[9/5, 9:12 PM] FA'IK: SONEEE.... (Silar Komai) Fage...1 (Book one) Mallakar 👇 Fa'IK ✍️ 07039676994 Typing.... GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Yanayine Na Hunturu Karfe Goma ne Amma Sai Kazaci Karfe 7 ne Saboda Tsananin Sanyi Daya Haddasawa Kowa Qiwar Fitowa Duk Kuma Wani Da Yayi Kundun Balar Fitowa Tau Dole ne ka hangeshi Lullube Da jibgegiyar Rigar Sanyi, Wani Santalelen Matashi Nahanga gefen Titi, Yayi Zaune Saman Wani Dan Kwalbati Dake Gefen Titin. Abin Mamaki Shikam Daga Shi Sai Farin Yadin Dake Jikinsa. Babu Rigar Sanyi A Jikinsa Kuma Ko Alama Bai Nuna Yama San Sanyin Akeyi. Abun Da keda Ban Mamaki Kenan. Kawai Naga Yayi Tsaki Yamike Yashiga Cikin Gidansu Yana Kokarin Share Hawayen Da ke Ta Kokarin Safka A kyakyawar Fuskarsa. A Tsakar Gidan Yatarar Da ita Tana Kokarin Kimtsa Jikinta Tana Hada Yan Kayanta A Bakko Wanda Hakan zai Nuna ma Alamun Fita Zatayi Tunda Matashin Nan Yashigo Tadaga Kai Ta kalleshi Bata Sake Kallonshi Ba Ta Ci Gaba da Sabgoginta. Abunda Yakara Daga Hankalin Wannan Matashin Kenan Yakuma Haddasawa Hawayensa Cigaba Da Gudu A Fuskarsa Ya durkusa Yana Mai dubinta Da Fuskar Nadama Yace, "Innarmu Dan Girman ALLAH ki ya......" Cike Da Fusata wacce Yakira Innarmu Din Takatsesa Ta Hanyar Daga Masa Hannu, Tace, "Bana Bukatar Jin Komai Daga Gareka. Ni Wallahi Da Zaka Kyaleni ma Sai In Fi Shakar Numfashi Cikin Sa'ada, Kuskure ne Nagane Nayi Kuma Baxan Kara Sake Yin Makamancinsa Ba. Shine Kawai." Cike Da Sheshhekar Kuka Da Tarin Nadama Yabuda Baki Zaiyi Magana Takara Katsesa Itama Din A Yanzun Muryar Ta Na Rawa, "Amma dae Nace Bana Bukatar Jin Komai ko? Ka kyaleni Yafi min Sa'ada In Kuma Haryanzun Bukatar kake KaCigaba Da Nuna min Iyakata Tau Bismillah!." Tadire Wannan Maganar A fusace Kafin Ta juya Zuwa Dakinta Wanda Da Ka kallesa Kasan Yana Cikeda Maraicin Abubuwan Da Zasu Qawata Shi. Shidinma Matsahin Jiki Ba kwari Yanufi Nasu Dakin Kafin Yazube A Yar Tsamurarrar Katifarsa Yana Mai Kyacewa da Wani Irin Kuka Dake Tasowa Tun Daga kasan Zuciyarsa. Wanda Kaitsaye Zaka yanke Masa Hukunci Cewa na Nadamar Abinda Ya Aikata ne. Can Kawai Yamike yasoma Gaura Kansa Da bango Yana Kuka Tareda Cewa "Nayi Nadama! Natsani Kaena! Nayi Nadama Innarmu Wallahi In Baki Gafartamin Zan Hala....." Kanensa Dake Cikin Toilet ne Yay Saurin Fitowa Ya tushe Masa Bakinsa Gamida Rikesa Shima Din Hawaye yake Yana Cewa, "Haba Yaya Kadaina Fadar Haka Ka Kuma Daina Abinda kake Kakuwa ga Yanda Kajiwa Kanka Rauni? Comon Big Bro in Rai ya bace Bai Kamata Ace Hankali Yadaina Aiki ba." Wanda Yakira Yayan Yadubesa Cikin Sharaftu Hawaye "Abubakar kabarni Na Girbi Abunda Na Shuka ban kyautawa Innarmu ba Ban kyauta ba Ban...." Yakasa Karasawa Sbda Kuka Yaci Karfin sa Abubakar yace Masa "Tun Farko ai Yaya Sai da na Nuna maka Gashinan Yanzu wa Gari Ya waya?" "Neni Abubakar Kuma Natabbata Sakarai Wanda Bai San....." "Yaya Duk Wannan Bata Taso ba, kabar Jifar kanka Da wayyanan muna Nan kalaman..." "Dole najefi Kaina Da wayyanan kalaman Inma Akwai Wasunsu kasanar Dani Danna Fadawa Kaina Ikram Ta Cuceni Taci Amanata Ta Kuma Wargaza Rayu...." Abubakar yasake Rufe Masa Baki Yace "is enough Yaya. Kana da Sauran Dama Haryanzun. Kazo Mu sake Gina Rayuwarmu Kamanta da Batun Wata Ikram...." Abdul Yadubesa Yace, " Tayaya Zan Manta Irin Wannan Tabon Tayaya Zan iya Gogeshi Eh ? Ka gayamun Abubakar Ina Sauraren ka?" Izuwa Yanzu Abubakar Yafara Tunanin da Kuma Fargabar Anya Abdul Dinsu Kuwa Nada Hankali? Inkuwa Yana Dashi Tau Yana Cikin Hayyacinsa? Da Wannan Tunanin yakamo Hannun Dan uwan Nasa ya zaunar Dashi Kan katifar Dakin Nasu, Kafin Yaje Yayi burkuce A Dakin Nasu Yasamo kyalle Yazo Yana Dorawa A Goshin Yayan Nasa. ALLAH yatakai ta Raunin Ba Sosai Bane. Kaitsaye Abubakar Yafita Daga Dakin Nasu Yanufi Inda Innarmu Ke Dafenta-Dafenta Yagama Bude-Budensa Babu Komai Cikin Tukanen, yadanyi Tsaki Kawai. Sa'anan Yakoma Dakinsu Yadauki Flaks Kai tsaye Gurin Mai Shayin Unguwarsu Yanufa Da zuwansa suka Gaisa Da Habu Mai Shayi Kafin Ya'amashi Flask Dinda Abubakar din ke Miko Masa Yana Cewa "Harna Cire Ran Yau zaka Zo ma Ai." Abubakar Yayi murmushi Yana Neman Gurin Zama Kan Bencin Da ke laye A Gurin Inda Cosmtomomin Habu Mai Shayi Ke Zaune Wani Na Shan Shayi da Bread Wani Kuma kwai ne Da Endomi Ke Gabansa Kuma Dukkaninsu Sunyi Shiru Sai Aikin Bama Ciki Hakkensa Suke. Habu Mai Shayi Yana Kokarin Zuba Masa Ruwan Liptom Din A Flask Yasake Cewa, "Takwara Lafiya kuwa Nidae bansanka Miskili ba Da Yayanka Ne Abdul Ma banayi Mamaki ba." Karo Na Farko Da Abubakar Yayi Dariya Yace, "Kaidai Habu Surutu bayama Wahla Shi Yaya Abdul Shaidar da Aka Masa Kenan ko? Abun da yasa kaga banyi Saurin Zuwaba Bana Da Zuwa Class Da safe Shiyyasa, Kuma Kaga Gari Da Sanyi Fitowa yau Sai Mutum Yayi Dagaske." "Indon wanna Da Wannan Kam, Gari Yau Antashi Da Sanyi." Habu Yafadi Hakan Yana mai bude Robar Da Yake Sa Shuga Da Nufin Yadiba Yasa Acikin Flask din Da yariga Yazubo Masa Ruwan Zafin Abubakar Yayi Maza Yace Masa "A'a Karka Sa Shugan Bana Bukata Samin Lipton Guda Biyu." Bayan Yasa Ya Miko Masa Yana cewa, "Wanna Ruwan Lipton Na Yayan Kane Abdul." Abubakar yakarbi Flask din Yana Cewa "Koma dae waye Ina Ruwanka? Kajimin Mutum Da Sa'ido?" Yasa Hannun Acikin Aljuhunsa Yaciro Kudi Yamika wa Habu Mai Shayin, Kafin Yajuya Yanufi Wani Mai Shagon Yabar Habu Na Dariya Gamida Cewa, "Baxaka Tsaya Ka karbi Canjin ba?" Shidai Abubakar ko juyowa Bai ba. Dan Yasan Inya Biyewa Habu Mai Shayi Sai Su Kai Yamma Suna Abu Dai. Shima Dae Habu Soke Kudin Yayi A Aljuhunsa Dan Yasan Suna Haka In har Yabar Masa Canji Tau Hakan Na nufin Da Yamma ko Da daddare Zai Dawo Ya karbi Ruwan Lipton. A Wurin Masu Shagon Bready Ya Siya Da Kayan Tea Sa'anan Yakama Hanyar Gida Cike Da Tunanin Yanda Cikin Gidan Nasu ke Cikin Matsala A Yan kwanakinnan. Dan Tsaki Yayi A ransa, Wanda Yayi Dai Dai Da karasowarsa Dakin Nasu. Abdul yadago Daga Tagumin da Yayi Yana Mai Cewa, "Kaima kanajin Haushi Nane ko? kayi Hakuri kanena Wallahi Duk Abinda Yafaru, Yafaru ne Cikin Kuskure Amma Bawai Dan Niyyah ba." Abubakar ya janyo Wani Cup Yashiga Hidimar Hada Shayin. Sai da Komai Yahadu Yakawo Gaban Abdul Din Yace, " Yaya Ga Shayi ka karya Sannan Muyi Magana. Ni Banyi Tsaki Dan Ina Jin Haushin ka ba Sai Dan Yanda Walwala Da Farinciki Suka Kaura Daga Gidannan Namu Tun Bayan Kunnowar wannan Matsalar Kuma Tun Farko Yaya Da ka karbi Shwara ta Tau Da Hakan Duk Bata Faru ba." Abdul Cikin Jin Takaicin kansa Yace, " Kuyi Hakuri kaida Innarmu Nasan nayi Ba dai dai ba Amma Wallahi SONEEE Silar Komai Bawai Dan Ina da Niyyah hakanba Amma Na....." "Yaya Mubar Wanna Maganar Zamuyi ta Daga Baya Abunda Nakeso Dakai Yanzu Ga Break Fast Nan Na hadaMa ka karya Kayi wanka Ka Kuma Canja Kaya Sai Mu Zauna mu San Ta Inda Zamu Gyara matsalar pls." Abdul Yadubi Qanin Nasa Ido Cikin Ido Yace "Da zaka Taimaka Qanina da Munyi Wannan Maganar tafiye min komai. A Yanzu banaji Ina Da Wani Bukata Sama Da Gyara wannan Kuskurenda Na'aika ta Ciki kuwa Harda Abinci da Komai Zan iya Hakura Dasu." Abubakar Yayi murmushi da Kai tsaye Kasan Ba na Dadi Bane Kafin Yadubi Yaya Nasa Yace, "Yaya Ko A wancan Kuskuren Da kake Neman Gyarawa A Yanzun Taurin Kanka ne Yajanyo Hakan Kakuma Yimin Afuwa Da wannan Furucin Banida Wani Harshe Da Zan Amfani Ne Bayada Wannnan. Dan Haka Yanzun ma Idan Kaki Karbar wannan Shawarar Watau tafara Gabatar da Cin Abincin ka Da Kuma kimtsa Jikinka Tau Bana Raba dayan Biyu Yar Gidan Jiya Za'a Sake komawa. Sabo da Haka Ina Mai Rokonka Da ka Karbi Kayan Karinnan Ka Karya." Abdul Bai Musa ba Yajanyo Kayana Shayin Ya Soma Sha Wanda Kai da Ganin kasan Yana Shane Kawai Bawai Dan Yanajin Gardinsa ba. A Kasalance Yake Komai Nasa. Bayan Yafito Daga Wanka Jallabiya Fara Kar! Yadauka Yasa Kafin Yajingina Da bango Yana Mai Kallon Qanin Nasa Watau Abubakar Da Yattara Duk Hankalin sa Akan Wani Littafi Na Biology. Cikin Murya Mai Nuna Alamun Ma Mallakinta Nacike Da Tarin Damuwa Abdul Ya Soma Magana, "Abbakar Na kammallah Sai Muyi Maganar Da kake Cewa Ko?" Abubakar yadan Rufe Littafin Biology Din Da Yake Nazari Kafin Yajoyo Ga Yayan Nasa Yana Mai Murmushi Kafin Ya Soma Da Fadin, "Duk Mai Faruwa ta Faru Yaya Dan Haka Duk Wata Damuwa Kayi Watsi Da ita Kafara Sabuwar Rayuwa Matakin Gyara Na Farko Da Zamu bi Shine Mufara Neman Gafarar Innarmu Sannan Mudora Na Gaba." Cikeda Tarin Damuwa Abdul Yalumshe Idanuwansa Kafin Yasake Budesu Yana Kallon Fuskar Qaninsa Mafi Kuma soyowa Gareshi, Yana Rayawa A Ransa Ina Ma'a ce Baya Zata Dawo? Wallahi Da ya Dawo da ita, Ya Hana Duk Wani Abu Da Yafaru Sake Faruwa. A Hankali Abubakar yakama Hannunsa Yana Rintse Sa Cikin Nasa Yace "Kada Kayawaita Damuwa da Tunani Yaya Kamanta Duk Abinda Yafaru Ka daukeshi Amatsayin Kaddarace Kawai Wannan Shine Zai Karfafemu Wajen Gyara Abubuwan Da Suka Lalace." Abdul Ya Sauke Wata kakkafar Ajiyar Zuciya Kafin Yadora da Cewa "Kana ga Yanda Innarmu Tadauki Zafi Dani Zatai Hakuri?" Cikeda karfafawa Abubakar Yake Girgiza Masa Kai game da Cewa "Da Izinin ALLAH Zamu Ciwo Kan Innarmu Zatayi Hakuri Kasan Itadin Mai Son muce Kuma Mai Sadaukarwa Akan Komai Namu Dan Haka Bana Zaton Zata ki Yafiya Gareka Yayana." Abdul ya Sunkuyarda Kansa Cikin Wani Bakinciki da Tsanar Kansa Yace "Qanina Daina Tunamin Hakan, Wallahi Kara Tsanar Kaina Nake Kana Kuma Tuna min Irin Butulcin Da Nayi wa Innarmu ne Akan Wata Macce Kaicona Ni Abdul Nayi Asa..." "Kash! Yaya Nagayama Kai Daina irin Wannan Tunanin Kabar Komai Yawuce Kama kanka Fata Nagari Kaji Yaya? Ba Wanda Baya Kuskure Kuma Ba Wanda Yake Tsallake Kaddararsa." Tau Da irin Wayyanan Kalaman Abubakar Yayi Ta Tausar Yayan Nasa Dasu Wanda Babu Shakka Sunyi Tasirin Akansa Sosai Dan Har Yasamu Yadan Jincira Har Kuma Gashi Barci Na fisgarsa Dan Haka Sai Kawai Abubakar Yamike Ya kunna Masa Karatun Kur'ani Acikin Kira'ar Maheer Zain Acikin Yar karamar Mp Dinsu Da Suka Hada Kuddi Suka Saya. Wannan Abun bakaramin Kara Samarwa Abdul din Nutsuwar Zuciya Yayi Wanda Harshi Kansa Abubakar din ya Amfana. Kafin Kace kwabo Sai Ga Abdul Yana Barci lakadan. Ko Banza Yayi Kwana da kwanaki Bai Runtsa ba. Ganin Hakan Abubakar Yayi murmushi Tareda Mikewa Ya sunce Kayan sa Yadibi Ruwa A boket Yanufi Bayinsu Dan yin Wanka Dan Karfe 1 Tana Karatowa Kuma lokacin Yake Da lakca A Makaranta. Yafito Sai karkrwar Sanyi Yake Sabo Shi Kansa Yasan ba Karamar Jarumta Yayi ba Na Wanka Da Ruwan Sanyi A Irin Wannan lokacin ba. Sai da Yagama Shiryawa Kafin Yahada Tea Da Bread Yasha Kafin Ya Rarumi Jikkarsa dake Cike Da Hand Out Yafita Yana karawa Jawa Abdul Kofar Dakin. Murmushi Yayi A sanda zai gota Kofar Dakin Innarmu A Ransa Yana Cewa, "Innarmu Badai Fushi ba, Gashi Ya Abdul yajamin Nadaina Samun Dumamen Mai Dan Dadi." Kai Kawai ya Girgiza Kafin Yafice A waje Yana Jiran Abokin Karatunsa Da Zai Biyo Masa Da Mashin. Bai Dau Dogon Lokaci Ba Sai Gashi Ya'iso Yaku Haye Suka Damki Hanyar Zuwa School. ************ Da Yamma ne Sosai, Sai Dai Rana A lullbe Take Sabo Da Sanyi Ko Ina Yayi Lumshi Mutane Sai Hada-Hada Suke Kowa Na Kokarin Ganin Yayi Saurin Kammallah Abunda Yake Dan Isa Gida Da Wuri Saboda Yasamu Ya Adana Kansa Tun Gabatowar Magarib. Innarmu Na Cikin Jirin Wayyanan Mutanen Dan Agaggauce Ta iso Gida Ta Soma Da ajiye Yar Bacconta Kafin Tashiga Share Gidan Tsaf Daga Bisani Ta Shiga Kiciniyar Girki Dan Kwana Biyu Batayi. Amma Ga Alama Yau ta Dan Sauko Daga Dokin Fushin Da Ta hau Tsakar Gida Ta Ajiye Yar Tsugguno Tazauna Tana Aikin Tsintar Shinkafa A ranta Sai Lissafin Sauran Kwana Nawa Yarage Azumi Yazo Da Kuma Irin Shirin Tarbarsa Da Yakamata Tayi. Tana Tsaka Da Wannan Tunanin ne Abubakar Yafado Gidan Da Sallamarsa Innarmu Ta'amsa Sallamarsa Batareda Tadago Ta kalle sa ba Murmushi Kawai Yayi. Yawuce Dakinsu Ya'ajiye Jakarsa Kafin yazube Kan Yar katifarsu Cike Da Gajiya da Kuma Tunanin ta Ina Zai Fara ne? Yana Cikin Wannan Nazarin Ne Aka Turo Kofar Dakin Nasu, Ga Tunanin sa Innarmu ce Haryana Murnar Ta Sauko Kenan Tunda Gashi Yau Ya ga har Girki Take Musu Sabanin Yan kwanakin da Suka Shude Sai Dai Taciko Cikinta Daga Gurin Da Take Aiki In kuwa Hakan Bai Samu ba Sai dai Tajika Gari Da Shuga Tasha Tayi kwanciyarta. Wata Irin Kakkafar Ajiyar Zuciya Yasauke Yana Mai Kallon Abdul Din Da Yashigo Duk Sukayiwa Juna Murmushi Irin Na Yake. Abdul Dae baice Masa Komai Sai Dai Yanufi Ina Suke Ajiye Jikkar Pure water Dinsu Wadda Sukan Siya Idan Gari Yayi Musu Dadi Inkuwa Baiyi ba Suje Randar Innarmu Suciko Jug Su Sha pure water Yazaro Kafin Yamika Masa Yana Mai Cewa, "Amshi Kasha Bawai Dan Kana Jin Kishirunwa A Irin Wannan Hunturu ba Sai Dan Irin Bushewar Da Makoshi Kanyi Idan Ana Cikin Irin Wannan bacin Rai." Abubakar din Yamika Hannun sa Yakarba Yana Cewa, "Kaji Ka da Wani Zance Ya Abdu Ai Yanzun Alamun Sauki Na Zuwa Kai Baka Ga Alamar Innarmu ta Sauko Ba Gashi Yau Har Girki Za'a Rangada Mana." Abdul Yayi Dariyar Da yadade Baiyi Ba Tun Faruwar Wannan matsalar Kafin Yace, "Kaifa Ja'iri ne Wani Lokacin Innarmu dince Tace maka Dammu Takeyi? In Kuma Baki Zatayi?" Abdul Yamike Yana Fadin, "Koma Dai Dan Waye Ni yau Sai Naci Girkin Nan Nayi Missin Dinsa Nakuma Gaji Da Ruwan Shayin Da Nake ta Durawa Cikana Sai Indome Wadda Bata Rikon Ciki." "Dama Ai Kai Indae Akan Cikine Nan Kafi Auki?" Abubakar ya waro Ido, "Tau Kaga Laifinane Ya Abdul Ai Komai Za'ayi Sai An koshi Akeyinsa. Ni Kaga Zomuje Ma." Yafadi Hakan Yana Mai Jan Hannun Yayan Nasa Inda Kai Tsaye Suka Fito Tsakar Gidan Inda Innarmu Ke Zaune Kan Yar Tsuggunonta Tana ta Aikin Tsintar Shinkafa. Ta gefen Ido Take Kallonsu Taga Ina Suka Nufa Wurinta Sukazo Kai Tsaye Suka Zube Kan Gwaiwowinsu Aikuwa Da Azama Tamike Tanufi Dakinta Suma Suka Mike Suka Bita Tasake Banke Labulen Dakin Tafito Zuwa Tsakar Gida Nan ma Suka Sake Biyota. Bata Kasa A Gwaiwa Ba Tasake Komawa Daki Abinta A Yanzun Kam Abubakar daene Mai Kwarin Zuciyar Binta Cikin Dakin Shikam Abdul Sai Ya Durkushe Nan Bakin Kofar Dakin Yana Fitarda Wasu Irin Zafafan Hawaye. Abubakar Din ma Na'isa Gabanta Yazube Yana Mai Dora Hannuwansa Kan Cinyoyin Innarmu Kafin Yace Komai Sai Ga Innarmu Tafashe Masa Da Kuka Dama Can Kwarin Zuciya Ce kurume Take. Kuka Riris Innarmu Tafashe Musu Dashi Wanda ko A Rasuwar Mahaifin Su Batai Irin Sa ba. Kai Suna Ma Iya Rantse wa Tun Wayon Su Basu Taba Jin Tayi Kuka ba. Saboda Itadin Innarmu Macce Mai juriya Da Kuma Hakuri Da Tsananin Ibada Dan Haka Ko Da Yaushe take Cikin Kamala. Dole Suma Kukan Yakwace Musu Dukda kuwa Taurin Rai Da Aka San Da Namiji Dashi Mussamman ma Abdul Da Yakara Tsanar Kansa Wai Yau Akansa Innarmu Ke Irin Wannan Kuka? Innarmu Mai Tsananin Sadaukarwa Akan Sha'anin su Idan Har Bai Sa that Farinciki Ba Anya Ta canci Irin Haka? Shikuwa wace Irin Rudewar Duniya ce Ta sameshi Haka? Wayyanan Tamboyoyin da Tunanunka Da Sukai wa Zuciyarsa Rubdugu Suka Bashi Kwarin Gwaiwar Mike wa Yanufi Dakin Amma me Yana Kan Niyyar Shigar Innarmu Tadaka Masa Tsawa Acikin Muryarta Da ta wadatu Da Bacin Rai Cewa, "Karka Kuskura kashigo min Nan Wallahi kana Shigowa Zan Sallamaka." kalamanda Suka Takawa Abdul Burki Kenan Yakuma Zube Bakin. Kofar Yana Wani Irin Rishin Kuka. Yana Ta Nana Cewar, "Ikram Kin Cuceni Kinci Amanata Kin Hada Ni Da Mahaifiyar mu Mafi Soyuwa Garemu Innarmu In Baki Yafemin Ba Ni Na San Nalalace Kawae. Wayyo ALLAH Na SONEEE (Silar Komai) Shine Ya Tarwatsa Rayuwata Da Ta Ahalina Ikram Kinci Yaudareni Menayi Miki Kika Zabi Cutar Dani Haka?" "ka Gyara Maganar ka Me Nayima Ka Zabi Kwarewa Kwarin Gwaiwa Ta Akanku? Abdul Na Hakura Da Kowa Nawa, Na Yafe Duk Wani Farinciki Saboda Dae Naga Rayuwarku Ta Inganta, Ashe Ni Bansani ba Kuskura Nayi? Na Dauke KU Komai Nawa Ashe Ni Bansani ba Ku A Gurinku Bahaka Bane? Zaku Sa Yan Uwana Sumin Dariya? Zaku Sa Yan Uwana Suce Dama Mun Gayamaki..." Kafin Tayi Shiru, Tasanya Gefen Zanenta Tana Fyace Majina. Abdul Nadama! Tsanar Kansa! Bakinciki! Duk Sai Suka Masa Dirar Mikiya A Zuciyarsa. Dan Haka Sai Yarasa Abunda Zaiyi kawae Sai Yazabi Yayi Kukan watakil Yasamu Sa'ada A Zuciyarsa Kuma A Yanzun Yana ga Shine Abu mafi Arha Da Sauki A Gareshi. Abubakar Dake Durkushe Gaban Innarmu Shine Kadai Keda Kwarin gwaiwar Magana Shima Acikin Kukan yake Cewa, "Kiyafe Mana Innarmu Wallahi Mu Badamu Ba Ya Abdul Shima Kuma ba Laifin Sa Bane SONEE......Silar Komai." Cikin Muryar Bacin Rai Innarmu Tace Masa, "KU Daina Yaudara ta Abbakar Da Cewa SONEE ....Silar Komai Kawai Kune Silar Komai Son Zuciya Ne Silar Komai Amma Meye Amafni Wannan Son? Nace Meye Amafnin Wannan Son indae Bai Zama Silar Alkairi Ba Ai Bai Kamata Ya Tarwatsa mu ba......" Abdul Ya Rarrarafo Kamar Dan Karamin Yaro Ya Iso Gareta Yana Cewa, "Natuba Innarmu Nabi ALLAH Nabiki Dan ALLAH Kimin Alfarmar Saurarena Kiji Ta Inda Abun Yafaro....kinji Innarmu? Dan ALLAH badanni Ba." Shima Abubakar Sai Yasako Bakinsa Yana Taya sa Roko Tareda Cewa, "Innarmu kidaina wannan Kuka Bazamu Taba Yafe Ma Kammu ba Indae Bamu Share Maki Hawaye ba Bai Kamata mu Sakaki Hawaye Dan ALLAH Innarmu Ki Saurare Ya Abdull Kiji Uzurinsa." Magiyarsu Da irin Kuka Da Rukumkumeta Da Sukayi Duk Da Irin GirmanSu Hakan Yakara narke Zuciyar Innarmu Tayi Laushi Dama Dauriya Kawai Take Kunsan Kuma Tsakanin 'Da Da Mahaifiyarsa Sai ALLAH Wurin Yadan Dau Shiru na wayyansu Yan Lukkutan Kafin........ ASALI DA TUSHEN LABARIN........👇 ........... Muje Zuwa Readers Nawa Muji Wai Tayaya So Yazama Silar Komai? In ma Yazamo Silar Meyesa Yazama? Kuma Ma Dame-Dame Yazamo Silar? Akwai Badakala Acikin SONEE....Silar Komai... Takin Karewa Ta Inda So Zai Sa 'Da Yacanzawa Mahaifiyar sa Duk_da Irin Tarin Alkairinta Garesa. Haka Budurwa ta Canzawa Saurayinta Duk kuwa Kasancewarsa Mai Sadaukarwa A gareta Yanda Kuma Ita Kanta Buduwar Son Zai Sata Canzawa Izuwa Wata ta Daban Ba Yanda Take ba. Kudai kubiyoni Page 2 Inda Zamu Ci Gaba Da TUFKA DA WARWARA Akan SONEE........ Dafatar Kuma zakuyi Hakuri Da Yanayin Rubutun Kasancewar Bansamu Nayi Edit ba. [9/5, 9:12 PM] FA'IK: SONEEE.... (Silar Komai.) Fage...2. Mallakar 👇 Fa'IK ✍️ 07039676994 Typing..... GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem ASALIN DA TUSHEN LABARIN. Mal Rabi'u Shine Cikakken Sunan Mahaifin Su Abdul Wahab Da Abubakar Da Kuma Auntynsu Mai Suna Aisha. Kuma Shine Miji Ga Fatima Wacce A Dangi Suke Kiranta Da Inno Diyanta Kuwa Suke Cema ta Innarmu. Kamar Yadda Tarihi Yanuna Su Din Yan Asalin Jahar Sakkwato Ne Acikin Kauyen Sayyinah. Mal Rabi'u da Matarsa Fatima Watau Innarmu. Auren Zumunci Sukayi, Wanda Bayan Aure Suka Tare Nan Cikin Gidansu Rabi'u Din. Gida Mai Cikeda Dangi Iyaye Da Surukai Duk Ake Curkude Guri Guda. Gefe Daya Ga matsalar Zama Gidan Taro, Tau A Haka dae Zaman Nasu Yamika Inda Innarmu Haifuwarta Ta Farko Tahaifi Yarta Macce Suke Kiranta Da Aisha Daganan Tasake Haifo Danta Santalele Suke Kiran sa Da Abdul Wahab Daganan Sai Mai bimasa Abubakar. Dagashi Kuma Bata kara Samun. Wani Cikin ba. Kasancewar Mal Rabi'u Mai Zafin Nema Da Kuma Himma Da hazaka Sai Iyalan Suka Fita Zakka Acikin Gidan Nasu Suka Banbanta Da Sauran Matan Yannensa Da Kannensa Dama Sauran Mata Dake Gidan. Saboda Shi Rabi'u Yana Kokarin Ganin Ya Wadata Su (Iyalinsa) Da Komai Na Rayuwa Wanda Shine Abu Na Farko Da yafara Jawowa Innarmu Tsana Da Tsangwama A Gidan. Suka Shiga Hassadar Ta Akan Yanda Tafisu Komai. Saboda Haka Zaman Gidan Sai Hakuri A Gurin Innarmu. Dama Can Ita Bamai Zafi Bace Akan Lamarin Rayuwa, Gashi Kuma Ko Da Yaushe Mijinta In Sun Samu Kebewa A Dakinsu Yana Kara Nuna Mata Muhimmanci Hakuri Komai Zai Wucewa ne. Acikin Haka Dae Suka Sanya Diyarsu Babba Watau Aisha Makaranta Cikin Ikon ALLAH Ta Kamallah Makarantar Secondary Wanda Tana Karewa Mutanen Gida Sukayo Caaa Akan Shi Mal Rabi'u Ya Aurar Da ita. Suna Cewa, Ga Sa'aninta Nan Duk Sunyi Aure Sai Ita Kadai. Babu Yanda Zasuyi Duk-da Kuwa ita Aishar Taso Ci Gaba da Karatun Amma Zatabi Umurninsu Babanta Ko Dan Nuna Masu, Su mutanen Gida Cewa Yanda Suke Cewar Ai Innarmu Bata Barshi A Haka ba. Bahaka Bane Babansu Ya'isa Da Iyalinsa. Akasha Buki Da Wani Saurayinta Dan Asalin Jahar Zamfara Suka Tare A Gidan sa Dakenan Sakkwato Da Tafiya Tai Nisa Sai Suka Koma Mahaifar Mijin Nata Watau Zamfara Tunda Dama Nan AIKI ne Kawai Yakawo Shi. Bayan Wata Biyu Mal Rabi'u Ya kwanta Jinya Jinyar Da Bai Tashi Ba Kenan Sai Darul Salam. Rasuwar Mal Rabi'u itace Abu Mafi Girma Da ta Samarda Wani Katon Gibi Ga Matarsa Innarmu Da Kuma Yayan ta Watau Abdul Wahab da Kuma Dan Kaninsa Abubakar Dan Ba'a Ce Da Aisha ba Tunda ALLAH Yanufa Tayi Aure, Dan Haka Ko da Gibin Ya sameta Kadanne Bisa Ga Yan Uwanta. Innarmu iya Chanjin Rayuwa Da Kuma Kin Zumunci Irin Na Mutanen Zamanin Nan Namu Taganeshi Tun Yan uwa Da Kannen Mal Rabi'u Na Taimakonsu Harta Kai Ga Sun Daina Dan Haka Karatun Da Suke Yalalace Abinda Suka Ci Shima Neman Gagararsu Yake. Rayuwa Dae Tai ma Su Innarmu Daurin Minti Dama Yan Uwan Su Dayane Da Mijinta. Balle Tace Bari Ta Nufi Nata Dangin, Yan Uwanta ma Wani Lkcin Sunfi Tausaya Mata Da taimakon ta. Dan Dama Ba'a Taruwa A Zama Daya. Itama Can Aunty Aisha Tana Taimakon su Ta Hannun Mijinta. Dama Can Ita Innarmu Itakadai ce Agurin Mahaifiyarta, Sai Gurin Babanta Ne Suke Da Yawa, Kuma Kowa Yasan Yadda Yan Uba Suke. Ba kasafai Ne Ake Samun Fahimtar Juna Haka ba. Tau Yau dae FARI Gobe BAKI Haka Rayuwar Taita Zuwar ma Innarmu, Dan Su Abdul Wahab da Kaninsa Abubakar ba Wani Wayo Suke Dashi ba. Akwai Sanda Innarmu Ke Hakura Da Abincin intaga ba Yawa tabarmusu Su Suci. Suma din Bawai Dan Yana isar Su ba Dan Wani Lkcin Har Kuka Suke Mata Mussamman ma Dae Abubakar din Da Shine Karamin Sosai. Haka Innarmu Zatayi ta Hawaye Tana Lallashin Sa Harta Samu Suyi Bacci Inda Daddare ne Kenan, Inkuma Da Rana ne Harsu Hakura. Gefe Daya Ga Dariyar Da Faccalolinta Suke Mata da Kuma Gori Harma Da Izgili Cewar, "Yaudae Matar So! Anzama Abun Tausayi. Yau Kuma Ina Galihun? Ai Karya Fure Take Bata 'Yaya, Wai Ita Ana Kula da Ita Tafimu Komai Tau Yau Ina Gatar? Ai Sai Abunda Kuma muka Dafa Muka Samma Ki." Sai A Bushe Da Dariya A tafa Can tsakaninsu Suke Wayyanan Maganganu. Dae dae Rana Daya Innarmu Bata taba cemusu Ta tafasa ba. Sai Dai Ma Tashiga yin Wasu Yan Sabgoginta kodai Ta Gyra Dakinta Ko ta Tattaro Wankin Yaranta Tayi, Ko ta Dauki Buta Tai Arwallah Tashige Tayi Nafila ta Soma Karatun Kur'ani. Ko Kuma Tadauki Yar wayarta Ta Itel Da Mijin Aisha Yasiya Mata Saboda Su Rika Gaisawa Da Aishar, Sai Takamo Fm Din Dake Cikin Wayar Tana Sauraren Wasu Shirye-Shirye Masu muhimmanci mussamman ma Dae Na Addini da Ake Hira Da manyan Malummamu. Wanna Kam Baya Wuce Innarmu Koda Yaushe Tana makale Da jin Su Saboda Tana Karuwa. Wannnan Kenan! Dare Yatsala Sosai Kowane Bawa Yana Makwanciyarsa Duk Gari Yayi Tsit! Sai Kukan Tsuntsaye DaKuma Haushin Karnuka Da Kake Ji Daga Can Gidajen Masu Su Jifa-Jifa. Wani Iska Akeyi Kadan-Kadan Gaskiyar Bahaushe Da Yace, 'Dare Mahutar Bawa.' Masu Barci Nayi, Masu Ibada Nayi, Masu Sabon ALLAH Nacan Nayi, Masu Wata Bukata Da Suke Ganin Tafi Dacewa Da Irin Wannan lkcin Suma Sun Dukufa Sunayi. Innarmu Ce Tai Kokarin Mikewa Sanda Taji Alarm Dinda Ta Sanya Abdul-wahab Ya Sanya Mata A Yar Itel Dinta. Wannnan Yake Tabbatar Mata Cewa Karfe Hudu ne Dae-dae. Dan Karfe 4 Tace Abdul-wahab Din Yasaka Mata. Bayan Tamike Kaitsaye Butarta Ta Dauka Tafito Tsakar Gida Inda Iska keta Kadawa Alamun Dae Akwai Yuyuwar Asamu Ruwan Sama A Wannan Dare, Dama Kam Wannan Zafin Da Ake Sha Sai Haka. Bayan Tafito Daga Toilet Arwallah Tayi, Kafin Tafito Da Robobinta Ta Tara A Inda Suke Tara Ruwan Sama Da Nufin In ALLAH Yasa Anyi Ruwan Saman Zata Samun Na yi Musu Wanki Kayansu Da Sauran Yan Bukatunsu. Sallayarta Ta shimfida Kafin Ta Fuskanci Alkibla Bayan ta Kimtsa Kanta Da hijabinta Dake Ja Har Kasa, Daganan Ta Dukufa Nafil-fili Wayyanda Tun Ina iya kiddidige Adadinsu Harna Gagara. Bayan Tayi Wayanda Take Gani Sun wadaceta Tazauna Jan Carbi Kafin Tadaga Hannayenta Tana Ta Adu'a Wanda Tayi Tayi Tun Hawaye Suna Kwaronyo wa A Fuskarta Har Yaxace Da Sheshahekar Kuka Wanda Hakan Yatilasta Mata Durkushe wa Kan Cinyoyin ta Tana Rufe Fuskarta Da tafukan Hannayenta (Ina Kuke? Kunji Yanda Salihan Bayi keyi Ko?) Daga Wannan Lokacin Bata Runtsa ba Sai Da taji Anfara Kiraye-kirayen Assalatu Sannan Ta Tayar Da Su Abdul-wahab Ta Tasa su Gaba Sukayi Arwallah Kafin Tasanya Hannun Abubakar Cikin Na Abdul-wahab Din Tace, "Kuje Massalaci, Kuma Banda Wasa Ana kammallah wa kudawo." Sukace 'Tau.' Tajuya ta Koma Daki Ta kabbara Tata Sallar. Gari Nafara Haske Aka Tsuge Da Wasu Irin Ruwa Masu Karfi Wanda Yahaddasawa Kowa Zama Cikin Daki Innarmu dae, Dole Tafito Zuwa Nema Musu Kalanzir Dinda Zata Yi Amfani Dashi. Dan haka Tajike Shataf! Da Ruwan Saman Da Ake, ALLAH Ma Yataimaketa Cikin Gidan Nasu ne Daga Cikin Matan Wata ke Sai da Kalanzir din. Dole Ta Canja Kaya Kafin Tayi Kokarin Zuba Kalanzir Dinda Tasiyo Acikin Dan Karamin Stove Dinsu Watau Risho. Ta daureye Tukunya Kafin Ta Dora Ruwan Zafi. Ayan kwanakinan Suna Cikin Wadatar Abubuwa, Saboda Ba'a Dade Ba Da Aisha tareda Mijinta Sukayo Masu Aike. Kunun koko Ta Dama Musu Kafin Tasake Dora Sanwar Dafa Dukan Macaroni, Irin Wacce Ake Aunowa Dinnan CE Tasa Aka Auno Mata Kwano Biyu. Kawo Yanzun Kuma Ruwan Da'ake Yadan Tsagaita Sai Dan Yam-Yam Da'ake. Su Abdul-wahab Da Kaninsa Abubakar Tafara Gabatarwa Da Kunun Bayan ta saka Musu Suga Tace Su Motsa. Ita Kuma Tafita Gyara Ruwan Saman Da Ta Tara, Tai Sa'a kuwa Duka Robobin Suncika. Bayan ta tarshe Su Guri Daya Tadawo Dakin Nasu Wanda Yayi Dae-dae Da Shigowar Hamza Yaron Gidan Ya'ajiye Mata Kwanon Da Sunan Dan Hasafin Da Suka Saba Samu Daga Gidan. Tace, "Hamza Ana Godiya." Kafin Kuma ta Dora Da karba Gaisuwar Da Yakeyi Mata. Bayan Su Abdul Wahab Sun Gama Shan Kokon Da tazuba Masu Sannan Tabasu Dumamen Da Hamza Yakawo Sukaci Kafin Ta SallameSu Suka Kama Hayar Zuwa Makarantar Allo, Bayan Tabisu Da gargadin Su kula Da Hanya Mussamman ma Dae Abdul-wahab Da yakasance Shine Babban. Sa'anan Tadawo Dakin Ta Duba Yar Jallof din Macaronin Data Dora Taga Yana Nan Yana Zabarbaka Dan Haka Sai Ta Zuba Kunun Koko Itama Ta Zauna Tasha, Kafin Taduba Dan Sauran Canjinta Taga Suna Da dan Kauri Dan Haka Tanufi Tsakar Gidan Tasiyo Tokar (Sabulun Wanki) Dan Nanma Akwai Mai Saida Tokar (Sabulu) Daga Cikin Matan Gidan. Kaitsaye Ta Soma Wankin Kayansu Gefe Daya Ta'ajiye Yar Wayarta Tana Sauraren Shirin Da ake Gabatarwa A Lokacin Mai Suna Zauren Fikhu Wanda Abdullahi Ibrahim Sokoto ke Jagoran ta Tareda Wani Kwararren Malami, Da Yake Bayani Akan Sabbuban Tsarki. Daga Baya Kuma Masu Saurare Suka Soma Kira Suna Tamboyoyi Akan Abinda Yashigemusu Duhu Daga Sallah Ko Wani Abu makamancinsa. Wanda ke Bukatar Karin Bayanin Kan Karatun Mal Kuwa Sai Yace Ga Inda Bai Gane ba. Hankalin Innarmu Yayi Nisa Acikin Saurare Kuma Tana Wankinta Taji Girkinta Yasoma Kauri Dole Tasaki Wankin Ta Nufi Dakin Dan Saukeshi. Bayan Ta Gama Wankin Ne, Tana Tsaka Da Shanya Wanda A Wannan Lokacin Agogon Dake Kan Wayarta Ke Nuna Karfe Dai!(1) Na Rana. Dama Kuma Yau Dole Lokaci Yayi Gudu Tunda An Wayi Gari Da Ruwan Sama Ga kuma Yanda Garin Duk Ya Rine Baka Ma Gane ma Rana Tayi. Wannnan lokacin ne Su Abdul-wahab Suka Dawo Da Makarantar Allo. Innarmu Ta Tarasu Gefe Daya Ta Zuba Musu Abinci Tana Cewa, "Abdul Kuci ku Gama Kazo Ka karbomin Katin Inkira Yayarku Naga Dazu Tana min Flashing Watakil Habibu (Mijin Aishar) Yayi nisan Kiwo Dole Kati Yay Mata Wahla." Duk Suka Hau Murnar Za'a Kira Auntynsu Suna Rikinci. "Innarmu Ni Za'a Fara Ba Inyi Magana Da ita" wannan Yace, "Ni Za'a Bawa." Innarmu Tace, "Bana Son Rigima Kuci Abincinku Yau Ba Wanda Zanba Yacinye min Kati." ************ Tau Irin Hakan Dae Shine Yanda Innarmu Ke Renon Yan Marayun Yaran ta, Da Basu Da Matallafi Sai Ita Sai Kuma Wani Daga Cikin Dangi Da In Yadubi ALLAH Yataimaketa Akan Sha'anin Su Da Auntynsu Aisha da Mijinta Dake Kan Nasu Kokarin Suma. Acikin Hakane Wani Daga Cikin Dangi Yafito Yana Mai Neman Aure Innarmu Cikin Abinda Bai Gaza Wata Biyu ba Suka Fahimci Juna Aka Daura Auren Su Saidai Baifi Wata Uku Ba Auren Nasu Matsaloli Suka Dabai bayesa Domin Dae Babu Jituwa Tsakaninsa Da Yayan ta, Kuma Data Shiga Hidimar Yaran Nata Yake Tashi Da Bala'i Kamar Anzubawa Fulawa Is. Hardai Takai Yace Indai Tana Son Zaman Nasu Yadore Tau Tabada Yaran Ga Dangin Ubansu Ai ba Ita keda Hakken Renonsu Ba. Abinda Innarmu Tasanar Masa Bazai Taba Yuwa ba. Domin A Nan In Duniyar In Ancire Iyayenta Da Kuma Mijinta Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya, Tau Bata Da Tamkar Yaranta. Dan Haka Rabuwa Dasu Ba'abune Mai Yuwa ba. Shiko Yace "Tau Taje Yasaketa." Tace masa "ALLAH Yasa Hakan Shi Yafi Zama Alkairi." Wannan Yasa Tasake Dawowa Tsofon Dakinta Wanda Take A Da. Duk-da Su Yan Uwan Rabi'u Sun So Hana Mata Shi. A Cewar su Abu Zasuyi Dashi Sai Suka Samu Rashin Goyon Baya Daga Sauran Dattijan Da Suka Rage Adangi Suka Tsawatar Musu Cewa, "Wannan Kuma Basu Isa ba Sunciye Gadon Yara. Sunyi Ribda Ciki Da Dukiyar Marayu Saboda Kin ALLAH Kuma Suce Matsugunni Ma Bazasu Barmu Su ba? Tau Innarmu Tawaye Ce In ba Tasu ba Tunda Ai Cikinsu Ba BARE Dan Haka Akul Dinsu Da Wannan Maganar." Jin Haka Yasa Suka Shafawa Kansu Lafiya (Dama In Akwai Tsoffi Masu Albarka Acikin Gida Akanci Albarka cinsu Wani Zubin A Raga maka ma DominSu. Wani Sa'in Bama Gane Hakan Sai Bayan Ransu Sai muga Abinda Bai Faru ba sanda Suke Raye Yau Yafaru Saboda ba Idonsu Nan Kusa.). Zaman Innarmu Karo Na Biyu A Gidan Taro (Family House) Kalubale Da Ta Tarar Yama Fi Na Farko, Sai Dai Imaninta Yashanye Komai. Tayi Tawwakalli Itadin Ko da Yaushe Baka Ganin Fuskarta Da Wani Kunci Zaka Ga Fuskarta ta Cikin Hasken Musulunci Da Kuma Tawwakalli Wanda Ko Da Yaushe Baka Raba Hannun ta Da Casbaha Ko Alkur'ani Hakanan Bata Gaza Akan Kai Kukanta Gurin ALLAH Ba Ako Wane Dare. Kari Ga Haka, Sallar Walha Bata Wuceta Sannan Tana Tuna Wata Kalmar Mamarta Datake Cemata "Fatima Ita Wannan Duniyar Dakike Gani Mumuni Yafi Shan Wahla Acikinta ALLAH Yana Jarabtar Mumini Da Abubuwa Masu Tsauri Amma In Yayi Hakuri Zaya Samu Daukaka." Kuma Sanda Mal Rabi'u ke Raye Komai Yana Yawan Cemata "Duniya Kurkun muminice Inno Saboda Haka Komai Yake Faruwa Muyi Hakuri Insha'allah watarana Zaya Wuce, Nidai ALLAH yaga Zuciyata Bani Da Wani Buri Da Yawuce Inga Na kyautata Rayuwarki Da Ta Yaran Nan Namu Ta Hanyar Sama Maku Ilimi Nagartacce Sai Dai Wani Lokacin Ina ji Ajikina Kamar Burina Baxai Cika ba inaji Kamar Nidin Bazan Dade Tare Daku ba." Aduk Sanda Yace Mata Hakanan Sai Ta tareshi Da Tattausar Muryar ta Cewa, "Kadaina Fadar Haka Insha'allah Burinka zaicika Kuma Zaka Kasance Taredamu Wayyanan Abubuwan Suke Tare Da Innarmu Suke Kuma Kara Karfafa Mata Akan Fuskantar Kalubalen Rayuwa. Bata Jima Sosai Ba Wani Manemin Yasake Fito Mata Sai Dai Shi Yasha Banban Da wancan, Danshi Cewa Yayi Tunda Tana Da Yara Dole 50-50 Zasuyi Ma'ana Raba Dae-dae Akan Daukar Nauyin Gida. Misali Zai Auno Gumi Ita Tayi Cefane Ko Kuma Dae Makamancinsa Kuma Nan Zata Zauna Dakinta Zai Dinga Zuwa Duk Sanda Girkinta Yazagayo Tunda Itace Matarsa Ta Ukku. Haka Innarmu Ta'amince Aka Sha Buki, Dafari Dae Yana Kwatantawa Da Tafiya Tai Nisa Kuma Sai Labari Ya Canza Salo. Ba Ruwansa Da Abinda Yadangace Ta Sannan Babu Zaman Lafiya Kullum Zagi Da Tsinuwa Dole Dae Shima Auren Ba Shiri Ya Tarwatse, Daga Karshe dae Innarmu Sai Hakuri Tayi Da Sha'anin Auren. Tunda Kowane Da Irin Tasa matsalar Kuma mafi Yawa Saboda 'Yayanta Ne. Kafin Nan Kuma Sai ga Tambarin Da Suka Mata Cewar Itadin Mai Farar Kafa Ce Waye -waye. Aka Zo Gabar Da Ta Kasa Hakuri Tayi Wa Yan Gidan Nasu Wankin Babban Bargo Wanda A Ranar Sun Sha Mamaki Ba kadanba. Dama Ance Mai Hakuri Bai Iya ba. Dole Kowacensu Tashiga Taitaiyinta Tana "ALLAH Baki Hakuri." Da Wannan Bacin Rai Ta Ziyarci Kawarta Akan Shawarar Meye Abinyi? Kawarta Tace Ta Tashi Suje Gurin Malaminsu Na Isalamiyyah. Bayan Gaisheshi Da Sauran Tambayar Ya Bayan Rabo Sai Kuma Tashiga Zayyana Wa Malam Abbas Halinda Take Ciki Takare Da Cema Sa Ita Gabaki Daya Garin Na Sayyinah Yafice Mata Daga Rai, Indai Ba Barinshi Tayi Ba, Tau Ko Da Yaushe Da Irin Abinda Zata Fuskanta. Kuma Dae Kai Itakam Ma Yanzun Kawai Bata Bukatar Ci Gaba Da Zama Garin Kawae." Malam Abbas Yashiga Nazarin Lamarin Tareda Girgiza Kai Kamar Kiski (Kadangare) Kafin Yace "Hakamma Dae-Dae ne, Tau Amma Ba Wannan Abun ji Ba, Inda Zata Nufa Kuma Tayaya Zata Rike Yan Marayunta?" Bayan dae Tunani Da nazarce-Nazarce Da Suka Zurfafa Itada Abokiyar ta Dakuma Malaminsu, Suka Tsaida Shawarar Ita Innarmu Ta Dawo Nan Cikin Garin Sakkwato A Shiyyar (Unguwar)Arkillah. Da Alkawalin Malam Abbas Zai Hada Ta Da Wani Amininsa Dazai Zame Mata Jagora Akan Komi Gefe Daya Kawarta Ma Tace kaunwar Innarta Na Nan Zata Hada Da ita. Nan Dae Suka Kitsa Suka Kimtse. A Wannan Ranar Innarmu da Abokiyar Ta Mai Suna Saudatu, Suka Tattara Duk Kayan Dakinta Suka Sai dasu Gurin Dillaliyyah Sa'anan Taso Har Gonar Da Take Gado Tahada Ta Saida Amma Saudatu Ta Nuna Mata tabarta Zatayi Amfani Wani Lokacin Mussamman Ga Diyanta. Zama Ba Kaddara Ba Dadi. Da Wannnan Shawarar Tabar Gonarta Hannun Wani Kawunta Wanda Tasu Tazo Daya. Yace, Za'a Dinga Mata Noman Rani Irin Su Kabaje, Da Salat, Da dai Sauransu. Adan Dinga Tura Mata Kudinta Itama Can Inta Samu Tana Iya Aiko Musu Sukara Cigaban Noman Ahaka Suka Rabu. A Wannan Ranar Innarmu Bata Runtsa ba Har Karfe 4 Nadare Tana Aikin Kimtsa Kayan Ta Bayan Kuma ta kammallah Shirinta Tashiga Nafil-fili. Karfe Bakwai Na safe Tashigo Motar Da Zata Kawota Cikin Birnin Sakkwato Itada 'Yan Yaranta. Bayan Tayi Sallama Da Duk Wanda Yakamata Tayi Sallama Dashi. Aminiyarta Saudatu Har Tashar Mota Ta Rakota Da Alkawalin In An Kwana Biyu Zata Zo Gurinta. Wannan Shine Dalilin Barowar Innarmu Mahaifiyar ta, Watau Sayyinah Zuwa Cikin Garin Sakkwato Daga Nan Kuma Tasoma Zama Gurin Kanwar Innar Aminiyarta Saudatu Kuma Sunyi Zama Na Mutumci Tunda Innarmu Bata da Qiwa Komai Na Gida Yimata Take Kuma Ga Yaranta Ta Dora Su Kan Tarbiya Mai Kyau Dan Haka Sai Zaman Su Yayi Dadi Da Inna Indo. Gefe Daya Ga Aminin Malam Abbas Yana Taimakon ta Akan Wadansu Al'amurrah Kuma Tana Ganin Haske Cikin Lamaru Nata Kafin Kace Komai Sai Gata Tadawo Cikin Hayyacinta Ita Da 'Yan Yaranta Suma Har Sun Fara Karatunsu Na Boko Da Isalamiyyah. Aiki Innarmu Take Tukuru Domin Ganin Ta kyautata Rayuwar Yan Marayunta. Itace Akawo Mata Wanki Tayyi Itace Surfe Itace Reno ma mutanen Yaransu Wasu Su biyata Harma Da Kyautatawar Sutura Da Abinci. Wanin Lokacin Har Inna Indo Ta Samma Ta Itama Danshine Take Cewa Zaman Innarmu Agurinta Alkairi ne. Gashi Ta rabata Da Aikin Gida Sannan Kuma Ga Kyautar Da Take Mata In AnyimaTa Itama. Suna tsaka Da Wannnan Kyakyawan Zaman Su Ne. Kwatsam Kuma Sai Ga.......... Taufa Readers Sai Ga Me? Muje Zuwa Labarin Fa Yanzun Aka Somasa.💪 Acikin Labarinan Akwai Lamurrah Masu Ban Sha'awa da Mamaki Harma Da Tausayi Da Kuma Wata Irin Gagarumar Soyyaya Da Zata Zo Taxama Silar Komai. Gefe Daya Zakuji Yadda 'Ya Mace Take Zama Jaruma Akan Matsalolinta Tayi Uwa Tayi Makarbiya Ta Zama Uba Ta Kuma Zama Uwa Sa'anan Kuji Yadda Tsagwaron Soyyaya Zaisa Itadin dae Haryanzun 'Ya Mace Zata Zamo Mai Sadaukarwa. Tashin Sanse Da kowace Irin Kwamacala Akwai Acikin Book Dinan Na SONEEE.....(Silar Komai) Ina Fatar Goyon Bayanku Wanda Shine Zai Karfafeni Wajen Cigaba da Kayatar Daku👌 [9/5, 9:12 PM] FA'IK: 💞 SONEEE....💕💕 (Silar Komai.) Fage....➡️3 Mallakar 👇 Fa'IK ✍️ Typing.....💻 GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. 07039676994 Bissmillahi Rahmanin Raheem Kwatsam! Sai Gasu Sun Wayi Gari Da Wani Bakon Al'amari Da Yazo Musu A Bazata Da Kuma Wani Irin Rudani Sosai. Inna Indo ce Sun Kwana Lafiya Amma Sai Wayuwar Gari Sukayi Da Inna Indo ta Karba Kiran Mahallici(Rasuwa). Bakadan Rasuwar Inna Indo ta Sanya su Al'ajabi ba, Duk-da Kuwa Cewa Itadin Mutuwar Wajibice Ga Kowa, Kuma Bata Sanarwa Balle Sallamar Gani Tafe, Kawae da Lokaci Yayi shikenan Kuma kamar dai Yadda Akace ne 'In Ajali Yayi Kira Tau ko Babu Ciwo A je." Haka Suka Shiga Zaman Makoki Na tsawon Kwana Ukku, Inda Inna Indo Tasamu Shaiadar Arziki Agurin Jama'a. Kowa ya budi Baki Alkairinta yake Fadi. Bayan Kare Zaman Makoki ne Kuma Aka Shiga Bincike Dame-Dame Inna Indo Tabari? Dawa-Dawa Ke biyarta Bashi?Da Waye take Biya Bashi Itama? Tau Dama Ita Inna Indo Diyarta Daya ce, Kuma Tana Aure A Garin Bernin Kebbi,Dan Haka Itace Jagoran Komai Sai Diyan Yanne Wanda Saudatu Aminiyar Innarmu Tana Cikinsu. Bayan dae komai Ya kammallah, Karshe Dae Sai Kitsawa Sukayi Kan Innarmu Taci Gaba da Zama Acikin Gidan Akan Sharadin Zata Biya Kudin Hayar Gida A Gurin Diyar Inna Indo. Innarmu Kuma Babu Tantama Ta'amince Kuma Anan Take Ta lissafe Kudinsu Kasa Tabasu. Dan Haka Yanzu Sai Gida Yadawo Gurin Innarmu Kadai Da Yan Yaranta Biyu. Daga Nan Sukayi Sallama Da Innarmu Kan Zasu Koma Gidajen Aurensu, Saudatu kadaice Ta Kara Kwana Biyu Bayan Sunyi Kama-Kama Wajen Shawarar Yadda Innarmu Zata Cigaba Da Zamanta Batareda Tanema Ta Rasa Ba, Shiyyasa ma Inda Inna Indo Ke Aiki Suka Je Akan Za'a Maye Gurbinta Da Innarmu. Aikinde Shine Wanke-wanke Da Kuma Yin Girki Wani Lokacin Da Wanki Da Sauran Yan Abubuwan da Kan Tusgo. Dan Sunce wa Gidan Ita Innarmu Diyar Inna Indo ce Mai Rasuwa. Dalili Da Yasa Suka Karbi Innarmu Kenan da Kuma Tayin Taci Gaba da Aikin da Ita Inna Indo Take. Dan Acewar Masu Gidan, Inna Indo Mutum ce Harda Rabi Kuma Sunyi Zama Da Ita Na Amana Tsawon Shekaru 20 Dan Haka Zuri'arta Abinso ce A Garesu. Wannan Kenan Bayan Dae Innarmu taraka Aminiyarta Saudatu wacce Bata Da kamarta Tasha, Sukayi Sallama Da yiwa Juna Fatar Alkairi. Innarmu Aka Dawo Aka Soma Fuskartar Sabuwar Rayuwa. Dafarko tadan Sha Wahla Sabo da Rashin Sabo Da Zamanta Ita Kadai A Gidan Da Kuma Gurin Aiki, Amma Da Aka Kwana Biyu Kuma Sai Ta Saba Tacigaba Da Aiki Tukuru Gefe Daya Tasamawa 'Yan Yaranta Makarantar Boko Da Isalamiyyah Suke Zuwa. Kuma ko Da Yaushe Cikin Hidimtawa Take Dan Dae Karsu Nema Su Rasa. Cikin Haka Aunty Aisha Tadawo Nan Mahaifi Tunda Wannan Shine Haifuwarta ta Tafarko. Zuwan Aunty Aisha A Gidan Yakara Dadi Suka Rage Kewa. Ga Kuma Mijinta Nayo Musu Aike, Dan Haka Suci Mai Kyau Su Sha Mai Kyau. Nanne Dai Kuma Suma Yan Yaran Innarmu Suka Dukufa Aikin Hannu. Abdul-wahab Yake Fita Aikin kaniKanci Shikuma Abubakar Ke Zuwa koyon Dinki. Izuwa Yanzu Rayuwa Ga Innarmu Sai Hamdala Dama Kowa Yasa ALLAH Gaba Lamarinsa Bai Lalacewa. Yanzun Kam Itada Sanyinnah Sai Dai Taje Ziyarar Yan Uwa ko In Buki Yatashi Wanda Take Zuwa, Kuma tamusu Sha Tara ta Arziki Wanda Hakanma Yakara Tabbatarmusun Itadin Dae 'ALKAMAR SAMAN DUTSE CE ALLAH KE BATA RUWA BADA SON MAKIYA BA🤗' Dan Haka Wasu Daga Cikinsu Suka Aje makaman Yakin Su Suka Dawo Ake Harkar Arziki, Wasun Kuwa Suka ki Sallamawa A Cewar su Yanzun ne ma Aka Fara. Dan Su Aganinsu Bai Kamata Ace Tafisu Komai ba Mussamman ma in Suka Tuna Cewa Sudin Ma Masu Iyaye Da Kuma Mazaje Basu Samu Irin Rufin Asirinta ba. balle Innarmu marainiya Ta Bangare Iyaye da Miji? ********* Tsakar Rana ne Sosai Ana Kuma Matukar Zafi In kaga Mutum Na Zufa (Gumi) Sai kace Ruwa ne Yakwarara Ajikinsa. Saurayine Kyakyawa Dashi Dan FULANI Sak Dashi. Naga Yana Ta Aikin Kwakwale-kwakwale Acikin Wata Kk Napep (Nufin Dae Yana Gyaranta ne) Yana Cikin Aikin su Naji Wani Mutum Na kwala Masa Kira Wanda nake kyautata Zaton Ogansu ne. "Abdul-wahab Ka Gama Gyara ma Matar can Motar ta Wai? Tunfa Daxu Nake Ganinta Nan Zaune?" Abdul-wahab Yace, "Oga ban kammallah ba Na'aika Asiyo Wasu Kayane Daza'a Samata A Motar, Kuma Haryanzun Dan Aiken Bai Dawo ba." Oga Yace, "Waye Ka Aika Halan?" "Samuel." "Samuel?" Oga Yamaimaita Sunan Cikin Takaici Kafin Yadora Da Cewa, "Kaima Ai kasan Abinda Kayi, Samuel Ai Ni in Ina sauri Bana Aikinsa Dan Nasan Halin Shiriri tarsa. Kaga?" Abdul-wahab Yadago Yana kallonsa Dan Jin Mai Zaice Masan "Kawo In Karasa Gyara ma Wannan Napep Danshi, Je kabi Sawun Samuel Kazo Kayi Hanzari Ka Gyara Wannan Matar Motarta Lokaci Yana Tafiya Kuma kaga Kila Sai ta Koma Zata Tanadi Abin Budin Baki." Hajiyar Tasako Bakinta Cikin Zancen Nasu Da Cewa, "ALLAH ma Albarka, Mutumin Nan Kamar kasani. Ina Zaune zullumin Danake Kenan. Mai min Aiki Kwana Biyu Tana Gida Jinyar Mahaifiyar ta Take." Oga Sunday Yace, "Tau in ba Damuwa Zaki iya Samun Abun Hawa kije Gida, saiki Bamu Address Dinki Shi Abdul-wahab Din in Ya Gama Gyara Zai Kai Miki Gida." "Aikuwa, Hakan Yayi." Hajiyar Tafadi Hakan Tana Mai Kokarin lalubo key din Motar Acikin Jakarta. Kafin Ta dago Kanta Tana Mai Mikawa Abdul-wahab key din Tareda Sanar Dashi Adreshinta. Daganan Kuma suka Tare Mata Mai kk Napep. Yayinda Shikuwa Abdul-wahab Yatafi lalubo Samueil. Gabda Shan Ruwa Yagama Gyara Motar Dan Haka Dole yabiya yakarbi Kayan fruit (lemu dasu ayaba) Da Yasaba Siya Masu Akullum Kafin Yanufi Gida. baishiga Gidan ba Yaro Yabawa Cewa Yakaima Innarmu Zaije Yadawo." Su Innarmu da Abubakar Suna Tsakar Gida Saman Tabarmar Da Innarmu ta Saba jere Musu Kayan budin Baki, Sanda Yaron Yakawo Sakon Yana Sanar Dasu Yanda Abdul-wahab Din Yace. Sae Suke Mamakin Hakan, Dan Sun Saba Duk Runtsi Gida Suke Shan Ruwa A Tareda Innarmu. Dan Haka Ran Innarmu A Bace Tamikowa Abubakar Yar Wayarta Tana Cewa "Nemomin lambarshi inji Dalilin shi nakin Zuwa Gidan." "Bari wayarki Innarmu Ina da Katy Cikin Tawa Wayar Bari inkirashi inji." Abubakar ne ke Wannan Maganar Yana Kokarin Fitarda Wayarsa dake Cikin Aljuhunsa. Kara day, Biyu, Ana Uku Aka Daga Wayar "Ya Abdul ......" "Dan ALLAH Karka Cika Ni da Surutu Oga Yasani maida Motar da na Gyara Gashi ma Na kawo wa Mai Motar Zan Dawo Yanzu." Abubakar yakashe Wayarsa Yana Dan Karamin Tsaki Gamida Cewa, "Kajimin Ya Abdul Sai kace Nima Bana Jin Kishirunwa azuminan ko Ni Nasa Shi yin Azumi..." Innarmu Na tsura Masa ido Tace, "Meyace maka halan? Ai Shiyyasa Nace maka Ka kiramin Shi A Wayata." "A'a Innarmu Bafa komai bane ba, Yace Motar da ya Gyara A Gurin Aikinsu ne Ogansu Yace ya mayarwa da Mai ita Kuma Yanzun Zai Dawo." "ALLAH maidashi Lafiya." Innarmu Tafadi Hakan Kuma Ga Alama dae Bata ji Dadin Hakan ba. Kafin Tamike Tana Cewa, "Tashi Kayi Arwallah." Tare Sukayo Arwallah Kafin Suka Zo Suka Fara Budin Baki. Ba Abdul-wahab Nan, Dan Haka Sai Sukaji Duk Abin Ba Dadi. Akwai Shakuwa Sosai A Cikin Iyalan Innarmu. Bayan Sunyo Sallar Magariba Suka Dawo Dan Cigaba da Budin Baki, Sai ga Abdul-wahab Din Yashigo Kaitsaye Kuma yararumi Kofin Da Abubakar Yacika Kunun tsamiya Dashi Dan yasha. Abubakar Yayi Saurin Fisge Kofin Yana Mai Matsawa Kusa da Innarmu Yace, "Kaji Ka dae Yaya Abdul Nima Fa Yunwar Nakeji." Abdul-wahab Yasake Yun kurowa Da Nufin Zai Amshi Kofin Innarmu Tashiga Zancen Nasu Da Cewa, "Wai KU meyasa bakwa Girma ne? Bazaka Dau Naka Cup din kadibi Wani Kunun ba Dole Sai Nashi?" "Innarmu Nashi Yahuce. Wanga(Wannan) Kuma da Zan Diba Yana da Zafi ne Shiyyasa Fa." Abdul-wahab Yafadi Hakan Yana Wani zunbura Baki Kamar Dan Yaron Goye. "Tau Amshi Bari Nazuba Wani." Innarmu Tamika Masa Nata Abubakar Yayi wuf Zai Amshe Yana Cewa, "Innarmu Wallahi Bazaki Bashi ba. Aikema Zubawa kikiyi kika Jira Yahuce Shima Yazuba." Abdul-wahab Yafisge Kofin Yana Kaiwa Bakinsa Yasha Yayi Masa Gwalo Yace, "Dan Ciki Baki (Bakinciki) Kawai." Itadai Innarmu Bata ce Komai ba Sai ma Tanemi Yuka Tana Yanka Kayan Fruit dinda Abdul-wahab Yasiyo Bayan ta wankesu. "Wayyo! Innarmu!" Tajuyo Afirgice, kafin Tai Magana Abubakar Yace, "Ya Abdul ne Ya Mitsile Mun Hannu Dan Zan Dau Dankalin Da ke Gabansa." "ALLAH yashiryaku." Abinda Innarmu Tace Kenan. Tau Haka dai Suka Gama Budin Bakin Sai Hayaniya Suke Mata. Dama Haka Suka Saba, Shiyyasa Daxun Da Abdul-wahab Din Bai Nan Sai suka Ji Ba Dadi. Haka Suka Kammallah Cikin Farinciki Kafin Suka Mike Abdul-wahab Yadauki Darduma Shida Innarmu Zasuje Masallaci Sallar Asham (Tarawihi) Shikuwa Abubakar Tela Dole Gurin Dunki Aka Nufa Dan Karkare Dunkunan Mutane Da Aka Amsa. Daza Su Rabu Har Abdul-wahab na Zolayarsa Cewar, "ALLAH Yasa Yaro yaki Gama Dunkunan Mutane Yasha Waju (Duka)Wurinsu." Abubakar ya Zunbura Baki, "Kina Jinshi Ko Innarmu ba?" Innarmu Tace, "Rabu Dashi Dan Autana, Lafiya Lau Zaka Gama Dinkuna In Yazo Hada Lefe Karka Masa Dinki." Abubakar Yabar ke Da Shewa! Kafin Yamasa Gwalo Yawuce Da Gudunsa. Yayinda Abdul-wahab Yace, "Zaka Dawo ne Ka sameni Ai." Innarmu Tace, "Nidae Wuce Muje Kanaji Har Antayar Da Salla." Koda Yaushe Haka Innarmu Take Tareda"Yan Marayunta Da Ayanzun Suka Girma, Suka Zama Santala-Santalan Samari Kowa Kuma Yake Da Sana'ar Hannunsa Gefe Daya Suna Ci Gaba Da Karatunsu Inda Abdul-wahab Yake Karantar Aikin Lawyer A Jami'ar Usman Dan Fodiyo Shikuwa Abubakar Yana Karatun sa A Umar Ali Shinkafi polytechnic Dakenan Sokoto Inda Yake Karantar Computer seince. A Tare suka Rubuta Jamb Tau Amma Shi Abubakar Makin Nasa Bai Kai Yanda Jami'ar ke Bukata ba Dan Haka Sai Yashiga poly din Amma Yinin Ranar Yaci Kuka Sai da Su Innarmu Sukai ta Lallashinsa Kan Karbar Kaddara. Tau Yanzu Karfinsu Yakawo, Dan Haka Komai Sun Daukewa Innarmu Sai Aikin ne Kawai Bata Bari ba, Dan Acewar ta Sun Saba Sosai Da mutanen Kuma Suna Girmama ta. Azumi Yayi Nisa Sosai Kowa Kuma A Yanzun Shirin Sallah Yake Mussamman Bangaren Dinke-Dinke. Anshigo Goma Ta Wuya Inji Malam Bahaushe. Danhaka Azumi Bugun (Dukan) Mutane Sosai. Yau Takasance Jumu'a Ce Ankuma Kwalla Rana Sosai Kamar Yadda Akan San Kowace Jumu'a Da Rana. Mutane Sai Sayen Pure water Ake Ana Zubawa A Jiki Yayinda Sauran Samari Suka Nabba'a Zuwa Tafki Suna Wuni Acikinsa. Abdul-wahab Yana Kasan Rumfar Wurin Aikinsu. Yau Basu Da Aiki Kwarai, Dan Haka Yayi Tunanin Bari Yakira Abokinsa Yusuf Mai Tukin Kk Napep Yazo Yadaukeshi Sufita Tare. Dan Wani Lokacin Hakan Suke In Yana Nishadi Yakan Kira Yusuf Din Yazo Yadaukeshi Sufita Aikin Napep Din Tare. Haka Shima Yusuf Din Duk Sanda Yabada Kk Napep Din 'Taba' Ga Wani Sai Yazo Garejinsu Yazauna. Yauma Suna Tare Suna Aiki. Ana ta Kiraye-kirayen Sallah Magrib Sukayi Parking Gaban Wata Mata Dake Gefen Titi Tana Tuyar Kwasai Da Dankali Dakuma Doya Harma Da Plantain Gefe Daya Ga Kunun Koko. Wurin Duk Yan Kk Napep Ne Da Masu Mashin-Mashin Dakuma Dai-Daikun Mutane Da Suke Ta Hada-Hadar Budin Baki Gurinta. Suna Parking Gurin Yusuf Yayo Musu Odar Komai d Komai Amma Abdul-wahab Din Yakasa Cin Komai Saboda Shi Inba Abinda Innarmu Tadafa Ba Bayaci Wannan Abinda Suka Sabane Shi Da kanensa. Yusuf Yakallesa Yana Danna Bready Da kwasai Abakinsa Yana Mai Cewa, "Meye Kayi Wani Zaune? Kaci Mana" Abdul-wahab Yace, "Ni Gaskiya Muyi Sauri Kawai Ka Kaini Gida inba Abincin Innarmu ba baxan ci ba." Yusuf Ya kallasa Yana Dariyar Nan Ta Shaidanun Abokai Yace, "Tau Yayi Dan Innarmu." Bayan Yaci Dabino Sai Yadauki Ruwan pure water Yasha. Dayan Pure Water kuwa Yafashe Yasoma Arwallah. Kamar Wacce Aka Jefo Yaganta Agabansa. Farace Tas! Kuma Tana Da Wushirya Tsakiyar Haurunta Na Gaba Gata Yar Madaidaiciya A Tsawo Baza'a Ce Mata Mai Tsawo ba Kuma Baza'a Ce Mata Gajeruwa Ba. Sai Dan Dumulmulallen Jiki Da Take Dashi (Yar Duma-duma 😀) Sanye Take Doguwar Riga Mai Matukar Laushi Ga Dan Karamin Hijab Da Mata ke Cewa Hapsunnah Ta Yane Jikinta Dashi Wanda Iyakarsa Bisa Kafadunta. Duk Acikin Abinda Bai Gaza Minti Biyar ba Abdul-wahab Yafahimci Hakan. Rike Take Da Flet Mai Dauke Da Soyyayar Doya Da Kuma plantain Gefe Daya Ga yaji, Sai Kuma Lemun kwali Mai Sanyi Da Take Rike Dashi Tace, "Bansan Meyasa Ba Tun Daxun Nakasa Sukuni Kan Naga Baka ci Komai ba. Shine Nace Bari Nayi maka Wannan Hidimar Ko Da ko Zaka Gwasalani ne." "Mexai Sa In Gwasalaki Bayan Karamci Kika min? Wanna Ba Halin Mutane Kirki Bane Dan Haka Nagode Kwarai da Wannan karamci Sosai." "Tau Ka Karba Kaci Abinda Nakawo Ma please?" Tafadi Hakan Da Wani Salon Rokonsa Kamar Inya ci Cikinta Zaiyiwa Aiki. Abdul-wahab yagirgiza Kai, "Kiyi Hakuri Ni Inba Innarmu ce Tayi Girki Banaci." Tabude Baki Da Nufin Yin Magana Mamarta Ta Kwalla Mata Kira Tana Ta Fada, Cikin Yarensu Da Abdul-wahab Bai San Wane Iri Bane Sai Dai komeye Take Cewa Baya Rasa Nasaba Da Tana Mata Fada Akan Tabarta Da Ayyuka Costumers Sun Mata Yawa Tazo Ta Sallami Wasun. Abdul-wahab Yace, "Kingani Ba, Yakamata Ki Koma Kan Aikinki." "Ba Zan Koma ba Kuma Bazanji Dadi ba Indae ba Karba Kayi ba." "Ai Nagaya Maki Tsarina, Inkuma Baki ji Da Kyau Bane Bari In Sake Gayamaki. 'Ni Bancin Girkin Da Ba Innarmu Bace Tayi Shi ba." Tadade Tana Kallonsa Kamar Baxatayi Magana Ba Kafin Ta Sauke Ajiyar Zuciya, "Tau Shikenan, Yanzu Bari Nasama A Leda Ka Kaima Innarmu Din injini." Yayi maza Ya Girgiza Kansa "A'a Gaskiya Tau A Wace Dankatar Zan Kai Mata Abu Ince Gashi?" "Bisa Ga Dangatar Musulunci Ko Itadin Ma Zaka Kawar Da Ita ne?" Yagaji Da Surutu Dan Yana ma Mamakin Yanda Suka Dade Suna Magana. Dan Haka Sai Yace Mata Takawo Zai Kai. Kafin Yamike Yanufi Masallaci dake Kusa da Gurin Dan Yin Sallah. Dama Shi Yusuf Tuni Suna Massalacin. Bayan Sunfito Sun Shiga Kk Napep Zasu Wuce Sai Gata Tana Miko Masa Ledar Tareda Wayarsa Tace "Niyyar Ka Katsere Ko? Tau Da Kayima Kanka Dan Dazu Kana Arwallah Ka Tafi Kamanta Da Ita." Batareda Yace, Komai ba Yamika Hannu Yakarbi Wayar Da Ledar A Ransa Sai Mamakin Yake Lalle Da Yatafi Da Yayiwa Kansa. Shikuwa Yusuf Harda Turo Kansa A waje Yana Mata Godiya Ita Kuwa Cewa Take "Ina Gaida Innarmu." Yusuf Yace, "Zataji." Kafin Suka Soma Tafiya Sai Shakiyanci Yake Yiwa Abdul-wahab Yana Kwasar Dariya. "Mutumin Kayi Kasuwa Fa? Lalle Wannan yarinyar Taciri Tuta Cikin lokaci Kankani Har Ka Gayamata Su Innarmu?" Shidai Abdul-wahab Shiru Yayi Masa, Burinsa Su Isa Gida Yaci Girkin Innarmu. Da Asuba Suna Suhur Sai Ga Kira Da Bakuwar Number Bayan Sallama Take Tambayarshi "Ina Innarmu Ka Kaima Mata Sakon Da na Baka?" Sai da Yacire Wayar A Kunnesa Yaduba Da mugun Mamakin Ina Ta Samu Number Kafin Yasake Maida Wayar A Kunnesa Da Nufin Tambayar ta "Ina Kika Samu Number Na?" Sai tarigashi Cewa "Karka Tambayeni Ina Nasamu Number ka, Ni Da Kaina Zanbaka Wannan Amsar Yanzun Ka'amsa min Waccan Tamabayar Dana ma." Jikin Abdul-wahab Yayi Sanyi Da Yanda Yagu Su Innarmu da Abubakar SunTsura Masa Ido Sai Yakasha Shan Kunun Da Ke Hannun Sa Yabuge Girgiza Cupin Kawae. "Ya Kayi Shiru? Katyna Fa Ke Tafiya." Dagacan Tace Masa Haka. "Ina Wani Uxurine Yanzun, Zamuyi Waya Anjima." Da Fadin Haka Da kashe Wayarsa Duk Lokaci Daya Yayi su. Yadauki Cupin Kunun Yasoma Sha A Hankali "Idan Bakayi Hanzariba Za'a Kira Assalatu Bakaci Komai ba." Yadago Yana Kallon Innarmu Dan Ya tantace Da Wane Kalar Yanayi Tayi Masa Magana.....Sai Kuma Jikinsa Yadauki Makarkata. Nima Jikin Nawa Makarkata Yadauka Wayar Tagagareni Riko Saboda Nima nashiga makamancin Rudanin Da Abdul-wahab Yake Ciki. Dan Haka Zan Dan Nissa Anan......... Muje Zuwa Raedars Nawa Shin Meye Yake A Rufe Wanda Bamu Sani ba? Kuma Meye Na Wannan Fargabar Da Abdul-wahab Keyi? Mutara Daku A page Na Gaba. [9/5, 9:13 PM] FA'IK: 💞💞 SONEEE....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....4 A....... Maimaikon Pages 123, Zankoma Da Yin Amfani Da Chapter.👌 Mallakar 👇 Fa'IK ✍️ Typing.....💻 GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. 07039676994 Bissmillahi Rahmanin Raheem Abdul-wahab Duk Sai Yarasa Nutsuwar Sa Amma, Da Yayi Wani Tunani, Kawai Sai Yamaze Yayi Mirsisi Dan Kar Yabada Da Kansa. Dan Haka Da Kuzarinsa Yabude Kular Dake Gabansa Yadibo Mal-Malar Tuwo Leda Biyu Yasaka A Flet Kafin Yazuba Bushashiyar Miyar Goro Da Wadatu Da Man Shanu Sai Kyalli Take, Yasoma Aikawa Cikinsa (Dama Can Shi Baya Wasa Da Ci😜) ππππππππ Cikin Kwana Ukku, Abdul-wahab Yakamu Da Wata Irin Zazzafar Soyyayar Da Baisan Ya'akayi Tayi Tasiri Akansa Ba. Ikram Gaba Daya Tabi Ta Mamaye Zuciya Da Ruhinsa Harma Da Tunanin Sa. Saboda Acikin Kowane Lokaci Cikin Kiransa Take Karramsa Takeyi Do Kowane Abu Da Yazamo Mallakinta, Kuma Komai Nata Soyyaya Yake Nuna Masa, Ayyukanta, Kalamanta, Gangar Jikinta, Ruhinta, Kai Har Idununta Idan Ya Kallah Ba'a Bunda Yake Hangowa Face Tsantsar Kauna Da Soyyaya. Tau Shikuwa Waye Shi da Zai iya Watsi da Wannan Masoyiya? Dan Haka dae Tuni Abdul-wahab Yakarbi Tayin Da Khaleesat Tayi Masa (Kamar Yadda Momynta Ke Kiranta) Suka Antaya Duniyar Masoya Suke Ci Gaba Da Lulawa. Azumi Dae Yangangara Har Yakawo Gangara Dan Yauma Kowa Kagani Da Dan Radionsa Yana Saurare Yaji Me Sarkin Musulmi Zaice Akan Ganin Wata? Dan Haka dae Yau Muna Sa Ran Daren Sallah ne, Mata Dai Mussamman ma 'Yan Mata Tuni Aka Baxama Ana Kitso Da Lallen Sallah, Wasun Ma Har Andawo Gida Anfara Shirye-Shiryen Abincin Sallah Gobe. Khaleesat Na Cikinsu Dan Ansha Lalle Yazauna Radau! A Yan Hannayenta Da Santala-Santalan Kafafunta Abinka Ga Farar Macce Sai Kyalli Take, Ga Kitso Anzubo Wasu Gaba Wasu Kuma Baya, Sai Kai Komo Take A Tsakar Gidan Nasu Domin Taya Momy Girki. Lokaci-Lokaci Tana Duba Wayar Momynta Dan Sunyi Da Abdul-wahab Zai Kirata. Shikuwa Abdul-wahab Yana Can Gida Wanka Ake Sha Bayan Andau Gayu Aka Fito Tsakar Gida Ana Daura Agogo Innarmu Dake Ta Kai kawo Tsakanin Dakinta Da Madafi(kitchin) Dan Tana So Ta kammallah Miyarta, Da Gari Ya waye Tuwon Laushinta Kawai Zata Tuka. Ta kalli Abdul-wahab Din Tace, "Kai Kuma Wannan Gayu Haka Sai Ina? Ko Duk Zumudin Sallarne Ka Kasa Bari Sai Gobe?" Yayi Dariya Kafin Yasa Hannun Yadauki Tsunkin Naman Miyar Da Inna Ta soya Yajefa A Baki Yace, "Kai Innarmu Wane Gayu ne Nayi? In Yusuf Yaji Kina Fadar Haka Ai Sai Yace Yafasa Baya Son In Rake Sa Gurin Budurwar Tasa." "Oh Tau Can Kuka Nufa Kenan?" Innarmu Ta tambayeshi Tana Kokarin juya Miyarta Kafin Ta debo Ta Dan Dana Danji Komai Yaji. Kafin Tace, "Sai Nake Jin kamar Miyar Nan Gishiri Yaso Yin Yawa Fa?" Abdul-wahab Yadan Tara Hannun Sa Yana Cewa "Dan Sammin Inji." Wanda Yayi Dae-dae Da Shigowar Yusuf Gidan Idonsa Yakai Kan Abdul-wahab din dake Ta Ayikin kwadai, Yayi Dariya Yace, "Innarmu Sarkin Kwadayin Nan Na Nan ya Hanaki Aiki ko?" Kafin Innarmu Tai Magana Abdul Yayi karaf Yace, "Eh Din Ya Ranka?" Innarmu Tace, " Ya Ransa ko?...." "Innarmu Raina Fari Sol." Yusuf Yafadi Hakan Yana Mai Kokarin Zama Kan Wata Kujera Dake Tsakar Gidan Abdul-wahab Yayi Maza Yace, "Kaga Dan ALLAH Karka Zauna, Tashi Zakayi Mutafi Yanzu Inkuka Fara Zance Kaida Innarmu Muda Tafiya Sai Safe." Dai Dai Lokacin Shima Abubakar yafito Daga Cikin Toilet Yayo Wanka Yace, "Kajimin Ya Abdul Tunda Kai ka Cika Cikinka Shi Baxaka Barshi Yacika Nashin Ba?" Kafin Yakalli Yusuf "Kaga? Ya Yusuf Bari Inzubo Mana Abinci Muci In Yaso Ko'ina Zakuje Sai Kuje. Kai da ma Za'ayi wa Rakiyar Baka Sauri Sai Shi?" Kafin Abdul-wahab Yace, Wani Abu, Innarmu Tarigasa Cewa, "Yawwa Dan Auta Na ALLAH Ma Albarka Zo Kazubo Maku Abincin Namanzo." Innarmu Takarasa Maganar Cikin Sigar Zolaya. Gaba dai Sukayi Dariya Banda Abdul-wahab Da Yayi Fuska Yana Cin Magani "Nidae Innarmu Nagano Abbakar Dinnan Yamana Farrakau Dole in Tashi Tsaye." Gaba Dai Sai Da Suka Bushe Da Dariya Kafin Innarmu Tace, "Ba Wani Farrakau Da yayimin Illah Gaskiya Da Yafi Ka so Kuma Yafika Aiki Da Ita..." "Cau! Innarmu Telan Ne Mai Gaskiya? Lalle ma Innarmu, Ko Yanzun Kinsan Iyakar Adadin Wayanda Gobe Zasuyi Sallah Ba Dinki Saboda Rashin Gaskiyar Tela?" "Tau Nidae Nasan Bada Dan Autana, Dan Tun Da Watan Azumi Yakama Kwana Gashi Bayayi, Kuma Ban Taba Jin Wani Ya Sallamo Masa Cewa Yasaba Alkawali Sai Dai Yace Yazo Yakarbi Dinkinsa." "Gaya Masa Dae Innarmu, Ai ba Duka Aka taru Aka Zam Daya ba." Yusuf Ne Mai Wannan Maganar Yana Kokarin Kai Cokalin Da yaciko Abinci Abakinsa. Abdul-wahab Yahararesa Yace, "Dan ALLAH Malam Yi Kagama Mutahi Dare Keyi Safiya Ba, Tunda Nidae Nagano Gidannan Kun Hade min Baki." Innarmu Ta Kalli Su Yusuf Tareda Cewa, "Kuyi A Hankali Har KU kammallah In Yagaji Da jira Yatafiyarsa." Kafin Tamikawa Abdul-wahab Wayarta Tana Cewa, "Kamomin Gidan Radio Naji Ko Sarki Yafara Sanarwar Ganin Watan," Yamikawa Innarmu Wayar Bayan Yakamo Mata Tareda Mikewa Suka Nufi Hanyar Fita Shida Yusuf Suna Yiwa Innarmu Sallamar Suntafi Sai Sundawo. Abubakar Yace, "Yusuf Kajira Akawo Mana Kunun Ayar Mana." Yusuf Kamar Zai Tsaya Abdul-wahab Yafisge Sa Da Sauri "Ai Wallahi Baka Isa Ka Tsaida mu Ba Kasha Kunun In mundawo." Suka Fice Ana ta Dariya. Abubakar Yamike Yana wanke Hannunsa, Dan Dae Sukam Innarmu Ta Sabar Musu Cin Abinci Da Hannun Dan Haka Ko kadan Basa Jin Dadin Ci Da Cokali Yana Mai Cewa, "Innarmu Nifa Nafara Zargin Rakiyar Nan Ya Abdul ne Za'ayi wa Kawai Dai Ya Layance Mana ne." "Fita Batunsa Ai Tuni Na hango Jirginsa Kawai Na Zura Masa Idone Inga Iya Gudun Ruwansa." "ALLAH Yahadashi Da Tagari, Bari Ni inkoma Shagonnan Akwai Kayan Da Zan Kamallah Masu Su Zasu Zo Su Karba Dama Nadawo In Dan Watsa Ruwane." Innarmu Tace, "ALLAH bada Sa'a, Aci Gaba Da tsare Gaskiya Dan Autana Banda hadaMa Azo Ancinye Kuddin Mutane Kuma Dunkunan Su Yamaka Yawa baka Gama Na Wasu Ba, Ka karbi Kudin Na Wasun. Saba Alkawali Ba Dadi." "Innarmu Ai in Nayi Haka Tamkar Cin Amana ne Ga Tarbiyar Da Kika Bamu. Duk Abinda Zanyi Nakan Yi Iya Abunda Nasan Zan iya Kuma Baza'a Ga Rashin Gaskiya ta ba. Shiyyyasa Ma Tun Wata Yanada Kwana Ashirin Nadaena Karbar Dinki Dan Ma Wannan Karon Abubuwan Sunzo Mutane Ba Kudi Da Ai Tun Goma Zan Rufe Tau Amma Saboda Rashin Kudi A Hannun Jama'a Wasun Sai Yanzu Ma Suke Samu Suna Kawowa." "Rashin Kudi Kam A kasarnan Ai Yazama Jiki Saidai Muyi Ta Adu'a." "Shine Kawai Fa Abinyi." Abubakar Yafadi Hakan Yana Kokarin Fita Daga Gidan Kafin Kuma Yadawo Yana Cewa "Yawwa, Namanta Innarmu Nagama Dinkunan Maman Walida (Auntynsu Aisha Suke Cewa Haka Dan Diyar ta Biyu Hakane Sunanta) Harma Daxun Naje Tasha Na Tura Mata Abubuwa ne Sukamin Yawa Bansamu Na Kirata ba Inji Ko Sakon Yazo." "Eh Sakon Yazo, Dan Takira Ni Dazun Tacemin Ma Ukku Ga Sallah Zasu Zo Dan Za'ayi Bukin Wata Abokiyar Karatunta Da Sukayi Makaranta Atare." "Eyyah Tau ALLAH Yakaimu Lokacin, Ni Naje Innarmu." "ALLAH bada Sa'a Auta Yakuma Bada Halal." Yafice Yana Cewa 'Allahumma Ameen Innarmu. ALLAH Barmana Ke." Tau Su Abdul-wahab Fa Iyayen Soyyaya? Bari Muji!👂 ******* Tunda Suka Fita Yusuf Sai Tsokanarsa Yake "Mutumina Khaleesat Ta Tafi Da Zuciyarka Da Yawa Fa? Ko Ni Da muka Jima Da Fa'iza Bamu Kaiku Sharbar Soyyaya Ba." Abdul-wahab yacije lebensa Nakasa Yana Cewa, "Naku Wasa ne." Yusuf Yakama Haba Kamar Mace, Cikin Mugun Mamaki Yace, "ALLAH Mutumena?" "Sosaima ko Ku Me Ma Kuka Sani A Son?" Abdul-wahab Yafadi Hakan Yana Kokarin Danne Dariyar Da Tazo Masa. "Aikuwa Dae. Tau ALLAH Samu A Danshin KU." Yusuf Yafadi Hakan Yana Fanshe Mamakin Da yakeji Na Abokin Nasa. "Ameen" Abdul-wahab Yafadi Hakan Batareda Yabawa Maganar muhimmanci ba. Yusuf Yace, "Dama Fa Naji Ance KU Ustaxzanann Baku Iya Son A...." "Kaga Mal Nidae Karka Cikani Da Tawilinka Da baya Karewa, Ina Zamu Fara Zuwa? Kasiyowa Fa'izar Mayafin Da Takalmin Da Kace?" "Nope Bansiya Ba Gaskiya, Yau Banyi Aiki Sosai ba Wallahi, Kasan Azumin Daren Sallah Sannan Gashi Kuma Umma Tayi Ta Aikena Cefane Sai Nadawo Tace Tamanta Ba'a Siyo Wannan Ba Ga Zubaida Uwar Iyayi Harda Zuga Umma Inbasu Kudi Zasuyi Zobo." "Kajika Tau Da can Wazai Musu Inba Kai ba. Muje Kasuwar, Akwai Yan Kudi Hannuna Inkuma Basu Ishemu ba Na Sato Atm Din Abubakar Sai Mushiga Account dinsa Muyi Masa Ta'anati Kasan Wannan Watan Su Kakarsu ce Tasamun Kudi." Gaba Dae Suka Farke Da Shewa Suna Cafkewa Irin Na Gayu Nan. Kafin Yusuf Yace, "Hooooo Abokina Kana Cinye wa Wallahi, Amma Naso Mu Fara Biyawa Muyi Aski." "Mubar Askinnan Kawai Sai Mun Dawo Dan Nasan Yanzun Shagon T Boy Baya kalluwa Dan Taron Jama'a." "Oh Right Never Damuwa." Yusuf Yafadi Haka Suna Bushewa Da Dariya Dan Wannan Shine Turancinsu In Suna Jin Shakiyanci. Kaitsaye Kasuwar Kanawa Sukaje, Bayan Sun Gama Shan Wahla Da Gow slow Da Suka Iske Wurin. Damma Karshe Dae Dole Wuri Suka Samu Sukayi Parking Din Kk Napep Dinsu, Suka Taka Da kafafunsu Saboda Cincinrodon Al'Umma Wani Kan Wani Mussamman Ma dae Yan Mata Da Ayanzu Ake Fitowa Karasa Siyayyar Da Ba'a Samu Anyi Ba. Su Abdul-wahab Suka Shiga Jerin Mutane Domin Siyayya Yayinda Yasuf Ya Darje Yazabawa Fa'izarsa Takalmi Da jakkarsu Tareda Sarka Da Yan Kune Harma Da Mayafi Masu Dan Karen Kyau. Lamarin Da Yabawa Abdul-wahab Sha'awa Shima Yashiga Tsintar Tasa Sahibar Kayan Da yake Ganin Sun Dace Da'ita Kai Ba Ita Kadai Ba Harda Innarmu Tasamu Nata Rabon Suma Sukayi Sayi Boxes Da Singilet Dakuma Takalmi Anan Kam Harda Abubakar Aka Siyawa Dan Kudin Nasu Basu Ishesu Ba Dan Haka Dole Dae Saida Suka Shiga Acc Din Abubakar din Sai Dai Basu Diba Da Yawa ba. Dan ma Sai Da Aka Zo Siyen Boxes Dinne Suka Bada Atm Aka Cire A Account din Abubakar. Abubakar Dae Na Dinki Sai Ganin Yayi Yan Banki Sun Masa Alart Na Cirar Kudi Da Akayi Account Dinsa, Da Yaduba Sai Bai Damuba Dan Yasan Ya Abdul-wahab ne. Kuma Shida Abinsa Duk Na Abdul-wahab ne. Acikinsu Babu Mai Yiwa Wani Iyaka Da Abin Hannunsa Dan Komai Nasu A hade Yake. Wannan ma Kuma Yana Daga Cikin Tarbiyar Da Innarmu Tarenesu Da Ita. (Uwa Tagari Itake Samarda Al'Umma Tagari. Dan Haka Kalubale Garemu Iyaye Mata🙏) ********** Karfe Daya Nadare Suka Baro Kasuwar Kanawa, Inda Suna Kan Hanya Muhawara Ta Barke. Yusuf Yace Gurin Sahibar sa Za'a Fara Zuwa Abdul-wahab Yaja Tunga Kan Shima Gurin Tasa Za'a Fara Zuwa. Karshe Dae Dole Yusuf Yayi Nasara, Bayan Sun Tsaya Sun Kalli Uzurin Shi Yusuf Din Cewa Iyayen Fa'izarsa Suna da Tsanani Ko Yanzun Ma Babu Dole Abarta Tafito Sai ma Dai Taci Albarkacin Yau Take Daren Sallah. Dan Tuni Sarkin Musulmi Yayi Sanarwar Anga Wata Insha'allah Gobe Daya Ga Watan Shawall. Da Zuwan Su Da ganawa Da Fa'izar Bai Wuce Minty Ashirin Ba Suka Mata Sallama Bayan Taciko Musu Leda Da Soyen Nama Miyar Sallah Da Kunun Zaki. Suka Nufi Gidan Su Khaleesat Kira Daya Tadaga Dama Takagara Abdul-wahab Yakira tan Kai! Jima Nakeyi Kamar Nayi Tsuntsuwa Inje Gareshi Jiya daene Bamu Hadu ba, Amma Sai Nake Ji Kamar Munyi Wani Lokaci Mai Tsawo Bamu Ga Juna ba. "ALLAH Yasani Abdul-wahab Yatafi Da Zuciyata." Bayan Na Ajiye Wayar Momy Dake Gaban katuwar Roba Tana Motsa kullun Wake Sai Hamma takeyi, Tacemin "Abdul din Yaxo ne?" Nadubeta Ina Murmushi Nace, "Eh Yazo, Momy Duk Naga Kamar Kin Gaji. Nace Maki Momy Ai Shinkafa Da Miya Itace Ba Wahla Miyarmu Kawai Zamuyi Da safe Shinkafarmu Kawai Zamuyi Kince A'a Ke Sai kinyi Wani Abincin Yan Garinku Na Al'adarku Gashi Ya......" Momy Ta Rarumo Takalmi Tana Jefata Dashi Tana Cewa, "Gidanku! Abincin Al'adarmu Yake Da Wahlar? Kawai Dai Ke Dan Baki Saba Dashi Bane Bari Nayi Abincin Kici Kiji Bazaki Kara Son Wani In Ba Shi ba ja'ira. Ko Dadynku Haka mukai Dashi Amma Yanzu Shi da Kansa Yabugo Waya Ayimasa Irin Abincin Garinmu Gobe Da Sunfito Sallar Idi Zai kamo Hanya." Na Nufi Daki Bayan Nasamu Nasarar Kaucewa Takalminda Momy tajefo Ni Dashi Ina Fadin, "Hum'um ALLAH sa Zan Iya Cin Wanna Abun Da Haryanzun Nakasa Gane Ya'ake Hadasa." Nadubi Kaina Sama Da Kasa! Siket Da Riga ne Yan Kanty Nake Sanye Dasu, Sunbi Jikina Sunyi Das Sai Kaina Da Yasha Kitson Sallah, Na Dora Hullar Yorubawa Akaina Najanyo Hijabi Nasa Dan Na kula Abdul Dina Nason Yaga Nasa Hijab. Wit Leaps Nadan Murzawa Labbana Suka Kara Sheki Kafin Nadan Murza Hoda Afuskata Nadan Mutsutsuka Turare Daga Can Barandarmu Naji Momy Nacewa, "Ai kina Wannan Feleken Harsu Tafi." "Momy Gani Fitowa." Nafadi Hakan Dae dae Sanda Nake Bakin Kofar Dakinmu Ina Zura Takalmi Nawuce Momy Tana Cewa, "Karfa Ki Dade Khaleesat Kizo Nayi Abinnan Gabanki Inkika Iya Zaimiki Anfani Nan Gaba." Nafita Inacewa, "Tau Momy." Araina Kuwa Nace "Zan Iya Indinga Yiwa Abdull Dina." Nakasa Boye Fara'ar Fuskata Sanda Hasken Farin Gluf Din Bakin Garkar(Kofar) Gidanmu Yahasko min Fuskar Abdul-wahab Dina Mai Cike Da Annuri Na'isa Gabansa Da Wannan Fara'ar Shima Dai Murmushi ne A Fuskar Tasa Yajima Yana Kallona Kafin Ya Sauke Ajiyar Zuciya Yace, "Baby Na Sannu Da Gida." Na Zunburi Baki Kamar Karamar Yarinya Tareda Cewa, "Nifa Fushi Nake, Saboda ALLAH Tun Karfe Tara Nake Dubin Kazo Amma Sai Yanzu Harna Fidda Tsamani." "Ayimin Hakuri Gimbiyata Nima din Badan Naso Haka Bane Kasuwar Kanawa Mukaje Kuma Kinsan Yau Garin Da Kwai Cinkoso." Kafin Nace Wani Abu Sai Ga Yusuf Yafito Daga Cikin Kk Napep Yakaraso Garemu Yana Goge Bakinsa Da Kyalle Yana Cewa, "Sahibar mu Sannu Da Gida. Ayi Hakuri Munyi Laifi ko?" Nace "Ba Wanin Nan Ai Duk Bakinku Daya." "Tuba Muke Ni Nayi Laifin Dan Ni Na janye Maki Mutumin nace Sai Nasiyowa Fa'iza Ta Kayan Kwalliya. Nasan Ai Kuma baxaku So Nima Na Rasa Tawa Soyyayar ba Tunda Kan Sharafinta kuke Ko?" Nadan Harareshi Cikin Sigar Wasa, "Tau Ni Mezance? Tunda Duk Ka lauyeni, Ai Wallahi Kaikam matarka ko, Tashiga Ukku Da Dadin Baki." Duk muka Kyalkyale Dariya Yusuf Yace, "Ke! Ni Duk Dadin Bakina Ai bankai Gwarzon Naki ba Daxun Fa Cewa Yayi soyyayar mu Ba....." Abdul-wahab Yayi Saurin Dafe Masa Baki Yana Cewa, "Aku Sarkin Magana Kaidai Ba Damar Ayi Sirri Da Kai?" Duk muna Dariya Nace, "Yanzun Habibi Na Niza Kayi wa Sirri?" "Ah Tau Nima dae Shi Nagani." Yusuf Yafadi Hakan Yana Yarfar da Hannayensa. Abdul-wahab Yahararesa Kafin Yaturesa "Dan ALLAH Malam Koma Cikin Kk Napep Dinka Duk Kabi Kacika mu Da Surutu Ka hanani Inga Na Da Tawa babyn Bayan Kai Da Mukaje Nabaka Guri." Muna Ci Gaba da Dariyar Nishadi Yusuf Yace, "Kinji Ba?" Abdul-wahab Yayi Saurin Juyowa Yana Kallon na Tareda Dafe Bakin sa Yace, "Au..." Bi Ma'ana Dae Yayi Azarbabi Da Yawa Wanda Yawuce Ka'idarsa. Banda Dariya ba Abunda Muke. Bayan mun Dan Natsa Yusuf Na kk Napep Yana latse-latse Acikin Wayarsa Ga Alama Kuma Chat Yake Dan Sai Murmushi Yakeyi, Mukuwa Muna Nan Sai Batu Muke Wanda Mafi Yawancinsa Nice Ke Jan Ragamar Labarin Dan Abdul Dina Ba gwanin Surutu Dinnan bane Sosai Mussamman ma Dae in muna Tare. Hannun na Yakallah Wanda Yayi Shar Da Zanen Fulawa, Yace, "Babyna Kinyi Kyau Kamar Nasaceki Na Gudu Dake Wannan Lallen Jinake Kamar Incire Hannayen Inje Da Abuna Gida Duk Motsin da Zanyi Sai Na kallesu." "Habibi Mekake Sauri Inda Rai Da Lafiya Ai Watarana Nidin Takace Sai Yanda Kaso Zakayi Dani." Yayi Murmushi, "Are you sure?" Yafada Cikin Wata Irin Murya Mai Cike Da mayen So. Nagirgiza Kai ma'ana Dae "Yes." Yace, "Kenan Dai Zaki Dinga min Irin Wannan Lallen?" "Sosaima ko Sai Wanda Kazaba Kake So Habibi Na." "Wow! Gaskiya Nacika Da Zumudin Ganin Wannan Lokacin." Abdul-wahab Yafadi Hakan Yana Cikeda Wani Irin Shaukin So! "Oh Afuwan Bari Dan ALLAH Nakawo Maku Ruwa Tun Daxu Na Saka Ku Gaba Da Surutu." "Kinga Ni kuwa Surutunan Yafiyemin Duk Wani Abu Da Zaki Kawomin.". "Duk-da Haka Babyna Idan Ga Ruwan Ai Sai Surutun Yafi Armashi Ko?" Nakarasa Maganar Cikin Zolaya. Abdul-wahab Yayi Dariya Yana Cewa, "Kinganki ko? Da Aikin Jarida Kawai Kika Karanta, Saboda na Tabbata Za'ayi Hazikar Yar Jarida Kuma Yar Baiwa." Cikin Farinciki Nace, "ALLAH ko?" "Sosaima." Yafadi Hakan Yana Mai Girgiza Kansa Dan Bani Tabbaci." Najuya Inafadin "Kaga, Infa ba Zuwa Nayi Ba Bazamu Taba Gajiya Da....." Yayi Saurin Cewa,"Kinga karbi Kayanan Kiwuce Dasu Ciki." Najuyo Nakarbi Ledar Ina Fadin, "ALLAH sa Ba Wahlar Da kanka Kayi ba dae Dan Ni dai Gaskiya Bai....." "Shiiiiiii!" Nayi Shiru Saboda Hakan Din Da Yayi min Kafin Yadora Da Cewa, "Dan Miji Yayi wa Matarsa Abunda Yake Ganin Yadece Shikenan Kuma Sai Yakoma Wahla?" Kafin Yagirgiza Kai Yace, "Abunda Kawai Zakimin Ki Burgeni Ki Karba Da Hannun Biyu Sa'anan Kiyimin Adu'ar ALLAH Ya sanyawa Nemana Albarka Ta Yanda Zanci Gaba Da Dawainiyah Da Innarmu Dakuma KE Harma Da 'Yan Yaramu Da Zamu Samu Nan Gaba Insha'allah." Maganarsa Takarshe Tabani Kunya Dan Haka Sai Narufe Fuskata Da Hijabi Na Nufi Cikin Gida Dan Kawo Musu Abin Tabawa. . Tau Raedars Kafin Khaleesat Tadawo Bari Nima Na Dan Sarara Insamu Abin Kaiwa Baka.😜 Zansake Dawo Maku A Chapter Ta Tagaba. Labarin Dae Haryanzun Ba'a Soma Ba, Batutuwa Na Gaba. 🚶🚶🚶🚶🚶🚶 [9/5, 9:13 PM] FA'IK: 💞 SONEEE....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....5 SADAUKARWA. Wannan Pages Din Na Kyautar Ga Wayyanan Bayin ALLAH Wayanda Sune Kwarin Gwaiwa ta Ina Godiya Irin Trillions Dinnan 😅😅 ABUBAKAR AK SARAKI da Kuma UMMU SADIQ Tareda Mr BABONI. Sai Kuma HAJARU.(Yar Uwa) A....... Maimaikon Pages 123, Zankoma Da Yin Amfani Da Chapter.👌 Mallakar 👇 Fa'IK ✍️ Typing.....💻 GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. 07039676994 Bissmillahi Rahmanin Raheem Bandade ba, Nadawo Dauke Da Faranti Wanda Aka Jera Gorar Ruwa Da Kuma Bigi Fanta Sai Flet Da Aka Rufe Da Dan Uwansa Flet Soyayyen Dankali Ne Da aka Nannade Da Masar Kwai (wainar kwai) Na'aje Ina Cewa, "Gashi Ku karba Da Hakuri Yau Kasan Ana Fama Da Hidimar Sallah Bamuyi Abin Budin Baki ba Yau Ko Shago Momy Bata Fita ba." Nadago Ina Kallon Abdul-wahab Ashe Nidae Ke Magana Ta, Abdul-wahab Ya Manta A Ina Yake Ya Shagala Da Kallona Nai Azamar Rufe Fuskata Da tafukan Hannayena Zara-Zara Da Suke Zagaye Da Bakin Lalle Ina Murmushi Kafin Nace, "Kallonfa Ya'isa Haka." Yasauke Ajiyar Zuciya Yadora Da Cewa, "Tuba Nake Tawan Kece Duk Kika Tafi Dani Har Nakasa Control din Kaina. Anya Tawan Bazamu Gaggauta Gabatar da Kammu Gurin Dady Abani ke Ba?" Nashiga Bude Masa Lemon Fantar Dana Kawo Kafin Namika Masa Ina Cewa, "Kaga Fara Sha Takwan Mayi Magana Inka Gama." Yakarba Ya kurba Sannan Ya kalleni Yana Cewa, "Yakamata Naji Amsarki Akan Wannan Maganar Fa?" "Ina Zuwa." Mikewa Nayi Daga Kan Dakalin Da Muke Zaune Ina Mai Daukar Gorar Cok Nanufi Inda Yusuf Ke Zaune, Namika Masa Nace, "Gashi Inafatar Baxaka Ki Karba ba?" Yayi Dariya Yana Amsawa Yace, "Wa? Ni Na'isa? Ai da Habibinki Yarufe ni." Mukayi Dariya Najuya Ina Cewa "Kaidai Oga Yusuf Baka Rabo Da Abin Dariya." Yace, "Tau Ki Tambayeshi Kiji Mana." Wajajen Karfe 2 Nadare Harma Da Wasu Yan Mintoti Suka Dawo Gida Sungaji Tibis! Dole Dai Yusuf Ya Kwana Gidansu Abdul-wahab Din Dan Dare Yaja, Dan Haka Sai Suka Bada Ajiyar Napep Din Yusuf Gurin Gidan Makwabta Dake Da yalwataccen Guri. Kafin Suka Shigo Cikin Gida Suna Ta Layi Itakam Innarmu Haryanzun Idonta Biyu Tana Bakin Kofar Dakinta Tajawo Soket Nan Bakin Kofar Dakinta Ta jona Fankarta Tana Daura Lallen Da Bata Samu Daurawa Da Rana Ba. Takallesu Sanda Suke Zama Kan Baranda Kofar Dakin Tana Cewa, "Sai Yanzun Kuka Dawo? Har Ina mitar Kun Tafi Kun Barni Nikadai A Gida Ga Wayata Ba Katy Balle Nakira ka." Abdul-wahab Yamike Yabude Frij Yana Jawo Kunun Ayar Da Innarmu Ke Saidawa Yamikawa Yusuf Gora Daya Kafin Shima Yabude Daya Yasoma Sha Sa'anan Yadubi Innarmu Yana Cewa, "Ina Autanki?" (Watau Abubakar Dan Shima Wani Lkcin in Yana Nishadi Yakan kirasa Da Haka). "Autana Yace Yau Can Zai Kwana Yace, So Yake Ya'ida Duk Dunkunan Mutane Dake Hannunsa." "Yana Da Kyau." Abdul-wahab Yafadi Hakan Yana Mai Yar Mika da Hamma Alamun Gajiya. Innarmu Ta dubeshi "Kai Kam Kacika Ragwantaka Wallahi, Yar Wannan Fitar Ce Duk Kake wa Raki Haka?" "Kema dai Ki Fadi Innarmu Bayan Kafin Mufita Kamar Zaiyi Tsuntsuwa." Yusuf Ne me Wannan Maganar. Innarmu Tace, "Taya Ni Gani Makaho Yaso Gulma." Abdul-wahab Yahararesa Kafin Yanufi Hanyar Dakinsu Yana Cewa, "Kai Mal Ni Ban iya Abinda Ka iyya ba. Innarmu Ni Zan kwanta Saboda Karna Makara Zuwa Sallar Idi." "Amma Yakamata Ku zuba Abinci Kuci Ko?" " Nakoshi Nikam, Saidai In Yusuf Ne Zaici." "A'a Wallah Nima Ba Guri, Wannan Ciye- Ciye-Da Mukayi Yau Ai ALLAH dae Yatsare Mu da Gurbacewar Ciki." Innarmu Tayi Dariya Tana Cewa, "Tau ALLAH ya Takai ta." Nan Dae Yabar Yusuf Da Innarmu Suna Firah Kan Yashiga Dakinsu Ya Tube Kayan Jikin Sa Ya Zura Jallabiya Mai Ruwan Zuma Yafito Waje Yadibi Ruwa Yafada Toilet Ya Watso. Kan Katifar sa Yazube Bayan Yafito Daga Wankan Kenan, Cike Da Gajiya Wacce Bawai Ta Tafiya Bace Ko Aiki A'a Wannan Kawai Ta Shaukin So ce Dake Nukurkusar Duk Wata Gaba Da Take Mallakinsa Ne. Ahankali Yalumshe Idanuwansa Kafin Yasake Budesu Yana Tsurawa Fankar Dakinsu Dake Ta Kai kawo Ido Domin Bawa Dakin Nasu Iska A Ransa Yakeji Cewa, Anya Bai Wuce Makadi Da Rawa ba Akan Son Khaleesat Ba? Wacce Baya da Tabbacin Ma Iyayen ta Zasu Bashi Aurenta In Sun Bashi Ma da Wane KWANJIN Zai Aureta? Suda Basu Da kowa Bayan ALLAH da Innarmu Da Yan Sana'o'i Hannun Da Sukeyi Wayyanda Suke Rufa Masu Asiri, A Ture Wannan ma Karatunsa Fa Wanda Yake Bukatar Kudi Da Lokacinsa Karatunda Yakula Matuka! Innarmu Tabashi Muhimmanci Da ko Shi Da yake yinsa Bai Bashi ba, Idan Akazo Abincinsu Yakare Ga Kuma Lalurar Karatunsa Innarmu Takance, "A Hakura Da Siyen Abincin Yaje Yayi Sabgar Karatun sa, Abincin Kuwa ALLAH Zai Rufa Asiri." Babu Shakka Yakwaso Jan Aiki Ma Kansa Wanda Bai Ma San Ta Inda Zai Fara Bullo Masa ba. Gashi Inka Cire Aminin Nasa Yusuf Ba Wanda Yagayawa Maganar, Tau Dae ire-iren Wayyanan Tunanen, Sune Suka Dami Zuciyar Abdul-wahab Suka Kara Saukar Masa Da Wata Irin Gajiya Harma Da kasala Bacci kuwa da Yace Zaiyi Ko kadan Bai Ziyarceshi Ba. Har Sanda Yaji Yusuf Da Innarmu Suna Sai Da safe. Dan Haka Dole Yatirsasawa Kansa Baccin Karya Hardasu Minshari. Dan Baya Son Surutu Kawai Yafi Son Yayi ta Tunaninka. Yusuf Dae Da Baisan Wainar Da Ake To Yawa ba Sai Yabawa Ransa Cewa Da gasken Abdul Din Bacci Yake Dan Haka Shima Yabi Lafiyar Katifa Ya kwanta. *************** Basuyi Wani Bacci Ba ma Aka Soma Kiraye-kirayen Assalatu Dan Haka Dole Suka Tashi Sauke Farali Suna Dawowa Daga Massalaci Yusuf Yawuce Dan Baizo Da Dinkin Sallah Ba Dole Yasamu Ya'isa Gida Dawuri Ya Shirya. Tunda Suka Dawo da Sallar Idi Suka Ci Abinci Shida Abubakar Suka kule Daki Sai Bacci, (Dama Shi Kunsan Ba'acin Bashinsa) Suka bar Innarmu Da Diyan Makwabta Masu Shigowa Yawon Sallah Sai Budiri Sukeyi. Dan Sun Samu Sakewa Gurin Innarmu Adalilin Itadin Mai Saukin Kai ce Kuma Ga Son Yara Dan Haka Sai Suke ta Shishshigowa Gurin Innarmu Gida Kuwa Yakacame. Abubakar da Abdul-wahab Basu Farka ba Sai La'asar Shima Bawai Dan Ya'ishesu ba Sai Dan Innarmu Da ta matsa Musu Su Tashin Saboda Suyi Sallah Ga Kuma La'asar Da Tayi. A BANGAREN KHALEESAT FA?🙄 Shin Wacece Khaleesat ma Dae? Nana KHADIJAT Shine Asalin Sunanta Iyayenta Auren So Sukayi, Dan Babanta Bafulatanin Adamawa ne Yayinda Mamarta Take Yaren 'Ibra' Yar Asalin Garin Kogi, Sunan Mahaifin ta Mustapha Mahaifiyar ta kuwa Sunanta 'Yawo. Haduwar Yawo da Mustapha Ya Samo Asali Ne Sanda Aka Turashi Aiki Can Kasancewar Shidin 'Mopol' ne, Sun Hadu Da Yawo Gurin Da Take Sai Da Abincinta Wanda Suka Kamu Da Zazzafar Kauna Akan Juna Ansha Gwargwarmaya Kafin Auren Su Kasancewarsu Ba 'KABILA' Daya ba, Sai Dai Jajirce wasu Ta shanye Komai Dole Aka Barsu Sukai Aure Bayan Da Shi Mustapha Sai Da Akayi Masa Auren Zumunci Da Yar Uwarsa Take Kuma Zaune Can Adamawa Garinsu Kenan. Zaman Su A Sakkwato Ya Samo Asali Ne Sanda Aka Dawo Dashi Aiki Nan, Sai Garin Yay Musu Dadi Mussamman Yawo Data Fara Sana'ar ta Ta Saida Kunu da kosai Dasu Dankali Harma Dasu Doya da Plantain Wani Lokacin har Kunun Zaki Takanyi Tasa A kula Kuma ALLAH yasama Abin Albarka Dan Duk Kazo Gurin Zaka Iske Cincirindon Yan Kabu-kabu(Yan Acaba) da Kuma Yan Kk Napep Da Sauran Tsirarun Mutane. Nuradden Shine Dansu Na Farko Yana Aiki A Legos Shi ma Aikin Kaki Yake Sai Kuma Nana KHADIJAT Wacce Kowanensu Ke Kiran ta Da Sunan Da Yayi Masa Dadi. Dadynta Nace Mata Ikram Momy Kuwa Takance Mata Khaleesat Tau Khaleesat Dae Shine yafi Samun Karbuwa Tunda Kunsan Dama Uwa Tafi Kusanci Da Diyanta. Khaleesat Tana Zuwa Skull Both Boko An Isalamiyyah Kuma dae Rayuwar Gidansu Akwai Yanci Dan Ba'a Cika Tsarara Musu ba. Rayuwar Dadynta Baya Zama Guri Dae Yau Yana Wannan gari Gobe Wancan Jibi Yana Daya Daga Garin Matan Sa In Yazo wa Wannan A Wannan A Wanin Karon Yazo Wa Wannan (Yanayin Hakanne In Yasamu Sarari Agurin Aiki Nasu) Haka Rayuwarsa Take Tafiya. Wannan Kenan 🤗 Kamar Yadda Kuka Sani Yaudin Ce Sallah Harma Yammaci Yayi, Kowa Ka Gani Ya kule A daka Ba Sauki😜 Gidanmu Ba kajin Kunne Saboda Hayaniya Da Yacika Gidan Namu, Mundade Ba'ayi Irin Wannan Haduwar ba Agidamu Watau Ga Babamu Ga Kuma Yaya Nuradden Duk Sundawo Gida, A Wannan Karon Ya Nuradden, Harda Iyalinsa Yazo Dasu wacce Tazamo yaren momy ce dan Haka tasu dazo daya da momy. Ga Kuma Kawayena Na Skull Da Suka Zomin Tayani Tarbar Daddy Da Kuma Ya Nuradden Munkule Dasu A dakina Da Yake Mallakina bakajin Komai Sai Sowa da Tafi. Abinci Kuwa Munyi Girki Yakai Kala Ukku Ga katan din Drinks da Ya Nuradden Suka Siyo Shida Daddy. Daddy Yakirani Dan Haka Nafito da Hanzarina Ina Amsawa Nashiga Falon Shida Momy Suna Zaune Abinci Yagama Ci Yace, "kwashe Kayan Nan ki Kawo min Ruwa in Wanke Hannuna." Bayan Nakwashe Na kawo Masa Ruwan Cikin Roba Yana Wanke Hannu Yace, "Ikram Cikin Daki Ki Duba Jikkar Da Nazo Da Ita ki Duba Wayarki Na Nan Nasiyo Ma....." Ai Kafin Yagama Magana Nakai Kuryar Daki Da Zumudi Na Ina Ihun Murna Shida Momy Me Zasuyi In Ba Dariya Ba Nadawo Dauke Da Waya Sabuwa Dal! Cikin kwalinta Kirar Samsung Da Murna ta Nake Cewa, " Wow! Dadymu I love you, Thank you! Nagode Nagode Daddy...." Cikin Haka Ya Nuradden Yashigo Falon Yana Murmushi Yace, "Diyar Dadynta Me Akayi?" Cikin Zumudi Na Nuna Masa Wayar Hannuna Ina koro Masa Jawabin Dady Yasiyomin. Yanemi Guri Ya Zauna Yana Cewa, "A 'a Lalle Yar Daddy An gwangwajeki." Na Fallah Da Gudu Ina Cewa "Bari Naje Na Nunawa Su Halimo Nima Nafaso Gari...." "Kinga." Ya Nuradden Yakirani Natsaya Jikina Na Tsuma Yashiga Laluben Aljuhunsa Yana Cewa, 'Bari Nayi Dobling Din Wannan Murnar ko." Yamiko min Yan Dari Biyu Sabbi Har Guda Biyar Yana Cewa, "Kya Sayi Katy, Yanzu Ba Kudi, Cash! Wahla Yake." Narungumesa Cikin Farinciki Sosai Gamida Cewa, "Wannan Ma Is Okay Yaya ALLAH yabarmin Ku Kaida Dady, ALLAH Ya....." Momy Ta Rarumo Fillo Kujerar Datake Zaune Tajefe Ni Dashi, "Mukuma Karya Barmu Ba Tunda Ba....." Nayi Saurin Isa Gareta Nace, "No no! Momy Harda ke Mana." Kafin Na Juya Da Hanzarina Dan Nuna Wa Kawayena Abin Arzikin Da Yasameni. Acan Ma Dakin Nawa Murnar ce Dae, Kowacensu Da Irin Abinda Take Cewa. Na kunna Wayar Na sa Abata Caji Cike Da Zumudin In Tayi Caji Zankira Habibina (Abdul-wahab) Kawayena Muna Tare Sai Da Yamma Lis Rana Ta Tafi Zata Fadi Sannan Kowace Su Ta Soma Rarumar Jakarta Da Mayafi Kan Zasu Gida Na Rakesu Dakin Momy Sukayi Musu Sallama Inda Dady Yabani Dubu Dai Da Dari Biyar(1500) Kan Cewa Suyi Hakuri Dasu Ba Cash! Har Ina Karasa Masa Kalmar, Dan Ba Cash Yazama Jiki Yanzun Mukaje Dakin Da Ya Nuradden Ya sauka Shida Matarsa Nan Ma Sun Samu Dari Biyar (500) Sai Godiya Suke Tayi. Har Bakin Titi Mukaje Sai Da Suka Shiga Kk Napep Sannan Na juyo Zuwa Gida Lokacin Wasu Masaalatan An Fara Kiran Sallar Magariba. Dan Haka Ina Shiga Buta Kawai Nazara Nafada Toilet Nakama Ruwa Nafito Nayi Arwallah Nashiga Dakin Domin Yin Sallah Bayan Na ida Ina Sunce Hijabi Wayata Kawai Na Nufa Naje Falon Momy Nadauko Wayarta Na kwafe Number Abdul-wahab Sai Dai Wayar tawa Ashe Ba Katy Dole Dai Da Ta Mommy Nakirasa Dai-Dai Lokacin Sunfito Masallaci Daga Sallar Magrib Yadaga Fuskarsa Cike Da wal-wala, "Babyna Barka Da Sallah!" Duk Mukayi Dariya Nace, "Dan Karna Rigaka Cewa Kabani Goron Sallah ko? Tau Sha Kuruminka Ni Yau Hajiya ce." "Eyyeeee Hajiya Khaleesat Nikam ko Zanzo A Sammani ne Dan Yau Haka na Wuni Yammata Duk Sunkarbe min Kudi Da Sunan Abasu Goron Sallah.." Nai Saurin Bata Fuska Kamar Yana Ganina Kafin Nace, "Yan Mata Kuma?" Yayi Hanzarin Cewa, "Au Sorry Yan Matan Fa Duk kwaila ne, Ko A Kwai Manya Ai ba Wadda Ta Isa ta Kama kafarki baby Na." Na Zunburi Baki Cikin Muryar Shagwaba Kamar Ina A Gaban sa, "Naji din Sai dai Duka Bana so, Dan ALLAH Habibi Na Kabar Kula kowace In Har Baka Son Nadinga Ma Kuka." Cikin Danne Dariyar Da Tazo Masa Yace, "Nabari Dama Ni Can Fa Zolayarki Nake Babyna." Nayi Shiru Kawai Ina Maida Numfashi Daga Can Da Yaji Ba Amsa Yace, "Hello! Are we Together My Baby?" Nace, "No!" Cikin Wani Irin Salo Mai Tafiyar Da Hankali Yace, "Ohhhhhh My Baby Nace Fa Zolayarki Nake Sorry Kinji?" Nace, "Tau Yayi Nahuce, Amma Karka Kara Kuma bana Son Kana kula Wasu Yan Mata manya ko kanana Kaji ko?" Yacemin, "Naji Zan Kula Baby." "Yawwa! Kai Nawa ne Nikadai Nima Kuma Takace Kai Kadai Zamu Rayu Tareda Juna Har Aljannah." Yayi Saurin Cewa, "Ina Fatar Hakan my baby." Kafin Dukamu Mukayi Shiru Sai Numfashi Mu Da Ke Tai Kai kawo Kowa Kuwa Da Irin Shaukin So Da Yakeji. Daga can Yasake Cewa, "Hello." Na'am Sa, "Uhummm" "Ilove you" Yafadi Hakan Cikin Wata Irin Cool Voice Dinsa Mai kamar Yanzun Yatashi Daga Bacci Sai Da Naji Duk Tsikar Jikina Ta Tashi. Nace "Me Too 😘" Kafin Nai Hanzarin Kashe Wayar Cikin Kunya Ina Rufe Fuskata Da Filo Jinake Kamar Ina Gabansa Wallahi Sai Wani Haki Nake. Daga Can Shima Jin Takashe Wayar Sai Kawai Yayi Murmushi Kafin Yarubuta Sako Ya'aika Mata. Sannan Yakama Hanyar Gida Gaba Dae Ya Manta Da Abubakar Da Suka Fito Massalaci Sai Da Yaji Abubakar Din Yadauko Sauri Yana Cewa, "Ya Abdul Jirani Mana." Yayi Saurin Tirjewa Yana Susar Kai Gaba Dai Kunya Takamashi Na Yadda Yamanta Da Abubakar. Abubakar Yamatso Gurinsa Yana Cewa, "Yaya You are In love Ba?" Abdul-wahab Yahararesa Yana Fuskewa Waishi Nan Gashinan Yaya, "Yaronan Kafa Raina Ni Da Yawa Wannan Wane Irin Batune?" Abubakar Yakama Hanyar Gida Yana Cewa, "ALLAH baka Hakuri Yaya." Kome Abdul-wahab Din Yatuna Yayi Saurin Jawo Kanin Nasa Yana Cewa, "Seriously Ina Cikin Wata Irin Zazzafar Soyyayar da bansan Yaushe Tashige ni ba A Yanzun Bani Da Wani Buri Kanina Face Nakasance Da Wannan Masoyiya Tawa A Inuwa Daya Matsayin Ma'aurata." Abubakar Yakallesa Sosai Yana Kara Tabbarda Cewa Lalle Ya Abdul Yayi Nisa Kamar Yadda Yafada Kafin Yace, "Maganar Gaskiya Yaya Da kasharwarceni Da Baka Yi Wasa Da Rayuwar ka Irin Haka ba? Inaga kamar ka Manta Waye Mu Da Kuma Irin Karatun Da kake Wanda Yake Bukatar Nutsuwar ka, Da Kuma Irin Burin Da Innarmu Taciwa Karatun ka A Ture Wannan Ma Yanzu Idan Ka tattago Maganar Aure Ina Zaka Sa Matar ka? Yaya Ni Ina ga Ba Wannan Yafara Kamarta mu ba, Mufara Gina Rayuwarmu Mu Samu Madogara Mai Kyau Da Muhalli Kafin Mu Nemi Matar Da...." Cikin Facin Rai Abdul-wahab Yadaga Masa Hannu "Meyesa Zaka Ta Kashimin Kwarin Gwaiwa, Duk Kalamanka Auta Basa da Dadin Saurare Why?" "Saboda Sudin Gaskiya Ce Gaskiya Kuwa Kasan Daci Gareta Saboda Sudin Sun Sabawa Bukatar ka Dan Haka Banga Yanda Zasu ma Dadi ba. Sai Dai Ni Ina Tunatar Da Kai Waye mune Da Abin da Yafi Kamantar mu Sa'anan Kasan Duk Duniya Nafi Kowa Sonka Da Duk Wani Abu Da Yadangaci Ci Gabanka Harma da Farinciki Ka." Abubakar Nagama Fadar Haka Yawuce Yabarshi Nan Tsaye Cike da Tunanunka Lalle Inzai Kauda Sonkai Yabar Gaskiya Tayi Aikin ta Tau Abinda Abubakar Yafada Masa Shine Yakama ceshi Tau Amma Zai Iya Barin Khaleesat? Zai iya Rayuwar da Ba Khaleesat Acikinta? "Kai! Never." Yafurta Haka Da karfi A Kuma fili Wanda Hakan ya Tilas tawa Wasu Kallato Sa Cikin Mamakin Sa. Ganin Haka yasa yasoke Kansa Yanufi Gida. KHALEESAT Fa? Ina Cikin Wannan Haline Naji Wayar Momy Tayi Kara Alamar Anturo Sako Dan Haka A Kasalance Na janyo Wayar Izuwa Fuskata Da Tunanin Yan Gidan Layine Suka Yo Sakon Sai Naga Sunan Habibina Ranga Dau! Dan Haka Da Zumudi Nabude Sakon Nasoma Karantawa Kamar Haka! Hummm Babyna Kunya ko? Ni Duk Kin Hanamun In Tambayeki Daddy Ya Suka Iso Da Ya Nuradden? In Dae Na Samu Sarari Zamu Bullo Gayarda Da Dadymu. Miss U my babyyyyyy. Naki Wahab." Wani Irin Sanyin So Ne ke Shigata Wanda Yatilasta Min Rumgume Wayar Kamar Itace Masoyin Nawa. Ina Cikin Laulayin So Ne Naji Momy Nakira Na. Dan Haka Dole Na wartsake Nafito Tsakar Gida Ina Cewa "Gani." Ta nuna Min Kulolin Mutane Da Suka Kawo Abincin Sallah Yakamata Ki Duba Kulolin Nan Asan Da Tawaye Da Tawaye Ce Sa'anan Afitar Da Abincin Da ke Ciki Aba Mabukata Dan Kar Yalalace Sai A Wanke Su A Mayar. Har Tawuce Sa'anan Ta Dawo "Yawwa Kiyiwa Auntynku Magana Ta Kama Miki." " To" Kawae Nafada . Kafin Na Nufi Dakin Da Matar Ya Nuradden Suka Sauka, Na'isko Ta Tana Kokarin Sakawa Danta Muyyidim Famfas Tadago Kai Tana Kallo na A Sanda Nashigo, Ashe Tanajimu Da Momy Tace, "Zo Ki Karasa Shirya Danki Bari Inje Iniyi Aikin Ai Kekam Kingaji." Murmushi Kawai Nayi Ina Cewa, "A'a Aunty Baza'a yi Hakaba, Ai kunfi Gajiya Kuda Kuka Debo Hanya Daga Legos." Murmushi Kawai Tayi Tafita. Nufin Dae Bata Bukatar Muyi Ta Jayayya Dan Haka Dole Dae Yanda Tace Din Akayi. Bayan Nagama Shirya Muyyidim Din Nasa Hijabi Nafita Shago Siyen Katy Saboda Kiran Habibi Na. Ina Fitowa Kuma Sai Ga kosassar Mota Na Dalle Ni Da Haske Daga Baya Kuma Sai Wanda Ke Cikinta Ya Soma Jera Horn......... Anan Zan Nunfasa Sai Muje Chapter Ta Gaba Muje Wace Irin Chapter Za'ayi. [9/5, 9:13 PM] FA'IK: Typin...... 💻 💞 SONEEE....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....6 Mallakar 👇 Fa'IK ✍️ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Duk Horn Ɗinda yayi Tayi ban waega ba Illa Na'isa Shagon dake Gefen Gidamu Namiƙa Kudi Tare da Cewa, "Abani kati." Babu jinkiri Yamiko min Nakarɓa da Nufin Injuyo Muyyidin Yasa Rigima ba Inda Zamu Sai na siye masa biskit Dole Namiƙa canjin Da'aka ban Nace Abashi Biskit Ɗin. Wannan ne Yasa Mutumin dake ta min Horn Ɗazu yasamu Sa'ar Riskar Mu Shagon Bayan Yaga Anmmiƙowa Muyyidin Biskit Ɗin Sai Yace A Ƙaro Masa. Muyyidin kuwa Sarkin Ƙwadayi Yanajin Haka Ya Wangale Baki Yabi Ya kanainaye Wannan Alhajin. Babu Yanda Zanyi Dole Najirashi Haka Muka jero Mutumin Yana ta Faman Zuba, Shikuwa Muyyidin Yamakale Masa Kamar Ubansa, Takaici Duk Yabi Ya Isheni Ni Ba intahi inbarsu ba yayi Awon Gaba Ɗan Mutane, Dole Haka Na Saurare shi Inda Yasoma gabatar min Da Kansa Cewa, "Sunana Alhaji Saminu Kuma Ni Ɗan Kasuwa ne, Babu Inda Bana Da Plaza A Nigeria Ina Da Mata Daya Dakuma Yara Biyu. Naganki ne Aɗazu Dakika Rako Ƙawayenki Kuma Daga Wannan Lokacine Na Rabu Da Nutsuwata Sai Da Nazo Na Bincika Aka Nuna Min Gidanku Inpact Dae Khaleesat Ina miki wani Irin So Wanda Kallo Guda Da nayimaki Naji Yashigeni Naji Kuma Bazan Iya Runtsa wa Ba Sai Nazo Na gayamaki ina Fatar Zan Samu Karɓuwa." Na Sauke Ajiyar Zuciya Cikeda Mamakin Mutane Watau Bayan Nuna Masa Gidan mu Da Akayi Harda Sunana Aka Gayamasa Kila Har Labarin Gidamu Anbashi. "Uhumm. Ke Nake Saurare." Yafadi Hakan Yana Mai Sonji Daga Gareni. Nace, "Alhaji Saminu Kace Sunan Ka Ko?" Nacigaba Da Cewa, "Maganar Gaskiya Nagode Da Irin Wannan ƙauna Dakake Yimun Nima Kuma Ina Ƙaunarka Saidai Wayanda Suka Gayamaka Wacece Khaleesat Sun Manta Su Gayama Cewa Anyimata Miji Dan Haka Kaga Yanzun Bakin Alkami Yabushe ko. " "Maganar Yabushe Ma Bai Taso Ba Wannan Kawai Karin Maganar Hauswace In Yanzun Aka Sake Tsomashi Zai Jike Cakab! Amma Bari In tambayeki Yaturo Kuma Yakawo Sadaki? " Ina Dariya Nace, "Tuni, Harma An Saka Mana Rana Lokaci Kawai Muke Jira... " Shima Dan Darawa Yayi Kafin Yace, "Jikina Yana Bani Ba Haka Bane, Kawai Kinfaɗa ne Dan Haka Ita Macce Allurace Cikin Ruwa Mai Rabo Ka Ɗauka Dan Haka Ni Na Gani Ina So Kuma Daga Yau Nashiga Layin Masu Nema Finish!" "Ina Maka Fatar Rashin Nasara." "ALLAH Bazai Karbi Adu'arki Ba." Dai-dai Nan Kuma Muka Kawo Bakin Kofar Gida Dan Haka Natsaya Ina Miƙa Hannu Nufin Yabani Muyyidin Shima Yafahimta Da Hakan Amma Sai Yashare Tareda Cewa, "Ki Bani Number ki. " "Bana da Waya" "Kina Fara Fadar Hakan? Big girl Dake? " Nalura Alhaji Saminu Dan Duniya ne, Bugu da Ƙari Dan Bariki ne, Ba Wuya Macce Tafada Tarkonsa Domin In Samu In Kaucewa Haka Bari Inyi Saurin Rabuwa Dashi In huta Dan Haka Na Karanto Masa Lambata Yasa A wayarsa Sai Da yakira Yatabbatar Itace Sanan Yamin Sallama Bayan Yabani Bandir Din Dari Biyu Dana Ƙi Karɓa Sai Yamikawa Muyyidin Yajuya Yashige Motarsa Yabarni Da Mamakin Irin Wayyanan Gallah-Gallahn Kuddi A Irin Wannan Lokacin Da Ake Fama Da Matsalar Cash! Watau Shi Mai Kuddi Lamarinsa Dabanne. Muka Shiga Cikin Gida Ina Cewa, "Ƙasata Nigeria Ho!" *********** Abdul-Wahab Kuwa Nashigowa Gida Kai Tsaye Ɗakin Innarmu Yashiga Ya'Isko Abubakar ɗin Da Innarmu Suna Zance, "yawwa Gashima Yashigo." Innarmu Tafaɗi Hakan Sanda Abdul-Wahab Yaƙaraso Abdul-Wahab Yazauna Jininsa A ƙumba A zatonsa Har Abubakar Yafaɗa Mata Halinda Ake Cikine Sai Yaji Sabanin Abunda Yake Hasashe Don Dae Suna Shawara Kan Ya Za'a Sarrafa Kuɗin Da Abubakar Yasamu Na Ɗinkunan Da Yayi A Watan Ramadan. Dan Haka Sai Yace, "Innarmu Bakince Maman Walida (Auntysu kenan) Na Nan Zuwa Jibi Ba?" "Eh" Su Innarmu Suka Faɗa A Tare. Abdul-Wahab Yace, "Tau Innarmu Ajira In tazo Mayi Shawarar Tareda Ita Zaifi Bisaga Mu Yanke Batanan Da'ace Bazata zo Bane Da Sai muyi Tunanin Meza'ayi." "Eh Hakan ma Dae-dae ne Kayi Tunanin Ko Can Tana min Kwakwazon Ba'a komai Da Ita. " "Tau Kingani? " Innarmu Tace, "Ai Shikenan ALLAH Yakama Mana. Sai Batun Kajinda Kake Kiwata Kaga Sun Tasa Yakamata Akwashe A siyar A Zuba Wasu." Abdul-Wahab Yace, "Suma A Bari In tazo Ayi Maganar. " "Nidae Innarmu koda Za'a Sai da Abar muna Biyu Mu Dan Yanka Muci." Abubakar ke Wanga Maganar Yana Tanɗe Harshe Alamar Kawaɗayi Nan Da'ake Jin Takaicinsa. Abdul-Wahab ya Hararesa Yana Cewa, "Maye! Ko ɗai Baza'a Bari Ba Sai Dawa Za'ayi, Zanyi Sabbin Ɗinkuna A Wannan Samester Da Zamu Koma." "Dan ALLAH Yaya Na." Abubakar Yafaɗa Cikin Nuna Kalar Nuna A tausaya Masa Ɗinan. Duk Suka Sa Dariya Innarmu Nacewa, "Rabu Dashi Ukku Ma Za'a Barmaka Kasha Farfesu." Abubakar Yakyalkyale Da Dariya Yana Yiwa Ya Abdul-Wahab Dariya. Da Gwalo Abdul-Wahab Ya Hararesa Tareda Cewa, "Mai Ƙaton Kai, Kawai Nidai Taso Muyi Magana." A Ɗakinsu Suka Baje Abdul-Wahab Na koro Masa Bayanin Duk Yanda Soyayyar Sa Da Khaleesat Ta Samo Asali. Yakarkare Masa Labarin Da Cewa, "Kaji Halin Da Nake Ciki Ƙanina, Kuma Wallahi Zan Iya Mutuwa In Kace In Rabu Da Khaleesat A Irin Wannan Halin."Jin Wannan Furuci Abubakar Sai Ya Rafka Tagumi Yana kallon Yayan Nasa Yama Rasa Mai Zaice. Sai Abdul-Wahab Ɗin Ya magantu, "Meye Ka Tasa Ni A gaba Haka kana Kallon Kamar Kasamu Tv? Nafa Gayama ne Dan A Samu Mafita." Abubakar Ya Sauke Ƙatuwar Ajiyar Zuciya, Kafin Yace, "Ya Abdul Da Kashawar Ceni Kafin Fara Wannan So Dana Baka Shawarar Karka Bada Imaninka Akansa Haka Saboda Akwai Matsololi Da Yawa Tatareda Wannan Son Naka Bayaga Haka Matan Yanzu Ya Abdul Basu Da Tab... " Cikin Ɓacin Rai Abdul-Wahab Yaɗaga Masa Hannu, "Wai kai Meyasa Bakinka Bai Iya Furta Alkairi Ba? Meyasa Baka Kwararamin Gwaiwa Sai dai Kacika Ni Da Kiran Matsala! Matsala!! Matsala!!! Why? Abubakar? " Abubakar Yalura Gaba dae Yaya Nasa Yayi Riga Yayi Nisa Baya Jin Kira Kuma Duk Wani Abu Yanzu Da zai Gayamasa Bazai Taɓa Fahimtarsa Ba, Indae Ba Mara Masa Baya Akan Hakan ba Dan Haka Bari Yabi Yarima Yasha Kiɗa, 'Masara Intaji Wuta Ita Ka Hwaɗi' Dan Haka Sai Yace, "ALLAH Yahuci Zuciyarka Ya Abdul Yasanya Alkairi Ya Kuma Mallaka ma Khaleesat. Yaushe Zamuje Inga Aunty Tawa?" Ga Mamakin Sa Sai Kawai Abdul-Wahab Yasaki Fuskarsa Cikin Fara'a Yace, "Tace Yau Dadynsu Da Yayan Su Zasu Dawo Zanso Muje Yau, But Yau Kaga Sallah Ne Ansha Hidima Angaji So Kawai Mubarshi Gobe Da yamma Haka Sai Muyi Wa Gidan Tsinke Kaga Furen Zuciyata Na tabbata Zaka Yaba Da Zabina." Yakarkare Maganar Kamar Da Ita Masoyiyar Tasa Yake Magana Cikin Wani Irin Shauki Abubakar Yace, "Seriosly Yaya?" "Sosaima Kuwa." Abdul-Wahab ne Mai Faɗar Wannan Maganar. Dole Ranar Khaleesat Ce Takasance Abin Firar Tasu. Shikuwa Abubakar Sai Mamaki Shin Dama Hakan Son Da Ake Faɗa Yake? Indae Haka Yake Baya Fata Yayi So. ************* Basu Samu Zuwa Biyu Ga Sallah Ba, Saboda A Ranar Abubakar ya Wuni Da Zazzaɓi Wanda Suke Zaton Wahlar Ɗunki ce Da'aka Sha Acikin Azumi Ta Sanya Hakan. Badan Haka Abdul-Wahab Yaso Ba Suka Dae Hakura Rana Ta Ukku Ga Sallah Abubakar Ɗin Yaɗan Farfaɗo Bawai Dan Yana Iya Zuwan Ba Sai Don Kula Da Ya Abdul Ɗin Nason Suje Yasa Ya ƙoƙarta Yanuna Zai Iya Zuwa. Dan Haka Da Zumuɗin Abdul-Wahab Suka Shirya Suka Caɓa Ado Cikin Wata Zazzafar Shadda Light blue (Watau Kalar Sararin Samaniya) Sai Maiko Shaddar Take Tana Kyalli Alamun Sabonci Ɗaya ce Daga Ɗinkunansu Na Sallah Wanda Duk Abubakar Ɗinne Yaɗinka Musu Su Dan Cin Bukin Sallah. Innarmu Takkalesu Takara Kallon Zuka-Zukan Samarin Nata Tace, "Masha'allah ƴayan Innarsu ALLAH yayi Muku Albarka Yau Kuma Sai Ina Haka?" Abubakar Na murmushi Yace, "Innarmu Taɗi Zamuje Ɗan Autanki Yafara Nema?" Innarmu Tace, "Auta Yayi Azarɓaɓi Meye Na Gaggauwa Haka? " Sanda Take Faɗar Hakan Zuciyar Abdul-Wahab Tai Wani Irin Bugawa Wanda Da Suna Kusa Da Juna Da Zasu Iya Jin Bugawarta Amma Sai Yalayance Yana Cewa, "Tau Meye Aciki Innarmu.?" "Babu Komai Sai Dai Komai Ai Lokaci ne, In Yazo Za'ayi Amma Ina Tunatar Da Ku Akwai Muhimmin Abu Gareku Kafin Aure Dan Haka Karku Yiwa Aure Gaggauwa, Ina Da Burin Kufara Gina Kanku Lokacin Ne Kuma Su Matan Su Zasu Nemeku Ba Ku ba. Amma Ku Tambayeku A irin Wannan Yanayi Damuke Ciki Aure Yakamace ku? Dan Haka Ku Kwantar Da Hankalinku Komai Yana Da Lokacinsa Kuma Ko Bayan Raina Zaku Fahimci Manufa Ta Ta Kufara Gina Kanku Kafin Aure." Abubakar Yaji Dadi Matuka Da Irin Bayanin Da Innarmu Tayi Wata Ƙila In Abdul-wahab Bai Fahimci Bayaninsa ba Tau Zai Fahimci Na Innarmu. Yayinda A ɓangaren Abdul-wahab Kuwa Sai Yake Ji Kaitsaye Dashi Innarmu take. Jikinsa yayi Wata Irin Mutuwa Kasala Ta Dabaibayeshi Amma Son Khaleesat Yana Ta ƙoƙarin Danne Komai Yana Nuna Masa Cewa, "Ai da Innarmu taga Yanda Suke Son Juna Dole Zata Aje Ra'ayinta Tabarsu Suyi Aure." Dan Haka Sai Wannan Tunanin YaƘara Masa Kuzari Dai Sanda Abubakar Ke Cewa, "Innarmu Gurin Matar Yusuf Zamuje Gaida Iyayenta." "ALLAH yakaiku Lafiya, ku Gaida Mana Surukar Tamu." Innarmu Ce Tayi Wannnan Maganar A Sanda Su Abdul-wahab Suka Miƙe Suna Nufin Fita. Kk Napep Suka Tare Ta Kai Su Hargidan Gimbiyar Tasa Suka Fito Yana Ƙoƙarin Lalubo Number Khaleesat Tareda Sanarda Ita Suna Bakin Ƙofar Gida. Ba'a Ɗau dogon lokaci ba Nafito Cikin kyakykyawar Shigar Da Takara Tafiyar Da Hankalin Abdul-wahab Yanaji A Ransa Inbai Aure Khaleesat ba Mutuwa ta Wajaba Gareshi. Yayinda Shikuwa Abubakar A Ransa Yake cewa, Masha'allah Lalle Khaleesat Kyakykyawa ce Ta Karshe Dole Ne Ya Abdul Yamace Akanta. Tau Da Wannan Saƙar Zuci Muka Nufi Cikin Gidan Namu Yayinda Tsakanina Da Abdul-wahab Muke Ci Gaba Da Jifar Juna Da Murmushi Da Kuma Saƙon So Kala-kala. Zubewa Sukayi Har Kasa Suna Kwasar Gaisuwa Sanda Suka Iso Falon Na Momy Tana Zaune Cikin Hijabi, Bayan Gaishe-Gaishe Take Umurtarsu Su Zauna Sosai Su Kuma Sha Ruwan Da Khaleesat Din Tajere A gabansu Kafin Baban Nata Ya'iso Yanzu Yana Kan Hanya. Daganan Kuma Sai Momy Tamike Tabar Musu Falon Abdul-wahab da Khaleesat Sai Satar Kallon Juna Ake Ana Murmushi Ana Cigaba Da Aikawa Juna Sakon So. Abubakar dae Na kule Dan Haka Yakatse Wannan Firar Ta kurame Da Cewa, "Aunty mu Barka da Wannan Lokaci. " Cikin Yanayin Kunya Take Amsawa, "Yawwa Ɗan kanenmu Ina Fatar Kana Lafiya Ya Kuma Innarmu." "Alhamdullah Muke, Innarmu Kuwa Tana Gaisheki kwarai da gaske." Abubakar ne Yayi Wannan Maganar Yana Mai ƙokarin Tsiyaya Ruwan Faro Acikin Cup Kafin Ya dauka Yakai bakinsa, Adaidai Lokacin Nake Cemasa "Ina Amsawa ALLAH karawa Innarmu Lafiya da Nisan Kwana Masu Albarka." "Aunty Kifa daena Jin Kunya Na Ni Nan Dakike Ganin Nine Ɗan Aikenki Da Zan Rika Yo Maki Cefane Dan Yanzu Haka Kina Tarewa Zan Yowa Innarmu Hijira Kular Abinci Na Gidan ku Zan Maidata Saboda Adinga Shan Man Shanu Tareda Ni." Cikin Dariya Nace, "Kai ka soma Yiwa Innarmu Haka? " "Yo meye Aciki Ki Tambayi Yaya kiji Ko Yan.... " "Kai Auta Kashiga Ukku Wannan Zuba Haka Sai Kace Radio?" Ya Abdul-wahab Ke Masa Wannan Maganar Yana Harararsa. Nikuwa Nai Maza Na Taresa Da Cewa, "Tau?... Kajimin Mutum Shikenan Tun Yanzun Zaka Fara Shiga Tsakanina Da ƊAn Kane na?" Duk Mukayi Dariya Abdul-wahab Yace, "ALLAH Bada Hakuri Mai Ɗan Kane Ina Gefe Sai Na Ganku A Rana." "insha'allah Ma Bazaka Gannmu Ba." Abubakar Ne Ke Wannan Maganar Nima Nace, "Gayamasa Dae." Shidae Abdul-wahab Sai Yafita Batun Mu Ya Buɗe Gwangon Maltina Da Yaketa Raɓar Sanyi Kamar Yanzun Aka Fito Dashi Daga Frij Ya soma Nikuwa Da Abubakar Sannu A Hankali Muna Cigaba Da Fahimtar Juna Ta hanyar Yar Tattaunawar Damuke. Acikin Wannan Halin Dady Yasamemu Dan Haka Sai Namike Nabasu Guri Su Gaisa. Bayan Gaishe-Gaishe Dady Yasoma Dan Yimusu Tambayoyi Wanda Mafi Yawa Abubakar Ne Ke Bada Amsa. Kafin Yayi Musu Fatar Alkairi Yamike Yabasu Guri Yana Mai Cewa, "Inkunje Gida ku Gaida Magabatan." Cike Da Karsashi Suka Amsa Saboda Yanda Duk Gidan Dai Kowa Yake Karramasu. Bayan Fitarsa Abubakar Yayi ƙoƙarin Matsowa Kusa Da Ɗan Uwan Nasa Yana Cewa, "Maganar Gaskiya Yaya Kayi Zaɓi Mai kyau, Badon Kalubalen Da Nake Ha.... " Abdul-wahab Yayi maza Yadaga Masa Hannu Yana Mai Cewa, "Kaga Auta Inba Alkairi Zaka Faɗi ba Kayi Shiru Ai Ko Manzo Yahore mu Da Haka ko?" Batareda Yajira Amsarsa ba Yaci Gaba Da Cewa, "Insha'allah ma Innarmu Zata Yarda Arziki Ai Na ALLAH Kuma Shike Komai Kuma Shi Yana Juyarda Tsanani Zuwa Sauki, Dan Haka Ni Nasani Innarmu Bazata Kasa Fahimta Ta ba Duk..." "A'a Yakikayi Tsaye Anan Baki Shiga Ba Muje Naga Surukin Namu." Ya Nuradden Ne Yakatsamin Laɓen Da Nakeyiwa Su Abdul-wahab Dan Na Nufo Ɗakin Naji Suna Wannan Maganar Dan Haka Sai natsaya In Saurari Maganar Tasu Tau Kuma Saiga Ya Nuradden Yakatsemin Hanzari. Jiki Ba kwari Muka Shigo Nakuma Saman Kujera Nazauna Ina Kallon Yanda Suke Gaisawa Da Ya Nuradden Nakurawa Kyakykyawa Fuskar Abdul-wahab Ta Yan Fulanin Asali Ido Ina Ji In Ban Auri Abdul-wahab Ba Irin Wannan So Danake Masa Mutuwa Ce Kawai Zanyi Nayi Nisa A Tunanin Sai Jinayi Ana Ɗan buga Hannaye A Gaban Fuskata Irin Yatsun Nasa Suna Bada Yar Kara Kas! Kas! Nai Firgigit Ina Sunne Kaina Tareda Murmushi Abdul-wahab Ya Zauna Gefena Yana Duk Wannan Tunanin Nameye Haka? Tunanin me kike Haka?" Murmushi Nayi Ina Kallonsa Harcikin Ido Da wani Irin Shaukin So Nace Masa, "Tunanin ka mana Nake." "Tau Ai Gani Kusa Dake Ko? Dan Haka Saiki Hutar min Da Zuciyarki Wajen Tunanin." "Yaushe Kake Tunanin Za'a Saka Mana Rana?" Abunda Naji Bakina kenan Yafurta Nayi Saurin Rufe Fuskata Cikin Matsainai Ciyar Kunya Ba'a Binda Nai Niyyar Faɗa ba Amma Wannan Tunanin Shine Yake Zuciyata. Cikim Murmushi Abdul-wahab Yace, "Kidaina Jin Kunya Ta My Fretty Kuma Ni Kaina Tambayar Danake Son Yi Maki kenan Saboda Naƙagara Inkai Wannan Kyakykyawan Fure A gidana." Nidae Nayi Shiru Ba'abun Cewa Face Na Sunkuyar Da Kai Ina Aikin Murza Zoben A zurfar Dake Hannuna Dan muddim Nace Zan Cigaba Da magana Tau Ba Shakka Zan Ta Baran-Bara Mana ne. Kamar Abdul-wahab Yasan Tunanin Danake Yace, "my Fretty pill free Kigayamun Abun Da Yake Ranki, In Bamu Gayawa Juna Sirrin Zukatan mu Waza mu Gayawa? " "Babu!! " Nafadi Hakan Ina Mai Sauke Wata ƙaƙƙafar Ajiyar Zuciya Kafin Nadora Da Cewa, "Zanwa Iyayena Maganar Duk Abunda Suka Yanke Zakaji? " "Da gaske? " Nagirgiza Tareda Bashi Tabbacin Da gaske. Tau Haka Firar Tamu Takasance Ta Iya Tsawon Lokaci Kowanenmu Na kokarin Nuna Wa Dan Uwansa Yanda Yake Da Muhimmanci Acikin Ransa Hardae Yamike Yana Mun Sallama Tunda Dama Shi Abubakar Tuni Yafita Waje Tareda Ya Nuradden. Namike Ina Cewa, "Baku Ci Komai Ba fa, Dan ALLAH ka Zauna Inkirawo Abubakar Yazo Ku... " Yayi Maza Yace, "A'a Munsha lemu Dan Haka muna Godiya Bari Kawai Zamu Wuce, " Nashagwabe Masa Ina Buga Kafafu "Kai Habibi Wallahi Su Momy Bazasu Ji Dadi ba Bakuci Komai ba ALLAH! Kuma Wallahi Ni Zata yiwa Faɗa Tace Laifinane. Sannan inda Kagani Tun Safe Muke Ta Aikin Haɗa Kayanan Nifa Harda ƙonewa Nayi." Ba Sai Abdul-wahab Yalalace Gurin Kallon Wannan Shagwabar Ba Yana Kara Jin Cewa Lalle Nann Duniya Bashi Da Mata Inba Khaleesat ba. Cikin Wani Irin Shaukin So Yace, "Tau Shikenan Yanzun Yakike So Ayi Baby? " "Yanda Za'ayi Kabari Na kwashe Muku A Leda Dan Nan Bazaku Sake Ba." "Kajita Da Wayo Mexai Hana Musake Nan Ma Ai Muma Gidanmu ne Ko?" "Eh Din Dai. " Batareda Najira Cewarsa Ba Nakwashe Duk Kayan Snacks Dinda Muka Toya Masu Nida Aunty Shahida (Matar Ya Nuradden) Kafin Muka Fito Tsakar Gida Nashiga Dakin Da Su Ya Nuradden Suke Shi da Abubakar Ina Sanar Musu Zasu Wuce Wai, Dan Haka Abubakar Yamike Yafito Suna Sake Yin Musabaha Da Shi da Ya Nuradden Nashiga Ɗakin Aunty Shahida Nasameta Da Ɗaurin Kirji Tana Shafa Mayuka Ga Alam Tafito Wanka Ne. Nace Mata Su Abdul-wahab Zasu Shigo Gaidata Dan Haka Tai Maza Tace, "Bani Hijabi Can. " Namiko Mata Tasaka. Sanda Su Kuma Suke Sallama A bakin Kofar Ɗakin, Muka Amsa Kafin Suka Zube Nan Bakin Ƙofar Suna Gaidata Sannan Suka Mata Sallama. Har Tsakiyar Gida Na Rakasu Muka Rabu Kamar Bazamu Rabu Da Hubbina Ba. Najuya Cikin Farinciki. Suma Suka Tafi Cikin Murna. Da Murmushi Nashiga Ɗakin Momy Ina Cewa, "Momy Kinga Abdul-wahab Ko? " "Eh Nagani, Amma Ai Kema Kinsan Baza'a Hadashi Da Alhaji Saminu Ba ko? Ke ƙuruciya Shi Ƙuruciya Wazai Ɗora Wani Akan Hanya? Ni Banga Wani Makosa Da Alhaji Saminu Keda Ita Dakika Fifita Soyayyar Wannan Yaron Akan Tasa ba." Jikina Yayi Mugun Sanyi Meke Shirin Faruwa Ne Karfa Alhaji Saminu Yazamowa Rayuwata Matsala Tunjiya Yazo Gidannan Nake Ganin Kamar Duk Ya Siyesu. Kuma Ni Wallahi Dana San Haka Zata Faru Da Ban Bashi Dama Yashigo Gaida Su Momy Ba. Dan Dai Shi Sarkin Naci ne Kuma Ba yanda Zanyi Dashi Namasa Iso A gurin Su Momy Da Sai Dai Ai Na banza Ne. Tunda Tun Kafin Ma Nai Masa Ison Sai Da Yasallama wa Dady Suka Fara Ganawa Dan Ma Dadyn Ne Yace Min Inje Waje Ina Da Baƙo Danshi A Tunanin sa Ma Shine Abdul-wahab ɗin Da Na Ishesu Da Labarinsa. Na numfasa Da Wannan Dogon Tunanin Danayi Kafin Nace, "Amma Momy Ab..... " "Kinga Karki Isheni Da Surutu Sallah Zanyi, Magarib Tana Karatowa Kije Dadyn ku Na San Ganinki Yana Can Falo. " Cikin Mugunyar Kasala Da Mutuwar Jiki Na Nufi Inda Dady Yake Sai Dai Shima Ina Zuwa Yana Fitowa yacemin Zashi Masallaci Inje Inyi Sallah Kafin Yadawo Inzo Zaiyi Magana Dani. Nace, "Tau. " kawai Kafin Na nufi Dakina Domin Yin Sallar Nima Ina zuwa Naga Waya ta Na Haske Alamar Anturo Sako Dan Haka Sai Najawo Wayar Daga Cajin Dake Take Naduba Abdul-wahab Ne Yasanar Dani Sun Isa Gida Da Kuma Sauran Yan Kalaman Ƙauna Haka. Murmushi Kawai Nayi Sai Dai Nakasa Samun Kuzarin Mayarmasa Saboda Maganar Da Momy Tayimin Ta Tsayamin A Rai Ga Kuma Dady Zai Gana Dani Ko Meye Hakan Ke Nufi? Dan Haka Komai A kasalance Nakeyinsa Har Na Ida Sallar Na Zauna Ina Lazimi Zuciyata Cike Take Da Wasu Wasi Da Tunane-Tunane. Adu'a Nayi Na Shafa Na Nufi Falon Baba Nasameshi Zaune Yana Kurba Shayin Cittah Da Momy Takai Masa A Cupi Guri Na Samu Na Zauna Ina Mai Jiran Inji Mai Dady Zaice. Saida Yakurba Shayin Kafin Yadubeni Yana Aje Cup Din Kan Center Table ɗin da ke Gabansa "Naga Abdul-wahab Nakuma Ga Alhaji Saminu Duk Kuma Na Yaba Da Zaɓinki Saidai Mu A Matsayin Magabatanki Mun Zaɓa Maki Alhaji Saminu...... Daradammmmmmm Shine Ƙugin Da zuciyata Tayi. Tirkashi!!!!!! Muje Chapter Ta Gaba [9/5, 9:13 PM] FA'IK: Typing....... 💻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....7 Mallakar 👇 Fa'IK ✍️ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Daram Dam Dam!! Shine Abun Da Zuciyata Tayi Naɗago Ina Kallon Dady Mu Cikeda Tashin Hankalin Da Nakasa Ɓoyewa Nace, "Dady Alhaji Saminu? " "Eh Alhaji Saminu Kuma Nabashi Damar Turo Magabatansa Saboda Haka Saiki Kula Banbancin Ki Da Matar Aure A Yanzu Kaɗanne. Ke Yanzu Ƙarama Ce Amma Nan Gaba Zaki Gano Alfanun da Mu Iyayenki Mukayi Maki. Alhaji Saminu Yagirmemiki Nesa Ba Kadan Ba, Sannan Shi Yake Da Kuɗin Da Zai Tallafi Bukatunki Amma Abdul-wahab Shi Ƙuruciya Ke Ƙuruciya Tau Waye Zai Kwaɓi Wani? Sannan Shi Kansa Meyaci Balle Yabaki? Babu Wani Abu Da Zaki Tsira Dashi Face Soyayyar sa Wadda Ita Ɗin Bata Iya Cika Guraben Ingantan Rayuwarki Ba. Banbanci Dae Zayyawa Tsakanin Alhaji Saminu da Abdul-wahab Kuma Duk Wani Mai hange Na Alfanu Zaya Yaba Da Zaɓin mu A gareki Banda Ke Da A Yanzu Da Soyayya Ta Makantar Ta Kuma Rufewa Ido." "Dady Kutaimaki Rayuwata Wallahi Bana Son Alhaji Saminu Ni Abdul-wahab Nake So. Wallahi Bazan Iya Rayuwa Babu Abdul-wahab Dan ALLAH dady Ku....." "Ke! Ke! Ke! Kin Ishi Mutane Da Hayaniya Oya Fice Daga Falon Nan Shasha Kawai Ana Nunamaki Gata Kina Wani Haukan Banza. " Dady Ke Fadar Hakan Cikin Fusata Sai Ga Momy Tashigo Falon Tana Faɗin, "Bari Nayima Maganin Yar Banza. " Tana Faɗin Wannan Ne Tana Dube-Duben Inda Zata Samu Wayar Wuta Ganin Hakan Yasa Nai Azamar Ficewa Daga Falon Ina Ta Kuka Tareda Ihun Wallahi Bana Son Alhaji Saminu "Ja'ira Daki Tsaya Ki Ga Yanda Zanyi Maganinki." Momy Ce Ke Wannan Maganar Ranta A ɓace Kan Katifa Nazube Inata Gurshuƙeƙen Kuka Kamar Raina Zai Fita Inajin Wannan Shirin Kamar A Mafarki Tayaya Zan Iya Rayuwar Da Ba Abdul-wahab? Sannan Shima Kamar Yanda Nafahimci Maganar Da Suke Can Gidansu Akwai Matsala Duk Meye Masababbin Wannan Damuwar Meye Laifin Sa? Dan Baya Da Kuɗi? Tau Ai Ba kuɗine Farinciki Ba. "Wayyo ALLAH Abdul-wahab Inba Kai Mutuwa Zanyi. " itace Kalmar Da Nake Ta Nanatawa Cikin Kuka ******* Sanda Su Abdul-wahab Suke Komawa Gida Ana Gabda Sallar Magarib Dan Har Wasu Massalatai Ansoma Kiran Sallah Adaidai Wannan Lokacin Ne Kuma Kk Napep ke Aje Maman Walida Da Yan Yaranta Guda Uku Ammar (mai Sunan Babansu) Da Walida Sai Kuma Hanifah. Cikin Farinciki Su Abubakar Suka Tareta Suke Kuma Tayata Sauke Kayan Suna Cewa, "Maman Walida Kinyo Tafiyar Dare." Cikin Gajiya Da zaman Mota Tace, "Kudai Ku Bari Kawai Motar Tamuce Ta Lalace Mana Dai-Dai Nan Garin Talatar Mafara Kafin Ta Saɓa Hanifa A Kafaɗa Tanufi Cikin Gida. Sukuwa Su Abdul-wahab Da Abubakar Suka Shiga Hidimar Shigarmata Da Kaya Cikin Gida. Innarmu Kuwa Sai Kai Kawo Takeyi Da Yan Jikokinta Cikin Farinciki Da Murnar Ganinsu Bayan Tsawon Lokacin Da AKa ɗauka Basu zo Sakkkwato Ba. Kowanensu Buta Yaɗauka Yayi Arwallah. Su Abdul-wahab Suka Nufi Massalaci Yayinda Sukuwa Su Innarmu Sukayi Haramar Tasu Sallar Nan Gida. Bayan Sungama Sallah Innarmu Tagabatar Musu Da Abinci Da Kuma Fura Mai Sanyi Itadai Maman Walida Furar Kawai Ta iya Sha Saboda Gajiya Kafin Innarmu Tadubeta Tana Mai Cewa, "Akwai Ruwa Ki ɗiba Ki watsa Ko kya Wartsake. " Dan Haka Sai Tamike Taɗibi Ruwan Ta watsa Tafito Ne Sanda Su Abubakar Suka Dawo Daga Massalaci Nan Kuma Aka Shiga Firar Yaushe Gamo? Inda Nanne Abdul-wahab Yazaro Wayar Sa Yaturawa Gimbiyar sa Sakon Sun Dawo Sai Dai Ga Mamakinsa Haryanzun Ba Reply Ɗinta. Abinda Kuma Bai Taɓa Faruwa Ba. Dan Haka Duk Sai Walwalarsa Tarage Yakeji Tamkar Yayi Tsunsuwa Yaje Gareta Yaji Meyake Faruwa. Sai Firar Tasa tazama Rabi da Rabi Hardae Maman Walida Ta Sanya Baki Da Cewa "Nikam Ƙanina Abdul Ko Da Wata Matsalane? Duk Nakasa Gamsuwa Da Yanda Nasameka menene?" "Badole Aunty Ki Kasa Gamsuwa Da Yanda Kika Samesa Ba Yaɗaukowa Kansa Abunda Zai Hargitsa Masa Lissafi." Abubakar Ne Ke Wannan Maganar Acikin Ransa Amma A Fili Sai Yake Cewa,"Maman Walida Ai Dole Ki Samesa A Haka Exam Zasu Soma Bayan Sallah Nan Fa?" "Eh Tau ALLAH Yataimaka Sai Adage Da Karatu Da Kuma Nafilfilin Dare Ko Mu Haka Mukeyi Sanda Muna Jarking" Ta Kammala Maganar Tana Dariya Wanda Sai Da Kowa Ya Dara Dalilin Haka Ma Sai Firar Tajuye Ta Koma Ta Skull Maman Walida Tashiga Basu Labarin Yanda Tayi Karatunta Can A Da Su Kuma Suna Gayamata Irin Sauyin Da Aka Samu Yanzu A Karatun Nan Kuma Tashiga Basu Labarin Irin Burin Da Taciwa Karatun Ta Taso Ta Kammallah Ta zama Ma'aikaciyar Jinya Dan Ta Tallefesu Saboda Taga Irin Banbancin Da Ake Nuna Musu A Dangi Sai Dai ALLAH Bai NuFa Ba. Sai Dai Kuma Tana Farinciki Da Cewar Gashi Yan Ƙannenta Zasu Cika Mata Burin Hakan Dama Burin Innarmu Na Son Ganin Sunyi Karatu Sun Zama Wani Abu. Sanda Take Maganar Abubakar Yaɗago Kansa Yana Mai Kallon Dan Uwansa Tareda Yimasa Alamar Ka Gani Ko Yaya? Shikuma Abdul-wahab Sai Yay Biris Tareda Yimasa Kallon 'Ku Ta Shafa Nidae Aure Nake So. ' Da Sanyin Safiya Innarmu Nata Kai Kawo Tsakanin Madafi Da Ɗaki Karin Kummalo Take Hadawa Kwatsam! Taga Santaleliyar Budurwa Tafado Gidan Da Sallamar Ta Innarmu Ta tarye Ta Cikin Mutumci Tana Mai bata Guri Tace Ta Zauna. Bayan Na Zauna Ne Muka Kara Gaisawa Cikin Kunya Nace Mata Gurin Abdul-wahab Nazo Cikin Mamaki Tai ta Nanata Sunan Kafin Tace, "Yana Ciki Bari Nai Masa Magana. " Kafin Innarmu Tanufi Ɗakin Su Abdul-wahab Ɗin tana Buga ƙofarsu Akai Sa'a Abdul-wahab Ɗin Yabude Ƙofar Kafin Innarmu Tace, "Kayi Bakuwa." Batareda Ta jira Cewarsa Ba Tai Juyawarta. Tana Zuwa Cikin Fara'arta Tace, "Yana Zuwa Kinji 'Ƴata? " Nace Mata "Tau. " Kafin Tajuya Taci Gaba Da Kai Kawonta Tsakani Kitchin Da Ɗaki Tana Kula Da Girkinta Duk Inda Ranta Yake Yaɓace Saidai Bazaka Taɓa Ganewa ba Saboda Tsananin Dangana Da Kuma Hakuri Irin Na Innarmu. Shikuwa Abdul-wahab Tsaye Yayi Cikeda Zullumi Da Tarardaddi Wacece Tazo Neman Shi Hargidan Su? Shida Ba Wasu Yan Mata Yake Dasu Ba Khaleesat Ce Kuma ko Sau ɗaya Bai Taɓa Gigin Kawota Gidan Nasu Ba Tau Wacece? Tambayar Da Yakasa Amsawa kansa Kenan Dan Haka Sai Yazaɓi Yazo Kawai Yaga Ko Wacece. Wani Irin Luguden Tara Zciyarsa Tayi Sanda Yayi Tozali Da Kyakykyawar Fuskarta Fara Fat Wacce Babu Wani Kwalli A kanta Sai Annuri Kyau Take Fitarwa Wanda Ake Kira Natural Ɗinan. "Khaleesat! " Yafurta Hakan Batareda Yasani Cewa A Fili Yayi Maganar Ba. Jin Amon Muryarsa Yasa Na Ɗago Ina Kallonsa Yakaraso Cikin Kasalar Jiki Kafin Yace, "Khaleesat Waye Yanuna Maki Gidanmu? " "In Banda Abunka Ai Matanbayi Baya Ɓata Habibi. " "Hakane, Sai dai Abin Da Mamaki Please Ki Gayamin Waye Yanuna maki Gid..... " Cikin Ƙosawa Nataresa Da Cewa, "Wannan Ba Shine Abinji Ba Kuma Dae Nice Nazo Gurinka Da Tawa Matsalar Dan Haka Kabari Nafaɗi Tawa Matsalar Kaima In Wannanne Yadameka Sai Ka sameni A gida Zangayama Wanda Yakawo ni. " Abdul-wahab Ba Baki Sai Kunne Yarasa Abin Cewa Face Kai Kawai Da Yake Ta Girgizawa Kafin Yadan Motsa Laɓɓansa Da Nufin Cewa Wani Abu.. Nataresa Da Cewa, "Abdul-wahab Matsala Gagaruma Ke Tunkarar Soyayyar mu Iyaye Na Suna Neman Hana Mana Cikar Burinmu Dan Sun Bada Aurena Ga Waninka Yanzu Haka Ansa Rana Nan Da Wata Ɗaya Shine Nazo Naji daga Gareka Meye Abinyi?" Abdul Duk Hankalinsa Yatashi Ya kuma Ruɗe Yace, "Tau Meyayi Zafi Haka Khaleesat? Meyasa Su Momy Bazasu Dubi Irin Soyayyar da muke Wa juna ba? Meyesa Su Momy Bazasu Kalli Makomar Rayuwar mu Ba idan Har Suka Rabamu Da Juna ba?" "Abdul-wahab Duk Ba Wannane Gabansu Ba, A Yanzu Kuɗi Suke Kallo A yanzu Zamani Yazo Da Kuɗi Sune Komai In Kana da Su Tau Ba'a Bukatar Wani Bincike. " "Hummm! " Abinda Abdul-wahab Yayi Kenan Domin Duk Inda Wani Tunani Nasa Yake Yatsaya Cak! "Habibi Nazo ne Muje A Ɗaura Muna Aure A Kowane Wurine Kaga Yadace Muje Sannnan Duk Inda Ka'ajiyeni zan Zauna. Wallahi Abdul Bazan Iya Jurar Rashinka ba Zan Iya Komai Dan Ɗorewar Soyayyar mu. " Abdul-wahab Yajuya Yakalli kowane Sashe Na Gidansu Babu Kowa Atsakar Gidan Nasu Sai Su Kaɗai Kafin Yadawo Da Kallonsa Gareni Yace, "Khaleesat Wannan Ba abune Mai yuwuwa ba Zo muje Gurin Innarmu. Gara Dai Aje Can Gidan Naku A gyara Matsalar. " "Matsalar Bata Gyaruwa Indae Gidanmu ne Da Tana Gyaruwa Bazan zo Gidanku A mamakance ba. Kaidai Wannan Kawai Shine Mafita." Abdul-wahab Bai Damu Da yabani Amsa ba Sai kawai Yajuya Ya Nufi Ɗakin Innarmu Yana Yafito ni Da Hannunsa Cewa, "Zomuje." Innarmu Takare Komai Nata Zaune Kawai Take Tana Juya Kunun Dake Gabanta Cike Da Boket Domin Tabbatarwa Yaji Sugan Da Tasa Masa Yayinda Su Walida Ke Gabanta Rike Da Cup Dinsu Jiran Tazuba Masu kallo Kawai Ta bimu Dashi Wanda kai Da Ganinsa Kasan Yana Cikeda Tarin Ma'anoni. Muka Durkushe Mu Duka Biyun Gabanta Kafin Naɗago Kai Dan Kara karantar Fuskarta Sai Dai Nafahimta Ita Wannan Matar Dae Komai Nacinka Baka isa ka gano Komai A Fuskarta ba Saboda Kwarjininta Da Haibarta Duk Sukan Ɓoye Komai. Abdul-wahab Yace, "Innarmu Wannan Itace..... " "Karka Ɓatawa kanka Lokaci. Naji Duk Abinda kuke Cewa na Kuma Fahimci Komai. Ai Kaga Abinda Nake Nuna Maka Ko? Cewar Ka Tsaya Kafara Gina kanka Takwan Ko? Rayuwar Ta sauya Yanzu Mutane Hannu Mai Miya Aka lasa. Sannan Inba Da Rigima Irin Taka Abdul-wahab Meka taka Yanzun Da zaka iya Aure? Sadaki Muhalli Ko Meye?. " Innarmu Ta numfasa Cikin Takaicin Halin 'Yayan Zamani. Da Rashin Kunyar Da Suke Da Ita Wai Abdul-wahab Ne Zai zo ko Budurwar ce Zata Baro Gidansu Taxo Gurin Saurayinta Duk A kan So! "Baiwar ALLAH. " Tafaɗi Hakan Tana Mai Kallo Na "Kiyi Hakuri Kije Kibi Umarnin Iyayenki Kinji? Mu Talakawa ne Bamu Da Abin Aurar Da Abdul-wahab, Domin Abdul-wahab Bashi Da Abin Aurenki, Sannan Bashi da Kuma Abinda Zai Riƙe ki. Iyayenki Sunfi ki Sanin Abinda Yafi Dacewa Dake Dan Haka Amatsayi Na Uwa Ina Baki Shawara Komawa kiyiwa Iyayenki Biyayya Kinji? " Innarmu Nagama Fadar Hakan Takarbi Kofin Walida Daketa Rigima A Zuba mata Kunu Ta Sanya mata Kunun Sannan Tamika Mata, Kafin Takama Hannun Hanifa Tanufi Da ita Waje, Dan Ita Yanzu tafarka Daga Barci. Abdul-wahab Yadurkushe Nan Ƙasa Wasu Hawaye Zafafa Suna Saraftu A Fuskarsa, Cikin Sanyin Jiki Namike Ina Mai Share Hawayen Da Ke Gow Slow A Fuskata Nakama Hanyar Fita Waje. Ina Gabda Fita Gidan Abdul-wahab Yaccimin Yana wani Tangaɗi Kamar Wanda Yasha Barasa. Najuyo Na kallesa Kafin Nasake Maida Idona Kan Titi Ina Neman Abin Hawan Da Zai Mai dani Gida. "Kiyi Hakuri Khaleesat, Komai Yayi Tsanani Maganin Sa ALLAH, Zanzo Gidan Idan Anjima Muji Yaza'a Mu ɓolluwa Lamarin " Shi ne Kalaman Da Abdul-wahab Yake Faɗamin Bayan Nahau Kk Napep Nadago Fuskata Cike Da Hawaye Nace, "Abdul Karka Wani Wahlarda Kanka Ni Nariga Na Samarwa kaina Mafita Kowa dae Kalmar Ɗaya ce Kuɗi! Kuɗi!! Kuɗi!!! Dan Haka Ni Zanyi Abinda Nake Ganin Yadace. Dan Haka Karka Ɓatawa kanka Lokaci Zuwa Gidamu Dan ko Kazo Bazan Saurare Ka ba." "Meyasa Zaki ce Haka? Haba Khale...." Naɗaga Masa Hannu "Karka Karyamin Gwaiwa Abdul Kaje Ka Kawai" Kafin Nayiwa Mai Kk Napep Umurnin Kawai Muwuce. Nan Muka Bar Abdul-wahab Tsaye. Kamar Iccen Da Aka Dasa Yarasa Gaba Zai Ko Baya Zuciyarsa Na Tafarfasa Hawaye Naci Gaba Da Gudu A Damdamalin Fuskarsa Yajuyo Yanufo Cikin Gida Wani Irin Duhu Gidan Ke Masa. Kai Tsaye Ɗakin Su Ya Nufa Ya Sami Abubakar Lokacin Yafarka Daga Barci Yanazuba Makilin A Brosh Dinsa Da Niyyar Zai Fito Ya Wanke Bakinsa. Turus! Abubakar Yayi Yana Kallon Abdul-wahab Ɗin Da Yashigo Duk A Firgice Kafin Yace "Yaya Lafiya?" Shiru Ba'amsa Daga Abdul-wahab Ɗin. Dan Haka Abubakar Yajuyo Yazo Ya Zauna Kusa Dashi Yana ƙara Tambayarsa, Ga Mamakin Abubakar Sai Ga Abdul-wahab Na Wani Irin Kuka Wanda Tunda Yake Bai Taɓa Ganin Yayi Irinsa ba. Lamarin Da Yatayarwa Abubakar Hankali Kenan Yafita Ɗakin Nasu Da Gudu Yana Kiran Innarmu Tazo Tagani. "Innarmu Zo Ki Gani Mene Yasamu Ya Abdul?" Yana Faɗar Hakanne Tare Da Ƙokarin Jawo Hannun Innarmu Yayinda Ita Kuwa Tafisge Daga Riƙon Da Yayi Mata Cikin Fushi Tace "Ba inda Zanje Ai Duk Wanda Baiji Bari Ba yaji Hoho Gashinan Dae Kuma Tun Ba'a je Ko'ina Ba Yaga Illar Abinda Nake Nuna Maku. " Cikin Rawar Murya Abubakar Yake Cewa, "Wai Me Yafaru Ne Innarmu? Kun Sani A Kwana Dan ALLAH kumin Bayani." "Babu Abinda Yafaru Yarinya Yaje Nema Sukuwa Iyayenta Suka ce Bazasu Bashi 'Ƴarsu Ba Dan Baida Kuɗi." Innarmu Nagama Faɗar Hakan kuma Taɗauki Buta Tashiga Arwallah Dan Yin Sallar Walha Kamar Yadda Tasaba. Shikuwa Abubakar Yayi Tsaye Cikin Zullumi Da Taraddadi Kafin Yasake Nufar Ɗakin Nasu Ya'iske Abdul-wahab Yahaɗe Kai Da Gwaiwa Yana Ta Aikin Sauke Numfashi Yadurkushe Gabansa Yana Mai Cewa, "Yaya Kaga Abinda Nake Nuna Maka Ko? Kaga Illar Abinda Nake Gayama ko? Tun ba'aje Ko'ina ba ko?. Shi..... " Wata Irin Tsawa Abdul-wahab Yayi Masa Yana Cewa, "Ka'isheni Auta Kafice Kaban Wuri Bana Son Jin Mugun Surutun Ka." Dole Abubakar Yamike Cikin Sanyin Jiki Yararumi Merkealin da Brush Dinsa Yafice Cikin Ƙunar Zuciya. Akan Wannan Halin Da Suka wayi Gari Dashi. Gashi Maman Walida Tunjiya Dataje Bukin ƙawar Tasu Bata Dawo ba Su Walida kawai Da Ammar Tabari. Kila Da Tana Nan Data Shawo Kan Matsalar Tunda Innarmu Najin Maganar ta Da Shi Kansa uban Gayyar Watau Abdul-wahab. Shikam Abubakar Baya Da Zaɓi Illai Yashirya Tsaf Kafin Ya Lalubo Yan HandOut Ɗinsa Yazo Yaɗibi Abin Ƙari Ya Karya Kumallo Kafin Yace, "Innarmu Naje Skull Sai Nadawo." Fuska Ba Yabo Ba Fallasa Tace, "ALLAH Yatsare. " Minti Biyar Da Fitarsa Shima Abdul-wahab Yafito Goye Da Jikkarsa Ko Wanka Baiyi ba Balle Aje Maganar Yayi Break Fast Ya'isa Gurin Innarmu Yace, "Innarmu Zanje Makaranta." Ko Inda Yake Bata Kalla ba Tace, "Adawo Lafiya." Ko'ajikinsa Yakama Hanya Yafice. Tirkashi! Lokacin Ƙanƙani Fa Komai Na Neman Wargajewa A Familyn Nan Kuma Duk SONEEE SILAR KOMAI Muje Zuwa muji Yazata Ƙarƙe! [9/5, 9:13 PM] FA'IK: Typing....... 💻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....8 Mallakar 👇 Fa'IK ✍️ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Wannan Al'amari Ya Matukar Ɓatawa Innarmu Rai! Watau Akan Ta Nunawa Abdul-wahab Hanya Shine Zai Ɗau Fushi Da Ita? Lalle Wannan Zamani Yakai Inda Ya Kai Abdul Mai Tsananin Ladabi Da Biyayya Gareta Mai Tsananin Sadaukarwa Akan Komai Nata Yau Shine Kan So! Yake Neman Ɓauɗe Mata? Tunanunka Barkatai Sukai Ta Ziyartar Zuciyar Innarmu Suka Ƙara Haddasa Mata Kasalar Tashi Tayi Abinda Zai Amfane Ta Karshe Dae Tace "Ba'a Komai! Komi Yafaru Da Sanin ALLAH. " A dae-dae Wannan Lokacin ne Maman Walida Tashigo Gidan 'Yan Yaranta Sukai Ta Tureneniya Gurin Yimata Oyoyo! Taɗaga Kowanensu Cikin Farinciki Saida Aka zo Kan Ammar Tace, "Kai kam Dattijo na (Dan In Tana Nishaɗi Tana Kiransa haka.) Ka Girma Dan Haka Ka Girmi A ɗaga Ka." Duk Sukayi Dariya Shikuwa Ammar Yashiga Buga Ƙafa A Kasa Yana Kukan Shagwaba Tareda Cewa, "Momy Ni Bazan Yarda Ba, Ai Dady Ɗagani Yake Shikam. " "Dady Kace Nikam Ina Nakai Karfin Dady Ne. Innarmu Sannu Da Gida. " Tamai Da Maganar ta Gurin Innarmu Ganin Inta biye ta Yaran Bazasu Gaisa Da Innarmu ba. "Yawwa Ƴan Buki kundawo? " Innarmu ke Amsa Mata Da Hakan "Eh! Duk Nagaji Wallahi. " Maman Walida ke Maganar Tana Nemawa kanta Inda Zata Zauna. "Ai Ba Zama Yakamata Kiyi Ba Ki Nemi Abinda Zakici Ko?" "A'a Innarmu Bana jin Yunwa Wallahi." Innarmu Tace, "Tau Ai Shikenan Ina Amaren Suna Can An kai ko? " "Amarya Na Can, Amma Innarmu Lafiya Kuwa? " "Da Akayi Me Fa?" Innarmu Ta Faɗa Tana Ƙokarin Nuna Bakomai. Maman Walida Tace, "Innarmu Naga Duk Idanki Yay Ja! Gashi Duk Dai Kamar Bakya Cikin Yanayi Mai Daɗi. Kodai Jikin ne Innarmu? " Innarmu Tace, "A'a Kawai Dai Ina Tunanin Sha'anin Yaran Zamani ne wai Kamar Abdul-wahab Dan Na Nuna Masa Abinda Zai Taimakesa A Rayuwa Shine Zai Ɗau Fushi Dani Baki Ga Yanda Yabar Gidan Ba." Cikin Rashin Fahimta Maman Walida Tace, "Kamarya Innarmu? Nifa Ban Fahimta Ba Gaba Ɗai." Innarmu Tace, "Wata Yarinya ya Jajibo Sukuma Iyayenta Suka Ce Bazasu Bashi Aurenta ba Dan....... " Nan Dae Innarmu Takwashe Iya Abunda Tasani Gameda Lamarin Ta Gayamata Maman Walida Tarafka Tagumi Cikin Mamaki Tace, " Amma A Fuska Kamar Abdul Bazai Aikata Hakan ba Shikuwa Meye Ya Matsesa A Lamarin Aure Da Yake Gaggawa Haka? Ko Bayan Haka Me Muka Aje Yanzun? Meya Tanadarwa Auren Da Zai Tunkari Wannan Maganar Hala?" Innarmu Ta Muskuta Cikin Takaicin Lamarin tareda Cewa, "Kema Dai Kin Gani 'Yar Nan." "Innarmu Daina Ɗaga Hankalin ki Kici Abincinki Ki ƙoshi Kiyi Baccinki Barni Dashi Yadawo Zamu Gauraya ne." Wannan Kenan!!!!! A Gidansu Khaleesat Fa? Tunda Kk Napep Ta Saukeni Na Shiga Gidanmu Ɗakina Na Nufa Nadaɗe Jingine Da Bango Cikin Tunani Da Makomar Rayuwata Wasu Hawaye Zafafa Ke Ta Gow Slow Kan Fuskata. Ban Taɓa Sanin Darajar Kuɗi Ba Sai Yanzun Ina Son Abdul Haka Shima Yana Sona Sai Dai Matsalar KUƊI Zata Kawo Mana Cikas! Koma Nace Takawo Mana Cikas! Ɗin. Tunani Barkatai Ke Zuwa Mani A Kwakwalwa ta. Najima Ina Tufka Da Warwara Kafin Natsaida Shawarar Dana Ke Ganin Bani Da Mafitar Da Tawuce Ta. Dan Haka Da Karsashina Na Mike Nafito Tsakar Gida Ruwa Naɗiba Nashiga Wanka Banyan Nafito Nayi Yan Shafe-shafe mu Na Mata Nasamu Doguwar Riga Nasaka Kafin Nafito Na nemi Ruwan Zafi Na Shiga Falon Momy Inda Canne Kayan Shayi Suke Naɗibo Na Haɗa Tea Mai Kauri Nasha Duk Abinda Nake Momy Na Kule Dani Na Kuma Lura taji Daɗin Sauyin Nawa Saboda Tun Kunnowar Rigimar Na Birkice Masu Ba Wanka Ba Cin Abinci Ba Fira Ba... Ba... Ba.... Zayyawa Ko Da Yaushe Ina Cikin Ɗaki Makure. Abincin Dare Yauma Tare Mukayi Kamar Yadda Muka Saba Momy Har Tana Cewa, "Ko kefa? Ja'ira Bazaki Gane Amfanin Zaɓin Da Mukayi Maki Ba Sai Nan Gaba Ko Bayan Rammu Zaki Shaidi Hakan." "Aikuma Yanzun Komai Yawuce Momy ALLAH Sa Hakan Shi Yafi Zama Alkairi. " Momy Tace, "Ameen Ƴar Albarka." Da Haka Girkin Namu Ya Kammallah Can Da Dare Yayi Kuma, Sai Ga Alhaji Saminu Yazo. Natsala Wanka Natafi Gurinshi Muka Sha Hira Sai Mamakin Sauyawa ta Yake Cikin Lokaci Ƙanƙani Haka. Nayi Murmushi Kawai. ********** "Haba Abdul-Wahab Ina Hankalinka Yaje Da Harzaka Manta ko Kai Waye Da Kuma Irin Gwagwarmayar Da Innarmu Tasha Dan Ganin Rayuwar mu Ta Inganta Amma Lokaci Ƙaƙanni Zaka Manta Wayyanan Muhimaman Abubuwa ko Ka Juya Masu Baya? Saboda Kawae Son Wata Yarinya Wadda Iyayenta Tamkar Tuni Suke Maka Akan Muhimmin Abu Da Kake Kokarin Mantawa? Tunda Suma Sunce Bazasu Baka Ƴarsu Ba Saboda Suna Ga Bakayi Kaurin Wuyar Da Zaka Riƙe Yar Tasu ba Ashe Duk Wannan Bai Kamata Yazama Iznah Gareka Ba Abdul?" Maman Walida Ta Numfasa Da Wannan Dogon Bayanin Datake Ta Korowa Abdul-Wahab Dake Zaune Gabanta Durkushe Da Kansa Zuciyarsa Na Wani Irin Suya! Yana ji A Ransa Tabbas Duk Abinda Take Gayamasa Gaskiyane. Tau Amma Yazaiyi Da Son Khaleesat Dake Azalzala Zuciyar sa? Anya Ma Zai Iya Rayuwar Da Babu Khaleesat Acikinta? Maman Walida Takatse Tunanin Nasa Ta Hanyar Cewa, "Duk Wayyanan Abubuwan Danake Gayama Abdul Ka Riga Kasan Da Su Sai Ma Ka Gayama Wani Su. Sai Dai Ina Tunar da Kai ne Saboda Inmma Ka Manta Ka Tuna In Kuma So Ke Ƙoƙarin Makantar Da Kai A Kansu Kai Ƙoƙarin Wartsakewa Kadawo Hayyacinka Sannan Ma Duk A Ture Wannan Abdul, Mu Kalli Irin Tashi Faɗin da Innarmu Tayi Danganin Rayuwar mu Ta Kyautata Yanzun Saboda ALLAH Yakamata Ace Yatashi A Banza Akan Wani Ɗan Ƙaramin Dalili Misali Shi Wannan Naka? Dan Haka Abdul-Wahab Kajini Da Kyau Daga Yau Baka Ba Wannan Yarinyar Ka ƙyalemusu 'Ƴarsu Suje Su Aurawa Wanda Suke Ganin Yadace Da Ita. Ina Fatar Abdul-Wahab Yajini?" Maman Walida Tafaɗa Tana Kama Kunnenta Irin Anji Da Kunnen Basira. Abdul-Wahab Yagirgiza Kansa Yana Cewa, "Insha'allah." Kafin Kuma Yamiƙe Ya'isa Gurin Innarmu In Da Take Damun Furar Da Takan Siyo Wani Lokacin intayi Sha'awar Sha. Yadurƙusa Yana Faɗin, "Innarmu Dan ALLAH Kiyafemin Natuba." Innarmu Ta Share Kwallar Da Ta Taru A Idanunta Tace, "Nayafe Maka ALLAH Maku Albarka Ku Duka." Wannan Yafaru Yawuce!!! Sai Ga Abdul-Wahab Ya Shiriricewa Makaranta Baya Zuwa Ko Yaje Baya Karatu Lokacin Exam Kuwa Da Anbashi Answer Sheet Sai Dai Yarubuta Sunan sa Yayi Submiting. Yauma Suna Cikin Hall Ɗin Da Suke Zana Jarrabawa Ana Bashi Yarubuta Sunan Sa Yaje Yayi Submiting Har Zai Fita embigilator Dinsu Yakira Sa Ba Musu Yadawo Yadaɗe Yana Kallon Abdul-Wahab Kafin Yace, "Kai Kana Ga Hanyar Da kabi Zata Fissheka Kuwa? Ina Fa Hankalce Da Duk Wani Motion Ɗinka Nazuba Ma Ido Ne Kawai Inga Iya Gudun Ruwanka. Amma Naga Baka Da Alamar Sauyawa, A Fuska Gaka Dae Kamar Mutum Amma In Mutum Yabincika Sai Ya Sameka Shasha.... " Abdul-Wahab Yafara Ƙoƙarin Kare Kansa Amma Sai Malamin Bai Bashi Damar Hakan Ba Yace, "Gate Out My Freind. Jeka Abinka, Dafuwar Mutum Mai ƙosar Dashi." Jiki Babu Kuzari Haka Abdul-Wahab Yafito Hall Ɗin Yanufi Ƙarƙashin wata Bushiya Yazauna Cikin Nazarin Ƙila Wa Ƙala Da Yakasa Ƙaremasa. Shi Kansa Ya San Abunda Yake Baya Kyautawa kansa Yasani Kuma Bai Dace Ba Amma Yazaiyi? Wallahi Duk Yanda Yayi ƙoƙarin Cire Son Khaleesat A Ransa Yakasa Sannan Yakasa Aiwatar Da Komai Ko A Gurin Aikinsu Duk Yabi Ya Sukurkuce Ko Ogan Sa Na Masa Ƙorafin Haka Har Ya Tambayesa Ko Lafiya Ce Bayada? Amma Shiru Babu Amsa. Shidai Kawai Yafi So Ne Yasamu Guri Shi Kaɗai Yazauna Ko Ya Kwanta Yayi Ta Tunani. Dan Haka Yanzu Da Yake Zaune Cikeda Tunanin Meye Mafita Ya Yanke Shawarar Yaje Gidan Su Khaleesat Yaroki Iyayenta Su Taimaki Rayuwar Sa Su Bashi Aurenta Insun Bashi Duk Yanda Za'ayi Dole Su Innarmu Su Yarda Ayi Auren, Dan Wallahi Baya jin Rayuwarsa Zata Yuwu Babu Khaleesat. Da Wannan Tunanin Yamiƙe Yanufi Gida. Yau Ko Bus Ɗin School Bai Iya Jira Ba, Yaɗauki Shatar Kk Napep Izuwa Gida, Sanda Yadawo Gidan Ba Kowa Innarmu Na Gurin Aiki Abubakar Kuwa Shima Na Shagon Ɗinki Dan Haka Yatsala Wanka Yafesa Turare Yafito Yana Ƙara Gyara Karin Fullarsa Dai-dai Lokacin Da Agogo Ke Nuna Karfe 5 Na Yamma Lokacin Rana Tayi Sanyi Sai Iskan Da Ke Kaɗa Manyan Bishiyoyi Dan Da Yuwar Za'ayi Ruwan Sama Dan Duk Gari Ya Rine Sai Kamshin Ruwan Sama Kakeji. Yanayin Yakara Saka Zuciyar Abdul-Wahab Cikin Wani Irin Nishaɗi Da Yadaɗe Baijishi Acikinsa Ba. Kai Tsaye Bakin Titi Ya'Iso, Yasake Tarar Ɗan Kk Napep Dan Yakaishi Har Shiyyar (Unguwar) Su Khaleesat. Yasauka Cikin Kk Napep Ɗin Yana Ƙoƙarin Lalubo Number Khaleesat Yakirata Gefe Daya Yana Murmushin Zai Mata Bazata Amma ga Mamakinsa Har Wayar Tagama Ɓurari Ba'a Ɗaga ba Amma Sai Yabawa Ransa Tana Wani Uzurine Dan Haka Sai Ya Sallami Mai Kk Napep Ɗin Da Yakawo Shi, Shikuma Yakarasa Gangarowa Bakin Kofar Gidan Nasu Khaleesat, Sai Dai Abinda Yayi Tozali Dashi Yafirgita Masa Lissafi Da Duk Wani Tunani Da Yakeyi Zuciyarsa Tai Wata Irin Bugawa Wanda Hakan Yasa Yadafe Saitin Zuciyar Tasa Da Tunanin Karta Faɗo Ƙasa! Saboda Irin Bugawar Da Yaji Tanayi Kafin Ya Soma Karanto "Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju'u!!!!" [9/5, 9:13 PM] FA'IK: Typing....... 💻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....9 Mallakar 👇 Fa'IK ✍️ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Haka Yayi Ta Nanata Kalmar Har Sanda Yasami Nasarar Dai-daita Bugun Zuciyarsa Kafin Yashiga Shawarar Shin Yaƙarasa Inda Suke Ko Ya Komawarsa Gida Kawai? "Gara Dae Kaje Karkayi Saurin Yanke Hukunci." Abunda Wani Ɓangare Na Zuciyarsa Kenan Ke Sanar Masa. Dan Haka Sai Ya Tunkari Motar Kai Tsaye Yana Musu Sallama Alhaji Saminu Na Masa Wani Malalacin Kallo Ya'amsa Sallamar Tasa Dan Dukda Bai Taɓa Ganin Abdul-Wahab Ɗin Ba Jikinshi Yabashi Cewa Wannan Shine. Hirarmu Muke Cikin Kwanciyar Hankali Ina Ta Dariya Saboda Labarin Da Alhaji Saminu Ke Bani. Shine Fa Abinda Abdul-Wahab Yagani Yafita Hayyacinsa. Ba Yabo Ba Fallasa Naɗago Kaina Ina Kallon Abdul-Wahab Da Yaja Gefe Yatsaya Yana Jiran Infito Nalumshe Idanuna Kafin Nasake Buɗesu Ina Kallon Alhaji Saminu Saboda Nasan Yana Son Wannan Salon Kafin Na Motsa Laɓɓana Cewar, "Baby Bari Naje Naji Da Wacce Yazo?" "Shine Abdul-Wahab Ko?" Alhaji Saminu Ya Tambaya Cikin Nuna Abdul-Wahab Ɗin Ba Kowa Bane. Nataɓe Baki Gamida Cewa, "Shine." Shima Bakin Yataɓe Yace, "Ina Jiranki Ina Fatar dae Bazaki Daɗe Ba ko Swetina?" Yaƙarasa Maganar Cikin Wani Irin Salo Na Jan Hankali Nace, "Sha Kurumin Ka Yanzun Nan Zandawo Ina So Ne Na Rabu Da Kwallon Mangwaro In Huta Da Ƙuda." Ina Gama Faɗar Hakan Na Ɓalle Murfin Motar Na Fito Na nufi Inda Abdul-Wahab Yake Tsaye Yana Jirana. Banda Kallona Ba Abinda Abdul-wahab Yakeyi Nace, "Sannu da Zuwa." Bai Amsa Sannun Da Nakeyimasa Ba Face Cewar Da Yayi, "Khaleesat Bai kamata Kina Sauraren Irin Wayyancan Mutanen Ba Mayaudara ne Kuma...... " Naɗaga Masa Hannu "Muyi Maganar Da Takawo Ka Dan Wannan Bai Shafeka Ba." Cikin mugun Mamaki Abdul-wahab Yace, "Mekike Nufi Khaleesat Nifa Ban ma Gane Kanki Ba Zuwa Nayi Fa Muji Yanda Zamu Ɓullowa Al'amarin mu A Yanzun Nashirya Aurenki Koda Su Innarmu Basu Amince Ba Dan.... " "Daga Baya Kenan Wannan Ba Khaleesat Ɗinda Ka Sani Bace, Nima kuma A yanzun Nagano Kuskuren da Natashi Afkawa Sai dai Ina Godiya Ga ALLAH da yaganar dani Tun Wuri." "Bangane mekike Nufi Ba Khaleesat?" Abdul-wahab Yafaɗi Hakan Cikin Wani birkicewar Tunani. Nikam Ko Ajikina Nace, "Abin da Nake Nufi A Yanzun Bana Sonka Nakuma Gano Wancan Yafi Dacewa dani Dan Haka Ina Mai Sanar Dakai daga Yau Bani Ba kai! Ina Fatar Yanzun Kagane Menake Nufi?" Jikin Abdul-wahab Yaɗau Kyarma Idanunsa Suka Kaɗa Sukai Jazir Kamar Gauta "Nagane ALLAH Yahaɗa Kowa Da Rabon Sa. " Abinda Kawae Abdul-wahab Ya Iya Cewa. Tau Mai Ma Zaice? Koda Yana Da Abin Cewar Bayada Dama Dan Kuwa kwalkwalwarsa Ta Kulle Tamau! Khaleesat Ta Shayarda Shi Mugun Mamaki Bai Taɓa Zaton Khaleesat Ɗinsa Da Yake Wuni da Kwana Da Tunanin Ƙaunarta Zata Iya Yi Masa Hakaba. "Ameen." Kawae Nace Kafin Najuya Na Koma Cikin Motar Alhaji Saminu Muka Ci Gaba da Hirarmu Cikin Nishadi Harda Kyalkylewa Da Dariya. Ina Kallon Abdul-wahab Ta Gilashin Motar Sanda Yazo Wucewa Sai Wani Tangaɗi Yake Na Kalli Alhaji Saminu Shima Kallo Na Yayi Dan Haka Sai Na Taɓe Baki Kawae. Shima Alhaji Saminu Hakan Yayi Cikin Jin Daɗin Yadda yaga Nayima Abdul-wahab Wulakanci Kafin Yazakuɗa Cikin Karsashi Yace, "Baby Kimin Wani promise Mana?" "Uhummm." Nafaɗi Hakan Ina Mai Kallonsa Da Wani Irin Salo Mai Tafiyar da Zuciyar Masoyi. Abunda Yake ƙara Ƙaunata Kenan Acikin Zuciyarsa Yace, "Ke Babbar Yarinya ce Bai Kamata kina Kula Kowane Irin Kilaki ba Musamman Irin Wayyanan Ƙananun Yaran ma." "Yanzun Kuma Andaina Dama Ai Wannnan Yafarune Kafin In Haɗu Da Alhaji Saminu Ai ko?" Naƙarasa Maganar Ina Kashe Masa Ido Irin Na Yan Bariki Ɗinnan Yalumshe Ido Alamun Dae Saƙon Nawa Yakai Harcikin Zuciyar sa Kafin Yace, "Hakane Tawan." Wai Abdul-wahab Fa? Ikon ALLAH Ne Kawai Yakaishi Gida Domin dai Inba Da Muryar Khaleesat Ba'abinda Ke Amsa Kuwa Acikin Kwakwalwar Kansa. Yaci Sa'a Babu kowa A tsakar Gidan Daga Innarmu har Abubakar ɗin ba wanda Yadawo yazube kan Katifarsu Yana mai fitar da Wani Irin Wahlallen Numfashi "DAN HAKA DAGA YAU INA MAI SANAR DA KAI BANIIII BAKAIII!!!!! " Muryar Dake Ta maimaita kanta Kenan Acikin kunnawa Abdul-wahab Hawaye Wasu na korar Wasu A Fuskarsa Cikin Rawar Murya Yace,"Babu Shakka Haƙƙenki Ne Ki Bibiyata Innarmu Babu Shakka Nayi Wasa da Rayuwata Kaicona!!!" Kafin Yarushe Da Wani Irin Gurshuƙeƙen Kuka. Kamar Wani Ɗan Ƙaramin Yaro Ko Wata Macce. Yinin Ranar Haka Yayishi Sukuku Kamar Wanda Bashi da Lakka! Innarmu dai na kule Saidai Batace Komai ba Hakama Abubakar. Yayin Da Acikin Zuciyar Abdul-wahab Yake ta Tufka da warwarar Sabuwar Rayuwar Da Zai Fara Na Mantawa Da Khaleesat Da Duk Wani Abu da yadanganceta Yamaida Hankalinsa kan Karatunsa Kamar Yadda Innarmu taso Yayi tunda Farko, Tau Saidai Yayi Fargar Jaje Dandai Yamaida Hankali Ga Yan tsirarun Jarrabawa Da Suka Rage Masa Amma Suka Kasa Hanasa Faɗuwa dan dai Sakamako Na fitowa Yafito Da Wani Irin Tashin Hankali Ga Abdul-wahab ga ma duk Wani Masoyinsa Dan dae Yazube Warwars Da Tarin Carry over Wayanda Suka Sababba Akayi Withdrawalce Dinsa A makaranta. Watau Dai An koreshi A Skull. Saboda Jp Ɗinsa Yagaza Tsallake Yanda Ake Bukata. Tashin Hankali Wanda Ba'a Sama Ka Rana. Duk yanda zan misalta Tashin Hankali Da Tsananin Damuwar Da Abdul-wahab yake Ciki Bazai Wadatar Ka gane ba mai karatu. Shikaɗaine Yasan Ya yakeji Saida Yagayama Su Innarmu da Abubakar Sannan Suma Sukabi Yarima Shan Kiɗa Wajan tayashi Shiga Damuwa Mussaman ma dai Innarmu Da Ta kwallafa Ranta Ga Karatun Kuma Take Fatar Suyi Nasara Akansa Tau Ga Abinda Abdul-wahab Yayi kuma Shi Yace SONE SILAR KOMAI! kundai Ji Mafari da Tushen Lamarin ko da kuma Asalin Wayyannan Taurarin ko? Tau muje Zuwa!!! MUN DAWO LABARIN. Innarmu Ta Sauke Wata Kakkarfar Ajiyar Zuciya Kafin Ta Soma Da Cewa, "Yanzun dai ai kagane Abinda Nake maku Nuni ko? Ka kuma gane abinda Yasa Nake Tsaye tsayin Daka Dan Rayuwarku Ta inganta ko? Kuma Yanzun Katabbatarda Babu Wata Rayuwar da Zata inganta sai da Ilmi? Yanzun Kun Fahimta da hakan Ko Sai Duniyar taci gaba da koya maku Darasinta? Yakamata Kagane Abdul-wahab Ina yin Komai Domin ku ne ba wai Dan kaina ba. Danni Yanzu saidai nai Fatar gamawa da duniya Lafiya Amma Duk Kature Wannan Kawatsa min Ƙasa A Ido Gashinan Yanzun Wa gari Ya Waya?" "Niya Innarmu. Innarmu Na'aikata Babban Kuskure Kuma Nayi Nadama Dan ALLAH Kiyafemin Ko Nasamu Naga Haske A Rayuwata." Abdul-wahab ke wannan Maganar Cikin Rawar Murya. Innarmu Tasoma Shafa Kansa itama Cikin Tata Rawar Muryar Tace, "Nayafe maka Kai Ku dukanku Nayafe Maku Ni Ban taɓa ƙullatarku ba Sai dai Nayi Hushi daku dan ku Gane Abinda Kukayi Badai Bane. Amma bawai dan Hakan Na Nufin Har A Raina Inajin Haushin ku bane. ALLAH yamaku Albarka.!!" Gabaki Ɗaya Suka Rumgume Innarmu Suna masu Sauke Ajiyar Zuciya Yayinda itama Innarmu ke cigaba da Shafar Kansu Cikeda Soyayyar Da Akasan kowace Uwa nada Akan 'ƴayanta. Gefe Ɗaya Tana Mai Cigaba da nusar dasu Akan Su kula da Halin Rayuwa. Innarmu dae Anhuce😅 ******** Nacaɓa Ado Kamar wacce zataje gasar Kyau Sai kai da kawowa nake Daga Ɗakina Zuwa tsakar Gida Inata Zuba Kamshi Tareda Tauna Cimgam yana Kas! Kas! Inbanda kallona ba Abinda Momy keyi Hardai tagaji ta sa Baki Takirani Zuwa Ɗakinta. Na'isa Ɗakin Nata Wayata A kunne Ina mai Dariya Ƙasa-Ƙasa Tareda Cewa, "Alhaji Lamarinka Azimunne, Nifa Tunɗazu Na Shirya Kai Kawai Nake Jira?..... ALLAH?..... Kai Amma ko danaji daɗi..... Ok Tau Sai Ka iso..... Nagodeeee. " wayannan Zantukkan Su nake tayi Kamar ba ina gaban Momy ba kuma ko Ajikina. Abinda Nalura dashi Kuma Gabaɗai Jikin Momy Yayi Sanyi Da irin Wannan Sabon Hali da natsiro Dashi A yan Lukkutannan Tun Abun na bata Sha'awa Haryadawo Bata Tsoro "Gidan Ubanwa Zakuje?" Momy ke Wannan Tambayar Cikin tsawa Da Ɓacin Rai. Na Zunburi Baki Cikin Shagwaba Gamida Cewa, "Momy Ba Fa Kowa bane nake waya dashi ba face Alhaji Saminu ku..... " "Eh Ai Nasani Shi Alhaji Saminu Ubanki ne? Wallahi Khaleesat ki kayayeni Da wannan sabon Iskanci dakika tsiro da Shi idan kika kaini maƙura Gamuwar mu dake bazata Kyau ba." Haryanzun dae da Salon Shagwabar Nasakecewa, "Momy Bafa Komai ne ba Alhaji Saminu yace min Zaizo Zamuje....." "Rufemin Baki Shasha Ba'inda Zakuje ni wannan Feleƙen Naku Yafara isata Bari Anjima Insa kati Zankira Mahaifin Naku Yaimaza yazo ayiwa Abun Tufkar Hanci." Najuya Afusace ina Faɗin, "Ni Wallahi Momy Sai Naje Haka ka.... " Momy Tafisgoni Da Karfi "Khaleesat ina Magana kina Magana? Nashiga Ukku Ni Ɗiyar Alhaji Bola. Khaleesat Yaushe kika iya irin Wannan Rashin Kunya Haka?". Nidai Bance mata Uffan ba Kawae Nayi Shiru ne Ina Zumbure-zumbure. Abinda Nalura ya bala'in Ɗagawa Momy Hankali Dan Ba Ɗabi'ata Bace Wannnan. Namike da Nufin komawa ta ɗakina Momy tasake Fisgoni Tana Huci Da Faɗin "Dawo Nan Ba inda Zakije Bani Wayar Nan. " Nace, "Momy Nifa ba fita zan ba Ɗa... " "Nace Kibani Wayar ko? " Momy tafadi Hakan Cikin Tsawa tana mai mika Hannunta gareni Nufin Inbata Wayar. Ganin bazan bata ba yasa ta sanya Hannu Tafisge Wayar Kafin ta Zaunar dani Nan kusa Da Ita. Taci Gaba Da Juya Ƙullunta Da Zatayi Ƙosan Gobe Dashi. Hakanan Bakinta Baiyi Shiru Ba kan Canjin Da tagani Tareda ni Sai Faɗa take kamar zata Ari Baki Tayi Hausa Takoma Yarenta. Wani Zagin Intamin Shi Sai Na Kunshe Baki Saboda Dariya. Dole Firar Danaso Fita Ranar Bata Yuwuba Saboda Momy Takasa Ta Tsare. Haka dae Alhaji Saminu Yayi ta jira da Aike Harya gaji Ya Tafi. ********** Tau tunda Safe Momy Nagama Lazimi Ba Wanda Takira Sai Dady Dama can kuma shine Mutum Nafarko Dasuke fara waya duk Safiya ta ALLAH Mafi Yawa kuma Shine mai Kiranta dan Yaji Lafiyar Gida Tau Yaudae Takasa Hakurin Yakira Itace Takirashi Harma Yana Tambayarta Lafiya? Cikin Ɗacin Rai Tace Masa, "Ina Fa Lafiya Alhajin Nan Na Son Sauyawa Yarinyarnan Hali? Duk Tabi Ta Susuce A kanshi?" Mustapha Yanumfasa Dan Shi Duk Baiji Wata Matsala Anan Ba dan Haka Yakara tambayarta da Cewa "Kamar Yaya? Nifa Bangane Inda Zancen Naki Yadosa ba?" "Alhaji Zancen Wayar Bazai Gamsar Ba Inaga kawai Ka Samu Lokaci Acikin Satinan Kashigo Inaga Abin Zaifi." Alhaji Mustapha Daga Can Inda yake Kishingiɗe Kan Gadonsa Ya musƙuta Kafin Yace, "Babu Damuwa Zanyi Ƙokari Inga Nazo ina Khaleesat ɗin Tana Lafiya?" Saida Momy Takyaɓe Baki Alamun Dae Tanajin Haushin Khaleesat ɗin tata kafin tace, "Tana Nan Lafiya lau. " "Masha'allah Badai Wata Matsala ko?" dady ke Tambayar Momy Hakan. Momy ta'amsa "Babu Bayan Wannan dana gayama." "Tau Shikenan Zanyi Ƙoƙarin Inzo Ina Khaleesat ɗin In tana kusa Bata Wayar Muyi Magana. " Momy Sai da Aka Harareni Kafin A mikamin Wayar Na'amsa Ina niyyar Miƙewa inbar Ɗakin Ta bugamin Tsawa "Dawo Nan Munafuka Ina Zakije?" Dole Bashiri Nadawo Na Zauna. daga can Dady Najinmu A Ransa yace 'Yawo Sarkin Rigima."......... Masu Karatu Muje daku Shafi Na Gaba Domin jin yaxata Kaya Rigima dae tayi Ƙamari Tsakaninta da Yar lelenta Khaleesat. [9/5, 9:13 PM] FA'IK: Typing....... 💻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....10 Mallakar 👇 Fa'IK ✍️ INA YIWA..... Ɗaukacin Al'ummar Musulmi BARKA DA SALLAH!!! ALLAH Yakarɓi Ibadarmu Yasa Kuma Mun Rabauta Yakuma Nufi Musake Ganin Wani Azumin Cikin Rai da Lafiya 🙏. GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Nidae Bance Komai ba Cikin Sanyin Murya Nagaida Dady Ya'amsa min Cikin Kulawa Kafin Yajefomun Tambayar "Meya Haɗaki da Momyn Ku?" Sai da Nakalli Momy Dake Tamin Kallon Kamar Intaso In Shaƙeki Kafin Nasake Riƙe Wayar Nace, "Ba'akomi Dady." daga can yasauke Ajiyar Zuciya Sa'anan Yace, "Kina jina ai? " "Eh Dady." "Ki nisanci Abinda zai batawa Mamanki Rai Bana son Fitina kinji ko?" "Dady Nifa banma ta Komai ba Alhaji ne yake Zuwa Ina....." "Bana son Wani dogon Bayani kiyi Kawae yanda nace Kinji ko?" Nace, "Shikenan Dady Insha'allah Zankula. " Daga Can ɓangaren Nasa Yace, "Yawwa ALLAH Yamiki Albarka. Ba Momy Taku Wayar." Na'amsa Da Amin Kafin Namika ma Momy dake Ta Aikin Hararata Wayar. Bansan Dame-Dame Suka ce Ba Don Miƙewa Nayi Nafito Nasoma Aikin Gidan da Nasan Ni ke Yinsa. Kawai dai Naga Momy taɗan Sake min Saɓanin Da can Farko Kamar Yadda ta Ɗau zafi Dani. Nima kuma naƙara bata Hakuri Tace Tayin Yauma Tare Muka Fita Wurinda Take Saide-Saidenta. Da Misalin Karfe Tara da kwata Lokacin muna Falon Momy muna kallon Arewa24 Yaron Makwabtanmu Yashigo Tareda Yin Sallama Kafin ya gaida mu Sa'anan Yaɗora da Cewa, "Wai Ana Sallama da Khaleesat." "Jeka ce waye ne?" Momy ce mai Wannan Maganar. Nidae Ƙala bance Ba Maimakon ma Hakan Sai naƙara Gyara Kwanciyata Saman Dogowar Kujerar Danake Kwance Akai Ina cigaba da maida Hankali Na Ga Kallon danakeyi. Ba'a wani Daɗe ba Yaron Yadawo Yana mai Sanar mata Cewa, "Wai Alhaji Saminu ne. " "Je kace Tana Zuwa." Amsar da tabawa Yaron kenan. Kafin tadubeni Tace "Ai sai kitashi Kije ko?" Ban musa mata ba nasakala mayafina nafice Zuwa Gurin Alhaji Saminu Muka Sha Hirarmu Kafin Yacika ni da kuɗaɗe kamar Yadda Yasaba Yamin Sallama Yawuce. Cikin Lokaci Ƙanƙani Natara Kuɗaɗe Masu Tsoka Daga Gurin Alhaji Saminu da Sauran Waɗɗansu Samarin Nawa. Wayanda Nakan Fito gurinsu A sace Batareda Sanin Momy ba nakan ce musu in sunzo Suce Sunan su Alhaji Saminu da wanan dubarar nake fitowa ta. Kwata-kwata Yanzu Bana Sauraren Wanda Nasan Bazan Samu Kuɗi Gurinsa ba. Inkaga Muna Ɗasawa Tau Kasakarmin Bakin Aljihunka Ne. Saidai Koda Kuskure Ban Taɓa Bari Wani Daga cikinsu Ya yaudareni ba. Ganin Kuɗin Dana ke Ajiyewa Gida Sun ɗanyi Kauri Na yanke Shawarar Zuwa Banki In Buɗa Accaunt Insasu Ciki Dan Gudun Ɓacewar Rana. Dan Haka da Sanyin Safiyar Litinin Na Shirya Na Nufi Banki Bayan Nayiwa Momy Ƙaryar Zanje Gurin Aminiyata Dubata batada Lafiya. Ban Samu Wani Jinkiri ba Akamin Bvn Number Bayan Nacika she Form Suka ce Inje Jibi Indawo In Anshi Atm. Tun Acikin Banki Na haɗu da Wani Alhajin Yamaƙalemin Yana ganin Nafito Shima yayi Zumut Yafito Waishi A Dole Zai ragemin Hanya. Ban musa ba Nashiga Dan dama irinsu Nake Nema😋. Kafin Mukai Gida Hira ta ɓarke A Tsakanin Mu Mukayi Musayar Number Asanda Yakawo ni Bakin Gida Ya'aje Da Alkawalin Zai dawo da Dare Nabashi Lokacin da Zaizo mukayi Sallama yaja motarsa Nikuma Nashiga Gida. ******* Tun Bayan Faruwar Wancan lamari Yayiwa Kansa Alkawalin Mantawa da Khaleesat da duk wani Abu da Yadanganceta Yanzun Aikinsa kawae yasa A Gaba Wanda in yadawo kuma yakanje Majalisar Wani Malami Ɗaukar Karatu. Wani Sauayawar Tasa ba ƙaramin daɗi tayiwa Innarmu ba harma da Abubakar Yanzu Walwalar Gidan Tadawo Sunci Gaba da harkokisu Kamar ma Komai bai faru ba. Sai dai A koda Yaushe Abdul-wahab Sai Yayi da gaske kafin ya yakice Tunanin Khaleesat A Ransa Saboda Shi Yasan Cewa Sonta ba Kaɗan Yamasa Ta'annati ba kawai yana maida komai ba komai bane Saboda Yasamu Yaci ribar Rayuwarsa Ko dan Kuma Ganin Farincikin Innarmu Mussaman ma in ya tuna Irin Wulakanci da Khaleesat ɗin tayi Masa. A koda Yaushe kwana yake Yatashi Da Tunanin Yaza'ayi Yasake Samun Damar Komawa Makaranta Yacigaba da Karatunsa Tunda Yatabbatar A Yanzun Ba wani Gata dazai yima kansa Wanda Yawuce Ya Tsaya Yayi Karatun. Ga Abubakar Nan paper Karshe Suke Zanawa Yanzun Abdul-wahab Yana Ji Ina Ma'ace Shine? Da Wannan Nazarin Dayake Yasamu Shiga Makarantar Lawyer dake Cikin ƙaramar Hukumar wamakko. Tunda Yasamu Yashiga Kuma sai yazama bashi da Wani Aiki sai Karatun ko da yaushe kaganshi inba wurin Aiki ba tau yana Karatun ne. Hakan kuma bakaramin daɗaɗawa Innarmu Yayi ba kullum Cikin yimasa Adu'a Take. Khaleesat Fa? Nazama Cikakkiyar Budurwar Manya Daka ganni Yanzu kasan Komai Yazauna Wayar da Nake Riƙe da ita ma kasan Takai balle Aje ga Maganar Suturar da nake Sawa Ƙawayena Kuwa Suma Sunsan Class yakaru Sai Huramin Kai Ake. Bana Harka da Ƙananan Mutane Sai Alhazai Masu Hannu da shuni. Alhaji Saminu kuwa Tuni Mukai Baram-Baram Saboda tafito Fili Bawai da Gasken Aurena Yake Nema ba Kawae JIKINA YAKESO Nikuma Yatarar Ba irin sa bace dan haka Mukai Fata-fata Lamarin da yakaimu Gabansu daddy Kenan Ƙiri-Ƙiri Kuma Yanuna masu Cewa shi yafasa Aurena. Abun ba kaɗan yayiwa Su Daddy Ciwo ba Sunyi Nadama iya Nadama na Amince Masa Baremma Momy. Lamarin Sha'anina da Alhazai kuwa Tuni Nabuɗe kasuwa da su Sosai Su Momy Sunyi Iya Nasu Ƙokari Harsun gaji Sun barni Wannan ma yasa sun Kara Nadama Akan Lamarin. Karfe Biyar ne Lokacin da nake Gyara Parking ɗin Motata Wacce Alhaji Tanko (Sabon Alhajin da muke Harka dashi ) Yasiyamin Nafito Cikin Wata irin Ƙasaita Wacce Nakeji Ba Yanayi Duk Cikin Ƴan mata. Narufe Motar Kafin Nashiga Gida Ina Ƙoƙarin Danna key ɗin Motar Tawa Tayi Wata Irin Ƙara Kai Tsaye Nashiga Gida ba Kowa A gidan Dan Momy Izuwa Wannan Lokacin tana Wurin Saide-saidenta. Kangado Nafaɗa Gajiye ina Hamma Wayata Najawo Wanene Yake Kirana Adaidai Wannan Lokacin? ALHAJI SHESHE! Sunan dake ta Yawo Kenan kan Fuskar Wayar Tawa Naɗan Tsurawa Wayar Ido Cikin Nazarin In ɗauka ko infita Batun sa? Karshe dai Harta Yanke bangama Shawara ba. Can sai ga Kiran Yasake Shigowa ɗan taɓe Baki Nayi Cikin Nazari Itama haka Ta Tsinke ban ɗaga ba. Ƙarshe dae Watsi Nayi da Wayar kan gado, nadafe Kaina da Duka Hannaye Biyu Cikin Tunanin Wannan Rayuwar Yakamata Ace Angama Wasar Hakanan Inje Ga masoyina Na Hakika Wanda Zuciya ke kwana da Yini Cikeda Ƙaunarsa Ina da Yaƙini Cewa A halin Yanzu Natara Kuɗin da Zasu Ishemu Rayuwa In Mukayi Businezz dasu Kuwa, Tau Har jikokin mu Basu Ba Talauci Tau Saidai Anya Abdul-Wahab Zai Yarda Dani Yanzun Zai Iya ma Saurarata Har Yafahimta da Wannan GAME ɗin dana Buga Wadda Ba Komai Yasa Sai Don Ceto SOYAYYAR MU ba? babu Shakka Akwai Aiki ja Agabana. Ganin Yanayin Garin Nakara rinewa tabbacin Kowa ne Lokacin Ana Iya Gocewa da Ruwan Sama Yasa Nayi Hanzarin miƙewa Na Sauya kaya Kafin Nararumi Jikkata Nasake Ficewa Kafin In Isa Gurin Motar Tawa har'an Fara Kaɗa Wani Iska Mai karfi. Kai Tsaye Dambu Store Na nufa Ina Isa gurin Nagyara Parking Nafito daga Cikin ta nashige Ciki Nasoma Jidar Abubuwan da nake Buƙata Turarukka Masu Asalin kyau Naɗauka Nakwashi Mayuka da Biskit da Chacolate Masu Ɗan Karen Kyau harsu complaks Sai da naɗiba Saida Nayi Siyayyata Yanda Raina keso Kafin Nakai Gurin Masu Lissafi Akamin lissafi Namiƙa masu Atm Ɗina Suka Cire Kuɗinsu Injiyo Haka mukayi Karo da Mutum Kayan da ke Hannuna da Nasa dake Hannunsa Suka tarwatse Suka faɗi Kasa Sukayi ɗai-ɗai A tafkeken Gurin Naɗago Kai cikin Masifar Wannan wane irin Mutum ne marar lissafi cikin Lamurransa Da har zaice Baya ganin Abinda ke Gabansa Saidai Wanda Idanuna Sukayi Tozali Dashi Ba Zato Yasa Na nemi Masifar Na Rasa Nayi Saƙare Ina ƙare masa Kallo! Abdul-wahab ne Sanye da wani tattausan Yadi Fari Kal! Kana Ma Iya hangen singlet ɗinsa saboda farin yadin Ga wani Mayen Kamshi da yake tashi A jikinsa Yarufe Kyakykyawar Fuskarsa da Wani Farin glass kana hangen kwayar idonsa Haka Kansa yana sanye da Fulla fara kal Irin ta Ustazai ɗinnan Wacce Sakkwatawa ke Cewa 'Taɓanni kasha Hadisi' "Abdul-wahab!!! " Naji Bakina yafurta Sunan nasa Batareda Nashirya hakan ba ko Nasan Na Furta ba. Shikuwa Abdul tun Kallon Farko Bai yarda munsake Haɗa ido ba illah Yadurkusa Yasoma haɗa kan kayan sa da suke zube Kan Farin Tayes ɗin dake Malali A tafkeken Wurin. Yana Kammallah kwashesu Yaje Aka masa Lissafi Yabiya Sa'annan yasake Juyowa yanufi Hanyar Fita. Duk Abinnan da'ake Ina nan Tsaye Kamar Wacce Aka dasa Gurin Inba Kallonsa Ba'abinda Nake. Ganin Zai Fice yasa Nayi Saurin Haɗa kan kayana da Taimakon Ma'aikatan Wurin, Nakwaso Sauri Nabi Bayan Sa Ina Kwala Masa Kira, dae-dae Lokacin da Ƙaninsa Abubakar ke gyaran parking ɗin Mashin Yana Cewa "Hau Muje Yaya." Nikuma Naƙarasa Ina Cewa, "Abdul Katsaya ka Saurareni." Abdul-wahab Yatsaya yana Kallo na Tacikin Farin glashinsa Wata Zuciyarsa Na Shawartarsa da Cewar Karka Tsaya yayinda wani Ɓangaren Nayi Masa gargaɗin "A Kul! Gara Ka tsaya Masoyiyarka ce Fa Wadda kake kwana da Tashi da Tunanin ta. Dan Haka sai Yatsaya Yana ji da Kallona. Ganin Haka Abubakar Yayi ƙoƙarin saukowa daga kan Mashin ɗinda Yake yanufo Gurin da Muke Dai-Dai Lokacin da Nake Cemasa, "Kayi Hakuri Abdul duk Abinda nayi maka Shirine Kuma duk Abibda kaga ya..... " Abubakar yafisgi Hannunsa yana Cewa, "Yaya Karya take Karka saurareta Itaɗin Mayaudariyace. " Abdul-wahab Yaso Ya'amince da Abinda Ƙaninsa Abubakar ke Gayamasa Amma kuma Soyayyar Khaleesat Nata yunkurin Hana Ya yardar dan haka sai Yafisge Hannunsa Acikin na Abubakar Tareda Cewa, "Kadakata mana! " Cikin Mugun Mamaki Abubakar Yake Kallonsa Kafin Wasu Hawaye Masu Zafin Gaske Suka Wuto Akan Fuskar Abubakar ɗin Cikin Rawar Murya Yace, "Yaya Wallahi karka Saurare ta Yakamata Kagane itaɗin ba Alkairi bace Gareka. Karfa ka manta Irin Tashi Faɗin Da Innarmu keyi Akanmu Tayi Wanke-Wanke Tayi Share-share kai tayi Kowane irin Aiki Dan ganin ta Kyautata Rayuwar mu Lokaci ɗaya Wannan muguwar tazo ta tarwatsaka wanda yazama Silar Rasa Farincikimu sannan ya rusa ma Karatu Amma duk Wannan Yanzun kana Ƙokarin Mantawa Yaya? Shikenan Ai Amma Kasani Wannan Karon Bana Tareda Kai! " Waɗɗanan Kalaman Sai Suka zama Farkawa ga Abdul-wahab Akan Halin da Yatafi dan haka da hanzarinsa Yajuyo Yarike Hannun Kaninsa Batareda ya iya Furta Komai yajasa Nufin dae Suwuce Kenan. Ganin haka Yasa Nabisu Cikin Wasu Irin Hawaye dakemin Saraftu A Fuskata Watau Mutanen nan irin Fassarar da Suka min Kenan? Nadubi Abubakar Cikin Hawayen da suke ta Faman Gow Slow A Fuskata ina Faɗin "Abubakar Kumin Mummunan Fahimta ne Amma Wallahi bahaka Bane Da zaka ku Tsaya kuji...... " "Meza muji? Wanda bamuji ba Acan ba? Eh? " Abdul-wahab ke Wannan Maganar Cikin Rawar Murya Kafin yadubi Abubakar Yace, "Kayi Saurin ɗaukeni Daganan Abubakar inba haka ba Komai zai iya Faruwa." Cikin Zafin Nama Abubakar yayiwa Mashin ɗin Siterta Suka Bar Gurin Yayinda Abdul-wahab yakife Kansa A Kafaɗar Abubakar yana mai ci Gaba da Sauke Wasu irin tagwayen Numfashi jere da Juna Kamar mai Asma. Ganin Sun Tafi ga kuma Yan tsirarun Mutane da Suka tsayu A gurin Suna kallon dramar da muke Yasa Nanufi Motata da Hanzari kafin Narufe ta Ruf Naja ta da Karfi Nabar Harabar Gurin. Ikon ALLAH ne Yakaini Gida Kasa fitowa nayi daga Motar Sanda Na'iso Gidan Sai Kawai Na rumgume Sitarin Nafashe da Wani Irin Kuka Mai ɗaci. Yanzu Irin SAKAYYAR da Abdul-wahab Zaiyimin Kenan? Nazamo mai Sadaukarwa Akan SOYAYYAR mu Amma Shine Zai kasa saurarata Yaji Uzuri Na? Ba'akomi duk Abinda Yafaru LAIFI NANE! Eh Mana Laifina Mana Nida Na Sadaukar Masa da Komai Nawa. No! Ba Laifin ki Bane SONE SILAR KOMAI! Wani Ɓangaren zuciyata ke cemin Hakan sai na samu kaina da girgiza Kaina cikin Murya Kuka ina Faɗin "ba Shakka Hakane.!!! " dai-dai Wannan Lokacin ne kuma Aka Gwafce da Wasu Irin Ruwa Masu Ƙarfi Harma da Iska Kasan Cewar Su Na Farko -Farkon Damina. A Wannan Lokacin Nasha Kuka harna gode ALLAH Yanzu Banda Ajiyar Zuciya ba Abinda Nakeyi ina kuma Cike da Tunanin MAKOMATA. Gashi dae Nayiwa kaina Tambarin Zama ƳAR ISKA! Saboda Abinda Mafi Yawan yan Unguwa ke kallo na dashi kenan Hakama Iyaye Na. duk-da Cewar Kuwa ni A Raina bahaka bane kuma duk Abinda Nayin Nayine domin ceto Soyayyar mu, Sai dai Gashi Wanda nayi DominSa Shikuma A MAYAUDARIYA yake Kallona Kenan dai BANI GA TSUNTSU BANI GA TARKO! Wannan Tunanin da Nayi sai Yakara mayarda Damuwata Sabuwa Fil! Nasake Fashewa da Wani Irin Gurshekeken Kuka kamar Raina zai Fita. Su Abdul-wahab Fa? ............ Readers Shin Meke Shirin Faruwa Ne? Kuma Meyasa Wai SONE keta Zama SILAR KOMAI? Ba Shakka!! Akwai wani Ƙullallen Ƙulli da Warwara sa keda Matuƙar Fa'idar da kuma dacewar ji ga mabiyin👇👇👇 Labarin. SONE SILAR KOMAI ❤️❤️❤️ Dan haka Muje Tareda Alkalamin FA'IK!!. ✍🏻✍🏻✍🏻 [9/5, 9:13 PM] FA'IK: Typing....... 💻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....11 Mallakar 👇 Fa'IK ✍️ INA YIWA..... Ɗaukacin Al'ummar Musulmi BARKA DA SALLAH!!! ALLAH Yakarɓi Ibadarmu Yasa Kuma Mun Rabauta Yakuma Nufi Musake Ganin Wani Azumin Cikin Rai da Lafiya 🙏. GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Lamarin Su Abdul-wahab Kuwa Sunshigo ne Sanda Innarmu ke Tsakar Gida kan Yar tsugunno tana Arwallah Sallar Magarib taɗaga tadubesu Yanda Suka Shigo Wani Iri Tace, "Lafiya?" "Ba'akomi Innarmu Cikinsa ne keyi Masa Ciwo." Abubakar ne ke Wannan Maganar. Yayinda Shikuwa Abdul yawuce ɗakinsu Kai Tsaye Tunda Yasamu Abubakar ya belesa. "ALLAH yasauwaka Ai Sai Yanemi Magani Yasha ko? Wannan Ciwon Ciki Haka yake ta Fama dashi Tun Yana Yaro. " Innarmu ke Wannan tarihin Kafin Tashiga Kwashe Kayanta Ganin Hadari Yagangamo Har Ansoma Yayyafi Inda Abubakar Yashiga tayatan. Kafin Su ida Aka gwace da Ruwan Dole Haka Cikin Ruwan Suka idasa Kwashe Kayan Kafin Innarmu tashige dan yin Sallah. Shima Abubakar ɗakinsu Yanufa yacire Kayan jikinsa da Suka Jiƙe Shataf! Yasa Jallabiya Yaɗauki Buta Yafito Bakin Baranda Yayi Arwallah Yakoma cikin Ɗakin Nasu Yana Cewa Abdul-wahab "ya Abdul Magarib Tawuce Yakamata Katashi Kayi Sallah." "Jira ni Muyi Jam'i. " Abdul-wahab Yafaɗi Hakan gamida Fita dan Yayo Arwallah "Okey Tau Bari Nayi Nafila Kafin Kazo." Bayan Sun Ƙare Sallar Abinci Abubakar Yaɗauko Musu Yayinda Ya'iske Abdul-wahab yaɗauki Handout Yana dubawa Dan Yana da Tex Goben Saidai Karatun baya Shiga Kai Kwata-kwata Baya ma Fahimtar me Yake Karantawa Muryar Khaleesat Kawae Ke Amsa Amo Cikin Kunnuwansa. Abubakar Ya jere kulolin Abincin Gaban sa Yakuma Kawo Masu Ruwan da Zasu Sha Yazauna Yana Cewa, "Tau Bismillah Muci Abinci." "Naƙoshi." Abunda Kawai Abdul-wahab Yace. "Ya Abdul baifa Kamata kana damun Kanka A Kan Tunanin Wannan Yarinyar ba Karka manta Wacece ita da kuma Ramin da Kafito." "Meka Sani ne Abubakar? Ka kuwa San Meye So?..... " "ALLAH ko yatsine Wa Wannan So Naka Yaya Inhar Haka yake Baya Barin Mutum Yasan Ciwon Kan...." Tas! Kakeji Abdul-wahab Yasauke wa Abubakar Mari A kumatunsa Kafin Yanuna Sa Cikin Fusata "Ka rena ni ba Abubakar ba? Ko dan Kaga Damata ne Kake Gayamin irin Wannan Maganar Banza!" Abubakar yadafe Kumcinsa Cikin Ƙunar Zuciya Yana Kallon Abdul-wahab Ɗin Kafin Yakaɗa Kai Kawai Yaɗauki Kular Abinci Yanufi Waje. Abdul-wahab yabishi da harara Kafin Yace, "da kazo Karama Marar Mutumci Kawai." Yayi tsaki Gamida Yin Jifa Da Handout ɗindake Hannunsa Yajawo Pure Water Dan Yasha Yaji Ruwan Sun Masa Ɗaci Dan haka Suma yayi Wurgi da ledar Batareda yadamu da Yanda yake Tsiyaya Acikin Kayansu ba. Yamike yana Ta kai kawo Acikin ɗakin Nasu Kafin Yakaiwa Hannunsa Naushi Gamida Cewa, "Khaleesat Kin Cuceni." (hummm! SO! Kenan) Kai Tsaye Yanufi tagar Ɗakinsu Yana mai Yaye Labulen dake Gurin Yatsurawa Wajen Ido Yana Mai Kallon Yanda Ruwan Saman Keta Kwarara Kamar da Bakin Kwarya Sai Walƙiya da Cida Ake Tayi. Yajima A haka Yana ta Sakar Zuci dana Kasa Gane Ta mecece har Ruwan Saman da Ake Suka Tsagaita Sai Yan Yayyafi -Yayyafi da Akeyi Awannan Lokacin ne Kuma Abubakar Yayi wa Innarmu Sallamar Sai da Safe Yanufo ɗakin Nasu Ko inda Abdul-wahab yake Bai Kallah ba yagyara Wuri Yayi Kwanciyarsa. Dai-dai Lokacin da Shikuma Abdul Yabaro Jikin Tagar Ya Sauya Kaya Izuwa Jallabiya Yaɗauki Kwando Wanka zai yo Wanka Dan Nufi In yayi wankan Shikenan Goben Asubancin Zuwa Skull Kawai Zaiyi. ********** Momy ce Ta Kwankwasa Gilashin Motar danake Ciki Nayi Saurin Tsaida Kukan da Nake Na yago Tisue Ina Goge Hawaye Kafin Na Buɗe Motar Nafito banyiwa Momy Magana ba Kawai Rufe Motar Nayi Nanufi Cikin gida Yayinda Momy Kuwa Sai da Tasanyawa Gidan Sakata Ta Rufe Sa'annan Tanufo Cikin Gida Zuciyarta Ta Babu Daɗi Da Irin Wannan Yanayi da Khaleesat ke Ciki Tau Amma Tunda Dady Ma da Yake UBA yakawar da Kansa Cewar Rayuwarta ce Tana da Yancin Yin Yanda Taso Ita Wace Power Take Da Ita Ta Shiga Rayuwar Ta Khaleesat? (Nikuwa Nace Kece ko Mai Power Momy Saidai Rashin Nesanta Tunani Yakawo Maki Wannan Hangen.) Kai Tsaye Ɗakin Khaleesat ɗin Tashiga Tasameni kan Sallaya ina Sallah. Ganin Hakan Yasa tasamu gefen Katifa ta zauna tana mai nazartar kowace Kusurwa ta ɗakin Taga Yanda Na Sauya Komai Na ɗakin. Nikuwa Saboda Ganin Momy Yasa naita Doka Nafilfili Wayanda Ni Kaina Bansan Iya Adadinsu Ba Dan dae Kar wata Maganar Tashiga Tsakaninmu dan A ganina duk Sune Suka Janyo min Faɗawa Wannan Halin da Nake Ciki Wannan yasa Hawaye na Suka Kasa Tsayawa Dana goge wasun zasuyi ta zubowa. Tun Momy najin daɗin Zaman datake harya soma Gundurar ta kai harta Soma doka hamma da gyangyaɗi dama Tagaji Musamman ma Aikin yanzun Yayi mata Yawa Itakadaece Yanzun keta ɗawainiya da costomer ɗinta tayi Wannan tayi Wancan hakan Yasa Momy Tamike Tafice Tabarni Da Sunan Inna San Wata Ai Bansan Wata ba. Yayinda Nikuma Tana Fita Nazube kan Katifa ta Ina Mai rera Wani Marayan Kuka Meyasa Abdul zai Kasa Fahimta ta? Meyasa Bazaimin Uzuri ba? Banyi Tsammani Soyayyar da mukewa Juna Ba Tana Iya Barin Ɗayan mu Yayiwa Waninsa Haka ba! Banyi Tsammani Cewa Abdul-wahab zai Iya Juyamin Baya ba Idan Nazo Gareshi ba. Tau Waɗɗanan Tunane-Tunanen Sune Suka Abokanci Zuciyata Har'izuwa Sanda Wani Bacci Marar daɗi Yazo Yaɗaukini Wanda Dukkaninsa Mafarkine Akan Artabun mu da Abdul-wahab.. Washe Gari Tunda Asuba Na Nemi Ruwan Zafi Nahada Shayi Wanda A Ynazun Shikaɗai Nakeji Abinci Mafi Sauki Da Zan iya Mu'amala dashi Nasha Kafin Nayi Ayyukan da Nasan Ko Dama can Nikeyi Dan Duk Wannan Taɓarar Danake Ban yarda Nabar Taya Momy Ayyukan Gida ba. Shiryawa Nayi Cikin Wani Swis Lace Mai Kalar Kwai Naɗan Shafa Hoda Sama-Sama Kafin Naɗauki Hijabi Harkasa nasaka Jakkata Naɗauka Bayan Nacire wayoyina dake Caji Najefa Ciki Naduba naga Atm ɗina nacike Saboda Banada Isasshen Cash Kuma Bana son Fita da Motar Saboda Jiya Ankwana Ana Ruwa Nasan Kuma Cabo yayi yawa Zata Lalace ne Kawai. Ban ma Nufi ɗakin Momy ba danna San intaganni Bazata barni in fita ba Shatar Mai Kk Napep naɗauka Harzuwa School ɗinsu Abdul-wahab har Hall ɗinda Suke Lakca Aka Kaini. (Nasan Wannan ne da Taimakon Yusuf Abokinsa. shi yake Sanar dani Komai kuma ko A Yanzun shi yahaɗani da Wannan mai kk Napep ɗin Yakawo ni) Nasha Wahla Sosai kafin inga Abdul-wahab inda Nasamesa Karkashin wasu bishiyo na dogon Yaro yana Zaune Kan Darduma Handout rike A Hannunsa Yana Karatun ta da bai Samu Yayi Jiya ba Kafin Ashiga Tex ɗin. Nesa Dashi Ma Wasu Ɗalibaine Suke Zaune Suna Karatun Wasu Gungu ne Wasu Kuwa Sukaɗai ne Yayinda Wasu Suke Zaune Kan Darduma Suma Wasu Kuwa Sun Kakkafe Mashunan Su Suka Zauna Akai. Abinda Na lura dae Wurin matattarar Ɗalibai ne Kuma Yana da Yalwa Irin Yanda Kowa Baya damuwar Wani Sai dai Ka hangi wani can Wani Nan Nesa da Kai duk Na Nazarci Wurinne Acikin Yan Sakkanin da Basu Wuce 30 ba, Abinda Na Lura dashi Abdul-wahab Baisan da Isowa ta A gurin ba Saboda yayi Nisa Acikin Karatunsa. Kamar wanda Aka Cewa ɗago Kanka Idanuwansa Sukai Masa Kyakykyawan Ganin Khaleesat ɗinsa tafe Izuwa gareshi tana Rangaji kamar Iska zai tafi da ita Shi harga ALLAH Yaba Ransa Cewa ba ita bace Kawai Gizo Ne Take Masa Saboda tsabar Damuwa da Yayi da Tunanin sa Wannan Yasa Kawai Yayi Tsaki Yamaida Idonsa Kan Handout ɗinsa Afili Yake Cewa, "Ya ALLAH ka yayemin Wannan Masifa." "Abdul Nice Masifar? Abdul Wace irin Tsana ce Kayimin harkake dangantani da Masifa?" Abinda Kunnuwansa Suka jiyo masa kenan Abinda kuma yaƙara Tabbatarmasan da Cewa Bafa Gizo Take Masa ba Khaleesat ɗin dai ce Zahiri Tau Amma Ya'akayi.... "Abdul-wahab Komeye Ina bibiyar ka Ai Yakamata ka Tsaya kaji Uzuri Na... " " Uzuri? " Yakatse ni da Furta Wannan Kalmar wadda yafurta tane Kamar ma baisan Metake nuhi ba. "Idan Har ke kinsan Uzurin Meyasa Kika Kasa Yimin Shi A Sanda Nake Bukatar sa daga gareki? Alhajin Naki Ya yaudarenki ne Ya Juya Maki Baya A Yanzun Shine Kike Dawo Gareni Ko Yaya? " "Abdul-wahab duk Ba Wannan bane Yakamata Ka Tsaya Ka Saurareni Wallahi Wallahi Baduk Abinda Kake Hasashe Bane Ni Banyi...... " Yaɗaga Mata Hannu Cikin Ɓacin Rai Kafin Yace, "Kinga Khaleesat bana Wani Bukatar Jin Komai Gareki ko kin Manta Abinda Kika ce Min A Waccan Ranar In tuna Maki? 'BANA SONKA NAKUMA GANO WANCAN YAFI DACEWA DANI. DAN HAKA DAGA YAU BANI BAKAI INA FATAR KAGANE YANZUN MENAKE NUFI' Ko bahaka kika ce ba? Saboda Haka Nagane Mekike Nufin Kuma Nafita daga Rayuwarki Bani Bake Dan ALLAH Ki Rabu Dani Kibarni Na Shaƙi Ɗaɗɗan Numfashi Bana Son Abunda Zai Hargitsa min Kwakwalwata." Yana gama Wannan Maganar yadurkursa Yahaɗa kan Kayansa Yaninke Sallayarsa Yamaida Cikin Jakkarsa Yagoya Zai Bar Gurin Nariƙo Rigarsa da Iya Ƙarfina Cikin Kukan da yazomin Nace, "Wallahi Abdu Bazan Fita daga Rayuwarka ba Meyasa Bazaka Tsaya ka Saurareni A Wancan Ranar Duk Abinda Nayimaka Bawai Nayishi Bisaga Doron Kiyayyarka ba Nayi ne Saboda Wani Shiri Dana..... " "Da kika Shirya Na cutata ko? Tau Aikin Cucinin dan Haka Ki kyaleni Mana Ko Wata Sabuwar Cutar kuma kika kullo A Yanzun Kuma? Tau Ina mai Sanar maki A Wannan Karon Bazaki yi Nasara ba. " Yana faɗar hakan yafisge daga Rikon da na Masa Yarataya Jikkarsa yawuce Bai ko Waiwayeni ba Balle Ya'amsa Kiran da Nake masa ba. Nadurkushe Nan Kasa Ina Mai Fashewa da Wani Irin Kuka dana kasa Hana Kaina yinsa. Ina Maicike da Nadama dana San Haka zata faru Da Ban Bari Naso Abdul-wahab ba! dana San Haka zata Faru da ban Ɓata Lokacina gurin Tariyar Abinda Nake Ganin Zan Faranta masa dashi Ba dana San haka ce Zata Faru da ban Shirya Wannan plan ba Marar ma'ana! Dana Sani!! dana Sani!! dae Gasunan Barka tai Sukaita Ziyartar Zuciya da Ruhina. Cikin Wannan Yanayi Marar daɗi Namike na Nufi Bakin gate ɗin Makarantar Tasu Natare Mai Kk Napep Sai Gida Muna isa Kuɗinsa kawai Namika Masa Yana "Ga Canjin ki." Amma ina! ban Tsaya Sauraren sa ba nashigewata Cikin Gida dai-dai Nan kuma Wani Irin Amai Yatasomin Na nufi Gurin Famfo dake Tsakar Gidanmu Nasoma Tsulashi Kamar Zan Amaye Yan Hanjina. Saboda Ruɗewa da Tashin Hankali da Fargabar da Suka Ziyarci Momy Bata San Sanda Tai Shuri Da Kwanon Ɗumamen dake Gabanta ba Tabi Ta Kan Cupin Kunu tashure shi Shima Duk Suka Zube Suka warwartse A Falon Idanunta Rufe Ta Nufo Inda Nake Durkushe Ina Yunkurin yin Amai Amma yaƙi Zuwa Saboda Babu Komai Acikin Cikina Shayi ɗaine Kuma Na Amayar Dashi. Momy Tariƙeni Cikin Karkarwar Jiki Tace "Khaleesat Meyake Faruwa dake ne? Nashiga Ukku Na Lalace mezan Ji ingani Khaleesat?" Kafin Ta Rushe da Wani Irin Kuka Ta'aza Hannu Saman Kai Tana Faɗin, "Heeee!!! Oh May Good!" Tayi Hausa Ta Koma Yarensu Ganin Bazai Hissheta ba Ta Jawo Hijabi Ta Rarumeni Ko Gyra Jikina banyi Ba Muka fice Waje Saida Mukai kai Get Ta Tuno Bata ɗauki Kuɗɗi ba Ta'ajiyeni Ƙasan Bushiyar dake Harabar Gidan Namu Tanufi Cikin Gida Kamar Zata Kifa Har Tana Tuntuɓe Yayinda Nikuwa Nakasa Tantance Halin da Nake Ciki Saboda Ga Yunkurin Amai Inayi Amma Baya Zuwa Irin dae Amanan Mai Azaba Da Kuka Sani. Dishi-Dishi Nake Hango Momy tana dawowa Gareni Can Cikin Maƙoshi Na Samu Nace "Momy Kitaimake ni Zan Mutu! Zan Mutu Momy Za... za.... Zan...." Iya Abinda Na Sani Kenan Sauran saidai Kuji Daga Bakin Momy da FA'IK. Duk Ƙokarin da Momy Tayi Kasa ɗaukarta tayi Dan Ayanzun Itama Duk Jikinta Amace Yake Batansan Ina ma take Takawa ba Tsoron ta ALLAH Tsoron ta Ace Khaleesat Nada Ciki Tunanin Hakan Ma Sai Yasa Taƙara Ɓarkewa Da Kuka Sai Gwalamniya take Cikin Yarensu Yayinda dae taga Hakab Bazai fissheta ba Tafice Da Hanzari zuwa Bakin Titi Tadawo Tareda mai Kk Napep Yakama mata Suka Shigar da Khaleesat ɗin Kafin Suka Naushi Hanyar Asibiti. Tayi ta Neman Number Dady Amma bata ganta ba cikin Wayarta ba. Tayi ta Mamaki Ya'akayi Bata ga Number ba. (Sai dai Abinda Bata Sani Ba Tana Zuwa kan Number Amma Sai Ta wuce ta Saboda Bata Cikin Hayyacinta.) ******* Duk Iya Ƙokarinsa Na Maida Komai Ba Komai Ba Yakasa Hakan Muryar Khaleesat keta kai Kawo Acikin Kunnuwansa Sanda Yabaro ta tana Kwla Masa Kira "Abdu! Abdul!! Abdul-wahab Katsaya Ka Saurareni Dan ALLAH!!!!! " "Bazan Tsaya ba ɗin Kin Dameni Fa.!!!! " Abinda Yafurta Da Karfi Kenan Sai da Hall ɗinda Suke Ciki Ya'amsa Duk Aka ɗago Ana Kallonsa Kamar Wani Mahaukaci. lecturer ɗinsu Ya'iso Gaban Kujerar Da Abdul-wahab ɗin ke Zaune Yace "Are U In Sanse?" Abdul-wahab Yadurkusar da Kansa Ƙasa Yana Cewa "Sorry Sir! " Lecturer ɗin Yatsurawa Abdul-wahab Ido Kafin Yagirgiza Yajuya. Ahmad dake Gefensa Yace, "Abdul-wahab Meke damunka ne Haka Kake Sambatu Irin Wannan kamar taɓaɓɓe? Ina Kule da kai Tun Kafin Mushigo nadai Bari Ne Kawae Harmu Kamallah tex ɗinnan." "Wallahi Ban Sani ba Nima Ahmad Ban Sani ba ina Cikin Tashin Hankali Wallahi. " Abdul-wahab Ke Faɗin Hakan Cikin ɗaga Murya Wanda Hakan Yasake Janyo Hankalin Yan Aji Kansu Ganin Lecturer ɗai Gabansa Yana masa Tsawa Cewar "Get Out! " Yarusuna Zai Bada Hakuri Lecturer Yasake masa Tsawar da Tafi Ta Farko "I Say Get Out My Freind!" Ahmad Yaɗago Yana Cewa, "Sorry Sir We..... " "Get Out both of U! " Lecturer Yafaɗi Hakan Cikin ɗaga Murya Yana mai Nuna Masu Ƙofar Fita Cikin Ƙufula Abdul-wahab Yafigi Jakarsa yafice Kamar Zai Tashi Sama Yayinda Ahmad Yakwantar da Murya Yashiga Rokon Lecturer Ganin Abinda Abdul-wahab Yayi Yasa Yadubi Girman Ladabin Ahmad Yayi Masa Afuwa. Yayinda Ya Ƙullaci Abdul-wahab Ƙullata Mafi Muni Da Cewar Sai Yaga Waye Uban Abdul A Makarantar! Abdul-wahab Kuwa Yana Fitowa Gate ɗin School ɗinsu Ya'isa Yasamu Bus ɗinsu Ancika Yashige Kawai Aka Kawoshi Inda yasaba Sauka Yaƙaraso Cikin Gida. Innarmu Daddawa take Gyarawa Wacce Ta shanya A Natsakar gida Taga Mutum Gabanta kamar Wanda Aka Jefo Yafashe da Kuka yana Cewa, "Innarmu Kitaimake ni Mubar Garinan da Ƙasar Nan Gaba ɗaya Inba Haka ba Khaleesat Zata Zamo Ajalina Kasheni Zata yi Innarmu! Hauka ta ni Zatayi Innarmu. " Duk Inda Hankalin Innarmu yake Yatashi In banda Mazari Ba Abunda Jikinta Keyi. Tayi Saurin Kamo Abdul-wahab Dake Zube Aƙasa Yana ta Aikin Maimaita "Kashe ni Zatayi Innarmu!! Hauka ta ni Zatayi Innarmu!!! " Inbanda Kalmar "Innalillahi Wa'enna Ilaihi Raju'un!!!" Ba'abinda Innarmu ke nanatawa..... Wai Yatakene Readers? SO! Shu'umine Fa! Gashi Dai yana Neman Tayarwa Mutanen nan Hankali Ko ince ma Yatayar Komai Zai Faru Yake Kuma Cikin Shirin Faruwa? ALLAH masani! Mudai Ci Gaba da Bibiyar Labarin SONE SILAR KOMAI Dan Ci Gaban da Jin TUFKA DA WARWARA Akan Wannan SO Da Yazamo SILAR KOMAI Gashi Kuma Yazamo Musu Babbar CUTA. Ko Meye MAKOMAR Wayyanan Taurarin? Ku kasance Tareda Alkalamin 👇 FA'IK. ✍🏻 [9/5, 9:14 PM] FA'IK: Typing....... 💻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....12 Mallakar 👇 Fa'IK ✍️ INA YIWA..... Ɗaukacin Al'ummar Musulmi BARKA DA SALLAH!!! ALLAH Yakarɓi Ibadarmu Yasa Kuma Mun Rabauta Yakuma Nufi Musake Ganin Wani Azumin Cikin Rai da Lafiya 🙏. GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Not Edating.... Cos Am 2 buzyyyyy. 🙏🙏🙏. Suna Cikin Wannan Halin Abubakar yafaɗo Gidan Cikin Tashin Hankali Yanufi inda Suke Yana "Innarmu meyafaru? Meyasa meshi? " Cikin Kukan da Yasuɓucewa Innarmu Tace, "Bansani ba Auta Kawai naga Yashigo min Cikin Wannan Halin." Yayinda Shikuwa Abdul-wahab Bakinsa Bai daina Ambatar "Kasheni Zatayi Innarmu!! Hauka ta ni Zatayi Innarmu!!" "Kama minshi Mukaishi Asibiti Ni Nashiga Ukku na Lalace..... " harta Nufi ɗaki Sai kuma Tadawo tana Cewa, "Abdul-wahab Ko Gamo Kayi? " Innarmu dae keta Sambatu Wayanda ke Nuni Ta ruɗe Yayinda Shikuwa Abubakar Yaɗauki Abdul-wahab Ɗin Zuwa ɗakin Innarmu. Innarmu tabiyo Bayan shi Tana Cewa, "Wane Ɗaki Zaka Kai shi Kai da nake Cewa Kaje ka samo mana Abib Hawa Mukai shi Asibiti." Abubakar yajuyo ga Innarmu Sanda Yashimfiɗe Abdul-wahab Saman Shimfiɗar dake Tsakiyar ɗakin na Innarmu Yace, "Innarmu ki Natsu Wannan lalurar bata Asibiti Bace Bani Ruwa cikin Cupi ki Gani. " Cikin Azama Innarmu tajuya taɗebo Ruwan Bakinta kuma bai Futa da Kiran ALLAH ba. Tasami Abubakar Rike da Abdul-wahab Ɗin yana ta karanto Adu'o'i yana Tofa Masa Yakarɓi Kofin Yasoma Karanto duk Wata Adu'a da yasani ta maganin Ƙunci Yana tofawa Acikin Kofin Yakaranto ayatul kursiyu Falaki da Nasi da Ikhlas Tareda Adu'a Annabi Yusuf (AS) sanda Yashiga Kurku da Kuma Adu'a Annabi Yunus (AS) Sanda Yashiga Cikin Kifi da duk Wata Adu'a da Yasani Sannan Yashiga Shafa ma Abdul-wahab Ajiki Musamman Saman Zuciyarsa Take Abdul-wahab Yayi tsit Yana maida Numfashi Ya runtse Idanuwansa Tamau Yan Tsirarun Hawaye Nata Sulmiyowa Tacikin Idonsa. Abubakar Yamike Yaɗauko Hisnul muslim Yabudo Masa Dai-dai Shafinda Yake Magana Akan Adu'ar Tafiyar da kuncin Zuciya da Damuwa Yamiƙa Masa Babu Musu Abdul-wahab Ɗin yasa Hannu yakarɓa yasoma Karantawa. Yayinda Innarmu Takoma gefen Gadon ta tazauna Tana maicigaba da Tasbihi ga ALLAH tana Mai Ƙara Godiya ga ALLAH da Yaba ta Ikon Tsayuwa Akan 'ƴaƴanta Har Sai da Sukayi Karatun Isilama. Abubakar Yamike yana mai Cewa "Bari ni Inje Inɗan Watsa Ruwa Innarmu dama Nashigo ne Inshirya Zamuje dubin Baban Aliyu Asibiti Nida Abokanamu. " "Ayyah! ALLAH Bashi Lafiya, Amma Kafin katafi Yakamata Kaci Abinci dan tun ɗazun na Kamallah." Abubakar Yadawo Yaɗauki Flet Yana Cewa, "Kuma Hakama dae-dae ne Innarmu. Dan dama Yunwa Nakeji Kawai naɗauka baki gama Bane. " "A'a tun ɗazu na 'ida. Daddawar da Zan Aikawa Auntynku Nake Shanyawa Yayanka Yashigo min A firgice." "ALLAH Ya kyau ta." Abubakar Yafaɗi Hakan Yana mai Zama Kusada Innarmu Bayan Yazubo Abincin. "Tau Ameen, Amma Yayanka Yahaɗu da lalura ALLAH dae Ya yaye Masa." "Allahumma Ameen Innarmu. " Haka dae Sukaci gaba da Tattaunawar Akan Matsalar ta Abdul-wahab Ɗin. Yayinda Shikuwa Abdul-wahab yayi Shiru kamar baya gurin Adu'o,in dake Cikin Littafin Hisnul muslim yake ta Duba wa yana Karantawa har Wani Irin ƙaƙƙafar Bacci Yazo yayi Awon Gaba Dashi. Ita kuma Innarmu Lokaci -Lokaci takan Yima sa firfita da mafefeci Saboda Zufar da yake tayi Kamar Ana kwarara masa Ruwa. Khaleesat Kuwa....... Tunda Suka Isa Asibiti Kai Tsaye likitoci Suka Amshe ta Saboda Dama Daddy yabuɗa Masu Fayel A gurin Dan haka duk Matsalar rashin Lafiya ta Taso Su Nan Suke Zuwa. Momy Kam Sai Safa da Marwah take Ta Kasa Tsayawa Takasa Zama Siyo Wannan Maganin Karɓo Wancan Resit. Bata Taɓa Jin Haushin Rashin Zaman Dady Harma da Ya Nuradden Agarin ba Sai Wannan Karon da Suna nan Ai da Suntaya ta Wannan Zirga -Zirga da kuma Sunyi Raba dae-dae na Wannan Tashin Hankalin. Bayan gwaje -gwaje da Aune-Aune Sakamako Yafito Likita Yakira Momy Zuwa Office ɗinsa Dan yi Mata Bayanin Abinda ke damun Khaleesat. Momy kamar Zata Kifa Tashiga Ofishi. Wani Irin Zullumi da Bugu Zuciyar ta keyi dahaka Tazauna Kan Kujerar dake Kallon Likitan. Dr Jabir Naduƙe Yana Yan Rubuce-rubuce Cikin Fayel ɗin dake Gabansa Kafin Yaɗan Kawar dasu Gefe Yaɗago Fararen Idanuwansa da suke Sakaye Cikin Farin glass Yana Kallon Momy "Kece Mahaifiyar Khaleesat Mustapha?" ya Tambayi Momy. "Eh....E.. H Eh.. Eh Nice Dr." Momy Tafaɗi Hakan Cikin Tsoron Me Kunnuwanta Zasuji. Kamar Shima Likitan Yakula da Hakan Kuma Yanga Dama Ɗabi'ar sa ce Kamar Wata Macce. Saida Ya bushi Iska Kafin Yace, "Ki Kwantar da Hankalinki Ba Wata Matsala Bace Mai Girma Tana da Miji?" "Shikenan Na Bani Na Lalace Yau ni YAWO nagama Yawon Duniya Heeee chinekeee Ere meleko Adaburo." Momy Ke Wannan Sumbatun Cikin Yanke Kauna Cewar Shikenan Khaleesat tagama jawo mata Abin kunya da Abin Faɗe Acikin Ahalinta. Dr Jabir Yayi Saurin Tushe Kunnuwansa Saboda Wannan Ƙyaƙyar Ta Momy Kafin Cikin Sauri Yace, "Bafa Komai Bane Yasa Natambaya Tana Da Miji Ba Saboda Kinga Shine Suke Tare Dan Haka Shi Yafi Kamata A gayama Dan Yakula. Kuma Olcer ce Kawai takama ƴarki Kuma Tayi Mata Kamun Kwarai Because batacin Abinci Shiyyasa Yanzun Ma Kummalo Yakamata Kingane?" Momy Cikin Farinciki Tadakata daga Kukan ta Tace, "Olcer?" Dr Jabir Yace, "Eh." Momy Tace "Tau Ai Alhamdullah!" Dr Jabir Cikin Hanzari Yaɗago Yana kallon Momy Yana Mamakin Furucinta. Momy dataga Kallon Da Yake Mata Tace, "Eh Ai da Acemin Ciki Gara Ace Olcer ne Sai Muyi Jinyar Abu Ɗaya." Abin Gwanin ban dariya ma Wallah yanda Momy Tawartsake Kamar ba Ita Ba Sai Bayani Take Korowa Dr Jabir. Shikam Rubuce- Rubuce- yayi Sannan Yamiko Mata Resit ɗin Tareda Cewa, "Wayyanan Magunguna ne Daza'a Saye Mata Tarika Sha. Wanna ɗayar Allura ce Asiyo Yanzun Sai Inyi Mata. " Cikin Hanzari Momy Takarɓi Takardun Tanufi Saye. A hankali Nabuɗe idanuwana Tareda Yin Miƙa Saboda duk Jikina tsami Yakeyi min Ina Mai Kara Tantance Ina Ne Nake? Jin Hannuna Na Tamke Yasa Nabi Wurin da Kallo Har'izuwa Sanda Nayi Tozali da Ƙarin Ruwa Da'akeyi Mani Yayinda Momy Ke gefen Nawa Rike da Hannun tana Cewa, "Yi A Hankali Khaleesat Karki tsinke Igiyar kijiwa kanki Ciwo. " Bance Komai ba Nakoma Kawai na Kwanta Fuskata Na Kallon Rufin ɗakin Ina Tunano Abinda Yafaru Tsakani na da Abdul-wahab Komai Yana zuwar min Kamar Yanzu ne Wasu Hawaye Suka Shiga Gangaro min Kan Damdamalin Kuma tuna Bandamu da Inshare Su Ba sai Ma Cewa da Nake "Abdul-wahab Kamin Mummunan Fahimta ne Amma Wallahi Bana Nufin Cutarka da ka tsaya ka Saurare ni Kaji Uzuri Na. " kafin Nafashe da Wani Irin Kuka. Momy Ta taso Tana Cewa "Khaleesat Natsu Mene Yake Faruwa ne? Ko Bakiga Ina ne Muke?" "Meye Ruwana da ina Muke Momy Ai duk Abinda Yafaru KUNE SILAR KOMAI Wallahi Inba Abdul-wahab ba Bazan Iya Rayuwa da Kowane ɗa namiji ba Nagwammace In Mutu Banyi Aure ba.... " Shigowar Dr Jabir Yasa Momy tarufe min Baki Tana Khaleesat "Subhanallah Khaleesat Ko Kin Taɓu ne?" Kasa Cewa Komai Nayi Saboda Ganin Ba mu kaɗai bane Sai Kawai Nayi Juyi Ina Funskatar Bangon ɗakin ina Ci Gaba da kuka Marar Sauti. Dr Jabir Yafashe wata Yar Ƙaramar kwalba Yasa Sirinji Yazuƙo Ruwan da ke Cikin kwalbar Kafin Ya saita Dai-Dai Yanda yake Ganin Zasuyi Mishi Kafin Yadubi Momy Yana Cewa "ina Fatar Ɗiyar Momy Bata Tsoron Allura?" Momy Tace, "Wannan Sarkin Rakin? Ai Inaga Sai Annemo Masu Danneta." Yanufo ni da Allurar Yana Cewa, "Haba ita Tasoma Duk Kwalisar Nan tata." Nidae Ƙala Bance Musu ba Harsanda Naji Yana Lalubar inda Zaimin Allura Nayi Saurin Miƙa masa Hannuna Nace, "Kamin Anan." Yayi min Wani Shu'umin Kallo Mai Cike da Tarin Ma'anoni Kafin Yace, "Nikam Koda Naji Nasan Yar Momy Jaruma Ce." Yariƙa Hannuna Yamin Allurar Sa'annan Yajuya ga Momy Yana cire Handglos(Safar Hannu) ɗinda ke Hannunsa Yana mai Cewa, "Zuwa Anjima Ruwan Suka Kare Zaku Iya Tafiya Gida Insha'allah. Sai dai Dan ALLAH Yar Momy.... " Yajuyo Gareni, "Ki Kula da Cin Abinci Saboda Karki Jamana Asara Muda Su Momy." Nai Masa Kallon Kai A Suwa Tau? Kafin Najuya Naci gaba da Lugwaiguwata Wurin da Yamin Allurar dan Nasan Bakaramin Jarumta nayi Ba Dan dai Kawai Ina cikin Damuwar da Tafi Ta Allurar ne Kawai Da Sai Mun kwashi Yan Kallo Nasani saidai A Wannan Halin da nake Ciki Ba Allurar ba Komeye Za'ayimin Banajin Girman sa Yakai Girman Halin da Nake Ciki. Shikam Dr Jabir Juyawa yayi yana duban Momy "Ko ba Haka bane Momy? " "Ah Tau Ai Tasani kam." Momy ke Mayar Masa Da Amsa. Yahaɗa Kayan Aikinsa Yana Cewa, "Tau Gara dae Ta kiyaye Inba Hakaba Aka Saki Kawo ta Asibiti Rike ta Zamuyi Sai Nan da Shekaru Aru-Aru Mun Tabbatarda Tayi Sabo da Cin Abinci Sannan. Mubata Sallama." "Dadai Yafi." Momy Tabashi Amsa. Yajuya Yafice Yana Cewa, "ALLAH ya sauwaka Momy. Na lura Yar Momy Bancin Olcer Harda Ciwon Baki Tana Fhama dashi. " "Momy Wallahi Bazan Jira Ruwan Nan Yakare Gida Zamuwuce Haka Kawai." "Ke! Kya Soma Ma. Dole ma kijira Ruwa Nan Ya..... " Wayar ta ce Tai Kara Dan haka takatse Zancen da Take. Ganin Dady ne Tayi Saurin Ɗaukar Waya Tasoma Kwararo Masa Bayani Ina Yashiga Tai takiran Wayarsa Bai ɗaga ba? Duk-da Bana A Yanayi Mai Daɗi Sai da Nayi Dariyar Momy. Araina Nace, "Momy Na Hoe!😁" Ina jin Su Suna Magana Dady Har Sanda Yace Mata Tabani Wayar Tabani Muka Gaisa Yamin Yajiki Sa'anan Yaɗora da Cewa "ALLAH Ya sauwaka Ina Nan Tafe Cikin Satinan Insha'allah." "Ameen Dady ALLAH kuma Yakawo ka Lafiya." Nafaɗi Hakan Ina Mai Miƙawa Momy Wayar Ina Jin Sanda Yake Cewa Ameen. Suka ɗan Taɓa Magana Yayi Ma Momy Sallamar Tareda Sanarda Ita Ma Kamar Yadda Ya sanarmin Watau "ALLAH Ya sauwaka Ina Nan Tafe Cikin Satinan Insha'allah." Basu Jima Da Gama Waya Ba Kiran Ya Nuradden Shima Yashigo Wayar Momy. Taɗaga Shima Suka Gaisa Kafin Tagayamasa Cewa Nice Bana jin Daɗi Muna Ma Asibiti. Yace, "Subhanallah Meyasa meta?" "A'a Ai Da Sauki Gata Ma Kwayi Magana." Momy tafaɗi Hakan Tareda mikamin Wayar. Ina Karɓar Wayar Nafashe Masa Da Kuka Nantake Yakara Ruɗewa "A'a Lafiya Me Yafaru Khalee (Sunan da Yake kirana Dashi Kenan). "Ya? Maganar Bazatayu A waya ba Dan ALLAH Kasamu Kashigo Ina Cikin Matsa..... " Momy Tafisge Wayar Tana Hararata Kafin Tasoma Magana dashi Shikuwa Sai Tambaya Yake "Please Momy Meyake Faruwa Ne? Dan ALLAH Ku..... " "Kaga Fa Karka Wani Tashi Hankalinka Taɓara ce Kawai Ta Khaleesat. Amai Takeyu Muka Zo Asibiti Shine fah Likita Yake Gayamana Olcer Ce Tamana Mummunan Kamu Kuma Yama ce Da Ruwan Da Aka ɗora mata Sun Kare Zamu Iya Wucewa Gida. " daga Can Ya Nuradden Yasauke Ajiyar Zuciya Kafin Yace, "Tau ALLAH Bata Lafiya Maganar Kuɗi Fa? Ko Zanturo Maku Ne?" "A'a Likita Yayi Magana da Dadyn ku Kuma Inaga Harsun Gayamasa Abinda Suka Caje Mu Ya kuma Turo Masu." "Tau ALLAH yasauwaka Sai Nakira Ina Gurin Aiki Ne." "Tau Shikenan Badamuwa." Momy Tasauke Ta Soma Min Faɗa Kamar Ba Wacce Ake Jinya ba. Wai Bana da Hankali Ina Legos Ina Sakkawato Da Zan Tayar Masa Da Hankali Haka? Inda Tashiga Banan Take Fita ba Nidai Bantan ka ba. Nayi Shiru Kawai Ina Sauraren ta. Gefe daya Na zuciyata Naci Gaba Sanarmin Shikenan Fa Narasa Masoyina Abdul-wahab. Da Sauri Na zabura Ina Faɗin, "Ina Bazai Taɓa Yuwa ba Abdul-wahab Nawane Nikaɗai Nima Tasa ce Shi Kaɗai An hallicemu Dan Junan Mu Kawai." Lamari Na Sai Yakoma Ba Momy Tsoro Yabar Bata Haushi Tashiga Karanta Duk Wata Adu'a da Tasani Tana Tofamun. Da Wannan Naɗan Natsu Nayi Lamo Kamar Mai Bacci Saidai Idanuwa Biyu Kawai dai Naɗan Samu releaf ne Nafaɗa Duniyar Tunani. Harsanda Ruwan da Akemin Ƙari Suka Kare Momy Takira Wata Nos Da Nufin Tazo Taciremin Amma Saiga Dr Jabir Kamar Wanda Aka Jefo Yace Taje Abunta Zai Ceremin Bayan Yacire Mun Saida Yatabbatar Yasa Mana Abun Hawa daga nan Cikin Harabar Asibitin Tasu Yabiya Kuɗin Sa'annan Yajuya. Wannan Karon Ba'a Wata Magana da Yayi Sai Ayyukan Sa dake Nunawa Girmamawarsa Garemu. Momy Kam Sai Godiya Takeyi Masa Iya Godiya. Sanda Zai Wuce ne Yajuyo Yamin Wani Irin Kallo Natsakar Ido Wanda Saida Naji Tsikar Jikina Ta Tashi duk yanda Naso Watsi Da Sakon Nasa Sai Nagagara Sai Kawai Nasame Kaina da lumshe Idanuwana Da Sukayi Luhu-luhu Saboda Kukan Nake Tilas tasu Dashi. Ganin Saƙon Nasa Yasamu Karɓuwa Yajuyawarsa Cikin Tafiyarsa Ta Ingarman Namiji Yana Wani Shu'umin Murmushi Wanda Shi kaɗai Yasan Ma'anarsa. Yayinda Mai Kk Napep ɗimu Yaja Muka Soma Tafiya Nalura Dr Jabir Miskili ne Na Bugawa A Jarida Kuma Daga Ganin Sa Dan Babban Gida Ne Kuma Kai Kasan Ilimi Yazauna Masa Sosai Ga Wasu Kyakykyawan Id... Subhanallah Meyake Shirin Faruwa Danine Ina Kuma Ruwana Da Dr. Jabir? Babu Shakka Wannan Kawai Sharrin Shaiɗain Ne. Dan Haka Nai Maza na Kawar da Tunanin Sa Ina Yin Istigfari Kamar Wacce Tayi Saɓo Ina Cewa Ni Ta Abdul-wahab Ce!! Wata Zuciyar Tace min "Tau Dama Yace Yana Sonki Ne? " Kawai Sai Nasami Kaina da Fashewa da Wani Irin Kuka Mai ɗaci Nasanya Hannaye na Afuskata Nadurkar Da Kaina Akan Cinyoyina Ina Mai Cigaba da rero Kukan da Nake Ganin Bani da Wani Abu Mafi Soyuwa Sama Dashi Mai Kk Napep Yaruɗe Yana "Subhanallah Mama Lafiya? " "Bata da Lafiya ne. " Momyn Da Yatambaya Tabashi Amsa Cikin ɗacin Rai Akan Tonon Sililin Danake Mata. Yajuya Yaci Gaba da Tuki Tareda Cewa, "ALLAH Sarki, ALLAH bata Lafiya." Momy Tace, "Ameen." Tirkashi! Ana Wata Ga Wata Ana dara Ga dare Yayi Inji Yan Caca Tau Waye Dr Jabir? Meye Kuma Manufarsa Akan Khaleesat? Duk-da Ma Khaleesat Tayi Hanzarin Cewa Itakam Nan Duniyar Sai Abdul-wahab Domin Junansu Kaɗai Aka Hallicesu Tau Amma Kuma Ai Baice Yana Sonta ba(Inji Khaleesat ɗin) Saidai Nikuma FA'IK Nace Inkaga Kare Na Shinshinar Takalme Tau Ɗauka Zaiyi. Kawae Readers Muci Gaba da Bibiyar Labarin SONE SILAR KOMAI dan Babu Shakka Akwai Tashin Sanse! Tsantsar Soyayya Tsagwaronta Da Kuma TAUSAYI ga Rayuwar Khaleesat harma da Shi Shalelen Nata Abdul-wahab Kudai Muje Zuwa Har'izuwa Matsayar Domin dae Komai nada Iyaka In Banda Ikon Jallah Sarkin Sarauta Dan Haka Ni FA'IK Nayi Gaba Da Alkamina Izuwa ga Fage Nagaba 👇👇👇👇 .......... [9/5, 9:14 PM] FA'IK: Typing....... 💻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....13 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Abdul-wahab Kuwa Tunda Yasamu Bacci Yaɗaukeshi Bai Farka ba Sai da Yamma Lis! Innarmu Ta kyaleshi ne Yayi Bacci Saboda yasamu Hutun Kwakwalwa da Gangar Jikinsa. Koda Yatashi Tana Tsakar Gida Tana Sanwar Girkin Dare Tadubeshi Sanda Yake Fitowa daga ɗakin Nata Yana Hamma Tace, "Katashi?". "Eh Innarmu Shine Ba'a Tasheni Nayi Sallah Ba?" Abdul-wahab Yafaɗi Hakan yana Yamutsa Fuska Alamun dae Baiji daɗi ba Anki Tashin sa yayi Sallah. Innarmu Cikin Kulawa Tareda Tarin Ƙauna da Akasan Kowace Uwa Dashi Ga Ɗanta Ko Yarta Tace, "Abdul Ai Lalura ce Tasa Ko? Ya Jikin Naka Yanzun?" "Da Sauki Innarmu." Abdul-wahab Yafaɗi Hakan Yana 'Yar Miƙa Irin dai Ta wanda Ya Tashi Da Bacci. "Jeka Kayi Sallar Ga Kunun Tsamiya Na Dama Ma." Yanufi Ɗakinsu Yana Cewa "Tau Yayi Innarmu Yau Mekuka dafane Da Rana?" "Shinkafa da Wake Ne." Innarmu Ta'amsa masa. Yace "Kai Amma Naji Daɗi Gaskiya ALLAH yabar Mana ke Innarmu Mu Kaɗai. " Innarmu dai Murmushi Kawae Tayi. Wanka Yayi Sannan Yayi Brush Kafin Yayo Arwallah Yarama Sallolin da Suka Kufcemasa Bayan Yagama Yafito Yasami Innarmu Tashirya masa Komai Har Kwai da Kwai (Awara) Ta'aika Ansiyo Masa Dan Tasan Indae Zaici Shinkafa Da Wake Tau Ƙa'idar Sa ne Sai Yasa Awara Aciki. Yazauna Yasoma Cin Abincinsa Cikin Kwanciyar Hankali da Nutsuwar Zuci Wayanda Yaɗan Rasa Acikin Yan Kwanakinan Yanaci Suna Fira Da Innarmu Wacce Mafi Yawanta Akan Aunty Su Ce. Suna Taren Har'aka Kira Sallar Magarib Lokacin Innarmu Harta Kammallah Girkin ta Suka yi Arwallah Tare Innarmu ta tayarda Tata Cikin Gida Shikuma Abdul-wahab Yawuce Massalaci Bayan Fitowar Sallar ne Suka Haɗu da Su Abubakar. Suka Shigo Gida Taren Amma Ko Inda Yake Abubakar Bai Kallah ba. Abin Yamasa Ciwo Sosai Yalura Daga Sanda Suka Samu Saɓanin Kwata-kwata Abubakar yaɗauke Masa Wuta Dan Haka Yanzun Suna Shigo Wa Yasoma Yima Innarmu Maganar, "Innarmu Dan Autanki Gaba Yake Dani." Innarmu Tatsaya Daga Abinda Takeyi Tace, "Gaba Kuma? " Abdul-wahab Yasamu Kusa da Ita Yazauna Yana Cewa, "Gaba ko Innarmu Saidai Ni ne Mai Laifin Dan Haka Natuba A Shirya mu." Innarmu Tadago Tana Kallon Abubakar dake Can Kusada Yar Karamar Tv Innarmu Tashar Rtv (Gidan Talabijin Na Jahar Sokoto) Yake Ƙokarin Kamowa "Kaji Abinda Yayanka Yace Dan Haka Batareda Nabi Ba'asi Ba Nace Abar Komai Yawuce Kayi Hakuri." Abubakar dae baice Ƙala ba, Madadin Hakama Sai Yanemi plet Yazubo Tuwo Yazauna Yasoma Ci Abinsa gefe ɗaya yana mai Kallon Labaran da Rtv Ke Gabatarwa Karfe 7:30pm. Yaɗago Yana Cewa, "Innarmu Kinga ni Ba Dama Nagayamaki Matsalar Wutar Nan da'ake Fhama da'ita kawai Gwamnati Bata Sa Baki Bane Amma Yanzu data sa Kinga Komai Yagyaru." Kafin yasakeɗibar Wata Loma Yakai Bakinsa. Zakin Miyar datasha Maggi da Daudawa nakai masa Har Kunne A Ransa Sai yabon daɗin Girkin Innarmu Yake. Cikin Al'ajabi Innarmu Take Kallonsa Kafin taɗora Da Faɗin, "Amma Ai Auta Kana jin Maganar danake Ma Ko?" "Naji Mana Innarmu." Abubakar Ya'amsa Yana Mai Cigaba da Bawa cikinsa Hakkensa. "Tau kuma Shine Kawani Shareni?" Innarmu ce ke Wannan Maganar. Abubakar yace "Tau Innarmu Yi Hakuri Andaina Insha'allah." Innarmu tayi Kwafa Kawai Kafin Tamike Tana Saka Carbinta Kan Ƙofar ɗakin. Tareda dubin Abdul-wahab da Yarafka Tagumi Yatsurawa Tv Ido Azahiri Kamar Kallon Yake Amma Ainhin Gaskiyar Hankali da Tunanin sa duka Basa Nan. Tace, "Kai Bazak Ci Tuwon Bane?" "Zanci Innarmu Amma Sai Anjima Nida Nagama Cin Abincin Yanzu? Adai Kwai Kunun Aya?" "Babu shi Dan Yau Duka Aka Saye." Innarmu Take Mayarwa da Abdul-wahab Amsa "Tau Kuma Dan ALLAH Innarmu Saiki Saida Duka? " "Kajimin Ɗa! Tau Kuma Sai Inƙi Kuɗi Ina ganinsu Meya hana Kabada Kuɗin Su Kace A ajiyema?" "Tau Aini Banɗauka zai Ƙare Bane Dan Naga Ko Jiya Da'akayi andawo Dashi Kuma Nan Cikin Frij Yana Cike." "Oh So Kake Kullum Nayi Tsimbo(Ba'a siyarba) Ko?" Abdul-wahab yayi Maza Yace, "A'a. bahaka nake Nufi Ba Innarmu." Innarmu Tace, "Tauwo Koda Naji, Nan da kake Gani Fa Tariya Nakeyi Daga Yanzu Zuwa Sanda Bukinku Zaitashi Saidai Kawai Aga Ina zaro Abina Ina lalurorina Batareda Na Nema Na Rasa ba. Banida Burinda Yawuce In Haɗa Aurenku Kaida Ɗan Auta Inga Kunkama Gidajen Kanku Kunfi Karfin Bukatar Ku Daganan Nikuma Zan Komawa ta Cikin Yan Uwana In Zauna. Shi kenan ALLAH Yacika Mani Burina!" Anan Kuma duk Sai Jikinsu Yayi Sanyi Ba Abdul-wahab ɗai Da'ake Hirar dashi Ba Harda Abubakar dake Can Gefe Yana Sauraro Dan Haka daga Can Yace, "Innarmu Ki Koma kuma cikin Yan Uwan ki Kuma Tau Mu Meye Amfa..." "A'a Nafison Komawa Mahaifata Kusa da Yan Uwa na Koda Kuka ga Nabarosu Nadawo Nan Saboda Ku Ne Ina Son Rayuwarku Ta Inganta Bana Son Wani Yatakura Maku Inga kuma Kun Samu Karatu Na Isilama da Boko Wanna Kuma ma Shine Burin Mahaifinku Har Yakoma ga mahallincinsa Ko Safiyar da Zai Rasu Mun Tattauna Wannan Maganar dashi Kuma Alhamdullah Ko Yanzu Yadawo Zaiyi Alfahri Burin mu Yacika Wanda Ni Nasani Ba Jajircewa ta bace Face Taimakon ALLAH danake Nema Ba dare ba Rana kuma Alhamdullah Ina Ƙara Godiya Ga ALLAH." Duk Jikinsu Yayi Wani Mugun Sanyi Da Wannan dogon Jawabin da Innarmu Ke Kwararo Musu Dan Haka Cikin Kasalar Jiki Abubakar Yataso yajingina Ga Jikin Innarmu Yana mai Cewa, "Nikam Innarmu Bazan Taɓa Zama Inda Bakinan Ba Duk Inda Naje Muna Tare." Cikin Zolaya Innarmu Tace, "Inkuma Matarka Bataso Fah Kasan Yayan Zamani Yanzu Ba Jituwa Sukeyi Da Surukai Ba Fa?" Abubakar Yace, "Innarmu Ba'ahaifi ɗiyar da Zan Aura tace Bata fi Son ki Sama Daniba Wallahi Bazan Zauna da Ita ba." "Kaidai Auta Banda Cika baki Fah?" Innarmu Tafada da Nufin kawar Musu Da Alhinin da Tasa su Takuma Yi Nasara dan Dukansu Saida Suka Dara Barin ma Abdul-wahab dake Can Gefe Cikin Tunanin Waɗɗanan Kalaman Na Innarmu Kamar Tsumagiya ne A gareshi. Shi dayake Kokarin sarayar da Wannan Kokarin Na Innarmu Harma Ashe da Mahaifinsu Mai Rasuwa Akan Wata Banzan Soyayyar Tashi marar Makama da Tushe! (Anashi Tunanin Fa?) dan Haka Sai Yakara jin Cewa Tabbas Abubakar yafishi Gaskiya Shine dai Yattabata Sakarai! Dan Haka da Karsashinsa Yataso Yarumgume Dan Uwansa Yana Mai Cewa "Autan Innarmu Nayarda da Abinda Kake Kokarin Nunami Dan Haka Kayafemin Da Mar...." Abubakar yayi Hanzarin Rufe Masa Baki Dan Baya Son Innarmu Taji Meyafaru Yace, "Yi Shiru Ya Abdul, Komai Yawuce Insha'allah! Nima Kuma Kayafemin Maganar da Nagayama dakake Ganin Kamar Raini Ce A Gareka." Cikin Kaunar dan Uwan Sa Abdul-wahab Yake Cewa, "Daina tunawa Komai Yawuce Kaji?" Innarmu Tasa Hannunta Tana Mai ɗauke kwallar da Ta taru A Idanunta Tareda Cewa, "Ya'isa Ai, Sai Kutashi Kuje Sallah Kar Jam'i Yakufce Maku Dan Kunji Har Anfara Iƙama." Tare Suka Mike Suna Haɗa Baki Gurin Cewa, "Yanzu Kuwa Innarmu." Kafin Suka Fice Suna Masu Share Hawayen da Suka Zobo Masu. Itama Innarmu Suka barta Cikin Mutuwar Jiki Kafin Tayi Karfin Halin Mikewa Izuwa ga Sallayarta Ta Kabbarta Sallar Ta Isha'i. (Ni Kaina FA'IK dake Laɓe Ina Ɗauko Maku Rahoton Sai da Nashare Hawayen Sbd Burgewar Wannan Familyn Ina mai cike da kwaɗayin Kowane Family yazama Irin Nasu.) ******** La'asar Ce Sakaliya Rana ta tafi Zata Faɗi, Gari Yaɗanyi Sanyi Sai Manyan Bishiyoyi daketa Reto Suna Kaɗa Wani Iska Kaɗan-Kaɗan duk-da kuwa yau Ankwallah Rana mai Zafi wanda Dayawa Suka Yi Hasashen Za'a Samu Ruwan Samane Kasancewar Dama Ana cikin Yanayine Na Damana. Acikin Katafariyar Asibitin FA'IK Hospital Dr Jabir ne ke fitowa daga Office ɗinsa wuyansa Saƙale Da Microscop Yayinda Gefe Ɗaya Yake Rike Labcoat (Fara Rigarsu ta Likitoci) ɗinsa A hannu Yana Tafiya Amutakar Gajiye Ya'iso parking space ɗinsu Rumfar da Suka jere motocinsu Yadanna danna remot ɗin motarsa Tayi ƙara Kafin Yasa Hannu Zai Buɗe Amma Sai Yadakata Yajuyo yana Kallon Nas ɗin da Ta'iso Gurin Nasa tana haƙi Tareda Cewa, "Dr Ka'oje Dan ALLAH kazo Kayi Attanden ɗin Wata paceint Wallahi tana Bukatar Taimakon Gaggawa." Yayi Tsam da Ransa Yana Kallonta kamar Bazaiyi Magana ba Kafin Yace, "Nas Zainab Wannan wane Irin Rashin Imanine Kuke Nunamin Tun Shabiyu Jiya Nabaro Gida ina cikin Asibitin Nan Ina Aiki da nawa da wanda ba Nawa ba Duk dan Taimako Still Yanzu Zankoma Gida Kuce kuma Yanzu Nazo nayi Wani Attanden Nimafa Ina Bukatar Taimakon Nan kuma Akwai Iyalina Gida Dasuke Suma Bukatar Taimakon Nawa ta Hanyar Basu Kulawa." yatsaigata Yana mai Sauraro daga Nas Zainab Yayinda tai Ƙasa da Kanta Tana Fhamar Ambata Masa "Sorry." Yace, "Ba Maganar Sorry Bace Maganar Amin Adalci ce Nima. Ina Dr Jabo Yake Ne?" "Yanzu Yafito daga Teater Yaje Massalaci Sallah?" Nas Zainab Tafaɗa tana Mai Rusunar da Kanta Ƙasa Tana Mai jin Bazata Iya Jurar Kallon Sihirtattun kyawawan Idanunsa ba. Yaɗan Dafe Goshinsa Alamar Tunani Kafin Yace "Tau Dr Gwadabawa Fa?" "Yana nan!" ta'amsa mashi A Taƙaice. "Meyake Yi Shi?" Yasake Jefo Mata Tambaya. Nas Zainab Tagaji da Amsa Wayyanan Tambayoyi Jikinta karkarwa Yake Mutumen nan Yanada Matukar Kwarjini da Haiba da kamala Da Kyawun da Kowace Ya macce Zata yi Sha'awar Yazamo Abokin Rayuwarta Batada Burin da Yawuce Itama tazamo Cikin Sahun Matansa Ita Ko Amatsayin Ta nawa zai Kata Tana So Wallahi Shiyyasa ma Yanzun Da'aka ce Akirasa Tayi Azarɓaɓin Cewa Itace Zata Kirashi Tau Gashi Kuma Tana Gabda Yin Nadama Akan Wayyanan Tambayoyin Da Yatasa ta A Gaba Yana yi Mata Kamar Wani Ɗan Jarida. Shidai Haka Yake da Baiwa Kowane Aiki Inzaiyi Sai Kaji Kamar Shi Yakaranta Kuma Yafi Dacewa Das....." Tunanin ta Yakatse ne Sanda Dr Jabir Yashiga Karkaɗa Mata Makullayen Motarsa A Fuskarta Tareda Cewa, "Heyyyyyyy Nas Zainab Are U Okey?" Tayi Wani Irin Firgigit Tare da Cewa, "Afuwant Dr." Yace, "Ina Tambayar ki Meyake Yi Shi?" "Eh... A'a Shi.... Shi Yanacin Abinci ne Sai Yace Inje Gaka can In Kiraka tun Kafin Kawuce." "Tau Kice Masa Koda Kikazo Nawuce Baki Sameni ba." Dr Jabir Yafaɗi Hakan Yana mai Faɗawa Cikin Motar sa Yarufe Tare da Bata Wuta Yawuce Yabar Nas Zainab Tsaye Tana Mai Bin Sawun Motar Tasa Da Kallo "Tau Kice Masa Koda Kikazo Nawuce Baki Sameni ba." Tasamu Kanta Tana Mai Mai-maita Abinda Yace Tareda Kwaikwayon Muryar sa. Kafin Taɗaga Hannu sama Tana Adu'ar "Ya ALLAH Kamallakmin Wannan Gay Amatsayin Mijina." Tadafe Saitin Zuciyarta Tana Lumshe Manyan Idanunta Tace, "Wow! Gaskiya Dana Caɓa." Tana Juyowa Sukayi Ido Huɗu da Nas Asma'u Tana Cewa, "Nas Zainab Lafiya Naganki Anan?" Suka Rankaya Ward ɗinsu Nas Zainab Nasanar Mata Wanda Tazo Kira Nas Asma'u Tace "Wannan Uban Miskilanci." Nas Zainab Ta'amsa Mata dacewar "Shifa!" Nas Asma'u Tace, "Sai dai Nan dakike Ganinsa Akwai Kirki dakuma Tausayi Fa." Antaɓo Ma Na Zainab Inda Ke Mata Kaikayi Dan Haka Da Ɗokinta Tace, "Ah Wannan Kam Ai Duk Asibitin FA'IK Hospital Ba Kamar sa." "Shiyyasa Ko da Yaushe Nake Ta Adu'ar ALLAH Yasa Da Rabon Yazama Mijina dan Irinsu Miskilai Dakike Ganin Nan Akwai Iya Tattalin Iyalinsu Zasu Sha Soyayya. " Jin Wannan Furucin daga Bakin Nas Asma'u Sai Nas Zainab Tahaɗe Girar Sama da Takasa Aranta Tana Cewa, "Kaji Munafuka Tau Kada ALLAH Ya'amshi Adu'ar taki." Da Wannan dai Hirar Tasu Ta Ƙare Har Suka zo Inda Zasu Rabu Nas! Zainab Ta Tafi Isarda Sakon Aikenta Itama Nas Asma'u Tashiga Hall ɗin Ɗakin da Majinya Ta Kwance Birjik Tanufi Teburen da Suke Zama Tana Gaisawa da Mutanen Ɗakin... Dr Jabir Kuwa Tuki Yake Cikin Wata irin Kasala dake Taso masa Tun Daga Kasan Zuciya Har'izuwa Ruhi da Gangar Jikinsa Komai Yakeyi Fuskar Ɗiyar Momy Keta Masa Gizo Bai Taɓa Haɗuwa da Macce Mai Kyaun Tsari Da zubi Ba Irin Nata Duk-da Kuwa Kansacewar Sa Likitan Mai Cuɗanya da Al'umma daban-daban. Yakai Hannunsa Yashafo Kansa Yana mai Lumshe Idanuwansa Kafin Yaɗan Furta A Fili "Ya ALLAH Ka Kawo Mani ɗauki." Yajawo Wayarsa dake ta Ɓurarin Neman Ceto Sai Yaga Sunan Dr Gwadabawa Ne Keta Yawon Kan Fuskar Wayar Tashi Yayi Tsaki Yana maida Wayar Kafin Yace "Saidai Kunemi Wani. " Ƙara Wayar Tasake Yi A Zatonsa Dr Gwadabawanne Dan Haka Bai Kula ba Sai da Tasake Ring Sannan Yamiƙa Hannun Cikin Ƙufular Indae Dr Gwadabawane Zai Caɓa Masa Magana Amma Sai Yanemi Fushin Yarasa Saboda Sunan da Ke Yawo kan Wayar 'NURUL KHALBI! ' Abinda Aka Rubuta Kenan da Manyan Harrufa Da Murmushinsa Yaɗauki Wayar Tareda Cewar, "Tuba Nake Hayatina Gani Kan Hanya So A Haɗa min Ruwan Wanka Kafin In Karaso." Yadanyi Jim Fuskarsa Cike da Walwala Kafin Yace, "Sereosly Nake Gayamaki Fa Hayatee dan Haka Kishirya Ko Kinyi Kwalliya ne Sai Mun Sake Wanka Tare." Dif! ta Kashe Wayar Tabarshi Rike da ita Wayar Yana wani Irin Murmushi mai cikeda Ma'anoni daban-daban Yasan Dama Za'ayi Haka Dan Kunyar Tsiya ce da Ita Sosai. Sanda Yashigo gidan Lokacin Take Fitowa daga Kichin Tallabe da Faranti Da Manyan-Manyan Wermars Dake Jere Akai. An Ko Sha Kwalliyar Nan Da yake Cewar Kamar Wacce Zataje Gasar Kyau. Murmushi Kawai Tayi Tana mai Nufar Danin Area da Kayan da Ke Hannunta Yayinda Ashraf dake Ƙame Kan Doguwar Kujerar da Sukayiwa Ƙayatacen Falon Ƙawanya Yayi Cilli da Remot ɗin Hannunsa Yana Kallon Cartoon ɗinda Tv Ke Watsowa Yanufo shi Yana "Oyoyo Dady!" Dr Jabir Yakamashi Yacaɓe Suna ta Murnar Ganin Juna Ashraf Yakkali Idanun Dadyn Nasa dake ta Lumshewa Saboda Tsabar Gajiya da Bacci Dake Cikin su Yace, "Dady karame... ko Mami?" Yaƙarasa Maganar Yana Kallon Mami tasa data Harɗe Tana Kallon su Fuskarta Cike da Walwala Yayinda Dady Ke Basa Amsa da Cewar "Badole ba my Son Nayi Missin Naku ne." Ashraf Ya Kyalkyale Dariyar Yarinta Yace, "Muma Haka Dady Harda Mami... Ko Mami?" Nan ma Mami Bamagana Sai Murmushi Kawai datake Aiko Masu Dashi Dan Haka Dr Jabir Ya'isa Gareta Tareda Ɗora Hannunsa kan Kafaɗarta Yana mai Cewa, "Ko Yar Momy Bata Jin Ashraf ne." "Ƴar Momy Kuma?" Ta Maimaita Tana Mai Kallonsa. Gabaɗai Sai Yadaburce Yasoma Inda-inda, "A.a.... Eh Wai Ina Na.. Nufin......... Readers Anan Zan ɗan Nisa Sai Muje Daku A Fage Nagaba Domin jin Yanda Zata Kaya Gadai Reshen Na Neman Juyewa Haryanzun dae Zamu Sake Tambaya Waye Dr Jabir Kuma Wace Barazana ce Ga Kyakykyawar SOYAYYAR Su Khaleesat? Makaranta Littafin SONE SILAR KOMAI Akwai fah BADAKALA Harma Curkuɗewar Al'amurrah Ga Wayyanan Mutanen Ataƙaice Zan Iya Cewa LABARIN Yanzun Ma Yasoma Kuma Akwai KWAMACALA Mai Cike da Ban Sha'awa Harma da Darussan Ɗauka Dan Haka Nayi Gaba Muje Zuwa Tareda Alkalamin 👇 FA'IK. ✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻 [9/5, 9:14 PM] FA'IK: Typing....... 💻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....14 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem "Eh Ina Nufin keɗin Ai Yar Momy Ce Ko?" Dr Jabir Yafaɗi Hakan yana Mai Ƙokarin Sai saita Nutsuwarsa. Maman Ashraf Tadubeshi Cikin Salon So Tace, "Hakane Amma Ni Nafi Son Wancan Sunan da Kakemin Yafimin daɗi." Takara sa Cikin Shagwabar ta dake Kara mata kyau da Kuma Wani Irin Matsayin Acikin Zuciyar Dr Nata Yace, "Tau Angama NURUL KHALBI!" Tayi Murmushi Kafin Tace, "Da Meza ka Fara Abinci ko Wanka? " Yakanne Mata Ido ɗaya Sa'annan Yace, "Duka Bada su Zanfara Ba." "Tau Dame Zaka Fara?" tafaɗi Hakan Cikin Yima sa Kallon Ƙasa-Ƙasa dan Bata Iya Jurar Kallonsa Cikin Ido Sai Taji Kamar Jiri Na Neman Kayarda Ita. Shikuwa Dr Jabir Ashraf Yakalla da duk yabi Yaɗale Jikinsa Yana ta Wasa da Key ɗin Motar Dadyn Nasa da Sauran Gwalanci Irin Na Yara kafin yaɗago Yakallo Maman Ashraf ɗin Yana Yafito ta Tareda Cewa, "Zokiji!" Tamatso Yakama Kunneta Yana Raɗa Mata Magana Tayi saurin Rufe Fuska Tareda Saurin Miƙewa Tanufi Bedroom ɗinsa Tabarshi Yana yimata Dariya Shi kam. ********* Cikin Kwanakinan Kwata-kwata Bana Tareda Sukuni tunda Muka dawo Asibiti Bana da Wani Aiki Daga Kwanciya sai Kwanciya Abinci Gashi Bana wani Cinsa Sai Innaga Yunwa Na Neman Yimin Lahni Sannan Insamu Abu Mai Ruwa Insha Nakama Wayoyina Duka Na Rufe Bana Mu'amala da Kowa da Komi Tun Abin Na ba Momy Haushi Tafita Harkata Harya dawo Bata Tausayi Tasoma Lallashina Saidai Duk-da Haka kwalliya bata biya kuɗin Sabulu ba Abin Kam Sai Yakoma bata Tsoro Takawo Ba mujiya Ta zuramin Bawai Kuma Dan Abin Baya damunta ba Sai dai don Tayi Duk Abinda Take Ganin Zatayi Amma Lamarin Ya faskara Gashi Dady Aiki Yarike shi Yana Son Zuwa Amma Ba Hali. Harma tagaji Da kai Masa Ƙorafi Shima Ya Nuradden Haka Dama Shi Bawani Cika Zuwa Yayi Ba. Sai Anɗau dogon Lokaci yake Zuwa Saidai Momy takudurce Matakin Ɗauka A Ranta Itakam Tagaji da Zaman Wanan Na nan Wannan na Can. Da Sanyin Safiya ne, Misalin Karfe Bakwai Nasafe Momy Na shirin Fita Wurin kasuwancin ta Nikuma Ina Tsakar Gida Yau Nawayi Gari Da Sha'awar Cin Kwai Dan Haka Nafita Shago Nasiyo Na Sulala Ina Zaune Sunake Ci Kamar wacce ke Cin Magani Yayinda Momy keta kai Kawo Wajen Haɗa Kayan da Zata Fita Dasu. Almajirinda Ta ɗauka Aiki Yana Tai Maka mata Gurin Haɗa Abubuwan, Jefi-Jefi Muna ɗan Fira da ita duk dai Ƙorafi ne AKan Rashin Zuwan Dady. Wanda Acewarta bai taɓa daɗewa kamar ta irin Wannan Karon Ba. Bayan Sun Gama Haɗa Kan Kayansu Taceda Sani (watau Almajirin dake Tayata) Yaje Ya Samo Musu Mai Kk Napep Tunda Haryanzun Wanda Yasaba Zuwa Ɗaukar Sun Bai zoba Kuma Takira Wayar sa Bata Zuwa. Sani Ya'amsa mata da Cewa "Tau." Bai ɗau Wani dogon Lokaci ba Yadawo da mai Kk Napep ɗin. Yasoma Kwasar Kayyakin Yana fitar masu dashi Yayinda mai kk Napep ke Aikin Lodasu Cikin Kk Napep ɗin. Momy tadubeni Sanda Take Kokarin Fita Tana Cewa "Mu munje Sai Nadawo Yau Ki Girka Mana Shinkafa da Miya Zan bawa Sani Salat da Nama Yakawo." Nayi Maza Nace, "Momy Adai sa Kifi Zaifi daɗi." Momy Tayi Saƙare Tana Kallona Dan Harta Manta da Rabon Ince Zanci Abinci Balle ince Ga Abinda Nake So Cikin Jin daɗin Sauyawar Tawa Tace, "Tau Yayi Zanbashi Yakawo Bayan Shi Akwai Wani Abu?" Nagirgiza Kai Gamida Cewa, "A'a Momy." Tajuya Tana Faɗin, "Tau Ni Natafi Sai Na Dawo." "ALLAH bada Kasuwa Yakuma Tsare." Nabita da Wannan Kalamin. Suka Fice tana Cewa, "Amin." Bayan Fitar Tasu Na Kammallah Cin Kwai ɗinda Nakeyi. Nakwashe Kayakin kafin Naje Famfo Na Wanko Hannuna Nadawo Ina Gyashi Alamun dai Na ƙoshi Kenan. Nayi Hamdala Ga ALLAH Sa'anan Nasoma Haɗa Soket ɗin dake Falon Momy Ina Ƙokarin Kunna Tv Wanda Rabona Da Hakan Harna Manta. Tashar Afrika tv3 Nakamo Naci gaba da Kallo Kafin Zuciyata Tayi Nisa Cikin Tunanin Farkon Haɗuwata da Abdul-wahab Cikin Azumi Gabda Shan Ruwa. Mukayi Sabo Mai Wuyar Mantawa Cikin Sauki. Na Soshi Sonda Bantaɓa Yiwa waninshi B, Muna Tsaka da Tunanin Cimma Burimu Su Momy Sukayi Mana SHAMAKI Tareda Taimakon Alhaji Saminu Wanda Babu Komai Tattare dashi Face Tsantsar YAUDARA Ni Atawa Wautar Momy Sun Hana mu Aure ne Saboda Bayada Kuɗɗi Nashiga Neman Kuɗɗi Wurin Manya Alhazai dan Nabawa Abdul-wahab Yasamu Yatsayu da Kafafunsa Kamar Yadda Momy harma da Tasa Innar Ke Cewa Shi Kaɗai ne Matsalar sa da zata sa Ba zaiyi Aure ba A Yanzun, Amma Bayan Nasamo Nazo In Kawo masa Cikin ɗaukina Shikuma yatareni da Mummunan Fahimtar da Yamin Harda Sharrin Cewa Ni MAYAUDARIYA CE Wanda Ko A Wancan Lokacin Nayima Sa Abunda Nayinne Saboda Samun Cikar BURIN RAINA Bawai dan Ina Nufin shi da Hakan ba Har Raina ba. Na Saɓawa Iyaye na Akan Hakan Na Saɓawa Mahallici Na Akan Hakan. Duk-da Bawai Nasaida Mutumci Nawa Na ƊIYA MACE Bane Amma Na YAUDARI Dayawa daga Cikinsu Ƙarshe dae duk BURINA Bai Cika ba Hasalima Wanda Nayin Dominsa Kallon MAYAUDARIYA Yakeyimin. Wasu Hawaye masu Zafi Suka Shiga Silalowa daga Cikin Kwayar Idanuna Zuciyata Namini Wani irin Zafi Dole Nadafe Zuciyar Tawa Ina Mai Kiran sunan ALLAH dan Neman Taimakon Sa. Babu Shakka Sai Yanzun Nagano Bangina Nawa BURIN kan Adalci ba Dan Haka Dole ne Nima naga Tawa SAKAYYAR Tunda daga Cikin Wayyanda Na YAUDARAR Harda Wayyanda Nayiwa Alkawalin Cewa Zan Aure Su Amma daga baya Na Tuɓure musu Shin Su Nasan Halinda Na bar Zuciyar su? Lalle Nayiwa BURINA Ginin TUBALIN TOKA Dan Haka Nine SILAR KOMAI Ba SONE ba dana ke Zargi. Kaiconah! Kaiconah! Yanzun Wa Gari Waya? ga Kuɗin Nasamu Amma Wanda nanemesu Dominsa niɗin ma baya da Lokacina balle kuma Su Kuɗin dana Sama daga Abokan Hamayyarsa dayake Ganin dasune Nahaɗa baki Naci Amanarsa. Babu Shakka Sai Yanzun Nagano Wautar dana Yi A Rayuwata Babu kuma Dalilin gyarata. Haka dai Nacigaba da Saƙar Zuci Tareda Ci gaba da Kuka Marar Sauti Har'izuwa Sanda Naji Sani Nakwaɗa Sallama A Tsakar Gida Nayi Maza nagoge Hawayen Fuskata Kafin Namike Nafito ina Mai Kokarin daidai ta Nutsuwa ta. Yamiko min Leda "Ga Cefanen Inji Momy." Nakarɓa Ina Faɗar "Tau Yayi Sani." Zai Juya Kenan Saiga Sallamar Dady Aiban Sanda nayi wurgi da ledan Hannu Na ba Natare shi Cikin Murnar Muka Rankaya Cikin Falon Momy Sai Surutu Nake Masa Yayinda Yaran Unguwa Suka Soma Shigowa da Kayansa Sani Na tayasu. Naciko Jug da Ruwa Masu Sanyi Nahaɗo da Ɗan Karamin Kofi Natsiyayawa Na'ajiye Gaban sa ina Mai kara Yimasa Sannu da zuwa. Shikuwa Yana Amsawa Tareda bina da Kallon Mamakin yanda duk Nafyaɗe Na Rame Kamar Ba Ikram ɗinsa ba, ƴar Duma-duma Yasanya Hannu Cikin Aljihunsa Yaciro Kuɗi Tareda Miƙawa Sani Yace Suje Yaraba masu Suda Sauran yaran da Suka Kwaso mashi Kaya Cikin Murna Suka Amsa Suna ta Zuba Godiya. Naje Na buɗe Tukunya Natarar Akwai Sauran Ɗumamen da Momy Tayi Nazubo Masa Cikin Kula Nakawo harda Cokali Na'ajiye Masa. Dady yace Kawomin Roba In wanke Hannu na Ni kinsan Nafison In Sa Hannu Fa. Nakawo Ina Cewa, "Aikam yafi Dady Dan Shine Sunnah!" Dady Yabuɗe Kular Tareda Cewa, "Masha'allah Kamar Kinsan Ina Tafe Ina Tunanin Ɗumamen Momynku Nayi Missin Nasa Sosai." nakyalkyale Dariyar Dady Ina Cewa, "Tau Dady Sai Gashi Katarar Yanzun kam Sai Kayi Iya Yinka Ko?" yace, "Aikam dai. " Nace, "Dady Ina su Umman Adamawa dasu Jamila?" Watau Matar Dady Ta Can Da kuma Ɗiyan ta. Dady Yakai Lomar Tuwo Mai laushi Da Sulɓi Tawuce Tacikin Makwogoronsa Yana Tantance Tsakanin Tuwon da Miyar Wanne Yafi daɗi? Kafin Yadubeni Yace, "Suna can, Suma Kuma Suna Kewarki." Ina Murmushi Nace, "ALLAH Sarki! Umman Adamawa Nayi Missin ɗinta Sosai itada Su Jamila." Dady Yace, "Ba Wani Nan Ai da kinbini Munje, Ni Har Bana Tuna Ma Yaushe Rabon Kije Har Umman Taku Na Tambayata Kotayi Maki Laifi ne? Nace Mata May be dai Kin Soma taya Momyn taki Kishine Kamar Yayan Naki Nuradden." Na Ƙyalƙyale da Dariya Gamida Cewa, "Kai Dady Wane Kishi Kuma? Bandai Samu Naje Bane Shima Ya Nuradden Ba Kishi Yake Taya Momy ba Irin dae Tasa Rayuwar Kenan Ta Rashin son Zumunchi Tunda Ko Wasu daga Cikin Ƙannen Momy Sun Shaida shi Da Hakan." "Haka Naji Lauya." Dady Yafaɗi Hakan Yana mai Ƙokarin Tsiyaya Ruwan dake Cikin Jug zai Sha. Cikin Dariya Nace, "ALLAH Dady." Yace, "Tau Naji. Momy Taku Tana Wurin Kasuwancin Nata Ne?" "Eh Dady." Na'amsa Masa Ina Kokarin Harhada Kayan da Yaci Abinci Da Nufin Kaisu Kitchin. Yace, "Ok Kwanaki Kinyi jin jiki Har Asibiti Kukaje ko?" "Eh Dady Baka Gani Ba Kaidai Kamar Zan Rasu." Yace, "Ba Wani Nan Raki dai Ne dake Harkika Tashi Hankalin Momy taki da Itama Tafiki Birkicewa." Yakarasa Maganar Cikin Sigar Wasa. Dan Haka Sai Nayi ta Dariya Naɗauki Kayan Nafito da Su Tsakar Gida. Zuwan Dady yakwashe kaso Mafi Yawa daga Cikin Damuwar Danake Ciki Saboda Yajanye Hankalina Da Hira. kasancewar Dady Irin Iyayen Nan Ne Masu Sauƙin Kai Wa Ƴayansu. Inkaji Yana hira Damu Sai kace Ƙannensa ne ko Wasu Abokansa Hakan Yasa Akwai Shaƙuwa Ta Haƙiƙa Tsakani mu Dashi Wannan ma yasa da yawa suke Ganin Yasakar Mana Dama muke Abinda Muka So! Kuma Naɗaya Daga Dalilin Yan Uwansa Naƙin Aure Momy Acewarsu Musulma ce Saidai Bai wani Sha Mata kai ba. Nikaina Nasani Abinda Muke Mukswashe Lafiya ɗiyan sa Dake Adamawa Bazasu Soma Ba. Karfe 1:30pm Na Rana Lokacin ma An Soma Sallar Azuhur A Wasu Massalatan Yayinda Wasu Massaltan Lokacin Suka Soma Kiran Sallah. Har Nagama Abincin Rana Ina Yanka Salak Ne, Shikuwa Dady Yayi Arwallah Yaje Massalaci. Momy Tashigo Sani Da Sauran Yaran da Suka Tayashi Kwaso Mata Kaya Suna biye da Ita. Suka'ajiye Kayan Inda Suka Saba Ajiyewa Kafin Ta Sallami Sauran Yaran Yayinda Tace da Sani Yajira Azuba Masa Abincin Rana In Na Kammallah kam. Dai-Dai Lokacin Kuma Nafito Kitchin dayan Hanunna Riƙe da Yuƙar danake Yanke Salat Dayan Kuwa Ina Rike da Salat Dake Cikin Kwando Nai Mata Sannu Da Dawowa Tareda Shaida Mata Dady Fa Yana gari Yadawo. Tanemi Guri Cikin Matukar Gajiya Ta Zauna tana Cewa, "Eh Kam Ai naga Alama Tun daga Fara'ar taki Ƴar Dady Sani Kuma Yagayamin." Nayi Murmushi Gamida Cewa, "Dady Wannan Karon Zuwan Bazata Yayi Mana." "Ai kam dae! Ga Ƙullon Dana Rago Nan, Yau Bazan Koma Ba dan Haka Maimaikon Abincin Dare Sai Ayi Alala dashi." "Yauwa Momy Kamarma Kinsan Ko Ina Sha'awar Cin Alalan." "Ai Fa Yau Komai Sha'awar Ci Kike, ga Alama Kuma Kina Fanshe Kwanakin Da Kikayine Kina Yajin Cin Abinci Na Ba Gaira ba Dalili." "Kai Momy Wane Yaji Kuma?" Nafaɗi Hakan Cikin Shagwabar da Nadaɗe Banyi Mata Irinta ba Kafin Nadubi Sani Dake Can Gefen ta Zaune Ina Cewa, "Sani Zo Ka zuba Min Ruwa In Wanke Salat ɗinnan Inyi In Sallameka." Sani Yasoma Zuba Min Ina ɗaureyewa daga Can Momy Tana Cewa, "Gaskiya kam Yasamu Yashiga Makaranta da Wuri tunda Yau Bamu Samu Mundawo Ma Da Wuri Ba." Ana Haka Dady Yashigo Gida Nan Suka Gaisa Da Momy Yawuce Falon Kafin Momy tayi Arwallah Azuhur Ta Nufi Dakin Ita ma. ========= Duk Yanda Yaso Yin Watsi da Lamarin Yar Momy Abin Yacutura! Komai Yakeyi Ƴar Momy Ce ke ta Kai Kawo Acikin Ransa! Ko Yanzun da Yake Cikin Office ɗinsa Saman Kujerar daketa Juyi dashi Idanuwansa A Lumshe, Ba komai Yake Tunanin ba Ilai Ita. kyakyawar Fuskarta, Zara-Zaran Yan Yatsunta, Yanayin Shagwabar ta Da kuma Miskilanci ta Wanda Itace Macce Ta Farko Da Yataɓa Haɗuwa da ita Batareda ta nuna Kyaun shi Yaburgeta ba Kuma Tayi Masa Miskilanci. A gurguje Yakamallah Aikinsa Kafin Yayiwa Motarsa Key Yadamƙi Hanya. Lokacin Karfe 5:30pm Tagota Sanda Ya'isa Shiyyar (Unguwar) Tasu Khaleesat Kafin Yashiga Tambayar Tsirarun Mutanen da Yake Haɗuwa Dasu Inane Gidan Su Khaleesat. Yaɗan Sha Wahla Kafin Yagane Gidan, Kafin Yafito daga Cikin Motar Tasa Yana Rabon Idanun Ina Yaron da Zai Aika Cikin Gidan Zai Ɓullo. Yajingina da Motarsa Tareda Fito da Wayar sa Yana Latsawa. Cikin Ikon ALLAH Sai ga Yara Suna tasowa daga Islamiyya dan Haka Yakira daya daga Cikinsu Ya'aikesa. Lokacin Niɗaice Tsakar Gida Ina Wanke-Wanke Su Momy kuwa Suna Falo Itada Dady Sun Ɓarke da Firar Bayan Rabo Har Ina ɗan Tsokanarsu da Cewa "Tsoffi Anyi Missin ɗin Juna." Momy tajefo ni da Pillon Kujera Lokacin da Nake Maganar Tareda Cewa, "Kin Maida Mu Kakkanin Ki ko?" Ina Samun Sa'ar Kaucewa Filon da tajefo ni dashi Sai Nayo Waje Nabarsu Sunata Dariya. "Salamu Alaikum." Sallamar Yarinyar Takatsaemin Tunanin Danake Naɗago Kaina Ina Amsa Sallamar Kafin Nace, "Sajida (Yar Makwabtanmu ce) Antaso daga Makarantar?" Tagyda Kai Gamida Cewa, "Eh Aunty Wai Wani Ne Awaje Yake Sallama." "Wayace Maki Yana Nema?" Natambaye ta Ina maida Hankalina Gareta. Takwaso Yamin Baki Irin Nasu Na Yara Da Cewar, "Im! Um!... Baice Kowa... ba." "Tau Je kice Masa Ana Zuwa." Nafaɗa Ina Kokarin Mikewa Daga Wanke-Wanken Danakeyi Na ɗaureye Hannaye na Sa'annan Na Nufi Falon Momy Tareda Gayawa Dady Cewa, "Wai Wani Na Sallama A Waje." "Wani?" Dady Yamai mai ta Maganar Cikin Mamaki dan Banda Makwabtanmu Na nan Kusa baiyi Waya da Abokansa Ko ɗaya kancewa Yana Gari Ba. Nagirgiza Kai Gamida Cewa, "Yanzun Sajida Da'aka Aiko Tafita." "Okey Bari Inga kowaye." Yafaɗi Hakan Yana Ƙokarin Sa Hullarsa Da Yajawo Saman Kujera. Daganan nima Na Juya Naci gaba da Wanke-Wanke Da nakeyi. Ba'a Jima ba Saiga Dady Yadawo Dai-dai Lokacin da Momy Taleƙo Daga Falon Tana Cewa, "Yakamata Ki Duba Alalar Nan Fah!" Na'amsa mata da Cewa "Eh Yanzun Nake Kokarin Zuwa In duba." Dady Yace, "Ashe Dr Jabir ne Na Asibiti FA'IK Hospital Ikram kije Yana jiranki." yana gama Gayamin Yashigewarsa Falo Yabarni da Bin Bayansa da Kallo. Inajin Sanda Momy Ke Tambayar sa "Meye Halan?" Banji Amsar Da Yabata Ba Saboda Sun Isa Cikin Falon. Naɗan Jima Cikin Nazarin Kila wa Ƙala Kafin Nasamu Kwarin Gwaiwar Mikewa Najawo Hijabi Na Dake Kan Igiyar Shanya Nasaka Nafita Zuwa Wajen. Yana Cikin Mota Zaune Kafarsa ɗaya A Waje Waya Yakeyi da Wani. Sanda Na'isa Gurinsa Ina Masa Sallama Yaɗago Kansa Yana Murmushi Batareda Yacemin Komai Ba Kafin daga can Yace ma Wanda Suke Wayar, "Bro Zamuyi Waya Anjima." Batareda Yajira mai Zaice Ba Yakatse Wayar Sa'annan Yadubeni "Shigo Ciki Mana." "Nan ma Yayi." Nafaɗi Hakan Ina Mai girgiza Kaina. "Ƴar Momy Daru ko?" Yafaɗi Hakan Yana Mai Kallona. Nidai Ban Tofa Ba Madadin Hakan ma, Sai Nagyara Tsayuwa ta Tareda Harɗe Hannaye na A Kirji. "Yazanyi Tunda Ni Nakawo Kaina?" Yafaɗi Hakan Gamida Fitowa daga Cikin Motar tasa Yajingina Gareta Yana mai Cigaba da Kallo na Kafin Yace, "Ƴar Momy Bata Iya gaisuwa Bane?" "Ina Wuni." Nafaɗi Hakan Cikin Zumburar Baki. "Bana so Tunda Sai da Na Roƙa." "Kayi Hakuri!" Nasake Faɗa Cikin Salon Shagwabar da Bansa Ina na Koyo ta ba. "kayi Hakuri!" Shima Yamai mai ta Abinda Nafaɗi. Kuma duk Mukayi Dariya Ni Dashi........... Tau fa Meke Shirin Faruwa Ne Masu Karatu? Hummm Akwai BADAKALA Taƙin Karewa kamar Yadda Nasanar da ku Cakwakiyar Na Can Gaba Da Nake da Ƴakinin cewa da Mai Karatu Yasan KALART? Tau da Zai Cika da Ɗaukin Jinta Sai dai Yanzun FA'IK Ne Kawai Ke Cikeda Ɗaukin Sanarda Ita ga mai karatu dan Haka Muje Zuwa dai............... [9/5, 9:14 PM] FA'IK: Typing....... 💻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....15 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem A Raina Nace Ashe Yana da Surutu Haka? Kamar Yasan Meke Raina Yace, "Bakiyi Zaton Ina Zuba Surutu haka ba ko? Tau Yazanyi Ƴar Momy Taɗaga min Hankali Kuma Gashi Ta Fini Miskilanci?" Yaƙarasa Maganar tasa Cikin Rausayar da Kansa Irin Kalar Tausayi ɗinan. Nan Ma Dariyar Nayi dan Wallahi Yabani dariya Cos Banyi Tsammani Irin Yadda yake da Tsare Gira Ɗinan Yana da Bakwanci Haka. Nasake dubansa Sanda Yake Cewa, "Izuwa Natabbata Yar Momy Ta san Meke Tafe da Likita Gurin dan dai Hausawa Sukace In kaga Kare Na Sunsunar Takalmi tau ɗauka Zaiyi Hakane.? Yaƙarasa Maganar yana dagemin Girarsa mai Matukar Kyau Nayi Murmushi Ina Sadda Idanuwa na A Ƙasa Saboda bana iya jurar Kallon Nasa Idanun dasuke ɗauke da Wani Irin Magana ɗisu Kafin Na motasa bakina Ina Cewa, "Hakane, Amma kuma Hausawane Sukace 'Waƙa Abakin Mai Ita Tafi daɗin Saurare ko?" Yasanya Duka Hannayensa Cikin Aljihun Wandonsa Yana Jifana da Wani Mayen Kallo Sa'annan Yayi Murmushi Tareda Cewa, "Kice Kawai So Kike In Miki Gwari-Gwari Ini Matar Bagware ko?" Wannan Karon Dariya Har Sunkuya Nake Tareda Tambayar Kaina Wai dama Haka Miskilan Mutanen Nan Suke? Dai-dai Lokacin Naji Yana Cewa, "Shikenan Tunda Hakan kike so Ni A Yanzun bani da Ja Bana da Kuma Kataɓus Saboda Sonki Yariga da yagama Zama Jinin Jikina Dan Haka Komai kikace Dole In bada Kai Bori Ya Hau." Kai Wannan Mutumen Ƙarshe ne Ashe Wallahi ku...." "Yar Momy...!" Yakatsamin Zancen Zucin da Nakeyi. "Na'am!" Batareda iya dago Kaina in kallesa ba. "Dubeni Mana!" Yafaɗa Yana Ƙokarin Rage Nisan dake Tsakani na Da shi. Nikuma Naɗan ja Baya Gamida Cewa, "Ni Bazan Iya Kallon ka ba?" "Saboda ni Mummunane Ko?" Nayi Saurin Girgiza Kaina "Bahaka Nake Nufi ba." "Tau me kike nufi My Ƴar Momy?" Naɗan Zumburi Baki Abinda Yazamemin Ɗabi'a Kafin Nace "Komai." "Komai!" Shima Yamai maita Kamar Yadda na Faɗa Muka danyi Dariya Yace "Yar Momy INA SONKI INA MURADIN KASANCEWARKI MATATA Kema kinada Wannan Ra'ayin Akaina?" Nayi Shiru gamida Sunkuyar da Kaina Ƙasa ina Wasa da ɗan ƙaramin Zoben Azurfar dake Hannuna. Yayi Murmushi Kafin Cikin dan Jidali haka-hakanan Yace "Ai Kuma Baki Isa ba! Kice in Miki Gwari-Gwari Sa'annan ke Kuma kizo kina Wani Sunne Kai kamar Wata Ma..... " "Saboda ALLAH tau Mekake So Ince Maka?" Nakatse da Faɗar Hakan Cikin Shagwabar da Bansan meye Dalilin yi Masa Ita. "Saboda ALLAH So Nake kema Kifurta Abinda Nafurta Bi Ma'ana kiban Amsar Tambayata In Har Kema Kina jin Abinda Nakeji Gameda ke." Na Nuna Masa "kaga Hadari Nahaɗo wa Kar Ruwan Sama Yama duka." Yayi Dariya Kafin Yace, "Na Lura Yar Momy Banda Miskilanci Harda Zama Yar Daru Ko? Tau ko Za'a Gwabce dasu Yanzun Su ɗauke Wani Hadarin Yasake Haɗowa Yasamemu Nan Bazamu ɗaga ba Harsai Kin Amsar Tambaya ta." Nakara Rumgume Hannaye na A Ƙirji Tareda Ƙara gyara Tsayuwa ta danake Jin Tana Neman Gagarata Saboda kwarjinin Wannan Talakin da Wani Irin So Nasa mai Shiga Da Zafi-Zafi Batareda Yanemi Izni Ba "Uhummm Ke Nake Saurare." Yakatse Min Tunanin da Nakeyi. Nace "Tau Kuma Shikenan Ba'a Barin Mutum Yayi Shawara." "Babu Wannan Damar Gudun Wani Yacanza Maki Tunani dan Nasan Yadda Kike da zubin Hallitar Nan Mai Kyau da Jan Hankali Bazaki Rasa Wasu Manema ba Tau Nikuwa Mezaisa Ni Abari Yahuce......" "Tau Shikenan Na'amce." Faɗar Hakan danayi Sai da Naji Tsawa Acikin Kwakwalwar Kaina Wanda Yayi Dai-dai Tasowar Wani Iska Mai Ƙarfi Alamun dae Kowane lokaci Ruwan Saman Zasu iya gwacewa. ^^^^^^^^^^^^^^^ Wannan Yayi Dai-dai da Abdul-wahab Na Tsaye gaban Wata Motar Acikin Garejinsu Yana Kwal-kwale-kwale Acikin Ingimin Motar Zuciyarsa Tai Wata Irin Bugawa Wanda Sai da Yayi Taga-taga Kamar Zaifi Faɗi Cikin Ikon ALLAH Yasamu Yadafe Wani Ƙarfe dake Kusa dashi Kafin yakai Zaune Cikin Sauri Gamida dafe Saitin Zuciyarsa Yana mai Karanto Innalillahi! Duk Mutanen Wurin Sukayo Ruuuu Akansa Tareda Subhanallah! Oga A Wurin Aikinsu Yariga Kowa ƙarasowa gareshi Kafin Yarike Sa Yana Cewa, "Abdul-wahab Meke Faruwa?" Abdul-wahab Cikin Runtse Ido Wanda Tuni Hawaye Sun Soma Zubo Masa Yace, "Oga Bansa ni Ba Nima." Ogan Yace, "Baka Sani Ba? Tau dama Baka da Lafiya ne ko da Kafito?" Abdul-wahab Yagirgiza Kansa yana Cewa, "Lafiya lau Nabaro Gida Kuma Nanma Lafiya lau Nake Aiki Na. Kawai dai Yanzun ne Naji Abun Yataso Mun." Kafin Kuma Yasoma Karkarwa Cikin Kiɗima Oga Yace, "Sunday Zo Ka Ƙarasa Gyaran Motar Nan Bari Naje dashi Asibiti." Abdul-wahab Yace, "Akaini Gida Kawai Zaifi." Ogan Nasu Cikin Rashin Hausasar da Bai Kware ba Yace, "Bazaiyu ba Abdul Wannan Ko kana Gida Ne Yasameka Ai Asibiti Aka Nufa dakai Balle Kuma Muna nan gurin Aiki Tashi Muje Kagani." Yakama Abdul-wahab Suka Fito daga Garejin Yayinda Mutanen Gurin Musamman Abokan Aikin sa Suke Biye dasu Cikin Sanyi Jiki Da Matukar Mamaki "Sannu!" Kuwa Sunyi Ta Karanto Masa Harba Adadi Kasancewar Abdul-wahab Mutumen Mutane A Gurin Baya da Abokin Faɗa Kowa Yana Zaune dashi Cikin Mutum ci Da AMANA. Wannan Ma Yasa Yazama YARO! Mafi Soyuwa A gurin Ogan Nasu Tun Abokan Aikin Nasu Na Hassada Har Wasun Suka Haƙura da Cewar Shiɗin Yaron Kirki ne Kuma Suma Yana Kyautata Musu Yayinda Wasun Kuwa Sukace Sai Sunga Abinda Yaturewa Buzu Naɗi. (Dama Haka ALLAH Yayi Mutanensa da Rayuwar!) Tuni wani daga Cikinsu yariga su Isa Bakin Titi yadawo masu da Kk Napep dan Haka Shida Ogansa da Wani Yaron Garejin Suka Hau Tareda Nufar Asibitin Suka bar Mutanen Gurin Cikeda Alhinin Lamarin. ========== "Ya dai?" Dr Jabir ke Tambaya ta Sanda Nayi Maza Nadafe Kaina Tareda Sunkuya wa Ƙasa Ina Karanto Hassbunallahu! Duk Ƙokarinda Nayi In Amsa masa Nakasa. Yaɗaga Kai Yakalli Yanda Gari Yayi Baƙi ƙirin Har ma An soma Yayyafi Kaɗan-kaɗan Yadurkusa Kusa Dani Cikin Zuciyar sa Yana Tunanin kodai Wannan Iskan ne da'ake yi Yatayar min Da Aljanu tunda Dama Su Mata baka Rabasu da Aljannu😂 Yayi gyaran Murya Gamida Cewa "Yar Momy Tashi Kishiga Gida Zamuyi Magana daga baya, Karɓi Ga ɗayan Wayata Zankira Ki Anjima Kinji?" Babu Musu Nakarɓi Wayar jikina duk Gumi(Zufa) yake Kamar Ba Ana Iska ba. Najuya na nufi Cikin gidan Batareda ko Wai waye sa ba. Yadaɗe Jingine da Motar sa yana Kallona Har Sanda yaga Nashige Gida Kafin Yasauke Ajiyar Zuciya Cikin Mamakin Sauyawa ta Cikin Lokaci Ƙanƙani. Ganin Ruwan Da'ake Yasoma Karfi Haryajiƙa Masa Jiki Yayi Hanzarin Shiga Cikin Motarsa Yatayar Da ita Yawuce. Sanda Nashigo cikin gida ba kowa A Tsakar gidan Sai Momy dana Hango can! A Cikin Kitchin Tana Rike da Lema Nasan Alalar dana ɗora Take Sauke wa. Ban Wani Saurara ba Na nufi ɗakin dayake Nawa ne, ina Zuwa kuma na faɗa kan ƙatuwar Katifa ta Na dunƙule Cikin Hijabi na Ina Makarkatar Sanyi. Can da jimawa Saiga Momy Tashigo ɗakin Nasan tayi Mamakin ganin kawai nawuto Ban bi Ta kanta ba. Tahayo kan katifar tawa Tana yaye lulluɓin da naye gamida Cewa, "ke Lafiya? Dama Ni tunda Naga Yanayin Shigowar ki Nasan da Walakin....." Naka ra Ruƙumƙume Jikina Ina cewa, "Momy ki Rufe ni Sanyi Nakeji." Momy tace Subhanallah Kodai Ruwanan da'ake Yajiƙa ki Yasaukar Maki da Masassara(Zazzaɓi) Kuma kema dai Kinga Alamun Hadarin Ba Sai kuyi Sallama Ki Shigo gida ba tunda Kin Sanu Ba wani Cikakkar Lafiya ce dake ba?" Nidai Bantaka ba Ko Inada Ma Niyyar Tankawar Nakasa Saboda Wani Irin Zazzaɓi da Yarufeni Anan Take. Momy Tajawo Bargo Tana Lulluɓeni Tana Cewa, "ALLAH Yasauwaka Bari Naje nagayawa Dadyn ku, Ana ma Ruwan Nan Wane Mai Chamist Ne Zaka Sama?... Bari A Samo Maki paracetamol Kisha Zuwa Sanda Ruwan Zai Tsagaita Sai A nemo maki Magani." Kafin Tajuya da Nufin fita Sai Kuma Tadawo "Ni Wannan, Ciwon Naki daki Yaƙi Ci Yaƙi Canyewa Tunda Kika Haɗu da Jarababben Yaro Nan (Abdul-wahab) Kikayi Ban kwana da duk Wani Farincikin ki Haba! Me Ake da Wannan ALAKAR? " Momy Tayi ta Yan Faɗace-faɗacen ta Tagaji Sannan Tafito Tabarni Acikin Yanayin da Nakasa Tantance Ina ne Nake Tsakanin Duniyar Mutane da kuma ta Masu CIWON SO! ********** Dai-dai Lokacin da Su Abdul-wahab Suke dawowa daga Asibiti Suna Bakin Gidan Su Abdul-wahab ɗin A Gwabce da Ruwan Masu Ƙarfi. Cikin Ruwan Kuma Suka Rika Abdul-wahab Sai Cikin Gida Suna Shiga Yazuɓe Kan Shimfiɗar Innarmu Sai Maida Numfashi Yake. Innarmu Tayi Hanzarin Sallame Nafilar datake Ta Iso Gareshi kafin Tajiyo Muryar Mutane A Ƙofar ɗakinta dake Cikin Baranda Sama-Sama. Dan Haka Sai Ta Fito Wajen. "Mama Ina Wuni?" Abinda Ogan Nasu Abdul-wahab Yatareda Shi Kenan Tace, "Lafiya Lau. Ah Zayyanu (Watau dayan Abokin Aiki Nasu Dayake Shi Sun Saba zuwa da Abdul-wahab Gidan Innarmu Tasanshi) Na Shima Ya Gaisheta Shima Kafin Kuma Yakoro Mata Jawabin duk Abinda Yafaru Innarmu Sai Girgiza kai take Tana salallami Daganan Suka Sake Gaisawa da Ogan Nasu Abdul-wahab Harma tayi Masa Godiya da irin Karamcinsa ga Abdul-wahab da kuma Wani Lokacin Aiken da Yake Yo Mata Ta Hannun Abdul-wahab ɗin. Ruwa kuwa Sai Ƙara Ƙarfi Yake duk Feshinsa dake Shigowa Cikin Barandar Yajiƙasu Hakan Yasa Sukayi Mata Sallama Tareda Miƙo Mata Ledar Maganin Na Abdul-wahab. Rokon duniya Innarmu tayi Masu kan Su Shigo ɗakinta ko ɗakinsu Abdul-wahab ɗin Harzuwa Sanda Ruwan zai Tsagaita Amma Sukaƙi. Dole Cikin Ruwan Tayi Masu Rakiya Tareda Binsu da Kalaman Godiya harba Adadi. Duk kuwa da irin Rokon da Sukeyi Mata Suma na Cewa Takoma Kar Ruwan Saman Yajiƙata. Dole Sanda Aka kawo Bakin Ƙofar Gidan Sukayi Sallama Yayinda Suka Rumtuma da gudu Suka Faɗa Cikin Kk Napep ɗinda Suke tare da ita. Itama Innarmu Tajuya Cikin Gidan Cikin Tarin Mamakin Irin Wayyanan Rashin Lafiyoyin Abdul-wahab Da Suka Ƙi Ƙarewa. Tama Lura Kai Tun Sanda Abdul ɗin Yahaɗu da Jarabbar Yarinyar Nan (Khaleesat) Sai kuma duk Yafita Hayyacinsa da Walwalarsa Tau Me Ake da Wannan Soyayyar Marar Kan Gado? "Tashi Kasha Maganin Sannnan ka Kwanta Zaifi." Abinda Innarmu ke Cewa Abdul-wahab Kenan Sanda Tashigo ɗakin Yayinda Shikuwa Yaƙara dunƙulewa Tareda Cewa, "Innarmu Nasha tun Acan Asibiti harma Allura Sukamin, Dan ALLAH ki lulluɓeni Innarmu Sanyi Nakeji." "Tau Bazakaci Abinci ba? Ai kasha Koda Kunun Zaƙi ne Ko?" "Innarmu Bana Bukata, Dan ALLAH ki Lullubeni." Abdul-wahab Yasake Faɗar hakan Yana Mai Ƙara dunƙulewa Guri ɗaya. Innarmu Tajawo Bargonta Ta lulluɓa Masa tareda Tofa masa Adu'a Sa'anan Tamike Takoma Kan Sallayarta Tana Cewa, "ALLAH ya yaye Maka Wannan Lalurar Abdul Dan Alfamar Ma'aiki (S A W). Kafin Tasoma jan Carbinta Tana Mai Sauraro daga Ruwan da Ake ta Ci gaba da Tsugawa Kamar da Bakin ƙwarya. *********** Shima dae Cikin Ruwan Saman Yayi parking ɗin Motar sa Yafito, Kafin Maman Ashraf Tafito da Lema ta taryeshi Yaɗora Hannunsa Kan Kafaɗar ta Suna Cikin Lemar Suka Nufi Cikin Gida. Sai Sannu Take yima sa. Shikuwa yana mata Murmushi Tareda Cewa, "Karki damu, Dama Shi Watan August Yagaji Hakan." Tace, "Wallahi Kam! Ni Nama ɗauka Bazaka Taso Yanzun ba Tunda Kaga Ruwan." "Bari Kawai! Saman Hanya Suka Riskeni Wallahi." Dr Jabir Yafaɗi Hakan Yana Mai Cire Jiƙaƙƙun Kayan dake Jikinsa Kasancewar Sun Shigo ɗakinsa Yayinda Maman Ashraf Tashiga Tayashi Cirewar Bakinta Kuma Bai Huta da Amba ta masa Sannu! Ba. Shikuwa yana Amsawa gamida Karramata da Wata irin Sahihiyar Ƙauna Wacce take Tasowa Tundaga Cikin Zuciyar sa Har Izuwa ga Maƙwagoro. Kaitsaye Toilet Yashiga Yagasa Jikinsa da Ruwan Zafi Sa'anan Yayi Wanka Da Ruwa Masu Ɗumi Kafin Yafito Ɗaure da Tawul A Ƙugunsa Yana kuma Rike da ɗaya yana Tsane Ruwan Jikinsa da shi. Maman Ashraf tamiƙo Masa Ruwan Lipton mai ɗan Zafi Da Yaji Haɗin Citta, ta'amshi Tawul ɗin tashiga Aikin Tsane masa Jikin nasa Yayinda Shikuma yake Kurɓa Ruwan A Hankali ɗaɗinsu Na Gauraye masa Maƙoshi Kafin Yace Mata "ina Mutume Nane(Ashraf)?" Tace, "Yana Bacci Tunda Aka Soma Ruwan Sai muka Shige ɗaki Muka Kwanta Kasan Mutumen da Tsoron Tsawa! Ingayama duk Yabi Yaruƙumeni daganan Sai Bacci." Dr Jabir Yayi Murmushi Tareda Cewa "Ɗan Baba Kenan!" Jallabiya Yazura Suka Fito Falo Lokacin Ruwan Sun ɗan Tsagaita Sai Yan Lam-lam Da'akeyi. Kan 3Searter Suka Zauna Atare Kafin Maman Ashraf tace dashi "Akawo Abinci?" Yadubi Agogo Kamin Yamai do Kallon Sa gareta Magarib Tagaba to, A Bari Har in dawo Sallah." Yajanyo Remote ɗinda ke Kan Hannun Kujerar Yana mai Ƙokarin Kunna Tv Kafin Yace, "Wai Nikam In Tambayeki 'ƴar Momy?" Yayi Saurin dafe Bakinsa Yayinda Maman Ashraf Kuwa Tahaɗe Girar Sama da ta Ƙasa Izuwa Yanzun Tasoma Gundura da jin Wannan Sunan Haka Jiya Suna Barci Yakwana Kiran Mata Yar Momy! Yar Momy!! Kamar Wanda Ke Mafarki Ta Tayar dashi Ya dinga Zamewa A'a Wai Ai itace yake Mafarkin Yana tsokana Haka da Safe Zai Fita "Sai Nadawo Yar Momy." Still Gashi Yanzun Yar Momy. Kuma ga dukkan Alamun Yanda Yasha Jinin Jikinsa A Yanzun da Yasake Suɓutar Baki Yaƙara Tabbatar Mata Cewa Kowacece dai Yar Momy ɗinan Ba Alkairi bace Itakam Gareta. Dan Haka Cikin Sanyin Jiki Tazare Hannunta Dake Cikin Nasa dai-dai Lokacin da Wasu Hawaye Masu Zafi Suka Sulalo Mata Tamike Tanufi Part ɗinta Shikuwa Sai Kiran ta Yake, Tayi Masa Banza dan Haka da Hanzari Yamike yabiyotan Ita kuwa tahaɗa Harda gudunta ta'isa ɗakinta Kafin Tarufo Ƙofar ta da ƙarfi Sanan tajingine da ƙofar Tana mai da Numfashi "Namiji Ƙanin Ajali Namiji ba ɗan goyo ba Namiji Ƙudan Zuma!!!" Wayyanan Kalamin Sukaita Mata Yawo A Kwakwalwar ta Bata san Sanda ta Sulale Ƙasa ba Jingine da Ƙofar Tareda Fashewa da Wani Irin Kuka Mai Ratsa Duk Wata Zuciyar Mai Sauraron ta. Bugun Duniya Da Kiran Sunan ta Dr Jabir Yayi Amma Taki Buɗewa Haka Yajuya Yakoma Falon Yana Mai dafe Kansa Tareda Tambayar Kansa "What is Wrong Wit me? Meyake Damuna ne?" Tau fa Readers Dr Jabir Na Tambaya Mu Gayamashi Ko Mubarshi? Hummm SO! Kenan! SO! BABBAR CUTA Meke Shirin Faruwa Ne? Wane Irin SONE Wannan da Yayi Musu Kamun Kazar Kuku? Shin Wai Haryanzun SO ƊINAN BAI GAMA ZAMA SILAR KOMAI BA? Haryanzun Muje Zuwa.......... Tareda Alkalamin FA'IK ✍🏻✍🏻✍🏻 [9/5, 9:14 PM] FA'IK: Typing....... 💻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....16 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Sai Bayan Sallar Isha'i Ruwan Saman Da'akeyi Yatsagaita Lokacin Su Dady Suna Cikin ɗakina Tareda Wani Mai Phamacy da kenan Cikin Unguwar Mu Dady Yakira shi Yazo yadubani Sa'annan Yabani Magunguna Yakuma Ɗora min Ƙarin Ruwa. Daganan Yayiwa Su Dady Sai da Safe! Bayan Dady Yasallamesa Suka Bishi da Kalamin Godiya Lokacin Ni kuma Wani Bacci Mai Ƙarfi Yayi Awon Gaba dani. Da Safe Natashi Jikina Garas! Yayimin Sauki Sosai In Ba Yunwa Ba Abinda Nakeji, Dan Haka Nahaɗa Shayi Mai Kauri Na Jawo Bready Nahaɗa Nasoma Ci Ina Karewa Kuma Momy Takawo Soyayyar Indomi Itama Natashi da Ita tas! Momy tace, "Masha'allah Sauki Yasamu Kenan dai." Nidai Murmushi Kawai Nayi. Kafin Namike Nayo Arwallah Nayi Sallah Lokacin Karfe shidda Na Safe Bayan Nagama Saiga Dady Shima A ɗakin da carbi A hanunsa Yazauna gefen Momy yana Mai Amsa gaisuwar Danakeyi Masa Yace, "Ikram Yajikin Naki?" "Jiki Yayi Sauki Dady." Momy ta Sanya Baki Acikin Maganar Tamu da Cewa, "Aikam Yayi Sauki, dan Tunda Asubar Fari Tahau Ciye-ciye." Duk mukayi Dariya Cikin Shagwaba Nace, "Kai Momy Wane Ciye - Ciye Tea ne Kawai Sai indomi fa?" "Oh Su ba Abinci bane? " Momy tafaɗa gamida Rike Haɓa. Dady yagra Zama Kafin yace, "Tau Alhamdullah, ALLAH Ƙara Baki Lafiya Amm Abinda Nake So dake Ikram, idan dae dagaske Wannan Yaron yake tau Kice Masa yaturo Magabatan sa Ayi A Kare Komai. Maganar Gaskiya Nagaji da Ire-iren Abubuwan dake Faruwa. Sauka Na Jiya Garinnan Duk fitar da Zanyi Sai Nasamu Mai Magana Akanki Kowa kuma da irin Abunda Yake tarbana Dashi Wani Ya'iya faɗar Magana Wani Kuma Zaki Samu Akasin Hakan Tau Amma dai duk Nashanye Na nuna Masu Ina Godiya da Hakken Makwabtaka da Suka Sauke Ƙari ga Haka Ina can Momy Tana kira na Akan Wayyanan Matsalolin duk-dai Nakawar da Kai ne Nakyale ki. Tau Yanzun dai Ina So Ayi ta Taƙare Bayaga Haka Motar nan da Kika Amso Bana Bukatar Sake Ganinta A gidan Nan Kodai Ki Mayarwa mai ita Ko Ku san Yanda Zakuyi da Ita. Sa'annan ina ƙara Jaddada maki Dr Jabir Yaturo Magabatan sa Indai da gaske Yake In kuwa bahaka ba Ni Zan Samarmaki Wanda Nake Ganin Yadace dake Ina Fatar Ikram Ta jini?" Kaina A Durkushe ƙasa Ina wasa da yatsun Hannuna Nagirgiza kai Kawai Batareda Na'iya Tofa Wani Abu ba. Tau Ma ko Inada Abin Cewar, Ba Dama Dan dai Dady nagama maganarsa Yafice daga ɗakin Momy ma Ta mara masa Baya Suka Barni Nikaɗai Cikeda Tarin Tunanin Irin Wannan Rayuwar tawa. Haryanzun Nakasa Tantance Halin danake Ciki Ko Nake ji Gameda Dr Jabir Saidai Inaji Zan Iya Zama dashi Fiye da duk Wani da Dady ke Shirin ƙakaba Mani. Saidai Natabbata Manta Abdul-wahab A Raina Shine Abu Mafi Girma da Zai Kawo wa Rayuwa ta Barazana. Naji ina ma'ace Banyi Sharholiyar da nayi ba dan tarawa Abdul-wahab Kuɗin Danake ganin Sune Gatan da zai sa Ya Aure ni? Wata kila da Dady Bai Matsa Akan Auren Nawa ba. Haka dae Na lume Cikin Tarin Tunani da Damuwa Wacce Bansan Ranar ƙarewarta gareni ba daga Wannan sai Wannan. Karo Na Farko A Rayuwa ta Namike Nayo Arwallah Nayi Nafila kafin Naɗauki Alkur'ani na danake Zuwa Islamiyya Nasoma Karantawa Lamarinda Yasoma Saukar min da Ita wata Irin Nutsuwar Zuci. Abdul-wahab Kuwa...... Gari Na Waye wa Yamike Yasoma Shirin Shiga Skull Innarmu tafito daga madafi Tana Kallon kai kawon sa Kafin ta Sanya baki Da Cewa "Badai Makaranta Zaka je ba?" Yana Kakkaɓe Jakkarsa Yace, "Itace Zanje Innarmu." "Aikuwa dae da Kabari Harka samu Kwarin Jikinka Komai Ai Saida Lafiya." yace, "Innarmu Jarrabawa Muke Kuma Wannan ma Itace ta ƙarshe Aikinga ko Ba Maganar Fashi Kuma ma ni Wallahi Naji Sauki." "Tau ALLAH Ƙara bida Lafiya, sai Kazo Ga Kummalon Ka Karya Ina Shi Auta Ko Haryanzun Bai tashi daga baccin Bane?" Innarmu tafaɗa gamida Juyawa Izuwa Kitchin ɗin. Abdul-wahab Yace, "Bai Tashi ba yana can Yana baccin ƙa'ida ni inaga bazan tsaya karin nan ba in Akwai Kunun Zanɗauka Innaje Zan Sami Bons In haɗa." "Wannan Kuma Shine Baka Isaba dole Katsaya kacika Cikinka." Innarmu Tafaɗa Sanda Take dakata wa daga Niyyar shiga madafin da Tayi. Ya zaiyi dole Yatsaya yacika Cikinsa Sa'annan yafice zuwa Skull ɗin Yana mata sallamar Sai Yadawo. Yana tafe Yana Zancen Zuci Kumafa Gara da Ya Tsaya ɗin Yacika Cikinsa. Koda yaje Skull ɗin da Sauran Lokacin kafin shiga hall ɗin da zasu zana Exam ɗin, dan haka sai Yasamu guri Yana ci gaba da Nazartar Handout ɗinsa. Karfe 2 Dai-dai Suka Fito Jarrabawa Fuskokinsu Akwai Alamun Gajiya sai dai kuma Suna cike da Annuri Alamun dai Jarrabawar Tayi daɗi dan haka Da Murna Ake ta Taɓewa da Abokai Anata shewa Irin Na ɗallibai Wayar sa ce Tayi ƙara Yaɗauka Yana Mai Cewa, "Shegen Sama Kamar Kasan Kaine A Raina!" daga can Yusuf yana Murmushi Yace "Ba Wani Nan ɗan iska Nidai da na Damu Da kai Nakira ka!" "Kai Abokina Haka Zaka ce Ma Kenan Wallahi Muna Exam ne Shiyyasa kaga naɗan daina kiranka Amma ai kasan Nafi Ka Kira ko?" Abdul-wahab Yafaɗi yana Kokarin Samun Gurin Zama dan Yaji daɗin yin Wayar. Yayinda daga Can Shikuma Yusuf yace, "Kaga Ni ɗan Iska Katyna Bai da Yawa dama Na Kira Ingayama Insha'allah Gobe Zan Taso.... " "Kai da gaske Nawan?"Abdul-wahab Yakatse sa da faɗin Hakan Cikeda ɗaukin Zaiga Abokinsa da Yadaɗe Basu Haɗu ba, Saboda Fatauci da yaje yi A kudancin Ƙasar Nan. Yanzun Kusan Wattani Yana Can. Daga Can Shima Yusuf Yana Mai Gyra Zamansa Yace, "Baka Bina Bashin Rantsuwa, kadai Kawai Jibi I war Haka Kasa A ranka Muna Tare! Kasan Kuma Ina Zamu Fara Zuwa?" Abdul-wahab Yagirgiza kai Kafin Yace, "Sai Ka Fa...." Kit!! Yaji Wayar Ta Yanke Watakil Katin Yusuf ɗinne Yaƙare. Dan haka Abdul-wahab da Kuzarinsa Yamiƙe yanufi Cikin Kafteriya ɗinsu, dan Yasamu Lemu Yasha daga nan yasa Kati Cikin Wayarsa Suƙarasa Magana da Abokin Nasa da Yake jinsa Tamkar Wani Rabi Na Jikinsa Saboda shaƙuwar dake Tsakani su. Tau Yana cikin Wannan taɗin Zuccinne saiga Kiran Na Yusuf Yasake Shigowa Yaɗaga Yana mai Murmushi Kana Sukaci Gaba da Tattaunawa Irin Tasu Ta Aminai. ******** Har yaje Sallar Isha'i Yadawo Babuta Babu Labarinta Falon Wayam! Haka Yasake Binta Har bedroom ɗinta Yana Yimata Magana Amma Shiru ba'amsa dole Haka yadawo Falon Shikaɗai Yazuba Abinci Acikin Flet yasoma Ci Amma duk sai yaji Abinci Baya yi Masa daɗi dan haka yadire plet ɗin yaɗauko Lemu Yatsiyaya Acikin Cup Yasoma Sha Shima ɗin Baiji Wani daɗinsa ba Dan Haka Kawai Sai Yamiƙe Yabaro Danin Table ɗin Cikin Rashin Kuzari da kuma Tunanin Meye Mafita? Nan Acikin Falon Yasamu doguwar Kujera Yakwanta Kafin Yajawo remot Yakamo Tashar CNN domin Kallon Labarai Wanda A Zahiri Baya cikin Nutsuwar Fahimta Me'ake Cewa A Labaran, Kawai dai Gashinan ne Yayi wa Tv ƙuru da Ido. yaɗan Sake Musƙutawa karo Na barkatai Yana mai Jan Tsaki! Taƙamaimai yarasa Meke damunsa? Shidai Yasan Yana Son Matarsa duk-da Kuwa ba Auren Nagani Ina So Sukayi Ba, Aure ne Na Zumunci (Watau Haɗin Iyaye) Amma Ƙauna da Kyakykyawar Mu'amala dake Tsakanin sa da Maman Ashraf ko Wayanda Suka yi Auren So! Basu Kaisu ba. Kuma Wannan Son da Yakeyi Yiwa Ƴar Momy bawai Yanayi ne dan Ya Wulakanta Matarsa ba, Yanayi ne da Yana son Itama Ƴar Momy Kuma Yana ji Idan har Bata Kasance Iyalinsa ba Tau Baya da Wani Sauran Sukuni. dan haka Tsakani da ALLAH bazai Fasa Abinda Yake Niyya ba Tunda ALLAH Ma Yahallata Masa. Ire-iren Wayyanan Tunanunka Suka ci Gaba da ƙara Masa ƙaimi Wajen Son Ƴar Momy gefe ɗaya Suka Nuna Masa Ai Matsalar Maman Ashraf Mai Sauƙi ce, Zai Ci gaba da Lallashinta Har'izuwa sanda Zata Sauko daga Kishin Nata. Dan Haka Cikeda Karsashi Yajanyo ɗayan Wayarsa Yashiga Kiran Wayarsa ɗaya Wacce Yabarwa Khaleesat, taɗaga Wayar tasa Gamida kwararo Sallama Cikin Sanyaryar Muryar ta data ƙara dulmiyar da Dr Jabir ɗin Cikin Kogin Ƙaunarta Yakuma ƙara Hakiƙancewa Inba Khaleesat ba Sai Rijiya! Sai da Yaja Fasali Kafin Ya'amsa Sallamar Tata Yace, "Tawan Ina Fatar Kin Zama Normal Yanzun?" daga can nace, "Alhamdullah Sai dai Zazzaɓi Yakoma min Sai da Ma Aka min ƙarin Ruwa!" Yace, "Ƙarin Ruwa Kuma?" "Eh!" nafaɗi cikin girgiza kai Kamar Yana Ganina. Yace, "Amma Wannan Rashin Lafiya tayi Tsaurin Ido dazata Kama Har Matar Likita Sukutum?" "Tau ba Dolenta ba tacika Umurni? Wanda Ya'aiko ta Ai shi yayi matar har Likitan Kuma Yake da iko akan Masarrafin Ƙaddarar Su ka ko ga ya wuce da haka ma ko?" nayi Masa Wannan Zancen Cikin Ƙara Natsuwa da Cewa Ko bana Son Wannan Likitan Zan Iya Zama Dashi. "Hakane Kuma Matar Likita Kinyi Gaskiya?" Yafaɗi Hakan Tareda Miƙewa Yanufi Danin Table "Natashi Daga Ƴar Momy Na Koma Matar Likita?" "Ke Bakiga Alamun Haka ba?" "Taya ya?" Nafaɗi Hakan Cikin Shauƙi "Ta Yadda Yanzun Bani da Wani Buri Sai Mallakar Ƴar Momy tazamo Matata Kuma Inace Tuni Na Nemi Wannan Alfamar Gurin ƴar Momy Tace ta'amince hakane?" Wannan Karon Nakasa Amsa masa Sai Kawai Na girgiza Kaina a Wautata Zai gane. Sai da Naji daga can Yace, "Yadai Kika yi Shiru?" Nasauke Ajiyar Zuciya Kafin Nace Masa "Hakane!" Yace "Tau Yanzun Alfamar ɗaya Nake Nema A gurin ki Kimin Izini Turo Magabata na Dan A tabbatar Min Cewa Yar Momy Tazama Matar Likita!" Naɗan gyara Kishingiɗata Ina ƙara maƙala Wayar a Kunne na dan Ba Shakka kai kana gani na kasan Wayar Nayimin daɗi Nace, "da Wuri Haka?" Yajanyo Ƙaton Flask ɗinda ke Girke A Saman Danin Table ɗin Cikeda Ruwan Lipton. Yatsiyaya Acikin Cup Sannan Yajawo kwalin Shuga Yaɗibi Masu ɗan Yawa Yajefa Acikin Ruwan Lipton ɗin Kafin Yasanya ɗan Ƙaramin Cokali yana Juyawa. Cikin Tunanin Ko Wayar ta tsinke ne? Najanye wayar daga Kunne na Naduba naga still yana kan Layi tau Meye ya... "Ke bakiji Ance da Safe-Safe Ake Zuwa kamun Fara ba?" Yakatse Tunanin nawa cikin Fadar Hakan. "Haka Naji Ana Faɗi." "Tau dan haka Kawai Kimin Wannan Izinin." yafaɗi hakan yana mai Juyowa da Nufin dawowa Falo, Gefe ɗaya yana mai Kurɓar Ruwan Lipton ɗinsa "Zamma Magana Insha'allah!" Nafadi Hakan Cikin Sanyin Murya. "Zuwa Yaushe kenan?" "Zuwa Sanda Nayiwa Su Momy Maganar." "Tau Shikenan Ƴar Momy." Naɗan Zaro Ido "ba Matar Likita ba?" Yakama Baki, "Au? Kumafa Hakane." Wayar dae da Muke tayi Itace Takwashe Kaso Mafi Yawa daga Cikin Damuwar da muke Ciki Yayinda Zukata mu Suka Samu Nutsuwar Cewar Lalle Muna Bukatar Rayuwa tare da Juna. Dan Haka ta ɓangaren Dr Jabir Yakeji Zai Iya Jure Fuskantar Kowa ne Irin Kalubale ne dan Ganin Ya mallaki Khaleesat. Yayinda Tawa Zuciyar Ki Ci gaba da Sanar dani Lalle Nan Duniya Bani da Wani Wanda Zai Cikemin Gurbin Abdul-wahab Sama da Dr Jabir Dan Haka Naji Na Amince Zan Rayu da Shi Muddin Rai! Da Wayyanan tunanunka Mukwa Kashwe Lokaci mai Tsawo Muna Waya kafin Mukayi Sallama. Kowanenmu kuma yakwanta Cikeda Saƙar Zuci da Tunanin Makomar Rayuwar Sa! Inda Ni Nake Ganin Cewa Babu Shakka! Dr Jabir Ya'isa Kuma Zan Mallaka Mashi Zuciyata Kuma Ai Dama A Rayuwa bai Zama Dole duk Abinda Kake So Kasamu ba! dan Haka Nabarwa Raina Cewa Abdul Kawai Ba Rabo Na Bane. Yayinda Shima Dr Jabir ta ɓangaren sa Yakeji Cewa Yazama Wajibi ne Gareshi Auren Khaleesat bcause Itace Farincikinsa dan haka Yafi Maida Hankali ga Tunanin Tayaya Zai Haɗa Kan Matan Nasa Su Zauna Lafiya? Yana kuma Ayyana cewa Yazama Dole gareshi Wannan Satin Yaje Gida Dan Yagana da Su Ummarsa Kan Wannan Maganar. Saidai Wani ɓangaren Zuciyarsa Na Sanar dashi Anya Iyayensa Zasu Karɓi Auren sa da Khaleesat Kuwa? Musamman Mahaifiyarsa da yake Ganin duniya Ba wacce take so Sama da Maman Ashraf? Baya Tunanin Mahaifinsu Saboda Yasan Shiɗin Baya da Wata Matsalar Tunda Yasan Sunnar Ma'aiki S A W zai Raya. Tau dai Haka Suka Kwana Cike da Tunani Mafitar Da kowane Yake Ganin Zata fisshe Shi. Rashin Kwanciyar shi Da Wuri Yasa Yayi Jinkirin Tashi dan Ko da Yafarka Massalaci Unguwar tasu Suna Sallame Sallah, dan Haka A gagauce Yayi Arwallah Ba tareda yayi Wanka Kamar Yadda yasaba Ba Yanufi Massalaci Bayan Sallah Kuma Yashiga Yin Lazimi Yadan Jima Yana Lazimin Kafin Yadawo Cikin Gida, Kaitsaye Kitchin Yanufa Inda Yake Kyautata Zaton Zai Sametan. Illai Ko Yahangeta Tsaye A Tsakiyar Kitchin ɗin, Sai Aikin ɗorawa da Sauke wa Takeyi. Fuskar Nan Tata Fara fes! Sai Annuri Take kamar Ba Wani Abinda Ke damunta Sai dai Idanunta da Suka Kumbura Sukayi Luhu-Luhu Tabbacin Tasha Kuka Harta Ƙoshi, Tajuya Masa Baya Dankalin turawa ne A hannunta Tana Ferewa. Sannu A Hankali Yalallaɓo Da Nufin Yariƙota ta Baya, Kamar Yadda Yasaba Yi Mata, Amma Sai tai Maza ta Koma Gefe Tana Kallonsa da Idanunta dake Wadace da ɓacin Ransa. Baƙar Magana taso Yaɓasa Masa Amma Suna Ido Biyu Sai kwarjinin Sa Yasa Takasa! Tabar Abinda Zata Faɗa Yabi Iska Taci Gaba da Motsa Laɓɓanta Kawai. Yafahimci Hakan dan haka Sai Yayi Murmushi yaƙarasa Inda Take da Murmushin A Fuskarsa Yana Cewa "Yana ga Idanunki Jawur Haka NURUL KHALBI?" "Fetur Aka Watsa musu Ko Zaka Kyasta Ashana ne su Kama da Wuta?" Tafaɗi Hakan Cikin Ƙufula Yamiƙa Hannu Zai Riƙota Taƙara Janye Jikin ta Tare da Cewa "Wai Meye Haka ne?" "Ah! Mutum da Matar shi?" Yatambaya Cikin Mamaki Kawai Sai Tafita Harkarsa Taci gaba da Abinda Takeyi tana jin Cewa duk Yasa ke Wani Yunƙurin Taɓata Kawai Yuƙar Zata Caka Masa! Kowa ma Yahuta. Dan A Yanda Zuciyarta Yanzun Ke Makance Da Kishi Tana ji Komai Zai Iya Faruwa!.......... Muje Zuwa Readers Tareda Alkalamin FA'IK.... ✍🏻 [9/5, 9:14 PM] FA'IK: Typing....... 💻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....17 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Shi Kanshi Yalura da Yadda take Cika Tana Batsewa dan haka sai Kawai Ya yanke Shawarar Bari Yatafiyar sa Kawai Yabarta Harta Huce, Sai dai Yana Juyawa Yaji Tafashe da Wani Irin Kuka Mai Razana duk Wani mai Sauraren sa Yadawo Da Hanzari Tareda Cewa, "Subhanallah Maman Ashraf Meyayi Zaf...." "Kada Kataɓa ni!" Tafaɗi hakan Cikin Muryar Kuka. "Haba Maman Ashraf! Wai Meke damunki Ne daga jiya duk Nakasa Gane Kanki Ne? Kinbi Kin ɗaga Mana Hankali?" "Oh Nine Ma Naɗaga Mana Hankalin? Tau Shikenan ai." Tana Faɗin haka kuma Tajuya cikin Hanzari Tabar Kitchin ɗin. Har Yabita Kuma Yasake dawowa Sai da Yakashe duk Wata Na'ura data Kunna Kafin Yafito dan Zuwa ɗakin Nata Yaji Meye Matsalar ta ne? Amma me Sai Ganin ta Yayi Ɗaɗɗake Da Akwatin Kayanta Ta Nufi ƙofar Falon tana Kuka. da Hanzarinsa Ya'isa Gareta Yakama Hannunta Yarike. Duk Ƙokarin da Tayi na kubcewa Riƙon Nasa tagagara Dan ƙarfin ba ɗaya ba dan Haka Sai Kawai Tazube Gurin Tana Kuka Sosai! Dr Jabir yarasa ta'inda Zai Soma dan Haka sai Kawai Yatafi Ya murza Wa Ƙofar Falon Nasu Key, Yajefa Key ɗin Cikin Aljihunsa Wanda Hakan da Yayi Yaƙara Fusata Maman Ashraf Tasake Zabura da Duk Karfin ta tana Faɗin "Ni Wallahi Gida Zani." "Tau Gida Zakije Dalili ne Na Sai kin tadawa Mutane Hankali? Ko Sanda Kika Saba Zuwa Gidan Sai Anyi Yaƙi Ne?" Dr Jabir Yafaɗi Hakan yana kallonta A wannan Karon Shima yaɗan Soma Hasala da Ita. "Ni ban tambaye ka Wannan dogon Jawabin ba Kawai Nace ma Gida Zanje dan...... " "Tau Bazaki je gidan Ba Inke kike da Iko da Kanki Sai Inji." "Ni kuma Wallahi Sai Naje." Tafaɗi Hakan Kana Takwa so Sauri Ta Nufi Kofa Sai ta tuna Ai Yarufe, dan Haka sai ta zube Bakin Ƙofar Tacigaba da Kuka Mai tsuma Zuciya Wanda Yayi Sanadiyar Tashin Ashraf daga Bacci Shima Yazo Yarumgume ta Yana Kukan Duk Sai Suka Sukurkucewa Dr Jabir Zuciya, Yayi Tsaye kawai Yana Kallon Su Kana Yana Tambayar Kansa Dama Su Mata Duk Hankalin Su In Aka Zo Maganar KISHI Sai Ka Nemi shi Ka Rasa? Wai Wannan Ma Mai Saukin Ce Saboda Maman Ashraf ce Kuma dama can Ita bamai Surutu Bace Kuma bata da Tsiwa, tau Yanzun da Mai Tsiwa ce Fin Haka ma Kenan? Cikin Rashin Kuzari Yatako Zuwa inda Suke durƙushe Ita da Ashraf Suna Aikin Kuka Yace, "Wannan Aikin Bai Kama ceki Ba, A Nawa tunanin Ba'abin da Yafi Karfin Fahimta Kuma A Sani na Muna da Wannan Agender Kafin Komai Yakamata Ki Gayamin Menayi Maki Maman Ashraf?" yadan yi Shiru Yana jan Fasali Kuma ga dukkan Alamun Maganar tasa tayi Tasiri Acikin Zuciyar Gimbiyar tasa dan haka Sai Yaƙara Kwantar da Murya tareda mai da kansa Kalar Tausayi yasoma Rattabo Mata Jawabi Wanda Afakaice Lallashinta Yakeyi, Hardai Yasa tattausan Hannun sa yana Share Mata Hawaye kafin Yariko Hannunta Yajawo Akawatin ta gefe daya Ashraf Nabiye dasu Shima tunda Mahaifiyar sa Tayi Shiru Shima Sai Yayi Shiru. Kan Kujera Suka Zauna Yana Ci gaba da gayamata Muhimmanci ta Acikin Rayuwarsa, da irin yanda Yakamata Su riƙa Fahimtar Juna Idan Irin Wannan Matsalar ta taso, yakare da Cewa, "Kin Fahimce ni Maman Ashraf?" Takasa Yin Magana sai dai Girgiza Kai kawai Alamun dae "Eh! " Yace, "Yawwa Tawan, izuwa Yanzun yakamata Kigane Cewa Bazan iya Rayuwar da babu ki Acikin ta ba. dan haka ki daina ɗaukar Rabuwar mu Abu ne Mai Sauki Ko Yiyuwa, kawai Inna miki Laifi Zaunar dani Ki Sanar dani Nikuma bazan ƙi Gyarawa ba Kin Gane?" Nan ma Girgiza kai Tayi yace, "Ba Girgiza kai Zakiyi ba, Baki Zaki Buɗe Muyi Magana." Taɗan Share Hawaye Kafin tace, "Amma kai Kana ga kayimin adalci Yin tarraya da Wata Bayan duk wata kula da ta kamata ina Ƙokarin ganin Nabaka ita hakanan duk wani Abu Dakake So Inayi. ka gayamin da me narage ka harda wata zata janye hankalin ka harka kazo Kana ta min mafarkin ta da Sumbatun Kiran Sunan ta?" takarashe Maganar tana tsura masa ido wanda ada can bata iya yin hakan. Dr Jabir yasami Kansa da jin Kunyar ta har hakan yasa ya rusunar da kansa ƙasa Cikin Nazarin Wace Amsa zai bata zai ce matane Wacce zai Aura ce? In har yace Wacce zai Aura ce Wace Hujja gareshi Na Iyayenta Sun bashi Aurenta? Ko zai ce Wadda yake So ne? Anya in yace Haka Cin Fuskar bai yi Yawa ba? Kuma ɗan Shirin da Suka Soma Yanzu bazai lalace ba? Haka dae yajima cikin Nazarin hardai Yazaɓi Kawai yabata Hakurin Kawai, dan Haka yaɗago kan Nasa Haryanzun Shi take kallo da Kumbararrun Idanunta Cikin Sanyin Murya Yace, "Ban kyauta ba, kuma kiyi Hakuri Insha'allah bazan ƙara ba." yakarasa Maganar yana mai haɗe Hannayensa guri ɗaya Alamun Ban Hakuri. Maman Ashraf Ta kawar da kanta Cikin Nazarin Duk Sanda Dr Jabir yace zai haɗa ta da Wata matar Mutuwa kawai zatayi, dan tana ji A ranta Cewa bazata iya raba dae-dai Akan Mijinta da kowace Macce ba. "Yakikayi Shiru ko Haryanzun baki Huce ba?" yafada Cikin ƙara Sanyaya Muryar sa. Tace, "Nahuce Yawuce Kuma." Yamike yadawo kusa da ita Yana mai kara Share mata Hawayen da takasa tsai da wa yace, "Tau Ya'isa Hakanan Kinji?" ta sake Girgiza kai Yaɗan Sake Kallon ta Yace, "I Love You my NURUL KHALBI!" shiru Kawai Tayi Masa Yasake Cewa, "Ko Baki Huce Bane? Yakamta Kiyi Murmushi Dan in tabbatar." Haka dai yayi ta Amfani da dubaru yana Lallashinta har sanda ya tabbatar komai Yawuce, sannan Yamike yaje ya shirya A gagauce. Koda Yafito harta Shirya Ashraf Cikin Uniform din skull dinsa. Braek kaɗai ne Bata Kamallah ba, tana ta Ƙokarin taga komai ya kamallah. Yadan gyara Wuyan rigarsa gamida Cewa, "Inaga yau Mun Makara Maman Ashraf Babu Lokacin da Zamuyi Break." tace "Haba dae Na kusa Kamalla wa Fa, Dan ALLAH Kujira, Shi Ashraf ban sa Masa Komai A Coolern sa ba fa?" Yasake Duban Agogon dake ɗaure A tsintsiyar Hannunsa Yace, "30 minute Kawai Muke da Kina ga zai Samu Kafin Lokacin?" Tayi Hanzarin Nufar Kitchin ɗin Tareda Cewa "Bazai ma kai Lokacin ba insha'allah Just One minute." Cikin yan mintocin ƙalilan Ta Wadata su Da Break ɗin, tayi Savin ɗin su Cikin Matukar Kula. Wanda Yaƙara Tabbatarwa da Dr. Jabir cewa Ba Shakka Kwanciyar Hankalin Iyalin sa Shine Nashi Kuma Farincikinsu Shine Nashi. ********* Yauma bayan Yataso Aiki Sai da Yabiyo Ta Gidanmu Kuma dai Na'isar Masa da Saƙon Dady Kuma Yayi Farinciki da jin Hakan Yayi Mani Alkwalin Cewa Cikin Satinan Zasu Iso Insha'allah. Munsha Hira Sosai Wacce taƙara tabbatar min Cewa Lalle shiɗin Na Musamman ne Ko Acikin Maza, kuma Zan iya ƙare Rayuwa ta Tareda shi. Ban taɓa Yardar wa kaina Cewa Ma Wai yana da Aure ba. Ni kwai Abinda Nabarwa Raina Harga ALLAH, Dr Jabir Saurayi ne. Shima Kuma bai min Magana makamanciyar Wannan ba. Tau haka dai Kuka Rabu Cikin Wata ƙauna da muhimmancin sa da yasamar Acikin raina. Ina shiga gida Na kimtsa Nayi ma Momy Sallama Kafin Na nufi Gurin Saloon dan Raben da In wani gyra kaina Harna Manta. Dady yaɗauko kuɗi Yabani harda na Kk Napep Tareda gargaɗin Kar na daɗe. ****** Bayan Sunfito Sallar Isha'i Shida Abubakar ne da kuma Abokin sa Yusuf da Yadira A garin Yau. Sune ke zaune kan Barandar gidan ta su Abdul-wahab ɗin Suna ta Firar Bayan Rabo, Yusuf yana ta basu Labarin Kudu da kuma Yanayin Al'adunsu. Wasun suyi ta mamaki wasun Suyi dariya, har zuwa sanda Jibril Abokin Abubakar yazo yajanye shi Suka Shige Suma Yin Sabgogin su, Suka Bar Yusuf da Abdul-wahab Nan nata taɗi Irin Na Aminan Juna. Acikin Firar tasu ne har Suka sauko Kan Abinda Yadanganci Tsakanin sa da Khaleesat Inda nanne Yusuf ke Cewa, "ya labarin Mutumniyar Taka Khaleesat?" da Yusuf Yakula yanda Abdul-wahab ɗin yahaɗe Girar Sama da Takasa da Yabar Zance tau amma da yake Bai Kula ba sai yaci Gaba da Cewa, "Abokina Wallahi Kai kam Kayi dace da Mai Sonka tsakani da ALLAH. ALLAH Yasa Nima Maryam ɗita Zata Soni Kamar Haka! Kai kaga yanda Khaleesat ke faɗin Tashin Akan Soyayyar ku takai Labari Akan fa An....." "excuse me! Excuse me!!" Abdul-wahab Yafaɗi Yana ɗaga Masa Hannu Kafin Cikin Fusata Yaɗora da Cewa, "Kaga Mal Karka Cika ni da Surutun wata Khaleesat kai ka Santa. Ni ban san ta ba." Yusuf Baki Yasaki Galala yana kallon Abdul-wahab Cikin Mamaki Kafin yace, "Abokina Lafiya? Kardai kacemin Haryanzun komai bai Wuce ba a taksanin ku?" "Bai Wuce ba, ba kuma zai taɓa Wuce wa ba indae Akan Wannan mayaudariyar ce."Abdul-wahab Yafaɗa Cikin ɗacin Rai! Yusuf Yace, "Amma ko Abdul kacuci Khaleesat kuma kai butulu ne Wallahi, kuma kasani ALLAH zai Saka Mata ha...." "Ya'isa! Yusuf ya Isa! Menayi Mata?" Abdul-wahab Ya tambaye sa Kamar zai tashi yashaƙe sa. Yusuf yace, "karka manta irin son da Khaleesat takeyi maka Abdul. A kanka ta saɓa da Iyayenta Akan Ance ba'a yin Auren ku da ita, Saboda baka da madogara Khaleesat tashiga tafita tadinga tatsar masu kuɗi dan kawae ta tara ma kuɗɗin da zaka ka tsayu A Ƙafafun ka. Abdul Akan Soyayyar ka Khaleesat ta kwana Kuka tayi Jinya Sa'annan ƙarshe tazo tana Bibiyar ka Amma kaƙi Saurarata ka koreta da Wulakanci. Kana ganin Haka kamata Adalci Kenan? Kana ganin A irin Wannan Lokacin da Zamanin Namu Za'a samu masoyiya Irin ta? Meya Haɗani da Na'ima tawa Lokacin Eh?" Yusuf yaɗan Tsagaita Cikin runtse ido yanajin wani bakinciki Na Taso masa kamar Lokacin ne abunda tayi masa Yafaru, kafin yamatso kusa da Abdul-wahab da yayi Shiru, yadafe Kansa dake Sara Masa kamar Zai rabe gida biyu, yana ji wai Akan sa Khaleesat Tayi Abinda tayin dan ta Samar masa kuɗi tunda Anyi Masa gorin baya da Kuɗɗi. Tau Amma meyasa Taƙi kulashi A Wancan Lokacin Meyasa Kuma Bata gaya ma.... Yusuf yakatse masa Tunanin sa ta hanyar Cigaba da Cewa, "Na Sani tayi Wauta Akan Abinda Tayin, Wanda ita Ana ta Kuskuren tana ga shine zai sa ku mallaki Juna A Matsayin ma'aurata, Amma Abokina mezai hana kadubi Girman So da takeyi maka? Abdul!...." Yusuf yaɗan Tsagaita kafin yaɗora da Cewa, "Wallahi Wallahi kaji na Rantse ma? Khaleesat na sonka kuma idan ka rasata bazaka sake samun Wacce take maka makamancin Son da takeyi Maka ba, duk Abinda Tayi tana gayamin kuma ina da labarin Komai, kawai Bangayama Ne ba, Saboda ta gargaɗeni Akan cewa Tagayamin Amana ce, Sannan ko A Sanda tazo gida da safe Ni Na kawo ta Sbd irin magiyar da tayi ta yimin da Irin tabbatar war da nayi cewa itaɗin mai sonka ce tsakani Da ALLAH. Dan haka Katsaya ka ƙara Nazari, A Rayuwar nan babu wani DACEWA irin ka Auri Wacce ke Son ka, Domin itace wacce zatayi hakurin Zama da kai Acikin Kowane Yanayi, itace Wacce Zata Riƙe ma Amana, kai itace zatayi duk wani abu da zai faranta ma Albarkacin Wannan Son da Takeyi ma, dan haka Abokina Ka gode ma ALLAH da yahaɗa ka da masoyiya ta haƙiƙa,kuma ka gaggauta Zuwa gareta dan ku SULHUNTA." Readers ɗina Anan zan Numfasa muje daku A gaba dan jin yanda Tirƙa-tirƙar zata Kaya dan dae Akwai KWAMACALA Harma da BADAƘALA!!!! Dan haka Muje Zuwa Nidae nayi gaba Acikin Littafin na SONE SILAR KOMAI......... [9/5, 9:14 PM] FA'IK: Typing....... 💻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....18 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Abdul-wahab Yayi shiru cikin Nazari da Tunanin Wannan Rayuwar da Mamakin Irin abinda Abokin sa Ke gayamasa Yanzun, babu Shakka shi kanshi yana matuƙar Son Khaleesat Sonda bai taɓa tunanin zai Risƙi kanshi acikin sa ba, tau sai dai Yana kawaici ne domin gujewa abinda zai tashi hankalinsa har hakan yashafi Dangantakar su Innarmu. hakanan baya son komawa ƴar gidan jiya acikin abinda Yadanganci karatun sa. Yusuf yadafa Kafaɗarsa Sa'annan yakallesa kallo na tsanaki Yace, "Abdul-wahab ka Saurare ni da Kyau. karka zurfafa Acikin Wani Nazari haryazama Silar jefa kanka cikin wata Matsala, mafita ɗaya ce Zuwa Biyu, Nafarko dole Ka iya fin karfin Damuwar ka dan karya zamo Silar wargajewar Al'amurranka Sa'annan Kaje ka gana da Khaleesat Ko da Bazaku dawo da Soyayyar ku ba, tau ku SULHUNTA kai da ita. Haka kuma Kuyafi Juna, ko ba komai Za'a samu Kafar yin Zumunchi kai da ita ko ba haka ba ma, Soyayyar ku bata cancanci kuyi irin wannan Rabuwar ba, yana da kyau Ace Kunyi RABUWAR ARZIKI ita kanta Abuce Mai daɗi. Wannan shine kawai Mafita." "Tau Amma tayaya kake ganin hakan zai Faru?" Abdul-wahab yake faɗin hakan yana mai kallon Abokin nasa. "Abune mai Sauki dai-dai ta danganta karku da Khaleesat, mai Wahlar shine yanda kai Zaka iya Kasancewa Mutum Mai kwarin Zuciyar da zai iya Shanye Damuwar sa ka kuma Kasance Wanda Zai Iya Mai da komai ba komai ba." "Yusuf Bansan Yaza'ayi Na kasance Hakan ba! Nima kuma Inajin Ciwon Zama na Mutum Marar juriya akan Matsalar sa, tau Amma abu ɗaya Nabarwa Raina Shine, Haka ALLAH yayi tawa Rayuwar kuma bani da yanda zanyi wanda yawuce Karɓar ƙaddarata." Yusuf Yasauke Ajiyar Zuciya mai Ƙarfi kafin yace, "Hakane Abdul, Amma dai ko yaya ne ka Ƙoƙarta ganin an ɗan samu Sauyi, Sa'annan mu Shirya zuwa gurin Khaleesat dan Ku SULHUNTA." "Bazan iya zuwa gurin Khaleesat because Nagayama Nayimata Maganganu cikin Rashin Fahimta Wanda A yanzun ina kunyar haɗa idanu da ita." Abdul-wahab Yafaɗi Hakan Cikin Tsananin Takaicin Maganganu da yagaya matan sanda Tasameshi A Makaranta. "Karka Damu Abokina Zanji da komai ni kawai kazo Muje. Kamar yadda Nafaɗa Abinda kawai Nake Buƙata a gurinka kazama mai juriya da fuskantar ƙalubale." Abdul-wahab Yace, "Shikenan Ai, ALLAH yamana Jagora." Yusuf Ya'amsa da "Ameen." Daganan shiru yaɗan Ratsa mazaunin Nasu Na yan sakkani kafin Abdul Yadubesa Yace, "Yaaa? Muje Ciki ku gana da Innarmu ba?" "Kaima kasani Ai." Yusuf yafaɗa yana harararsa. Suka Nufi Cikin gidan Suna ci gaba da tattauna Yanda Abubuwan Zasu Kasance Musamman bukin Na Yusuf dake ƙarato wa. Sun sami Innarmu Gaban Ƙatuwar Frizer ta, tana Aikin Jera Kunun Zaƙi dana Aya datake Sai dawa. Sukayi Sallama Innarmu ta'amsa Tareda Cewa, "Lale Marhabin da Mutanen Ondo State." suka Zauna Yusuf na Cewa, "Innarmu Mutanen Sakkawato dai, Ni mi A haɗina da Ondo kuma?" "Kasuwanci Mana!" Innarmu tabashi Amsa. "Tau kuma hakane Innarmu, mun same ku Lafiya?" "Ah Lafiya Lau, tun ɗazun nake Dakon Shigowar ku dan Auta Yagayamin kuna A Waje." Yusuf yace, "Wallahi kuwa, sarkin Surutun nanne yahana mu shigowa muna can bakin Garka (ƙofa) muna ta zuba Surutu." Innarmu Tace, "Aikam dai naga Alama." Shikuwa Abdul-wahab Sai Aikin Zabga wa Yusuf harara yakeyi, dan yace masa Sarkin Surutu. "Ga Kunun Nan Fa?" Innarmu tafaɗa Tana mai cigaba da gyara jera Kunun Acikin Frezar. "Innarmu Sanda Ina can Ba ƙaramin Missin ɗin Kunan naki nayi ba Wallahi." Yusuf ke wannan Maganar dai-dai Lokacin da yake buɗe gorar Kunun Ayar yana korawa A makwagoron sa. ********* Karfe 8pm Nadare Suna bakin Gidan mu Ni Sanda ma Nafito Naci karo dasu Ba ƙaramin Mamaki nayi ba. Nayi ta Kallon Abdul-wahab da irin yanda yarame ga wani Uban Fari da yaƙara yi sai dogon Hancinsa yaƙara fitowa tamgarau. Yusuf ne Yakatse Shirun Namu da Cewa, "Gamu munzo ban Hakuri Akan duk Abinda Yafaru muna Fatar Gimbiyar tamu zata dubeni mu da idan Rahma tareda mantawa da Laifin da Mukayi?" Murmushi Nayi Sa'annan nace, "ka ganka Yusuf? Kai ko? Kai ko? Wallahi Kowaye yahaɗu da kai Zai shafa ma kanshi Lafiya." Duk Sai Muka Shiga Dariya wannan Karon har Abdul-wahab yana tayamu dariyar. Na Juya Tareda Cewa, "Ina Zuwa." Fararen kujerun Roba guda Uku Nacewa Sani Yaɗaukarmin, Sa'annan Nikuma na tallabi plet ɗinda Najera Gorar Faro guda biyu Da Kuma glass Cup suma Biyu. Bayan sun Zauna Na'ajiye Gaban su Gamida Cewa, "Bismillah Kusha Ruwa." daganan nima Naja Kujerar Na Zauna. Yusuf ne Yatsiyaya Musu Ruwan Acikin Cup Kafin Kowanensu Yaɗauka Yana Sha, Daganan Yusuf yasake Cewar, "Tau Aka ce dai Labarin Zuciya A Tambayi Fuska daga ma Irin Wannan tarbar da'aka mana Yanuna mana cewa komai Yawuce dan haka Ina dai ƙara bada hakuri Amadadin Abokina." Nace, "Kaine mai bakin, Shi Abokin Naka bayada Baki ko?" dai-dai Lokacin Abdul-wahab Yaɗago dara-daran Idanunsa Na Asalin ɗan Fulani Yakalleni dasu yasake kauda kai Nima Nakawar da Kaina gefe. Yasake ɗago kansa Nima naɗago Muka Haɗa Ido yayi Hanzarin kawar da Kan Nasa nima kuma hakan Nayi. Yaɗan Furzar da Iskan bakinsa, Yaɗago da Nufin Cewa Wani Abu Amma kuma muna haɗa ido sai Yakasa cewa komai. Hakan da yayi Sai Yabani dariya Ashe Shima Abin Yabashi dariya Sai Muka Shiga yin dariyar tare. Yusuf Cikin Al'ajabinmu Yakama Bakin sa Kamar Wata Macce Yace, "ikon ALLAH Abun Kuma kurman ci Yakoma? Tau Bari Kagani." Yamiƙe glass Cup Riƙe A hannunsa "Ni kunga Tafiya ta Kunga sai ku sake Sosai Kusha Soyayyar Taku, daɗin Abun dai Ina da tawa Masoyiyar, Bari Ma na Kira Abata A waya." Cikin Sanyin Murya Nace, "kai kam Kashiga Ukku Yusuf..." Yace, "Tara ma Kai!" Cikin Abinda Bai Fice Sakkani ba Khaleesat da Abdul-wahab Suka Tsunduma Cikin Wata Irin Sarƙaƙƙiyar Soyayyar da a gurin su Za'a iya Cewa, ta zarce Zuma daɗi, tuni Muka manta laifukan Juna. Muka Cika kunnawa mu harma da Zukatan mu da Kalaman Irin kewar da mukayi ta Juna. Hira Muke sha kamar ba gobe, Sai da Mukaji Yusuf Yana ta mana Magana Cewar, "Malamai Dare fa Yayi Ni Kun Barni Sai Sauro Ke cizo na ....." "Maganin ka Kenan ni da Zan Samu Ganawa da Sauron Da Na Biyashi Yaƙara Cizon Naka!" Abdul-wahab ke wannan Maganar cikin tabbatarwa da Yusuf cewa So ya kai so. Yusuf yace, "lalala! Sakkayar tawa kenan?" "Au Namanta Sorry Abokina tuba Nake." gaba ɗai Mukayi Dariya. Daganan dae Mukayi Sallama Suka Barni Cikeda Tarin Farincikin Akan dai-dai tawar damukayi Da Abdul-wahab Wanda Zaƙin Soyayyar yasa Shaf! Na Manta da Maganar Dr Jabir. Yayinda Sukuma Can suke tafe Hira ta ɓalle Tsakaninsu. Yusuf Yace Masa "Shikenan fa Anyi mai Wuyar da kana Cewa bazaka zo ba." Abdul-wahab yaɗan Lumshe idonsa Cikin Mayenso Kafin Yace, "Banzaci Abun Zai Zo Mana da Sauƙi Har Hakaba, Ban kuma zaci Zata Sauko Haka da Wuri Ba." Yusuf Yadaki Kafaɗarsa Sa'annan Yace, "Ai Nagayama Kai kam Kadace Da Masoyiya Mai Sonka Da Gaskiya, gata kuma da Saukin Kai." "Tau Kuma Shine Zaka Nemi Ciremin Kafaɗa." Abdul-wahab Yafaɗi hakan yana mai Harar Yusuf ɗin. Hakadai Salon Hirar tasu Ta Kasance Har izuwa Sanda Suka Samu Kk Napep Zuwa gid. Acikin kk Napep ɗinma dai Hirar ce ta Yan Matansu Wanda Har Shima Mai Kk Napep yatsoma Masu Baki A Firar Sukayi tayi. Dama Ance "Hirar Samarin Bata Wuce ta 'Ƴan Mata! Hakanan Suma Yan Matan Hirarsu Bata Wuce Ta Samarin Su😅 ************* Da Sanyin Safiya Kuma sai ga Manyan Motoci Guda Kusan Biyar Suna Jerawa A Bakin Ƙofar Gidanmu. Mutanen Ciki Suka dinga Fitowa Wayanda Mafi Yawancin su Dattijai ne Sanye da Malun-malun (watau Babbar riga) Sai Tsirarun Samari Da Suka Dinga Fitowa da Kwalayen Biskit da Alewa da kuma na chacoolate Gefe ɗaya Ga Kuma Katin-katin ɗin Lemu da Na Ruwan Faro Sai Kwandon Goro Wanda Nakasa Tantance iya Adadinsu. Yayinda Anan cikin Gida Kuma Dady Sai Kai Kawo Yake Tayi. Inda Tuni Ankai Tabarmi An shimfiɗa Masu Sun Zauna Sai Waya Yakeyi da Amininsa Cewar "Ya'akayi Haryanzun Alhaji baka Karaso Ba Har Bakin Sun Iso." ban san Me Aka Cemasa daga can bangaren da Suke Wayar ba, kawai dai Ya sauke Wayar Yana ɗan Tsaki. Zuwa can Kuma saiga Dattijan Unguwar mu Suma Suna Shigowa Aka Soma Gaisawa Cikin Fara'a da Mutanen da Suka Zo. Cikin haka Shima Aminin Dadyn Namu Ya'iso Aka Shiga Musabaha Yana mai Bada Hakurin Rashin karasowar sa Da Wuri kan Cewar Mai Ne Yatsaya Yasha tau Kuma Yatarar da Layi A Gidan Mai. A Hankali Na saki Labulen windor nawa Wanda tun ɗazu Nake tsaye ina Kallon Abinda Ke Wakana Atsakar Gidan Namu, Na Zube Kan Kujerar ɗakin Nawa Ina ƙara tabbatarwa Kaina Cewa Iyayen Dr Jabir ne Suka zo dan Acikin Samarin da Suka Rakko Dattijan Naga Wani Mai bala'in Kama dashi Wanda ko Shakka Bana yi Ƙanin sa Ne. Tau Meke Shirin Faruwa ne? Readers ɗina Muje Zuwa........ Tareda Alkalamin FA'IK ✍🏻 [9/5, 9:14 PM] FA'IK: Typing....... 💻 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....19 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Tau Meke Shirin Faruwa Ne? Tambayar da Nasake yiwa Kaina kenan Ko Shakka bana yi Auren Na Ne da Dr Jabir ke Shirin Tabbata. Tau Amma Ya Makomar Shirin mu da Abdul-wahab? Tau Yanzun ke Kin isa Ki tunkari Su Dady ma Da Wannan Maganar, in ma kinje Kice Musu Meye? Haka nayita Karatun Wasiƙar Jaki wanda Ko ƙaɗan Nakasa Gane Bakin Zaren Ƙarshe dai Zuciyata Ta na Sanar min Babu Abinda Yakamace ni Face TAWAKKALI da Kuma barwa ALLAH Lamari na. Tau Amma Zan Iya Jure Rashin Masoyina Abdul-wahab? Tau ko Zakije Ki Gayawa Su Dady bakya Son Dr Jabir Abdul-wahab Kike So? "Never! Kai Bazan Iya Ba Wallahi!" Nafurta Hakan Afili Kamar Wata Wacce Ki Shirin Kamuwa da Hauka, Haukarma Sabuwar Kamu. Nayi Lamo Acikin Kujerar Zuciyata Naci gaba da Zantuka Masu Kama da TUFKA da WARWARA! Ƙarshe A Fili Nake Tambayar Kaina Tau Wai Ita Kuma Wannan Rayuwar haka take Cike da Kalubale? Ina Cikin Wannan Halinne Momy Tashigo ɗakin Nawa Fuskarta Cike da Fara'a Tasha Gayu Sai ƙamshi Take Bazawa Alamun dai Itakam Suna Cikin Farinciki Tadubeni Tareda Cewa, "Kije Falo Dadynku Nason Ganin ki Kuma Yayanki Yace Yana kiran Wayarki Baya Samu Lafiya dai Ko?" "Lafiya lau Momy Na Kashe Wayar ne Kawai." Nabawa Momy Amsa Ina Mai Ƙoƙarin Samo Wata Jarumta Inya Yafa Kaina ita dan Ɓoye Halin da Nake Ciki Anawa Ganin Iyaye na Basu Cancanci Wannan Rainin Hankali daga gareni ba kuma koma mey........ "Aiko Yakamata ki buɗa Wayar Sa'annan Ki Tashi kiɗan Watsa Ruwa Ki ɗan Kimtsa!" Momy ce ke Wannan Maganar tana Kokarin Juyawa Harta Kai Bakin Ƙofar Fita Tadawo gamida Cewa, "Yawwa Haryanzun banga su Hauwa'u da Laila Sunzo ba (ƙawaye na) kin kuwa Sanar Musu?" "Ban Sanar Musu Ba, Abinda Ni Ban Ma sani Ba Momy Sai dai Kawai Naga Mutane?" Nakarashe Maganar cikin Shagwaɓa "Ai kuwa dai Yakamata yanzun Ki Kirasu Ki Gayamusu." Momy tafaɗi Hakan Tareda ficewa daga cikin ɗakin Nawa. Batareda ta Bawa Wancan Maganar danakeyi Mata Muhimmanci ba. Sarai! Na Lura Momy Tafahimceni Amma Sai tai Kamar Ba ta ta Kaina Alamun Wannan Karon dai Bazata Saɓu ba. Ganin Tunanin nawa ba mai Karewa bane Najanyo Hijabina Nasa, Kafin Na Nufin Cikin Falon Su Momy Inda Na Samu dady Shima Yaci Ado da Babbar Riga Shida Amininsa Suna Zaune Momy tacika Gabansu da Abincuccuka Kala-kala Ga Kayan sha nan Kala-kala Sai Tauna Naman kaza Sukeyi Gefe ɗaya Dady Nata Wayoyinsa Ga Alama Kuma Yan Uwa da Abokan Arziki Yake Sanarwa. Nasamu Gefe na Rakuɓe Na Zauna Cikin Yan kewar Buri Da Ƙara Tabbatar wa kaina Auren Dr Jabir ya wajaba Gareni kamar Yadda Rasa Abdul-wahab Ya wajaba Gareni. Cikin Sanyin Murya Nagaida Aminin Dady Ya'amsa Min Cike da Fara'a Kafin Ya sanyamin Albarka Tareda ƙara Gayamin Lalle Na tabbata Ƴar Halak! Tunda Fidda Surutun Mutane Kuma Kowa Yaga dangin Dr Jabir Yasan Nazaɓo Irin Albarka Zan Kuma Shiga Dangin da Yadace. Kwata-kwata Bana wani Jin daɗin Wayyanan Kalaman na Aminin Dady Hasalima Wani Bakinciki ne Ke turnuke Zuciyata saidai Ina Ƙokarin danne wa ne. "Yawwa Kina Ji Ba?" Naɗago Na Kalli Dady Sanda Yake Faɗar Hakan Bayan ya kamalla Wayar da Yakeyi Yakuma Ajiyeta Gefe. Yaci gaba da Cewa, "Kamar dae yadda kika gani Iyayen Dr Jabir Sunzo Harma Munkai Karshen Magana Nan da Sati Biyu Insha'allah Za'a ɗaura Auren ku." "Sati Biyu????" Cikin Wata irin Kiɗima Na Furta Hakan. "Eh Sati Biyu Saboda Shi Jabir ɗin Wata ɗaya Yarage Masa Zashi Ƙasar Indiya Ƙaro karatu Akan Wani Kwas! Kamar Yadda Suka Faɗa Tau Suna so Ayi Komai A Kammallah Kafin Lokacin Kuma Nima Haka Yayimin." "Amma Dady Sai Kace Kun Gaji dani Sati Biyu Fa." Hawaye Suka Ɓallemin Dama Mai Neman Kuka ne Anjefe Shi da Kashin Shanu Dady Yamurtuƙe Fuska Kafin Yace, "Dubi Wani Sakarci Kuma? Wane Irin Gajiya kuma Kin taɓa Ganin Nagge ta Gaza da Ƙahon ta? Akwai kuma wata Ƙauna da zamu nuna maki Wacce Ta wuce Mu sadaki Izuwa gidan Aurenki Ikram?" Hawaye Nacigaba da Gowslow A Fuskata Nace, "Amma Dady..." "Amma me? Kinga Ikram Hakan da Akayi Shine Dai-dai, Insha'allah Babu Abinda Zai Gagara duk Abinda Kike so Kije Ki rubuto Zanyi Maki Kai Har kayan ɗaki Anjima Kishirya Muje Ki zaɓa Ina fatar Kinji?" Nagirgiza Masa Kaina Wanda Haryanzun Nakasa Daina Hawayen Wanda ni Natabbatar Bawai dan Ance Sati Biyu Bane. Yace, "Yawwa Karɓi Ga sadakin Ki Naira dubu 50 Anjima Kuma Mata Na Nan Zasu Kawo lefe." Nakara Girgiza Kaina "Dady Kawai Kavar Kuɗin A Hannunka Ni Ba'a bunda Zanyi dasu." Dady yace, "Jeki Ki Kaiwa Momynki Can Ku Shawarta Abinyi dasu, Ni Ta Wajena Ba'a bunda Zai gagara Insha'allah dan Nadaɗe da Shirya wa Wannan Ranar tunda Dama Nasan Tana Zuwa." Nasa Hannu Nakarɓi Kuɗɗin Kafin Namike Ina Cewa, "Tau Yayi." haka Hawaye na Basu Tsaya ba. Dady Yace,"Yawwa ALLAH yamiki Albarka." Koda Nafito Tsakar Gida Ba Kowa bansan Ina Momy taje ba Dan Haka Nanufi Dakina Ina Zuwa nayi Watsi da Kuɗin A Tsakiyar Gadona. Nazube ƙasa kafin Na Fashe da Kukan da Ni Kaina Bansan dalilin sa ba, Amma Wani Sashe Na Zuciyata Yana Rayamun Cewa Halin Ko Inkula Ne Dasu Dady Ke Nunamin Akan Damuwa ta Ko wanen Su Bai damu da Ya lallasheni ba. Shine Yake Sani Kuka. Kafin Kace Kwabo Gidamu Yacika da Makwabtanmu Da Sauran ƙawayen Momy. Sai Saukewa Da ɗorawa Suke dan Ganin Abinci Yawadaci Kowa. Momy kam sai kai kawo take Cikin Farinciki Ba'abinda Ya shalleta Dani. Zuwa can Sukuma Sai ga Su Hauwa da Su Laila harda su Zubee Kawayen Amana. Inaga dae Momy ta kirasu Wannan ma dai Yaƙara tabbatarmin da Cewa Momy A wannan Karon Sunɗauki Mataki A kaina Ne Kuma Suna Sane da Halin da Nake Ciki Musamman ma Momy dai. Zuwan su keda Wuya Ɗakina Yakamace Da Shewar Ƴan Mata Kafin Suka Tasani Gaba da Surutu dolena Nayi Wanka Nayi Shirya Cikin Wani Matirial Kalar Purpul Sai Wani Kyalli Nake Kamar Yaune Amarcin. Duk Suka ɗauka "Haba Koke Fa? Amma Kin Zauna Mana kamar Wata Wadda Aka Kwanto Daga Bakin Kura?" Daganan Laila Taɗauko Turare Tana Fesa min. Nature ta Ina Cewa, "wai meye Hakane?" duk Suka Kama Baki Kafin Hauwa Tataso daga inda Take Zaune Tace, "Bani Nan! kin taɓa Jin Wanka Yacika Ba Turare." Hakadai Sukaita Min Iskanci Iri-iri Kamar Yadda Kukasan Kowayenne Kawaye Nayiwa Ƙawarsu. Su A Zaton su Kawaici ne Nake. Gidan Yaƙara Kacamewa ne Sanda Yan Kawo Lefe Suka Iso Wata Daga Cikinsu Taƙarkare Iya Ƙarfinta ta Rangaɗa Guɗa Aaaaayirrrrrr! Nan Fa Aka Shiga Ina Aka saka da Su Ana Ta Jere Musu Abinci Iri -Iri. Da Abubuwan Sha Kala-kala dai-dai Lokacin Wayata taɗauki Kara Najawota Ina Mai Ƙokarin Tantance Waye Yake Kirana. Sunan DR. JABIR! Nagani Yana ta Yawo Kan Scereen ɗin Wayar Nayi Kamar Bazan ɗaga ba Sai Kuma Naɗaga. Duk Yanda Naso Yimasa Shariya Sai Abun Yagagareni Saboda Shiɗin Wani Irin Mutum ne da ba Kowane irinsa ba. Muka gaisa Cikin Mutumci haryake Sanar dani Naji Sati Biyu da Aka Ajiye? Ai kuwa kamar Jira Nakeyi Na Hau Bakina Ina Cewa Yazasu Sa sati Biyu Sai Kace Wacce Aka Gaji da Ita? Shi Sai Abun Ma Yabashi dariya Shine Yake Tambaya ta "Tau Acikin Nida Su Dadyn Waya gaji dake?" Ni Kaina Sai Lokacin nagano Wautar Maganar tawa Sai Kuma Nayi Shiru. Yace, "kinga? Wannan Ba Wani Abun Damuwa Bane. Ai Angayama ki Uzurin da Yasa Akayi Hakan ko?" Nagirgiza Kaina Kamar Ina gabansa. Daga can Yace, "Banji Kince Komai Ba." Nace "Eh Dady Yagayamin." "Tau Kingani So Nake Ayi komai Cikin Tsanaki, Yanzu Hakan Abubuwan Sun Haɗe mi Ina Ƙokarin ganin Yanda Zan tsara Su Bayaga Wannan Akwai Wani Muhimmin Abu Da Yadace Ingayamaki Duk-da bansan Yazaki Karɓeshi ba Saboda Na Sanar Maki A kurarren Lokaci amma Ni A Nawan Tunanin Ko Yanzun Ba wata Babbar Matsala bane." Yaɗan Numfasa Kamar Wanda ke Shakkar Abinda Zai Faɗa Kafin Yace, "Khaleesat Ina da Mata Harda ɗa Ina Fatar Idan Kikazo Zakuyi Zama na Fahimta da Juna." Wani Irin Faɗuwar Gaba Yariskeni Wanda Sai da Na Zauna kan Kujera Ba tareda Na Shirya Hakan ba, Kafin na lalubo Yawu Acikin Bakina Na Lashe Laɓɓana Da Suka yi Bushewar Nan take Nace, "Kana da Mata?" Yace, "Bafa Wata Matsala Maman Ashraf Tana da Hankali kuma Zaki Sameta Mai Saukin Kai Nima Kuma Zanyi Adalci A Tsakanin ku Abunda ɗai Nake So Ga........" "Haka kake Zato ba? Haka kuma Mahaukacin Tunanin ka yake Saƙa ma Macuci Kawai!" Tafaɗi Hakan Tana Kokarin Fisge Wayar dake Hannunsa Yakalle ta Amamakance Yana Cewa, "Ke Kina Hauka ne ko...... "Dif! Naji wayar taɗauke Namike Tsaye Ina Karanto Innalillah! duk yan ɗakin Sukayo Caaa A kaina Lafiya Wanda ni Kwata-kwata Ma Na Manta da Cewar ba Ni kaɗaice Aɗakin Ba. Wanda A dazun Kowa harkar Gaban sa Yake Innalillahi da Sukaji Ina Karanto wa ne Yadawo Da Hankalin su Kaina. Dole Nayi Murmushi Nace, "Kai Ba'a Komai fa Ni dashi ne Kawai." Gabaki ɗaya Suka Sa Shewa Gamida Taɓewa Kafin Hauwa Tace, "Lalle Dr Nan Ƙarshe ne." Nan Fa suka Shiga Dariya ta. Yayinda Nikuma na Sulale Nashige Toilet Ina Rufe Kofa Wani Kuka Yazomin Nikam Wace Irin Rayuwa ce Hakane? Meke Shirin Faruwa Danine? Meyasa Dr Jabir Zai yaudareni Yaƙi Gayamani Cewa Yana da Mata sai Yanzun? Shin Su Dady ma Sunyi Bincike Ko Waye Shi? Ko Kwai Sun gaji dani ɗinne dagaske Mararraba Suke Biɗa Dani??? Muje Zuwa Readers ɗina...... [9/5, 9:14 PM] FA'IK: Typing....... 💻 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....20 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Wayyanan tarin tambayoyin Naci gaba da yiwa kaina Kuma Narasa Samun Amsar ko guda ɗaya Acikin su tau mezanyi? Kuka? Fita Neman wanda zai bani Amsar su? Inna Fita ina zan Sameshi? Dan haka sai nazaɓi Nayi Kukan Ko Sanyi Naji Azuciya ta. Sai dai dole ne Innemawa kaina Mafita domin duk yanda takai Takawo Nice zan kwana cikin Matsalar duk yanda wani zai koka min Baikai nawa kukan ba! Inaji Araina wannan Karon Ma zansake Wani Yunkuri! Zan sake wata Sadaukarwa! Zan Sake Wani plan Karo Na ƙarshe Matuƙar Bai Kuɓutar dani Ba, tau Na Hakura Zanbi wannan Rayuwar duk Yanda ta zomin Kawai. Zuwan Wannan Tunanin Acikin Zuciya ta, Sai Yasamarmin Salama Sosai Naji yakwashe Kaso mafi yawa na ƙuncin da zuciyata take ciki, Nasamu Wani kwarin Gwaiwa A yanzun dan haka Nafito Toilet ɗin da Wani Irin Karsashi duk-da Kuwa wata Zuciyar na Tsoratar dani Kan Wannan Plan Nawa Amma wacce take Son Abdul-wahab So Na hakika Tana kore Wannan Tsoron Kuma tana ƙarfafa Tareda nuna min Cewa Rayuwar Aure babu Abinda Yafi Dacewa Acikinsa Face Samun Wanda Kake SO! Sanda Nafito Aka Yayyameni Da Cewa, "Ina Kika shiga dangin Ango Yan Kawo Lefe Suna ta Neman suga Amarya Amma Babuki ba Samatarki? " Nadubi zubee wacce Ke Maganar Tareda ce mata, "Mesuke Yiwa Gaggawa? In Sukayi HAKURI Nanda Sati Biyu Ai kuma Ina cikin su Tsamo-tsamo sai sungaji da ganina." Faɗar hakan da Nayi duk sukayo Caaa Akaina "Eyeeeee! Yar Is...(Haka muke ɓacin/zagin Juna in Muna jin shaiɗaincin mu)Watau dai Nafahimci Yarinyar nan Kin Taki wani Abu ko?" Nakoma Kan Kujera Na zauna Ina kuma dafe Kaina Tareda Cewa, "Kinga Hauwa Dan ALLAH ni ku ƙyaleni da Wannan Iskanci naku Wallahi kaina ke Ciwo." Laila Ta Caɓe, "Aikuwa Ciwon Nan ƙaryarshi tasha ƙarya dan Kuwa Dr Yafi ƙarfin Shi?" "Tau ke kika Sani Ciwo kan Aiken Dr ɗin ne?" Hauwa Ke faɗar hakan Cikin Salon Tsokana. Itama Zubee Tace, "Ah tau, duk Sanda Suka Haɗu muka kai masa Ita Ai sai ke Neme shi Ki Rasa." "Kuma fa Hakane." Laila ke Faɗar Hakan Tareda kama Haɓarta Alamun Gulma. "Wani Aikin Sai Likitanmu." Hauwa ce mai Wannan Maganar Kafin duk Suka ɗauke da Shewa da kuma Dariya Suka Taɓe Har Suna Faɗomin A jiki Namiƙe Ina Cewa, "Ni kunga Karku jimin Ajiki gara ku Ƙashin ku Yana da Ƙwari yan Islamiyya Kawae." Nan ma Suka yo Caaaa A kaina. Haka dai Muka Yini Da Ƙawayena Muna ta Caɓta! Wanda Mafi Yawanshi Faɗa yafi Yawa. Nidai Sai ce Musu Nake Sun ɗau Bashi ALLAH kaimu Auren wata daga Cikinsu Sai Na Fanshe Iya Shegen da Suka min Nam dai dariya Mukayi. Sai gabda Magariba Kowacen Su Tayimin Sallama Suka wuce Da Alkawalin dawowa jibi dan jin Tsare - tsaren da Zamuyi Na Buki. Hakanan Ma Gurin Momy duk Bakin Sun Watse, Sai Ƴan Tsiraru Makwabtanmu Da Basu Samu Shigowa ba Saboda Ayyukan Gida Da Dai sauran uzurori. Sune Ke Shigowa Yanzun Suna Ganin Lefe Wanda Sai da Nafito Arwallar Magrib Na Hangi Akwatan Anjerasu Sai Ƙyalli Sukeyi. "Ba Shakka yayi Kokari, Amma Gaskiya Dr jabir bazan Iya Auren ka ba. Shiga Tsakanin Miji da Matarsa harda Albarka ɗa Ai Matsala ce. Gara ke Ashigo A sameki da Mijin da Ace kece kika shiga. ƙari ga haka ma Ni ina da Jarumi na, In Ba Abdul-wahab ba ina jin sai Rijiya, Ko Ya suka ƙare da Matar tasa? Kila ta Rotse Masa Kai, hhhhh" Zance zucin da Nake tayi kenan A Lokacin da Nake Arwallah. Ina gamawa Na Nufi ɗakina dan Yin Sallah Nabar Makwabtanmu da suka Shigo A Lokacin sai ɗaga kayan Suke Suna "Kai!! Masha'allah! Wallahi Yayi Ƙokari ALLAH yabasu Zaman Lafiya.". Yayinda Momy take ta Murmushi. ********* Suna Cikin Kafteria ɗin Makarantar su A Zaune Shida Abokan Karatun sa kowanen su kuma Nakaiwa Cikinsa Abinda Yasiya. Wani Shinkahwa da Miya ne Wani kuma Kwai da kwai(Awara) ne da dankali dakuma Kabeji Wani Kuwa kok ce da Bons sai Donoth. Abdul-wahab Na cikin Wayanda Ke Shan Kok da Bons da kuma Donoth. Dama Shi ba Ɗabi'arsa bace, Cin Abincin Waje wannan ma dai dan Sun fito ne da Yunwar da Aka san kowane ɗalibi Nafito wa da ita in Aka tashi daga Skull ko aka kammallah Lakca ga Masu karatu A manyan Makarantu Kenan. Tj ne yadubesa yana Cewa, "Wai Saura Wata Nawa ne bukin Abokin ka (yana nufin Yusuf)da Kake gayamuna Za'ayi?" Abdul-wahab Yaɗan kora Kok ɗinsa kafin Yadubesa Yace, "Wata fa? Kace Sati dai." Tj Yace, "A'a Kace Bukin ma Yaƙarato, Ai gara ma Haka dan Kar yazo Mana Gabda Exam ɗinmu Ko Ma Ana cikin Yinta." "Wallahi Kaidai Ai ni zance Haka ma." Abdul-wahab Yafaɗi Hakan Yana Mikewa gamida Sa Hannun Cikin Aljihunsa Yazaro ƴar dubu daya yana mai Mika ma Mamallakin Wurin Yace, "Kacire Har kuɗin Wannan." yafaɗa Yana nuna Tj. Bayan Ya karɓi Canji Yadubi Tj Tareda Cewa, "Ya? Zamu tsaya Mujira Lakcan Wancan Karfar Malamin Ko mu Fice?" Tj Yamike Yana Goge Hannunsa da Tissue gamida Cewa, "Allaji Kawai Mutafi Abun mu Ma kaura dashi Wani Satin, Yau Ba wanda Nabaro A shago kaga kuwa ai Yakamata in koma in buɗa." Tboy Yasako Baki A Cikin zancen nasu da Cewar, "Kaji Daher ba Ai Karatun Naka ma Shagon Naka ne Rufin Asirinsa. Bro Ware Kawai Kaje Abinka Ka nemi Kuɗi Karatu A Ƙasarnan Ai Sai da kuɗi." "A Lafiya dai Nawan! ALLAH shi kiyaye min Kai." Tj ke wannan Maganar Cikin Salon Gayunan Na Yan Skull in An Haɗu guri ɗaya Ana Cabta. Kafin duk Wurin suka ɗauke da sowa irin Wacce aka san Samari da Ita. Dahaka Dai Sukayi Sallama Da Sauran Abokan Nasu Suka Fito Get ɗin Makarantar Tareda Samun Kk Napep dan Tayi dropin Nasu A gida. Acikin kk Napep ɗinne Abdul-wahab Yazaro Wayar sa dan Yakira Shalelen Tasa(Khaleesat)dan Yagayama ta cewa yau Zasu Zo Hira.. ********** "Maman Ashraf Kina Hauka ne? Meke Damunki ne?" Dr Jabir ke Faɗin hakan Yana mai Ƙokarin Maida Wayarsa Aljihunsa sai dai ina? Tuni Ta shamace Shi ta Fisge Wayar Ta watsa ta A bangon ɗakin Ji Kake Tatsatsatsa!!! Wayar tayi ɗai-ɗai Ko wane Yanufi Wani Muhalli. B3 yayi gefe haka marfin Wayar Shima yayi nasa Gefen. Tas! Tas! Kakeji Saukar Maruka A Fuskarta Yana mai ci gaba da Nuna ta Cikin ƙunar Zuciya Cikin ɗaga Muryar sa yana Cewa, "Maza kifece daga ɗakin Nan kafin In buɗa ido dan Wallahi Zan iya kakkarya ki." Maman Ashraf ta Durkushe Sai kuka Take Mai cike da Sauti tana Tunanin Matakin ɗauka. Yayinda Shikuwa Yanufi Wayar sa yana Ƙokarin haɗa Kanta. Wayakam Taci Screen. Sai ganin Yayi Tamike Harta kai ƙofa Kuma Tadawo kafin ta soma Cewa, "Zanfita ɗin ba'ama A iya ɗakin ba, har Gidan Gaba ɗaya Kai Harma Rayuwarka duka Dr, Amma Sai Kabani Takarda ta dan Inba Munafunci Ba Tayaya Za'a Auren ka banji daga Gareka ba sai A dangi? Hummm!" tayi Shiru tana mai goge jini dake ɓulɓulowa Abakinta dan ba Kaɗan Yayi Mata marin Ba. duk Jar Fatar ta Shatin Yan yatsun sa Ne. Abinka da Fara Fata da basa Rena Abu. Tasake dubansa karo na Biyu Abinda Bata iyayi Ada Amma yau Saboda halin KISHI taji Bata Shakkar Hakan. Kafin Tasoma Cewa, "Dama ai sai da Ƴan Uwa na Suka Gayamin Matar Cushe bata Daraja Amma Naki kula Maganar su, gashi kuma Naga SAKAYYAR Zancen Nasu Domin dai Banga Abinda Narage ka dashi ba. Duk dai domin In gamsar da kai Amma da yake dai 'NAMIJI ƘANIN AJALI ne. Sai da ka tabbarmin da Hakan kuma Wai Ka kasa gaya....." "Tau wai ke Waya Gayama ki Zan ƙara Aure ne dan Bana Sonki Ko kuma Dan Kin gaza Kyautata Tamin ne? Shi Aure Sunnar Manzo Rahma ne kuma kamar yadda Yayi mana Koyi Muyi Na Farkon Hakama Ya Sunnan Tama na Yin Na biyu ko Uku kai Har Huɗu ma Sa'anan ya horemu da amma in mun san Zamuyi Adal....." Maman Ashraf Ta dakatar dashi ta Hanyar ɗaga Masa Hannunta, "Kaga Mal ni Bana wani son Wa'azinka Kabani Takarda ta inɗare Inbar Maka gidan ka Harma da Rayuwar ka, Wa'azinka Kuwa In Amaryarka Matar So Ta'iso Sai Ka soma yi mata Tun daga Daren da Aka Kawo ta har Yauma Tanadi wannan Matsalar kune ba tawaba." Dr Jabir Yayi Saƙare Yana Kallon wai Yau Maman Ashraf ce ke Gabansa da irin Wannan Siffar Tana Gayamasa Wayyanan Baƙaƙen Maganganu Kawai Saboda tsabagen KISHI Abinda In kafin Hakan ce Tafaru Aka Gayamasa Bazai Yarda ba Saboda kallon da yakeyi Mata Na Ko Farce (yatsa)Aka Sama ta Abaki Bazata Ciza ba. Sannu A Hankali Yatako Zuwa Inda Take Tsaye, Yayinda ita ma taja da baya Saboda yanda takejin tsanarsa A Yanzun ko Ganin sa bata Son yi Balle kuma Ya raɓe ta. "Ki Tsaya ki Saurare ni Maman Ashraf Shifa Wannna Ab....." "Wallahi ni Yanzun babu wani yare da zan Fahimta daga gareka Illah Yaren Ka Sawwake min Auren ka Inje ni gidamu Shine Kawai." Ta faɗi hakan tana mai ci gaba da Zubar da Hawaye. Yamika Hannu da Nufin Riƙota Tareda Cewa, "Naji Zan miki Abinda Kike So Amma...." "Amma me? Kanka Tsaye kawai Kamin Abinda Nake so Shine Kawai HALLACIN Da Zakayimin A Yanzun." Kafin taƙara ja da baya Tana Nuna sa da Yatsa "Kada kataɓani Banaso!" Shi Sai Abin Yadaina Ɓata masa Rai Yakoma Bashi Dariya. Ta Lura Sarai Dashi Dan Haka Sai Kawai Tajuya tabar ɗakin. Yana kiran ta Amma Ina Makullin Motarsa dake Falon Tafiga Tafice daga gidan. Sai jin Tashin Motarsa Yayi koda Yafito har maigadi Ya wangale Mata Ƙofa Tafice A Matukar Gudu wanda ke bayyanar da Irin Ɓacin ran da Take Ciki, Yakuma Sani Sarai! Irin Wannan Tuƙin datake yi SAI ALLAH! Dan dama can Ba wani kware wa tayi da jan motar ba dan bai daɗe da koya mata ba dan haka da hanzarin sa Yaƙaraso Yana yiwa Maigadin Nasu Faɗa Kan Mezai sa Yabuɗe mata Get ɗin? Maigadi Yarusuna yana Cewa, "Ayi Hakuri Yallaɓai Naɗauka Fitar Arziki ce Shiyyasa Na buɗ...." "Fitar Arzik? Haka Ake Fitar Arziki A garinku?" Dr Jabir yatare sa da Faɗin Hakan Cikin Ɓacin Rai! Kafin Yayi Tsaki Yajuya Izuwa cikin Gida Yana Neman Makullin Mashin ɗinsa Wanda In yayi Sha'awa Yake Hawa ya zaga Gari. Kaitsaye Yabawa Mashin ɗin Wuta Yabi Sahun Maman Ashraf. Tau fa!🤔🤔 Ƙaƙa ƙara ƙaƙa tau Yaza'a Ƙerke ne Wai? Muje A Chapter ta gaba my Readers..... Nayi Gaba Tareda Alkalamina FA'IK ✍🏼 [9/5, 9:14 PM] FA'IK: Typing....... 💻 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....21 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Gwaggo Halima Tana Zaune Tsakar Gida Nama Take Yankawa Safiyya Na Rike Mata Suka Ga Mutum Yafaɗo Musu Acikin gida Kamar Wacce Aka Cillo Haka ta zube Gaban Gwaggo Halima tana ta Rusar Kuka Kamar Ranta Zaya Fita. Gwaggo Halima da Safiyyah Sai da Suka Firgita Gwaggo Halima Tadubeta cikin firgici tareda Cewa, "Asiya Wannan wane irin Hauka ne kuma? Ki Faɗo ma Mutane gida A irin Wannan Yanayin?" Gwaggo Halima tayi shiru tana mai ci gaba da Kallon Maman Ashraf ɗin. Dama tayi Tunanin hakan zai Faru tunda taji Cewa Ankai Lefe nan tasan A Rina wai An saci Zanen mahaukaciya! Ganin Kukan Yayi Yawa Tana Neman tara Mata Mutane Yasa Gwaggo Halima Ta Tsawace Ta, "Wai ke Kanki ɗaya Kuwa? Wallahi Kimin Shirun da Bakinan naki tun kafin Na Taso na tattakaki?" Itakam Safiyya Ta rafka Uban Tagumi Tana Aikin Kallon Yayar tata Cikin Zullumi da Taraddadi Tanaji A Ranta Lalle Ya Jabir Bai Kyauta wa Auntyn Tata ba, dan haka Cikin Kasalar Jiki Ta taso Izuwa ga Maman Ashraf ɗin Tana mai Share mata Hawaye Kafin Tasoma Cewa, "Aunty Kiyi Hakuri Dan ALLAH Komai Yayi Zafi Maganin sa ALLAH!" Izuwa Yanzun Tarage Sautin Kuka Sai Gumji Takeyi. Dan Haka Safiyyah Taja Hannunta Zuwa ɗakin Gwaggo Halima tana mai ci gaba da bata Baki Suka samu guri Suka Zauna. Itama Gwaggo Halima wanke hannun ta tayi daga cikin Naman kafin Taduba Girkinta Taganshi Yana Ci Gaba da Turiri! Dan haka Itama Sai ta nufi Ɗakin Kafin Ta zauna Gefen Gado Tana Mai Kallon su Safiyyah Na Aikin Rarrashin Maman Asharaf. Taɗan Numfasa Kafin Tace, "Banyi Tsammanin Wannan Rashin Hakuri daga gareki Ba Asiya, Kin Manta shi Namiji Mijin Macce Huɗune Halan? Sannan Kin mance da Irin Tarbiyyah da Muka baki? Meye Abin Mai Zafi Aciki?" Cikin Sheshshekar Kuka tace, "Amma Umma fa Kina Ganin Mutumen Nan Bai gayamin Batun Auren nan Sai Acikin Dangi Da'aka kai Lefe Naji Sannan Kinga yanda Yake Rawar Kai Akan ta Tun Kafin ta Shigo? Sannan Dan Allah menene Banayiwa Baban Asharaf da zai Sakamin da Wannan?" duk Su gwaggo Halima Suka Nutsu Suna Saurarenta. Bayan ta tsagaita Gwaggo Halima Ta musƙuta daga Inda take Kafin ta Soma Cewa, "Naji duk Abinda Akai Maki Amma Kin Manta Shi Aure Sunna ne, ai ba dole Sai Ka ɓata ma Namiji ko Ka kyautata masa Zaisa ya Ƙaro Aure ba, a'a Shi Aure Kawai Sunnah ce Yanda Nagayama ki In kin Manta In Tambeyeki Ma'aiki (S A W) Matansa Nawa? Sannan Wacce daga Cikin su Kikaji Tayi Kishin Hauka? Wannan ma Ai Abun da kike Shi zai bawa Amaryar Damar Mayarda ke Bora Acikin gidanki Hakanan Shima Maigidan yaji kin Fita Ransa. Kishi Halak ne! Kuma Yana da Azaba Nasani, Tau Amma In Ka Iya Masa Sai Kaci Riba in Kuwa Baka Iya sa ba Sai ka Kwashi Asara. Dan Haka ki Nutsu da Kyau Kijini." Gwaggo Halima tayi Shiru tana ƙara muskutawa daga Zaunen da Take yayinda Maman Asharaf da Safiyyah Suka Ƙara Nutsuwa Suna Sauraronta Duk-da Kuwa Kanajin Ajiyar Zuciyar da Maman Asharaf keyi Akai-Akai. "Yanzu ne Yakamata Ki ƙara ɗamarar Kusantar Mijinki da kyautatawa Harma wacce Bakya yimasa Ada Sa'annan Kizama Macce Mai Fin Ƙarfin Fushin ki Akan Abinda Yadangaceshi Ko Kishi Yarki. Wayyanan Abubuwan da Na faɗamaki (gaya maki) Bazasu yuwu ba Saikin Jajirce Kin kuma Jure Wani Malami Mai hikima yana Cewa, Namiji Yakan Kara Aure Inji Yaji daɗin Auren Saboda Yaƙara Samun Jin daɗin Auren Hakanan In bai Samu jin daɗin Auren ba zai ƙara Aure dan Yasamu Jin daɗin dan haka KISHIYA Tilas ce Ga Ƴa mace. Dan haka ina mai nusar dake tun wuri Kije kigyara Gidanki tun Kafin Wata tashigo Tafiki Tasiri Acikinsa dan dai kinga Bakida Wani Yaƙinin Auren Wanda Bazai Maki Kishiya ba, in kuwa Hakane Gujewa Kishiyar Bashine Mafi Muhimmanci ba A'a tsayawa Kiyi Tunanin Abinda Zai ƙara maki Martaba gurin maigidanki da Kuma Kishiyar taki Amma Ba wannan Haukan da Babu Abinda Zai Hana illai yaja maki Rushewar daraja." Haka dai Gwaggo Halima tasa Maman Asharaf da Misalai da Nasihohi Irin Nasu Na Dattijan Mata dakuma Suka Cuɗanya da Rayuwa Suka San Menene Rayuwar. Wanda Babu Shakkah Misalan da Nasihohin Sunyi Tasiri Matuƙa Akan Maman Asharaf harma da Safiyyah ƴar taya Yayarta KISHI kai Harma da Dr Jabir da tun ɗazun Ya'iso Gidan Kalaman da Yaji Gwaggo Halima Nayiwa yarta ne Yasashi Jan burki Yatsaya tsakar gidan Har' A ransa Yana ƙara Jadadda Albarkar dake kwai Cikin Auren Ƴar Babbar Gida ƴar Dattijan Mutane da Suka San Abinda Sukeyi. Ƙaurin Da Gidan Yacika dashine Yatabbatarwa da Su Gwaggo Cewa Miyar Tasu dai ta ƙone, dan haka Cikin Hanzari Gwaggo Halima tafito da nufin Zuwa Kitchin ɗin Wanda tsirit Yarage Tayi Tuntuɓe da Dr Jabir Dake nan Tsugunne Bakin Ƙofar Tayi Hanzarin Cewa, "A'a Subhanallah! Jabiru zuwan Yaushe?" Ta leka Cikin ɗakin gamida Cewa, "Ke Safiyyah zo ki kawowa Yayan naku Abun Zama." Kafin Takaɗa kai Zuwa kitchin Tareda Cewa, "ina Zuwa Jabiru Miyata ce Ta ƙone." Shikam Dr. Jabir Duk Yawani Ƙara Mutuwar Zaune Saboda Girma da Darajar da Yaƙara Ganin Gwaggo Halima da Ita. Yana ƙara ji A ransa Cewa Samun irinsu Gwaggo Halima yanzun sai An tona, dai-dai lokacin ne kuma Safiyyah ke ƙoƙarin Shimfiɗa masa Tabarma Nan gefen Ƙofar ɗakin. Kafin Tagaidashi Ta Nufi Ɗaki Inda Tabaro Yar Uwarta Sai dai Kafin tashige daga kitchin Gwaggo Halima ta kwalo Mata kira Kan Cewa ta Kawo Mata Allayahun da Ta Yanka Azuba Cikin Miyar. Dan Haka taɗauki Robar Nama da Allayahun Ta Nufi Gurin Gwaggo Halima Hakan Yaba Dr Jabir Damar Miƙewa Yanufi Cikin ɗakin Yasami Maman Asharaf ta Rafka tagumi Haryanzu takasa Tsaida Hawayen da ke Zubo Mata Duk-da A Yanzun Tana jin Tasamu sassauci da kuma kwarin gwaiwar cewa Zata iya Zama da Mijinta Cikin Juriya dakuma Jajircewa Kan....... Rusunawa Yayi Agabanta yaɗora tafukansa Akan Cinyoyinta Kafin Yakira ta Cikin Sanyi Muryar da inba Dagaske kayi Bazakaji ba. Maman Asharaf taɗago kai tana kallonsa Batareda ta'iya Amsawa ba, Tasani Tana son Mijinta Shiyyasa ma take Matuƙar Kishin Abinta Amma Gwaggo tace mata Hakan da Takeyi Shine Zubar da ƙimarta. Tau meye mafita Kenan Gareta? HAƘURI! Wani Sashe Na Zuciyarta Ka gayamata Hakan. Kwata-kwata tayi nisa daga duniyar Mutane Tunani takeyi Kawai Yayinda Shikuma Dr Jabir Yayi mata Zuru da Ido Yana Kallo. Shikanshi Tunanin yakeyi Yana kuma Gaya masa Kansa Cewa Zaiyiwa Maman Asharaf Kishiya ne Kawai dan shiɗin Yana Son Khaleesat bawai dan Yagaji da Maman Asharaf ɗin ba ko nufin Wulakanci gareta ba. Tau. Kowanensu dai da Abinda Yake Saƙawa Acikin Ransa Amma da zaka Shigo Ka Risƙesu A yanayin da Suke zaka Zaci wani batu sukeyi Ko suke tattaunawa A tsakanin su. Kuma an rasa mai ƙwarin gwaiwar da Zaiyiwa ɗan uwansa Magana Wannan Kenan........ ********* Tunda Na sanarma Da Abdul-wahab Halin da Ake Ciki duk Yabi Ya Sukurkuce Yayi Zuru Yarasa Maganar Cewa, Yayinda Nima Nayi Shiru Cikin Tsura Masa Ido da Tunanin Ko in Sanar Masa da Matakin da Nake Shirin ɗauka? Tau Amma In Bai Bani goyon baya Bafa? "Kai! Shima bai cancanci Jin Wannan Plan ɗin ba dan Ba Shakkah Shima Ina Son In Auna Irin Zurfin Son da Yakeyimin dan Haka Shima Bari Na kawo Na Mujiya Na Zuba Masa, dan Inga Iya Gudun Ruwan sa Shima." Kawai Sai Nazaɓi Inyi Shiru Nima Yayinda Yaɗago Idanuwan sa Jajir dasu Yana mai kallona Kamar Wanda Ya Warke Daga Makanta A yau ɗinan Kuma Yasamu Sa'ar Ganawa da Abun da Yadaɗe Yana son Gani. Kafin wani irin Tauhidi Yazowa Abdul-wahab Cikin Alhini Yaɗan Motsa laɓɓansa Yasoma Cewar, "Tamu Ƙaddarar Kenan Khaleesat, Muyi Hakuri In Har muɗin Rabon Juna ne duk Runtsi da Wahla Zamu Kasance Amatsayin Mata da Miji idan Kuma Har muɗin Ba rabon Juna Bane Tau duk Wani Ƙokarin da Zamuyi Baza mu taɓa Zama Mata da Miji ba Saboda haka Abinda Kawai Yakama cemu Hakuri da Adu'a." "Amma sai inga Kamar Baka sona kamar Yadda ni Nake Mutuwar Sonka Abdull Bansan Meyasa ba? Ko dan kaga Nacika Sonka da Yawa ne? In ma Haka ne tau Ka......" Abdul-wahab Yakatse ni Ta hanyar ɗagamin Hannun Kafin Yasoma cewa, "In ma Ina Sonki Khaleesat Sai Kuma Nagoyi Bayan Ki Saɓawa Iyayen ki? Da bakin ki Fa Kika cemin Dadynki Har Yasa Rana Lokaci kawai Ake Jira ko ba haka kika ce Ba?" Nagirgiza Kaina Gamida Goge Kwallar da Tacika Idanuna Batarda Na samu Zarrar Yin Magana ba. Yace, "Tau Kinga ni In Har Ni MASOYI Ne Na Haƙiƙa bazan So Naga Dadyn ki Yazama Karamin Mutum. Meye Ƙaramin Mutum? Shine Yayi Magana Kuma A samu Yasaɓa Alkawali ko Yacanza Maganar Wanda Nasan hakan Abu ne da bazai taɓa yiwuwa ba. Sannan Ko Bancin Hakan ma Sunce Bancanci Zama Mijinki ba Saboda Ni Ban tara Abin Duniya ba Nima dai Kawai Naci ne Irin Na SO! Inba Shi ba Irin Wannan wu....." Jin Abdull Yasoma Sakin Layi Saboda Ɓacin Rai da Yashiga Yasa Nayi Saurin Toshe Kunnuwa Najuya da Gudu Zuwa Cikin Gida Yana Kiran "Khaleesat! Khaleesat!! Khaleesat!!! " Amma Ina Ban saurare Shi Ba. Cikin Matuƙar ƙunar Zuciya Yazube Ƙasa Yana maida Numfashi Tamkar Mai Ciwon Asma wanda Ganin Hakan Yasa Yusuf Cikin Hanzari Yanufo Shi Yana Cewa "Abdul-wahab!" Yakamo Kafaɗarsa Tareda Cewa, "Abdull Meyafaru Naga Itama Khaleesat Ta tafu Tana Kuka?" "Yusuf Khaleesat Wani Za'a Aura mata Wanda Bani Ba Nan da Sati Biyu, Yusu Menayi Wa Iyayen Khaleesat da basa sona ne? Ko ina da wata muguwar ɗabi'a ce?" Duk inda Jikin Yusuf Rawa yake Shi Kanshi yashiga Tashin Hankali kan Wannan Maganar Cikin Muryar Kuka Abdul-wahab Yake Cewa, "Dama Talauci Na Iya Zama Aibu? TALAUCI Nan Nima fa Bani Liƙawa Kaina ba ARZIKIN DA TALAUCI Nan Duk Na ALLAH ne kuma Shi Yake Badawa Ga Wanda Yaso Bawai dan Yin Zalunci Ba Sai don Jarabba Kowane daga Cikin Bayin sa... "Yafashe Da Wani Kuka Mai ban tausayi Kafin Yasoma Cewa, "Yusuf Manayiwa Iyayen Khaleesat Meye Nayi Wa Iyayen Khaleesat Mena ci Musu me....." Yusuf Yayi Hanzarin Toshe Masa baki Yana Basa Hakuri Kafin Yajasa Suka bar Cikin Gidan Yana mai ƙaƙarin Nema musu Abun Hawa da zai kaisu Gida. A wannan Karon Shi Kanshi Yana jin Ya tsani Iyayen Khaleesat Harma da Ita Khaleesat ɗin Saboda Sunci Amanar Abokin sa. Gidansu Yacema Mai kk napep ɗin da Yatara Yakaisu Yayin da Abdul-wahab Yace, "Ni Ka Kaini Gida Ba'inda Zanije." Yusuf Bai Kula sa Ba yace Mai Kk Napep Yaja Suje. Tunda Suka shiga Kk napep ɗin Abdul-wahab Yahaɗe Kai da Gwaiwa Shi Ba Kuka yake ba Amma Yanda Zuciyarsa Ke Suya Gara Yayi Kukan Ƙila Yasamu Sassauci. Taufa My Readers Muje Zuwa Danjin Yazata Kaya Nikam Nayi Gabaaaaaaa [9/5, 9:15 PM] FA'IK: Typing....... 💻 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....22 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem NOT EDITIN.... A hankali Na sauke Labulen Windor Nawa da tun ɗazu Nake tsaye ta gurinsa Ina Hangen Irin Tashin Hankali da Abdul-wahab ke Ciki Ina Mai kuma Ƙara Amincewa Zuciyata Irin Son da Abdul-wahab Yake yimin. Cikin Sanyin Jiki Nasanya A hannuna Nagoge kwallar tausayin Kammu davTa taru A idona Kafin Na Koma Kan Kujera Na zauna Batareda Nasan Taƙamammen Abinda Nakeyi Ba, Kawai dai Nasan Ina Cikin Wani Irin Ƙunci da Tambayar Kaina Shin Meye Illar Aure na da Abdul-wahab ne da Har Iyayenmu Suke Yimana SHAMAKI ne? Meye ne dan Mun SO Juna ta Hanyar da Tadace ne? Yanzun Basa Tsoro ko Tunanin Mudinga Zaman Banza? (Wa'iya zubillah) eh Mana Tau Ai Wannan Sunshiga Haƙƙemu. Ire-iren Wayyanan tunannuka Su Suka Abokanci Zuciyata Har'izuwa Wani dogon lokacin da Halin Damuwar da Nake Ciki yasa nakasa Tantace Yaushe ne ma kuma bana ma Buƙatar In sani dan ni A Yanzun tunda Narasa Abdul-wahab Komai ma Na Duniyar Na Hakura dashi Kawai dan Haka sannu A hankali Na Sulale Ƙasan Carpet ɗinda Ke malale A tsakiyar ɗakin Nawa Naciga ba Zubbda Hawayena Wayanda Nakejin Ba Ranar daina Su Harsai Sanda Aka cemin Anbarni Ko Lalle Yau Bana da Miji Sai Abdul-wahab Lamarin da Nakeji Kamar da Wuya Inji Masu Iya Magana Sukace "Gurguwa da Auren Nesa." ******* Tunda dai Suke Cikin dakin Ba'abunda Sukeyi Illah Tufka da Warwara! Kuma An rasa daga cikinsu Mai Yiwa ɗan Uwansa Wata Magana Musamman ma dai Dr Jabir Da shine YAFI CANCANTA yace Wane Abun tunda Shine Yaɓallo Ruwan Dan Haka Shi Yafi Kamata Yatare su. Ana Cikin Hakan Har kiran Sallah Magarib Yariƙsu A Haka Wanda Yayi dai-dai da Dawowar Alhaji daga Kasuwa Kuma Suka Ji Muryarsa A tsakar Gida Yana Magana da Su Gwaggo Halima dan Haka Cikin Sanyin Jiki Duk Suka Miƙe Suka Fito Kafin Suka Rusuna Gefe Suna Gaidashi Yayinda Shikuma Yabisu da Kallon Mamaki Kafin Yaɗago Kansa Yana mai Kallon Gwaggo Halima Cikin Alamun Tambaya Amma Sai Gwaggo Halima takawar da Kanta madadin Hakamma Sai taɗauki Buta Tanufi Dromm ɗin Ruwansu dake Girke Tsakar Gidan Nasu Taciko Masa da Ruwa Takawo Gabansa Nufin Dai Zaiyi Arwallah Zuwa Masjid dai-dai lokacin da Shikuma yake Amsa Gaisuwar Tasu Daga bisani Yake Tambayarsu Lafiya Kuwa? Dr Jabir ne Mai kwarin gwaiwar Cewa, "Lafiya lau Alhaji Mundai Zo Gaishe ku Ne Kawai." Alhaji Badan Ya yarda da Maganar tasa Ba yagirgiza Kansa Kafin Yace Masa, "Tau Madallah Aikun Kyauta zo ɗauki ga Buta Kayi Arwallah muje Sallah Naji Har Sun Tayar Ke Asiya Zoki Cikomin Wata." Maman Asharaf da Dr Jabir ɗin duk Tare Suka Miƙe Shi Yaɗauki Butar Yasoma Naɗe Lonk slive ɗinsa Bayan Yacire Tsadadden Agogon dake Kan Kyakykyawan Hannunsa iTa Kuma Taɗauki Butar Zuwa cikowa Alhaji Dan Shima Yayi Arwallah. Ganin Hakan Yasa Su Gwaggo Halima Da Safiyyah Suka Nufi Kitchin dan Ƙarasa Aikin Nasu. Tare Sukaje Masallaci Bayan Angama Kuma Suka Jero Suka dawo gida Alhaji Na Tambayarsa Yanayin Aikinsu Shima Yana Amsawa masa Cikin Girmamawa, Lokacin Gwaggo Halima Na Kan Yar Tsuggonunta Tana Raba Abinci Yayin da Safiyyah Ke Aikin Tayata Ita Kuwa Maman Asharaf tana ɗaki Kan Darduma Dan bata jima da gama Sallar ba Ita. Alhaji Yazauna Kan Shimfiɗarsa Yayinda Dr Jabir Yadawo Gefen sa Ya zauna Cikin Nutsuwa Yana Sauraron Jawabin Na Alhajin Can Yajefo Masa Tambayarsa Kwana nawa ne Suka Rage ne Auren sa? Dr Jabir Yace, "Bazai Wuce goma ba yanzun." Dai-dai Lokacin ta'ajiye Masa Farantin Abincin dake Jere Cikin Kwanonin Silba da Kuma Kofin Sulba Da'a ka Cike da Ruwan sha Shima, dan Haka Alhajin Ya'Umurci Dr Jabir Da Ya Wanke Hannun sa Suci Abinci Dr Jabir Ba Yanda Zaiyi Dolen sa Ya Wanke Hannun Nasa. dan Yariga yasan Waye Alhaji da Kuma irin Nasa Aƙidun Suka tsoma Hannayensu Acikin Kwanon Tuwon Suna Ci Sannu A Hankali Kuma Alhajin Naci gaba da Bugun Cikin sa Dan jin Matsalar da Takawo su Gidan. Hakanan ko Cikin Hikima da dubara irin Tasu ta Manya Haryajiyo Abinda Yake Son Ji daga Bakin Dr Jabir ɗin A wannan lokacin Kuma shi Alhajin Yatsame Hannun sa daga kwanon Abincin Yajawo buta ya wanke Hannun sa kafin Yakuskure Bakin sa sa'anan Yafuskanci Dr Jabir. "Dama ni Nasan Abinda Yakawo Jabiru Kawai Zuru Nayi Maku dan Dama Can Na Nasa Tun Kafin Kuzo ɗin Sai kunzo Dan Nasan Halin Mata Na Kuma Kaidin Su Akan Kishi Shiyyasa ma Tun Kafin Irin Haka Naja Ma Mahaifiyar tasu Kunnen da Sauran dukkan Yan Uwan ta, dan Haka kaima Abinda Zan Sanar da Kai Yanzun Shine Sai ka Ƙara Hankuri Buhu-Buhu Sai kuma Kazamo Namijin duniya Acikin Gidanka In ba Hakaba? Tau Wallahi Kana Kallo Gidan ka Zai Tarwatse Saboda Kayi Adalci a tsakanin Iyalan ka Itace Mallaha Ta Farko Gareka Sannan Kazauna Katsara Yanda Zaman takawar Iyalin ka Yakamata ta Kasance, Kada Kazamo Maiyin Abu Gaba-gaɗi Ai Kana Fahimta ta ko?" Dr Jabir da Tuni Shima Yawanke Hannnun Nasa Daga Cin Abincin Da suke Yana Nan Rusune Gaban Alhaji Ya sunkiyar da Kai Kamar Mai Neman Gafara Yagirgiza Kansa Batareda Yace Uffan ba. Dan Haka Alhaji Yaɗora da Cewa, "yawwa Idan Kafahimci Hakan Shine Maganin Matsalar Karka Musgunawa Ko Wacce daga Cikinsu Domin Dukkansu Matan ka ne Kuma Amana Aka Baka Kuma ɗiyan Wasu ne Kaima Kuma Zaka Haifa Kuma Zaka Bada Auren So duk irin Riƙon da Kayi Masu Shi Za'ayi Wa Nakan Saidai Kuma Bance Akan Tsallake Jarrabawa ba Asamu Akasin Naka Halin Ba Wannan kuma Jarrabaw ce daga Min indillah Idan Akayi Hakuri Aka Karɓi Jarrabawar Ta Fuskar data Dace Sai Ka An Samu Sakamako Mai Kyau." tau Haka dai Alhaji Yasaka Dr Jabir Gaba da Nasihohi da Shawarwari Harma kuma da Faɗakarwa Akan Halin Duniya da Kuma Irin Zaman da Yacancanta Yayi da Iyalin Nasa. Wayanda Dr Jabir Yaƙaru dasu Sosai Hakanan Iyayen Na Maman Asharaf Sun Ƙara Wata Irin Ƙima da Darajar duk Yanda Yaso Yakwatanta Abun Yafaskare sa. Cikin hakan Alhaji yasa Aka kira Masa 'Yar tasa Itama ya zauna da ita ba faɗa ba kyara Dan yayi Mata Uzuri Kan shi ya Yarda KISHI Halak ne kan Abinda kake So, Abun buƙata dai baifi Kasamu Ma'abota Hankali da Zasu Fahimceka Su kuma ɗora ka kan Hanya managarciya. Tau Itama dai haka Yayi mata nasiha da Lurarwa Irin Tasu ta dattijan Sannan Yagargaɗeta Cewa Babu Yaji dan Yana Zubar da Ƙimar Ya mace. Daganan Ya cikata da tarin Kyaututtuka Na turare da Yan Ƙayatattun kayakin da Campunan da suke Mu'amala ta saye da saisuwa ke Basu Irin Botikai da robobi Da dai sauran su Sannan yace tayi List ɗin duk Abinda Take Buƙata Zai Siya mata kada ta matsawa mijin Hidimun Sunyi Masa Yawa. Haka dai Suka Shigo Motarsu Suka Nufi Gidansu Cikin tarin Alkairi Albarka daga SURUKAN KIRKI Wani gefe kuma Dattijan Kirki Shi Kanshi Dr Jabir A yanzun Yanajin Cewa Ko A iya wannan Idan Yacuci ɗiyarsu Haƙƙensu Bazai Barshi ba. Saida Suka biya Gurin Ƙanwarshi Suka ɗauko Asharaf Kasancewar School ɗaya Yakeyi da Yaranta Dan Haka In Ba'aje ɗaukar Daga Cikinsu ba Sai Wanda Yazo ɗaukar ɗayan Yahaɗa duka Yaɗauke su Inyaso Shi Dr ɗin ko Ita Maman Asharaf Sai taje gidan ta ɗaukoshi hakanan Itama Ƙanwar ta Dr Jabir Mijinta ko direban ta Ke Zuwa ɗauko Yaranta In Sunbi Asharaf Can gidan Su. Nan ma saida Suka ɓata Lokaci Kafin Sukayi Musu Sallama Suka Nufi Gida Suka Bar Sajida(Ƙanwar Dr Jabir ɗin) Cikin Mamaki da Tunanin Shikuwa Yayan ta Mezaisa Shi Wani ƙarin Aure Suna Zaman su Lafiya da Matarsa Yaje Kawai Yajajibo wa Kansa Wata Rigimar? Karshe dai Tawatsar da Hannayen ta Alamun Shi Yaga zaya Iya. Kafin Afili ta Furta, "Mudai Asiya ce Tamu bamu San Wata Amarya ba dan Ko Banza Itace Ƴar Uwar mu Ta jini." kafin Tajuyo ta koma Ciki dan Tana Wannan Tunanin ne A sanda Motar tasu taɗaga Tabar ta tsaye Nan Harabar parkin space ɗin gidan su. ************ Su Abdul-wahab Kuwa Kai tsaye Mai Kk Napep ɗin gidan Su Yusuf Ya'ajiye Su Yusuf Ne Yasallameshi Kafin Yabi Abdul-wahab Da ɗan gudun sa Danshi Abdul-wahab Suna Sauka Wucewarsa Yayi Cikin Gidan. Dakin Yusuf Suka Zube Abdul-wahab Yatallafe Keyarsa da duka Hannayen Sa Biyu Tareda Tsurawa Fankar dake Saman Rufin Ɗakin Tana ta Aikin Bada Iska Hawaye ne Ke Silalowa A Fuskarsa Kunci Nakara Samun Muhalli Acikin Zuciyarsa, Gefe ɗaya Yana ALLAH Wadai Da Irin Wannan Zuciyar Tasa da Takasa Cire Son Abinda Bazata Taɓa Samu Ba. Can Kuma Sai Yake Tambayar Kansa Wace Irin Ƙiyayya ce Iyayen Khaleesat Keyi Masa? Meyasa Suka Kasa Gano Irin Tsantsar Soyayyar Da Yakeyi Wa Ƴarsu? Tabbas Yasan Baya da Kuɗi Amma Yanada Sana'ar da zai Fita Yanema Yazo Yaci dasu Yana kuma Da Yaƙinin Zata Iya Riƙesu da Duk Wani Lalurorinsu Amma Su Sunce ƘUƊI! Tau Mey..... Yusuf Yashigo da Kular Abinci Ya'ajiye Da Ruwan Pure water guda Tareda Gorar Soɓo guda Biyu Sai Raɓa Sukeyi Alamun dai Sunyi Sanyi. Kafaɗar Abdul-wahab Yabuga Tareda Cewa, "Kaman ta Komai dan ALLAH Taso Muci Abinci Sa'annan Muyi Magana." Batareda Yaɗago Ba Daga kwancen Yace, "Yusuf A Yanzun Bana Sha'awar Komai Bana Jin Kuma Zan Iya Cin Komai." Yusuf Yayi tsaki Kafin Yace, "Matsala ta da Kai fa Kenan Rashin Tawakkali Dan ALLAH Ka...." "Kaga Malam Karka Wani Isheni da Surutu Abinci Nace Bazan Ci Ba Dan Haka Karka Wani dameni Kawai Ka ƙyaleni Inji da Abunda Ke Damuwa ta Ni Da Zaka Ma Fice Daga ɗakinan Kaci Abincin Zanji daɗi Wallahi dan ko Warinsa Bana son Ji!" "Abincin Ne Ke Wari Abdul-wahab?" Yusuf Yafaɗa Cikin Sakin Baki Akan Mamaki. Banza Abdul-wahab ɗin Yayi Masa Yana Mai Ci Gaba da Tunanin sa da Nufin Bazai Taɓa Kammalla shi Ba Harsai Yasamawa Kansa Mafita. "In Bazakaci Abinci Ba Saika Sha Ga Soɓon Ko dan Ka sanyaya Zuciyarka Dan Yana da Sanyi." yaƙare Maganar Gamida Miƙawa Abdul-wahab Gorar Soɓon. Daga Inda Abdull Yake Kwance Yamiƙo Hannunsa Yakarɓi Gorar Kafin Yamiƙe Yaɓalle Murfinta Kafin Yakai Bakinsa Yasoma Sha Bai Dire Gorar ba Sai da Ya shanye Tas Ya'ajiye Gorar Yakoma Yayi Kwanciyarsa Irin Ta ɗazu. Kaida Gani Yasha ne Kawai Dan Kada Yusuf ɗin Yacika Shi da Surutu. Gefe Yusuf Yakoma Yasoma Cin Abinci Rayuwar Tasa Shima duka Babu daɗi Akan Irin Halin da Abdull ɗin Ke Ciki Saidai Babu Abunda Zasuyi Wanda Yawuce Haƙuri Hakanan Kawai Su Rufe Babin Khaleesat A Rayuwar su. Hakadai Yatsakuri Abinci Shima Yatarka ta Kayan Yanufi Cikin gidan Nasu Ummarsa Ke Tambayar sa Yabasu Ci Abinci Ba Shine Fa Yake Gayamata Halin da Ake Ciki Tashawo Lulluɓi Suka Zo Tare A ɗakin na Yusuf Suka Tarar Abdul-wahab Na Nan Yanda Yake Yayi Nisa Cikin duniyar Tunani ga Hawayen na Cigaba da Kwarara daga Cikin idanuwan sa Wayanda Yake ji tamkar Ruwan zafi ne tafasassu ne Ake Kwarara Masa Akan Fuskarsa. Sallamar Ummarsu Yusuf Yasa Yayi Firgigit Yasoma Share Hawaye Kafin Yashiga Gaisheta. Cikin tausayin sa Take Amsawa Kamin Tasoma Yimasa Nasiha Kan yayi Hakuri, Komai Na Duniya Muƙaddari ne daga ALLAH duk Abinda Yaso Shi Yake Faruwa dan Haka indai Da Rabon Zasu Auri Juna shida Khaleesat duk Ƙin Iyayen ta Akan Abun Insha'allah Sai Sun Auri Juna idan Kuma Bai Ƙaddara ba Duk Son Su Da Abun Bazai taɓa Faruwa ba." taƙare da Cewa, "Saboda Haka Kasawa Ranka dangana Ka Kuma Ci Gaba da Adu'a Komai Yayi Maganin sa ALLAH Kaji Ɗana? (Dama haka take cemasa) Abdul-wahab Yakasa Magana Sai girgiza Kawai Yakeyi. Daganan Ummarsu Yusuf ɗin Takoma Cikin gida yarage daga shi Sai Yusuf ɗin, Yusuf ɗin Ma Yana ganin Shirun Nasu Yayi Yawa kawai Sai Yamiƙe Ya kunna Masa Karatun Ƙur'ani Cikin Mp ɗin da Ke ɗakin Sa'anan Shima Yafice Zuwa waje. *Muje zuwa dai Readers........ * [9/5, 9:15 PM] FA'IK: Typing....... 💻 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....23 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Sai da Aka Kira Magrib Yusuf Yazo Yana Tashin sa, Dan Baccine Yatafi Dashi Sosai Wanda Baima Zata ba, Arwallah Sukayi Suka Rankaya Zuwa Massalaci Bayan Sun idarda Sallah Suka Nufo Gida Bakin Ƙofa Suka Samu Abubakar Yayi parkinq da Mashin Yana Jiransu. Saida Suka Gaisa Kafin Abdul-wahab yahau Mashin ɗin da Nufin su Wuce kawae Yusuf Yacakumeshi Tareda Cewa, "Ai Wallahi Baka Isa ba, Yazaka Wuce Bamu ci Abinci Kuma Bakaje Kayiwa Umma Sallama ba?" Abdul-wahab Yahararesa Sa'annan Yasauka daga Mashin ɗin Yanufi Cikin Gidan Batareda Yace Uffan Ba. Shidai Abubakar Sai Aikin Kallon su Yakeyi Yana Murmushi dan Duniyar ALLAH Yusuf da Abdul-wahab Suna Burgeshi Hardai Inyaga Suna Drima Kamar Bazasu Shirya Ba. Tau Suna nan dai Har Saida Suka Yo Sallar Isha'i Sa'annan Suka Wuce Duk-da Kuwa Cewar Abdul-wahab Baiso Hakanba Amma Yusuf ya Rinjaye Shi. Bayan Sun Iso Gidan Abubakar Yaje Maida Mashin ɗin Abokin sa Da Ya'aro Yayinda Shikuwa Abdul-wahab Yashigo Cikin Gida Yasami Innarmu Zaune A tsakar gida Tana Aikin ɗaura Lalle Wata Yar Makwabtansu Na Tayata. Kallo tabishi dashi Kafin Ta'amsa Gaisuwar da Yakeyi Mata Kai tsaye ɗakin su Yanufa Innarmu Takaɗa Baki takirasa "Abdull!" Cak! Ya tsaya Kafin Yayi Ƙoƙarin Saita Nutsuwarsa Sannnan Yajuyo Gareta Gamida Cewa, "Na'am Innarmu?" "Yanaga Kashigo gida Hajaran Majaran ne Haka Lafiya?" "Ba'akomi Innarmu Kawai Nagaji ne Wallahi." ya'amsa yana mai Ƙokarin Nuna Ba Komai ɗinan. Innarmu tagirgiza Kai Kafin Tace, "Tau Amma ai Ka Nemi Abinci Kaci ko? Kila bacin Gajiyar harda Yunwa Naciki." Ɗan Murmushi Abdul-wahab Yayi Kafin Yace, "Eh Zanci Wai Ina So inɗan Watsa Ruwa Ne." Innarmu Tasake Girgiza Kan ta Gamida Cewa, "Shikenan Ai ina Shi Auta? (Tana Nufin Abubakar)" Abdul-wahab yanufi ɗakin Nasu Yake Cemata Yaje Yamaida Mashin ɗinda Ya'amso. *********** Mai Karatu Yakamata Musan Waye Dr Jabir da Ahalinsa. Dr Jabir dai Ɗane ga Malam Badaru Haifafen Garin Birnin Kebbi. Dr Jabir Shine ɗa na Farko A gurin Iyayen sa Sai Ƙannensa mata Ukku da Suke Binsa. Mahaifinsu Mal. Badaru Mahaifiyarsu ce Kaɗai Matarsa Suma Kuma Su Huɗu ne Rak! Mata Biyu Maza Biyu Dr Jabir Shine Ɗa Na Farko Sai Kuma Ƙanwarsa Sajida Mai Bimata Mu'az Sai kuma Ƴar Auta Fa'izah. Asiya (Maman Asharaf) ɗiyar Kawun sa Ce, Mahaifinta Shine Yayan Mahaifiyar Su Dr. Jabir Asiya itace Babba Sai Kuma Ƙanwarta Safiyyah Sukaɗai ALLAH Yaba Mahaifinsu duk Sauran Rasuwa Sukeyi. Dan haka Auren Dr. Jabir da Asiya (Maman Asharaf) Auren Zumunchi ne Wanda Yasamu Asali Tun Sonda Shi Mahaifin Asiyar Keyiwa Dr. Jabir Kuma Yakasance Ma A Hannunsa Dr. Jabir Yatashi Har zuwa Sanda Akayi Auren Nasu Kuwa. Faɗar Kuwa Irin Kamalar da Kuma Tsagwaron Ilimi na Islam da Boko da Suke dashi ma ɓata Lokaci ne Hakanan Arziki dai Suna dashi gwargwado Cikin Family Nasu Ba Hayaniya Sosai Duk-da Baza'a Rasa Ƴar tawayar dake Tare da su ba tunda dai Munsan Rayuwar Ba Hundret Pacent Bace. ALLAH ɗai Ya'ishi Kanshi. Wannan Kenan!! Tunda Aka tsaida Ranar Aure na Yazama Gidan Namu Ba'abunda Suke Sai Shiri Ko Tsintsiya Kaga Anshigo da Ita Gidan Katamabaya Za'a cema Ta Buki Ce. Yau Saura Kwana Uku Buki Tuni Komai Ya Kam-Kama Na Abinda Yadangaci Buki Tuni Dangi na Nesa yan Adamawa da Kogi Suka Soma Isowa Gida Yasoma Albarkar Jama'a! Sai Jike-jike da Hade-Haɗe Ake Bani Wasu Insha Cikin daɗin Rai Wasun kuwa Sai Momy da Ƙanneta Sun tasani Gaba da Masifa Sannan Fa Zansha! Ta ɓangaren gyaran Jiki Shima ba Kama Hannun Yaro. Ƙawaye Na Jiki kuwa Kullum Nan Suke Wuni Ana Tsare-tsare Yanda Abubuwan Yakamata Su tafi. Nidai Nawan dasu Ido ne Kurum! Saidai Inaji Ajikina Bazata Saɓu ba Raba Kaina da Soyayyar Abdul-wahab! Wannan Wani Abune Tsararre Acikin KUNDIN ƘADDARATA tun daga 'Lauhul Mahfuz' sbd Haka Nashiga Tufka da Warwara Kan Yanda Zan Samarwa Kaina Mafita. Waya Kuwa Kullum Sai Mun Raba Dare Munayi da Abdul-wahab Yana Mai Ƙara Sanarda ni Irin Tsantsar Ƙaunar da Yakemin Tareda Cewa Babu yanda Zamuyi da Ƙaddarar mu Saidai Mu Karɓa da Hannu Biyu. Dr.Jabir Kuwa In Yakira Sai Naga Dama Nake ɗagawa Sanda Yazo Hira Kuwa Haka zai ƙarashe Surutunsa Yawuce Batareda Yagane kaina Ba! ******** Suma dai Su Abdul-wahab Shiri Sosai Sukeyi dan Bukin Yusuf Yana ƙaratowa dan haka Basu ba Zama Kullum Cikin tsare - tsare Ake. Dan Haka sai Kan Abdul-wahab Yaɗau Caji Sosai! Komai Kuma Yaƙara Rincaɓe Masa Har Wata Yar Rama Yayi Ga Wani Uban Fari Kal! Da Yaƙara Yi Sai Siririn Hancinsa Yaƙara Fitowa Yana Ƙokari iya Ƙokari dan Ganin Yamanta da Khaleesat A ransa Hakanan Baiyi Ƙasa A Gwaiwa ba Wajen Yin Adu'ar ALLAH yacire masa Sonta indai har itaɗin ba rabonsa bace Kuma ba Alkairi Bace Agareshi! Saidai Kullum Kamar Wanda Ake ƙara yiwa Allurar Son Khaleesat ɗin dan haka sai yayi Tawakkali Ya fawallawa ALLAH Komai Ta ɓangaren Yusuf ne Kawai Yake Samu Matallafi Mai Bashi Shawara Yana kuma ƙara tunatar dashi Alfanun Fin Ƙarfin Damuwar Tasa! Tuni dai da Aka Soma Bukin kamar yadda Aka san Al'adar Basakkwace Akan Sanya Amaryar Lalle ne Ranar Laraba sauran Ranakun da Kan Biyo Baya Amarya da Yan gidan su Kan Shirya yan Bukukuwansu Irinsu Ƙauyawas day, Fulanis Day, Party, Kamu, Deener, da Dai Sauran su harzuwa Ran Assabar inda nanne Ake Tuƙewa da Ɗaura Aure da Dare Kuwa 'JIRGIN SUNNAH' Yatashi da Amaryar zuwa gidan Mijinta! Tau A wurin su Ma Haka ce Takasance Kuma Komai yana tafiya lokaci guda (ina Nufin Gidan su Khaleesat da Kuma Nan Suma Yusuf) Saidai A ɓangaren Su Khaleesat Ansamu Cikas! Domin dai Ana tsaka da Buki Wanda Yazo dai-dai Ranar Jumu'a Ranar Kuma Akayi Ƙayatacen 'Kamu' Ana jiran Gobe Assabar Aɗaura Auren Amaryar ta Tare. Tau Amma me? dare liss Angama 'Kamun' Kowa yagaji Sai Ma huta Yake Nema Amma Mezai Faru? Amaryar daga Dawowa Kamun tashiga ɗakin dan cire Kayan tana Mitar Sun Isheta da Zafi Kawai Akaga tazube ƙasa babu Alamun Numfashi Tareda Ita Lamarin da Yajanyo Hankali Ƙawayenta suka Yo tururuwa Akanta Suna Kuwar kiranta Kamar Maƙwagoronsu Zai Tsage! Amma ina Amarya Khaleesat bataji sai Wani Kumfa ke Antayowa daga bakinta yana kwarara A Ƙasa! Momy kamar Zata Tashi Sama ta ratso ɗakin da Mutane suka sanya Khaleesat ɗin Atsakiya Suna Kuka! Momy ta durƙushe Gabanta Tana Aikin Shafa Mata Ruwa A Fuska bakinta bai Futa da Faɗin "Innalillahi Wa 'innalaihi Raju'un!" Amma ina Ihunka banza dan Babu Alamun Rai Tare da Ita. Momy Cikin Kuka tamike Tanufi ɗakinda Dady Yake Tana Kuwar kiransa,"Dadynsu Khaleesat Ta Mutu! Nashiga Ukku Zo Kagani Dadynsu! Khaleesat ɗita Babu Ciwo ba Komai Amma ta Mutu!" Kalaman Sunzowa dady Kamar Saukar Aradu da Ya Nuradeen dake can Shima ɗakin da suka saba Sauka dan Haka A Sakwane Suka Fito Har suna Karo da Juna Wajen Shiga ɗakin. Wanda Tuni yarikice da Koke-Koken yan Uwa da Abokan Arziki! Ya Nuradeen yaɗaga Hannun ta Amma sai Yakoma Yaraf! Yafaɗi tabbacin Babu fa Numfashin Tareda Ita. Wasu Hawaye Masu Zafi Suka Fito daga Cikin idanunsa da gudu suka Soma Anbaliya A Fuskarsa yaɗago yana Cewa, "Shikinan Momy Kun kashe Khaleesat da Kanku Zuciyarta ta buga! dama Nace Muku Ku Bar Lamarinan Tunda Bata so Abata wanda takeso Amma Kunƙi tau Gashinan Kun Kasheta!" yaƙarasa Maganar Cikin Rawar murya! Duk Ilahirin Jikin Momy Rawa Yakeyi yayinda Shi kuwa Dady Duk Wuta taɗauke Masa Hankalinsa In Yayi Dubu duk Yatashi! Yace, "Wace irin Maganar Banza ce Kakeyi Nuradeen?" Yayinda Momy Kuwa Sai karkarwa Jikinta Ketayi Tana Mai Cigabada Share Hawayenta. Ƙanwar Momy ce Watau Mami Iyabo Cikin Hausarta da bata Fita Sosai Tace, "Ba Wananne Yakamata Ayi Ba Muɗaukesi Zuwa Asibiti domin Ceto Rayuwar si..." Kamar Jira Suke tayi Maganar Dady Yajuya Yana Mai Cewa "Bari Naje Na samo Mana Abin Hawa Kutallafo ta Mugani!" Sai Ƙokarin Sharce Zufa Yakeyi. Mami Iyabo ce Ta Sunkuci Khaleesat ɗin dake Miƙe Samɓal Babu Alamun Numfashi Tareda ita Zuwa Waje. Lamarin da Yaƙara Tunzura Zuciyoyin Mutanen da ke Gurin Kenan ganin Cewa Yanzun Fa Ake Tareda Ita Ƙalau! Kai Mutum Ba bakin Komai yake ba A gurin ALLAH! Momy kam biye ɗai take dasu Batareda tasan ma inda take jefa ƙafarta ba Balle tagano Cewa bata da Mayafi ko Takalmi ba. Ɗaya daga cikin Ƙawayen Amaryar ne ta lura da halin da Momy ke ciki dan Haka tayi hanzarin Lalubo Hijabi tabawa Momy da kuma Silifat ɗinda tagani Batareda tasan Wa yake dasu ba! Tau waye yake tasu ma Yanzun? Illai dai komai Kasamu Ka yaɓa! Gudan Amarya da Aka taru domin ta ba Lafiya? Koda Suka fito Dady Yayiwa wani Makwabcinsu Magana Harya fito da Motar sa dan haka Su Momy da Mami Iyabo Shigewa Sukayi Baya Tareda Amarya Khaleesat Dama Shi Dady Tuni Yana gidan Gaba. Duk Yadda Wasu Suka So Zuwa ba Wuri, dan Amaryar Mike take Samɓal! Ba Wurinda ke Motsawa Dole haka Suka Haƙura Suna mai Fatar ALLAH yakawo mata Sauki! Ya Nuradeen Kuwa Titi Yanufa Yasamu Mai Kabu-kabu (Ɗan Acaɓa) Yatara Yabi Bayansu. Gidan Uwargida Fa Sarautar Mata? (Maman Asharaf) Uwargida Tayi Kyau Abinta Cikin Wani Tsadadden Les! Kalar Mlik Sai Ƙyalli Takeyi Tana ta Kai Kawo Cikin yan Uwa da Abokan Arziki da Suka zo tayata Shirya Abinda Zatayi Taron Bukin Ta Na Gobe. Kayan Snack ne Annan Suna ta Aikin Tuyawa, Harda Su Sajida Ƙannen Dr Jabir ɗin Suna Nan Ita Suke ta Taya KISHI. Dan Haka Ko Wannan ɗai yana ƙara kwantar mata da Hankali Taji Cewa lalle Itace Sarautar Mata Donoth ɗinda Ake Toyawa ne taɗebo Cikin Flet Kafin Tabuɗe ɗan Ƙaramin Frij dake Girke A Kitchin ta Jawo Gwangon Maltina Mai Sanyi Har Yana Raɓa tadora Akan Farantin Tanufi ɗakin Oga, Yan Uwa sai Tsiya Sukeyi Mata Ana ta Dariya! Masu Karatu Anan Zan Numfasa Muje daku A Gaba Tareda Alkalamin FA'IK. [9/5, 9:15 PM] FA'IK: Typing....... 💻 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....24 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Gefen gado tasameshi A zaune Yana Aikin duba Wasu takardu da Yake Shirye-shiryen Tafiya ta dalilinsu Daga shi Sai Gajeren Wando Da Yar Singlet Fara ƙal! Jikinsa Fari tas Shima Sai Walwali Yakeyi Kamar Ka lashe Saboda Fari da Taushin sa Yaɗago dara-daran Idanunsa Masu Yiwa Ƴan Mata Kwarjini Yazuba su Gareta cikin Wata irin tarin Ƙauna! Ta kula dashi Sosai Amma duk Yanda Farinciki Hakan Yataso Mata Sai ta tuna daga gobe fa Farinciki Raba dedensa Zasuyi da Wata Matar duk Sai taji Baƙinciki yamaye Gurbinsa Yanzu ma Hakan ce tafaru harta ɗebo Fara'a Tana Tuno wa sai Kawai ta gimtse Fuskarta Shima Yasan Abinda Yasa hakan dan Haka Cikin Sigar Lallashi Yawatasar da Takardun Yanufo ta Gamida Cewa, "Sai ni Mijin Ummu Asharaf kuma ɗan lelenta Abin daɗin da kuek Girkawa ne Aka ɗebomin Inyi Tastin?" Yasa Hannunsa Yakarɓi Farantin Yadauki Donoth din Bakinsa Yana Tauna Hankali dai-dai lokacin wayarsa dake Gefe ta Soma Neman Ceto kamar Bazai ɗauka ba Amma ganin Number Dadynsu Khaleesat ne yasa Yayi Hanzarin ɗauka daga Can Dady ke kwararo Masa Bayanin Abinda Yafaru Kai! Ai Babu Shiri yamiƙe Yana "Subhanallah! Ganin Nan Zuwa Yanzun Dady!" yakashe Wayar Cikin Hanzari Yasoma Jawo Jallabiya Yasaka bai ko Saka dogon Wando ba! Maman Asharaf Cikin Mamaki tariƙosa dan kamar Ma yamanta da ita Acikin Ɗakin Tace, "Menene Yafaru Baban Asharaf?" "Wallahi Khaleesat ce Akace Ba Lafiya Sosai Kuma Harma Suna Asibitin Mu..." yana mai Ƙokarin Ficewa daga ɗakin Yake Faɗar hakan. Cikin Ƙokarin danne Abunda Yataso mata Tace, "Ai Ka tsaya Kasa Complet Kaya Amma Kafita Haka?" Ji Yakeyi Kamar ya Faskara Ma Maman Asharaf Mari Amma Me Ya tuna Sai Kawai Yanufi Drowar Kayansa Yana Ƙokarin Zaro Riga da Wando Na Adidas. Cikin Hanzari yasanya Kayan Kafin yaɗebi wayoyinsa da makullin Motar sa Tareda ficewa yana Cewa, "Maman Asharaf naje Sai na dawo!" "ALLAH Yatsare!" Can Cikin makwashinta tai Maganar Wacce Ma Bana Tunani Shi Uban gayyar Yaji Maganar tata wanda Ko yajin ma Bana Tunanin Yadamu da Jin balle Aje ga yakula Yanda Maganar tazo. Sannu A Hankali ta Sulale ta zauna Kafin Tasanya Hannunta Biyu ta dafe Kantan Dai-dai Lokacin da Wasu Irin Hawaye Masu Zafin Gaske Suka Soma Sharafto Akan dan damalin Fuskarta Yayinda Tarin Tambayoyi Birjik Suka Soma Kara Kaina Acikin Zuciyarta Cewa Anya kuwa zata iya Jurar Irin Wannan Zumuɗin Na Dr Jabir? Shin ma Kuwa zata Iya Karawa da Amaryar Irin Wannan Masifaffen So da Dr Jabir keyi Mata wanda baya iya ɓoye shi ko Gaban Waye? Anya Ba Sallama Zata Nema Takoma Gidansu ba? Tau Inba Haka ba Fa Akwai Yuwar Ciwon Zuciya Zai Sheƙata Barzahu Matuƙar Amaryar ta'iso Gidan Kuma Dr Jabir ɗin yaci Gaba da nuna Haka. Balle Kuma Ba tasan Halin Amaryar ba Wacece ita? Kila ba Mutumniyar Kirki Bace Su taru ita Dr Jabir Su Saka mata Ciwon Zuciya Koma Zuciyarta Ta Buga Lokaci ɗaya! Ta Mutu Murus Kuma su Basuda Asara! Kai Bazai yu ba. Tau in Bazai yu ba Mezai yu? Wannan Tambayar Taƙarshe Samun Amsarta yayi mata Wahla wanda hakan Yasauya Akalar Kukan Nata daga ZUBAR HAWAYE zuwa Kuka Sosai Mai Sauti Tana mai Nadamar Kasancewarta Matar Dr Jabir Watakil da Irin Hakan duk bai Faru da ita ba. Tajima Tana Kukan Kafin Taji Anzauna gefenta Gamida Rumgume Kafaɗarta tace, "Ya'isa Hakanan Kinji? Nabarki kiyi Kukane Saboda Shima ɗin Rahamane ga bawa A sanda Yake Cikin Matsi hakanan Yana Rage Nauyin Baƙinciki da Zuciya take kunshe dashi So Ina Fatar Kin Samu releaf?" Maman Asharaf takasa Magana Sai Ajiyar Zuciya Takeyi. Cikin ɗacin Rai Sajida Ta Numfasa Kana Tace, "Har muna Yabon Kin Warware Kin Manta Komai Sannan Kuma Zaki zo Yanzun Ki Ɓata rawarki da tsalle?...." Cikin rishin Kuka Maman Asharaf ta Tari Numfashinta gamida Cewa, "Haba Sajida taya zan Juri Wannan Kinaga fa Muna Cikin Magana Cikin Salama Dadyn Amaryar nan Yakira shi Cewa Batada Lafiya Suna Asibiti Inkika ga Yanda Yaburkice Yana wani Rawar Ƙafa Ko Umma Ce Sai Haka Da Nayi Masa Maganar ya natsu Yashirya Kamar Zai Kifamun Mari tau A hakan Tun Kafin Tashigo fa Kenan? Kiyi Tunanin idam Tashi go Wane Irin Cin Kashi ne Zasuyi min Shi da Ita? Yanzun ma A Nashin kaɗai yana ƙare Balle Ga Nashin ga Nata? Gaskiya bazan iya jura ba Wallahi Bazan Iyaba Kawai Yasak......." Kuka Yaci Ƙarfinta Yayinda Sajida Ta toshe Bakinta Tareda Cewa, "Ko Kusa kidaina Irin Wannan Maganar Ko Sa Tunanin ki Akanta Maman Asharaf! Wanna ba hanya bace mai ɓullar dake ba Bakuma Shine Sulotion ɗin problem ɗin ba Kingane? Yanzun Kuma keda ya Jabeer MUTU KA RABA Takalmin kaza dan haka ki daina jin rauni Acikin Zuciyarki. Dan Haka Nafison Kisamu Compedience Kizauna Sosai! Kiji A ranki Cewa kece da gida duk wadda Zata zo Bayanki Zatabi Ko babu Aure Keda Yaya Jabir Yan Uwan Juna ne JINI ƊAYA kuwa Ai Yawuce Wasa! Ire-iren Wayyanan Tunanin Yakamata Kiyi Wanda Sune Zasu ƙarfafi Gwaiwar ki Bawai Wayanda Zasu Sa Ki Sare ba Ina Fatar Kin Fahimce ni Maman Asharaf?" Sannu A Hankali Maman Asharaf ta girgiza kai Cikin Gamsuwa da Shawarar da ƴar uwarta ta Bata. Fahimtar Hakan da Sajida tayi yasa ta ɗora da Cewa, "Yawwa Tawan dan Haka Tashi kije ki wanke Fuskarki Kizo ki Sake ɗanɗasa kwalliyarki Ta yanda ba wanda zai gane Abinda Yafaru Ki kuma Manta da Komai Ki maida Komai ba Komai ba." Cikin ƙwarin gwaiwa da Kuma Karsashi Maman Asharaf tamiƙe Zuwa toilet ɗin dake cikin ɗakin Na Dr Jabir ɗin Tana Wankin Fuskarta Zuciyarta Naƙara tuna mata Shawarar Ƙanwar Mijinta Wanda Ko A Iya kulawarsu gareta kaɗai A yaci Ace Tasamu FARAGA Akan Baƙincikin KISHIN Da ke Ruruwa A Zuciyarta dan Nawa ne Ma Suka samu Kulawar Irin Tata? Dangin Miji Basa sonsu Hakanan Kuma zasu Sa shi yaƙaro Mata Kishiya dan ƙara cin Zarafinta Amma A Hakan ta Hakure tau Ina ga ita ba Ahaka yazo mata ba? Ire-iren Tunanin da Shawarar Sajida Suka Asassawa Maman Asharaf Kenan Wanda hakan yaƙara Ƙarfafa mata gwaiwar dawowa cikin walwalarta Kamar dai komai Bai Faru ba. Abinda Yasa taji Babu Shakkah Kasamu Wanda Zai Tallafeka Yakuma Agajeka da Shawarwari Nagartattu A Sanda kake Cikin Halin Damuwa Ba ƙaramar Rahma bace Ga BAWA dan haka sai ta Ƙara yiwa ALLAH godiya Tareda ƙara Rokon sa juriya da kuma Hakuri Akan Lamarin KISHIN Mijin ta. ********* Daga sanda Suka Shigo da ita Asibiti Aka ɗora ta kan gado Aka turata Zuwa Emagyncy Room Basu Sake Sanin halinda take ciki ba, hakanan su Kansu Basu Sake Sanin Halinda Zukatansu Suke Ciki ba. Sudai Kawai Gasunanne Zube A Ƙatoton Reception ɗin Asibitin. Momy dai takasa Zama Abinda Yakaita ƙofa Yadawo da Ita Cikin Falon. Mami Iyabo ce Mai Tausarta da Lallashinta Yayin da Dady Yayi Tawakkali Yazauna Aɗaya daga kujerun dake jere gurin hakanan Bakinsa bai Futa da Faɗar duk wata Adu'a da ya sani ba ta Neman Samun Sauƙi ga Wanda Musiba ta Faɗama. Shikuwa Ya Nuradeen Jingine kawai Yake A bango yarumgume Duka Hannayensa Biyu A Ƙirji Yana Aikin Kallon Mutanen dake kai kawo A gurin bawai dan Hankalinsa Na kansu ba! Awowi Biyu Suke Shuɗe A Haka Kafin daga can Aka Buɗe Ƙofar ɗakin da Aka Shiga da Khaleesat ɗin Dr Jabir Yafito Duk Yahaɗa gumi. A Lokaci ɗaya duk Suka nufeshi da Tambayar "Yaya Ta tashi?" Tambayar da Yakasa Amsa Musu Illai Kawai Yakaɗai kansa Yawuce Yana mai Share Hawaye da duk Yanda yayi Ƙokarin karsu Zubomasa Sai da Suka Zobo! Wannan Yasa Duk Suka ƙara Firgita Ciki Kuwa Harda Dady da Ada Yayi ɗan Ƙarfin Halin Nuna Juriya. Wanda Kuma Hakan Yasa Suka Shiga Turereniyar juna dan ganin Ƙowanensu Yashiga Acikin ɗakinda Khaleesat ɗin Take Adai-dai Lokacin Idanuwansu Sukayi Musu MUGUN GANI Wanda Har'abada Bazasu Taɓa Mancewa da Irin Wannan ganin Harma da RANAR da Sukayi Wannan Ganin ba! Khaleesat Kwance Samɓal! Likitan dake Kanta yajawo Farin Zane Gamida Rufeta tundaga Ƙasa Har Saman Fuskarta ruf! Kafin Shima Yaɗauke kwallar da taru A idonsa na tausayin Wannan Family! Ya dafa Kafaɗar Ya Nuradeen Tareda Cewa, "Am Sorry!" da Hanzari kuma yafice ɗakin dan Ba Shakkah Shima Zai iya tayasu Kuka in ya Tsaya. Wutace ta ɗaukewa Momy Cikin Firgici Take Tambayar Dady "Dadynsu Meyafaru da Ita? Eh dan ALLAH Kumin Bayani Mene ne?" Dady Yasharce Hawaye da Rabon Yayisu A Rayuwar sa Harya mance Yace da Momy, "Kullu Nafsin Za'iƙatu Mauti!!! Khaleesat Ta RASU ALLAH da yabamu Ita ya Amshi Abinsa dan Haka Muyi H......" Ina Momy bata gama jin Abinda Ya'am bata ba Ta Nufi Gadon da Gawar Khaleesat ɗin ke kwance Ta Rumgume ta Tana ihun, "Wayyo ALLAH Nashiga Ukku! Khaleesat Karki Mutu Ki Barni Ku Biyu ɗaine ALLAH Yabani. Jama'a Ku taimakeni Karta Mutu!!!!" Babu Shakkah Izuwa Yanzun Kowa Yasan Momy Tafita Hayyacinta Kuma daga Cikin su Ankasa Mai ƙwarin gwaiwar da Zaizo Yakamata Ya Lallasheta Ko yadakatar da ita daga Girgiza GAWAR datakeyi. Ya Nuradeen Haɗe kai da bango Yayi tayi Yana ƙwala kansa ga Bangon Yana Kuka Mai Cin Rai da ban Tausayi ga duk Wani kunne da ke Saurarensa dan Kai Kasan da jin Irin Wannan muryar Na Kuka tau Abun Yakaine. Ɗakin Yaruɗe Yashiga Wani Irin Ruɗu da Ruɗani Dama Mami Iyabo ce Mai ƙwarin Zuciyar Lallashin Itama Yanzun ta Nemi ƙwarin tarasa Musamman idan Taɗago kai tayi Tozali da Gawar Khaleesat ce Acan, Khaleesat Amarya! Amaryar da ɗazu-ɗazu Suka dinga yiwa liƙin Kuɗi Suna Cashewa Cikin Nishaɗi Kai Lalle ALLAH ALLAH NE kuma Shiɗin Buwayi ne Gagara Misali. Tau Dadyn ma dai Ba Kuka Yakeyi ba Kuma Shi Ba Wani Ihu Yakeyi ba Kawai dai Gashinanne Wuta ta ɗauke masa yarasa Nayi! Ya Tuno ɗazu ne fa Yake mata Raha Akan Yan tsallen da Tasa Kan Cewa Irin Wannan Tsulun Haka? Bakya Tsoron Faɗuwa Ikram?" Khaleesat Tayi Murmushi Tace, "Dady Wane irin faɗuwa Ai Har Wayanda ma Suka Fisu Ina Sawa." duk Sukayi Dariya. Zuwan Wannan Tunanin Acikin ƙwaƙwar Dady Yaƙara Tayar masa da Hankali Wanda Sai da Yayi da Gaske Kafin Yasamu Yafi Ƙarfin Zuciyarsa Yasoma Anbatar Innalillahi Wa Innah Ilaihi Raaju'un! Da Ƙarfi! Tirkashi!!!! Tashin Hankali Wanda Ba'a Samasa Masa Rana! Masu Karatu Muje Zuwa danjin Yazata Kaya....... Nidai Nayi Gaba......... Tareda Alkalamin FA'IK. [9/5, 9:15 PM] FA'IK: Typing....... 💻 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....25 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Hakanne yazaburar da Mami Iyabo Itama Takama Kalmar tariƙe Daganan ta Nufi Yar uwarta (Momy) Takamo ta tana mai Lallashinta Tariƙe ta tamau Adai-dai Lokacin Dr. Jabir Yasake Shigowa ɗakin Idanunsa Jaziri Kamar gauta Kai da ganin Kasan Garama Yasamu Yayi Kuka Bisaga Wannan Kunar Zuci da Yake Tareda Ita! Kai tsaye Ya Nuradeen Yajawo A Jikinsa yana Bashi Baki Tareda Nuna Masa Muhimmacin Tawakkali gamida Cemasa Idan Harshi Yayi Haka Waye Kuma zai Tsaya Ya Lallashi Wayyanan Tsoffin wayyanda Ruhi da gangar Jikinsu ke Cike da Rauni! "Khaleesat dai tarigamu gidan Gaskiya Babu Wani Gata da Zamuyi mata da Yawuce Mu Kama GAWAR ta mu Suturta ta mu Sada ta da Makwancinta Mu Bita da Adu'ar ALLAH Yayi Mata RAHMA!" Wayyanan Kalaman Kalilanne Amma Abinda Suka haddasa Acikin Zuciyoyin Mutanen Nan Yafi A Ƙirga Hakanan kuma baya da ma Adadi dan dai Kawai Sunyi Ƙarfin Haline Kila da Sai sun zagi Dr. Jabir ɗin dake gaya musu Wannan Baƙar Maganar mai Ƙokarin Raba su da jinsu. Tau Amma yazasuyi? Tunda Gaskiya ce Yake gayamusu dama dai Ita gaskiyar ɗaci ne da ita Kamar yadda masu iya Magana Kance. Dole dai Abinda Nan da Yace Shine Akayi. Motar Ambulance Aka Kawo dan dai Dama shi Makwabcinsu da dady yanemo Yana kawo su Yakoma. Suna gani Aka Turo Gawar Kan gado Zuwa Cikin Motar Lamarin da Yaƙara Tunzura Zukatansu Kenan. Wanda Yasa Momy tasake Ɓarkewa da Wani Irin Kuka da duk Wani Mahaluƙi dake Cikin Asibitin Saida Yaji! Kasancewar daman Asibitin Bawani Girma ne dashi Ba Falo ɗayane Mai ɗauke ɗakukka daban-daban. Hakanan Gashi tsakar Darene Daman Komai Yayi tsif! Ko ƙaramin Motsi Akayi Zakaji. Haka Suka Shigo Motar zuwa Gida Cikin Wani Irin Tashin Hankali Marar Misaltuwa. Nanne ma Dady Yasamu yaɗan dawo Hayyacinsa Yasoma Buge-Bugen Waya Yana Sanarda Yan Uwa da Abokan Arziki Rasuwar Khaleesat ɗin. Dawowar Su Gidane Kuma Fa Komai Yaƙara Kacamewa Harda Masu Some-Some Ciki Kuwa harda Matar Yaya Nuradeen dan Itama Khaleesat Mutumniyar ta ce Suna ɗasawa Sosai. Bata tuna wani Abu da Khaleesat tayi mata tun Sanda ALLAH yasa ta Auri Yayan Khaleesat ɗin, Saima Girmamata da Kuma Son ɗansu da Takeyi take kuma Bashi Kulawa kamar itace ta tsugguna tahaifeshi. Kafin Kace Kwabo Mutuwar Amarya Khaleesat Yayi Tambari Acikin Lungu da Saƙo Na Ilahirin Masu ALAƘA da Ita. dama dai Ance Inkaji Shiru Tau LAFIYA Ne. Da Safe Kowa yazo Ɗaurin Aure Sai Ya turje Jin Cewa Abu Yakoma Jana'iza. Kai dole Ka Tausaya Wannan Lamarin Mai Imani ma Sai Yazubar da Hawaye Saboda Tsabar Tausayin Al'amarin Dady da Ya Nuradeen Duk Sunyi Firgai-Firgai Daga Jiya Zuwa Yau da Safe Kamar Wayyanda Suka Shekara Acikin Jinya babu ci Babu Sha! Itakam Momy ma Ba'a Maganar ta! Dan Yan Uwanta Ne Taushe da Ita Ruwa ma Sai Sun ɗura Mata. Shikuwa Abdul-wahab Ana gama ɗaurin Auren Amininsa Yusuf, Yasulale yanufo nan Gidan su Khaleesat ɗin domin Halartar Ɗaurin Auren ta duk kuwa da Irin Tullin Aikin dake gabansa Amatsayin sa Na Babban Aboki Ga Angon Amma Haka ya Watsar! Wayarsa ma dan Karsu Isheshi da Kira Sai Yasa ta A Flightmode(Jirgi) Daga Sanda ya doso Gurin Yakejinsa A Wani Iri. Bugun Zuciyarsa Na Ƙara Tsanan ta Saidai Yana dangan ta Hakan da Cewa Kawai Bai Wuce Damuwar da Yake Ciki na Gimbiyarsa Kuma Masoyiyar sa Khaleesat Zata Auri Wani A Yau Wanda Ba shi ba. Wanda hakan Na Nufin Yarabu da Ita Rabuwa ta Har'abada wanda Hakan Yasa Yakeji Shida Aure Kuwa koda Ba Har'abada tau Ba Yanzun ba. dan Baiga Wacce Zai so Makamancin Son da Zaiyiwa Khaleesat ba. Haɗa Idanu Sukayi da Ya Nuradeen Ganin sa Yasa Ya Nuradeen ɗin Nufosa Cikin Hanzari Yana Mai Ƙokarin danne Kukan da ke Neman kufce Masa Sai Shima Abdul-wahab Yaji Jikinsa Yaɗauki Makarkata Yana Neman Faɗowa Ƙasa, Amma Sai Yayi Hanzari Yadafa Bangon dake kusa dashi Yana Mai Kiran Sunan ALLAH. dai-dai lokacin ne Kuma Ya Nuradeen ya iso Garesa Yana gayamasa Maganar da Yakejin tunda Innarmu Tahaifoshi Duniya baitaɓa Jin Magana Mafi ɗacin ɗanɗano Irin ta ba! Maganar da Yakejin ko A MUGUN MAFARKI Bai Kamata yaji Irinta ba dan Haka Sai Yabar Abun Akan Baiji Abinda Ya Nuradeen ke Sanarda shi Bane dan Haka Cikin Ruɗani Yake Tambayar Ya Nuradeen Cewa, "Nakasa Gane Mekake Nufi Ya Nuradeen Shin Abinda Naji kana Faɗa dai-dai ne Kodai Nine ke Neman Haukace wa?" Ya Nuradeen Yace, "Abinda Kajin dai Shine dai-dai Abdull Khaleesat ta tafi tabarmu Har'abada Muda Ganin ta Sai A Hoto Dan ALLAH Kayafemata duk Abinda Tayi Maka." yaƙarashe Maganar yana mai haɗe Hannayen sa guri Biyu Alamun Neman Afuwa! Kafin Yaɗora da Cewa, "Auren ku da Baiyu ba kuwa, Kada ka zargeta ba Laifinta Bane Ni Na shaida Khaleesat tasoka da Zuciya ɗaya Kawai Laifin Su Dady ne da Suka ƙi Fahimtar ta, Gashinan yanzun Sunsa Zuciyarta ta Buga Tabarsu Musu duniyar gabaɗai yanzun kuma Sai Su nemi Wacce zasu Yiwa Auren dole...." Shi kam Abdul-wahab Ganin Kawai Yakeyi Bakin Ya Nuradeen Na Motsawa Amma Bayajin Komeye Yake Cewa Illai Bayanin sa kawai Nafarko da yaji Cewa "Khaleesat TA RASU!" Bayan Shi babu Abinda Yasake ji. Mezai Gani? GAWAR ce Kuwa Aka Fito da ita Mutane Na Ƙokarin gyara sahun su dan yin SALLAH Gareta Can Kuma Gungun Mutane ne ke ta Fahma da Momy dake ta Kururuwar Ba Inda Za'a kai Mata ɗiya Wallahi bata Mutu ba "WALLAHI BATA MUTU BA!" Kalamin da Momy keta nanatawa kenan Wanda Kai da Ganin Momy Kasan Ba Hayyacinta take ba! Wata irin Kururuwar Abdul-wahab Yayi Yanufi Makarar Da Iya gudunsa Wanda Yasanya Fullar dake kansa tafaɗi tanemi Gurinta Yarike Makarar Yana Wani Irin Gunjin Kuka da Surutai "Khaleesat Bamuyi Haka dake ba! Munyi Alkawalin Zamuyi Hakuri Mu Rumguni Ƙaddarar mu da Hannu Biyu Mu Yarda Cewa ALLAH Bai Nufa Zamu Auri Juna Ba Amma Bakice min Zaki Mutu ba. Dan Girman ALLAH Khaleesat Kitashi Ni Ko Baki Aure ni Ba BURINA naji Ance Kawai Kina raye A ɗakin Mijinki Kinyi Ma Su Dady Biyayya Hakanan Kiyiwa Mijin ki Biyayya Wannan Shine Alkawalin da kikayimin Meyasa Zaki Karya? Meyasa Baki Gayamin Zaki MUTU ba! Nima inzo Mu Mutu Tare Mezanyi A duniyar da Babu ke? Khaleesat!!!" Yafaɗi Hakan da Wani Irin Sauti Mai Ratsa dukkan Wani Bil'adama dake Gurin Harcikin tsoka da ƙashi Balle Kuma ZUCIYA. Duk Juriyar Dady Saida Yafashe da Kuka Wiwiwi Shikam Ya Nuradeen Nan Take A Gurin Ya Faɗi Some Abinda Yaƙara Karya Zuciyar Jama'ar dake Wajen Kenan. Masu Raunin Zuciya Suka Shiga Tayasu Kuka Masu Karfin Kuwa Suka Soma Sharar Ƙwalla! Tashin Hankali Wanda Ba'a Samaka Rana!!! Dole Wasu Suka Tallafi Ya Nuradeen Akayi Dashi Cikin Gida Ana Ƙokarin Yayyafa Masa Ruwa Shima dai Nan Abdul-wahab dakyar Aka ɓanɓare sa Daga GAWAR Mutane Suka Rufu Akanshi Ana ta Bashi Baki. A haka dai Suka Samu Suka Taushe Shi Suka Sakashi A tsakiyar su Yashiga Sahun Sallah Bawai dan Yana da Nutsuwar Yinta ba. Liman Na Sallame wa. Wasu daga Cikin Yan Uwa Aka ɗaga Makarar Gawar Zuwa Motar da Za'a Tafi Maƙabarta da Ita. A wannan Lokacin ne Wani irin duhu Ya Mamaye Ganin Abdul-wahab Daganan Kuma Bai Koma Sanin Meke Faruwa dashi Ba. Kai Jama'a Sunga MUTUWAR da Suka daɗe Basuga Mai Alhinin Irinta ba. Haka aka Kai Amarya Khaleesat Maƙabarta Aka Yi Abinda Akanyiwa Kowane Mamaci Kafin Suka Juyo Cike da Kewa da Tarin Tausayi. Aka Dawo Aka Shiga Zaman Makoki NADAMA Mai Suna Nadama dai Tashiga Dady Yayi Dana Sani Babu Adadi Tabbas da Yasani da Yadubi GIRMAN SO da Ke Tsakanin Wayyanan Yaran Yabarsu Sun Auri Juna Gashi Akan ɗan Karamin Dalilin su Shida Momy ya salwantar da Ran Ƴarsu Shima dai Abdul-wahab Tunda Su Yusuf Sukayi Ta Neman sa Basu Ganshi Ba Yusuf Ya Ayyana A ransa Cewa Tabbas yana nan Gurin da Ake ɗaurin Auren dan dama Yace Masa Shifa Sai Yazo! harya Zolaye sa da Cewa Baya Kishi Ne? Dan Haka dai da Suka Lalube sa basu Ganshi Ba sai Suka biyo Sahunsa Shine Fa Suma Suka Ci Karo Da Abinda Ke Faruwa Suka tattaleshi Rai kwakwai Mutu kwakwai! Lamarin Uwargidan Dr Jabir Fa? (Maman Asharaf) Tunda Dr Jabir Yadawo Musu da Labarin Mutuwar Amarya Khaleesat Jikin su Yayi Sanyi Ƙalau! Duk Wani Toye-toyen da Girke-girke da Sukeyi Aka Ajiye. Aka Shiga Zullumin Wannan Lamarin. Tsakani da ALLAH Maman Asharaf Har Ranta Taji Wannan Mutuwar Takuma Shiga Alhinin Abun. Ga Mamakinta Sai gata tana Hawaye Shaɓe-Shaɓe A Fuskarta tana mai Nadamar Ayyukan Da Ta Aikata Ashe Ita Amaryar ma Ba mai Tsawon Rai Bace. Yanzun kam Ba Ma Dr Jabir Ba Duniyar ma Gaba ɗai Tabarma ta Ta tsinci duk Abinda Zata tsinta Acikinta! Yanzun Inda Bata Samu Iyaye tsayayyu ba Tana Gida Tana Yaji Ita A dole Wacce Za'a Yiwa KISHIYA Lalle tasani da Kunyar da Zataji Sai ta Fi Wannan ma Kenan. Kamar Yadda Dr Jabir Yayi ta Juyi Akan Gadon Haka itama tai ta Juyi Cikinsu Aka Rasa mai Baiwa ɗan Uwan Sa Magana. Dole Shi Yamiƙe Yasanyo Arwallah Yashiga Doka Nafil-fili Yana mai Nemawa Khaleesat Gafara Da Rahmar ALLAH Wanda A gurin Adu'ar duk Juriyar sa Saida Yafashe da Kuka! Kuka dai Wanda Ake Cema Kuka. Da Hanzarin Maman Asharaf ta Runtomo daga kan gadon Tazo Ta Rumgume Shi Itama Tashiga Yin Kukan Dama ita ma A wuya Take. Mai Neman Kuka ne Aka jefeshi da Kashin Awaki. Sai Nanatawa Takeyi, "Naji KUNYA Baban Asharaf Kayafemin Kai Mani gafara! ALLAH YAJIKAN KHALEESAT!!!!" Abun Tausayi Abun Alhini ga Zuciyar Mai Imani. Sun ɗau Dogon Lokaci Acikin Wannan Halin Kafin Dr. Jabir Ya Umurci Maman Asharaf Cewa taje tayo Arwallah Tazo Suyi Sallar Zai Fiye Masu Fa'ida. Bata Musa ba tayi Yanda Yace Suka Shiga doka Nafilfili Har Kiran Assallatu Yariske su A Haka. Raka'atanul Fajri Yayi Kafin Yamiƙe Yanufi Massallaci dake Jikin gidan Makwabcinsu! Ko A Massallaci Yajima Yana Nemawa Khaleesat gafara Kafin Yanufo Gida Lokacin Karfe 6 Nasafe Yatarar Maman Asharaf Tana Shirya Asharaf ɗin Tayo Masa Wanka Mai Take Shafa Mashi. Bayan Sungaisa Yakarɓi Asharaf ɗin Yace Kawo Naƙarasa Shiryashi Je ki haɗa Masa Lonchbox ɗinsa. Hakan kuwa Akayi. Yashirya Asharaf ɗin tsaf Acikin uniform ɗinsa Na Isilamiyyah Sai Surutu Yakeyi Ma Baban Nasa (Yaro Kenan Shikam baisan Halin da Ake Ciki ba)Lokacinne Maman Asharaf ɗin Tashigo Ta'ajiye Abincin Nasa na Zuwa Skull ɗin da tashirya masa Kafin Ta nufi Juyawa. Cikin Sanyin Murya Dr Jabir Yakira ta Tajuyo Yace, "Kizo Kishirya da Wuri Mu'aje Shi Skull Ina so Mutafi Gidan su ..... Sai Yayi Shiru Yana Tunanin tau Mezai ce Ma Khaleesat ko Marigayiya?" Masu Karatu Zan ɗan Nisa Anan...... Muje A Shafi Na Gaba Tareda Alkalamin FA'IK. [9/5, 9:15 PM] FA'IK: Typing....... 💻 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....26 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Kai Shidai da Bakinsa Wallahi Bazai iya Cema Khaleesat ɗinsa Haka ba. itakanta Maman Asharaf ɗin Tafahimci Sa Sarai! Dan haka Ta juya Tareda Cewa, "Ok Ina Zuwa minti Biyu." Ba'ajima ba Kuwa ta dawo ɗauke da Farantin Da tajera Soyayyen Ƙwai da Shayi Mai Matuƙar Ƙauri da Kuma Bread Gefe. Ta'ajiye Gaban Dr. Jabir Tareda Rusunawa Gabanshi Cikin Tsantsar Tausasa Murya Tace, "Dan Girman ALLAH Kayi break Badanni ba! Baban Asharaf Tunda Lalurarnan ta taso Kake yiwa kanka Horo Da Yunwa Mussaman daga jiya Zuwa Yau. Kaine Likita Kaine Yakamata Ace Kana faɗakar damu Kan Haka Bawai Mu Ba." Lumshe Idanuwan sa Yayi Yanaji A Ransa Abunda tafaɗa gaskiya ne. Kawai dai Abun ne Yafi Ƙarfinsa babu yanda zaiyi da Rayuwar sa wacce A Yanzun Tafita daga Ƙarfin Ikon Sa domin dai Acanda Shike Sarrafata yanzun kuwa Yadawo Itace ke Sarrafashi. Sannu A Ahankali Yasake buɗe idanun nasa Fes A kanta tana durƙushe Gabansa Tareda Juya Shayin dake Cikin Glass Cup taɗebo Shuga Zata sa Yadakatar da ita Kan Cewa, "Sunyi Yawa Maman Asharaf Sa ƙwara Biyu Kawai." Haka tasa taɗan juya shayin da spoon Sa'annan taɗauko ta miƙa Masa Yakarɓa Yakai bakinsa Yana sha kamar Mai shan magani Saboda ɗacin da Shayin Keyimasa. Matsa masa tayi sai da yashanye tas! Kafin ta turo masa Soyayyen ƙwan Shima A gabansa. Dago Fararen Idanunsa Masu Launin Madara Yayi yazuba su ga Matar tasa Batareda Yace Uffanba dama dai can Miskili ne balle kuma Yanzun da Komai Nasa ma Nauyi Yakeyi Masa. Maman Asharaf Tasan Halin Yan Kayanta dan haka saita bi dashi ta Yanda tasan Tana Karya lagonsa. Haɗe Hannayen ta tayi Guri ɗaya Irin mai Roƙonan dai Kafin Tace, "Dan Girman ALLAH!BabanAsharaf." Ba Musu Yasake jan flet ɗin Soyayyen ƙwan Yasa Fork(Cibi mai Yatsu)Yasoma ci. Shima ɗin dai Kamar Wanda ke cin Magani Haka yadinga Cinsa. Bread Tafitar A ledarsa Tana mai Ƙokarin Tura masa A Gaban Nasa wai A nufinta Yahaɗa, Amma Harar da Yawatsa mata Yakatse Hanzarin Nata ta sadda Kanta ƙasa Cikin Matuƙar Jin Ƙwarjinin da Idanun nasa keyi Mata dubanta yayi Yana Cewa, "Amma nace Kiyi Hanzari Ki Shirya Zamuje Gidan Mutuwar Nan tare ko?" Miƙewa Tayi Tareda Cewa, "Kayi Hakuri Bari Na Shirya ɗin." daga nan Kuma tafita Zuwa ɗakin ta. Can Ta Sami Su Sajida Na Shiri Kan zasu Wuce Tunda ga yanda Lamari Kuma Ya Rincaɓe. Gefen Gado ta Zauna Gamida Cewa, "Wai da Gasken dai Wucewar Zakuyi?" "Tau me kuma Zamu Tsaya yi Asiya?" Aunty Asabe Ta'amsa mata tana Ƙokarin Sakawa Yarinyar ta Kaya Ajikinta. "ALLAH dai yajikanta Yayi mata Rahma Shine Kawai Abin Cewa dan Abin da Matuƙar ban Tausayi wallahi." Sajida ce Mai Wannan Maganar A Yanzun itama tana Ƙokarin Cusa Kayanta da na Ƴar Yarinyarta Yar Shekara 6 Acikin Jakkah! Aunty Asabe Tace, "Tau Yaza'ayi da Lamarin Ubangiji? Wa'azi dai Ai Ana Ganinshi A duniyar Nan Saidai Zukatan Mu ne Suka Koma Kamar Na dutse Muna ƙin ɗaukar Darasi." "ALLAH dai Yasa Mucika da Imani." Abinda Maman Asharaf Tafafa Kenan Kafin Tamiƙe Tana Faɗin, "Kedai Safiyyah Ba inda Zakije Dole Kijira Indawo." Safiyyah Ta Zumburi Baki Alamun dai bata so ta Zauna itaɗima tafi so Tawuce Shiyyasa Tayi ta Kallon Su Aunty Asabe dan Susa Baki Amma sai Sukayi Biris da ita Alamun dai Suna Goyon Bayan Maman Asharaf Kenan Suma dai. Dan Haka Kawai Tamiƙe tabar Masu Ɗakin Tanufi Falo Tana Ƙunƙuni. Maman Asharaf dai Bata Sake mata Magana ba, madadin Hakamma Sai Ta Nufi Bathroom dan Yin Wanka Harta kama Ƙyauren Ƙofa Sai kuma tatsaya gamida Juyowa tana fadin, "Yawwa Aunty Asabe Nace Yaza'ayi da Wannan Kayan Tau Yanzun?" "Nima Abunda Nake ta Nazari Kenan Wallahi! " Sajida ce Mai Wannan Maganar. Aunty Asabe Tace, "Ki Rabasu Kashi Ukku Kashi ɗaya Ki Ajiye Muku Zai Maku Amfani ɗayan Kuma Tunda Safiyyah Na Nan Ko kuma Kafin Mutafi Zamu Shirya Su A Leda-Leda Ki Rabawa Makwabtanki Musamman Masu Ƙaramin ƙarfi daga Cikin Su Sauran Kuwa Akai Can Gidan Rasuwar dan Zai Musu Amfani dan Ba Wani Girki Zasuyi ba Nasani." "Good Idea! Aunty Asabe ALLAH yabar Mana ke dai wallahi." Maman Asharaf da Sajida Suke Faɗin Hakan. Murmushi Kawai Auntyn Tayi because Basa Yanayi Mai daɗi da Shaƙiyancin Sai Ya wuce Haka. A gaggauce Maman Asharaf Ta Shirya Tayiwa Su Sajida Sallama Kan Sai Sunzo dan Sune Zasu Kawo Kayan Gidan Gaisuwar Idan Suka Gama Shirya Sun Kamar Yadda Suka Tsara. ************ A Hankali Yake Ƙiƙorin buɗe Idanuwan sa Yana Mai Ƙokarin Tantance A Ina Yake? Ya Yunƙura da Nufin Tashi Yaji Duk Jikinsa A Tankwashe babu Wannan Damar, dan Haka yabi Hannun Nasa da ke Maƙale da plaster Harzuwa ga Inda Aka Saƙala Gorar Ruwa da Ake Masa Ƙarin Su. Sa'annan Yadawo ga Kallon Nasa ga Wanda ke Riƙe da Hannun Nasa Ƙaninsa ne Abubakar Sai Yasami Kansa da lumshe idununsa Cikin Ƙokarin Tambayar Kansa Dalilin Zuwan Sa Asibiti. Daga gefensa Yaji Innarmu Na Tambayar Abubakar Cewa, "Ya Farka ne?" Abubakar Yagirgiza mata Kansa Nufin dai Yafarkan Kenan. Innarmu Ta dinga Yin Hamdala ga ALLAH Tareda Ƙara tsarkake sa Kafin Tace, "Tau Ai Saika Kira Likita Ko? Tunda Yace Musanar dashi In Yafarka." Wayyanan Kalaman Suka Sanyawa Ƙwaƙwalwar Abdul-wahab Caji Hakanan Komai Yasoma Dawo Masa Tiryan-Tiryan. Idan Zai Tuna Fa Gidan Su Khaleesat Yaje Domin Halartar Ɗaurin Auren ta Aka Cemasa ta RASU!!! Da Sauri Yamiƙe Zaune Yana dube-dube Kafin Yakalli Su Innarmu Gamida Cewa, "Innarmu da Gaske ne Abunda Naji? Eh Dagaske ne Khaleesat Tarasu? Ko kuwa Mafarki Nayi?" Duk Suka Rufu A Kansa Suna Masu Ƙokarin Dannarsa Akan Zabure-Zaburen da Yakeyi. Abubakar Nacewa, "Yaya Inaga Mafarki ne Kayi Amma Khaleesat Bata Mutu ba Tana Ray...". "KARYA NE!!! KHALEESAT TARASU NAGAN GAWARTA DA IDONA!!!!" Kai da Ganin Yanda Yake Maganar Kasan Baya Cikin Hankalinsa Ƙokarin Ma Yake Ya Turesu Yafice daga ɗakin. Dole Innarmu Tafice da gudu Zuwa Kiran Likita Kan Yakawo Masu Agaji. Tare Suka Dawo da Likitan Inda Tuni Abdul-wahab Yayiwa ɗakin Kaca-kaca Sai Ihu! Yakeyi Yana Sambatu. Dole Sai da Suka Samun Ƙarin Wasu Likitocin Kafin Aka Danne sa Aka Turtsa Masa Allurar Bacci. Duk Ƙokarin da Yakeyi Na Yatashi Yayi Hargagin, Allurar Tahana Masa Wannan Damar. dan Haka sai Ya Koma Yana mai Lumshe Idanunsa Jikinsa duk Ya Mace. Ahakan idanun Nasa Suka Lumshe gabaɗai Yayinda wasu Hawaye Suka biyo ta Gefen Idon Nasa. Daganan Kuma Yayi tsit! Alamun dai Baccin Yatafi dashi Karfi Da yaji. Gefe Likitocin Suka Koma Suna Sauke Ajiyar Zuciya Kafin Suka Sharce Gumi Tareda Ficewa daga ɗakin. Innarmu Kam Kuka take Tayi Haka Zalika Shima Abubakar Sai Hawaye ke kwararo Masa. Yarasa ƙwarin gwaiwar Lallashin Innarmu. Suna Cikin Wannan Halin ne Ango Yusuf da Tawagar Abokan su Suka Iso Dubiyar Jikin Abdul-wahab ɗin. Wanda Hakan yatirsasawa Innarmu toshe Kukan Nata Tajawo tasbaharta Taci gaba da salati. Shima dai Abubakar ɗin Share Hawayensa Yayi Yajawo Gilashinsa Baƙi Yaɓama A Fuskarsa. Duk Suncika ɗakin Sai Surutun Su Ketashi Abubakar Yajawo musu Kujerun Roban dake Gurin Wasu Suka Zazzauna Yayinda Wasun Sukai Tsaye dan Bazai Isheshu Ba. Duk dauriyar da Yusuf Yakeyi Sai da Yakasa Yafashe da Wani Irin Kuka Kafin Yakifa Kansa Kan gadon da Abdul-wahab ɗin ke Kwance Yana ta Aikin kukan Kamar Macce. Gabaki ɗaya ɗakin Yayi tsif Innarmu kam da Dama A Wuya take sai Tayi Hanzarin Fita daga ɗakin Zuwa Harabar Asibitin Tasamu Ƙarƙashin Dalbejiya ta Zauna Tana Mai Ci Gaba da Jan Carbinta Kuka Nata Ƙokarin taso mata Yayin da Tawakkalin ta Ke Kokawa dashi domin Hana Sa Zuwan. Acan Kuwa ɗakin Duk Abokan Nasu sai Sukai Caaa! Akan Yusuf ɗin Suna Aikin Basa Magana. Yayinda Abubakar Yarasa Wannan Jarumtar Illai Hannayen sa da Yaharɗe A Kijinsa Yakoma Gefe Yana Kukan Zuci Wanda Akace Yafi Na Zahiri Ciwo. Hankincip Yusuf Yasa yana Share Hawayen sa Kafin Yaɗago Yadubi Abubakar Yace, "Tunda Muka Kawoshin Ya farka Kuwa?" "Ya farka, Saidai Allurar Bacci Sukayi Masa da Ya farkan Dan Sunce Amfi Son Yayi Baccin." Abubakar yabashi Amsar Batareda Yadamu Yasan A Yaya yayi Maganar ba. "Amma Ayi Haka Mutum Yayi ta Bacci Ba Ci Ba sha..." Wani daga Cikin Abokan Kansu da Ake Kira Shamsu Shine Yayi Wannan Maganar Yayinda Wanin Shima daga Cikin Su Mai Suna Abba Yace dashi, "Ai tunda Kaga Sun Masa Hakan tau Shine Dai-dai tunda Aikin Sune Su." "Hakane Kuma. Tau ALLAH yatashi Kafaɗunsa Yabashi Lafiya!" Shamsu ne Mai Wannan Maganar. Yayinda Duk Sukayi Tarrayah Gurin Cewa, "AMEEN YA ALLAH!" Sunɗan ɗauki dogon Lokaci A gurin Kafin Sukayi Musu Sallama Kan Zasu Wuce Abubakar ne Yayo Musu Rakkiya Suka Biyo ta Inda Innarmu Ke Zaune dan Yima ta Sallama Sai Suka Sameta Tana Sallah! dan haka Sai Suka bar Sallahun Abubakar Yasanar Mata Cewa su Sun Wuce. Kusa da Zasu Hau Baburan su wasu kuwa Kk Napep Ango Yusuf Yaja Abubakar gefe Suna Tattaunawa kan Ciwon Na Abdul-wahab ɗin. Abubakar Yace, "Ya Yusuf Wallahi Yaya yana Cikin Wani hali Kasan shi dama da Halin Nasa ba Komai yake Iyama Juriya Akai ba. Sanda Yafarkan Kamar Wani Taɓaɓɓe Shine ma dalilin da Yasa Likitocin Suka Danna Masa Allurar Bacci. Ni Tsoro na Kar Yayamu Yagamu da Ciwon Hauka ta Sanadi yar Wannan Masifaffen Son da Ban Taɓa Ganin Irin sa A Wannan Zamanin Namu Ba... " Abubakar Yaƙarshe Faɗar Hakan Cikin Rawar Murya Kamar zai fashe da Kuka. Masu Karatu Zan ɗan Nisa Anan Muje Zuwa A page na Gaba Tareda Alkalamin FA'IK. [9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....27 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Yusuf da Jikinsa Shima yayi sanyi Yace, "Kadaina Tunanin Hakan Auta Insha'allah Zaiji Sauki. Damuwa Ce Kawai Tasashi Haka Bi'iznillah Zai Warware, Kaidai Kawai Muyi ta Adu'a ba Abunda yagagari Ubangiji." Abubakar Yacire gilashin da ke Fuskarsa Kafin Yasa kyalle Yashare Hawayen da ke Zubo Masa Gamida Cewa, "Insha'allah Muna Fatar Hakan Yaya." "Yawwa Auta Sannan dan ALLAH kadinga Ɓoye Damuwar ka Saboda Kaine ƙwarin gwaiwar Innarmu Kaine kuma Mai Lallashinta Kaga In Kaima Aka Gagara Samun Hakan daga Gareka Damuwar Sai tayi wa Innarmu Yawa." Abubakar Yagirgiza Kansa Yanajin Tabbas Abinda Yusuf Ke Gayamasa Gaskiya ne. "Ina Maman Walida Kun Sanar Mata ne?" Yusuf ya Tambaya "Eh Tana Ma Kan hanya! Nama kirasun ɗazun tace Suna Dai-dai Lambar Tureta." Yusuf Yace, "Ah Sun Kawo ma Yanzun ma Zaka ganta Sun Iso. ALLAH Yakawo su Lafiya, Bari Inje Suna jira na Anjima Zandawo Insha'allah." "A'a Ya Yusuf Kai Zaman ka dan ALLAH Zirganiyar Ai Tayi Yawa!" Yusuf Yahararesa tareda Cewa, "Amma ma Kaɓatamin Rai Auta. dan Ma Ga Ayanayin da Abun Yazo da Akwai Wanda Zai Zauna da Abdul-wahab ɗinne Sama dani? Pls karka Sakemin Irin Wannan Zancen Bana so!" Abubakar Yace, "Dan ALLAH kayi Haƙuri Ya Yusuf ban Faɗa da Nufin ɓatama ka Rai ba Nima Yanayin ne na duba." Yusuf Yace, "Duk-da Haka Nidai. Amshi Ga Abinda Ke Hannuna Koda Za'a Buƙaci Wani Abun." Har Abubakar Yatashi Cewa Yabari Amma da Ya tuno Yanda suka kwashen Yanzun. gudun Sake Wani Laifin Sai Yasa Hannu Yaƙarɓi Kuɗin Gamida Cewa, "ALLAH Yaƙara buɗi Ya Yusuf Yakuma bawa Abdul-wahab ɗinmu Lafiya Yakuma Fitar Masa da Wannan Masifaffen Son A Ransa Ya Bashi Wata Yarinyar Wadda Tafi Wannan da Yake So." Cikin jin daɗin Adu'ar Tasa Yusuf Yarumgumo Kafaɗar Abubakar ɗin Suka Nufo Inda Abokan Nasu Shida Abdul-wahab Ke Jiransa Yana Cewa, "Ameen Autan Innarmu Autanmu Muma, Amma Kadaina Zargin Masifafen So Ne ALLAH Kaɗai Yasan dalilin sa Nayin Haka Kuma Ƙiyayya ma Tana da tata Ranar Balle Kuma Soyayya dan Haka Mu kyautata masu Zato Mu Kuma bisu da Adu'ar Fatar Alkairi daga Shi har MARIGAYIYAR Kaji Auta?" Abubakar Yagirgiza Kansa Cikin Gamsuwa da Maganar ta Yusuf ɗin. Yusuf yaɗan Bubbugi Kafaɗarsa Gamida Cewa, "Yawwa Sai Anjima!" Nandai Sukai Hannu da Yusuf Tareda Sauran Abokan Yana Mai Yi Musu Godiya daganan Yajuya Yabarsu Suna Ƙokarin tayarda Ababen Hawan Nasu dan Su Wuce. Tafe Yake Yana Tambayar Kansa Kan Maganar da Yusuf Yai Masa Wai Ƙiyayya ma Tana da Tata Ranar tau Ta Ina? Can Cikin Kunne sa Yaji FA'IK Na Raɗa Masa Cewa, "Maganar Yusuf Gaskiya Ce dan In Ana Nuna Ma Ƙiyayya Kafi Sanin Ciwon Kanka dan Bazaka Yarda kai Abinda Zaisa Maƙiyan Nan naka Suyi maka Dariya ba." Afili Abubakar Yace, "Hakane kuma Fa!" Kafin Yajawo Wayarsa dake Cikin Aljihu tana ta Ringin Number Maman Walida Ce yagani nata Yawo Kan Fuskar Wayar Tashi dan haka Yaɗaga Tareda Yin Sallama Bayan Ta'amsa Masa Sallamar Take Sanar da shi Gata Cikin Asibitin Suna ta Wane Waje ne? Jin Hakan Sai yajuyo zuwa bakin Gete Yana mai Yi Mata misalin Inda Zasu Haɗu. Tau Abdul-wahab Nima dai Nace ALLAH Yabaka Lafiya Saidai Anya Zaka Samu Wacce Kafi So Fin Khaleesat? Tau Bazan ja ba Tunda ALLAH Aka Ce. *********** Gidan Makokin Fa? Ga Alama Yau Ake Adu'ar Ukku dan Taron Yau Yafi Na Kowane Lokaci Ga Kuma Malamai Nan Sai Ƙus! Ƙus! Sukeyi Atsakanin Su Alamun dai Yaza'a Tsara Abun? Can gefe Na Hango Dady Zaune Riƙe da Carbi Yana ta tasbihi Cikin Kwana Ukku duk Yazube Kamar Wanda Yayi Shekara yana Jinya. gefen sa Ya Nuradeen ne Ke Zaune Shima Sai Aikin Kallon Mutane Yake. A iya Cewa Yama fi Dady Ramewa dan shi Harda Ɓaki Yayi Kuma Har Yanzun Idanunsa Basu daina Zubar da Hawayen KEWA Da SABO ba yana dai Ƙokarin ɓoyewa Mutane ne Halinda Yake Ciki! Ƙara Tambayar Kansa yake Shikenan fa dai Dagasken Khaleesat ɗinsu Ƙanwarsa Abar Ƙaunar sa da Baya da Wata Ƴar Uwa sai Ita ta tafi Tafiya kuma ta Har'abada Tabarshi Shikaɗai Ba Ƴa ba Ƙanwa. Nan take Yashiga Karanto "Innalillahi waa inna Ilaahin Raaju'un." Karanto tan da Yakeyi Sai Yasamu Nutsuwa. Cikin Gidan Na Nufa Inda Matan Suke Birjik! Momy ce Zaune Tsakiyar Yan Uwanta da Abokai Harma da makwabta tana Cikin Hijab Hannunta Kuwa riƙe Yake da Carbi Duk wanda ya San Momy Yakuma ganta A Yanzun Tabbas Zai shaida Cewa Ba kaɗan Mutuwar Ta Taɓata Ba dan ta Rame Sosai Haryanzu Kuwa idanun ta Basu daina Zubar da Hawaye ba. Daga Wajen dai ɗan Aike Yashigo Yana Sanar Musu da Cewa Za'a Fara Adu'a. dan haka Kowa Yanutsu daganan Cikin Matan Wata Malama Tasoma Karanto Adu'o'i Masu Ratsa Zuciyar duk Wani Mumuni. A Can ma Wajen hakance Takasance Wani Malami Yasoma Kafin Yaba Ma Wani Shima Yayi Tasa. Haka dai Aka Kammallah Adu'ar Cike da Alhini daganan Mutane Suka Soma Haramar Tafiya Musamman ma Na nesa Irin Yan Uwan Dady na Garin Adamawa da kuma Na Momy Yan Kogi. Nanne fa Mutuwar Tadawowa Su Momy Sabuwa Fil Momy dai Tashiga Kuka Wiwiwi Dole Yan Uwanta Sukayi Shawarar Mami Iyabo Ta Zauna taɗan Kwana Biyu Hakanan Ya Nuradeen Shima Yabar Matar Tasa Nan In Yaso Sai yadinga Zuwa. Tau Zaman Nasu Anan Yayi Ma Momy Rana dan dai Sune Masu Tausarta Musamman ma Mami Iyabo. Hakanan Dady Yaɗan Jima Kafin Yakoma Bakin Aiki Saidai Kullum Yana kan Kira Dan Ƙara Kwantarwa da Momy Hankali! Hakanan Shima Ya Nuradeen Bai Fasa Kira ba ko yaushe! Wannan yaɗan Samarwa Momy Salama Acikin Rai Ba wai dan ta Manta da Khaleesat ɗin ba. ********* Ta ɓangaren su Dr. Jabir Kuwa Tun Bayan Kamallah Zaman Makoki Yasoma Shirye-shiryen Tafiyar da Zaiyi, Shi Kansa Idan Kagansa Zaka Shaida Cewa Mutuwar Ta Taɓa Shi Shima Saboda Komai Yanayin sa ne Sukuku! Komai dai Na Tafiyar tasa Ya Kammallah. Da Yammacin Yau da Yakasance Jibi Zasuyi Tafiyar, Maman Asharaf ce keta kai Kawo A cikin gidanta Inda Take Ƙokarin haɗa kan gidan Abunda Zai lalace tuni Tafitar ta kyautar ga Maigadin gidan Hakanan duk Wani Abu da zata buƙata A tafiyar tata tahaɗa Gidan ma Ta kimtsa shi Sosai. Yanzun Girki da Zasuci takeyi Musu Tana ta kai kawo daga Kitchin ɗin zuwa Falo Asharaf kuwa Yana kan Kujera Yana ta Aikin Buga Tv game Sai Surutu Yakeyi. Yanzun Zaman Lafiya A gidan Yadawo dai-dai Lokacin Yayi parkinq ɗin Motarsa Yafito rike da Wasu Fayel gefe ɗaya kuma Labcaot ɗinsa Ce Fara kal! Yariƙe. Maigadin gidan Yakira Yakwashe ledojin Suka Nufi Cikin gidan. Da da gudu Ashraf Yarumgume Baba Nasa Yana masa Oyoyo, Shikuwa yacaɓeshi Yaɗora Kan Kafaɗa Yana Tambayar sa Yau Me Momynsa Tadafa Musu ne da Yacika Gida da Kamshi Ne Haka? Maigadin kuwa na Ajiye ledojin Yajuya Yakoma Wajen Aikinsa. Yayinda Dr Jabir yabishi da Kalmar "Sannu da Ƙokari, Inna Fito Sallar Magrib Zamuyi Magana." Maigadin Yarusuna yana Cewa, "Tau Shikenan Allaji Afito Lafiya." Dai-dai Lokacin ne Maman Asharaf Tafito daga Kitchin Tallabe da Faranti da tajere Manyan Kololi A sama da Jug! Wani Kallo Aka bita dashi Mai Tafiyar da Hankali Kafin Yace, "Madam Sannu da Aiki?" sai da Ta Mayar masa da Martanin Kallon Itama Kafin Tace, "Oga barka da Zuwa." "Barka kade Madam." yafaɗa Tareda Zaman kan dogowar Kujera dake Falon Asharaf kuwa Na cakume dashi Kamar Wanda Za'a ƙwace Masa Shi. Remot Yajawo Yasoma Laluben Tashar ALJAZEERA Dae-dai Lokacin Maman Asharaf ta Tsiyayo Ruwa Farare tasa daga Cikin gorar Faro da Taɗauka daga cikin ɗan Karamin Frij ɗinda ke Girke Acikin Falon Nasu. Karɓar Cup ɗin Yayi Yana Kaiwa Bakinsa Sai da Yashanye tas Yamiƙa mata kopin Gamida Cewa, "Alhamdullah Matar Kirki ALLAH yayi maki Albarka." Murmushi tayi tareda Cewa, "Ameen Tareda kai Mijin Kirki." "Ga dukkan Alamu Komai Is Ready dan Falon Ma Naga Yanuna Alamar Hakan." Dr Jabir yafadi Hakan Yana mai Ƙarewa Falon Kallo da Shaƙar daddaɗan Kasmhin turaren dake tashi A kowane Saƙon Na Falon. "Insha'allah! Gobe Sai Kitso da Lalle Munyi Waya ma da Sajida Tace Inje Goben Unguwar tasu Za'a Min Kaga Gobe Inzaka Fita Saika Ajeyimu Ko?" Maman Asharaf Tadire Maganar Tareda Kallonsa. Lumshe Idanunsa Yayi Cikin Alamun Yar gajiya dake Tareda shi Kafin yabuɗesu Tar Akanta Sa'anan Yace, "Ba Wannan Maganar Coz Gobe Ina da Abubuwan yi da Yawa Kuma kinga Goben Kaɗai Ce Damu A Ƙasarnan, So In Zaiyu Ita Mai Lallen da Kitso Tazo Nan gida ta mike Za'a Biyata Ko Nawane." Ta Zumburi Baki Irin Shagwabar Nan Tareda Cewa, "Kai HUBBI! Bafa Guda Bace Mai yin Kitson daban Mai Lalle daban....." "Tau duka Biyun Suzo Kowa Yayi Aikinsa Sai Abashi Haƙƙensa." Yakatse ta da Faɗar Hakan. A Bazata Suka ji Shima Asharaf Ya Maimaita Abinda Baban Nasa Yafaɗa. Bashiri duk Sukayi Dariya. Anan Zan Nisa Muje daku Chapter ta Gaba. Tareda Alkalamin FA'IK. [9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....28 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. NOT EDITIN....... 🙏 Bissmillahi Rahmanin Raheem Dai-dai Lokacin Kuma Masaalatan Unguwar Suka Soma Kwallah Kiraye-kirayen Sallar Magrib. Dan Haka Dr Jabir Yamiƙe Yana Cewa, "Kun Shiririta ni Har An Soma Kiran Sallah da Kuma Naso naɗan Watsa Ruwa Inɗan Rage Gumi Nan (Zufa)Kafin Inje Massallaci." Maman Asharaf Ta Kwashe Fayel ɗinda Yashigo dasu da Kuma Labcaot ɗinsa Tabisa dasu Tareda Cewa, "Bawani Gumi da Kayi! in Ma Kayin Ai Gumin Naka daɗi ne Dashi Dan Yafi Almiski Kamshi." A hanzarce Yajuyo Yana Kallonta Cikin Son Tabbatar wa Kansa Itace Kuwa Tayi Wannan Maganar? Itama ta Fahimce shi dan Haka ta Maze Abinta Ta Raɓashi Zata Wuce yayi Hanzarin Jawo ta Jikinsa Tareda tsare ta da Manyan Idanunsa da Ke rikita duk Wani Mutum da ya Kalle sa Yace, " Sereously Maman Asharaf Ki Maimaita Abinda Kika Faɗa Nayi Missin ɗin Jin irin Wayyanan daddaɗan Kalaman daga gareki tun Sanda Aka Soma Shirin Aurena da Marigay...." Tai Hanzarin taresa ta hanyar Cewa, "Kaga Dr Anfa Soma Haramar tayarda Sallah Ko So Kake Shima Sai Ka Rasa Jam'i Kace Laifin Mu ne?" Hannunsa Yakai Kan Lips ɗinta da Yasha witlips Sai Maiƙo Sukeyi, Tayi Hanzarin Kwalawa Asharaf kira Dr Jabir Yayi Hanzarin Saketa Suna Dariya. Dai-dai Lokacin Asharaf ɗin Yazo Yana Cewa, "Momy Jani(gani)" Taja Hannunsa Haryanzun Bata Bar Dariyar ba Tana Faɗin Zomuje Kayi Arwallah Kabi Dadyn ka Zuwa Masjid. Ɗan Harar ta Dr Jabir Yayi Tareda Nuna Kirjinsa Yace, "Ni Ko? Zamu gauraya ne. Sanda Wata Zata Shigo Hanunna Asharaf Na Ina?" Gwalo tayi Masa Tareda Cewa, "Yanzun dai Natsira ɗin." Duk Suka ɗunguma Zuwa Cikin Sukayi Arwallah Shida Asharaf ɗin Suka Nufi Massallaci Bayan Yacanza Suit ɗinda Ke jikinsa Zuwa Jallabiya Kalar Ruwan Zuma Sai Tashin Ƙamshi Takeyi. Ita Kuwa Nan Ta Kabbarta Tata Sallah Acikin ɗakin. ********** Duk Yanda Mamar Walida taso dauriya daga Halinda ta Sami Ƙanin nata Ciki Sai Takasa Tafashe da Wani Irin Kuka Mai tsuma Zuciya. Kai da ganin Yanda Abdul-wahab ɗin Yake Baccin Kasa Bana Lafiya bane Kuma Ba Acikin Hayyacinsa Yakeyin sa Ba. Abubakar ne Yake Tausarta Yana "Aunty Idan ke Kinyi Haka Mu Muyi Yaya Kenan? Kiyi Hakuri Dan ALLAH ya Abdull Adu'ar mu Yafi Buƙata A Yanzun Ba Kuka ba." "Tayaya Bazanyi Kuka ba Auta? Wannan Wace Irin Jarabar SONEE? Dubi Kaga Halinda Abdull Yake Ciki, duk Wanda Yasan Abdull Ada Yazo Yanzun da Wuya Ya shaidashi Duk Dalilin SO! Sukuwa Iyayen Khaleesat waɗanne Irin Mutane ne Mararsa Imani ne da......" "Aunty!!!! Dan ALLAH Kibar Wayannan Maganganun Tunda dai Yanzun duk Mai Faruwa ta Faru Abu Mafi Muhimmaci Shine Yaza'ayi Mu Samawa ɗan Uwan mu Lafiya Yadawo Hayyacinsa Shine Magana." Abubakar ne Mai Wannan Maganar Yana mai Ƙokarin maida Kwallar da Ke Son Zubo Masa Shima. Babu Shakkah! Abdul-wahab Yana Cikin Wani Hali da Kowaye kai Inka Ganshi A Yanayin Zaka Tausaya Masa. Cikin Barcin Nasa Sai Surutu Yakeyi, "Khaleesat Bamuyi Wannan dake Ba Baki Gayamin Zaki Mutu Ba Fa? Munyi dake Zamu Rumgumi Ƙaddarar mu Muyi Hakuri Akan Hukunci su Dady Akamu. Amma Meyasa Zaki Karya Alkawalin Nan Khaleesat? Mezai Sa Ki Mutu Ki Barni Acikin Wannan duniyar? Me Zanyi A Wannan Duniyar da Babuki?" Duk Sun Rufu A Kansa Suna Sauraren Sambatun Nasa. Cikin Kasalar Jiki Abubakar Yakai Tafin Hannunsa Kan Bakin Abdull Tareda Furta,"Innalillahi Waa Inna Ilaaihi Raju'un! ALLAH Yakawo Maka Ɗauki Ya Abdull." Dai-dai Lokacin ne Kuma Innarmu Tashigo Hannunta Riƙe da Carbi dan Sanda Maman Walida Ta'iso Tana Sallar Isha'i Kafin Kuma taɗora da Shafa'i da Wutiri. Shiyyasa ma Basu Gaisa Ba da Maman Walida Ba. Ta kalle su daga Yanda Sukayi Cirko-Cirko Tana Tambayar Su Lafiya Kuwa? Maman Walida ce Tashare Hawayenta Tace, "Yanzun Mama Haka Abdull Yakoma? Wannan wane Irin Masifa Ce?" Innarmu tagirgiza Kai Cikin Alhinin Abun Kafin taɗora da Cewa, "Kindai Gani Ɗazun Ma Da Yafarka Nema Yayi Yafice daga Asibitin nan Sai da Likitocin Suka danna Masa Allurar Bacci, Ai kedai Lamarin Abdul-wahab Sai du'i Kawai." Maman Walida Tajawo Kujera Tazauna dan dai A Halin Yanzun Jitake inta ci Gaba da Tsayuwa Itama Zata Faɗi dan dai Babu Shakkah Ƙafafunta A Yanzun Baza su Iya ɗaukarta ba. Dan haka Ta rafka tagumi Cikin Salalar Hawaye. Innarmu Tace, "Bafa Haka Yakamaceki Ba Auntynsu Adu'a ce Kawai Abunyi." Maman Walida ta Girgiza Kai kawai Tareda Sanya Hannuta ta Share Hawayen da keta goslow Afuskartata. Innarmu Tace, "Ina Yaranne Kardai Kice Bakizo da Ko ɗaya ba?" Cikin Nauyinda Bakinta Yayi Mata Tace, "Su Walida Suna gida tareda Babansu Kinsan Makaranta Shikuwa Hanif Yana nan gida Nabaro Inda Maman Nuwaila(Makwabciyar Su Innarmu )." " Tau Kinyi Sallah?" Innarmu taɗora da Wannan Tambayar. Girgiza kai Kawai Maman Walida Tayi. "Tau tashi Kije kiyi Ruwa Na Nan Cikin Buta ta Gurin Shimfiɗa." Maman Walida ta tashi Tanufi Yin Arwallah Tana Tafiya tana Waigen ɗan Uwan Nata. Haka Suka Kasance Cikin Juyayi da tarin damuwa Akan halinda Ɗan Uwan Nasu Ke Ciki, Ko ƙadan Basu Runtsa ba domin dai Abdul-wahab Hauka Yakeyi tuburan! Wanda Kuka kam! Sun Shashi Harsun godewa ALLAH. Dole Bashiri da Safe Bayan Dogon Bincike da cike-ciken Fayel da Akayi Aka Turasu Asibitin Mahaukata dake Cikin Ƙaramar Hukumar Kware. Zo kaga Tashin Hankali Wurin Wayyanan Bayin ALLAH! Surutu Kala-kala Yakeyi Yayi Kuka? Yayi Dariya Yayita Harare-Harare. Wallahi Abun Gwanin ban Tausayi Musamman ma dai Ada Kasan Abdul-wahab ɗin Mutum mai Matuƙar Natsuwa!. Bayan Isarsu Asibitin ma dai dogon turanci ne Aka tsaya yi Siye wannan Kati Cike Wannan Rasiti Yi Wannan Tes! ɗin Kafin Fa Kuma Aka dangana su da inda Za'a Kwantar dashi. Nanma dai duk wanda kagani Gwanin ban Tausayi Saboda ga Mutum dai Har Mutum Amma Yana Hauka. Wasu Sha-shaye ne Sila Wasu Kuwa Asirine Wasu kuwa Rashin Lafiya ce Ya allah Haɗari ko dai Ciwon Kawai. Su Innarmu Fa Sunga Rayuwa Irin wacce tunani da Hasashen Su bai taɓa kawo Masu Cewa zasu Riski Kansu Acikinsa ba. Su Innarmu da Maman Walida Sun Kasa daina Hawaye Yayinda Abubakar ke Kukan Zucci Wanda Akace Yafi Na Zahiri CIWO. Haka Suka Zauna Asibiti Na Tsawon Lokaci Suna Jinya Wanda Suka tsayu ba dare ba Rana Wajen Kai Kukansu ga ALLAH Wanda Babu Shakka sai suce Adu'ar ma tafi tasiri Sosai Sama da Maganin da Akeyi Masa. Kuɗi Kam Ancajesu Sosai wanda duk wani ɗan Tanadi da Sukayi Jinyar Ta laƙume Shi. Damar su Basu Nema Gurin Kowa ba. ALLAH yarufa Musu Asiri Hakanan Yan Uwa da Abokan Arziki Suna Kan Hanya Gurin Ziyartarsu Gwargwado Kuma Kowa yazo Yakanyi Musu Hasafi. Zuwan Mijin Maman Walida Ukku Gurinsu. Yan Garejin su Abdul-wahab ma Mota guda Sukayo harda Ogan su Aka zo duba Abdul-wahab! Hakanan Abokan Karatun sa Bus ɗin Makaranta ta kawo su Suma. Shikuwa Yusuf Kullum tafe yake Tsakanin Kware da Cikin Birnin Sakkwato Hargida Yaje Yasami Su Momy Yasanar dasu Irin Halinda Abdul-wahab Yake Ciki Ai kuwa Suma Sunzo dubinsa Momy Kam da Kuwa Wiwiwi Tabar Asibitin NADAMA Iya NADAMA Tayita. Dady ma da Ya Nuradeen da Suka Shigo Gari Sunzo Dubiyar Sa. Wannan Na ɗaya daga Abinda Yaragewa Su Innarmu Raɗaɗi daga halinda Suke Ciki dan Al'umma Sunyi Musu kara Suka ƙara yarda Cewar da'akayi, AL'UMMA RAHMANE. Tau Cikin Ikon ALLAH dai Abdul-wahab Yadaina Sumbatun da Yakeyi da Surutai da Yawan Firgice-Firgece da Yakeyi. Shidai Gashinan Sukuku ne ba Magana Sai Ido da yake bin mutane Dasu, Tau Amma me? Suna Zaune Yau da Sanyin Safiya. Yayinda Shikuwa Yake Kwance Kan Gado Yana Lumshe da Idanunsa A hankali Yabuɗe Su yana Kallon bakin Ƙofa, Ai bashiri Yamiƙe Zaune Zumbur! Tareda Cewa, "Khaleesat?" da Wani Irin Mugum Mamaki Su Mama Suka Juya Suma Suna Kallon Inda Yake Kallon Khaleesat ɗince Kuwa Suma Suka Gani Tana tafe Yayinda Hawaye Ke Ci Gaba da Shatata A Fuskarta. Abdul-wahab Wata irin Zabura Yayi Yamiƙe Tsaye Tareda Nufar Inda Take Yana Mai Cewa, "Dama Ni Nasani Baki MUTU ba Khaleesat! Dama Ni Nasani Wallahi Bazaki Mutu Ki Barni Ba Dama ni Nasani Ƙarya Akeyi." Tare Suka Iso ga Juna Suka Rumgume Juna Cikin Wata Irin Matsainaiciyar Soyayya Mai haɗe da Wani Irin Zazzafan Shauƙin da Komai Ƙoƙarin Zuciya bazata iya danne sa Ba, Kawai Yazama Wajibi gareta ta Sallama. Kuka Wanda Ake Kira Kuka Suka Sanya Shida Khaleesat, Yayinda Bakin Abdul-wahab Yakasayin Shiru, "Khaleesat Ni Nasani Bazaki Tafi Ki Barni ba Ni Nasani Ƙarya Akeyi." Sai kuma Yajawo Hannunta Zuwa Wurinsu Innarmu da Maman Walida da Sukayi Mutuwar Zaune Wanda Ko kwakwaran Motsi Sunkasa Yi Duk Inda Jikinsu Yake Ɓari Yakeyi Tambaya Iri Ɗaya Sukeyi wa Kansun Shin Suma Sun Haukace ne Komeye? Suna Nan Cikin Wannan Halin Har'izuwa Sanda Abdul-wahab Ya'iso Garesu Fuskarsa Cike da Hawaye, Yasoma Jawo Hannun Innarmu Tareda Cewa, "Innarmu Taɓa Kiji Wallahi Khaleesat ce Dama Nace Muku Ƙarya ne Bata Mutu ba Khaleesat ɗita bazata MUTU ta Barni Ba Kuka ƙi Yarda Kuka ɗaukeni MAHAUKACI." Innarmu Muƙut! Tahaɗiye Wani Mugun Yawo da Yamaƙale Mata A Maƙwashi A sanadiyar tsayawar Wucin Gadin da Komai Nata Yayi. Tabbas Ga Hannunta Cikin Na Khaleesat Fa Kuma Ga Khaleesat ɗin Ita ma Gabanta Cikin Wani Irin Firgici Maman Walida Tamiƙe Tana Furta A'uzzubillah! Laaa'ilaha ilallahu Muhammadu Rasullullah! S A W. innahu Min Sulemanu Waa....."Kai Kasa Ƙarasa Tayi Tafice da Gudu daga ɗaƙin Tana Ihun Tashiga Ukku Itama ta Haukace. Yo Inba Hauka Ba Yaza'ayi Wanda Yamutu Yadawo harma Kaganshi? Dai-dai Ƙofa Taci Karo da Abubakar Yadawo daga Siyen Maganin da Likita Yarubuta Masu Hannunsa Riƙe da ledar da ke ɗauke da Tambarin Chamis ɗin da Yaje Siyen Magani. Aikuwa Maman Walida tacakumeshi Tana Kuka Sosai "Auta Nima Na Haukace Nakamu da Irin Ciwon Abdul-wahab Dan ALLAH Auta Kumin Gata Karku Barnin Inshiga Duniya Har In koma tsirara Kamar yadda naga Wasu Mahaukatan Nayi Ku Taimakeni Ku Kamani Ku ɗaure A Wuri ɗaya Har'izuwa Sanda ALLAH Zaiyi Ikonsa Akaina Kaji." Misalata Irin Tashin Hankalin da Abubakar Ke Ciki Bazai taɓa Yuwa ba Abun Kawai Sai Wanda Yagani. Tirkashi!!! Meke Shirin Faruwa ne Masu Karatu? Muje Zuwa Tareda Alkalamin FA'IK. [9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....29 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem Sai Kawai Yakama Auntyn Tasu Yarike Sosai! Yana karanto duk Adu'ar da tazo Bakinsa Yana tofa Mata, Kafin Ya'ankara Ta zube A Sume. Tashin Hankali Wanda Ba'a Samaka Rana Cikin Wata Irin Kuwa da Ƙaraji Yake Kira "Aunty!!!!!" yadurƙushe gabanta Yana Cigabada Cewa, "Duk Tafiya Zakuyi Ku Barni ne?" Dai-dai Lokacin Al'umma Suka Hankalta da Abinda Ke Faruwa Na take Kuma Suka Kawo ɗauki. Aka Tallabi Maman Walida Saman ɗan Gadon tura marassa Lafiya Zuwa Imerginycy Room Domin Bata taimakon Gaggawa. Dai-dai Lokacin ne Kuma Abubakar Yajuyo Yana ƙarewa Cincirindon Mutanen dake Gurin Kallo Ga Mamakinsa Kuma Sai Yaga Abdul-wahab ne Cikinsu Shima Cikin Tashin Hankali Akan Halinda Maman Walida Tashiga. gefen sa Kuma Khaleesat ce Itama dai Hankali Tashe. Dubawa Yasakeyi Domin Ƙara gasgata Abinda Idanunsa Ke Gane Masa Shin Mafalki Yakeyi Ko dai Shima Haukar Ce Ta Raɓeshi? A wanna Lokacin ne Abdul-wahab Yamatso Kusada Shi Yana Cewa, "Auta Kaga Abinda Nake Gayama Ku ko? Kaga Ƙaryar dai ce Khaleesat ɗita Bata Mutu ba ko? Ina Fatar Kai kam zaka Nutsu Ka Fahimce ni Ba Kamar Yadda Su Innarmu da Maman Walida Suka Kasa Fahimta ta ta ba." Wata Irin Hajijiya ce ke Neman kai Abubakar Ƙasa, Amma Sai Yayi Hanzarin dafe Bango Sa'anan Yalalubi Kujera Yazauna Lokaci ɗaya kuma Yasa duka Hannayen sa Biyu yadafe Kansa Yana Mai Ƙokarin Karanto "Innalillahi Wa Inna Ilaaihi Raju'un!!!" Kalmar da Yaketa Nanatawa Kenan Babu ji Ba gani Yana ji Duk duniyar na Juya Masa. Innarmu Kuwa Tunda Suka Baro ɗakin Suka Biyo Maman Walida da tayiwa ɗakin Fitar bindiga. Cikinta yaƙulle tamau Kafin Kuma Wata Irin Guduwa Mai Matuƙar Sauri ta Tasoma mata Dole Tadinga Kai Kawo tsakanin ɗaki da Toilet tana Fyace Majina da Gyafen Zanen ta Tareda Ƙara Tabbatarwa Kanta A Yau Wata Annoba Tafarmusu Sukam Sai Yanda ALLAH Yayi dasu Kawai. Acikin Wannan Halin ne taɗaga ƙafarta dakyar Tafito zuwa inda tun ɗazun takejin Hayaniyar. Kai tsaye gurin Abubakar ta Nufa tadafashi Tareda Cewar, "Auta Meke Shirin Faruwa Damu ne?". Dai-dai Lokacin Itama Khaleesat ta matso tana Kuka Tadurƙushe Gaban Innarmu Tareda Cewa, "Innarmu Ku Nutsu ku Saurare ni Wallahi Ban MUTU ba Akasine Aka Samu...." Innarmu tai Maza takoma Gefe tana kallon Khaleesat ɗin Yayinda Shima Abubakar Yaɗago A Firgice Yana Kallon ta Yana Kuma Ƙokarin tattaro dukkan Wata Jarumta tasa domin Karya Fece da Gudu Shima. Itama Innarmu Sai Kallon Khaleesat Takeyi ba ko kyaftawa. Tana Kuma Tambayar kanta Dama Haka FATALWA Take? Amma taji Ance FATALWA nada Siffa Mai Ban Tsoro Kuma Ita Bataga Haka ga Khaleesat ɗin ba? Ita kuwa Khaleesat Kukan ta Yatsananta, Yinsa Takeyi Kamar Ranta Zai Fita Saboda yanda taga Mutane Na Tsoro da ƙyamarta. Abdul-wahab yaƙaraso Gurinta Yana Cewa, "Khaleesat Kidaina Kuka Koda Kowa zai guje ki ni Ina Tareda ke! Ba MUTUWA Kikayi kika dawo ba ko fin Hakan kikayi bazan taɓa gudun ki ba." tajuyo tana Cewa, "Yawwa Abdul-wahab Ni Nasani Ko Kowa Yakasa Fahimta ta Kai Zaka Fahimceni Kuma Koda Kowa ya gujeni Kai Bazaka Gujeni ba." Tahaɗa Hannayen ta guri ɗaya tacigaba da Cewa, "Dan ALLAH Innarmu Ku Nutsu ku Saurare ni Wallahi Wallahi Nice Ba MUTUWA Nayi ba." Kalaman da Khaleesat keyi Kenan Wayanda Suka ɗan Fara Samarmawa Innarmu da Wata ƴar nutusuwar da Suka rasa tun a ɗazun, Suka Kuma jefa Su Innarmu Cikin Nazari da Tunanin Yakamata su Natsu su Saurareta. A wannan Lokacin ne kuma Likitan da ke Duba Maman Walida Yafito Yana Ƙokarin Cire Facemaks ɗinsa, Gurin Su Abubakar ɗin Yazo Yace, "Kune Yan Uwan Waccan patien ɗin Tamu Ko?" Abubakar Yaɗago kansa dake Matuƙar Sara Masa Kamar zai Rabe Biyu Saboda Halin Ruɗanin da Suke Ciki Yace, "Eh Mune." Likitan Yace, "Yawwa Mun Samu Yar Uwar taku ta farfaɗo, Tashiga Firgici ne Wanda Yasa daba dan Suman Tayi ba, tau Zata Iya Samun Bugun Zuciya Na Nan take. Tau Kuma Sai ALLAH Yagajarta Mata Wahlar ta Yatsaya A Suman Yanzun Ma Komai Ya dai-dai ta Zuwa Anjima Idan taɗan Ƙara Samun Hutun Ƙwalƙwalwa da Na Jiki Zaku Ganta tadawo Sumul." "Tau Likita Zamu Iya Shiga Muganta Yanzun?" Abdul-wahab Ya watso Masa Wannan Tambayar Batareda La'akari da Waye Yayi Masa Tambayar ba Yace, "A'a 4Now Tana Buƙatar Hutun ƙwalƙwalwa Dana Jiki Kamar Yadda Na sanar Daku, dan Haka Akwai ɓukatar Kubarta ɗin Zuwa Anjima." "Tau yayi Likita Muna Godiya! ALLAH yayiwa Rayuwa Albarka." Innarmu ce Mai Wanna Jawabin. "Ameen." Likitan ya'amsa Harya Wuce Kuma Sai Yadawo Yana ƙare Musu Kallo Cikin Mamaki Yace, "A'a Wannan Ba Patien ɗinmu Bane da Ba Lafiya?" Yayi Maganar da Kallon Abdul-wahab. Abubakar Yace, "Shine." Likitan Yayi Saurin Kama Hannun Abdul-wahab Da Tun Faruwar Lamarin Ketsiyaya Jini Saboda Fisge ƙarin Ruwan Da Akeyi Masan da Yayi Ba Bisa Ƙa'ida Ba. Yace, "Wannan Ai haɗari ne Yazaku Barshi Yataso Cikin Irin Wannan Halinne?" yana Wannan Maganar Yana Ƙokarin danne Hannun na Abdul-wahab da Plaster Kafin Yajashi Suka Nufi ɗakin da Aka Kwantar Abdul-wahab ɗin. Innarmu Tabibayansu Tana Faɗin, "Yaro Ai Mu Muna Cikin RUƊANI. wanda Ko A Rayuwar Mafarki Bantaɓa Ganin Irin sa Ba." Bai Saurari Abunda Innarmu Take Sanar dashi Ba Sai da Yadangana Abdul-wahab da Gadon sa Yaga Ya dai-dai Ta Komai, Sannan Yajuyo Yana Cewa, "Inna Kudaina Barin Irin Hakan Na Faruwa Yakamata Inkunga Irin Hakan Kuyi Ƙokarin Sanardamu Dan Mu Ɗauki Mataki da Wuri." Innarmu Tafahimci Sukaɗaine Suka San Ruɗanin da Suke Ciki Kuma Su Kaɗaine Suka San Halinda Suke Ciki Dan Haka Babu Wani Bayani tsayayye da Zatayi Masa dan Haka sai tazaɓi Amfani da Wayyanan Kalmomin Da Zasu Sanyaya Zuciyar Likitan Itama Kuma Su Hutar da Ita. Wayyanan Kalaman Kuwa Sune. "DAN ALLAH LIKITA AYI HAKURI INSHA'ALLAH ZAMU KULA!!!" daganan ta Lalubi Buta dan Komawa Toilet. Kallo ɗaya Likitan Yayiwa Khaleesat Kamar bai santaba Kamar Kuma ba Komai A tsakanin su Yajuya Yafice daga ɗakin. Ita kuwa Khaleesat Sai ta Nemi Kujera taxauna tana mai Ci Gaba da Fuskantar Abin Ƙaunarta Cikin Wani Irin Bugun Zuciya da Zallar DAMUWAR da Tayiwa Zuciyarta Kane-Kane. Tana ƙara jin Cewa Komai ma Yafaru SONEE SILLAR SA! Da Taimakon Iyayensu da Suka Kasa gano Girman Soyayyar dake Tsakanin su da Masoyin ta Abdul-wahab. ********** Tsakar Dare Suka Sauka A Ƙasar ta Maleshiya gama Lokacin Agogon Ƙasar ke Nuna Ƙarfe 2 Nadare Dai-dai. Tafe Suke A Matuƙar gajiye Musamman ma dai Maman Asharaf da Yakasance Wannan Shine Karo na Farko A Rayuwar ta da Tashigo Jirgi da Nufin Barin Ƙasar Nigeria, Kasancewar Shi Dr Jabir Sunsha Fita Zuwa Yin Wasu Kwasa-kwasai Akan Abinda Yadangaci Cututtuka. Shine ke Janye da Akwatinsu da Sauran Yan Shirginsu Yayinda Maman Asharaf ke Saɓe da Asharaf ɗin A Kafaɗarta Wanda Tuni Yayi Bacci. Taxi Yake Ƙokarin Tarar Musu Cikin Sa'a Kuwa Yasamar Musu Shatar Mai Tax ɗin da Zai Saukesu Har Masaukinsu. Kyawon Ƙasar da Tsarin ta Suka Sa Maman Asharaf ta daina jin gajiyar da take ji ɗazun, tabaza na mujiya tana Kallon Farar fata daketa kai Kawo A Ƙasar Kamar ba Dare ba Kowanensu Jibge da Coat. Ga dogayen binaye da Kuma Shuke-Shuken da Sukayiwa Titunan ƙawanya. Dai-dai Wasu Flat ɗin Gidaje da Korayen Ganye Suka Mamaye Gurin, Mai taxi ɗinsu Yayi Parkinq. Suna fitowa, Wani Irin Sanyi Yabuso su Wanda Sai da Maman Asharaf Taƙamƙame Jikinta Tana mai daɗa Shakar Iskar Mai Tafe da Kamshin Shuke-Shuken Itace Kala-kala da Sukayi wa Wurin dabaibayi. A ranta Tana ƙara tasbihi ga ALLAH Mai Falala Harma da Ni'imomi daban-daban, Lalle Maganar Nan ta Bahaushe Gaskiya ce, 'ALLAH ɗaya gari banbam' dan itakam taga zahirin Hakan. Dr Jabir Sallamar mai taxi Yayi Kafin Suka nufi Cikin Flat ɗin Kaitsaye Hawa Na Biyu Suka Nufa Bayan Sunkawo Wata ƙofa Suka Tsaya Dr Jabir Yafitar da Wani Samfurin key Mai Kama da Takarda Yaɗan Manna A Ƙofar Sai gata Ta buɗe. "Aljannar duniya!" Abinda Maman Asharaf Tace Kenan Sanda Suka kutsa Kai Cikin Gidan. Faɗar Irin Tsarin Gidan da Kuma Kyanshi Sai Ya cinye Mana yan Shafuka Namu dan Haka mai Karatu Nabarka da Wannan Hasafin Amma dai Falo ne ƙato da yake ɗauke da ɗakuna daban-daban Sumaɗin Kuma Cikin tsari akayi Su. Tsakiyar sa Wani Lallausan Carpet ne ke malale A gurin da kuma wasu Zafafan Kujeru da Suka fi Kama da Na gidan Sarauta suke Zagaye A Falon. Ga Kyakykyawan Center table ɗin Glass dake Gurin, Shima Sai ƙyalli Yake. Ko'ina Na Falon Sai Hasken Gluf Keta Fita. Faɗar Abinda Ke Zuciyar Maman Asharaf Gameda Risƙan Kanta A matsayin Wacce Zata Kasance Ma Mallakiyar Gidan Na Yan Shekarun da Gwammanti taɗaukar Ma Su Dr. Jabir Su Ƙara Ilimi Akan Wani Ciwo da Ya ɓulla kwana nan, Ba'a Bune Mai yuwa Cikin ɗan ƙanƙanin Lokaci ba. Ilai dai kawai Harta fara Ƙissima Irin gyran da Zata dinga yiwa Gidan. Wani Murmushi Yasubuce Mata batareda tasan Cewa Dr Jabir Na hankalce da ita ba. Sai da Taji Yace, "Baƙauya Kawai!l." Tayi hanzarin dubansa tana Dariya Kafin tace, "Naji dai, Ai da Kaine Ni Kila ma Fin Hakan Zakayi." Yakama Bakinsa yana Cewa, "Nine Ma Zaki ce Wa Haka? Lalle ma Yarinyar nan, Nifa Nama Lura Kwana nan Wani Reni Yashiga Tsakanin mu Fa? Kodai dan...." Sauran Zancen Yaraɗa Mata A Kunne. Me Zatayi Inba Dariya ba Tareda Rufe Fuskarta Cikin Matsanaiciyar Kunyar da Zancen Nasa Yasaukar Mata Kafin taɗora da Cewa, "Nidai Wallahi Bance Ba." "Ba Waninan Ai Nagane ki Kuma Wallahi In....." Maman Asharaf Tayi Wani Irin Sufa ta Rufe Masa Baki tana Cewa, "Dan ALLAH Kabar Zancenan, Wai Kai Kam Meyasa Baka gane Ka Girma Yanzun?" Yadanna Mata Cizo A Hannun Nata Tayi Saurin Janyewa Tana Kukan Shagwaba. Yakanne Mata Ido ɗaya Yace, "Meye Girma....?" Maman Asharaf Ta Taresa Wurin Cewa, "Nidai dan ALLAH Gajiya Nakeji Muje Kanuna min gurin, Inɗan Samu Inwatsa Ruwa Inyi Sallah In Sama mana Abinda Zamuci Ko Kai duk Baka Buƙatar Wannan?" Yasaƙalo ta Tareda Karɓe Asharaf ɗinda ke kwance Kan Kafaɗarta tun ɗazun Batareda Yasan Wainar da'ake Toyawa ba. Yana mai Cewa, "A'a Nima Ina Buƙata Uwargida Ran gida." Tau Dr Jabir da Maman Asharaf Asha Soyayya LAFIYA! Anan Kuma Zan Nisa Masu Karatu Muje daku Gaba Tareda Alkalamin FA'IK. [9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....30 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem!!! Shikuwa Abubakar Tun Wucewar Su Innarmu Bai Tashi ba Nan Yaci Gaba da Zama Cikin Kasalar Jiki da kuma Wani Irin RUƊANI Da Yayi Masa dabaibayi A Zuciya Sai Saƙe-Saƙe Kala-kala dake Zuwar Masa Cikin Zuciya, Wanda Taƙaimame Yakasa Na dafawa Akan MUTUWAR Khaleesat da DAWOWAR Ta Shidai Baiga Jana'izarta Balle dama can Yace Ya Tabbatar da MUTUWAR Tata, Labari Yaji Kuma Yayi Imanin Cewa, Bazai duk Mutane Su Taru Suyi Ƙarya Ba, Wani Sashe Na Zuciyarsa Yace, "Tau Suyi Ƙaryar Mutuwarta A Wanne Dalili? Saboda Basa Son Bawa Yayan ka Ƴarsu. Yaji Wata Zuciyar Tace Masa Hakan Sai Kuma Watar Tace Masa Su da Ƴarsu Inbasa Badawa Dole Sai Sun Mata Taɓon MUTUWA Harsu Sa Ta Makara? In ma Hakane Meyasa basuyi Wannan Hukunci ba A Wancan Karon da Suka Tashi Aurar da Ita ga Alhaji Saminu ba? "Kai!" Abubakar Yafurta Hakan Afili Tareda Ƙara dafe Kansa Ganin Kansa Zai Kulle Tamau Koma Yaƙulle Tamau Baya da Wata Mafita da Ta Wuce Karantar Innalillahi Wa Inna Ilaaihi Raju'un!!!" dan Haka ita Yariƙe Yaci Gaba da Yi Har'izuwa Sanda Likitan Nan Yasake dawowa Tareda Bashi Umurnin Zai Iya Shiga Gurin Maman Walida Yanzun Dan Haka Yamiƙe Cikin Kasalar Jiki da Na Zuciya Yashiga ɗakin Yasami Maman Walida Idanunta Biyu Sai Aikin Kallon ɗakin Takeyi Tana Ganishi Tasoma Ƙoƙarin Mikewa Zaune. Fahimtar Hakan da Yayi Yasa Ya'isa gareta da Hanzari Yataimaka Mata Tareda Jinginata da Filo Ta dai-dai ta Sosai, Kafin Shikuma Yajawo Kujera Yazauna Gabanta A Sanda Ita Kuma Take Tamabayar sa Meye Gaskiyar Abunda Tagani da Gaske ne Ko Mafarki ne Tayi? Girgiza Mata Kai Yayi, "Ba Mafarki Bane Gaskene, Amma Dan ALLAH Ina Son Mmn Walida Ke Saka Nutsuwa A Ranki Mubi Komai A Sannu, Nima Ina Cikin Makamancin Halinda Kike Ciki dakuma Nazurfafa A Bincike Sai Naji Kamar Ƙwaƙwalwata Zata Tarwatse Sbda Nakasa Gane Komai gudun Faɗawa Irin Halin da kika Shiga Yasa Nayi Ƙokarin Raba Kaina da Irin Wannan Tunanin Abunda Kawai Nabarwa Raina Yanzun Kawai Khaleesat Ba MUTUWA tayi Ba Akwai Wani Ƙulallen Ƙulli da Bamu Sani ba, Wanda Mukabi Tq Lumana Zamu Sanshi Amma Mukai Garaje tau Zamu Nakasta Kammu ne kurum Dan Haka Kema Nake Shawarta Ki da Bin Wannan Hanyar dan Tsira da Lafiyarki." Babu Shakkah Wayyanan Kalamin Sunyi Tasiriri Sosai Acikin Zuciyar Mmn Walida Yaune Kuma Taƙara Tabbatarwa Maganar nan Da Ake Cewa, "Tunanin Macce Baya ɗaya da Namiji Komai Girmanta Komai Kuma Shima Ƙanƙarta Sai In Shi Mijin ne Yayi Watsi da Wannan Baiwar ta Hanyar Gurɓata Tunanin Nasa. Dan Haka Sai Taƙara Gyara Ƙishingiɗar da Tayi Cikin Rashin Ƙarfin Jikin Nata Kana Tace, "Auta Maƙoshina Yabushe Taimake ni da Ruwa Masu Sanyi Insha Dan ALLAH!" "Ok Bari Na Kawo Maki." Yamiƙe Zuwa Waje Sai da Yagayama Likita Halinda Ake Ciki Cewa Patien Tana Buƙatar Ruwa Masu Sanyi Za'a Iya Bata?" Likitan Yace, "A'a Kar Abata Masu Sanyi Adai Bata Matsakaita In Ma So Samu Ne Asamo Mata Ayaba Abar Ruwan." dan Haka Abubakar Yajuya Zuwa Harabar Asibitin Yasiyo Ayaba Mai Laushi Yadawo Yana Bata Tareda Sanarda Ita Umurnin Likita Kenan. Tau itama bata Musan ba Tunda Tasan Aikin Sune Kuma Suna Yi ne Dan Lafiyarta Kuma dai Ma itakam Taga Zurfin Tunanin Ƙanin Nata da Yaje Ya Tambaya. Da Taci ayabar Kuwa Sai Taji Lalle Ta Ƙara Samun Nutsuwa. Bayan Yakawo Mata Tacin Yafita Zuwa Masallaci Saboda Azahar Takawo Jiki daga Masallacin Kuwa Inda Su Innarmu Yanufa Yasamu Abdul-wahab Na Zaune Kishingeɗe da Fillow Kayan Fruit ne Gabansa Yayinda Khaleesat Ke Aikin Ɓare Masa Ɓawon Ayaba Ko Lemu Yanaci. sai Ka Rantse Kamar Ba Abinda Yafaru. I zuwa Yanzun Kuma Innarmu ma Ta Nutsu Itama Tana Riƙe da Carbinta Sai Abinda Ta Manta Nadaga Tsabihin da Takeyi Itama Ko Tayi Irin Tunanin Nasa ne? Ko kuwa dai ta Saduda ne Sbda Taga ba Abunyi? ALLAH Masani Sai Kuma Innarmu da Ita Kaɗaice Tasan Halinda Take ciki. Gudawa Kam dai Bata Tsaya ba Gama Lokaci -Lokaci Ka Kanganta da Buta Zuwa Bayi(Toilet). Yana Ma ɗaya daga Cikin Abunda Tayiwa Abubakar Ƙorafinsa A Yanzun Bayan Sungaisa da Tambayar Juna Yanayin Al'amurrah da ke ta Cuɗawa dasu Ayanzun Tamkar A RAYUWAR MAFARKI Ko Shirin FILM. Bayan Yagama ji daga Innarmu Yace, "ALLAH Ya Sawwaƙa Bari Naje Na samo Maki Magani, Amma Abinda Yafi Kamata Kawai Ki Koma Gurin Maman Walida dan Macce Sai Macce Haka NAMIJI ma Sai Namiji ɗan Uwanshi." Innarmu Tagirgiza Kai Cikin Gamsuwa da Zancen ɗan Nata Kana Taɗago Tadubeshi Cikin Tausayinsa Akan duk Yanda Yayi Wani Firgai-Firgai Ko Babu RUƊANI Jinya Ba Abuce Mai Sauƙi ba ga duk Wanda Yayi Yasani. Balle Kuma Ga Nasu Da Yazo Musu da Wani Irin RUƊANIN da Harsun Rasa Abin Misaltawa Dashi. Tace, "Auta Ina Fatar Ka Ƙara Juriya da Haƙuri Akan Wannan Halin da Muke Ciki Kaji? ALLAH Yana Ganin Halinda Muke Ciki Hasalima Shine Yajarabcemu Bawai Dan Yazaluncemu ba Saidon Yana Nufin Mu da Rahma Wadda Kila Nan Duniya ko Kuma Lahira Wannan Shine Yabarwa Kansa Sani Amma dai Ni Nasani Dukkanin Tsanani Yana Tareda Sauki Hakanan Bahaushe Yace BAYAN WUYA.... SAI DAƊI dan Haka Abubakar Ina Ƙarama Wasiya da HAKURI Akan Wannan Halin da Muke Ciki. Ina da Yaƙini Yanzun Ko Anjima Kai Koma Yaushe ne Taimakon ALLAH Zaizo Garemu." Wayyanan Kalaman Na Innarmu Sai Suka Kasance Kamar Wata Allaura ta Ƙwarara Gwaiwa ga Abubakar Hakanan Suka Samarmasa Da Wani Irin Tawakkali Maigirma Acikin Zuciyarsa. Bama Shi Kaɗai ba Har Abdul-wahab da A yanzun Yayi Ras! Kalaman Innarmu Sun Ratsa sa Balle Kuma Khaleesat da A yanzun Takejin ITACE SILAR KOMAI. Saidai da Zata Iya Duban Innarmu Tayi Mata Magana Da tace Mata, "Nima Ba Yin Kaina bane Innarmu SONEE SILAR KOMAI." Saidai Bazata iya ba Innarmu nayi Mata Wani Irin Ƙwarjini Hakanan Tana da Ƙima ta Surukuta A Gareta. Dan Haka Sai ta Ture ledar Fruit ɗin da Ke Gabanta Tamiƙe Tsam! Tanufi Waje. Duk Suka Bita da Kallo Batareda ko Wanen su Ya'iya Ce da ita Uffan ba. Hakanan Anrasa Mai Jarumta Tunkarata domin Tambayar Ainihin Abinda Yafaru. Ita Kuwa Khaleesat Bayan tafita Hannunta ta Wanke Kafin Ta Sanyo Arwallah Tadawo Tareda ɗaukar Sallayar Innarmu ta Shimfiɗa Ta Soma Sallah. Ajiyar Zuciya Abubakar Yasauke tareda Cewa, "Innarmu Bari Inje In Samo Maki Maganin." "Tau Yayi Abubakar Bari inZo Muje daga can Ka Rakani ɗakin da Yayar Taku Take." Harta Sa Kai Zata Fice Sai Kuma Tadawo Tana Kallon Abdul-wahab da A yanzun Yakoma Kan gado Yalafe Tareda dafe Kansa da Hannu Idanun sa A Lumshe Shi ba Bacci Ba Kuma Shi ba A Farke ba. Kawai Sai Innarmu takaɗa Kanta Kafin Tajuyo Gurin Khaleesat da Nufin Tayi Mata Magana Sai taga Bata idar da Sallah Ba Dan Haka Tabi Bayan Abubakar da Shi Tuni Yayi Gaba. ********* Washe Gari Tunda Sassafe Dr Jabir Yahau Shirin Fita Gurin Aikin Nasa da Yakasance Yaune Rana ta Farko da Zasuje Suji Ta'inda Program (Shirin) Nasu zai Soma. Dan Haka Maman Asharaf Tashiga Kai Kawo Dan Haɗa Masa Abinda Zaici Kafin Yafitan. Ƙwai Ta Soya masa da Irish Sannan ta dafa Masa Shayi(tea) Nan inda yake Zaune Yana ɗaura Tie ɗin Coat ɗinsa da Yabi yalafe ɗas Ajikinsa Kamar dan shi Akayi Su. Takawo ɗan Madai-daicin Farantin ta'ajiye Kafin Kuma ta zauna Gefensa Tana Cewa "tau Food is Ready!" dubanta yayi Cikin Soyayyar ta dake Ƙara haɓɓaka Acikin Zuciyarsa Bakuma dan Komai ba, Sai dan Yanda Take Matuƙar Hidimta Masa kowane Lokaci Batareda Nuna ƙosawarta ba, Hakanan Kuma A Ko da Yaushe Tanayi ne Cikin Nuna Masa Zallar Ƙauna. Ɗan Busa Masa Iskan Bakin ta Tayi Tareda Haɗa yan yatsunta Biyu Suna bada Sautin Ɗas! Ɗas!! Kana Tace, "Maigida Irin Wanna Nisan Zango Fa?" Firgigit!! Yayi Yana mai ƙara Kallon ta da Mayu Idanunsa Masu Matuƙar ƙwarjini Kafin Yasauke Wata Ƙatuwar Ajiyar Zuciya Gamida Cewa, "Eh Tau Ai keɗin ce Maman Asharaf Kullum Sai naga Kamar ƙara Maki Kyau A keyi, Ko Meye Sirrin?" Wal!! tayi da idanunta Cikin Jin daɗin Kalamin Nasa Saidai A Furincinta Bata Nuna Hakan ba dan Cewa Tayi, "HUBBINA Akwai ka da Zolaya Wani Sa'in wallahi." Yaɗan Sunkuya yaɗauki Kofin Shayin dake Ta Suracin Zafi Tareda ɗan Juya Shayin da ɗan Karamin Cokalin da ke Cikinsa Kafin Yakai Shayin Bakinsa Yana Kurɓawa A Hankali Kamar Bazai bada Amsar Maganar ba. Sai Yace, "Hummm! Haka Kike Tunani? Tau ɗauko Madubi Ki Gani Indai Zolaya Ce tau Nayarda A Hukunta ni ta Hanyar Ha....." Ganin Zai Ɓaro Wata Magana Data Girmi Kunnen ta tai Hanzarin Taran Numfashin sa Da Cewa, "HUBBINA Lokaci Na Tafiya, Kuma Bacin Haka fa Bakyau Magana A Sanda Ake Cin Abinci." Sarai Yafahimceta Maganar Ce Kurum Bata So, Dan Haka Sai Yamiƙe Yana Murmushi Tareda Yago Tisue ɗinda Cikin Kwalinsa Akan Center Table Yasoma Goge Bakinsa Kafin Yace, "Maman Asharaf Ni Naga Sanda Zaki Daina KUNYAR Nan Tawa Mutum Harda Albarkar Ɗa Amma Kuma Kamar Jiya Kika Zo Gidan?" Maman Asharaf Batabi Ta Kan Zancen Nasa ba Madadin Hakan ma Flet ɗin Irish taɗauko Tareda Kosanto Shi tana Cewa, "Kai HUBBINA Yanzun Dan ALLAH Bazaka Ci Abincinan Ba Haka Zakaje Yunwa Ta Nakastamin Kai?" harararta Yayi Cikin Sigar Ƙauna Yace, "Anƙi Aci ɗin, Ni Nagane ɗuren Naki Harda Mugunta Acikinsa Wallahi." Yanda Yaƙare Maganar Sai da Yabata Dariya dan Haka Cikin dariyar Tace, "Taufa Wace Mugunta Kuma daga Abun Arziki?" "Ba Wani Abun Arziki Nagane So kike Nayi Ɓulele ta yanda duk Wadda taggani Tace Bata So...." Habawa Me Maman Asharaf Zatayi Inba Dariya ba dan Yanda Yake Maganar Kamar Wani Kwarkwasinu Yace, "Tau Nagane Wayo Naki daga yau Ai." Maman Asharaf Tace, "Kai Ai Yanzun Yammata Ma Sunfi Son Ɓulele In Baka Sani Ba In Baka Labari." "Inji Wa?" Tace "In Ji Su Yan Matan!" "Tau Ban Yarda ba Sai Na Binceke Su Inji." Yafada Yana Ƙokarin Kwaikwaiyon Muryar ta. Dai-dai Lokacin Asharaf Yafito Falon Sanye da Kayan Barci Sai Mutsutsuke Ido Yake Alamun dai daga Bacci Yatashi Yana Zuwa Kuwa Ya Rarumi Kofin tea ɗayan Hannun Kuwa Yaɗebo Irish Zai kai Baki Ai da Zafin Nama Maman sa Ta Fisge Tana Faɗin, "Tau Acici Mala'ikun Tukunya Daga Tashi Barci Ko Brush Bakayi ba?" Asharaf Ya Yamutse Fuska Zai Fashe da Kuka Yadubi Baban Sa Cikin Gwaracinsa Yace, "Dady Ce Momy Wunya Aji Tabani Tea." Dr Yadurƙusa Gaban Asharaf Yana dafa Kafaɗarsa Yace, "Sorry My Boy Zata Baka but Kabari Kayi Brush Kaji?" Asharaf Yagirgiza Kansa Cikin Tunzure Baki. Dr Jabir Yamiƙe Yana Faɗin "Yawwa My Boy Bakyau Cin Abinci Ba'ayi Brush ba Kaji." Yaƙarasa Maganar Cikin Sigar Lallashi Still dai Asharaf Sake Girgiza Masa Kan Yay, Dan Yaron Akwai Misƙilanci Kamar Baban Nasa. Dr Jabir Yazura Hannunsa Zai ƙarɓi Jakkar Labpton ɗinsa dake Hannun Maman Asharaf Ita kuwa ta Noƙe Tareda Cewa, "Muje Ai Sai Na Rakaka!" Murmushi Yayi Sannan Yajuya Yanufi Ƙofa Yana Cewa, "Lalle Kam Gara kiyi da Kuka Inba Hakaba Turawa Nan Suyi Awon Gaba Dani." Hannun Asharaf tariƙo Suka Mara Masa Baya Tana Cewa, "Taɓ! Su Sun Soma ma?" "Tau Yi Wasa ki ga Yadda Zatayi Wuff dani Wallahi." Yakarasa Yana mai Taka Burki Bai Bata kuma damar Cewa Wani Abun Ba Yace, "Tau tsaya daga Nan dan Karwani Baturen Yaganki Yace Zai Maki Magana Nikuwa In Faskare Masa Kai." Masu Karatu Zan ɗan Tsahirta Anan Muje Daku A Shafi Nagaba Tareda Alkalamin FA'IK. [9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....31 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem!!! Maman Asharaf Takama Baki "Kai HUBBINA Ina Wani Zai Yimin Magana ma Kuma Munatare?" "Tau Ina Ruwan su tunda Ba Addinine dasuba Sufa Agurin su Komai Ƴanci ne." Maman Asharaf Tace, "Baban Asharaf Baka da Dama, Nidai ga Jakkar Ka." Taciro ta Tana saƙala Masa ita A Kafaɗarsa Taɗora da Cewa, "Asauka Lafiya ALLAH Yatsare Mana Kai." Sai Ji Sukayi Shima Asharaf Yace, "Ashauka Lafiya Ayya Yashale Mana Kai." Mezasu inba Dariya ba? Dr Jabir Yaɗan Sunkuyo Yana ɗan Tsakulan sa A kumatu Gamida Cewa, "Ameen ɗan Dady." daganan Yajuya Suna Gaisawa da Wani Bature da Yafito daga Nasa Part ɗin, Cikin Shirin Fita Shima. Da Ido Kawai Yayi Ma Maman Asharaf Alama Cewar Su Koma Ciki. Sbd Ganin Baturen Yanufo Inda Suke. dan Haka Sai Taja Hannun Asharaf Suka Koma Cikin Tana Kullo Kofar Part ɗin Nasu. Shi kuwa Dr Jabir Gaisawa Sukayi da Baturen Daganan Suke Gabatar da Junansu Yayinda Baturen Yace Sunan Sa Jacob Shima Dr Jabir Yasanar Masa Da Sunan Sa Daganan Kuma Suke Sauka Akan Step ɗin gidan Saman Suna Ci Gaba da Ba Juna Sanayyah. Ƙarshe dai da Motar Jacob ɗin Suka Fice. Baturen Mutum Akwai Son Mutane ga Iya Tsari da Kuma Tsayuwa Akan Aƙida. Maman Asharaf Kuwa Asharaf tayi Ma Brush dan dai ma Wanka Taso Yimasa Amma Sai Ya'azazaleta Shi Tea Zaisha. Dole Tamasa Brush Tabashi Tea ɗin Da Nufin Inyaƙare Tamasa Wankan. Daganan Kuma Tashiga Aikin Kwashe Kayan da Ta Kawo Ma Shalelen Nata, Zuciyarta Fal Tunanin Irin Dacen MIJI Da Tayi da Yakanyi Komai Don Samun Farincikinta. Abunda Yan Lokkutan da Suka Wuce Yaso Shuɗewa Saboda Auren Sa da Khaleesat da Yataso Ashe Kuma Auren Bama Mai Yuwa Bane. Tayi ta Tuna Artabun da Suka Sha A Lokacin. Wani Tayi Dariya wani Taji Kunya A Yanzun. Duk-da Kuwa Harga ALLAH Bata Yi Murna da Mutuwar Khaleesat ɗinba, Hakanan duk Abinda Tayi A Wancan Karon, Tayishi ne Akan Kishin Mjinta Wanda Ba'a Raba Kowace Macce Dashi. ********* Mmn Walida Ta Warke Sumul! Sai Ƙarfin Imani da Tawakkali da ke ɗawainiya da Zuciyoyin Su. Hakanan Yanzun Sun daina Tsoron Khaleesat ɗin, Sun Saduda Kan Tunanin da Abubakar Yaɗora su Akai. Bugu da Ƙari Likitan nan da ke ta ɗawainiya dasu Tundaga Sanda Abin Yafaru Yazo Yasame Su Tareda Sanar dasu Cewa, "Abdul-wahab Yasamu Sauƙi Kuma Kowane Lokaci Zasu Bashi Sallama Bayaga Haka Yana da Magana Dasu Mai Muhimmaci Akan Abinda Yadangaci Tsakanin Khaleesat da Abdul-wahab Hakanan Su Kwantar da Hankalinsu Khaleesat Ba MUTUWA tayi ba Gaskiya, Akwai dai Wani ƘULLALLEN ƘULLI da Yake Buƙatar Warware Masu Shi Tau Amma Fa Sai Lokaci Yayi. Maganar Sa Tasake Jefa Su Innarmu Acikin Wani ƘULLIN Bayan Wancan ƘULLALLEN ƘULLI da Yace Zai Warware Masu, Tau Amma Basa Son Hayaniya Kuma dai Sunyi Amanna Cewa, "Komai Nisan Jifa Ai Ƙasa Zai dawo." dan haka Bari Su Jirayi Lokacin Sugani. Daganan Kuma Sai Alakarsu ta Dawo Lafiya tsakanin su da Khaleesat ɗin Suke Komai Tareda Ita Lafiya -Lafiya. Hakanan daga Cikin Masu Zuwa Dubin Nasu Ba Kowane Yasanta Ba, Balle Yasan Matsalar da Ake Ciki. Yusuf ne Tau Kuma Shima Kwana Biyu Mura Ta Kwantar dashi Zazzaɓi Yakeyi Sosai Harma Saida Akayi Masa Ƙarin Ruwa. A Sanda ma Innarmu Taji Sai Cewa Tayi Ai dole ne ma Yayi Mura Ai ko Kai-kawo ɗinda Yakeyi Cikin Sanyinan daga Sokoto Zuwa Kware Ai Yasashi Mura. Saidai Abinda Innarmu bata Saniba Shine, Yusuf Yanayin Mura ne Irin Wacce Kowane Ango Sabon Aure Kanyi, A Farkon Kwanukan Angancinsa(Wannan Sirrin Kuma Maza ne Kurum Suka Sanshi😜) Tau Kwana Biyu da Yin Wannan Maganar Da Sanyin Safiyar Yauɗin da Ta Kasance Ranar Litinin Aka Bawa Abdul-wahab Sallama Bayan Likitocin Ƙwaƙwalwa Sun ɗora shi Akan Shawarwari da kuma Magungunan da zai Ci Gaba da Sha Har Izuwa Sanda Zai Ƙara Warware wa. Sun Kuma yimasa Huɗubar Ya Rage Sa Abu Acikin Ransa Sannan Yarage Yawan Tunanin da Dai Sauran Tsare-tsare Irin Nasu Na Likitoci daga Bisani Kuma Akayi Cike-Ciken Takardu Aka Basu Sallama. Duk Wannan ne Dai Yana Faruwa ne Ƙarƙashin Jagorancin Likitanan dai Mai ƁOYAYYEN Suna Wanda Tun Sanda Suka zo Asibitin Shi ke Basu Kulawa Akan Komai Nasu. Yanzun Haka Office ɗinsa Suke Zaune yayinda Yake Hakimce Kan Kujerar Sa Yana Yan Rubuce-Rubuce Akan Fayel ɗin Marassa Lafiya dake Gabansa. Bayan Yakamalla Kuma Yaɗago Yana Mai Ƙokarin Cire Medical glass ɗinsa dake Kan Fuskarsa Yaɗan Busa Shi Kamar Wanda Yayi ƙura Sa'anan Ya'ajiye Gefe Yana Mai Ƙare Ma Su Abdul-wahab ɗinda Ke Zaune A Gabansa Kallo Inka Cire Mmn Walida dake Can Tana Ƙoƙarin haɗa musu Kayansu dakuma Abubakar da kecan Gurin Nemo Musu Motar da Zata Kwashe su Zuwa Gida. Murmushi Yayi Sannan Yace, "Innarmu Ina Tayaki Murna da Ganin Wannan Ranar da Fatar Kuma ALLAH Yatsare gaba. Yaƙara Bawa Abdul-wahab Lafiya." Innarmu tace, "Allahumma Ameen Kuma Muma Muna Godiya Ƙwarai da Gaske Bisa ga ɗawainiyar da Akayi tayi Damu Tun Sanda Mukazo Asibitin Nan ALLAH Yataimake ka Akan Aikinka Yakuma Yimaka Albarka Yajiƙan Magabata." "Ameen Summa Ameen Innarmu Nagode." Likitan Yafaɗi Hakan Cikin Matuƙar Farinciki da Adu'ar Innarmu Kafin yaɗora da Cewa, "Kamar Yadda Nasanar da Ku Ƴan Kwanaki Biyun da Suka Shuɗe Cewa, Khaleesat Ba MUTUWA tayi ba Akwai dai Wani ƘULLALLEN ƘULLI da In Lokaci Yayi Zan Warware Maku Tau Lokacin Yayi, Sai dai Yanzun Kafin Azo Gaɓar Warware Muku ƘULLIN Ina Neman Alfarmar Kuje da Khaleesat Gidanku Tazauna gurinku Zuwa Sanda Nake Son Komai Ya dai-dai ta Sai Inzo Ayita Ta Ƙare. In Ma Goben ALLAH Yasa Abunda Nake Tsarawan Yadai-daita A Goben Tau Karku Cire Tsammanin Zaku Ganni A Goben Insha'allah." Innarmu Takawo Gwauron Numfashi Ta Sauke Cikin Jin Irin Wannan Murɗaɗɗen Al'amari Tace, "Badamuwa Likita Zaka Samemu Da Yimaka Yanda Kace Ɗin, Muma Kuma Muna Fatar Komai Yatsarun Gobe dan Fita daga Cikin Wannan Ruɗu da Ruɗanin da Muke Ciki." Ɗan Murmushi Likitan Yayi Gamida Ɗan Juyawa Akan Kujerasa Sa'annan Yace, "Tau Shikenan Innarmu Ina Godiya da Wannan KARAMCI Kuma Karku damu da Yawa Harku Zurfafa Cikin Wani Tunani da Zai Iya Sababba Maku Wani Tention! Insha'allah Komai Yakusa Zuwa Ƙarshe." "Muna Fatan Hakan!" Innarmu ta Faɗa. Dai-dai Lokacin Kuma Abubakar Ya'iso Office ɗin Bayan Wata Nas tayi Masa Iso Gurin Likitan. Ya Sanar dasu Cewa, Ga Mai Motar Ya'iso. Dan Haka Likitan Yamiƙe daga kan Kujerar da Yake Zaune Tareda Cewa, "Tau Innarmu Zaku Iya Tafiya Ga Wannan."Yamiƙo Mata Farar Ambulance Kafin Yaɗora da Cewa, "Kuɗine Ba Yawa Ku ɗan Ƙara Kuyi Na Mota ALLAH Yakai ku Lafiya." Innarmu Tace, "Ɗannan Irin Wanna Hidima Haka Batayi Yawa ba?" "Batayi Ba Innarmu Badan Aikin Yayimin Yawa ba Ma Ni Zan Kaiku Hargida." "Tau ALLAH Yayi Albarka Yasa Agama da Duniya Lafiya, Yakuma Sanya Muku Albarka Acikin Aikin Ku." "Ameen!!!! Innarmu Abunda Muke Buƙata kenan A Gurin ku." Likitan Ya'amsa da Hakan Kafin Yaɗan Tako Masu Zuwa Wajen Office ɗinsa Yadafa Kafaɗar Abdul-wahab Tareda Cewa, "Abdul-wahab yau Sai Gida Ko?" Abdul-wahab Ba Baki Sai Fara'ar Da Yake tayi Kamar Wanda Akayiwa Bushara Da Kujerar Hajji. (Kunsan fa daɗi ne Ga ita ga Wanda Baije ba Kuma Ba Kuɗin Zuwa😅) Murmushi Kawai Likitan Yayi Tareda ɗan Bubbuga Kafadar Abdul-wahab Kafin Yace, "ALLAH Yakaiku Lafiya." Yaɗan Juyo Yana Miƙawa Abubakar Hannu Sukayi Musabaha Kana Yaɗora da Faɗin, "Wish U All d best Abubakar." Yajuya Yatafi Abinsa Yabarsu Suna Ta zabga Masa Godiya da Tarin Fatar Alkairi. Sunaji Nan duniya Ba Mutum Mai Kirki Kamar sa. Innarmu Suka Shiga Yin Sallama da Mutanen da Akayi Sabo dasu Na ɗan Zaman da Akayi Suna Masu Yimusu Adu'ar Suma ALLAH yakawo Masu Wa'adin Zaman. Haka Suka Raba Masu Sauran Kayakin su Irin Su Jikkar Pure water da Sukan Siyo da Kuma Kayan Fruit ɗinda Tun da Suka Zo Asibitin Basa Rabo dasu da Dai Yan Sauran Tarkace Hakanan. Wayanda Aka Shaƙu dasu Sosai Kuwa Aka Shiga Musanye Number Tareda Bawa Juna Adrees. Daganan Kuma Sukayi Haramar Tafiya. Abdul-wahab dai Sai Kallon Mahaukatan dake Gurin Yakeyi. Yana Ayyana Daɗa Shima Haka Yayi Tayi ko? Kai ALLAH Yabar Masa Mahaifiyarsa Harma da Yan Uwansa. Haka Suka ɗunguma Cikin Mota Cikin Wani Irin Farinciki Ma Bayyani. Daganan Suka Kama Hanya yayinda Hira Ta Ɓarke Tsakaninsu Inka Cire Khaleesat da Tayi Nisa A Duniyar Tunani Kala-kala. Duk-da Kuwa Sukan Haɗo da Ita Acikin Firar Tasu Saidai Nata Raddin Baya Wuce Uhumm Ko A'a Ko Kuma Murmushi. Karfi Goma Shabiyu (12:00pm) Motar tasu Tayi Parkinq Acikin Unguwar Tasu Bada Wani Jinkiri Ba Suka Shiga Fitowa Yayinda Mmn Walida da Abubakar Suka Shiga Firfito da Kayan Su. Yaran da Suka Baibaiyesu Suna Oyoyo Ga 'Innarmu (dama Innarmu Mutuniyyarsu ce Sosai Kullum Baka Rabata dasu Cikin Gidan ta dan Haka Sanda Batanan Sai Sukayi Maraicinta.) Sune Sukai ta Shigar Musu da Kayan Cikin Gida. Inda Hayaniya da Murnar Yara Tasanarda Iyayen Su (watau Makwabtansu Innarmu) Cewa An Sallamo Su Innarmu daga Asibiti. Take Nan Fa Suka Shiga Shigowa Yiwa Innarmu Barka Musamman daga Cikin su Wayanda Basu Samu Zuwa duboshi (Abdul-wahab)Ba. Tsakar gida Suka yi Shimfiɗa Iskar Hunturu Nata Kaɗasu dan Muna Yanayin Sanyi ne Kuma Yau Antashi Garin Yayi Dum!(Babu Rana). Mmn Walida da Khaleesat Suke Aikin Kakkaɓe ɗakunan Nasu Innarmu Wani Abun Ma Yayi Hunhuna Sbda Rashin su A gidan. Haka Suka Shiga Wanke-wanke Duk-da Ma Innarmu da Mmn Walida Nata Ƙokarin Hana Khaleesat ɗin Aiki Amma Ina Taki Tare Sukayi Komai. Abinci Kuwa Basu da Matsalar sa dan Tuni Makwabta Suka Dinga Yo Masu Aiken sa Gashinan Iri-iri. Humm Ku Tambayeni Zuciyar Abdul-wahab? .................... FA'IK. ✍🏼✍🏼✍🏼 [9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....32 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem!!! Abun Sai Wanda Yagani Ji Yakeyi Kamar yalula Sama Yayi ta Yawo Cikin Gajimare Saboda Tsananin Farinciki da Yake Cikinsa. Yau ga Khaleesat ɗinsa Cikin Gidansu Tana Ta Kai Kawo ji yake Ina Ma'ace Da Igiyoyinsa Ukku Akanta? Duk Inda Tayi Yana biye da ita da Murmushin da Yakasa Ɓoyuwa A Fuskar sa. Ita kanta Khaleesat tana cikin Wannan Yanayin Saidai Ita kam Kunyar da Aka San Kowace ɗiya mace Ƴar Mutumci Takan Yima ta Burki Akan Komai. Yayinda Su Innarmu Suka Ƙara Tabbatarwa Cewa Khaleesat da Abdul-wahab Haɗin ALLAH ne Shiga Tsakaninsu Kuwa Nufi ne Na Ba'a Son ɗaya daga Cikin su Yarayu. Hakanan Aɗan Zaman da Sukayi da Ita ALLAH yasaka Masu Wani Irin Sonta Acikin Zuciyoyinsu Sbda Kunyarta, Ladabinta, Son Addinta, ga Kuma Yawan Fara'a da Faran-faran da Mutane. Itakanta Innarmu Jitake A wannan Karon Sai Inda Ƙarfinsu Yakare Wajen Nemawa Abdul-wahab Auren ta. Ruwa da Iska Ba'abinda Zai Rabasu da Khaleesat ɗin Tunda Sun Fahimci Muddin Suna Son Kwanciyar Hankali Abdull ɗin tau Abarsa da Abar Ƙauanarsa. Bayan Kamallah Ayyukan Nasu ne Kuma Khaleesat ɗin Tacika Ruwa da Boket Taje Ta Wanke Bayin Nasu Tas! Kafin Kuma taɗebi Wasun Taje Tayi Wanka. Bayan tafito kuma Tayi Yan Shafe-Shafen ta da Yake Ita Ba Mai Son Kwalliyyah Bace Itadai Barta da Shafe-shafen Mayuka Masu Ƙamshi da Kuma Turarrukan Humra. Hakanan da Ka Kalli Khaleesat Kasan Tana Cikin Sahun Matanan da Suka Kasance Masu Natural Kyau Koda Kwalliya ko Babu. Fararen idanunta da ɗan Siririn Hancinta Kaɗai Ma Abin Kallo ne Balle Kuma Aka Zo Kan Fuskarta Fara Tas! Wacce Babu Kwarzane Ko Kaɗan A Kanta, Hakanan Kamar ka Latsa Jini Yafito Sbd Taushin Fatar Fuskarta da Kyaunta. Bayan gama Shafe-shafen doguwar Riga Tasaka Wayanda Tun Bayan Barinta gida Bata da Kayan Sawa Sai Su. Dan Sune Likita Mai ƁOYAYYEN Suna Yashiga butiuqe yakwaso Mata da Hijabai Harƙasa. Kowace Kuma Riga da Hijabinta Kalarsu Kuma ɗaya ga Kuma Tsanani Laushi da Yadin Keda Shi. Bayan Ta Kimtsa Jikinta ne Tana Maida Kayan Cikin Yar Madai-daiciyar Akwatinta da duk Cikin Sayayyar Likita Mai ƁOYAYYEN Suna ne. Abdul-wahab Yafaɗo ɗakin Shima Cikin Shigar Jallabiya Kalar Ruwan Zuma Yaɗora Fullar Taɓanni Kasha Hadisi Inji Sakkwatawa😂(Ƴar Pakistan) sai Kamshi Yake baɗawa (Kamar Bashine Wanda Yayi Jinyar HAUKA BA.😜) Yamiƙo mata Rigar Sanyi Yana Cewa, "Kiɗora da Wannan Kinga Yau Akwai Sanyi Garin." Kallonsa Tayi da ɗan Murmushi nan da Ko Yaushe Baya Rabo da Fuskarta Koda Kuwa Tana Cikin Ɓacin Rai Ne. Ta'amshi Rigar Tana Ƙokarin Sakawa Tace, "Nagode!" Abdul-wahab Yajuya Yana Cewa, "Kedai Bakya Gajiya da Godiya Komai Ƙanƙantar Abu? Naje Massallaci Naji Suna Ƙokarin Tayarwa." "Adawo Lafiya." Abunda tafaɗa kenan Agajarece. Kafin Itama ta Shimfiɗa Sallaya Tasoma Tata Sallar. Bayan Ta Idar Kuma Tasamu Su Innarmu Tsakar gida Suma Sun Idar da Tasu Sallar Jifa-Jifa Makwabtansu ne Ke Shigowa Haryanzu dan Musu Barka da Dawowa. Innarmu Tadubi Khaleesat Sanda Take Ƙokarin Zama tana Cewa, "A'a Ai Bazama Zakiyi ba Kitashi Ga Abinci Nan Kiduba Wanda Yayi Maki Kici, Ina Lure dake Tun Sanda Muka Dawo Komai Baki Saka A Baki ba. Gamu Kila Cin da Mukayi Yakai Goma." Duk Wurin Sukayi Dariya Jin Yanda Innarmu ta Karashe Maganar. Cikin Kunyar Khaleesat Tamiƙe Zuwa gurinda Aka Ajiye Cololin taɗauko Wace Taga Shinkafa da Wake Aciki Tadawo Gurin su Innarmu Tazauna. Innarmu tace, "Kema dai Irin Cimakar Wancan ne Kikafi Sha'awa ko? (Tana Nufin Abdul-wahab) tau Bari A Aika Maki Kwai da Kwai(Awara) dan Naga Dashi Yake Haɗawa. Itadai Khaleesat Ba Baki Saboda Tana Kunyar Innarmu Sosai. Yayinda Ita Kuwa Innarmu Ke Ƙokarin Jawo ta Ajiki Saboda Tasake Sosai. Tau Tunda Suka Dawo Sai Suke Wani Irin Zama Mai daɗi A Tsakanin Su Hakanan Jefi-jefi Baka Rasa Wayanda Suka Zo Yimusu Barka Har Mutanen Sanyyinah Sukan zo Suma. Wasun Su Kwana Wasun Kuwa Yini Kawai Sukeyi Su Koma. A Irin Haka Sukayi Sati ɗaya Cif! Da Dawowa Wanda Zama Mai daɗin da Sukeyi Har Yasa Sun Sha'afa Da Zancen Likita Mai ƁOYAYYEN Suna. Zamantakewa Suke Maidaɗin Gaske Hakanan Su Abdul-wahab da Abubakar Sun Koma Kan Ayyukan Su Yayinda Innarmu Ta'azazzali Mmn Walida data Koma Itama Nata gidan Auren, Acewarta Ko Yanzun Ai Mijin Nata Yayi Musu Kara. Yayinda Ita Kuwa Mmn Walida Takan Noke Kafaɗa Cewar Gaskiya Ita Sai ta ƙara Hutawa A Irin Hakan Harta Haɗa Sati ɗaya. Yaudai Dole Innarmu Kuma ta tuɓure mata Tayi Mata Jan Ido kan Dole Gobe ta Koma Gama ta Lura da Yawan Wayar da Babansu Walidar keta yowa Akai-Akai Yana Son Maiɗakin Nasa Takoma Ne. Dan Haka Mmn Walida Tashiga Shirin Komawar Gobe Tuni Tayi Banyar Kai Wata Makbaciyarsu Tashigo Ta Yarfa Mata Kitso. Suna Gamawa Kuma Khaleesat Tahau Yimata Siffah (Lalle mai Zanen Fulawa.) Sai La'asar Suka Kammallah Mmn Walida taɗauki Buta Ta Tafi Wankewa. Yayinda Ita Kuwa Khaleesat Tayi Sallah Sa'anan Taci Abinci Daganan Kuma Tasoma Yiwa Innarmu Cirar Akaifa (Yankar Farce) Jefi-jefi Suna ɗan Taɓa Hira. Innarmu Tace, "Yaudai Su Auta Shiru Ba Wanda Ya dawo." "Humm! Kila Kuma Sunyi Nisan Kiwo ne Yau ɗin." Khaleesat ce Mai Yin Wannan Maganar Tana Karkare Farcen Na Innarmu. Innarmu Ta'amsa da Cewa, "Ga dukkan Alama Kam." Shiru yaɗan Ratsa Gurin Nasu Kafin Innarmu taɗan Nisa Tace, "Nikam Ƴar Nan Intambayeki Wa...." Sallamar da Aketa Kwaɗawa Bakin Kofar Gidan ne Yakatse Innarmu daga Maganar da Ta Soma. Tadubi Khaleesat tana Cewa, "Kamar Fa Sallama Nakeji Anayi A Bagin Gida Ko?" Khaleesat Tace, "Lalle Nima Na...." Sallamar dai Aka Sakeyi. Innarmu Tashiga Ƙokarin Miƙewa tana faɗin, "Bari Induba Inga Waye." Itama Khaleesat ta miƙe Tana Jawo Hijabinta dake Kan Yaggiyar Shanya dake Tsakar Gidan Tasaka Tareda Cewa, "Bari Inje Ni Innarmu." Innarmu Tace, "A'a Nice Yafi Kamata da Inje Bari Inje Ingani." daga Haka Innarmu tafice Bakin Kofar Gidan. Wata Ƙatuwar Jeep Ce Take Parke A Bakin Kofar Gidan, Jingine da Ita Dr ne Mai ƁOYAYYEN Suna Yana ɗan Karkaɗa Makkullan Motarsa A Hankali Yayinda ɗayan Hannunsa Ke Riƙe da Wayoyin sa. Innarmu Takwaso Fara'a Tana, "Lale da Zuwan Dr. Maraba-maraba." Shikuwa Dr Sai Murmushi Yakeyi Cikin jin daɗin Irin Tarbar da Yasa mu. Innarmu Tasake dubansa Karo Na Biyu Tace "Bismillah Mana Kushigo daga Ciki Mana! (Kasancewar ba Shi Kaɗai ne ba) Tare Suke Da Wani Dattijo Mai Matuƙar Kamanni da Dadyn Khaleesat. Ɗan Yunƙurowa Dr Yayi Tareda Duban Baba Tanimu Yace, "Baba Bismillah Muje ko?" Yaƙareshe Maganar Cikin Ladabi da Tsantsar Girmamawa ga Dattijon da Yakira da Baba Tanimu. Bayan Sun Shigo gidan Innarmu Ta Malale Musu Tabarma Suka Zauna Nan Aka Ci Gabada Gaisawa Cikin Mutuntawa. Kafin Innarmu Taɗora da Faɗin, "Likita Ni Naga Kayi Kyaun Kai Da Ka Iya Gane Misalin Gidan Namu da Mukayi ma Fa?" Dariya yayi Sa'annan Yace, "Kai! Innarmu Ai Shiyyar Arkillah Gurin Zuwa Nane Kullum dan Kamar Gida Take Gareni Dan Momy na(Ƙanwar Mahaifiyata)Nan Take Zama Inaga Ma Kinsanta." "Yana Yuwa Kila, Amma Meye Sunan ta?"Innarmu Tafaɗa Tana Ƙokarin Zama Kan Yar Tsuggunon da Ta'ajiye Gefen Su. "Haj. Luba Mai Turare" Yafada Shima Cikin Murmushi. "Ohhhh Ah Nasan Haj Luba Mai Turare Sosai Mutuniyar Kirki Ko Wallahi." Innarmu Tafaɗa Fuskarta Cike da Fara'a. Shikuwa Dr Mai ƁOYAYYEN Suna Yayi Murmushi Yana Mai Ƙokarin ɗaga Wayarsa da ke ta Ɓurari. Bayan Amsa Sallamar Yace, "Abdul-wahab Gamu Fa Mun Iso Gidan Ku Kaɗai Muke Jira?" Yaɗan Yi Shiru Yana Sauraro. kafin Yace, "Ok Tau Sai Kun Iso pls Sai Ku ɗan Hanzarto." Yasauke Wayar Yana duban Baba Tanimu Cikin Ladabi Yace, "Baba A ɗan Ƙara Haƙuri Suna Zuwa Yanzun Suka Ce Insha'allah." dai-dai Lokacin ne Kuma Khaleesat Take Ajiye Jug ɗin Ruwa Agabansu Tareda Tsugunnawa Tana Gaishesu Batareda ta ɗago Kanta ba, Tacigaba da Rusunar da Kanta tana Wasa da Yan Zara-zaran Faratanta. Dai-dai Lokacin da Baba Tanimu ke Kallonta ba ko kyaftawa. Wai Khaleesat ce dasuka Turbuɗe da Hannunsu Sukayi AMMANA Ta MUTU Itace nan Gabansa. Babu Shakkah badan Kafin Yagantaba Dr Mai ƁOYAYYEN Suna Yariga Yafaɗa Masa Komai ba, da Bazai Taɓa Yarda Cewa Itace Ba. Sannu A Hankali Yashafi Furfurarsa Mai Albarka Yace, "Khaleesat Hoe!" Cikin Wani Irin Bazata Taji Muryar Baba Tanimu Wanda Komai daɗewa da Zatayi A Doron duniya Basu Haɗu ba, Bazata Taɓa Mance Muryar ba. taɗago Kanta Tana Kallon Baba Tanimu da Wani Irin Yanayi da Nakasa Tantance Wane Iri ne. Kafin Cikin Rawar Jiki da Kukan da Yazo Mata Kai Tsaye Tanufi Gefen Nashi ta Zube tana Rera Wani Irin Kuka Mai Ban Tausayi Kafin Cikin Kukan Take Cewa, "Baba Kuyafemin Dan ALLAH....." Shima Lallashenta Yakeyi, "Ya'isa Daina Kukan Iyayen Ki Duk SUNE SILAR KOMAI Ko Kinada LAIFI kaɗanne." Cikin Matuƙar Tashin Hankali Mmn Walida Ta Samu Idar da Sallar da Takeyi Batareda Yin Azkar Ta Runtomo Zuwa Waje dan Jin Meye Musababbin Wannan Kukan Na Khaleesat. ******* Momy ce A Tsakar Gidan Tana Ta Kai Kawo Domin Yin Hidima da Baƙin BAZATA da Sukayi daga Adamawa Yayinda Aunty Shahuda(Matar Ya Nuradeen)Ke Tayata. Bayan Aunty Shahuda Takai Masu Abin Jiƙa Maƙoshi Tadawo Kitchin ɗin dan ɗaukar Abincin da Momy Tashirya Musu A Ƙaton Faranti. Bayan taɗauka Momy ta Biyota da Sauran Kayan Suka Shiga Falon Yayinda Muyiddim Ke ta tsallen-tsallen sa A Falon Na Rashin Jin Magana. Dole Aunty Shahuda Tajanye sa Bayan Ta'ajiye Kuma Ta Gaishesu Suka Fice Tare Tana Cewa, "Muje In Maka Wanka, Dubi Kayan jikinka Kamar Ba Ɗazun-Ɗazun Nan Momy Tayi Maka Wanka Ba." Dai-dai Lokacin Shima Ya Nuradeen Yake Shigowa Falon domin Gayar da Ƙanne da Yannen Dadynsa Da Suke Cike Maƙil A Falon. Kasancewar Dady Ɗan dangi kuma Masu Yawan Family. Duk Sukayo Caaa!! Akansa "Ja'iri Marar Son Zumunchi....." "Ai Ba Laifin Sa Bane. "Baba Tanko Ya katse Baba Bukar da Yafaɗi Hakan. Baba Ado Ya'ajiye Cupin da Yasha Lemu Yana Cewa, "Tau Waye ne Mai Laifin?" Muje Gaba Masu Karatu Dan Jin WAYE MAI LAIFIN? Hakanan Kuma Muji Meke Shirin Faruwa Da Irin Wannan Zuwan Bazata da Su Baba Sukayi Ma Dady. Inda Nanne Zakuji Warware war ƘULLALLEN ƘULLIN da Aketa Magana. Tareda Alkalamin FA'IK.. [9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....33 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Na Sadaukar Da Wannan Chapter Ga Yar Uwa A Harkar Rubutu HADIZA SALISU SHARIF. Wacce Tarigamu Gidan Gaskiya Ya ALLAH Ka Karɓi Bakwancinta Ka Kyautata Tamu In Tazo. 🙏 Bissmillahi Rahmanin Raheem!!! Baba Bukar Yace, "Gashinan Zaune." Yana Mai Nuna Dady. Kafin Yaɗora Da Cewa, "Saboda ALLAH da Ya Nuna Musu Darajar mu Da Suna Ƙin Zumunchin?" Kowa Falon Yaɗauka "Lalle Laifin Dady ne." Yayinda Dady Ke Aikin Bada Haƙuri Dan Shi Sun Gama Masa Komai Irin Wannan Zuwan Bazata da Sukayi Masa, Duk-da Kuwa Yana Cikeda Mamakin Irin Wannan Zuwan Nasu na Ban Mamaki. Shima dai Ya Nuradeen Shiru Yayi yaɗan Sunkui da Kansa ƙasa yana Murmushi dan Yasan Shi Mai LAIFI ne, Baya Tuna Rabonsa Da Zuwa Adamawar dan ko A Wancan Lokacin Marigayiya Khaleesat ce Mai Ƙokarin Tilas ta Masa Suje. Anan Kuma Saida Yaji Wani da Ya Tuno da Yar Uwar Tasa da Babu Garin ALLAH da Zaizo Yawaye Yawuce Batareda Yatuno da Ita ba, Wanda Yanaji Har Tashi Mutuwar tazo bazai Taɓa Mantawa da Mutuwarta ba. Cikin Dubara Yasanya Hannunsa Yana Mai ɗauke Hawayen da ke Zobo Masa Kafin Yaɗan ɗago Kansa Yana Kai Kallonsa Ga Wani Ƙatoton Tangamemen Hotonsu dake Maƙale Aɗakin. Sunfito Sosai Kamar Zakayi Magana Su Amsa Ma. Dady ne Zaune Gefensa Na Dama Momy ce Zaune Yayinda Ya Nuradeen ɗin Ke Gefen sa Na Hagu Shima Ita Kuwa Khaleesat Tana Gefen Momy Taɗan Rumgumota Dukkanin Su Suna Murmushi. Anɗauki Foton ne Sanda Yasamu Aiki A Legos. Falon Yayi tsit! Bakajin Komai Sai Ƙarar Cukulla dake tashi Dattijan dai Kowane Sai Aikin Ba Cikinsa Hakke Yakeyi. Ya Nuradeen Ya Yunƙura da Nufin Fita Baba Bukar Yadawo dashi Yace, "Maza Zauna, Ina Kuma Zakaje?" "A'a Da Zanɗanje ne Harku Kammallah Wai." Ya Nuradeen Yafaɗa Cikin Girmamawa. Baba Tanko Yamiƙo Masa Flet Tareda Cewa, "Kaima Zuba Abinci Kaci, Kana Gudun mu Haka Ina Za'a Shaƙu?" Dole Ya Nuradeen Yayi Yanda Suka ce ɗin Kuwa Yasoma Cin Abincin Shima. Dan Dama Yunwar Yakeji Tunda Shima bai daɗe da Sauka Gidan Ba. ********** Turus Tayi Ganin Baƙin da Ke Wajen Dr ne Kawai Ta Iya Shaidawa Kasancewar Shi Ta Sanshi, Saidai Baba Tanko ma Taba Ma Ranta Cewa Mahaifin Khaleesat Ne tun daga Yanda Taga Suke Ɗibar Kama dan Haka taja burki Jikinta Na Tsuma. Dai-dai Lokacin Abdul-wahab Yashigo Gidan Bayansa Abubakar ne Sannan Yusuf Yashigo Shima. Duk Sukayi Cirko-Cirko Kukan Khaleesat Na Tsuma Zuciyoyin Su Musamman ma Sahibin Nata(Abdul-wahab) Da Yakejin Kukan Nata Tamkar Dalma Ake ɗiga Masa Ajiki Saboda Yanda Yakijin Damuwar Kuka Nata da Bayaso. Dr ne Yaɗago Kai Yana Kallon Su Cikin Son Tantance Halinda Abdul-wahab Ke Ciki Kan Kukan da Khaleesat Keyi, Yaɗan Sauke Ajiyar Zuciya Kana Yace, "Tau Ai Zamu Iya Tafiya Ko?" Kafin Yajuyo Gurin Su Innarmu Yana Mata Ƙarin Bayani Cewa, "Innarmu Yaune Ranar da Nake Ce Maku Zan Warware Muku ƘULLALLEN ƘULLI Akan MUTUWAR Khaleesat Saidai Yanzun Zamuje Canne Gidan Nasu Ayi ta Gaban Kowa." Kaitsaye Suka Miƙe Harda Baba Tanimu da Haryanzu Khaleesat take Maƙale dashi. Saidai Yanzun Tadaina Kukan Ajiyar Zuciya ce Kurum Takeyi Akai-Akai. Haka Suka Fice Aka Rufe Gidan Su Innarmu da Khaleesat Mmn Walida Dr Baba Tanimu Suka Shiga Mota Abdul-wahab, Abubakar da Yusuf Kuwa Suka Shiga Cikin Kk Napep ɗin Yusuf ɗin. Gasunan-Gasunan Har Cikin Shiyyarsu Khaleesat Yayinda Sukayi Parkinq Suka Soma Firfitowa, Khaleesat Itace da Fitowa Lokacin Ba Kowa A Layin Nasu Tsit-tsit. Dan Haka Basu Samu Yaron da Zai Musu Iso Cikin gidan ba sai Kawai Baba Tanimu Yajagorance Su Zuwa Cikin Gidan. Dam! Dam!! Dam!! Shine Sautin da Zukatan Su Momy Sukayi Sanda Idanuwansu Sukayi Musu Arba da Su Baba Tanimu Tareda Khaleesat. Baba Tanimu duk Yana Hankalce dasu Yayi Murmushi Kawai Kafin Yakara Rangaɗa Sallama Cikin Fara'a Yajawo Hannun Khaleesat Gamida Cewa, "Zo ki Zauna Nan ɗiyata." Anan fa Aka Shiga Kallon-Kallo Tsakanin Momy, Dady Ya Nuradeen dakuma Matarsa Aunty Shahuda, Sukam Su Baba Bukar da Baba Tanko Da Baba Manu Murmushi Kawai Sukeyi Kasancewar Damar Suna Sane da Komai. Muyyudim kuwa Yasheƙo da gudu yaɗale Jikin Khaleesat Yana Oyoyo Momy na(In baku manta ba itaɗin mutunniyar sa ce.) ga Khaleesat ɗinma Haka Lamarin Ya Kasance Duk Ilahirin Jikinta Rawa Yakeyi Yayin da Take Wasu Hawaye Suka Ɓalle Mata Tamkar Anbuɗa Famfo. Kafin Su Ankara Kuwa Ihun Momy Kawai Sukaji Tafaɗi Sume Dole Sukayi Kanta da Hanzarinta Suna Masu Ƙokarin Shafa Mata Ruwa, Yayinda Haryanzun Dady da Ya Nuradeen Harma da Aunty Shahuda Sukayi Mutuwar Zaune Wuta Ta ɗauke Musu Ɗif Suka Kasa Tantance wace Irin Duniya ta Suke Anasu Sanin dai Ba'a Taɓa Mutuwa Aka dawo ba Kuma Lalle In ma Ba Yaudarar Kansu Sukayi ba Khaleesat ce Suka Gani Tareda Su Baba Tanimu da Kuma Yan Gidan su Abdul-wahab Tau Meke Shirin Faruwa Kenan? Tambayar da Suka Kasa Amsawa Kansu Kenan. Sukuwa Innarmu Daƙyar da Taimakon Dr Suka Samu Momy ta dai-dai ta Inbanda Zabure-Zaburen ba'abunda Takeyi. Tana Faɗin, "Shikenan Ita Ma Ta Mutu dan dai Inba DUNIYAR MATATTU BA. Ba Yanda Za'ayi Ta Koma Ganin Khaleesat ɗinta Wadda Takeda Tabbacin Cewa Ta MUTU. "Tau Meke Shirin Faruwa danine?". Tafurta Hakan A Fili. Baba Tanimu Yayi Murmushi Yana Cewa, "Ba Abinda Zai Faru dake Sai Alkairi dan Haka Ki Nutsu Kiji Abinda Ke Faruwa Ko ya Farun Khaleesat dai bata MUTU ba Tana nan Raye." Wayyanan Sune Kalamai Mafi Razani da Girma Ga Su Momy Harma Su Dady da Ayanzu Wutar su data ɗauke ta Dawo, Inbada Gumi Ba Abinda Dady keyi Kamar Ba Muna Cikin Lokacin Sanyi ba. Dole Baba Bukar Yamiƙe Ya Kunna Fanka Tasoma Bama Dady Iska. Ya Nuradeen Kuwa da Aunty Shahuda Suka Kafe Khaleesat da Idanu Ko Ƙyaftawa basayi. Momy Tamiƙe Zata Fice Falon da Gudunta Su Innarmu Sukayi Hanzarin Riƙota Suka dawo da Ita Cikin Falon, Momy Ta Fara Sarewa Cewa da Mafarki ne Takeyi, Tafara Yarda Cewa Wanda Abun dai Yana Son Zama Gaske. Tau Amma Ai A gidan su Take. Dady Yadafe Kansa da Ke Shirin Tarwatsewa Gida Biyu Haka Shima Ya Nuradeen Yayi Yayinda Aunty Shahuda Take Kuka Wiwiwi Cikin Wani Irin RUƊANI Da Ta Matsu Ya Ƙare Ta Mastu Ace Da Ita Tafarka Daga Baccin da takeyi dan Wannan Abun Babu Ko Tantama MAFARKI NE kawai Irin Na da Daɗin Bacci. Yo Inba Bacci Ba Waya Taɓa Ganin Mutum Ya MUTU kuma Yadawo Ko Acikin Fina-Finai da Littafai da Suka Kasance Rayuwar Ƙarya Indai Akace Mutum Ya Mutu Tau Shikenan Fa Ya Mutu Balle Kuma Duniyar Tasu ta Gaskiya. Kai Haka dai Sukayi ta Fama da Tashin Hankali Wanda In Zamu Ƙai Yaushe Bazamu Iya Bayanne Adadinsa ba Wanda Kuma Babu Wani Rubutu da Zai Iya Bayyane sa Harma Ya Misalta Irin RUƊANIN Da Suke Ciki Harma da Iface-Ifacensu. Saidai Kawai Abarwa Mai Karatu da Ƙyiyasta Irin Hargitsin da Su Momy Suke Ciki. Sun Kasa Yarda da Kalamin da Su Baba Tanimu ke ta Nanata Masu Cewa, "KHALEESAT BA MUTUWA TAYIBA KHALEESAT TANA RAYE Illai Kawai Akwai ƘULLALLEN ƘULLI Da In Suka Nutsu Za'a Warware Musu Tau Amma Sun Kasa Samun Nutsuwar Sun Nemi Nutsuwar Sun Rasa. Haka Akai Ta Fama da su Acikin Falon Kafin Aka Samu Suka Natsa Saboda Faɗan da Baba Tanimu Yatasa Gaba Yanayi Musu Kasancewar sa Mutun Mai Zafi da Faɗa Shiyyasa ma duk Familyn Nasu Sunfi Shakkarsa. Cewa Yakeyi, "Karku Maida Mu Ƙananu Mana Ai Kunsan dai Bazaiyu Tsofai-tsofai Damu Muzo Gurin Da Maganar Banza Ai Bazai Yu Bane." Khaleesat dai Sai Kuka Take Mai Matuƙar Tsuma Zuciya Takuma Rasa Wa zata Tunkara Acikinsu Momy, Dady ko kuma Ya Nuradeen? Kawai Sai Ta Sami Kanta A tsakiyar Falon Tana Cigaba da Rera Kuka Tamkar Ranta Zai Fita. Hakan Yasa Falon Yayi Tsit! Inbabda Kukan Nata Ba'abunda Kakeji. Taɗago Kanta Ta Kalli Momy Taga Yadda Duk Momyn Tafita Hayyacinta Tayi Wata Irin Rama Mai Ban Tausayi Kamar Ba Momynta Da Ta Sani Mai Matuƙar Jiki da Ƙwalisa Ba Kai Lalle Tayi Yawo Da Hankalin Iyayen ta Mafi Soyuwa Agareta Wanyanda Nan Duniya Takeji Bata da Kamar Su tau Amma Yazatayi Ita Kanta Ba Laifin ta Bane SONEE SILAR KOMAI. Sannu A Hankali ta Rarrafa Izuwa ga Jikin Momy Tafaɗa Tana Cigabada Kukanta Cikin Kukan Tace, "Momy Kuyafemin Natuba Nabi ALLAH Nabiku. Wallahi duk Abinda Yafaru, Yafarune Bisaga SILAR SO Wanda Nabari Ya Rinjayi Zuciyata Har Yazama Nakasa Tafiyar dashi Yazamana Shine Ke Jagoranci na Har'izuwa Sanda Ya Makantar da Idanuna Ga Manta Muhimmancinku da Irin Fifikon da Kuke dashi Akan Wanda Na Aikata Hakan Ta sanadin Na Rayu dashi, Saidai Nasani Rayuwa taredashi Gareni Dolene Inba Hakaba Nina Nasani Mutuwa Ta Wajaba Gareni domin dai Nasani Walwala da Kwanciyar Hankali Zasuyi Bankwana Dani." taɗan Sarara Cikin Ƙunar Zuciya da Ta Ruhi Kafin Taɗora da Bayanin da A yanzun take Ganin Bata da Mafitar da Tawuce Yinsa Kodan Irin Fa'idar da take Hangowa Tattare da Bayanin Ko Bayan Hakan Ma Ai Akace "Ranar Wanka Ba'a Ɓoyon Cibi." dan Haka Ta Kalli Dady Gamida Cewa, "Dady Kaima Ina Neman Yafiyarka, ALLAH Shine Shaidata Nayi Iya Ƙokarina Na Fahimtar da Ku A Hakan A Irin YARE Mai Sauki Saidai Kun Kasa Fahimtar sa Shiyyasa Muka ZAƁI Fito Muku Ta Wannan YAREN Domin Muna da Tabbacin Zai Nuna Maku Zahirin Abinda Kuke Son Aikatawa BAIDACE BA." Taufa Wasa Farin Girki Kallo Kuma Yakoma Sama Akace Shaho yaɗau Giwa. Gabaki ɗaya Mutanen dake Cikin Falon In Kacire Dr Mai ƁOYAYYEN Suna Dakuma Almajirin Gidan Su Khaleesat ɗin Watau Sani tau Sauran Kam Duka Sunkasa Fahimtar Wannan Zaurancen Na Khaleesat domin Kuwa ko Su Baba Tanimu Wani Suka Sani Wanin Basu Sani Ba. My Readers Wai Ya'ake Ciki ne? Meke Shirin Faruwa Ko Kuma Yafaru Wanda Ba Kowa Yasani Ba? Muje Tare da Ku A Fage Na Gaba Domin Jin Warwarar Lamarin Tareda Alkalamin 👇 Fa'IK ✍ [9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....34 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Na Sadaukar Da Wannan Chapter Ga Yar Uwa A Harkar Rubutu HADIZA SALISU SHARIF. Wacce Tarigamu Gidan Gaskiya Ya ALLAH Ka Karɓi Bakwancinta Ka Kyautata Tamu In Tazo. 🙏 Bissmillahi Rahmanin Raheem!!! Taufa Wasa Farin Girki Kallo Kuma Yakoma Sama Akace Shaho yaɗau Giwa. Gabaki ɗaya Mutanen dake Cikin Falon In Kacire Dr Mai ƁOYAYYEN Suna Dakuma Almajirin Gidan Su Khaleesat ɗin Watau Sani tau Sauran Kam Duka Sunkasa Fahimtar Wannan Zaurancen Na Khaleesat domin Kuwa ko Su Baba Tanimu Wani Suka Sani Wanin Basu Sani Ba. Hakan Yasa Gaba ɗaya Falon Suka Ƙara Shiga RUƊANIN TUNANI Ƙwaƙwalwar Su da Tunanin su Yaɗaure Tamau! Dr Mai ƁOYAYYEN Suna ne Yalura Da Hakan Dan haka Ya Musƙuta Cikin Murmushi Kafin Yasoma Cewa, "Inaga Yanzun Khaleesat Yakamata Ki Warware Masu Wannan ƘULLALLEN ƘULLI Hakanan." Yana Ajiye Zancen Nasa Khaleesat Taɗora Da Cewa Abinda Yafaru Shine....... 👌👇 >- - - - - - -----------------------> Da Yammacine Bayan Angama Ruwan Sama da Aka Wayi Gari Anatayi Kamar da Bakin Ƙwarya. Ina Cikin ɗakina Wayata ce A hannu Na Inata Saƙe-Saƙe Acikin Raina Sai ga Kiran Dr Jabir Yashigo Acikin Wayar Tawa Kamar Bazan ɗaga ba Saboda Haushin sa Danakeji Ina ga Kamar Shine Yazama SILAR Wargaje Alakata da Masoyina Abdul-wahab. Naja ɗan Karamin Tsaki Sanda Wancan Kiran ya yanke Waninsa Yasake Shigowa Naɗaga Wayar Tareda Kaiwa A Kunne na Ina Saurare daga Gareshi Batareda Nayi Tunanin Cewa Ni Yakamata Infara Magana. Shiru Na ɗan Mintoci Yara tsa Tsakanin mu Kamar Ba Katin sa Ake Cinyewa ba. Na yunƙura Cikin Hasala da Nufin In Katse Wayar Shikuwa Kamar yasan Abunda Nake Niyyar Aikata wa Yayi Saurin dakatar dani Ta Hanyar Cewa, "Karki Kuskura Ki Kashemin Waya Nida Ake Jnayewa Kati Bankashe ba kece Zaki Kashe?" Tsaki Nayi Niyyar Yimasa Amma Sai Naji Nakasa Sbd Harga ALLAH Dr Jabir Na Matuƙar Yimin Ƙwarjini. Dan Haka Sai Na Samin Kaina Da Cewa, "Kayi Haƙuri." "Anƙi Ayi Haƙurin." Dr Jabir Yamayar Min A Ƙufule. Wani Irin Takaicinsa Yataso Yarufeni Inda Zan Iya Wallahi tas! Zan Zageshi Dan Haka Nakeyi Wa Su Alh Saminu Amma Shi Nakasa Ko Meyasa? "Saboda Shi Ya Yi Musu Finti Kau."daga Can Wani Ɓangaren Na Zuciyata Yace Hakan. "Kina ji Ba?" Dr Jabir Yakatse ni daga Tunanin danaje. Nace, "Uhummm!". "Tau Kisameni A plus Center." Yace dani Haka Batareda Kuma Yajira Cewa ta Ba Yakashe Wayarsa. Yabar ni da Kallon Wayar Kamar Yau Nafara Ganinta Saidai Idona ne Kawai Ke Kanta Amma Hankali na Bayanan Yana can Wurin Tunanin Tau Me Dr Jabir ke Nufin Da In Sameshi Plus Center? Kodai Yagaji da Tsiwar da Nakeyi Masa Zaiyi Maganin Abun? Ai kuwa Bazanje Ba. 'Tau Ai ko kije ko Karkije Nan da Wasu ƴan Kwanaki Kina Hannunsa A Wannan Lokacin Kin'isa Guje Masa ne? Rashin Zuwan ki Ma Yanzun Zaiƙara Maki Wani Laifi." Wannan Saƙe-Saƙen Nayi Tayi Hardai ɗayan Ɓangaren Zuciyata tayi Rinjaye Akan Inje Kawai. Dan Haka Nashirya Cikin Wani Farin Less ɗina Mai Matuƙar Ƙyalli Nazuba Hijabi Mai Hannaye Kafin Naɗan Mutsutsukawa Fuskata ƴar Hoda Nayi ƴan Shafe-shafen Na Da Aka Sanni Dasu Kana Nafito Zuwa Gurin Momy Nasameta A Kitchin tana Aikin Sanwar Dare Ban Ɓoye Mata Komai ba Nasanar da ita cewa da Dr Jabir Zamu Haɗu Tace, "Adawo Lafiya. Kuma dai A Kula Banda Yin Dare." Na Zumɓuri Baki Cikin Shawagaɓa Gamida Cewa, "Kai momy Wane Dare Kuma?" Tace, "Nadai Gayamaki Dan Wallahi In Dadyn Ku Yadawo Yatarar Bakyanan Kinsan Sauran." Nace, "Zankula Momy." Tace "Dadai Yafi." Kafin Tasa Hanun Cikin Jikkar Cinikin ta Na Ƙwasai da Dankali Taɗauko Kuɗin Kk Napep Tabani. Na'amsa da Godiya Natafi Ina Yimata Sallamar Sai Na dawo. Gane Tafe Har Plus Center Aka Ajiyeni Nakira Dr Jabir Gamida Sanar da shi Cewar Na'iso. Yace, "Jirani Ina Zuwa." Minti Biyar Sai Gashi Yana Tambaya ta Ina Mai Kk Napep ɗin Nace, "Na Sallame Shi." Murmushi Yayi Tareda Cewa, "da kyau Hajjaju." Cikin Ƴar Shagwabar da Bana Rabo Nace, "Momy ce Fa Tabani." Kallona Kawai Yayi, Kafin Yayi Hanzarin Kauda Kansa Yajuya Yanufi Cikin Nikuma Ina Binsa Abaya Cak! Ya tsaya Sai da Na Iskesa Sannan Muke Tafiya Tare. Ƙarkashin Wata Rumfa Muka Zauna Kan Wasu Fararen Kujerun Roba, Rumfar An Lailayeta da Wani Irin Grass Carpet Sai Iska dake Hurowa Akai-Akai. Lemu da Met pie Dakuma Donoth Yasa Aka Kawo Mana. Bayan Ankawo Yasoma Cin Nashi Nikuwa Na Harɗe Kawai Kan Kujera Riƙe da Wayata Batareda Nasan Taƙamammen Abinda Nakeyi da ita. Gabaki ɗaya Na Matsu Inji Me Wannan Haɗuwar Tamu Take Nufi Ko dan Yalura da Hakanne Yasa Yakemin Jan Aji Oho. "Me Kike Jira Bakici Ba?" Naji Muryar sa ta Ratsa dodon Kunnena. Naɗago dara-daran Idanuna Tareda Kallon Sa Shima Yaɗago Kai Yana Ƙokarin Kallo na Aikuwa Nayi Hanzarin Maida Nawa Ƙasa Saboda Bana Iya Haɗa Ido Dashi. Kwata-kwata Tsoron Mayyun Idanunsa Nakeyi Masu Wani Irin Maganaɗiso. "Nace Me Kike Jira Bakici ba?" Yasake Maimaita Maganar Sa. Na Zumɓuri Baki Cikin shagaɓwar Tawa Nace, "Ni Bana cin Abinci A Waje." "Da Kyau, Sanda Kike Fita Yawon Holewa da Ire-iren Su Alh Saminu Keke Iya Cin Abinci A Waje Ko? " da Wata Irin Razana Nake Kallon Sa Mutumen Nan Shu'umi ne Ya'akayi Yasan da Wannan Maganar? "Nikam karki Haɗiye ni Irin Wannan Kallo Haka." Nayi Hanzarin Ruzunar da kaina Ƙasa Cikin Kunyar Yanda Nasaki Baki da Hanci Ina Kallon Sa. Nasoma Wasa Awarwaron da Ke Hannuna. "Khaleesat!" Karo Na Farko Da Na Soma Jin Suna na A bakinsa Kamar Kuma Shi Yaƙirƙiri Sunan Saboda Iya Fadarsa. Kai Dr Jabir Karshe ne. Naɗago da Kaina Tareda Cewa, "Na'am!" "Ɗauki Abincin Nan Ki ci." Yafaɗa Cikin Wani Irin Bada Umarni. Haka Nasoma Cin Mitpie ɗin Sannu A Hankali Kamar Wadda Ke Cin Kashi. Yayinda Shikuwa Yagama Cin Nashi Yaɗauki Lemun Yana sha. A Raina Nace, 'Shidai Baya Wasa da Cikinsa Kenan.' Gyaran Murya Yayi Sannan Yasoma Magana. "Nasani Kina Cikeda Mamakin Haɗuwarmu Nan da Kuma Son Sanin Meye SILAR Haɗuwarmu Anan ɗin." Kafin Yaɗan Numfasa "Tau Ba Komai bane Yasa Na Nemi Da Mu haɗu ba Saboda Ina Son Yi maki Wani Taimako ne Tau Amma Ina Son Kimin Alkawarin Gayamin Gaskiya Sa'anan Ki Saki Jiki Mu Tattauna Sosai Cikin Fahimta." Yakarasa Maganar Yana Mai Tsura Min Ido. I zuwa Yanzun Na dakata daga Cin Mitpie ɗina Shi kawai Nake Saurare Batareda Wani dogon Nazari Ba Nace, "Nayima Alƙawari." Yace, "Good! Dafari dai Ina Son Insan Wane Plan Kike Shiryawa A Yanzu?" Nayi Shiru Ina Kallon Sa Kamar Ban Fahimci Maganar tasa ba Saidai Nafahimcesa Tsabagen dai Mamaki ne Na Irin Wannan Kaifin Tunanin Nasa ne Nake. "Ina Nufin Wanda Kika Saba Shiryawa Aduk Sanda Kikaga Wani Abu Da Ke Ƙokarin Rabaki da Masoyinki Abdul-wahab." Muka ɗanyi Shiru Cikin Nazari Yana Kuma Jiran Cewata Saidai Haryanzun Bance Komai Ba. Zan Tsahirta Nima Anan Kafin Suma Suɗan Tashi Cewa Wani Abun Na dawo Maku A Chapter ta Gaba Kuci Gaba da Kasancewa Tareda Alkalamin 👇 FA'IK. ✍🏼 [9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....35 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Na Sadaukar Da Wannan Chapter Ga Yar Uwa A Harkar Rubutu HADIZA SALISU SHARIF. Wacce Tarigamu Gidan Gaskiya Ya ALLAH Ka Karɓi Bakwancinta Ka Kyautata Tamu In Tazo. 🙏 Bissmillahi Rahmanin Raheem!!! Ya Sauke Ajiyar Zuciya Kana Yace, "Ok! Bari Nayi Maki Gwari-gwari Inji Matar Bagware. Daga Sanda Momy Ta Kawoki Asibiti Ranar Farko kenan da Muka Fara Haɗuwa Na Ganki Nasan Akwai Tarin Abubuwa A tattare da Rayuwar ki daganan Nikuma Nafara Bibiyar Rayuwar ki Harna Gano Irin Soyayyar dake Tsakanin ki da Abdul-wahab Da Yanda Iyayenku Suka Ki Amincewa (Musamman Iyayen ki)Har zuwa Sanda Alh Saminu Yazo da Niyyar Aurenki Kika Masa Korar Kare Wanda A Zaton Iyayen ki Shine Yaƙi. daganan Kikaji Cewa Ai Ga Dalilin da Yasa Iyayen ku Basa Son Auren Naku Watau Suna Ganin ME NA SAMA YACI.... Balle Na Ƙasa Yasamu. Watau Bayada Aiki Mai ƙwari Da Zai Riƙe kiyi Rayuwa Irin Wacce Suke Buƙata. Sai ke Kuma Kika Shiga Bin Maza Musamman Alhazai Kina Tatsar su KUƊI Kawai dan ki tara Ki bawa Abdul-wahab Saboda Shima Yayi Kuɗin da Iyayenki Suke Buƙata Abarki Ki Aure shi Tau Nan Ma Plan ɗinki Bai Ci Ba dan A Sanda Kikaje Gurin Abdul-wahab ɗin Shi Kuma Amatsayin Mayaudariyah Yake Kallon Ki. Mutanen Unguwar Ku Suka Miki Mummunan Shaida Harzuwa Sanda Dady Yazo Yaji Ya Fatattakeki Kika Maida Mota Amma Kuɗin Haryanzu Suna Nan A Wancan Acc ɗin Baki Maida Ba Kuma Baki Taɓa Su Ba Hakane?" Cikin Wani Irin Sanyi jiki da Matuƙar Mamakin yanda duk Akai Yasan Wannan Na Girgaza Masa Kai Tareda Cewa "Eh." Shikuwa Yaɗora, "Indai Taƙaice Maki Zance Harkawo Yanzu Da Na Shigo Rayuwar ki Da Tawa Manufar Nima Baki Saduda Ba. Kina Nan da Ƙudurin Na Bazaki Auri Kowa Ba Sai Abdul-wahab Hakanan Nasan Kina Nan Kina Shirya Wani Plan Yanzun da Akace An Sanya Ranar Auren Mu Shine Kuma Bansani Ba Menene Kike Shiryawa?" Shiru Nayi Cikin Nazari da Tunanin Harzuwa Sanda Naji Yana Cewa, "Karki Manta da Alkawarin da Kikayimin." Jin Hakan Yasa Naɗago Ina Cewa, "Hakane Ina Shiryawa Saidai Wallahi Nayi Mamaki yanda duk Kasan Wayyanan Abubuwan, Saidai Ba Wannan ba Kafin Nabaka Amsar Tambayarka. Bari In Fara Sanar Dakai Dalilin da Yasa Na Aikata duk Wayyanan Abubuwan Nafarko ALLAH Yajarabceni da Wani Irin Son Abdull Wanda Nima Ban San Iya Adadin sa Ba tun A Ranar Farko da ALLAH Yaɗora ƙwayar Idanuna Akanshi Kuma duk Yanda Nayi Ƙokarin Cire Hakan A Raina dan Bin Umurnin Iyayen Nawa Sai Inji Nagagara Yin Hakan. Hakanan Shima Yana Min Irin Wannan Son Shiyyasa Ma Mukayi AMMANA Cewa Bazamu Iya Rayuwa Matuƙar Bama Tare da Juna Saboda Shima Yasamu Matsalolin Sosai da Gidan Nasu Akaina. Gameda Plan ɗinda Ka Tambayeni Kuwa Maganar Gaskiya Abunda Na'aje A Raina Kawai indai Har Kuka Matsa Sai Anyi Auren Nan Tau Kawai Ana Gobe Ɗaurin Auren In gudu Zuwa Wata Duniyar Bazan dawo Ba Har sai Sanda Su Dady da Momy Suka Gane MANUFA TA Ko Kuma Inshi Abdul-wahab Ya yarda Kawai Mugudu Zuwa Inda Za'a Fahimce mu Muyi Auren mu Wannan Shine Plan ɗinda Na Tsara." Nayi Shiru Ina Kallon Sa Yayinda Shikuwa Yayi Shiru Cikin Nazari Kafin Yayi ɗan Murmushi Yaɗago Ya na Kallo na "Kin gamsu da Wannan Hanyar da Kika Bi?" "Nagamsu Sosai Nasan Kana Jiyemin Faɗawa Wani Hali Inna Bar Gidan Ko?" Nacigaba Batareda Najira Amsarshi Ba Dan Bana Buƙata "Idan Na Zauna Ma Cituwa Zanyi Bana Tunanin Zan Iya Rayuwa da Wani Ɗa Namiji Inba Abdul-wahab Ba, Bana Tunanin Zan Iya Biyayya Ga Mijin da Zan Aura, Bana Tunanin Zai Samu Kulawa ta Bana Tunanin Kasancewa Cikin Walwala Komai Daren daɗewa ko Kai Babu! Babu!! Da Yawa Dr Ka Kuwa San Babu Mijin da Zai Juri Hakan dai Ko? Bugu da Ƙari Ga Babban Zunubi Ina Gidan Wani Amatsayin Matar Sa Amma Ina Alaƙa ko Tunanin Wani. Shiyyasa Kawai Na Zaɓi Bin Wannan Hanyar Tunda Nayi Iya Nawa Ƙokarin Dan Fahimtar da Momy Sun Kasa Fahimta ta. Dr Zuciya Bata da Ƙashi Haka Kuma Shaiɗan Fa Ba Rago Bane In Har Aka Hana Mana Rayuwa Ta Hallatacciya Hanyar Muna Iya Kuma Risƙar Kammu Ta Hamratacciya Hanya Idan Muka Yi Hakan Kana ga Zai Mana Kyau? " A Wannan Lokacin Muryata Ta Soma Rawa Tuni Hawaye Ke Kwarara A Idanuna Kamar An buɗe Famfo Cikin Kukan da Ke Tasomin Ina Ƙokarin danne shi Na ɗora Zancen Nawa Da Cewa, "Ai Kaga Ko gudun Faruwar Hakan Yana Sa Ingudu Ko? Bansan Meyasa Su Momy Suka Kasa Fahimta ba Meye Illar Abdul-wahab Yana da Aikinsa Gwargwado da Zai Fita Yasamu Muci Shikuma Arziki Na ALLAH ne Ba Wanda Yasan Inda Rana Zata Faɗi, Tana Yuwa Mai Kuɗin da Suke So In Aura ɗin Zuwa Gaba Yasamu Karayar Arziki Abdull ɗinda Baya da Yayi ARZIKIN. Haka Kuma Tana Yuwa Ko Bai Samu Karayar Arzikin ba Shima Abdul-wahab Yayi Nasa ARZIKIN Bayan Haka Tana Yuwa Ina Auren Wani Can Amma Saboda Soyayyar da Mukeyi wa Juna Yazamana Muna Tare Kaga Kuma Haka Ai Baidace Ba Ko?" Kai Haka Nayita Kawowa Dr Jabir Misalai daban-daban Gwargwadon Iya Nawa Tunanin da Kuma Yanda Zai Fahimci Illar Abinda Su Momy Ke Sonyi Mana Wanda Kuma Tuni Zuciyata Ta Karye Na Soma Kuka Wiwiwi dan Haka Nakifa Kaina Kan Center table ɗin dake Gabamu Nacigaba da Yin Abuna Saboda Wani Irin Ƙunci da Nakeji Yana Tasomin Mussaman In Na Tuno Irin Rabuwar da Mukayi da Abdul-wahab A Wancan Ranar da Kuma Yanda Suka Bar Gidanmu. Idanun Dr Jabir Suka Kaɗa Sukayi Jazir Kamar Barkwano Aka Watsa Masa Cikinsu Saboda Yafi Kowa Sanin Abinda Takeji Tunda Shima Tashi Masoyiyar Aka Raba Shi da Ita Akayi Masa Auren Zumunchi da Maman Asharaf Har Kuma Gobe Yanaji Cewa In Masoyiyar Tasa Zata Fito daga Gidan Auren ta Koda Takai Tsufan Kwando ne Zai Iya Auren ta. Cikin Sanyin Murya Yace, "Is Ok, Kukan Ya'isa Haka Karɓi Wannan Kishare Hawayenki." Ba Musu Na Karɓa Ina Goge Hawaye na Saidai Ina Gogewa Wasu Na Zuwa. Dan Haka Ƙyallen Yajiƙe Sharƙaf da Hawaye na. Yace, "Baifa Kamata Kina Wannan Kukan Haka Ba Dan Bazan Samu Nutsuwar Yimiki Bayanin MAFITAR Da Nasamo Miki da Kuma Irin Taimakon da Nake da Ƙudurin Yi Maku Ba." Jin Wannan Kalamin Yasa Hawaye Suka Kafe Kaf Babu Abinda Nake Buƙata da Muradin Ji Irin Mafita da Taimakon da Yace Zaiyi Mana. Ganin Hakan Yasa Yaɗan Nisa Gamida Cewa, "Yawwa Ko Kefa." Kafin Yaɗora Da Faɗin, "Na Gamsu da Kalaman Ki Sarai Kuma Ko Bacin Hakan Kullum Ana Nuna Mana Illar Auren dole Duk-da Bance Bayada Fa'ida ba, Amma dai Yana da Kyau Ake Sa Kula Cikin Abubuwan dan Gudun Kilu ta Ja Bau Nawa Ne Aka Yiwa Auren Suka Sawa Mazajen Guba? Nawa ne Akayi wa Auren Suka Shiga Duniya Yawon KARUWANCI Nawa Ne Aka Yiwa Auren Yakasa Daɗi Aka Rabu? Kai gadai Matsaloli Nan Barkatai." Naɗago Kaina Ina Mai Sake Kallon Sa Ina Ji A Raina Nan Duniya Ba Mutum Mai Fahimta Kamar Dr Jabir Hakan Yasa Darajar sa Da Nake Gani Ta Ƙaru A Idona. "Tau Kagani Kaima dai Ga Ma Wayyanan Matsalolin Wayanda Ni Nawa Tunanin Ma Bai Kai Kansu Ba." Acikin Zuciyata Nake Maganar Batareda Nasan Cewa Ashe Tafito Fili ba, Sai Ji Nayi Dr Jabir Yace, "Wayyanan Ma Wayanda Nasanine Nima Wani Ma In Zai Gayama Maki Nashin Sanin Sai Kiji Mu Bamu Faɗo Komai ba." "Hakane." Nafaɗa Cikin Sanyin Muryar da Duk Wanda Yaji ta Zai San Taci Kuka Harta Shaƙe. Shikuma Dr Jabir Yaci Gaba da Koromin Nasa Jawabin. "Tsakani da ALLAH Ni Bana Son Wani Na Aure Ki." Nayi Hanzarin ɗago Kaina Ina Kallon Sa. Yagirgiza Kansa Irin Na Tabbatarwa ɗinan. Yaci Gaba, "Kamar Yadda Kikaji Bana Nemiki Bane Dan Na Aure ki Bane Na Nemi ki Ne Dam Na Taimaka Maku Domin dai Daga Sanda Kuka Zo A Rana Ta Farko daga Asibiti Nafahimci Irin Halin da Kike Ciki Wannan Yasa Na Shiga Bibiyar Rayuwar ki Har Na Gano Komai Sai Nazaɓi Bin Wannan Hanyar dan Na Taimaki Soyayyar ku Keda Abdul-wahab Kuma Bawai dan Bana Sonki Ba A'a Nadai Lura Indai Son Gaskiya Nakeyi Maki Tau Na Taimaka Maku Ne Kawai Ta Wannan Hanyar Saboda Haka Duk Abinda Kika Ga Ina yi Na Abinda Ya Danganci Aurenki Wallahi Plan ne Sai dai, Babu Wanda Yasan Wannan Maganar Dagani Sai Mahallicina Sai Kuma Ke Yanzun da Nasanarwa Saboda Anzo Gaɓar da Yakamata Ki Sani bugu da Ƙari Kuma, Ki ɗora Daga Inda Natsaya Domin Yanzun Aikin Ke Zaki Cigabada." Yaɗan Yi Shiru Tareda Jawo Gwangwanin Maltina dake Gabansa Yatsitsiya A Cup Yana Sha. Yayinda Nikuma Nake Kallonsa Cikin Ƙullewar Kai A Kan Maganganunsa Da Kuma Jin Mamakin Cewa Wai Duk Neman Aure na Da Yakeyi Ba Gaske Bane Plan Ne. "Kallon Ya'isa Haka fa." Yafaɗi Hakan Cikin Sigar Wasa. Yayinda Nikuwa KUNYA Tayi Min dirar Mikiya dan Haka Sai Na Sunkuyar da Kaina Ƙasa Tareda Ci Gaba da Wasa da Awarwaron Hannuna. Ina Mai Cike da Zumuɗin Son Yaci Gaba da Gayamin Inda Maganar Sa Ta Dosa. Ina ga Hakan da Yafahimta Ne Yasa Yayi Shiru Yana ɗan Jamin Aji Ko Miskilancin Nasa ne Kawai Ya Motsa? Oho! Ina Cikin Wannan Nazarin Ne Naji Muryar sa Tacigaba da Ratsa Kunne Na. Yana Mai Cewa, "Tunda Su Momy Sun Kasa Fahimtar Wancan YAREN Dole Zamu Fahimtar dasu Ta Wannan YAREN da Indai Basu Fahimce sa ba Tau Babu Wani Yare Kuma da Zasu Gane. Gameda Cewar da Nayi Anzo Gaɓar da Kece Zaki Ci Gaba da Buga Wasar Kuwa Shine... Akwai Wata Allura da Mu Likitoci Mukeyi. Tana ɗauke Ma Mutum Numfashi Na Tsawon Zuwa Lokacin da Aka Buƙata dan Haka Wannan Allurar Ita Zaki zo Wurinane Inmaki Ita Adai-dai Lokacin da Yarage Saura Kwana ɗaya Buki. Za'a Tafi Akan Kin MUTU Aɗaukeki Zuwa Maƙabarta Bayan An binne ki Mutanen Sun Watse Sai A Tono ki Muje dake Wani ƁOYAYYEN Wuri da Sai Komai Yadai-daita Mun Kuma Tabbatar da Su Momy Sunyi Laushi Sun Kuma Yi Nadama Akan Abinda Suka Aikaita Sai Ke Kuma Ki Dawo Ina Fatar Kin Gane Karatun?" Yaƙare Maganar Yana Mai Kallo Na. Yayinda Ni Kuwa Zuciyata ke Dukan Ukku -Ukku Tun Daga Sanda Yazo Gaɓar Da Za'a Binneni Ina Mai Tambayar Kaina Anya Kuwa Zan Iya Wannan Babbar Kasadar Kuwa? Kamar Ya Fahimci Tunanin da Nakeyi dan Haka Yaɗan Musƙuta Cikin Son Ƙarfafa min Gwaiwa Yace, "Tabbas Akwai Babban Ƙalubale Sosai Acikin Aikinan Amma In Kika Jajirce Zaki Iya, Sannan Yin Hakan Fa'ida Biyu Gareshi. Nafarko Zaki Samu Cikar Burin ki Sa'annan Zaki Ƙara Tabbatar da Irin Sonda Abdul-wahab Keyi maki Hakanan Suma Iyayen Naku Zasu Tabbatar da Irin Girman Soyayyar Dake Tsakanin Ku Su Barku Kuyi Auren Ku Cikin Farinciki. Saidai Bazan Matsa Maki ba, Nabaki Nan da Kwana Biyu Kije Kiyi Shawara Saidai Da Sharaɗin Bazakiyi Wannan Maganar da Kowa Ba Hakanan Bazaki Shawarar Ta Da Kowa ba, Because Wannan Ko Acikin SIRRI SIRRINE Maigirma dan Haka Da Zuciyar Ki Kawai Na'amince Maki Kiyi Shawara Sannan Karki Manta ni Kawai Inayi Ne Dan Na Taimaki SOYAYYARKU Bayaga Wanna Bana da Wani Abu da Zan Ƙaru Dashi." Kafin Yaɗan Tsahirta Da Yin Maganar Yana Mai Duban Agogon sa dake Ɗaure A Tsintsiyar Hannunsa Yaɗago Yana Kallona Gamida Cewa, "Tashi In Maida Ki Gida Lokacin Sallar Magarib Na Matsowa Ga Kuma Yanayin da Muke Ciki Yanzun Kowane Lokaci Ruwan Sama Na Iya Tsugewa." Kuzo Muje Musamu Mafaka Kar Ruwan Yatsuge damu Sai Muci Gaba da Labarin Tareda Alkalamin👇 FA'IK. ✍🏼 [9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....37 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem!!! Fahimtar Hakan da Nayi Nikuma Naci Gaba da Ribatarsa da Kalamai Masu taushi Wayyanda Nake Ganin Zasu Sashi Yafahimci Halinda Nake Ciki da Kuma Halinda Zanshiga Idan Ban Samu Wannan Taimakon daga Gareshi ba Da Kuma Makoma ta Akan Auren da Su Dady Ke Shiri Yimin da Irin Mutumci da Girmama Juna dake Tsakanin mu dashi Haryasa Na Zaɓeshi Amatsayin Wanda zai Taimaka Min. Wayyanan Lamuran Su Sukayi Tasiri Ga Sani Harya Amince Zai Min Wannan Taimakon Zai Kuma Nemi Amintattun Abokan sa dan Su Tayashi Yin Wannan Aikin. Daganan Nikuma Na bashi Sabulai da Mayukan da Naɗauko Masa Wayyanda Ko Dama Can Nasaba Yimasa Irin Wannan Kyautar. Mukayi Sallamar Cikin Girmamawa da Mutunci Kowane mu Yanufi Inda Zashi. Yayinda Nadawo Cikin Gida Da Tunanin Yanda Al'amurrah Zasu Gudana Tareda Adu'ar ALLAH Ya Bani Nasara Su Tafi Dai-dai Yanda Nake Buƙata. Tau Haka dai Akayi Washe Gari Sai ga Sani Yazo da Amintattun Nasa Muka Kashe Muka Binne Akan Abubuwan da Za'ayi Batareda Kowa Yasani Ba. Nakawo Kuɗɗi Masu Tsoka Na basu Kyauta Sa'annan Nadawo Gida Cikin Farinciki Cewa Aikina Zai Tafi dai-dai. Daganan Na Kira Dr Jabir A Waya Nasanar Dashi Duk Halinda Ake Ciki Ya Jinjina min Sosai Akan Irin Tawa Hazaƙar Nima. Tau Shine Kafin Afara 'Kamu' Naje Gurin Dr Jabir Yayi min Wannan Allurar Tareda Faɗamin Sanda Zata Fara Aiki da Kuma Sanda Zata Ƙare Aiki dan Haka In Kula Sosai Fa Kar Asamu Matsala Kuma Na Jadadda wa Su Sani Karsu Yi Ƙwaurin Zuwa Su Tononi Sbda In Suka Wuce Lokacin Za'a Iya Samun Matsala. Nace, "Insha'allah. Zan Kula." Haka Nayima Sa Godiya Iya Godiya Nabaro Wurin Sa Nadawo Gida Bayan Naga Sani Naƙara Jadadda Masa Shima Yace, "Zasu Kula." Sa'annan ne fa Hankali na Ya kwanta Nadawo Cikin Jama'a Aka Shiga Harkokin Buki." Haka Kuwa Akayi, duk Yadda Muka Tsara Abubuwan Haka Suka Kasance Har'izuwa Sanda Su Sani Suka ɗauko ni daga Maƙabarta Zuwa Gidan Dr Mai ƁOYAYYEN Suna da Kuke Ganin Mu Yanzun Atare Wanda da Taimakon Sa Komai Ke Tafiya. Nanne Nasamu Labarin Halinda Abdul-wahab Yake Ciki Nashiga Tashin Hankali Matuƙa Tun Suna Asibiti Naso Inje, Amma Sai suka Hana ni da Cewar, 'Ba yanzu ne Yakamata In Bayyana ba Harzuwa Sanda Aka ce Ya Haukace Tuɓuran DuK Ina Samun Labari ne ta Wajen su Dr Harzuwa Sanda Aka Kaishi Asibitin Mahaukata Ta Ƙaramar Hukumar Kware. Ranar Nayi Kuka Harna Ba Ukku Lada, Haka dai Su Dr Sukayi ta Tausa ta Da Cewar Haƙuri dai Zaniyi In Ba Haka ba Zan Iya Wargaje Mana Shiri Dahaka dai Na Haƙura Har Lokacin da Dr Mai ƁOYAYYEN Suna Ya Buƙaci Inzo Yaukam Lokaci Yayi Zamuje ne Asibiti Infara Ganawa da Su Abdul-wahab Gama Yana Ganin Yanzun Jikin Nasa Yayi Sauki. Tau Shine Fa Muka Zo Suma Kuma Innarmu Sun Shiga Kwatankwacin Irin Wannan tashin Hankalin da RUƊANI A Sanda Suka Ganni Abdul-wahab ne Kawai Bai Wani Nuna ba Wanda Ni Kaina Nayi Mamakin sa, Tau Amma Sai Nabar wa Raina Cewar Maybe Saboda Tsananin Soyayyar da Mukeyi Wa Juna ne Yasa. A gurin su Na Zauna Har'izuwa Sanda Yauɗin Dr Mai ƁOYAYYEN Suna Yaje Shida Baba Tanimu Mukazo Nan Gurin ku. yayinda Na Kawo Nan A Jawabina Sai Muryata Ta Soma Rawa Nacigaba da Cewa, "Tabbas Na Aikata Babban Kuskure Wanda In Baku Ya...." Baba Tanimu Yakatse ni Ta hanyar Cewa, "Ya'isa Haka Khaleesat Zamu Zo Wannan Gurin." Yajuya Gurin Dr Mai ƁOYAYYEN Suna Yace, "Munji daga Khaleesat Yanzun Kaine Muke Buƙatar Ji Daga Gareka Kamar Yadda Ka Buƙaci Mu Taro Anan ɗin dan Kayi Mana Bayani." Gabaki ɗaya Falon Yayi Tsit! Kowanen mu da Irin Al'amurrah da Ke Kai Komo Acikin Zuciyarsa. Wasu Kuwa Hawaye ne Shaɓe-Shaɓe (Irin su Momy Kenan da Ya Nuradeen) Yayinda Tsantsar Mamakin Ɗan Yau da Tarin NADAMA Suke Shinfiɗe A Fuskar Dattijan Gurin (Musamman Dady) Duk Mun San Wannan BayanineTa Hanyar Dr Mai ƁOYAYYEN Suna dake Bin Kowanen su da Ido Yana Kuma Karantar Yanayin da Suke Ciki. Daganan dai Yayi gyaran Murya Kafin Yasoma Cewa, "Da Fari dai Sunana Dr Faisal Kuma Ni Abokine na Ƙut-Ƙut ga Dr Jabir. Baya Ɓoyemin Komai Nasa Kamar Yadda Nima Bana Ɓoye Masa Maganar Gaskiya Akwai Fahimtar Juna Sosai Tsakaninmu. " Yaɗan Nisa Acikin Zancen Nasa Yayinda Kowa Na Falon Ke Binsa da Kallo Lura Da Hakan da Dr Faisal Yayi Yasa Yaɗan yi Murmushi Sa'annan Yaci Gaba da Cewa, "Tau Kamar dai Yadda Khaleesat tafaɗa Maku Haka Abin Yake Kuma Abokina Watau Dr Jabir Yana Tsaka da Aikin Nanne Kuma Saiga Sunan sa Yafito daga Jerin Sunayen da Gwammanti Zata Tura Ƙsar Waje domin Ƙaro Ilimi Akan Abinda Yadangaci Wata Sabuwar Cuta da Ta Ɓulla. Dan Haka A Wani Dare Bayan Nadawo daga Aikina Inagida Tareda Iyalina Yaziryaceni Bayan Sungaisa da Matata Takuma Gabatar Mana da Abin Motsa Baki Sai Tabamu Waje. Domin dai Su Matan Namu Sun san Mafi Yawa Indai Muka Ziyarci Juna A Irin Wannan Lokacin, Tau da Kwai Magana Mai Muhimmaci da Zamuyi. Dan Haka Bayan Mun Keɓe Dai Dr Jabir Yake Sanar dani Wannan Maganar da Kuma Buƙatar da Yake da Ita Na Barin Lamarin A Hannuna Dan In Kammallah Abinda Yafara. Da Fari Na Nuna Masa Rashin Amincewa ta Saboda Ina Ganin Rashin Dacewar Abin Domin Ai Baidace Ayiwa Iyayenta Irin Wannan Yawo da Hankali ba. Tau Amma da Yamatsa min da Bayani da Kuma Nusar Dani Ire-iren Abubuwan da ke Nan Ya Ƙara Gayamin Shirin Na Yarin Na Guduwa Zuwa Wata Duniyar Da Rashin Sani Abinda Illar Hakan Zai Haifar Ga Iyayen da Ita Kanta Yarinyar da Sauran Matsaloli Ma Banbanta da Ya Lissafa Min A Wancan Ranar Kawai Sai Na'amince. Muke Gudanar da Aikin Tare Harzuwa Sanda Lokacin Tafiyarsa Tayi Yabar Komai A Hannuna Nake Ci Gaba da Aiwatar Dashi Ko A Wancan Ranar da Kuka Kawo Khaleesat ɗin Asibiti Ina Cikin Jerin Likitocin da Sukai ta Kai-kawo Akan Halinda Tashiga Saidai Yana yin da Kuke Ciki Bazai Bari Ku Lura Ba. Haka Abubuwan Suka Ci Gaba da Tafiya Kamar Yadda Muka Tsara Harzuwa Sanda Muka ga Yakamata Khaleesat ta Bayyana dan Haka Naɗauke ta da Mota Zuwa Asibitin da Dama Can Nake Aiki Kuma Nike Lura da Abdul-wahab Bawai dan Wasun Basa Lura dashi Ba Saidon Ni Dai Nashiga Lamarin Sosai da Nunawa Yan Uwana Likitocin Cewa Ai Family nane Su. Bayan Nakai Khaleesat ɗin Su Innarmu Sun Shiga RUƊANI Irin Wanda Bazai Misaltu ba Sai Wanda Yagani Kawai. Dan Ita Yayar Tasu Sai da Ta Kwanta Gado Saboda Tsabar Rikicewa da RUƊANIN da Tashiga. Zan dakata Anan Kuma Ina Fatar Muje daku A Chapter Na Gaba Tareda Alkalamin FA'IK. ✍🏼 [9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....36 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem!!! Maimakon Inmiƙe ɗin Kamar Yadda Yabuƙata Sai Na Gyara Zamana Gamida Cewa, "Ai Bamu Gama Maganar ba Ko? Zaɓi Kabani In Bazan Iya Yanke Hukunci Yanzun ba Inje Har Inyi Shawara da Zuciyata." Naɗanyi Shiru Ina Mai Ci Gaba da Yawo Da Idanuna A Harabar da Muke Zaune Kafin Nadawo da Kallona Gareshi Shima ɗin Ni Yatsura Wa Mayun Idanun Sa Masu Matuƙar Kwarjini Wanda Kwarjinin Nasu Yataimaka Wajen Kasa Ci Gaba da Kallonsa Da Nayi Niyyar Yi Sai Kawai Na Ruzunar da Nawa Idon Ƙasa Gameda Cewa, "Shi Ruwan Kashe Gobara Ba'a Tsayawa La'akari da Kyaunsa Ko Akasinsa Kawai dai Amfani Za'ayi dashi dan Kashe Gobarar Dan Haka Na'amince daga Yau Zanfara Aiwatar da Nawa Shirin Duk Yanda Nayi Zan Ma Bayani." "Da kyau Ta Abdul-wahab Ina Miki Fatar Nasara." Yafaɗi Hakan tareda Yimin ɗan Tafi Na Ƙarfafawa. Tau Daganan Kuma Muka Miƙe Bayan Yasallami Masu Gurin Akan Abubuwan da Muka Ci, Yashiga Wasu Shagona dake Cikin Plus Center ɗin Yayiwa Iyalansa Shopin dangin Su Makilin da Su Brush Kayan Tea Dakuma Kayan Makulashe Harda Nima Sai da Yayiwa Nawa Shopin ɗin Yafito Hannayen sa Rike da Manya-manya Ledoji dake ɗauke da Tambarin Shagon da Yashiga Yasameni Ina Jingine da Motar sa da Yayi parkinq ɗinta A Wajen Harabar. Yabuɗe Gidan Baya Yasaka Ledojin Sannan Muka Shiga Gidan Gaba Muka Soma Tafiya. Da Fari Motar Tsit Tayi Inbada Muryar Mai Labarai Da Yakamo A Radion Motarsa Bakajin Komai. Daga Bisani Kuma Muka ɗora Hirar Tamu Wacce Mafi Yawanta Muna Tattauna wa ne Akan Yanda Plan ɗinmu Zaije Batareda Ansamu Akasi ba. Gamunan-gamunan Hargida Yayi Parkinq Nafito Kamin Yamiƙo min Ɗayan Ledar Tareda Cewa, "Ki Gaida Su Momy Ban Shiga Nagaishe su Ba Yau Nayi lattin Komawa Gida Nakuma San Hukunci na Nacan Najirana." Murmushi Nayi Ina Faɗin, "Ai Gara hakan, Sabida Kuɗinne Sai da Hakan dan Bakwa da Tabbas." Yace, "Lalala Lalle Yarinyar Nan Kinyi Baki yanzu Saboda ALLAH Macce Batafi Namiji Rashin Tabbas ba?" Nace, "Uhummm Kadai Faɗane Kawai Amma Ni Nasan Munfiku Tabbas." Dariya Yayi Yana Mai Shafa Sumar Kansa Kafin Ya tayarda Motar sa Yana Cewa, "Shikenan Ai, MAUDU'I Nan Yana da Girma gashi Ba Lokaci Amma Tabbas Sai Na Samu Lokaci Nahaɗu da ƊAN JARIDAR NAN ABDULLAHI IBRAHIM SOKOTO Su Saida Mana Fili A Radion su Dan Mu Tattauna Wannan Matsalar dani dake dashi A Kuma Buɗe Layi Jama'a Sukira Muji Su Waye da Nasara." Nima Cikin Dariya Nace, "Tau ALLAH Yabaka Iko Amma Ni Nasan Zaku Faɗi Warwas Ne." Yaja Motarsa Yana Ta Dariya Tareda Faɗin "Baki da Dama Ni Kinga Tafiya ta Karki Sa Amini Hukunci Mai Yawa." Yabarni Nan Tsaye Ina Bin Motarsa da Kallo Nima Kuma Dariyar Nakeyi Hakanan Zuciyata Na Ƙara Gayamin Cewa Ba Mutum Mai daɗin Sha'ani Yakuma San Darajar ɗan Adam Kamar Dr Jabir. Ni Ina Masa Mummuna Kallo Ashe Yashigo Rayuwata Ne Kawai dan Yataimake ni, Sai Nake Tambayar Kaina Ko Ina Yasamu Irin Wannan Hazaƙa Shida Yakaranci Fannin Likitanci? Kila Kuma ABOKIN Nasa ɗan Jarida Abdullahi ibrahim Sokoto Yafaɗa Masa Irin Wannan Idaeyar. Gama Ni Ma'abociya Sauraren Shirye-shiryen Sa Ne Musamman Shirin sa Na 'LAMBUN MASOYA' Inajin Yanda Yake Warware wa Masoya Matsalolinsu Sosai. Hakanan Wani Lokacin Nikanji Shi Yace Yasadaukar da Wannan Waƙar Ga Abokin sa Likita Bokan Turai (Watau Dr Jabir)Ina Cikin wannan Karatun Wasiƙar Jaki Har Dady Yafito Zuwa Massallaci Zaiyi Sallar Magarib Yana Mai Riƙe da Hannun Muyiddim Zasu Masallaci Tare. Nayi Hanzarin Rusuna Wa Ina Gayar Dashi Ya'amsa Cikin Fara'a Wacce Banyi Tsammani ba, dan Nazata Zaimin Faɗa Ne, Amma Sai Yacemi, "Kun Dawo? " Nace, "Eh." Yace, "Ok Shi Jabir ɗin Yawuce ko? Ai Yakirani Yace min Zakuje ne Ki zaɓo Wasu daga Kayakin da Za'a Samaki Cikin Lefe Sbda Yafi Son Yasiyo Maki Zaɓinki." Nace, "Eh Hakane Dady." Yajuya Yana Faɗin "Tau Ai Saiki Hanzarta Shiga Gida Ki Samu Kiyi Sallah." Da Faɗin Haka Yaja Hannun Muyiddim da Nufin Suje Masallaci Tare Amma Sai Muyyudim Ya taɓure Ba'inda Zashi Yaggani da Ledar Kayan Kwaɗayi. Dady Yasake Hannunsa Yawuce Abunsa Gamida Cewa, "Kai Kasani Sarkin Kwaɗayi." Yabarmu Muna Ta Dariya. Tunda Nashiga Gidan Nakuma Fitar wa da Muyiddim da Bisket da Chocolat ɗinda Ke Cikin Ledar Nabashi. Sai Nashiga Nima Haramar Sallah. Bayan Na Kammallah Kuwa Nafito na ɗebi Abinci Na Nufi ɗakina dan Nasan Innace Bazan Fito ba Momy Zata Zargi Wani Abin. Abincin Kuwa Banbi Ta Kansa ba Sai Da Naɗauko Biro da Memo Na Tsara duk Yadda Nake Bukatar Abubuwan Suje Batareda Ansamu Cikas! ba. Sa'annan Nazauna Cikin Farinciki da Kuma Gamsuwa Kan Yadda Natsara Abubuwan. Ina Gama Cin Abinci Kuwa Aka Ci Sa'a Sani(Almajirin gidamu)Yazo Karɓar Abincin sa Nai Maza Nafito Tsakar gidan Ina Cewa "Sani Kashigo?" Yace "Eh Aunty." Bayan Na ɗauko Masa Abincin Nasa Nace, "Ina So Muyi Magana da Kai Sani In ka gama Cin Abinci Kasameni Ɗakina." Cikin Matuƙar Mamaki Hakan Yace, "Magana Kuma?" dan Bamu Taɓa Ƴar Haka dashi ba Komai Za'ayi Tsakar gida ne. Ganin Hakan Yasa Nace, "Kai Karka damu Bafa Wani Abu Bane ba, In ma Baka Nutsu da Muje ɗakin ba Bari Muyi Maganar A Harabar Gida." Yace, "Aha Zamu Iya Maganar Kawai Yanzun dan Banan Zanci Abincin ba Sai Naje Makaranta." Nace, "Tau Yayi Jirani A tsakar Gidan Ina Zuwa." Kafin Na Nufi ɗakina "Bari Nayiwa Su Momy Sai da Safe Kafin Kifito." Sani Yafaɗi Hakan Yana Mai Nufar Ɗakin Nasu Momy. Ledar da Muka Dawo da Ita Na buɗe Nadebo Sabulai Na Wanka da Na Wanki da Mayukan Shafawa da Turaren Nazubo su A leda Nafito. Dai-dai Lokacin da Sani Shima Yafito Zuciyarsa Cikeda Saƙe-Saƙe Yabiyo Bayana Harzuwa Sanda Muka Samu Wuri daga Cikin Harabar Gidan Namu Na Zauna Ina Mai Kallon Sani Da Yayi Tsaye Yana Kallo na Cikin Maɗaukakin Mamaki, Saboda Irin Wannan duguwar Hulɗar Bata Taɓa Shiga Tsakanin mu ba. Duk Hulɗar da Zamuyi Mukan Yita Ne Idan Aiki Yahaɗa mu Kamar Inyazo Taya mu Aiki Nan Gida Ko kuma Muna Wurinda Momy Ke Saye da Sai Suwanta. Nadubeshi Yana Tsayen Nace, "Zauna Mana." Ba Musu Yazauna Naci Gaba da Magana "Sani Wani Taimako Nake So Ka yimin Basai Na Tsaya Yima Bayanin Aure na da Ake Kusa da Yinsa Ba Nasan Kasani Kuma Kasan da Irin Matsalolin da Nake Fuskanta da Su Momy Kan Su Bani Wanda Nake So Amma Sunƙi Sudai Sai Na Auri Zaɓin Su Duk-da Kuwa Irin Bayanin da Nake Tayi Musu Da Magiya Saidai Sun Kasa Fahimta ta Dan Haka Na Yanke Shawarar Ɓullo Musu Ta Wata Hanyar da Nake Kyautata Zaton Zasu Fahimta Insha'allah Wannan Kuwa Ita ce 'Zanyi MUTUWAR Ƙarya Aje Abinneni Tau Ina Son Bayan Mutane Sun Watse Kuje Kaida Wayansu Amintattakunka Ku TONO NI Kuɗaukeni Zuwa Wani Wuri Da Nan Gaba Zanbaka Adireshin Sa." Tunda Na Fara Wannan Maganar Sani Yake Kallon Na Cikin Mamakin da Yafi Wanda Yake Ciki A tun ɗazun Dan Saida Ya Firgita Sosai. Zan ɗan Numfasa Muje daku A Page Na Gaba. Tareda Alkalamin 👇 FA'IK. ✍🏼 [9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....39 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem!!! "Tau Ai Gashi Takaika ga Zubda Hawaye Ko?" Baba Tanko Yafada Yana Mai Kallon Dady. Yayinda Dady Yagirgiza Kai Kawai. Baba Bukar Yace, "Ba'a haka Mustapha, Ɗan Hakin da Ka Raina Shi Zai Tsole Maka Idanu Yanzu da Ka Sanar Damu Matsalar Ai dai Komai Girman ta da Ƙanƙantar ta Za'ayi Wa Abun Tufkar Hanci Amma Sai Kayi Watsi damu Saboda Yanda Yaya Yace ɗin Ko?" "Dan ALLAH Ku Gafarceni Na Tuba." Dady Ke Wannan Maganar Cikin Girgiza Kai. Baba Tanimu Yace, "Bukar Mubar Wannan Maganar dan Ba A Muhallin da Yadace Muyi ta Bane Yanzun Saboda ɗiya da Jikoki dakenan Mayi ta Daga Baya. Baiwar ALLAH!" Baba Tanimu Yafaɗi Hakan Yana Mai Juyowa Gurin Innarmu Nufin dai da Ita Yake Kafin Yace, "Kundai Ga Sakamakon Ƙin Fahimtar Ƴaƴanku yanda Yakasance Shi Ya Haukace Saboda Rashinta Ita Kuwa Ta Munafunci Iyayenta Shin Haryanzu Kuna Nan Kan Bakarku Ko Yaya Hardakai Mustapha Nake da Ke Yawo(Watau Momy)" Gaba ɗaya Suka Shiga Girgiza Kai. Innarmu Ce Tasoma Magana "Wallahi Bama Kai. Kuma Nidai Ko da Na Matsa Akan Karatun Su Samu Aiki Mai ƙwari da Kuma Muhallin Kansu Saboda Kaucewa Irin Abinda Yafaru Yanzun Watau Iyayen Khaleesat da Suka Hana Masa Ita Khaleesat ɗin, Amma Bacin Hakan Ni Bana da Wata Matsala Akan Wannan Lamarin Kuma Kullum Abinda Nake Sanar Dasu Kenan." Baba Tanimu Yagirgiza Kai Cikin Gamsuwa Kafin Yakalli Su Momy da Dady, "Tau Ku Kunji Fa?" Dady Ne Yayi Magana Yace, "Munji Kuma Ni Yanzun Yaya Bana da Ta Cewa Sai Abinda Kuka Ce Na Kuma Fahimta A Baya Nayi Kuskure Na Tsame ku Acikin Lamarina Saidai Yanzun Ina Mai Baku Hakuri." Gaba ɗaya Falon Yaɗauki Shiru Kafin Baba Tanimu Yakalli Momy Yace, "Kefa?" "Mijina Yagama Magana Yaya, Nida Ƴaƴana Mallakarsa ne dan Haka Muna Nan Ƙarƙashin Ikonsa." Momy ce Mai Wannan Maganar Haryanzun Kuwa Bata Daina Share Hawaye A Fuskarta ba. Cikin Wani Irin Yanayi Mai Cikeda Mamakin Sha'anin Duniya. Baba Tanimu Yanumfasa Sa'annan Yace, "Tau Ai Shikenan Yanzu Ni Abinda Nake So Kufahimta Yaranan Suna Son Junansu Kuma Gadai Abinda Ke Bayyane Yaron Nan Bayada Wani Mugun Hali Hakanan Yana da Sana'ar sa Ko Ba Hakaba?" Gabaɗai Falon Suka Amsa da Cewa, "Hakane." Baba Tanimu Yaɗora, "Shi Arziki Na ALLAH Ne Abu Mafi Muhimmaci A Sha'anin AURE Kyaun Hali Mutum, Addinin Sa Sannan Kuma Sana'ar Yi Gashi Ɗa Namiji Kenan. Tun Amma Kafin Ma Azo Ga Wannan Batun Babu Shakkah Yakamata Mu Kalli Matsalar Nan Ta Fuskoki Daban-daban Na Farko dai Harga ALLAH Ku Iyayen Kune JIGO Dan Haka Sai Bango Yatsage Ƙadangare Kan Shiga Ku Yafi Kamata Ace Kun Zama Jarumai Wajen La'akari da Abubuwan dake Kai Komo Nadaga Dangane da Ƴaƴanku da Kuma Zamanin da Muke Ciki Bawai Yin Abu Gaba gaɗi ba. Bansan Ba Ko Kun Fahimce ni ba?" Baba Tanimu Yafaɗa Yana Mai Kallon Su Dady, Momy dakuma Innarmu Duk Suka Girgiza Kai Nufin Sun Fahimta. Yace, "Madallah! Saboda da Kun tsaya Kun Kalli Lamuran Ta Fuskoki Mabanbanta Bana Tunanin Za'a Kai Ga Haka Sannan Kai Mustapha Kan Yanke Zumunchi da Yan Uwanka Batareda Ka Nemi Ku Haɗu Ku Kashe Ku binne Tare ba Kasan Wai Mal Bahaushe Yace, "Aikin Mai Shawara Baya Ɓaci." Haka Zalika Kema Baiwar ALLAH Duk-da Naki Laifin Ba Yawa Saboda Duk Abubuwan da Kika Lissafa Ba Wanda Ya'isa Yayi Inkarin su. Aka Kuma yi Dai-dai da Kunci Karo da Mai Irin Wannan Halin Da Kike Jiye Musu. Sannan Kekuma Khaleesat Baki Kyauta ba Darajar Iyaye Tawuce duk Wata Daraja da Kike Gani Sannan Duk Son da Kike Ikirarin Kina Yiwa Abdul-wahab Bai Kai Wanda Iyayen ki Keyi Maki ba Babban Abun Ma Ki duba Duk Yaƙin Nan da Sukeyi Sunayi Ne Dan Suga Sun Kai Inda Bazaki WAHLA Ba Inda Za'a Kula Masu Dake Kamar Yadda Suke Kula da Ke Ko Ma Fin Haka Amma Kika Zaɓi Yimusu Wannan Sakayyar Yaya Zakiji Sanda Naki Ƴaƴan Sukayi Maki Haka? Iyayen da Suka Reni Ki Cikin Tsantsar Ƙauna da Soyayya Kulawa Harma da tattali Tun Kina Ciki Harkika Zo Duniya Harkika Girma Basu Taɓa Ƙosawa Ko Gajiyawa ba Hargashi Zakiyi Aure A Hakan Ma Ƙokarin Suke Suga Sun Samar Maki da Inda Wannan Ƙaunar Zata Taɗore Mutane Masu Irin Wannan KARAMCI Gareki Shin Sun Cancanci Irin Wannan Sakayyar daga Gareki? Shin Basu Cancanci Kiyi Komai Domin Farinciki su Ba? Gama Ƙaramin Misali Dr. Faisal da Dr. Jabir Abokai ne Amma Yacemaki Dr. Jabir Yacancanci Komai AgareSa Amma Duk Ke Baki zo Ghana Kika Ghano Ba?" Baba Tanimu Yayi Shiru Yana Mai da Numfashi Yayinda Kukan Khaleesat Yatsanan ta Tarin Dana Sani da NADAMA Sukayiwa Zuciyar ta dabaibayi. Taji Tabbas Tayi Butulci Mai Girma Ga Iyayen ta Lalle Kuma So Ya Makantar da Ita Ga Tarin Alkhairin Su Wanda Takasa Gano Cewa Fa Sonda Abdul-wahab Keyi Mata Bai Kai ko Rabin Rabin Wanda Su Momy da Dady Ke Yi Mata Ba. Cikin Kuka Shaɓe-Shaɓe Ta Nufi Momy Tarumgume tana Faɗin, "Momy Nayi Babban Kuskure Wanda In Baku Yafemin Ba Bazan Taɓa Gafartawa Kaina Ba. So Ya Makantar da Ni Na Aikata Abinda Baku Cancanci Inyi Gareku ba. Momy Dan ALLAH Kuyafemin Wallahi Nayi NADAMA Kuma Wallahi Bazan Ƙara ba Nama daina Son Abdul-wahab ɗin Ku Aura min Koma Waye Wallahi Nayi Maku Alkawalin Zama Dashi." Yanda Khaleesat take Kuka Wiwiwi Dole ne Ka Tausaya Mata Hakanan Ma Momy Tarumgume ta Itama Inbanda Hawaye Ba'abunda Takeyi. Gurin Dady Khaleesat Takoma Ta Rumƙumeshi "Dady Dan ALLAH Kuyimin Gafara Bana Son Abdul-wahab Ku Aura Min duk Wanda Kuke so Nayi Maku Alkawalin Zama Dashi Muddin Raina Indai Hakan Zaisa Ku Farinciki Kamin Tajanyo Hannun Ya Nuradeen da Inbanda Hawaye Shima Ba Abunda Yakeyi. "Ya Nuradeen Katayani Bawa Su Momy Haƙuri Nayi Musu Butulci Bansan Meyasa Tun Farko Nakasa Ganen Abinda Yanzun Baba Tanimu Yaganar dani ba. Dan ALLAH Kaima Yaya Kayafemin Duk Na Cutar daku Akan Mahaukacin SO da Nabi Naɗorawa Kaina Na Manta da Irin Wanda Kuke Yimin Natuba! Natuba!! Nabi ALLAH Nabi ku Kuyafemin Aunty Shahuda Ku Yafemin Kuyi Ha....." Kuka Yasarƙeta Yayinda Ita ma Aunty Shahuda Tashiga Tayata Kukan Shima Ya Nuradeen Hawaye Kawai Ke Kwarara A Idanunsa Hakanan Duk Wanda Ke Falon. Saboda Dole Khaleesat Zata Baka Tausayi Kuma Kai da Ganinta Zaka Tabbatar da Lalle Har Ranta Tayi Dana Sani da NADAMA Akan Ina Hankalinta Yaje Ta'aikata Hakan ga Mutane Masu Darajar da Babu Mai Irinta. Ya Nuradeen Ne Yajata Jikinsa Yana ta Aikin Lallashinta Tayi Shiru Dan Shima dai Muyyudim Tuni Yaruɗe da Kuka Ganin Mamansa Khaleesat da Momyn sa Sunayi. Saida Su Baba Tanko Suka Sa Baki Taɗan Tsagaita da Kuka Tadawo Ajiyar Zuciya Itada Aunty Shahuda dakeTaya ta. Ganin Sunyi Shiru Sai Shima Muyiddim Yayi Shiru Sai Ajiyar Zuciya Yakeyi Dady Sai Aikin Shafa Kansa Yakeyi Yana Ƙara Lallashinsa Shima Kuma Dady Jifa-jifa Yakansa Hankicip Yagoge Nasa Hawayen Cikin dubara Batareda Kowa Ya Lura Ba. Sai A Yau Yaƙara Tabbatar wa Kansa da Cewa Rayuwar ta Wuce Yanda Yake da Zato Da Tsammanin ta. Babu Shakkah Acan Baya Yanda Baba Tanimu Yace Haka Yake Kallon Su Ashe Tunanin da Hangen Nesan su Yazarce Duk Yanda Yake Zato da Hasashe Kai Shi kam Yayi NADAMA Mai Suna NADAMA Ashe Shine Bai San Komai ba. Ashe Shine Baƙauyen Ba Su Ba. "Shin Tunda Lamarinan Yataso Kataɓa Irin Wannan Zama da Khaleesat Ka Nusar da Ita Da Irin Wannan Nusurwar Da Nayi Mata?" Baba Tanimu Yakatse Wa Dady Tunanin da Yakeyi. Dady Yagirgiza Kai "Ban Taɓa yi Ba Yaya." Baba Tanimu Yace, "Tau Kagani Shiyyasa Nace Sai kun Zama Masu Kula da Lamurran da Kuma Zamanin da Muke Ciki Da Irin Yanda Abubuwan Suke Kai Komo Kenan dan Haka Yanzun Ni Bana Son Ka'amince da Auren Wannan Yaran dan Kanajin Saboda Mu Ka Yarda A'a Ni Nafison Ka'amince da Zuciyar ka ɗaya Inma Bai Maka Kana da Damar Hanawa Kuma Ko Kaɗan Baka Ɓata Rammu Ba Wallahi." Khaleesat Tayi Karab Cikin Maganar Tareda Cewa, "Ni Wallahi A Yanzun Nadaina Sonsa Nafasa Su Dady Su Bani Wanda Suke SO Ko Meye Shi Zan Zau......" Tau fa Me Khaleesat ke Shirin Aikatawa Kuma? 🤔 Muje Tareda Alkalamin FA'IK. ✍🏼 [9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....38 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem!!! Duk Wannan Abun da ke Faruwa Dr Jabir Yana Sane Yana da Labari, Saboda Kullum Muna Waya Dashi, Daganan Nagaya Masa Cewa, Ga Khaleesat Nakawo Asibiti Harsun Gana da Su Abdul-wahab Meye Plan Nagaba? Yacemin Yanzu In Zauna da Khaleesat Ita ce Zatamin Bayani Sun Riga da Sun Tsara Komai. Daganan dai Na Keɓe da Khaleesat ɗin Nake Gayama ta Yanda Mukayi Da Dr. Jabir Tace, "Tabbas Hakane, Plan Na Gaba Yanzun Shine Kamar Yadda Suka Tsara Zata Koma Gida Ta Gayamasu Gaskiya Tasan Izuwa Yanzun Iyayen ta Sunyi NADAMA Kuma Tabbas Zasu Bata da Ga Wanda Takeso. Najima Cikin Nazari Kafin Nace Mata "Ba Haka Za'ayi ba." A Wannan Lokacin Taɗago Kanta Take Kallona da Alamar Buƙatar Ƙarin Bayani daga Gareni Nikuma na Musƙuta Cikin Murmushi Kafin Nace, "Yanda Za'ayi Shine Nasan Kuna da Family Kuma Baza'a Rasa Wanda Iyayen ki Suke Ganin Girma da Mutumci su ba Dan Haka Su Zamu Sama Sai Muje Tare Dasu dan Ƙara Wayar wa Da Su Iyayen Naki Kai Harma da Na Abdul-wahab ɗin." Cikin Murmushi Tacemin, "Tabbas Hakane, Tau Amma Tayaya? Haɗasu Ba Abune Mai Sauki Ba, Bayaga Haka Nida Zan Bayyana A Matsayin FATALWA Garesu Tayaya Kake Ganin Aikin Zaiyu Gareni?" Nima dai Murmushin Nayi Nace, "Kibar Komai A Hannuna Abunda Nake Buƙata Kawai A Gurinki Yanzun Zaki Sanar dani Inda Dangin Naku Suke Sai Inje In Samu Su." Tazaro Ido "Wallahi duk Suna da Nisa Familyn Dady Suna Adamawa Momy kuwa Kogi." "Badamuwa Zanje, Amma Tunda Suna da Nisa Zanje ga Na Dadynki." Khaleesat Ta Kalleni Cikin Mamakin Irin Wannan Sadaukar wa Da Mukeyi Akan ta Nida ABOKINA Nace, "Karki Damu YIWA KAINE Hakanan Dr Jabir Yana da Wata Irin Daraja Gareni Ina Iyayin Komai domin Farincikinsa Kamar Yadda Nake da Yaƙinin Shima Zai Iya." Khaleesat tasauke Ajiyar Zuciya Tareda Cewa, "Hakane, ALLAH Yabar So da Yarda. Nima kuma Ina Godiya gareku ALLAH yabiya ku da gidan Aljannah bisaga Wannan Taimakon Naku Gareni." Naɗan Kurɓa Lemun dake Gabana Kafin Nace, "Allahumma ameen Khaleesat Kema Kuma ALLAH Yanuna Burin Nan Naki Yacika." Cikin ɗan Murmushi da Kuma Kinya Tace, "Ameen." Nace, "Yanzun Saiki Bani Cikakken Adereshi Inda Familyn Dady Yake Hakanan Ki Bani Number Wani Wanda Zan Dinga Waya Dashi Har In Isa Wurin Nasu." Tabani Number Baba Tanimu Tareda Gayamin Shine Babban Wa a Familyn Nasu Dady. Daganan Nikuma Nasa Rana Naje Har Adamawa Bayan Na Kimtsa A hotel ɗinda Nasauka. Bayan An Sauko daga Masallacin Jumu'a. Na Nufi Family House ɗin Nasu Dady da Taimakon Wayar da Mukeyi da Baba Tanimu. Nasamu Tarba Mai Kyau Agurin Sa Daganan Kuma Nakoro Masa Bayanin Abinda Ke Tafe Dani Yayi Mamaki Sosai Yayinda Nikuma Naduƙufa Fahimtar dashi Cikin Taimakon ALLAH Yafahimci ni daganan Kuma Yasa dani da Sauran Dattijan Gidan Suma Nayi Masu Bagani Kamar Yadda Nayi Masa daganan Muka Aje Ranar da Zasu Zo Bayan Sun Kira Dady Sun Samu Tabbacin Ranar da Yake Gida Batareda Sun Nuna Masa Cewar Zasu zo Ba. Bayan Nadawo Nakira Khaleesat Nasanar Mata da Yanda Akayi Kasancewar Dama Nagayama Su Innarmu Suje da Ita Can Gida Har'izuwa Sanda Abubuwan da Nake Tsarawa su Dai-dai ta In Zaku Tuna Innarmu Munyi daku Haka Ranar da Aka Sallame ku Ko?" Yaƙare Maganar da Kallon Sashen Da Innarmu Take. Cikin Sanyin Jiki Innarmu Tagirgiza Kai Tareda Cewa, "Hakane." Shikuwa Dr. Faisal Yaɗora, "Bayan Su Baba Tanimu Sun IsoYake Sanar dani Gasu Sun Sauka Tasha dama Kuma Tun Suna Kan Hanya Muke Waya Dasu. Dan Haka Naɗauki Motata Naje Naɗauko Su Bayan Mun'ajiye Su Baba Bukar Nan Sai Muka Wuce da Baba Tanimu Kan Cewar Zamuje ne Muzo da Khaleesat da Kuma Iyayen Abdul-wahab Harma dashi Kanshi Abdul-wahab ɗin." Yaɗan Numfasa Yana Mai Nazarta Foskokin Mazauna Falon Kafin Yaɗora Da Cewa, "Kunji duk Yanda Abubuwa Suka Kasance Idan Har Munyi Maku Ba dai-dai ba Dan Girman ALLAH Amadadin Abokina Ina Mai Baku Haƙuri, Mudai Munyi Abunda Muke Ganin Da Khaleesat Taje Yawon Duniya Tau Gara Mu Ɓullo ta Wannan Hanyar tunda Wancan Ta zama dan Yiwa Su Dady Bayani Bai zama Dole Su Fahimta ba. Bugu da Ƙari dai MUTUWAR Khaleesat ɗin dai Yanuna Maku Abinda Zai Faru dan Gashi Shi Abdul-wahab Yasamu taɓin Hankali Sannan Ku Kanku Kunshiga Tashin Hankalin da Ba Sai An Tsaya Yin Bayani Ba. Dan Haka kuyi Tunani Idan Wannan Mutuwar ta Kasance Ta Ƙarya Tasa Irin Haka Yafaru Tau Sanda Kuka Dage Kan Aura Mata Wanda Ku kuke Muradi Koda Bata Gudu Ba Tau Intaje da Baƙinciki Zata Zauna Gidansa In Kuma Hakan Baiyuba Wataƙil Suci Gaba da Mu'amala da Junan Su Ita da Abdul-wahab Tunda Suna Son Juna, da Dai Sauran Wasu Dalilai Daban-daban da Ban Lissafo ba Wayanda Wasun Tunanina da Naku Yasani Wasun Kuwa Sai Sun Faru Sannan Zamu Sani Adawo Ana Tunanin da Ba'ayi Ba da Hakan Bazata Faruba. Dan Haka A Shawarce Ina......" Baba Tanimu Yaɗaga wa Dr. Faisal Hannu Kafin Yasoma Cewa, "Yi Shirunka Ko A Iya Haka Kuma Ai Kariga da Kabada Bayanin da duk Mai Hankali Zai Iya Ganewa. Kai Kuma Mustapha." Yajuyo Gurin Dady Da Yaketa Sharɓa Zufa Kamar Ba Lokacin Sanyi ba. Baba Tanimu Yacigaba da Cewa, "Yanzun Hukunci Yarage Gareka Duk-da Nayi Mamaki da Samun Ka da Wannan Ra'ayi Batareda Mun Sani Ba Wai dan Mutum Baya da KUƊI Bai Isa Ya'auri ɗiyarka ba Dan Bayada Kuɗin da Zai Jiyarda ita daɗi. Shin Ko Kasan Da Auren Wasu Masu Kuɗin gara Auren Talaka Wanda Yake da Kyakykyawar Zuciya. Nawa ne Suka Aurin Mai Kuɗin Amma Sai ka ga Matar Wani Talakan Tafi ta Mai Kuɗin Wadata Saboda Hali Ba ɗaya ba. Yakamata Kagane Bawai Kuɗin Bane A'a daga HALINE Koda Yana da Kuɗɗin indai Baida Hali Mai Kyau tau Bazai Wadatar da Ita Ba Hakanan koda Talaka Ne Indai Yana da Hali Mai Kyau Sai Kaga Yarka Ta Samu Kula Mai Kyau Hakanan Tana Yuwa Kuma Asamu Mai Kuɗin Kuma A Sameshi da Hali Mai Kyau Na Kula da Iyali dan Haka Ba Yanda Bata Iya Kasancewa. Amma dai Abinda yafi Kamata Muyi La'akari dashi Shine Shin Wanda Zan Ba Yata Yana da Sana'ar yi? Yana da Hali Mai Kyau? Yana da Addini? Idan Kasamu Wayyanan Sun Wadatar Sai Ka Haƙura da Sauran dan Ba Wanda Zaka Sama Ɗari Bisa Ɗari. Bayaga haka Jikina Yana Bani Wannan Ba Tunanin NAMIJI Bane. kawai Kabi Shawarar Matarka ne Kurum. Gashi Mu ko ɗai Rana Baka Taɓa Sanar da Mu Wannan Lamarin ba Ko dan Baka ɗauke Mu Yanda Muka ɗauke bane Saboda Kana ganin Kaine Kayi Boko Ka Goge Ka Waye, Muko Bamu San Komai ba Inba Noma da Kiwo ba Sai Kuma Zama Massalaci Ko?" Dady Yayi Maza Yagirgiza Kansa, "Wallahi Bahaka Bane Yaya Ku Gafarceni Dan ALLAH Kawai dai Ni Banyi Tunanin Wannan Matsalar Girman ta Yakai Haka Bane Shiyyasa Ban Faɗa Maku Ba." "Tau Ai Gashi Takaika ga Zubda Hawaye Ko?" Baba Tanko Yafada Yana Mai Kallon Dady. Muje Zuwa Readers Man Kaina Na Hayaƙi Wallahi 😫 Tareda Alkalamin FA'IK. ✍🏼 [9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....40 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem!!! Khaleesat Tayi Karab Cikin Maganar Tareda Cewa, "Ni Wallahi A Yanzun Nadaina Sonsa Nafasa Su Dady Su Bani Wanda Suke SO Ko Meye Shi Zan Zau......" Baba Bukar Ya Watsa Mata Yatsun Sa Biyar Yana Cewa, "Ungo Nan, Wayasa Bakin Ki Manya Na Magana Ko Kinfi duk Wayanda Ke Nanne." Hakan Yasa Khaleesat Tayi Mui! Da Bakin ta Tunda Dama Can Ita Mai LAIFI ce Karta Ƙara Yin Wani. Yayinda Shikuwa Dady Ya Musƙuta Sa'annan Yace, "Wallahi da Zuciya ɗaya Nake Sanar da Kai Nabaku Yuƙa Da Nama Duk Abinda Kuka Zartar Shikenan Ina So Ingyara Kuskuren da Nayi A Baya Ina Kuma Neman Gafarar Ku Akan Wancan Ma Da Nayin. Dan Haka Ga ku Ga Ikram Duk Abinda Kuka Zartar Akanta Dai-dai ne In Kuma Kumma badata Ga Wannan Yaron (Abdul-wahab) Zanji daɗi Sosai In Ma Kun Hana Bazance Komai Ba." Baba Tanimu Yace, "Tau Maddallah! Yanzun dai Babu Buƙatar Tone-tone Ina Son Amanta Komai Abarshi Yawuce Baiwar ALLAH Mun ba Abdul-wahab Khaleesat Kuma Yanzunan Ba Anjima ko Gobe ba Za'a ɗaura Auren Su Meye Ra'ayin ki?" Yaƙare Maganar Yana Mai Kallon Innarmu. Yayin da Innarmu Kuwa Ta Musƙuta Cikin daɗi da Farinciki Kafin Tace, "Wallahi Nayi Farinciki Sosai Nima Kuma da Ƙudurin Da Nazo Dashi Kenan Sai dai Wani Hanzari Ba Gudu ba Muna Neman Alfarmar Aɗaga Mana Ƙafa Mu Sanar Da Iyayen Yaron Na Wajen Ubansa Dan Karsu Zarge mu da Yin Abu Gaban Kammu, Sa'annan Kuma Bamu Riƙe da Sadaki Yanzun Bugu da Ƙari Dole Sai Munje Munɗan Tanadi Muhallin da Zai Zauna da Matarsa." Baba Bukar Yayi Karaf Yace,"Batun Sadaki Naɗauki Nauyi Zanbiya Masa Batun dangin Mahaifinsa Kuwa ɗauki Waya Ki Sanar dasu Halinda Ake Ciki Yanzun." "In Ma Katyne Babu Ga Tawa Wayar Ki Kira Ko ga Kuɗi Asa Maki A taki Wayar." Baba Tanko Ne Me Wannan Maganar Shima. Dr. Faisal Yace, "Batun Gida Kuwa Kubar Komai A Hannuna Insha'allah Ba'abinda Zai Gagara." "Ballatana Ma Ko Babu A ɗaura In Sun Kimtsa daga Baya Ai Ta Tare Ko?" Abinda Shima Baba Tanimu Yace Kenan. Dr Faisal Yace, "Insha'allah Ma Ba Abunda Zai Gagara." Nandai Innarmu Takarɓi Waya Takira Baba Lado Kasancewar sa Babban Wa Ga Dangin Baban Su Abdul-wahab Wanda Tayi Musu Bayani Dalla-dallah Kafin Kuma Ta Haɗasu da Baba Tanimu Ya Ƙara Kora Masu Bayani. Basuyi Wani Ja'Inja ba, Suka Amince Tareda Fatar A Hari Na Gaba Watau Na Abubakar. Dan Haka Nan Take Dady Yatashi Ya Nuradeen Akaje Aka Siyo Dabino da Alewowi Goro ɗaine Ba'a Samo ba Wai Suntashi. Bayan Gama Sallar Magarib A Massallacin Unguwar Su Khaleesat ɗin Liman Yayi Sanarwar Kowa Ya tsaya Akwai Ɗaurin Auren da Za'ayi Na Khaleesat. Take Kan Mutane ya Ƙulle Wace Khaleesat kuma Bayan Wacce Ta MUTU? Liman Yace, "A saurara Khaleesat Ashe Bata Mutu ba duguwar Suma ne Tayi Ga Kuma Bayin ALLAH da Suka Ci Karo da Ƙabarinta Nan Bayan Sun Kai Nasu Mamacin Sukaji Numfashin ta Shine Fa Sukayi Jarumtar Cirota Da Harzasu Gudu Tau Amma Jajircewa da Kuma Shawarwarin Wasu Yasa Suka Tsaya tau tadai Jima Hannun su Tana Jinya Kafin Suka Samu Bakinta Tayi Musu Kwatancen Gida Shine fa Suka Maidota Gida tau Bayan Maidota Aka Buƙaci Kawai Aɗaura Auren Nata da Ake da Niyyar Kafin Ta Rasu." tau da Haka dai Aka Rufe Bakin Jama'a Aka Barsu Cikin Tarin Al'ajabi. Nan dai Kuma Aka Ɗaura Auren Khaleesat da Abdul-wahab. Auren da Akasha Gwagwarmaya Kafin Tabbatuwarsa Auren da Aka Sha Artabu Kafin Tabbatuwarsa Auren da Aka Kai Ruwa Rana Kafin Ganin Yauɗin. Bayan Ɗaura Auren Kuma Aka Shiga Rabon Dabino da Alewowi Harma da Cimgam Ga Masu Ci Kenan. Kunun Ayan da Momy Tayi Na Saisuwa Shi Tafitar Aka Shiga Rabawa Jama'a Harma da Almajirai. Inda Nantake Momy Tahura Wuta Taɗora Tunkuyar Tuwo da Miyan Kuɓewa Kafin Ƙarfe 9 Harsun Gama Cikin Taimakawar Su Aunty Shahuda da Kuma Mmn Walida da Tazama Ƴargida Sunƙulle da Aunty Shahuda Dama Gasu Kai ɗaya. Sai Aikin ƙuƙƙula Tuwon Akeyi Cikin Leda. Ya Nuradeen Kuwa Suka Haɗa Kuɗi Shida Dady Nan Take Kuma Ya Nuradeen ɗin Yaɗauki Sani Cikin Motar sa Suka Kwaso Kayan Drinks Su Pop Cola ne Wow! Ce dakuma Cok Kai Harma da Lemun kwalbar Da Baka Taɓa Gani ba. Aka Shiga Kwasa Ana Kaiwa Cikin Gida. Makwabta Kuwa Tuni Suka Shiga Ɓarkowa Cikin Gidan Saboda Samun Labarin Yanda Al'amari Yakasance Watau Kan Yanda Liman Yasanar da Mutane Unguwa. Sai Jaje da Barka Sukeyiwa Su Dady da Momy. Kowa Kuma Yashigo Zaici Yaƙoshi Yakuma Yi Guzuri dashi. Habawa Tuni Gida Yacika Maƙil da Jama'a. Dama Kuma Irin Wannan Yanayin da Ake Ciki Na Halin Rayuwa Wani Rabon Sa da Abincin Tun Safe Wani Ko Na Safen Ma Bai Samu ba. Saboda Halin Matsin Tattalin Arziki da Ake Fuskanta ga Babu Tsaro Ga Yunwa Ga Fatara da Tayiwa Al'umma Ƙatutu😥 (Kai ALLAH Yataro Mana Ƙasarmu Ka Kawo Mana Mafita Harma da Sauran Ƙasashen dake Cikin Irin Wannan Yanayin Musamman Na Musulmamu.) kai Ranar Fa Anga Dandazon Jama'a Cikin ɗan Ƙanƙanin Lokaci. Kai Hatta Almajirai Saida Suka San Ana Sha'ani. Momy da Dady Kuwa Cewa suke, "Buƙin Karshe ne Sukeyi daga Khaleesat ɗin kuma Saidai Suyi Sha'anin Jika. Ai Kuwa Gara Su Zage Damtse. Gara Ma Shi Dady Akwai Wasu Gurin Matarsa Ta Gida Tau Kuma Suma duk Ya Aurar Sai Tsirarun Ƴaƴan da Take Riƙo ne. Haka Fa Buki Yatashi Haiƙan Gida Yayi Albarkar Jama'a. Nikuwa Sai Nan nan Su Momy Keyi Dani Mezakaci Mekike So Ina Zaki? Wani Abu? Haka dai Suke Cemin Akan Duk Wani Motsi da Nayi Inda Nikuwa Naƙara Shiga NADAMA da Ganin Wautar da Natafka A Rayuwata Na Mance Irin Wannan Tsafatattaciyar Ƙauna da Iyayena Kimin. Wannan Tunanin Kan Ƙara Jefani Cikin Raunin Zuciya da Har Hakan Kan Haddasa min Sake Ɓarkewa da Kuka. Sai Su Momy Sun Tsawatarmin Kan Indaina Ai Komai Yawuce. Kai Ku Tambaya Ni Labarin Abdul-wahab (Angon Ƙamshi😅) Wohoho Faɗar Farincikin da Ke Cikin Zuciyar Abdul-wahab ma Ɓata Lokaci ne. Tun A Massallaci Yana Jin Anshafa Fatiha Yakamo Abubakar Yarumgume Cikin Wani Irin Maɗaukakin Farinciki. Abubakar Yalafe Ajikinsa Yanajin Yanda Zuciyar Yayan Nasa Keta Bugawa Kafin Yaji Saukar Hawaye Akan Kansa. Yayi Hanzarin ɗago Kansa Yana Kallon Abdul-wahab Yace, "Ya Abdull Ai Kuka Kuma Yaƙare." Murmushi Abdul-wahab Yayi Yace, "Ai Wannan Na Farin Cikine." Shima Kuma Yusuf Ya Matso Suka Rumgume Juna. Daganan Fa Su Baba Tanimu Ke Gabatar Dashi Wurin Jama'a Cewa Shine Angon Nanfa Aka Shiga Musbaha dashi Ana 'ALLAH Sanya Alkairi' Kamar Za'a Tsinke Masa Hannu. Bayan Anɗan Sarara Kuwa. Can Bakin Titi Gurin Mai POS Suka Nufa Yabawa mai Pos ɗin Atm ɗinshi da Cewar Afitar Masa da Duk Wasu Kuɗinsa Dake Ciki Inda Hali Kuma Abashi Sabbi Fil. Yusuf Yazaburo Yana Faɗin, "Kai Kana Hauka ne, Mezaka yi Dasu?" In kun tanka Shi Tau Abdul-wahab ma Yantanka. Daga Sanda Mai Pos Yabashi Sabbin Ɗari-ɗari Kuwa Nan Yashiga Fallo Su Cikin Aljihu Yana Rabawa Sadaka Ga Almajirai Kai Harda Wayyanda ba Almajiran ba, Sai Karɓa Sukeyi Suna Sokewa (Haba Yanda Garin Nan Yayi Zafi😅) Nan fa Yusuf Yashiga Tareshi Yana Ƙokarin Hanawa. Abubakar Yariƙe Yusuf Gamida Cewa, "Ƙyaleshi Yayi, Irin Wannan Ranar Ko Ba'a Sha Gwagwarmaya ba daɗi ne Da Ita Balle tasu da Ka Sani Ba Sai Angayama ba Saidai Kaba Wani Labarin ta, Kumama Wlh Ga Wayanda Yake Ba Nan Suna Ma Kallon Ɗan Baƙinciki Zaka Hana Musu Samu." Abubakar Yaƙarasa Maganar Cikin Raha. Yusuf Yayi Dariya Yace, "Tau Kuma Fa Hakane, Tau Ai Bari Kagani." Nan Yazaro Ƙatuwar Wayar sa Yarumgomo Abubakar Sukayi Salfe Kafin Kuma Yaruga izuwa Ga Angon. Yashiga Ɗaukar Hotuna da Vedio Me Abubakar Zaiyi Inba Dariya Ba? Yayinda Wasu Hawayen Farinciki da Tausayin Ɗan Uwan Nasa Ke Zobo Masa. Dr Faisal Ma Na Gefe Sai Vedio Call Yakeyi da Dr Jabir Yana Nuna Masa Yanda Sha'anin Ke Guduna. Suna Dariyar Farinciki. Kai Abun Fa Sai Wanda Yagani. Buki dai Ya ƙayatar Gaskiya, Sai Fatar ALLAH Yaba Ango da Amarya Zaman Lafiya. Buki dai Bai Tashi Ba Sai Karfe Goma Shaɗaya Inda Nan Innarmu Suka Haɗu da Faisal Sukayi Godiya Iya Godiya daganan Baba Tanimu Yahaɗa su Yayi Jan Hankali da Kuma Nasiha Mai Tsawo Kafin Kuma Aka Aje Ranar Tariyar Khaleesat Nan da Sati Biyu Shima Da ƙyar Baba Tanimu Ya Yarda Dan Shi Cewa Yayi Kawai Abdul-wahab Yaɗauki Matarsa Suje. Alabashi Tazauna Can Inda Suke Harzuwa Sanda Zasu Kimtsa. Sukuwa Momy duk Abinda Suke da Niyyar Yimata Sa Aika daga Baya. Tau Amma Sai Mutane duk Suka Taru Akan dai Abarshi Kan Wata Ɗaya Baba Tanimu Yace Ko Alama Ahakan dai Aka Samu Aka Kai Matsaya Kan Sati Biyun. Dr Faisal Shine Yakwashi Su Innarmu da A Motar Sa Zuwa Gida Bayan Yayi Sallama da Su Baba Tanimu Kan Cewar Goben Kafin Su Tafi Zai zo Suyi Sallama. Washe Gari Kafin Yatafi Gurin Su Baba Tanimu Nan Yafara Sauka Gurin Su Innarmu Bayan Tarba Mai Kyau da Yasamu Daga Garesu dagana Ya Buƙaci daga Abdul-wahab Me'ake Ciki Dangane da Inda Zasu Tare. Innarmu Ta Musƙuta Ta Soma Rattabo Masa Bayanin Kan Matsayar da Suka Kai Kan Cewa, 'Tunda Yanda Abubuwan Suka zo Gidan Na Innarmu Akwai Fili Gwargwado Ga Wani ɗaki Can Spare Nan Zai Ja Gina Yayi Masa Falo Gefe Kuma Afitar Masa Toilet Store da Kuma Kitchin Misalin dai Gini Irin Na Talaka. Dr Faisal Ya Girgiza Kai Cikin Yabawa da Hazaƙarsu Kafin Yakarkace Yazaro Farar Ambulance Ɗin Takarda Yace, 'Tau Ga Tasu Guddumowa Shida Dr Jabir. Shi Dubu ɗari 5 Dr Jabir Ma Dubu ɗari 5 Kuɗɗi Sun Tashi Miliyan ɗaya Kenan. yakara da Cewar Suyi Haƙuri Ana Cikin Yanayi ne Na Ba Kuɗi Ga Abubuwa ne dai Barka tai. Su Innarmu Ma Sai Suka Rasa Bakin Magana Saboda Tsananin Mamaki. Abubakar Ne Ma Yayita Jarumtar Bufe Baki Yashiga Kwarara Masu Godiya Shi da Dr Jabir. Nanne Suma Su Innan Suka Samu Bakin Magana Harma da Uban Gayyar Watau Ango Abdul-wahab Sukayi Cikin Mutumci da Girmamawa Bayan Sun Karɓi Number Dr Jabir Kan Cewa Zasu Kirashi Shima Sumai Godiya. Bayan Sun Dawo daga Rakiyarsa Abdul-wahab Yatafi Raka Maman Walida Zuwa Tasha Ta Koma Gida Dan Yin Shirin Buki ta Dawo, dan Har tace Bama Zata Koman ba Sai Buki Innarmu Tace Lalle Tafiya Ba Fashi Saidai Taje Ana Gobe Buki Tadawo. Daganan Fa Suka Tasarma Aikin Gyara Muhallin da Abdul-wahab ɗin Zai Zauna Cikin Rufin Asirin ALLAH. Hakanan Sai Guddoma wa Suketa Samun Daga Gurin Jama'a Daban-daban Ko Ƴan Garejin su Kuɗin da Suka Haɗa Masa Yakai Dubu ɗari Maigidan sa Kyauta Sosai Yayi Masa. Innarmu Tayi Godiya ALLAH Har sai da Ta Zubar da Hawaye Ta Kuma Ƙara Tabbatar wa duk Wanda Yariƙe ALLAH Dagaske Tau Lamarin sa Bai Ɓaci Takuma Ga Ranar Tashin Dare Datake Tayi Tun Suna A Kauyen Su Na Sanyyinah Kan ALLAH Yashiga Lamarin ta Yataimaka Mata Wajen Kula da Marayun Ƴaƴanta Kar Yabarta da Wayon ta Ko dubarar ta Gashi Kuma Ubangiji Mai Tausayi Yakarɓa Dan Rasuwar Mal Rabi'u Uban ƴaƴanta Bata Taɓa Cewa Yau ya Zasuyi? Kullum Suna Cikin Rufin Asirin ALLAH. Yauda Mal Zai Dawo ta Tabbata Zaiyi Farinciki da Ita. Wannan Kenan!!! Akwai Wata Magana Fah Masu Karatu Akwai Wani Sirrin da bukinnan Zai Ɓangaɗo Ku muje Zuwa Tareda Alkalamin FA'IK ✍🏼 [9/5, 9:16 PM] FA'IK: Typing....... 💻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....41 Mallakar 👇 Fa'IK ✍ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 GARGADI. Duk Wata Dama A Littafin Nan A Kare take, komai Za'a Aiwatar Sai da Izinin Mai Littafin Dan Haka Akiyaye. FADAKARWA. Yima Rubutuna Kyakyawar Fahimta Banyishi Dan Kowa ba. Nayi Dan Ilmantarwa Da Nishadantar wa. A Kuma Shirye Nake Wajen Karbar Kowane Irin Gyara Cikin Fahimta bada Cin Zarafi Ba🙏. Bissmillahi Rahmanin Raheem!!! Wannan Kenan!!! *********** Tau Ɓangaren Na Nima Sai Hamdalah Domin Iyayena Jarumai Ne Masu Zafin Nema Dama Kuma Komai Akwai, Wasun Kawai Aka Sabunta Lefe Kuwa Tuni Abubakar Yazo Yaƙarbe su Kan Zaiyomin ɗinkuna Kala-kala Dan Dr Jabir Yace Komai Da Yayi Ba Kansa Yayiwa ba Dama Can Abdul-wahab ɗin Yayiwa. Walwalar Gidanmu Tadawo ALAƘATA Tagyaru da Iyayena Muna Cikin Zammamu Mai Daɗi Bugu da Ƙari Yanzun Shima Dady Sanadin Wannan Abun da Yafaru Alaƙarsa ta gyru da Yan Uwansa Zumunchi Suke Yanzun Sosai Komai kuma Kowanen su Zaiyi Sai da Shawarar Yan Uwansa Hakanan Dady Yakwashe Mu Zuwa Adamawa Kwana Biyu Asabar da Lahdi Mukayi Muka Dawo Daganan Ya Nuradeen Yadamƙi Hanyar Legos Da Burin In Yaje Zaiyi Ciku-Cikun Adawo Dashi AREWA Saboda Yagaji da Zirga-Zirga. Yanzun Haka Momy Suna Zumunchi da Matar Dady Ta Adamawa Saɓanin da Da Basa Wani Yi Harma Tayi Alkawalin Zuwa Buki Inya Tashi. Ana Gobe Buki Yan Uwa da Abokan Arziki Aka Shiga Ɓarkowa Gida Yaɗauki Harami Komai Yakacame Sai Shagali Akeyi Tunkuya Aɗora Wannan A Sauke Wancan Saboda Buhu guda Dady Yagir Mana Agida Da Kayan Miya Birjik. Yayinda Mami Iyabo Tazo da Fulawarta Domin Yimin Kayan Gara dasuka Danganci Dibilah Cin-cin Alkaki da Donoth da Dai Sauran Su. Dataji Abunda Nayin Kuwa (dan Ita Momy Ta Faɗa Mata Kasancewar ta Ƙanwarta Da Suke Rabon Fhara Guda) Nasha TiƘa Gurinta Akan Wahalar Da Na Basu Shine Tace Sai Rama Kukan da Nasa ta Mukayi ta Dariya. Yanzun Ma Zaune Take Kan Ƴar Tsuggonunta Tana Suya Cin-cin Yayinda Sauran Sukenan Ana Gwarzar Fulawa Tacemin, "Miƙomin Wani Mazubin Wannan Yacika In tsame Kar Cin-cin Yaƙone." Namiƙo Mata Ina Cewa, "Mami In ɗanyi Maki Tastin Inji Yayi daɗi?" Taharareni, "Shiɗai Kika Iya Gawa Taƙi Rame Kawai(Sabon Sunan da Take Kirana dashi Kenan Tunda Kowa Ce Masa Akayi Dogowar Suma ce Nayi Kamar dai Yadda Liman Yasanar da Mutane.) Tana Faɗar Hakan Kowa Yakwashe da Dariya Nikuma Na Zumɓuri Baki, "Ni Wallahi Mami Bana Son Wannan Sunan Nafasa Maki Tastin ɗin." Tace, "Meye Ruwana Daga Kawai Ma ALLAH Yahutar dani?" Nayi Hanzarin Dawowa Tareda Tsumbula Hannun na Cikin Robar Cin-cin ɗin Ina Cewa, "Eh Lalle Nagano." Mutane dai Sai Dariya Suke Mana Saboda Mami Iyabo Akwai Barkwanci Shiyyasa Wani Lokacin Kamar Jika da Kaka Muke. ********** Ɓangaren gidan Ango Ma Haka Sha'ani Keta Gudana Su Mmn Walida Sai Kai Kawo Ake Kamar Yadda Su Yusuf da Abubakar Aka Kasa Zama Yaudai Gidan Angon Komai Yayi Fes ɗankaramin Gida Mai Kyau An Malale Ko Ina Na Gidan Da Tayels (Irin Haɗin Gambizar Nan) Ciki da Falo ne Sai Kuma Kitchin da Store dakuma Toilet da ke Jere daga Gefe Sai Ƙamshin Fenti Da Akeyi Yauɗin Ke Tashi. Saboda Zuwa Anjima Ƴan Jere Zasu Zo. Innarmu Kam Sai Kai Kawo Takeyi Cikin Yan Uwa da Abokan Arziki Ana Ƙokarin Ganin Komai Yatafi Dai-dai. KASHE GARI....... Data Kasance Ran Assabar Aka Tashi Da Buki Haiƙan Aduk Gidajen Biyu Kowa Sai Kai Kawo Yakeyi Cikin Matuƙar Farinciki da Nishaɗi. Gidan mu Yacika Tamƙam da Al'umma Sai Hidamar Buki Ake Tayi Nikuwa Sawa da Hissuwa Nakeyi Insaka Atamfa Insa Les Insa Shadda. Harzuwa Sanda Aka Zauna 'Walima' Malama Zuwairiyyah (dan Ita Momy Ta Gayato)Tayi Wa'azi Akan Haƙƙoƙin AURE A Musulunci Da Irin Yanda Mace Yakamata Ta Kasance A Gurin Mijinta Lakaca Guda Tasauke Akan "Wace Macce Mafi Soyuwa A gurin Mijinta?" Kai Mutane Sunƙaru Sosai Sai ALLAH Shiyi Mata Albarka Ake Harma da Momy da Tazama Sanadiyar Kawota. Yayinda Su Aunty Shahuda da Mmn Walida (da Yake da Lokacin Walima Yayi Yan Gidan Ango Sunzo.) Suka Shiga Rabon Kayan Buki Irin Su, Take Awaye da Ƴan Ƙananan Botikai Wasu Abin Kwasar Shara Suka Samu Kuma Kowane na Manne da Stikacs ɗin Sunayen mu. Aka Tashi Walima Cikin Farinciki da Annushuwa. Misalin Ƙarfe Takwas Motocin Ɗaukar A Marya Suka Hallara Gidamu. Ɓangaren Ango Kuwa Suna Can A Wani Masallacin Jumu'a Inda Malamai Kusan Biyar Sukeyin Lakca Akan Abinda Yadangaci AURE. (Kasancewar Abdul-wahab ɗalibi Mai Kuma Zama Majalisin Malaman Ahlis Sunnah. Shine Fa Aka Sa Wannan Walimar Wadda Tasoma Gudana Bayan Gama Sallar Magarib) Malamai Sunyi Lakcoci Masu Zafi Akan Aure daga Cikin Su Akwai Mai Taken, "Wanene MIJI Mafi Daraja Agurin Matarshi." Wani Malamin Kuwa Yayi Lakca Akan "Falalar Aure" Wane Kuwa Yayi Akan "AURE BAUTAR ALLAH." Taƙarshen Itace "Yanda Yakamata Ma'aurata Su Kasance A Rayuwarsu Ta Aure." Suma dai Anci Ansha Anyi Hani'an. Kuma Kowa Kagani Yaci Ado Sosai (Kunsan Maluman Ahlus Sunnah Akwai Gayu Dama😅) Tau Itama dai Haka Tashi Cikin Farinciki da Nishaɗi Ango Nacikin Abokai Baki Yaƙi Rufuwa Sai Ƙyalli Yakeyi Cikin Wata Tsaleliyar Shadda Fara Tas! Shi da Abubakar Baka Gane Waye Angon. Karfe Tara Dai-dai Aka Ɓanbaro ni Jikin Dady da Akai Kaini Gurinsa da Nufin Yayimin Nasiha Aka Shigar Dani Mota Sai Kuka Nakeyi. Ƙawayena Suna Tayani Musammama Na Unguwar mu Kasancewar Su Kullum AnaTare. Ina Zaune Tsakiyar Tattausan Gadona Nasha Lulluɓi Haryanzu Hawaye Nakeyi Yayinda Sukam Ƙawaye Na Suka Gyagije Suna ta Sha'anin su na Shaƙiyanci. Saiga Ango Da Tawagar Abokan Su Sunshigo Nanfa Guri Yaƙara Kacamewa Aka Shiga Siyen Baki Nidai Duk Abinda Suke Inaji Harsuka Gama Aka Kwashe Ƙawayena da Nufin Kaisu Gida Angon Yaɗaga da Nufin Musu Rakiya Suka Maidashi Suna Masa Shaƙiyancin Su da Akasan Kowayen Abokan Ango Nayi. Bayan Fitarsu Yakasance daga Ni Saishi, Sai ɗakin Namu Yaɗauki Shiru Inbanda Ƙarar Fanka dake Aikin Bada Iska Aɗakin Baka Jin Komai. Sannu A Hankali Abdul-wahab ɗin Yamiƙe Tareda Cire Hullarsa da Babba Rigar dake Jikinsa Ya'ajiye Gefen Gado Yafita Zuwa Falo. Sai Gashi Yadawo Da Ledoji Ya'ajiye Sa'annan Yahayo Gadon Tareda Yayi Mani Rufin Mayafin da Ke Kaina Nikuwa Nayi Saurin Runtse Idona Tareda Saukowar Wasu Hawaye Akan Fuskata Suka Wuce da Gudu. Murmushi Yayi Tareda sa Yatsansa Ya Lakuci Hawayen Yakai ga Fuskarsa Yana Duban Yatsansa Nasa Yace, "Ina Fatar dai Wayyanan Hawaye Na Farinciki ne Ko?" Nidai Ban Tanka Sa Ba. Yace, "Barka mu da Ganin Wannan Ranar da Kafin Risƙar ta Sai da Muka Tsallake Siraɗi daban-daban." Nanma dai Nayi Shiru. Yasake Cewa, "Ina Cewa Bakin Nan Tunɗazu Muka Sayeshi Ko Bai Sayu Bane Insake Saye?" dagama Faɗin Hakan Yakaimin Wata Sumba(Kiss) Wanda Bansan Sanda Na zabura Ba Nace, "Meye Haka dan ALLAH?" Mezai Inba Dariya ba "Ai Yanzun Kin Magantu." Yace, "Tashi Ki Nemo Mana Flet Mana." Miƙewa Nayi Muka Fito Tare Na Nufi Inda Nake Kyautata Zaton Nanne Kitchin ɗin Yayinda Shikuwa Yafice. Ina Tsakar Gida Flet da Cup Nake ɗaureyewa Axuciyata Ina Yaba Irin Ƙoƙarin da Su Momy Sukayi Min Acikin Kitchin ɗina. Babu Abunda Babu Kuloli Kala-kala Ga ɗan Ƙaramin Gas da Suka Siyamin Dasu Blanda, jug-jug Da Kuma ɗam Madaidaicin Oven. Maganar Gaskiya Sun Shaƙemin Kitchin ɗina Makil da Kayan Aiki Wanda A Wannan Zamanin da Muke Ciki Kitchin ne Abin Kallo ga Mutane. Ina Cikin Adu'ar ALLAH Yasaka Masu da Alkairi, Abdul-wahab Yashigo Gidan Ɗauke da Faranti da Wasu Sabbin Kuloli Jere A Sama. Ya Kalleni Yayi Murmushi Yace, "Afuwant Nasa Amarya Aiki." Ya'ajiye Farantin Gefe Yana Naɗe Hannun Rigarsa Kafin Yace, "Ɗauki Faranti Shiga dashi Ciki Bani Wannan Inƙarasa." Nace, "A'a Nikam Ibada Ce Kuma Nariga Nasoma ta Daga Yanzun Sai Sanda Kaɗaga Min Ƙafarka Na kuɗe Aljannah." Yakama Baki Kamar Wata Macce Gamida Faɗin, "Tau, Bakin Kuma Yabuɗu Yanzun Kenan?" Falo Muke Zaune Ina Aikin Zuba Masa Lallausan Tuwon Semo da ɗanyar miyan Kuɓewa da Ta Wadatu da Nama ga Kuma Ƙamshin Manshanu dake Ta Tashi Cikin ta. Natura Flet ɗin Gabansa, "Bismillah!" Nafaɗi Hakan Can Cikin Maƙoshi Dan Bana Tsammanin Yamaji. Yakalleni Ya Kalli Felt ɗin Abincin Kafin Yayi Murmushi Yace, "Amarya Kinsha Kamshi. tau Ai Matsowa Zakiyi Muci Ko?" Nace, "Ai Ni Naƙoshi." yayi Maza Yahaɗe Fuskarsa, "Amma ɗazun Kince Min 'Ibada Ce Kuma kin Riga Kin Soma daga Yanzun Sai Sanda Naɗaga Kafata Kika Kuɗe Aljannah'." Yayi Shiru Yana Mai Sauraro Daga Gareni Nace, "Lalle Haka Nace." Cikin Nutsuwa Yace, "Tau Kuma Yiwa Miji Musu Yana Cikin Ibadar ne?" Nayi Maza Na Girgiza Kaina Nufin dai A'A Yace, "Tau Matso Muci Abinci Innarmu ce Tagirkashi da Kanta, Kuma Tasan Wayeni Ƙwalama Bata Ƙosar dani Hakanan Bana Cin Wani Girki In Ba Nata Ba, Shiyyasa Duk Ruɗun Buki Bai Hana Ta Tashiga Kitchin Tayimana Wannan Girkin ba. A Sanda Tabanin Kuwa Cewa Take Intabbatar Kinci Kin Ƙoshi Saboda Tasan Irin Wannan Ranar Ba Komai Amarya Kanci Ba." Muna Cin Tuwon Mai Laushi da Matuƙar Daɗi Nace, "Hakane Kam." Yakai Loma Yana Faɗin, "Tau Wai Meyasa? " Nai Maza Nace, "Oho Karka Tambayeni Nikam." Ƴar Dariya Kawai Yayi. Saida Mukaci Muƙoshi Dan Abdul-wahab Bai Barni Nayiwa Cikina Ƙyata ba. Muje daku Muji Ya Amarci Zai Kaya? Tareda Alkalamin FA'IK ✍🏼 [9/7, 11:53 AM] FA'IK: Typing....... 💻 ❤❤SONEEE ....💕💕 (Silar Komai.) Chapter.....42 ➡➡➡ ENDING(ƘARSHE) Mallakar 👇 Fa'IK ✍ 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo 💪🏻J.A.W 💪🏻 GARGADI. Duk wata dama a littafin nan a kare ta ke,komai za'a aiwatar sai da izinin mai littafin dan Haka a kiyaye. FADAKARWA. Yi wa rubutu na kyakyawar fahimta B banyishi dan kowa ba. Na yi ne dan ilimantarwa da nishad'antar wa. A kuma shirye na ke wajen kar'bar kowanne irin gyara cikin fahimta ba da cin zarafi ba🙏. Godiya ta musamman ga ALLAH sarkin sarauta da ya bani aron rai da lafiya na kammala wannan litaffin. 🙏🙏🙏 BUGU DA ƘARI!!! Littafin nan nawa bazai kammala ba har sai na jadadda godiya ta ga 'yar uwa Hajaru M Bello Abubakar Ak Saraki, tare da Basira AB Musa UMMU SHUKURAH (shugaba) tare da dukkan wani member na k'ungiyar mu mai albarka kuma gagara gasar masu gasa end of discotions wato. JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION. Haka nan ina miƙa godiya ga mutanen arzik'i da suke taya ni yad'a wannan rubutun irin su, Haulat Abubakar, Nana (ƴar Saudiyah) da kuma Nafeesat (itama tana taya ni duk da kuwa babu sanayya a tsakanin mu) da sauran dukkan wad'anda ajizanci na d'an adam yasa ban samu na lissafo su ba ina godiya ALLAH ya yi muku sakayya da gidan ALJANNAH MAƊAUKAKIYA 🙏🙏🙏 Bismillahir rahamanin raheem!!! Domin dai tsakani da ALLAH yadnlda Innarmu ta ce haka ne zullumin bai bar ni na ci komai ba. Kazar ma abaki ya rik'a ba ni mukaci sosai muka kora da tsaftatacciyar madara mai sanyi sannan kuma ya shiga taya ni kwashe kayan zuwa kitchen. Bayan na ɗauraye kayan shi kuwa a lokacin ya fito daga shi sai Jallabiya ya cika ruwa a boket zaiyi wanka. Ni kuma na ɗauki brosh ina matsa maclean sannan na soma wanke baki na. "Karki taɓa bari mijinki ya shaƙi wani abu a gare ki wanda ba k'amshi ba." Huduɓar Momy ta faɗomin a rai kamar yanzu ta ke faɗamin ita. Na samu kaina da yin murmushi a fili na ce, ALLAH ya saka ku Aljannah Momy da ke da Dady da kuma Yaya Nuradeen har......" " Da Sauran Al'ummar musulmi." Abdul-wahab ya ƙarasa wannan maganar lokacin yana miƙo min kwandon da ke ɗauke da soso da sabulun wanƙa mai k'amshin strawbeery. Dariya Mukayi dukkan mu sannan ya ce, "Ga ruwan wanka can na kai miki Toilet jeki ki yi wanka amarya." 'Dariya na yi,amma ai ni nafi can_canta da inyi maka haka ko?".Ya yi murmushi shi ma yana matso maclean a brosh ɗinsa sannan ya ce, "Ita kyautatawa tana can_canta akan kowa Ma." "Abdul-wahab ya dafe kai na ya na karanto addu'o'i kala-kala bayan mun gama nafila kenan. Ya kuma yi min tambayoyi akan addini na inda na sani na bashi amsa inda ban sani ba kuma ya yimin k'arin bayani a nan ne wani daɗi ya ƙara lulluɓe ni jin cewa angon nawa Malami ne sosai. Kallo na ya yi ya ce min. "Kin iya wankan haila ko?". Na kaɗa kai na alamun eh." Ya ce, "To haka akeyin na janaba ma ban_bancin su kawai niyah ce." Daga nan muka canza kaya zuwa na bacci. Na ɗan tsaya gaban madubi ina shafe-shafen da suka zamo min al'ada ta shi kuwa ya na gefen gado zaune riƙe da wayar sa.Saƙon ban gajiya da kuma godiya ya ke turawa abokan sa, kafin kuma ya ajiye yayar ya laƙato wani lotion wai zai taya ni shafawa. Tun daga nan komai ya rikice mana saboda numfashin mu da ke dukan juna ga kuma k'amshin juna da muke shaƙa wanda yana kankaro duk wata k'auna da soyayya da muke yiwa juna tana saukar nana da kasala. Ban yi aune ba sai jin nakinsa na yi cikin nawa ya na min wani irin tsotsa kamar wanda ya samu alawar lolipop daga nan kuma abin da ya biyo baya bazan iya tan_tance sa ba saboda wani hali ne na shiga wanda na rasa gane Duniyar da na ke ciki. Tun ya na kiran suna na ina amsawa har amsawar ta gagare ni. Duk wata tsantsar k'auna da take maƙale a cikin zuciyar Abdul-wahab a ranar sai da ya fitar da ita a wannan daren ne kuma sukaji ashe can da ba son juna sukeyi ba, sai yau ne suke k'aunar juna domin dai kowanne daga cikin su ji yake kamar ya haɗiye d'an uwan sa aaboda k'auna. Kuka kam nasha shi y'an gidan mu kuwa ba wanda ban kira ba dan neman ceto. Idanun Abdul-wahab biyu lokacin da Ladanin Masallacin unguwar ya kwaɗa kiran sallar asuba na farko ya miƙe cikin wani irin karsashi ya ɗauro alwala bayan ya yi wanka ya fito da Gas ɗin su waje ya kunna sannan ya ɗora ruwan zafi Bayan sunyi zafi ne ya juye ruwan cikin boket ya ƙara ɗora wasu ya tafi ya sirka ruwan dai-dai yanda za'a iya amfani da su. Sannan kuma yaje ya tallafo ni ya shigar da ni bayin navsoma yin wankan na gasa jiki na. Sai da na fito sannan na kimtsa kai na,ina kan sallaya ne ya tabbatar da ya taimaka min sannan shi ma ya nufi Masallaci. ******* BAYAN WASU ƳAN SHEKARU............ Abubuwa da dama sun faru wasu sasu daɗi wasu kuma marasa daɗi haka kuma rayuwa tana shurawa sosai ta kuma sauya sosai an kuma samu cigaba akan rayuwar su Khaleesat. Abdul-wahab dai ya kammala karatun sa bayan k'alubale da gwagwarmayar da aka sha yanzu ya zama cikakken Lawyer mai zaman kansa. In da Shi ma dai Abubakar ya gama na sa karatun ya zama babban Enginier da ke zana manya-manyan gidaje har wajen Nigeria akan nemesa da aiki. Arzik'i dai ya ɓalle musu sosai yanzun. Tuni kuma Shi ma Abubakar d'in ya ke tare da amaryar sa Safiya 'yar gidan su Dr Jabir k'anwar Maman Asharaf da a yanzu Dr Jabir da Dr Faisal da kuma su Abdul-wahab tare da su Yaya Nuradeen da kuma abokin Abdul-wahab ɗin wato Yusuf suka k'ulle suka zama ZURI'A ƊAYA. Suke kuma fantamawa a Duniya ba inda sunan su bai kai ba baboda kujba_kujbar nema da sukeyi da kuma gidauniyoyi da suke dasu na taimakon al'umma. Hakanan yanzu sun gina wani katafaren gida a cikin unguwar Sama road wanda masana sukayi ittifaƙin cewa babu irin sa a faɗin jahar Sokoto a yanzu in dai gurin kyau da tsaruwa ne. To abu na ka..... Enginer sukutum ya yi wa wasu balle kansa Kuma? Yanzu haka Maman Walida sun dawo Sokoto da zama saboda mijinta da su Abdul-wahab suka bawa jagorancin Companyn su mai sarrafa shinkafa. Companyn da mutane da yawa ke ci k'arkashin sa ciki kuwa harda y'an uwansu na sanayyah. A cikin shekarun nan dai Abdul-wahab suna da y'a'ya biyar maza uku mata biyu yayin da Abubakar ke da ukku mata Biyu namiji ɗaya. Innarmu kuwa girma ya kamata ta koma KAKALLIYAH. Yanzu haka 'yan mata da mazan na su Abdul-wahab ɗin, suna shashenta suna ta tsula tsiya dai-dai lokacin na ke k'ok'arin shigowa sanye da wani tsadadden less sai k'yalli na keyi. Na zama babbar mace ina tare da mijina abin k'aunata Alhaji Abdul-wahab na rakoshi ne gurin Hajiya Innarmu da ke zaune a sashenta kan lallausan kujerun da suka yiwa falonta k'awanya. Shari'a ta keyi tsakanin yaran yayin da Asharaf ɗin Dr Jabir ke gefe sanye da Suit sai shan k'amshi ya ke yi. Yaron akwai misƙilanci ba inda ya baro Dadyn sa. Na durƙusa gefe ina faɗin Innarmu barka da hutawa. Ta ce, "Ina naga hutu yaran nan sun tasa ni a gaba da iya shege? Wai Afrah('yar wajen Abdul-wahab) ta ce zata min kitso shine fa Rumana(ƴar wajen Abubakar) ta hana ai aikin ta ne ita ta saba yimin shi ne na ce duka su bari bana so zan kira Malika ('yar wajen Abdul-wahab mai bin Afrah kenan) na ke so tayi min kinga ita kuwa sai wani shan k'amshi take yimin ala dole gata 'yar izzah ko ina ta gaji wannan shan k'amshin oho, dan dai Auta da Abdul-wahab basu da wannan miskilancin. Nuwaila 'yar gidan Yusuf ta yi maza ta ce,"Wallahi mijinta Yaya Asharaf ne ya koyamata." Gaba ɗaya yaran da ke parlon sukayi dariya da shewa. Shi kuwa Asharaf harara ya watsamata kamar zaiyi magana sai kuma kawai yavhaɗe abinsa ba tare da ya yi maganar ba ya cigaba da dannar wayarsa. Dai-dai lokacin kuma Malika ta shigo d'auke da faranti ta ajiye gaban Asharaf ɗin har ta miƙe ya ce, "Ina spoon?" Ta kama baki "Lahh!! Bara na ɗauko." Me yaran zasuyi idan ba ihu ba. Yayin da ni da Abbansu mukayi murmushi ita kuwa Innarmu ta toshe kunnenta ta na faɗin, "Ni dai na shiga uku yaran nan zasu toshe min kunne." Dai-dai lokacin Abubakar ya shigo parlorn ya na saɓe babbar rigarsa wai zashi ɗaurin auren 'yar wani abokin su. Safiyah ta na biye da shi ta na riƙe da hularsa dama k'a'ida ne duk zasu fita zasu biyo gurin Innarmu. Ya ce, "A'a me ye haka yara kuna neman maida mana gida kamar gidan kallon k'wallo?" Nan take kuma suka shiga taitayin su dan sun san Baba k'arami baya wasa. Daga can Asharaf na cin abincin sa ya ce, "Maganin ku kenan." In banda Malika da ke kusa da shi ba wanda ya iya jinsa. Nan fa duka samu parlorn ya ɗan natsa suka samu hankalin KAKALLIYAH(Innarmu) ya dawo kansu ta dube su cikin farinciki da har abada idan tana ganinsu a wannan matakin da bata taɓa tunanin ganinsu akai ba baya gushewa. Ta yi murmushi tare da cewa, "Sai ina sojojin Inna?" Suma dai murmushi sukayi Abdul-wahab ne ya fara magana ya ce, "Zan je Abuja ne Innarmu domin akwai wata shari'a da zanyi handling kuma ina ganin shari'ar zata ɗauke ni tsawon sati ɗaya." Abubakar kuwa ya ce, "Ni kam ba nisan kiwo zanyi ba,d'aurin auren 'yar abokin mu zamuje nan Tamaje." Innarmu ta sakeyin murmushi ta ɗan muskuta cikin jin daɗi da BURIN ina ma marigayi zai dawo yaga marayun da ya bari cikin kulawar Ubangiji da ta ke kai kukanta gurin sa ba dare B ba R rana matakin da yak aisu ta ce, "Masha Allah,amma kai mai zuwa Abuja jar sati ɗaya baka ganin yafi kamata ka tafi da iyalin ka?" Ya ɗan musƙuta ya ce, "Ni ma na so hakan amma sun ce suna da shirin fita siyo kayan d'akin auren y'ay'an su." "Ƴay'ansu kuma?" Innarmu Ta maimaita maganar cikin son tuno su waye. Abubakar ya yi murmushi ya ce, "Innarmu girma ya fara shiga ko? Batun Walida(Walidar Maman Walida) da Haroon (dan Dr Faisal) da za'ayi, to kuma jiya ma mun aama yanke hukuncin haɗa na Asharaf (d'an wajen Dr Jabir) da Malika (y'ar wajen Abdul-wahab) da kuma Rumana(y'ar wajen Abubakar) da Abdulrazak (d'an wajen Dr Jabir mai bin Asharaf kenan) sai kuma Afrah (ƴar wajen Abdul-wahab) da Musty (ɗan Wajen Yusuf) Nuwaila(y'ar wajen Yusuf)da Affan(d'an wajen Abubakar)." Innarmu ta yi murmushi a karo na barkatai ta ce, "Masha Allah abu ya yi kyau kuma ya yi sha'awa to amma kun binciki Yayan?" Abdul-wahab ya ce, "A'a bamu bincika ba sai dai muna kyautata zaton haɗin na mu mun yi sara kan gaɓa kuma dama mun ce ke zamu bari da wannan aikin ki bincike su kiji tun da ai k'awayen ki ne sai abokan ki ko?" Ya k'arasa maganar cikin raha. Duk sukayi murmushi kafin ta ce, "Ni ma ina kyautata zaton haɗin da ku kayi kunyi dai-dai sai dai zan ƙara bincikar su muji,amma duk da haka bazai yu ba,ita ce ta ce bazata bika ba kuma wannan ba hujja bace kuje kawai alabarshi idan sun tashi siyayyar ta su su biya ta can wurin ta(Abuja)sai su wuce. Dan haka tashi kije ki haɗo kayan ki kibi mijin ki." Innarmu ta k'arasa maganar tana kallo na yayin da ni kuma na shawagaɓe kamar ba ni ce mai surukai ba. ta ce, "Ƴar nan aure ibada ne Aljannah kuwa sai ka dage,maza tashi." "Miƙewa na yi zuwa part ɗin mu ina wani bana so. Shi kuwa Alhaji Abdul-wahab ya faki idanun mutanen ya yimin gwalo.Ni kuma nai masa kallon zaka santa ne. Nan kuwa cikin raina zallar farinciki ne dama ina son bin mijina kawai dai kar su Maman Walida suga a zarɓaɓi na ne. Shi ma kuma in ɗan ja aasa ajin nan namu na mata. Wannan kuma na ɗaya daga cikin dalilin da ke k'ara kimar Innarmu a cikin ran mu dan ta ɗauke mu duka kamar y'aƴanta. Duk yanda zata yi wa Maman Walida muma haka zata yi mana. Shiyasa ko da yaushe gidan mu muke zaune lafiya kuma cikin albarka. Minti biyar na haɗa kaya na na fito janye da troly na. Daga nan Innarmu ta ce kowa ya matso ayiwa su ABBA addu'ar sa'a zasu Fita. Nan kowa ya matso ta soma kwararo addu'a muna cewa ameen. Wanna jazamun ne dama! Duk zamuyi tafiya tau takan yi mana hakan. Idan yaran sunanan basuje School ba ayi dasu idan kuma sunje daga mu sai mazajen mu ne za'ayi. ALHAMDULILLAH!!! Masu karatu anan na kawo k'arshen wannan labarin nawa mai suna SONEE SILAR KOMAI. Ina fatar kuma ya k'ayatar da ku kuma za'a faɗakartu dashi A wa'azantu a kuma nishaɗantu. Ina fatar samun goyon bayan ku dan shi ne zai k'arfafe ni domin cigaba da zak'ulo muku labarai masu k'ayatarwa. Sai n afito muku a.............. Muje zuwa tare da alk'alamin FA'IK. 🙏🙏🙏