[10/08, 6:38 pm] Baby Aysher: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION* _(Home of expert & perfect writers)_ *SO DA ALAƘA....!* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ *Wattpad:@ummishatu* Free page *1* *DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI* ~~~Gudu take yi a hankali kaɗan kaɗan tana motsa jikinta cikin salon jan hankali da burgewa, shi ɗinma da yake biye da ita a hankalin yake yin nasa gudun inda yake ƙarewa halittar da ubangiji Allah yayi mata kallo, duk da cewa gudun tsere suke yi amma ya kasa zuwa ya wuceta saboda nishaɗin da yake samun zuciyarsa a ciki duk sa'ilin da yake kallonta, Sake ƙurawa bayanta ido yayi sanye take cikin ƙananan kaya riga da wando blue black, rigar iyakacinta cibiyarta shi kuma wando a cinyarta ya tsaya sai dai kayan sun kamata matuƙa, shi kuma sanye yake da riga armless da wando boxer dukkaninsu kalar ruwan madara, Sake rage gudun tayi tana ɗan numfarfashi cikin kissa da jan hankali, dariya yayi ya ƙarawa gudunsa mai yazo ya wuceta hakan da ta gani ya sata rakwarkwaɓe fuska tabi bayansa, kwance ta sameshi saman korayen ciyayin dake shimfide awurin kamar carpet ya wani baje yana shaƙar iska, kansa ta faɗa tana turo baki alamun yin fushi, hannu biyu yasa ya rungumeta yana faɗin, "what's wrong with my baby?" "Me yasa yau ka wuce ni?" ta faɗa cikin muryarta mai sanyi da rashin hayaniya, "I told you kinyi ƙiba da yawa tun bayan da kika haifi Ajmal kika buɗe gaki nan daƙyar kike ɗaya ƙafa...." Duka ta kai masa a ƙirji tana shusshura ƙafa kamar zata yi kuka, hannun ya riƙe bai barta ta dakeshi ba, a madadin hakanma sai ya soma sunbatar hannayen nata da lips ɗinshi masu tsananin taushi, " Kin san ina son ki.... Babu ruwana da ƙibarki zan cigaba da sonki koda zaki ninka haka ƙiba sau goma..." Murmushi tayi ta kwantar da kanta saman ƙirjinsa ta sake rungumeshi ƙam, "thank you darling..... Thank you for making my heart smile and my eyes shine...." "I love you..." ya faɗa yana sunbatar goshinta, mayar masa da martani tayi ta hanyar sunbatar wuyansa, "Lokacin salla ya kusa, kuma na bar baby na shi kaɗai a bedroom yana bacci may be yanzu ma ya tashi...." "Za kiyi min wayo dai kawai.... Oya let's go" ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa riƙe da ita, Maƙale kafaɗa tayi alamar ba zata tafi ba, ya san abinda take nufi shiyasa cikin salon so ya duƙa ta haye bayansa ya nufi ciki da ita bayan ya rufe garden ɗin. Kwantar da kanta tayi tana mai lumshe idanuwanta dan idan da akwai abinda ke sanyata nishadi a duniya bai wuce tajita kwance cikin jikinsa ko gadon bayansa ba. A hankali yake tafiya da ita har cikin bedroom ɗinsu, kan gado ya sauketa idanuwansa na kan ɗan ƙaramin gadon ɗansu Ajmal ɗan kimanin wata biyu wanda ke kwance yana bacci, wurin da yake kwance ya ƙarasa ya sunkuya ya manna masa kiss a kumatunsa sannan ya ɗago fuskarsa ɗauke da murmushi yana kallonta, "Ada kince dake Ajmal yake kama... Yanzu fa?" "yanzun ma da ni ɗin dai yake kamar" ta faɗa tana tashi zaune, "To zo ki gani.... Wallahi yanzu da yake baccin nan dani yake kama, these days ma gaba ɗaya kamanninshi sun koma nawa.... Ko jiya abinda hajiya ta faɗa kenan" Tashi tayi taje ta bayanshi ta rungumeshi ta karkatar da kanta ta leƙa dan ya fita tsayi nesa ba kusa ba, "Yanzu a hakane zaka ce kuna kama? Dan dai kawai kace hajiya ma ta faɗa ne shiyasa ba zan musa ba" "Kalli idon shi ki kalli nawa...." ya faɗa yana juyo da ita gabanshi, "Na san idon shi irin naka ne..." "Hancin shi fa?" "shima irin naka ne" "Bakinshi fa?" "irin nawa ne..." Dariya yayi ya ɗagata sama yana faɗin, "kin dai faɗi son ranki kawai malama.... Muyi wanka ko tunda gashi can naji ana kiran salla" Dariyar itama take tana harharba ƙafafu sakamakon cakulkulin da yake yi mata ta hanyar cusa kansa a cikinta. Cike da so da ƙauna suka yi wankan suka fito daidai lokacin Ajmal ya tashi, ɗaukarsa tayi tana daure da towel ta zauna gefen gado dan shayar dashi tana kallon gogan nata wanda yake tsaye gaban mirror yana goge jikinsa da ɗan ƙaramin farin towel body spray kaɗai ya feshe jikinsa dashi kusan kala biyar kasancewarshi ma'abocin ƙamshi daga bisani yawuce closet ya buɗe, juyowa yayi yana kallonta bayan ya riƙe ƙugunsa,ta gane nufinsa so yake ta shirya shi domin da haka ta sabar masa, langaɓar da kai tayi tana kallonsa, "Ayya daddy kayi haƙuri ka shirya da kanka mana..... Ajmal yunwa yake ji" Juyawa yayi yana kallon jerin tarin kayansa dake shirye cikin closet ɗin, yafi mintuna biyu amma ya kasa ciro wanda zai saka, "Ciro wannan blue ɗin trouser ɗin da maroon ɗin t shirt pls" ta faɗa daga nan inda take zaune, hakan yayi kamar yadda tace sannan yazo gabanta ya shirya, "zan je salla... Ki shirya kafin na dawo zamu fita dinner....." "a dawo lafiya" Kissing ɗin goshinta yayi ya juya ya fita yana balle botiran gaban rigar shi. Da murmushi ta rakashi har sai da ya ɓacewa ganinta sannan ta mayar da hankalinta kan Ajmal, bayan ya ƙoshi ta kwantar dashi ta miƙe, salla tayi bayan ta idar ta wuce gaban mirror ta soma shiryawa simple make up tayi dan iya powder kadai ta shafa sai gazal sannan ta shafa lips glow akan leɓenta, turarenta mai sanyin ƙamshi da daɗi na arabian oad ta shafa, doguwar riga ta saka baƙa ta sake komawa kan abun salla domin gabatar da sallar ishah dama shi kam ta san ba zai dawo yanzu ba har sai yayi sallar ishah kamar yadda ƙa'idarsa take, Tana zaune kan prayer mat taji motsin shigowarsa, addu'ar da take yi ta shafa tare da miƙewa tsaye hakan yayi daidai da shigowarsa, "Sannu da zuwa...." Ta bayanta yayi hugging ɗinta sannan ya sumbaci kumatunta kafin ya amsa da "Yawwa Darling" Ajmal ya ɗauka ya fita tana biye dashi har gaban motarshi, sai da ya buɗe mata ta shiga ta zauna ya miƙa mata Ajmal sannan ya zagaya mazaunin driver ya zauna, a hankali yake tuƙin yana riƙe da hannunta guda ɗaya har suka isa wurin cin abincin, yanzunma shine ya buɗe mata ƙofar motar ta fito ya karɓi Ajmal sannan suka shiga cikin restaurant ɗin, da kanshi yayi musu order ɗin abinda zasu ci bayan sun kammala ya biya suka nufi gida. Tare suka yi shirin bacci yana maƙale da ita a gefenshi laptop akan cinyarshi yana duba wasu ayyuka da zai yi, juyawa yayi ya kalleta idanuwanta a lumshe kanta bisa kafaɗarshi, "Darling..... Kinyi bacci ne?" Kai ta girgiza masa bayan ta buɗe manyan fararen idanuwanta, "kwanakin baya na taɓa faɗa miki akwai wani aikin hanya da zan yi a Niger ko?" Kai ta sake ɗaga masa tana kallonsa, "yawwa to yanzu maganar aikin ta taso.... Insha Allah zuwa Friday zan je inga ta yadda aikin zai kasance" Sake ƙanƙameshi tayi ta shige cikin jikinsa, "Zamu bika" Dariya taga yayi kafin ya shafi fuskarta, "Zan so hakan nima" "Allah yasa kayi aikin ka gama cikin nasara" "Amin Darling..... Me kike so in siya miki idan na gama wannan aikin" "Mota" ta faɗa tana kissing hannunshi, "Angama.... Nayi miki alƙawarin sabuwar mota insha Allah idan na dawo..." "Yehhhh" ta faɗa tare da faɗawa kanshi gaba ɗaya, janye laptop ɗin yayi ya tureta can gefe yayi mata masauki a jikinsa sosai yana dariya. Washe gari kamar yadda ya saba bayan ya gama shiryawa zai tafi office sai da ya fara biyawa ta gidan mahaifiyarshi domin ya gaisheta, Ƴar kyakkyawar dattijuwar tana zaune saman sallaya da alama sallar walaha ta idar hannunta riƙe da carbi tana ja, har gabanta ya ƙarasa ya zauna yana murmushi, "Hajiya barka da hutawa" Murmushin itama take yi tana binsa da kallo, "Imran..... An fito?" "Allah ya nufa Hajiya.... Ina kwana?" "Lafiya lau, ya iyalin, ina Angon nawa da alama rowarsa ake yimin ko?" Dariya yayi har sai da haƙoransa suka bayyana kumatunsa suka lotsa ciki, "Haba hajiya ai da kai da kaya duk mallakar wuya ne, idanma cewa kika yi ya dawo nan da zama gaba ɗaya to hakan za ayi" "A'a, har yanzu ku ɗinma baku gama ɗokinsa ba ai" Murmushi ya sake yi ya sunkuyar da kanshi ƙasa kafin ya ɗago cike da farin ciki yace "Hajiya albishirinki...." "Goro fari tas Imrana....." "Hajiya wannan babbar kwangilar da zanyi ta samu.... Insha Allah zuwa nan da juma'a zan je Niger..... Bayan na kammala aikin zaki sake komawa umarah" Faɗaɗa fara'arta tayi cikin murna da tsantsar farin ciki tace "Alhamdulillah..... Kai kai kai, Lallai kam dole a koma umarah ayiwa Allah godiya.... Allah yasa ayi lafiya agama da tarin nasarori Imran.... Allah ya sake ɗagaka, ya ƙarawa rayuwarka albarka" "Amin hajiya... Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana" Sallama yayi mata ya fita, tun yana hanya yake kiran gimbiyar tasa kamar yadda ya saba, wayar na dab da tsinkewa yaji ta ɗaga a kasalance, "Baccin ne?" Ya tambaya a hankali, "uhmmmm" "Ayya sorry na tasheki..." "Dama ina son jin muryarka ai" "An fara missing ɗinane?" "Over ma" "To ko in dawo...?" "uhmmmm uhmmmm kawai ina missing dinka ne fa" Murmushi yayi kafin ya bata amsa da "I miss you more.... Ina Ajmal?" "Yana bayan Dija ta goyashi.... Yana ta bacci" "Ok, sai na dawo, I love you" "I love you much more" Ta faɗa tare da katse wayar, da farin ciki danƙare a zuciyarsa ya ƙarasa office, shi dai haka rayuwarshi take baya taɓa haɗa komai da iyalinsa, wani irin so yake yi musu mai tsanani wanda sam baki ba zai iya faɗarshi ba. Cikin ƴan kwanakin ya gama shirye shiryensa na tafiya amma sai ya fara zuwa birnin tarayya Abuja wanda daga can ne zai bi flight, Yana maƙale da ita ajikinshi ya haɗasu ita da Ajmal ɗin gaba ɗaya ya rungume lokacin da ta iyo masa rakiya domin tafiya, "Zaka biya ta gidan hajiya ne?" "No, munyi sallama da ita tun daren jiya lokacin da naje, amma yanzu idan na fita zan kirata awaya" "To Allah ya kiyaye hanya ya kaika lafiya ya kuma dawo da kai lafiya" "Amin darling.... Am already missing you my Angel" Sai da ta ɗora kanta a ƙirjinsa sannan tace "same here sweetheart" Kissing ɗinsu yayi babu adadi sannan ya tafi, tana tsaye tana kallonsa har motarshi ta fita daga cikin gidan mai gadi ya mayar da gate ɗin ya rufe sannan ta koma ciki, bayan kamar mintuna 15 da tafiyarsa ya kirata yake sanar da ita ya kama hanya, wannan itace wayarsu ta ƙarshe da ita daga nan bata ƙara jinsa ba, idan ta kira wayar sai taji a kashe da haka har dare yayi anan ne kuma hankalinta ya soma tashi daga ƙarshe ta kasa jurewa har sai da ta kira hajiya ta sanar da ita, Yanda hajiya bata runtsa ba haka itama ta kasa runtsawa sai uban tashin hankali da tunani iri iri dake faman kai komo acikin zuciyarta. Washe gari tunda sassafe hajiya tazo gidan nan suka zauna tare sunata tsammanin warabbuka, amma shiru idan an kira wayarsa ma zancen ɗaya ne wai a kashe, sai zuwa yamma suka samu labarin wai ƴan ta'adda sunyi garkuwa da mutane sama da 10 a hanyar Abuja wannan labarin shi ya sake gigitasu ya ɗimautasu, dukkansu su biyun suna cikin mawuyacin hali, "Ruhaima sai haƙuri da addu'a... Addu'a za mu yi masa a halin yanzu dan ita yafi buƙata, Allah ya kuɓutar dasu....." Hajiya ta faɗa tana share hawayenta, ita dai bata iya cewa komai daga ƙarshe ma tsintar kanta tayi a gadon asibiti dan bata san me yake faruwa ba. Kwana da kwanaki ta kwashe a gadon asibiti kafin suka dawo gida amma ko bayan da suka dawo ɗinma babu wanda ya kira su yayi musu maganar Imran ko maganar kuɗin fansa kamar yadda aka tsammata shiru shiru tun ana kwanaki har aka share watanni da haka har aka shekara shiru babu wani sabon labari tun ana saka rai har aka fara cirewa, wasa wasa ƙaramar magana sai ta zama babba domin kamar an shuka dusa ko kuma an aiki bawa garinsu shiru babu labarin ko wanda ya ga Imran bare shi kansa.......✍🏻 *_Ummi Shatu_*👌🏻 [12/08, 10:06 am] Baby Aysher: ©️ *H.W.A* Paid Book *SO DA ALAƘA!* *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* *Wattpad:@ummishatu* 2 ~~~Tun bayan ɓatan Imran rayuwarta ta shiga cikin mawuyacin hali da ƙunci gaba ɗaya an kasa gane kanta, kusan kowa ita yafi tausayawa ko hajiya da take mahaifiyarsa kamar ta fita dauriya akan lamarin. Yau ma kamar kullum tana kwance saman gado da Ajmal kwance a jikinta, wayarta ce a hannunta ta tsura mata ido ko kiftawa bata yi, hoton Imran take kallo wanda suka ɗauka tare ranar sunan Ajmal, hawayene ya soma bin kumatunta babu ƙaƙƙautawa, har aka buɗe ƙofa hajiya ta shigo bata sani ba kuka kawai take yi sautin sansanyar muryarta yana fita a hankali, zama hajiya tayi a gefen gadon ta dafa kafaɗarta itama tana jin kanta kamar zata fashe da kukan, "Ruhaima..... Kiyi haƙuri kiyi haƙuri..... Lokaci yayi da zaki daina zubar da hawayenki haka, addu'ar nan dai da muke yi ita zamu cigaba da yi ba zamu fasa ba, insha Allah duk inda Imran yake yana cikin tsarewar ubangiji..... Kiyi haƙuri ki share hawayenki ga Umaima can tazo tare da baƙi tace dama kin san da zuwansu..... " Da ƙyar ta iya tsayar da hawayen ta ɗauki tissue ta goge fuskarta ta tashi, karɓar Ajmal hajiya tayi ita kuma ta gyara zaman dogon hijabinta wanda yake har ƙasa ta fita tana goge hawaye hajiya na biye da ita, Umaima ta hango zaune a cikin babban falonta, tun daga nesa ta fahimci cewa itama Umaima kukan take yi dan gashi nan idanuwanta sunyi ja baya da luhu luhu da suka yi, kusa da ita taje ta zauna kasancewar kujerar da take kai mai mazaunin mutum uku ce, Rungume juna suka yi suna sake yin wani sabon kukan a haka hajiya tazo ta iskesu, "Assha..... Nan ɗinma wani kukan kuke yi Ruhaima? Haba Umaima, wai shin wannan kukan da kuke yi zai ba mu mafita ne? Kuka fa baya magani...... Addu'a zaku yi masa" Daga haka hajiya ta wuce bedroom wanda yake mazaunin nata a halin yanzu tun bayan da aka samu labarin ɓatan Imran tana tafe tana share nata hawayen itama. Sai da su Ruhaima suka ci kukan su suka more sannan suka haƙura, "ga baƙin can na zo dasu..." Umaima ta faɗa tana kallon Ruhaiman, "kunyi magana dasu?" ta buƙata tana kallonta da jajayen idanuwanta, "Ehh sunce insha Allahu tsawon watanni biyu zasu kwashe suna gudanar da saukar alqur'ani da addu'o'i..... Kuma anan gidan zasu zauna, idan sun kammala za a basu abin sadaka dubu ɗari biyu" Ɗaga kai tayi alamun gamsuwa da bayanin da umaiman ta gama yi mata, "Wannan ba matsala bace sai akaisu can B/Q a saukesu, ni dai dama abinda bana so shirka da kauce hanya.... Amma tunda su karatun alqur'ani ne da addu'a hakan yayi min" "Nima wannan dalilin ne yasa na kawo su, ubangiji Allah ya wuce mana gaba yasa mu dace" "Amin Inlaw" ta faɗa tana murmushin yaƙe saboda halin da zuciyarta ke ciki, Umaima ƙanwar Imran ce kuma Allah ya haɗa jininsu da Ruhaima, tashi suka yi gaba ɗaya suke je wurin baƙin Ruhaima ta gaisa dasu sannan suka ɗan tattauna tasa aka rakasu B/Q, jin hayaniyar almajirai a ƙofar gida ya sanyata komawa cikin bedroom ɗinta ta buɗe drawer ɗin jikin mudubinta ta ɗauko kuɗi ƴan dari bibbiyu rafa biyu ta fito, da kanta ta fita ta rarrabawa almajiran sadaka kamar yadda ta saba kullum ta Allah, sai da ta tabbatar almajiran sun ƙare babu wani sauran wanda ya rage bai zo ya karɓa ba sannan ta koma ciki tana tafe tana tasbihi da carbin dake makale a yatsanta, Hajiya ta iske a falo tare da Umaima wadda ke ƙoƙarin haɗawa Ajmal abincinshi,zama tayi gefen umaima tana kallon yanda suke kokawa da Ajmal yanata zillo yana miƙa hannu zai kamo ɗan ƙaramin vowel ɗin da take dama masa kunun madara, "wait mana my dear... Yunwa kake ji ne haka?" umaima ta faɗa tana dariya, "Ba dole yaji yunwa ba..... Uwa bata ci ta ƙoshi ba bare shima ya samu.... Ni yau sam sam ma banga ta ci wani abu ba a cikin nan nata ko ruwa banga ta sha ba...." Juyawa umaima tayi ga Ruhaima ta kalle ta idanuwanta a lumshe tana istigfari sai dai tana sauraren duk abubuwan da suke faɗa, " inlaw bakya cin abinci why? Dan Allah ki rinƙa daurewa komai ƙanƙantarshi ko dan Ajmal.... Yanzu me zaki ci? Sai in dafa miki" "Azumi nake yi" ta faɗa cikin taushin murya idanuwanta a lumshe, "Hajiya kinji wai azumi take yi" "Ni na kasa gane kan wannan azumi na wannan yarinya, kullum azumi babu hutawa? Wannan wanne irin azumi ne?" Jin abinda hajiya tace ya sata buɗe idonta tana murmushi, "Hajiya jiya fa banyi ba,irin azumin Annabi Dawud nake yi, yau kayi azumi gobe ka huta, jibi kayi gata ka huta.... Jiya banyi ba dan har kika sa Mama Saude ta dafa min zogale naci ko kin manta?" "Eh anyi haka.... Ban manta ba" "Inlaw adai yi ta haƙuri dan Allah, a cigaba da haƙuri da rayuwa... Haka Allah ya ƙaddaro mana" Bata sake cewa komai ba ta miƙe ta fita ta ƙofar kitchen ta nufi babban kitchen wanda su mama Saude ke kwarafniyar girke girke, Aiki ta samesu suna yi na abincin sadaka da ake kaiwa gidan marayu da gidan yari kullum ta Allah, ɗan dafe kanta tayi wanda ke yi mata ciwo koda yaushe sanadiyyar kukan da take yi a kai akai shiyasa kowanne lokaci bata rabo dashi, "mama Saude idan kun kammala dan Allah akwai baƙi a B/Q mutum huɗu sai akai musu abinci da dukkan abinda ya kamata, zan ɗan shiga in kwanta daren jiya ban samu bacci ba watakila shiyasa kaina ke ciwo" "To shikenan hajiya... Babu komai, Allah ya sauwaƙe, a fito lafiya" Juyawa tayi ta nufi hanyar komawa ciki mama Saude ta bita da kallo tare da girgiza kai alamun tausayawa, ita dai tana tausayin wannan baiwar Allah domin tana cikin babbar jarrabawa, Sai da ta ɗan zauna wurin su hajiya sannan ta tashi ta shiga ciki ta kwanta wai ko za ta ɗan samu baccin amma ƙyamas yaƙi zuwa a madadin haka ma sai faman tunane tunane iri iri da ke bijirowa cikin zuciyarta, ita abinda yafi tsaya mata arai shine baka san halin da mutum ke ciki ba, ya mutu ko yana raye? Idan yana raye to a wanne yanayi yake? Wanne hali yake ciki? Wannan shine abinda ke sakata zubar da hawaye koda yaushe wanda ta kasa dainawa. Tana nan kwance tana ta faman juye juye ahaka umaima ta shigo ɗauke da Ajmal a kafadarta wanda ke bacci,duk a tunaninta bacci take yi shiyasa ta kwantar da Ajmal ɗin a gefenta ta fita, a hankali ta buɗe idanuwanta bayan taji fitar umaima ta zubawa Ajmal ido wanda sai yanzu ne take hango tsantsar kamanninsa da Imran wanda ada bata gani ba amma a ƴan watannin nan gaba ɗaya yaron ya juye kamar ubansa fitik, ajiyar zuciya ta ajiye a hankali tana jin ƙwalla tana ciko mata ido, "Allah ya bayyanaka Imran.... Allah ya tsareka a duk inda kake kuma ya kareka..... Jikina yana bani cewa kana raye.... Ban taɓa ji ajikina ka mutu ba....." hawayen ta goge kafin ta tashi ta shiga toilet, alwala tayi tazo ta fara jera salloli kamar yadda ta saba dan hakanne kaɗai ke ɗauke mata hankali daga halin da zuciyarta ke ciki, Sosai taji ta samu nutsuwa sannan zuciyarta tayi sanyi, nan inda tayi sallar wani bacci ya ɗauketa wanda ta wuni tana yi sai la'asar ta farka, ba ƙaramin daɗin baccin da ta samu taji ba saboda ta tashi zuciyarta wasai kuma nauyin da yake cikinta ma ya ragu, wanka tayi tai salla ta fita wurin hajiya, babu kowa atare da ita sai Ajmal dan da alama umaima ta tafi nan ta zauna wurin hajiya suna hira jefi jefi har zuwa lokacin da suka ji horn alamun mota zata shigo cikin gidan, Tana ta nazari acikin ranta tana tambayar kanta to kuma ko waye yazo mai gadi ya shigo cikin rissinawa da girmamawa yace, "Ranki ya daɗe baƙone yazo, zai iya shigowa?" "Ehh ya shigo baba" ta faɗa a taƙaice, juyawa yayi ya fita bayan fitarshi babu jimawa baƙon ya shigo kallo ɗaya tayi masa ta gane cewa daga cikin abokan Imran ne domin ba zai fishi ba ko a haife,da sallama a bakinsa ya shiga suka amsa atare ita da hajiya, "Ya abunda ya faru kuma? Ubangiji Allah ya bayyana shi, ai Imran mutumina ne sosai akwai kyakkyawar alaƙa tsakanina dashi..." "Allah sarki, mun gode madalla Allah ya bada lada" hajiya ta faɗa kuma kusan ma da hajiyan suke hira duk da gaba ɗaya hankalinsa yana kan Ruhaima wacce ke can duniyar tunani bata ma san yana yi ba, ita kanta hajiya ta fahimci hankalinsa yana ga Ruhaima amma dai bata nuna komai ba, kudi ya ajiye musu dami guda yayiwa hajiya sallama ya fita yana sake jaddada musu wai idan suna buƙatar wani abu a gaggauta sanar dashi...................... . ✍🏻 *HASKE! HASKE!! HASKE!!!*💡 IT'S *HASKE WRITERS*💡AGAIN THE HOME OF EXPERTS AND PERFECT WRITERS ✍🏻 HAƘIƘA JIMIRIN ZAMAN JIRA YA ƘARE MASOYA DOMIN ƘUNGIYARKU MAI FARIN JINI TA AMANA WATO *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 ITACE TA MOTSO KUMA TA DAWO DAN NISHAƊANTAR DAKU KAMAR YADDA TA SABA, *TAURARI HUƊU* SHINE TAKEN TAFIYAR TAMU A INDA ZAMU GABATAR MUKU DA FASIHAI, HAZIƘAN MARUBUTA GUDA HUƊU DA ALƘALIMANSU CIKIN TAFIYAR DA BABU NADAMA ACIKINTA, *1.AYUSHER:-* Writing by FERTYMERH XARAH *2.ƘAZAFI NE:-* Writing by RAHAMA NALELE *3.DA UBA AKE ADO (Bada riga ba):-* Writing by ZAINAB BAWA *4 SO DA ALAƘA:-* Writing by UMMI A'ISHA WAI WAI WAI... 🔥BAHAUSHE YAYI GASKIYA LALLAI TAFIYA DA GWANI MAI DAƊI, NIMA DAI GA NAWA GWANAYEN 4 STARS DUKKA WAƊANNAN LITTATTAFAN GUDA HUƊU ZAKU SAMESU CIKIN FARASHI DAIDAI DA ALJIHUNKU....MY SISTER WHAT ARE YOU WAITING FOR?? MAZA HANZARTA KI GARZAYA KI NEMI NAKI DAN ZASU FARA NAN BADA JIMAWA BA, KAR KI BARI A BAKI LABARI..... COMING TO YOUR WAY SOON, DON'T MISS IT 😘😘 Guda 4:- 1500 Guda 3:-1200 Guda 2:- 800 Guda 1:- 400 7033027658 Palmpay Bank Aisha Muhammad Salis Katin wayar MTN ta... 07044644433 da shaidar biya *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 *_Ummi Shatu_*👌🏻 [13/08, 7:08 am] Baby Aysher: ©️ *H. W.A* *SO DA ALAƘA!* *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* *Wattpad:@ummishatu* Free page 3 ~~~Rayuwa na tafiya, lokaci na wucewa, komai yana sauyawa, kullum sababbin al'amura ke sako kai sai dai hakan bai sauya rayuwar Ruhaima daga kan doron da take kai ba, addu'a yinta ake ba dare ba rana haka sadaka da sauran ayyukan alkhairi dan Imran ya bayyana amma Allah bai ƙadarta ba, lissafa adadin kuɗin da suka kashe wurin biyan malamai su yi addu'a ba zai lissafu ba domin malamai sun zo gidan babu adadi wasu ma tun daga uwa duniya, dan bata mantawa waɗannan malaman da suka tafi na ƙarshe tun daga ƙasar Mali suka zo, tayi kuka har ta gaji ta fawwalawa Allah lamarinsa. BAYAN SHEKARA BAKWAI *** Rayuwar Ruhaima ta sauya cikin waɗannan shekarun, ada tana cikin arziƙi dumu dumu amma yanzu rayuwar sai dai a lallaɓa domin ita ba aikin gwamnati take yiba, haka kuma bata da wata ƙwaƙƙwarar sana'a da zata taimaka mata ta riƙe kanta da Ajmal wanda yanzu yana buƙatar asakashi a makaranta, Yau tun da garin Allah ya waye da tunanin neman mafita ta tashi, so take ta saka Ajmal a makaranta dan idan ta kalli yaron ma tausayi yake bata. Suna falo suna karyawa ita da Ajmal ɗin baba maigadi ya shigo yana sanar da ita wai tayi baƙi,cewa tayi su shigo, Manta inda ta san fuskar mutumin tayi amma dai kamar ta sanshi, murmushi yake yi mata mai ma'anoni daban daban, hijabin jikinta ta gyara ta bar karyawar da take yi ta maida hankali ga mutumin suna gaisawa, "Sai kuma naji ki shiru... Keda nace miki idan kuna da buƙatar wani abu asanar dani kuma sai inji shuru? Haba Madam.... Baki da buƙatar komai ne? Yau shekara nawa da ɓatan mijinki...." Murmushin yaƙe tayi dan sam ita bata fahimci abinda yake nufi ba, "Babu komai mun gode Allah ya saka da alkhairi..." "Haba madam.... Menene abin godiya? Yaushe zaki cigaba da rayuwa cikin ƙunci da damuwa? Ki ajiye komai a gefe kiyi rayuwarki kiji daɗinki..... Kina da kyau, kin mallaki komai wanda ake buƙata a wurin ƴa mace, idan kika bada dama ba zaki ƙara kukan rashin mijinki ba.... " Sai lokacinne ta fahimci inda maganar tasa ta dosa, nan take ta ɗaure fuska ta kalleshi kamar yadda yake kallonta, " Wannan ne ya kawoka? To mun gode zaka iya tafiya, sannan bana buƙatar sake ganinka acikin gidana idan kuma ba haka ba wallahi zaka ga abinda zai biyo baya" Jiki babu ƙwari ya miƙe ya fita yana ƴan kame kame wanda hakan ya sake ɓata mata rai, wani dogon tsaki taja bayan fitarsa hawaye na bin kumatunsa, wai dama haka matan da suka rasa mazajensu ke fuskantar ƙalubale? Dama haka wannan zamanin namu ya lalace da butulci mai cike da tsantsar cin amana? Tashi tayi ta wuce cikin bedroom ɗinta ta kwanta kamar yadda ta saba kukan baƙin ciki a duk lokacin da wani yazo mata da magana makamanciyar wannan, Kuka tayi wanda ita kanta bata san yawan lokacin da ta kwashe tana yinsa ba daga ƙarshe bacci ya kwasheta bayan ta tashi tayi wanka ta shirya shima Ajmal ta shiryashi ta kama hannunsa suka fita, gidan umaima ta nufa dake unguwar Sulaiman crescent, tana tuƙi tana tunanin rayuwa, a haka har Allah ya kaita gidan lafiya, Rungume juna suka yi cike da murnar ganin juna, "inlaw shine baki sanar dani zaki zo ba?" umaima ta faɗa tana ƙoƙarin ɗaukar Ajmal wanda ke sanye cikin jeans da farar t shirt, "zo nan sweetheart, mommy bata kawoka kunyi wasa dasu Abid ba ko?" "Na cema mommy zan dawo wurin su Abid" Murmushi Ruhaima tayi tana sauraronsu, surutun Ajmal yafi gaban haka wannan dalilin ne yasa ta ƙagu ta sakashi a makaranta. Cikin mintuna kaɗan umaima ta cikasu da kayan motsa baki, dambun nama, cake, meat pie da sauran dangin kayan sanyi,da kallo Ruhaima ke bin ko ina na cikin falon saboda yanda gidan ya sake haɗuwa kuma ya ƙawatu da yake mijin umaiman mai kuɗi ne sosai kuma rayuwar tana gara masa daidai gwargwado,sai bayan da umaima ta dawo ta zauna sannan suka gaisa Ruhaima ta kalleta da murmushi tace, "inlaw wurin mijinki na zo.... Ina son ganinsa kan wata muhimmiyar magana" Ajiyar zuciya umaima ta sauke kafin ta kalleta tace "Gashi kuma kin daki gurbi.... Ina fata dai lafiya babu wata damuwa?" "lafiya lau amma zuwa yaushe zai dawo?" "A gaskiya inlaw zai yi 2 weeks kafin ya dawo dan aiki ya tafi kuma dazun nan yayi tafiyar" Ɗan dafe goshinta tayi cikin rashin jin dadi da damuwa ƙarara wadda ta bayyana kan fuskarta, "To shikenan babu matsala, sai ki bani phone no ɗinsa sai in kirashi kawai" Ɗan damm umaima tayi amma sai tayi murmushi tace "ok to ai babu problem bari na saka miki no ɗin nasa" Wayar hannunta ta bata ita kuma ta saka mata sannan ta mika mata ta karɓa tayi saving, sun jima a gidan suna hira Ajmal yana wasa da su Abid waɗanda suka dawo daga makaranta, sai magriba sannan tayi musu sallama suka tafi, Sai bayan da ta idar da sallar ishah sannan ta samu zarafin kiran Alhaji Sabo wato mijin Umaima kuma abokin hulɗar mijinta Imran, har ta gama ringing ta tsinke bai ɗauka ba, nan ta sake kira amma har tayi ta gama ba a ɗauka ba, yanke shawarar tura masa saƙon karta kwana tayi, nan tayi masa sallama tace itace Ruhaima matar Imran tana son yin magana dashi dazu taje gidanshi bata sameshi ba, Bai dawo mata da reply ba sai can misalin ƙarfe 10 na dare lokacin har ta gama shirin bacci sai ga kiran sa, kamar ba zata ɗauka ba amma sai wani ɓangare na zuciyarta ya shawarceta da ta ɗauka domin wataƙila da yuyuwar lokacin da ta kirashi har ta tura masa text massage yana can yana ganawa da mutane tunda matarsa tace mata aiki ya tafi, "Assalamu alaikum....." ta faɗa cikin muryarta mai sanyi, "Wa alaikumussalam..... Hajiya Ruhaima, yagida, ai sai yanzu naga kiranki da saƙonki.... Lokacin da kika kirani na shiga meeting ne wallahi" "Ayya nima nayi wannan tunanin, dama dazu ma naje gidan sai umaima ke fada min kayi tafiya, kuma gashi ina son Magana da kai" "To karki damu insha Allah da zarar na dawo zan sanar da ke, babu matsala" "Ai babu wani abu koma awaya ne zamu iya maganar" "a'a... Haba haba, ai idan nayi haka to ban mutuntaki ba kuma ban baki darajar da ta kamaceki ba Ruhaima.... Karki damu zamu tattauna face to face idan na dawo" "to shikenan nagode, Allah ya kaimu, sai da safe" ta faɗa ataƙaice kuma bata jira cewarsa ba ta gintse wayar sannan ta kasheta gaba ɗaya, Bata sake kiransa ba ko tura masa saƙo har sai bayan sati biyu ya kirata da kanshi yace mata ya dawo gari, "ok to yaushe zan zo gida na sameka?" "Ai matsalar bana zama a gida munata ayyuka tunda na dawo sai dai mu haɗu wurin aikin....." Misalin ƙarfe uku na yamma ta kammala shirinta kamar yadda suka alƙawarta da Alhaji Sabo, doguwar riga ta saka ta atamfa purple color ta yafa milk ɗin mayafi kasancewar akwai ɗigon milk a jikin atamfar, bata yi wata doguwar kwalliya ba, iya gazal da lipstick kaɗai ta saka ta fita rataye da handbag ɗinta dama tun kwana biyu da suka wuce Ajmal yana gidan hajiya, Drop ta ɗauka na napep har inda Alhaji sabo ya kwatanta mata, sauka tayi ta sallami mai napep ɗin sannan tayi knocking a ƙofar guest house ɗin, ɗaya daga cikin masu tsaron gidanne ya leƙo sannan ya buɗe mata, "Dan Allah nazo ganin Alhaji sabo ne..." "eh yana nan bari asanar dashi" Sai da yakirashi a wayarshi ta hannu ya sanar dashi yace ta shiga sannan ya nuna mata hanya, cikin ƙarfin hali da kuma dakiya ta buɗe ta shiga, duk a tunaninta zata ga falon cike da mutane kamar yadda ya sanar da ita amma sai taga sai shi kaɗai sanye da ƙananan kaya, "Barka da zuwa" yace da ita fuskarsa dauke da fara'a, "Yawwa barka Alhaji" Ta faɗa tana zama akan kujerar dake kallon tasa, "Yagida ya kike" "lafiya lau, dama nazo ne akan maganar kuɗin Imran dake hannunka, ya taɓa sanar dani akwai kuɗinsa a hannunka..... To muna da buƙata ne ina so zan saka Ajmal a makaranta ga kuma sauran buƙatu na yau da kullum...." Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ɗan tashi daga kishingiden da yake yana binta da wani shu'umin kallo, " Hmmmm, Ruhaima kenan ai ko babu kuɗin Imran awurina ni mai taimakawa rayuwarki ne mutuƙar kin amince..... Gaki da kyau.... Kina da tsananin kyau Ruhaima, tun lokacin da na fara ɗora idona a kanki naji kishin Imran ya kamani..." Wani kallo tayi masa cikin firgici sannan cikin dimuwa tace, " Ban... Ban fahimceka ba" Murmushi yayi ya juya gefensa ya ɗauko wani ɗan ƙaramin brief case ya buɗe ya ciro rafar kuɗi yan dubu dubu guda biyar ya tashi ya miƙa mata, "ga wannan ki fara dasu... Wannan somin taɓi ne matsawar zaki yarda dani to zan rinƙa baki adadinsu babu yankewa..... Ni dai buƙatata ki bani dama ki barni in ɗanɗani zumarki...." Cikin gigicewa ta kalleshi jin ya dawo kusa da ita ya zauna, "Alhaji ban fahimci abin da kake nufi ba, nifa matar yayan matarka ce... Yanzu idan muka aikata haka da wanne suna za a kira wannan kwamacala da ƙazantar da muka aikata? Kenan dama da biyu ka gayyato ni nan babu wani aiki ko meeting da kake yi?" "Kawai na kawo ki nan ne dan mu more rayuwar mu na san kema kina da buƙatar hakan.... Yaushe rabonki da mijinki.... Ki manta da batun matata kawai ki saki jiki mu more rayuwarmu" Zabura tayi ta tashi da sauri jikinta yana kyarma yana rawa karkar, idanuwanta duk sun fito waje alamar firgici da tashin hankali, "Ka bani lokaci zanyi tunani" ita kanta bata san lokacin da ta faɗi hakanba saboda bukatar ta a halin yanzu ta ganta a waje, "Haba Ruhaima... Ya kike yin abu kamar wata sabon shiga ko ƙaramar yarinya? Kefa ba budurwa bace bare kiji tsoron wani abu...." Kafin ta ankara ya damƙo hannunta, ƙoƙarin fusgewa ta shiga yi amma ya riƙeta gam tare da haɗata da jikinsa ta ƙarfin tsiya, kokawa suka shiga yi amma da yake ƙarfin namiji da mace ba ɗaya ba nan ya riƙeta gamgam daga ƙarshe ya jefata kan kujera, ƙoƙarin ceton kanta ta fara yi ta hanyar dube duben abinda zata ɗauko, yana ƙoƙarin cire belt ɗin jikinsa tayi ido huɗu da kwalbar giya dake ajiye can gefe ɗaya cikin azama haɗe da zafin nama ta rarumota ji kake tasss ta buga masa akai take jini ya ɓalle shi kuma ya ɗagata babu shiri yana sakin ƙara, da masifar gudu tayi hanyar waje bayan ta suri handbag ɗinta, shima bai zauna ba duk da jinin dake zuba rufa mata baya yayi yana ihu, "kar ku barta ta fita.... Ku riƙeta ku kira police" Hakan kuwa akayi cikin mintuna kaɗan sai ga motar ƴan sadda take suka ingiza ƙeyarta suka tafi da ita, idanuwanta jajur ko kukanma ta gagara yi, ba zata taɓa yafewa Sabo wannan abun da yayi mata ba, a bayan kanta aka sakata har magriba lokacinne Alhaji sabo yazo, kansa ya sha ɗinki inda ta kwaɗa masa kwalbar, Ofishin DPO aka shiga dasu, nan tayi shiru ta zuba musu ido tana sauraren uwar ƙaryar da Alhaji sabo yake shiryowa akanta........... ✍🏻 *HASKE! HASKE!! HASKE!!!*💡 IT'S *HASKE WRITERS*💡AGAIN THE HOME OF EXPERTS AND PERFECT WRITERS ✍🏻 HAƘIƘA JIMIRIN ZAMAN JIRA YA ƘARE MASOYA DOMIN ƘUNGIYARKU MAI FARIN JINI TA AMANA WATO *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 ITACE TA MOTSO KUMA TA DAWO DAN NISHAƊANTAR DAKU KAMAR YADDA TA SABA, *TAURARI HUƊU* SHINE TAKEN TAFIYAR TAMU A INDA ZAMU GABATAR MUKU DA FASIHAI, HAZIƘAN MARUBUTA GUDA HUƊU DA ALƘALIMANSU CIKIN TAFIYAR DA BABU NADAMA ACIKINTA, *1.AYUSHER:-* Writing by FERTYMERH XARAH *2.ƘAZAFI NE:-* Writing by RAHAMA NALELE *3.DA UBA AKE ADO (Bada riga ba):-* Writing by ZAINAB BAWA *4 SO DA ALAƘA:-* Writing by UMMI A'ISHA WAI WAI WAI... 🔥BAHAUSHE YAYI GASKIYA LALLAI TAFIYA DA GWANI MAI DAƊI, NIMA DAI GA NAWA GWANAYEN 4 STARS DUKKA WAƊANNAN LITTATTAFAN GUDA HUƊU ZAKU SAMESU CIKIN FARASHI DAIDAI DA ALJIHUNKU....MY SISTER WHAT ARE YOU WAITING FOR?? MAZA HANZARTA KI GARZAYA KI NEMI NAKI DAN ZASU FARA NAN BADA JIMAWA BA, KAR KI BARI A BAKI LABARI..... COMING TO YOUR WAY SOON, DON'T MISS IT 😘😘 Guda 4:- 1500 Guda 3:-1200 Guda 2:- 800 Guda 1:- 400 7033027658 Palmpay Bank Aisha Muhammad Salis Katin wayar MTN ta... 07044644433 da shaidar biya *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 *_Ummi Shatu_*👌🏻 [13/08, 9:07 pm] Baby Aysher: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION* ( _Home of expert & perfect Writers_) *SO DA ALAƘA....!* *_NA_* _*UMMI A'ISHA*_ Free Book 4 *Wattpad :@Ummishatu* ***Wasu zafafan hawaye ne suka sauka akan kuncinta lokacin da ta ji irin ƙarya da ƙazafin da Alhaji Sabo yake shirya mata, Sai da ya sake gyara zamansa sosai ya kalli DPO cikin salon yaudara da ƙarya tsantsa yace, "Yallaɓai wannan yarinyar taci mutuncina mutuƙa, ka duba ka ga irin ɗanyen aikin da tayi min......duba goshina da kaina duk naɗe suke da bandeji sakamakon aika aikar da tayi min, so tayi ta ɗauki rayuwata ranka ya daɗe Allah bai nufa ba, jibi yanda ta illata ni da kwalbar lemo dan kawai ta zo akan in taimaka mata ni kuma nace me yasa bata sameni a gida ba wurin iyalina kamar yadda na sanar da ita tun farko, sai tace min wai bata so iyalina ta sani ni kuma babu wani abu da nake ɓoyewa iyalina komai nawa is open, yarinyar nan ta fito ƙarara ta nuna min abinda take nufi dani nace a'a yanzu dai zan bata dubu ɗari taje ta kashe matsalar gabanta domin akwai alaƙa tsakaninta da iyali na, lokacin da na bata kuɗin nace ta tafi gida muka yi sallama ashe ba tafiya tayi ba laɓewa tayi dan tayi min sata, ina shiga toilet na jiyo alamar motsin mutum, fitowar nan da zanyi sai na hangeta tana ƙoƙarin yin awon gaba da jakata wadda aciki ta ga na ɗauko waɗannan kuɗin na bata.... Yallaɓai to cut the story short wallahi daƙyar na ƙwace jakata.... Kai garin in ƙwace ɗinne ma ta ɗauko makami tayi amfani dashi ta jimin wannan ciwon da kake gani wanda sai da ta kaini ga zuwa asibiti...... " Kallonta DPO yayi na ɗan wasu sakanni yayin da ita kuma idanuwanta ke kallon ƙasa tana zubar da hawayen baƙin ciki da ɓacin rai, wannan wacce irin ƙaddara ce? Alhaji sabo ya yaudareta ya so yaci amanarta ya keta mata rigar mutuncinta Allah ya tsallakar da ita amma yanzu kuma yazo yana yi mata sharri da ƙage,muryar DPO ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, "Hajiya kin aikata laifi kan laifi.... Laifinki da yawa, ta yaya zaki nemi yiwa mutum sata, sannan dan ya kare dukiyarsa kiyi yunƙurin ɗaukar rayuwarsa? This is a very serious case.... We can take it as criminal offense....." "Ni banyi niyyar yi masa sata ba, asali ma shine ya gayyace ni zuwa guest house ɗinsa duk da na kawo maganar mu haɗu a gidansa amma yaƙi yace baida lokaci..... Wannan ciwon da naji masa yunƙurin keta min haddi yayi shiyasa nayi amfani da kwalbar giyar dake cikin sitting room ɗin na buga masa..... " " sharri zaka yimin Ruhaima? Abin naki harda sharri ya koma? Saboda kin buƙaci mu ƙulla mummumar alaƙa naƙi amincewa na nuna miki wannan ba halayyar mutanen ƙwarai bace shiyasa yanzu zaki zo nan kiyi min sharri? Alhaji sabo ya faɗa cikin hayaniya kamar gaske, "Ya isa haka Yallaɓai... Amm Ruhaima kika ce yayi yunƙurin keta miki haddi ko?" DPO ya buƙata yana Kallonta, "Ehh yallabai haka nace" "To a lokacin me ya hana ki kiyi ihun neman taimako? Wanne yunƙuri kika yi dan ankarar da mutanen dake maƙotaka da wurin dan akawo miki ɗauki?" "Banyi ihu ba kawai dai nayi ƙoƙarin ganin na kare kaina...." ta bashi amsa hawaye na bin kumatunta, "wannan ba hujja bace.... Sannan wannan maganar taki ba wacce hankali zai ɗauka bace Ruhaima... Idan har dagaske kike abinda kika faɗa cewar yayi yunƙurin keta miki haddi to kamata yayi kiyi ihu a matsayinki na mai hankali, sannan ni sai nake ganin babu abinda zai sa ki ziyarci guest house ɗinsa mutukar abinda kike faɗa gaskiya ne, me ya hana kije gidansa? Duk wanda aka ce mace taje guest house abinda zai fara zuwa ransa shine kinje taya shi hutawa ne..... Yanzu dai duk ba wannan ba, Alhaji sabo babu buƙatar mu fitar da maganar nan waje ko mu tura court, kamata yayi kuje gida kuyi sulhu, zamu bada belinta sannan dole zamuyi rubutu saboda gaba, domin case irin wannan bama ɗaukarsa da wasa..... " Har suka yi suka gama bata sake furta koda kalma guda ɗaya ba saboda tama rasa me zata ce, binsu kawai take da ido har zuwa lokacin da DPO yace ta bada no wanda za a kira yazo yayi belinta, bata da zaɓi wanda ya wuce ta bada no din hajiya. Hajiya aka kira lokacin tana zaune kan sallaya bayan ta idar da sallar magrib tana azkhar, tana jiyo hayaniyar su Ajmal wanda ke ta ƙiriniya dasu Abid wanda suka zo weekend, A gigice hajiya ta fita da wayar a hannunta bayan ta saurari bayanin da aka yi mata a wayar wai daga police station ne aje ayi belin Ruhaima, part din da ke kusa da nata ta nufa a kiɗime dan ƙafarta ko takalmi babu tana tafe tana cin tuntuɓe, Fitowarshi daga wanka kenan yana goge jikinsa da towel yaji shigowar hajiya tana ƙwala masa kira cikin tashin hankali, "Sameer..... Sameer..... Kana ina ne? Wai ko baka ciki?" Jin kiran da take yi masa kamar bana lafiya bane yasashi saurin fitowa a yanda yake daga shi sai gajeren wando da towel a hannunsa, "Hajiya lafiya......?" "Babu maganar lafiya Sameer.... Yi maza ka shirya ka tafi police station Ruhaima aka kama.... Sauri kaje ka jiyo me ya faru...." Saida yaji gabansa ya tsinke ya faɗi amma sai ya dake bai bari hajiya ta fahimta ba, "Hajiya..... Kuma ni zan je?" "To wa kake so yaje? Ni zanje ko wa?" Shiru yayi bai amsa ba, sannan cikin halin ko in kula ya kawar da kai, "kayi maza ka shirya nace maka kaje, ko baka ji?" hajiya ta fada cikin faɗa, "Naji" Daga haka ya juya ciki, tsaki ya ja ya wuce gaban mirror ya fesa body spray sannan ya wuce gaban closet dinsa, farar jallabiya kar ya ciro yasaka yana jan tsaki, gefen gadonsa yaje ya ɗauki wayar shi da key ɗin mota ya fita yana ta faman ciccin magani, Part ɗin hajiya ya shiga, bai bi ta kan yaran dake ta faman guje guje ba a cikin babban falon gidan sannan da alama suma ɗin babu wanda ya ankara da shigowar tashi, Samun hajiya yayi ta kasa zaune ta kasa tsaye sai faman safa da marwa take ta faman yi tana ta kaiwa da kawowa a falonta, "Hajiya wanne division ne?" ya fada fuska ba fara'a, faɗa masa tayi ya juya ya fita yana ta ɓaɓɓata rai, tafiyar mintuna 30 ce ta kai shi division ɗin, Lokacin da yaje iya DPO kaɗai da Alhaji sabo ya samu bai ga Ruhaima ba, kamar yadda Alhaji sabo ya tsare dpo ƙarya da gaskiya haka ya tsare Sameer wanda kusan gaba ɗaya ma zancensa ƙarya ne, Sai da suka yi rubutu kowa yasa hannu daga ƙarshe aka shigo da Ruhaima dan itama ta saka hannu, kawar da kai Sameer yayi lokacin da take shigowa, fuskar ta jajur da idanuwanta saboda taci kuka har ta gaji, ɗankwalinta a hannu sai ko gyalenta dake kanta wanda ta yafa, hannu tasa Sameer yayi sallama dasu ya fita tabi bayansa, handbag ɗinta aka bata da takalminta, a hannu ta riƙe su dan tsabar baƙin ciki ko takalmin bata saka ba, tana biye dashi har gaban motarsa, ko Kallonta baiyi ba ya buɗe ya shiga itama ta shiga ranta a cunkushe kuma a dagule me yafi wannan tozarci da kunya? Ayi mata ƙazafin sata da bin maza? Yanzu ta san bata da wata hanya wacce zata wanke kanta sai abinda hali yayi, amma dai abinda ta yarda dashi shine Allah baya zalunci sannan baya bacci, ta san komai daren daɗewa Allah zai tona asirin alhaji sabo, Tunda suka fito daga police station ɗin bata yi gigin kallon ko inda yake ba sai yanzu da suka hau titi sannan ta saci kallonsa ta gefen ido, sai da tayi danasanin kallonsa saboda yadda taga ya haɗe girar sama da ƙasa ya cika fam kaɗan yake jira ya fashe, Tuƙi kawai yake yi gaba ɗaya ya tattara nutsuwarsa akai kamar babu wata halitta acikin motar sai shi ɗaya, ransa a ɓace yake tuƙin cikin tsananin baƙin ciki, kai tsaye gidanta ya wuce da ita, har cikin gidan ya tura hancin motarsa lokacin da mai gadi ya buɗe musu ƙofa, birki yaci da ƙarfi wanda sanadiyyar hakan har sai da ta buge kanta amma bai ko kalleta ba, buɗe ƙofa tayi ta fita dan jikinta ya bata hakan kawai yake buƙata ahalin yanzu, tafiya kawai take bata ko sake marmarin juyowa ba taji alamun fitowarsa daga cikin motar shima, tana dab da hawa barandar falonta tajiyo amon muryarsa cikin kaushi yake yi mata magana, "Be kamata ba sannan kuma ba daidai bane ki rinƙa bin mazajen mutane awaje ciki harda mijin ƙawarki, mijin ƙanwar mijinki dan kawai mijinki ya rasu, sannan saboda tsabar rashin tunani da toshewar basira harda sata..... Tirr.... Akwai mata da yawa da suka rasa mazajensu kuma suka daure suka yi hakuri suka kame kansu suka killace mutuncinsu, idan ba zaki iya haƙuri ba ki rungumi azumi a matsayin magani..... " daga haka ya juya ya nufi motarsa cikin tsananin fushi da ɓacin rai, tana tsaye tana kallonsa takalminta da jakarta da ɗankwalinta duk sun zame sun faɗi awurin saboda jinta take kamar ba ita ba, waɗannan baƙaƙen maganganun da Sameer ya faɗa mata su suka fi yi mata ciwo fiye da abinda Alhaji sabo yayi mata, yanzu ta san ba iya Sameer kaɗai ba kusan kowa kallon da zai rinƙa yi mata kenan, jarababbiya marar haƙuri ta kasa jure rashin mijinta tana neman wasu mazan, mai halin ɓera wadda Allah Allah take taga wasarere ta sata, tana nan tsaye kamar an dasata tana zubar da hawaye har motar Sameer ta fita, tafi mintuna 20 tsaye bayan tafiyarsa dan baƙin ciki dan har ƙafafuwanta saida suka yi tsami suka ƙage, daƙyar ta jasu ta shiga ciki sauran kayanta da ta zubar kuwa nan ta barsu ko bi ta kai bata yiba sai maigadi ne ya shigo mata dasu, zaman dirshan tayi a tsakiyar bedroom ɗinta tana kuka wiwi saboda baƙin ciki, daƙyar ta rarrashi zuciyarta bayan taci kuka ta ƙoshi, tana ƙoƙarin yin shirin bacci lokacin misalin ƙarfe 9:30 na dare taji wayar ta dake cikin jaka tana faman neman agaji sakamakon ƙarajinta da ya karade ko ina na cikin dakin.......✍🏻 *HASKE! HASKE!! HASKE!!!*💡 IT'S *HASKE WRITERS*💡AGAIN THE HOME OF EXPERTS AND PERFECT WRITERS ✍🏻 HAƘIƘA JIMIRIN ZAMAN JIRA YA ƘARE MASOYA DOMIN ƘUNGIYARKU MAI FARIN JINI TA AMANA WATO *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 ITACE TA MOTSO KUMA TA DAWO DAN NISHAƊANTAR DAKU KAMAR YADDA TA SABA, *TAURARI HUƊU* SHINE TAKEN TAFIYAR TAMU A INDA ZAMU GABATAR MUKU DA FASIHAI, HAZIƘAN MARUBUTA GUDA HUƊU DA ALƘALIMANSU CIKIN TAFIYAR DA BABU NADAMA ACIKINTA, *1.AYUSHER:-* Writing by FERTYMERH XARAH *2.ƘAZAFI NE:-* Writing by RAHAMA NALELE *3.DA UBA AKE ADO (Bada riga ba):-* Writing by ZAINAB BAWA *4 SO DA ALAƘA:-* Writing by UMMI A'ISHA WAI WAI WAI... 🔥BAHAUSHE YAYI GASKIYA LALLAI TAFIYA DA GWANI MAI DAƊI, NIMA DAI GA NAWA GWANAYEN 4 STARS DUKKA WAƊANNAN LITTATTAFAN GUDA HUƊU ZAKU SAMESU CIKIN FARASHI DAIDAI DA ALJIHUNKU....MY SISTER WHAT ARE YOU WAITING FOR?? MAZA HANZARTA KI GARZAYA KI NEMI NAKI DAN ZASU FARA NAN BADA JIMAWA BA, KAR KI BARI A BAKI LABARI..... COMING TO YOUR WAY SOON, DON'T MISS IT 😘😘 Guda 4:- 1500 Guda 3:-1200 Guda 2:- 800 Guda 1:- 400 7033027658 Palmpay Bank Aisha Muhammad Salis +447894142004 Katin wayar MTN ta... 07044644433 da shaidar biya *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 *_Ummi Shatu_*👌🏻 [15/08, 8:58 am] Baby Aysher: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *SO DA ALAƘA....!* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ *Wattpad:@Ummishatu* Free page 5 ***Driving yake amma tunaninsa na wani waje, shi gaba ɗaya lamarin mata yanzu tsoro yake bashi ba mamaki ba, banda lalacewar zamani ta yaya mace zata rinƙa ƙasƙantar da kanta tana ajiye darajar da Allah yayi mata tana cire kunyar da aka santa da ita tun tale tale tana kaiwa namiji kanta? Tsaki yaja a karo na ba adadi tun bayan da yabaro gidan Ruhaima, shi dai idan da abinda ya tsana a duniya to zina ce, yaƙi jinin zina sannan ya tsani duk wani mai aikatata amma yanzu yaga kamar tama zama ado dan idan mutum ba yayi wai gani ake bai waye ba, sannan masu yi basa kunyar bayyana kansu ya fahimci hakanne dalilin yawan kawo masa hari da mata keyi shi dai ya rasa wannan masifa ya rasa me suke gani atare dashi da suke yawan kawo masa farmaki, da zancen zucin da yake yi ya shiga unguwar su ransa a cunkushe kuma a ɓace, sallar ishah ya tsaya yayi sannan ya shiga gida, tun a hanya yaketa ganin kiran hajiya amma bai ɗaga ba. Kamar yadda ya tafi yabarta hankali tashe yanzun ma haka ya sake dawowa ya sameta, duk bata da cikakkiyar nutsuwa, yana shiga ta miƙe daga zaunen da take bayan ta ajiye Ajmal a gefe wanda ada yake kwance a jikinta yana bacci, "Ina Ruhaiman take? Me ya faru? Me ya hadata da ƴan sanda har ta kaisu ga zuwa police station? Yanzu ya aka ƙare?" Duk da a cikin fushi yake sai da yayi murmushi jin irin tarin jerin tambayoyin da hajiya ta jero masa lokaci guda kuma ya san kowacce tambaya tana buƙatar amsarta, " Sameer..... Kabani amsa mana " " Hajiya ba wata matsala bace babba... Harma ai an kashe case ɗin, tana can gidanta na sauketa..." Daga haka ya wuce kitchen, zama hajiya tayi a ranta tana juya wannan al'amari, kwata kwata Sameer yaƙi wayar mata da kai ya sakata a duhu yaƙi ya bata gamsasshiyar amsar da take buƙata, kiran da ya shigo wayarta ne ya katse mata tunanin da take yi, " Umaima....." "Hajiya kinji badaƙalar da Ruhaima tayi ko? Wallahi sai na yi mata rashin mutunci sai na nuna mata true color ɗina.... Ta rasa wa zata bi sai mijina?" Jin abin da Umaima ke faɗi yasa hajiya zaro ido cikin duburburcewa dan sam ma sai ta kasa fahimtar inda zancen ya dosa, " wai Umaima me kike faɗa hakane.... Meyake faruwa? " " Hajiya Sameer bai sanar dake abinda yake faruwa ba?? " " Bai sanar dani komai ba, kin ganshi shigowarshi kenan ya bani amsa a dunƙule yaƙi ya fayyace min komai...." Daidai lokacin Sameer ɗin ya shigo cikin falon riƙe da filet wanda ya zubo abinci aciki, jin abin da hajiya ke faɗa a waya ya tabbatar masa da Umaima suke waya, ji yayi ransa ya kuma ɓaci, bai zauna ba ya wuce ya fita shi koma maganar fa ya tsana baya son yaji ana sake maimaitata dan hakan sake ƙona ransa yake yi, wannan wacce irin fitina ce ke damun Ruhaima? Koda yake kusan haka yanzu gaba ɗaya zamanin ya koma, wasu matan ma suna da auren amma hakan bai hanasu bibiyar wasu mazan ba a waje, shi kansa ba dan kariyar ubangiji ba matan aure nawa ne suka kawo masa hari? Kasa cin abincin yayi saboda damuwa. In banda salati babu abinda hajiya ke yi jin labarin abinda ya faru da Umaima ta kwashe ta sanar da ita yanzu kamar yadda itama Alhaji sabo mijinta ya sanar da ita babu abinda ta ragewa hajiya ta sanar da ita komai, jiki a sanyaye kuma a mace hajiya ta kashe wayar bayan ta gama jin abinda ya faru, tabbas ta san Ruhaima tana da nutsuwa da kunya da halin ƙwarai to amma yanzu ba a shaidar mutum shine matsalar, mutum yana iya canjawa akoda yaushe sannan kowanne mutum tara yake bai cika goma ba, haka kuma wani abin ƙaddara ce wadda babu yadda mutum zai yi da ita, ita ta ɗauki Ruhaima tamkar ƴar da ta haifa ta cikinta ba wai sirika ba, duk abinda zata yiwa ɗan cikinta shi zata yiwa Ruhaima,wayarta ta sake ɗauka ta fara kiran layin Ruhaima, Jiki a sanyaye ta ƙarasa gaban handbag ɗinta ta ciro wayar ganin hajiya ce me kiran yasata jin kunyar duniya ta lulluɓeta ta san Sameer yaje ya sanar da ita halin da ake ciki, "Haba Ruhaima.... Ya ina yabon ki salla amma zaki kasa alwala.... Dan kina cikin wani hali Ruhaima sai ki kifara ƙoƙarin ɓata rawarki da tsalle?? Ai ko wani ne awaje Ruhaima bai dace ki kai masa kanki ba harda yunƙurin sata bare mijin Umaima....." "Hajiya dan Allah ki fahimceni ke kadai na san zaki fahimceni akan wannan lamari wallahi yanda ake tunani ba haka abin yake ba...." ta faɗa cikin kuka, "Wannan ai ya wuce Ruhaima sai dai a kiyaye gaba, dukkan ɗan adam ajizi ne amma ki kiyaye, dan Allah.... Ni tunda Sameer ya dawo naji yaƙi magana dama naji hankalina bai kwanta ba sai da Umaima ta kirani yanzu, Allah ya rufa asiri amma ki kiyaye dan Allah" daga haka taji hajiya ta katse wayar, take kuma wani kiran ya sake shigowa kamar dama jira ake, ganin Umaima ce sai da gabanta yai muguwar faɗuwa, "Hello inlaw....." "Karki fara... Karki kuskura ki sake kirana da haka Ruhaima... Ai baki ɗaukeni a hakan ba tunda har kike bibiyar mijina, dama wannan shine dalilin da yasa kika zo har gida neman sa?" "Dan Allah ki fahimceni Umaima, kema kin san wallahi ko a mafarki bazan taɓa aikata hakan ba...." "Daga yau sai yau wallahi babu ke babu mijina, idan kika sake yunƙurin kusantar mijina zaki gane shayi ruwa ne......" "Umaima karki bari shaidan ya shiga tsakaninmu dan All....." ƙitt taji Umaima ta datse kiran, wasu hawayen baƙin ciki ne suka sake ɓarke mata, daman ta san yanzu babu wanda zai yarda da ita kowa kallon mai laifi yake yi mata duk da irin kokarin da hajiya ke yi a kanta ace ta aikata haka ai da ta tabbata butulu, kukan nan dai shi take ta yi har tsawon wani lokaci da ita kanta bata sani ba. Samun kansa yayi cikin wani ƙarin ɓacin ran a duk sa'ilin da ya tuna wayar da yaji hajiya suna yi da umaima, wato Alhaji sabo sai da ya kwashe duk abinda ya faru ya fadawa umaima kenan saboda tsabar rashin kara, Meyasa bazai rufa mata asiri ba sai ya sake zubar mata da mutunci acikin family? Haushi ne ya kamashi ya ja tsaki, "Kawai salon ta jawowa mutane magana..... Sai da ta dauko mana magana dai hankalin ta ya kwanta" ya faɗa cikin ɓacin rai yana tashi daga kwancen da yake kan madaidaicin gadonsa, Kukan magensa ne ya sake tunzura shi, dan shi yama manta da ita, ba dan ya so ba ya miƙe ya buɗe ƙofa, yana buɗewa ta shigo tana shinshina ƙafarsa sunkuyawa yayi ya ɗauketa yana shafata, ganin tana lasar baki yasa shi dafe kai, "am sorry pretty.... Yau ban baki abinci ba sai sau ɗaya... Wallahi kaina ne a caje daren yau ɗinnan...." Saman gadonshi yaje ya ɗorata sannan ya fita, part ɗin hajiya ya sake komawa bai jima ba ya fito riƙe da glass cup cike da madarar kwali sai abinci a wani ɗan ƙaramin filet, part ɗinsa ya koma ya ɗauki magen ya ɗora akan cinyarsa ya soma bata abincin da madara tana ci,har ta cinye tas ya kwantar da ita kusa dashi, haka dama yake rayuwa da wannan magen wadda ya sakawa suna pretty tun tana yar ƙarama da ya tsinceta a lambun gidan ya ɗaukota, tare suke kwana. Da ƙyar ta samu bacci daren ranar dan sai bacci ɓarawo, bayan asubah ta samu ta farka, amma tana farkawa abinda yafara zuwa ranta shine abinda ya faru jiya, take ta ji wani sabon bakin ciki ya sake turnuƙeta sai da ta share hawaye sannan ta shiga bathroom ta ɗauro alwala tazo tayi salla, bayan ta idar ta ɗauki alqur'aninta dake ajiye gefe ta karanta abinda ya sawwaƙa sannan ta rufe ta soma azkhar. Wunin ranar gaba ɗaya acikin ɗaki tayi shi duk da dama hakan ɗabi'arta ce yanzu amma na yau kam kamar na dabanne, shigowar baba saude mai aikinta wadda yanzu ita kaɗai ta rage acikin ma'aikatan gidan dan duk sauran ta sallamesu tun jimawa,shigowarta ne yasa ta tashi zaune da koɗaɗɗun idanuwanta take kallon baba sauden, "Ruhaima... Lafiya kuwa yau duk baki fito ko falo ba? Ko wani wurin ke yi miki ciwo?" "Wallahi lafiya lau baba saude.... Kawai dai akwai abinda ke damuna" "Hakane.... Kowa ka gani dama akwai abinda ya dameshi sai dai hakuri, duk abinda yake damun bawa idan yayi hakuri zai wuce, na san kina cikin damuwa amma ki kara haƙuri akan wanda kikayi abaya Insha Allah ubangiji Allah zai baki mafita sannan yana tare dake a koda yaushe... Allah ya fiki sanin damuwarki Ruhaima kuma zai kawo miki ɗauki Insha Allah " Duk da bata bayyanawa baba saude damuwarta ba amma kalaman na baba saude sun samar mata da nutsuwa kuma sun sanyaya mata zuciyarta haka kuma sun rage mata wani kaso mai yawa daga cikin damuwarta, ƙwarin gwiwa taji ta sake samu akan ƙudurinta da kuma nufinta, Bata san lokacin da ta ɗauki wayarta ta kira hajiya ba, da sallama hajiya ta ɗauki wayar tata lokacin suna tare da Sameer acikin bedroom ɗinta yana kwance kan gadonta Ajmal yana kan ruwan cikinshi yana doki dashi, Saida ta gaida hajiya sannan cikin sanyin muryarta wanda ya gaurayu da damuwa tace "Hajiya dan Allah ina son magana da Umaima da Sameer da kuma ke harma da Alhaji sabo idan zai yuyu... Ma'ana dai ina so mu haɗu gaba ɗayanmu anan gidan ki kuma gabanki dan akwai wata sarƙaƙiya da nake son warwarewa....." "To shikenan Ruhaima amma ni da sai nake ganin idan har akan waccar maganar ce ta abinda ya faru da kin barshi..." "a'a hajiya a dai taimaka min a saurareni...." "to shikenan sai mu barshi asabar ko saboda kinga suna zuwa aiki...." "hakan yayi hajiya nagode Allah ya ƙara girma..." Sallama suka yi, ɗan tashi zaune Sameer yayi yana kallon hajiya, "me kuma ya faru?" "Ruhaima ke son Magana damu gaba ɗaya.... Ina jin zata koma gida ne amma dai bata faɗi hakanba kawai hasashe na ne..." "zata koma gida kuma? To amma hajiya ai bai kamata mu barta ta tafi ba..." ya fada cikin damuwa yana ƙarasa tashi zaune, "to ya za ayi Sameer? Bari dai lokacin yayi sai muji me take tafe dashi" Bai ƙara cewa komai ba ya tashi ya fita cikin damuwar dashi kansa bai san ko ta mecece ba, farfajiyar gidan ya fita ya samu ya jingina hannayensa cikin aljihun bakin trouser ɗin dake jikinsa..........✍🏻 *_Ummi Shatu_*👌🏻 [16/08, 7:32 am] Baby Aysher: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *SO DA ALAƘA...!* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ *Wattpad:@Ummishatu* Free page 6 ****Rasa abinda zai yi yayi sai faman zancen zuci yake ta yi shi kaɗai, "to ko maganar da na fada mata ne ta ɓata mata rai? Na faɗa mata wani abu mai zafi ne?" ya tambayi kansa yana kallon harabar gidan, "amma ni a iya sanina ai gaskiya na faɗa mata, bai kamata ta rinƙa ɗauko mana magana ba dan kawai tana missing mijinta...." ya sake bawa kansa amsa, "oho dai..." daga haka ya fita daga ma gidan baki ɗaya a ƙafa batare da ya ɗauki motar shi ba, sai dai duk da ya zurfafa tunaninsa ya kasa gano dalilin da yasa Ruhaima tace tana son ganinsu gaba ɗaya, tafiya yayi sosai acikin unguwar yana zagayawa daga ƙarshe ya yada zango a masallacin wani ƙofar gida dake da maƙotaka da unguwar tasu ganin lokacin sallar magariba yayi. Sai da yayi salla sannan ya koma gida, sashensa ya wuce kai tsaye yayi wanka sannan ya fito riƙe da magensa pretty, lokacin da ya koma part ɗin hajiya samu yayi Ajmal yana tv game a falon hajiya nan ya biyeshi suka yita yi tare kamar wani sa'ansa har saida Ajmal ɗin yayi bacci. Washe gari itace ta kama ranar da Ruhaima zata zo domin ganawa dasu kamar yadda ta roƙa, duk da tana cikin tsananin fargaba da da tsoro amma ta dake ta daure tana ta addu'a da haka ta shirya, navy blue color na leshi ta saka mai duwatsu ɗinkin riga da skirt, turare kaɗan ta ɗan fesa sama sama sannan ta kawo blue ɗin mayafi ta yafa, sam bata ɓatawa kanta lokaci ba wurin yin kwalliya domin ko mai bata shafa ba saboda a haƙiƙanin gaskiya bata cikin nutsuwa da farin ciki tun daga ranar da Alhaji sabo yayi mata wannan sharrin, Misalin ƙarfe 12 na rana ta isa gidan hajiya duk da dai gabanta sai faman faɗuwa yake, a falo ta tarar da hajiya da umaima wadda ko kallo bata isheta ba, duk sai ta sake jin babu daɗi ga kuma yaransu nan suna wasa tare wato su Abid tare da ɗanta Ajmal, daurewa tayi bayan ta gaisar da hajiya ta saki fuska tace, "umaima ina wuni?" Kamar ba zata amsa ba dan aciki ciki ta amsa gaisuwa, duk da hakan yayiwa Ruhaima ciwo amma sai ta basar ta danni zuciyarta, itama hajiya ganin haka yasata kiran Sameer awaya aganinta gara yazo su yi su yi abinda ya tarasu kowa ya koma gidansa bata son irin wannan zaman na doya da manja, Ita dai Ruhaima a ranta tunani take to ya taga umaima ita kaɗai? Ina mijin nata ko dai ba zai zo bane? Tana son ta sani amma babu damar tambaya, jin horn acikin gidan ya tabbatar musu da zuwan wani baƙon, "yawwa ga abbansu Abid ɗin nan ma ya ƙaraso hajiya" inji umaima, Wani sanyi Ruhaima taji acikin ranta, Zuwan Alhaji sabo yayi daidai da fitowar Sameer daga part ɗinsa, sanye yake cikin ƙananan kaya farar t shirt ta polo sai blue ɗin wando jeans, gaisawa suka yi da Alhaji sabo sannan ya jagoranceshi zuwa ciki, Bayan gaishe gaishe Sameer ya dubi hajiya wadda ke zaune ɗan gaba dashi kaɗan, "Hajiya Nifa inada uzuri.... Dan Allah ayi abinda za ayi" Kallonsa Ruhaima tayi ta ƙasan ido ita dai a rayuwa ta rasa me tayiwa bawan Allahn nan da bata burgeshi tsakaninta dashi ko yaushe sai harara sai ɗaure fuska sannan babu wata magana mai daɗi da take shiga tsakaninsu dan ko gaishe shi tayi tun lokacin da yayansa yana nan a ciki ciki yake amsawa kai kamar ma a dole yake amsawar dama kuma bama zuwa gidan nata yake yiba sai da ƙwaƙƙwaran dalili, "to ai Ruhaima ce ta taramu dan haka ita muke saurara...." maganar hajiya ta ratsa kunnuwanta nan ta dawo cikin hankalinta daga tunanin da take yi, gaba ɗaya kowa ita yake kallo kuma yake saurare banda Sameer wanda ko kallo bata isheshi ba dan wayar shi ma yake dannawa, shi kuwa alhaji sabo ido ya ƙura mata acikin ransa yana bakin ciki da takaicin rashin cikar burinsa yaso ya ɗanɗana kayannan yaji dan ya san zai samu cikakkiyar nutsuwar da yake so, amma yanzun ma bai haƙura ba kuma bai sare ba zai sake jarraba wata hanyar har sai ya dace, "Kamar yadda kowa ya sani, ni marainiya ce na taso cikin maraici, cikin babu......" "To sai me? Kowa ya san wannan, idan dan shi kika taramu muna da abin yi..." Sameer ya faɗa ta hanyar ɗaga mata hannu alamar dakatarwa, bata kula shi ba taci gaba da faɗin abinda take da niyyar faɗa, "Duk da na taso cikin babu, babu cin yau babu na gobe, babu suttura babu kayan ƙyale ƙyale ko more rayuwa hakan bai taɓa sani tunanin inyi sata ko in ɗauki abin wani ba, ban taɓa ji araina zan saci kayan wani ko in bada mutuncina dan in mallaki wani abu ba.... A koda yaushe kakata tana faɗa min cewa wadatar zuciya itace babban arziƙi koda mutum baida cin yau baida na gobe, nasha wahalar rayuwa iri iri a lokacin da nake tasowa saboda babu, amma haka na jure nayi hakuri har zuwa girmana, wallahi tallahi kayan wani ko dukiyar wani bata taɓa burgeni ba bare har inji araina zan iya ɗauka da sunan sata..... Abban Ajmal ya taɓa sanar dani sunyi haɗin gwiwa da Alhaji sabo wurin gina wani kasuwanci, nikuma a halin yanzu inada buƙatar kuɗi dan in gina rayuwar ɗana, lokacin da naje gida nemansa umaima tace yayi tafiya, ganin maganar ko a waya zan iya yi masa shiyasa na buƙaci da ta bani no wayarsa, shi da kansa yace bazan iya ganinsa ba a gida saboda yana da meeting amma zan iya samun ganinsa a guest house ɗinsa dan kusan gaba ɗaya harkokinsa yanzu acan yake gudanar dasu, wallahi zuciyata ɗaya na shirya naje ban taɓa tunanin wai da wata manufa ya gayyaceni can ba, lokacin da naje ya fito min da ƙudurinsa ban amince ba dan aganina wannan cin amana ne amma sai ya nemi da yayi min ta ƙarfi..... " wani kuka ne yaci ƙarfinta dama kuma tun lokacin da ta fara maganar hawaye ke bin kuncinta, duk jikin kowa yayi sanyi da kalamanta duk da wai basu gaskata cewa alhaji sabo yayi yunkurin yi mata fyaɗe ba, " Ta yaya zamu yarda da abinda kike faɗa? Kina da wata shaida?" umaima ta faɗa a kufule saboda jin abin da ake faɗa akan mijinta, yayin da shi kuma alhaji sabo kallon Ruhaima kawai yake yana tunanin ta inda yakamata ya soma wanke kansa ya sake ɗaureta sannan ya ɓatata a idon kowa, Handbag ɗinta ta buɗe ta ciro wayarta tana goge hawaye, "wannan itace maganar da muka yi awaya...." ta faɗa tana kunna recording ɗin da tayi, bayan duk an gama saurara ta sake kunna wani tana cewa "wannan shine abinda ya faru a guest house ɗinsa" Kowa nutsuwa yayi yana sauraren maganganun alhaji sabo wanda suke fita tar kamar yanzu yake yi, duk abinda ya faru tun daga zuwanta har lokacin da suka yi magana da mai gadi ya kirashi awaya har shigarta da yadda ya rinƙa hilatarta tana ƙi da kokawar da suka gwabza da komai kai har zuwan ƴansanda duk sai da kowa yaji, kunya ce ta lulluɓe alhaji sabo yaji kamar ƙasa ta buɗe ya shige dan tsabar kunya, bai taɓa jin kunya irin ta yau ba, da ya san wannan ranar zata zo tabbas da bai aikata abinda ya aikata ba, ita kuwa umaima kuka ta fashe dashi, babu wanda ya iya magana daga hajiya har Sameer, itama Ruhaima kukan take yi duk da bata so ta tona masa asiri ba amma bata da wani zaɓi illa hakan ko dan ta wanke kanta daga kallon da kowa ke yi mata, miƙewa tayi ta ciro kuɗin da ya bata dubu ɗari, ta ajiye a gabansa tace, "waɗannan sune kuɗin da ka bani.... Bani da buƙatarsu a yanzu, gashi na dawo maka dashi...." Shi dai alhaji sabo kansa na sunkuye a ƙasa gumi sai yanko masa yake tako ina saboda tashin hankali,ganin ta juya tana ƙoƙarin barin falon tana kuka umaima tace, " Ruhaima dan Allah ki yafe min.... Nabi daɗin bakin namiji na biyewa kishi idanuwana sun rufe na kasa fahimtarki... Wallahi koda wasa ban san mijina yana da irin wannan halin ba" tsayawa tayi cak tana sauraren maganganun umaima, kai kawai ta ɗaga mata alamun gamsuwa amma daga haka bata iya cewa komai ba ta fita daga falon tana share hawaye......✍🏻 *_Ummi Shatu_*👌🏻 [17/08, 9:41 am] Baby Aysher: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *SO DA ALAƘA....!* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ Free page 7 ***Ita kanta bata san a halin da take ciki ba ahalin yanzu dan ko shakka babu da za a tambayeta ba zata iya kwatanta yanayin da take ciki ba, baƙin ciki da farin ciki duk a lokaci guda duk da cewa dai baƙin cikin yafi yawa amma duk da haka taji daɗin yanda Allah ya kawo mata mafita har ta samu zarafin wanke kanta, dama ita gaskiya haka take duk daren daɗewa sai ta bayyana kanta sannan bata buƙatar taron dangi wurin bayyanarta saɓanin ƙarya, tana tafe tana share hawayenta har ta samu ta fita daga cikin gidan. Yanda Ruhaima ta fita ta barsu haka duk suke zaune kowa ya gaza koda ƙwaƙƙwaran motsi bama kamar ya alhaji sabo da gaba ɗaya yake jinsa kamar an dasa shi a wurin da yake zaune, shi yanzu koda magana zai yi baima san me zai ce ba, sannan ba zai yuyu ya tashi ya fita haka kawai ba tare da yace wani abu ba, bugu da kari baida koda kalma ɗaya da yake ganin zai iya amfani da ita wurin kare kansa, gaba ɗaya Ruhaima ta gama kunce masa zani acikin kasuwa, ta gama tona masa asirin da ya jima yana binnewa wannan fa shi ake kira da rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tak ta mai kaya, gaba ɗaya ilahirin falon yayi tsit baka jin komai sai shassheƙar kukan umaima wanda ya fara karaɗe falon, "wallahi ka cuceni.... Amma ka sani kaima ka cuci kanka kuma na gama zama da kai dan bazan iya cigaba da zama da mazinaci ba....." daga haka ta yi ciki tana rusar kuka bata ko sake bi ta kansa ba, Sameer kam kallonsa kawai yake a ƙule zuciya ta zo masa wuya amma dai bai yi magana ba dan ya san kome zai faɗa to ba mai daɗi bane a wannan lokacin shiyasa ya zaɓi yayi shiru, miƙewa ma kawai yayi ya fita, fitarsa babu jimawa itama hajiya ta shiga ciki ba tace da Alhaji sabo ko kanzil ba, nan ya sha zamansa ya gaji daga ƙarshe ya tashi yabar gidan. Yanda ta fito daga gidan hajiya haka taci gaba da tafiyarta tana kuka duk da masu napep na tsaya mata wai ko zata shiga amma sam bata tanka su dan bata jin zata hau abin hawa, tana dab da fita daga cikin unguwar su hajiya taji alamar mota a bayanta ko juyawa bata yi ba duk da uban horn ɗin da ya addabi kunnuwanta da ƙara, har ya ƙaraso kusa da ita bata kalli motar ba sai da ta jiyo sautin muryarsa, "Shigo in kaiki gida....." Cak! ta tsaya kamar mai nazari, wai shi wannan wanne irin murɗaɗɗen mutum ne? Salon ta shiga yau ma ya yaɓa mata duk maganar da tazo ransa? Daurewa tayi ta zagaya ta buɗe gaban motar ta shiga, Tun bayan shigowarta taji ƙamshin turarensa wanda ita dai zata iya cewa tun ranar da ta fara ganinsa taji wannan ƙamshin kuma har yau bata ƙara jinsa awurin wani ba, Shiru motar tayi kamar babu kowa aciki wanda har hakan saida ya takurata, shi ɗinma kamar kusan hakan ƙila ma wannan dalilinne ya sanya shi kunna radion dake maƙale cikin motar, daga ita ita har shi ba wani sauraren radion suke yiba, ɗan satar kallonsa tayi ta gefen ido, fuskar shi yau babu yabo babu fallasa saɓanin irin yadda ta saba gani ko yaushe, a fisge dai yana yi mata kama da Imran sosai sai dai akwai ta inda suka bambanta da yawa, shi Imran fari ne dan za a iya saka shi cikin layin farare amma Sameer baƙi ne bawai chocolate color ba a'a baƙine sosai amma duk da hakan tana mamakin yadda mutane tun ba yanzu ba suke faɗin kyawun Sameer fiye da na Imran koda yake ita bata taɓa tsayawa tayi masa kallon ƙurulla ba sai dai ta kalleshi a sace shi ɗinma sau ɗaya take bata ƙarawa, amma dai ta san yanayin tsayinsu da jikinsu kusan duk iri ɗaya ne dan yanda Imran yake a tsaye shima haka Sameer ɗin yake sannan wani abu dake sake ruɗata shine muryarsu kusan iri ɗaya dan duk lokacin da taji yayi magana sai taji kamar Imran ne yayi, Har suka isa gidanta babu wanda yace uffan, bayan yayi parking tana ƙoƙarin fita yayi ta maza wurin dakatar da ita bayan ya gama tattaro juriyarsa wuri guda dan shima kunyar ta yake ji na maganganun da ya fada mata ba tare da taunawa ba, "amm.... Dama nace.... Kiyi haƙuri da abinda ya faru ranar nan..... Raina ne a ɓace shiyasa...... Kiyi hakuri" "babu komai.... Ya wuce" daga haka ta fita ta rufe masa ƙofar motar, bai tafi ba saima fita da yayi domin yin sallar azahar yabar motar tashi nan cikin gidanta. Ita dai ciki ta shiga bata sanma yabar motarshi a gidan ba, ko ba komai yau dai ta samu nutsuwa cikin ranta sannan ta samu sauƙin halin da take ciki, alwala tayi tai salla bayan ta idar ta yiwa Allah godiya da ya kubutar da ita sannan kuma ya wanketa daga zargi, tana zaune kan abin sallar taga kiran mukhtar ya shigo cikin wayarta, mukhtar wani matashin magidanci ne dake rike da matsayin manager na wani babban store wanda yayi suna sannan yake kan shura har yanzu cikin wannan jaha mai albarka, tunda ya ƙyalla ido ya ganta lokacin da suka je shopping ita da Ajmal yabi ya liƙe mata, a zahiri dai ta san ba shida makusa duk da bai kai tsohon mijinta ba amma shi dinma zata iya sakashi sahun mazan ƙwarai sai dai da yake zahiri daban sannan baɗini daban haka kuma mutane yanzu sanin haƙiƙanin waye su sai ubangiji domin shi kaɗai ne masanin sirrin ɓoye da fili, ji tayi har cikin ranta ta gamsu da mukhtar yanzu sannan tana ganin lokaci yayi da zata bashi dama su sasanta su fahimci juna har su kai ga aure tunda dai yana mutuƙar ƙaunarta, gara dai kawaima tayi auren nan ta huta ko ba komai igiyar auren zata tare mata abubuwa da yawa, ayanda dai ya faɗa mata matarshi ɗaya wacce ta kasance cousin ɗinshi ce domin auren zumunci suka yi sai yaran su guda biyu mace ɗaya namiji ɗaya suna zaune a unguwar court road, Da sallama a bakinta ta ɗauki wayar, ita sam bata saba da irin wannan hirarrakin ba da samari tun farko balle yanzu da take zawarci duk dai take jinta wata iri kamar sabuwar Ruhaima bawai waccan Ruhaiman ta asali ba, wani lokacin ma kunya ce ke hanata sukuni bare har ta tsaya ta saurari bazawari sai ta jita duk a takure dan bata saba ba, kai zata ma iya cewa tun tasowarta har tayi aure bata taɓa tsayawa da saurayi ba har shi kansa Imran ɗin basu taɓa tsayawa dashi ba, jin amsar da ta bashi wacce ya jima yana jira daga gareta ai bai san lokacin da yace mata gashi nan zuwa yanzu ba, murmushi kawai tayi ta kashe ranta acikin ranta amma wani irin raɗaɗi da ciwo take ji,tabbas babu abinda yafi mutuwa ciwo kuma a rashin uwa akanyi uwar ɗaki, ko a mafarki bata taba zaton irin wannan lokacin zai risketa ba domin ta gama shirya rayuwarta gaba ɗaya da mijinta amma da yake kana naka Allah na nashi sai gashi rayuwar ta juya mata, haƙura tayi da wannan zancen zucin da take ta tashi ta shiga wanka ta soma shiri, bata yi doguwar kwalliya ba amma dai ta shafa powder da kwalli sai man leɓe, baƙar doguwar riga ta saka ta yafa ƙaramin mayafin rigar akanta bayan ta saka pink ɗin hula mai ƴar tuta wacce aka yi ta kwalliya a jiki, turare ta ɗan feffesa sannan ta fita, kitchen ta wuce ta tsaya tana haɗa masa ɗan kayan motsa baki, fruits ta yanyanka sai drinks masu sanyi ta haɗa ta ɗauka ta fita, hakan yayi daidai da zuwan baƙon, a kunyace ta shigo dashi duk ta gagara sakewa shikuma sai faman kallon ta yake kamar yaga wata sabuwar halitta, "yanzu dama ranki ya daɗe za a bani wannan damar amma shine aketa faman ja min rai? Yanzu to me kike shirya mana? Ina nufin zuwa nan da yaushe kike ganin yadace a ɗaura aure?" ya tambaya cikin zumuɗi yana kurɓar juice ɗin dake hannunsa, "wannan kuma ai a hannunka yake Kaine zaka faɗa" ta faɗa cikin kunya kanta yana ƙasa tana wasa da ƴan ƴatsun hannunta, "ni ai ko yanzu kika ce nima a shirye nake sai in bada sadaki kawai a ɗaura aure..." Murmushi tayi ta ɗan sake ƙasa da kanta kafin tace "Ahh da wuri haka?" "to ai ni ba wasa nazo yiba Ruhaima.... Idan har kin amince ko nan da sati biyu sai kawai a ɗaura aure" "to bari dai mu ga abinda hali zai yi, zamu shawarta da manyan mu gani" ita kanta bata san dalilinta na faɗar hakanba, Gaba ɗaya bata sake dashi ba shiyasa hirar sama sama suka yi ya tashi zai tafi dan dama daga office yake kuma office ɗin zai koma, bin bayansa tayi domin yi masa rakiya, suna tafe suna ɗan sake tattaunawa duk da ita dai babu abinda take cewa sai dai murmushi, shigowar Sameer ce tasa duk hankalinsu ya koma kansa, shima daga nesa yake kallonsu dan lokacin da yaje salla can tsallake sai ya gamu da wani abokinsa wanda suka yi B. U. K tare shine suka jima tare suna hirar yaushe gamo sai yanzu suka rabu bayan sunyi exchanging contact ɗin juna,itama Ruhaima da mamaki akan fuskarta take kallonsa tana tambayar kanta wai dama wannan bai tafi ba?, "shi kuma wancan waye?" Tambayar da mukhtar yayi mata ta katse mata tunaninta, "Ƙanin abban Ajmal ne...." ta bashi amsa tana kawar da kallon ta daga kan Sameer wanda ya nufi motarshi rannan a cunkushe, "ayya Allah sarki.... To yayi bari in wuce" ya faɗa yana ƙwallawa mai gadi kira, nan ya taso a sukwane ya buɗe masa bayan mota ya soma fito da kaya kamar da gangan to masu abu da abunsu duk abinda ke faruwa akan idon Sameer wanda ke zaune yana cikin motarsu yana kallonsu ta mirror, ita dai juyawa tayi ta koma ciki yayin da mai gadi ya rinka shigar mata da kayan wanda duk na ciye ciye ne sai ko na shafe shafe da sabulan wanka, gel, da man wanke gashi da sauran tarkace irin na amfanin mata, akan idon Sameer mukhtar ɗin ya fita saida yaga fitarsa sannan ya fita daga motarsa yashiga ciki wanda rabonshi da shiga har ya manta, yana shiga da kayayyakin yafara arba a falo gasu nan kamar za a kasa a siyar dan yawa duk ledodin da kayan suke ciki suna ɗauke da tambarin store ɗin na su mukhtar, idonsa ne ya kai kan wata leda wadda ta tintsire nan ya hango tissue da pad, "harda waɗannan abubuwan ya kawo mata? Wannan ai iskanci ne...." ya faɗa acikin zuciyarshi amma har lokacin idanuwanshi na kan ledar, sam bata san shigowarshi ba ta fito da zummar ganin kayan arziƙin da mukhtar ya kawo mata bayan ta tuɓe doguwar rigar da ta saka ta sake saka ƙaramar riga marar nauyi iya gwiwa kanta ko ɗan kwali babu, tana fitowa tayi arangama dashi tsaye ya riƙe ƙugunsa.............. _*Ummi Shatu*_👌🏻 [18/08, 9:08 am] Baby Aysher: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *SO DA ALAƘA......!* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ TAURARI HUƊU Free page 8 ***Duk da ta san yaganta dan harma haɗa idanuwa suka yi ƙarewa amma hakan bai hanata komawa ba da baya da baya, cikin bedroom ɗinta ta shiga gabanta yana faɗuwa to shi wannan bawan Allahn me kuma ya sake dawowa yi? Wani dark blue ɗin dogon hijabinta ta ɗauka ta saka sannan ta sake fita, yana nan tsaye inda ta tafi ta barshi yanzun ma fuskarsa babu annuri ko kaɗan, "waye wancan da ya fita?" taji ya tambayeta ba tare da ya kalleta ba, "baƙona ne...." ta bashi amsa acan ciki, "ehh dama na san baƙonki ne.... Me yazo yi? Sannan wannan kayan kuma na menene?" ya sake tambayarta har lokacin idanuwanshi na kan kayan, Shuru tayi masa bata amsa ba dan gaba ɗaya tambayoyin nasa sun fara bata haushi da ɓata mata rai, ya za ayi yazo ya wani tisata a gaba da tambaya yana titsiyeta kamar wani wan miji alhalin shi ƙanin miji ne, "waɗannan kayan ki faɗa masa ya zo ya kwashe kayansa...." Juyawa yayi ya fita bai jira amsarta ba kamar ya san dama bata da niyyar bashi amsar, zama tayi tabi bayanshi da kallo har ya fice mintuna kaɗan taji alamar fitar motarshi daga cikin gidan, tuɓe hijabinta tayi a ranta tana tunanin maganar da ya faɗa wai mukhtar yazo ya kwashe kayansa tab ai abinda bama zai taɓa yuyuwa ba kenan, kowacce leda sai da ta buɗe taga abubuwan da ke ciki daga bisani ta shisshigar dasu ciki kowanne ta kaishi inda yadace ta adana. Driving yake amma hankalinsa na kan Ruhaima sufa mata zurfin tunaninsu kaɗanne shiyasa babu wahala an yaudaresu ko anyi musu wayo, abu kaɗan ke jan ra'ayinsu har su amince da mutum su bashi yarda ɗari bisa ɗari alhalin da yawa da suke yiwa kallon masoya ba masoyan nasu bane wanda suke kallon sune maƙiyansu a haƙiƙanin gaskiya sune masoyan nasu, Bayan la'asar ya isa gida, sai da yaga umaima sannan ya tuna da abinda ya faru, shifa wallahi ko tuna maganar nan ma baya son yi bare maimaitata, bece uffan ba kan lamarin ya nemi wuri ya zauna yana kallon hajiya wacce ke yankewa Ajmal farce, "hajiya nace ya dace a saka yaron nan a makaranta....." Dakatawa daga abinda take yi hajiyan tayi ta zuba masa ido na ɗan wasu lokuta sannan tace "wannan tunani ne mai kyau Sameer.... Ni ɗinma abin yana raina dama kuma mune muka fi dacewa da cancanta wurin kula da gina tarbiyarsa ba wai iya mahaifiyarsa ba, mune zamu tallafa mata har ta cimma burinta wurin gina tarbiya da rayuwarsa..... Allah yayi maka albarka, wacce makaranta kake ganin ya dace a saka shi? " " Amin hajiya..... Akwai wata nan kusa sai akaishi " " to Allah ya bada sa'a " Farin ciki yaji yana mamaye ilahirin zuciyarsa sakamakon ganin irin farin cikin da Ajmal ɗin ya shiga jin za asakashi a makaranta dan har ya garzaya ya tafi sanar dasu Abid. Daren ranar ya ɗauki Ajmal suka tafi shopping duk wani abu da ya san yaron zai buƙata ko mahaifiyarsa sai da ya siya daga nan suka wuce wurin Ruhaima, bai shiga ba iya Ajmal ɗinne ya shiga sai ko kayan da ya sissiyo musu wanda ya barwa mai gadi ya shigar mata dashi, Tana kwance falo kan kujera lokacin da Ajmal ɗin ya shigo, cemata yayi wai shi da uncle ne bakinsa ta ɗan mara kaɗan tace, "Daddy ne ba uncle ba, na faɗa maka daddy zaka rinƙa ce mishi...." "yace zan fara zuwa school" Murmushi tayi ta tashi zaune jin alamun buɗe ƙofa, ganin mai gadi da kayayyaki niƙi niƙi ya sata kallon Ajmal, "ina kuka fara zuwa kafin ku zo nan?" "shopping...." Ba tace komai ba ta karɓi kayan duk da ta san ba dan ita yayi ba sai dai ko dan ɗan ɗan uwanshi,miƙewa tayi ta leƙa window nan ta hango shi tsaye shida mai gadi ko me suke cewa oho sai su sai Allah, yana sanye da ƙananan kaya jar t shirt da baƙin wando, komawa tayi ta zauna bata sake jin ɗuriyarsa ba dan bata ma san lokacin da ya tafi ba saboda ko shigowa baiyi ba. Haka ta kwana zuciyarta cunkushe da tunani kala kala, ta saka wancan ta kunce, duk ta rasa me ma ya dace tayi kan maganarsu da mukhtar, ita dai ta san ba wai sonshi take ba to ita yanzu ma ai babu batun wata soyayya a gabanta kawai dai zata yi aure ne aure irin na rufawa kai asiri bawai dan soyayya ba sannan har yanzu ta kasa jin nutsuwa a cikin ranta na ta amince ko karta amince, daren ranar dai sai bacci ɓarawo amma tajima tana juye juye. Washe gari da safe misalin ƙarfe 11 ta gama shirya Ajmal bayan itama ta shirya cikin atamfa super Holland coffee color, ɗinkin riga da skirt ne, yau tunda garin Allah ya waye mukhtar ke faman turo mata saƙonni, jin yace wai yana nan zuwa anjima ya sata yin murmushi tare da mayar masa da amsa cewa unguwa zata je, kamar jira yake sai ga kira, a ƙagare ta ɗauka don kunya take ji duk sai ta rasa me zata ce, "ayi min alfarma in zo inyi rakiya...." Ɗan jim tayi kafin ta bashi amsa "ba wai naƙi bane amma...." "dan Allah kar akatse min hanzari sannan kar a sace min gwiwa.... Idan kika ce a'a bazan ji daɗi ba" "to shikenan sai ka zo...." Sallama suka yi ta katse wayar tana jin aranta hakan bai dace ba, ta yaya zai kai ta gidansu abban Ajmal? Idan taƙi kuma shi yaji babu daɗi yaga kamar ko tana ɓoye masa wani abune, ita kuma zuwan nan da zata yi ma zata yi shi ne dan umaima so take taje ta rarrasheta tayi haƙuri ta koma ɗakin mijinta ko dan farin cikin yaranta, Ita dai gaba ɗaya a ɗarare take da mukhtar ko hirar ma da Ajmal suke yi ita dai kunnene nata, har suka ƙarasa gidan hajiya maganarta bai fi a ƙirga ba, a waje ya ajiye su suka shiga shikuma ya tafi,iya hajiya kaɗai suka samu a falo ta gama karyawa bayan sun gaisa ta wuce bedroom wurin umaima, ganinta tayi kwance kamar marar lafiya duk idanuwanta kumbure saboda kuka, Zaune ta tashi tana kallonta fuskarta asake, "in law kune kuke tafe?" "in law ai ni fushi nake.... Ya za ayi ki ɗauki abu da zafi har haka? Wannan hukuncin da kika ɗauka baiyi ba gaskiya, kiyi haƙuri ki share komai ki koma gidanki..." Ido umaima ta zuba mata har na tsawon wani lokaci kafin ta girgiza kai tace, "Ruhaima kin san kuwa abinda nake ji? Kin san irin baƙin cikin da zuciyata ke ciki? Miji irin wannan babu amfanin cigaba da zama dashi..." "wallahi na san yanda kike ji in law.... Karki faɗi haka, kiyi haƙuri ki koma gidanki kicigaba da addu'a Insha Allah wata rana sai labari.... Abubuwa da yawa kana haƙuri dasu ne kana shanyewa ba wai dan kanka ba a'a sai dan yaranka kar su shiga wani hali... " Haka tacigaba da yi mata kalamai da faɗa mata maganganu masu daɗi har ta sauko ta yadda zata koma amma wai sai ta huta, dariya Ruhaima tayi tace hakanma ta gode, suna ƙule a ɗaki tana sanar da ita maganar mukhtar da kuma irin yanda ya matsa shi so yake ayi biki cikin ƙanƙanin lokaci har azahar tayi sai da hajiya ta aiko Abid wai yazo ya kira su suje suci abinci, fita suka yi suna dariya, hajiya suka hango saman dining kusa da ita Sameer ne suna cin abinci tare a faranti ɗaya, "a'a yau ma ƙaunar ce ta motsa kenan..." umaima ta fada tana dariya, "to ai dama koda yaushe wannan ƙaunar tana nan" hajiya ta bata amsa, ita dai Ruhaima ba tace komai ba, haka in banda gaisuwa babu abinda ya haɗasu da Sameer itama sama sama suka gaisa dan ta kula sai faman haɗe girar sama da ƙasa yake,a falo taja birki ta zauna nan umaima ta kawo musu abincin, jalop ɗin shinkafa da ɗanyen kifi amma su kuma su hajiya taga kamar macaroni suke ci, "kin san shi waccan patient ɗin baya cin kifi....." umaima ta faɗa lokacin da suka fara cin abincin, "kuma ko ansaka bai ganiba sai ya gane?" "ai tun daga nesa zai jiyo dan jaraba..." Dariya suka yi gaba ɗaya atare hakan ya janyo hankulan su hajiya gaba ɗaya ya dawo garesu, "ya aka yi kuma?" hajiya ta buƙata, "hajiya in law ta samu bazawari, yanzu maganar aure ake" Tunda yaji abinda umaima tace ya sake ɓata rai, ita kuma Ruhaima ji tayi kunya ta kamata. Tamkar wanda ya ƙware take ya soma tari mai rikitarwa harda faɗowa daga saman kujerar da yake zaune a kai, nan fa hankula suka tashi musamman na hajiya dan tafi kowa sanin irin baƙar azabar da yake sha a duk lokacin da wannan lalurar tashi ta motsa, "yaya Sameer..... Yaya Sameer attack ka samu?" Umaima ta faɗa cikin tashin hankali, kai kawai ya iya ɗaga mata yana kokawa da numfashinsa wanda ke ƙoƙarin yankewa......... *HASKE! HASKE!! HASKE!!!*💡 IT'S *HASKE WRITERS*💡AGAIN THE HOME OF EXPERTS AND PERFECT WRITERS ✍🏻 HAƘIƘA JIMIRIN ZAMAN JIRA YA ƘARE MASOYA DOMIN ƘUNGIYARKU MAI FARIN JINI TA AMANA WATO *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 ITACE TA MOTSO KUMA TA DAWO DAN NISHAƊANTAR DAKU KAMAR YADDA TA SABA, *TAURARI HUƊU* SHINE TAKEN TAFIYAR TAMU A INDA ZAMU GABATAR MUKU DA FASIHAI, HAZIƘAN MARUBUTA GUDA HUƊU DA ALƘALIMANSU CIKIN TAFIYAR DA BABU NADAMA ACIKINTA, *1.AYUSHER:-* Writing by FERTYMERH XARAH *2.ƘAZAFI NE:-* Writing by RAHAMA NALELE *3.DA UBA AKE ADO (Bada riga ba):-* Writing by ZAINAB BAWA *4 SO DA ALAƘA:-* Writing by UMMI A'ISHA WAI WAI WAI... 🔥BAHAUSHE YAYI GASKIYA LALLAI TAFIYA DA GWANI MAI DAƊI, NIMA DAI GA NAWA GWANAYEN 4 STARS DUKKA WAƊANNAN LITTATTAFAN GUDA HUƊU ZAKU SAMESU CIKIN FARASHI DAIDAI DA ALJIHUNKU....MY SISTER WHAT ARE YOU WAITING FOR?? MAZA HANZARTA KI GARZAYA KI NEMI NAKI DAN ZASU FARA NAN BADA JIMAWA BA, KAR KI BARI A BAKI LABARI..... COMING TO YOUR WAY SOON, DON'T MISS IT 😘😘 Guda 4:- 1500 Guda 3:-1200 Guda 2:- 800 Guda 1:- 400 7033027658 Palmpay Bank Aisha Muhammad Salis Katin wayar MTN ta... 07044644433 da shaidar biya *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 _*Ummi Shatu*_👌🏻 [19/08, 7:47 am] Baby Aysher: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *SO DA ALAƘA......!* *NA* *UMMI A'ISHA* TAURARI HUƊU free page Wattpad:@Ummishatu 9 ***Da taimakon umaima da na hajiya ya samu ya kai ga kan gadon hajiya domin bedroom ɗinta shine mafi kusa daga inda ya samu attack ɗin, Ita dai Ruhaima gaba ɗaya ji tayi tausayinsa ya kamata lokaci guda, ita dai ta san sau da dama Imran ya kan ce mata Sameer ne baida lafiya ko kuma yasamu attack amma idanuwanta basu taɓa gani ba sai yau, wani irin kai komo taga numfashinsa nayi, lallai in dai hakane masu irin wannan lalurar suna buƙatar tsananin kulawa ta musamman, Yanda su hajiya suka ruɗe ita ɗinma a ruɗen take dan jikinta gaba ɗaya in banda karkarwa babu abinda yake yi. Hankula basu kwanta ba har sai da aka yi masa allura bayan an kira likita, bacci ya ɗan samu na tsawon wani lokaci, Tagumi Ruhaima tayi tana kallon umaima wacce ke cin abincin da suka bari, ita kam gaba ɗaya tama kasa ci, "wai in law dama haka yake fama da wannan ciwon?" "wallahi in law... Kuma kinga shi kaɗai keda shi duk familynmu,ƙaddara dai kawai" "Allah sarki, Allah ya bashi lafiya ya yaye masa, amma maganin ba ayi masa na hausa?" "amin, ana yi mana ai yanzu ne ma hajiya ta ɗan lafa amma ada duk inda taji mai maganin hausa ko aka ce wannan maganin asthma ne sai ta karɓowa Sameer, tazo su yi ta daru shi baya son maganin hausa amma haka zata tsare shi sai ya sha" "to Allah ya bashi lafiya yasa a dace" "amin" Tashi tayi ta sake leƙawa bedroom ɗin hajiya dan ganin halin da yake ciki dan ita wallahi haka kurum taji ya bata tausayi, wannan shine leƙawarta na wurin biyar tun bayan da ya samu bacci, har yanzun bacci ta ganshi yana yi ya wani ƙanƙame jikinsa wuri guda kamar mai jin sanyi, fita tayi ta koma wurin umaima wadda har lokacin bata gama cin abincin ba, "wai in law dagaske ba zaki ƙara abincin nan ba?" "wallahi duk ya fita a kaina inlaw" Dariya kawai umaima tayi ta san dan ruɗewa ta ruɗe amma kuma kamar Ruhaima ta fita ruɗewa tunda gashi ko abinci ta gagara ci, sannan mintuna kaɗan sai taje ta gano halin da yake ciki da haka har la'asar tayi, sake shiga ɗakin tayi bayan ta idar da sallar la'asar yana zaune kan gadon hajiya ya tashi daga baccin ya ziro ƙafafuwansa ƙasa yana shirin saukowa ta shiga, bata yarda sun haɗa ido ba duk da dai taga bai kalleta ba dama, tsaye tayi ta kasa yi masa magana kamar yadda shima baiyi ba, ganin ya tashi ya shiga toilet yasa itama ta fita daga cikin ɗakin, ganin umaima bata idar da sallar da ta tafi ta barta tana yi ba yasa ta komawa falo, wayarta ta ɗauka wadda ta isheta da ƙaraji tun ɗazu kuma ta san maganar gizo dai bata wuce ƙoƙi bazai wuce mukhtar ba domin shine ke addabarta da masifar kira yanzu tun daga lokacin da ta bashi dama, saka wayar tayi a silent bayan kiran ya katse ta mayar da ita cikin handbag. Ita kanta bata san takamaimai me take tunani ba sannan ta rasa wanne irin tausayi take ji game da Sameer, a iya saninta dai babu wata shaƙuwa ko kulawa tsakaninsu in ka cire ƴar shan ƙamshin dake wanzuwa tsakaninsu tun daga ranar da ta fara ɗorashi a idon ta har kawo yanzu, fitowar shi ce ta katse mata tunanin da take yi game dashi nan tayi ƙasa da idanuwanta kamar yadda ta saba gudun kada asamu rashin dace su haɗa idanuwa, sai da ta tabbatar da ya wuce sannan ta ɗago tabi bayanshi da kallo lallai babu abinda ya kai lafiya, duk abinda mutum zai yi ko zai samu sai da ita, tunani tayi a ranta tunda har taga marar lafiyar ya tashi ai gara itama ta tattara sawunta a likkafa ta koma inda ta fito dan dama anan ɗin a takure take a duk lokacin da akace yana nan, shiyasa da mukhtar ya kirata tace yazo su tafi kamar yadda ya buƙata amma yace sai yayi sallar magrib, bata sake saka Sameer a idonta ba har lokacin da suka fito zasu tafi, Shi kuwa Sameer duk abinda yake faruwa akan idonshi sune basu ganshi ba amma shi yana hangosu daga inda yake zaune cikin motarsa wacce ke ajiye cikin farfajiyar gidan, a ransa kawai sake jaddada taurin kan Ruhaima yake, yayi mata hannunka mai sanda akan mutumin nan, yayi mata wanka mai kama da jurwaye akan mutumin nan amma duk a banza dan tsabar jaraba ta toshe kunnenta, ko idan sunyi auren me wannan mutumin zai bata oho, tsaki yaja ya cigaba da daddanna wayarsa, shi bashi ma ko lambar wayarta kuma ya dace ace yana da ita fa, "me zanyi da no dinta ma" ya fada cikin zuciyarsa kamar da wani ne yace sai ya mallaka, akan idonsa suka bar gidan wanda bai wuce dasu gida direct ba sai da yafara biyawa da ita wurin wani gashin kaza yayi musu take away sannan ya mayar da ita gida, ita dai ta gama amincewa zuciyarta cewa kawai zata yarda ta auri mukhtar ba wai dan tana sonsa ko tana ƙaunarsa ba, ba kuma wai dan yayi mata ba a'a kawai dai halayensa sunyi mata dan mutum ne mai haƙuri da rashin fushi sannan ga barkwanci da fara'a, Lokacin da tayi shirin bacci sai taji ta gagara domin babu abinda take tunawa a wannan lokacin sai halin da Sameer ya kasance ɗazu, ko yanzu yana cikin wanne hali oho? Ko ya samu yayi bacci ko kuma har yanzu yana cikin damuwar ciwon Allahu a'alamu, Ajmal ta rungume wanda ke gefenta yana bacci, a can ƙasan zuciyarta kuma tana yi masa addu'ar rabuwa da wannan ciwon rabuwa ta har abada. Shima Sameer a nasa ɓangaren lokacin da ya hau kan gadonsa domin yin bacci ji yayi Ruhaima ta faɗo masa gaskiya ya zama dole ya sanar da hajiya yakamata a tattaro Ruhaima ta dawo gidan nan ko dan kare mutuncinta da darajar ta, yanzu tana can tana rayuwa ita kaɗai sannan ta baiwa wani fuskar da zai je mata hira gida tofa komai zai iya faruwa yanda mutane yanzu basu da tabbas, shi tausayi ɗaya take bashi idan ya tuno irin yanda tayi sabo da mijinta yanzu kuma tazo ta rasa shi, lumshe idanuwanshi yayi amma ya san bacci kam ba yanzu ba, wani ɓangaren na zuciyarshi kuma alla alla yake gobe tayi domin yaje ya sauke nauyin da yake kan shi. Kasancewar bata yi bacci da wuri ba shiyasa ta kasa tashi dan sai bayan da tayi sallar asuba sannan ta samu bacci, shima Ajmal ɗin da ya saba tashi da wuri har ya dameta yau bai tashin ba bare ya hanata rawar gaban hantsi,baccinsu suke kamar za a sake yi musu wani daren. Agogon hannunshi ya kalla misalin ƙarfe 10 har da rabi na safe agogon ya nuna masa, sake gyara tsayuwarsa yayi yana tunani a ransa to ko dai sun fita ne? To amma tayaya zasu fita ba tare da maigadi ya sani ba? Maigadi ya tabbatar masa da suna ciki, ƙofar falon ya sake zuwa a karo na huɗu ya ɗan bubbuga, cikin bacci taji muryar Ajmal yana cemata, "mommy inje in buɗe? Ƙofa ake bugawa" "uhmmm jeka" ta faɗa tare da sake jan bargo dan jin maganganun Ajmal ɗin take yi kamar a mafarki, da gudu ya sauka daga kan gadon ya fita, saida ya jima yana murɗe murɗe sannan ya buɗe, ganin Sameer tsaye hannayensa cikin aljihun wandonsa yayi saurin rungumeshi, ɗaukarsa Sameer yayi yana kallonsa dan ya fahimci daga bacci ya tashi, falon yake bi da kallo ganin komai a karkashe alamar itama Ruhaiman bata fito ba, wuri ya samu ya zauna yana gyara zaman face mask ɗin dake fuskarshi dan tun jiya numfashinsa babu ƙarfi, Kimanin mintuna 15 ya shafe zaune a falon amma babu ko motsinta kai babu ma ko alamar cewa zata fito hakan yasa shi duban Ajmal dake lilo akan ƙafafunsa, "mommy bata da lafiya ne?" "uhmm.... Uhmmm...." Kasa gane amsar da Ajmal ya bashi yayi, ehh yake nufi ko a'a? Cikin azama ya miƙe shi kansa bai san lokacin da ya tashin ba yana tambayar Ajmal tana ina? Tiryan tiryan yake biye dashi har cikin bedroom ɗinta inda take kwance tana bacci...... *HASKE! HASKE!! HASKE!!!*💡 IT'S *HASKE WRITERS*💡AGAIN THE HOME OF EXPERTS AND PERFECT WRITERS ✍🏻 HAƘIƘA JIMIRIN ZAMAN JIRA YA ƘARE MASOYA DOMIN ƘUNGIYARKU MAI FARIN JINI TA AMANA WATO *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 ITACE TA MOTSO KUMA TA DAWO DAN NISHAƊANTAR DAKU KAMAR YADDA TA SABA, *TAURARI HUƊU* SHINE TAKEN TAFIYAR TAMU A INDA ZAMU GABATAR MUKU DA FASIHAI, HAZIƘAN MARUBUTA GUDA HUƊU DA ALƘALIMANSU CIKIN TAFIYAR DA BABU NADAMA ACIKINTA, *1.AYUSHER:-* Writing by FERTYMERH XARAH *2.ƘAZAFI NE:-* Writing by RAHAMA NALELE *3.DA UBA AKE ADO (Bada riga ba):-* Writing by ZAINAB BAWA *4 SO DA ALAƘA:-* Writing by UMMI A'ISHA WAI WAI WAI... 🔥BAHAUSHE YAYI GASKIYA LALLAI TAFIYA DA GWANI MAI DAƊI, NIMA DAI GA NAWA GWANAYEN 4 STARS DUKKA WAƊANNAN LITTATTAFAN GUDA HUƊU ZAKU SAMESU CIKIN FARASHI DAIDAI DA ALJIHUNKU....MY SISTER WHAT ARE YOU WAITING FOR?? MAZA HANZARTA KI GARZAYA KI NEMI NAKI DAN ZASU FARA NAN BADA JIMAWA BA, KAR KI BARI A BAKI LABARI..... COMING TO YOUR WAY SOON, DON'T MISS IT 😘😘 Guda 4:- 1500 Guda 3:-1200 Guda 2:- 800 Guda 1:- 400 7033027658 Palmpay Bank Aisha Muhammad Salis Katin wayar MTN ta... 07044644433 da shaidar biya *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 *_Ummi Shatu_*👌🏻 [20/08, 11:53 am] Baby Aysher: ©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION* 4 stars...... *SO DA ALAƘA.....!* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ Wattpad :@Ummishatu Last free page 10 ***Sake juyi tayi lokacin da taji Ajmal yana kiranta bayan ya hayo kan gadon "mommy.... Mommy" Bata amsa ba sai ma sake jan bargo da tayi amma kamar acikin mafarki sai kuma ta fara jiyo amon muryar Sameer, "bari tashinta Ajmal.... Daina...." ya fada yana bin cikin bedroom ɗin ta da kallo duk da babu wani wadataccen haske sosai domin ko ina ɗiɗim yake da duhu haka duk da hancinsa a toshe yake bai hana shi jin irin sanyin ƙamshin da cikin ɗakin keyi ba, ai bata san lokacin da ta zabura ba ta tashi zaune kamar wacce aka tsikara sai kuma ta tuna da kayan bacci ne a jikinta cikin azama ta sake ƙudundune kanta, Yanda ta tsorata shi ɗinma tsoratar yayi sai dai ya dake, cikin tausasa murya kamar yadda ya saba magana taji yana faɗin, "sorry.... Mun tadaki... Am... Am.... Dama nazo ɗaukar Ajmal ne sai naji shiru kuma na kasa gane amsar da ya bani lokacin da na tambayeshi ko baki da lafiya...." "lafiya ta ƙalau" ta fada cikin kiɗimewa wadda shi kansa ya fahimci hakan, bai ƙara cewa komaiba ya juya ya fita Ajmal ya rufa masa baya, tafi mintina biyu ahaka kafin ta samu ta tashi ta zira hijabinta ta fita, suna zaune falo Ajmal na kan cinyar sa,ita dai tana mamakin yadda yake sakarwa Ajmal bayan ayadda ta lura baya son raini, "ina kwana...?" ta fada kanta a ƙasa bayan ta zauna can nesa dasu, "lafiya lau.... Ina so zan kai Ajmal makaranta ne, ki shirya shi" Bata ce masa komai ba ta miƙe ta shiga ciki Ajmal yabita, wanka tayi masa gashi matsalar ko breakfast basu yi ba ga baba saude bata nan ita fa yau abin yayi mata yawa, shirya shi tayi cikin jeans da t shirt duka baƙake ta fesa masa turare kaɗan sannan ta saka masa baƙin combos, Kamar yadda suka tafi suka barshi haka suka fito suka sameshi sai dai yanzu hankalinsa akan waya yake yana lallatsawa, "zaku jira in haɗa breakfast ne?" ta tambayeshi tana gyarawa Ajmal belt ɗin wandonshi, "no.... Zan kaishi yaci abinci" "to shikenan..." Kiss Ajmal yayi mata a kumatu yana haddane dasu amma shi abin mamaki ya bashi ya aka yi yaron yasan kiss? Koda yake ta yuyu itace take yi masa amma duk da haka ya kasa mantawa shiyasa a hanya lokacin da suka tafi sai da ya tambayi yaron wai a ina ya gani, "mommy ce take yi min" murmushi yayi dama yasan hakan mai yuyuwa ne. Kasancewar shima bai karya ba sai da ya fara biyawa dasu ta restaurant suka ci abinci sannan suka wuce makarantar sa zai saka Ajmal, makaranta ce mai tsada dan ta ƴaƴan masu kuɗi ce kuma ƴan gata dan babu students ma da yawa sosai, registration yayi masa sannan ya biya dukkan abubuwan da suka dace kuma bugu da kari makarantar haɗe take da islamiyya dan haka sai 5:30 ake tashi idan yaro ya tafi tun safe, Koda suka gama gidan hajiya ya wuce da su kai tsaye dan sai gobe zai fara zuwa lokacin komai nasa ya zama ready kama daga kan uniform, school bag, lunch box, sandal da sauransu dan komai a makarantar ake badawa yana cikin kuɗin registration,lokacin da suka isa gidan sun samu umaima tana shirin komawa gidan mijinta bayan hajiya ta jajja masa kunne domin yazo shi dai Sameer har yau ya kasa daina ganin baƙin mutumin nan tun bayan da yaji irin aika aikar da yai niyyar yi Allah ya kare. Bai ce komai ba kawai ya wuce part ɗin shi yaje ya kwanta dan wani mashahurin bacci ke shamayarshi tunda safe amma ya daure bai yi ba wannan dalilin ne ma ya haddasa masa ciwon kai kadan kadan, baccin ya ɗan samu ya rage zuwa yamma lokacin da ya shiga wurin hajiya sai ita kaɗai ya samu da Ajmal domin su umaima sun tafi, abinci ya zubo ya zauna yana sauraren hirar da hajiya keyi masa wacce ta shafi matsalar umaima zuwa can ta ɗan sauya akalar hirar daga wacce take yi masa zuwa wata ta daban, "wai Sameer har yanzu shiru baka samo budurwar ba?" Sai da ya lumshe idanuwansa sannan ya buɗe kan filet ɗin abincin da yake kan cinyarsa yana ci, ita dai hajiya ayita magana ɗaya koda yaushe ba canji? "Sameer baka jina ne?" "hajiya ina jinki mana...... Ai maganar ce nakan rasa amsar da zan baki wani lokacin" "ban gane kana rasa amsar da zaka bani ba?" "to hajiya maganar budurwa yaƙi ƙarewa.... Ni har yanzu Allah bai nuna min wadda tayi min ba" "kullum haka kake faɗa, koda yaushe maganar kenan baka ga wadda tayi maka ba....... Ni ina ganin tunda kai dubawar awurinka ta gagara ni inada idon da zan dubo maka, ɗazu hajja Maimuna ta kirani wai Arfat ta samu admission anan BUK, wai zata zauna a hostel nikuma nace a'a ga gida yaushe zata zauna a hostel, kawai tazo nan ta zauna, to ni yanzu wani tunani ne ma yazo min, Sameer tunda ka rasa budurwa ni ina ganin kawai ka nemi Arfat..... " Tunani yafara yi acikin ransa wacece ma Arfat? Idan bai manta ba tun yarinyar bata san kanta ba rabon da ya sake ɗora idanuwansa akanta, ƴar ƙanwar hajiya ce uwa ɗaya uba ɗaya domin hajja Maimuna itace autar su hajiya, yanzu haka tana can Gombe da yaranta, ji yayi ya tsani Arfat ɗin tun kafin ya ganta, shi kansa bai san me yake damunsa ba a duk lokacin da hajiya tayi yunƙurin haɗashi da wata sai yaji ya tsani yarinyar, ko wani ne ya kawo masa maganar wata haushi abin yake bashi, shi fa baya maraba da irin wannan haɗe haɗen, "kaji abinda na faɗa maka ko?" muryar hajiya ta katse masa tunanin da yake yi, "eh naji hajiya amma gaskiya wannan maganar a barta" "koda yaushe abinda kake faɗa kenan... Sameer nima fa ina son inga iyalinka, ina son inga ƴaƴanka" "zaki gani hajiya Insha Allah amma sai lokacin yayi, har yanzu ni banga wacce tayi min ba kinga babu amfanin inyi auren favor daga baya inga irin type ɗina hankalina ya karkata can ta farkon ta rinƙa ganin kamar banyi mata adalci ba..." "duk mace macece Sameer duk abinda zaka samu a wurin wadda kake kira da type ɗinka itama wannan ɗin zaka samu awurinta, Arfat yarinya ce mai nutsuwa mai hankali mai addini.... Insha Allah zaka ji daɗin zama da ita, sannan idan har nice na haife ka kuma na isa da kai to ita na zaɓa maka a matsayin mata " " hmmm ji hajiya tana maganar wai duk mata ɗaya suke, wallahi mata suna suka tara especially ma matan yanzu " ya fada a cikin zuciyatarsa, shi dai yau yaga ta kansa wallahi da ya san irin abinda zai biyo baya kenan da baima shigo part ɗin hajiya yanzu ba, yana jinta taci gaba da yi masa ƴar nasiha akan ya sakawa zuciyarsa so da ƙaunar wannan zaɓin da tayi masa Insha Allah ba zai yi nadama ko dana sani ba, ji yayi abincin da yake ci ya fita daga ransa dan haka ya tashi ya fita ya kai abincin kitchen ya koma sashensa dan bashi da wurin zuwa, pretty ya ɗauka dama itace abokiyar wasan shi. Sai da yayi sallar magrib sannan ya tafi mayar da Ajmal gida, abin ya bashi mamaki mutuƙa sannan ya saka shi cikin tunani mai zurfi lokacin da yaga Ruhaima cikin kwalliya sosai a wannan daren,falonta sai ƙamshin turaren wuta yake yi ko ina da komai a gyare, banda gaisuwa babu abinda ya sake shiga tsakaninsu sai dai irin yanda yake kallon falon ta san akwai magana acikin zuciyarsa, miƙewa yayi dan tafiya amma sai ya zuba duka hannuwanshi cikin aljihu ba tare da ya kalleta ba yace, "kiyi hankali da irin mutanen da kike kawowa gidan nan wai da sunan zawarci..... Sannan ki guji bin mutum da sunan kai ki unguwa" Da kallo ta bishi ba tace masa komai ba kamar yadda shima bai so tace ɗinba dan yana gama faɗar abinda ke ransa ya juya ya fita, maida hankali tayi kan Ajmal wanda ke bata labarin irin abubuwan da suka faru a makaranta tun daga farko har ƙarshe, taji daɗi sosai dan dama wannan shine burinta taga ya samu ingantaccen ilmi wanda kowa zai yi alfahari dashi kuma zai amfana, kai ai Sameer halinsa sai shi haka kawai ya dage yayi ta kafa mata dokoki da sharuɗɗa kamar wani wanda yake aurenta, harda wani ta kiyayi bin mutane su kaita unguwa, lallai ma, duk waɗannan maganganun tana yin su ne cikin ranta. Kamar yadda Ajmal ya sanar da ita wai yau zai fara zuwa makaranta tunda tayi sallar asuba bata koma ba, abincin da zai ci da wanda zai tafi makaranta duk ta haɗa tayi masa, 7 saura ta tashe shi tayi masa wanka ta shirya shi cikin kaya personal saboda uniform ɗin sai yau, suna falo yana yin breakfast duk sai murna yake ɗoki ya cika shi suka ji alamun shigowar Sameer, kayan bacci ne ajikinsa blue color daga waje ya tsaya bai shiga ba, tare suka fito da Ajmal ɗin tana riƙe da flask ɗin abincinsa, abun ya bata mamaki duk da ba sabon abu bane ganin tana gaida shi amma bai ko kalleta ba koda yake dama haka ya saba wannan halinshi ne sai dai ta bawa wani labari shan ƙamshi da ciki ciki ajininsa yake, Sai da taga fitarsu daga gidan sannan ta koma ciki, bacci ta koma, haka ta wuni tana bacci daga ƙarshe ta rasa ma me zata yi gashi sunyi wayar har ta gaji da mukhtar, kallon ma ta kunna duk bai wani yi mata ba, kiran umaima ne ma ya ɗan ɗebe mata kewa dan ta kirata tana sanar da ita ta koma gidanta, sai da suka ɗan taɓa hira sannan take sanar da umaima Ajmal ya fara zuwa school yau, duk gidan babu daɗi yayi mata shuru ta rasa me zata yi dariya umaima tayi tace, "haka abinfa yake, idan suna nan su dameka bakinka bazai huta ba idan basa nan kuma kaɗaici ya takura maka.... Kawai ki faɗa social media, zaki fi ɗebe kewa yanzun nan lokacin zai ɗan rinƙa tafiya, kije can kiyi ta kallon films da karance karancen novels" Wannan shawarar tabi ta umaima kuma hakan ya taimaka mata dan tabbas tana cikin nishaɗi, ita social media bata taɓa burgeta ba dan akwai abubuwan da bata ma taɓa amfani dasu ba kuma suna kan wayarta dan ada gani take kamar ɓata lokacine ko kuma rashin aikin yi ne. Sai 6 na yamma Sameer ya dawo da Ajmal yanzun ma bai shigo ba, iya Ajmal ɗinne kaɗai ya shigo da kayansa a hannu kashi kashi dan an bashi komai yau sai murna yake tsabar ɗoki tun a daren ranar ya gwada kayan (uniform) bai bari gari ya waye ba, washe gari kam sai da tayi masa pics kafin Sameer yazo bayan ta shirya shi ya sha uniform ɗin shi wanda ya amshe shi yayi masa masifar kyau, milk color ɗin riga da necktie blue black sai blue black color ɗin wando, kamar jiya yau ma bai shigo ba itama bata fita ba sai iya Ajmal ɗin ta tura masa suka tafi. Rabon da ya shigo ciki harta manta dan ba zata iya tunawa ba amma kullum zai zo ya ɗaukeshi babu fashi sannan zai dawo da shi sai ko a weekend shine zai huta, yau dai kam ta kwana da ciwon nata na gado kuma ta tashi da shi dan ko bacci bata samu ba sai juye juye ta kwana tana yi shiyasa ma ba zata iya shirya Ajmal ba, tana jin lokacin da Sameer ya shigo gidan domin ɗaukarsa, cikin ƙarfin hali ta tashi Ajmal tace yaje ya faɗa masa yau ba zai je school ba bata da lafiya, yana zaune cikin mota sai ga Ajmal ɗin ya fito babu shirin makaranta, tun kafin ya tambayeshi ya sanar dashi abinda mommy ta aiko shi, "bata da lafiya meke damunta? Ina wannan baban dake yi muku aiki?" Ba dan Ajmal yarone mai wayo ba da bazai iya amsa masa waɗannan tambayoyin ba domin sunyi masa yawa, kama hannunsa yayi suka shiga ciki ya tsaya a falo yace yaje ya kirata, Da ƙyar da dafa bango ta samu ta fito a durƙushe ma take tafiya kuma daƙyar, koda tazo falon a ƙasa ta zauna ta kifa kanta a kujera, sam bata damu da a yadda take ba dan ita kaɗai ta san abinda take ji, "sannu.... Meke damunki?" Kai kawai ta ɗaga masa amma yadda yaga ta dafe cikinta hakan kaɗai ya bashi tabbacin ciwon ciki ne,ya san ciwon ciki ya san yadda yake dan shima lalurarsa ce shiyasa yaji ya tausaya mata sosai, "kinsha magani?" ya buƙata cikin kulawa, kai ta girgiza masa, "sannu.... Bari na kai Ajmal school sai na dawo na kai ki clinic" Bata amsa ba sai ko ciccije lips ɗinta da take yi, Ajmal ya tura ya kwaso uniform ɗin shi da school bag da komai ya ɗaukeshi suka fita, yau kam ya makara dan gidan hajiya suka je aka shirya shi sannan ya rakashi shiyasa lokacin da suka je makarantar har an gama assembly yara zasu shiga class, dropping ɗin shi yayi ya kama hanyar gidan Ruhaima wacce keta faman murƙususu, yadda ya tafi yabarta haka ya dawo ya sameta, da ƙyar ta buɗe ido ta kalleshi ga babu damar magana domin bakinta cike yake fal da yawu sannan amai take ji tun ɗazu, ganin ta kasa buɗe baki sai motsa shi take yi yasa shi fahimtar yawune ya taru a bakinta, tissue ya ɗauko wacce ke ajiye kan tv stand ya miƙo mata, tana zubar da yawun kuma yaga ta fara yunƙurin amai............ Alhamdulillah laifin dadi karewa, anan na kawo karshen free pages, ga duk wadda ke da bukatar jin cigaban labarin sai ya tuntubemu 👇🏻👇🏻 *HASKE! HASKE!! HASKE!!!*💡 IT'S *HASKE WRITERS*💡AGAIN THE HOME OF EXPERTS AND PERFECT WRITERS ✍🏻 HAƘIƘA JIMIRIN ZAMAN JIRA YA ƘARE MASOYA DOMIN ƘUNGIYARKU MAI FARIN JINI TA AMANA WATO *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 ITACE TA MOTSO KUMA TA DAWO DAN NISHAƊANTAR DAKU KAMAR YADDA TA SABA, *TAURARI HUƊU* SHINE TAKEN TAFIYAR TAMU A INDA ZAMU GABATAR MUKU DA FASIHAI, HAZIƘAN MARUBUTA GUDA HUƊU DA ALƘALIMANSU CIKIN TAFIYAR DA BABU NADAMA ACIKINTA, *1.AYUSHER:-* Writing by FERTYMERH XARAH *2.ƘAZAFI NE:-* Writing by RAHAMA NALELE *3.DA UBA AKE ADO (Bada riga ba):-* Writing by ZAINAB BAWA *4 SO DA ALAƘA:-* Writing by UMMI A'ISHA WAI WAI WAI... 🔥BAHAUSHE YAYI GASKIYA LALLAI TAFIYA DA GWANI MAI DAƊI, NIMA DAI GA NAWA GWANAYEN 4 STARS DUKKA WAƊANNAN LITTATTAFAN GUDA HUƊU ZAKU SAMESU CIKIN FARASHI DAIDAI DA ALJIHUNKU....MY SISTER WHAT ARE YOU WAITING FOR?? MAZA HANZARTA KI GARZAYA KI NEMI NAKI DAN ZASU FARA NAN BADA JIMAWA BA, KAR KI BARI A BAKI LABARI..... COMING TO YOUR WAY SOON, DON'T MISS IT 😘😘 Guda 4:- 1500 Guda 3:-1200 Guda 2:- 800 Guda 1:- 400 7033027658 Palmpay Bank Aisha Muhammad Salis +447894142004 Katin wayar MTN ta... 07044644433 da shaidar biya *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 _*Ummi Shatu*_👌🏻