🌹 SIRIKATA🌹 Story nd writing by: SADIKA IBRAHIM Momsani.......✍️ Bismillah rahmanir raheem. *Wannan littafi me suna SIRIKATA kirkirarrene banyi dan cin zarafin wata ko wani ba,Allah yasa yadda nafara a sa,a nagamashi cikin amincin me duka* Note:*wasu zasuga Ina yawan yin labarai na da garin kontagora,yes hakane sbd Ina alfahari da kasancewata yar cen besides ma bansan kowane gari ba bayan namu😀😀ni kifin rijiyace iya garinmu kawai nasani,Kuma Ina fatar Hakan ze baze Dami me karatuba,sannan Ina fatar darasin dake ciki dasakon da labarin ya kunsaya isa inda ake bukata ngd*🤲 Pg 01_02 Kontagora Niger state. Zaune suke agaban wani shirgegen mutum yasha babbar riga da rawani hannunsa rikeda katuwar charbi irin me dubu dinnan, idonsa yasha kwalli ranbadau katon mutum ne bakin kirin dashi fuskarsa cikeda gashi buzuzu lebensa manya dasu kamar biredi dan dari da hamsin se mui-mui yake da baki kamar me karanta wani abu gabansa wani farantin kasa ne idan yaja charbin nan se ya dangwala kasa se zare ido yake, sukuwa se kallonsa suke suna jiran suji abinda zece, cen daya gama gungunin sa yace "ke Idiyatu, kozaki mutu matar danki seta haihu Kuma idan kika matsa akan hana faruwar haka to tabbas mala,ika azara,ilu ze ziyarceki,domin akwai rabo me zafi atsakani inkika cika matsa lamba hahahaha margaya Sala" Jikinta na rawa tace "to Allah yatemaki mlm buzu bawata mafita ne" dole seta haihu? nifa kozanyi yawo tsirara wannan shegiyar bafulatanar banason ta haihu da dana" Kallonta mlm buzu yayi yace "lalle bakida hankali kikace ko Zaki yawo tsirara ne ko? to ai se kina raye ne Zaki yawo tsirarar ko? Wakika ga yana shiga hurumin ubangiji har haka? Kin taba ganin Sara da sassaqa yahana gamji toho? To ko gurin wa zakije magana guda ce za a fada Miki matar danki seta haihu sede in kudinki za aci afada Miki sabanin hakan, ni kaina duk hatsabibancina bana matsawa akan irin wannan Al amarin saboda da aure da haihuwa idan kadage akan dakatar dashi sekiga Allah ya daukeka anyi babu Kai to mekenan akayi badi ba rai? to badaniba nide na fada miki abinda yake akwai kuma me yuwuwa inkinji kanki in bakijiba ruwanki nide na fada Miki gsky kafurar banza bacemin dagani anan" yafada yana kwalalo mata kananan idonsa da sukasha kwalli. Jiki na rawa daya matar me suna Biba tace "gafarta mlm ayi hakuri bata sani bane,tayi kuskure ayi mata afuwa yanzu menene abinyi bawata hanyar da za abi?" Kallonsa yamayar kan Biba yace babu amma za,a iya yima su farraqu da juna ko an haifi yaro ko yarinyar baze sotaba zema iya cewa ba danshi bane ko 'yarshi". "Yawwa mlm buzu ayi hakan,hakama yayi,to yanzu nawane kudin aikin?" Yana hura hanci yace "dari uku ne ba yawa" zugurar idiyatu Biba tayi tace "kibada kudin mana kinyi zugum kamar me tunani" sauke gauron numfashi tayi "hmmm Allah temaki mlm ba ragi"? Idon mlm buzu cikeda bala,i yace "nafasa Miki aikin makwadaddiya 'yar munafuka baqar muguwa tashi kibar min guri kafin na sauya Miki kama marar godiyar Allah" Jikina rawa Biba tace"Allah ya huci zuciyar mlm buzu me abin ban mamaki batasan ba a tayin aikin ka bane namanta ban mata wannan bayanin ba gafarceni mlm zamu Bada kudin" idiyatu jiki na rawa ta dakko kudin acikin Jakarta tamikosu dubu dari uku cif, duk irin rudewar da tayi da tsoro mlm buzu Daya shigeta besa tayi zuren kudin ba dari uku cif tabashi lols, sannan ta tashi jikina rawa tafita tabar Biba aciki tana Kara bawa mlm hakuri. A hanyarsu ta barin kauyen ma haka Biba keta sababi kamar zata ari baki, "ni wlh Idiyatu wannan halin makon naki yana bani mamaki da haushi, haba ayi mutum me shegen son abin duniya haba Dan Allah, ga bakin Hali,ga son abin duniya duk ke kadai kika hada wannan abin ga hassadar tsiya wacce koni da muke tare baki raga min ba,to wlh nagaji da mugun halinki sekace ke kadaice bayerbiya adoron kasa kinuna kinfi kowa son abin duniya,to wlh nagaji da halinki,gurin malamai kusan uku kikamin wannan abin inbanda ke ma ai ranar biyan bukata rai ba abakin komi yake ba keda zaki samu makudan kukade Amma kike ta wani tsumulmular fidda dubu dari uku haba dan Allah wannan ba girmanki bane" Idiyatu de ba baka se kunne ita gsky ba haka taso ba taso ace kwata-kwata Rabil be Sami da ko daya a duniyaba,ita gsky acikin agenda dinta babu da ko 'ya saboda tana ganin ko bajima koba dade Rabil ze waiwayi wannan yaron, musamman idan ta tuna yadda yake bala,in son yaga da ko 'yar sa aduniya,yasha fada mata cewa idan Allah yabashi da ko ya ze raba dukiyarsa biyu yaba wannan dan ko 'yar, kenan ita ko oho to bazata taba bari Hakan ta faruba bayan tabiyo ta karkashin kasa ta rabashi da danshi ko 'yarshi to zata hada harda makirci da tuggi gurin ganin ta hanashi amsar wannan abin da za,a Haifa masa. Da wannan tadagawa Biba daketa zuba kamar kanya hannu tace "pls sararamin hakanan,inace duk jirgi daya ya kwasomu? Kefa kadanki ne kike zubarwa matar danki da ciki Kuma kika lakaba mata sharrin cewa itace batason haihuwa har seda kikasa danki yasaketa Kuma kika aura masa wata itama Baki cenza zani ba haka kike sashi yanata aure aure kamar daddawa, to sahirtamin hakanan ehe" Haka sukata yiwa kansu tone tone har suka fito titi sannan suka cigaba da kitsa yadda zasu Kara zage dantse gurin ganin sun Hana sirikansu zaman lfy. ___________________ Unguwar dadin kowa. Masifa take kamar zata ari baki bakinta har kumfa yake kamar an kada mata Omo aciki saboda bala,i, wayace kare a kunnenta fadi take " wlh na gwaggo ko ka maidoni minna nan ko kuma kaga bacin raina iskancin banza da wofi, nizaka nunawa aure to sannu tattabara wlh idan har bazaka kaini minna ba kaima sede ka tattaro karuwar matarka Kuma juya kudawo nan indinga ganin ku,inga wacce waina kuke toyawa acen din azo nan ayi agabana ingani, ga dakin da muke ajiyae itace cen ashare muku ku zauna, ai dama daga Kai se ita tunda taki haihuwa sede aci akai masai se uwar kiba da take narkawa kamar jaka," Dan tsayawa tai tana sauraron me ake fada kafin ta lailayo wata uwar ashariya ta narka zanci burar...... Dan kaniya kawai na gwaggo ni kake fadawa naji tsoron Allah? Ni na gwaggo? To idan ban daga Maka nono akan karuwar matarka ba me nake,kace mudi me walda bada jini ya haifeni ba" sekuma tasaki kuka "yiiiiiii na gwaggo ba lefinka bane nasan an gama dakai an wanke Maka buje ka shanye a jiqa Maka jinin al,ada kasha wayyo ni Allah na na gwaggo yiiii" Gidan baban nera. Gidane na Gani na fada, gidane me shegen kyau hawa biyu kamar gidan wani me muqami yahadu gidan over kamar a turai. Zaune take akan daya daga cikin Maka makan kujerun da aka kawata falon dashi tasha less peach color hannunta yasha zobunan diamond masu kyau farar mace me kyau wiyanta sanyeda wata siririyar sarka idonta sanyeta gilashi Kara karfin gani (*medicated*) falonko yagaji da haduwa komi na falon black nd white ne tun daga kujerun Wanda suka kasance set uku har zuwa curtains da center carpet,kafar ta Daya akan daya hannunta daukeda glasscup tana siffing din strewberry jus akalla zatayi Shekaru 37 zuwa da takwas, wata dattijuwa ce zaune akasan carpet din kusada kafafunta kanta akasa kamar zatayi mata sujjada tace "hjy dije lemon yayi Dede ko?" Cikeda fusata da izgili tace "sede in kece dije ko kuma tsohuwar ki bade ni ba, ni sunana hjy DEEJA ko kokuma kice beauty kamar yadda danki yake fada" Kan wanna dattijuwa akasa tace to "jija kiyi hakuri hjy jija" afusace DEEJA tawatsawa wannan tsohuwar lemon dake hannunta tasa kafa ta shureta tace "jeji zakice ba jija ba uban waye jija? Matsalar dan kauye kenen kina zamanki akauye inda yafi dacewa dake Amma saboda kawai son atakuramin daga zuwa gaisheki kika kwaso kafa kika biyomu kamar gidan ki, Koda yake gidan danki ne bakida iko dashi balle kizo ki share duwawu ki zauna, dan naki ma nikeda sitiyarin juya rayuwarsa da duk abinda ya mallaka. Kuma inason kisawa ranki cewa ukubata itace ajalinki fitinanniyar tsohuwa kawai kwadayya mtwsss " Tasa kafa ta take yatsar wannan tsohuwar tajuya zata wuce kanan sukaji sallama abayansu wani mutum ne yashigo da alama shine me gidan yasha babbar rigar wata danyar shadda sea green se kamshi yake fuskarsa daukeda fara,a yake cewa "barkan kude da gida" idonsa yasauka akan matarsa abin sonsa durkushe gaban mahaifiyarsa tana kokarin dagata ta tashi tana fadin "ayyah inna seda nafada Miki kidinga kirana idan Zaki sakko Saman matakalar nan saboda santsin tiles din kar ya kada ke ga jikin tsufa sannu kinji daure ki tashi" Ai dasaurinsa yakaraso yakama mata suka daga inna suka zaunar Saman kushin, Fadi yake "inna bakideji ciwoba ko? Sannu" yafada yana zaro wayarsa daga cikin aljihun babbar rigarsa ya dannawa likitansa kira ringing daya ya dauka yace "pls Dr kazo kaduba min inna tsantsin tiles ne y dibeta ta Fadi,ok sekazo" ya ajiye wayar yamaida dubansa kan inna daketa sharar kwallan, yayin da DEEJA ke gefe tana zuba mata uwar harara ganin ze juyo ne yasa taci gaba da goge idonta kamar me hawayen gaske tace" sweetheart nacewa inna tadinga min magana idan tanason wani abu base tafito ba saboda bata Saba taka tiles ba kar taje ta Fadi gashi yanzu ta Fadi har ma jus dinda ta dakko ya zube mata ajiki Kila zata Sha ne tunda kaga ai basaba shansa tayiba may be ma gurin Shane zakin yadebeta tafadi batasan takawo gurin steps ba" tafada tana share kwallan karya. Memakon yaji zafin maganarta akan mahaifiyarsa sema Jin yayi takara kima a idonsa gani yadda ta damu akan faduwar mahaifiyar tasa harda kukanta. "Bakomi beauty zata kula next time ai in Sha Allah,ok stop wasting ur preasious tear umm" yafada yana janyota jikinsa kamar ba agaban uwarsa yakeba Yama manta da wata inna agurin seda Dr yayi sallama tareda Neman izinin shigowa shine ya tuna da inda suke yayi saurin sakinta tareda bama Dr izinin shigowa, Koda suka juya wayam ba inna ba dalilinta... Kara kara Kaka... Wannan tafiyar ta dabance wannan salon na daban ne... Tafiyar me zafice akwai darasi sosai acikin wnn tafiyar kude ku biyoni domin Jin yadda zata kaya acikin wannan zazzafan labarin. SIRIKATA! SIRIKATA!! SIRIKATA!!! Hmmm wnn labarin akwai taba zuciya da nishadi kude ku biyoni domin mu nutsa tare acikin labarin.... Shin su wanene idiyatu da Biba? Wacece hjy DEEJA? Wacece innah? Wacece mahaifiyar na gwaggo? Duk kubiyo ni domin Jin suwaye su... Momsani......✍️ 🌹 SIRIKATA 🌹 By SADIKA IBRAHIM Bismillah rahmanir raheem. Pg 03_04 Wacece idiyatu.... Garin Lagos. Kasan gadar legas gurine daya kunshi mutane daban daban masu yare maban banta kama daga hausawa, yarbawa, inyamurai dade sauran yaruka da dama kowa harkar gabansa yake kowa yasan wasu irin mutane ne mazauna kasan gadar legas, mutane ne da dama Wanda suka baro garuruwansu da mahaifarsu Wanda suka baiwa duniya gaba dakuma amanar rayuwarsu, yawancin mazauna wannan guri basa tina makomar rayuwarsu sude kawai gasunan ne suna rayuwa irin yadda sukaso. Taye wata bayerbiyace me kananun shekaru a duk cikin matan dake zaune suna sana, ar su ta karuwanci itace karamar yarinya sosai dan duka duka shekarunta 15 kawai. Tun tana yarinya iftila'i yafada mata kanin babanta yamata fyade daga nan tafara Sha,awar Maza harta Kai shekaru goma Sha uku daga nan ne kuma ta tarkata tabi wata mata me suna funke suka tafi legas kasan gada suka cigaba da karuwancin su, itade taye ta kasance mace ce karfin jini bakowane kwayoyin planning ne yake karbar taba, Hakan ya janyo mata yawan samin juna biyu tayi abortion kusan sau tara, ana goma ne tahaduda wani bahaushe inda ya dauketa Yakama mata gida suka dawo nan cikin unguwar surulere suka cigaba da dadironcin su, ana haka kwasam Sega ciki ajikin taye har na tsawon wata biyar, ta tada hankali kan cewa ita lalle seta zubar inda wannan bahaushen me suna murtala yace tabar masa abinsa yana so kuma inta yadda shi ze aureta bayan ta haihu, taye ganin cikin sauki Allah yakawo mata miji dama tagaji da karuwanci tuni ta amince, yadauketa suka dawo arewa garin kontagora Niger state. Bayan taye ta haihu Allah yabata mace aka Sanya mata suna Idiyatu duk da cewa taye tanada aure hakan be hanata cigaba da hulda da wasu mazan ba, Shima baban idiyatu yacigaba da kula matan sa abinsa, ahaka rayuwar idiyatu ya taso uwa bin Maza uba bin mata, sannan idan zasuyi rayuwar auratayyar su baruwansu da idiyatu ko tanajinsu zasuyi abinsu su gama suyi ta faman ihu da nishe nishe tanajinsu baruwanta itama har abin yafara bata Sha, awa. ______________ Ahaka har ta taso har tagirma tafara kidayar dangi halin iyayenta be cenza ba,. Muktar... Muktar makotansu Idiyatu ne. Kasancewar yadda iyayenta suka sakar mata ragamar rayuwarta hakan yasa har takwana a makotansu gidansu Biba kawarta wacce takasance kanwar muktar ce, muktar tun yana bawa Idiyatu minti intazo gidan su yasamu ya lalibe mata 'yan gidayar danginta har yafara bata kudi tayi yana cewa tacire wandonta,da haka abin nasu har yakai wata ran setayiwa Biba sallama kan cewa ta tafi gida,dazarar Biba Takoma gida se Idiyatu tadawo tashige dakin muktar Wanda yake asoron gidan tun suna abin dawasa dawasa har tafara kwana a dakinsa da asuba yarakota kofar gidansu tashige,bawanda yasan abinda suke aikatawa har Biba kawarta batasan cewa Idiyatu da yayanta suna wannan rayuwarba. Haka zatazo da kudi tayi abinda takeso iyayenta Basu taba tambayar Ina take samo kudiba, wataran har taye tana amsar kudi a hannun Idiyatu wai ta ara batareda tasan daga Ina yarta ya samo wannan kudinba Kuma bata damu tasaniba. HARIRA... HARIRA makociyarsu idiyatu ce itama bafulatana ce da mijinta zayyad yanada rufin asirin sa sede mutum ne matafiyi yana sana, ar hatsi ne ya dakko daga kauyuka yakawo cikin gari, da sassafe yake fita se kusan goman dare yake dawowa. Biba tana yawan shiga wurin harira saboda Biba batada kyuiya harira tana aiken Biba ko ina, Hakan yasa suka Saba sosai. Ashe Biba son zayyad take idan akayi sa, a yadawo gida da rana Biba seta ruga gida Tasha wanka tadawo taita yiwa zayyad iyayi kala kala, aita masa fari da karairaya, idan Yana nan ma har cenza salon magana da tafiyarta take ashe zayyad yagano nufinta Hakan yasa yadena sakar mata fuska itakuwa harira baiwar Allah batasan me ake cikiba. Biba de ganin hakarta yaki cimma ruwa hakan yasa tanemi shawarar kawarta idiyatu wacce ita batama San harira ba sosai saboda ita batada shige shigen gidan mutane ba kamar Biba ba itakam kusan kowa na unguwar tasansu, abinda yasa ma batasan hariraba saboda Basu dade da dawowa unguwarba. Biba ce tashigo gidansu idiyatu tanata rabka sallama amma shiru ba amsa, kasancewar taye maman Idiyatu Bata cika zamaba tana cen wurin yawon tallar maganin basir Wanda take fakewa dashi tana Sha, aninta, Biba Kai tsaye dakin Idiyatu ta fada da tunanin ko bacci take kamewa tayi na wasu yan mintoci sakamakon ganin idiyatu da yayan ta muktar turmi da tabarya basama cikin hayyacinsu basusan tashigoba.. Seda Biba ta daddage ta sambada wata uwar ashariya sannan sukasan da wanzuwarta agurin, se a lokacin ne suka fara neman abinda zasu suturta jikinsu, cikeda borin kunya Idiyatu tafara kukan karya, Fadi take "seda nace Maka banso bansaba ba amma kaki ji kanatayi yiiiii wayyo nashiga uku" ta dora hannu aka, da mamaki yake kallonta yace "munafuka bakece kika kiraniba kikace mamanki ta tafi tallah ba, babanki dama se angansa" Idiyatu de se matsar kwallah take, Biba ce taja numfashi cikeda mamaki se kallon su take, a iya saninta gaisuwa ce kawai take hada Idiyatu da yayanta amma yau segasu kamar wasu ma aurata. Jan numfashi Biba tayi tace " nide sa kayanki kizo muyi magana wani lamarine yakawoni wurinki". Tajuya tafita tabarsu sunata zare ido, shiru shiru Idiyatu zata fito bata fitoba muktar ma shiru, seda aka dauki kusan 5mins kafin taji anyi wani irin Nishi kamar na raguna, sannan sega muktar yafito yana daura tazugensa yawani daure fuska dan ma karta kawo masa wargi, cikeda Al, ajabi Biba take kallonsa tareda mamakin dadewar su bayan yanzu suka gama gaddama atsakaninsu kan cewa basuda lefi, kowa se mannawa dan uwansa lefi yake,alhalin duk Wanda yagansu kamar yadda ita tagansu to tabbas zegane cewa abinsu babu tursasawa aciki,komi dasuke aiwatarwa da son ran junansune, tajisu shiru kamar basusan da zuwanta ba, sannan Kuma yanzu yafito yana wani Sha mata kunu, hmmm abin al,ajabi baya karewa me rai. Tanaganin muktar kamar ustaz ashe kwallon shege ne, tuno yadda taganshi dare dare akan Idiyatu take, abun kamar majigi yazauna mata radam a kwakwalwar ta, Idiyatu ce tafito tanata yan matse matsen kwallah, wai ita wlh ba yar iska bace muktar ne yace..... Kafin takarasa Biba ta daga mata hannu tace"dakata dan Allah" cikin kasa kasa da murya Biba tace "da dadi abin dan Allah?" Cikeda mamaki idiyatu ta dago miri mirin idanunta Wanda suke abushe ba alamar kuka tace "mene?, Mekike ce?" Cikin Kara kasa da murya Biba tace "abinda naganku kunayi da yaya nace da dadi kuwa?" Ai se idiyatu tagyara tsayuwa tace "wai ma meya kawo kine?" Cikeda son Jin kwaf Biba tace"nide tambayar ki nayi yakikaji lokacin da yaya na yake eh yane?"ta fada tana kashewa Idiyatu ido daya,"lumshe ido idiyatu tayi tace "ummmmm me ma zance dake ne, wlh duk duniya banajin akwai abinda yakai sex dadi, yayanki karshene wurin hakar hole, kinsan Allah wannan maganar da muke dake yasa nakara jikewa" takai karshen zancenta tana tusa hannunta cikin pant dinta tana lumshe ido. Cikeda al, ajabi Biba ke kallon idiyatu, Jan hannun Biba tayi tace muje kiji.... _______________________ "Shakuruminki kawata inde Ina numfashi bakida miji se zayyad, Amma fa ni banma sanshi ba fa ban taba ganinsaba", Biba tace " nide ba wannan ba kawai inason zayyad Kuma zan iya aikata komi domin insameshi". Kasancewar taye maman Idiyatu mace ce me biye biyen malamai inde har taga namijin daya birgeta Kuma taga zebata wahala wurin shawo kan sa to da malamai take hadasa, hakan yasa idiyatu ta iya shige shige itama,Wanda da Hakan nema tasamu kan muktar yayan Biba, saboda betaba gwada kwanciya da itaba sede ya dan tattabe mata kirji yakyaleta,ranarda tanuna masa tanason su kwanta tare yaki amincewa a cewarsa bayason ya aikata zina,wannan din ma da suke yakasa rike abinda yake ji ne,amma sutsaya ahaka kawai Allah ya yafe musu, tadaga Kiri Kiri yanason yadena ko tabamata kirjin gashi Kuma ita tanada Sha,awa sosai sekawai wataran takai sunansa wurin wani malami daya daga cikin Wanda take raka mamanta ya mata aikinda yasa muktar yakwanta da ita,tuntaga ranar Kuma se suka zama kamar mata da miji wataran takwana a dakinsa wataran shiya biyota gidansu su shige dakinta sukwana suna abu daya se asuba yake bitowa yakoma gidansu, koyanzu da Biba takamasu cemasa tai tunda tariga tagansu kawai su gama abinsu shiyasa Biba taga sun dade basu fitoba. Idiyatu tace "zankaiki wani wuri inde zayyad kin auresa angama". Harira baiwar Allah batasan meyake faruwaba tadega kwana 2 Biba tadena zuwa, Hakan yasa taje har gidansu Dan taji lafiya, bayan sun gaisa da maman Biba harira tace taji Biba shiru kwana2 shine tace bari tazo tagani lafiya kuwa, lafiya lau wallahi harira dama sunfara jarrabawane a makaranta shiyasa dake wannan ce jarabawar su ta fita karamar secondary. Bayan harira tabar gidansu Biba da kwana 2 se harira suka fara samun matsala da mijinta zayyad, Abu kadan fada sannan yatsiri dawowa dawuri duk abinda yake karfe shida yadawo gida yasha wanka yafita se karfe goma ko Sha daya ze shigo gidan sannan Babu maganar arziki tsakanin su, tana cikin wannan hali tarasa Wanda zata fadawa taji dadi tana zaune darana tazuba uban tagumi sega sallamar Biba itada idiyatu sunshigo gidan sallama sukayi shiru ba amsa seda suka shiga har dakin suka zauna harira batasaniba tayi zurfi a tunanin wane laifi tayiwa mijin ta yacenza mata. Seda Biba ta tabota sannan tayi firgigit ta tasauke numfashi tace 'yaushe kuka shigo banjiba? Sannunku dazuwa"ta tashi takawo musu ruwa me sanyi na tulu, gaisawa sukayi Biba tasha wanka se yatsina takeyi tana karewa dakin harira kallo kamar yau tafara ganin dakin. Suna zaune suna fira sama sama Sega sallamar zayyad, da mamaki harira ta amsa tana masa sannu da zuwa tareda tambayar sa ko mantuwa yayi Taga yadawo ba lokacin da yasaba ba, budar bakinsa se cewa yayi matarda zan aura ce tace muhadu agidana yau da rana shiyasa kika ganni yanzu, yafada yana Maida kallonsa kan Biba wacce tayi wani irin zama kamar dakinta se hura hanci take. Cikeda mamaki harira take kallon zayyad tamaida kallonta inda taga Yana kallo straight kan Biba tadawo da kallonta kan zayyad Wanda yamatsa kusada Biba kamar ze shige cikinta yana mata magana kasa kasa, yayinda idiyatu daya kasance yau ne farkon ganinta da zayyad tayi mutuwar zaune tasaki Baki da hanci tana kallon zayyad kamar zata cinyesa danye..... Momsani......✍️ 🌹 SIRIKATA 🌹 Na SADIKA IBRAHIM. Bismillahirrah manirrahim. Pg 05_06 Wani irin kukan kura harira tayi, tafada kan Biba dan kallon da taga tanawa zayyad dakuma yadda yazaune kusada ita kamar ze mata sujjada shikadai ya isa yasanar da ita cewa Biba itace macen da yake ikirarin matar da ze aura, batareda tunanin komiba cikeda tsananin fushi da zuciya take dukan Biba,akiyayi fushin me hakuri, Basu iya fushiba idan aka cimma tsautsayi suna iya kisa,,,, dukan Biba take kamar Allah ya aikota Fadi take "nizaki ciwa amana, duk yadda nake dake duk temakon da nake Miki, sau nawa kina zuwa min nan da yunwa indau abinci nabaki sabulun wanka, da wanki bawanda bana baki amma Dan rashin tsoron Allah kirasa wa zakiciwa amana seni....... Kan ta karasa taji anyi sama da ita fauu fauu kawai kakeji zayyad yana wanke fuskar harira da Mari dukanta yake kamar yasamu namiji irinsa, seda yawa harira mugun duka kafin yakoma kan Biba wacce bakinta da hanci yake zubar da jini idonta daya har ya tasa saboda wuya bakinta kamar ganda ya suntume yayi himm gaba daya fuakarta ta sauya kamanni, kamata yayi ya dagota zaune ganin yadda fuskarta tayi dameji abin yakara harzukashi yajuya kan harira dake yashe gefe daya se kukan bakin ciki take yace " kije nasakeki, kafin in dawo kitattara yanaki yanaki kibarmin gidana". Idiyatu da tunda aka fara jibgar Biba ta daka tsalle takoma gefe tana kallo aranta fadi take yawwa kashe min yar banza kiragen aiki(aikin me idiyatu 🤔) seda taga zayyad yafara dukan harira kafin tanemi hanyar guduwa kar azo ahada da ita, amma tana zuwa soron gidan ta tsaya tanajin duk abinda yake Wakana har sakin da yawa harira tanaji. ___________________ Bayan kamar sati biyu anata hidimar batun bikin zayyad da Biba su idiyatu kirjin biki komi tare ake musu na kwalliyar auren hatta kayan gyaran amarya idan aka bawa Biba to tareda idiyatu sukesha acewar idiyatu yayan Biba takewa gyara, Hakan Kuma be taba damun Biba ba, ita damuwartama yadda kwana2 zayyad yacenza mata gaba daya yadena zuwa wurinta sede ya aiko mata abokinsa da kudi yace suyi abinda sukeso shi hidima tamishi yawa. Akwana atashi yau takama daurin auren Biba da angonta zayyad, jama'a suntaru makil a babban masallacin unguwar ta sabon gari, kamar a mafarki maroka suka fara sheda an daura auren zayyad da amaryar sa idiyatu akan sadaki dubu hamsin lakadan ba ajalan ba..... Anata guda kamar an dauke nepa kowa yayi tsit Jin wacece amaryar da aka daura aure da ita, kafin kace me gidan biki yakoma gidan danbe tsakanin amare biyu Biba ta dukan Idiyatu take itama tana ramawa damben su sukasha me rai da lafiya bawanda yayi yinkurin rabasu seda suka gaji dan kansu suka koma gefe suna maida numfashi kamar zakaru, cen bayan sun huta suka cigaba,daga baya ma se suka koma jifan junansu da duk abinda suka samu kan kace mekenan an watse anbar amare da uwayensu sunata rabon fadan se jifan juna suke da mugun alkaba,i suna tonawa junansu asiri, atakaicedai Idiyatu tazama matar zayyad batareda kowa yasan dalili ko kuma makasudin juyewar wannan al, amari ba yayinda kowa yayi shiru da bakinsa kamar an mantar dakowa zancen kamar ma babu abinda yafaru. Inda bayan auren da kwana 2 Idiyatu ta tare adakinta sannan Kuma akanemi iyalan gidansu Biba sama ko kasa Babu su ba labarin su, kawai wayar gari akayi aka ga gidansu kulle kamar ba a taba zama cikin gidanba, sannan bawanda yaneme su. Amarya Idiyatu an tare gidan zayyad Wanda sukeshan amarcinsu kamar ba gobe, yamanta da zancen wata Biba balle Kuma matarsa harira wacce bemasan wacce duniya tashiga ba, yamanta irin soyayyar da sukasha ya manta cewa itadin amanar baffanshice kasancewar ta yar wan babansa daya basa aurenta tunda aka haifeta, kunsan fulani da auren dangi to haka ta kasance da zayyad da harira asalinsu yan kauyen gombene amma kasancewar fulani basa zama guri daya haka sukayita zama gari gari inda suka yada zango a garin sokoto garin shehu, acen suka kafa zuriar su har aka haifi su zayyad da harira Kuma aka hada su aure yawon karatu yakawo zayyad kontagora inda har yagirma yasami sana, ar Saida hatsi bayan Allah yasa masa albarka ne ya dakko matarsa harira yadawo da ita nan garin kontagora inda yake sana, ar sa kasancewar yafijin dadin zaman nan din. *********************** Harira bayan ta farfado tasamu gidan wayam bakowa se ita kawai ga sakin da zayyad yamata tana kuka tahada kayanta dake tanada yan kudi a hannunta tahada tayi na mota takoma cen sokoto wurin iyayensu tafada musu duk abinda yafaru ran baban zayyad yabaci yayi fushi sosai yace tayi hakuri tazauna ze zo yasame shi da batun auren inde shi ya haifeshi bashida mata aduniya bayan harira, da wannan tasamu saukin zuciya, kwasam bayan sati da dawowar ta gida Sega zayyad yazo da batun aje nemar masa auren Biba babansa yamasa tas Kuma yace masa inde shine mahaifinsa ba hannunsa ba kafarsa acikin aurensa, hakama mamansa tamasa fada sosai inda shikuma yayi zuciya yataho yasamu tsohon malaminsa dayayi almajiranci agurinsa yazama waliyyinsa aka nemar masa auren Biba inda a yanzu reshe ya juye da mujiya idiyatu itace amarya.... Haka rayuwa takasance wa zayyad da amaryarsa Idiyatu bayaji baya gani akan Idiyatu yama manta da iyayen sa balle wata aba wai harira ba a ma zancen biba, yazama bawan idiyatu shine wankinta bautar duniya ba wacce bayawa Idiyatu da iyayenta inda yagyara musu gida komi yasamo Idiyatu ko mamanta hakama baban Idiyatu abu kadan zece Idiyatu yar albarka kicewa mijin ki inason kaza, shiko jiki na rawa ze dauka yabayar har yana tambaya ya isa ko akaro.. Bayan shekara biyu da faruwar wannan al, amari kwatsam zayyad yatashi dason ganin iyayensa Amma yana fadawa idiyatu tace me zasu masa bayan ga nata iyayen ai iyayenta nasa ne so kawai yayi zaman sa, haka sukayita yi har aka kwashe sati biyu. Zayyad yana tashi kawai sede ya hau mota se sokoto wurin iyayensa yanata kuka yana rokar gafararsu Dakyar da sudin goshi suka yafe masa inda yasamu labari me dadi daya kusa zautar dashi, labarin shine harira tahaifar masa yaro namiji, bayan tafiyarsa da wata uku ciki ya bayyana ajikin harira har na tsawon wata biyar haka bayan ta haihu ba yadda iyayen basuyi da ita akan tasake aureba amma taki fafur tace itafa ko tsufa zatayi tagama aure inde ba zayyad bane mijin,(first love never dies😍). To bayan ta yaye yaronta me suna Abubakar Sadik takoma makaranta inda dama tayi karamar secondary se kawai ta dora da karatunta gashi yanzu tana s.s.3 matakin karshe na secondary. Sadik yayi wayo abinsa, haka zayyad ya rude ya rikice akan takoma gidansa seda tagara sa son ranta harda kukansa iyayen ko sukace baruwansu inta yarda shikenan haka zayyad ya share duwawu yayi zaman saboda cemasa tayi se sanda tagama makaranta sannan zata Kara aurensa, Kuma ita tana gida kusada iyayen ta sede in ze dawo nan sokoto da sana, ar sa kokuma yatafi yafinga zuwa ganinsu, da haka ya yarda yayita zamansa tsawon wata uku Yama manta yanada wata mata Idiyatu. _______________________________ Acen kontagora kuwa Idiyatu hankalin ta yatashi matuqa rashin zayyad yazamar mata wani babban gibi a rayuwarta, dafarko tayi zaton kauye yatafi gurin kasuwancinsa sedaga baya sannan takeji gurin abokanan sana, ar sa cewa sokoto yatafi tofa daganan ne tasan cewa duk wani alkadari nata ya karye, hankali tashe suka koma wurin bokan su itada taye anan ne bokan yake sheda musu duk abinda akayiwa zayyad yakarye saboda yataka kasar haihuwar sa, sede asake musu wani aikin Wanda zeci makudan kukade ko kuma sukawo idon jariri sabon haihuwa, tofa daganan ne hankali su ya tashi matuqa don su basuda wannan kudin sannan basusan inda zasu samo idon jariri ba. Dama da zayyad suka dogara komi nasu shine cinsu, shansu, sitirarsu komi na rayuwa gashi sanda ze je sokoto basu saniba balle su Sami wani abu ahannunsa sannan duk abinda yarage musu agidan sun siyar sunci dadi. Shiru shiru zayyad bedawoba har tsawon wata takwas lokacin harira tagama makarantar ta har an daura musu aure sun tare a gidan da yagina musu acen sokoto domin batareda sanin Idiyatu ba yazo kontagora shigar dare ya tattare komi nasa har gidan da suke aciki nashi yasiyar kwanan shi 3 agarin ya tattare komi nasa yakoma sokoto.. suna zaune suna ta hamma sunsiyarda komi nasu basuda sana, ar komi baban Idiyatu yakara calewa Lagos abinsa yabarsu nan,, suna ta zabga hamma ga yunwa ga zafi sejin sallama sukayi dafa waje Idiyatu bako mayafi ta tashi taleqa seganin wasu Maza biyu tayi daya dan saurayi dayan Kuma dattijo, tace musu "lafiya kuwa wa ake nema?"Atakaice dattijon yace mata yazo ganin gidansa ne saboda haka ga notice yikawa Idiyatu wata yar takadda yace nanda sati daya yanaso subar masa gidansa zeyi gyara saboda dansa zeyi aure. Baki sake Idiyatu ke kallonsa kamar Yaya gidansa, tace "wannan fa gidan mijina ne zayyad Kode batan Kai kukayi?" tsohon yace mata ai yasani zayyad din da kansane yasiyar masa da gidan kwana 6 da suka wuce, idiyatu tace "to idan ma dan anga mijina baya nan ne akeson aci zalina to wallahi ba a isaba bazamu fitaba", tayage takaddar tazubar takoma ciki. Tanata banbamin fada tana gayawa taye abinda yafaru, taye tace kyalesu macutan banza ba inda zamuje Muna nan zanga Wanda ze fitar damu agidan nan. Bayan sati Daya da faruwar hakan yau su Idiyatu ansamu abinci me rai da lafiya anaci harda kazarsu kasancewar taye ta hada idiyatu da wani tsohon kwartonta dasuka hadu gurin Saida maganin basir, ranar tafita ko tasamo musu abinda zasuci tahadu dashi suka gaisa yace mata kwana2 andena ganinta, nan fa ta labarta masa cewa mijin yartane yagudu yabarta gashi itama yanzu batada jari balle tafara wata sana,a shinefa yace tazo Sudan sakaye se asamu abinda aka bata, ba musu tabisa bayan sun gama yabata 4k,sannan yace takawo yar tata se asamar mata dan abinyi, taye na murna takoma ta labartawa Idiyatu wannan albishir shinefa yau ya dauki Idiyatu ganinta bawata babba bace ya kaita cen gidansa seda sukayi kwana 2 yana gurje Idiyatu sannan yamata sayayya yakawota gida shinefa ake Shan dadi yau. Sallamar Maza suka faraji suna tsaka dacin dadinsu, wannan karon taye ce taje taduba katti tagani sunyi su biyar tace musu "lafiya kuwa wa ake nema?" Daya daga cikin su ne yace "mata yau wa, adin zamanku yakare ko kufito dakanku ko mufito daku"......... 🌹 SIRIKATA 🌹 Na SADIKA IBRAHIM. Momsani. Bismillahirrah manirrahim. Pg din nakune kawayen idiyatu. Ummu zee Khadija Musa Miemie Reema Pg07_08 Ja da baya taye tayi tadakata da sudin hannun da take tace "kamar yaya mufito ko kufito damu, banganeba? Nan din gidan mijin 'yatane, gidan sirikina ne zayyad". Wani daga cikinsune Wanda yadan fisu sauki da alama ya matsa yace mata "hakane gidan sane amma a daa yanzu kuma yasaidashi wa alhaji lawan me kekuna, sannan yabada wannan abawa matarsa Idiyatu", yafada yana mikama taye takarda an nadeta da envelope. Jikina rawa taye ta amsa tajuya cikin gidan hankali tashe, tana zuwa tamikawa Idiyatu takaddar tace takaranta musu Maza Maza, Idiyatu na tambayarta suwaye a waje amma Ina hankalin taye baya jikinta itade kokarinta taji me ke cikin wannan takaddar Allah yasa de ba abinda take zargi bane, dan ita harga Allah batason auren idiyatu ya mutu.. Tana wannan tunanin ne taji Idiyatu tasaki ihu da ashariya, kuka take sosai dan Allah ne kadai yasan irin son da takewa zayyad. Bakomi wannan takaddar ta kunsaba face Sako daga zayyad kamar haka "*Ni zayyad Abubakar nasaki matata idiyatu murtala sakamakon Allah ya dawo dani cikin hayyacina, dama na auretane bada sanina ba Kuma bada sanin iyayena ba, saboda haka nasaketa saki uku, Allah ya hada kowa da rabonsa na alheri Kuma nayafemata duk zaluntata da tayi Allah ya yafe mana baki daya*" Wani iru kuka idiyatu keyi kamar ranta ze fita se fatali takeyi da yan komatsansu da suka saura basu siyarba, har abincin duk ta watsar taye se hakuri take bata,Dan itama kadan yarage bata sa kukan ba, suna cikin wannan halin ne wannan kattin mazan suka shigo suka fara musu fatali da yan kayansu waje seda suka watsa komi waje sannan sukace musu "zaku fitane ko se mun fitar daku kamar yadda mukayiwa kayanku? matsiyatan banza maciya amana karuwai, Allah wadaran zuri, a irin taku ba uwa ba Uba ba yar ba kowa tambadadde, in Sha Allah karshen ku baze kyauba kamar yadda na mijinki beyi kyauba" suka fada suna nuna taye, a haukace taye tace " me kuke nufi da kamar yadda na mjina beyi kyauba? Meya Sami murtala ku gayamin?". Daya daga cikinsune ya dubi idiyatu a wulaqance yace " ranarda yadawo aranar yaga lokacinda tsohon kwartonki yadauki diyarki Idiyatu acikin motarsa, dama ai yasan wannan mutumin kwartonki ne, to sekuma gashi yagansu da Idiyatu sunshiga hotel din colony, aranar ne yarugo aguje dan yasamu wannan mutumin yamasa warning kan cewa meyasa ze dunga bin uwa da diya, Aiko Yana Hawa titi wata kanta tabi ta kansa nan take kafafunsa suka fita daga jikinsa, muduk Muna wurin muka taso da sauri dan mukawo masa dauki, a lokacin ne yaketa kwarara ihun azaba, Yana fadin a je a dakko masa yarsa Idiyatu tashiga wancen hotel din na colony tareda tsohon kwarton uwarta, shin batasan kwarton uwarta bane,? Se ihu yake kafin ayi wani yunkuri ya kama aman jini ta hanci ta baki, Koda aka isa asibiti dashi rai yayi halinsa, kuma me motar da ya bigeshi be tsayaba ya gudu, muma da muka kaishi asibiti Muna ganin ya mutu muka zame daya bayan daya muka gudu ato bame kudin da ze biya ayi masa wani abin, anan ne mukasan abinda yake faruwa kude kunyi asarar rayuwarku". Yakai karshen maganarsa yana wani karkace baki irin na yan jagaliya. Wani irin ihu Idiyatu tasaki nan take ta sume agurin itakuwa taye kamar an zare mata lakka ta dena motsi agurin, seda wannan samarin suka fara balbalin masifa kan cewa zasu kaisu waje sannan taye tayi kamar an mintsineta ta tashi dagudu tayi hanyar waje tana ihu irin nasu na yarbawa idan an musu mutuwa, ihu take tana gudu kamar zararra har takawo kan titi itama tana Kiran sunan murtala tana cewa ta shiga uku se kallonta ake kamar kwancen hauka tana gudu tana ihu, wani me Hilux ne ya shararo aguje yayi tafiyar yaji da raye ji kake timm ta tashi sama ta fado nan take tasami kariya a hannun ta na dama da cinya, kanta ya fashe, ganin haka mutane suka taso ruuu akayi kanta wannan me motar Daya bigeta ya fito hankali tashe yace "Dan Allah kutemaka min nakaita asibiti" haka aka kama taye batasan inda kanta yakeba aka kaita general hospital... Koda wannan samarin sukaga Idiyatu taki farkawa suka dibo ruwa a katon buket suka lema mata, numfashi taja se Kuma ta tashi tana dube duben inda zataga taye, daya acikin wannan samarin ne yace mata ga uwarki cen tafita da gudu tana ihu kamar ta haukace seki tashi ki bita ko kuma yanzu mu fitar dake Da gudu itama ta fita tarufawa uwarta baya, haka tayita gudu tana ihu tana Kiran sunan uwarta, wani saurayi ne ya tsaida ita se Kuma take kamar zata shide bala,i goma da ashirin itakam yau Taga ta kanta duniya tajuya musu baya kamar juyin waina a tanda, wannan saurayin ne yagaya mata abinda ya faru da taye dakuma kaita asibiti da akayi, Kara rushewa tayi da kuka idonta har yafara rufewa saboda kumburi, rokarsa tayi yatemaka mata yabata ko dari biyuce, tausayi tabashi matuqa ya dakko dari biyar yabata, gdy tayi ta tare napep ta wuce asibitin da aka Kai taye. Wannan me motar shiya biya komi da akayiwa taye, dama sauri yake zeje meeting wani gari segashi Kuma wannan Abu ya faru, yana zaune a reception yana waya Sega idiyatu ta shigo da kuka wii Wii dasauri ta tambayi wata nurse ko an kawo wata mata me suna taye, hatsari tayi, nurse din tace batasaniba Amma de ankawo wata takakkarye sede batasan sunan ta ba, tanuna mata block din yan hatsari dasauri idiyatu tanufi block din tana zuwa kuwa taga taye kwance kan gadon marasa lfy an daure mata hannu da kafa da Kai kamar ma Bata numfashi, dasauri cikin kururuwa tanufi gadon da taye take Kai se ihu take abinka da yarbawa lols, nurses ne suka fara yimata fada kan cewa zata tayar da marasa lfy ba a son hayaniya sannan idiyatu tayi shiru se hawaye take. Tana nan zaune tayi tagumi sega wannan mutumin da wata mata babbar mace sunzo wurin direct gadon taye suka nufa matar nata alhini tana magana, idiyatu de batajin mesuke cewa sbd tadanyi nisa da tana waje ne suna ta cikin dakin,tasowa tayi tazo wurin tana kallonsu, babbar macen ce ta kalleta tace "sannu ko yarinya yar uwarkice ko?" "Mama na ce" cewar Idiyatu, "Allah sarki Dan Allah kiyi hkr kinji tsautsayi ne Dan Allah kiyi hkr in Sha Allah zata samu lfy" cewar matar,daga Kai idiyatu tayi wannan mutumin Kuma ya matso kusa yace "kiyi hkr sister wlh ban ganta ba inata sauri" " bakomi" tafada tana share hawayenta. Kwana2 dayin hatsarin taye tarasu Idiyatu tayi kuka kamar bazata denaba daga baya tayi hkr tabar wa Allah. Wannan matar da danta ya bige taye da mota su suka dauki idiyatu suka Kai gidansu saboda tausayi suka riqeta. Yau watan ta biyar taredasu, bayan tabasu labarin karya tace musu batada kowa se mmn ta babanta yadade da rasuwa tun tana karama, tayi aure Shima mijin ya rasu shine gidan da suke haya aka koresu, sbd bakin ciki shine mmn ta ta fito tana kuka shine muhsin yabigeta da mota. Sunan wannan saurayin Daya nige taye da mota muhsin. Saurayi me kyau yanada rufin asirin sa Dede gwargwado, a cikin watannin nan biyar yasamowa idiyatu gurbin karatu a FCE bayan yasiya mata jarabawar gama secondary, tayi jamb shine yasata a makarnta, suna zaune lfy da ita kamar ta Allah ba abinda tarasa, ahaka tafara son muhsin kullum tana dan nuna masa amma kamar baya ganewa ahaka aka fara batun auren muhsin dawata yar uwarsa me suna zainab, ranarda aka Kai kudin sadakin sa Idiyatu seda tayi zazzabi. Shiko bemasan tanayiba kanwa ya dauketa. Tasami sabuwar kawarta wadda tayi amakaranta tafada mata damuwarta, kawar me suna zahida tace kifada masa mana maybe ya fahimta. Da wannan tasamesa ya dawo da daddare yana Shan iska a barandar dakinsa tasamesa Tasha kwalliya, takai masa coffee tahaishesa bayan gaisuwa tai shiru yace "sister akwai abinda kk so ne?" Dama haka yake kiranta, kanta akasa tace "yaya dama..... Dama uhm uhm cewa nai uhm ko zaka iya aurena? Wallahi Allah ya jarabceno d sonka me tsanani narasa yadda zanyi na fada Maka, gashi anata Shirin aurenka da wata". Kallonta yake sosai kamar meson gano wani Abu a fuskarta, seda tagama ya ce " kiyi hkr sister gsky ni banjin zan iya aurenki, besides ma xainab yar uwa tace, tun tana yarinya aka bani ita, so kiyi hkr Allah yabaki miji nagari, sannan kimaida hankali akan karatunki kinji, kicire wannan maganar aranki Babu ita dan ba abune daze yiwuba". Idonta cikeda kwallah ta tashi ta ruga aguje tana kuka, tausayi tabashi ya girgiza Kai dan de Allah yagani Bata masa ba, shibama rashin asalinta ya dameshiba aa kawai Bata masa ba. Haka Idiyatu taci gaba dason muhsin da bawa rayuwarta wahala dan shi bemasan tanayiba, shigar ta university yasa takara wayewa tayi kawaye wayayyu Kuma tambadaddu irinta samari kala kala kowa kulawa take yan iskan makaranta kowa tasanshi amma Bata taba Bada kofar fa za a gane Hakan a gidan ba. Bikin muhsin da zainab yamatso haka akasha biki nagani na fada tunda baban zainab me kudine Hakan yasa yabawa muhsin MD a kampanin San na sarrafa Mai, arziki yakaru Kuma ya wadata idiyatu da komi na rayuwa suna zaune lfy da maman sa har takai matakin 200level lokacin kan har shaye shaye tanayi ba Wanda yasani, Kuma bata dena son muhsin ba kullum kamar Kara mata sonsa ake. Bayan shekara biyu lokacin takusa yin graduate amma saboda dakikanci c.o dinta sun hana ta yin graduate har an koreta a makaranta batareda su maman muhsin sun saniba, kullum Kuma seta fita dasunan zuwa makaranta. Lokacin muhsin dan sa me sunan Rabil an yayesa. Wata Rana da daddare Idiyatu tayo gayyar abokanta 'yan dabar makarantarsu Wanda aka koresu tare sakamakon dabancin da sukayi wa wata malama suka mata mugun duka mazan Kuma suka mata fyade Hakan yy sanadiyyar mutuwarta, an Sami nasarar kama wasu yayin da kafin azo kansu Idiyatu ta tattaro su sukazo gidansu muhsin, yasha mamaki matuqa ganin Idiyatu cikin bakaken kaya kamar 'yar fashi, murmushi tamasa tace "kayi mamakin ganina ko muhsin? To ba abin mamaki bane ganin cewa kaki karbar soyayya ta nikuma har yanzu Ina sonka Hakan yasa zan Maka adalci guda shine ko kabani kudade kimanin billion dari ko kuma..... " Takai karshen maganarta tana shafa wuyan zainab alamun yanka. 🌹 SIRIKATA 🌹 Na SADIKA IBRAHIM. Momsani. Bismillahirrah manirrahim. Pg09_10 Pg dinkine Ayshu kawar idiyatu. Ina Mika sakon godiya ta gareki *YUMNERH* nagode sosai Allah bar tare. Cikin rawar jiki da murya Muhsin yace "sister dagaske zaki iya kashe rai? Dagaske zaki iya kashe matata zainab? Duk irin halaccin da nai miki a rayuwa,innalillahi wa inna ilaihi raji'un" "shiiiiiiiiiiii"idiyatu tafada tana dora hannunta akan lips dinta alamar ya yi shiru. "Ai baka nemi zaman lafiyaba tunda kace bakaso na, my friend kinɗly nd silently go nd bring d money i demanded,or else..." tayi fito tana kallon sama tanuna zainab daketa kwakwume yaronta akirji. Bamusu muhsin yatashi wani daga cikin ƴan daban ya na binsa da wata sharbebiyar wuqa a hannu, sama suka haura har dakin muhsin yajawo side drower dinsa ya dakko wata ƴar jaka karama shaqe da kudi,dama banki ze kaisu besami dama ba yabari har gari yawaye se yakai, mikawa wnn ɗan dabar ya yi,amsa ya yi suka juyo zasu fito kenan sukaji jiniyar motar police, ai jiki na rawa ya ture muhsin ya sakko a tamanin kan kace me sauran ƴan dabar sunfara fita aguje aiko duk wanda ya fiya jikake fass an harbeshi,ashe me gadin da suka daure ne yasami nasarar kwancewa ya yi sauri yakira ƴan sanda. Jin anata sheqesu yasa Idiyatu tadaki kan zainab da bayan wuqar dake hannunta ai dasauri Muhsin ya yi kan matarsa,kasancewar basuda bindiga ko daya sede wukake da adduna, aiko nan take zainab ta sume kanta yafashe dauke yaron Idiyatu tayi da jakar kudin ta rataya tasawa yaron wuka a wuyansa wanda yafarka sakamakon faduwar da ya yi sanda aka daki mamansa akai, a hankali Idiyatu tafito riqeda yaron tasamishi wuqa a wuyansa fuskarta rufe rub da face mask. Ganin haka ƴan sandan sukaja da baya suna cewa "you are under arrest young woman, ki ajjiye yaron nan ko kuma muyi harbi" kara seta wuyan yaton tayi da wuqar hannunta aiko yasaki kuka muhsin yace "dan Allah karki cutar da yarona,baimiki komiba pls ki bani shi kitafi da kudin, i promise u ba wanda ze harbeki pls" yakarasa yana zamewa kan gwiwoyinsa, ko ajikinta haka tacigaba da tafiya da yaron yanata tsala ihu ga wuqa a wuyansa har tafata jimasa ciwo. Tana kaiwa waje tashige motarsu taja aguje tabar wurin aguje,aiko suna ƴan sandan suka rufa mata baya,haka taketa tsala gudu acikin wnn daren,gudu take iyakar iyawarta,bata tsaya ba har seda tabacewa ganin ƴan sandan nan,shiyoyin asuba takawo maƙera, Rabil ya yi kuka har ya gaji ya yi bacci, wani kauyen makera tashiga wani karamin garine babu yawaitar mutane. Koda gari ya waye tasami wasu ƴan tsirarun mutane tafada musu cewa ita bakuwace, tana neman gidan da zata saya ne,ƴan kauye baruwansu ganin ta da yaro kuma tafada musu dantane tabaro garinsune sakamakon fadan hausawa da yarbawa a garin ibadan. Gida madedeci tasamu tasiya, haka tabawa wani saurayi agarin sako yazo cikin gari ya siya mata komi na abinci da kayan da Rabil ze saka,komi na abinci tasiya motar kuwa wani guri tasamu taboyeta acikin kauyen. A cen bangaren su muhsin kuwa an baza jami'ai tako ina neman Idiyatu an rufe kowacce hanya da tashoshin mota,hatta airport ko ina an baza nemanta. Sam tunaninsu be basu zata iya zuwa kowane kauye ba ganin irin maƙudan kudin da ta amsa fiyema da yanda tayi demanding. Zainab tayi kuka kamar idonta ze fita itade koda yaushe batada abin fadi se sunan ɗanta Rabil da Idiyatu. Wani abin mmk shine an nemi hoton Idiyatu ko daya babu ataredasu,shidama muhsin bashida hotonta a wayarshi,mama ce hotonta dayawa amma abinda yabawa kowa mamaki shine babu hoton idiyatu ko guda a wayar mama,su dama ƴan sanda basusan fuskartaba, wayon tsiyane da ita ko a school bata hoto bata yadda da hoto ko video ba,hakan yasa aka rasa ta yadda za,a samo koda me kama da ita,har school anje ko alamar takaddunta babu balle asami koda irin ɗan karamin hotonta na passport. Haka Idiyatu tayi ta zama a wannan kauyen dako sunansa bata saniba sedaga baya da hankalimta yakwanta ta aminta cewa koda wasa baza a iya zuwa nan dasunan nemantaba sannan tasan sunan ƙauye, har tsawon shekara hudu lokacin sana,arta ta tireda yabunƙasa sosai,Rabil kuma ya yi girma abinsa shekararsa shida cikin na bakwai yaron akwai wayo sosai betaba sanin ba idiyatuce mahaifiyarsa ba tsawon wnn shekarun ba abinda yarasa yana zuwa islamiyyar garin tareda yara ƴan uwansa harda ƴar primary din garin wadda a yanzu an ɗan sami cigaba a garin har boko akwai sannan an musu famfuna ga wutar nepa da sukeda ita available. BAYAN SHEKARA GOMA. A wannan lokacin Idiyatu tayi haramar barin garin BODIN SADAU,shine kauyen da take zama da Rabil ɗanta, takoma ibadan da zama acen tasa shi a makarantar boko ta Barrak da islamiya. Rabil yarone me matuqar hankali da nutsuwa,bagashiga abinda ba bu ruwansa,sannan becika tsawwalawa akan lamariba ko wanne irine,baya shiga abinda ba bu ruwansa ko kadan. Wani abin al ajabi shine Idiyatu tanason yaron Muhsin da ta sace tamaidashi ɗanta,tabashi ilimi sosai na boko da islama. Har ya yi sauka, afannin boko kuwa yana shekarar kashe a secondary, idiyatu makwadaddiyar mace ce ga zafin nema,duk yadda kake da ita bakacin abinta ta sauƙi,ta iya maida taro yakoma sisi,amma akan ɗanta Rabil zata iya kashe ko nawane. Haka taci gaba da zama a garin ibadan cikin unguwar sabo,inda duk hausawa sunfi yawa a gurin. Rabil yafara soyayya da wara yarinya ƴar makotansu fulani ne, yarinyar marainiya ce babanta ya rasu, Fatima shine sunanta, Idiyatu batason yarinyar ko kadan acewarta fulani mugayene. Ahaka soyayyar fatima da Rabil tayi nisa sosai har manya suka nemi yaturo. To anan nefa akeyinta,dama a koda yaushe idan Rabil ya tambayi Idiyatu ina ƴan uwansu da babansa, seta ce masa basuda kowa a rikicin fulani da makiyaya na cen kauyen da suka baro aka kashe kowa nasu,hakan yasa be takura kansaba sbd Idiyatu ta masa komi a rayuwa tazama uwarsa,ubansa,danginsa,hakan yasa baya wani damuwa. A shagonta na saida drinks dake ita bata zauna hakaba tun kudin da tayowa baban Rabil fashinsu take jujjuyawa kuma se Allah yasawa abin albarka,dawowarta ibadan tabude babban shago kato nasaida duk wani nau'i na drinks ba bu kalar da bata siyarwa. A cen tasami wani mutumi cikin wadanda suke sana'a tare tabiyasa akan yaje nemawa Rabil ɗanta auren Fatima duk da cewa ba wani son ta takeba amma yaxatayi tunda ɗan lelenta naso. Itama ɓangaren Fatima wani maƙocinsu ne ya amshi matsayin babanta tunda ana zaman mutunci,abinka da auren marasa asali cikin ƙanƙanin lokaci akasha bikin Fatima da angonta Rabil. A lokacin Rabil yafara kasuwancin saida shaddodi kala kala da yaduka different design. Daga baya ma da abin ya yi albarka harya bude katon shago ana kawo masa kaya daga garuruwa daban2,da kasashe. Cikin shekara biyu da auren Allah yamasa wani irin nudifi ya bunƙasa sosai. Sede har lokacin babu alamun ciki atareda Fatima, abinda basu saniba shine....... # FLASH BACK# Wata biyar kafin auren Rabil Idiyatu taje wani shopprite ta sai mayukanta na bleacing,wanda Rabil ya yi fama akan ta dena taƙi, tana tafe tana zaɓen wanda yamata tana ƴan wakokinta,taji an dafata tabaya ance wanake gani kamar Idiyatu kawata.. Juyowar da zatayi idonta yasauka fess cikin na Biba kawarta. Mamaki,tsoro, da shock su suka rike Idiyatu na ƴan mintoci, seda Biba taɗanyi waving hannunta agurin idanun Idiyatu sannan tayi firgigit tadawo daga dogon tunanin da ta lula,kawai seta fashe da kuka tafada jikin Biba,kuka take mecikeda kissa da makirci,fadi take "ki gafarceni kawata, dan Allah kimin aikin gafara an cuceki kuma an cuceni nima, sebayan tafiyarki nagane cewa ashe malamin da muka kaiwa aiki ashe akaina ya yi aikin ba akankiba, nima wlh bada sanina hakan tafaruba,kuma bayan tafiyarki zayyad yadinga kuntata min,dukan yau daban na gobe daban,wahala kala kala ba bu wadda bansha ba a hannun zayyad ga tsohon ciki yabarni dashi karshe yamin duka kuma yamin sakin wulaqanci babana saboda baƙin ciki yafadi yamutu,bayan rasuwarshi da wata daya mamana ma takasa juran rashin mahaifina itama tarasu,haka naita wahala nikadai babu matemaki daga bayan nakama wanki da surfe har Allah ya saukeni lafiya na haifi namiji daga nan nacigaba da wanki na da surfe har Allah yamin arziki nadawo nan da zama,yanzu hakama auren yarona saura watanni kadan". Se yanzu tasauke numfashi daga karyar da take shararowa........ 🌹 SIRIKATA 🌹 Na SADIKA IBRAHIM. Momsani. Bismillahirrah manirrahim. Pg11_12 Biba kallon Idiyatu kawai take da madaukakin mamaki, Amma bata bari Hakan ya nu na ko a fuskartaba. Cikin ranta fadi take lalle Idiyatu takai makirar mace, Kuma zata nuna ma ta lalle itama ba baya ba ce gurin makirci. Murmushi tasaki itama cikeda kissa tace "ayyah kawata karki damu komi yawuce, Allah ya yi ni ba matar zayyad bace kece matarsa, karki damu komi ya wuce nayafe miki". "Nagode sosai kawata bani labari bayan barinku garin kontagora ina kuka shiga?" Ta tambaya tana tsare Biba da ido tarda Jan hannunta suka koma gefe inda aka tanada domin zama. Ajiyar zuciya Biba ta sauke kafin tafara bawa Idiyatu labarin bayan barinsu garin kontagora da iyayenta.... "Muna zaune munata jimamin yadda al'amarin auren yakasance dama baba ya fita kawai seganinsa mukayi yadawo afujajan yana cewa maman mu muhada kayanmu zamu bar wannan garin yanzu base anjimaba,munata tambayar sa ko lafya amma baba babu abinda yake iya fadi se kuyi hanzari mu are garin na,haka muka hada kayanmu cikin wannan daren baba ya yo shatar mota muka kama hanya Wanda shikansa baba besan Ina muka nufaba,seda mukayi nisa sosai kafin direba yake tambayar baba in muka nufa, budar bakin baba se cewa ya yi duk inda kanufa ka kaimu cen,kideda mamaki muke kallon baba gashide a zaune amma daganinsa kasan ba kalau yake be,Muna fita daga cikin garin kontagora baba ya ja wani dogon numfashi kamar a lokacin ne yake samun 'yancin shaqar ta. Bayan mun bar garin kontagora nida iyayena a wannan daren bamu tsaya a ko inaba se suleja, cen kauyen *SULEJA* me suna *LAMBATA* Dake direban dan cen ne Koda muka iso asuba tayi wani wurin an idar da sallah, kinsan a wancen lokacin abubuwa basi tsada kamar yanzuba haka baba yasami hayar gida karami yakama da temakon wannan direban,. Bamu dade a garinba baba yakama sana,ar Saida kayan miya da yan kudin da suka rage masa, haka muka cigaba da zama a wannan kauyen har tsawon wata biyar Muna mutunci da wannan direban kasancewar makotan muke dasu,Shima yana zaune da mamansa da babansa saurayi ne, munsaba dashi sosai dan yazama abokin yaya muktar munzama kamar yan uwan juna ahaka muka fara soyayya har takai aka mana aure, da fari muna zaune lafiya da iyayensa watan mu uku da aure SIRIKATA tasani a gaba wai banyi cikiba, kullum setamin gori kamar na shekara, tun ina kuka har na dena, mijina me suna Lukman yayi ta lallashina idan tana min gori, daga baya na kile nafara tsula mata iskanci San raina idan takama min fada Sena faki idon danta in mata gwalo, ranarda na fara mata haka ranar munga tijara kamar zata dake mu nida Lukman, fada take kamar me nikuma inata fakar ido Ina mata gwalo da dakuwa, daga na ga ze juyo se in hau share ido azuwa kuka nake. Wata rana da na gaji da halinta nashiga bandaki zanyi fitsari tafara sababi wai naki haihuwa se de inci in buga katon kashi, Kuma nayi na bata guri zata yi wanka, nagama uzurina na fito tashiga tanata banbamin fada kan ta fito na kada kuka da ruwa na zuba mata a dede kofar fitowa daga ban daki aiko tana fitowa santsi ya kwasheta ta zame jikike dibbb tasha kasa tasaki ihu me karfi sekuma tayi shiru. Ina labe Ina kallonta nayi dariya nace Allah Kara munafuka, nashige daki na narufe nahau bacci, se wajajen la, asar naji hayaniya kamar ana kuka, tashi nayi aiko naji muryar Lukman yana kwalamin kira da gudu na fito Ina mitsike ido Aiko nayi arba dashi rikeda mamansa Babu alamar rai atare da ita nanfa hankalina yatashi karde tun faduwar da tayi wajen 12 na rana bata tashiba aiko nashiga uku... "Kikama min mana kintsaya kina kallona ko tunanin me kika tsaya yi a wannan yanayin" muryar Lukman tadawo dani daga duniyar tunanin da na afka. Kamata mukayi muka kaita asibitin cikin gari dake da motarsa shiyasa muka isa cikin kankanin lokaci. Likitoci dayawa akanta tunda Lukman ya dawo da kudi dayawa a hannunsa aka hau dubata, seda aka dauki lokaci me tsayi sannan suka fito still suna tattauna wani abin a tsakaninsu, nide Ina gefe duk na tsure, ga babansa a gefe se Jan charbi yake, kasancewar Muna hanya Lukman din yakirasa yake fada masa abinda yafaru da maman Wanda yagani da idonsa. Inda suke muka isa Lukman d babansa har suna hada Baki wurin tambayar meya sameta. Kallonsu likitan yayi ya ce subiyoshi office dinsa, bayani yake musu cewa mama fa tasami matsala a spinal cord dinta, sannan saboda dadewa da tayi a kwance sakamakon faduwar da tayi tasami shanyewar barin jiki sbd haka sede hakuri. Kuka Lukman yake kamar karamin yaro likitan se hkr yake bashi baba ma kukan ne kawai beyiba. Nikuma nayi tsuru tsuru kamar banda gaskiya, to Ina na ganta" tafada tana kashewa da dariya kafin tacigaba da fadin! "Haka akacigaba da jinyar mama wadda ko magana Bata iyayi sede tabi mutune da kallo ga bakinta Daya karkace se miyau kw dilala,yan gidan mu suna kokarin zuwa kullum har aka sallameta bayan mundawo gida se Kuma jinyarta yadawo kaina sbd baba baya iyawa jikin girma ga maman Lukman ba kadanba, nice wankanta tsarkin kashi, abincinta yayinda Lukman yake fita nemo mana abinci, nafara gajiyawa sbd kullum seta kima kashi ba kadanba nikuma duka kayanda tayiwa kashi sede in zubar bana wankew itama wataran SE inbarta da kashinta inje in kwanta abina seta dankare mata ajiki kafin inzo insaka tsintsiya dashi zan mata tsarkin bayan nasa face mask ato Ina zan iya wankin kashin gardiya, ga wari kamar mecin mushe wallahi,. Ahaka nafara laulayi me zafi sosai lokacin shekararmu daya da rabi da aure hakan yasa bana iya mata komi se Lukman yasamo wasu manyan mata biyu a nan cikin kauyen suke mata komi Nima suna dan yimin wani abin dan bana son girkinsu sbd kazantarsu nakeji. Haka cikina yakai watan haihuwarsa mama sede ta kalleni da tsiririn ciki abinda take so Amma ba halin magana Baki ya karkace. Watan haihuwata nace zani gida babanmu yahana wai sbd SIRIKATA ba lfy, Aiko mamanmu tace ba hakaba ai me jinya daban sbd haka Sena dawo Lukman besoba haka yakyaleni nakoma gida cikin iKon Allah na haifi dana namiji me kyau kamar babansa aranar da aka fadawa maman Lukman na haihu tayita kuka alamun murna Amma ba bakin Fadi, ga jikinta kullum ba sauki abinka dame karamin karfi, haka mama ta lalace takare akwance wataran masu jinyarta daya tafita dayar Kuma tana sallah aiko mama tafado daga kan gado wuyanta ya karye ko shurawa batayiba. Bayan tayi sati da rasuwa nadawo gidan haka naketa renon yarona me suna Awwal shekararsa daya da wata bakwai na yaye sa, daga kansa Kuma bankara haihuwa ba. Daga baya muka dawo cikin garin SULEJA nan akasa Awwal a school har yagama primary Allah yayiwa Lukman budi akasa Awwal a private school yayi ya gama lokacin mijina Lukman ya Yi kwari yazama oga sede yaransa su ja masa motocinsa yana zaune akawo masa kudi. A lokacin da Awwal yagama secondary school ya nuna yafison kasuwanci akan ya yi karatu shikuwa Lukman ba mutum ne me tsanani ba duk abinda muke so shi mukeyi dagani har yarona Awwal. Haka aka Bude masa babban boutique yana Saida kaya kana nan kaya masu kyau latest har yazo ya abin yayi albarka ya karawa ahagonsa girma yazama babban dealer Yana kawo duk wani sabon design na kaya irin na yaran masu kudi kala kala. A haka yasamo wata yarinya acikin garin Abuja yarinyar ba masu Hali bane sunade da rufin asirin su Amma Basu kaimu ba agidansu yarinyar ma mamanta itace bolar gidan shiyasa bana sonta amma Lukman yadage shi abinda yaronsa keso Shima shi yake so banaso amma hakanan yashige gaba tarda temakon babana aka nemowa Awwal auren mufida aka daura musu aure. Watansu biyu da aure tafara laulayi nikuma Ina fahimtar cikine da ita kawai nasa mata magani a abinshanta Tasha ya zube Kuma nabiya likitan kan cewa ya tabbatar wa Awwal cewa ita Tasha dakanta, dalilina shine banason tahaihu da dana Sena samo masa mace yar masu kudi sannan zan bari ta haihu. Aiko ranar Awwal kamar ze saketa, haka babansa yayita tausarsa har ya hakura daganan Kuma nasami dama seda na zubar mata da ciki sau biyar, yar banza kamar akuya Se saurin daukar ciki, daga baya ma Sena koma ta karkashin kasa nahanata haihuwar kwata kwata, Amma dake Awwal nason matarsa yaki sakinta nikuma bazan bari ta haihuba. Yanzuma nashigo ibadan ne dan naji ance yarbawa sunfi iya asiri inasone insamu Awwal ya auri wata yar abokin babansa me suna alhaji Tukur dollars, yarinyar wayayyiya ce yar gayu gashi babanta me kudi ne sosai Kuma ita kadai Allah yabasu". # Karshen labarin Biba# Sauke ajiyar zuciya Idiyatu tayi aranta tana cewa ayyah Biba u r still silly nd naive little girl I know year back. Anan itama idiyatu take fadawa Biba yadda ta tsani yarinyar da Rabil danta ze aura ahaka suka ajiye kan cewa zasu wurin bokan tare kowa yaje da bukatarsa. Seda su Biba sukaje gurin malamai ko ince bolaye har biyu sannan Biba takoma Abuja, a gurin zuwa wurin malaman ne sukayita fada sbd Idiyatu tanuna halin ta na mako lols. # End of flash back# Itade Idiyatu abinda yasa batason matar Rabil ta haihu shine tana tsoron Rabil yafara tara yara yadena damuwa da ita Gani take kamar idan ya haihu bazata Sami gadonsa da yawa ba, sannan ya Sha fada mata cewa idan Allah yabashi yarinya ko yaro komi na dukiyarsa da sunan dan ko yar ze mayar akan komi na dukiyarsa. Kenan ita ta tashi a tutar Babu duk wahalar da tasha gurin renonsa ace Allah yamasa arziki tana kallo yamayar da dukiyar sunan iyalansa ita kuma ko oho. Ita tayi ruwa tayi tsaki ta hana matar Rabil haihuwa ta hanyar bin malamai da bokaye. Dalilin zuwansu kauyen kontagora kuwa shine Fatima matar Rabil tayi barin cikin wata biyu, Hakan yatayarwa da Idiyatu da hankali kenan asirinta y karye kenen, hankali tashe takira Biba take fada mata shine Biba tace mata ta shirya suje kontagora ansami wani mashahurin malami, arikice Idiyatu tace "kontagora? Eh.... Umm... Aa... To yaushe zamu dake umm.... To yaushe?, Kode nabaki kudin kijemana in yaso base najeba" Biba tace allanbaran se Idiyatun tazo sunje inba hakaba abarshi dan ita yanzu batada matsalar komi. A dasauri Idiyatu tace zataje, sbd tayi wani tunani aranta cewar yanzu kilama Muhsin baban Rabil Kila basa garin kontagora a yanzu, fa wannan suka ajiye ranar da zasuje kontagora, shine da akaje gurin malam buzu idiyatu ta nuna halinta na mako lols. Bayan duk inda zataje da katon hijabi da face mask take zuwa kar azo asamu Wanda yasanta taganta asami matsala. Wanda ko Biba batasan dalilin Idiyatu ba na yin wannan shigarba ta dauka kawai sbd yanayin garin ne sbd hunturu da ake..... # Karshen labarin idiyatu da biba# ____________________________ # Wacece mahaifiyar na gwaggo #??? 🌹 SIRIKATA 🌹 Na SADIKA IBRAHIM. Bismillahirrah manirrahim. Pg13_14 WACECE MAHAIFIYAR NA GWAGGO??? Fatima zarah, shine cikakken sunan ta, yar asalin kauyen Babban rami ce, ana cikin garin kontagora suna zaune da iyayenta acikin garin kontagora unguwar Bagaya babanta principal din makarantar Maidubu primary school ne. Tayi primary da secondary school dinta a wata makarantar kudi me suna Mustapha Bello comprehensive school. Tana karamar secondary wato j.s.s 3 sun Sami Hutu me dogon zango shine taje kauyen Babban rami domin tayi hutunta acen tareda kakannin ta, kakanta mahaifin babanta me suna mlm Abubakar shine me garin wnn kauye a wancen lokacin, inda mahaifiyar babanta me suna mama Laure suke zaune a cikin kauyen. Mahaifin na gwaggo wato Sani yaje hutu kauyen shina kasancewar Shima dan asalin kauyen Babban rami din ne. Tafito tazauna dan nesa kadan da dandalin inda take hangen yan mata yan kauye da samari anata rawa da gada a dandalin matan rigunansu daban da zanin jikin su hakama Dan kwali daban, itakuwa shigar riga da Zane ne na atamfa ajikinta se wani dan gyale kalar kayanta data yafa akanta tana kallonsu tana murmushi fuskarta Babu digon kwalliya ko kadan, yayinda yan matan kauyen kowacce fuska cikeda kwalliya irinta yan kauye. Yana gefe Shima cikin kayansa kanana riga da wando masu kyau yau karo na uku kenen yana ganinta zaune akan wannan dutsen ita bata shiga cikin masu rawarba sede tayita kallonsu tana murmushi, sallama yayi mata ta amsa tana kauda Kai gefe, yace "barkanki da hutawa yan mata" bata amsashiba tamatsa cen gefe murmushi yayi yace " Yan mata ke bazaki shiga cikin yan uwanki kuyi rawar ba? " Kallonsa tayi tace " mtwsss did I look lyk a villager's lyk dem? " Koda yake ma ta Ina kasan me nace mtwsss" tayi gaba abinta mamaki ne yacikashi Jin tayi turanci dama a wannan zamanin akwai mace karama kamarta wacce tayi karatun boko har take Jin turanci har haka a wannan kauyen? Ganin bashida me amsashi ne yajuya yabi hanyar tabi da kallo har tayi nisa yacimmata da Dan gudunsa yana mata magana tamasa banza yace " hey young lady koba kyajin hausa ne? " Juyowa tayi da mamaki tana kallonsa dama yanajin turanci tab ashe akwai me Jin turanci a wnn kauyen, mamakin ta yakasa boyuwa tace "dama kanajin turanci?" "Kadan ba" yabata amsa murmushi sukayiwa juna suka cigaba da tafiya. "Anan kauyen kikeda zama ne?" Yajefa mata tambaya. "Aa Hutu nazo agurin kakannina mlm Abubakar me gari" "Wow dama kece jikar me gari da akace tazo hutu yar gayu naji anata maganarki agari, Ashe kece"? "Nice" tabashi amsa. " Ni sunana Muhammad Sani Lawal, ni jikan dagaci Lawal ne nazo hutun karshen shekara ne agurin kakannina kasancewar sukadai suka rage min, narasa iyayena a hatsarin mota, inada mata da yara biyu mata farisa da Farida". Kallonsa take da mamaki be Santa ba amma yake gaya mata duk wannan kamar wata wacce suka dade dasanin juna. Murmushi yayi yace "kina mamakine Jin na fada Miki abubuwan da suka shafeni ko? To ba abin mamaki bane tunda kike zuwa kallo dandali kullum Ina lura dake bande tana miki magana bane se yau nide nayaba da hankali dakuma nutsuwarki Kuma nide kinmin amatsayin mata sbd haka idan badamuqa zanzo dakaina gurin kakan naki na nemi izinin zuwa wajenki idan ba damuwa Fatima zarah". Mamaki sosai yabata Jin yakira sunan ta , murmushi yasake yi yace "jinayi ana cewa sunan jikar me gari Fatima zarah Kuma yar gayu ce" Murmushi ne yasubuce mata, har seda tadara batareda tasaniba. Dede lokacin suka kawo kofar gidan me gari tamasa sallama zata shige yace" Baki bani amsaba Ina je inga kaka?" Aguje ta ruga cikin gidan tana kulle fuska, itakam ya birgeta sosai gashi dan gayu gashi ya iya turanci, sannan yafada mata gsky yanada mata harda yara, itakam bata shirya auren me mataba amma yabirgeta sosai. Kwanci tashi soyayya me karfi ta kullum tsakaninsu batareda tasaniba itade tasan kawai suna shiri sosai amma basoyyya take ba. Seda tayi wata uku cur Babban rami sannan tayi azamar tafiya lokacin ne kuma tayadda tanason Sani sosai, ada bata Sha awar auren me mata Amma yanzu gsky tanason Sani sosai. Hakan yasa tabashi dama yaje yaga kakanta shikuma yasanarda mahaifinta Wanda ita kadai Allah yabasu, be jaba saboda yanawa mahaifinsa biyayya sosai yace duk abinda akayi Dede ne. Ahaka kakan Fatima zarah da kakan Muhammad Sani suka yanke komi na auren Fatima da sani ansa lokacin biki nan da wata uku masu zuwa. Ahaka aka daura aure Fatima zarah isah da angonta muhmmad sani Lawal. Kasancewar da sunan kakansa yake bearing. Seda Fatima ta kwashe shekaru biyar Bata haihuwa lokacin harta gama secondary school ta dora da university, lokacin yaran uwar gidan sani naima uku mata, takara haihuwa bayan auren fatima, daganan Bata karaba, seda Fatima takai 200lv sannan tahaifi danta namiji santalele me kyau sosai kamar tayi kaki ta tofar aka sa masa suna Sufyan. Aranar sani yi yayi kamar ba a taba masa haihuwa ba seda yayi sadaka da rabin kudin account dinsa raguna biyu y yanka akayi sadaka Sanna ranar suna aka yankawa Sufyan raguna biyu da katon saa, itade naima idone nata batada hayaniya ko kadan hakama yaranta me hayaniyar dayace batula wacce aka Haifa bayan auren fatima. Haka Sufyan ya taso cikin kulawa kamar me kowa sonshi yake gashi bulbul abinsa kyakkawa, yannensa mata sunaji dashi komi suka samu Sufyan. Mahaifiyar Sufyan takasance masifaffiyace sosai fadane da ita kamar me, ga Neman fitina yayinda uwar gida naima takeda sanyi batada matsala da hayaniya ko Fatima ta takaleta Bata kulata har ta gaji tabari daga baya dataga ba riba seta koma kan yaran Abu kadan duka da fada kuma tahanasu daukar Sufyan gashi sunason daukarsa amma tahana wai karsu yarda shi. Harta gama karatunta na university tasami aikin teaching lokacin ta yaye Sufyan yana tafiyarsa ko ina, agidan take barinsa gurin naima. Bayan shekara goma.. Lokacin Sufyan yana ajin karshe ta primary a school dinda Fatima mahaifiyar sa take koyarwa, ana musu graduation na gama primary 6,angama sunkama hanyar zuwa gida suka hadu da hatsari inda nan take mahaifinsa Sufyan wato Muhammad Sani Allah yamasa rasuwa, itakuma naima tasami matsalar Karaya a cinyoyinta duka biyu, yaran kuwa babbar ma tarasu me suna zainab, se tabiyun me suna fatiha, se batula da autansu Sufyan da Fatima mahaifiyar Sufyan din su babu abinda yasame su, Fatima ce ma tabugu akanta Shima ba sosaiba. Wannan ahalin sunji mutuwarnan matuqa Fatima kamar bazata dena kuka ba, ahaka akayi arba'in inda bayan tagama takaba zata koma bakin aikinta, abokan marigayi suna temaka musu da kayan abinci harta gama takaba takoma bakin qikinta, alokacin ne Kuma akamata transfer zuwa wata makaranta tareda mukamin principal. Itake riqeda yaran naima uwar gida ita yan uwanta sun dauketa acen gurinsu take jinya tace abarmata sauran yaran zata riqe, tacigaba da zama agidan mijin nasu itada yaran. Haka rayuwa tayita shurawa inda Sufyan ya girma yannensa mata duk sunyi aure a hannun fatima, Shima aurensa yamatso se shiri suke ba kama hannun yaro auren dan gata Sufyan, Fatima tana nan da azabar masifarta Babu abinda ya ragu sema karuwa da yayi. Bayan auren Sufyan da shekara daya aka fara samun matsala da Fatima uwarsa, acewarta bataga amarya Aisha tana amai da tofar yawu ba, me ake nufine, ita tanason jikoki sbd haka idan ma planning suke to adena bataso. Tun suna daukar abin da wasa, suna cewa ai Allah ne bekawoba har Aisha tafara gajiya da abin, A shekarar su biyu da aure ne abin Fatima yafara tsamari badama Aisha tasake se habaici da masifa, Anki haihuwa se shegen cii kamar gara da katon kashi kamar yan firsin amma anki haihuwa. Dalilin da Sufyan na gwaggo ya dauke matarsa suka koma inda yake aiki wato garin Minna. Sunan na gwaggo da ake kiransa kuwa yasamo asaline alokacinda aka yaye sa aka Kaisa wurin mahaifiyar Fatima wacce ake cemata gwaggo itace take kiransa da na gwaggo shine sunan yabisa har girma. WACECE HAJIYA DEEJA??? Hadiza lashe money shine cikakken asalin sunanta. Yan asalin kauyen SULEJA ne suna Nisa sosai da cikin gari tana zuwa tallah cikin gari Amma idonta akan manyan motoci, duk wacce ta wuce seta auno kanta aciki wai itace me wnn motar, kullum tana mafarki da kula lissafin dukiyar rano, seta gama iyayi abakin titi tukunna take zuwa tallarta. Kyakkawar gaske ce fara kamar ba a kauye takeba, sede shigarta ce kawai zata sheda maka daga inda tafito. Tallar maganin daji take amma idonta idon me kudi itada uwarta karime mayun kudine gasuda munafircin tsiya, da tsananin Munafurci uwarta karime tasa mijinta yasaki matarsa uwar yayansa, takawo agolar yarta hadiza Kuma ta gallabi yaran. Ahaka wata rana tana talla tahadu da muktar yayan biba alokacin yana aikin tsaron wani katon gida,nawani baturene ana cikin garin SULEJA, balefi yana da kyau ga karya, ahaka ya yaudari hadiza lashe money da motar da ya tuko ta wannan baturen,yazo gari kasancewar baya zama sede yazo yakoma,shiyasa yadauki motar yabashi yakaimasa gyara gurin makanike shine ahanyarsa ta dawowa yahaduda hadiza lashe money, batawani yi karatu ba shiyasa batasan ma anar kayan jikinsaba, Dan kayane irin na masu tsaron kofar mall, ko restaurant haka, irin uniform din nan na masu gadi. Kullum se sunhadu adede kan junction susha hirarsu sannan yasiya mata ice cream da meat pie tayi take away taje suci d uwarta, daganan kan karime yakara girma ita me sa,a ce yarta tasamo me kudi, har maganar aure tashiga tsakanin su basusan me gadi bane, haka yasa babansu yaje nemar masa auren hadiza uwarta tayi Kane Kane tahana ayi kwakkwaran bincike, acewarta su masu kudi basa son yawan bincike, dama mijin nata ta shanyesa haka aka basu auren hadiza,akan sadaki dubu hamsin,tace ai albarka ake nema bayawan kidinba,dogo baban nera shine sunan da duk Yan kauyen dama ita kanta amarya sukasan muktar dashi, aka kaita gidan wannan baturen, kasancewar sa ba mazauniba Kuma yana barin makullin gidan a hannun babban me tsaron gidan wani inyamuri, shine muktar yabiyasa kudi suka hada baki aka kaita cikin gidan da niyyar idan bature me gida yakira ze dawo se yadauki hadiza akan zasuje ganin mamansa, seya wuce sudawo. Haka kuwa akayi ankawo amarya gidan da kowa seda yaji tsoro anata gulmar karime tasiyarda yarta wa me yankan Kai. Watansu biyar anacin amarci bature yasanar ze dawo, muktar betaba bari mahaifiyarsa tasan irin zaman da sukeyi da amarya ba, cemata yayi ai ogansa ne yabasu daki daya suzauna. Kuma duk tsawon watannin nan Bata taba zuwa ba, Shima Kuma be Kai hadizaba. Dawowar bature me gida shiyasa muktar ya tsiri tafiya shida amaryarsa wai zasuje kauye agaida mamansa,. Seda sukayi kwana 6 akauyen LAMBATA inda iyayensu sukeda zama sannan aka kira muktar kan cewa bature yakoma, shinefa suka tattara ya hau aniyar komawa. Seda suka kwashe tsawon shekara uku acikin wnn auren karyar, har yau batasan asalin waye Shiba tade lura suna zuwa kauye lokaci bayan lokaci.inda acikin wnn shekarun duk sanda bature zedawo se yasa akwashe kayansu bayan tafiyarsa akai boys quarters,in zasu dawo akwasao amayar,komi nagidan dakayan sawar na matar baturene,ake amfani dashi,. Yayinda yatare agindin matarsa komi yasamu natane itada uwarta, Yana mantawa da tasa uwar se in bature ze dawo inzasu kauye. Dake becika zuwa ba, seyafi shekara bezoba. Wani zuwa dasukayine kwanansu uku sukace zasu tafi, inda mamansu tadage setaje taga inda sukeda zama, aiko DEEJA tace batasan zanceba, seda muktar yayita lallashi shine fa ta yarda da sharadin bazata dade agurinsuba, ya yarda sbd Yana sonta matuqa, duk da haka ita abin bemata ba tana gudun tsohuwa taje tace bazata dawo kauyeba, waya ta dauka takira mahaifiyar ta karime tafada mata komi, aikuwa karime tadinga sababi wai za atakurawa yarta, bashiri tayi gurin nakan tudu akan amallake mata dogo baban nera da mahaifiyar sa,. Kwanan su biyar da dawowa taga tsohuwa taki tafiya aiko takara Kiran uwarta, uwarce tanuna mata karta nuna Bata son uwarsa agabanasa tanuna ai uwarsu ce gaba daya, daganan tamaida ita yar aiki. ______________________ Wannan shine tarihin kowa nacikin wannan labarin yanzu zamu tsuduma da kyau cikin labarin, muje zuwa. 🌹 SIRIKATA 🌹 Na SADIKA IBRAHIM Pg15_16 Bismillahirrah manirrahim. CIGABAN LABARI..... Bayan Idiyatu takoma gida da sati biyu fatima matar Rabil tafara wani shegen laulayi me zafi sosai Wanda yakai ko tashi bata iyawa, ga wani tari me tsanani idan tafara setayi amai da fitsari a gurinda take, sannan bata iyacin komi. Idiyatu bata temakon ta da komi sede in Rabil na nan y temaka mata, inko bayanan haka zata wuni tana wahala da Jan ciki take zuwa toilet tasamu ta gyara kanta tadawo kafin kace me wani tarin yasake tirniqeta laulayi take me azabar gaske, Idiyatu tasan laulayi take amma Fatima da Rabil basu saniba . Hankalin Rabil duk yakoma kanta yayi2 akan suje asibiti taki satinta daya ciwo yaqi cinyewa ya dauketa bisa dole sukaje asibiti gwajin farko ya nuna ciki wata uku da sati biyu Kuma yana cikin koshin lafiya, farin cikin da yayi baya misaltuwa, agaban Dr yayi sujudul shukur, Dr nata masa dariya tun a asibiti yakira Idiyatu da murnar sa yafada mata atinaninsa zatayi murna amma seyaji akasin haka dan wani irin ashar ta lailayo ta saki tacikin wayar kamar wata yar tasha sekuma ta kashe wayar diff. Jikin sa a mugun sanyaye ya dauke wayar a kunnensa, dama so yake yafara fada mata kafin yakira mahaifiyar Fatima amma abinda Idiyatu tayi yasa jikinsa yin sanyi harya manta bekira maman Fatima ba. Biba ma Koda Takoma gida tasami labarin daya kusa juya duniyarta, mijinta Lukman ya auro wata tsaleliyar yarinya budurwa wacce bazata wuce shekaru ashirin ba, yayinda mufida matar Awwal danta takeda cikin wata biyar. Abin yamata mugun bugu, an shammaceta iya shammata, tanacen tana fafutikar hana matar danta haihuwa ashe mijinta Yaena nan Yana gina mata kabarinta, abi mamakin ma bakowa bace yarrinyar da Lukman ya auro face yar abokinsa datakewa Awwal danta kwadayin aurenta wato Ihsan Tukur dollars. Suma Biba tadingayi ana zuba mata ruwa, daga ta farfado ta kalli mufida zaune kusa da ita da Dan cikinta Daya fara tasawa Wanda bata taba lira dashiba se yau, gefe Kuma ga mijinta Lukman da yar matarsa ihsan zaune kusadashi se manne masa take kamar mage, tana arba dasu seta koma duniyar sunanta Lols. Abude yaki ci yaki cinyewa seda aka dangana Biba da asibiti Wanda duk mufida ke dawainiya da ita dan Lukman kamar abin tsafi yatare gindin yar amaryarsa me shegen shagwabar tsiya, sede yazo yadubata yakoma, daga mufida se Awwal suke kulawa da ita tayi kuka hartaba uku lada, Kuma ta kudiri aniyar muddin tana numfashi adoron kasa se ta juya farin cikin Lukman da Ihsan zuwa bakin ciki. ******************* Abangaren hjy DEEJA kuwa,.. Da Koda Dr yashigo cemasa tayi bawata matsala yana iya komawa sbd mara lafiyar ma ba taji ciwoba muktar yanaji ba yadda ya iya Dr yajuya yatafi. Family Dr din baturene idan yazo Nigeria, yabada damar aduba duk wani ma, aikacinsa idan bukatar hakan ta taso bisa umurninsa. A bangaren innar muktar kuwa tanacen daki tanata matsar kwallah bame lallashin ta, yaranta biyu ne aduniya, muktar shine babba se Biba, dukansu gasunan de se gyaran Allah Biba tunda tayi aure mijinta Allah yamasa budi bata waiwayarsu acewarta ai tana musu aike duk karshen shekara, tanacen daga ita se danta, Wanda bata nuna masa darajar suba, shikuma muktar bata ma san inda yasa gaba ba, tarasa gane masa shine wannan gidan nasane ko Kuma uban gidan nasane ya ara masa?, Ita wnn Al amarin yana daure mata Kai. Ga azababbbiyar matarsa Bata ganin darajar kowa, Bata ganin kimarta amatsayin ta na SIRIKARTA, gashi takasa barin gidan kamar andaureta agidan. Kuma ma ko ba komai ai tanasamun jar miya ga katifar ta me laushin tsiya ga rabar AC Kodan wannan ai tazauna. Takai karshen tunanin ta tana zamewa takwanta akan katifarta katuwa. ____________________ "Assalamualaikum, assalamualaikum". "Amin wa alaikimussalam, haba mutum kamar makaho inata amsawa ko ba ajibane? Waye? Shigo ni nariga nazauna ban iya tashi wlh". Sanyo kansa yayi cikin dakin bakinsa dauke da wata sallamar, "wanake gani haka kamar nagwaggo? Aa maraba, maraba da babban bako yaushe a gari dan albarka? Tafada tana leka bayansa ganinsa shi kadai abin yaharziqata tafara banbamin fada, "Ina ita rasa kunyar take? Wato shine kazo Kai kadai dan karkazo da matarka na cinyeta wato ga bakar mayya ko? Wlh na gwaggo idan baka fita idona akan wannan munafukar matar taka ba ko hmmmm" "Dan Allah ki hkr mama batajin dadi ne shiyasa na barta amma wlh har kuka seda tayi akan mutaho tare ninace tayi zamanta tunda batada lfy" " Rasulullahi manzo dan Amina, na gwaggo yaushe kazama sallamamme sbd ba uwarta bace ni shiyasa kahanata zuwa wato dan karkazo da ita nahata komawa ko? To wlh ko kaso ko karka so se kadawo da yar iskar yarinyar nan cikin garin nan, wato ga yar Lele ko? Juyar mace har wata abin lallashi ce, amma balefinka bane zan San abinyi". Shide kansa akasa bece komiba harta gama kunfar bakin tagama, sede yace mata " kiyi hkr mama". Agefen oganniya idiyatu kuwa, tana kashe wayar takira mlm buzu tace " mlm maganarka ta tabbata wannan tsinanniyar cikine da ita", dariya yayi ya ce mata " me na fada miki tuntuni? seta haihu Koda zakiyi menene, Kuma wannan karon kisaurari abinda ze biyo baya" kit ya datse Kiran, safa da marwa takama yi acikin dakin nata, agaskiya bazata sabu ba taya zata bari matar Rabil ta haihu? In tabari ta haihu Hakan yana nufin duk dukiyar da yatara takoma mallakin abin da aka haifar masa, ita kenan ta tashi a tutar babu? No hakan bame yuwuwa bane bazata taba bari Hakan ta faruba bari tasan abin yi. Idiyatu ta manta maganar mlm buzu akan haihuwar Fatima, cewa inta matsa tofa ajalinta nakusa. Daga waya tayi takira Biba, a lokacin Biba tanacen tana saqe saqen yadda zata wujijjjiga rayuwar mijinta da Ihsan amarya sa. Kiran idiyatu ne yashigo wayarta inda nan take ta dauka, ba sallama tafara magana "Biba nashiga uku Fatima cikine da ita, da gaske maganar mlm buzu ta tabbata". Sauke ajiyar zuciya Biba tayi tace "ke matsalar ki jaririya ce akan tawa, ko kinsan irin ta addadancin da natarar agidana?, Ko kinsan irin wulaqancin da Lukman ya aikata min?" Hawaye ya biyo kuncinta take ta fashe da kuka nan talabartawa Idiyatu irin halinda take ciki da irin yadda Lukman ya banzatar da ita, dakuma labarin cikin matar danta Awwal Wanda batasan dashiba se yanzu. Wata irin ashariya Idiyatu ta lailayo tace " kan babban bujen dakarkari, mu za aiwa haka? Biba idan bamu miqe tsaye ba to lalle wata tonon asirinmune yatsaya". "To yanzu meye abin yi?" Biba ta tambayi Idiyatu,"abinyi shine kudi Zaki tanada muhau jirgi muje cen kasar nijer akwai wata bokanya nasan da munje gurinta komi yazo karshe". "Yaushe zamuje dan ni inaga yau bazan iya bacciba" cewar Biba. "Gobe gobe kishirya cewar Idiyatu" Koda rabil suka dawo dg asibiti direct dakin su suka wuce fushi yake da Idiyatu Jin batayi murna da samun cikin da Fatima tayiba se yayi fushi a tunanin sa zatazo tasamesa tunda batason bacin ransa ko kadan, Amma shiru har garin Allah yawaye, ganin shirun yy yawa ga sashen ta shiru kamar ba mutum aciki Tunani yayi kancewa bari yaje ya dubata, ko banza fishida iyaye babban zunubi ne balle uwa,koda yashiga shashen nata wayam babu kowa ko Ina arufe mamaki yakamashi to Ina taje da sassafen nan? Babu me bashi wnn amsar, juyowa yayi yakoma sashen su yana trying number din Idiyatu amma is not reachable. Abangaren idiyatu da Biba kuwa a hotel din Abuja suka kwana tun asuba suka gama Shirin su na tafiya nijer dake tun dare sukayi booking flight Wanda ze tashi karfe takwas. A airport takwas din tamusu suka Lula se kasar nijer, cen cikin wani kungurmin daji, a wani karamin kauye wajen gari ne sosai sunkashe kudi sosai kafin su Sami drop din taxi din da ze kaisu gurin bokanyar, a hanya suka tsaya suka dauki wani mutum Wanda shine zeyi musu rakiya har kauyen, mutumin Idiyatu ne run a Nigeria suka San juna, shi dan nan garin Niger ne. A gefen hanya me taxi y saukesu dan garin ko shinshinin kwalta babu, da kafa suka fara takawa har zuwa cikin dajin ga nisan tsiya duk sun gaji Amma sbd taurin rai da mugun nufi ko alamar gajiya basu nuna ba. Dede wani katon iccen kuka me ban tsoro ga duhu inuwarsa ta mamaye katon Fili acikin dajin dede wannan iccen suka tsaya, se gani sukayi wnn mutumin yafara cire kayansa yana ajiyewa agefe, seda yayi zigidir sannan ya kallesu sunyi tsuru tsuru kamar kace arr su fece aguje wage katon bakinsa yayi seda suka firgita wata mahaukaciyar dariya yakece da ita seda dajin ya amsa nan take wannan mutumin yazama wata katuwar tsuntsuwa yatashi sama yabarsu nan jikinsu na wata irin makyarkyata, duk sun jiqe jikinsu da fitsari Biba harda zawo tasaki. Dajin ne yadauki wata irin Kara kamar na ihun mace, daganan basu Kuma ganin komiba se duhu.... *Tofa Ina su Biba da Idiyatu suka kawo kansu? Mugun nifinsu Ina yajefo su? Kude kuci gaba da bibiyar labarina anan ne zakusan wane ruwa wadannan matan suka ballowa kansu* Share fisabilillah 🤲 Momsani ......... ✍️ 🌹 SIRIKATA 🌹 Bismillahirrah manirrahim. Pg17_18 A mugun firgice Idiyatu ta farka daga mummunar mafarkin da take, tafarko da ihu da wulle wulle harseda ta fado dg kan gadon hotel din da suka kama a Abuja itada Biba, ihunta ne ya farkar da Biba ta tashi agigice itama tana neman gurin buya. Wayar Idiyatu ce tadauki Kara har seda ta firgita jikinta na karkarwa ga wata zufa data wanke mata jiki kamar tayi wanka, ga zaninta da takeji da danshi alamar kamar tayi fitsari a kwance, wayarce ta sake daukar ruri alamar ankara kira da sauri Biba ta dakko wayar tamikowa Idiyatu wadda jikinta be bar bari ba har yanzu. Amsar wayar tayi jikinta na masifar rawa faduwa kasa wayar tayi ta dakko hannu na rawa ta dauka, muryar Rabil ce ta dakin dodon kunnenta inda yake cewa "assalamualaikum mom Ina kika shiga baki kwana a gida ba? Hankalina yatashi sosai dana duba banganki ba, baki fadamin Zaki fitaba balle ki kwana" Tattaro yar ragowar jarumtarta tayi tace "son Ina nan cikin garin Abuja ne Biba kawatace batada lfy an kwantar da ita asibiti shine nazo, sorry hankalina yatashi shiyasa ban fada maka ba amma in Sha Allah nan da karfe 2:00 na rana zan dawo". Seda yamata magana kafin ya kashe wayar. Jikin Idiyatu na rawa ta tashi aguje ta afka toilet ba soso ba sabulu ta watsa ruwa tafito aguje kamar zomo se guje guje take, ba sallar asuba har karfe 10:00 na safe, ta hau hada kayanta a cikin yar Jakarta Biba de se kallonta take cen de takasa hakuri tace " wai idiyatu ban gane mikiba kin tsoratani da iface ifacenki yanzu Kuma kin kama guje guje kamar bera yaga mage Sanna Kalli gadon ki da alama fitsari kikayi akwance, baya ga haka kin hau tattare kaya gashi naji kina waya cewa nanda karfe 2 na rana kinkoma gida, me kike nufine? Batun zuwanmu nijer din fa? " Idiyatu ba baki se hada kaya take duk a tsorace take, Biba de abin ya isheta amshe jakar Idiyatu tayi tace " kinsan Allah sekin fadamin abinda kike Shirin yi". Idon Idiyatu jajur cikeda bala'i tace " bani jakata Biba, yau koda zankoma insamu Fatima ta haihune wallahi wallahi bazanje nijer din nan ba, kinkosan bala'in da nagani? Kinsan abinda nagani cikin mafarkina gameda zuwan mu nijer kuwa? To wallahi sede ke kije nikam bazaniba in Sha Allah yau agidana zan kwana" takai karshen zancenta jikinta na bari dan har yanzu yadda wannan mutumin yazama wata katuwar tsuntsuwa yana mata gizo acikin kanta da idanunta. Cikin muryar lallashi Biba tace "haba kawata kinfasan kudirinmu, kinsan abinda zekaimu garin nan bakaramin abu bane taya haka kwatsam dagayin mafarki Wanda kowa yasan ba gaskiya bane sekice kinfasa tafiya? Dan Allah kiyi hakuri kidaure muje mudawo, Dan wlh ban hakura ba Kuma bazan hakura ba, duk abinda Lukman yamin Sena masa fiyeda yadda yamin, Sena gana musu azaba shida munafukar amaryarsa ke hatta iyayen ta bazan barsu ba". Idiyatu Bata tsaya wata wata ba ta dauko wani kati acikin Jakarta tabawa Biba tace "duk abinda kike nema gameda zuwa kasar nijer idan kika kira wannan lambar an gama, Amma nide bazaniba nafasa Kinga tafiya ta Allah yabada sa, a". Taja Jakarta tayi waje drop tadauka na mota daga Abuja zuwa ibadan, sbd babu jirgin da ze tashi a lokacin itakuma duk bala,i yau seta kwana a ibadan cikin gidanta. Biba kuwa ba Bata lokaci Kuma batareda ta damu da tafiyar Idiyatu ba ta fara gwada Kiran wnn numbers din na jikin katin. _________________________________ Kontagora Niger state. MUHSIN BAGO'S RESIDENTS... Tsaye take ajikin window din dakin ta dage Hawa na uku, idonta sanye da glasses fari medicated, Jan numfashi tayi tana sauke ajiyar zuciya sakamakon Jin hannuwa akan kafadarta, "my zee wai yaushe Zaki dena wannan tunanin ne umm? Kullum kuka da tunani tsawon shekaru 30 haba dan Allah karki kasance mara tauhidi mana, Allah daya bamu Rabil yafimu sonsa shiyasa ya amshesa, kisawa ranki dangana, Dan Allah kindeji abinda Dr yace akan ciwonki ga idonki ma sbd kuka har sun fara samin matsala, pls kibarwa Allah komi, gashinan Allah yakara baki wasu yaran har biyu ga Aziza ga Radiya, Kuma duk Allah yabasu mazaje kowacce tayi aurenta sbd haka dan Allah kidena damuwa kinji? Kuma Rabil in Sha Allah me ceto ne" Da hanzari tajuyo tana dora hannunta aka bakinsa tace " a,a yarona yana raye be mutuba in Sha Allah yakusa dawowa gareni yarona is still alive he's alive he's aliveeeeeeee" se tazube ajikinsa tana mimmikewa kamar me farfadiya, innalillahi "zainabbbbb Kinga abinda nake gaya Miki ko? Innalillahi yayi saurin lalubo gefen drower din gefen gadon ya dakko wata allura nanda nan ya tsira mata ita a hannunta dede jijiya, nan take jikinta yasaki sekuma ta tafi duniyar bacci, bacci me cikeda mafarkan danta tilo namiji wato RABIL.... Muhsin kenan mahaifin Rabil Wanda Idiyatu tasace sa tun yana yaro, zainab mahaifiyar Rabil takamuda cutar damuwa(depression) dakuma cutar jijjiga (seizure) idan ta tuna da Rabil nan take zata Sami attack tafara jijjiga Hakan yasa seda likitoci suka Samar mara da allura wacce dazarar ta fara jijjigar idan ayi mata ita take samin bacci Koda zata farka Kuma normal ne kamar bata yi ba. Acikin wnn yanayin takara haihuwar mace aka Sanya mata Aziza seda tayi shekaru biyar sannan ta haifi Radiya wacce daga kanta bata Kuma haihuwaba, tsakanin Rabil da Aziza shekara ukune sbd sanda aka sace Rabil shekararsa biyu Kuma alokacin zainab nada shigar ciki Wanda basu San dashiba se bayan faruwar al'amarin Wanda iKon Allah ne kawai yasa cikin be fitaba shekarar Aziza ashirin da tara, Radiya Kuma 25. Dukkansu sunyi aure, Radiya tana aure a sokoto tana auren Abubakar Sadik zayyad. Itakuma Aziza tana aure nan cikin kontagora unguwar GRA phase 1. __________________& Karfe uku na rana Biba ta sauka a garin nijer a cikin birnin niamey. Da kwatance wannan mutumin harta kusa isa inda yake tana kan mashi suna waya, Dede wani karamin kauye Sega gungun shanaye wani bafulatani yana kiwonsu,wasu shanaye guda biyu ne suka hauro kan hanya suna ta fada wanna fulanin yayi yayi sunki rabuwa har kan hanya sunata fada, jama a se gudu ake dan bil hakki suke fadan kamar bazasu dena ba, shikuma dan acabar da Biba tahau irin yan takife din nan ne ya fafaro aguje da ita ji kake cuss anyi Karo da dan acabar daya dauko Biba da wannan shanaye. Salatin mutane kawai Biba takeji akanta daganan Bata Kuma sanin inda kanta yakeba.... **************** Nigeria...... Se karfe taran dare sannan Idiyatu ta isa garin ibadan, duk ta galabaita tun dare rabonta da abinci gashi an tarbi wani daren,sallamar me mota tayi ta hau mashin yakaita gida, da sallama tashiga gidan inda tasami Rabil da Fatima zaune a garden din gidan tayi matashi da cinyarsa, yayinda shikuma yake Kara Kiran number din idiyatu tana fara ringing segata ta shigo gidan afujajan, se haki take duk tayi zuru zuru, dasauri Fatima ta tashi Shima da saurinsa suka tarbota Fatima duk da batajin karfin jikin ta amma dasauki ta daure ta amshi jakar Idiyatu suka nufi part dinta tana gaba suna baya Rabil tana tambayar ta akan dadewar ta bawan tace darana zata dawo, fada masa tayi a mota ta dawo shiyasa ta Dade har suka karasa part dinta yana tambayar ta jikin kawartata. SULEJA. Gidan alhaji muktar. Yana kwance dakin amaryarsa ta kanainayeshi ta hanashi fita se uwar shagwaba take zubawa wai seya mata goyon Doki, ba musu y ajiye gwiwowinsa akasa yace tahau yanata yawo da ita aransa yana tunani wai da girmansa amma shine yakewa yarinya goyon Doki sbd kawai ya aureta kamar a da ba ladabi take masa ba, baba sama baba kasa tana sunne Kai amma yanzu ta zanzare wai shi take sawa Doki gashi yakasa yimata gardama dan wlh tunda yakwashi garar amarci yake bala, in ji da ita baya iya mata musu gata da kyau yar karama fara tas da ita fa iya shagwaba Kuma abin mamaki kamar ba yar me kudi sosai ba ta iya girki sosai Kuma tana kokarin ibadan. Yana cikin tunani kawai yaji tasaki kuka yiiiiiii ta fado kasa daga goyon tana birgima akasa, ai dasauri a sukwane ya dawo daga tunanin da yatafi ya tallafota yana tambayarta lafiya me takeso me aka mata, cikeda tabara tace "bakaine kadena tafiyar dokin ba Kuma bakayin kukan Doki ba yiiiiii" taci gaba da kukan ta rungumeta yayi yanata aikin lallashi seda ta wainasa da kukan shagwaba sannan tadage hannuwa sama wai yacire mata riga zafi takeji ita yamata wanka. Haka ba yacce ya iya ya dauketa kamar baby yakaita toilet yamata wanka Wanda dole sukayi tare bayan ya kwashi gara ya goyota kamar yar yarinya yafito da ita waje kamar wai haka ya sauketa Saman bed zasu cigaba da aikin lada Sega Kiran waya, kamar baze daukaba sekuma yadakata da abinda yake Jin Kiran yaki yankewa daya yanke wani ze shigo, yana daukar wayar yaga bakuwar number Kuma bata Nigeria ba, picking yayi kawai yaji ana masa yaren french, kashewa yayi aka sake kira Yana dauka da Dan fadan sa yace "wrong number please" daga cen akace "dan Allah Ina magana da alhaji muktar Nigeria mijin Biba ne? " Gabansane ya fadi yace " eh shine Amma Kai wayene? " " Kana magana da Dr Mansoor Al mustapha daga nan niamey kasar nijer, mu Sami matarka ne tayi hatsari ankawota daga nan wani kauye kusada cikin gari, kwana 6 kenan Muna neman wani Wanda yasanta bamu samuba kasancewar tayi dogon Suma sakamakon hatsarin da tasamu acen Kuma mun nemi wayarta mun rasa se jiya muka samu ta dawo hayyacinta shine yau ta bamu number din ka muka nemeka dafatan zakazo nan niamey dake kasar Niger domin tafiya da matar ka Kuma kabiya kudin aikin da aka Yi mata? " Arikice yace " what Biba akasar nijer no ba matata bace matata tana nan Nigeria tana SULEJA taje gaida iyayenta yau kwananta takwas kenan" kuka yaji an saki daga gefen tacikin wayar sekuma aka amsa tana kuka tace " alhaji takemata min nice Biba matarka uwar danka Awwal Ina kasar nijer naje amsowa mama maganin ciwon kafarta shine tsautsayi ya afkamin nasami hatsari yanzu haka maganar da nake maka kashin cinyata ya karye seda aka Sanya min karfe ajikina" tafada tana rushe masa da kuka... Dogo baban nera residents. Hjy deeja ce taga mijinta muktar SE harhada musu yan kayansu yake hankalinsa duk atashe jikinsa SE rawa yake sakamakon Kiran gaggawa Daya Sami dg chief security na wannan gidan cewa megidan yana hanyar zuwa gidan Kuma wannan karon da iyalansa ya taho yanzu hakama an daukosa daga airport. Yana hanya yakusa isowa shine yaketa sauri sukwashe kayansu sukoma boysquaters kafin bature ya karaso. Karar motoci yaji Wanda seda cikinsa ya Murda kafin kace me anfara shigowa da kayan su, Sega matar bature me suna Isabella da yaranta biyu maza Fredrick da Danielo sun sanyo Kai cikin falon turus sukayi ganin wata mata zaune akan sofa sin falon ta kure ac tana kallo jikinta sanyeda wasu kananan kaya yar vest pusher pink karama da wandonta dede gwiwa ta mimmike ta bararraje ga lemo a gefe tana siffing.. ______________ Tofa yau ake yinta HAJIYA DEEJA gamasu gida sundawo faaa🏃🏃🏃 Share fisabilillah 🤲 Momsani........ ✍️ 🌹 SIRIKATA 🌹 Na SADIKA IBRAHIM. Momsani. *Takabbalallahu Minna wa minkum eidil MUBARAK alaina wa alaikum* # Kamar yadda muka tafi hutun ramadan kamar jiya yau gashi Allah ya kawomu munyi sallah lfy, inawa daukacin al'ummar musulmi barka da sallah, Allah ya maimaita mana# Ina Kara mika sakon ta'aziyya ta ga oum shaheed akan rashin bango Kuma mijinta Allah ya jaddada rahama agaresa. Haka zalika Ina mika sakon ta'aziyya ta ga 'yan uwan Rukayya surajo (*ummu Ameera*) Allah yajikanta da rahma, Allah Kuma yaraya abinda tabari. Bismillahirrah manirrahim. Pg19_20 Niger republic.... *Niamey* An sallamo Biba tareda dan ta Awwal Wanda shiyaje y dakkota, domin fafur alh Mansur yaki zuwa yace sede ta dawwama acen idan taji sauki ta dawo tunda be aiketa, dalili kuwa shine zuwan Awwal cen garin suleja dan Jin wani aikene kakarsa tayiwa mahaifiyar sa har niamey gashi tahadu da tsautsayi, Amma se yasami labarin cewa ai mahaifiyar Biba kusan shekara kenen bata gidan tabi danta muktar cen garin da yake aiki, shikuma mahaifinsu wato kakansa kenen yatafi kontagora watannni biyu kenen babu kowa acikin gidan su. Bayan fadawa alh Mansur wannan zance shine ya yanke hukuncin bazai tafi niamey duba Biba ba sede ya biya duk wani hospital expensive Daya dace yace tayi ta zama acen har sanda ta warke tadawo da kanta, Kuma ya gargadi likitocin kan cewa karsu Kara nemansa idan sungaji da ita su wurgota waje. Wannan dalilin yasa Awwal tafiya nijer ya dakko mahaifiyar sa wacce ta rame kamar kudin guzuri, gata babiyan bukata gashi tarasa kafa,ga bakin cikin idiyatu ta tadena kiranta ko ta kiratama bata samunta kamar ma block nata tayi, tun bayan da ta ari waya a cen nijer takira ta tafada mata cewa tasami hatsari har yayi sanadiyyar rasa kafarta, yayinda idiyatu taji wnn batu abakin Biba tasaki ihu da kururuwa tana cewa "dayanzu Nima banda kafar, da yanzu Nima sun halakani kamar yadda aka Miki", dif takashe wayarta tun ranar Biba Bata sake ji daga idiyatu ba, data ari waya takira ta tanajin muryarta seta zabga ihu tana cewa aceceta, daga baya ma karya layin tayi tayar, wnn shine dalililn dayasa Biba Bata samun Idiyatu. Sannan taki zuwa ta dubata, itakuma gashi batada no din kowa na Idiyatu ko no din Rabil batada. Da wnn ta kullaci idiyatu sosai acikin ranta, Kuma ta alakabta tsautsayin da yasameta da Idiyatu ce. # SILAH#( aysha danjuma). Sabo Ibadan.. Tunda Biba takira tafadawa Idiyatu cewa tayi hatsari tarasa kafarta shikenan Idiyatu ta tsure se gudawa take tana iface iface, tana zaune seta yanka ihu ita kadai ko bacci take seta farka afirgice tana tsala ihu kamar wata yarinya, bayan firgicin abinda yasami Biba, tana cikin tashin hankali Wanda tun ranarda tadawo bata bi Biba Niger ba take wasu mafarkayya masu ban tsoro matuqa. Zainab mahaifiyar Rabil take gani da wuqa tabiyo ta tana cemata kibani yarona, tana binta da wuqa tana kuka Wanda hawayen yakasance na jini,. Wannan yasa talalace ta yi baki gawata uwar rama da tayi, shikansa Rabil ya rame sbd abun ya hade masa biyu, ga ciwon Fatima lauyayinta me wahala, ga ciwon Idiyatu Wanda yakasance kamar shafar aljanu, Hakan tasa dole yamayar da fatima gida gurin mahaifiyar ta tana kula masa da ita, shikuma ya dakko wasu yarbawa biyu suna kula masa da Idiyatu wacce takoma kamar kazar mayu duk tarame se katon Kai da ido kwalakwala, idan ze tafi aiki se suzo,. Gidan baban nera. (Bature mansion) A gigice muktar ya afka ban dakin dake falon kasa, yanata gudanawa, dan wlh bakaramin razana yayi ba da ganin Isabella da yaranta, Dan yasanta farin sani batada mutunci, kadan acikin aikinta tasa akullesa bayan yasha tsinannen duka,. Danielo yakalli wata yar matashiya a cikin falonsu yace "wat d hell is that?" Yafada yana juyoda kallonsa kan uwarsa Isabella, kallonsa tayi takalli hjy Deeja wacce ke sanye da kayanta,sannan tayi daddaya acikin falon, kamar gidan ubanta. Bata Sami zarafin bashi amsaba bature ya sanyo Kai acikin falon,yayinda Deeja tamike tsaye cikeda gadara take kallonsu kamar bakin halitta,tana cewa "ku Kuma daga ina,Kode batan Kai kukayi ne?" Tafada tana kwalawa muktar kira da "baby kana ina ga wasu arna nan sun shigo mun gida har cikin falo kamar basuda hankali,wai inama securities din gidan ne?zaku shigowa mutun har falo mtwssssss" Kafin tarufe baki Danielo dan zafin Kai harya sauke mata mari abakin kuff, aiko nan take jini yabiyo bakin sharr, ai hjy Deeja ana kyalla ido akaga jini nan take tayanka wani uban ihu da kururuwa fadi take " wayyo nashiga uku barayi yan fashi da makami wayyo Allah atemaka min" taruga aguje tashige dakin da muktar mijinta yashige yaki fitowa. "Danny wat have u done huh,? Why r u always...." Be karasa ba uwarsu ta tari numfashin mijinta wanda yakewa dansu Danny fada akan dukan matar da dukansu basusan wacece ba, da fadin "am confused Hector wat is all dis? Who r dis people living in our house? Did you rent d house to dem or wat is all dis am seeing? and if i could remember well she's wearing my clothes as well?" Tafada tana kama dan tsukakken kugunta dayasha dauri da belt na mata me shegen kyau, jikinta sanyeda shigarsu ta masu jajayen kunnuwa. Kasa bata amsa yayi tunda bashida ita Shima, shi a iya saninsa Koda yaushe gidansa part dinsa a rufe yake, yana kasancewa abude ne kawai yayin da yake gari, Amma duk sauran parts din gidan ko ina abude ake barinsa tunda akwai masu aiki da securities, amma kamar ganin mace yayi acikin falon nasa Kuma idan ya fahimci maganarta kamar tana claiming cewa gidanta ne. Kasancewar shi yana dan Jin yaren hausa jifa jifa. Daga wayarsa yayi yakira chief security na gidan gaba daya kasancewar shi aka baiwa ragamar kula da komi na gidan, duk wani ma'aikaci kama dg mata har mazan, masu bawa flowers ruwa har masu kula da abincin gidan duk shine babban su, daga cen cikin wayar aka daga ana cewa "oga please wait for me, I dey for toilet doing shit oga" bature me suna Hector betaba Jin chief security nashi yayi pidgin English ba se yau Kuma da alama arude yake, dan tunda yasanar masa cewa ya iso airport aturo security suzo su dakko su shida iyalansa yaji wani wawan ihu da chief security yasaki har seda ya dauke wayar akunnensa, kafin ya kashe dan ya tabbatar yaji abinda ya fada, yasan akwai wata yar matsala, Amma atunaninsa Kila fita yayi yabar tsaron a hannun yaransa ashe wata tsiyarce suka kulla agidan Kuma yau zasu warware masa komi dan gidan su,, yafada aransa tareda fadin yazo maza yasameshi acikin babban falon gidan dashida duk wani ma'aikacin gidan. Aikuwa Sega chief security yana kuka akan sitter din toilet dinsu na ma'aikata, wandonsa a hannu fadi take "nashiga uku yau son abin duniya ta yajamin rasa aikina, Ina zaman zamana nabiyewa wancen shashashan me katon Kai gashi nan yajamin bala'i yuuuuuuhhuiii" yasaki sabon kuka haka yataso dagashi se dan wando da suit wandon suit din rataye a wuyansa, baya cikin hayyacinsa kwata2, haka yadanna kararrawar kiran duk wani me aiki acikin gidan, haka suka sameshi tsaye rataye da wandon suit din sa awuya gashida dan ciki kwai, se matsar kwallah yake, haka yayi gaba suka bisa abaya zuwa falon gidan seda seka Kai bakin kofa sannan yadawo baya yana muzurai yace " meye kuke kallona kamar na cenza muku wani yabude kofar nan Maza yanzun nan. Acen dakin da muktar da hjy Deeja suka boye kuwa, tasamesa yanata keta zawo dakin duk ya dume da wani gigitaccen wari, s magana take masa yaki kulata jikinsa duk yajike sharkaf da gumi, Fadi take "hubby baka ganin yan fashi ne agidan nan, Amma ka gudo kabarni dasu salon sumin fyade, dubi bakina yadda Daya acikin su ya zabgamin mari"tafada tana turo masa bakinta da yafara tasawa, duk wannan bayanin da take masa hannunta akan hancinta ta toshe sbd warin gudawarsa, snn kasa kasa take magana wai kar yan fashin suji. __________________ Idiyatu jiki Kam se a hankali duk tafara komawa kamar wata psycho, idan tana zaune kawai sede aga tasaki kuka tana fadin "wayyo Allah na, kidena bina wlh ba danki bane Dana ne wayyo karki daukemin dana" ire iren wannan abin yasa Rabil yashiga damuwa sosai gashi batacin abinci, Shima seya zabge kamar me cuta, idan anason samin sauki sede amata allurar bacci, Shima bawani jimawa takeyiba ta tashi tana ihu akan kar akwace mata yaronta, Se an riketa domin gudu take kwasawa kamar fa zararriya. Seda Rabil yafara amso mata rubutu sannan aka fara samin kanta kadan, domin anyi zarya asibitoci kala kala amma suce normal take kawai stress ne ke damunta da rashin bacci. Ahaka aka kwashe tsawon watannin biyar, lokacin tafara samin sauki sosai Se dan abinda ba a rasaba, amma totally tacenza kamar ba Idiyatu ba mace tsayayya fara tas ta bleaching, ga kwalliya amma yanzu tazama so silent shagon nata ma tadena fita se yaara ne kezama, Fatima kuwa haihuwa ko yau ko gobe, dan harta wuce edd dinta. Agidan alhaji Mansur mijin Biba kuwa, danta Awwal yasa anyi mata kafar roba ba inda Bata zuwa da kanta, Amma bazuwa unguwa tunda ta dawo mijin ta yadena kulata baya zuwa inda take amma komi na rayuwa yana Bata, kawai de ita dince tafice masa arai, sbd munanan halayenta Wanda a daa cen betaba lura dasuba se yanzu, da irin yadda tasashi yarabu da kowa nasa harda ubansa mahaifi, daga ita se dansa batason kowa yarabesu. Dakyar aka samu yafara kulata Shima sanadiyyar haihuwar da matar Awwal tayi tahaifi namiji yaci sunan alh Mansur, shine sanadiyyar kulata da yafara yi, sbd itace takewa me jego da yaronta wanka, dan tahana amaidasu gida, wani irin son yaron take kamar me, hakama alhaji Mansur yana matukar son yaron shine dalililn da yasa idan yazo duba yaron yadaukeshi Yana masa wasa kamar babba yayuta masa magana seta dinga Sanya baki, tun yana shareta har ya fara kulata kadan2. Bature Hector mansion.... Zaune suke jigum jigum kowa ya yi mukus, an gama rattabawa bature yadda muktar yamaida gidan kamar gidansa, komi da hjy Deeja take amfani dashi na Isabella ne. Muktar agefe ya sunne Kai kamar wani mumini, ga chief security Shima agefe wannan karon yayi gammo da wandonsa yadora Saman kansa se gyada Kai yake kamar kiski duk abinda Labaran me wanki da guga yafada se ya gyada Kai alamar hakane. Shi Hector gabaki dayama dariya suke basa, yadda Labaran me wanki ya daddage cikin pidgin English dinsa inda takakare masa yahada da Hausa ya kwaba, yana bada labarin yadda aka hadawa hjy Deeja plan kancewa wnn gidan na muktar ne har akayin auren, da yadda muktar yake biyan chief security kudin hayar gidan komi be gareba kakaf seda ya zayyana,sukansu muktar da chief security sunyi matuqar mamakin yadda akayi yasan duk abinda suka kulla,kamar agabansa akayi komi,kagansa sidi-sidi kamar Wawa ashe da hankalinsa kallon biri suke masa yana musu kallon iccen hawa, sauran ma'aikatan ma kansu mamaki suke sbd wani abin ma basusan yafaruba, sbd dayawansu tunanin su yana basu cewa megidan ne yabawa muktar damar zama adaya dg cikin dakunan part din ashe muktar dinku na Allah duka gidan ya mamaye tareda sahalewar chief security. Dadin dadawa ma hatta kayan sawar Isabella be bariba komi da komi hatta kayan hausawa Wanda Hector yabayar ayiwa matarsa bella daniyyar idan sunzo Nigeria tadinga sawa sbd shigar hausawa ta atamfa na birgeta, se yabayar ayima ta akwati kusan biyar yaso yamata surprised dasu, to su muktar yakwashe yabaiwa hjy Deeja take sakawa,. Isabella, Danielo, Fredrick, duk kallonsu suke dansu bakomi suke fahimta acikin bayanin da Labaran me wanki yakeba, bature Hector kuwa tsananin mamaki yahasa magana, gabaki dayama karfin halin muktar ne yake Kara daure masa Kai, idan be mantaba a lokacin da ya temaki muktar yabashi aikin gadi lokacin haka yazo kofar wannan gidan kamar almajiri kullum seyazo amma su chief security da sauran masu tsaron kofar gidan sukoresa kamar kare amma haka ze wanke kafa gobe yadawo sbd kawai yanaso adaukesa aiki,. Watarana yadawo daga unguwa yaga anata dukan mutum a kofar gidan sa, ashe chief security ne yasa yaransa suka Zane muktar saboda sungaji da nacinsa, shikuma yaki dena zuwa shine suka zanesa, haka Hector yamusu kaca kaca har yakusa korar su, sbd yadda suka yiwa muktar rudu rudu da jiki, dukda kasancewar sa nasara bayason wulaqanta mutum, haka yadauki muktar yakaisa asibiti aka masa treatment din ciwukamsa, sannan ya tambayesa meyasa kullum yake zuwat masa kofar gida gashi masu gadi sundakesa, cikin marairaita muktar yake fadawa Hector cewa shi bakone a garin besan kowa ba yaxone ko zasu temaka subashi Koda aikin gadi ne shima yadingayi yasamu yarike kansa, kasancewar muktar yanajin turanci cikin harshen turanci yake fadawa Hector damuwarsa, haka yaji tausayinsa yace yakoma gida idan yaji sauki yadawo shi zebashi aiki, yamika masa katinsa yace yakirasa, Kuma yabashi kudi dayawa domin yakula da kansa har zuwa lokacin da zedawo amsar aikin. Dahaka muktar yafara aiki agidan bature, farko wuya yakesha gurin su chief security sbd sunji haushi ankaro musu me gadi suna bakincikin yasami alherin da suke samu sbd Hector bashida keta Sam kusan dubu dari yake bawa duk masu masa gadi a wata, shiyasa suke masa mugunta, seda Hector yamusu barazanar kora dukkansu snn muktar yasami lfy ashe kwallon shegene tsiyarda ke wandonsa tafi kaefinsa. Sauke ajiyar zuciya hector yayi, yayinda Danny ke sake tambayar sa "dad is everything alright? U have been quite for while, wat r dis people saying? I can't understand anything". Gaya masa abinda muktar yy briefly, cikeda mamaki suka juyo suna kallon muktar Wanda zuwa yanzu jikinsa har diga yake da zufa, rigarsa tajike sharkaf da zufa. Wani kukan kura Deeja tayi ta afka kan muktar tana....., Barka da sallah once again ma people. Momsani...... ✍️ 🌹 SIRIKATA 🌹 Na SADIKA IBRAHIM. Pg 21_22 Bismillahirrah manirrahim. A yanzu Biba ta saduda kamar ba itaba tanata fama da kafar robarta, amaryarta ma tsohon cikine da ita, Biba tayi kuka kamar me tayi takaicin yadda duniya tajuya mata baya, ahakan ma tagode wa Allah tunda alh Mansur be saketa ba, daya saketa batasan Ina tanufaba sbd har yanzu batasan inda iyayen ta suke ba baban ta bata samin wayar sa, mamanta Kuma tunda Awwal yaje akace masa tabi muktar basu sake Jin duriyarta ba, gashi ita Biba saboda tsananin rashin zumuncinta ko abaya bata damu da muktar yayanta ba, saboda kar yarabeta tasami nakasu acikin dukiyarta, shiyasa bata taba sanin inda yake aiki ba acikin garin Abuja gashide agari daya suke amma batasan yadda yake rayuwa ba. Ko aurensa batajeba sede ta tura masa kudi, Shima seda Awwal yayi ta magana sannan tabashi acct number din muktar yatura masa makudan kudade yace ga gudunmuwar mamansa nan, aiko Biba tayi bakin cikin yawan kudin da Awwal yabawa muktar, shikuma d kudin yayita facaka a lokacin bikinsa da hjy Deeja. Shikuma alh Mansur har yau sama sama yake da ita balle yadamu da ita da damuwarta. Kullum tana tunanin Ina iyayenta suka shiga suka barta da duniya gashi yanzu tana ta koya mata darasi alokacin da yadace, shikuma Awwal danta kasuwancinsa yasha masa Kai, kullum ta Allah ze shigo yadubata ya gaisheta yatambayi bukatunta idan yafita kuwa se tayi bacci ma yake dawowa, hakama iyalansa kullum suna hanyar gaisheta da dan jikanta yaro me kyau bulbul dashi,. ********************** Idiyatu jikinta alhamdulillah tasami sauki sosai sede duk tayi la'asar tadena batun bin bokaye duk shafe shafen mai yanzu babu duk tayi baqi tarame shagonta ma tadena fita yara ke zama aciki suna kula mata da shagon. Yau Fatima matar Rabil ta tashi da wani azababben ciwon nakuda ankaita asibiti abu tun safe har yamma tayi tagalabaita matuqa batada sauran wani kuzari idiyatu ana gefe da charbi se jaa take dan yanzu batada aiki se istigfari, mahaifiyar Fatima ma haka Rabil kuwa duk ya susuce yafita hayyacinsa kamar shike nakudar, yakasa Sanya komi abakinsa tun daren jiya rabonsa d cin wani abu sede ya amshi ruwa yasha ragowar ya tofa addua abaiwa Fatima tasha amma haihuwa shiru. Har likitocin sun fara Shirin yimata aiki dakayar aka samu Rabil yasanya hannu aka shiga da ita aiki tanata neman gafarar sa, Idiyatu se hawaye take itama tana neman gafarar Fatima. Haka aka gungurata Saman gadon asibiti zuwa theatre room. Anyi aiki lfy anciro mata yaranta biyu duka Maza, masu tsananin kyau abin haryaso firgita doctors din dayan yaron idonsa ocean blue kyakkawa sosai kamar ba jaririba, dayan Kuma bezo da lafiya ba yazo da ciwon zuciya gashi yafi kyau ma, shi ko kwayar idonsa basu samu ganiba dan ko kuka yakiyi, gasu manya kamar ba twins ba, they look identically. Cikin kwarin gwiwa tarda murnar samin nasara wata nurse tafito da sauri tazo gurin Rabil tace "yallabai albishirinka"? Kan Rabil a sunkuye Wanda tun sanda aka shiga da Fatima dakin theater yaji kansa ya Sara ya zauna ya sunkiyarda Kai, dago kansa yayi idonsa sunyi matuqar jaa abin tsoro har seda nurse din ta firgita taja baya jiki na rawa tace " sorry sir matarka ta haihu anyi aikin cikin nasara tasami twins duka Maza". "Alhamdulillah" shine abinda Idiyatu da mamar Fatima suke furtawa, tareda matar makocinsu Wanda ya yayiwa Fatima waliccin aure, tazo bayan shiga da Fatima operation, mamar Fatiman ce takira ta sheda mata shine ta karaso. Cak suka dakata da murnar da suke sakamakon abinda sukaji Rabil yana furtawa kamar amafarki. "Wacece ta haihu? nisam ba 'ya'ya na bane, banida wata alaqa dasu". Yafada yana nuna wannan nurse din da tafadi haihuwar, idonsa jajur kamar Gauta. To fa Dan Dan Dan Dan Dan My people ya kuke ganin wnn Al amarin ze kasance da alama aikin malam buzu yayifa. Idan me karatu be mantaba shafin farko Idiyatu ta sahalewa mlm buzu yin farraqu tsakanin Rabil da abinda za, a Haifa masa, gashide kamar idiyatu ta shiryu Amma Kuma aikin da tasanya ayi Yana nan yana firering....... Nadatse pg din ne anan sakamakon yimuku dayawa bashida wata fa, ida. Inada ayyuka dayawa Amma nake takure kaina namuku typing, Amma common react ya gagari me rai haba Dan Allah mudinga yiwa juna adalci. Am a busy soul too, yadda kuke da uzuri Nima haka nakedashi Amma na ajiye nawa namuki typing, sbd Allah ban cancanci soyayyar ku ta hanyar comment ba, Kuma abun haushin shine wnn littafin free ne, Babu ko sisinku ku ko tunanin datar da nake kararwa bakwayi. Shiyasa tunda bakwason yin KOMAL 🤣Nima nake kyuiwar yin typing 😤mutaru mugyara pls nd pls my people 🙏 In Sha Allah idan kukamin zafafan KOMAL nikuma namuku alkawarin gobe akwai zazzafan update 💪 Share fisabilillah 🤲 Momsani...... ✍️ 🌹 SIRIKATA 🌹 Na SADIKA IBRAHIM. # Dan Allah ayi hkr jiya mabuda wuta ne bansamu nacika alkawarinaba, Amma yau gashinan namuku me yawa. Masu kirana Dan suji lafiya nagode sosai da kulawarku Allah yabar zumunci.# Pg23_24 Bismillahirrah manirrahim. Wnn pg din nakine kadijat Musa ki yayyagashi inkinso🥰 "Wacece ta haihu? Ni Sam ba 'ya'ya na bane banida wata alaqa dasu". Kafin sudawo daga suman wucin gadin da sukayi yasakai yabar asibitin ido rufe ya afka cikin motarsa ko ganin gabansa ba ya yi, dawani irin speed yaja motar haryana bude mutane da qura, mutane se kallonsa ake wasu na cewa Kila mutuwa aka masa, aguje me gadin gate din asibitin yabude masa yasa kai yafita ikon Allah kadai yakaishi gida dan wani irin tukin ganganci yake se shara uban gudu yake kamar ze bar duniyar. Yana isa gida dakinsa ya fada idonsa jajur abin tsoro he look like he was possessed, yana zuwa yafada kan makeken bed dinsu yadafe kansa dake barazanar rabewa biyu yalumshe idonsa zuciyarsa suya take matuqa ga jikinsa ya yadau wani masifar zafi kamar ana hura masa wuta acikin zuciyarsa nan take zazzafan zazzabi ya rifesa, se karkarwa yake yanaso y ambato sunan Allah yakasa, bakinsa SE bari yake hakuransa suna hadewa da junansu. Acen asibiti kuwa jikin Idiyatu na kyarma tace "innalillahi wa inna ilaihi raji'un hasbunallahu wa ni'imal wakil, allahumma ajirni fii musibatii wa kalifnii Khairan Minha, ya Allah wat have i done,? Dis is all my fault,I did dis, innalillahi wa inna ilaihi raji'un," ta maimaita wnn Kalmar yafi akirga sbd tsananin tashin hankali su maman Fatima basuji abinda take fada ba, sukansu shock din abinda Rabil ya aikata ke begama sakinsuba. Cen makociyar maman Fatima me suna maman inaya tace "kan bala,innan me wannan yaron yake nufine? Ko yafara shaye shaye ne? To wallahi be isaba muze nunawa kwaya iye? Ubanwa yahaifar masa yaran dazecewa mutane bashida wata alaqa da wnn yaran? Tun ma bega fuskarsuba ze fara karantawa mutane wasikar hauka, to wallahi billahil azeemu be isaba," juyowa tayi kan Idiyatu wacce jikinta ke masifar kyarma kamar ana kadata tace "iya Rabil" dake haka akece mata a unguwar duk makota sunanda suke fada mata kenan tunda yawancin su sun chakude da yarbawa da hausawa ne shiyasa SE suka zama kamar duk daya suke, tacigaba da fadin "kinajin haukar d danki ke Shirin aikatawa ko? Dan uwar ubansa yaran nawaye dazecewa mutane ba 'ya'yansa bane iye? Ubansa ne yayi cikinsu ko Kuma ke uwarsa? To wlh tun wuri kifada masa yadawo hayyacinsa kafin yaga haukar datafi tasa idan ma yafara afa kwayoyine to yasawa kansa birki tun kafin alhaji yadawo yaji wannan bakin furucin da yake akan Fatima da 'ya'yansu". Hankalin mutane har yafara dawowa kansu sbd masifar da maman inaya take zazzagawa gashi se daga murya take damacen masifaffiyace. Jikin Idiyatu na bari hakama bakinta tace "Dan Allah maman inaya kiyi hkr muzauna asasanta wannan Lamarin ni zan masa magana in Allah ya yarda komi zezo cikin sauki dan Allah kiyi hakuri"tafada tana hade hannayenta guri daya alamar roko sannan muryarta kasa kasa. Maman Fatima bata iya cewa komiba se ajiyar zuciya datake saukewa akai akai, bude baki mmn inaya tayi da niyyar sakeyin wata maganar sega Doctors din ne suka fito suna cigaba d magana atsakaninsu, mmn inaya ce ta tarbesu da sauri tana fadin"likita yajikin 'yata? nurse tace mana anyi aikin cikin nasara, ina take da abinda ya haifa?" Seda likitan yagama magana da sauran doctors din sannan yace "sorry ma'am ina mijin ita me jinyar yake inason ganinsa yanzu a office dina, seda ta harari gefen da Idiyatu take wacce tayi zuru kamar ace Kee ta arce, sannan tace "yafita bashida lfy likita kafadamin duk abinda zaka fada masa ina sauraronka ni zan masa bayani". Seda likitan yakare musu kallo dukkansu sannan yace "Ina mahaifin ta?" Mmn inaya tace "yakusa karasowa dama baya garine" " ok idan yakaraso yasameni a office dina yanzu za a Maida ita dakin hutu tukun yaran Kuma idan aka gama shiryasu za a miko muku su" Dr yafada yana wucewa zuwa office dinsa. Minti biyar tsakani mmn inaya tana gefe tana hura hanci idan ta tuna Rabil yace wai bashida wata alaqa tsakanin sa da yaran wani irin bakin ciki ne yake turbuketa, yanzu ma se sakarwa Idiyatu magana take, Idiyatu kuwa tayi mus ba baki, burinta kawai shine tasamu kebewa domin tafara Shirin zuwa kontagora dole ma taje tasanya mlm buzu ya warware wannan aikin don ita Kam yanzu harga Allah take kaunar Rabil da yaran sa, tagaji da aikata zunubi hakanan, tundaga farkon rayuwarta babu wani aikin kwarai data taba aikatawa,ga mafarkin nan da tayi akan shirinsu na zuwa Niger tafara tsorata sannan Kuma Biba data dage setaje ga abinda yafaru d ita wannan shine babban dalilinta nafara tsorata da lamarin duniya sannan kobayan haka ita kadai tasan yadda take bacci da daddare har yau bata dena hunted dreams ba,. Kawai she was just pretend to be normal amma deep down ita kanta tasan she's not normal, kullum setasha maganin yara don tasamu bacci amma haka zata karaci zamanta ko kyafta ido batayi dasunan bacci har yafara taba mata kwakwalwa, aboye tana ganin likita batareda Rabil yasaniba, Abu daya takasa jurewa Wanda takeji dole ta aikatashi kafin mutuwarta ta risketa shine tasada Rabil da mahaifansa na gsky, yin hakan tasan ze iya sanadin rayuwarta amma tagwammaci faruwar hakan sbd tana tsoron mutuwa ta risketa acikin wnn yanayin. Kuma zata nemi Biba in Sha Allah tafada mata komi sbd halin rayuwa, Kuma tanemi afuwarta akan cutar da tayi mata na aure zayyad da tayi, duk da alokacin itama Biba cutar tasoyi amma daga karshe itace ta amshe komi, sannan tasa akayi musu ingije tayadda sukabar garin kontagora batareda sun shiryaba. ******************* Hjy Deeja sehada kayanta take tana kuka tana durawa muktar zagi ta uwa ta Uba, Fadi take "munafuki algungumi, mugu azzalumi, natsaneka Kuma wlh karubutamin takaddar sakina yiiiiiii", muktar na gefe bakinsa a suntume sakamakon dirar mikiyar da Deeja tayi Saman kansa batareda ya shiryaba aiko ta shammacesa tasamu bakinsa da goshinsa ta dinga kwala masa takalmin Isabella me shegen tsini, Wanda ita kanta bella batasan sanda Deeja ta wafce shi akafarta ba. Fadi yake "aikema kwadayinki yaja miki banda kina makwadaiciya ko primary bakiyiba amma kice ke seme kudi Zaki aura uwar ki lashe money Kuma ta daure maki kugu Kuma wlh idan kika ga nasakeki kin biyani duk kudaden da na kashe mikine, bari ma in samu littafi narubuto duk abinda nakashe miki dan nasan paper tayi kadan tadauki yawan abubuwan da na muku keda uwarki lashe money". Duk wannan bidirin da ake mahaifiyar muktar tana boys quarters tana sheqa bacci bayan taje kitchen ta dauko lafiyayyen abincinta da lemon kwali taci tayi hani'am daganan se bacci, duk tsiyar da aka tsula agidan bata saniba har dawowar bature duk batasan anayi ba. "Muktar ni kake fadawa Sena biyaka duk abinda ka kashemin? Ni kake kiran uwata lashe money? Bayan ta aura makani uwata muktar? " Tafada tana nuna kanta. " Ahab uwa tafi uwa ne? Inace nan saboda samun wuri kika ce sede uwata takoma bq d zama tunma bakisan gidan ba nawa bane, koba haka akayi ba munafuka gashinan saboda in faranta miki bantaba yiwa uwata biyayya ba tunda na aureki, bayan masifar dana jefa kaina ta aron gida harda masifar kauracewa uwata d kikasa nayi, gashi yanzu duk a silar ki na rasa aikina, Kuma yanzu ma ni bansan ta inda zan fara Neman gafarar uwata ba, balle in sanar d ita abinda ke faruwa dani, Kai da kunyama ince mata ga abinda yasameni tunda sanda nake amatsayin me wannan gidan ban kyautata mata ba" yakarasa cikin raunin murya kamar zeyi kuka, shi wallahi bema san abinda yakaishi yin wannan danyen aikin ba, idan ya tuna yadda me gidan y temakeshi batarda wani tunaniba da yadda ya banzatar da mahaifiyarsa SE yaji inama yana iya maida hannun agogo baya daya mayar ya kyautata rayuwarsa data uwarsa, koba komi yanzu daya shiga wani hali itama ta tausaya masa, amma yanzu ko giyar wake yasha baze fara tunanin tausayawa daga garetaba. Zuciyarta na tafarfasa tace "wlh yau a gidan mu zan kwana zakasan kayi da ni wlh seka sakeni dan ni ba kalar talaka bace". Azuciye ta kwashi akwatinta Wanda bayan bature yagama Jin bayanin kowa akan abinda muktar da chief security suka aikata ya sallami chief security da tawagarsa, Shima muktar ya sallamesa Kuma yace duk kayanda sukayi amfani dashi na gidan sukwashe su tafi dashi, iya adalcin da yamusu kenan daga haka be musu komiba Kuma yace yabasu daga yaunzu zuwa dare sukwashe komatsan su subar masa gida, shine fa hjy Deeja wacce ayanzu takoma Deeja tsura ba hjyr sbd dama samun guri yasa tasanyawa kanta hjy Deeja, takwashi akwatina niki niki zata tafi kauye gidan su da alh muktar baban nera Wanda Shima a yanzu y koma muktar tsurar sa ya gyara musu dakyar ta iya Kai akwatinan main falon gidan sbd girmansu dakuma yawan kayan dake cikinsu muktar de yana kallon ikon Allah kuma yana biye da ita ko ajikinsa dan zata tafi sbd yasan tsiyar da ya shirya mata, ko kadan beyi yunkurin hanata tafiyaba. Suna kaiwa bakin main door na falon yajuya yayi hanyar boys quarters domin tasar da mahaifiyarsa tazo su cikawa wandonsu iska dan yaga Danielo se hararsa yake daganinsa beda mutumci yasan idan ya yarda yakara awa daya acikin gidan to ba shakka seya masa dan banzan dukan mutuwa. Dan yafusata kwarai Jin hukuncin d babansa ya yanke musu batareda ya dauki mataki akansu ba lefin d suka aikataba. Yana zuwa yasamu maman ta idar da sallar la'asar wacce shi ko azahar be Sami zarafin yi ba, tana ganinsa tace "subhanallahi wannan yaron lafiya? Meta sameka? Ko hadari kayi naga fuskarka duk a kumbure" sunkiyarda kansa yayi idonsa na cikowa da kwallah yace " mama kiyafemin dan Allah kigafarceni bisa Saba mikin da nayi, dan Allah mama ki yafemin" yakarasa kuka na kufce masa,jiki na rawa tace "subhanallahi muntari lafyarka kuwa Kode hjy Dije ce ba lafiya iye? Anya lafiyarka kalau kuwa? " A raunane yace " mama lafiyata kalau hadiza ma lafiya lau take dan Allah mama kiyafemin duk abubuwan da na aikata agareki," "bakamin komiba muntari duniyace ai budurwar Wawa, Wanda be zo bama tana jiransa duk da nasan cewa akwai abunda ke faruwa amma nayafe maka, koba komi baka ki zamana kusa da Kai ba bakamar yar uwarka habiba data gujeni ba ita Sam bata kaunar ma nunawa duniya nice na haifeta, amma Kai koba komi muna rayuwa aguri daya, nayafe maka muntari" tadaga hannu sama tana gdy ga Allah dayasa danta yadawo cikin hayyacinsa koma menene dalilin dayasa yadawo hayyacinsa itakam ta godewa Allah da zuwan wannan dalili tasan adduar ta bata tafi abanza ba. " Mama anbani daga yanzu zuwa kankanin lokaci nabar cikin gidan nan domin masu gidan sun dawo Kuma ya koreni daga aikin ma" muktar yafada yana Kara sunkui da Kai, "bangane ankoreka ba me kayi da aka koreka?". Kansa akasa ya zayyanewa mamansa duk abinda yafaru tundaga neman da yayiwa Deeja har yau da bature yadawo, cikeda mamaki da al'ajabi take kallon muktar gaba biri yayi kama da mutum, ashe zuwan da suke kwana 2 gaisheta ashe ba banzaba, ita abinma harda dariya yaso bata. Cikin mamaki tace "yanzu harda kudin da Awwalu dan gidan habiba yaturo maka masu yawa kahada kayita karya agari, Gani cen wani lokacin ma garin kwakin nan idan babanki yafita ba samowa yakeyiba, to Allah ya kyauta nagodewa Allah da Zuwan wannan rana koba komi kadawo cikin hankalinka, Kuma ina fatar ace kashiryu kenan har abada, domin Allah yaba son tuban muzuru,ka tabbatar kayi taubatan nasuha". Tana kaiwa karshe tafara hada yan kayanta acikin yar gana mustgo dinta tanayi tana Kara yiwa muktar nasiha, suna haka sukaji cirin motoci a harabar gidan, ai jikin muktar na masifar rawa yace "mama yi sauri bar kayan nan haka taho muje" da sauri yadau gana mustgo dinta sukayi hanyar waje yana riqeda hannunta, motocine na sojoji sunkai biyar, gawasu vans agefe kusan guda biyar shake da kayan furnitures da komi na bukatar gida, bayan bature yasallami duka ma,aikatansa abisa tursasawar iyalansa kan cewa sede yasallami dukansu acewarsu ai duka bakaken fata maciya amana ne saboda hk sede ya sallamesu aka yo hayar wadannan sojojin kafin gobe securitynsu na cen kasar waje su iso, Sadaf Sadaf muktar yataho riqeda hannun mahaifiyar sa sunkai dab da gate zasu fita aka daka musu wata uwar tsawa "hey intruders" agigice muktar yasaki bakkon kayan maman yadaga hannu sama yana fadin "wallahi yanzu zantafi bazan Kuma dawowa ba dan Allah kuyi hakuri" yama kasayin turancin se tsilli tsilli da ido yake ga bakinsa da goshinsa har lokacin a suntume, Danielo yace "you jerk u remain here despite all the warning i did to you huh?" Jikin muktar ba inda baya zubarda gumi ga wata irin gudawa data Kara taso masa, sukuwa sojojin jira kawai suke ace wani abu su farwa muktar, kamar Danny yasani dan shi wlh har yanzu haushi yake ji na yadda babansa be dauki wani kwakkwaran mataki akan mutanen gidan ba yacewa sojojin nan "guys get him" ai atake muktar yasaki fitsari awandonsa. "Dan Allah kiyi hakuri kitaho mutafi banga amfanin cigaba da zamanmu a cikin wannan garin ba, tsawon shekaru masu yawa kinkasayin tawakkali sanadin haka cutuka dayawa sun sanyaki agaba amma har yau kinkasa fawwalawa Allah lamiranki kin ki daukar kaddarar d Allah yadora miki, nasha fada miki idan har Rabil yana raye in Allah yaso Zaki gansa koba jima koba dade" araunane tajuyo rungume da katon hotonsa tun na 1year birthday dinsa, yasha kaya masu kyau kamar ba hoton daa ba yarone me kyau yana murmushi ga cake agabansa. "In Sha Allah zan dauki kaddarata daga yau hannu bibbiyu idan Rabil dina Yana raye nasan zamu hadu wata Rana" tafada tana ajiye hoton akan katon gadonta Wanda aka rufeshi da farin kyalle, komi na gidan an rufeshi da farin kyalle. Juyowa tayi kyakkawar mace wacce akalla zatayi shekaru sittin da yan kai, zainab kenan mahaifiyar Rabil suna shirin tafiya airport jirginsu ze tashi karfe 11 Dede zuwa kasar Qatar. Sakamakon takasa dena tunanin danta Rabil shiyasa mijinta mahaifin Rabil wato alhaji Mohsin ya yanke shawarar komawa Qatar da zama na dan wani lokaci dama yanzu acen yake aiki. _____________________ Acen garin Ibadan kuwa Dr ne yagama yiwa alhaji bayanin halinda twins din Fatima suke ciki dayan yazo da lafiya dayan Kuma yazo da ciwon zuciya yanzu haka yana dakin gwaji dan anaso aga matakin da ciwon yake saboda sunaso zasu dorashi akan magani, sauke ajiyar zuciya yayi cikeda tausayawa Allah baruwansa ace jariri yana fama da ciwon zuciya wannan SE iKon Allah. Fitowa yayi bayan yagama Jin bayanin likita, dasauri mmn inaya takaraso tana tambayar sa akan abinda likita yafada zaunawa sukayi akan waiting chairs dake bakin kofar dakin da aka kwantar da Fatima aciki yana mata bayanin abinda yake faruwa maman Fatima taje gida tayi wanka tadawo, kuka mmn inaya tasaki tana fadin "innalillahi wa inna ilaihi raji'un wannan wace kalar jarabawace ace jariri da ciwon zuciya bayan wannan mummunar tabon da ubansu ya musu, alhaji kanajin fa wai cewa Rabil yayi yaran Fatima bandashi bane bashida wata alaqa dasu" "what?" Alhaji yafada yana mikewa "mekike son kicemin ne shi Rabil din ne yace yaran nan ba banashi bane? To na uban waye? To wllahi be isaba Ina yake ne?" Yafada yana wurga idon sa ako ina nawurin idonsane yasauka akan Idiyatu wacce har yanzu takasa wani kwakkwaran motsi. Tambayar yamayar kanta " iya Rabil me nakeji ne mmn inaya tana fada Rabil din da kanshi ne yace wadannan yaran banashi bane?". Bejira amsartaba yaciro wayarsa yafara dialing no din Rabil amma switch off. Kallon Idiyatu yayi wacci ta taso tana bashi hkr akan bari taje gidan in Sha Allah komi ze dedeta. Fitowa tayi daga asibitin tahau taxi tayo gidan adaki tasami Rabil kwance zazzafan zazzabi ya rifesa, tashi hankalinta ya yi dakyar tasamu wasu samari suka fito mata dashi aka sashi amotarsa ta tuka takaishi asibiti dasauri likitocin suka karbeshi akayi addmiting nashi aka sa masa drip bacci me nauyi y daukeshi, office din Dr Idiyatu taje sukayi wata magana dake asibiti dayane da inda aka kawo Fatima. Fitowa tayi jikinta har rawa yake tanajin wani masifaffen guilt kamar takashe kanta. Komawa gida tayi tadauki kudade masu yawa agurguje tawatsa ruwa tashirya ta fito t rufe gidan tashiga makotan ta tayi magana dawata bayerbiya tafito tahau taxi rabiya ta shagonta tadudduba abin da zata duba tafito me taxi y wuce da ita se tashar mota, yau komin dare in Sha Allah agarin kontagora zata kwana, zataje malam buzu ya warware wannan aikin kar alhakin Rabil yakasheta, gana yaran da basusan hawaba balle sauka. 🌹 SIRIKATA 🌹 Na SADIKA IBRAHIM Bismillahirrah manirrahim. Pg 25_26 Karfe 11:00 na dare idiyatu ta iso garin kontagora, mashin tahau yakaita hotel takama daki salloli yafara yi kafin tayi oder abinci me sauki source din anta me ruwa ruwa se coffee me zafi Shima dakyar taci tasamu wuri takwanta tunanika da dama suna kawowa kwakwalwar ta hari, jitakw inama tana iya maida hannun agogo baya data mayar da Rabil gurin iyayensa tun yana yaron sa. Sede Kash aikin gama yariga ya gama, itakam duk cikin kaddarorinta babu me kyawon da zata tuna balle tace kodanshi Kila zata iya shiga aljanna, amma ba a yanke kauna daga rahmar ubangiji, tana rokon Allah karya kasheta batareda ta sada Rabil da iyayensa ba, ita ko bazasu yafe mata ba ta gwammaci ko kulleta zasuyi tayarda akan de tamutu da wannan nauyin Saman kanta. Kamar wasa bacci yafara daukar Idiyatu yau ko maganin yaran batashaba Sega bacci yana daukarta, carbi ne a hannunta tana jaa cen bacci me nauyi yayi awon gaba da ita, kamar wasa kamar a farke taga Rabil yana kuka yana kallonta yana cewa "why? Why?? Whyyyyyyyy??????" Kawai seyafada wani wawakeken rami me masifar duhu,Afirgice tafarka ta hada uwar zufa tana kwala kira sunansa "Rabillllll yaronaaaaaa" ganin kanta da tayi kan dadduma a dakin hotel din da tasauka yasa tasan mafarki tayi, hamdala tayi tunda ba gaske bane aguje tafada bayi ta dauro alwala tazo ta tada sallah yi take har kafafuwamta suka gaza, se azaune takomayi hakanma tagaji sekawai tasaki kuka yitake ba kakkautawa, Idiyatu tarame sosai daka ganta kasan she is totally depressed nd devastated. gyangyadi take tana farkawa dan bataso bacci yakuma daukarta dan batasan mezata kuma mafarki dashiba, Ahaka wani baccin yakara kwasheta lokacin karfe 4:59am, wannan karon batayi mafarkin komiba har sanda aka kira sallar subh sannan tafarka mamaki yakamata ya akayi tayi bacci yau, daga hannuwa sama tayi tana hawaye tana fadin alhamdulillah., Alwala takara yowa tazo tayi raka'atainil fijr sannan tayi sallah asuba, bata Kara kwanciyaba ta hada komi nata ajaka tayi oder abinci tea kawai da bread lokacin karfe 6:30am tafito tabiya bill dinta takara tarar mashi SE kauyen su mlm buzu. %%%%%%%%%%%% Bibace zaune Saman gadon ta kanta duk ayamutse se zabga kuka take duk tahada uwar zufa jikinta se kyarma yake, yanzu babu halin bacci ya dauketa seta dinga mafarki da sirikar ta mahaifiyar alhaji Mansur tana miko mata hannu tana fadin "Biba! Biba!! Biba!!! Mena mikiiiiii" haka take fama tsawon kwanaki uku kenen gata mayyar bacci minti kadan bacci ya debeta harda minsharinta siii sii fii fii kirr kirr" Amma dazarar bacci yasoma dadi seta farka afirgice tana tsala ihu yanzuma zaune take tana kuka akan gadonta gashi karfe 2 na dare ne yanzu, dama mirror dinta yana kallon gadone tana dago kanta da niyyar sauka daga kan gadon aiki tayi arba da kanta ayamutse acikin mirror ga fuska jage jage da hawaye da majina ai take ta kwallara wani azababbben ihu tazube akasa ba numfashi, itade harga Allah firgita tayi da taga kanta a mirror, setaga kamar fatalwar sirikar natane take gani azahiri. Ihunta ba inda be karadeba acikin gidan tayadda duk Wanda ke rayuwa acikin gidan seda yaji arikice suka taho part din nata Koda suka iso a kwance suka ganta akasa babu alamar numfashi atareda ita. Koda tafarka ta ganta akan gadon asibiti matar Awwal zaune tana bawa danta friso tana ganin ta farka ta taso tana mata sannu da saurinta ta fita taje ta kirawo dr tare suka shigo da Awwal da alh Mansur duddubata yayi yana tambayarta yatakeji yanzu tace batajin komi yajuyo ga alh Mansur yace Kila anjima mubata sallama. ........................... "Idi sonake ka kaini gidan na gwaggo" "Kai wallahi idan yasan nina kaiki seya koreni daga aiki Kuma wlh ni da aikin nan kawai na dogara dashi nake ciyar da iyayena, Kuma wlh oga baya mana keta dazarar lokacin biyan ma'aikata yayi baya kwana da haqqin kowa akansa, Kuma ma muna cen Muna aikifa ni yatayar ya aikeni kasuwa yace naje duk abinda kika lissafa asai miki ko kyalle kar na rage idan kudin sunkare nakirashi y turomin wasu, duk wayar da kikeyi da Wanda yaje kasuwa jiya dani kikeyin ta wallahi oga yana matukar kaunarki da yimiki biyayya kema kibarshi ya sarara mana haba". "Idi na gwaggo dana ne ko na ka? Munafuki algungumi, to wallahi ko ka kaini ko nasa yakoreka daga aikin naga ta rsiya, ai tunda naga yayimin wannan uwar siyayyar nasan waccen munafukar juyar matar tasa bakaramin chabawa take ba, kadubafa yanzu kwanon gyada yakai dubu daya da dari uku haka nace masa yasaimin kwano ashirin amma ko musu beminba ya siya, nace yakara biyar ashirin din na lissafa bazai isheniba ko tari beminba ya amsa da to, nace inason biredi guda goma dukda de ba uwar da zanyi dashi karshentama su lalace tunda ni bawani ci nake ba, gashi ya siyomin, nakara da kayan tea gashinan ya laftomin kamar zan bude kanti, nace masa na ci bashin katin waya na dubu ashirin agurin garbati me kanti ba musu ga ya aikomin da dubu talatin wai nabiya bashi narike sauran, irin wnn hidima to Allah kadai yasan uwar juyar matar sa me taci, sbd haka yau base gobe ba ka kaini garin minna in yaso ka ajiyeni ka tafi nikuma bazan fada masa Kai ka kaini ba". Baki sake idi yake kallon maman ogan nasa, shi wallahi be taba ganin muguwar mata wacce batason kwanciyar hankalin danta irin wnn matarba. Gashide be rageta da komi ba duk bala'i da tujarar da take masa be hanashi yimata biyayya ba, amma ita batada buri daya wuce kullum ta muzguna masa. " Kayi shiru idi, kode ka kaini walh ko Kuma aikinba ahaka" tafada tana cira Kai gefe. Idi yaron makotanta ne babanshi yarasu se nauyin iyayensa wato matan babansa su biyu da kannensa yakoma kansa, da mamarsa da kishiyarta dake suna zaman lfy se yake fita yana saukale(dako)din kaya akasuwa yana dan samo musu na abinci kasancewar shine babba Kuma namiji agidan kannensa duk matane, wata rana na gwaggo yakawo mata ziyara seya gansa yadawo daga saukale dinsa suka gaisa yataya shi shigowa da kaya cikin gida, anan na gwaggo ke tambayar sa aikin da yake yace masa dako yakeyi yanzu a sabuwar kasuwa to anan de na gwaggo yace masa yahada kayansa idan ze koma minna sukoma tare yabashi aiki acen kamfanisu da yake aiki bangaren shinkafa, shine dalilin zaman idi yaron na gwaggo Kuma duk idan ze aikowa da mahaifiyarsa Sako to idi yake bawa kasancewar shi mutum ne amana,. "Dan Allah kiyi hkr karkije tunda ya yo miki sakon Kuma duk abinda kikace Wanda yafishima aka kawo miki". Daukar wayar ta tayi tana neman no din na gwaggo tace "barima kagani, yanzu kila daga nan base ka koma gurin aikiba zaka Sami sakon sallamarka, kaga seka cigaba da dakon da kakeyi" tafada tana cuno baki gaba kamar wata yarinya wannan mata bade masifar tsiyaba. "Kiyi hkr in Sha Allah goben kishirya Sena kaiki amma dan girman Allah karki fada masa nina kaiki dan Allah". " Inde wannan ne idi shakuruminka bazan fada masa ba kaide kawai ka nunamin gidan kodaga nesa ne nisena shiga Kai kajuya abinka". " To Allah yakaimu goben". " Amin kadauki biredin nan guda uku katafi muku dashi, idan Allah yatsaga da rabon wani inya shigo Shima nabashi haka zan rabar dashi". Gari na wayewa tun karfe 6:00am tagama shirinta tsab tana jiran idi, karfe 6:30 ya yi sallama yashigo daga ita se kayan jikinta se kudinta da wayarta a cikin yar pose dinta, titi sukaje sukahau taxi se tasha, 7:00 dede motarsu ta daga, dake hanyar bakyau se karfe 1:20 suka isa garin dukda gajiyar datake ji a cikin jikinta hakan behata Jin karfiba idan ta tuna kudirin da yakawota. Adede kofar gidan me adedeta yasauketa, dasauri Kuma idi yacewa me adedeta yayi maza subar wurin karma wani ya gansa asan shine yakawota. Kallon yanayin unguwar take wacce ko sunanta bata saniba,ko ina tsit unguwar akwai tsari gidajen kusan duk iri dayane, saboda zakwadi sanda idi ke fadawa me adedeta ko saurare batayi hankalinta na cen ta matsu ta isa tayi cin mutunci. Kwankwasawa gate din tayi me gadi ya bude yana tambayar ta daga ina watake nema tace masa "nice uwar me gidan" kallonta yayi sama da kasa yace "to ai oga be cemin mamarsa zatazo ba" rike haba tayi tace "saboda yazama solobiyo dan ana gadin wannan juyar matar tasa har se yafada maka ga Wanda ze shigo ga Wanda zaka bari yashiga? Tab lalle na gwaggo inacen sake da baki an maisheka sauna huhulahu" kafin me gadi ya yi wani yunkurin ta bankadesa ta afka cikin gidan, afarfajiyar gidan ta gansa akan wata resting chair me Lilo shida matarsa Aisha tana kan cinyarsa tana matse masa kurji agoshinsa se dan shagwaba yake mata yana matsa ass dinta jikinta sanyeda bomshort se wata yar riga shoulderless fara, jikinta yayi luwai luwai farar fatarta takara fresh, Shima jikinsa sanyeda dan boxers na Maza medan fadi. Sunyi nisa gurin shafe junansu daga matsar kurji aka cenza jaha, Jin salati kawai sukayi akansu fadi take "sallallahu alaihi wa sallama, kalu innalillahi na gwaggo mezan gani haka? Yaushe ka koma cikakken dan bariki ? Dama abinda take maka kenan shiyasa kaki ka Kara aure balle kaga gudan jininka nima insamu naga 'yan jikokina ko?" Masifa take kamar zata ari baki kamar wacce takamasu suna aikata zina, asukwane suka bar jikin junansu dasauri ya dauki jallabiyyar sa yasanya yamatso kansa akasa yana fadin "barka da zuwa mama yaushe kikazo?" "Rufemin baki bunsurun banza da wofi tunda kazama sallamamme yaushe zakasan nazo, yau gani agidanka da ka hanani sani yau Allah yakaso ni Kuma nazo kenan sallamamme sha3 maloho". Kansa akasa be iya cewa komiba aransa mamaki yake ya akayi tasan gidansa, shin wama yakawota garin ne, tambayar da yakasa baiwa kansa amsa dan ko kadan besawa ransa idi ne yakawotaba. Aisha ce tamatso bayan ta Sanya kimono dinta ta suturta jikinta tace "sannu da zuwa mama, Bismillah mushiga ciki......" Bata karasaba mama ta kwashe fuskarta dawani lafiyayyen mari hagu da dama, tace " munafuka algunguma jinin fir'auna juyar banza da wofi, ta Ina nazama mamanki? Nace ta Ina nazama uwarki? Uwarki nacen de jinin munafukai masu asircewa mutane 'ya'ya". Taga taga tayi zata fadi yayi saurin tarota idonta arufe bakinta har ya fashe, idonta yayi kwanciyar jini, dagowa yayi cikin sanyin murya yana fadin "haba mama nine bakya kauna ba Aisha ba duk wannan abin da kikeyi ba ita kike yiwa ba ni kike yiwa, Kuma in Sha Allah zan saki Aisha Kuma bazan Kuma aureba zan zauna nikadaina tunda haka kikeso, idan nafada halaka kinka kinada naki kamashon kenan". "Na gwaggo ni kake fadawa wadannan maganganun? Ni ?" Kafin yayi wani yunkurin ta ruga aguje kamar mahaukaciya ta karyo ganyen gwandar da aka kawata compound din gidan dasu different types na bishiyu, ta hau lafta masa kamar karamin yaro yana kare fuskarsa ko kadan beyi yunkurin kwatar kansa ko yahana taba, tana ta zuba masa tana zaginsa kamar ba dantaba yana durkushe akan gwuiwoyinsa ko motsi bayayi idonsa arufe, shiru yaji kafin Kuma yaji ihun maman tasa, bude idonsa yayi, aiko yayi arba da Aisha ta daga mama da hannu daya kamar ta daga kaza, idonta duk jinine kwance aciki gwanin tsoro dagani kasan ba cikin hayyacinta take ba lyk she's been possessed. 🌹 SIRIKATA 🌹 Na SADIKA IBRAHIM. Pg27_28 Not edited Bismillahirrah manirrahim. Dakyar Idiyatu tagano haryar daze sadata da gurin mlm buzu saboda tun ranarda sukazo da Biba bata sake zuwaba, Kuma dama zuwan farko kenan se yau data dawo. Agajiye ta karasa bukkar mutane tagani sosai agurin kamar ana biki wasu azaune wasu atsaye wasuma bacci suke acen gefe sbd layi bezo kansuba faduwa gabanta yayi, ita da take son tasamu ganin mlm buzu ayau Kuma har takoma ibadan duk a yau da alama hakan bazata samu ba, ganin yawan jama'ar dake gurin, yanke shawarar zama tabi layi kawai tayi, tana zaune se kallon mutanen gurin take aranta tana ayyana yadda mutane suka shagala dason abin duniya kamar de yadda tayi abaya,wasu ko tunanin zasu mutu basayi. A ina? A yaushe?kana me?,aikin alheri ko aikin sharri duk bakasaniba kaide kawai duniyarce agabanka, "hmmmm" tasauke ajiyar zuciya tana furtawa afili "Allah ya sa mudace", tana zaune wata mata tafito tana daura dankwali se wage kafa take amma dan masifa fuskarta sanyeda nikaf wai batason wani agurin yaganeta, gashide da ganinta kasan me ta aikata amma wai nikaf ne sanye afuskarta. Wasu mata agefe suka kalleta suka kwashe da dariya Fadi suke "gawata karamar 'yar tasha nan, ai idan kika kuna bazki tarar kauriba, hjy ta tunda kika iya debo kafa kikazo nan ai kawai nafsi2 ne kowa yayi takansa bawanda zakiwa wani fi'ili kowa abinda yakawosa kenan neman duniya" suka fada suna tafawa, ko kallonsu batayiba tayi hanyar barin gurin. Jikin Idiyatu a sanyaye take kallon kowa na gurin, se dab da magrib sannan tasamu ganinsa Shima seda taroki wani alhaji cewar ita ba 'yar gari bace kafin yabarta dakyar tahau layinsa, sallama tayi tashiga gurin bakinta dauke da 'yan addu'o'in da ta iya jikinta banda rawa ba abinda yake wani mugun kallo tareda wata gigitaccen tsawa aka daka mata "karki kuma yimana sallama anan munafuka", jiki na rawa ta tsugunna akan gwiwar ta tana bashi hkr, kallonta yayi sosai kamar yadda itama take kallonsa sede shi kallon dayake mata ma daukeda fassarori ne masu wuyar ganowa itakuma tagaza ma kallonsa sosai, amma a dan kallonda tamasa taga cenji sosai a tattare dashi wannan karon ba babbar riga bace ajikinsa wani abune kamar buhun albasa sanye ajikinsa anmasa dinkine ko saqace batace ba, Amma abin haka yake kamar dinkin rigar Maza irin tazarce dinnan har kasa me fadi, ga dakin yaceza sosai yanzu abubuwane dayawa kamar na bokaye sabanin zuwan fari datagansa sanye da babbar riga dakuma rawani ga carbi a hannunsa, wannan karon Babu ki daya. "Idan kin gama kallon naki zan baki amsar abinda yakawoki, wannan aikin da kika sa akayiwa dan mutane da kika sato kika mayar dashi naki baze taba warwarewa ba har se ranarda Rabil yahaduda iyayensa na jini, saboda haka tashi kibani wuri" hankali tashe ta bude baki zatayi magana ya daga mata hannu "tashi kitafi, nagama magana", jikinta na kyarma tafito da saurinta lokacin gari yayi duhu sosai batama San hanyar inda zata fita takoma cikin gari ba. Tana nan zaune se hawaye take badamuwarta takasa komawa gariba aa damuwarta itace yadda zata rabuda Rabil dinta cikin kankanin lokaci, sannan batasan yaze dauki abinda ta aikata masaba, koze yafe mata ko aa, Allahu aalam. Tama sani yaudarar kanta kawai take baze taba yafe mataba, Kuma tasani nan da lokaci kankani zata tafi gidan yari, wata qilama life imprisonment za'a yanke mata, watever koma menene tayi Shirin amsarsa hannu bibbiyu babban tashin hankalinta yanzu shine Bata saniba Rabil ze yafe mata ko aa. Wannan alhajin ne yafito daga cikin bukkar mlm buzu ko tace boka buzu shimade babbar rigarsa a hannu yanata gyara tazugensa yazo yakama hanya batareda wani dar dar ba, cikin azama ta taso tana kwala masa kira, "bawan Allah,dan Allah katemaka min mufita tare bazan iya wucewa ba bazan gane hanya ba". "Ok muje"yafada yana daure tazugensa tana mayar da babbar rigarsa,tafiya suka farayi yana haska musu torch light din wayarsa se uban surutu yake zabga mata kamar ta tambayesa,Fadi yake " Amma zuwan ki na farko kenan ko?" " Eh" ta amsa masa atakaice," to Amma ke kuwa meya kawokine? Nikinga abinda yakawoni nan shine wasu mahaukatan kudi nakeson samu awata kwangilar titi dazan amsa a hannun gwauna Amma da alama munafukai har sun kaiwa gwauna tsegumin cewa ina sama da fadi da kudin al'umma, ni nan da kika ganni cancellor din kauyen..... " Be karasaba Idiyatu takwala wani ihu tana cewa " wayyo maciji innalillahi wa inna ilaihi raji'un munshiga uku" agigice ya juyo yana kallon katon macijin da yafasa Kai se huci yake yana kallonsu, jikin Idiyatu na rawa tafara karanta ayatul kursiyyu shiko wnn alhajin yana fadin " wayyo Allah menake gani haka kamar gajere?, Wallahi wannan mugun macijine idan yacijeka sede wani ba Kai ba, yanzu musan yadda zamuyi mu tsere masa batareda ya cijemuba". Kuka Idiyatu tafara dan ita tsoron datakewa maciji har yabaci mugun tsoron macijine da ita, sanda alhajin nan yafara yanaso yabi ta gefen macijin nan wata wawuyar Sara macijin yakawo masa aiki yasamesa akafa nan take alhaji yafara jijjiga dafara tafara fita ta bakinsa duk wata kafar gashi ajikinsa tafara fitarda wani irin jini bakikirin, ko sakan 50 beyiba yace ga garinkunan. Idiyatu tarasa me zatayi itama kawai jiran sarar macijin take shiru2 ba a saretaba kodata duba babu maciji ba alamarsa ai aguje tafara neman hanyarta gudu take ba kama hannun yaro bata tsayaba seda taganta akan dogon titin dayake nuna mata alamun ta iso cikin gari sannan tadantsaya haryanzu jikinta rawa yake Kuma bata dena ganin yadda wnn mutumin yamutu murus agabantaba. Tana tuna yadda yamutu ai taci gaba da gudu har Allah yasa yakawo cikin mutane ko taxi bata nemaba akafa taketa tafiya hartakai kanta hotel din jiya seda takara kama daki sbd tariga ta sallamesu da tunanin bazata dawoba SE gashi kaddara tasa bata koma ba, agajiye tabude dakinta toilet tamike direct bayan tazubar da komi atsakar dakin ruwan sanyi tasakarwa kanta abubuwa da dama suna zuwar mata a ka,. Har yanzu tana ganin yadda wannan alhajin yamutu agabanta gashi yagama zayyana mata mugun aikin da yake Kuma da dukkan alamu wani mummunan abu y shiga tsakanin su da boka buzu, subhanalla batakosan tuna yadda yake gurnanin azabar fitar rai, yanzu yamutu kafuri fasiki wa iyazubillah, Allah kasa muyi kyakkawan karshe. Alwala tadauro tafito sallaoli ta tayi tana yankewa kanta shawarar gobe bazata bar garin kontagora ba setaje gidan iyayen Rabil Wanda ko shekaru dari za ayi bazata manta hanyar zuwa gidanba, zataje tafada musu komi Kuma tasa subita domin suga dansu ko mugun asirin dake jikinsa ya karye. Da wannan mafitar bacci yakwasheta akan sallaya ko abinci bata nemaba tun Karin safen da tayi. ********************** "Wlh na gwaggo seka Kara aure nibazan Kuma cewa kasaki basamudiyar aljanar matarkaba amma seka Kara aure Kuma nizan Nemo maka matar da zaka aura, Kuma bazaka koma yauba, wlh na gwaggo har yanzu bayana ciwo yake min Kai wnn matar muguwa ce yiiii haka kawai tagwauce mini agudi wallahi bazan yafe mataba yiiiii" gadariya nacinsa ga takaici, na gwaggo jiyake kamar ya dara, uwa uwace amma yadanji dadin yadda aljanun Aisha sukadan wujijjjiga maman tasa yasan in Sha Allah zasu samu saukin wani takurar, abinda yafi damunsa shine auren da ta nace yakara shi gaskiya baya ra'ayin mace fiyeda daya, zeta lallaba maman harta hakura da batun Kara auren nan, dan shikansa yasan bazeyi adalciba sbd yanason Aisha dayawa bayajin ze iya hada soyayyar ta da wata. Yau kwanansa biyu agarin kontagora tunda akasamu Aisha yajefar da ita daga daukar kazar datayi mata tace wlh bata kwana gida daya dame garken aljanu yau seya mayar da ita gida, dakyar yasamu yashiga makota yaroki alfarmar makocinsa akan yabashi aron matarsa taduba masa Aisha dake matar malamar islamiyya ce, shikuma yaje yamayarda mamansa kontagora aranar dan kin kwana tayi tace ko Ina bazata kwanaba se agidanta, Dan bakaramin riqo Aisha tamata ba, hakan ya darsa wani mummunar tsoron ta aran mama, musamman yadda taga idon Aishar yajuye kamar na wata halitta. _________________________ "Dan Allah mlm Ina masu wannan gidan suke? Wani mutumi nake nema me suna muhsin da gidansa anan yake yanzu Kuma naga wannan gidan na bene ne dan Allah ko kasan inda muhsin din yake? yanada mata zainab". Kallon Idiyatu mutumin yayi yace " to ai wannan gidan ma nashine hala kindade baki zo garin bane? Ai arzikinsa yaci uwar nada yanzu hakama sunkoma Qatar da zama saboda waide naji ana cewa antaba sace musu yaro tun yana karami, wai shine dansu na fari, sanadin haka ita matar tasa takamu da ciwarwata da dama saboda takasa mantawa da yaron, gashi ance wai har idonta sunsami matsala, Kuma made wai kamar harda kwakwalwarta, to hakade naji ana fada. Hala ke 'yar uwarsuce? To lalle de sunkoma Qatar da zama kusan wata daya kenen da tafiayrsu". 🌹 SIRIKATA 🌹 Na SADIKA IBRAHIM. Not edited. Pg29_30 Bismillahirrah manirrahim. "Malama kibani kudina natafi inada aikin yi ba kallonki nafito yiba" me taxi yafada yana kallon Deeja wacce tayi sororo tana kallon gidansu da aka sanyawa dan madedecin gate yasha fenti sosai kamar ba a kauyeba, kafin tabashi amsa wasu yara suka fito aguje kamar agwagi sukayo kan Deeja jikake timm sun shatile kafafun Deeja segata akasa warwas basu tsaya ba sukayi wata hanyar aguje da alama dayane yakeson yakama dayan kamar mugun wasa suke kotakan Deeja wacce take yashe akasa basubiba sukayi gaba abinsu aguje, me taxi mezeyi ba dariyaba yi yake ba kakkautawa kamar sabon kamu yadda yaga 'yan wadannin yaran nan sun kwashe kafar Deeja abin ba karamin dariya yabashiba, dama tabashi haushi sosai ganin yadda ta tareshi jikina rawa yatsaya yaga kyakkawar mace da alama airport ze kaita ganin yadda take ta yauki da iyayi akan titi ga dan mayafi karami akanta, yana tsayawa yaji takira masa sunan wani kauye sekuma yayi tunanin Kila ziyara zata Kai, shinefa suna isowa yaga tanuna masa wani gida me dan kyau duk yafi gidajen kauyen kyau yaga tafita tayi tsaye tanata kalle kalle kamar bakuwa tabarsa zaune yana jiran kudinsa shine yake tambayarta tabashi kudinsa kafin tayi wani yunkurin shine wasu yara ne ko wadanni bataceba suka kifar da ita akasa, shiko me taxi mezeyi ba dariyaba ganin yar gayu wanwar akasa takasa ko tashi. Deeja da kyar tasamu ta tashi ta sallami me taxi bayan takare masa zagi tas se kutuntuma masa ashar take kamar shine muktar. Zuwa tayi bakin kofar gidan takama zata jaa gate din kamar ansa remote taga yabude dakansa ajiyar zuciya tayi takama hanya kanta asama zata shiga jitayi tabuga uban tuntube ta wani abu kamar dutse sauke kanta kasa tayi aiko tayi arba da wani wadan mutum mara kyan fasali ko kadan Wanda ko acikin wadanni muninsa yabaci gashi bakikirin, dafe kirji tayi taja da baya ido waje bakinta na rawa take nunasa ta yatsa "waye Kai? Me kakeyi agidan mu? Innalillahi wayyo nashiga uku" harga Allah tsoro yabata yadda yakafeta da jajayen idonsa kamar maye. Duk da cewa yaji haushin yadda tayi data gansa sekace wacce taga abjn tsoro, hakan behanashi karewa kyakkawar fuskarta kallo ba, matsowa yayi kamar ze riketa yana fadin "yi ahankali 'yan mata karki fadi" jaa baya tayi taruntuma aguje tabar kayanta yashe agurin gidan me unguwa ta afka kamar mahaukaciya tana haki. Kallonta iyalan gidan sukayi Wanda suka kasance zaune a tsakar gidan yuuu sukayo mata da idanu gasu da uban yawa, daya daga cikin matan gidan ne tace "baiwar Allah wacece ke kika fado mana haka bako sallama kamar wacce aka biyo?". Dago kanta tayi tace "inayini baba kandala nice hadizan karime ta gidan mlm audi", " hadiza, hadiza, banganeba wlh", " hadiza me maganin ciwon daji tagidan mlm audi na kan layin habu me kanti". " O, o haka au kice dani hadizan karime lashe money, to yau Kuma kece aguje haka? ina motocin alhaji muktar dogo baban nera? "Tafada tana kama haba. Kan Deeja akasa batareda ta amsa tambayar tace "baba kandala dan Allah Ina mamana take naje gidan mu bansametaba wlh sede wasu wadanni ne kawai suke fitowa daga gidan ko shiga bansamu nayiba yanzu ma daya daga cikin sune ya biyoni shine nagudo nan". " Hahaha hadiza kenan wace irin tambaya ce wnn Kuma tun yaushe kika sa mijinki yazo har cikin garin nan yasiyarda gonakin ku dagidan da kuke zaune aciki kikasa yasiyawa mahaifiyar ki wani gidan acen cikin garin SULEJA? Kozakice duk bakisan da wnn ba? To munan my muka raka karime har gidan ta na suleja ta tare me kyau dashi Wanda mijinki yagina mata, duk gonakinku Wanda kika gada daga gurin mahaifin ki da na mahaifiyarki yasiyar yadauketa yamayar da ita cikin gari wannan gajerun mutanen kuwa sune masu gidanku ayanzu sunansa alh Mande big moo, shiya Siya gidan yau kusan wata uku kenan da tarewarsa, dama mlm audi ya dade da rabuwa da karime lashe money yakoma gidan matarsa Wanda yaransa suka gina da guminsu, yanzu shikam Allah yasa yadawo hayyacinsa yanacen suna zaman lfy da uwar yaransa". Idon waje Deeja ke kallon baba kandala wacce se yanzu tagama rattaba zancen ta kafin tadasa aya, hannu tadora aka zata zunduma ihu cen Kuma kome ta tuna se tayi shiru, awayance tace "oh gosh wlh baba kandala mantawa nayi alokacin da akayi hakan ina cen Switzerland naje wani taro kinsan matan manya da safgogi may be shiyasa na shafa'a, amma bakomi, toko Zaki hadani da wani cikin yaran nan yakaini cen gidan? sbd saukata kenan daga airport nan nayo direct ko gida banjeba". Dan jimm baba kandala tayi kafin tace " Koda naji ninasan Kam taya Zaki kwaso jiki kiyonan bayan kin dauke uwarki daga kauye aikam de se mantuwa", yake Deeja tayi kafin baba kandala takara cewa " to gashi ba Wanda yasan guri acikin yaran nan sede idan ni zanzo narakaki barin tambayo me gidan, ince de da motarku me sanyin nan kikazo? " Ta tambaya tana washare baki, " cikin dan mazewa Deeja tace "no taxi nahau dg airport zuwa nan yanzuma inaga sede mudau wata taxi din dan nariga nasallami wancen". "To to bakomi aisemuhau kurar Adamu musamu ko titi yakaimu sannan musami taxu din ko?" Tafada tana dauraye kafarta jikina rawa har tamatsu su isa Kila tasami ko 'yar jallop ce me manja taci, dan ita atunaninta idan tasami jallop din manja tasami cimar yan gayun birni, tunda akauyen bakowa ne yake samun arzikin dafa shinkafa agidan Saba, Suma dasuke matan me unguwa tuwon datsar masara shine abincinsu me dan kyau da dadi, Allah yasa mudace. Koda suka fito akwatunan Deeja kusan guda takwas babu se wani wadan yaro cikin Wanda suka kifar da ita ne sukaga yana Jan dan kit din ta daya rage zeshige gida dashi aikuwa asukwane Deeja ta fafaro ta mauje masa Kai ta amshe akwatinta tana ihun Ina sauran kayanta, sbd idan Bata mantaba harda yan sarkojin Isabella da ba a bataba ta zundume amma gashi babu awaktunan ta se dan kit din da kayan ciki basuda yawa, ihu take tana karawa Fadi take "wayyo nashiga uku sarkokina kayana nashiga uku namutu na lalace", baba kandala sakato tayi tana kallon yadda Deeja ke sambada ihu, tace "kekuwa hadiza wasu irin kayane aka sace haka?" "Wlh baba kandala kayana masu tsada harda gwalagwslaina aciki wayyo nashigesu wlh se anbiyani" cikin gidan su tayi dagudu wanda ayanzu yake mallakin alh Mande big moo (Dan wada)kamar dazu tabude zata shiga Sega wata wadar matar tafito aguje aiko sukayi Karo da Deeja jikake timm takara faduwa itako wannan wadar matar ko gezau batayiba fadi take "luku waya bugeka nunamin hii" wannan wadan yaron yana kuka yanuna Deeja da ke yashe kasa yana fadin "Wagga tabbugan gatanan yashshe akasa ke kada ita" (sakkwatanci suke sbd mutanen Hausa ne). Juyowa matar tayi kan Deeja tace "mi yammiki kinka bugai?" Se huci take, baba kandala ce tamatso tace "yi hkr jummai wlh kayantane taga luku yanaja shine tadan make masa keya, kiyi hkr idan yakawo sauran kayan cikin gidan kutemaka kubata tafiya zatayi takawo mana ziyara ne,wacce aka kira da jummai wato wnn wadar matar tace " sunanan ciki ina Bata kayanta amma SE luku yarama bugun tammai" , " bakomi inde zaku Bata kayan yarama bakomi" Deeja ce tadago fuska jage jage duk majina zatayi magana baba kandala tamata alamar tayi shiru. " Matso luku tau nanniyagga rama bugun da tayyima" Aiko ba kunya wadan yaro ya matso kafin Deeja ta ankare ya lafta mata kututturen hannunsa a kumatunta seda taga taurari kafin tadawo daga suman datayi Sega jummai ta dire mata akwatunanta agabanta, da sauri baba kandala takama Deeja wacce tunda tazuba ihu sanda luku yamareta bata Kuma cewa komiba se dafe kuncinta datayi bata Kuma cewa komiba har me kura yazo irn wacce ake daurawa shanaye din nan , aka loda mata akwatunanta se a sannan baba kandala ta sauke ajiyar zuciya tadafa Deeja wacce se yanzu tadawo cikin hayyacinta Bude baki tayi da niyyar magana kawai Sega jini shaa ta hanci da baki, kuka tafashe dashi tanatayi abin dariya abin tausayi ga bakin da kimatun sun kumbure kamar biredi, baba kandala nata bata hkr tace "wannan Marin da luku yamiki shine rufin asirinki, Babu Wanda besan bala'i da masifar jummai wada ba idan tafara masifa akan yaranta tunsafe wlh seku kwana kunayi bata gajiba gata da karfi makar shara'a. Haka tayita tallaba Deeja har tayi shiru lokacin da suka iso cikin gari anfara Kiran magrib suka tare taxi yakaisu har kofar gidan da akace muktar yasiyawa karime maman Deeja akofar gidan suka ganta zaune tanata sheqa bala'i itada wani busasshen mutumi yanacewa yabata nanda jibi kota bar masa gidansa kota Nemo kudin hayarsa tabashi... Tikashi me Hakan ke nufi me wnn mutumin yake nufi bayan ance wnn gidan na karimene mamar Deeja, baba kandala ke tmbyr kanta. Suna wnn tunanin me taxi yace abarshi kudinshi, juyowa Deeja tayi tacewa baba kandala "kibiyasa mana kinata kallona", "kamar yaya nabiyashi Kode kibiyashi bake barakoba ?" Ko kallon inda suke batayiba,aiko me taxi yafito yafara nade hannun riga yana karkace Baki yace "yane ko abani kudina konayiwa mace zigidir wlh" kafin kace mekenan Deeja tazaro dubu biyu Wanda suka saura mata acikin yan kudinta tabashi, ya amshe Kuma yaki bata cenjin dari biyar dinta yace ladan Bata masa lokacin da sukayi,. ************************* Jiki ba kwari idiyatu ke kallon Rabil Wanda tun jiya shekaran jiya data kawoshi ranga ranga sau daya kawai ya farka, drip ne kawai ke dawainiya dashi, duk ya zabge yarame kamar yayi kwanaki yana jinya,. Gurin su Fatima taleqa Suma jikin alhamdulillah gobema ake sakaran basu sallama, tayi sallama tunda su maman inaya suka amsa basu Kara mata mgn ba sbd atunaninsu tadauke kafane sbd danta yace bashida alaqa da yaran, fatimace kawai take mata mgn. Juyowa tayi garesu ta fuskancesu tace "kugafarceni dan Allah nadauke kafatame kwana2 sakamakon nayi tafiya naje nahadu da baban Rabil wato mahaifinsa, namuku karyar cewa baya raye dan Allah kugafarceni akan hakan, mahaifinsa yana nan araye naboye mukune sbd wani dalili nawa Wanda nan bada jimawaba zaku sanshi, amma yanzu naga kamar bukatar yazo ga dansa yatasone shiyasa natafi cen gurinsa Kuma cikin rashin sa'a nasamu baya kasar yabar kasarnan gabaki daya ba tabbacin ze dawo nan kusa". Maman inaya ce tace " Amma ko kin cuci wannan yaron dakika kashe masa uba bayan yanada ransa,"sababi take kamar zata ari baki wai dan ma bataji ainahin abinda Idiyatun ta aikataba. Dama harda haushin dake cinta tasamu tasauke wa Idiyatu duk da haka bawai ta huce akan Rabil bane tana nan tana jiransa yazo yasameta, seta masa kwando kwandon rashin mutunci. .......................... Muktar yanzu ya shiryu lafiyar Allah suna zaune da mamansa lafiya lau, babansama yadawo dg kontagora ashe dama yana zuwa lokaci zuwa lokaci, a lokacin da sukecen gidan bature, har yanzu jikin muktar begama sakiba daga dukan da yasha a hannun sojojin nan. Biba kuwa a yanzu babu abinda yake bukata samada iyayenta, kullum kuka take kamar karamar yarinya batada aiki se Kiran akaita gida gurin mamanta, zuwan Awwal sau biyu lokacin basu dawoba, yauma kamar kullum haka ta matsa musu da koke kokenta na fama bashiri alh Mansur Wanda ayanzu shikansa tausayin Biba yake tarame tayi duhu dukta fice a hayyacinta, batacin abinci se an matsa takeshan ruwan Lipton, yasa aka tattarata akasa amota hardashi da matarsa wacce yake jego satinta uku kenen da haihuwa aka dunguma aka tafi se gidansu Biba acen garin SULEJA dake bawani nisane dashiba dg Abuja zuwa SULEJA bawani Nisa. Koda suka iso a sukwane Biba tasanyo kafarta me lfyr ta sakko tana sanyo tabiyu wacce itace ta robar aiko cikin tsautsayi ta gurde tadafi kanta y bugu da kasa, nan take tasume, Dede lokacin da muktar yarikowa mamansu dan bakkonta zata kasuwa cefanen kayan miyar datake siyarwa, Wanda yayi2 tabashi yaje mata taki yadda Shima yadage akan sede suje tare, shine suna sanyo Kai sukayi arba da Biba yashe akasa ba alamun numfashi atare da ita ga sauran mutanen gidan zagaye da ita. 🌹 SIRIKATA 🌹 Na SADIKA IBRAHIM. Not edited. Pg31_32 Bismillahirrah manirrahim. Dakyar na gwaggo yasamu mamansa tadena maganar Karin auren sa,seda yakara kwana 4 sannan yatafi bayan yakara kwantar mata da hankali. Abangaren Idiyatu dasu Fatima ma anbasu sallama lokacin Rabil yafarko Shima sede be fiya yin magana idan ba tazama dole ba, anyi anyi idan baze amshi yaran fatimaba to yasaketa amma yaqi yace shi wlh ko kashesa za ayi baze taba sakintaba amma fa yaranta banashi bane baya sonsu bayason ganinsu, anrasa gane kansa akan yaran kullum Idiyatu batada aiki se kuka itace tayiwa yaran yanka itada alhaji mijin maman inaya yara Kam sunsami gata na ban mamaki kamar yadda ubansu ze musu haka aka musu fiyeda yadda ma ze musu, gasu da shegen kyau kamar ba yaran hausawaba, komi na shagalin sunansu daga Idiyatu da alhaji yafito, yara kam basu rasa komiba se soyayyar ubansu, Kuma bayan Idiyatu bawanda yake masa uzuri domin bawanda yayi tunanin wai tsafine yake dawainiya dashi, duk atunaninsu kawai haihuwace bayaso, ita kanta Fatima takasa yimasa uzuri tace sede yahada duka yatsanesu har ita dan ita bazata zauna da Wanda bayason yaranta ba, ita abinma wani lokacin mamaki yake bata ganin yadda idan yazo gidansu ganinta duk wulaqancin da zata masa taki fitowa baya gajiya, dazarar tafito zeyi kamar yamata sujjada yayita bata hakuri akan tadawo gida hakanan domin yanzu tayi arba'in harma da doriya, idan kuwa tanason ganin tashin hankalinsa to ta dakko yan biyu yanzun nan ze rikice yayi kamar ze dauke numfashi, ranar da ta ce seya dauki Hassan dake ba a cenza musu sunaba aiko ranar taga tashin hankali ganin idonta don ba zato tadora masashi akan kafarsa aikuwa yayi wani irin ture yaron yako fadi kasa hannunsa ya amsa shikuma yazube agurin asume tarikice tarasa wazata kama cikin da da Uba aikuwa sede tayita zunduma ihu tana neman agaji dan takasa temakon ko dayansu ga Hassan akasa se tsandara ihu yake ga Rabil asume agefe ita Kuma tana riqe da Hussain Wanda shine yake ciwon zuciya ba aso yana kuka ko kadan Kuma ba ason hayaniya dayawa ataredashi. Gashi dazarar Hassan yakama kuka Shima ze kama, ga ihun uwarsu daya cika masa kunne gashi tariqesa akafadarta ihun ta yana kaiwa kunnensa sosai ai take Shima yakama kuka duk ta rikice Hussain bedade Yana kukaba yayi luf yalangabe mata ajiki ai data Kuma yanka wani wawan ihu alhaji da shigowarsa kenan aikuwa yarugo aguje ya afko cikin dakin ko sallama ba tsaya yiba, yana arba da Fatima riqeda Hussain ga Hassan da Rabil yashe akasa ai dawani irin gudu yakarasa shiga dakin ya dakko Hassan lokacin mutanen gidan duk sunji ihun Fatima Suma aguje suka shigo dakin mmn inaya ce arikice take tambayar lafiya bawanda ya amsata se ihun Fatima dayaki karewa kamar tazare se callara ihu take, alhaji ne yy karfin halin cewa Osman babban dansa yakama masa Rabil yasanya amota sutafi hospital. Idiyatu na gida mummunar labarin nan yarisketa, arikice tabaro shagonta Wanda ayanzu take dan zuwa ba sosai ba, ta tafi asibitin, Koda ta isa tasami mmn inaya, alhaji, Osman, sunyi jigum jigum ga Fatima idonta harya kumbura sbd kuka, Kuma har yanzu bata dena kukanba, kanta akan kafadar mmn inaya, likita ne yafito dasauri duk suka mike suna tambayar sa lfy be amsa musu ba yashige office nasa ya dakko wani abu yadawo yasake shigewa seda yakusan 2h sannan suka fito. Kallonsu likitan yayi yana tambayar sune suka kawo yaran ko, suka amsa masa, yace ma alhaji yabiyosa ofis alhaji yace "banida wannan kwarin gwiwar likita kafadi koma menene anan dukanmu iyalai guda ne Kuma kome yafaru da yaran zamu dauki kaddara, fadi kawai likita". Numfashi Dr ya sauke yagyara tsayuwarasa yace "dafarko dai zance alhamdulillah munsani nasarar dedetuwar numfashinsu dukansu daga yaran har uban, shi baban nasu tsananin firgicine da kaduwa da yayi sakamakon gani ko jin wani mummunan abu shine yayi sanadiyyar sumewarsa Wanda Allah yatemaka faduwar batazo da wata matsala ba yanzu haka yasami bacci in Sha Allah nan da 1h ze iya farkawa cikin koshin lafiya". Sauke ajiyar zuciya Fatima da Idiyatu sukayi atare, aransu fadi suke alhamdulillah. Dr yacigaba "sukuma yaran dayan da yafadi yasami gaucewar kashine ahannunsa amma yanzu komi normal alhamdulillah munsani nasarar dedetuwar kashin nasa Shima yana bacci zaku iya ganinsama yanzu, shikuma dayan wato Wanda muka fada muku tun farko yanada matsalar ciwon zuciya munsamu ya farfado yanzu haka ana Kara masa gwaje2 ne dan mu Kara tabbatar da yana cikin stable condition, amma fa akiyaye abinda yake sanyashi irin wnn kukan dahar yake sanya numfashinsa yana daukewa sbd munriga munfada muku condition dinsa pls akiyaye next tym kar ana barinsa yana irin wnn kukan idan ba hakaba idan yana samun irin wnn attack din wata rana ba lalle ne ya farkaba sede ayi hkr dashi kawai". " Alhamdulillah" shine abinda kowa na wurin yafurta, wata wawuyar ajiyar zuciya Fatima takara saukewa, gdy alhaji yaketa yiwa likitan, likita yace bakomi yanzu ma zasu iya shiga sugansu idan angama yiwa Hussain gwajin se akawo musu shi. Ai dasauri Fatima da Idiyatu har suna rige rigen shiga dakin ganin Idiyatu yasa Fatima tayi kan Hassan dasauri Wanda yaketa shara baccin wahala hannunsa nade da plasta, Idiyatu Kuma kan Rabil tayi tana shafa kansa idonta cikeda kwallah, itama idonta har ya tasa sbd kukan da tayita yi dazu, kiss tamasa agoshi tace "in Sha Allah zan gyara komi Koda hakan yana nufin numfashina na karshe aduniya, I will correct my mistakes nd I will resurrect wat i have killed inside you my son" kamar amafarki yakeji maganganun ta akunnensa bude idonsa yayi yana kallonta itama shi take kallo tana hawaye sosai, maida kallonsa yayi kan Fatima wacce taketa kallonsa idonta cikeda kwallah mika mata hannu yayi dasauri tamatso takama nasa, janyota yayi tafado kansa rungume juna sukayi ita tana kuka Shima ji yake kamar yayi kukan, bayason yaranta yarasa meyasa amma ko kallonsu bayason yi, ita Kuma taki fahimtar sa, magana yafara kamar haka adede lokacinda su mmn inaya da alhaji, da mmn Fatima suke shigo sbd ita se lokacin tazo kasancewar agidan mmn inaya Fatima take jegonta " pls teema karki Kara bani yaran nan banaso, wlh banaso idan na kallesu jinake kamar na shaqe kaina ko na shaqesu, pls karki sake banisu, alokacin da kika doramin daya ajikina jinayi kamar gaushin wuta kika sanyamin, kiyi hkr bansan na yardashiba" dago Kai Fatima tayi daga kan kirjinsa tazuba masa idonta Wanda suka kumbura tana kallonsa da tsananin mamaki, kallon cikin idonsa rayi taga tsantsar gaskiyar sa yake fadi, bayason yaransu akan me to? Wannan itace tambayar da batada amsarta duk wani Wanda ne cikin dakin ma bashida wannan amsar se mutum daya Idiyatu. Jiki a sanyaye tadaga masa kai tana Saka wani abu acikin ranta, kowa dake dakin kallon tsantsar mamaki suke musu Wanda ko sanin anshigo basuyiba Idiyatu ce tarufe baki da tafin hannunta tafita wani irin kuka na kucce mata, se a sannan Fatima tasan da mutane adakin Jin karar kofa, ganin wadanda suke tsaye yasata dagowa da sauri tana sauke Kai kasa, kasa cewa komi sukayi dukansu kowa da abinda yake sakawa acikin zuciyarsa, lamarin Rabil abin dubawa ne kamar Wanda jinnu suka shafa, haka sidda bazaka tsani yaranda kayi cikinsu Kuma kasha wahalar tarairayar cikinsu ba, se bayan sunzo duniya ne zaka ji katsanesu? Wannan Lamarin abin a dubane abunda kowanne su yake sakawa kenan acikin ransa, dukansu gurin gadon Hassan suka nufa suna kallonsa cikeda tausayi. **************************** Haka lokaci yayita shurawa inda daga karshe aboye batareda sanin kowaba Idiyatu tayi hayar private investigator tasashi yana bincikar mata lamarin MUHSIN mahaifin Rabil inda suka Sami labarin ankara yimasa canjin gurin aiki yakara komawa Florida da aiki, gabaki daya takasa samun wani makama akan lamarin iyayen Rabil. Kuma sbd karancin ilimin addini datake dashi bata wani yi tunanin hada masa da temakon malamai akan dagewa da addua da rokon Allah, akan ya sanyaya lamarin ba, tafi believing kan cewa tabbas karyewar wnn sihirin yana tareda haduwar Rabil da mahaifansa na gsky. Agefen su Fatima da iyayenta su mmn inaya kuwa sun Sanya malamai sudinga yimusu rokon Allah akan ya sanyaya koma menene dake tareda Rabil din, sbd wani malami yasheda musu lalle Rabil akwai sihiri ajikinsa Kuma yabasu addu'o'in da za a dinga masa aruwa yana Sha, Kuma alhamdulillah yarage wannan firgitar idan yaga yaran sede har yau baya daukarsu, itama Fatima bata fasa yimasa adduar ba, har yanzu Kuma bata koma gidansaba gashi yaran har sun shekara suna yawonsu ko Ina, sunyi wayo Hassan bade kiriniyaba, Hussain ne ma becika yawan dariyaba shine me ciwon zuciya, Koda yaushe zaka gansa acukule, idan yayi dariya yaga Hassan ne ko alhaji ko Kuma Osman babban da mmn inaya. Yaran akwai shiga rai kowa sonsu yake acikin unguwa kamar yaran turawa Allah yamusu baiwar kyau gasu very identical baka taba ganesu sbd kamarsu tayi yawa, gasu dukansu blue eyes garesu, sede na Hussain batakai na Hassan duhuba, bazaka taba gane hakan ba se idan suna tare aguri daya,ko agida ana ganesune kawai ta halayyarsu Hassan akwai dariya ko cemasa akayi kaii to yanzu ze bantare baki yana dariya,Hussain kuwa ga kyuiya ga rashin fara'a,shekararsu daya da wata biyu aka yayesu sbd girmansu kamar ba twins ba dama bawani damuwa suke da nonoba, idan aka kaisu gurin Idiyatu tun safe se dare suke dawowa, shiyasa ma tayayesu. Wani abin al'ajabi shine yadda Idiyatu keson yaran nan harya baci, Ashe sonsa takewa Rabil shafim maine,haka zata kashe musu kudi kamar batasan zafinsuba, Karin mamakin shine duk ranarda aka kawosu gidan ta, to Rabil baya fitowa adaki ze wuni ashe labewa yakeyi ajikin labule yayita kallonsu duk kiriniyar da sukeyi yana kallo wani yayi murmushi wani yayita mamaki sbd wayone dasu, haka Idiyatu zata zuba musu kayan wasa afarfajiyar gidan suyitayi, idan suka gaji takwashesu tamusu wanka acenza musu kaya adaukesu amota afita aiko haka Rabil ze shiga tashi motar yayita binsu abaya duk inda sukaje yana biyedasu batareda saninsuba, har sugaji sudawo gida, se anmayardasu sannan yake samun mutsuwa yakwanta yayita tunaninsu yana murmushi shikadai amma ko inda suke baya zuwa balle ya daukesu. Se bayan an yayesu snn ne Rabil yaje har gida yayita magiya abasa matarsa haka ba yadda suka iya aka bashi matarsa domin itama tanuna tanason komawa ga mijinta. Agurin mmn inaya aka bar yaran, amma Idiyatu tazo tanemi alfarmar duk abinda suke bukata arayuwa ita zata yimusu, taroki alfarmar ko pampers sukeda bukata itace zata Siya. Haka rayuwa tayita shurawa har su Hussain suka isa shiga school lokacin Fatima nada shigar wani cikin bawanda yasani harshi uban gayyar Rabil tsoro takeji gashi bazata iya zubarwaba, batason irin kaddarar su Hussain tafadawa wnn cikin Shima, haka zata boye adaki tayita kuka, kasancewar wnn cikin lafiya lau tayisa ba amai ba komi, sede 'yan kwadaye2 dacin abincinta daya karu. Idiyatu itace komi na makarantar su Hussain taki barin alhaji yatemaka mata da komi hatta sock dozen uku uku ta ajiye musu, haka pencils, litattafai Kuma duk a school ake basu, makarantacs me mugun tsada, komi da komi acen ake baiwa yara har abinci, idan Kuma baka bukatar ba makaranta seka dinga kawo naka amma idan ka kawo sekaje gurin social master kanuna masa Kuma ka dandana agabansu sannan ka ajiye katafi, haka Idiyatu tadaukarwa kanta wannan larurar, Fatima tayi tayi tabari suci na school taki wai kar aje abawa buddies nata naman alade kasancewar school din ta arnace, sukuma haka take kiransu buddies. Ahaka har cikin Fatima yakai wata bakwai SE a sannan yafito shikansa Rabil se a lokacin ya tabbatar da cikine da Fatima sbd ada ya dauka tumbine kawai tayi, ganin bata laulayi ko kadan sannan bata taba cemasa tanada cikina ko tanajin ciwon Kai, idanma taji abinta sede tasha magani batareda saninsaba. Aiko ranarda yagane cikine yayita masifa wai taki sanar masa, budar bakinta kuwa tace "sokake nafada maka inada ciki ka shegantasa tunma kafin yazo duniya ko?" Sekuma jikinsa yayi sanyi bekara cewa komiba haka yayita yallabata Kodan tari tayi yanzu ze mike tsaye yace yaya muje asibiti ne ko kuwa, abin nashima har dariya yake bata wani lokacin. Cikinta yashiga watan haihuwa amma kullum fargaba take, Hakan yasa tafara ramewa kullum Rabil na nan nan da ita amma hankalinta yakasa kwanciya, ranarda ta tashi da nakuda se rokon Allah takeyi ita ciwon baya damunta kamar yadda take fargabar yadda Rabil ze amshi wannan dan dako haihuwarsa ba ayiba, tana tausayin wnn yaronko yarinyar, Kuma a wnn karo ta Sanya aranta idan har Rabil yace wannan dan ko 'yar banashi bane to ita dashi sede a lahira. Lafiya lau ta haifi yarta mace me kama da Rabil sak kamar yayi kaki ta tofar, itama blue eyes gareta, Rabil kamar zeyi hauka harda hawayensa ya rungums 'yar yana mata addua nan take ya Sanya mata suna Nadhira yana bala'in son sunan. Kowa mamaki yake don da gayya mmn inaya takwaso su Osman niyyarta idan Rabil yace wannan ma b 'yarsa bace tasa sumasa shegen duka se gashi agaban kowa yake kukan sonta harda Sanya mata suna. Anan take suka gano lalle akwai wani Al amarin akansa gameda su Hussain. Allah shine mafi sani. Anyi shagali nafitar Kai a wnn haihuwa kamar shine haihuwar fari. Daganan Kuma Fatima bata Kuma haihuwa ba. **************** BAYAN SHEKARA GOMA.... "Likita dan Allah kiyi iya yinki aceci rayuwar matata, dan Allah, idan kunga da matsala ayima ta CS kawai acire babyn amma wnn wahalar tayi yawa"na gwaggo yafada gumi na karyo masa. "In Sha Allah karka damu zata haihu dakanta base an mata aiki ba in Sha Allah zata haihu dakanta, kude kuci gaba dayinata addua". Gefe daya kuma wata gajeriyar matace se gyatsine fuska take tana hura hanci magana take kasa kasa " hmm niza a nunawa haihuwa nida ba haife maza hudu, dan ma ba tsayawa suke ba iskancin banza wnn har nakuda take". Gefe daya kuma mmn n gwaggo ce se jab tazbaha take tana kwalalo ido tanaso tayi mgn amma tana tsoron bala'in murja dawo END OF BOOK 1.