[10/4, 11:13 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba. Ban yi shi don cin zarafin kowacce ƙabila da Masarautunsu ba. SHAFI NA ƊAYA Masarautar Huddam Shekara Saba'in Baya (1953) Wani irin zafi take ji yana ratsa ta tun daga tafin ƙafarta har zuwa tsakiyar kwanyarta, dalilin haka ya sabbaba mata karkarwar jiki tamkar wacce ta ji kiɗan gangi. Wanda hakan ne ya haifar mata gumin da ke tsatssafowa daga kowacce kafar da ke cikin ilahirin jikinta. Ba yau ne karo na farko da haka ya taɓa faruwa da ita ba, sai dai a wannan ranar ji take tamkar an saka ta a tukunya ana dafa naman jikinta da ruwan zafi. A hankali ta cije baki tana yarfe hannu haɗe da lumshe idanu. Baiwa Maimuna da ke bayanta tana mata fifita cikin ƙwarewa a makirci ta fakaice ta, ta yanki ƙasan jelar gashin kanta ɗan ƙanƙani ta yadda ba za ta fahimci hakan ba. Da sauri ta soke shi a jikinta haɗe da sauke ajiyar zuciya don ko babu komai ta san ta tsira daga siraɗin Fulani Umaima. Ta ɗan numfasa a hankali. "Ki gafarce ni uwar ɗakina zan ƙarasa sashen Takawa na ce Jakadiya ta karɓo miki magani kamar yadda na ji kin ambata a baya, ranki shi daɗe lamarin ciwon nan na ki ƙara ƙamari yake yi amma tuba nake idan da kuskure a kalamaina uwar ɗakina." Ta so musa mata kamar yadda ta yi kafin zafin jikin ya fara galabaitar da ita, dalilinta na yin haka bai wuce yadda take gudun kada Bayin cikin masarautar su fuskanci zaman doya da manjar da ke tsakaninta da Mai martaba ba. Gyaɗa mata kai ta yi haɗe da ruƙo hannunta ta furta, "Idan kin fita Maimuna ki turo mini Baiwa Zainaba." Cike da girmamawa ta russana, "Allah ya ƙara wa Fulani lafiya, Ubangiji ya buɗi ido lafiya ya kawo mana Yarima mai jiran gado cikin yalwar ariziƙi da ƙoshin lafiya." Da hanzari ta fice a gaggauce don ko kaɗan ba ta son wargaza shirin ɓoyayyar uwar ɗakinta. Sai da ta turo wa Fulani babba Zainaba sannan ta wuce sashen Fulani Umaima cike da firgici, tana tafe tana waige kamar sabuwar munafukar da ta yi gulma a fada. Da yake Fulani Umaima ta kwana da sanin shirinsu, tun da doshin magriba ta sallami bayinta suka wuce sashensu na bayi. Tamkar wacce aka jefo daga sama haka ta faɗa ɗakin Fulani Umaima da ke tsaye tana kai kawo don gudun samun matsala a shirinsu, duk da tana da yaƙinin Baiwa Maimuna ba za ta iya shallake wa umarninta ba. A ƙasa ta zube tana sauke numfashi ta furta, "Hutawarki lafiya Fulani mai magajin masarauta, zinariyar Mai martana haskenki bai tsaya iya shi kaɗai ba kin haske lungu da saƙon cikin Masarauta. Ina gwanar wani ga tawa? Kin yi taki kin yi ta kowa, garnaƙaƙin dutse kike kowa ya ja da ke shi zai faɗi..." Fulani Umaima ta katse ta da cewar, "Ina fatan komai ya tafi yadda ya kamata?" Baiwa Maimauna ta saki murmushi, dalilin haka ya sa Fulani Umaima ta sauke ajiyar zuciya duk da ba ta kai ga jin amsar Maimuna ba amma ta fahimci sun yi nasara domin kuwa labarin zuciya a tambayi fuska. "Ranki shi daɗe an gama aiwatar da komai, ga wannan." Maimuna ta ƙarasa maganar tana kunto gashin kan Fulani Babba ta miƙa wa Fulani Umaima. Wani yalwataccen murmushi Fulani ta saki, Baiwa Maimuna ta ci gaba. "Yanzu haka tana can magashiyan har ta umarce ni da na aika Jakadiya ta karɓo mata ragowar maganinta a wurin Mai martaba." Wata irin dariya ce ta suɓuce wa Fulani Umaima wacce ba ta tsammace ta ba, tuna wacce take gabanta ya sa ta tsuke fuska haɗe da furta. "Ki jira ni." Uwar ɗakinta ta shiga can ƙarƙashin gado ta zura hannunta, ta ɗauko wani ƙoƙon kan ƙwarangwal. Wani garin magani ta ɗebo a ciki ta kulle a cikin wata 'yar busasshiyar ƙaramar fata. Ta fito zuciyarta fes cike da takun isa da ƙasaita. Sai da ta koma kan ƙasaitacciyar kujerarta ta zauna sannan ta miƙa wa Maimuna. "Ki fara zuwa ki karɓo maganin wurin Mai martaba, amma ki tabbata wannan kika ba ta ta yi amfani da shi, za ki zuba mata a ruwa ko abinci kuma ki tabbatar da ta shafe jikinta da shi. Duk dare ina buƙatar ganinki domin akwai fitar sirrin da nake so mu yi." Cike da girmamawa Maimuna ta russuna. "An gama ranki shi daɗe, fansar kaina gare ki ya shugabata domin kai da kaya duka mallakar wuyane. Ki sa a ranki na aiwatar da duk abin kika buƙata na gama, Allah ya taimaki giwar Takawa ɗawusu mai yawan ado." Fulani Umaima ta gyaɗa kai sannan Baiwa Maimuna ta miƙe, har ta je bakin ƙofa Fulani ta furta. "Ki tabbata ba a samu matsala ba, idan aka samu matsala ki kuka da kanki." Baiwa Maimuna ta russuna. "Godiya nake uwar gijiyata." Sai da Maimuna ta ɗaure maganin wurin Fulani Umaima sannan ta nufi sashen Mai martaba, Jakadiya ta samu ta sanar da ita saƙon Fulani Babba. Kai tsaye Jakadiya ta tunkari turakar Takawa. Sai da rangaɗa sallama haɗe da kirarin girmamawa sannan ta isar da saƙon Fulani Babba. Kamar ba zai amsa mata sai kuma ya miƙe ya nufi wata jakar fata da ke saƙale a jikin bango ya zura hannunsa, wasu ƙullin magunguna biyu ya ciro ya miƙa wa Jakadiya, ta karɓa tana godiya. Har ta fara tafiya ya furta. "Daga yau a sanar da ita ta riƙa karɓar magani kafin almuru, ba a koyaushe muke da buƙatar hakan ba." Jakadiya ta amsa sannan ta fice ta damƙa wa Baiwa Maimuna tana jaddada mata saƙon Mai martaba. Maimuna na shiga sashen Fulani Babba ta same ta kamar yadda ta bar ta, Baiwa Zainaba na gefe tana matsa mata ƙafafuwanta da suka ɗan kumbura. Cike da girmamawa ta miƙa mata maganin da Fulani Umaima ta bata sannan ta furta, "Allah ya ƙara wa Fulani lafiya, Ubangiji ya shiga lamuranki uwar ɗakina. Mai martaba ya ce a jiƙa rabi, rabi kuma a shafe miki jiki da shi." Idanun Fulani jawur kamar sabon barkono ta buɗe su a hankali ta furta. "A yi yadda ya da ce Maimuna." Zuciyar Maimuna ƙal ta tashi jiki na rawa ta jiƙa maganin kamar yadda Fulani Umaima ta gaya mata, ta taimaka wa Fulani Babba ta tashi zaune haɗe da kai mata ƙoƙon bakinta. Tas ta shanye shi sannan Maimuna ta shiga shafe mata a jiki gabaɗaya, sannu a hankali ta ji wata sassanyar iska na ratsata. Ta koma ta kwanta sakamakon jin daɗin jikinta da ta fara yi. Ta dubi su Baiwa Maimuna. "Maimuna za ku iya tafiya, Zainaba a tabbata an gyara makwanci su Khadija." Cikin girmamawa suka zube ƙasa, "An gama ranki shi daɗe, Allah ya ƙara lafiya ya kawo mana Yarima lafiya." Ba ta iya amsa musu ba sai ma runtse ido da ta yi sakamakon jin wata irin hayaniya da ta yi a tsakar kanta, ga wani irin jiri da ke ɗaukanta. A ɓangare ɗaya kuma wani abu mai tsini ya fara fusgar can cikin ƙasanta. A gurguje Maimuna ta fice haɗe da sake ba wa Zainaba umarnin gyaran ɗakin su Khadija da yake ita ce gaba da ita, ta juya ta fice daga ɓangaren 'yayan Fulani Babba. A sanyaye Baiwa Zainaba ta bi Maimuna da kallo don haka kawai take jin zuciyarta na wasuwasi a kan Baiwa Maimuna tun da ta taɓa ganinta ta shiga sashen Fulani Umaima sau biyu. Kai tsaye sashen Fulani Umaima ta faɗa, kuma a wurin da ta tafi a nan ta koma ta same ta. Fulani Umaima na ganin Baiwa Maimuna ta faɗa uwar ɗaki, wani sirrintaccen akwatinta ta ɗauko ta buɗe cikinsa. Kamar kullin idan za ta ziyarce shi haka take saka wannan sihirtacciyar rigar da Boka Bamagujen dutse ya bata, a lokacin ma sai da ta tube kayanta gabaɗaya sannan ta zura rigar mai ɗauke da launin ja, baƙi, ruwan ɗorawa da launin ruwan ƙasa. Rigar ɗinke take da waɗansu ƙananan layu sai kuma wasu ƙananun rubutu da aka yi da larabci, wani ɗan ƙaho ta riƙe a hannunta sannan ta fito wurin da ta bar Baiwa Maimuna. Hannu ta miƙa wa Maimuna babu musu da yake ta san kwanan zancen ta ɗora tafin hannunta a saman na Fulani Umaima, wanda ta tabbata ba don wannan sirrintacciyar tafiyar da suke yi ba babu dalilin da zai kai hannunta jikin Fulani Umaima, musamman yadda take nuna ƙyamar bayi da talakawa ƙarara a fili. Saka hannun Maimuna cikin na Fulani babu jimawa, ta runtse idanunta ta ɗaga hannunta da ta ke riƙe da ƙahon ta busa sau uku sannan ta kira sunan Bamagujen dutse sau uku. Wata irin guguwa ce ta karaɗe cikin ɗakin kamar ƙiftawar ido sai ga su a bakin wani ƙaton farin dutse mai ɗaukar ido, wurin kamar rana tarwai babu abin da ba ka iya gani. Kamar yadda yake bisa al'ada a duk lokacin da suka ziyarce shi, sai da suka saka ƙafarsu ta hagu a tare a kan wani jini da ke malale a gabansu. Sun ɗan ɗauki kamar minti biyu a haka sannan suka ji an bushe da wata irin dariya wacce take alamta musu aikin da ya da ce su yi a gaba. Ƙafarsu suka sake ɗagawa suka ɗora a kan wani kabari da ke gaban wannan jinin sannan suka fara takawa suka haye can sama dutse. Zaune suka hango shi babu ko ɗigon sutura a jikinsa, Maimuna ta kawar da kanta gefe don har cikin zuciyarta ba ta son ziyartar wannan shu'umin bokon don dai ba ta da yadda za ta yi ne. Suna ƙarasawa wurin wata ƙaramar bishiyar kuka Maimuna ta russuna tana faɗin, "Fatan nasara a kodayaushe ya shugabata." Fulani Umaima ta ci gaba da tafiya don Maimuna ta san ko karen hauka ne ya cije ta ba ta isa ta ƙara koda taku ɗaya ba. Fulani na zuwa sai da ta fara ɗiban wani jan ruwa a cikin wani ƙoƙon kan ƙwarangwal ta wanke fuskarta, sannan ta nemi wuri ta zauna tana fuskantar Boka Bamagujen dutse. "Barka da aiki uban gidana." Jinjina kai ya yi ya furta. "Barkanki Fulanin Sarki Abdul'aziz." Shiru ne ya ratsa Fulani Umaima ta kawo ido ta sa wa Bamaguje, ya saki murmushi don ya san wace ce Umaima. Ga tsananin buƙata fal ƙirjinta ga kuma taƙama da izzar mulki, kallo ɗaya ya yi mata ya fahimci halin da take ciki. "Umaima kin yi ƙoƙari." "Sanin haka ya sa na kawo ziyara a ranar da ka buƙata." Ta amsa masa a taƙaice. "Kin aiwatar da komai yadda ya kamata, don haka kishiyarki ita da Sarki Abdul'aziz sai kallo sai hange daga nesa. Matuƙar ba asirin nan ne ya karye ba, ba na jin kishiyarki za ta sake ɗaukan ciki a doron ƙasar nan. Ke ba ma ciki ba ina mai tabbatar miki ita da sake yin wata mu'amala da Sarki Abdul'aziz sai dai a lahira idan ana yi. Ina ragowar kayan aikin?" Ya wurga mata tambaya. Jin haka ya sa Umaima ta saki malalacin murmushi ta ɗebo gashin Fulani babba da gashin Sarki Abdul-aziz, haɗe da ƙasar maƙabarta da ta gidan tururuwa ta miƙa masa ba tare da ta tanka masa ba. "Mun sakar mata lalurar fitsarin kwance, kuma mun saka mata lalurar mantuwa da warin jiki." Bamaguje ya faɗa yana jefa tarkacen da Fulani Umaima ta bashi a cikin wata tunkunya da ke cike da jini tana tafasa. Kusan duk abin da suke tattaunawa Maimuna tana jin su, haka kawai ta ji tausayin uwar ɗakinta ya ɗarsar mata. Musamman da ta tuna zallar cin amanar da take yi mata mai haɗe da zagon ƙasa. "Ina maganar cikin jikinta ya kwana?" Fulani ta tambaya cike da izza. Bamaguje ta ɗebi wani jini mai yauƙi ya watsa a jikin wani allon farin ƙarfe. Take waɗansu inuwoyi suka bayyana, yana fara nazartarsu sai gani ya yi ɗuff komai ya ɗauke. Cikin da damuna ya sake ɗiban jinin ya watsa har sai da ya yi haka sau uku sannan ya dubi Umaima cikin damuwa. "Kishiyarki a daren yau za ta haihu!" Dum! Fulani ta ji tsakiyar kanta ya sara kamar wacce aka buga wa guduma. Rai a ɓace ta dube shi. "Wanne irin mugun labari nake ji haka, zancen banza kenan ƙafa ta mutu ta bar takalmi. Cikin jikinta ya fi komai ɗaga mini hankali..." Da sauri ya katse ta. "Tun fil azal kundunsa rubuce yake da zanen ƙaddararsa, cikin kishiyarki shu'umin ciki ne lulluɓe yake da almara tamkar yadda masarautarku ta kasance SHU'UMAR MASARAUTA. Kamar yadda na gaya miki a yau za ta haihu..." Duk dakiya da ƙarfin zuciya irin ta Fulani Umaima sai da hawaye ya suɓuto mata, Bamaguje ya tsaya yana kallonta haɗe da jinjina kai. "Yau shekarata biyar kenan a cikin masarautar nan ko ɓatan wata ban taɓa yi ba, tun Fulani babba na da goyon fari Takawa ya auro ni. Bamaguje kana son na ƙare rayuwata cikin ƙasƙanci da rashin mamora?" Girgiza kai ya yi, ya sauke ajiyar zuciya. "Wa ya ce miki ba za ki haihu ba?" Fulani ta zuba masa idanu zuciyarta na bugawa. "Yanzu haka kina ɗauke da juna biyu na tsawon makwanni uku." Kamar a mafarki haka ta ji kalaman Bamaguje na ratsa majiyar sautinta. "Ki yi imani da ni Umaima matuƙar ina numfashi ba za ki tozarta ba." Sanyi ta ji har cikin ranta. "Da kai na dogara Bamaguje na yi imani da kai tun da ba ka kunyata mahaifiyata ba na tabbata ba za ka tozarta ni ba." Ta yi maganar a raunane. Wata ƙatuwar kunama ya ɗauko da hannunsa ya ce, "Ba ni hannunki." A firgice ta wurga masa kallon baka da hankali, ya saki murmushi don ya fahimce ta. "Umaima kenan kura kike ga tsoro ga ban tsoro." Umaima ta haɗe fuska kamar ba ita ba. "An ya kuwa? Kar fa ka manta ko kura ta rame ta fi ƙarfin gawurtattun karnuka, dalilin haka ya sa masallacin kura ba a ba wa kare limanci." Murmushi Bamaguje ya yi. "Kwantar da hankalinki kamar kin faɗa rijiya. Matso kusa ki ji." Bamaguje ya furta. Tun bai rufe baki ba Umaima ta matsa kusa da shi, raɗa ya yi mata a cikin kunne lokaci ɗaya ta bushe da wata iriyar dariya cike da farinciki. Ta koma mazauninta na farko tana sauraronsa. "Ki tabbatar da kin aiwatar da abin da na umarce ki, don kuwa kowa rai ya yi wa daɗi ba ya mai shi ba." "Bamaguje kenan! Ai ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba." Umaima ta furta cike da nishaɗi. Kashe mata ido ɗaya ya yi yana ƙare mata kallo, ganin haka ya sa ta fahimci inda ya dosa. "Tukwina fa?" "Ka sallame ni kenan?" Ita ma ta wurga masa tambaya. Gyaɗa mata kai ya yi Umaima ta miƙe babu ko kunya ta sauke rigar tsubbun jikinta, Maimuna ta sunne kai ƙasa zuciyarta na bugawa. A fakaice take ƙare wa tsohon kallo cike da ƙyanƙyami don ko ita da take baiwa gani take ba za ta iya haɗa jiki da shi ba. Bamaguje na shirin ɗora hannu a jikinta ta ɗan ja da baya haɗe da sakin murmushin mugunta. "Na sadaukar maka da kishiyata a wannan daren, shi ne tukwicin da zan iya yi maka." Ba ta jira cewarsa ba ta ɗora rigar a jikinta. Bamaguje ya gyaɗa mata sannan ya furta. "Za ku iya tafiya." Umaima ta yi masa jinjina da hannu sannan ta sake ɗiban ruwan da ta wanke fuska da shi ta nufi wurin da Maimuna ke zaune hannunta ɗauke da kunamar da Bamaguje ya damƙa mata. Abin da suka aiwatar a farkon zuwansu yanzun ma haka ne ya faru, sai da suka koma daidai wurin da suka buɗe ido suka gan su tun farkon zuwansu sannan, Fulani Umaima ta ɗaga ƙahon ta runtse ido ta busa haɗe da kiran sunan Bamaguje. Ƙamshin ɗakin Fulani ne ya ankarar da Maimuna dawowarsu gida, cike da girmamawa ta zube ƙasa ta furta. "Allah huta gajiya uwar gijiyata." "A kullin ina sake jaddada miki bakinki ƙanin ƙafarki Maimuna, duk ranar da kika bari kwaɓarki ta yi ruwa na ji sirrina ya fita za ki bambamce mini tsakanin tsaba da tsakuwa." Fulani ta yi maganar cikin sigar gargaɗi. "Maimuna ta duƙa kai ƙasa. "Wace ni uwar gijiyata? Kada Allah ya nuna mini ranar da zan aikata miki wannan zunubin ranki shi daɗe." Fulani ta taɓe baki, "Za ki iya tafiya." Da sauri Maimuna ta fice ko waige ba ta yi. Har za ta nufi sashen su na bayi sai uwar ɗakinta Fulani babba ta faɗo mata. Haka kawai ta ji sam ba ta kyauta ba. Zuciyarta ta ci gaba da azalzalarta da ta je ta ga halin da take ciki. Cikin sanɗa ta nufi sashen Fulani babba gabanta na faɗuwa. A haka ta ci gaba da tafiya har cikin ɗakin, ras! Ƙirjinta ya buga jikinta ya ɗauki karkarwa sakamkon ganin Fulanin a yashe babu sutura a jikinta. Wani tafkeken maciji ta gani a tsakanin ƙafafuwanta ya kafa kansa a saitin ƙasanta, ga wani irin gurnani da macijin ke yi. Idanun Fulani a rufe amma sai mutsu-mutsu take yi, da alama ma bacci take yi. Daga bayanta ta ji an dafa kafaɗarta, wani abu ne ya tsarga mata ta yi mutuwar tsaye cikin sanyin jiki ta waiwayo. Karaf idanunta suka sauka a kan Fulani Umaima da ta haɗe girar sama da ta ƙasa. _Ummou Aslam Bint Adam_🌚 07062062624. [10/4, 11:30 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba. Ban yi shi don cin zarafin kowacce ƙabila da Masarautunsu ba. SHAFI NA BIYU Ras! Ta ji gabanta ya yi mummunan faɗuwa, lokaci ɗaya ta nemi yawun bakinta ta rasa. Cikin firgici ta buɗe baki za ta yi magana Fulani Umaima ta katse ta. "Me kike yi a nan kuma uban me kike leƙe?" Maimuna ta zube a ƙasa jiki na rawa ta furta. "Ki yi mini aikin gafara uwar gijiyata, na zo na ji ko Fulani nada buƙatar wani abu kafin na tafi." Da hannu Fulani Umaima ta nuna mata hanya, sum sum sum Maimuna ta fice jiki na karkarwa. Fulani Umaima ta leƙa Fulani babba da ke kwance, ta saki murmushi mai ɗauke da ma'anoni a hankali ta furta. "Mu zuba mu gani idan tusa na hura wuta, in dai ni ce yanzu kika fara gani." Daga haka ta fice daga ɗakin. Fulani babba ta jima a haka sannan ta farka, a hankali take sauke ajiyar zuciyata. Duk da a mafarki ta ga Mai martaba yana kusantarta abin ya yi mata daɗi, ta ji farinciki matuƙa saboda idan ba mantawa ta yi ba rabon da wani abu ya shiga tsakaninta da Takawa tun cikin jikinta bai fi wata biyu ba. Danshin da ta ji a jikinta ne ya sa ta kai hannunta, da mamaki take kallon makwancin nata. Da ƙyar ta yunƙura ta tashi nan take fitsarin da ke naɗe da zaninta ya fara ɗiga, da farko ta yi tsammanin ko faya ce ta fashe mata tun da a halin da take ciki tana iya haihuwa a kowane lokaci, musamman da take jin ciwon mara sama-sama. Sai dai zarni-zarnin da ta ji ne ya sa ta shinshina hancinta. A hankali ta furta. "Fitsari? Ni kuma? Kai ina jin dai faya ce ta fashe." Gudun wasu-wasi ya sa da kanta ta ɗebo ruwa ta sa a katifar ta sauya kayan jikinta amma har lokacin gani take faya ce ta fashe mata. Banɗaki ta shiga ta yi wanka ta fito sannan ta ɗan ci abinci, a hankali ta ji mararta na ci gaba tsikararta daga baya bacci ya sake yin awon gaba da ita. Fulani Umaima kai tsaye sashenta ta wuce don a ranar ba ta jin sha'awar zuwa wurin Mai martaba. Da shigarta babu jimawa sai ga Jakadiya ta shiga ɓangarenta da saƙon Mai martaba na gayyatarta zuwa turakarsa, ba don ta so ba haka ta amsa mata. Jakadiya har za ta tafi Fulani ta dakatar da ita. "Jakadiya ba na son ki yi nisa da sashen Fulani babba." Jakadiya ta amsa mata sannan ta fice. Cike da kissa Fulani Umaima ta shirya kanta da sihirtattun turarrukan da Bamaguje yake haɗa mata, ta ƙarasa turakar Mai martaba. Zamanta babu jimawa suka ji wata ƙarar busar sarewa. Da sauri Fulani da leƙa kusurwar turakarsa idonta ya sauka a kan ƙaton shurin da gudajen turuwa suka zagaye da ke cikin ɗakin, gabanta ya yanke ya faɗi don ta san tun da ta ji wannan sarewar a yau mai afkuwa za ta afku. Mai martaba ya saci kallonta, haka kawai yake jin shakkarta a zuciyarsa. Amma ko shakka babu wannan busar sarewar da shuri ya saki na da alaƙa da cikin jikin Fulani babba wanda yana da yaƙini za ta iya haihuwa a cikin daren nan. Ya so ya tanka wa Fulani Umaima amma sai ya fasa, hakan ya sa ta saki murmushi cikin kissa. "Jikina yana ba ni Fulani babba na gab da kawo mana Yarima, wannan abin farinciki ne. Tun da shuri ya saki sarewa na tabbata a yau za mu iya samun ƙaruwa a gidan nan." Faɗaɗa murmushinsa ya yi, ya janyo Fulani Umaima jikinsa ya furta. "Wannan haka ne yanzu me kike ganin ya kamata a yi?" "Ina ganin zai fi kyau a yi dakan ɗaka shiƙar ɗaka... sai a kira Jakadiya ta zauna a wurinta koda ciwon zai tashi tana kusa da ita, a madadin a kira Ungozoma. Amma sai yadda kace ranka shi daɗe farin jakada." Fulani Umaima ta ƙarasa magana tana sunkuyar da kai ƙasa. Ajiyar zuciya Mai martaba ya yi, "Na baki wuƙa da nama mai farar zuciya Allah ya yi miki albarka." Fulani Umaima ta amsa sannan hirar tasu ta fara sauya salon faranta ran ma'aurata. Zuciyar Fulani Umaima ƙal ta je ta samu Jakadiya da zancan Takawa, Jakadiya na gama sauraronta ta yi ƙasa da murya tana ɗan waige sannan ta ce. "Wani ma ya yi rawa ma ballantana ɗan makaɗi? Ai wallahi sai mun ga abin da ya ture wa buzu naɗi. Ina mai yi miki albishi tauraruwar Mai martaba gobe war haka Fulani Babba na nan cunkushe da baƙin ciki fal ƙirjinta, idan an isa a yi Yarima ba a ɗakinki ba shegiya nake." Fulani Umaima ta saki dariyar ƙeta. "Jakadiya tamkar zuma haka kike ga zaƙi ga harbi. Na aminta da ke fiye da haka ma za ki iya aikatawa." "Ai shi abin kasuwa na mai ciniki ne, ni ta ki ce Fulani har abada ina bayanki. Fulani kin manta ɗayan kirarin nawa kaska rabi mai jini ki bar shi da gashi." Fulani Umaima ta jinjina kai alamun gamsuwa. Jakadiya ta sake ƙasa da murya. "Allah ya taimake ki ni zan ƙarasa zan biya na taso Baiwa Maimuna da zarar haihuwa ta taho gadan-gadan zan turo miki ita." Murmushi Fulani Umaima ta yi har Jakadiya ta yi gaba ta sha gabanta da sauri ta furta. "Jakadiya a kawo mini kayan Bayi sashena, sannan a tabbatar an bawa Maimuna ta kawo mini cikin hanzari." Shiru Jakadiya ta yi tana nazaratar Fulani. Cikin zuciyarta tana ayyana ƙwarewarta a mugun makirci da ƙuduri. Da sauri Jakadiya ta wuce ɓangaren Fulani Babba a lokacin da ta ƙarasa dare ya tsala sosai, sai da ta yi sallama sannan ta shiga har cikin ɗakinta. Shigar Jakadiya ya yi daidai da farkawar Fulani babba, ƙarasawa ta yi gabanta ta ce. "Allah ya taimaki uwar ɗakina ya ƙarawa Fulani lafiya. Yanzu haka Mai martaba ne ya turo ni a kan na kwana da ke saboda yanayin da kike ciki, domin tuni shuri ya saki sarewa." Murmushi Fulani ta yi don ko ba komai ta ji daɗin yadda Takawa ya ba ta kulawa, hannu ta miƙa wa Jakadiya alamar ta taimaka mata. Wani abu ta ji ya tsira wa mararta haɗe da bayanta. Cije baki ta yi jin ciwon na ƙara tsanani gadan-gadan. A haka ta miƙe ta ƙarasa banɗaki da ƙyar don ta gyara jikinta, a lokacin da ta tashi ta sake lura da fitsarin da ya jiƙe makwancinta sharkaf, na wannan lokacin har ya fi na baya yawa da wari. Fulani na dawowa kafin ta shiga ɗakin ta ci karo da wata mata baƙiƙƙirin a tsaye a dokin ƙofa. Hannu ta miƙa mata cikin wata irin murya ta furta. "Ba ni cikin jikinki!" Da Mamaki Fulani ke kallonta har lokacin ciwo na cin ta, "Wace ce ke? Me ya sa zan baki cikin jikina?" Tana rufe baki ta ga matar ta miƙa hannuwanta masu ɗauke da waɗansu irin baƙaƙen farata da zaƙwa-zaƙwan yatsu, ta miƙa hannun da niyyar shafa saman cikinta, Fulani da sauri ta ja baya haɗe da furta. "A'uzubillahi, Innalillahi..." Da gudu ta ga matar ta shige cikin sashenta, wata uwar ƙara ta ƙwalla nan take sai ga Jakadiya ta nufo wurin da gudu. Jiki na karkarwa Fulani ta ce, "Jakadiya baki ganta ba?" Jakadiya ta waiga hagu da dama ta ce, "Wa kenan ranki shi daɗe?" Dum! Fulani ta ji kanta ya yi nauyi tana son tuna a kan abin da Jakadiya take tambayarta amma ta manta, gumin da ke tsattsafo mata ta share ta ce, "Ba komai mu je Jakadiya marata ciwo take. Wash! Bayana zai ɓalle." Jakadiya ta taimaka mata suka ƙarasa ciki, kafin fitowar Fulani daga banɗaki tuni Jakadiya ta gyara wurin ta haɗa gabaɗaya kayan karɓar haihuwa. Ganin zaƙi haɗe da jini ya fara bin ƙafar Fulani ya sa Jakadiya ta shimfiɗa mata ƙatuwar leɗa, Fulani da ƙyar ta yunƙura ta hau kai tana jin ƙasanta tamkar ɗa zai faɗo. Fulani Umaima ce ta yi sallama daga bayanta Baiwa Maimuna na biye da ita, yadda Fulani Umaima ta marairaice tana yi wa Fulani babba sannu sai ka rantse zuciyarta cike take fal da tsoron Allah. Wani jan ƙoƙo ta miƙa mata ta furta, "Mai martaba na cikin tsananin damuwa da jin halin da kike ciki, musamman da ya tuna da mutuwar Marigayya Fulani Samira. (Matar Sarki Abdul'aziz ta uku ce da ta rasu wurin haihuwa.) Ya umarci da a kawo miki wannan yanzu na karɓa a hannun Shamaki." Ɗago kan Fulani babba ta ga Fulani Umaima ta sauya mata a kammani, har take ganin kamar ta taɓa sanin kamannin, sai dai kuma ba ta jin za ta tuna kalar fuskar. Baiwa Maimuna da ke tsaye jikinta ya yi sanyi don ta san garin maganin ba ya wuce na wurin Bamaguje. Fulani Babba ta karɓe za ta kai baki ta ji wani irin nishi ya taso mata, cikin tsananin azaba ta wurgar da ƙwaryar gefe ta riƙe Jakadiya da ke gefenta, take jaririn ya faɗo ya fara mutsu-mutsu yana tsanyarewa da kuka. Wani irin baƙin ciki ya turniƙe ta Jakadiya ta waiga tana kallon Fulani don sanin irin hukuncin da za su yanke, da sauri Fulani Umaima ta fita sakamakon manta kunamar da Bamaguje ya bata. Jakadiya ta tsugunna ta sa reza ta yanke masa cibiya, a tunaninta ko Fulani Umaima ta zubda makamanta ne tun da jaririn ya riga da ya zo duniya. Ta gama yanke masa cibiya kenan Fulani Umaima ta faɗo ɗakin hannunta ɗauke da wata ƙatuwar kunama, a daidai lokacin Fulanin ta sake wani yunƙurin babu jimawa wani jaririn ya faɗo. Kusan mutuwar tsaye gabaɗaya suka yi, fuska babu walwala Fulani Umaima ta ƙarasa ta ɗora kunamar a kan jinin da ke zuba daga ƙasan Fulani Babba, kunamar na fara zuƙar jinin Fulani babba ta yanke jiki ta faɗi jikinta na wani irin karkarwa. Fulani Umaima ta saki shu'umin murmushi, sai dai kuma ganin jariran biyu ya sa ta samu shakkun wanda za ta aiwatar da mugun ƙudurin a kansa, na farkon da jakadiya ta yankewa cibi ta naɗe a zani ta ɗauka, take zuciyarta ta ƙwaɗaita mata wata shawara. Kiran Baiwa Maimuna ta yi ta damƙa mata shi, sannan ta ƙarasa gaban ɗayan jaririn da ko cibiya ba a yanke masa ba. Wutsul-wutsul yake yana kuka ta ɗauki kunamar da ke cikin jinin ta buɗe bakinsa da ƙarfin tsiya ta matse kunamar a cikin bakinsa. Take wani irin ruwa mai yauƙi haɗe da jini ya fara ɗiga a bakinsa. Kamar yadda yaro yake kama mama haka jaririn ya riƙa tsotsar jini da ruwa mai yauƙin. Ya jima yana sha sannan jaririn ya fara wani irin kakari wani farin ruwa mai haɗe da jini na fita daga hanci da bakinsa. Fulani ta waiga wurin Baiwa Maimuna ta furta, "Ina buƙatar ki fita ta ƙofar baya a sirrince, ki samu ƙaton kogi ki jefa shi ko kuma ki samu wani ƙaton ramin ki binne mini shi. Duk rintsi kada ki bar shi da sauran numfashi, idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci." Baiwa Maimuna da jikinta ya gama sanyi ta ce, "An gama ranki shi daɗe." Har Maimuna ta yi gaba Fulani Umaima ta katse ta, "Iya ruwa fida kai. Kowa ya biya allonsa ya wanke. Ki tabbatar ba a samu matsala ba, wallahi matuƙar asiri ya tonu sai kin gayyaci mutuwarki da bakinki. Ni da kika ganni ba na ƙwaina sai da zakara don haka ki bi sannu, shawara ce na baki don kar ki bari kwaɓarki ta yi ruwa." Baiwa Maimuna ta russuna rungume da jaririn ta furta, "Tuba nake ragamar damisa a ja ki da nisa. Na yi tsammanin kin fahimci somu-somun hauka zubda yawu. Mai ƙafa ɗaya ma ya yi rawa ballantana mai biyu? Indai ni ce har gaban abadan ba zan taɓa baki matsala ba." Fulani Umaima ta saki malalacin murmushi ta furta, "Na aminta da ke Maimunatu, idan kin kammala komai ki samu Jakadiya akwai kyakkyawar kyauta. Amma ina buƙatar ganinki da zarar kin kammala." Cike da girmamawa Baiwa Maimuna ta ce. "Godiya nake giwar Takawa fara mai farar aniya, sikari baki yi farin banza..." "Ba mu da isasshen lokaci ki hanzarta ki fita." Fulani Umaima ta katse ta a taƙaice. Daga haka Baiwa Maimuna ta fita daga sashen Fulani ta ƙofar baya, cikin duhu haka ta ci gaba da tafiya tana ratsa bishiyoyi da ƙayoyi har ta samu ta fita ta can bayan Masarauta. Ganin har lokacin jaririn bai daina kakarin da yake yi ba ya sa Jakadiya ta dubi Fulani Umaima. "Ranki shi daɗe me zai hana mu ƙarasa shi tun da har yanzu bai ƙarasa mutuwa ba?" Da ido Fulani ta kafe jaririn. "Bamaguje bai ba ni damar haka ba, ki tsaya kawai mu zura wa sarautar Allah ido. Kuma ni kaina ba na son ya mutu yanzu, na fi son na dasa wa Fulani Babba ɓacin ran da har ta mutu ba za ta manta da shi ba." Jakadiya ta jinjina kai a daidai lokacin da jaririn ya tsagaita da wannan kakarin, a lokacin Fulani Babba ta farfaɗo. Ta yunƙura a hankali da niyyar tashi da yake jikinta babu ƙwari sai Jakadiya da Fulani ne suka taimaka mata. "Sannu Yaya, barkanmu da arziƙi Allah dai ya kawo mana Yarima lafiya." Fulani Umaima ta furta tana sakar mata murmushi, wani irin yammm take ji a jikinta kamar tafiyar kiyashi, jiki babu ƙwari ta sakar wa Fulani Umaima murmushi. Idonta ne ya kai kan jaririn da ke kwance ta kafe shi da idanu, wani abu take son tunawa amma kanta ya yi nauyi ta gagara tunawa. Jakadiya ta saki guɗa da ƙarfi tana ɗaukan jaririn da ilahirin jikinsa ya haɗe da gumi, ga wani irin zafi zam a kan fatar jikinsa. Guɗar da Jakadiya ta yi ce ta alamta wa Dogaran da ke kewaye da sashen saukar Fulani babba, kafin wani lokaci tuni labari ya isa wurin Mai martaba. Fulani da Jakadiya tuni suka gyara jariri da mai jego, an turare ɗakin da turaren wuta ko ina sai buga ƙamshi yake yi. Sai dai Fulani babba tana ƙare wa yaron kallo ta fahimci kamar idanunsa ba daidai suke ba, ga yawu da yake ɗan ziraro masa ta gefen bakinsa hancinsa na yoyon majina. Ƙura masa ido ta yi tana son tuna wani abu da ya shafi lokacin da take naƙuda har zuwa haihuwarta, sai dai nauyin da kanta ya yi ne ya haddasa mata ciwon kai ɓari ɗaya take jin kamar zai tarwatse mata. A hankali ta kalli Fulani Umaima cike da murmushi, "Na gode sosai da kulawarki ƙanwata." Fulani Umaima ta saki murmushin yaƙe don saboda rufewar ido har gani take babu abin da maganin Bamaguje ya yi wa jaririn, amma saboda kissa sai ta furta. "Haba Fulani babba me ye abin godiya ina ce da kai da kaya duka mallakar wuya ne?" Fulani babba ta jinjina kai cike da jin daɗi ta ce. "Amma kuma yaba kyauta tukwici in ji masu iya magana." "Ai lamarin tuwona maina aka yi, ni dai bari na wuce Fulani na ji asuba ta fara ƙaratowa." Fulani Umaima na zuwa sashenta ta faɗa gado cike da tashin hankali. "Ya zame mini dole na ziyarci Bamaguje kuma a yau ba sai gobe ba sai ya hallaka mini Fulani da abin da ta haifa, idan ba haka ba zuciyata bugawa za ta yi." Ta ƙarasa maganar tana shiga cikin uwar ɗakinta. Tafiya mai nisa Baiwa Maimuna ta yi har sai da ta yi nisa da masarauta, ta shiga cikin wani daji mai duhun bishiyoyi. Kuka jaririn ya fara yana wutsul-wutsul, bankaɗa zanin ta yi ta ji tausayinsa ya mamaye zuciyarta. Da yake asuba ta yi haske ya fara mamaye cikin dajin, wani ɗan rami ta hango da ke gefen wata murgujejiyar bishiyar kuka, kallon bishiyar kukar kaɗai ya isa ya tsoratar da gangar jikin mammallakiyar ƙwayar idon. Da sauri ta ƙarasa wurin ta tsugunna sai a lokacin ta lura da zagayyan gidan tururuwar da ke wurin, taku ta fara jiyowa a ɗan nesa da ita da sauri ta saka shi a ciki ta bar wurin ta ɓoye a bayan wata bishiya, amma ga mamakinta sai ta ji shiru babu kowa. Gudun kada asirinta ya tonu ya sa ta fara zabga gudu ta nufi hanyar gida, a yadda take ji ba ta jin za ta iya kashe jaririn da bai ji ba bai gani ba, don rashin imaninta bai kai nan ba. Tana cikin gudun ta ji ta yi karo da wani abu garam! Har sai da ta faɗi ƙasa. Tsoro, firgici da matsanancin tashin hankali ya mamaye ta, take jikinta ya hau karkarwa sakamakon ganin bishiyar kukar da ta kwantar da jaririn a gabanta ta tsaya dass kamar yadda ta baro ta a baya. _Ummou Aslam Bint Adam_ 🌚 07062062624. [10/4, 11:45 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba. Ban yi shi don cin zarafin kowacce ƙabila da Masarautunsu ba. SHAFI NA UKU Fulani Umaima har ta zura hannu za ta ɗauko ƙahon ta busa sai kuma ta ayyana ta bari idan Maimuna ta dawo ta ji yadda ta ƙarke idan ya so sai ta ziyarci Bamaguje, saman gadonta ta faɗa ta kwanta babu jimawa bacci ya yi awon gaba da ita. Sannu a hankali ta fara jin dariya sama-sama, sai dai kuma yanayin dariyar ya tababtar mata da dariyar ƙaramin yaro ce. Ba ta tsinke zaren tunaninta ba ta hango wani jariri tube tamkar a lokacin ya zo duniya, tunkaro ta yake yana ci gaba da ƙyaƙyata dariya hannunsa da wata murtukekiyar igiya yana jan waɗansu murtuka-murtukan shanu, hannunsa ɗaya ɗauke da kwari da baka. A tsorace ta miƙe tana ja da baya ganin jaririn na saita ta da niyyar harba mata, jin bango ya tokare ta ta baya ya sa hankalinta ya sake kai wa matuƙar ƙololuwar tashi. Sai da yaron ya zo gabanta ya furta, "Ba yanzu ba! Zan ƙara miki lokaci." Yana gama maganar ta ga ya juya yana ci gaba da ƙyaƙyata dariya. Firgigit Fulani Umaima ta tashi daga nannauyan baccin da ya ɗauke ta har ya gayyato mata mafarkin da ke neman wargaza kwanyarta. Ajiyar zuciya take saukewa akai-akai sannan ta jingina da bango, da ta ga zaman ba zai kai ta ba ta faɗa banɗaki ta yi wanka ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar asuba, a lokacin da tuni rana ta jima da fitowa. Kamar a mafarki haka ta ga bishiyar na sake tunkaro ta, a yadda take a zaune a ƙasa ta fara ja baya ilahirin jikinta na karkarwa. Wata irin iska mai haɗe da guguwa ce ta taso, Baiwa Maimuna ta sa hannuwa biyu ta rufe idanunta jin ƙura na shigar mata ido. Kamar an yi ruwa an ɗauke haka Maimuna ta ji wurin shiru tana buɗe idanunta ta nemi bishiyar ta rasa, a zabure ta tashi ta ci gaba da gudu kamar wacce ake bi a baya za a zare ranta. Ta jima tana abu ɗaya sannan ta ƙarasa ta bayan masarautar, a lokacin tuni gari ya waye. Sai da ta fakaici idon Dogarawan da ke gefen hanya sannan ta yi sauri ta shiga cikin gidan, tafiya take kamar za ta tashi sama don kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci kwanciyar hankali ya yi ƙaura daga gangar jiki da ruhinta. A haka da samu ta ƙarasa sashen matan sarki tana gab da shiga sashen Fulani Umaima ta ci karo da Uwar bayi, ƙare mata kallo ta yi sama da ƙasa sannan ta ce. "Maimuna daga ina kike haka?" Marar gaskiya ko a ruwa gumi yake, take Maimuna ta yi fiƙi-fiƙi baki na rawa ta furta. "Amm da ma... Yanzu..." Daga can baya Jakadiya ta katse ta, "Uwar Bayi tare muka kwana da ita a sashen Fulani babba yanzu haka gyare-gyare ta gama yi mana." Jinjina kai Uwar bayi ta yi sannan ta wuce, Jakadiya ta ƙarasa wurin Maimuna ta ce. "Ya kamata ki riƙa sara kina duban gatarinki, ki riƙa gayyato nutsu kina yafa wa a gangar jikinki. Kin san sarai wace ce Fulani Umaima." Ajiyar zuciya Maimuna ta sauke ta amsa wa Jakadiya sannan ta wuce sashen Fulani Umaima jiki a saɓule. Tun da ta doshi sashen take jin gabanta na faɗuwa ta rasa dalili, gani take kallo ɗaya idan Fulani ta yi mata asirinta zai iya tonuwa. A haka ta lulluɓa mayafin jarumta ta shiga cikin gidan tana karkaɗe jikinta da ya yi butu-butu da ƙasa. "Barka da hutawa ranki shi daɗe." Ƙuri Fulani Umaima ta yi wa Maimuna tana karantar yanayinta. "Binne jariri tamkar wacce ta yi dambe da jarumai biyar, Maimuna me yake faruwa na ga jikinki kamar wacce aka tono daga rami?" Ras! Gaban Maimuna ya faɗi, murya na rawa ta ce. "Ranki... Shi daɗe... Dama... zuwa na yi na sanar da ke an aiwatar da komai... Cikin nasara." Shekararta kusan hudu da Maimuna, ta karanci halaye da ɗabi'unta sarai. Take ranta ya yi mummunan ɓaci don ta fahimci zallar ƙarya a saman harshenta. "Me ya sa na amince za ki iya yi mini komai ban aiwatar da kaina ba?" Fulani Umaima ta yi maganar cike da murmushin yaƙe. Ɗakinta ta faɗa ta ɗauko ƙaho cikin shigar ziyarar Boka Bamaguje, ba ta tanka wa Maimuna komai ba ta miƙa mata hannu, zaro idanu Maimuna ta yi ta ji wani abu yana tsarga mata. Babu yadda za ta yi ta ɗora hannunta a kan nata, ba su jima ba sai ga su a fadar Boka Bamaguje. A wurin da ta saba zama koyaushe yanzun ma a nan ta zaune, gumi ya jiƙe jikinta sharkaf zuciyarta na dakan lugude kamar za ta hudo ƙirjinta. Fulani Umaima ta ce, "Bamaguje ina zargin Maimuna da cin amanata." Bamaguje ya saki murmushi. "Ba zargi ba ne domin yanzu haka duka jariran Sarki Abdul'aziz suna raye a doron ƙasar nan. Ba ta kashe shi ba kamar yadda kika buƙata." Wani yawu mai ɗaci Fulani Umaima ta haɗiya, ta wurgawa Maimuna kallon tsana. A firgice Maimuna ta zube bisa gwiwoyinta hawaye bibbiyu na zuba, "Ki gafarce ni uwar ɗakina wallahi..." Daga wurin da Fulani take ta ɗaga mata hannu. "Kin wargaza mini shirina Maimuna. Na yi rantsuwa da abin da ya busa numfashina sai na shayar da ke ruwan uƙuba mai tsanani." "Faɗuwa ce ta yi daidai da zama." "Ban fahimci kalamanka ba Bamaguje." "Ina nufi sarane za a yi a kan gaɓa. Kin san akwai muhimmin aikin da na alƙawarta miki kwanaki, zan sadaukar da shi a kan baiwarki. Idan kuma za ki samo wata sai a aiwatar a kanta." Jin kalaman Bamaguje ya sa Fulani Umaima dariya ta sauya fuska cikin damuwa. "Amma kafin aikin Bamaguje ya aka yi aka haihu a ragaya? Na yi tsammanin kunamar da ka ba ni za ta hallaka jaririn Fulani? Ina fa tsoron kada wankin hula ya kai ni dare." Wata baƙar mujiya Bamaguje ya ɗauka ya sa hannu ya fige fukafukanta da ranta, ta saki wani kuka cike da azaba sannan ya jefa ta cikin wani daskararran jini. Ya shiga gudanar da al'amuran tsubbunsa, yana cikin yi ya ga tukwanen gabansa sun rushe. A razane ya ɗago yana ɗan ja da baya, ya sake kai hannun da niyyar sake aiwatarwa kamar saukar aradu ya ga wata baƙar kwari da baka ta faɗo tsakiyar tukwanen. Tashin hankalinsa ne ya tsananta, ya ɗago yana sharce gumin fuskarsa da ke cike da gashi. Garin wata farar ƙasa mai walwali da ɗaukan ido ya ɗebo ya watsa, nan take wata narkekekiyar baƙar saniya ta bayyana jingine da kwari da bakar nan. Da bayyanarta babu jimawa duka wutar wurin ta ɗauke, ƙirjin Bamaguje ya buga ya ɗago ya dube ta. "Tabbas wanzuwarsa a doron ƙasa akwai sanadi, ban san wacce kalar baiwa da matsayi ruhinsa ke ɗauke da shi ba. Sai dai a duk bincikena na garara gano taƙamaimai wane ne shi? Abu ɗaya shafin ƙaddararsa ya buɗe mini shi mai nasara ne, sai kuma samun goyon baya da taimakon ruhi da ke lulluɓe da fatarsa..." Cikin rashin fahimta Fulani Umaima ta katse shi, "Ban fahimci gurbin da kalmanka suke neman samun zama ba, wane ne shi wanda kake magana a kansa?" "Jinin Sarki Abdul'aziz wato jaririn da kika sa aka fitar da shi, tabbas akwai ɓoyayyan al'amari a tattare da wannan yaron. Babban kuskuren da kika tafka kenan, da kika sa aka fitar da shi daga masarautar ba tare da shawara da ni ba. Zancan da nake yi miki yanzu ruhinsa ya yi nisan kiwon da babu hallitar da ta isa ta kawar da shi daga doron ƙasa. Ba zan ɓoye miki ba, daga ni har sauran matsafan da ke doron ƙasa ba na jin akwai wanda zai iya bankaɗa miki labuben sirrinsa, ba ina miki magana a kan masakin ɗan'uwansa ba domin wannan da shi da gawa marabarsu sauka da hawan numfashi. A yadda kika gan shi a haka zai ƙare rayuwarsa a nannaɗe, hatta ruwa da abinci idan ba a ba shi ba sai dai ya dauwama da yunwa. Shi kuwa wance ingarma ne mai ɗauke da rikitattun al'amura, amma ba zan yi miki iyaka ba Umaima idan har kina ganin za ki jarraba wani masanin fiye da ni ga fili ga mai doki." Wata gwauruwar ajiyar zuciya ta sauke fuska ɗauke da damuwa ta ba shi amsa, "Ba zan ja da kai ba Bamaguje domin na tabbata zaɓenka da mahaifiyata ta yi a matsayin madogara ba za ta yi zaɓen tumun dare ba, a halin da nake ciki babban burina bai wuce masarautar Huddam ɗin nan ta dawo ƙarƙashin ikon abin da zan haifa ba wala Takawa yana raye ko baya raye." Bamaguje na ƙarasa jin kalamanta ta ɗauko wani baƙin ƙaho ya kai shi saitin idonsa na hagu ya haske wani allon farin ƙarfe mai ɗauke da rubutun jini, ƙahon da ke hannunsa na fesar da wani tartsatsin jini a jikin kaskon. Ƙuri ya yi yana kallo yana sake fahimtar al'amuran da ke wanzuwa a kwarmin ƙwayar idonsa, kamar kazar da aka jefa da gishiri haka Bamaguje ya ajiye ƙahon ya dube ta. "Za ki haifi gawurtacce kuma ingarman matashin saurayi, mai cike da isa ƙasaita da izzar mulki. Kuma zai kasance sarki wato magajin karagar sarki Abdul'aziz..." Murmushi da murnar Fulani ya katse kalaman Bamaguje ta ce. "Tabbas da kuwa mun shimfiɗa mulkin da wani mai numfashi bai taɓa aiwatar da makamancinsa ba. Sai na shayar da Fulani babba ruwa mamaki domin sai na gasa mata tsakuwa a tsakiyar tafin hannunta." Bamaguje ya kafe ta da idanu yana faɗin, "Haba Umaima me kike ci na baka ma zuba, ai duk gaggawar ungozoma ta bari a haihu. Kuma duk gaggawar asara ta jira yi samu. Kamar yadda na gaya miki jininki zai kasance sarkin ƙasar Zazzau ne kaɗai bisa taimakon jini da ruhin wata hallita, ban san ya zan fasalta miki ita ba amma ta kasance mai ɗauke da rikitattun al'amura. Wanzuwarta a doron ƙasa sanadi ne, kuma ta kasance abar farautar al'umma da dama ciki kuwa har da mahaifina wanda ya shafe shekara da shekaru cikin halwar tsafinsa yana dakon zuwanta. Ban gama tabbatar da abin da nake zargi ba amma tabbas na ga walƙiyarta a cikin masarautar Sarki Abdul'aziz, wannan zai sauƙaƙa miki cim ma muradinki..." Da sauri Fulani ta katse shi cikin ƙagauta. "Wacce irin hallita ce? Me ne ne alaƙarta da masarautar Huddam? Shin dole sai da taimakonta ne abin da zan haifa zai kasance Sarkin masarautar Huddam?" "Akwai ɓoyayyun al'amura game da ita, a sura ta zahiri ta kasance bil'adam kamar kowa. A baɗini tana da ɗauke da al'amura masu hautsina kwanya. Halwar tsafina bai fayya ce mini komai ba, sai dai ina mai shawartar ki da ki tabbatar kin yi nasara a kanta. Ina daga nan zan ci gaba da dafa miki domin ni ba iya boka kaɗai nake a wurinki ba, akwai wata ɓoyayyar alaƙa mai ƙarfi a tsakaninmu. Ba don na yi wa mahaifiyarki alƙawarin binne wannan sirrin ba da tuni na fayyace miki shi, amma ko ga iya haka na dakata na yi miki jurwaye mai kamar wanka don haka dabara ta rage wa mai shiga rijiya." Da yake hankalin Fulani ba ya jikinta ya sa ba ta fahimci inda kalaman Bamaguje suka dosa ba, tana shirin yi masa magana ta ji ya ci gaba da ce wa. "Tana da matuƙar hatsarin gaske don haka dole ki yi takatsantsan, wannan shawarar ina baki ita ne ba a matsayina na bokanki ba ina ba ki ita ne a matsayina na makusancinki. Wani abin da ɓatattu da dama irina ba su sani ba wannan hallitar na da wata tawaya ɗaya wacce da a ce an santa da tuni an yi galaba a kanta..." "Wacce irin tawaya gare ta?" Bamaguje ya wara hannuwansa haɗe da faɗin, "Ni kaina ban santa ba, sai dai allon tsafina ne ya alamta mini haka. Ammma zan baki wannan sirrintaccen littafin mai ɗauke da labarin abin da ya taɓa faruwa a masarautar Daura, wannan al'amarin ya faru a shekara ɗari da hamsin baya da suka shuɗe. Ƙa'idar littafin ba a karatunsa kowacce rana sai ranar Lahadi ko Laraba daga bayan la'asar zuwa sallar isha'i. Ki bi shi a sannu ki karanta zai taimaka miki matuƙa. Umaima!" Boka Bamaguje ya ambaci sunanta cikin wani irin yanayi. Fulani Umaima ta dube shi cike da ƙwarin gwiwa babu alamar karaya ko tsoro a tattare da ita. "Jarumta da dakakkiyar zuciyarki na matuƙar birge ni, tabbas kin cancanci shiga sahun mace mai kamar maza. Na yi imani da abin bautar da nake bauta tare da siddabarun da na gada a wurin iyayena da kakanni sai na ci gaba da dafa miki kin kasance mai nasara har ƙarshen rayuwarki." Fulani Umaima ta saki murmushi. "Ai dama duka ɗaya baya kada sadaukan jarumai, don haka na dulmiya kogin azaba na yayyafa wa ruhi da gangar jikina don kada wani hatsari ko firgici ya razana ƙwarin gwiwata." Umaima ta ɗora tafin hannunta a saman tukunyar tsafinsa ta runtse idanunta ta ci gaba da cewa, "Na yi imani da kai Bamaguje kuma na yi maka alƙawari wallahi sai jinina ya mulki ƙasa da masarautar Huddam bakiɗaya." Bamaguje ya jinjina kai sannan ya ɗauko wani irin littafi mai ɗauke da bangon ƙarfe wanda yake ɗauke da launin ruwan zaiba. A tafin hannunta ya ɗora mata, wani irin zuuuu ta ji a tafin hannunta kafin ta ankara ta ji wani sauti na furta. "Hidayaaaa!" A razane ta buɗe idonta suna haɗa ido Bamaguje ya jinjina mata kai, "Kamar yadda majiyar sautinki ta jiye miki haka ne wato Hidaya ba zan ce miko komai ba, domin amsar tambayar ki na cikin kundin littafin." Fulani ta rungume littafin ƙam kamar wani zai ƙwace shi, sannan ta waiga wurin da Maimuna ke zaune kamar gunki ta gagara motsa koda yatsanta ne. "Bamaguje ka aiwatar mini da duk abin da ka yi niyya a kan waccan la'ananniyar." Bamaguje na jin haka ya bushe da dariya, Maimuna ta fara mutsu-mutsu tana son tashi ta gudu amma ta gagar tashi. Yana daga wurin da yake zaune ya turmutsa hannunsa a cikin wani kabari, ya ɗauko ƙoƙon kan mamacin da ke ciki ya fara takawa har ya isa wurin da take zaune. Ɗora mata kan ya yi a kanta na ɗan lokaci take jikinta ya fara karkarwa, ya jima a haka sannan ya saka wata ƙaramar tsafatacciyar wuƙa ya yanki tsokar jikinta. Wajen kabarin ya koma ya tura fatarta a cikin kabarin sannan ya furta. "Wannan da kike ganinta a zahiri ne take tamkar rayayya amma ba ta da amfanin komai kuma za ta zame miki tamkar raƙumi da akala. Yanzu ki tafi da ita zuwa turakar Sarki Abdul'aziz, kuma a wannan ranar nake son ki sa Sarki Abdul'aziz ya kusanceta ta gaba da baya." A firgice Fulani Umaima ta ɗago ta kalle shi cikin tashin hankali. _Ummou Aslam Bint Adam_ 🌚 07062062624. [10/4, 11:48 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye. SHAFI NA HUƊU Wani irin kallo Fulani Umaima ta watsa wa Bamaguje, shi ma ya yi ƙuri yana kallon ta da daƙwa-daƙwan idanunsa jawur kamar sabon barkono, ta katse shirun da ce wa. "Ka na nufin Baiwata Maimuna ce Takawa zai kusance ta? A saboda wanne dalili kuma ba ka ganin tamkar na miƙa kai a kan hanyar da asirina zai tonu?" Bamaguje ya girgiza mata kai. "Matuƙar ina numfashi kullin za ki kasance lulluɓe cikin bargon rufin asirin da babu wani mai numfashi ya isa ya yaye miki shi, dalilin da ya sa na ce ki aiwatar da wannan aikin matuƙar Sarki Abdul'aziz ya kusanci Maimuna ta gaba da baya za ki sha gaban kowa. Wane na mai faɗa a ji a cikin ƙasar Huddam?" "Sarki Abdul-aziz." Umaima ta amsa masa. "Ki saurare ni da kyau. Ba akwai wata baƙar rijiya mai baƙin murfi a turakar Mai martaba ba wacce suke kallon juna ita da tsohon shuri mai tsohon tarihi?" Umaima ta gyaɗa masa kai. "Mai martaba na gama mu'amala da ita ki tabbatar kin ɗebi najasar jikinsu sai ki shafa ta akan saman murfin take murfin zai buɗe, ki zura Maimuna cikin rijiya ki koma gefe su zuba ido zai koma ya rufe kamar yadda yake da farko. Maruƙar kika aiwatar da komai yadda ya kamata za ki sha gaban duk wata hallita da ke cikin ƙasar Huddam, kwarjini da tsoronki zai mamaye zuƙatansu ta yadda kina faɗar maganar za a aiwatar miki. Sai dai akwai sharaɗi duk ranar da aka fito da Maimuna daga cikin wannan rijiyar wannan asirin ya karye, amma kuma abu ne da kamar wuya gurguwa da auren nesa domin yanzu haka rabon da a buɗe rijiyar yau kimanin shekara ɗari da hamsin kenan." Umaima ta sauke ajiyar zuciya. " Duk wannan ban ɗauke shi abu mai wahala ba, shin ya za a yi na wuce da Maimuna har turakar Takawa ba tare da wani ya gan ni ba, kuma na sa shi ya yi mu'amala da ita?" "Umaima a kullin kin fi son a yi miki ciki a yi miki goyo, za ki saka hannu ki ƙwaƙwalo ƙwayar idonta ki jefa a cikin wancen sihirtaccan ruwan, yadda za ta makance ta daina gani haka za ki ci karenki babu babbaka ba tare da wani ya kawo miki cikas ba. Kuma daga wannan lokacin hatta uwar da ta kawo ta duniya ba za ta sake tambayarta ba, yadda matacce ke mantawa da rayuwar baya haka duk wanda ya santa zai manta da shafinta." Umaima ta yi masa jinjina da hannu. "Na gode sosai Bamaguje faɗi kowanne irin tukwici kake buƙata." Bamaguje ya saki murmushi, "Ki je Umaima zan fanshi aikina a cikin masarautarku." Umaima na gama sauraronsa ta miƙe ta ƙarasa gaban Maimuna da ke zaune kamar butum-butumi, ƙaramar wuƙa ta saka ta ƙwaƙwalo idanunta ta watsa cikin wani koren ruwa kamar yadda Bamaguje ya faɗa mata. Ta koma gabansa ta yi masa sallama da faɗin duk abin da ake ciki za ta sake ziyartarsa. Ta rungume littafin a jikinta hannunta ɗaya riƙe da Maimuna na biye da ita kamar raƙumi da akala. Duk wani abu da take gudanarwa na siddabaru sai da ta gudanar babu jimawa sai ga su a cikin ɗakinta a tsaye. Kai tsaye uwar ɗakinta ta wuce da Maimanuna ta buɗe wani akwatinta na ƙarfe da take ajiyar abubuwanta na sirri ta ajiye littafin, sannan ta koma falo ta zauna tana ta zuba murmushi don gani take ƙiris ya rage haƙonta ya kai ga cim ma ruwa. Bayan fitar Fulani Umaima daga sashen Fulani babba, Jakadiya da kanta ta ɗan tattara wurin. Ta leƙa madafa tana tambayar su Baraka ko ruwan zafin ya tafasa, a daidai lokacin ta same su sun fara kwashe ruwan. Bayan an zuba aka kai banɗakin Fulani babba, shi kuma jaririn Jakadiya ta zauna ta sulle shi tas. Sai da gari ya waye tangararan sanna Jakadiya ta ɗauki Yarima ta wuce da shi turakar Mai martaba. Farinciki fal fuskarsa ya karɓi jaririn yana jin son shi a zuciyarsa don ya jima yana mafarkin samu ɗa namiji. Huɗuba ya yi masa da suna Abubakar sannan ya ba wa Jakadiya ta mayar da shi, Jakadiya na mayar da shi Fulani ta rungume jaririnta suka kwanta bacci. Jakadiya da kanta ta sanar da Baiwa Zainaba a kan duk wanda ya zo mata barka a ce masa tana hutawa. Sai a lokacin ita ma Jakadiya ta wuce can sashensu na Bayi ta samu ta yada haƙarƙarinta don ta yi ramuwar baccin daren da ba ta yi ba. Fulani Umaima tun da ta dawo ta kasa zaune ta kasa tsaye don burinta bai wuce ta ga ta aiwatar da abin da Bamaguje ya umarce ta ba. A yadda ta jingine Baiwa Maimuna a haka ta same ta a bayan ƙofa, bayan ta idar da sallar asuba ta riƙo hannun Maimuna tana faɗin, "Wuce mu je sashen Mai martaba." Babu musu Maimuna ta fara tafiya tana biye da Fulani. Duk da ta aminta ɗari bisa ɗari da hatsabibancin Bamaguje, a lokacin da ta fita harabar da Bayi suke kai wa da kawowa sai da gabanta ya faɗi, jikinta ya ɗauki rawa tana tsoron kada su ankara da Maimuna wacce take tafe da ƙwaƙwulallun idanuwa asirinta ya tonu. Amma ga mamakinta duk wurin da ta gifta sai dai Bayi su riƙa zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa. Cike da izza, ɗagawa, faɗin rai da alfari Fulani Umaima ta ci gaba da taku ɗaiɗai tana kallonsu a banzace ba tare da ta amsa ba ta wuce. Ba su yi mamaki ba domin ba wannan ne karo na farko da ta saba yi musu haka, wulaƙanci da tozarta na ƙasa da ita kamar a jininta yake don haka kowannensu ya sake shiga taitayinsa. Lokacin da ta isa sashen Sarki Abdul-aziz shiru ta ji wanda hakan ya alamta mata baya nan, can gefen gadon sa ta zaunar da Maimuna sannan ta fara jiyo motsi daga jikin windonsa. Tana leƙawa ta hango Takawa a cikin lambun shaƙatawarsa zaune a kujera a gefensa ɗawisu ne da ƙananan tsuntsaye suke ta kaiwa da kawowa. Har ta nufi ƙofar da za ta sada ta da lambun ta tuna ba ta ɗauko sihirtaccen turarenta, da sauri ta fice don kar Sarki Abdul'aziz ya dawo ba tare da ta kammala shirinta ba. Da fitarta ba a ɗauki minti biyar ba Sarki Abdul'aziz ya taso kai tsaye ya nufo cikin turakarsa, gabansa ya ji ya yanke ya faɗi ƙwarin gwiwar da ke tattare da shi ta tarwatse. A razane yake bin kan gadonsa da kallo, sakamakon ƙwaɗayin idanunsa da suka hango masa abin da ba yi tsammani ba. Fulani Umaima na zuwa ta wuce ta zaro akwatinta da ke ƙarƙashin gado, ta buɗe ta da niyyar ɗaukon turaren amma zuciyarta ta fara kwaɗaita mata son sanin abin da yake ƙunshe a cikin littafin da Bamaguje ya damƙa mata. Ta sake tuna matuƙar ta rasa karatunsa a wannan ranar sai dai ta bari zuwa wani makon mai zuwa. Ɗaukan littafin ta yi ta koma gefen gado ta zauna, za ta sa hannu ta buɗe ta tashi da sauri ta je ta saka kuba a ƙofarta ta rufe sannan ta sake komawa ta buɗe shafin farko daga cikin littafin, ƙwayar idonta ta sauka a kan jimlar farko da aka yi rubutunta da ajami. BAN SAN KAINA BA Da mamaki ta sake furtawa da bakinta, "Ban san kaina ba! Me hakan yake nufi?" Duk harsashen kwanyarta ta gagara lalubo mata amsar tambayarta don haka ta sake mayar da kanta ta ci gaba da karatun. Ban san mizanin tubalin ginin da ya dace na jingine rayuwata ba, balle na san kaina da abin da rayuwata ta ƙunsa, abu ɗaya na sani ban san kaina ba. Ban san wace ce ni ba domin kuwa wata hallita ce ke sarrafa zuciya da ruhin gangar jikina. Ban san asalina ba ballantana na binciki dangina, hasali ma kusan duk wani Bawa ko Baiwa da za ka gani a cikin masararutar Kabbab kusan kowa akwai tushe da asalin yankin da ya fito, nawa asalin ya yi rauni dalilin da ya sa ko a cikin Bayi na kasance ƙasƙantacciyar baiwa. Wacce take fuskantar tsangwama, kyara da duk wani nau'in cin zarafi saboda babu mutum ɗaya da zan kalla da sunan dangina. Har ya zame mana jiki a kowacce rana idan rana ta take muna karkasuwa ɓangare-ɓangare domin gudanar da ayyuka daban-daban. Ni da su Dije muna ɓangaren bangon yamma muna sirfen geron da za a yi wa su Fulani fura da shi, a lokacin rana ta take sosai daga bayana na ji an saka hannu an dafa kafaɗata wacce na ke kai taɓarya ina yin surfe da ita. A hankali na waiga ƙwayar idona ta sauka a kansa, cike da fargaba da sake waro idanuna haɗe da tattaɓa gefen fuskarsa don tabbatar da ƙwayar idona ba yaudarata take ba. Tun ban fi shekara biyar a duniya ba nake mafarkinsa ba dare babu rana, domin a duk lokacin da zan yada haƙarƙarina gangar jikina ta samu hutu bacci ya yi awon gaba da ni sai na yi mafarki da wannan hallitar. "Ki taya ni murna da farinciki domin na samu 'yancina, na zama kamar kowa mai ɗauke da rayuwar gashin kai. Na yi miki alƙawarin sai na karɓo miki karagarki, a kullin Kaka na sake jadadda mini mu tabbatar da mun ba wa alƙawari muhimmanci kuma mun cika shi, wannan zai dawo da ƙima da martabar ahalinmu, wacce zuri'armu ta tarwatse silar cin amanar da aka yi mana." Kalamansa suka mamaye masarrafar jina, mamakina ya ninku dalilin ganin ƙwalla na zuba daga ƙwayar idonsa. "Ke Hidaya kar ki raina wa kanki hankali, kina nufin mu za mu ci gaba da surfen kina can kina kalle-kalle banza da wofi? Wallahi kika bari muka surfe na cikin turmin nan sai dai ki surfe wannan kwano ukun ke kaɗai." Kalaman Safare suka katse ni, da sauri na waiga wurinsu kowaccensu ta sakar mini harara kamar idanunsu zai faɗo. A zuciyata na furta. "Ko dai su Safare ba sa ganin wannan saurayin?" Daga bayana na ji ya sake taɓo ni. "Ba za su taɓa ganina ba, saboda wasu muhimman abubuwa. Ke ma akwai dalilin da ya sa kike rayuwa a cikin Masarautar nan har kike mu'amala da su. Ki ci gaba da haƙuri kin san idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi." Yana gama furta mini waɗannan kalaman na neme shi na rasa. Wata irin azaba ta riyarci ƙafata sakamakon wurgo mini taɓarya da su Safare suka yi, na sunkuya cike da azaba ina matsa ƙafata. "Ga shi nan ki yi ki surfa ragowar, kuma kin fi kowa sanin halin Uwar tuwo matuƙar aka gama surfen aka bar ki a baya za ki yaba wa aya zaƙinta." Idanuwana na kai kan ƙwaryar da ke cike da gero har kusan kwano uku, tausayin irin wuyar sirfen da zan sha ya mamaye ni. Dole ƙanwar na ƙi, na sunkuya na ɗauko taɓarya kafin na ɗago na ji saukar bulala a tsakiyar bayana, azaba ta sa na wurgar da taɓaryar ina ihu haɗe da soshe-soshe. Ragowar mutanen da ke wurin babu wanda ya motsa ballentana na saka ran wani daga cikinsu zai kawo mini ɗauki, sai da Uwar tuwo ta gaji da dukana don kanta sannan ta nuna ni da murtukekiyar dorina. "Ki yi gaggawar ƙarasa surfen gabanki idan ba haka ba wallahi sai na sa Balele ya kai ki ɗakin duhu, shegiyar yarinya da idanu kamar na ƙwanƙwamai." Tun ba ta ƙarasa zagina ba na suri taɓaryar da a tsaye ta kusan tsayina, jiki na karkarwa na fara daka cike da tashin hankali. Ganin haka ya sa Uwar tuwo ta yi gaba tana buga wa sauran Bayin da ke tsaitsaye tsawa, da tafiyarta babu jimawa waɗansu zaratan samari biyu suka kewaye ni. "Shugaba wannan ba aikinki ba ne." Mamaki ya lulluɓe ni domin ko a mafarki ban taɓa cin karo da su ba, haka kuma suturun jikinsu bai yi kama da kayanmu na bayi ba. Na sake mamakin kalamansu da suke kirana da shugaba. Tsaye na yi ina bin bayan Uwar tuwo da kallo samakon har lokacin ina hango ta sai da ta ɗan yi nisa da ni, takaicin dukan da ta yi mini ya mamaye ni na fara ayyana da ina da hali sai na karɓi doriyar hannunta na zane ta ita ma ta ji irin abin da muke ji. Ihun da na ji Uwar tuwo na yi ne ya dawo da ni hayyacina, na kai ƙwayar idona wurin cikin mamaki nake bin ta da kallo. Kamar yadda na ayyana haka Uwar tuwo ke tsalle tana ihu, hatta ni da nake nesa da ita haka na riƙa jiyo sautin saukar dukan da ake yi mata.Ta jima cikin wannan halin sannan ta faɗa gefe ɗaya tana sauke ajiyar zuciya, kamar wacce aka ce na waiga ina juyawa wurin turmin na yi tozali da abin da ya daskarar da ni. Gabaɗaya geron da ke wurin an surfe shi an dake mini tas, tsoro ya mamaye ni da ganin wannan lamarin. Duk da ba sabon abu bane a wurina na ji kalamai daga cikin zuciya, amma a wannan karon na razana, "Kada ki tsoro ta Shugaba domin firgici ba hali ko ɗabi'ar ahalinku ba ne." Jin haka ya ƙara mini ƙwarin gwiwa na ɗauki ƙatuwar ƙwaryar na ɗora ta a kaina da ƙyar, kafin na ƙarasa wurin da Uwar tuwo ke kwance tuni Bayi suka taimaka mata aka kai ta can ɓangarenmu na Bayi. Kallo ɗaya za ka yi wa Bayin da ke wurin ka fahimci kowa ya sha jinin jikinsa, don babu hayani tsit wurin ya yi kamar an yi mutuwa. Kamar kullin idan kowannenmu ya dawo daga sashen da yake yi wa hidima, mukan taru a sashenmu na Bayi. Zaune muke gabaɗaya a tsakar gida, wasu daga cikinmu na zaune kusa da yayyansu suna wasa. Waɗanda suke da ƙanƙarta shekaru kamar nawa da ba su wuce sha uku ba suna kwance a jikin iyayensu, idanuwana suka ciko da ƙwalla sakamakon ganin ni kaɗai ce wari ɗaya ba ni da makusanci. Ko da ba ni da iyaye ya kamata wasu su tausaya mini su ƙaunace ni kamar yadda na ga wasu Bayin da aka samo marasa iyaye ake kula da su, me ya sa na kasance mai baƙin jini kowa ba ya ƙaunata?" Ba zato daga gefen kunnuwana na ji an furta mini. "Ke kike da kowa Hidaya! Kada ki karaya domin lokacin na nan da za ki tabbatar da haka." Abin ka da mai shirin kuka an jefe shi da kashi awaki nan take hawaye ya fara kai-kawo a ƙwayar idona. Jiki a sanyaye na miƙa zuwa gaban Jakadiya na tsugunna, da mamaki gabaɗaya suka juyo suna kallona. Ban damu da irin ƙalubalen da zan fuskanta ba, babban burina bai wuce ni ma na san wace ce ba. "Lafiya kika zo kika saka ni a gaba kamar tsohuwar mayya?" Gabana na dakan lugude na tattaro kalaman bakina da na guntso na fesa mata. "Don Allah Jakadiya su waye iyayena?" Kamar haɗin baki haka na ji sun tuntsire da dariya, sai da suka yi mai isar su sannan Jakadiya ta nuna wurin da Uwar Bayi ke zaune. "Akwai tarin bayanai dangane da samuwarki, ki tafi wurin Uwar Bayi za ta warware miki zare da abawa." Cike da ƙwarin gwiwa na miƙe cikin sassarfa na isa gaban Uwar Bayi, na baje tagwayen kunnuwana ina sauraron makoma da tushena. Ajiyar zuciya Fulani Umaima ta sauke ta kai hannu ta rufe shafin littafin ba don ta gaji da karatun wannan hargitsattsan labarin mai cike da rikitar da kwanyar mai karatu ba. Mayar da littafin ta yi cikin akwatinta sannan ta ɗauko turaren da take amfani da shi a duk lokacin da za su yi wata mu'amala da Mai martaba. A cikinta ta soke shi sannan ta rufe ɗakinta ta fice kai tsaye ta wuce sashen sarki Abdul'aziz, haka kawai ta ji gabanta na faɗuwa ba tare da ta san dalili. Babban tashin hankalinta bai wuce kada laƙanin jikin Takawa ya wargaza mata shiryayyan shirin ta a kan Maimuna ba. _Ummou Aslam Bint Adam_ 🌚 07062062624. [10/4, 11:48 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye. SHAFI NA BIYAR Cikin mugun yanayin ta kafe shi da ƙwalaƙwalan idanuwanta masu razana duk wanda ya yi tozali da ita, a hankali Sarki Abdul'aziz ya fara ja da baya jikinsa na karkarwa. Bai yi tsammani ba ya ji bayansa ya bugu da bangon ɗakin, cikin tsinkewar zuciya yake sauke ajiyar zuwa. Da wata irin sanɗa ta taso daga kan gadon tana durfafo wurin da yake tsaye, ganin tana gabda cin masa ya sa ya fice da sauri daga cikin ɗakin ya ƙarasa wurin dogaran da ke tsaron sashensa. Yanayinsa kaɗai ne ya tabbatar musu da tabbas Takawa yana cikin damuwa, tun bai ƙarasa wurinsu ba suka zube cikin girmamawa. "Allah ya taimake ka ya ƙara lafiya da nisan kwana, ɗawisu sarkin ado mai taƙama da ikon Allah..." "Ya aka yi kuka bar waccan hallitar ta shiga har cikin turakata?" Mai martaba ya katse su fuska a tamke babu ɗigon fara'a. "Tuba muke ranka shi daɗe, Allah ya huci zuciyar amale a gafarce mu wannan ne na farko na ƙarshe." A daidai lokacin Jakadiya ta ƙarasa ita da Baiwa Saro hannunsu ɗauke da kayan lambun da ake kai wa Sarki Abdul'aziz kamar wannan lokacin. Dogaran ta gani sun nufi turakar Takawa kafin su ƙarasa su ka ga wata baƙar mage ta fito daga cikin turakar idanuwanta jawur kamar gauta tana bin mutanen wurin da wani irin kallo. A zabure Jakadiya ta furta. "Ka gafarce ni uban gidana ka yi mini afuwa, amma ba ni da masaniya game da sakacin Dogaran ƙofa da har suka bar kyanwar nan ta shiga cikin turakarka." Jakadiya ta yi maganar jikinta na karkarwa don ta san a duniya babu abin da Takawa ya fi tsoro sama da mage, wannan ɓoyayyan sirri ne da ba kowa ne ya sani ba saboda gudun kada magauta su fahimci lagonsa. Ita ma Jakadiya abin da ya sa ta sani tun wani lokacin da ta taɓa shiga sashen Mai babban ɗaki (Mahaifiyar Takawa.) wata mage ta shiga har suma ya yi a wurin, kuma ko da ta ga haka sai da Mai babban ɗaki ta tsawatar mata a kan wannan sirrin. "A kiyaye gaba, ba na buƙatar sake ganin kowacce hallita a sashena." Gabaɗaya suka amsa masa cikin girmamawa. Jakadiya da kanta ta shiga ta jera kayan lambun kamar kullin sannan suka fice bayan ta tambayi Takawa ko akwai wani abin da yake da buƙata, ya ba ta amsa fuska babu walwala. Har bayan wani lokaci Sarki Abdul'aziz bai saki jikinsa ba, ganin bai sake jin motsin komai ba ya sa ya ɗan saki jikinsa. Cike da ƙwarin gwiwa Fulani Umaima ta ƙarasa cikin turakar Mai martaba, ganinsa zaune a gefen gado kusa da baiwa Maimuna ya sa ta zaro idanu cikin fargaba har sai da ya fahimci ruɗewar da take ciki. "Lafiyarki Umaima?" Cikin kissa ta daidaita nutsuwarta ta ce, "Dama na yi mamaki ne ganinka shiru, kar dai ka jima kana jirana." Murmushi ya sakar mata haɗe da girgiza kai. Ta ƙarasa wurinsa asirtaccan ƙamshinta ya ratse hancinsa, ya lumshe ido cike da jin daɗin ƙamshinta. "Ki tabbata kin sa shi ya shiga bayan gida kafin ki saka wa Maimuna turare a gabanta." Kalaman Boka Bamaguje ya dawo mata raɗau a cikin kunnuwanta. Miƙe wa ta yi ta furta. "Sarkina bari na haɗa mana ruwa mu ɗan watsa ko?" Ba ta jira cewarsa ba ta nufi banɗaki ta haɗa komai da kanta sannan ta zuba turaren da Bamaguje ya bata, bayan dawowarta ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa sannan suka wuce banɗaki. Da kanta ta ɗebi ruwan ta watsa masa cikin sigar tsokana, sai kuma ta yi farat ta furta. "Na yi mantuwa." Kallon da ya yi mata ne ya alamta mata yana buƙatar ƙarin bayani daga gare ta. "Ina zuwa." Kawai ta furta ta fice a gaggauce. Sai da ta tabbatar da ta rufe ƙofar ta baya sannan ta koma turakarsa cikin sauri ta ɗaga doguwar rigar Maimuna ta kwara mata turaren a ƙasanta sannan ta shafa mata a fuskarta, ita ma ta murtsuke jikinta da shi ta rage kayan jikinta ta sake komawa cikin banɗakin. Tana shiga ƙamshinta ya daki hancinsa, take ya ji wani irin yanayi ya tsarga masa. Buƙatar ya kusance ta ta yunƙuro masa, ganin saƙwannin da yake aika mata ya tabbatar mata da haƙonta zai cim ma ruwa, don haka ta fara neman shawarar da za ta yanke wa kanta. A hankali ta yakice shi tana faɗin, "Sarkina a banɗaki muke mu ƙarasa turaka." Bai musa mata ba, ta ƙarasa sheƙa musu ragowar ruwan sannan suka fito hannunta na riƙe da shi, idanuwansa a rufe suka ƙarasa don haka ko da ta zaunar da shi a gefen gado ta ga ya rarumo Baiwa Maimuna da ke zaune kamar gawa. Fulani Umaima ta koma gefe ta zuba masa ido zuciyarta ƙal, tana nan tsaye Takawa ya gama mu'amalarsa da Maimuna ya koma gefe ɗaya sai gani ta yi numfashinsa ya ɗauke. Da sauri ta ƙarasa ta ɗebi najasar jikinsu ta isa bakin rijiyar da tun da take shiga cikin turakar ba ta taɓa taka wurin ba, wata irin kuɗa ta fara ji a cikin kunnuwanta ga wata 'yar juwa-juwa da take ji sama-sama. A haka ta samu ta zuba najasar a kan rijiyar take murfinta ya buɗe, wata baƙar ƙura ta turnuƙe ta. Sai daga baya komai ya washe, ganin haka ya sa Fulani Umaima ta koma ta janyo hannun Baiwa Maimuna sai da suka je bakin rijiyar Fulani Umaima ta furta. "Maza ki shiga rijiyar nan da ƙafar hagu." Ba musu Maimuna ta ɗaga ƙafarta ta zura cikin rijiyar ta zauna a kan wani mulmulallan baƙin dutse. Kamar yadda Bamaguje ya gaya mata Maimuna na gama shiga murfin ya taso da kansa ya rufe ruf. Ta koma can gefen Sarki Abdul'aziz ta kwanta tamkar da ita Takawa ya gama mu'amala. Bayan ɗan wani lokaci Mai martaba ya fara motsawa, jin haka ya sa Fulani Umaima ta fara sauke ajiyar zuciyata tana rarumo shi cikin kissa da kisisina. Wani irin nauyi dum! Kansa yake yi masa don haka ya gagara tunano abin da ya faru a baya, ganin yanayin da suke ciki ya sa ya sakar mata ajiyar zuciya ya yunƙura suka wuce banɗaki don tsaface jikinsu. Irin rawar jikin da yake yi a kanta ne ya sake tabbata mata da tabbas alƙaluman tsafin Bamaguje ba su zube a ƙasa banza ba, ta ci gaba da narke masa tana cin karenta babu babbaka. Daren ranar a sashen Sarki Abdul'aziz ta ƙarashe shi har zuwa wayewar gari. Cikin abin da bai fi wuni biyu ba, maganar haihuwar Fulani ta yaɗu cikin da wajen Masarautar Huddam, musamman da ya kasance an san Takawa ba shi da ɗa namiji sai a wannan lokacin. Manyan mutane da masu kuɗi haka suka dinga zuwa suna bada gaisuwa haɗe da yi masa barka da samun ƙaruwa, mafi yawa daga cikinsu har da sha tara ta arziƙi suke kawowa. Duk da Fulani Umaima ta san jaririn a nakashe yake hakan bai hana ta jin ƙyashi, baƙin ciki da ƙunci a kan kyaututtukan da Fulani Babba take samu ba. A lokacin sai ta tsiri kwanciya da tsirfar ciye-ciye wani lokacin har amai take ƙaƙalowa a turakar Mai martaba, duk da cikin jikinta babu abin da yake saka ta. Ganin haka ya ɗaga hankalin Takawa har ya aikata sashen magunguna aka kira masa Ungozoma da jikar Baushe don su duba ta su ba ta magani. Tashin farko aka sanar wa da Sarki cikin da ke jikin Fulani Umaima, farin ciki kamar zai zuba ruwa a ƙasa ya sha. Ita kuwa Fulani Umaima ko kaɗan ba ta nuna wa Takawa ta san da cikin jikinta ba, nan ta shiga gwalangwaso da feleƙe wani lokaci hatta ƙamshin Turakarsa ce wa take ba ta so. Cikin wannan yanayin aka ɗebi kwanaki mai jego tana ɓangarenta tana jego ita kuma Fulani Umaima tana rainon cikinta, gabaɗaya gidan sarautar ya zagaye da ƙananan maganganu. Jin labarin cikin Fulani Umaima da Fulani Babba ta yi ba ƙaramin faranta ranta ya yi ba, kuma rashin ganinta kwana biyu a ɓangarenta ko kaɗan bai dame ta ba don ta san yadda laulayin ciki yake ba shi da daɗi. A ɓangare ɗaya Fulani Babba na cikin matsanancin tashin hankali sakamakon yadda fitsarin da yake zuba daga jikinta yake sake ta'azzara, tun tana ɓoyewa har ya zamana sai da Baiwa Zainaba ta fahimci halin da take ciki, ga shi abin kullin gaba yake yi da ta kwanta ko bacci minti biyar ba ta yi tana farkawa sai dai ta ji ta sharkaf da fitsari, ga kuma jinin biƙi duk shimfiɗarta ta haɗu ta dagule. Ana gobe suna da asuba bayan ta tashi ta sake ganin wurin ya yi sharkaf da wani irin zarnin da ke tashi har ya wuce misali. A wannan lokacin take zuciyarta ta karye ganin lalurar tata a kullin gaba take yi ba baya ba, a daidai lokacin yayarta da suka zo daga Masarautar Bassar ta shiga ɗakin, ganin ta a zaune ya sa ta ɗan yamutsa fuska. "Fatima wai mene ne yake wari ne?" Da yake mai shirin kuka ne aka jefe shi da kashi awaki take Fulani Babba ta fashe da matsanancin kuka, da mamaki Halima ta furta, "Fatima me yake faruwa ne?" Sai da ta yi mai isarta sannan ta miƙe tana nuna wa yayarta ta ce. "Ki duba ki gani Yaya Halima wai ni ce yau nake malala fitsarin kwance. Ni dai na fi zargin tun ranar na haihu na haɗu da wannan iftila'in, duk yadda zan yi takatsantsan ina runtse idona duk gajarta bacci sai dai na tsinci kaina a cikin fitsari." Jakadiya da ta zuro kanta da niyyar sanar da Fulani Babba ruwan wankanta ya yi zafi ta yi fakare tana sauraronsu. Yaya Halima cike da damuwa ta jinjina kai. "Kin sanar da Mai martaba?" Girgiza mata kai kawai ta yi don ba ta son ta buɗe baki har ta iya sanar da danginta zaman doya da manjar da ke tsakaninta da Takawa. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta furta, "Ya zama wajibi na sanar da Yakumbo a nemar miki magani, domin wannan fitsarin ba na lafiya ba ne. Ni fa dama zuciyata da hankalina ba su taɓa aminta da wannan kishiyar taki ba..." Da sauri Fulani Babba ta katse ta. "Yaya kada ki zargi Umaima domin ban taɓa zarginta a kan wani mugun abu ba, zamana da ita babu wata matsala ni dai a yi mini magani amma Allah ya sani babu sa hannun Umaima a lalurata." Inuwar da Yaya Halima ta hango a wurin labule ya sa ta furta. "Waye a wurin nan?" Jikina na rawa Jakadiya ta faɗa ɗakin tana faɗin, "Allah ya taimaki Fulanin Takawa, uwar yariman gobe da yardar Allah. Dama ruwan wanka na kwashe na zo sanar da uwar gijiyata." Daga cikin ɗakin Fulani Babba ta furta. "Saƙonki ya isa Jakadiya." "Godiya nake zinariya fara mai farar aniya bangon talakawa da marasa gata, Allah ya raya mana yarima ya gaji karagar da babu kamarta a faɗin nahiyar nan." Yaya Halima ta amsa tana bin Jakadiya ta kallon tuhuma. Sai da ta ga Jakadiya ta fita sannan ta furta. "Da alama wannan farar zuciya taki na iya kai wankin hula ya kai ki dare, jikina yana ba ni idon masarautar nan yana kanki." "Yaya Halima shi zato zunubi ne! Don haka..." Da sauri ta katse ta. "Dama ki ajiye zurfin cikinki kin amayar mini da abin da yake cikinki domin abokin kuka ba a ɓoye masa mutuwa." Idanun Fulani Babba ya ciko da ƙwalla don ita kaɗai ta san zafin da zuciyarta take yi mata, amma sanin Yaya Halima na daga cikin irin marasa haƙuri ya sa ta danne damuwarta ta furta. "Babu wani abu da yake damuna Yaya Halima, idan ma akwai na fauwala wa Allah saboda saniyar da ba ta da jela Ubangiji ne ke kore mata ƙuda." Yaya Halima ta taɓe baki ta fice ba tare da tanka mata ba, Fulani Babba da ta yi shirin wanka tana kai idanunta kan jaririnta. A kullin ta kalle shi zuciyarta na wasu-wasi a kan ingancin lafiyarsa, sai dai babu yadda za ta yi tun da ba fada gare ta a wurin Takawa ba balle ta yi masa bayanin halin da jaririn yake ciki. Kamar za ta tashi sama haka Jakadiya ta yi sashen Fulani Umaima a lokacin Fulani na shaƙar bacci ko sallar asuba ba ta yi ba duk da gari ya waye garau, da farko Bayin da ke kula da ita sun sanar da Jakadiya Fulani na bacci. Amma da yake bakinta cike yake fal da tsegumi a dole haka ta shiga tana ta rangaɗa sallama. Kamar a mafarki Fulani Umaima ta ji sallamar Jakadiya wanda hakan ne ya alamta mata akwai wani muhimmin abin da yake tafe da ita, tana daga kwance ta sa a yi wa Jakadiya iso har cikin turakarta. Jakadiya na shiga ta zube a ƙasa, "Hutawarki lafiya tauraruwar Mai martaba uwar yariman gobe da yardar Ubangiji. A yi mini aikin gafara na tashi uwar gijiyata a farar safiya..." Da hannu Fulani Umaima ta katse ta, kamar ba za ta yi magana ba sannan ta ce. "Akwai magana a bakinki Jakadiya don na tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa." Jakadiya ta yi mata jinjina da hannu. "Allah ya ƙara yawan rai wannan yarinyar da nake ganinta mai hankali ashe lumbu-lumbu ce wutar ƙaiƙayi?" "Jakadiya tafi kanki tsaye. Fulani Umaima ta faɗa a gajarce. "Halima yayar waccan ragowar fitsarin, ita na ji tana shirin ɓallo mana ruwa. Ni kuma na ce har gaban abada kwaɓarmu ba za ta yi ruwa tsululu ba, sai dai a mutu har liman kowa ya rasa sallah..." Jakadiya ta kwashe duk maganganun da ta ji Fulani Babba suna yi ita da Yaya Halima. Murmushi Fulani Umaima ta saki. "Daga kallon da na ga tana bi na da shi ya sa na fahimci ruwa ba zai taɓa tsami banza ba. Ta shi ki je Jakadiya idan hantsi ya fito ki dawo akwai kyautar samirar alkaki da nakiya, zan haɗa miki da fallan zani da gorar maɗi. Na rantse da Allah sai na tabbatar wa Halima ba a taka shuri kowanne iri a zauna lafiya." Jakadiya ta sake zubewa. "Godiya nake uwar ɗakina, godiya nake zinariyar Mai martaba uwar duka mazauna ƙasar Huddam da kewayenta. Allah ya buɗi ido lafiya ya kawo mana Yarima cikin ƙoshin lafiya." Fulani Umaima ba ta amsa ba, inkiya ta yi mata da ido. Ganin haka ya sa Jakadiya ta fice daga ɗakin don ta san ba za ta amsa mata ba. Washegari ya kama suna jaririn Fulani Babba ya ci suna Abubukar Sadiq, haka kawai Sarki Abdul'aziz ya tsinci kansa cikin farin ciki duk ba ya iya nuna soyayyarsa game da yaron, ya so a gayyaci masu wasannin al'adar bahaushe amma wata irin fargaba yake ji da tsoron Fulani Umaima a zuciyarsa. Da ya yi wani yunƙuri sai ya ji kamar idan ya aikata bai kyauta wa Fulani Umaima ba. A haka aka ci taron suna sai dai hatta Bayin da ke cikin masarautar ranar sai ta zame musu daban sakamakon walwala da suka samu ta hanyar sauya abinci da sakewa. Fulani Umaima ta saki jiki sosai a ranar da kanta ta gayyaci 'yan wasan tauri aka gudanar da wasanni, tamkar babu wani mugun ƙuduri a zuciyarta. Bayan suna da kwana biyu 'yan uwan Fulani Babba suka tattara kayansu suka koma masarautarsu, ko a ranar da za su tafi sai da Yaya Halima ta jaddada wa Fulani Babba suna komawa za a aiko mata da magungunan da suka da ce. Ita ma kuma Fulani Umaima a ranar da suka tafi a ranar ta dira wurin Bamaguje ta shimfiɗe masa bukatunta, kuma take ya zartar mata da su, haɗe da jinjina mata bisa aikin Baiwa Maimuna da ta aiwatar ba tare da an samu matsala ba. Sai dai abu ɗaya da ya sanar mata ne ya nemi hargitsa kwanyarta har ta koma gida ta gagara runtsawa tana tunanin makomar abin da zai biyo baya. *Masu ganin laifin Fulani Babba na rashin yin addu'a kada ku manta labarin an sanya ya faru a shekaru saba'in baya da suka wuce (1953) Kun ga a lokacin ilimin addini bai yawaita ba, ba kamar yanzu da ilimi ya zaman ruwan dare ba. A mafi yawan wancan lokacin, camfi da tsubbace-tsubbace sun fi ƙarfi a kan yawaitar addu'a, babu wayewar kan da idan abu ya same ka kace bari ka duƙufa ba dare ba rana ka kai wa Allah kukanka.* _Ummou Aslam Bint Adam_ 🌚 07062062624 [10/4, 11:48 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye. SHAFI NA SHIDA Ajiyar zuciya Fulani Umaima ta sauke ta zauna a gefen gado, wani irin gumi ya fara tsattsafo mata. "Binciken da nake kan yi dangane da abin da kike ɗauke da shi a cikin cikinki, na shafe tsawon kwanaki ina bincike har yau na gagara sanin mene ne a ciki. Kullin duhu nake mai ɗauke da rashin alkairi, duhu ne mai ɗauke da tururi da ke ƙone duk wani makusancinsa. Ba ke kaɗai ba ni kaina ina da burin sanin me za ki haifa domin amfanar gobena. Ina buƙatar Magaji a halwar tsafina Umaima." A razane ta ɗago tana kallonsa, "Ban gane kalamanka ba Bamaguje, me ye alaƙar abin da yake cikina da gadon halwar tsafinka?" Bamaguje ya saki murmushi. "Wannan sirrintaccan sirri ne tsakanina da mahaifiyarki, ba alaƙar abin cikinki ya kamata ki tamabaya ba. Amma mu jirayi lokacin kin san ko ba daɗe ko ba jima akwai lokacin da ya za ta ɗakin ƙanwa." Sallamar Baiwa Salame ta katse Fulani Umaima daga duniyar taunanin abin da suka tattauna da Boka Bamaguje. Ba ta amsa mata ba don haka Baiwar ta koma, Fulani Umaima ta miƙe ta ci gaba da kaiwa da kawowa damuwa cunkushe a zuciyarta. Kamar wacce aka tsokara haka ta miƙe ta ƙarasa ta ɗauko akwatin sirrinta, ta ɗauko littafin da Bamaguje ya bata. Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta buɗe shafin da ta tsaya da karatu. Na jima a tsugunne gaban Uwar Bayi ina tsammanin kalamanta har sai da na fara yanke ƙauna da samun abin da nake buƙata, ba zato na ji muryarta a tsakiyar kaina. "Hidaya labarinki cike yake da almara, al'ajabi da ban mamaki. A tsammanina ni ce mace ta farko da na fara tozali da ke a cikin masarautar nan, ban sani ba ke 'yar cikinta ce ko akasin haka. Abu ɗaya na sani watarana na tafi isar da saƙon Fulani Hauwa na gan ki tsaye a jikin bishiyar kukar da ke bayan ɗakunan Bayi kina rusa kuka, gudun kada na yi latti a aiken da aka yi mini ya sa sai da na kai na dawo har lokacin ba ki daina kuka ba. Da yake a ranar an shigo da sababbin Bayi sai na yi tsammanin 'yar ɗaya daga cikinsu ce yawo ya kawo ta nan take kuka ta gaza gane hanya wurin mahaifiyarta. Sai na riƙe miki hannu muka wuce sashen Bayi na ƙaraci cigiya babu wanda yace 'yarsa ce, to da yake a cikin Bayin da aka kawo akwai wasu mata biyu da suka rasu sai na yi tsammanin mahaifiyarki na ɗaya daga cikinsu. Amma daga baya sai na ga 'yan uwansu suna cewa sam ba tare da su aka kawo ki ba, wannan dalilin ya sa kika ci gaba da zama a sashen Bayi ba tare da iyaye ba." Kalama Uwar Bayi suka zo ƙarshe a daidai lokacin da ni kuma bakin ƙomar idaniyata ta ɓalle, sai da na yi kukana mai isata na dube ta. "Haka zan ƙare rayuwata ba tare da sanin makomata ba." Uwar Bayi ta wara hannuwa. "Abin da na sani kaɗai na sanar da ke, idan Allah ya sa akwai rabo sai ki gansu ko a nan gaba ne." Yau ita ce rana ta farko da na ji daddaɗan kalamai daga bakin wani daga cikin Bayin da nake mu'amala da su, don haka na ƙirƙiri murmushin da bai kai zuci ba na furta. "Shi kenan ina godiya Uwar Bayi da wannan bayanin naki." Babu wanda ya sake tanka mini haka na tashi jiki a sanyaye kamar kazar da aka jefa da wuƙa na koma mazaunina na farko na zauna ina jin zuciyata babu daɗi. Ina jin su suka ci gaba da hirarsu sai dai ko kaɗan ba na fuskantar koda kalma ɗaya, zuciyata ta yi nisan kiwo a fannin tunani da na gagara janyo ta balle ta gane in da hirarsu ta dosa. Wani farin tsoho mai ɗauke da farin gemu na gani yana tunkaro ni, tsananin kammanin da muke yi da shi ya sa na tsaya cak ina kallonsa. Tun da na zo duniya ban taɓa ganin mai kamceceniya da ni ba, ban yi tsammanin ya kusance ni ba don haka na ji hannuwansa a cikin nawa. "Kada ki damu da sai kin san wace ce ke, kina da kowa kuma wannan masarautarki ce gadonki ce halak malak, sai dai ina mai ta'ajibin sanar da ke har duniya ta tashi ba za ki ga mahaifiyarki ba. Ni ne mahaifinki! Ni ne mahafinki!! Ni ne mahaifinki!!!" Firgigit na farka daga mafarkin da nake yi, na juya ina kallon yadda mutane ke baccinsu hankali kwance. Mamaki ya kama ni, cikin damuwa na furta. "Ya aka yi ka zama mahaifina? Kuma me ya sa kuka guje ni." Kamar alamara na ji an furta mini. "Ba mu guje ki ba, mun kawo ki karagarki ne don ki karɓi abarki." Waige-waige na fara yi don ganin mai tanka mini a cikin tsohon daren nan, har na yunƙura zan tashi sai na ji tsoro ya mamaye ni, ba shiri na koma na zauna bacci ya ƙaurace mini. A lokacin da bacci ya fara fisga ta na ji Uwar bayi tana tashinmu cikin hargowa da masifa kamar yadda ta saba duk asubar fari. A haka na ci gaba da gudanar da rayuwa cikin rashin daɗi, rashin 'yanci da ƙangin bauta. Mu Bayi ba mu da wani gata ba musan ci mai kyau da sha mai kyau ba, ana cikin haka watarana saƙo ya iso gare mu ana san Uwar bayi ta sake zaɓen Bayi ta kai sashen Fulani Hauwa kulu, haka kawai na ji gabana yana tsananin faɗuwa. Aka saka mu muka yi layi cikin tsautsayi ƙaddara ta yarfo mini hannunta, Uwar Bayi ta zaɓa har da ni a cikin mutane ukun da Fulani Hauwa take buƙatar ƙari.Tun da nake rayuwa a cikin Masarautar ban taɓa shiga sashen Fulani ba, hasali ma ban taɓa tozali da ita ba, sakamakon rashin imanin da nake jin ana faɗa game da ita. Wannan ta sa nake takatsantsan a kan abin da zai sa na kai kaina sashenta. Tun da muka dumfari hanyar sashen Fulani nake jin jikina yana yi mini wani irin zafi, hayaniya na fara ji sama-sama a kaina ga wani kiɗan tambura da nake ji yana tashi a tsakiyar kunnuwana. Sai dai yadda na lura ni kaɗai nake jin waɗannan baƙin al'amuran da ke yi wa duniyana dirar mikiya. Take gumi ya fara keto mini sakamakon yadda nake jin zafin na ratsani kamar wacca aka tsire a tukubar tsire. A babban ƙofar rumfar (Falo) Fulani Hauwa na coge, sakamakon yadda nake jin ana fisgata. Hayaniyar da nake ji ta fara rikiɗa zuwa muryar da nake jin tamkar na taɓa sanin mamallakiyar muryar. "Barka da zuwa Sarauniya." Na ji an furta. Waige na fara yi amma ban ga kowa ba, na riƙa jin busar sarewa a tsakar kaina ba tare da na ga masu yi mini ba. Ina nan tsaye na ji Uwar Bayi na faɗin. "Ku yi hanzari kada ku fusata Fulani kuke tafe laƙai-laƙai kamar marasa laka a jiki." Da sauri na ci gaba da tafiya har muka ƙarasa babban rufar Fulani da ta ƙayatu da kayan alatu kala-kala. Kaina na ji ya yi girma wata irin ƙasaita, isa da tsantsar izzar mulki na ratsa ni, da ƙyar nake taku cikin ƙasaita. Uwar Bayi da sauran Bayin da muka taho tare suka tsaya cak a bakin wata mashinfiɗa wacce bayi suke tsayawa idan sun shiga wurin Fulani Hauwa kulu. Ban kalle su ba na zarce kan ƙasaitacciyar karagar da ke cikin falon, na zauna ina kallon su Uwar Bayi ɗaiɗai. Da zamana na ji wani abu ɗau! Yana zagaye ƙoƙon kaina. Uwar Bayi kusan mutuwar tsaye ta yi ganin ɗanyan aikin da na aikata, bakinta na rawa ta furta mini. "Hidaya...hankalinki ɗaya kuwa? Kin san a fadar wacce kike?" "Ya kamata ki gyara linzamin harshenki, idan ba haka ba sai na sa an datse shi nan take. Wannan fadata ce..." Ashar ɗin da Fulani Hauwa kulu ta saki ya katse kalamaina, na dube ta cikin tsadaddiyar shigarta ina ƙare mata kallo. "Uban waye ya halatta wa wannan ƙasƙantaciyyar zama a karagata?" Cikin isa da ƙasaita na ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, kamar ba zan amsa ba na ɗago ina kallonta a wulaƙance. "Wannan karagar iyaye da kakannina ce don haka ki gyara kalamanki." Na lura da razani a saman fuskarta, ɗan yatsanta na rawa ta nuna ni. "Ta tabbata ke ce Hidaya ko?" Na jingina da jikin kujerar na furta. "Ba tsammani ba ne ni ce Gimbiya Hidaya." Wata gwauruwar ajiyar zuciya na ji ta sauke. "Tabbas da alama tarihi zai kuma maimaita kansa. "Tarihi tuni ya sake maimaita kansa tun da gani na wanzu a gabanki." Fulani Umaima ta rufe littafin tana jin kanta na sarawa don a kullin labarin Hidaya ƙara hargitsa kwanyarta yake. Ta wurga shi cikin akwatinta tana sakin tsaki a fili don ba ta jin za ta sake ci gaba da karanta wannan rikitaccan labarin. Komawar su Yaya Halima Masarautarsu da kwana ɗaya labari ya dawo wa Fulani Babba na sabuwar lalurar da ta afka wa Yaya Halima na kurumcewa da makanta, hankalin Fulani Babba ba ƙaramim tashi ya yi ba. Da yake jego take yi babu damar ta tafi dubiya haka ta zauna ta ci kukanta a cikin ɗaki, ta sake ayyanawa zuciyarta ko da wasa ba za ta sanarwa da mahaifiyarta halin da take ciki ba don kar damuwa ta yi mata yawa. BAYAN SHEKARA GOMA Tafe suke a cikin wani baƙin ƙasurgumin daji mai matuƙar hatsarin gaske, su kansu sukan yi takatsantsan wurin shiga irin waɗannan dajijjikan sakamakon miyagun hallitu da iskokin da ke cikinsa. "Mai gado wai ni kam kin taho mini da baƙar bakata?" Umaru ya faɗa yana sake leƙen wani koren maciji da ke saƙale da wata koriyar bishiya. "A'a Malam tsakani da Allah ni kam na manta ka san sai da na ce idan za mu fito ka tuna mini." Da sauri ya ciro wata ƙanƙanuwar kwari da baka daga cikin ƙugunsa, bai cika harbi da ita ba don haka ya so Mai gado ta taho mata da farar bakar wurinta. Ya kalli macijin haɗe da matsa wata laya da ke saƙale a wuyansa, ya sakar wa macijin harbi nan take ya tsire shi wani koren ruwa mai kauri ya fara fita daga jikinsa. Yana shirin miƙa hannu ya ciro kibiyar daga can gefensu suka fara jiyo numfarfashi, Mai gado da sauri ta fara matsawa don tabbatar da zarginta. "Wash wayyo! Ku taimaka mini, ku kawo mini ɗauki tsafi zai taimake ku. Tsafi zai shiga lamarinku, ku taimaka mini kada na mutu idan na mutu tsafi zai yi fushi da ku." Gaban Mai gado ya faɗi ganin wata matashiyar mace mai tsohon ciki tsugunne babu kaya a jikinta, ƙugunta ne kaɗai ɗaure da ganye sai saman ƙirjinta. Kanta da wani irin cukurkuɗaɗɗan gashi ya zubo har ƙirjinta. "Malam zo ka ga." "Kada ki taɓa komai Mai gado, har yanzu ba ki gama sanin sharrin daji ba. Wannan ba kamar sauran dajijjika ba ne, ki yi takatsantsan." Yana ƙarasawa idanunsa suka yi tozali da matar, ta galabaita da alama naƙuda take duba da yadda jikinta ya ɓaci kace-kace. Mai gado ji ta yi ba za ta iya daurewa ba don haka ta ƙarasa ta ruƙo ta tana faɗin. "Baiwar Allah me ya kawo ki naƙuda cikin dokar dajin nan?" Wani irin nishi suka ji ta yi cikin galabaita da fita hayyaci tana faɗin. "Tsafi, tsafi ka dafa mini. Abin bauta ka tserar da jinina ko ɗon ta gagara magautana, tsafi ka taimaka mini." Rufe bakinta babu jimawa suka ji ta ƙwalla ƙara nan take ta haifo jaririyar 'yarta mai tsananin kama da ita. Mai gado na shirin taɓa jaririyar da sauri matar ta dakatar da ita, ta hanyar ture hannunta tana girgiza mata kai. "Zuri'ar RUMZU daban take da sauran al'umma, idan muka haihu tashin farko jinin wata al'umma ba ta isa ta taɓa mana 'ya'ya ba har sai mun gama da 'ya'yanmu ake taɓa mana su. Idan ba haka ba yanzu za ki mutu, abin bauta zai hallaka ki." Mai gado ta ɗan zaro idanu cikin tsananin mamaki. Umaru da ya juya bayansa ya jinjina kai yana taɓe baki. Hannu ta sa a ƙugunta ta ciro wata ƙaramar baƙar aska ta yanke wa jaririyar cibiya, ta sa wata siririyar fata ta ɗaure cibiyar tamau. Hannunta ta saka ta lakuto jinin da ke fita daga ƙasanta ta shafa a saman goshin jaririyar lokaci ɗaya jaririyar ta tsanyare da wani irin matsanancin kuka, jinin da ta lakata mata a goshi ya shiga wata irin tafarfasa a kan goshin jaririyar. Wani irin baƙin jini ya fara zuba daga cikin hancin jaririyar, kunnuwanta da ƙasanta. Mai gado tana tsaye tana kallon abin da matar take yi cikin al'ajabi da tsananin mamaki har sai da tsoro ya fara kamata. Ganin jinin ya zarce ƙa'ida ya sa matar ta saka bakinta ta zuƙo shi sannan ta fesar a gefe, take ciyawar wurin ta ƙone ƙurmus. Ta jima tana zuƙe jinin jikin jaririyar tana ɗiban jinin gabanta tana zubawa a goshinta, idan ya tafasa sai ya shige jikin jaririyar. Sai da matar ta gama ta ɗago ta dubi Mai gado cikin karyewar zuciyata tana faɗin, "Ban san ku su waye ba, amma na tabbata daga yanayinku ku masu karamci ne kuma tsafi zai shiga lamuranku ya dafa muku..." Da sauri Umaru ya waigo ya katse ta. "Baiwar Allah mu ba mu dogara da tsafi da sihiri ba, mun dai dogara da Ubangijin sammai da ƙassai." Jinjina kai ta yi tana murmushi ta furta. "Koma da wa kuka dogara ban damu da na sani ba, zan bar muku amanar 'yata domin na san dangina ba za su bar ni ba mutuwa zan yi, don na hangi tsinin mashin tsafin da Mahaifina ya wurgo min, idan ban damƙa muku ita ba tabbas har ita za su hallaka mu. Ba a nan doron ƙasa ba, ko ƙarƙashin ƙasa na nutse matuƙar ina numfashin na tabbata zuri'ata ta Rumzu ba za su bar ni ba." A firgice suke kallonta. "Wace ce ke? Mutum ce ko aljan?" Mai gado ta wurga mata tambaya a tsorace. "Sanin matsayin hallitata ba shi ne mafita ba, domin a yanzu ba lallai ya amfane ku da komai ba. Ga amana zan bar muku ku dubi darajar abin bautarku ku riƙe ta amana, na so a sanya mata suna HAIZAT amma dalilin mahaifinta ya nunke nawa don haka ya ce mini ya fi son a saka mata sunan JAWAHIR, ban san ma'anar sunan ba don ba ya daga cikin sunan zuri'ata. Sai dai na tabbata wannan sunan zai amfane ta zuwa nan gaba, idan ta isa zama budurwa ku ɗauke zuwa bakin kowacce irin bishiyar kuka akwai ajiyar da mahaifinta ya taɓa yi wanda ita za ta tono gadon da zai bayyanar da ita jininsa ce da hannunta. Wannan jaririyar ita za ta sanar da ku asalin wace ce ni har zuwa zuri'ata ta Rumzu, tun daga zubin hallita har zuwa tushenta. Na san dangina da bibiya, kafiya da matsanancin ruƙo duk rintsi kada ku bayyana ba kune asalin iyayenta ba matuƙar za ku shiga baƙon wuri ko al'umma, wataƙila ta iya tsira da rayuwarta daga kaidinsu." Tana gama maganar ta ɗora jaririyar a kan saman wani ƙaton gidan tururuwa, ta damƙi ƙasar gidan tururuwar tana runtse idanunta haɗe da furta waɗansu irin kalaman tsafi da su Mai gado ba su taɓa ji ba, tana gamawa ta shafa a jikin jaririyar gabaɗaya, take jinin da ke saman goshin jaririyar ya ɓace ɓat. Ta sunkuya saitin kunnen jaririyar tana yi mata raɗa, lokaci ɗaya jaririyar ta yi shiru tamkar wacce take sauraron kalaman mahaifiyarta. Wani irin jini ne ya ɓalle wa mahaifiyarta amma duk da haka cike da ƙwarin gwiwa da dakiyar zuciya ta ɗauki jaririyar ta fara takawa har zuwa bakin ramin kwarmin bishiyar kukar da ke gefenta ta ɗora jaririya a ciki, ta saka hannu ta dafa saman goshinta nan take suka ga ta fara wata irin jijjiga, idanunta suka firfito numfashinta ya ɗauke rai ya yi halinsa. Daga Umaru har Mai gado kusan mutuwar tsaye suka yi saboda al'ajabi don tun da suke a duniya ba su taɓa ganin makamancin irin wannan lamarin ya faru a gabansu ba. Mai gado ce ta iya motsawa ta ƙarasa ta ɗauki jaririyar da mamaki ta kalli Umaru jin jikin jaririyar ya yi wani irin sanyi kamar ƙanƙara. "Malam yanzu ya zamu yi da wannan gawar?" Ajiyar zuciya ya sauke yana shirin yin magana suka ga gawar matar na matsawa haɗe da nutsewa cikin bishiyar kukar da take jigine a jikinta. Cikin tsoro suka ja da baya suna kallo, kafin wani lokaci babu gawar babu alamarta ta nutsa cikin bishiyar kukar sai shatin jinin da ke manne a jikin bishiyar. Jiki na karkarwa Mai gado ta ajiye jaririyar a ƙasa tana ja da baya ta furta. "Mai gida Allah ya sani ba zan iya riƙon wannan abin ba, domin ba na ko tantama mahaifiyar yarinyar aljana ce ita kanta yarinyar dubi irin siddabarun da mahaifiyarta ta yi mata kafin ta mutu." Cike da gamsuwa Umaru ya ɗago zai yi mata magana, gabansa ne ya yanke ya faɗi sakamakon mugun gamon da ƙwayar idonsa ta yi. Da sauri ya ja hannun Mai gado suka faɗi can gefe haɗe da kurma ihun neman taimako. _Ummou Aslam Bint Adam_ 🌚 07062062624 [10/4, 11:49 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye. SHAFI NA BAKWAI Koren macijin da Umaru ya kashe tun kafin haihuwar matar nan suka hango ya sulalo ya kafe su da ido yana kallo tamkar zai far musu da sara, suna nan cikin tsinkewar zuciya suka ga ya ƙarasa wurin jaririyar ya kanannaɗe ta, suna daga wurin da suke a gefen Umaru ya ce. "Mai gado an ya yau mun shigo dawa a sa'a kuwa?" Da sauri ta girgiza masa kai. "Tun wuri mu kama hanyar gida." Cikin sanɗa suka miƙe da niyyar tafiya sai dai bisa ga mamakinsu babu macijin babu alamarsa, don haka suka nufi hanya da niyyar tafiya. Cak Mai gado ta tsaya tana waige. "Tsayawar me kika yi Mai gado?" "Mai gida zuciyata ta karaya, ba zan iya tafiya na bar yarinyar can ba. Ka dubi yadda mahaifiyarta ta aminta har ta damƙa mana amanarta. Ba mu sani ba wataƙila samunta babbar rahama ne a tattare da mu, ta wani fannin ma gani nake Allah ne ya azurta mu da samunta ka duba ka gani haihuwata huɗu duk yanzu babu rayayye, idan muka bar ta a wannan ƙungurmin dajin ba mu san wacce irin rayuwa za ta gudanar ba." Jikin Umaru ya yi sanyi ya waiga yana hango jaririyar da ke tsala matsanancin kuka. "Mu je na ɗauko ta In Shaa Allah, Allah zai kare mu tun da ya ga kyakkyawar niyyarmu." Da haka suka rankaya suka wuce har gaban jaririyar suka ɗaukota, Mai gado ta kunto ɗankwalinta ta nannaɗe ta a ciki sannan suka nufi hanyar da za ta sada su da gida. Sai da fargabar da Umaru yake ciki ba wuce irin tarbar da mutanen ƙauyensu za su yi musu ba, musamman idan aka samu akasi wani al'amarin almara ya faru kamar yadda suka gani daga wurin mahaifiyarta. Sai dai sun ɗaukar wa kansu alƙwari babu wanda za su furtawa silar samuwar yarinyar don kada ta taso cikin tsangwama da ƙyara. Masarautar Huddam Ɗan matashin ne mai kimanin shekara goma zaune a cikin fadar Sarki Abdul'aziz a kan shimfiɗaɗɗiyar shimfiɗar alfarma yana sanye da rantsattsiyar alkyabba. Kallon mutane yake yi ɗaiɗai fuska a murtuke babu walwala, kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar da mulkin gadarsa ya yi ba taka-haye ba. Gajiyar da ya yi da zaman cikin fadar ya sa ya miƙe cike da izza yana taku kamar ba zai taka ƙasar ba. "Takawarka lafiya Yariman masarauta, a huta lafiya sarkin gobe da yardar Allah." Fadawa suka ɗauka a lokacin da suka lura Muhsin ya miƙe da niyyar fita daga fadar, wasu daga ciki suka ƙarasa suna take masa ba. Hannu ya ɗaga haɗe da tsayawa wuri ɗaya cak, ya kusa minti ɗaya a haka sannan ya furta. "Ba na buƙatar rakiya." Lokaci ɗaya suka ja da baya sannan ya ci gaba da taku, duk hanyar da ya bi haka bayi da fadawa suke zubewa suna kwasar gaisuwa amma ko kallansu ba ya yi ballanta su saka ran zai tanka musu. Yana gab da shiga sashen mahaifiyarsa bisa tsautsayi wata baiwa ta fito da sauri don isar da saƙon Fulani Umaima, a rashin sani ta bangaje shi har sandar hannunsa ta faɗi ƙasa. Jiki na karkarwa ta zube ƙasa. "Tuba nake shugabana, a gafarce ni uban gidana ni mai laifi ce ba tare da..." Marin da ya ɗauke kuncinta da shi ya sa haƙoranta suka datse harshenta har sai da bakinta ya fashe, idanunta suka fara zubar da ƙwalla ta sake zube wa a ƙasa tana faɗin. "Godiya nake Sarkin gobe." Ɗaga kansa ya yi ya hango wani Bafade hannunsa ɗauke da murtukekiyar bulala ya furta, "A hora ta na tsawon wuni guda da alama ba ta gama sanin a gidan masarauta take rayuwa ba tun da ba ta san aikinta ba." Yana gama maganar ya wuce ba tare da ya jira cewarsu ba. A kishingiɗe ya tarar da mahaifiyarsa tana huatawa, wasu 'yan matan Bayi na tsugunne wurin ƙafarta suna yi mata tausa. Ganin yanayinsa ya sa ta tashi zaune haɗe da sallamarsu. "Wa ya ɓata ranka Muhsin?" Fulani Umaima ta tambaye shi. Bai tanka mata ba sai da ya zauna. "Wata baiwarki ce ta ɓata mini rai amma komai ya wuce." "Wace ce ita na sa a hukuntata?" Muhsin ya fara rage kayan jikinsa. "Na sa a hukuntata, ina Ruƙayya ban ganta ba?" Fulani Umaima ta yamutsa fuska, "Za ta wuce sashen Fulani babba ne, yarinya sai baƙin nacin tsiya kamar tsohuwar mayya." Take idanunsa suka yi jawur rai a matuƙar ɓace ya saki guntun tsaki, ba tare da furta komai ba. Ihun da Ruƙayya ke ƙwallawa ne ya ja hankalin Fulani babba da sauran bayin da ke harabar gidan, turus bayin suka yi suna kallon juna duk da ba yau ce rana ta farko da suka ga Abubakar na kama gashin duk wani mutum da ya kusance shi ba ciki kuwa har da mahaifiyarsa. Ruƙayya ƙanwar Muhsin ce ita take binsa shekararta bakwai a duniya, Allah ya haɗa jininta da Abubakar ba ta iya wuni guda cir ba tare da je sashen Fulani babba ta shiga ɗakin Abubakar ta tsaya yana yi mata gwaranci tana mayar masa ba. Babbar matsalar da ke damun Fulani Babba bai wuce yadda Abubakar yake cizgar gashin kansa yana ci ba, idan na kansa ya ƙare kuma duk wanda yake da tsautsayi idan ya damƙe ka haka zai dinga cizga har sai an kwace ka. Abubakar ya shiga shekara ta goma sha ɗaya, sai dai har lokacin a zaune yake ko motsi ba ya iya yi komai sai an yi masa. Fari ne sol kamar mahafiyarsa sai dai kammaninsa sak da Sarki Abdul'aziz, tun da ya taso ba ya iya magana sai dai gwaranci kuma har kawo lokacin yawu na dalala daga bakinsa. Idanunwansa duka biyun a juye suke, hannuwa da ƙafafuwansa suma a shanye suke babu abin da yake iya aikatawa hatta wanka da tsarki yi masa ake yi. Fulani Babba da sauri ta ƙarasa gaban Abubakar ta sa hannu cike da ƙunan rai ta ɗauke fuskarsa da mari, wannan ne karo na farko da ta taɓa sanya hannu a jikinsa da sunan duka. Zafin marin ya ratsa shi hakan ya sa ya ƙarasa cizge kitson kan Ruƙayya da ke bakinsa, sai kuma ya fashe da kuka yana gwara kansa da ƙasa. Cikin azaba ta sake ƙwalla ƙara take numfashinta ya ɗauke ta sume a wurin. Tamkar mayuwancin zakin da ya samu nama haka Abubakar ya tura sillin jelar kitson kan Ruƙayya da ya cizge cikin bakinsa ya fara tauna kafin wani lokaci ya haɗiye shi gabaɗaya. A firgice Fulani Babba ta shiga yayyafa wa Ruƙayya ruwa ta jima a kanta sannan ta sauke ajiyar zuciya a galabaice, ganin ta buɗe ido ya sa Fulani Babba ta ji farinciki har cikin ranta sai dai kuma wurin da ya ɗaye mata kitson tuni gefen kan ya kumbura suntum. Wani irin sara ta ji kan yana yi mata a daddafe ta iya miƙewa ganin haka ya sa Fulani ta ba wa Bayin da ke gefe umarnin su ɗauke ta zuwa cikin turakarta. Duk dauriya irin ta Ruƙayya sai da ta dinga zubda ƙwalla sakamakon yadda take jin kanta na sara mata kamar zai tsage gida biyu. Duk yadda Fulani babba ta so zaman Ruƙayya a ɗakin zuwa lokacin da zugin zai sarara mata fir ta ƙi yarda, don haka ta sake saka Bayi suka ɗauke ta tana gaba suna biye da ita a baya har cikin sashen Fulani Umaima. Ganin a halin da aka shiga da Ruƙayya ya sa Fulani Umaima miƙewa zumbur! Bakinta har rawa yake ta furta. "Me ya faru da ita?" "Laifi ne yayanta Sadik ya yi mata, wallahi tsatsayi ne Fulani don haka na zo da kaina ba saƙo ba..." "Dakata Fulani! Hawainiyarki ta kiyayi ramata. Ba tun yau ba na lura da take-takenki dangane da kiranyen da kika yi wa Ruƙayya. Lokaci ɗaya kin sa an lashe kurwar yarinya ba ta ƙaunar zaman wurin mahaifiyarta, wannan fa ba shi ne karo na farko na ji labarin wancen shagirigirbau ɗin ya maƙure ta yana yi mata ƙamshin mutuwa ba. Amma an yi ta yanke ta gille, wannan shi ne karo na farko kuma na ƙarshe da zai sake taɓa kowanne bil'adama a sashenki." Fulani Umaima ta ƙarasa maganar tana kai kallonta wurin bayin da ke riƙe da Ruƙƙaya. "A samu Jakadiya ta gaggauta sanar da Mai martaba ina buƙatar ƙwararrun masu magani, don ban san dafin da haƙoransa suke ɗauke da shi ba." Da sauri suka shimfiɗar da ita suka fice, Fulani Babba ta ƙarasa gabanta ido cike da ƙwalla ta furta. "Wallahi ko a mafarki ban taɓa jin Ruƙayya ba 'yata ba ce, tamkar yadda na ɗauki su Khadija haka nake jin ta, ta ya ina sane zan bari Abubakar ya illatata." Sai da Fulani Umaima ta saki murmushin takaici ta furta, "Me ya sa bai kama Khadija ko Sakina ya illata ba, saboda kina baƙincikin kin haifi sauna, wawa, shashasha shi ne ni ma kike burin ƙarfi da yaji na rasa waɗannan biyun da Allah ya ba ni." Tsoron hukuncin da Fulani Umaima za ta yanke ya sake mamaye Fulani babba, ta tsugunna bisa gwiwoyinta don ta san kome Fulani ta gaya wa Takawa hawa yake ya zauna ɗaram. Ba tun yanzu ba ta jima da dawowa daga rakiyarta, don ta lura sai abin da Fulani Umaima take so Takawa yake zartarwa. "Tabbas Abubakar bai kyauta ba amma ki dubi girman Allah ki yi haƙuri..." "Idan ba ki yi gaggawar fita daga sashena ba wallahi sai na shayar da ke ruwan mamaki." Fulani Umaima na gama magana ta yi ciki cike da zafin rai. Fulani babba ta sunkuyar da kanta ƙasa tana zubar da ƙwalla, dama ya ya lafiyar kura ballantana ta yi zawo. Gari banza ma Takawa ba ƙaunar Abubakar yake ba ina ga an ce ya taɓa 'ya'yan gaban goshi. Cike da zullimi ta fara yunƙurin tashi, daga bayanta ta hangi Muhsin na zaune yana aika mata da saƙon harara cikin kallon tsana. A haka ta ƙarasa sashenta gwiwoyinta a sanyaye, ta windo ta leƙa Abubukar da ke zaune yawu na dalala. Sai a lokacin ta samu damar fashe wa da matsanancin kuka duk da tana da tabbacin bayin da ke zagaye da ita suna sauraronta. "Ya Allah ba don ba ka so ko ƙaunata ka jarabce ni da wannan bawa Naka ba, Ya Ubangiji ina godiya bisa baiwa da wannan ni'imar da ka yi mini domin dubbunaina na buƙatar ko da makamancinsa ne. Ya Allah idan rayuwar wannan bawa naka mai tsayi ce Ubangiji ka yalwace shi da lafiyar ya zama kamar kowa, saɓanin halin da yake ciki. Idan kuma mai gajeren kwana ne Ubangiji ka gaggauta ɗaukar kwanakinsa ko na samu salama a rayuwata..." Kukan da ya ci ƙarfinta ne ya datse ragowar kalamanta. "Allah ya sanyaya zuciyar uwar ɗakina Ubangiji ya ƙara wa Yarima lafiya." Baiwa Zainaba ta furta jiki a sanyaye kamar kazar da tono wuƙa. "Zainaba na ɗauka ko kowa zai furta son ransa ke mai faɗa mini gaskiyar abin da ke cikin zuciyarki ne? A haka kike kiran Abubakar da Yarima kina ga ko a mafarki za a damƙa wa Abubakar karagar mulki ne." Tabbas kalaman Fulani Babba a turba suke domin kowa ya san halin da Abubakar yake ciki kuma ko a garin gaɓa-gaɓa babu wanda zai damƙa masa kujerar sarauta, ina ya san kansa ma balle ya san matsalolin talakawa? Sai da ta ƙara rissinawa ta furta. "Tuba nake ranki shi daɗe, In shaa Allahu Allah zai ba shi lafiya." Fulani babba ta amsa mata sannan ta wuce cikin sashenta. Ganin har zuwa dare babu wani saƙo ya sa Fulani babba ta ɗan fara sakin zuciyarta, har ta zauna su Khadija na soko mata hira wani ta amsa musu wani kuma ta yi musu shiru. Suna cikin wannan yanayin Jakadiya ta iso da kiran da Maimartaba yake yi mata. Take ƙirjinta ya buga dum! Zuciyarta kamar za ta yi tsalle ta fito daga ƙirjinta, da ƙyar ta tattaro jarumtar haɗa kalmomin da ta iya furta wa Jakadiya. A gurguje ta watsa ruwa ta ɗan gyara jikinta, don saboda yadda lalurar fitsarin da yi mata kamun kazar kuku har ji take haka kawai kamar zarni na tashi a jikinta. Da kwalliyarta fes ta ƙarasa turakar Mai martaba ƙamshi na tashi, haka kawai wani lokacin yake jin kamar yana tauye haƙƙinta ko yana yi mata ba daidai ba, musamman yadda ya ga ta fige ta lalace kamar ba ita ba. "Barka da hutawa Sarkina." Kalamanta ya ji na sauka a kunnuwansa, wani ɗaci ya ziyarci zuciyarsa kamar wanda ya haɗiyi maɗaci. "Barka!" Daga haka shiru ya biyo baya, ganin yanayin tarbar da Mai martaba ya yi mata ya sa jikinta ya yi sanyi. Cikin sanyin murya ta furta. "Allah ya taimake ka na ji saƙon kana son ganina." "Wani hukunci muka yanke da muke ganin shi ne mafi alfanu babu cuta babu cutarwa." Mai martaba ya faɗa fuska a haɗe kamar dafaffan kwanannan kunun tsamiya. Ƙirjinta ya hau dakan lugude, gumi ya fara keto mata ta ko ina. "Don haka ba ma buƙatar jayayya. Abubakar Sadiq zai koma ɗaya daga cikin ɗakunan gidan ajiya da gyaran hali, na sa a ware masa ɗaki guda wanda zai zauna a ciki, idan ya so duk wani abu da yake buƙata a aiwatar masa a can. Mun yanke wannan hukuncin ne domin sama wa lafiyayyun gidan nan mafita, idan yau ya nemi nasaka wannan jibi wancan watarana ina tunanin kaina zai dawo." Kafin dirar kalaman Takawa tuni hawaye ya gama wanke fuskarta. Cikin kuka ta zube a ƙasa hannuwanta biyu a saman cinyarsa ta furta. "Don Allah kada ka yi mini haka ranka shi daɗe, Allah ya sani Abubakar ba shi kaɗai na haifa ba akwai yayyansa Khadija da Zainab amma wallahi babu wanda na ke jin ƙaunarsa har a cikin jinina kamarsa. Wannan ƙasƙanci ne a ce jininka zai ƙare rayuwa a gidan ajiya da gyaran hali saboda ya kasance mai nakasa, in dai a kan Ruƙayya ne na yi maka alƙawari ko inuwarsa ba za ta ƙara gani ba ballanta shi. Don Allah ka..." Cikin tsawa ya katse ta. "Ba mu san lokacin da raini ya gifta a tsakaninmu ba Fulani, da har ake neman yin jayayya da mu. Mu ba ƙananan mutane ba ne sanin kanki ne ba tun yau ba; ba ma taɓa magana biyu. Tashi ki ba mu wuri, wannan hukuncin ba zai tɓa canzawa ba." Fulani babba duk yadda ta so dakatar da hawayenta abin ya gagara, don haka ta fice daga turakar zuciyarta na tuƙuƙin ɓacin rai. Tana shiga ɗaki ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ganin kukan na ta ba na ƙare ba ne ya sa su Khadija rungume ta suka fashe da matsanancin kuka! Yau ita ce rana ta farko da ta ji zama a cikin gidan ya gama fita daga ranta, ta kuma ji wani abu ya tokare mata maƙoshi game da Fulani Umaima sai dai kuma a ɓangare ɗaya shakka da tsoronta ya hana zuciyarta sanar da ita gaskiyar abin da ke ranta. Sun jima ita da yaran a haka sannan ta miƙe ta nufi ɗakin Abubakar, ta same shi a kwance kamar yadda ta barci. Sai da ta share ƙwallah sannan fito daga ɗakin. Washegari tun safe Dogarawa suka cika umarnin Mai martaba, tun lokacin da aka fara jidar kayan Abubakar Fulani Babba take share hawaye don dai ba ta da yadda za ta yi. "Idan kika matsa mana da magana wallahi ranki zai yi mummunan ɓacin da ba ki taɓa gani ba Fatima." A razane ta dubi Mai martaba, yanayinsa kaɗai ya tabbatar mata babu alamar wasa a tattare da shi. Dole ƙanwar na ƙi ta zubar da makamanta, ta rungumi ƙaddarar da ta afka musu babu sallama. Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta tuna yadda suka kwashe da Takawa, a daren ranar da ta sake zuwa sashensa tana yi masa magiya a kan ya bar Abubakar ya ci gaba da zama a sashenta. Hawaye ya gangaro mata sakamakon ganin wata irin birgima da Abubakar ya fara yi a cikin jar ƙasar da ke ɗakin saboda ɗakunan kowannensu babu daɓe a ciki. Wata ƙasar ya ci wata kuma ya burtune jikinsa da ita, tana ji tana gani bayan ta gama kallonsa ta fice daga ɗakin. Abin ka da gidan masarauta take labarin kai Abubakar gidan yari ya gama zagaye gidan kowa da abin da yake tofawa, sai dai mafi yawa daga cikin shakkun Fulani Umaima ya hana su faɗar gaskiyar abin da yake cikin zuciyoyinsu. "Allah ya taimake ki ni fa don kada a ce na saki linzamin harshena amma Allah ya sani na fara ɗora zargi a kan Fulani Umaima. Lamarin zamantakewar da ke tsakaninki da Takawa akwai fa ayar tambaya." Jakadiya ta yi wa Fulani babba maganar tana yin ƙasa da murya. "Jakadiya tafi kanki tsaye ba mu fahimce ki ba." Jakadiya ta sake yin ƙasa da murya. "Bari na fito miki a mutum Fulani, an ya kuwa Fulani Umaima ba ta bi ta ƙarƙashin ƙasa a kan Takawa ba, duba da yadda take cin karen ta babu babbaka a gidan nan kamar wacce ta wanke masa hannu aka. Yanzu musakin yaron nan Bukari me ya yi da zai fuskanci zama a sashen gidan ajiya da gyaran hali." Jin haka ya sa hawaye ya zubo wa Fulani Babba. A fakaice Jakadiya ta saki murmushin cin nasara, don babban burinta ita ma bai wuce ta samu sanadin dandalar arziƙin da su Fulani suke ci ba a matsayinsu na matan Sarki. "Jakadiya al'amurana a yanzu haka na miƙa su a wurin Ubangiji, duk ma wanda ya nemi ya ƙuntata wa rayuwata Allah ba ya bacci yana sane da abin da yake faruwa." Jakadiya ta taɓe baki a fakaice. "Amma ya kamata ke ma ki tashi tsaye domin kin san da sanyin safiya ake kama fara." Fulani babba ta ɗan sauya fuska don haka kawai ta ji ba ta aminta da waɗannan shawarwarin na Jakadiya ba. "Ni fa hatta ciwon yaron nan wallahi na jima da ɗora zargina a kan Umaima, saboda Allah yaro shi ba aljanu ba amma an mayar da shi wani iri. Kwanaki fa har barbaɗe na ga tana yi a turakar Mai martaba wai don ya daina jin ɗanɗanonki." A ɗan razane Fulani babba ta dubi Jakadiya sai kuma ta haɗe fuska. "Jakadiya muna buƙatar hutawa a ba mu wuri." Ganin babu fuska ya sa Jakadiya ta fice tana wurgawa Fulani babba mugun kallo. "Sakarai da ba ta gaji arziƙi ba kya ƙare a wahale cikin warin jiki da fitsari." Jadiya ta faɗa cikin jin haushin rashin samun nasara a kan Fulani Babba bayan ta fita waje. Wacce ta shirya biyan kuɗin karatun ci gaban littafin *SHU'UMAR MASARAUTA* Ƙofa buɗe take, za ta iya turowa ta wannan Acc ɗin da ke ƙasa domin free pages na gab da ƙarewa. Waɗanda suka fara biya su min afuwa zuwa lokacin da zan buɗe group bayan na kammala free pages. *Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* [10/4, 11:49 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye. *Masu ƙorafe-ƙorafe ta pc da groups zan rage 100 daga yau zuwa ranar da zan gama free pages. Free pages za su ƙare a page a 10 daga yanzu zuwa ranar duk mai son karanta littafin za ta turo 400* SHAFI NA TAKWAS RIGAR ARƊO A gajiye tuɓus suka dawo gida sakamakon yawon kiwon da suka je cikin dokar daji, zamansu babu wuya wata farar dattijuwa ta ɗauko ƙorai guda biyu sai da ta fara zuba nono a cikinsu ta miƙa wa mai gidanta Baffajo. Ta jima a tsugunne tana jiran ya karɓa tana ɗagowa ta lura da yadda ya dulmiya cikin kogin tunani, a sanyaye ta kai hannu ta taɓa shi. "Yanzu Baffajo ba za ka daina wannan tunanin ba? Idan kai kana yi ni kuma sai ƙaƙa?" Ajiyar zuciya ya sauke. "Inna wuro aradun Allah lamarin yaron nan ƙara ci mini tuwo a ƙwarya yake, yanzu a ce ɗan mutum ba shi da abokan rayuwa sai gidan tururuwa da dokar daji? An ya Inna wuro ba za mu kai Kamalu wurin Malamijon farar riga ba?" Inna wuro ta yi jim cike da damuwa sanna ta furta, "Eh to hakan ma wani abu ne amma ni sai na ga kamar har da sabon shiga dawa..." "Kayya mu ba a dawa muka yi rayuwa tun daga ƙuruciya ba? Kin manta a lokacin baya tsakiyar dare nake tsintoshi a bayan rumfar can wurin shurin da ke gabas da shi." Kamalu ya ɗago fuska a haɗe don jin abin da Iyayensa suke furtawa, motsa baki yake kamar wanda zai yi magana, amma sai ya gimtse ya kawar da kai gefe. "Kamalu kai fa ba yaro ba ne a ƙalla shekarunka sun haure goma, mahaifinku girma ya kama shi ba ka ganin sauran 'yan uwanka ba haka suke ba." Kamalu ya sunkuyar da kai ƙasa ba tare da ya kalle su ba, A'iru da ke gefe ta furta. "Kwarankwasa dubu rannan har gani na yi yana ɗibar wani abu a kan gidan tururuwa yana sha, dubi wancan zobe." A'iru ta yi maganar tana nuna hannun Kamalu mai ɗauke da wani zoben azurfa mai ɗauke da wani irin zane. "Da bakinsa ya ce mini tsintarsa ya yi a kan shuri wai gadon Masarautarsu ne." A razane su Inna wuro suka dube shi, Baffajo ya ce. "Kamalu wa ya ba ka wannan zoben?" "Tsintarsa na yi." Kamalu ya furta kai tsaye ba tare da ɗago ya kalle su ba. Haushi ya fara kama Baffajo don haka ya ce, "Kai Kamalu hai ka shiga taitayinka, ba ka san dawa ba ko?" Kafin Kamalu ta ya ba shi amsa daga sama suka fara jin gudun dawakai da iface-ifacen mutane, kafin su yi wani yunƙuri tuni waɗansu Dogarai da sojojin masarauta suka farmusu cikin shammata suka riƙa taɗe su suna ɗaure su da wasu murtuka-murtukan igiyoyi a jikin manyan itatuwa. Lokaci ɗaya garin ya hautsine ban da ƙura babu abin da yake tashi, waɗanda suke da rabon tsira tuni suka shuɗa daji. Waɗanda aka riga da aka rubuta zanen ƙaddararsu kuma tuni aka damƙe su, a cikin waɗanda suka tsira har da Salele ɗan gida Baffajo. Shi kuwa Kamalu ko da ya ga abin da yake faruwa ko gezau bai yi ba, yana nan zaune wani Dogari ya isa gare shi ya fisgo shi da niyyar taɗe shi, ɗayan hannun nasa ya sa ya bigi gefen hannun Dogari, wata irin azaba ya ji tamkar an zuba masa ruwan dalma. Da kansa ya ƙarasa wurin wasu Dogarawa da ke tsaitsaye suna ɗaure ragowar mutanen da aka kama wanda ko tantama babu sun riga da sun zama bayi. Sai da aka ɗaure Baffajo da waɗansu mutane biyu sannan aka ɗaure Kamalu, a ɓangaren mata kuma tuni aka ɗaure Inna wuro da sauran mutanen da ke cikin rigar. Kafin wani lokaci rigar ta yi fayau sai kukan dabbobi da ƙananan tsuntsaye da ke tashi. ƘAUYEN GANGARE Jiki a matuƙar sanyaye suka ƙarasa cikin ƙauyen gangare hannun Mai gado ɗauke da jaririya, tun daga ƙofar gari aka fara jefa musu tambayoyin inda suka samu jaririya sabuwar haihuwa. Sai dai amsa ɗaya suke bayarwa tsintarta suka yi a cikin gona, da haka suka samu suka ƙarasa gida. Da zuwansu babu jimawa gidansu ya cika maƙil da mutane, wasu na taya su murna ya yin da wasu suka fara tsegungumi da ƙananan maganganu. Wani tunani Umaru ya yi take ya sa Mai gado ta ɗauki jaririya har ta ɗora ruwan da za ta yi mata wanka ya dakatar da ita kai tsaye suka wuce gabaɗaya wurin Mai gari. Umaru yana zuwa fadar Mai gari ya zube ya kwashi gaisuwa sannan ya gabatar da jaririyar hannunsu da mahaifiyarta ta yi mata laƙabi da Jawahir, bayan ya tsahirta ya karɓe ta daga hannun Mai gado ya miƙa wa Mai gari, sanƙira yana raɓe a gefensa. Tun da aka ɗago jaririyar Malam Malmo ya zura mata idanu ko ƙiftawa ba ya ni, wannan ya haddasa fargaba da tashin hankali a zuciyoyin Mai gado da Umaru, sakamakon sanin Malam Malmo sarai da mugun aikinsa. A sakaye Umaru ya ɗan yi gyaran murya ya furta. "Allah shi ba ka yawan rai yanzu haka Mai gado ta ɗora mata ruwan wankan da za a yi mata wanka da shi." Mai gari ya jinjina kai tare da yi musu nasiha a kan su riƙe ta da riƙon amana. Su Umaru har sun miƙe bayan mutane sun watse yana waigawa ya ga Malam Malmo yana yi wa Mai gari raɗa a kunne, haka kawai ya ji zuciyarsa ba ta aminta da wannan raɗar da yake yi wa Mai gari ba. Tsawar da sanƙira ya yi masa ce ta sa shi zura takalman fatarsa ya yi gaba jiki a sanyaye kamar kazar da aka watsawa gishiri. "Mai gado ina tsoron Malam Malmo a kan yarinyar nan kada fa a ce ya gano wani al'amari game da ita." Umaru ya faɗa bayan Mai gado ta yi wa Jawahir wanka tana shafe mata jiki da mai. "Ni kaina ina tsoro amma In shaa Allah babu abin da zai faru sai alkhairi." Wannan ƙawarin gwiwar da ya samu daga wurin Mai gado ya sa ya tashi ya fita don tatso wa Jawahir nonon akuyar da za a shayar da ita. Sannu a hankali suka ci gaba da rainon ta, tun suna ɗari-ɗari da ita har suka saki jikinsu sakamakon babu wani abu da suke gani na ban tsoro a tattare da ita. A ɓangare ɗaya kuma wata irin soyayya suke nuna mata, ga shi sai ta wuni ba a ji kukanta ba idan ba yunwa take ji ba. Abu ɗaya ne ya fara damun Mai gado da yake faruwa da Jawahir cikin dare, duk lokacin da ta farka don ta ba ta nonon akuya da dare sai ta ga wani baƙin jini ya tsattsafo a goshinta, idan kamar bacci ya ɗauke ta har asuba ta yi, sai da ga goshin na ta ya yi ɗan duhu amma babu jinin a jiki, zuwa wayewar gari kuma sai ta nemi komai ta rasa jinin ya washe. Tun tana barin maganar a ranta har ta taɓa tashin Umaru ta sanar da shi, shi kansa ya yi mamaki amma gudun kada ƙilu ta ja bau! Ya ce su zuba wa sarautar Allan ido tun da ba ta kuka wataƙila abin ya mata ciwo. Kwanan Jawahir goma Mai gari ya aika a kira masa Umaru, tun da Umaru ya ji kiran Mai gari gabansa ya faɗi har sai da Mai gado ta ƙarfafa masa gwiwa sannan ya nufi gidan Mai gari cikin wasuwasi. Yana zuwa aka yi masa iso har cikin shagonsa da yake hutawa a soro, ganin Malam Malmo ya sake tsinka zuciyarsa. Dole ƙanwar na ƙi ya zuba wa fuskarsa murmushin yaƙe cike da girmamawa ya gaishe su. "Umaru ka sani a gaban Mai gari kake don haka muke son duk maganar da muka tambaye ka ta zama gaskiyarka za ka faɗa. Wace ce yarinyar da ka zo da ita kuma a ina ka same ta?" Malam Malmo ya jefa masa tambaya. "Allah ya baka yawan rai wallahi tsintarta muka yi..." "Idan tsintarta kuka yi ina mahaifiyarta? Ko kuna nufin jaririya ɗanyar haihuwa za ta kawo kanta ne?" Mai gari ya katse Umaru. Shiru Umaru ya yi yana tsoron kada ya ba da kai bori ya hau, yana cikin nazari ya tsinci kalaman Malam Malmo. "Sanin kanka ne Umaru duk yankin nan babu wanda ya kai ni sanin sirrin tsafi da sihiri, na bincika kuma na gano waɗansu bayanai tun ranar da na ɗora ƙwayar idona a kan yarinyar nan. A zahiri ne kuke ganinta ƙanƙanuwa amma a baɗini basarakiya ce, shu'uma ce kuma tana ɗauke da rikitattun al'amura. Ita ba kamar kowa ba ce dalilin da ya sa mahafiyarta ta yo gudun fanfalaki da ita kenan daga cikin danginta, mukuma a ɓangarenmu na masu aikin tsubbace-tsubbace wannan yarinyar ta kasance tamkar taki ce da ke farfaɗo da shukar da ke cikin gona. Ya zama wajibi ka mallaka mana ita domin cikar muradinmu, a zahiri Mai gari zai karɓi riƙonta ta koma gidansa da zama. A baɗini kuma zan aiwatar da aikin da za ta kasance a ƙarƙashin ikona. Sharaɗi na biyu ya zama dole ka nuna mini daidai wurin da gawar mahaifiyar yarinyar nan take, idan ba haka ba wallahi sai na shayar da kai ruwan mamaki." Gumin da ya shiga keto wa Umaru ne ya bankaɗa sirrin da ke cikin zuciyarsa, cikin matsanancin tsoro ya ɗago jiki na rawa ya furta. "Duk abin da kuka buƙata haka za a yi ranka shi daɗe, da kai da kaya duka mallakar wuya ne." Malam Malmo ya saki murmushi cikin jin daɗi don ya ga tsoro malale a saman fuskar Umaru don haka ya furta. "Ba zan barka haka ba Umaru dole za mu aiwatar maka da naka tukwici mai tsoka." Umaru ya saki murmushin yaƙe yana godiya, sannan Mai gari ya sallame shi. Kamar zai tashi sama haka ya ƙarasa gidan yana alla-alla ya ɗauko Jawahir ya kai musu ko ya yarda ƙwallon magwaro ya huta da ƙuda. Masarautar Huddam A ranar da aka kai Abubakar ɗakin da ke ɓangaren gidan ajiya da gyaran hali ko runtse Fulani babba ba ta runtse ba, baƙinciki da ɓacin rai ya mamaye zuciyarta. Sai gabannin asuba sannan ta samu hawaye ya zubo mata, zuciyarta cunkushe da ɓacin rai. Wani abu da ya so ɗaure mata kai ganin ta wayi gari lafiya ƙamas babu fitsari a shimfiɗarta, ba ta ankara da haka ba sai da aka kira sallar asuba da za ta yi wanka kamar yadda ta saba duk asuba sai ta wanke fitsarin jikinta. Amma wannan ranar da ta kwana idonta biyu sai ta ga babu komai a jiki, mamaki cike da zuciyarta ta yi alwala bayan ta gabatar da sallah a gurguje ta nufi sashen da Abubakar yake kwance ɗauke da kayan sawar da za ta sake masa kamar yadda ta saba tsaftace shi. "Waye nan?" Aka furta mata cike da tsawa a lokacin da ta ƙarasa jikin babban ƙauren ƙofar. Baƙin ciki ya kama ta jin ƙasƙantaccan bawa na buga mata tsawa, da ace a sashen ta yake babu wanda ya... "Ina magana waye nan?" Kamalan Dogarin suka katse mata tunani. Sai da ta sauke ajiyar zuciya ta furta. "Fulani ce na zo wurin Abubakar." Cikin girmamawa Dogarawan suka zube. "A gafarce mu uwar gijiyarmu, muna neman afuwar saƙon da zai fito daga bakunanmu." Zuciyar Fulani ta fara azalzala kamar za ta hudo ƙirjinta, fargabarta ɗaya kada su ce mata wani abu game da Abubakar. "Allah ya taimake ki, ki yafe mu amma Takawa ya ja kunne da kada a sake buɗe ƙofar nan har sai hantsi ya ɗaga wurin ƙarfe tara." Da sauri ta dube su. "Yaushe ya bada wannan umarnin?" "Ranki shi daɗe jiya da dare." Sai da ta haɗiyi yawu mai ɗaci sannan ta miƙa musu kayan hannunta da akushin abincin da ta taho da shi. "A gyara Abubakar da shi a tabbatar da an yi masa wanka, wannan abincinsa ne." Jim suka yi sannan ɗaya daga cikinsu ya furta. "Allah ya taimake ki koda mun karɓi kayan nan sai lokacin da Takawa ya zartar za mu buɗe ƙofar, amma a gafarce ni ranki shi daɗe." Wani irin kukan takaici ne ya taso mata, gudun kada ta bar abin faɗa ya sa ta juya da sauri ba tare da ta amsa musu ba. Fulani babba na zuwa sashenta ta fashe da matsanancin kuka, tana tsaka da kuka ta ji Khadija mai kimanin shekara goma sha shida ta dafa kafaɗarta. "Ummi me ya sa kullin cikin kuka kike? Ummi kin san idanun masarautar yana ko ina a lungu da saƙo don Allah kada ki bari a samu a bin faɗe, komai ya yi tsanani maganinsa Allah kamar yadda na ji kina faɗa. Wuya ba ta kisa na san a kan Sadiq kike wannan kukan don Allah ki kwantar da hankalinki na tabbata babu abin da zai faru da shi." Khadija yarinya ce mai nutsuwa da sanin ya kamata, idan tana magana kamar babbar mace, a hankali ta goge wa mahaifiyarta hawaye ta ci gaba da tausarta har damuwar da take ciki ta yaye. Haka ta haƙurƙurtar da zuciyarta har lokacin da ya dace, sannan ta ɗauki kayan da kanta ita da Khadija suka nufi wurin Abubakar. Tun tasowar Abubakar ko da wasa Fulani ba ta taɓa yunƙurin ba wa wata baiwa hidimarsa ba, haka ta sawa ranta har zuwar ƙarshen rayuwarta za ta ci gaba da kulawa da shi ba tare da ta sare ba. A lokacin da suka ƙarasa ɗakin duk da kasancar safiya ce ƙudaje ne suka fara yi musu maraba, a kwance suka same shi kamar yadda Fulani ta bar shi da dare sai dai ya fitsari da kasaye duka kayan jikinsa. Ƙudajen da ke kai-kawo a kansa yake ɗaga kai yana cafko duk wanda ya zo hannunsa ya kai bakinsa ya cinye. A fakaice Khadija ta share hawayenta, sannan suka gyara masa jikinsa. Khadija ta kira Baiwa Salamatu ta damƙa mata kayan Abubakar don a wanke su, sannu a hankali Fulani babba take ba shi abinci wani ya karɓa wani ya zubar bayan sun gama suka tashi suka rufo shi suka fito daga sashen zuciyoyinsu babu daɗi. Tsaye take hannunta ɗauke da wata irin sharɓeɓen tsafaffiyar takobin da Boka Bamaguje ya bata don kare kanta da shi, ta hango ƙurar ɗan matashin yaron ya tunkaro ta da bai fi sa'an Muhsin ɗin ta a shekaru ba, duk yadda ta so hana shi shiga cikin ƙofar Masarautar Huddan sai abu ya gagara. Ganin haka ya sa ta zaburo da sauri kafin ta aiwatar da abin da yake ranta ya sa hannuwansa biyu ya mauje ta, ta faɗi ƙasa warwasa. Ɗagowar da za ta yi ta hangi Baiwa Maimuna a bayansa tana sakar mata murmushin mugunta, sai wata inuwa da ta gagara tantance wace ce ita. "Ban yafe miki abin da kika yi mini ba kuma sai na ɗauki fansa a kanki." Rufe bakin Baiwa Maimuna ta sa hannu ta fara jan Fulani Umaina a ƙasa kanta sai kurjewa yake jini na zuba, ko da ta hango Bamaguje yana tsaye a gefe yana kallonsu cikin magiya da tashin hankali ta fara roƙonsa. "Da kai kaɗai na dogara Bamaguje ka taimaka mini za su kashe ni." Wata irin mahaukaciyar dariya ta ga ya bushe da ita, ya juya mata baya ya fara tafiya yana faɗin. "Na riga na gaya miki kin yi sake wannan yaron ba kamar ɗan uwansa yake ba." Firgigit Fulani Umaima ta farka daga mummunan mafarkin da ta yi, a 'yan kwanakin nan ta rasa dalilin waɗannan miyagun mafarkai nata. Kusan kullin sai ta yi mafarkin wannan yaron yana barazana da rayuwarta. "Waye wannan da yake ƙoƙarin kutsowa cikin rayuwata har yake neman dagula lissafina?" Ta tambayi kanta ba tare da ta san amsar tambayarta ba. Ƙirjinta ya buga a lokacin da ta tuna jaririn da baiwa Maimuna ta fitar da shi yana nan a doron ƙasa, "Ƙarya ne ba shi ba ne! Ba zai taɓa razanar da ni ba." Fulani Umaima ta furta tana kai wa da kawowa. *Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* [10/4, 11:49 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye. *Masu ƙorafe-ƙorafe ta pc da groups zan rage 100 daga yau zuwa ranar da zan gama free pages. Free pages za su ƙare a page a 10 daga yanzu zuwa ranar duk mai son karanta littafin za ta turo 400* SHAFI NA TARA Ayarin dakarun masarautar da ke tafe da su Baffajo tafe suke cikin gajiya sakamakon doguwar tafiyar da suka yi, a farfajiyar wata bishiya suka yada zango suna hutawa sai bayan sun huta sannan suka ci gaba da tafiya, cikin zuciyarsu kowa da abin da yake ayyanawa. Ganin magriba ta fara dosowa ya sa suka yanke shawarar kwana a cikin dajin washegari da asuba sai su ɗora daga inda suke tsaya. Ƙauyen Gangare Ganin yanayin da Umaru ya koma gida da shi ya sa Mai gado shan jinin jikinta. "Mai gida ya kuka yi da Mai gari na ganka duk a sanyaye." Ƙasa ya yi da murya ya furta. "Ina yarinyar nan take? Zan kai ta gidan Mai gari" Kallon rashin yarda ta bi shi da shi ta sake gyara goyon Jawahir da ke bayanta. "Me za ta yi a gidan." Kamar zai yi kuka Umaru ya ce, "Malam Malmo Mai gado ban san ya za mu yi ba, sun buƙaci na mallaka wa Mai gari ita." Rass! Ta ji gabanta ya faɗi, sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta yi ƙasa da murya. "Ba zan iya rabuwa da Jawahir ba Mai gida, na san Malam Malmo sarai ba zai wuce tsubace-tsubbace zai yi da ita ba." Umaru ya waiga kamar wanda ake kallo duk a tsorace ya ce. "Ya zamu yi yanzu? Mene ne mafita?" Masarautar Huddam Wuni guda haka Fulani Umaima ta yi shi cikin rashin ƙwarin jiki, ba ta san dalili ba amma haka kawai za ta ji gabanta na faɗuwa. Har ta so dannewa ta ji zuciyarta na azalzala ba za ta iya jure rashin zuwa wurin Bamaguje ba. Tsufansa ya sake fitowa sosai don jiki da hannuwansa har karkarwa suke yi. "Ta zo duniya da ƙarfin iko, shi kuma yana gab da dawowa gidansu na gado." Bamaguje ya furta bayan ya gama sauraron ƙorafin Fulani Umaima. Ta ɗago a hargitse bakinta na rawa, ƙirjinta na dakan lugude. "Su waye? Kuma daga ina suke." "Garaje ga dami, daɗina da ke gaggawa Umaima. Na ɗauka za ki tambayi alaƙar shi da masarauta da ita kanta yarinyar." Ajiyar zuciya ta sauke. "Tamkar tagwaye haka suka kasance tsakaninta da Hidaya, sai dai waccan ruwan sanyi ce salam a kan wannan. Ban san a wanne muhalli zan tirke ta ba, abu ɗaya na sani ita ta kasance daga cikin wata irin zuri'a masu matuƙar hatsarin gaske. Na ga takobi a cikin jininta sannan wuta na gewaye sashenta, takaicina ɗaya Mahaifiyarta ta riga da ta binne duk wani al'amari da sirrin da ke ƙunshe a cikin rayuwarta. Daga ni har sauran matsafan duniya duk wani bincike da za mu yi ba za mu tantance takamaiman ainihin tushenta ba. Sai dai kuskure guda mahaifiyarta ta tafka wanda da shi kaɗai za mu iya cin galaba a kan wannan yarinyar." Cike da zumuɗi Fulani Umaima ta furta. "Mene ne shi? Duk wuya duk tsaninsa zan nemo shi..." "Bincike ya bayyana mini tana da matuƙar tasiri a rayuwarsa. Ina nufin jaririn da kika sa Maimuna ta fitar da shi shekara goma sha ɗaya baya, shi yake gab da shigowa gidan sarautarku. Sai dai kuma ita da shi za su kasance tamkar wuta da ruwa a fannin gaba, kowannensu ba zai ƙaunaci ɗan'uwansa ba. Shigarsa tamkar dasa nakiyar da ke tashin zamani da alƙaryarki ne, ba tun yau ba; na gaya miki shi ba kamar ɗan uwansa ba ne. Ruhinsa ɗauke yake da zaratan dakarun da ke sarrafa zuciya da tunaninsa, tun ranar haihuwarsa na fahimci zanen ƙaddararsa ya wanzu dalilin da ya sa na baki shawarar matse kunamar nan a cikin bakinsa, ashe tagwaye ne halwar tsafina ya gagara nuna mini. Tun yana jariri ya sauka a fadar Sarkin fararen aljanun doron ƙasa, da ke tsakiyar dajin Wuruju a daidai wurin da Baiwa Maimuna ta dire shi. Sun naɗa masa kambun da babu mai iya sauke shi sai mutum ɗaya wato wannan yarinyar." Bamaguje ya ƙarasa maganar yana haska wa Fulani Umaima inuwar wata yarinyar. Ta tsinci muryarsa ya ci gaba da faɗin. "Mu koma maganarmu ta baya na kuskuren da mahaifiyar Fargi ta tafka. Ta bar tauraron 'yarta a sake wanda duk wani matsafi kallo ɗaya ko bincike ɗaya idan ya yi a kanta zai fahimci muhimmancinta gare sa. Duk wanda ya mallaki ruhinta shi zai kasance mafi shahara a faɗin yankin nan a ɓangaren gawurtar tsafi da sihiri, runduna ce guda a tare da ita domin mahaifiyarta kafin ta mutu ta riga da ta juye mata nata jinin a jikinta." "Mene ne mafita, don ta ni gabaɗaya a mutu har liman a rasa mai jan sallah." Cewar Fulani Umaima da zuciyarta ta gama ƙeƙashewa. "A baya na fid da rai da samun wannan ɗaukakar, amma idan kin yadda me zai hana mu jefi tsuntau biyu da dutse ɗaya?" Mai Gado "Guduwa ita ce mafita, sai dai mu bar garin nan amma ka san muddin muna cikin ƙauyen nan Malmo ba zai bar mu da sauran numfashi ba." Shiru ya yi yana tunanin shawarar da ta kawo, ganin ya tsaya yana nazari ya sa Mai gado ta faɗa ɗaki ta ɗaura kayansu a cikin ɗankwali ta fito. "Allah ya sani na ɗauki aniyar kula da yarinyar nan, Malmo azzalumin mutum ne, na san halinsa sarai tun da ya ƙallafa rai a kan yarinyar nan ko mun damƙa musu ita sai sun hallaka mu don gudun tonuwar asirinsu." Mai gado ta faɗa tana miƙa wa Umaru ƙullin kayansu, sai da ya karɓa sannan ya furta. "Na gode wa Allah ya sa kika fahimtar da ni da tuni na sa mun yi tsalle mun afka cikin rijiya gaba dubu. Yanzu dai babu sauran lokaci mu bi ta ƙofar baya." Cikin sauri Mai gado da Umaru suka hankaɗe katangar karan da ke gewaye da gidan, kamar masu shirin tashi sama haka suka dinga sauri suna kutsawa ta ciki bishiyu duk da a lokacin magriba ta kawo kai. Sai da suka yi tafiya mai nisan gaske sannan suka ƙarasa wani ƙaramin gari a lokacin dare ya tsala sosai babu haske sai na farin wata, a gajiye suka zube a gefen ganuwar garin suna sauke ajiyar zuciya. Cike da galabaita Jawahir ta fara mutsu-mutsu sai a lokacin suka shiga damuwar abin da za su sama mata ta sha. Gorar ruwa Mai gado ta kunto ta ba ta sannan suka yi jigum-jigum, har sun zauna da sunan hutawa Umaru ya furta. "Mai gado an ya wurin nan yana da kyau kuwa? Me zai hana mu ƙarasa cikin garin nan mu nemi alfarma?" Mai gado ta yi murmushin takaici, "Duk in da za mu je matuƙar za su fahimci ba na shayar da yarinyar nan dole za su harbo jirginmu, kuma su ɗora mana zargi da tambayoyi a kanmu. Abin da muke gudu kuma ya faru ka ga an ƙi cin biri an ci dila." Umaru ya yi jum sannan ya furta. "Ina ganin mu ƙarasa bakin kasuwa mu kwana asubar fari sai mu bar garin, mu ɗora daga inda muka tsaya." Ta gamsu da shawararsa don haka suka yi gaba suna tambayar kasuwar garin har Allah ya datar da su, suna gab da shiga kasuwa suka ga wata mai fura da nono suka siya nono sannan suka ƙarasa. A bayan rumfunan kasuwar suka yada zango bayan sun take wa Jawahir cikinta da nono, babu jimawa baccin gajiya mai nauyi ya yi awon gaba da su. Sanyin asuba ne ya bige su suka farka don haka kamar marasa gaskiya suka sake nufar doguwar hanyar suka ci gaba da tafiya. Ba su yi tafiya mai nisa ba suka tsaya suka gabatar da sallah sannan suka ɗora daga inda suka tsaya. Sai da suka yi tafiya mai nisan gaske sannan suka tarad da wani ayarin mutane, yara, manya, maza da mata. Sai kuma Dogarawan da ke kai kawo a kansu, kallo ɗaya Umaru ya yi musu ya fahimci bayi ne aka kama. Da yake suna ɗan nesa da su da sauri Umaru ya ja hannun Mai gado ya furta, "Maza zo mu gudu idan Dogaran nan suka gan mu na tabbata kashinmu ya bushe don mun zama Bayi na har abada." Yana rufe baki suka juya da sauri. Cak! Suka tsaya cikin faɗuwar gaba, Mai gado ta riƙo hannun Umaru jiki na karkarwa. "Gidan uban wa za ku gudu?" Kalaman Sojan masarautar mai ƙirar samudawa ya ratsa su, gabaɗayansu aka rasa mai bakin magana. Ganin haka ya sa Dogarin tsula wa Umaru bulala a baya, cikin azaba ya hau susar baya yana faɗin. "Tuba nake ranka shi daɗe ba guduwa za mu yi don Allah ku yi mana rai." Da hannu Dogarin ya nuna musu hanyar da sauran mutanen da ke zaune a ƙasa suke, babu musu Mai gado da Umaru suka bi hanyar ba tare da sun furta komai ba. Tun da suka tunkari wurin mutanen wurin suka zuba musu na mujiya suna kallonsu. Bai san dalili ba haka kawai yake jin ƙirjinsa na bugawa, zuciyarsa kamar za ta yi tsalle ta hudo ƙirjinsa. Duk taku ɗaya da Mai gado take yi tana kusanto shi ji yake kamar ana ɗana wa zuciyarsa ruwan dalma, da wata irin ƙuda da wani surutai da ya gagare tantance harafi ɗaya ballantana ya yi wa kalaman nasu hisabi. Da yake hannunwansa biyu a ɗaure suke a jikin itace, kansa ya tura cikin ƙafafuwansa yana runtse ido. Bai yi aune ba ya fara jin sautin kukanta a tsakar kansa, yana yunƙurin buɗe idonsa kamar a mafarki ya ji an furta. "Ita daban ce don haka ta fito daga cikin wani irin ahali, tarayyarku alheri ce mai samar da taimakon juna a koyaushe. Sai dai zuciyoyinku za su gagara ba ku haɗin kan da za ku cimma manufarku ta alheri. " Firgigit ya ɗago kansa cikin mamaki, ba yau ce rana ta farko da ya fara jin waɗansu irin surutai a kansa ba. Amma na yau sun matuƙar dagula lissafinsa. "Wace ce ita?" Ya furta a fili. A daidai lokacin aka kama Umaru aka ɗaure ita kuma Mai gado aka kama ƙafarta ɗaya aka ɗaure, ta ci albarkacin jaririyar da ke bayanta. "Idan muka kama hanya a yanzu babu wani sauran hutu da za mu ƙara yi a hanya, domin mun kusa shiga cikin ƙasar Zazzau." Wani turɓunannan mutum ya furta fuskarsa a murtuke babu fara'a. A galabaice cikin yunwa, ƙishirwa da wahalar tafiya suka ɗauki hanyar da za ta sada su da ƙasar Huddam. Sai da suka yi tafiya ta kusan sa'o'i shida sannan suka ƙarasa cikin masarautar ta Huddam. A lokacin da suka je daidai ƙofar shiga Jawahir da ke a bayan Mai gado ta fara wata irin jijjiga idanuwanta suka fara yunƙurin kakkafewa, cike da tashin hankali Mai gado ta sauko ta, ganin halin da take ciki ya sa ta ƙwallah kururuwa cikin neman agaji. Da sauri Dogaran da ke wurin suka buga mata tsawa. "Hattara dai muna gab da shiga masarauta..." Ganin Jawahir na ci gaba da shiɗewa ga wani irin jini da ke tsiyaya daga hanci da kunnenta ya sa Mai gado ta furta. "Ku taimaka mini ɗiyata za ta mutu." A fusace wani Dogari ya ƙarasa da niyyar zubga mata bulalar da ke hannunsa, gannin halin da Jawahir ke ciki ya sanyaya jikinsa, yana shirin yayyafa mata ruwa suka ji gijif alamun faɗuwar abu. Suna waigawa suka hangi Kamalu ya faɗi ƙafarsa ɗaya na jijjiga, daga ƙugunsa zuwa tafin ƙafarsa take ya sauya launi zuwa jawur, jini ya fara zuba daga cikin kunnuwansa. Ganin haka ya sa Dogarawan suka sa aka ɗauke shi aka shiga da shi ciki, jiki a sanyaye Mai gado ta rufa musu baya hannunta rungume da Jawahir da har lokacin ba ta daina kakkafewa ba. Fulani Umaima Da yanayin damuwa ta dube shi, "Ban fahimci kalamanka ba Bamaguje." Bamaguje ya tattara nutsuwarsa wuri ɗaya ya furta. "A lokacin da nake ƙarami burin mahaifina kenan ya mallaki ruhin wannan yarinyar, sai dai kash binciken farko da ya yi ya bayyana masa lokacin da yarinyar za ta zo duniya ba ya raye. Ni kaina na yi tsammanin a farkon rayuwata za ta wanzu, amma sai ga shi sai da tsufa ya make gangar jikina. Ina son ko ba yanzu ba idan kun haɗu da yarinyar nan ki ribace ta har zuwa wannan tsibirin nawa. Domin ba za mu iya kamata da alƙaluman tsafi da sihiri ba, idan kika yi haka tamkar kin kawo ƙarshen rayuwar yaron da kika sa aka fitar da shi daga cikin masarautar ne. Wannan kaɗai za ki aiwatar mini sauran bayanan zan yi miki su daga baya." Fuska ɗauke da damuwa ta furta. "Ban santa ba ban taɓa ganinta ba ta yaya kake tunanin zan gane ta har na ribace ta na kawo maka ita?" Murmushi Bamaguje ya yi ya furta. "Daga shi har ita ba su kasance kamar kowa ba, kuma shigarsu cikin masarautarku zai ƙara tayar da rikitattun al'amuran da ke cikinta. Masarautarku shu'umar masarauta ce da ke raye a ƙarƙashin ikon waɗansu ɓoyayyun hallitu. Ko ban faɗa miki ba shurin da ke cikin turakar Takawa akwai dalilin wanzuwarsa, tun da kin san banza ba ta kai zomo kasuwa. Zan sake bincike game da wasu al'amuran ko za mu da ce a wannan karon." Bamaguje yana rufe baki ya watsa wani baƙin jini a cikin wata tukunyar ƙasa take wuta ta fara ci gangan-ganga, shiru ya yi yana nazartar abin da yake faruwa zuwa can ya saki wata irin dariya. Shiru Fulani Umaima ta yi tana kallonsa cike da ƙosawa. "Wani abin farinciki da ban za ta ba, kusan gabaɗayansu ruhinsu na da kusanci da juna..." Kalamasa suka katse sakamakon ganin wutar gabansa ta ɗauke yo kansa kamar za ta ƙone shi sai kuna ta ɗauke ɗif, bai so haka ba amma ko babu komai ya tsinci waɗansu abubuwa da za su ba shi narasa a game da yarinyar. "Ki sa ido sosai a wurin da kika binne jariran da kika taɓa binnewa a bayan ɗakin Sarki Abdul'aziz. Matuƙar kika ga an tone ta ba kowa ba ne face jininsa, ina nufin jininsa da kika fitar da shi. Idan har kika ga kan tinkiyar da kika rataye a ɗakinki wanda a kullin jini yake ɗiga a kan zanin kishiyarki ya fara tsutsa ta tabbata gabaɗaya su biyun suna da kusanci da ke, wato suna rayuwa a cikin masarutarku. Idan ba ki manta binciken da na yi miki a baya na gaya miki akwai wanzuwar rayuwar waɗansu ruhi masu ɗauke da rikitattun al'amura a cikin masarautarku waɗanda suke yunƙurin shiga al'amuran masarautarku. Lokacin ganawata da sarkin baƙaƙen aljanin ƙarƙashin ƙasa ya yi, zan ba shi aikin matar wani attajiri akan kishiyarta, ki ba ni wuri sai wani lokacin idan kin sake dawowa." Fulani Umaima guntun tsaki ta saki cike da takaici, ta yi masa bankwana ta koma ɗakinta. Lokacin da aka shigar da su Baffajo sashen Bayi aka wuce da su, kusan gabaɗaya jikinsu a sanyaye yake sakamakon ganin halin da Kamalu da Jawahir suke ciki don a tsammanin mutane da yawa mutuwa za su yi. A hankali Kamalu ya fara buɗe idanuwansa yana ganin mutane dishi-dishi, ajiyar zuciya ya sauke ya yunƙura da ƙyar; da sauri Baffajo ya ɗago shi yana zubda ƙwallah. Mutanen da ke wurin suke bi su da kallo cike da mamaki, Inna wuro ta share ƙwallah tana faɗin, "Na faɗa maka Kamalu ba zai mutu ba." Baffajo ya jinjina kai yana tallafo haɓarsa, "Amma har yanzu jikina yana ba ni za su iya halaka mini shi, wataƙila ba za su bar mana shi ba." Kamalu da ke zaune bai tanka musu komai ba sakamakon wata irin juwa da ke ɗibansa, waani dattijo tsoho ya gani a gabansa ya sakar masa murmushi tare da faɗin. "Muna ta ya ka murnar dawowa cikin ahalinka, ka tashi ka ƙarasa bakin rafin can ka ɗebi ruwan cikinsa ka ɗura a kunnenka, ka damƙi ƙasar cikinsa za mu yi maka iso har bayan turakar Mai martaba yanzu, aikin da za ka zartar sai kai domin abin salsala yake bi." Kamar wanda aka ƙara wa ƙarfi haka Kamalu ya miƙe daƙau, Dattijon ya kama hannunsa ya fara tafiya Baffajo da Inna wuro suna ƙwala masa kira, ko waiwayensu bai yi ballantana su saka ran zai tanka musu. *Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* [10/4, 11:50 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* *Masu ƙorafe-ƙorafe ta pc da groups zan rage 100 daga yau zuwa ranar da zan gama free pages. Free pages za su ƙare a page a 10 daga yanzu zuwa ranar duk mai son karanta littafin za ta turo 400* LAST FREE PAGES SHAFI NA GOMA *🤔WAI NA CE KINA DA WAƊANNAN MATSALOLIN AMMA KIKE ZAUNE DA TARUN TUNANI FAL KWANYA?* *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin* *5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14. Supplement na whitening/glowing skin* *15. Supplement for Acne, dark spots remover* *Da duk wasu nau'in supplement da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* Ba iya su Baffajo ba hatta sauran Bayin da ke wurin sai da suka rufa musu baya, sakamakon ganin wurin da Kamalu yake ƙoƙarin kai kansa. A tarihin masarautar babban kuskure zuwa rafin tsamiya da doshin magriba, hasali ma a ranar juma'a akwai abubuwa biyu da suka haramta ga mazauna cikin masarautar. Na farko, duk ranar juma'a haramun ne shan nonon shanu, awaki ko na raƙumi. Duk wanda ya yi gangancin karya wannan ƙa'idar kuma zai iya tsintar talatarsa a laraba, domin a labarin da yake yawo a cikin masarautar an ce shekara sama da ɗari an taɓa samun turka-turka tsakanin Sarkin da ke mulki da Bafulatanar Aljana kafin daga baya aka sasanta, amma wannan labarin kusan na kunne ya girmi kaka ne don babu wanda kai tsaye zai ce maka ga daga wurin wanda ainihin labarin ya fito. Shi kuma wannan rafin ana kiransa da rafin tsamiya sakamakon wata narkekiyar bishiyar tsamiya da ke girke a tsakiyar rafin, shi wannan rafin yana daga can gefen sashen bayi kuma rafi ne mai hatsarin gaske. Ba a taɓa ganin ya ci mutum ba, sai dai duk wanda ya yi gangancin shiga cikinsa ranar juma'a, zai fito lafiya ƙalau daga cikinsa amma a ranar za a neme shi sama ko ƙasa a rasa. Wasu daga cikin mutanen gidan masarautar sun ce faɗan Bafulatana ne ya shafi rafin yayin da wasu suka ce alƙwarin babban sarkin Aljanin ruwa ne yake cika dalilin wata yarjejeniya da ke tsakaninsa da Sarki Muhammad Safwan wato Kakan Sarki Abdul'aziz na uku. Sarki Muhammad Safwan ya yi mulki kafin hawan Sarki Abdul'aziz da shekara ɗari da biyar, har zuwa wannan lokacin babu tsayayyiyar wannan magana. Sai dai duk mazaunin cikin masarauta ya kwana da sanin masarautarsu ta sha bambam da sauran masarautun da ke wannan nahiyar musamman a kan al'amura masu rikitarwa da ban mamaki. Da sauri Baffajo ya sha gaban Kamalu cike da damuwa ya furta, "Kamalu hai ina za ka je ne, can ba ka ganin kududdufi ne?" Tsohon da ke riƙe da hannun Kamalu ya sakar masa murmushi haɗe da faɗin. "Tabbas sun kasance iyaye masu baka kulawa amma ka sani dakatarwarsu tamkar komawar cigabanka baya ne." Jin Kamalu ya yi shiru ya sa Inna wuro ta furta, "Kamalu ko wani abu yana damunka ne?" Girgiza kansa ya yi ya furta, "Inna wani ne ya ce na je cikin ƙoramar can." Ras! Gaban Inna wuro ya faɗi, tana shirin yin magana daga bayansu suka ji an furta. "Tun wuri ku kama ɗanku idan ba haka ba wallahi matuƙar ya shiga cikin wancan rafin a yau sai dai nan gaba ki haifi wani." Uwar Bayi ta yi maganar cikin halin ko-in-kula. Take jikinsu ya ɗauki karkarwa, Kamalu na kai dubansa wurin tsohon ya ga ya tsuke fuska rai a ɓace ya furta. "Kai ba kamar kowa ba ne, jininka yana da bambamci da nasu don haka ba koma ne za ka riƙa bankaɗa musu sirrinka ba." Yana gama faɗar haka ya ɓace masa. A lokacin tuni Baffajo sun riƙe hannuwansa bibbiyu sun koma da shi cike da tsoro. Komawarsa babu jimawa Jawahir ta farfaɗo tana yin wata irin shaƙuwa mai ƙarfi, duk wanda yake wurin sai da jikinsa ya yi sanyi ganin halin da ƙanƙanuwar yarinya take ciki. A hankali take sauke numfashi, Mai gado ta sa ruwa da ɗankwalin kanta ta goge mata jinin fuskarta. Buɗe baki ta fara yi alamar tana buƙatar abinci, a nan ne kuma hankalin mai yankan kaba ya koma ga rina domin Mai gado ta manta sam da batun nonon da za ta bai wa Jawahir. Cikin damuwa ta kalli wata Dattijuwa. "Baba don Allah ku taimaka mini ko da nonon akuya ne yarinyar nan shi nake bata." Kusan lokaci ɗaya suka kalli juna a firgice, Uwar soro ta ce. "Baiwar Allah sai dai kam ki bata wani abin ba nono ba domin yau juma'a kuma duk ranar juma'a ba a shan nono a gidan duk wanda ya sha ya dinga aman nono har a zare ransa." Mai gado na jin haka ta rushe da kuka, don ɗan kwanakin da ta yi da Jawahir ta shiga ranta sosai. "To ke me ya sa bakya ba ta nono?" Mai soron baƙi ta sake wurga mata tambaya." Mai gado har za ta fallasa alaƙar da ke tsakaninsu da Jawahir sai kuma ta tuna da kalaman mahaifiyarta a lokacin da ta haife ta. "Tun lokacin da na haife ta babu ruwan nono a jikina, kafin zuwanmu nan har magani mun nema amma a banza kare ya sha tsamiya." Waɗannan kalaman na Mai gado suka ƙara dasa tausayin Jawahir a zuciyoyin mutanen da ke wurin, "Bakin da Allah ya tsaga na tabbata ba zai hana shi abinci ba, akwai baiwa Zinaru da ke shayarwa mai zai hana a roƙi alfarmar yau ɗaya ta shayar da ita?" Uwar tuwo ta furta. Zuciyar Mai gado ta yi ƙal ta ƙarasa wurin Baiwa Zinaru da ke goyon ɗanta mai kimanin shekara guda. Take Zinaru ta amsa ba ta musa ba, sai dai tana ɗaukar Jawahir ɗanta da ke gefenta ya ƙanƙame mahaifiyarsa yana tsanyare wa da matsanancin kuka haɗe da cusa kansa cikin jikin mahaifiyarsa. A lokacin babu wanda ya kawo komai a ransa don a tunaninsu ma kishine irin na yara yake yi don ya ga an ɗauki wata yarinyar, kai tsaye Zinaru ta rungume Jawahir ta fara shayar da ita, wani irin zuuu! Zinaru ta ji tamkar wacce aka kafa wa shocking har tsakiyar kanta. Ga wata irin zuƙa da take ji Jawahir na yi kamar za ta fige maman jikinta, suna nan tsaitsaye ruwan nono ya fara dawo wa Jawahir ta hanci da kunnuwanta. Wannan yanayin da ta shiga ya sake faɗar da gaban mutanen wurin, cikin masifa Jakadiya ta fara magana. "Wannan wacce irin masifa aka kawo mana saboda Allah, yarinyar tun da aka kawo ku sai faɗar mana da gaba kike yi." Mai gado jiki a sabule ta karɓi Jawahir ta fita zuwa bakin wata bishiya ta zauna cikin sarewa ta fara zubar da ƙwallah. Jawahir ta jima a haka sannan nonon da ke fita daga jikinta ya dakata da zuba, ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta sake goge mata haɗe da saka ta a baya ta goya ta. A ranar kusan kwanan zaune mai gado ta yi cike da rashin sabo da zaman baƙunta, uwa-uba rashin kyakkayawan makwancin saɓanin wanda suka saɓa kwana a ciki. Cikin Dare. Wata doguwar hanyar ya bi samɓal yana tafiya wacce babu komai sai dogayan bishiyu, tsawo da girmansu ya haddasa wa wurin duhu mai ban tsoro. Daga bayansa ya ji kamar ana bibiyarsa don haka ya yi saurin waigawa cikin tsoro da tashin hankali, wata baƙar mage mai ratsin fari ya gani tana tafe tana shinshina sawunsa. Tun bai yi wayo ba yake ƙaunar kyanwa don haka ya tsugunna da niyyar kai hannu kanta, da sauri ya ji an fisge shi gefe waɗansu surutai na tashi sama-sama a cikin kunnuwansa. Waigawa ya yi bai sake ganinta ba, ya ci gaba da tafiya. A jikin wata murgujejiyar bishiyar kuka ya hangi wata rantsatstsiyar karaga, "Je ka ƙarasa kan karagarka." Ya ji an furta masa. Wani irin sanyi ya ji yana ratsa shi, jiki a sanyaye ya fara takawa da niyyar hawa kan shimfiɗar da ke ɗauke da karagar, ga mamakinsa sai ji ya yi wannan baƙar magen ta hankaɗa shi gefe ɗaya. Ta ɗora wani mulmulallan abu mai kama da ƙawai a kan karagar, sannan ta fara zagaye karagar cikin ƙasaita. A can ƙasa ya faɗi kansa ya bugu da wani farin dutse take jini ya fara ɗiga, dafa wurin ya yi cikin azaba sai gani ya yi magen ta ƙaraso tana lasar jinin da ke zuba daga goshinsa. Ta fara ɗaga kanta tana da alamar tana son kai wa kansa farmaki wurin da ragowar jinin yake ɗiga. Ganin ta dumfaro shi ya sa ya ci gaba da ja baya zuciyarsa na dakan luguje, ganin haka ya sa magen ta fara wata irin dariya fiƙoƙinta na zubowa ƙasa ɗaya bayan ɗaya. Duk wurin da fiƙar ta faɗa sai ƙasar wurin ta rufta har ta yi tsalle za ta damƙi saman goshinsa. Firgigit Kamalu ya tashi cikin matsanancin tsoro, firgici da tashin hankali. A lokacin dare ya tsala sosai, ban da munsharin mutanen ɗakin da kukan tsuntsaye babu abin da yake tashi. Jin abu na gangaro masa a goshi ya sa ya kai hannunsa ga mamakinsa ya ji ya taɓa abu, da sauri ya yunƙura zuwa wurin aci-balbal ɗin da ke kunne a gefen ɗakin ya haske. Rass! Gabansa ya faɗi, jikinsa ya ɗauki karkarwa kamar mazari. "Jini!" Ya furta a kiɗime. Yana shirin komawa ya tashi Baffajo ya sanar da shi abin da faru ya ji an dafa kafaɗarsa. "Wannan gidan ba irin kowanne gida ba ne, sai ka ɗaura ɗamarar juriya da jajircewa. Gadon gidanku ba a sansu da sarewa ba, ka zama jarumi mara tsoro a haka ne za ka ƙwaci kanka. Ka gode wa Allah da ba ta yi nasarar yagar naman jikinka ba, kuma kada ka ɗauka za ta haƙuri. Wannan daɗɗaɗiyar mummunar manufa ca tunkafin haihuwarka, zan yi takaici ƙwarai matuƙar ta yi nasara a kanka kamar yadda ta ci galaba a kan mahaifiyar..." Sam Kamalu baya fahimtar kalaman da farin dattijon ke gaya masa, cike da damuwa ya katse shi. "Don Allah wane ne kai? Ya aka yi ka san mafarkin da na yi?" Murmushi Dattijon ya yi, "Yaro man kaza! Da sannu za ka fahimci turbar da nake son ɗora ka, izza da ƙasaitar jinin Sarki Muhammad Safwan ba za ta tashi a banza ba. Ba ni zan bayyana wa duniya waye kai ba, izza da tasirin jinin sarautar da ke jikinka ne zai bayyana wane ne kai. Ni Aminin Kakankakanka ne, ina bibiyar al'amarinka saboda waɗansu muhimman abubuwa da tasirinsu. Ta so mu je ka wanke ciwonka a wancan rafin, idan gari ya waye kada ka sanar da kowa mummunan mafarkinka hatta Baffajo da Inna wuro, domin wannan gidan sarautar cike yake da idanu mabanbanta." Tamkar raƙumi da akaɗa haka Kamalu ya bi bayan tsohon yana gaba shi kuma yana biye da shi, lokacin da suka ƙarasa bakin rafin wani irin sanyi ne ya fara ratsa shi har sai da jikinsa ya ɗauki rawar ɗari. Kaf kaf kaf haƙoransa suka fara rawa, ga wata irin juwa da take ƙoƙarin fisgar shi ko ta halin ƙaƙa, ɗagowa ya yi a wahalce ya furta. "Ba zan iya ba, ba zan iya zuwa ba sanyi nake ji." Rufe bakin Kamalu sai dajjijon ya sa hannunsa a tsakiyar goshinsa, a hankali ya ji sanyin da yake ji yana raguwa, "Ba na jin daɗi a duk lokacin da ga karaya a ƙwayar idonka, daga yau kada na sake jin ka furta kalmar gazawa. Tabbas za ka iya domin duk tsawon lokacin da muka ɗauka lokacinka muke jira, mu je ka aiwatar da abin da yake gabanka." Dattijon ya faɗa yana kama hannun Kamalu ya sanya ƙafarsa ta dama a cikin rafin, wani irin zuuu! Ya ji har cikin kwanyarsa. Gabansa na faɗuwa ya tsugunna a ɗebi ruwan ya wanke ciwonsa kamar yadda tsohon yake ba shi umarni, yana gamawa ya sake ba shi umarnin wanke fuskarsa ya ɗura masa ruwan a cikin kunnuwansa. Ruwan ya gani ya fara kaɗawa a hankali, daga baya kuma ya ga igiyar ruwan tana katantanwa da su. Yana shirin guduwa tsohon ya riƙe shi tsam a jikinsa, ganin a kowanne lokaci yana iya halaka ya sa Kamalu runtse idonsa. Sannu a hankali ya ji komai yana lafawa, hakan ya sa shi buɗe idonsa suka fara takowa suka fito daga ciki. Wani irin sauti yake ji cikin sigar kururuwa da neman ɗauki, lokaci ɗaya ya ji zuciyarsa na fisgar gangar jikinsa. Tafiya yake yi ba tare da ya san wurin da yake jefa ƙafafuwansa ba har ya zagaya wurin da yake jin ƙarajin sautin na kusantarsa a bayan ɗakin Mai martaba. A saitin kusurwar yamma ya hangi wani mulmulallan abu baƙi saboda duhu bai tantance takamaiman mene ne ba. Cikin dakiya da ƙarfin zucuya ya sa ka hannu da niyyar tonowa take zoben hannunsa ya mamaye wurin da haske, a nan ya yi tozali da wani abu mai tsananin wari da siffar jarirai har sai da ya ji tamkar ya amayar da kayan cikinsa. Tsaki ya yi cike da jin haushin abin da ya aikata, shi kansa bai san dalilin da ya sa shi aikata haka ba, ya dai ji ba za iya haƙura ba har sai ya taimaki abin da yake cikin ƙarƙashin ƙasar. Koda ya koma sama da ƙasa ya nemi Dattijon ya rasa, a bakin ƙofar ɗakinsu ya hangi Baffajo yana kai wa da kawowa yana ganin Kamalu ya ƙarasa yana tambayarsa inda ya je. "Baffajo fitsari ne ya tashe ni, na ga kana bacci shi ya sa ban tashe ka ba." Ya tsinci kansa da ƙin faɗa wa Baffajo gaskiyar abin da ya faru. Riƙo hannunsa Baffajo ya yi tsam kamar wani zai ƙwace shi suka ƙarasa cikin ɗakin, ƙwallah ce ta ciko idanun Baffajo ya furta. "A wannan farautar da aka yi mana mun rasa Salele Kamalu yanzu haka ban san duniyar da ya nufa ba, don Allah kada ka yi yunƙurin abin da zai raba ni da kai, ka ga wancan rafin dai an ce hallaka mutane yake don Allah koda wasa kada na ga gilmawarka a wurin." Kamalu ya jinjina kai sannan ya koma ya kwanta cike da tausayin mahaifinsa. Tun da asubar fari aka tashi duka Bayin da ke sashen kamar yadda aka sunnanta musu, bayan sun idar da sallar asuba Uwar Bayi ta shiga raba wa sababbin Bayi aikin da za su gudanar, waɗanda suka san aikinsu kuwa suka ci gaba ɗorawa daga inda suka tsaya. Sai da rana ta fara fitowa sannan suka samu zarafin kai abinci cikin bakunansu, Mai gado ita da Inna wuro kusan ɗura suka yi wa kansu da sauran baƙin Bayin da aka kawo su rana ɗaya. Baiwa Fatsim na ganin yadda suke cin abinci ta saki shewa tana yi musu kallon sheƙeƙe ta furta. "Ahayye! Allah na dawo inji kishiyar mai yaji, duk wannan feleƙen da kuke yi gumi ce ba ta yi gumi ba. Amma da sannu za ku gane karatuna." Gabaɗaya babu wanda ya tanka musu, wata Dattijuwa da suka ji ana jira da Uwar tuwo ta ƙarasa wurin ta ce, "Tun wuri ku cire kawaici da kara ku fara ƙwatar wa kanku 'yanci idan ba haka ba kowa takaku zai yi kamar takalmin sawarsa. Wannan gidan yana da matuƙar bambamci da wuraren da kuka fito..." Sallamar Jakadiya ta katse ta, fuska a haɗe ta dube su ɗaya bayan ɗaya. "Zan ɗebi sababbin Bayi gabaɗayanku zan kai ku sashen Fulani Umaima tana son zaɓar waɗanda suka yi mata domin tana buƙatar ƙarin masu yi mata hidima." Jin babu wanda ya tanka mata ya sa ta buga musu tsawa, jiki na rawa duka suka miƙe sai Inna wuro da ke faman jera loma da sauri don ita idan tana cin abinci tana tashi duk daɗin abinci ba ta iya cinsa, ballantana a nan da abincin dare da suka ci ko kaɗan bai ishe su. Jakadiya ta leƙa ganin Inna wuro na zaune. "Ke ce shafaffiya da mai ba ki ji abin da na ce ba?" Baki na rawa Inna wuro ta sanar da ita uzurinta, ai kuwa lokaci ɗaya ta ji an kwashe mata da dariya. "Ke a tsammaninki tun da kika shigo masarautar nan kina da sauran ikon da kanki? Ko kin manta matsayinki na Baiwa ne? Idan ba ki sani ba ki sani a yadda kika a cikin gidan nan sai yadda aka yi da ke, idan aka so ki kwana a tsaye dole ki kwana, gara tun wuri ki yakicewa kanki ɗan guntun 'yancin da kike taƙama da shi." A sanyaye Inna wuro ta tashi, idanunta suka ciko da ƙwalla. A duniya babu abin da ta tsana sama da yarfi da tozartawa. Babu yadda suka iya haka suka bi bayan Jakadiya haka kawai Mai gado ta tsinci gabanta na matsanancin faɗuwa, tun da suka nufi sashen Fulani Umaima Jawahir ke wani irin mutsu-mutsu har zuwa lokacin da Jakadiya ta sa suka jeru ɗaya bayan ɗaya. A hankali ta fara bin Bayin tana duba su a wulaƙance cikin yarfi da ƙasƙantarwa. Tana zuwa daidai kan Mai gado gabanta ya yanke ya faɗi, ta dube ta a yamutse. "A sauko da wannan jaririyar." Ba musu Mai gado ta kunto Jawahir da jikinta ya yi wani irin sanyi kamar wacce aka ciro daga ƙanƙara. Sauke idanun Fulani Umaima a kan ƙwayar idon Jawahir ya haddasa mata matsananciyar faɗuwar gaba, kalaman Bamaguje suka faɗo mata. Ba ta sake tsinkewa da lamarin ba sai da ta yi tozali da goshinta. 😁😁 Yanzu ne za a fara buga wasan, Shin me yake shirin faruwa tsakanin Fulani Umaima da Jawahir. Wai ma wace ce Jawahir ɗin nan kuma mutum ce ko Aljan? Ina Dattijon nan kuma me ye alaƙarsa da Shu'umar Masarauta, wai ma me ye silar wannan abubuwan da ke faruwa? Akwai ɓoyayyan sirri mai ƙarfi da Dattijon nan ya sani mai ya sa bai aiwatar da komai ba sai da Kamalu ya zo. Wai shin Bayin Masarautar da shi Kansa Sarki Abdul'aziz za su gane shi ɗin jinin masarauta ne? Idan Fulani Umaima ta fahimta me kuke tunanin za ta aiwatar? Ina labarin Abubakar zai warke a nan gaba ko a'a?😢 Fulani babba tana warkewa daga cutar fitsari ko bata warkewa? Maza hanzarta kada ki bari a yi babu ke, salon labarin daban yake. Namu ba irin nasu ba ne💃🏼💃🏼💃🏼 na san ba ku manta da BAƘAR DAULA ko AN YA BAIWA CE da ZAUJATU JINNUL-ASHIQ ba. Kar ki bari a yi babu ke wannan kafcan.🥳🥳🥳💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼 *Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* [8/20, 7:22 PM] Ameera Adam🌚: *BAƘAR DAULA*       ©AMEERA ADAM FIRST CLASS WRITER'S ASSO...   Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️                   1      A duk lokacin da Allah (S.W.A) ya ƙaddara wanzuwar hallitar Ɗan adam a doran ƙasa, ko ya ƙi ko ya so akwai waɗansu abubuwa da suke yin jerin gwano a gangar jiki da ruhinsa. Inuwa! Wata aba ce da Ubangiji ya ke ƙaddara wanzuwarta manne a jikin kowanne abu, walau mai rai ko akasin haka. A kodayaushe tana bibiye da su matuƙar bawa zai zuba maganansa zai lura da haka. Kalmar ƙaddara! Kalma ce mai ɗauke da rassa biyu walau ƙaddara mai kyau ko kishiyarta. Ƙaddara abokiyar tagwaitakar inuwa ce domin bawa ba ya taɓa shallake wa ƙaddararsa, sanin haka ya sa na fahimci karin maganar Malam bahaushe ta: 'Tun ran gini tun ran zane." ta zauna ɗaram kwatankwacin yadda ake ɗora ƙwarya a gurbinta. 10/06/1022    Shekara Dubu Ɗaya baya.   Hankalinsa ya fi na kowanne lokaci kai wa matuƙar ƙolokuwar tashi, yana tafe yana taku da sandarsa Waziri da sauran muƙarraban cikin daular suna take masa baya. Tamkar waɗanda saƙon mutuwa ya dirar wa haka fuskokinsu suka fasalta saƙon da ke ƙunshe cikin birnin zuciyoyinsu. Sarki Damina yana kai ɗora ƙafarsa kan jan dutsen da ke a matsayin matattakalar benen hawa tsauni tsidik! Wani gajiyayyan talakansan ya  dira a gabansa cikin firgice da tashin hankali, kuka yake tamkar hawayen idanunsa za su ƙare. Ya ruƙo ƙafafuwan Sarki Damina a ɗimauce yana faɗin, "Ya kai babban Sarki, Sarkin sarkunan duniya bakiɗaya sarkin da yake share mana hawaye. Ka taimaka ka roƙar mana afuwa wurin Sarauniya Sha-kundum, yanzu haka ɗana Rabo yana can yana aman jini ta hanci ta baki don mai ɗakina naƙuda take jini ya ɓalle mata tana gangarar..." Tun bai rufe baki ba Sarki Damina ya daka masa razananniyar ƙarar da sai da hantar cikinsa ta kaɗa, yana shirin sake magana Sarki ya fisgi takobin da ke maƙale a kafaɗar Waziri kafin Bawan ya yi wani yunƙuri tuni ya sauke kansa ƙasa. Da sauri wasu ƙaratan Dogarai suka ƙarasa wurin suka zube suna yi wa Sarki godiya, "Godiya muke Sarki Damina mai masoya da yawa, Sarauniya Sha-kunduma ta yi ruƙo da hannayenka. Haushin zuciyarta ya gushe domin ta faɗa mana hanyar maganin samun lafiyar Yarima, idan wannan bai wadatar da kai ba ka yi mana umarni mu kawo maka wani ko da a cikin mu ne ka sake datse rayuwarsa matuƙar zai sanyaya zuciyarka" Bai tanka musu ba ya miƙa wa Waziri takobin da ke ɗigar da jini, har sun cicciɓi gawar bawan da kansa tuni ta samu mutsuguni a gefen wata bishiya, Sarki ya dube su yana cewa. "A gaggauta ƙone gangar jikinsa tare da yaron nasa da ba shi da lafiya. Ita kuma mai ɗakinsa a zaro jaririn cikinta a kai wa babban dodo sannan a salwantar da gangar jikinta" Yana gama magana ya haye kan tsibirin maƙarrabansa suna biye da shi a baya. Kamar yadda yake farillah a wurinsu duk lokacin da za su shiga cikin kogon dutsen a yanzu ma sai da suka aiwatar, sai da kowannensu ya saka ƙanƙanuwar aska ya yanki gefen ɗan yatsan hannunsa suka yarfar da jinin a jikin wani sassaƙaƙƙaen gunki, hannun gunki ɗauke yake da kwari da baka daga bayansa an jingina masa takobi a jiki. Kansa a sunkuye yake alamar ƙasƙantar da kai ga wani dungulmin kan mace da suka ɗora masa a gadon bayansa. Sarki Damina ne ya fara yin gaba sannan su Waziri suka rufa masa baya, daga bakin shiga dutsen suka tsaitsaya don sun san ko karan hauka ne ya cije su ba za su taɓa haure bakin ƙofar dutsen ba. Kai tsaye Sarki Damina ya kutsa ciki sandarsa ta zame masa abokiyar tafiya. Daga tsakiyar kogon dutsen ya hangi Boka Mai zamani zaune da wasu ƙanana tukwane a gabansa, daga shi sai ganyen ayaba wanda ya yi makari don rufe al'aurarsa. "Yau ba ranar zuwan ka ba ce kamar yadda yake a bisa al'ada, me yake tafe da kai don na tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa." Boka mai zamani ya faɗa yana karkatar da hankalinsa wurin Sarki Damina. Duk tsananin izza da taƙama irinta Sarki yau ya sauke ta a gefe ya fusakanci Boka yana mai bayyana damuwarsa, Sarki Damina ya zube gwiwowinsa kamar wanda ya aikata wani mummunan zunubin da yake neman gafara. Murya ɗauke da damuwa ya furta, "Ya kai Boka Mai zamani lamarin halin da talakawanmu suke ciki tabbas tura ta fara kai bango. A yau mun wayi gari da samun ɓillar annobar haɓo a cikin gari fiye da tsammani, babban abin da ya ɗugunzuma hankalina abin bai tsaya iya waje ba hatta ahalina na fuskantar wannan barazanar, a taimaka a roki Sarauniya Sha-kundum ta yafe mana tun da laifin wani ba ya taɓa shafar wani." Boka mai zamani ya miƙa masa busasshen hannunsa mai ɗauke da zaƙwa-zaƙwan farata, taurin hannunsa tamkar busasshen katako sannan ya ce, "Ina tukwicin ziyarar Sarauniya Gunki Sha-kundum kafin na san abin yi? Domin sanin kanka ne tuni bakin alƙami ya riga da ya bushe." Sai a lokacin Sarki Damina ya tuna da ƙoƙon tukwicin ziyara, cikin sake ƙanƙan da kai ya furta. "Sha-kundum ta dafa aikinka ta shiga lamuranka boka mai dogon zamani. Ka ga taka ka ga ta kakanninmu, iyayenmu duka sun wuce sun barka. Ya kai wannan boka mai dauwamamman ruhi da dogon zamani a yi mini afuwa bisa mantuwar da na yi, amma duk wani hukunci da Sha-kundum za ta yanke ni mai biyayya ne." Boka na gama jin haka ya miƙe ya tunkari bakin wata rijiya wacce faɗinta ya fi girman ƙaramin ɗakin, yana zuwa ya fara taka matattakalar da ke cikinta ya shige. Shigarsa ke da wuya bakin rijiyar ya shafe tamkar ba a taɓa wanzar da komai a wurin ba. Yana shiga kai tsaye ya tunkari gunkin wata mace da ke tsaye da tulelen tsohon ciki a jikinta, hannunta ɗaya tallafe da tsohon cikin ɗayan kuma yana riƙe da garkuwa alamun ta kare kanta da shi. Sai da ya sunkuya ya miƙa gaisuwa sannan ya furta, "Ya ke Sarauniya sha-kundum! Ya ke mammallakiyar wannan Daular a yau ma na sake dawowa da neman yafiyar al'ummarki.Na tabbata kina saurarena kamar yadda kika daɗe kina jina. Haƙiƙa talakawanki sun dawo da wata buƙata domin a yau sun wayi gari da samun annobar haɓo shin wane taimako za ki yi musu?" Hawayen ne ya ziraro daga cikin idanun gunkin, boka ya ƙarasa ya kanga kunnensa a jikin ƙirjinta. Ya jima a haka sannan ya ɗago cike da girmamawa ya ce, "Tabbas zan isar musu kamar yadda kika buƙata, ki ƙara haƙuri nan ba da jimawa ba za ki dawo cikin ainihin hallitarki ta zahiri. Za ki ci gaba da mulkar al'ummarki kamar yadda kika mulke su a ɗaruruwan shekarun da suka gabata. Komai ya zo ƙarshe tun da ke kika tabbatar min da haka, sarauta da izzar mulki na baibaye da rayuwarki. Taɓewa da hallaka tana ga Maharba da Mafarauta har ƙarshen rayuwarsa." Yana gama maganar ya juya jiki a sanyaye kamar kazar da aka jefa da gishiri, yana taka matattakalar bene ɗaya rijiyar ta fara dawowa kamar yadda take da farko a wurin. Kan shimfiɗarsa ta farko ya koma ya zauna ya dubi Sarki Balarabe yana faɗin, "Ta faru ta ƙare..." Da sauri Sarki ya katse shi da cewar, "Allah sa ba laifinmu ne ya sake hauhawa ba." "Ka buɗe kunnenka da kyau ka saurari abin da Sha-kundum ta gaya min game da ku." Boka mai zamani ya faɗa fuska babu walawa. Shiru Sarki ya yi yana sauraron Boka. "Tabbas Sarauniyarmu Sha-kundum ta sake dawo wa kamar yadda ta faɗa a lokacin da numfashin zai ɗauke..." Baki na rawa Sarki ya katse boka da cewar, "A ina aka wanzar da ruhinta? A wane yanki ne mu sa a kawo mana ita? Idan ta kai bangon duniya na rantse da hatsabibanci Sarauniya da izzar mulkina sai na sa an ɗaukota a faɗin duniya." Boka ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya har yana birgima a ƙasa tamkar jakin da yake birgima a cikin sahara. Sarki sai da ya fusata ya doki ƙasa da tafin hannunsa sannan Boka mai zamani ya koma kan buzunsa  ya furta, "Haba Sarki Damina ai duk gaggawar ungozoma ta bari a haihu, haka duk mai niyyar yin sammako ya bari duhun dare ya gifta. Sarki Damina a kwai gaggarumar matsala, kamar yadda duk faɗin garin nan babu wanda ya taɓa gani ko jin sautin Sarauniya Sha-kundum sai ni, to tabbas a wannan karon ko ni ba ni da masaniyar a ɓangaren da wannan sabuwar sarauniyar take. Babban abin baƙincikin ma waɗanda suka sulwantar mana da ruhinta a cikinsu halitar Saruniya ta sake wanzuwa..." Tun bai ƙarasa magana ba jikin Sarki Balarabe ya fara rawa kamar wanda ake kaɗa wa gangi, a fusace ya miƙe tsaye yana huci tamkar kumurcin macijin da ke tsaka da fusata. A fusace ya furta, "Boka mai zamani ka na nufin Sarauniyarmu ta ɓullo daga cikin zuri'ar maharba da mafarauta ne?" Boka ya jinjina kai yana faɗin, "Ba harsashe ba ne Damina domin Sha-kundum ta tabbatar mini kuma kai shaida ne bata taɓa yin ƙarya, ta ba ni muhimmin saƙo gare ku na farautar Maharba a ko ina suke a faɗin duniya. Sai dai babban tashin hankalin ta yi alƙawarin ba za ta sake magana ba har sai na sada da ta da ainihin ruhinta. A sanyaye Sarki Damina ya furta, "Tirƙashi! Ana dara ga dare ya yi. Bayan wannan ina tafe akan buƙatar Yarima Nomau, babban boka lamarin ciwon yaron nan a kullin ƙara ta'azzara yake. A da muna haɗa shi da ƴan mata ɗaya zuwa biyu a rana amma yanzu har ta kai ga mata biyu ba sa iya gamsar da shi, kafi kowa sanin shi kaɗai na mallaka kuma har abada ba zan sake haihuwa ba. Idan na tuna ba ni da magaji lamarin na sake ɗugunzuma hankalina." Boka mai zamani ya hura ƙasar gabansa nan take wata ƴar ƙorama ta bayyana a wurin, sai da ya barbada wani garin magani sannan ya zura hannunsa ya warasu haɗe da runtse idanunsa tare da fara karanta waɗansu irin ɗalasuman tsafi, ƙirjin Sarki Damina ban da bugawa babu abin da yake yi saboda fargabar abin da Boka zai sanar da shi. Boka mai zamani ya jima a haka sannan ya buɗe idonsa yana kallon Sarki Damina haɗe da furta, "A kodayaushe maganar ɗaya ce! Kamar yadda na sanar maka Yarima Nomau ba zai taɓa warkewa ba matuƙar bai sadu da da inuwar wannan macen da nake gani a tattare da shi ba. Tabbas zai warke sai dai bazan taɓa ce maka ga wa'adin lokacin da zai ɗauka cikin wannan tuburewar ba. Na ga haske jingine da su daga inuwar yarinyar nan na ga akwai rabo a tsakani, sai dai ka fi kowa sanin yadda aka yi aka samu Yarima Nomau don haka idan har ya samu rabo da wannan yarinyar Ɗa ko Ƴar da za su haifa dole zai zama mallakin Babban dodo ne, idan ba haka ba duk daren daɗewa za su zama masifa a daular nan. Kuma wannan hasken ba komai yake bayyana mini ba illa kusantowar warakarsa, don na lura akwai yuwuwar samun waraka nan ba da jima wa ba." Ajiyar zuciya Sarki ya yi don tun da yake zuwa wannan kogon bai taɓa jin labarin da ya faranta ransa kamar na wanan ranar ba  Ya dubi Boka fuska ɗauke da murmushi ya furta, "Ya kai babban malamin madogararmu shin zan iya sanin wacece yarinyar nan kuma a wane yanki take?" Boka Mai zamani ya girgiza kai yana cewa, "Lamarin Yarima Nomau ya wuce duk yadda kake tsammani, daga ni har bokayen duniya babu wanda yake da wannan amsar don haka ina mai baka shawara kar ka wahalar da gangar jiki da ruhinka akan abin da babu takamaimar amsa. Wani hanzari ba gudu ba, daga bayan wannan inuwar na hango wata baƙar ƙura wacce ta lulluɓe sarararin samaniya sai dai ni kaina ban fahimci wacce irin ƙura ba ce koma dai wacce iri ce ina fatan za ta zame mana alkairi." Sarki Damina ya miƙe ya fara zagaye cikin kogon dutsen sai da ya zagaye boka mai zamani sannan ya ce, "Wannan ba zai zame mana matsala ba domin mun dogara da Sarauniya Sha-kundum da babban dodo na tabbata su za su kawo mana waraka a rayuwa. Yanzu wanne irin magani ta ba mu wanda za mu aiwatar mu da al'umnarmu?" Boka mai zamani ya miƙe ya ƙarasa bakin rijiyar ya miƙa hannu ciki nan take ruwan cikinta ta kawo har sama sannan ya ɗebi ruwan da ƙoƙo ya miƙa wa Sarki Damina yana faɗin, "Wannan ruwan a je a zuba shi cikin kogon Ɗanbille duk wanda wannan annobar ta same shi ya ɗauka ya sha kai koda bata kama mutum ba zai iya wanka domin yin rigakafi. Wannan ce iya maganar da ta umarce ni na sanar da ku don haka za ka iya tafiya ya sarkin sarakunan duniya." Sanin ƙa'ida da dokar Sarauniya ya sa Sarki bai musa ba ya miƙe ba tare da ya furta koda kalma ɗaya ba, har ya je bakin ƙofa ya ji muryar Boka yana faɗin, "Ka da ka manta a kai wa Babban dodo Mai tsohon ciki biyu da idanun dattijai biyu." Gyaɗa kai kawai Sarki ya fice daga kogon dutsen. Garin Dabur    Daga cikin bukkar da nake kwance ina bacci na fara jin hayaniya sama-sama, ina yunƙuri tashin na ji muryar mahaifiyata ta karaɗe majiyar sautina da cewar, "Yau wacce baƙar rana muke gani da yammacin haka? Ya abar bauta kada ki yi fushi da wannan mummunan zunubin domin ba mu da sa hannu a ciki, ka hukunta masu wannan zunubin da gaggawa don sun cutar da ƴar tsintuwar da bata ji ba bata gani ba." Ihun da Kandala take jerawa ne ya sa ni fito wa saboda duk wanda ya ji kukan nata ya san ba na lafiya ba ne. Jikina ne ya ɗauki tsuma sakamakon ganin halin da take ciki kace-kace da jini, a gefe ɗaya mutane daga jinsin maza da mata sun yi carko-carko a kanta suna kallon halin da take ciki. A gabanta na tsugunna raina ya kai ƙololuwar ɓaci, na dube ta fuska babu walwala na furta "Waye ya yi miki haka Kadala?" Ilahirin jikinta rawa ya ke don haka na kama hannunta na haɗa su da nawa na sake furta, "Babu abin da zai faru da ke ki gaya min waye ya yi miki haka?" Cikin yanayin azaba ta furta, "Ban san sunansa ba amma na ji wasu suna ce masa Barde." Ban jira ragowar maganar ta ba saboda tun farkon ganin halin da take ciki shi ne mutum ba farko da ya fara faɗo min a rai, saboda sanin hali ya fi sanin kama. Barde riƙaƙƙen ɗan akuya ne baya iya kwana biyu ba tare da ya kusanci wala macen bil'adam ko dabba ba.  Ina miƙe wa na riski muryar Goga ya fara fito yana busa ƙaho wanda yake alamtawa sauran ƴan uwa na nesa da na kusa akwai fita ta gaggawa. Kafin ya gama busar da yake tuni gidanmu ya cika damƙam da sauran ƴan uwa maharba da mafarauta kowanne yana tafe cikin shirin dawa, ɗaya bayan ɗaya na kalle su kowannen su yana jiran umarnin da zan bayar. Jin na yi shiru ya sa Goje  ya ɗaga gorarsa sama da hannun ɗaya, ɗayan hannun mai riƙe da kwari da baka ya sauke ya fara zabga mini kirari. "Burugu ce da kanta ba aike ba mace mai kamar maza ko cikin maza sai an tona. Cau cau cau cau ƙurungu mugun kifi sa'a a dawa sa'a a cikin gari wani aiki sai jan wuya makutsa daji, a lafiya uwar gidan kere amanar kura kyaci da gashi. Dawa dai, dawa gidan maza tsanani yana dajin Gurɓu ku bar faɗa musu wahalar sanar da su daɗin maza na cikin dawa mata na gida suna yin girki, wuya a dajin gwiɓau wuya a dajin fatalaki wuya ta ƙare a kan Barde yau ya taɓo ajalinsa." Ilahirin jikina ban da rawa babu abin da yake yi saboda tsumin da ya tayar min har nake jin da ace Barde na gabana babu abin da zai hana ban tsarge ruhinsa gida biyu ba, duk da kowa ya san Barde a cikin garinmu ba kanwar lasa ba ne.   Da sauri na faɗa bukkarmu na ɗabo gurun damatsan hannuwana da wuya, na kunce fatar mesar da ke ɗaure a ƙuguna na ɗaura ta damisa sannan na ɗauko kwari da baka haɗe da zabgegiyar adda na fito wurin da su Goga suke tsaitsaye. Suna ganina suka yi yunƙurin saka kai a hanzarce na dakatar da cewar, "Wannan fitar ba taku ba ce saboda Barde gidanmu ya taɓo ba ku ba, na yi rantsuwa da abar bauta ba zan dawo gida ba sai na sauke kan Barde daga gangar jikinsa, weeeehuuuuhuuuuu sai ni sarauniyar baka jikar marigayi Baushe amanar kura kawanciyarka ka huta muna tafe idan dabbobi sun ƙare. Sai ni yaƙi ban san wasa ba Abar bauta ta buɗa mana matuƙar na saka kai ko yau ko yanzu ban san namiji ba sai na ga tabo a jikinsa, wahala a hanyar tugu wuya a hanyar badake wuya ko da magani babu daɗi ko ana ha maza ha mata sai na dawo da kan Barde a hannuna." Ina gama zabga kirari cikin haɗin baki tawagar da ke wurin suka furta, "Dawa dai Sarauniyar kwari da baka, Abar bauta ta buɗa miki a dajin Gurɓu." Har na saka kai zan fita na dawo wurin Mahaifiyata na russuna saitin kunnenta ina faɗin, "Ki roƙar mini abar bauta da ta rinjayi ɗayan ruhin kar ya ziyarce ni ina tsoron kada Barde ya yi nasara akaina." Cike da ƙwarin gwiwa ta furta min, "Sa'a dai Sarauniya abar bauta ta buɗa miki ɓoyayyan ruhi ba zai ƙara ziyartar ki ba." Ina gama sauraronta na fice daga cikin gidan cike da ƙwarin gwiwa na nufi wurin da na tabbatar Barde na zama da ƴan koronsa. Daular Sarki Damina.    Daga kogon boka mai zamani ya so kai ziyara bukkar babban dodo amma sai ya ga mafi dacewa ya fara zuwa wurin al'ummarsa ya umarci rundunar mayaƙansa da su fita yi masa farautar duk wata halitar bil'adam, musamman daga tsagin maharba da mafarauta kamar yadda suka saba yi a baya. A tsaitsaye suke dubbanin mutanen daular don a zatonsu maganin warakar annobar da ke damunsu aka kawo musu, Waziri ne ya yi gyaran murya sannan ya furta, "Ya ku waɗannan jama'a ya kamata kowa ya nutsu don jin saƙon da Sarauniya sha-kundum ta aiko." Tamkar ɗaukewar ruwan sama haka wurin ya yi tsit, Sarki Damina ya yi gyaran murya sannan ya dube su ɗaya bayan ɗaya  ya sanar da su duk yadda suka yi da boka Mai zamani sannan ya ɗora da cewa, "Ina umartar manyan mayaƙan dakarun daular nan da su hanzarta fita cikin gaggauwa don yi mana farautar bayi kamar yadda suka saba a baya, kuma su yi sani cewa ya zama wajibi su farmako mana La'anannun hallitar can ta maharba da mafarauta a ko ina suke a faɗin duniya. Wannan umarni ne daga Sarauniya sha-kundum idan ba haka ba bala'in da muka shiga da wanda muke ciki a yanzu shafar mai ne akan abin da zai faru da mu a gaba." Yana rufe baki zaratan dakarun mayaƙan suka fara fita a guje zuwa mahallansu kowanne na fito wa da manyan makamai, runduna guda suka yi tsaya a gaban sarki Damina. Sai da ya ƙare musu kallo sannan ya kasa su gida huɗu, manyan zaratan mayaƙan ya ce su bi gabas hanyar da za ta sada su da ƙasar Dabur. Runduna ta biyu ya ce su bi Yamma hanyar da za ta sada su da ƙasar Baƙasud, runduna ta uku ya ce su bi kudu hanyar da za ta sada su da ƙasar Mubali sai tawaga ta huɗu da ya umarce su da Arewa wacce za su isa da Ƙasar Surima. Lokaci ɗaya suka bazama a yunwace da farauto kowanne irin bil'adam kamar yadda Sarkin da yake mulkarsu ya ba su umarni. *KU MATSO KU TAHO*💃🏼 Wannan labarin salonsa na daban ne💃🏼 cike yake da sarƙaƙiya da tsananjn ban tausayi😰  ku dai kar ku bari a yi babu ku.🏂 Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN. Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne. Idan kin san kin sayi ɗaya daga cikin litattafan nan *AN YA BAIWA? KO DUBU JIKAR MAI CARBI KO ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* za ki biya 300 wannan ragin na waɗanda suka sayi wannan littafan nan ne kaɗai.💃🏼 Na ɗaga hannuwa riƙe da takobi da kwari da baka na salaƙe na sunkuyar da kai ina miƙa gaisuwa da kirari cau cau cau cau, sai ni Ameera 'yar Alhaji Adamu Amiriyan Mamanta, uwar Aslam da Ayman Amanar Oganta turmi sha daka 🥰 Wiiiiiiihuuuuuuhuuuu mace mai kamar maza ko cikin maza sai an duba domin wuya ake yi wa lissafi daɗi sai an jinkirta. Allah dai ya biya wuya a ƙofar Na'isa, wuya a ƙofar Kabuga wuya a ƙofar Nasarawa wuya a doka wuya, wuya a ƙofar kansakali mun buga a dajin Jemagu mun buga a dajin Falgore ko dajin Sambisa albarka. Sai ni ƴar Kanawan dabo amanar mutanen Rigana, idan ka ga matsoraci ko rago a Rugana baƙo ne domin jarumi ba'a nuna masa hanya, sa'a dai 'yar gaban goshin *FIRST CLASS WRITER'S* Amanar Marubuta La'ilaha'illahu. Sai ni ta hannun Matar Habibu ni ce dai ƙawar Mum Amnash amanar Masoyanta, cau cau cau cau makaranta ku matso ku ji wannan kafcan don idan kika bari aka yi babu ke an barki a baya. Domin duk wacce ta bari aka yi wannan tafiyar babu ita ta fita daga cikin jaruman mata masu aji.🌚 *Ummou Aslam Bint Adam*🌚 [8/20, 7:26 PM] Ameera Adam🌚: *BAƘAR DAULA*       ©AMEERA ADAM FIRST CLASS WRITER'S ASSO...   Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️                   2 Fita ta ke da wuya na ci karo da Mahaifina da ya sawo kai ciki kafaɗarsa maƙale da barewa da ingarman zaki, ganin yanayina ya tabbatarsa masa akwai wani abu da yake faruwa don ya san fitarsa ban yi da shi zan shiga dawa ba. Cike da ladabi na miƙa masa gaisuwa irin tamu ta maharba ina faɗin, "Dawa dai Sarkin sarakuna uban dawa ga tsini ga mashi, ina gwanin wani ga nawa gamji kake ka fi ƙarfin saran maƙiya ɗan butar uban nan. A lafiya garnaƙaƙi uƙubar Gabatarawa, Abar bauta ta buɗa maka ka ci gaba da maganin munafukan mafarauta, sha zamanka ka ci gaba da kai dabbobi ƙasa wallahi ko yau ko gobe ko baka nan muna yi maka yaƙi." Cikin jin daɗi Mahaifina ya jingina gorar hannunsa da tawa sannan ya furta, "Dawa dai Sarauniya Abar bauta ta buɗa miki ko dare ko rana a dokar daji. Cau cau cau amanar Baushe wata wuyar sai a tsakiyar tsaunin Mani." Ɗora kokarata na yi a wuya na saɓi hanya tare da furta, "Sa'a dai ruwan saman mai dukan basarake da faƙiri, shawarar Duba amanar Duna." Kai tsaye mazaunin Barde na tunkara da ke cikin ƙasurgumin dajin Gurɓu, duhun almuru har ya fara karaɗe gari don haka na ƙara ƙaimi domin na cin musu don ba na son Barde ya sake shaƙar doguwar iskar numfashi.  Ganin dajin na sake yi min nisa kuma ina gudun rasa Barde a yammacin, ya sa na lalubi ramin bushiya cikin nasara na fisgota da ƙarfi tsiya, ƴar ƙaramar aska na ciro ya tsaga bayanta sannan lalubi ganyan tunfafiya na murje a bayanta, na damƙi ƙayoyi na soka a tsakiyar kanta. Sai da na kalli kusurwa huɗu da ita a hannuna sannan na saita hanyar da za ta sada ta da mazaunin su Barde na dire ta a ƙasa tare da furta, "Bisa ga Barde amanar Lado, ko tsuntsu kika gani kar ki bar shi ya kubce."   Tun ban rufe baki ba ta zabura da matsanancin gudu sannan na rufa wa sawunta baya. A lokacin da na ƙarasa wurinsu tuni na riski zaren carbin rayuwarsu ya kusa tsinkewa, ilahirin jikinsu ƙayoyi ne kwatankwacin yadda suke lulluɓe a jikin bushiyar da na aika musu, ganina ya harzuƙa Barde ya dube ni cikin huci yana cewa, "Uwar dawa me ye haɗina da ke da za ki aikata min haka ina cikin shaƙatawata? Ba don ina ganin mutumcinki ba da tuni na roki Abar bauta ta la'anci ruhinki kamar yadda kullin muke yi wa Baƙar Daula wannan addu'ar..." Tun bai rufe baki ba na ƙarasa wurinsa haɗe da yi masa mahangurɓar da ta kusa gigita lissafin rayuwarsa, a fusace na sake kai masa duka a maƙoshi ina faɗin, "Barde yau akuyancinka ya kai ka wurin da ba za ka sake sanin wata ƴa mace ba sai a rayuwarka ta gaba idan ka na da rabo, ka roƙi Abar bauta da ta yafe maka zunubinka wataƙila ka samu sauyi a rayuwar da za ka dawo nan gaba." Wata sakaran dariya Barde ya saki sannan ya ce, "Wai kina nufin ƴar shilar da na latsa ta gidan ku ce? Ya aka yi haka bayan na san ke kaɗai kika wanzu a cikin gidanku?" Ban ba shi amsa ba sai wani mahaukacin duka da riƙa kai masa ta ko ina, ganin haka ya sa ya damƙi ƙasar gabansa haɗe da ɗaukan cinnaka ya ɗora a kai ya dunƙule su wuri ɗaya sannan ya ɗaga hannunsa sama ban yi aune ba na ji ya watso min ƙasar da ta rikiɗe zuwa jinsin cinnaku. Nan take muka fara sabon artabu kowanne yana son nuna ƙwarewarsa da ƙarfin jarumta da na tsatsuba, ganin hanyar da ya ɓullo da ita ba mai ɓille wa ba ce ya sa ya dube ni cikin hakki yana faɗin, "Kin cika zabuwa mai tsoro don na tabbata da ace ƙarfin damtse za mu gwada babu abin da zai hana ban yi nasara a kan ki ba, ya ke ƙasƙantacciya la'ananniya marar rabo, ya ke gajiyayyiya watsatssiya ƴar taka hayen maharba ba ƴat na koya ba. Wallahi ko giwa ta yi mushe ta fi ƙarfin bakin karnuka, dawa dai  dawa ga mazaje ba mata ba Aradu mai tarwatsa ƙananan la'anannu ni Barde kabari nake duk daren daɗewa ina sauraronka." Wata irin kuɗa na ji har tsakiyar kaina yayin da maganganun Barde suka fara amsa-amo a majiyar sautina, daga bayana na fara jiyo sautin haniniyar dawakai tare da ƙarar ƙarafa da miyagun makamai, sannu a hankali na waiga don ko kaɗan na ƙi jinin wannan yanayin da nake riskar rayuwata a ciki. A duk lokacin da wannan yanayin ya riske ni na kan gaza sarrafa gangar jiki da ruhina don na banzatar da abin da nake gani a zahiri ba tare da wanda nake mu'amala da su sun riski abin da nake tozali da shi ba. Kamar wacce guguwa take fisga haka na riƙa jin ana fisgar gangar jikin da ke jingine da ruhina zuwa ga mayaƙan da nake riska suna tunkaro ni gadan-gadan, a koyaushe ina jin baƙincikin yadda nake yaƙar ƴan uwana wato jinsin Maharba da Mafarauta waɗanda su ne nake ganin rundunarsu cikin ƙwayar idona. Ƙaddara wata abada ce da take sarƙe da gangar jiki da ruhi! Ni tawa ƙaddarar salonta mai tafiyar kura ne, ko a tarihi ban taɓa riskar makamanciyar irin tawa ƙaddarar ba.   Na fito daga cikin jinsin Maharba da Mafaruta, don haka na fi jin daɗin rayuwar cikin dabbobin daji akan mutane. Sai dai kash! Na tsinci ruhina a jikin wani gangar jikin da ba ta ahalina na Maharba ba, na rasa yadda aka yi nake iya rayuwa cikin jinsi biyu. Ko na aikata wani mummunan zunubin a rayuwata ta baya ban sani ba? Idan haka ne na cancanci hukunci irin wannan tun da gangar jikin da nake rayuwa da ita bata ji ba bata gani ba? Ban gama zayyana wa kaina jerun gwanon tambayoyin ba na hangi yadda suka zagaye ni tamkar yadda ale zagaye bakin rijiya, kamar yadda kullin nake ji a wannan karon haka gangar jikina ta riƙa ingiza ruhina ba don na so ba tafi da gudu na riƙa kai sara ina kare kaina. Da alama Barde mamakin abin da nake aikatawa yake don duk wanda yake tare da ni ba ya gani ko fuskantar abin da nake gani a maganaina. Ganin ya samu wannan damar ya sa ya biyo ta bayana a zabga min sara a kafaɗata, wanda fitar jini daga jikina ya haddasa wata irin gigitacciyar tsawa a dajin kamar yadda yake faruwa a duk lokacin da jini ya fita daga jikina. Abin sai ya haɗe min hagu da dama don na rasa wanne daga ciki zan kare duba da rundunar dake kawo min sara ga Barde da yake niyyar yin galaba a kaina. Ban yi aune ba wata irin juya ta fara katantawa da ni tun iya daga tsaye har na gagara mallakar kaina, wani saran na sake riska a gadon bayana wanda silar haka ya sa na durƙushe a wurin ga rundunar da ke gabana na son hallaka ni nan take. Daular Sarki Damina.    Bayan watsewar tawagar rundunar mayaƙan Sarki Damina, daga harabar wurin kai tsaye keɓaɓɓan gida ya nufa wurin da Yarima yake rayuwarsa a ciki. Gidan an keɓe shi ga Yarima kaɗai saboda gata da kulawar da ake bashi sakamakon mummunar larurar da yake fama da ita, idan kuka zauna kuna ma'amala da shi ba za ka taɓa tsammanin yana da wannan ciwon ba har sai ya motsa za ka tabbatar da haka. Tun daga bakin ƙofar gidan har zuwa ƙofar ɗakin Yarima Maza ne suke gadinsa sakamakon mummunar lalurar da yake tare da ita, wannan dalilin ya sa hatta masu yi masa hidima maza ne don gudun abin da kaje-ya-zo. Saboda kafin a farga da lulararsa a baya mata ne suke yi masa hidima wani abin mamaki duk ranar da aka wayi gari sai an samu gawarwakin ƴanmata waɗanda ya yi musu fyaɗe, waɗansu su galabaita gudun ƙarin wahala Sarki ya sa a ƙonne su ko a binne su da ransu. Ba wannan ne dalilin da ya sa Sarki Damina ya kwashe mata ya sa aka zuba masa maza ba, saboda duk wani abu da zai faranta ran Yarima shi ya ke so bai da mu ba ko da matan yankin za su ƙare. A lokaci wata jarabta ce ta same su matan daular suka daina haihuwar ƴaƴa mata sai maza, wannan ne ya fargar da Sarki Damina ya taka tsibirin Boka mai zamani ya tuntuɓe shi game da haka, nan take ya sanar masa da matuƙar Yarima zai ci gaba da salwantar da rayuwar ƙanana yara mata tabbas za su wayi da ƙarewar ƴaƴa mata a gabaɗaya yankin. Idan kuwa haka ta kasance Sha-kundum za ta yi fushi da su fushi mai tsanani. Wannan dalilin ya sa Sarki yake saka ake zaɓar cikakkun mata da ƴan matan da suka isa ake kaiwa Yarima duk lokacin da larurarsa ta motsa.   Shigar Sarki ɗakin ya tarar da Yarima na ta wani irin kakari tamkar wanda yake gargarar mutuwa, hakan ce take faruwa a duk lokacin da larurar Yarima ta tashi idan ka ga yana wannan halin sai ka rantse ba zai ƙara rayuwa ba. Cike da tausayawa Mahaifinsa ya ƙarasa gabansa yana zura masa ido, duk dakiya irinta Sarki Damina sai da ya zubda masa ƙwallah. A haukace Yarima ya cakumo Mahaifinsa cikin fitar hayyaci da ɗimauta yana yunƙurin haike masa, da sauri Sarki Damina ya fara yunƙurin ƙwatar kansa amma tsananin ƙarfi irin na Yarima ya sa ya kasa, a kan dole dogarawan da ke kewaye da ɗakin suka runƙuro suka taimaka wa Mai martaba. A wahalce Sarki ya ke sauke ajiyar zuciya sannan ya furta, "Ku ɗebo masa ƴan mata biyar don ba na son na rasa yarima, shi kaɗai na mallaka ko matan garin nan za su ƙare sai an nemo masa wasu a faɗin duniyar nan." Tun bai kai ga rufe baki ba wata gihitacciyar tsawa ta ratsa ciki da wajen ma'adanar sautinsu. A razane Yarima ya rungume mahaifinsa don wannan ita ce tsawa karo ta biyar da suka sake riskar irinta. A baya duk ranar da aka yi musu tsawa irin wannan lokaci ɗayamatan Daular suka riskar kansu cikin ɓallewar jinin Al'ada har tsofaffi waɗanda lokacin yin su ya gushe musu, a gaggauce ya fita don isa ga bukkar babban Dodo don ya sanar musu wannan tsawar da wacce irin masifa ta zo musu. A daidai ƙofar keɓantaccan gidan Yarima ya tsaya ya ɗaga kansa yana kallon sararin samaniya, kururuwar dattijuwar ce ta dawo da shi daga duniyar harsashen da yake yi. Waɗansu manyan barada ne riƙe da gashin wata mai tsohon ciki da alama naƙuda take jini na bin ƙafarta, ɗayan yana riƙe da wani matashin saurayi da fuskarsa ke fidda habbon jini daga hancinsa. Tsohuwar na riƙe da su ana jan su tare tana kururuwa da roƙon Dogaran akan kar su aiwatar da abin da Sarki ya umarce su, gyaran murya ya yi lokaci ɗaya Dogarawan suka tsaya cak kamar waɗanda suka haɗiyi taɓare nan take. Bawan da ke tsugunne a gabansa ne ya lura da inkiyar da Sarki ya yi don haka ya furta musu, "Sarki na buƙatar ganin ku a gabansa." A gaggauce suka ƙarasa gabansa bisa lura da yanayinsa suka fahimci ƙarin haske yake nema game da busasshiyar tsohuwar da take riƙe da mutanen da ya bayar da umarni a binne su. Wani narkeken Dogari mai ƙirar samudawa ne ya kwanta a gaban Sarki Damina, sai da ya lashi saman ƙafarsa sau bakwai sannan ya yi sujjada a gabansa yana faɗin.   "Abar bauta ta ja da zamanin adalin Sarki mai cikakken iko. Wannan tsohuwar mahaifiyar baiwarcen ce, muna ƙoƙarin cika umarninka ta nemi..." Bai ƙarasa maganarsa ba Sarki Damina ya ɗaga masa hannu tare da faɗin, "A kawo min ita." Tun Sarki bai gama maganar ba Tsohuwar ta yunƙura cikin tsananin firgici, ganyen da ke maƙale a ƙugunta wanda ya kasance shi ne tufafin da suke rufe al'aurar su, tuni ya samu matsuguni a ƙasa. Tun daga sama har ƙasa gudawa ce take bin ƙafafuwanta, jan ciki ta fara yi cike da tashin hankali da nadama tana cewa. "Ya Abar bauta ki yi gaggawar kawo min mafita daga wannan baƙin zalincin azzalumin bawan na ki." Da ƙarfin gaske Dogarin ya ƙarasa ya fisgi ƙafarta ɗaya wacce nan take ta yi ƙara ƙaras! Da alama ya karya ta ya fara ja bai dire ta ko ina ba sai a gaban Sarki Damina. Sandar da ke hannunsa ya saka ya dokare wuyanta nan take ta fara kakari sannan ya miƙa hannu zuwa idanunta, zaƙwa-zaƙwan faratansa ya saka ya zaro ƙwayar idanunta nan take ta ƙwalla wata gigitacciyar ƙara jini ya wanke fuskarta. A cikin wani ƙanƙanin ƙoƙo ya jefa ƙwayar idon sannan ya yi gaba, Fadawan da ke take masa baya ne suka bi shi sannan ya juyo ya ce, "Kada a binne ta a kaina ɗakin zuma ta ƙarasa tsokar jikinta." Daga haka kai tsaye ya wuce Bukkar babban dodo don lamarin tsawar da ta saba haddasa musu tashin hankali ba ƙaramin tsinka hantar cikinsa ta yi ba.    Tattakawa ya yi har ya shige gidan ƙasa wanda a nan ne bukkar babban dodo ta samu matsuguni, sai da ya yi sujjada sau bakwai a gaban bukkar sannan ya zura idanun tsohuwar a wata ƙanƙanuwar ƙoramar da ke gefen bukkar. Ta gefen tagar ya fara zayyane buƙatar da ke tafe da shi, sai da ya gama bayanin matsalolinsa daga cikin bukkar aka fara magana da wani irin yare cikin murya mai matuƙar ban tsoro. Ga wanda zuwansa ne na farko a lokacin da ya saurari muryar za ta iya kurumta sauraronsa, sai da aka yi yare sama da goma sannan aka fara maganar cikin harshen hausa.   "Tabbas jinin sarauniya Sha-kundum ne yake zuba a daidai wannan lokacin, hasalima rayuwarta tana cikin wani hali. Rasa rayuwarta a karo na biyu tamkar rushewar daular na ne gabaɗaya, na yi rantsuwa da tsabbun da na gada a wurin iyaye da kakannina matuƙar sakacinku ya sa kuka sake rasa Sha-kundum shakka babu kun rinƙa ganin masifu kala-kala kenan har ƙarshen rayuwarku." Hankalin Sarki Damuna ya fi na kowanne lokaci tashi, ga rabuwar shawarwari da ya samu daga wurin Boka mai zamani da babban dodo. Cikin damuwa ya furta, "Ya babban Dodo mai share mana hawaye kai ne mai ciyar da mu da shayar da mu a wane yanki wannan Sarauniya tamu take saboda na..." A tsawace aka furta, "Idan za ka zagaye faɗin duniya babu wanda zai tabbatar maka a nahiyar da take. Hasali ko da za ka yi tozali da ita ba za tantance fa ba sai dai alamu su nuna mana da isowarta ga mahaifarta, a kaf faɗin duniyar nan Boka Mai zamani ne kaɗai ya san kalar surar Sarauniya Sha-kundum kasamakon abin da ya faru a shekara ɗari biyar baya da suka shuɗe, kuma ko da ta ƙaraso daular nan ba na jin jinin da ta sake wanzuwa a ciki na Maharba da Mafarauta zai bar jinin daular nan ya yi tasiri a jikinta. Sarainiyarku ta sake wanzuwa a cikin jinsin Maharba da Mafarauta, haka kundin ƙaddarar yake don haka ba mu da damar ninke babin ƙaddararta. Game da lalurar matan Daular nan ka ɗauki Mahaifiyarka mai babbar turaka kai ta wurin Yarima ya mu'amalanceta ni nake gaya maka ciwonsa zai daɗe bai sake tashi ba kuma munanan al'amura za su jima ba su sake faruwa ba. Idan ya gama ka kawo min dattin al'aurarsu zan taimaka muku na yi wani aiki da shi amma idan na gama haɗa shi wajibinka ne ka sadu da Mahaifiyarka domin kammalar aikin bakiɗaya."   Ajiyar zuciya Sarki ya sauke sannan ya furta, "A duk lokacin da aka ambaci wannan jinsi na Maharba zuciyata da raina na matuƙar ɓaci, amma babu komai haka shafin ƙaddarar yake za mu karɓe shi hannu bibbiyu. Ya kai babban dodon mai azurta wannan daular ka yi sani ko jinin Mahaifiyata ka ce na bawa Yarima zan bashi matuƙar sarautar nan ba za ta kuɓuce daga ahalina ba." Yana gama maganar ya sake yin sujjada sau bakwai sannan ya fice daga bukkar, kai tsaye ya wuce gidan mahaifiyarsa da suke yi mata laƙabi da mai babbar turaka. Yana shiga bayin da ke yi mata hidima suka fice don haka suke yi a duk lokacin da Sarki Damina ya ziyarce ta duk da sun fahimci a mafi yawan lokuta zuwansa ba alheri ba ne. Mahaifiyarsa Ladi na ganinsa gabanta ya faɗi tana shirin yin magana ya ce, "Ta so mu je na sadaki fa yarima." Idanunta ne ya ciko da ƙwalla ta ce, "Har gobe ba zan daina dana-sanin haihuwarka ba Damina, Mai martaba ya cuce ni shi da baƙon bafulatani..." Bata rufe baki ba Sarki Damina ya fisgi hannunta daga wurin da take zaune ya furta, "Saboda kin ci darajar Mahaifiyata shi ya sa na tako da kaina, wannan girma ne da daraja na baki da a cikin bayi ne Dogarai zan aika musu. Ki gode wa Abar bauta da ba dauwama za ki yi da Yarima yana mu'amala da ke ba, babban dodo ya kawo mana waraka ko ki taso ko na sa dogarai su fitar min da ke." Hmmmm Wace ce sha-kundum kuma meye alaƙarta da ƴar maharba? Waye baƙon Bafulatani? Kuma ƴar maharba na mutuwa ko yaya? Me ye silar ciwon yarima kuma yaushe zai warke? Amsoshin na gaba ku dai kar ku bari a yi babu ku🏂💃🏼 Na gaishe ku kyauta Cau cau cau cau, Allah buɗa mana fans🏂 *KU MATSO KU TAHO*💃🏼 Wannan labarin salonsa na daban ne💃🏼 cike yake da sarƙaƙiya da tsananjn ban tausayi😰  ku dai kar ku bari a yi babu ku.🏂 Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN. Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne. Idan kin san kin sayi ɗaya daga cikin litattafan nan *AN YA BAIWA? KO DUBU JIKAR MAI CARBI KO ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* za ki biya 300 wannan ragin na waɗanda suka sayi wannan littafan nan ne kaɗai.💃🏼 Na ɗaga hannuwa riƙe da takobi da kwari da baka na salaƙe na sunkuyar da kai ina miƙa gaisuwa da kirari cau cau cau cau, sai ni Ameera 'yar Alhaji Adamu Amiriyan Mamanta, uwar Aslam da Ayman Amanar Oganta turmi sha daka 🥰 Wiiiiiiihuuuuuuhuuuu mace mai kamar maza ko cikin maza sai an duba domin wuya ake yi wa lissafi daɗi sai an jinkirta. Allah dai ya biya wuya a ƙofar Na'isa, wuya a ƙofar Kabuga wuya a ƙofar Nasarawa wuya a doka wuya, wuya a ƙofar kansakali mun buga a dajin Jemagu mun buga a dajin Falgore ko dajin Sambisa albarka. Sai ni ƴar Kanawan dabo amanar mutanen Rigana, idan ka ga matsoraci ko rago a Rugana baƙo ne domin jarumi ba'a nuna masa hanya, sa'a dai 'yar gaban goshin *FIRST CLASS WRITER'S* Amanar Marubuta La'ilaha'illahu. Sai ni ta hannun Matar Habibu ni ce dai ƙawar Mum Amnash amanar Masoyanta, cau cau cau cau makaranta ku matso ku ji wannan kafcan don idan kika bari aka yi babu ke an barki a baya. Domin duk wacce ta bari aka yi wannan tafiyar babu ita ta fita daga cikin jaruman mata masu aji.🌚 *Ummou Aslam Bint Adam*🌚 [8/20, 7:28 PM] Ameera Adam🌚: *BAƘAR DAULA*       ©AMEERA ADAM FIRST CLASS WRITER'S ASSO...   Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️                   3   *KU MATSO KU TAHO*💃🏼 Wannan labarin salonsa na daban ne💃🏼 cike yake da sarƙaƙiya da tsananin ban tausayi😰  ku dai kar ku bari a yi babu ku.🏂 Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN. Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne. Idan kin san kin sayi ɗaya daga cikin litattafan nan *AN YA BAIWA? KO DUBU JIKAR MAI CARBI KO ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* za ki biya 300 wannan ragin na waɗanda suka sayi wannan littafan nan ne kaɗai.💃🏼 Na ɗaga hannuwa riƙe da takobi da kwari da baka na salaƙe na sunkuyar da kai ina miƙa gaisuwa da kirari cau cau cau cau, sai ni Ameera 'yar Alhaji Adamu Amiriyan Mamanta, uwar Aslam da Ayman Amanar Oganta turmi sha daka 🥰 Wiiiiiiihuuuuuuhuuuu mace mai kamar maza ko cikin maza sai an duba domin wuya ake yi wa lissafi daɗi sai an jinkirta. Allah dai ya biya wuya a ƙofar Na'isa, wuya a ƙofar Kabuga wuya a ƙofar Nasarawa wuya a doka wuya, wuya a ƙofar kansakali mun buga a dajin Jemagu mun buga a dajin Falgore ko dajin Sambisa albarka. Sai ni ƴar Kanawan dabo amanar mutanen Rigana, idan ka ga matsoraci ko rago a Rugana baƙo ne domin jarumi ba'a nuna masa hanya, sa'a dai 'yar gaban goshin *FIRST CLASS WRITER'S* Amanar Marubuta La'ilaha'illahu. Sai ni ta hannun Matar Habibu ni ce dai ƙawar Mum Amnash amanar Masoyanta, cau cau cau cau makaranta ku matso ku ji wannan kafcan don idan kika bari aka yi babu ke an barki a baya. Domin duk wacce ta bari aka yi wannan tafiyar babu ita ta fita daga cikin jaruman mata masu aji.🌚       Takunsa mai girgiza hankulan ƙananan dakuru ne ya karaɗe majiyar sautina, haniniyar dokinsa ta musamman ce a duk lokacin da ya ziyarce ni don ya kasance zara a cikin dubbannin taurari. A kodayaushe na kan rasa wane ne shi da yake faɗo wa cikin duniyata har ya kawo mata agaji a duk lokacin da nake yunƙurin sare wa da miƙa wuya ga mutuwa. Idanuwan suna kan fuskarsa ya yin da na faɗa duniyar tunanin samuwarsa, ban yi tsammani ba na riski sautinsa ya karaɗe dodon kunnena yana faɗin. "Sare wa da rashin nasara ba taki ba ce, a kullin ina gaya miki ke ɗin mai nasara ce! Ke ta daban ce don haka rayuwarki ma ta daban ce! Don haka kada ki sallama wa mutuwa rayuwarki don ba ki cancanci mutuwa yanzu ba, ki taimaka ki cika muradi da burinki. Surarki, nasabarki, tsatsonki, zuciyarki da asalinki ba sa daga cikin jerin masu rauni." Nutsuwata da hankalina gabaɗaya na sallama masa ina sauraron maganganun da yake furta min, ba yau na saba jin haka daga gare shi ba sai dai kalaman yau sun sha bambam da waɗanda yake sanar min. Ina yunƙurin yi masa magana cikin tsawa na ji ya furta, "Ki tashi na ce ki aiwatar da ƙudurunki cikin jarumta domin ke ba ki kasance gajiyayyiya ba." Tamkar wacce aka ƙarawa ƙaimi haka na ji wani masifaffan ƙarfi ya mamaye ilahirin jikina, a zabure na waiga wurin Barde da ya yi yunƙurin kawo min duka sai dai ɓarin makauniyar da na yi masa a fuska ne ya azabtar da ruhinsa. Ƙaraji yake tamkar wanda ake zare wa rai saboda azaba, kamar yadda na ƙudura a zuciyata haka na sake jadaddawa. Daga jikin ƙuguna na zaro wata ƙanƙanuwar wuƙa na ƙarasa gaban Barde kafin ya yi wani yunƙuri na kauda kai gefe haɗe da tsige al'aurarsa daga gangar jikinsa. Maƙarrabansa su baƙi-baƙi na ganin haka kowannensu ya cika wandonsa da iska saboda sun lura a yunwace nake da su ina iya tsalle na dira a gabansu na yi musu makamancin abin da na yi wa Barde, saboda duk tafiyarsu ɗaya hallayarsu ɗaya duka tare suke aikata kowanne irin ɓarna sai dai Barde ya fi su yin ƙaurin suna wurin aikata badaƙala.    Ina yunƙurin juya wa wurun tawagar da ke farmakar rayuwa na neme su na rasa tamkar ɗaukewar ruwan sama, jinin da ke ci gaba da zuba daga jikina ne ya haddasa min raunin garkuwar jikina, na fara takawa ina layi ga idanuna da suke yi mini dishi-dishi har ta kai ba na iya bambamce takamaimar hanyar da zan bi na koma ga muhallina. Kwatsam! Ban yi aune ba na ji na faɗa jikin makamanciyar halitata ta bil'adam wanda hakan ya haddasa min sakin ragowar jikina a jikinsa. Muryarsa ba baƙuwa ba ce a gare ni hasali ma takan faranta zuciyata domin shi ɗin wani ɓangare ne daga tsakin zuciyata, ya kasance jini da tsokata ta yadda a kowanne hali nake ciki ina iya tabbatar da siffarsa mai cikar haiba da kamala. Idanuwana ne suka fara lumshewa, na riski ya huro min iskar bakinsa akan fuskata yana faɗin, "Abar bauta ta dafa miki a duk lamuranki ya ke sarauniyar maharba amanar Goje, ba kyau ba daɗi murucin kan dutse baki fito ba sai da kika shirya. Wane Mutum wawan mutum rana mai haske duniya kowa ya ƙarasa a bar shi ya kawo ƴar tsatson maharba. Cau cau cau cau sai ke Damisa amanar Duna, da wuya a dajin Gurɓu da wuya a dajin Dagumba wata wuyar sai mun tsallaka dajin Bagege. A lafiya shawarar Goga a lafiya amanar Goga, a lafiya wakiliyar Goga ko yau ko gobe kwarankwatsa dubu ko bakya nan ina yi miki yaƙi." Kirarinsa ne ya sake ƙarfafa zuciyata na ɗago a wahalce na jingina  kerena (Ɗaya daga cikin makamin maharba ne.) A jikin Barandaminsa cikin amsa gaisuwa irin tamu ta Maharba na furta, "Sa'a dai mai dawa amanar Shamuwa amana sai ɗan amana, amana ta kai maka har dajin Gaduru." Ina rufe baki ya cicciɓe ni ya ɗora a kafaɗa sannan ya wuce gida da ni. Tun a cikin dajin na ji yana yagar ganyayen magunguna da zan yi amfani da su, muna ƙarasawa gida aka kwantar da ni akan fatar kura wacce ta zame mana mashinfiɗin da muke hutawa. Hayaniya ce ta fara tashi a wurin matasa maza da mata suka cika damƙam, ganin halin da nake ciki ya sa Mahaifina ya sallami sauran mutanen da ke tsaitsaye a kaina, cike da takaici ya tsugunna a daidai kaina ya yin da ya yi tozali da irin jini da yake fita daga jikina sakamakon mummunan saran da Barde ya yi, yanayin fuskarsa ne ya bayyana min ɓacin ran da ya ziyarci zuciyarsa. Runtse ido ya yi ya furzar da iska mai zafi sannan ya furta, "Abar bauta ta ci gaba da dafa wa lamuranki ya ke sarauniya. Haƙiƙa ina baƙinciki raunin da yake ziyartar ruhinki, wanda dalilin haka yake sa a yi yunƙurin yin galaba a kan ki." Hannunsa na kama da hannuwana biyu, ina jin hawayen baƙinciki na neman ɗiga daga idanuna. Sarewa da karaya ba hali ko ɗabi'ata ba ce amma a wannan karon ina jin ƙwarin gwiwata ta yi rauni fiye da kullin, Mahaifina na lura da halin da nake ciki don haka ya shafa kaina tare da furta, "Namiji ba ya sarewa da ƙarfin magauta. A zahiri ke macece amma ni nasan nagartaccen jarumin namiji na haifa. Kada ki taɓa bari wani ya lura da rauninki, ko da wasa kar na sake ganin ruwan hawaye a ƙwayar idonki domin zai ba wa magautanki ƙwarin gwiwa a kan ki har su yi nasara su kai ruhinki kushewa." Daga wurin da nake kwance na dube shi sannan na furta, "Wuya bata raunata zuciyar 'yan maza koda kuwa a tsakiyar rundunar mayaƙan maƙiya ne, raunina ya dogara a kan ɓoyayyan lamarin da yake faruwa da ni ta yadda ba na iya mallakar gangar jiki da ruhina. Na yi rantsuwa da abar bautar da ke raya dare zuwa rana ta samar da yalwatacciyar ni'ima da kyautata noma, ba zan sake bayyana raunin da zai bawa magauta dama akaina ba koda kuwa rikicitaccen al'amarina zai ci gaba da farmakar rayuwata." Mahaifiyata  ce ta miƙo masa ƙaron marke da ganyen zaƙami, ya saka su akan fatar zomo ya ƙwanƙwasa su da dutse sannan ya fara shafa min a wurin da yake zubar da jini. Ba a ɗauki lokaci ba jinin ya tsaya na riski muryar mahaifiyata tana faɗin, "Baushe me za a yi wa yarinyar nan a kan karyewar asirin jikinta, tun da abar bauta ta wanzar da ruhina ban taɓa bada maganin ƙarfe ya karye ba. Amma yarinyar nan babu abin da ba a bata ba duk lokacin da wannan al'amarin zai same ta sai ta rasa duk wani tsarin jikinta." Da kansa ya ɗauke ni ya kaina cikin bukkar mahaifiyata sannan ya tsaya a bakin ƙofar bukkar yana faɗin. "Kyauta ita kaɗai gare ni a faɗin duniya, don haka ba zan yi ƙasa a gwiwa ba don sake roƙar mata abar bauta akan ta shiga lamurunta idan akwai zunubin da ta aikata ta shafe mata shi. Ban san zunubin da ta aikata ba da farauta take yi mata gudun mutuwa, ban san ya aka yi tsatson maharba yake son bijirewa zuri'arsa ba. A duk binciken da na yi babu tasirin tsafi ko asiri a jikin Kyauta, rauhanai sun sanar mini akwai wani ɓoyayyan al'amari game da ita sai dai sun garara sanar da ni komai daga cikin al'amuranta. Zan ziyarci abar bauta da mataimakanta ta taimaka min domin ita ce madogararmu mai taimaka mana da kawo mana mafita, ba zan rasa ki ba Kyauta domin lokacin mutuwarki bai zo ba har sai mun shiga Dajin Mugazu ta karɓo kambun sarauta da hannunta." A hankali na yunƙura na tashi zaune azabar da nake ji ta sa na cije bakina sannan na furta, "A taimaka a sada ni da Abar bauta akwai maganar da nake son tattaunawa da ita." Da mamaki ɗauke a fuskokinsu na ga sun kalle ni, Mahaifiya ta ƙaraso wurina ta ɗago ni tana cewa. "Abar bauta za ta saka miki albarka ziyararki babbar nasara ce albarkacin tsafi da farauta." Mahaifina ne ya kama ni muka wuce tsaunin Abar bauta ya yin da Mahaifiyata ta ci gaba da ba wa Kandala kulawar da ta da ce tana gasa ta da ruwan zafi don warkewar raunin da ke ƙasanta. Daular Sarki Damina.   Duk yadda Mai babbar turaka ta kai ga ƙin amince wa da buƙatar Sarki fir ya ƙi sauraronta, da ƙarfin tsiya ya fisge ta ganin tana son kunto masa matsala ya cicciɓe ta ya ɗora a kafaɗa. Ciccila ƙafa ta rinƙa yi tana dukan kafaɗarsa bai saurari roƙonta ba ya fice da ita, a tsakar gidan keɓaɓɓan gida ya dire ta sannan ya kalli waɗansu ƙosassun dakaru masu siffar adawa ya ƙwala musu kira, tun bai rufe baki ba suka ƙaraso wurinsa sannan ya ce, "A gaggauta sada ta da Yarima almuru ya ƙarato zan kai gaisuwar ibada da roƙon ruwa." Kuka Mai babbar turaka take rusawa kamar ranta zai fita, yana shirin tafiya ta rarrafa tana jan ciki haɗe da ruƙo ƙafarsa tana faɗin, "Damina ni ce fa mahaifiyarka wacce ta ɗauki cikinka tsawon lokaci yanzu da kanka za ka sada ni da Yarima ya haike min ina ji ina gani?" Taɓe baki Sarki Damina ya yi ya tsugunna sannan ya ruƙo haɓarta ya furta, "Ban fiya son ja'inja da ke ba don ina matuƙar ganin mutumcinki." Ya ɗago yana kallon dogaran tare da furta, "A yi gaggawar wuce wa da ita." Daga haka ya fisge ƙafarsa mai babbar turaka ta faɗi gefe haɗe da kifa kanta a ƙasa tana ci gaba ta rusa kuka mai cin zuciya. Da ƙarfin gaske suka fisge ta duk irin magiyar da take yi musu bai sa sun saurara mata, saboda sanin kansu ne matuƙar suka saɓa wa umarnin Sarkin Damina tabbas za su tsinci talatarsu a laraba domin na su hukuncin sai ya ninka nata sau dubu. Suna gab da shiga ɗakin, Mai babbar turaka ta dubi Nalami dogari cikin karayar zuci ta furta, "Ka taimaka ka bar ni ko na taƙi kaɗan ne zan bar musu wasiyyar da ba na son ku buɗe ta har sai bayan babu rayuwata. Jikinsu ne ya yi sanyi duk da kasancewar ba sa daga cikin masu tausayi, ganin tausayi na neman tasiri a zuciyarsu ya sa suka fisge ta da ƙarfin tsiya. Kamar mayunwacin zaki haka Yarima ya kurma wata uwar ƙara haɗe da janyo Mai babbar turaka da ƙarfin tsiya, ganyan da ke maƙale a ƙugunta da ƙirjinta ne ya faɗi gefe Yarima ya haɗe ta da jikinta tare da sauke buƙatarsa a haukaca akanta. Cikin fitar hayyaci ta riƙa ambatar sunan Damina tana tsine masa da aibanta shi da miyagun kalamai marasa daɗin saurare, sai da  Yarima ya dawo cikin hayyacinsa ya fahimci Mai babbar turaka ta galabaita. A wahalce ta dubi Yarima yana faɗin, "Yarima mahaifinka ya yi min abin da ba zai taɓa albarka ba, akwai laƙanin da nake son taimakon wannan daular da shi amma yana cikin turakata..." Da sauri Yarima ya tallafo kanta yana faɗin, "Laƙanin me ye kar ki tafi ba ki gaya min ba." Cikin kakari ta furta, "Ka tabbatar da ka yi tozali da sabuwar sarauniyarmu kuma ita ce za ta ɗauko..." Daga haka harshenta ya sarƙe idanunta suka ƙafe ta faɗi matacciya. Zuwanmu tsibirin keda wuya muka samu dubbannin jama'ar yankinmu sun yi dafifi akan tsiribirin, da yake duk ranar talata da daddare muna taruwa akan tsibirin domin miƙa buƙatunmu ga abar bauta. Mun yi amanna akan duk wanda ya faɗi buƙatarsa a kan tsibirin tabbas buƙatarsa za ta biya. Kasancewar sun lura da halin da nake ciki ya sa suka buɗe min hanya muka wuce  don isa ga abar bauta saboda akwai ƙudurin da nake son sanar da ita duba da rikitattun al'amuran da suke baƙuntar rayuwata. Muna gab da ƙarasawa muka riski sautin wakiliyar Abar bauta, ba mu sake tsinkewa daga lamarin ba sai da muka yi tozali da ita ta fito matsayar da ko a tarihin rayuwa ban taɓa jin ta fito harabar wurin ba. Kamar ɗaukewar ruwa  sama haka wurin ya yi tsit kowanne ya baje majiyar sauti da maganansa, ko a mafariki ban taɓa tozali da siffar wakiliyar Abar bauta ba sai dai labarin da magaba suke ba mu akan samuwarta da tasirinta ga rayuwarmu.Tun bayan kafuwar yakinmu a tarihin da muka taɓa fuskanta, abar bautar wancen yankin bata taɓa fito wa ba sai a ranar da wani mummunan al'amari ya faru da su wanda sanadin haka ya sa aka kafa tarihi har muka mayar da ranar Talata a matsayin ranar karɓar addu'a kuma ranar biyan buƙata, domin a cikinta ne al'ummar Maharba suka samu ƙarfin iko da nasara akan Baƙar Daular da ke gaba da yankinmu. Sannan mahaifina ya tabbatar min a bisa al'ada duk lokacin da Abar bauta ta bayyana akwai wani mummunan al'amari da zai faru wanda zai hargitsa al'ummarmu.  Ban gama dawo wa daga duniyar tunani ba na riski sautinta tana faɗin, "Ya waɗannan al'aumma yau na bayyana kaina ne domin na shaida muku mummunan al'amarin da yake tunkaro mu kwatankwacin mummunar ƙaddarar da ta faru a baya. Kogon bincike ya ƙone ƙurmus! Hasken wutar abar bauta ta ɗauke. Buzun zakin abar bauta ya miƙe yanzu haka yana cen yana fidda aman wuta.   A yau na tsaya a gabanku domin na tabbatar muku da bala'in da yake tunkaro rayuwarku, ga taron rundunar baƙar inuwa tana tunkaro mu don haka ya zama wajibi mu haɗa ƙarfi da ƙarfe mu sake tserartar da yakinmu domin gujewa abin da ya faru ɗaruruwan shekarun da suka gabata, a zahiri dukkan alamun da suka bayyana a baya sune suke sake bayyana a wannan lokacin domin yanzu haka tazarar da ke tsakaninmu da wannan baƙin yaƙin bai fi taƙi kaɗan ba. Ina jin tsoron kada farmakin Baƙar Daula ya wanzu a gare mu duk da muna da tsarin da ko tsuntsu ba za su iya gani da idanunsu ba matuƙar ya kasance ɗaya daga cikin ahalinmu na Maharba." Ras! Na ji gabana ya faɗi musamman da na tuna Kandala bata daga cikin zuri'ar Maharba, hasalima tsarinmu ya katange da ita." Ina tsoron kar wani mummunan al'amari ya faru da ita. Hankali a tashe na furta, "Ba zan bari ba Kandala! Ba zan taɓa bari a cutar da ke ba tun da kaina na ɗauki alƙawarin kulawa da rayuwarki. Zalincin baƙar Daula ba zai taɓa ɗarsuwa a kanki ba koda zan rasa rayuwata tun da ni ce sillar salwantar iyayen da suka haifo ki don haka zan bada jini da ruhina akan ki. *Ummou Aslam Bint Adam*🌚 [8/20, 7:28 PM] Ameera Adam🌚: *BAƘAR DAULA*       ©AMEERA ADAM FIRST CLASS WRITER'S ASSO...   Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️                   4   *KU MATSO KU TAHO*💃🏼 Wannan labarin salonsa na daban ne💃🏼 cike yake da sarƙaƙiya da tsananin ban tausayi😰  ku dai kar ku bari a yi babu ku.🏂 Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN. Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne. Idan kin san kin sayi ɗaya daga cikin litattafan nan *AN YA BAIWA? KO DUBU JIKAR MAI CARBI KO ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* za ki biya 300 wannan ragin na waɗanda suka sayi wannan littafan nan ne kaɗai.💃🏼 Na ɗaga hannuwa riƙe da takobi da kwari da baka na salaƙe na sunkuyar da kai ina miƙa gaisuwa da kirari cau cau cau cau, sai ni Ameera 'yar Alhaji Adamu Amiriyan Mamanta, uwar Aslam da Ayman Amanar Oganta turmi sha daka 🥰 Wiiiiiiihuuuuuuhuuuu mace mai kamar maza ko cikin maza sai an duba domin wuya ake yi wa lissafi daɗi sai an jinkirta. Allah dai ya biya wuya a ƙofar Na'isa, wuya a ƙofar Kabuga wuya a ƙofar Nasarawa wuya a doka wuya, wuya a ƙofar kansakali mun buga a dajin Jemagu mun buga a dajin Falgore ko dajin Sambisa albarka. Sai ni ƴar Kanawan dabo amanar mutanen Rigana, idan ka ga matsoraci ko rago a Rugana baƙo ne domin jarumi ba'a nuna masa hanya, sa'a dai 'yar gaban goshin *FIRST CLASS WRITER'S* Amanar Marubuta La'ilaha'illahu. Sai ni ta hannun Matar Habibu ni ce dai ƙawar Mum Amnash amanar Masoyanta, cau cau cau cau makaranta ku matso ku ji wannan kafcan don idan kika bari aka yi babu ke an barki a baya. Domin duk wacce ta bari aka yi wannan tafiyar babu ita ta fita daga cikin jaruman mata masu aji.🌚     Gudun kada Abar bauta ta fahimci abin da nake faɗa ya sa Mahaifina ya damƙi hannuna mara ciwon sannan ya yi min raɗa a kunne da cewar, "Ɗaure bakinki ya fi miki alheri akan mummunan fushin da abar bauta za ta yi da ke." Idanuwana na ɗago ina kallonsa, har ƙwayar idona ta ciko da ƙwallah sai na haɗiye abina don na tuna gargaɗin da mahaifina ya yi min akan zubar ƙwallata. Muryata na rawa na furta, "Ina gudun abin da zai faru da Kandala don ka san tsarinmu ba zai taɓa tasiri a tattare da ita ba. Ta kasance bata daga jinin Maharba da mafarauta, idan baka manta ba da bakinka ka gaya min Abar bauta ta tsarkake iya zuri'ar wannan yankin namu ne kawai, ka na ganin idan wani abu ya faru da Kandala zunubi da munanan abubuwa ba za su ƙaru a kaina ba duba da abubuwan da suke faruwa da ni? Na yi sanadiyar mutuwar iyayenta, kuma tun da dokar dajin na lashi aniyar kare haƙƙinta kamar yadda iyayenta za su kula da ita. Don Allah kada ka dakatar da ni saboda ina tausayin rayuwarta, ta rasa iyayenta a yankinmu, ta rasa zuri'arta a yankinmu, ta rasa budurcinta a yankinmu shin wannan kaɗai bai isa ya sa a tausayawa rayuwarta ba?" Jikin mahaifina ne ya yi sanyi tamkar wanda aka zare wa laka, ya dube ni haɗe da sauke ajiyar zuciya sannan ya furta, "Shi kenan Kyauta! Abar bauta ta kawar da muguwar rana a kan ki, za ta shiga lamuranki ba za ta da mu kunya ba albarkacin tsafi da farauta." Jin daɗin kalamansa ya sa na sakar masa murmushi a daidai lokacin na ji Abar bauta ta sake cewa, "A daren yau zuwa gobe za a katange yankin nan daga baƙar guguwar da ta taso mana. Ya zama wajibi a zubar da jini ga rauhanai don su sake dafa mana akan sha'anin rayuwarmu, wannan shi ne abin da zan iya sanar da ku don na taimaka muku. Idan kuka bijirewa umarnina zan iya sauya sheƙa daga wannan yankin zuwa wani na kafa daulata, munanan abubuwa za su yi ta faruwa a kan ku haɗe da farmakai daga sauran ƙasashe musamman Baƙar Daular da kullin burinta ta shafe tarihin Maharba a faɗin duniya." Cikin aminta da kalaman abar bauta da ba ta yarda ya sa muka amsa mata da faɗin, "Uwar gijiya abar bauta ta dafa mana ta shafe matsalolinmu, mun dogara da ke don haka ke ce mai yaye mana damuwa da ba mu waraka a kowanne lokaci. Mun ji mun amince za mu yi abin da kika ce domin mu ma su bin umarninki ne, mun dogara da tsafi da sihiri sune madogarar abar bauta ita kuma ita ce madogararmu a koyaushe." Fuskar abar bauta ce ta fasalta irin farincikin da ta yi da mu, don haka ta ɗaga hannunta sama ta wara ƴan yatsunta nan take wani mulmulallan haske ya dira a kai. Ta dube mu ta sake kallon haske sannan ta furta, "Albarkacin tsafi da sihiri, albarka da tabbata a gare ku ya ku wannan zuri'a ta mafarauta masu albarka. Shin akwai mai son a bincika gobensa don sanin abin da zai faru da shi? Akwai mai ciwo mu warkar da shi? Ko akwai mai son mu ninka nasara da tsaririn tsafinsa don ya gagari kowanne rauhani a dajin farauta?" Tun bata rufe baki ba mahaifina ya ɗaga hannu sama, kasancewar mahaifina sarkin Maharbin yankinmu ya sa mutanen garinmu suke matuƙar ba shi girma domin mutum ne mai adalci da son talakawansa. Ganin mahaifina ya yi magana ya sa alummar da ke wurin suka fara  kai masa gaisuwa cikin girmamawa, "Sarki ya zo mutuwa ta zo, mutuwa mai kai ƴan maza ƙasa ko da son rai ko babu. Abar bauta ta riga da ta buɗa maka kwarankwatsa dubu sai ka gama lafiya amanar ƙauran garin Dume, amana ta kai mana amana ta kai maka mun baka amana ka ba mu gaskiya ko sun ƙi ko sun so sai mun bar wuya a dajin Gagarar maza. Sa'a dai maza sa'a dai uban dawa wuya mai sa ƙarar kwana ga ƙananun maharba uban dawa sai ya kai labari ko da daɗi ko babu." Sunkuyar da kai Mahaifina ya yi alamar gaisuwar tana kai masa sannan ya ɗago ya amsa musu da cewar, "Dawa dai mazaje! Ba kyau ba daɗi, idan wuya ta yi wuya yaro ke guduwa ya bar babansa. Kwarankwatsa dubu ranar Talata mai zuwa sai na kai hallitun dawa dubu biyar da ɗoriya ɗan butar uwa, Abar bauta ta buɗe mana dai." A hankali muka riƙa takawa har kan tudun tsira sannan mahaifina ya tura ni daga gabansa kaɗan ya fara yi mata magana."Abar bauta ta yafe min kada ta yi fushi da ni a yau ma na sake dawowa da 'yata Kyauta domin ta shiga lamuranta. Ɓoyayyun al'amura na sake bayyana a tattare da ita, don haka na sake dawowa da ita don na ji ko akwai wani taimako da Abar bauta za ta yi domin Kyauta ta rinƙa rayuwa kamar kowa." Daga can duhu-duhun wurin da mutane ke tsaitsaye na hango wani matashin saurayi yana ƙara kutso kai sakamakon jin bayanin da Mahaifina ya yi, muna haɗa ido ya sakar mini murmushin da ban san dalilinsa ba, sai dai abin da ya ɗaure min kai ba kasafai na cika tozali da matashin ba sai a ranaku makamantan waɗannan da muke kai wa Abar bauta kukanmu.Hasali ko kaɗan ba ya daga cikin zuri'armu domin gabaɗaya mun san kanmu waɗanda suke rayuwa a yankin. Ina cikin wannan tunanin na riski muryarta tana faɗin, "Akwai ɓoyayyun lammura game da Kyauta don haka nake gagara bincika abin da yake damunta, a duk lokacin da na bincika gobenta ba na samun biyan buƙatata. A duk faɗin yankin nan babu wanda zan bincika rayuwarsa ta gaba na samu tangarda sai Kyauta, ina mai yi maka albishir da cewa ita ɗin ta musamman ce don haka waɗansu abubuwa suke baƙuntar rayuwarta. Babban abin da za mu saka a gaba shi ne, mu mayar da hankali wurin zagaye garin nan domin idan muka zagaye gari na yi ammana da tsafi da sihiri babu abin da za same mu." Wurin ne ya yi tsit muna sauraron ci gaban bayanin da abar bauta take. Sai da ta sake hawa can ƙololuwar samman tsauninta sannan ta ci gaba da cewa, "Albarkacin ranar talata da nasarorin da ke cikinta muna miƙa wuya ga alƙaluman tsafi akan zan sanar da talakawa su nemi waɗannan kayan tsarin su aiwatar da shi domin neman warakar su. Da farko za ku saro kan wani ƙasurgumin kumurcin maciji da ke Dajin Bawaya, sai ku kawo min na jiƙa shi da ruwan sihiri haɗe da tumfafiya, idan ya kwana ɗaya a jiƙe sai a dake kan macijin ku samo mana ruwan kogin haladu a wanke idon matasan makafi a haɗa da ƙasar kabarin Jarumi Baushe uban Yaɗiya, idan kuka yi haka ku kawo min na haɗa sauran mahaɗin da kaina. Zan baku shi ku je ku zagaye garin nan da shi kuma duk abin da za ku gani kada baki ya furta ko zuciya ta tsorata, duka waɗannan abubuwan za a same su ne a cikin ƙasa da kwana biyu." Duk da zuciyoyinmu sun fara karaya bai hana mun amsawa abar bauta ba, tana gama jawabin ta dafa raunin da ke jikina haɗe da ɗaura min wata baƙar fata wacce da alama ta baƙar wahainiya ce. Nan take raunin jikina ya warke wani ƙarfi ya ratsa ni tamkar wani abu bai taɓa faruwa da ni ba, daga haka ta sallame mu sannan kowa ya watse gidansa.   Sannu a hankali na rinƙa waige-waige don ganin na lalaubo matashin da nake ɗora zargi a kansa, amma sai haƙana ya gagara cim ma ruwa. Na neme shi sama da ƙasa na rasa! Dama na san za a rina wai an saci zanin mahaukaciya. A duk lokacin da na yi tozali da shi haka ce take faruwa don haka nake tunanin yana tattare da mummunar manufa game da yankinmu. Saboda na tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa, kuma tamkar wanda yake wa rufa ido ban taɓa ji wani ya yi magana ko ƙorafi akansa ba. Kasancewar ba a ranar na saba ganin hallitun da ƴan uwana ba sa iya ganinsu ba ya sa na ja bakina na yi shiru, amma haka kawai jikina ya ba ni ziyararsa a gare mu ba alheri ba ce. Matashin saurayin na barin wurin kai tsaye ya bi ta wata ɓarauniyar hanya da ke ƙarƙashin ƙasa, cike da fargaba ya rinƙa falfala gudu don yana tsoron tonuwar asirinsa musamman da ya tuna irin kallon zargin da Kyauta take yi masa. Sai da ya yi gudu mai nisa sannan ya isa wurin wasu rundunar dakarun mayaƙa, haki yake yi kamar ransa zai fita sannan ya sanar da su duk abin da ya ji game da yankin su Kyauta sannan ya ɗora da cewa, "Matsala dai ɗaya ce kamar yadda na gaya muku a baya, duk lokacin da na shiga yankin nan ba na iya ganin kowacce halita da idona face manyan dabbobi da ƙanana. Da taimkon Shugaba Usaina ta ba ni wani laƙani shi ne nake iya ganin yarinya ɗaya da idanuna kuma nake iya jin sautin abin bautarsu, ita ma a yadda na lura tana ganina sai dai ina tsoron kar asirinmu ya tonu." Shugaban Dakarun ne ya bushe da dariyar ƙeta sannan ya furta, "Ka gama aikinka don haka za ka iya tafiya ga Daularmu mai albarka, na tabbata idan muka kai wa Sarki wannan zuri'a ta Maharba sai ya yi mana ƙarin girma ya ɗaukaka darajarmu. Runtse idonsa matashin ya yi tare da faɗin, "Shugaba Usaina! Shugaba Usaina." Nan take wani haske ya mamaye wurin babu jimawa ya ɓace ɓat. Gurfane yake a gabanta yana sauraron abin da za ta faɗa, sanin faɗin rai da izzarta ya sa ya ƙagara har ya ɗago don a tunaninsa ko ta bar wurin bai sani ba. Suna haɗa ido ya sauke kansa ƙa sa cikin girmamawa ya furta, "Sha kundum ta dafawa aikinki." Miƙewa ta yi ta fara taku ɗaiɗai ta rinƙa zagaye shi sannan ta furta, "Na saurari bayaninka don haka ina mai umartarka da ka iya bakinka idan ba haka ba sai na fisge rai daga gangar jikinka. Tabbas Boka mai zamani ya yi gaskiya Sha kundum ta sake bayyana a wannan yankin da kake min leƙen asiri sai dai babbar matsalar da har yau ya gagara bayyanar da suffar yarinyar. In dai ina numfashi Sarki Damina ba zai taɓa samun cikar burinsa na jininsa ya gaji karagar mulkinsa ba, na yi rantsuwa da abar bauta sai dai zuri'arsa ta ƙare a wahale yana ji yana gani zan gina Daular nan da jinin da ba na shi ba." Ta kai ƙarshen maganarta a tsawace kamar wacce aka ɓata wa rai, a razane matashin ya gyaɗa kai yana shirin sake magana ta katse shi da cewar, "Fitar da sirrina tamkar ka sanya takobi ka datse rayuwar da kake ciki ne, ka kiyaye idan ba haka ba wankin hula zai iya kai ka dare." Godiya ya yi mata sannan ya tashi zai fita ta sake katse shi da cewar, "Ka tabbatar da ka bawa yarima mugunyar ruwan sihiri a daren nan kafin wayewar gari." Amsa mata ya yi cikin ladabi sannan ya fice daga ɓangarenta. Dare ne ya tsala sosai ban da kukan tsuntsaye da na ƙananan dabbobi babu abin da yake tashi, cikin sanɗa da ɓadda-bami take tafiya a hankali tana waige don kar wani ya ganta har ya fahimci abin da yake tafe da ita. Kamar yadda ta saba a duk daren da take neman biyan buƙatarta haka ta tunkari tsaunin Boka Mai zamani, kamar yadda ya ga zuwanta a cikin ƙoramar sihirinsa haka ya ji takunta zuwa kogon dutsensa. Tun daga bakin ƙofa Boka Mai zamani ya rungume ta a yunƙurinsa na son su fara aikata masha'arsu kamar yadda suka saba duk lokacin da ta ziyarce shi, a hankali ta zame shi daga jikinta tana faɗin, "Sha kundum ta ci gaba da rufa mana asiri dangane da ɓarnar da muke aikatawa Sarki Damina." Boka mai zamani ya bushe da mahaukaciyar dariya sannan ya furta, "Wane mutum In ji mutuwa shalelena? Asirinmu ba zai taɓa tonuwa ba don ba na jin wancan sakaran zai iya kusanto da Sha kundum cikin wannan Daular, hasalima rashinta tare da mu shi ne mafi alheri domin na tabbata idan tana yankin nan asirinmu ya gama tonuwa. Yanzu dai ya kamata a baiwa kura ajiyarta." Takawa ta fara yi a hankali tana zame ganyen da ke jikinta daga wanda ya rufe al'aurarta har zuwa na ƙirjinta sannan ta furta, "Ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai ya ke ba mudubina. Indai wannan ne ai ta kwana gidan sauƙi jariri a ɗakin mayya. Amma abin da yake tafe da ni bai wuce kan maganar wancan sakaran Yariman ba, shin maganar da na ji Sarki ya faɗa gaskiya ne zai iya warkewa? Saboda ina ɗagawa Sarki Damina ƙafa ne don na san a halin da yarima yake ba zai iya mulkar Daular nan ba." Boka mai zamani ya ƙarasa wurinta yana yawo da hannunsa a sassan jikinta sannan ya furta, "Tabbas a bincikena matuƙar Sha kundum ta bayyana a Daular nan zai iya warke wa amma da sharaɗin sai an bankaɗo sirrin da ba kowa ne ya sani ba kuma ba kowa ne zai gan shi ba. Mai wannan ikon yanzu haka ta bar duniya, Mai babbar Turaka ita ce ta san da wannan ɓoyayyan sirrin wanda ko da Sha kundum ba ta dawo daular nan ba matuƙar aka bankaɗo shi Yarima zai warke, yanzu haka gawar Mai babbar turaka na ɗakin yarima na kashe ta ne a lokacin da take ƙoƙarin sanarwa da Yarima sirrin ɓoyen da bankaɗe shi ba alheri ba ne a game da ke, ni kuma duk abin da zai muzanta shi zan iya kawar da shi. Sarki Damina yana kallonki a matsayin mahaifiyar Yarima alhalin Hasana ita ce Mahaifiyarsa kece Usainarta, Ko kin san har gobe Mahaifiyar Yarima tana raye a faɗin duniyar nan? Ko kin san Yarima ba shi kaɗai ne Ɗan da Sarki Damina ya mallaka ba? Ko kin san ƴaƴan Sarki Damina Uku ne a faɗin duniya? Idan bacci kike ki farka domin a duk lokacin da Damina ya gano kece kika nemi salwantar da rayuwar yarima da mahaifiyarsa na tabbata kashinki ya bushe. Ki yi duk abin da za ki yi ki nemo tagwayen jarirai ki kawo min domin na cika miki wani aiki da su idan ba haka ba komai zai iya faruwa, kuma ki tabbata jariran sun fito daga cikin jinin Maharba domin har gobe jininsu na tasiri akanmu tun da sune suka yi galaba a kan mu a lokacin da mummunan al'amari ya faru da Sarauniya Shakundum." Jakadiya da tun shigar Mai ɗakin Sarkin Damuna take laɓe a ƙofa ta riƙe bakin cikin mamaki, a hankali ta furta, "Tabbas Usaina ta cika tattaciyar marar imani amma na yi rantsuwa da Sarauniya Sha kundum da mulkinta sai kwaɓarta ta yi ruwa, a kullin fata da burina bai wuce Sarki Damina ya auri Jummai don na tabbata ko da tsiya da azziki sai Jummai ta haihu a gidansa. Jakadiya bata ƙarasa wannan tunanin ba ta hango harshen wutar itace kafin ta yi wani yunƙuri Bayin Sarki Damina suka haske ta da shi, a tsawace babban bawansa ya furta, "Jakadiya Lami me kike yi a wurin Boka mai zamani a talatainin tsohon daren nan duba da kin san haramun ne matuƙar ba a sanar da Sarki Damina wannan ziyarar ba?" Daga cikin kogon dutsen cikin Boka mai zamani da Usaina mai ɗakinsa ne ya kaɗa, nan take zufa ta fara keto musu cikin faɗuwar gaba ta furta, "Halaka ta zo mini matuƙar Sarki Damina ya san da ni a kogon dutsen nan." Kafin boka mai zamani ya yi magana daga cikin rijiyar da gunkin Sarauniya Sha kundum take suka ji wata irin tsawa wacce ta haddasa razanar Jakadiya ta faɗo cikin kogon dutse a hargitse. Ganin haka ya sa Sarki Damina da Fadawansa suka rufa mata baya, don ya kawo ziyarar cikin dare ne sakamakon mummunan mafarkin da ya yi akan Yarima da wata matashiyar buduwa mai ɗauke da kwari da baka a hannunwanta." *Ummou Aslam Bint Adam*🌚