[3/4, 22:15] 🥰Nanameera🥰: *🌹SHEIKH HEESHAM🌹* *Royal Star Writer's Association* Nanameera. 01. Yola/ Jimeta.. Tsugune take bakin kogin tayi shuru kana ganinta kasan tunani take, wata yarinya ce tazo wucewa wacce aƙalla bazata shige shekaru goma sha huɗu ba kallonta ta yi sai kuma ta ce" Jiddoh " wacce aka kirada Jiddon ta juyo sai a sannan na ƙare mata kallo farace tass amma kana ganinta kasan a cikin wahala take bazata huce shekara goma sha biyar ba tana round face da ɗan siririn hanci sai bakinta jajur dashi ganin yanda take kallonta yasa ta buɗe dara-daran idanunta masu matuƙar ɗaukan hankali. Batace mata komai ba ta juya tayi gaba abunta, sunkuyawa tayi ta ɗau ruwan da ta ɗiba sannan ta kama hanyar da ƴar uwartata tabi.... Da gudu ta shiga gidan nasu wanda bukkace kawai tana faɗin "Ammi!! Ammi " fitowa tayi daga wani waje tana kallon ɗiyar tata ta ce" lpia hanne kina yimin irin wannan kiran?" tana riƙe ƙugu ta ce" ba kin aiki Jiddoh ba?, to wlh ganinta nayi tana wasa awajen shanun arɗo bata tafi ba tana ganina ta gudu" bata rufe baki ba Jiddo ta shigo gidan da tulun ruwan akanta, ajiyewa tayi ta tsaya ganin irin kallon da take mata, ƙarasowa wajenta tayi ta murɗe kunnenta tana magana cikin gurɓatacciyar hausarta ta ce" wato ke ban isa na aike ki kije ba ko?, saboda bani na haifeki ba shiyasa kikemin irin wannan rashin mutuncin ko toh wlh bari baffan naku ya dawo yau saidai ya tsaɓa ko ni ko ke tunda ke kin gaji hali irin na uwarki" tana gama faɗin hakan ta tunkuɗata. Waɗuwa tayi tana kuka dan idan da sabo to tasaba da irin wannan, shigewa cikin bukkar sukai suka barta nan tana kuka..... Kano State. Ɗaukan wayarta tayi ƙirar iphone 13pro max ta zauna gefen gadonta a hankali kuma cikin isa ta fara dialing number, ganin har ya katse bai ɗagaba yasa ta ajiye wayar ta tashi ta sanya takalmknta sannan ta fito parlon. Zaune ta sameta itada wata friend ɗinta wacce kuma daman gidan gidan zuwantane, zama tayi kusada Mami sannan ta ce" Mommy ina yini" murmushi tayi ta ce" lpia loa Shareefat ya gida ya karatun?" tana kwanciya cinyar Mami ta ce" lpia Alhamdulillah ina Nihal?" ta ce" wai yau za'a musu orientation that's why bata biyoni ba" ok tace sannan ta kalli Mami ta ce" Mami nakira Sheikh fa kuma bai ɗauka ba" Mami ta ce "maybe wani abun yake anjima sai ki sake kiran kije kici abinci Shareefat" kwaɓe fuska ta yi ta ce" wlh Mami i'm full saidai anjima" ok Mami ta ce tana kallon Hajiya Zainab ɗin ta ce" yawwa sai akayi me Hajiya?" ta ce" wlh ina baki labari kin san yaron ashe wai hacker ne to ankamashi shine take ta kuka" girgiza kai Mami ta yi ta ce" Allah Sarki Nihal Allah yasa hakane mafi alkhairi" ta ce "Ameen"....... Ganin da tayi rana ta faɗi yasa ta miƙe a hankali ta shiga inda nake zaton shine banɗakinsu, cire kayan fulanin dake jikinta tayi ta ɗebi ruwa ta watsa a jikinta sannan ta ɗaura alwala ta fito. Wata tabarmar kaba ta samu wajen ƙuda sai bi yake ta ɗauka ta shimfiɗa ta tada sallah. Tana idarwa ta tashi a hankali dan da kyar take tafiya saboda tsananin yunwar da takeji ta fita daga cikin bukkar tasu, tafiya kawai take batareda tasan inda zata jeba ita dai tasan yunwa takeji kuma abinci ta fito nema, ji tayi tafiyar na neman gagararta yasa ta nemi wani waje ta zauna ta kifa kanta kan gwuiwoyinta ta fashe da kuka, haka ta zauna wajen mintuna talatin a hankali kuma bacci ya ɗauketa..... Sanyin asuba ne ya farkar da ita a firgice ta tashi tana kalle-kallen inda ta kwana, jiki babu kwari ta miƙe ta kama hanyar tafiya gidansu. Duk suna cikin bukkah kowa na kwance babu wanda yayi noticing bata kwana gidan ba ta shiga cikin tata bukkar wacce ita ɗaya take kwana, babu komai cikinta sai tabarmar kaba ta kwanta akai tana tunanin rayuwarta bata taɓa samun farinciki ba batasan mene ne jindaɗi ba abunda kawai ta buɗi ido ta tarar shine wahalar rayuwa, tabbas rashin mahaifiya babban giɓine a rayuwa domin da tanada uwa da tasamu sauƙin wani abun amma ita bata tadda tata mahaifiyarba dalili kuwa sanadiyyar haihuwarta Allah ya karɓi ranta dunga sanda aka haifeta har zuwa yanzu babu wani abu mai daɗi cikin labarin rayuwarta, da waɗannan tunanin bacci ya sake awon gaba da'ita....... Fitowa tayi da shirinta na tafiya makaranta, kallonta Mami ta yi ta ce "Shareefat kiyi sauri fa karki makara" Toh ta ce sannan ta ajiye cup ɗin tea ɗin ta ce "tom Mami bye" Murmushi Mami ta yi ta ce"bye dear Allah ya tsare" waje tayi tana cewa Ameen.... A firgice ta miƙe tsaye dalilin ruwan sanyin da taji an watsa mata, tsayawa tayi jikinta na kyarmar sanyi domin lokacin weathern sanyi ake tana mata wani shegen kallo ta ce "zaki zo ki wuce ko saina bigeki" ahankali ta ratsa ta gefenta ta fita jikinta sai ɗiga yake, tulun ruwan ta ɗauka kawai tayi waje...... Tunda ta fito yake kallonta har ta ƙaraso gabansa sosai yarinyar take bashi tausayi yana kallonta ganin yanda take rawar sanyi yasa ya ce" Jiddo meyasa zaki jiƙa jikinki a wannan sanyin?" sunkuyar da kanta kawai ta yi tana goge hawayen fuskarta, ganin babu mutane dayawa wajen yasa ya ce" ina zakije?" bata kalleshi ba ta ce" ruwa zan ɗebowa Ammi" girgiza kai ya yi dan tsananin mugunta ce tasaka wannan aiken da sassafe ya ce "toh muje na raka ki" sai a sannan ta ɗago ta kalleshi da idanunta da sukayi Ja ta ce" kabarshi kawai ngd" murmushi ya yi ya ce" karki damu Jiddoh muje" bata kuma magana ba tayi gaba yana binta abaya har suka ƙaraso kogin. Karɓa tulun ya yi ya ɗebi ruwan sannan ya ɗora akafaɗarsa yana mata murmushi ya ce" mu tafi" toh kawai ta ce ya yi gaba tana binsa a baya, tana ganin sun kusa zuwa gidansu ta kalleshi ta ce" kabani kar Haule ta ganka" bai yi mata musuba saboda yana guje mata a doketa ya miƙa mata ruwan ya ce "kin ci abinci kuwa?" ɗaga masa kai ta yi kawai sannan a hankali cikin cool voice ɗinta ta ce" nagode Laminu" murmushi ya yi kawai sannan ya juya ta tafi........ Tana shiga ta tararda Baffa tsaye yana tambayarta da gudu ta ƙarasa wajensa ta tsaya tana kallonsa dan rabon da tagansa har ta manta, kallonta ya yi ya ce" Hauwa'u daga ina kike?" tana murmushi ta ce" Baffa na ɗebo ruwane" kallon Ammi ya yi ya ce" yanzu Hanne wannan abun ya dace da sassafe zaki aiketa ɗiban ruwa kuma ita kaɗai ina ita Haulen?" wani kallon sheƙeƙe tamasa sannan ta wani karkace baki cikeda faɗa take faɗin da harshen fulatanci " to bazan aiketa ba naga bacci Haule take kuma ba ƙanwarta bace ai dolene ta taimaka mata, har wani zakace an aiketa da safe idan yawonta ya tashi kasan inda take zuwa" girgiza kai kawai ya yi ya kalleta ya ce" jeki ki zauna" tafiya tayi kamar yanda ya ce mata ta zauna kan tabarma shikuma ya juya ya fita..... Yana fita yayi hanya wani ɗan ƙaramin garke, yana shiga ya tsuguna jikin wata saniya ya tatsi nononta yana gamawa ya fito. Inda ya barta nan ya sameta amma banda Ammi dan tayi shigewarta bukkah, zama ya yi gefenta yana kallonta ya ce" karɓi kisha kinji" batayi musuba ta karɓa tunda ta ɗaga kanta bata saukeba sai da ta shanye nonon tass sannan ta ajiye kwaryar, kallonta yake cikeda tausayawa yasan batada kwanciyar hankali kwata-kwata kuma haƙiƙa da yasan inda zai kaita da tuntuni ta bar wajen. Kallonsa ta yi ta ce" Baffana" murmushi ya yi mata ya ce" na'am Hauwa'u " ta ce "Ka bani labarin Ammina Baffa" Shuru ya yi bai ce mata komai ba ta kwaɓe fuska a hankali ta ce" Baffa me kake tunani?" juyowa ya yi yana kallonta taga hawayen kwance akan idanunsa, sosai hankalinta ya tashi ta shiga goge masa tana cewa "Dan Allah Baffa kayi haƙuri bazan sake tambayarka ba kaji" hannun da take goge masa ya riƙe yana kallonta sosai taga ya saki murmushi, tsayawa ta yi tana kallonsa dan ba ƙaramin kyau murmushin ya yi masaba kasancewarsa asalin bafulatani, ya ce "Aduk sanda na kalleki sai naga kamar Hauwa'u ce gabana, domin babu abinda kika manta nata da baki ɗaukoshiba yanda kike da haƙuri haka take koda cutarta kake kuma tasan cutarta kake bazata taɓa nuna makaba, sannan bata riƙo a rayuwarta tana iya yafe laifi duk girmansa na tabbata Hauwa'u ƴar Aljanna ce, inaso ki ɗora daga inda kika tsaya Hauwa'u kisani babu wanda aka taɓa zalunta kuma Allah ya barshi haka ki cigaba da haƙuri kinji watarana sai labari" Kuka kawai take ta gyaɗa masa kai a hankali ya fara goge mata hawayen yana murmushi yace" Allah ubangiji ya jiƙan Hauwa'u" ta ce" Ameen"..... Wajejen ƙarfe sha biyu tana zaune cikin garken shanun nasu bata damu da yanda jikinta ya ɓaci ba, dan babu inda takejin dadi sai wajen waɗannan dabbobin indai Baffanta bayanan. Fitowa tayi tana kalle-kalle sai kuma ta ƙaraso gabanta tana kallonta ta ce "Kee Jiddoh kizo inji Ammi" bata jira amsarta ba ta juya ciki abinta. Tashi Jiddah ta yi ta shiga cikin gidan nasu, zaune ta sameta tana dama fura ta tsuguna gabanta cikin ladabi ta ce "Ammi gani" kallonta ta yi ta ce "Ki tashi kije gidan Arɗo Adda zata aikeki" tashi ta yi batareda ta ce komai ba ta fita daga gidan..... Zaune take kusada Mami tana cin abinci ta ce" toh yanzu kina ganin Sheikh zai amince ya auri Nihal kinfasan halinsa Mami" kallonta Mami ta yi ta ce "Ai ni ce na haifi Heesham ba shine ya haifi kansaba kuws this time around dole ne ko yana so ko baya so ya yi abinda nace" taɓe baki Shareefat ta yi ta ce "Kindai san halinsa wlh kuma abinda yakeso shi za'a yi inda Dad na nan" girgiza kai Mami ta yi ta ce " dole ne ya yi abinda na ce ko shi babanku bai'isa ya hana ba" dariya Shareefat ta yi ta ce" Hajiya Mami kenan, ai ya cemin gobe ma zai dawo Nigeria" "me zai kawoshi?" Ta ce" maybe Dad ne ya yi kiransa amma nidai ba cemin ga abinda zai dawo yiba kindai san yaya Sheikh" sallama da akayi ne yasa suka yi shuru, zama ta yi gefen Shareefat sannan ta ce" Mami ina yini" cikin sakin fuska Mami ta ce "lpia lao Nihal ya Mommyn taki?" ta ce " tana nan klao tace tana gaisheki" murmushi Mami ta yi ta ce" ina amsawa" sannan ta tashi ta hau sama. Kallonta Shareefat ta yi ta ce " sirikarmu" dariya Nihal ta yi ta ce" kinga ranki zai ɓaci tom" murmushi Shareefat ta yi ta ce" har na ganoku ranar wow wayaga kyau da kyau" harararta ta yi ta ce" banson irin wannan rashin mutunci ina wani kyau?" tashi Shareefat ta yi ta ce "plx muje ciki"....... Kallonsa take har ya gama shiryawa ya kalleta ganin irin yanda take kallonsa yasa ya yi murmushi ya ce" mene ne Hauwa'u?" kwaɓe fuska ta yi ta ce" dan Allah Baffa karka daɗe kaji" shafa kanta yayi sannan ya ce" in sha Allah Hauwa'u, amma dan Allah ki ƙara haƙuri kinji komai zai zo ƙarshe da yardar Allah" toh ta ce sannan ta ɗaukar masa kayansa ta ce" muje na rakaka hanya Baffa" daga haka ta yi waje. Suna zuwa ƙarshen hanya ya kalleta ya ce" Hauwa'u ki koma kinji" murmushi ta yi sai kuma hawaye ya biyo bayansa ya kalleta ya ce "Banson kina wannan kukan kamar zan mutu?" ta ce" Baffa a dawo lpia Allah ya tsare ya kiyaye" ya ce" Ameen Allah ya albarkaci rayuwarki" tana murmushi ta ce " Ameen. Tsayawa ta yi har saida ya ɓacewa ganinta sannan ta juyo ta kama hanyar gida, a hanya taga wani ɗan abun wuya ƙarami mai kyau ɗauka tayi tana kallonsa dan tabbas tasan na Baffa ne ya yardashi saboda a wuyansa yake sakawa, ɗaurawa tayi a wuyanta ta ce" idan Baffa ya dawo saina bashi abinshi" sannan ta cigaba da tafiyarta tana ƴan waƙoƙinta..... A hanya ta haɗu da Laminu yana ɗiban kara dan kunna wuta, tana murmushi ta ce" bari na tayaka" girgiza kai ya yi ya ce " haba Jiddoh kina mace kuma ke zaki tayani" haɗe rai ta yi ta hau ɗeban waɗanda ya rage tayi gaba ta barsa wajen, murmushi kawai ya yi sannan yabi bayanta...... Hayaniyar da ya ziyarci kunnenta yasa ta buɗe idanunta a hankali, mamaki ta yi ganin har gari ya waye kuma Ammi batazo ta tasheta ba, ta miƙe jin kamar hayaniyar ƙaruwa take ta fito daga cikin bukkar tata kallon ko'ina tayi amma bataga alamar Ammi ko Haule ba yasa tayi waje dan ganin meke faruwa..... Mutane ta hango sunyi ƙawanya sun zagaye abu amma bata ce ka abinda suka zagaye ba, hakan yasa ta ƙarasa wajen cikin tafiyarta a hankali kamar koda yaushe. Tana zuwa taji kamar ana kuka mutanen na ganinta suka matsa mata hanya, kwance ta gansa cikin jini kana ganinsa kasan kasheshi akai, da gudu ta ƙarasa wajen ta tsuguna tana sake buɗe idanunta dan tabbatar da abinda tagani, shafa fuskarsa tayi tana kallonsa kamar mahaukaciya muryarta na rawa ta ce "Ba..Baff.Baffana" sai kuma ta fashe da wani raunataccen kuka kamar ranta zai fita ta ɗago tana sake kallonsa a karo na biyu dan gani take kamar a mafarki ta ce "Baffa ka tashi kaji kadaina irin wannan wasan kaji, nasan kana jina katashi kar nayi kuka" shuru taji babu amsa hakan yasa hankalinta ya sake tashi sai kuma ta miƙe da gudu dan kafin takai inda zata ta yanke jiki ta faɗi kasa..... Share it plx. [3/4, 22:15] 🥰Nanameera🥰: https://chat.whatsapp.com/LSYEkQgVkLKDQyheA6YWH4 *🌹SHEIKH HEESHAM🌹* *Royal Star Writer's Association* Nanameera. 02. Farka warta kenan ta tashi zaune tana kallon cikin bukkar da take, tashi tayi ta fito tsakar gidan nasu ta tararda mai gari zaune sai Arɗo sai kuma wani abokinsu, ƙarasowa ta yi ta tsuguna tana kallonsu dan gani take kamar zataga Baffanta a cikinsu, ganin yanda take binsu da kallo yasa Arɗo ya ce" Jiddoh tashi ki tafi wajen Adda zata baki abinci" tashi tayi jiki a sanyaye tayi waje..... Kusan sati ɗaya da mutuwar Baffa kenan kuma sai a yanzu takejin mutuwar sabuwa mussamman yanda batada kowa da zata ce wannan natane ko zaiji tausayinta babu dangin Uwa dan bata taɓa ganinsu ba dangin uban kuma su Arɗo ne dan shi kaɗai ya rage masa ɗan uwa, babu wata wacce zata bata shawara ko kuwa ta rarrasheta kullum sai dai ka ganta cikin shanu tana zaune dan sunfi ɗebe mata kewa. Haule ce ta fito tana shan fura ta kalleta dan rabonta da abinci tun shekaranjiya kallonta ta yi ta ce "Jiddoh zaki sha?" Gyaɗa mata kai tayi ta harareta ta ce "mayya to ko zaki mutu bazaki sha ba" tana gama faɗin haka ta juya ta koma ciki. Shuru Jiddah tayi tana tunani haka zata ƙare rayuwarta har ta mutu babu wani abun arziƙi?, haka zata zauna har yunwa tayi ajalinta?, zama ya yi gefenta ta ɗago a ɗan firgice tana kallonsa. Murmushi ya sakar mata ya ce "Gani nayi kin zauna kinyi shuru shine na ce bari nazo na tayaki zama" shuru tayi dan ita yanzu magana sai ta kama take yinta ya ce" Jiddoh zaki aureni?" da sauri ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta ya ce "idan har kin amince zanwa Baffana magana Jiddoh kuma nasan bazai ƙiba" share hawayen fuskarta tayi a hankali ta miƙe batace komai ba tabar wajen, kallon kawai ya yi dan shi harga Allah tausayin Jiddoh yake kuma zai cigaba da faɗa mata har ta amince ya aureta...... Wata irin azababbiyar yunwa ce ta tasheta daga baccin buɗe idanuwanta tayi wadanda ko buɗuwa sosai ba su yi saboda tsananin yunwa, fitowa tayi daga cikin bukkar batareda taji tsoron komai ba har ta fito daga cikin gidan nasu, garin ya yi tsit babu abinda kake iyaji sai kukan karnuka amma kwata-kwata Jiddah bataji tsoron wannan dare ba ta fara tafiya batareda tasan inda ta nufa ba..... Tafiya kawai take cikin garin jimeta sai kace aljana ce, jitayi kamar ta taka wani abu hakan yasa ta tsuguna tana kallon ƙafarta, ƙaya ce ta soketa ta zauna tana cirewa sam bata lurada wadanda suka zo suka mata ƙawanyaba. Ɗago kanta tayi taganta tsakiyar maza sunkai su biyar, ji tayi gabanta ya waɗi abinda kawai yazo ranta shine ranar mutuwarta ce tazo, kasa kwakkwaran motsi tayi har sannan su kuma kallonta suke. Wani daga cikinsu ne ya ce "Me muke jira kawai mu aikatata mana lokacifa na ƙurewa kuma munada yawa" Batayi zaton yanda zuciyarta ta buga ba mutuwa zatayi ba amma sai taga ta samu kanta da kallonsu dukkan ninsu ƴan fulani ne kamar ta kuma duk basuda wani jiki, batayi aune ba taji sun fara janta har cikin wata bukka ƴar madaidaiciya...... Banda tsuma babu abinda jikinta keyi amma kwata-kwata ta kasa kuka sai kallonsu take dan ta tabbatar da yau zatabi Baffa da Amminta...... Fuskokinsu ɗauke da annuri suke kallonta dan gani suke sun samu nama a banza, ɗaya daga cikinsu ne ya fara cire rigarsa ɗayan ya kalleshi ya ce "Kai bangane me kake nufi ba" Harararsa ya yi ya ce" nufi nake ni zan fara" wani mugun kallo na ukun ya yayi masa ya ce"_ kama isa ai aradu nine nan zanfara" wanda ya tsaya daga bakin bukkar ne yazo duka ya hankaɗesu ya ce "Tunda nine nake muku gadi ni ne wanda zai fara saina koma wajen zamana, cecekuce suka fara akan wanda zai zama na farko hakan yasa suka fara faɗa i junansu, fita sukayi daga cikin bukkar sunata faɗace-faɗace...... Zama tayi da farko sai kuma wata zuciya ta raya mata "ga dama kinsamu kawai kiyi guduwarki bai kamata ace a cikin nan kika mutu ba" da wannan tunanin ta fara kalle-kalle ai kuwa tayi sa'a daga can ƙarshen bukkar ta ɗan yage, da sauri ta ƙarasa wajen dukda batada wani kwari amma haka tayi jarumta tana zuwa ta saka kanta ciki amma inaaa bazata iya fita ta ciki ba. Fashewa tayi da kukan baƙin ciki ta haɗe hannanyenta biyu waje guda tana kuka ta ce "Allah na roƙeka ka taimakeni nabar nan wajen da mutuncina dan darajar Annabi" ta ƙarasa maganar tana rushewa da kuka, har sannan kuma tana jiyo hayaniyarsu suna faɗa kamar ba dare ba..... Sake gwada fita tayi amma still taji ta kasa, can wata dabara tazo mata ta zauna ta fara kakkarya karan jiki da hannunta kasancewar tsohuwar bukkah ce yasa duk inda ta karya yake karyuwa saida tayi hanya data tabbatar zata isheta ta fita sannan ta saurara. Tana ƙoƙorin zura kanta ciki suka shigo, da sauri ta ƙarasa fita suka biyota da gudu...... Gudu kawai take babu ƙaƙƙautawa kuma har sannan suma binta suke har ta fara galabaita, batasan sanda ta waɗi ƙasa sumammiya ba......... Tsayawa Driven ya yi da tuƙun, ahankali ya ɗago idanunsa daga kan computern hannunsa juya idanunsa ya yi kamar zai yi magana sai kuma ya yi shuru da bakinsa kusan 2mins amma bai ce komai ba cikeda ladabi driven ya ce "Sheikh motar ta samu matsala kuma gashi dare ya rigada ya yi saidai mu samu wani wajen mu zauna zuwa safiya" Sai a sannan ya kalleshi da fararen idanunsa kuma manya, sunkuyar da kansa drivern ya yi domin duk rashin kunyarka baka isa ka haɗa idanu da Shaikh Heesham ba. A hankali ya buɗe bakinsa yana tasbihi ga ubangiji kusan mintuna biyar sannan ya ce cikin tsantar nutsuwar data gama ratsashi "Allah ya kaimu" Abinda kawai ya furta kenan bai kuma sake wata maganar ba ya lumshe idanunsa masu kyau. Sheikh Heesham Muhammad kenan babban malami a ƙasar saudia yankin larabawa, ya kasance kyakykyawa dan asalin balarabe ne mahaifinsa Alhaji Muhammd ɗan asalin ƙasar saudia ne amma bai rayu acan ba kasancewar duka danginsa mutanen Nigeria mahaifiyarsa ta haifeshine a ƙasar dalilin zuwa omrah. Sanda aka samu cikin Sheikh Heesham sai mahaifiyarsa Hajiya Amina ta tafi saudia dan rainon cikin jikimta har kuma ta haihu ƙasar hakan yasa shima ya kasance indigin na ƙasar saudia saboda haka sanda ya fara tasawa sai mahaifinsa ya kaishi karatu ƙasar, ya kasance ya rayu a ƙasar tun yana ɗan karamin yaro har girma shiɗin likitane gefe guda kuma babban malami a ƙasar. Wannan shine ƙadan daga tarihin rayuwarsa.. Ganin dare na ƙara yi yasa drivern ya ce "Sheikh ko zamu samu wani gurin mu zauna?" Ba zaka taɓa cewa da Sheikh Heesham ake magana ba dan ko kallonsa bai yiba bare ya saka ran zai bashi amsa saima cigaba da danna cazbahar hannusa da yayi.. Hadarine ya haɗo ganga-ganga kuma kana gani kasan ba ƙaramin ruwane zai sauka ba, ɗaya daga cikin securities ɗinsa dake ɗaya motar ne ya fito yana tafiya kamar wani zaki yazo gaban motar ya sunkuyar da kansa ya ce "Sir wannan hadarin zai iya sakawa ayi ruwa mun samu wani waje zaka je ka zauna saboda lafiyarka" Sai a sannan Sheikh ya kalleshi amma bai ce komai ba, buɗe masa motar ya yi yana kallonsa. A hankali kuma cikin nutsuwa ya zuro ƙafarsa waje sannan ya fito daga motar yana gyara zaman al-kyabbar jikinsa ya ce "Ya Allahu" Shine abinda ya furta yana sake kallon yanda garin ke yin duhu na haɗowar hadari sannan ya fara tafiya yana goya hannunsa a bayansa.... Wata bukkah ce suka nuna masa ya sunkuya domin kwata-kwata bukkar batayi rabinsa ba, zama ya yi kan carpet ɗin da suka shimfiɗa masa kamar kuwa jira ake ruwan ya fara sauka da ƙarfinsa... Ba ƙaramin ruwa akayi a jimeta ba ko'ina ya yi daɗin gwanin ban sha'awa ganyayyaki da shuke-shuke duk sunyi kyau, yanayi ne wanda zai sanyaka cikin nishaɗi da annashuwa haka kuma har Allah ya wayi garinsa..... Zaune yake inda ya yi sallar domin bai iya bacci ba yana azkar ɗinsa wani guard ya shigo ya sunkuya cikin girmamawa ya ce "Barka da safiya Shaikh!" Ba tareda ya kalleshi ba ya ce "Barka" Abinda kawai ya iya furtawa kenan, guard ɗin ya ce "Sir ya kamata mu tafi dan jirgin ya kusa tashi" Batareda ya yi magana ba ya miƙe yana ambaton sunayen Allah a ransa kamar koda yaushe ya yi waje..... Sosai take mamakin inda taganta kwance, ahankali ta miƙe zaune tana kallon kusan duk mutanen rugar da suka zagayeta ana ƴan ƙananun maganganu, mai garin ne ya fito yana kallon kowa ya ce "Ina fatan kowa ya shaida abinda wannan yarinya ta aikata?, saboda haka za'ayi mata hukunci daidai da laifinta saboda kada ƴan baya suce zasu kwaikwaya " gyaɗa kai duk suke alamar gamsuwa da abinda ake faɗa d'in ita kuwa sai idanuwa take binsu dashi dan bata gane inda zance ya dosa ba.... Wata zabgegiyar bulala aka ɗauko irin wacce suke amfani da'ita idan za'ayi shaɗi tasha manshanu sai kyalli take, kallon bulalar kawai take dan batasan me zasuyi da itaba, mai gari ne ya kalli mutumin ya ce "Zaka yi mata bulala 80 shine hukuncinta da kuma kora daga cikin garin nan". Karɓar bulalar ya yi yana sake gyara zamanta a hannunsa ya ce"za'a riƙetane saboda kar ta wahalar dani?" Girgiza kai ya yi ya ce " Ai bata isaba dole ta tsaya ayi mata hukunci tunda shi ya zama ɗan iska" Allah sarki Jiddah banda kallo babu abinda take amma zuwa lokacin ta gane inda maganar tasu ta dosa, wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata ta saka hannunta tana sharewa Allah ya sani bata aikata komai ba kuma batasan ya akayi ta zo wajen nan ba amma wa zata faɗawa ya yarda da ita?!, babu.......... Tafiya kawai suke acikin motar, idanunsa a lumshe suke dan wani azabbaben ciwon kai yake ji, ji yayi zuciyarsa tayi wani kyakyawan bugu ya buɗe idanuwansa yana kallon garin daidai nan kuma ya hango wasu cuncurundon mutane kuma fulani ya yinda har sannan yake jin bugun zuciyar na sake tsananta. "Stop the car" Ya faɗa ba tareda ya kalli drivern ba cak kuwa ya tsaya yana juyowa dan yasan ba ƙaramin abune zai sa Sheikh ya magantuba. Kamar wanda akama tilas haka ya kama murfin motar ya fito, nan take duk guards ɗinsa suka fito kowanne ya yi cirko-cirko dashi... Tafiya ya fara yi torward direction ɗin da yake hango mutanen, yana kusantar wajen yanajin bugun zuciyar na ƙaruwa fiyeda na baya a haka har ya ƙaraso..... Ganin balaraben mutum yasa duka suka dare masa hanya, a hankali ya matsa har inda yarinyar ke kwance sai zabga mata bulalar ake, duk jikinta jini ne kana gani kasan ba ƙaramin duka suka mata ba.. Ba tareda ya yi magana ba ya ƙarasa wajenta yana kkallon mutumin, ahankali kuma ya zare bulalar daga hannunsa cikin yanayinsa nason kamewa ya ce "Ka bari babu kyau zalunci" Sakar baki sukai dan basu ɗauka ya iya hausaba, mai garin ne ya ƙaraso gabansa wani guard ya daka masa tsawa "leave that place" Zabura ya yi Sheikh Heesham ya riƙoshi yana kallonsa ya ce "Mene?" Cikin inda-inda ya fara faɗin "Daman..Dama..Daman wannan yaron ya mana laifi ne an kamashi da maza da daddare kuma hukuncinsa shine bulala 80 sannan a koreshi daga garin" Kamar bazai magana ba sai kuma ya ce "Ku rabu da'ita" Girgiza kai ya yi ya ce "ai saidai ka tafi da'ita dan indai tana garin nan to sai angama mata bulalar nan kuma bulala 20 aka mata" Shuru Sheikh Heesham ya yi sai kuma ya sakeshi ya juya dan komawa mota.... Da gudu arɗo ya bishi kafin ya isa motar ya cimma sa cikin magiya ya ce "Dan Allah dan Annabi yaro ki taimaka ki tafi da Jiddoh ko zata samu rayuwa me kyau zata mutu anan aradu indai suka gama yi mata wannan bulalar to bazata tashi ba, ki taimaka yaro" Ya ƙarashe maganar yana kuka... A nutse ya saka tattausan hannunsa ya ɗago arɗo yana kallonsa sai kuma ya yi murmushi ya ce "Shikenan zan kula da'ita" Ajiyar zuciya arɗo ya sauke sannan ya ce "Amma baza su barka ka tafi da'ita ba har sai ka aureta" Da sauri ya kalleshi sai kuma ya girgiza kai alamar bai yarda ba. Tsugunawa arɗo ya sakeyi ya ce "taimakawa zakayi idan kuka bar garin nan sai ka saketa kaji yaro" shuru Heesham ya yi arɗo ya ce "Naga kayi kalar taimako yaro ka taimakawa marainiyar nan batada kowa sai Allah sai kuma kai yanzu" Bazai iya cewa A'a ba dukda yasan bazai zauna da ita matsayin mata ba amma zai taimaketa yayi jahadi....... Murmushi ya yi yana kallon Arɗo ganin yanda yake kuka da idanunsa ya ce "Shikenan na amince"....... Kama hannunsa arɗo ya yi jikinsa har rawa yake suka koma wajen.... Yana kallon mai gari ya ce "Zai tafi da'ita" "Amma yasan saidai ya aureta?" Gyaɗa masa kai ya yi ya ce" shikenan" Anan aka ɗaura auren Sheikh Heesham Muhd da Hauwa'u Ahmad sadakinma zoben hannunsa suka karɓa....... Kallonsa Ardo ya yi ya ce "Na yarda dakai yaro nasan zaka kula da rayuwar Hauwa'u kada ka barta ta yi kuka kaji" Riƙe hannunsa Sheikh ya yi ya ce "Har ƙarshen rayuwa" Kwance take dan har sannan bata farfaɗoba ya saka tattausan hannunsa ya ɗauketa yana tafiya har suka isa cikin motar, tsayawa arɗo ya yi yana musu addu'a har suka ɓacewa ganinsa......... Share it plx. *Paid book #500.* *SHEIYK HEESHAM* [3/4, 22:15] 🥰Nanameera🥰: https://chat.whatsapp.com/LSYEkQgVkLKDQyheA6YWH4 *🌹SHEIKH HEESHAM🌹* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Nanameera. 03. Tafiya kawai suke inda shi kuma tunaninsa ya ke wani wajen daban, "Ya Allahu, ya Rahmanu" Shine kawai abinda bakinsa ke furtawa har suka ƙaraso filin jirgin.... A vip yake ya kishingiɗa da bayan kujera idanunsa a lumshe shi kaɗai yasan iya abunda ke damunsa gashi kuma ciwon kansa nason hargitsashi, ahaka yana wannan tunanin bai san bacci ya ɗaukeshiba dan baccin Sheikh sai dai ɓarawo...... A nutse yake tafiya guards ɗinsa na biye dashi har ya'isa gaban motar suka buɗe masa, zama ya yi yana kiran sunan Allah a cikin ransa kamar koda yaushe. Ganin drivern yaƙi tafiya yasa ya ce "lpia?" "Sheikh daman yarinyarce ba'a ɗauko ba" Sai asannan ya tuna dan kwata-kwata ya manta da wata yarinya ya ce" ina take?" tana can kwance har yanzu bata farfado ba za'a saka guard ya ɗauketa ya kaita asibiti" Bai ce komai ba ya sauka daga motar ya bisa da kallo yana daɗa jinjina hali irinna Sheikh Heesham..... Kwance ya tarar da'ita har sannan kuma batada niyyar farfadowa, a hankali ya sanya hannayaensa duka biyun ya ɗauketa, ji yayi kamar bai ɗauki komai ba saboda rashin nauyinta ni kuwa nace ya za'ayi tayi nauyi??????.. Kai tsaye asibitin Abdullahi wase dake nassarawa ya kaita, sosai sukayi murna ganin babban malami a asibitin cikin mutuntawa kuma suka karɓeta shikuma ya shiga mota dan tafiya gida...... Tsaye take saman benen gidan taga motocin na reton shigowa, da gudu ta sauko ƙasa tana kallon Mami ta ce" Mami Sheikh" Murmushi Mami ta yi ta ce" ai naji ajikina ya dawo tun ɗazu" bata rufe baki ba ya shigo parlon ɗaukeda sallama, da murmushi afuskarsu suka amsa masa sannan ya zauna kan kujerar yana kallonsu ya ce "Mami ina yini" "lpia lao Heesham ya hanya?" Ya ce"lpia lao Alhamdulillah" da murmushi a fuskarta ta ce" yaya ina yini" "lpia lao ya karatu?" Shine abinda ya tambayeta sannan ya miƙe ya ce" zan watsa ruwa" daga haka ya shige apartment ɗinsa....... Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da hancinsa ya shaƙi daddaɗan ƙamshin airfreshner da akayi amfani da'ita a ɗakin, a hankali ya shige bedroom ɗinsa yana jan jiki dan ya gaji sosai........ Zama ya yi gefen royal bed ɗin dake ɗakin, ko ina tsaf yake gwanin sha'awa kuma yasan babu wanda zaiyi wannan aikin sai Mami dukda yasan wajen a gyare yake amma wannan sabon gyarane, ganin lokaci na shigewa yasa ta tashi yana sakin ajiyar zuciya a karo na babu adadi ya shiga banɗakin...... Fitowa ya yi jikinsa yana ɗiga alamun wanka sumar kansa ta zubo har fuskarsa, ga wani faffaɗan ƙirjinsa sai gashi da ya yi luf akai a hankali yake goge jikin nasa kamar wanda kwai ya fashewa ajiki har ya gama sannan ya sanya wasu riga da wando farare sol dasu ya shafawa sumar kansa mai sannan ya tufketa da ribon ta zubo har bayansa, sosai take damunsa kuma ahakama ana rage masa ita, ya taje gemunsa wanda yake dogo kuma atsaye irinna riƙaƙƙun malaman nan. "Alhamdulillah" Shine abinda ya furta sannan ya hau kan royal bed ɗin nashi ya kwanta nan da nan bacci ya yi awon gaba dashi......... A hankali ta fara ƙoƙarin buɗe idanunta waɗanda suka mata nauyi sosai, sosai ta firgita ganin inda take dan bata taɓa ganin makamancin irin wannan waje ba a rayuwarta iya kacin abinda tasani bukka, sai kogi. Yunƙurin tashi tayi amma taji wata irin azaba ta ziyarci kwakwalwarta dole ta haƙura ta cigaba da kwanciya nan take kuma duk inda jikinta ya fara mata ciwo, batasan ina take ba kuma batasan dalilin kawota wajen ba duk zatonta ma ko siyar da'ita su Ammi sukai, wasu hawaye ne suka wanke mata fuskarta babu abinda take tunawa sai irin yanda aka dunga dukanta akan laifin da bata aikata ba, tunanin hakan yasa ta sake fashewa da kuka dan ita kaɗai tasan yanda takeji a zuciyarta...... Murmushi ta yi tana kallonsa ta ce "Laaa yaya Bilal sai yau kazo?" Fuskarsa a sake ya ce" Eh mana ina Sheikh?" Dariya ta yi ta ce"daman nasan saboda Sheikh kazo wlh Mami tana ta zancenka amma gashi kanaji ance Sheikh ya dawo shine kazo, ai shikenan ina Junior?" Murmushi ya yi yana shafa kansa ya ce "wlh yana gida ina Mamin?" "batanan taje gidansu Nihal" Ta bashi amsa gaba ya yi yana cewa " ok ina nan har ta dawo ai"....... Zaune ya same shi yana danna system kana gani kasan abu mai muhimmanci yake yi, zama ya yi kan bedside drawer ɗin yana murmushi ya ce " su Sheikh manya wato shine sai yanzu kaga damar zuwa ƙasar ko?" Shuru yayi masa kamar bdashi yake ba, girgiza kai Bilal yayi dan yasan hali ya ce "Wai kai harnima ɗaukemin kan ka keyi?" Shuru Shaikh ya yi kamar bazai magana ba sai kuma ya ce" amma kana sane da bakayi sallama ba" Kwaɓe fuska ya yi ya ce" sorry i forget assalamu alaika" "Wa alaika salam" Shaikh ya amsa masa, murmushi ya yi ya ce" yanzu sai a kulani ko?" Murmushin sa mai kyau ya yi dan yana matuƙar girmama abotar dake tsakaninsu dukda cewa shiɗin ɗan uwansa ne dan ɗan ƙanwar Mami ne kuma bazai wuce shekara 35 ba dan kusan tare aka haifesu da Sheikh Heesham......... Hira suka fara yi akan rayuwarsu amma duk rabin hirar Bilal ke yinta dan shi Sheikh sai Umh, un'un, har lokacin kiran sallah ya yi. Miƙewa Shaikh ya yi ya shiga toilet dan ɗauro alwala domin shine yake jan sallar masjid ɗin gidan nasu............ Zaune suka tadda Mami suna taɓa hira da Shareefat, Bilal ya ce "Mami ina yini" harararsa tayi ta ce" yana gidan biki, sai yau kaga damar zuwa?" shafa kansa ya yi yana murmushi ya ce" sorry Mami wlh abubuwane suke riƙeni" ta ce" amma ai dayake ɗan uwanka ya dawo gashi na ganka yanzu babu abinda ya riƙeka kenan" kasa magana ya yi sai sunkuyar da kansa ya ce banda dariya babu abida Shareefat ke yi ta ce "Toh yanzu ba gashi yazo ba Mami?" ta ce" yimin shuru kina goyan bayan yayanki kawai" "Sheikh akawo maka abinci?" Girgiza kai ya yi ya ce "azumi" ta ce" toh Allah ya haɗamu a ladan".......... Shigowa ya yi ya ce" Sir yarinyar ta farka" "Wace yarinya?" Mami ta tambaya, tashi Sheikh ya yi yay gaba batareda ya amsa tambayar Mami ba, Bilal ne yabi bayansa yana cewa "Wai bazaka tsaya niba" Driver sit ya zauna bakinsa ɗaukeda addu'a ya yiwa motar key ya fara tafiya cikin nutsuwa, ganin yanda yake tafe slowly yasa Bilal ya ce" wai dan Allah kayi sauri mana" kamar bazai magana ba sai kuma ya ce" so kake natafi da gudu wani ya mutu?" "wane zai mutu?" murmushi ya yi ya ce" ni mana" da mamaki Bilal ya ce" Eh lallai kaga kuwa bai kamata ka mutu ba bayan baka tara iyaliba, wai yaushe zakayi aure ne?" "sanda Allah ya yi" Sheikh ya bada amsa. Murmushi Bilal ya yi ya ce"wlh inada wata yarinya zan baka ka aura plx" girgaza kai Sheikh ya yi sanda yake parking ya ce" Allah ya tsare" dariya ya yi ya ce" au hakama zakace?" bai ce masa komai ba ya sauka daga motar shima ya fito......... Tafiya kawai yake amma shi yasan yanda zuciyarsa ke wani irin bugawa ya ce" ya Allahu ya rahmanu" shine abinda yake furtawa har ya kai bakin ƙofar ward ɗin, a hankali kuma ya murɗa kofar bakinsa ɗauke da sallama........ *SHEYKH HEESHAM* *Paid Book 500#*[3/4, 22:15] 🥰Nanameera🥰: https://chat.whatsapp.com/LSYEkQgVkLKDQyheA6YWH4 *🌹SHEIKH HEESHAM🌹* *Nanameera*. *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *AMMEY LAYLERH DETA SERVICES* *Azo asai DATA kan farashi mai sauqi, cikin rahusa👌🏻🤗* *Data* *Available* *MTN* *AIRTEL* *GLO* *9MOBILE* *MTN* 500MB-175 1GB -350 2GB - 700 5GB - 1750 10GB -3500 *AIRTEL* 500MB - 175 1GB - 350 2GB - 700 5GB - 1750 10GB - 3500 *GLO* 500MB - 175 1GB - 350 2GB -700 5GB - 1750 10GB - 3500 *9MOBILE* 500 - 175 1GB -350 2GB - 700 5GB - 1750 10GB - 3500 Account number: 3206656358 Account name: Maryam Nasiru first Bank *MORE Information 08104493215* Paid book Free page 4. Kallonsa kawai take tunda ya shigo, da mamaki Bilal yake kallon yarinyar dan kwata-kwata bai taɓa ganin yarinyar ba kuma baisan inda Sheikh ya samo yarinya mace ba, murmushi ya yi mata ganin yanda take kallonsa ya ce "Sannu ya jikin naki?" Tana kallonsa ta ce" da sauƙi" Doctor ne ya shigo yana kallon Sheikh cikeda girmamawa ya ce " Sir za'a iya discharging nata saidai a dinga kula da lafiyarta" jinjina kai kawai Sheikh ya yi sannan ya ce" a fito da'ita ina jiranta " daga haka ya juya ya fita, da kallo kawai Bilal ya bisa har ya fita sannan ya kalli Jiddoh ya ce" taso mu tafi dear" batayi musu ba ta tashi tana tafiya ahankali saboda har sannan jikinta babu wani kwari ta bi bayansa suka fita......... Zaune suka tadda shi cikin motar yana danna cazbahar hannunsa, kallonsu kawai ya yi har suka shiga motar sannan ya yi mata key ya cillata kan titi............ Murmushi Nihal ta yi ta ce" to ai naga bangansa ba ina ya tafi?" taɓe baki Shareefat ta yi ta ce" wlh dai karki zaƙe dan Sheikh halinsa sai shi" ta ce" nikam ko dukana zai dinga yi inasonsa haka"tashi Shareefat ta yi ta ce "aikuwa zakisha wahala" sannan ta shige toilet....... Kallon makeken gidan kawai take dan gani take kamar ba'a duniya take ba, dan ko a mafarki bata taɓa ganin abu mai kyau irin wannan gidan ba, lura da hakan yasa Bilal ya yi murmushi ya ce" what's ur name?" kallonsa kawai tayi amma bata bashi amsaba dan batasan abinda ya faɗaba ma, ya ce" nace ya sunanki?" sai a sannan ta sunkuyar da kanta ta ce" Jiddah" murmushi ya yi ya ce "masha Allah Hauwa'u kenan?" gyaɗa masa kai kawai ta yi, girgiza kai kawai Sheikh ya yi ya buɗe ƙofar parlon bakinsa ɗauke da sallama........... Murmushi ɗauke a fuskarsa ta ce" welcome back yaya" ba tareda ya kalleta ba ya ce" thank you", sannan ya zauna kan royal sofa ɗin dake zagaye a parlon "Ya Allahu" Shine abinda yake faɗa akaro na babu adadi, tsayawa tayi tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, Shareefat ta ce" yaya ina kasami ƴar fulani?" shuru ya mata kuma daman tasan bazai amsa mata ba yasa bata wani damu ba. Mami ce ta fito daga part ɗinta hannunta riƙe da waya tana dannawa da alama magana mai muhimmanci take, zama tayi kan kujerar batareda ta kallesu ba ta ɗaga kiran da ake mata. Murmushi ta yi ta ce"ok kawai ki barta ta kwana gobe sai ta tafi makarantar tanan" Daga ɗaya bangaren ta ce" tom shikenan Allah ya kaimu" Ta ce" Ameen" sai a sannan ta kallesu kai tsaye kuma idanunta ya sauka akan Jiddarh wacce har sannan bata samu ta zauna ba, da mamaki Mami ta ce "Wannan yarinyar fa?" Kamar bazai magana ba sai kuma ya ce" idan anjima zan miki bayani in sha Allah" yana gama fadin hakan ya miƙe yana sake tattare al-kyabbar jikinsa ya shige ɗaki yana cewa "Shareefat ki kaita ɗakinki ta yi wanka"...... Bai fito ba sai lokacin sallar magrib ya fito cikin wata shadda ash colour ya ɗora al-kyabba orange mara nauyi akai, zaune ya tadda ita kamar yanda ya barta ɗazu babu alamar tayi wankan ko ta sake kayan jikinta. Kallonta ya yi sai kuma ya kalli agogon hannunsa kawai ya yi waje....... Yana shigowa gidan shi kuma ya fito daga masjid ɗin, murmushi ya yi yana zuwa ya shige jikinsa yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya a karo na babu adadi ya furta" Alhamdulillah" shafa bayansa Daddy ya yi yana murmushi ya ce" saukar yaushe Sheikh?" Saida ya raba jikinsa da nasa sannan ya ce" ɗazu na sauka Daddy" murmushi Daddyn ya yi ya ce" sannunka da zuwa ya hanya?" "Alhamdulillah" shine kalmar daya furta yana sakin fuskarsa. Sosai suke kamada Daddynsa dan babu abunda ya raba su suka jera gwanin sha'awa suka shiga gidan............. Zaune suka sake tadda ita amma wannan karan tayi tagumi ita kanta batasan kuka take yiba, da mamaki Daddy ya ce "Wannan yarinyar wace?" murmushi Sheikh ya yi ya ce" zanyi muku bayani later" ok Daddy ya ce sannan ya shige part ɗinsa dan dawowarsa kenan. Kallonta ya yi ya ce" keeee" ɗago kanta tayi tana kallonsa da dara-daran idanuwanta ta ce" dan Allah malam ka maidani rugarmu kaji" kamar bazai ce komai ba sai kuma ya kama hannunta cikin nutsuwa ya yi waje da'ita........ A bakin wani makeken shopping mall ya tsaya sannan ya sauka daga motar, shuru tayi ganin bai ce mata tafito ba kuma bai buɗe motar ba ta zauna kawai tana kalle-kalle.............. Bayani kawai ya gama yi mata sannan ya ce" plx pink, white, coffee colour" cikin girmamawa ta ce "Okay Sir" sannan ta juya dan haɗa masa kayan......... Kayane aka haɗa mata kamar hauka amma duk yawanci abayas ne sai inner wears kala-kala sai mayuka masu kyau da tsada irinna ƴaƴan manyan nan, ni kuma nace idan tana tareda Sheikh ai kuɗi ba'a magana......... Suna tafiya a hanya yana tuƙinsa a hankali ya yinda ta shagalta da kallon kyakkyawar fuskarsa, ajikinsa yaji ana kallonsa ya juya suka haɗa idanu. Murmushi ta sakar masa ya ɗauke kai dan shikam bai shirya haka da'ita ba, ganin bai kalleta ba yasa ta ɗauke kanta tana kallon hanya har suka ƙarasa gidansu............ Banda ƙarar cokula babu abinda ke tashi a parlon kowa ya yi busy banda Sheikh Heesham wanda yake zaune ƙasan carpet yake cin nasa abincin, daga can gefe na hangota ta takure jikinta dan ko abinci takasa ci kuma daman babu wanda ya bata abincin sai Daddy. Kallonsa kawai take dan Allah ya gani wata irin yunwa takeji kamar ta mutu amma babu wanda zata iya tambaya abinci haka tana kallo suka cinye kuma bataci wanda Daddyn ya bata ba......... Yana gamawa ya tashi a nutse ya shige apartment ɗinsa dan kwata-kwata bashida nutsuwa ji yake kamar ba shiba. Suna gamawa ta ce" nifa bangane wannan yarinya da Sheikh ya kawo ba, banson irin hakafa ka sani" murmushi irinna manya Daddy ya yi sannan ya ce" Amina kenan, kinsan ai tunda ya kawota dole akwai wani abu ko, kuma ai bacewa ya yi zata zauna a gidan nan ba bare kice" haɗe rai tayi dan ita arayuwarta ta tsani ganin wanda taba saniba a gidanta tunda wata ƴar aike ta taɓa cutarta, saboda haka bata yadda da duk wanda bata sani ba. Ganin kamar ta tafi tunani yasa ya ce" Aminaa!", a ɗan firgice ta kalleshi ta ce" na'am" "tunanin me kike?" Ɗauke kai ta yi ta ce" nifa tunda ta shigo naji na tsani yarinyar kawai bata yimin ba wlh gwara yazo ya mayar da'ita inda ya ɗaukota" girgiza kai ya yi dan yasan halinta da kafiya ya miƙe ya ce" Allah ya kyauta" Ameen............ Yana gama shiryawa ya yi kwanciyarsa yana lumshe idanunsa dayake jin suna masa nauyi koda yaushe........ Ita kaɗai ce a parlon kuma har sannan batayi wankan ba shurun ne ya mata yawa ta miƙe a hankali tana tafiya a hankali har ta hau kan stairs ɗin benen, tafiya take a hankali dan a tsorace take da benen tunda ba taɓa hawa tayi ba har ta isa ɗakin Shareefat........ Tura ƙofar tayi a hankali, zaune suke suna hira da Nihal ta shigo da sallamarta cikin gurɓatacciyar hausarta ta ce" dan Allah in zauna anan tsoro inaji" ta yi maganar tana langwaɓar da kanta. Kallonta Shareefat ta yi sai kuma ta ce" A'a malama ɗan fita banda wari babu abinda ki keyi wlh bazaki zauna min ɗakiba kisa ya yita wari, sannan duk kayan da Sheikh ya kawo naki ki kwashe su muje na nuna miki ɗaki" tom ta ce sannan ta firfito mata da kayan ta ɗiba itama ta ɗibar mata wasu............. Wani ɗakine a downstairs ɗin gidan wanda babu kowa aciki dan ɗakin ƴar aikinsu ne kuma ta tafi, shiga sukayi tana kallon Jiddarh ta ce" ki zauna anan, amma ki shiga banɗaki kiyi wanka" gyaɗa mata kai kawai tayi, ganin batasan yanda zatayi komai ba yasa ta shiga da ita banɗakin ta nuna mata yanda zatayi wankan da yanda zatayi brush, sannan ta fito............. Kasancewar tanada saurin riƙe abu yasa batashi wahala ba tayi wanka ta fito tana tafiyar ta anutse kamar koda yaushe....... Zama tayi gefen bed ɗin tana ƙarewa ɗakin kallo dan yanda aka gyara ɗakin bazaka taɓa cewa ba ɗakin ɗan gida bane, a hankali ta buɗe ɗaya daga cikin ledojin tana kallo. Rasa wane kaya zata saka tayi ta zaro wata riga dogowa amma batada nauyi pink colour. Sanya rigar tayi wacce tayi masifar yi mata kyau dan tabi jikinta sosai, turare ta gani ta ɗauka tana kallo dukda batasan mene ne ba amma kawai ta fara ƙoƙarin buɗewa,sauran ƙiris ta fasa shi Allah ya taimaka ta buɗe tana kallonsa a ɗan tsorace ta danna wajen fesawar. Ganin yanda yake fitowa yasa abun ya bata dariya ta buɗe baki tana dariya ta ce" lahhh kamar ruwa" ta faɗa tana faɗaɗa fuskarta har saida beauty point ɗinta ya loma. Sosai ta shafa turaren dan har yaso ya mata yawa sannan ta ajiye ta haɗe komai a gefe........... A ɗan tsorace ta hau kan gadon daga gefe ta kwanta ta lumshe idonta nan da nan bacci ya ɗauketa......... Wata irin azababbiyar yunwa ce ta tasheta, ta miƙe tana riƙe cikinta lokaci ɗaya kuma ta fashe da wani irin kuka tana sake riƙe jikin, a hankali ta sauko daga kan gadon ta fito daga ɗakin...... Tafiya kawai take ba tareda tasan inda zata ba, haka har tahau benen, tsayawa ta yi tana ƙarema ɗakunan kallo a hankali kuma ta fara tafiya zuwaga wanda yake kallonta. Riƙe numfashinta tayi saboda wani ƙamshi daya daki hancinta lokacin data buɗe ɗakin, babban parlon ne wanda ya wadatu da kayan more rayuwa, kalle-kalle tayi ta hango wata ƙofar kamar kuwa ana turata taje ta buɗe ƙofar........... Bataga kowa ba sai ƙamshi lokaci ɗaya kuma idanunta ya sauka kansa, kwance yake ya rufe duka jikinsa da blanket dukda an kunna a.c....... Ƙarasawa tayi gabansa ta tsuguna tana kallon fuskarsa wacce bai rufeta ba, wata kyakkyawar ƙara ta saki da tasa ya buɗe idanunsa bakinsa ɗauke da addu'a yana kallonta. Tashi ya yi zaune ganin yanda take kuka kamar ranta zai fita, tattausan hannunsa yasa ys ɗagota ya zaunar gefensa yana magana cikin sanyin jiki ya ce" lafiya?" sake fashewa ta yi da kuka ya kwaɓe fuska yana kallonta ya ce" ki yiwa Allah karki fasamin kai" shuru tayi da kukan tana sauke ajiyar zuciya, sai da yaga tayi shuru sosai sannan ya ce "ke dawa?" kwaɓe fuska ta yi ciki shagwaɓa ta ce" koba yunwa nake jiba" sakar baki ya yi yana kallonta jin akan yunwa take masa wannan kukan ya ce" to kiyi haƙuri saida safe ko" sake fashewa tayi da kuka ta ce" ni wlh zan mutu yunwa nake ji" dafe kansa ya yi dan nema take tasaka shi ciwon kai ya miƙe a nutse ya buɗe frigde ɗin ɗakin...... Babu komai aciki sai kayan marmari sai kuma fresh milk , fresh milk ɗin ya ɗauko mata har lokacin tana riƙeda cikinta. Miƙa mata ya yi shi kuma ya shige banɗaki..... Kafa kanta tayi ta fara sha tana lumshe ido saboda garɗin madarar da yake zuwa har cikin kwakwalwarta, fitowa ya yi bayan ya ɗauro alwala ya kalli inda take, mamaki ya yi ganin ta kwanta tana bacci bayan ta yarda empty robar madarar girgiza kansa kawai ya yi sannan ya yi waje....... Prayermat ya shimfida a parlon ya hau sallolinsa na nafila wanda ƙa'ida ce duk dare sai ya yi su......... *SHEIKH HEESHAM* *Paid Book 500#* [3/4, 22:15] 🥰Nanameera🥰: https://chat.whatsapp.com/LSYEkQgVkLKDQyheA6YWH4 *🌹SHEIKH HEESHAM🌹* *Nanameera*. *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *I Dedicated this book to yhu Aunty Sarauta my nimcyluv, much luv* Paid book Free page 5. Sai wajen ƙarfe 6am sannan ya shigo gidan bayan ya gama wa'azi a masjid ɗin kamar yanda ya saba, kai tsaye ɗakinsa ya wuce yana kiran Allah aransa kamar koda yaushe............ Kwance ya tarar da'ita da alama har sannan bata tashi daga baccin ba, girgiza kansa kawai ya yi dan da alama yarinyar zata wahalar dashi. A nutse ya ƙarasa yana kallon fuskarta wacce ta kwaɓeta kamar zata yi kuka yake yi yana sake riƙe kansa akaro na babu adadi, ahankali ya ɗan bubbaga gefen pillow aukuwa ta buɗe ido kasancewar batada nauyin bacci. Kallonsa take tana murza idanunta dan ta manta inda ma tayi baccin, "Tashi ki tafi" Abinda ya furta kenan sannan ya juya ya shige toilet, shagwaɓe fuska ta yi sai kuma ta miƙe kamar mai tsoron tafiya haka tafara yinta............. Fitowarta kenan daga ɗakin Shareefat ta kalleta da mamaki, ƙarasowa Jiddah ta yi ta mata murmushi, bata amsa mataba haka kuma bata daina kallonta ita dai ta ratsa ta gefenta ta sauka daga benen ahankali dan har sannan tsoronsa takeji..... "lafiya?" Shareefat ta tambaya ganin yanda ta tsaya, murmushi Nihal tayi ta ce" nothing kawai jiranki nake" daga nan ta sauka, ɗaga kafaɗa Shareefat tayi alamar bai dameta ba sai kuma tabi bayanta.............. Kallonsa take har ya gama shiryawa sannan ta ce" wai dan Allah ina zakaje da safen nan dear?" yana saka hularsa ya ce " wajen Sheikh zani zamuje unguwa" Murmushi ta yi ta ce"daman ai tunda Sheikh ya dawo shikenan yanzu ganinka zai mana wahala, to kace masa ina miƙo saƙon gaisuwa" light kiss ya mata a goshi sannan ya ce" in sha Allah, bye" ɗaga masa hannunta itama tayi sannan ya juya ya fita, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta koma bedroom ɗinta........... Zama tayi daga gefen kujera ta rakuɓe bayan ta gaida Daddy dan shine kawai ya amsa, kallonsa Daddy ya yi yace" Sheikh muna sauraronka ina kasamo yarinya?" Ajiyar zuciya Sheikh Heesham ya sauke sannan ya ɗago yana kallon iyayen nasa wanda suma shi suke kallo. Ahankali kuma cikin nutsuwar da tagama ratsashi ya fara basu labari tun daga farko har ƙarshe, abu ɗayane bai faɗa musu ba shine an ɗaura masa aure da'ita...... Ajiyar zuciya Daddy ya sauke amma bai ce komai ba dan haƙiƙa yaji tausayin Jiddah, "Allah ubangiji ya jiƙan iyayenta yasa sun huta, amma bari kaji bazai taɓa yiwuwa ba ta zauna agidan nan ka ɗauki ƴar mutane ka mayar da'ita cikin ƴan uwanta dan banjin zan iya zama da'ita cikin gidan nan" Tunda ta fara magana yake kallonta bashi kaɗaiba harda Daddy, Shareefat, Nihal, Bilal sai kuma Jiddah. Hankalinsa a matuƙar tashe yake amma bazaka taɓa cewa shine ake yiwa maganar ba saboda iya riƙe kansa............ Girgiza kai Daddy ya yi cikin dattako ya ce "Wannan wace irin magana ce Amina?, madadin ace kinji tausayinta kin jata ajiki kamar ƴar da kika haifa shine zakice bazata zauna tare dake ba, toh bari kiji gida dai gidana ne kuma ni nakeda iko da duk wanda yake cikin gidan nan saboda haka matuƙar ina raye to tabbas zan kulada rayuwarta kamar ƴar dana haifa kuma nasan ko bayan mutuwa ta Heesham zai ɗora daga inda na tsaya, kuma wannan umarni ne bawai shawara ba saboda haka take note" yana gama faɗin haka ya kalli Jiddah wacce tayi shuru kanta a ƙasa ya ce" ki saki jikin ki daughter ki ɗauka nima babanki ne da ya rasu, duk abinda kike buƙata ki sanar dani ko Heesham kinji" gyaɗa masa kai tayi sannan ya shige apartment ɗinsa........ Kowa na parlon ya yi shuru sai kallo da ido, ahankali ta miƙe tana kallonsa ta ce "Bazan koreta daga gidan nan ba tunda ba gidana bane kamar yanda mahaifinka ya faɗa amma ka sani babu abinda ya haɗani da ita koda wasa karna kuskura naganta a inda nake idan ba haka ba ran kowa zai ɓaci" fuuuuu tayi benen gidan....... Tashi sukai atare suka tafi ɗakinsu wajen ya rage daga Sheikh, Bilal sai Jiddah. Kuka kawai take a hankali, kallonta Bilal ya yi dan tabashi tausayi sosai yarinyar, kamo hannunta ya yi ya ce" ki daina kuka kinji Jiddah, zaki bini gidana?" gyaɗa masa kai ta yi ya ce" ok ɗauko hijab a ɗaki mu tafi" cikin sanyin jiki ta tashi ta shige ɗakin nata.......... Sai a sannan ya kalli Sheikh wanda zaka ɗauka baya wajen ya ce" zan tafi da'ita, can i?" tashi Sheikh ya yi daidai lokacin ta fito sanye da hijab ɗin yana batareda ya yi magana ba ya kama hannunta a hankali ya fara taka stairs ɗin benen tana biye dashi............. Girgiza kai Bilal ya yi dan daman yasan da kyar ya barshi ya tafi da'ita, ya miƙe kawai ya ɗauki car keys ɗinsa ya yi waje.... Fitowa ya yi daga bedroom ɗin har sannan tana zaune kan kujerar da yabarta tana kuka, dafa kansa ya yi bai ce komai ba ya zauna kan kujerar dake facing ɗinta ya yi mata alama da tazo da hannunsa...... Cikin tafiyarta ta nutsuwa ta ƙaraso gabansa zata tsuguna ya kamo hannunta ya zaunar da'ita kan cinyarsa yana yin baya kaɗan ya ce "kukan na mene?" Turo baki ta yi sai kuma ta sake fashewa da wani sabon kukan, shuru ya yi yana sauraronta har wani runtse idanu yake sabida tsananin azabar ciwon kai. Saida tayi mai isarta da kanta tayi shuru tana sauke ajiyar zuciya, kallonta ya yi cikin kasala ya ce" kin gama?, kin kusa fasamin kai fulani" kwaɓe fuska tayi ta ce" toh ni kamayar dani rugarmu kaji" cikin son shawo kan rigimar da take masa ya ce" shikenan ki kwanta zuwa anjima zansa a maida ke" shuru ta yi ba tace masa komai ba wajen 2mins ya kalleta ta ɗauke kai, bai san sanda ya yi wani kyakkyawan murmushi ba amma bata gansa ba ya juyo da fuskarta yana ƙare mata kallo ya ce "ki daina rigima zan saka ki makaranta" Riƙe hannayensa ta yi da murna ta ce" irin wanda su Adda suke zuwa?" bai gane wace makaranta take nufi ba hakan yasa ya yi mata shuru, haɗe rai ta yi sai kuma ta ce" to wai kai bakayin magana ne?" buɗe gajiyyayun idanunsa ya yi ya sauke akanta tayi saurin ɗauke nata saboda wani kwarjini da ya yi mata. Sauketa ya yi daga jikinsa yana faɗin "Astgfirullah" leƙa fuskarsa ta yi ta ce" mene wannan ka faɗa?" kallonta ya yi da mamaki da alama dai batasan komai ba gameda addini, a ransa ya yi alƙawarin mayar da'ita cikakkiyar malama kuma mai tarin ilimi............. Ganin lokaci na tafiya yasa ya ce" tashi kije" Miƙewa tayi tana kallonsa ya nuna mata hanyar waje ta juya ta fita, a hankali ya furta "Ya Allahu, Ya Rahmanu". Da mamaki ta ce" to yanzu yarinyar tana gidan?" Gyaɗa mata kai Nihal ta yi ta ce" wlh Daddy ne ya ce babu inda zata amma Mami sai faɗa take" ajiyar zuciya ta sauke ta ce" ina Heesham ɗin?" "yana gidan shima" ta bata amsa, shuru sukayi duka sai kuma Nihal ta ce" Mommy bari naje nayi wanka nikam" ok Mommyn ta ce sannan ta shige ciki......... Zaune suke a company ɗin Bilal ya ce" yanzu ya zakayi da ita?" shuru ya yi masa ya ce" wai dan Allah bazaka daina wannan abunba kanaji ana maka magana kayi shuru" numfasawa Sheikh ya yi sai kuma ya ce" zan kaita makaranta ne saboda na fuskanci batasan mene ne karatu ba ma both boko da islamiyya tanada flaws sosai". Ajiyar zuciya Bilal ya sauke sannan ya ce" toh meyasa ka karɓo musu yarinya?" murmushi Sheikh ya yi amma bai bashi amsa ba, tashi sukayi dan daman magrib ya kusa kuma zasu tafi gida............ Sai wajen ƙarfe 10pm sannan yashigo gidan kai tsaye kuma apartment ɗinsa ya nufa dan ba ƙaramin gajiya ya yiba. Yana gama shiryawa ya yi kwanciyarsa dan sam ya manta da wata Jiddah.......... Washegari wajejen 9am kowa yana parlon suna breakfast Daddy ya ce" ina Hauwa'u naga bata fito ba?" kallonsa kawai Mami ta yi amma bata bashi amsa ba ya ce" Shareefat jeki kirawota" tashi tayi kawai ta shige ɗakinta dan kiranta kamar yanda ya umarceta......... Zaune ta tadda ita tana kallon mudubi wanda azahiri bashi take kallo ba tunani kawai take ki, tsaki Shareefat ta yi sai kuma ta ce" keee" juyowa ta yi tana kallonta dan batasan tashigo bama, tana tattare fuska ta ce" ki zo ina kiranki" ta juya ta fita........... Da sallama ta shigo parlon ta tsuguna ta gaishesu suka amsa banda Mami as usual, kallonta Daddy ya yi ganin yanda ta tsuguna ya ce" tashi ki zauna anan" ya nuna mata kusadashi, batayi musu ba ta zauna kamar yanda ya ce ya miƙa mata abincin yana kallonta. Ahankali take cin abincin saboda rashin sabo da cinsa, har tagama sannan ta tashi ta koma ɗakinta......... Da daddare ya dawo gidan lokacin kusan ƙarfe 9pm shida Bilal, zaune suka tadda ita a parlon tana kallo a tv, murmushi Bilal ya yi ya ce" kallo ki keyi?" gyaɗa masa kai ta yi ta ce" ina kwana" cikin harshen fulatanci langwaɓar da kai ya yi ya ce" Ayya Hauwa'u ai ni ban'iya ba saidai ko Abbanki" juya fararen idanunta ta yi sai kuma ta ce "Abba" Murmushi ya yi ya ce" Eh mana ai Sheikh Abbanki ne, saboda haka daga yau Abba zaki dunga ce masa" murmushi tayi har saida fararen haƙoranta suka fito ta ce "Abbana" Ya gyaɗa mata kai yana murmushi shima ya ce" yees Abbanki". Kallonsu kawai Sheikh yake amma bai ce komai ba, Bilal ya miƙo mata wata takarda ya ce"admission later nki" kallonsa tayi da rashin fahimta ta ce" ni bangane ba" dafa kansa ya yi ya ce"ohh sorry, gobe zaki fara zuwa makaranta".dariya tayi ta ce" da gaske nima zan fara zuwa makaranta?" gyaɗa mata kai ya yi yana dariya ta ce" nagode" ya ce" Abbanki zaki yima godiya"................ Tashi ta yi ta ƙarasa gabansa ta tsuguna cikin harshen fulde ta ce" nagode Allah ya ƙara arziƙi" murmushi ya yi ya shafa kanta ya ce" Ameen Fulani".......... *SHEIKH HEESHAM* [3/4, 22:15] 🥰Nanameera🥰: https://chat.whatsapp.com/LSYEkQgVkLKDQyheA6YWH4 *🌹SHEIKH HEESHAM🌹* *Nanameera*. *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *I Dedicated this book to yhu Aunty Sarauta my nimcyluv, much luv* *Paid book* *Free page 6* Da sassafe ta farka saboda zumuɗin zata fara zuwa makaranta, ahankali take tafiya cikin sanyin jiki kamar batason taka ƙasar har ta ƙaraso ƙofar part ɗinsa. Tura ƙofar tayi bakinta ɗauke da sallama, zaune ta sameshi yana karatun al-qur'ani mai girma cikin daddaɗar muryasa mai tsinka zuciya, zama tayi gefen gadon tana sauraren karatun nasa har ya kammala sannan ya kalleta. Tsugunawa tayi cikin ladabi ta ce "Abbana ina kwana" "lafiya lao, kintashi lpia?" Sheikh ya tambaya lokacin da yake miƙewa tsaye dan shiryawa, murmushi ɗauke a fuskarta ta ce" yau zan fara zuwa makarantar Abba?" gyaɗa mata kai kawai ya yi dan ya lura nema take ta sa kashi magana. Shiryawa ya yi cikin wata dakakkiyar shadda ash colour ɗinkin jampa da babbar riga ya ɗora hirami akansa sannan ya fito, kallonsa kawai take dan sosai ya yi mata kyau "Mefa?" Ya faɗa ganin irin kallon da take masa, girgiza kai tayi ya miƙa mata hannunsa ta kama sannan sukai waje. Mami ce zaune sai Daddy suna breakfast, da murmushi a fuskarsa ya ce" ƙaraso mana Hauwa'u" ahankali ta fara tafiya tana zuwa ta tsuguna gabansa ta ce" ina kwana?" kamo hannunta ya yi ya zaunar gefensa sannan ya ce" kintashi lafiya?" gyaɗa masa kai tayi saboda batason magana musamman ganin irin kallon da Mami ke mata. "Ina kwana?" ta faɗa tana kallon Mami, shuru Mami tayi dan bazama kace da'ita take ba sunkuyar da kanta tayi lokaci ɗaya hawaye ya fara zubuwa a fuskarta Lura da hakan yasa Daddy ya ce" ci abinci kinji karki makara" "na ƙoshi" ta furta cikin sanyin jiki. Girgiza kai Daddy ya yi ya ce" noo dole sai kinci abinci tukunna idan kingama sai akai ki makarantar kinji" batasan yin musu dashi yasa ta fara cin abincin wanda kwata-kwata baya yi mata daɗi Bata wani ci dayawa ba ta ce" na ƙoshi" gudun karya takura mata yasa ya ce" shikenan ayi karatu dayawa dear" tashi tayi tana satar kallon Sheikh wanda ya zauna tun ɗazu akan kujera yana jiranta Gaba yayi hakan yasa tabi bayansa tana sauri gudun karya tafi ya barta A harabar gidan suka tadda Bilal wanda daman shine zai kaita makarantar, da murmushi a fuskarsa ya ce" ƴar makaranta" sai asannan tayi dariya tana rufe fuskarta ta ce" ina kwana?" "lafiya lao" ya amsa mata Kallonta Sheikh ya yi sannan ya ce "akula banda wasa, kiyi karatu da kyau" gyaɗa masa kai tayi ya zaro wani abu a hannunsa, batace ga abinda ya zaro ba saida taga ya kama kafaɗunta a nutse kuma ya fara saura mata afuska Kallonsa kawai Bilal yake har ya gama sanya mata niƙaf ɗin wanda yayi mata kyau sosai, murmushi tayi ta cikinsa ta.ce" laaa! Kamar dodo" girgiza kai kawai ya yi sannan ya juya ya fara tafiya hannunsa goye a bayansa kamar koda yaushe, guards ɗinsa ne suka fito suka buɗe masa motar ya shiga sannan suka bar harabar gidan. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kalli Bilal ya sakar mata murmushi ya ce" mu tafi ko?" ya kama hanyar wajen motarsa tana biye dashi. A harabar makarantar Sheik Bashir dake cikin garin kano ya yi parking, sosai makarantar ta birgeta musamman daya kasance suna koyarda both boko nd islamiyya, a office ɗin principal suka zauna aka ƙarasa cike-ciken da za'ayi sannan suka bata aji Jss 1 domin acewarsu batasan komai ba a harkar karatun Wata prefect akace ta kaita aji, suna fitowa ya ce" banda wasa kinji Jiddah" ɗaga masa kai tayi hawaye na taruwa a idanunta ya ce" mene ne?" "tafiya zakayi kuma?" ta faɗa da zallar gaskiyarta Dariya ya yi sannan ya ce" to ai daman ke kaɗai za'a dinga kawowa idan antashi amaida ke gida, karkiyi kuka kinji" goge hawayen ta da yasamu damar zubowa ta yi ta ce" to ni dawa zan zauna?" dafa kansa ya yi ya ce" Jiddah ki daina rigima da akwai mutane a cikin ajin" bata kuma cewa komai ba ya ce"please ki riƙe hannunta" tom prefect ɗin tace sannan ta kama hannun Jiddah suka fara tafiya tana juyowa har suka bar section ɗin. Fitowarsa kenan daga wanka ya tsaya yana ƙaremata kallo ganin yanda take bacci kamar jaka, tsaki kawai ya yi sannan ya girgiza kai yazo gabanta, "Nabeela!!Nabeela!!Nabeela" A firgice ta buɗe idanu tana mutstsiƙesu ta ce"please kabarni nayi bacci mana" sakar baki ya yi yana kallonta sai kuma ya ce" amma kinsan lokacin sallah ya yi ko?, kuma bakida alamar tashi kiyi" turo baki ta yi ta ce" to naga idan mutum bacci yake ai ba'a tashinsa saboda sallah ni gaskiya ka daina tashina haba" ta tashi ta shige toilet ɗin Girgiza kai ya yi sannan ya ce" Allah ubangiji ka shiryi Nabeela" Tana gama zuba masa abincin ta kallesa ta ce" Doctor nagama" murmushi ya yi ya ce" thank you dear Allah ya yi albarka" Ameen ta amsa sannan ta koma kitchen d'in dan ƙarasa abinda take Murmushi ya yi yana kallon yanda yake zuba masifa ya ce" haba prince wannan fa ba girmanka bane" wanda aka cewa prince ɗin ya kallesa ya ce"ok haka ma zaka ce?, nayi ƙafa da ƙafa tun daga bauchi nazo wajenka amma shine zaka cemin haka babu komai thank you" Murmushi Khalil ya yi sannan ya ce" ba haka nake nufiba Ajmal abinda nakeso ka gane ita rayuwa a hankali ake binta bada faɗa ba tunda kaji mai martaba ya ce haka dole akwai abinda ya faru dan Allah ka dinga yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi". Kallon kawai ya yi sannan ya ce" ni idanma ya yi haƙuri ƙasar zan barmasa sai ya ƙarata shida su, kuma fa wai har Fulani koyon bayansa take" murmushi ya yi ya ce" haƙuri zakayi friend karka ɗauki abin wani personal kaji, Allah ya yi mana jagora" ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce" Ameen, nagode amma wlh bazan koma yanzu ba" dariya Khalil ya yi ya ce"shikenan sai ka zauna gidana" da sauri ya kallesa sai kuma ya ce" waye zai zauna gidanka?, Allah ya tsare wannan ƙazamar matar taka tana gidan, tab" girgiza kai ya yi ya ce" tunda bazaka zauna ba karka zagarmin mata agaba ahaka ina sonta kuma itama tana sona" kallonsa ya yi sai kuma ya fashe da dariya ya ce"ina wata soyayya bayan babu tsafta?, kana dai fama" tada motar ya yi ya ce"E, naji". Kallon motar da tashigo suke har tayi parking, fitowa tayi da niƙaf kamar yanda ta tafi sai kayan makarantar da suka bata a hannunta sai school bag ɗinta, murmushi ta sakar musu, haɗe rai Shareefat tayi Nihal ta ce" sannu dazuwa" "yawwa" Jiddah ta faɗa sannan ta shige gidan. Harararta Shareefat ta yi ta ce" banza mene ne na gaisheta?, wlh wannan sai ta shiga tsakanin ki da Sheikh" murmushi Nihal ta yi sannan ta ce" ke bakida wayo idan muka nuna bama sonta ai za'a iya fahimta, amma idan mun sakar mata fuska ta saki jikinta damu sai mu rabata da gidan nan" dariya Shareefat ta yi ta ce" muguwa kawai" juya idanunta ta yi ta ce" nafi hakama" Da sallama tashiga parlon nasa wanda banda ƙamshi babu abinda yake, zaune ta sameshi ya rufe idanunsa ya yi shuru. Zama tayi a ƙasansa ta ce" Abbana" Buɗe gajiyyayun idanunsa ya yi akanta amma bai ce komai, littafin hannunta ta buɗe ta ce "Abbana ka koyamin ban iyaba" Kallonta ya yi sai kuma ya kalli littafin ya miƙa mata hannu, tagane abinda yake nufi hakan yasa ta miƙa masa littafin nata. Ajiyewa ya yi agefensa sannan ya tashi ya shige bedroom ɗinsa Not too long ya fito hannunsa riƙeda al-qur'ani ya zauna aƙasan carpet ya tankwashe ƙafafunsa "Zo nan" Ya furta a nutse.Tasowa tayi cikin sanyin jiki ta zauna gefensa tana kallon al-qur'anin "Daga yau idan kindawo daga makaranta zamu dinga yin karatu" murmushi tayi sannan ta ce"tom, zaka koyamin Abbana?" gyaɗa mata kai kawai ya yi dan gudun kar taja maganar da tsayi. Sosai yayi mamakin ganin yanda take karatun kamar antaɓa biya mata kuma hadda bata yimata wahala duk abinda ya biya mata to haddacewa take, kuma yasa ya dinga godewa Allah. Dariya tayi ta ce"ai naganesa shine wanda ya dinga liƙa dollar ranar bikinmu" "exactly ashe baki mance saba" murmushi Ajmal ya yi ya ce" ai nima ban mance amarya ba to ya gida?" "lpia lao Alhamdulillah" ta bashi amsa sannan ta miƙe tashiga kitchen. Kallonsa ya yi ya ce"yanzu zaka kwana anan friend?" girgiza kai ya yi ya ce" nifa bazan kwana ba narigada na kama ɗaki tun da safe kuma anan zan dinga kwana period" girgiza ka Khalil ya yi ya ce" Allah ya rabaka da gaddama prince" harararsa ya yi ya ce" ba Ameen ba". Kallonta kawai yake har tagama kwanciya akan gadon sannan ya ce "Dare nayi aje akwanta" Tura baki tayi ta ce" ni Abba ka barni anan" girgiza kai ya yi y ce" banson rigima" shuru tamasa tana sake rufe jikinta da blanket ɗinsa, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya juya ya fita daga bedroom ɗin Zaune suke acikin ajin kowa da ƙawarsa amma banda ita tayi shuru abinta, taɓata Hajar tayi ta ce" hyyyyy" shuru tayi mata dan batasan mene ne abinda ta faɗaba, bata kawo komai aranta ba ta ce" ya sunanki?" Hauwa'u Heesham ta bata amsa dan shine sunan da Bilal ya faɗa mata. Murmushi Hajar tayi ta ce" ni sunana Hajar inason ki zama ƙawata" batasan mene ne ƙawaba ta ce"tom" kamo hannunta ta yi ta ce" zo muje muyi break" bata mata musu ba suka jera tare abin su. Buɗe ƙofar ɗakin akai ta ɗaga kanta tana kallonsu zama sukayi gefenta da murmushi a fuskarsu Nihal ta ce" karatu ki keyi?" gyaɗa mata kai Jiddah tayi har sannan tana riƙeda al-qur'anin ganin kamar bata saki jiki da suba yasa Shareefat ta ce" daman zuwa mukayi muganki taso muje ɗakina" murmushi ta sakar musu dan daman batason zamanta ita kaɗai indai ba Sheikh yana nan ba kamo hannunta Nihal ta yi tace"taso mana" tashi tayi cikin tafiyarta a nutse kamar koda yaushe ta ajiye al-qur'anin sannan suka fita daga ɗakin. Ƙarar shigowar motoci taji yasa ta miƙe da mamaki Nihal ta ce" A'a Jiddah ina zakije?" gaba tayi tana faɗin "Abbana ya dawo zai min karatu" harararta Shareefat ta yi ta yi ta ce" kinji munafuka ko, daman ƴan fulani da tsafi wlh inaga ta tsaface Sheikh" tsaki Nihal ta yi ta ce"ni bari Mami ta fito kawai azo ayi maganar nan dan wlh jinake kamar zuciya ta zata fashe saboda baƙin ciki wlh na tsani yarinyar nan" dariya Shareefat ta yi ta ce"wlh kam idan kin aureshi shikenan kin huta da fargaba, yarinya ƴar ƙarama sai makirci" tashi sukayi saboda yin sallar isha'i. Yaukam da wuri tayi karatunta yana jinta dan bai mata ƙari ba, tana gamawa ya ce "Allah yayi miki Albarka Fulani" Murmushi ta yi har saida beaty point ɗinta suka lotsa ta ce"Ameen Abba". Kusan wata ɗaya kenan tana zuwa makaranta kuma sosai ta bawa kowa mamaki dan tanada saurin fahimtar duk abinda ka koya mata, har malaman makarantar sun fara saninta, yauma suna zaune da Hajar suna karatu dan indai ba lokacin wasaba to zaka samesu suna karatunsu abinsu. "Wai kee ina ne gidanku?" Hajar tatambayeta kwaɓe fuska ta yi ta ce" nima bansan sunan unguwar ba saidai na tambayi Abba idan na koma gida" dariya Hajar ta fara mata ta ce"yanzu bakisan unguwarkuba?" haɗe rai tayi ta ce" E, ɗin" shuru tayi saboda tasan next reaction ɗinta kukane ta ce"shikenan mu cigaba da karatunmu".. Murmushi tayi ganin wanda yazo ɗaukanta bayan sun shiga mota ta ce" uncle ina Abbana?" yana kallon titi ya ce"bayanan yaje Abuja shine ya ce nazo na ɗauke ki" kwaɓe fuska ta yi ta ce"yaushe zai dawo?" dariya ya yi ganin yanda tayi da fuska ya ce"gobe" fashewa tayi da kuka ta ce"dan Allah kace masa ya dawo yau" dariya kawai yake saboda yanda take kukan ya ce"shikenan calm down dear anjima zai dawo yanzu gidana zamuje dake ki zauna ko bazaki ba?" ɗaga masa kai tayi ta ce"zani" ya ce" good gurl". *SHEIKH HEESHAM*[3/5, 16:00] 🥰Nanameera🥰: https://chat.whatsapp.com/LSYEkQgVkLKDQyheA6YWH4 *I Dedicated this book to yhu Aunty Sarauta my nimcyluv, much luv* *Paid book* *Free page 7-8* Murmushi Ameera ta yi ta ce"yau ɗiyar Sheikh ce a gidan namu?" zama Jiddah ta yi ta ce" ina yini y gd?" "lpia lao" kalle-kalle ta yi sai kuma ta ce "Ina junior?" "Yana makaranta maybe suna hanya" Okay Jiddah ta ce sannan ta yi shuru dan damaan ita ba gwanar magana bace. Har kusan isha'i tana gidan Bilal, dan tare suka dafa abinci da Ameera tana koya mata wasu abubuwan "Mom" Juyowa tayi tana kallon ɗan ƙaramin kyakkyawan yaron ta ce "Toh sarkin tambaya yanzu kuma mene ne?" Turo baki yaron ya yi sannan ya ce "Dad ne ya ce wai aunty Jiddah tazo zai maida ita gida" Kallonsa Jiddah ta yi ta ce"ka ce masa gani nan" Juyawa yaron ya yi Ameera ta ce" bazaki kwana ba?" Girgiza kai tayi ta ce" Abba zai min faɗa" Murmushi Ameera ta yi ta ce "Kaga ɗiyar Sheikh" Rufe fuskarta ta yi da hannunta sannan ta ce"na tafi" "Tom sai anjima " Sannan ta fito parlon ta ɗauki school bag ɗinta sannan tayi waje. Har suka isa gida ba tace dashi ƙala ba saboda kwata-kwata ta matsu taga Abbanta ji take kamar tayi shekara bata gansa ba Tsaye ta tarar dasu a parlon kowa ya yi shuru, da mamaki take kallonsu dan ta ɗauka wani abunne ya faru "Daughter me yasa kika bi Bilal baki sanarwa kowa ba?" Rarraba idanu ta yi sai kuma ta ce" ai na ɗauka ya faɗa muku shiyasa Daddy kuma.. Wata kyakkyawar tsawa da Sheikh ya daka mata yasa ta yi shuru jikinta nata ɓari, lokaci ɗaya kuma ta fashe da kuka "Idan baki yimin shuru ba i'll deal with you" Tsit ta haɗiye kukan nata tana sauke ajiyar zuciya, ya juya yana tafiya dan dauriya kawai yake a haka har ya haura benen Girgiza kai Daddy ya yi dan yasan halin Heesham kawai ya juya ta tafi, Shareefat ce ta ƙaraso gabanta ta dafata "Kiyi haƙuri kinji Jiddah ki tashi ki tafi ɗaki gobe sai ki bashi haƙuri" Ɗagowa tayi tana kallon Shareefat da idanuwanta da suka kumbara ta ce "Wlh bansan bai faɗawa Abba ba da bazan bisa ba" Gogo mata hawayen ta yi ta kama hannunta suka shiga ɗakinta Saida ta tabbatar ta daina kukan sannan ta fito daga ɗakin lokacin ta shiga banɗaki Juyi kawai take akan gadon amma kwata-kwata ta kasa bacci ko meyasa????? Da wuri ta tashi kamar kullum ta gama shirin makarantar ta sannan ta fito, kallon ƙofar ɗakin kawai take tanajin kamar ta shiga kamar kuma karta shiga. Jiki asanyaye ta buɗe ƙofar bakinta da sallama ta shiga, zaune ta hangeshi kan carpet ya tankwashe ƙafafunsa ya yi shuru dan bazakace ga abinda yake ba. Zama ta yi gefensa kanta ƙasa ta ce "Abbana ina kwana?" Shuru ya yi mata hakan yasa taji ta ƙara tsinkewa da lamarinsa hawaye suka fara rige-rigen zuba daga idanunta, kuma har sannan bai ɗago ya kalleta ba kusan 5mins hakan yasa kawai ta miƙe jiki babu kwari tayi waje "Heeshama" Sunan da taji ya furta kenan sanda take shirin fita daga ɗakin, batasan wace yake kira da wannan sunan ba amma kawai ta juya ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da nata idanun, da hannu ya yi mata alama da tazo aikuwa da saurinta ta tafi kamar zata waɗi. Tana zuwa ta tsuguna gabansa "Heeshama!" Ɗago idanunta tayi dan tana son tabbatar da wacce yake kira da wannan sunan, numfasawa ya yi sannan a nutse ya ɗora hannunta ɗaya saitin zuciyarsa. Sosai zuciyarsa take wane irin bugawa da ƙarfi ta runtse idanunta "Naji zafi Sosai, akiyaye" Fashewa ta yi da kuka ta ce"kayi haƙuri Abbana wallahi bansan Dad ɗin Junior bai sanar dakai ba dan Allah ka yafemin Sheikh" "Na yafe miki duniya da lahira Heeshama" Sai asannan ta saki fuskarta ta kama gemunsa tana murɗawa ta ce "Abbana ni ce Heeshama?" Gyaɗa mata kawai ya yi ta yi murmushi har saida beauty point ɗinta ya loma ta ce "Abbana sunan da daɗi sosai ina sonshi, Heeshama" Shuru sukayi duka na rashin abin faɗa kusan minti 5 sannan ya ce "Tashi ki tafi dare nayi" Kwaɓe fuska ta yi ta ce" Abbana ka barni anan " Girgiza kai ya yi dan yasan rigima takeji da, gyara mata zamanta ya yi kan cinyarshi ta ɗora kanta kan ƙirjinsa idanunta a lumshe, ajiyar zuciya ya sauke wadda shima baisan ya yi hakan ba saukar numfashinta da yaji yasa ya tabbatar da tayi bacci. Anutse ya miƙe da'ita yafara tafiya. Babu kowa a parlon banda tv dake aiki har ya kaita ɗakin amma haka kawai ya ji bazai iya barinta ita kaɗai ba a ƙasa alhalin kowa ya sama. Kallonsa take har ya kwantar da'ita gefen gadon sannan ya ce "Daga yau tare zaku dinga kwana understood?" Gyaɗa masa kai tayi ya juya ya fita. Kallon Jiddah ta yi wacce take barcinta hankali kwance, haka kawai taji tausayinta ya shigeta girgiza kai ta yi sannan ta kwanta itama. Dariya kawai tayi ya ce" wlh ina baki labari wife kinganki kuwa ranar?" murmushi ɗauke a fuskarta ta ɗago kanta dake kirjinsa ta ce"Allah Doctor banaso, bayanma ka fini yin kyau ranar" Riƙe bakinsa ya yi ya ce" kin taɓa jin inda ango yafi amarya kyau?" gyaɗa masa kai tayi tana murmushi ya ce "To ban yarda ba" "Wlh da gaske nake maka Doctor wata friend ɗita da mukayi bikinta kwata-kwata batayi kyau ba angon kuwa handsome guy dashi" Dariya kawai ya yi sannan ya ce" shikenan kiyi bacci kinsan gobe zan fita da wuri" "Ayya doctorna zan raka ka" Waro idanunsa ya yi ya ce" so kike wani ya ganki haka kawai yaji kin masa, kinsanfa inada kishi sosai" Rungumeshi ta yi ta ce"I Love you so much doctor" Shafa kanta ya yi ya ce" nima haka Nabeela, Allah ya nuna min randa zaki haifamin Twins, can't wait" Da sauri ta kalleshi ta ce" nikam bazan iya ba Doctor" murmushi ɗauke a fuskarsa ya ce" zamu gani". Da mamaki take kallon inda ta ganta, murmushi Shareefat ta yi mata ta ce" Abba ne ya kawo ki jiya" ba tace komai ba ta tashi a hankali ta nufi kofa ta fita. Tana gama shiryawa ta fito lokacin Dad ne Mami zaune suna ɗan taɓa hira "Ina kwana?" ta faɗa a sanyaye, "lpy ƙlao Hauwa'u kin tashi lpy?" Dad ya tambayeta Da murmushi a fuskarta ta ce"lpy klao Dad" "Masha Allah" kallon Mami tayi wacce ta ɗauke kai dan bama zaka ce tana wajen ba lokaci ɗaya jikin Jiddah ya yi sanyi, tsugunawa ya yi cikin girmamawa ya ce" Mami ina kwana?" murmushi ɗauke a fuskarta ta ce" lpy lao Sheikh ya ayyuka?" "Alhamdulillah" ya furta sannan ya koma gaban Dad, a hankali ya zame hular kansa ya ɗora kansa kan ƙafafun Dad ɗinsa yana sakin ajiyar zuciya "Muntashi lpy?" Shafa kansa Dad ya yi sannan ya ce" lpy lao Heesham ka tashi lpy?" "Alhamdulillah" ya bashi amsa sannan ya miƙe yana kallon wrist watch ɗin hannunsa ya ce" sai na dawo" "Allah ubangiji ya tsare" suka bashi amsa, gaba ya yi har sannan ta na tsaye bata motsa ba "Hauwa'u tashi ki bisa" Tom ta ce sannan tabi bayansa kamar yanda Dad ya ce mata. Tsaye ta samesa suna magana da wani managern company ɗinsa bayan sun gama ya kalleta ganin yanda ta haɗe rai ya kama hannunta bai ce komai ba suka shiga mota "Heeshama!" Sunan da ya furta kenan yana matse hannunta dake cikin nasa, shuru ta masa kamar ba da ita yake ba ya tallafi haɓarta yana ƙarewa cute face ɗinta kallo ya ce "ke dawa?, rigimar me ce?" ya yi baya yana jingina da kujerar motar. Kallonsa ta yi sai kuma ta fashe da kuka, shuru ya yi mata yana sauraren kukan nata wanda yake jinsa har ƙasan zuciyarsa saida tayi mai isarta sannan ta fara sauke ajiyar zuciya, sai da yaga ta yi shuru duka sannan ya ce "Now tell me ke dawa?" Kallonsa ta yi da kwaɓaɓiyar fuskarta ta ce" ko bakai bane ba" Wara idanunsa ya yi yana nuna kansa da yatsa ya ce "ni kuma menayi Heeshama?" tana wasa da gemunsa ta ce "Shine ka mai dani ɗakin Shareefat bayan nace maka a ɗakinka zan kwana" tana kaiwa nan ta sake fashewa da wani sabon kukan, ɗauke kansa ya yi yana murmushi dan ya gama gano zallar rigima ce take ɗawainiya da ita ɗan bubbaga bayanta ya yi ya ce "Sorry Abba bai ƙarawa" "Promise?" ta tambaya cikeda shagwaɓa, shuru ya yi mata da farko ai kuwa ta sake buɗe bakinta akaro na uku zata zumduma ihu, tattausan hannunsa yasa ya rufe mata bakinta yana kallonta ya langwabar da kai ya ce "Ki yiwa Allah karki fasamin kai Heeshama" haɗiye kukan ta yi tana kallonsa ita kaɗai tana tura baki har suka isa makarantar tasu "Abbana ka kaini har cikin makarantar" ta faɗa tana wasada fingers ɗinta, girgiza kai ya yi ya ce" ki bari sai an tashi yanzu zan makara" zatayi magana ya nuna mata hanyar waje batayi musu ba ta sauka sannan ta shige makarantar, saida ya daina ganota sannan ya saki ajiyar zuciya "Ya Allahu" Shine abunda yake furtawa har suka bar makarantar. Kallonsa yake har ya ƙaraso ƙofar office ɗin yana murmushi ya ce "Dr Khalil daman ana ganinka?" Harararsa Khalil ya yi ya ce" dani dakai aga wanda ba'a ganinsa" shafa kansa Bilal ya yi sannan ya ce" toh ya kake ya gida ya bayan rabuwa, ina Nabeela?" murmushi Khalil ya yi ya ce" wlh komai lpy dole ka tambayeni Nabeela tunda bakazo aurenmu ba" da mamaki Bilal ya ce" daman kunyi aure?wlh ban saniba" "Eh daman ya za'ayi ka sani tunda baka damu ka sani ba baka neman mutane, ina ɗan namu?" dariya Bilal ya yi ya ce " daman kasan inada ɗa?" tsaki Khalil ya yi ya ce" tunda baka damu kaji na mutane ba ka ɗauka mu bamu jin naka wlh ina sane na ƙi zuwa saboda bakada mutunci sai kace ba'a rayu tare ba" girgiza kai Bilal ya yi ya ce "Sorry friend wlh ba haka bane amma in sha Allah yanzu zamu dinga zumunci" "Allah yasa har zuciyarka" Dariya ya yi ya ce" Ameen na Nabeela" harararsa ya yi ya ce " naji kuma gashi na auri Nabeela" "Allah ya bada zaman lpy Friend" Murmushi ɗauke a fuskarsa ya ce "Ameen Bilal daman nan asibitinka ne?" Gyaɗa masa kai Bilal ya yi ya ce "Ai ban saniba nima asibiti kusada nan yake tom wani friend ɗina nazo dubawa" Kama hannunsa Bilal ya yi yana cewa "Muje ciki sai mu ƙarasa hirar". Shuru Dad ya yi ta ce" Alhaji kayi shuru?" ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce" kinsan banason azo ayi abunda za'aji kunya nan gaba amma zanga yanda za'ayi idan Heesham ya yarda dan bazan masa auren doleba yana namiji kuma kinsan Sameer ma bazai bari ba" Numfasawa ta yi ta ce" ni dai dan Allah kasan abun yi dan wlh nagaji da kallon Heesham babu aure yaro kamar ba namiji ba sa'anninsa daga mai ƴaƴa biyu sai mai uku haba" "Na tabbata Heesham bai yi haka da ganganba dole there must be a reason da yasa bai yi aureba coz yanada ilimi shiba jahili bane kinga kuwa dole something fishy" Ruwan hannunta ta ɓalle ta sha sannan ta ce "Wlh Nihal batada matsala she is fine gurl batada flaws ko kaɗan" "Allah yasa hakane" "Ameen". [3/6, 14:03] 🥰Nanameera🥰: https://chat.whatsapp.com/LSYEkQgVkLKDQyheA6YWH4 *I Dedicated this book to yhu Aunty Sarauta my nimcyluv, much luv* *Paid Book* *Free page 9-10* *Last Free Page* Da sauri ta kalli Mommy sai kuma ta ce "haba Mommy dan Allah ki mata magana wlh da gaske ina son Sheikh wlh" sakar baki ta yi ta na kallonta ta ce" toh ta ce min sunyi magana da babansa sai ki bari sai sun yanke hukunci tukun na " zumɓura baki ta yi sai kuma ta tashi ta shige ɗakinta, girgiza kai Mommy ta yi ta ce" Allah ubangiji ya shirya". Rungumeta Shareefat ta yi ta ce" oyoyo Sister sannu da zuwa" zama Nihal ta yi sannan ta ce" thank you sis ina Mami?" "ba tanan taje unguwa" gyaɗa kai Nihal ta yi sai kuma ta ce" ina Sheikh" riƙe haɓa Shareefat ta yi ta ce" har anfara tambayarsa toh baya nan" murmushi kawai ta yi sannan suka cigaba da hira. "Wai ke bazaki faɗamin ina ne gidanku ba?" dariya Jiddah ta yi ta ce" wlh nima bansani ba kuma na manta ban tambayi Abba ba" harararta Hajar ta yi ta ce" ay shikenan tunda bakiso nazo gidanku" murmushi Jiddah tayi ta ce" haba friend wlh zan tambayo" okay ta ce sannan suka cigaba da karatunsu. A gajiye ta dawo gidan dan ba ƙaramin yawo ta sha ba, zama ta yi kan kujera "Wash" ta furta daidai lokacin suka fito daga kitchen ɗin, zama suka yi gefenta suna mata sannu da zuwa amsawa ta yi sannan ta ce "Bari naje nayi wanka wlh na gaji sosai" "Ayyyah Mami sannu, kin kuwa siyo?" gyaɗa mata kai tayi sannan ta haye sama. Kallon Nihal ta yi ta ce" wai ke me kike nufi?" ƙasa ta yi da murya ta ce" ina nufin ta bar gidan nan yanda Sheikh bazai sake ganinta ba saboda nifa ina tsoron watarana yace zai aureta wlh" ajiyar zuciya Shareefat ta sauke sannan ta ce" haba wlh bai kamata ba nifa babu ruwana idan kika aikata abinda zai zo ya dameki kinsan babu yanda za'ayi Mami ta bari ya auri wannan yarinyar kuma ma tayi masa ƙanƙanta kwata-kwata bazata shige 15-16yrs ba kinga kuwa da'ace yaya yayi aure da wuri to da tabbas ya haifi kamarta saboda haka ki daina wani damun kanki ki saka aranki kin auri Sheikh an wuce wajen" shuru ta yi batace komai ba kuma badan ta yarda da duk abinda Shareefat ta faɗa ba. Murmushi ɗauke a fuskarta ta buɗe motar tana kallonsa ta ce" Abbana kazo ɗaukana?" gyaɗa mata kai ya yi dan baya son surutu sannan suka cigaba da tafiya. Suna shiga gida bayan anyi parking ta fito bata tsaya shiba dan ita haushin bai kulata ba ne ya dameta, girgiza kansa kawai ya yi yana kallonta har ta shiga gidan sannan ya sauke ajiyar zuciya Da sallama ta shiga ɗakin, zaune ta tarar dasu suna hira ta ce" sannunku" fuska a sake suka amsa mata Shareefa ta ce" sai yanzu kika dawo?" gyaɗa mata kai ta yi ta ce" na tsaya jiran Abba ne shiyasa" ji tayi gabanta ya wani yanke ya faɗi duk zuciyarta ta dagule amma ta yi ƙarfin halin cewa" ina Sheikh ɗin?" tura baki Jiddah ta yi ta ce" nima ban saniba ai bana kula shi" dariya shareefa ta yi dan yadda Jiddah ta yi dole abin ya baka dariya wai sunyi faɗa Sheikh. Bata kuma cewa komai ba ta shige toilet dan yin wanka dan zafi take ji. "Amma yaya mai zaka zo yi a kano?" Daga ɗaya ɓangaren ya ce" zanzo na tafi dakai ne saboda Mimi ta matsa" haɗe rai ya yi kamar yana gabansa ya ce" nifa bazan koma gidan nan ba daga nan ma US zan wuce baza su sake ganina ba" kwantar da murya ya yi ya ce" haba Ajmal wannan fa ba daidai bane abunda kake abunda ya faru ya riga ya faru kuma ya wuce dan Allah ka shirya gobe zanzo ɗaukarka" tsaki Ajmal ya yi sannan ya ce" Allah ya kawo ka" "Ameen " ya amsa sannan ya kashe wayar, daidai nan Khalil ya shigo yana kallonsa ya ce" kai da wa naga kana mafan masifa?" cilli ya yi da wayar hannunsa sannan ya ce" wlh Sultan ne zai dameni" murmushi Khalil ya yi dan yasan halin Ajmal da saurin fusata ya ce" dan Allah to kayi haƙuri kazo zamu ci abinci" "I'm full" Ya furta sannan ya yi kwanciyarsa kan royal bed ɗin yana kallon sama, girgiza kai ya yi dan yasan tunda ya ce bazai ci ba to ko za'a kasheshi bazai cinba. "Kaiii wlh Mami ya yi kyau sosai gold ɗin, nima ki siyamin irinsa" Shareefa ta yi maganar tana shagwaɓe fuska, dariya Nihal ta yi ta ce" baza'a siya ba ɗin?" harararta ta yi ta ce" dalla babu ruwanki dani tom!" murmushi Mami ta yi tana kallonsu duka ta ce "shikenan duka zansa akawo muku" rungumeta sukai atare suna faɗin "Thank you Mami" Goge hawayen idanunta ta yi tana sake kallonsu cikeda sha'awa, ji take inama ace ita ce mai mahaifiya, wataƙila bata rabon samun farinciki daga uwa mace yasa duk inda taje bata samun wacce zata riƙeta matsayin ƴa, kallonta Shareefa ta yi sai kuma ta sunkuyar da kanta dan sosai Jiddah take bata tausayi inama Mami ta ɗauketa matsayin ƴa, kama hannunta taji anyi batareda ya yi magana ba ya jata har cikin ɗakinsa. Zaunawa ya yi ya zaunar da'ita kan cinyarsa yana kallon fuskarta, fashewa ta yi da kuka tana rungumeshi ƙam-ƙam, sosai take kuka kamar ranta zai fita kuma bai yi ƙoƙarin hanata ba dan tabbas tana buƙatar tayi kukan ko tasamu sauƙi a zuciyarta. Sai da tayi mai isarta sannan a hankali ta fara sauke ajiyar zuciya kuma taji sanyi a ranta "A daina kuka komai zai shige kinji Heeshama" Kallonsa ta yi tana shashsheƙar kuka ta ce " Abbana meyasa ni bazan taɓa farin ciki ba?, meyasa bana samun wacce zata ɗaukeni matsayin ƴa?, meyasa Ammina ta mutu ta barni?, meyasa nima ban mutu ba sanda ta haifeni?, banida gata Abba, banida uwa Abba, bansan mene ne farincikin da ɗa yake ji ba idan yana tareda uwarsa wlh Abba ji nake kamar...... Saurin rufe mata baki ya yi yana girgiza mata kai ya ce "Ba'a cewa haka Heeshama, a rayuwa duk abinda kaga ya sameka to damaan haka Allah ya rubuta maka, ƙaddararka ce a haka, kuma sannan kinada kowa Heeshama, ki ɗauka ni ne Abbanki, Amminki, kuma yayanki duk abinda kike so a rayuwa ki sanar dani Heeshama na miki alƙawarin tsaya miki akan komai saboda haka banson kina furta irin waɗannan kalaman isn't good Heeshama" ya faɗa ya sauke numfashi dan rabonda ya yi magana mai tsayin haka har ya manta. Shuru ta yi ahankali kuma ta ɗora kanta akan ƙirjinsa not too long bacci ya yi awon gaba da'ita, kallon kyakkyawar fuskarta ya yi yana sake rungumeta dan yana matuƙar jin yarimyar har cikin ransa. Shuru ya yi har Dad ya gama faɗa sannan ya ce "amma Dad.. Dakatarda shi ya yi ta hanyar yi masa alama da hannunsa sannan ya ce " Heesham dolene kayi aure kuma not too long saboda zamanka a haka ba abu bane mai yiwuwa kuma kamar yanda mahaifiyarka ta zaɓa maka mata idan ta hali kana iya aurenta amma ni bazan maka dole ba abinda kake so shi zakayi kana iya zuwa kayi tunani ka yankewa kanka shawara amma tabbas inason kafin nan kafin 2months kayi aure idan kuma baka fito da mata ba kuma baka ɗauke wacce aka zaɓama ba to zaka wayi gari ka tarar an kai maka mata gidanka kuma babu saki, ɗazu munyi waya da Sameer kuma shima abinda ya ce kenan karma kayi tunanin guduwa duk inda kaje zansa a nemoka understood?" gyaɗa masa kai kawai Sheikh ya yi dan ji yake kamar kansa zai rabe biyu saboda tsananin ciwon da yake masa, a daddafe ya haura saman yana shiga ɗakinsa ya shige banɗaki, ruwa ya sakarwa kansa saida yaji hankalinsa ya fara dawowa jikinsa sannan ya yi wanka ya fito. Wata armless ɗin riga ya saka da wadonta ya kwanta nan da nan bacci ya ɗaukesa. Murmushi ya yi ya ce" wato dai kana jin maganar yaya Sultan ko?" harararsa Ajmal ya yi ya ce" wlh kawai saboda shi zan koma, amma yanzu yaushe zaka zo?" "sai da bikin ka" wani shegen kallo ya yi masa yana rufe trolley ɗin ya ce"kada Allah yasa kazo" murmushi kawai ya yi yazo ya rungumeshi ta baya ya ce" in sha Allah friend nan bada jimawa ba zanzo harda Nabeela" murmushin shima ya yi ya ce" Allah ya sa" dariya sukayi duka sannan ya ce" amma dai please ka ci abinci yau kafin ka tafi" "idan naƙi fa?" "Sai nasa ayi maka duka dan ni bazan iya dukanka ba" fashewa ya yi da dariya sannan ya yi waje. Throughout ranar haka ta yini a makaranta tana jinta wani iri bata ce ga exactly abinda yake damunta ba amma jinta take duk wani lonely hatta Hajar basuyi wata hirar arziƙi ba har aka tashi, sosai tayi mamaki ganin yazo ɗaukanta yauma, bayan sun ɗanyi nisa ya kama hannunta batareda ya yi magana ba ya zaro wani diamond ring mai kyau kuma mai matuƙar tsada sai sheƙi yake yi ya zura mata a ɗan yatsanta na tsakiya sosai ring ɗin ya yiwa farar fatarta kyau kamar an dasashi, murmushi tayi ta ce" Abbana ya yi kyau sosai nawane?" gyaɗa mata kai ya yi ya ce" na kine Heeshama promise me bazaki manta dani ba" da sauri ta kalleshi ta ce" Abba meyasa zaka ce haka?" numfasawa ya yi amma bai ce komai ba, ta riƙe gemunsa ta ce " Abbana!" juyowa ya yi taga yanda idanunsa suka rini kamar gauta da sauri kuma cikin tashin hankali ta ce" Abbana bakada lpy?" girgiza mata kai ya yi dan ya gagara yin magana haka kawai taji gabanta yanata faɗuwa har suka isa gidan Kallonta ya yi ya ce" ki shiga Heeshama zani unguwa?" kallonsa ta yi sai kuma ta kwaɓe fuska ta ce" Abba zan bika" girgiza mata kai ya yi ya ce" kije gida kinji Allah ya Albarkaci rayuwarki" murmushi ta yi ta ce" Ameen Abba na, Allah ya dawo dakai lafiya" "Ameen" ya furta da kyar, a hankali ta sauka tana tafe tana waigowa taga shima kallonta yake har ta shige parlon. "Ina zamuje Sir?" "Airport" Sheikh ya furta yana lumshe idanunsa shi kaɗai yake furta "Ya Allahu Ya Rahmanu, Ya Zul-Jalalu wal ikhram". "Mami banfa gansa ba" harararta Mami ta yi ta ce "wlh idan naje na ɗaukoshi sai ranki ya ɓaci" gyaɗa mata kai Shareefa ta yi sannan ta zauna suna hira da Nihal. Duba sosai Mami ta yi amma bataga gold ɗin ba, sosai kuma abun ya ɗaure mata kai dan tasan babu kowa a gidan idan ba itaba, Shareefa, Nihal a parlon. Sakkowa ta yi tana kallonsu ta ce" bakuga inda na ajiyesa ba jiya ko na canza masa waje ne?" da mamaki suka ce "wai kema baki ganshiba Mami?" gyaɗa musu kai tayi Shareefa ta ce "Kuma naga babu wanda ya shigo gidan nan jiya" "Nima abunda yake bani mamaki kenan" Mami ta faɗa. Shuru suka yi sai kuma Nihal ta ce "To ko za'a tambayi Jiddah ne ko ta gansa?" da sauri Shareefa ta ce" a ina Jiddah ta ganshi batama san mene gold ba bare ta ɗauka". "Nifa cewa nayi a tambayeta ko ta ganshi, ko ya kika ce Mami?" Da sauri Mami ta yi hanyar ɗakin Jiddah ba tareda ta sake yiwa koma magana ba. "Mu koma gida i forget something" Sheikh ya faɗa lokacin sun kusa kaiwa Airport ɗin, okay kawai drivern ya ce sannaa ya yiwa sauran motocin umarnin dasu koma suka kama hanyar gida. Bata cikin ɗakin amma ruwa na zuba a banɗaki alamar wanka take, dube-dube Mami ta hau yi a ɗakin, time ɗin Shareefa suka shigo da Nihal da sauri Nihal ta ce" lemme help you Mami" daga nan ta fara bincike duka cikin ɗakin ita kuwa Shareefa sai binsu da kallo take. "Mami i got it" Nihal ta faɗa da ƙarfi, da sauri duka suka juyo suka kallonta tana riƙeda sarƙar gold ɗin a hannunta, tsabar shock sun kasa rufe bakinsu hatta Shareefa kallon sarƙar take da sauri Mami ta karɓa tana cewa "Ina kika ganta Nihal?" Daidai nan Jiddah ta fito daga banɗakin tana kallonsu da mamaki "A cikin wasu kayanta ta ɓoye Mami" Iyaka ɓacin rai ran Mami ya ɓaci ita kuwa Jiddah kallonsu take da rashin fahimta da sauri Shareefa ta shaƙe mata wuya ta figeta har parlon tana mata wani shegen kallo ta ce "Ɓarauniya kawai, kin bani mamaki Jiddah ki rasa me zaki sata sai gold wlh kinyi asara daman ance tsintacciyar mage bata mage, no wonder Mami ta tsaneki ashe ɓarauniya ce bamu sani ba wlh kin yi asara banza kawai ƴar matsiyata" Allah sarki Jiddah kallonta kawai take tama kasa magana ko kuka dan batasan akanme take mata magana ba, Mami ce ta fito tana kallonsu ta ce "Shiyasa tun zuwanta nace bana sonta daman wlh ni nasan tabbas tanada wani mugun hali da take aikatawa yasa naji na tsaneta Heesham ya kawo mana masifa" Da mamaki ya ce"what's wrong Mami?" kallonsa ta yi sai kawai ta fashe da kuka ta ce" Heesham sanda nake faɗa ai ƙarya kuke ɗauka nace na tsani yarinyar nan amma kuna min kallon mara imani" da rashin fahimta ya ce" Shareefa meya faru?" da sauri ta ce masa "yaya Jiddah ce ta satarwa Mami gold ɗinta data siyo jiya" "Sata?" Ya maimata kalmar a fili sai kuma ya kalli Jiddah wacce ta fashe da wani raunataccen kuka dan sai a sannan tak abinda ake zargin ta aikata, girgiza kansa kawai ya yi sai kuma ya juya ya fita daga parlon ta bisa da kallon amma ta kasa magana Babu irin tijarar dasu Mami da Shareefa basu yimata amma duk wannan abun da ake Nihal bata saka baki ba tayi shuru abinta har suka gama maganarsu suka shige sama. Zaune ta tarar da ita gefen wata flower sai kuka take kamar ranta zai fita "Jiddah" Ta kira sunanta, da sauri Jiddah ta ɗago tana kallonta sai kuma ta sunkuyar da kanta tana share hawayen fuskarta, zama ta yi gefenta ta ce" kiyi haƙuri Jiddah ki ɗauka hakan ƙaddararki ce, amma ina son baki wata shawara" Da sauri ta kalleta ta ce cikin kuka "dan Allah wace shawara zaki bani?" numfasawa Nihal ta yi sannan ta ce" tunda kikaga Sheikh ya fita bai kula ki ba toh yan sanda zai kirawo su kama ki, kuma yanzu na baro su Mami suna faɗawa Dad kuma bai kamata ace Dad ya ganki da wannna laifi ba" hankali Jiddah idan ya yi dubu to ya tashi ta ce" dan Allah ki bani shawara" "Shawara ɗaya zan baki shine ki gudu kafin su dawo kiyi tafiyar ki garinku" da sauri ta kalleta ta ce" ni bansan hanya ba kuma banida kuɗi" kuɗaɗe ta zaro wajen bandir ɗaya na ƴan dubu ta ce" ungo kiyi tafiyar ki idan kika fita saiki tambayi tasha idan aka kaiki sai ki hau motar garinku" goge hawayen fuskarta ta yi sannan ta ce" nagode" murmushi Nihal tayi mata sannan ta mike jiki a sanyaye ta fara tafiya har ta fita daga cikin gidan daga ita sai hijab har ƙasa ajikinta wata ƙaramar riga ce. Ajiyar zuciya Nihal ta sauke sannan ta tashi ta koma gidan. Allah sarki rayuwa tafiya kawai Jiddah take yi batareda tasan inda zata ba, murmushi ɗauke a fuskarsa ya ce" dallah ka daina min ko bakaga tuƙi nake ba?" dariya Ajmal ya yi ya ce" wato bakason ka mutu yaya Sultan bakai aure ba?" kafin ya bashi amsa ya sake kai hannu zai taɓashi da sauri ya kalli gabansa amma kafin ya tsaya har ya rigada ya kaɗeta, cikin tashin hankali suka fito daga motar, kwance suka tadda ita dukda basu wani bigeta sosai ba amma ta suma, ɗukanta Sultan ya yi ya saka a mota suka cigaba da tafiya. Basuda ishashen lokacin da zai ishesu su kaita asibiti anan garin hakan yasa kawai suka hau private jet ɗin da aka kawo musu zuwa garin bauchi....... *Shin wace irin ƙaddarace ta raba Jiddah da Abbanta?* *Shin da gaske Jiddah itace wacce ta saci gold ɗin ko A'a?* *Shin da gaske Sheikh yan sanda ya tafi ɗebowa Heeshamarsa?* *Shin meyasa Jiddah tabar garinsu kuma suwane Ajmal da Sultan?* *Shin ya Heesham zai ji idan ya dawo ya tarar babu Heeshamarsa?* *Duka zaku samu amsoshin tambayoyinku a yayinda kuka biya kuɗin littafin Sheikh Heesham 500# via 9086030007 evidence via 09086030007 or contact me direct via 09086030007 whatsapp only* *Taku har kullum Nanameera sai mun haɗu a paid group*