COMPILED BY ESHAAT SMILER HOM OF HAUSA NOVLS DOCUMNTS WASAPP 08066360176 FOR MORE.. 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 _*SHAK'UWA CE*_ 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 01 *漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�* _馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_ *Hallo lovers I'm back again 馃槃馃拑馃徎, wannan shafi naku ne kyauta masoya na masu bibiyan labarai na, musamman wad'an da suka karanci ZUBAIDAH 馃挐馃槏* *Bismillahi Rrahmani Rraheem* Gudu take kan faman sherawa cikin k'ungurumin dajin da baka jin komai sai kukan tsuntsaye. Haki ta tsaya tana yi sabida tsananin gajjiya da tayi, sunkuyawar da zatayi sai ji tayi an d'auke ta da mari had'i da fizgo ta.... Ja da baya ta soma hawaye masu zafi suna ci gaba da bin k'uncin ta kafin ta soma fad'in "Shema'u don Allah kar ki kashe ni, kiji tausayi na, ki tuna I'm your only sister pls kar ki rabani da iyalai na... " Ta k'arashe tana tsananin kuka. Wacce ta kira da Shema'u dariya ta tuntsire mata dashi kaman tab'ebb'iya kafin ta soma girgiza kai tana fad'in " Aysha dole ki mutu, and your family kar ki damu they're in good hand, nayi alk'awari babu abinda zai same su zan kula maki dasu fiye da yanda zakiyi, kinyi kuskure Aysha tunda kika amince kika auri Man of my dream, Aysha kin tab'a tambayar kanki me ya hanani aure all this while, nasan baki damu kiyi ma kanki wann tambayar ba tunda burin ki ya cika kin auri mijin da kike so, and you even gave him children bayan kinsan cewa ni na soma had'uwa dashi ni na fara sanin shi, I should be the one in your place, ni ce ya kamata na kasance da AT not you Aysha..." Ta k'arashe tana mai fitar da hawaye tana murmushi tana girgiza kai tamkar tab'ebb'iya.... Aysha taci gaba da girgiza kai kurum hawaye na bin k'uncin ta don kuwa wannan wani Al'amari ne da bata tab'a zaton zai iya faruwa a gaske ba, kai ko a film bata tab'a ji ba, sai gashi yana faruwa akanta, 'yar uwa ke farautar rayuwar 'yar uwa sabida namiji... Cikin rashin yarda da tunanin da zuciyar ta ke karanto mata ta shiga goge hawayen ta kafin ta soma fad'in " Shema'u kar ki kashe ni pls you can have AT, zan bar maki shi but pls don't hurt me and my children.." Cikin tsananin kuka tana mai had'e hannayen ta waje guda alamun rok'o take maganar amma kaman cewa take Shema'u ta k'ara sautin dariyar ta... Ganin Shema'u tayi nisa cikin dariyar ta yasa Aysha soma ja da baya a hankali, jini na ci gaba da bin k'afarta sakamakon k'aramin cikin dake jikin ta.... Kan tayi wani katab'us sai ji tayi Shema'u ta kuma finciko ta had'i da watsa mata mari mai ji da lafiya har guda biyu ta shak'e wuyar ta hawayen taurin rai na bin k'uncin ta take fad'in "You are so delusional Aysha da kikayi tunanin zan barki da rai, kin sace soyayyar kowa nawa daga gare ni, Aysha you always stealing from me, kowa ke yake so, Aysha tun muna makaranta k'awaye sunfi sonki, sanda Abbah yake da rai yafi sonki snn Momma tafi sonki, you are always the good one, ni kuma ni ce maras jin magana ni ce wacce ba'a so, Koda Abbah ya zo da AT kai tsaye ke akace ya Aura despite the fact nice gaba dake, nice ya kamata na soma aure ba ke ba Aysha... Why why Aysha meyasa kika sace komai daga gare ni.. " Girgiza kai Aysha keyi hawaye na bin k'uncin ta, ga azaban da marar ta ke mata tamkar zata mutu, fuskar ta tayi jajazir sabida azaba. Cikin wani irin murya mai cike da azaba take fad'in " Shema'u have mercy pls, ki tausaya min ko don alhakin dake ciki na, Shema'u kar ki hukunta wanda baida laifi...." Dutsen gefen ta Shema'u ta jawo tayi saitin goshin Aysha dashi tana kuka shar shar da hawaye tana girgiza kai take kallon 'yar uwan nata take fad'in.." Aysha ina sonki ina sonki sister but bani da zab'in da ya wuce na kashe ki, hakan ne kawai zai sa na mallaki duk abinda na rasa ta dalilin ki..." ta k'arashe maganar had'i da kwad'a mata k'aton dutsen dake hannun ta akan ta... Wani k'ara Aysha ta saki lokaci guda Shema'u taci gaba da kwad'a mata dutsen nan jini na bin goshin Aysha, babu d'and'anin imani haka Shema'u take hura hanci tana mai ci gaba da rabza wa Aysha dutsen nan da iyaka k'arfin ta.... Hisham dake tsaye gefe ya kafe su da idanu dariya ya fashe dashi kafin ya shiga tafe hannayen sa yana fad'in" What an interesting show, you really are something Shemah, gaskiya na jinjina maki yanzu kin nuna min zaki iya komai domin ki mallaki that damn Dr.. Wannan ya nuna min you don't feel anything for me.." Ya k'arashe yana matso wa daf da ita... Shema'u kuwa cike da firgici take duban Aysha tana kallon aika aikan da tayi, ganin bata mosti bata numfashi yasata saurin sakin ta tana wani irin b'ari tamkar mazari. Cikin wani irin murya mai cike da firgici take duban Hisham tana zazzare idanu take fad'in " Oh no no no, na kashe ta, I killed my sister, Hisham na kashe 'yar uwa ta..." Ta k'arashe tana waige waige tamkar wacce take tsoron kar a kama ta... Ganin she's going out of control yasa Hisham saurin rik'o kafad'un ta kafin yace " Kee.! Put yourself together, don't be such a daft, ashe baki shirya ma aikin da kika yin ba, barin fad'a maki, what's done has already been done, gwara ma kisan yanda zakiyi ki k'arasa abinda kika riga kika soma.. " Ya k'arashe yana wata kafiran dariya... Fincikewa Shemah tayi tana girgiza kai tana waige waige tana karkad'a masa yatsar ta manuniya take fad'in "Kar kayi tunanin tsame kan ka cikin mess d'in nan Hisham, we are into this together, wllhi if you dare think of betraying me, I have my ways to get rid of you.... " Dariya Hisham ya fashe dashi yana mai jinjina taurin zuciya irin na Shema'u kafin ya matso daf da ita ya rungumo ta cikin jikin sa duk da rawa da jikin ta keyi don har lokacin tsoro da firgicin abinda tayi basu bar jikin ta ba... Saitin kunnen ta yake rad'a mata " Idan kika taimake ni na mallaki abinda na jima ina farauta daga wajen AT kin gama min komai, ina mai tabbatar maki your secret is safe with Dr Hisham...." Ya k'arashe yana wata irin dariya... Gyad'a masa kai Shema'u ta shiga yi, cikin rawar murya take fad'in "You can count on me , wllhi wllhi zanyi komai ganin ka Mallaki _Sajmal Clinic_." Hisham ya kuma murmusawa kafin yace "Deal? " da sauri ta gyad'a masa kai tace "Yeah deal". A rud'e ta kuma fad'in "Dr ka taimaka min yaya zanyi da ita?.." "Aw dama baki shirya ma abin ba kika soma yi?? Yaya kike aiki da ka ne babu lissafi Shema'u??. " Gajeren tsaki ta d'an yi tana duban Aysha dake kwance lifeless a k'asa jini na faman kwarara a goshin ta da k'afafun ta kafin tace "Ko hak'a rami zamuyi mu tura ta ciki..? " Hisham ya kuma tuntsurewa da dariya kafin yace "Daga gani you're very poor when it comes to mathematics, anyway leave this to me, I'll take care of it, yanzu abinda nake so dake tayani mu janyo ta zuwa cikin motar naku. " Babu musu Shema'u ta shiga yin yanda ya umarce ta. " ********* _Sajmal Clinic Kano_ Zaune yake saman kujeran sa na duba marassa lafiya, lokaci zuwa lokaci yake jin k'irjin sa na wani irin yankewa yana fad'uwa. Kasa ci gaba da ganin marassa lafiya yayi dole yayi excusing kansa ba don yaso ba... Wayar sa naga ya d'auka dake saman table d'insa gefen wasu files wanda ba sai ance maka na majinyata bane kafin ya kafe wayar da idanun sa yana shafa saman screen d'in da d'an yatsar sa... Sai sannan na samu na k'are masa kallo, sanye yake cikin faran yadi k'al mai laushin gaske, wuyan rigar da d'an gaban rigar sun sha sirirn aiki da zare golden colour, haka nan hannun rigar an zagaye ta da irin aikin wuyar rigar. Fari ne amma ba can ba, dukda idanun sa naga kan screen d'in wayar sa zaka gane yanada yalwan idanu, dogon fuskar sa ya dace da siririn hancin sa wanda yake zat kaman an zana, haka nan d'an k'aramin labb'an sa tamkar ya shafa Jan baki... Duk yanda kyakkyawan mutum ya kai toh fah wannan mutumin ya kai, gashin kansa a kwance suke luf bak'ik'irin sai ka lura ka hangi d'an furfura da suka soma fitowa daga wasu sassa na sumar nasa, a ido zaka iya bashi shekaru 36 zuwa 39, amma a zahiri Dr AT is at his late 40s, magidanci ne d'an shekaru 48 a duniya.... Mik'ewa naga yayi yana mai ci gaba da shafa wayar sa, sosai fuskar sa ta cika da damuwa... Sai snn nayi nazarin k'irar jikin sa, tabbas shekarun sa sunfi jikin sa tsufa, ko kusa idan baka sani ba, bazaka zaci yakai shekarun da yake a yanzu ba, ko da shike abinka da likita sun iya kula da motsa jiki da yanayin abincin da suke ci... D'an tsaki naga yayi had'i da shafe goshin sa, ga dukkan alamu bai samu wanda yake nema a wayan bane, ko kuma wayar bata shiga ba.. ********* "MARYAMA don Allah muje mu tari a daidai ta mu tafi gida, k'ila dai yau Daddy Ya mance ne damu." Cewar wata yarinya da bazata wuce shekaru 16 zuwa 17 . Wacce ta kira da Maryama ta juyo tana duban wacce ta ida magana kafin tace " Haba Sajida bafah lallai bane Uncle yazo d'aukar mu, k'ila Aunty ce zata zo mu d'an k'ara hak'uri kin san Aunty tanada uzurin gida a gaban ta. " Sajida ta d'an turo baki had'i da yin still kafin tace "Wllhi na k'osa muyi SSCE d'in nan mu huta, kawai ma bin su Momma da Aunty Shema'u zanyi mu tafi Jalingo tare. " Ta k'arashe tana mai dariya had'i da d'an tafe hannaye. Maryama ta murmusa kafin tace " Ashe su Momma sun zo.? " Sajida ta gyad'a kai kafin tace " Ehen shiyasa nake fad'a maki Momy yau dole ta mance damu koda Daddy zaice ta d'auko mu tunda yau Aunty Shemah da Momma sun zo, ba lallai ta tuna da mu ba.. " Ta k'arashe tana sab'a jakar makarantar ta a kafad'. Mik'ewa Maryama tayi ta kakkab'e rigar uniform d'inta kafin tace " Shikenan muje, Allah sa mu sami a daidaitan don kin san idan yamma tayi layin nan ba'a faye samu ba." Suka jera suna tafiya yayinda Sajida taci gaba da fad'in "Wllhi har wani dad'i nake ji gobe babu wann shegen lesson d'in mutum zai koma gida da wuri. " Murmushi kawai Maryama tayi sanda suka k'arasa bakin titi don neman abin hawa." ******** A razane ya mik'e had'i da damk'e wayar jikin kunnen sa cikin hannayen sa yana fad'in "Hisham me kake cewa, Innalillahi wa inna ilaihirraj'un,." Bai gama jin abinda Hisham ke fad'i ba yayi jifa da wayar ya fito a guje cikin tsananin birkicewa, gaba d'aya duk yanda ya wuce cikin asibitin kallon sa suke cike da firgici, basu tab'a ganin sa cikin irin yanayin ba... Wasu nurses maza guda biyu suka biyo bayan sa suna masa magana, inaa ko kulasu baiyi ba, bai ma san me suke cewa ba, motar sa dake ma'ajiyan ta kurum ya k'arasa, ya mata key kafin ya fice a guje cikin tsananin tashin hankali... ************** Sanda Dr Ahmad Tahir ya iso wajen daidai lokacin Ambulance ta iso, chan k'asar gada ya hangi motar matar sa ga mutane sunyi chaa a wajen, ciki harda aminin sa kuma coworker d'in sa wato Dr Hisham.. Hisham dake tsaye yana matsan k'wallan munafunci yana hango AT yayi saurin k'arasowa yanda yake, AT d'inma k'ok'arin gangarowa k'asar gadan yake cikin tsananin tashin hankali, tamkar mutum mutumi haka yake tafiyar.. Rik'e sa Hisham yayi yana k'ok'arin saita kansa kafin yace "Friend, I shouldn't have called you in the first place, but babu yanda na iya ne Tahir ka..." Saurin katse sa Tahir yayi kafin yace "Hisham ina Aysha? " Daidai sanda aka soma fito dasu daga cikin motar.... Hango Ayshar sa da zaiyi ana zak'ulo ta cikin jini ya sauk'ar masa da wani irin jiri.. Ya nemi kalma guda saman harshen sa ya rasa, baisan sanda ya k'arasa wajen a guje ba ana d'aura ta saman gadon ambulance ya jawota ya rungume cikin jikin sa.. Shema'u da aka d'dd'ura mata bandage d'in k'arya sai nishin munafunci take sai ka rantse jin jiki take... Cikin wani irin tsananin tashin hankali yake fad'in " No no Aysha, don Allah kar ki tafi ki barni, bazan iya ba...." bai kai aya ba wani irin kuka ya kufce masa yana rungume da ita cikin jikin sa. *Sameena Aleeyou Mrs* [2:49PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 _*SHAK'UWA CE*_ 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 02 *漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�* _馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_ "Maryama don Allah ki bari mu wuce gida mana gaba d'aya." Sajida tace sanda suke shiga kwanar Janbulo. D'an jim Maryama tayi kafin tace "Kar ki damu Sajida idan dai naga jikin Ummi da sauk'i sosai zan biyo Uncle idan yazo gaida Hajiya sai mu kwana tare." Sajida ta murmusa kafin tace "Shikenan na amince, Ki gaida (Maama Juu) da jiki." _Maama Juu shine sunan da Sajida da k'annen ta suke kiran Ummin Maryama da shike itace ta raine su gaba d'aya tun daga kan Sajida har zuwa kan autar su Ni'ima._ Maryama ta gyad'a kai tana mai amsawa da zata ji, kafin sukai sallama ta shige gida, Sajida na fad'in "Ki gaida birkitacciyan tsohuwar nan." Dariya sukayi gaba d'ayan su Maryama tace "Zaki sani ne ai idan dai Hajiya ce." Ta shige gida suna masu waving ma juna. Zaune Maryama ta hangi Hajiya k'asar bishiyar mangwaron da ya zamto wajen shak'atawar ta a can farfajiyan gidan. Hajiya na hangota ta washe baki tanai mata lale domin kuwa Allah Ya had'a jinin ta dana Maryama.... Duk tsangwama da masifah irin ta Hajiya batayi ma Maryama, hasali ma ita ke taya ta kwana, dukda kuwa cewa harta mahaifiyar Maryaman ba wai ta sha bane a hannun Hajiya. "Hajiya ta barka da yammaci." Ta fad'i sanda take kwab'e sandals d'inta tana mai zama bisa darduman. "Yauwa barka Maryama d'iyar albarka, an taso daga bokokon." Hajiya ta amsa sanda take karyan goro.... Maryama ta d'an tab'e fuska kafin tace " Wai ke Hajiya bazaki daina cin goro kina tara cuta ma cikin ki ba koh, kin dai ji abinda Uncle yace makomar mai cin goro.." Tsegege kurum Hajiya ke kallon ta kafin tace "Tohhh wato kema Attahiru ya koya maki felek'e da firirta irin tasu ta 'yan bokoko ko,..? Ke kekam kikayi nisa a bokon bansan k'ak'a za'a k'are ba, inaga shinkafa ma sai kin haramta mana cinta... Kodashike ba laifin ki bane, SHAK'UWA CE da kikayi da Attahiru shi ya cusa maki wannan ra'ayin, inyi haba..... " Maryama saida tayi datasanin soma maganar nan domin kuwa tasan shikenan yau kuma Hajiya ta sami maudu'i, idan ta soma batayi shiru ba. Mik'ewa Maryama tayi had'i da d'aukar Jakarta kafin ta furta "Bismillahi.... Hajiya ni na shiga ciki.." Hajiya ta k'ek'ashe idanu tana duban ta kafin tace "Ina Attahirun inji shi ya kawo ku?" Maryama ta girgiza kai kafin tace "Adaidaita muka biyo." Hajiya ta tab'e baki kafin tace "Agogo sarkin aiki yana can yana aikatuwa saikace inji." "Toh ai lada yake samu a aikin nasa." Maryama ta fad'i sanda take saka sandals d'inta. Hajiya ta kuma tab'e baki kafin ta warware bakin zaninta ta ciro wayar ta ta mik'a wa Maryama tace "Ungo maza kira mani lambar sa." Maryama tasa hannu ta amshi wayar snn ta soma dialing layin AT. Ta kira yafi abinda yafi ba'a d'aga ba. Haba nan fah Hajiya ta soma sababi babu ji babu gani, wai da gangan yak'i d'aga wayar ta.... Ummi dake can sashen su saida tajiyo sababin da Hajiya take, ta fito don ganin da waye Hajiya take fad'an nan, ganin babu yara masu d'iban ruwa sai Maryama abin ya bata mamaki don tasan ko meye Maryama ta mata basa fad'a, kai idan sunyi fad'ar ma Maryama ta mata yaji da kanta take zuwa tayi bikon ta ta dawo da ita, don kuwa ba kad'an take k'aunar Maryama ba..... Kai harta Ilu mai gadi saida ya baro benchin sa ya nufo wajen shima.... Haba nan fah ta kuma kaure su da fad'a... Maryama kam me zatayi banda dariya, kai har tana Alla Alla Uncle yazo ta labarta masa. ********** Sajida tana shigowa ta tarar da Momma zaune a parlor tana kallon tashar wasan kwaikwayo. Fad'awa jikin ta tayi a guje had'i da zama bisa cinyar ta.... Momma ta rungume ta tana fad'in "Inye lallai jikar tawa ta k'ara girma sosai, saura kawai ta kawo mana miji mu sha biki." Sajida ta turo baki kafin tace "Haba Momma 'yar ni d'in nan, ai yanzu na soma karatu, sai na gama karatu na soma aiki kaman Aunty Shema'u kafin nayi aure..." Momma dai murmusawa kurum tayi kafin tace "Bani fatan ki dad'e babu aure kaman Shema'u, duk maneman ta koran su take, toh yanzu dai da alama wannan likitan abokin mahaifin ki bazata korasa ba." Sajida ta mik'e tana fad'in "Wai ina suke ne ma, nasan yau Momy da Aunty Shemah za'a k'ule a d'aki ana labarai." "Auw! Ba tare kuke bane? " Momma ta tambaya. Sajida ta girgiza kai kafin tace "A'a ni yanzu sauk'ata daga adaidaita, Daddy baije ba Momy ma haka, kuma malam iro bashida lafiya kwana biyu dama baya zuwa. Ce maki tayi zata d'auko mu ita Momyn.?" Momma ta jinjina kai kafin ta dubi agogon bangon dake mak'ale a parlorn tace "Oh ni Kulu, wato dai Shema'u da Aysha idan suka had'u sai yanda mai ya k'are masu, wai fah gidan k'awarsu zasu a nan Hotoro amma kinji shiru har yanzu, kuma ita Ayshan da tayi waya ma Daddyn ku ta fad'i masa zasu fita tabbas yace su biya su d'auko ki makaranta, sunje sun shantak'e sun sami surutu." Sajida ta murmusa kafin tace "Momma ai gashi na dawo, dama Aunty Shemah da Momy suka fita kam ai sai an gansu, nasan gaba d'aya Malls d'in garin nan sai sun zaga tas..... Bara naje na cire uniform" ta k'arashe tana d'an tsalle jaka da hijabi duka a hannu ta nufi upstairs. Momma na nan zaune na tunani, haka kurum take jin gabanta na fad'uwa kaman wani abu zai sami yaran nata, musamman idan ta tuna Aysha ba k'oshin lafia bane da ita, k'aramin juna biyu gareta.... Tana cikin tunanin wayar ta dake saman center table Ya d'auki ruri ... Saida ta d'an firgita kafin ta d'au wayar. Ganin bak'uwar lamba ce ya kuma sauk'ar mata da wani matsanancin fad'uwar gaba... Hannu na b'ari ta d'auki wayar tana amsawa. Wani k'ara Momma ta Saki babu salati balle ambaton Allah ta shiga rusa kururwa tana fad'in "Wayyo ni Kulu na shiga uku, 'ya'ya na, wayyo 'ya'ya na... Wayyo Allah na...." Ai a tamanin Sajida dake d'akin ta tana zura riga ta nufo downstairs, su Jamal da Ni'ima harda Baba Delu suma suka nufo parlorn a tamanin... Hajiya tana ganinsu ta k'arasa ta rungume su gaba d'aya tana kuka.... Tambayar ta suke meke faruwa amma ko kad'an bata sami zarafin amsa su ba... Ta dubi Baba Delu kafin tace ta tsaro masu tasi su tafi.... Momma ko la'akari da k'arancin shekarun Jamal da Ni'ima batayi ba haka ta dinga kuka ta kwashe su suka tafi asibiti, suma yaran haka suka dinga kuka ganin kakar tasu na kuka...... ********** Yana rungume da ita cikin jikin sa, kansa na kwance bisa k'irjin ta haka yake kuka kaman k'aramin yaro, su Hajiya Ummi da Kuma Maryama suna gefe suna nasu kukan suma, Dr Hisham sai k'ok'arin janye AT yake amma fir yak'i sakin Aysha, dole haka ya k'yalesa still yana rungume da ita yake kuka tamkar k'aramin yaro. Ai su Momma suna shigowa wani sabon kuka ya kaure, Maryama ta k'arasa da sauri ta rungume Sajida data koma tamkar gunki ganin mahaifiyar ta kwance saman gado bata numfashi idanunta a rufe ruf ga kuma mahaifin ta rungume da ita yana kuka wanda bata tab'a ganin hakan daga garesa ba... Tuni su Jamal da Ni'ima sun k'arasa wajen suna kuka, cikin sauri Ummi ta d'auke su ta fice dasu... Da k'yar Hajiya ta janye AT daga jikin matar sa. Su Dr Hisham sai kai komo ake sai ka rantse aminin arziki ne. AT rungume mahaifiyar sa yayi yana kuka sosai yana fad'in" Hajiya Aysha ta tafi.... Ta tafi ta barni... " Hajiya ta matsi k'walla tana rik'e dashi take fad'in" Kayi hak'uri, kayi hak'uri Attahiru, kayita karanto innalillahi kaji....." Momma ta k'arasa kan d'iyarta sanda za'a fita da ita, tana kuka tamkar ranta zai fita... Sam babu wanda yabi takan Shema'u dake kwance d'aya d'akin... Tana kwance tana tunani taji an tab'a k'ofa... A tamanin tayi saurin sakin jiki irin ta mai jinya ta rufe idanun ta... Dariya ya kwashe dashi kafin yace " Bud'e idanun ki abinki ba wad'anda kike tunani bane. " Ya k'arashe yana mai zama gefen ta.. Bud'e idanunta tayi kafin ta dubi Dr Hisham tace " Ina AT, yanacan yana kuka akan gawar matar sa koh?" "Keda kika sani, yana can yana rungume da ita da k'yar aka b'anb'are su, kaman a bisne su tare... " Hisham ya fad'i sanda yake warware drip d'in k'aryar da aka d'aura wa Shema'u. Shema'u tayi k'wafa kafin tace "Aysha dukda ta mutu wato sunfi sonta, AT da yaranta suna tareda ita, Momma da banida kowa sai ita itama tana can tare da ita,.." tayi wani murmushi mai cike da ma'anoni kafin tace "Yanzu ne zan kafa soyayya ta cikin zukatan ku, one by one sai kun so ni da duka zukatan ku." Hisham ya murmusa kafin yace "Kar ki damu kinada ni, a hankali ya sauk'o da fuskar sa saitin nata yanai mata wani irin shu'umin kallo, hannu yasa ya janye masu labulan window kafin ya soma kissing d'inta.... *Sameena Aleeyou Mrs* [2:50PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 _*SHAK'UWA CE*_ 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 03 *漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�* _馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_ Ganin yanda Hisham ke pulling d'inta ga dukkan alamu ma ya mance a yanda suke. Turesa tayi daga jikinta tana wani irin yamutsa fuska kafin tace "Not here hungry Dr." tayi maganar tana wani murmushi had'i da kad'a masa d'an yatsan ta manuniya saman fuskar sa. Murmushi Hisham yayi yana mata wani irin mayaudarin kallo, su duka biyun kowa da kalan abinda yake sak'awa cikin ransa. Hisham ne ya katse shirun da fad'in "A gaskiya my whole life ban tan's ganin maras imani irinki ba, ki kashe 'yar uwanki babu ko d'an tunanin soyayyar dake tsakanin ku.... " Da sauri ta kaste sa da fad'in "No Dr you're quite mistaken, abinda ke tsakanina da Aysha ba soyayya bace SHAK'UWW CE kurum, difference na shekaru dake tsakanin mu babu yawa, shekara d'aya ne da 'yan watanni, so kaga mun taso tare like twins, tunda muka taso komai tare ake mana, ko ina tare muke zuwa, ga wad'anda basu sani ba sukanyi tunanin mu 'yan biyu ne, harta class d'inmu a makaranta d'aya ne, abu guda da Aysha ta fini dashi shine ci gaba, she was always ahead of me bayan kuma ni ce gaba da ita, I should be the one ahead of her... Aysha was always stealing from me, tundaga wannan lokacin na tsane ta na tsani 'yar uwata. Kaji abinda yasa nace maka ba soyayya bace a tsakanin mu SHAK'UWA CE kawai.." Ta d'an ja fasali kafin taci gaba "Sannan Tahir.." ta murmusa kafin taci gaba "Tahir ni na soma sanin shi, ni na soma had'uwa dashi wani rana sunzo gidanmu da mahaifin sa nayi serving nasu drinks... Koda nazo na sanar da Aysha naga man of my dream sosai ta tayani murna, washi gari da Abban AT ya kuma dawowa Aysha tayi serving nasa, ita bata had'u da AT ba so bata sanshi ba a wancan lokacin. Mahaifin AT ya yaba da hankalin yaran Abbah na musamman Aysha da shike ta k'ware wajen makirci da saye zukatan mutane. Kai tsaye ya nema ma d'ansa Ahmad Tahir auren d'aya daga cikin mu , Abban mu yayi farin ciki da hakan sabida lokacin AT bai jima da dawowa daga India ba ya kammala karatunsa na likitanci. Abba da yazo kai tsaye ma Aysha yayi maganar bayan ni ce gaba da ita , a cewar sa itace bata tara samari kaman ni, sannan tafi nutsuwa da hankali , baison abinda za'azo ana jin kunya tunda yasan halina na rashin jin magana. Ni kuwa a lokacin inaji da k'uruciya ta da tashen kyau tunda nafi Aysha kyau babu had'i.... Aysha ta amince wa buk'atan Abbah ita a dole ga d'iya mai biyayya.... Ka fad'a min Hisham, ta yaya bazan yi burin d'aukan fansa ba... ka fad'a min Hisham.... " Hisham dai kallon ta kawai yake cike da mamaki. Shema'u taci gaba da fad'in "Tun wancan lokacin na k'udiri niyyan d'aukan fansa akan 'yar uwata." Ta murmusa kafin taci gaba da fad'in "Ina son AT soyayyan da ban tab'a yiwa wani d'an Adam irinsa ba, akan AT ni na kashe Mahaifin mu don ya min sauk'in mallakan abinda nake so, tun daga wancan lokacin zuciyata ta k'ek'ashe ta bushe, sannan banyi aure ba duk a saboda shi, sannan na k'udiri niyyan rabashi da Aysha da 'ya'yan data haifa masa, ban sami chance d'in ba sai yanzu... Sannan nayi alk'awari sai na mallake sa ni kad'ai ba tareda kowa ba, even his children wllhi sai na raba sa dasu, ni kad'ai ya kamata na mallaki AT, dagani sai 'ya'yan da zan haifa masa nan bada jimawa ba.... Sannan nayi rantsuwa who ever crossed my way I'll kill him.... " Ta k'arashe tana wani irin hura hanci tana muzurai da dara daran idanun ta... Tsoro abin ya bawa Hisham, nan yaga ashe shi k'aramin k'waro ne. Duk wani iskancin sa a bayan Shema'u yake. Ta kashe mahaifin ta da 'yar uwanta na jini duk a sabida namiji.... Nan ya soma tsoron anya Shema'u batada mental case.... Bai gama tunanin ba yaji tana kad'a masa yatsu a fuskar sa... A firgice ya d'ago yana dubanta. Amma da shike shima wani shak'iyin ne nan ya gwada kaman baiji tsoron abinda tayi ba, saima dariyan da ya fashe dashi ya d'aga mata babban yatsa alamun jinjinawa kafin yace "Bravo, gaskiya na yarda kina son Tahir, anya kuwa zaki bari na d'auki fansa na da na jima ina nema akan sa...? Mik'ewa tayi sosai tana duban sa kafin tace "Don't even start, don't mess with my man, wllhi idan wani abu ya samu AT zan halak'a ka.." Hannu yasa ya jawota cikin jikin sa yana wata irin murmushi yake fad'in "Don't be such an idiot, nida ke are team, tare muka soma, and you must help me take back what's rightfully mine from AT..." Kallon sa Shemah keyi tana k'ok'arin k'wacan kanta daga irin rik'on da ya mata amma ta kasa.. Cike da masifa take fad'in "Me yayi maka da tsanani...?" Hisham ya murmusa kafin ya soma fad'in "That idiot is always ahead of me, tare mukayi karatu but Ya fini samun nasarori da ci gaba a rayuwa. Nida shi mun zama kaman 'yan uwa, sabida babu wanda bai sanshi a gidanmu ba haka nima babu wanda bai sanni a gidan su ba... Nida Tahir burin mu shine mu gina asibitin kanmu, mu mallaki asibitin kawunan mu. Mahaifi na yanada wani babban fili wanda Tahir yasan cewa banida burin da ya wuce na gina nawa asibitin a wannan filin, shida kansa yana fad'in tabbas wajen zaiyi kyau da asibiti..." Ya d'an ja fasali sanda idanunsa suka kad'a sukayi jazir kafin yaci gaba da fad'in "Mahaifi na ya rasu ban mallaki filin ba, tunda ya rasu fili ta zama na magada.... A lokacin banida kud'in sayan wannan filin, su kuma 'yan uwana sun dage saidai a sayar da fili.... Ganin rikici na neman b'arkewa a family yasa Tahir ya saya filin sabida hankalin kowa ya kwanta... I thought da ya saya zai barmin filin koda aro ne daga baya na biyasa, tunda yasan burina na mallakan filin domin na gina asibiti na.... Kafin na dawo daga Germany yin wani course domin a zahiri ya fini karatu, kwatsam na tarar Tahir sai ginin asibitin sa yake a very same filin. I was quite devastated then, I was like, how could my very own best friend betrayed me kaman haka. He knew yasan yanda nake burin gina asibiti a wann filin, meyasa zai min haka...... Babban abinda yafi bak'anta min rai shine na rasa aiki k'arshe dole nayi joining nasa a nasa asibitin muna aiki tare..... Ever since then, my plan is to ruin him, and you'll be my ally in doing that.... Da ke zanyi amfani wajen cimma buri na, and you've no option than ki bi umarni na, if not... " Ya wani murmusa kafin yace "I'll ruin you too, and I won't back down until I see him on the ground.... I'll take back Sajmal Clinic, I'll take back this very hospital sabida nawa ne, DREAM d'ina ne.... " Ya k'arashe yana mai matse mata fuska yana hura hanci. Sauk'e ajiyan zuciya tayi cike da tsoro kafin ta ware hannaye tana muzurai take fad'in "Okay okay fine, naji but you've to promise me bazaka tab'a lafiyan sa ba, coz ni ba abin hannun sa nake so ba, shid'in kawai nake so. Zan taimake ka ka mallaki Sajmal, ni kuma zaka taimake ni na mallake sa ni kad'ai...." Murmushi Hisham ya sakar mata had'i da wani shu'umin kallo. Daidai nan suka jiyo ana tab'a k'ofa.... Cikin sauri ya mik'e yana tab'a drip ita kuwa Shema'u lumshe idanun ta tayi tamkar maras lafiya.. Wata nurse ce ta shigo da wani drip a hannun ta... Ganin Dr Hisham yasata d'an sadda kai kafin ta gaishe sa. Ya wani sha mur kafin yace "Don't you know how to knock.?" Hak'uri ta shiga basa tana fad'in batasan yana ciki ba. Karb'an drip d'in hannun ta yayi lokaci guda Shemah take nishi uwa majinyaciya tana fad'in "Momma... Momma na, ku kira min ita..." Hisham ya dubi nurse d'in yace "Oya pls ki kira mata mahaifiyar ta, tun tashin ta take a birkice." Nurse d'in ta d'an rusuna kafin tace "Sir, ai sun riga sun tafi gaba d'aya harma da Dr AT." Gyad'a kai Hisham yayi kafin yace "Shikenan you can go." Nurse d'in tana fita Hisham da Shema'u suka kalli juna. Ta tab'e baki kafin tace "Kaga abinda nake fad'a maka ko, gaba d'aya sun d'unguma sun bi gawar Aysha, harda mahaifiya ta. Babu wanda ya tuna Ya duba ni tunda had'arin nan tare mukayi." Hisham ya murmusa kafin yace "Ni ai na duba ki, kar ki damu kiyi zaman ki a nan idanyaso idan naje sai na sanar dasu na tsaya a nan ne sabida ke, nasan yanzu baza'a sami kan AT ba sam.." Tab'e baki kurum Shema'u tayi ba tareda ta furta komai ba. ************ Komai tareda Hisham akayi, kama daga sallan gawa har zuwa mak'abarta, for second bai bar side d'in AT ba, haka ya ringa basa baki yana calming nasa sai ka rantse aminin arziki ne. Tun dawowar su daga mak'abarta ya k'ule a d'akin sa, har dare bai fito ba, sosai abin yayi affecting nasa. Su Hisham da wasu abokan su da 'yan uwa suke kan karb'an gaisuwa. A b'angaren iyalan gidan ma sosai abin ya shiga jikin su, tabbas wannan tragedy d'in da bazasu tab'a mantawa ba a rayuwar su. Hankalin ta sam bai kwanta ba , tana son sanin halin da uncle yake ciki tabbas tasan he must be having a difficult time.... Jigum tayi har wajajen k'arfe 1:00am, ta kalli Sajida dake kwance gefen ta wacce itama baccin bai jima da satan ta ba... Jin mosti a downstairs yasata mik'ewa ta d'au hijabinta ta zura kafin ta nufo k'asa.. Jikin stir case ta rakub'e tana hangosa cikin parlorn yana sallah. A hankali ta soma sauk'owa har ta isa ta zauna daga can gefen carpet... Tana jin yanda yake karanto suratu Maryam yana hawaye. Tausayin sa ya cika mata zuciya, haka kurum taji wani abu na fizganta jin yanda yake karanto suratu Maryam cikin nustuwa da dad'in saurare... Har ya idar da sallan ya sallame baisan Maryama na zaune bayan shi ba.. Ida sallan sa keda wuya ya kifa kansa saman gwiwoyin sa yana kuka sosai.... Maryama kam batasan sanda itama kuka ya kufce mata ba.. Dif ya tsaya da kukan nasa sakamakon jiyo sautin kukan da yayi a bayan sa.. Juyowan da zaiyi ya hange ta ta rufe fuskar ta da hijabin ta sai sharan kuka take... *Sameena Aleeyou Mrs* [2:52PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 _*SHAK'UWA CE*_ 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 04 *漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�* _馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_ Ya jima sosai yana duban ta yanda take shak'an kuka harda shid'ewa. Tsintar kansa yayi da jin zafin kukan nata dukda halin da yake ciki. A hankali ya mik'e ya k'arasa gaban ta yayi irin zaman rak'umi had'i da tsura mata idanu.... Jikinta ne ya bata Uncle AT na kallon ta, aiko tana bud'e idanu sukayi ido hud'u, k'irjinta ya yanke ya fad'i, dukda a fuzge ta kalle sa tabbas ta lura da yanda fuskar sa ya nuna rama, idanun sa sun dad'a fitowa, hancin sa ta kuma yin tsini.... Sosai ya bata tausayi... Gaba d'aya daburcewa tayi tama rasa me zata soma fad'i masa.... Kaman daga sama sai jiyo muryar sa tayi yana fad'in "Maryama me ya faru bakiyi bacci ba har yanzu.?" Maryama ta rasa wani amsa zata basa kawai ta kuma fashe masa da kuka. AT ya mata k'uri tausayinsu gaba d'aya na ratsa sa. A hankali ya soma fad'in "Kiyi hak'uri kinji, haka Allah Ya k'addara, muyi mata addu'a, Allah Ya karb'i bak'wancin ta..." Maryama ta shiga gyad'a masa kai tana goge hawayen ta ba tareda iya furta koda kalma ba, sai shan zuciya take alamun taci kuka. AT ya mik'e kafin yace "Tashi kije ki kwanta." Babu musu ta mik'e kaman yanda ya umarce ta, ta d'an d'ago kai tana duban sa, gaba d'aya sai ta tsinci kanta da fad'uwan gaba. So tari Uncle d'in nata yanai mata k'warjini dukda SHAK'UWA dake tsakanin su, bata d'auki hakan komai saiko don kasancewar sa Mahaifin k'awarta da suka taso tare.. Murmushi ya d'an sakar mata kafin yace "Saida safe ko Maryam... " Bata kaiga amsawa ba suka jiyo kukan Ni'ima tana sauk'owa daga stirs tana kiran Daddyn ta... Da sauri Maryama ta k'arasa ta rik'ota suka dawo cikin parlorn.. Rungumeta tayi tsam cikin jikinta tana lallashinta... Ni'ima sai kuka take tana fad'in ita saidai a kaita Momy... Maryama ta rungumeta sosai tana lallashin ta, ta kwantar da ita saman k'irjinta tana shafe kanta tana lallashi har bacci yayi gaba da ita, abinka da yarinya. AT ya tsare su da idanu ba tareda ya iya furta komai ba... Kallon Maryama yake kanyi yanda ta rungume Ni'ima itama baccin ya soma d'aukan ta. A hankali ya durk'usa gefe dasu kafin yace "Maryam kawota kije kiyi bacci. Maryama da barci ya soma satan ta, tayi saurin ware idanunta kafin tace "Uncle don Allah kaje ka huta ni zan kula da Ni'ima kaji, Uncle kana buk'atan hutu, don Allah kaje ka d'an sami barci. Gajeren murmushi yayi kafin yace "Toh Maryam zan kwatanta amma kawota na kai maki ita d'aki sai ku kwana tare." Babu musu Maryama ta mik'a masa Ni'ima, ya d'ora ta bisa kafad'arsa suka nufi stirs... Momma dake tsaye bakin corridor d'in da zai sadaka da d'akin bak'i akan idanunta komai ya faru... Haka kurum taji mugun tsanar Maryama ya sauk'o mata, dama taga yanda Jamal yak'i yarda da ita yace sai tareda Maama Juu zaiyi barci, kai da alama wann shegiyar yarinyar da uwarta sunada matsayi mai girma a wannan gida.... Cikin sauri ta k'arasa fitowa tana fad'in "A'a Ni'ima barci ya gagara koh, Allah sarki 'yar marainiya, kawo ta nan..." A tare Maryama da AT suka juyo. Maryama ta k'araso had'i da mik'a wa Momma Ni'ima. AT dai bai kuma cewa komai ba ya nufi hanyar d'akin sa. Momma ta raka Maryama da wata kafiran harara kafin tace "Kawota jikin kakarta taji d'umin mahaifiyar ta." Maryama dai wucewar ta tayi ba tareda ta tanka wa Momma ba, don haka kurum take jin sam matar bata kwanta mata ba... Tana shiga d'aki cire hijabinta tayi ta linke ta kwanta tana mai tuno AT, tausayin sa na dad'a ratsa ta.... Ita kad'ai ta d'an Saki murmushi sanda ta tuna wai AT ne mai lallashinta d'azu a parlor instead itace zata basa baki shida aka masa babban rashi amma shi ke lallashin ta... Murmusawa ta kuma yi kafin ta dubi Sajida dake barci gefen ta tana mai tausaya ma rayuwar da zasu shiga cikinta, tabbas iyaye babban gurbi ne a rayu, idan ka rasa guda dole kaga canji a rayuwa... A hankali ta furta "Allah Ya jik'an ki Aunty Aysha." Saida akayi kwana uku kafin aka sallamo Shema'u, har wani makeup Hisham ya mata da dabara irin tasu ta likitoci, sai ka rantse jinya tayi. Haka har akayi bakwai cikeda alhini na rashin Aysha. ************** Bayan sati guda Maryama ta dawo gidan Hajiya snnan sun soma rubuta jarabawar su ta kammala sakandare. Shema'u da Momma wani kulawa na musamman suke bawa AT da iyalan sa. Babu kaman Shema'u wacce tayi dedicating lokutan ta gaba d'aya wa iyalan AT. A rananr da Aysha ta cika sati guda da rasuwa saida Hisham yazo har gida ya sakawa AT drip, don gaba d'aya babu abincin kirki a system d'insa. ************ Tunda Sajida ta dawo daga school ta k'ule a d'aki, bata komai sai aikin kallon hoton Momyn ta tana hawaye... Shema'u tayi tsaye jikin k'ofa tana watsa mata wani irin mugun kallo, banda sak'e sak'e da k'ulle k'ulle bata komai cikin zuciyar ta... Jin alamun tab'a k'ofar AT yasata saurin k'arasawa cikin d'akin yanda Sajida ke zaune saman gado. Da gangan ta bar k'ofar d'akin a bud'e don AT ya hango su, dama fitowar sa take jira. Zare pic d'in tayi a hankali daga hannun Sajida kafin ta zauna dab da ita ta rik'o hannayenta ta shiga share mata hawaye tana fad'in "Sweetheart kiyi hak'uri kinji, Momyn ku is in better place, kiyi hak'uri Sajida.... You need to be very strong for your siblings da kuma Daddyn ku, what would you expect idan Jamal ko Ni'ima suka ga kina kuka haka.. Huh? Kiyi hak'uri kinji, kece babba kece ya kamata kija k'annenki jiki ki kula dasu ki nuna masu they are not alone kinji my dear...." Ta k'arashe tana satan kallon k'ofa da wutsiyar idanunta, ai kuwa tarkon ta yayi kamu, plan d'inta went perfect, abinda take so ya auku,... AT tsaye yayi yana binsu da kallo... Sajida tasa bayan hannu ta kuma goge hawayen ta kafin ta dubi Shema'u tace "Aunty I still can't believe Momy is gone, I don't know... Bansan yaya zanyi ba yanzu, bansan mecece makomar rayuwata ba. Aunty Shemah bansan ko zan iya rayuwa without Momy ba.... She was my inspiration sabida soyayyar da nake mata yasa nak'intafiya boding school, na tsaya yin day school... Aunty I just can't do without one of my parents... Ina son su sosai.... " Shema'u ta rungumo kan Sajida cikin k'irjinta fuska fal tausayi kafin ta soma fad'in " Sweery, we are here, we are here for you.... Dukanmu muna son Aysha but Allah yafimu son ta... Sajida I promise I won't leave your side, both you and your siblings kinji... " Sajida ta d'ago kai tana dubanta kafin tace " Aunty ki min alk'awari zaki zauna a nan tare da mu both you and Momma kinji Aunt pls kuma kar ku tafi ku barmu please.... " Ta k'arashe cikin rawar murya. "Ohh sweetheart, come here..... Ta fad'i tana kuma rungumo Sajida had'i share mata hawaye kafin taci gaba da fad'in "Sajida ina sonku keda 'yan uwanki, I'll do everything for you, zanyi komai ganin 'ya'yan 'yar uwata sun sami good life sannan baza kuyi kukan rashin mahaifiya ba insha Allah... I promise you that kinji sweetheart... " Murmushi Sajida tayi kafin tace "I love you Aunt." Shema'u ma ta murmusa kafin tace "I love you too sweetheart, oya tashi muje mu had'a ice-cream gaba d'aya tareda su Jamal, I know it'll be fun..." Suka mik'e a tare fuskokin su cike da fari'a... Tsaye suka hangi AT na k'ok'arin barin wajen.. Sajida ta k'arasa da gudu tayi hugging nasa kafin tace "Daddy zamu had'a ice-cream will you join us..?" D'an d'ago kai yayi yana duban Shema'u da murmushi ya wanzu saman fuskar ta kafin ya dawo da dubansa ga Sajida yace "Baby.... Em.... " 'yan kame kame ya soma yi dai. Sajida ta rik'o hannunsa tace pls Daddy don't say no, ka tuna tare fah mukeyi da kai da Momy gaba d'aya family... Daddy pls kar ka canza mana don Momy bata nan..." Ta k'arashe cikin rawar murya alamun zatayi kuka. Kasa ce mata komai yayi sai kallon da yake binta dashi.. Shema'u kuwa ganin haka yasata saurin k'arasowa tana murmushi kafin ta rik'o hannun Sajida, tana mai duban AT take fad'in "Sweetheart karki damu pls understand your Daddy, he still needs some space to recover.... why not muje muyi, since I'm here... " Ko kuma mu fita mu sayo a waje, ni ke da kuma su Jamal, what do you see." Sajida ta gyad'a kai kafin tace "Eh Aunty Shemah, hakan ma yafi, dama gidan nan is kind of boring... " Shemah ta d'an dara tana rik'o hannun Sajida tana duban AT take fad'in "Dr pls anyi mana izini..?" D'an gajeren murmushi yayi had'i da gyad'a Kai kafin yace " Yeah... Yeah sure zaku iya zuwa..." Yasa hannu a aljihu yana k'ok'arin zaro kud'i Shema'u ta wani murmusa kafin tace " Em don't worry Dr I can take care of everything, burina shine naga yarana cikin farin ciki...." Daga haka ta dubi Sajida dake kan kallon ta tana murmushi sannan tace "Oya muje mu shirya su Ni'ima suna wajen Momma...." Haka suka jera ita da Sajida suna mak'ale da kafad'un juna suka nufi downstairs suna hira gwanin sha'awa. AT ya bisu da kallo har suka b'ace ma ganin sa, tabbas har ransa yaji dad'in abinda Shema'u tayi. For the first time da yayi murmushi mai tsawo tun bayan mutuwar matar sa... Sauk'e deep breath yayi kafin yaci gaba da taka matakalan. ************** "Hajiya fah zanyi latti." Ta fad'i baki a ture. Tab'e baki Hajiya tayi kafin tace "Aiko babu yanda zakije sai kin kamo min arewa tonti po (Arewa 24), Yo shi wannan malamin naku baisan kin girma bane, k'irji sur nono yace zai na dukan zagada zagadan 'yanmata haka inyi...." "K'wafa Maryama tayi kafin ta kuma turo baki tace "Nikam wllhi Hajiya ki daina irin wannan maganganun don Allah kar watarana bakin ki ya sub'uce kiyi a gaban Uncle." Hajiya ta sake baki da hanci tana duban ta kafin tace "Tooh, auho wato gaskiyar ce bakiso a fad'i inyi, toh ai sai kuje yayita lallasa maku duka zagada zagadan 'yammata daku, inji Ma'awuya ne d'an gidan Laminde, me wuya uwa Mark'en lema, ni Fatsuma banma san sanda yaron yayi karatu ba wai har ya zama Malami, imm abun babu wuya, girman d'an mutum..." Ta k'arashe tana goga aswakin ta a hak'waran ta..." Marayama dai bata kuma tanka ta ba har saida ta gama had'a mata talabijin d'in kafin ta mik'e ta d'au jakar makarantar ta saman kujera... Ko sallama batai ma Hajiya ba ta nufi k'ofa. Hajiya ta bud'e murya tace "Bakya amshi kud'in istira'in ba, ko fushi ne kikayi... Haba Maryamu Daso, haba ta gaban goshin Hajiya... Yaki abinki, ungo zo ki amsa..." Ta shiga sunce bakin zaninta tana k'ok'arin zaro kud'i. Fozewa kurum Maryama tayi a wajen still bakin nan a ture, kaman bazata dawo ba sai kuma ta dawo cikin parlorn, tasan idan bata tsaya ta karb'a ma ba k'aramin aikin Hajiya bane ta bita har makarantar ta kai mata tunda a unguwar ne. "Yauwa Maryama d'iyar albarka, bak'a mai farin zuciya, fitilan gidan Hajiya.... Amshi abinki.. " Saida Hajiya tasa Maryama ta dara, idan tana mata wannan kirarin dole takan yi dariya, ba ita kad'ai bama, harta AT yakanyi dariyan draman Maryama da Hajiya.. Musamman idan Maryama ta dage da fad'in ita ba bak'a bace wankan tarwad'a ne... AT yakance babu wankan tarwad'a a kaloli, daga bak'i ne sai fari... Idan Maryama tayi fushi toh haka Hajiya zata salle AT tass dukda ita Hajiyan ita ta kawo zancen... Yakanyi murmushi yace " Maryama ta Hajiya, ba'a shiga tsakanin ku. Sauri sauri take tafiyar nata don kuwa already tayi latti kam gashi Malam Mu'awuya nada karb'an hadda, gashi nata Ya taru don tunda akayi rasuwar nan bata samu ta bayar ba. Kaman daga sama tajiyo horn kaman za'a had'e da ita a markad'e. Gajeren tsaki tayi gamida matsawa gefe.. Nan fah taji horn d'in ya kuma biyo ta... A hasale ta juya zatayi masifah ganin mak'ocin su ne yasata fasa masifar, ta sakar masa murmushi a tak'aice kafin tace " Amma Buzu wllhi ka d'auki hakki na, yau kuwa da kasha masifah don wllhi a k'ule nake. Buzu, matashin sauri irin k'wara d'in Kanon nan dake zaune cikin motar sa k'irar Camry Anaconda yayi murmushi kafin yace " 'Yar kunama ba, ai ta nan kukafi kauri, masifa ba... Yanzu dai shigo na kaiki islamiyan don wllhi yau kam kinyi latti, yanzu na wuce gate d'in islamiyar naku naga sai jibgan 'yan latti ake." Idanun Maryama sukayi rau rau kafin tace "Buzu don Allah da gaske kake, wayyo Hajiyata wayyo Ummita, wai da gaske kake har an tsare latti.." "Kindai san haka kurum bazan sharara maki k'arya ba.." Ya fad'i yana taje sumar sa da k'aramar cumb wanda dama d'abi'ar sa ce.... Toh kodai ta shiga Buzu ya sakata ne, tunda ko wani minti ya shud'e yawar dukan ka ne ke k'aruwa. ... Buzu kuwa ganin ta tsaya tayi jigum tana tunani yasa sa mik'a hannu ya bud'e mata front seat... Hancin motar sa tana karyo kwanan ya hangeta tana k'ok'arin shiga wata mota... K'irjinsa ya yanke ya fad'i, baisan sanda ya k'ara wuta wa motar nasa ba ya shigo layin cikin sauri. *Sameena Aleeyou Mrs* [2:52PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *SHAK'UWA CE* 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 05 *漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�* _馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_ Cak ta tsaya sai faman muzurai take ganin AT na zuge glass d'in motar sa. Fuska babu walwala yake duban su, itakam Maryama tunda Aunty Aysha ta rasu tayi noticing wannan canzawan da Uncle yayi, sam duk SHAK'UWAR dake tsakanin su a baya yanzu babu ita, kai gaba d'aya ya canza ya kuma zama miskili na k'arshe, magana ma ba kasafai yake yinta ba har sai ta zame masa dole. "Emm barka da yammaci Dr." Cewar Buzu had'i da d'an sunkuyar da kansa. Tsaf AT ya gane Buzu, yaron layin ne wanda yake tunanin courting Maryama yake, domin so tari yakan gansa har gidan Hajiya yana shiga ya gaishe ta. Saida ya d'anyi still kaman bazai amsa ba sai kuma yace "Barkan ka." A tak'aice. Maryama kam k'irjinta ne keta faman lugude. A hankali ta bud'e murya tace "Uncle sannu da zuwa." D'an dubanta yayi kafin yace "Ya baki tafi islamiyan ba kika tsaya a nan." Maryama ta kuma rungume K'ur'anin ta dake rik'e hannun ta kafin tace "Uncle dama latti nayi shine Haris yace bari ya saka ni." _Haris shine asalin sunan Buzu._ Kallon Buzu AT yayi kafin yace "Kana iya tafiyar ka ko, zan kaita." Buzu ya d'an murmusa had'i da sadda kai kafin yace "Toh Dr babu matsala, Allah Ya taimaka." Maryama sai k'yafta masa idanu take kan yayi ta'aziya ma AT. Har ta zaga mazaunin mai zaman banza zata shige ta jiyo muryan Buzu yanai ma AT ta'aziya... Still babu walwala saman fuskar sa haka ya amsa wa Buzu. Kai tsaye Buzu gidan su ya gangara yayinda AT da Maryama suka d'au hanyar islamiya. Cikin tsanaki yake driving d'in idanun sa naga bisa kwalta. Gaba d'aya sai ji tayi she's not comfortable, ta fi saba da wasa da dariyar da suke a baya, sam bata jin dad'in wannan changes d'in nashi, tausayin sa na rashin matar sa kuma uwar 'ya'yan sa ya kuma rufe ta. Muryar sa ne ya katse ta sanda yake fad'in "Maryam ba na hanaki shiga motar saurayi ba ko wani iri ne?" Maryama tayi shiru tama rasa masar da zata basa.... Jin ta soma 'yan kame kame yasa shi ci gaba da fad'in "Kar ki sake attempting shiga motar kowa idan dai bana gida ba kinji, komin rashin nisar wajen da zaku je." Gyad'a masa kai tayi kafin tace "Bazan k'ara ba Uncle insha Allah, dama yanzun ma tsoron duka nake shiyasa zan shiga ya rage min hanya." AT ya d'an juyo ya dubeta yanda tayi maganar cike da tsoro, shakka babu tsoron dukan take ji. Bai kuma fad'in komai ba har suka iso k'ofar Makarantar. Yana gama parking ta bud'e k'ofar ta sauk'o cike da tsoro, ga wasu Malamai kuwa sai tsaron latti suke. Ga mamakin ta sai ganin AT tayi ya sauk'o ya nufi Malaman, bayan sun gaisa bata jiyo maganar da ya masu ba, kawai dai ta hangi fuskokin su sai murmushi suke suna girgiza kai alamun babu komai. Juyowa yayi yanda ya barta nan tsaye, itama shi take duba.... Tana jiyo muryar Malam Kabiru yana fad'in "Maryama kizo ki shige ai ke baki latti sai ta b'aci." Da murmushin ta take kallon AT dake k'ok'arin bud'e marfin motar sa tace "Na gode Uncle." Murmushi kawai shima ya mata kafin yace "Allah bada sa'a koh." Daga haka Ya shige motar sa ya bar wajen. *************** Gidan da yaga Haris ya shige nan ya k'arasa yayi parking motar sa a k'ofar gidan, kafin ya bud'e motar sa ya fito.. Kaman daga sama saiko ga Buzu ya turo gate ya fito. AT ya tsaya yana karantar yanayin yaron sosai da yanayin dressing d'in sa.. Buzu ya fad'ad'a murmushin sa yana mai k'arasowa wajen AT dukda Charsman AT ya cika masa idanu. AT ya d'an Saki fuska kafin ya mik'a ma Buzu hannu sukai masabaha. Kaman babu mai cewa komai sai kuma AT ya katse shirun da fad'in "Malam Haris ko." Buzu ya gyad'a kai yana murmushi alamun eh haka. AT ya d'anyi jim kafin yace "Nasan kai mak'ocin Maryama ne sannan har gida ka kan je ka gaida Hajiya." Buzu ya kuma gyad'a masa kai. AT ya d'an saka makullin mota ya sosa kunnen sa kafin yaci gaba da fad'in "Toh Malam Haris kayi niyyan taimako Allah Ya saka, ban hanaka zumunci da Maryama da Hajiya ba amma ina so daga yau kada ka kuma attempting d'aukar Maryama a mota ita k'wallinta d'aya ka gane." ya k'arashe yana mai duban Buzu. Gyad'a masa kai Buzu yayi cike da shakku kafin yace "Insha Allah hakan bazata sake faruwa ba Dr za'a kiyaye." AT ya d'an murmusa da gefen bakin sa kafin yace "Yauwa madalla da fahimtar da kayi min koh..." Ya kuma mik'a masa hannu sukayi masabaha kafin Buzu yace "Allah Ya tsare, a sauk'a lafiya..." Sanda AT ya k'arasa motar sa ya tada ita ya nufi gidan Hajiya. Buzu ya bisa da kallo har motar sa ta shige gidan Hajiya kafin ya zauna saman benchin mai gadin su yana tunanin tsarewa irin na Dr Tahir. ************* "A'ah, maraba lale lale... Attahiru yau kaine a gidan namu, Masha Allah tunda yau har ka samu ka fito." Hajiya dake zaune bisa darduman ta k'asar bishiyar ta na hutawa ta fad'i. D'an murmushi AT yayi kafin ya zauna daga can gefe yana mai gaida Hajiya. Sai nan nan Hajiya take dashi, duk masifan da take masa sam yanzu ta rage tunda Aysha ta rasu, hasali ma yanzu tausayin sa take ji sosai sosai. Ta soma k'ok'arin mik'ewa domin kawo masa abin tab'awa. AT ya girgiza kai kafin yace "A'a Hajiya da kin barshi kawai, ai ban jima da cin abinci ba ma." Hajiya ta tsare sa da idanu tausayin sa na kuma ratsa ta kafin tace "Anya Attahiru, kafah duba kaga yanda duk ka rame ka lalace, ko gado ne kam za'a baka a asibiti." D'an murmushi yayi kafin yace "Lafiya lau nake Hajiyata, Hajiyan Maryama." Ganin ya d'an Saki ransa har yana k'ok'arin raha yasa Hajiya taji d'an dama dama, komawa tayi ta zauna a mazaunin ta tana tambayan sa jikokin ta. AT yace "Ai duk sun fice, Shema'u ta fita dasu ko zasu d'an mance abin." Nan da nan Hajiya tayi kicin kicin da fuska jin an anbaci Shema'u, bata san dalili ba amma sam tak'i jinin Zabiyar dadar Ayshan nan, kai yanda taki jinin Kulu, haka tak'i jinin Shema'u, dama Aysha ce zakka cikin su a cewar Hajiya. "Toh, toh toh, ai yayi kyau." daga jin yanda tayi maganar zaka gane ba har ranta bane, don kuwa Hajiya sam bata da b'oye, idan tak'i jinin ka kai tsaye take fad'a maka, ko ya maka dad'i ko kar ya maka, yanzu ma sabida 'yan jikokin ta ne ta fad'i hakan, amma sam tak'i jinin Shema'u. Gani take shantak'ewar ta kurum take tak'i aure, tayi boko har ta digirgire. Ta d'an muskuta kafin tace "Nikam Attahiru nace ba, yaushe ne Kulu da d'iyarta zasu tafi tunda dai naga har anyi bakwai ana harin ashirin." AT ya d'anyi jim kafin yace "Hajiya ai inaga zamansu a nan d'in na d'an wani lokaci har abin ya samu ya bar jikin yaran kaman zai d'anfi, tunda ba iyalai ne dasu ba koda sun koma can Jalingon." Tsegege kurum Hajiya ke kallon sa, tana son sille sa tana tausayin sa. "Uhm haka ne, hakan yayi." Abinda ta iya fad'i kenan had'i da kauda kai gefe tana mai tab'e baki. Shiru ne ya d'an biyo na wasu lokuta kafin AT ya d'an gyara zaman sa yace "Hajiya nikam nace ba, shi wannan yaro na nan mak'otan ku, farin yaron nan menene tsakanin su da Maryam?." Hajiya ta murmusa kafin tace "Au wai Harisu, Allah sarki Harisu yaron kirki, ai kana ganin sa watarana a nan." AT ya gyad'a kai kafin yace "Eh hakane, shiyasa nake son sanin ko akwai wata alak'a a tsakanin su." "Munadai mutunci, har mahaifiyar sa ma muna mutunci da ita, ai mutane ne masu karamci, ni banida burin da ya wuce ma su daidaita tsakanin su shida Maryama, kaga da zaran ta gama karatun ta sai a soma maganar biki tunda naga shi yaron kaman najin wani abu gameda ita." Ta k'arashe tana mai murmushi had'i da goga aswaki a bakin ta. Dumm! Haka AT ya tsinci maganganun Hajiyan. Ya jima yana kallon wani waje guda kafin ya soma girgiza kai yana fad'in "A'ah Hajiya, Maryam ba yanzu zatayi aure ba sai ta k'ara girma da karatu, sannan ni zuciyata bata kwanta da wannan yaron ba gaskiya. Karma a soma barinta tana zance tun yanzu, don inada tsarin da na masu daga ita har Sajida." Karan aswakinta kurum ta rik'e tana dubansa ba tareda ta furta komai ba. Kai Attahiru fah ya kusan kaita bango, ya kusan sakata ta sille sa. B'angare na zuciyarta ta shiga tausan ta tana nuna mata shid'in har yanzu cikin damuwa da alhinin rashin matar sa yake. Bata ce masa komai ba sai rangad'a kirawa Atine mai mata aiki data shiga yi. ********* Yaran sai yawo suke cikin Mall suna zab'an abubuwan da suke so, fuskokin su sun cika da annuri, ko meye suka nuna suna so Shema'u zata ce su d'auka da murnan ta without any hesitation..... Daga ganin su zakasan they are having a great time. Wayar Shema'u ne ya soma ringing, nan taga Hisham ne mai kira. D'an satan kallon yaran tayi taga hankulan su gaba d'aya naga shopping, cikin sauri ta d'aga wayar tana mai matsawa gefe kafin tace "Ehen ina jinka, what's new, what's on the ground." K'asaitacciyar murmushi yayi kafin yace "I can see you're having such a great time with your kids. Abu ya soma tafiya perfect kice." Murmushi ta d'anyi kafin tace "Na fad'a maka zan yi komai to win AT and his kids... Wait yaya akayi ka ganmu.?" Murmushi ya kuma yi kafin yace "Na fad'a maki I've eyes everywhere. Na ganku sannan naga masoyin ki tareda wata a mota." Dumm! Sautin da k'irjin Shema'u ya bada, cikin rawar murya take fad'in "Hisham wacece ita, wacece ka ganta da AT.? Whoever that bitch is, I swear I'm gonna kill her.. Hisham ka fad'a min pls." Gaba d'aya ta birkice lokaci guda. Dariya Hisham ya kuma yi kafin yace "Idan kinason jin komai in details, then you should come to my apartment, ni kuma sai na fad'a maki ko wacece harma na k'ara maki da ways d'in da zaki zama rid of her.." Cikin daburcewa wayar na damk'e a kunnen ta take fad'in "Wllhi zan zo, nayi maka alk'awari zan zo..." Hisham yayi dariya kafin yace "I'll be expecting you tonight." Daga haka ya kashe wayar d'if yana wani irin shu'umin dariya. Cak Shema'u ta tsaya tana rik'e da wayar a hannun ta tana wani irin turiri da huci ita kad'ai, tana tunanin irin kisan gillan da zatayi ma duk matan dataji an ganta tare da AT... Kaman daga sama ta jiyo muryar Sajida tana fad'in "Aunty Shemah lafiya, me ya faru kika tsaya ke kad'ai a nan, and you don't seem well." K'ak'aro murmushi Shema'u tayi gamida k'arasowa ta rik'e hannun Sajida tana fad'in "Ah em, is nothing sweetheart, I just received a call from my boss, wai yana gaya min banzo office ba na tsawon kwanaki nayi neglecting aiki na. Sweetheart ni kuma wllhi kunfi min aiki na, I can't abandon you sabida aiki na. He can go ahead and fire me idan dai akan farin cikin ku ne." Ta k'arashe tana gyara ma Sajida zaman rap round d'in dake kanta. Murmushi Sajida tayi soyayyar Auntyn nata na kuma ratsa ta, kafin ta rungume ta tace "I love you Aunt, you the best." Shemah ta murmusa itama tana mai hugging Sajida take fad'in "Nima ina sonki Sweery, both you and your siblings." Cikin zuciyarta kuwa tamkar ta shak'e Sajida haka take ji, babban burinta a yanzu shine ta ganta gaban Hisham, taji wata mai neman barin duniya ne take rab'an AT. *Sameena Aleeyou Mrs* [2:53PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *SHAK'UWA CE* 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 06 *漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�* _馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_ Suna fitowa daga WELLCARE kai tsaye gida suka wuce. Daga ganin yaran kasan sunji dad'in fitar da sukayi, sai ciye ciye suke a motar. Shema'u kuwa hankalin ta duk baya garesu, burin ta kawai taji da waye AT ke tare. Ta d'an saci kallon Sajida dake faman bud'e wani novel d'in James Hardly Chase me suna A COFFIN FROM HONGKONG. Duk cikin shopping d'in da sukayi ta d'auka, don dama ita Allah yayita mai son karance karance, kama daga English novels har zuwa Hausa novels. Shema'u ta lura hankalin su Ni'ima da Jamal naga kayan mak'ulashen da suke kan faman bubbud'ewa. Ita ko Sajida dake zaune gefen ta nata hankalin naga littafin hannun ta ne. D'an gyaran murya tayi idanunta naga kwalta, a hankali kafin tace "My Sajee, ina tsoron Daddyn ku yace zai sake aure, don nasan Stepmothers are always wicked, kar ta rabaku da Daddyn ku harma da mu... Sweery banso wani abu ya same ku..." Ai bata kai aya ba Sajida tayi saurin rufe littafin hannunta ta juyo tana duban Shema'u da damuwa ya nuna k'arara saman face d'inta kafin tace "Aunty Daddy ne zai k'ara aure, tabb! Ai wallhi Daddy Ya gama aure tunkan Momy, wllhi yace zai k'ara aure barin gidan zanyi, don ni bazan zauna da wata muguwar mata ba sai ke da Momma Aunty Shemah...." Ta k'arashe tana hura hanci. Shema'u da farko ta d'an ji drum! A k'irjinta amma dataji Sajida nason zama da ita tasan tabbas zata amince kai tsaye ta auri mahaifin ta. Murmushi ta d'anyi a fili kafin tace "Yauwa Sweery shiyasa nake sonki, nasan you can do everything to keep your mother's memories, nasan bazaki bari a kawo wata cikin gidan ba ta ringa amsa Lady of the house, rabaku zatayi da Daddyn ku koma ta salwantar daku gaba d'aya. Amma kinga nida Momma duk duniyar nan bayan Daddyn ku baku da masoyan da suka fimu tunda mune shak'ik'an Momyn ku, mune Flesh and Blood d'inta, we would never turn our backs on you, amma kowace mata da kuka gani, duk soyayyar da zata nuna maku one day eventually zata betraying naku sabida babu jinin mahaifiyar ku a tattare da ita. Kin gane abinda nake nufi Sweery..?" Ta k'arashe tana sakar ma Sajida murmushi. Gyad'a kai Sajida tayi kafin tace "Aunty pls pls don't ever leave us kinji." tayi maganar kamar zatayi kuka. Shemah ta murmusa kafin tace "Don't you ever worry dear, I'll always be here for you kinji." Ta k'arashe tana mai shafan gefen face d'in Sajida. Murmushi Sajida ta d'anyi amma k'asar zuciyar ta cike take da tunanin kar maganar Aunty Shemah ya zama gaskiya, kar Daddy yace zai k'ara aure don yanzu babu Momy,... Ita kad'ai ta shiga girgiza kai, cikin zuciyar ta taci gaba da fad'in "No, ina hakan bazata tab'a faruwa ba.. Wllhi da Daddy Ya kawo masu wata mata cikin gidan, kai ai gwara ma a fitar da gawar ta a gidan itama.... Haka Sajida ta dinga tunane tunane iri daban daban... Shema'u kuwa sai karantar ta take, tabbas tasan ta dasa dafi mai k'arfi zuciyar yarinyar, she's so easy to manipulate, bazata sha wahala wajen brainwashing nata ba. A hankali ta Saki wani murmushi mai cike da ma'anoni kafin ta maida hankalin ta ga driving... *************** Tana sako hancin motar ta a layin ta hangi motar AT ana hangame masa gate, haba nan fah ta kuma tsuma, alla alla take ta isa taga da wata shegiyar yake tare. Malam Audi me gadi, bai rufe Gate ba Motar Shema'u ta sako kai... A tare a tare suka shigo gidan da AT. Fitowar sa kenan daga cikin motar yana tsaye yana danna security lock ya hange su sai fitowa suke nik'i nik'i da kaya shopping bags daban daban. Ni'ima 'yar shekaru hud'u ta k'araso da gudu ta rungume sa tana fad'in "Daddy oyoyo." Rungume ta yayi had'i da d'aukan ta ya rik'eta a kafad'an sa yana tambayar ta ina taje haka, ina tsaraban sa... A tare su Shema'u dasu Sajida suka k'araso wajen. Fuskan Shema'u dake fente da kwalliya kuwa sai murmusa shi take. Hannun Jamal na rik'e cikin na Shema'u tana tsakiyan su shida Sajida. Gaba d'aya gaisar dashi suka soma yi, Ni'ima sai tura masa Malteezars cikin bakinsa take tana fad'in saidai ya sha. Su Shema'u su Sajida kuwa sai dariya suke.. Momma dake mak'ale window d'in d'akinta tana hango su, dad'i ya rufeta, tabbas AT da Shema'u da yaran sun dace, like a real family.. Kai Allah dai ya tabbatar da hakan sai tafi kowa farin ciki... Jamal ma ya soma mik'a ma AT bigbom sweet yana fad'in "Daddy nawa zaka sha, pls Daddy kaji... Duk yaran suka rikita sa,.. Su Shemah kuwa sai dariya suke tana rik'e da kafad'un Sajida. Jamal yace "Daddy Aunty Shemah tanda kirki..." Caraf Sajida tace "Eh Jamal, she's really kindhearted, we love her..." Ta k'arashe tana kallon Shema'u... Itama Shema'un Sajidan take kallo kafin tace "And I love you too My Sajee keda k'anenneki gaba d'aya." D'an jim kawai AT yayi yana kallon su ba tareda ya furta komai ba. Shafa kan Jamal da Ni'ima yayi kafin yace "Su shige gida Magrib ta kunno kai... Gaba d'aya suka nufi cikin gida harma da Sajidar. Da gangan Shema'u ta d'an lank'washe k'afar ta kaman zata fad'i, ta soma ciza lab'e... AT dake k'ok'arin nad'e hannun rigar sa don gabatar da alolan magarib da sauri ya d'ago yana duban ta... K'arasawa yayi yanai mata sannu yana tambayarta bataji ciwo ba. Shema'u ta d'an yi murmushi wanda yafi kama da yak'e kafin tace "No, banji ba... Thanks." Saurin Kauda kansa gefe yayi don kuwa wuyar rigar ta Ya d'an sab'ule... Ita kuwa a nata b'angaren da biyu tayi hakan. Har ya juya ya soma tafiya itama ta nufi cikin gida ta jiyo killing voice d'insa ya ambato sunan ta, kai batama tab'a jin ya kira sunanta ba sai yau. D'an juyowa tayi tana duban sa... AT ya d'an tako kad'an kafin ya dube ta yace "Thank you, thank you for keeping the kids company.... And pls next time kar ki sake kashe kud'i haka da yawa akan su.... You can save your money." D'an murmushi Shema'u tayi kafin tace "Doc you don't have to thank me for anything though, duk abinda na masu kaman nayi ma kaina ne, tunda abinda yayi Aysha shi ya yini, those kids are my kids koda Aysha ko babu Aysha. So pls ka daina min godiya, snnan maganar kashe kud'i kuma, duk abinda suke so idan har baifi k'arfina ba zan masu shi, tunda nasan kana masu fin haka. Yanzu ne suke buk'atan kulawa more than ever." Ta k'arashe tana mai saka fuskar tausayi sai ka rantse har zuciyar ta, iyakacin gaskiyar ta kenan. D'an jinjina kai yayi ba tareda ya iya furta komai ba, Shema'u ta rakasa da mayen kallo kafin ta murmusa tace "Ni zan shiga ciki Dr, have a good evening." Kallo ya bita dashi har ta b'ace ma ganin sa kafin ya nufi bakin famfon da ake bayi ma flowers, tun kan ya iso Malam Audi har ya tara masa ruwa a buta... Daman ya saba masa hakan, tun AT na hanasa har ya hak'ura, watarana idan AT d'inma ya riga Malam Audi toh shi yake tara wa Malam Audi ruwan. Haka suke gudanar da rayuwar su cikin girmama juna, babu nuna k'ask'anci, wannan d'aya ne daga cikin d'abi'un AT masu kyau, rashin d'aukan kai wani abu, dukda tarin nasara da Allah Ya basa a rayuwa, wanda haka ake so bawa na k'warai ya kasance. ***************** Suna shiga gidan wajen Mama Juu suka nufa suka wuce kakarsu Momma dake tsaye tana jiran shigowar su, gaba d'aya harta Sajida wajen Maama Juu suka nufa kowa yana nuna mata tsarabar da ya kawo mata.... Ita kuwa sai rungumar su take d'aya bayan d'aya. Momma kuwa haushi kaman ya kar ta, kai ta k'osa wannan mayyar matar ta koma gidan ta, tunda dai ita da Shema'u kad'ai sun isa su kula da yaran. Murmushi kawai Shema'u take tana kallon Momma data had'e rai ta fita sabgan yaran, a zuciyar ta take tabbatar da wautar mahaifiyar ta, tabbas idan wannan hanyar zata bi bazata sami soyayyar yaran ba kaman yanda take so su so ta.... Da sauri ta k'arasa wajen su kafin ta shiga ciro kaya cikin jaka tana mik'awa Maama Juu tana fad'in itama ga tsarabar ta.... Haba nan Momma ta kuma kawowa wuya. ************** "Don't be stupid Hisham, ka fad'a min ta yaya zan fito a daren nan, ai sai su soma zargina da wani abin. Na riga na soma cusa wa yaran soyayya ta cikin zukatan su, kar ka b'ata min plans d'ina." Cikin k'asa da murya take maganar bayan ta k'ule a d'aki. Daga d'aya b'angare Hisham ya murmusa kafin yace "Take your time My Ally, na maki uzuri na yau, amma ina tsammanin ganin ki gobe da safe sannan kar ki kawo min excuse." D'an tab'e baki tayi had'i da juya idanu kafin tace "Alright, hakan yayi kar ka damu I'll keep my word..." Jin an murd'a handle d'in k'ofar d'akin ya sata sakin zancen da fad'in "Oh oh oh, kar ka damu Sir, I'll see what I can do, maybe zan zo koda next weekend ne, kasan na fad'a maka nike kula da yaran.. Okay okay yauwa na gode, have a good evening sir." Daga haka ta katse wayar ta juyo tana duban Momma datayi zaune saman Couch. Murmushi Momma ta sakar mata kafin tace "Shema'u gaskiya kin burgeni da d'awainiyar da kike da yaran 'yar uwanki, I never thought zaki tab'a zama very responsible haka, gaskiya kinyi tunani daughter.... " Ta k'arashe tana murmusawa. Zama Shema'u tayi bisa gado tana wata irin murmushi kafin tace "Momma me anfanin SHAK'UWAR da mukayi da Aysha idan har ban rik'e yaranta ba, as they say "Blood is thicker than water, koda aure AT yayi bazan bari kishiyar uwa ta gallaza ma yarana ba...." Kan ta kai aya Momma tayi saurin fad'in "Allah tsari bakin ki, Tahir yayi aure kike fata, haba Shema'u idanma zaki masa fatan aure ai addu'an ya aureki zakiyi, ba wata shegiya ba." Shema'u taji dad'in maganar Momma dama nata view d'in take son ji, tunda watak'ila bazata so ta auri AT tunda mijin k'anwarta ne, dukda a addini hakan bai haramta ba amma a Al'ada yayi wani iri saidai k'anwa ta auri mijin ya. Bata furta komai ba sai murmushin da take, Momma kuwa taci gaba da fad'in "Ke bakiga yanda kuka dace bane gaba d'aya dashi da yaran, gwanin sha'awa, Karma ki bawa ma wata banza k'ofa tazo tayi taking place d'in da nake so ki samu a gidan nan.... Koda baki son shi kar ki damu a hankali zaki so shi don Tahir miji ne da ko wace Mace take fatan samu. Mik'ewa Shema'u tayi tana murmushi kafin ta k'arasa ta rungume Momman ta ta baya kafin tace "Anything for my kids Momma." Tayi maganar tana wani irin murmushi. Shigowar sa parlorn kenan ya hangi littafan Sajida na karatu, dangin su questions and answers da ya danganci Waec, novel ya hanga saman littafan da alama karatu take ta tashi... K'arasawa yayi ya d'aga novel d'in yana juyawa kafin ya shiga doka mata kira. Tun bayan rasuwar matar sa basu ji yayi irin wannan kiran ba, A tare Sajida dasu Shema'u da Momma suka fito. Cirko cirko sukayi suna kallon AT, yayinda Sajida ke sauk'owa da stirs kaman kazan da k'wai ya fashe ma. D'aga novel d'in yayi yana jefa mata mugun kallo kafin yace "Me kike yi da wannan bayan kina jarabawa.?" Shiru bata iya amsa sa ba, sai k'walla dake neman ciko idanunta don kuwa tasan halin mahaifin nata idan ransa ya b'aci, duk wasa da dariyar da yake masu akwaisa da tsayarwa musamman akan karatu..... Muryarsa ya kuma dakan dodon kunnen ta. "Answer me! Me kike da wannan..." Shema'u ta dubi Sajida dake faman zuban hawaye da sauri ta k'arasa gaban AT tana wani yauk'i da murmushi kafin tace "Oh that's mine, ni na barshi wajen, don tare muke zaune d'azun, ba nata bane don't scold her pls." Kallo ya bisu dashi ba tareda ya furta komai ba ya ajiye novel d'in ya nufi stirs. Suka bisa da kallo har ya shige kafin Shema'u ta k'araso tayi hugging Sajida. Sajida na murmushi take fad'in "Aunty yau kin cece ni, wayyo thank you Aunty na, da Daddy yasan nawa ne yau da na yaba wa aya zak'i, thank you Aunty Shemah.... " Murmushi Shema'u ta sakar mata kafin tace "Anything for you sweetheart, yanzu ki sai ki kiyaye kinji kar ya kuma gani. " Da sauri Sajida ta gyad'a mata kai suna masu sakar ma juna murmushi. Wani sabon dad'i ya kuma mamaye Momma. **************** Har wajajen 8:am su Sajida basu zo sun d'auketa ba, gashi 9:00am zasu shiga jarabawar. Takwas d'inma har ta gauta da 'yan dak'ik'ai.. "Hajiya kawai zan shiga adaidaita." ta fad'i tana rufe littafin hannun ta. "Maryama yaushe kika fita, yaushe kika sami adaidaita, ai zakiyi latti, bari dai na kira Attahirun naji dalilin da yasa su Sajidan basu zo ba." Hajiya ta fad'i sanda take ciro wayar ta a bakin zani. Mik'a ma Maryama wayar tayi kana tace maza nemo min shi. Maryama ta d'an turo baki kafin tace "Kai Hajiya yanzu fah Uncle yana wajen aiki, haka kurum a kira sa, ya bar aikin sa kenan ko me, aidai gwara na shiga adaidaita, k'ila sun mance ne." "Ke bana son iyayi fah tam, kaiki makarantar ba aiki bane, idan bazaki kira sa ba, bani kiga na kai ma Ilu ya kira min shi." Girgiza kai kurum Maryama tayi kafin tayi dialing lambar AT ta mik'a ma Hajiya baki a ture. *Sameena Aleeyou Mrs* [2:53PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *SHAK'UWA CE* 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 07 *漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�* _馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_ *Fatan Alkhairi a gareku masoya littafin Shak'uwa馃槏馃* Yana tafe bisa kwalta hanyar TH ya nufa, domin akanyi booking nasa a TH ya kalli patients. Yau Surgeries daban daban ma yake dasu a TH d'in.... Wayar Hajiya ce ya shigo masa, Saida ya rage speed kafin ya d'aga wayar da hannu guda, hannu guda naga steering wheel. Gaisawa sukayi nan Hajiya ta sanar dashi buk'atar ta... Sosai AT yaji mamakin rashin d'aukan Maryama da basuyi ba, koda yake Shema'u ce ta kaisu ba lallai idan yaran sun fad'a mata ba, shima shaf ya mance bai fad'awa Shema'u zasubi gidan Hajiya su d'au Maryam ba. Dole AT ya d'auki hanyar gidan Hajiya don ko kusa baiso Maryam tayi missing exams d'in ta. Yana ida waya da Hajiya wata wayar ta kuma shigowa. Dr Ashfaq ne wanda suke ganin mutane tare a TH. "Dr ya muka jika shiru ne, hope all is well?.. Komai ya zama ready, the room and everything, so kai muke jira a shiga da patient d'in." Cewar Dr Ashfaq daga d'aya b'angaren. Cike da miskilanci ya soma maganar domin kuwa d'abi'ar sa ce, bada raini ko wulak'anci yake yin hakan ba, hasalima duk wanda ya sanshi toh kuwa yasan wannan d'abi'ar nasa "Em lafiya Ashfaq, ka gane just go ahead with the preparations, get the first patient ready I'll be there in a bit,... Okay, yauwa na gode Dr." Ya k'arashe wayar had'i da d'an fuzar da iska.... Yana shiga kwanar Janbulo wata wayar ta kuma shigo masa, daga can asibitin sa ake kiran sa.. Nan aka kuma sanar dashi jikin wani patient ya tashi.. Sosai hankalin AT ya tashi don shi akwai son kula da marassa lafiya. Cikin sauri ya shiga neman layin Hisham don yasan Hisham da lattin fita office. Hisham na kwance saman gado Shema'u na gefensa suna aikata masha'a wayar AT ya shigo masa... Kaman bazai d'aga ba sai kuma Shema'un ta tirsasa masa d'agawa. Murya irin ta mai barci ya soma magana. "Hello Doc.." Ya fad'i yana wani matse idanu tamkar mai barci. Daga d'aya b'angaren gajeren tsaki AT yayi kafin yace "I knew it, nasan baka tashi ba, bayan kasan yau kaine a clinic ni zan tafi TH... Hisham don Allah ka tashi ka tafi, patients na buk'atan ka. "Relax Doc, idan kabi na mutane tas sai sun k'arar maka da k'arfin ka, sam AT baka huta ma rayuwar ka, kullum cikin aiki... Yanzu kana can TH d'in ne.?" Ya k'arashe yana kallon Shema'u data kafe sa da idanu. D'an tsaki ya kumayi kafin yace " Naje zan ajiye Maryam a school amma daga can TH d'in zan wuce.... Wai ma Me amfanin karatun daka jima kana yi idan bazaka dedicating lokutan ka ma Al'umma suma su anfana ba... Pls Hisham no time for jokes, ka tashi ka shirya pls.... Sai munyi magana." Daga haka ya kashe wayar daidai sanda yake horn a gate d'in gidan Hajiya. A gurguje suka gaisa da Hajiya, sauri sauri suka fice shida Maryama Hajiya na masu addu'an Allah Ya tsare. Sai faman satan kallon sa take da wutsiyar idanu, shikam kullum k'uriciyar sa dad'a fitowa take ta rufe tsufar sa, sam bazakace ya aifi d'iya kaman Sajida ba. Yana sanye da Jampa ruwan k'asa kansa babu hula, sajen nan nasa a kwace luf, ta kai dubanta ga hannayen sa dake rik'e da steering kaman ka tab'a jini ya fito, so fresh, ga agogon Rolex dake d'aure a hannun nasa, kai gaskiya Uncle d'an gayun k'arshe ne, shi k'anshin sa ma daban ne, ko yaushe cikin k'anshi da gayu yake, duk yanda ya zauna toh k'amshin sa yakan rinjaye wajen, tabbas shida Aunty Aysha sun dace da juna, dukansu 'yan gayun k'arshe ne, Allah sarki mutuwa mai raba tsakani, tausayin sa ya kuma ratsa zuciyarta..... Gabanta ne yayi mugun fad'uwa, ta shiga tambayar kanta. Anya lafiyanta kuwa , meyasa take jin tana tsintar kanta wani irin yanayin duk sanda suka keb'e da Uncle, sannan meyasa take yawan tunanin sa har tayi k'ok'arin wuce gona da iri..? Tabbas ita kanta zuciyarta da take faman shek'o mata wad'annan tambayoyi bata da amsar su, abu guda da tasani shine SHAK'UWA CE sosai a tsakanin su ..... Tana cikin tunanin ta jiyo muryar sa yana fad'in "Wani exam zakuyi yau.?" A d'an tak'aice ta amsa masa da "Chemistry practical." Jinjina kai yayi kafin yace "Har yanzu baku gama practicals d'in ba.?" "Eh ni idan nayi yau ahikenan su Sajida ne masu yin Food and nutrition su kuma sai Thursday." ta kuma yin maganar duk ba'a sake ba, sam bata saba da wannan canzawar da yayi ba, ta sani tuntuni miskili ne dukda SHAK'UWAR dake tsakanin su amma yanzu abin ya kuma yawa, k'ila rashin matar sa ne. AT ya kuma jinjina kai kafin yace "Meyasa ke bakiyin Food and Nut d'in, ko Hajiya ta koya maki girkin ne?" Yayi tambayar teasingly. D'an murmushi tayi tana mai kallon 'yan yatsun ta kafin tace "Ai Hajiya bata barina nayi girki." D'an karkato da fuskar sa yayi ya dubeta kafin yayi murmushi ya maida fuskar sa ga kwalta sannan yace "Ai kinyi k'arama ma yin girki ne shiyasa, saidai irin ta makaranta banda na gida." D'an ware idanunta tayi kafin tace "Laa Uncle fah masu shekaruna ma suna girki." Ya juyo ya dubeta yanda tayi maganar cike da yarinta kafin yace "Nawa ne ma shekarun naki.?" Still idanunsa naga kwalta yayi tambayar. "18 fah zan cika Decembern nan." Murmusawa kurum AT yayi yarintar ta na burge sa kafin yace "Au ashema kin d'an fi Sajida, toh ke kin kusa fara gwada girkin amma sai kin cika 18 d'in." Bata kuma cewa komai ba sai murmushin da tayi kanta a k'asa lokaci guda kuma taji wani iri, don harga Allah sosai yanzu take jin nauyin sa. K'arfe 8:45am daidai suka iso makarantar. Ta bud'e marfin mota tana fad'in "Na gode Uncle." Kallon ta Ya d'an yi kafin yace "I hope babu dukan latti." Murmushi tayi kafin ta girgiza masa kai tace "No ba'a tare 'yan SS3." Gyad'a kai yayi kafin yace "Allah bada sa'a koh." Ta amsa da ameen kafin ta shige. Saida yaga shigewar ta kafin yaja motar ya bar wajen. *********** "That imbecile is always bossing me around. Nunawa yake kaman yafi kowa iya aiki da son taimaka ma mutane, I'm sick of him already, kaman na shak'esa na huta haka nake ji." Hisham ya fad'i sanda yake had'a boturan rigar sa. 'Yan kunnayen ta take sakawa kafin tace "You watch your mouth Hisham, ina gargad'in ka don't mess with my AT...." ta k'arashe tana yawo da d'an yatsar ta saman fuskar sa. Murmushi Hisham yayi kafin yasa hannu ya kamo k'ugunta ya had'e da nasa waje guda, dab da fuskarta yake magana cikin sigan rad'a "Kiyi a hankali my Ally dukda nasan baki fed'e min sirrinki gaba d'aya ba amma ki sani Hisham ya wuce tunanin ki." Murmushi ta d'anyi kafin ta sauk'e masa light kiss a lips d'insa tace "Dangantakar wancan bak'ar yarinyar da AT zaka fad'a min, dukda nasan AT ya ninka ajin wannan yarinyar sau babu adadi I still need to take precautions, don irin wad'annan munafukan yaran sunfi manya iya makirci." Hisham ya murmusa kafin yace "Next time zan fad'a maki, kinga yanzu fita zanyi. D'aukar handbag d'inta tayi had'i da gyara mayafinta kafin suka fito a jere.. Cikin zuciyarta tsantsan tsanar Maryama da uwarta ne zalla, tun yanzu gwara ta soma tunanin ways d'in da zatabi ta rabu dasu, musamman data tuna yanda yaran AT ke son uwar yarinyar, sannan ita kanta Sajida tana tsananin son yarinyar.... Kai dole ma yau taje d'aukan su makaranta don ta kuma ganin yarinyar sosai, tabbas ta ganta lokacin rasuwar Aysha amma sam tama mance kamannin ta, ko banza she feels at ease, don dai wannan yarinyar ne ai batada mastala, ta zaci wata babbar mace ce mai aji irinta Hisham ya gansu da AT d'inta... Da wannan tunanin ta isa jikin motar ta k'irar Accord... **************** Da gudu Sajida ta k'araso ta rungume ta tana dariya take fad'in "Maryama don Allah kiyi hak'uri, wllhi Aunty Shemah ce ta kawo mu, sai surutu muke a motar shaff na mance da ke, sorry pls." Harara Maryama ta galla mata kafin tace "Da nayi missing exams ai bakida damuwa." Dariya Sajida tayi had'i da janyo kafad'an Maryama suka nufi bakin hall d'in tana fad'in "Ai da bakizo ba ma bazan shiga ba nima saidai nayi missing.." Da haka suka k'arasa don already an soma shiga. ************* Zaune take cikin motar ta sai faman hangen ta ina su Sajida zasu fito take, burinta bai wuce taga Maryama ba. Can ta hangesu suna tahowa itada Sajida, sai yanzu ta samu ta k'are ma yarinyar kallo. Chocolate ne in colour, don kai tsaye baza'a kirata bak'a ba sannan sam bata a layin farare. Shakka babu dukda uniform ne a jikinta zaka fahimci Allah Ya mata diri mai kyau, bata faye tsawo ba sannan ita ba gajeriya bace, irin mutanen nan ne da bature ke kira average, batada wani tsananin kyau sai manyan idanu da d'an k'aramin lips d'inta, sannan koda murmushi tayi kumatun ta suka d'an lotsa, wannan shine iyaka qualities d'in da Shema'u ta hango tattare da ita.... Wani murmushi ta saki don kuwa wannan ai ko makaho ya shafa yasan bata dace da AT ba, aima ruwa ba sa'an kwando bane, Babban goro sai magogin k'arfe, bayan k'aracin shekaru akwai rashin wayewa a tattare da ita, AT da ita ya dace, yanda yasha boko ya k'oshi ma bazai tsaya soyayya da k'aramar yarinya 'yar cikin sa irin wannan yarinyar ba. Dama bata tsaya damun kanta ba idan dai don wannan yarinyar ce. Abu guda da zatayi kawai shine ta dasa ma Sajida tsanar ta cikin ranta..... Muryar Sajida ce ya katse ta sanda suka k'araso tana fad'in "Oyoyo Sweet Aunt, ashe har kin iso." Shema'u ta bud'e marfin mota ta tafi tayi hugging Sajida tana gogge mata fuska da hanki kafin tace "Na iso tunkan ku tashi My Sajee, kinsan I don't wanna keep you waiting, sabida banso ki wahala, yaya exams, me kike son ci..?" Ta k'arashe tana wani ware idanu tana sakar ma Sajida sassanyar murmushi. Maryama dai jinin jikinta tasha, don harga Allah itakam sosai Aunty Shema'u ke bata tsoro, bata san dalilin hakan ba..... Tana cikin tunanin ta jiyo muryar Sajida tana fad'in "Maryama ga Aunty Shemah baku gaisa ba." D'an murmushi Maryama tayi kafin ta rusuna ta gaida Shema'u. Da sakin fuska Shema'u ta amsa mata hannun ta still rik'e cikin na Sajida kafin tace "Okay girls mujen ku koh.." A sanyaye Maryama dai ta nufi backseat yayinda Sajida ta nufi front seat sai faman murna take tana fad'in "Wllhi Aunty don kece da tada Daddy ne sam sai ya mance damu, ina sonki Aunty yanda kike son mu... Shema'u murmushi kawai take tana driving kafin tace "Sweetheart anything for you, you and your siblings are my top priority... Faranta maku ya fiye min komai.." ta k'arashe maganar tana satan kallon Maryama datayi jigum a bayan mota ta cikin mirror. Kashe AC d'in motar Shema'u tayi tana tara miyau a baki kafin tace "Baby ya sunan k'awar taki ma.?" Sajida tace "Maryama Aunty. Baki ganeta bane, gidan Hajiya fah take." Shema'u ta zubar da yawun bakinta kafin tace "Oh na ganeta, itace d'iyar Nannyn su Jamal koh, sannu Maryama, amma dai kina sure da body spray koh, kinsan fah kun zama 'yammata, idan baku kiyayewa wari zaku keyi duk yanda kuka shiga. Nasan My Sajee bata wasa da kayan k'amshi, kike k'ok'ari kina amfani da kayan k'amshi kinji Maryama, yanzu kiji yanda gaba d'aya motar nan ta hamame sabida shigowar ki... So nake ki gyara shiyasa na fad'a maki kinji." Ba Maryama kawai ba harta Sajida saida taji babu dad'i abinda Aunty Shemah tayi, ta yaya zatace Maryama tana wari, bayan tsafta irinta Maryama, kai duk yayen d'alibai ma da akeyi ita take karb'an wacce tafi kowa tsafta... Kuma itakam sam bata tab'a jin wari a jikin Maryama ba tsawon shekarun da sukayi a tare. Iya k'uluwa Maryama ta k'ulu, tsanar matan ya kuma shiga ranta, itace mai wari... A duniya babu abinda ta tsana irin wari, amma shine yau har ita akece ma me wari, tana son mutum d'an gaye, amma Sam banda Aunty Shema'u dukda gayu da take ji dashi..... Sajida ta d'an lek'o tana duban ta zatayi magana Shema'u tayi saurin fad'in "Me kuke son ci, ko a biya daku eatery ne, Maryama ko bakujin yunwa ne..?" Ta d'an juyo tana duban Maryama datayi zaune kurum cikin motar kafin tace "I hope dai ba abinda na fad'i bane ya b'ata ranki, kiyi hak'uri ni na d'auke ki ne kaman Sajida, duk abinda na gani na gyara zan maku both ke and Sajida tunda ku d'in tamkar sisters kuke, right my Sajee.?" ta k'arashe tana duban Sajida. Haba nan fah Sajida ta kuma jin dad'i ta kuma yarda lallai Aunty Shemah tana son su da gaske, tunda gashi soyayyar ta shafi har mutanen da suke so. Murmushin yak'e kawai Maryama tayi wanda hausawa ke cema tafi kuka ciwo, Alla Alla take ta isa gida ta tambayi Hajiyar ta ko da gaske tana wari. Marayama suka soma ajiyewa, tai masu sallama kafin ta fice ta nufi gate, a daidai k'ofa suka had'u da Buzu, nan suka tsaya suna magana... Sajida tayi saurin rik'e hannun Shema'u dake saman steering wheel tace "Wayyo Aunty don Allah d'an tsaya.. " Ta k'arashe maganar tana kallon Buzu had'i da sakin sassayanyar murmushi, shiko sai magana yake da Maryama da alama cikin raha suke zancen. Shema'u ta kafe Sajida da idanu tana karantar ta yanda take kallon Buzu kafin ta saki wata murmushi tace "Baby shi kuma wancan d'in waye. Your crush I guess?" Murmushi Sajida tayi had'i da rufe fuska alamun jin kunya. Shema'u ta murmusa sanda taci gaba da driving kafin tace "Sajee tsakanina dake babu wani kunya, ina so ki zama very free da ni, mu zama tamkar k'awaye, ki dinga fad'a min damuwar ki sabida bakida mahaifiyar data fini a yanzu, sannan yanzu ne kike buk'atar Uwa da zata guiding naki, tunda kin soma girma Sweery." *Sameena Aleeyou Mrs* [2:54PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *SHAK'UWA CE* 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *08* *漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�* *_馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_* "My Sajee ina sauraren ki, go ahead fad'a min abinda ke ranki, nai maki alk'awarin I'll support a duk abubuwan da kike so, irin support d'in da uwa zata bawa d'iyarta, sabida bakida wacce ta fini." Shema'u ta fad'i sanda suke hawa babban kwalta. D'an muskutawa Sajida tayi cike da jin k'arfin gwiwar fayyace ma Shama'u abinda ke zuciyar ta kafin ta soma fad'in "Aunty I'll be honest with you, ina fatan ki fahimce ni pls." Shema'u ta murmusa had'i da gyad'a kai kafin tace "Ina sauraren ki daughter, don't hesitate pls kinji, kar ji d'ar d'in fad'a min ko meye, mother's daughter's talk muke yanzu so kar ki b'oye min komai, I promise to guide you to the right path insha Allah." ta k'arashe maganar in a serious tune, sai ka rantse iyakacin gaskiyarta kenan. "Aunty,... Magana ta gaskiya ban tab'a son wani namiji ba kaman yanda nake son Buzu, tun lokacin dana soma ganin sa Allah Ya jarabce ni da son shi Aunty bansan yaya zanyi ya gane irin soyayyar da nake masa ba, farkon dawowar su unguwar Hajiya sam Maryama bata shiri dashi, idan ya mata magana ma bata amsawa, ni ce dai na dinga rok'onta kan ta bari ko gaisawa suna yi tunda kowa a layin yasan kirkin sa da son mutanen sa, da k'yar Maryama ta amince mun suka soma mutunci da Buzu har gidan Hajiya yanzu yana zuwa, sun saba sosai." Shemah tayi murmushi kafin tace "Oh kice Baby na ta iya soyayya.?" Sajida ta d'an rufe fuskar ta. Shemah ta kuma murmusawa kafin tace "Don't be shy, that's natural dear, at your age zaki sami first love d'inki dama, and ya tabbata Buzu shine masoyin ki. Amma meyasa ake ce masa Buzu, bashida asalin suna ne.?" Girgiza kai Sajida tayi fuskarta cike da murmushi kafin tace "No Aunty sunan sa Haris, wllhi Maryama ce dai tasa masa Buzu sabida yana kiranta 'Yar Kunama, toh yanzu Buzu ya bisa, idanma kika shigo layin nan wani sa'in idan bakice Buzu ba baza'a gane ba,... Amma ai yaci sunan sa Buzu ko Aunty, kin gansa fari k'al kaman balarabe." Shema'u tayi murmushi kafin tace "Aah gaskiya yaci sunan sa Buzu, sannan shida d'iyata would make a perfect couple, dukanku farare kyawawa..." Wani murmushin jin dad'i Sajida tayi, har ranta taji dad'in furucin Aunty Shemah.... Muryar Shema'u ya katse mata murmushin nata sanda take fad'in "Amma kuwa kin tabbata babu wani abin tsakaninsa da Maryama.?" tayi tambayar idanunta naga kwalta. D'an jim Sajida tayi tana dubanta kafin tace "SHAK'UWW CE kawai a tsakanin su, sannan Maryama tayi hakan ne sabida ni, don kinsan Daddy bazai bari na fara soyayya yanzu ba, kinsan shi allazi boko, mafarkin sa bai wuce nima na zama Likita kaman shi ba, ko fah waya Android bai bari mun soma rik'ewa ba wai sai mun kammala Waec, kiji fah Aunty, wake yayin haka yanzu...Shiyasa nake so tun yanzu a saba da Buzu harda Hajiya baki d'aya, tunda yanzu na kusan kammala WAEC d'ina ai zai cika alk'awarin sa ya mallaka min waya." Cikin ran Shema'u wani irin haske da dad'i yayi mata, tabbas amfani da Sajida sam bazai mata wahala ba, don ta lura yarinyar asalin d'iyar fari ce, akwai wauwauta sosai akanta. Saida ta d'anyi gyaran murya kafin ta soma fad'in "Haba Daughter kaman bakije school ba, wake yin haka yanzu, wake trusting wata k'awa a wannan zamani da muke ciki, ke bakisan duniyar nan baki da aminiya sai mahaifiyar ki ba ko, har yaushe zaki yarda da k'awa ki barta ta sami kusanci da saurayin da kike so kike mafarkin kasancewa tare dashi..? Toh bari kiji na fad'a miki, ki bud'e kunnuwar ki da kyau kiji ni, the moment kika bawa k'awa dama har SHAK'UWA ta shiga tsakanin su da saurayin da kike so before you know it shak'uwar ce zata rikid'a ta koma soyayya,. Ke bakiga irin kallon da yake ma Maryama ba, sannan itama bakiga yanda take gwale masa baki tana murmushi ba, only lovers can do that. Ki kula da kyau kiyi nazarin abinda na fad'a maki, sannan da ace tana sonki dashi, da tuni ta soma yin wata hanya koda dabara ne kun soma soyayya koda a b'oye ne, da zaran lokaci yayi kinga yasan yanada ke kema kinada shi, saidai kawai a gabatar da iyaye.." Sajida ta d'an dubeta kafin tace "But Aunty bana son na zama me b'oye rayuwar da nake ciki wa iyaye na, sabida Momy da Maama Juu kullum gargad'in da suke min kenan kar na zama mai yin wani abu maras kyau bayan idanun su..." Parking a gefen titi Shema'u tayi kafin ta karkato sosai tana mai duban Sajida, fuskarta fal damuwa kafin ta soma fad'in "Sweetheart try to understand me, I'm not saying you should be hiding things, shiyasa ma nace maki ki zama free ki zama open dani, yau da ace Momyn ki tana nan, the same abinda zata fad'a maki kenan, besides sonshi kawai kike da manufa mai kyau ba da niyyan lalacewa ba right.?" Sajida ta gyad'a kai tana duban Shema'u. Shema'u ta kuma shafa fuskarta kafin taci gaba da fad'in " Ehen, ni na sani, My Daughter is a good girl, bazaki tab'a yin wani abu maras kyau ba tunda kinsan makomar wanda ya lalata rayuwar sa, sannan hanaki yin abinda kike so da Daddyn ki zaiyi shine zai jefa ki cikin rayuwa maras inganci, sannan hanaki yin abinda kike so zaisa ko karatun ma da yake so kiyi kizo bakiyi ba, kinga kuwa ai ba'aci riba ba ..... ki saurare ni da kyau ki gane me nake nufi, shi Daddyn ku namiji ne, ba lallai ya fahimci irin hakan ba, shiyasa ake cewa ciwon d'iya Mace ta d'iya Mace ne, shiyasa Uwa take zama babbar aminyar D'iya da zaran ta doshi irin shekarun ki, ni na tabbata if Aysha was still here hakan zata fad'a maki.. Sajee I love you and I want your happiness, bana son wani abu da zai ruining maki rayuwa, daga baya na tabbata Daddyn ki zai fahimci hakan, sabida tak'ura ma yaro bashida wani alfanu especially a Teenager like you..... Kin fahimce ni Sweery.?" Ta k'arashe cikin tsantsan sadda murya tamkar mai shirin yin kuka. Sajida ta gyad'a kai kafin tace "Wllhi haka ne Aunty, tak'urawar bashida wani alfanu. Toh yanzu yaya zanyi nayi grabbing attention nasa Aunty.?" Shema'u ta d'anyi murmushi kafin tace "Thanks for understanding me, kar ki damu duk lokacin da kike sonyin waya dashi zan rik'a baki wayata kuyi waya har lokacin da Daddyn ki zai sai maki naki tunda saura k'alilan ne ki kammala Jarabawar k'arasa sakandaren. Sannan yanzu ki sami ita Maryama da zancen cewa tasan yanda za'ayi ta had'aki da Buzu, duk yanda kukayi sai ki sanar dani. Kinga idan kinyi haka baki zama mai b'oye Al'amranki ba tunda kin sanar dani, sannan da Aysha ta tana nan da ma ita zaki fad'i, tunda bata nan sai ki sanar dani, bazan daina fad'a maki bakida masoya kaman dangin mahaifiyarki ba kinji Sweetheart.... Hakan yayi maki.?" Da sauri Sajida ta shiga gyad'a kai tana fad'in "Aunty wllhi shiyasa nake jin ina k'ara sonki sabida kina fahimta ta a koda yaushe. Thank you Aunty Shemah, please kar ki bar rayuwar mu sabida bansan yaya zamuyi ba.." Rungumeta Shema'u tayi tana mai fad'in "Ohh My Sajee insha Allah bazan tab'a barinku ba.. Oya zo ki tuk'a mu.." Sajida ta ware idanu tana dariya kafin tace "Aunty ai ban iya driving ba, da idan nace ma Momy take koya min sai tace sai na kai 18,." Shema'u ta murmusa tana mai goge k'wallan makirci kafin tace "Allah sarki My Aysha my Baby Sis, I never thought zan tab'a rabuwa da ita, tunda tayi aure na kasa Aure sabida SHAK'UWAR dake tsakanin mu, yau gashi mutuwa tai mana me kankat.... " Nan fah Shema'u tayi bursting cikin tsananin kuka. Sajida ma hawaye ne suka soma kwararo mata kafin tayi saurin rungume Shema'u tana fad'in "Aunty ki daina kuka pls, idan kina kuka ni kuma me zan yi, don Allah ki daina kuka... " Ta k'arashe itama cikin kuka. Da sauri Shema'u ta rungumeta tana lallashin ta, kallon glass d'in marfin mota kurum take tana wata kafiran murmushi mai cikeda ma'anoni..... Saida ta tabbata Sajida tayi shiru kafin ta soma cheering nata da zantuka masu dad'i tana sanar da ita zata soma koya mata driving kwanan nan tunda ta kusan harin 18. *************** "Wai ni meye ke damunki kika saka abinci gaba kika kasa ci ne inyi.?" Hajiya ta tambaya Aswakin ta na mak'ale a bakin ta, ( Kar kuji inata cewa Aswakin Hajiya na mak'ale a bakinta, sosai ta rik'i wannan Sunnah na goga Aswaki shiyasa ma dukda tana cin goro kullum hak'waranta k'al suke babu dottin goro) Kaman bazata amsa Hajiya ba sai kuma ta mik'e k'afafunta tana kuma shinshina hammatar ta kafin tace "Hajiya wai don Allah ina wari.?" Tayi tambayar fuskarta cike da damuwa. Mik'ewa Haiya tayi ta k'araso dab da Maryama tana k'ok'arin kai hanci jikinta... Maryama ta kauce tana fad'in "Haba Hajiya bafa cewa nayi ki manna hancin ki a jiki na ba." "Auho inji cewa kikayi naji maki ko kina wari, nidai banji warin bane sai k'amshi shiyasa kika ga ina kawo hanci na, kuma banda iyayi da felek'e duk zamana dake, yo ai idan kina warin kinsan zan fad'i tunda kinsanni banida b'oyo." "Toh fah, yau kuma ta sami Maudu'i" ta fad'i a hankali kafin taci gaba da fad'in "Nifa kurum tambayar ki nayi Hajiya..." "Fad'a min uban waye yace kina wari.?" Hajiya ta fad'i tana gyaran d'aurin kallabin ta. Maryama ta kalleta kafin tace "A bar zancen tunda kince banayi." "Auw bazaki fad'i min ba ko, naji ko a gidan uban sa ake k'eran man k'anshi da yafi naki tsada da kyau, yo ko agwagwa nan ya ganki ya barki wajen wanka, dukda wankan bak'i asaran ruwa ne, amma ke naki ba asaran bane, ki fad'i min wa yace kina wari...?" Cike da masifa take maganar. Kaman bazata fad'a ba, tasan ma idan bata fad'a ba wllhi maganar bazai tab'a mutuwa wajen Hajiya ba. Baki a ture tace "Aunty Shema'un nan bane tace wai bana shuwa da body spray, kuma wllhi kullum sai na saka, Hajiya ai ke shaida ce." Sakare Hajiya tayi tana dubanta kafin tace "Au dama wancan mai suffan aljanai da mayun ne tace kina wari, Meye kuma Shuwa d'in ince man hammatan nane,... Ki sha kurumin ki Allah kai mu gobe suzo d'aukar ki tsaf zan rama maki, Karma ki b'ata ranki." "Hajiya don Allah kar kice mata komai, dama dai kawai ina son sanin ko da gasken warin nake shiyasa na tambaye ki... " Ko tankata Hajiya batayi ba ta nufi uwar d'aki tana tunanin kalan rashin mutuncin da zatayi ma Shema'u tunda ta tab'a mata Maryaman ta. *Sameena Aleeyou Mrs* [2:54PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *SHAK'UWA CE* 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *09* *漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�* _馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_ Misalin k'arfe takwas da wasu 'yan dak'ik'ai su Sajida suka iso gidan Hajiya d'aukan Maryama. Shema'u sai kareraya ake mayafi rufe saman kanta sai ka rantse wata mutuniyar aziki ce. Sajida ce akan gaba sai faman rangad'a kira ma Hajiya take. Hajiya na Kitchen tana taya Atine karin kumallo ta kafe Shema'u da idanu tana karantar ta, murmushi tayi a hankali kafin ta wanke hannunta ta fito daga Kitchen d'in. "Hajiyar mu kinaji inata rattaba maki kira kikak'i amsawa koh." Sajida ta fad'i baki a ture daidai lokacin da Maryama ta fito tana saka hijabin ta. Hajiya ta kalli Sajida ta watsar don daga ita har Shema'un haushi suka bata. Saida ta isa saman farin kujera dake barandar ta zauna kafin tace "Yo wannan kira da kike min sekace makahon da ya rasa d'an jagora." Dariya Sajida tayi kafin suka soma gaisawa don wannan dama halin Hajiya ne tsaf ta saba da hakan... Kaman daga sama sai jiyo muryar Shema'u sukayi tana gaida Hajiya daga nan yanda take a tsaye. Musamman Hajiya ta kaikaito tana duban Shema'u kafin tace "Lafiya, Almiski sarkin k'amshi.." Ganin Hajiya zata Saki layi yasa Maryama saurin d'aukar jakkan ta kafin tace "Aunty Shema'u ina kwana." Shema'u ta amsa da sakin fuska, cikin sauri Maryama ta soma fad'in "Hajiya mun tafi kar muyi latti.." Hajiya bata sami zarafin amsa Maryama ba sai k'are ma Shema'u kallo da take, tun daga sama har k'asa wanda hakan yasa Shema'u shan jinin jikinta sosai ta tsargu da wannan kallo da Hajiya ke mata..... Jiyo muryar Hajiya sukayi tana fad'in "Yo ashema warin man Bilica (Bleaching) kike." Tayi maganar baki a tab'e.. Sajida sam bata gane ina Hajiya ta dosa ba hankalinta yafi karkata kan Solution d'in wani equation da Maryama ke nuna mata, Maryama kuwa tuni ta d'ago Hajiya, kai wato dai Hajiya bata barin kota kwana. Sai faman k'yafta idanu take ma Hajiya sam tak'i kallonta balle tayi shiru. Hajiya ta jawo sandar dake gefenta ta shiga d'aga k'asan skirt d'in Shema'u dashi tana fad'in "Haba haba, duba sawayen ki ki gani, duk sun k'one sun dauje, yo dama wannan farin naki uwa toka ai nasan na man kanti ne, tun daga shigowar ki gidan nan Ya hamame da warin arna, da kika ce Maryama tana wari yo ai ga wari nan jikin ki .. Kina shiga rana ta soya wannan roba robar fuskar taki wari ne zai kuma tashi...." Baki sake kawai Shema'u da Sajida suke duban Hajiya... Maryama kuwa janye Sajida ta shiga tana fad'in "Aunty Shema'u don Allah kiyi hak'uri muje , kar ki saurari Hajiya. "Rufewa mutane baki ke kuma, wato kar ta saurare ni sabida ga mahaukaciya ko, ince 'yancin ki nake karb'a maki, gobe bazata sake duban ki tace kina wari ba.. " Sai lokacin Sajida ta gane meke faruwa, wato maganar da Aunty Shemah tayi ma Maryama jiya a mota shine har tazo ta beza wa Hajiya... Sosai abin ya bawa Sajida haushi, itakam sam bataga laifin Aunty Shemah ba don tana son gyara su, kuma ai tayi apologizing ma Maryama tun a jiyan. A kufule Sajida ta soma fad'in "Haba Hajiya, haba Hajiya, gaskiya ki daina irin haka..." bata kai aya ba Hajiya ta watsa mata mugun kallo kafin tace "Rufe min baki ke kuma kafin na hamb'are bakin." Kan kace me hawaye sun ciko idanun Maryama. Shema'u kuwa cikin kissa ta soma bawa Hajiya hak'uri tana fad'in "Kiyi hak'uri Hajiya wllhi ni bada cin zarafi na fad'i hakan ma Maryam ba, pls kiyi hak'uri Hajiya..." Sam basuji sallaman AT ba dake shigowa cikin shirin tafiya aiki.... Tsaye yayi kurum yana kallon yanda Shema'u ke durk'ushe gaban Hajiya tana bata hak'uri ga Maryama rakub'e gefe tana hawaye. Ita kuwa Sajida ita ta kula da shigowar sa. Cikin sauri ta k'arasa ta rik'o hannun sa tana fad'in "Daddy please kazo ka bawa Aunty hak'uri wllhi Hajiya tayi addressing nata sosai, it's unfair, it is totally unfair..." Jin haka yasa Shema'u fashewa da kuka sosai tana nan durk'ushe gaban Hajiya, haba nan fah hankalin Sajida ya kuma tashi, ta shiga jan hannun AT da yayi tsaye kurum yana kallon yanda Maryama ke hawaye, haka kurum yaji k'irjinsa na bugawa da sauri da sauri ganin hawayen Maryam na zuba. Kasa cewa komai yayi har lokacin idanunsa naga Maryama, Sajida kuwa banda watsa wa Maryama mugun kallo bata komai,... Kan yayi magana Hajiya ta soma karanto masa abinda ya faru tsaf, sannan ta k'ara da "Wllhi ko gobe ta kuma b'ata ran Maryama ta, nata ran itama sai ya b'aci, banda naci da bak'in iyayi su tattara mana su koma garin su tunda yara sunada masu kula dasu..." Kuka Sajida ta fashe dashi tana fad'in "Wllhi wllhi babu yanda zasu tafi, wllhi idan Aunty Shemah ta tafi nima binta zanyi, wllhi barin gidan zanyi..." AT ya saba da fad'an Hajiya amma sam bai saba da tashin hankali irin haka ba, yama rasa da waye zai soma cikin su... " Cikin kissa murya irinta mai kuka Shema'u ta soma fad'in "Sajee kiyi hak'uri, ina sonku keda k'annen ki, but I have no choice dole na tafi, I can't stay here and be causing problems with your family.... Baby ko bana nan nasan you'll always be good girl.. Ki... " bata kai aya ba Sajida dake girgiza kai tana kuka ta fincike hannayen ta daga rik'on da Shema'u ta mata ta fita waje da gudun gaske tana fad'in "Wllhi saidai ni na rigaki tafiya, ko kuma mota ta markad'e ni... " Ai gaba d'aya cikin tashin hankali suka bi bayanta, AT yana fad'i ma Ilu kar ya bari Sajida ta wuce gate, inaaa , tuni Sajida ta nufi waje har ta kusan isa babban titi... Hajiya ma zani a hannu ta fito, haka Maryama dake kuka shar shar da hawaye.. Shema'u kuwa itace kan gaba, kan kace me tayi kan Sajida dake shirin tsallake babban kwalta ga babbar mota ta tink'aro... Hankalin AT sosai yayi mugun tashi, mutuwar matarshi bai gama fita daga jikin sa ba, kansa tuni ya soma juyawa yana tuno sanda yaga Aysha cikin jini, gaba d'aya bai gane meke faruwa... Kaman daga sama sai ganin Shema'u sukayi tayi ta maza ta rik'o Sajida sun zube gefen kwalta... Hajiya kuwa isarta wajen ta d'auke Sajida da mari mai ji da lafiya... Shema'u ta tare ta tana fad'in "Hajiya kiyi hak'uri don Allah yarinya ce,.." Hajiya huci kawai take tana turiri take fad'in "Don ubanta kashe kanta zatayi ne ko kuma kashe mun nawa d'an zatayi inyi, b'acin rai hauka ne, Allah yasa jaririya ce ita ba yarinya ba... " Kuka kawai Maryama keyi sai karkarwa da jikinta keyi. Sajida na rungume cikin jikin Shema'u, a hankali AT ya k'araso kafin ya mik'a ma Sajida hannu yace "Come here Baby, mak'e masa kafad'a tayi still tana hawaye. Shema'u dake rungume da Sajidar ta d'ago tana duban AT kafin ta dubi Sajida tace "Sajee kije wajen Daddyn ki kinji sweetheart. Ta k'arashe cikin tsananin damuwa. Mak'e kafad'a Sajida tayi a karo na biyu kafin tace "Aunty don Allah kar ki tafi ki barni kinji." AT ya dubi Shema'u ya dubi Sajida yanda suke rik'e da juna k'am, saida Shema'u tayi da gaske kafin Sajida ta mik'a hannu ma AT, kai tsaye motar sa ya nufa da ita.. Hajiya wangale baki tayi tana kallon ikon Allah, da k'yar ta iya furta "Yo naga bariki da k'afafun ta.." tab'e baki tayi kafin ta nufi Maryama dake tsaye gefe tana hawaye ta janye hannun ta tace "Shige muje, su suka sani, kuma daga yau idan babu me kaiki makaranta sai wannan aljanar ni zan wanke k'afafuna na kaiki tunda Allah yasa da K'arfi na rass.." Ta fige hannun Maryama suka wuce ciki.. Suna shigewa Shema'u tayi wata kafiran murmushi kafin tace "This is just the beginning Shemah, kiji dad'in ki da sannu zaki sami abinda kika jima kina buri. Karkad'e jikinta tayi ta tashi ta nufi motar ta, zuciyar ta fari k'al. ********* Duk maganar duniyar nan tayi Maryama tak'i amsa mata, sai faman shan zuciya kurum take alamun taci kuka. Hajiya duk sai taji babu dad'i don kuwa bata jure fushin Maryama. D'an matsowa tayi kafin tace "Tashi muje na kaiki kar kiyi latti." Baki a ture tace "Na fasa zuwa." "Jarabawar fah, inyi.?" "Bamuda yau, dama karatu zamuje." tayi maganar tana mai mik'ewa had'i da shigewa d'aki.... ********** "Hello kana ina ne.?" ta fad'i tana saka trafficator. Daga d'aya b'angaren Hisham ya fashe da wata irin muguwar dariya kafin yace "Shema'u annoba, wani improvement d'in kika samu don nasan haka kawai bazaki kirani ba, saidai kin sami wani ci gaba ko kuma you're planning for something." K'asaitaceccen murmushi tayi kafin tace "Kaida ka sani, komai yana tafiya yanda nake so, I'm pretty sure yanzu AT zai amince gidansa baza'a tab'a zaman lafia ba muddin babu ni. Nasan wannan Uwar tasa itace zata zame min matsala, but I have my way to get rid of her. ..." Cikin sauri Hisham ya katse ta da fad'in "No Shema'u, don't hurt Hajiya, ko kinsan AT yana son mahaifiyar sa fiye da komai a duniyar nan,? ...wait what's wrong with you ne kam, You said you love him, but meyasa kike cutar da mutanen da yake so, first kin rabasa da matar sa uwar 'ya'yan sa, kina k'ok'arin rusa tarbiyar da ya bawa d'iyar sa, and now his Mother..? Shema'u are you human.? "...... Katse sa tayi da fad'in "Hisham don't tell me you're backing down, toh idan ma ka hak'ura da k'udirin ka ne, ni zanfi kowa farin ciki coz bana so kayi hurting AT, abu guda da nake gargad'in ka dashi shine, don't you dare think of betraying me.. Wllhi Hisham kayi tunanin turning back d'inka on me I won't go down alone, tare da kai zamu tafi k'asa... " Tunstirewa da dariya yayi kafin yace "Stop being so sensitive, haba my Ally kema kinsan hakan bazata tab'a kasancewa ba.. Ban janye k'udiri na ba kuma bazan janye k'udiri na ba. Yanzu me kike so kika kirani. Murmushi tayi kafin tace "Yanzu naji bayani, akwai wani yaro a nan Janbulo, Haris Buzu, ina son ka taimaka min nasan komai a gameda shi, I want to work with him.. " Ta k'arashe tana murmushi. Murmushi Hisham yayi ya shafi kansa da yasha aski low-cut kafin yace "What can I have in return..?" Murmushi ta kuma yi kafin tace "Nasan matsalar ka, gani nan zuwa apartment d'inka, dama inaso na d'an b'oye masu, su nemeni su rasa nasan Sajida zata d'aga masu hankali har sai na dawo gidan..." Hisham ya murmusa had'i da kashe wayar kafin a hankali ya soma furta, "AT I'll ruin you completely..." *Sameena Aleeyou Mrs* [2:55PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *SHAK'UWA CE* 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *10* *漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�* _馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_ *_REMINDER..!_* _(This book is a work of fiction. All names, Characters, locations and incidents are products of the author's imagination or have been used fictitious. Any resemblance to the actual persons living or dead, locales or events is entirely coincidental.)_ Tsareta da idanu AT yayi yanda ta tak'ure waje guda sai faman shan zuciya take alamun taci kuka. Cike da masifa yaci gaba da fad'in "Answer me! Kinyi hauka ne huh..!" Kafad'unta ya rik'e yana jijjgata yana ci gaba da mata fad'a, gaba d'aya fuskar sa tayi jazir sabida b'acin rai, jijiyoyin goshin sa sunyi rud'u rud'u. Girgiza masa kai Sajida take still tana hawaye, ba tareda ta iya fad'in komai ba sai kuka da take. D'an dafe kansa yayi had'i da fuzar da iska, gani yake kaman he's going to far... A hankali ya durk'usa a gabanta yana kallonta, tausayin su gaba d'aya ya rufesa, yana tsananin son yaransa musamman yanzu da suka rasa mahaifiyar su. Hannu yasa ya kamo hannayen ta kafin yace "Sweetheart, what you did out there was crazy, haba Sajida, da girman ki.... If to say Jamal ne ko Ni'ima sukayi abinda kika yi zan masu uzuri nace su yara ne, but you at your age, haba Sajida, have you forgotten what this family had been through lately.. Huh? Or do you want the same tragedy to repeat it self huh..? Har kin manta Sajida, if your Momy was here, do you think she will be proud of you, no sweetheart, bazataji dad'i ba... " Sajida dai hawaye ne kawai ke kwaranya a idanunta... AT ya kuma kamo hannayen ta kafin yaci gaba da fad'in "Sajida my family are my first priority, bazan tab'a yafewa kaina ba idan na bari wani abu ya same ku da ganganci, but I can't do this alone, kece babba kece zaki taimaka min na kula daku da k'anenn ki, pls sweetheart kar ki sake irin wannan tunanin kinji." Ya k'arashe maganar fuskar sa dab da nata mai zuban hawaye. Gyad'a masa kai tayi kafin tace "Daddy kayi hak'uri, bazan sake ba insha Allah... But pls Daddy ka min alk'awari zaka rok'i Aunty Shemah ta zauna damu a nan for good, pls Daddy kar ka bari ta tafi kaji Daddy..." Dummm! Haka k'irjin AT ya buga, yama rasa me zaice ma Sajida, tattaro naman goshin sa yayi had'i da d'an fuzar da iska kafin yace "Sajida Auntin ku tanada tsarin rayuwar da tayi ma kanta, and she can't be here for good, sabida mace ce ita, sooner or later zata soma tunanin gina nata family d'in itama, sannan ta baro aikinta a can gida which is ya kamata da tuni ta koma bakin aikinta, she also need to prioritise her own happiness.. Sajida.... " Bai kai aya ba ta soma ci gaba da wani sabon kuka ta rik'e hannayen sa tana fad'in "Daddy pls this is all I'm asking of you, Daddy don Allah kar ka bari ta tafi, wllhi Aunty Shemah tana sonmu tana son zama damu, pls Daddy kar ka bari Hajiya ta koreta, do this for us please." Ta k'arashe cikin rawar murya. Sauk'e deepbreath AT yayi kafin ya gyad'a mata kai yana murmushi kana yace "Okay, I'll see what I can do, I'll talk to your Aunt, hakan yayi maki.?" Saurin gyad'a kai tayi cike da murna tace "Daddy na gode, Allah saka da alkhairi." Bai iya amsa mata ba sai ficewa da yayi daga d'akin jiki babu laka. Yana fita Maama Juu ta shigo Sajida ta tafi da sauri tayi hugging nata. Rik'eta Maama Juu tayi suka k'araso suka zauna saman gado. Kafin ta soma tambayar ta abinda ke faruwa. Sosai tayi fad'a ma Sajida jin rashin hankalin da tayi.. "Inyi, haba yaya ma zakiyi haka Sajida, baki tausayin mahaifin ku ne, da wanne zaiji, da rashin mahaifiyar ku, ko kuma da fitinar da kike neman b'ullo masa...Haba, haba Sajida wannan aiki ko Jamal bazaiyi ba balle ke...." Jikin Staircase Shema'u ta mak'ale tana sauraren su tana murmusawa ita kad'ai, Har Momma shigowa tayi tana salle Sajida akan abinda tayi, gaba d'aya sai fad'a suke mata. Jin Sajida ta soma masu kuka tana fad'in ba da gangan tayi hakan ba yasa Shema'u saurin shigowa d'akin ta k'arasa cikin tashin hankali tana fad'in "What's going on here, Momma meke faruwa.? " Da sauri Sajida ta tafi ya rungume Shema'u tana fad'in "Aunty Shemah pls tell them to stop scolding me.." Rungumeta Shema'u tayi kafin tace "Oh Sajee na, yi shiru abin ki, kema ba son ranki bane kikayi hakan, bedsides thank goodness I was there, and I was able to save you.... " Maama Juu dai ficewa tayi cike da shakku gameda Shema'u. Momma kuwa surfa masu masifa taci gaba da yi daga Shema'un har Sajidar. Shema'u sai faman k'yafta idanu take wa Momma inaa Momma tak'i yin shiru. Nan ta soma fad'in "Haba Momma yarinya ce dai, sann mu duka 'yan Adam ne muna kuskure, for crying out loud give her break Momma..." Cikin kuka Sajida take fad'in "Aunty yanzu na gane keda Daddy ne kawai masu sona, Hajiya ta mare ni, Momma ma ta min masifa, har Maama Juu ma masifa take min..." Shema'u ta kwantar da kan Sajida cikin jikinta tana lallashi, lokaci guda tana aika ma Momma kallon kin k'i saurare na, kin ga abinda nake ji maki. ************* Da yamma lis ya nufi gidan Hajiya yana sanye cikin k'anan kaya da shike lokaci ne na zafi. Red Armani shirt da bak'ar jeans, sosai kyaun sa da k'uruciyar sa suka fito. Sanye take cikin purple top kanta babu d'an kwali, gashinta mai cika wanda bai faye tsawo ba amma ba guntu bane tupke cikin ribbon, zani ne d'aure a jikinta tayi rigingine saman tabarma ta bararraje sai faman karatu take, sam bataji sallamar sa ba. Haka kurum ya tsinci kansa da fad'uwan gaba hangota a haka da yayi.... Still yayi a wajen ya kasa ci gaba da tafiya.... Kaman daga sama ya jiyo muryar Ilu Mai gadi ya nufosa cikin sauri yana basa sak'o....Cikin sauri Maryama ta mik'e zaune zumbur tana kallon su daga can k'asar bishiyar Hajiya da suke tsaye... AT kuwa cike da takaicin shigowar da Ilu yayi har cikin harabar gidan ya soma masa fad'a... Sosai Ilu ya shiga basa hak'uri yana basa sak'on... _Wato ma Ilu ya saba shigowa haka kenan_ AT ya fad'i haka cikin zuciyar sa ... Gajeren tsaki kawai yayi, don kuwa sam Ilu bashida nitsuwa, irin mutanen nan ne masu barkwanci sosai. Hajiya kuwa bazata tab'a bari a sallame sa ba don tasu tazo d'aya. Zuru tayi tana kallon yanda AT ke sille Ilu, gaba d'aya kasa tashi ma tayi har saida ya iso yanda take. A d'an daburce ta soma gaishe sa. A tak'aice ya amsa kafin yace "Ina d'ankwalin ki, ba hanaki zama babu d'ankwali ba..." Mik'ewa tayi zunbur cike da kunya ta nufi palorn Hajiya ta d'auko hijabi ta saka. Fitowa tayi ta same sa yana nan zaune saman faran kujera. K'ara gaishe sa tayi kafin ta zauna a mazaunin ta, haka kurum ta sami kanta da jin nauyin sa mussaman ganinta a haka da Uncle yayi. "Hajiya bata nan ne.?" ya tambaya sanda yake ciro waya a aljihun sa sakamakon k'arar shigowar sak'o da yaji. "Eh ta tafi dubiya gidan Baaba Dije nan mak'ota jikarta ta karye." Idonsa naga wayarsa yana karanta sak'on da ya shigo masa yake gyad'a mata kai kafin yace "Allah bata lafiya." Sajida ta amsa da "Ameen." "Ya karatun, hope kina yi.?" Gyad'a masa kai tayi ba tareda ta iya furta komai ba. Saida ya d'an gyara zaman sa, ya had'e yatsun hannun sa waje guda, hannayen sa na d'aure saman laps d'insa kafin ya d'an yi gyaran murya yace "Maryam." D'ago kai tayi tana dubansa lokaci guda k'irjinta ya kuma yankewa ya fad'i, cikin sauri ta sadda nata kan k'asa. Muryan AT ta jiyo yana fad'in "Regarding what happened earlier, kiyi hak'uri kinji." Saurin girgiza kai tayi kafin tace "Uncle ni ce mai laifi, ni ya kamata na apologizing, dan Allah kayi hak'uri uncle, I know you still having a hard time..... Kayi hak'uri kaji Uncle." Baice komai ba sai tsareta da idanu da yayi, abubuwa da dama ne suke yawo a kwanyar sa wanda bazai ce ga ma'anar su ba... Muryar Maryama ya jiyo tana fad'in "Uncle barin kawo maka ruwa." Bai sami zarafin amsa ta ba, sai mik'ewa da yayi ya d'an matsa gefe yana amsa wayar Dr Ashfaq, matashin likitan da yake so ya sami gurbin aiki a asibitin AT. AT ya yarda da qualification d'in Ashfaq tunda sukanyi aiki tare a TH, duk matashi ne da bazai wuce 32 ba amma yanada k'wazo da sanin aikin sa, shiyasa samun aiki bazai masa wahala ba a ko ina, shi kansa AT yaji mamakin yanda Ashfaq ya nace saida shi zaiyi aiki, koda yake ta yuyu hakan nada alak'a da sabon da sukayi na yin yawancin ayyuka tare a Teaching Hospital. Shigowar Hajiya yayi dai-dai da ida wayar sa. A tare suka jera suna shigowa da Hajiya, sai faman hura hanci take, tana a'a'amsa shi a ciki-ciki, ita a dole fushi take dashi, don Hajiya tak'i jinin d'abi'ar AT na sakalta yara da yake, a cewar ta d'abi'ar yahudu ne. A verandan suka yada zngo, ta kwab'e hijabinta tana fifita dashi lokaci guda tana rangad'a kira ma Maryama. K'arasowa Maryama tayi had'i da ajiye trayn ruwa gaban AT dake faman gaida Hajiya tana amsa masa a ciki. "Uncle ga ruwan." Ta fad'i sanda take ajiyewa. Murmushi ya d'an sakar mata kafin yace "Sannu Maryam, na gode ko." Maryama na murmushi ta juya tanai ma Hajiya sannu da dawowa. Hajiya ta amsa kafin ta warware k'ullin bakin zaninta ta ciro k'ullin goro a leda ta mik'a wa Maryama tace "Ungo wanko min su yanzun nan." Tayi maganar fuskar nan tamau, a tare AT da Maryama suka kalli juna, sarai sunsan don AT yaji haushi Hajiya tayi haka. Ko ta kansu Hajiya bata bi ba ta ciro karan aswakin ta ta soma goga hak'waran ta. AT ya gane kallon da Maryama take masa na tambaya ne, don dama sun saba 'yar haka, watarana yakan k'yafta mata idanu, ko yabi bayanta yace ta fad'awa Hajiya goron dakwai tsutsa. Amma yau kam sam babu fuskar wasa a tattare da Hajiya, don haka gyad'a ma Maryama kai yayi alamun ta wanko goron. Saida suka sakar ma juna murmushi kafin ta wuce. Maryama tana wucewa AT ya tattaro nutsuwar sa ya maida su ga mahaifiyar sa. Da 'yan kame-kame ya soma yana mai bata hak'urin abinda ya faru safiyar yau. Shek'ek'e ta kalle sa kafin tace "D'an boko mai hak'waran ABCD, naji ai na hak'ura tunda ba yau ka saba irin hakan ba. Toh nidai ka jini da kyau, bazan zauna inaji ina gani su susutaka ba, su gurb'ata maka tarbiyan yara, don Kulu da wannan d'iyar tata, mai fuska kaman an bad'a wa agwagwa toka ba tarbiya bane dasu, dama zakkan kenan Aisha kuma ta tafi abinta. Don haka dole su tattara su tafi, don wllhi basuda muhalli a gidan ka." Ta k'arashe dai-dai sanda Maryama ta aje mata plate d'in goro kafin ta kwashi books d'inta ta shige ciki. Saida AT ya sauk'e deep breath kafin yace "Hajiya, kiyi hak'uri don Allah, ki duba halin da yaran suke ciki, sannan kiga yanda Sajida tayi reacting d'azu, idan na kuma zuwa masu da wannan maganar Allah kid'ai yasan abinda zatayi. Hajiya zaman Shema'u a gidan sosai yake taimaka wa yaran... Dama so nake idan abin ya bar jikkunan su, da wai sai su koma, but for now Hajiya ki d'an yi hak'uri don Allah. Ki mana nida yarana, Don Allah Hajiya..." Ya k'arashe cikin sanyin murya. "Attahiru bazan zuba ido Kulu da d'iyarta su d'aid'aita min ku ba kaida yaran ka.. Idan kaga na d'aga maka k'afa toh fah Uwa ta gari ka kawo wa yaran nan cikin gidan su, ma'ana Aure kayi." Kaman sauk'an aradu haka yaji maganar Hajiya, shi take ma zancen aure Matar sa ko wata biyu batayi da rasuwa ba...... Tamkar gunki haka ya d'ago yana duban Hajiya. *Sameena Aleeyou Mrs* [2:55PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *SHAK'UWA CE* 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *11* *漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�* _馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_ Bakinsa har na rawa yake furta "Hajiya Aure.... Aure fah Hajiya.? Haba, haba Hajiya, Aysha ko wata biyu, kai ko wata guda ma bata cika da rasuwa ba kina min maganar aure.? Hajiya idan wani ne daban yayi maganar nan ba ke ba sai yafi min sauk'i.... Kiyi hak'uri Hajiya amma harga Allah bazan iya aure ba, mace guda nake so gidan duniyar nan kuma ta tafi ta barni ina fatan na had'u da ita a rayuwar da zamuyi gaba... Hajiya don Allah kiyi hak'uri kiyi maganar komai amma don Allah bada aure kiji tausayi na dan Allah kinji." Tamkar k'aramin yaro haka ya k'arashe maganar. Jikin Hajiya ya d'anyi sanyi, kuma sai yanzu take ganin tamkar ta masa hanzari sosai, amma kam sam bata son zaman Kulu da d'iyarta a gidan Attahiru. Saida ta d'an muskuta kafin tace "Shikenan Attahiru naji bazakayi aure yanzu ba, amma kasa a ranka bazaka tabbata a haka ba, dole wata rana zakayi aure ko don inganta rayuwar iyalanka.. Sannan magana ta gaba shine sam ban yarda wannan zabon ta ringa kai Maryama makaranta ba, idan dreban nasu bai dawo bakin aiki ba ka nemi wani ko kuma kake zuwa da kanka kana kaita. Ka fahimce ni." Gyad'a kai AT yayi kafin yace "Insha Allahu ma gobe drivern nasu zai dawo, za'a kiyaye insha Allah." Saida ta jinjina kai kafin tace "Yayi, Allah shi maka albarka." AT ya amsa da "Ameen Hajiyata, Hajiyar Maryama." Har ransa yake jin dad'in albarkan da Hajiya ke saka masa dukda wani sa'in tanada wuyan sha'ani. Murmushi Hajiya ma tayi don kuwa sosai take son d'an nata, tunda shi kad'ai Allah Ya mallaka mata. *************** Washe gari Sajida sam bata wani sake da Maryama ba, sai faman tattamke fuska take. Har aka fito exams Maryama kuwa bata daina bata hak'uri ba. Fuska a d'aure Sajida tace "Maryama wllhi idan Aunty Shemah ta tafi bazan tab'a yafe maki ba, don kece sila. Maryama ta murmusa kafin tace "Sajida insha Allah Aunty Shema'u bazata tafi ba, zata zauna tareda ke.. Na kula SHAK'UWA CE mai k'arfi a tsakanin ku.". D'an tab'e baki Sajida tayi kafin tace "K'warai kuwa, SHAK'UWA CE mai k'arfi a tsakanin mu wanda babu wanda ya isa ya tsinka ta." Sauk'e ajiyan zuciya Maryama tayi kafin tace "Sajida no matter what happens ki sani I'll always be your friend kuma 'yar uwarki, don Allah kar ki tab'a mance wannan." D'an kallon ta Sajida tayi don kuwa tabbas akwai Shak'uwa da soyayyan juna tsakanin ta Maryama, basu da shirgin k'awaye sai su biyun su tun tasowar su, saiko wad'anda ba'a rasawa. Tunawa tayi she needs Maryama now more than ever, ta tuna abinda Aunty Shemah ta fad'i mata cewa ta tambayi Maryama ta had'ata da Buzu. Cikin sauri tayi murmushi kafin ta kamo hannun Maryama tace "Hakane 'yar uwa. Nima kiyi hak'uri pls." Murmushi Maryama tayi kafin tace "Mu k'arasa mazaunin mu..." A tare suka jera suna tafiya kaman babu wani abu da ya shiga tsakanin su, nan suka hangi k'awarsu Fadila Talba ta nufi motar su anzo d'aukar ta, sai faman d'aga masu hannu take alamun sai gobe, suma waving d'in suka mata Sajida ta bud'e murya tace "Fadee don't forget to study hard." Daga can Fadila tace "Wannan saidai ki gaya ma Maryama allazi boko, tunda bokon ba do or die bane..." Gaba d'aya sukayi dariya don haka nan Fadila take sam babu ruwanta da b'oyo. Bayan sun zauna a mazaunin su Sajida ta dubi Maryama kafin tace "Maryama waini ya labarin Buzu ne.?" "Yana nan mana, ko shekaran jiya ma nasha kin gansa sanda kuka ajiye ni. Meyasa kika tambaya. ?" Shek'eke Sajida ta kalleta kafin tace "Ban gane meyasa na tambaya ba, kaman baki san dalilin da yasa nayita nacin kuke gaisawa da mutunci dashi ba." Tsaf Maryama ta gane ina Sajida ta dosa, gyara zamanta tayi kafin ta soma fad'in "Sajida wai har yanzu baki mance da zancen Buzu ba, wllhi da na d'auka tsaban k'uruciya ce dai kawai yasa kike son sa." Murmushi Sajida tayi kafin tace "Lallai da alama har yanzu bakisan menen soyayya ba. Maryama ta murmusa kafin tace "Aah gaskiya ban san soyayya ba kam amma nasan SHAK'UWA." "Kinga Maryama joke aside pls, muyi magana ta gaskiya , yanzu yaya za'ayi na ringa had'uwa dashi ba tareda sanin Daddy ba." "Ban gane ba tareda sanin Uncle ba, since when kika soma b'oye masa abubuwa.. Sajida we're writing our final Exams kiyi hak'uri mu kammala before ki fara ire-iren wad'an nan tunanin, sannan had'uwarki da Buzu a b'oye bashida wani alfanu, idanma auren kike so ai kin kai auren... Na tabbata idan kin gama secondary d'inki Uncle will listen to you, and he'll understand you, na sani mahaifin ki d'an boko ne kuma yana valuing karatu fiye da komai, tunda shi irin iyayyen nan ne da sam basu da matsala, kiga yanda yake daku yaransa very friendly, kai bama ku ba harta nima, pls Sajida karki betraying that trust da yake dashi akanki...." Gajeren tsaki Sajida tayi kafin tace "Kinsan burin da Daddy yaci min na karatun likitanci, kinsan ban isa na je masa da maganar wani saurayi yanzu ba ko... Toh wai ma aure nace maki zanyi yanzun, kawai dai son shi nake, kinga ai gwara yasan dani tun yanzu gujema kar ya fad'a ma soyayyar wata." Sauk'e ajiyan zuciya Maryama tayi kafin tace "Amma nidai a ganina ki bari namiji ya fara furta maki kalman so kaman zaifi akan ke ki fara, dukda dai bansan meye so d'inba. Tsaki Sajida tayi kafin ta mik'a don already anzo d'aukan su, saida ta watsa ma Maryama mugun kallo kana tace "Ke ai naga irin SHAK'UWAR da kikayi dashi, Maryama wai son Buzu kike ne.?" tayi tambayar tana tsareta da idanu. Dariya ma tambayar ta bawa Maryama kafin tace "This is ridiculous, haba Sajida kar kiyi magana haka, wllhi ni Maryam banga namiji da zai shiga tsakanina dake ba, babu shi.... Kawai dai ina so ayi abubuwa ne the right way, abinda kike son yi ba haram bane amma baki biyo ta hanyar da ya dace ba... Kiyi tunani akan maganar da na fad'a maki. Sai yanzu ta yarda da maganar Aunty Shemah, Maryama is just keeping Buzu for her self ne. Kallon Maryama tayi kafin tace " Shikenan with or without you Haris zai soni, he's mine, ni kad'ai... Idan ma kin fad'a ma soyayyar sa ce ina mai gargad'inki da ki ciresa a ranki... " Daga haka fuuu ta wuce ta nufi mota. Sauk'e ajiyan zuciya Maryama tayi cike da mamakin canzawan da Sajida tayi a 'yan kwanakin nan, girgiza kai kurum tayi kafin ta wuce mota. ************ Hisham ya kalle sa a karo na biyu kafin yace "Dr wai meke damunka ne kam, kana looking dull tun shigowar ka, idan tunanin Aisha ne, hak'uri zakayi Tahir, Allah shi ya tsara hakan sannan yafika sonta tunda shi ya hallice ta, Tahir don Allah kake rage ma kanka tunain nan, you are perfectly aware of the consequences, yanzu sai ciwo ya rafke ka, kaga ba'ayi riba ba." Fuzar da iska AT yayi had'i da zuba hannayen sa gaba d'aya saman table d'insa kafin yace "Hisham, no matter how hard I try not to think of it...... I just couldn't.. Amma haka ne yanda kace ne, Allahn da ya d'auketa ya fini sonta sannan Allah yana tareda masu hak'uri da tawakkali, what worries me the most , Hajiya ce." Hisham ya k'araso ya zauna a kujera mai kallon na AT kafin yace "Hajiya kuma, me Hajiya tayi.?" AT ya d'an girgiza Kai kafin yace "Could you just imagine, wai ta fara min maganar aure, na sani sooner or later zata kuma yin batun tunda ta fara, abin ya dameni sosai. Sannan she's asking me na sallami su Shema'u daga gidan, kasan bazan iya ba, aside from that yaran sosai suke son Shema'u, tana d'ebe masu kewar mahaifiyar su, I was even thinking of asking her to stay a bit longer har sai yaran sun k'ara recovering, amma kaji abinda Hajiya take fad'i. Shiru Hisham yayi kaman bazaice komai ba sai kuma yace "Toh kai baka son auren ne.?" Galala AT ya kallesa kafin yace "Aure kuma ni yanzu, ai babu batun aure yanzu kam a gaba na, mace guda nake so kuma ta tafi, kai kasan da hakan." Hisham ya jinjina kai kafin yace "Haka ne, amma kasan kaman yanda Hajiya tace bazaka tabbata a haka babu mata ba, for the sake of your children, tunda Shema'u ba tabbata zatayi a gidanka ba .....you've to keep this in mind." AT dai baice masa komai ba sai mik'ewa da yayi ya nufi k'aramar fridge d'in dake a cikin office d'in. Hisham kuwa wani irin dad'i ne ya ziyarce sa, burinsa ya kusa cika, Sajmal ya kusa zama mallakin sa, all he needs to do now shine yayi updating Shema'u wannan daddad'an labarin. Daga nan store suka nufa don duba magaungunan da basu dashi a asibitin. ************** "Hello, kina jina.." cewar Hisham bayan Shema'u ta d'aga wayan. Yamutsa fuska tayi kafin tace "Ina jinka mana, meke faruwa, what's on the ground.?" Murmushi Hisham yayi kafin ya labarta mata duk zancen da sukayi da AT. Mik'ewa tayi tamkar wata zautacciya, ta k'arasa tasa key ma k'ofarta kafin ta soma fad'in "I'm sick of that old woman, she's getting on freaking nerves, wllhi wllhi if she keeps on getting on my way zan b'atar da ita..." Sai huci take tana maganar tana zazzare idanu. Hisham ya murmusa kafin yace "Kwantar da hankalin ki and don't think of doing anything stupid, idan kika ci gaba da saye zukatan yaran AT ina mai tabbatar maki kece zaki zama matar sa, tunda shid'in bashida wacce yake so a halin yanzu, duk macen da zai so tabbas tayi grabbing affection d'in yaran sa ne. Don haka kar ki b'ata shirin ki by hurting Hajiya, just keep on killing her with kindness na tabbata itama eventually zata soki, koda kanta da k'aho ne." D'an dafe kanta tayi had'i da zama saman couch kafin tace "Hisham baka san wannan uwar tasa bane, she's insane wllhi batada hankali, ba abu mai wahala bane ta zab'o masa mata a k'auye... Amma nasan yanda zanyi, Shema'u nake, da kanta zata soni ta zab'a ma d'anta da jikokinta zama dani.." Daga haka katse wayar tayi tana wani irin huci... Wata wayar ce ta kuma shigo mata. Ganin ogan ta ne a wajen aiki yasata d'agawa da k'yar sai faman yatsina fuska take. Daga d'aya b'angaren Alh Aminu yace "Rankishidad'e kin mance dani, sai kewarki nake." D'an murmushin yak'e tayi kafin tace "Haba my Alhaji kasan ai bazan mance da kai ba, wllhi yaran ne sam basu saba da kowa ba sai ni, mussaman k'aramar cikin su, wllhi my Alhaji idan ka gansu sai ka zubda k'walla sabida tausayi." Ta k'arashe maganar kaman me shirin yin kuka. Sauk'e ajiyan zuciya Alh Aminu yayi kafin yace "Shema'u magana ta gaskiya kinsan dai kinyi neglecting aikin ki, sannan albashi bai yanke maki ba tunda ni ne babba a waje, amma ki sani duk randa Governor ya kawo ziyara ministry d'inmu akwai babban matsala, sannan nima ina buk'atan ki tunda kinsan idan ban jiki a jikina ba sam banida kwanciyar hankali, Shema'u don Allah ki bari muyi auren nan na huta..." Dumm! Haka taji maganar Alh Aminu, cike da masifa ta soma fad'in "Lallaima Alhaji, waye zai aureka yaje cikin wad'an nan locals wives d'in naka, kaga na maka kama da zama cikin su ne, sannan da kake min maganar aure yanzu yaran 'yar uwatan ma waye zan barsu, idan gorin abubuwan da kake min zakayi fine sai mu rabu it's not a big deal ai, kaima kasan duk yanda na shiga bazan rasa masoya ba." A daburce Alh Aminu ya soma bata hak'uri "Shema'u kiyi hak'uri sam ba haka nake nufi ba, sannan maganar matana kinsan bazan tab'a had'aki gida guda dasu ba, yaran 'yar uwanki kuma kina iya rik'esu koda a gidana ne, amma don Allah kar kice zaki rabu dani." Murmushin cin nasara tayi kafin tayi k'asa da murya kaman mai shirin kuka ta soma fad'in "My Alhaji kasan bazan tab'a rabuwa da kai ba, kasan ina sonka sosai, sannan naso zuwa Jalingo dubaka amma motata ta tawarwatse kasan da ita mukayi had'arin, wllhi shi ya hanani zuwa, kuma banida enough cash da na biyo jirgi.." Alh Aminu yayi wata murmushin jin dad'i kafin yace "Yauwa sanyin rayuwa ta, shiyasa a kullum nike k'ara sonki, ai bansan da motarki akayi had'arin ba da tuni an aiko maki sabo, ki kwantar da hankalin ki, mota da kud'u suna nan tafe cikin satin nan." "Allah my Alhaji, wayyo shiyasa nake k'ara sonka.." Tayi maganar full of excitement. Nan suka b'uge da hiran soyayya, tana gama wayar dogon tsaki taja kafin tace "Banza kawai, ina ni ina kai, babban baho." tana gama fad'in haka ta mik'e ta nufi d'akin Sajida. *Sameena Aleeyou Mrs* [2:55PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *SHAK'UWA CE* 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *12* *漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�* _馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_ Zaune take saman gadon ta tayi tagumi da hannayen ta biyu saman pillow. Saida Shema'u ta gama karantar ta tsaf kafin ta shigo cikin d'akin, da alama Sajida tayi nisa duniyar tunani. Saida Shema'u ta lellek'a corridor ta tabbatar babu mai zuwa kafin ta maida k'ofar ta rufe ta k'araso cike kissa fuska fal damuwa ta zauna gefen Sajida ta dafata tana fad'in "Sweetheart lafiya na ganki haka, kinsan I hate to see you cikin damuwa, com'on Sajida kinyi k'arama ma shiga damuwa, kar ki manta you have me, kinadani pls ko me kike so ki sameni ki fad'a min Sajida bawai ki dinga shiga damuwa ba." Ta k'arashe maganar tamkar zatayi kuka. Da sauri Sajida ta rungume ta kafin ta soma fad'in "Aunty meyasa abubuwa suke faruwa haka, Aunty ina son Maryama bana so wani abu ya raba mu, but it seems SHAK'UWAR mu da ita yana gab da yankewa, Aunty you were right da kika ce Maryama ba sona da Haris take ba, sam bata son alak'ata dashi, I was stupid da na yarda da ita a baya, gaskiyar ki ne Aunty yanzu ne zan gane masu sona tsakani da Allah tunda yanzu ne na soma girma na soma sanin ciwon kai na." Shema'u tamkar ta zuba ruwa a k'asa tasha sabida farin ciki, tuggun data shirya ya tafi yanda take so, perfect inji bature . "Ohhh Sweery come here..." ta fad'i sanda take rungumo Sajida kafin tace "My Sajee har raina naji dad'i da idanuwan ki suka bud'e kika gane wannan Maryama she's nothing but a Social climber, k'ok'ari take ta sace soyayyar kowa naki daga gareki, tana kai kanta yanda Allah bai kaita ba , ki duba yanda Hajiya kakar ki take sonta, ko ku jikokin ta Albarka, har marinki Hajiya tayi amma na tabbata ko zungurin Maryama bata tab'ayi ba, Daddyn ki yakanje da kansa ya kaita school, har wani nunawa take ta fiki son karatu sabida tsaban makirci irin nata, wllhi nan gaba ina mai tabbatar maki Daddyn ki sai yafi sauraren ta fiye dake, uwa uba kin aminta da ita kin had'ata da saurayin da kike so ta zaga tana cin amanar ki, kuma zakiga ko cikin k'awayen ku zasufi sonta sabida ta k'ure a makirci da munafunci, amma dai ni banaso ki rabu da ita tunda kina sonta sannan tare kuka taso, abinda zance maki dai shine you should be careful with her. From now on ba komai zakina sharing da ita ba tunda true color d'inta ya fito fili kin gane ko wacece ita. Maganar Haris kuma ni nai maki alk'awari duk iya makircinta sai Haris yaso ki ke kad'ai, you've my word, kinji sweetheart, so kima daina saka ma ranki damuwa tunda kinadani." ta k'arashe tana sakar ma Sajida sassanyar murmushi. Murmushi Sajidar ma tayi kafin tace "Aunty, thank you for always been here." Girgiza kai Shema'u tayi kafin tace "Sajee ki daina min godiyar nan pls, me anfani na idan yaran tilon 'yar uwata basuji dad'i ba. Oya kar ma ki damu, Haris kaman yaso ki an gama." ta k'arashe maganar zuciyarta fari k'al, inama duka mutane can easily be manipulated kaman Sajida. *********** A 'yan kwanakin nan sam Sajida ta canza wa Maryama, sunadai gaisawa Hi hi, amma sam bata bari suyi dogon zance, Maryama ma bata d'ago mata zancen ba sai ta share kurum, tunda yanzu jarabawar su dake gaban su yafi komai mahimmanci a garesu. A haka kwanaki suka shud'e. Yau Shema'u na zaune a d'aki sai faman fente-fenten fuska take, don har wani alla alla take AT ya dawo yayi araba da ita. Kaman daga sama ta jiyo wayarta na ringing, k'arsawa tayi ta d'aga tana mai washe baki da kashe murya don kuwa ba kowa bane illa Bahon ta, wato Alh Aminu. "Hello giwan mata." ya fad'i daga d'aya b'angaren yana washe baki. Saida ta wani murmusa kafin tace "My Alhaji yaya akayi ne, naji shiru fah banji alert ba har yanzu." Dariyar jin dad'i yayi kafin yace "Cash d'inki da ride d'inki sun sami isowa yau d'in nan." "Wow, da gaske kake my Alhaji?" ta fad'i tana mai mik'ewa tsaye. "K'warai kuwa Tauraruwa ta, kinsan komai idan naki ne jikina har rawa yake." Shema'u tayi murmushin jin dad'i kafin tace "My Alhaji kenan, sam baka gajjiya da d'awainiya, toh yanzu waye ka aiko don nasan yanda zanyi na amshi aikan." Amsar da ya bata ne ya sanyata d'aure fuska tamau, cike da b'acin rai ta soma fad'in "Haba Alhaji, haba, yaya zaka min haka, me zai kawoka Kano, nida nace maka zanje har gida na sameka, kasan Momma bata san da kai ba har yanzu, kuma kaga gidan wani nake, bana so su soma zargina." Alh Aminu ya tattare naman goshin sa had'i da fuzar da iska kafin yace "Shema'u a gaskiya I'm tired of your excuses, why are you hiding me from your family, meyasa baki so 'yan uwanki su San dani, Shem'au sonki nake da aure ba zallan daduro ba ke kinsan da hakan." Sam bataso ta sami sab'ani da Alh Aminu a yanzu, don kuwa yanzu ne take buk'atansa more than ever, she really needs to put up with his stupidities ... D'an gajeren murmushi tayi kafin tace "My Alhaji kenan, sam baka fahimce ni bane, amma yanzu text me your location I'll be on my way." Cike da jin dad'i yana baje saman gadon hotel yana shafa tunbinsa yake k'yalk'yale dariya kafin yace "Shiyasa nake k'ara sonki, yanzu zan turo maki right away." Daga haka sallama sukayi. Wata uwar tsaki Shema'u taja cikeda takaici, yanzu shikenan wannan kwalliyan a iska tayishi her AT bazai gani ba. K'arasawa tayi jikin bagrag ta d'au jaka ta zari mayafinta, saida ta lek'a parlorn AT tana mai tunanin watarana da yardan Allah suna cikin nan suna shan soyayyar su, wani murmushi tayi kafin ta nufo downstairs fuskar nan tasha heavy makeup. A farfajiyan gidan ta hangi Momma na zaune saman faran kujera, k'arasawa tayi tana dubanta daga yanda take tsaye kafin tace "Momma ni zan fita." Baki sake Momma tace "Ke wannan kwalliya da kikayi haka ai gwara ki tsaya Tahir ya gani tunda ya kusa dawowa, ina mai tabbatar maki har kama yau kikayi da marigayiya Aisha ta." K'atutun bak'in ciki ne ya tokare mak'oshin Shema'u jin Momma na had'ata da Aysha, wato dukda ta mutu baza'a daina kawo tunaninta first ba, harta kamanni ma wato ba'ason nata sai na Aysha, miji ma sai sauran na Aysha ake neman lik'a mata, kodayake ai ta riga Aysha fara son AT don haka dama AT nata ne since from the very beginning. Kai ta tsani Aysha wllhi, dolema ta d'aid'aita rayuwar Sajida kota halin k'ak'a ne. "Momma kenan kinsan nace maki zanje gidan k'awata a Sabon gari, tun d'azu taketa min waya.... Ba jimawa zanyi ba insha Allah." Ta k'arashe maganar tana ciro waya a jaka tana duba sak'on Alh Aminu da ya shigo mata. "Toh ai shikenan, kardai kiyi dare kuma ki kula da kwalta." D'an murmushi Shema'u tayi kafin tace "Momma kenan wani sa'in idan kinyi magana kina bani dariya, yanzu ni ce sai an fad'a min na kula da kwalta, kodayake tun bayan accident d'in nan sai kin fad'i haka kullum idan zamu fita, ki kwantar da hankalin ki Mommata yau kam ma da taxi zan fita don motata babu enough fuel kuma yanda zanje kinga da d'an nisa." Momma ta jinjina kai kafin tace "Shikenan Allah Ya tsare,." ko amsa mata Shema'u batayi ba taci gaba da tafiyarta. Momma tayi jigum tana kallon Shema'u, a kullum idan ta tuna bata sanar da Shema'u asalin wanene mahaifin ta ba, hankalin ta yana matuk'ar tashi, gani take kaman duk randa Shema'u tasan asalinta zata tsaneta na har Abada. Allah sarki Alh Mukhtar marigayi mijinta mai rasuwa kuma mahaifin Ayshan ta, ya rik'i Shema'u amana, har ya koma ga ubangiji Shema'u batasan bashine mahaifinta ba,. Momma tasa bayan hannunta ta share k'wallan da suka zubo mata tunowa datayi yau babu Mukhtar babu Aysha, duk sun tafi sun barta. Jikinta yayi sanyi sosai da wannan tunani ta mik'e ta nufi cikin gida. Sauri-sauri ta soma tafiya da sawu a layin, alla-alla take ta sami abun hawa ta d'ale amma shiru bata samu ba, kaman daga sama ta hangi motar AT na shigowa layin, k'irjinta ya yanke ya fad'i. Gaba d'aya daburcewa tayi don bataso suka had'u da AT ba, tasan zai iya cewa ta shigo ya ajiyeta. Parking ya d'anyi sanda ya hangeta, cike da murmushin k'issa ta k'araso yanda yake, d'an rage glass yayi suka gaisa kafin ya tambayeta ina zataje. A d'an daburce ta sanar dashi gidan k'awarta zataje kaman yanda ta sanar da Momma,. AT ya d'an murmusa wanda yake kashe Shema'u kafin yace "Toh banda abinki Shema'u me anfanin motar ki, kije a ciki mana." D'an murmushin yak'e tayi kafin tace "Dr kenan, ai motar tawa tana buk'atan ziyartan gareji ne ma, amma babu matsala zan sami ko taxi ko adaidaita ne na shiga." AT ya d'an dubi agogon jikin motar sa kafin yace "Toh shigo na ajiyeki, ko kuma ki karb'i tawa motar kije da ita." Shema'u ta k'walalo ido waje, dad'i kaman ya karta, wai yau ita AT kema magana haka har yana cewa zai kaita anguwa. "Em... Em wllhi ka barshi kawai Dr I can manage, haba ka dawo daga office ga gajjiya, kana buk'atan hutu pls ka shiga ka huta." Murmushi ya kuma yi a karo na biyu kafin yace "Karki damu ni nace zan kaiki ai, this is the least I can do after all the sacrifices you've done for my family. Pls ki shiga na ajiyeki." Murmushi ta d'anyi zuciyarta fari k'al lallai AT yana appreciating abubuwan da takeyi wa yaransa, tabbas sune her key to his house. Suna tafe babu mai cewa komai, sai binsa da mayen kallo take da wutsiyar idanu, wayyo Allanta gaskiya ta matsu tana tsananin buk'atar AT a shimfid'arta, sosai take kwad'ayin shi... Muryarsa ne ya katse mata tunanin ta. "Na gode da devoting lokutanki masu anfani da kikayi ma iyalai na sannan ina fatan hakan won't affect your job." Idanunsa naga kwalta yayi maganar. Rausayar da idanu tayi kafin tace "Haba Dr, saikace wani abin nayi, yaran nan fah are my obligation tunda yaran 'yar uwatace, ko a shari'a ne sunada hakki akaina a matsayina na yayar mahaifiyar su, Dr bazan b'oye maka ba wllhi ina son yaranka so na hak'ik'a, soyayyar da nakejin sam bana son rabuwa dasu." Saida ya d'an kaikaito da fuska ya dubeta kafin ya maida idanunsa ga kwalta. A tak'aice ya furta "Na gode da soyayyar da kike masu." tundaga haka bai kuma cewa komai ba har suka isar unguwar da suka nufa. Gaba d'aya ta daburce ta soma tunanin ina zata sauk'a, wata dabara ta fad'o mata, Shagon gyaran gashi dake a bakin titi ta hanga, tayi saurin ciro wayarta tamkar mai karanta sak'o kafin ta d'anyi murmushi ta furta "Kai Salma dai akwai shirirta, waifa kaga tun d'azu nake jira ta turo min location na gidan nasu amma shiru. Sai yanzu take ce min na jirata a wancan saloon d'in." Baice komai ba don kuwa sam bashida hayaniya, karya kan motar kurum yayi ya k'arasa bakin shagon gyaran gashin yayi parking. Sai wani kwarkwasa take sanda take masa godiya had'i da sallama, shikam sam hankalinsa ma baya gareta, a tak'aice ya amsata kafin ya tada motar sa ya bar wajen. ************* Aaa'ah, mamaki ya cika Ashfaq ganin tulin fake d'in magungunan da akayi ordering, kai anmayi banning wasu magungunan an hana amfani dasu. Cikin sauri ya shiga neman layin AT. AT yana gama parking motar sa wayar Ashfaq ya shigo masa, nan take Ashfaq ya fad'a masa halin da ake ciki. "What!" AT ya furta cikeda tashin hankali kafin yace "Ina Hisham ya bari hakan ta kasance, shine alhakin sayan magunguna suke wuyarsa..... Okay, ka gane zamu gudanar da bincike, zan kira Hisham d'in, kar ka bari a sauk'e kayan ko k'wayar magani ce. Sosai hankalin AT ya tashi wannan ka iya jefa asibitinsa cikin had'ari mai girma, amma yasan Hisham bazaiyi haka ba, duk yanda akayi hakan ta faru ne bada saninsa ba. Neman layin Hisham ya shiga yi. "Hisham ya akayi hakan ta faru, kasan irin had'arin da hakan ka iya jefa hospital d'inmu?" In a furious tune yayi maganar. Gaban Hisham ya yanke ya fad'i amma yayi saurin saita kansa kafin yace "Tahir kasan dai da sanina bazanyi hakan ba, amma kar ka damu zanyi magana dasu distributors d'in, in short zamu daina sayan magunguna a company d'insu... Oh my god I'm really sorry Friend, nasan hakan zai janyo fad'uwa sosai." Gajeren tsaki AT ya d'anyi kafin yace "Ba kud'in da za'a rasa bane damuwar, what matters shine b'ata sunan asibitin da hakan ka iya haifarwa da kuma amfani da magungunan... Thank goodness Ashfaq was there sanda suka delivering, kasan meye zai faru mu had'u a asibitin yanzu." Daga haka katse wayar sa yayi. Wani uban tsaki Hisham ya buga yana wani huci yake buga kujera yana furta "Dammit! Damn that Bastard." a hankali ya furta "Ashfaq" yayi wata murmushi kafin yace "That imbecile bazai bari na cimma burina ba muddin yana asibitin, I really need to get rid of him." buga kujera ya kumayi yana mai ci gaba huci. ************* "Haba giwar mata, yanzu bazaki bari na k'ara koda round guda bane. " Yayi maganar yana shafa tuleliyar tumbinsa. A d'an yatsine Shema'u ta kallesa tana mai ci gaba da jan zip d'in rigarta take fad'in "My Alhaji kasan uzuri na, ka fahimce ni don Allah. Nai maka lak'awari gobe kafin ka tafi zan zo." Murmushi yayi ya shafi gefen fuskar ta kafin yace "Ai na yarda dake d'ari bisa d'ari tauraruwata." yasa hannu a bedside ya ciro car keys da Check ya shafawa Shama'u a fuskarta.. Ware idanu tayi batasan sanda tayi wani tsalle ta haye kansa tana murna ba. Kai tsaye gidan Hisham ta wuce da motar ta ajiye a can, bata sami Hisham ba don suna asibiti dasu AT suna fixing issue na magungunan. *************** *Bayan kwana biyu* Jinta take cikin kud'i, suna zaune itada Hisham a parlonsa aka shigo da Buzu idanunsa a rufe. Mik'ewa Hisham yayi ya mata alama da idanu kafin ya shige d'aki. Murmushi ta sakar masa kafin ta masa alama da idanu itama. "Ku bud'e masa idon." Ta fad'i sanda take zama bisa sofa. ************ Ashfaq ne zaune saman sofa a 'yar k'aramar apartment d'insa, k'aramar madubi ya d'auko ya shiga cire makeup d'in da yakeyi a fuskar sa na b'atar da kamanni... Kaman daga sama yaji wayarsa na ruri. Ganin sunan da ya bayyana jikin screen d'in yasa sa sakin murmushi kafin ya d'aga wayar yana fad'in "Assalamu'alaiki the most amazing mother on earth." *Sameena Aleeyou Mrs* [2:56PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *SHAK'UWA CE* 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *14* *漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�* _馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_ Matseta jikin garu Hisham ya kuma yi yana wata mayaudariyan murmushi ya d'ago hab'arta suna kallon juna cikin ido kafin yace "Da ace kinga shed'an da bansan yaya zaki zama ba, kai ni duk iya tsawon ratuwata da yawon da nayi a duniya ban tab'a gamuwa da shed'aniya irinki ba, duk abinda kike so sai kin samu da k'arfin gaske." Murmushi Shema'u keyi kafin ta shiga zagaye fuskar sa da fingertips d'inta tana fad'in "Rantsuwa nayi sai na tarwatsa iyalan Aysha and keep AT for myself." Dariyan rainin hankali Hisham yayi kafin yace "Idan kina sonshi ai zaki so 'ya'yan shi, sannan barikiji na fad'a maki wacce sai tafi zama illa ma rayuwar ki fiye da yaran AT. I'm afraid tana iya zama matar AT ke baki zama ba." K'walalo idanu waje Shema'u ta shigayi tana girgiza kai tana kalle-kalle tamkar mai tab'in hankali kafin ta soma fad'in "No no no, wllhi ba'a haifeta ba, ince wancan shegiyar Nurse d'in kake nufi mai suffan karan rake. B'atar da ita mai sauk'i ne." Dariya Hisham ya kumayi kafin yace "Dad'ina dake bakida imani wajen kisa, kina manta cewa akwai mutanen da idan kin kashe su bazakiyi succeeding abinda kike buri ba, bari kiji na fad'a maki akwai certain people da dole kiyi hak'uri dasu don rashin su ka iya kawo nak'asu ma abinda kike nema. Sannan ni ba Huda nake nufi ba, idan ita ce ai da sauk'i tunda kinsan irinsu AT dole 'yanmata nurses suyita rushing akansu, ko a TH ma akwai masu mutuwar sonsa, amma kinsan basa gaban sa, wacce nake nufi ba kowa bace illa MARYAMA, AT da mahaifiyar sa Kai harma da yaransa suna son yarinyar nan da uwarta tamkar sun had'a jini.... So ina mai baki shawari kiyi taka tsan-tsan dasu SHAK'UWA CE mai tsanani tsakaninsu da Family d'in... Kar ki ganta k'arama kiyi tunanin he can't fall for her, k'aramin gashin ido yakan shiga ido ya hanaka zaune ya hanaka kwance." Jikin Shema'u yayi sanyi da maganganun Hisham, saurin d'ago idanu tayi tana dubansa yana k'ok'arin had'e boturan rigarsa kafin tace "Hisham wllhi yau babu yanda zakaje sai ka gaya min WACECE MARYAMA, who is she to AT and his family.. I need to know who she really is..???" Murmusawa yayi yana kallonta da wutsiyar idanu kafin yace "You are unbelievable, how comes baki sansu ba bayan k'anwarki tana auren AT." Hannayenta biyu ta d'aura a duka kafad'unsa kafin tace "Don't be such an ass, tunda Aysha tayi aure zuwana gidanta baifi a k'irga ba, nasan sau biyu ne zuwa na tun bayan aurenta sabida bazan iya jure ganinta a gidan AT ba, zuwata na farko lokacin data haifi Sajida ce nazo bikin suna, daga nan ban kuma zuwa ba sai sunan Ni'ima, toh tun daga wannan lokacin da na kuma yin arba da AT na k'udiri niyyan next zuwa da zanyi, salwantar da Aysha da iyalanta zanyi na mallaki AT, ka fahimta..." ta k'arashe tana tale masa fuska kaman wani toy. Hisham ya jinjina kai kafin yace "I see, okay zauna na fad'a maki wacece ita." Zama tayi saman gado ta zubawa Hisham dake zaune saman stool idanu. "Kaman yanda kika sani, washe garin auren AT, Allah Ya karb'i ran mahaifin sa Alh Muhammad Shattima. Babu yanda AT baiyiba Hajiya ta koma gidansa da zama bayan ta gama takaba fir tak'i tace ita a nan gidanta zata zauna har itama tata ta sameta. Hajiya tanada fad'a sosai hakan yasa duk mai aikin da aka samata ko 'yar tayin zama sai sun gagara zama da Hajiya sun gudu, ke k'arewarta har Rano asalin garin mahaifan AT. ... AT da Aisha sunje sun d'auko 'yar uwa ta zauna da Hajiya amma abu yaci tura, babu mai hak'urin zama da Hajiya sabida tsananin fad'anta, ada fad'an Hajiya ya ninninka wanda takeyi a yanzu, ai yanzu tayi sanyi sosai babu ma had'i da da....." cikin sauri Shema'u ta katse sa da fad'in "Au yanzu matar nan da tafi haka fad'a..? Kace anyi annoba jarabebbiya. " Hisham ya murmusa kafin yace "Ai saura kika samu, Ayshan kanta sosai tayi hak'uri da Hajiya kafin daga baya Hajiya ta sota sosai, me yake hana Momman ki zaman bayan haihuwa ma Aysha, masifar Hajiya ce kurum ke korarta sabida halinsu baizo d'aya ba, ba sai na fad'i ba kinsan keda mahifiyarku halinku yayi shige, Aysha ta fita zakka cikin ku, kinga ko ai bazasu jitu da Hajiya ba.... " Ya d'anja fasali kafin yaci gaba da fad'in "Mu dawo cikin labari.... Ana nan a haka kowa ya kasa zama da Hajiya sabida fad'anta, ranan da Aisha ta tashi da nak'udan babbar 'yarta Fatima Sajida, sosai hankalin AT ya tashi driving ma da k'yar yakeyi, yanayi yana juyawa baya yana kallon Aisha yanda take mark'usoso Hajiya na rik'e da ita. Kaman daga sama suka hangi Mace Kwance tsakiyar titi.... Horn AT ya ringayi mata tak'i matsawa, a zaton sa mahaukaciya ce, ga tashin hankalin da yake ciki.... Da k'arfin gaske yabi ta gefen matar ya wuce. Nan suka hangi jaririya 'yar shekara d'aya tana zaune gefen matan ashe, matar kuma tamkar ta mutu, yarinyar sai tsalla kuka take ga duhu na dare ga Aysha na murk'usoson nak'uda, gaba d'aya ya rasa da wanne zaiji ga Hajiya sai salle sa take tana fad'in yazo su tafi asibiti. AT ya tsaya cirko-cirko a tsakiyan titi kafin ya d'aga hannayen sa sama yace "Ya Allah kaga zuciyata, bansan wanne zanyi ba wanne zan bari, k'aramar yarinya tana kuka a tsakiyan titi da duhu na dare, Mace mai tsananin buk'atan taimako tana kwance tamkar gawa a tsakiyan kwalta, ya Allah ka kawo mun d'auki, matata bazata iya haihuwa da kanta ba saidai a cire abinda ke cikin, idan na barta a haka zan iya rasata ya Allah nasan duk abinda kayi there must be a reason, Allah ka kawo min mafita.. AT bai sauk'e hannunsa k'asa ba yaji kukan sabuwar jaririya na fitowa daga cikin mota, ma'ana Allah Ya sauk'i Aisha lafia.... Hawayen farin ciki ne ya shiga keto masa, k'arasawa yayi ya sungumi yarinyar dake zaune saman kwalta ya rungumeta kafin ya nufi mota tareda yanda ya tarar Hajiya sai murna take don bata tab'a ganin haihuwa mai sauk'in na Aisha ba. Kallon yarinyar dake rik'e hannunsa yayi yana mai murmushi had'i da hawaye kaman daga sama ya jiyo muryar Hajiya tana fad'in Attahiru tabbas kayi tunani da baka bari mun tafi mun bar bayin Allahn nan a nan ba, Allah yaga niyarka na taimako kuma ya yassare maka damuwar ka. Attahiru daga yau bazan k'ara hanaka taimako ba, kuma insha Allahu ni zan zauna da wad'an nan bayin Allah cikin aminci da k'aunar juna......" Shiru Haisham ya d'anyi don baisan yaya akayi zuciyarsa ta shiga jero labarin nan yana mai jin rauni na ratsa sa ba, tabbas bazai iya k'arya zai fad'a ma Shema'u iyaka abinda ya sani, don bayan shi baya jin akwai wanda AT ya basa wannan exact labarin tunda shine aminin sa..... Kaman daga sama ya jiyo muryar Shema'u tana fad'in "Kar kace min wai imani ne ya soma shigar ka don kana labari mai tab'a zuciya, k'arasa labarta min nasan ta yanda zan b'ullo masu." Dariya Hisham ya fashe dashi kafin yace "Zan tuba amma sai na amshe asibitina daga hannun AT. Daga nan yaci gaba da fad'in "Koda mahaifiyar Maryama ta farfad'o a firgice ta farfad'o ta ringa masu wasu irin sunbatu tamkar na tab'in k'wak'walwa, ta jima tana asibiti Hajiya ita ke kula da Maryama, bacci tare komai tare, kinji yanda SHAK'UWAR Maryama da Hajiya ta samo asali, sannan AT tun daga wannan lokacin idan yaje gidan Hajiya yana tare da Maryama yanai mata wasa don dama shi Allah yayisa mai son yara, Sannan shi ya fara ambatan ta da MARYAM sabida son suratu Maryam mahaifiyar annabi Isah da yake a cikin Alk'ur'ani, tunda mahaifiyarta babu lafiya balle ta fad'i masu sunanta, Jaririyar d'iyarsa kuwa taci sunan mahaifiyar sa Fatima. idan ya koma gida ga Sajida, Idan yaje gidan Hajiya ga Maryama. Kinji dalilin da yasa nace maki SHAK'UWA CE mai k'arfi a tsakanin su....." Shema'u ta kafesa da idanu kafin tace "Nifa banji kace min ga asalinsu ba, ita Maryaman da Uwarta, ko kan street shine asalin su.?" Hisham ya murmusa kafin yace "Ana baki kina rok'o, ai ce maki nayi mahaifiyarta ta kwana biyu a asibiti, tayi kusan watanni biyu kafin ta dawo dai-dai. Sanda ta dawo hayyacinta nan ta sanar dasu cewa Su d'in asalin su 'yan Jihar Katsina ne, Zaizayan K'asa da akayi a wancan lokacin shi ya kashe masu kowa nasu, daga ita sai d'iyarta sukayi saura. Koda ta farka taji suna ambatonta da Maryama tasha mamaki sosai domin kuwa Maryam shine sunanta na asali. Toh fah tun daga wannan lokaci mahaifiyar Maryama ita ta raini yaran AT gaba d'ayansu shiyasa suke tsananin sonta kinji yanda SHAK'UWAR su ta samo asalin " Ya k'arashe yana mik'ewa tsaye kafin yace "Toh kina iya barina na fita, ko akwai sauran abinda kike son ji.?" Jinjina kai tayi kafin tace "Now that I learned more about them yanzu ne zan tattaro makaman yak'ina, I'll destroy them one after the other." D'ago face d'inta Hisham yayi kafin yace "Ke meyasa bazaki bi bikaye da malamai ba don cikan burinki cikin gaggawa kaman yanda matan zamani suke. Huh...?" Bursting tayi cikin dariya kafin tace "Ai ni nan nafi ko wani shegen boka da Malam iya tuugu da makirci, da zasu zo wajena ma da na basu tips d'in da zasuke bawa masu zuwa wajen su suyi su sami biyan buk'ata..." Ta k'arashe tana d'aga masa gira sama. Hisham na fita itama ta fice, bata zarce ko ina ba sai shagon saida waya. Android mai kyau ta saya kafin ta nufi gida. ****************** "Ummi yanzu yauma ba kwana zakiyi ba duk kun tare gidan Uncle, gasu Aunty Shema'u da Momma duk basu isa ba kema sai kin koma." ta k'arashe maganar baki a ture. "Haba Maryama ai ganin mutane haka yana d'ebe masu kewa, kuma Momma satin nan da zamu shiga zata tafi." D'an jim Maryama tayi cikin zuciyarta addu'a take Allah yasa harda Aunty Shema'u zasu tafi don Allah Ya gani sam tak'i jinin matar. *************** Tana shigowa gidan ta jiyo hayaniyan yaran a parlorn AT na sama, saurin ciro turare tayi cikin jakarta ta feffeshe jikinta kafin ta canza taku ta soma haurawa sama. Can cikin parlorn sa take hangosu ta cikin sliding door d'in dashike k'ofar ta glass ne. Sosai suka burgeta Jamal da Ni'ima sai d'alewa wuyar sa suke yayinda Sajida ke zaune gefe tana tayasu dariya, idan ka gansu dole kaji sha'awarsu..... Kaman ance Sajida ta kalli k'ofa nan ta hangi Shema'u tayi tsaye tana kallon su fuska fal murmushi.... Da gudu ta mik'e ta nufi k'ofa tana fad'in "Yoyoyo Aunty... " Nan Ni'ima ta mik'e itama ta nufi bayan Sajida a guje.... Jamal kuwa rik'e yake da wuyar AT suka bisu da kallo. [2:56PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *SHAK'UWA CE* 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *13* *漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�* _馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_ Shiru Ashfaq yayi yana sauraren mahaifiyar sa daga d'aya b'angaren. A hankali ya sauk'e nannauyan ajiyan zuciya kafin ya soma fad'in "Mummy don Allah ki daina saka ma ranki damuwa I'm very well here, yanzu ne zansan rayuwa da kuma k'alubalen da ake fuskanta a cikinta, sannan Mummy hakane kawai zaisa na sami wacce take sona tsakani da Allah ba don kud'i da muk'amin mahaifina a gwamnati ba, Mummy idan na zauna a gida I'm quite sure Daddy arrange marriage zaimin kaman yanda suka saba shida abokan siyasar sa da kasuwancin sa." Daga d'aya b'angaren Mummy ta sauk'e ajiyan zuciya kafin tace "Haidar, kana ganin hakan shine maka mafita. Idanma asibitin kanka kake so ko ni nan zan gina maka shi but pls ka dawo gida Son, I'm afraid to lose a child again." Shiru Ashfaq ya kuma yi zuciyar sa na tafarfasa yana mai tuna har abada k'wandala da ta fito daga wajen mahaifin sa bazai kuma anfanuwa da ita ba sabida k'azanta irin ta dukiyar, if only zai iyar sanar da mahaifiyar sa abinda ya gani da ya sanar da ita, amma bashida hali..... Muryan Mummy ta kuma katse masa tunani da fad'in "Daddyn ka yayi fushi sosai da kai tunda ka watsa masa k'asa a idanu ranar da ya kamata ace ya kasance ranar bikin ka, yace sam babu shi babu kai muddin baka dawo ka nemi yafiyar sa ba kuma ka aminta da auren Fairuza ba." D'an murmushi yayi kafin yace "Mummy pls ki daina damuwar nan kinji, it shall all pass, zan dawo amma ba yanzu ba, na fad'a maki har sai na sami macen da take sona ba don kud'u muk'ami ko kyau na ba. Sannan ina so na tashi tsaye ma rayuwata banaso na kasance kullum dogaro da mahaifina nake." Jinjina kai tayi tana goge k'wallan da suka zubo mata kafin tace "Shikenan Haidar, kana tare da addu'o'ina a duk yanda kake, Allah Ya maka albarka." Ashfaq ya amsa da Ameen kafin sukayi sallama. Tagumi ya rafka idanunsa sunyi jajazir a duk lokacin da ya tuna abinda ya gani a d'akin sirrin mahaifin sa, shakka babu k'ok'on kan tilon k'anwarsa ce Nabila, shin yaya Mummy zatayi idan tasan Daddy shi yayi tsafi da Nabila, Nabila ba mutuwa tayi kawai ba tsafe ta akayi daga ita har mai rainonta, shin yaya zataji idan tasan tsafi ne yakai Daddy matsayin da yake na mataimakin shugaban k'asa a yanzu...... . Ya tuna sanda zai koma makarantar kwana k'arshen ganinsa da Nabila kenan tana 'yar k'aramar Baby. Share wasu hawayen ya kumayi kafin ya furta "Zanyi aiki ba tareda taimakon ka ba Daddy, bazan huta ba har sai na had'a kud'ad'en da nasan zasu isheni shari'a dakai." ************** Fincika Buzu yayi yana fad'in "me kike nema a wajena, wacece ke.?" Kafiran dariya Shema'u tayi kafin tace "Relax boy, kai baka sanni ba, amma ni nai maka farin sani. Sunan ka Haris amma anfi saninka da Buzu a layin ku, mahaifiyar ka mijinta ya mutu ya bar mata ku biyu, kaida yayar ka dake auren tsohon sanata Kamilu Ashir, tun kuna k'anana mahaifanku suka dawo k'asar nan da zama, amma asalin ku 'yan k'asar Yemen ne..... A iya sani na mijin yayar ka shike d'awainiya daku don harta motar da kake shiga shi ya saya ma mahaifiyar ka..." Ta d'an ja fasali kafin taci gaba da fad'in "Tooh gashi yanzu Kamilu Ashir ba Sanata mai ci bane, an sauk'esa shi kansa ya fad'a a kwata taimako yake buk'ata. "..... Kallonta kawai Buzu yake baki sake cike da mamakin yanda akayi tasan abubuwa da dama a gamedashi, ko da yake ba abin mamaki bane, k'ila itama d'aya ce daga cikin irin matan manyan mutane da suke neman sa ya biya masu buk'atunsu su basa kud'i, amma kuwa ai da ba sai tabi ta hakan ba tunda dama sana'ar sa ce.... Kaman tasan tunanin da yake, ta k'araso gabansa tana murmushi kafin tace "Kana mamakin nasan abubuwa da dama gameda kai ko.? Toh ba a nan ta tsaya ba, nasan kai d'in matan manya suna nemanka daga nan har Abuja, basai na lissafo maka su ba tunda kasan na sani, sannan duk club d'in garin nan babu yanda bakayi k'aurin suna ba, while on the other hand a unguwar ku kana acting innocent, kana nuna kai yaron arziki ne kuma na kowa, da wannan d'abi'a ka saye zukatan mutane da dama ciki harda Maryama da Hajiya Fatima mahaifiyar Dr Ahmad Tahir Shattima. Am I right?" ta k'arashe tana wata munafukar murmushi. Zufa ne ya shiga keto ma Buzu ta kota ina, ina bazai bari a b'ata tsakanin su da Maryama ba ko a bak'antasa a idanunta da na Hajiya ba.. Don kuwa son Maryama yake da gaske bada wasa ba..... Cikin sauri ya soma girgiza kai baki har na rawa yake fad'in "Baiwar Allah don Allah wacece ke, sannan me kike nema a wajena, pls ki fad'a min ko meye zan maki shi amma pls don't ruin my reputation especially a idanun Maryama da Hajiya, pls kar ki b'ata min suna a idanun su." ya k'arashe yana d'aga mata hannu bibbiyu alamun rok'o. Murmushi Shema'u tayi tana shafa fuskar Buzu tamkar tab'ebb'iya take fad'in "Are you sure Baby boy, are you zakayi duk abinda na umarce ka, I can even pay you sannan na b'oye maka sirrin ka, no one will learn about it." Buzu dai kallonta kawai yake cike da tsoro, don kuwa duk taurin kansa bai tab'a gamuwa da macen data firgita sa ta basa tsoro irin Shema'u ba. D'an yatsanta ta saka ta shiga gyara masa kwancecciyar sumar sa tana fad'in "Aikin me sauk'i ne Malam Buzu." Wayarta ta latsa hoton Sajida ya fito cikin screen d'in kafin tace "Ka ganta, isn't she sweet, yeah tanada kyau da k'uruciya, tafi sugar Mummies d'in da kake spending nights dasu. Ko ba haka bane.?"..... Jin yayi shiru ya kasa amsata yasata juyowa tana dubansa yanda yayi mutuwar zaune yana bin hoton Sajida da kallo. Murmushi tayi kafin tace "Oh... I know you'll like her Boy, she's every Man's type right." Ta k'arashe tana d'aga masa gira alamun tambaya. Girgiza kai Buzu ya soma kafin yace "Wannan ai Sajida ce, 'yar uwan Maryama ce kuma d'iyar Dr Tahir ce, I'm afraid but I can't mess with her." Shema'u ta tuntsire da dariya kafin tace "Ashe kai k'aramin d'an iska ne kuma bakayi shirin yin bariki ba idan har akwai wanda yake baka tsoro." Kamo fuskar Buzu tayi suna facing juna kafin tace " The girl is madly in love with you, she's the reason why you and Maryama are in good terms.... Zan baka mota da kud'i, just love her, make her feel like she's a Queen, daga farko, daga k'arshe inaso kayi ruining d'inta, ka koya mata zuwa club, if possible ka koya mata shan duk wani miyagun k'wayoyi, sannan daga k'arshe get her pregnant." Ganin yayi sakare yana kallonta yasa ta d'auko key d'in sabuwar motar da Alh Aminu ya bata ta shiga shafawa a fuskar Buzu tana wata mayaudariyan murmushi... ************** "Oyoyo Ummi nayi missing d'inki da yawa." Ta fad'i sanda ta tafi ta rungume Ummin nata. Hannunta ta rik'e kafin tace "Oh wato Maryama bazaki girma da d'ale jikin mutane ba." D'an turo baki tayi kafin tace "Ai wllhi Ummi idan dai keda Hajiya ne sam bazan daina d'ale jikin ku ba....... Tsulum Hajiya dake zaune saman Sofa tana wurga d'anwake a baki tace "Yo idan na aurar ki ai saidai ki d'ale jikin mijin." Maama Juu dai murmushi kawai take yayinda Maryama tayi kicin-kicin da fuska tace "Waike Hajiya da anyi magana sai kice wani aure, wllhi nidai koma auren nayi tareda zamu tafi gidan mijin." Hajiya ta dara kafin tace "Aiko ga kutiri na ga naki dole mijin ya gina mini nawa d'akin inko ba haka ba saidai ya kora mu don babu wanda ya isa ya rabamu." Gaba d'aya sukayi dariya kafin Maama Juu ta zauna tana gaida Hajiya sanda Maryama ta nufi madafi kawo ma Umminta abin tab'awa. *Sameena Aleeyou Mrs* [2:56PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *SHAK'UWA CE* 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *15* *漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�* _馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_ *_Fatan Alkhairi a gareki Fauxia MB marubuciyar LOKACI NE 馃槏馃_* Shema'u ta sunkuya ta d'auki Ni'ima tanai mata irin maganganun 'yan yara kafin ta dubi Sajida dake mata sannu da zuwa ta amsa had'i da shafa fuskarta tace "Sweetheart naji dad'in ganinku haka cikin raha jin dad'i da farin ciki, wllhi sosai naji dad'i ina fatan family d'in ta kasance cikin haka kullum." Hannunta Sajida ta shiga janyowa suka nufi cikin parlorn AT. Shema'u sai washe baki take tana kwarkwasa. A haka ta gaida AT, ya amsa a tak'aice. Ta dubi Jamal dake sakale da wuyan Baban shi yana mitan Maama Juu bata dawo ba, don dama yaron sosai yake k'aunar Maama Juu. "Champ, babu gaisuwa ne.?" ta fad'i tana duban Jamal... D'an murmushi yaron ya sakar mata kafin yace "Aunty Shemah meyasa bakije gidan Hajiya kin d'auko Maama Juu ba, ina missing d'inta, I thought itace ta dawo not you." Hannu Shema'u ta mik'a masa tana mayaudarin murmushin ta kafin tace "Zo abinka my Jamal, kayi hak'uri kaji soon zata dawo...." Kallo tabi AT dashi wanda ke faman shafa wayar sa lokaci guda ya mik'e ya manna wayar a kunne yana amsawa kafin ya shige corridor d'in d'akinsa. Shema'u kaman ta had'iyesa haka taji. Sauraren yaran na dole kurum take amma hankalinta kacaukam naga mahaifin su. Suna nan a haka da yaran ya fito cikin shiri, k'anan kaya ne a jikinsa, black long sleeve shirt da kuma faded Blue Jeans.... Baki sake Shema'u ke binsa da kallo tamkar ta had'iyesa. K'arasowa yayi ya mammana ma yaransa kiss a goshi had'i da shafan kansu kafin ya dubi Sajida yace maza ta tabbata tayi karatu. Sai ce masa suke "Daddy sai ka dawo." Ni'ima kuwa binsa tayi ta rik'o k'afarsa ta baya kafin tace "Daddy zan bika." D'an duban agogon Gshok dake d'aure a hannunsa na hagu yayi kafin ya rage tsayin sa ya rik'o hannayenta yace "Precious Asibiti zanje ko kinaso a maki allura.?" Kuka ta soma masa tana fad'in ita sai ta bisa. Ganin haka yasa Shema'u saurin tasowa ta k'araso yanda suke, tsugunawa tayi itama gaban Ni'ima kafin ta shafi kanta tace "Baby Daddy fah allura zaije, kuma idan kika bisa anjima zamu tafi shan ice-cream babu ke.... Right guys? " ta k'arashe tana duban su Sajida. Murna suka soma yi nan Ni'ima ta janye hannunta daga na AT ta tafi wajen Shema'u ganin yanda sauran 'yan uwan nata ke murna. Sai satan kallon AT da ya bisu da kallo take, mik'ewa yayi ya soma tafiya yana zura wayar sa a aljihu. Nan Shema'u ta hangi car keys d'insa saman center table, kafin yaran su kula tayi saurin k'arasawa ta d'au keys d'in. Har ya kai k'ofa ya jiyo Shema'u ta ambato sunansa "Dr." Juyowa ya d'anyi ya dubeta. Cikin salo da kissa ta tako har yanda yake kafin ta d'ago masa keys d'in tana murmushi tace "You forgot this." D'an murmushi yayi kafin yace "Thank you." Yasa hannu zai karb'a ta saki keys d'in a k'asa cikin salo. "Ohh sorry,." ta fad'i sanda tabi keys d'in k'asa.... Daidai lokacin da yakai hannunsa kan keys d'in Shema'u ma ta sako nata, nan hannayen su suka mannu da juna, d'ago idanu sukayi suna duban juna, cikin sauri ya janye hannun sa yana bata hak'uri. Cike da kissa itama ta soma basa hak'uri irin a daburcen nan, sai ka rantse har ranta ne. Cikin sauri ya mik'e ya fice, k'irjinsa na bugawa cikin sauri, rabonsa da jikinsa ya shafi jikin wata macen daba tasa ba tun Ayshar sa na raye... D'an shafe goshinsa yayi had'i da k'ok'arin yakishe hakan a zuciyar sa cikin sauri. Shema'u dad'i kaman ya kar ta, cike da farin ciki ta shige cikin yaran suna masu ci gaba having fun, sai jefa throw pillows suke a tsakanin su. ***************** Kallon wayar data sayo d'azun da yamma ta zauna tana yi, kai anya yanzu ne ya kamata ta bama Sajida wayan nan.? What if AT finds out.... Kai ya kamata tayi abu da tunani tunda dai yanzu confirm tanada Buzu a k'asa, umarni kawai yake jira ta basa ya soma gudanar da aikinsa.. Wani tunani ne ya fad'o mata ta Saki murmushi had'i da kwanciya saman gado zuciyarta fal nishad'i...... Wasa-wasa SHAK'UWA CE sosai ta shiga tsakanin yaran AT da Shema'u. A b'angaren AT kuwa sosai yake duk iya k'ok'arinsa ganin yayi avoiding duk wani abinda zai had'asa da Shema'u amma abu yaci tura, ko ya keb'e kansa yaransa zasu had'asu, bazai iya k'aurace ma yaransa ba da yayi hakan. Shi kansa baisan me yake ji ba, amma tabbas zaman mace haka a cikin gidansa yana matuk'ar jefasa cikin wani irin yanayi da tunani kala daban-daban tunda shidai ba waliyi bane. Tabbas shed'an yayi jagora ma Shema'u don kuwa AT ya sami kansa da matsananciyar Sha'awar ta duk iya k'ok'arinsa na ganin ya yakice hakan a zuciyar sa abu yaci tura, musamman idan ya tuna 'yar uwar matar shi ne, kai ko zaiyi aure don kare kansa daga fad'a ma tarkon shed'an bazai auri 'yar uwar matar shi ba, gani yake kaman yaci amanar Aysha ce. Ganin tunanin hakan bazai ficce sa ba ya sanya sa dagewa da azumin litinin da alhamis. Shema'u kuwa dama ta samu, ado da kwalliya babu kama k'afan yaro. *************** Rai b'ace ta turo k'ofan d'akin ta shigo kaman zatayi kuka. Cike da makirci Shema'u ta mik'e ta rik'ota tana fad'in "Baby lafiya, meke faruwa.?" "Aunty wai Daddy bazaije graduation d'ina ba... Aunty ina so na ganku duka a wajen, all my family..." Murmushi Shema'u ta sakar mata tana shafa fuskar ta kafin tace "Sweetheart kinsan Daddyn ku da kafiya, gashi yanzu sam ba sosai yake son shiga sabganmu ba, bansan ko zamana ne a gidan sa baya so ba, amma dai kar ki damu anything for you my dear, zan yi iya k'ok'arina na nuna masa mahimmacin zuwan nasa, ai nasan da zaije, amma sani nima zanje inaga shiyasa ya fasa, Baby bansan me nayi ma Daddynku yake avoiding d'ina haka ba, ko dai ina wani abin maras kyau ne.?" ta k'arashe tamkar zatayi kuka. Jikin Sajida yayi sanyi, tak'i jinin taga Shema'u cikin damuwa. Da sauri ta soma girgiza kai kafin tace "Aunty don Allah kar kiyi kuka." Cike da kissa Shema'u tace "Ba dole nayi kuka ba sweetheart, kinsan dai yanda nake sonku nake ji daku, yanzu idan Daddyn ku yace na bar masa gidan sa ai bazan iya rayuwa babu ku ba, ina sonku sannan na shak'u daku, bazan iya barin ku ba, never. " ta k'arashe tana mai rungumar Sajida idon ta harda kawo ruwan makirci kafin tace "Amma dai kije ki bisa a hankali ki nuna masa mahimmancin zuwan nasa, nasan he'll listen to you." Nan ta kitsa mata me zata ce. Cikin sauri Sajida ta mik'e ta fice daga d'akin ta nufi parlon mahaifinta.. Shema'u ta bita da kallo, kafin ta daka tsalle tana fad'in "Yesssss." kwanciya tayi bisa gado had'i da lumshe idanu. Bata samesa a parlor ba hakan yasa ta nufi bedroom d'insa, k'wank'wasa k'ofar tayi had'i da sallama kafin ya mata izinin shigowa, yana zaune yana research a computer, kunsan likitoci ba'a rabasu da bincike. Cire medicated glasses d'in idanunsa yayi kafin ya karkato yana dubanta yace "K'araso mana Mama ta." Baki a ture kaman zatayi kuka ta tako ta zauna gefensa kafin tace "Daddy sanda na gama primary, you were there, harda Mummy da Jamal. Daddy meyasa yanzu bazaka je ba, sabida babu Mummy, wllhi zanyi kuka idan ban ganku gaba d'aya a wajen ba. Nasan kana valuing aikin ka but pls Daddy do this for me... Don Allah kaji Daddy Tura laptop d'in gabansa yayi kafin yace "Sajida sam ba haka bane, ranar tayi dai-dai ne da ranar ziyarta ta asibitin Bauchi kinsan ni visiting Dr ne a can. Amma I'll see what I can do, kinji...." ya k'arashe yana sakar mata murmushi. Murmushi itama tayi kafin tace "Daddy na gode. You the best. " Ta mik'e ta fice cike da farin ciki. Ya bita da kallo yana murmushi kafin ya girgiza kai kawai yaci gaba da abinda yake. Da gudu ta shigo d'akin had'i da d'alewa jikin Shema'u tana mai sanar da ita ya yarda zaije shi. Murna Shema'u ma ta shiga yi tana fad'in "Kinga abinda nake fad'a maki idan kin bisa a tsanake tsaf zai yarda." Sajida na murmushi take fad'in "Allah barmin ke Aunty." Shema'u ta kuma hugging nata. **************** Yau ce ranar su ta k'arshe a Makarantar, ranar bukin yayen su. Sunyi kayu cikin graduation gowns d'insu. Kana iya hango tsan-tsan farin ciki a fuskar gaba d'aya d'aliban da ake yaye su. Fadila ce ta kuma tab'o Sajida tace "Wai har yanzu Maryama bata iso ba, kinga fah the program is about to start, yaya zamuyi kar a soma kiran sunan ta don nasan confirm zata karb'i kyaututtuka." Tab'e baki Sajida tayi ba tareda tace komai ba, tsaki Fadila ma tayi tace "Kar Allah sa ki tanka, kuma kyauta ne dai sai ta karb'a.... Su Fauziya sauran k'awayen su sai dariya suke masu. Don dama sun saba 'yar haka da Fadila, wacce suka fi shiri dama Maryama ne. AT yayi kyau cikin faran yadi mai laushin gaske, ya saka hula dark ash zanna bukar, dark covers ne a k'afafun sa yayinda ya d'aura agogon Aldo zallan silver, k'anshin rantsatstsun turarruka ne kurum ke tashi a jikinsa. Shema'u dake tsaye dasu Jamal a parking lot baki ta sake kawai tana hangosa. Tun daga nesa ya bud'e masu security lock amma Shema'u bata san ya bud'e ba, tayi nisa cikin duniyar kallon sa. Saida ya k'araso ya bud'e masu Jamal k'ofar motar kafin hankalin ta Ya dawo jikinta, cike da kissa ta bud'e front seat ta shige tana binsa da mayen kallo, shi kuwa AT sam baison yama kalle ta. Sai biye ta yaransa yake. Suna tafe suna hira da yaransa Shema'u tana tsomo baki, a dai-dai kwanan shiga makarantar wayarsa ta soma ringing, Hajiya ce mai kira. Da fad'a ta soma masa don ko zsrafin gaisheta bai samu ba, nan ta sanar dashi Maryama tana gida bata je ba, yauma su Sajidan basu biyo mata ba. "Subhanallah Ya akayi haka?!" ya furta sanda yake karyan kwanar, Shema'u kuwa k'uri ta masa tana son jin menene ya d'aga masa hankali haka..... Muryarsa ta kuma jiyowa yana fad'in. "Okay, gani nan zuwa yanzun nan, barin ajiye su Jamal." Koda ya gama wayan kallo Shema'u ta kuma binsa dashi tana son tambayar sa wa ya kirasa amma babu fuska, iyaka abinda ta fahimta kiran nada mahimmaci a gurinsa. Sanda ya gama parking a farfajiyan makarantar, ya dubi su Jamal yace "You guys should behave okay, zan dawo bada jimawa ba, just stay with your Aunt okay." Jamal yace "Daddy ina zakaje, Adda Sajida bazataji dad'i ba idan taganmu babu kai. D'an turo kansa yayi ta k'ofar motar kafin ya shafi kan Jamal yace "Champ, zanje d'auko Addan ku Maryam ce, she supposed to be here by now, tunda harda ita akema yayen. Ku zauna da Aunty ku, yanzu zan dawo.. Kad'an ya rage Shema'u bata saki fitsari a wandonta ba jin yanda AT zaije sabida tsananin tashin hankali...... Tayi nisa duniyar tunani ta tsinkayo muryar AT yana fad'in Ta kula dasu da Allah. Murmushin yak'e tayi kafin tace "You don't have worry Dr, mu jenku ko babys d'ina, ta rik'o hannayen su suka shige. K'irjinta sai tafarfasa yake. Cikin sauri AT ya tada motar sa ya bar wajen. Tana tsaye jikin glass d'in window dashike irin mai kaman madubin nan ne tana gyara d'aurin kwalinta ya hangi bayanta. Kasa ci gaba da tafiya yayi sai mutuwar tsaye da yayi a wajen. Da sauri da sauri zuciyar sa ke bugawa. Ta cikin mirrorn ta hangesa yayi tsaye yana kallon ta wanda hakan ya sauk'ar mata da fad'uwan gaba. *Sameena Aleeyou Mrs* [2:56PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *SHAK'UWA CE* 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *16* *漏Sameena Aleeyou....鉁嶐煆�* _馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_ *Fatan Alkhairi k'awayen k'warai Sweetheart Rally Garba 馃槝 and Shawty 馃挄 Darling.... Love you guys from the bottom of my heart 馃槏* Sajida tana hangosu ta tafi da sauri tana welcoming nasu had'i da basu wajen zama. Su Jamal tuni sun d'ale kan seats sun zazzauna. Shema'u ta wani juya idanu had'i da mik'ewa kafin ta shiga gyara ma Sajida zaman hular nata, with that fake smile on her face, fad'i take "Sweetheart I'm proud of you, kinyi kyau." Sajida ta murmusa kafin tace "Aunty naji dad'i kinzo,.... Amma ina kuka baro Daddy.?" Saida Shema'u ta d'an saci kallon su Jamal da hankulansu yafi karkata wajen d'alibai masu Cultural Dance sunyi shiga k'abila daban-daban kana tace "Baby you know your Dad when it comes that social climber,.... Uhm sorry nasan dai k'awarki ce kin d'auketa 'yar uwa, I just couldn't stand her ne, haba Daddyn ku fah har mun iso nan dashi kawai Hajiya ta masa waya ta ringa salle shi da masifa wai Maryama bata taho ba, babu yanda Daddyn ku baiyi ba ta hawo ko adaidaita ne ko taxi ta taho shi zai biya kud'in amma fir tak'i wai saidai shi yaje ya kawota, hmm Sweetheart I'm afraid she's stealing your Dad away from you... Amma kar ki damu kinada ni, bazan tab'a barinta tayi succeeding ba." Tuni idanu Sajida ya soma kawo ruwa domin kuwa ana iya kiranta karb'an kyauta a koda yaushe, gashi tasha burin mahaifinta ya gani ya rakata su karb'a tare. Ganin haka yasa Shema'u saurin rungumota kafin tace "Oh no My Sajee, kinsan bana son ganin ki cikin damuwa, this is your Day, don't let anything ruin it for you, besides mu munzo ai, gani ga Siblings d'inki, we're all here for you sweetheart." Gyad'a kai Sajida tayi kafin tace "Aunty what if aka kirani karb'an kyauta babu Daddy, Aunty babu Mummy na sannan shima baya nan, wa zai raka ni amsar kyautan.?" Hannayen ta Shema'u ta rik'e cike da kissa kafin tace "My Sajee ni zan raka ki karb'a kar ki damu, I'm here, I'm here for you sweetheart, karma ki b'ata ranki kinji, oya koma seat d'inki, nida su Jamal zamu raka ki gaba d'aya da zaran an kiraki." Haka Shema'u ta ringa calming Sajida da makirci har ta yarda ta koma wajen zamanta, amma zuciyarta fam yake da haushin Mahaifin ta da Maryama. ***************** Kasa ci gaba da abinda take tayi, gaba d'aya sai ta tsinci kanta da jin nauyin sa. A hankali ta juyo idanunta naga k'asa take fad'in "Sannu da zuwa Uncle." Har lokacin murmushi bai gushe saman kyakkyawan fuskar sa ba, d'an takowa yayi yana mai karantar yanayin ta kafin ya amsa mata gaisuwar ta Ya k'arada "Congratulations, Allah Ya sanya Albarka." D'an murmushi ta kuma yi kafin tace "Ameen, na gode Uncle." Kasa cewa komai sukayi daga ita har shi kowa da abinda yake sak'awa a zuciyar sa. Ita dai Maryama nauyinsa take ji, yayinda AT ya rasa meke faruwa dashi a Al'amarin Maryama.... Hajiya ce ta k'araso cikin cancatewar ta leshi mai jida kyau da tsada, abinka da farar fata sai tayi kyau sosai, yanyin jikinta AT ya d'auko sam jikinsu bai nuna tsufa. Takowa take tana fad'in "A'a Attahiru har ka iso d'in ne, ai sai muyi mu tafi kar mu kuma lattti ko." ta k'arashe tana gyara d'aurin kwalinta jikin madubin window.... Ba Maryama kawai ba harta AT saida Hajiya ta basa dariya yanda take karkata d'aurin kwali. D'an durk'usawa yayi kafin ya gaidata, Hajiya kam hankalinta fa sam naga cancad'a d'auri take amsa ma AT gaisuwar sa. "Hajiya kema zaki bukin yayen ne." Ya tambaya sanda ya mik'e tsaye. Karkatowa tayi ta dubesa da kyau kafin tace " Attahiru wuce mu tafi babu lokaci, bana son dogon zance, yo kaima kaje balle ni." Maryama kam tuni ta shige ta d'auko graduation gown d'inta da d'an hulan. AT da Hajiya suka k'arasa yanda ya paka motar sa. Daga can yake hangota yanda tayi kyau sosai, ta d'an nad'e wuyar ta da farin Vail, sosai rigar bukin yayen nasu ya mata kyau. Tana shiga AT ya tada mota suka wuce. *************** Shema'u dai sam hankalinta baya jikinta, burinta kawai taga b'ullowan AT da wannan tsinanniyar yarinyar. Nan aka soma kiran d'alibai ana basu kyaututtuka da kuma testimonial d'insu na kammala sakandare. Anata kiran d'alibai d'aya bayan d'aya har aka iso kan Sajida. Shema'u ta rik'o hannun su Jamal da Ni'ima suka nufi Stage gaba d'aya harda Sajidar daketa faman kallon k'ofar hall d'in ko Daddyn ta zai shigo shiru. Haka ta karb'i takardan shaidan k'arasa karatun ta na sakandare da kuma kyaututtukan ta babu Daddyn ta, k'walla da takaici tab suka taru mata, Shema'u sai karantar ta take tana jin dad'i. Sanda su AT suka shigo Hall d'in dai-dai lokacin aka soma kiran Maryama ta karb'i nata ktaututtukan a matsayin ta na d'alibar da tafi ko wani d'alibi k'wazo.... Ana kiranta daga can baya ta d'aga hannu ta amsa, gaba d'aya Hall aka juyo ana duban su daga can yanda suke tsaye a bakin k'ofa. Babu abinda yafi k'ona ran Shema'u kaman yanda taga hulan Maryama a hannun AT, wato ma shi ya rik'e mata. Sajida kuwa babu abinda yafi k'ona ranta kaman yanda taga Daddynta da Hajiya sun d'unguma sun raka Maryama karb'an kyaututtukan ta, sai hotuna ake masu don babu shakka ta amshi kyaututtuka masu yawa, Jamal ma ya rik'o hannun Ni'ima suka kutsa anayin hotunan dasu, AT ya kasa rufe baki, nan ya d'auki Ni'ima ya rik'e a kafad'an sa yayinda Maryama ta kamo hannun Jamal aka masu hoton, Hajiya na gefe ta cakare... Lol. Su Fadila kuwa sai fad'i suke sunyi kyau, banda hararansu babu abinda Sajida take, Shema'u kuwa sai karantar ta take, a hankali ta sid'ad'e ta fice ta wani k'ofar dake gefe da ita kad'an. Wayar ta ta ciro ta latsa bugu biyu ya d'aga. "Hello kana jina, yanzu zata fito, kayi duk yanda zakayi ku bangaji juna, ka gane ai, I don't have to remind you." daga haka katse wayar tayi kafin ta dawo cikin hall d'in ta k'arasa yanda Sajida ke zaune can baya tana hawaye. Ta zauna had'i da dafata kafin ta kai dubanta ga AT dake faman gaisawa da manyan mutane irinsu Deputy Governor su Speaker State House of Assembly. Sajida ta d'ago tana dubanta kafin tace "Aunty ki gani fah ko nemata basuyi ba, wllhi na tsane su." Shema'u ta dafi kafad'unta cike kissa kafin tace "Kar ki tsane su, wancan makiran zaki tsana, ita ta rabaki da kakar ki sannan tana k'ok'arin rabaki da Baban ki, amma ta Allah ba tata ba, Allah yaga zuciyarki baki rik'eta da komai ba sai alkhairi ita kuma ta maki halin 'yan adam butulu. Yanzu abinda nake so dake, kar ki nuna ma Daddyn ki komai, ki tashi kije waje kiyi refreshing don karma su gane kuka kikayi, they might be thinking you're jealous of Maryama tunda ta fiki yawan kyauta , especially Hajiya. Sannan da yamma I've a surprise for you." ta k'arashe tana wani murmushi. Gyad'a mata kai tayi kafin ta mik'e ta fice. Hajiya tana zaune tareda su Jamal sai raba masu snacks da drinks ake. Maryama kuwa sai tambayan su Fadila take ina suka gano Sajida. Fadila ta tab'e baki tace "Ask me again, ni ina ruwana nasan yanda taje, k'ila tana wajen wannan Antin nata mai k'irar aljanai." sauran k'awayen sai dariya suke, Maryama kuwa b'ata fuska tayi. Fadila ta tab'e baki tace "Na you Sabi, ta dubi camera man tace "Ci gaba da d'aukar mu. Maryama ta sauk'e mata dundun wasa tace "Zaki sani ne." "Eh d'in na sanin, kunfi kusa keda ita, nikam ba k'yaleta zanyi ba kin sani." Cewar Fadila. Fitowar ta kenan tana faman share hawayen ta taji ta bangaji mutum, saurin d'agowa tayi da niyan masifa don dama a wuya take. Fuskar da tayi tozali dashine ya hanata furta koda kalma, Cak ta tsaya tana bunsa da kallo. Durk'usawa yayi ya d'ago mata hanki d'inta da ya fad'i k'asa ya karkad'e kafin ya mik'a mata yana murmushi mai kashe 'yan mata da manyan mata yace "Sorry pls, kiyi hak'uri it wasn't intentional..." Bata san sanda murmushi ya kufce mata ba, cikin sauri ta shiga girgiza kai tana fad'in "Kar ka damu babu komai." Buzu ya murmusa kafin yace "Are you sure.?" Bata sami zarafin amsa masa ba sabida tsaban k'warjinin sa da ya cika idanunta sai gyad'a masa kai tayi alamun eh. "Kaman na gane fuskar ki." ya fad'i yana k'ura mata idanu. D'an murmushi tayi kafin tace "A gidan Hajiya koh." "Exactly." ya fad'i yana mai fad'ad'a murmushin sa had'i da shafa kwantaceccen bak'in sumar sa. "Congratulations, ashe kema harda ke cikin d'aliban da ake yayewan." D'an murmushi tayi wanda yafi kama da yak'e kafin tace "Na gode, ka k'arasa ciki, Maryama na ciki, inace wajenta ka zo." D'an jim yayi kafin yace "No ai banma san tana candy yau ba, don ba ita ta gayyace ni ba, wata cousin d'ita ce nazo mata, kuma mun had'u har munyi pics.... Amma ya na ganki haka, yau ranar farin cikin ki ne kina looking sad, lafiya dai koh..? " Kasa ce masa komai tayi, sai kallon sa a fuzge da tayi. D'an gyara tsayuwar sa yayi ya shafi sajen sa kafin yace "Kiyi hak'uri idan na maki tambayan da baki so bane, or maybe na shiga hurumin da ba nawa ba, I'm only concerned about you ne, a beautiful girl like you fushi bai kamace ta ba.." Cikin siga mai cike da jan hankali yayi maganar. D'ago kai Sajida tayi tana mai tambayan kanta _Did I hear him right, ya kirani Beautiful._..... Ganin tayi sakare tana kallonsa yasa shi sakin wata murmushi kafin yace "Miss Beauriful idan bazaki damu ba mu k'arasa k'asan bishiyar can, inada muhimmiyar magana da nakeso muyi. " Daga yanda take zaune ta hangesu d'aga masa babban yatsa tayi alamun jinjina, ganin Sajida tabi bayansa kaman rak'umi da akala. Saurin mik'ewa Shema'u tayi ta lab'e a wani k'ofa don tasan idan su AT basu ganta ba zasuyi tunanin tana tareda Sajida don Karma su nemeta, dad'in da taji AT manyan mutanen nan sun hanasa barin wajen su, Hajiya kuwa tana tareda jikokin ta, Maryama kuwa su Fadila bazasu barta ta fita neman Sajida ba tunda sunsan da gangan ta taho ta bar Maryaman. "Kinyi shiru Miss Beauriful, nifa friendship kawai na tambayeki nothing more, ko shid'in bazan samu ba." cike da yaudara yake kalaman nasa. D'an murmushi tayi had'i da rufe fuska da tafukan hannu kafin tace "A'a ba haka bane, kawai dai I'm not comfortable ne tsayuwata da kai a nan don ban saba ba, kuma Daddy na na cikin hall yana iya fitowa any moment, idan ya ganni da kai a nan, he might be thinking otherwise. " Gyad'a kai yayi kafin yace "Na fahimce ki Miss Beauriful, yanzu bara na baki lambata tunda kince min bakida waya, idan kin sami hali sai ki kirani." yayi maganar had'i da bud'e backseat d'in sabuwar motarsa da Shema'u ta basa ya d'auko takarda da pen ya rubuta mata lambar ya mik'a mata. Karba tayi tana kallon takardan da murmushi a saman fuskar ta, ta d'ago ta dubeshi kafin tace "Wani suna zan saka maka, ko Buzu zan saka maka.?" ta k'arashe teasingly. Dariyar shima yayi kafin yace "Duk sunan da kika saka min is okay by me Miss Beauriful." Ganin AT ya mik'e yana masabaha da mutanen alamun sallama yake masu yasa Shema'u saurin ciro waya ta shiga neman layin Buzu. Ganin Shema'u ce mai kira yasa bai d'aga ba, sai duban Sajida yayi kana yace "Miss Beauriful Mumsy ta tana kira, ni zan wuce, sai naji daga gareki." Nan sukayi sallama cike da farin ciki, Sajida ji take kaman ta zuba ruwa a k'asa tasha sabida murna, kai gaba d'aya ta nemi bak'in cikin da take ciki ta rasa. Ganin ta tunk'aro k'ofa yasa Shema'u saurin fitowa ta nufi Sajida don ta jiyo AT na tambayan su Hajiya. "Sajee where have you been, munata neman ki a ciki daga ficewa freshing up.?" ta tambaya cike da nuna damuwa. Hannunta Sajida ta rik'e cike da farin ciki take fad'in "Aunty zan fad'a maki idan munje gida." Shema'u ta wani juya idanu kafin tace "Daughter da gani dai kina cikin farin ciki, oya mu k'arasa." A tare suka k'arasa cikin hall d'in, sai sann Sajida ta k'arasa ta gaida AT da Hajiya, Mai hoton da Shema'u ta kirane ya soma d'aukan su, Sajida ta rik'o hannun Shema'u tace "Aunty Family pic." Murmushin yak'e Shema'u tayi ta k'arasa gefen AT ta tsaya had'i da dafa kan Jamal, Sajida na d'aya gefen yayinda Ni'ima ke hannun AT. Koda akazo tafiya Hajiya cewa tayi su tafi abunsu zasu shiga tasi, don dama motar ba isan su zaiyi ba. Fir AT yak'i tafiya ya dage saidai ya kai su Hajiya da Maryama, Hajiya ma k'in aminta tayi tace "Ko don Ni'ima ai gwara ya kaisu, don dai ita da Maryama ne zasu shiga tasi. AT ya d'anyi Jim, rashin driver d'in nan ya soma damunsa, kai dole ma ya canza driver ya sama ma Hajiya standard. Wayar sa ya ciro a aljihu ya shiga neman layin Ashfaq. Yako yi sa'a Ashfaq na kusa da makarantar. Suna gama waya da Ashfaq ya k'araso rumfar dasu Hajiya da Maryama suke kafin ya sanar dasu, abokin aikin sa zaizo har nan ya d'auke su, yanzu zai k'araso. Hajiya ta amsa masa kafin tai masu a sauk'a lafiya. Suna wucewa ta tab'e baki, ina itama ina had'a hanya da wannan mai roba-robar fuskar, fuska uwa anyi b'arin hoda. Tsaki tayi had'i da kauda fuska. Maryama ta bita da kallo tana mamaki da dariyar halin Hajiya. *Sameena Aleeyou Mrs* [2:57PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *SHAK'UWA CE* 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *17* *漏Sameena Aleeyou...鉁嶐煆�* _馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_ *On Your Birthday, Today, I Wish You a Year With Loads Of Fun, Excitement and Beautiful Memories......馃帀馃帀馃帄馃帄 Happy Birthday K'awata Aysha Sada Machika..... This one's yours my commander ontop 馃拑馃徎馃挊馃槣* Wasu 'yan mata biyu Ashfaq ya tambaya ko sun san Maryama, akayi sa'a juniors d'insu ne masu shirin shiga aji shida nan sukayi directing Ashfaq har rumfar dasu Maryama suke. Mutuwar tsaye Ashfaq yayi yana duban Maryama dake k'ok'arin bubbud'e kyautukan ta Hajiya na hanata, tana fad'in ta bari sai sunje gida. Baisan dalili ba amma ganin wannan budurwa yasa shi tsananin fad'uwar gaba, gani yake tamkar ya tab'a ganin fuskar a wani wajen.... Saida Hajiya ta dubesa tsegeg ganin yanda yake bin Maryama da kallon k'urilla kafin tace "Malam lafiya dai koh, inji kai ba Maye bane don yanzu duniya babu yarda." Nan Hankalin Maryama ya dawo ga mutumin da Hajiya ke masa magana. Saurin saita kansa yayi kafin ya soma gaida Hajiya ya sanar da ita, shine wanda Dr Tahir ya turo don ya tafi dasu.. Hajiya dai dubansa kawai take, don taji Attahiru yace abokin aikinsa zai turo, toh wannan baiyi kama da likita ba sam, ya tara k'asumbi sannan da alama ba'a taje k'asumbin, duk sun dunk'ule waje guda, domin kuwa duk wanda zai bar k'asunbi yana gyarawa ba k'aramin kyau yake k'ara masa ba amma na wannan sam babu gyara,.. Tasan dai likitoci da tsafta da son gayu, wannan kam ba haka yake ba..... Jiyo muryar Maryama tayi suna gaisawa da mutumin... Cikin sauri Hajiya ta kaste su da fad'in "Kai wannan kai ba likita bane, yo likita ne zamu gansa haka babu gayu... Kai ko bature nan yaga likita ya bari wajen gayu..." Maryama sai tamke hannun Hajiya take tana mata magana k'asa-k'asa cewa tayi shiru amma Hajiya ta kasa, sai zuba take. "Kai wannan kai d'an yankan kai ne da ganin ka, ko kuma masu garkuwa da mutane kinafas (Kidnappers)...." "Hajiya don girman Allah kiyi shiru." Maryama ta fad'i cikeda b'acin rai. Shek'ek'e Hajiya ta dubeta kafin tayi magana Ashfaq yayi saurin fad'in "Em babu damuwa barin kira Dr d'in sai ya maku bayani...." Ya k'arashe maganar yana ciro waya a aljihun sa, Maryama kuwa takaicin Hajiya ya cikata fam. AT na d'aga wayar Ashfaq ya mik'a ma Maryama yace "Ga Dr d'in nan." Hajiya kuwa fad'i take "Ya daifi da mu shiga motan d'an yankan kai." Maryama kam mik'a ma Ashfaq wayar sa tayi bayan sun gama magana da AT, ta dubi Hajiya baki a ture kafin tace "Muje Hajiya, kar mu b'ata masa lokaci k'ila nada wurin zuwa." "Yo shi Attahirun yasan yanada wajen zuwa ya kira mana shi, ke nifa wannan sam bayada zubin likitoci..." Cike da takaici Maryama ta soma tafiya don tuni Ashfaq ya nufi yanda ya paka 'yar Henacy d'insa. Har suka iso gida Hajiya bata daina zuba ba. Maryama kam saida ta bari Hajiya ta shige ciki kafin ta dubi Ashfaq tace " Uncle Dr don Allah kayi hak'uri, wllhi haka Hajiya take, don Allah kayi hak'uri. And mun gode sosai." D'an murmushi yayi kafin yace "Haba dai ki daina bani hak'uri pls, ai Hajiya tayi gaskiya domin yanzu duniya babu yarda... Ganin tunanin ganin k'ok'on Kan Nabila da yayi a d'akin Daddyn sa na neman fad'o masa yasa sa saurin kauda zancen da fad'in "Kinga sunana ba uncle Dr ba, sunan Ashfaq, just call me Ashfaq." K'walalo ido waje Maryama tayi kafin tace "Toh ai kai abokin Uncle d'ina ne, kaga kaima ka zama Uncle d'ina." Murmushi ya kuma yi kafin yace "Ai Uncle d'inki Ya fini tsufa, amma tunda kince haka, ki kirani da Yaya Ashfaq." Murmushi itama tayi kafin tace "Shikenan, Yaya Ashfaq." Murmushi yayi kafin yayi congratulating d'inta, bata tsaya biyema surutun sa ba ta shige ciki don tasan yanzu Hajiya sai ta kawo wani zancen. Ashfaq kuwa kallo ya bita dashi har ta shige kafin ya shige cikin motar sa ya tada ya tafi. ************* Sosai aka k'awata gidan da decorations, Shema'u bata sama bata k'asa. Tsayin daka tayi a wajen ganin komai ya tafi dai-dai. Kai tsaye d'akin Sajida ta wuce yanda ta tarar Sajidar na shiryawa cikin sabuwar gown d'in da ta saya mata. "Wow my Daughter is now a young lady, Sajee kinga yanda kikayi kyau, son kowa k'in wanda ya rasa, Masha Allah d'iyata." Ta k'arashe maganar tana d'aura ma Sajida belt d'in dake tsakiyar rigar. Sajida ta rungumeta cikeda farin ciki, don yau wani dad'i takeji Buzu ya kusa zama mallakin ta. Rik'e hannun Shema'u tayi suka zauna saman couch dake d'an gefen wardrobe kafin ta soma fad'in "Aunty, hak'ik'a lokacin da Mummy ta rasu na d'auka shikenan bazan kuma samun gurbinta ba, sai gashi Allah Ya kawo mana ke, Aunty we can't repay you what you're doing for Us, you sacrifices alot for us, you prioritised our own happiness first, kin yi neglecting aikin ki duk a saboda mu, kin baro Home d'inki kin dawo namu duk don muji dad'i... Aunty kaman yanda kike son farin cikin mu nima ina son ganin ki cikin farin ciki, ina fatan wata rana nima nai maki abinda zakiji dad'i, cos good people like you deserve to be happy." ta k'arashe tana kallon cikin udanun Shema'u da tuni sun kawo k'walla. Saurin rungumeta Shema'u tayi tana k'ok'arin mayarda k'wallanta take fad'in "Sajida I'm not doing this to get something in return, abinda ya cancanta nakeyi, this is one of my obligations na kula daku, nayi guiding naku, yau idan Aysha ce take nan na mutu na bar yarana she would do the same ne, so pls ki daina min godiyar nan kinji Sajida." Ta k'arashe tana goge ragowar hawayen ta. Murmushi Sajida ma tayi tana goge k'wallan ta kafin tace "Hakane Aunty, still thank you for throwing me this special liyafa. Na gode. Shema'u ta murmusa kafin tace "K'arasa shirin ki, tunda Malam Habu yazo zaije ya d'auko Maryama." Zaro ido waje Sajida tayi kafin tace "Aunty are you inviting that social climber ne, no gaskiya I don't want her here." Murmushi Shema'u tayi kafin tace "Sajee let her be, nothing will change the fact that you're the real member of this family, as they say Blood is thicker than water, so kar ki damu, kiyi kaman yanda suke fad'i Kill the haters with kindness...." Jim dai Sajida tayi ba tareda tace komai ba, don idan akwai wacce tafi tsana a yanzu toh fah Maryama ce. Shema'u har ta kai k'ofa ta jiyo muryan Sajida ta ambato sunanta. D'an jiyowa tayi cikeda kulawa kafin tace "Akwai wani abinda kike so ne sweetheart.?" Sajida ta d'anyi still tana tunanin ta yaya zata soma tambayarta. Dafata Shema'u tayi kafin tace "Daughter I thought mun gama wannan maganar dake cewa duk abinda kike so ki fada min ko ki tambayeni without any hesitation." Murmushin samun k'arfin gwiwa Sajida tayi kafin tace "Aunty wayarki dama.... Zaki d'an ara min, I need to call a friend." Shema'u ta murmusa kafin tace "I thought wani babban abu ne, bara na d'auko maki na barta a d'aki. " Sajida say murna take, Shema'u kuwa tana isa d'akinta ta d'au wayar ta tayi dialing lambar Buzu, yana d'agawa ta sanar dashi Sajida zatayi amfani da wayarta yanzu, don haka karma ya zaci ita ce ya b'ata masu plans. Suna gama waya da Buzu tayi deleting lambar sa daga wayan, da duk wani kiran da sukayi. Saida ta tabbata babu duk wani abinda zaiyi linking nata da lambar Buzu kafin ta fice ta nufi d'akin Sajida. "Daughter here you go, ta fad'i sanda take dank'a mata wayar a hannu kafin tace tayi amfani dashi har lokacin data gama. Sosai Sajida ta ringa murna tanai mata godiya. ********** Shema'u tana fitowa daga d'akin Sajida ta shiga waige-waige, da sauri ta shige kitchen had'i da saka lock. Kallon Iya Kande tayi kafin tace "Iya Kande bana fah so a sami matsala, kinga idan wannan shegiyar matar ta bar gidan nan kema zakifi samun 'yanci tunda dukda ga kinan yaran nan da shegen kinibibi basu cin abincin kowa sai nata, Na tsaneta, zatabi sawun 'yarta yau su koma gidan wacce ta jajib'osu." Murmushi Iya Kande tayi kafin tace "Hajiyan sake hannu wllhi kina burgeni, bakiji yanda na tsani matar nan ba dama, wani felek'e take saikace ta had'a jini da Datta (Doctor) tak'i ta tsaya a matsayin mu duka na ma'aikata." Murmushi Shema'u tayi kafin tace "Ki kwantar da hankalin ki k'arshen ta a gidan nan ya zo, kawai ki tabbata kinyi yanda nace.Daga nan d'akin Momma dake faman had'a kayan tafiyar ta ta shige. Momma sai mitan ta tsani Maama Juu take, don daga window tana hango yanda su Jamal da Ni'ima suka kewayeta. Batada burin da ya wuce wannan matar ta fita daga rayuwar jikokin ta. Shema'u ta murmusa sanda ta dafa kafad'un Momma kana tace. "My Momma, just wait and see yanda zata tarkasa kayanta ta fice, I promise you before you leave sai kinga tafiyar ta....." Ta k'arashe tana wata kafiran murmushi... Momma ta bitada kallo tana tunanin me take shiryawa. Saidai kafin ta tambayi Shema'u tuni ta fice. Suna gama k'ulle-k'ullen su Shema'u ta fito ta nufi can filin gidan yanda su Mamaa Juu dasu Jamal suke, dama tuni ta aika Malam Habu ya d'auko Maryama. Irin fari'a da barkwancin da take ma Maama Juu sai ka rantse har cikin ranta ne. Cikin sauri dabara da sand'a Iya Kande ta bud'e d'akin marigayiya Aysha, wargaza d'akin ta ringayi tana barbaza kaya da drawers. D'an k'aramin kit d'in dake ajiye cikin wardrobe ta d'auko ta bud'e cikin sa'a kuwa saiga dank'areren sark'an gold d'in Aysha. Murmushi Iya Kande tayi kafin ta bar 'yar akwatin a bud'e ta kuma bar d'akin a hautsine yanda kana shigowa zaka gane anyi b'arna...... Malam Habu na ajiyeta Shema'u tayi saurin mik'ewa ta isa wajen Maryama tayi hugging nata tana fad'in "Oyoyo sannu da zuwa Maryam, and congratulations, ban samu na maki d'azu ba a can school d'inku, gaskiya kinyi k'ok'ari na yaba da k'wazonki sosai yanda kika amshi manyan kyaututtuka." D'an murmushi Maryama dai tayi zuciyarta cike da k'in aminta da kindness d'in Shema'u kafin tace "Na gode Aunty Shema'u, barin k'arasa wajen Sajida. " Don har alla-alla take su had'u da juna, zuciyar ta na bata SHAK'UWAR su bazata tab'a yankewa ba. Kaman daga sama ta jiyo muryar Shema'u tana fad'in "Aiko Sajida na cikin d'aki bata fitoba tukunna, inaji isowarki take jira..." Ai bata gama yin shiru ba, cikeda zumud'i Maryama ta nufi cikin gidan. Murmushi Shema'u tayi zuciyarta na mata dad'i... Ba tareda ta kawo komai ba ta ajiye handbag d'inta a parlor ta haye sama. Iya Kande dake mak'ale bayan k'ofa ta fito a sad'ad'e ta soma gudanar da aikin da Shema'u ta sakata.... Dai-dai shagon electronics ya paka motar sa ya nufi cikin shagon, nan ya ma masu shagon umarni da su basa waya guda biyu iri guda, haka aka ringa d'auko masa Android masu kyau yana dubawa. Yana gama zab'a ya umarci masu shagon su masa wrapping kwalayen wayoyin, hakan kuwa sukayi. Cikeda farin ciki ya nufi motar sa ya saka ledar a gefen mai zaman banza kafin ya soma tafiya. *Sameena Aleeyou Mrs* [2:57PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *SHAK'UWA CE* 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *18* *漏Sameena Aleeyou... 鉁嶐煆�* _馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 馃_ Jin ana k'wank'wasa mata k'ofa yasata saurin sallama da Buzu kafin ta katse kiran ta nufo k'ofa, duk a zatonta Aunty Shemah ce. Ganin Maryama ce yasata murtuk'e fuska tasa kai zata juya Maryama tayi saurin bin bayanta cikin d'akin.... "Da kin jirani a downstairs don yanzu zan sauk'o, shiryawa nake." Sajida ta fad'i sanda take k'arasa gaban dressing mirror tana gyara rigar ta. D'an fuzar da iska Maryama tayi kafin ta mik'e ta isa gaban Sajida ta zuba mata idanu tana karantar canzawar da tayi all of sudden. Dafata tayi kafin tace "Sajida pls let's talk sensibly, idan wani abin na maki ki fad'a min sai mu patching up koma menene, idan kuma akan maganar Buzu ne kiyi hak'uri, zan masa magana, I'll even introduce you to him kinji, amma don Allah kar mu bari shed'an ya datse SHAK'UWAR MU.." Dariyan takaici Sajida tayi kafin ta karkato tana dubanta kana tace "Au kin gama, toh bara kiji na fad'a maki, idan a baya kin sace zuciyata da munafurcin ki yanzu kan mage ta waye, nasan abinda nake Maryama, yanzu ne true color d'inki ya fito, ke bama computing kike dani ba, kai tsaye rayuwata kike son sacewa. First kin rabamu da Hajiyar mu, Hajiya ta fifita ki fiye damu jikokin ta, and now Daddy,... Shima kina nema ki rabamu dashi mu 'ya'yansa, his Flesh and Blood... Keko tsoron hakkin mutane bakiji, haba Maryama me na maki da tsanani haka..? Sannan maganar Buzu kuma ni ban aike ki ba, nima Mace nake, inada hanyoyin da zanyi winning heart d'insa.... So if you may excuse me ni zan sauk'a k'asa.." Baki sake Maryama ke binta da kallo, kai this is not the Sajida that she used to know , she's something else now, she's not herself , duk yanda akayi someone's been brainwashing her.... Wllhi wannan ba halin Sajida bane sam.... Kallo ta bita dashi don tuni ta nufo downstairs... Cak Sajida ta tsaya tana hango d'akin Mummyn ta da yake a bud'e, k'irjinta ya yanke ya fad'i... Shema'u dake lab'e k'asan staircase ta tsare Sajida da idanu tana kallon yanda ta k'ura ma idanu... Cike da kissa ta fito daga mab'oyarta tamkar daga waje take, ta nufo stirs tana fad'in "My Sajee hope all is well, ya kamata ku fito ina Maryamar gasu Fadila su Fauziya suna waje suna jiranku.... " Muryar Shema'u ya sark'e ganin Sajida tayi k'uri ma d'akin marigayiya Aisha dake hangame very messy... "Oh my goodness, meke faruwa.. Innalillahi, Sajida meyasa kika shiga d'akin mahaifiyar ki kika wargaza haka.." tayi maganar cikin tashin hankali tamkar gaskiya. Girgiza kai kawai Sajida take tana fad'in "Aunty bani bace, bansan waye ya shiga ba, shigowata d'aki na, k'ofar d'akin Mummy ba'a bud'e bane...." Cikin rud'ewa Shema'u ta soma doka salati tana tafe hannaye tana k'walla ma ma'aikata kira... Jin haka yasa Maryama dake tsaye har lokacin tana mai mamakin canzawar Sajida saurin fitowa ta nufo yanda suke tsaye carko-carko. Tuni su Momma dasu Iya Kande sun nufo wajen. Maama Juu kuwa dama tana waje tareda su Jamal. "Ke lafiya kike wannan doka salati haka.?" Momma dake kama staircase tana k'ok'arin k'arasa haurowa ta tambaya. Shema'u cike da rud'ewa take fad'in "Momma d'akin Sis ne, Momma we've been rubbed, Momma lek'a kiga d'akin Aysha na tabbata b'arayi ne suka shigo." Momma ta lek'a d'akin tana mai tafe hannuwa kafin ta maida dubanta ga Iya Kande tace "Kin shiga d'akin da sunan gyarawa ne..?" Iya Kande tayi saurin girgiza kai baki a tab'e tana mai tafa hannuwa take fad'in "Hajiya, ni Haramiya, me zaikaini d'akin Marigayiya da sunan gyara idanba umartata akayi ba tunda bata nan, saidai ko ta bakin *Hajiyan sake Hannu* (Shema'u) b'arayi ne suka shigo." Ta k'arashe tana lek'e-lek'e. Momma kuwa cikeda b'acin rai tace "Yo wani b'arawo ne zai shigo gida ko ta ina tsaro..." Cikin sauri ta shiga d'akin ta tarar k'aramar akwati 'yankunnayen Aysha a bud'e... D'aukan d'an kit tayi ta shiga tafe hannaye tana salallami. "Toh wllhi babu mai barin wajen nan sai na caje ku gaba d'aya, tunda babu wanda suka shigo nan sai ku." Ta k'arashe tana nuni da Maryama da Iya Kande.. Girgiza Kai Maryama ta shiga yi idanunta na k'ok'arin kawo ruwa take fad'in "Wllhi Momma bani bace, yanzu shigowata kuma kai tsaye d'akin Sajida na wuce.. Pls ki yarda dani bazan yi abu makamancin haka ba.." Tsaki Momma tayi ta fincikota ta shiga cajeta ta ko ina.... "Shema'u kuwa cikeda makirci take fad'in "Haba Momma let the girl be, bazata yi haka ba tunda tana tareda su da jimawa batayi ba.." "Ke dalla rufe min baki, tsintacciyar mage bata 'ya'ya, kika sani ko ta jima tana shirya hakan, yanzu dama ta samu tunda babu mai d'akin... Wllhi wllhi sai an caje kowa. Cikeda makirci Shema'u rai b'ace take duban Hajiya kana tace "Toh idan dai haka ne saidai nima ki caje ni.." Sajida kam downstairs ta nufa ganin ran Aunty Shema'u ma ya b'aci da abinda Momma keyi, tasan tana fushi da Maryama amma tasan bazata shiga d'akin Mummyn su tayi sata ba..... Nan Shema'u tabi bayanta tana kiran sunan ta. Momma kuwa bakin skirt d'in Maryama da bakim zanin Iya Kande ta kamo ta nufo k'asa tana fad'in "Wllhi duk wacce na sameta da tsinken Aysha cikin ku hukuma ce zata rabamu." Tuni hawaye ya wanke idanun Maryama, tunda take a rayuwarta ba'a tan's cin zarafinta kamar yau ba, sata, Allah Ya tsareta da d'aukan kayan wani... Babu yanda Shema'u da Sajida basuyi ba Momma ta bar maganan caje fir tak'i, k'arshe dai harda Shema'u aka caje.. Ba'a sami komai a jikin kowa ba.. Sajida ta d'an girgiza kai tace "Momma kin gani koh, ta yuwu buglers ne suka d'an hauro window..." Ta k'arashe maganar tana satan kallon Maryama dake goge hawaye ta d'auki jakarta ta rataya... Zata fice Momma tayi saurin jawota baya tace "Aiho ashe wannan jakar ki ce, toh ko baki isa tafiya ba sai an duba jakan nan..." AT sai sallama yake sam basu jisa ba.. Shema'u data hangi shigowar sa tayi saurin k'arasawa tana janye Maryama daga rik'on da Momma ta mata tana fad'in "Haba Momma duk fa kinyi searching d'inmu baki sami komai ba, this is not fair, pls ki k'yaleta.." Maryama kam sai kuka take tana fad'in wllhi bata d'au komai ba. AT ya k'arasa shigowa cikin parlorn sosai kafin ya bud'e murya yace " What's going on here..." Shema'u ta k'arasa gabansa da sauri cikeda makirci take fad'in "Thank goodness ka iso, inaji buglers ne suka hauro window sukayi b'arna a d'akin Sis, and Momma tak'i yarda ba d'aya daga cikin mu bane ta shiga d'akin, tayi searching namu bataga komai ba still bata yarda ba..." Katse ta Momma tayi da fad'in "Shema'u wllhi kinji na rantse sai na duba jakan yarinyar nan don ban yarda da ita ba, kuma ai ban duba jakar nata ba, da kike maganar ki dole na damu na cajeku tunda nima inada hakki a gadon d'iyata..." ta k'arashe tana huci. Sai sannan AT ya sauk'e idanunsa kan Maryama da tayi tsaye hawaye na bin k'uncin ta... Ji yake kaman ya rungumeta ya share mata hawayen ta sabida tsananin tausayin ta da ya lullub'esa. Tunda yake bai tab'a wani sa'insa da Momma ba amma yau kam har cikin k'ahon zuciyar sa yaji zafin abinda tayi ma Maryama. Cikeda b'acin rai yace "Momma pls ki sakar mata jakanta, babu wanda za'a k'ara cajewa.. Sakar mata jakarta ta, nasan Maryama wannan ba halinta bane... Sannan ko meye ya b'ace a d'akin Aysha zan biya, so pls banaso a sake d'aga wannan maganar." Zuciyar Shema'u kaman ta fashe sabida takaici ganin yanda AT yake defending Maryama. Girgiza kai Maryama tayi still tana hawaye kafin tace "Uncle pls ka bari ta duba jakan.." Kallonta yayi kafin yace "Maryam." Da sauri tace masa "Please." Bai kuma cewa komai ba sai wani mugun kallon da yake watsa ma Momma, babu kunya babu tsoron Allah Momma ta bud'e jakar ta shiga zazzagewa. Kaman daga sama sai kuwa ga sark'an zinaren Aysha ya fad'o daga cikin jakar. Iya Kande ta soma salati tana sallalami ta d'ago sark'ar tana fad'in "Wllhi ga sark'ar Marigayiya cikin jakar, Oh ni Kande..." Momma sai faman tafasa take tana huci fad'i take "Zan kira 'yansanda yanzun nan kuwa su rabamu dake, algunguma anammimiya b'arauniya." Shema'u da Sajida baki sake suke kallon ta, tsanar ta ya kuma shiga zuciyar Sajida. Maryama kam ta kasa fad'in komai sai girgiza kai kurum take da tsananin mamaki.. AT ya kasa motsawa daga yanda yake, ya tabbata wannan aikin Momma ne tunda dama ya kula bata son Maryama da Maama Juu... Har cikin b'argo da tsoka yake jin zogi da rad'ad'in abinda ya faru ga Maryama... Maama Juu dake tsaye bakin k'ofa ta gama ganin komai, goge hawayen da suka zubo mata tayi kafin ta k'arasa shigowa.... Da sauri Maryama ta tafi ta rungume Ummin ta..... Sosai Maama Juu ta rik'eta idanunta da suka kad'a sukayi jazur k'yam akan Momma... K'arasawa tayi gabanta kafin tace "Maryama ba b'arauniya bace, Maryama bata d'auka ba, na tabbata kece kika yi hakan, domin ki cimma burinki na ganin na fita daga rayuwar yaran gidan nan, ki sani duk iya makircin ki SHAK'UWA da soyayyar dake tsakanina dasu daga Allah ne, bazasu tab'a sonki kaman yanda suke sona ba, sannan idan zaki k'ala sharrin ki mani zaki k'ala ba d'iyata ba...." Huci Momma take tana jin zafin maganganun da Maama Juu ke watsa mata.. "Yo sai me, sata ne tayi kowa ya shaida bari ma ki gani wllhi 'yansanda zan kira su zasu rabani da wannan b'arauniyar.." Ta k'atashe tana k'ok'arin shafa wayar ta tana faman girgiza... AT gaba d'aya kansa ya kwance yama rasa wanne zaiyi... Tsakiya ya tsaya yana fad'in "Enough pls.." Parlorn yayi tsit sai kallon kallo da ake aika ma juna.... AT yaci gaba da fad'in "Momma ki daina maganar kiran police this is family issue...." Momma tayi saurin katsesa da fad'in "Waye family d'in, Allah fidda k'wad'o daga rogo...." AT ya dafe kansa hak'urinsa yana gab da k'arewa... Maama Jun ta rik'o hannun Maryama tace "Wuce mu tafi.." AT yayi saurin tsaresu yana bawa Maama Juu hak'uri.. Tak'aitaccen murmushi tayi kafin tace "Dr kayi hak'uri, ina son yaranka ina k'aunar su, amma ya zama dole na bar gidan nan sabida d'iyata..." Daga haka bata kuma sauraren AT ba ta fizgi hannun Maryama suka wuce zuciyarta na tafarfasa... Sajida tayi saurin rik'o hannun Maama Juu tana fad'in "Maama Juu tafiya zakiyi ki barmu, pls don't leave, don Allah ki tsaya, wllhi bazamu iya rayuwa babu ke ba..." Ta juyo tana watsa ma Momma mugun kallo kafin tace "Momma meyasa zakiyi haka, wllhi na tabbata kece kika saka a jakar Maryama, gashi kin jawo Maama Juu zata tafi, Kinyi searching har Aunty Shema'u hakan ya tabbatar min kece kika saka Momma just admit..." Haba nan fah Momma ta daburce, reshe ya juye da mujiya, gaba d'aya suka mata k'uri suna jiran amsar ta.. Kallon Shema'u Momma ta juya tanayi, Shema'u ta kauda kanta had'i da rik'o hannun Sajida. Inda-inda Momma ta soma ta rasa me zata ce.. Maama Juu kuwa girgiza kai tayi kafin tace "Kinji kunya Hajiya Kulu, daga haka janye hannun Maryama tayi suka fice cikin sauri.. Sajida ko sai bin Momma da mugun kallo take. Juyowa AT yayi yana watsa masu mugun kallo gaba d'ayansu kafin ya nufi Upstairs zuciyar sa na masa zogi, kaman zai kifa da k'asa. Liyafar da ba'ayiba kenan Sajida ta sallami k'awayenta. A d'aki Shema'u ta sami Momma sai faman huci take don kuwa babu wanda yabi bayanta harta Shema'u da take tunanin ita ta k'ulla wannan k'ulelliyar.. Mik'ewa tayi tana huci take fad'in "Me kike tunanin kinyi Shema'u, meyasa kika kasa bin bayata alhali kina gani kowa ya juyan baya, meyasa kika bari laifi ya dawo kaina.?" Murmushi Shema'u tayi kafin ta rik'o kafad'un Momma ta zaunar saman gado kafin tace "Relax Mom, and keep it down, someone might here you, abinda yasa nayi haka sabida ke kad'aice ya dace kiyi taking responsibility, nima bansan abin zai koma haka ba, amma koma an d'aura maki laifi ai kwalliya ta biya kud'in sabulu tunda buk'ata ta biya, we got rid of them... Sannan I'm only doing this ne for your grandchildren, kinga idan laifi ya dawo kaina AT da yaransa bazasu kuma aminta dani ba.... " Tayi wata murmushi kafin tace "Momma ta kar ki damu, ni ce fah I'll make it up to you... Inaji a jikina aurena da AT yazo..." Ta k'arashe maganar tana wata kafiran murmushi tana kallon Momma da tayi jigum tana sauraren d'iyar tata.. Chan k'asan zuciyar Shema'u kuwa fad'i take _Momma kenan kin d'auka bansan abinda kike b'oye min bane, nasan kinfi son Aysha kin fifitata akaina sabida itace 'yar halak while I'm the Bastard, oh my dear mother, if you flipping think you getting away with that damn crime of yours you're mistaken, I'll also make you pay... All of you must pay, Jikar ki d'iyar Aysha mafi soyuwa a gareki sai ta hafi shege itama,... Saikinyi nadamar haihuwata bata tsaftacecciyar hanya ba.._ Ta k'arashe tunanin nata tana murmusawa still kanta na dafe a kafad'an Momma... Mik'ewa tayi tace "Barin duba yaran nan.." Gyad'a mata kai kawai Momma tayi kafin ta fice. Parlorn AT ta lek'a nan ta hangesa yana zaune saman carpet, ga goran ruwa a gabansa da alama yayi nisa a duniyar tunani. Saida ta kintsa kanta ta gyara zaman rigarta da mayafin dake kafad'arta kafin tayi knocking had'i da sallama. ************ "Batan ubanchan... " Hajiya ta fad'i tana girgiza.... "Toh wllhi Kulu ta gama zamanta gidan Attahiru, wllhi yau sai anyita ta k'are..." Daga haka mayafinta ta fiza ta nufi waje... Maryama tana rik'ota tana kuka tana rok'onta kar taje, inaaa Hajiya ko saurarenta bata yi ba.. Ta dawo wajen Umminta tana fad'in "Ummi kin gani koh, wayasan abinda Hajiya zataje tayi pls Ummi kibi bayanta ki taro ta... Ko kulata Ummin ma batayi ba ta shige sashen su..... *Sameena Aleeyou Mrs* [2:58PM, 3/4/2018] 鈥�+234 703 300 1537鈥�: 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *SHAK'UWA CE* 馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊馃挊 *19* *漏Sameena Aleeyou... 鉁嶐煆�* _馃寛KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_ A tak'aice ya amsa mata sallaman nata ba tareda ya kuma cewa komai ba. Shema'u tasha jinin jikinta ganin sam babu walwala saman fuskar sa. A hankali ta soma takowa cikin parlorn. Can gefe ta nemi waje itama ta zauna. Sai lokacin AT ya d'ago ya mata kallo guda ya watsar. Murya a dake yace "Ina jinki, meke faruwa? " Shema'u ta d'an muskuta nan take tayi kalan tausayi kafin ta soma fad'in "Doctor regarding what happened earlier dan Allah kayi hak'uri, nasani Momma bata kyauta ba kuma nai mata magana na nuna mata illan yin hakan, don Allah kayi hak'uri Dr, and insha Allah zanje har gidan Hajiya na bawa Maama Juu da Maryama hak'uri." Ta k'arashe maganar kaman zatayi kuka. Baice komai ba sai kurb'an ruwan sanyin da ya kumayi, gaba d'aya ya kusan d'age babban goran Faro... Shi tunda suka zo masa gida abubuwa suka sauya, duk baisan tashin hankali ba sam sai yanzu. Gyad'a kansa yayi kafin yace "I hope zata tafi soon don bana so na rasa respect d'in da nake bata gaba d'aya, Sannan I care so much about Maryama and her mother, sunada matuk'ar mahimmanci a gareni, kin fahimta..?" Ya k'arashe yana mai firfito da idanunsa waje. Gaban Shema'u ya yanke ya fad'i, saida ta had'i miyau d'in bak'in ciki "muk'ud" tabbas an kawo peak d'in da hak'urin AT zai k'are, ka guji fushin miskili domin idan yayi abun baiyin kyau... Cikeda kissa taci gaba da fad'in "Eh dama jibi ne zata tafi idan Allah Ya kaimu...... " Shema'u bata kai aya ba suka jiyo muryar Hajiya tana doka sallama.. Ai daga ita har AT mik'ewa sukayi zunbur suka nufo downstairs... Hajiya sai huci take tana k'walla ma Hajiya Kulu kira tana fad'in ta fito.... AT ya k'araso da sauri yana tambayar Hajiya lafiya meke faruwa?.. Shek'ek'e Hajiya ta dubesa ta kuma duban Shema'u dake take masa baya kafin tace "Uwar matarka da wancan mai suffan karuwan nake so su bar gidan nan yanzun nan bada b'ata lokaci ba..." Kuka Shema'u ta fashe dashi ta durk'usa gaban Hajiya tana fad'in "Haba Hajiya, meyasa kika tsaneni haka, meyasa kike jifata da munan kalamai, karuwa fah Hajiya, ko me na maki ban cancanci ki kirani karuwa ba balle babu abinda nayi, burina shine faranta ran yaran 'yar uwata da ta tafi ta bari idan baku gode min ba kwabini da mugayen kalamai ba..." Hajiya ta Saki baki tana kallon salon makirci... Shi kuwa AT tausayin Shema'u ne ya rufesa, duk sai yaji babu dad'i, d'awainiyar da Shema'u keyi da yaransa yasa shi bata wani matsayi cikin zuciyar sa, don bazai tab'a mance wannan babban halarci data masa ba shida yaransa.. Saida Hajiya ta daka masa tsawa tana fad'in "Nace ka sallami Kulu da d'iyarta yanzun nan ko kuma kaga b'acin raina... Yara sunada masu rik'esu... Ta juya tana kallon Shema'u dake goge hawaye da bakin mayafinta kana tace "Bari ma kiji na shaida maki Attahiru uwa ta gari zai kawo masu cikin satin nan......" AT tamkar gunki haka yake duban Hajiya.... Dai-dai lokacin da Momma ta fito daga corridor d'in da zai sadaka da d'akin bak'i.... "Lafiya nike jin hayaniya haka na tashi..?" cewar Momma bayan ta k'arasa shigowa cikin parlorn sai wani pankan-pankan take.... Saida ta murmusa kafin ta dubi Hajiya tace "Hajiya Fad'ime mun wuni lafiya, da fatan b'arauniyar yarinyar can bata tab'a yasheki ba..." Ai batakai aya ba Hajiya ta k'araso gabanta sosai tana fad'in "Ke Kulu wllhi kinyi kad'an bokanki yayi kad'an, kece jinin tsiya amma Maryama kam tafi k'arfin ta d'au wani abu naki, ban mata wannan tarbiyar ba kuma zaman Juwaira daram a gidan nan ke baki isa ki rabata da yaran nan ba, SHAK'UWAR da Allah Ya riga ya had'a yafi k'arfin d'an mutum, nan gani nan bari, sannan abu na k'arshe shine awa guda bazaki sake yi cikin gidan nan ba, tunda shi Attahirun bakida gadonsa... Banda asara kin tattaro kin tare gidan surkin ki ke ko kunya bakiji, wllhi kinji jiki kuma kinji kunya....." Shewa Momma tayi kafin tace " Ko baki nemi na tafi ba zan tafi tunda na raba jikokina da wancan alak'ak'ai d'in, masu gadon tsiya marassa asali balle tushe...." AT ya dafe kansa yana karanto innalillahi.... Duban Shema'u dake faman share hawayen k'arya yayi murya can k'asa yace "Pls take Momma to her room." Da sauri Shema'u ta gyad'a masa kai kafin ta shiga janye Momma suka nufi d'aki. Allah yasa sauk'in abin yaran sun tafi islamiya. Hajiya bata daina balbala masifa ba tana fad'in "Wllhi Kulu sai kin bar gidan nan." "Hajiya don girman Allah kiyi shiru haka nan, don Allah kiyi hak'uri." AT ya katse ta da fad'in haka kafin ya nemi waje saman carpet ya zauna. Har lokacin dai bata daina huci ba, saman kujera ta zauna kafin ta dubesa da kyau tace "Attahiru, ka bud'e kunnuwanka da kyau ka saurari abinda zan fad'a maka. Ka zauna mata sai juyaka suke, inyi, waini yaushe ka zama lusari haka ne, toh wllhi idan kai asirin Kulu yayi tasiri akan ka ni baiyi ba, wllhi bata isa ba..." AT ya shafi goshinsa kafin yace "Hajiya please enough of this, give me break please..." Hannu ta d'aga masa alamun katsewa kafin tace "Um um karma ka soma min turancinkan nan da baka tashi yi sai ranka ya b'aci... Kaji na rantse maka ka gama zama babu mata, wllhi aure zakayi, bazan zauna inaji ina gani Kulu da d'iyarta su shanyeka ba ehe.." Ta k'arashe tana gyara zaman mayafinta. Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana, tabbas AT ya shiga tsaka mai wuya..... Gaba d'aya ya nemi kalma guda saman harshensa ya rasa, gaba d'aya kansa na neman kwacewa, abubuwa sun cakud'e a kwanyar sa... Bai ankara ba sai ganin Hajiya yayi ta mik'e tana gyara mayafinta kafin ta dubesa tace "Kadaiji abinda na fad'i maka Jumma'a mai zuwa d'aurin auren ka, ya rage maka ka samo matar cikin satin nan, idan baka samu ba ni zan sama maka..." Daga haka ta suri posanta dake ajiye saman sofa tayi ficewarta cikin sauri.... Tamkar wanda aka dasa haka yayi zaune a wajen. Shema'u da Momma dake lab'e a corridor kallon juna sukayi, tuni idanun Shema'u sun firfito waje, duk iya shegenta tana mugun shakkan Hajiya, amma tabbas Hajiya ta kawota iya wuya, tana gab da salwantar da rayuwar ta... Kallon Momma tayi tana girgiza kai tamkar tab'ebb'iya take fad'in "Momma aure zata masa, wllhi jarabebbiyar nan aure zata masa, Momma we need to do something bazan iya barin yaran 'yar uwata hannun kishiya ba, Momma pls we need to save your grandchildren,...." Gaba d'aya tamkar ta zare lokaci guda. Hannun Momma tasa da sauri ta toshe bakin Shema'u don kar a iya jiyota... A hankali cikin rad'a ta soma fad'in "Ki dubesa yanda yayi zaune, this your best chance, he really needs company, yana buk'atan wanda zai masa magana yaji sanyi, kar kiyi wasa da wannan damar, kinga dai ni tafiya zanyi, and dole na tabbata na barki akan yaran nan for good, kinsan sune farin ciki na... Shema'u na yarda dake I know you can do it, pls don't fail me... Oya kintsa kanki ki k'arasa garesa..." Ta shiga goge ma Shema'u hawayen ta tana gyara mata fuskarta, ita kuwa Shema'u sai gyad'a kai take tana zazzare idanu tamkar mai tab'in hankali... A hankali ta soma takowa cikin parlorn... Har ta zauna ta d'an gabansa baiyi noticing ba, gaba d'aya hankalin sa bai tareda shi.... Muryar Shema'u ya jiyo cikeda kissa tana fad'in "Damuwa bai cancanceka ba sannan bai kamace ka, kayi hak'uri sannan ka sani sam babu laifin Hajiya ko k'ank'ani, wannan duk laifin Momma ce, at times idan Momma tayi wani abin nakanji mamaki sosai, amma idan na tuna girma ya soma sauk'o mata sai na mata uzuri, shakka babu Hajiya ma harda girma a abubuwan da takeyi, AT kayi hak'uri, ka k'ara akan wanda kake Allah yana son masu hak'uri sannan sukeda nasara a rayuwa, watarana komai zai wuce ya zama sai labari... Sannan if you need someone to talk to kar ka mance that I'll be right here kaji..." D'ago kai yayi yana dubanta sosai, she sounds like Aysha, tabbas kalamanta sun d'anyi calming nasa... Bai iya ce mata komai ba sai gyad'a kai da yayi ya mik'e ya nufi sama. Shema'u ta bisa da kallo tana wata kafiran murmushi... Jim kad'an ya sauk'o da makullan motar sa.. Yasa kai zai fice daga parlorn Shema'u tayi saurin bin bayansa har tura k'ofar ya fice ya jiyo muryar ta tanai masa a dawo lafiya had'i da addu'an Allah Ya tsare.... Juyowa yayi ya dubeta kafin ya d'an murmusa yace "Na gode" a tak'aice.. Daga haka yayi saurin sa kai ya fice... Bayansa tabi da kallo tana mai cikeda jin dad'i ganin sam baya gwaleta, ita kad'ai ta dinga murmushi tana sak'a abubuwa da dama cikin zuciyar ta.... Iya Kande ta k'araso ta sameta nan tsaye tana washe baki take fad'in "Kai Hajiyan sake hannu, ina mai tabbatar maki keda Datta ba k'aramin dacewa zakuyi ba, dukanku farare sol-sol wanke hannu ka tab'a...." Shema'u tayi murmushin wanda yafi kama dana rainin hankali kafin ta dubi Iya Kande tace "Kande bari na tuna maki don kar ki mance,." Iya Kande tayi saurin gyad'a kai alamun toh. Shema'u ta murmusa tana dafa kafad'an Iya Kande kafin tace "Ba'a cin amanata idan na aminta da mutum don haka ki kiyaye..." Ta k'arashe maganar tana mai bud'e tafin hannun Iya Kande ta dunk'ula mata 'yan dubu-dubu guda uku.. Haba nan fah Iya Kande ta washe baki ta shiga kod'a Shema'u..... *************** Hisham I'm lost, I'm completely lost... I...i just don't know what to do anymore.. Wllhi bansan yaya zanyi da Hajiya ba bansan me zan fad'a mata ta fahimce ni ba.." Ya k'arashe zancen yana hura iska a bakinsa. Mik'ewa Hisham yayi daga saman sofan da yake zaune akai ya dawo gefen AT kafin ya dafa kafad'ansa yace "Tahir, you better take things easy, don't stress yourself, kabi komai a sannu, abokina nasanka nasan yanayin ka, wllhi nasha mamaki da naga ka zauna baka k'ara aure ba tun bayan mutuwar matarka tunda nasan kai ba bin matan banza kake ba, don I can still remember sanda muke sch azumi bai wuceka... Baka biye mana.." Ya k'arashe yana murmusawa. Gajeren tsaki AT yayi kafin yace "Tuzuru banza kak'i aure kak'i canza hali... Wllhi Hisham kaji tsoron kamuwar Allah. Ni bama wannan bane a gabana, I can hold myself, yarana sune min gaba da komai ka gane." Ya k'arashe maganar yana lank'washe 'yan yatsun hannunsa. "Okay fine naji, your children are your top priority, amma Tahir kayi auren mana kaman yanda Hajiya ta buk'ata, yin auren sai kaga ya kawo maka kwanciyar hankali da iyalanka, all this tashin hankula-hankula da kuke shiga sai kaga Allah Ya sauwak'e maka albarkacin auren." AT yayi shiru yana sauraren sa yana nazarin maganganun nasa, fuzar da iska ya kumayi ya shafi goshinsa kafin ya had'e tafukan hannayen sa waje guda yana mai duban Hisham yake fad'in "Toh Hisham wa zan aura for goodness sake, you're fully aware of banida macen da nake so a halin yanzu, and you know what the worse part is... Waifa Hajiya cewa take zata samomin matar, kaifa kaji saikace k'aramin yaro a shekarunan nan, yo banda abun Hajiya ko Rano taje ta samesu da batun zata min aure ai dariya zasu mata, kaman wani matashin saurayi..." Ya k'arashe yana girgiza kai. Hisham ya jinjina kai kafin yace "Eh toh nasan kanada masoya masu sonka amma kai baka sonsu, idan zaka daure ka zab'i d'aya daga cikin su fine, idan kuma ba haka ba toooh fah saidai ka karb'i zab'in Hajiya wanda I'm pretty sure gida zataje ta samo maka...." Ya d'anja fasali kafin yaci gaba da fad'in "Tahir auren magidanci kaman kai yana buk'atan lokaci sosai to think of wa zaka auro ka kawo kan iyalanka, it should someone da ka yarda da hankalinta, wacce bazata raba maka kan yaranka ba koda ace Allah Ya azurtaku da rabo kaida ita, sannan wacce zata so yaranka with all her heart, ita ya kamata ka auro ka kawo gidan ka..." Zuru AT yayi masa kafin ya shiga jinjina kai yace "Haka ne, you are right... Shiyasa banaso Hajiya ta kwaso min ko wace iri." Hisham ya murmusa kafin yace "Aaff, ina yarinyar can ta gaban Hajiya kodai ita ce ta ajiye maka...." Zaro idanu waje AT yayi yana dubansa kafin yace "wai Maryama kake nufi, amma bakada hankali Hisham, if not you are a therapist wllhi da na nemo maka therapist ya duba ka, Maryam, Maryam fah... K'aramar yarinya k'awar Sajida..." yayi murmushi kafin yace "You're insane Hisham this is ridiculous." Tak'aitaccen dariya Hisham yayi kafin yace "Tahir ka daina denying you care so much about her ko ba haka bane.?" "Yes I care so much about her, sabida tareda Sajida na rainesu, kai kasan da hakan... All I can say SHAK'UWA CE sosai tsakanina da ita ..... Waima ta yaya zakayi wannan maganar, ta ina ni AT zan soma batun aure tsakanina da Maryam, me na zamo... I wonder what's going on on that Skull of yours..." Ya k'arashe yana mik'ewa tsaye. Hisham ya murmusa don yaji abinda yake sonji kafin ya mik'e shima had'i da zura hannaye a aljihu sannan ya dubi AT yace "Doc ga shawari na k'arshe da zan baka." AT ya kallesa without saying a word. Hisham yaci gaba da fad'in "Shema'u is the perfect and right person for you...." *Sameena Aleeyou Mrs* [2:00PM, 3/12/2018] ‪+234 803 533 3121‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *19* *©Sameena Aleeyou... ✍🏽* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_ A tak'aice ya amsa mata sallaman nata ba tareda ya kuma cewa komai ba. Shema'u tasha jinin jikinta ganin sam babu walwala saman fuskar sa. A hankali ta soma takowa cikin parlorn. Can gefe ta nemi waje itama ta zauna. Sai lokacin AT ya d'ago ya mata kallo guda ya watsar. Murya a dake yace "Ina jinki, meke faruwa? " Shema'u ta d'an muskuta nan take tayi kalan tausayi kafin ta soma fad'in "Doctor regarding what happened earlier dan Allah kayi hak'uri, nasani Momma bata kyauta ba kuma nai mata magana na nuna mata illan yin hakan, don Allah kayi hak'uri Dr, and insha Allah zanje har gidan Hajiya na bawa Maama Juu da Maryama hak'uri." Ta k'arashe maganar kaman zatayi kuka. Baice komai ba sai kurb'an ruwan sanyin da ya kumayi, gaba d'aya ya kusan d'age babban goran Faro... Shi tunda suka zo masa gida abubuwa suka sauya, duk baisan tashin hankali ba sam sai yanzu. Gyad'a kansa yayi kafin yace "I hope zata tafi soon don bana so na rasa respect d'in da nake bata gaba d'aya, Sannan I care so much about Maryama and her mother, sunada matuk'ar mahimmanci a gareni, kin fahimta..?" Ya k'arashe yana mai firfito da idanunsa waje. Gaban Shema'u ya yanke ya fad'i, saida ta had'i miyau d'in bak'in ciki "muk'ud" tabbas an kawo peak d'in da hak'urin AT zai k'are, ka guji fushin miskili domin idan yayi abun baiyin kyau... Cikeda kissa taci gaba da fad'in "Eh dama jibi ne zata tafi idan Allah Ya kaimu...... " Shema'u bata kai aya ba suka jiyo muryar Hajiya tana doka sallama.. Ai daga ita har AT mik'ewa sukayi zunbur suka nufo downstairs... Hajiya sai huci take tana k'walla ma Hajiya Kulu kira tana fad'in ta fito.... AT ya k'araso da sauri yana tambayar Hajiya lafiya meke faruwa?.. Shek'ek'e Hajiya ta dubesa ta kuma duban Shema'u dake take masa baya kafin tace "Uwar matarka da wancan mai suffan karuwan nake so su bar gidan nan yanzun nan bada b'ata lokaci ba..." Kuka Shema'u ta fashe dashi ta durk'usa gaban Hajiya tana fad'in "Haba Hajiya, meyasa kika tsaneni haka, meyasa kike jifata da munan kalamai, karuwa fah Hajiya, ko me na maki ban cancanci ki kirani karuwa ba balle babu abinda nayi, burina shine faranta ran yaran 'yar uwata da ta tafi ta bari idan baku gode min ba kwabini da mugayen kalamai ba..." Hajiya ta Saki baki tana kallon salon makirci... Shi kuwa AT tausayin Shema'u ne ya rufesa, duk sai yaji babu dad'i, d'awainiyar da Shema'u keyi da yaransa yasa shi bata wani matsayi cikin zuciyar sa, don bazai tab'a mance wannan babban halarci data masa ba shida yaransa.. Saida Hajiya ta daka masa tsawa tana fad'in "Nace ka sallami Kulu da d'iyarta yanzun nan ko kuma kaga b'acin raina... Yara sunada masu rik'esu... Ta juya tana kallon Shema'u dake goge hawaye da bakin mayafinta kana tace "Bari ma kiji na shaida maki Attahiru uwa ta gari zai kawo masu cikin satin nan......" AT tamkar gunki haka yake duban Hajiya.... Dai-dai lokacin da Momma ta fito daga corridor d'in da zai sadaka da d'akin bak'i.... "Lafiya nike jin hayaniya haka na tashi..?" cewar Momma bayan ta k'arasa shigowa cikin parlorn sai wani pankan-pankan take.... Saida ta murmusa kafin ta dubi Hajiya tace "Hajiya Fad'ime mun wuni lafiya, da fatan b'arauniyar yarinyar can bata tab'a yasheki ba..." Ai batakai aya ba Hajiya ta k'araso gabanta sosai tana fad'in "Ke Kulu wllhi kinyi kad'an bokanki yayi kad'an, kece jinin tsiya amma Maryama kam tafi k'arfin ta d'au wani abu naki, ban mata wannan tarbiyar ba kuma zaman Juwaira daram a gidan nan ke baki isa ki rabata da yaran nan ba, SHAK'UWAR da Allah Ya riga ya had'a yafi k'arfin d'an mutum, nan gani nan bari, sannan abu na k'arshe shine awa guda bazaki sake yi cikin gidan nan ba, tunda shi Attahirun bakida gadonsa... Banda asara kin tattaro kin tare gidan surkin ki ke ko kunya bakiji, wllhi kinji jiki kuma kinji kunya....." Shewa Momma tayi kafin tace " Ko baki nemi na tafi ba zan tafi tunda na raba jikokina da wancan alak'ak'ai d'in, masu gadon tsiya marassa asali balle tushe...." AT ya dafe kansa yana karanto innalillahi.... Duban Shema'u dake faman share hawayen k'arya yayi murya can k'asa yace "Pls take Momma to her room." Da sauri Shema'u ta gyad'a masa kai kafin ta shiga janye Momma suka nufi d'aki. Allah yasa sauk'in abin yaran sun tafi islamiya. Hajiya bata daina balbala masifa ba tana fad'in "Wllhi Kulu sai kin bar gidan nan." "Hajiya don girman Allah kiyi shiru haka nan, don Allah kiyi hak'uri." AT ya katse ta da fad'in haka kafin ya nemi waje saman carpet ya zauna. Har lokacin dai bata daina huci ba, saman kujera ta zauna kafin ta dubesa da kyau tace "Attahiru, ka bud'e kunnuwanka da kyau ka saurari abinda zan fad'a maka. Ka zauna mata sai juyaka suke, inyi, waini yaushe ka zama lusari haka ne, toh wllhi idan kai asirin Kulu yayi tasiri akan ka ni baiyi ba, wllhi bata isa ba..." AT ya shafi goshinsa kafin yace "Hajiya please enough of this, give me break please..." Hannu ta d'aga masa alamun katsewa kafin tace "Um um karma ka soma min turancinkan nan da baka tashi yi sai ranka ya b'aci... Kaji na rantse maka ka gama zama babu mata, wllhi aure zakayi, bazan zauna inaji ina gani Kulu da d'iyarta su shanyeka ba ehe.." Ta k'arashe tana gyara zaman mayafinta. Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana, tabbas AT ya shiga tsaka mai wuya..... Gaba d'aya ya nemi kalma guda saman harshensa ya rasa, gaba d'aya kansa na neman kwacewa, abubuwa sun cakud'e a kwanyar sa... Bai ankara ba sai ganin Hajiya yayi ta mik'e tana gyara mayafinta kafin ta dubesa tace "Kadaiji abinda na fad'i maka Jumma'a mai zuwa d'aurin auren ka, ya rage maka ka samo matar cikin satin nan, idan baka samu ba ni zan sama maka..." Daga haka ta suri posanta dake ajiye saman sofa tayi ficewarta cikin sauri.... Tamkar wanda aka dasa haka yayi zaune a wajen. Shema'u da Momma dake lab'e a corridor kallon juna sukayi, tuni idanun Shema'u sun firfito waje, duk iya shegenta tana mugun shakkan Hajiya, amma tabbas Hajiya ta kawota iya wuya, tana gab da salwantar da rayuwar ta... Kallon Momma tayi tana girgiza kai tamkar tab'ebb'iya take fad'in "Momma aure zata masa, wllhi jarabebbiyar nan aure zata masa, Momma we need to do something bazan iya barin yaran 'yar uwata hannun kishiya ba, Momma pls we need to save your grandchildren,...." Gaba d'aya tamkar ta zare lokaci guda. Hannun Momma tasa da sauri ta toshe bakin Shema'u don kar a iya jiyota... A hankali cikin rad'a ta soma fad'in "Ki dubesa yanda yayi zaune, this your best chance, he really needs company, yana buk'atan wanda zai masa magana yaji sanyi, kar kiyi wasa da wannan damar, kinga dai ni tafiya zanyi, and dole na tabbata na barki akan yaran nan for good, kinsan sune farin ciki na... Shema'u na yarda dake I know you can do it, pls don't fail me... Oya kintsa kanki ki k'arasa garesa..." Ta shiga goge ma Shema'u hawayen ta tana gyara mata fuskarta, ita kuwa Shema'u sai gyad'a kai take tana zazzare idanu tamkar mai tab'in hankali... A hankali ta soma takowa cikin parlorn... Har ta zauna ta d'an gabansa baiyi noticing ba, gaba d'aya hankalin sa bai tareda shi.... Muryar Shema'u ya jiyo cikeda kissa tana fad'in "Damuwa bai cancanceka ba sannan bai kamace ka, kayi hak'uri sannan ka sani sam babu laifin Hajiya ko k'ank'ani, wannan duk laifin Momma ce, at times idan Momma tayi wani abin nakanji mamaki sosai, amma idan na tuna girma ya soma sauk'o mata sai na mata uzuri, shakka babu Hajiya ma harda girma a abubuwan da takeyi, AT kayi hak'uri, ka k'ara akan wanda kake Allah yana son masu hak'uri sannan sukeda nasara a rayuwa, watarana komai zai wuce ya zama sai labari... Sannan if you need someone to talk to kar ka mance that I'll be right here kaji..." D'ago kai yayi yana dubanta sosai, she sounds like Aysha, tabbas kalamanta sun d'anyi calming nasa... Bai iya ce mata komai ba sai gyad'a kai da yayi ya mik'e ya nufi sama. Shema'u ta bisa da kallo tana wata kafiran murmushi... Jim kad'an ya sauk'o da makullan motar sa.. Yasa kai zai fice daga parlorn Shema'u tayi saurin bin bayansa har tura k'ofar ya fice ya jiyo muryar ta tanai masa a dawo lafiya had'i da addu'an Allah Ya tsare.... Juyowa yayi ya dubeta kafin ya d'an murmusa yace "Na gode" a tak'aice.. Daga haka yayi saurin sa kai ya fice... Bayansa tabi da kallo tana mai cikeda jin dad'i ganin sam baya gwaleta, ita kad'ai ta dinga murmushi tana sak'a abubuwa da dama cikin zuciyar ta.... Iya Kande ta k'araso ta sameta nan tsaye tana washe baki take fad'in "Kai Hajiyan sake hannu, ina mai tabbatar maki keda Datta ba k'aramin dacewa zakuyi ba, dukanku farare sol-sol wanke hannu ka tab'a...." Shema'u tayi murmushin wanda yafi kama dana rainin hankali kafin ta dubi Iya Kande tace "Kande bari na tuna maki don kar ki mance,." Iya Kande tayi saurin gyad'a kai alamun toh. Shema'u ta murmusa tana dafa kafad'an Iya Kande kafin tace "Ba'a cin amanata idan na aminta da mutum don haka ki kiyaye..." Ta k'arashe maganar tana mai bud'e tafin hannun Iya Kande ta dunk'ula mata 'yan dubu-dubu guda uku.. Haba nan fah Iya Kande ta washe baki ta shiga kod'a Shema'u..... *************** Hisham I'm lost, I'm completely lost... I...i just don't know what to do anymore.. Wllhi bansan yaya zanyi da Hajiya ba bansan me zan fad'a mata ta fahimce ni ba.." Ya k'arashe zancen yana hura iska a bakinsa. Mik'ewa Hisham yayi daga saman sofan da yake zaune akai ya dawo gefen AT kafin ya dafa kafad'ansa yace "Tahir, you better take things easy, don't stress yourself, kabi komai a sannu, abokina nasanka nasan yanayin ka, wllhi nasha mamaki da naga ka zauna baka k'ara aure ba tun bayan mutuwar matarka tunda nasan kai ba bin matan banza kake ba, don I can still remember sanda muke sch azumi bai wuceka... Baka biye mana.." Ya k'arashe yana murmusawa. Gajeren tsaki AT yayi kafin yace "Tuzuru banza kak'i aure kak'i canza hali... Wllhi Hisham kaji tsoron kamuwar Allah. Ni bama wannan bane a gabana, I can hold myself, yarana sune min gaba da komai ka gane." Ya k'arashe maganar yana lank'washe 'yan yatsun hannunsa. "Okay fine naji, your children are your top priority, amma Tahir kayi auren mana kaman yanda Hajiya ta buk'ata, yin auren sai kaga ya kawo maka kwanciyar hankali da iyalanka, all this tashin hankula-hankula da kuke shiga sai kaga Allah Ya sauwak'e maka albarkacin auren." AT yayi shiru yana sauraren sa yana nazarin maganganun nasa, fuzar da iska ya kumayi ya shafi goshinsa kafin ya had'e tafukan hannayen sa waje guda yana mai duban Hisham yake fad'in "Toh Hisham wa zan aura for goodness sake, you're fully aware of banida macen da nake so a halin yanzu, and you know what the worse part is... Waifa Hajiya cewa take zata samomin matar, kaifa kaji saikace k'aramin yaro a shekarunan nan, yo banda abun Hajiya ko Rano taje ta samesu da batun zata min aure ai dariya zasu mata, kaman wani matashin saurayi..." Ya k'arashe yana girgiza kai. Hisham ya jinjina kai kafin yace "Eh toh nasan kanada masoya masu sonka amma kai baka sonsu, idan zaka daure ka zab'i d'aya daga cikin su fine, idan kuma ba haka ba toooh fah saidai ka karb'i zab'in Hajiya wanda I'm pretty sure gida zataje ta samo maka...." Ya d'anja fasali kafin yaci gaba da fad'in "Tahir auren magidanci kaman kai yana buk'atan lokaci sosai to think of wa zaka auro ka kawo kan iyalanka, it should someone da ka yarda da hankalinta, wacce bazata raba maka kan yaranka ba koda ace Allah Ya azurtaku da rabo kaida ita, sannan wacce zata so yaranka with all her heart, ita ya kamata ka auro ka kawo gidan ka..." Zuru AT yayi masa kafin ya shiga jinjina kai yace "Haka ne, you are right... Shiyasa banaso Hajiya ta kwaso min ko wace iri." Hisham ya murmusa kafin yace "Aaff, ina yarinyar can ta gaban Hajiya kodai ita ce ta ajiye maka...." Zaro idanu waje AT yayi yana dubansa kafin yace "wai Maryama kake nufi, amma bakada hankali Hisham, if not you are a therapist wllhi da na nemo maka therapist ya duba ka, Maryam, Maryam fah... K'aramar yarinya k'awar Sajida..." yayi murmushi kafin yace "You're insane Hisham this is ridiculous." Tak'aitaccen dariya Hisham yayi kafin yace "Tahir ka daina denying you care so much about her ko ba haka bane.?" "Yes I care so much about her, sabida tareda Sajida na rainesu, kai kasan da hakan... All I can say SHAK'UWA CE sosai tsakanina da ita ..... Waima ta yaya zakayi wannan maganar, ta ina ni AT zan soma batun aure tsakanina da Maryam, me na zamo... I wonder what's going on on that Skull of yours..." Ya k'arashe yana mik'ewa tsaye. Hisham ya murmusa don yaji abinda yake sonji kafin ya mik'e shima had'i da zura hannaye a aljihu sannan ya dubi AT yace "Doc ga shawari na k'arshe da zan baka." AT ya kallesa without saying a word. Hisham yaci gaba da fad'in "Shema'u is the perfect and right person for you...." *Sameena Aleeyou Mrs* [2:00PM, 3/12/2018] ‪+234 803 533 3121‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *20* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ "Adda Sajida fah kinsan Daddy yace munyi k'anan muke dawowa gida mu kad'ai, meyasa zakice mu tafi mu kad'ai. " Yayi maganar fuska a b'ace. Tsaki Sajida tayi kafin taja kunnensa tace "Kai wllhi bansan yaushe zaka girma ba, shekarar goma, goma fah Jamal amma bazaka iya kulada Ni'ima a hanya ba, nace maka Hadda zan tsaya badawa, wllhi saura naji wani zancen daban sai kaga abinda zan maka, oya rik'e hannunta ku tafi..." Ta k'arashe tana had'e hannayen su waje guda. Baki a ture Jamal yaja hannun Ni'ima suka soma tafiya, sauk'in abin isalmiyar a layin bayansu yake. Daga can yanda yayi parking ya toshe idanunsa da bak'in shades ya sauk'e tint glass d'in motarsa had'i da danna horn (pim pim) yana mai sakar mata murmushi. Murmushi itama tayi suna wuce ta k'arasa wajensa tana faman waige-waige. Front seat ya bud'e mata ta shiga kafin ya rufe, sai ka rantse babu kowa cikin motar, sai AC dake tashi da k'amshin turarruka. Sosai yayi kyau cikin red polo shirt da blue jeans, farin fatar sa har kashe idanu yake, yayi kyau har ya gaji. *********** Karkatowa AT yayi da kyau yana duban Hisham yanda yayi maganar da iyakacin gaskiyar sa. Tak'aitaccen murmushi yayi kafin yace "Wai kai meke damunka ne, Shema'u, Shema'u fah , yar Aysha fah.....Kai a ina ka tab'a ganin haka ta faru Ya ta auri mijin k'anwa, if to say ita ce k'anwar da sauk'i amma ta ina hakan zata fara kasancewa..." d'an jan fasali yayi kaman ya tuna wani abin kafin yaci gaba da fad'in "Waima tsaya! Ba kaine kwanaki kace min kana son ka nemi aurenta ba ka tuna.?" Ya k'arashe fuskar sa cikeda alamun tambaya. Murmushi Hisham yayi kafin ya dafa AT yace "Of course anyi haka, but Bro you need her morethan I do, kana buk'atan ta fiye dani Tahir. Shema'u 'yar uwar matar ka ce, she loves your Kids and na tabbata bazata tab'a hurting d'insu ba, think about it... Da kaje ka auro wacce bakasan yaya take ba ka kawo kan yaranka gwara wacce ka sani, kuma a iya zaman da tayi a gidanka na tabbata kana iya gane wacece ita.... Sannan ni bama sonta nake ba kadaisanni ne kawai da iya k'yalla idanu akan farar mace, bamuyi magana ba balle wani soyayya ya soma shiga tsakanin mu, AT koda ace nida ita are in a relationship me anfani na idan banyi sacrificing soyayyar ma kai ba, ka tuna ka min halacci da dama a rayuwa, ka wuce aboki a wajena kai d'an uwa ne and this is exactly what brothers are for.... Pls AT kar ka bari wannan DAMAR ya wuceka, do this for your children, wllhi idan na kalli Ni'ima babu Uwa ina tsananin tausayinta, AT ka auri 'yar uwan mahaifiyar su ko don inganta rayuwar su tunda dama sabida su d'in kake da buk'atan auren." Ya k'arashe fuskar sa fal damuwa sai ka rantse har cikin ransa iyakacin gaskiyar sa kenan. Shiru yayi yana nazarin kalaman Hisham kaman bazaice komai ba sai kuma ya d'ago yana dubansa kana yace "Na fahimce ka Hisham, but what if it turns out tana da wanda take so... Quite alright nasan Shema'u zata amince ta aureni koda bata sona sabida soyayyar da take ma yarana.... Amma Hisham gaskiya I don't want to be a burden to her sabida she already sacrifices alot, maganar da nake fad'a maka ina tunanin har ajiye aikinta tayi just to be with my children, kaga kuma nazo mata da batun aure alhali tanada plans d'inta maybe da wanda take so kaga ai abu baiyi ba gaskiya sam banason na zame mata nauyi ko na tak'urata.." Hisham kallonsa kawai yake yana tunanin da ace AT yasan rayukan da Shema'u ta d'auka duk don ta mallake sa ta kasance dashi da bai fara wannan tunanin ba. Murmusawa yayi kafin yace "Abokina give it a try, ka gwada ka gani, na tabbata ko don marayun nan Al'amran zasu tafi da sauk'i.." AT yayi shiru yana tunanin idan yajema Hajiya da wannan batu anya zasu kwashe lafiya..? Tabbas yasan da kaman wuya, amma he needs to think first. Sallama sukayi da Hisham don already an soma kiraye-kirayen sallan magrib kafin ya nufi gida. Jamal da Ni'ima ne rik'eda hannun juna suka shigo gidan. Shema'u dake zaune tana jiran dawowar AT tayi saurin k'arasawa ta rungumesu tana fad'in "Sannun ku da dawowa yarana, da fatan kunyi karatu sosai." ta k'arashe tana cire ma Ni'ima d'an k'aramin hijabin ta, had'i da amsar jakan Jamal. "Ina kuka baro Adda Sajee.?" ta tambaya tana kwab'e ma Ni'ima riga ya rage saura vest... Jamal baki a ture yace "ba cewa tayi wai malamin su zai karb'i hadda ba waima mu mu fara gaba, kumafa Aunty Allah 'yan ajinsu ma ina gani suna tafiya gida.." ya k'arashe yana cire 'yar hularsa... Shema'u tayi saurin jawosa ta shiga b'alle masa boturan rigarsa ta waiga gefe da gefe kafin tace "Amm my Boy, kar ka fad'a ma Daddy kaji nasan Addarku da gaske take, I'll take care of everything kaji koh, oya muje ku canza uniform..." ta k'arashe tana d'aukan Ni'ima tana fad'in "Baby na ta gaji..." Daga Ni'iman har Jamal tambayarta Maama Juu suka shigayi, Ni'ima tana fad'in ita wajen Maama Juu zataje ita zata mata wanka. Shema'u sai faman lallashin su take. ************ Tunanin maganganun da sukayi da Hisham shike faman yawo a kwanyar sa, a b'angare guda kuwa tunanin halin da Maryama take ciki a halin yanzu yake, yasan tabbas yau tasha kuka har ta gaji, take yaji zuciyar sa nai masa zafi da zogi, lokaci guda yaji yana son ganinta yana son sanin halin da take ciki, cikin sauri ya karya kan motar sa ya nufi gidan Hajiya. Isarsa ya samu har an shiga sallan Magrib a masallacin unguwar, don haka kai tsaye paka motar sa yayi ya wuce masallaci. ************* "Miss Beauriful dukda banga kwalliyarki na liyafarki ba naji dad'in sake ganin ki, and I hope zanci gaba da ganinki har k'arshen rayuwata." Yayi maganar fuskar sa dab da nata. Gaba d'aya jin abubuwa na tsarguwa a jikinta take, bata tab'a jin irin hakan ba, ga kyaun halittar sa na firgitata. Gyad'a masa kai tayi cikeda kunya kafin tace "Ni zan k'arasa gida kar Daddy ya dawo nasan zai nemeni, sannan Aunty Shemah ma bata san nida kai are seeing each other ba..." Buzu ya zaro fararen idonsa masu narkar da 'yanmata da manyan mata waje kafin yace "Haba Miss Beauriful, we ain't doing anything wrong right, gaskiya banji dad'i ba da baki sanar da Aunt d'inmu ba, at least idan ta sani yafi, this is legal banaso kina b'oye mata abu tunda babu Mummy.." Ya k'arashe in a serious tune. Cikeda jin dad'i Sajida ta gyad'a masa kai kafin tace "Insha Allah zan sanar da ita." Buzu ya murmursa kafin yace "Good hakan yayi, toh yanzu sai yaushe na sake ganinki Miss Beauriful.?" A shagwab'e yayi mata tambayar. Murmushi ta kumayi cikeda jin dad'i kafin tace "Gobe babu islamiya jibi ma babu sai weekend kenan, ko kuma idan nayi magana da Aunty na tasan da zaman ka zan iya nemanka a waya sai na sanar da kai.." Buzu ya kuma marairaice mata fuska kaman zaiyi kuka yana wani matso da jikinsa kusan seat d'inta kafin yace "Miss Beauriful bazan iya kwana biyu mai kyau ban ganki ba sai nayi ciwo, amma babu matsala ki sanar da Antyn namu things will be easier..." Ya k'arashe yana kasheta da mayen kallo.. Abunka da budurwa mai ji da tashen budurci da k'uruciya duk sai ta ringa jin wani irin feelings na fizgar ta. Gaba d'aya a tak'ure take, d'an d'ago idanu tayi ta dubesa kafin tace "Ni zan wuce gida kaga yanzu za'a fito daga sallah ina son na shige gida kafin a yi sallama nasan Daddy na masallaci." Buzu ya gyad'a mata kai kafin ya turo hannunsa daf da k'irjinta yana k'ok'arin bud'e mata marfin mota, wani irin abu taji yanai mata yawo a jiki dukda hannun nasa bai shafi jikinta ba. Abunka da tsohon d'an bariki sai karantar ta yake, tsaf ya lura yarinyar batada wayo, she's so naive and innocent, and babban weak point d'inta shine she fell for him completely, samun kanta bazai masa wuya ba sannan yasan duk abinda ya sata da wanda ya kwab'eta zatayi.... Koda sukayi sallama bai shige ba saida yaga ta karyi kwanan layin su kafin yaja motar sa ya bar wajen... ****************** A veranda ya samesu sun sallame sallar magrib, Hajiya na gefe tana lazimi Maryama kuwa Al'Qur'ani ne k'arama a hannunta da alama shigar da Hadda take. Jiyo sallamar sa da tayi yasata dasa aya ma karatun nata dukda dama ba da sauti takeyi ba, ta amsa masa sallamar kafin ta masa sannu da zuwa. Dukda hasken k'wan wuta ne ya haske masa fuskar tata hakan bai hanasa gano kumburi da idanunta sukayi ba alamun taci kuka. Samun kansa yayi da fad'uwan gaba mai tsanani, gaba d'aya ji yayi tausayinta ya rufesa, gaskiya ba don Momma ita ta haifi marigaiya Aysha ba da kuman yana ganin girman tsufa da yau d'in nan sai yanda k'arfinsa ya k'are wajen karb'a wa Maryama hakkinta. "Lafiya ka mana tsgege haka aka uwa bashi kazo amsa." Muryar Hajiya ya katse sa, gaba d'aya baisan ma yayi tsaye yana bin Maryama da kallo ba. Saita kansa yayi kafin ya janyo k'aramar kujeran zaman kitchen dake gefe ya zauna had'i da gaida Hajiya. A tak'aice ta amsa masa don shima a wuya take dashi. Maryama ta gaishe shi ya amsa har lokacin idanun sa na kanta, harta Hajiya saida ta lura da kallon da yake bin Maryama dashi dukda duhu da ya soma. Qur'an d'inta ta d'auka ta nad'e abin sallanta kafin ta shige parlour ta barsa shida Hajiya zaune a verandar. Hajiya ta kaste masa kallon nasa da fad'in "Meye kake binta da kallon k'urilla ko kaima baka yarda da ita bane, ko sharrin satan kaima zaka k'ulla mata inyi.?" cikeda fad'a tayi maganar. AT ya tura hular kansa baya kafin ya gyara zama yace "Hajiya don Allah kiyi hak'uri maganar nan ta wuce har abada, Momma zata tafi jibi-jibin nan insha Allah, kiyi hak'uri dan Allah." Tab'e baki tayi kafin tace "Ai ko kotu akaje Kulu ce batada gaskiya idan Alk'ali bai d'aureta ba zaici taranta sabida sharrin data k'ulla ma Maryama ta ehe..." Hajiya taso basa dariya jin harda batun zuwa kotu amma sai ya d'an dake don yasan dariyar sa ka iya zama wani chapter daban. "Hajiya me ya kawo batun zuwa kotu kuma, Momma ai me tafiya ce...." Dakatar dashi Hajiya tayi ta hanyar d'aga masa hannu kana tace " Dakata Attahiru, wai naji kanata cewa Kulu ce mai tafiya, ita kuma wancan mai roba-robar fuskar fa uwar me zata zauna tayi, ko d'akin k'anwartar ne zata shige inyi.?" Gaban AT ya yanke ya fad'i, k'ok'arin had'a kalmomi saman harshen sa ya soma yana fad'in "Amm dama Hajiya wai da zata d'an kuma zama da yaran....." "Rufe min baki banason ji, gaka uban 'yan son 'ya'ya ko, irinku ne masu d'auko rayuwar nasara ku d'ora yaranku akai , yaro sai abinda yaga dama zaiyi, da anyi magana kace gaka d'an boko ko, toh naji yayi kyau, halan ni haka kaga na tayar da kai ko?" Ta k'arashe tana rik'e da hab'arta. Kasa cewa komai yayi don bayaso aja maganar.... Karyar goronta tayi kafin tace "Nidai bazan daina maka addu'an Allah Ya warware asirin da Kulu da d'iyarta suka maka ba, ta kirkin cikinsu ta tafi abinta, Allah Ya tsare yaranta daga koyi da halin Kulu da d'iyarta.." Idan Hajiya tayi maganar an masa asirin nan sosai abin yake basa dariya da mamaki, bil hakk'i da gaskiya take fad'i abinta......Idonsa ya hangi tray na abinci ta cikin parlour. Hajiya ta bisa da kallo taga yanda idanunsa ke kalla. "A kawo maka abincin nan ne ko kuma zaka shiga kaci." Ta tambayesa tana mai mik'ewa tana k'ok'arin linke sallayar ta, saurin karb'an sallayar yayi ya linke mata kafin yace "Maryam ta kawo min nan, ta fito mun da darduma kawai, barin shiga na gaisa da Maama Juu." Hajiya ta jinjina kai kafin ta bisa da kallo har ya shige, ita sam wannan sanyin hali na Attahiru na bata mamaki, saikace ba ita ta haifesa ba, kodashike mahaifinsa Alh Shattima ya biyo.. Hajiya harda d'an murmusawa gamida goge k'walla an tuno tsohon soyayya.. Lol.... Sanda ya fito daga sashen Maama Juu ya samu har ta shimfid'a darduman, zama yayi bisa had'i da cire agogon hannun sa. Cikin tsanaki ta k'araso ta ajiye masa tray d'in sallama a saman bakinta. Tak'aiteccen murmushi yayi had'i da amsa mata sannan yayi mata sannu, don ya lura da rashin sakewanta gaba d'aya dashi. Zata mik'e taji ya kira sunanta da irin sigar da shi kad'ai ke kiranta dashi. *Sameena Aleeyou Mrs* [2:00PM, 3/12/2018] ‪+234 803 533 3121‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *21* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ *For my Avid Readers😍💘* *Kufah bar Shema'u ta shana ehe lokacinta ne 🤣 irin wannan zagi ai zaku karta kafin ran mutuwarta 😹🙆🏻‍♀* D'an kallonsa tayi gabanta ya yanke ya fad'i, cikin sauri ta sadda nata kan k'asa. "Zuba min abincin." ya fad'i idanunsa naga wayarsa. Bud'e flask d'in tayi ta d'au serving spoon da plate ta shiga serving nashi. Kallonta yake kanyi yanda take zuba abincin tamkar wacce k'wai ya fashe ma a ciki..... Saida ta gama kafin ta mik'a masa plate d'in tuwon shinkafa da miyar taushe cikin tsanaki. Ssannu ya mata kafin yaja plate d'in gabansa sosai.... Zata mik'e ta kuma jin ya kirawo sunanta. Murya can k'asa ta amsa masa. "Maryam, kiyi hak'uri kinji, nayima Momma magana insha Allah abu makamancin haka bazai kuma faruwa ba.." Gyad'a masa kai tayi had'i da k'ak'aro murmushi tace "Babu komai Uncle ai ya wuce." AT ya gyad'a kansa kafin yace "Me ya sameki a idonki, yana ciwo ne...?" yayi tambayar idanunsa naga plate yana juya spoon.. "Emm a'a babu komai..." "Are you sure.. " ya fad'i yana mai tsareta da idanu. Gyad'a masa kai ta kumayi alamun tabattarwa..... Sallaman da Ilu keyi ne ya katse su.. AT ya amsa murya a dake don sam baya wasa da Ilu. "Datta dama bak'on da ya kawo su Hajiya d'azun da rana ke sallama yace shi abokin aikin ka ne..." Ilu ya fad'i cikeda ladab. Kallon Maryama AT yayi kafin yace "Tashi ki shiga." ya dubi Ilu yace "Ce masa ya shigo." Ilu ya amsa da "An gama rankashidad'e.." Da sallama Ashfaq ya shigo hannunsa d'auke da shopping bag. AT ya amsa masa babu yabo babu fallasa kafin yace "Ah Dr bismillah, k'araso mana." Ashfaq ya fad'ad'a murmuahin sa ya k'araso yana fad'in "Ah Ya Doctor (haka yake kiran AT wani sa'in) ashe kana nan kenan.." ya k'arashe yana mik'a ma AT hannu sukayi masabaha had'i da gaidashi. AT ya amsa yana masa nuni da gefensa yace "Bismillah zauna mana bari a kawo maka plate..." Ashfaq ya d'an murmusa had'i sosa k'eyarsa kana yace "A'a na gode Ya Dr a k'oshe nake." AT ya jinjina kai sannan "Da fatan dai lafiya ko...?" ya k'arashe yana kai spoon bakinsa..... Ashfaq baikai ga basa amsa ba domin kuwa shi kansa baisan me zaice ma AT ba, Hajiya ta fito don taji kaman muryar AT da wani ne. Burki tayi tana kallonsa da kyau kafin tace "A'ah Keenafas (Kidnappers) ka kuma dawowa ne.." cewar Hajiya da ta masu tsaye aka.. "Keenafas" abinda AT ya nanata cikin zuciyar sa kenan. Ashfaq kuwa murmushi yayi kafin ya soma gaida Hajiya... Da fari'anta ta amsa masa don ta lura yaron sam bashida fushi tabbas zamansu zai zo dai-dai da Hajiya. Ajiye spoon d'in hannunsa yayi ya d'an dubi Hajiya kana yace "Hajiya sunansa fah Ashfaq naji kin kirasa da wani suna daban." cewar AT "Yo baka ga yanyinsa bane kaman keenafas masu garkuwa da mutane, ai d'azun k'in yarda dashi nayi, amma kaga gwara yanzu yayi fasali harda d'an gayu yayi ba kaman d'azun da rana ba.." Sosai abin ya bawa AT dariya, wai Keenafas, d'an girgiza kai yayi kafin yace "Hajiya sunan sa Ashfaq kuma abokin aiki na ne, shi ba kidnapper bane." "Yo na sani ai, keenafas maza taso ka shigo daga ciki a kawo maka naka abincin ciki." ta k'arashe tana komawa cikin parlorn. A ladabce Ashfaq ya amsa kafin yabi bayan Hajiya... AT ya bisa da kallo yana tunanin toh me ya kawo Ashfaq kuma.... Yana jiyo yanda Ashfaq da Hajiya suka sake sai hira suke kaman sun jima da sabawa da juna... Maryama ma ta fito daga uwar d'aki suka gaisa da Ashfaq tana mai shan mamakin yanda Hajiya ta sake dashi kaman ba ita bace d'azun ta sursurfa masa fad'a ba. Hajiya ta umarceta da ta kawo masa abinci, babu musu tayi yanda Hajiya tace.. AT sai binta da kallo yake sanda ta fito ta nufi kitchen, shifa sam bai aminta da zuwan Ashfaq ba, toh wata gulmar ta kawo sa bayan yayi abinda ya saka shi, b'angare na zuciyarsa ta shiga kokonton anya Ashfaq ba sawun Maryam ya biyo ba, take yaji gabansa ya yanke ya fad'i, gaba d'aya ji yayi ya kasa ci gaba da cin abincin, mik'ewa yayi ya d'auki wayoyin sa da agogon sa ya nufi cikin parlorn, don kuwa gwara ko menene yake tafe da Ashfaq ya fad'esa a gaban idanunsa.... ************* A hankali ta tura k'ofar d'akin tana mai d'an k'wank'wasawa da yatsun hannunta biyu kana tace "May I? " Sajida dake tsaye gaban wardrobe tana neman kayan sakawa saurin k'arasawa tayi ta rungume Shema'u kana tace "Aunty luv, I thought baki gida don d'azu nayi knocking a k'ofarki banjiki ba." Shema'u ta murmusa kafin tace "Ina nan sweetheart kawai dai fushi nake dake.." ta k'arashe fuskarta babu walwala. Idanun Sajida yayi rau-rau. "Aunty me ya faru, pls don't be mad at me." kaman zatayi kuka tayi maganar. Shema'u ta tsareta da udanu kafin tace "Ina kika tsaya bayan an tashi a islamiya, kindai san nace maki tsakaninmu babu secrets you're my daughter and my best friend, oya fad'a where 've you been..? " Sajida ta d'an muskuta kafin tace "Aunty wllhi dama I was about to tell you, kin tuna maganar Haris da mukayi." Shema'u ta gyad'a kai tana mai ci gaba da dubanta.. Sajida taci gaba da fad'in "Toooh dama shine muka had'u yau a school d'inmu shima yaje ma wata cousin d'insa, in short we're friends now.." ta k'arashe tana murmushi. Murmushin jin dad'i Shema'u tayi kafin tace "Sweetheart naji dad'i da kika zama opened dani, amma dai kinsan your Dad won't welcome the idea Haris ya zama friend d'inki, amma kar ki damu, kinsan nace maki you can always count on me, for now tunda kin sanar dani no need Daddy Ya sani, don idan ya sani zai iya rabashi dake, tunda shi bazai kawo ba wani abu maras kyau kukeyi ba, you know how Daddies are when it comes to their daughters, they're over protective gani suke kaman lalata masu yara za'ayi while idan ba'a bar yara sun d'ansha iska ba at this age of yours shine suke lalacewan, but ni nayi trusting d'inki sweetheart nasan bazakiyi wani abu maras kyau ba.." Sajida ta murmusa had'i da rik'o hannun Shema'u kana tace "Aunty Shemah na gode da yanda kike fahimta ta, sannan sunan uwa kawai na rasa, amma tabbas ke d'in kin maye min gurbinta, na gode k'warai.." Hugging d'inta Shema'u tayi fuska fal murmushi.. Nan Sajida ta fayyace ma Shema'u gaba d'aya yanda sukayi da Buzu, Shema'u kuwa sai biyeta take tana nuna mata zatayi guiding nata in everything. Magana Shema'u ta rad'a mata a kunne tana murmushi... Waro idanu waje Sajida tayi kafin tace "Aunty kinsan na mance gaba d'aya, toh cake fah ya zamuyi..." Shema'u ta murmusa kafin tace "Na riga na shirya komai sweetheart, tashi muje wajen su Jamal suna downstairs mu ci gaba da preparations, tsalle Sajida tayi suka rungume hannun juna itada Shema'u suka fice a tare. ************* Wayarsa yake kan faman shafawa amma hankalin sa naga Ashfaq da Hajiya dake faman zuba zance, shi kansa baisan Ashfaq ya iya surutu haka ba, sosai Ashfaq yaci tuwon kuwa, yana ci suna labari da Hajiya yana fad'a mata shi d'in d'an Katsina ne, iyayen sa da 'yan uwansa gaba d'aya suna can Katsinan, shine dai aiki ya kawosa garin Kano. Maryama dake d'aki tana jiyo hiran nasu nan gabanta ya yanke ya fad'i jin Ashfaq d'an Kastina ne, garin da Ummi ta fad'a mata asalinsu da tushen su kenan, garin da take mafarkin zuwa amma har yau Ummi sam bata son ko labarin garin ayi, Allah sarki ko don ta rasa kowa nata a zaizayan k'asan ne k'ila shiyasa sam bata so a d'ago mata zancen garin.. Maryama ta sauk'e ajiyan zuciya tana mai ci gaba da rayawa a ranta watarana insha Allahu zataje, wata k'ila ta sami sauran danginta tunda tasan tabbas baza'a rasa wasu ba koda wasu sun mace. Gaba d'aya AT ya gundura da hiran Ashfaq d'in, shi sam baida hayaniya, shafa wayarsa yake kan faman yi, nan yaga wata lamba ta whatsapp ana turo masa pictures.. Bud'ewa ya shiga yi yana murmushi, hotunan yaransa ne ga dukkan alamun cikin jin dad'i suke, shi kad'ai sai faman murmushi yake yana bud'e pics d'in, nan ya bud'e wani wanda suka d'auka harda Shema'u, wasu da funny faces abin sai ya basa dariya, sosai suka burgesa like a real family, k'asan pictures d'in ya bud'e wani message _Daddy pls come home soon, we've a surprise for you.... Sajee*_ Murmushi kawai ya kuma yi kafin ya koma yana sake kallon pics d'in. Kiraye-kirayen sallan isha aka soma, AT da Ashfaq suka mik'e suka nufi masallaci.. Nan Hajiya tasa Maryama ta tattara kwanukan da suka ci abincin, sosai Maryama tasha mamakin ganin AT bai wani ci abincin kirki ba, ita kanta ta gundura da Ashfaq ta lura akwai shi da zak'ewa, bacin haka miye nashi na dawowa bayan ya riga ya kawo su kaman yanda Uncle ya umarcesa.. Sanda suka shigo tana gaban socket tana had'a ma Hajiya chajin wayar ta. AT sai bin Ashfaq da kallo yake yanda yake faman satan kallon Maryama, shifa abun na Ashfaq ya soma damunsa, idan gaisuwa ne ya kawosa ya tafi mana tunda yayi.... Kaman Ashfaq yaji zancen zucin da AT keyi, nan ya mik'e ya jawo ledar da ya shigo dashi kafin ya rusuna ya mik'a ma Hajiya yace "Hajiya ga wannan na Maryama ne kyautar ta ta k'arashe makaranta..." Daga AT har Maryaman dake k'uryan d'aki saida k'irajensu suka buga, shi sai yanzu yama tuna wayoyin da ya sai masu itada Sajida a matsayin kyautar su. "A'ah keenafas harda wahala haka, ayya toh Maryama ta gode, kayya da baka tak'ura kanka ba." ta k'arashe tana bud'e jakar turarruka ne masu kyau da tsada had'i da bangles da sark'a ruwan silver, da gani sunada d'an kud'i.. Wannan kyauta da Ashfaq yayi ma Maryama har wuya ya kawo AT, banda iyayi ina ruwansa da ita da har zai mata kyautan kammala makaranta. Shi haushin Hajiya ma yaji data amshi kyautar. Hajiya kuwa ko a jikinta ta mik'e tana fad'in "Ayya keenafas, kayi hak'uri fah sunan naka ne ke bani wuyan fad'i, amma dai kar ka damu zan koya, bara na kira maka Maryam d'in tai maka godiya ko.." Maryama tana jin haka tayi saurin rufe idanunta kaman tana bacci, Hajiya ta fito tana fad'in "Oh Maryama sam bacci baya mata wahala, da zaran ta kishingid'a toh shikenan tayi bacci, idanba kallon shirin nan na Dad'in kowa wanda ake nunawa a Arewa tonti po zamuyi ba." AT har ransa yaji dad'in barcin da tayi. Ashfaq ya d'an murmusa had'i da shafa kai kana yace "Ai babu komai Hajiya, idan ta tashi ace mata na wuce, sai wani lokacin kuma." "A'ah keenafas kazo abinka ko yaushe ai nan gida ne, karkaji komai kaji koh..." Takaicin Hajiya ya cika AT, yasan Hajiya ba kasafai take yarda da mutane ba amma yasha mamakin yanda lokaci guda ta aminta da Ashfaq,... Ashfaq ya katse masa tunanin nasa da fad'in "Ya Dr ni zan wuce, Allah ya bamu alkhairi." Mik'ewa AT yayi yana zura wayarsa a aljihun gaban riga sannan yace "I'll walk you out.." Tare suka jera suka fito bayan Ashfaq da Hajiya sunyi sallama. Har wajen motar Ashfaq suka k'arasa, sosai Ashfaq ya sha jinin jikinsa ganin yanyin AT d'in. AT ya dafe jikin motar suna facing juna shida Ashfaq idanunsa naga wani b'angaren ya soma fad'in "Emm Ashfaq, you shouldn't have bothered buying presents for Maryam in the first place, amma tunda kayi, pls this should be the first and the last, banaso kai ko ita wani idea ya soma shiga kwanyar ku, kaga Maryama is still young, and kai kuma tamkar k'ani na d'auke ka, so pls banson wani abunda zai kawo mana sab'ani nida kai, pls ka kiyaye." Cikeda mamaki Ashfaq ke duban AT, d'an k'ak'aro murmushi yayi kafin yace "Insha Allah zan kiyaye Ya Dr, kayi hak'uri, inajin Maryam tamkar k'anwata ta jini ne shiyasa na kawo mata kyautan, amma insha Allah za'a kiyaye." AT ya gyad'a kansa kafin yace "Good, kana iya tafiya, I'll see you tomorrow...." Ashfaq ya kuma mik'a masa hannu sukayi masbaha had'i da sallama kafin ya wuce. K'uri AT yayima Hajiya tana bud'e kyautar tana fad'in "Ah'ah d'iyar tawa fah farin jini ne da ita, daga gama makarantar ta ta soma amsar kyaututtukan samari, wannan yaro da ganin toshi ya kawo..." Hajiya tana mik'ewa ya shiga tattara kayan rai b'ace.... "A'ah kai menene haka nan, ina zaka da kayan.?" ta tambaya tana k'arasowa. "Haba Hajiya, kan wani dalili zaki amsa kyautar sa, mayar masa zanyi don bata buk'ata, idanma da wani manufa ya kawo mata ba aure zatayi yanzu ba karatu za......" Fuzge ledar Hajiya tayi tana watsa masa mugun kallo sannan tace "Toh malgofak uban 'yan boko, wai kai lafiyan ka Attahiru, yo idan batayi aure ba zama zatata yi, wllhi ka bud'e kunnuwan ka da kyau kaji yau d'iyata ta sami mijin aure aurarta zanyi, ai da biyu na amshi kyautar, sarai naga yanayinka tun shigowar Ashafak baka so ba, Kai duk wanda ya nuna damuwarsa akan Maryama idan dai na miji ne saika nuna baka so, kaje ka k'araci son bokokon ka akan Sajida amma Maryama kam aure zan mata da zaran ta sami miji ehe, kuma yaron nan yaron arziki ne tunda duk kalan abinda na masa baiyi zuciya ba sannan na lura yanada hankali da ganin dattako..." AT ya d'an lashi leb'en bakinsa ka kafin yace "Hajiya rana guda fah tak kuka had'u shine har kin aminta dashi..." Bai kai aya ba ta jeho masa amsa "Eh na aminta dashi, tunda naga amintaceccen ka ne, idan da baka yarda dashi ba bazaka turosa ya kawo mu gida ba, kai Attahiru ka fita a idanu na fah tam..." Shafe goshinsa yayi kafin yace "Kiyi hak'uri, ni zan wuce..." ya fad'i yana mik'ewa tsaye. "Toh Allah shi bamu alkhairi, ka gaida min yaran sannan idan Allah ya kai mu gobe kazo min da batu mai dad'i kan maganar da mukayi d'azun." Saida gabansa ya yanke ya fad'i bai iya amsa mata ba sai sallaman da sukayi ya fice yana mai tunanin maganar Hajiyan. *Sameena Aleeyou Mrs* [2:00PM, 3/12/2018] ‪+234 803 533 3121‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *22* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ *Fatan Alkhairi Asma'u Galadima (Ummu Fatima) 💘* Mamaki ne ya isheshi jin babu mostin yaran ko kad'an sanda ya shigo parlorn k'asa, kai tsaye upstairs ya nufa parlorn sa na sama, hannu ya kai ya danna switch d'in wuta haske ya gauraye parlorn.... Sosai yasha mamakin ganin 'yan decorations a parlorn, harda cake a saman center table... A hankali ya taka ya isa har gaban table d'in yana murmushi... Suna nan lab'e bayan cottons a dinning area, Shema'u ta dubesu kafin tace "Now" Gaba d'aya mik'ewa sukayi suna fad'in "Surpriseeeee..." AT sai murmushi yake mai bayyana hak'wara... Suka k'araso suna fad'in "Happy Birthday Daddy." Pecking d'insu ya ringayi a kumatu yana fad'in ya gode, Shema'u ma sai k'wark'wasa take tana fad'in "Happy Birthday Doctor, murmushi ya sakar mata had'i da mata godiya. Ya dubesu gaba d'aya kafin yace "I thought kun manta yau birthday na graduation d'in Sajida ya mantar daku." Sajida ta murmusa kafin tace "Daddy Aunty Shema'u ce ta tuna mana..." AT ya d'an saci kallon Shema'u cikeda mamaki ya akayi tasan birthday d'insa, murmushin yak'e kawai yayi kafin yace "And who's responsible for the cake..?" Sajida ta kuma kamo hannunsa kafin tace "Aunty Shemah ce Daddy, kaga cake d'in yayi kyau.." Nan ma murmushin yak'e yayi had'i da duban Shema'u daketa faman juya idanu.... Kan ya sami zarafin magana su Jamal suka soma jansa suna fad'in a yanka cake d'in zasu ci... Duk yanda AT yaso yayi dodging yaran sun hanasa, haka yayita biyesu ba don yaso ba.... Shema'u harda masu pictures, Sajida ta jawo hannunta itama ta shiga suka d'au selfie, shiko AT gaba d'aya jinsa yake ba'a sake ba, quite alright yasan babu d'igon soyayyar Shema'u cikin zuciyarsa amma Allah Ya jarabce sa da tsananin sha'awarta... Haka dai k'arshe ya zame ya nufi d'akinsa ya barsu sai hayaniyar su suke, can jimawa ya jiyo muryar Shema'u tana fad'in su shiga suyi ma Daddy goodnight is getting late... Abun ya burgesa jin har tsarin kwanciya tana masu kaman yanda Aysha ke masu, dama sam baison rashin kwanciyar yara da wuri koda babu school... Shema'u ta shiga tattara wajen gaba d'aya Sajida na taya ta, saida sukayi tas-tas da parlorn, Sajida ta d'au sauran cake d'in ta nufi kitchen dashi.... Ledan wayoyin su Sajida da Maryama ya hanga yanda ya ajiye, nan ya suri ledan ya fito parlorn da niyyan bama Sajida nata nan suka kusan karo da Shema'u da shigowarta kenan. D'an ja da baya tayi tana wani mad'e da rausaya ta shiga basa hak'uri tana fad'in bata san na zuwa bane. K'ak'aro murmushi shima yayi sannan yace "No babu komai, ya juya ya shiga kalle-kallen cikin parlorn nasa kafin yace "Kin manta wani abu ne.?" Murmushi Shema'u tayi cikeda kissa kafin ta d'ago paper bag d'in hannunta ta mik'a masa kana tace "Na manta ne ban baka wannan ba." AT yabi d'an jakan da kallo kafin ya murmusa yana mai girgiza kai yace "What's that...?" Ta kuma murmusawa cikeda rausaya kafin tace "Ka duba da kanka." D'an tab'e baki yayi had'i da d'age giransa sama kafin ya ajiye ledar dake hannunsa saman sofa ya amshi paper bag d'in hannun Shema'u, hannu yasa ya ciro abinda ke ciki.. Wata arniyan *Armani Shirt* ne gray color wanda ak'alla zaikai dubu goma an rubuta Armani a gaban rigar da rubutu ruwan madara. AT yabi rigar da kallo sannan ya kalli Shema'u. "It's your birthday gift." ta fad'i ganin irin kallon da ya mata, taci gaba da fad'in "Na tabbata da Aysha tana nan zata baka gift, toh wannan ma ita nayi, kasa a ranka wannan kyautar Aysha ne." D'an jim AT yayi kafin yace "look Shema'u, you shouldn't have bothered, duk wad'anan d'awainiyar da bakiyisu, it's not necessary.." D'an b'ata fuska tayi idanunta naga ledan da ya ajiye saman sofa kafin tace "Banyi da wani manufa ba sai don faranta maka kaida yaranka, especially the kids, nasan zasuji dad'i shiyasa nayi, and the gift, it should be rude idan kak'i karb'a... Amma babu komai, kayi hak'uri idan bakaji dad'i ba inaso wannan family ta kasance cikin jin dad'i ne da farin ciki shiyasa.." ta k'arashe tana k'ok'arin juyawa. Duk sai yaji babu dad'i, bud'e murya ya d'anyi ya kirawo sunanta, nan ta tsaya cak had'i da jiyowa. AT ya d'an shafi goshin sa kafin yace "Kiyi hak'uri, and thanks for the gift..." ya k'arashe with a smile on his face. Murmushi itama tayi kafin ta d'auki ledan da ya ajiye saman sofa tana juyawa take fad'in "Saidai kuma kak'i karb'an kyauta ta sabida wannan, da alama someone special ne ta kawo maka kasan kai d'in yanzu bazauri ne.." ta k'arashe teasingly. Tak'aitaccen dariya yayi wanda yafi kaman da murmushi donko dariyar nashi baida sauti kana yace "Kema kika ce bazauri, wa zata damu ta kawo ma bazauri gift, wannan kyautar Sajida da Maryama ne na kammala karatun sakandare d'insu." Wani dad'i ya lullub'e Shema'u, tana murmushi take jujjuya kwalin da shike anyi wrapping nasu, d'an girgizawa tayi tana son sanin menen a ciki. Murmushi AT yayi kafin yace "Someone's curious..." Ta murmusa had'i da ajiyewa kafin tace "Kawai dai so nake nasan menen kyautar d'iyata." "Tohm kiyi guessing.." ya fad'i yana k'arasawa jikin TV ya kunna socket had'i da d'aukan remote kafin ya zauna a 3seater. Zama tayi bisa armchair tana fad'in "I guess jewelries ne." AT ya murmusa idanunsa naga TV yana canza tasha yace "Baki canka dai-dai ba, idan kin bada gari a fad'a maki,.. Wani smile d'in jin dad'i tayi kafin tace "Gaskiya na bada gari." Ya kuma murmusawa kafin yace " Toh tunda kin bada gari cellphone ne." Take annurin fuskar Shema'u ya d'auke, sam bataso ya bawa Sajida freedom ai plans d'inta zasu tarwatse.... D'an gyara zama tayi kafin tace "Cellphone Dr, gaskiya a ganina is too early Sajee da Maryama su mallaki waya, a ganina instead da Laptop ka saya masu da zaman banza da zasuyi na jiran results sai su shiga computer school, kasan wannan zamani namu wllhi waya itace ummul haba'isin lalata tarbiyan yara, 90% wayace ta lalata su, ni dai gaskiya ban aminta d'iyata ta rik'e waya babba kaman wannan at her age ba, makarantar kawai ta gama da wuri amma har yanzu yarinya ce mallakan waya irin wannan ka iya haifar mata da wani tunani, pls Dr ka duba lamarin." Shiru AT yayi yana nazarin kalaman Shema'u, tabbas da computers ya saya masu da sai yafi masu amfani, kuma tunda yaga Ashfaq ya soma kawo hari ma Maryama mallakan waya zaisa maza su ci gaba da kawo mata hari... Toh waima meyasa baiso wani yayi tarraya da ita, yayi ma kansa wannan tambayar, zuciyarsa ta shiga raya masa ai har yanzu ita d'in yarinya ce... Kallon Shema'u yayi ya jinjina kai kafin yace "You're right, banyi wannan tunanin ba, laptop shine dai-dai kyautarsu sannan zan saka su a computer school d'in, na gode da wannan shawari naki." Murmushi kawai Shema'u keyi zuciyarta fari k'al "Babu komai Dr, you can always count on me a duk wani abu da ya shafi yaranka tunda nima yarana ne.." ta k'arashe tana mai mik'ewa kafin tai masa saida safe... Jigum AT yayi tsananin buk'atar Shema'u na fizgarsa, dad'i da k'ari nuna kulawanta a lamran yaransa sosai yake burgesa, hiransu da Hisham ya shiga yawo a kwanyar sa. Tana shiga d'akinta tsalle tayi ta haye kan gado kafin ta jawo wayarta ta shiga neman layin Hisham. Bugu biyu ya d'aga kaman wanda yake jiran kiran nata. "My allied ya akayi." ya fad'i daga d'aya b'angaren. Dariya Shema'u ta tuntsire dashi kafin tace "Komai na tafiya perfect yanda na tsara kuma nake so, Hisham thanks for your help..." Hisham ya murmusa kafin yace "Aidai kinsan godiyar da ya kamata ki min, so I'll expecting you gobe.." K'asaitaccen murmushi tayi kafin tace " Sai mun had'u uban 'yan jaraba." Hisham ya murmusa kafin yace "A bayanki nake ina tausayin AT randa aka kai masa ke a matsayin amarya inaga ranar sai ya had'a da powerhose.." Gaba d'aya dagashi har ita dariya sukayi..." ************** Washe gari AT daga Clinic shagon electronics d'in ya wuce yanda aka canza masa wayoyin da laptop Hp masu kyau na yayi... Kai tsaye gidan Hajiya ya nufa alla-alla yake ya bawa Maryama kyautar ta... Ai kuwa sosai tayi murna da kyautar, Hajiya ma sosai taji dad'in kyautar AT d'in, nan kuma yake sanar da Hajiya zai saka su a makarantar koyon computer ita Maryam d'in da Sajidar kafin jarabawar su ta fito, Hajiya tayi na'am da hakan. Maryama ma taji dad'i sosai tai masa godiya, cikeda zumud'i ta kinkimi laptop d'in ta wuce sashen Maama Juu don ta nuna mata.. Tahir ya bita da kallo har ta shige yanda taketa murna, sosai zuciyarsa tayi sanyin ganinta cikin farin ciki, gyara zamansa yayi da kyau ya dubi Hajiya kafin yace "Hajiya dama akwai maganar da nake so muyi gameda maganar aure da kika min jiya." Hajiya ta washe baki tace "Kai Masha Allah, yau dai Attahiru ka faranta min rai, kai naji dad'i sosai, asirin Kulu da d'iyarta Allah Ya warware maka, toh wacece surkan tawa kuma a ina take..?" Dummm! K'irjin AT ya buga yana tunanin yanda zasu kwashe da Hajiya.. Daurewa yayi ya soma magana domin kuwa bashida zab'in da ya wuce ya sanar da Hajiya dukda baiji ta bakin ita kanta Shema'un ba... "Kai nake saurare Attahiru." muryar Hajiya ya katse sa. "Dama... Dama Shema'u ce nake tunanin ko zan nemi aurenta tunda naga yaran suna k'aunar ta kuma....... 'yaruwan mahaifiyar....... " Bai kai aya ba Hajiya dake faman huci tana jin zancen nasa kaman sauk'an aradu ta dakatar dashi da fad'in "Rufe min baki shanyayye kawai, yo ko mata sun k'are a duniya zan barka ka auri wannan zabon ce, kod'add'iyar da ta gama gantalinta a titi, Attahiru anya basu juya maka kwanya ba..." Ta shiga tafe hannaye tana sallallami... Maryama da ke tsaye k'ofa k'arasowarta kenan batasan lokacin da hawaye suka shiga zarya a kumatunta ba.. *Sameena Aleeyou Mrs* [2:00PM, 3/12/2018] ‪+234 803 533 3121‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *23* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ Ta yanda take shiga bata nan take fita ba, sai faman huci kurum take tana salle AT. "Inyin, don ka rasa mafad'i a doron k'asa sai na zuba maka idanu ka auri sauran titi, wannan da k'yar idan aka aunata ba'a sameta da cutan zamani ba, banda jaraba irinta d'anamiji har uwan me ka hanga a jikinta kaji ta maye gurbin Aysha, inyi. ...." AT ya d'ago idanu cikeda mamaki yana dubanta, harga Allah halin Hajiya ya soma isan sa, yaya tana mahaifiyar sa zatake fad'an maganganu haka, shi ko nauyin 'ya'yan fari da manya keyi da yaransu sam Hajiya batayi dashi, k'ila don bashida k'anne ne shiyasa take yin hakan... Muryarta ya kuma dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi.. "Tashi, tashi ka fice min daga gida nace, shanyeyye kawai, idan da batun da zaka zo min kenan kar na kuma ganin sawayenka a gida na..." ta k'arashe tana sauk'e labulen k'ofa da k'arfin gaske. Daga yanda take tsaye hawaye sharkaf a k'uncinta, tausayin sa ya cikata ganin ya fito jikinsa babu laka.... Saurin juyawa tayi a tunaninta AT bai ganta ba... Shi d'inma bai iya tab'uka komai ba sai kallo da ya bi bayanta dashi har ta shige... Da k'yar yaci gaba da d'aga k'afafunsa har ya isa yanda motar sa take... Driving kawai yake amma harga Allah baijin yanada buk'atar wata mace bayan Shema'u baisan dalilin ko don ita 'yar uwar Aysha bace yake jin wannan feelings d'in a game da ita ba oho, all he knows shi ne yana tsananin buk'atar Shema'u abin har mamaki yake basa... Da haka ya isa gida ana kiraye-kirayen sallan La'asar... A can wajen swing ya hangesu gaba d'aya suna zazzaune su Momma dasu Shema'u da Sajida suna saman grass carpet suna hiran tafiyar Momma da zatayi a gobe, yayinda Jamal da Ni'ima ke saman lilon.. Idanunsa k'yam akan Shema'u, take ya soma karanto addu'o'in tsari daga shed'an ya nufi cikin gida, gaba d'ayansu babu wanda ya kula da dawowar sa don ko k'aran bud'e gate basuji ba dashike ana tonon borehole a mak'otansu. Tunanin abubuwa da dama suke yawo a kwanyar sa, hawayen da ya gani kwance fuskar Maryam shi ya hanasa kwanciyar hankali, yana son tambayarta meke damunta, yana son sanin halin da take ciki, toh waima me yasata kuka..? Wata zuciya ta basa amsa da _Fad'an da Hajiya tayi maka ne.._ A hankali ya lumshe idanunsa abubuwa da dama suka cigaba da yawo a kwanyar sa... Kotakan sabon laptop d'in nata bata bi ba, itakam sam bataso Uncle ya auri Aunty Shema'u, idan ya aureta shikenan bazata daina ganinta ba har abada, sam zuciyarta bata son Aunty Shema'u da Momma ta tabbata Aunty Shema'u is playing innocent ne, jikinta na bata she's wicked ba son yaran Uncle take ba, meyasa Uncle zaice yana son aurenta.... Wani sabon hawaye ya kuma wanke mata fuska, jin Hajiya ta bud'e labule ta shigo tana mai ci gaba da sababi don har lokacin bata daina sababi ba, tuni Maryama ta lumshe idanunta tamkar mai barci.. ***************** *Abuja, birnin tarayya* Misalin k'arfe 3:00am Vice president ya shigo gidan, idan da sabo Hajiya Maryam ta saba wani sa'in mijin nata a wajen meeting yake kwana. Yasha mamakin ganinta yau idanunta biyu batayi bacci ba, da murmushi saman fuskar sa ya k'araso ya zauna gefenta had'i da kwab'e babbar rigar sa... Ganin bata kulasa ba yasa shi kamo 'yan yastun hannunta yace "Ayimin hak'uri Maryama kinsan yanayin aikin nawa da kuma hidima da jama'a ga election na k'aratowa bama so mu rasa muk'anman mu.." Hannu tasa ta goge hawayen da suka zubo mata kafin ta soma fad'in "Ni jimawanka a waje sam baya damuna tunda idan da sabo na saba tun ina damuwa ina tunanin ko zaka daina tun kana deputy governor baka daina ba balle yanzu da kake a matsayin mataimakin shugaban k'asa, ni abinda ke damuna kawai shine yanda ka fifita muk'aminka a gwabnati fiye da iyalanka, fisabilillahi yanzu haka zamu ci gaba da zama babu Haidar.." Bata kai aya ba ya mik'e yana cire links d'in hannun rigar sa... Hajiya Maryam ta mik'e tana dubansa kafin tace "Your excellency magana nake maka, na gaji da zama babu d'ana don Allah ka janye k'udirinka na aura masa Fairuzah k'ila ya dawo garemu..." ta k'arashe cikin rawar murya.. Kallonta yayi yana huci don shi kad'ai yasan irin hukuncin da ya tanadar ma Haidar, murya a dake ya soma fad'in "Maryama, a yau idan ina so a zak'ulo min Haidar a fad'in k'asar nan za'a zak'ulo min shi amma bata nasa nake ba tunda rayuwar da ya zab'a ma kansa kenan yaga yafi masa sauk'i fine yaje yayi tayi amma nidai kam bazan bisa ina lallashinsa ya dawo gareni ba, yaron da na masa rana a rayuwa, yaron da na fifita sa fiyeda......" Shiru yayi bai k'arasa maganar nasa sannan ya fuzar da iska yace "Maryam kiyi wa Allah ki cire damuwar Haidar a ranki, abu guda tak na tambayesa bayan duk halaccin da na masa Ya kasa min ya watsa min k'asa a idanun duniya bayan na gama tara jama'a, ya nuna min shid'in ba d'an halak bane, ko kinsan har yau mahaifin Fairuzah na kallona da abin, sannan ba lallai ya amince ya kawo mana k'uri'un da muke samu na manyan 'yan kasuwa daga garesa ba, Haidar failed me yayi niyan yayi ruining d'ina ne if not meyasa tuntuni baik'i amince ma auren Fairuzah ba sai ranar d'aurin auren a wayi gari baya nan, ko kinsan zafin ka tara manyan mutane daga k'asashe daban-daban ai maka irin wannan cin fuska... Koda shike ba laifinsa bane dama dole yayi irin hakan.... " Da sauri Hajiya Maryam tasa hannu ta toshe masa baki tana girgiza masa kai take fad'in "Dan Allah kar ka tab'a fad'a mishi, Haidar d'anmu ne wllhi d'anmu ne,..." ta k'arashe cikin kuka.. Saurin rungumota yayi yana mai jin zafin kukan da take, tabbas yana tsananin son Maryama soyayyar da bazai tab'a bari tasan babban laifin da ya tapka ba..... ***************** *Kano* Tsaye yayi gaban doguwar mirror dake manne cikin closet d'insa yana k'are ma kansa kallo, kana ganin fuskar sa ba sai ance maka yanada damuwa ba, babban abinda yafi d'aga masa hankali shine a daren jiya har mafarki da Shema'u yayi wanda dama baccin satansa tayi, wannan wani irin masifa yake k'ok'arin aukawa ciki, tabbas Allah Ya jarabce sa, bashida mafita da ya wuce ya auri Shema'un idan har zata yarda dashi..... Yana tsaye yana wannan tunani kunnensa ke jiyo masa kaman hayaniya daga k'asa, kuma muryar tamkar ta Hajiya, gabansa ya yanke ya fad'i. Cikin sauri ya nufi downstairs k'irjinsa na ci gaba da bugawa, saida ya sauk'o parlor yaga ashe hayaniyar ma daga waje take shigowa... Cikin sauri ya nufi k'ofa.. Nan ya hangi kayan Momma jikin trunk d'in motar SShema'u na gefe ta rik'e Sajida dake zuban hawaye yayinda Hajiya da Momma aka rasa mai bama wani hak'uri, ko wacce gaya ma 'yaruwarta magana take... "Wllhi Kulu duk tsiddabarun da kuka zuba wa d'ana sai Allah Ya maidashi kanku, bacin haka har yaushe Attahiru zai soma maganar auren wannan mai suffar agwagwan..." ta k'arashe tana nuni da Shema'u... Daga Shema'u har Momma a sama suka tari zancen, kenan AT yana son auren Shema'u, dad'i ya lullub'e Shema'u ta kuma rik'o hannun Sajida tace "Muje ciki sweetheart kinji.... " Ai kan tayi wani yunk'uri Hajiya ta fizgo wuyar ta baya tana fad'in "Ki shiga ina, ai yanda kikaga uwarki ta fito toh kuwa binta zakiyi, annoba kawai, tunda kuka zo gidan nan hankula basu kwanta ba, munafuka ni tunda naga kina nan-nan da yaran nan nasan da biyu kikeyi, kin lik'e ma mijin k'anwa banda asara, gadon jaraba gadon Kulu..." Har wuya AT yazo ganin a gaban Sajida Hajiya take wad'an nan maganganun, cikin sauri ya juya ya koma cikin gidan... Shema'u ta bisa da kallo kaman ta zuba ruwa a k'asa ta sha, cikeda makirci take bawa Hajiya hak'uri tana rok'onta tayi shiru ko don Sajida.... Gaba d'aya Hajiya ta had'e su gaba d'aya taci gaba da sille su... Momma kuwa tunda Shema'u ta kwab'eta ta had'iye bak'incikinta don kuwa tabbas ta yarda da shawarin Shema'u ta ringa hak'uri da Hajiya har su sami biyar buk'atar su... Shema'u ta gyara zaman hijabin kanta don dama kayan barci ne a jikinta, cikin zuciyarta ji take tamkar ta damk'o Hajiya ta mak'ureta a wajen kowa ya huta, har tana hasashen irin kisan gillan da zatama Hajiya, daurewa tayi kafin ta lank'wasa murya tana kuma bawa Hajiya hak'uri, Sajida kam tsanar kakan nata ne tab ya cika zuciyar ta, jiyo kukan Ni'ima da sukayi daga cikin gida yasa Shema'u saurin shigewa a rud'e tamkar gaskiya Sajida ta take mata baya da sauri... Momma ta murmusa ta dubi Hajiya kafin tace "Fad'ime kin koma tamkar zararriya, barikiji na fad'a maki nafi k'arfin nayi asiri ma uban jikoki na, saidai idan ina numfashi baki isa ki auro ma Tahir wata ta zauna kan jikokina ba tunda Allah yasa mahaifiyar su tanada 'yaruwa... Ta murmusa kafin taci gaba da fad'in "Ayyiriri, Alhamdulillah Masha Allah tunda shi da kansa ya gane abinda yafi masa kyau yafi dacewa dashi, nikam saidai nace Allah sanya alkhairi na bisu da fatan khairan, kuma tafiya ne dole na d'ageta sai nasan matsayin da d'iyata take a gidan nan..." Daga haka ta shiga janye akwatinta ta nufi cikin gida. Zuciyar Hajiya kaman ya fito waje ya tawarwatse, yau ita za'a ma wannan cin kashi a gidan Attahiru. Gyad'a kanta tayi kafin ta juya ta soma tafiya bata ko ganin gabanta, idan anyi duniya don manzo ta gama shiga hidiman gidan Attahiru, yaje yayi duk yanda yake so da rayuwarsa tunda shi ba k'aramin yaro bane... Kusan karo suka kusanyi da AT suka jima suna kallon juna, tuni Sajida ta shige ta d'ago Ni'ima... Cikin sauri Shema'u ta saita kanta ta shiga murmushin yak'e tana basa hak'uri, bata jira cewar sa ba tayi saurin k'arasawa yanda Ni'ima da Sajida suke ta amshi Ni'ima tana rarrashinta don da alama firgita tayi ta tashi a baccin. Cikin sauri AT ya nufo downstairs ya nufi motarsa yayi mata key ya fice daga gidan, yabi bayan Hajiya. Yana gani ta patattake malam Habu dake rok'onta ta tsaya ya kaita.. Hankalin AT idan yayi dubu ya tashi.. Cikin sauri ya fice daga motan ya nufeta da sassarfa... *Sameena Aleeyou Mrs* [2:00PM, 3/12/2018] ‪+234 803 533 3121‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *24* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ Kaman ya durk'usa saman gwiwoyinsa haka yabi Hajiya yana bata baki yana rok'onta tayi hak'uri ya kaita... Tasi na tsayawa tayi shigewarta sai faman huci take, AT yayi saurin kama gaban tasi d'in zai shiga ta watsa masa mugun kallo kafin tace "Wllhi ka shiga motar nan kai ba d'ana bane..." Gaban AT ya yanke ya fad'i, jiki a mace ya saki marfin motar, Hajiya ta dubi d'an tasi tace "Muje Malam." Nan mai tasi ya ja motar suka wuce. Jigum yayi a wajen yabi bayan motar da kallo, tunowa yayi fah Hajiya nada mota amma tsaban masifa da fad'a irin nata direbobi basu iya zama da ita, da an kawo su sati d'aya sati biyu yayi yawa sun k'ara ma kansu gudu sabida Hajiya..... A hankali ya ambaci sunan Allah kafin ya nufi motar sa ya tada ya nufi gidan nata. *********** Maryama na zaune a parlor tana kallon wani series film mai suna *Jenifer's Diary* a sabon laptop d'inta don dama Buzu ya jima da bata plate d'in kyauta sabida yaji yanda take labarin a makaranta su Fadila na gani suke bata labari hakan yasa ya sai mata CD d'in, sai faman shan dariya take don film d'in akwai abin dariya lokaci guda tana goge inners d'inta dangin pants.... Ganin Hajiya ta shigo fuska babu walwala yasata dakatawa da abinda take.. "Hajiyata lafiya, Allah sa ba wajen Momma kika je ba..." Maryama ta fad'i tana mai saka pause ma kallon nata. Hajiya bata furta komai ba sai k'wafa da tayi had'i da cire hijabinta ta d'aura saman hannun kujera.... Tabbas idan kaga Hajiya bata amsa ka ba toh kuwa ranta ya kai k'ololuwa wajen tashi. Kasa furta komai Maryama tayi sai sanyi da jikinta yayi, tana son Hajiya duk fad'a irin nata bata son ganin ranta a b'ace.... Kaman daga sama sai ganin AT sukayi ya d'aga labule ya shigo sallama saman bakin sa... Ai tun kan ya gama shigowa Hajiya ta mik'e ta fad'a uwar d'aki had'i da tura k'ofan. Maryama ta bisa da kallo ganin yanda ya shigo a birkice, gaba d'aya kaman ba Uncle ba, blue long sleeve ne a jikinsa da alama suite zai d'aura a saman bai sami zarafin yin hakan ba... Shi d'inma kallonta yake lokaci guda idanunsa suka sauk'a kan kayan da take faman gogewa.. Ganin yanda idanunsa ke kallo yasata jin kunya sosai..... Cikin sauri ta tattari kayan tana turawa bayanta, shi kuwa AT sam hankalinsa ba'a wajen yake ba, gaba d'aya rasa meke masa dad'i yayi... Jiyo muryarta yayi tana gaida shi, ya d'an saita kansa kana ya amsa mata gaisuwar nata had'i da zama bisa sofa. Maryama sai kallonsa take yanda ya dafe goshinsa, tausayin sa ya cikata tama rasa me zata soma fad'a masa, tambayar sa zatayi ne ko hak'uri zata basa, toh ma tace me?. Gabanta ya kuma yankewa ya fad'i, ita harga Allah Uncle na matuk'ar bata tausayi don tunda Aunty Aisha ta rasu bai huta ba.... Su biyu d'in jigum sukayi aka rasa mai magana ma wani cikinsu.... Jin shiru yasa Hajiya fitowa don a tunin ta ya tafi ne... Aiko tana ganinsa tasa kai zata juya Tahir yayi saurin mik'ewa yabi bayanta... Zama tayi bakin gado ta cika tayi fam, sautin huci da turirinta kawai kake jiyowa... Kaman wani munafuki haka ya k'araso da sand'a, zuba gwiwoyinsa a k'asa yayi saman rug dake gaban gadon yana fuskantar ta jdanunsa a k'asa, Hajiya kuwa idanunta naga gefe ko kallon kirki bai samu ba, sai faman girgiza hannunta take wanda d'abi'arta idan ranta ya b'aci... "Hajiyata kiyimin afuwa pls, Hajiya ki fahimce ni ki fahimci halin da nake ciki, bazan iya kawo wata macen da zata tarwatsa min kan gida ta rabani da yarana ba, na d'auka idan nace zan auri Shema'u zan sami goyon bayanki, Hajiyata ki duba lamarin Sajida itace babba cikinsu wacce ita kanta tana buk'atar uwa ballantana Jamal da Ni'ima wanda na tabbata ganin su haka babu uwa yana karya maki zuciya.... Hajiya a halin yanzu ba auren soyayya zanyi ba na wuce wannan babin tuntuni, aure zanyi sabida yarana sannan nasan kema sabida su kike so nayi auren, yau idan nace zan kawo wata mace cikin gidan na tabbata fitintunu ne zasuta tashi especially with Sajida, sannan.......suna son Shema'u suna so ta zauna dasu for good, hakan bazai tab'a yuwuwa ba idan ba aurenta nayi b........" D'aga masa hannu tayi alamun dakatarwa kafin ta jinjina kai tace "Yayi Attahiru tashi kaje, Allah Ya sanya Alkhairi ya bada zaman lafiya...." Daga haka mik'ewa tayi ta nufi bathroom, ta barsa nan durk'ushe uwa maraya... Cikin sauri ta fice daga parlorn tana k'unshe kukanta, shikenan da gaske uncle auren Aunty Shema'u zaiyi, shikenan Aunty Shema'u zata zama matar Uncle..... Wani sabon kuka ya kufce mata sanda take shiga d'an madaidaicin parlorn Maama Juu... Mik'ewa Maama Juu tayi tana tambayarta lafiya.... Cikin kuka ta soma fad'in "Ummi wllhi da gaske Uncle yake aurenta zaiyi, Ummi meyasa zai aureta wllhi ni na sani akwai bak'in k'ulli a cikin zuciyarta ba soyayyan gaskiya take nunawa su Sajida ba, Ummi ni dai wllhi banaso Uncle ya auri Aunty Shema'u...." ta k'arashe tana mai zama dirshan a saman tiles... Mamaki ne ya cika Maama Juu, toh banda abin Maryama Tahir shi ya zab'i hakan ma kansa kuma yanada tabbacin hakan shine masa dai-dai.. Hannun Maryama ta rik'e tana duban idanunta da tsan-tsan gaskiyar kukan da take kana ta soma fad'in "Maryam, Ahmad shi ya zab'i hakan ma kansa sannan nima idan da zai nemi shawari na zan amince masa da auren Shema'u domin kuwa a iya zamana da ita kyautatawa ne kawai ke shiga tsakanin mu, itada marigayiya Aysha sam basuda halin mahaifiyar su ke shaida ce, ki duba ranar yanda sam bata goyi bayan Hajiya Kulu ba sanda ta k'ala maki sharri, sannan har ita saida Hajiya Kulu ta caje a gabanki, ni na zauna dasu a gidan naga yanda take kula da yaran sosai, koma babu wannan 'yaruwar mahaifiyar su ce ita yafi cancanta rik'onsu ya koma hannunta domin kuwa jini ya wuce wasa, dole ta kula da yaran tamkar ita ta haifesu, sannan Tahir bai kamata ya auro k'aramar budurwa ya had'a da yaransa ba don kuwa sabon raino zai k'ara ma kansa amma kinga babba kamar Shema'u sai tafi kula masa da yaran...." Girgiza kai kawai Maryama keyi still hawaye na bin k'uncinta, ji take inama kowa zai fahumci Shema'u kaman yanda ta soma fahimtar ta, don tun farkon had'uwarsu da ita takeda wannan feelings d'in gameda ita, bata kuma cewa komai ba sai shigewa k'uryan d'aki datayi.... Maama Juu ta bita da kallo cikeda mamaki.... ************** AT ya girgiza kai a karo na biyu kafin yace "Hisham gaskiya ina tsoron fushin mahaifiya, Hajiya tayi fushi yanda baka tsammani, kawai inaga dai zan janye maganar neman auren Shema'u tunda dama bamuyi wata magana da ita ba, zan bata go ahead kawai ta Aura min koma waye d'in tunda ni dama ba auren soyayya zanyi ba...." ya k'arashe maganar yana bud'e maidaidaicin fridge dake a cikin office d'in nasa... Hisham yayi shiru yana sauraren sa kafin yace "AT ya kamata ka sake tunani akan lamarin nan, fad'a da fushi halin Hajiya ne wanda i zuwa yanzu yaci ace ka saba da hakan, Allah yaga zuciyar ka yaga niyyar ka, kuma na tabbata daga baya Hajiya zata fahimici baka yanke mummunar hukunci ba, think about it, yaya yaranka zasuji idan sukaji 'yaruwar mahaifiyar su da take d'auke masu kewar mahaifiyar su itama zata tafi ta barsu, zasu fara tsoron SHAK'UWA da mutane tunda kowa tafiya yake ya barsu, kai kanka kasan dagan da aka sha da Hajiya kafin ka auri Aysha, Allah Ya jik'an Baba Shattima shi yayi tsayin daka har auren nan ya yuwu, grudges d'in dake tsakanin Hajiya da Momma shine kurum yake kawo cikas amma ba komai ba, kai ai kasan zaman hak'urin da Aysha tayi da Hajiya har tayi winning nata over, toh ina mai tabbatar maka hakance zata kasance da Shema'u ma, ..... Sannan AT you can't deny the fact kanada feelings for Shema'u, ko ba haka bane....?" ya k'arashe fuska cikeda alamun tambaya... AT ya d'an yamutsa sumarsa da ystaun hannun sa kafin yace "Am I that obvious..?" Hisham yayi wata murmushi kafin yace "Mutumi na idan kowa bazai fahimce ka ba kasan banda ni, ba jiya ba na sanka Tahir, so shawarin da zan baka ka sami Shema'u kuyi magana ta fahimta sannan ka tafi Rano kazo ma Hajiya dasu Baffa Ado tunda nasan su zasu fi mata bayani ta gamsu...." Ya k'arashe yana tsiyaya ruwa a cup... Nazarin maganganun yake kafin ya shiga gyad'a kai yace "Na gode Hisham, I'll see what I can do..." Hisham ya gyad'a kai yana mai kurb'an ruwansa.. A zuciyarsa kuwa fad'i yake _I won't rest till you're completely ruined, wllhi AT sai na rabaka da filin mahaifina kaman yanda ka rabani dashi..._ *********** Tunda AT yazo ma Shema'u da maganar aka rasa wa yafi wani farin ciki tsakanin ita kanta uwar gayyan wato Shema'u da kuma Momma kai harta yaran AT su Sajida,... Tsalle Sajida tayi ta rungume Shema'u tana fad'in "Aunty na fiki farin ciki, dama idan Daddy zai yi aure toh it should be someone like you, yanzu bamuda fargaban zaki tafi ki barmu wata rana, you're staying here for good..." ta k'arashe tana k'ara hugging Shema'u.... Ai Shema'u kam har yanzu gani take tamkar a mafarki, ko iya amsa magana batayi sabida murna sai gyad'a kai kurum uwa k'adangariya.. Shi kansa AT yasha mamakin ganin Shema'u ta amince dashi lokaci guda, wata zuciyar tace " k'ila tsananin son yaranka da take yasata amincewa da kai lokaci guda... Washe gari ya d'auki hanyar Rano, Baffah Ado k'anin mahaifin sa da kuma Kawu Sunusi yayan Hajiya sunji dad'in batun Attahirun sosai, gaba d'aya sun goyi ba suka kuma d'unguma suka taho Kano don mara ma d'ansu baya, tsarin da Attahiru ya yanke shine dai-dai ko a shari'a hakan yayi babu laifi.. Hajiya kuwa cewa tayi ai da bai sha wahalan d'add'ago su ba, daga nan iyanin da d'aurin aure suka shige don ita tuni ta masa addu'an dacewa, bata nuna masu komai ba, su kansu sun sha mamaki don sun san fad'anta sunyi tunanin bazasu wanye lafiya ba... Shirye-shirye ake babu Kama k'afan yaro idan ka d'auke Maryama da Hajiyar ta wad'anda suka koma gaba d'aya babu walwala... Maama Juu tuni ta koma gidan AT kasancewar Momma tareda Shema'u zasu wuce Jalingo don gudanar da shirye-shiryen biki... Tana zaune saman gadon Hisham yana shafe bayanta kaman tsohon maye yana fad'in "My Allied yanzu zakiyi tsada sosai idan kika shiga gidan AT." Shema'u ta murmusa had'i da juyowa suna fuskantar juna kana tace "Kar ka damu nida kai bazamu rabe ba ai, amma ka sani da zaran ka mallaki abinda kake so daga gareshi zaka k'yale min shi..." Ta k'arashe tana rungumo wuyar sa.. Dariya ya fashe dashi kafin yace "Niko zanga yanda za'ayi ki mallaki Tahir shi kad'ai ki rabasa da mahaifiyar sa da 'ya'yan sa.." Shema'u ta murmusa sannan taci gaba da fad'in "Wannan mai sauk'i ne don na gama tsara yanda zanyi, Jarabebbiyar tsohuwar can zan d'an sa ayi brushing bakinta ne a rage mata wargi, ita kuwa babbar d'iyarsa mai shirin zama k'aramar karuwa da zaran ta haife masa shege zai sallameta, su kuwa k'ananan idan basubi hanyar da uwarsu tabi ba zan salwantar dasu ta wani hanyar..." ta k'arashe maganar tana tuntsirewa da dariya.. Hisham kuwa wata kafiran murmushi yayi cikin zuciyarsa yake fad'in _Ni kad'aine nakeda abunda zanyi destroying d'inki lokaci guda Shema'u, idan kika betraying d'ina I won't think twice, zan shayar dake mamaki..._ ya k'arashe zancen zucin nasa yana kai mata capka... *Sameena Aleeyou Mrs* [2:00PM, 3/12/2018] ‪+234 803 533 3121‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *26* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ A zabure ta mik'e tana kuma karanta sak'on, ita kad'ai take girgiza kai ba tareda ta iya furta koda kalma ba. Mata mai mata gyaran jiki dai kallo ta bita dashi ganin yanayin ta, a d'an kid'ime ta furta "Lafiya Amarya..?" Shema'u ta d'an saita kanta kafin ta sakar mata murmushi tace "ba komai Dakura, ina zuwa..." Bata jira amsarta ba tayi ficewarta zuwa wani d'an store dake tsakanin corridor, tana shiga ta maida k'ofar ta rufe sai waige-waige take, Momma da fitowar ta kenan ta sallami wasu bak'i ta hangi Shema'u ta shige store, gabanta ya yanke ya fad'i, me Shema'u zatayi cikin store?.... Bata gama tunanin ba wasu 'yanuwansu suka yi sallama haka dole tayi ta kansu ta fita sabgan Shema'u amma zuciyarta sam bai kwanta ba da yanyin da taga Shema'un. "My Alhaji pls ka tsaya ka saurare ni wllhi nima bansan su Momma na shirya wannan auren ba sai da abin ya k'arato, kaga yaran nan ne sam basu yarda da kowa ba sai ni basu SHAK'U da kowa ba sai ni ever since their mother passed away, pls ka tausaya min kar kayi....." Bata kai aya ba yace "Rufe min baki and don't take me for a fool, jiya na sanki da zaki wani kashe murya kina min k'aryar banza, dama tunda naga kin mak'ale a gidan Daktan nan nasan da abinda kike shiryawa, kin maidani ATM machine d'inki koh tun yaushe nake binki da maganar aure amma kink'i amince min da shike idanunki sun rufe da soyayyar mijin k'anwarki koh... Ko ki fasa auren nan ko kuma nazo har wajen d'aurin auren na fad'a ma mijin who you really are.." Huci kawai Shema'u keyi ga zafin store da ya addabeta, zufa tako wani sak'o tsattsafo mata yake, take wani tunani ya fad'o mata ta Saki wata kafiran murmushi kafin ta soma fad'in "Alh Aminu don't you dare do that, I won't go down alone, tareda kai zamu ruguje idan kayi tunanin rusa min rayuwata, Shema'u nake, komai nasa a gabana sai nayi nasara, kasan inada labarin zaka tsaya takarar d'an majalisa...." ta kuma yin murmushi kafin taci gaba da fad'in "Wllhi wllhi zan maka sharri irin wanda imagination d'inka bai tab'a baka ba, zan ruguza maka rayuwarka dana iyalanka, wllhi idan kayi yunk'urin rabani da Tahir da iyalansa sai na rabaka da kowa naka, kai sai na maida kai abin kwatance, wllhi 'ya'yanka sai sunji su kashe ka da hannayen su shi yafi masu sauk'i..... So a shawarce mu ci gaba da rufawa juna asiri tunda ni nasan jikina kake so kar ka damu bazaka daina samu ba muddin zakabi dokoki na..." ta k'arashe tana kashesa da murmushi... Tsoro ya cika Alh Aminu, tabbas baya fatan ya rasa kujeran da yake nema tunda gashi har ajiye aikinsa yayi ya shiga siyasa tuk'uru, sannan yana son 'ya'yan sa fiyeda komai a duniyar nan... Murmushi ya sakar mata kafin yace "Toh ai ke d'ince kinsan bana jure rashinki, ina jiranki a guest house d'ina tunda kin hanani fitowa..." Tab'e baki tayi kafin tace "Ta ina zan fito bayan 'yan d'aurin aure sun cika ko ina..." Alh Aminu ya dara kafin yace "Haba giwar mata wai dama so nake kizo kinga sai na baki nawa gudumawar sannan idan zaki min adalci ai ya kamata kizo muyi sallama,." Ta d'an juya idanu kafin tace "Cash ne ko check.?" "Sai wanda kika zab'a" ya bata amsa kai tsaye... Murmushi tayi kafin tace "Ka saurare ni." daga haka ta katse wayar... Tana cikin waige-waige tana k'ok'arin fitowa ta ji an jawota an shige d'aki da ita, ba kowa bace Momma ce, sai faman huci take tana watsa ma Shema'u mugun kallo kana tace " Jarabebbiya babu yanda zaki je, banda shegen fitina inji gidan wani za'a kaiki yau uwar me zaki fita kiyi da wani inyi.." Shema'u ta buga tsaki kafin tace "Momma kinafa shige gona da iri, idan banje ba cewa yayi zai fallasa ma AT halina na bin maza sannan kinsan idan wannan aure ta fasu ba AT kawai ba harta su Sajida jikokin ki sai sun tsane mu daga ni har ke, don haka a shawarce ki barni na fita kuma ki rufa min asiri sabida dolenki ne..." ta k'arashe tana juya idanu hannu rik'e a k'ugu... Idanun Momma sukayi rau-rau, kai Shema'u bala'i ce, harga Allah ita batayi wannan bin mazan ba gashi Allah Ya jarabce ta da samun 'ya haka, Kuskure d'aya tayi tak a rayuwarta, ji take kaman a fasa wannan aure amma babu yanda ta iya, jikokin ta zasu tsaneta...... Bata gama tunanin da take ba ta jiyo muryar Shema'u tana ci gaba da fad'in "Momma duk lalacewan naka naka ne, nasan tunanin ki bai wuce kar nabawa jikokin ki wannan tarbiyar ba, kar ki damu wllhi bazan tab'a abu makamancin haka ba, ina sonsu tamkar yanda nake son 'yaruwata mahaifiyar su, hasalima zuwa wajen Alh Aminu da zanyi sabida su zanyi, and I promise you wannan shine na k'arshe bazan kuma pls Momma kifahimce ni, nasan kina sona kina son su Sajida pls kar kiyi abinda zai zame mana tarin danasani dagani har ke..." ta k'arashe tamkar zata runtuma ihu idanunta sur k'walla. Momma dake zaune kurum k'walla sun ciko idanunta, a hankali tasa bayan hannunta ta goge hawayen bata iya furta komai ba sai sanyi da jikinta yayi tamkar an tsoma a freezer.... Shema'u tana ganin haka ta mik'e tana wata kafiran murmushi ciki-ciki kafin ta shafi fuskar Momma tace "Anfani uwa kenan kullum ta tsaya ma family d'inta, ta zama very responsible.." daga haka mik'ewa tayi ta bud'e wardrobe ta d'auko hijabi har k'asa sannan ta d'au black Vail tayi nik'ab dashi.... Har ta kai k'ofa Momma ta k'araso gabanta ta rik'e hannayen ta tace "Goggonayen Attahiru zasu tafi dake da zaran an gama d'aurin aure don basu so ayi dare..." Shema'u ta murmusa kafin tace "Kar ki damu Momma komai zai tafi yanda na tsara, ki dai san yanda zakiyi ki kare Amarya just in case ana nemanta..." Daga haka ficewa tayi cikin sauri ba tareda kowa ya ganeta ba... Komawa Momma tayi ta zauna saman gado hawaye taji suna bin k'uncinta, ta sani ita d'in mai laifi ne ta sani ita d'in mai yawan son nata ne tak'i na wani, ta sani ita d'in mai son abun duniya ne amma tana tsoron kar hakkin Tahir ya kamasu, anya ta kyauta ma d'iyarta Aysha idan ta bar Shema'u ta zauna akan iyalanta.... Wata zuciya tace "Bakida zab'i muddin kika hana wannan aure toh har abinda kika jima kina b'oye ma Shema'u zai iya bayyana, sannan jikokin ki zasu tsane ki, ita kanta Shema'u zata tsaneki, Hajiya Fad'ime zata maki dariya, gashi babu Mukhtar babu Aysha, wad'annan su kad'aine family d'inki a yanzu, yin shirun ki shine maki mafita, iyakaci kibi Shema'u da addu'an shiriya.... Kifa kanta a wajen tayi hawaye suna sauk'o mata.... *************** *Kano* Gidan a d'an kwai mutane wanda yawanci 'mdangin Hajiya ne da na mahaifin AT wato mutanen Rano 'yan taran Amarya. Tana kwance saman gadonta suna chatting da wayar da Shema'u ta bata, nan yake sanar da ita ya d'an fita shan iska sabida zafi, Sajida sai murmushi take tana jinta a uwa wata duniya, nan ya tambayeta abinda take itama, kai tsaye ta sanar dashi tana d'aki tana kwance chatting with him, ya turo mata bugun zuciya wato Heart, nan yace ta turo masa pic d'inta a yanda take kar tayi makeup kar tayi komai..... Alamun rufe idanu ta tura masa kana tace tana jin kunyar sa... Ya tura mata sad face kafin yace shi bari ya tura mata nasa...Hotonsa ya turo mata yasha kyau a bakin pool , babu riga a jikinsa sai wando 3quater gashin nan nasa sun kwanta luf-luf, babu macen da zata gansa a haka bai burgeta ba... Sajida ta tsinci kanta da fad'uwan gaba, saida taji wani yarrr a jikinta ganinsa a haka da tayi... Kiran da taji Maama Juu na k'walla mata ya katse masu hirar tasu, nan ta d'aga k'asar pillown ta ta tura wayar ciki... Gyare-gyaren d'akin Babanta Maama Juu ta sakata tunda ita ba shiga zatayi ba, Sajida dai gaba d'aya hoton Buzu ya kasa b'ace mata a k'wayan idanunta, kyaun halittan sa na fizganta, har alla-alla take ta gama gyaran su ci gaba da hirar su... Tana gamawa ta dawo ga wayarta, zamanta a d'aki har ya d'an dami Maama Juu tunda tasan Sajida da son shiga mutane musamman yanda 'yanuwan su yau suka d'an cika gidan, wata zuciya tace "K'ila tunowa da mahaifiyar ta tayi shiyasa ta k'ule a d'aki, don haka Maama Juu bata kuma bin ta kanta ba... Daga chatting k'iranta yayi ya sanar da ita gashi a layinsu tunda tak'i nuna masa hoton ta yazo ya ganta da idanunsa, sabida he's dying to see her pretty face... Dad'i kaman ya kasheta, mik'ewa tayi ta soma shiryawa, harda wani d'an makeup tayi akasu fesa turare.... ************ *Taraba, Jalingo* Toilet ta shige ta kintsa kanta bayan sun k'arashe bidirinsu da Alh Aminu, tana tsaye k'ofar toilet d'in tana jan zip d'in rigarta take jiyo muryar sa yana waya. "Allah Ya taimaki his excellency, yayi wata murmushi cikeda rusunawa kafin yace "Wasu kala kake buk'atan 'yanmatan , farare, bak'ak'e ko wankan tarwad'a.... Ya gyad'a kai kafin yaci gaba da fad'in "Toh an gama rankashi dad'e, 'yan Sha biyar zuwa shatakwas kenan, yauwa an gama.. Allah Ya taimake ka your excellency, yauwa za'ayi duk yanda za'ayi su isa Abuja a gobe, daga haka yayi hanging... Shema'u ta k'araso tana wata kafiran dariya kafin tace "Kace ba'a nan kawai ka tsaya ba my Alh, toh shi kuma waye ka gama waya dashi..." Alhaji yayi dariya kafin yace "Ai yau ko me kika tambaye ni kai tsaye zan baki amsa domin kin jiyar dani dad'in da baki tab'a jiyar dani a baya ba... Wannan manyan mu kike ji na Abuja, bokayen su suna sakasu lalata da k'anan yara a ko wace wayewan gari sabida cimma burinsu, ba mata zalla ba wani jik'on harda yara maza..." ya k'arashe yana k'ok'arin kai mata wani sabon capka... Dariya ta fashe dashi a zuciyarta ba komai ta tuna ba sai yanda za'ayi ta mik'a Sajida... Sauri-sauri ta tarkasa ya nata ya nata tayi wucewar ta don idan ta biye na Alh Aminu sai ya kusan had'iyeta a yau sabida naci da jaraban sa...D'an gyaran da akayi ma ango ya kwashe... Tana isowa ta samu 'yan d'aurin aure suna dawowa alamun an d'aura, daga cikin napep d'in da take tana hango AT yanda yaketa gaisawa da jama'a yayi kyau cikin faran shadda k'al da hula ash color, wani dad'i ya mamayeta yau wannan mutumi maiji da class ya zama mallakin ta, lallai tanada sa'a a rayuwa, cikin sauri ta fice ta shiga gida a sace tamkar bak'uwa.... ************ Buzu ya karkato da kyau yanai mata wani irin duba kafin yace "Miss Beauriful kinmin kyau.." Sajida ta murmusa had'i da rufe fuskarta da tafukan hannu.. Murmushi shima yayi kafin yace "No pls ki bud'e min fuskar ki don bana gajjiya da kallo, those lips, those eyes.... Kai komai na fuskar ki na min kyau Miss Beauriful, wani kalan lipstick ne kam kika shafa don gaskiya ni ban tab'a ganin lips d'in da suka min kyau irin haka ba, kodai bakin naki ne haka, shiba red ba shiba pink ba, okay pitch ne koh..." ya k'arashe yana wani kashe idanu... Murmushi Sajida ta sakar masa kafin tace "Ban shafa komai ba sai lipgloss..." Buzu ya murmusa kafin yace "Toh gaskiya kinada kalan baki mai d'auke hankalin samari, nifa har naji kishin ki kar wani ya gane min ke haka tunda kince bikin Daddyn ki ake nasan maza zasu zo.." Murmushin jin dad'i ta kuma yi kafin tace "Ai Daddy bazai yi wani event ba, Aunty Shemah ce dai zatayi liyafa gobe." Buzu ya murmusa kafin yace "Har naji sanyi a cikin raina." ya sauk'o da idanunsa yana k'are ma jikinta kallo, saida ya d'an muskuta kafin yace "D'inki ki yayi kyau sosi dukda kin rufe da mayafi bana gani, amma dai ya kamata a nuna min na gani..." yayi maganar cikeda shagwab'a... Shiru tayi bata ce komai ba sai murmushi k'asa-k'asa da takeyi... "Pls mana Beautiful, gani fah kawai zanyi.." Ba tareda ta kawo komai ba a zuciyarta ta d'an bud'e gyalenta tace "Ka gani ..." Kallo ya bita dashi kafin ya murmusa cikin ransa yace _Not bad_ a fili kuwa cewa yayi tailor d'in nan yaci na masa kyauta, kodayake bama fah d'inkin bane yayi kyau jikin ki ne yasa d'inkin yayi kyau, you're beautiful..." Murmushi kurum tayi kafin tace "Ai ka fini kyau.." "Inji wa, ai ni my whole life ban tab'a ganin mai kyaunki ba, and babban buri na shine ki zama matata, da Daddy zai gane ma da an had'a bikin mu da nashi ne..." yayi maganar uwa gaskiya. Zaro ido waje Sajida tayi kafin tace "Tab! Ai Daddy bazaimin aure yanzu ba zaice I'm still young kuma karatu yake so nayi sosai, Daddy ko waya bai bani ba har yanzu, wayata ma Aunty Shema'u ce ta bani without his knowledge." Buzu ya gyad'a kai kafin yace "Na lura kinaji da Auntyn nan naki nima har kinsa naji ta burgeni, sabida a koda yaushe tana share ma princess d'ita hawaye, she's indeed kindhearted." Sajida ta gyad'a kai tana murmushi kana tace "Gaskiya ne tana sonmu sosai.." "Miss Beauriful nima fah na matsu ki zama matata, anya zan iya jira har lokacin da Daddy zaiyi accepting d'ina..." ya k'arashe kaman zaiyi kuka.. Idan yana mata shagwab'a dariya yake bata a wani b'angare kuma sosai yake burgeta sannan tana jin wasu feelings na musamman idan yana mata hakan. Hira sosai suka sha kafin Buzu ya dage sai ya masu hoto kafin ta sauk'a a motar, sam bata son mata musu sabida tsananin soyayyar sa dake fuzganta, tanaji ya matso daf da ita jikinsu na gogan na juna ya masu hoton, zata kai hannu jikin marfin mota ta bud'e yayi saurin rungumo cikinta yana fad'in "Saura d'aya mana Princess.." Saurin d'ago idanu tayi tana dubansa ganin yanda ya rik'e mata ciki... Cikin sauri ya saketa kafin ya soma bata hak'uri yana fad'in he didn't mean it. Fuska babu walwala tace masa ita zata tafi gida.. Haka yayita marairaice mata yana bata hak'uri yana fad'in bada nufi yayi ba, tak'aitaccen murmushi kurum ta masa kafin ta kama marfin motar ta fice... "Baby zamu waya.." ya fad'i yana turo kai ta glass, ko kulasa batayi ba tayi shigewarta.... Buga steering wheel yayi yana furta "Damn it.!!!" Shigowar ta gida yayi dai-dai da shigowar Ashfaq zai ajiye cartons d'in juices da Tahir Ya umarce sa tunda dama shi baije d'aurin auren ba... Ashfaq ya bita da kallo don tun daga bakin layinsu da yake shigowa yaga daga motar da ta fito, sam baiyi tunanin gidan zata shigo ba, saida ya kalle ta sosai yaga kamanninta da AT, k'ila wannan itace d'iyarsa Sajida, amma me takeyi cikin bak'ar motar can mai bak'in tint wanda da gani sun jima a ciki domin tun d'azu da zai wuce ma yaga motar, haka kurum yaji zuciyar sa bata kwanta ba... Zata shige cikin gida yayi saurin katseta da fad'in "Emm da Alla sannu koh.." Wani juyowa tayi had'i da jifa masa kallon raini... *Sameena Aleeyou Mrs* [2:01PM, 3/12/2018] ‪+234 803 533 3121‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *25* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ Misalin k'arfe tara da wasu Dak'ik'ai Shema'u ta lek'a d'akin Maama Juu da sallama yanda Ni'ima ke kwance saman gado, murmushi suka sakar ma juna itada Maama Juu uwa mutuniyar arziki, ta k'arasa ta rank'wafa saman kan Ni'ima tamkar tanai mata addu'a, cikin zuciyarta kuwa da zata sami halin mak'ure Ni'ima da tayi ta huta... Maama Juu na kallonta har ta k'arashi addu'o'in ta ta gyara ma Ni'ima kwanciya kafin ta masu saida safe, daga nan d'akin Sajida ta nufa... Zaune ta sami Sajida gaban laptop d'inta tana upgrading Apps. Zama Shema'u tayi gefenta fuska fal murmushi, Sajida tai mata sannu kafin tace "Aunty ya shirin tafiya..?" Shema'u ta d'an rausayar da idanu had'i da sauk'e ajiyan zuciya kafin tace "My Sajee, I'm nervous fah, gani nake anya zan iya auren Daddyn ku, gani nake tamkar naci amanar 'yaruwata idan na auri mijinta, Sajee ji nake kaman na fasa auren mahaifin ku...." ta k'arashe maganar kaman zatayi kuka... Saurin ture laptop d'in gabanta tayi kafin ta kamo hannayen Shema'u tana girgiza kai take fad'in "Haba Aunty, pls don't say no, Aunty idan baki auri mijin Mummy ba kika bari aka kawo wata mace cikin gidan ta maye gurbinta shine kinci amanarta kuma kinci amanar yaranta, but auren Daddy na nufin kin amanar da aka bar maki, Aunty don Allah kar ki fasa, idan domin Hajiya ne nasan kwananan zata fahimci ke wacece, zataga kyakkgawan zuciyar da kike da ita ba kaman yanda take tunani ba, sannan gaba d'ayan mun nan hak'uri da Hajiya mukeyi harta Daddy, Aunty do this for us please..." ta k'arashe kaman zata runtuma ihu... Shema'u tayi saurin hugging d'inta kafin tace "Bazan tab'a barinku ba Sajida, never.... Ta d'agota ta shiga share mata 'yan hawayen da suka soma zuba kana tace "Oya banason ina ganin damuwa a fuskar ki, ya labarin Haris kuwa..?" ta tambaya tana d'aura murmushi saman fuskar ta... Take annuri ya wanzu a fuskar Sajida, d'an murmusawa tayi kafin tace "Aunty kinsan na fad'a masa da wayarki muke anfani gashi yanzu zaki tafi shiyasa nike upgrading laptop d'in mu samu muke magana dashi, bansan meyasa Daddy yak'i saya min wayan ba bayan yace da zaran na gama secondary school zai saya min..." Shema'u ta d'an sauk'e ajiyan zuciya kafin tace "Sajida kinsan mahaifin ki ya sha boko ya k'oshi, shi gani yake duk abinda bazaki k'aru dashi ba b'ata lokaci ne, shiyasa ya sai maki wannan computer instead of waya, ko nima na masa magana is high time ya barki ki rik'e waya amma sai ce min yayi baiso wasu rubbish ideas su soma shiga kwanyar ki tun yanzu, amma ban sani ba ko sai kin shiga Jami'a ne ya barki ki soma rik'e waya ba, kinsan dole yasa idanu akanki musamman da ya ga kin rasa mahaifiya, ni wllhi har nayi tunanin sai maki iPhone X latest a matsayin gift d'inki naji wannan doka da Daddyn ki ya kafa kurum sai na fasa..." Sajida ta d'an turo baki cikeda rashin jin dad'i kafin tace "Aunty wllhi da hankali na da wayona, lalacewa fa sai mutum yaso ne, bana tunanin waya zai iya lalata budurwa har sai idan ita taso hakan, haba tun muna sec school fah k'awayen mu da yawa sunadashi kuma babu abinda ya lalata su, ni dai pls ki saya min ko babu sanin sa.." Shema'u ta d'an tab'e baki tace "Nima dai abinda na gani kenan, kar ki damu tunda har kinsan hakan, zan baki tawa da sabon layi ni kuma idan naje Jalingo na sai wani, amma this should be between us..." Tsallen murna Sajida tayi had'i da hugging Shema'u kafin tace "Aunty you're my Fav.." Shema'u kuwa sai murmushin jin dad'i take... Tana komawa d'akinta layin Buzu ta nema, "Hello kana jina, kafin na dawo daga Jalingo ina so a sami improvement, duk wani salo da kaloli na yaudarar ka ka tabbata ka had'asu, yanzu hankalin magaifinta zai kasu sabida biki dake k'aratowa, kayi amfani da wannan damar, and don't fail me....." Daga haka bata jira cewar sa ba, ta cire sim d'in ta jefa a jaka... Ita kad'ai sai nishad'i da annashuwa take... ************* Washi gari kafin su wuce Jalingo suna zaune itada AT a parlorn sa na sama, gaba d'aya jinsa yake ba'a sake ba, everything is happening so fast, shi baima san ta yanda zasu soma zancen ba.. wata b'angare na zuciyarsa dai har yau bata gama aminta da hukuncin da ya yanke ba, wata sashi kuwa ce masa take ya rabu da kokonton zuciya sharrin shed'an ne, domin so tari hakan ne yake faruwa idan za'ayi abin alheri musamman aure... Shema'u kuwa an sha babban lullub'i kan nan a k'asa, sai ka rantse mutuniyar arziki ce, sai faman wasa da 'yan yatsun hannunta take, Ni'ima da tashinta kenan ta shigo da gudu ta d'ale cinyar sa, hakan sai yafi masa sauk'i gaba d'aya sai suka soma hiran da Ni'ima... Sauk'ar da ita Tahir yayi yace maza taje Maama Juu ta mata brush sai tazo ta nuna masa, Ni'ima ta fice da d'an gudu irinta yara tana mai gyad'a kai... Gaba d'aya suka bita da kallo, Shema'u kuwa har wani cewa take" Baby ki tafi a hankali koh.." AT ya gyara zamansa ya d'an tattaro nutsuwar sa kafin ya soma fad'in "Malam Habu zai kaiku, idan yaso sai ki bar motar ki a nan tunda ko kin tafi da itama wahalan dawowa za'ayi da ita, sannan banaso kina long journey irin haka yanada had'ari though nasan kin k'ware a driving amma kiyayewa ne.." Ya d'anyi shiru.. Shema'u kuwa sai gyad'a kai take cikeda jin dad'i jin AT har ya soma mata umarni, wayyo komai nasa abin burgewa ne... Muryar sa ya kuma dawo da ita daga duniyar soyayyar sa data lula yanda yake fad'in "Ammm Shema'u ina so nasan more about you, dukda nasan ke 'yaruwar Aisha ce amma kinsan nidake bamusan juna sosai ba sannan bamu saba da juna ba..." ya k'arashe yana d'aura hab'ar sa saman hannayen sa. Shema'u ta d'an murmusa kafin ta soma fad'in "Dr yanda ka ganni haka nan ni d'in kenan, saidai abu guda da baka sani ba shine na tab'a aure tun kafin Aysha tayi aure, na auri wani Alh Aminu, kishiyoyi suka hanani zaman gidan, toh shiyasa ma batun aure ya fita daga tsari na, ban kuma yin wani aure ba tun wancan lokacin don na wahala sosai hannun kishiyoyi, sai yanzu da ka zo min da maganar, sannan abinda ya k'arfafa min na amince da kai sabida yaran 'yaruwata ce, both nida kai nasan munayi ne sabida su.." ta k'arashe tana sadda kai k'asa,. AT ya d'an tausaya mata, ashe dole taji tsoron auri tunda bataji dad'in gidan aure a baya ba... Gyad'a kai yayi kafin yace "Haka ne sabida su zamuyi, and I trust you, na tabbata zaki rik'e min su amana.." Shema'u ta murmusa kafin tace "Bakada haufi Dr, yaran nan are my life, insha Allahu bazasuyi kukan rashin uwa ba..." AT ya jinjina kai cikeda jin dad'i kafin yace "Toh ya batun aikin ki, ko zan nema maki transfer of service ne..?" Girgiza kai tayi cikeda kissa kafin tace "Ai a halin yanzu aikina shine kula da kai da iyalanka, wllhi sam babu batun aiki a gabana, da d'inma don banason zaman banza ne shiyasa...." Ran AT ya kuma yin fari, murmushi yayi mai bayyan hak'wara kafin yace "Toh shikenan, naji dad'in hakan sosai, Allah ya wuce mana gaba..." Shema'u ta rausayar da idanu kafin tace "Ameen Dr." Su Sajida ne suka shigo suna gaida su, suna fad'i ma Shema'u Momma ma ta fito, a tare suka nufo downstairs gaba d'ayan su AT na rik'eda 'yar autar sa... Momma kanta har wani sabon hankali ne ya shigeta.... Gaba d'aya har wajen mota sukai masu rakiya harda AT da yaran... ************ Tunda suka zo Jalingo ko shi bai kirata ba sai ta kirasa, wasu kalaman girma saye zuciya da soyayya take karanto masa, Shema'u tayi nisa a iya makirci... Momma ta kuma dubanta kafin tace "Kedai shashasha ce sam keda Aysha tamkar baku had'a jini ba, ni nasan wannan shegen gantalin naki bin maza dama kike, bacin haka meyasa zaki shera masa k'arya cewa kin tab'a aure, ke ko tsoron k'aryar ta k'are maki ba kyaji..." ta k'arashe tana watsa mata mugun kallo.... Tsaki Shema'u ta buga a karo na babu adadi kafin tace "Momma kinga ki daina min ihu akai, ai ke ban tab'a abin arziki kika yabeni ba sai Aysha, kuma da kike cewa bin maza nake lokacin da nake kawo maki kud'ad'e kin tab'a tambayata ina nake samun kud'ad'en da suka ninka salary na ?? Baki ttab'a ba, sai yanzu zakizo ki sakani gaba, sannan wannan aure fah don jikokin ki zanyi ba don kowa ba, idan kin amince wancan jarabbabbiyar tsohuwar ta aura masa ko wace iri ta zauna kan jikokin ki fine sai na fasa ba abin tashin hankali bane, tunda duk abinda nake baki gani...." Momma ta share zufan da ya keto mata kafin ta shiga bawa Shema'u hak'uri, tabbas idan da laifin Shema'u harda nata, sannan wannan gaskiya ce kayi k'ok'ari ka samar da iyalanka ta tsaftacecciyar hanya, domin kuwa duk abinda ka shuka sai ka girbe... Ta fad'a duniyar tunanin yanda Mukhtar ya taimaketa sanda kowa ya gujeta sabida cikin Shema'u, Mukhtar shi ya share mata hawaye ya kuma jadadda mata Shema'u bazata tab'a sanin ba shine mahaifin ta ba, kaico dukda hud'ubar samari tabi a wancan lokacin abin saida ya bibiyeta,.... _Allah ka rabamu da sharrin samari masu neman yaran mu domin sharri, ameen_ ************* Ranar d'aurin aure abokansa likitoci, 'yan uwa da abokan arziki gaba d'aya sun hallara, su Goggo Asabe ma motoci na musamman Hisham ya sama masu dukda AT baiso a wani d'aukaki bikin saida mutane suka hallara, Hisham baya k'asa baya sama, sai hidima yake sai ka rantse aminin arziki ne... Alh Aminu ya kad'a kai a karo na biyu kafin ya kwararo wata ashariya, har shine Shema'u zata masa 419 a cikin garin nan toh kuwa wllhi k'aryarta tasha k'arya, ya kirata yafi sau abinda yafi tak'i d'agawa, k'arshe text ya tura mata kaman haka..... *Sameena Aleeyo Mrs* [2:01PM, 3/12/2018] ‪+234 803 533 3121‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *27* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ Ashfaq ya d'an dake kafin yace "Pls ke 'yar gidan nan ne.?" Ya tambaya yana dubanta. Rasa me zata ce masa tayi gashi dama tana ji da haushin abinda masoyinta Haris ya mata, wannan kuma ko waye shi oho, ya tsaya yana mata tambayar rainin sense. Ashfaq ya d'an k'araso jikin bishiyar umbrella dake tsakiyar farfajiyan kafin yace "Kiyi hak'uri da Allah, dama Dr ne ya aiko ni da kaya so pls idan bazaki damu ba kiyi magana wa mutanen gidan su fad'i yanda za'a zuba.." D'an jim tayi kafin tace "Menen aikan.?" K'arasawa jikin motar sa yayi ya d'aga both kafin yace "Kin gansu.." Sajida ta gyad'a kai kafin tace "Bara na shiga na tambaya a ina za'a zuba.." Daga haka ta barsa nan tsaye ya bita da kallo yana mamakin jin kanta... Shiganta gida neman Maama Juu ta soma tana son tambayarta ko Daddy ya sanar da ita za'a kawo aika, bata sameta ba don suna can sashen bak'i suna shigar da warmers na taran bak'i... Daga yanda yake tsaye yana dafe da motar sa ya hangi gefen fuskar wata mata da tayi mugun masa kama da wata, kai gaskiya yanayin matar ma yai masa kama da ya tab'a ganinta, toh a ina yasan mai kama da wannan matar..... Yana nan tsaye ya fad'a duniyar tunani sai jiyo muryar Sajida yayi tana fad'in "ka zubasu a nan kawai za'a shiga dasu later..." bata kuma jiran amsar sa ba tayi shigewar ta, murmushi yayi cikin zuciyar sa yace wannan duk yanda akayi masifar Hajiya tayo.... Yana gama sauk'e kayayyakin ya kira AT ya sanar dashi, AT ya masa godiya kafin yace "Suna hanyar Kanon suma. Ashfaq ya masu fatan sauk'a lafiya kafin ya shige motar sa ya bar gidan, tunanin yanda ya tab'a ganin mai shigen fuskar matar can yake, wata zuciya tace k'ila dai ka had'a kanninta dana wata ne, d'an tab'e baki yayi kafin ya maida hankalin sa ga driving... ************ Basu suka iso Kano ba sai wajajen isha, gaba d'aya a gajjiye suke, amarya sai k'anshi turarruka ake, an tsuma da maganin mata iri da kala, batada burin da ya wuce a barta a d'akinta daga ita sai angonta... Ta d'aga idanu tana duban d'akin k'anwarta Aysha wanda yake a matsayin nata a yanzu, murmushi tayi mai tarin ma'ana, cikin zuciyarta take furta _Aysha inama kina gani na, yau gani nan na mallaki gidanki, mijinki da kuma yaranki, tabbas ni ce nafi cancanta da wannan rayuwar ba ke ba, da sannu Tahir zai zama nawa ni kad'ai.._ ta kuma murmusawa kafin ta haye saman gado. Babu k'awar data rako Shema'u don dama ita bata yarda da wata k'awa ba sabida ita kanta bata yarda da kanta ba, wani sa'in har tsoron kanta take sabida zata iya k'ulla sharri ma kanta, tunda Aysha tayi aure ta yaye k'awaye dama yawanci sabida kirkin Aysha suke zuwa dashike duk tare sukayi sch.. AT kuwa suna isowa gidan Hajiya ya nufa, sam bai gane kansu ba daga Hajiyar har Maryamar, sama-sama Hajiya ta masa barka fuska babu walwala kafin ta kunna radio d'inta ta shige uwar d'aka tana sauraren zab'en dare, don ya fiye mata sauraren Attahiru. Parlorn ya rage saura shida Maryama, yana hankalce da ita yanda ta koma sukuku gaba d'aya yana son tambayarta meke damunta. D'an duba agogon hannunsa yayi kafin yace "Maryam ina so ki fad'a min gaskiya, be honest with me.." Gabanta ya yanke ya fad'i, toh me Uncle zai tambayeta yanda yayi maganar sounds serious... Tana cikin tunanin ta jiyo muryar sa na fad'in "Hajiya tayita fad'a ko, tayi fushi sosai koh..?" Jikinta yayi sanyi don sam bata kawo abinda zai tambayeta kenan ba, d'an saita kanta tayi kafin tace "A'a batayi fad'a ba, bata ce komai ba..." AT ya sauk'e ajiyan zuciya kafin ya shafi goshinsa yace "And you yaya baki tafi can gidan bikin ba, ko kema taya Hajiya kike ne...?" D'an murmushi tayi gamida sadda kai kana tace "A'ah ba haka bane, kawai banjin dad'i ne.." AT ya kafeta da idanu kafin yace "Meke damunki...?" Nan fah ta tuna ashe fah Uncle likita ne, tasan bazai k'yaleta ba har sai ta fad'i masa abinda ke damunta... Kame-kame ta soma tama rasa me zata ce, cikin sauri tace kanta ne ke ciwo.. Ya k'ura mata idanu kafin ya soma jero mata tambayoyi gameda ciwon kai d'in "Gefe ne ke maki ko kuma gaba d'aya ne, yaushe ya soma maki, kinsha wani magani ne...?" Gaba d'aya ma ta rasa wanne zata amsa masa cikin daburcewa tace "Eh eh na sha paracetamol, yama daina..." Yayi shiru yana dubanta kafin yace "Idan bai daina ki sanar dani kinji koh." Gyad'a masa kai tayi alamun toh, daga nan ya sata ta kawo masa abinci ya zauna yana ci yana jefo mata hira jefi-jefi wanda akasarin hiran gameda karatu ne,... Maryama dai um da um-um kawai take amsa masa don kuwa gaba d'aya ji take ta kasa sakewa dashi, kaman ba shine Uncle d'inta wanda suka shak'u a baya ba, wanda suke hana Hajiya cin goro tare da plans d'in su...Shi kansa AT ya lura da hakan.. Wajajen nine ya mik'e ya lek'a d'akin Hajiya zai mata sallama nan ya samu tayi barci, daga nan kuwa ba bacci Hajiya tayi ba jin lek'owar sa ne yasata lumshe idanu... Kallon Maryama dake tattara plates d'in da yaci abinci yayi kafin yace "Muje mota ki karb'i sak'o,." amsa masa tayi da toh, bayan ya fice tabi bayansa... Front seat ya bud'e ya ciro wani shopping bag kafin ya mik'a mata yace "here tsaraban ki, and gobe Shema'u zatayi event don't tell me kanki na ciwo, Malam Habu zaizo ya kaiki..." K'ak'aro murmushin k'arfin hali tayi kafin ta shiga gyad'a masa kai, da k'yar ta lalumo kalmomi saman harshenta tai masa godiya.. Har ta juya ta soma tafiya ta jiyo daddad'an muryar sa ya ambato sunanta "Maryam" Juyowa tayi suna duban Juna, hasken wutan lantarki ya haske fuskokin su, a hankali ya furta "Baki min murna ba." Nanma k'ak'aro murmushi tayi kafin tace "Kayi hak'uri Uncle, congratulations Allah Ya bada zaman lafiya, Allah Ya kad'e fitina." Har cikin ransa yaji dad'in addu'an data masa, murmushi ya sakar mata kafin ya amsa da amin had'i da mata godiya, sallama suka kuma yi kafin ta soma tafiya cikin yanayin tafiyar ta.. Gaba d'aya sai yaji jikinsa yayi sanyi, ya jima a wajen shi kansa baisan tunanin me yake ba kafin ya shige motar sa ya tada... Tana shiga gida ta bud'e jakan ta zaro abinda ke ciki, riga ce Navy blue mai kyau irinta larabawa wanda tasha ado da duwatsu, haka kurum ta tsinci kanta tana mai yin murmushi, rungume rigar tayi tana shak'an k'amshin turaren Uncle da tuni ya kama jakan da rigar.... Yana isowa gida saman sa ya nufa ya shiga bathroom ta sakar ma kansa shower don a gajjiye yake lib'is.. Shema'u kuwa tana jin shigowar sa ta d'aura hijabi saman rigar baccinta ta nufi nasa parlorn, bata gansa a parlor ba hakan yasata shigewa master bedroom d'insa kai tsaye irin batada shamak'i d'in nan... Tana jin alamun tab'a k'ofa zai fito tayi saurin rarumo abin sallah ta haye kai tamkar mai sallan gaskiya... AT da fitowar sa kenan daga bathroom towel d'aure a kunkumin sa sai d'an k'arami yana goge sumar sa har ya d'an razana da ganin mutum saman abin sallah, gabansa ya yanke ya fad'i don ba kowa ta tuno masa ba illa Aysha... Nan yayi tsaye yana kallonta, ganin tana k'ok'arin sallamewa yasa sa saurin komawa cikin closet d'insa, jallabiya fara k'al ya zura kafin ya komo cikin d'akin, zuciyar sa k'unshe da tambayoyi me ya kawota d'akinsa, b'angare na zuciyar sa tace yaya zakayi ma kanka wannan tambayar, ko ka mance matar ka ce, wata zuciyar tace toh ai ko 'yan biki basu watse a gidan ba, wata b'angare ta basa amsa kai tsaye ka mance bazaura fah ka aura ba budurwa ba, koma yaya ne zata jira ya soma zuwa gareta.... Muryar ta Ya jiyo tanai masa sannu da gajjiyan hanya... A d'an tak'aice ya amsa ba tareda ya k'ara da komai ba, kaman tasan tunanin da yake nan ta soma fad'in "Wllhi su Inna Larai ne wai zasu kwana a d'akin nawa, gaba d'aya sun cike d'akin shiyasa nazo nan, I hope bazan tak'ura ka ba.. Murmushi ya sakar mata kafin yace "Ko kad'an this your house ai..." Wayyo dad'i kaman ya kar Shema'u.. Akan idanunsa ta yaye hijabin jikinta, AT yayi saurin d'auke idanunsa domin kuwa wata kafiran rigar bacci ne a jikin Shema'u.. Ta nufi k'ofan bathroom tana satan kallon sa, nan ta d'ebi jiki ta zube a k'asa da gangan, cikin sauri ya nufeta yanai mata sannu yana tambayarta bataji ciwo ba, k'in tashi tayi sai d'an kama kunkuminta da take yi cikeda k'issa. Ya d'an rank'wafo yana k'ok'arin d'agota kaman wacce take jira nan ta shige cikin jikinsa..... *Sameena Aleeyou Mrs* [2:01PM, 3/12/2018] ‪+234 803 533 3121‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *28* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ *Anmunah* *Aysher cool* *Fatima Tasi'u* *Maman Ikram* *Mum Izaddeen* *Ummu Jawad* *Xee Mako* *Suwaiba* *Miss k'anwar AT* *Mum Hisham* *Mum Mus'ab* *Da sauran members na MUSHAA KARATU wannan shafi damarku ce ina k'aunarku da zuciya guda ❤ A ringa ragar ma amaryar AT 😹* Gaba d'aya ta cukwikuyesa ta shige cikin k'irjinsa sai kukan shagwab'a take tana kuma narke masa, da k'yar AT ya samu ya masu masauk'i saman _chaise lounge_ irin kujeran Aina'un nan dake can gefe a wani angle cikin d'akin. Sannu yake kan faman mata don a zatonshi ciwo wajen ke mata, ya yunk'ura zai tashi yana fad'in bari ya d'auko man zafi..... Tana ganin ya mik'e ta kauda kai gefe tana murna harda wani karkashe idanu tsaban nishad'i da take ji... Fairst aid d'insa ya bud'e ya ciro man zafi kafin ya dawo gareta, k'ank'amesa ta kuma yi tana fad'in kujeran ya matse ta ya kaita gado... AT ya d'anyi jim kafin ya kamota yayi mata masauk'i saman gado, mik'a mata man zafin yayi yace ta shafa a wajen.... Kuka ta fashe masa dashi tana fad'in bazata iya ba... Shi kuwa gaba d'aya da zata gane data k'yalesa domin kuwa gaba d'aya jinsa yake wani iri tamkar bashid'in ba... Hannunsa ta kamo ta d'aura saman waist d'inta yanda ke mata ciwo a k'aryarta. Gyara zamansa yayi k'irjinsa na bugawa sanda ta yaye masa d'an b'ingilan d'in rigar tata wanda da kad'an ya wuce kanpai dama, wani ikon Allah duk wani sha'awarta ya addabesa a baya sai ya nema ya rasa, harga Allah k'yamarta ya soma ji ba tareda sanin dalili ba, ba don yaso ba ya soma shafa mata man a wajen tsikar jikinsa sai tashi yake, baisan dalilin da ya haifar masa k'yank'yaninta lokaci guda ba. Shema'u kuwa sai faman lumshe idanu take taji lallausan hannu irin wanda bata tab'a jiba a jikinta, ba irin nasu Alh Aminu ba, gaba d'aya lokaci guda ta wani susuce, yana yunk'urin tashi ta d'ale jikinsa gaba d'aya ta soma masa wasu salo, tun yana k'ok'arin k'watan kansa har ya kasa, gaba d'aya shi k'aik'ayi ma jikinsa ya soma masa dama haka yake something small can irritate him, kuma duk k'ank'antan abu idan yayi irritating d'insa take zai soma developing allergy, lokaci guda skin d'insa yakan turning red yayi ruhu-ruhu tamkar mai borin jini. So yake ya k'wata kansa daga irin mayen sunbatan da take masa ya kasa ga d'an banzan k'aik'ayi da jikinsa ke masa, kan kace me amai yaji na yunk'urin yi, wani irin mik'ewa yayi ya nufi bathroom a tamanin..... Shema'u ta mik'e tana rarraba idanu tana tambayar kanta lafiya, meke damunsa... Cikin sauri ta nufi bathroom d'in yanda ta gansa sai k'waza amai yake ga skin d'insa yayi jazur yayi ruhu-ruhu tamkar borin jini, murya na rawa ta k'araso ta dafasa tana masa sannu... Taimaka masa tayi ya kintsa kansa kafin ta rik'oshi zata dawo dashi cikin d'akin yace mata zai iya... Kallo ta bisa dashi har ya fice daga bathroom d'in yana mai goge fuskar sa da k'aramar towel... "Bantan ubancan!! " ta furta a hankali, ciwo bai tashi zuwa masa ba sai daren amarcin su, haushi ya taru ya turnuk'e Shema'u, ga wani kafiran buk'atar sa da take ji na kuma taso mata, gyara bathroom d'in tayi ta nufo d'aki ta tarar baya d'aki, a parlor ta hangesa yana waya.. "Hello ka shiga gida ne..?" Daga d'aya b'angaren Hisham yace "Ango kasha k'amshi, hope komai normal, ai ban zaci zaka iya kirana ba kana can kana kwasan gara mutumina..." ya k'arashe teasingly. Gajeren tsaki AT yayi kafin yace "Kaga calamine lotion da Antibiotic zaka kawo min pls..." Hisham ya had'iyi dariyar da yake kafin yace "Badai amarya bace babu lafiya koh.." "Kaikam ka kawo min yanzu pls, sai na jika.." daga haka katse wayar yayi. Nan Hisham ya soma tunanin AT yanada Allergy wanda duk abinda ya gani ya d'aga masa hankali ya basa k'yank'yani toh fah yana tashi, a fili ya furta "Allah sa shegiyar nan ba k'azamin salon karuwanta ta tashi nuna masa ba.." cikin sauri ya zari car keys d'insa ya fice.... Fitowa Shema'u tayi duk jikinta yayi sanyi kaman ta cinyesa haka takeji, ta k'araso yanda yake cikin salo na tafiya, zama tayi gefensa tanai masa sannu, nan taga gaba d'aya fatar sa tayi jazir... K'ak'aro murmushi AT yayi don shi harga Allah tausayi ta basa baisan dalilin da ya haifar masa k'yank'yanin ta ba duk da cewa ita d'in 'yar gayu ce ta ajin k'arshe, a zahiri baijin k'yank'yanin ta amma kusantar ta da ya tasamma yi shi haifar masa da k'yank'yanin.. "My Dr kana son wani abu ne..?" ta tambaya tana kashe murya. D'an girgiza kai yayi kafin yace "No babu komai kije ki kwanta akwai gajjiya a tattareda ke, sannan kema bakida lafiyan, ko wajen ya daina maki ciwon ne?" Murmushin yak'e tayi kana tace "Eh ya daina, kaine patient yanzu, amma dama kanada allergy ne Dr, kodai kaci wani abinda baka saba ci bane a garinmu or maybe you're allergic to it baka sani ba...?" tayi tambayar cikeda nuna damuwa. D'an murmusawa kurum yayi kana yace "Kar ki damu zai daina wani sa'in haka yake min, Hisham zai kawo min magani yanzu, na duba first aid d'ina babu, kije ki kwanta kinji I'll be fine.." Marairaice fuska tayi tana wani babbank'arewa uwa gashashhiyar kaza kana tace "My AT wllhi bazan iya bacci kana cikin wannan hali ba pls let me take care of you..." AT ya d'anyi jim kafin ya sakar mata murmushi cikeda tausayinta, kai shi wannan k'yank'yani nashi shi kansa na damunsa shiyasa ba ko ina yake iya cin abincin ba sabida yasan kansa, ko abincin restaurant ba ko wanne yake ci ba don wani jik'on yana cin abincin da bai kwanta masa ba allergy d'insa zai tashi, gashi yanzu abin yayi tsamari har kan matar sa.... Suna nan zaune wayar Hisham ya shigo masa, mik'ewa yayi ya fice ya karb'o magaungunan, Hisham yasha mamaki ganin yanda jikin AT yayi, tabbas jikinsa ya basa yanzu haka Shema'u ce tayi irritating nasa don yasan waye AT d'in.... Ba don yaso ba Shema'u ta shafe masa maganin uwa zata had'iyesa, dukda maganin dake shafe a jikinsa bai hana Shema'u shigewa cikin jikinsa ba a haka bacci ya d'auketa AT kam sam babu bacci a idanunsa, a hankali ya zare jikinsa yana k'are mata kallo, ikon Allah ga Mace har Mace amma wllhi ji yake bazai iya kusantar ta ba, wato da can da sha'awarta ya addabesa sharrin shed'an ne, shi ya ringa k'awata masa ita ko zai nemeta da alfasha sai kuma Allah yasa shid'in baya daga cikin mazinata, sai gashi da ya aureta ya nemi sha'awar ya rasa saima akasin haka. Sauk'e nannauyan ajiyar zuciya yayi kafin ya koma saman couch yayi kwanciyar sa.... Da asuba koda ya tasheta tayi sallan asuba komawa tayi taci gaba da baccinta don dama sallan ba wai ya dameta bane, koda ya dawo a zatonsa tayi sallah k'arshe ma a parlor ya k'araci kwanciyar sa gari na soma haske ya tsala wankar sa ya shirya tsaf cikin lallausar yadi ruwan k'asa da b'akar hula, kumburin jikin nasa sun b'ace sai rod'i-rod'in ja da skin d'in nasa yayi.... ********* Tun daga veranda yake jiyo muryar Hajiya tanai ma Maryama fad'an ta tashi taje ta cire abinda ta d'aure k'irjinta dashi, taci gaba da fad'in "Inyi banda taurin kai irin naki, sarai kin sani muddin kina al'ada k'irjinki kumburi suke suyita maki ciwo ai sai ki sarara ma kanki koh, banda felek'e kin matse kanki kin tak'ure ba dole suke maki ciwo ba , haba wannan tak'ura kai har ina, idan ba fita zakiyi ba sai ki kwab'e rigar maman kisha iska ai tunda a cikin gida kike inyi..." Sallaman AT ne ya katse Hajiya... Duba d'aya Hajiya ta masa ta tab'e baki had'i da d'auke kai gefe, Maryama kuwa kamar ta nitse a k'asa haka taji, takaicin Hajiya ya turnuk'eta , kai Allah yasa Uncle bai jiyo maganganun da Hajiya take ba... Waje ya nema ya zauna yana satan kallon Maryama yake gaida Hajiya. Hajiya ta wani foze sai amsa masa take a dake, ta jawo ledar goron bikin 'yar mak'otansu da aka kawo mata ta wangale ledar gaba d'aya don AT ya gani yaji haushi... Da k'yar Maryama ta gaida shi sabida ciwo da k'irjinta suke mata... Kaiii! Karkatowa Hajiya tayi tana duban Attahiru don d'azu a fige ta kalle sa gaba d'aya bataga sauyin da fatar tasa tayi ba... Baki sake ta bisa da kallo.. Tafe hannaye ta shigayi tana sallalalmi wanda yasa daga AT har Maryama suka bita da kallo suna jira suji abinda ya sata jero salati "Attahiru yanzu kaima duk hasken fatar taka bata isheka ba saida kod'add'iyar can ta shafe ka da man bilicha (bleaching) d'in kaima, na shiga uku ni Fad'ime kaima ka koma roba-roba fuska uwa kakin soji, Oh Allah dai ya yaye maka mugun k'ullin da suka maka..." ta k'arashe tana rik'e hab'a Ba AT kawai ba harta Maryama dake faman cije-cijen labb'a saida ta k'unshi dariyar ta.. AT ya d'an shafi k'eyarsa baice komai ba. Domin baima san me zai soma ce mata ba, sai lokacin Maryama ta d'ago tana dubansa suka kuwa had'a idanu, saurin sadda nata kan k'asa tayi don ba komai ta tuna ba illa Uncle fah yanzu mijin Aunty Shema'u ne... "Kai nake saurare Attahiru ko salon naka asirin da su Kulun suka maka kenan iyi..?" "A'a Hajiya kin mance tun ina k'arami ai inayin ciwo makacin haka, me zai had'ani da bleaching kuma Hajiya.." ya bata amsa still yana satan kallon Maryama da keta tamke idanu alamun zogi. Ganin hankalin su ya karkata kan zancen da suke yasata mik'ewa a sulale ta wuce uwar d'aka... "A'ah yo dole nace haka tunda ka zama shanyayye sai yanda Kulu da d'iyarta sukayi da kai, an tofa maka a ruwa ka sha..." AT ya d'an shafi goshin sa yanaso ya kawar da zancen, mik'ewa yayi ya isa gaban flask d'in ruwan zafi dake gefe tareda kayan kari ya shiga k'ok'arin bud'e flask d'in. "Meye haka, ko ajiya kayi ne a ciki, inyi.." ta fad'i tana watsa masa kallo. Komawa yayi ya zauna baice komai ba, uwa maraya. Ta mik'e tana ci gaba da sababi tana fad'in "Banda bak'in gulma da munafunci ka baro amaryar taka kazo kana neman abin kari a nan, ai sai kaje amaryar ta dafa maka ruwan shayin wannan kam k'walelen ka ehe.." Tagumi ya rapka uwa wanda akai ma mutuwa. ************* Da lalaume ta soma sai faman shafa gado take tana son rungomo angon nata, saidai fah wayam taji babu ango babu dalilin sa, ta mik'e a zabure ta nufi bathroom nan ma baya nan, parlor ta nufo nan ma sammakal, bak'in ciki ya taru ya turnuk'e mata mak'oshi, harga Allah da matsanancin buk'atar AT ta kwana gashi bata sami yanda take so ba, babban abinda yafi d'aga mata hankali shine kardai ace Office ya fice ranar amarcin su, Shema'u fah ta cika tayi fam... For the first time data soma neman abu bata samu yanda take so ba, itafah so na hak'ik'a take so AT ya nuna mata, a ajiye maganar wad'annan shegun yaran nasa don ita ba domin su ta auresa ba ma kanta tayi tanadin sa, sai faman girgiza take ita kad'ai tana huci, wayarta ta rarumo ta shiga neman layin Hisham don shine kawai zai gaya mata ina AT ya tafi da uwar safiyan nan, tasan bazai wuce yana office ba. Yana ganin wayarta saida yayi wata kafiran dariya kafin ya d'aga.. "Amarya kinsha mai..." ya fad'i yana murmusawa. Tsaki Shema'u ta buga sabida takaici kafin tace "Ina Ahmad.?" "A'ah yaya zaki min wannan tambayar keda kuka kwana tare.." Tsaki ta kuma yi kafin tace "Hisham ka fad'a min idan AT office ya taho.." Hisham yayi dariya kafin yace "Shege AT salihi mai ra'ayi kikeji, wllhi bai taho office ba, amma nasan idan dai bashi a gida toh gidan Hajiya ya tafi..." bai kai aya ba ta katse wayar tana tururri, Kai ina da sakel, bazai yuwu tayi sharing AT da kowa ba, AT nata ne, ya kamata tayi taking next step akan gina soyayyar ta a zuciyar AT da kuma raba Hajiya da AT, tana nan tsaye tana huci ta jiyo kukan Ni'ima a parlor tana neman Daddyn ta.. Wani uban tsaki ta buga kafin ta nufo parlorn a fusace, kafiran tsawa ta daka mata wanda ya sata had'iye kukan babu shiri ta shiga matsawa da baya cikeda tsoro. Tuni Sajida ta nufo parlorn sabida ta jiyo kukan Ni'ima, Shema'u tayi saurin k'arasawa ta d'auki Ni'ima dake faman shan zuciya tana jijjigata take fad'in "Sorry Baby Daddy gidan Hajiya ya tafi, bari yanzu zan kaiki ki gansa ko, yi shiru Baby na, zaki je Daddy..?" Ni'ima tayi saurin gyad'a kai alamun Eh.. Sajida sai murmushi take ta k'araso tana gaida Auntyn nata tana fad'in "Iyye Ni'ima 'yar gatan Daddy da Aunty.." Shema'u ta kuma rungume Ni'ima dake k'ok'arin k'watan kanta, ta saci kallon Sajida ta zare ma Ni'ima idanu tuni yarinyar ta lafe a jikin Shema'u, "K'warai kuwa 'yar gatan mu ne 'yar auta ba yanzu ma kuwa zan kaita Daddy..." Sajida dai dariya tayi cikeda jin dad'i... ********** Tausayin sa ya cikata domin kuwa sai lek'en sa take ta labule, wannan shiri nasa tasan k'ila office zai wuce tunda ya fito da sassafe, gaskiya bazata iya barinsa ya tafi aiki haka da yunwa ba, daurewa tayi ta mik'e ta zura hijabinta kafin ta fito parlorn.. Idanunsa naga wayar salulan sa amma jikinsa ya basa ta fito parlorn, d'ago kai yayi suna duban juna.... *Sameena Aleeyou Mrs* [6:53AM, 3/13/2018] ‪+234 803 315 3757‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *29* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝_ *ZAUREN BIEBEE ISA (ZBI) ina yinku ina k'aunarku da zuciya guda, and this spectacular chapter is yours guys 💘 aradu kuyi yanda kuke so dashi amma banda tsinema Amaryar Attahirun Hajiya hilis 😹❤* Sauk'e idanunta tayi don harga Allah Ya bata tausayi yanda taga fatarsa tayi rod'i-rod'in ja, kenan bashida lafiya... "Ammm me za'a kawo maka uncle.?" ta tambaya tana wasa da 'yan yatsun hannunta. Shikam AT sosai ta burgesa dukda yaji Hajiya tana fad'in batada lafiya hakan bai hanata fitowa nema masa abinda zaici ba, lallai SHAK'UWAR SU da Maryama daga Allah ne. Murmushi ya sakar mata kafin yace "Ba naji Hajiya na cewa bakida lafiya ba, kar ki damu jeki kwanta abinki kinji..." Gabanta ya yanke ya fad'i shikenan yaji maganganun Hajiya, wayyo Allahn ta, wani sabon kunyarsa ya sauk'o mata. AT na hankalce da ita yanda ta tsaya uwa dogariya ta kasa gaba ta kasa baya, ya gane kunyar sa taji. D'an gyaran murya yayi kafin ya kuma cewa "just go and rest kinji..." Tayi k'ok'arin saita kanta kana tace "Ai na warke ma bari na kawo maka shayin." Bata jira amsar ba ta soma tafiya... Bud'e murya ya d'anyi ya ambato sunanta. Cak ta tsaya had'i da komowa ta rusunar da kanta... AT yaci gaba da fad'in "Kin gane just black tea with honey zaki kawo min.." Gyad'a masa kai tayi kafin ta shige.... Hajiya da mai masu d'an aikace-aikace na gida ta samu a kitchen d'in sai hira suke wanda akasarin hiran maganar auren AT ya shafa. Maryama bata bi ta kansu ba ta shiga k'ok'arin had'a shayin Uncle... Hajiya na hankalce da ita, karkatowa tayi tana dubanta yanda taci magani sabida tsaro tasan ba k'aramin aikin Hajiya bane ta hanata had'a masa shayin... Aiko bata gama tunanin hakan ba Hajiya ta katse ta da fad'in "Uwar me ya fito dake kike wani k'ok'arin had'a masa shayi keda bakida lafiya inyi...?" Maryama dai bata amsa ta ba baki a ture take gudanar da aikin nata... Fizge mug d'in Hajiya tayi ta soma sababi tana fad'in "Bazaki had'a masa ba, banda shegen gulma da iyayi ya wani kwaso k'afa jiki duk a daddauje wayasan uwar me su Kulu suka shafe shi dashi fatar sa ta koma haka, uwar me ya hana matar tasa had'a masa inyi..." Tana soma magana muryarta ya soma rawa sai kuka.. " Ni dai wllhi Hajiya sai na had'a masa, haba haba bakijin tausayin sa ne, bashida lafiya fah, fisabilillahi Hajiya idan baizo gidanki ba gidan wa zaije shi, wllhi gaba d'aya kin daina tausayin Uncle...." Daga Hajiya har Baaba pause sukayi suna kallon Maryama data dage harda kukan ta, shi kansa AT d'in lab'e yake yana lek'en su, dad'i ne yaji ya mamaye illahirin zuciyar sa ganin yanda Maryama take kare shi a wajen Hajiya, saidai a wani b'angare na zuciyar nasa yana jin zafin zuban hawayen nata... Hab'a ta kame tana dubanta kafin tace "Tooh.!!! Eh ina ganin salo ni Fad'ima, idan baka mutu ba kasha kallo, toh yayi, daina b'ata hawayen ki idan dai tausayin Attahiru kikeji kin d'auko aiki ma kanki tunda shi ba tausayin kansa yake ba, da ace yana tausayin kansa da bai soma yunk'urin auren d'iyar Kulu ba, maza had'a masa ai kunfi kusa.." Baaba dai sai dariyar su take, idan kana gidan Hajiya bakayi hawan jini ba. Ganin ta kusan k'arasa had'awa yasa sa saurin dawowa parlor yayi zaman sa... Da sallama ta shigo ta ajiye masa k'aramar parantin a gaban sa. Sannu yayi mata had'i da godiya, zata shige d'aki ya kuma kiran sunanta, komowa tayi ta zauna daga can gefe still idanunta a k'asa. "Yaya jikin naki..?" ya tambaya yana juya teaspoon cikin mug. A hankali cikeda kunya ta furta "Naji sauk'i.." D'agowa yayi ya dubeta ba tareda ya furta komai ba kafin ya soma kurb'an shayin.. Har ta cire rai bazai kuma cewa komai ba ta kuma jiyo muryar sa yana fad'in "Dama haka ne yake maki every month.?" Wayyo Allahnta haba Uncle shi meyasa ya faye tambaya ne, ko duka likiticin haka suke... Ta fad'i cikin zuciyarta... Shigowar Hajiya ne ya cece ta bata amsa tambayar ba... Tahir saida ya kusan k'warewa jin Hajiya ta shigo, ta dubesa tayi k'wafa. Shiko sai sansan da kai yake uwa munafuki, tashan NTA yake kallo program d'in da ake da sanyin safiya wato _good morning Nigeria_ . Hajiya ta d'auki remote saman hannun kujera ta shiga canza tasha kawai don ta bak'anta ma AT, har ransa yake son Hajiyar sa, gaba gad'i take lamranta.... Maryama ta k'unshe dariyar ta ta silale d'aki tana satan kallon AT dake faman sipping shayinsa, yanayi yana satan kallon Hajiya yanda take dangwala remote control d'in da k'arfi tana manna sa jikin decoder d'in uwa zata shige ciki, magana ne bai kuma isa yayi ba... ********** Saman chaise lounge ta ajiye Ni'ima dake faman shan zuciya alamun taci kuka, bushesshun hawaye kwance saman fuskar yarinyar abin tausayi. Ta gama fente-fenten da zatayi a fuskar nata uwa zabo bakin nan yasha jan janbaki sosai tayi kama da tsoffin kilaki, tana shafa powder ta juyo ta watsa ma Ni'ima wani kafirin kallo ganin yanda taketa shan zuciya... Tuni yarinyar ta had'iyi d'an sauran kukan da take.. Wayarta ne ya soma ringing ta k'arasa ta d'aga, ganin Hisham ne ya sata shigewa bathroom bayan ta bud'e murya tace ma Ni'ima "Idan kika fita sai na yanka ki da Knife, ai kinsan Knife koh..?" Ni'ima ta gyad'a kai cikeda tsoro. Shema'u tayi murmushi mai firgitarwa kafin ta gyad'a kai tace "Good, you stay right there kinji koh..." ta kuma nodding kan nata a tsorace. "Hello ya iso office d'in ne.?" ta tambaya tana muzurai. Fashewa da dariya Hisham yayi kafin yace "Iska na wahal da mai kayan kara, ke wai ya akayi haka ne, tell me what really happened last night." ya k'arashe yana wata ja'iran murmushi. Tsaki Shema'u tayi kafin tace "You stay out of this Hisham, sirrina da mijina zan fad'a maka ko me kake nufi iyi.." Dariya Hisham yayi ya wani shafi hab'arsa kaman tana ganin sa kafin yace "Ai nafi mijin naki sanin sirrinki, don't forget we are allied..." Gajeren murmushi tayi kafin tace "Kana b'ata min lokaci, gidan uwar sa na nufa zan dawo dashi don yau ranata ce bazan sharing da kowa ba.." Hisham yayi murmushi mai sauti kafin yace "Billahillazi kar kiyi gigin zuwa gidan Hajiya yanda take cikeda haushin auren ki da AT, duk barinki ki ina mai shawartanki kiyi wani makircin daban amma kar ki kwashi sawayenki zuwa gidan Hajiya, kin gannin nan namu batazo d'aya ba shiyasa ma kiga ban faye zuwa ba, idan kikaje kuma you'll regret..." Shema'u sai faman huci take takaicin Hajiya ya cikata, kafiran murmushi tayi kafin tace "Nasan abinda zanyi, sai munyi waya..." Daga haka ta katse kiran. D'aki ta dawo ta sami Ni'ima a kwance saman kujeran ta tak'ure waje guda har kaman baccin wahala na son d'aukanta... Hannu tasa ta mintsileta, yarinyar ta tashi firgit zatayi ihu Shema'u ta toshe mata baki da hannun ta... Zare idanu tayi tace mata "Quite" shiru Ni'ima tayi tana kallon Shema'u uwa taga dodo.. Shema'u ta sassauta rik'on data mata lokaci guda ta marairaice fuska ta rik'e hannayen Ni'ima kafin tace "Baby I'm sorry, I'm sorry kinji, I'm not a monster, spirit d'in Mummyn ku ne ya shige ni shiyasa na zama Monster, itace real monster, and idan kika fad'a ma Daddy abinda ya faru zata dawo ta kuma shiga jikina tasa na yanka ki da knife kema ki tafi yanda ta tafi ki dawo Monster kema, kina so ki dawo Monster..?" A razane Ni'ima ta girgiza kai alamun a'a. Shema'u ta murmusa kafin ta gyad'a kai tace "that's my girl, oya let me call your Daddy, kiyi kuka sosai kice masa you want see him, kinji koh, idan bakiyi duk abinda na saka ki ba, spirit d'in Mummyn ku Monster zai shige jikina na yanka ku gaba d'aya harda Daddy dasu Jamal..." tsoro ya bayyana a idanun yarinyar.. *********** Yana shirin mik'ewa wayar Shema'u ke shigo masa, aiko yana d'agawa yaji kukan Ni'ima tana fad'in ya dawo gida, Shema'u daga can sai zare mata idanu take tana mintsilinta lokaci guda ta kashe murya ma AT tana fad'in "My AT pls kazo gida tak'i yin shiru and kaman tanada fever ma...." Ai a sukwane ya mik'e yana fad'in "Fever!! Gani nan zuwa, pls Shema'u don't leave her side, just take care of her yanzu zan iso" daga haka katse wayar yayi yanai ma Hajiya sallama... Ta bisa da kallo kurum cikeda tausayi a fili ta furta "Ya Allah bana cutar da kowa da harshe na idanba shiga hurumita kayi ba, Ya Allah ka yaye ma Attahiru k'ullin dasu Kulu suka masa.." ta k'arashe zuciyarta cikeda tausayin d'an nata. ... *********** Bata bar Ni'ima ta tafi wajen Maama Juu ba koda suka gama wayan da AT, saima kunna mata cartoon d'in _Moana_ da tayi a iPad d'in kafin ta mata umarni da kar ta fice, d'akin Sajida ta nufa yanda ta ganta tayi jigum dukda ga hayaniyar mutane 'yan biki a parlorn k'asa amma Sajida ta k'ule a d'aki tasan akwai wata a k'asa, tana son ji ko akwai improvement da aka samu tunda har yau bata samu tayi waya da Buzu ba tunda aka soma biki . [8:09AM, 3/14/2018] ‪+234 803 315 3757‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *30* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ Zaune ta hangi Sajida tayi jigum ta k'ura ma window idanu da alama ta jima a hakan. Maida k'ofar tayi ta tura a hankali kafin ta d'aura murmushi saman fuskarta ta k'arasa shigowa cikin d'akin, zama tayi gefen Sajida had'i da dafe kafad'un ta, sai sannan Sajida tasan Shema'u ta shigo.... Fuskar tausayi Shema'u ta saka lokaci guda ganin Sajida ta kasa furta mata komai sai rungumarta da tayi... "My Sajee meke faruwa, pls sweetheart share it with me, kinsan bana son ganinki cikin damuwa, fad'a min meke damunki sweetheart..." ta k'arashe fuska uwa zata kurma ihu. Sajida ta goge hawayen da suka zubo mata kafin ta soma fad'in "Aunty wllhi ina son shi, bansan abinda na mashi zai b'ata masa rai ba, he's not answering any of my calls, na masa text bai min replay ba, Aunty pls banaso na rasa shi wllhi kullum k'ara sonshi nake..." Shema'u ta shiga had'e tunani tana waresu kafin ta kamo hannun Sajida tace "Sajee tell me, fad'a min me ya had'a ku...?" D'ago idanu Sajida tayi kaman zatayi magana sai kuma ta fasa, don batama san me zata soma fad'a mata ba. Shema'u ta tsareta da idanu sai sak'e-sak'e take tana warwarewa... Ganin Sajida ta kasa fad'a mata komai yasata tunanin wani babban abin Buzu ya mata, kuma ga dukkan alamu Sajida bataji dad'in abin ba... Murmushi ta sakar mata kafin tace "Sweetheart idan baki so ki sanar dani fine, na fahimce ki, sannan wannan shi ya nuna min kina son Haris sosai, karki damu relationship ya gaji hakan, ki kwantar da hankalin ki kinji babu wani abu, dole dama zaku samu sab'ani sannan ku fixing abunku da kanku kin fahimta, yanzu kar ki sake kiransa zakiga da kanshi zai nemeki, kamar yanda sukace if they love you they'll come back. Kar ki damu kinji sweetheart, trust me kiyi yanda nace da kanshi zai nemeki, don nasan babu namijin da ya kai ya wulak'anta min daughter ta sabida every man's type ne..." Sajida ta murmusa kafin ta rik'e hannun Shema'u tace "Aunty wllhi bansan yaya zanyi ba without you, thanks for everything, Allah Ya baku farin ciki mai d'aurewa keda Daddy, ke kad'ai tol babu k'ari, our family is complete bamu buk'atan wata..." Dad'i kaman ya kashe Shema'u, hugging Sajida ta kuma yi tana wani kashe murya take fad'in "Oh sweetheart Allah Ya amshi bakin ki..." Tana ficewa daga d'akin nata d'akin ta wuce har lokacin Ni'ima na zaune tana kallo, Shema'u ta sakar mata murmushi kafin ta shige bathroom, layin Buzu ta shiga dialing, bugu uku ya d'aga murya a tamke.. Cikeda masifa tana huci ta soma fad'in "You such an imbecile, banga wani improvement ba saima tsoronka da ka haifar mata, fad'a min what really happened..." Saurin katseta yayi yana fad'in "Hey.. hey just hold on, don't you dare call me an imbecile or whatever, you talk to your niece first, kinsan ban saba hark'a da k'anan yara irinta ba, hugging d'inta kawai nayi shikenan tayi fushi, ina kiranta har tana rejecting, babu macen da take min haka coz duk macen da kika ganni da ita nemata tayi, mace d'aya nake so and ita kad'aice zatayi yanda take so dani... Maryama, Maryama ce kawai zan d'auki duk abinda zata min, sannan idan kika tak'urani zan ajiye maki aikin ki..." Shema'u ta shafi goshinta had'i da d'anyi k'ara kafin tace "Wllhi k'arya kake, wllhi sai ka lalalata ta idan kana so ka mallaki Maryama, remember Dr AT shine a matsayin mahaifinta and nice matar sa ni zan bada shaida akan ka, idan mun gama da Sajida ni nasan yanda zamuyi mu zama rid of her, daga nan kai kuma sai ka mallaki Maryama.... Amma idan kak'i bin umarni na...." tayi wata kafiran murmushi kafin tace "Wllhi kana ruwa, zaka tashi a tutan babu, bazaka tab'a samun Maryama ba, the love of your life, so ina mai shawartan ka mu k'arasa abinda muka fara... Tana sonka take advantage of that love, if not I'll take advantage of the situation and ruin you, so is up to you boy, kaci gaba da aiki da ni ka sami biyan buk'ata..." Daga haka bata jira cewar sa ba ta katse wayar tana wani irin huci takaici ya cikata, don by now ta zaci Sajida ta k'ware a iya romance, ita wllhi sam ta raina ma barikin Buzu, yanda yake huld'a da manyan mata ta zaci yafi haka iya bariki... Tsaki ta buga had'i da finciko k'ofa ta fito dai-dai lokacin da AT ya murd'a k'ofan d'akin ya shigo da sallama. Abunka da maras gaskiya tuni ta razana da ganinsa, shi kuwa a tamanin yayi wajen Ni'ima yana tattab'a jikinta yana tambayarta meke damunta.. Rungumesa yarinyar tayi tana satan kallon Shema'u dake narka mata harara a sace tana mata alamu da tayi shiru.. Gefen AT ta zauna tana k'ok'arin shigewa jikinsa take fad'in "My AT wllhi fever d'in ya sauk'a kaga har kallo ma take. AT ya murmusa yana rungume da Ni'ima kafin ya dubi Shema'u yace "Nasan you'll take care of her, idan kina tareda su banida haufin wani abu zai same su..." ya k'arashe maganar with a smile on his face. Shema'u sai wani kwarkwasa da mad'e take, Ni'ima na son tafiya wajen Maama Juu AT yak'i sakinta don tsoronsa d'aya kar Shema'u ta kusanto sa, har addu'a yake cikin zuciyar sa... ************** Bayan azahar aka soma gudanar da liyafar da Shema'u ta had'a. Tana d'aki tana shiryawa ta kira layin Buzu bugu biyu ya d'aga. "Hello kanajina, ka cika aikin ka yanzu, take her out and treat her like a queen... Yauwa ka dai gane, no hankula sun kasu sabida hidima, just take advantage of the situation... Yauwa, don't fail me pls..." Daga haka katse wayar tayi tana wata kafiran murmushi... ********** Shiryawa tayi tsaf cikin sabuwar rigar da Uncle ya kawo mata, tayi kyau har ta gaji, Hajiya ta dubeta ta tab'e baki ba tareda ta furta komai ba domin kuwa sam bataso Maryama taje bikin wannan watsesttiyar matar. "Hajiya nayi kyau.?" ta tambaya tana kuma duban kanta a mirror. "Yo bikin rahama zakije da zan ce kinyi kyau, ai koma kinyi kyau ni dai baki yimin ba tunda bikin sharri kika nufa, wannan aure sam banji akwai albarka a tattareda shi, shi dai Attahiru da Allah Ya riga ya jarabta da auren tsautsayi saidai na bisa da addu'a don bana masa baki ba, wannan bakin uwa ya kamasa saidai kuma yabi bola, tunda Kulu sun riga sun juya masa kwanya baya gane gabas baya gane yamma, addu'a dai shi zan tayi masa har Allah Ya warware wannan bak'in asiri da suka masa...." Tunda ta fara magana Maryama tayi kicin-kicin da fuska, tasan batason auren Uncle da Aunty Shema'u amma sam bataso taga Hajiya na fushi da Uncle tunda ko bata tofa ba fushinta ka iya tasiri a rayuwar sa... Jin bata amsata ba yasata karkatowa tana dubanta, ta yab'e baki tace "An tab'o ubanki Attahiru ai dole ki gimste fuska, toh kifi shanu, ke nifa had'e ku zanyi daga ke har Attahirun na wanke ku tsaf babu ruwana ehe, wllhi idan dai akan maganar aurensa da wancan mai k'irar jiminar ce saidai kuyita fushi, idan kun gama zaku sauk'o da kanku...." ta k'arashe maganar tana goga ashwakinta a bakinta... Sallaman Ashfaq ne ya kaste Hajiya, mik'ewa tayi tana gyara d'aurin zani ta nufo parlor tana fad'in "Ah'ah wa nake ji kaman Keenafas, lale-lale maraba likita bokan turai, shigo abinka..." Ashfaq yayi sallama had'i da d'ago labulen parlorn ya shigo fuskar sa cikeda fari'a. Saman carpet ya zauna yana gaida Hajiya, ta amsa masa cikeda sakin fuska suka soma tab'a hira don Ashfaq babu laifi akwai barkwanci, nan yake tambayarta Maryama.. Tab'e baki Hajiya tayi ta yunk'uro ta lek'a k'ofar d'akin kafin ta rage murya tamkar mai rad'a take fad'in "Gata can ta d'ane bakin, wai fushi take dani nace kar taje bikin Attahiru.." Ashfaq ya murmusa yana mai jin dad'in hiran Hajiya kana yace "Ai ya kamata taje Hajiya, tunda nazo ai sai na kaita..." Hajiya ta kuma tab'e baki kana tace "I yayi, ai sai ki fito keenafas ya kaiki, nasan idan bakije ba kwana zakiyi kina min zunb'ure zunb'uren baki,... Ina kike ne.." ta fad'i tana d'aga labulen d'akin. Still fuskarta babu walwala ta fito, ta d'an k'ak'aro murmushi tana gaida Ashfaq da ya kafeta da idanu yana sakar mata sassanyar murmushi... Kallon Hajiya ta d'anyi don ita sam ba so take Ashfaq ya kaita ba tunda tasan Uncle baison irin hakan. "Hajiya fah Uncle yace zai turo malam Habu ya kaini, nasan k'ilama yana hanya." ta fad'i a shagwab'e. "Yo saidai idan kin fasa zuwa muyi zaman mu, ke wai yaushe kika koyi wannan felek'e da d'an banzan ra'ayi irin na Attahiru ne, idan baki zuwa keenafas kayi zamanka abunmu mu sha hira." Marayama ta turo baki ta cika tayi fam, Ashfaq duk sai yaji babu dad'i, baison ganin ranta a b'ace. Duban Hajiya yayi kana yace "A'a Hajiya mu jira mai zuwa d'aukan nata ya iso tunda Ya Dr zai turo sa..." yayi maganar yana satan kallon Maryama. Ita kanta Maryaman sai taji babu dad'i, kaman bata kyauta ma Ashfaq ba. Mik'ewa tayi don tasan idan taci gaba da zama yau sunyita haurawa da Hajiya kenan, ta d'auki d'an handbag d'inta tace "Ya Ashfaq muje ka kain pls.." Ta juyo ta dubi Hajiya baki a ture tace "Na tafi..." "Toh Allah Ya tsare, Keenafas ka kula min da d'iyata, idan suka k'ala maki wani sharrin wllhi ko zan masu diran mik'iya don na sansu dangin Kulu dangin jaraba, dangin tsiya.." Maryama tazo wuya, yanzu a gaban Ashfaq Hajiya ke maganar nan ko oho babu ruwanta, cikin sauri ta fice tana fad'in "Hajiya sai na dawo..." Ashfaq ma sallama yayima Hajiya ta kuma jadadda masa ya kula da walta. Shaf ya mance da batun kai Maryama event d'in Shema'u, cikin sauri ya tattara files d'insa ya katse ganin patients ya fice, sosai yake falfala gudu saman kwalta. ********* Ba k'aramin dad'i taji ba ganin yanda ya kuma damuwa da ita, ta nemi bak'in cikinta ta rasa, a hankali ya bud'e mata marfin motar ta shige fuskar sa d'auke da mayaudarin murmushi mai narkar da 'yanmata, tana shigewa ya tada motar. Ashfaq da karyo kwanar su kenan yaga sanda Sajida ta shige cikin wannan bak'ar motar, tsaf ya gane motar jiya a ciki ya ganta ta fito, yau gashi sun fice. Zuciyarsa ta cika da shakku, ya juyo ya dubi Maryama data dafe face d'inta daga kauce ma hasken rana, da alama bataga abinda ya faru ba, baice komai ba ya had'iye zancen amma sam zuciyar sa bata kwanta ba da wannan bak'ar mota mai bak'in gilashi ba dukda bai tab'a ganin mai motar ba. Sosai Maryama ta masa godiya zata shige ya ambato sunanta a hankali, juyowa tayi tana dubansa ganin ya mata k'uri yasata sadda nata kan k'asa. Murmushi yayi kafin yace "Inaso na ce maki sunan mahaifiyata gareki so ina respecting sunan sosai, if you don't mind zan fara kiranki lil sis." Murmushi itama ta masa kafin tace "Babu komai Big bro..." a tare suka sakar ma juna murmushi kafin sukayi sallama.... Yana tada motar sa ya soma tunanin ta wani hanya zaibi ya cimma su cikin sauk'i dukda abinda yake shirin yi shisshigi ne bana kad'an ba.. ************ Sai faman huci AT yake jin Ashfaq ne ya fita da Maryama, wato bata jin maganar sa saida yace mata baya son tana shiga motar kowa idan ba shi ya umarta ba, tabbas zata sa yayi firing Ashfaq... Ya d'ago a karo na biyu yana duban Hajiya kafin yace "Amma Hajiya ai na hana tana shiga motar kowa ko, meyasa kika bari Ashfaq ya kaita ba tareda sani na ba...?" Jakar uba, tsegege Hajiya ke dubansa baki a hangame, "Eaaah...! Sannu Malam Sallau Mai Hula uban Fad'ima, Kaine ma ka haife ni Attahiru dole ka gindaya min sharad'i, toh ba'abi dokar taka ba, kai dokan wa ka bi, kai ank'i abi dokar taka sai ka had'e mu gaba d'aya ka daka,. Kai wllhi ka fita a idanu na kaji na fad'a maka, toh waima meye nufinka na tak'ura ma yarinya inyi, kan wani bokon banza, kai da anyi magana sai kace karatu kake so tayi, toh alimantari d'in ma yaci uwashi (alimentary), bazatayi karatun ba, wanda tayi ya isheta, aurarta zanyi idan yaso ka had'iye zuciya... Kai uban waye ya tsare maka naka jin dad'in, ince kaima auren kayi, toh na gane take taken ka shine ka hanata manema koh, toh koh wllhi baka isa ba kayi kad'an ehe, kai shanyayye ma irinka.. Fice min a gida, kuma wllhi kayi wani abin ma yaron nan nida kaine.." ta k'arashe tana d'aga masa labule... *Sameena Aleeyou Mrs* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *31* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ *Aysha Balarabe (My fastidious friend aka Maman Shema'u 🤣) and Aysha Malumfashi shafin yau naku ne ❤🤝🏻* Gaba d'aya zuciyarsa a cunkushe take, tamau ya d'aure fuska babu alamun walwala a tareda shi, shi abin na Hajiya wata rana sosai yake damunsa, at least sai ta ringa ragar masa tunda shi ba k'aramin yaro bane amma idan ta soma tsefe sa bataji bata gani, kai shi da ace yanada k'anne yasan da ta rage wani abin... "Zaka fice koko.?" Muryarta ya kuma kaste masa tunani. Mik'ewa yayi jiki babu laka kafin ya furta "Kiyi hak'uri.." "Ai ko Damo nan ya ganni ya barni wajen hak'uri tunda na k'yaleka ka auri wancan roba-robar, maza fice min a gida ehe.." ta k'arashe tana gyara labulen sosai. D'an jim kawai yayi kafin ya soma tafiya uwa kazar da aka tsamo a ruwa. ************ "Malfar uba.!!" Shema'u ta furta a hankali ganin Maryama da kayan da AT yayita kwad'aita mata ta d'auka rananr da suka shiga store domin shi ya rakata sayyan kayan auren nata, bata d'auka ba ta d'auki wani kalan ashe ya zaga ya saya ma wannan shegiya bak'ar yarinyar mai ido uwa ta mujiya, zufa ya shiga keto mata take ta soma tunanin karfa hasashen Hisham ya zamo gaskiya, AT son wannan yarinyar yake, d'iyar cikinsa, yarinyar da ko hankalin kanta bata gama mallaka ba.. Taci gaba da huci tana tafarfasa sanda Maryama ta k'arasa wajen Maama Juu tana tambayar ta Sajida.. Shema'u dai zuciyarta tamkar ta fito waje ta tawarwatse haka take ji, lallai kuwa watan cin uwar yarinyar nan ya kama, tayi wata kafiran murmushi a hankali kafin ta furta "Maryama" _daga ke har uwar tasa mai d'aure maki gindi sai nayi maganin ku, sai na b'atar daku a kwanyar AT wllhi sai na shafe ki a babin rayuwar sa, babu wanda ya isa ya shiga tsakani na da Tahir, he's mine...._ a zuciya tayi wad'an nan maganganu kafin taci gaba da k'are ma Maryama kallo, tayi wata kafiran murmushi sanda tuna ta raba AT da matar sa uwar 'ya'yan sa kuma 'yaruwa a gareta balle wannan k'aramar yarinyar wanda tasan da salo da kaloli na makircin ta zata shafeta.. Ta fuzar da iska kurum ta shiga jona wayoyi suna spark a kwanyarta.... *********** Yama rasa ta wani hanya suka bi, gaba d'aya ya zama lost... Runtse idanunsa yayi sanda traffic lights ya nuna masa Koren wuta, cikin sauri ya karya kan motar ya soma bin hanyar da yake tunanin nan suka bi. Buzu ya shafi red lips d'insa yana wani tamke fuska irin bai gama hucewan nan ba.. Ta d'an turo baki tace "Kayi hak'uri mana pls, nimafa ba son raina bane..." Saida ya shafi sumarsa da suke a kwance luf kafin yace "Ya wuce amma ki sani ba'a rejecting kirana, gwanda Karma ki d'aga da kiyi rejecting, and na maki uziri is like baki tab'a soyayya da wani a baya ba . Na kula ni ne first love d'inki, ki gane tsan-tsan soyayyarki ce a cikin zuciyata banida bad intentions, amma kaman baki yarda dani ba, sannan irin haka a soyayya is norms ba wani abu bane tunda ni aurenki zanyi, amma idan baki sona fine I won't force myself on you..." ya k'arashe yana d'aga gira sama had'i da d'aga kafad'u da tab'e baki... Idanun Sajida yayi rau-rau jin har an kawo peak d'in da Haris masoyinta ya soma irin wad'annan kalaman, gaskiya she don't wanna lose him, tana son shi sosai.. Satan kallonta yayi yaga kaman hawaye a udanunta, cikin sauri yayi parking a gefen hanya. Cikeda kulawa ya soma fad'in "Baby me ya faru kuma, why those tears, com'on fad'a min me yasaki kuka, na fad'i wani abinda bai maki ba koh... Oh I'm sorry I didn't mean it kinji, oya come here bana son ganin hawayen nan...." ya k'arashe maganar yana rungumota tsam cikin jikinsa... Ita kuwa narkewa tayi tana mai ci gaba da kuka harda shesshek'a, ga sanyin k'amshin turaren sa ya sai yawo yake cikin hancinta don kuwa tsam ya matse ta cikin k'irjinsa.. Yana jin yanda k'irjinta yake bugawa da sauri-sauri.. K'ofar wani joint yayi parking yana mai ci gaba da lallashinta, harda goge mata hawayen, d'ago hab'arta yayi kafin yace "I'll pay a reservation, ina so na nuna maki how important you are to me, zan nuna maki cewa ni d'in masoyinki ne.. Ki jirani a nan mota okay, yanzu gidan Aunt d'ina zan kaiki daga nan sai mu dawo muyi lunch kinji my love..." Gyad'a masa kai tayi tana murmushi kanta har wani fashewa yake ganin wannan had'dd'en saurayi yana treating d'inta tamkar sarauniya, Allah sarki abinka da yarinta had'i da wauwauta. Cikin hanzari ya gama parking motar sa domin joint d'in da yaga motar ta tsaya ba abin arziki ake a wajen ba, wajen rage lokacin shasshashun matasa ne babu kalan kayan mayen da ba'a sha a wajen. Gaban Ashfaq ya yanke ya fad'i cikin sauri ya k'arasa jikin motar ya shiga k'wank'asa glass. Gaban Sajida ya yanke ya fad'i idan bata b'ata tunani ba wannan mutumin kaman shine jiya Daddy Ya aiko sa da kaya, tabbas abokin aikinsa ne, ta rasa wanne zatayi ga Buzu ya shige cikin joint d'in nan... Hannu yasa ya funciki marfin motar ta bud'e ashe basu saka security lock ba sun mance.. Ashfaq yasha mur yana watsa ma Sajida mugun kallo ganin cikin motar yanda yakeda duhu sosai sai sanyin AC ne kawai ke fitowa... Cikeda masifa ta soma fad'in "Malam wai lafiya kake bibiyata.." Ashfaq ya murmusa dabara ta fad'o masa. "Dr ne yace na biyo ki na dawo dake gida." Gaban Sajida ya yanke ya fad'i shikenan ta mutu, yau Daddy kasheta kawai zaiyi.. Ganin ta birkice gaba d'aya yasa Ashfaq gyara murya kafin yace "Fito muje Dr na jirana." Idanun Sajida suka kawo ruwa ta soma fad'in "Dan Allah da gaske kake Daddy ne ya turoka, don Allah ka fad'a min gaskiya..." Murmushi Ashfaq yayi don dama da biyu ya fad'i hakan, kenan Daddyn ta baisan tana fita da saurayi ba kuma tana tsoron ya sani, tabbas koma waye saurayin niyyan b'ata ta yake yi.. Gyaran murya yayi ya kuma shan mur kana yace "kina b'ata min lokaci ni inada wajen zuwa, ko dama Dr baisan kina fita yawo bane...?" Bata sami zarafin amsa sa ba jikinta har na rawa ta fito daga motar sai faman waige-waige take tana tunanin yanda zasu wanye da Daddyn ta yau. Buzu ya gama booking tarkacen kayan mayen da zai d'irka mata da dare, fitowar sa ya hangeta ta shige motar Ashfaq, sarai ya gane motar yana ganin motar na zuwa gidan Hajiya, a tunanin sa AT ne, gabansa ya yanke ya fad'i, kasa fitowa yayi sai neman wajen fakewa da yayi... Yana ganin motar ta bar wajen ya daki k'afarsa da garu yana furta "Damn it...!!!" *********** Hisham ya kalli AT a karo na biyu kana yace "Toh kai banda abinka Tahir ka k'yale yarinya mana tayi rayuwarta ai gaskiyar Hajiya ne, kabi ka tak'ura yarinya ka hanata manema, toh saidai kuma idan kaine zaka aureta, naga alama ma kanka kake tanadi." Mugun kallo AT ya watsa masa kafin yace " You're insane, ni ba son Maryama nake ba, this is not the right time for her ta soma kula samari, she's still young for that, idan lokaci yayi ni da kaina zan samo mata mijin aure wanda na yarda dashi, wanda bazai ci amanarta ba sabida ita d'in amana ce a gareni..." Hisham ya sauk'e ajiyan zuciya yana wata kafiran murmushi yana shafa hab'arsa. _Lallai Shema'u tanada aiki_ ya furta a zuciyar sa. ************* Goge hawayen ta taci gaba da yi, fargaba da tsoro suka cikata. Ashfaq ya saci kallonta kafin ya mik'a hannu backseat ya zaro tissue paper ya mik'a mata ba tareda ya kalleta ba. K'in karb'a tayi don ita wani mugun tsanar Ashfaq takeji. Ashfaq ya murmusa kana yace "Next time idan zakiyi wani abu kiyishi da ilimin iyayenki, ni bazan fad'a ma Dr ba for now, I'll be watching you duk randa na kuma kamaki da laifi makamancin haka zan sanar da mahaifin ki domin kuwa zaman amana kenan." idanunsa naga kwalta yayi maganar dai-dai lokacin da yake karyan kwanar layinsu. Yana gama parking ta finciki marfin motar ta fice tana huci, kaman zata tashi sama ta shige gida. Ashfaq ya bita da kallo had'i da sauk'e ajiyan zuciya, tabbas kowa da abinda Allah zai jarabce sa wani takan 'ya'ya wani takan iyaye, tuno nasa mahaifin da yayi yasa sa d'aura kansa saman steering wheel, ya jima yana wajen yana tunanin rayuwa. A wajen AT ya k'araso ya samesa, horn ya masa Ashfaq ya d'ago kansa had'i da saurin fitowa daga motar. AT ma yayi parking a bakin gate d'in ya fito dai-dai lokacin da Ashfaq ya k'araso. Fuskar AT a tamke yake amsa gaisuwan Ashfaq. Gaba d'aya Ashfaq yasha jinin jikinsa da ganin yanayin AT d'in. D'an key d'insa yasa yana sosa k'eyarsa kafin yace "Jiranta kake ka maida ta...?" Daga sama Ashfaq ya tari tambayar, baima gane me AT yake nufi ba, kardai yasan Sajida ta fita ne.. Kan ya sami zarafin magana AT ya gyara tsayuwar sa yace "Kar ka damu kana iya tafiya zan maidata,..." Ashfaq ya d'an rusuna kana yace "Toh Ya Dr, a huta gajjiya..." Yayi masa sallama ya soma tafiya, har ya bud'e motar sa ya kuma jiyo Tahir ya kira sunansa. Wannan karan Tahir d'in ne ya k'araso yanda Ashfaq d'in yake kana yace "Ashfaq da Allah ko Hajiya ce ta saka fita da Maryama inform me first kaji, da Allah banso muzo muna samun wani misunderstanding ka gane, pls respect my decision.." D'an jim Ashfaq yayi kafin ya jinjina kai yace "Za'a kiyaye insha Allahu Ya Dr. AT ya jinjina kai cikeda jin dad'i kafin suka kuma yin sallama ya shige ciki. Hango Maryama da Sajida Shema'u tayi sun saka Maama Juu a tsakiya Ni'ima na saman cinyarta.. Tambayar kanta ta soma me ya faru taga Sajida a gida, zufa ya shiga keto mata, a yayinda hankulan mutane yayi wajen shagali ta mik'e ta nufi uwar d'akinta ta saka key ya shige bathroom kafin ta soma shafa wayarta, ana haka wayar Hisham ya shigo mata, hannu har na rawa ta d'aga wayar. "Hello ina jinka.." ta fad'i cikeda k'osawa. Hisham ya murmusa kafin yace "Ai kuwa gwara kijini da kyau domin kuwa abubuwa gab suke da kwab'e maki.." Dariyan rainin hankali Shema'u tayi kafin tace "Wllhi nafi k'arfin abubuwa su kwab'e min, kasan take na Murucin kan dutse ban fito ba saida na shirya, oya fad'a meke faruwa." "I love your courage.." ya fad'i yana wani shafa hab'arsa. "Ina jinka Hisham akwai abinda zanyi yanzu pls ka fad'a min meke faruwa..." Dariya ya kuma yi kafin yace "Wllhi dukda k'arancin shekarunta she can steal AT away from you, idanma bacci kike you better wake up..." Bai kai aya ba ta dakatar dashi da fad'in "Wata 'yar shegiyar kenan, wata mai neman rasa numfashinta ne..." ta k'arashe tana muzurai uwa mage cikin buhu. Saida ya kuma yin dariya kafin ya labarta mata yanda sukayi da AT akan Maryama... Haba nan fah hankalin Shema'u ya kuma tashi dama a cike take fam da ita. Cikin sauri ta soma fad'in "Ina wad'annan yaran da suka kamo min Buzu...?" Hisham yace "Wai su Jarka kike nufi...?" Har gyad'a kai take tamkar yana ganinta kana tace "Ka gane don Allah ina so su min aiki, wannan karan harda morewa zasuyi, domin kuwa zasu sami abin hutawa...." tayi maganar fuskar ta d'auke da murmushi. Hisham ya k'walalo idanu waje kafin yace "Au barikin naki har ya kai ki bada kanki ma k'azamai irinsu Jarka...?" Dariya tayi kafin tace "My allied kenan ka gane me nake nufi, hutawa zasuyi da wancan shegiyar yarinyar, I want them to rape her, su mata kaca-kaca ita kuma tsohuwa su d'anyi brushing hak'waranta acire mata ko guda biyu ne domin nasan ganin incident d'in da zai faru da Maryama sai ya haifar mata hawan jini tunda tana sonta, ita kuma yarinyar nasan abun will deform her and break her, rayuwarta zai zama miserable ta yanda sai ta gwammaci ta mutu ta huta..." ta k'arashe tana kallon kanta a mirror na toilet d'in. Dariya Hisham yayi kafin yace "Ina ji maki tsoron ranar da zaki k'ulla sharri ma kanki baki san kin k'ulla ba, anyway zasu zama ready, kiyi transferring kud'in to my account ni zan k'ara masu ma..." tayi dariya kafin tace "Da ilimi nake komai, a ankare nake komai, nasan me nake gudanarwa.... Ta k'arashe tana murmushi. Sallama sukayi kowa da abinda yake k'ullawa cikin zuciyar sa Murmushi kawai Hisham keyi domin kuwa ya sami hanyar mallakan asibitin AT cikin sauk'i, tabbas yasan wannan tsautsayi ya sami Maryama toh kuwa tamkar AT ya sama , zaiyi amfani da damar ya cimma burinsa cikin sauk'i.... Ita kuwa Shema'u yana daga cikin plans d'inta ta k'ak'aba ma Hisham sharri ya rabu da AT ta huta dashi, she'll finally get rid of Hisham tunda ta gama amfani dashi ta mallaki AT. Sanda ta ida waya da Haris Buzu ba k'aramin takaici taji ba, ta ringa buge buge ita kad'ai wanda ya janyo hankalin AT dake can d'akinsa.. Knocking ya soma mata yana tambayarta lafiya.. Saurin kintsa kanta tayi ta fito tana murmushi kafin tace "My AT ai bansan ka dawo ba wllhi spider na gani shine na ringa binsa ina bugesa ina son korarsa ka sanni da tsoron insects.." ta k'arashe tana kashe murya. Gajeren murmushi yayi wanda yafi kama da dariya amma maras sauti kana yace "Haka mata kuke gaba d'aya, da kin kira Jamal ya kora maki ai.." ya k'arashe teasingly.. Murmushi tayi ta k'araso ta rungumo wuyar sa tana wani lank'washewa had'i da mad'e take fad'in "My AT bansan ka ahigo gida ba ai, nayi missing d'inka da yawa, yaya jikin naka, hope kaji sauk'i. " Bai sami zarafin amsata ba sabida miyau da ya k'unsa a bakinsa, don ko had'iyewa ya kasa, sosai take basa k'yank'yani... Ganin tana k'ok'arin had'e bakin su yasa sa saurin zaunar da ita saman sofa ya had'i da ciro wayar sa a aljihu tamkar wani na kiransa... Da hannu ya mata alama excusing kansa yana nuna mata wayar kafin ya k'ara a kunne ya shige parlorn sa kaman mai wayan gaske. Mayen kallo ta bisa dashi kaman ta lashe sa, har ta k'agu dare yayi ta jita jikin AT d'inta. Ta window ta hangi su Maryama dasu Sajida har lokacin suna tare, tayi wata kafiran murmushi sabida tunanin da ya fad'o mata, saurin d'auko rigarta irin na Maryama tayi kafin ta nufo kitchen tayi alama ma Iya Kande ta k'araso cikin sauri, keb'ewa sukayi Shema'u ta bata rigar had'i da mata rad'i a kunne , Iya Kande ta jinjina kai tana kafiran murmushi tuni ta sauk'a k'asa ta nufi wajen su... Yanda take haba-haba da mutane sai ka rantse har cikin zuciyarta kenan. Hannun Maryama ta rik'e tana mayaudarin murmushi kana tace "I'm glad you came by, wllhi naji dad'i sosai Maryama, banida burin da ya wuce na ganki da Sajida kun koma tamkar yanda kuke a baya, SHAK'UWAR ku daga Allah ne.." ta k'arashe tana duban Sajida da murmushi. Daga Sajida har Maama Juu murmushi suke yayinda Maryama ta koma tamkar gunki, domin kuwa fuskar Shema'u sosai yake firgita ta. Iya Kande ce ta k'araso tana rusunawa kafin ta shiga d'ago rigar tana tambayar Shema'u "Aunty wannan rigar ce za'a goge maki...?" Yanda ta d'aga rigar gaba d'aya ta warwareta, kala ce kawai ta banbanta da ta Maryama. Gaba d'aya suka bi rigar da kallo, Sajida ta kuma kallan rigar ta kuma kallan ta jikin Maryama. "Aunty kinga rigar ku iri d'aya color ne kawai ya banbanta..." cewar Sajida da tayi k'uri ma rigar. Shema'u ta murmusa kafin tace "Haka ne my Sajee, ai Daddyn ki ne ya saya mana, tare mukaje shopping ranar, ya so rigar sosai har naso d'auka ma yace min yana son rigar ma someone special, so I thought ma ke ya d'auka ma tunda nasan idan bani bace special toh saidai ke..." Gaba d'aya kasa tab'uka komai sukayi, babu kaman Maryama da tayi mutuwar tsaye, Maama Juu dai sai karantar Shema'u take, sannan ta lura da canjin da Sajida tayi a d'an kwanakin tabbas Shema'u tanada wani bak'in k'ulli a zuciyarta wanda bai fito fili ba, bazata bar gidan ba da yardar Allah sai ta gano wacece Shema'u.... Muryar Shema'u ya katse mata tunani yanda take fad'in "Kar ki damu Sajee zan baki nawa sai kuyi anko da k'awarki..." Sajida dai bata tankata ba sai kallon tuhuma da take bin Maryama dashi, k'arshe ma wucewa cikin gida tayi abinta ta barsu nan tsaye.. Shema'u ta rakata da kallo tana murmushin cin nasara. Maama Juu kuwa hannun d'iyarta ta kama suka bar wajen. Bayan la'asar 'yan Jalingo suka wuce, gaba d'aya Sajida bata fito ba tana can tana tunanin me Daddynta yake nufi da Maryama?" rasa amsar tambayar tata tayi. Uwarta Shema'u kuwa yau ba'a sama ba'a k'asa domin taran angonta ne a gabanta, kotakan Sajida bata bi ba m. Tasha gayu cikin wasu arnan kayan bacci masu d'aukan hankali ta nufi d'akin sa... .AT dake zaune saman gado laptop a gabansa yana research saida k'irjinsa ya buga ganin Shema'u ta shigo, shikenan ya shiga tara, shi har tausayin ta yake ji... Ba don yaso ba ya tura laptop d'in gefe had'i da k'ak'aro mata murmushin k'arfin hali, ai kuwa kaman jira take ta fad'a jikinsa tanai masa wasu salo.. Ba'a je ko ina ba AT ya soma developing allergy, hattushawa Ya ringa yi babu k'kk'autawa fuskar sa tayi jazir, jikinsa sai k'aik'ayi.... Mik'ewa Shema'u tayi dafe da k'irji tana kallonsa yanda yaketa jero hattishawa uwa ta kurma ihu... *Sameena Aleeyou Mrs* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *32* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ Shema'u ta masa k'uri cikeda tsoro da al'ajabi ganin yanda ya soma shid'ewa tamkar numfashin sa zai d'auke, a guje ta mik'e ta nufi fridge ta d'auko masa bottle water ta basa, har lokacin atishawa yake a jere a jere, da k'yar ya iya amsar ruwan ya shiga kwankwad'a. Shi kansa AT abun nasa ya soma damunsa, what's wrong with him, kodai bashida lafiya ne...? Bai kai ga samo amsar tambayar sa ba ya jiyo Shema'u tana shafa bayansa tana d'an bubbugawa take masa sannu. Bai iya amsata ba sai runste idanunsa da yayi, tausayin ta ya rufe sa, mai ma zai soma ce mata, that he's allergic to her or what... Muryarta ya jiyo tana fad'in "Dr make damunka, gaskiya ina tsamman bakada lafiya, toh ko dai perfumes d'ina ne basu maka ba, or maybe humra da nake shafe jikina dashi ko shine baka so.." ta k'arashe kaman zata kurma ihu... K'ak'aro murmushi AT yayi domin kuwa da tasan yanda yake son k'amshin turaren humra da batayi wannan tunanin ba, k'ok'arin rungumeta yayi cikin jikinsa yana tattamke idanunsa kafin ya furta "I'm sorry, kiyi hak'uri kinji.." Jin yanda yayi hugging d'inta yana bata hak'uri with all his heart yasata kuma narkewa cikin jikinsa, kafin ta soma fad'in "My AT zan I promise you zan kula da kyau na gane meke irritating d'inka, insha Allah ko menene zanyi avoiding kaji..." ta k'arashe murya can k'asan mak'oshi.. AT bai sami zarafin amsata ba sabida itches... So yake ya fad'a mata ga gaskiyar lamarin amma baisan me zai soma ce mata, zamansu a haka akwai alaman tambaya, tausayinta ya kuma rufesa don sam baiso ya shiga hakkin ta sannan sooner or later zata fahimci gaskiya, dole yasan abin yi dole ya samo masu mafita... Sauk'in abin jikin nasa baiyi ruhu-ruhu d'inba sannan k'aik'ayin ma ba sosai ba, haka dole ya tilasta ma kansa kwanciya cikin jikinta ya matse ta na dole ba don yaso.... ************* Abu kaman wasa an sahafe sati haka na faruwa tsakanin AT da Shema'u, hankalinta idan yayi dubu ya tashi, duk wasu turarrukanta ta daina amfani dasu haka nan cream d'inta dasu shower jell d'inta dole ta k'aurace masu amma babu abinda ya canza, ko yayi forcing kansa don sauk'e nauyin da shari'a ta d'aura masa bai iyawa.. Shi kansa yasan i zuwa lokacin Shema'u ta fahimce sa, harga Allah bazai iya bud'e baki ya fad'a mata ita ce ke irritating d'insa ba, it's unfair... Shema'u kuwa gaba d'aya ta rasa meke mata dad'i ga d'an banza buk'atan AT dake damunta, gashi duk tayi bak'i fuska ta daddauje babu shafe-shafe, jigum tayi a uwar d'aki tana tunanin lamarin, ba komai ya fad'o mata zuciyarta ba illa Hajiyar AT tasan itace kawai zata kai sunanta gaban Malamai don kar AT ya kusance ta, ta mik'e tana huci ita kad'ai tana zagaya uwar d'aki, wllhi dole ta koya ma matar nan hankali, ta yanda sai ta koma da k'afafunta tasa an warware sammon da tayi masu itada AT, annoba mutuwa ma ya kamata tayi tunda taci nata lokacin... Taci gaba da tafarfasa tana huci... Yau kam ko attempting nuna buk'atar ta batayi ba, koda ta gama shirin baccinta peck ta manna masa a kumatu ta haye gado tayi kwanciyarta, AT dake gaban laptop d'insa ya bita da kallon tausayi, sauk'e ajiyan zuciya yayi yaci gaba da abinda yake, sanda ya kammala aikinsa kwanciya yayi gefenta ba tareda ya rik'ota ba. Shema'u tana jin sanda ya kwanta, kaman ta had'iyi zuciya ta mutu, banda la'antar Hajiya da tsine mata babu abinda take cikin zuciyarta, kai wllhi ma cire hak'wara hukuncin yayi kad'an ma Hajiya, kamata yayi tayi kidnapping shegiya ta gallaza mata kafin ta karta.. Ta juyo tana duban AT dake baccin sa peacefully ga miji har miji amma ta kasa samun sa, bak'in ciki ya kuma turnuk'eta, k'ura ma kyakkyawan fuskar sa idanu tayi tamkar ta had'iyesa.. ************ Har wajajen 12:am batayi bacci ba sai chatting suke da masoyinta Buzu, voice note suka soma tura ma juna, daga voice note yace muryarta duk ya kashe masa jiki yana son ganinta, daga nan video call suka soma.. Tana sanye da yalwateccen kayan baccin ta harda 'yar hula saman kanta, shiko gogan daga shi sai faran singlet.... Sai kasheta da salon yaudara yake.. "Baby I'm dying to be with you.." ya fad'i cikeda salo. Murmushi tayi had'i da rufe fuskarta. Ya murmusa kafin yace "Idan munyi aure bazaki ke saka min irin wad'annan kayan baccin ba, kin dai sani koh..." yayi maganar cikeda umarni. Murmushi tayi kafin tace "tabb lallai ma toh wani iri kake so...?" tayi tamabayar cikeda sangarta . Buzu yayi wata murmushi yana d'aga hannayen sa ya maida su baya, jikinsa ya kuma bayyana kafin yace "Wanda mata ya kamata ta saka don mijinta, wanka ma ni zan ke maki, harta shiryaki duk ni zan ke yi..." Sajida ta k'walalo idanu alamun taji kunya, da sauri tasa tafukan hannayen ta ta rufe idanun... Haka ya ringa janta da hira wanda sam basu a hanya, har wajajen k'arfe d'aya, nan ma saida ya sata ta masa kiss a screen d'in kafin ya k'yaleta. Ni'ima na bacci tana firgita haka Maama Juu ta ringa mata addu'o'i tana mamakin yanda a baccin nata take ambato sunan Shema'u... Bacci yake amma gaba d'aya ya had'a zufa, sauti yake jiyowa tamkar na Aysha tana kuka take fad'in _"'Ya'ya na, 'Yaya na Tahir....."_ A firgice ya farka ga zufan da ya wanke sa dukda sanyin AC dake hurawa. Addu'a ya karanto kafin ya kunna side lamp ya kalli time, k'arfe biyu da wasu motsi ya nuna. Sauk'e deep breath yayi har lokacin zuciyarsa bata daina harbawa ba, gaba d'aya mafarkin ya firgita sa, mik'ewa yayi ya nufi corridor d'in d'akin yaran, ya kai dubansa ga d'akin Ni'ima bazai yuwu ya shiga ba tunda da Maama Juu take kwana, ya kuma duban k'ofar d'akin Sajida nan ma bai shiga ba, da k'yar yaci gaba da d'aga k'afarsa har ya isa k'ofan d'akin Jamal, hannu yasa ya murd'a k'ofan nan ya hangi yaron na baccin sa peacefully... Saida ya sauk'e nannauyan ajiyan zuciya kafin ya k'araso cikin d'akin, zama yayi gefen Jamal ya karanto masa addu'o'i ya shafa masa. Ya jima yana zaune a d'akin yana tunanin mafarkin da yayi da Aysha. Koda ya koma d'aki ma bathroom ta shige ya d'auro alola yazo ya tada sallah, nan yayita jero nafilfili yana rok'on Allah Ya sawwak'a masa lamuransa. ************ AT yana fita ta fice dama ta sanar dashi zata gidan k'awarta, bata zarce ko ina ba sai gidan Hisham.. Saida ya razana da yaga Shema'u, har wani rama tayi ga fuskarta ta koma multi color nan ja can bak'i can coffee... A razane yake tambayarta lafiya..? Huci kawai Shema'u keyi kafin ta soma fad'in "Hisham su Jarka bazasu iya aikin nan ba sun min k'anana, High Killers nake so ka samo min, wllhi sai na shayar da Hajiyar AT mamaki, sai tasan ba'a shiga gonata..." ta k'arashe tana girgiza. Murmushi Hisham yayi kafin ya k'araso yayi hugging nata ya zaunar saman sofa ya fara fad'in "Wannan daliline yasa duk kika fita hayyacin ki kika d'aid'aice..." Tana huci taci gaba da fad'in "Hisham AT ya kasa kusanta ta har yau, could you imagine... Duk dare da zaran nayi niyyan kusantsa zai soma ciwo, Hisham bazan iya ba wllhi ji nake mutuwa zanyi idan ban samu biyan buk'ata ta ba, kasan irin gwagwarmayar da nasha kafin na mallake sa, a zahiri na mallake sa amma a bad'ini ban mallake sa ba.... Hisham wllhi zan iya kashe ko waye akan shi...." ta k'arashe tana rarraba idanu tamkar mahaukaciya Saurin rungumeta Hisham yayi yana lallashinta, kaman jira take nan ta soma responding suka d'aura daga yanda suka tsaya.... Hisham ya dubeta bayan ya gama ja mata zip d'in rigarta kafin ya soma fad'in "My allied ba laifin Hajiya bane, idan baki sani ba ki sani AT is allergic to you, ni tun rananar farko na gane, sannan abinda kike buk'ata kike nema zaiyi wuya... " Baikai aya ba ta mik'e tana girgiza kai had'i da wani irin murmushi take fad'in "Wllhi k'arya ne, this is ridiculous, wllhi asiri aka masa, babu lafiyayyan namijin da zai kasa biyan buk'atar sa yace allergy ne, wllhi wannan ko a wasan kwaikwayo ban tab'a gani ba, ko a labarai ban tab'a ji ba, wannan aikin Hajiyar AT ne ba ita ta iya asiri ba.... Toh wllhi sai mun tafi har gaban bokan nata naci uwarsu gaba d'aya, da kansa zai nad'e buzun sa ya bar bokanci domin kuwa ko shed'anu masu nuna masa sharri a bayana suke, ita kuma her days are numbered..." daga haka fincikan mayafinta tayi ta fice bata kuma bi takan Hisham ba. Tunanin wayar da sukayi tareda Buzu take kan yi, amsoshin tambayoyin data masa suka shiga yawo a kwanyar ta, idan kuwa haka soyayya ne toh tabbas Daddynta son Maryama yake ba SHAK'UWA CE ba kenan soyayya ce... Girgiza kai ta soma ita kad'ai tana wani irin huci kafin ta zari mayafinta ta fice ta nufi gidan Hajiya ba tareda ta sanar da Maama Juu ba.... Zaune suke k'asar bishiyar shak'atawan Hajiya Maryama na ma Hajiya tsifa sai ganin Sajida aukayi tsgege saman kansu tana wani irin huci Baki Hajiya ta bud'e tana kallon ikon Allah yanda ko darajar sallama basuci ba balle gaisuwa.... Jiyo muryar Maryama Hajiya tayi tanai ma Sajida sannu da zuwa. Bata amsata ba sai fincikota da tayi tana ci gaba da huci take fad'in "Wllhi tallhi sai kin bar gidan nan, wllhi baki isa kiyi soyayya da Daddy ina raye ba..." bata kai aya ba Hajiya ta mik'e tana d'aura kwalinta take fad'in "Ke lafiya kike kuwa, tarbiyar da tambad'edd'iyar can ta soma baki kenan koh.. toh kuwa kinsan bana d'aukan rashin d'a'a sam.... Cikata kafin naci maki mutunci yanzun nan, sokuwa maras wayo da hankali..." Kuka Sajida ta soma tana cigaba da fad'in "Hajiya wllhi dake da Daddy duk kunfi sonta, Hajiya me Daddy yake nufi da ita, soyayya suke a b'oye su duka biyun." ta juyo tana duban Maryama dake zuban hawaye taci gaba da fad'in "munafukar banza munafukar wofi kinji kunya Maryama, kuma wllhi daga ke har Daddy babban kuskuren da zaku tapka kenan don wllhi ina numfashi bai isa......." bata kai aya ba taji an d'auketa da wani wawan mari.... Gaba d'aya suka d'ago suna dubansa ba kowa bane illa Tahir..... *Sameena Aleeyou Mrs* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *33* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ _Assalam makaranta SHAK'UWA CE, ina mai baku hak'uri bisa kuskuren da aka samu a shafin da yazo kafin wannan, kamata yayi nayi numbering d'inshi *32* sai na kuma rubuta *31*. Amma dai labarin bai canza ba saidai wannan shafi zai kasance 33 sabida abin ya tafi da tsari. So Sorry for the inconvenience pls.._ *HASIYAT IMAM sak'onki ya iso min, na gode k'warai da addu'o'inki da kuma k'aunarki a gareni. Rabbi ya bar k'auna, Sameena tana sonki tsakani da Allah ❤* Huci kawai AT keyi yana kallon Sajida disbelievingly, yaushe ta zama haka, har ita ke irin wad'annan maganganun akansa saikace sa'an wasan ta... Tsawa ya kuma daka mata "Shige mu tafi stupid..!!!" Rik'e da k'uncinta ta soma tafiya kaman zata fashe har lokacin hawaye bai daina zuba mata ba. Hajiya ta bisu da kallo baki a tab'e kafin tace "Yo bakaga komai ba idan dai wancan gogeggiyar ka d'auko masu matsayin uwa.." ta dubi Maryama dake nan tsaye itama tana hawaye kana tace "Ki k'yaleni da ita idan dai tace halin wancan kod'edd'iyar ta d'auka toh kuwa ta d'auki Dala ba gamo.." ta k'arashe tana rik'e da hannun Maryama suka nufi cikin gida.. D'aki Maryama ta shige tana hawaye, toh kodai har mutane sun fahimceta son Uncle take, wannan wani irin jarabawa Allah Ya jarabceta dashi, tabbas tana son Uncle tana jin soyayyar sa har cikin jini da tsokar ta, toh wai dama hakan takan faru da mutane ko ita d'in ne dai kawai Allah Ya jarabceta da son Uncle, mutumin da yafi k'arfin ajinta nesa ba kusa ba, mutumin da ya raine ta tun tana k'arama, mutumin da ya kasance gata a gareta, sannan uwa uba mahaifi ga babban aminiyar ta, tabbas zuciyarta batayi mata adalci ba sannan batayi ma Sajida adalci ba, inama zuciya tana shawartanka kafin ta soma son abu, inama ziciyarta soyayyan wani ta kamuda ba Uncle ba.... Hawaye suka ci gaba da kwaranya mata, wannan abu ne da bazai tab'a yuwuwa ba koda a duniyar tunani ne... *************** Hannunta ya rik'e yana fincikarta da iya k'arfinsa zuciyar sa na tafarfasa, har yanzu ya kasa yarda da kalaman da yaji Sajida 'yar cikinsa nayi a gamedashi... Doka kira ya ringa yi ma Shema'u, ta fito babu shiri domin kuwa itama bata jima da dawowa gidan ba, yanayin da taga AT da Sajida yasa gabanta fad'uwa, ta k'araso tana tbayar lafiya.. Fuska a dake Ya dubi Shema'u yace "Daga yau ko k'ofa ban yarda ki kuma barinta ta fita ba..." daga haka saman sa ya wuce zuciyar sa naci gaba da tafarfasa.. Shema'u ta bisa da kallo cikeda mamaki kafin tayi saurin k'arasowa tayi hugging Sajida tana tambayarta me ya faru.. Sajida ta goge hawayen ta kafin ta soma fad'in "Wllhi bazai tab'a yuwu ba, wllhi na tsani Maryama kuma sai ta bar gidan Hajiya...." daga haka ta wuce ta nufi d'akinta. Shema'u ta lek'e gabas ta lek'a yamma kafin ta nufi d'akin AT, Zaune ta samesa ya k'ura ma goran ruwa idanu, har lokacin mamakin abin yake. Zama tayi gefensa ta kalallame kafin ta soma fad'in "My AT dukda bansan me ya faru ba kayi hak'uri kasan yara, sannan nima ban jima da dawowa ba kasan na sanar da kai zanje gidan Karima k'awata, toh na barsu a gida tareda Maama Juu bansan me ya faru ba....." Katseta yayi ta hanyar d'aga mata hannu kafin yace "Ya isa daga yau kar ki kuma barinta ta fita ko k'ofa ne, zan sami Maama Juu ma na mata magana..." ya k'arashe yana kwanciya cikin kujera had'i da lumshe idanunsa... Abunda zuciyarsa ke fad'a masa tabbas k'arya ne, babu yanda za'ayi soyayya ya shiga tsakanin sa da Maryam, SHAK'UWA CE kawai... Shema'u ta bisa da kallo tana karantar sa. ************ A d'aki ta sami Sajida tana zaune ta had'e kanta da gwiwoyinta tana hawaye, yau kam ko takan Buzu batabi ba thought d'in Daddyn ta is in love with Maryama ya hanata sukuni. Zama Shema'u tayi gefenta ta dafata.. Suna had'a idanu Sajida ta kuma fashewa da wani sabon kuka. Rungumeta Shema'u tayi itama tana k'ok'arin rau-rau da idanunta. "Let it out my Sajee, yi kukanki ki sami sa'ida dukda bansan musababbin abinda ya had'aki da Daddyn ki ba, sannan Sajida bai kamata ki fita ba tareda sanin mu ba, wani abin ka iya samun ki, Daddyn ki yana sonki ne baison wani abu ya sameki... " ta k'arashe tana k'ura ma Sajida kallo babu ko k'yafta idanu. "Aunty wllhi barin gidan nan zanyi muddin hasashe na ya tabbata, Aunty wllhi bazan iya zama inaji ina gani Maryama my childhood friend ta zama matan Daddy ba, wllhi gwamma na shiga duniya..." ta k'arashe tana kauda fuskarta gefe wasu hawayen na zubo mata. Murmushin yak'e Shema'u tayi kafin tace "Sam kar kiga laifin mahaifinki wannan yarinya tun ba yau ba na gane k'udirinta akan mahaifin ku, amma sam banso na shiga tsakanin ku tunda naga yanda kuka d'aukesu daga ita har mahaifiyar ta, tun kafin ya tabbata soyayya suke yafi nuna kulawansa akanta fiye daku yaransa, toh mai zai faru ranar da ya auro ta matsayin mata. Wannan yarinya sam bata bar kanta yanda Allah Ya ajiyeta ba bacin haka ina ita ina soyayya da mahaifin ku, wannan yafi k'arfin cin amana ma ya zama zalunci.. Sajida ina sonku ki sani insha Allahu Daddyn ku bazai tab'a falling mata ba duk da k'warewa a salo na yaudaran ta... Oya zo nan." ta k'arashe tana mai hugging nata. ************ "Mummy pls ki daina kukan nan, kiyi hak'uri don Allah naji zan dawo, zan dawo sabida ke, Mummy don Allah kar kisa ma kanki wani ciwon pls kinji Mummy na.." Ya k'arashe muryar sa har rawa..." "Haidar yaya bazanyi kuka ba sannan yaya bazanyi ciwo ba bayan kaima na rasa ka kaman yanda na rasa Nabila." Ashfaq ya shafi goshinsa, da gaske mahaifiyar sa har gado aka bata a asibiti, shi wai yaya zaiyi ne, tabbas ya koma ma Daddy babu mata zai aura masa Fairuzah yarinyar da ta gama barikancinta a VICTORIA UNIVERSITY OF MANCHESTER, ENGLAND. Aside from wannan ma sam bai yi shirin confronting mahaifin nasa ba, toh wai ya zaiyi ne..... Baffah Yawale ne kawai ya fad'o masa a rai, shi kad'aine yasan Haidar na living wata rayuwa, shi kad'aine yasan Haidar na b'oye kansa saidai shi a iya saninsa Haidar na b'oye kansa ne sabida 'yanmata masu son shi da muk'amin mahaifin sa ko kuma da kyaun halittan sa, amma bayaga wannan baisan akwai wata dalilin ba. Sauk'e nannauyan aniyan zuciya Ashfaq yayi, tabbas Baffah Yawale zai tsaya masa a neman aurensa ba tareda sanin mabaifin sa ba, zasu fita da Mummy zuwa k'asar Germany in a couple of weeks, yanaso da zaran sun dawo yaje ya duba mabaifiyar sa sannan a lokacin da matar sa zaije yasan idan Fairuzah taga yayi aure ta hak'ura dashi kenan har abada sabida yasan zafin kishi irin na Fairuzah, koda suke school tasha attempting hallak'a 'yanmata masu kawo masa hari. Da wannan tunani Ashfaq ya kwanta, ya jima yana tunanin ta shi kad'ai yake murmushi yana tuna yanda AT yake son hanasu alak'a ta k'arfin tsiya, tunowa yayi yanada Hajiya. Take ya saki wata sassanyar murmushi had'i "Keenafas" mik'ewa yayi ya shiga manna gashin bakinsa ya shafa wata irin hoda da yake amfani da ita mai b'atar da asalin kalan fatan mutum kafin yayi shirinsa cikin k'anan kaya mai dogon hannu kana ya fice ya nufi gidan Hajiya. Sosai Hajiya taji dad'in zuwan nasa, tabbas Allah Ya had'a just jinin Hajiya da Keenafas. Maryama da wuni guda tayi kusan yinsa a d'aki sosai take dariyan hiran nasu, saida ta jiyo muryar Ashfaq na tambayar ta kafin ta mik'e ta fito parlorn, kallo ya bita dashi don kaman ya lura wani abu na damunta. Hajiya sai satan kallon sa take, cikin zuciyarta take fad'in _Zama ka fad'i ne da bakinka Keenafas, son d'iyata kake kaman Pep alop (five alive)_. Dabara Hajiya tayi t mik'e ta barsu a parlorn, tunda ta gaishesa bata kuma cewa komai ba, shi kuwa sai jefo mata tmbayoyi yake uwa d'an jarida.. **************** Gidan Dr Ahmad Tahir Shattima dai haka kowa ya wuni babu walwala, idan ka d'auke Shema'u dake faman k'ulle-k'ullen step d'inta na gaba, Maama Juu dai an bata da tunanin abubuwan da suke kan faman faruwa, ita kuwa Sajida wuni tayi d'akinta a kulle tak'i magana ma kowa tak'i bud'e k'ofa. Shi kuwa AT tunda ya kad'e k'afafunsa ya tafi _Sajmal_ bai waiwayo gidan ba. Uwar d'aki ta k'ule ta shiga waya da Buzu tana sanar dashi Dama ta samu, babu haufi yanzu Sajida zata bisa duk yanda yake so... Daga nan waya tayi dasu Jarka su Spider ta sanar dasu su cika aikin su yau, dama jiya data fita saida suka had'u a wani uncompleted building ta basu kud'in su cash. Ita kad'ai sai annashuwa take, abubuwa suna tafiya mata yanda ta shirya ta kuma tsara. *********** Yau dai sosai Ashfaq yaja Hajiya da Maryama da hira, har dinner saida yaci a gidan. Dr Bilyamin abokin aikinsa ne ya masa waya zai basa wasu takardu gobe ya shiga dasu TH da sassafe akwai wani taron likitoci da zasuyi, Dr Shattima (AT) ya sanar dashi yanada ziyartan asibitin koyarwa na Bauchi a gobe, so ba lallai ya halarci taron ba.. Ashfaq ya kwatanta masa yanda yake Dr Bilya ya tsaya ya basa har yana masa tsiya ya tare gidansu Dr Shattima kodai kamuwa yayi. Ashfaq dai sai dariya kawai yake sukayi sallama da Dr Bilya, komowa cikin gidan Hajiya yayi suka d'an kuma tab'a hira kafin ya masu saida safe, ba don Maryama taso ba Hajiya ta sakata dole ta raka Keenafas har wajen motar sa. ********* Jin knocking d'in Daddynta a k'ofa yasa gabanta ya yanke ya fad'i, tayi saurin katse wayar da suke da Buzu ta cilla wayar k'asar gado kafin ta k'araso ta bud'e masa k'ofan bakinta a ture... Shi d'inma babu walwala a fuskad sa ya shigo. Zama tayi bisa gado kafin ta gaida shi. Kaman bazai amsa ba sai kuma ya amsa ta a tak'aice. Hard'e hannayen sa yayi a k'irji yasha mur sosai kafin ya soma fad'in "Bazan lamunci rashin kunya daga wajen ki ba , sarai na sani kina kan gab'ar ne har yanzu, toh ki sani I'm your father not your brother, don na baki room ina sharing abu daku yarana doesn't mean zakiyi duk abinda kike so, be careful . Ki shiga hankalin ki, bansan yanda kika samo wancan idea d'inba amma ki sani duk abinda zanyi ku nake fara tunowa first my family, sai na duba yin abin wani implications zai haifar sai nasan matsayin abun kafin nayi. Kwanan nan na auri 'yaruwar mahaifiyar ku sabida ku sabida na inganta maku rayuwar ku, sabida na faranta maku, ashe ke kina babba bazaki kula da hakan ba har kina bud'an baki kina fad'an magana akaina Sajida!! Mahaifin ki, toh wllhi ki shiga hankalinki bazanyi tolerating rashin kunya koda wasa, kina jina..." ya k'arashe cikin daka tsawa. Jinjina kai tayi hawaye na k'ok'arin zubo mata don tunda take da mahaifinta bai tab'a yin fushi irin haka da ita ba, da k'yar ta iya furta "Daddy I'm sorry." Still yayi bai amsata ba... Tana jin sanda ya fita daga d'akin still ransa a b'ace... Wayarta ta kuma lalumowa ta kulle k'ofarta ta shiga neman layin masoyinta Buzu domin shi kad'aine zaiyi calming nata taji sanyi. Tsaye yake cikin closet d'insa yana sanye da inner white da lallausar wando na bacci, bayan ya gama feshe jikinsa da body spray na AXE ya k'araso cikin d'akin, nan ya samu Shema'u har ta kwanta, kaman daga sama sai jiyo sautin kukanta a hankali yake. Gaba d'aya jikinsa yayi sanyi, d'an zama yayi gefenta yama rasa me zai soma fad'i mata, hannu ya mik'a ya d'agota nan yaga hawaye kwance saman fuskar ta sai faman k'ok'arin b'oye fuskar take.. AT ya k'ura mata idanu kafin yasa hannunsa ya shiga goge mata hawayen yana fad'in "Kiyi hak'uri nasan matsalar kukan ki bazai wuce nawa matsalan ba, I'm sorry kinji believe me nima abun ya dameni sosai sannan ina research akai kullum kinji koh, I promise you komai zai zama normal insha Allah kinji...." Bursting ta kuma yi cikin kuka ta shige cikin jikinsa cikeda salo na makirci.. Matse ta yayi cikin jikinsa his heart's beating so fast, yana tsoro kar Allah Ya kamasa tunda ya kasa sauk'e nauyin da ya d'aura masa. A hankali ya soma furta, "Shema'u banso na zama azzalumi a gareki, ina so muyi magana na fahimta nida ke, idan auratayya bazai yuwu a tsakanin mu ba, zan sawwak'e maki sabida ko kad'an banson shiga hakkin ki...." D'ago watery eyes d'inta tayi tana dubansa yanda yayi maganar, k'irjinta ya buga uwa an sauk'e mata guduma, girgiza kai ta soma tamkar tab'ebb'iya tana kuma cukwikuye masa riga take fad'in "No, no my AT I love you, I can't do without you, zan jira har lokacin da zaka sami lafiya, pls kar kace zamu rabu kaji...." Cikeda mamaki yake kallonta kaman ba ita bace tace sabida yaran 'yaruwarta zata aure sa ba... Ya shiga yin wasu irin tunani sarara, jin tak'i daina kuka yasa sa hugging d'inta still tunanin maganar nata yak'i barinsa. Shaf ya mance takardun da Dr Bilya ya basa a gidan Hajiya, gashi gobe da sassafe ake buk'ata gashi go slow d'in da ake samu da safe a titin unguwar Hajiya zuwa TH ka iya jawo masa ya rasa meeting d'in kuma takardun are very important.. Agogon hannunsa ya duba yaga har goma ta wuce amma gwara yaje, domin zuwan nasa yau zaifi, idan ya kai gobe komai ka iya faruwa. *Sameena Aleeyou Mrs* [9:08PM, 3/21/2018] ‪+234 703 300 1537‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *34* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ *Jinjina, Fatan Alkhairi tareda gaisuwa a gareki gwanata Biebee Isa, ina matuk'ar jin dad'in yanda kike biye da wannan labari nawa.... Rabbi ya kareki da kariyar sa, Ubangiji ya bar k'auna❤* Saidai ya shigo layin ya kuma duba agogon jikin motar sa, k'arfe goma da kusan rabi harta gauta, d'an jim yayi kafin ya soma tunanin ta yaya zai soma masu sallama a wannan daren, wannan ma ai sai yasa suji tsoro, gaskiya sam hakan baiyi tsari ba. Ashfaq ya karya kan motar sa ya fito daga close d'in gidan Hajiya, dama gidan nata shine yanda kwalta ya k'are shine a k'arshen layi. Clash Ashfaq yayi da wata bak'ar mota sai faman danna masa full light suke suna kashe masa idanu, d'an tsaki yayi kafin ya basu hanya suka wuce... Sannan shima yayi wucewar sa.. Bacci suke dukansu biyu hankali kwance, jin ana buga masu k'ofa yasa Hajiya ta mik'e zunbur bakinta d'auke da salati tana k'ok'arin lalumo tocilanta, nan Maryama ma ta bud'e idanu tana k'ok'arin mutstsuka su. Hajiya ta haska tocilan ta tana tafe take fad'in "Ilu sam bakada saiti, yo ko uwar me kake nema talatainin daren nan oho....." muryarta ne ya carke ganin tik'a-tik'an k'arti kusan guda uku dukansu da bak'ak'en kaya sannan fuskokinsu a rufe.... Salati ta soma tana fad'in "K'alu innalillahi wa inna ilalihirraji'una ku kuke ganin mu bamuke ganin ku ba......" bata kai aya ba Spider ya bud'e murya yace "Shut up! kar ki cika mana kunne..." Firgit Maryama ta kuma farkawa ta mik'e tana k'ok'arin saka hijabinta... Oga IK ya kalli Spider yace "Shiga ka zak'ulo mana yarinyar..." Spider ya gyad'a kai kafin ya soma bud'e k'ofofi.... Hajiya tayi wuf ta tare masa hanya tana fad'in "Halan ajiya kayi cikin d'akin??" yanda tayi maganar sam babu tsoro a tattareda ita.. Spider kallo kurum ya tsaya yana binta dashi... Oga IK ya kalli Jarka da tuntuni yake jiran umarnin sa kafin yace "Ka buge buhun nan ka danna min kan wannan tsohuwar ciki, kai kuma Spider ka shige ka fito min da yarinyar nace maka..." Ya k'arashe yana karya k'afafu saman kujera yana hura bakin bindiga... Hajiya tayi masu k'uri tana kallon ikon Allah yanda Jarka ke warware k'aton buhu wai ita za'a danna kanta ciki, jakar uba! Bud'e murya tayi zatayi ihu IK ya daka mata tsawa kana yace "Kika kuma yin fit sai na fasa kanki da bakin bindiga...." Dai-dai lokacin Spider ya fito da Maryama daketa faman tarjewa.... Wani mayen kallo Oga IK ya bita dashi... Haka kurum yaji gabansa ya yanke ya fad'i, ji yayi bai yarda da mutanen da ya gansu layin su Hajiya ba, cikin sauri ya juya kan motar sa ya koma... Kasancewa sautin injuna sun cika unguwar don babu wutan lantarki yasa baza'a iya sauraren draman dasu Hajiya keyi dasu Spider ba.... Kokawa suke kan faman sha da Hajiya tana kare Maryama da tuni Jarka ya fincike hijabin jikinta. Hajiya fad'i take, "Idan kud'i kuka zo nema sai mu baku 'yankunnayen mu da sark'ok'in mu amma ahir d'inku kuyi tunanin tab'a lafiyar d'iyata." Oga IK ya fashe da wata kafiran dariya, domin kuwa k'arfin halin tsohuwar ya basa mamaki. Tsawa ya kuma daka masu daga ita har Maryamar dake b'oye a bayanta tana kuka yace "Ke kinada kud'in da har zamu shigo sata ne, umarni muka zo cikawa don haka karki damu an riga an biya mu...." Ya k'arashe yana k'ok'arin finciko Maryam Hajiya na janyeta, Spider na k'ok'arin janyo wuyar Hajiya ta d'ago k'afarta ta hagu ta sai kai masa harbi take still tak'i sakin Maryama. Mamaki ya cika Ashfaq ganin Ilu a d'aure da sunkuceciyar igiya a k'ofar d'akinsa ga bakinsa rufe da wata tsummar... Cikin tashin hankali ya shiga kwance d'aurin da akama Ilu, ai yana gama kwancesa Ilu ya soma fad'in "Meke faruwa..?" Ilu sai haki yake yana nuna masa cikin gida ya kasa furta komai, duk yayi fitsari a jikinsa sabida tsabagen tsoro... Ai a tamanin Ashfaq ya nufi cikin gidan.. Nan ya tarar Spider sai kokawan tura kan Hajiya cikin buhu yake, ga Maryama k'artan maza har biyu suna kokawan rabata da suturan dake jikinta... Ai take yayi wata tsalle ya cakumo IK ya soma kai masa naushi, shiko Jarka bai fasa k'udirinsa akan Maryama ba, Spider tuni ya tura kan Hajiya cikin buhu sai shure-shure take tana fad'in "Keenafas ci uwar su...." dama taga shigowar Ashfaq a birkice... Hannu tasa ta lalumo dutsen da take daka goro a bayan k'yaure aiko nan ta zage k'arfinta ta sauk'e ma Spider kan k'afarsa.... Ya saki wata k'aran azaba, a tamanin ya saki kan Hajiya yana rik'e da k'afarsa da aka dandantsa... Hajiya tayi k'ok'arin ciro kanta cikin buhun... Ashfaq ya sami daman k'watar bindigar IK nan ya soma pointing nasu dashi, suka soma jada baya.... Ai tuni Spider ya soma k'ok'arin rarrafe da niyar barin parlorn, saidai Hajiya a ankare take dashi, gyara d'aurin zaninta tayi tana fad'in "Ai baka isa gudu ba sai ka fad'i uban da ya turo ka... Ta shiga janyo k'afarsa yana k'ok'arin k'wacewa, dama veranda d'inta akwai buhuhunan shinkafa na Zakkan gona Spider ya shiga kama buhun dake can k'asa yana son tsira, aiko nan buhanen suka shiga runtumo masa d'aya bayan d'aya, Hajiya tayi baya a tamanin.... Hakan yabawa su IK daman tserewa babu shiri... Ashfaq ya bisu a guje saidai inaa, tuni sun tsere... Shiko Spider tamkar maras numfashi haka ya koma, wayar AT Ashfaq ya shiga kira yana mai duba Spider ko yana numfashi abinka da likita... Maryama kam can k'uryar parlron ta tak'ure tana kuka har lokacin tsoro bai bar jikinta ba... ************* Sam AT bai razana da ganin kiran Ashfaq da dare ba tunda yasan k'ila a hospital ne ake neman wani abin.. Jin wani zance na daban daga bakin Ashfaq yasa sa mik'ewa zumbur babu shiri yana karanto innalillahi wa inna ilaihirraji'un.. Shema'u ta mik'e a birkice tana tambayar sa lafiya..? Fuskarta fal damuwa cikin zuciyarta kuwa fal murna ne, don a zaton ta su Spider sun cika mata aikin da ta saka su ne.... K'arasa closet AT yayi bai ko sami zarafin amsata ba, still waya manne a kunnensa yake fad'in "Okay Ashfaq I'll be right there, ka kula min da Hajiya da Maryama, make sure they are safe..." Daga haka katse wayar yayi ya zari jallabiyar sa ya kwab'e inner white d'in dake jikinsa ya zura jallabiyar... Gaban Shema'u fah ya yanke ya fad'i, saurin mik'ewa tayi tasha gabansa tana tambayarsa me ya sami Hajiyan..? Kafad'unta ya d'an rik'e kana yace "zan maki bayani idan na dawo, inaga b'arayi ne suka shiga gidan Hajiya, amma Allah ya taimaka Ashfaq yana can basu masu komai ba, and guda d'aya is unconscious yana can gidan Hajiya d'in sauran sun gudu... Ki kula da kanki da yara..." Daga haka ya fice cikin sauri. Ai gaba d'aya Shema'u bata fahimci me yake fad'i ba, kenan shirinta ya rushe, kenan Hajiya da Maryama suna nan lafiya, jar uba...! Kai ina da sakel, bama wannan ba an kama guda d'aya kenan, asirinta na shirin bankad'uwa kenan.. Ita kad'ai ta shiga girgiza kai ta soma sambatu tana fad'in "Wllhi k'arya kenan, ni Shema'u nafi k'arfin asirina ya tonu, ban fito ba saida na shirya, wllhi babu wanda ya isa yaja dani..." ta shiga muzurai tana zagaye d'akin tana k'aran takaici, barbaza gashin kanta tayi tana huci. Abubuwa suna neman kwance mata, meyasa duk sanda ta shirya wani abu sai ya ruguje, meyasa yanzu take rasa sa'a kaman da..? Zuciyarta ta shiga shaida mata sabida kin bar mutane da yawa suna rab'arsu, "Ashfaq" ta furta a hankali, ta tuna shine mutumin da ya kub'uto da Sajida daga hannun Buzu gashi yanzu ya kub'utar dasu Hajiya da Maryama, tabbas babu haufi shine tunda ranar da ya kawo aika ma AT tana jinsa da Sajida sai zolayarta yake ita kuma tana basarwa sannan Hisham ya bata labarin yanda Ashfaq yake ruguza masa duk wani shirinsa na cutar da AT a asibiti, a da taji dad'in taimakon AT da yake don guje ma sharrin Hisham amma a yanzu battle d'inta dashi zai soma, muddin Ashfaq na jikin AT she won't succeed, she really need to get rid of him before he causes hell for her... Fuzar da iska tayi idanunta suka kad'a sukayi jazir, fuskar Ashfaq kawai take hangowa... ******* Sanda ya isa tuni Ashfaq ya kira 'yansanda sun wuce da Spider asibiti, Hajiya na gefe tana lallashin Maryama AT yayi sallama ya shigo Ilu na biye dashi na basa ba'asi saika rantse wani abin kirki ya tab'uka. A rud'e ya k'araso ya durk'usa gaban Maryama yana tambayar ta "Did they hurt you? Sun maki wani abu,...?" gaba d'aya Hajiya wangale baki tayi tana kallon yanda Attahiru ya susuce akan Maryama.. Girgiza masa kai kurum Maryama keyi alamun babu abinda ya sameta. AT kuwa ji yake kaman ya rungumeta ko zaiji sanyi cikin zuciyarsa sosai kukan nata yake tab'a masa zuciya.... D'aki Hajiya ta kaita kafin ta dawo parlorn suna tattauna lamarin da AT. Hankalinsa ya kuma tashi jin abinda ya kawo b'arayin bama sata bane, shi kad'ai yake tsuma yana jin dukda basu cimma burinsu akan Maryama ba, runtse idanunsa yayi yana tuna dole sun tab'a mata jiki da k'azantattun hannayen su... Fuzar da iska yayi ya mik'e ya dubi Hajiya yace "Hajiya barinje asibitin nan, sai ya fad'i waye ya turosa...." Daga haka ficewa yayi zuciyarsa naci gaba da tafarfasa. Hajiya kuwa tai masa addu'an kariya da samun nasara. Sosai take mamakin ganin yanda hankalin AT yayi mugun tashi.. *Sameena Aleeyou Mrs* [9:21PM, 3/21/2018] ‪+234 703 300 1537‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *35* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ *HBD My Little Miss AKA Firdausi Abdullahi, Ubangiji ya Albarkaci rayuwarki 😘❤* Tunda ya karyo kwanar unguwar su yasha mamakin ganin motar AT na fitowa daga layin, daga can k'ofar gate d'in Hajiya kuwa Ilu ne sai faman lek'e-lek'e take. Ai Buzu na k'arasowa a guje Ilu ya koma cikin gida ya turo k'ofa yana k'ok'arin gark'ama sakata yake karanto addu'an shiga band'aki.... Jin haka yasa Hajiya fitowa cikin sauri domin gaba d'aya Ilu muryar sa ya bud'e yana karanto addu'ar ida alola da ta shiga band'aki.... Hajiya tana tambayarsa lafiya..? Inaa fad'in yake "Sun kuma Hajiya, aradu sun kuma dawowa.. Sosai abun ya bawa Buzu dariya yana mai ci gaba da bugun gate d'in yana fad'in "Ni ne Ilu, Haris Buzu ne..." Hajiya ta watsa wa Ilu harara kana tace "Kauce min dalla naga alama kaikam dai maza ka rako...." Hajiya ta bud'e k'aramar k'ofar Haris ya shigo yana gimste dariyar sa. "Harisu ina ka fito talatainin daren nan...?" Hajiya ta tambaya tana d'aura hannaye k'asan k'irjinta.. "Hajiya hayaniya naji shiyasani fitowa.." Cewar Buzu dake danno kai cikin gidan. "Kai ashema kaine, ai wllhi na zaci b'arayin nan ne suka dawo da na shayar dasu mamaki, aradun Allah sandar shad'ita ta gado zan d'au....." Bai kai aya ba Hajiya da ta sake baki tana kallonsa tace "Rufe min baki, saikace gaskiya, aikin da ka iya kenan cika baki uwa d'an marok'i, inji yanzu ka canza kayan fitsarin naka, kai wannan inaga gidan gona ya kamaceka sam bakada saiti..." Ilu ya wage hak'wara uwa gonar auduga yana dariya yake fad'in s"Hajjaju namu wanda sukaje Madina suka gaida Manzo ai idan babu mu bakwa iya zaman unguwar ba, muna nan dai mutu ka raba, Dapta yayi iya yinsa ya hak'ura...." "Kai tafi can da Alla..." Hajiya ta katse sa. Buzu ya gaida Hajiya kafin ya soma jajanta lamarin, Hajiya ta kwashe labari tsaf ta basa. Gabansa ya yanke ya fad'i, ba kowa ya fad'o ransa ba illa Shema'u, that witch zatayi abinda yafi haka. D'an kintsa kansa yayi kafin yace "Hajiya Maryama fah, da fatan tana lafiya..?" Hajiya ta kuma turo baki still tana jinjina lamarin kafin tace "Ai wato Harisu ina fad'a maka b'arayin turen nan sam basuda mutunci fah, yo cikin buhu dai da ka sani nan suka dannan kaina suna k'ok'arin ficewa dani saikace wata Mage, Allah dai ya rufa asiri wannan yaro abokin aikin Attahiru da shi mukayi hira ya mance takardun sa , toh da ya dawo d'auka saifah ya taimaka mana, Allah Ya rufa asiri basu tafi dani ba basu ci mutuncin Maryama ba kaman yanda suka so. Ohh ai wannan yaro Asheefak yaron kirkirne ina kiransa Keenafas ai yaune naga Keenafas d'in gaskiya, kaina cikin buhu uwa Mage ni Fad'ime..." Ilu sai faman k'unshe dariyar sa yake yayinda hankalin Buzu yayi mugun tashi, shi kad'ai ya shiga jero tunani iri da kala, lallai Shema'u bata gaji mutunci ba, wato rayuwar Maryama take yunk'urin lalatawa, macen da yake so yake mafarkin kasancewa tareda ita.. Muryar Hajiya ne ya katse masa tunanin nasa. "Harisu kaje gida abinka, babu komai kaji, Allah dai ya dad'a karewa." Buzu ya d'an yi still kafin yace "Shikenan Hajiya, Allah Ya dad'a kiyayewa, dan Allah a gayar min da Maryama insha Allah gobe zan shigo..." Sallama sukayi da Hajiya tace ya gaida Hajiyar sa kafin ya wuce gida zuciyar sa nai masa zogi... Buzu yana shiga gida lambar Shema'u ya soma kira. Tana d'agawa ya soma fad'in "What the heck is wrong with you, wllhi wllhi don't you dare hurt Maryama, shaye-shayen ki bai gaya maki gaskiya, babban kuskuren da zakiyi kenan ki lalata rayuwar Maryama..." "Stop being silly, kar kayi magana haka, meyasa zan lalata mata rayuwa, on the contrary nima abin ya dameni kar ka mance Hajiya uwar mijina ce..." Dariyar rainin hankali Buzu yayi kafin ya gimtse yace "Don't play innocent with me, I wasn't born yesterday... Wllhi abinda ya faru gidan Hajiya aikin ki ne, since when kika soma damuwa da damuwar iyalan AT, ni dai inai maki gargad'i kar ki cutar da Maryama idan kuma ba haka ba...." yayi wata murmushi kafin yace "I'll bring you down..." A hasale ta katse sa da fad'in "Shut the hell up! kai waye da har zaka ke d'aga min murya, yes aiki na ne, kuma wllhi idan bata bar min mijina ni kad'ai ba zan b'atar da ita kaman yanda nayi da sauran..." tayi wata murmushi mai cikeda ma'anoni kafin taci gaba da fad'in "You still don't know me, do you..? Haris idan baka daina jada umarni na ba wllhi zaka tsinci kanka daga cikin marassa sa'a, idan banda abinka that mere girl doesn't have eyes for you, idan baka sani ba ta makance da soyayyar mutumin da yafi k'arfin ajinta, idan ka kwantar da hankalin ka abinda nake yi amfanin ka ne kaima sannan ko kace zakayi fad'a dani you will never defeat me, because whatever you does you can't bring me down..." daga haka katse wayar tayi tana wata kafiran dariya... Tunowa da tayi boys d'inta d'aya na asibiti yasata saurin kiran layin Hisham... Yana d'agawa ta masa breaking news d'in.. Hisham baiso haka ba, ya gama sakewa wannan karan zai sami dama akan AT.... A birkice ya soma fad'in "yaya akayi hakan ta kasance...?" Shema'u dake faman zagaya d'aki ta shafi goshinta kana tace "That's precisely why I called you, Hisham saida na fad'a maka bazasu iya aikin nan ba kace kayi trusting d'insu, yanzu duk bama wannan ba ko kasan d'aya daga cikinsu yana asibiti, and definitely idan ya farka ya bada statement d'insa ta k'are mana, we really need to do something right away..." Hisham ya mik'e yana zura riga yake fad'in "Ba dai kince na asibiti ba, ki bar min wannan I'll take care of it...." Daga haka katse wayar yayi ya d'auki car keys d'insa ya nufi ma'ajiyar motar sa, yana driving yake kiran layin AT... Parlor ta sauk'o ta d'auki ruwa a kitchen tana rik'e da goran ruwan take huci tana fad'in "Wllhi duk sai na gama daku, one after the other, Aysha I won't stop until your family is completely ruined, bazan huta ba har sai na mallaki Attahiru ni kad'ai, just me and only me... Da sannu zan aika yaranki gaba d'aya yanda na aika ki...." Jiri ne ya soma d'iban Maama Juu ta sauk'o d'auka ma Ni'ima ruwa, kasa yarda tayi da abinda kunnuwanta ke jiyo mata daga bakin Shema'u tayi.... Jikinta kuwa tamkar mazari haka yake rawa hawaye suna bin k'uncinta.... Juyawan da zatayi ta bige flower vase hakan yayi dai-dai da juyowar Shema'u... Gaban Shema'u ya yanke ya fad'i sanda sukayi ido hud'u da Maama Juu, dashike zuciyarta a taurare take nan tayi saurin kintsa kanta tana mai sakar ma Maama Juu mayaudarin murmushin nan nata. Maama Juu ta soma jada baya tana nuna Shema'u da d'an yatsa take fad'in "Kece wllhi kece, ke kika kashe Aysha...." hawaye na ci gaba da zuba a idanun Maama Juu taci gaba da fad'in "Kin cika babbar muguwa azzaluma, ban tab'a tunanin duniya akwai irinka ba..... Wllhi Allah bazai baki sa'a ba, wllhi Allah sai ya kare iyalan Aisha daga mummunar bak'ar sharrin ki..." ta k'arashe tana mai taka matakala cikin sauri cikeda tsoro.. Shema'u tabi bayanta cikin wani irin taurin zuciya ta shiga janyo Maama Juu tana fad'in "Comeback here, kinyi kad'an ki bayyana sirrina..." Kokawa suka soma Maama Juu na k'ok'arin haurawa domin kare 'yan yaranta... Shema'u kuwa jawota take da iya k'arfinta, sam babu k'arfi jikin Maama Juu, tsoro da firgici gaba d'aya sun gama cikata... Saida suka isa can sama k'arshen matakala Shema'u ta fincikota da k'arfin gaske ta wurgota ta shiga gangarowa k'asa.... Lokaci guda Maama Juu ta saki wani irin k'ara... A tamanin Shema'u ta koma d'akin AT cikin sakanni... Ni'ima kuwa a guje ta fito daga d'akinsu da Maama Juu jiyo sautin k'aran Maama Juu da tayi, ganin Maama Juu kwance k'asan matakala ga jini na bin goshinta yasa Ni'ima k'walla wani irin firgiteccen k'ara ta k'ame waje guda.. A tare Shema'u da Sajida suka fito, harma da Jamal dake faman mustukke idanunsa alamun bacci.... Gaban Sajida yayi wani irin yankewa ya fad'i, cikin sauri ta soma sauk'owa daga matakalan ta k'arasa wajen Maama Juu jikinta na rawa hawaye na bin k'uncinta... Wani irin k'ara ta Saki sanda ta mirgina ta taga jini na malala a goshinta.... Tuni Shema'u ta suri Ni'ima ta rungumo Jamal dasuke faman kuka da iya k'arfinsu. Kuka Sajida keyi tana jinjigata take fad'in "No, no pls noo... Maama Juu you can't leave us right, kin tuna kince zaki kasance tareda mu, ki tashi don Allah.... Mummy already left us, don Allah ki tashi....." Iya Kande ta fito jikinta na k'yarma sabida abinda ta gani itama, Shema'u sai matse k'walla take, ta k'arasa tana k'ok'arin janye Sajida saidai inaaa, gaba d'aya yaran kwanciya sukayi saman k'irjin Maama Juu suna kuka sosai... Shema'u ta dubi Iya Kande tace "Kula dasu barin d'auko wayata..." cikin sauri ta haura sama ta d'auko wayarta ta shiga dialing lambar AT. AT suna kan Spider suna shirye-shiryen shiga dashi theater domin ceto rayuwar sa sabida spinal cord d'insa is badly injured bai farfad'o ba sai an masa aiki... Ganin wayar Shema'u yasa gabansa mugun fad'uwa. Yana d'agawa yaji muryarta cikin kuka ga sautin kukan yaransa a gefe... Kasa furta komai yayi sabida tashin hankali sanda take fad'in "Tahir ka dawo gida don Allah... It's Maama Juu... Dan Allah kazo...." Daga haka katse wayar tayi tana sharan hawaye... Innalillahi wa inna'ilahirraji'un kurum AT ke nanatawa, Hisham dake tsaye gefensa yana zura hand gloves kallonsa yayi kana yace "Doc is everything alright..?" Girgiza kai kurum AT keyi jiri na neman kadashi yake fad'in "Hisham nothing is alright, I've to go.... Just take care of everything here okay....." Daga haka kwab'e gloves d'in hannayen sa ya soma yana cire rigar theater da suke sakawa na likitoci ya suri car keys d'insa... Dai-dai nan Ashfaq ya k'araso yana turo keken kayan aiki, ganin AT cikin tashin hankali ya nufi waje yayi mugun d'aga masa hankali, a tamanin yayi kansa yana fad'in "Dr lafiya...?" girgiza masa kai AT yayi kafin yace "Gida zanje.." Ai a tamanin Ashfaq ya gungura keken yana kwab'e gloves d'in hannayen sa yake fad'in "I'll drive you Dr..." Bai jira cewar AT ba ya nufi parking lot a tamanin.. A zaton Ashfaq wani abin ne ya sami Sajida ko saurayin nata ya gudu da ita, gaba d'aya hankalin sa ya tashi... Hisham kuwa murmushin cin nasara yayi kafin ya yaci gaba daga yanda suka tsaya.... *Sameena Aleeyou Mrs* [9:27PM, 4/5/2018] ‪+234 806 652 0501‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *36* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ Jini ya rufe fuskar Maama Juu gaba d'aya baka iya tantance fuskarta sabida yanda jini ya b'ata fuskar sosai.... Ashfaq na daga bakin k'ofa AT na k'ok'arin aune-aune don tabbatar da tana numfashi ko kuwa batayi, Shema'u rungume da yaran sai lallashinsu take hawaye na sauk'o mata itama sai ka rantse iyakacin gaskiyarta kenan. Gaba d'aya AT ya kasa ci gaba da aune-aunen da yake sai hawaye dake gangaro masa, sosai Maama Juu ta zubar da jini. Ya kasa yarda Maama Juu ma is gone, mutuwar Aysha ya dawo masa sabo, meyasa rayuwa ta kasance haka, good people suke tafiya... Ganin tunanin sa na neman kaucewa daga hanya yasa soma jero innalillahi wa inna'ilaihirraji'un... He needs to be strong for his family and also for Maryam, tabbas wannan babban rashi aka kuma masu. Hannu yasa ya warware d'ankwalinta kafin ya rufe fuskanta dashi gaba d'aya... Sajida ta fincike a guje ta nufo wajen mahaifinta tana kuka take jijjigasa take fad'in "Daddy she's alive right..? Bata mutu ba ko Daddy, Daddy don Allah kace min zata tashi, pls Daddy do whatever you can, we can't lose her.... Pls Daddy.." kuka sosai ya kubce mata.. Rungumeta AT yayi yana k'ok'arin k'arfafa mata gwiwa da lallashinta.. "Sajida I'm sorry, Maama Juu is gone, sweetheart you need to be very strong okay, your siblings needs you..... kuyi hak'uri...." ya kasa k'arasawa sabida muryarsa da ya soma rawa... Sajida ta k'uma k'ank'ame mahaifinta tana girgiza kai take fad'in "No... No.. no Daddy...." AT ya d'ago idanunsa yana duban Jamal da Ni'ima yanda suka kwanta saman gawan Maama Juu suna kuka, abin ya wuce abin tausayi, harta Iya Kande saida imani ya ratsa zuciyarta k'walla ya shiga gangaro mata. Ashfaq dake tsaye daga bakin k'ofa kasa ci gaba da tsayuwa yayi a wajen, ya fice hawaye na gangaro masa, rasa tilon k'anwarsa ya fad'o masa mussaman da ya tuna wai mahaifinsu shi yayi tsafi da ita sabida biyan buk'atarsa ta duniya, kai kaico halin d'an adam a yau ya zama abin tsoro. Shema'u ta d'ago idanu tana duban AT yanda ya rungume yaransa, yaran sai kuka suke gaba d'ayansu, shi kansa ya kasa basu baki, sosai zuciyarsa ta raunana.. Ta k'araso tana goge fuskarta da yayi jazir sabida kuka kafin ta dafa kafad'an Sajida tace " Sajida kuyi hak'uri kuyi mata addu'a shine kawai gatan ta a halin yanz.... .." kasa ci gaba da maganar tayi sabida kuka da ya kuma b'alle mata. AT kam Bai iya ce mata komai ba sai kallo da ya bita dashi, yana rungume da 'yan 'ya'yansa lokaci guda tunanin Maryama da tausayin ta na ratsa zuciyarsa. K'unshe bakinta Shema'u tayi saika rantse irin kuka ne yaci k'arfinta kafin ta haye sama ta d'au wayarta hawaye na bin k'uncinta take wata kafiran murmushi, waya suka somayi da Hisham ta sanar dashi abinda ke faruwa, sosai ya razana da hidiman Shema'u, amma mutuwan Maama Juu da Spider shine rufin asirin sa shima. Suna gama waya dashi ta soma murmushi tana tunanin kiran Hajiya ta mata breaking news d'in cikin salo na makirci da kashe jiki, tabbas idan ta kira Hajiya tana kuka k'ila ta soma saye zuciyar jarabebbiyar tsohuwar, kawar da ita a doron k'asa bayan ta saye zuciyarta sai yafi mata sauk'i. Cikin kuka Shema'u ta kira Hajiya ta sanar da ita abinda ke faruwa, yanda take kuka harda shesshek'a saika rantse har cikin ranta iyakacin gaskiyarta kenan.. Hajiya gaba d'aya jinta take tamkar a wata duniyar, bakinta ya kasa furta komai, kwanyarta na barazanar juyewa. Meke faruwa dasu ne, Aysha bata jima da mutuwa ba, yau b'arayi sun far masu sannan GA wani tashin hankalin kuma, anya ba wani laifi sukayi ma Allah yake jarabtansu haka ba... Cikin sauri ta furta "Astagfirullah" domin kuwa ikon Allah Ya wuce gaban wasa, shi d'in kunfa yakun ne, sannan fad'insa ne _Kullu man alaiha faan_ tabbas Allah baya k'ara ma rai tsawon kwana idan lokacinta yayi d'if zata tafi koda ciwo ko babu ciwo... (Allah ka bamu k'arshe mai kyau, ameen.) Hawaye suka shiga gangaro ma Hajiya, bata ma san me zata soma fad'i ma Maryama ba. Ta sakata gaba ta tsura mata idanu hawaye na gangaro mata... Maryama daketa sararan mafarkai don tunda b'arayin nan suka tab'a mata jikinta bata dawo normal ba, baccinma satan ta yayi, farkawa tayi taga Hajiya ta baza tagumi tana kallonta tana hawaye.. Cikin sauri ta mik'e ta isa gaban Hajiya ta durk'usa saman gwiwoyinta tana tambayanta "Hajiya lafiya...? Hajiya sun maki wani abu ne, Hajiya meke faruwa... Don Allah ki min magana...?" Hajiya bata iya amsata ba sai sabon kuka da ya kuma b'arke mata. Hawaye suka soma bin k'uncin Maryama sanda taci gaba da fad'in "Hajiya don Allah ki fad'a min meke faruwa, Hajiya kukanki tashin hankali ne a gareni, wani abune ya sami su Uncle, b'arayin nan sun harbi su Uncle da Ya Ashfaq koh, Hajiya ki fad'a mun? Don Allah ki fad'a min. Kallon tausayi Hajiya ta bita dashi kafin ta rungumeta sosai tana mai ci gaba da kuka, kaman wacce aka sinkaya kuma sai d'ago kafad'un Maryama tayi kana tace "Tashi, tashi muje... " Maryama da har lokacin kuka take ta mik'e tana zura hijabi had'i da d'auko slippers d'inta dana Hajiya wari-wari batama san ta had'a ba... Ilu ya tsorata sosai da ganin yanayinsu, duk tambayan da yake masu babu wanda ya sami zarafin amsa sa cikin su, gaba d'aya basu san yanda suke jefa k'afafun su ba. Ilu cikin sauri ya k'arasa gate d'in su Buzu ya shiga bugawa ganin Hajiya da Maryama sun nufi bakin kwalta suna neman abin hawa ga dare ya ja.... Mai gadinsu yana fitowa Ilu ya shaida masa halin da ake ciki.. Cikin sauri ya nufi sashen Buzu ya tada shi. Shi kansa Buzu ya razana da lamarin, motar sa ya d'auki ya nufi yanda su Hajiya ke tsaye. Cikeda tashin hankali yake fad'in su shigo ya kaisu. Gaba d'aya suka d'unguma cikin motar Buzu, sai basu baki yake dukda baisan musababbin abinda ya faru ba, lokaci guda zuciyarsa ta cika da firgicin abinda Shema'u ka iya yi don cimma burinta, sam Shema'u ba abin yarda bace, sosai yake tsoron kaidinta... Hajiya rik'e da Maryama suka nufo cikin gidan, Ashfaq dake tsaye daga waje yana hangosu gabansa ya yanke ya fad'i. Su kuwa sam basuma lura dashi ba suka nufi cikin parlorn... Abinda idanunsu ya gane masu sai yafi d'aga masu hankali, AT rungume da yaransa Jamal da Ni'ima yayinda Sajida ke rungume cikin k'irjin Shema'u gaba d'aya basu a hayyacin su, hankalin Maryama bai gama tashi ba saida ta hangi mace kwance a k'asa an lullub'e kanta.. K'irjinta yayi wani irin bugawa. Batasan sanda ta furta "Ummmiiiiii!!!!!" da k'arfin gaske. Wanda hakan ya janyo hankalin su AT suka kai dubansu ga bakin k'ofa yanda Maryama da Hajiya suke a sandare. A guje ta tafi kan gawan ta yaye rufin fuskar, jinin da ta gani sai ya kuma d'aga mata hankali... Take ta zube a wajen sumammiya.... A tamanin AT yayi kanta yana jijjigata yana kiran sunata inaaa bata bud'e idanu ba... Ya mik'e ya nufi saman dinning ya suri goran ruwa ya dawo ya durk'usa nan gabanta yana yayyafa mata gaba d'aya ya rikice..... Shema'u sai uwar harara kurum take watsa masa yanda ya daburce sabida Maryama. A hankali ta soma bud'e idanunta kafin ta mik'e ta kwanta saman Maama Juu tana kuka mai tsuma zuciya. "Umm.... Ummi, Ummi na ki tashi don Allah, kar ki tafi ki barni, Ummi kince min kowa namu sun mutu ke kad'ai kika rage min meyasa kema kika tafi kika barni, Why Ummi, why....." kuka ya kuma kufce mata.. Shema'u ta k'arasa tana k'ok'arin janye Maryama tana bata baki, Hajiya ta k'arasa kan Maama Juu tana hawaye take tuno tun farkon had'uwar su har zuwa rana mai kaman ta yau... Addu'a ta shiga jero mata hawaye na bin k'uncinta.. AT ya dubi Shema'u ya mata alama ta haura da Maryama sama. Babu musu ta gyad'a masa kai kafin tayi yanda yace.. Suna tafe take fad'i ma Maryama "Ki dinga karanto innalillahi kinji, ki daina kukan nan kinji koh..." A wannan bak'in dare haka akayi kwanan k'unci tareda tarin alhini a gidan Dr Ahmad Tahir.... Allahu Akbar, dukkanin mai rai mamaci ne, 'Yan uwa mubi duniya a sannu. Washe gari aka mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya, Hisham da Ashfaq harma da Buzu tareda su akayi komai. Maryama da Hajiya dole suka tare gidan AT. Gaba d'aya Maryama ta zama abin tausayi, harta Sajida tausayinta take, AT kuwa shiga goma fita goma sai ya tambaya taci abinci kuwa? Kacaukam hankalinsa na kan Maryama da yaransa musamman Maryama data kasance d'iya ga Maama Juu. A b'angaren Shema'u kuwa ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba ganin yanda AT ke ririta Maryama yana sakata a gaba taci abinci na dole, koda tace masa ya bar mata kulada Maryama a hannunta bai kula zancen nata ba. Yana ahigowa gida daga wajen 'yan karb'an gaisuwa d'akin Hajiya da Maryama yake nufowa, yaran ma gaba d'aya sun k'aura d'akin. Hankalin Shema'u ya soma tashi, dole tasan abinyi, ga Ashfaq ma kaman competition suke akan Maryama, sabida shid'in ya zama d'an gida wajen Hajiya.... AT da Hisham basu sami zarafin maganar halin da Spider ke ciki ba sai bayan kwana uku. Nan Hisham ya shaida masa aikin Was successful zai iya farkawa nan da wasu kwanaki... AT ya jinjina kai kurum ba tareda ya furta komai ba. Hisham sai faman karantar yanayinsa yake kafin ya gyara zama had'i da d'an gyaran murya ya soma fad'in "Tahir kai d'an uwa ne a gareni, a gaskiya bazan zauna ina ganin abubuwa suna faruwa da kai ba nayi shiru ba tareda na maka magana ba. Tahir kanada saurin yarda da mutanen wann zamani, kowa jawosa kake jikin ka, kai da niyyan taimako kake su kuma su cutar da kai, regarding abubuwan da suke faruwa da Family d'inka lately a gaskiya ka bud'e idanunka da kayu kasan waye kake jawowa jikinsa.... Ya d'an ja fasali kafin yaci gaba da fad'in "Good example mu d'auki wann yaron Ashfaq, from no where yazo shi ka karb'esa hannu bibbiyu ka yarda dashi lokaci guda har ka had'asa da iyalanka... Tahir ka bud'e idanunka da kayu before it is too late... *Sameena Aleeyou Mrs* [9:27PM, 4/5/2018] ‪+234 806 652 0501‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *37* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ D'ago idanu AT yayi yana duban Hisham ba tareda ya iya furta komai ba. Da k'yar ya k'ak'aro murmushi kana yace "Hisham kenan ni da ka ganni ban tab'a yarda wani d'an Adam zaimin abunda Allah baiyi mun ba, walau ta cutarwa ko akasin haka. Duk abunda kaga ya sami bawa a rayuwa toh fah ka tabbata Allah Ya hukunta faruwan hakan. So bazan d'aura blame d'in abinda ke faruwa dani ga wani ba. Ashfaq yanada matuk'ar mahimmanci ga rayuwata, kar ka mance a sanadin sa Allah Ya tsare Hajiya da Maryam, Ashfaq alkhairi ne a garemu. So pls ka daina irin wad'an nan maganganun saikace ba musulmi ba, ansan musulmi da yarda da k'addara a duk yanda tazo masa, iyakaci muyi addu'an Allah Ya bamu jarabawar da zamu iyaci a rayuwa." Hisham ya k'ura ma AT ta mujiya yana mamakin k'arfin imani irin na AT. Gyara zama ya kumayi kafin yace "Tahir bank'i maka ba, amma kai baka ganin zuwan Ashfaq nada alak'a da abubuwan da suke faruwa, ka sake tunani Tahir, me ma ya kai Ashfaq gidan Hajiya da daddare idanba shi ya tsara zuwan b'arayin ba. I'm not saying kayi firing nashi a wajen aiki, but ka saka masa iyaka da iyalanka... Shawari ce..." ya k'arashe yana k'ok'arin mik'ewa tsaye. D'an jim AT yayi kafin yace " I'll think about it, amma ka sani zuwan Ashfaq gidan Hajiya baida alak'a da b'arayin da suka shiga gidan hasalima zuwan nasa alkhairi ne..." ya k'arashe maganar nasa yana mik'a ma Ashfaq hannu sukayi sallama. Kafin Hisham ya nufi ma'ajiyar motar sa yayinda AT ya nufi cikin gida yana mai tunanin maganganun Ashfaq. Koda Hisham ya labarta ma Shema'u yanda sukayi da AT a waya sosai hankalinta ya tashi, kenan tabbas AT bazai rabu da tsinannen yaron nan ba? Lalallai kuwa gwara tasan abinyi tun wuri. Abu guda da ya faranta mata rai shine, Hisham ya sanar da ita yama Spider wata allura wanda a hankali zai mace ba tareda kowa ya fahimta ba, wato slow dying zaike yi. *************** Bayan sati guda Hajiya da Maryama suka tattara suka koma Janbulo, babu yanda AT baiyi ba su zauna Hajiya tak'i hakan a cewarta idan don yaransa ne akwai mai kula dasu tunda yanada Mata sannan 'yaruwa ga mahaifiyar su. AT kuwa daga asibiti kusan kullum a gidan Hajiya yake yini. Maryama ta shige d'akin Umminta tana kallon kayayyakin ta da wasu abubuwan ta, tanayi tana hawaye, gaba d'aya ta zama abin tausayi. Idanunta suka sauk'a kan wani d'an k'aramin akwati wanda Marigayiya ta haneta da tab'a akwatin tun tana k'arama. Gaban Maryama ya yanke ya fad'i, cikin sauri ta shiga goge hawayen ta kana ta nufi yanda k'aramar chase d'in take cikin wardrobe. D'aukowa tayi ta dawo saman gado ta zauna. K'irjinta na bugawa da sauri da sauri ta soma bud'ewa. Wata sark'a ta gani wanda ba sai ance maka na zallan Diamond bane, tasha mamakin ganin wannan sark'a cikin 'yar akwatin dukda batasan yanayin tsadarta ba tanada kyau sosai. Murmushi tayi ta rungume sark'an cikin k'irjinta kafin ta furta "Ummi ina sonki, na tabbata wanda ya d'auke min ke ya fini k'aunarki, Allah Ya gafarta maki ya had'a fuskokin mu a darussalam, yanda zamu dawwama muna rayuwa babu mutuwa." Samun kanta tayi tana mai jin nutsuwa cikin zuciyarta bayan ta k'arashe karanto addu'o'i ma Ummin nata. A hankali ta soma saka sark'an a wuyarta tana mai murmushi bushesshen hawaye saman fuskar ta, tabbas itada wannan sark'a mutu ka raba ne, babu abinda zai sakata cirewa sai mutuwa. Bata kuma bincike akwatin ba ta rufe dukda akwai kaya a k'asa an rufe da wani zani, sam Maryama bata lura da hakan ba, hankalinta yafi karkata kan wannan sark'an. Ciccib'an akwatin tayi ta maidasa wajen zaman sa. ********* Sosai Ahsfaq ya shiga matsanancin tashin hankali da mutuwar mahaifiyar Maryama, kullum ya kwanta sai yayi mafarki da matan tana kiransa da asalin sunansa tana fad'in _Haidar ka kula min da d'iyata Maryam, kar ka bari rayuwarta ta salwanta, ka kasance miji kuma garkuwa a gareta ta haka ne kurum zaka iya bata kariya._ amma bai iya tantance fuskar ta sannan muryar yana masa kama da ya tab'a ji wani wajen, Sosai abin ya damesa. Duk ya had'a zufa sharkaf ya zauna saman gado, a hankali ya karanto addu'ar tashi a bacci. Toh idan matar da yake mafarki da ita mahaifiyar Maryama ce kenan tasan sa kenan, meyasa muryar ke kiransa da Haidar. Ya ja numfashi sannan ya fuzar, kai kodai tsaban son Maryama da yake yi ne ya sakata cikin ransa har yake irin wad'an nan mafarkai...? Toh amma ba sau d'aya ba sau biyu ba yayi, kai gaskiya yana son Maryama sannan zai nemi aurenta koda hakan ka iya jawo fallasan asalin sa...... Da wannan ttunani ya mik'e yana k'are ma asalin kamannin sa kallo jikin mirror. A b'angaren Buzu kuwa gaba d'aya yayi la'asar, duk barikancinsa bazai iya kashe rai ba, hasalima shi ko yanka ne baiyi ma Hajiyar sa Malam Sallau mai gadinsu keyi, gaba d'aya jinsa yake wani iri, duk wani d'abi'un sa na banza ya watsar dasu. K'arewa ma canza sim d'insa yayi sabida Sajida da Shema'u, shi a halin yanzu tausayin Maryama da soyayyar ta yafi cika zuciyar sa, son gaskiya da aure yake mata. Ya k'udiri niyyan zai nemi aurenta ya zame mata garkuwa daga Shema'u koda hakan na nufin rasa numfashin sa, tunda shi yasan waye Shema'u sannan muddin Maryama ba aure tayi ba Shema'u bazata k'yaleta ba, data salwantar mata da rayuwa gwara ya aureta ko Yemen ne wajen dangin iyayen sa gwara su koma..... Yini zubur tunanin da Buzu yake kenan, yana neman mafita ta yanda zai rabu da Sajida cikin sauk'i. ******* Sosai abin ya soma damun AT ganin Ashfaq da Buzu basuda wajen yini da ya wuce gidan Hajiya, shima gashi nan rabin yininsa bayan tashi daga wajen aiki a gidan yake, watarana ma tareda Ashfaq suke isowa gidan. Sannan kowa nuna damuwar sa sosai yake akan Maryama, kowa so yake ya burgeta ya mantar da ita halin k'unci da take ciki. Koda Hajiya taga Maryama da sark'an sam bata hanata sakawa ba, sosai taji dad'i ganin Maryama ta soma sakewa, sannan Sajida ma ta rage hantaran Maryama da take a baya. Har wuni AT ke kawosu gidan Hajiya gaba d'aya yaran don suma su rage kewar da suke ciki.... ********** Tunda ta kwanta take wasu irin mugayen mafarkai, wasu halittu na binta basuda kai balle ta gane kamannin su... Firgita take sosai, idan ta farka tayita gumi kenan kaman an jefata cikin wuta. Ga wani irin zafi da jikinta keyi muddin tayi mafarkin... ********* Bayan wasu satattuka su Jamal sun koma makaranta, Maryama da Sajida sun shiga computer school, rayuwa ta soma koma masu kaman ta baya, musamman dukan su biyu idan suka tuna sun rasa iyayen su, daga Maryamar har Sajidar, wani sabon SHAK'UWA CE ta soma shiga tsakanin su, Sajida a kullum da tunanin Buzu take kwana take tashi, gaba d'aya ta rasa ta yanda zata sameshi nan ta yanke shawarin sanar da Maryama ko zata taimaka mata. ************ Wani irin muguwar fad'uwar gaba ne ya sauk'o masa jin Mummyn sa na kuka da hawayenta sabida shi. _Haidar don Allah ka dawo gareni kafin ka rasani..._ Kalman dake kan faman yawo a kunnensa kenan wayar da sukayi da Mahaifiyar sa a daren jiya. Wata b'angare na zuciyar sa kuwa muryar mahaifiyar Maryama ya kasa b'ace masa. _Haidar kai kad'aine zaka iya zama garkuwa a gareta, ka auri d'iyata domin ka zame mata kariya.._ Runtse idanunsa yayi bugun zuciyarsa na k'aruwa da sauri da sauri, ga kansa da yayi masa nauyi yana neman mafita. ******** Sajida ta gyara zamanta ta kuma rik'o hannun Maryama cikin nata kafin ta soma fad'in "Ki yafe min duk wasu abubuwan da na maki, kinsan zuciya batada k'ashi, all I was thinking shine Daddy sonki yake amma yanzu na aminta SHAK'UWA CE kawai a tsakanin ku da Daddy sannan yana maki irin son da yake mana ne a matsayin d'iya. Maryama pls ki yafe min kinji." ta k'arashw tana k'ak'aro murmushi Murmushi Maryama ma tayi tausayin kanta ya lullub'e ta, da ace Sajida tasan yanda Allah Ya jarabceta da soyayyan mahaifinta da bata soma fad'in haka ba, but this shows itada Uncle can't never be together, dole ma ta cusa ma ranta ta tursasa ma ranta cireshi daga cikin zuciyarta.... Dole ta amince SHAK'UWA CE kawai a tsakanin su. Kaicon zuciya irin tata wanda bai hasasho abu dai-dai. K'ak'aro murmushi Maryama tayi had'i da hugging Sajida cikin rawar murya take fad'in "Sajida ban rik'eki da komai ba, nima ki yafe min don Allah kinji..." Sajida tasa hannu ta shiga share ma Maryama hawayen ta. Hajiya dake zaune cikin parlor tana hangosu daga veranda ta sa hannu ta goge k'wallan da suka zubo mata tausayin yaran ya cika zuciyarta. Kaman daga sama suka jiyo sallaman Buzu.... Gabansa ya yanke ya fad'i ganin Maryama da Sajida a tare... *Sameena Aleeyou Mrs* [9:28PM, 4/5/2018] ‪+234 806 652 0501‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *38* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ *Gaisuwa da babban murya gareku masoya wannan labari, Sameena na k'aunarku a duk yanda kuke ❤👌🏾* _Masu k'orafin na bud'e shafi a wattpad sabida labarin ya ringa isa maku cikin sauk'i naga sak'onku, banyi alk'awarin bud'e shafi a wattpad amma insha Allah zan duba na gani idan da hali zan bud'e, na gode k'warai da nuna k'aunarku 🤝_ Shafa kansa Buzu ya d'anyi kafin ya isa k'ofar parlorn Hajiya yana sallama. Hajiya ta masa iso ya shiga ya soma gaida ta, gaba d'aya hankalinsa naga waje yanda su Maryama da Sajida ke zaune, sam bai samu sakewa a gidan ba. Koda ya fito Maryama ce kawai ta sami zarafin gaidashi Sajida kam k'uri ta masa tana jira taji ko zai mata magana shiru..... Bai sami zarafin jimawa a gidan ba, sauri-sauri yayima Hajiya sallama ya fice. Sam Maryama bata lura da yanayin k'awar tata ba, sai bayan sun k'ule a uwar d'akin Hajiya Maryama ta lura da canzawan Sajida. Dole Maryama ta tasa Sajida a gaba ta fad'a mata abinda ke damunta. Sosai Maryama ta tausaya ma Sajida, tabbas ta sani tana tsananin son Haris sannan ta sanadiyan Sajida suka saba da shi, wannan karan kam ta d'au alwashin zatayi iya k'ok'arinta wajen ganin Haris ya sauk'e idanunsa kan 'yaruwarta kuma k'awarta, sam bata k'aunan abunda zai kuma kawo masu sab'ani musamman yanzu da Sajida da k'annenta suka tareda zama gidan Hajiya, idan kaga sun tafi gidansu toh weekend ne, hakan yasa attention d'in AT kacaukam ya koma gidan Hajiya, sam Shema'u bata gabansa, wani sa'in har fad'a yakema kansa kar Allah Ya hukunta sa da hakkin Shema'u. Daga Ashfaq har Buzu yanzu AT ya d'an d'aga masu k'afa ba kaman da ba, ko yayi niyyan fatattakan su ma Hajiya ke hanasa. *********** Hankalinta duk ya gaza kwanciya, Buzu yayi disappointing d'inta, ga wayan da Alh Aminu ya matsa mata dashi yana so yazo wajenta, nan ta soma tunanin ai gwara yazo ma ta samu kud'i tasan ta yanda zata soma b'ullo ma Al'amarin Haris Buzu da kuma Ashfaq, babban abinda yafi d'aga mata hankali shine yanda yaran gaba d'aya suka gujeta lokaci guda suka koma gidan Hajiya, kai dolema tasan abinyi if not k'ura babba na neman b'arke mata.... ********** Bayan kwana biyu Maryama na faman zullumin maganan da Buzu ya fad'a mata, ta kasa aminta wai shi tuntuni k'aunarta yake, sam bata tab'a kawo soyayya yake mata ba, a iya tunaninta SHAK'UWA CE kawai a tsakanin su. Tirk'ashi lallai Haris yana neman ya jangwalo mata wani aikin. Tunda wannan magana ta shiga tsakanin Maryama da Buzu ya rage zuwa gidan, domin kuwa cikeda fad'a ta sanar dashi sam babu d'igon soyayyar sa a zuciyarta, sannan ita ba aure zatayi yanzu ba, sai ta cika ma Uncle burinsa na ganin cewa tayi karatu sosai.... Wani sa'in harejajensa Hajiya keyi. Kwana biyu da faruwan haka Ashfaq ma yazo da nasa batun, sosai hankalin Maryama ya tashi, me suka maidata? Dama duk wannan kulawa da suke bata sunada wata manufa akanta, lokaci guda ta canza masu gaba d'aya ba kaman da ba, idan suna waje ma bata zama. Tamkar me juju haka ta koma, wani irin tasanar su take ji. Koda Hajiya ta sami AT da batunma yaji dad'in hukuncin da Maryama ta yanke, sannan ya k'arada sam bazai tak'urata ba, duk wanda take so shi zai Aura mata.... Tunda Shema'u ta sami labarin Buzu yana son neman auren Maryama tayi wata dariyar mugunta domin kuwa tuggu da makircin da zata had'a masu sai sun kuka da kansu. Duk wannan bidiri da ake Sajida bata da labari domin kuwa satin baya da ya wuce suka dawo gida daga gidan Hajiya. Shema'u ta turo k'ofan d'akin Sajida ta shigo da sallama fuskarta fal fari'a. Murmushi Sajidar ma ta sakar mata kana tace "Aunty lallai kinsha kewar mu sosai sanda muke gidan Hajiya." Shema'u ta d'anyi tak'aitaccen murmushi kana tace "Ba dole nayi kewar ku ba, gaba d'aya gidan baimin dad'i, amma tunda kuka dawo sai gida ya koma kaman da... Ina tunin duk randa kikayi aure shikenan daga ni sai su Jamal da Baby Ni'ima." ta k'arashe tana wani narkar da fuska kaman zatayi kuka. Sajida ta d'an murmusa had'i da rufe fuskarta kana tace "Aunty ai ba yanzu zanyi aure ba kinsan Daddy bazai bari ba...." Bata kai aya ba Shema'u ta d'anyi tak'aitaccen murmushi mai sauti kana tace "Kai haba Sajida, bayan ya amince wa Maryama meyasa ke bazai amince maki ba.... Koda yake ba laifin Dr bane ya amince wa Maryama ta tsaida manemi sabida gaba d'aya dukansu biyu soyayya ce tsakanin su ba SHAK'UWA CE ba...." Sajida ta d'an karkato tana dubanta da kayu kafin tace "Aunty yaushe akayi hakan banida labari, sannan su waye kike nufin soyayya ce tsakanin su da Maryama...?" ta k'arashe fuskarta fal alamun tambaya. D'angelo dafata Shema'u tayi kana tace "Dr ba laifinsa bane ya amince sabida Hajiya ta masa hud'ubar cewa sam bazata k'yale Maryama tayita karatun boko ba kaman yanda yaci maku buri sai tayi aure. ..." ta d'anja fasali kana taci gaba da fad'in "Sajida both Haris da Ashfaq idanunsu ya rufe da soyayyar Maryama, and to tell you the truth gaba d'aya tak'o aminta dasu sabida soyayyan da take ma Daddyn ku, domin sanda ya zaunarta ya mata maganar cewa tayi ita karatu zatayi yanzu kaman yanda yake sonku dashi ba aure ba... Sajida I'm telling you this based on experience, na zauna da mutane da dama sannan shekaru na da naki ba dai-dai bane, abinda babba ya hanga yaro sam bazai hanga ba..... Sajida wllhi baki bina bashin rantuswa tsananin soyayyar da Maryama keyima mahaifin ku shiyasa ta kasa aminta da buk'atan zaratan Maza har guda biyu, she's playing innocent with you.... Ya kamata ki bud'e idanunki da kyau kisan cewa ke yanzu kin girma ke ba yarinya bace kuma, Saurayinki ya makance da soyayyar ta, sannan ita ta makance da soyayyar mahaifin ki..." ta kamo hannayen Sajida wacce tuni k'walla sun ciko idanunta kafin ta marairaice murya ta soma fad'in "My Sajee, ina sonki and I don't want you to get hurt, idan Saurayin ki ya auri Maryama you'll end up getting hurt, haka idan mahaifinki ya aureta same abu zakiji, the only abinda ya kamata kiyi shine ki kwad'aita mata auren Ashfaq, kinga idan ta auri Ashfaq Buzu dole ya hak'ura ya k'aunace ki tunda dama yana sonki ba wai baya sonki ba, kawai dai idanunsa sun makance ne akan Maryama. Sannan Daddyn ku will forget about her, kar kije mata da hantara ko fad'a, no bita a sannu, I assure you idan kika sauk'e kanki kika nuna mata muddin bata auri Ashfaq ba bazaki tab'a samin attention d'in Haris ba na tabbata zata saurareki tunda tana sonki, and your Dad kar ki canza masa, kici gaba da zama good girl, sai yafi jin dad'i kema ya k'yaleki ya baki freedom d'inki kinji koh...." ta k'arashe murmushi saman lips d'inta. K'ak'aro murmushi Sajida tayi kafin tace "You're absolutely right Aunt, duk abinda hak'uri bai bada ba tashin hankali bazai bada ba, I agree with you.... Na gode da shawarin ki Aunty you the best." ta k'arashe suna masu hugging juna. ************** Washe gari bayan sun fito daga computer class, jigum Sajida tayi had'i da rapka tagumi, Maryama ta gyara laptop bag d'inta ta tura pen cikin jakar kafin ta k'araso ta zauna gefenta ta dafata kana ta soma fad'in "Sajida lafiya kikayi tagumi haka, sistu fad'a min meke damunki pls." K'ak'aro murmushi Sajida tayi had'i da goge k'wallan da suka zubo mata kafin ta girgiza kai tace "Babu komai kawai na tuna Maama Juu da Mummy ne." Murmushin k'arfin hali Maryama tayi domin kuwa ta tunada Umminta harma da Aunty Aisha itama. Kafin ta rik'o hannun Sajida tace "Insha Allah yanda suke a yanzu yafi masu nan. Maryama ta ciro book d'inta tana duba abinda aka masu kafin a zo d'aukan su, sai bayani take ita kad'ai sam hankalin Sajida baya wajen. Rufe littafinta tayi ta d'an kaikaito sosai suna facing juna itada Sajida kafin ta dafa kafad'anta tace "Sajee meke damunki wllhi nasan akwai, abinda kika fad'a min earlier ba shine kawai damuwar ki ba, kinada wani damuwa and bakiso ki fad'a min, kar ki mance munce zamu koma tamkar yanda muke da, if we're hiding things from each other bazamu koma kaman a baya ba, so just share it with me pls, maybe I can help." ta k'arashe labb'anta d'auke da murmushi... Murmushi Sajida tayi kafin tace "Maryama you're the one keeping things from me, duk abinda ya faru ina sane, nasan komai....." Gaban Maryama ya yanke ya fad'i kafin Sajida taci gaba da fad'in "They both love you.... I mean Ashfaq da Haris, nasan har sunyi magana but keda Daddy baku goyi bayan abun ba, I wonder yanda zaki k'i aminta da soyayyan zarantan maza har guda biyu, Haris da Ashfaq.. Is it because you're in love with my Dad...?" ta k'arashe tana d'aga gira sama. Gaba d'aya Maryama ta daburce cikin sauri ta soma girgiza kai tana fad'in "Haba Sajida, I thought you've already talked about that, haba haba.... Don Allah ki daina irin wannan maganar, ta yaya zaki soma wannan tunanin, Uncle fah Daddyn mu ne gaba d'aya daga ni har ke so inaga bai kamata muke magana makamanciyar haka akansa ba... Pls...." Katse ta Sajida tayi ta hanyar d'aga hannu. Ga mamakin Maryama murmushi ta gani saman fuskar Sajida. "Shikenan that's what I want to hear, yanzu na yarda SHAK'UWA CE tsakaninki da Daddy na.. What about Haris, shikuma kina sonsa ne yasa ko labarin baki min ba bayan kinsan matsayin sa a wajena...?" Murmushi Maryama tayi kafin tace "Would you stop being silly, Haris kam ai naki ne ke kad'ai da yardar Allah...." Sajida tayi murmushin jin dad'i kana tace "Shikenan tunda kince haka na yarda dake, toh Ashfaq fah meyasa kika k'isa...?" Kasa ce mata komai Maryama tayi sai kallon data bita dashi, sam batasan yaushe Sajida tayi wayon da har take tambayoyi irin haka ba sabida tasan wautan Sajida tuntuni. Ganin bata bata amsa ba yasata sakin wani murmushi kana tace "Keda Ashfaq will make a perfect couple, dukanku Hajiya tana sonku tana ji daku, and you know ya bada rayuwar sa fansar taki rayuwar sanda b'arayi suka shiga gidan Hajiya, if I were you I won't reject him..... Sannan idan kika amince da aurensa ta haka ne kawai zan yarda ba son mabaifina ko saurayina kike ba, only then zamu koma tamkar da... Amma idan har kika k'i aminta da amsar soyayyar sa toh kuwa zanci gaba da kallonki a matsayin maciya amana, me neman aure mun saurayi ko mahaifi.." Daga haka Sajida ta mik'e tsaye fuskar ta babu walwala, ba sai ance maka har cikin zuciyarta iyakacin gaskiyarta kenan ba. Maryama ta bita da kallo dai-dai lokacin da Malam Habu ya iso d'aukar su... **************** Gaba d'aya yau da zancen ta wuni, itakam ta gaji da dakon soyayyar wanda baisan tanayi ba, koma ya sani shid'in ba tsaranta bane, sannan koda gigin wasa bazata tab'a fatan aure ya gifta tsakanin su ba, ta yarda tsan-tsan SHAK'UWA CE kawai tsakanin su wanda har takai ga hakan na haifar mata da wani negative tunani, sannan fatan ta da burinta a yanzu shine su reconciling SHAK'UWAR SU itada Sajida, sannan duk abinda Sajida ta fad'i gameda Ashfaq gaskiya ne, ya kamata ta basa chance tunda dama tana jin wani al'amari a tattareda dashi dukda babu d'igon soyayyar sa a zuciyarta da sunan su kasance inuwar aure... Har dare Hajiya sam bata gane kan Maryama ba. *********** Mafarkin da yayi a daren yau yafi na kullum firgita sa, Mummyn sa da Maryama ya gani a tare duka suna kuka suna fad'in ya ceci rayuwar su.. Sosai hankalin Ashfaq ya tashi, kenan Mummyn sa tana cikin tashin hankali na rashinsa, he's afraid kar Daddy Ya tsafe ta itama, Mummy tabbas tana buk'atar sa, sannan Maryama ma tana buk'atarsa.. Abinda ya d'aure masa kai ya rasa gane meyasa yake mafarki da mahaifiyar Maryama da ita kanta Maryamar, wani taimako suke nema wajen sa...? Tabbas yana buk'atan yayi tunani sosai, bazai daina jarabba neman auren Maryama ba har sai yanda k'arfinsa ya k'are. Tabbas akwai wani babban Al'amari dake faruwa gidan Dr AT only Allah's knows what.... Baccin da Ashdaq bai koma ba kenan ya mik'e ya d'auro alwala ya shiga jero nafilfili.... ************ Jikin Hajiya gaba d'aya yayi sanyi ganin yanda Ashfaq ya susuce gaba d'aya yana fad'in irin soyayyar da yake ma Maryama. Tun Hajiya tana d'aukan abin nasa kaman wasa hardai ta soma jin tausayin sa sosai. Allah Ya had'a jininta da Keenafas tana jinsa tamkar d'an data haifa a cikinta, koda Attahiru zaik'i auren Maryama da Ashfaq muddin Maryama ta amince da soyayyar da Ashfaq ke mata toh fah sai yanda k'arfinta ya k'are... Ashfaq ya kuma marairaice fuska yace "Hajiya wllhi da gaske nake son Maryama, Hajiya mahaifyata ta damu nayi aure sannan ni Maryama kawai nake so wacce Daddy na yake so na aura sam batada kamun kai, Hajiya ki taimaka min don Allah....." Sauk'e nannauyan ajiyan zuciya Hajiya tayi kafin ta d'ago ta dubesa. *Sameena Aleeyou Mrs* [9:28PM, 4/5/2018] ‪+234 806 652 0501‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *39* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ "Ni sam bazan k'i aurenka da Maryama ba mai sunan larabawa, kasan sunan naka wahalan fad'i yake bani nafi ganewa na kiraka da Keenafas..." D'an murmusawa Ashfaq yayi domin sosai Hajiya ke burgesa. Hajiya taci gaba da fad'in "Ni hakanma da sai yafi min dad'i, amma muddin d'iyata bata amunce ba toh fah gaskiya babu abunda zan iya akai domin amincewarta shine nawa..." Ashfaq ya sauk'e nannauyan ajiyan zuciya kafin yace "Shikenan Hajiya kiyita mata addu'an alkhairi, Allah Ya zab'ar mata da abinda yafi alkhairi, iyayena suna k'asar Saudi mahaifiyata ta tafi jinya muddin suka dawo banyi aure ba mahaifina zai Aura min waccan yarinyar da nake fad'a maki....." Da sauri Hajiya ta katse sa da fad'in "Allah Ya tsareka da auro irin matar Attahiru, shidai da Allah Ya jarabta da auren Roba-roba bana fatan wannan wak'i'a ta kuma sauk'a kan wani nawa, insha Allahu sam bazaka auri fentettiya ba....." Allah shi maka albarka ya zab'ar maka abinda yafi alkhairi...." Ashfaq ya amsa da ameen Hajiyar mu... Tana k'uryar d'aki tana sauraren conversation d'in nasu, tausayin Ashfaq ya cika zuciyarta, lokaci guda tana tuno yanda suka rabu da Sajida, this the only way for her, ta haka ne kurum Sajida zata aminta cewa ita d'in mai k'aunarta ne, sann Ashfaq ya cancanci ya mallaketa koda babu soyayyar sa a zuciyarta, sannan haka ne kawai zaisa ta daina yaudaran kanta da rud'in kanta wajen tunanin Uncle. Mik'ewa tayi ta zura hijab d'inta k'irjinta na dukan tara-tara ta nufo parlor... Daga Hajiya har Ashfaq kallo suka bita dashi..... Ashfaq ya d'an mik'e yana fad'in "Hajiyar mu ni zan wuce...." Hajiya ta amsa masa kana sukayi sallama, ya kuma kallon Maryama kafin ya nufi k'ofa.... Har ya d'aga labule ya jiyo muryarta tana kiran sunansa. "Ya Ashfaq" Juyowa yayi yana dubanta ba tareda ya iya furta koda kalma ba. Cikin sanyin muryarta ta soma fad'in "Na amince ka zama miji na....." Baki sake Ashfaq ke dubanta, maganar tamkar ba daga bakinta ya fito ba... Hajiya kuwa kaman talabijin haka suka zame mata wajen kallo, ta dubi wannan ta dubi wancan. Fari'anta ya kasa gushewa, farin cikinta ya bayyana sosai... K'arasowa tayi ta rungume Maryama tana fad'in "D'iyar albarka Allah dai ya saka ki a aljannah, ni na sani bazaki watsa min k'asa a idanu na ba..." Ashfaq dai samun kansa yayi da raahin yarda da abinda Maryama tace, gaba d'aya yama kasa furta komai.... Bai bar gidan ba saida ya sami yin magana da Maryama. Sosai abin ya dami Ashfaq yanda Maryama ta sauya lokaci guda tamkar ba ita ba, abun nata akwai ayan tambaya amma sam baiso yayi wani matsalan rashin yarda ya shiga tsakanin su. Bayan ya tafi suka k'ule a d'aki itada Hajiyarta, Hajiya na tambayarta ta tabbata tana son Keenafas.? Maryama ta gyad'a kai kana tace "Hajiya inaso kowa ya kasance cikin farin ciki, na tabbata idan Allah Ya yarda aurena da Ya Ashfaq shi zai haifar da farin ciki ma kowa, sannan kin manta tun ina k'arama na sha fad'a maki cewa duk abinda kike so nima shi nake so, tunda kina sona da Keenafas d'inki nima ina sonsa, sabida nasan bazaki tab'a zab'a min abinda zai cutar dani ba, Ummi ta Allah Ya gafarta mata, haihuwa ta kawai tayi amma rainona gaba d'aya kece kikayi, banida tamkar ki bayan Ummi a dinuya..." Hajiya dai kallonta kawai take tana murmushi k'walla na neman ciko idanunta, gaba d'aya ta kasa fad'in komai sai rungumar Maryama da tayi su duka suna k'ok'arin zuban hawaye. Hajiya ta rik'e hannayen Maryama kana tace "D'iyata kenan kin amince bazaki ci gaba da karatu ba kaman yanda kikeda burin hakan, sai kinyi auren ki ci gaba kenan...?" Maryama ta murmusa tasa hannu ta goge hawayen da ya gangaro ma Hajiya kana tace "Hajiyata, duk abinda kike so nima shi nake so, nasan kina so kiga aurena tun da sauran k'arfinki, ina so na faranta maki shine samun albarka na..." Gaba d'aya jikin Hajiya ya kuma yin sanyi tabbas ranar da aka ce Maryama zata bar gidan zata sha kuka, domin kuwa tsan-tsan SHAK'UWA CE a tsakanin su.. AT dake daskare bakin k'ofa ya gama sauraren su, kasa motsa koda d'an yatsan k'afarsa yayi, shin da gaske abinda yake jiyowa gaskiya ne, Maryam d'insa bata bari ya zab'a mata miji ba kaman yanda yake da buri,.. Shin ta yaya zai soma aurar da Maryam yanzu, gani yake she's too young for that, aside from that he's afraid ko wani irin miji take so sai yayi k'wakk'waran bincike akansa sabida Maryama marainiya ce amana ce a hannunsa... Kasa shiga parlorn yayi sai komawa da baya da yayi..... Yana tafe cikin motarsa yana ci gaba da tunanin, dole ya nutsu yasan ma waye zai damk'a wannan amana da Allah Ya bar masa. Tabbas namiji da macce ba d'aya bane, tunanin mata ya banbanta dana maza su idan suna son mutum shikenan, k'wakk'waran bincike akansa bazai zame masu abin damuwa ba, bacin haka ta yaya Hajiya zata aminta da Ashfaq kai tsaye ba'ayi k'wakk'waran bincike ba, dukda shi Ashfaq d'in baida matsala ga dukkan alamu amma ya kamata ayi bincike akansa kafin a soma maganar aure..... Gaba d'aya tunanin da ya kusan kwana yanayi kenan. ************ Yau tunda Mummy ta d'auki wayar Haidar ta gane na cikin farin ciki nan ya labarta komai duk abinda ya faru. Mummy ta sauk'e ajiyan zuciya kafin tace "Haidar anya bakayi kuskure ba, ina ka tab'a jin anyi wannan irin aure da b'oye kai, aure fah abune da yake buk'atan gaskiya a komai, ka bayyana asalinka nasan they'll accept you for who you are. Amma b'oye kai bashida wani alfanu.." Ashfaq ya d'anyi jim kafin yace "Com'on Mummy na fad'a maki dalilina, ke kinfi kowa sanin idan Daddy yasan zanyi aure wllhi bazai bari ba, sannan ni kuma rantsuwa nayi kwabon sa bazan kuma ci ba, we're just related by blood nidashi bacin haka bana fata wani abin ya kuma had'ani dashi..." ya k'arashe kaman zaiyi kuka... Cikin d'an fad'a ta soma fad'in "Bakada hankali ko Haidar, wacce irin magana kakeyi, idan kak'i dukiyarsa sabida shi politician ne sabida kana tunanin dukiyarsa tana gauraye da haramun ne da kuma hakkin jama'a ka tabbata da hakan, ka tabbata Daddynka ba guminsa yake ci ba... Haidar ka rage wannan zuciyar taka fah kullum ina maka fad'a. Hak'uri ya soma bata don baiso plans d'insa su wargaje kafin yacigaba da fad'in "Mummy pls don't say no, kinga zan had'aku da Maryama da Hajiya a waya sai ku gaisa, karfa ki mance ki kirani da Haidar, my name's Ashfaq to them, daga baya gyaran da nake son yi idan ya tabbata kowa sai yasan ko ni waye, .. And maganan biki kuma banso ki saka family ciki, Aunty Deena k'awarki kawai ta isa tunda nasan aminiyar ki ce, and na gama magana da Baffah Yawale zai tsaya akan komai pls Mummy kar ki bari ku baro Saudiya sai anyi auren nan kinji...." Gaba d'aya dai Mummy kam gani take anya kan Haidar bai kwance ba, ita ina ta tab'a jin irin wannan aure kai ko a wasan kwaikwayo, yama maida auren wasa kenan... Gwara ta lallab'asa idan hakan yake so tunda ya tabbatar mata idan dai yayi auren zai dawo gare su... _Maryama and Mummy I'm doing this for the both of you, nasan mafarkina bazai zama shirita kawai ba, there must be something behind it...._ ya fad'i haka cikin zuciyar sa. ************** Sanda AT ya tari Hajiya da zancen tass ta salle sa... "Inyi, saika hana yarinya yin aure, ka fice a idona Attahiru, da yardan Allah sai naga d'iyoyin Maryama kafin na bar duniya, banda felek'e kasa ido akan taka d'iyar mana, Maryama d'iyata ce, kai idanma baka bada auren nata ba ni nan zan bada idan yaso ka had'iyi zuciya....." Gaba d'aya bai gane me take fad'i illa zuciyarsa dake masa zafi, sam Hajiya bata tsayawa ta fahimcesa sai ta soma fad'a shi kuwa sam baison abinda zaisa ranta yake b'aci, hak'uri kurum ya bata kafin ya mik'e ya fice yana neman layin Ashfaq, sanar dashi yayi yana nemansa ya same sa a gidan sa ... Cikeda ladabi Ashfaq ya amsa masa... Ta window d'in d'aki Maryama ke hangosa gaba d'aya sai taji babu dad'i, ko kad'an bata son yanda Hajiya kema Uncle fad'a, tana jin Hajiya ta shigo tana ci gaba da sababi tayi kwanciyarta tamkar mai bacci... ************* Saman fararen kujerun roba dake farfajiyan gidan suka zauna, Shema'u na mak'ale daga window tana hangosu.... Tun daga ganin yanayin AT Ashfaq ya sha jinin jikinsa, tambayoyi ya ringa masa uwa d'an jarida fuska babu walwala, haka Ashfaq ya ringa amsa masa tambayoyin nasa ya k'arada Wan mahaifinsa zaizo shi daga Katsina cikin satin nan.. AT ya jinjina kai kafin yace "Shikenan dukda zaizo shi zan kuma bincikawa kaji koh..." Ashfaq ya jinjina kai alamun amincewa cikeda ladabi. AT ya dubesa kafin yace "Kana iya tafiya.." Godiya Ashfaq yayi ya mik'e cikeda rusunawa... Har ya soma tafiya Tahir ya kira sunansa. Dawowa yayi ya zauna mazaunin sa. AT ya d'an gyara zamansa kana ya soma fad'in "Ashfaq don't hurt her, promise me zaka kula da ita sabida ita d'in amana ce a hannu na, ka min alk'awari zaka iya rik'e min wannan amanar....?.... Ashfaq idan kaci amanata bazan tab'a yafe maka ba, for Maryama zan iya yin komai, duk namijin da ya wulak'anta ta wllhi wllhi sai yanda k'arfina ya k'are, so be careful." Kallon cikin idanun AT Ashfaq yayi wanda baka iya gano komai sai tsantsan gaskiya....... D'an murmusawa Ashfaq yayi kafin yace "Insha Allah bazatayi kuka ba sabida ina sonta ina k'aunarta with all my heart, I'll cherish her and love her till my very last breath..." Kasa cewa komai AT yayi sai kallo da ya bi Ashfaq dashi can k'asan mak'oshinsa maimakon kalaman Ashfaq su faranta masa rai tunda ya masa alk'awarin kula da Maryama sai ma zogi da rad'ad'in kalaman Ashfaq d'in da suka dabaibaye masa zuciya... D'an fuzar da iska yayi gamida k'ak'aro murmushi kafin yace "Ba don kai d'in ka zamto tamkar k'ani a gareni ba, ba don ka zama family a garemu ba da nace baza'ayi auren nan ba har sai mahaifan ka sun dawo, but nima mai nema maka aure ne.... Ina so muyi magana da Dad d'inka kafin lokacin..." Daga haka mik'a ma Ashfaq hannu yayi sukayi sallama ya shige gida ya bar Ashfaq a nan yana zullumin yanda zai had'a AT da Daddy suyi magana, yasan komai ka iya rushewa all his plans... AT yana shigowa gida Shema'u ta kalallame sa tana tambayar sa abinda ke faruwa. Bai sami zarafin mata bayani iyakacin abinda ya fad'i mata shine Ashfaq yana neman auren Maryam... Kasa b'oye farin cikinta tayi, lallai plan d'inta went perfect, gaba d'aya har wani nishad'i takeji, finally zata rabu da Maryama kuma Ashfaq zai fita daga rayuwar su ta cimma burinta kan iyalan Aysha, tabbas tasan AT bazai juri ganin Ashfaq na aiki a k'ark'ashinsa ba, dole ya ringa tunawa cewa Maryama fah matar Ashfaq ce, duk wanda ya fahimci AT kaman yanda tayi zai hangi tsan-tsan soyayyar Maryama a idanunsa.... Wasa-wasa maganar aure ya kankama, Baffah Yawale da wasu abokansa Dattawa su suka zo nema ma Ashfaq auren Maryam. Gaba d'aya AT ko maganar ya kasa yi da Maryama, kullum da Hajiya suke zancen, Mummy tayi waya da Hajiya har kusan sau biyu saidai bata sami zarafin gaisawa da Maryamar ba. Sajida babu wanda ya kaita farin cikin kasancewar hakan, Shema'u kuwa duk wasu shirye-shiryen biki na sayan kaya ma Amarya ita keyinsu, AT har Katsina yaje bai samu mummunar shaida akan Ashfaq ba, Baffa Yawale shi yayi komai ya toshe duk wani kafa da zai fito da asalin wanene Ashfaq.... A b'angaren Maryama kuwa kullum ta k'ule a d'aki bata komai tunanin Uncle, takanyi murmushi idan ta tuna kalan SHAK'UWAR dake tsakanin su, koda shike tunda ta soma girma ma Shak'uwar tasu ta ragu, aure shine mafi mata sauk'i akan ta zauna jiran abinda ko a mafarkima ba kasancewa zaiyi ba, Allah yaga zuciyarta da sannu zai koyar da ita soyayyar Ashfaq.. Su Sajida abin nema ya samu ba'a sama ba'a k'asa, dama akwaita da son hidima balle bikin 'yaruwarta Maryama, k'awayen Amarya su Fadila Talba su Aysha cool su Anmunah kullum cikin sintiri suke dukda amaryar tasu sam bata d'auki wani damuwa ta d'aura ma ranta ba, idanma sun dameta saidai tace masu ita simple wedding kawai take so tunda shima Ashfaq d'in abinda yake so kenan. Ana sauran sati guda Hajiya ta d'auko mai gyara mata amarya, a satin su Aunty Deenah da kuma Aunty Faty suka zo daga Abuja manyan k'awayen Mummy 'yangayu wanda kana ganinsu basai ance maka hamshak'ai bane dukda sun zo a matsayin average people... Hajiya ma da mutanen ta daga Rano da kuma mutanenta na unguwa su suka shirya karb'an kayan. Sosai hankalin Buzu ya tashi shi gani yake tamkar anci amanar sa ne, hakan yasa sam Hajiyar sa batazo amsar kayan ba dukda Hajiyar AT ta tura mata gayyata, Hajiya fah babu sauk'i kullum cikin cakarewa take kaman itace amaryar, _Ina ruwan su Hajiya za'a aurar da d'iya... Lol_ *********** Idanunsa sunyi jazir yake dailing lambar Shema'u.. Saida ta yastina kafin ta d'aga da k'yar.. Daga d'aya b'angaren Buzu yace "You'll pay for what you did, Maryama tawace, ki sani from this very moment na daina maki aiki, you're nothing but a trader...." Dariya tayi kafin tace yaro dai yaro ne, you're so stupid, toh waye zai yarda da maganar da zakayi, bazan gushe ba ina warning naka, ka ci gaba da yimin biyya domin wllhi I can destroy you within a second without being pathetic, you've no idea what I'm capable of..... Wllhi nasha gabanka a iya bariki nayi da wa'enda suka damaka basu nasara ba balle kai, kai kasan farkon had'uwarmu da kai yanda aka kawo min kai, kaji yanda na baka details akan ka, so be careful boy, kar ka soma yak'in da bazaka iya k'arasawa ba, idan akan Maryama kake wannan kumfar bakin kar ka damu at the end zaka sameta bayan buk'atata ta biya...." Daga haka d'iff ta kashe wayan ba tareda ta kuma cewa komai ba.. VP ya kalli orderly d'in matar sa Hajiya Maryam a karo na biyu kafin yace "I asked you to spy on her ba shiririta na saki ki min ba, I know my wife, I perfectly well know her, nasan she's hiding something bata so na sani, and tabbas nasan bazai wuce akan Haidar ba, ina so ki kawo min komai in details within 24hrs kin fahimta..." Saurin gyad'a kanta tayi kana ta sara masa tace "Yes Sir consider it done.." daga haka ya bata izini ta fice... Shi kad'ai yake juya glass cup d'in hannunsa yana tunanin kalan hukuncin da ya kamaci Haidar, wllhi sai ya shayar da yaron nan mamaki sai ya nuna masa shid'in k'aramin yaro ne, har yanzu bai gama sanin duniya ba. ****************** Yau asabar tayi daidai da ranar da ake saka ran d'aurin auren Maryama da angonta Ashfaq.... AT gaba d'aya yama kasa tashi daga saman gadonsa, Shema'u ta shigo cikin shiga ta alfarma tana k'ok'arin bud'e manya-manyan cottons 'yan k'asar Turkey da aka k'awata windows dasu take fad'in "My AT you still on bed, haba Bride's Father ai kai ya kamata ku isa ku amshi bak'i ga wayarka nan Hisham sai faman kiranka yake.." ta k'arashe tana k'arasawa bedside yanda wayar AT d'in ke ajjiye, juyowa tayi taga gaba d'aya hankalinsa baya wajen... Murmushi ta d'anyi kafin ta k'araso tayi hugging d'insa ta baya tace "Muje na maka wankan..." Gajeren Murmushi yayi da gefen bakinsa kana yace "Kar ki damu zan iya yi, just get my clothes rady..." daga haka ya nufi closet ya d'auki bathrobe sannan ya shige bathroom d'in, Shema'u ta bisa da mayen kallo tana wani fari da idanu. A kullum taga AT Sha'awarsa k'aruwa mata yake. Tana ficewa daga d'akin waya tayi da Allied d'inta Hisham. Su Sajida su Ni'ima gaba d'aya suna gidan Hajiya, hidima babu kama k'afan yaro, Amara Maryama kuwa gaba d'aya sukuku take jinta tamkar maras lafiya. ******* Tsaf ya gama shiryawa cikin wata d'anyar boyel fara k'al wanda ya d'inka zai saka a aurensu da Shema'u bai saka ba sai yau a auren Maryama da Ashfaq ya saka, AT yayi kyau har ya gaji idan ka kallesa dole ka kuma sake kallonsa, shi kansa ya jima cikin closet yana k'are ma kansa kallo a full length mirror kafin ya fito, wani daddad'an k'amshi kawai yake bulawa duk yanda ya wuce.. Shema'u bata ko ji fitowarsa ba tana nan a kitchen tana had'a masa break sai ficewar motar sa data jiyo, tamkar ta Kumar ihu haka fuskar ta ya koma. Yana shigowa gidan Hajiya kaji yanda mutane ke gaidashi, ita kanta Hajiya yaukam sosai take shiri da Attahiru bai watsa mata k'asa a idanu ba. Yaransa su Jamal da Ni'ima suka ringa zuwa suna hayewa jikinsa. "Daddy kaima kazo auren Adda Maryama ne? Daddy kayi kyau kayi kama da amarya..." cewar Ni'ima dake rik'e da piece d'in masa a hannunta. Gaba d'aya mutanen wajen saida sukayi dariya wasu na tausayin AT da yaransa don sunga Shema'u da aka soma hidimar biki haka Hajiya ta ringa fad'in ga roba-robar matar Attahiru ko a jikinta, da gani sun gane Shema'u ba mace ta gari bace, abinka da manyan mata wad'anda sukayi huld'a daemutane daban-daban. Murmushi shima AT d'in yayi kafin ya dafa kan Jamal yace "Champ kira min Addar ku Sajida ko." babu musu Jamal ya shige yana d'an tsalle.. AT kuwa rik'o hannun Ni'ima guda suka nufi babban parlor wanda ba'a bud'esa sai taro. Bayan Sajida ta shigo ta gaishesa ta kawo masa abin kari text ya tura ma Maryama kaman haka. _Ki sameni a parlorn bak'i..... Uncle_ Gaban Maryama ya yanke ya fad'i domin kuwa rabonta da suyi wani k'wakk'waran magana itada Uncle tun kafin a tsaida aurensu da ya Ashfaq... *Sameena Aleeyou Mrs* [8:52PM, 4/5/2018] ‪+234 806 652 0501‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *40* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ Ta karanta sak'on yafi sau abinda yafi, ita batama san Uncle nada layinta ba domin kuwa dududu wayar bata wuce sati guda a hannunta ba, angonta Ashfaq ne ya sai mata sabida su sami sauk'in yin magana da juna. A hakama da k'yar ta amsa saida ya nuna mata su d'in sun zama abu guda. Juyawa tayi ta dubi friends d'inta da hankalinsu yafi karkata wajen mai zana masu k'unshi sai faman hayaniyar su suke, ciki harda Sajida wacce itace bisa layi ita akema k'unshin domin kuwa jiya bata samu zama an mata ba sai yau. Mik'ewa tayi ta fice ba tareda sun lura ba, kai tsaye parlorn Hajiya ta nufa yanda mutane 'yan biki sai zolayarta suke, itako sai sunne kanta cikin mayafi take. A uwar d'aki ta sami Hajiya nan ta sanar da ita Uncle na kiranta. Hajiya data cakare cikin wata jan leshi mai duwatsu harda d'aurin ture kaga tsiya tayi, ta murmusa kafin tace "Allah sarki Attahiru nasan nasiha zai maki, shakka babu zaiyi kewarki sosai ni kaina nasan tsan-tsan SHAK'UWA CE a tsakanin ku,..." ta kuma murmusawa tana k'ok'arin maida k'wallanta kana tace "Duk tsiyan da kuka min a baya na yafe ku, b'oye ledar goro na, yau kuce da tsutsa gobe kuce ta rub'e duk don kar naci...." I zuwa lokacin idanun Maryama ma ya soma rau-rau, itama ta tuna wad'ancan lokutan.... Allah sarki Hajiya da Uncle zatayi kewansu domin kuwa ko Umminta bata shak'u da ita ba kaman yanda ta shak'u da Hajiya da Uncle. Albarka Hajiya ta kuma saka mata, tasa hannu ta goge k'wallan da suka zubo ma Maryama kafin tace "Maza tashi kije ki koh nasan yana jiranki tunda lokacin d'aurin auren ya kusa." Jiki babu laka ta mik'e ta nufi parlorn bak'i daga Maryama har Hajiya saida suka bawa mutane tausayi... Tsaye ta hangesa ya bada baya yana fuskantar window, hannayen sa zagaye da bayansa, gabanta yayi wani irin mugun fad'uwa domin kuwa tunda take uncle bai tab'a mata kyau kaman na yau ba, kayan ya amshe sa ga wani golden brown hula zanna bukar da ya zauna akansa tamkar akan nasa aka k'era, kwantattun sumarsa wanda suke gauraye bak'i da furfura kad'an sai dai bak'in yafi yawa sun d'an fito ta bayan hular tasa, gaba d'aya k'amshinsa da k'warjininsa sun cika wajen. Jikinsa ne ya bata tana wajen, a hankali ya kaikaito yana dubanta, tana sanye cikin leshi kalan hulan kansa wato golden brown da kuma yalwateccen mayafi fari k'al kalan shaddar dake jikinsa, har wani girma ta k'ara masa. D'an saita kanta tayi had'i da yin sallama kana ta soma shigowa. K'ak'aro murmushi Tahir yayi yana mai amsa sallamar tata ya k'araso saman Couch ya zauna, abincin da Sajida ta kawo masa ko bud'ewa baiyi ba. Can k'asan carpet ta zauna kanta a k'asa. Gaidashi ta soma yi cikin sanyin muryar ta yana amsawa fuskar sa d'auke da murmushi, tabbas yau d'in d'iya ko ince k'anwar tasa ta canza masa gaba d'aya, ga wani kyau na musamman da wani daddad'an k'amshi da take. Shiru ne ya d'an biyo baya kafin AT ya d'an muskuta ya ambato sunanta da irin sigan da ya saba kira. Saida ta d'an d'ago ta dubesa kafin ta amsa, cikin sauri ta maida nata kan k'asa, itakam sai yanzu ta lura shiga iri guda sukayi da Uncle. Tahir yaci gaba da fad'in "Tunda aka saka aurenki da Ashfaq ban samu zama munyi magana ba, sabida Hajiya ta tabbatar min kin zab'i Ashfaq d'in a matsayin miji...." ya d'anja fasali kafin yaci gaba "Ina so na kuma tambayarki kafin a d'aura auren, kin tabbata kina son Ashfaq....?" Bugun zuciyarta ya k'aru, wayyo Allahnta yaya Uncle yake mata tambayar da yasan bazata iya basa amsa ba. Shiru na wasu dak'ik'ai suka gifta. Shi kansa mai tambayan k'irjinsa tamkar zata faso ta fito waje haka yakeji, addu'a yake kan faman yi Allah yasa kar ta amsa masa, shirunta sai yafi masa sauk'i akan amsawarta... Saida ya d'an kuma yin gyaran murya kafin yace "Ko a shari'a shirun budurwa is acceptance.... Masha Allah, Allah yayi maki albarka.... Allah Ya baku zaman lafiya mai d'orewa tareda......" kasa k'arasawa yayi sai d'an murmushi da yayi wanda yafi kama da yak'e kafin yaci gaba da fad'in "Maryam, ki sani koda ace kinyi aure we're still your family, duk wani rashin fahimta ko na cin zarafi ko na wani abu makamancin haka don't hesitate to tell me right away kinji, you can always count on me..... I'll always be there kinji koh...." ya k'arashe cikin rawar murya wanda hakan yasa Maryama ta d'ago tana dubansa, take ta gano sauyawa da idanunsa sukayi... K'walla ne suka ciko idanunta cikin sauri ta sadda nata idanun k'asa. Saurin daidaita kansa yayi had'i da d'an fuzar da iska kafin ya soma mata nasiha mai ratsa zuciya wanda ba Maryama kawai ba harta shi AT d'in saida yaji zuciyarsa na neman karaya..... Ganin tana hawaye yasa sa soma lallashinta yana fad'a mata idan tana so zaisa Ashfaq yake kawota wajen Hajiya kullum ko kuma shi yaje da kansa. _(Ni kuwa Sameena nace, inaga dai AT ya mance Maryama aure zatayi zata zama mallakin wani shiyasa yake fad'in haka... Lol)_ Ita kanta Maryama statement AT d'in saida ya sakata nishad'i, yana kallon yanda take murmushi har cikin ransa yaji dad'i. Duban abincin gabansa yayi kana yace "Toh Maryamar Hajiya ayi serving Uncle na k'arshe koh..." Murmushi tayi cikeda kunya kafin ta k'arasa gabansa ta soma bud'e warmers d'in, sai bin zanen lallen hannunta da kallo yake, flowers d'in sunyi kyau sosai, take yaji zuciyarsa na k'una, wai duk wannan lalle domin Ashfaq tayi su... Saurin kawar da kansa gefe yayi don hakan ne yafi masa sauk'i. Bai k'yaleta ta tafi ba har saida ya d'an ci abincin, Maryama kuwa gaba d'aya ta kasa sakewa dashi. Wayar da Hisham ya ringa damunsa dashi ne yasa sa dole ya mik'e ba don ya gaji da kallon Maryama ba don yasan daga yau zata zama mallakin wani.... K'ura mata idanu yayi kafin ya fice sannan yace "Zanje na bada aurenki Maryam.." Kasa ce masa komai tayi sai kallon tausayi data bisa dashi, he's acting strange, gaba d'aya Uncle ya canza mata.... Muryarsa ta jiyo yana fad'in "Bazaki min fatan Alkhairi ba..?" K'ak'aro murmushin k'arfin hali tayi kana tace "Allah Ya kaika lafia yasa ayi a sa'a..." ta k'arashe kaman zata kurma ihu. Murmushi ya sakar mata da gefen baki kafin yace "Ameen..." Daga haka ficewa yayi cikin sauri. Maryama tabi bayansa da kallo lokaci guda da durk'usa saman gwiwoyinta tana kukan da batasan dalili ba. Shema'u da isowarta kenan taga AT ya fito daga parlorn bak'i ga kuma takalmin mace a wajen, cikin sauri ta nufi parlorn k'irjinta na bugawa da sauri da sauri. Turus ta tsaya ganin Maryama durk'ushe a wajen na kuka, saida ta bita da wani mugun kallo kafin ta k'arasa ta dafata tana fad'in "Haba Amarya yaufa ranarki ne, kuka bai kamace ki ba." Jin Muryar Shema'u yasa gaban Maryama ya yanke ya fad'i cak ta had'iyi kukanta, Ji take kaman Aunty Shema'u ta fahimci sabida Mijinta take kuka. Lallashinta Shema'u ta ringayi tana watsa mata mugun kallo, duk yanda taso Maryama ta fad'a mata abinda ke damunta Maryama ta kasa fad'a mata.... Kallo kawai Shema'u ke binta dashi, Jakar uba!! Ai sai yanzu ta lura AT da Maryama anko sukayi. Wani k'atutu ya tokare mata mak'oshi, ita kad'ai take huci tana watsa ma Maryama kafiran kallo.. Allah sarki Maryama kanma batasan tanayi ba..... ************* Taro yayi taro, uban gayya kurum ake jira a gabatar da d'aurin aure, Ashfaq dasu Dr Bilya su Dr Nicolas da sauran abokanayen aikin su tuni sun sami hallara. Ashfaq yayi kyau cikin shigar sa ta angwaye, tunda ya hango AT gabansa ya yanke ya fad'i. Hisham ma kallo yake kan faman bin Tahir d'in dashi yanda yake kan faman gaisawa da Jama'a. Zama AT yayi bayan sun gama gaisawa dasu liman aka soma k'ok'arin gabatar da abinda ya tarasu....... Kaman daga sama sai jiyo sautin jiniya suke gaba d'aya ya gauraye unguwar tako ta ina... Dama auren a farfajiyan babban masallaci ne, gaba d'aya jama'a aka soma mik'ewa ana hange-hange da kalle-kalle... Gaban Ashfaq yayi wani irin yankewa ya fad'i, suka kalli juna shida Baffah Yawale.... Kafin su sami zarafin magana sai gani sukayi tirk'a-tirk'an motici na alfarma suna shigowa... Kankace me Mopulawa sun soma durowa daga motocin su suna ba ma uban gidansu tsaro... Mamaki ya cika mutanen dake wajen ganin mataimakin shugaban k'asa ne sukutum a wajen, wasu a nasu tunanin shima gayyatar sa akayo.... Ashfaq da ya kasa furta komai sai huci da yake ga wani irin gumi dake karyo masa, ya kasa gasgata abinda yake gani, kenan Daddy bazai tab'a k'yalesa ba... Kallo guda VP ya watsa ma Baffah Yawale wanda dama sam basu shiri kana yace "Ina Haidar....?" A'a gaba d'aya mutanen wajen sun rasa gane meke faruwa, AT kam ko motsawa daga yanda yake ya kasa... VP ya cakumo kwalan rigar Baffah yana fad'in "Yawale ka fad'a min ina Haidar...." Haidar da tuni idanunsa sun kad'a sunyi jazir ya k'araso ya fincike hannun VP 'yansanda suka yunk'ura zasu kai mai duka VP yayi saurin dakatar dasu kafin yasa hannu ya fincike hular Ashfaq nan gashin da yake sakawa a kansa ta zame tabi hular asalin halittar sumarsa ta bayyana... Murmushi Daddy yayi idanunsa sun kad'a sunyi jazir kafin ya d'auke Ashfaq da wata lafiyayyar mari wanda yasa tuni gashin bakin da yake mak'alawa ta fice ta fad'i k'asa, gemun ma tabita lokaci guda.... Asalin kalan fatarsa ta bayyan sosai.... Mamaki ya cika mutanen dake wajen. VP yaci gaba da fad'in "Kayi kad'an Haidar, har kana tunanin zaka b'ace min a cikin k'asar nan.... Yau na tabbata zakaji zafin ka tara mutane a kunyata ka kaman yanda kamin a baya..." ya juyo yana duban Baffah Yawale kafin yace "Kai kuma ka saurare ni." Ya dubi 'yansandan sa yace "Ku d'auko min Haidar..." AT dake tasye idanunsa sun kad'a sunyi jazir k'arasawa yayi ya cakumo babban rigar Ashfaq yana jijjiga sa yake fad'in "Who are you...? Wanene kai? Me kake nema daga wajena....??? Answer meeee!!!!!" *Sameena Aliyu Mrs* [8:53PM, 4/5/2018] ‪+234 806 652 0501‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *41* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ *OMG! Just unbelievable, wai dama haka SHAK'UWA CE keda masoya... Hayam just.... Speechless guys❤❤ Allah dai ya bar k'auna, ina sonku gaba d'aya da zuciya guda 💘* Jijjiga sa AT yake da iya k'arfinsa yana fad'in "Ka amsani nace, tell me who you really are...?" Yanda yake huci yana fitar da gumi dole mutum yaji tsoro idan yaga yanayinsa... AT yaci gaba da fad'in "I trusted you.... I even introduced you to my very own Family.... K'arewa na d'auki babban treasure ina yunk'urin damk'a maka amma ka rasa me zaka min sai butulci.... Why! Why!! Just tell me whyyyy...!!!!" Yanda yayi maganar saida hawayen zafin rai ta tsattu a idanunsa... Ashfaq ya kasa fad'in komai sai hawaye dake bin k'uncinsa... Hisham ne ya soma janye AT lokacin da VP ya kuma daka ma mopalawan sa tsawa yana fad'in "Kunsan bana jiran wani, just get the idiot I said..." daga haka ya soma tafiya... Nan suka soma janyo Ashfaq dake d'igan hawaye yana k'ok'arin had'e hannayen sa waje guda yake fad'in "Dr pls let me explain... Don Allah ka barni nayi bayani but kar ka rabani da Maryama pls, I beg of you..." Fincika Ashfaq yake yana duban mopalawan yake fad'in "Let go.... Let me gooo...." Inaa basu tsaya sauraren sa ba tuni suka ciccib'esa suka nufi mota dashi, domin daga wajen his excellency Airport ya nufa jet d'insa na can.... Mutane take waje ya kaure da maganganu kowa na tofa Albarkacin bakinsa.... AT kam zama dirsahan yayi saman carpet had'i da cire hulan kansa, tunanin abubuwa daban-daban ne suka shiga yawo a kwanyar sa. D'ago rinannun idanunsa yayi yana duban Hisham kafin yace "You were right, kayi gaskiya Hisham, I shouldn't have trusted him, he made a fool out of me...." kasa ci gaba da maganar yayi yana tunanin yanda wannan abu zaiyi hurting Maryam, ace anzo aurenta ga abinda ta faru.... Lallai wannan aya Allah Ya gwada masa, Maryam amana ce a hannunsa tun daga ranar da ya tsince ta, batada kowa sai shi, tunda abu makamancin haka ya soma faruwa tabbas zaiyi wuya ya sami mai rik'e masa ita bisa gaskiya da amana, Ashfaq yaci amanar su, ya yaudare su...... Tabbas bazai tab'a yafe masa ba.... Yana cikin tunanin ya jiyo muryar liman yana fad'in "Dr Ahmad kar ka damu, lallai komai muk'addari ne daga Allah, ka sani Allah yana tareda masu hak'uri, ka gode ma Allah da yasa komai ya bayyana kafin ayi auren.... Lallai Allah yana sonka da alkhairi, kayi addu'an Allah yasa haka shine mafi alkhairi ita kuma yarinyar Allah Ya bata wanda yafi zama alkhairi a gareta, muyi addu'a sai mu watse... Domin manzon mu tsira da aminci su k'ara tabbata a gareshi ya koyar damu yin addu'a bayan ko wace zama da mukayi daga abinda ya kai mutum biyu...." AT gaba d'aya baya gane me ake fad'i, Maryama ce cikin zuciyarsa, tunani yake yanda zataji, tunanin halin da zata kasance ciki yake idan wannan labari ya risketa, fad'i yake cikin zuciyar sa _I won't call off your wedding Maryam_, zakiyi aure insha Allah... Bai ankara ba sai gani yayi yana shafe addu'a ana mik'ewa... Cikin sauri ya mik'e tamkar wanda aka tsinkaya kafin ya dubi Liman yace "Allah gafarta malam a tsaya akwai d'aurin auren, ina zuwa.." Bai jira cewan Liman ba ya kutsa cikin mutane ya nufi motar sa. Hisham dai kallon mamaki yake bin AT dashi, kafin AT ya dawo farfajiyan d'aurin auren yayi amfani da damar yayi dialing lambar Ally d'insa... Hajiya na gefen su Sajida ta mik'a hannu tana fad'in "Maza zana mani k'unshina kiga, farar mace alkyabban mata, faran Mace lantarkin gida, na tabbata nawa k'unshin sai yafi na amaryar ma kyau..." gaba d'aya k'awayen amaryar sai shan dariyar Hajiya suke, gashi har hoda pankeke Sajida ta shafa mata, harda foundation, Maryama tana hanawa Sajida tana k'i... Hajiya ko cewa take "Shafa mani bud'a jakar naku, amma kar ki maidani roba-roba, don wannan ba irin ta zamanin mu bane..Abinka da farar fata kuwa sai tayi kyau sosai ... Hajiya ta murmusa ta lakuci fuskarta taga jan hoda ya bayyana, foundation ya lakaci yatsanta, sai ka rantse abin arziki zata fad'i "K'ura ma yatsun nata idanu tayi yanda ta lakaci hodan kana tace "Oh ni Fad'ime Allah ka kiyasheni zama roba-roba.... Ke 'yar nan gane mani banyi zubin zabon can ba koh..." ta k'arashe tana nuni da Shema'u dake zaune can gefe tana shafa wayarta... Gaba d'aya son k'unshe dariyar su suke sun kasa don sunsan sarai Shema'u ta jiyo Hajiya, don tunda tazo gidan Hajiya ke yab'a mata magana ko ajikinta, sai Maryama ta d'an b'ata raine ma Hajiya ke yin shiru.... Kaman daga sama suka jiyo muryar Shema'u na salati ta mik'e tsaye had'e da rik'e k'irji tana fad'in "Mun shiga uku mun mutu mun lalace....." Hajiya kallabinta a kaikaice ta mik'e tana fad'in "Allah Ya tsari bakinki kedai kika lalace bamu ba, banma san uwar kinibibin da yasa kika d'ebo wannan sawayen naki uwa ta d'an marini sabida tsaban shafe-shafe kika zo mana bikin mu ba, muguwa mai halin tsiya wato kizo ki mana mugun kaba'iri toh Allah Ya tsari bakin ki.... Aniyarki ya biki mai mummunar fata, bamu shiga uku ba saidai muga alheri ehe...." Mutanen Hajiya sai tausanta suke yayinda Sajida tasha kunu ta k'arasa wajen Aunt d'inta tana tambayarta meke faruwa... Cikeda makirci Shema'u ta soma fad'in "Sajida waya aka min yanzun nan daga wajen d'aurin aure ana sanar dani taron aure ya watse an fasa auren Maryama da Ashfaq, shine na birkice gaba d'aya banma san me nake fad'i ba amma Hajiya bata saurareni ba...." Bata kai aya ba Hajiya dake kaikaita kallabinta ta d'ago tana watsa mata mugun kallo kafin tace "Me kika ce...!!! Ke ahir d'inki nayi imani da Allah kinyi kad'an kizo ki mana barikanci a nan... Aure babu fashi, saidai naki auren da Attahiru ne ya k'are....." Maryama da juwa ya soma d'ibanta, sama-sama take jin batun su Hajiya domin kuwa tuni labari ya soma yad'uwa ta wayar salula.... Ba Shema'u kawai aka kira ba har da wasu daga cikin 'yan biki... Kan kace me Maryama ta d'ibi jiki ta fad'i, nan hankula yayi kanta.. Sajida da k'annenta sai kuka suke... Hankalin Hajiya idan yayi dubu ya tashi, haka aka shigar da Maryama d'aki ana mata fifita still bata farfad'o ba... Hajiya sai matse hawaye take tana jero sallalami, gaba d'aya tama rasa wanne zatayi, kai da zataga Keenafas yau da ta cukumesa sun dambatu da kyau..... Friends d'inta sun kewayeta sai mata fifita suke, kowa ya cika da al'ajabin wannan lamari. Hajiya ma zubewa kurum tayi cikin kujera kallabi a hannu anai mata fifita, rabonta da ganin irin wannan tashin hankali tun mutuwar mijinta Alh Shattima, gani take tamkar zata rasa Maryaman ta. Shema'u na gefe banda addu'an Allah sa zuciyar Hajiya ya buga bata komai, zuciyarta ya cika da farin cikin ganin Hajiya cikin tashin hankali, yanda take mashassharan nan da zata sami hali data k'arasata daga ita har Maryamar ta huta.... Tana cikin wannan tunani wayan Hisham ya kuma shigo mata. Mik'ewa tayi ta fice can waje kafin ta amsa wayar. .... Hankali tashe Hisham ya soma fad'in "An d'aura auren....." Saida ta waiga gefe taga babu mai zuwa kafin ta sauk'e ajiyan zuciya tace "Haba hakan ai yafi gwara a d'aura, amma ko banza naji dad'in mishkilan da aka samu daga farko tunda dukansu biyu zukatansu k'iris ya rage basu buga ba......" Gajeren tsaki Hisham yayi kana yace "Ki saurareni kiji waye mijin..." Hayaniyar Ilu data jiyo daga can veranda yasata katse kiran Hisham ta nufi wajen cikin sauri don ta jiyo muryar Hajiya. Ilu mak'ale da hularsa a hammata irin tashi ka faye naci d'in nan yaci gaba da fad'in "Aradu Hajiya ban tab'a ganin maraimakin shugaban k'asa ido da ido ba sai yau, har jikin motar sa saida na shafa...." Hajiya dake zaune saman faran kujera ji take kaman ta tashi ta rufe Ilu da duka.... Gaba d'aya mutanen wajen sai mamaki suke jin Ashfaq wai d'an vice president ne ciki harda Shema'u wanda tabbas bata fatan Maryama ta aurin d'an mataimakin shugaban k'asa... Take kuma ta soma tambayar kanta toh ai Hisham yace an d'aura auren kuma yanzu Ilu yace VP ya tattari d'ansa ya tafi dashi.... Bata gama tunanin da take ba ta jiyo muryan Ilu yana ci gaba da fad'in "Ai Hajiya da rabon aure dai ta gidan nan zai dawo, wllhi Dapta yayi tunani bai bari jama'a sun taru a banza ba tuni aure ya juya kansa..... Hajjaju namu ai anyi tuwona maina da Dapta......." Kan bala'i!!!!! Bata fahimci me ake fad'a ba kaman zautacciya haka ta tako har gaban Ilu tana girgiza kai kaman wata mahaukaciya ga fuskarta uwa mage ta fad'a a talge take fad'in "Me kake cewa, mijina, Tahir d'ina ne yayi aure.....?" Ilu ya wage baki uwa gonar auduga kana yace "Au dama kece matar da Dapta ya aura kwanaki..... Yo murna zakiyi anyo maki k'anwa ta gida, ko Hajajjun mu...." ya k'arashe yana kai dubansa ga Hajiya da tuni ta mik'e tsaye... Kallon Ilu da kyau Hajiya ta kuma yi kafin tace "Kai Ilu banason sakarci, kana nufin Attahiru ne mijin Maryama, Maryama tawa...?" Ilu ya kuma wage baki kafin yace "Insha Allahu Hajajjun mu.... Abu yayi kyau ai..." Kasa furta komai Hajiya tayi lallai Attahiru hankali bai ishesa ba, yo ita ina zata bari ya kwashi Maryama ya had'a da wannan matar tasa mai suffar kafirai, wannan da ganin idanunta tsaf zata salwantar da rai, yo shi kansa fata da addu'a take ya rabu da wannan kod'edd'iyar kafin ta watsa masa cututtukan zamani shine yanzu kuma zai had'a harda Maryama yakai a karsu gaba d'aya ta yab'a masu cuta ta kashesu gaba d'aya.... Inaaa ba da ita ba.... Huci kawai take tana jiransa ya iso ya warware wannan aure da ba d'orewa zaiyi ba..... Bata gama tunanin da take ba ta jiyo kukan Shema'u tana fad'in "Kai Ilu kake ko wa, wllhi wannan kuma k'arya kenan... Wllhi ni nasan Mijina bazai tab'a yin abinda kace ba......" Fitowar Sajida daga d'aki yasa Shema'u ta kuma kurma wani ihun tana jijjiga uwa tab'ebb'iya. A tamanin Sajida tayi kanta tana tambayarta lafiya...? Shema'u cikin kuka ta rungume Sajida tana fad'in "Sajee wai Daddyn ku shine ya auri Maryama, wayyo Allah na Sajee mutuwa zanyi.... Sajida ta d'ago idanu tana dubanta cikin rashin yarda da abinda take ji, kallon illahirin mutanen wajen take ta shiga girgiza kai tana jada baya take fad'in "No.... That's not true, wllhi wannan ba gaskiya bane, Daddy na bazaiyi abu makamancin haka ba......." Shema'u ta rik'ota tana hawaye take fad'in "Sajee gaskiyar kenan, aure my AT yayi kuma wai Maryama for that matter.." Tamkar wacce aka zabura haka Sajida ta fice a guje Shema'u tabi bayanta, Hajiya ta rungumo Jamal da Ni'ima ta wuce dasu d'aki.... Lokaci guda gidan biki ya tarwatse kowa na fad'in albarkacin bakinsa, wasu gani suke Tahir yayi dai-dai yayinda wasu ko suke ganin sam bai kyauta ba duba da yanayi Maryama tare suka taso da d'iyarsa Sajida. K'awayen amarya aka barsu da Al'ajabi harta Fadila k'awar fad'an Sajida saida taji tausayin Sajida yau, sam hakan bai kamata ba a cewar su dukda hakan bai sab'a ma Shari'a ba.... Duk wannan wainar da ake toyawa Maryama bata san yanda hankalinta yake ba, tana nan a kwance... Shema'u tana ganin Sajida ta nufi kwalta ta soma addu'an Allah sa trailer tabi kanta.... Aiko mai machine ne ya kwashe Sajida nan ta zube a k'asa sumammiya Shema'u tayi kanta, mutane sukayi chaaa.... Kai tsaye aka kwashi Sajida aka wuce da ita asibiti mafi kusa Shema'u sai huci da turiri take tana tunanin kalan tuggun da zata k'ulla.... AT ya shafi goshinsa a karo na biyu kafin yace "Toh Hisham wai ya zanyi ne, ya zanyi ne fisabilillahi.... Ni kaina ba son auren Maryam nake ba but banida choice...." Hisham ya jinjina kai kana yace "AT don't say I didn't warn you, domin kai kanka kasan abinda kayi is a big mess...." "Enough pls Hisham! Kar ka k'ara min more headache pls......." bai kai aya ba waya daga asibitin da aka kai Sajida ya shigo masa.... A zabure ya mik'e yana amsa wayar... Cikeda tashin hankali ya dubi Hisham yace "Sajida tana asibiti, I've to go....." daga haka k'ofa ya nufa Hisham ya mik'e cikin sauri yabi bayansa. ******************** Tsaye suke cirko-cirko cikin parlorn Haidar wanda yake a Penthouse d'insa..... Mari ya kuma watsa ma Haidar a karo na biyu, kafin ya d'ago hab'arsa yace "Ka sani there's a good and wrong way of doing things....." Mummy dake gefe tana sharan kuka cikin sauri ta k'araso ta janye Haidar tana kallon yanda fuskar sa tayi jajazir abinka da farin fata... Fad'i take "Fu'ad kayiwa Allah ka k'yale yaron nan haka, kowa yana kuskure, ko so kake ka illata min shi...." Kallonta VP Fua'ad Mainasara yayi kafin yace "Duk laifinki ne, ke kika sangarta sa gaba d'aya shiyasa yake ganin yayi girman da zaici gashin kansa. Kuma na gama magana Haidar k'ofa bazai kuma ficewa ba har sai lokacin da ya nustu yayi hankali....." Daga haka kallon Chief security na kula da al'amaran cikin gida yayi kafin yace "Make sure you locked him up..." daga haka ficewa yayi ya nufi sashen sa cikin sauri.... Mugun kallo ya rakasa dashi zuciyar sa na masa zafi, ji yake tamkar ya shak'esa ko zai huce takaici. Ba don health condition na mahaifiyar sa ba wllhi da ya sanar da ita Daddy shi ya kashe Nabila... Sanar da hukuma is pointless sannan sanar da Mummyn sa na nufin rasa rayuwarta..... *Sameena Aliyu Mrs* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *42* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ Hankali tashe AT suka isa asibitin, kai tsaye Dr d'in da ya amshi case d'in Sajida suka samu, daga shi har Hisham d'in Dr baiji wani d'ar d'in sanar dasu komai ba sabida yasan su duka likitoci ne.... Daga office d'in Dr ward d'in da Sajida take suka nufa... Shema'u na zaune saman faran plastic chair ta cika tayi fam, kana ganinta kasan hankalinta baya jikinta gaba d'aya a birkice take, Sajida na kwance saman gado drip mak'ale a hannunta na hagu... Kallo d'aya Shema'u ta watsa masu had'i da kauda kai gefe zuciyarta na mata wani irin zogi da rad'ad'i.... Kallo Hisham ya bita dashi yana karantar yanayinta yayinda AT yayi kan Sajida a tamanin ko takan Shema'u bai bi ba.. Bandage d'aure a goshinta da hannunta maras cannula.. Tausayinta ya cika zuciyar AT, shafa goshinta yake a hankali yana furta "I'm here sweetheart, meyasa zakiyi haka ma kanki, why Sajida....?" A hankali ta soma bud'e idanunta don kaman a mafarki take jiyo muryar mahaifin nata, aiko suna had'a idanu ta fashe da wani irin kuka ta fincika zata tashi AT yayi saurin rik'eta... Kuka take sosai tana fad'in "I don't want to see you ever again, just get out of here.... Ka tafi Daddy banson ganinka.... Bana sonka, I hate you....." Da sauri Shema'u ta matso ta rik'e Sajida sosai daga fincikan da take, rungume Shema'u tayi tana ci gaba da kuka take fad'in "Aunty I want to die, I don't wanna live anymore..... Aunty ina so nima na tafi na sami Mummy zaifi mun wannan rayuwa mai k'unci da zanyi...." kuka yaci k'arfinta. Shema'u ta k'ak'aro hawaye tana girgiza kai take fad'i ma Sajida "Ki daina fad'in haka Sajee, kiyi hak'uri kinji sweetheart.... I'm here kinji koh, ki daina fad'in mutuwa yafi maki kar Allah yayi fushi dake...." Hisham ya janye AT suka fice daga d'akin, kana ganin AT kasan a birkice yake gaba d'aya, idanunsa sun kad'a sunyi jazir... Fuzar da iska ya kuma a karo na babu adadi kafin ya dubi Hisham yace "Hisham she's not normal, she need a therapist, muyi transferring nata to hospital d'inmu tunda kana....." Hisham ne ya katse sa da fad'in "Karma ka soma wannan tunanin AT idan akwai mai buk'atan therapist toh kaine, ai dama kasan dole irin haka ta kasance.... Kaima kasan definitely dole reaction d'inta ya zama haka, implications d'in da nake jiye maka kenan, sannan ita kanta Maryamar bakasan yaya zaka kwashe da ita ba...." Mugun kallo AT ya watsa masa kafin yace "Shut the hell up Hisham! don't give me more headaches here.... Just pls give me a breathing space, you are not helping at all .... Gajeren tsaki yayi sannan yayi ficewarsa daga asibitin gaba d'aya... Hisham ya bisa da mugun kallo kafin ya tab'e baki.... Tunani ya somayi, tabbas yanzu Shema'u bata gaban AT gwara tun wuri yasan me yake ciki, wllhi yanda ya taimaka mata ta mallaki AT dole ta taimaka masa ya mallaki abinda ya jima yana buri, dole su k'arasa abinda suka riga suka soma.... Yana cikin wannan tunanin Shema'u ta fito ta riske sa. Murmushi ya sakar mata kana yace "Kin fito a dai-dai ina muka kwana, kinsan gwara nasan matsayi na tunda ga dukkan alamu kin kusa zama stohuwar yayi...." Saida ta waiga gefe da gefe taga babu mai zuwa kafin ta janyo Hisham suka d'an fice wani k'ofa. "Meye kika kawo mu nan.?" ya tambaya yana dubanta... Gajeren tsaki tayi kafin tace "Muna tsaye a can wani zai iya jiyo mu, ina Tahir...?" Hisham ya dafe hannunsa da garu kafin yace "Ya tafi wajen sweet 18 d'insa...." Murmushin yak'e Shema'u tayi wanda hausawa ke cema kafi kuka ciwo kana tace "Kutumar uwar 18 d'in, wllhi yarinyar nan sai tasan ta aurin mijin wata, sai na maidata abin kwantance, dukkansu sai na shayar dasu mamaki har shi mai budurwar zuciyar...." Hisham yayi tak'aitaccen dariya kafin yace "Ni dai damuwata ki tabbata na mallaki takardun filin nan tun kinada sauran amfani kafin ki k'arasa komawa k'arfan 'yan gwan-gwan..." Shema'u ta kuma murmusawa kafin tace "My Ally kenan, kasan without me bazaka cimma burinka ba, sannan nima idan babu kai burina bazai kammala cika ba, yanzu mu d'au next step, zamuyi utilizing wannan opportunity d'in na rashin lafiyan Sajida, kasan AT yaransa sune rayuwar sa...." Tuni Hisham ya d'ago me Shema'u ke nufi, Murmushi ya sakar mata kafin yace "Allah rabamu da kaidin ki..." Itama murmushin tayi kafin tace "Kaga na samu hanyar rabashi da shegiyar yarinyar kafin na bijiro mata da wani bala'in da hankalinta bazai d'auka ba..." ta k'arashe tana wani kafiran murmushi... ************ Gidansa ya wuce kai tsaye domin ko zarafin zuwa gidan Hajiya bai samu ba, gaba d'aya abun ya d'aure masa kai, Aysha ce ta fad'o zuciyarsa. A hankali ya lumshe idanun sa, sam Sajida da ba haka take ba, quite alright yasan batada wayo but baisan wautan nata har ya kai haka ba, sau biyu kenan tana attempting abu makamancin haka.... Dafe kansa yayi da duka hannayen sa biyu lamarin ya hanasa sukuni gaba d'aya. Sallah kurum AT yake tashi yayi don ko fita ya kasa... Yana nan zaune a parlorn har wajajen k'arfe 9:30pm kaman daga sama yaji ana tab'a k'ofa. D'ago idanu yayi yana dubansu cikeda mamaki don bai zaci za'ayi discharging nata yau ba idan da tashine da an barta a asibiti ta k'ara recovering, sannan ko sallaman ta akayi bai zaci zata yarda ta dawo gida cikin lumana ba, yasan wannan aikin Shema'u ne, akan yaransa zata iya yin komai sabida k'aunar da take masu.. Shema'u na rik'e da Sajidar suka k'arasa shigowa.... Ko darajan gaisuwa bai samu daga Sajida ba tayi wucewarta upstairs, Shema'u ta dubeta tace "Sajee are you sure zaki iya haye matakalan ko na rik'e ki....?" Girgiza kai Sajida tayi murya can k'asa tace "Zan iya Aunty..." daga haka ci gaba da d'ingisawa tayi har ta haye bene.. Ko kallo AT bai ishi Shema'u ba tasa kai zata shige.... Saurin mik'ewa tsaye yayi ya sha gabanta, k'warjininsa ya hanata kasa furta komai sanda idanunsu ya had'e waje guda. A hankali ya furta "Thank you, thanks for everything..." Idanun Shema'u yayi rau-rau amma ta dake tace "I only did what I had to do...." Daga haka bata jira amsar sa ba tayi wucewarta upstairs tana matsan hawaye... AT yabi bayanta da kallo jikinsa duk a Mace, gani yake sam bai kyauta ma Shema'u ba... Kaman daga sama ya jiyo knocking cikin sauri ya k'arasa ya bud'e, ganin Hisham ne yasa sa basa hanya ya shigo. AT bai ce masa komai ba don har yanzu a shak'e yake dashi, ya k'arasa saman couch ya zauna, Hisham d'inma zama yayi cikin d'aya daga cikin kujerun ya k'urawa abokin nasa idanu. AT ya d'an dubesa kaman bazaice komai ba sai kuma yace "So kai ka kawo su kenan.?" Hisham ya jinjina kai kana yace "Nayi magana da Sajida da taimakon Aunt d'inta Shema'u. From what I observed she's quite devastated, and nothing is wrong with her sanity, kawai dai tana buk'atan space domin kuwa abun da ya faru yayi matuk'ar b'ata mata rai, just put your self in her place zaka gane me nake nufi.... Sannan magana ta gaba da nake tsoron sanar da kai shine...." shiru yayi baici gaba ba sai dunk'ule hannayensa da yayi ya d'aura hab'arsa akai. AT ya gyara zama kafin yace "umhum go ahead, me tace..?" Hisham ya fuzar da iska kafin yace "Cewa tayi the moment aka kawo Maryama cikin gidan nan a matsayin matar ka zata sha poising ko kuma ta shiga duniya, don bazata iya zama gida guda da aminyarta a matsayin matar Babanta ba...." Daga haka mik'ewa tsaye yayi hannayen sa cikin aljihu.. Mik'ewa AT d'ima yayi zuciyarsa cikeda shakkun abinda abokin nasa ya gama sanar dashi... Har farfajiyan gidan AT ya raka Hisham kafin ya komo cikin gidan. Ya jima yana kallon k'ofar d'akin Sajida kafin ya nufi d'akin Shema'u, tana zaune bakin gado tana shafe jikinta lotion ya shigo.... Sarai taji shigowar sa tayi masa banza. Cikin takunsa na k'asaita ya k'araso har gabanta, da sauri ta mik'e zata shige bathroom AT yayi saurin rik'ota yace "Shema'u pls we've to talk..." Kallonsa tayi da rinannun idanunta kafin tayi murmushin yak'e tace "Idan dai akan Sajida ce kar ka damu zan ci gaba da kula da ita, domin wannan alk'awari nayi ma 'yaruwata amma idan akan kawo amaryar ka cikin gidan nan ne kasani bazan hana Sajida making decision d'inta ba, the girl had enough already...." ta k'arashe tana k'ok'arin k'wace kanta daga rik'on da yayi mata... Cikeda mamaki AT ke kallonta, yanda tayi maganar kaman ba ita ba, sam bai zaci zata goyi bayan Sajida ta aiwatar da abinda Hisham ya sanar dashi ba.... Da mamaki yake fad'in "Why are you sounding this way...?" A harzik'e tace dashi "How am I sounding...?" AT ya kuma rungumota kafin yace "I mean you are speaking in a strange manner, meke faruwa ne My Shemah..." Da mamaki take dubansa lallai kaga namiji ka k'yalesa, tunda suke da ita bai tab'a kiranta his Shemah ba sai yau, gashi yanda ya fad'i ba k'aramim dad'i ya mata ba.. Ta ci gaba da k'ok'arin k'watan kanta ta fashe masa da wani irin kuka tana fad'in "Kar ka yaudareni da kalaman ka Tahir, kayi aure babu sani na ina a matsayin matar ka, sannan nima yaushe ka sauk'e min hakkina da har zaka auro wata, nikam na gaji da zam......" bata kai aya ba taji ya had'e lips d'insu waje guda... Take ya soma kasheta da wasu irin salo, jikin Shema'u ya d'auki k'yarma shi kuwa AT lokaci guda ya soma jin aches ta ko ina anjikinsa... A kasalce ta turesa daga jikinta tana ci gaba da hawaye take fad'in "Karma ka soma abinda bazaka iya ba...." ta yunk'ura zata tashi ya kuma rungumota murya can k'asan mak'oshi yake fad'in "Shema'u I'm sorry, I'm sorry kinji but pls kar kice zaki rabu dani my children still needs you, auren Maryama da nayi banida option ne, Maryam amanace a hannu na kinga tun daga yanzu an soma samun matsala irin haka inaga na Aura mata wani, pls ki taimaka min na tsare amanar da Allah Ya bani idan har kina sona kinji....." Gashi dai with a cool voice yake mata maganar cikin kwantar da hankali amma banda suya babu abinda zuciyarta keyi. Lallai ma AT ya raina mata hankali, wato sabida yaransa dai take zaune dashi, sam batada wani amfani da ya wuce ta kula masa da yaransa, gashi yanzu yayo aure kenan ya auri wacce yake so, har wani wai bashida option ne shiyasa ya auri Maryama, har yana wani cewa ta taimaka masa ya rik'e amanar sa... Uwar amanar ma!.. Tayi murmushi a hankali kafin taci gaba da tunanin nata, da sannu zata shayar dasu mamaki kuma wllhi wllhi sai AT ya sota ko naman jikinsa ne yake gutsirewa ya fad'i... Cikin jikinsa yau tayi bacci dukda babu wani abinda ya shiga tsakaninsu amma kam taji jiki don da k'yar bacci ya sace ta. Washe gari rigar da ta sai mashi birthday gift d'insa ya saka don kawai ya faranta mata .... Ko fitowa Sajida batayi ba, Shema'u ce ta ringa sintirin kai mata abinci. Koda AT ya shiga ma rufe idanunta tayi kaman tana bacci, bai damu ya tasheta ba sai ficewa da yayi.... Ko sallama yauma baiyi ma Shema'u ba sai jin k'aran rufe gate tayi... Zuciyarta tamkar ta fito waje ta fashe..... AT kuwa yana ficewa gidan Hajiya ya nufa, a veranda ta sami 'yan yaran shi, Jamal da Ni'ima nan suka tafi a guje suna hayewa jikinsa suna gaida shi. Fuskar sa ya cika da annuri ya d'aga Ni'ima sama yana shafa kan Jamal yake tambayar su suna lafiya..? Jamal yayi saurin gyad'a kai kafin yace "Daddy mu muna lafiya amma Adda Maryama bata da lafiya tana kwance d'akin Hajiya tun jiya ma batada lafiya.... " Gaban AT ya yanke ya fad'i! Duban Jamal ya kuma yi kafin yace "Hajiya fah? " Hajiya wai taje sayo mata magani saidai Baaba Delu ce take nan.." Ya jinjina kai yana tunanin wato dai Hajiya bazata daina self medication ba, saikace wata likitiya kai tsaye sai tayi ma kanta prescribing magani, ya zaci ta daina tunda ya tab'a d'ura mata ruwa a ciki ashe bata daina ba. "Champ, princess kuje wajen Baaba Delu ko, barin duba Addar taku." Gaba d'aya suka gyad'a masa kai suka wuce suka nufi sashen Baaba Delu... Gabansa na dukan tara-tara ya nufi d'akin don baisan yaya zasu kwashe ba sannan baisan labarin ya risketa ko kuma bai risketa ba. Kwance ya hangeta saman gado ta duk'unk'une cikin bargo sai rawan d'ari take idanunta a lumshe. A hankali ya k'araso har gaban gadon had'i da k'ura mata idanu, saida ya d'iba wasu mintoci kafin ya zauna dap da ita ya kai hannunsa goshinta, nan yaji jikin nata k'auuu, zafi sosai. A hankali ta bud'e idanu ta sauk'e su kansa, dukda tana cikin ciwo hakan bai hana gabanta yankewa ya fad'i ba. Cikin sauri ya mik'e ya nemo bowl da ruwa da handtowel, sosai ya razana da jin zafin jikin nata abinka da likita, temperature d'in nata is very high... Zama yayi ya yaye bargon data rufu dashi yasa hannu ya d'agota.... Ba Maryama kawai ba shi kansa AT cak ya tsaya yana kallonta.. Itakam bata gane me Uncle keyi ba, tsoro ne ma da firgici suka rufeta, meyasa Uncle zai rik'eta haka, ko ya zaci har yanzu ita d'in k'aramar yarinya ce. Gaba d'aya ya kasa tab'uka komai sai kallon k'urilla da yake binta dashi. Ita kuwa Maryama ko bud'e bakinta ta kasa sai kallon itama take binsa dashi, zuciyarta ta raya mata k'ila tausayin abinda Ashfaq ya mata Uncle yake... Yana nan rik'e da ita a hannunsa sam basuji shigowar Hajiya ba, sai salati data soma lokaci guda ta k'arasa ta fincike Maryama tana fad'in "Toh uban 'yan rashin kunya tashi min a saman gado, ko kunya bakaji ba god'e-god'e da kai ka wani shigo ka kallame yarinya salon ka mata wani abin ko, toh ahir d'inka, kul ka d'aga idanunka akan d'iyata... Kuma kaji da kyau asaran sadaki kayi ehe Maryama ba MATARKA bace......" Daga AT har Maryama saida k'irajensu yayi wani irin bugu.... Ta kasa gasgata abinda take ji sai kallon mamaki databi Hajiya dashi tana girgiza kanta hawaye na zubo mata Cikin sauri AT ya fice daga d'akin.. Hajiya ta rik'i bakinta domin ita kanta batasan tayi wannan sub'ul da bakan ba don dama bata so Maryama ta sani ba sai AT ya rubuta mata takardan sakin Maryama..... *Sameena Aleeyou Mrs* [8:53PM, 4/5/2018] ‪+234 806 652 0501‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *43* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ Kuka take sosai tana girgiza kai tana kallon Hajiya ba tareda ta iya furta koda kalma ba, har lokacin ta kasa yarda da abinda kunnenta ya jiye mata... Uncle, Uncle dai a matsayin mijinta na aure.... Bata iya furta koda kalma ba sai wani sabon kukan da ya kuma kufce mata, Hajiya gaba d'aya jikinta yayi sanyi sai lallashinta take amma kaman cewa take ta k'ara.. Shi kuwa AT har cikin k'ahon zuciyar sa yake jin rad'ad'in kukan da Maryama keyi... Hajiya taci gaba da fad'in "Haba Maryama ta kiyi hak'uri ki daina b'ata hawayen ki kinji koh, idan dai auren Attahiru ne ina mai tabbatar maki ni da kaina zan saka shi ya rubuta saki ehe, da yak'i da ya so......" AT bai iya ci gaba da sauraren kalaman Hajiya ba sai mik'ewa da yayi ya fice daga parlorn.. Maryama ta dubi Hajiya da watery eyes d'inta murya na rawa take fad'in "Hajiya da gaske Uncle ne mijina...?" Hajiya ta kasa furta komai sai kallon tausayi databi Maryama dashi, zuciyarta gaba d'aya zafi yake mata domin a duniyar nan bata k'aunan ganin b'acin ran Maryama balle har taga hawayen ta.. Lallashinta Hajiya taci gaba da yi gaba d'aya ma ta mance magungunan data sayo mata a chemist d'in Ema, gyara mata kwanciya ta kuma yi sai huci take tana yin k'wafa... AT kuwa yana nan lab'e yana jin Hajiya ta shige bathroom ya sad'ad'o ya shigo, fuskar Maryama naga d'aya b'angaren bata gansa ba sai k'aran tab'a ledan magani taji... Tana juyowa sukayi ido hud'u, tattara magungunan yayi kafin ya d'aura d'an yatsa a lips d'insa alamun tayi shiru don ya jiyo Hajiya na k'ok'arin fitowa... Cikin sauri ya kwashi magungunan sannan ya fice... Maryama ta bisa da kallo tana ganin lamarin tamkar a wasan kwaikwayo wai ita Uncle ya aura. Tabd'ijam! Ko kusa Allah Ya gani bazata iya zaman aure da Uncle ba. Koda Hajiya ta fito tana neman magungunan shiru Maryama tayi mata bata sanar da ita Uncle ne ya tattara ba, haka ta k'araci nemanta k'arshe tayi tunanin k'ila to jefa wani wajen. ************* Shema'u ta kuma kallon Sajida a karo na biyu kafin tace "Sweetheart abunda ya faru ya riga ya faru, kedai kawai kiyi abinda na fad'a maki shine kawai zai lalata auren Maryama da Daddyn ki but idan ba taimakon Maryama kika samu ba Daddyn ki namiji ne, kiga maza ki barsu yanda kika gansu shi ko ajikinsa zai yada kai gaban k'aramar yarinya idandai buk'atarsa zai biya, b'acin ranki won't solve anything saidai ma ya k'ara maki k'unci da takaici... Sajida ina sonki ne shiyasa nake sanar dake wannan abu, muddin kika sami goyon bayan Maryama I assure you komai zai wargaje kin gane, sannan Daddyn ki ki basa hak'uri kinji koh ta haka ne kurum bazaiyi suspecting wani abu daga gareki ba kinji koh....." Sajida ta gyad'a kai tana murmushi kafin tace "Aunty you always ve solution for everything, ina sonki...without you bansan yaya rayuwa zata kasance mana ba..." Shema'u tayi murmushi kana tace "Nima ina sonku farin cikin ku shine nawa, idan don ta nine zan bar AT ya kawo Amaryar sa cikin gidan nan babu wani abu a ciki, tazo mu fafata ko ni ko ita, amma sabida nasan zuwanta na nufin tashin hankalin ki ne shiyasa nake nema maki solution kin gane...." Sajida ta kuma murmusawa kafin ta rungume Shema'u, saida Shema'u ta bata magungunanta ta sha kafin ta gyara mata kwanciyar ta tace ta sami bacci kafin ta fice... ************** Kaman wani munafuki haka yake lek'en su, Hajiya dasu Jamal zaune tacan gefe wajen flowers... Yaran suna wasan su yayinda Hajiya da Baaba Delu keta faman labari... Saida ya tabbata basa hangosa kafin ya shige cikin sand'a. A hankali ya tura k'ofar d'akin ya hangeta tana nan kwance ga mug na tea a gefenta.... Suna had'a idanu gabanta ya yanke ya fad'i.. Ya k'arasa shigowa cikin d'akin kafin ya maida k'ofar ya rufe a hankali. Kanta a k'asa ta kasa furta koda kalma guda.... Saida ya d'an fuzar da iska kafin ya d'aga mug d'in yaga bata wani sha abin kirki ba.. Bata ankara ba sai gani tayi ya zauna dab da ita, bugun zuciyarta ya k'aru, sarai ya gane ya haifar mata da tsoro amma hakan baisa ya canza position d'in zaman nasa ba. Fuskar sa babu yabo babu fallasa yace da ita yaya jikin naki.?" Cikeda tsoro ta d'an matsa gefe kad'an, da k'yar ta lalumo kalamai saman harshenta tace "Da sauk'i..." kana jin yanda tayi maganar zaka gane a razane take... AT ya kai lallausar hannunsa saman goshinta.... Take ta lumshe idanunta abubuwa da dama suka ziyarceta lokaci guda. Shid'inma hakan ce ta kasance dashi..... Nan yaji zafin jikin nata ya ragu, B'alle magunguna ya shiga yi yana mik'a mata yace "Oya karb'a ki sha and make sure kin shanye wannan tea d'in..." Idanun Maryama yayi rau-rau domin idan akwai abinda ta tsana shan magani ne uwa uba allura.... AT ya tsareta da idanu domin yasan halinta wajen k'in magani. D'an gyaran murya yayi ya kaikaito yana dubanta sosai kafin yace "Idan baki sha magani saidai a maki allura... Kina son allura..?" Yanda yayi maganar tamkar da Ni'ima yake magana, yanda ake ma yara idan ana so susha magani... Baki a ture tana goge hawayenta ta girgiza masa kai alamun a'a. Yayi nodding kansa kafin yace "Oya toh karb'a kisha idan baki so na maki allura..." Ganin ta kasa amsar maganin yasa sakin wani numfashi kafin yace "Barin koya maki logic d'in shan magani, just close your eyes and open your mouth..." ita kanta Maryama saida ta d'ago ta dubesa domin gaba d'aya da sigan yara yake mata maganar... Manyan idanuwan sa ya d'an ware kafin yace "Oya do as I said..." Runtse idanunta tayi sosai kaman wacce za'a caka ma allura kafin ta bud'e bakinta... AT ya bita da kallo yanda take shivering, harga Allah ta burgesa sosai wanda hakan har saida yasa saki wata silent smile... A hankali ya jefa mata maganin a baki kafin ya kwara mata da Tea d'in cikin wata irin kasaltecciyar murya yake fad'in "There you go... Good...." Har saida ya gama bata maganin kafin yace "Oya bud'e idanunki toh an gama....." Sanda ta bud'e idanunta akan fuskar AT ta bud'e su tsaf, wani irin charisma taga ya kuma mata, cikin sauri ta sadda idanunta k'asa. Shi d'inma d'an jim yayi kafin yayi gyaran murya yace "Allah baki lafiya koh...." bata iya basa amsa ba saidai ta amsa cikin zuciyarta. Saida ya kuma kwasan wasu mintoci kafin ta jiyo muryar sa ya soma fad'in "Maryam, I'm sorry about what happened, da ace nasan abunda Ashfaq or whatever zai maki kenan da banyi trusting d'inshi ba from the very beginning, kiyi hak'uri kinji koh, na sani it's not easy to overcome this na sani.... But na maki alk'awari ni Ahmad bazan barki ke kad'ai a dai-dai wannan lokacin ba, together we will go through this... Allah yasa haka shine alkhairi..." Shiru yayi ya kasa ci gaba da maganar yakai dubansa ga Maryama yaga kaman share hawaye take... Bazai iya juran ganinta cikin wannan yanayi ba, baisan yaya akayi ba baisan lokacin da ya janyota ya rungume cikin k'irjinsa ba... Hankalin Maryama gaba d'aya ya tashi gaba d'aya ta kuma daburcewa, ai tuni ta kuma fashe masa da wani sabon kuka... AT ya kuma matseta yana fad'in "It's okay, I'm here.." cikin wani irin sigan da baisan ya iya ba... Gaba d'aya ya mance kukan Maryama ta yuyu sabida aurensa takeyi yafi bada zaton sabida abinda Ashfaq ya mata take kukan... Wani irin sanyi da nutsuwa ne yaji sun dabaibayesa yau Maryam d'insa ce cikin k'irjinsa, a koda yaushe idan yaga tana kuka yakanso rungumarta ya rage mata pain d'in gashi yau Allah Ya basa wannan damar tabbas Allah buwayi ne gagara misali... A hankali ta ringa sakin ajiyan zuciya tana nan rungume cikin k'irjinsa, itama d'in samun kanta tayi k'uncin dake cikin zuciyarta ya ragu sai wani sanyi da ya mamaye zuciyar nata... Hajiya dake tsaye bakin k'ofa kasa shiga tayi ganin yanayin data gansu a ciki, gaba d'aya jikinta ya mace, a hankali ta Saki labulen ta dawo parlor ta zauna had'i da rapka tagumi, "Oh d'an yau sai Allah" ta furta a hankali... A haka Ni'ima ta shigo ta tadda Hajiya bata bi takan Hajiya ba sai kutsawa cikin d'akin Hajiya da tayi tana k'walla ma Adda Maryama kira... Cikin sauri Maryama ta soma kiciniyar k'wace kanta daga rik'on da AT yayi mata, bai saketa ba har saida yaji Ni'ima na share masa hawayen idanunsa tana fad'in "Daddy kuka kuke yi, Daddy kuma kar ku mutu, Aunty Shema'u tace duk wanda ya mutu zai dawo Monster......" shiru yarinyar tayi ta kasa ci gaba da magana sabida tuno fuskar Shema'u datayi tana fad'in saita yankata da knife idan ta fad'i... Daga AT har Maryama kallon Ni'ima sukayi cikin rashin gane ina zancen nata ya dosa, saurin rik'ota yayi domin ba komai ya tuna ba illa matarsa Aysha a lokacin da ya rungumi Maryama cikin k'irjinsa... Jin maganar Hajiya a parlor yasa sa saurin mik'ewa ya rik'o hannun Ni'ima suka nufo parlor don baiso Hajiya ta shigo ta same sa.. Zama yayi kujera mai kallon na Hajiya kafin ya shafi kan Ni'ima yace "Princess oya jekice ma Baaba Delu ta shirya maku kayan ku zamu tafi gida koh, gobe akwai school.." Da sauri yarinyar ta gyad'a kai had'i da ficewa... AT ya d'an d'ago ya dubi Hajiya yana sosa k'eya ga k'irjinsa dake bugun tara-tara, kaman mai shirin koyon magana haka ya soma k'ak'aro kalamai... Hajiya ta dakatar dashi ta hanyar d'aga hannu kafin taci gaba da fad'in "Attahiru tun kafin ta kaimu ga ja'inja ka wareware wannan auren wasan yaran da kayi da Maryama kana jina koh, rubuta mata rasidi yanzu ka bani don dama na fad'a maka asaran sadaki kayi." Da k'yar ya had'o kalamai ya soma fad'in "Haba Hajiya, a ina kika tab'a jin anyi auren wasa, auren Maryama da nayi da gaske nayi, Hajiya Maryama amana ce a hannun mu bai kamata mu dank'ata hannun wanda bazai iya rik'e amanar nan ba, Hajiya ki duba lamarin, kiga dai irin abinda Ashfaq ya mana shima da muka yarda dashi kenan balle kuma wani daban.... Hajiya don Allah ki taimaka min na k'arasa rik'on amanar da Allah Ya dank'a min har i zuwa lokacin da zan bar numfashi... Don Allah Hajiya..." yanda ya k'arashe maganar kaman zaiyi kuka... "Yo sai na zuba ma roba-robar matarka idanu ta karku gaba d'aya don wannan ban yarda batada cutan zamani ba ehe...." Yanda tayi maganar yaso bawa AT dariya, sai yanzu ya d'ago nufin Hajiya, Allah sarki har yau batasan Shema'u bane sam da bazata na mata irin zato ba... Banda Hajiya ma da nata tunanin yaushe auratayya zai shiga tsakanin sa da Maryam a halin yanzu, ai tayi k'arama sosai a ganinsa, kawai dai so yake ya koyar da ita soyayyar sa a halin yanzu.. Magiya yaci gaba da mata yana rok'onta har saida Hajiya ta gano tsan-tsan soyayyar Maryama cikin idanunsa kafin ta jinjina kai tace "Shikenan Attahiru naji, bazan tilasta maka sakinta yanzu ba, amma ka sani Maryam babu yanda zataje, tana nan zaune da ni a gidan nan, idan kaga Maryama ta tafi gidanka a matsayin mata toh kuwa babu shakka rasidi ka kawo min na gwajin jinin matarka tabbacin bata d'auke da wata cuta ehe...." AT ya k'unshe dariyar sa don gaba d'aya yasan characteristics of old age ne ke d'awainiya da Hajiya... Akan wannan sharad'i Hajiya ta janye maganar sakin Maryama, sannan ta k'arada sai taji daga bakin Maryama idan bata son sa dole ya saketa, AT ya amince da hakan domin shima tsantsan soyayyar sa yake ganowa cikin idanun Maryam tun ba yau ba LOKACI NE dai bai basu damar ba sai yanzu, domin wannan karan kam sam bazaiyi wasa da Damar sa ba, zai nuna mata shi d'in mai k'aunarta ne.. Kafin ya kwashi yaransa su wuce gida saida ya kuma lek'a Maryama, ya samu idanunta a lumshe tamkar mai bacci, a hankali ya sad'ad'a ya sauk'e mata light kiss saman chick d'inta wanda tajishi har cikin zuciyar kafin ya furta "Allah baki lafiya Maryam..." cikin wani irin siga yayi maganar. Cikin zuciyarta ta sami kanta da amsa masa da _Ameen Uncle_ gaba d'aya jinta take wani iri ta kasa yarda da al'amarin, wai yau ita Maryama da Uncle a matsayin miji da mata... Da gudu ta duro daga saman gado kaman ba itace maras Lafiya ba ta k'arasa gaban dressing mirror tana ganin yanda ya sunbata tana shafa wajen a hankali k'irjinta naci gaba da bugawa... Lokaci guda k'irjinta ya tsinke sakamakon tuno maganar Ni'ima da tayi cewa Shema'u tace duk wanda ya mutu yana dawowa monster, toh Me wannan maganar take nufi??? Zama tayi dirshan bisa gado tana tunanin lamarin..... Yau gaba d'aya jinsa yake cikin farin ciki, harta Shema'u saida ta fahimci hakan, wani babban abinda ya kuma masa dad'i shine Sajida ta basa hak'uri akan abinda tayi, sannan ta amince masa ya kawo matarsa cikin gidan ko sa'a Ni'ima ce zata zauna da ita kuma zata darajata insha Allah... Ta kuma sadda kanta k'asa tana saman gwiwoyinta kafin tace "Daddy I'm sorry, kayi hak'uri kaji...." AT yana murmushi ya mik'e ya d'agota kafin yayi hugging d'inta yace "Thanks for understanding me sweetheart, Allah maki albarka kinji koh..." Tayi murmushi ta d'an rik'e hannunsa kafin tace "Ameen Daddy" ta juyo ta dubi Shema'u tace "Aunty na gode da kyawawan shawarwarin ki a gareni, Allah Ya barmu tare gaba d'aya." Shema'u ta murmusa kafin ta k'araso tayi hugging Sajida tace "Anything for you sweetheart, burina shine family d'in nan ta dauwama cikin farin ciki mai d'orewa..." AT murmushin jin dad'i yake yana dubansu gaba d'aya kafin Ya bud'e hannayen sa yayi hugging d'insu su duka biyu, cikin kunnen Shema'u ya rad'a mata "Thank you my Shemah" Shema'u cikeda jin dad'i ta kuma lafewa cikin jikinsa.... ********** Washe gari Sajida ta shirya tsaf ta tafi gidan Hajiya, saida tayi timing lokacin da Hajiya ke islamiya kafin ta tafi gidan... Maryama na kwance a parlor ta gama karance sak'on da Uncle ya turo mata ta jiyo sallamar Sajida... Gabanta ya yanke ya fad'i, cikin sauri ta mik'e zunbur ta zauna tana rarraba idanu... To her greatest surprise murmushi Sajidar ta sakar mata kafin ta k'arasa shigowa ta zauna a gefenta... Maryama ta rasa me zatace mata sai sadda kanta k'asa da tayi.. Murmushi Sajida ta kuma yi kafin ta kamo hannayen Maryama ta soma fad'in "Kar ki damu nasan ba laifinki bane, Maryama ki sani har abada ke 'yaruwa ce agareni, Daddy Ya aureki sabida ya raba alak'ar dake tsakanin mu, amma nasan nida ke bazamu tab'a rabuwa ba, nasan idan damuwa ya sami d'aya daga cikin mu toh babu shakka ya sami d'aya haka ne ko ba haka ba...?" ta k'arashe kaman zatayi kuka.. Maryam da hawaye ke gangaro mata cikin sauri ta shiga gyad'a mata kai alamun haka ne... Sajida tasa bayan hannu ta goge hawayenta kafin tace "idan har hakane alk'awari d'aya nake so ki min..." Maryama cikin muryar kuka take fad'in "Ki fad'a Sajida zan maki ko menene insha Allah..." "Ki min alk'awari har abada auratayya bazai tab'a shiga tsakanin ku da Daddy na ba, idan kin min haka kin gama min komai, sannan idan kika sab'a alk'awarin wllhi wllhi nida ke har abada...." Kaman an buga guduma haka k'irjin Maryama ya buga... *Sameena Aliyu Mrs* [8:55PM, 4/5/2018] ‪+234 806 652 0501‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *44* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ *Assalamu alaikum makaranta wannan littafi ina mai baku hak'urin jina da kukayi shiru na tsawon kwanaki biyu hakan ya faru ne sakamakon dakatar da rubutu da nayi sabida wasu uzururruka nawa da suka sha gaba na..... Amma duba da k'orafe-k'orafen ku zanyi k'ok'ari duk lokacin da na sami dama nai maku typing koda ba akai-akai kaman yanda aka saba ba.... Na gode k'warai da nuna k'aunarku a gareni.....🤝* _Haly Mom Farhan_ _Sholingaye_ _Sadnaf_ _Maman Aysha_ _Halima MK_ _Mrs Mansoor_ *Ina mik'a gaisuwata a gareku ❤🤝* Girgiza kai Maryama keyi tana duban Sajida cikeda mamaki, ta kasa yarda wad'annan kalaman daga bakin Sajida suke fitowa.... Kai tasan halin Sajida tasan kalan sangartar ta da kuma wautanta wannan tunani ya girmi tunanin Sajida duk yanda akayi akwai wata a k'asa, akwai mai neman gurb'ata mata tunani.... Likaci guda Aunty Shema'u ta fad'o zuciyarta, tabbas zuciyarta ba kowa take zargi ba illa Aunty Shema'u..... Muryar Sajida ne ya katse mata tunanin nata.... "Sanda ta mik'e tsaye tana gyara zaman Vail d'in abayarta take fad'in "Ni zan tafi, Maryama this should be between us, babu wanda zaisan abunda muka tattauna koda Hajiya ne, na barki lafiya...." Daga haka tasa kai ta fice... Maryama ta kuma binta da kallon mamaki, yini guda na wannan rana haka Maryama tayishi sukuku gaba d'aya maganganun Sajida sun d'aure mata kai, haka kurum taji tana son sanin meke faruwa a gidan Uncle tsakanin iyalansa da Aunty Shema'u, lokaci guda maganar Ni'ima ya kuma tsaya mata a rai cewa Aunty Shema'u tace duk wanda ya mutu spirit d'insa ne yake dawowa monster.... Tana nan zaune tana tunanin, Hajiya ta tasa ta gaba tanata mata fad'an tak'i shan magani gashi yau da ciwon k'irjinta tashi da shike watan ta ya zagayo... Nan suka jiyo sallaman sa cikin dadd'an sautin sa... Gaban Maryama ya yanke ya fad'i, kaman wata munafuka tayi saurin jawo hijabin dake gefenta ta rufa a kanta.... Kallo ya bita dashi kafin suka soma gaisawa shida Hajiya.... Hajiya ta mik'e tana k'ok'arin linke sallayan ta casbaha a hannu take fad'in "Toh ai tunda kazo sai ka sata tasha maganin...." AT yayi saurin karb'an abin sallan ya linke mata ya d'aura hannun kujera sai wani sanne kai yake yana satan kallon Maryama. Hajiya tana shigewa d'aki ya jiyo yana dubanta sosai... Da k'yar ta bud'e baki ta gaishesa, ya amsa yana mai k'arasowa yanda take. Zama yayi kusan k'afafunta da shike saman 3seater take kwance, a hankali ta janye k'afafun nata... Kallo d'aya AT ya mata ya gane cikin kwanakin ta take.... Bai kuma cewa komai ba sai mik'ewa da yayi ya k'arasa saman d'an wani stool dake gefen parlorn yanda Hajiya ke ajiye magunguna, k'ullin goro da wasu 'yan k'ulle-k'ullen ta na tsofi da ba'a rabasu... Maryama sai satan kallonsa take yanda yake gudanar da Al'amran sa, yana sanye cikin gray shirt da bak'ar Jeans ba k'aramin kyau da haske k'ananan kaya ke k'ara masa ba sam bakace ya haifi Sajida ba.... Tayi saurin sadda idanunta k'asa ganin ya k'araso ya zauna saman carpet saitin kujeran da take kwance bisa. Irin zaman cin abinci yayi kafin ya b'ula ledar ruwa ya tsiyaya a cup, ya shiga b'alle magungunan... Ganin tayi rau-rau da idanu yasa shi cin mur sosai murya a dake yace "Sauk'o kisha magani...." Dad'a marairaice fuska tayi kaman zatayi kuka, ganin sam babu wasa a tattare dashi sannan cikeda umarni yayi maganar ya sanya Maryama silalowa saman carpet d'in bakinta a ture, dama naturally idan tana period toh ranta a b'ace yake, uwa uba idan ta tuna maganganun da Sajida ta fad'a mata, gaba d'aya haushin Uncle d'in takeji ya rufeta... Ganin sam babu walwala a tattare da ita ya sanyasa yin wata murmushi a hankali kafin ya sassauta murya yace "Oya irin logic d'in da na koya maki jiya shi zakiyi, just close your eyes kiyi imagining sweet kike sha kinji koh..." ya k'arashe yana mik'a mata maganin.. Itakam idan yana shagwab'ata haka abin har dariya yake kusan sakata, saikace wata Ni'ima, wai za'a mata wayo ace tayi imagining magani sweet ne... Wani ikon Allah kuma sai ta sami kanta da biye masa tana shagwab'ewa yana riritata.... Ya k'arashe bata maganin kafin yace "Yaya jikin naki...?" Da k'yar ta amsa masa murya a ciki... AT ya tsareta da idanu kafin yace " Kirjin fah suna maki ciwo...?" Gabanta ya yanke ya fad'i, toh ya akayi ya sani.. Bata sami zarafin amsa masa ba sai sadda kanta k'asa da tayi cikeda kunya... Ya d'an gyara zama kafin yace "Zo na gani sai na maki prescribing magani...." Maryama ta d'ago ta dubesa a razane, nan taga da gaske yake maganar bada wasa ba... Ta d'an sunkuyar da kanta cikeda kunyarsa kaman k'asa ta tsage ta shige ciki, murya can k'asa tace "Na warke...." kana jin yanda tayi maganar zaka fahimci a birkice take... AT ya kuma d'aure fuska tamau kafin yace "The earlier the better, gwara a duba tun yanzu asan wani irin ciwo ke damun ki ko kina so akai peak d'in da za'ace sai an yankesu gaba d'aya...." yanda yayi maganar sam babu alamun wasa a tattare dashi.. Maryama kuwa tsoro ya cikata, hawaye suka ciko idanunta, cikin rawar murya take fad'in "Uncle mutuwa zanyi koh...." Ganin yanda ta tsorata sosai abun yaso bawa AT dariya amma ya gimtse ya jawota cikin jikinsa murya can k'asa yace "BABY bazaki mutu ba shiyasa zan duba ki yanzu..." Maryama ta rintse idanunta tana jin yanda AT ya yaye hijabin data rufa yana k'ok'arin rabata da suturan dake jikinta, k'irjinta sai lugude yake, ita sam bata ko kula da sabon sunan da AT ya kirata dashi ba... A hankali ya mik'e ya lek'a Hajiya yaga tayi nisa a bacci, ya saki labulen a hankali had'i da jawo k'ofa, har lokacin idanun Maryama suna nan a runtse, bata san me likitan nata keyi ba sai hanneyensa data jiyo cikin jikinta..... ********** Shema'u kaman wacce aka bugama guduma haka taji k'irjijta ya buga sanda ta kuma duban agogon bangon dake mak'ale a d'akin ya nuna k'arfe goma saura, ta shiga zagaye d'akin cikin tsananin tashin hankali tana tunanin kardai AT wajen Maryama ya tafi... Tamkar wata zararriya, cikin sauri ta rarumo wayarta ta shiga neman layin Hisham.. Hisham yana d'agawa ya soma fad'in "Da fatan labari mai dad'i zaki sanar dani, don wllhi sati biyun da na d'ibar maki suka cika baki mallaka min takardun asibitin nan ba wllhi wllhi zan k'ona asibitin harma da majiyantan dake ciki sannan na d'aura blame d'in akan Tahir kinsan dole kowa ya yarda muddin akaji zancen daga bakina ya fito, kinga finally zan mallaki abinda na jima ina buk'ata shi kuma he'll rot in jail domin babu mai yarda dashi, mutum d'aya ne dama zai kawo min cikas, that counterfeit Ashfaq toh shima I got rid of him kinga cikan burina bazaimin wahala ba a yanzu, so idan kinason Attahiru bakiso ya tafi jail ki dank'a min takardun nan In two weeks time..." Shema'u ta shiga muzurai tana zare idanu take fad'in "No, no no Hisham bazaka min haka ba, AT bazai tafi jail ba he's my whole life, wllhi wllhi bazan tab'a k'yaleka kayi abu makamancin haka ba, kasanno kasan halina akan AT zan iya yin komai....." Dariya Hisham ya fashe dashi kafin yace "Nasanki farin sani ma kuwa, you're smart but such an idiot, har yau bakisan me nake shirya maki ba, amma duk ranar da kikace zaki takala fad'a dani rannan ne zaki san ko wanene Hisham, na baki sati biyu idan baki cika min alk'awarina ba I won't think twice....." Daga haka katse wayar yayi yana wata irin kafiran dariya.... Shema'u tamkar tab'ebb'iya haka ta shiga cisge gashin kanta tana wani irin k'ara tana buge-buge tana wargaza kayan d'akin... ******* Wani irin yanayi ne ya ziyarce su su duka biyun, tunowa da kalaman Sajida ya sata saurin ture AT daga jikinta tana mai ci gaba da hawaye... Ya d'ago idanunsa a galabaice kafin yace "Baby mammography nake maki just calm down babu abinda zan maki kinji..." Baki a ture tace "Nidai ciwo suke min kuma ni bacci zanyi...." AT ya kuma jawota ya d'aura saman laps d'insa kafin yace "Kar ki damu saura kad'an, nama gano maganin da zan baki, yanzu fad'a min yaushe zaki fara sallah domin sai kin fara sallah kisha maganin I mean sai an gama period ake shan maganin daga nan bazai kuma maki ciwo ba..." Jim ta d'anyi kaman mai tunani don tsoro take ji sosai kar ace za'a yanke mata breasts d'inta, cikin sanyin murya tace "Saura kwana 4..." AT ya murmusa kafin yace "Allah Ya kaimu, da zaran na baki maganin kin daina ciwon kinji koh..." "Da gaske Uncle..? " ta fad'i tana duban sa, gyad'a mata kai yayi kafin yace "Amma zaki bari mu k'arasa mammography d'in sabida na tabbatar da maganin..." Jiki a sanyaye ta runtse idanunta tana jin sanda ya kwanto da ita saman k'irjinsa.... Murmushi AT yayi yarintar ta yana kashe sa, banda yarinta yaushe zata wani biyesa wai mammography yake mata, iyakaci yasan aurene zai sawwak'a mata ciwon da take fama dashi lokacin al'ada..... Lumshe idanunsa yayi yaci gaba da koya mata salon soyayyar sa. ********* A tamanin su Sajida suka shigo d'akin suka tarar Shema'u tayi kaca-kaca da komai, Jamal da Ni'ima tsoro ya cika su, domin Jamal kanma bacci yake ya jiyo k'aran fashe-fashe ya fito a razane, waje guda suka tak'ure shida Ni'ima yayinda Sajida ta nufi wajen Shema'u dake durk'ushe tana kuka, ta dafata a d'an tsorace kafin tace "Aunty lafiya, meke faruwa, meke damunki...." Shema'u tayi saurin rungume Sajida tana mai ci gaba da kuka take fad'in "Sweetheart I'm scared, I'm so scared banaso ta rabamu, zata rabani da Daddynk ku, kinga time gashi har yanzu bai dawo ba, nasan wajenta ya tafi, Sajee ki kiramin Daddyn ku pls kinji sweetheart...." Yanda take maganan kaman wata tab'ebb'iya, cikin sauri Sajida ta rik'eta sosai tana girgiza mata kai take fad'in "Aunty haka bazai tab'a kasancewa ba, bazamu tab'a rabuwa ba, nayi yanda kikace and Maryama nasan zatayi abinda na umarceta pls ki kwantar da hankalin ki..." Shema'u taci gaba da k'walalo idanu tana girgiza kai take fad'in "Sajee pls just call him, I'm scared I'm so scared..." Sajida da tuni hawaye sun soma ciko idanunta ta shiga girgiza kai tana fad'in "Aunty you're scaring us too, pls ki daina kuka.... Ai kafin Sajida ta rufe baki Ni'ima ta soma kuka tana fad'in "Aunty pls kar ki mutu kema kar ki zamo monster kaman yanda Mummy da Maama Juu suka zama, pls Aunty kar ki mutu kinji...." Kallon mamaki Sajida tabi Ni'ima dashi tana nanata abinda ta fad'i a zuciyarta... Ganin Sajida tayima Ni'ima k'uri yasa Shema'u saurin k'arasawa ta rungume Ni'ima tana mai ci gaba da kuka da iya k'arfinta.. Saurin jawo wayar Shema'u Sajida tayi kafin ta shiga dialing layin AT... Daga shi har Maryama saida suka razana da kiran... Ta cikin wayar yake jiyo sautin kukan Shema'u da Ni'ima ga Sajida tana masa magana a birkice... Cikin sauri yace da ita gashi nan zuwa... Ya dubi Maryama da tayi tsaye tuk'wik'une da hijabinta tana dubansa, itama d'in hawaye ta soma murya na rawa take tambayar sa lafiya.. Don gaba d'aya mutuwar Ummin ta ne ya dawo mata sabo.. Kafad'unta ya dafa ya zaunar da ita saman sofa kafin ya shiga calming nata, yana sanar da ita babu komai insha Allah zaije yanzu ya duba su..... saida ya tabbata ta sami nutsuwa ya rakata har k'ofan d'akin Hajiya kafin ya mata sallama harda manna mata kiss a kumatun ta na hagu bayan ya saci idanunta... Tausayin su daga ita har Uncle ya dabaibaye mata zuciya, wani sabon k'aunarsa takeji na ratsa zuciyarta idan ta tuna yanayin da suka kasance ciki, lokaci guda kuma kunyar sa sai ya dabaibayeta... Lumshe idanu tayi kafin a hankali ta furta "Allah Ya tsareka da iyalanka Uncle..." ********** Sajida tana ganin mahaifin nata ya shigo ta janye 'yan k'anneta suka rab'a ta gefensa kafin tace "Daddy is Aunty Shemah, she's not well..." kaman mai rad'a haka tayi maganar... AT ya jinjina mata kai yana duban Shema'u da tayi durk'ushe a wajen tana kuka, ga d'akin ta wargaje shi gaba d'aya.... *Saminah Aliyu Mrs💖* [8:55PM, 4/5/2018] ‪+234 806 652 0501‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *45* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ _Maryam T Baliya_ _Zee Virus_ _Anty Hajir Minjibir_ _Hafsat winner_ _Surayya_ _Maman Safiyya_ _Wannan shafi tukwici ne a gareku, na gode da nuna k'auna da kulawa ❤🤝_ A hankali ya tako yana bin d'akin da kallo kafin ya kamota ya d'agota, suna had'a idanu ta kuma fashewa da wani kukan had'i da shigewa cikin jikin sa, jiki a sanyaye AT ya rungumeta cikin jikinsa.. Cikin muryar kuka Shema'u take fad'in "Tahir kar ka rabu dani pls, ko me zai faru kamin alk'awarin bazaka rabu dani ba.... Tahir ina sonka ina son yaranka don Allah kar ka rabu damu kaji pls my AT....." ta kasa ci gaba da maganar sabida kuka da yaci k'arfinta... AT ya masu masauk'i saman armchair dake gefe kafin ya d'ago fuskar ta yana dubanta kana yace "Shema'u meyasaki fad'in all those things, bazan tab'a rabuwa daku ba daga ke har yarana, we are family akwai strong bond a tsakanin mu bazai yuwu na rabu daku ba...." Shema'u ta kuma dafe face d'insa tanai masa wani irin kallo lokaci guda tana tunowa da Hisham kafin ta soma girgiza kai tana fad'in "My AT mafarki nayi wai Maryama zata rabamu gaba d'aya, pls kar ka bari ta rabamu kaji pls pls...." D'an murmushi AT yayi kafin ya kwantar da kanta cikin k'irjinsa murya a taushashe ya soma fad'in "Maryama ba haka take ba Shema'u, mafarki ne kawai ba gaskiya ba kinji koh, ki kwantar da hankalinki, ni Tahir bazan tab'a rabuwa daku ba....." Shema'u dai ta jisa ne kawai amma kalaman Hisham ba k'aramin d'aga mata hankali sukayi ba, idan ya k'ona asibitin AT ya d'aura masa blame ta rasa AT har abada, idan ta bata kai masa takardun ba zai iya fallasa ta wajen AT.... Take wani tunani ya fad'o mata... Ai Hisham bashida wani prove da zai tabbatar ita ta kashe Aysha don haka babu mai yarda dashi sabida abune da sam hankali bazai kama ba, saidai ma AT ya masa wani zargin daban.... Da wannan tunani ta samu hankalinta ya d'an kwanta dukda sam bata sami nutsuwa ba.. Shema'u na kwance cikin jikin AT ya kasa bacci shi kad'ai sai murmusawa yake yana tuno moment d'in da suka kasance shida Maryama, abubuwa da dama suka cika masa zuciya, shi kad'ai sai nishad'i yake ji.... A b'angaren Shema'u kuwa zuciyarta turnuk'e take da bak'in ciki, ita kad'ai sai k'ulle-k'ullen da neman hanyar b'ullowa ma rayuwarta take.... Ita ko Maryama yanda ya kasance da AT hakan ne ta kasance a gareta, data lumshe idanu kyakkyawar fuskar mijinta take gani, ita kad'ai sai faman murmushi take tana tuno lokutan da suka kasance ciki, lokaci guda sai ta saka tafukan hannunta ta rufe idanunta... Kuma wani ikon Allah ta nemi ciwon da take ji ta rasa.... Kewar mijinta ya cika mata zuciya, _Shin SHAK'UWA CE ko kuwa SOYAYYA CE tsakanin su da Uncle_ tambayan da ya haifar mata da fad'uwan gaba domin kuwa gani take tausayi da SHAK'UWA su suka saka Uncle aurenta ba soyayya bace... Jikinta yayi sanyi ta janyo pillow a hankali ta shige ciki cikeda tausyin kanta...... ************* Abu kaman wasa Shema'u tana bacci tana ihu, hankalin AT gaba d'aya ya tashi, zaune yayi dirshan saman gado yana mata addu'a Fad'i take "Wayyo kar ku kashe ni, don Allah kar ku kasheni..... Wayooooo....." ihun da tayi na k'arshe ta mik'e ta had'a gumi gaba d'aya jikinta sai kyarma yake dukda sanyin AC da ya gauraye d'akin. AT ya rik'eta sosai yana fad'i mata tayi addu'a.... Kallonsa tayi lokaci guda kuma ta shiga bin bangon d'akin da kallo kana ta rungume shi tana fad'in "I'm scared Tahir..... I'm so scared..." AT ya rungume ta k'irjinsa na bugawa da sauri da sauri, gaba d'aya ya kasa gane meke faruwa... A wannan dare kusan kwana zaune sukayi da Shema'u, data kwanta zata mik'e tana ihu... Hankalin AT gaba d'aya ya tashi abu kaman wasa yana neman zama babban abu.. Washe gari ya kira Hisham yana sanar dashi.. Hisham yayi wata kafiran murmushi kana yace a ransa _Baki haukace ba ma sai kinga abinda nake shirin maki Shema'u_ A fili kuwa cewa yayi, "Okay ba damuwa zanzo na dubata insha Allah.." AT yayi masa godiya kafin sukyi sallama,. Shema'u tana ganin yanda ko k'ofa bai fita ba yana nan tareda ita, tayi wata kafiran murmushi kafin tace a ranta _Ai kuwa na sami abun fakewa, da wannan zan hanaka zuwa ganin Maryama..._ Lokaci zuwa lokaci AT ke duba agogon hannunsa, yana kallon Shema'u datayi lamo cikin jikinsa, Sajida ta kawo abinci , AT ya soma bata a baki, har lokacin bata daina matsan hawaye ba .... Da ya yunk'ura zai tashi zata kuma cukwikuyesa tana fad'in "Zasu kasheta...." Haka dole ya hak'ura da fita, ga zuciyarsa cike take da son ganin abin k'aunar sa.... Hisham na isowa AT ya rik'o Shema'u suka sauk'o parlorn k'asa... Hisham ya tsareta da idanu yanda tayi wani lamo cikin jikin AT, abin yaso basa dariya ya gimste dariyar sa yana jinjina tamtiranci da shed'anci irin Shema'u, wato ta nan ta b'ullo... AT nama Hisham bayani, yayinda Hisham da Shema'u tuni sunyi nisa da zance ta idanunsu.. Hisham na mata alama da _Bakima fara hauka ba idan hauka kika zab'a muddin baki cika min alk'awarina ba..._ Shema'u ta kuma shigewa jikin AT tana zazzare idanu take fad'in "My AT waye wannan..." Hisham yace a ransa _your Ally don uwarki._ AT ya dubi Hisham yace "kaga irin abinda take tun jiya..." "Toh banda abinka AT cewa kayi mafarki tayi shiyasa take hakan, ai ni a gani na Malamai masu ruk'uya zaka d'auko mata ba likita ba, tunda ba wani had'ari tayi ba ko wani tashin hankali na musamman ne ya haifar mata da hakan.." Jakar uba! Gaban Shema'u ya yanke ya fad'i, lallai Hisham ya cika d'an bariki wato so yake a kira malami idan ma Malam duba ne su gano cewa ita ta kashe Aysha ko zuba mata wani abin tayita fad'e-fad'en duk muggan abubuwan da tayi... Cikin sauri ta soma fad'in "My AT had'arin da mukayi da Aysha shi yake dawo min sabo wayyo 'yar uwata..." ta k'arashe tana shigewa cikin jikinsa.. AT ya dubi Hisham yace "Kaji koh, ka tuna babban ditch d'in da motar tasu ta hantsila ciki, pls Hisham do something.." Hisham ya d'an ware hannayen sa kafin yace "Zan shiga TH dama yau, idan yaso sai na ganta a can...." wayar da akayima AT ne yayi interrupting nasu, ya k'wace jikinsa da k'ayar daga jikin Shema'u kafin ya matsa yana amsa wayar... Yana ficewa Hisham yayi saurin matsowa jikin kunnen Shema'u kafin yace "Kinyi haukan a daidai, kisan yanda za'ayi ki zak'ulo min important documents d'insa, tunda ke mahaukaciya ce ko kin salwantar dasu bazai damu ba..." Hannu tasa ta cakumo rigarsa kafin tace "Kasan abinda zaka ce masa, just tell him idan bai saki Maryama ba bazan warke ba, kaga daga nan burin kowa zai cika..." tayi saurin sakesa ya koma mazaunin sa sakamakon jiyo tafiyan AT da sukayi.... ********* Huci kawai Haidar keyi yana kallon mahaifin nasa, baiso ya sanar dashi yasan sirrinsa domin shima zai iya kashe sa tunda ya kashe Nabila, sam babu Allah a al'amarin Daddy sai duniya... Cikin tsan-tsan b'acin rai Daddy yaci gaba da fad'in "Na maka sutura, na baka ilimi na inganta maka rayuwa amma ka rasa me zaka saka min dashi sai rashin godiya..." Haidar da jijiyoyin wuyansa sukayi rud'u-rud'u, ya d'ago yana watsa ma VP mugun kallo kafin yaci gaba da fad'in "Da ace zan iya biyanka duk abubuwan daka lissafo ka yimin da na biyaka, kayita kulle ni nasan bazan dawwama a nan for good ba, abinda kake so nayi ne dai bazanyi ba, wllhi wllhi bazan auri Fairuzah ba, Maryama nake so kuma ita kad'ai nake da burin aur...." Bai kai aya ba VP ya d'aukesa da mari, nunasa da d'an yatsa yake kafin yace, nan da sati biyu zan Aura maka Fairuzah ko kanaso ko baka so..." Daga haka ya buge babbar rigar sa ya fice... PA d'insa yayi saurin mik'a masa waya kana yace "Sir Alh Aminu ne mai neman takaran Senator d'in nan...." VP ya amsa wayar yana wata murmushi kana suka soma magana da Alh Aminu, wanda akasarin maganar akan confidential meeting d'in da zasu gudanar ne a garin Kano domin basuso suyishi a Abuja basu so mai girma president ya sani domin so suke su bar tafiyan sa tunda sunga shi mai girma president akwai Allah a Al'amransa.... ********* Gaba d'aya yau yinin haka tayisa sukuku, har Hajiya saida taso d'agota, samun kanta tayi da son ganin Uncle. Har wajejen k'arfe goma na dare batayi bacci ba tana nan kwance tana kallon talabijin idan taji k'aran tab'a gate d'in mak'ota sai ta zata shine yazo... K'arshe dai har ta cire ranta akan bazai zo ba, ta mik'e ta kashe fitilan parlorn kenan taji hannunsa a jikinta ya rungumota ta baya dashike dama switch d'in wutan a bakin k'ofa yake... K'amshin turaren sa ya cika mata hanci... Toh wai yaya akayi ya shigo gidan bata kula ba... Lumshe idanunsa yayi had'i da kwantar da kansa saman kafad'anta, cikin wata irin kasaltacciyar murya yake fad'in "I'm sorry Baby nasan kinyita jirana ko,." Bata sami zarafin amsa shi ba sabida taji salon da ya soma mata... D'an ture shi tayi kad'an kafin tace "Ni dai ba jiranka nake ba kallo na gama yi..." yanda tayi maganar cikeda shagwab'a ya birgesa. Kuma matseta yayi kafin yace "Okay na yarda, Hajiya tayi bacci ne..." Kai ya gyad'a masa alamun eh.. Ya jinjina kai kafin ya d'aura da kinsha maganin...?" Nan ma Kai ta gyad'a masa alamun eh.. "Toh zo na duba jikin naki..." ya k'arashe yana masu masauk'i saman sofa.. Kukan shagwab'a ta soma masa jin abinda yake shirin yi kafin tace "Nifa na warke Uncle..." baki a ture tayi maganar.. AT ya waro idanu waje kafin yace "You mean kin fara sallah zan iya baki maganin..." Ta girgiza masa kai alamun a'a. Saida ya sauk'e wata ajiyan zuciya kafin yace "Okay yau magana nake so muyi, ina so ki bani hankalin ki sosai..." Ta d'an kallesa cikeda fad'uwan gaba sabida he sounds serious *Saminah Aliyu Mrs💖* [8:56PM, 4/5/2018] ‪+234 806 652 0501‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *46* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ Hannayenta AT ya kamo suka jima suna kallon juna, murmushi saman fuskar sa ya soma fad'in "SHAK'UWA CE.... SHAK'UWA CE ta haifar da soyayya a tsakaninmu Maryam, I can't deny it anymore, I must confess it to your face... that, that I love you...." kallon cikin idanun juna suke sanda AT yaci gaba da fad'in "Maryam ina sonki, ina sonki da duka zuciyata, Na sani koda ace Aysha tana nan I'll still feel the same, tun ranar da na d'auke ki a hannu na soyayyarki ta shiga zuciyata..... And kema nasan you love me, kina sona.... Right?" ya k'arashe maganar yana dad's damk'e 'yan yatsun hannunta had'i da matso da fuskar sa dab da nata.... Bata iya amsa masa ba sai sunkuyar da nata kan k'asa da tayi..... AT ya kamo fuskar ta ya d'ago yana dubanta kafin yace "I love you..... I love you Maryam kinji..." daga haka rungumeta yayi tsam cikin jikinsa.... Hawaye suka shiga kwararo mata sanda ta tuna Sajida, nan tayi lamo cikin jikin AT...." D'umin hawayen ta yaji na sauk'a cikin jikinsa yayi saurin d'agota yana dubanta, jikinsa yayi sanyi don gani yake kalaman da yayi su suka sakata kuka.... Murya can k'asa yace "Baby did I say anything that hurt you..?" Baki sona koh, Ashfaq kike so koh, na maki tsufa koh....?" Yanda yayi maganar sai ya kuma bata tausayi, cikin sauri ta shiga girgiza kai tana goge hawayen ta kafin tace "Ba haka bane Uncle, ina sonka ina sonka nima, hasalima nayi zaton SHAK'UWA CE a tsakanin mu ashe soyayya ce, sabida bansan kana sona ba....." muryarta ya sark'e ta kasa ci gaba da magana....." AT ya tsareta da idanu yana kallon bakinta yanda yake furta kalaman tana son sa..... Muryarta yaci gaba da jiyowa cikin rawar murya wanda yafi kama da na mai kuka tana fad'in "I don't know, but you and can't be together..... I'm sorry bazan iya zame maka macen da kake so ba sanyin idaniya.... I'm sorry..." Murmushi AT yayi had'i da d'an girgiza kai kafin ya kuma kamo hannayen ta yace "Maryam kalle ni...." Watery eyes d'inta ta d'ago tana dubansa, su duka biyu tsan-tsan soyayyan juna suke hangowa cikin idanun su, murmushi ya sakar mata kafin ya soma fad'in "Nasan abinda kike tunani, nasan abinda ya saka ki fad'in haka, kina tunanin abinda mutane zasu ce musamman Sajida koh... But Maryam its not our fault that we fell in love with each other, sannan ba haramun bane, hasalima Allah ne ya k'addara hakan.... Maryam we can't escape our destiny, if Allah destined us to be together, no one can separate us.... Mutane ya kamata su gane this can happen, zai iya faruwa da kowa, ba ko wacce budurwa ce Allah zai saka mata soyayyan saurayi d'an uwanta ba wata Allah sai ya jarabceta da soyayya sa'an mahaifinta sannan shima magidanci Allah yakan jarabce sa da soyayyar sa'an 'yar cikin sa.... A koda yaushe mutum ya kasance fata na alkhairi yake ma rayuwar sa... Come here." ya k'arashe yana bud'e mata hannaye.... A hankali ta shige cikin jikinsa tayi lamo... AT yaci gaba da fad'in "Maryam you don't have worry about Sajida, domin ta fahimci komai, Shema'u ta fahimtar da ita komai...." Gaban Maryama ya yanke ya fad'i jin AT ya ambato Shema'u, itakam tanada bad feelings gameda Shema'u... Bata ce komai ba sai lumshe idanunta da tayi, AT yaci gaba da magana har ya sanar da ita rashin lafiyan Shema'u, wajajen k'arfe goma da rabi ya bar gidan kaman kar su rabu da juna domin yau wani sabon tattali da soyayya yake nuna mata.... Washe gari Maryama ta sanar da Hajiya rashin lafiyan Shema'u, tab'e baki Hajiya tayi kafin tace "Allah bata lafiya" a tak'aice.... Babu yanda Maryama batayi ba Hajiya ta bari taje ta gaida Aunty Shema'u Hajiya fir ta hana, ta d'ago tana dubanta kafin tace "Yo sai na barki ki tafi wajen matar da da hankalinta ma yaushe ta barki balle babu hankali wannan ai sai turu ni nasan asirin da aukama Attahiru shine Allah Ya soma maida masu kansu, ahab nasan addu'o'i na bazasu tashi a banza ba... Kad'anma ta gani, wannan daujejjen fuskar nata sai ya zamo bak'ik'irin sannan ta gane...." Maryama ta d'an turo baki kafin tace "Haba Hajiya kiyimata addu'an samun sauk'i mana..." Hajiya ta dubeta a kaikaice kafin tace "Yo nayi ai, daga nan sai turu..." Daga haka ta d'au aswakin ta tana gogawa..." Maryama ta dubeta kawai tana murmushi.. ********* Shema'u fah mafarkin ihu ya zame mata jiki k'arshe dole AT yayi waya Jalingo Momma ta taho... Ga Hisham ya bud'e mata wuta, gaba d'aya ta rasa wanne zatayi, ita kad'ai zakaji tana sunbatu idan ta tuna Hisham her Ally is capable of betraying her.... AT kuwa kullum yana mak'ale gidan Hajiya suna shan soyayyar su shida amaryar sa, musamman yanzu da Momma tazo ya sami sauk'i da manne masa da Shema'u keyi.. Hajiya tun tana kauda idanu har ta fara korarsa da gaske, wani sa'in ma ko asibitin bai tafiya zama yake har Hajiya ta tafi islamiyya kafin ya baje kolin sa... Yau kafin su rabu tana kwance cikin jikinsa yake rad'a mata "Ki shirya gobe zan baki maganin ki don naga tun last three days kika fara sallah.." Ta d'ago idanu ta d'an dubesa had'i da turo baki kafin tace " Uncle nifah banson magani mai d'aci pls.." AT ya dad'a matseta kafin yace "Ba nace ki ringa imagining sweet kike sha ba, kar ki damu I promise you maganin babu d'aci kinji koh..." Gyad'a masa kai tayi kafin ya sakar mata murmushi had'i da manna mata peck a gefen bakin ta... Tayi saurin rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta... *********** Neman duniya tayi ta rasa yanda zata sami takardun asibitin AT, duk wani safe datasan yana ajiye important documents d'insa ta duba bata samu ba, gashi tasan baya kaisu bank domin ya tab'a sanar da ita... Gaba d'aya hankalinta ya tashi wa'adin da Hisham ya d'ibar mata sun cika... ********** Mummy ta kuma duban Haidar da ya shirya tsaf cikin sky blue shadda kansa babu hula kafin tace "Son abin ya bani mamaki ganin kai da Daddyn ka kun shirya lokaci guda har zakuyi tafiya tare..." Haidar ya k'arashe brushing sumar sa kumatunsa d'auke da murmushi domin yau zai tafi Kano zai gano Maryamar sa, juyowa yayi yana duban Mummy kana ya dafa kafad'unta yace "Mummy naji shawarwarinki insha Allah I'll fix everything kinji I promise you...." ya k'arashe yana d'an fito da idanunsa waje.. Murmushi tayi ta mik'a hannu ta shafi kumatun sa lokaci guda ta tuno mahaifyar sa da d'iyarta Nabila wanda suka mace shekarun baya kafin tace "Allah maka albarka Haidar, Allah maka albarka....." Hannu yasa yana d'an goge mata hawayen dake neman fitowa kafin yace "Ameen Mummy na...." rage tsayin sa yayi ya d'an bata light hug kafin yace "You take care okay, ki sha maganin ki pls kinji Mummy nah..." Gyad'a masa kai tayi kafin tace "Insha Allah zan sha Son, I promise you Dr..." Murmushi ya kuma yi sanda suka jiyo tawagar mahaifinsa sun fito.... Mummy ta bisa da kallo kaman mai masa kallon k'arshe, ta tuna kallon k'arshe da tayima Nabila... Da gudu ta k'arasa window tana gani Daddy da Haidar suka shige wargajejiyar jeep d'in, da shike tafiyar ta sirri ce, babu tawagar motoci, mota d'aya tak suka fita da ita.... Haidar yayima Daddy k'uri yana murmushi cikin ransa, domin yasan hakan da yayi shine daidai, amince masa da auren Fairuzah da yayi shi zaisa ya sami kusanci dashi har Allah Ya tainake shi ya karya sa kab'as, domin idan baiyi kusa dashi ba bazai tab'a iya ganin bayansa ba tunda yanada mulki da dukiya... *********** Jinsa wani iri yake gaba d'aya, kaman kullum saida ya tsaya yayi masu sayyan kayan mak'ulashe dangin su fresh milk kafin ya nufi gidan Hajiya.... Maryama na zaune tana kallo Hajiya ta tafi islamiya... tayi kyau cikin doguwar riga na atampa d'inkin ya zauna a jikinta, lokaci zuwa lokaci gabanta ke fad'uwa ba tareda tasan dalili ba, jiyo sallaman sa da tayi yasata mik'ewa zunbur ta zauna. Shid'inma ya jima yana binta da kallo daga bakin k'ofa kafin ya soma takowa, ta masa kyau sosai yau d'in, shi har wani girma yaga ta k'ara masa... Bai iya cewa komai ba sai rungumeta da yayi cikin jikin sa... Sun jima a haka kafin ya masu masauk'i saman kujera, dab'as ya d'aurata saman cinyoyin sa... Da k'yar ta iya gaidashi ganin irin kallon da yake binta dashi, ya amsa yana kwaikwayon muryar ta. Gaba d'aya sukayi dariya... Fuskar ta Ya dafe da duka hannayen sa biyu kafin yace "Baby kinyi kyau da yawa..." Ta d'an turo baki tace "Ai ka fini kyau, kaifa fari ne ni kuma bak'a ce..." Murmushi ya kuma yi kafin ya lakaci hancinta yace "Inji waye, ai bak'i yafi tsan-tsan kyau na fad'aki, fari na saurin attracting mutane ne, but real beauty is black... I love you..." Kallonsa take yanda yake maganar abin burgewa kafin ta kwantar da kanta saman k'irjin sa.... Ledar da ya shigo dashi ya soma bud'ewa, duk a tunaninta magani ne, har ta soma ya mutsa fuska, nan taga shirgin kayan k'walama ne ga tarin na jiya a fridge gashi yauma ya kuma taro wasu... Da kansa ya shiga bata a baki, tun tana nok'ewa har ta Saki jikinta, shiru-shiru bata ga an fito da magani ba.. Dubansa tayi da mamaki kafin tace "Uncle ina maganin...?" AT ya kamo kunkuminta suna fuskantar juna kafin yace "Zan baki kafin na tafi, promise Me bazakiyi kuka ba Baby, kinji pls..." Abin har yaso bata dariya ganin ma ita za'a bada magani amma shine mai marairaicewa. A hankali ta gyad'a masa kai kana tace "Bazan yi ba Uncle..." Murmushi yayi kafin ya d'an ja kumatun ta yace "Ai dai kinsan ni mijin ki ne koh, sannan kinsan hakkin miji akan matar sa da kuma hakkin mata akan miji koh, anyi maku a islamiya koh..." Gabanta ya yanke ya fad'i da jin wani sabon zance da Uncle d'in nata yazo mata dashi.. Ganin tayi jigum yasa AT yin murmushi kafin yace "Don't panic it's nothing kinji koh, tashi muje muyi sallah I'll teach you everything..." Bai jira cewarta ba ya sunkuce ta suka shige d'akin bak'i mai kallon na Hajiya... Jikinta duk yayi sanyi dama jiya kafin ya tafi saida ya sata ta gyara masa d'akin, wllhi itakam bata kawo komai ba, sai yanzu take recalling abubuwan, sai yanzu ta gane maganin da Uncle yake nufi, Innalilhai itakam batasan yaya hakan zata soma kasancewa tsakanin su ba, tasan tana son sa kuma tana tausayin sa but ina alk'awarin su da Sajida.... Bata k'arasa tunanin nata ba taji hannun AT a goshinta yana karanto mata addu'o'i... Saida ya mata nasiha mai ratsa zuciya wanda har saida ya sakata zuban hawaye... AT ya jawota cikin jikinsa yana lallashi, daga nan zance ya soma canzawa.. So take ta hanasa abinda yayi niyya ta kasa, so take ta dakatar dashi bazata iya ba, shin idan ta k'yale Uncle ya ida nufin sa ina matsayin alk'awarin da tayima Sajida... Wata zuciya tace toh idan kika yini kika kwana cikin tsinuwar Allah da Mala'ikun sa fah? Maryama ta rinste idanunta hawaye na gangaro mata... A hankali yake rad'a mata "I'll be gentle..." Tsam ya matseta cikin jikinsa yana lallashinta don yasan tayi namijin k'ok'ari, abubuwa da dama suka ziyarci zuciyar AT, tabbas yau ya bud'e amanar sa da kansa, sannan ya tuna da matarsa Aysha, ya sami nutsuwar da ya rasa tun bayan mutuwar ta... Albarka yaci gaba da saka mata ita kuwa ta kasa yin shiru sai kuka take, jikinsa yayi sanyi gaba d'aya gani yake bai kyauta ba, gani yake she's still young, gani yake ya sab'a alk'awarin da ya d'aukar ma kansa... Shi gaba d'aya gani yake ya ji mata ciwo ne ma.... Tak'i daina kuka tak'i d'ago fuska su had'a idanu... AT ya marairaice murya yana mai ci gaba da bata hak'uri... Ita kuwa Maryama sam ba abinda ya sata kuka sosai kenan ba, karya alk'awarin Sajida da tayi shi ya sata kuka babu ko k'akk'autawa, laifin kanta take gani, tana tsananin son Uncle bazata iya hanasa kanta ba, gashi hakan ya jawo ta karya alk'awarin 'yar uwanta, shikenan tasan har abada Sajida bazata tab'a yafe mata ba... Yana nan rik'e da ita yana aikin lallashi suka jiyo Hajiya ta tasaya daga gate suna magana da Ilu da alama tambayar sa take ko Attahiru ya zo gidan ne... Gaba d'ayansu saida k'irjinsu ya buga, ai sai yanzu suka tuna a yanda suke, ashe gidan Hajiya ne..." Maryama ta kuma fashe masa da wani sabon kuka, shikenan itkam, ta mutu ta lalace, shikenan Hajiya zatace ta zama 'yar iska wayyo Allahn ta, Uncle ya shammace ta..... Cikin sauri ya gama zura rigarsa shi sam bai kawo Hajiya zata dawo yanzu ba... Duban Maryama dake duk'unk'une cikin bedcover kafin ya sassauta murya yace "Baby let me take you to bathroom, kiyi hak'uri kinji Hajiya won't find out.." Mak'e masa kafad'a tayi tana mai ci gaba da kuka.. Sai faman share zufan goshinsa yake bazaiso Hajiya ta shigo ta gansu a wannan yanayin ba, cikin sauri ya nufo k'ofa jin muryar ta parlour sai bin parlorn da kallo take, ga d'ankwalin Maryama saman kujera yanda suka gama ciye-ciyen su... Turus suka kusa cin karo shida Hajiya a bakin k'ofa.... Ya kasa bata hanya ta shige ya kasa ficewa... Kallo ta bisa dashi shek'ek'e kafin ta had'e giran sama da k'asa tace "Meye haka kai kuma inyi, sai faman muzurai kake uwa kayima sarki k'arya, bani hanya na wuce ni... Waima ina Maryama ko bataji na dawo bane..." AT yasa hannu ya goge zufan goshin sa kafin yace "Ki k'arasa d'akinki Hajiya, dama dama tana.... tana kitchen...." Yanda yake maganar sarai zaka fahimci bashida gaskiya.. Gyara tsayuwarta Hajiya tayi don gaba d'aya bata yarda dashi ba kafin tace "Kai bafa na son sakarci, matsa min na shige nace, yo gidana ne ko ina naga daman shiga zan shiga ko iyaka zaka min..." AT ya soma girgiza kai yana shafa k'eya ko zarafin magana bai samu ba ya kuma jiyo muryar Hajiya tana fad'in "Matsa min nace ban yarda da wannan sunne kan naka ba..." Jiki a sanyaye ya matsa ta nufi d'akin tana ci gaba da sababi..... AT kuwa tuni ya suri car keys d'insa ya fice... Turus Hajiya taja tayi birki ganin Maryama kwance cikin gado baka jin sautin kukan ta sai hawaye.... *Saminah Aliyu Mrs💖* [8:56PM, 4/5/2018] ‪+234 806 652 0501‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *47* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINIWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ Tafe hannaye Hajiya ta shiga yi tana sallallami.... "Eh lallai mana, haba ai biri yayi kama da mutum, ni tunda naga wannan kame-kamen da yake yi nasan za'a rina..." ta kuma duban Maryama da har lokacin sharan hawaye take kafin ta yab'e baki tace "Toh ke kuma hindiya sarkin kuka ke ba 'yar soyayya ba, ai kinga soyayya da idan ina korarsa har haushina kike ji kega Hemamalin sarauniyar soyayya koh, ai kinga soyayya dama shikam ai wayo zai maki.... Zai dawo gidan nan ya same ni ne..." ta k'arashe tana shigewa bathroom don had'a ruwan zafi wa Maryamar ta, zuciyarta ya cika da nishad'i dukda a fili fad'a take..... ************ Yana driving yana tunanin Maryamar sa, a hankali yake sakin murmushi idan ya tuna yau shida Mariam sun zama cikakkun ma'aurata, lokaci guda tausayin ta Ya cika zuciyar sa, inama suna tare shi yake jinyar kayansa, inama suna tare yayita riritata she's indeed a Queen to his heart.... Ya kuma sakin wata murmushi sanda ya tuna kalan yarintar ta... Har ya iso gida tunanin da yake kenan, Shema'u tana cikin d'akinsa ta wargaza sai binciken neman takardun asibiti take don batayi tsammanin yanzu zai dawo ba tunda tasan sai yamma k'arfe hud'u yake dawowa daga office... Sam ko k'aran tsayuwar motar sa bataji ba don gaba d'aya Hisham ya d'aga mata hankali... Tana cikin bincike drawer tajiyo muryarsa a bakin k'ofa yana amsa waya.... A tamanin ta Saki takardun hannunta tayi saurin warware gashin kanta kaman mai haukan gaskiya... AT yana shigowa yayi karo da ita a bakin k'ofa uwa birin wasan tashe... Wani sabon k'yank'yanin ta yaji ya taso masa haka kurum.. A b'angaren Shema'u kuwa haka kurum taji gabanta ya fad'i domin yanayin datagan sa ciki yayi bala'in firgitata.. Murmushi ta soma masa tana sosa gashin kanta kafin tace "Gyara nake maka my AT, daga ina kake...?" Kai tsaye ya sami kansa da bata amsa "daga gidan Hajiya nake..." Gaban Shema'u ya kuma bugawa, baki sake take dubansa kafin tace "Gidan Hajiya kuma, gidan Hajiya fah, kaida kace ka tafi office kofah karyawa bakayi ba, toh me kaje yi gidan Hajiya..?" Tambayar nata ya basa mamaki, shi take tambaya me yaje yi gidan mahaifiyar sa, bai amsata ba sabida zuciyarsa da yaji yana k'una lokaci guda, zai wuce Shema'u tasha gabansa uwa mahaukaciyar gaske tana fad'in "Wllhi sai ka fad'a min me kaje yi gidan Hajiya, wllhi sai ka fad'a min..." A tunanin sa haukan nata ne ya motsa, d'an matsar da ita gefe yayi kafin yace "Barin yi wanka koh sai nazo na fad'a maki...." "Wanka!!" ta nanata da k'arfi... Kuka ta fashe masa dashi tana fad'in "Wllhi wllhi baka isa ba, wankan me zakayi bayan wanda kayi d'azu, wllhi sai ka fad'a min idan amanata kake ci da wancan shegiyar yarinyar, wllhi bazan yarda ba tunda kaga banida lafiya shine kuke cin amanata kaida uwarka da wancan tsinanniyar yarinyar...." bata kai aya ba taji ya d'auketa da wata mahaukaciyar mari.... Yana huci yana dubanta cikeda mamaki, idan za'a ce masa Shema'u zata fad'i maganganu makamancin haka zai musa, sai gashi akan idanunsa tana fad'i, ko kad'an yak'i ba wa zuciyarsa haukan ne yasata fad'in haka.. Yana huci yake nunata da yatsa kafin yaci gaba da fad'in "Idan kina hauka kar ki kuskura ki kuma sako magaifiyata ciki, sannan Maryama matata ce banci amanarki da ita ba, tun ba yau ba na fad'a maki na sawwak'e maki idan zamana dake zai kasance akwai cutarwa kikak'i amincewa kika ce kinji kin gani zaki zauna dani haka... And yess wankan sunnah zanyi da matata na kwanta Mallaki na ba da karuwa ba don haka ki iya bakin ki... Daga haka ya finciketa ta fad'i k'asa tana kallonsa cikeda mamaki, ruhinta da zuciyarta suna barazanar tarwatsewa... Wani irin ihu ta kurma tana birgima take fad'in "Na shiga uku na mutu na lalace, wllhi AT Allah bazai barka ba, sai ya saka min, watanni na nawa a gidanka da aurenka ka kasa sauk'e min hakki na shine zakaje ka kwanta da k'aramar yarinya 'yar cikin ka wllhi wllhi duk sai kunyi nadama.." AT kam baima san tanayi ba don tuni ya shige cikin cubicle ya sakar ma kansa shower yana tuno abar k'aunarsa da kalan soyayyar su abin birgewa.... A stirs ta had'u da Sajida don ta jiyo ihun Shema'u su Momma da iya kande suna can kitchen d'in waje basu jiyo Shema'u ba, Allah yaso su Jamal da Ni'ima sun tafi school... A razane Sajida ta k'araso don a zaton ta ciwon Shema'u ne ya tashi.... Tun kan ta soma magana Shema'u cikin kuka take fad'in "Sajida Daddyn ku yaci amanata, Sajida AT ya zalunce ni, tunda nake aurensa a gidan nan babu abinda ya tab'a shiga tsakanin mu sabida gani nake kaman idan wani abu ya shiga tsakanin mu naci amanar 'yar uwata Aysha Mummyn ku, shine daga auren wancan k'aramar karuwar har tayi seducing d'insa sun kwanta tare... Wllhi Sajida yanzu mahaifin ku bashida sauran kima a idanun Maryama tunda taga girmansa balle ku yaransa... Wayyo ni Shema'u AT ya gama da ni..." Girgiza kai Sajida keyi cikin rashin yarda da kalaman Shema'u, zuciyarta ya shiga mata zogi, kenan duk plans d'insu sun wargaje, duk iya k'ok'arinta not gani ta raba mahaifinta da Maryama saida suka kasance tare.... Tamkar wacce aka zabura haka ta fice daga gidan hawaye na bin k'uncinta... Shema'u tabi bayanta da kallo had'i da yin wata munafukan murmushi.. Kallo tabi k'ofan d'akin AT dashi kafin ta shige nata d'akin had'i da banko k'ofa, bata damu ba Hisham ya banka ma asibitin wuta idan AT ya tafi Prison Maryama za'a bari da k'uncin rayuwa tana 'yar k'aramarta, sannan yaransa kuma gaba d'aya saita d'aid'aita su... ********* Tana kwance saman doguwar kujera har lokacin hawaye basu daina bin k'uncinta ba, Hajiya ta gama kintsa ta ta koma tana kintsa d'akin suka ji an banko k'ofa an shigo.... Zunbur Maryama ta mik'e ta zauna dukda ciwon da take ji daga k'asanta... Ganin Sajida a wannan yanyi ba k'aramin tsoro ya haifar mata ba... Kan kace me Sajida ta d'auketa da wani wawan mari ta shiga kai mata duka ta ko ina tana fad'in "You hypocrite na tsane ki, na tsane ki Maryama, kin cuce ni.... You should be ashamed of your self, wllhi kinji kunya tunda kika bari abu ya shiga tsakanin ki da mutumin da ya raine ki tamkar d'iya...." Maryama dai bata iya cewa komai ba sai hawaye dake kwarara mata babu k'kk'autawa... Hajiya tayi tsaye bakin k'ofa tana sauraren Sajida.. Zuciyar Hajiya kaman ya fito waje sabida takaici... A fusace Hajiya ta fito parlorn tana huci, daga Maryamar har Sajidan basu ankara ba sai jin k'aran gark'ame k'ofa da Hajiya tayi.... B'allo igiyan jikin decoder Hajiya tayi ta shiga laptar Sajida dashi tamkar wacce aka aiko.... Sajida na ihu Maryama na kuka tana k'ok'arin rik'o wayan Hajiya ta dubeta sanda ta kuma mak'uro hannun Sajida tace da Maryama idan baki matsa min a nan ba wllhi sai na had'a dake..." laptan Sajida Hajiya keyi da iya k'arfinta tana huci take fad'in "Don ubanki ko uban naki bai isa yazo har gidana yayi sakarci na k'yalesa ba, mahaukaciyar k'anwar uwar taki da take koya maki bariki itama tayi kad'an, shashasha kawai maras hankali, Attahiru ya auri Maryama ki had'iyi zuciya kuma wllhi tunda iskancin da kika tsira kenan da k'afata zan kaita har d'akinta, roba robar uwar taki ta kuma kitsa maki wani abin doluwa kawai, tashi, tashi ki fice min a gida....." ta k'arashe tana kuma zuba mata waya a gadon baya... Jikin Sajida rud'u-rud'u abinka da farar fata, tana kuka haka ta finciki k'ofa ta fita a guje mayafi a Hannu... Buzu da bai jima da shigowa unguwar ba don tunda AT ya auri Maryama Buzu ya k'aurace ma zaman unguwar, nan ya hangi wata kaman Sajida ta fice a guje, cikin sauri yabi bayanta... Bagazam-bagazam Sajida ke jefa k'afafunta a kwalta tana kuka tana goge hawayen ta da mayafinta, Buzu yayi parking gefen Kwalta ya biyo bayanta gudu-gudu yana kiranta. "Baby! Miss Beauriful !! Miss Beauriful Pls ki tsaya, Ni ne Haris d'inki ne..." Jin muryar Buzu ya sakata tsayuwa cak still mayafi a hannu tana goge hawaye... Kallo d'aya Buzu y mata zuciyarsa ta yanke ganin kalan tabon da jikin Sajida yayi, gaba d'aya yayi jazir tako ina. Shaye da mamaki yake fad'in "Beauriful wa ya maki haka... Bata iya cewa komai ba sai kukan da ta kuma fashe masa dashi, Kallo yake binta dashi ga mutane masu wucewa jefi-jefi sai kallon su suke, d'an sassauta murya yayi kafin ya soma fad'in "Baby, Beautiful pls ki daina kukan nan oya zo muje, ya janyo hannunta suka shige mota... Hannu yasa ya ringa share mata hawayen ba tareda tayi yunk'urin hanasa ba, tsanan Mahifinta Maryama da Hajiya shi ya taru ya cika zuciyar Sajida, Buzu ya ringa lallashinta yana bata baki yana nuna mata Sam ba'a kyauta mata ba, anci amanar ta... Sajida ta kuma d'alewa dokin fushi, ji take tana dai-dai da kowa cikinsu gaba d'ayansu sai ta shayar dasu mamaki... Buzu yace bari ya kaita gida ta mak'e masa kafad'a tace bazata koma wannan gidan ba, bai tak'urata ba yaja mota suka d'auki wani hanyar a zuciyar sa yake furta _It's payback time Dr AT yanda Mallake min abin k'aunata zan fansa a wajen d'iyarka koda dark'arfi ne...._ ya k'arashe yana sakin wata kafiran murmushi.. ******* Bai wuce asibiti ba sai gidan Hajiya da ya kuma nufowa, don ko Hajiya zata sillesa dole yazo yaga halin da ya bar Maryam a ciki.. A parlor ya sami Hajiya sai faman huci take tana kad'a kai.... Kallo d'aya ta watsa masa ya zube saman carpet... Baki na rawa yake k'ok'arin gaidata don shi duk a zaton sa fushi take dashi sabida abinda ya shiga tsakanin sa da Maryama.... A hasale Hajiya ta dakatar dashi cikin d'aga hannu.. "Yimin shiru nace kafin na sassab'a maka yanzun nan, banda sakarci baki ka bud'e ka fad'a ma d'iyarka abinda ya shiga tsakanin ka da matarka ko me, ko kai ka turota tazo tayima d'iyata cin kashi a nan iyi..?" Gabansa ya yanke ya fad'i bai fahimci me Hajiya ke nufi ba... Girgiza kai ya soma a hankali kafin yace "Hajiya ban fahimci me kike nufi ba..." Ta kuma harzuk'a tace "Ina kuwa zaka fahimta, ka koma tamkar lusari a cikin gidanka ka d'auko tantiriya ka dank'a mata tarbiyan yaranka..." Gaba d'aya abinda Sajida tazo gidan tayi Hajiya ta sanar dashi tana mai cika gaba da bambami ta yanda take shiga bata nan take fita ba... Hankalin AT idan yayi dubu ya tashi, zuciyarsa ta shiga tafarfasa, gashin jikinsa suka mimmik'e idanunsa suka kad'a sukayi jazir cikin sauri ya mik'e ya lek'a d'akin Hajiya nan ya hangi Maryama na kwance uwa marainiya da alama ta gama jiyo maganganun da Hajiya ke fad'a masa, cikin sauri ya saki labulen zuciyarsa na ci gaba da tafarfasa ya nufi motar sa, suna jiyo yanda ya finciki motar ya fice daga gidan... Da k'yar Sajida ta amince Buzu ya maidata gida bayan ya gama lallashin ta, tana shiga gida d'aki ta wuce ta kulle kanta ciki... Hisham ya kuma kallon gallons d'in petur dake gabansa a store d'in magunguna kafin ya danna layin Shema'u yace "Kin tabbata zamu sami kud'ad'en..." Shema'u ta murmusa tana kallon Alh Aminu dake shirin tafiya meeting da VP kafin tace "Kasha kurumin ka my Ally na shirya mu tarwatsa Tahir kuma wllhi sai mun tarwasta sa dashi da iyalansa, kawai ka cika aikin ka ka banka ma asibitin wuta...." Hisham ya fashe da wata kafiran dariya kafin ya katse kiran, shi kad'ai yake fad'in "Shema'u the Devil, tabbas kin shiga tarko na, da zaran kin dank'a mani kud'ad'en nan nikuma zan cin amanarki kafin kici nawa..." ya k'arashe yana mai kuma fashewa da wata dariya, lokaci guda ya tokari galan d'in petur guda ya fad'i k'asa ya shiga zuba tamkar mai.... Kallon ta Alh Aminu yayi kafin yace "Giwan mata kenan, ai ni yanzu bani huld'a da manyan mata irinki sai dai na kaiki ma uban gidana..." Shema'u ta fashe da dariya kafin tace "hakan ma yafi mun..." Kai tsaye wargajejen guest house d'in VP suka nufa.. ******** Ko parking bai gama ba ya shiga gidan yana doka kira ma Shema'u da Sajida, don yasan Shema'u ce ta fad'a ma Sajida abinda ke faruwa... Daga Iya Kande har Momma saida suka fito a bikice, tambayar su yayi ina Shema'u da Sajida.. Murya na rawa Momma tace "Sajida dai tun safe ban ganta ba inaga bata sauk'o k'asa ba tana d'akinta Shema'u kuma tace min ta tafi asibiti....." Bai gama saurarenta ba ya nufi upstairs kaman zai kifa da k'asa.... Tana kwance saman gado tana matsan hawaye taji an tokari k'ofar d'akinta, ta mik'e zunbur tana raba idanu... Bata tab'a ganin mahaifin nata cikin irin wannan yanayi ba. Kifa mata mari ya ringa yi yafi sau abinda yafi ya shiga k'wallo da ita, .... Ihun Sajida dasu Momma suka jiyo yasa suka nufi sama a tamanin.... ****** Gaban Haidar ya yanke ya fad'i ganin harda Shema'u a masu zuwa meeting wajen mahaifin sa, dukda tsaro da suke bama wajen saida yayi yasan yanda ya kutsa ya mak'ale jikin k'ofa don dama tuntuni shi bai yarda da matar ba.. VP yayi murmushi yana dubanta kafin yace "Ni a k'a'idana bana huld'a da macen data haura shekaru sha takwas bayan matata, amma tunda kin matsa kina son kud'in, kije ki nemo min Yarinya 'yar shekara biyar da kuma yaro d'an shekara goma, umarni aka bani idan nazo garin nan nayi amfani dasu burina na mallakan kujeran Shugaban k'asa zai cika, don haka idan zaki iya aikin fine zaki sami kud'ad'enki cash..." Murmushi Shema'u tayi don ba komai ta tuna ba illa Jamal da Ni'ima, saida ta juya idanu kafin tace "An gama Your excellency..." Daga haka aka sa guards suka fice da ita... Haidar na nan mak'ale zufa na keto masa tako ina don baisan arnancin ubansa ya kai har haka ba.... Cikin sauri ya silale jikinsa ya fice daga wajen.... *Saminah Aliyu Mrs💖* [8:57PM, 4/5/2018] ‪+234 806 652 0501‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *48* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ A tsorace Momma ta shiga tsakanin AT da Sajida wacce har shid'ewa take sabida kuka, jikinsa ya kuma yin jazir kan wanda Hajiya ta mata.... Momma na kuka Sajida na kuka... Huci kawai AT yake yana dubanta kafin ya d'ago wayar hannunsa yana nunata dashi yace "Kinji na rantse aure zan maki da duk wanda naga dama sannan ita mai koya maki rashin kunyar zata dawo gidan ta same ni... Useless kawai...." daga haka jifa yayi da bulalar yana mai ci gaba da huci ya fice daga d'akin.... Sajida ta rungume Momma tana kuka lafin tace "Momma Daddy is a big disappointment, wllhi na tsane shi, na tsane...... Saurin toshe mata baki Momma tayi ta jawota suka zauna saman gado tana goge mata hawayen da suke kan fama zubowa daga idanunta, jikin Momma gaba d'aya ya kuma yin sanyi.... Suna nan zaune suka hange AT ya fito ya nufi downstairs cikin tsananin tashin hankali waya manne a kunnen sa yake fad'in "You mean the Hospital's on fire...? Ina Hisham,... Okay pls KB kar ku bari wani abu ya sami patients..... I'll be on my, na gode...." yana katse kiran fire service ya shiga nema.... Momma hankali tashe ta mik'e tana duban Tahir da tuni ya fice cikin tsananin tashin hankali hannayenta dafe a k'irji... Mahaifinta na fita ta jawo wayarta tayi dialing lambar Buzu.... Cikin tsananin kuka take sanar dashi yazo ya d'auketa bazata iya ci gaba da zaman gidansu ba aure Daddyn ta zai mata sabida abinda tayima Maryama... Buzu da bai k'arasa gida ba parking motar sa yayi a daidai garun Hajiya ya fito yana amsa wayar tamkar wanda basira ta b'ace masa...... Hajiya na jikin pampon bayi ma flowers ta jiyo muryar Buzu yana amsa wayar yana ambato sunan Sajida yana lallashinta yana fad'in zaizo ya d'auketa yanzu su tafi yanda babu mai sake ganin su..... Ai Hajiya zani a hannu tayi patali da butan da take shirin alolar azahar, mayafinta dake mak'ale saman igiya ta fincika ta rufa ko sallama batayima Maryama ta fice, Ilu sai magana yake mata inaa bata ko kulasa ba. Tana fita ta hangi motar Buzu na shirin fita daga layin... Hannu bibbiyu Hajiya ta d'aga tana kiran mai adaidaita..... ********** Burinsa ya cimma Shema'u baya fatan ta sato yara a lalata masu rayuwa innocent souls.... Hankalinsa yayi mugun tashi ganin bai cimmata ba dashike a motar take, Haidar ya rasa wanne zaiyi, cikin sauri ya zak'ulo wayarsa ya shiga neman layin Maryama, ga mamakin sa yau sai ya jita a kunne... Ya kira yafi sau biyar ba'a d'aga ba, k'arshe text ya tura mata yana neman taimako, matar AT tana shirin salwantar da rayuwar k'anan yara kuma baisan wasu yara zata kawo ba, ko yaran gari ko kuwa yaran AT.... Dukda Maryama bata fahimci sak'on nasa ba saida gabanta yayi mummunar yankewa, hannunta har na rawa ta soma dialing layin Ashfaq.... *********** AT yana isowa asibiti yaga hayak'i ya turnuk'e ko ina gaba d'aya, mutane wad'anda 'yanuwansu ke cikin asibitin sai kuka suke suna hango AT wasu suka soma bore suna fad'in sam bazasu yarda ba wannan wutar kunnawa akayi ba tashi tayi haka kurum ba,... AT cikin tsananin tashin hankali ya nufi cikin asibitin su KB da sauran Nurses d'in sai turo gadajen marassa Lafiya suke, mutane sun jirkita bana wasa ba, ga wuta dake ci fal-fal... Dai-dai lokacin fire service suka iso aka soma mik'a taimakon gaggawa... Hisham bai zaci abin zai zama haka ba domin gaba d'aya hayak'i ya turnuk'e store d'in sannan wani k'arfe ya kama masa gefen riga yayi yayi ya keta ya kasa, tun yanada sauran k'arfi har yaji babu k'arfi a jikinsa... AT shiga cikin fire service d'in yayi suka dinga k'ok'arin kashe wutan, gaba d'aya idan ka gansa kasan a birkice yake k'arshe dole ya kuma komawa wajen wad'anda had'arin ya shafa yana basu kulawa shida Nurses d'insa.... ********** Dukda ciwon da take ji hakan bai hanata fitowa ta sami Ashfaq a waje ba, dubanta yayi kafin yace "Maryam bamu da time ina muka nufa, ina kike tunanin zamu samu Shema'u....?" Maryama ta ringa recalling abubuwan da sukayita faruwa a rayuwan gidan Uncle kafin ta soma girgiza kai tace "Ya Ashfaq wllhi ta yuwu su Ni'ima zata kai, su zata sayar muguwa ce ta k'arshe,...." ta k'arashe hawaye na nema zubowa daga idanunta... Haidar ya girgiza kai kafin yace "Idan nayi ido hud'u da ya Dr nasan kasheni ne kawai bazaiyi ba, bazan iya zuwa gidan sa ba, sannan ko na fad'a masa ba lallai ya yarda dani ba, kar mu tsaya b'ata lokaci ni yanzu zan tafi nazo da 'yan sanda ke kuma ki tafi can gidan nasa pls ki bi bayansu..." Gyad'a kai Maryama tayi kafin tace "K'warai Aunty Shema'u makira ce ta k'arshe Uncle bazai yarda da kai ba, amma nasan makarantar su Jamal zata nufa tunda yanzu k'arfe d'aya ta wuce lokacin tashin su yayi.... Ni zan wuce makarantar nasu kai kuma ka tafi ofishin 'yan sandan kazo dasu...." Shafe kansa yayi kafin yace inada layin orderly d'in Mr President zan kira sa yanzu , domin basu san abinda ke wakana ba zan sanar da Mr President komai domin Daddy na shed'anan sa yafi k'arfin 'yansandan garin nan, sai an turo cover-up daga Abuja..... Amma still suma zasu tsare mana Shema'u.... Gyad'a masa kai tayi cikin sauri, Haidar yayi saurin tsare mai adaidaita baima san yawan kud'in da ya damk'a ba Maryama ta shige ciki a tsorace... Yayi masu addu'an kariya kafin shima yasa hannu ma d'an acab'a ya d'ale.... ************* Napep d'in su Hajiya tana shigowa layinsu AT ta hangi Sajida sun shige motar Buzu har wani rirrik'eta yake...... Ai a tamanin taceda mai adaidaita "Yaro mubi bayansu, mubi bayansu nace, jikata ce tsinanne zai lahanta min ita..." Cikin sauri mai adaidaita yace "Toh Baaba an gama, gaskiyarki ne kam gwara ki tsare mutuncin jikar ki, irin wad'an nan gurb'atattun samarukan lalata 'yanmata kawai suke.... Ko zarafin amsa sa Hajiya bata samu ba idanunta k'yam kan motar Buzu yanda yake kwasan gudu da jikarta Sajida cikin motar..... ********** Da taimakom Allah suka samu wutan ya mutu, AT gaba d'aya fatarsa tayi ja, bak'in hayak'i duk ya rina masa fata... Dole aka kawo masu d'auki daga Teaching Hospital.... Kai tsaye CCTV FOOTAGE na cikin asibitin ya bud'e ya soma dubawa domin shima kansa bai yarda wutan ba kunnata akayi ba, don tafi kama da kunnata akayi... Duk abinda ya faru a asibitin tun daga safiya ya soma gani.... Har isowan Hisham saida ya gani, wani ikon Allah basiran Hisham gaba d'aya ya shafe bai yi hacking cameras d'in ba kodashike sam bai zaci asibitin bazata k'one gaba d'aya ba... Jiri ya fara neman kada AT ganin Hisham na fito da gallons d'in petur ya nufi cikin Store dasu yana gani ya saka su a last store kafin ya fito parlorn yana fashewa da wata irin dariya.... Tashin wutan saida yayi jifa da Hisham gefe, wutan bata biyo ta parlorn yanda Hisham yake ba sai ta shige cikin asibitin cikin ward d'in majinyata... Hisham kwance a wajen sai k'ok'arin janye rigarsa data rik'e k'arfe yake ya kasa ga hayak'i ya soma gauraye wajen..... Kasa ci gaba da kallo AT yayi sai hawaye dake kwaranyo masa, yak'i aminta ma zuciyarsa cewa Hisham ya gani, Hisham dai his very own best friend wanda ya zame masa tamkar d'an uwa..... Cikin wani irin huci yayi jifa da computer d'in, hawaye na bin k'uncinsa ya fito ya nufi store d'in magunguna, su KB na ganinsa ya nufi wajen sukayi saurin take masa baya, sabida sun razana da ganin yanyin nasa... Yana isa ya daki k'ofar da hannunsa yaji zafi.... Cikin sauri KB da Alonso suka jawo k'arfe suka bugama k'ofar nan ta bud'e... Hango Hisham da sukayi kwance a k'asa yayi mugun d'aga masu hankali, cikin sauri suka k'arasa kansa suna k'ok'arin ceto rayuwar sa... AT kuwa yana k'arasowa ya finciko Hisham ya kai masa wata wawan naushi a hanci wanda saida yasa sa bud'e idanu babu shiri tamkar d'an maye.. Alonso da KB gefe suka matsa suna kallon ikon Allah, yau Dr AT ne da Dr Hisham a wannan yanyi.. Dukansa AT yake da iya k'arfinsa hawaye na bin k'uncinsa yake fad'in "You Animal I'll kill you, you're despicable wllhi Hisham sai na kashe ka..." Da k'yar su KB suka janye AT ganin na shirin aika Hisham lahira... Hisham ya tsuguna saman gwiwoyinsa yana tarin azaba... AT yaci gaba da fad'in "You're unbelievable, Hisham bansan kai meye a gareni ba, duk shekarun nan ashe kanada shirin da kake yi akaina, you're not Human Hisham kai ba d'an adam bane.... You'll rot behind bars and pay for what you did..." Ya k'arashe yana kuma yunk'ura zai capko Hisham... Mik'ewa Hisham yayi yana layi yana nuna AT da yatsa yake fad'in "You're a coward AT, baka san su waye masu sonka ba bakasan su waye masu k'inka ba, abunda zan fad'a maka sai yafi komai d'aga maka hankali..." yasa hannu ya share jinin da ya gangaro daga bakinsa kafin yace "Aysha ba a had'arin mota ta mutu ba.... She was killed by your wife Shema'u, her very own sister..." Girgiza kai AT yake yana duban Hisham yake fad'in "You gone insane, baka san me kake fad'a ba, hatred ya cika maka zuciya shiyasa kake magana marassa kan gado...." Hisham ya fashe da dariya kafin yace "Shema'u ba iyaka abinda tayiba kenan, ta kashe Maama Juu sannan ita ke yunk'urin gurb'ata tarbiyan Sajida and lastly k'anan yaranka rayuwar su na cikin had'ari domin maganar da nake maka a yanzu zata kaisu..... Za'ayi masu fyad'e gaba d'ayansu daga Ni'ima har Jamal, so if I were you I won't waste time here zan tafi ceto rayuwar yarana..." Bai kai aya ba AT ya kuma kai masa wata wawan naushi yana fad'in "You imbecile I'll kill you...." Alonso ya dubi KB yace "Buddy let's call the cops let's go..." KB ya gyad'a masa kai suka fice a tamanin... Hankad'e AT Hisham yayi yana dariya kafin yace "You miserable Coward na fad'a maka sai na karb'i land d'in mahaifina, it's mine... Snann idan kana ganin abinda nake fad'a maka k'arya ne nasan idan ka gani bazaka k'aryata ba...." Daga haka ya zaro wayarsa a aljihu yayi playing videon da Shema'u take k'ok'arin kashe Aysha... Tamkar gunki haka AT ke bin Video d'in da kallo..... Momma da ahigowar ta wajen kenan itama daskarewa tayi had'i da k'unshe bakinta da duka hannayen ta biyu... *Saminah Aliyu Mrs💖* [8:57PM, 4/5/2018] ‪+234 806 652 0501‬: 💘💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *49* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ Sosai hankalin Maryama ya tashi sanda ta isa makarantar su Jamal aka sanar da ita cewa Aunt d'insu tazo ta d'aukesu, idanunta sukayi rau-rau lokaci guda bugun zuciyarta ya k'aru... Innalillahi kawai bakinta ke furtawa, gaba d'aya ta birkice ta rasa wanne zatayi.... Wayarta dake hannunta ne yayi k'ara wanda hakan saida ya firgita ta, tana ganin Ashfaq ne tayi saurin d'agawa lokaci guda ta fashe da kuka tana fad'in "Ya Ashfaq basu nan Aunty Shema'u ta d'auke su... Wllhi ta d'aukesu..." Haidar ya dubi commissioner of police kafin ya girgiza kai yace "Sir sun baro makarantar na tabbata wajen Daddy na suka nufa...." commissioner ya gyad'a kansa kafin ya dubi ASP yayi masa alama da hannu... Sara masa ASP yayi domin tuni ya gane me yake nufi kafin ya wuce cikin sauri.. Wayar Maryama Haidar ya kuma dannawa kafin yace ta jira shi a wajen yana zuwa yanzu.... Commissioner ta wagan sa kuwa tuni sun d'auki hanyar guest house d'in VP.. ********* D'an napep gaba d'aya ya cika Hajiya da surutu ga traffic ya raba tsakanin su dasu Buzu.... Hajiya bata san sanda ta shiga sille sa ba, ita gaba d'aya tama rasa wani hanya suka nufa ga gari ya canza ko ina flyover.... Kaman ance ta kalli gefen hagu nan ta hangi Buzu na shiga wani guest in.... Talle k'eyar mai Napep tayi ta shiga nuna masa motar tana fad'in "Kaga mu shiga gidan karuwan can da ya shiga, maza muje nace idan bakayi sauri ba kuma ka bani..." Mai napep ya shiga sosa k'eyarsa yanda Hajiya ta talla masa mari yana fad'in "Baaba bafa gidan karuwai bane Hotel ne...." A harzuk'e Hajiya tace "Uwar otel ne ma, yo me ake a ciki banda bad'ala da b'arna ko kaga masu kamun kai a wajen ne inyi...." ta k'arashe tana huci... Mai napep dai bai kuma cewa komai ba domin kuwa Hajiya ta zarce tunanin sa, duk son surutun sa dole yayi shiru.... ******** Girgiza kai AT yake yana naman zubewa k'asa.... Murya na rawa yake furta "No... no, wannan ba gaskiya bane, No no no.... This can't be happening......" ya k'arashe yana dafe k'irjinsa dake barazanar rabewa..... Momma kuwa tuni ta zube a k'asa sumammiya..... AT yayi kan Hisham zai kai masa duka Hisham ya ciro bindiga a bayan wandon sa yayi pointing AT dashi, kan kace me ya harba masa a kafad'anshi yana wata irin kafiran dariya yake nuna AT da bindiga d'in yake fad'in "I've always known you to be a coward, be a man for once AT, ka kalle ka bazaka iya komai ba saidai kallo da ido....." ya kuma fashewa da dariya yana kallon AT dake durk'ushe rik'e da wajen da ya harbesa jini na zuba yana cije baki.. Da k'yar yake fad'in "You're an Animal Hisham.... Wllhi sai ka girbe abinda ka shuka....." Hisham ya kuma fashewa da dariya ya k'araso yanda AT yake ya kai masa naushi a hanci nan AT ya fad'i k'asa ga zafin bullet ga jini na kan zuba.... Dariya Hisham keyi yana nuna sa da bakin bindiga yake fad'in "Tashi ka rama.... Da zafi koh nasan da ciwo, zan maka kisan gilla bayan na wulak'anta k...... Bai kai aya ba yaji sauk'ar katako a gadon bayansa..... A tare shida AT suka juyo suna dubanta ba kowa bace illa Momma, hawaye na bin k'uncinta tana rik'e da katakon da gani zaka gane k'arfin hali kawai tayi amma tana jin jiki.. Ganin Hisham ya nufi Momma yasa AT yayi ta maza ya mik'e ya kai mai naushi wanda saida yasa Hisham ya fad'i akan fuskar sa.... Duka AT yake masa irin dukan huce takaicin nan.... Bai ko kula da jini dake bin hannunsa ba sai dukan Hisham da yake tamkar an aiko sa, baka ko ganin fuskan Hisham jini ya rufe gaba d'aya... A haka su KB suka iso da polisawa suka taddasu, da k'yar aka k'waci Hisham hannun AT domin kuwa ya kusan aikasa lahira.... Take akayi arresting Hisham 'yansanda AT bai daina fimcika yana so a barshi ya k'arasa Hisham ba.... KB na rik'e AT yana fad'in "Dr you're bleeding pls ka bari ayi treating naka..." Girgiza kai kurum AT yayi yana nunawa KB Momma dake durk'ushe a wajen rik'e da k'irjinta sannan yace "KB just take care of her... My children need me... I've to go... Kar ka damu I'll be fine, bazan iya tsayuwa a nan ba alhali rayuwan yarana na cikin had'ari..." Da k'yar ya k'arasa gaban Momma dake dafe da k'irjinta idanu rufe, jin ta ambato sunansa a hankali.. Momma taci gaba da fad'in "Tahir jikokina don Allah, Tahir kar ka bari Shema'u ta masu abinda tayi wa mahaifiyarsu, Tahir ka kula dasu don Allah, sannan ka rok'a mun su yafiya domin nice silan komai, kaima ka yafe min, ku yafe ni gaba d'aya hak'ik'a ban kasance uwa ta gari ba, sannan ban zamto Kaka abin alfahari ma jikokin ta ba.... Tahir kar ka bar Shema'u ta kuma kusantar jikokina na rok'i arzikin ka....." Momma ta kasa ci gaba da magana sai tattamke idanu da take tana dafe k'irjinta... AT dake zuban hawaye yana damk'e da wajen harbinsa saurin ficewa yayi a guje cikin tsantsan tashin hankali.... Gudu yake a tsakiyan kwalta cikin tsananin tashin hankali. ********* Haidar na isowa ya hangeta tsaye bakin kwalta, da sauri ya bud'e mata bayan taxi yace shiga muje... Cikin sauri Maryama ta shige tana fad'in "Ya Ashfaq naga wulk'awan motar ta mubi bayanta...." Haidar ya gyad'a kai kafin ya dubi mai taxi yace "Malam mubi direction d'in da take nuna mana...." Shema'u daketa faman kwasan gudu a kwalta tsawa ta kuma daka ma yaran tace "Zaku mutu yau zaku bi uwarku yanda ta tafi, shegu annoba kun hanani sakat...." Jamal dake faman huci da d'an k'aramin hancin sa jawo Ni'ima yayi yana lallashinta kafin ya bud'e murya yace "Aunty pls kar ki kashe k'anwata kill me instead kinji....." Dariya Shema'u ta fashe dashi sanda ta waigo ta dubi yaran kafin ta kwaikwayi maganar Jamal ta maimaita abinda yace... Kunnensa ta jawo had'i da buga kansa jikin seat kana tace "All of you must die, no one should survive among you, makiri mai halin kakar sa....." Jamal ya zuciya ya soma k'ok'arin bud'e lock Shema'u ta ciro takalmin k'afarta ta rik'e steering da hannu guda ta shiga tura d'aya hannun baya tana jibgan yaran da k'afar takalminta mai tsini.... Allah sarki sai kuka suke sun tak'ure waje guda... Kan kace me tuni Mr President ya turo jet guda na soji garin Kano suna hanya basu sami isowa ba, IG kuwa da kansa suke communicating da Commissioner.... Sanda suka isa gidan already masu lek'en asiri masu tsaro daga main gate sun hango abinda ke wakana cikin unguwar ta hanyar amfani da cameras d'insu, take suka sanar da mai girma VP ... Ransa idan yayi dubu ya b'aci domin tuni 'yansanda sunyima unguwar zobe... VP ya shak'o wuyan Alh Aminu yana huci yake fad'in "Laifinka ne, duk laifinka ne, matar nan bamu santa ba haka kurum ka jona mu da ita yanzu ga abinda hakan ya haifar mana wllhi ina mai tabbatar maka idan 'yansandan nan mu suke farauta zaka bar tafiyar mu, tun wuri kasan yanda za'ayi ka tsare matar nan from coming to this place, just do whatever you can to stop her... I can't lose my carrier.." ya k'arashe yana huci kafin ya doka kira ma Chief security d'insa yace ya dubo masa Haidar a penthouse d'insa... Alh Aminu da ransa ya gama b'aci da hidiman Shema'u, layin d'aya daga cikin 'yan dabansa na garin yayi kafin ya sanar dashi aikin da yake so yayi masa, kalan motar Shema'u ya fad'a masa sannan ya sanar dashi zasu ganta da yara... Take Cuna yace "An gama mai gida...." Cuna ya dubi yaransa yayi masu pito had'i da masu alama da kai cewa su ware ta samu... Cikin sauri suka d'auki kayan aikinsu suka fice daga uncompleted building d'in... ********** Masu tsaron gate firfir suka hana Hajiya shiga domin su kansu yanayin matar ya basu tsoro...... Mai napep ma harda shi a magiya amma sun hanasu shiga, Hajiya data cika tayi fam sai aunasu kawai take da idanu... Basu ankara ba sai hangota sukayi tayi tsalle ta cab'e k'arafunan gate tana k'ok'arin haurawa ga wayan wuta a sama.... Ai a tamanin d'ayan yayi jifa da kulkin dake hannunsa ya durk'usa saman gwiwoyin sa yana rok'onta Allah Annabi ta sauk'o don idan wayan wuta Ya ja ta ta mutu shi za'a Kama.. D'ayan inyamurin kame kansa yayi yana ambato Chineke... Bahaushen kuwa yaci gaba da fad'in "Iya kiyiwa Allah ki sauk'o..." Hajiya tana cab'e da gate take fad'in " Bani sauk'owa don uwarka sai ka k'yaleni na shiga nan na fito da jikata..." Mai napep me zaiyi banda dariya fad'i yake "Baaba wllhi kar kika sauk'o sai sun bud'e maki...." Ganin draman Hajiya bazai k'are ba yasanya inyamurin nan saurin bud'e mata k'aramar k'ofa jikinsa har k'yarma yake don baison biafara ta maimaita kanta... Sai sannan Hajiya ta sauk'o ta shige cikin hotel d'in tana fad'in "Dama baku bud'e min ba kuga yanda ake d'ale katanga, masu taimakawa ma yad'a fasadi kawai....." Mai napep daga chan yana dafe da napep d'insa yake fad'in "Yauwa Hajjaju Baaba shiga ki fito ina nan ina jiranki...." ****** Jini sai faman d'iga a hannunsa yake kaman daga sama sai ganin KB yayi ya paka mashin d'insa Kimko a gefe kana yace "Dr dan Allah ka hau muje zaka iya fad'i kaga jini na ta zuba, pls ka hau muje...." AT baima fahimci me KB ke cewa ba shidai kawai yasan ya d'ale mashin d'in, bai fad'a destination ba bai iya fad'in komai ba don already sama ta soma juya masa k'asa... KB kuwa bai yi wata-wata ba ya koma dashi asibiti don yasan ogan nasa na buk'atan taimakon gaggawa.... ******** Gudu Shema'u kema shararawa a kwalta, ganin Jamal ya kusa bud'e k'ofa yasata yin parking a gefen hanya don wajen babu mutane sosai, wani igiya ta rarumo a gefen kwalbati uwa zararriya tana niyyan d'aure yaran kaman daga sama taji saukan itace a gefen fuskar ta saida jini ya tsarto... Lokaci guda ta saki wani jahilin ihu.... Daidai lokacin da taxi d'in su Maryama ya iso... Haidar da mai taxi suka fito a guje suka nufo wajensu Shema'u.... Oga Cuna kuwa ganin mutane sun nufosu yasa sa saurin ciro ruwan acid d'in dake aljihun sa ya watsa ma Shema'u sai gefen kunnenta da wani b'angare na jikinta..... Wani wawan ihu Shema'u ta kurma ta shiga fiffincike jikinta tana rawan alanta uwa wacce tayi wanka da ruwan k'arara... Ihu take tana dafe kunnenta ga fuskanta gaba d'aya halittan ta canza sabida sauk'e mata itace dasu Cuna sukayi.... Jamal da Ni'ima sai ihu suke suna kuka yayinda su Cuna tuni sun cika ma rigarsu iska a guje... Maryama da k'yar take takawa sabida itama lafiya bai isheta ba, ta k'araso wajen motar da sauri ta bud'e su Ni'ima suna ganinta suka rungumeta suna kuka itama kukan take... Haidar da mai tasi kuwa sunbi bayan su Cuna saidai basu cimmasu ba... Duban Shema'u dake birgima a gefen titi sukayi lokaci guda wayan ASP ya shigo ma Haidar nan ya sanar dashi abinda ke faruwa... ASP ya sanar dashi zasu turo masu cover-up cikin gaggawa..... ******* Gaba d'aya Buzu ya canza mata lokaci guda, bai b'oye mata ko abu guda ba na shirin da suke akanta shida Shema'u, sannan ya sanar da ita fansan abinda mahaifinsa ya masa na auren Maryama zai d'auka akanta... Sajida ta shiga jada baya tana hawaye... fyad'e yake shirin mata da k'arfin da Allah Ya masa, Sajida ta kuma dubansa idanu na zuban hawaye kafin tace "Haris na d'auka kace kana sona...." Dariya Buzu ya fashe dashi kafin ya soma fad'in "Da shike ke doluwar k'arshe ce ba, koda yake tunda evil Aunt dinki ta iya manipulating d'inki kowa ma zai iya, you such a daft... Bari kiji na kuma fad'a maki Maryama is the love of my life.... Kuma wllhi kinji na rantse sai na rama abinda munafukin ubanki ya min akanki ya hanani aurenta ya aura ma kansa sabida son zuciya irin nasa... Sai na maki kaca-kaca ta yanda idan yaga illa da na maki sai zuciyar sa ya buga tunda shi likita ne...." Sajida tana huci hawaye na bin k'uncinta take fad'in "Kar ka kuskura ka kuma zagin mahaifina da wannan la'anannen bakin naka, kuma Maryama ba ajinka bace bari kaji, matar manya yace, baka cancanceta ba, Daddy shi kad'ai ya cancanci ya mallake ta...." Bata kai aya ba Buzu ya d'auketa da wani wawan mari... Cikeda tsoro ta nufi k'ofa a guje tana kuka.... Nan taji k'ofa a gark'ame... Ya fashe da wata dariya kafin ya fincikota ya jefa ta saman gado yana k'ok'arin zuge belt d'in wandon sa.... Tsalle ta kuma yi ta nufi jikin window tana bubbuga glass d'in tana neman d'auki nan ta hangi Hajiya a k'asa sai bin tapka tapkan benayen take da kallo.... Kuka Sajida take don babu mai jiyota already ya kunna TV ga k'ofofi da winduna a gark'ame... Hajiya ta warware bakin zaninta lokacin da wani dabara ya fad'o mata kafin tayi addu'a ta nufi wani k'ofa, akako yi sa'a reception ta nufa, nan ta danna wayarta hoton Sajida ya bayyana ta shiga nuna masu tana tambayar su, matse hawaye take yi tana rok'onsu su taimaka jikarta ce tanada matsalan k'wak'alwa sato ta saurayin yayi... Receptionists d'in wannan ya kalli wannan wancan ya kalli wannan, Hajiya ta basu tausayi ganin tana neman zuba gwiwoyinta a k'asa.. D'ayan yace Baaba zamuje dake mu duba idan abinda kika fad'i ba haka bane ki kuka da abinda zamu maki domin yin hakan na nufin rasa aikin mu ne idan Oga ya sani.. Hajiya ta gyad'a kai tace ta yarda... D'aya ya zaro key a shell kafin suka nufi bene... Aiko suna zuwa wajen d'akin sukaji hayaniya sosai gana TV gashi kaman harda kukan mace... Hajiya ta zare idanu had'i da d'aura hannu a k'irji tace "Na shiga uku ni Fad'ime! Bud'e min don uwarka nace.." ta k'arashe tana had'e kan receptionist d'in da jikin k'ofa wanda keta faman manna kunnensa a jikin k'ofar yana son jiyo meke faruwa cikin d'akin... Jiki har na rawa yake gyara hulan security d'in dake kansa wanda tuni ya zame sabida had'e kansa da k'ofa da Hajiya tayi, tuni ya shiga zura Key nan k'ofa ta bud'e... Hajiya hango Buzu tayi yana kokawan raba Sajida da suturanta ya danneta gaba d'aya... Saida ta kwararo wani ashar kafin ta waiga gefe da gefe tana neman abin lapta masa nan ta hangi irin dogon flower vase d'in nan aiko shi ta rarumo tana fad'in "Zakaci gwafar ubanka yau ka gama bariki.... Gadon bayansa ta samu wanda yake jazir sai shek'e yake kafin ta sauk'e masa Vase d'in nan lokaci guda ya tale had'i da sake k'aran azaba.... *Saminah Aliyu Mrs💖* [8:58PM, 4/5/2018] ‪+234 806 652 0501‬: 💘💘💘💘💘💘💘 *SHAK'UWA CE* 💘💘💘💘💘💘💘💘 *50* *©Sameena Aleeyou...✍🏼* _🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_ *_FINALE_* Jikin Sajida har na rawa ta mik'e tana goge hawaye tayi bayan Hajiya data shak'o Buzu da iya k'arfinta tana k'ok'arin ka dashi, bil hakk'i da gaskiya kokawa Hajiya ke shirin yi dashi saida securities suka k'araso suka k'waci Buzu domin kuwa da k'yar idan k'ashin bayansa bai karye ba... Sai Huci take tana gyara d'aurin kwalinta da zaninta take nuna sa tana fad'in "Kaji jiki munafuki algungumi mai fuska biyu.... Allah Ya tsaremu da mugaye irinka watsetstse kawai.... Ke kuma wuce ki daina mun kuka ai kinga irin abinda nake fad'a maki kink'i yin hankali wauwata da sokanci sun taru sun maki yawa wuce nace...!!!" ta k'arashe tana daka tsawa ma Sajida dake cazgan kuka.... Bata iya tafiya ba sai rungume Hajiya da tayi cikin muryar kuka take fad'in "Hajiya ki yafe min, wllhi na yarda nayi dolanci amma ki yafe min dan Allah duk abinda nayi bada son raina bane kuma na yarda mutum bai wuce k'addaransa, ki yafe min pls Hajiya tah...." Hajiya jikinta yayi sanyi d'an rungumar Sajida itama tayi tausayinta fal zuciyarta kafin tace "Na yafe ki takwarata Allah Ya k'ara tsare min ku....." Ta dubi Buzu dake nishi da k'yar hannun securities kafin tace "Yan sanda zaku kira min wannan barin su a gari masifah ne...." D'aya security d'in ya gyad'a kai kafin yace "K'warai Hajiya already ma suna nan tafe amma wannan kin illatasa sai an kaisa asibiti....." Hajiya ta tab'e baki kana tace "Sakamakon irinsu kenan nidai bana barin nan sai naga 'yansanda sun kame sa....." Bata kai aya ba wayarta ya shiga ruri tana dubawa taga bak'uwar lamba abinda aka fad'a mata a wayar shi yayi mugun d'aga mata hankali.... Cikin sauri ta shiga janyo hannun Sajida suka fice hawaye na gangaro mata take fad'in "Sajida Mahaifin ki, mahaifinki ne muje.... Muje kar mu rasa shi..." Sajida na kuka take girgiza kai tana fad'in "Hajiya Aunty Shema'u fuska biyu gareta ki fad'a min me tayi wa Mahaifina... Ina Daddy na...?" Hajiya sam bata sami zarafin amsata ba sai janyota data ci gaba da yi suka fito suka sami mai adaidaitan su nan ta umarce sa ya wuce dasu Sajmal Hospital.... ******** Kuka Haidar keyi shar-shar da hawaye sanda aka zura hannayen Daddyn sa cikin handcuffs da muk'arraban sa su Alh Aminu... Ya tako har gaban VP fuskar sa tayi jazir kafin yace "Tun ba yau ba, Daddy tun ba yau ba nasan bak'in zaluncin da ka aikata shekarun baya, ka kashe min tilon k'anwata sabida neman duniya, duniyar da bazata tabbata maka ba, ka kashe ta ka kashe Mama Juwaira sabida ka sami cimma burin ka.... Meyasa su meyasa Nabila meyasa ni baka kashe ni ba ka k'yale Nabila tayi rayuwarta...." Bai kai aya ba VP dake huci yana nuna sa da d'an yatsa ya kaste sa da fad'in "Because you're not my son, kai ba d'ana bane Aliyu, you don't have my single blood running in your veins....... Sannan Nabila ni nasan ban kashe su ba uwarka wacce ta bada kyautar ka wa Maryam wacce take rainon Nabila babu dare babu rana ta gudu da Nabila.... Skulls d'in daka gani d'auke da sunayen su ba Skulls d'insu bane ba k'ok'on kayukan su bane, Boka ya tabbatar min idan na tsafe tilon gudan jini na zan dawwama ina mulki, b'acewar da sukayi shiyasa na boka ya manna sunayen su jikin wad'ancan k'ok'on kayukan da ka gani.... I don't owe you any explanation boy.... Iyakaci Haidar saidai nace ka cika butulu sabida na maka gata ka kasance ungrateful daga k'arshe.... Abu guda da nake son sanar da kai shine kwabo na ban yarda kaci ba while I'm in jail......" Haidar da sama ke neman juya masa k'asa baisan sanda ya durk'ushe a wajen ba yana raba idanu ya kasa fahimtar komai.... Shin wanene shi..? Tambayar da ya ringa yima kansa kenan .... Baisan sanda aka fice dasu Daddy ba bai kuma sanin yanda kansa yake ba... ***** Maryama na rik'e da hannunsa gefe guda yayinda su Sajida ke d'aya gefen, gaba d'aya kuka suke Hajiya ita kad'aice mai k'arfin halin k'arfafa masu gwiwa hak'ik'a yau sun had'u da iftila'i wanda ba'a saka masa rana.... A hankali AT ya bud'e idanunsa ya sauk'e su kan iyalansa, hannunsa d'aure cikin bandage.... Hawaye na gangaro masa.... Lumshe idanunsa ya kuma yi yana fad'in "She killed them... Ta kashe su, Shema'u ta kashe su gaba d'aya..." wani sabon kuka ya kuma kufce masu gaba d'aya domin i zuwa lokacin magana ta gama fitowa fili..... Hajiya ta dafe goshinsa tana karanto masa addu'o'i Al'ajabi ya rufeta gaba d'aya... Su Sajida da Maryama kuwa ko wacce mahaifiyarta ta tuna, lallai Shema'u abin tsoro ne ba 'yaradam bace.... Hannun Hajiya ya rik'e still idanunsa a lumshe yake fad'in "Hajiya ki yafe ni, ki yafe min, hak'ik'a bijire ma umarnin ki yana d'aya daga cikin abinda ya jefani cikin halin da na tsinci kaina a yau, ki yafe ni Hajiya...." Hajiya tasa bakin mayafi ta goge hawayen da suka zubo mata kafin ta kuma dafa sa tace "Attahiru na yafe ka, idan da laifin ka nima da nawa laifin, hak'ik'a na kasance mai kausasa harshe a gareka, bana la'akari da cewa ni mahaifiyar ka ce.... Ka yafe ni Attahiru ka yafe ni kaji.... Allah shi kad'ai zai mana sakayyan abinda roba-roba tayi mana....." ta k'arashe tana kuka.... A hankali ya mik'e ya zauna yana dubansu gaba d'aya yanda suka tak'ure waje guda suna kuka daga Maryama har su Sajida... Takowa yayi yana dafe da hannunsa ya k'araso har gabansu.... Cikin sauri yaran suka k'arasa suka rungume sa suna kuka sosai.. Lallashin su yake kuka shima ya carke masa murya... Sajida ta d'ago tana dubansa take fad'in "Daddy I'm sorry, it's all my fault... Da ace ban aminta da ita ba duk da batakai ga aurenka ba, I Was stupid and naive, she was only using me..... If only I knew..... Da ace nasan ita ta kashe mahaifiyata da ban barta ta kusance mu ba... Daddy don Allah ka yafe min wauta na shi ya haifar mana da tashin hankalin da muka tsinci kanmu ciki.... Forgive me pls for all the pains I caused you.... Wllhi duk ita ke sakani yin abubuwan da nayi....." Hugging d'inta AT ya kuma ya shiga share mata hawaye yana fad'in "It's okay sweetheart, we all are victims here, non of this is your fault... She manipulated us all, she played innocent with all of us..... Amma Allah bazai barta ba zata girbe abinda ta shuka koma nace ta soma girba.... Zata tafi yanda suka tafi itama..... Oya kuzo nan...." ya had'esu gaba d'aya yayi hugging.. Ido suka had'a da Maryama tayi saurin saka bayan hannunta ta share hawayen ta... A hankali ya k'araso gabanta.... Ta kasa d'ago idanu ta dubesa, hannayenta AT ya kamo murya can k'asa ya furta "Thank you, thank you Maryam ...... Banida bakin maku godiya keda Ashfaq Allah Ya saka maku da aljannah, sannan.... Sannan kiyi hak'uri kashe mahaifiyarki da Shema'u tayi, ku yafe min daga ke harsu Sajida I couldn't protect.....Na.... Na kasa tsare iyayenku..." Maryama ta d'an girgiza kai tana goge hawayenta kafin tace "Uncle ka daina min godiya sannan kuma babu laifinka ko d'aya a mutuwan Aunty da Ummi nah, tuntuni hakan ya jima a rubuce.... Nasan chan d'in yafi masu nan saidai mu bisu da addu'a...... Bata kai aya ba AT ya rungumeta hawaye na gangaro masa.... A haka Sajida ta jawo hannun k'annenta suka rungumesu gaba d'aya. Hajiya dake gefe share hawayen da suka zubo mata tayi lokaci guda fuskar ta Ya cika da murmushi...... Ihun Shema'u dake kwance wani d'aki suka jiyo don ba'a jima da kawota asibitin ba... ********* Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana, haka Mummy ta biyo jirgi ta nufo garin Kano, idan kaga Mummy sai ka tausaya mata.... Kuka ta ringa yi shar shar da hawaye tamkar k'aramar yarinya don labarin kwatsam kawai ya risketa cewa anyi arresting mijinta.... ******* Idan ba muryar Shema'u kaji ba bazaka shaidata ba gaba d'aya ta canza ta koma wata halitta ta daban.... Taci gaba da kuka daga saman gadon da take kwance take fad'in "AT ka yafeni wllhi sonka nake yi, ka yarda dani duk abinda nayi nayisu ne out of love, dan Allah kar ka juya min baya kaji my love..." Jijiyoyin jikinsa gaba d'aya sun mimmik'e idanunsa sunyi jazir... k'arasowa yayi yana toshe hanci sabida wari da Shema'u keyi.... Da k'yar ya soma furta "Kin cuce ni kin zalunce ni kin ha'ince ni kin ci amanata in the most horrible way.... Yaya kike tunanin zan tab'a yafe maki bayan duk abubuwan da kikayi..... Meyasa Shema'u Why..... Ki sani wannan shine dalilin da ubangijina ya hanani kusantarki, sabida shi ba azzalumi bane sannan ya sanya zalunci ta zamo haramun a tsakanin bayi..... Ban tab'a ganin mugun d'an adam irinki ba.... Allah bazai barki ba Shema'u koda na yafe maki...." Aysha was pregnant.... Muryarsa ya sark'e ya kasa ci gaba da magana sai kuka yana dafe da wajen ciwonsa daidai lokacin dasu Maryama Hajiya da kuma Sajida suka shigo.. Maryama tayi saurin k'arasawa ga mijinta yayinda Sajida ta k'arasa gaban Shema'u.... Idanunta jazur hawaye na zubo mata.. Shema'u ta soma d'ago hannunta da ya k'one da ruwan acid tana fad'in "Sajee my Sajee ki yarda dani nasan bazaki tab'a juya min baya ba sweetheart pls believe me....." Sajida tasa hannu ta goge hawayen da suka zubo mata tana wani irin huci ta soma fad'in "Allah Ya Isa tsakanina dake Shema'u, wllhi wllhi wannan kad'an kika soma gani, kin kashe mutanen da nafi so a rayuwata kin kashe mahaifiyata kika jani a jiki don kin salwantar da rayuwa ta, kika nuna mana soyayyar k'arya don ki saye zuciyar mahaifin mu, toh ki sani Allah shine masanin al'amuran da muke k'ulla a fili da kuma a bayyane.... You know Shema'u I don't feel sorry for you, babban burina shine naga kinfi haka wulak'anta sannan ki k'are miserable days d'inki a gidan kurku..... You shameless witch...." ta k'arashe tana kuka sosai tana k'ok'arin kaima Shema'u duka saida Hajiya ta rik'ota.... Daidai lokacin aka turo Momma aka shigo da ita tana zaune saman wheelchair. Kallonsu one by one Momma tayi hawaye na gangaro mata kafin ta k'arasa gaban Hajiya, tana kuka take bawa Hajiya hak'urin duk wasu abubuwan da suka shiga tsakanin su a baya, ciki harda taimaka ma Shema'u da auren Tahir da tayi, da ace tasan bak'in k'ullin dake cikin zuciyar Shema'u da bata kai ga had'asu ba.... Hajiya ta durk'uso ta kamo hannayen Momma kana tace "Kulu nima ki yafe min nasan nayi maki abubuwa da dama na yafe ki nima ki yafe ni.." Momma ta share hawayenta kafin tace "Tabbas mu iyaye muke kula da rayuwar yaranmu, na zalunci yarana tun daga lokacin da nafi nuna fifiko akan guda, sannan kuskure d'aya tak nayi ta bibiye rayuwata hak'ik'a 'yanmma kuyi hattara domin kuskure d'aya zaki iya yi ta bibiyi rayuwarki har abada..." ta k'araso ga Sajida ta kamo hannayenta kana ta soma fad'in "Ku yafe ni Sajida ni na kawo maku annoba cikin gidanku, ku yafe ni jikokina, na sani I don't have much time left, amma inaso na kuma rungumar ku sannan na samu yafiryar ku ko ubangiji na zai sassauta min lamura na...." Saurin rungumarta Sajida tayi tana hawaye take fad'in "Momma ki daina fad'in haka, kema Victim ce, kema kin fad'a tarkon Aunty Shema'u.... Mu gode ma Allah da ya ganar damu komai...." Momma tayi murmushi had'i da hugging Sajida dukda k'arfin hali kawai take... Koda suka fice daga d'akin Momma bata fice ba saida ta k'arasa wajen d'iyarta Shema'u, Shema'u ta ringa surfa mata ashar tana fad'in duk laifinta ne ita ta jawo, itace silan komai, nan Shema'u ta sanar da ita cewa ita ta kashe mijinta Alh Mukhtar sabida ta jima da sanin ba shine mahaifinta ba shiyasa suke wareta suke nuna sunfi son d'iyarsu Aysha sama da ita.... Momma ta soma gani bibbiyu lallai Shema'u ta wuce tunanin mutum cikin kuka take gungura kekenta ta k'arasa tana kai duka ma Shema'u dake faman dariya ta ko ina.... K'arfen abin drip Shema'u ta jawo ta shiga ruza wa Momma a tsakar ka duka zogin ciwo dake addabanta... K'arshe ta k'are ta hankad'e Momma ta fad'i akan zuciyarta lokaci guda ta Saki wani k'ara... Gaba d'aya suka nufo d'akin nan suka ga Shema'u sai dariya take ga Momma rik'eda k'irji tana salati.. Shema'u kuwa sai dariya take uwa tab'ebb'iya k'arshe fiffincike bandage d'in da aka rufa mata da jikinta ta ringa yi tana had'awa harda naman jikinta tana ihu....." Dole aka kwasheta aka canza mata asibiti.... Momma kuwa mintoci kad'an ta k'ara tace ga garinku, rai yayi halinsa.... A gidan AT akai ma Momma komai taredasu Hajiya, gaba d'aya sunsha kuka barin su Sajida, haka su Maryama da Hajiya suka ringa lallashin Su suna basu baki.... ***** Hannun Mommy ya rik'e yana kuka tana kuka sanda ya sanar da ita duk yanda sukayi da Daddy... Haidar yaci gaba da fad'in "Mummy pls ki sanar dani asalina , wanene ni....?" Mummy ta shafi gashin kansa tana mai ci gaba da kuka take fad'in "Gaskiya ne Haidar Juwariyya itace ta haifeka, ta kasance tana yimin aikatau a lokacin dtazo da kai kana jariri domin mahaifinka ya rasu tun kana ciki ma'ana tun ba'a haifeka ba, ni kuma tuntuni inada son yara saidai Allah bai bani haihuwa ba.... A dalilin haka ta damk'a mana kai kyauta ko bayan ranta, koda nazo na sami cikin Nabila na haifeta sai na damk'a mata rainon Nabila gaba d'aya har zuwa ranar da muka wayi gari wuta ya k'one su..." Haidar ya share hawayen sa kafin yace "Mummy basu k'one ba, Daddy bai cimma burinsa akansu ba Allah Ya tseratar dasu kuma suna rayuwa a wani waje nasan watarana Allah zai had'a mu...." Mummy ta gyad'a kai kafin tace "Haka ne Haidar, sai yanzu nasan dalilinka na bijire wa Mahaifinka, hak'ik'a mutane sun zama mushirikai sabida neman duniya, sun fifita duniyar su sama da lahiransu wacce lahira itace rayuwa ta har abada, Fu'ad ya zalunce ni, ya cutar damu.... Bana k'aunar na kuma ganin fuskar sa har abada...." ta k'arashe cikin tsananin kuka... ******* Gida suka zo ita da Hajiya don d'iban kaya sabida Tahir da iyalansa suna tsananin buk'atar su, nan Maryama ta wuce sashen Maama Juu ta d'auko d'an akwatin tan nan na sirri... Hannunta dafe a wuyanta tana shafe sark'anta tana mai mata addu'a cikin zuciyarta ta shiga bud'e akwatin... 'yan kunnaynta ne yawanci tun tana Baby irin a yaye lafiya d'in nan, abun har saida yasanya Maryama yin murmushi... Har zata rufe kaman ance ta karkad'e nan wata wasik'a ta fad'o.... Gaban Maryama ya yanke sanda ta d'auki wasik'ar zata soma karantawa kenan ta jiyo sallaman Ashfaq da wata Mace wanda ya sanyata fad'uwan gaba... Hajiya ta fito daga d'aki tana fad'in wa nake ji kaman Keenafas... Haidar na murmushi ya k'arasa shigowa Mummy ta take masa baya.. Hajiya da Haidar na ma juna barkwanci Maryama kam da Mummy tuni sun makare a kallon juna... Idanun Mummy suka sauk'a kan sark'an dake mak'ale wuyan Maryama, take ta soma recalling komai sanda tabawa Mama Juwaira wannan sark'an tace ta ajiye mata domin a ranar Nabila wuni tayi tana wasa da sark'an... Mummy na hawaye ta k'arasa har gaban Maryama baki na rawa take nunata tana furta "NABILA!! " Ba Maryama da tayi turus ba tana kallon Mummy gaba d'aya su Hajiya ma tsareta da idanu sukayi.... Haidar ya k'araso yana duban Mummy da kyau kafin yace "Mummy itace Nabila koh, Maryama itace Nabila koh.... Kenan matar da na zata mahaifiyarta ce wacce nake gani a mafarki itace mahaifiyata koh.... Mummy mahaifiyata ta rasu, bazan ganta ba kenan..." Rungume Maryama Mummy tayi tana fad'in "Nabila Nabila ta, Allah yayi zan kuma ganin ki, ina Mama Juwaira...." Hawaye Maryama keyi tana bin matar da kallo tana girgiza kai, ta kuma saurin sunkuyawa ta d'au wasik'ar da take k'ok'arin karantawa wasik'ar da Maama Juu ta fayyace mata komai a ciki, asalinta da sunan mahaifanta da kuma ita d'in ko wacece da dalilin da ya sanyasu gujewa daga gida... Kuka Maryama take shar-shar da hawaye sanda Ashfaq ya amshi wasik'ar yana karantawa da bud'edd'iyar murya.... Gaba d'aya parlour ya kaure da kuka..... Al'ajabi ya cika Hajiya.... Nan kuma bayan hankula sun dawo jiki aka zauna aka soma fahimtar juna, Mummy da Haidar sosai sukaji mutuwar Maama Juu, Babu kaman Haidar da bai sami Chance d'in kasancewa da ita ba a matsayinta na mahifiyar sa.. Allah Ya k'addari hakan saidai su bita da addu'a...Allah sarki Maama Juu ta cika mai halin k'warai Allah ya kai haske makwancinta.. Mummy tamkar ta maida Maryama cikinta haka take ji, gaba d'aya suka d'unguma sukayi gidan AT... Mamaki da Al'ajabi ya cika su gaba d'aya, kodashike ba'a mamaki da ikon Allah lokaci guda ya warware komai.. Mummy gaba d'aya rasa bakin godiya tayima Hajiya da Ahmad Tahir... Babban abinda yafi mata dad'i shine auren Tahir da Nabilar ta, lallai sun cika mutane masu karamci... Maryama dai bata wani sake da Mummy ba tana nan mak'ale da Hajiyarta, saida Hajiya ta tilasta mata ta tafi wajen mahaifiyarta su kwana tare suji d'umin juna kafin Maryama ta mik'e ta tafi wajen mahaifiyarta... Hira Mummy ta ringa janta dashi na labarin rayuwarta kafin daga bisani tace maza ta tashi ta tafi wajen mijinta yafi kowa buk'atan ta a hali yanzu tunda bashida lafiya... Maryama ta d'an turo baki had'i da zaro idanu tace "Mummy fah zai iya kwan, nidai ki barni naji d'uminki..." Mummy tayi murmushi ta shafi kumatunta kafin tace "Baby babu kalan d'umina wanda bakiji a jikin Hajiya ba, yanzu d'umin mijinki yafi d'umina mahimmanci a gareki kinji koh..." Cikeda kunya Maryama ta sadda kanta k'asa.. Har k'ofa Mummy tayi mata rakiya had'ida saka mata albarka... A stirs ta had'u da Sajida zata sauk'o k'asa... Gaban Maryama ya yanke ya fad'i don gani take Sajida ta fahimci d'akin mahaifinta zata tafi... Murmushi Sajida ta sakar mata kafin ta iso yanda take, a kunnenta ta rad'a mata... "Aunty Sis kin k'yale min Daddy na shi kad'ai bayan kinsan bashida lafiya..." Dariya Maryama tayi ta kai mata dukan wasa tace "Zaki sani ne..." Dariya Sajida ma tayi kafin tace "Eh mana ai gaskiya na fad'i koh, ga wannan yayan naki Keenafas d'in Hajiya ina cikin bacci na ya dameni da waya wai sai na had'a masa shayi... Likitoci akwai kad'ifiri wai basu cin solid food da dare..." Ganin Maryama na watso mata kallo yasata k'unshe baki tace "Oh I'm sorry ashe ke matar likita ne..." ta k'arashe tana wucewa da gudu... Murmushi kawai Maryama tayi kafin tayi wucewarta d'akin masoyinta.... Yana tsaye gaban full length mirror yana k'ok'arin cire rigarsa da hannu guda sabida ciwon sa, kaman daga sama sai jiyo hannunta yayi tana taimaka masa... Annuri ya cika zuciyar sa, gently ta k'arasa cire masa rigar... Juyowa yayi ya d'an kamo kunkuminta da hannu maras ciwon kafin yace "Allah Ya maki albarka Baby.." Bata iya amsa sa ba sai sadda kai k'asa da tayi domin kuwa gaba d'aya nauyinsa take ji... AT ya murmusa kafin yayi masu masauk'i saman chaise lounge, tana zaune saman laps d'insa ya d'ago fuskar sa yana dubanta kafin yace "Why the face Baby, ko baki so zuwa wajena bane, I thought da Hajiyarki zaki kwana har na cire rai...." Turo baki ta kuma yi kafin tace dashi a shagwab'e "Ba Mummy bace tace sai na zo..." AT ya murmusa had'i da d'an jan hancinta kafin yace "Gaskiya Mummy ta kyauta min, ai Mummy ta fiku gaskiya keda Hajiya, ku kun faye son kanku yanzu nima kunga na sami mai sona tunda tana tausayi na..." Maryama ta kuma turo baki.. Rungumeta yayi cikin jikinsa had'i da lumshe idanu... Nan yaji hawayenta na sauk'a a kafad'ansa.... SSaurin d'agowa yayi yana tambayarta meke faruwa.. "Ko kina son ki tafi wajen Hajiya ne..." Girgiza kai tayi kafin tace "Uncle na kasa aminta mahaifina mutumin banza ne, shin dama hakan ka iya kasancewa ga mutum, meyasa mahaifina why him... Rayuwa ta mana sauk'i, mun zama family d'in da muke mafarkin zama na samu Mahaifiyata, na auri mijin da nake so but.... I'm still hurting deep inside....." AT da jikinsa yayi sanyi saurin rungumeta yayi kafin yace "Ki daina irin wannan tunanin Baby, Allah yakan jarabci bayinsa tako ina, babu laifinki ko na mahaifiyarki don mahaifinki ya kasance haka, kar ki manta Allah yana cire rayayye a cikin matacce sannan yana cire matacce a cikin rayayye wannan fad'insa ne, kasancewar mahaifinki haka doesn't mean you can't be accepted by other people, because we all are imperfect no one's perfect sannan babu wanda zai sami irin rayuwar da yake so perfectly dole ta wani wajen ka sami nak'asu.... Kar ki manta Annabi Nuhu alaihissalam Annabi ne kuma manzo sannan d'ansa da matar sa sun kasance 'yan wuta... Asiya matar fir'auna wanda yafi kowa kafirci a duniya ta kasance cikin mataye masu daraja kuma 'yan aljannah dukda cewa daga iyalan gidan Fir'auna take.. So ki daina damuwa Baby wannan shike tabbatar wa mu 'yan Adam ne bazamu sami komai yanda muke so ya kasance ba kinji koh..." Murmushi tayi had'i da gyad'a masa kai kana ta kwanta cikin jikinsa a hankali ta furta "Ina sonka Uncle..." Ido a lumshe shima ya furta "Ina sonki nima Baby..." "Keenafas ka k'yaleni naje nayi bacci tunda na kawo maka shayin pls..." ta k'arashe tana had'e hannayen ta waje guda.. Murmushi Haidar yayi kafin yace "Saifah kinmin labarin saurayinki Buzu kafin na k'yaleki..." Harara ta galla masa kafin tace "Kaga ka daina tam, ni dai bana so...." Haidar ya k'unshe dariyar sa kafin yace "Toh saurayin ki Keenafas fah...?" Dariya itama tayi kafin tace "Kai gaskiya Hajiya ta iya saka suna sosai, kuma fah kayi kama da Kidnappers d'in...." Dariya ya kumayi kafin yace "Gashi kuma zanyi keenafas d'inki ba...." Kaman daga sama sai ganin Hajiya sukayi ta lek'o tana goga aswakinta kana tace "Kafin kayi keenafas d'inta ka tabbata ka biya sadaki ehe....." Daga Haidar har Sajida dariya suka ringa yi harda sunkuyawa... Hajiya kuwa ko a jikinta ta fad'i ta koma d'aki abinta..... ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!! *A nan na kawo k'arshen wannan littafi nawa mai taken SHAK'UWA CE, kurakuren da nayi cikinsa ina rok'on Allah Ya gafarta mani, fad'akawan dake cikinsa Allah Ya amfane mu dashi baki d'aya.* *Dukkan yabo da godiya sun tabbata GA Ubangijin talikai wanda ya aramin rayuwa da lafiya har na kammala wannan rubutu nawa...* *K'ungiyata ta KAINUWA na gode maku k'warai bisa goyon bayanku da jajircewan ku a gareni har wannan sak'o da nake son isawar ya kammala, Allah Ya saka maku da alkhairi ya k'ara had'e kanmu baki d'aya... Ameen!"* *''Yar uwa aminiya k'awa a gareni RALIYA GARBA aka RALLY GARBA, banida bakin godiya a gareki saidai naci gaba da maki addu'an alkhairi.... Allah Ya rabamu da sharrin mutum ko aljan... Wannan littafi nawa mai taken SHAK'UWA CE kacaukam d'insa sadaukarwa ne a gareki My Sisi... Tabbas SHAK'UWA CE mai k'arfi abtsakanin mu, Allah Ya bar k'auna... Amen...!* *Masoya na a duk yanda kuke a fad'in duniya nima ina sonku ina k'aunar ku... Nasan cewa SHAK'UWA CE mai tsanani a tsakanin ku da wannan labari zakuyi kewan shi kaman yanda shima zaiyi kewarku.... Alkhairin Allah Ya kai maku a duk yanda kuke...* _*SAMEENA ALEEYOU aka QUEEN SAMY ke maku fata na alkhairi 🤝*_