https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw 12/4/2025 🪻SAWUN KEKE Season 2🪻 EP .......1 By INDO (SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU) *Ba zan iya cewa wannan labarin cigaban wancan bane, domin kowanne Maudu'insa Daban.........👌🏻👌🏻👌🏻 Salon Wannan Daban,,, Salon Wancan Daban...... Sai dai ya zama dole in gaya muku cewa....... Wancan Labarin Shine asalin Tushen Wannan.👏🏻 Da Fatan Zaku Bibiya tun daga Farko har Ƙarshe don jin Yaya Abun Yake..................* Bismillahirrahmanirrahim. Ihu ta kurma a karo na ba Adadi tare da tattaro dukkan ƙarfinta ta bangaje shi da Ƙarfi har sai da yayi baya taga-taga kamar zai faɗi ............ Bata tsaya jiran komai ba ta falla da gudu tana dafe da ƙirjinta da ya bayyana sakamakon Yaga mata riga da yayi..... a tunaninta gudunta zai iya tseratar da ita, sai da ta ji ƙafafunta sun harɗe ta faɗi ƙasa tim!! sannan ta gane bahagon tunani take yi. ihu ta ƙara kurmawa tare da yunƙurawa zata miƙe, sai lokacin ta lura wani kalar ganye me yaɗo ne ya ɗaɗɗaure mata ƙafa har ya jaza mata faɗuwa. cikin zafin nama da bata zata tana dashi ba ta fara ƙoƙarin cire ganyen sai taga ya ƙara kame hannunta ya ɗaure, "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" ta furta cikin ɗaga murya, tashin hankali ba a sa masa rana, Ko sau ɗaya bata taɓa tunanin irin wannan zai faru da ita a rayuwa ba, bata taɓa zaton laifin da tayi zai sa ta girbi irin wannan ɗanyen hukuncin ba......... Muguwar cafkar da ya ƙara yi mata ce ta dawo da ita hayyacinta, ta saki wani matsanancin kuka tana cewa "Ban yi maka komai ba don Allah kar kai min haka, wallahi ban faɗa ba ka yi haƙuri!!, ba zan ƙara shiga rayuwarku ba, ka duba girman Allah ka ƙyale ni kar ka lalata min rayuwa!" Idanu ya zuba mata ƙur!!! yana jin wani irin bahagon yanayi yana ziyartarsa. Idanunsa da suka koma Blue color tuni sun cika taf da ruwan hawaye, wani sashin na zuciyarsa na tunzura shi wani sashin kuma yana shirin fara tausayinta. Wata gagarumar guguwa ce ta tunkaro wajen da ƙarfi ta sure shi ta watsar a ƙasa,,, "Abeeee!!!" ta ƙwala masa kira cikin tashin hankali da ruɗani. guguwar tana wucewa ta faɗa kan wata bishiya daga haka ta dena ganin ƙyallinta sai dai jinsa tayi yayi sufa akanta Tamkar wani yunwataccen Zaki......... Ihu da neman ɗauki gami da jero Addu'o'i shine abunda take iyawa dan kuwa gabaki ɗaya ji tayi kamar an ɗaure mata hannaye da ƙafafunta a cikin ƙasa....... Tana jinsa yana nashi gurnanin gami da wasu Surutai wanda bata taɓa jin irin Yaren ba a duk tsayin Rayuwarta. Lokacin da ya gama wulaƙancinsa ya sauka daga kanta ta riga ta zama marabarta da Gawa kawai ita akwai rai a jikinta, sai sa'a ɗaya idanunta da suke a buɗe suna gani dishi-dishi da kuma tunaninta da bai gushe ba..... tana iya ganin lokacin da ya miƙe yana bubbugar kansa da ƙarfin gaske yana kuka , kai tsaye Wajen Tafkin Ruwan da ya ƙawata wannan Yankin na Dajin ya nufa yana tafe yana haɗa hanya, daga haka bata ƙara sanin inda kanta yake ba.................... ******************************************** "Yanzu kamar ni in faɗi magana ki ƙi yarda Kyakkyawa?.... kin sa Zuciyata ta tsinke fa" Murmushi tayi gami da taɓe baki tace "Ai maganar taka ce bata yi kama da gaskiya ba, wancan Abokin naka uban faɗin rai shi ne zai so ni?, da wasa kake yi; kalli fa irin sutturar jikinku ka kalli irin Motar da kuke zuwa da ita Unguwar nan, ni kuwa fa sana,ar Awara nakeyi akan layi ka ga babu haɗi tsakaninmu" "Wayyo Allah Beauty kina breaking heart na fa!" ya ƙarasa maganar cikin sigar shagwaɓa. murmushi ta saki wanda ya tawo daga can ƙasan zuciyarta, tana shirin yin magana Ammar ya dakatar da ita da cewa "Ya kamata ki san cewa bamu ɗauka cewar da bambanci tsakanin mu daku ba. In akwai bambanci me zai sa mu dinga zuwa Uguwarku ?, ko ba ki yarda ba har yanzu?" "Na fara yarda mana" ta faɗa tana murmushi gami da yin ƙasa da kanta. Ammar ma murmushin yayi gami da kallon inda Umar yake, tare da cewa "Ji mana Abok.....!" kasa ƙarasa maganar yayi saboda jin wani sauti wanda yafi kama da na takun ingarman doki yana tunkaro inda suke, ganin Umar ya sume yana kallon wajen yasa yayi sauri ya kalli inda Umar din yake kalla don ganin me ya gani.... zumbur ya miƙe tare da dawowa kusa da Umar suka ci gaba da kallonta. Cikin Wata sumammiyar murya Umar ya ce "Subhanallah !, Girma da tsarkaka su ƙara tabbata ga Ubangijin da ya halicci Kyau domin ya kasance Adon Duniya da Lahira!" cikin sanɗa Ammar ya riƙe hannun Umar yana cewa "Kam bala'i yaushe Ƴan China suka fara kafa Masarautu a Nigeria?. PAID BOOK NE👏🏻 https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw 🪻SAWUN KEKE Season 2🪻 EP .......2 By INDO Bismillahirrahmanirrahim. Waya Umar ya zaro daga cikin Aljihunsa ya fara yiwa Budurwar da take tinkaro su akan Ingarman Dokinta bidiyo, sannan ya bawa Ammar amsa da cewa "Abunda ba zai yuwu ba kake faɗa; ni kayi min shiru dalla!" daidai lokacin Budurwar ta iso inda suke sai dai da tazara a tsakaninsu. Cak! ta tsaya tana zuba musu zaratan idanunta masu matukar kyau da ƙawa, sai dai kallon da take watsawa Umar yafi kama da na tuhuma ko kuma gargaɗi. dogon suman da ya tafi saboda kallonta yasa bai fahimci hakan ba. Ganin yaƙi dena abunda yakeyi yasa Zuciyarta ta fara tafarfasa, cikin sauri ta zaro kibiya dake cikin mazubinta a rataye a bayanta, tana zarowa ta shillata inda Umar yake, Kai tsaye ta sauka akan wayar hannunsa tare da shafar Yatsansa guda ɗaya. ƴar ƙara ya saki saboda azabar da ta ratsa shi har cikin kansa, ƙasa ya kalla don ganin halin da wayarsa take a ciki, idanunsa ne suka ƙara girma ganin yadda ta tarwatse babu batun za a iya gyara ta ma. tuni jikinsa ya fara tsuma sabida wani yanayi da ya ziyarce shi , yanayin da ya kasa bambance irinsa. zai iya cewa duk tsawon rayuwarsa bai taɓa tsintar kansa a cikin makamancin hakan ba. cikin tsoro da fargabar abunda zai ƙara biyo baya ya ɗago idanunsa da suka kawo ruwa ya ƙara ɗora su akanta. har lokacin kallo me cike da fushi da ɓacin rai take yi masa, ganin ya ƙara tsura mata ido yasa ta ƙara zaro kibiyar tana shirin ƙara masa. "Kubraah!!!" kiran gaggawar da aka yi mata ne yasa ta fasa abunda take shirin yi tare da runtse idanunta da ƙarfi. a sukwano Matashin ya ƙaraso inda take tare da yin tsalle daga kan Dokinsa ya sauka a gefenta ya janyota suka faɗi tim!! a wajen. "Me yasa taurin kanki yayi yawa ne?!" yayi mata tambayar cikin tsawa. cikin tsawar ta bashi amsa da cewar "Na gaya maka bana so kana yi min tsawa ko?" "Nayi ɗin mara kunyar banza" Bangaje shi tayi daga jikinta tare da artawa da gudu zata sake hawa Dokinta yayi saurin ƙure mata gudu ya cafkota tare da matse ta a cikin faffaɗan ƙirjinsa. wutsil-wutsil ta fara yi tana cewa "Ka Sake ni, bana so !!, ni ba zan koma ba" surutan ta cigaba da yi, tun tana motsawa da karsashinta har ta dena motsi jikinta ya saki salaf. kallon wani Da yake bayansu yayi gami da cewa "Ahmadi ka tawo da Dokin nata." Ahmadi ya amsa cike da girmamawa. saɓata yayi a kafaɗarsa tare da yin sufa ya haye kan dokinsa sannan ya kalli inda Umar yake ya ce "Ka kula da kanka!" Daga haka ya sukwani dokin ya wuce. Da Ido Umar,, har ma da duk ilahirin Mutanen wajen suka raka su, sai da suka ɓace sannan Umar ya numfasa ya ce "Ammar mu bar unguwar nan" sai a lokacin Ammar ya iya yin motsi ya shiga Mota. Umar ne a mazaunin Driver amma ya kasa ko motsi da sunan jan motar. Mutanen wajen kuwa tuni sun karaɗe da muhawara tare da maida yadda akai, kowa na tofa albarkacin bakinsa. "Umar idan ba zaka iya ba ni ka bani in ja" ba musu ya fice daga motar yana shirin zagayawa, ganin haka yasa Ammar ya koma sashin driver, Umar yana shiga ya bawa Motar wuta. shiru ne ke famar ɗawainiya dasu har tsayin wani lakaci, sai da suka kusan shiga Unguwar su Umar sannan yace "Yau rana ta farko da idona yayi tozali da abunda yasa na tsinci kaina cikin wani yanayi mai wuyar fassaruwa" Ammar yace "Naga alama ai, ni kuma zan iya cewa abunda ban taɓa gani ba yau shi na gani, wallahi suman tsaye nayi, ko wacece wannan Kuma??? kayan jikinta suna da bambanci da kayan da Matan Hausawa suke sakawa a wannnan zamanin, gashi yanayin shigarta yafi kama da na sarauta; Abokina ka manta da wannan yarinyar wataƙila Aljanu ne suka fara shigowa jinsin Bil,adam" Umar ya murmusa kafin yace "Mantawa da ita ba abu ne me sauƙi gareni ba, wallahi ko Aljanar ce ma na kamu da tsananin kwaɗayin ƙara ganinta" "A'uzubillah! Umar anya kuwa kana Azkhar yanzu?, ina ga ka dena yi ne shiyasa Aljanar take nema tayi nasara akanka" shiru Umar yayi don ba zai iya cewa komai akan hakan ba. Suna yin parking a harabar gidan Umar ya ɓalle murfin Motar ya fice, Ammar ne ya katse masa hanzari da cewa "Gidanmu zan wuce fa!" "Okay see you letter" Umar ya faɗa a taƙaice, wasu lokutan yakanji ba daɗi sabida nuna ƙyama da Ammar yakewa gidansu, sanin Ammar ɗin ya fi shi hujja yasa baya ɗago zancen. a Falon farko ya tarar da Mommy ta ci Ado ta hakimce kan sofa tana famar danne-dannen waya. "Good evening Mommy" ya faɗa tare da yin shirin shigewa ciki. wani mugun kallo ta watsa masa kafin ta ja tsaki tace "Shashasha wanda bai san Mutuncin kansa ba!" shiru yayi mata, kawai ya dangana da Bedroom ɗinsa, masauki yayiwa kansa a bakin gado gami da dafe kansa da yake wani irin hargitsi gami da juyawa. zazzafar iska ya furzar gami da yamutsa Ƴar sumar kansa da ta fara fitowa, "Wai me yasa iyayena suke ɗaukata tamkar babu alaƙa koda kaɗan a tsakaninmu?" wani sashi na Zuciyarsa ne ya jefo masa tambayar, daga wani sashin kuma ya samu amsa da cewa "Saboda kana kula Talakawa kana Abota dasu!" murmushin takaici ne ya suɓuce masa, a sarari yace "Tunda kuwa haka ne lallai ina da sauran aiki, yana da muhimmanci gareni in ganar da iyayena Muhimmancin ɗan Adam a rayuwa, gashi tin kafin tafiya tayi nisa na yi Gamo da wata ban san ma wacece ba gashi tunaninta ya tsaya min a raina" A ɓangaren Ammar ma haka yaje gida sharaf-sharaf jikinsa duk babu ƙwari, koda Ummi ta tambayi lafiyarsa sai yace ba komai. _______________________________________ Cike da fargaba Abee yake takawa tare da kutsa kai cikin wani makeken Falo wanda tsayawa zayyano irin kyawu da kayan alatun dake tare dashi aiki ne babba. a duk takunsa ɗaya Zuciyarsa ƙara gudu takeyi yayinda tsoro yake ƙara ɗarsuwa a cikinta. Lokacin da ya iso tsakiyar Falon ya lura babu kowa don haka ya sauke kyakkyawar ajiyar zuciya tare da sauya akalar tafiyarsa zuwa Bedroom ɗin Kubrah da nufin yaje ya kwantar da ita. "Abee!" zazzaro idanu yayi tare da fizgar numfashinsa da kyar..... sai daga baya ya gane Mammi ce me kiran, ɗan gyarawa Kubrah zama yayi akan kafaɗarsa sannan ya juyo tare da ɓoye duk wani tsoronsa, cikin ƙarfin hali yace "Rankiyadaɗe!" fuskarta babu alamum wasa ta ce "Menene haka!?, ina kake shirin zuwa, kuma daga ina kake?, me ya sameta da ba zata iya tafiya da kanta ba?" ɗan murmushin ƙarfin hali yayi cikin son kawar da zancen ya ce "Mammi tambayoyin sun yi min Yawa " "Ya zama dole ka amsa min su, idan ma baka bani amsa ba za....." bai barta ta ƙarasa ba ya katse ta da cewa "Don girman Allah Mammi kiyi haƙuri!, Yawo ta tafi yi a Daji shine na dawo da ita" Ɓoyayyar ajiyar zuciya Mammi ta sauke kafin ta ce "Ɓace min da gani, ka je ka ajiyeta ka fito ka nemo min Su Zahra" da "To " ya amsa tare da juyawa ya ci gaba da tafiya cikin gaggawa. Yana ajiyeta ya fito domin aiwatar da abunda Mammi ta Umarce shi. Sai da aka fara kiran Sallah sannan ta samu Ƴancin Farkawa daga nannauyan baccin da ya sure ta, bayan ta ajiye addu,ar bakinta "Abee" shine wanda ta fara kira tare da juyawa gefenta da nufin ta ganshi amma sai taga fayau babu kowa. idanunta ne suka ƙara girma lokacin da ta tuno Fuskar Umar , Nan take zuciyarta tayi wani ƙwaƙƙaran duka wanda ya motsa duk ilahirin masarrafan jikinta, "Yasalam!" ta faɗa tare da ɗora hannayenta duk biyun a kanta. ta ɗauki tsawon mintuna akalla biyu kafin ta samu ta dena ganin hotonsa da Zuciyarta take haska mata, jiki a sanyaye ta sa ƙafa ta sauka daga kan tafkeken gadon wanda ya sha shimgiɗar alfarma. Daidai lokacin aka hankaɗo Labulen ɗakin da ƙarfi, sai da Zuciyarta tayi tsayawar wucin gadi sabida tsoro da ya rikito mata tamkar saukar aradu. Sai da Zahra ta ce "Yaya! Ki tashi kiyi Sallah mana!" Sannan ta sauke gwauron numfashi gami da cewa "Zan yi mana, ki dena shigowa ɗaki da sauri haka" Zahra ta murmusa kafin ta ce "Dake da Yaa Abee yanayinku ya nuna akwai abunda ke faruwa wanda ya kasance sirri a tsakaninku!" "Zahra ya isa haka!, Affah ya dawo ne?" "Yana Masallaci, kuma na tabbata gaf yake sa shigowa" Zahra ta bata amsa tare da juyawa ta nufi hanyar fita. Sai bayan ta idar da sallar ne ta samu nutsuwa har ta iya yin numfashi me dadi.... Bata gama hutawa ba Saim ya shigo cikin sauri gami da cewa "Yaya! Affah na kira" dim!!! Zuciyarta ta buga, idanunta sukayo waje, cikin wani ƙaramin tashin hankali da ta tsinkayi kanta a ciki ta ce "Da gaske?" Yana shirin fita daga d'akin yace "Ai ba zan yi Miki k'arya da irin wannan ba " Bai jira cewar ta ba yayi gaba. ''Innalillahi Allah gani gareka" ta fad'a gami da yunk'urawa ta mik'e don gudun ƙarin laifi. (SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU!!) *Ba zan iya cewa wannan labarin cigaban wancan bane, domin kowanne Maudu'insa Daban.........👌🏻👌🏻👌🏻 Salon Wannan Daban,,, Salon Wancan Daban...... Sai dai ya zama dole in gaya muku cewa....... Wancan Labarin Shine asalin Tushen Wannan.👏🏻 Da Fatan Zaku Bibiya tun daga Farko har Ƙarshe don jin Yaya Abun Yake..................* PAID BOOK NE......👏🏻 SHARE FISABILILLAH https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw 🪻SAWUN KEKE Season 2🪻 EP .......3 by INDO Yana tsaye k'ik'am tamkar wanda ya had'iyi ta'barya, Abee, Zahra, Mammi, Saim, duk suna tsaye a gefe curko-curko kamar wasu zakaru. Cike da fargaba tace "Affah Good evening!" Juyowa yayi yana fuskantar ta tare da zuba mata idanunsa masu matukar kaifi, murya can k'asa ya amsa da cewa "How are you Princess!" Sai da ta had'iyi wani k'ullutun yawu da yayi kaka-gida a mak'oshinta sannan tace "Am fine!" Shiru ne ya ratsa Falon na tsawon lokaci kafin Affah ya kalli Mammi cikin murya me cike da barazana yace "Where'd they go today?" 'dan numfasawa tayi kana tace "Basu gaya min ba, sai bayan sun dawo ne na tambayi Abee kuma ya gaya min Kubrah ta shiga Daji ne" "K'arya ya gaya Miki, Kuma Ina bukatar sanin gaskiyar yanzun nan!!" Ya karasa maganar cikin tsawar da ta sa Zahra da Kubrah suka k'ank'ame juna. Cikin in-ina Abee ya ce "Af... Affah....bab...ba.. nisa muka yi ba!" Cikin rawar baki Kubrah tace "Abee ya fad'i gaskiya" "Idan zaku kara magana ku tabbatar gaskiya kuka fad'a min; me kuka je d'aukowa a inda kuka je??, waye ya baku izinin fita??!!" Affah ne yayi maganar tare da binsu da kallon da yake nuna tsantsar fushinsa a zahiri. Abee ya ce "Ni ne , dama......" Tasss!! Ya d'auke Kubrah da wani lafiyayyen Mari Wanda yasa ganinta d'aukewa na wucin gadi, "Don Allah kayi hakuri!!" Shine abunda bakinta ya furta cikin daga murya....... Da sauri Abee ya dawo kusa da ita gami da rik'o hannunta idanunsa tuni sun kawo ruwan hawaye, cikin d'aga murya ya sake cewa "Affah Ni ne! Laif........." A wannan karon ma kasa k'arasa maganar yayi saboda saukar Wani zazzafan Mari akan kumatunsa. Cikin sauri yayi gefe da fuskarsa gami da saka hannunsa ɗaya yana shafar kumatun nasa...... cikin tsawa Affah ya ce ''Yi bayani mana!!!!" Cikin k'arfin hali Abee ya kara d'aga baki zai yi magana Affah ya Kuma dakatar dashi ta hanyar kifa masa wani k'erarren Mari Wanda ya tilasta masa sakin hannun Kubrah ya fara laluben iska. Kafin Affah ya k'ara d'aukar wani matakin Kubrah ta ce. "Zanyi bayani Affah,!!,    Ni ce na fita shi kuma ya bini ya dawo dani, kuma banida wani dalilin fita wanda ya wuce ina son ganin Mutanen da suke rayuwarsu tamkar Sakakkun tsuntsaye!,  don Allah ka yi hak'uri Affah!"  Numfasawa Affah yayi kafin ya bar musu wajen ba tare da ya ce kanzil  ba. Mammi ce ta kalle su cike da jin zafin dukan da suka sha tace "Ba kwa jin magana!, kun sani ba a shigowa Kuma ba a fita ba tare da izininsa ba, ta yaya ma kuke tunanin zaku iya fita Cikin Dubban Al,uma kuma ku dawo ba tare da ya sani ba?, ba na so ku k'ara maimaita wannan kuskuren" Cikin k'arfin hali Abee da bai gama warkewa daga rad'ad'in marukan da ya sha ba ya ce "Amma Mammi duk da na baki hak'uri meyesa kika gaya masa?". Cike da tausayawa ta ce  "Da ka lura da tambayarsa ta farko da ba zaka tuhume Ni ba, ba ka ji Ni ya fara tambaya ba?, da ace nayi k'arya domin kare ku nima sai na fuskanci nawa hukuncin" tana kaiwa nan tabi sawun Affah...... Zahra da Saim ne suka temakawa Abee da Kubrah suka mik'e daga k'asa duk suka nufi Bedroom domin Kuwa sai sun ji ruwan d'umi zasu iya jin dama-dama. A tsaye ta same shi Ya tsirawa window idanu hannayensa goye a bayansa. 'dan gyaran murya tayi sannan ta fara magana cikin nutsuwa..... "Amma Akhee! da yaya rayuwar yara ƙananu haka,,, zata yuwu a killatacciyar Duniya irin wannan?, kenan dai!, su basu da y'ancin yin rayuwa kokuma shiga cikin Mutanen da suka danganci kowane irin nau'i na Mutane??" Shiru ne ya ratsa tsakaninsu har na d'an lokaci.... Ganin ba shi da niyyar amsa mata yasa ta zagayo gabansa suna fuskantar juna, idanunta ta wulla cikin nasa kafin ta sake cewa "Ba kowace amsa bace shiru take gamsarwa!, akwai buk'atar fashin bak'i bayan yin shirun,,,, Kodai ka manta cewa Zahra ma ta fi shekara Uku ne?" Murmushin da bai wuce gefen laɓɓa ba yayi kafin ya ce "Na haifi Y'ay'a ne domin nayi farinciki tare dasu!, ba don Duniya tayi dasu ba..." 'Dan tsahirtawa yayi kafin ya ci gaba da cewa "Ni dake ba mu ishe su rayuwa bane?, Ko kuwa duk dangin da muke dasu basu isa a rayu dasu ba har sai an shiga wasu dangin daban?" Jinjina kai Mammi tayi sannan ta ce "Tana da kafiya da jajircewa akan abunda take son cimmawa ,na kamu da ts......." Kallo yayi mata me nuni da baya son zancen dole ta had'iye sauran maganar sannan ta tarkata ta fice". Washegari.... Duk wunin ranar Abee da Kubrah haka sukayi shi cikin sanyin jiki gami da damuwa wadda Basu san asalin ta ba. Musamman Kubrah duk ta firgice ita kad'ai take zabura har da kaiwa iska naushi. Bayan kwana Hud'u....... Kubrah tana zaune a gefen ƙawataccen swimming pool Wanda ke a Tafkeken Garden din gidan, k'afunta suna cikin ruwan tana lilo dasu a hankali a hankali. A zahiri dai tana zaune a gurin ne amma a gaskiyance kwata-kwata hankalinta baya cikin yankin ma gabaki daya bare cikin gidan, tayi matuk'ar zurfi cikin tunanin da yake shagaltar da ita a cikin kwanakin nan, ba zato ba tsammani taji an dafa kafad'arta , dogon numfashi me cike da firgici ta ja gami da zazzaro idanu waje ta tsaya ƙiƙam ko motsin kirki bata yi ba. Sai da ya zauna kusa da ita yayi irin zaman da tayi sannan ya ce "Firgicewar taki har ta kai haka?" Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce "Ban san kai ne ba" Murmushin kan la'b'ba yayi kafin ya ƙara sassauta murya ya ce "Meye damuwarki?" kasancewar basa ɓoyewa juna abunda ya shafe su yasa ta yanke hukuncin gaya masa. "Ni fa ina matuƙar son in ƙara fita, ba tare da kowa ya sani ba" kyawawan idanunsa ya zaro akanta a razane yana faɗin "What!??...... are serious?" "Yeah" ta bashi amsa kaitsaye, hannunta ya cafka da sauri gami da cewa "Why Kubrah!!? Ke bakya gudun 'bacin rai wai?" 'Dan numfasawa tayi kafin ta ce "I want to see him again, because I always think about him " "Yasalam!!" Ya furta cikin kad'uwa, cigaba yayi da cewa "What Are You think?, what will you say to him !?" (SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU) *Ba zan iya cewa wannan labarin cigaban wancan bane, domin kowanne Maudu'insa Daban.........👌🏻👌🏻👌🏻 Salon Wannan Daban,,, Salon Wancan Daban...... Sai dai ya zama dole in gaya muku cewa....... Wancan Labarin Shine asalin Tushen Wannan.👏🏻 Da Fatan Zaku Bibiya tun daga Farko har Ƙarshe don jin Yaya Abun Yake..................* SHARE FISABILILLAH https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw 🪻SAWUN KEKE Season 2🪻 EP .......4 By INDO Shiru tayi tare da zubawa hannunsa da yake k'ank'ame da nata ido, tana son yin maganar amma abun ya ci tura sai da ya k'ara maimaita tambayar sannan ta iya cewa "Hak'uri!!! Kalmar da zan fad'a masa kenan!!,,, bayan ita ba Ni da wani abun faɗar gareshi a yanzu, amma fa da zan samu dama,,,,, Allah ne kad'ai yasan adadin kalaman da zasu fito daga bakina". Dogon tsaki ya doka tare da janye hannunsa daga nata ya juya mata ƙeya zuciyarsa na wani irin tsalle.......... "Abee ! can't you help me?, babu wani abu daban da nake tunani bayan wanda na gaya maka!, ko kuskure ne bada hak'urin?" "Bada hak'uri ba zai taba zama kuskure ba, karya dokar Affah shine kuskure mafi had'ari, kiyi hak'uri Ni kam shirme na bai kai matsayin nan ba, ba nak'i bane k'arfina ne bai kai na gasgata hakan ba" Hawayen da sukayi kwanton 'bauna a cikin idanunta ne suka samu nasarar saukowa kan kumatunta , cikin sauri ta rik'o hannun Abee da yake shirin tashi ya barta, cikin rawar murya tace "Ban ce dole sai ka temaka min ba, nima ba na so laifina ya shafeka, sai dai yana da kyau in gaya maka kafin na aikata,,,,, amma da zaka temaka min zan yi farin ciki sosai! " ta k'arasa maganar tana murmushin k'arfin hali ga kuma hawayen da suka cigaba da ambaliya a fuskarta...... Tuni idanunsa sun kawo ruwan hawaye , Zuciyarsa tayi wata k'wak'k'warar tsinkewa. Cikin murya mai kama da raɗa ya ce " Kubrah ke ce Raunina, ganin hawayenki yakansa na manta cewa Ni namiji ne, faruwar wani abu gareki daidai yake da a sanya Takobi a tsaga Zuciyata, Ni zan cutu Indai har kika fad'a wani hali walau a cikin gida ko kuma a waje,,, Kubrah!!,,,,, Ganin ki cikin wannan yanayin yasa naji ina son shiga lamarin yanzu ba na tsoron abunda zai je ya zo burina shine kiyi farin ciki, amma wajibinki ne ki kula min da kanki sannan ki gujewa Had'uwar mu da Affah, kuma karki manta Affah ya gaya mana cewar Mutum ya fi Aljani illa don haka ki kula" "Na gode Abee zan yi duk yadda ka ce" ta fad'a tana murmushi. "In Allah ya kaimu gobe zan shiga Kasuwa daga nan zan sa a yi mana Bincike akansa da inda yake rayuwa, to daga nan ne zan baki dama ki fita, amma zuwa da dawowarki kar ya wuce 1 hour " gyad'a kai tayi gami da sauke nannauyar ajiyar Zuciya. ****************************** Umar da Ammar suna zaune suna fafata Muhawara kamar yadda suka saba a duk tsawon kwanakin nan tun bayan haɗuwarsu da Kubrah,,,,, "A karo na barkatai ina k'ara gaya maka cewa watarana zan k'ara ganinta,,, hakan Zuciyata take gaya min" Umar ya faɗa cike da son tabbatar da gaskiyarsa... "Ita dama Zuciya ai itace me tsara labarai da wanda zai yiwu da wanda ba zai taba yuwuwa ba,,, nima a karo na barkatai ina ka'ra gaya maka cewa Aljanu ne suka fara bud'e maka ido , Kubra ɗinnan sam ba Mutum ba ce, gabaki d'aya ka zare ka zauce sai surutai da tunane-tunane ! Duk ka dameni" "Ka zuba ido, da yardar Allah watarana za ka ganta kai ma" Yana shirin yin magana Yasmin ta shigo tsugul!.. babu ko sallama, tsayawa tayi ta rike ƙugu tana kallonsu kamar yadda suke kallonta sai dai yanayin kallon ya sha bamban , ita kallon raini take musu yayin da suke Binta da Kallon tuhuma. Taɓe baki tayi gami da doka musu harara ta ce "Mom tana kira" Daga haka ta juya ta fice tsigal-tsigal tana wata kwarkwasa. Tsaki Umar ya ja tare da tashi ya bi bayanta yana cewa "Ina zuwa Ammar" A d'an nesa da Mom ya zauna yana k'ara sauke rumfar ido, ganin yadda take wannan hucin ya tabbata yau Allah ne kaɗai zai ƙwaceshi. "Ban hana ka shigo min da ƙazamin Yaron can cikin Gida ba?, Don ubanka me yasa ba ka jin magana?" "He's my best friend Mom, Me yasa wai ni bani da Y'anci a Gidan iyayena komai nayi ba daidai bane?" Sakin baki tayi galala kafin ta ce "Okay har na fara fad'e kana mayar min? Kuma akan wancan kayan dattin?, wai anya kuwa kai ne d'an da na haifa ba canja min kai akayi ba?" Cikin kad'uwa ya d'ago idanunsa wanda suka cika taf da tarin damuwa ya zuba mata gami da cewa "Subhanallah! Mom....." Katse shi tayi ta hanyar ɗaga masa hannu gami da cewa "Don't tell me anything!, Kuma yau ya zamo na k'arshe da zan k'ara ganin ka shigo min da wani Matsiyaci gidana; ina so ka je ka yi masa korar kare ka nuna masa kai da shi akwai bambanci!" Cike da son barin wajen ya mike da sauri ya fara tafiya, tsayar dashi tayi da cewa " "Kuma gobe ka shirya akwai inda za mu je Ni da kai" Kasa magana yayi kawai ya ci gaba da tafiya, yana jinta ta cigaba da zazzaga Bala,i Yasmin tana tayata. Katari yayi da Ammar yana shirin fita, cikin sauri ya ce "Ya dai?" Ammar yayi murmushi fuskarsa ɗauke da damuwa yace "Na biyo bayanka ne da nufin in gaisar da Momy sai in yi maka sallama in wuce Gidanmu, yanzu baka buƙatar sake faɗa min saƙon Momy!, Ni a kowane lokaci ƙofar gidanmu a buɗe take gareka, zaka iya shiga lokacin da kake so kuma ka fita lokacin da kaso , saboda kai ma ɗa ne a gidanmu, amma gidanku in sha Allahu ba zan ƙara zuwa ba, ba zan temaka maka mu bujirewa umarninta ba, sai dai hakan sam bai taɓa alaƙarmu ba" shiru yayi gami da ɗaukar idanunsa da suka ciko taf da ruwan hawaye ya zubawa Ammar. Dafa kafaɗarsa Ammar yayi gami da cewa "Kar ka ji komai, ni ina tare da kai , kuma nasan kai ma haka" gyaɗa kai yayi cike da son gazgata abunda Ammar ya faɗa, ɗorawa yayi da cewa "Ka faɗi gaskiya, amma hakan ba zai hana ni baka haƙuri ba Ammar!, a madadin dukkan Ƴan Gidanmu ina me baka haƙuri, kuma ina fatan wataran zaka sake ziyartata a cikin gidan........" katse shi yayi da cewa "Umar indai lafiya ƙalau to babu abunda zai sa na zo gidanku, Ba zan yi fatali da Umarnin Momy ba!, ni yanzu nake son tafiya in zaka kaini to mu je" Hawayen da yake ta ƙoƙarin dannewa ne suka yi nasarar kwararowa kan kumatunsa, "Ina zuwa, zan kai ka da kaina" ya faɗa gami da nufar hanyar komawa sashinsa domin ɗauko key. washegari..... Kasuwar Kwari..... misalin ƙarfe 3:21pm Ammar yana zaune a shagonsu wanda ya kasance na haɗin gwiwa tsakaninsu , Umar ya faɗo kamar wanda aka jefo daga sama, cikin mamakin ganinsa Ammar ya ce "Laa!" Kafin ya rufe baki Umar ya ce "Meye wani laaa! sai kace wani Mace ??" "To ai ban yi tsammanin ganinka ba ne" ya faɗa yana dariya nemar waje Umar yayi ya zauna sannan ya ce "Momy fa ta kaini inda take son kaini, wai Aure take so in yi ni kuma gaskiya bana ra,ayi" Ammar ya Ajiye wayar hannunsa ya dawo da hankalinsa kan Umar sannan ya ce "Ina ganin kawai ka yi biyayya, kai ma kanka zaka fi samun kwanciyar hankali, maybe zaka dena ma tunanin wannan Aljanar" Murmushin takaici Umar yayi kafin ya ce "Da a ce wata Matar ce daban da zan Aure ta, amma wannan dai ba ta yi min ba, ina son kusanci da wanda zai dinga mutunta ni ya mutunta Abokaina da duk wanda nake mu'amala dashi,,, na rasa hakan daga ƙannena da iyayena zan so in samu daga Matata, amma in na sake na Auri wannan yarinyar zan rasa wannan mafarkin har Abada" ɗan ƙaramin tsaki Ammar yayi kafin ce ""Ba na so ka tsallake wannan damar Bro, kana buƙatar ƙarin kusanci da iyayenka, ina ganin yin hakan zai kawo maslaha amma kai ba ka ganewa" "Indai akan haka ne ba zan gane ba, abu ɗaya ne kawai,,,, nasan na fi su gaskiya, Ammar ko ni bata mutunta ni ba bare kai bare kuma sauran mutanen da suke tare damu, domin Allah in ka ga na Aureta sai tsananin rubutun ƙaddara wanda bana fatansa, don haka ka janye wannan maganar taka, ka ga wata shigar banza da tayi kuwa? wai a hakan zatayi haɗuwar farko da Bahaushen Saurayi irina, haba ! Impossible wallahi" Ammar ya ce "Kana da kafiya Umar, don Allah ka dinga tausasawa akan wani abun mana, Aure fa ba zai taɓa zama kuskure ba" "Amma Aurar Matar da zata haifi Ƴaƴan da basu da rana kasan dai shine mafi girman kuskure ko?, ka manta da ita kawai Ammar,,,,,,, ni fa wallahi da na san Gidan su Aljanar nan da ba shakka ita zan ɗauko in nunawa iyayena a matsayin wadda zan Aura!" ido Ammar ya zaro tare da faɗin "What!? kai fa ka gama zaucewa Aboki, na gaya maka Aljana ce ba zaka ganta ba!" ya ƙarasa maganar cikin ɗaga murya, Umar ya ce "Ni fa ban yarda ba, kuma in baka sani ba yanzu kullum ji nake tamkar na ƙara kusanci da ita , a duk lokacin da nake tunaninta nakanji tamkar tana kusa dani, haka bugun Zuciyata yake nuna min" "To Allah ya bada sa,a tunda na faɗa ka ƙi yarda, inda zaka yarda ko iya hakan ma ya isa tabbatar maka Aljana ce" "Sai kayi kuma" Umar ya faɗa gami da miƙewa ya nufi wajen Yaron Shagon wanda yake ta fama da costumers. ___________________________________________ Yau......... akan hanyarsa ta komawa Gida, yana driving yana tunane-tunane bai ankare ba sai da ya kusa yin awon gaba da wani ƙoshashshen Doki a gabansa, da sauri ya taka burki tare da zazzaro ido, a take Zuciyarsa ta fara wani bugu da ƙarfi kamar wanda aka sanyawa wuƙa a maƙoshi ana shirin yankawa. Cikin sauri ya fito daga motar ya nufo wajen Dokin cike da fatan yayi tozali da wadda Zuciyarsa take marari. "Umarh!" sai da numfashinsa ya ɗan samu tangarɗa lokacin da zazzaƙar muryarta ta bashi ƙararrawar sanarwa a cikin kunnensa, da sauri ya juyo baya inda yaji muryar ta fito, tuni jikinsa ya fara wata irin karkarwa wadda bai san sanadinta ba, abu ɗaya kawai zai iya bada shaida shine muryarta da kuma yadda ta furta sunansa cikin salo mai matuƙar taɓa zuciya da ƙwaƙwalwar Ɗan Adam sun fi komai dagula masa lissafi, sai da yaji tsigar jikinsa ta tashi yarrr!!!. Babu shakka da yana da nutsuwa a wannan lokacin da ya yi nazari akan kalaman Ammar na cewar Aljana ce , sai dai ba shi da wannan ƙwarin gwiwar a yanzu. Ido ya zuba mata yayinda ita ma take kallonsa idanunta cike taf da hawaye, Cikin rawar baki ya furta sunanta cikin salo makamancin nata sai dai shi ya haɗa da alamar tambaya "Kubrah!!!?" gyaɗa masa kai tayi alamar eh, kafin ta sakar masa murmushi wanda ya ƙara susuta shi, "Ka yi haƙuri Umar!!" ta faɗa tare da yin gefe da kanta. ɗan numfasawa yayi kafin ya ce "For what?! me kikai min?, wai Kubrah don Allah wacece ke??" (SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU) *Ba zan iya cewa wannan labarin cigaban wancan bane, domin kowanne Maudu'insa Daban.........👌🏻👌🏻👌🏻 Salon Wannan Daban,,, Salon Wancan Daban...... Sai dai ya zama dole in gaya muku cewa....... Wancan Labarin Shine asalin Tushen Wannan.👏🏻 Da Fatan Zaku Bibiya tun daga Farko har Ƙarshe don jin Yaya Abun Yake..................* SHARE FISABILILLAH https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw 🪻SAWUN KEKE🪻 Season2 EP .......5 By INDO Shiru bata bashi amsa ba sai ma kallon Ahmadi dake gefenta takeyi. Umar bai fahimci me yake faruwa ba sai da ya ga Ahmadi ya fara zayyano masa cewar Gimbiyarsa tana da muradin bashi haƙuri ne koda babu silar hakan. "Amma ai ita na tambaya ba kai ba, ba zan ƙara samun kyautar Jin zazzaƙar muryarki bane Kubrah!" sai da yayi ƙoƙarin gaske sannan ya iya zuwa ƙarshen maganar duba da yadda take futowa da ƙyar tamkar wanda bai taɓa kurɓar ruwa ba. Ahmadi zai ƙara magana ta dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu, ta sauke ajiyar Zuciya sannan ta fara magana tana kallon Ahmadi "Ahmadi ka gaya masa na Fasa masa abunsa ranar nan, ni ban san meye daɗinsa ko akasinsa ba, abu na biyu kuma nasan dole sai yayi jinya Bisa wurga masa Kibiya da nayi duk da bata same shi sosai ba amma dole zata taɓa shi!, sai abu na uku shine shigowa rayuwarsa da nayi, dole in bashi haƙuri akan hakan domin ban sani ba Farar Sa'a ce ko akasinta" Tuni Umar ya zagayo kusa da Ahmadi don ya fi kallonta da kyau ko zai fahimci halin da yake ciki, lissafin bai warware masa ba sai ma ƙara shiga wani lulluɓin da yayi, ya fahimci cewa tana magana ne akan wayarsa da ta fasa da kuma ganinsa ma da tayi gabaki ɗaya, cike da ƙarfin hali ya ce "Amma wacece ke? a ina kike, meyesa na ga kin bambanta da Matan da na sani a wannan Nahiya tamu?, kuma meyesa ba zaki yi magana dani kai tsaye ba dole sai ta hanyarsa?" murmusawa tayi kafin ta ce "Ahmadi ka gaya masa cewa na yiwa ɗan uwana Alƙawarin kalmar haƙuri kawai zan faɗa masa, sauran tambayarsa kuma basu da amsa domin gabaki ɗaya Rayuwata Tambaya ce babba, wadda ni kaina ban san amsarta ba; Bayan ka isar da saƙon sai mu tafi don gudun saɓa lokaci" da sauri Umar ya ce "Na ji ki, ba sai ya faɗa ba, hakan ma na gode, iya ganinki ma babbar Ni'ima ce Allah yayi min Allah ya kai ki gida lafiya yake wannan kyakkyawar halitta!!" Ya ƙarasa maganar gami da sakin murmushi wanda yayi daidai da zubowar hawayensa ba tare da ya shirya ba. Lumshe idanunta tayi gami da jan dogon numfashi ta sauke shi tare da nannauyar ajiyar Zuciya, hawaye sun so ɓalle mata amma tayi ƙoƙarin dakatar dasu, ba tare da ta ce komai ba ta haye Dokinta ta zabure shi. Ya ɗan jima a wajen yana tunane-tunane har sai da wani me mota ya fara masifa akan cewar ya tsaya kan hanya sannan ya koma Motar ya janyeta, don ma cikin unguwa ne da Allah ne kaɗai yasan go slow da zai tara. fasa shiga Gidan nasu yayi ya sauya akalar tafiyar zuwa gidan su Ammar domin ya bashi tabbacin yau ya ƙara ganin Kubrah. koda ya zayyana masa abunda ya faru ƙin yarda yayi sai cewa yayi Aljanun ne dai suka ƙara buɗe masa ido. Dolensa ya haƙura tare da fatan Allah yasa wataran tazo a lokacin da suke tare. ____________________________________ Abee ne ya kalli Kubrah wadda tayi zurfi a cikin tunani, ya murmusawa gami da cewa "Yanzu kin yi farin ciki ko?, kuma mun yi sa,a Affah bai gane ba" "Ba ƙaramar sa,a muka yi ba , kuma nayi farin ciki amma bai kai yadda nayi tunani ba; nayi zaton bayan haka zan manta dashi kwata-kwata amma sai naga ashe ba haka bane, sai ma sauya salo da tunanin nawa yayi" "To fa!, kin iya tarairayar masifa ke kam; to ni dai bana son ƙara jin wani abu akansa, ki manta dashi kawai" ɗan kallonsa tayi ta ɗauke kai sannan tace "Dole ne hakan ai, duk da cewar akwai wuya, yau fa 1 week kenan da haɗuwarmu amma har yanzu komai sabo yake a wajena" "Kin ga , canja wata maganar na gaji da wannan" murmushi ta saki kafiin ta ce "Wadda zan kawo ɗin ma ba mai kwantar da hankalj ba ce, ina son Waya ne kuma da gaske nake, in ban sameta ba hankalina ba zai taɓa kwanciya ba!" zaro ido yayi yana cewa "Waya dai irin wadda kika fasa wa Umar??!!" gyaɗa kai tayi tana cewa "Ba shakka ita nake nufi , inaso in san amfaninta da kuma haɗarin nata" ya wangame baki zaiyi magana tayi saurin tsayar dashi ta hanyar riƙo hannunsa tana cewa "Don Allah kar ka ce min a'a, ka temaka min in samu!" Idanu ya tsira mata jiki a sanyaye yace "Amma ke meyasa ba kya ƙauracewa abunda ya zamo tashin hankali ?" marairaicewa tayi tace "Abee don Allah!, nasan akwai rigima amma fa sai in Affah ya sani, kuma ba za mu bari ya sani ba" nazari ya ɗan yi kafin ya ce "Kin tabbata ba zaki bari ya sani ba?" gyaɗa kai tayi tana murmushi, ya ɗan numfasa sannan ya ce "Na san Uncle Isah ya kusa zuwa, in ya zo sai mu yi masa maganar, kin ga ba mu san inda ake siyarwa ba" da sauri ta ce "Yawwa hakan yayi, Allah yasa yazo yau" "Ba zai zo ba ma karki sa rai" Ya bata amsa gami da jan hannunta suka bar wajen. Duk wannan lokacin zaman saurare Kubrah take yi, bata da burin da ya wuce ta ga Uncle Isah ya zo, yaci ace yayi zuwa uku amma a wannan karon ko ɗaya bai yi ba, ko da tsara shirin nasu yau kwanaki uku kenan. Har ta gaji ta fara cewa zata je ta nemo da kanta. Suna zaune a tafkeken Falo wanda ke a tsakiyar Gidan suna hira sai ga Affah ya shigo , kallon inda suke yayi gami da cewa "Uncle Isah ya zo" bai jira cewarsu ba ya wuce gaba, da sauri Kubrah ta miƙe tana cewa "To bari in kai masa abun sha" dakatawa yayi da tafiyar hakan bai wadatar ba har saida ya juyo ya ƙare mata kallo bai ce komai ba ya ci gaba da tafiya. Ɗan numfasawa tayi kafin tace Abee zo ka raka ni. Saim ma miƙewa yayi yana cewa , "Ni ma bari in tashi tun kafin a tashe ni" A Falon da suka saba zaman karatu suka same shi, tuni har an kawo masa kayan ciye-ciye, Kubrah tafi kowa matsawa kusa dashi, ko gaisawa bata bari sun yi ba ta ce "Uncle Don Allah irin wannan abun nake so!" Fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "Wanne kenan Ƴata?!" Abee ta kalla cike da son ƙarin bayani, ɗan sosa ƙeya yayi sannan yace "Uncle,! She's talking about phone" shi kansa maganar ta girgiza shi, bai san lokacin da ya zazzaro ido gami da maimaita sunan "Phone?" ɗin ba, gyaɗa kai tayi domin ba shi tabbaci. a gefe guda Saim da Zara suka haɗa baki wajen jefo mata tambaya Saim ya ce "What will you do with it?!!!!!" Zahrah ta ce "Me za kiyi da waya kuma??" "Nothing ! kar ku damu kanku, kawai ina so ne" shiru ne ya ratsa tsakani mamaki ya hana su ƙara yin magana, Abee da Kubra kuwa jiran amsa suke daga Uncle Isah. sai da ya sauke gwauron numfashi sannan ya ce "Gaskiya ba zan iya baki wannan goyon bayan ba, ba naƙi bane amma kiyi haƙuri kawai!" sai da ya rufe baki sannan ta ɗauke kallonta daga kansa gami da cewa "Shi kenan, zan nema da kaina bana buƙatar goyon bayan kowa tunda Abee yana tare dani" Bai ƙara yin magana akai ba sai ma cewa da yayi "Yau kawai na zo ganinku ne, ba zan iya baku kowane darasi ba don banida isasshiyar lafiya" Saim ya ce "Ai na ga alama, me yake damunka ne Uncle?" rausayar da kai Uncle Isah yayi tare da yin dukkan ƙoƙarinsa wajen danne sirrin dake ɓoye a Zuciyarsa, '"Saim koda na yi maka bayani ba zaka gane ba, idan ba damuwa zaku iya tafiya ku turo min Yallaɓai?" Kubrah ce ta fara tashi fuuuuu!! tayi gaba Abee ya bi bayanta yana kiran sunanta. Saim da Zahra ma tashi sukayi suka nufi cikin gidan dan isar da saƙonsa. Nannauyar ajiyar Zuciya ya sauke yana rarraba idanu. Duk da Sanyin AC dake dukansa hakan bai hana zuffa tsatstsafo masa ba, duk lokacin da ya tuna ƙudurinsa akan mai gidan nasa yakanji Zuciyarsa ta buga da iya ƙarfinta!. Yana nan zaune yana tufka da warwara Affah yayi sallama, a ɗan firgice ya amsa gami da gyara zamansa yana kakalo fara,a. Zama Affah yayi yana tsura masa ido kafin yace "Me ya faru da kai ne?" da ƙyar ya nemo jarumta ya aza sannan yace "Babu komai kwana biyun nan ne nake wani Ɗan zazzabi, amma ba wata damuwa" gyaɗa kai yayi alamar ya gamsu da hakan, ya ƙara da cewa "Ina saurarenka da fatan dai ba Yara ne sukayi wani shirmen ba!" daidaita nutsuwarsa yayi sosai sannan yace "Alfarma nake nema in ba damuwa!, Ƴata Fatima ita kaɗai ce nake zama in bata labarinka,,,, a wannan lokacin ta ce min tana so tazo nan ta ɗan kwana biyu , shine nace zan nemi wannan Alfarmar!". Murmusawa Affah ya ɗan yi kafin ya ce "Shine abun neman Alfarma?, a gaya mata nan ma gidansu ne!" shiru Uncle Isa yayi saboda wani mashi da ya soki Zuciyarsa...... "Me yasa rayuwa ta canjani haka? wanda yake zaune dani da zuciya ɗaya shi nake shirin cutarwa!" abunda ya faɗa kenan a zuciyarsa, Affah ne ya katse shi da cewa "Akwai wani abun ne bayan wannan?" cikin sauri ya girgza kai gami da cewa "A'a babu, so nake in tambaya Yaushe zan kawo ta?" "Duk lokacin da ta shirya ƙofa a buɗe take" ya faɗa yana ƙoƙarin tashi, ƙarawa yayi da cewa "Na gode da ƙoƙarinka gare ni" Uncle Isah yayi murmushin ƙarfin hali kafin ya ce "Nauyi ne wanda ya rataya a wuyana, ka dena yi min godiya Yallaɓai!" Affah ya ɗan murmusa ba tare da ya ce komai ba. Yau Tun da Safe ta shirya ta saci hanya ta fice daga gidan, babu wanda ya san ta fita sai Abee shi ma don ya zame mata dole ta faɗa masa. Kai tsaye Ƙofar gidan su Umar Ahmadi ya ci burki da ita, cike da girmamawa ya kalleta gami da cewa "Wannan shine gidan da Suke rayuwa shi da iyayensa!" "Yanzu ta yaya zan ganshi?, gashi Gidan Babba ne sosai, ban san a wane sashi zan iya samunsa ba!" Ahmadi ya ce "Gimbiya kuma Uwar Masu gida!! wannan gida duk girmansa bai kai ya Gidanku ba! don haka memansa ba zai mana wahala ba Ranki-ya-daɗe , naga idan Baƙo ya zo aika yake yi cikin gidan ayi sallama, ina ga hakan zamuyi ko ?" ɗan tsaki tayi tace "Ashe ka san da hakan ka zo ka ajiye ni a nan?". "A gafarce ni" ya faɗa yana rusunawa. Waige-waige ya fara yi ko zai samu ɗan aike amma fayau kasancewar Unguwar manyan gidaje ne zalla shiru babu masu fitowa zaman kan layi" ganin wankin hula yana neman kaisu dare ya sa Kubrah ta sa kai ƙofar gidan ta fara nocking. ta ɗan jima tana yi kafin Mai Gadi ya buɗe ya leƙo yana cewa "Kai Bana son hayya-hayya!! waye ne!!??" ganin wata sabuwar halitta a gabansa ya sa yayi saurin saita nutsuwarsa ya gyara tsayuwa yana zuba mata ido. "Na ce ko zaka kira min Umar?" caraf! ya amsa da cewa "Ke a suwa? Umar gadan-gatsai babu taunawa?! Yallaɓai ko kuma Me gida haka za ki ce, ki bar gani Allah ya hore miki kyau ɗinnan wallahi in ba a ban izini ba ba zaki shiga ba ehe!". murmushin takaici tayi kafin ta ce "A gurinka ne yake da wannan sunan, amma ni a wajena da kai dashi duk bayi ne!" yadda ta faɗi maganar cike da ƙwarin gwiwa yasa Mai gadi ya sarara don kuwa irin kuɗi da ƙarfin ikon da Mahaifin Umar yake dashi ko masu kuɗin ba zasu iya ɗaga baki su kira shi bawa ba, jin hakan daga gareta kuwa ya tabbatar masa bata fito ba sai da ta shirya. ƙare mata kallo yayi sama da ƙasa kafin ya jinjina kai yana cewa "To yanzu na gane!, Girl friend dinki ne shi ko?, bari in kira shi yi haƙuri Hajjaju" kafin ya juya tace "Malam! ni Mace ni ce girl friend ɗin ba shi ba, ƙato sukutum dashi" ,, Yanzu zaka iya kira min shi?" "An gama!" ya faɗa gami da nufar inda zai samu ƴan aikin da aka sahalewa shiga gidan. (SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU) SHARE FISABILILLAH https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw *🪻SAWUN KEKE🪻* Season 2 EP .......6 By INDO Fitowarsa kenan Parlour da shirin tafiya Wajen nemansa Shamsiyya ta ƙaraso tana raɓe-raɓe a can gefe ta sanar masa saƙon. Bata faɗi suna ba sai suffanta kamanni kamar yadda Mai gadi yayi mata. yana jin haka zuciyarsa tayi wata ƙwaƙƙwarar bugawa. Da sauri ya nufi hanyar fita yana gyara zaman bag ɗinsa akan kafaɗarsa. "Wata Matsiyaciyar ka gayyato mana kuma?" Mommy da ke kan stairs tana saukowa ta jefo masa tambayar . jim! ya ɗan yi kafin ya ce "Duk da ban san asalinta ba amma na tabbata ta fi ƙarfin Tsiya Mommy!, ko ni da nake ɗan masu arziƙin ni ba Komai ne a wajenta ba! matsayina bai wuce na Boyi-boyinta ba!" suman tsaye Mommy tayi hakan yasa ta gaza furta wani kalamin, shi kuwa hakan dama ce ta fitarsa. tuni ya fice harda gudu-gudu. Tana tsaye a inda take ɗazu fuskarta babu alamun annuri. "Kubrah!!" bakinsa ya furta a lokacin da idanunsa suka sauka akan fuskarta. Ɗago idonta wanda ya fara rikiɗa yana sauya kala tayi ta zuba masa kafin ta ce "Shine sai an wulaƙanta ni saboda na zo neman alfarma wajenka?" kallon kallo suka yi shi da mai gadi wanda yake maƙale a bayansu yana kallon ikon Allah. Da sauri ya ce "Wallahi umarnin Hajiya Babba na cika Yallaɓai!" maida hankali Umar yayi zuwa kanta, cikin tattausar murya ya ce "Amma ni ban san da hakan ba bare in wulaƙanta ki, kuma bana fatan ki nemi Alfarma a wajena Kubrah!, saboda nasan alfarmarki ta wuce ki tsaya nemanta!, ina yi miki barka da zuwa ƙofar gidanmu!" ya ƙarasa maganar yana murmushi. bata san lokacin da ta saki murmushin ba, ta ɗan numfasa sannan tace "Ai Kowa a Fadarsa Sarki ne Umar!, ina gaisuwa!" . Lumshe idanunsa yayi gami da jan dogon numfashi , jin kansa yake kamar me shirin faɗawa dogon suma, Zuciyarsa sai dukan sittin saba'in take amma duk da haka yau a nutsuwarsa yake ba kamar wancan lokacin ba. "Amma akwai Wanda in Sarauta ta kai Sarauta duk inda ya shiga ma Sarki ne, hatta Sarakunan ma gani za kiyi suna zube gwiwoyinsu a ƙasa suna ɗibar Gaisuwa" murmusawa tayi gami da cewa "Amma dai anan kai ne Sarkin!, don haka zan je maganata kai tsaye, ina son siyen Waya ne da fatan kai ma ba za ka ƙi bani goyon baya ba" Kasancewar bai san dawan garin ba buɗar bakinsa yace "Abu me sauƙi ma irin wannan shine sai kin tsaya wahalar da kanki??,,,,, amma wani hanzari ba gudu ba waye bai baki goyon baya kan siyenta ba?" farr! tayi da ido kafin ta ce "Wannan abunda ya shafi rayuwata ne, yanzu dai ka raka ni in siya don sai na zaɓa" ta ƙarasa maganar tana miƙawa Ahmadi hannu, da sauri ya ƙaroso gami da miƙo mata wata ƙaramar jaka dake hannunsa. buɗewa tayi ta zaro wata narkekiyar Sarƙa wadda kallo ɗaya Mutum zai mata ya ganeta muddin yasan gold... Idanun Umar kamar zasu faɗo ƙasa sabida zaro su da yayi. miƙa masa tayi tana cewa "Karɓi wannan, duk da ban san kan abun ba kawai ina sakawa ne , amma nasan yana da Daraja, idan muka siyar muka ga kuɗin bai kai a siyi wayar ba Sai in haɗa da wanda yake wuyana!, ga ma wannan !!" ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin saɓule awarwaron hannunta. "Yasalam!!" Umar ya furta yana me ƙara buɗe idanunsa a kanta, a duk wani motsi nata ƙara jefa shi cikin ruɗani take yi, ga tarin tambayoyi da Zuciyarsa ke son yi mata kuma a ƙalla duk yana buƙatar amsar su,,, sanin ba lallai ya samu ba ya sa shi danne mamakinsa ya ce "Haba Kubrah! in banda ƙuruciya ai ko ni zan siya miki Waya ba sai kin Ɓatar da wannan Dukiya haka ba, ki mayar ki ajiye zan siya miki da kaina!" girgiza kai tayi ta ce "A'a ina da Dukiyar da zan iya siya da kaina wallahi ba roƙonka na zo yi ba Umar, dan dai Affah baya so ne amma da ba abunda zai sa Wayata ta biyo ta hannunka, don ban san yadda ake siyowa ba ne da can zan tafi kai tsaye " "Oh!! Ya Allah, haba Kubrah ! bana nufin haka, na san kin fi ƙarfina wallahi, amma duk da haka nasan baki da girman kai, shiyasa ma nace zan baki Waya a matsayin kyauta ba wai don na isa ba,,,,,,, ki karɓa don Allah". Shiru ne ya ratsa tsakaninsu kafin ya katse shirun da cewa "Idan akwai matsala a cikin hakan to ba damuw...." katse shi tayi da cewa "Ba komai, zan iya samu yanzu?" " Sosai ma kuwa, za mu iya tafiya tare? " "Zuwa ina?" "Oh Kasuwar nake nufi ki tafi tare dani, nima a yanzu fita zanyi, bari in fito da Mota ko?" girgiza kai tayi gami da cewa "A'ah! nafi son na tafi a inda na zo, kayi gaba zan biyo bayanka, kuma ina ba ka haƙuri a bisa hakan" rausayar da kai yayi kafin ya ce "Shi kenan, karki damu akan bani haƙuri ni hakan bai zama laifi gareni ba, ki jira ni zan fito yanzu" sai da ta gyaɗa kai alamar ta amsa maganar tashi sannan ya juya ya shige cikin gida. Kafin ya fito ya kira wanda yake siyen waya a wajensa tare da gaya masa ya kai masa ita Wajen Sana'arsu. Haka suka yi tafiyar daban-daban ita da Ahmadi a Doki suka saba yawo don haka a shi ne suke biye da Umar wanda yake cikin Motarsa. sai da suka je wajenn tsayawa sannan duk suka Tsaya Umar ya ƙara jan su zuwa Inda makeken shagonsu yake. Wasu lokutan sai dai ya juyo ya ga Kubrah ta tsaya ƙiƙam tana kallon jama,ar da suke kaikawo da kuma Kayayyakin da ake saidawa. Haka yayi ta lallaɓarta har suka isa Shagon. Sallama ya rangaɗa kafin ya kutsa kai ciki, Ammar yana zaune yana mita akan wayar da ya ga An kawo, ganin Umar yw sa shi cewa "Yawwa dama jiranka nake, Mai Kuɗi Uban Fuƙara'u!, bayan waccan wayar kuma meye haɗinka da wannan? kuma fa irin waccan ce, ni bana son Almubazzaranci" Dariya ya ɗan yi kafin ya ce "Ita wannan ɗin ba tawa bace, tawan gata a hannuna" "A'a to wai wa ka siyowa ne??" ya jefa masa tambayar cike da mamaki, wata Budurwa da take tsaye gefensu ta bashi amsa da cewa "Haba kai ka fiye tambaya , mutum da kuɗinsa??" kallon sama da ƙasa Umar yayi mata kafin yace "Too! ikon Allah!" Hankalinsa ya mayar kan Ammar kafin ya ce "Yau dai Allah ya nufa za ka ga Kubrah da idonka, a karo na biyu" Zumbur! ya miƙe tsaye yana zazzaro ido gami da tambayar "Wadda na sani dai???, nifa wallahi gabana sai da ya yanke ya faɗi!" Dariya Umar yayi kafin ya fita bakin shagon ya yiwa Ahmadi da Kubrah iso. Ba iya Ammar ba duk ilahirin Matan da suka ɗan taru a Shagon suna zaɓen kayan siya sai da suka yi Suman tsaye gami da tsayawa kallon Ikon Allah. ganin irin Kallon da ake yi mata na Mamaki ya sa taji gabaki ɗaya ta fara tsarguwa, Bayan Ahmadi ta koma ta maƙale ta ci gaba da zazzaro ido daga nesa. Cikin sanyin jiki ta kalli Umar ta ce "Ina so in tafi gida" hannu ya ɗora kan kafaɗar Ahmadi yana shirin ture shi don yafi ganinta , Ahmadi ya ture hannun nasa yana cewa "A'a Yallaɓai!, yarda da kai da Uwar Ɗakina tayi shi yasa aka bani amanarta don in kawo ta ku gana, amma naga ka kawo mu wani guri daban" Ɗan shafar sumar kansa yayi cikin sanyin jiki ya ce "Allah ya bada haƙuri!" Ammar ne ya matso wajen yana cewa "Kubrah! wai ke ce dai wadda na gani rannan?" gyaɗa kai tayi alamar Eh , sai da ya haɗiye yawun bakinsa da ya fara bushewa sannan ya ce "Sunana Ammar ni Aboki ne ga Umar!" Umar yayi saurin katse shi da cewa "Kubrah wannan Shine Ammar!, ba iya Aboki yake a wajena ba shi ɗan Uwa ne mafi soyuwa gareni!, a cikin gajeriyar rayuwata a wajensa ne kawai nake samun farinciki, akanki ne dai ya kasa Yarda da maganata sai yake gani na tamkar Mahaukaci, kuma hakan ya samo asali ne saboda baki gaya min wacece ke ba!" Murmushi tayi sosai kafin ta ce "Sannu Ammar!, ni rayuwata Sirri ce! ba wai gabagaɗi ake yin zurfi a cikinta ba, amma in lokacin sani yayi maybe zaku sani" mayar da hankali tayi kan Umar ta ce "Ko zan iya samun wayar yanzu?" Jiki na rawa Ammar ya ɗauko ya miƙo yana cewa "Komai ya kammala har layi an saka akwai lambar Ɗan Uwana a ciki nasan......" da sauri Umar ya katse shi da cewa "Haba kai kuwa ka bari in yi bayani da kaina mana?!" miƙa masa wayar yayi yana cewa "Sai kayi ai" Murmusawa yayi kafin ya damƙa mata tare da yi mata bayanin layin da ya saka mata. Godiya tayi masa sannan ta ɗauki hanyar komawa gida.......... (SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU) WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE SHARE FISABILILLAH *🪻SAWUN KEKE🪻* season *2* EP .......7 By INDO https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw Sai bayan ta tafi ne Ammar ya samu damar cewa "Lallai ka fi ni gaskiya Umar, dukkan Yabo da godiya su ƙara tabbata ga Allah!!,,, wallahi Umar gabaki ɗaya yarinyar nan ita kanta Al'ajabi ce" dariya kawai Umar yayi don ganin yadda Ammar duk ya ruɗe, shi dai yayi sa'a wannan lokacin bai yi wannan burkicewar ba kodan za a iya cewa zuwa yau ya ɗan saba da ita. Budurwar da ta saba shishshigi cikin maganar su ce ta kalli Umar tana cewa "Wanda yake soyayya da wannan Baiwar Allah babu wata mace da zata ƙara burgeshi a Duniya, wallahi dama ni ce" Sakin bakuna sukayi suka kallonta cike da takaici, daman tun ba yau ba Ammar ya gane take-takenta hakan ya sa suka dena sakar mata fuska sosai saboda rashin kamun kanta. Kubrah tayi sa'a har ta fita ta dawo babu wanda ya gane.... Hakan yayi musu daɗi sosai ita da ƴan Uwanta sai murna suke sun samu abunda za su dinga leƙen Duniya daga ɗakinsu. Har akayi kwana biyu Babu abunda ya faru hakan ya sa suka saki jiki suka fara raƙashewa. Wani lokacin Duk su huɗun suke haɗuwa a Ɗan madaidaicin Falonsu su kulle ƙofa sannan su fara latse-latse a wayar. Misalin ƙarfe 9:12PM Umar yana zaune a bakin Gado ya doka tagumi ya zubawa lambarsa wadda ta zama tata ido, sai yayi kamar ya kira amma sai ya fasa sabida raɗe-raɗe da zuciyarsa take ta famar yi masa...... a karo na ƙarshe dai rufe ido yayi ya tura kiran zuciyarsa na ta famar tsalle amma ya jure duk da hakan. Kiran farko Network ya hana shi shiga, sai da ya kuma kira sannan ya shiga, ta daɗe tana ringing sannan ta ɗauka ba tare da tayi magana ba. Sallama ya yi kafin ya ɗora da ambaton sunanta wanda ya kusa zabe masa ɗabi'a,,,, cikin sauri ta cafki hannun Abee ta riƙe shi gam tana cewa "Abeeh!! Umar ne!" Fasa tafiya Abee yayi ya zauna kusa da ita yana cewa "Ki haɗa ni dashi muyi magana" cikin sauri ta miƙa masa wayar jikinta na karkarwa , dama ba lallai ta iya magana ba don kuwa tayi matuƙar kaɗuwa da jin muryarsa. ɗan gyaran murya Abee yayi sannan ya ce "Da fatan kana lafiya!" sai da Umar ya furzar da zazzafar iska sannan ya amsa "Ina lafiya!" ''Okay nice, na gode da karrama Ƴar Uwata da kayi kuma har ta samu kyauta daga gareka, amma don Allah na roƙe ka ka dena mafarkinta! sannan ka dena tunaninta" zumbur! Umar ya miƙe tsaye kamar an tsikare shi, wani duhu ne ya fara zagaya masa tun daga cikin ƙwaƙwalwarsa har zuwa idanunsa hakan ya tilasta masa durƙushewa kan gwiwoyinsa, cikin wata sarƙaƙƙiyar murya wadda take nuni da tsananin hargitsin da ya shiga ya ce "Amma me yasa??, baka yi tunanin cewa ba ni na zaɓawa kaina hakan ba Yaya!" kallon-kallo Abee da Kubrah sukayi suna haɗa ido tayi ƙas da kai hawayen da take ta ƙoƙarin dannewa suka fara silalowa kan kumatunta, janyota ya ƙarayi ya rungumeta acikin ƙirjinsa yana ɗan bubbugar bayanta a hankali...... sai da sakanni suka shuɗe sannan Abee ya mayar da raddi ta hanyar cewa "Na san ba zaɓinka bane, don inda hakan ne babu yadda za a yi Kubrah ta dinga tunaninka, Amma zaka iya ƙoƙartawa ka dena ta hanyar mantawa da ita, itama a nata ɓangaren hakan zata faru; Na gode da karamcinka garemu!" Daga haka ya katse kiran gami da jefar da wayar can gefe. Zazzafar iska ya furzar kafin ya ce "Kin gani yanzu wayar tana nema ta zama wani sabon makami da zai Yaƙi rayuwarmu, Kubrah don Allah ki manta dashi!" "Zan yi ƙoƙari sosai don ganin nayi hakan, amma idan na kasa ba zaka kasance a tsagina ba Abee?!" ta ƙarasa maganar tana rushewa da kuka,,,,, girgiza mata kai yayi yana ƙara rungumeta tuni hawaye suka fara aikin kwarara daga idanunsa. Umar ...... Kuka kawai ya saki daga zaunen da yake, don kuwa ba ya jin zai iya wani abu bayan haka. Ranar haka ya kwana yana tunane-tunane kala-kala har da mafarkai. Washegari kamar lokacin da ya saba tashi yau ma ya tashi, bayan yayi shirin fita ya nufo Falo.. Yasan bai fiye samun Breakfast ba hakan yasa bai wani damu ba da shirin fitarsa yake fitowa. Sai dai yau abun ya sha bamban, duk da ba baƙon abu bane ya fito ya ga babu motsin Kowa a Parlour amma da kamar wuya ace ko alamar mutane babu a gidan Musamman Mommy . Sauya akalar tafiyarsa yayi zuwa ɓangaren Mommy koda ya isa bai ganta ba,. Sai da ya karaɗe gidan da nema amma bai ga Mommy ba, Haka Yasmin da Yaseer, duk da shi Yaseer daman ba fiye kwanan gida yayi ba. Jiki a sanyaye ya dawo Falo zuciyarsa cike da tunane-tunane kala-kala. Inda Mommy ta saba zama yaje ya zauna kamar zai fashe da kuka, karaf! idonsa ya sauka kan wata falleliyar takarda dake kan center table ɗinta, cikin sauri ya sa hannu ya ɗauka ya buɗe ta, karo ya ci da rubutun Mommy ya tsaya karantawa "Mun tafi Spain da ni da Ƴaƴanmu wanda suke jin maganar mu kuma suke bin tsarinmu!" iya abunda ya gani kenan, wurgi yayi da takardar ya miƙe bai san sanda ya fara rero kuka ba. Da ace da me rarrashinsa a gidan da ba abunda zai hana shi ya zauna ya ci kukansa ya tsire sai dai kashh!.... gidan ma jinsa yake kamar kango gabaki ɗaya yayi masa ƙunci kamar an jefa shi a kurku. Ficewa kawai yayi ya kama hanyar kasuwa, tun yana kukan har ya gaji ya share hawayensa don ya san babu mai rarrashinsa. Koda ya dawo da yamma yayi niyar zama amma sai ya kasa, gidan ya zame masa tamkar Ƙaya, haɗa Ƴan Kayansa yayi a travel bag ya ɗauki Key ya nufi wajen Mota, sai da ya shiga ya bata wuta sannan ya kira Ammar, cikin sa,a kuwa ya ɗaga yana cewa "Yanzu nake bawa Ummi labarin Aljanarka! sai gashi ka kira!" cike da damuwa yace "Aljanar wasu zaka ce, ni na riga na manta da ita, ba itace damuwa ta ba yanzu" gyara zama yayi yana cewa "To meye damuwar?" "Tambayarka zanyi Wane Hotel ne ya ɗan fi abun mutunci a garin nan? bana son wanda ƴan iska sukayi yawa a cikinsa" Tsaki Ammar ya ja yana cewa "An gaya maka ni Karuwa ce da zaka tambayeni Hotel?, ni banga abunda zai haɗaka da Hotel ba ma in ba neman jaraba irin na Ƴaƴan Masu kuɗi ba!" tuni hawayen da yake ta yiwa shamaki suka samu damar fara aiki akan fuskarsa, cikin rawar murya ya ce "Ammar kai ma ci min mutuncin zakayi kenan?, ni in zaka faɗa min ka faɗa min in tafi, iskancin nake so na fara nima" jin alamun kuka acikim maganarsa yasa Ammar ya saita nutsuwarsa yace "Ƙarya kake wallahi!, ka gaya min gaskiyar abunda ya faru!" cikin muryar kuka ya ce "Su Mommy duk sun tafi Spain sun barni ni kaɗai a wannan Gidan!, ni kuma ba zan iya zama ba gaskiya gwara nayi garari a titi har zuwa lokacin da zasu dawo!, Wallahi Ammar ni ban taɓa Alfahari da kuɗin Babana ba hasalima gani nake kamar Dukiyarsa ce silar rasa farin cikina!, na kasa samun gatan da kowane Ɗa yake samu a wajen iyayensa, kar ka ƙara kira ɗan masu kuɗi bana so!, ni ga Allah nake gareshi na dogara, ƙoƙari nake kullum don ganin na inganta kaina har in samu damar inganta Ƴaƴan da zan haifa!, ni ba zan yi rayuwa irin ta iyayena ba Ammar!! , b..... !" ganin bashi da niyar yin shiru yasa Ammar dakatar dashi ta hanyar cewa "Ya isa haka mana Umar, ɗakinmu nida Al'amin yana da ɗan girma zai ishe mu ka tawo nan kawai" "A'a Ammar ai abun kunya ne ma hakan!, ranar nan fa ina ji ina gani Mommy ta kore ka daga Gidanmu, kuma ta ce kar ka ƙara zuwa, sai kawai in tawo gidanku to da wane idon zan kalli su Ummi kenan?!" ɗan ƙaramin tsaki Ammar yayi kafin ya ce "Ranar nan da ka faɗawa Kubrah cewa ni Ɗan Uwanka ne na ɗauka fa da gaske kake, ashe ƙaryar banza ce!" da sauri ya ce "Kar kayi min gurguwar fahimta, ba haka bane ba fa" "Okay to in ba haka bane ka tawo Gidanmu da zuciya ɗaya, kuma Ummi ma ta ce tana nemanka yanzun nan " daga haka ya katse kiran yana cewa Ummi "Na gaya masa, nasan zai tawo tunda yaji kinyi magana"... Umar ..... In banda yaji Ummi ta magantu da ba abunda zai sa shi zuwan, haka nan ya tattara ya tafi can. (SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU) SHARE FISABILILLAH *🪻SAWUN KEKE...🪻* season *2* EP .......8 By INDO https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw *SAWUN KEKE...(Ba a Gane Gabanka!......)* Kubrah....... Duk suna zaune kaf a Babban Parlour suna hira har da Mammi,,, sai ga Affah kamar an jefo shi, a tsakiyarsu ya tsaya fuskar nan a murtuke kamar anyi yaƙi akanta cikin dakakkiyar murya ya ce "BA NI WAYAR HANNUNKIi!" a tare sukayi kallon kallo su duka huɗun yayin da Zuciyoyinsu suka fara luguden Bugawa a tare...... Kasa magana Kubrah tayi sai girgiza kai da tayi alamar a'a. Cikin sigar mamaki Mammi ta ce "Meye haɗin Kubrah da waya kuma Akhee!? gaskiya ina ga ka saɓa fahimta n...." ɗaga mata hannun da yayi ne yasa tayi yin shiru da bakinta, maimaitawa Kubrah tambayar yayi hallau dai ta ƙara girgiza masa kai. Mariam ta buɗe baki zatayi magana tayi saurin rufe shi sabida mahangurɓar da Affah ya bawa Abee, ƙara Kubrah ta ƙwalla gami da zamewa daga kan Kujera ta durƙushe a ƙasa tana faɗin "Affana don Allah ka tausaya mana don Allah!" .... Zahra da Abee da Saim ma durƙusawa sukayi kan gwiwoyinsu suna famar zazzare ido, ganin haka ya sa Mariam ta zube a ƙasa itama jikinta na wani mugun ɓari da karkarwa... Duka Abee ya shiga rarraba musu a tsakanin su biyun amma hakan bai sa sun magantu ba sai aikin bayar da haƙuri wanda yake ƙara tunzura Zuciyar Affah. Tun Mammi bata magana har ta gaji ta fara magiya da roƙon yayi haƙuri amma ko gezau beyi ba don kuwa ba ta ita yake ba. Sun ɗauki lokaci suna shan duka amma taurin kai ya hana su fito da wayar, ganin abun nasu yayi yawa yasa Affah ya finciki hannun Abee ya fara jansa ƙiririri!!!,,,, rufa masa baya sukayi suna magiya da roƙon sassauci, zuwa yanzu Zahra da Kubrah tuni kuka ya ci ƙarfinsu, Mammi ma bin bayansu tayi tana cewa "Ya kamata ku faɗi gaskiyar abunda kuka aikata Kubrah!, na tabbata da bakuyi komai ba ba abunda zai faru" Cikin kuka Kubrah tace "Don Allah Mammi ki ce ya ƙyale Abee, be yi laifin komai ba!" ai kafin Mammi tayi wani yunƙuri tuni Affah ya shige inda yake son zuwa wato Kitchen,,, kai tsaye Cooker gas ya kunna gami da jan hannun Abee ya ɗora akai..... Zuwa yanzu har Mammi ma sai da ta fashe da kuka tana cewa "Haba Akhee in ba kai ba waye yake yin izaya da wuta saikace wani kafiri?!! don Allah ka bari kar ka nakasta min shi don Allah!, in ka tambayesu a hankali zasu gaya maka ba sai ka azabtar dasu ba!! " Banza yayi mata kamar be san tana yi ba, Abee dai yana karɓar azaba iya azaba sai ɓarza kuka yakeyi. A burkice Kubrah ta miƙe tana cewa "Af.. Affah!! zan ɗauko! wallahi zan ɗauko don Allah ka ƙyale shi, Affah ! don Allah!!" janye hannun Abee yayi daga kan wutar yana cewa "Okay Go ahead!" mayar da kallonsa yayi kan Mammi kafin ya ce "You See?! waɗannan da kike ganinsu Zuma ne sai da wuta!" mamaki da al'ajabi ya hana Mammi cewa komai sai ido da take rarrabawa cike da mamakin tana zaune haka turus! a gidan ashe har waya suka kawo suka ajiye bata sani ba. Afujajan Kubrah ta dawo Kitchen ɗin jikinta sai rawa yake kamar mazari, duk numfashinta ya susuce. miƙawa Affah Wayar tayi tana shirin yin baya taji ya haɗa da hannunta nata ya ɗora akan wuta,,, da sauri ta yarda wayar akan wutar aikuwa ta shiga ƙonewa, ihu ta fara kurmawa tana bashi haƙuri,,, "Waye ya siya miki ita??, na ce waye ya baki?????" ya yi tambayar cikin tsawa da barazana!" haɗa baki suka yi wajen bashi amsa Abee ya ce "Ni ne!!" ita kuma tace "Abee ne!" sakin hannun nata yayi kafin ya kifa mata wani zazzafan mari wanda yasa ta fara majaujawa a filin wajen, Saim ne ya ƙoƙarta ya riƙe ta suka faɗi rajaf!! a ƙasa. A kausashe Affah yace "In na ce A'a ina nufin A'a!!, muddin aka samu wanda yake jin ya isa ya karya doka ta a cikin gidan nan babu shakka zan taka shi in yanka masa wuya!, ni ba a nuna min taurin kai!" yana kaiwa nan ya nufi hanyar fita a fusace! kamar zai tashi sama. Mammi ma dasa nata faɗan tayi, ta inda take shiga ba tanan take fita ba. Sai da ta gama sannan ta nemo magani ta basu suka sha, ta shafa musu na shafawa. misalin ƙarfe 2:00am......... Cikin sanɗa Mariam ta buɗe ƙofar bedroom ɗin da ya kasance masaukinta, leƙawa tayi waje ta kalli ko'ina sai da ta ga babu motsin kowa sannan ta koma ciki ta danno ƙofar gami da saka mukulli ta rufe. Wajen kayanta ta koma ta fara laluben Ƴar wayarta da Abbi Ya bata a sirrince,, tana cirowa ta lalubo Lambarsa wadda ita kaɗai take karakaina a cikin wayar. Duka ɗaya Uncle Isah ya ɗauka yana ambaton sunanta, sai da yaji ta amsa sannan hankalinsa ya kwanta, ya sauke ɓoyayyar ajiyar Zuciya kafin ya ce "Tunaninki nake yi, nan zaman da nayi jiran kiranki nake yi, haka kawai jikina yake bani kamar wani abun na faruwa" haɗiye yawun da ya tokare mata maƙoshi tayi kana ta ce "Abbi Ya jikin Rahma?, da fatan dai duk kuna lafiya!" "Muna lafiya , Rahma kuma tana cigaba da shan Magani da Alluran da suka ce a dinga yi mata" "To Alhamdu lillah!" ta faɗa kafin ta cigaba da cewa "Abbi ina matuƙar jin tsoron zaman Gidan nan Don Allah ku sauya wata shawarar nidai in dawo Gida!, wallahi Abbi duk ranar da ya gane muna yi masa zagon ƙasa ko shakka Babu sai ya ƙona ni da raina!, ashe haka yake Abbi?! Ƴaƴan cikinsa ma ba zaka so ka ga izayar da yayi misu ba Ɗazu saboda sun siyo Waya!" ta ƙarasa maganar cikin rauni tamkar zata fashe da kuka, Uncle Isa ya ce "Haka yake tamkar Garwashi! kallonsa daga nesa abun marmari amma da zarar ka taɓa zai saɓule maka fata!!, idan kuma kika iya binsa a hankali akansa zaki dafa Abincin da zaki ci ki rayu,,, wannan ita ce Suffarsa, baya duba da wanda ya taɓa shi kawai hukuncinsa yake ga kowa" Kuka ta saki tana cewa "Abbi nidai ina so in dawo Gida don Allah!" "Kiyi haƙuri Maryam, Banida zaɓin da ya wuce hakan, ki duba halin da ƙanwarki take ciki mana!'' "Amma....." katseta yayi da cewa "Calm down Mariam, nasan kafin safiya zeyi kamar ya manta abunda ya faru, to haka nake so ki manta ke ma, ba na so wani abu ya dinga firgita ki, ki saki jiki a cikinsu kin ji ko?, in sha Allahu ba abunda zai faru!" gyaɗa kai tayi tana cewa "Shi kenan !" Uncle Isa yace "Wayar tana hannunsu ne?" "A'a ya ƙona ta haka ya dinga ƙona musu hannu fa Su Abee" "Kar ki damu, komai zai wuce, zamu yi nasara in sha Allah, good night!" yana kaiwa nan ya katse kiran. Jiki a sanyaye Ta mayar da wayar zuciyarta cike fal!!! da tunane-tunane, babu shakka in banda tana son lafiyar ƴar uwarta da ba abunda zai sata wannan aika-aika. Ta daɗe tana tunanin ta yaya ma zata samu kyakkyawar alaƙa tsakaninta da su, Don kuwa ba wani janta a jiki suke yi ba musamman Abee, sai me binsa Kubrah!. Washegari Sai lokacin da ta tabbatar zata samu Mutane a Falo sannan ta fito bayan ta gaisar da Mammi ta ƙara da cewa "Ina son in dubo Abee da Kubrah!" ido Mammi ta zuba mata kafin tace "Kar ki damu sun ji sauƙi kuma suna samun kulawa sosai, in kuma ganin nasu ya zama dole zan shiga in fito miki dasu sai ku gaisa" girgiza kai tayi alamar a'a duk sai taji ta tsargu lokaci ɗaya, duk da ba wannan ne karon farko na nuna mata iyakarta ba. Cigaba tayi da ƴan sabgoginta sai dai hankalinta ya karkata sosai kan su Abee, musamman dai shi don ta tabbatar yafi shan izaya, tun tana sa ran ganinsu cikin sauƙi har ta fitar don kuwa dare yayi amma ko motsinsu babu. Kasa jurewa tayi sai da ta tambayi Mammi, Mammi ta kalli inda Abbi yake cike da son samun amsa, ɗan jim tayi kafin tace "Za ki dubo su ko?" da sauri ta gyaɗa kai, Mammi ta miƙe tana murmushi gami da cewa "Abokin faɗa yau babu lafiya ko?, na ga ma ba kwa wani jituwa da Abee sosai!" Mariam ta ce "Laifinsa ne wallahi, ya fiye girman kai gashi miskili ne ɗan rainin hankali jin kansa yayi yawa!" Mammi ta ce "To yau dai kam Babbar giwa ta faɗi!" rasa amsar da zata bayar tayi don haka ta rufe bakinta, Bedroom ɗin Kubrah suka fara zuwa tana kwance ta dunƙunƙune a cikin Bargo sai sautin kukanta ke tashi a hankali. Jiki a sanyaye Mammi ta janye Bargon tana cewa "Wai ke an ce miki kuka yana yaye damuwa ne? duk wannan ciwon kan da kike yi bai isheki ba sai kin ƙaro wani!" ƙoƙarin tsayar da kukan ta fara yi tana cewa "Abee fa bashida lafiya!, in nayi laifi ni ya kamata a hukunta ba wai a hukunta shi akan laifina ba" Mammi ta ce "Ke ma ba lafiyar gareki ba fa, kuma ke ce zakiyi ƙoƙari ki sama masa zaman lafiya, gardamarki ce take sawa ake yawan ƙuntata masa, shi da yake bashida wannan gardamar taki ai kin fishi samun zaman lafiya, tunda kin riga kin san irin hukuncin da ake muku" Mariam ta ce "Kuma haka ne gaskiya ki rage Kubrah tunda kun ga Abbi yana da fushi sosai" shiru tayi don kuwa ba ta san ma abunda zata faɗa ba, Mammi ta juya tana cewa "Ki dena kukan nan ya isa haka, kuma ki sha magani kafin kiyi bacci" bata jira amsarta ba ta fice Mariam na biye da ita. Abee yana zaune a bakin gado ya zubawa hannunsa wanda ya sha wuta ido, Mammi tayi sallama tace "Ga Mariam zata duba ka" da sauri ya janyo Blanket ya lulluɓawa jikinsa kasancewar daga shi sai wando three quarter. a bakin ƙofa ta coge tace "Sannu Allah ya sawwaƙe! ya kamata ku rage fitina!" zuro kai yayi ta cikin bargon ya zuba mata wani shegen kallo kafin ya ce "Bana son shishshigi ba kwarjini!, abunda ya shafe ni ne nida ƴar uwata , bana buƙatar tsarinki a ciki" jiki a sanyaye tace "Yi haƙuri, bakin nawa ne akwai surutu amma ba zan kuma ba in sha Allah" Mammi ta ce "Ka sha maganin kuwa?" gyaɗa kai yayi, ta ƙara da cewa "Amma dai baka ƙara yin zazzaɓin ba ko??, kuma ƙunar ta dena raɗaɗi?" "E, yanzu ba inda ke min ciwo" tace "Yayi kyau, sai da safe" amsawa yayi yana maida hankalinsa kan Mariam wadda jikinta yayi matuƙar sanyi, taɓe baki yayi ba tare da yayi wani sharhi akai ba. (SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU) SHARE FISABILILLAH Ep.......9 https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw Umar........ Sai da Ummi ta fara haɗawa da faɗa bayan nasihar da take yi masa sannan aka samu sauƙin damuwar da ya jefa kansa a ciki Abun ya haɗe masa da yawa ga tunanin su Mommy ga tunanin Kubrah, yayi iya bakin ƙoƙarinsa don ya cireta daga tunaninsa amma ya kasa, sai dai yanzu abun ya ragu ba kamar Da ba don kuwa an ɗauki tsawon sati biyu harda ƴan kwanaki bai ƙara jin ɗuriyarta ba. "Kamar wani Jariri haka ka zama yanzu" Ammar ne yayi maganar yana ƙoƙarin zaunawa a kusa da shi.. Murmusawa yayi kafin ya ce "Ina iya ƙoƙarina don ganin na jure Hukuncin da ƙaddarata ta yanke akaina, menene kuma abunda banyi ba?" "Na ga ba yau ne farko ba da su Mommy suka tafi wani wajen suka barka, amma naga borin naka da rigima na wannan karon yafi na kullum" Ɗan jim!! yayi kafin ya ce "Kullum fa sa rai nakeyi in ga rayuwar ta canja, burina in ga an samu cigaba amma sai naga baya ake yi, a lokacin da nake cikin damuwa lokacin da ya kamata Iyayena su yi min addu,a su dinga kwantar min da hankali a lokacin ne suke duk meyuwa don ganin sun ƙuntata min kawai don suna fushi dani akan gaskiyata!" Ammar ya ɗan numfasa sannan ya ce "Haƙuri zaka yi, ni ina ji a jikina komai zai dawo daidai" "To yayi, Allah yasa" Umar ya faɗa sannan ya cigaba da cewa "Nayi Sa'a Allah ya rufa min Asiri ban ƙara ganin Aljanata ba, yanzu na rage tunaninta kuma na rage yin mafarki da ita kamar dai yadda Yayanta ya faɗa" "Barka da arziƙi , Allah yasa ta tafi kenan, shiyasa naga har ka ɗanyi ƙiba ashe?" Umar ya fashe da dariya yana cewa "Kaji iskanci, wato har nayi ƙiba!, Allah ya shiryeka!" Cigaba sukayi da hirarsu cikin nishaɗi gami da bawa juna kulawa. haka rayuwar ta cigaba da tafiya a kowane ɓangare wataran daɗi wataran akasinsa...... Ammar yana duk ƙoƙarinsa wajen mantar da Umar damuwar da take barazana ga lafiyarsa. a ɓangaren su Kubrah ma tarzoma ta lafa, Affah yakan zauna su ci Abinci tare su yi hira tare har da Raha, sai dai Ɓoyayyen sirrin dake tsakanin Kubrah da Abee yakan yi barazana ga farin cikinsu a wasu lokatan. a ɓangaren Maryam ma tana iya bakin ƙoƙarinta wajen zayyanawa Abbinta duk wani Motsi da akeyi a gidan, cikin sa,a Affah bai gane halin da take ciki ba. Abee Yana Zaune kan sofa ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya yana ƴan ciye-ciye ,Maryam tana tsaye a gefensa ta zuba masa wata uwar harara kamar idon zai faɗo ƙasa, a ranta tana tunanin Dalilin da yasa gabaki ɗaya baya ƙaunarta, a zahiri Kubrah ta fishi Barazanar Jinkai da Izza tare da ƙin shiga sabgar Mutane , tunda shi har Boyi-boyin Gidan ma yana sakar musu fuska ya saurare su amma ita ko Ƙuda ma ya fi ta Mutunci a idonsa. Ba ta ankare ba sai ji tayi ta zabga tsaki. Cike da mamaki ya juyo yana binta da wani irin kallo me cike da salon bambanta tsara, "Wato tsayin Bakinki har ya kai ki jawo min tsaki ko?, sabida baki da Kunya har ki kalli tsabar idon ƙannena kina gaya musu kin tsane ni ko?, to nima na tsaneki!!" ya ƙarasa maganar tare da wurga mata Apple ɗin da ya fara gwaguya, cikin sa,a ta sauka akan bakinta jikake ɓam!!!...... Danne bakin tayi da duk hannayenta a take idanunta suka kawo ruwa saboda azabar da ta fara sagaraftu a cikin ƙwaƙwalwarta. Mammi ce ta ƙaraso wajen da sauri tana cewa "Abee ubanka kenan! , kar ka ƙara harinta da duka ka san dai zafin hannu gareku, sai ka je ka illata mata baki a banza!" ƙarasawa tayi wajen Mariam ta riƙo hannunta tana bata haƙuri. Tuni Yawu da jini sun haɗe sun fara tsiyaya zalalala!! , Mammi ta runtuma salati ta cigaba da cewa "Abee! baka da hankali ne? me tayi maka!!?" "Mammi ta raina ni ne, har da cewa ta tsane ni!" tsaki kawai tayi bata ƙara bi takansa ba sai ta shiga rarrashin Mariam...... Miƙewa yayi yana cewa "Gobe ki ƙara zuwa kiyi min tsaki, kuma naji daɗi da kika tsane ni don nima na tsane ki!" raka shi sukayi da idanu har saida yayi nisa daga wajen sannan Mariam ta cigaba da kukanta ....... A zahiri kukan takeyi a cikin ranta kuwa jinjina izzar Ubangiji takeyi da ya halicce su tamkar Kaifin Takobi, Dukkansu babu na banza sai dai Abee da Kubrah sun fi Saim da Zahra tsauri, duk da ba sanin Affah tayi sosai ba amma takanji labarinsa a wajen Abbinta, idan ta kalli hakan kuwa sai taga babu abinda suka bari daga Mahaifinsu daga kan kamannin fuska har zuwa Miskilancinsa da tsarinsa da kuma Kaifin da yake dashi akan abu............ Kaitsaye inda yake tunanin zai samu Kubrah can ya nufa sai dai kash!!! bata nan, sai da Zuciyarsa ta yi wani wawan tsalle kafin ta fara harbawa da gudu-gudu. Cikin sauri ya fito yana tambayar duk wanda yaci karo dasu amma kowa cewa yake bai ganta ba....... Haɗawa yayi da gudu ya fita daga cikin gidan ya nufi cikin Daji yana surfa mata kira......... sai da ya sha bulayi sannan ya samota a gefen ruwan Kogin dake cikin Dajin tana zaune ta sa shi a gaba tana kalla...... da gudu ya ƙarasa wajen gami da dire gwiwoyinsa a ƙasa ya zube a gabanta yana maida numfashi, ,,,,, sai da ya ɗan sarara sannan ya ɗago idanunsa da suka canja Launi zuwa kalar zaiba sai sheƙi sukeyi tamkar ba na ɗan Adam ba. Hawayen da ya gani layi-layi akan fuskarta ne ya tsayar masa da tunanin abunda zai yi wani mugun kallo ya zuba mata me cike da fusata, buɗe baki tayi zatayi masa magana ya dakatar da ita ta hanyar wanka mata wani Rantsatstsen Mari,,,,,, ba shiri ta miƙe tsaye hannunta na kan kumatun nata. shi ma miƙewar yayi ya juya mata baya ,,,,,, da sauri ta nufo inda yake tana shirin faɗawa jikinsa yayi saurin dakatar da ita da cewa "Karki taɓani tunda bani da amfani a wajenki!!! " "Abeeeee!!!!" ta kira sunansa cikin mamakon firgici! cigaba tayi da cewa "Abee please listen to me Abee please!!" kukan da ya ci ƙarfinta ne ya hana ta ƙarasa maganar, a fusace yace "Me zaki gaya min??!!! me yasa zaki zauna kina kuka anan?? kenan ba za ki iya faɗa min damuwarki ba koda kuwa banida ƙarfin da zan temaka miki?!!! ko kuwa a tunaninki don kin ɓoye min farin ciki zanyi da hakan!! ! ! ! !!" ya ƙarasa maganar cikin tsawa,,,, girgiza kai ta shiga yi tana cewa "A'a Abee! ba zan so nauyin laifina ya cigaba da ɗoruwa akan kafaɗunka ba Abee" sassauta murya yayi kamar zai fashe da kuka ya ce "Ke fa dole na ce Kubrah!, duk da ban baki tazara ba amma fa ni ne babba a cikinku, nauyi ne akaina na hana zubar hawaye a idanunku, bare ke da tun Ina Cikin Mahaifiyata bani da Abokiyar wasa sai ke, babu wanda nake iya faɗawa Abunda ke kwance a cikin Zuciyata sai ke!, me yasa yau ɗaya zaki ɓoye min" cikin muryar kuka tace "Abee!! faɗanka baya min daɗi Abee!!! kayi haƙuri don Allah!, babu abunda na yiwa ƙaddara amma ta haɗani da son wanda gwara in so Bawan dake Bauta a gidanmu zai fi Mutunci a idon Affah!,, Abee wallahi ina son shi, ina son kasancewa dashi har ƙarshen rayuwata,,,,, Abee!! ina so kullum idan na buɗe ido in dinga ganinsa, idan ban samu hakan ba kuma babu shakka farin cikina zai samu tangarɗa!!" Lumshe idanunsa yayi gami da kwasar gefen leɓensa na ƙasa ya taune shi da ƙarfin gaske... Buɗe mata hannayensa yayi aikuwa ta yi saurin faɗawa jikinsa tana sakin wani sabon kukan,,, sai da ƴan sakanni suka shuɗe sannan ya buɗe idanunsa hakan yayi daidai da zubowar hawayensa, ,,,, "In Allah ya kaimu gobe ki je ki gayawa Umar Abunda kika gaya min yanzu,,, amma da sharaɗi ɗaya akansa muddin ya mutunta soyayyarki bai wulaƙanta ki ba zan so shi, amma idan wulaƙanci ya biyo baya zan tsane shi, hakan kuma Barazana ce ga duk wani farin cikin rayuwarsa , in kuma ya Amince da kaina zan sanarwa Affah domin babu amfanin zaman jira" "Na gode Abee!" "Kar kiyi min godiya , kawai ki dena kukan shine abunda bana so!"..... "Ƙwarai kuka bai dace da ku ba Domin kun fito ne daga tsatson Gwarzon da Muke Kira Namijin Duniya,,,,, babu abunda yake firgita shi bare har ya sa shi Zubar da hawaye, don haka nake jin matuƙar raɗaɗi idan naga damuwa ta bayyana akan fuskarku, bayan hakan ba Ta'adar gidanku bace, ba a taɓa gane raunin Affanku akan fuskarsa, ku zamo masu dakakkiyar Zuciya tamkar shi,,,,, jinjina ga Sarakan Gobe!!" Ahmadi ne yake zayyano jawabin cike da girmamawa gwiwoyinsa zube a ƙasa. Murmusawa Abee yayi kafin ya ce "Ahmadi idan Mutum bai san halinka ba babu shakka zaka sa kansa yayi girman da shiga Ƙofar Masarautar Garin nan sai ya gagare shi, In Allah ya kaimu gobe ka kaita wajen Umar cike da kulawa, ka kasance tare da ita a kowane saƙo da lungu ka zamo shaida akan duk motsinsu!" ƙara russunawa yayi yana cewa "Indai Allah ya aramin lafiya babu shakka zan aikata abunda ka Umarce ni Shugaba!". *🪻SAWUN KEKE🪻* season *2* By INDO (SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU.....) Ep........10 *Ɗaya daga cikin Ƙauyuka mabambanta dake Ƙasar China.............................* Kamar Yadda aka sani a cikin kowace Masarauta akan Fuskanci ƙalu-bale, haka saɓanin fahimta, kokuma bambancin ra'ayi, sannan akwai guru-gubji a cikinta ta yadda har akan iya rasa rai domin cimma wata manufa........... Itama Masarautar da SARKI YIZHENG yake Jagoranta a wannan ƙarnin,,, cike take taf da irin waɗannan Ƙalu-balen , sannan cike take da Manyan MATSAFA da Masu SIHIRI, hallau sukanyi amfani da wannan damar wajen Mallakar duk wani abinda suke son cimmawa kokuma kawar da dukkan Ruhin da zai kawo Tsaiko ga Muradinsu.................... _______________________________ Daidai wannan lokacin zamu iya kiransa da Yamma yayin da rana take shirin gushewa daga sararin Samaniya ta koma Makwancinta wanda Allah ne kaɗai Yasan ina ne.......... https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw King Yizheng yana Zaune cikin sirrintaccen Ɗakinsa wanda yake aiwatar da Tsafe-tsafensa, idanunsa na kan wata tafkekiyar Taswira.... Yadda yake kallon Taswirar kaɗai ya isa tabbatar da muhimmancinta gareshi. "Yi Zheng!! Kana wasa da damarka, muddin Bakayi sauri ba zaka rasa Ƙarfin ikon da kake son samu,,,, Kamar yadda muka gaya maka indai bakayi amfami da wannan Yarinya ba to ba zaka taɓa dawwama akan wannan Mulki ba, ɗan uwanka zaiyi nasarar Kawar da kai, sannan Ba zaka taɓa zama Babban Sarki a Ƙasan China ba...." wata murya mara daɗin amo ke yi masa tuni akan aikinsa na gaba,, Nannauyar ajiyar Zuciya ya sauke bayan Hasken da ya bayyana akan Taswirar ya ɓace. ""Yizheng! ! !!" Kyakkyawar Matarsa kuma kamalalliya, wadda ta sha ado irin na Sarauta itace ta katse masa tunanin da ya tafi. Yadda ta kira sunansa cikin razani yasa shi saurin miƙewa yana Zuba mata idanunsa da suka ƙara girma. Cigaba tayi da cewa "Meyasa kake son tarwatsa rayuwar wasu don cikar muradinka?, Ba na so ka dinga aikata waɗannan zunuban, ka zauna iya matsayinka, kar ka cutar da Ƴar Mutane!" Ɗan Murmusawa yayi kafin ya tako Zuwa inda take yasa hannu ya ɗauki ɗan cup ɗin dake kan tray a hannun Hadimar Queen Xiang. Sai da ya kurɓi Haɗin lemon Fruit ɗin ciki sannan ya kalleta cikin muryar raɗa yace "Hakan Mafarkina ne, cikar shi kuma ya zama nauyina, Kawar da duk wanda baya goyon bayana hakan haƙƙina ne; Kin sani ina sonki Queen Xiang abun alfahari ne gareki in Zamo Sarkin da Duniya take labarinsa kuma take matuƙar tsoronsa, kuma hakan zata faru ne bayan Yarinyar ta zama mallakina , Itace Mahaɗin Ƙarfin ikon da Duk Manyan Hatsabiban Duniya suke nema; Karki damu akan hakan cikin sauƙi zan kammala komai ba wata Yarinya ce me galihu ba ta kasance Ƴar Nigeria kin ga ba zan sha wahalar samunta ba!" Hawayen baƙin ciki ne suka fara silalowa kan kumatun Queen Xiang, cike da ɓacin rai ta ce "Indai ina raye ba zan bari hakan ta kasance ba, ka kasance Azzalumin Sarki wanda baya tausayin Talakawansa, indai na bari ka shahara tabbas Al'umar Duniya zata yi Kuka da kai , kuma ka sani ka ci Amanata ka ci Amanar Mahaifina da ya baka Amanata, Tabbas zan dakatar da kai koda hakan na nufin rasa raina ko kuma naka!" Idanunsa ya ware akanta cike da mamakin furucinta, da sauri ya riƙo hannunta gamida fincokata ta faɗa jikinsa ya matseta da ƙarfi sannan ya murmusa ya ce "Ke ba komai bace a wajena Xiang, tunda kika furta nasan zaki aikata min har fin haka, don haka zan aika ki inda ba za ki san abinda nayi ba bare ranki ya ɓaci.." Kafin ta gama fahimtar inda ya dosa ya zaro ƴar ƙaramar wuƙa a jikinsa ya soka mata a maƙoshi. Ihu Hadimarta ta kurma tare da yin kukan Kura ta cukume shi tana shirin ɗaukar tashi rayuwar sai dai kash!!! cikin sauƙi itama ya aikata inda ya aika Queen Xiang wato Lahira, sai da yayi mata kaca-kaca da wuƙar sannan ya koma gaban Matarsa ya rungumeta ya kurma gagarumin ihu sannan ya fara Kuka kamar ransa zai fita .... Ihun da ya kurma bai zame ko'ina ba sai cikin Kunnuwan gudan jininsa wato PRINCE JIEHONG Shigowarsa kenan cikin Masarautar ya dawo daga Farauta , jin haka ya sa shi fallawa da gudu ya nufi sashin Mahaifin nasa. Kasancewar Yasan inda yake tun kafin ya fita yasa bai sha wahalar iske su ba sai dai tashin hankalin da ya gani bai taɓa Tsammanin irinsa ba a duk tsawon rayuwarsa. "Maaa!" Ya furta da ƙarfi tare da cukumar gawarta yana duba jikinta, ɗago ido yayi yana yiwa Mahaifinsa kallon tuhuma, da hannu yayi masa nuni da Hadimar Queen Xiang, cikin muryar kuka yace "Itace ta kashe min Sarauniyata! saboda tazo zata kashe ni Queen Xiang ta shiga tsakani shine ta kasheta ba tare da duba yardar da mukayi da ita ba!" kukan ya cigaba da yi na tsawon sakanni kafin ya cigaba da cewa '"Na kashe ta, kuma zan kashe duk wanda yake da sa hannu aciki, sai da na gaya mata ta dena zuwa nan da kowa amma bata ji yanzu kalli abunda ya faru..." Kuka me ƙarfi ya ƙara saki tare da ƙanƙame hannun Queen Xiang....... Zazzare ido a tsakanin Mutane ukun kawai Prince Jiehong yake yi, yayin da Zuciyarsa take zaɓalɓala, babu ko shakka ba zai taɓa ragawa duk wanda ya zamo silar Mutuwar Mahaifiyarsa ba....... sun daɗe cikin wannan yanayin kafin Prince Jiehong ya miƙe ya nufi hanyar fita, ganin haka yasa Sarki ya bi bayansa da gudu-gudu yana ɗan murmushi, ya tabbata da ta hanyar Tsafi ya kashe Queen Xiang da sai Yarima ya gane shi ya aikata, shiyasa yayi dubarar saka wuƙa dan ya wanke kansa daga zargi, yanzu kuwa tarkonsa ya kama Zaki. Kaitsaye muhallin Hadimar Queen ya nufa ya zaƙulo Ƴar Budurwar Ƴarta dake cikin gidan ya watsota waje. a gaban kowa yayi mata kisan Gilla sannan ya watsar da gawarta ya koma..... A zahiri King Yizheng nuna baƙin ciki da Alhini yake yi, Zuciyarsa kuwa farin ciki ne fal a cikinta, ya tabbata Ɗansa baya zarginsa sannan kuma a yanzu duk Umarnin da ya bashi da hanyar da ya ɗora shi su zai bi tunda babu me rusa masa shiri. Kafin ka ce me! Masarauta ta rikice an kasa gane menene yake faruwa a cikinta, hankalin Mutane da dama yayi matuƙar tashi..... Sai da King yasa aka tara Mutane sannan ya sanar da Mutuwar Matarsa da kuma silar Mutuwar tata,,,, tuni tsanar Duk wanda yasa hannu aka aikata tayi tsiro a zukatan al'uma. Mutuwar tayi majaujawa da Mutane, Masu kuka nayi masu alhini nayi wasu ma tashin hankalinsu ya wuce suyi kukan. Ta samu wannan gatan a wajen Mutane ne saboda tausayinta ga talakawanta da kuma Adalci da take yi ga kowa. *🪻SAWUN KEKE🪻* season *2* By INDO (SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU....) WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE.... SHARE FISABILILLAH Ep.........11 Kaitsaye inda gawar Queen Xiang take ya koma gami da tsayawa akanta yana kalla,,, duk da cewar a burkice yake amma sai yaga kamar akwai bambanci da yadda ya barta ɗazu..... kamar wadda aka motsata kokuma ta motsa kanta, Tunowa da yayi cewar lokacin da suka fita King Yizheng ne ƙarshen fita sai ya kwantar da hankalinsa bisa cewar King ne ya motsa ta don dama yana rungume da hannunta. https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw Haka akaita Bikin Mutuwar Queen har na tsayin kwanaki biyu sannan Ƙura ta Lafa a lokacin ne King Yizheng ya mayar da hankali wajen fanɗarar da halayen Prince Jiehong tare da dasa masa son Mulki da ƙarfin iko gami da tsanar dukkan wanda yayi yunƙurin dakatar dashi zuwa ga manufarsa............... Nigeria...... Wannan daren na yau Abee da Kubrah jinsa suke tamkar daren Mutuwarsu duba da yadda yayi musu ƙunci tamkar wanda aka jefa a kurkukun bala'i,.... Kubrah tunaninta akan Abun ƙaunarta ne sai kuma wani yanayi da take ji a jikinta mara daɗi, Abee kuwa abun ya tarar masa da yawa Ji yake tamkar wani gagarumin abu na shirin Faruwa dashi ko kuma ga Ƴar Uwarsa, sai dai duk iya nazarinsa ya kasa gane ko wane irin abu ne kuma ta ina zai ɓullo. Washegari.... Tun safe ta fita domin Haɗuwa da Umar..... Kaitsaye gidan su Ammar suka nufa kamar yadda Ahmadi ya gaya mata ya koma kwana acan. Zuwansu yayi daidai da fitowar su Umar da nufin tafiya Kasuwa, Umar yana cewa Ammar "Su Momy sun dawo, na kusa komawa Gida" Ammar ya ce "Amma da zaka ɗauki shawarata kawai ka je ka Auri wadda Mommy tace, ina ganin hakan zai kawo zaman lafiya tsakaninku, saboda........" maƙalewa Maganar tayi lokacin da idanunsa suka sauka akan Kubrah dake famar kallon Umar kamar wani Jaririn Watan Ramadan. "Umar gata nan fa!" sai lokacin Umar ya juya saitin inda take don bawa Zuciyarsa tabbacin abunda take gaya masa. Ido ya zuba mata suka shiga yiwa juna kallon-kallo . Ahmadi ne ya katse shirun da cewa "Tuba nake Uwar Ɗakina, bamu da isashshen lokaci don nasan akwai dogon bayani a gaba!" Numfasawa ta yi kafin ta fara takawa zuwa inda yake, cikin takunta irin na Ƙasaita me nuni da zallar izzar dake yawo a cikin jininta. sai da taje gab dashi sannan ta tsaya gami da kawar da kanta gefe, ta ɗan lumshe ido ta buɗe sannan tace "Ko zan iya samun lokacinka a yanzu?, ba Umarni bane kana da damar zartar da ra'ayinka!" Sai da ya sauke zazzafar ajiyar Zuciya sannan ya samu zarrar cewa "Barka da zuwa ƙofar gidanmu... kina da damar dakatar dani daga dukkan wani uzuri da nake dashi domin lokacinki yana da matuƙar Daraja a gareni" murmushin gefen baki tayi ba tare da ta ce uffan ba..... shiru ne ya ratsa wajen na ɗan lokaci har Ammar ya je ya ɗauko Kujerun Roba guda biyu ya kawo ya ajiye sannan ya ce "Ina ganin ku zauna maganar zata fi daɗi!" Umar ya ɗan murmusa kafin ya kalli Kubrah ya ce "Bismillah!" Juyawa tayi ta kalli Ahmadi kallo irin na neman izini ko kuma shawara,,,,, rusunawa yayi yana cewa "Umar Amintacce ne gareki Shugabata!" ɗan matsakaicin numfashi ta ja ta sauke sannan ta ƙarasa kan kujerar ta zauna gami da harɗe ƙafafunta Tamkar a Fadar Kakanta....... Zama Umar yayi sannan ya ce "Ina saurarenki, Allah yasa ba laifi nayi ba!" jim!! tayi kafin ta ɗan girgiza kai ta ce "A'ah, Kawai dai abunda nake tunani nake son gaya maka" ya buɗe baki zaiyi magana ta katse shi da cewa "Zaka iya zamowa Bango gareni?,,,,,, zaka iya zama Jigona daga yanzu Har Bayan raina?" idanu Umar ya zazzare akanta tare da yin suman Zaune , gabaki ɗaya wutar kansa ta ɗauke ba abunda yake ganewa sai Kalamanta da suke maimaita kansu acikin ƙwaƙwalwa da Zuciyarsa..... sai da Ammar ya ɗan ranƙwashi kansa sannan ya dawo hayyacinsa, tsananin mamakin Abunda ya ji yasa shi kasa gazgatawa, "Am.... amma Kubrah me yasa kika ce haka, na kasa gane inda kaina yake bare har in fahimci me kike nufi!" ya yi maganar cikin kiɗima, ga wata zuffa da ta fara keto masa kamar wanda yayiwa Sarki ƙarya....... Murmushin da bai wuce kan laɓɓa ba tayi kafin ta ce "Dama Abee ya gaya min cewa a rayuwarmu ta Ƴan Adam, laifi ne Mace ta furtawa namiji tana son shi, ba Allah ne ya rubuta hakan a cikin Ƙur'aninsa ba,,, mu dai Mutane mu ne muka ɗauki hakan a matsayin laifi, hakan yana jawowa Mace ƙasƙanci da wulaƙanci har da tozarci a wajen Namiji; Amma Umar me yasa baku ɗauki Mace a matsayim me Ƴanci ba?, me yasa sai namiji ne kawai zai cewa Mace yana sonta ita kuma saboda tana da Imani da Tausayi sai ta karɓa har ta zamowa Namiji Gata a rayuwarsa!,,, ko kuna tunanin ita Mace Allah bai halicceta da Zuciya ba? kuma be yi mata Shauki a cikin halittarta ba?; Ba ina nufin ka yi min laifi ba, Tambaya nayi maka ka dawo min da Tambaya saɓanin Amsa, hakan ne ya karya min Zuciya, kai ma Ɗan Adam ne, mai daraja da Ƴanci, sannan kana da shaukin da zai iya bambanta maka ra'ayi Musamman akan rayuwa ta har Abada, kayi Tunani sosai, duk lokacin da ka shirya Amsoshin da zaka bani Sai ka neme ni ka gaya min!" tana kaiwa nan ta miƙe Da nufin barin wajen............ *🪻SAWUN KEKE🪻* season *2* By INDO (SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU) WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE.... naira 400 (idan zakiyi payment tare da SEASON 1 a lokaci ɗaya, akwai Discount, Naira 600 duk biyun) SHARE FISABILILLAH Ep..........12 "Kubrah!!" ya kira sunanta cikin wata kalar murya wadda tayi matuƙar tasiri akanta, cak!! ta tsaya ba tare da ta juyo ba haka kuma bata yi yunƙurin ƙara tafiya ba. "Kiyi Haƙuri ba zan iya Karɓar Soyayya daga gareki ba, banida wannan ƙwarin Zuciyar,,,, amma don Allah ina neman Alfarmarki!" runtse idanunta tayi da Matuƙar ƙarfi gami da cije gefen leɓenta........ Zagayawa yayi gabanta ya durƙusa kan gwiwoyinsa sannan ya haɗe hannayensa waje ɗaya, cikin raunin murya ya ce "Ki temaka ki zamo wani tsagi na rayuwata Kubrah!!!,, Ki Aure ni, ki kasance Tare dani Har Abada Don Allah!!!; Darajarki ta wuce ki nemi soyayyata sai dai ni in nemi Alfarma ki So ni, na baki haƙuri ne saboda kasa gaya miki da nayi har sai dai kika sha wahalar zuwa nemana, Tabbas da na san Inda zan nemi ki in baki amsoshinki da tuni na je har Wajen komai nisan sa Sannan da tuni na roƙe ki ki zamo Gatana, amma ko yanzu duk da na Makara ina Fatan zaki Zamo Haske gareni ki zamo silar Yayewar duhun da yayiwa rayuwata Ƙawanya Kubrah!!! don Allah!......" daidai lokacin Hawayen da suka cika idanunsa suka samu damar zirarowa suna sauka ƙasa...... Tunda ya fara magana idanunta suna kansa har sai da ya kai ƙarshe sannan ta numfasa, a hankali ta durƙusa saitinsa sannan ta ce "Baka makara ba!, yanzu ne daidai lokacin da ya dace,,, amma me yasa kake kuka a memakon kayi farin ciki Bayan ka gina Fadarka a Masarautar da kake Mafarkin Zama Sarki a cikinta?" ''Na kamu da matuƙar tsoron kar wani furci nawa ya zamo abun fushi gareki, ina matuƙar Sonki Kubrah!!" Yalwataccen murmushi ta saki kafin ta ce "Nayi farin ciki sosai da jin dukkan kalamanka, na ƙara samun ƙwarin gwiwa, musamman da ka yarda dani kuma ka so ni duk da baka san ko ni Wacece ba hakan kaɗai ya isa ya tunzura ni,,, in tunkari Duniya in sanar kai ne zaɓina!!" "Sonki daga Allah ne Kubrah, ba ni nayi Dashensa ba da kansa ya tsiro, ke kaɗai nake so shiyasa ban damu da bibiyar Tarihinki ba Duk da cewar ina son ji, ba zan tilasta miki wajen Faɗa min ba, sai lokacin da kika yi niyya!" Ɗan Murmusawa tayi kafin ta miƙe ta koma kan Kujera ta zauna, ganin haka ya sa shi miƙewa shi ma ya zauna......... https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw Sai da ta ɗan yi gyaran murya sannan ta ce "Khadijatul-Kubrah Ɗiya ga Muhammad Rislan !, Ina rayuwa a wata Ƴar Ƙaramar Duniya kuma keɓantacciya, Ba zan iya cewa ga Shiyyar da Muke ko kuma wani Local Government da ya jiɓance mu ba, abu ɗaya kawai na sani shi ne a Jihar Kano Muke, takamaimai ban san Yaya zan yi kwatance a gane Gidanmu ba, sannan Mutanen da muke mu'amala dasu a ƙayyade suke haka wanda suke rayuwa a ƙarƙashin Ikon Affana, Gidanmu Baya ɗaya daga cikin jerin Masarautun Duniya amma ya kasance Tamkar Masarauta sabida girmansa da kuma ɗumbin Dukiyar da ke cikinsa, sannan akwai Bayi da Hadimai a cikinsa,,, Affana ba Sarki bane amma Mutane da yawa da hakan suke kiransa ko su ce Mai Martaba ko kuma Shugaba, mu kuma sukan bamu Matsayin Ƴaƴan Sarki,,,, A Masarautar mu akwai kowa amma babu Waziri ko Galadima Affana shi kaɗai yake Mulkinsa kuma yake zartar da hukunci; Affa yana da tsauri musamman akan ra'ayinsa ko kuma Dokokinsa, ba ga Mutanen Gari ba kaɗai har mu Ƴaƴansa manta alaƙarmu yake yi a yayin da ya tashi Hukunta mu bisa Laifinmu, hakan ne yasa damu da Al'uma muke matuƙar tsoron Fushinsa,,,, Daga cikin gida sai Daji nan ne kaɗai inda Affa ya sahale mana mu je mu yi Wasa;, koda acikin Dangin Mamma ko kuma dangin Affa wasu suke son ganinmu sai dai su zo gidanmu su same mu, sai jefi-jefi ake kai mu gidajensu shi ma ta sigar da ba zamu iya mayar da kanmu Gidan ba" Shiru ta ɗan yi tare da sauke nannauyar ajiyar Zuciya sannan ta cigaba "Na taɓa gaya maka cewa gabaki ɗaya rayuwata Tambaya ce, gashi yau ina ƙara maimaita maka, Ni kaina ina da Tambayoyi akan rayuwata sai dai banida me bani amsar su, a taƙaice dai ni kaina ban gama sanin Wacece ni ba!!" Ɗan tsagaitawa tayi sannan ta ƙara da cewa "Ina fatan babu wani dalili ko wani tsanani da zai sa ka guje ni Umar!!!, ina fatan zaka iya Fuskantar Mahaifina da kuma Sauran Mutanen dake gareshi ka faɗa musu cewa Ka zaɓe ni a matsayin Abokiyar rayuwarka komai wuya komai runtsi, sannan fatana na ƙarshe shine,,,, koda zan kasance Musaka ko kuma in kasance cikin wani Jinsi daban hakan ba zai sa ka juya min baya ka ƙaurace min ba !" Gwauron numfashi ya sauke gami da lumshe idanunsa ya murmusa sannan ya ce "Indai haka ne zanyi, ko yanzu in zaki kaini zan faɗa masa, kuma ko ina za a shigar dani ba zan canja maganata ba, dukkan Fatanki zan cika shi Bi'izinillah, ba zakiyi da na sanin Sona da kikeyi ba zan zamo miki Bango a rayuwa da ikon Allah " Miƙewa tayi gami da cewa "Lokacin tafiyata yayi ba don na gaji ba!" shima tashi yayi yana cewa "Yaushe zan ƙara ganinki?" "Ba ni ke yanke wannan hukuncin ba, in dan ni ce gobe ma zan dawo, amma ba zan iya hakan ba har sai na samu izinin Abee!" ya buɗe baki zaiyi magana ya dakata don ganin idanun Abee a kansu........... Ware mata hannayensa yayi aikuwa ta falla da gudu ta ɗafe shi ya rungumeta tsam gami da lumshe idanunsa, sai da ya ji sautin kukanta sannan ya ɗan janye jikinsa yana cewa "Kin san na hana ki kuka ko?" share ƙwallar tayi tana cewa "Yaushe ka zo?" Murmushinsa na gefen baki yayi kafin ya ce "Na daɗe da zuwa, hankalina ya kasa kwanciya ne, alhaki ne a wuya in mayarwa Affah Ɗiyarsa Gida lafiya!" "Na ji daɗi da ka zo, daman ina tsoron komawa ni kaɗai!" Bai ce komai ba ya sungume ta ya ɗorata kan Dokinta sannan ya haye nasa yana cewa "Ahmadi ka ƙara ninka kulawarka akanta" Ahmadi ya rusuna yana cewa "Zanyi hakan da izinin Allah" Bai ce komai ba yayi gaba hannunsa ɗaya riƙe da Linzamin Dokin Kubrah, Ahmadi kuma ya bi bayansu ..... Har suka ɓace Kubrah tana waiwayen Umar shi ma yana ta famar kallonta. Da baya da baya Umar ya ƙarasa jikin bango ya jingina tare da furzar da wata zazzafar iska kamar wanda ya kawo Ƙarshen Yaƙi. Ammar ya kalle shi sama da ƙasa kafin ya ce "Danƙari maƙari, gaskiya sai na nemo Marubuta sun rubuta labarin Soyayyarka Abokina, na san hakan zai zamo Darasi ga Mutane daga nan har Ƙarni Casa'in Masu zuwa!" Murmusawa Umar yayi gami da sauke nannauyar ajiyar Zuciya sannan ya ce "Ba na son Zolaya Ammar, ni anan ban ga abun da zai zamo Darasi ba bare har a rubuta, ba fa a kaina aka fara So ba kuma ba a kaina aka gama ba" "E, na san da hakan, amma ni kai na gani kuma kai na sani, nima na ɗauki nawa Darasin saura ƴan baya!, ni bari ka ga ma in koma in gayawa Ummi da Abba su yi shirin zuwa neman Aure, yau na fasa fita kasuwar ma!" yana kaiwa nan ya juya da gudu zuwa cikin Gida ba tare da tsayawa saurarar kiran da Umar yake masa ba. Sin...... Cikin Sanɗa take takawa tana yi tana waige-waige gami da laɓewa da zarar ta ji wani motsi yana shirin tinkarota..... Jikinta a rufe yake ruf!! cikin kaya na Alfarma irin na Ƴaƴan Sarauta a Ƙasar China, bayan duk adon da ta sha ta lulluɓe Fuskarta da Farin Mayafi sai iya idanunta wanda suka sha Gazal kaɗai ake iya gani, Daga yanayin Zubin Jikinta da kuma ƙwayar idanunta za a gane Yarinya ce wadda ba ta wuce shekara Ashirin ba..... Shigowarta Sashin Yarima Jiehong ne ya sa ta ƙara sauya taku gami da ƙara taka-tsantsan don gudun Dakarun da suke aikinsu a wajen. Ta shagala wajen tunani kawai taji Ƙafarta ta riƙe ƙam!! ko motsata ta kasa yi, a hankali tayi ƙasa da kanta ta duba ƙafafun nata, ko shakka babu Wani hatsabibin Matsafin ne ya riƙe mata ƙafa. Ɗagowa tayi tana rarraba ido cike da son ganin ta inda za a ɓullo mata, Ganin Farar Takobi na walƙiya a saitin wuyanta ne ya sa Ƙara buɗe idanunta cike da razani, "Bayan kun Kashe mana Sarauniya yanzu shi ma so kuke ku kashe shi??" Muryar Ɗaya daga cikin Sojoji mafi kusa da Prince Jiehong ta ratsa kunnuwanta,, cike da ƙarfin hali ta ce "Ba don kai na zo nan ba, don haka ka bar ni in je gurinsa, kuma baku da Hujjar cewa Daga Ɓangarenmu aka kashe Sarauniya!" murmushin gefen baki yayi sannan ya ce "Babu wani Ɗa daga Gidanku da zai iya shiga nan koda Mahaifinki ne!" "Sai na shiga!" ta faɗa tare da sunkuyawa ƙasa ta zame daga tarkon nasa ta falla da gudu...... Ruwan Kibbau suka fara bata daga ko'ina ana kawo mata hari sai dai sun kasa samunta don ƙwararriya ce ta fannin tsalle-tsalle...... ganin hakan ba zai yi musu ba ya sa suka baza Tarko na Sarƙa suka zarge ƙafafunta...... Haukan ƙarya ta fara yi musu ta hanyar kai musu duka da fizge-fizge, ba shiri suka aika Mutum Ɗaya don sanarwa Yarima halin da ake ciki, ba daɗewa ya dawo yana numfarfashi yana cewa "Ku barta ta shiga!" Kwance ta suka yi ba don ransu ya so ba, ita kuwa ta miƙe ta kakkaɓe gefen zumbulelen skirt ɗinta ta hararesu sannan tayi ciki.... Yana Tsaye gaban wani Ƙaton Table yana shirin Ɗaukar glass cup wanda ke ɗauke da ruwan Giya a ciki, da sauri ta zuro hannu zata ɗauke cup ɗin sai dai batayi sa'a ba don kuwa duk yadda ta kai ga zafin namanta ya fi ta, wata kyakkyawar damƙa ya yiwa hannun nata sai da ta saki ƙara sabida azabar da ta ratsa ta har cikin kanta. Da ɗayan hannun ya ɗauki cup ɗin ya kurɓi abunda ke ciki sannan ya watsa mata guntun a fuskarta. Runtse idanunta tayi da ƙarfi tana ƙoƙarin gogewa da ɗayan hannunta don kuwa ya shiga idonta sosai. Bai bata damar hakan ba ya fizgota da ƙarfi ta faɗo jikinsa ya matse ta da ƙarfi,,, hakan ya tilasta mata buɗe idanun nata ta jefa su cikin nasa, sai da ya cire mayafin da ta rufe fuskar dashi sannan ya ce "Raina ya fi na Mamata Ƙwari, ba za ku iya Kashe ni ba!" "Koda kowa zai iya yin hakan ni ba zan iya ba!" da ƙyar ta fizgo maganar don tuni numfashinta ya fara sarƙe saboda muguwar matsar da ya yiwa ƙirjinta a cikin nasa..... Murmushin gefen baki yayi wanda in mutum ba ya da lura sosai ba zai gane yayi ba ma. "Ƙiyayyar da nakewa Mahaifinki ta sa bana son in dinga ganinki" "Ni kuma ba zan ƙauracewa idanunka ba komai yawan azabar da zaka yi min, kuma ba zan taɓa dena sonka ba" ɗan sunkuyawa ya ƙara yi fuskarsa ta kai daf da tata sannan ya ce "Ranar da na na kashe ku ke da shi za ki dena ko?" kawar da kanta tayi gefe ta ɗan girgiza kai ba tare da ta yi magana ba, wasu zafafan hawaye na azaba gami da ƙunar Zuciya suka fara tsiyayowa daga idanunta. Hannunsa ɗaya yasa ya matse kumatukanta da ƙarfi irin yadda ake wa yaro ɗurar magani,, sai dai salon ya bambanta don shi nashi yadda yasan zataji zafi yayi, juyo da fuskarta yayi saitin tasa sannan ya ce "Har kin kai matakin da zanyi magana kiyi shiru ko?" "Za ka kasheni fa!" ta faɗa cikin muryar da take nuna ta kusan shiɗewa. Murmushin nasa na masifa yayi ya ɗan sumbaci laɓɓanta sannan ya ce "Na fi so ki Mutu, amma ba yanzu ba sai lokacin da na gama cikawa Babana Muradensa sannan zan Kashe ki in kashe Mamanki don ina so Zhengyu ya san zafin Mutuwa" bai bata damar yin magana ba ya rufe bakinta da nasa ya fara kissing ɗinta..... Zuwa yanzu hawayen nata sun tsaya cak idanunta sun firfito waje guru-guru ta fara kokawa da numfashinta wanda yake barazanar ficewa ya barta...... Sai da ya tabbatar ta kusa sumewa sannan ya janye bakinsa daga kan nata ya hankaɗa ta da ƙarfi ta faɗa kan Table sannan ta dawo ƙasa ta baje tana wani mugun tari kamar me shirin barin Duniya. Juyawa yayi ya fice cike da rashin imani , bai damu da halin da ya barta a ciki ba hasalima burinsa kenan a kullum ya dinga yi mata izayar da wataran za a wayi gari da kanta ta ce bata Ƙaunar ganinsa. Aikinsa kenan kullum in suka haɗu sai ya tabbatar yayi mata abinda zata daɗe yana mata ciwo. tana cikin wannan halin na uku Bala'i Ƙartin Sojojinsa suka shigo suka ɗaure ta tamau da Sarƙoƙi suka kinkimo ta suka fitar da ita can bainan-nasi sannan suka yasarta a wajen. Ta daɗe tana majaujawa a wajen Sannan ta iya miƙewa tana tafiya tana haɗa hanya ta nufi sashinsu. Kafin ta isa labari ya iske Prince ZhengYu, a tsaye ta same shi yana safa da marwa, tsoro ne ya fara ɗarsuwa a Zuciyarta tuni jikinta ya ƙara ɗaukar tsuma, kasa ƙarasawa wajensa tayi don ta san shi akwai baƙar Zuciya ga saurin hannu. Duk da haka bata tsira ba bata san ta ya akai yazo kusa da ita ba sai jin saukar Yatsunsa biyar tayi a kumatunta, sai da yayi mata uku kyawawa sannan ya fara zazzaga bala'i ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba........... *🪻SAWUN KEKE🪻* season *2* By INDO (SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU) WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE.... naira 400 (idan zakiyi payment tare da SEASON 1 a lokaci ɗaya, akwai Discount, Naira 600 duk biyun) SHARE FISABILILLAH Ep...........13 https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw Nigeria..... Kubrah da Abee yau ma a karo na barkatai sun yi sa'a babu wanda ya san sun fita har suka je suka dawo, sai da suka daɗe da dawowa ne Mamma ta fara nemansu sai suka nuna mata bacci ma suke yi. "Ni fa ina ganin gwara mu faɗawa Affah Alaƙarki da Umar!" Abee ya faɗa yana kallon Kubrah, numfasa tayi sannan ta ce "A'a gaskiya ina jin tsoro, ina ganin hakan ba zai sauya komai ba, kuma jikina yana bani ba lallai ya amince da shi ba, ka ga in ka faɗa yanzu kawai zai raba ni dashi ne, ni kuma ban shiryawa hakan ba!" Shiru ne ya ratsa tsakani kafin Abee ya ce "Amma kin iya wauta Kubrah!, kin san kina jin hakan kuma kika fara? kuma me yasa zaki sako Umar a cikin rayuwarki indai kin san za ki rabu dashi?, ai da kin sani baki faɗa masa kina son shi ba" "Ba ni da zaɓi ne!, ina matuƙar son shi Abee, koda zan rabu dashi ina son alaƙarmu ta yi tsayi fiye da haka, shi yasa na zaɓi ɓoyewa Affah!" "Shi kenan, na fahimce ki amma Allah yasa hakan ya haifi Ɗa me ido, kin san halin shi ba sai na gaya miki ba, ni ina mamaki ma da kike fita ba tare da ya sani ba a wannan lokacin" ''Ni ma ina wannan mamakin, amma nafi tunanin hakan yana da nasaba da Tasirin da Umar yake dashi gareni, Allah ne kaɗai yasan me ke ɓoye a cikin hakan!" Shiru suka ɗan yi na wucin gadi sannan Abee ya ce "Ban san da wane yare ya kamata in miki bayani ba, amma jikina yana bani akwai abunda zai faru a nan gaba kuma ba lallai ya zamo me daɗi ba, sannan ina ganin kamar rayuwa zata ɗan canja mana koda na ɗan lokaci ne" a take jikinta ya ƙara yin sanyi ƙalau, ita ma takan fuskanci irin yanayin da Abee yake fuskanta sai dai bata ɗauki hakan matsayin komai ba face ruɗanin Soyayyar Umar. Ta buɗe baki zatayi magana Mariam ta riga ta da cewa "Tsuntsun da ya ja ruwa dai shi ruwa ke jibga!" Dukkansu suka zuba mata kallo cike da son fashin baƙi akan kalamin nata, ƙarasowa tayi tana girgiza da kwarkwasa ta zauna kan Kujerar dake fuskantar 2seater ɗin da suke kai, "Rana Dubu ta ɓarawo, rana ɗaya tak! ta me kaya..." ta ɗan murmusa sannan ta cigaba da cewa "Ba ni na faɗi hakan ba fa Hausawa ne suke faɗe, na ga kun fara fusata!" cikin mamaki Kubrah ta ce "Amma me yake damunki ne ? na ga kin canja fa" taɓe baki tayi ta ce "Murna nake na san wani ɓoyayyen Sirri naku, kuma gaf nake da tona muku asiri kowa ya san abunda kuke shukawa" kallon kallo Abee da Kubrah suka yi cike da mamaki da rashin fahimtar abunda take son faɗe. "Na san kuna fita kuma ku bar shiyyar nan, abu ɗaya na kasa ganewa shine inda kuke zuwa, to ina son sani idan kuma kun ƙi faɗa min babu shakka zan tona muku asiri har in ƙara da sharri!" ta ƙarasa maganar tana murguɗa baki. Murmushin kan laɓɓa Abee yayi gami da gyara zamansa ya kashingiɗa a jikin tattausan Filon kusa dashi, Kubrah ta buɗe baki zatayi magana ya ɗaga mata hannu tayi shiru. Ganin haka ya sa Mariam ta fara shan jinin jikinta, duk da tana da makamin da zata iya Yaƙarsu amma tana matuƙar tsoron Shu'umancin Abee.... Katse mata tunanin yayi da cewa "Yarinya ! idan ba ki san waye Abee ba baki san Kubrah ba ki je ki bibiyi Tarihi!, ba ke ba ko Babanki Uncle Isah bana jin yana da zarrar da zai sa mu faɗa masa inda muke zuwa, idan kin shirya faɗe Bismillah ki je ki taka bakin Faranti abun ciki ya tarwatse ayita ta ƙare, ni zanyi murna da hakan yayin da ke kuma zai zamo miki silar zubar hawaye daga nan har ƙarshen rayuwarki, ko shakka babu sai na zamo miki alaƙaƙai a rayuwa kuma sai na yi silar rabuwarki da jin daɗin Duniya!!" Dim! dimm!!! Zuciyarta ta fara tsalle tana faɗuwa tana tashi, lokaci guda jikinta ya fara tsuma ga wata zuffa da ta fara keto mata..... da dafe-dafe ta tashi ta nufi hanyar fita idanunta har wani duhu-duhu suke nuna mata, haka kawai bata san dalili ba tayi matuƙar firgita da jin kalamansa, wata Zuciyar tana gaya mata ya riga ya gane zaman Leƙen asiri take a Gidansu wata Zuciyar kuma tana gaya mata bai gane ba kawai wani mugun ƙullin zai yi mata. Ɗakinta ta koma ta rufe ƙofa ruf! sannan ta lalubo wayarta ta kwanta kan gado tayi lif! tana sauraran yadda ƙashushuwanta da jijiyoyinta suke ƙoƙarin daidaita kansu. ta daɗe a haka ko motsi bata yi kafin ta samu ƙwarin gwiwar turawa Abbinta kira. Ba ɓata lokaci ya amsa muryarsa a ƙasa-ƙasa ya ce "Ina Asibiti Mariam!, sun ƙara yiwa Rahma Allura ciwonta ya ƙara tashi yanzu an kwantar da ita ma, don Allah kiyi ƙoƙari mu samu wata makamar ko dan lafiyar Ƴar Uwarki!" "Abbi kar ka damu zata warke in sha Allah" jinkirtawa tayi saboda kukan da yake shirin kufce mata, sai da tayi da gaske sannan ta hana shi fitowa sai dai ta kasa dakatar da ƙwallarta wadda ƙunci da tashin hankali suka sa tayi zafi gami da raɗaɗi a cikin idanunta. "Zan cigaba da ƙoƙari akan wanda nake yi, amma fa nima zan iya fuskantar haɗari a rayuwa, matsalar da take faruwa komai nasu sirri ne a tsakaninsu bana iya gane wani abun da suke yi, kuma na tambayi inda suke zuwa ɗin kamar yadda ka ce amma ban samu amsa ba sai ma barazana da na fuskanta" Abbi ya goge ƴar ƙwallarsa sannan ya ce "Kar ki damu Mariam, abinda nake so dake kar ki ƙara tambayarsu don in suka ce za su yi miki abu to yana iya faruwa, haka nan zamu haƙura mu fawwalawa Allah koda hakan na nufin Rahma za ta rasa ranta, kar kiyi dai abunda za ki jefa kanki cikin matsala nima ki jefa ni, in akayi haka anyi mutuwar kasko kenan, gwara waninmu ya mutu wani ya tsira, gwara waɗannan azzaluman su kashe ni su kashe Rahma, na san zaki kula da Mamanki da Ƙaninki, idan hakan ta faru kuma kar ki yarda ki bar inuwarsu, anan ne zaki fi samun tsar..........." ɗif! network ya ɗauke gashi dai kiran na aiki amma bata jinsa shi ma baya jinta, dolenta ta katse ta ƙara kira sai dai network ya ƙi bata damar kaiwa gacci,, tura wayar tayi ƙarƙashinta ta fashe da kuka me tsuma Zuciya, lallai abun ya ci tura tunda har Abbi ya fara bar min wasiyya, wai kuwa shi Wannan Mutumi wane irin Mutum ne da manyan Hatsabibai na Duniya suke nemansa???? ........ wannan tunanin ne ke famar kaikomo a cikin ƙwaƙwalwarta. Affah....... Cikin Ƙasaitaccen Takunsa yake ratsa sassa daban daban na cikin Masarautar, wadda ta sha ado ta ko'ina kamar ba za a Mutu ba, duk inda ya ratsa gaisuwa ake miƙo masa ta ko'ina har ya isa Babban sashi Na wadda ake yiwa laƙabi ga Uwar Masarauta!. kai tsaye ya nufi tafkeken Gadonta wanda da an kalla za a hango tsantsar Mulki da gadara a tare dashi, duba da yadda ya sha kyakkyawar shimfiɗa ta Alfarma ga adon Gold ta ko'ina a jikin Gadon... Durƙusawa yayi a Gabanta tare da ɗora hannunsa kan Kyakkyawar Fuskarta wadda ta nuna alamun Manyanta, "Mother!!!" ya furta cikin muryar raɗa......... cikin nutsuwa ta dafa hannun nasa sannan ta buɗe gwara-gwara idanunta ta zuba a kansa, kamar ba zata yi wani motsi ba sai kuma Ta yunƙura ta tashi zaune, lallausan murmushi ta sakar masa gami da shafar kansa sannan ta ce "Kubrah da Abee sun ƙwace min Ɗa,,,,, He forgot his Mother!" "Ban isa in manta da ke ba Ammyna!, fatana lafiya ce tasa kika kwanta a wannan lokacin" ɗan numfasawa tayi sannan ta ce "Haka ne,! lafiya ce ta sa na kwanta duk da cewar tunaninka ne ya sa nake jin rashin walwala amma yanzu i'm Okay tunda na ganka" "I'm so sorry my Mother!" ya faɗa cike da ladabi...... Murmushi ta yi kafin ta miƙe ta gyara zaman Zankaɗeɗiyar doguwar rigarta sannan ta fara takawa one by one Tamkar wadda take gaba da ƙasa, miƙewa Affah yayi ya bi bayanta yana cewa "What Happen!" ya tabbata akwai wata a Ƙasa. Tana tafe yana binta har suka ƙarasa wajen Window sannan ta tsaya tana leƙen tsirarun Mutanen da ke kai komo a can ƙasa, nannauyan Numfashi ta sauke sannan ta fara magana "A wajena kai ne wanda kula dai kai ya zame min dole, a wajenka kuma Su Kubrah su ne Dole!, Kai kana da ni su kuma suna da kai, ka cigaba da kula da su ka ji Ɗana!!" gyaɗa kai yayi alamar To sannan ya ce "Kubrah tana bani ciwon kai Mommah!, gashi na tarar da canji akan Fuskarki" Murmushi me ɗan sauti tayi kafin ta fara magana "Nasan ka san Rayuwa takan iya canjawa, sai dai sanin lokacin canjawar tata sai Rabbissamawati, wani abun duk Dabararmu sai ya faru har mu dinga ganin kamar sakacin mu ne ya jawo haka, kar ka ɗauki wani abun a matsayin Gazawarka ka dinga dangana shi da Mu'ujizar Ubangiji , kasan Alƙawarin Allah ba ya gushewa ba tare da ya cika ba!,,, wani abun sai ka kawar da kai sannan ka zamo me haƙuri akansa amma Tabbas akwai Abunda yake shirin Faruwa sai dai sanin abun da kuma lokacin faruwarsa Sai Allah; abu ɗaya nake so ka ƙara riƙewa shine ninka Kusancinka da Ubangijinmu Allah; sannan kulli-yaumin ka dinga tuna cewa Ƙaddarata daban Taka daban haka ta Ƴaƴanka daban, ina fatan ka fahimta !" jinjina kai yayi kafin ya ce "Na gane Mommah! amma me yasa wani abun daban yake bibiyar rayuwata da IYALINA ??" "Ƙaddara kenan kowa da kalar zanen ta shi, ka sa a ranka komai zai wuce watarana sai dai aji Tarihi!" ya numfasa sannan ya ce "Shi kenan!, ina Ɗan Uwana?" "Yana Sashin Sarki, zaka je ne mu tafi tare ?" da kai ya bata amsa, ta ɗan numfasa kafin ta fara tafiya, bayanta ya bi Zuciyarsa cike taf da tunane tunane kala-kala. *🪻SAWUN KEKE🪻* season *2* By INDO (SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU) WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE.... naira 400 (idan zakiyi payment tare da SEASON 1 a lokaci ɗaya, akwai Discount, Naira 600 duk biyun) SHARE FISABILILLAH Ep............14 Sin........ Prince Jiehong yana Zaune kan kujera da take fuskantar wadda King Yizheng yake kai sun saka Table a tsakiya suna famar kallon Takardar Taswira dake kan Table ɗin, sun ɗan jima suna nazari sannan King Yizheng ya katse shirun da cewa "Dajin yana da Sarƙaƙiya sosai sai ka nutsu zaka iya shiga cikinsa don kuwa akwai Sojoji masu tsaronsa!" cikin nutsuwa ya ɗago kai ya kalli Mahaifin nasa kafin yayi magana cikin salon miskilancinsa "Zanyi yadda ka ce !" King ya saki murmushin jin daɗi, duk duniya gani yake nasararsa tana tare da mutuwar Matarsa tunda gashi yanzu Prince Jiehong baya tsallake duk wani umarni na shi, ta haka ne kuwa zai yi nasarar cimma muradensa. Bayani ya cigaba da yi masa sosai akan Taswirar, wani abun yana fahimta wani abun kuwa tunani ya hana shi gane me ake nufi........ .................... https://chat.whatsapp.com/BnCaQxCqE3qGM4y4y3IVOw Prince Zhengyu zaune yake kan hamshaƙiyar Kujerarsa ya dafe Sandarsa ta ƙasaita da duk hannayensa biyu. Kasancewar ya lula Duniyar Tunani bai san lokacin da Prince Jiefan ta shigo ba har sai da ta kira Sunansa, cikin nutsuwa ya ɗago idanunsa da suka sauya launi ya zuba mata cikin salon son jin ta bakinta. "Tunanin me kake yi me zurfi haka?" kawar da kai yayi gefe kafin ya fara magana "Ban san ta yaya akai Ɗan Uwana ya fi ni da komai ba!, gashi ya gaje Kujerar Mulki gashi ya fi ni sanin Sirrikan Tsafi a yanzu, da fa na fi shi iyawa, dole hankalina ya tashi tunda nasan Yaƙata zai yi!" taku biyu tayi ƙwarara cikin ƙasaita fuskarta ɗauke da wani sirrintaccen shu'umin Murmushi, cikin nuna rashin damuwa ta ce "Ba na damuwa akan duk wani motsi na shi, saboda na san ka fi ƙarfinsa!" zumbur ya miƙe kamar an tsunkule shi, ya ɗan ɗaga murya yana cewa "Kin san kuwa illar da Yizheng yake da ita?, da kike magana amma yanzu ya tsere min, gashi yana da ɗansa mai temaka masa, ni kuwa tawa ƴar bata da amfanin komai gareni!, duk abunda nake so bata so, ko ke kina goyon bayana amma ita babu ruwanta sai ma So da ta ɗorawa Jiehong shi kuma yake wahalar da ita, na tabbata da zarar burinsa ya cika kasheta zai yi!"   NOTE....   (Kar dai a Manta da Yarensu suke magana ba da Yarenmu ba,👌🏼🤓 kasancewar Ni INDO da nake Rubutun ina baku labari da ku masu Karatu dukkanmu Hausawa ne shi Yasa nake yi da Hausa👏🏻🤭 ato kar a dinga tunanin Sinawa ma Hausawa ne lol.......😜😜) Maganar tashi ta taɓa Zuciyar Princess Jiefan ta yadda da abunda ya faɗa ɗari bisa , lokacin guda fuskarta ta sauya launi daga murmushi zuwa ɓacin rai, "Ya kamata ka yi ƙwaƙƙwaran motsi ka gane me yake shiryawa, don kuwa labari ya sameni cewar akwai shirye-shiryen da yake yi!" "Ni ma an sanar min akwai wani sabon Sirri me girma da ya samu, wanda in ya kammala haɗa shi to Duk Duniya ma zai iya zama me haɗari a cikinta don ba zai bari a zauna lafiya ba, zai ga bayan duk wanda yake son ya ɓatar ba iya ni kaɗai ba!" Prince Zhengyu yayi maganar cike da damuwa. Jim!! ta ɗan yi kafin ta numfasa ta ce "Mu yi ƙoƙari mu gano Sirrin idan zai yuwu sai mu riga shi mallaka!" kai kawai ya jinjina ba tare da yayi magana ba........... GABA "Haka kake gani?" gyaɗa kai yayi ya ce "Ƙwarai kuwa, Kuma yana matuƙar burge ni sosai fa, har ina jin dama Ni ne na Kasance ƊANSA, a gaskiya kin yi sa'ar Iyaye, suna fahimtarki har suna Gatanta ki, amma ni na rasa hakan daga Nawa Iyayen" Ɗan jim! tayi kafin ta ce "Ban gane me kake son cewa akan su Mommy ba" murmushin takaici yayi kafin ya ce "Shi Daddyna wai shi Ɗan Kasuwa ne, kullum ba shi da lokacin Iyalinsa sai na kasuwanci, sai kuma Mummunar ta'adarsu shi da Mummy wai ba za su haɗa hulɗa da TALAKAWA ba, ni kuma tun ina Yaro ba ni da Aboki a Ƴaƴan Masu kuɗi sai dai Talakawa, rayuwa a cikinsu shi ya fi burge ni, hakan ne ya sa Iyayena suka fara tsangwama ta, tunaninsu hakan zai sa in dawo bin ra'ayinsu in dena kula Talakawa, sai dai har zuwa yanzu ba su yi Nasarar hakan ba don gani nake na fi su gaskiya, Su basa Daraja Ɗan Adam duk Darajarsa indai ba me kuɗi bane; a ɓangaren Ƴaƴansu kuma babu kwaɓa babu Harara, sai su sakarwa Yaro kuɗi kawai yayi ragamar komai nasa da kansa, sannan Basa laifi bare ayi musu faɗa, ina magana ne akan Yasmeen da Yaseer, yanzu gashi nan Yaseer ba shi da aiki sai shan Giya sa Bin Mata, ba ya kwana uku a jere a gida sai ya tafi Hotel ya kwana, Ita ma Yasmin Ƙawaye kala-kala fitinannu za ki ganta dasu, ita ma Mommyn aikinta kenan bin Ƙawayenta wanda na tabbata su suke ƙara ɗora ta akan duk Tsiyar da takeyi; Kin ga asalin Iyayena dukkansu Ƴan Kaduna ne, daga baya suka zauna a Abuja lokacin tun ina Yaro, da ta ƙara cimaɗo su kuma suka dawo Kano shine fa yanzu muke Kano, batun danginsu kuma babu ruwansu dasu, ba wai Talakawa bane kuma, kawai su Sharafin gabansu suke yi, son kansu ya fi son komai, Ba sa neman Danginsu su ma Danginsu ba sa nemansu kawai idanunsu ya rufe akan neman Duniya; To kin ji abunda ya haɗa ni da Iyayena da Ƴan Uwana sam bama Jituwa da juna, saboda na dage sai na gyara musu rayuwarsu!" gwauron Numfashi ta sauke kafin ta ce "A ganina hakan ba abun damuwa bane, Ka cigaba da yi musu Addu'a in sha Allahu za su dena" "Haka dai Ammar yake faɗa min, Allah yasa hakan zata faru" ta amsa da Amin sannan ta cigaba da cewa "Ina Matuƙar sonka Umar!, Ina tsoron wataran ka gaji da wahalar da Mahaifina yake baka, ka tafi ka barni cikin Masifar So" yayi murmushi me sauti kafin ya ce "Kubrah kenan!, Da izinin Allah ba zan tafi in barki ba, har sai in ke ce kika ce in tafi, ban ƙi ba ko Affah in ya ce in tafi dole zan tafi don ba zan iya karya Umarninsa ba!" Cikin murya irin ta wanda yake shirin fashewa da kuka ta ce "Koda wani abun zai faru dani ba za ka guje ni ba Umar?, koda ƙaddara ta sa ina daga cikin wani Nau'in halittar?!" sosai Zuciyarsa ta karye musamman da jin Furucinta na ƙarshe, 'Me hakan ke nufi kenan?' ya jefawa kansa tambayar, sai dai duk yadda ya kai ga ƙoƙarin yiwa maganar tankaɗe da rairaya ya kasa, a gefe guda kuwa wutar sonta ce ke ƙara ruruwa a Zuciyarsa, yayi ƙoƙarin ma ya hango ko akwai wani abu da zai sa ya gujeta amma bai ga komai ba sai tsantsar so da sadaukarwa, ya bawa kansa yaƙini kan cewar babu abunda zai sa ya juya mata baya koda kuwa hakan na nufin rasa ransa. Ɗago idanunsa wanda alamun tausayi ya cika su yayi ya zuba mata kafin yayi magana cikin tattausar murya, "Kubrah ba ni na zaɓe ki ba Allah ne ya zaɓa min ke!, ni kuwa me zai sa in Butulcewa masa akan Baiwar da yayi min?, ki kwantar da hankalinki ni na shirya Rayuwa da ke indai akan wannan tunanin naki ne hakan ba zai tsorata ni ba, ki cigaba da farin ciki abunki kar komai ya dame ki" ta saki lallausan murmushi, ta ma rasa amsar da zata bashi, ji take ina ma tana da damar da zata rungume shi tayi kuka ko zata ji saukin Yaƙin fa ake yi acikin Zuciyarta. Ahmadi ne ya ƙaraso wajen cike da Ladabi ya ce "Gimbiya Uwar Masu gida ina gaisuwa gami da neman Sulhu!, don na tabbata aiken nawa ba mai daɗi bane Ranki-yadaɗe!" duk suka zuba masa ido suna jiran abunda zai faɗa.... "Tuba nake Gimbiya a Gidanmu!, wato Mai martaba ne ya ce in zo in sanar da ke ba ya kawo Umar Gidan nan bane don ki je ki dinga tarewa a wajensa, don haka ki tashi ki je yana nemanki" Sallama ta yiwa Umar sannan ta tashi jikinta a bala'in sanyaye. Umar kuwa kuka ne kawai bai fasa ba, kawai sai ya bita ido. a Haraba ta samu Affah fuskar nan tamkar hadarin da ya gangamo yake kaikoma yana rugunɗimi a sararin samaniya...... "Kar na ƙara gani kin je wajensa, ba don hakan na kawo shi ba, bare har ki kai masa Abinci!" ya faɗa yana tsare ta da idanu, gyaɗa kai tayi kanta a ƙasa kamar munafuka. Tsaki ya doka sannan ya cigaba da Tafiya ya nufi Dokinsa, da alamu fita ze yi. Da sauri ta shige cikin gida tana raɓe-raɓe don kar ta ƙara katari da faɗan Mammi...... China.... Lisha har ta rame saboda damuwar da ta addabi rayuwarta.... tayi bala'in takaici da aka ce mata Prince Jiehong ya riga ya tafi. a gefe guda kuwa ganin ta rikice akan tafiyarsa yasa Babanta ZhengYu ya ɗora ransa akan sai ta gaya masa dalilinta na nemansa, ƙarshe ma ya ce ta san inda zai je sai ta gaya masa. Ta san yin hakan kuma wani sabon bala'in ne shiyasa ta ƙi faɗe ta jurewa Masifarsa , don ba daga nan ba indai wajen Masifar faɗa ne Allah ya hore masa. A wani ɓangaren kuwa matsanta tsaro da tayi don kar a gane tana da ciki yakan jawo mata mugun damuwa da ƙunci ga tunane-tunane . Haka nan ta ci gaba da ƙurƙura rayuwa tana famar katangala. Nigeria Jiki a sanyaye Ammar ya zame ya kwanta kan Katifa yana kallon sama, fuskar Abokinsa ko ma a ce ɗan uwansa, ita ta fara dawo masa sabuwa fill!,,, idan ya kasance abunda Umar ya faɗa cewar ba lallai na sake ganinsa ba ni kuwa ina na sa ƙafa a rayuwar nan?, wai wacece ma wannan da take wahalar da rayuwarsa haka? Tambayar da yake yiwa kansa kenan sai dai ba shi da amsar. ______________________________________ Prince Jiehong.... Bayan fafatawa da Abokan takararsa akan hanya ya samu Nasarar isowa amma ya sha wahala dan an so hallaka shi, da temakon Dakarun Aljanun Babansa da kuma tsafinsa ya samu ya sha fa ƙyar. Karo uku ana kawo masa hari, kuma duk masu neman abunda yake nema ne. Lokacin da ya dira a cikin Dajin tare da Ƴan Daban Aljanunsa, hatta bishiyu sai da suka girgiza sakamakon Ɗaurin da aka yiwa Dajin an karya shi lokaci guda,, hakan ya rugunɗima ya bada turnuƙun hayaƙi da guguwa mai ƙarfi.... Tun daga kan tsuntsaye har zuwa wasu ƙananun dabbobin sai da suka firgita suka fara gudun neman tsira.... Yarima Jiehong ya ƙara yin zaman dirshen don rufe ƙofar da ya buɗe, domin kuwa ya lura akwai masu son sace Kubrah ba shi kaɗai bane. Sai da ya gama sannan suka nemawa kansu Masauki suka haɗa Tanti suka yada zango baje-baje hankali kwance. Ba daɗewa Prince Jiehong ya fito yana ƙarewa Halittun dake cikin Yankin da suke kallo, ya saba ganin Dazuka iri-iri amma sai ya ji wannan ya fita daban a cikinsu. Tafiya ya fara yi yana kalle-kalle tare da shaƙar iska gami da ƙamshin tsirrai da yake kaɗawa, tuni ya fara lulawa Duniyar tunani kuma bai fasa tafiya ba don bai ma san inda yake jefa ƙafarsa ba bare lissafin komawa Masaukinsa. Yayi nisa sosai a tafiyar sannan ya farga, ya dakata yana duba ko'ina don ganin ta inda zai koma. Zuciyarsa ce tayi wani kyakkyawan tsalle saboda Kibiyar da ta tinkaro shi, cikin sauri yayi gefe ta wuce ta gefensa ya juya yana binta da kallo, jiyayi an ɗora tsinin Takobi a gadon bayansa kamar za a huda shi, yayi fakare yana saurarar motsin wanda yake shirin yi masa aika-aika. Sai da ya shammace ta ya juyo tare da sa ƙafa ya doki ƙwaurinta, ta saki ƴar ƙara tare da yarda takobin tana ƙoƙarin hana kanta faɗuwa, ido ya zazzaro tare da riƙo hannunta yana ƙarewa bayanta kallo, bai yi tsammanin zai ga Mace ba kuma sai gashi ya ganta, juyowa tayi ta tsira masa ido suka fara yiwa juna kallon-kallo, ta rufe fuskarta sai iya idanunta ne a waje, hakan yasa ya fi mayar da hankali kansu, wani irin bugu zuciyarsa ta fara yi mai tashi a hankali a hankali, ga wani baƙon yanayi da yake ratsa shi tun daga cikin idanunsa har zuwa duk ilahirin jijiyoyin jikinsa....... Gyara tsayuwarta tayi sannan ta fizge hannunta ta yi baya, sanin idan tayi hausa ma ba zai ji ba ya sa ta yi magana cikin Harshen turanci...... "Who are you?!" Kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce "I'm Jiehong from China, please show me your face!" Cikin zafin nama ta durƙusa ta suri Takobinta tare da kai masa sara, da sauri ya kauce gami da yarfa hannunsa gefe, nan take wata haɗaɗɗiyar Takobi ta bayyana a hannunsa nan fa suka kacame da Kaiwa juna Farmaki...... Mamakin zafin kanta da kuma ƙwarewarta a fannin sarrafa Takobi ya hana shi tasirin komai a kanta, zuwa yanzu ba shi da burin da ya wuce ganin fuskarta don haka yayi amfani da Tsafi wajen ƙwace Takobinta ya jefar gefe sannan ya fincikota ta faɗo ƙirjinsa. Mutsil-mutsil ta shiga yi tana ƙoƙarin ƙwatar kanta amma ta kasa. a hankali ya kwance Maɗauron fuskartata ya wurgar gefe kafin ya maida duk ilahirin hankalinsa kanta, ƙuri yayi mata da ido kamar bai taɓa ganin halittar ɗan Adam ba, shi kansa bai yi tunanin zai tsaya kallonta har haka ba amma sai yaji gabaki ɗaya ma ba ya son ɗauke ido daga kanta. Ita ma kallonsa take yi ba tare da tasan me take tunani ba, sai da Mintuna suka shuɗe sannan ta farga, ta fara ƙoƙarin hankaɗe shi. Cikin wata raguwar murya ya ce "Tell me Your name, Boss Lady!" cikin sarƙewar Murya ta ce "Okay leave me!" sakinta yayi ta ɗan ja baya sannan ta ce "My name is Kubrah!" daga haka ta falla da gudu iya ƙarfinta, Sai da ya kusa faɗuwa ƙasa don yadda zuciyarsa ta buga da mugun ƙarfi, cikin muryar raɗa ya maimaita "Kubrahh!!!" lokaci guda ya tsinci kansa cikin wani irin yamutsi tun daga ƙwaƙwalwarsa har cikin ƙashi. Sai da yayi da gaske kafin ya nemo nutsuwarsa ya fara neman inda Masaukinsa yake. Hankalinta bai kwanta ba sai da ta koma cikin Gida, kai tsaye Bedroom ta wuce tana maida numfashi, bata san dalili ba kawai ta tsinci kanta da gaya masa sunan Yayarta wato Kubrah. Tambayoyi ne da dama gareta a kansa sai dai bata da amsar ba ta da me amsa mata. ______________________________ Masu Kula da Dajin kuwa tuni suka sanarwa Affah wani ya shigo sai dai sun kasa gane waye da kuma inda yake. Hakan yayi bala'in Girgiza shi, sai dai da ya tuno bayanan Mother sai ya yi banza da lamarin kawai. Bayan wasu kwanaki........ Yarima Jiehong..... ya duƙufa sosai wajen neman abunda ya kawo shi, sai dai babu sa'a, duk yawan Tsafinsa da kuma fitinannun Aljanun da suke tare dashi ko Inuwar Kubrah sun kasa gani bare inda take kwana. a ɓangaren Kubrah kuwa hankalinta kullum yana kan Umar, sosai take shiga damuwa akan irin wahalar da ake ba shi, ta ƙarfin tsiya wai sai an koya masa Farautar Dabbobin Dawa duk da cewar ba aikinsa bane, gashi haɗa shi ake yi da gagga-gaggan Mafarauta kuma a ce sai yayi abunda suka yi, in bai yi ba ya sha rashin Mutunci. A ɓangaren Umar kuwa tun baya sakin jiki har ya fara don ya lura hakan ya zame masa dole, wataran har ciwo yake ji, amma sai a haɗa shi da magunguna washegari a kuma yin zabarinsa a fita. Zahra Tun ranar da ta haɗu da Yarima Jiehong kullum ba ranar banza da bata tunaninsa, wani lokacin har gizo yake mata musamman in tana bacci. Saim kawai ta faɗawa abunda ya faru tare da yi masa gargaɗi kar ya gayawa kowa, shi ma ja mata kunne yayi akan Dagewa wajen Addu'a musamman tunda in tana bacci ma ganinsa take yi...... *🪻SAWUN KEKE🪻* season *2* By INDO (SAWUN KEKE SABON SALO..... SABON TAKU) WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE.... naira 400 (idan zakiyi payment tare da SEASON 1 a lokaci ɗaya, akwai Discount, Naira 600 duk biyun) don ƙarin bayani 09079885632 SHARE FISABILILLAH *Ep..........15* Last Free Page Yau Saƙon Gaggawa King Yizheng ya aikowa Prince Jiehong ta hanyar tsafi, akan ganin Gilmin Kubrah da yayi, sannan kuma za ta shigo cikin Dajin, in anjima don haka ya kasance a shirye , shi kuma zai turo da tsafinsa wanda zai hana ta yin tasirin komai har su yi nasarar Saceta........ Abee Cikin shirinsa na fita Farauta ya fito yana takawa ɗaya bayan ɗaya, Yau fuskarsa a sake take babu haɗe rai , hakan ne ya bawa Mariam ƙwarin gwiwar tinkararsa, cikin ɗari-ɗari ta ce "Ina son zuwa inda za ka je" ya ɗan kalleta ya kauda kai sannan ya ce "Ba za ki iya ba!" yana rufe baki ta ce "Zan iya mana, don Allah ka temaka, in na cewa su Zahra ina son zuwa ba sa zuwa dani" murmushin mugunta yayi kafin ya ce "Shi kenan, amma kiyi sauri don tafiya zanyi, sannan kuma ki gaggauta haɗa shirginki ki bar gidan nan na gaji da ganinki!" "To, daman na kusa tafiya, mu je ni a shirye nake ga Hijab ɗina a hannuna" bai ce komai ba yayi gaba, ta rufa masa baya tana murna... ta daɗe tana son shiga Daji ta ji abunda ake ji, amma basa tafiya da ita yau dai kam tayi sa'a. Mammi ce ta tare su tana cewa "Ina za ka tafi da ƴar Mutane??" "Ita ta ce tana son zuwa" ya faɗa yana yin gaba, da sauri Mariam ta ce "Don Allah Mammi ina son zuwa, ki barni please" ba don ranta ya so ba ta ce "'Allah ya tsare" ta ɗan ɗaga murya ta ce "Kai Abee ka kula da ita sosai" da To ya amsa ba tare da ya juyo ba. Mariam ta runtuma da gudu don kar ya ɓace mata. Tun basu yi nisa ba ta fara gajiya, tafiyar mugunta yake mata ya fita sauri amma ba ruwansa da tsayawa saurarenta gashi akwai tudu da kwari a hanyar wani wajen kuma yashi, dole take haɗawa da gudu don a ganinta in ta bari ya ɓace mata sai dai uwarta ta haifi wata. Sun yi nisa don har sun fara cimma ƙananun Dabbobin Dawa , sai lokacin ya rage saurin tafiyarsa, hakan ya bata damar ƙarewa Wajen kallo, farin ciki ne ya lulluɓe ta ta fara dariya har da tsallen murna, yau gata ta zo inda sai a Film ko a labarai kawai take jinsa. Murnar ce ta koma ciki saboda ganin wata baƙar guguwa me cike da almara ta yo kansu da mugun ƙarfi, nan take hankalita yayi fitar burgu ya tashi ta tsaya ƙiƙam tana sauraren abunda zai faru. Tana iya hangen wasu abubuwa tamkar inuwa a cikin guguwar sai motsi suke suna cakusawa. hankali a tashe ya fisgo hannunta yana ƙwalla mata kira, ƙasa suka zube su duka, Guguwar kuma ta shafe su ta wuce. Yau ɗaya dai ta tabbatar Abee yana ɗaukarta a matsayin Mutum don a zatonta a wajensa bata da maraba da Dabba. Jin yana wani irin ƙaƙari yasa ta zaro ido gami da yin kansa tana tambayar lafiyarsa, ji tayi ya riƙo hannunta da ƙarfi ya janyota cikin jikinsa. Ta Tattaro dukkan ƙarfinta ta fizge tana ƙoƙarin tashi ya riƙe ƙafarta, ihu ta kurma ko akwai wanda zai iya kawo mata ɗauki sai dai kashh!!. Ya tashi ya zauna yana zuba mata idanunsa da suka koma wani kala daban kamar ba na Mutum ba, sai da ta kusa sumewa saboda tsoro da tashin hankali, ƙara yunƙurawa tayi zata gudu amma ta kasa don ba ruƙon wasa yayi mata ba, kuka ta fasa tana roƙonsa ya ƙyaleta amma ko a jikinsa sai ma rungumarta da yayi da wani irin ƙarfi, bakin kukan nata ya cafke da nasa bakin ya fara sumbatarta cikin fitar hayyaci.... numfashin kirki ma sai da yaso ya gagareta sai da tayi sa'a ya sake ta da kansa ya fara kiciniyar yayyaga kayan jikinta. kuruwa gami da magiya ta cigaba da rero masa, ganin hakan ba ya yi masa aiki ya sa ta hankaɗe shi ta tashi.... kafin ta gudu shi ma ya tashi ya ƙara cakumota... Ihu ta kurma a karo na ba Adadi tare da tattaro dukkan ƙarfinta ta bangaje shi da Ƙarfi har sai da yayi baya taga-taga kamar zai faɗi ............ Bata tsaya jiran komai ba ta falla da gudu tana dafe da ƙirjinta da ya bayyana sakamakon Yaga mata riga da yayi..... a tunaninta gudunta zai iya tseratar da ita, sai da ta ji ƙafafunta sun harɗe ta faɗi ƙasa tim!! sannan ta gane bahagon tunani take yi. ihu ta ƙara kurmawa tare da yunƙurawa zata miƙe, sai lokacin ta lura wani kalar ganye me yaɗo ne ya ɗaɗɗaure mata ƙafa har ya jaza mata faɗuwa. cikin zafin nama da bata zata tana dashi ba ta fara ƙoƙarin cire ganyen sai taga ya ƙara kame hannunta ya ɗaure, "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" ta furta cikin ɗaga murya, tashin hankali ba a sa masa rana, Ko sau ɗaya bata taɓa tunanin irin wannan zai faru da ita a rayuwa ba, bata taɓa zaton laifin da tayi zai sa ta girbi irin wannan ɗanyen hukuncin ba......... Muguwar cafkar da ya ƙara yi mata ce ta dawo da ita hayyacinta, ta saki wani matsanancin kuka tana cewa "Ban yi maka komai ba don Allah kar kai min haka, wallahi ban faɗa ba ka yi haƙuri!!, ba zan ƙara shiga rayuwarku ba, ka duba girman Allah ka ƙyale ni kar ka lalata min rayuwa!" Idanu ya zuba mata ƙur!!! yana jin wani irin bahagon yanayi yana ziyartarsa. Idanunsa da suka koma Blue color tuni sun cika taf da ruwan hawaye, wani sashin na zuciyarsa na tunzura shi wani sashin kuma yana shirin fara tausayinta. Wata gagarumar guguwa ce ta ƙara tunkaro wajen da ƙarfi ta sure shi ta watsar a ƙasa,,, "Abeeee!!!" ta ƙwala masa kira cikin tashin hankali da ruɗani. guguwar tana wucewa ta faɗa kan wata bishiya daga haka ta dena ganin ƙyallinta sai dai jinsa tayi yayi sufa akanta Tamkar wani yunwataccen Zaki......... Ihu da neman ɗauki gami da jero Addu'o'i shine abunda take iyawa dan kuwa gabaki ɗaya ji tayi kamar an ɗaure mata hannaye da ƙafafunta a cikin ƙasa....... Tana jinsa yana nashi gurnanin gami da wasu Surutai wanda bata taɓa jin irin Yaren ba a duk tsayin Rayuwarta. Lokacin da ya gama wulaƙancinsa ya sauka daga kanta ta riga ta zama marabarta da Gawa kawai ita akwai rai a jikinta, sai sa'a ɗaya idanunta da suke a buɗe suna gani dishi-dishi da kuma tunaninta da bai gushe ba..... tana iya ganin lokacin da ya miƙe yana bubbugar kansa da ƙarfin gaske yana kuka , kai tsaye Wajen Tafkin Ruwan da ya ƙawata wannan Yankin na Dajin ya nufa yana tafe yana haɗa hanya, daga haka bata ƙara sanin inda kanta yake ba.................... a ɓangaren Kubrah kuwa tana kwance kan Kushin tana kallon sama sai gani tayi wani turnuƙun harshen wuta ya tawo kanta yana tuƙuƙi gami da hayaƙi..... kafin ta kauce daga wajen tuni ya faɗo yif!!" a saitin ƙirjinta kuma ya shige ciki. A take tayi kukan kura ta tashi tana zunduma ihu, a take jijiyoyin jikinta suka fara tashi rututu suna bayyana kansu daga cikin farar fatarta sun koma baƙaƙe wulik, idanunta kuwa farin yana nan a farinsa baƙin kuma ya koma Ja da yarfi-yarfi Baƙi. Miƙewa tayi ta runtuma da gudu tayi hanyar waje. Babu kowa a Falon sai Mammi, bin bayanta tayi da gudu tana ƙoƙarin riƙota amma ta kasa tuni ta fice ta sa kai cikin Dajin tana falla gudu, ba takalmi ba Ɗankwali....................... *Last free page* *ƙarshen fejin kyauta* *🪻SAWUN KEKE🪻* season *2* (*Daga yanzu sai wanda ya biya kudin Karatu ne zai karanta. Naira 400 ne kacal)* Ga wanda suke son Karantawa ga lambar wayata nan 09079885632 SHARE FISABILILLAH