🐘🐘🐘 *SAWUN GIWA*🐘🐘🐘 Book 2 Duk wanda yakaranta min book batareda yabiyani hakkinaba banyafeba🙏 Page 35 & 36 "Cikin mugun gudu Akabar gidan....Aisha ce tafito daga cikin parlor gidan manne da waya akunnenta tana magana da sahibin nata wato yah muhseen setaga motar maisoon ajiye cikin mamaki tace "affuwan my only bro ga sweetheat na tazo barana ganta tafaɗa tareda yanke wayar.... murmushi yah muhseen yayi kana yace "Allah yaƙara sakamin sonki my Isha daga Hakan yatashi zuwa sha'anin gabanshi. Nufar motar Aisha tayi tana faɗar "sweetheat bazaki shigobane ashe harkin ƙaraso, ganin motar wangalam yasa tace au to ina taje kotashiga ne bansaniba tayi maganar tana dannawa maisoon ɗin kira, sedai me atsakanin kafafuwanta Raji ƙarar wayar maisoon ɗin, azabure tayi baya tana kallon ƙasanta aiko jakar maisoon ɗin ce da wayarta anan yashe ƙasa, ɗaukar kayan tayi tana waro ido waje cikin mugun mamaki tanufi cikin gidan tana kiran sunanta maisoon maisoon maisoon, da umma taci karo tafito daga bedroom ɗinta tace "ke lafiyarki kuwa? A,ina kikaga maisoon dakike mata wannan kiran? Bata shigoba? Aisha tajefawa umma tambayar batareda ta amsa tambayar ummar ba. Cikin mamaki umma tace "kamar ya bata shigoba bayanzu kike zaune a parlor ba kikemin wannan tambayar? Ido Aisha taƙara warowa tana maimaita innalillahi wa'innailaihiraji'un wlh maisoon tashigo gidannan umma ga motarta can awaje kuma kinga wayarta da jakarta ayashe nasamesu waje. "Da mugun mamaki umma tace "to ina taje kuma ta yada kayan? "Nima bansaniba umma Aisha tafaɗa cikin muryar kuka kana takwasa aguje zuwa wurin maigadi Tana zuwa tace "baba iro ina gaka maisoon taje bayan tashigo gidannan? Maisoon kuma aiciki tashiga da motarta. Nasani baba iro to bayan tashigo waye yashigo? Bakowa gaskiya domin bayan na buɗe mata sena shiga banɗaki to bayan ma nafitone narufe get ɗin. "Innalillahi wa'innailaihiraji'un 😲 wlh wani abun yafaru da ƴar uwata nashiga ukku ni Aisha, taƙarasa zancen cikin kuka tareda rugawa aguje takoma cikin gidan, tofa tashin hankali kenan wanda ba'a saka mishi rana, domin kuwa tashin hankali kam umma da aisha sunshigeshi, cikin giɗima umma tashiga kiran Abba yayinda Aisha tashiga kiran yah fawan, Shidai Abba umma nagama kaya mishi yashiga kiran ƴan uwanshi dudda cewar yanajin haushinta amma yakaɗu da ɓatanta.....shi ko yah fawan cikin mugun razana yamiƙe yana faɗar whatt? A ina Hakan tafaru kuma yoshe? "Cikin kuka Aisha tace anan gidan mana kuma yanzune wlh domin ga motarta nan da jakarta hardama wayarta. "Hum ina zuwa yanzu yafaɗa tareda yanke wayar yanufo gidan. Cikin ƙanƙanin lokaci ɓatan maisoon yazaga ilahirin family ɗinsu faɗin tashin hankalin da wannan ahalin suke ciki ɓata lokacine, musamman mom tayi kuka harta gode Allah hakama dady da yah jawwal, agidan Abba ma dukkansu hankalinsu atashe yake domin fadeel ne dakanshi yacewa ummansu yanaga yah fawan ne yasace maisoon dubada abinda ke tsakaninsu gaya kuma acikin gidan aka sace ta, umma ma tana wannan tunanin sedai tace yayi shiru da bakinshi gudun kar abbansu yaji wata matsalar takunno kai.....yah fawan dakanshi yatasa maigadi gidan agaba akan seya faɗa mishi yadda akayi har aka sace maisoon cikin gidan....shikuwa yace besan ya abin yafaruba Hakan yasa ya ɗauke shi izuwa office ɗinsu domin yatuhumeshi.... gabaki ɗaya wannan ahalin sun birkice akan wannan tashin hankalin kuma duk wannan abin dake faruwa yaseer bayada labari domin baya samun wayar maisoon tunda Aisha takashe wayar. Kuma yazo gida mom tacemai tana gidan Zainab yayar Aisha Hakan yasa duk abinda akeyi besaniba. Saudia Matsalar Sheck Sudais tagirma domin yanzu abin harya kaishi ga fara jinya kullun cikin tunanin maisoon yake yarinyarda besan asalintaba balle inda ze same ta, gaya duk abinda akeyi sarki bilal besaniba domin memartaba sarki Hassan yahana agaya mishi, tofa abin yabirkice sosai, domin yau koda yarima basam yashiga bedroom ɗinshi yana duƙe yana aman jini, jin shigowar yarima basam yasa yayi sauri saka hankey ɗinshi yagoge jinin kana yashige bathroom ɗinshi, sedai beɗauke hankey ɗin ba. Shikuwa yarima basam gyara mishi ɗakin yashigayi haryazo gunda hankey ɗin yake cikin mugun tashin hankali yake kallon jinin dake kai kafin yaduba aƙasama gashinan, bece komaiba kuma be ɗauke hankey ɗin ba gudun kar yah Sheikh ɗin yagano yaganeshi, sauri yayi yagama kana yafice daga ɗakin domin yabashi damar shiryawa atsanake, yana fita turakar mahaifinshi yanufa sedai kuma kafin yakaiga shiga yajiyo sautin maganar antyn su gimbiya saudat, Hakan yasa yafasa shiga kawai yakoma pert ɗinsu kana ya shiga kiran memartaba sarki Muhammad bilal domin yasanar mishi halinda ɗansa keciki....cikin girmamawa yagaida sarki Muhammad bilal kana ya shiga yimai bayanin abinda kefaruwa tun dawowar Sheikh Sudais saudia. Haryanzu...Tunda yarima basam yafara magana memartaba ke maimaita "innalillahi wa'innailaihiraji'un kafin yasauke ajiyar zuciya yace "ka kula dashi sosai basam kakira doctor yadubashi zanshigo saudia gobe in sha Allah...to abbey in sha Allah zanyi yadda kace Allah yakawoka lafiya. Nigeria Abufa yarikice sosai, gaya bikinsu maisoon seƙara matsowa yakeyi yanzu saura kwana biyar ayi bikin yayinda har yau babu labarin inda amarya ɗaya take, itako ɗayar duk tabirkice kamar wata zararriya....yau dasafe abban fawan yazo gidan abbey yasameshi zaune shida jafar da muhseen. Cikin girmamawa suka gaidashi kana suka tashi domin subawa iyayen nasu wuri. Bayan sunɗagane Abba yadubi abbey kana yace "yaya Ishaq inagafa yadace agayawa iyayen wannan yaron dakeson maisoon zancen ɓatanta domin kuwa kaga lokaci na ƙurewa karyazama se ranar ɗaurin aure Susan babu amarya kaga za'asamu matsala gara tun wuri susani idan ma fasawa zasuyi to mundai gaya musu domin afita hakki. Yaƙarasa zancen yana kallon yayan nashi domin yaji ya ze ɓullowa lamarin....ajiyar zuciya Alhaji Ishaq yasauke bayan yagamajin bayanin ɗan uwan nashi kana yace "karka damu Umar in sha Allah komai zezezo dede maisoon zata dawo cikin amincin Allah domin kullum muna addu'a Bama Fatar ɓatan maisoon yafita waje sabida wani dalili wanda fitar ɓatanta kamar kwarewa ahalinmu bayane, koshi Usman nagaya mishi cewar kar wanda yafaɗawa mijin nata zancen ɓatanta kawai muyita addu'a domin kuwa itace maganin komai. Tunda abbey yafaɗa magana Alhaji Umar yaƙanƙance ido yana kallonshi cikin rashin sanin ciwon kai yace "au kenan dai kunsan inda take yaya Ishaq tunda har bakwaso wani yasani awaje domin idan ba hakaba tayaya za'ace dan yarinya ta ɓata wai yazama kwarewar baya wa ahalinmu? Sedai idan tun farko akwai abinda anka ƙulla domin tun lokacinda ka hanawa fawan aurenta nasan cewar akwai abinda kuke ƙulli kaida Usman tunda bakwason ƴaƴana Hakan kuka watsawa yaronnan ƙasa a ido tunda bakune kuka haifeshiba yanzu kuma ga dama tasamu da ze iya mallakar maisoon domin idan iyayen wannan yaron sukasan cewar yarinyar da dansu ze aura ɓata tayi nasan bazasu bari ya aure taba kaga se amaidawa fawan abarshi dama can dashi tadace, amma dayake wani ƙullin kukayi shine kuke zancen wai a ɓoye zancen, to zanga wanda ya isa yahana auren maisoon da fawan idan Allah ya hukuntoda Hakan. Yafaɗa cikin ɗaga murya kamar meyi da sa'arshi. Da mugun mamaki Alhaji Ishaq ke kallon ƙanen nashi wanda yake ganin kamar ƙwaƙwalwarshi tadena aikine kamin yace "Kanada hankali kuwa Umar ? Kasan mi kake faɗa kuwa? Humm lallai yau na yadda basirarka tatoshe sabida sonkai, tobara nafaɗama abinda bakasaniba kasani ayanzu, bawai dan wani dalili ne yasa nace aɓoye ɓatan maisoon ba sedan cewar agidanka ne aka saceta wanda duka yayanmu suna zargin cewar fawan ne yasaceta sabida ƙudurinshi akanta wanda na tabbata idan wannan maganar tafita tozalcine agaremu Ace ɗan mu yasace ƙanwarshi, shine abinda yasa aka ɓoye zancen, kuma duk abinda suke faɗa beyi tasiri agareniba domin kuwa bana aiki da zargi senaga zahirin abu tukkunna amma yanzu wannan zantukan dakayi anan sunsa na yadda da wannan zargin tobara kaji ingayama wlh wlh wlh Allah kaji rantsuwar Musulmi idan fawan naɗa hannu wurin sace yarinyar nan kagayamai yayi gaggawar fito da ita saɓanin Hakan kuwa duk hukuncin dana ɗauka akanshi Kaine kasiya mishi. Abbey nagama faɗar hakan yabar wurin cikin mugun ɓacin rai....wani irin gumine keyankowa Abba Tako ina seyanzu yake dana sanin yiwa Alhaji Ishaq wannan maganar gaya yaɗaure ɗanshi babu gaira balle dalili, to ina maisoon tashiga? Waye yasaceta? Yafaɗa afili yana ƙoƙarin barin parlor.....! To muma dai munce ina maisoon tashiga ko awanne hali take ayanzu?🙄 Autar alheri ✍️ 🐘🐘🐘 *SAWUN GIWA*🐘🐘🐘 Book 2 Duk wanda yakaranta min book batareda yabiyani hakkinaba banyafeba🙏 Page 37 & 38 "Tunda Abba yafita muhseen yadake zaune a bedroom ɗin shi yadafe kanshi yana maimaita duk addu'ar datazo bakinshi domin yasan wannan abin baƙaramin tashin hankali zekawoba acikin zuri'arsu kuma shi harga Allah baya zargin fawan duba da yadda shima hankalinshi yake atashe gaya duk wani mataki daya dace aɗauka yaɗauka kuma shine yataso tareda fawan yafi kowa sanin waye shi, dayanzu fyaɗe akace yayiwa maisoon to ze yadda sabida yadda ya ƙwallafa rai akanta amma baya tunanin ze iya saceta, da wannan tunanin dai yabar gidan domin samo mafita kafin abin yakoma tsakanin iyayensu. Dubai Hankalin sarki Muhammad bilal baƙaramin tashi yayiba akan matsalar tilon ɗanshi hakan yasa washe garin ranarda sukayi wayada yarima basam yashirya zuwa saudia,,,,,lokacinda jirginahi yasauka adede lokacinne ake tada sallar azahar a masallacin harami Hakan yasa daga ireport yanufi masallaci, domin gabatar da sallah bayan an idarne manyan malaman harami suka shiga martabashi tareda kawo gaisuwa agun adilin sarkin, kafin yasamu haɗuwa da sarki Hassan wanda yayi mugun mamakin ganinshi a wannan lokacin bayan aikin hajji, Hakan suka rankaya zuwa masarautar cikeda farin cikin ganin junansu, gefe ɗaya kuma na zuciyar memartaba sarki Muhammad bilal na cikeda mamakin rashin ganin Sheck Sudais a masallacin harami kuma lokacin sallah, wannan abin yaƙara tabbatar mishi dacewa lallai akwai babbar matsalar dake damunshi....bayan sun isa masarautar ne suka wuce turakar memartaba sarki Hassan anan kuyangi da hadiman gidan suka shiga kawo gaisuwa gun aminin sarki tareda hidimta masa, kana iyalan sarkin ma sukazo domin sugaisa da sarki bilal, gimbiya zaitun ce tafara zuwa tareda rakiyar samarin ƴaƴanta, bayan sungaisa kamar da minti 10 Sega gimbiya saudat tareda fitsararriyar ƴarta kursum, Hakan suka zube gaban memartaba sarki Muhammad bilal suna zuba iyayi da fadanci kamar wasu maroƙa duk dan neman samun wuri...shidai da murmushi kawai yake binsu yana amsa musu kafin daga baya suka fice,,,,betambayi Sheck Sudais ba Shima sarki Hassan beyimai zancenshiba sebayan sallar la'asar kana sarki Hassan yadubi aminin nashi yace "ranka yadaɗe wai kokamanta da yarona ne naga baka nemeshiba kokun haɗu? Ɗan murmushi manya sarki Muhammad bilal yayi kana yace "a'a ranka yadaɗe banganshiba nabarine idan nayi sallar la'asar senaje gunshi tunda nasan bayada lafiya....jinjina kai sarki Hassan yayi cikin gamsuwa yace "tobara na rakaka ɓangaren nashi ko? "Yawwa to muje, Shima yafaɗa cikin murmushi,,,Hakan suka nufi pert ɗin Sheck Sudais inda suka samu yarima basam da yarima Junaid zaune a parlor shi....cikin girmamawa ga iyayen nasu suka miƙe suna gaidasu, bayan sun amsa musu ne sarki Hassan yace "Sheck Sudais fa? "Yanaciki pappu wanka yakeyi, Junaid yafaɗa cikin girmamawa. "Basuce mishi komaiba suka nufi bedroom ɗinshi inda sarki Muhammad bilal yazauna shikuwa sarki Hassan yace zeje anjima zeƙara shigowa kafin Sheikh Sudais ɗin yafito, yayi hakanne dan yabasu dama sugana maybe koze iya gayawa mahaifinshi damuwarshi...jinjina kai kawai sarki Muhammad bilal yayi yana murmushi, Hakan memartaba yafita yabarshi yana jiran fitowarshi. Kusan minti 15 dazaman memartaba sarki Muhammad bilal kana Sheikh Sudais yafito ɗaure da towel aƙugunshi ɗayan kuma a hannunshi ya rufo jikinshi, turus yayi ganin mutum zaune a gefen gadonshi domin daga farko ya ɗauka yarima basam ne seda yaware cat eyes ɗinshi akan kyakkyawar fuskar mahaifinshi mecikar haiba da kamala, ɗan warosu yayi waje cikin mamaki yace "Abbey yafaɗa cikin happy kana yayi kan mahaifin nashi tareda rungumoshi yana sauke ajiyar zuciya.... murmushi kawai sarki Muhammad bilal keyi kafin yashafa fuskarshi cikin tsananin son yaron nashi yace "Sheikh ɗin Abbey, yafaɗa cikin sakin fuska.....ajiyar zuciya Sheikh Sudais yaƙara saukewa akaro na biyu kana yakwantarda kanshi jikin memartaba, kafin yabuɗe baki cikin sassanyar muryar shi me ɗauke da amo meratsa zuciyar me sauraronshi yace "Abbey na nayi kewarku dayawa ina mamey na? Tana lafiya? Yayi maganar asakarce, wanda kenunida yana tsananin kewar iyayen nashi kuma yana zuba shagwaɓa muddin yana agabansu. Kanshi memartaba keshafawa kana yace "haba Sheck ɗin Abbey idan kayi kewarmu dagaske miyasa bakazo inda mukeba? Mudai mukayi kewarka kuma ai gaya nazo, Sedai kuma banji daɗin yadda naga Sheikh Sudais ɗina ba duk karame kayi wani iri dakai Sheikh ɗin Abbey kofa masallaci yau banganba wannan wacce irin damuwace kehana yarona kusanci da mahaliccinshi? Memartaba yayi maganar cikin alhini.....cat eyes ɗinshi yawaro kafin yarufe bakin Abbey cikin sauri yana girgiza kanshi yace "babu wata damuwa dazata shiga zuciyar Sheikh Sudais Muhammad bilal tahanashi kusanci da Ubangijinshi wlh Abbey na naje masallaci Sedai abakin kofa nake sahon ƙarshe sabida banaso aganni ahanani dawowa da wuri koɗazu ma naje Sedai duka shigar da nakeyi bansan Abbey na yanacikiba dabazan fitaba harse naga abinsona, yaƙarasa zancen cikin gajiyawa yana ƙara mayarda kanshi jikin Abbeyn nashi yana sauke nunfashi ɗakyar irin yagaji da maganar dayakeyi ɗinnan. Ajiyar zuciya memartaba yasauke yana jinjina kanshi cikin yadda da kalaman yaron nashi domin yasan Sheikh Sudais kaifi ɗaya ne yace "Sudais, yakira asalin sunanshi yana ɗagoda kanshi daga jikinshi...Shima zama yayi dede yana tattaro sauran jarumtarshi da ƙarfin hali yake kallon mahaifin nashi kafin ya amsa cikin sanyi murya, "na'am Abbey. Kallonshi memartaba sarki Muhammad bilal keyi sosai yana karantar yanayinshi kafin ya numfasa yace "miyake damunka? Inaso kagayamin matsalar ka ayanzu domin kasan kwanakin baya natambeka tun abin bekai hakanba kacemin Kanada damuwa amma nayima addu'a idan kadawo zaka gayamin, tun alokacin nake addu'ar Allah yakawoma sauƙin koma minene. Sedai abinda yarima basam yagayamin akanka da wanda nagani ayanzu ya tabbatar min dacewar akwai babbar matsala Sudais miyasa zakabar damuwa aranka hartana neman haddasa maka ciwo? Miyasa sokakeyi nima kakwantar dani jinyar? Domin kasan tabbas ka kwanta jinya nima kwanciyar zanyi miyasa Sudais? Miyasa Hakan? Kagayamin minene damuwarka aduniya? Yafaɗawa cikin ɗan faɗa faɗa domin sam beji daɗin yadda yarima basam yace Sheikh Sudais na aman jiniba, kenan so yakeyi yakashe kanshi da damuwa. Shiru Sheikh Sudais yayi har mahaifin nashi yagama maganarshi kana yaɗago ahankali yace "Abbey kayi haƙuri please naɗauka zan iya maganin abin shiyasa ban gayamaba kuma banaso kushiga damuwa kamar yadda nima nashiga, yafaɗa cikin rauni....kamoshi memartaba yayi yamaidashi jikinshi yana shafa kanshi zuwa bayanshi cikin rarrashi yake faɗar "karka damu Sheikh ɗin Abbey duk tsanani yana tareda sauƙi kuma babu abinda zesakamu damuwa muddin munada maganin matsalar ka kai koma bamudashi zamu tayaka da addu'a har Allah yakawoma mafita gayamin damuwarka yarona in sha Allah komai zezo dasauƙi...ƙara ƙanƙame mahaifin nashi yayi kana yabuɗe baki cikin rawar murya yace "narasata Abbey bansan minayi mataba take bibiyar rayuwata kuma yanzu nanemeta domin nasan matsalar dake tsakaninmu amma tayi tafiyarta Abbey daga farko naɗauka mafarkinta danakeyi matsalace ataredani ashe bansaniba shine sauƙi agareni gabaki ɗaya narasa yazanyi Abbey, yaƙarasa zancen cikin muryar kuka...tunda yafara magana Abbey ke sauraronshi harya gama kana yanisa yace "wacece Sheikh ɗin Abbey? Kuma mikamata? Miye haɗinka da ita? Kuma I ina kasanta? Duk atare yajero mishi tambayoyin domin yagano soyayya ce keneman rayuwar ɗan nashi.....kusan minti 10 da abbey yayi masa tambayar bece komaiba kamar bazeyi magana ba, kafin kuma yafara bawa mahaifin nashi labarin maisoon tun farko da yafara ganinta a harami dakuma zuwanta gidan har haɗuwarsu asibiti harkawo mafarkinta dayake yawanyi dakuma yanayin mafarkin harkawo zuwanshi Dubai dakuma dawowar dayayi nemanta Dr hareesh yacemai takoma Nigeria.....tunda yafara bawa memartaba labarin yake jinjina abin cikin mamaki yana kuma auna kowacce kalima tashi abisa mizani haryakai ƙarshe. Wani irin murmushin manya memartaba sarki Muhammad bilal keyi kafin yanisa yace "karka damu Sheikh ɗin Abbey inaga surukace muka samu daga Nigeria kuma acikin mafarki, yayi maganar cikin zolaya wa yaron nashi... ƙasa Sheikh Sudais yayi da kanshi afili yace "suruka kuma Abbey? "Eh mana Sheikh ɗin Abbey bara kaji ingayama bawani abin dakayi mata take bibiyarka domin Bama itace ke bibiyarkaba Kaine ke bibiyarta kuma ina kyautata zaton sontane kakeyi baka saniba ayanzu zamanta kusa dakai shine kawai maganin wannan damuwar sabida Hakan zamu nemi shi wannan doctor ɗin dakace agidanshi take seya gaya mana wacece ita kuma yayi mana jagora zuwa Nigeria domin muyi bincike akanta tareda nema maka aurenta, yaƙarasa zancen yana sakin murmushi....arazane Sheck Sudais yaɗago yana kallon mahaifin nashi kafin yabuɗe baki cikin rawar murya yace "aure kuma Abbey? Ayanzu? Ni aiba sonta nakeyiba, yafaɗa fuskarshi ɗauke da damuwa....hummm yaro yarone cewar memartaba kana yace to shikenan naji kodai basonta kakeyiba za'a aurota indai tanada nasaba mekyau daganan semuzo da ita kayita kallonta tana kusa dakai daga ranarda tunaninta yadena damunka kaga ai seku rabu idan bakada buƙatar zama da ita. "Abbey. "Ɗaga mishi hannu Abbey yayi alamar karyace komai kana yamiƙe yana faɗar "kashirya sekazo muci abinci tare domin yaudai kam da ɗan lelena zanyi dinner, yafaɗa cikeda Raha...daga kai kawai Sheikh Sudais yayi batareda yace komaiba domin yarasa miyakeji ayanzu farin ciki ko akasin Hakan? Shidai yasan nauyin dazuciyarshi kemishi kawai yarage sosai, da wannan tunanin yamiƙe domin yashirya bakinshi ɗauke da tasbihi kamar yadda yasaba...shi ko memartaba yayi ficewarshi zuciyarshi ɗauke da farin cikin sanin damuwar ɗanshi. Nigeria Wani madaidaicin gidane acikin unguwar gwagwalada dake garin Abuja gidane wanda baze wuce zaman mace ɗaya ba abakin get ɗin gidan wasu tiƙa tiƙan gardawane ketsaye kamar dogarai kowacce se muzurai sukeyi kamar suci mutum daranshi,,,,,daga cikin bedroom ɗin gidan kuwa maisoon ce zaune an ɗaure mata baki da ido....ɗas ɗas ɗas Hakan takon takalmi ketashi yana tunkaro bedroom ɗin wata hamshaƙiyar matace tashigo fuskarta manne da ƙaton glass wanda yacinye Rabin fuskar da chingum abakinta tana ɗallashi kamar wata karuwa, seda taƙaraso kusan maisoon kana tasaka hannu tabuɗe mata ido tareda jannye abinda ke rufeda bakin maisoon ɗin itama tazare glass ɗin idonta tana sakin murmushi...ɗagowa maisoon tayi itama tana murmushin wanda zaka rasa gane kona minene kuma wanda yayi sanaɗin ɗaukewar murmushin dake kwance akan fuskar matar....cikin tsiwa darashin tsoro maisoon tace "Rukky dikko dillah, humm iya wayon nakikenan? Tatambaya idonta nakanta...ƙuttt😱 Rukky dikko dillah?? Mahaifiyar yaseer?. 🙆 Autar alheri ✍️ 🐘🐘🐘 *SAWUN GIWA*🐘🐘🐘 Book 2 Duk wanda yakaranta min book batareda yabiyani hakkinaba banyafeba 🙏 Page 39 & 40 "Wani banzan kallo Hajiya Rukayya dikko tawatsawa maisoon ɗin kana tace "ba iya wayonaba kenan Dr maisoon Usman maina aiyanzune wasan zefara, bawai tunaninki ki auri yaronaba domin kiruguzamin daulata? Humm yaro yarone haryanzu ke yarinyace maisoon amma zan nuna Miki aikin manya, domin kuwa nida kaina zangayawa yarona cewar ƙinshiga duniya kuma iyayenki sun ɓoye mishi, daganan na tusawa mahaifinshi ƙiyayya da aurenki bayan nayi Hakan kuma nacimma manufata akanki, kinga najefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, kuma duk acikin kwana ukku nakeda muradin yin Hakan ƴamanta idan kin isa kidakatar dani dagayin hakan, tafaɗa cikin gadara. Haryanzu akwai murmushi kwance a fuskar Maisoon seda tagamajin mummunan ƙudurin Rukky dikko akanta wanda ita agunta kyakkyawa ne domin tana neman hanyar rushewar auren yaseer Sedai nufinta na biyu ne yake mummunan gaske agareta amma tabbas bazata bata damar cimma ko ɗaya ba, cikin wani ɗan iskan sexy voice tace "Allah sarki babba da ƙwaƙwalwar tumakai zanga yadda wannan banzar ƙwaƙwalwar taki zatabaki shawararyin nasara akaina tabbas ni yarinyace baki faɗi ƙaryaba amma yarinyar data zame Miki sinwon ido domin kuwa ɗan Hakim daka rena shine kezama matsalar rayuwarka, ɗan shiru tayi tana taune lips ɗinta naƙasa kana taɗago da murmushi kwance akan kyakkyawar fuskarta tace "wlh wlh wlh Allah Rukky dikko dillah sena nuna Miki asalin aikin yarinta irin kuma na firgitattun yara, daga Hakan tamaida idanuwanta ta lumshe...wani mugun takaicine yaciyo Hajiya Rukayya wanda yasata ɗaga hannu zata wanke maisoon da mari kome tatuna kuma setayi saurin janye hannunta tana jan dogon tsaki tareda juyawa tafice daga gidan. Seda matsaya bakin get taƙara suburbuɗawa garadan dake tsaron gidan gargaɗi tukkunnah tashiga mota tareda ficewarta. Saudia Dr hareesh ne zaune gaban manyan sarakunan Larabawa,,,cikin girmamawa yake basu amsar tambayarsu agareshi. "Allah yatemaki memartaba wlh ƙanwar matatace uwarsu ɗaya ubansa ɗaya sunanta maisoon Usman maina suna zaune ne Nigeria agarin Abuja, aikin hajji ne yakawota ƙasarnan kuma kasan cewarta doctor babba wanda aƙasarnan tayi karatunta itada sister ɗinta Aisha Umar maina, harsuka ɗan taɓa aiki a SS hospital tukkunna suka koma Nigeria, Hakan yasa har nanemi temakonta wurin yiwa gimbiya kursum aiki amma bada wata manufarba dan Allah kugafar cemu, wlh maisoon batada wani mummunar halayya abinda nasani tanada tsiwa Hakan yasa harsuka sam.."ya'isa Hakan doctor abinda muka tambeka kawai wacece ita dakuma inda zamu sameta. Cewar memartaba sarki Hassan cikin dattako...afuwan ranka yadaɗe, doctor hareesh yafaɗa cikin girmamawa. Ajiyar zuciya suka sauke atare kana sarki Muhammad bilal yace "gobe in sha Allah zamuyi tafiya zuwa Nigeria doctor hareesh kuma abisa jagorancinka...arazane yaɗago yana dubansu cikin tsoro da kaɗuwa.... murmushi yagani kwance akan fuskar kowannesu Hakan yaɗan sanyaya ranshi, kafin yaji muryar memartaba sarki Muhammad bilal yana faɗar "kakwantar da hankalinka doctor bafawani abin tashin hankali bane kaide kaje kashirya zuwa gobe jirginmu zetashi in sha Allah...ajiyar zuciya yasauke kana yace "Allah yakaimu gobe lafiya, yafaɗa jiki a sanyaye kafin yayi musu sallama yatafi. Yana zuwa gida hankali atashe yashiga bawa Anty meenah labarin abinda yafaru yau da aka kirashi gidan sarki...itama Anty meenah hankalinta yatashi sosai amma seta dake tace "karka damu abban Jawad in sha Allah ba abinda zefaru se alheri kuma kaga ai munada zancen zuwa Nigeria bikinsu maisoon ɗinko? Tunda yau saura kwana ukku ai semuyi tafiyar dukkamu...humm shikenan Allah yasa muji alkhairi. Ameen y Allah. Daga Hakan yashige warshi wanka. Nigeria Yau saura kwana ukku bikinsu, hankalinsu dady in yayi dubu to yatashi gabaki ɗaya sunrasa mafita inbanda addu'a babu abinda sukeyi daneman ɗauki agun uban gijin talikai....afannin Hajiya Rukayya kuwa yaune tashirya sanarda mijinta abinda kefaruwa da maisoon domin tuni tagayawa yaseer inda tace mai damacan maisoon batada tarbiya rufa rufa ne akeyi domin aliƙa mishi jaraba yanzu kuwa tashiga duniya sabida bata shirya aureba, tareda nunamai wasu picture na maisoon ɗin itada Aisha wasu kuma itada wasu ƙawayensu Larabawa suna cikin hostal ɗinsu wasu duk ƙananun kayane ajikinsu, kuma wannan hotunan tun suna makaranta sukayisu wanda wata ƙawarsu ce taturawa Hajiya Rukayya su tun suna saudia sune yanzu tanunawa yaseer wanda tasaku abin yayi tasiri sosai agunshi kuwa haryaje yayiwa yah muhseen rashin mutunci akan cewar ƙanwarsu karuwace za'a aura mishi domin Aisha yaje zagewa yata radda yah muhseen acan shine dalilin yimasa rashin mutuncin....shiryawa tayi tsab tanufi pert ɗin abban yaseer domin shima tagama tsara abinda zata gayamishi Zaune tasameshi bakin bed ɗin shi cikeda kissa dason ida mummunan ƙudirinta taƙarasa wurin shi, tareda zaunawa tana faɗar "sannu da hutawa Abban yaseer. Ɗagowa yayi yana kallonta batareda yace komai ba. Ganin hakan yasa tasan ba magana zeyiba, shiyasa bata jira cewarshiba tacigabada maganarta kamar hakan. "Shin Alhaji wai kasan abinda ke faruwa kuwa da yarinyar da yaseer ze aura? Da mamaki yaɗago yana kallonta kafin yace "a'a wani abunne? "Humm tasauke ajiyar zuciya kana tace "ai dama nayi tunanin iyayenta bazasu gayamaba domin kuwa cutar ɗanka akesonyi, ahaɗashi da baragurbi shiyasa ba wanda zeyima zancen. Taƙarasa zancen cikin alhini..."wai bangane mikikeson faɗa ba Rukayya ƴar aminina cefa kikeyiwa wannan mummunan ƙalaman....itama cikin jin haushi tace "kaine kake kallon ƴar amininka ce za'a aurawa ɗanka amma su azuciyarsu ba haka bane domin cike suke da yaudara acikin lamarinsu, sabida yarinyar lalatacciya ce kuma sunsan hakan amma suka rufeka domin yanzu hakan yarinyar bata gidansu taje yawon banzanta haryanzu iyayen basusan inda takeba kuma kaga ai basu sanarda kaiba amatsayinta na wadda zata zamo surukarka nanda kwana uku idan ɓatan Allah ne aidoline sugayama domin kaima kasan halinda ake ciki, amma dayake damacan sunsan tana yawonta na tazubar shiyasa basufaɗa ba yanzu hakan zamu zuba ido wannan tashigo gidannan amatsayin suruka wadda zata zamo uwar jikokinmu, tafaɗa tana matsar ƙwallah....wani irin faɗuwa gaban abban yaseer yayi atake yaji ranshi yayi mugun ɓaci cikin wani irin ƙunar rai yace "ni Alhaji Ishaq ze muna furta aiko wlh basu isaba dani suke zancen, wato shine ze aurawa ɗansa wadda yasan tanada kirki niko yabawa ɗana watsatsiya humm aiko wlh bazata saɓuba, yafaɗa yana janyo wayarshi tareda neman contact ɗin abbey, amma harta yanke beɗagaba sabida darene, ajiye wayar yayi da zimmar gobe idan Allah yakaimu zeje gidan...ganin hakan yasa Hajiya Rukayya fita daga bedroom ɗin nashi fuskarta ɗauke da murmushin nasara.. Humm ƙalu bale garemu iyaye bawai mazaba har mata mudena ɗauka jitajita akan komai na rayuwar ƴaƴanmu duk abinda yatun karo ko aka gaya mana koda kuwa makusancinmu ne to mufara bincike tukkunna kafin yanke hukunci, Allah yasa mudace.🙏 Saudia Yau ne jirginda yadauko manyan sarakunan ƙasa metsarki yataso daga Makka zuwa Nigeria, wanda yayi dede da saura kwana biyu ɗaurin auren su maisoon....ɗauke yakeda manyan ƙasa metsarki, memartaba sarki Hassan, da memartaba sarki Muhammad bilal tareda yarima junaid serakiyar wasu daga cikin hadimansu dakuma masu tsaron lafiyarsu,,,sekuma wanda ke jagorantar tafiyar doctor Hareesh anty meenah dakuma yaransu, semuce Allah yasauke matafiya lafiya. Yah muhseen nazaune a parlor gidansu misalin ƙarfe 1 narana, kawai wani tunanin yazo mishi da sauri yamiƙe zaune tareda janyo wayarshi yashiga kiran Aisha wadda kullun safiyar Allah cikin kuka take, bata ɗaga wayar kowa seta yayan nata kuma mijinta in Allah yace,,,,tana zaune koyanzu tana sa'ar tata wato kuka kiran yah muhseen yashigo wayarta, ahankali tasaka hannu ta ɗauki wayar tareda karawa akunne tayi sallama....daga gefen muhseen kuwa ko sallamarta be amsa mataba yashiga faɗin "Aisha wannan zoben dana baku ranarda kuka ƙare scondry school yana hannunki? "Eh yana,nan..."okey na maisoon yana hannunta kota cireshi? Yasake jefa mata tambayar? Yana hannunta yaya ai tunranarda kasaka munashi bamu taɓa cireshiba sedai idan yanzu ne da akasaceta akacire..."okey good kawai yah muhseen yafaɗa yana yanke wayar tareda miƙewa da sauri yanufi bedroom ɗinshi,,computer ɗinshi yaɗauko tareda saka wasu nombers yana saching aiko ko minti 3 beyi yanayi ba sekawai lucation ɗin da zoben hannun maisoon yake ya bayyana a computer ɗin..."yess nasameta wlh yafaɗa cikin ihu kafin yamiƙe cikin hanzari yasaka kayanshi na soja kana yaɗauki wayarshi tareda kiran yaranshi dawasu daga cikin abokanan aikinshi yana sanar musu inda yakeso su haɗu, yana gama wayar yaɗauki bindigarshi ya maƙala agefen wandonshi kana yafice daga gidan cikin saurinshi irinna jaruman sojoji.....! Autar alheri ✍️ 🐘🐘🐘 *SAWUN GIWA*🐘🐘🐘 Book 3 Duk wanda yakaranta min book batareda yabiyani hakkinaba banyafeba 🙏 Page 41 & 42 "Yana fita yafaɗa motarshi tareda harbata akan kwalta yanufi unguwar gwagwalada cikin aza babben gudu...Aisha kuwa sororo tayi da wayar a hannunta jin yadda yayan nata ke magana a tsaitsaye kuma yayanke wayar batareda sunyi sallamaba, afili tace Allah yasa lafiya.....gudu sosai muhseen keyi Allah kawai yakaishi unguwar lafiya, afarkon layin yasami yaranshi da abokinshi khamis suna jiran karasowarshi...fitowa yayi Shima tareda fitoda laptop ɗinshi yashiga duba gidanjen dake wurin, Sedai aɗan akwai tafiya daga inda suke ganin lucation ɗin...Hakan yasa suka koma cikin motocinsu khamis na duba inda sukebi har sukazo bakin ƙofar gidan da maisoon take, baya sukayi kaɗan kana suka fito, gadan gadan khamis da yah muhseen suka nufi get ɗin gidan, turawa sukayi domin su shiga Sedai yaƙi buɗewa Hakan yasa sukayi nocking, kusan minti 3 kana ɗaya daga cikin gardawannan yazo yana muzurai yabuɗe gidan..ai idonshi na sauka akan zaratan sojojin yayi wani irin gurnani tareda turo get ɗin daƙarfi zerufe, Sedai duka ɗaya khamis yayiwa get ɗin harshi suka zube ƙasa, dagudu sauran yan uwanshi suka ƙaraso suna finda bindigunsu, akuma dede wannan lokacin sauran yaran yah muhseen suka shigo gidan, nanfa aka fara artabo da harbe harbe, kafin kace me sun har gitsa unguwar. Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci sukayi nasarar kama mutun biyu daga ciki sauran kam sun gudu...yah muhseen kuwa cikin gidan yanufa shida khamis, anan suka shiga duba inda ke kusantosu da zoben hannun maisoon, kaitsaye kuwa suka nufi bedroom ɗin dasuke tunanin tana ciki, dasauri yah muhseen yabuɗe ƙofar yashiga inda khamis yayi tsayuwarshi baƙin ƙofar domin besan a yaya zasu sameta ba...shikuwa yana shiga yaganta zaune a ɗaure an rufe mata baki Sedai ido kawai. Dasauri yaƙarasa gunta yabuɗe mata baki kana ya kwance dauren da aka mata..aiko tanajin bakinta asake tasaka mishi kuka. "Yah salam I'm very sorry my little sister zomuje gida kinji, yafaɗa yana riƙo hannunta wanda dakyar take iya takawa sabida yunwa gakuma tsaminda kafafunta sukayi, ahakan suka fito khamis namata sannu, mota yasakata kana yaja motar da azabar ƙarfi yanufu gidansu da ita. Suna shigowa harabar gidan sukayi Perking dukkansu suka fito. Da kallo abbey dake tsaye bakin barandar pert ɗinshi yabisu, ganin muhseen yafito kuma yana ƙoƙarin fitowa da wani Ido yawaro ganin yafotoda maisoon cikin sauri yayi wurinsu har yana tuntuɓe bakinshi narawa yake faɗar "muhseen maisoon cefa a'inakaganta Hakan? Miyasameta? Duk atare yake jeramai tambayoyin...murmushi yayi kana yace maisoon ce Abbey bara mushiga daga ciki zanyima bayani,,,Abbey dai basamu damar cewa komai ba illa kallonda yakebinsu dashi,,,ahakan suka nufi cikin gidan abbey na biye dasu abaya har suka shiga. Mama naganinsu tataso dasauri tana salati, yah muhseen bebata damar cewa komaiba yace "mama ruwan zafi kitayata tayi wanka please agasa mata kafafuwanta sabida ɗaurin dasukasha, idan tagama setaci abinci..to kawai mama tace tanabin bayansu domin tuni yawuce da ita bedroom ɗin mamar. Suna shiga ya'ajiyeta bakin gadon kana yace "my lovely sis kiyi wanka kici abinci barana samo Miki magani idan nadawo semuyi magana ko? "Kai kawai taɗaga mishi tana share ƙwallar idonta domin koba'a faɗa mataba tasan ahalinta sunshiga tashin hankalin rashinta, dubada yanayin mama da abbey ayanzu to inaga mom ɗinta da dady kuma wani hali suke ciki kenan....shikam ficewa yayi inda mama tahaɗa mata ruwa tatemaka mata suka shiga bayin. Shikuwa muhseen parlor yadawo inda yasamu Abbey zaune yayi tagumi yana tunani...zama yayi kusanshi kana yariƙo hannun mahaifin nashi cikin girmamawa yabashi labarin yadda akayi yasamo inda maisoon take harya ɗauko ta yanzu...ajiyar zuciya abbey yasauke yana sakawa muhseen albarka kana yace "to waye yasaceta muhseen? Nima bansaniba abbey mujira tahuta semuji daga bakinta..to shikenan Allah yayi muku albarka. Ameen ameen, daga Hakan muhseen yafice. Baƙin saudia Misalin ƙarfe 5 na yamma jirginsu asauka Nigeria acikin garin Abuja,,,inda shugaban ƙasar Nigeria dakanshi yazo tarbar manyan sarakuna masu daraja acikin ƙasar data kasance lamba ɗaya acikin jerin kasashe masu albarka dake cikin duniya, domin tun kafin sutaso hukumar jekadancin Nigeria dake Saudia tasanarda zuwansu....sosai sukayi farin cikin ganin tarbar da suka samu agun manyan Nigeria inda aka ɗauke su cikin mutocin alfarma izuwa bilah dake cikin unguwar asokoro,,,,sudai su Anty meenah kallo ne kawai nasu domin ba yadda basuso suwuce gidaba inyaso daga baya sudawo idan sarakunan sunhuta amma sam sarki Muhammad bilal yaƙi amincewa domin gani yakeyi kamar bazasu dawoba,,,,sosai akashiga karrama sarakunan abin birgewa shugaban ƙasar dakanshi yake gabatar musu da komai cikin mutuntawa da girmamawa. Seda suka huta akayi Isha'i tukkunna sukayiwa megirma shugaban ƙasar abinda yakawosu inda sukace kuma yanzu sukeso tafiya gidansu yarinyar domin ganawa da iyayenta...sosai megirma shugaban ƙasa yayi farin ciki dajin cewar babban malamin addini kuma ɗa ɗaya tilo agun sarkin Dubai keson auren ƴar ƙasar shi wannan abin alfaharine ga ƙasar Nigeria, Sedai ya lallaɓasu akan suyi haƙuri zuwa safe se ashirya tafiyar zefi..Hakan suka haƙura badan sunsoba. Gidan abbey Bayan maisoon tayi wanka taci abinci muhseen yakirata parlor abbey bayan duk sun zauna ne yace "ƙanwata yanzu daga office nake ƴan ta addan damuka samu suna gadin ƙofar gidan da aka ajiyeki mun tuhumesu akan waya sakasu dafarko sunƙi faɗa daga baya dasukasha wuya shine sukace wai Hajiya Rukky tasakasu, shine nakeson sanin wacece Hakan ? Kinsanta ne? Kuma mikika mata harta aikata miki hakan? Yatambaya idonshi na kanta...Tunda yafara magana kanta yake aƙasa har yakai ƙarshe kana ta buɗe baki cikin sweet voice ɗinta tace "nasanta my one bro maman yaseer ce Hajiya Rukayya dikko dillah....ido suka zaro atare daga Abbey har yah muhseen suna haɗa baki wurin faɗar maman yaseer dai....! Autar alheri ✍️ 🐘🐘🐘 *SAWUN GIWA*🐘🐘🐘 Book 3 Page 43 & 44 "Suna haɗa baki wurin faɗar maman yaseer dai? "Eh ita abbey itace tasaka aka saceni wai ɗanta yafi ƙarfin ya aureni shinefa bazata iya hanashiba tasaka asaceni, taƙarasa zancen idonta na cikowa da ƙwallah. "Innalillahi wa'innailaihiraji'un shine kawai abinda Abbey ke faɗa Shikam muhseen mutuwar zaune yayi cikin mugun mamaki yace "to sabida me seta saceki? Idan tanaso afasa auren ai itace da yaron kuma yazo yayimin rashin kunya bayan ashe uwarsace babbar sheɗaniya aiko wlh seta gane kurenta daga ita har ɗan nata.....cikin sauri abbey yace "a'a muhseen abarzancen bari kawai zan nemeka kutashi kuje kuma karku gayawa kowa wannan zancen kunjiko. Kallon juna sukayi kafin sukace "In sha Allah suka faɗa atare dudda kowannensu zuciyarshi tafasa takeyi nasan ɗaukar mataki akan Hajiya Rukayya dikko amma abbey yahana, zasu zuba ido suga wanne mataki ze ɗauka akai, da wannan tunanin kowanne su yabar wurin. Washe gari dasafe Dr hareesh yakira Dadyn maisoon yana faɗa masa sun sauka suna Nigeria amma suna fadar shugaban ƙasa zasuzo yanzu tareda baƙi...da mamaki kwance akan fuskar Dady yace "baƙi kuma hareesh suwaye? Sarkin Saudia ne Dady...arazane Dady yamiƙe zaune daga kishin giɗen dayake yana faɗar sarkin Saudia dai lafiya kuwa? Yatambaya aɗan ruɗe "wlh nima bansaniba dady sedai idan munzo maybe ku sugaya muku, cewar Dr Hareesh cikin alhini, domin har yanzu cikin fargaba yake akan zuwansu Nigeria...nisawa dady yayi kafin yace "to Allah yasa muji alkhairi amma kuwuce dasu gidan yaya Ishaq yanzu zankirashi in sha Allah seku samemu acan..."to dady badamuwa, daga hakan sukayi sallama.......abbey nazaune a parlor shi suna wayada dady inda yake shaida mishi zancen zuwan mutanen Saudia Sega megadinshi yashigo yana sanar dashi cewa yayi baƙo awaje...seda abbey yaƙarasa wayar tukkunna yace wayene? "Alhaji dikko ne abokinka. Okey ceyashigo,,,,daga hakan megadi yafice, bayan minti 3 dafitarshi Sega abba yaseer yashigo parlor fuskarshi babu yabo babu fallasa...miƙewa abbey yayi yatarbeshi kamar yadda suka saba aduk lokacinda suka haɗu batareda yanuna mishi komaiba,,,bayan sungaisane abban yaseer yashiga yiwa abbey magana kamar hakan. "Alhaji Ishaq wani zance naji akan yarinyar ku da yaseer ze aura, ashe yarinyar batama gida shine kuka rufemu baku sanar manaba? Yayi maganar fuska ahaɗe akuma dede wannan lokacin abban fawan yashigo parlor shima zuwanshi kenan yaji wannan abin da abban yaseer ke faɗa sekawai yasamu wuri yazauna bece komaiba....shi kuwa abbey murmushin takaici yayi kana yace "haba Alhaji sam bahaka abin yakeba dama ai inada niyyar nemanka koda kai baka nemeniba domin sam wannan zancen ba hakan yakeba...tun kafin abbey yakai ƙarshen zancenshi abban yaseer yakarɓe dacewa "kamarya zaka nemeni? Idan dagaske zaka nemeni aida kanemeni tun lokacinda abin yafaru bawai seda akazo gobe ɗaurin aure ba, kaga tun daganan kanunamin ɓatan nata bedamekuba tunda damacan tasaba abinta ta kunyi tunanin zata dawo a ɗaura auren kawai batareda bansaniba, segaya tayi abinda bakuyi tunaniba gaya kuma har labari yazo min wlh Allah kaban mamaki Alhaji Ishaq sam banyi tunanin zaka rufeni a aurawa yarona karuwaba koda kuwa take ƴar ƙanenka. Cikin tsawa da ɗaga murya abbey yace ya isa hakan Alhaji dikko karka sake ka aibatamin yarinya wlh kab zuri'ata babu karuwa ba'ahaifetaba kuma baza'ataɓa haifartaba har abada, kasani ƴata saceta akayi kuma narufe zancenne sabida wani dalili nawa amma kasani cikin iyawar Allah da buwayarsa tadawo garemu sedai kuma zakayi matuƙar girgiza idan kaji wanda yasace tan dudda cewar Allah yaƙi bashi nasara akan mummunar ƙudirinshi, amma hakan behana yayanta san ɗaukar mataki akaiba ninenan nahanashi, sabida mutunci da zumunci amma inaga kai bakasan ko ɗaya ba barana tabbatarma dacewar ƴata tana hannuna. Yanakaiwa nan azancenshi yabuɗe baki daƙarfi yace "maisoon. "Na'am abbey, ita kuwa ta amsa tana daga bedroom ɗin mama....wani rass rass gaban abba yayi domin tunda yaji abbey yace wanda yasace maisoon gabanshi ke faɗuwa domin atunanin shi fawan abbey zece kuma gaya ba'agantaba, amma yanzu da yaji abbey yakirata sehankalinshi yatashi...shima dai abban yaseer jikinshi yaɗanyi sanyi amma benunaba ko afuska...ahakan tashigo parlor sanyeda dogon hijab ɗinta harƙasa taduƙa tana gaidasu kafin tace gani abbey...bece mata komaiba illa kallon abban yaseer dayayi yace "kaganta da idonka? Sekuma yamiƙe tsaye tareda takowa haryazo gabanshi yadda zasu iyajin nunfashin juna kana yace "kuma matarka Hajiya Rukayya mahaifiyar ɗan naka itace tasaka Aka saceta komiye dalili? Abbey yayi maganar cikin tuhuma.. Wani irin waro ido Alhaji dikko yayi tareda zabura lokaci ɗaya kaɗan yafaɗi, irin yayi mugun kaɗuwa ɗinnan kana yabuɗe baki zeyi magana amma taƙi fitowa,,,ganin hakan yasa abbey yin guntun murmushi kana yace "mutuncinka da darajar abotarmu yasa nahanawa muhseen da ita kanta yarinyar ɗaukar wani mataki, amma yanzu zan janye hanasun danayi nabaka nanda kwana ukku inaso katambayarmin matarka dalilinta nasacemin ƴa takaiwa ƙartin banza suna gadinta kuma idan baka dawomin da amsar tambayata acikin kwana ukku ba to tabbas zansaka yayunta sutambayeta wato fawan dakuma muhseen inadaida tabbacin cewar kasan jami'an tsaro ne? Sekuma zance na ƙarshe nasoke auren maisoon da ɗanka yaseer wanda za'ayi agobe domin bazankai ƴata cikin ahallin da basusan mutunci ba.Yaƙarasa zancen yana ɗagawa Alhaji dikko gira ɗaya....acikin kaɗuwa da dabircewa Alhaji dikko yabuɗe baki daƙyar yace "dan girman Allah Alhaji Ishaq tsaya kaji wlh duk bansan wannan abin hakan yake ba kuma koda bakaceba doline zan tuhume Rukayya akan wannan al'amarin amma dan Allah kajanye kallimar soke aure wannan sam badede...kafin abbey yace wani abun cikin sauri abba da tunɗazu yayi mutuwar zaune ganin maisoon yakarɓe zancen da cewa "ai wlh baka isaba Alhaji dikko kazo hargida kacimana mutunci kana kacewai ayi haƙuri zancen aure kam babushi kaji zance ɗaya kuma katashi katattara kabar gidannan kafin yanzu nasaka yarana susa ayimin waje dake, yaƙarasa zancen yana tasa ƙeyar Alhaji dikko agaba sam yaƙi bashi damar yin magana domin sosai Alhaji dikko yaso bawa abbey haƙuri akan zancen janye auren dudda cewar shima ya hau sosai...seda yarakashi har motarshi driver shi yaja sukabar gidan kana shima yashiga tashi mota cikin farin ciki yanufi gida domin yayiwa fawan albishir ɗin fasa auren maisoon da akayi. Humm abba kenan 😥 wato dakasan abinda tafiyarka zehaifar batareda kakoma ganawa da abbey akan zancen maisoon da fawanba tabbas dabazaka tafiba. Bayan fitarsu abba yazauna yana mamakin mutanen yanzu da sam basuda kunya balle kawaici, wai shi damatarshi tasa aka sacewa yarinya beyi maganaba ko ɗaukar wani mataki, seshi zezo mishi dazancen renin hankali, to hauka yakeyi daze yadda ya aurawa ɗanta ƴarshi ? idan dai ba gawarta yakeso akawo musuba...yana cikin wannan tunanin dady ya iso gidan yasameshi shi kaɗai a parlor domin maisoon tunda suka fara taƙaddama tabar wurin...shigowar dady da minti 3 jiniya tafara karaɗe gidan inda manyan motocin megirma shugaban ƙasar Nigeria suka sawo kai harabar gidan bayan megadi yawangale musu get... abbey nacikin bawa dady labarin yadda sukayi da abban yaseer yanzu sukaji wannan jiniyar hakan yasa suka Miƙe dukkansu sukayo harabar gidan...! Autar alheri ✍️ 🐘🐘🐘 *SAWUN GIWA*🐘🐘🐘 Book 3 Page 45 & 46 "Suka fito harabar gidan...da sauri secrety ɗin suka fito suna buɗe motocin, megirma shugaban ƙasar ne yafara fitowa se menistern tsaro Alhaji Ahmed buba, sekuma manyan sarakunan wato memartaba sarki Muhammad bilal da memartaba sarki Hassan, daga ƙarshe junaid yafito tareda yaron sugaban ƙasar wato mujaheed, tareda Dr Hareesh se anty meenah da yaransu. Habawa zukuga murna gunsu abbay cikin farin ciki dasakin fuska suke tarbar manyan mutanenda duniya gabaki ɗaya ke alfahidasu yau gasu agidansu, sunrasa inda zasu ɗorasu kamar zasu maidasu ciki,,,ahakan sukayi musu jagora har general parlor, suka zauna aka sake sabuwar gaisuwa kana abbay da dady dakansu suka shiga gabatar musu da abin motsa baki wanda abbey yasaka mama da maisoon suka haɗa cikin hanzari...bayan sungama ne suka zauna suna ƙara yiwa manyan baƙin nasu sannu dazuwa dakuma gaisuwa ta girmamawa ga sara kunan dudda basajin larabci seyakasance komai da Turanci sukeyinshi tunda shine yarenda kowannensu keji. Bayan duk angama gaisawa ne Alhaji Ahmed buba yafara gabatarwa su abbey da sarakunan suda basu saniba, kana yagaya musu buƙatar dasukazo da ita bayan yabasu labarin sheck sudais kamar yadda memartaba sarki Hassan yabasu labarin suma...tunda suka fara zancen abbey yayi shiru kawai yana saurarensu har suka gama, nandai suka tattauna wanda basu bani damar jin abinda suka tattana ɗin ba, sedai kawai naga sunfito su abbey na musu Rakiya amma fuskokinsu dukansu kamar ba walwala irinna ɗazun, hakan suka shiga motocinsu suka tafi bayan suyiwa abbey alƙawarin zuwa ɗaurin auren yaransu agobe kamar yadda suka sanar dasu. Shima dady ciki yakoma suka ƙara tattaunawa da yayan nashi kafinnan yatafi shima. Maisoon kuwa koda Anty meenah tashiga bedroom ɗin mama zaune tasameta tana risgar kuka kamar ranta zefita,,,domin Allah yagani taji baƙin cikin abinda Hajiya Rukayya dikko tayimata gaya asanaɗinshi Ana gayawa iyayenta magana har cikin gidansu,,,,sosai hankalin anty meenah yatashi ganin yadda ƙanwar tata ke kuka babu ƙakkautawa, abinda keda bala'in wahala ganin hawayen maisoon yau kan gasu a arha...cikin tashin hankali tajanyota jikinta tana bubbuga bayanta domin tasan muddin tana wannan kukan inzasu kwana tana tambayarta damuwarta ba tanka mata zatayiba, kusan minti 15 suna ahakan seda taji tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya ne kana tafara tambayarta abinda ke faruwa? Aiko tashiga bata labari tundaga farkon fara zancen auren itada yah fawan harkawo ga auren yaseer ɗin dakuma abubuwan da abba yarinƙa yimata a hospital ɗinshi, duk yau seda tagayawa yayar tata har inda akazo Hajiya Rukayya dikko tasaceta....damugun mamaki anty meenah ke saurarenta hartakai ƙarshe inda tace ita idanma anty meenah tatashi komawa saudia biyarta zatayi se hankalinta ya kwanta tukkunna tadawo,,,azahiri hakan tagayawa Anty meenah amma a baɗili bahaka abin yakeba da biyu zatayi tafiyar na farko ta haɗu da wannan ustaz ɗin acewarta nabiyu kuma tasamu damar yin maganin Hajiya Rukayya dikko domin inda aka fara anan ake ƙarewa. Tofa 🤔 komiye tsakanin maisoon da Hajiya Rukayya dikko dillah??🤔 To muje zuwadai idan ana zuwa ruwa ai ɓari akeyi🤷 Itadai anty meenah haƙuri kawai take bata amma aranta tana mugun mamakin wannan al'amarin daga gefe ɗaya kuma zuciyarta fal fargabar abinda yakawo su sarki Hassan gun iyayensu akan maisoon ɗin. Abba kuwa yana isa gida yasamu fawan bayanan seda yakirashi awaya, Aisha ma batanan domin yana shigowa itakuwa tana fita zuwa gidan abbey gun maisoon....abba kuwa yakasa zama jira kawai yakeyi fawan yadawo yayi mai albishir, ai yana shigowa parlor dasauri abba ya rungumeshi yana faɗar "congratulasion my son burinka zecika na mallakar maisoon kosunƙi ko sunso kuwa...ai wani irin ihu fawan yasaka yana faɗar miyafarune abbana gayamin nidai asanina gobene aurenta miyafaru? Wata irin dariya abba yasaka kana yashiga bawa fawan labarin abinda yafaru agidan abbay na zuwan abban yaseer. Aitunkamin abba yakai ƙarshe fawan ya ɗauke shi sama yana juyi dashi cikin farin ciki da jin daɗi, tofa haka suka ɓata lokaci suna murna da farinci, kafin fawan yashiga kiran abokananshi yana faɗa musu gobene ɗaurin aurenshi sabida yasan abbey baze canja lokaciba, wannan kenan. Gidan Alhaji dikko dillah Abirkice yashigo gidan ko sallama babu tun abakin ƙofar parlor yake faɗar "Rukayya Rukayya Rukayya, hakan yake kiranta babu ƙakkautawa...atare suka fito itada Hajiya kakar yaseer agiɗime suna haɗa baki wurin faɗar lafiya? Wani mugun kallo ya watsa mata cikin tuhuma da takaicinta yace "mi ƴar mutane tamiki zaki saka asaceta? Kuma ma yoshe kika koma mesatar mutane bansaniba? Wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi cikin inna inna tace "wace ƴa kuma Alhaji? Mikake magana akai? Dasauri ya katse ta da faɗar "kinfini sanin abinda nake nufi Rukayya karki wani renawa kanki hankali, shine kikazo kikamin zancen banza da karfarku ta mata a she kece babbar munafuka kuma makira, to seki tanadi amsar bawa yayunta tundani bazaki gayaminba su zasu tuhumeki dakansu, sekuma babba albashir izuwa gareku sun suke auren ƴarsu da ɗanki seki zuba ruwa aƙasa kisha munafukar banza me fuska biyu,,yana gama faɗar hakan yawuce fuuuu kamar yakifa dan baƙin ciki,,dudda yanajin Hajiya na kiranshi amma ko waigowa beyiba, babu tunanin dayakeyi aranshi irin yazeyi da taron jama'ar daya gayyata gobe? Yazeyi da kunyar aminin nashi daya aminta dashi wato Alhaji Ishaq, wanda yahanama ayi binciken ɗanshi kawai suka bashi auren ƴarsu batareda wani fargaba,,,amma yanzu shi yakasa fahimtarsu ma balle yayi musu uzuri akan abinda matarshi ce ma silar komai, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un da wannan tunani yakwanta yana saƙawa da kwancewa......yaseer kam mutuwar tsaye yayi jin kalamanda abban shi ke faɗa, domin ze shigo kenan yaji wannan zantukan masu rusa ƙwaƙwalwa, ganin Alhaji dikko yawuce batareda yasamu taka mammiyar maganar kamawaba yasa yanufi Hajiya Rukayya yana faɗar "momsy mi abba ke faɗa hakan? Wakika sace? Auren waye aka fasa? Duk atare yake jera mata tambayoyin y Yana Fatar Allah yasa kar abinda zuciyarshi ke gaya mishi yazama gaskiya, domin Allah yasani dudda rashin mutuncin dayayiwa yah muhseen becire rai daga auren maisoon ba tunda yasonta sedai kimarta dayake gani kaso 60 yafita acikin ɗari,...amma kuma yamakaro domin ko kallonshi batayiba tawuce bedroom ɗinta cikin mugun fargaba,,,hakan yamara mata baya amma kafin ya isa tarufe ƙofar ta da key....hakan yazube a bakin ƙofar yana nocking amma tayi banza dashi..Hajiya kuwa binsu kawai takeyi da kallon mamaki domin ita tama rasa abin faɗa.. Washe garin ɗaurin aure...afarfajiyar gidan Alhaji Ishaq maina, jama'ane tako ina ancika cinjim babu masoƙa tsinke domin har tawagar gidan shugaban ƙasa sun hallara a wannan ɗaurin auren ko ina kaduba jami'an sojojine se moba, abindai se wanda yagani,,, ancika babu masoƙa tsinke su yah muhseen, yah fawan, yah jafar, yah jawal dukkan yayunsu maza sunzuba shiga taban girma gwanin sha'awa, hakama su abba iyayen ango😅 ga abbey maɗauri auren gakuma dady baban amare💃💃 acikin parlorn abbey anan akayiwa duk wani babban mutun masauki ciki kuwa hadda manyan baƙi kuma manyan sara kunan duniya masudaraja, anyi addu'a daduk abinda yadace na ɗaurin aure inda dubbannin jama'a suka shaida ɗaurin auren MUHSEEN ISHAQ MAINA DA AISHA UMAR MAINA, AKAN SADAKI DUBU ƊARI BIYU,,,,,sekuma *SHEIKH SUDAIS MUHMD BILAL DA MAISOON USMAN MAINA AKAN SADAKI DUBU ƊARI BIYU* 😱 sena ukku, wanda aka Daura kuma naƙarshe FAWAN UMAR MAINA DA HUMAIRAH AHMAD BUBA SHIMA AKAN SADAKI DUBU ƊARI BIYU 😱, tab dijam chakwakiya kenan semuce Allah yabasu zama lafiya💃💃💃 wata irin muguwar zabura abba yayi jin wannan ɗaurin auren hakama fawan acan waje se riƙeshi abokananshi keyi amma yanason kuɓucewa yaje cikin parlor....acan ciki kuwa wani irin kallo abba keyiwa abbey kafin yabuɗe baki cikin tashin hankalin da rashin M yace...! Autar alheri ✍️