SARTSE BOOK 3 Sayyid. (1) Gidan Big Daddy. 04:40pm. “Wai ina tambayarku lafiya kun bini da ido dukkanku? Ke Seemah kin ɗauko yarinya daga gidan mijinta, kai ma Turaki kazo kai dai Nana, kuma duk kun zauna jigun jigun, ke kuma Islaha yaushe kika sami ciki babu sanarwa?” Mama Amina ta faɗa, ganin dukkanmu mun zo kuma mun yi shiru, Sister Seemah ta ce. “Mama, ki ɗan jira dan Allah, yanzu zasu zo zaki ji komai ma.” “Ba dai wani abin kuke son tayar wa ba ko? Kuna gani halin da ake ciki, na jinyar Hajiya.” “Ba wani abu ba ne Mama.” Miƙewa na yi na ce da Turaki. “Habiby ni dai zan tafi dan Allah.” “Babu inda zaki na faɗa miki.” Yaban amsa, sister Seemah ta ce. “Me ya sa zaki tafi?” “Ni bana son su zo su same ni anan.” “Me kika aikata mara kyau? Da zaki ji tsoron haɗuwa da su?” Na girgiza kai, ta ce. “To ki koma ki zauna.” Ba musu na zauna, Mama Amina ta sake cewa. “Yaran nan dan Allah kar da ku ƙullo mana abinda ba zamu iya ba, kun ga dai jinya ce a gabanmu.” Daidai lokacin Hajiya Falmata ta shigo tana faɗin. “Wane irin iskanci ne haka? Ina son ganin ‘yata a ce na yi nan na yi nan.” A lokacin Islaha ta miƙe tsaye, ta ruga wajen Hajiya Falmata ta fashe da kuka, Hajiya Falmata ta riƙe tana faɗin. “Me ya faru? Me ya sa meki? Kukan me kike?” Ta girgiza kai, sannan ta ce. “Mommy komai lafiya.” “Wancan mara mutuncin ya ce ya sake ki ko? To zaman uban me kike a gidan Seemah?” Ta faɗa tana nuna Turaki, Mama Amina ta ce. “Bangane ba? Turaki kaine ka saki Islaha? Akan wane dalili?” A lokacin ne kuma idon Alisha ya kai kan cikin Islaha da ya fito ya yi ƙato, ta ce. “Sai da ka yi mata ciki shine zaka sake ta?” Sai a lokacin na ɗago kaina, shima kuma ya ɗaga ya kallesu sannan ya ce. “Ta yi wa kanta ciki dai, ni aina na yi mata, ku tambayeta, wannan cikin shine abinda ya sa na sake ta.” “Kan ub*nk* Turaki.” Hajiya Falmata ta danna masa ashar, sanna ta ce. “Uban me kake nufi? Kana nufin ba cikinka ba ne jikin Islaha, to na ubanka ka ne?” “Ke fa matsala ta dake zagi, Haba Hajiya Falmata ki nustu mana.” “Kinga Amina ƙyale ni, ai kinsan da komai tun da ‘yar a gidanki na sameta, kuma kinsan da ƙullin da suke shirin ƙullamata, amma baku ce komai ba sai yanzu, na zage shi to.” “Mu babu wani abu da muka ƙulla mata, sai ma rufin asiri, Turaki ya kama Islaha da ciki, amma ya rufa mata asiri sabida gudun karta tozarta, amma kun zo nan kuna zaginsa.” Sister Seemah ta faɗa, Hajiya Falmata da Alisha har haɗa baki suke wajen faɗin. “To cikin waye? Me kuke nufi?” Alisha ta ƙara cewa. “Seemah bana ciki da baƙin hali, har da ke za a zauna a ƙulla wannan sharrin? Bansan baƙin cikin da kike yi damu ya kai haka ba.” Sister Seemah ta miƙe a fusace ta ce. “Baƙin ciki! Akan me? Me kuke fini? Cima mai kyau? Suttura mai kyau? Aikin yi? Ilimi? Ko aure? Idan baku fini ɗaya anan ba, to babu abinda zai sa na yi muku baƙin ciki, ita ‘yar taku ku tambayeta mana, me ya sa da duk baku ce da ita komai ba, ku tambayeta cikin waye a jikinta? Mugun ƙazafin da kuka je kuna yaɗawa akan Turaki da matarsa Nana, shine ya juye muku, ya koma kan taku ɗiyar da shi uban da yasa ku yaɗa sharrin.” “Seemah, Turaki ku nutsu, ku yi min bayanin komai cikim hausar da zangane.” Mama Amina ta faɗa, Seemah ta ce. “Mama ya dai yi miki, ko ita Islaha ko Nana, amma nima babu wani abu da nasani wanda har zan iya ba da bayani yanda za a gane, nasan dai Turaki Islaha.” “Islaha.” Mama Amina ta kira ta, ta amsa, Mama Amina ta ce. “Me ya faru ya sake ki?” “Me kuwa ya faru, kuna so ku ɗaura mata wani sharri na daban dai, ke Islaha baki da hankali ne?” Hajiya Falmata ta faɗa, Islaha fa fashe da kuka, a taki na ji wani iri tausayinta ya mamaye rayuwata, bana son naga mace na kuka, sai kawai na tuno kaina a cikin halin da na shiga shekarun baya, cikin muryar kuka ta ce. “Cikine da ni.” “Ciki ai duk mun gani.” Alisha ta faɗa, Mama Amina ta ce. “To ai ciki abun farin ciki ne, ban taɓa ganin inda aka yi saki akan sami a ciki ba, tun bayan wajen Habibun Fargar Jaji sai kuma kai Turaki.” “A’a Mama, ciki kowanne abun so ne a wajen mahaifinsa, amma ni dai bazan amshi ɗan da ba nawa ba, tun da ita kanta tasan babu wani abu da ya taɓa haɗani da ita na mu’amalar aure, kwatsam sai ganinta na yi da ciki.” “Hasbunallahu wani’imal wakil.” Mama Amina ta faɗa, Hajiya Falmata ta ce. “A gidan ubanwa? Turaki wallahi baka isa ka hulaƙanta min ɗiya ba, kana nufin cikin a ruwa ta sha? Ko a wani wajen ta samu?” “Gatanan ku tambayeta.” Turaki ya faɗa, Mama Amina ta ce. “Dan Allah duk ku nustu abun nan ba na haka ba ne, kusan a yanzu hankalin mazajen mu baya jikinsu, yana wajen mahaifiyarsu, dan Allah ku nustu mu samar da mafita a tsakaninmu.” “Ai wallahi babu wata mafita, Turaki ka hulaƙanta ni, ka hulaƙanta ɗiyata, ka ci mutuncin ‘yan uwanta dake tsakanin iyayenku maza, a yanzu nasan suna hanyar dawowa ƙasa to wallahi suzo sai dai amincin dak tsakaninsu ya tarwatse, amma wallahi Turaki sai na yi shari’ah da kai.” “A’a Hajiya Falmata, dan Allah ki sauke zuciya ƙasa, fushi da zafi babu inda zasu kai ki, har yanzu ita yarinyar ba aji ta bakin ta ba.” Ni dai na zama ‘yar kallo, daga na kalli wannan sai na kalli wannna, duk inda baki ke motsi idona na kai, Alisha ta ce. “To me zata ce? Bayan an ƙaƙabata mata sharri, an shirya mata tarko, ana so ayi mata mummunan Sartse a rayuwa.” “Idan har kuka bar nan baku tsaya an fahimci magana ba, wallahi babu abinda zai ƙara shigar dani wannan maganar, haka Turaki haka matarsa.” Sister Seemah ta faɗa, a fusace Islaha ta ce. “Sabida gaki uwarmu? To ba zamu tsaya ba, sai dai kuma mu haɗu a gaban alƙali.” “Kuje to, zaku sha kunya ne da cikin shige, tun da ita kanta ‘yar taku bata musu ba, ta faɗi wanda ya yi mata cikin, ko kuma wanda ta bawa kanta suke aikata abunda suka ga dama, har ta kaisu ga samin ciki.” Sister Seemah ta sake faɗa, a daidai lokacin Big Daddy ya shigo, bai ma san da mutane a cikin falon ba ya shigo yana cewa. “Hajiya, ‘yan biyu fa sun sauka, yau dai gasu anan ba tare da sun ɗibe wata uku uku da suka saba ɗiba ba….” Maganarshi ta katse ganin falon ciki da mutane, kallon ɗai ɗai ya yi mana, sannan ya ce. “Lafiyanku?” Mama Amina ta ce. “Sannu da zuwa, lafiya Alhamdulillah.” “Me ya tara ku haka, gashi kowa rai a ɓace?” “Sharri suke son ƙullawa ɗiyata, kuma wallahi babu wanda ya isa, ni dai wannan aure na Islaha da Turaki ba shi da wata rana.” Sai da ya sake ƙare mana kallo, ya sauke idonshi a kaina na ji jikina ya fara ɓari, bansan me ya sa mutumin nan baya sona ba, gani yake duk wata fitina ni ce nake taso musu da ita. “Me ya faru?” Ya tambaya, Mama Amina ta ce. “Ni dai ina zaune naga Turaki da Nana sun zo, nazata ma ziyara ce suka kawo min, can sai ga Seemah da Islaha, na fara tambayarsu me ya faru sai ga Hajiya Falmata da Islaha, shine fa cacar baki ya fara, sunƙi tsayawa ma a fahimci kan komai, abinda kawai na fahimat shine Turaki ya saki Islaha, sabida ya ganta da ciki wanda ya ce bana shi ba ne.” “Ta ya ya gane bana shi ba ne?” Big Daddy ya katse ta. “To shi dai ya ce, babu wani abu na mu’amalal aure a tsakaninsu, kuma a kafin yanzu ma wancan zama da suka yi tabbas ya faɗi haka, kuma Islaha bata musa ba, a duba da girman cikin da ke jikin Islaha ya kai wata takwas, to kuma ko wancan zaman na so banajin anyi wata huɗu, tabbas maganar abar a tsaya a duba ce.” Waje ya samu ya zauna, sannan ya ce. “Falmata, Islaha, Alisha dukkan ku ku zauna.” Zama suka yi, suna ta haɗe rai ya ce. “Turaki wannan maganar ta shafi wannan matar taka? Idan ta shafe ta ta zauna, idan ba ta shafe ta ba ta tashi ta tafi.” Ji na yi gaba ɗaya na muzanta, ba fara ƙoƙarin miƙewa na bar wajen, Sistr Seemah ta ce. “Daddy ta shafe ta, tun da abokiyar zamanta ce, kuma sun tattauna da ita akan cikin.” Ya kau da kai daga kallona, ya kalli Turaki ya ce. “Me ya faru daga farko?” “Big Daddy, kamar yanda na faɗa tun a wancan zaman namu, Islaha tun aurenmu ba ta taɓa bari ko magana na yi da ita ba, da ta ganni zata ɓoye, ba ta fara magana da ni ba sai da na auri Nana, shima ba magana ce ba kwai neman faɗa ne, haka nake raba musu kwana da Nana, amma duk ranar kwanan Islaha a falo nake kwanciya, sabida bana samun ɗakinta a buɗe, abinci kafin na aure Nana ni ke yi da kaina, bayan na auri Nana ya zama ko da yaushe ita ce ke yi, babu ranar kwananta da ba na ta ba, ana haka na daina ganin ko jin motsin Islaha a cikin gidan, tun ban fargaba Nana ta farga, ta yi min magana sai na ce ta bari kwananta ya zagayo zan duba ta, kwana biyu Nana ta daina yi min zancen Islaha, idan naje ɗakin Islaha kwana zan dai ji mostinta amma bazan yi ido biyu da ita ba, sai wata rana na dawo daga ofis zan ɗauki file da na manta, har na fita sai na ji ina son ganinta, sai kawai na shiga part ɗin nata, abinda na gani yaban mamaki, wai Islaha sai tsaye ga kuma ƙaton ciki a jikinta, a take na tambayeta wannan mene, kuma na waye, ta fara kuka sai da na yi mata jan ido, sannan ta ce da ni cikin Sardauna ne a tare da ita, har ma Nana ta sani ita tabata shawarar kar ta faɗamin ta bari zata gaya min da kaina, a farko ban yarda ba, tin da naga ba magana suke da Nana ba, babu abinda zai sa ta rufa mata asiri, bayan ta tabbatar min da cikin Sardauna ne na ga bazan iya ba, na yanke shwarar zan kawo ta nan, na sake ta saki ɗaya, a lokacin kuma Nana ta dawo, ta tabbatar min ta san da zancen kuma abinda yasa bata faɗan ba, tana tsoron kar na shiga ɓacin rai na saki Islaha, sai dai kuma bata san na riga na saki Islaha ba, daga nan ta bada shwarar a ajiyeta wajen Sister Seemah zuwa ta haihu a bawa Sardauna ɗan sa, ni kuma na mayar mata da aurenta, amma kuma Mamanta da Alisha sun matsa, sai zageni suke suna cewa na fito musu da ‘yar su, ƙarshe dai na ce musu suje tana gidan sister Seemah.” Big Daddy ya juya ya kalleni, ya ce. “Ke ta ina maganar ta shafe ki?” Bakina yana rawa na fara magana. “Ni.. ni.” “Alhaji duk ka kiɗima yarinyar nan, ka sanya mata tsoronka na ba gaira ba dalili.” Mama Amina ta faɗa, Sister Seemah ta ce. “Eyh wallahi Dad, gani kake kaman ita ke kunna faɗa a tsakaninsu, kuma ba haka ba ne.” Ƙwalla na ji ta fara zuba a idona na yi saurin gogewa, na yi ƙasa da kaina. “Islaha.” Ya kira sunanta, ta amsa da. “Na’am.” “Faɗamin naki ɓangaren.” Itama muryarta kamar za ta yi kuka ta ce. “Tun farko ni bana son Yaya Turaki, ban taɓa son shi ba, ban taɓa jin sonsa a raina ba, Yaya Sardauna nake so, shi nake ji a raina, kuma shi nake son aura, lokacin da na ji ya yi aure na shiga damuwa kuma na ji babu wadda na tsana kamar matarsa, ina cikin tsanarta ya zo ya same ni ya ce da ni, wai na shiga na fita nasan duk yanda zan yi na na taɓata Nana a cikin ‘yan uwa, ɓatawar da kowa zai tsaneta, har a sa shi ya sake ta ni kuma sai ya aure ni.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (2) “Husbunallahu wani’imal wakil, duk Sardauna ɗin?” Mama Amina ta faɗa, Big Daddy ya miƙe ya ce. “Duk ku jira ni, ina ga yau ƙarshen kowacce ƙarya zai ƙare, kowa sai ya hallara a wajen nan.” Yana faɗin haka ya fice. ******* Bayan awa uku. Ɗakin ya cika da duk wani ahali na Ta’ambo da ya mallaki hankalinsa, Big Daddy ne babba da Matarsa Mama Amina, sai kuma Musa wanda yake mahaifinsu Islaha da matarsa Hajiya Falmata, sai Alhassan mahaifinsu Turaki da matarsa Mommy, sai Alhussain wanda yake a matsayin mahaifin Sardauna da matarsa Nafisa. Sai kuma ‘ya’yansu duka. Seemah babba daga gidan Big Daddy, Alisha mai biye mata daga gidan Abbah Musa, sai Sardauna daga gidan Second Daddy (sunan da ake kiran Alhussain a cikin gidan gaba ɗaya) sai Turaki daga gidan Frist Dad (shima sunan da ake kiran mahiafinsa kenan) sai kuma sauran ‘yan gidan, ciki har da ni. Big Daddy ya yi gyayan murya sannan ya fara magana. “Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki da ya hallice mu cikin zuri’ah guda ɗaya, tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammadu. Ya ‘yan uwana, abinda ya sa na tara ku anan da dukkan ahalinku shine, ina so mu warware wani zare da ya daɗe yana ƙulli a tsakaninmu, wanda ni kaina na gaza gane asalin gaskiyyar zaren. Islaha ta so nan.” Ya faɗa yana nuna mata kusa da shi, ta miƙe ta taku, a take na kai idona kan Sardauna na ga yanda ya yi matuƙar kaɗuwa da ganin cikin a jikin Islaha, dan daman tin da yanzo tana zaune waje ɗaya ba ta ko motsa ba, idanunsa suka fito waje gaba ɗaya, a take ya fara fitar da zufa, na yi murmushi a raina na ce. ‘Sardauna yau ƙarya ta ƙare.’ Sai da Islaha ta ƙarasa ta zauna, sannan ya yi ƙasa da kansa, Big Daddy ya ce. “A tarihin gidan nan muna zaune lafiya, ‘yar rigimar dake tsakani ba ta taɓa shafar mu ba, ba a taɓa zuwa gabana an kawo ƙara ba sai akan wannan yarinyar.” Ya faɗa yana nuna ni, a take na ji gabana ya faɗi, bayan idon mutane ya yi kaina baki ɗaya, na yi ƙasa da kaina a take na ji jikina ya fara karkarwa, sai da na ji Lamrah ta sannu ta dafe ni, sannan na iya nutsuwa. “Ina zaune na fara jin ƙana nan magana akan cewar matar Sardauna tana yawo bin maza da aurenta, na shiga tsananin tashin hankali da kiɗima, mace mai bin maza da aurenta a cikin ahalinmu? Abun gaba ɗaya ya ɗaga min hankali, na ji duk yarinyar ta fitar min a rai. Sannan na ji kuma ana cewa wai Abubakar Turaki take bi, anan na fara shakku akan al’amarin amma ban nuna ba, ana haka Sardauna yazo da zancen ƙarin aure, na yi farin cikin jin haka sosai, sabida yarinyar duk ta fitar min a rai, na amince masa yaje ya yi sabon aure, bayan auren da watanni na samu labarin ya saki matarsa ta farko, na yi hamadala da cewar komai ya ƙare. ‘Yan wattani kaɗan Sardauna ya sameni da zancen Turaki ya ci gaba da bin tsohuwar matarsa, har da hotona na shaida duk ya kawo min. A wannan lokacin na ji yarinyar ta ƙara fita a raina matuƙa, ana haka Islaha ta tare ni da zancen tana son Abubuakar da aure, na yi murna sosai sabida a ganina zumunci ne da zai ƙara ƙulluwa cikin ahalinmu, bayan na yi magana da Abubakar aka yi aure, watanni kaɗan ya zo min da zancen ƙarin aure, yana so ya aure Nana tsohuwar matar Sardauna, anan na ƙara tabbatar da abinda Sardauna ya faɗa a baya, na kuma dage akan ba zaayi ba, amma da yake ubangiji ya tsara za ayin, gashi anyi. Tun a bayaj auren Yarinyar nan Nana, aka fara sintirin kawo ƙara wajena, ba a zauna ba. A yau kuma an zo da wani gagarumin abu da ya girmi tunani na, shine wai Turaki ya saki Islaha, sabida tana ɗauke da cikin da bana shi ba.” A take kowa ya ya ɗauki Salati, ana tafa hannu, Mommy ta ce. “Turaki! Wannan wace irin banzar magana ce marar tushe? Ya za ayi ka ce cikin dake jikin matarka bana ka ba ne?” Big Daddy ya ce. “Ki yi haƙuri, ki saurari komai mana, kowa ya yi haƙuri. Kai Abubakar me ya sa ka ce cikin dake jikin Islaha ba naka ba ne?” Turaki ya yi gyaran murya ya ce. “Kamar yanda na faɗa a wancan zaman namu, a yau ma zan sake maimaitawa, tun aurena da Iskaha babu wani abu da ya taɓa haɗani da ita, ko da maganar fatar baki ce, sai a bayan na ƙara aure, shima ba wai magana ba ce, rashin mutunci ne kawai take kawowa, rana ɗaya kwatsam naganta da ciki a jikinta, ko da na tambayeta sai ta fara kuka tana bani haƙuri, zuwan Nana yasa ta sanar da ni wai cikin Sardauna ne.” “Ita aina ta sani dan ubanta?” Maman Sardauna ta faɗa a fusace, Big Daddy ya ce. “Dan Allah duk wanda ba a bashi izinin magana ba ya yi haƙuri, komai zai fito wannan zaman zai kawo ƙarshen komai. Ke Nana.” Ya kira sunana, na ɗaga kai na kalleshi, ya ce. “Aina kika san cikin jikinta na Sardauna ne?” Cikin rawar murya na ce. “Ita ta faɗa min, na shiga ɗakinta na ganta da ciki kuma bata da lafiya, shine na fara taimakata da wasu ayyukan da zuwa asibiti, shine take faɗamin kuma wai tana tsoron sanar da Turaki, shine na ce zanyi ƙoƙari na faɗa masa yanda zai fahimta, kuma ban samu dama na faɗa masa ba har Allah Yasa ya gani.” Big Daddy ya ce. “Islaha.” “Na’am.” Ta amsa, ya ce. “Mene gaskiyyar waɗan nan maganganun?” Ciki murya kuka ta fara magana. “Tun farko ni bana son Yaya Turaki, ban taɓa son shi ba, ban taɓa jin sonsa a raina ba, Yaya Sardauna nake so, shi nake ji a raina, kuma shi nake son aura, lokacin da na ji ya yi aure na shiga damuwa kuma na ji babu wadda na tsana kamar matarsa, ina cikin tsanarta ya zo ya same ni ya ce da ni, wai na shiga na fita nasan duk yanda zan yi na na taɓata Nana a cikin ‘yan uwa, ɓatawar da kowa zai tsaneta, har a sa shi ya sake ta ni kuma sai ya aure ni. Tun daga nan na shiga ɓata sunan Nana ta ko ina, bana ji bana gani kullum cikin yi mata ƙage da sharri nake, duk da ita batasan anayi ba, amma abun ya zama trend a family, ana haka yazo ya ce zai auri Bilkisu, da na yi masa magana ya ce ranar da ya auri Bilkisu ranar zai saki Nana, da yake soyayya ta rufe min ido sai na yarda, aka yi sa’a ranar da ya auri Bilkisu ya saki Nana, amma bai aure ni ba. Ya ci gaba da ɗaurani akan keken ɓera na cewar zai aureni, ni kuma ina ta yarda har akazo lokacin da ya ce na auri Yaya Turaki, na dage akan sai na aureshi shi nake so. Ya faɗamin dalilin shine Yaya Turaki zai auri Nana, idan har ban bari ya auri Nana ba to shine tabbacin aurena da shi, na ƙara yarda da hakan na zo nasa daru akan ina son Yaya Turaki, ranar ɗaurin aurenmu Yaya Sardauna ya zo ya dinga cemin yana sona, yana ƙaunata, kuma duk tsanani yana tare da ni kuma zai aureni, a ƙarshe ya ce na taimaka na bashi abu mafi tsada da zai tabbatar da soyayyarmu, ko a lokacin ma bangane ba amma ya ce dani na bashi kaina kafin akaiwa Turaki, sabida son da nake masa na amince masa muka aikata saɓon ubangiji, tun daga wannan lokacin babu ranar bazan da ba zata zo ba, sai mun kasance tare da Yaya Sardauna, ya mayar da ni kamar matar da yake aure, har aka auro Nana ya ce dani idan na dage Yaya Turaki ya saki Nana, to a ranar shima zai sanya a sake ni kuma ya aureni, ko wannan ƙarar dana kawo ƙarar Nana ma duk sharri na haɗa musu. Ana haka nagane inda ciki na shiga damuwa na fara ɓoyewa har ranar da Nana ta gani, ita tabani shawarar na kula da lafiyata kar na faɗa ma Sardauna dan tsaf zaiyi duk abinda zaiyi dan cikin ya zube, wanda zai iya jamin matsala ko na mutu ko mahaifata ta sami matsala kamar yadda ya yi mata.” Ɗakin ya yi shiru gaba ɗaya, sai da aka ɗauki mintina sannan Hajiya Falmata ta ce. “Amma Islaha kinyi asara, wace irin soyayya ce wannan kike yi, sai ka ce baki da hankali? A tarihin rayuwata ban taɓa ganin soyayya ta jahilci ba irin taki, kai kuma Sardauna Allah Ya isa tsakanina da kai, kuma wallahi sai ka karɓi ɗan nan, kuma ka biyata duk wata wahalal da ta sha.” Sai a lokacin na kalli Sardauna da ya yi tsuru-tsuru kamar shege a rabon gado, zufa ce kawai ke zubo masa ta ko ina, wani irin tausayinsa na ji ya ratsani ta ko ina, yanzu Sardauna ya fara girbar abinda ya shuka. Hajiya Nafisa (Maman Sardauna) ta ce. “Ya Allah ka gani ba akan tarbiyar da na ɗaura ɗan nan ba kenan, Ya Allah karka kamani da haƙƙinsa, Sardauna ka cuceni, ka kuma cuci yarinyar mutane, ka sanya wa kowa tsanarta ba tare da ta aikata komai ba, Ya Allah.” Ta faɗa tare da fashewa da kuka, kowa na ɗakin ya yi shiru. “Tabbas Nana mun tsaneki, munƙi ki akan laifin da baki yi ba, Islaha kin bamu kunya, kin watsar da ilimin da kike taƙamar kina da shi, kin biyewa zugar ɗa namiji, Wallahi Sardauna Allah Ya isa tsakanin mu da kai.” Alisha ta faɗa, Hajiya Falmata ta ce. “Sardauna tun kana ƙarami na fuskanci kai sheɗani ne, kai ne sillar fara jin haushin Hajiya Amina da muke yi ni da Hajiya Nafisa, a kullum idan kazo sai ka ce sun zagemu sun aibata mu, hakan yasa muka haɗe kai mu ka fara jin haushinsu na babu gaira babu dalili, tabbas tsintacciyar mage bata mage, kuma barewa bata taɓa gudu ba ɗan ta ya yi rarrafe, bazan manta ba mahaifiyarka ma haka take da baƙin hali da baƙar zuciya, kullum cikin ƙulla sharri take har ta koma ga All…..” “Hajiya Falmata dakata!” Big Daddy ya faɗa a tsawace. “Wannan ba maganar nan wajen ba ce, magana ce akan abinda Sardauna da islaha suka yi, bana jin an zauna nan ne dan ayi wani tashin tashina, dan haka kar wanda ya kuskura ya canja mana abinda muke magana akai” “Ni kam da an canja, wallahi Sardauna ka kunyata ni, ko da yake da laifin na tun a farko, na kasa fahimtar irin baƙar zuciyar da kake da ita, na dinga biye ma. Tabbas Hajiya Falmata kin faɗi gaskiyya, sabuda abunda Sardauna ke faɗa mana yaja muke jim haushinsu, mussaman Hajiya Amina, duk idon mu ya rufe gaba ɗaya.” Maman Sardauna ta faɗa, Mama Amina ta ce da ita. “Duk da haka bai cancanci ayi wancan batun ba a yanzu, mu tsaya akan wannan tun da alƙwari ne a kai, kuma hausawa sunce hannunka baya ruɓe ka yanka, duk abinda Sardauna ya yi ko ya zama, har abada sunan sa namu, babu yanda muka iya, namu ne shi, rainon mune, tarbiyar mune.” Sai a lokacin na ji Abba musa ya yi magana, bar ‘yan biyu daman da su kwata kwata basa magana a waje indai Big Daddy yana nan, ni har mamakin irin haɗin kansu nake yi, yanda suke zama akan umarnin mutum ɗaya, idan ka zauna da su sai ka yi tunanin dukkan iyaye mazan sun mutu Big Daddy ne kawai ke raye, in dai ba gidansu kika je ba ba kya ganinsu, mussaman ‘yan biyu da suke ke kula da kasuwancinsu na ƙasar waje, sunfi zama can akan nan. “Tabbas Sardauna bai kyauta ba, kuma bai yi hallarci ba, ya cutar da rayuwar yarinyar mutane, amma abin godiyar shine ba ta yi mana nisa ba, bare ace neman afuwarta ya zama abu mai wahala, a yanzu duk mai son gyara laifinsa yana da damar nuna mata soyayyar da ta cancanta, sai kuma zancen Islaha da shi, ni banu da abin cewa amma a hukuncin da zan iya shine, dole ka auri Islaha, ku raini yaronku a tare.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (3). “Wallahu Daddy a’a, ni bana son sa yanzu, ya cutar da rayuwata, na tsane shi.” Islaha ta faɗa tana kuka, Mama Amina ta ce. “Haƙuri zaki yi Islaha, ni kaina wannan tunanin nake yi, tabbas a yanzu zuciyarki ta kai ki tsani Sardauna fiye da kowa, amma idan kika yi haƙuri komai zai wuce.” “Ni dai aduba lamarin nan Alhaji.” Hajiya Falmata ta faɗa, Alisha ta ce. “No Mommy, that’s is the best solution.” Big Daddy ya ce. “Tabbas shawararka ta yi, kuma Sardauna babu wanda zai ɗaukar maka nauyin komai akan wannan cikin, kai zaka yi komai da kanka, sannan wannan ya zama na ƙarshe a wajenka, kuma hukuncin da zanyi maka shine soke visa ɗinka, na shekara biyu, ba kai ba sake fita kowacce ƙasa har sai bayan shekara biyu, sabida hakan ya zama izina ga ‘yan baya, sannan ka je ka nemi yafiyar mahaifiyarka.” Ya faɗa yana nuna masa Hajiya Nafisa, wadda ta ci kuka ta gode Allah, daga haka zaman ya tashi kowa ya miƙe ya nufi gidansu akabar Sardauna zube a ƙasa ya kasa ko kyakywan motsi, a mota Turaki ya ce da ni. “Habibty ko yanzu mu godewa Allah, baƙin fentin da Sardauna ya shafa miki a cikin family ya goge, ki nutsu ki kwantar da hankalinki, in sha Allah yanzu zaki fara samun soyayya daga ‘yan uwana kamar yanda nake samu daga naki ‘yan uwan.” Na yi murmushi mai bayyana jindaɗi na ce. “Allah Alhamdulillah.” A haka muka ƙarasa gida muna hirar mu ta soyayya, ran mu fes haka muka shiga gida muka kwanta, muna fatan kowacce matsala tazo ƙarshe, mu gina sabuwar rayuwa mai cike da farin ciki da albarka, babu wata damuwa a yanzu da ta rage sai ta haihu, dan tabbas ina jin ɗar ɗar a cikin zuciyata na rashin haihuwar nan, duk da bana son nuna damuwar sabida kar ran Turaki ya ɓaci, amma a cikin raina ina nan shimfiɗe da wannan damuwar. A haka aka ci sati da zaman da aka yi na su Sardauna, tun daga wannan lokacin ban sake sanya Sardauna a idona ba, ita Bilkisu daman ba akai ba, babu wanda ya isa ya sata tazo, sharrin da Sardauna yake yi min ada yake cewa halina ne, a yanzu gashinan ya samu mata mai ainahin halin. Bayan Sati biyu. Tun daga wannan zama da aka yi na fara samun sauyi, dan a yanzu har su Hajiya Falmata sun daina nuna wani abu a gareni, idan mun haɗu zamu gaisa faran faran ba, duk da banje gidansu ba amma mun haɗu dasu sau biyu a asibiti, Maman Sardauna kam ko ada ta so ni a farko daga bayane ta janye ta daina sona, to a yanzu ta dawo da son, da zarar mun haɗu zata dinga faɗin Daughter Daughter! Su Sister Seemah kam abu ya ƙaru a yanzu ma idan naga Big Daddy faran faran muke gaisawa a asibiti, Bilkisu dai har yau bata zo dubiya ba kuma babu wanda ya nemeta, shi kanshi mijin nata a yanzu ya ja baya da familyn, yana dai zuwa ofis kuma yana zuwa asibiti, gidanmu babu wanda bai zo ba, Hajiya har wajen sau uku, hakama Yaya Ridwan. Ra’is yazo shi da amaryarsa itama tana ɗauke da juna biyu, Yaya Rumaisa da Yaya Radiya duk sun zo, ranar da naga ciki a jikin matar Ra’is na yi kuka kamar na gobe, a lokacin kuma na ƙara tabbatarwa kaina mahaifata ba ta warke ba, rashim haihuwa da Sardauna ya ƙaƙabamin ya zama babban cikas a rayuwata, Sai da Hajiya Maimuna ta yi wata ɗaya a asibiti sannan aka sallamota ta koma Abuja, Sardauna ne ma yaje kai ta da kansa, bayan kwana biyi da tafiyarta, ina zaune a asibiti wajen ƙarfe huɗu da rabi Lamrah ta kira ni a waya, ina ɗaga na ce da ita. “Lamrah barka da rana.” “Barka Anty Nana, yanzu aka sanar a family group Anty Islaha ta haihu, ta haifi mace.” Har cikin raina na ji daɗi, mussaman da ta sauka lafiya, na ce da ita. “Aikuwa ina tashi daga nan zan zo, kuna can?” “A’a, yanzu muma dai zamu tafi.” “Toh shikenan Lamrah, sai mun haɗu.” Ina kashe wayar na kira Turaki, yana ɗagawa ya ce. “Islaha ta haihu.” Na yi murmushi sannan na ce. “Yanzu Lamrah ke faɗa min, zaka je ne?” “A’a Habibty kema ba zaki ba.” “Me ya sa Habibi?” “Kawai, mu bari sai gobe in sha Allah, na ji Big Daddy ya ce yau za a ɗaura musu aure, a gidanta ma za ayi suna.” “Nan zata dawo kenan?” “Eyh, kinga ai ba sai mun je ba.” “Hakane kuma Allah Ya sanya alheri, yaushe zamuje wajen ‘ya’yanmu.” “Wai Habibty har yanzu ba a yaye su ba, nagaji fa.” Na yi dariya, sannan na ce. “Wai basukai ba har yanzu, ni tsorona ma kar suƙi zama, kaji yanda suke kuka idan muna waya, ta ce duk sun isheta, wannan tanayin shiru wannan zata fara.” Shima sai da ya yi dariya sannan ya ce. “Cika musu ɗaki zamuyi da kayan wasa, kuma ke zaki dinga kula da ɗaya nima ɗaya.” “To Habiby ya zaayi dasu idan zamuje aiki?” “Zamu samo mai kula dasu mana.” “Eyh hakan ya yi, amma babbar mace ko?” “Ko wacce ma, amma kaman babba zatafi kula dasu ko?” Na ce. “Eyh Habiby.” “Ni har naji ma ina son ganinsu, ko mu tashi muje.” Aikuwa jikina har ɓari yake na miƙe, shima ya miƙi muka fice. Da mukaje ma sun fara bacci, Yaya Ridwan ya ce. “Wannan zuwan na dare ai sai ku tsorata mutane.” “Yaranmu mu kazo gani.” “To ai sunyi bacci, idan kuma tafiya zakuyi dasu shikenan.” Dariya muka yi ni da Turaki, a haka muka ɗauke su suna baccin, sannan muka tafi. Washe gari aka sallami Islaha daga asibiti, kuma kai tsaye gidanmu aka yo da ita, sabida a daren jiya aka ɗaura musu aure da Sardauna, shigowa ta daga ofis kenan ko fitowo daga mota banyi ba, motarsu ta shigo. Fuskata a washe na tare su da faɗin. “Har kunzo?” Alisha ta ce. “Eyh, yanzu muka iso.” “Nima shigowata kenan, Islaha ya jikin ina babyn.” “Gata hannun Mommy.” Na kalli Hajiya Falmata da ta riƙe babyn na ce. “Ina yini.” “Lafiya ƙalau.” Ta amsa, ni kuma na kama hanya zan wuce nawa ɓangaren, Islaha ta ce. “Nana bazaki shiga ba?” Na ce. “Zan shigo ko da daddare ne.” Alisha ta ce. “Ai da kinzo an raka ki da ita.” Ba musu na bi bayansu muka shigo, na yi mamakin ganin kayan Islaha dake part ɗina anan, ko da yaushe aka dawo dasu oho? Muryar Bilkisu ce ta ƙaraɗe ɗakin. “Daman jiranku nake, wallahi ku fitar da ita daga gidan nan, dan wallahi babu wajen kowacce shegiya, wace irin amarya ce ma haka marar albarka, babu wanda ya rako ta.” Tsaki Hajiya Falmata ta ja, ta shige inda yake mallakin Islaha ɓangarena na da, ni dai duk jikina ya mutu, ganin haka ya sa na fice na yi namu ɓangaren. Ina jiyo hayaniyar Bilkisu tana ta masifa wai ita ta kasa gane kan wannan al’amarin, wannan ai Islaha ce matar Turaki, kuma mai ya kawo ta nan da jariri. Su dai duka suka yi mata banza ta yi ta surutanta, wajen ƙarfe shida ina cikin na ji an shigo ana ƙwallamin kira. “Nana, Nana, Nana.” Fitowa na yi na zo falon. “Nana faɗan gaskiyya, mai kishiyarki ke yi a part ɗina, kuma jaririn dake wajenta na waye?” Kallon Bilkisu na yi, kamar ta fara fita daga hayyacinta, na ce. “Bilkisu ki nutsu mana, Shi mijin naki bai faɗa miki ba?” “Ina ya faɗan munafuki, sai kiran shi nake ma yaki ɗauka gaba ɗaya.” “To ki jira ya dawo, me ya sa ranar da aka yi zaman nan baki zo ba?” “Ni zan shiga cikin ‘yan uwansa? Wani ya yi min kallon banza, wallahi a’a. Kawai ki faɗan.” “Da kinje da yanzu ba kya cikin duhu, Islaha dai a yanzu matar Sardauna ce, sauran bayani kya ji daga wajensa.” “Bangane ba, aina ya aureta, yaushe aurensu da Turaki ya mutu?” “Nima bansaniba, amma idan kika ga shi Sardaunan zai faɗa miki nasan.” A fusace ta fice fuuuuuuu, kamar wadda iska ta ɗauka, ni kuma na koma kicin na ci gaba da abinda nake yi. Sardauna da ya saba dawowa kafin magariba shiru har Turaki ya riga shigowa, sai wajen ƙarfe takwas sannan Turaki ya ce na shiga na yi wa Islaha barka, shi ba zai shiga ba, ba yanda banyi da shi ba amma yaƙi shiga. A lokacin da na shiga Bilkisu na zauna a falon farki tana ta faman wuci kamar wata zakanya, ban ko kalleta ba na shiga ciki na tarar da Islaha ita da wata dattijuwa, tana yiwa yarinyar wanka. Bayan mun gaisa na ce. “Ya babyn?” “Gatanan tana ta kuka.” Islaha ta faɗa, nan na zauna wajen minti goma sannan na miƙe zan tafi, daidai lokacin kuma naji Sardauna ya shigo falon, muryar Bilkisu ta karaɗe ko ina na gidan. “Jira nake ka dawo, Sardauna ni zaka ci amana, ka cuta? Ni zaka ƙarawa kishiya, a gidan ubanwa matar Turaki ta zama matarka?” “Bilkisu ku nutsu na miki bayani.” “Bayanin me? Sardauna wannan jaririn da tazo da shi kuma fa? Na waye ko nakane?” “Nawane Bilkisu.” Ta lailaya wata uwar ashar, sannan ta ce. “Shege? Ɗan shege Sardauna, iskanci kake da matar aure, shine xa a kawo ma ɗa ka riƙe, wallahi nafi ƙarfin zama da kishiya.” “Bikisu ki fahimce ni, nima bayi na ba ne.” “Ƙaramin yaro ne kai? Ko mace ne kai da zaayi ma auren dole? Wallahi Sardauna sai ka sake ta a yau, ba muyi alƙwarin ƙarin aure da kai ba, kwata kwata dan haka wallahi sai ka saketa, bandamu ba ko duka karuwan duniya naka ne Sardauna, bai dame ni ba, bai isheni ɗaga hankali ba, amma wallahu kishiya ɗaya bata isheni zama a gidan nan ba, gashi har ɗa, ni ina zaune ba haihuwa amma ace ga wata ta haihu da kai kuma babu aure a tsakani, lallai Sardauna.” Jin abun nasu bana hankali ba ne ya sa na fice na bar musu part ɗinsu, ina shiga na tarar da Turaki zaune kan kujera yana waya, yana ganina ya kashr wayar ya ce. “Habibty kin daɗe.” “Dawa kake waya haka?” “Abokina ne, me ya faru kika daɗe, na ji hayaniya acan.” “Uhm a tskananinsu ne, waj Bilkisu ta ce sai Sardauna ya saki Islaha, Habiby kasan me?” Ya girgiza kai, “Wai Bilkisu bata ƙi duk karuwan duniya su zama na Sardauna ba, amma kishiya ɗaya a gidan bazata ɗauka ba, wannan ai shirme ne, Habiby ni yanzu ai mace ko ɗaya bazan iya jure ganinka da ita ba, bare wai duk na duniya, Allah Ya tsare mana zuciyoyinmu.” “Habibty bazaki iya gani na da wata macen ba?” Na girgiza kai, sannan na ce. “Gaskiyya bazan iya ba.” “Amma kika yiwa Sardauna aure da kanki? Ko kinfi son shine?” “Ai sai yanzu nake gani ban so Sardauna a baya ba, sabida Habiby a yanda nake jin ka ai ko mutuwa yarinya za ta yi akanka sai dai ta mutu, amma bazan iya bari ba.” Ya yi dariya, sannan ya ce. “Habibty ni naki ne, ke ɗayarki in sha Allah.” “Allah Ya yarda Habiby na.” Na faɗa ina miƙewa, amma wata razananniyar ƙara ta fito daga part ɗinsu Sardauna, wacca ta girgiza mu baki ɗaya, a take kuma muka ji an buɗe ƙofar part ɗinsu anfuto, ihun ya fito sarari, ga Muryar Turaki yana faɗin. “Ke Bilkisu nutsu.” Ita kuma tana cewa. “Wallahi sai na kashe jaririn nan, wallahi yanda bazan haihu ba, kaima banu wacca ta isa ta haihu da kai har abada.” “Na faɗa miki dai Bilkisu kar ki cutar min da mata ko yarinya.” “Au Sardauna har mata kake ce da ita, mazinata bayan kun gama zina kun haifi ‘yar shege, to wallahi sai na kashe ta, kaima na kashe ka, sai dau nima a kashe ni daga baya, amma bazan zauna da kishiya a cikin gidan nan ba.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (4). Ƙoƙarin fita na fara Turaki ya riƙe ni. “Wai mene haka ne? Ka barni mana.” “Habibty wannan ne karo na ƙarshe da zance miki babu ruwanki da lamarin gidan Sardauna, duk abinda zasuyi idone naki, idan zaki kalla idan bazaki kalla ba ku barshi, na faɗa miki.” Buɗe baki na yi zan magana, amma sautin marin da Sardauna ya tsinkawa Bilkisu ya tsayar da ni, na sake mayar da kaina taga, a lokacin kuma Sardauna ya ce. “Wallahi Allah Bilkisu akan yarinyar nan, zan iya sakinki ki tafi can, nagaji da wannan mugun halin naki.” “Ni ka mara Sardauna? Wallahi sai kasan ni ka yi wa haka.” “Me zan sani Bilkisu, na gaji da zama dake wallahi, na yi dana-sanin saninki a rayuwata Bilkisu, na yi dana-sanin aurenki a rayuwata, aurenki bai amfane ni da komai ba sai masifa.” A daidai lokacin Islaha ta koma ɗakinsu, shima ya bi bayanta akabar Bilkisu tsaye, nima sai a lokacin na kula ashe Turaki ma baya nan, waigawa na yi gaba baya falon baki ɗaya, ba shiri na bishi ɗaki, yana zaune kan gado yana danna wayarsa. “Habiby.” Na faɗa ina tura baki, bai ɗago baya amsa da. “Na’am, Habibty me ya faru?” Zama na yi daga gefenshi, sannan na ce. “Naga ka dawo nan?” “To Habibty mene amfanin kallon abinda bai shafe ka ba? Muna da tarin abubuwa a gabanmu, me zai sa mu tsaya kallon na wasu?” “Hakane Habiby, amma wani aiko ba kaso ba, sai ka ji.” “Wani kuma kana so kake jin ma.” “Shikenan Habiby, na daina.” “A’a idan kina jin daɗi ki ci gaba kawai.” “A’a na daina.” “Allah Yasa.” ************ Washe gari ko da na tashi ban shiga wajen Islaha ba, sai da Turaki ya fita wajen ƙarfe tara ni kuma nagama shiryawa, sannan na shiga. Ban wani jima ba na fito na yi wajen aiki, ina ofis na ga kuɗi dubu ɗari uku sun shigo account ɗina daga Turaki, ina kokarin kiran shi ya kirani, bayan mun gaisa ya ce. “Gashinan na tura miki 300K, ki samu ki shiga ki fara siyan kayan twins ɗinmu, tun da kinga sun kusa dawowa.” Har cikin raina na ji daɗi na yanda Turaki yake ƙaunar twins ɗinan, “Tom shikenan, an gode Allah Ya ƙara buɗi.” “Amin.” Ƙarfe uku na tashi na nufi naje wani babban shagon siyar da kayan yara, komai biyu biyu na siya, tun daga kayan sawa da na wasa, har sai da na ƙara da wasu nawa kuɗin, daga nan na yo gida. Ina shiga part ɗina Su Lamrah suka shigo. “Anty tun ɗazu muka zo, ashe kinje aiki.” “Eyh wallahi, kuma na biya na yi siyayya shi ya sa ma ban dawo da wuri ba.” “Sannu da zuwa, siyayyar baby aka yi kenan, ko an kusa sauka ne?” Na yi murmushin yaƙe, sannan na ce. “In sha Allah.” “To Allah Ya kawo masu albarka.” Daga nan muka taɓa hira, har nagama girki ta ci sannan muka shiga part ɗin Sardaunan tare, har muka tafi Bilkisu ba ta dawo ba, na yi mamakin yanda Sardauna yake ta kashewa jaririyar kuɗi, sonta yake kamar ransa, idan kuma aka haɗa da yanda Sardauna yake son yara sai kaga ma wannan ba komai yake ba, a yanzu haka ya cika akwati wajen uku da kaya masu tsada na baby na fitar suna, kuma Islaha tana samun kulawa daga wajensa sabida wannan yarinya da ta haifa masa, lokacin da Su Mama Amina suka tafi nima lokacin na dawo nawa part ɗin ban sake komawa ba. Turaki yaga kayan da na siyo, kuma ya yaba da yawansu da zaɓen da na yi mai kyau, sannan ya ce na yi magana da Hajiya sai asama mun mai zama da yaran, dan so yake bayan anyi sunan Islaha da kwana ɗaya muma zamu ɗauko namu, nima kam na amince, a lokacin ya ce da ni. “Wai kinsa Matar Ra’is ma ta kusa haihuwa.” Dariya na yi, sannan na ce. “Wai Ra’is autan Hajiya.” Shima ya yi dariyar ya ce. “Autan Hajiya fa, ai ɗazu naje gidan nasu ya matsa ban taɓa zuwa ba.” “Ni ai bai taɓa nemana ba, yaron nan dani yake zancen.” “Ai na faɗa masa na ce, bai taɓa kawowa yayarsa amaryar ba, wai yana nan zai kawo ta yana shiri ne.” “Shi dai ya sani, Allah Ya sauke ta lafiya.” Tun zuwan Islaha kullum sabuwar Dirama ake yi a gidan Sardauna, Bilkisu kullum tana kan bakanta na cewa sai Sardauna ya saki Islaha, kuma sai ta kashe Jaririyar, shi kuma ya dage ba ta isa ba, haka zamu yi ta jinsu suna hayagaga, dan ma Turaki ya nuna ba ya so shi ya sa na rage leƙa su, amma duk da haka ban taɓa yin farin ciki da abinda Sardauna yake fuskanta ba, duk da nasan zallan haƙƙi na ne ke ɗauwainiya da shi, a duk lokacin da na tuna Sardauna bai da alaƙa da wannam familyn da yake taƙama da tinƙawo dashi, sai na ji na fara tausayinsa, har hango halin da zai shiga nake yi, a waje ɗaya kuma na ƙara tabbatar da Sardauna bai da tunani, bai da lissafi, yana ji su Hajiya Falmata suka ɗauko magana Big Daddy ya ce kar a canja musu topic, kuma yana ji hajiya Falmata ta ce barewa ba ta yi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba, aiko ba a ƙarasa maganar ba, wannan kalmar ta isa ta sa shi ya yi tunani akai, amma ya yi shiru ko ajikinsa. Yau ‘yan matan familynsu Turaki suka zo barka, daga ƙannen Turaki da na Sardauna, har da ma manyansu su Sister Seemah, ganin sun cika gidan ya sa nima na shiga cikinsu na saki jiki ana ta hira da raha, girki ma a nawa ɓangaren na yi musu duka, aka ci aka sha ana ta hira. Wajen ƙarfe uku na rana Bilkisu ta shigo ita da wasu mata wajen su biyar, tunda naga fuskarsu naga kamar nasan su, amma na kasa tuna inda nasan su. Wani banzan kallo suka yi mana gaba ɗayanmu, wata cikinsu ta ce. “Munzo barka ne, abamu ‘yar mugani.” Alisha ta ce. “Ba za a bada ba? Su waye ne ku?” “‘Yan uwana ne, ku basu isa su zo bane?” Bikisu ta faɗa, sister Seemah ta ce. “Ba za a bada ba, idan zakuyi barkar a haka ku yi idan bazaku yi ba ku tafi.” Sai a lokacin nagane fuskarsu, wasu a cikinsu sune ‘yan matan da Bilkisu tasa suka yi min rashin mutunci a lokacin da naje nemawa Sardauna aurenta. “Ke ma Bilkisu wallahi kina ban mamaki, akan ‘yar shege kika damu kanki? ‘Yar shege ce fa, ita ba gado ba, mutuwarta ma tafi rayuwarta alheri a wajenta, sabida abar kyara da tsangwama zata zama a cikin ‘yan uwa, kuma babu ta inda zata ci gadon Sardauna.” Wata cikin ‘yan matan ta faɗa, Bilkisu ta ce. “Ni duk ba wannan ba, rashin kunya ma irin ta su, wai shege ake yi wa wannan taron har da zuwan mutane, sabida su abun kunya baya suka bashi ba gaba ba.” Duk cikin mu babu wanda ya kula da tashin Alisha, sai kawai ji muka yi ta bawa Bilkisu wani uban mari fas a fuska, marin da ya yi matuƙar shigar Bilkisu ya sa ta dafe kuncinta, Alisha ta ce. “Wallahil azim, idan baki matsa daga nan ba sai na yi miki dukan da bazaki iya numfashi ba.” Wata cikin ‘yan uwan Bilkisu mai zafin nama tabawa Alisha lafiyayyen mari itama a fuska, aikuwa Alisha ta kaima ta ita, nan fa kowa ya tashi tsaye, ni dai na yi tsuru tsuru, Turaki ya hanani shiga lamarinsu, ga kuma abu yana neman zama faɗa. “Ai wallahi tun da kika mareni kin jan gwalowa kanki masifa da bala’i.” Bilkisu ta faɗa, Sister Seemah ta ce. “Masifa da bala’i akanki ke ɗai wallahi, yanzu nan zan sa akama ki kuma a ɗaure ki.” “Karki fasa sawa, an gaya miki ku kaɗai kuke da kuɗi? To ko bamu da kuɗi muna da bariki, wallahi duk kuɗin akwai inda zamu shiga musa a kulleku kar ku fasa.” Inji Wata cikin ‘yan uwan Bilkisu, nikam na saki baki ina kallonsu. ‘Oh ‘yan uwan Bilkisu sheɗanu ne.’ Na faɗa a raina, a fili kuma na ce. “Dan Allah ku yi haƙuri, su waɗan nan basu sa naraba da sheɗanu, basu ƙi ku biye musu ayi ta faɗa ba.” “Ke dallah ‘yar kore rufemin baki, marar zuciya, me son abun duniya, an sake ki kin na ce.” “Karki ƙara ce mata dallah.” Lamrah ta faɗa, Sister Seemah ta ce. “Wallahi na baku minti biyu ku fice daga gidan nan, idan ba haka ba sai kunyi da kunsanin shigowa cikin gidan nan, tun da bana uwarku ko ubanku ba ne.” “Babu wanda ya isa ya kore su, tun da gidan da ‘yar uwarsu ke aurene, dan haka babu wanda ya isa, kuma mari da aka yi min wallahi bazan haƙura ba sai na rama.” “Ashe kuwa zaki rame.” Alisha ta faɗa, Bilkisu ta yi yinƙurin kawo mari amma Alisha ta matsa. “Na faɗa miki wallahi karki kuskura ki ce zaki kai hannu jikina, dan naga kamar baki da hankali.” Alisha ta faɗa, amma ba ta rufe baki Bilkisu ta kai mata wani marin wanda ta yi sa’a ta same ta, aikuwa a take faɗa ya kaure a tsakaninsu, ‘yan uwa Bilkisu duka suke kawowa kowa, Sister Seemah ta fita waje tana faɗin. “Me gadi! Me gadi!!” ‘Yan mintina kaɗan sai ga me gadi ya shigo, sister Seemah ta ce. “Kaga waɗan nan biyar din, walahi ka fita da su ko ta wane hali ne, idan kuwa ba haka ba to wallahi sai ka bar aiki a gidan nan.” Aikuwa me gadi ya nufi su yana faɗin. “Ku zo ku fita, na ce ku fita.” “Kar ka kuskura ka taɓa ko ɗaya nan, tun da baka da hankali bakasan shari’a ba.” Afrah, ƙanwar Sardauna ce ta ce. “Bara na kira Yaya Sardauna kawai, naga abun ya zama out of control.” Sister Seemah ta ce. “Lallai Sardauna yana fama. Da, da wannan annobar yake zaune a gidan nasa? Allah Sarki Nana wallahi haƙƙin ki ke ɗawainiya da Sardauna, kuma ya tsaya girman kai ba zai zo ya nemi afuwarki ba.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (5). "Hello Yaya." Afrah ta faɗa, hankalin kowa ya yi kanta. "Yaya, wannan matar ta ka mentel ce, gata nan ita da 'yan uwanta sun zo sai dukan mutane suke, ya kamata kazo akan lokaci fa." Tana faɗin haka ta kashe wayar, cikin ƙasa da mintina goma Sardauna ya shigo gidan, yana zuwa bai tsaya ya bi ta wani abu ba ya hau tsinkawa Bilkisu mari, aikuwa ta tare ita ma suka fara 'yar mare mare ya dake ta tarama. 'Yan uwanta kuma na ta zagin Sardaunan, sai da ya jiyo kansu a fusace ya ce. "Duk shegiyar da bata barmin gida ba, sai na ɓaɓɓalata." Ba musu suka fara ficewa, aka bar shi daga shi sai Bilkisu, tana ta faman danna masa ashar, Sister Seemah ta ce. "Sardauna itama ka koreta mana, mene amfanin zama da ita a haka bata san darajarka ba, batasan darajar aurenta ba?" "Ina tara ta ne, rana ɗaya zan sallameta wallahi." "Ashe zaka iya sakina Sardauna, ai wallahi bazan sako ba, yanda ka auro ni haka zamu mutu tare, kuma wannan yarinyar ce sai ta bar gidan nan daga ita har abinda ta haifa wallahi." Bilkisu ta faɗa, tana zagaye ɗakin, sabida bin ta da Sardauna yake. "Wallahi gida ne ta shigo sai dai ki mutu, ke ba a auren aka aure ki? Ina ce kema kishiya aka yi wa wata dake, shine zaki ce ke ba a isa ba?" Alisha ta faɗa, Bilkisu ta ƙara cewa. "Ko ana kishiya nikam ba wanda ya isa ya yi min wallahi, yanda nake zaune gidan nan ni kaɗai zan rayu ciki, kuma ni kaɗai zan mutu cikinsa, Sardauna kuwa a tare da ni zai rayu ni ka ɗai wallahi." "Mitchewww." Sister Seemah ta ja tsaki, sannan ta ce. "Ni kam tafiya zanyi ba zan iya wannan zaman ba, takaici zai kashe ni wallahi." Tana faɗin haka ta ɗau jakarta, su Lamrah duk suka miƙe aka bar Islaha da 'yan gidansu kawai, nima na bi bayansu Sister Seemah na fito. Suka shiga mota ni kuma na yi nawa part ɗin, ina shiga na watsa ruwa na kwanta, wani ɓarawon barci ya ɗauke ni, wanda a cikinsa na yi wani mafarki. Ni da Turaki zaune a falo ga yara guda huɗu maza da mata suna zaune suna wasa, ina kallon yaran ina jindaɗi a cikin a raina, kwatsam sai wata mata ta fito daga cikim ɗaki ta far ɗaukan yaran, n kalli Turaki na ce. "Habiby, kaga tana ɗaukan yaran mu?" Ya kalle ni ya yi murmushi, ya ce. "Habibty ai na tane, za a hana uwa ɗaukan 'ya'yanta?" "Na ta?" Na tambaya ina miƙewa, shima ya miƙe ya ce. "Habibty wannan fa amarya tace, ko baki gane ta ba?" "Banganeta ba." Na faɗa ina girgiza kai, sannan na sake cewa. "Habiby yaushe ka yi aure? Rashin haihuwar tawa ne ya sa ka ƙara aure?" Ya girgiza kai zai yi magana, ƙarar kiran waya ya tashe ni daga barcin da nake yi, na tashi a firgice na ɗau wayar. “Habibty ina ta knocking ko ba kya nan ne?” Muryar Turaki ta fito daga cikin wayar. “Gani nan.” Na faɗa ina tashi, ina buɗe ƙofar naganshi a tsaye yana kallona. “Ina kika shiga?” “Bacci ne ya ɗauke ni, na yi wani mummunan mafarki, Allah Ya tsare.” “Amin Habibty.” Ya faɗa muka shigo ciki, sai da ya yi wanka sannan ya fito cin abinci, muna cikin ci ya ce. “Habibty mafarkin me kika yi ne?” “Uhm, Habiby bar ni dan Allah, bana son ma tunawa.” “Mara kyau ne? Ki faɗan na iya fassarar mafarki fa.” Na yi dariya sannan na ce. “Bana son ma fassarar abarta.” “Toh shikenan, Habibty kin san me?” Na girgiza kai kawai, ya yi gyaran murya sannan ya ce. “Ina so mu canja gida, sannan kuma ina son na biya miki aikin Hajji ke da Hajiya da Twins ɗinmu.” “Wow Ma sha Allah, Allah Ya saka da alheri, amma kai fa?” “Zanje Umara nan da sati biyu, ta wadatar tun da ko last year ma naje aikin Hajji ai.” “Eyh hakane kam, shi canja gidan fa? Ni ina ga wannan ai ya ishemu rayuwa daga ni sai kai, sai ‘yan ‘ya’yanmu.” Ya yi murmushi sannan ya ce. “Ina dai son canjawar Habibty, bamu san me Allah zai yi gaba ba.” Na yi shiru ina kallonsa, haka kawai na kasa gane ma’anar abinda ya faɗa, ni dai ina tsoron Turaki ya ƙara aure, bazan iya haɗa soyyyar da wata ba, bazan iya ba kwata kwata wallahi. “Habibty mene?” Na girgiza kai. “Kin tabbata?” “Eyh.” “Me zaki kai na barkar Islaha ne? Gobe suna.” “Wallahi kam, naso na siya musu wani abun kuma na sha’afa.” “To ko zamu fita yanzu? Sai mu biya mu tawo musu da shi ko?” “Eyh to, bari na shirya.” Na faɗa tare da miƙewa, na shiga ɗaki na sanya doguwar riga da mayafi na fito, muka shiga zagaya gari daga nan muka tawo musu da kayan barka, a daren har gidan Hajiya muka je amma Turaki ya ce kar na sanar da ita zancen na bari komai ya kammala, daga nan muka yo gida. Tun kafin mu shiga gidan na ce. ‘Yau ko da me zamu tarar dasu oho?.’ Turaki ya kalle ni ya ce. “Kina son sa damuwar su a ranki.” Na ce. “A’a, kawai na saba kwana biyun nan kullum dare, da tashin hankalinsu muke samar su.” “To mene naki?” Ya faɗa dai dai lokacin da motar ta shiga gidan, aikuwa dai ihun Islaha ne yau, sai dai na yau ya bambamta domin ihun kamar na ceton rai. “Ta kashe min yarinya!” Abinda ya shiga kunnenmu ni da Turaki a lokaci ɗaya kenan, na kalleshi na ce. “Kasan ko ɗazu sai da ta ce sai ta kashe yarinyar nan?” A tsorace ya ce. “Wannan wane irin rashin imani ne? Yanzu takashenta kenan?” “Ina nasani, yanzu fa muka shigo.” “Kinga Habibty mu wuce kawai, babu ruwanmu.” “Habiby maganar kisa fa ake, amma mu wuce a hakan?” “Eyh, ai yafi haɗari, da ace ceto take nema zamu iya zuwa, amma tun da aka ce ta kashe ta ai shikenan, mu bar su kawai.” Ba don raina ya so ba, na bi bayan Turaki muka shiga ciki, sai dai ko da muka shiga ma na kasa zaune na kasa tsaye, shi kan shi Turakin duk ya rasa nutsuwarsa, muna tsaye muka ji ana buga mana ƙofa, jikina har rawa yake na tashi na nufi ƙofar, ina buɗewa na ga Islaha tsaye tana kuka. “Islaha me ya faru?” “Ta kashe baby, ta kashe ta.” “Innullahi wa’inna illahir raji’un, a yaushe?” “Yanzu nan, ta danne ta da folo.” Ƙwalla na ji ta fara zuba a idona, na ce da Turaki. “Habiby fito ka ji, wai ta kashe musu yarinya ta danne ta fa fulo.” “Wallahi ta kashe ta.” Islaha ta faɗa tana ci gaba da kuka, nima na fara kukan har Turaki ya fito. “Kin sanar da babban yarinyar?” Islaha ta girgiza kai, ya ce. “Ki sanar da shi, yanzu.” Part ɗin su ta shiga ta ɗauko wayarta ta fito, muna tsaye ta kira, yana ɗagawa ta ce. “Yaya Sardauna, Bilkisu ta danne Baby har ta mutu.” “What! Gani nan.” Ya faɗa tare da kashe wayar, Turaki ya ce. “Ki yi haƙuri ki jira yazo, bari ni kuma na kira muku likita.” Ya faɗa tare da shiga ciki ya ɗauko wayarsa, can ‘yan mintina ya fito ya ce. “Gashinan zuwa, idan Allah Yasa da sauran numfashi gaba sai a ceto ta.” “Ai ta mutu ma, ta mutu ko numfashi ba ta yi.” “Innullahi wa’inna illahir raji’un, wane irin rashin imani Bilkisu take da shi?” Na faɗa ina kuka, sai kuma can na ce. “Ki kira Momynku mana.” Sai a lokacin ta tuna, ta tashi ta shiga ciki ta ɗauko wayarta ta fito, tana tsaye ta danna wa lambarsu kira, bugu ɗaya aka ɗauka. “Mommy, Bilkisu ta kashe Baby.” Ta cikin wayar Hajiya Falmata ta ce. “Ta kashe ta? Garin ya dan ubanta ba ta da hankali.” “Wallahi Mommy ta kashe ta.” “Gani nan zuwa.” Ita ma ta faɗa tare da kashe wayar, daidai lokacin kuma Sardauna ya shigo gidan, yana zuwa ya ce da Islaha. “Tana ina?” “Ciki.” Ta faɗa, ya wuce ta bi bayan shi. “Habibty mu koma.” “Haba Habiby, mutuwa fa. Duk wanda yazo yaga bama nan ai zai ce wani abun.” Ihun kukan Bilkisu mu ka ji yana tashi, Sardauna yana dukanta tana ihu. “Kika kashe ta, wallahi nima sai na kashe ki.” “Habiby ka yi masa magana, kar ya kashe ta fa.” “Matarsa ce ai.” “Ka yi haƙuri, amma idan ya kashe ta muma duka ba zamu tsira ba, kawai ya miƙa ta ga hukuma.” “Bana son shiga lamarin Sardauna, da bayanan tsaf zan wakilce shi, amma a gaban idonsa ina tsoro.” “Ka yi haƙuri.” Na faɗa. “Shikenan.” Ya faɗa tare da shiga ciki, na bi bayansa muka shiga, muna zuwa muka ga Sardauna yana dukan Bilkisu da ƙafa yana haurinta. “Wallahi yanda kika kashe ta kema sai na kashe ki.” Da sauri Turaki ya ƙarasa inda yake, ya sa hannu ya tare shi. “Idan ka kashe ta kaima kashe ka fa za ayi, ka nutsu ka miƙa ta ga hukuma mana.” “Haba Turaki, ‘yata fa ta kashe min, ita ta ce bazata haihu ba, na ƙyale ta to mene haɗin ta da ‘yata zata kashe?” “Hakane, amma idan ka kashe ta yanzu ribar me zaka samu? Ai ba kai aka ce ka hukunta ta ba, ka miƙa ta ga hakuma su zasu san yanda zasu yi da ita.” Daidai lokacin Hajiya Falmata da Alisha suka shigo, har da ma sauran ƙannen Islaha. Hajiya Falmata na shigowa ta ce. “Ina yarinyar? Ke kina me ta danne ta?” Nuna mata inda yarinyar ke kwnace na yi, sabida Islahan tana zaune a ƙasa tana kuka, daga gefe kuma Turaki riƙe da hannun Sardauna, Sardauna zai zubar da hawaye yake, ga Bilkisu a zube a ƙasa ta riƙe ciki, Alisha ta ce. “Tana ina ita sheɗaniyar, wallahi yau itama sai mun kashe ta.” Turaki ya ce. “Kar ku ɗau doka a hannunku, kuzo ku yi danasanj, a miƙa ta ga hukuma kawai.” “Aiko za a miƙa ta ga hukuma wallahi sai na ci ubanta.” Hjiya Falmata ta faɗa tana ƙarasowa inda Bilksu ke kwance, ta sa hannu ta fara ɗaka ma ta duka, jin zafin a hannunta ya sa ta sa takalmi ta fara dukanta. “Wallahi sai ankashe ki kema, muguwa kawai.” “Ki ƙara mata Mommy.” Wata cikin ƙannen Islaha ta faɗa, Alisha ta matso ita ma tasa ƙafa suka fara dukan Bilkisu wacce ta yi ƙasa da kanta, ita dai a ranta nasan murna take ta ci riba tun da ta kashe yarinyar, a raina na ce. “Bilksu baki ci riba ba, haƙƙin rai ai babbar masifa ce.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (6) Sai da suka yi wa Bilkisu Lilis, sannan suka ɗauki babyn da Islaha suka tafi, Hajiya Falmata ta ce. “Wannan auren ya ƙare, daman ni da yarinyar na amince aka yi shi, yanzu tun da babu ita komai ya ƙare, zama da Sardauna ai babbar masifa ce, wannan mutuwar ma haƙƙi ne ke bibiyarsa.” Suna tafiya muma muka fita, muka bar Sardauna da Bilkisu su kaɗai a su ci kansu. Washe gari a gidansu Islaha aka yi duk abinda yakamata, sai da na tashi daga aiki sannan na biya na yi mata gaisuwa, Hajiya Falmata ta tambayeni wai naga an kama Bilkisu, na ce ni dai sanda na fito ban gani ba, amma bansaniba ko bayan fita. “Shi ya sa ni cansuƙarata, daman duk tsuntsun da ya janyo ruwa shi ruwan kan doka, Sardauna shi ya jajibo ma kansa masifa, kuma shi ka ɗai za ta ci, wannan yarinyar ai babu alheri a tare da ita.” Ni dai bance da su komai ba, har dare sannan na koma gida, a harbar gidan namu na tarar da Sardauna, kallo ɗaya na yi masa na ɗauke kai, amma tabbas a wannan kallon ɗayan naga abun mamaki, fuskarsa ta yi wani irin ja, idanunsa sun hautsine, duk ya fita hayyacinsa kamar ba Sardauna ba, ya jagwale ya fita a hayyacinsa. Na ɗauke kai na shiga part ɗinmu, ina shiga na yi sallar la’asar na shiga kicin, ina tsaka da aiki na ji ana yi mij bugu, sai da na ji tsoro kafin na buɗe sabida ƙofar. Sardauna ne idonsa cike da hawaye, ya kalli ni na ɗauke kaina gefe na ce. “Lafiya?” “Nana.” Ya kira sunana cikin wata murya me karyar da zuciya, jin muryaf kaɗai ya isa ya tabbatar ma Sardauna yana cikin wani hali na damuwa. “Na’am.” “Nana, kinga yanda rayuwa ta yi da ni ko? Nana komai ya juye min, Bilkisu da naso na aura ta zame min ƙarfin ƙafa, komai ya zame min baƙi cikin ƙanƙanin lokaci, bana jin daɗin komai na rayuwar nan, Nana wallahi naga rayuwa, bana son komai na rayuwa, Nana dan Allah ki yafe min dan Allah.” Sai da na goge wata ƙwalla da ta maƙale a idona, sannan na ce. “Daman ita rayuwa haka take Sardauna, ka yi haƙuri babu wani abu da zai dauwama, wannan yanayin da kake ciki shima zai wuce, zai tafi kamar ba ka yi ba, karka karaya ka ci gaba da zama jarumi kamar yanda kake a ko da yaushe, ka ci gaba da saka ran ganin wasu abubuwan ma, domin idan Allah ya tashi jarabtarka, abubuwa ne suke zuwar maka daga wannan sai wannan, sai ka ji kamar ma kai kaɗai ne a kake fuskantar damuwa duniyar.” Ina faɗin haka na koma ciki, ina shiga na fashe da kuka, yanayin Sardauna ya taɓa min zuciya, haka rayuwa take babu wani abu tabbatacce, komai fararre ne kuma ƙararre. “Allah Ka yi mana mai kyau.” Na faɗa ina komawa cikin ɗin, magangunun da Sardauna ya faɗa suka dinga dawomin cikin raina akai akai, na rasa abinda ke min daɗi, har cikin zuciyata nake tausayawa Sardauna, sai dai kuma idan na tuna cewa akwai sauran rina aka ba, sai na ga Sardauna bai ma fahimci komai ba na rayuwa, idan na tuna nima ina da nawa ƙalubalen na rashin haihuwa, sai naga ma bani da lokacin da zan tausayawa Sardauna, gwanda na tausayawa kaina. Ji na yi an a buɗe ƙofar nasan Turaki ne, sabida yanzu ya ɗauki spare key sabida ranar da yadawo ina bacci. “Habibty! Habibty.” A raina na ce. ‘Yau ina sallamar.’ Sai da na fito na ce. “Lafiya? Ko sallama babu.” “Na yi sallama mana, me wannan yake yi anan zaune?” “Waye kuma?” Na faɗa ina duba bayansa. “Sardauna mana, gashinan a tsugunne a bakin ƙofa kamar zai yi bara.” “Ƙofar mu wai? Ko can tasu?” “Idan tasu ne mene damuwata? Tamu.” “To Habiby nima bana ce ba, amma da ka yi masa magana.” “Hhhm, nifa hankalina bai kwanta da Sardauna ba Habibty gaskiyya.” “Can ya ƙarata, Habiby da ina so gobe mu yi walima anan ta kawo Twins, amma ya ka gani.” “Fara bani abinci sai mu yi magana.” Sai da na haɗa masa abincin ya gama ci, sannan muka dawo kan kujera muka zauna ya kalleni ya ce. “Habibty taron zaiyu gobe kuwa? Ko mu bari sai jibi bayan sun kwana ɗaya anan, gobe zan tura event planner ku tsara komai, da masu decoration ayi mana komai, Habibty har irin wannan banner din asa hoton me jigo da mijinta da ‘ya’yan za ayi mana, sannan ayi set na abokai na da ƙawayenki, duk shagalin da kika hanamu yi da auren mu sai munyi, dan haka duk wata ƙawarki ki faɗa mata, bari nasa yanzu ayi mana invitition card mu fara turawa.” “To hakan ma ya yi Habiby, an gode sosai.” “Wane suna za a sa mana jikin card ɗin.” Na yi dariya sannan na ce. “Asa komai ma.” “A’a bari asa, Alhaji Abubakar Ta Ambo (Turaki) angon Rawasiya.” Na girgiza kai na ce. “Kar asamin wata Rawasiya, asamin Hajiya Nana matar Turaki ikon Allah.” Shima ya yi dariya, haka muka yi ta hira muna da dariya, ƙarshe da aka fito da kati mai kyau, a tare muka sa a status ni da Turaki, aikuwa cikin ƙanƙanin lokaci ‘yan uwa suka fara resharing, kati ya fara zagaye ko ina, ƙawayena duk na bi na tura musu a dare. Washe gari Turaki bai fita ba sabida kawo twins, muna gida ya kira event planner ya zo, ya kira mai decoration da masu girki kowa aka cika shi da kuɗi, ɗakinsu Twins ya sha gyara, ya kuma cika da kayan ado, dake ɗaki biyu ne na so, dana baccinsu da na kayan wasan su. Ƙarfe huɗu daidai Yay Ridwan yazo gidan, shi kaɗai ba mamansu Twins ɗin, gaba ɗaya sai jikina ya yi sanyi ko tana wane hali ne, a take na ɗau waya na kira ta. Ban bari mun gaisa ba na ce. “Maman twins yana ga bake aka zo?” Ta yi dariya, sannan ta ce. “Sabida kar su yu kuka shi ya sa, amma babu wani abu.” “Dan Allah idan baki ji dadi ba ki yi haƙuri, banga amfani ni na yi farin ciki ba ke kuma kina cikin ɓacin ran rabaki da yaran ki.” “Babu komai fa, a yanzu haka nasami wani cikin har ya fi wata uku.” “Kai Ma sha Allah, Allah Ya raba lafiya, na gode.” Daga haka na kashe wayar na fito, na tarar da Yaya Ridwan da Turaki suna ta hira, nima na shiga muka sha hira, anan ne Turaki yake faɗa masa yana so shi ya ɗauki Hajiya zai haɗa shi da wani yakaita inda za ayi mata passpord, sabida ya biya mata aikin Hajji, da ni da twins. Yaya Ridwan ya ji daɗi sosai da sosai, kuma ya yi masa godiya. Twins tun da na kaisu ɗakinsu na wasa suka zauna, mussaman da suka ga ɗakin cike da hotonansu, sabida yaran suna da matuƙar wayo sai suka sake har Yaya Ridwan ya zo tafiya, ya shiga yaga yanda suke ta wasa hankalinsu a kwance ya tafi ya barsu. Yana tafiya muka shiga ɗakin ni da Turaki, muka fara wasa da su suma suna wasa damu, sai na ji duka duniya ta yi min daidai, farin ciki ya mamayeni fiye da ko yaushe, haka shima Turaki kana ganinsa yana cikin fara’a, haka har dare twims ba su ne mi iyayensu ba, dan sun ce. “Mamma.” Zan ce. “Na’am.” Sai su yi shiru, ko idan suka ce. “Papa.” Nanma Turaki ya ce. “Na’am.” Wani abin daɗin ma sun yi cin abinci, da muka zo cin abincin dare suna ta wasa jikin Turaki kowa aka bashi na shi, da kansu suke shan custard din, amma suna ɓata jikinsu, sai wajen tara suka yi bacci, kowacce aka kaita gadonta sannan muma muka kwanta, Turaki ya ce. “Habibty, yau kina cikin farin ciki ko? Nima haka.” “Eyy Habiby, daman haka yara suke da daɗi?” “Haka suke mana, gashin yanzu kin samu ko? Allah Yasa ƙarshen damuwarki kenan.” “Amin Habiby, na gode da ƙwarin gwiwarka.” “Babu komai Habibty, ki sani ni Abubakar Turaki ina matuƙar ƙaunarki, wallahi Habibty ba ni da bakin da zan iya bayyana miki adadin son da nake miki, ina jinki cikin kowanne numfashi na, ina wajen aiki ke, ina tare dake ke, ina bacci ke, Habibty ban taɓa jin kin isheni ba ko na minti ɗaya, a kullum muradin zuciyata ke ce, ina sonki, ina ƙaunarki wallahi Habibty, rayuwata idan bake mutuwa ce.” “Nima haka, ina son ka Habiby, ina ƙaunarka, Allah Ya barmin kai har abada.” “Amin Habibty.” Ya faɗa tare da janyoni jikinsa. Washe gari da safe ƙarfe takwas masu decoration suka zo, ta wajen bayan part ɗin mu zaayi, inda ba za a taɓa ɓangaren su Sardauna ba, sai da suka share wajen ya yi kyau sannan suka hau decoration suna gyara wajen, ni kuma na shiga na tashu Twins. A tare muka yi musu wanka da Turaki, muka shirya su, suka koma ɗakinsu suka hau wasa, muma muka je muka shirya. Wajen ƙarfe goma da rabi masu decoration suka gama komai suka tafi, wajen ya yi kyau sosai da sosai. Wajen ƙarfe sha biyu Yaya Radiya ta zo ita da yaranta, sun yu kyau sun canja abinsu, ina yabon yanda suka canja, itama tana yabon yanda na canja. “Nana dole mu sake godewa Allah, burin mu duk sun cika, aure dai gashi kinyi, kina rayuwa cikin jindaɗi.” “Wallahi Yaya, a yanzu dukkanmu hankalinmu a kwance, Allah Ya amsa addu’ar Alhaji.” “Hakane Nana, ni dai dan Allah ki ci gaba da yin biyayya ga Turaki, ji yanda yake son komai kike so, yanzu ji ɗakin yaran nan, ji abinda yake musu kamar shi ya haifesu, ga Ridwan ya ce min, wai Ya biyawa Hajiya dake da twins, aikin Hajji “ “Wallahi Yaya.” “Allah Ya ƙara masa arziƙi.” “Amin Ya Allah, shi Umarar azumi zai je, muku babbar sallah.” “Ai abun kamar yau ne Nana, Allah dai ya saka.” “Amin amin.” Muna zauna Yaya Rumaisa ta zo, tare da matar Ra’is na ce. “Wai Ra’is dai bazai zo gida na ba.” Ta yi dariya sannan ta ce. “Zuwa na mussaman zai yi ya ce.” “Uhm.” Na faɗa, muna nan zaune event planner yazo, suka fara tsara wajen da yanda komai zai tafi a tsari a wajen, can kuma mutane suka fara zuwa, mai kwalliya ma tazo ta tsantsaramin kwalliya, har da su Twins. 04:30pm Harabar gidanmu ta cika ta batse da mutane, ‘yan uwa da abokan arziƙi ta ko ina, wajen ya tsaru yanda event planner ɗin suka yi ƙoƙari akan haka, ko ina na wulga ‘yan uwana ne, da ‘yan uwan Turaki, ƙawayena da abokansa. Ni da shi muna zaune sai twins suma a zaune, abokan Turaki sai kuɗi suke zubawa, wannan ya fito ya ce ya bawa Twins 2million, wannan ya ce 5million, har da wanda ya basu 15Million shine yafi kowa, sai kuma masu basu gold, haka aka yi ta abu, tun ina lissafa miliyoyi har na gaji na daina, abinci anci, an sha, Twins sun ga sabuwar rayuwa kowanne su sai farin ciki yake. Haka ka aka tashi daga taro kowa ya watsa muka zauna ni da Turaki muka fara tattaunawa akan abinda abokansa su ka yi, na ce. “Habiby, abokanka haka suke daman?” “Ai Habibty mun saba, duk wanda aka yiwa haihuwa haka muke yi, yanzu ko wasu aka ƙara haifa haka zaayi musu, amma na farko sunfi mora.” Na girgiza kai na ce. “Chaɓ.” “Habibty yanzu kuɗin ya kusa 60million, ina tunanin ko asiya musu filaye na 20/20 million, ragowar kuma abawa Yaya Ridwan.” “Ai ba zai amsa ba, zai ga kamar mun nuna ba ‘ya’yanmu ba ne.” “To Habibty me za mu yi da su? Idan muka cire musu 40M a ciki, ai yawadatar.” “To Habiby ko za a biya musu Umarar azumi shi da matarsa, ace da kuɗin da aka samu ne.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (7). Cikin kwana biyu Turaki ya siyawa Twins manya manyan filaye guda biyu na kimanin miliyan 20 kowacce ɗayansu, sannan kuma ya fara ƙoƙarin biyawa Yaya Ridwan da matarsa Umarar azumi, Twins basu bamu wahala ba wajen zama damu, sun saba da mu cikin ƙanƙanin lokaci, sun kuma shiga ran mu duka. Suna kirana da Maamah, suna kiran Turaki da Papah, ranar da naje dasu gidansu Turaki basu sami wata tsangwama ba, kowa ya karɓe su hannu biyu, kuma na ji daɗin hakan sosai. Cikin ƙanƙanin lokaci aka sama musu mai kula da su, inda aike kai su gidan idan zan fita, idan na dawo kuma na biya na ɗauko su. Mun fara shimfiɗa rayuwa cikin farin ciki, hankali kwance. A ɓangaren Sardauna dai Islaha ba ta dawo ba, sabida Hajiya Falmata ta dage kan Islaha baza ta dawo ba, har sai Sardauna ya ɗau mataki akan Bilkisu, abinda ya gagare shi kenan, a yanzu maganar ma ta mutu har wajen su Big Daddy, a raina na ce. ‘Idan Bilkisu ba ta yi haka ba ai ba ta cika mai bin malamai ba.’ Shiru magana kowa ya manta da ita, ta ci gaba da rayuwa da Sardauna cikin faɗa, kullum cikin tashin hankali gashi yawo ta ci gaba ba zama, abun nata ma ya fara gaba dan sai ta kwana acan ma inda ta tafi yawon, ta mayar da Sardauna sallau, ba abinda ya isa ya yi mata, sai dai mita su yi ta ɗaga murya. Nikam na mai da hankali kan kula da ‘ya’yana da kuma aikina, shine abinda ke gabana yanzu, sai kuma kula da Turaki. Lokacin da aka sanar da Yaya Ridwan da matarsa zancen tafiyar Umarar azumi har da ƙwallarsu ta jin daɗi, haka ma Hajiya sai a lokacin aka sanar da ita zuwan mu aikin Hajji, in sha Allah. Cikin ikon Allah watan azumi ya gabato, Turaki zai tafi goma ga azumi ya dawo biyu ga Sallah, su Yaya Ridwan kuma zasu tafi farkon azumi ne. Shirye shiryen azumi sun yi nisa, na roƙi Turaki akan ya barni na sami masu aiki da zasu dinga min kunu da ƙosai na sadaka, idan anyi sai a ɗauka a fita da shi can ayi sadaka, ba tare da ya yi wani musu ba ya amince, har ya bada wasu kuɗaɗen shima a matsayin na shi gudumawar, nasa aka sama min masu aiki mutum uku. Cikin ikon Allah aka fara azumi ranar talata, a ranar mu ka yi abincin sadakar mu aka fita da shi ya ƙare tas, washe gari mu ka ƙara yawan shi sabida matar ta ce min akwai mutane marasa ƙarfi da yawa daga wajen unguwar. Ranar azumi na huɗu Yaya Ridwan da matarsa suka ta shi, ranar azumi na shida Yaya Rumaisa ma da mijinta suka ta shi, wannan shekara sai ta zama shekara mafi farin ciki ga ‘yan gidanmu, har mutum biyu sun tafi saudiyya kuma ana saka ran nida Hajiya zamuje aikin Hajji. Ranar da aka yi azumi na goma Turaki ya tashi, gida ya zama daga ni sai Twins, har da kukansu da muka dawo, aka ci gaba da abin sadaka har azumi ya ƙare aka yi sallah Turaki ya dawo, tun tafiyar Turaki na yi ƙoƙari wajen ɗauke kai daga al’amarin Sardauna da Bilkisu, kamar basa gidan haka na mayar da su, kuma suma sun rage abinda suke yi, dan shima Sardauna ya tafi saudiyya ƙarshen azumi. Haka aka yi bikin sallah cikin farin ciki, a lokacin bikin sallah matar Ra’is ta sauka inda ta sami ɗa namiji, an sha taron suna anyi farin ciki, inda aka yi wa Alhaji takwara aka sanyawa babyn sunan Alhaji, ranar suna na a gajiye tilas na dawo, ga Turaku ya maida hankali akan gina sabon gidan da zamu koma, wajen ƙarfe tara na dare na dawo gidan, ina sauka a mota na ga ‘yan sanda a harabar gidan namu, da sauri na tura su Twins cikin part ɗin mu, ‘yan sanda suka ƙaraso inda nake. “Ranki ya daɗe barka da dawowa.” “Barka dai, wa kuke nema haka?” Na faɗa fuskata da alamar tsoro, danni a rayuwata ma magana bata taɓa haɗamu da ‘yan sanda ba. “Muna neman matar gidan nan ne?” “Ni ce matar dake zuane a wannan part ɗin.” Na faɗa ina nuna part ɗinmu, sanna na ce. “Matar dake zaune a wancan part ɗin kuma, tana ciki ko bata nan ni ban sani ba, wacce kuke nema?” “Bilkisu.” Na nuna musu part ɗin na ce. “Ita ce me nan, ni sunana Nana.” “Ai mun buga tun ɗazu ba a buɗe ba.” “Eyh da yake ba zama take yi ba, babu tabbacin ta nan, sai dai kujirata tun da ba kwana take a can ba.” “A’a idan ba ta zo ba zamu tafi dake.” Na yi musu wani kallo, sannan na ce. “Akan wane dsalili kenan?” “Akan dalilin neman ta dake ayi, kun ɓoye me laifi.” “Ina ba a gidan na zo na sameku ba? Ta ina zan ɓoye ta to? Ku jira ko ita ko mijinta wani na zuwa.” “Mu DSS ne, muna bincike ne akanta, sabida an zargin ta da harkar dillanci ƙwaya.” “Dillancin ƙwaya kuma?” Nai maimaita a tsorace, sannan na ce. “Ita Bilkisun? Lallai.” “Eyh ita, to kinga wannan case din babbane. Idan babu ita za a iya tafiya dake?” “Malam ni a wa? Kishiyata ce ko me? Nifa bani da wata akaƙa da ita, mijina da mijinta ke da alaƙa, dan haka ni bani da wani alaƙa da ita.” “Duk haka, kinsan inda za a same ta.” “Tare muke yawon ko me? Ni zan shiga ciki, kuna nan tsaye mijinta zai shigo, zaku ganshi wani ja kamar ƙosai.” Ina faɗin haka na shige ciki, ina mamakin yanda mutanen nan suke neman shafa min kashi awaki, ina shiga na kira Turaki a waya, yana ɗagawa na ce. “Habiby da matsala gida.” “Me ya faru Habibty?” “Jami’an DSS ne a gidanmu, wai zasu tafi dani sabida suna neman Bilkisu basu ganta ba.” “To ke awa? Kar su kuskura, ki faɗa musu na ce idan suka tafi dake duk sai na yi shari’a da su, gani nan zuwa.” Daidai lokacin na ji ana buga min ƙofa, aikuwa na yi kamar ba na ji naƙi buɗewa, suna tsaka da bugun na ji Turaki yana ce musu. “Bayin Allah lafiya?” Sai a lokacin na taso na buɗe ƙofar, ina ganin shi na ce. “Sai bugu suke min, na nuna musu part ɗin Bilkisu amma sunki haƙura.” “Ina tambayar ku lafiya, kunzo kuna tayarwa da matata hankali kuma kunyi shiru.” “Mu jami’an DSS ne, munzo ne muna neman Bilkisu.” “Ga can, nan ne part ɗinta, mijinta da ita duk basa nan, dan haka kar ku zo nan ku ɗaga mana hankali.” “A tsarin ƙa’idar aiki idan akan wannan case ɗin ne ana kama waɗan da ke kusa da mai laifi.” “Wanda ke kusa da ita ai bai wuce iyayenta ba ko mijinta, mu da zama ya haɗa mu kuma mene a tsakanin mu?” “Ka yi haƙuri yallaɓai, amma dole zamu tafi da wani cikinku.” “Babu wanda zaku tafi da shi, nina jami’i ne.” Turaki ya faɗa yana ɗauko musu id card ɗinsa, sannan ya ce. “Akan wannan abun zan iya shigar da ƙarar ku, bama ku kaɗai ba, har da hukumar ku.” Shiru suka yi, a daidai lokacin kuma Sardauna ya dawo, Turaki ya ce. “Ga mijinta nan.” Yana faɗin haka ya kama hannuna muka shige, muna shiga ya ce. “Wane lefe ne ta yi?” “Wai dilal ƙwaya ce.” “Ƙwaya kuma? Ita Bilkisun?” Na gyaɗa kai, sannan na ce. “Ita fa, ni na rasa gane kan matar nan, mugayen ayyukunta sunyi yawa, mene haɗin ta da dillanci ƙawaya tana mace, tana matar aure dan Allah?” “Sardauna idan baiyi wasa ba, Bilkisu sai ta ja masa rayuwa a gidan yari,” Bugu ƙofar mu aka fara yi, hakan ya sa Turaki ya fita ni kuma na bi bayansa. “Turaku ka ji wai tafiya zasuyi da ni, ka yi musu magana dan Allah.” Sai da Turaki ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, sannan ya ce. “Ba shine kuke nema ba, matarsa ce.” “Mun sani, amma ai taƙi dawowa.” “Shima ta gagare shi, bai isa ya sa ta ko yahana ta ba, amma ku yi haƙuri ku ƙyaleshi, idan ta dawo zai kawo ta.” “To, amma muna so ya bi mu can ya sa hannu.” “Kuje zan kawo shi yanzu.” Turaki ya faɗa, sannan ya kalle ni ya ce. “Habibty, miƙomin key ɗina.” Na shiga ciki na bashi key ɗin, sai da notarsu ta fita daga gidan sannan na koma ciki, sai dai ba afi minti uku da fitar su ba, motar Bilkisu ta shigo gidan, ko a lokacin goma na dare ta kusa, wayata na ɗauka na yi wa Turaki text na ce. ‘Ga Bilkisu ta dawo.’ Ya yi min reply da okay. Kasancewar basu yi nisa ba ya sa suka dawo, dan ta zarar ba tafi minti biyar ba suka fara hon, ina tsaye bakin taga na ga sun fito dasu da ma’aikatan, abinda yake bureni da Turaki yanda baya ɗaukan al’amarin mutane, yana fitowa daga mota ya nufo part ɗin mu, maimakojn ya je can ya ga ƙwal uwar daka, amma ya zaɓi ya dawo nan ba ruwansa, ina ganin zai shigo na koma kan kujera na zauna, yana shigowa na miƙe na ce. “Kun same ta?” “Ni bansani ba, na dai dawo kawai.” Na buɗe baki zanyi magana, muka jiyo muryar Bilkisu tana faɗin. “Me na yi da zaku kamani? Kai Sardauna kaine ka kai ƙara ta ko me? To wallahi ba inda zani.” Ɗayan cikin ma’aikatan ya ce. “Mu jami’an DSS ne, dan haka bincike ne ya biyo ta kanki, an sami sunan a cikin gidan da ake dillanci ƙwaya, kuma akwai tabbaccin cewa kullum kina zuwa gidan.” “A’a malam kar ka yi min sharri, abinda ke kaini gidan ai daban ne, dan haka ban san ana wani dillanci ƙawaya ba, dan haka ka rabu da ni kawai, babu inda zani, ko ita Hajiya Zinariyar wallahi ba ta isa ta yi min sharri ba.” “Idan anje can sai ki yi bayani, amma anan kam babu abinda zamu fahimta, dan haka kizo mu wuce, kuma kaima ka biyo mu.” Kallon Turaki na yi na ce. “Amma yakamata kaima ka je fa, babu wanda zai karɓi uzirinka tin da kana gidan, ace an tafi da ɗan uwanka kuma baka yi komai akai ba, alhalin kuna zaune a gida ɗaya.” “Abinda nake tunani kenan, amma bana son shiga lamarim Sardauna, mussaman a yanzu da nagane babu wata alaƙa a tsakanina da shi, daman can ina haƙuri da shi ne, sabida ina kallonsa a matsayin ɗan uwana, amɓa yanzu duk na ji komai ya fita a kaina dana gane gsky.” “Duk da haka Habiby, ba a taɓa canjawa tuwo suna, alaƙar ka kai da Sardauna tana nan a matsayinta, babu yanda za ayi, Sardauna naku ne har abada.” “Shikenan Habibty zo muje tare.” “Twins fa?” “Ai basa tashin dare, kawai muje.” Mayafina na shiga na ɗauka na fito, muka tafi a mota ɗaya ni da Turaki da Sardauna, karo na farko a rayuwa kenan, su biyu suna gaba ni kuma ina baya a haka muka ƙarasa ofishin, wanda ake ta hada hada kamatr tsakar rana. A lokacin da muka je anfito da sauran, matane manyan hajiyoyi, kina ganinsu kin ga masu faɗa a ji, duk kansu fatarsu har wani sheƙi take yi, duk jikinsu gwala gwalai ne suka yi ado dasu, ofishin ya zama kamar wajen biki, ana fito da su Bilkisu ta ce. “Hajiya zinariya sharri zaku yi min, nasan kuna harkar ƙwaya a gidan nan?” “Kinsani mana, ai ba karen da ba bara ba, dan haka ki shigo nan mu jeru, idan ta kama ma mu buga harka anan, tun da akwai kuɗina akanki.” “Ke a haka zaki yi harka da ita? Kina ji Turai tana ɗauke da ciwo, kuma Turan jiya suka rabu da ita , shine zaki nemawa kanki, ai kwai ta biyaki kuɗinki.” Wata cikin matan ta faɗa, kana ganinsu ka ga ‘yan duniya, babu tsoro babu mutunci a tare da su. Legendspen 0812955391 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (8). “Nan ba wajen mai da magana ba ne, abinda yake gaban mu shi zamu yi, nan duk wakilanku ne zasu saka hannu.” Wani jami’a wajen ya faɗa, nan aka bawa kowa ya sa hannu har da Sardauna, sai bayan sungama sa hannu, wani babban ma’aika ci ya ce. “Waɗan nan matan sun kasance ‘yan duniya na gaske, suna da gida mai zaman kansa, gidan da suke kwallci suke harkar maɗigo.” Ji na yi kaina ya wani buga, ‘yanzu abinda Bilkisu ke yi kenan?’ Na tambayi kaina. Mutumin ya ci gaba da cewa. “Ba iya abun da suka saba suke yi ba, a cikin gidan suna yin harkar dillancin ƙwaya, dan haka za a riƙe su duka anan, har sai an kammala bincike akam case ɗin.” “Wallahi ranka ya daɗe babu ruwana, yau ne zuwa na gidan na farko, Hajiya zinariya ce ta gayyace ni, ita ta ce nazo amma bansan suna harkar ƙwaya ba, Hajiya zinariya dan Allah ki faɗa musu gaskiyya, wallahi a gida ba a san na fito ba.” Wata matashiyar yarinya ta faɗa tana kuka, Hajiya zinariya ta yi wani murmushi sannan ta ce. “Ai kowa ya mutu wallahi, ƙarshen bariki kenan.” “Amma Zinariya kin cucemu, wallahi ke kaɗai kike harkar ƙwaya a gidan nan, mu nan duk ba ma yi, wallahi mugunta ta shirya mana.” Wata hamshaƙiyar mata ta faɗa, jami’in ya ce. “Koma mene ne bincike zai bayyana, mu anan akan iya harkar ƙwaya zamuyi binciken mu, sauran maɗigo da kuke tsakaninku da ubangiji ne.” “Ni yanzu ciwon da na kwasa ma kaɗai ya isheni, na shiga uku na lalace.” Wata mata ta faɗa, tana kuka tana sa hannunta cikin siket ɗinta tana sosawa, a take na runtse ido na na kawar da shi, sai a lokacin Bilkisu ta fashe da kuka. “Wallahi Turai ta cuce ni, ta shafa min cuta.” “Ko dai kin cuceta kin shafa mata, ai daman Hajiyar Saudiyan nan da ta zo, ku ka yi kwanakin nan kowa bai yarda da ita ba, amma ke kika fi kowa harka kika amice mata, wallahi Bilkisu idan har kin shafin min wannn ciwon ƙurajen sai kinyi dana-sani.” “Aina zata yi dana sani, wallahi duk wanu hukunci da za ayi min akan ƙwaya tare za ayi mana daku, mazajen ku ne zasuyi dana-sani sabida kun goga musu masifa.” Sai a lokacin na kalli Sardauna, na tuna ɗazu tabbas naga yana sa hannu a jikinsa, har yake juya baya sabida ka da wani yagansa, gaba ɗaya a yanzu idonsa ma ya cika da hawaye. “Waye mijin Bilkisu a cikinku? To wallahi kasanu Bilkisu ‘yar maɗigo ce, bata da aiki sai bin mata, gashinaj yanzu ta kwaso cuta duk ta shafawa matan da suke gidan namu, kuma kaima da kake mijinta tabbas ta shafa ma, ko ban faɗa ba nasan kana ganin ƙuraje a jikinka masu ruwa, to cuta ce ta kwaso ta shafa maka, daman ƙarshen mace mai maɗigo kenan, dukkan mu nan mun san ƙarshen mu bazai yi kyau ba, tun da muka zaɓi saɓon ubangiji, muka take sani.” Ƙoƙarin faɗuwa Sardauna ya yi, Turaki ya yi saurin riƙoshi. ‘wannan wace irin masifa ce, ace matarka ta sunna ta goga ma cuta? Hasbunallahu wani’imal wakil, ba za banza ba Bilksu ba ta zama, ba a bazan ba taƙi ta haihu, ta zaɓi saɓom ubangiji, aiki mafi muni shine ta zaɓa, gashi yanzu ta faɗa komar cuta da kuma sharrin siyar da ƙwaya.’ Abinda na faɗa a raina kenan. “Bilkisu…. Bilkisu Allah Ya isa tsakanina da ke, Allah Ya isa, bazan yafe miki ba, kin cutar da ni, kin cutar da rayuwata.” “Nima ai ka cutar dani? Sardauna kaima ai bin mata kake, kana bin mata da aurenka, har da haihuwa, to mene dan na yi abinda na yi, cuta ce kuma zamu warke ba zamu mutu ba akanta, kawai ina zaman ƙalau kasa na ɗau haƙƙin Nana, kasa na shiga rayuwarta na cutar da ita, kafin na aureka ai ban maɗigo, amma haƙƙin Nana ya sa na fara sha’awar mata, kuma na shiga cikin harkar har na zama gogaggiya, gashi na ɗauko mana sakamakon mu, wannan farashin haƙƙi ne kuma gashi muna biya Sardauna, kaina ka ja mana komai, kai ne wallahi, kuma bazan yafe maka ba.” Kukan ya ci gaba da yi, a lokacin jami’an suka ce. “Zaku iya tafiya, gobe ku dawo.” “Waye zai dawo? Ku cire ni akan lamarin ta, babu ni babu ita, Allah Ya isa da saninki da na yi Bilkisu, na tsane ki wallahi, kin cutar da rayuwata.” “Mun cutar da raywuar juna dai, nima a yawon bin matanka nasan wace cuta kasha fa min?” “Bilkisu na sake ki Saki Uku.” “Wallahi ban sako ba, ni dai kai mutu ka raba, zina kake yi, maɗigo nake yi, cikin shege ka yi wa wata har da ‘ya, cuta na ɗauko na shafa maka, haƙƙin wata ne akaina, kaima haƙƙinta ne akan ka, Wallahi Sardauna baka ga komai ba, kasan me? Ka je ka tambaya mene asalinka? Waye ubanka? Wace uwarka? Mene alaƙar ka da wannan familyn da kake tun ƙawo da su, Sardauna kai ba kowa ba ne face mitsiyaci, kai ba kowa ba ne face talaka, ɗan masu aiki, nasan komai akan ka, nasan baka da alaƙa da wannan gidan, idan kasani kasani, idan baka sani ba yau kasani.” Wani irin zafin nama Sardauna ya yi ya cakumi Bilkisu ya fara duka, tunu aka yo kansa ana riƙe shi amma ina bai ji, wani ihu da ya yi duk masu riƙe shi sai dai suka firgita suka yi baya, ya jawp Bilkisu ya fara taka ta da ƙafa, yana ball da ita, tun tana ihu har ta fara kakari, ma’aikatan gaba ɗaya suka yo kanshi suns riƙe shi, amma Sardauna ya cije, ya fusata kamar wani tsohon zaki, da ƙyar aka ɗauke Bilkisu, wadda ina da kyakywan tabbacin ta karye hannu da ƙafa, Turaki ya riƙe shi yana faɗin. “Mene kake yi haka Sardauna, idan ka kashe ta fa? Ka nustu mana. “Kana jin abinda take faɗa, kana ganin abinda ta yi min.” “To ka barta mana, a yanzu halin da take ciki a rayuwa zata koya mata darasi, kana gani fa ko nadamar abinda ta yi ba tai ba, har tinƙawo take tana faɗa, dan haka ka barta mana, duniya zata tafiyar da ita hanya madaidaiciya.” “Karku fita ku tsaya.” Wani ma’aikaci ya faɗa, tsayawa muka yi baki ɗayanmu, a lokacin aka fito da Bilkisu tana wani irin kakari, ga jini yana zuba daga jikinta me ɗoyi. “Wannan ku ɗauke ta ku kaita asibiti, an cire ta daga case ɗin gaba ɗaya.” A take Hajiya Zinariya ta ce. “Ai wallahi a’a, Bilkisun ɗin ita ce fa take amso ƙwayar, kawai akai ta ta yi jinya an yanke mana hukuncin mu anan.” “Kin tabbata ita ce?” Wani ya tambyae ta, ta gyaɗa kai. “Na tabbatata ita ce.” “Shikenan you can go, idan wani abu ya sameta dai zamu nemeka, idan kuma ta miƙe shikenan tin da ka sake ta har saki uku, ka raba komai tsakaninku, Allah Ya saka ma.” Babban jami’in ya faɗa, ita kuma aka sa ta a wata mota aka yi asbiti da ita, a motar muka koma shiru ba wanda ya ce komai sai sautin kukan Sardauna kawai, yanayi yana jan hanci abun tausayi. “Turaki.” Sardauna ya faɗa, Turaki ya kalle shi ya ce. “Na’am.” “Dagaske ne abinda Bilkisu ta faɗa? Na tuna ranar da aka je wannan zaman Momy ta ce halin uwata na yi, wai barewa ba ta yi gudu ɗanta ya yi rarrafe, tun a tasowa ta na san ni ba ɗan Mommy ba ne, akwai lokacin da muka je bikin a danginta na ji suna zagi na, suna cemata sannunta da riƙe ɗan riƙo, na yi tunanin Daddy mahaifina ne, mahaifiyata ta rasu shine na zauna a hannu kishiyarta, shi ya sa a lokacin ma da ta ce barewa ba ta yi gudu ɗan ta ya yi rarrafe ba na yi tunanin abinda take nufi kenan, amma a yanzu kalman Bilkisu sun tsaya min a rai, dan Allah ka faɗa min gaskiyyar komai.” “Sardauna, nima banda masaniya akan komai, amma ka tambaye su Big Daddy zasu iya sanar da kai, ko su granny, amma mene amfanin binciken? Idan ma ba haka ba ne idan kasani me zai canja? Zaka je ka nemi iyayenka na asali ne? Ko zaka bar gidan Ta Ambo? Sardauna abinda ya wuce ya wuce, ka fuskanci abinda zai zo maka gaba, rayuwar ka ka gina ta akan ginin son zuciya da son rai, ka tsani kowa ka raina kowa, a yanzu sauran lokacin da kake da shi ka yi amfani da shi ka gyara abinda ya rage maka, cuta ce aka ce jikinka, ya kamata ka mai da hankali ga lafiyarka, ka gyara komai, ka shimfiɗa sabuwar rayuwa da ragowar lokacin da ya rage maka, binciken da zaka yi ba lallai ya haifar maka da ɗa mai ido ba, sai dai ya dawo da kai baya a tsarim rayuwarka, ba ka da sauran lokacin ɓatawa Sardauna.” “Amma nasan asalina Turaki, nasan iyayena.” “Ba zan hanaka ba, amma ina shawartarka da ka bar abinda ya wuce ya wuce, ka fuskanci abinda ke gaba kawai.” A haka muka ƙarasa gida, lokacin sha biyu ma ta kusa, ba mu yi wata magana ba muka kwanta. Washe gari da safe ma haka ba mu sami damar yin wata maganar ba ya shirya ya fita, nima na shirya twins na kai su inda nake kaisu na wuce asibiti. Babban labarin dake tashi a asibitin shine na wata mara lafiya da aka kawo ta yi kara duka hannyenta biyu da ƙafarta ɗaya, sannan ta na fama da cutar ƙuraje a jikinta ta na wannan halin a ɗaure amma faɗi take asosa mata a sosa mata, ga jini dake zuba daga jikinta kuma a haka shari’a ake yi da ita, zancem sai ya ɗuwa yake cikin asibitim ko ina yaɗa shi ake yi, ga case ɗim nasu ya bazu a social media cewar an kama mata masu zaman a gidan kansu suna maɗigo da siyar da ƙwaya. Hotonan su sun zagaye media ga cutar da suke ɗauke da ita har da dukan da Sardauna ya yi wa Bilkisu akam cutar da ta kwaso, komai ya zagaye media, mutane da suka dinga yawo sa hotonan su an aure ya sune suke yawo da zancen sakin da kuma cutar da ta shafa masa, cikin lokuta kaɗan komai ya bazu a duniya, mutane sai kirana suke amma bana ɗagawa, kiran Yaya Rumaisa da ya shigo yanzu, shine kawai kiran da na ɗaga, ina ɗagawa ta ce. “Ke abinda ke faruwa da tsohon mijinki da matarsa gaskiyya ne?” Kamar tana kallo na na ɗaga kai, sannan na ce. “Gaskiyya ne Yaya, jiya muna wajen aka yi dukan da sakin, wai Bilkisu ‘yar maɗigo ce ga kuma siyar da ƙwaya, yanzu ta shafu musu cuta.” “Ai Allah shi ƙara, ƙarshen mace amana kenan, kamar yanzu duniya ta yi ta yawo da hotonansu na soyayya da na aure, har aka yi ta zaginki, yau gashi duniya tana yawo da videon saku da duka, duniya tana zaginsu, sai ga shi a yanzu wata ta ɗauko hotonan aurensu da yanzu tana magana akai, har take cewa ƙarshen cin amana kenan, dan a yanzu zance ya fita fes na cewa Bilkisu ƙawarki ce kuma ke kika nema mata auren Sardauna, har sakin da ya yi miki a ranar auren yanzu ya fita, ga hotonan ku na na taron twins sai yawo suke a media kowa yana miki fatan alheri, ko a haka aka tsaya Nana ki godewa mai sama, da ya yi miki sakayya, shima Sardauna yana nan zaiga sakamako, ni nasan ba iya wannan cutar ba ce sakamakon da zai gani.” “Ni Yaya Wallahi tausayi ma yake ban, Sardauna yaga sakamako, Yaya kinsan Sardauna ba ɗan asalin familyn nan ba ne? Ɗan ma’aikatan gidan ne suka rasu bayan an haife shi, shine aka riƙe shi a gidan fa.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (9). “Ke Nana ina kika ji wannan maganar?” “Wallahi Yaya dagaske na faɗa miki, kinga kuwa ai Sardauna yaga sakkayya.” “Wallahi ya gani, ni kaina ya fara ban tausayi Nana, amma hakan zai zama izina ga azzaluman gaba.” “In sha Allah.” Daga haka na kashe wayar, na ci gaba da aikina. A lokacin summy abokiyar zamana ta shigo ofis ɗin. “Nana.” “Na’am.” “Yanzu nake ganin labarai, wannan matar tana da alaƙa da ke?” “Eyh ada ba, amma yanzu komai ya wuce.” “Yanzu nake bibiyar labarai, gaskiyya Nana kin sha wuyar aure, Allah sarki.” “Amma yanzu Summy sai dai godiyar Allah, ni har mantawa nake da wancan lokacin.” “Amma Nana kinsan akwai ƙaryar media, dagaske ƙawarki ce kuma ke kika haɗa aurensu?” Na girgiza kai, sannan na ce. “Bansantaba sai bayan na yi aure, ta zo gidan ta ce anan baya take tana so mu zama ƙawaye. To kinsan amarya ba yara ba kowa zaman kaɗai ce duk ya isheni, na amince mata ta fara zuwa har ta zama ƙawatah, kuma bani na haɗa aurensu ba, tun kafin nasanta da soyayyarsu a ƙasa, tin da shi ya turo ta, kawai suny amfani da wauta tace na shiga abun na haɗa auren, kinsan lokacin ina da ƙana nan shekaru ko 20 ban rufa ba.” “Allah Sarki na tausaya miki Nana, Allah Yasaka miki.” “Haba Summy, wace sakayya kuma? Ni yanzu ai na yafe musu tuntuni.” “Hakane kuma Nana, amma dai still akwai wani abu shima ina jin shi kamar ƙaryar media.” “Mene?” “Wai a ranar da aka ɗaura auren aka saki ki? Kuma wai kin shiga difreshon sabida sakin?” Na yi murmushi sannan na ce. “Ranar da aka yi auren ya sake ni, amma zuciyata ta kasa karɓar hakan shine ya haifar min da cutar.” “Allah Sarki Nana.” Ta faɗa, ni kuma na miƙe ma fita ba yanda zuciyata bata raya min ba amma ba nakasa zuwa wajen Bilkisu haka na koma gida, sai dai babban abun mamaki shine, hirar da muka yi da Summy ashe recording ta yi, cikin ƙanƙanin lokaci hira ta bazu a media, ina ganin haka na kira Turaki na faɗa masa, nan ya hau da ni faɗa me ya sa na saki baki aka yi hirar. Cikin kwana biyu zance ya yi trending ko ina ka duba wannan maganar ake, wasu su yi ta gidan da aka kama, wasu su yo ta dukan Bilkisu, wasu su yi ta cutar da Sardauna ya yi min, sai da ya zama idan na zo asibiti mutane zuwa suke kallona, sabida yanda zancen ya yaɗu a kafafen sada zumunta, a gida kuwa Sardauna yana ta fama da jinyarsa, dan Turaki ne ma ke ƙoƙari wajen sama masa magunguna na ciwon, sabida a yanzu ƙuraje ne masu ruwa suka fito masa a jiki, su ka cika ko ina, duk rashin imanin ka kaga Sardauna sai ka tausaya masa, ba mata, ba ‘ya, ga ciwo, ga ba asali, duk da shima bai da wani tabbaci akan rashin asalin nasa. Amma gaba ɗaya ga canja kullum cikin kuka yake, duk da ni ban taɓa zuwa inda yake ba ko sau ɗaya. Sai da su Big Daddy ma suka ga ciwon suka haɗa shi da babban likita anan nigeria, idan ba a sami sauƙi ba zasu wuce ne ƙasar waje. Ranar wata lahadi da safe, muna zaune kan dinning muna breakfast, ni da Turaki da Twins ɗin mu wayata ta fara ringing, ina dubawa naga Yaya Rumaisa na ɗauka ina faɗin. “Hello Yaya.” “Nana, duba wani video da na tura miki.” “Tom.” Na faɗa tare da kashe wayar na kunna data, ina shiga na ji labarin wai kotu ta yankewa su Bilkisu zaman gidan kaso na shekara 20, a fili na furta. “Innullahi wa’inna illahir raji’un.” Turaki ya ce. “Me ya faru?” “Habiby ka ji wan an yakewa su Bilkisu shekaru 20 gidan yari.” “Daman ai wannan ne hukuncinsu.” “Amma Habiby kaman fa ba sa hannunta a abun.” “Eyh tayu ba sa hannunta, domin ita matar nan da dukkam alamu sharri ta yi musu, amma idan kim tuna haƙƙin rai ne fa akanta, ga wasu abubuwan da take yi, yanda ta azabtar da mijinta ai Allah bazai barta ba.” “Hakane kam, Sardauma ua wahala wajen Bilkisu ba ƙarya, ga ciwon da ta shafa mai. Kai Allah ya yi mana mai kyau.” “Amin Habibty, dan ma a yanzu an samu sauƙin cuwon, ƙurajen sun daina ruwa, kuma sun daina masa zafin, sai sai ga sunan faca-faca.” “Allah Sarki, Allah Ya bashi lafiya.” “Amin Ya Allah Habibty.” Kasancewar yau lahadi ce muna gidan dukkanmu daga ni har Turaki bamu fita ba, sai can yamma ya ce da ni. “Habibty ku shirya muje muga aikin gidanmu, ina son nan da wata ɗaya fa mu koma, dan daga can zaki tafi Hajjinki.” Na yi murmushi, sannan na ce. “To bari mu shirya.” Muka shirya ni da twins da shi muka fice, gidan babban gidane kuma aikin yana sauri, dan ko a haka ma tsaf za a iya zama, sai dai na kasa gane kan tsarin gidan. Tun ɗazu nake zagaye shi sai na ga kamar part biyu ne. “Habibty ya kika ga gida?” “Ya yi sosai Habiby, amma gidan kamar part biyu ne ko?” “Eyh Habibty part biyu ne mana.” “Shima mu da Sardauna zamu zauna?” Ya girgiza kai, sannan ya ce. “A’a ni ɗaya zamu zauna.” Na yi murmushi, sannan na ce. “Amma dai kayan mu da su zamu dawo, sabida kaga sabbabine, lokacin da Islaha ta yi wannan abun aka canja.” “Eyh Habibty, dasu zamu tawo sai dai za a ƙara komai set ɗaya, wannan falon naki na nan zamu zuba sabbabin kujerun ciki, su kuma na falon mu sai musa su a wancan falon, na falon ciki kuma akwai wani ɗaki daga nan sai mu sanyi shi ciki, kayan gado kuma ɗakin bacci namu uku ne sai na twins biyu, sabida ko ƙannensu.” “To amma wancan part ɗin fa?” “Ba yanzu zamu zauna ciki ba, zamu barshi ne kawai.” “Hhhm, Allah Ya sa.” Na faɗa, sanna muka ci gaba da zagaye part ɗin muna kalla, komai ya yi sosai da sosai. Daga nan muka wuce gidan Hajiya, bayan nan mukaje gidan Yay Ridwan, anan muka ga cikin matarshi ya girma sosai, twins kamar basu san su ba, ba kuka ba wani abu haka muka dawo gida. Bayan kwana biyu da yanke hukuncinsu su Bilkisu muka tashi da wani sabon abu a cikin family, wanda ba a san daga inda yake ba, ina zaune ofis Lamrah ta kira ni a waya, kamar bazan ɗauka ba amma dai na ɗauka, ina ɗagawa ta ce. “Wai kinji Sardauna ya sha guba.” “Guba kuma?” Na faɗa a tsorace. “Guba dai, daman jiya yazo gidanmu yana ta kuka, wai Big Daddy ya taimaka ya ce masa dukkan zancen da yake ji ƙarya ne, ya ce masa shi ɗan family ne, Big Daddy ya ce masa ko me ya ji ko gaskiyya ne ko ƙarya hakan ba zai canja shi daga sunan ɗan family ba, kuma an faɗa masa karya zurfafa bincike amma Sardauna yaƙi. Afrah ta ce min yau da safe ya sake zuwa gidansu ya dimga roƙon Momynsu ta faɗa masa gaskiyya, aikuwa ta faɗa masa wai ashe shi ba ɗan Abbah ba ne, wai babbanshi amininsu Abbah ne wanda ya muti sakamakon cetom ran granny, mahaifiyarshi kuma ta mutu yayin haihuwarsa shine aka bawa Momynsu ta riƙe shi, Anty Nana wannan zancen ya jijjiga family gaba ɗaya, ace the whole Sardauna babban jika ba familyn Ta Ambo ba ne, bare ne shi.” “Lamrah amma ko mene ai bai kamata ya sha Guba ba, idan ya mutu kuma fa? Yanzu yana ina?” “Big Daddy fa har da kukansa, wai Momy ba ta kyauta ba, Sardauna kamar amana ne a wajen su, Haka Mamanmu ma, yanzu sun tafi asibiti.” “Allah Sarki, Allah Ya bashi lafiya, Allah Ya tashk kafaɗunsa amin.” Na faɗa tare da kashe wayar, sai da na kashe wayar na shiga tunani. ‘Amma Sardauna bau kyauta ba, me ya sa zai yi yinƙurin kashe kansa, akan shi ba ɗan wannan ahalin ba ne? To mene a ciki da zafi haka?” Haka na yini tunani, ina son kiran Turaki ina tsoron kar ya ce me ya dame ni da case ɗin? Ta dole na haƙura na bar zancen har muka dawo gida, sai dai bai dawo ba har wajen takwas, ta dole na kira shi a waya amma taƙaraci bugunta bai ɗauka ba, abinda ya yi matuƙar tada min hankali. Ina ƙoƙarin sake kira ya kira ni. “Hello Habiby, ina kashiga haka?” “Habibty muna asibiti ne, Sardauna ya sha guba, kuma abun sai addu’a.” “Innullahi wa’inna illahir raji’un. Yanzu zaka dawo?” “Ta ina zan dawo? Tun safe likitoci ke sintiri akansa, amma abu ya ci tura, har babban likita Big Daddu ya kira daga indiya, yanzu haka ya ƙaraso shima ya shiga kusan minti talatin shiru.” “Ya salam, Allah Ya bashi lafiya amin.” “Amin Habibty ku ci abinci ku kwanta, idan na dawo to, idan badawo ba gobe da sassafe zan zo.” “Tam Habiby, Allah Ya tsare ka.” “Amin na gode.” Yana faɗar haka ya kashe wayar, aikuwa na fashe da wani irin kuka mai ƙarfi, a take twins suka tawo sula zagaye ni suna faɗin. “Maamah! Maamah!” Amma bana ko jinsu, kuka kawai nake daga ƙasan zuciyata nake tausayawa halin da Sardauna yake ciki, abubuwan sun masa yawa, da me zai ji? Dan ya yi ƙoƙari kashe kansa ma ai ba wani abu ba ne, ace abubuwa daga wannan sai wannan, Allah sarki. Sai da na yi kuka na ishashe twins suna ta ya ni, sannam na dawo na rarrashe suka yi bacci, na ɗau waya na rasa wa zan kira, sai can na kira Ra’is, bugun farko ya ɗauka bayan mun gaisa na ce. “Ra’is kasan me?” “A’a sai kin faɗa, na ji kamar kina kuka.” “Uhm, wai Sardauna ya sha guba.” “Akan me? Ina ruwanki?” “Akan bashi da asali.” “Bangane bai da asali ba, agola ne a gidan?” “Yafi ƙarfin agola, shi ba shi da uwa ba shi da uba, kuma dukkansu babu mai alaƙa da gidan.” “To shine ya sha guba, sabida bai da hankali? Y- mutu?” “Ra’is, Sardauna yana fuskantar rayuwa kwana biyu.” “To ai haƙƙi kenan, kinga ki kwanta ki yi baccinki.” “Kana ganin babu laifi na a ciki?” “Laifi kin kuma? Me kika yi? Ke kika hanashi asalin?” Na girgiza kai, sannan na ce. “A’a.” “To karki sawa kanki wata damuwa, ina Yaya Turakin?” “Suna can asibitin, ƙila ma can zasu kwana, jikin nashi sai addu’a.” “To Allah Ya ƙara afuwa, ki yi kwanciyarki kawai, shine ma mai haƙƙi, amma dai dan Allah ki yafe masa ko ya sami sauƙi ta wani wajen.” “Ai na yafe masa, na yafe masa tuntuni.” “To Allah Ya yafe mana baki ɗaya.” “Amin amin.” Na faɗa tare da addu’a na kwanta, sai dai gaba ɗaya na kasa bacci, da na rufe ido Sardauna nake gani akan keken guragu yana kiran sunana. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (10). Da na rufe idona Sardauna nake gani akan keken guragu yana turu shi zuwa inda nake, sai na yi sauri na buɗe idona, daƙyar na samu bacci ya ɗaukeni na yi shi. Da safe ina ta shi na hau haɗa breakfast, ganin har ƙarfe takwas Turaki bai dawo ba na shirya idan zan tafi asibiti zan kai mai breakfast sai na wuce. Wajen ƙarfe goma na isa asibitin, yanda naga mutane kowa jigun jigun ya yi matuƙar tsorata ne, kana kallonsu kasan ba lafiya ba, duk wanda na gaisar ma baya samun damar amsa min har na ƙarasa inda Turaki yake. “Habiby, ina kwana? “Kintashi lafiya?” Na gyaɗa kai kawai, sannan na ce. “Ya mai jikin?” “Mai jiki sai godiyar Allah, har yanzu babu wani sauƙi Habibty.” “Ya salam, in sha Allah zai tashi, ka samu kaci abinci gashinan.” “Bana jin yunwa Habibty.” Na kama hannunsa, na ce. “Yaushe rabonka da abinci? Tun jiya da rana ko?” Ya gyaɗa kai alamar eyh, na ce. “Ka daure Habiby dan Allah, idan baka ci ba kaima kwanciyar zaka yi, ka yi haƙuri mu ji da iya wannan.” “Tom zan ci ajiye min, ki tafi ofis idan ki tashi sai ki dawo.” “Tom Habiby.” Na faɗa tare da ficewa, ko a can ofis da wannan damuwar ta Sardauna na wuni, gaba ɗaya abun ya dame ni, fatana dai Allah ya tashi ka faɗun Sardauna, ko da zai mutu bana so ace ya mutu ta hanyar kisan kai, gwanda ya mutu ta wata hanyar daban. Karfe huɗu saura na tashi daga ofis na nufi asibitin Sardauna, da naje ban sami Turaki ba amma nasami ‘yan uwansu acan, har yanzu dai jikin sai addu’a, likitan indiyan har ya tafi amma bai farka ba, ana sa ran farkawarsa kowanne lokaci, har na gama zamana na tafi dai Sardauna bai farka ba. Abu Sardauna kamar wasa, sai da ya kwana biyu bai farka ba abun ya dami kowa cikin familyn duk jikinsu ya yi sanyi, sai a rana ta huɗu Allah Ya nufe shi da farkawa, sai dai a yadda Turaki ya ke faɗamin farkawar tashi tazo da wani irin abu, a tsorace na ce. “Habiby wane irin abu kuma?” “Habibty Surutai kawai yake, harda sunan ki yake kira.” “Sunana kuma Habiby?” Na tambaya, ya ce. “Uhmmmm, sunanki fa Habibty.” “Me yake cewa?” “Abun dai duk ba daɗi, idan na dawo zan faɗa miki.” “Yaushe zaka dawo? Wai dan Allah kana cin abinci kuwa?” “Habibty babu wanda yake da kwanciyar hankalin da zai ci wani abu, baki ga a yanayin da ya farka ba.” “Innullahi, to dan Allah ka samu ka dinga dawowa gida.” “Zan dawo in sha Allah, sai anjima.” Ya faɗa tare da kashe wayar, na yi shiru na tsurawa wayar ido, ko ciwon ƙwaƙwalwa ne yake son kama Sardauna kamar yanda ya yi min? Ko da yake ance shi surutai yake, Allah Ya sauƙaƙa masa na faɗa tare da miƙewa, ni zuwa asibitin nema na gaji da shi, shi ya sa na daina zuwa gaba ɗaya, amma idan Turaki bai dawo ba kam zanje yau zuwa dare, tashi na yi na shiga ɗakinsu twins suna ta wasan mu. Suma jira muke mu koma sabon gida sai a sanyasu a makaranta tun da a yanzu sun kawo shekara uku, bayan na gama basu abinci na dawo falo na ɗau wayata, na yi mamakin ganin tarin uban missed call daga ‘yan gidanmu, haka kawai na ji gabana ya faɗi sabida yawan kiran, a tsarin ‘yan gidanmu ba sa taɓa yi wa mutum kira sama da biyu amma yau wajen kira bakwai daga mutum ɗaya, ina cikin tunanin na ji wani kiran ya sake shigowa, ban ma tantance mai kiran ba na ɗauka. “Hello.” “Nana, ina kika sanya wayarki ana ta kira?” A muryar nagane Yaya Radiya ce, na ce. “Yaya na bawa twins abinci ne.” “To kinji Hajja ce Allah Ya yi mata rasuwa.” “Ya salam, yaushe?” “Yanzu haka ma ni ina hanya.” “Bari na faɗa ma Turaki, yanzu zan tawo nima.” “Tom.” Ta faɗa tare da kashe wayar, na kiraTuraki bai ɗauka ba, kawai na sanya Hijab ɗina na ɗauki twins na kai su gidan mai rainonsu na faɗa mata kakata ce ta rasu idan na dawo yau to, idan ban dawo ba su kwana, na ɗauki kuɗi dubu biyar na bata, daman kuma suna da kayan abinci a gidan. Sai da na ƙarasa gidan Turaki ya kira ni, hayaniyar da ya ji kasancewar glass din motar a sauke yake ne yasa shi cewa. “Habibty me ya faru? Kina ina?” “Hajja kakarmu ce ta rasu.” “Ya salam Allah Ya jiƙanta, ƙarfe nawa za ayi janaizar?” “Yanzu nan za ayi.” “Tom Habibty gani nan zuwa.” Ya faɗa tare da kashe wayar, ni kuma na fito daga mota na shiga gidan, su Yaya Radiya da sauran ‘yan uwa sai kuka suke, nima dai mutuwar ta taɓani amma ko ɗigon hawaye bana ji a idona, to ni ba wata shaƙuwa a tsakaninmu, daman sabo shine babban abinda ake yiwa kuka, shi kuma sabo shaƙuwa ke kawo shi, har mamakin yansa Yaya Radiya ta zauna tana ta zubar hawaye nake, haka Yaya Rumaisa ma idonta ƙamas, ni yanda take rarraba idanu ma yasa na kusa fashewa da dariya. Muna zaune a gidan aka yi wa Hajja suttura aka tafi da ita, bamma san Turaki yazo ba sai da suka dawo suka shigo, bai wani jima ya koma asibitin, washe gari naje gida na ɗauko twins na dawo, sai bayan addu’ar uku sannan muka dawo gida, a ranar kuna na ce zanje naga Sardauna, a yanda Turaki ya ce abun na shi ma gaba yake yi, sai dai naga kamar yana ɓoye min ma wani abu, sai dai ganin bani da alaƙa da Sardauna yasa ban damu ba da komai ba, da daddare wajen ƙarfe takwas na je asibitin, Turaki ma kawai ganina ya yi asibitin, ban ƙarasa shigowa ba ya ce. “Habibty me ya kawo ki?” Ganin yanda ya nuna damuwa yasa na ce. “Lafiya Habiby?” “Lafiya kawai bana son kowa ya ganki anan ne.” “To me ya sa?” “Kawai.” “Ah, Anty Nana kin dawo?” Afrah ƙanwar Sardauna ta faɗa, na kalle ta sannan na ce. “Eyh na dawo.” “Ya ƙarin haƙuri? Ki shigo mana.” “Haƙuri Alhamdulillah.” Na kalli yanda Turaki ya haɗe rai, na ce. “Komawa zanyi.” “A’a bazaki koma ba, bakisan nemanki ake yi ba? Jiya Big Daddy ya ce za a biki kanon.” “Kano kuma?” “Kakar taku da ta rasu ko ba a kano ba ne?” “A kano ne.” Na faɗa ina kallon Turaki, “Shige mana, kin wani bi ni da ido.” Ya faɗa yana harara Afrah, na ce. “Tom, Afrah muje.” Afrah ta yi gaba, ni kuma na tsaya a baya. “Wai mene ya faru?” Na tambaye Turaki ƙasa ƙasa, ya watsa min harara sannan ya ce. “Ke kika sani, sai da na ce kar ki zo amma kika ƙi, duk abinda ya faru ke kika sani.” “Habiby mene zai faru?” “Oho miki.” Ya faɗa ya yi gaba, kamar mara laka haka nake takawa har na shiga babban ɗakin da kowa ke zaune, a take ido ya yi kaina, Lamrah ta ce. “Yaushe kika dawo?” “Yanzu nan.” Na faɗa, duk da na rasa gane kan zancen baki ɗaya, nan fa kowa ya yi min sannu da dawowa, na ce. “Ya mai jikin?” “Mai jiki da sauƙi, dan Allah tashi ki shiga ki ganshi, kullum ba shi da aiki sai kiran sunanki.” “Sunana kuma?” Na faɗa ina miƙewa, Turaki ya biyo bayana muka shiga, Sardauna na kwance akan gado idonsa a rufe, a hankali na taka inda yake na zauna akan kujerar dake gefe Turaki ya ce. “Sardauna.” Da sauri ya buɗe idonsa ya ce. “Turaki dan Allah ka kawo min Nana, wallahi zuciyata zafi take min, ka taimakamin naga Nana ko zanji sauƙi a zuciyata.” A hankali Turaki ya ce. “Ga Nanan anan.” Da sauri ya buɗe ido ya ce. “Nana, Nana, Nana.” Ya tashi ya kamo hannuna ya riƙe da ƙarfi, na fara ƙoƙarin ƙwace hannuna amma Sardauna ya riƙe katamau. Idona na kai ga Turaki, naga yanda ya haɗe rai, fuskarsa ta yi wani ja, haka idanunsa. Na ce. “Sardauna, cika ni mana.” Ya ƙara riƙe ni katamau, ya ce. “Nana, ina sonki dan Allah, Nana ki ce kina sona, zuciyata zafi Nana.” Na kau da kaina gefe, ina ƙoƙarin ƙwace hannu na ce. “Sardauna hannuna zafi, Habiby kazo ka ce ya sake ni.” Tsaƙi ya ja ya miƙe ya fice, a raina na ce. ‘Innullahi wa’inna illahir raji’un, ni Nana naga masifa.’ “Nana dan Allah.” “Tom Sardauna, ka nustu ka cika ni ka ji.” Sardauna dai ya gagara cikani, ba yanda banyi ba amma abu ya ci tura, har sai da na fara ihun neman ceto, da sauri su Lamrah suka shigo suna faɗin. “Me ya faru?” Hannuna na nuna musu da Sardauna ya matse, duk suka fara cewa. “Ka cika ta mana.” “Kira min Turaki dan Allah.” Afrah ta fito tana faɗin. “Yaya Turaki ya riƙe mata hannu fa.” Ba shiri su Mama Amina suka shigo, ganin yanda Sardauna ya riƙe min hannun katamau yasa suka fara ƙoƙarin ƙwace ni, da ƙyar aka fusge hannuna daga jikin Sardauna. Ana ƙwacewa na miƙe na fice ina haki sai kace wacca ta yi tseren gudu, ina fita na ga Turaki ya haɗe rai, na nufo shi ya yi gaba ya ƙyale ni, nima na bi bayan shi na tadda shi a mota, har muka isa gida bai ce dani ci kanki ba, duk yanda na so na yi magana da shi amma yaƙi, da na matsa masa ma ya hau faɗa, ta inda yake shiga bata nan yake shiga ba. “Kinji daɗi ko ya riƙe miki hannu, shine daman abinda kike so to ya riƙe.” “Haba Habiby, ya za ayi na so ya riƙe min hannu? Kana ganin fa yanda aka yi da shi.” “Tun da ya farka yake kiran sunanki, yake wasu maganganu wai yana sonki, kinji zafin da nake ji? Na faɗa musu rasuwar Hajja, na ce musu akano ne, amma daga dawowarki shine kin kwashi ƙafa kin tafi, daman hankalinki yana kansa ko? To gashinan kingan shi ya ganki, ya ce yana sonki, ya taɓa miki hannu, sai kuma me ya rage? Ko so kike kema ki ce kina son sa? Daman ba yau kika saba faɗa ba.” “Haba Turaki! Me na yi duk da zaka dinga faɗan waɗan nan maganganun? Nasan halin da yake ciki? Komai fa ɓoye min kake? Dan shi naje wajen? Na je ne fa dan ka ci abinci, kwana nawa bana ganinka, nasani kana ci ko baka ci, shine naje amma kake min wannan abun, dan ya ce yana sona to sai me? Sai aka yi me? Ni son sa nake? Me ya sa kake min haka ne?” “Ni kike faɗawa waɗan nan maganganun? Ni kike wa magana da tsawa haka?” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (11). “Ni ba wani abu da na faɗa maka, kaine gaba ɗaya ka rufe ido, ta inda kake shiga bata nan kake fita ba, da ace tun a farko ka faɗa min komai ai da bazan je ba, amma ka rufe komai, nasan me yake faruwa?” “To yanzu ai kinje kingane sai kuma me?” “Hhhhm.” Na faɗa tare da ficewa daga ɗakin na koma wani ɗakin, gaba ɗaya Turaki ba shi da uziri akan al’amarin Sardauna, ni da ba son sardauna nake ba, ba wani abu ba, ko magana ba yi nake da shi ba, amma gaba ɗaya ba iya yin uzuri akan abubuwan da suka haɗani da shi, ni gwanda ma mu tashi mu bar gidan kowa ya huta, bani da wata alaƙa da zata sake haɗani da shi. A daren ba nemi Turaki ba shima kuma bai nemeni ba, washe gari ma da sassafe ya shirya ya fita, duk da haka ni ban wani damu ba, yanda yake fushi nima haka nake yin nawa fushin, har rana ba muyi waya ba, ƙarshe ma asibitin ya kwana, wannan ita ce rana ta farko tun auren mu da muka taɓa yini tun safe har dare har kwana ma wani bai nemi wani ba, amma dai still haka na jure na ce naji na gani, dan banyi komai ba bazan ɗauki laifi ba wallahi, mu yi ta fushin har atashi duniya, sai dai tun kwana na ɗaya, da na biyu na ji bazan iya ba kwata kwata, ina zaune a ɗaki na rasa me yake min daɗi, gashi tun da ya zo sau ɗaya bai sake zuwa ba, waya ta na ɗauka na danna lambarsa, sai dai har ta gama kukanta bai ɗauka ba, takaici ya isheni da haushin kaina, me ma ya sa na kira shi, ba fushi muke ba mu yi ta yi. Wajen minti 20 sannan ya kira ni, kamar ba zan ɗauka ba dai na ɗauka, na kuma yi shiru bayan na ɗauka. “Hello, salamu alaikum.” “Wa’alaika salam.” Na faɗa murya ciki-ciki, sai kuma na ce. “Bansan na danna kiran ba.” “Tom.” Kawai na ji ance, sannan aka kashe wayar. ‘Hhhm.’ Na sauke ajiyar zuciya na ce. “Lallaima Turaki, ya yi abinda ya ga dama, dan yaga yana jinya shine zai zo min da wannan salon to daidai nake da shi.” Da yamma lis na sake shiryawa zan tafi asibiti, ina ƙoƙarin fita nagan shi ya shigo, na matsa ma ya wuce ni kuma na nufi ƙofa. “Ina zaki?” Ba tare da na juyo ba na ce. “Zanje asibiti mana, ko an sallameshi ne?” “Asibiti kuma Nana?” “Eyh asibiti.” “To adawo lafiya, Allah Ya tsare.” Na ce. “Amin.” Na nufi hanyar fita, aikuwa ya yi sauri ya jawo ni. “Wai Habibty mene haka?” “Me na yi? Naga kaine ka daina sona, ka zaɓi zama a asibiti da Sardauna ka watsar dani, to nima ba sai na koma asibitin ba.” “Lallai, baki ga abinda kika yi ba kenan?” “To ai kai…” “Ya wuce Habibty, amma kar a sake, na ji ba daɗi.” “Tom.” “Ba a sallame shi ba, sun tafi babbban aisibitin Delhi na ƙasar indiya, ciwon na shi sai addu’a kawai.” “To Allah Ya bashi lafiya, Allah Yasa kaffara ne.” “Amin Habibty, na yi kewarki.” “Bawani nan, ɗazu wai ka kashe min waya.” “To kin ce ba ni zaki kira ba, shi ya sa. Wait wai wama zaki kira?” “Mijina na faɗa.” Daidai lokacin twins suka fito daga ɗaki, suna ganinsa suka tawo da gudu suna faɗin. “Papa, papa.” Ya tsugunna ya ɗauke su duka, suka miƙe tsaye ya ce. “Yau dai zamune shan ice cream, amma yanzu wanka zanyi na kwanta.” “Habiby ba a bacci da yamma fa.” “To ni dai sai na yi, yanda nagajin nan.” “Amma ana kiran magariba zan tashe ka.” “Na yarda.” Ya faɗa tare da shiga ciki, sai dai ya yi wanka ya ci abinci kafin ya kwanta aka yi magariba, sai bayan magariba ya kwanta. Ba shi ya tashi ba sai wajen goma saura, lokacin twins ma sunyi bacci. “Habibty bamu fita ba.” Kallonsa na yi, sannan na ce. “Sai bayan isha ka ce ai.” “Yanzu ƙarfe nawa?” “Bakwai saura.” “Yawwa, shirya twins din bari na yi wanka.” “Tom.” Na faɗa duka ban ɗauke idona daga kan laptop ɗita ba, bare ma na kalle shi. Ya miƙe ya sauka daga kan gadon, ya ɗau wayarsa ya duba. “Kai Habibty, goma saura fa.” Sai a lokacin na tsayar da laptop ɗin na ce. “Kai ka ce kar na tashe ka fa, zaka tashi da kanka.” “Amma da kika 8 ma ai sai ki tasheni.” “A’a gwanda ka huta, ni ka ga yanzu zanyi nawa baccin.” Na faɗa tare da kashe laptop ɗin, na ajiye ta gefe na kwanta. “Zaki ga bacci kuwa, bara na yi sallah. Idan na dinga tsalle a gadon sai kin farka dan kanki.” Na yi dariya na ce. “Taɓ, bari na tafi ɗakin can.” “A’a dan Allah, yi baccin ki anan.” Na yi murmushi na kwanta, washe gari da safe tare muka yi aikin komai da Turaki, har na tafi asibiti na barshi gida, wai shi ba zai fita ba yau hutawa zai yi. Wajen ƙarfe uku ya zo asibitin namu ya ɗauke ni, wai zamuje mu fara duba kayan da zamu sanya a sabon gidanmu, haka muka yini daga wancan shagon zuwa wancan, sai bayan magariba muka dawo gida. Bayan sati biyu. Shirye shiryen tashinmu ya yi nisa, kullum cikin siyayya kayan sabon gida muke, mu siya wancan mu siya wancan, ga kuma tafiyar mu tana gabatowa, shirye- shirye sunyi nisa sosai. Haka shima sabon gidan aikin duk ya yi nisa, saura kaɗan agama, pary ɗin da Turaki yake cewa ba zamu zauna ba, shima har nan ake aikin ya yi fes kamar a yanzu za a zauna, kayan gado na duk ɗaukan su ya yi ya kai su wani company aka yi musu ciko suka bamu sababbi, haka ma kujerun suma aka kai musu, da ba ayi niyar canjawa ba amma ganin sauƙi campany yasa muka bada su aka yi cikon, hatta twins suma sai da aka yi musu sababbin kayan ɗaki, mussaman waɗancan na yara ne, waɗannan kuma da aka sanya musu ba lallai acanja musu bar sukai shekaru 20, sabida gadon ma na ‘yan mata aka sanya musu, har da mudubi. Cikin ƙanƙanin lokaci aka gama gyara sabon gida, aka sanya komai, sannan muka koma aka yi gagarumar walimar tarewar mu, gida ya amsa gida ya ci uban gida, tun daga gidan Sardauna na farko da na zauna, da part ɗinsa na wancan gidan da muka tashi, da part ɗin da muka zauna da Turaki, yau kuma ga wannan gidan shima mun dawo, Allah Ya zaunar. Rayuwar mu a sabon gida ta fara tafiya cikin farin ciki, Turaki ya ƙara ninki na kulawa da yake ba ni a wannan gidan, sai na ji kamar sabon gidan nan ya kasance wata sabuwar duniya ta farin ciki, ƙaunar gidan ta cika min zuciyata. Ga wani irin son Turaki da yake ƙara kama zuciyata, nutsuwa ta shegi ne da kwanciyar hankali, bani da wata damuwa a yanzu, ga soyayyar dangin miji. Babu gidan da basayi na babu gidan basa so na, har da gidansu Islaha ma, dan ciwon Sardauna da kuma al’amarin Bilkisu ya yi matuƙar ta da musu hankali. Tun daga nan suka kama hanyar gaskiyya, haka Hajiyar Sardauna, daman ita ba mai hayaniya ba ce, kawai dai bata zumunci da Maman Turaki da Mama Amina, shima kuma ta janye a yanzu suna gaisawa. Islaha ta karɓi ƙaddara kuma a yanzu ta shirya idan Sardauna ya dawo zata aure shi a haka, dan duk abinda ya faru har yanzu zuciyarta bata daina son sa ba, sai ma tausayinsa da take ji, dan lokaci zuwa lokaci takan yi magana da ni ta ce, na yafewa Sardauna dan Allah, sai na ce mata bakomai Allah Ya yafe mu baki ɗaya, danni daman tun kafin yanzu na yafewa Sardauna, dan ban riƙe shi a zuciyata ba, mussaman lokacin da na ji shi ba asalin ɗan wannan gidan ba ne, na wanke zuciyata na ci gaba da rayuwa hankali a kwnace babu wata damuwa, ga mutuwar ‘yar sa ga kuma ciwon da ya samu, sannan kuma ciwon da ya samu na ƙwaƙwalwa wanda sanadiyarsa aka fitar da shi waje. Na sami nutsuwa da kwanciyar hankali, ga kyakywar kulawa daga mijina wanda take ɗebemin dukkan damuwar da take shirin damuna ta rashin haihuwa, kwata kwata Turaki baya bani damar damuwa akan wannan abun. Ranar da muka cika sati biyu a sabon gida, ji nake kamar na shekara cikin wannan gidan. Mun fara zuwa bita ni da Hajja, banda twins tun da su me suke ganewa ma bare ace za a kaisu bita. Sai da lokacin tafiya ya zo sai na ji gaba ɗaya bana son yin nisa da Turaki, sai nake jin kamar idan na tafi saudiya kafin na dawo wani abun zai same shi, gaba ɗaya sai na daina marmarin tafiyar ma. Haka kawai zan sha a gaba nai ta kallonsa, yau ma kamar ko yaushe kallonsa nake yi, sai da ya gaji da kallon ya ce. “Habibty kallon fa?” Na girgiza kai, sannan na ce. “Nifa bana son na yi nisa da kai Habiby, ji nake kamar wani abu zai sameka idan na tafi.” Ya yi murmushi ya taso daga kujerar da yake ya dawo kusa dani. “Habibty babu abinda zai same ni sai alheiri, kawai kewa ce, kinsan ba mu taɓa nisa ba, mussana irin wannan wajen wata guda zaki yi.” “Kaima da zaka tafi haka ka ji?” “Eyh Habibty, naji kewar ku sosai da sosai.” “Habiby dan Allah karka yi wani abun idan na tafi, kar ka dinga fita kana yin dare, ni dai gaba ɗaya na rasa me ke damuna.” “Tom Habibty, ki nustu ki kwantar da hankalinki dan Allah, ibada fa zaki yi, ibada mafi muhimmanci a rayuwarki, karki sa wani abu, kar sheɗan ya rusa miki ibada fa.” “Tom Habiby in sha Allah, Allah Ya tsare min kai.” “Amin Habibty.” Haka na yi ta fama da fargaba da rashin nutsuwar zuci, ana zaune sai na ce masa. “Yau saura kwana biyar tafiyarmu.” Ya kalleni ya yi murmushi, da na sake masa maganar sia cewa ya yi. “Habibty ko dai na biyo ku?” Na girgiza kai na ce. “Ai lokaci ya ƙure Habiby, amma ba inda zan sake zuwa ni kaɗai ba tare da kai ba, gaskiyya.” “Nima bazan sake gangancin tura ki wani wajen ke kaɗai ba, Allah Yasa dai ki iya ibadar nan Habibty.” Na yi murmushi, sannan na ce. “Zan iya mana.” “Allah Yasa ayi ibada karɓaɓɓiya Habibty.” “Amin Habibyna.” Haka na yi ta fama har Allah ya kawo mu ranar tafiyarmu, tun daren jiya nake kuka, ni da gaba ɗaya zuciyata babu nutsuwa a ciki, sai nake jin kamar ma ni ce zan mutu acan idan naje, gaba ɗaya na kasa zama na nutsu. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (12). A filin jirgi ma dai haka na kasa nutsuwa, hannuna na cikin na Turaki, ‘yan gidanmu da sauran ‘yan uwa sun cika airport, amma ni dai hankalina gaba ɗayansa yana kan Turaki, har aka zo lokacin da aka fara tantance alhazai kafin tafiya filin jirgi, Hajiya bakin ta a washe zata koma aikin Hajji ita ta riƙe twins muka shiga cikin jirgi, jirgin kai tsaye madina zai nufa hakan yasa ba musa harami ba, tafiyar awa huɗu da rabi ta sauke mu a Filin Jirgin Sama na Yariman Masarautar Mohammed bin Abdulaziz da ke Madina, muna sauka mu ka bi layin tantancewa shima kusan awa ɗaya da rabi sannan suka sake mu, tun da muka sauka a madina na ji wata nutsuwa ta shige ni, wani sanyin da farin ciki suka lulluɓe ni, muna gamawa da masu tantancewa wasu manyan motoci na Kamfanonin sufuri na aikin Hajji karkashin hukumomin aikin Hajji na jihar jigawa suka ɗauke mu, bayan an gama yi mana duk abinda ya dace. Kwananmu takwas a madina muna gabatar da ibada, sannan muka je ziyara. Bayan munyi kwanaki takwas a Madina, muka daura Harami daga Miqat na Dhul-Hulaifah (Abyar Ali) mula nufi Makka a mota tafiyar a ƙalla awa 4 zuwa 5. Ko da muka je makkah, bayan mun sauka a masauki, muka wuci harami kai tsaye domin yin Ɗawafi, bayan mun gabatar da ɗawafi muka fita daga harami muka shiga jiran kwanakin aikin Hajji, Ranar takwas ga watan Dhul-Hijjah muka daura niyyar Hajji daga hotal dinmu, motoci su kwashe mu zuwa Mina, inda muka kwana a tantuna muna ibada da sallah. Ranar 9 ga watan Dhul-Hijjah Ranar Arfa wacca take Jigon aikin hajji da safe muka fito daga Mina muka wuce filin Arfa. Anan ne muka yi ya yin addu'o'i tun daga azahar har zuwa faduwar rana. Anan na buɗe duk wata buƙata na zube, bayan faduwar rana muka wuce zuwa Muzdalifah. A nan muka yi sallar Magriba da Isha a hade, anan ne ake kwana a dandaryar kasa filin babu tantuna, sannan muka tsici tsakuwa na jifan Shaidan. Ranar 10 ga watan Dhul-Hijjah da take Ranar Sallah, da safe bayan asuba, muka koma Mina. Anan ne muka yi jafi Shaidan da tsakuwa guda 7. Bayan an yi aski/yanke gashi kuma an yi layya, sai kuma muka cire harami. Sannan muka koma Makka muka yi Dawafur Ifadah da Sa'ayi na Hajji, muka dawo Mina muka kwana. Duk wannan ibadar da su twins ake yi, ba ma su ba har da yara da basu kai shekarun su ba, iyayensu sun saki su suna ibada, zai anzo wajen ɗaura niya ne nake tsayawa na faɗa musu abinda zasu faɗa. Ranar 11, 12, da 13 ga wata Kwanakin Tashriq ne, muka ci gaba da zama a Mina muna jifar shaidan guda uku Kuskure, Tsakiya, da Babba kowace rana da tsakuwa bakwai bakwai. A ranar 13 muka kammalawa muka dawo hotal dinmu na Makka. Sai bayan mun dawo hotek muka fara gaisawa da yan uwa, dan wayar tawa ma acan na barta a hotel ɗin, sabida na mai da hankali ga ibada. Haka muka ci gaba da gabatar da ibada, muna waya da Turaki muna video call sosai, lokacin da aka cika sati biyu da idin babbar sallah na tashi da wani irin nauyi a zuciyata, na rasa me ya sameni gaba ɗaya, gashi sai kiran wayar Turaki ne ba ta shiga gaba ɗaya, ta whatsapp na yi magana da Ra’is, sallama na yi masa naga yana online, ban jira ya bani amsar sallamar ba na ce. “Kana ina?” “Ina gidana mana?” Ya dawo min da amsa a take, na sake ce masa. “Kaga ina kiran Turaki ba ta shiga kwata kwata.” “To Network ne babu mana.” Ya sake dawo min da amsa, kamar yana kallona na girgiza kai na ce. “A’a jikina bai ba ni haka ba, dan Allah ka duba min ko lafiya.” “Ke ki kwantar da hankalinki ba mutuwa ya yi ba, da ya mutu au zamuji.” Sai da na fara tura mai sticker duka, sannan na ce. “Nima banji mutuwa ba, dan Allah ka dubamin na rasa me ya sa, duk jikina babu daɗi.” “Ina Hajiya?” “Sun tafi massallaci ita dasu twins.” “To kitashi ki bi su, ki yi addu’a amma bakomai wallahi.” “Allah Yasa.” Na faɗa tare da kashe wayar, daidai lokacin kuma naga Lamrah online itama na yi mata sallama, ina mata sallama ta kira ni whatsapp call, na ɗaga tare da cewa. “Salam Lamrah.” “Anty Nana mutanen saudiyya.” “Lanrah ya gida?” “Alhamdulillah, Ya ibada.” “Ibada Alhamdulillah.” “Allah Ya amsa mana, dan Allah ayi mana addu’a.” “In sha Allah Lamrah, ya gidan naku?” “Lafiya ƙalau wallahi, yaushe ne dawowarku?” “Nan da kwana takwas, amma wallahi lamrah na ƙagu na dawo gida.” “Kai subhanallahi, saudiyya guda.” “Bazaki gane ba ne, hankalina yana gida wallahi ji nake kamar wani abu ne yake faruwa.” “Hhhhm, babu abinda yake faruwa ki kwmatar da hankalinki, ki mai da hankalinki akan ibada, kina inda addu’a bata jinkiri.” “Hakane Lamrah, a gaida su Mama.” “Zasuji ina twins din mu? Fatan dai har da mu suka sanya a addu’a ko?” “Har daku kam, suna massallaci nima yanzu zan tashi.” “Tom shikenan, Allah Ya karɓi ibada.” “Amin.” Na faɗa tare da katse kiran, sai da na sake gwada number Turaki bata tafi ba, na sauke wata ajiyar zuciya mara daɗi na tashi na nufi cikin massallaci, acan na yi ta addu’a ina roƙon ubangiji da ya kaɗe min duk wata fitina a gidana, ƙarfe takwas daidai na dawo hotel, wanda yake ƙarfe goma anan nigeria, sai a lokacin naga missed call ɗin Turaki barkatai, na ɗau waya na shiga whatsapp, ina duba naga tarin message ɗinsa kala kala, danna alamar kira na yi ta ringing biyu ya ɗauka, na ce. “Salamu alaikum.” “Wa’alaiki salam Habibty.” Kawai na fashe da kuka, wanda ya yi matuƙar tsorata shi, a rikice ya fara magana. “Habibty me ya faru dan Allah? Kukan me kike yi?” Cikin kukan na ce. “Haba Habiby, tun safe nake kiran wayarka ba ta shiga.” “Ki yi haƙuri Habibty, yau wani aiki ne ya tsare ni, kuma wayar cikin mota na barta daman ba chaji har ta mutu, kinsan data na a buɗe yake, to sai da na tashi naganta, na kuma sata a chaji na kira baki ɗauka ba, nasan kina massallaci.” “Amma ai da tun kafin ka fita kake min magana, amma yau kaƙi, gaba ɗaya zuciyata babu daɗi sai ji nake kamar wani abu ne zai faru, dan Allah Habiby idan wani abu ya faru ka faɗa min dan Allah ko zan sami nutsuwa a zuciyata.” Ya yi shiru kusan minti biyar baice komai ba, sai da na sake cewa. “Habiby…” “Na’am.” “Menene?” “Babu komai fa Habibty, kawai ina mamakin yanda kika ɗaga hankalinki, kika hana kanki nutsuwa kina ƙasa mai tsarki, kinsan dai duk runtse duk wuya ba zanyi wani abu da zai baƙantaki ba, bazai ɓata miki ba, dan haka Habibty ki sawa ranki salama dan Allah.” “Bangane ba fa.” “Habibty babu abinda ya faru, dan Allah ki nutsu ki yi ibada, sauran lokaci ƙalilan ya rage miki, dan Alla ki cire komai a ranki, ki kwantar da hankalinki, ki yi ibada kinji, koma menene idan kika dawo nasan zamu magance shi ko?” “Me zamu magance kuma? Ni banaganewa.” “Ki kwanta ki yi bacci kinji, da safe zan sake kiranki kinji.” “Uhmmmmm.” “Habibty.” Ya kira sunana, na amsa da. “Na’am.” Ya sauke wata ajiyar zuciya, sannan ya ce. “Ki yi haƙuri, ni banyi wani abu da zau ɗaga miki hankali ba ko ya ɓata miki rai, ina so dan Allah ki kwanta kinji, babu wani abu.” “Tom.” Na faɗa tare da kashe wayar, a lokacin kuma twins da Hajiya suka shigo, su sai lokacin suka dawo, Hajiya ce ta yi min wani kallo. “Wai ke mene haka? Kukan me kike yi? Ɗazu ma haka na ganki wata kala.” “Babu komai Hajiya.” “Koma mene ni dai na faɗa miki, ki mayar da hankali akan gajeren lokacin da ya rage miki a wannan ƙasar, bamu da tabbacin sake dawowa, bamu da shi. Tayu wata shekarar duka bama raye, tayu bamu samu damar zuwa ba ne, yanzu ma ba wayon ba dabararmu ba ne ya kawo mu, Allah ne ya kawo mu, dan haka ki mai da hankali ki yi ibada, ki roƙi Allah Ya baki zuri’a idan ya baki ki roƙi shi ya baki na gari, idan ya baki ya yi miki tarbiyarsu, ki roƙi shi ya baki lafiya, arziƙi da ilimin da zaku amfanar da al’ummar annabi, amma ba wai ki zauna kina kuka akan abun duniya ba, akan wani kishi na banza marar amfani ba, nasan duk abinda kike jin yana damunki bazai wuce kishi ba, wanda shaiɗan yake so ya kitsa miki, sabida karki yi ibada. To tun wuri ki miƙe, ki cire komai a ranki ki yi ibadarki na faɗa miki.” Tana gama faɗin haka ta nufi firji ta buɗe, twins suka yo kaina suna faɗin. “Maamah, ina papa.” Na ce. “Yana gida, muma mun kusa komawa, kuxo ku kwanta.” Na tashi na canja musu kaya, bayan nasu sunyi alawala na kwanatar da su, Hajiya bata sake ce min komai ba ta tada sallolinta, ni kuma na kwanta ina ta faman tunani a zuciyata, na saƙa wancan na kwance wancan, duk tambayata me ya kawo kishi cikin raina, bayan babu wani abu da ka ayi da zai kawo shi. Legenspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (13). Washe gari haka na tashi still dai raina ba daɗi, ina yin karin kummalo na nufi massallaci na fara sallah, ina addu’o da roƙon ubangiji da ya sanyaya min zuciyata, ya kuma bani zuri’ah ta gari, sai da na yini a massallaaci sannan na dawo hotel ɗinmu, duk da ina son na fara shiga siyayya ta kayan da zanyi na tsaraba, tun daman ina da kuɗin a ajiye, wayata na duba naga missed call ɗin Turaki, ban kira shi ba sai na yi masa message a whatsapp na ce. “Naje massallaci ne, yanzu na dawo.” A take ya yi min reply da. “Habibty kin tashi lafiya?” Na ce. “Alhamdulillah, ka fita?” Ya yi min reply da “Ina gida.” Na ce masa. “Tom, yanzu zamuje kasuwa mu fara siyayya, suara kwana biyar mu dawo.” “Allah Ya dawo min daku lafiya, idan anjima zmauyi waya.” Na ce. “Tom shikenan.” Na faɗa tare da tashi na shiga bayi na yi wanka na fito na shirya na ɗau twins muka nufi kasuwa, ba mu yi wata siyayya ba mussaman da naga kayan basu da wani bambamci da nan nigeria mussamman idan ka haɗa da kuɗin jirgi, haka na tawo gida ba tare da na yi siyayar da na yi niya ba, ina zuwa naga Hajiya bata nan ta tafi massallaci, ina zama na yi sallar la’asar na yi wa Turaki magana, nasan lokacin bakwai ta kusa a nigeria. Bai amsamin ba ya kira ni a waya, yana kira na ɗaga muka gaisa ya ce. “Duk na ƙagu ku dawo, na yi matuƙar kewarki.” Na yi murmushi, sannan na ce. “Ni kaina na yi matuƙar kewarka Habiby, ji nake kaman na yi tsuntsu na dawo nigeria.” “Habibty Saudiyya fa tafi daɗi.” “Idan tare da kai ba.” “Habibty.” Ya kira suna na, na amsa da. “Na’am.” “Ina so kisan wani abu guda ɗaya a rayuwarki, Habity ina so ako da yaushe ki dinga tunawa da shi dan Allah.” “Mene?” “Habibty wallahi ina sonki, ke kaɗai ce macen da nake so a zuciyata, ke kaɗai ce nake gani a matsayin sanyin idanuwa na, Habibty ki yarda da ni, ki yarda da soyayyar da nake miki.” Na yi shiru, duk kalamansa sun sanya min fargaba, sai na ji kamar wani abu ne zai faru. “Habibty, ko da bana nan ki dinga tuna cewar na so ki, tun bansan ki ba, kuma wallahi babu wata mace da naso ko zan so a rayuwata kamar ke.” “Wai mene dan Allah, kana samin tsoro da fargaba wallahi Allah Habiby.” “Babu komai Habibty, karki tsorota karki firgita, kawai ina faɗa miki ne ko zanji sauƙin abinda nake ji a raina, sonki ya taru a zuciyata ya hanani yin komai, a ko dayaushe tunaninki nake wallahi.” “Nasan kana sona, kuma nima ina sonka, so mai girma, dan Allah ka riƙe min amana dan Allah, wallahi ina sonka, ina kishinka a raina Habiby, ko hasaso ka na yi da wata ina jin zafi a raina, ana cewa ba a nunawa namiji ana son sa, to ni kam na faɗa ma Habiby, ko sani zaka yi a gabas kayanka sai dai ka yanka, amma tabbas ina sonka kuma bazan iya ɓoye maka ba, kaine kaɗai mutumin da nake ji a zuciyata, nasan ba kai ne na farko a rayuwata ba, amma tabbas kaine fatana na ƙarshe, babban fatana ga ubangiji ya barmin kai a tare da ni.” “Nima haka, fatana na kasance tare dake har abada Habibty, Allah Ya amsa mana.” “Amin.” Daga haka muka ci gaba da hirar my ta soyayya, kowa yana bayyana yanda yake jin ɗayansa a rai, yana bayyana yanda yake fatan kasancewa tare da shi har abada, sai wajen ƙarfe takwas anan sannna ya ce zai kwanta can goma ta gota, ya ce dani. “Habibty, ko xa ayi miki gyara ne anan?” Na ce. “A’a, share share ne kawai, kuma Yaya Rumaisa ta ce zata turu ayi, kawai ka bar musu key ɗin.” “Tom Habibtyna.” Haka muka yi sallama, kowa cike da so da ƙaunar ɗan uwansa, washe gari da safe bayan mun dawo daga massallaci na sake shiga kasuwa na siyo abinda xan iya siya, ni dai hankalina gaba ɗaga ya yi can nigeria kamar wani abun zan ɗauka, ina zaune a ɗakinmu bayan mun gama chat da Turaki, Sardauna ya faɗomin a rai, haka kawai na raya a zuciyata idan kuma ƙaddara ta sake haɗani da Sardauna fa, da sauri na ce. ‘Aina? Bana fatan kowacce ƙaddara ta sake haɗani da Sardauna.’ Wani ɓari na zuciyata ya ce. ‘Akwai mutuwa fa.’ “Kai innullahi wainna illahr raji’un, me yake damuna haka?” Na faɗa a fili ina miƙewa, gaba ɗaya wasu tunane tunane marasa daɗi nake yi, me ya kawo Sardauna tunani na gaba ɗaya, gaba ɗaya na ji zaman saudiyyan yasake fice min a rai, ko massallaci ban samu na sake leƙawa ba, Allah Allah nake washe gari ta yi ya zama saura kwana uku dawowarmu. Haka kuwa washe gari ta yi, tun safe na tafi massallaci sabida lokaci ya yi sauri, bani na dawo ba sai huɗu, haka na fita zagaye ni da su twins, har muka jira dare ya yi kasuwanni suka buɗe muka sake yin siyayyya kamar ko yaushe, wannan daren ya kasance dare mafi tsayi a rayuwata, sai naga kamar garin yaƙi wayewa, washe gari ina tashi na ce da Hajiya. “Saura kwana biyu.” Ta watsamin harara, sannan ta ce. “To ni bana farin ciki zan bar ƙasa mai tsarki, bana farin ciki ko kaɗan zan bar ƙasa da aka haifi shugabana annabi Muhammad (S.A.W) bana farin ciki zan koma nigeria ƙasa mai cike da tarin matsaloli, da Allah zai ɗauki raina a wannan ƙasar, da kuwa tabbas zan so hakan, ke da kike farin ciki sai ki yi ta yi.” “Ni Hajiya ba wani abu nake nufi ba.” “Kima nufi mana Nana, ni dai zan roƙi ubangiji ya sake dawo dani, ya ƙara ƙara dawo da ni, ke da kika zaɓi sakarci sai ki koma nigeria, zafin gari da hayaniyar jama’a ya isheki, bare azo ga rashin wuta, uwa uba matsalal tsaro, ko da kai ba a kamaka ba, zaka ji an kama wanda kasan wani na shi, idan baka ji ba zaka ji a radio, ko a social media, ko wannan fargabar kaɗai ta isheka, nan kina zaune cikin rahamar ubangiji, ko massallacin harami kika kalla abun da zai sanyaya miki rai ne, ya kwantar miki da hankali ya sa miki nutsuwa, amma ina ke miji miji ko? Sai ki yi ta yi, dan kin zo yanzu ba ki da tabbacin sake zuwa.” Jikina gaba ɗaya ya yi sanyi, tabbas Hajiya kam gaskiyya ta faɗa, kuma sheɗan ne yake tunzura zuciyata yake haifar min da rashin nutsuwa, ni dai a ko da yaushe ina bawa sheɗan dama shi ya sa duk matsala idan ga fuskanto ni nake shan wahala, sai na ji gaba ɗaya komawar ya fita a kaina, duk da tabbas nasan na yi addu’a iyakar addu’a, na yi kuka sosai da sosai, amma tabbas sheɗan yana raya min munanan abubuwa a zuciyata, tabbas a yanzu lokaci ne da zan yaƙi sheɗani dake zuciyata. Tun daga wannan lokacin na sa ƙarfi na tsarkake zuciyata, na fara sabuwar ibada kamar yau na sauka a birni, massallaci da nake tafiya sabida lokaci ya yi sauri, a yanzu na koma zuwa sabida kar lokaci ya ja, idan na shiga massallaci ba ni da abinda nake sai ibada, addu’o i ji nake kamar ban taɓa yi ba, gaba ɗaya zuciya ta ta yi laushi, na sake mai da hankali ga ibada. Sai dai duk abinda zanyi lokaci ya riga da ya tafi, dole mu koma nigeriya a gobe, sai na ji zuciyata ta yi rauni, bana son barin ƙasar gaba ɗaya, na koma na ci gaba da ibada sosai, daren ranar da zamu dawo haka muka kwana a massallaci ni da Hajiya muna addu’a muna kuka, muna roƙon Allah da ya sake dawo da mu a wani a lokacin, sai bayan asuba muka koma hotel din mu muka kwanta, tin da jirgin namu sai biyu na rana zai tashi, shigar dare zamuyi wa nigeria. Ƙarfe goma na safe muka tashi daga baccin da muka yi, muka fara shiri muna haɗa kayanmu, Hajiya na yi na zubar ƙwalla, tana ta nana ta addu’a ɗaya. “Ya Ubangiji ka kiramu gobe, ka sake kiran mu, Allah mun tuba Ya Allah.” A haka muka gama haɗa komai namu, bayan mun ci abinci, muka yi sallama da ɗakin mu na hotel, Hajiya ta kusa minti biyu tana kallon ɗakin tana zubar da hawaye, haka duk inda muka wuce sai ta ce. “Ya Allah ka kira mu gobr, ja sake kiran mu, Allah mun tuba Ya Allah.” A haka har muka ƙarasa filin jirgi, a lokacin da aka gama tantance kayanmu zamu wuce, sai da Hajiya ta saki zubar da wani hawayen, gaba ɗaga jikina ya yi sanyi, shikenan kuma sai Allah Ya sake kiranmu, idan muna da rabo. Allah ka kira mu ka amsa mana, a haka muka gama jira muka shiga jirgi. Ƙarfe takwas na dare jirginmu ya shiga nigeria. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (14.) Muna fitowa daga filin jirgi na fara baza ido ta ina zan ga Turaki, sai dai babu shi Yaya Ridwan ne a motarshi, sai Ra’is ma a tashi motar, ina cikin raba ido na ga shigowar motar Turaki, na sauke wata ajiyar zuciya a lokacin da yake fitowa daga motarsa, yana sanye da wata doguwar rigar jallabia ash kala, kanshi sanye da hula mai baƙi da ash, ya yi kyau sosai, ya yi fari ya yi ɓulɓul abunsa. Haka na ƙarasa inda yake ba kunya na rungume shi abuna, ya yi murmushi tare da faɗin. “Welcome Babytah, na yi kewarki sosai Habibty.” “Nima haka Habibynah.” Daidai lokacin twins suka ce. “Papah.” Ba shiri ya cika ni ta rugunmesu tare da faɗin. “My Babies.” Yaya Ridwan ne ya ce. “To mu dai zamu tafi, da alama nan zamu barku.” Hajiya ta ce. “A’a, aban tagwaye na tafi dasu, idan sun huta a dawo dasu.” Ra’is ya ce. “Gaskiyya dai kam.” “Me ya sa bazamu tafi dasu ba?” “To Habibty nima bana ce ba, kinji abinda suka ce, ko suna so muje mu huta ne.” “Tam, yanzu ko yaushe zaka zo.” Yaya Ridwan ya ce. “Gobe zamu shigo in sha Allah.” “Tom.” Na faɗa, tare da fara sa kayan mu a motar Turaki, yana taya ni, na Hajiya kuma a motar Yaya Ridwan, sai da kowa ya kammala sannan muka shiga mota muka fita a tare, sai dai muka yi nisa Turaki ya ce. “Habibty.” Na kalleshi, ina jin wani son sa yana huda zuciyata, so nake kawai muje gida mu sami ishashen lokaci tare dashi, sabida na yi matuƙar kewar shi. “Habibty an dawo.” “An dawo fa Habiby, wallahi na yi kewar ka kawai so nake mu koma gida, na yi ta kallonka.” “Nima haka Habibtyna, ina so a koda yaushe ki yi ta sona, karki daina dan Allah.” “Me zai sa na daina ni kuwa? Ai mutu ka raba.” Muna tafe muna shan hirarmu ta ƙauna har muka isa gidan, muna zuwa ya yi horn aka buɗe mana, daidai lokacin na duba wayata na ga ƙarfe tara da rabi daidai na dare, muna yi parking na buɗe na fito, shima ya fito ya fara sauko mana da kayanmu, ina fara taka ƙafata na ji zuciya tana wani irin bugu da ƙarfi, har sai da na runtse idona a daidai lokacin da nasa ƙafata a bakin ƙofar shiga falon, idona na kai kan wancan ƙofar da bama zama naga wajen da haske, na juyo na kalleshi na ce. “Naga haske?” “Aina?” Ya faɗa, yana shiga da jakar ciki. “Wancan part ɗin mana.” “Eyh.” Ya sake faɗa yana fita, ina tsaye na kasa gaba na kasa baya ya gama shiga da jakun kunan kayan nawa, sai da ya gama ya ce. “Ki shigo mana.” “Habiby ina maka magana ka yi min banza.” “Da yaushe? Me kika ce? Kuma anan zaki min maganar?” Hanyar part ɗin na ƙarasa na fara ƙoƙarin buɗewa. “Habibty mene haka kike yi ne wai? Ki nutsu mana.” Banza na yi da shi na fara murmurɗa ƙofar, ina fatan Allah Yasa ba abinds sheɗan ke ƙoƙarin raya min ba. “Wai me kike nema anan?” “Hasken mene a wajen?” “Hasken wuta mana, ko baki gani ba?” “Nagani, shi ya sa nake tambayarka me ya sa aka kunna haske a wajen.” “Shine na ce ki je na yi miki bayani.” Cika ƙofar na yi na nufi part ɗina, ina shiga na zauna akan kujera na haɗe rai ina jiran shi, yana shigowa ya zauna a kujerar da nake kai ya ce. “Habibty wai mene haka duk kika ɗaga hankalinki? Kinje kina ta buga can?” “Habiby waye acan ɗin, ni jikina ya bani mutum ne a wajen.” “Eyh Habibty mutum ce a wajen.” Na miƙe tsaye a tsorace. “Mutum? Wace?” “Habibty dan Allah ki fahimce ni.” “Wace kalal fahimta, wace irin fahimta kake so na yi maka?” “Kina ji, wallahil azim na rasa ta yanda zan faɗa miki tun kina nan, Habibty tun muna wancan gidan namu, Big Daddy ya ɗaura min aure.” Ji maganar na yi kamar an buga min guduma a akaina, wai an ɗaura masa aure, shine dalilin da yasa ya kaini aikin Hajji kenan, ni da mahaifiyata da ‘ya’yana? Ya kaini aikin hajji sabida na basu dama su ci amarci shi da matarsa? Shine zai siya ni da daɗin baki, me ya sa duk maza suke haka ne? Wai ni Nana yaushe zan ji daɗin rayuwa? Yaushe wahala zata yanke mini ne? Wan irin abu ne wanna Turaki ya yi min, ace ya tura ni aikin Hajji kawai ina dawo na tarar da shi da wata matar, to tukwicin aikin Hajji ne ƙarin auren? Ko kuma tukwicin ƙarin auren ne aikin Hajjin, ni bangane ba. “Habibty! Habibty!” Na ji muryarshi tana shiga kunnuwa na, sama sama. “Habibty dan Allah ki sauareni, ki ji me zance miki mana.” Na fara zubar da hawaye, ina jin wani ɗaci a raina, nama kasa magana sabida wani irin bugu da naji zuciyata na yi da wani irin ƙarfi, wanda zai iya cutar da lafiyata, da sauri na sami waje na zauna, na haɗa kai da gwiwa na fara janyo kuka, amma ina ya gagara zuwa, sai wani yaji yaji da nake a cikin idona, wani raɗaɗi da zafi, ga zazzafan bugu da zuciyata take yi. Hannuna ya fara shafawa yana faɗin. “Habibty, Nana, kina jina.” Kamar wacca aka tsikara na miƙe tsaye na ƙwace hannuna, sai da na kalli Turaki na kusa mintuna goma, kawai na juya na kalli ƙofar fita, na yi waje a guje, ba shiri ya biyo ni yana faɗin. “Habiby ki tsaya dan Allah, Habibty ina zaki?” Waje na nufa na fara ƙoƙarin buɗe ƙofa zan fita, Turaki ya yi saurin kama hannuna. “Habibty ina zaki a daren nan?” “Ka cika ni, ko ina nema wallahi gwanda naje, amma Turaki ba zan zauna a gidanka ba, bazan sake zama da kai ba, sabida kai macucine, kai mugu ne, ka zalunce ni, wallahi ban yafe maka ba.” “Hasbunallahu wani’imal wakil, Nana dan Allah ki fahimce ni, ki ji me zance miki dan girman Allah.” “Me zaka ce? Raina min hankalin zaka ci gaba da yi? Ka ce min Big Daddy ne ya yi maka aure, ko me? Ka yaudareni ka yi min ƙarya, a ko dayaushe ina tambayarka, amma sai ka ce zaka iya zama da a haka, ashe duk ƙarya ce, duk yaudara ce? Tun farko kasan bana haihuwa amma kazo ka yi min daɗin bakin cewa ka rayu da ni a haka, zaka aure ni a haka, amma kaje ka yi aure da wacca kake so, wacca kake tunanin zata haihu ta tara ma zuri’a, to ni zan tafi zan haƙura da rayuwa da kai, zan je na yi wata sabuwar rayuwa, ko da babu farin ciki a ciki.” “Nana dan girman Allah ki yi min kyakyawar fahimta, ƙarin aurena ba shi da nasaba ko wata alaƙa da rashin haihuwrki wallahi, ga yarinyar nan ki shiga ki ganta, ta faɗa miki gaskiyya.” “Har abada bana fatan Allah Ya haɗa idona da na ta, kai kanka Turaki wallahi bana son nasake ganim fuskarka, idan kana da haƙƙi akaina Allah Ya saka maka, idan ni nake da shi akanka na yafe maka, amma ka rabu dani, ka rabu da rayuwata, aure idan katashi ka auri goma su haifa ma ‘ya’ya dubu.” Na faɗa ina buɗe ƙofar, ya yi sauri ya riƙe ni ya yi baya da ni, yasa key ya kulle ƙofar. “Nana ba kya ganin dare ne?” “Ko menene tafiyata yafi min.” “Dan Allah ki yi haƙuri, ki bani dama na yi miki bayani.” “Bana son bayaninka, ka riƙe bazai amfane ni ba, ka rabu da ni dan Allah.” Na faɗa ina jingina da jikin gate ɗin, ba yanda Turaki bai yi ba na shiga ciki amma naƙi, na ce wallahi anan zan kwana asuba na yi na tafi gidanmu, sabida wani irin zafi da nake ji a cikin zuciyata, ko ganin Turaki bana son yi kwata kwata, babu abinda yake yawo a zuciyata sai zallan rashin mutunci da Turaki ya yi min, wai ya tura ni aikim Hajji sabida ya ci amarci, duk akan bana haihuwa, Allah Sarki ni, Allah ya kawo min mafita, amma tabbas nasha wahalal rayuwa, baya ga abubuwan da na fuskanta a rayuwata da Sardauna, yanzu ina fatan nasamu nustuwa da farin ciki, ina ganin kamar rayuwar wahala ta zata ƙare, kamar labarin zai shuɗe ashe yanzu ya fara, shikenan wahala da wahala ni Nana, cikin murya kuka na ce. “Allah na tuba Ya Allah, Allah karka maimaita min wahalal rayuwa da na shiga abaya Ya Allah, Allah na tuba Ya Ubangiji, Allah ka bani ƙarfin da zan fuskanci wannan rayuwar.” Haka na yi ta faman kuka, babu yanda Turaki bai yi ba, amma na yi banza dashi ko waigowa ma banyi ba, kawai so nake garin Allah Ya waye na tafi gidanmu, na je na yi kuka na gode Allah, Burina kawai Turaki ya sake ni, na yi iddah nagama na shiga wata rayuwar, amma tabbas har abada har gaba da abada ma babu ni babu wani auren. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (15). Da me zanji, Sardauna ya cuceni, wannan rashim haihuwar bazai barni na zauna a ko ina ba, daman ya faɗa ya ce bazai taɓa barina na aure wani ba, ga kalamansa sai tabbata suke, duk da yana halin jinya, amma Sardauna ya shuka mumunnan irin mai zafi a rayuwata, ya yi min SARTSE mai raɗaɗi cikin rayuwata, ya gana min azaba, ya cutar da ni, ina tsaye anan dare ya yi nisa, yanda nake tsaye haka Turaki yake tsaye yana kallona, ni kam nama juya masa baya, bayan wasu awowi ya matsu ya ce da ni. “Habibty dan Allah ki shiga ciki mu yi magana, ki tuna kin fa ce zaki yi min uziri akan komai, kar ki manta da kanki kika shaida irin son da nake miki, da kanki kika ce zaki rayu da ni duk tsanani da wuya, kin ce bazaki taɓa barina ba, sabida kin tabbatar da irin ƙaunar da nake miki, dan Allah ki sauƙaƙa zuciyarki, ku sanyaya ta karki yi min SARTSE a zuciyata. Habibty rashinki zazzafan SARTSE ne ga rayuwata dan Allah dan Annabi Habibty.” Maimakon sanyi, sai na ji wani zafi a maganganunsa, na maka masa wata uwar harara na juya baya, na sake rusa wani ihun ina faɗin. “Wallahi Turaki ka rabu da ni, ka ƙyaleni duk wasu maganganunka yaudara ne a ciki, ka ƙyale ni dan Allah.” “Babu ƙarya, babu yaudara, babu algus a dukkan maganata Nana, wallahi sonki nake kinsani, kim yarda, dan Allah ki bani dama na faɗa miki gaskiyya, na yi miki bayanin komai.” “Mitchewwww.” Na ja wani dogon tsaki, a raina na ce. ‘Dan ya mayar da ni sabuwar shashsha shine zai ce wai ya yi min bayani, da ya samu ya yi min kalamai shikenan zanji sanyi, su maza da sunga mace na son su shikenan sai su yi duk abinda suke so, sun san suna zuwa su yi mata daɗin baki shikenan, da raunin mu suke amafani wajen zaluntrarmu.’ Abu kamar wasa har aka fars kiraye kirayen sallah asuba, sai dai a yanzu na tsgunna daga jikin gate din, shima Turaki ya zauna daga gefe, har aka yi sallah muna nan, gari yanayin haske na fara bubbuga gate ɗin, Turaki ya fito bayan ya shiga yin sallah ya ce. “Habibty ki tsaya na sauke ki a da kain.” “Turaki wallahi ba zan shiga motar ka ba, ka rabh da ni dan Allah, ka buɗe min na tafi ko na haura ta sama wallahi.” “To ka taki motar nan dan Allah ki hau.” “Na bar maka kayarka, ai daman da kuɗinka ka siya, to bana so.” Na faɗa ina ƙoƙarin fara ɗane gate ɗin na haura, ganin ina ƙoƙarin hawa gate ɗin ya sa Turaki ya ce. “Bari na buɗe miki, amma dan Allah ki karɓi wannan ki yi na mota.” “Mitchewwww.” Na sake jan wani tsaki, sannan na matsa gefe ya buɗe, yana buɗewa na fita na fara tafiya, tin kafin naje bakin titi ma fara gajiya amma haka na daure na ci gaba da tafiya, ni da na fito kafin bakwai amma har tara ban ƙarasa gida ba, duk na gaji na fita hayyacina, fuskata ta yi ja tana fitar da wani gumin wahala, ina tafe ina hutawa, har na ƙaraso cikin unguwarmu, nasa mayafina na rufe fuska ta yanda babu wanda zai ganni ya gane ni, a haka har na shiga gidanmu, wanda yake cike da mutane masu shigawar Hajiya, kasamcewar jiya saukar dare ce, ina shiga ko sallama banyi ba na faɗa ɗakim gadom Hajiya, inda naga twins a kwance suna bacci, faɗawa na yi kan gadon daga gefe na fara kuka, ina jin Hajiya tana cewa. “Waye ya shigo? Waye.” Amma ta ji shiru, muryar Maman Amir na ji tana cewa. “Anya kuwa Hajiya wani ya shigo, da an shigo ai nan za ayu.” Hajiya ta ce. “Wallahi kamar sautin tafiya na ji.” “Gaskiyya ba kowa, amma bari a duba.” Ina jinta ta gama leƙe leƙen ta tsakar gida, taje ta tura ƙofar waje ta dawo, ni kam kuka na ke yi ƙasa ƙasa, idona yanayin min zafi ma rashin bacci ga kuma uwar gajiya, ga gajiyar zama a jirgi, ga rabin kwana a tsaye, ga kuma uwar tafiya da na yi a ƙasa. Ba jimawa wani wahalallen bacci marar daɗi ya ɗaukeni, wanda banyi shi cikin daɗin rai ba, ina cikin baccin na ji ana cewa. “Maamah! Maamah.” Na buɗe idona naga twins ne, na maka musu uwar harara na ce. “Ku fita ku tafi wajen Hajiya.” Ba musu suka sauka suka yi wajen Hajiya suna kuka, a loakacin na ji muryar Yaya Rumaisa tana cewa. “Daman suna nan?” “Eyh nan muka yo da su, jarabar uwarsu wazai iya.” “Aifa ana can ana tashin hankali, ni na rasa me ya sa Turaki yake tsoron Nana wallahi, idan suka jera sai ki gansu kamar ‘ya da uba, amma idan kika ga yanda yake rawar jiki idan ta yi masa magana sai ya baki takaici.” Hajiya ta ce. “Aini bana ma iya kallon shiriritarsu, yanzu dai suna can suna fama, tun muna can yarinyar nan ta fuskanci wani abu ya faru, ta bi ta ɗaga hankalinta, kai kishi masifa ne.” “Babba ba ƙarama ba Hajiya, amma ita nata da iskanci.” Wani abu na ji ya tokaremin maƙoshi, wato duk sun san da zancen auren na shi, shine ko a jikinsu lallai mutanen nan, to wallahi dani suke zancen Turaki ne ko shine autan maza na haƙura da shi, aure kam na yi abinda zan iya Allah Ya bada lada, amma tabbas na gama, na zauna na yi rayuwata na kula da tarbiyar twins, na sama musu farin ciki, shine kawai. Ji na yi jikina yanayi min wani irin tsami, ba shiri na tashi ma fito zan shiga kicin na ɗaura ruwa, na ji salatin Hajiya, sai da ta gama rangaɗa salati sannan ta ce. “Ke yaushe kika shigo gidan nan?” Na yi mata wani kallo, na ce. “Tun safe.” “Me kike yi to anan? Ina gidan naki?” “Ya sake ni.” Na faɗa ima fara juyewa ruwan zafin da nasamu akam tukunya, cikin bawon wanka. “Innullahi wa’inna illahir raji’un, Rumaisa fito kiji wani mugun zanci.” Ɗaukan ruwa na yi, na nufi bakin famfon na kuna masa ruwa sanyi ya fara zuba, Yaya Rumaisa ta ce. “Nana kin cuci kanki, akam kishin banza kin rasa mijinki, miji mai sonki, nagartacce.” “Na rasa ɗin, ke kije ki aure shi.” Na faɗa ina ƙoƙarim shiga toilet. “Sai kinci gidanku, kuma ki yi duk abinda kika ga dama, in Allah Ya yarda bazan sake sa baki a lamarinki ba.” “Kar ki sa ɗin.” Na faɗa tare da shigewa ban ɗaki, a yanda nake jin zuciyata cikkn gidanmu Hajiya kawai banza iya tsyaawa mu yi musayar yawo ba, amma duk kansu a wuya nake da su, wai sun san Turaki zai yi aure, amma ko a jikinsu suna jin daɗi anyi min kishiya, rashim haihuwata duk bai dame su ba. Haka na yi wa kaina ruwan zafi sosai, sannan na watsa ma fito, cikin jakar kayan Hajiya na duba doguwar riga na ɗauka na sanya, na dawo na zauna, dole naje gidan Turaki na ɗauko kayana, da waya ta da duk wani abu nawa, kuma babu wani a gidan nan da zan sanya dan duk basu da gaskiyya, ina cikin ɗakin na ji zuwan Yaya Radiya, tana zama Hajiya ta ce da ita. “Kinji yarinyr nan ta kashe auren, wai ya sake ta.” “Kai innullahi, yanzu tana ina?” “Tana ciki, amma karki fara zuwa wajenta, yanzu zata zage ki kamar yanda ta yi min.” Yaya Rumaisa ta faɗa, Yaya Radiya ta ce. “Zagi kuma?” “Ga Hajiya nan ki tambayeta, har da ce min naje na auri Turakin, tsabar ta raina ni.” “Lallai Nana, to ta ci kanta ita ta sani, babu wanda zai mata magana, ita ta yi asarar miji ba wani ba, har ta manta wahalal da tasha wajen Sardauna, tazo nan ta sami gata amma ina, shine akan ya ƙara aure take wannan abun.” Ni haushin Yaya Radiya ma nasake ji da ta gama wannan maganar, na miƙe tsaye na ce. “Ni Nana na gama shan wahala a rayuwa, zan tsaya na yi rayuwa cikin farin ciki ko da kuwa babu taimakon kowa a ciki.” Ina faɗin haka na fito daga ɗakin, na shiga ɗakin da suke ciki, Yaya Radiya ta ce. “Sannunki Nana, kin kyauta kin kashe aurenki.” “Hhhhmmm, yanzu ku abinda kuka yi kyautawa ne? Akan bana haihuwa shine kuka bada gudummawar ayi min kishiya? Bance baya ƙoƙarin zama dani ba, amma a zaman ba dole sa ya ji bazai iya ba sai ya sake ni, yafi min sauƙi akan yaje ya yi min kishiya, rashin haihuwa ai na Allah ne, wallahi kun ban mamaki kuma kun ban kunya, ina matsayin ƙanwarku jini ɗaya, amma akan abin duniya koka goyi bayan ayi min kishiya.” “Ke Nana kama bakinki? Kina tunanin akwai wani abun duniya da zai sa ‘yan uwanki su cutar da ke?” “To Hajiya mene? Duk sun sa za ayi min kishiya sabida bana haihuwa, amma babu wanda ya sanar dani.” “Wai waye ya ce miki akan rashin haihuwa aka yi miki kishiya? Da alama baki samu zama da mijinki ba, kawai kina ganin mace a gidan kika takura ya sake ki kenan?” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (16). “Nifa Hajiya ban ta kura shi ba, kawai mafita ta na duba, duk kun haɗe min kai akan abun duniya, babu wacca zata fahimci halin da nake ciki a cikin ku? Da ace ina haihuwa dan Turaki ya ƙara aure babu abinda zai sanya ni na bar gidansa, amma babu haihuwa duk soyayyar da yake min wacce ya aura tana fara haihuwa shikenan, namiji ne fa.” Yaya Ridwan ne ya shigo gidan shi da matarsa, bayan mun gaisa ya ce. “Nana yana ganki.” Na yi shiru ban ce komai ba, Hajiya ta ce. “Ta haƙura da auren.” Ya ce. “Kina ganin haka zai fi?” Na gyaɗa kai alamar. ‘Eyh.’ Ya ce. “Daman tun a farko na faɗawa Hajiya cewar idan har kika ce bazaki zauna ba, to babu wanda zai takura miki, domin rayuwarki ce kuma ‘yancin ki ne, amma kafin ki yanke kowanne hukunci ya kamata ki zauna ki yi tunani, wallahi muma bamu san da ƙarin auren ba sai gab da tafiyarku, Hajiya mai sai a filin jirgi na sanar da ita, daga ni har Ra’is bamu goyi bayan ki ci gaba da zama da Turaki ba idan ba kya so, duk abinda wani zai faɗa miki ki tsaya akan abinda zuciyarki ta yarda dashi, wanda kinsan bai saɓawa addini ba, Nana ana yin kishiya, ana zama da kishiya, amma ke taki tazo a wani irin yanayi na daban, duk da ba cewa aka yi bazaki taɓa haihuwa ba, amma haihuwar ki ta yi jinkiri, kuma babu lallai babu dole a lamarin ubangiji, amma ki tuna da bambamci dake tsakanin aurenki na farko da na biyu, ki haƙa ki yi wa kanki alƙalancin da kike ganin zai fi.” “Ni dai Yaya na haƙura da auren Turaki kawai, bazan iya jure ganin shi da wata matar ba, har ta haifa masa yara ni ina zaune, wallahi duk soyayyar da ta ‘yan uwansa da nake gani yanzu duk sai ta bar kaina, shi kuma Big Daddy Allah Ya saka min, wallahi bazan yafe masa ba, tun farko ba sona yake ba, gwanda na haƙura na bar musu familinus tun da daman ba can aka haife ni ba.” Na faɗa ina goge ƙwallar da ta taru a idona, Yaya Rumaisa ta ce. “Nana kina ganin haka zaifi?” “Eyh Yaya zaifi, ni abun duniyar Turaki baya gabana, a yanzu ina da ‘yanci ina da damar da zauna na riƙe kaina, na riƙe ‘ya’yana, bama iya Turaki tabbas aure na haƙura da shi har abada, wanda na yi Allah Ya bada lada.” “Amma me ya sa?” Yaya Rumaisa ta sake tambayata. “Akwai mutanen da kwata kwata basu da dace a soyayya, wasu a aure, wasu a rayuwa ma baki ɗaya, aurena na farko na ya kasance auren da na sha wahala mafi yawa a rayuwata, na biyu na sami farin ciki amma matsalal haihuwa taƙi barina na zauna, idan na sake wani a gaba ma matsalal rashin haihuwar ba bari na za ta yi ba, bazan sake yarda da wani daɗin bakin namiji ba, har sai dai idan wanda ba ya haihuwa shima na samu, amma muddin namiji yana haihuwa babu abinda zai sanya ya zauna da macen da ba ta haihuwa, da me zanji? Ciwo da raɗaɗin rashin haihuwa? Ko kuma da zama da kishiya? Na haƙura wallahi.” Na faɗa ina kuka, tare da tashi na koma cikin ɗaki. Tun jiya sai yanzu na sami damar yin kuka, ai kuwa na saki baki na dinga yin shi da ƙarfi har cikin zuciyata, sai da na yi ishashe sannan na samu bacci ya ɗauke ni, wanda ban farka ba sai wajen ƙarfe biyu. Ina tashi na sake ɗaura alwala na yi sallah na dawo ɗaki na sake kwanciya, su twins suna gefe suna wasa ni kuma ina kallonsu, wani irin so da ƙaunar su yana taɓa min zuciya, a raina na ce. ‘Ko da babu aure akaina babu me raba ni da ‘ya’yana, zan baku kulawa, soyayya da gata.’ A daidai lokacin na ji sallamar Yaya Radiya, hannunta riƙe da plate ɗin abinci, na kauda kaina gefe ina jin ɓacin rai, duk da Yaya Ridwan ya yi min bayanin komai amma kawai na ji haushinsu, sun nuna son abun duniya. “Nana.” Ta kira sunana, na waigo na kalle ta ban tanka mata ba, ta zuane gefen gadon tana kallona. “Ki tashi kici abincin?” “Na ƙoshi.” “Bangane kin ƙoshi ba, me kika ci?” “Ina ruwanku idan ma naci wani abun? Ina ba kun zaɓi dukiyar Turaki ba to mene a ciki?” “Nana wai mene haka? Ke kina tunanin akwai wani kuɗi ko wani abu na duniya da zamu so da ‘yar uwarmu? Nana muma fa matane mun san komai, munsan raɗaɗi da dukkan zafin kishi, amma baki tsaya kin saurari Turaki ba kamar yanda muka saurareshi, kuma a lokacin sai da muka ce dashi idan kin amince zaki zauna da shi haka muke so, idan baki zauna ba haka Allah Ya yi, amma zamu nusar dake cewar zama da auren yafi zama babu auren, amma wallahi bamu zaɓi abin duniya sama dake ba Nana.” “To ni bazan zauna ba ya sake ni kawai, kinsan irin alƙwarin da ya dinga yi min? Yana cewa zai zauna da ni ko babu haihuwa, ni kaɗai ce a zuciyarsa, ni kaɗai yake so ashe duk ƙarya ne. Ni ɓoye ɓoyen da ƙaryace ƙaryacen da ya yi min sunfi ƙona raina, haba baya sonta ya tare da ita, a baya son nata ya yi mata part daidai da nawa, a baya son nata zaki ga ta haihu, maza munafukai ne, duk halinsu ɗaya wallahi, natsani Turaki ko sunansa bana son tunawa, SARTSEN da Turaki ya yi min yafi wanda Sardauna ya yi min a rayuwa.” “A’a Nana babu haɗi wallahi, kawai a yanzu kina cikin zafin zuciya ne, amma idan kika nustu kika sami sauƙi komai zai daidaitar miki in sha Allah Nana, mu dai ‘yan uwanki ne, kisani a ko wanne lokaci muna tare da ke, kuma zamu kasance tare dake, kuma zamu tsaya miki mu baku dukkan ƙwarin gwiwa da ƙarfi a dukkan hukuncin da kika yanke.” Zuciyata ta yi rauni, jikina ya yi sanyi sosai da sosai, na ce. “Na gode Yaya.” “Bakomai Nana, ki ci abincin kinji.” Karɓar abincin na yi na fara ci, duk da bakin babu wani daɗi babu ɗanɗano haka na dinga tusa abincin kamar in shan magani, a haka na ci abincin sosai, ima cikin cin abinci Yaya Ridwan ya shigo ya kalleni, ya kira sunana. “Nana!” Na ɗaga kai na kalleshi, shima kallona yake sannan ya ce. “Turaki ya ce ba sake ki ba, da gaske ne ko a’a?” “Bai sake ni ba, amma na haƙura da aurensa kawai ku ce ya sake ni.” “Kina ganin sakin yafi?” “Eyh yafi.” “Shikenan, gashinan a waje idan ya shigo sai ki faɗa masa, duk yanda kuka yanke.” Ya faɗa tare da fita, Yaya Radiya ma ta ɗauki plate ɗin ta fita, yana shigowa twins suka yi kansa suna faɗin. “Papa.” Ya rungumesu ya ce. “Twins ɗin papa.” “Papa Good morning.” “Morning daughters.” “Maamah Papa.” Suka faɗa suna nuna min shi, na watsa musu uwar harara na ce. “To ba ubanku ba ne, ku matsa daga kusa da shi.” Na faɗa ina janyo su, ya riƙe su yana faɗin. “Haba Habibty, mene haka?” Banza na yi da shi na ci gaba da jan ‘ya’yana, su kuma suna wani manne masa kamar cingam, sai da na daka musu wata uwar tsawa na ce. “Dan ubanku ku cika shi, baku da wata alaƙa da shi ta kusa ko ta na nesa, ba ubanku ba ne kuma ba mijin uwarku ba ne.” Ba shiri ya cika su ya matso kusa da ni, na miƙi ina shirin matsawa ya kama hannu. “Habibty dan Allah ki saurareni, mene amfanin wannan duka, me ya sa kike haka ki tsaya ki fahimce ni ki yi min adalci dan Allah.” Na fara ƙoƙarin fisge jikina ina son miƙewa, ni ko magana sa shi ma bana so, kallon fuskarsa ma bana so, gaba ɗaya kamar annu sanya min soyayyar Turaki a zuciyata zuwa zazzafar ƙiyayyarsa, na ci gaba da mutsu mutsu na ina son ƙwacewa. “Wai bazaki ji ni ba?” Na gyaɗa mai sa kai kawai, dan bazan iya magana da shi ba. “Habibty karku hukunta nu ta hanyar ƙaurace min, ki yi min ko wanne hukunci ne dan Allah, amma karki haramtamin kanki, karki haramtamin ganinki, idan babu ke ban san idan zan kama ba, bansaniba.” Ji na yi inama zan iya yin magana da shi, na ce masa Yakama ko ina, da na faɗa masa maganganun da bazai iya ɗauka a kunnesa ba, da na faɗa masa zallan ƙiyayyarsa da nake ji a zuciyata, amma tabbas shiru na shine alheri a gareshi, ya cika ni ya sake ni kawai, domin bana son sa ko ɗis a cikin zuciyata. “Ki yi magana dan Allah, ki ce wani abu Habibty, idan baki yi magana ba shirun zai azabatar da ni, shirun ki azaba ne agareni dan Allah.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (17). Da ƙyar na iya buɗe baki na ce. “Ka cika ni Turaki, ka sake ni dan Allah.” Ya girgiza kai ya ce. “Dan Allah a’a Habibty bazan iya ba, bazan iya rayuwa babu ke ba, ki ce farin cikina, ke ce dukkan rayuwata dan Allah.” “Turaki na gaji da waɗan nan kalaman yaudarar naka, nagaji da wannan kalaman naka na ƙarya wallahi nagaji, bazan iya ɗaukan son zuciya irin naka ba, ka sake ni kawai dan Allah.” “Habibty bazan iya ba, bazan sake ba wallahi.” “Wallahi sai ka sake ni kaji ma na rantse.” “Haba Habibty me ya sa zaki yi min haka, ki yi min kowanme irin hukunci ne amma banda wannan, bazan iya ɗauka ba wallahi, ko kusa ko alama bazan iya rayuwa babu ke ba, bazan iya ba, ke nake so ke kaɗai ke ce nake so, ke ce a raina.” “Ni kaɗai kake so ka aureta? Ko iya ‘ya’ya kake si ta haifa ma? A baka son nata ka yi mata part tun a gina gidan? A baka son nata ka ajiye ta a gidanka ka tare da ita? A baka son nata zata haifa ma ‘ya’ya, namiji ne fa kai Turaki ƙanin ajali, ko Islaha ma da kanka ka ce bata baka fuska ba amma ka je wajenta, shine yanzu za ka raina min hankali, zaka zo ka ce zaka yaudare ni da wasu kalaman na ƙarya? Ai ƙaryarka na gama ɗauka, na ɗauki waccan zan ɗauka, ka ce da ni zaka rayu da ni, zaka mutu dani da haihuwa ko ba haihuwa, amma duk ka kasa, wallahi ka cutar dani ka azabtar da ni Allah Yasaka min, amma wallahi Turaki ki kaɗai ka yi saura a duniya na haƙura da kai, na haƙura da aurenka.” “Wallahi Habibty ba son ta nake ba.” Na ɗaga masa hannu cikin fushi na ce. “Dakata Turaki, nagaji da jin waɗan nan maganganun wai ba sonta kake ba, idan baka sonta shi wanda ya aura ma ai yana sonta, kuma baya sona, to Turaki na bar muku ahalinku, ai ba dole sai na rayu cikinku ba, ko da dole? Wallahi Turaki ganinka ma bana son na yi, ka yaudareni.” “Habibty ban yaudareki ba wallahi, ki yi haƙuri.” “Ka sake ni saki uku, sannan ka tashi ka fita zama da kai nagama har abada, duk halinku ɗaya, maza mugaye ne ku kanku kawai kuka sani.” “Haba Nana, wallahi ban kanmu muka sani ba, munsan kowa, nasan abinda ya faru ba a kyauta miki ba, an cutar dake, amma dan Allah k saurareni ba abinda ba shi da mafita, wallahi a shirye nake da na yi duk wani abu da kike so wanda zai sanya ki farin ciki wallahi. Kece nake so ke ɗaya babu wata, a yau da gobe da jibi har abada Nana, dan girman Allah karki hukunta ni ta hanyar cewa na rabu da ke, wallahi bazan iya ba.” “Ai daman bazaka iya ba.” Na tare shi cikin fusata, sabida jin yanda kalamansa suke neman raunatar da banzar zuciya irin tawa, su maza da sun sami raunin mace shikenan ta kaɗe, ta bushe. “A son zuciya irin naka sai ka ƙara min kishiya kuma ka ce na ci gaba da zama da kai, wai kana sona, ni kaɗai ce a ranka, as how? Idan nu kaɗai ce a ranka zaka zauna da ita tun tafiyata, kana bata ci, kana bata sha, kana bata dukkan lokacinka, kai burinka ta haifa ma ‘ya’ya, to sai mene wai a ciki? Ni bana haihuwa haka Allah Ya yi dani, bani na ɗaurawa kaina ba Allah ne ya ɗaura min, ta sanadiyar ɗan uwanka me son zuciya, amna ko haka baku gani ba, da shi Big Daddy da ya aura ma, idonku ya rufe ku sami jika to Allah Ya bada masu albarka, au daɗinta ba ita mata bane basa haihuwa, akwai maza da yawa da basa haihuwa, zanje na nema cikinsu mu yi auren mu babu wani tashin hankali ba hayaniya, ba ƙiyayya daga ‘yan uwa miji, me na yi masa da yatsaneni haka? Wani laifi na taɓa masa bayan ma duk kune kuka yi min laifi, amma ya tsaneni kuma ya yi alƙwarin ba zan zauna a gidan mijina ni kaɗai ba, to daɗinta shima ya haifi ‘ya’yamata gasu Seemah da Lamrah nan, bana fatan haƙƙina ya bi su tunda basu yi min komai ba, amma tabbas idan ina da haƙƙi akan Big Daddy sai Allah Ya yi min sakayya, sabida wani girma da Allah Ya bashi a cikin ku sai ya ce ga yanda yake so ayi, wannan mulkin mallakane ko me? To ni bazan iya ci gaba da zama a ƙarkashin mulkinsa ba, wallahi ko sabida Big Daddy dole na haƙura da kai, nagaji da wannan wahala rayuwa, gaba ɗaya aure wahala ce a gareni, damuwa ce, dame zanji, ko da lalura da aka ƙaƙabamin ta isheni, ta isa ta sani a damuwa. Ina son naji daɗi a rayuwata nima, ina so nasan cewa ni macece mai ‘yanci, na gode maka sosai da ka yi namijin koƙari wajen tabbatar min da farin ciki, amma a wannan gaɓar tabbas bazan haƙura ba, nagama aure da kai Turaki, ga amarya can Allah Ya baku zuri’a ta gari ɗayyaba.” “Wallahi bazan iya rabuwa dake ba, zanyi komai da na saki farin ciki, zan haƙura da komai da na rayu dake ne, ko da kuwa ‘ya’yan da kike tunani ne, zanje na yi abinda nima bazan haihu ba shikenan ko? Sai mu yi ta zama ba ‘ya’yan, twins sun ishemu.” Na ɗaga kai na kalleshi, wai zai je ya yi abinda shima ba zai haihu ba, kaman dagaske amma nasan da cewar maza dai macuta ne, namiji tsamiya ne, idan ya jiƙo ya ishe kowa ya sha, dan haka bazan sake gangancin sake yarda da wani daɗin bakim namiji ba, bama iya Turaki ba dua maza, dan babu gaskiyya a maganar su sai zallan san zuciya, kuma duka haka suke. Wallahi sunfi mata rashin tausayi, basu da tausayi akan son zuciyarsu, idan abu ya yi musu to ya yi musu ba ruwansu. “Habibty zan tabbatar miki da cewar tunaninki ba haka bane, mu maza ba haka muke ba, ba duka maza ke da son zuciya ba, zan tabbatar miki da idan namiji yana son mace to yana sonta har abada, zan tabbatar miki cewa dukkan namiji ɗan goyo ne, wallahu Habibty bazan taɓa saka miki da wani abu ba face alheri, ina sonki kuma zan ci gaba da sonki, za kiga hallaci Habibty, dan Allah ki janye kalaman sakin nan.” “Turaki ko me zaka yi ka yi, amma ni bazan sake zama da kai ba, ba iya ƙarin auren ka ba nagaji da zama idan ba a sona, Big Daddynku mutum ne mai son zuciya, idan yana kana da shi kai ne na shi, idan baka da shi kai bare ne, duk abinda Bilkisu ta yi bai taɓa tanka mata ba, bai taɓa zama a kanta ba, duk rashin mutuncin su Islaha bai taɓa zama akansu ba, sabida su ‘ya’yan wasu ne, ni kuma ana ganin ni ba ‘yar kowa ba ce, ubana ba wani ba ne shi ya sa duk zama ni, har da ƙara ma aure sabida ban cancanci zama da kai ba? Sabida darajata ba ta kai taka ba.” “Habibty duk wanda ya faɗa miki wannan ƙarya ne, karki saka wannan tunanin a ranki dan Allah.” “Hhmmm, Turaki wane dare ne jemage bai gani ba? Duk abinda yake faruwa banda masaniya ne? Dan bantaɓa faɗa ma ba? Na duba irin soyayya da kulawar da nake samu daga wajenka, shi ya sa na cirw komai a raina na kuma yi alƙwarin zan baka farin ciki da zai mantar da kai dukkan damuwar dake kake ciki. Tun lokacin ɗauko su twins da kunnena na ji wayar da kuke yi da Big Daddy yana umartaka akan kar ka kuskura ka kawo ‘ya’yan nan cikin gidanka, bayan nan na duba wayarka na ga irin maganganun da kuke yi da shi, duk ai bata ni da iyayena da yake yi duk nagani, har lokacin da ya sanar da kai lallai ka ƙara aure, Turaki naga message ɗin da ya ce Bana son wannan yarinyar da kake aure, naga message ɗin da idona, duk irin maganganun na ƙi da yake faɗi a kaina nagan su Turaki, na zaɓi na ɓoye duk wata damuwa ta sabida naga yanda shi kanshi kake tirje masa kake nuna masa son da kake min, da muhimmanci na, shi ya sa na zaɓi na baka farin ciki na mantar da kai duk wata damuwa a rayuwa. Dan haka ni a yanzu na gaji na gwammaci na kawo maka ƙarshen komai, tunda har ka biyewa son zuciya kaima, ka zaɓi ka cutar da ni, ka karya dukkan yarda da amanar da na baka, ka ci amanar yarda, wallahi Turaki ko ganinka bana son yi, ko wata muryarka ko wani abu da ya shafeka, ka rabu da ni dan Allah ka sake ni.” “Wallahi Habibty bazan iya sakin ki ba, bazan iya rabuwa dake ba, bazan iya rayuwa da wata ba idan bake ba, ina son ki.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (18). “Sai ka yi ta son nawa, amma dai zama da kai ni Nana na gama shi har abada.” Ina faɗin haka na fito daga ɗakin, na shiga ban ɗaki na fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya na zallan tausayin kai na, me na yi ne da duk aka tsane ni a rayuwa, ko dan ina son rayuwar aure shi ya sa bana dacewa, ko ya aka yi ne? Haka na yi ta faman tunani kala kala a cikin toilet ɗin nan, daga ƙarshe na watsa ruwa na fito, a lokacin da na fito baya nan, kuma ya fita da twins a raina na ce. ‘Wallahi sai ka dawo da su.’ Wata doguwar riga na sake ɗauka cin kayan Hajiya na sanya, dole sai naje na kwashe kayana duka a gidan Turaki sabida nasami na sawa, kuma idan babu kayana a gidan sai nafi ƙoƙari wajen cire Turaki a raina, sabida a yanzu babban burina shine na cire Turaki a raina, na fuskanci sabuwar rayuwa na manta da duk abinda ya faru da ni a baya, tabbas a yanzu lokacin kuka ya wuce min, lokacin shiga ciwon damuwa ya wuce min, lokaci ne da zan miƙi tsaye na tsaya da ƙafafuna na fuskanci gaskiyyar cewa ni macece, kuma rauni na shine rashin haihuwa, sai dai banzan taɓa bari wannan raunin nawa ya zama ajalina ba, na gama yarda da maza, namiji ya gama yi min SARTSE. Sai da na yi sallar la’asar sannan na fito falo, har lokacin su twins basu dawo ba, na kalli Hajiya na ce. “Ina son zanje na kwaso dukkan kayana dake gidan Turaki.” “Auren ya ƙare ne?” “Eyh Hajiya ya ƙare, bazan iya zama da Turaki ba ya cutar da zuciyata.” “Tom Nana, amma dai ki ƙara nazari,karki cutar da kanki da saninki, idan kika yi haƙuri komai zai daidaita, idan kuma kin haƙura ne Allah Ya baki wanda yafi shi alheri.” “Amin Hajiya, amma na haƙura.” “To yanzu kece zaki kwaso kayan? Ko Ra’is zaki sanya.” “Sai dai muje da Ra’is ɗin, iyakacin kayan sawa ne zan kwaso, sauran inaga duk nasane.” “To babu damuwa, sai ki kirashi ki sanar masa.” “Hatta wayata tana can Hajiya, sai dai ki bani taki.” Ba ta ce komai ba ta miƙomin wayarta, na buga lambar Ra’is ya ɗauka, yana ɗagawa na ce. “Kazo gida ina nemanka.” “Wane gidan?” “Gidan ubana.” Na faɗa tare da kashe wayar, na ajiye ta a gefe na kwanta akan kujerar da nake zaune, sai gab da magariba ya shigo gidan, kallo ɗaya na masa na ɗauke kai, Hajiya ta ce. “Gashinan yazo kuma kin ɗauke kai.” “Kaina ne ki yi min ciwo.” Na faɗa, Hajiya ta ce. “Gidan mijinta zaka kai ta, zata kwaso kayanta.” “Tam.” Ya faɗa kawai tare da miƙewa ya fice, nima na miƙe adaddafe na bi bayansa muka yi waje, ina shiga mota na ce. “Allah Sarki rayuwa, kamar jiya mukaje kwaso kaya gidan Sardauna, wai gashi yau zamuje gidan Turaki.” Tafiya muke ba wanda ya ce da wani ƙala, har muka isa ƙofar gidan, zai shiga da motar na ce. “Ka barta anan mana?” “A’a mu shiga dai.” Ya yi hon me gadi ya buɗe masa muka shiga, muna shiga na fito na yi ɓangaren da yake nawa, komai yana nan yanda na barshi jiya, jaka ta na fara ɗauka na duba wayata da komai nawa a ciki, na ɗauka na nunawa Ra’is jakunkunan da na dawo dasu na ce. “Kaga waɗan nan.” Ya ɗauka ni kuma na yi ciki, na sauke akwati na zuba kayana duka, sannna na sauke wata na fara zuba kayansu twins, sai da na cika su duka sannan na fito da su falo, Ra’is yaja ya fita. Ina shirin fita na ji an shigo part ɗin nawa, an buga ƙofa fa ƙarfi. “Wai wace ke? Me kike ji da shi? Wace irin macece ke mai sonki?” Kamar bazan waigo ba, na waigo dai na sauke idona akan wata yarinya da bazata wuce sa’a ta ba, na kai idona saitin idanunta na ga sunyi ja alamun ta ci kuka ta gode Allah, ɗauke idona na yi daga kallonta na nemi hanya zan fita, ta sa hannu ta riƙe ni ta jawo ni baya, cikin wani irin zafin rai na sa hannu na ɗauke wata wani zazzafan mari, ina wuci na ce. “Ko da wasa karki kuskura ki sake kai hannu jikina, ni ba sa’arki ba ce.” Kamar jira take ta fashe da kuka, cikik kuka ta ce. “Me kike taƙama da shi? Da kike azabtar da rayuwar aurena, idan bazaki zauna da kishiya ba karki zauna ɗin, amma ki ƙyale min miji dan Allah, tun aurenmu har yau ban taɓa samun kalma ko ɗaya daga bakinsa ba, ranar da kika dawo ina sa ran komai zai ƙare, amma kika ƙara hargitsa komai.” Kalmar mijina da ta ce ta haifar min da wani zafi a cikin zuciyata, na kama ƙofa na buɗe na fita, ina fita na tarar da Ra’is yana zuba kayan a cikin mota. Na buɗe motar na shiga shi kuma ya tsaya yana ci gaba da zuba akwatin a motar, daidai lokacin Turaki ya shigo da motarsa, na haɗe rai kaman ban ganshi ba Ra’is ya ƙarasa kusa dashi yana faɗin. “Yaya Turaki barka da dawowa.” Hannu ya miƙa masa yana faɗin. “Barka Ra’is me ya faru?.” “Na rako ta ne ta kwaso kayanta.” Na sa hannu na zuge glass ɗin motar, sabida ma na daina jin me suke cewa, sai dai ina ganinsu suna magana, ina ganin Turaki ya tunkaro motar na haɗe rai gaba ɗaya, ya fara buga glass ɗin amma na yi banza da shi kamar bangani ba. Sai da Ra’is ya buɗe mai motar da key ɗin hannunsa ya shigo, kafin ya ƙarasa shigowa na ce. “Dan Allah Turaki karka ɓata lokacinka anan, kaje matarka na buƙatarka, ka rabu da ni da rayuwata dan Allah, a yanzu ka wuce a rayuwata kazama tarihi, dan haka ka rabu da ni na fuskanci sabuwar rayuwata dan Allah.” “Amma ki sani Nana bazan taɓa rabuwa dake ba, bazan taɓa sakin ki ba.” “Ai idan kafi ƙarfina baka fi ƙarfin hukuma ba, dan haka zan shigar da kai ƙara.” Ina faɗin haka na ce da Ra’is. “Zaka shigo ne ko na fitar ma daga mota?” Simsim ya shigo ya tada motar muka tafi, har muka isa gida bance masa komai ba, ina shiga gida na kama kunnen twins na murɗe suka fara kuka, suna kuka na ce musu. “Duk ranar da kuka sake kuka ƙarabin Turaki wallahi sai na zane ku, dan ubanku baku da wata alaƙa da shi, ba ubanka ba ne shi.” “Kin haɗa kanki da aiki, dan ba abinda zasu gane.” Hajiya ta faɗa, ni miƙe na ce. “Yau da gobe zasu gane, in sha Allah gobe zan sanya su a makaranta, nima litinin zan komai aiki.” “Ai idan kika ga kina yi min yawo a gidan nan to wallahi mijinki ya sake ki, amma bazaiyu kizo kina min yawo a gida ba da aure akanki.” “Ni Hajiya idan yaƙi sakina, kawai zan shigar da shi ƙara.” “Wace irin ƙara kuma?” “Kotu mana Hajiya, alƙali zai iya raba auren.” “Amma kuwa da anyi shari’ar da ba a taɓa sokuwa shari’a irin ta ba, da mutane sun yi miki kallom jahila, sabida babu wacca ta taɓa zuwa kotu raba aure akan anyi mata kishiya sai akanki, Nana karki yi abinda duniya zata zage ki mana.” “Hajiya wai kinsan yanzu zuwan mu amaryar ta shi zata yi min rashin kunya, aikuwa na ɗauke ta da lafiyayyen mari, wai na rabu da mijinta.” “Mijinta mana, tun da a yanzu ta fiki iko akan shi, dan ita gida ɗaya suke zaune.” Na yi tsaki, na tuna kalaman ƙarya da yaudara irin na Turaki, wai ni kaɗai yake so, kai namiji mugun hallita, namiji mugun irin. “Ni dai Hajiya zan koma aikina, kuma zan shigar da ƙara kotu a raba mana auren, dan ni bazan iya zama da shi da wata matar ba, kuma tana haihuwa ni bana haihuwa, kema kinsan wannan zaman ai ba adalci a ciki, ni aure ma na yi wanda zan iya, Allah Ya bani lada.” “Ki dai dage da addu’a, haihuwar nan fa ba cewa aka yi bazaki yi ta ba, zaki haihu kawai ta yi jinkiri ne, amma duk kin sakawa ranki bazaki haihu ba, itama fa matar da ya aura babu tabbacin zata haihu anan kusa, kaɗan daga hukuncin ubangiji dan shi ba ayi masa dole kuma kin sani.” Na yi shiru, ina tuna son zuciya da zalunci irin na ɗa namiji, ko kuma na ce irin na ɗan Adam, dan ba iya maza ke da son zuciya ba, ko da ace ina haihuwa Turaki yazo zai ƙara aure ba zanji daɗi ba, amma kuma me ya sa a lokacin Sardauna banji komai ba? Ko da yake banso Sardauna ba a baya, kamar yanda na so Turaki, amma ya yi min wannan mummunar sakayyar, hhhm ɗan Adam. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (19). Bayan kwana uku da zuwa gidan Turaki na kwaso kayana, amma ba Turaki babu takardar saki, twins ma ranar da na ɗauke sun zan kai su makaranta wata school Bus tazo ɗaukansu, wai Babansu ya sa su a makaranta, har makaranta naje muka yi magana da shugaban makarantar na ce a faɗim kuɗin zan basu sai su mayar masa amma suka ce su ba haka ba, ta dole na ƙyalesu na dawo na ci gaba da zaman jiran takardar sakina amma shiru har kwana uku, dagaske dai Turaki dai dagske yake bazai sake ni ba kenan, Hajiya kuma ta dage wai babu inda zanje da aure a kaina, amma duk da haka na yi niyar gobe littinin duk abinda zai faru sai dau ya faru amma sai na fita wajen aiki, idan ma ba haka ba ni kawai zance kotu na shigar da ƙara, ina cikin wannan tunanin na ji wayata tana ƙara, na kai hannu na ɗauka naga lamba ba suna, na ɗaga nasa handsfree aka fara magana. “Dan Allah dan Annabi idan ba kya son Turaki wallahi ni ina son sa, dan Allah ki rabu da mijina ya yi rayuwa cikin farin ciki.” Wani abu ya tsayamin a rai, ‘Na rabu da shi? Riƙe shi na yi ko me?.’ Na ja tsaki na kashe wayar tare da dannawa lambar block, nu na fara gajiya da wannan yarinyar gaba ɗaya, wani mugun haushinta nake ji, musaaman idanta faɗi kalma mijina idan ta faɗa sai na ji duk duniyar ta yi min zafi, ni Turaki zai rainawa hankali kenan? Yana can yana rayuwa da yarinya shine zai zo yana yi min wannan shirmen, maza mayaudara ne ko mahaukaciya aka aura masa biyan buƙatarsa zai yi da ita indai zata ba shi abinda yake so, shine zai raina min hankali, ko da yake yarinyar ma ni banga marabarta da mahaukaciya ba, a take na tuna lokacin da Turaki ya ce zai yi duk wani abu da zai sani farin ciki, nasan so yake ya ji na ce ya sake ta sabida bani da hankali ko me? Ai dukkan yarda ta ƙare a tsakanina da Turaki tun ya gwada auren wannan to babu shakka nan gaba kaɗan ma zai sake auren wata, ba ma abinda zai kaini na ce ya sake ta ya yi ya zama da ita, idan ya ga dama ma ya jere mata hudu, bayan shekara ɗaya ya cire su ya sake zuba wasu huɗun shi ya ga dama, ni dai nagama yarda da karatun maza. Kwantawa na yi na fara hasaso rayuwata, tun daga lokacin da na fara haɗuwa da Sardauna, ɓacewa ganina da ya yi, da irin wahalal da na sha, sannan zuwa sa na biyu bayan mun dawo daga makaranta, da kuma haɗuwar mu da shi da Hajiya ta aike ni, irin soyayyar da ya nuna min har ta kai ga na aure shi, irin ɓoyayyiyar azabtarwa da ya yi min, wauta da na nuna a rayuwar auren har da zuwa gidansu Bilkisu, sai kuma na yi shiru a fili na ce. “Yanzu duk suna ina? Bilkisu ta girbi abinda ta shuka, Islaha ma ta girba, shima Sardaunan yana kan girba.” Sai kuma hawaye ya fara zuba a fuskata, cikin kuka na fara cewa. “Na ɗauka da ƙuncin da na shiga a gidan Sardauna na gama, na yi tunanin aure na da Turaki buɗewar dauwamammen farin ciki ne a rayuwata, amma ashe ba haka ba ne? Ni dai bana son rayuwata ta ƙara shan wahala, ina son hutu, ina son sauƙi a rayuwa, ina son na ji daɗi ko ya ne, Allah na tuba.” Na kifa kaina da katakon gado na ci gaba da raira kuka na, ina yi ina sharɓar hawaye ina ta tuna abubuwa marasa daɗi da yawa a rayuwata, ƙalubale da na sha tun haihuwata nake shan wahala wajen Hajja kakata, na girma na zo na faɗa tarkon Sardauna, haka na yi ta kuka na babu mai ce min Nana daina, har bacci ya ɗauke ni. Washe gari da safe na tashi na yi aikina na gida, bayan na shirya su twins sun tafi makaranta, nima na hau nawa shirin tafiya ofis ɗin, Hajiya na kallona bata ce min komai ba har nagama shirina, na zo yi mata sallama. “Nana, wai kina ganin hakan ya dace? A addinan ce fa hakan bai kamata ba, idan da aurensa akanki bai kamata ki fita ko ina ba, ba tare da kin nemi izini wajensa ba.” “Nasani Hajiya, amma zanje kotu ne na shigar da ƙara.” “Nana bazaki ji shawara ba ko?” “Hajiya ki yi haƙuri dan Allah.” Na faɗa tare da ficewa, sai da na fara zuwa kotu na nemi lawyer ma shigar da ƙara ta akan ina so mijina ya sake ni, akan dalilin na daina son sa kuma bazan iya zama da shi ba, daga nan na wuce wajen aiki. Nan ma ban wani jima ba na tashi na dawo gida, sai dai ko da aka kai takardar sammaci wai Turaki baya ƙasar ma baki ɗaya, na shiga tashin hankali sosai, me Turaki yake nufi? So yake ya barni na yi ta gantali da aurensa a kaina ko me? Haka na yi ta zaman ɓacin rai, sabida kar nasami matsala da wajen aikin yasa Hajiya ta barni na ci gaba da zuwa, ana wannan yanayin na yi wata biyu cif a zaune a gida da auren Turaki akaina, ina zaune ni ba mai aure ba, ni ba marar aure ba. Sai da aka yi wata uku sannam aka nemeni a kotu akan wanda na shigar da ƙarar sa ya dawo gari kotu tana nemana, domin yin zaman farko. Ba kunya ranar da za ayi zaman farko na shirya tsaf, ban nemi kowa a gidanmu ba na shirya na tafi kotu, kafin ƙarasowar alƙali ina zuane daga gefe Turaki yana zaune a gefe sai kallona yake, ni kuwa na ɗauke kaina, kamar ma bansa an hallice shi a wajen ba, sai dai abinda yake ta yi min yawo a zuciya shine yana can amaryar tasa ta sami ciki, idan kuma na tuna da ciki sai na ji na sake tsanar shi, sabida muguwar ƙarya irin tasa. Mu da muka zo kotu za a yi shari’ah ƙarfe goma ba a fara ba sai ƙarfe sha ɗaya da rabi, ina shiga ɗakin shari’ar na ji gabana yana wani faɗuwa, na ji gaba ɗaya jikina ya yi evening. ‘wai yau ni ce zan tsaya gaban alƙali ina shari’ah da Turaki? Duk abinda Turaki ya yi min bai kai na Sardauna ba, amma ban iya tsayawa da Sardauna ba sai Turaki, anya babu son zuciya nima a lamarina, anya kuwa akwai hallaci? Anya na yi tunani na mai kyau, na yi shawara da inda ya kamata, a take hawaye suka fara zubo min a fuska, bazan iya ba wallahi, bazan iya tsayawa da Turaki na yi shari’a da shi ba, na fasa.’ A hankali na fara zame jikina ina yin baya, na dawo na sami wani benci na zauna na kifa kaina da gwiwa na fara rusa kuka mai taɓa, zuciya kawai ni Turaki ya sake ni, amma babu zuwa gaban alƙali, Turaki har yanzu ɗawainiya yake da iyayena da ‘ya’yana da ‘yan uwana, duk da nagama auren sa bai kamata na tsaya gaban alƙali da shi ba, bai kamata na yi irin wannan rabuwar da shi ba, muryar barrister na naji yana cewa. “Ranki ya daɗe.” Na ɗaga rinannu idanuna na kalleshi, ya ce. “Mai shari’a yana nemanki.” Na girgiza ma sa kai, ya matso kusa da ni ya ce. “Mene bangane ba, ya yi miki barazana ne?” Na ce. “A’a, bazan iya shari’a da Turaki ba, bai cancanci wannan ba, ya yi min abubuwa da yawa a rayuwa bai kamata na tsaya da shi a gaban alƙali ba da Turaki ba gaskiyya.” “To yanzu mene abun yi?” “Nima bansani ba, amma bazan iya ba.” “To ki zauna anan zance baki zo ba, za a wuce shari’arku a tafi ta gaba, amma kisan kuɗin da kika bani bazasu dawo ba.” Na gyaɗa ma sa sama kawai alamar badamuwa, ya tashi ya tafi, ni kuma na ci gaba da kukana, sai da ya kusa minti talatin da shiga, sannan na miƙe na yi waje daga kotun, kai tsaye gida na nufa na shiga ina kuka, Hajiya ta biyo ni tana faɗin. “Ke me ya faru kike rusa mana kuka?” Cikin kukan na ce. “Hajiya ni kawai ku yi masa magana ya sake ni, bazan iya shari’a da shi ba, kawai ya sake ni.” “Au, wai da shari’a kika je?” “Eyh Hajiya, amma ni dai ku yi masa magana, kawai ya yi min sakina na ci gaba da rayuwata, dan Allah.” “Nana aure fa raine dashi, ba wanda ya isa ya yanke shi sai lokacin sai ya yi, ni bazan shiga maganar raba aure ba, idan da rabu tsaf sai kika ga rabo ya kashe ni, ba zan shiga ba, kuma babu wanda zai shiga cikin gidan nan, ki je dai ku yi yanda zaku yi a tsakaninku, amma mu dai babu mu gaskiyyar zance kenan.” Legendspen 08129553971. SARTSE BOOK 3 Sayyid. (20) Na kalli Hajiya, na ce. “Yanzu kenan kun cire hannunku? Duk abinda. Zai faru da ni ya faru ku babu ruwanku kenan?” “A’a ko ɗaya Nana, bamu isa mu ce mun cire hannunmu ba, amma a zancen kashe aure ba a zura kai Nana, tsakanin miji da mata ma sai Allah, yanzu da ace azaba kike sha, ko zaluntar ki yake yi to da zamu shiga, amma Nana zancen ƙarin aure ne, hukunci ne na zuciya, adalci da rashinsa, babu ruwanmu a ciki, yanda baza mu yi milki dole ba, to shima fa baza mu yi masa dole ba Nana.” “To Hajiya na gaji da zaman da shi, Yayan mahaifinsa baya sona Hajiya, duk wani abu shi yake ƙullo shi, yana namiji ya dinga abu kamar na mata Hajiya, zamana da shi wani sabon matsalal ne a gareshi Hajiya, shi ya sa na zaɓi na haƙura da shi, kuma ni bazan iya zama da kishiyar da take haihuwa ba.” “Idan kika yi wa kanki baki ai shikenan Nana, likitoci sun tabbatar miki da mahaifarki zata iya ɗauka jariri zaki iya haihuwa, kawai dan ta yi jinkiri sai ki ce haka? Allah zaki yi wa Butulci ne ko me? Da kina da hankali wallahi godiya zaki yi wa Allah, idan kika haɗa rayuwarki ta baya da ta yanzu, Allah Ya yi miki kyakyawan sauyi, amma duk kin kasa ganewa, kinsan da cewar shima ce masa aka yi an ɗaura masa aure? Sannan aka bashi zaɓin ko ya zauna da ku ku biyun ko ya haƙura dake, duk wani abu da zai ɗauke miki damuwar wannan kishiyar Turaki ya yi shi, kinsan da cewa ya buɗe miki babban shagon siyar da abaya? A niyar shi idan kika dawo duk ya faɗa miki ya nuna miki, har alfahari ya yi akam cewar matarshi na son shi kuma zata fahimci, amma Nana kin kasa fahimta, tabbas kishi halal ne, kishi da zafin zuciya gaskiyya ne, kuma soyayya ce ke kawo shi, amma idan rai ya ɓaci hankali ba ya gushewa, da kin zauna kin cire son zuciya kinyi tunani na gaske da zaki sami amsar komai da komai, amma kin kasa.” Jikina na ji ya yi sanyi, amma duk da haka napi bari waɗan kalaman bogin da ya shimfiɗawa su Hajiya su yi tasiri akaina, tabbas zancen shagon abaya ya buɗe dan naga wasu irin ledojin na shago da idan ansiya kaya ake zubawa a ciki da yawa a motarsa lokacin da kafin mu tafi Saudiya, ansa NANA’S DAR, amma da na tambayeshi sai ya ce na matar abokinsa ne take yin online bussiness a gida, shine ya sa akayi masa zai basu gudummawa, sannan kuma da muna saudiya naga yasa dp na logo ɗin NANA’S DAR, amma banyi tunanin komai ba, amma dai duk haka ƙanzon kurege ne irin na Turaki, ni sharrinsa ma tsoro yake ban, ya ƙware a yaudara. Tashi na yi jikina babu ƙwari na tafi ɗaki na kwanta, ni dai tabbas sai Turaki ya sake ni, bazan iya ba, ko da na yi niyar yin tunani akan hakan sai ma tuna wani mafarki da na yi Ni da Turaki zaune a falo ga yara guda huɗu maza da mata suna zaune suna wasa, ina kallon yaran ina jindaɗi a cikin a raina, kwatsam sai wata mata ta fito daga cikim ɗaki ta far ɗaukan yaran, n kalli Turaki na ce. "Habiby, kaga tana ɗaukan yaran mu?" Ya kalle ni ya yi murmushi, ya ce. "Habibty ai na tane, za a hana uwa ɗaukan 'ya'yanta?" "Na ta?" Na tambaya ina miƙewa, shima ya miƙe ya ce. "Habibty wannan fa amarya tace, ko baki gane ta ba?" "Banganeta ba." Na faɗa ina girgiza kai, sannan na sake cewa. "Habiby yaushe ka yi aure? Rashin haihuwar tawa ne ya sa ka ƙara aure?" Tabbas wannan mafarkin ne yake son zama gaskiyya kenan, na girgiza kai na ce. “To baza ayi haka da ni ba.” Haka na yini a kwance ina ta famam tunane tunane, duk da haka na takure zuciyata waje ɗaya, naƙi bata damar da za ta yi tunani bayan wanda na ɗaura ta kai, kawai a sake ni. Wajen ƙarfe takwas na dare muna zaune a tsakar gida ni da Hajiya sai Yaya Ridwan, daga gefe twins ne suka gama kukansu wai su wajen Papa zasu, takaici ya kaini na dake su shine suka koma gefe suka yi fushi, wayata ce ta fara ƙara alamar kira na shigowa, ina dubawa naga Lamrah, a take na tuna dukkan abinda Big Daddy ya yi min, wani haushinta ya rufe ni baki ɗaya. “Ba kiranki ake yi ba ne?” Na taɓe baki na ce. “Lamrah ce, ‘yar gidan Yaya Babansu Turaki.” “Ke mutanen nan suna nemanki kina gudun su.” Yaya Ridwan ya faɗa, Hajiya ta ce. “Ki ɗauka mana.” Na ɗauka ina tura baki gaba. “Hello Anty Nana.” “Na’am Lanrah ya gida?” “Lafiya ƙalau, ashe ba kya gida ɗazu amaryarki tazo tana yiwa Daddy kuka.” “Kukan me?” “Wai Yaya Turaki baya gidan gaba ɗaya, kema kuma ba kya gidan, wai ashe tun da suka yi aure bai su taɓa magana da ita ba.” “To ni ina zan sani, ni kawai dawowa na yi naganta a gidan, dan bana haihuwa shine Turaki zai yi min kishiya, to na barta mishi ta cinye duka.” “Waya faɗa miki? ‘Yar gidan Aminan Daddy ce fa, shima Yaya Turakin bai san da auren ba, nan Mama ta yi ta yiwa Daddy magana wai bai kyauta ba, itama sai da ta ce matarsa zata ga kamar sabida bata haihuwa aka yi mata haka, to amma kinsan ya riga da ya yi abinda yaga dama.” “Allah Sarki, ni kinga ina gidanmu ma, jira nake kawai ya aiko min da takardarta bazan iya ba wallahi.” “Wallahi Mama ma haka ta ce, wai da ‘yar ta ce bazata zauna ba, ranar sunyi faɗa da Big Daddy sosai fa, har take ce masa gashinan yaja mana duk babu masu auren mu, ji Yaya Seemah ta girmi Yaya Turaki fa wajen shekara 40 amma bata taɓa aure ba, Yaya Nadrah ce kawai ta taɓa aure itama yanzu ya mutu, shi kawai ya dinga takurawa sirinkansa dan yaga kowa yana bashi girma, Mamansu Sarauna ta ce ma Sardauna kar ya zauna da Laila ɗin ina ga, tun da daman ta zo nan sunyi kaca kaca da Big Daddy, muma nan duk haushi muke ji wallahi.” “Allah Sarki Lamrah, ku daina jin haushinsa mahaifinku ne, ni ce ba ya so kuma gashi na tafi.” “Wallahi bake kaɗai ba duk sirikan gidan maza da mata ba son su yake ba, gani yake kowa dukiyarsu yazo ci.” “Allah Sarki.” “Dan Allah ki yi haƙuri ki dawo, wallahi duk gidan ya hargitse in faɗa miki.” “Ki dai barni kawai.” Ba yanda Lamrah ba ta yi ba naƙi bata fuska, ƙarshe ma na kashe wayar baki ɗaya, ina kashe wayar hajiya ta ce. “To kin ji dai.” “Hajiya bakisan wannan duk tsarin Turaki ba ne? Ni fa Hajiya yanzu tsoronsa nake ji, Allah ɗaya kawai zai faɗan na yarda, amma Turaki babu abinda zai faɗan na yarda, duk wasu maza ma.” “Har da mu kenan dan ubanki.” Yaya Ridwan ya faɗa, na yi dariya na ce. “Banda ku.” Miƙewa ya yi zai tafi ya ce. “Nana adai yi tunani mai kyau dan Allah.” “Ni dai ina kan bakana Yaya.” Bai ce min komai ba ya fice, nima natashi na koma ɗaki na kwanta, sai dai tun da na shiga ɗaki maganganun Lamrah suke dawo min a raina, na hana kaina sakat ina ta faman tunani, da gaskiyyarsu baƙin halin babbansu Ya hana su aure, kuma a cikin familin babu wata ko wani suriki da kake jin bakinsu, nima sai da aka fara case sannan aka kira ni, amma kafin lokacin ko a family meeting ma baya baya muke zama, kuma har agama ba me ce mana ƙala, sai a yanzu da na yi jan wuya aka sanni, amma a wancan lokacin ma ba wanda yasan ni ko kallo ban ishe su ba, ashe gani yake kowa zuwa ya yi ya cinye musu dukiya kenan? Wani ɓari na zucuyata ya ce min. “Idan kuma dagaske take Turaki bai san komai ba fa?.” Na yi shiru ina son na yu tunanin akan hakan, sai dai kuma wanu ɓari na zuciyata ya ce. “Ai zai iya sakinta, amma ya zauna da ita. Wannan ma a kallon da na yi mata babu makawa tana ɗauke da juna biyu na Turaki.” Haka na yi ta tarawa da kwashewa a cikin kaina kafin wani irin wahalalen bacci ya ɗauke ni, wanda na dinga farkawa cikin dare, da ƙyar gari ya waye. Washe gari bayan twins sun tafi makaranta, wajen ƙarfe sha ɗaya na rana Maman Turaki da ƙannensu su Hajara suka zo, kasancewar sune suka san gidan, na yi matuƙar mamakin ganinsu. Bayan mun gaisa sun zauna Mama ta ce. “Nana, ba fa aga mijikin ba.” “Mijina kuma? Turaki ne ba agane ba?” “Shi fa.” Hajiya ta saki wani salati, tare da ɗaura hamnu akai, ta ce. “To ina ya tafi?” “Muma nan babu wanda ya sani, idan aka kirashi sai ya ɗaga ya ce dan Allah a ƙyale shi, yanzu ma wayar bata tafiya.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (21) Gaba ɗaya na zama kamar wata sokuwa, na shiga kallon ɗaya bayan ɗaya, sai nake ganin kamar duk tsari ne abun na su, Hajiya ta ce. “Muma nan ya kwana biyu bai zo ba.” “Ita Nana yaushe ta bar gidan?” Mommy ta tambaya, Hajiya ta ce. “Ai a ranar da muka dawo.” “Ni dai duk abinda ya sami ɗana wallahi Ismail ya ja min, ya dinga abu kamar shine ya hallice su, haka kawai ya ɗaurawa yaro aure, yanzu gashi an nemi yaron an rasa shi ko a jikinsa.” “Haƙuri zaayi, ke Nana yaushe rabonki da shi?” Hajiya ta faɗa, cikin sanyi murya na ce. “Ni an kwana biyu.” “To ki gwada lambarsa ko zata shiga.” ‘Na ce masa me?.’ Na faɗa a raina, a fili kuma na ce. “Ai ba zata shiga ba, sabida na rufe shi.” “Yaya Nana bai kamata ki ɗauki wannan hukuncin ba, da kin tsaya kinyiwa Yaya Turaki uziri.” Hajara ta faɗa, Mommy ta ce. “Gwanda da ta ɗauka, ni kaina abubuwan Isma’il sun fara kaini bango, ni yanzu zan tafi idan Allah Yasa an ganshi tanan sai ku sanar da ni.” Ta faɗa tana tashi, duk muka fita rakata ni da Hajiya, gaba ɗaya jikina ya fara sanyi na rasa gane kan al’amarin, haka na yini duk jiki ba daɗi. Abu kamar wasa sai da aka yi sati ba a sami Turaki ba, abun tun a ganinsa ƙarami har ya girma, ni kaina tun ina ganin abun a matsayi shiri, na dawo na fara ganinshi a zahiri ya fara bani tsoro, sai da aka yi kwana goma cif sannan aka sami labarin shi, shima ta bakin likitan asibitinsu, ina zaune a tsakar gida na yi jigun jigun kamar ko yaushe Ra’is ya shigo, yana shigowa ya ce. “Nana.” Na ɗaga kai na kalleshi, na ce. “Ya aka yi? “An sami labarin Yaya Turaki, amma kuma yana asibiti cikin halin jinya.” A razane na miƙe tsaye, duk na tsorata na kiɗime na ce. “Me ya same shi?” “A yanda Lamrah ta faɗa min wai yaje anyi masa allura kashe ƙwayoyin haihuwa ne, shine ta haifar masa da matsala a jikinsa.” “Kashe ƙwayoyin haihuwa kuma? Kai a ina kasan Lamrah ɗin? Aina kasami lambarta?” “Ita ta yi min magana da kanta tun kwanaki, wai ina burgeta na ce mata ina da aure.” A take na haɗe rai na ce. “To wallahi ka fita sabgarta, ba zakaje ka kwaso mana ‘yar wannam ahalin ba, ubanta ya dinga maka kallon cinye musu arziƙi ka zo yi, kuma mu a gidanmu ma ba ƙara aure. Yanzu shi yana wane aisibtin ne?” “Ai acan Abuja ne ma.” Jikina ƙara yin wani sanyi, na rasa me ke damuna. ‘To kenan Turaki dagaske yake akan maganar? To me ya kai shi zuwa ayi masa wata allura, ko dan ya tabbatar min da cewar ni kaɗai yake so? Amma fa namiji munafuki ne tsaf zai iya shirya abunsa, ni gaba ɗaya na kasa yarda da abun.’ Idan kuma na tuna zuwan mahaifiyarsa da kuma kwanakin da aka ɗauka ana nemansa sai naga gaskiyya ne, amma na rasa ta yanda zuciyata zata karɓi zama da wata a matsayin kishiya a gidan Turaki, duk da idan na duba Turaki ya sadaukar da abubuwa da yawa domin ni, kuma ko sau ɗaya bana fatan ace ya yi wa kansa wani abu da zai hana shi haihuwa, idan kuma na mutu fa? Shikenan ba zai sake aure ba ko me? Gaba ɗaya jikina ya yi wani irin sanyi na rasa abinda yake min daɗi. Sai na ɗauki wayata zan kira lambarsa sai na fasa, haka na yi ta faman danna waya har bacci ya ɗauke ni, washe gari ma da abinda na tashi a raina kenan, na kasa yin komai sai faman tunani, twins ma ƙarshe Hajiya ra shirya su suka tafi makaranta, babu abinda yake yawo a akaina kamar idan bayan na koma gidan Turaki amaryarsa ta haihu, tabbas akwai mazajen da basa juyawa matansu baya, akwai ‘yan goya da zani, amma kuma akwai ‘yan iskan da ko ciki aka samu shikenan kin zama sauna, kin zama sakarya, kin zama mara daraja. Duk da bana hango Turaki da wannan halin amma tabbas ba kowanne namiji ba ne ɗan goyo da zani, amma kuma idan na yi haƙuri na zauna ki da Turaki ya juya min baya zan iya ci gaba sa rayuwata ko babu shi, zan ci gaba da duk abinda nake yi, idan kuma na koma da sa’a fa? Ina komawa na sami ciki na haihu shikenan fa. Amma dai duk da haka zan kalli wata a matsayin kishiya ta, ko da yake kishi ance kai kake sa shi a rai, idan har ban ɗauke ta a matsayin kishiyata ba tun a yanzu babu abinda zai sa na ɗauketa a kishiya a ko da yaushe, idan na yi rayuwata hankalina kwance ba ta isa na kalleta a matsayin kishiya ba, idan kuma na bari Turaki ya suɓuce min babu tabbas na zan sake samun wanda zai so ni kamar Turaki, duk da bance ba lallai ba amma babu tabbas, dole na nutsu na yi tunanin da zai ɓulle min. Na sa hannu na dafe goshin sabida wani irin sarawa da na ji kaina yanayi min, na fara ƙoƙarin miƙewa amma na ji jiri yana son kwasata, da sauri na dafe bango amma kaman bango ma baya yake, na ji kaina yana wani irin abu. ‘Tsit! Tsit! Tsit.’ Da sauri na shiga ƙwalawa Hajiya kira, na buɗe dukkan muryata ina kiranta, ta shigo ɗakin tana cewa. “Nana me ya faru? Ihun me kike?” “Hajiya kaina, ɗakin juyawa yake, kaina zafi.” *********** Sama sama nake jin maganarsu, nasan dai muryar Yaya Radiya ce da ta Hajiya, a hankali na fara ƙoƙarin buɗe idona da ya yi min wani irin nauyi, ina buɗewa na yi saurin mayar da shi na rufe sakamakok wani irin yaji da na ji ya shiga cikin idon, sai da na yi kusan minti biyar sannan na sake ƙoƙarin buɗewa a hankali, ina buɗewa na kalli gefe naga Hajiya da Yaya Radiya, na skae kallon wajen tsaf naga ashe asibiti ne, cikin gajiyawa na ce. “Hajiya.” Da sauri suka yi kaina, Hajiya ta ce. “Sannu Nana.” Na gyaɗa kai kawai, Yaya Radiya ta ce. “Bari na kira likitan.” Ta faɗa tare da ficewa, Hajiya ta ɗaga hannu sama ta ce. “Allah Na gode maka da ka tashe ta, Allah na gode maka.” “Hajiya me ya faru da ni?” Ma faɗa, muryata cike da gajiya kamar wacca ta yi wani babban aiki. “Mene ma bai faru ba? Kwanan mu nawa anan duk hankalin kowa ya tashi.” “Kwana? Kwana nawa?” “Tun ranar alhamis kika faɗa, sai yau lahadi kika farka.” Wani irin shock ne ya ziyarce ni, a take na ji kaina ta fara juyawa, na sake dafe shi ina faɗin. “Kaina zafi Hajiya.” “Sannu, bari likitan ya ƙaraso.” A lokacin kuma Yaya Ridwan ya shigo, yana shigowa Hajiya ta ce. “Ɗan bi Radiya wajen likitanan, ya yi jinkiri.” Tuni shima ya fita, sai dai yana fita ya dawo tare da Yaya Radiya da kuma likitan, matashin likitan ya yo kaina ya fara dubani, bayan ya yi abinda zaiyi ya yi min allura wacca ko minti biyu banyi ba bacci ya ɗauke ni. Ban sake farkawa ba sai can dare, a lokacin kowa ya tafi sai Hajiya da Ra’is suna hira, ina buɗe ido na ji Ra’is ya ce. “Shima sun dawo da shi gida, nifa na fara ganin abubuwan Nana kamar rashin imanin, dan taga yana sonta shine ta ɗauke wannan hukuncin haka? Shima kuma kamar wani sakarai, Allah ne ya taimake shi fa allura ba ta yi aiki ba, da yake yana da ƙarfin jini to shine allura taƙi daidai ta da jininsa ta haifar masa da kumburin jiki, wai borin jini, baki ga yanda jikinsa ya kumbura ba, sai allura ta gama fita daga jikinsa zai dawo daidai.” “Hhhhm ita ma fa tana son shi, daga jin yana asibiti shine ta shiga wannan halin, kawai kishi ne ya hanata zama, kuma ni haka ina bayanta gwanda ta karɓawa kanta mutunci, kawai ina nuna mata bana bayanta ne sabida kar ta ga na yi mata haka ta sami damar hulaƙanta miji, amma tabbas abin da ciwo miji ya yi miki kishiya, katsahan kin dawo daga tafiya ki tarar da ita a gida, sai mai ƙarfin zuciya zata danne wannan, ga matsalal jinkiri da haihuwarta ta yi, abubuwan zasu haɗe mata.” “Hakane Hajiya, amma kinji komai dai da ya faru, kuma a yanzu abinda ya yi ya tabbatarwa da kowa Nana ce kaɗai a cikin zuciyarsa, kuma ita kaɗai yake so.” “Hakane ai namiji baka canja masa raayi akan abinda yake so, shi dai wancan kawun nasa ba shi da hali kwata kwata.” “Kai Hajiya sirikina ne fa? Kinsan yarinyarsa ta mutu a kaina.” “Ƙaniyarka ja’irin yaro, nikam bana yi maka sha’awar ƙara aure a yanzu da ƙana nan shekaru, kuma ga uwarka can ma ta ce bazaka auri ‘yar wannan ahalin ba.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (22) Ya yi dariya sannan ya ce. “Wallahi Hajiya ni bana bata fuska ma, sabida ban shirya ƙarawa matata kishiya ba, amma yarinyar tana nace, itace kira, ita tura saƙo, baki ga kayan da ta kaiwa Ayaan ba ranar nan.” “Ita matar taka tasan da ita kenan?” “Ta je gidan ta ce mata wai abokiyar aiki na ce ita.” “Kai matan zamanin nan basu da kunya, amma dai ka ci gaba da baya baya da ita.” “Nifa Hajiya ta yi min.” Sai a lokacin na tsoma musu baki, na ce. “To bazaka aure ta ba na faɗa ma, ubanta ba shi da kirki, kuma in sha Allahu zai yazo yanemi alfarma wajena, da yasan ba iya mai kuɗin ba ne ke da dama, har da muma.” “Ke kuwa ki farka daga halin rayuwa ko mutuwa, amma ki rasa da me zaki tashi a ranki sai zancen wasu? Ki raba kanki Nana.” Hajiya ta faɗa, Ra’is ya ce. “Da su ta kwanta ai, ki tashi ki yi sallah tun da daman tun ɗazu kina laɓe kina sauraren hirar mutane.” Tsaki na ja, na maida kaina gefe na kwanta, bama na son hirar kwata kwata, sai can dare ba samu damar yin sallolin da suke kaina, sannan na samu na ci abinci, sai da na ƙara kwana uku a asibiti sannan na dawo gida na ci gaba da jinyata. Gaba ɗaya jinyar ta cire min duk wani fushi da nake yi da Turaki, na yanke kawai zan koma mu ci gaba da zama da shi, amma da sharaɗin sai ya raba mana gida ni da amaryar ta sa, wannan shine abinda na yanke kawai, sai da aka yi sati biyu sannan Turaki ya zo, bansan haka na yi kewar ganinsa ba sai a lokacin, sai na ji kamar na tashi naje na rumgume shi, ya yi wani haske kuma ya yi ƙiba, duk da ance ba ya gidansa yana gidan Mommy anan yake jinyar, sai da suka gama wasa da su twins sannan ya kalli ni ya ce. “Habibty.” Na ɗaga kai na kalleshi ba tare da na ce komai ba, ya sake kiran sunana. “Habibty.” Kawai na fashe da kuka, kukan da bansan dalilinsa ba, wani irin abu nake ji a zuciyata, ta yi min wani irin rauni tausayinsa da na kaina duk ya cikina, ina son Turaki yana sona, amma matsaloli ko ta ina suna so sun hanamu rayuwa a tare. “Kukan mene? Har yanzu baki sauko ba? Ki yi haƙuri dan Allah.” Na goge hawayena, na ci gaba da kallonsa. “Habibty dan Allah ki yi haƙuri, ki zo mu koma gidanmu, mu yi rayuwarmu a tare dan Allah, wallahi ko me kike so zanyi, ko Laila kika na ce na sake ta zan sake ta, wallahi Habibty babu wani abu da ya taɓa haɗani da ita ko da magana ce, Habibty ko a jiya na yi yinƙurin sakinta sabida idan nazo miki ki karɓeni, amma Mommy ta ce na dai yi haƙuri nazo miki, bata son sakin nan, an riga anyi auren nan, amma wallahi ko yanzu idan kince a’a zan sake ta, dan Allah.” Na girgiza kai na, sannan na fara magana cikin sanyi murya. “Ba son ka ne bana yi ba ya sa na haƙura da rayuwa da kai, son ka shine dalilin da ya sa na haƙura, ku maza kuna da son kan ku fiye da komai, a yau dukkan soyayyar da kake min zata iya komawa ga amayarka indai kasami abunda kake so a wajenta, ni kuma zuciyata bazata iya ɗaukan ganin ka juya min baya ba, bazan iya jure ganin wannna lokacin na, halin ku na maza abin tsoro ne, babu ruwanku da bakwa so indai ta fannin biyan buƙatar ku ne, zaku cire kalma ƙi da kuke faɗa ku yi abinda kuke so.” “Habibty wallahi ba haka nake ba, zuciyata taki ce ke kaɗai wallahi, dan Allah ki yi haƙuri mu koma gida.” Duk yadda na so bijirewa na kasa, sabida zuciyata da gangar jikina suna matuƙar son Turaki, kuma sunyi kewarsa sosai da sosai. Duk yanda na so ma ba ya bari gobe na koma Turaki yaƙi, haka na shirya muka tafi da kayana, aka bar twins da cewar zai zo ya ɗauke su gobe. Tun da muka shiga cikin gidan na ji raina ya fara ɓaci, bana son tunawa kwata kwata da cewar akwai wata a gidan, sai da na yi alƙwarin bazan taɓa kallonta da idon kishiya ba, sai dai na kalleta da idon wani abun daban. Tare muka mai da dukkan kayana cikin sif, muna jera kayan a cikin sif ɗin yana cewa. “Habibty wannan ne na ƙarshe dan Allah.” Sai dai kawai na gyaɗa masa kai, a raina kuwa ina ta faman tunanin dole fa sai Turaki ya raba mana kwana, dole sai ya tafi wajen wacca yarinyar, to ta ina zan yi mata kallon wani abu daban ba kishiya ba, bayan ana raba mana kwana? Kuma a yanzu babbar soyayyar da zan nunawa Turaki ita ce na bashi damar sauke duk wani haƙƙinta mu dake kansa, ya yi adalci a tsakaninmu mu biyu. “Yanzu ya ka tsara girkin?” Na faɗa bayan na yi dogon yaƙi da zuciya, ya kalleni ya yi nurmushi. “Nima bansani ba, amma har yanzu zuciyata ba ta bani damar zama da ita a matsayin mata ba, ina son na rabu da ita, sai kuma ina duba cewar muma ‘ya’ya ne damu, yanda bama son a hukaƙanta su itama bazamu hulaƙanta ba.” Na gyaɗa kai, sannan na ce. “Hakane kam.” “Amma ke ya kike gani?” “Ah duk yanda ka ce haka za ayi.” “A’a kema yanda kika ce haka za ayi, ranki ya daɗe.” Na yi murmushi, sannan na ce. “Kamar yanda addini ya tanada ana yi wa amarya wasu kwanaki, sannan ajuyo a raba musu kwana.” “Na ta ba sun wuce ba? Ni dai Big Daddy ya cuceni wallahi.” “Wai me ya sa baya sona? Sabida mu talakawa ne kome?” Ya girgixa kai, sannan ya ce. “Muma ai ba son mu yake ba, a haka ne kike ganinsa kamar yana son kowa, babu wanda yake so sai nasa, sai kuma Sardauna shima sabida mugayen halayensu sun zo ɗaya, amma kinga matarsa da ‘ya’yansa duk ba su biyo halinsa ba, Mama Amina duk kanmu ka ɗaya take son mu, babu wariya ko wani abu a tare da sonta, haka ‘ya’yansa.” “Nagani duk ba haka suke ba, kuma yana claming cewar shi Big Daddy ne, amma yakasa playing role ɗinsa as Big.” “Wallahi, ita fa wannan yarinyar ‘yar amininsa ce, kawai sabida nuna isa ya aura min ita, sai kawai sanar da ni ya yi, ita kuma yarinyar kamar ba zuciya a ƙirjinta wai ta kamu da sona, ki ji fa har zuwa take ta na yi wa Mommy kuka a gidan fa, ni kwata kwata ba burgeni take ba.” “Ta riga da ta zama matarka ko ma dai yayane, to kawai ka karɓi ƙaddarar da ta baka ita, bamu san irin alherin da take tafe dashi ba.” “Hakane Habibty, amma ba zan taɓa ɗaukan rashin kunya daga wajenta ba, muddin ta taɓa ki to za ta bar gidan, ki shirya bari na yi mata magana ta zo.” Yana faɗin hala ya tashi ya fice, sai da na daɗe a zaune sannan na miƙi na shiga wanka, bayan na fito na shirya cikin doguwar rigr atamfa, na yi shirya na yi kyau abuna, tun ina shiryawa Turaki ya shigo ya ce da ni tana falo, sai da na gama shirina sannan na fita, sai a lokacin na yi mata kallon tsanaki, wannan dai zata iya girma fa tabbas, ko da kuwa na shekara ɗaya ne, amma ko ma mene ni tazo ta tarar dan haka biyayya dole agareni, duk da dai na ɗauki niyar babu wani abu da zai haɗa ni da ita ko da kuwa na magana ne, ko da sharri tazo ko da alheri, to sai dai ta ci kayanta ita kaɗai ba dani ba, asalin uwar gida mai capacity za ta gani. Sallama na yi musu na zauna akan kujerar dake gefe, ita kuma na barta a kujerar dake kusa da shi, ina ganin wani irin kallo da Turaki ya yi min na ɗauke kai kamar bangani ba. Buɗar bakinta ta ce. “Sai yau na sami damar magana da kai kenan a matsayinka namiji na? Ni abinda bangane ba wa nake aure? Kai ko ita? Tun da ta fita ta bar gidan nan ban sake ganinka ba, sai da ta dawo, adalcin ka kenan?” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (23) Ina kallon Turaki ya yi wani irin murmushi, ya gyara zama sannan ya ce. “Malama Laila, kafin auren mu kin taɓa ganina?” “Eyh na taɓa.” Ta faɗa cikin tsiwa, ya sake wani murmushin sannan ya ce. “Ni ban taɓa ganinki ba, ko da kin taɓa ganina bana jin wata magana ta taɓa haɗani da ke, amma kika ce kin ji kin gani zaki aure ni a haka, to ina ga duk abinda kika gani bai kamata ki yi ƙorafi ba.” “Amma ai tun da aka ɗaura mana aure na zama matarka, haƙƙoƙina da yawa sun hau kanka, kamar yanda naka suka hau kaina. Amma tun da aka kawo ni kana wani abu kamar matarka ta aure ni, kai fa namiji zaka dinga wani abu kamar mijin tace.” Ba Turaki ba ni kaina sai da na yi murmushi, na kalleta na kalle shi, ganin nan dai ‘yar ƙarama amma na cika wajen gaba ɗaya, idan ka ganmu tsaf zaka ce na girmeta sosai. “Ni ai nafi ƙarfin mijin tace, tun da shi mijin tace sai an faɗa yake yi, ni mijin kan tace ne, motsin ta kaɗai ya isa ya sani na nutsu a ko Ina, bani da wani ra’ayi ko umarnin kaina sai abinda matata ta ce.” “Chaɓ.” Ta faɗa tana tura baki gaba, ni dai bance musu komai ba, ɗakin ya yi shiru na wasu ‘yan mintina sannan Turaki ya sake cewa. “Laila, wannan matata ce Nana, uwar gidana kuma uwar ‘ya’yana, ki bata duk wani girma da yakamata, itama nasan zata baki duk wani da yakamata, matata bata da hayaniya bata da son rigima bare tashin hankali, a ko ina zan shaide ta, dan haka duk wani tashin hankali bazan ɗauke shi ba, gidana ƙofa a buɗe take idan kinga dama ki zauna, idan kinga dama ki fita.” Sai a lokacin na buɗe baki, cikin wani irin yanayi na taƙama da ya ziyarce ni, sabida yanda Turaki yake yabona gaban kishiya, kamar bansan sharrin ɗa namiji ba, na ce. “Habiby ba haka yakamata ba, amarya ce fa.” “Kya faɗi duk abinda kike so mana, tun da kin gama da miji, an kai suna wajen malamai an mallakeshi.” Banyi niyar bata amsa ba daman, na ja bakina na yi shiru, sai dai na ji Turaki ya ce. “Ai duk malamin da ya mallake mata ni, to taimako na ya yi.” “Habiby duk ba wannan ba, ga amarya ka kawo na karɓa hannu biyu, Allah ya zaunar, Allah Ya kaɗe duk wata fitina, ni dai a matsayina na uwar gida, na bawa amarya kyautar ango har na tsawon wata guda, sabida ran amarya ya yi haske bisa ga ɓata mata rai da aka yi, ni dai ina so mu zauna lafiya, kowa ya mutunta ɗan uwansa.” Ina faɗin haka na miƙe zan tafi, ya yi saurin riƙe hannuna, fuskarsa babu alamar wasa ya ce. “Koma ki zauna.” Na koma na zauna, ya kalle ni sosai sannan ya ce. “Da yake niɗin abun wasa ne shine za a bayar da ni? To ban badu ba. Kwanakin da addini ya tanadar na amarya zanyi, sannan na dawo na raba muku kwana faƙat.” “Hhhhhm.” Ta faɗa tare da miƙewa ta fice, tana fita ya watsa min wata uwar harara. “Ji wani abu da kika yi, kinsan da yanda zanyi kwanakin nan wajenta shine sabida ki nuna mata ba so na kike ba wai kin bata ni na wata ɗaya.” “Eyh mana wata ɗaya, aci amarci lafiya ango mijin amarya.” “Hhhhm.” Shima ya faɗa ya fice, yana fita na ji wani zafi ya ziyarce ni, raina ya shiga ɓaci a take na fara jan wani tsaki da bansan dalilinsa ba, zuciyata ta shiga raya min munafuncin ɗa namiji, na kusa minti talatin anan kafin na tashi na shiga cikin ɗaki, nan ma na daɗe zaune duk raina a jagule, kafin bacci ya ɗauke ni. Washe gari da safe iya cikina na yi abinci karyawa, dan banga dalilin da zai sani na ciyar da wata ƙatuwa ba, duk da Turaki ya shogo da asuba amma ban wani ba shu fuska munyi magana ba, haka ya gama borin kunyarsa ya koma, yana fita na ja tsaki. Yanzu ma wani tsakin na ƙara ja bayan na tuna yanda yake wani sunkuyar da kai. “Habibty tsakin me kike?” Na ji ya faɗa, ba tare da na juyo ba na ce. “Bana jin daɗi.” “Kai Habibty nine?” “Me ka yi min? Kai me ma ya kawo ka nan?” “Haba Habibty ki jiyo ki kalleni mana, abinda kike yi min fa bana jin daɗi.” “Uhmm.” Na faɗa tare da ci gaba da aikina, yana tsaye yana ta surutai na gama haɗa abincin na na juye a plate na ɗau kofi na fita, ya biyo bayana yana magana. “Wai Habibty ba zaki saurareni ba, ina abincin nawa?” “Yana wajen amaryarka mana, ni kake tsammanin na yi maka girki ne kai da ita? Ko ba zata iya girkin ba ne?” “Wai mene haka dan Allah?” Banza na yi da shi na zauna kan dinning na fara cin abincina, har na kammala yana zaune yana kallona, ina gamawa na ɗauke plate ɗin na nayar kicin na shiga ɗaki na yi wanka na shirya fita ofis, lokacin da na fito baya nan ya fita, na ja tsaki na ce. “Maza duk haka kuke.” Ina ƙoƙarin shiga mota na ga ya fito, tsayawa na yi ganin kamar matarsa tasa tana leƙe ta taga. “Habibty da wuri yau?” “Eyh.” “Me ya sa zaki fita da wuri?” “To me zanyi a gidan? Ai kana da amarya zata iya yi maka wanka ta shirya ko?” “Wai Habibty mene haka? Kince fa abar maganar amma kina ta dawo da ita.” “Hhhhm to ni dai zan tafi, zanje makarantarsu twins na faɗa musu anyi sunyi relocating zuwa nan, sannan zanje na kwaso musu kayansu na can.” “Tom Allah Ya tsare.” “Amin.” Na faɗa tare da shiga mota na nufi wajen aiki, ko acan duk na rasa abinda ke mun daɗi, ina nan amma hankalina da tunani suna gida, ina faman tunanin me Turaki suke yi da amaryarsa, agogon wayata na duba naga sha biyu da kwata. Nasan Babbar likita bata da mutane yanzu, dan haka na tashi na nufi ofis ɗinta, na yi sa’a kuwa ita kaɗai ce a cikin ofis ɗin, bayan mun gaisa ta ce. “Nana akwai wata damuwa ne?” “A’a babu.” “To ya me gidan? Har yanzu haihuwar shiru ko? Ki yi haƙuri tana nan tafe.” “Ai yanzu ma babu wannan matsalal, tun da ya riga da ya ƙara aure.” “Ya ƙara aure kuma, yaushe?” “An kwana biyu.” “Allah sarki, ki yi haƙuri kinji Allah Yana ji yana gani, kuma zai baki haihuwa anan kusa in sha Allah, a yanzu sai kinyi haƙuri kin ci gaba da bashi kulawa, mussaman yanzu da yake da wata kuma ana sa ran za a sami abinda ake so daga wajenta.” “Mommy ni ai haushinsa nake ji, ko magana bana iya tsayawa na yi da shi, sai na ji raina duk yana ɓaci.” “Hakane daman wannan shine kishin Nana, amma yaƙi zaki yi da shi dan tabbas idan kika ci gaba da banzatar da shi tofa zata ƙwace miki shi, kuma wannan idan kissa kike nufi ai ba haka ake yi ba, a gabanta ki ja shi a jiki, ki nuna mata ke kike da iko da shi, a bayan idonta kuma sai ki yi duk fushin da zaki yi da shi, shima kuma ba wai dogon fushi ba ko faɗar maganganu, haka dai ɗan nuna i don’t care, kingane.” “Nagane Mommy, Allah Ya saka da alheri.” “Amin amin daughter, stay strong kinji? Komai da kika gani zai wuce zai zama labari, kamar yanda rayuwarki da tsohon mijinki ta zama labari, wannan jinkirin haihuwar shima zai zama labari, i promised.” “In sha Allah Mommy, na gode.” Na faɗa tare da tashu na fito, ban wani jima a ofis na na tashi zuwa makarantar su twins, na basu sabom address ɗin mu sabida zuwa ɗaukansu da dawowa da su, principle ɗin ma ya ce wai da address ɗin aka yi musu rijista tun farko, daga nan na wuce gidan Hajiya na ɗauko musu kaya, ban wani jima gidan Hajiya ba na dawo nawa gidan.” Ina parking ɗin mota ta na ga an buɗe part ɗinta a fito, a raina na yi tunanin ganin Turaki sai kuma naga ita ce da kanta, na buɗe mota ta na fito ina jan akwatin su twins zuwa part ɗin na, babbar ƙofar mu ɗaya ce amma babu wanda zai shiga part ɗin wani ko ya ga abinda ke cikin na wani, kowa rayuwar shi kaɗai ce, wata ‘yar iskar tafiya naga tana yi, ta wani daƙire tana cije baki tana kallona, kamar wata mai koyan tafiya, na yi wani murmushi mai ban haushi na sa key zan buɗe part ɗina. “Wash, ni matar cushe uwar ‘ya’yan so.” Ta faɗa bayan ta zo gab da inda nake, na yi kamar ban ji ta ba na buɗe ƙofar da key, a iya bakin wajen na sanya akwatin sannan na juya janyo ɗaya. “Allah ka sauke ni lafiya, na haifewa Baby Turaki ‘ya’ya kyawawa.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (24) Nan ma dai na yi banza da ita kamar banji ta ba, na koma na janyo ɗaya akwatin na shigo da ita, ina ƙoƙarin shiga kuma ta ce. “Allah karka sa na zama su o’o mu ci mu kasayar, mu bar miji da asarar kuɗin magani, da suna muna kan ganin likita, bayan munsan ba haihuwar zamuyi ba.” Wani abu mai zafi ne ya tsaya min a raina, na juyo a fusace zuwa inda take, nasa hannu na ɗauke ta da wani lafiyayyen mari, wanda na tabbatar sai da ta ga taurari a idonta. “Idan kina cin ƙasa ki kiyaye ta shuri, duk ƙaryar hauka da jahilci da zaki yi ki yi abunki amma karki kuskura ki ce zaki sani, ni ba sa ar ki ba ce ba tsarar ki ba ce, haihuwa kuma dan Allah idan kin fara karki daina, ki zama tinkiya.” Daga haka na shige ciki, nasa mukulli na kule ƙofa ta, ina shiga na haɗa kai da gwiwa na fara rusa kuka, lallai Turaki daga kwana ɗaya wajen amarya shine zaka je ka saki baki ka fara faɗa mata abubuwan da za ta yi min gori kenan, tun da dai idan ba shi ba, babu wanda zai faɗa mata, kuma ita ba duba take ba, bare ta buga ƙasa ta gani, ta inda Turaki zai fara kenan, to ya dawo ni duk bazan ɗauki wannan ba wallahi. Kamar daga sama na ji horn ɗin motarsa, ina zaune na ji kuma ya fara buga min ƙofa. Tashi na yi na buɗe, ina buɗewa na gashi tsaye, ita kuma tana bayanshi, shigowa ya yi ta sake biyo bayansa, sai da suka karaso tsakiyar falon sannan ya ce. “Habibty ta ce kin mare ta.” “Eyh.” “Me ta yi?” “Iya marin kika iya faɗa masa? Baki faɗin abinda ya ja marin ba? Ni babu ruwana da matarka, ta yi rayuwarta na yi tawa, duk habaici da ƙananan maganganunta basu dame ni ba, amma ba zan ɗauke gorin akan haihuwa ba, shine kawai.” “What! Ita haihuwar take ko kin sami ciki ne? To idan har kina da ciki ba nawa ba ne.” “Ni cewa na yi ciki ne da ni? Cewa na yi in Allah Yayarda sai na haifa ma ‘ya’ya kyawawa, shine ta mareni.” “To ina ruwana dan ta haifa mai ‘ya’ya kyawawa? Ni babu abinda ya dame ni, amma muddin zaka je ka ci gaba da gaya mata matsalal dake jikina shine abinda ba zan taɓa yafe maka ba Turaki har abada wallahi.” “Bangane matsalal dake jikin ki ba, me ta ce na faɗa mata.” “Ka tambayeta mana, aina tasan ina yi maka asarar kuɗi a asibiti? Wai ina kan magani Hhhm.” “Laila, aina muka yi wannan zancen? Nifa bazaki zo ki haifar min da matsala ba a cikin gidana wallahi, muddin kika ce haka zaki yi a shirye nake na rabu dake, na faɗa miki.” “Turaki wannan wane irin rashin adalci kake min? An mare ni kuma kazo kana ce min wani abu daban? Anya zaka iya adalci a cikin gidan nan.” “Ai na faɗa miki matata bata da matsala, duk waata matsala daga wajenki ne, kuma gashi an fara samu, sannan na faɗa miki wannan shine abinda bazan iya ɗauka ba wallahi.” Ni dai banza na yi dasu, suka gama abinda zasu faɗa bance musu komai ba, ƙarshe yazo yana banu haƙuri, tun daga wanann ranar bansake sata a idona ba, kuma nima ban nemeta ba. Sai da Turaki ya yi sati guda wajenta, sannan ya fara raba mana kwana, na cire raina na ɗauke ta a lissafina kwata kwata, har mantawa nake tana gidan sabida gaba ɗaya bana bi ta kanta, lokacin da Turaki yake gunta shima mantawa nake da shi sai lokacin da ya dawo wajena, kwata kwata ban sami wani sauye daga wajensa ba na kulawar da yake ba ni, mussaman da na ɗauke idona daga kanta, sai hakan ya zama wata kafar shan iska agareni, na riƙe yara na hannu biyu ina kula da su, na kuma dage da addu’a na daina kwanciya irin da kamar kasa, idan na kwanta sai safiya. Na mai da hankali na dage matuƙa da ibada da roƙon ubangiji. Yau tun safe Lamrah ta kira ni zata zo, kasancewar yau weekend ne ina gida twins kuma suna tahafiz, ba wani aiki na yi nazo azo a gani ba, amma na gyara gidan sosai. Sannan na shirya yin wainar fulawa, na haɗa komai na ajiye ina jira tazo mu yi tare, sabida wainar fulawa tafi daɗi ana soyawa ana ci. Sai dai zuwanta ita da Ra’is ya tsayar min da duk wani zumuɗi da nake yi, Ra’is wai ya manta yana da aure ne? Kuma ni har cikin zuciyata ma bana son mu’amala sa da Lamrah, bawai dan tana da wani mugun hali ba ko wani abu, kawai mahaifinta ba mutum arziƙi ba ne. “Kin wani tsare mu da idona, ki bamu hanya mu shigo.” Ra’is ya faɗa, sim sim na matsa musu hanya suka shigo cikin falon. “Baby wai baki faɗa mata tare zamu zo ba?” Lamrah ta gyaɗa masa kai, ni kam da naga bazan iya shiru ba na ce. “Baby aina? Ra’is baka taɓa kawo min matarka gidana ba, amma ka iya biyo Lamrah ku tawo, har kana wani kiranta da Baby, to kasani zaren ba kalal yadin ba ne.” “To matata zuwanta nawa? Ni zan kawo ta da kaina? Kuma ma ko mene ai na kawo amaryata ba shikenan ba.” “Kai ka sani marar kunya.” “Anty Nana ina wuni?” “Eyh dole ki ce anty bayan kusan abinda kuke ƙullawa, ke kina tunanin Big Daddy zai barki ki aure Ra’is ne? Ni kaina yana ke fama da shi bare kuma Ra’is? Kar ku fara ɗaurawa ranku abinda bazai yu ba, shawara.” “Mu dai munji mun gani ko?” Ra’is ya faɗa. “Ai sai ku yi, ke kuma ki tashi ki shiga ki soya mana wainar, dan banza iya ba.” Dariya ta yi sannan ta tashi ta nufi kicin ɗin, Ra’is ya miƙe zai bita na ce. “Kai Namamajo.” Dariya ya yi ya zauna, ni kuma na tashi na shiga kicin ɗin, sai da na haɗa mata komai ta fara soyawa, sannan na fito falon. Kasancewar nasan kicin ɗin yana ɗan ciki ciki yasa na ce da Ra’is. “Kai baka da hankali wai? Kasan sharrin baban yarinyar nan? To duk wata matsala da nake fama da ita gidan nan shi ya ƙullata, baya son talaka ko kaɗan, bazai taɓa baka ‘yar sa ba ƙarshe ya ci maka mutunci, muma ya ci namu.” “Wallahi Yaya ni ba sonta nake ba, kawai naga abinda take yi min ne, baki ga yanda take sona ba wallahi, tun bana kula ta har na fara jin tausayinta, shi ya sa na fara biye mata, amma nasanar da ita magana ɗaya daga wajen mahaifinta da ita za ayi amfani, yana cewa a’a na haƙura, yanzu ma baki ga magiyar da ta yi min ba na kawo ta nan.” Legenspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (25) “Allah Sarki, Ai mutuniyar kirki ce wallahi, haka ma Mama Amina akwai son jama’a, da ace babu matsalal Big Daddy ni kaina zan so maka ita, amma tabbas amincewar Big Daddy aiki ne ja.” “To Yaya Nana a dage a sanya mu a addu’a, ina twins?” “Suna Tahafiz, nan ba da jimawa ba zaka gansu.” Na faɗa tare da tashi na koma kicin ɗin, a lokacin da na koma na tarar da ita har ta yi wainar sosai ma, bayan na duba na gani na ce. “Ai wannan ma ta isa ko?” “Eyh nima haka na gani, sai dai ko za a yiwa Yaya Turaki da su twins.” “Turaki yau acan yake, sai dai su twins suma sai ɗaya da rabi zasu dawo, idan sun dawo a soya musu ko?” “To shikenan.” Ta faɗa tare da kashe gas ɗin muka fito falon mu ka fara ci, muna ci muna hira Turaki ya shigo na yi mamakin ganin shi a gida, dan ni tun safe bai shigo min nan ba, na yi tunanin ba ya nan ma. “Ah kana nan ashe? Barka da safiya.” Ra’is ya faɗa yana miƙawa Turaki hannu, murmushi ya yi masa sannan ya ce. “Ina nan, ai yayar taka ta watsar da ni yanzu, idan banzo ba fa bazata neme ni ba.” Lamrah ce ta ce. “Yaya ina kwana?” “Lafiya ƙalau Lamrah, yau duk kune a gidan?” “Eyh wallahi, ya amarya?” “Ai baki shiga kin ganta ba, ta ina zaki tambaye ni?” “Zan shiga ai.” Cikin ɗaki ya shiga ba tare da ya amsa mata ba, nima na miƙe na bashi, ina shiga ya ce. “Habibty kinsan me?.” “Sai ka faɗa.” “Laila fa ciki ne da ita.” Ji na yi maganar ta shige wani girin gin, amma na dake na ce. “Kai ma sha Allah, abin nema ya samu, Allah Ubangiji ya raba lafiya, ya yi masa albarka.” “Amin Habibty.” Ya amsa, farin cikin dana gani ya gaza ɓoyuwa a fuskarshi, sai yasa naji jikina ya yi sanyi. A raina na ce. ‘Allah Sarki ni, Allah ka duba ni.’ “Habibty karki damu kinji, in sha Allah kema naki suna nan tafe, suna hanya in sha Allah.” Na yi wani iri murmushin da ni kaina bansa fasaarar shi ba, na ce. “Ai ni ko ban samu haihuwa ba Allah ya sallameni, ya bani twins kaima kuma ya bawa Laila.” “Hakane Habibty, amma ina son na wajenki sosai, in Allah Ya yarda suna hanya.” “Allah Ya yarda, bari naje wajensu ko?” “Tom, nima bari na shirya anan na fita, ‘yan uwanta ne suka zo.” “To shikenan bari na haɗa ma ruwan wanka.” Na faɗa tare da shiga banɗakin, ina shiga banɗakin na fashe da kuka, da sauri na kunna famfo ruwa ya fara zuba, wani irin abu me zugi na fara ji a cikin ƙirjina, mai matuƙar zafi da raɗaɗi wanda yafi wanda na ji ranar da Turaki ya ƙara aure, ina kuka ina haɗa masa ruwan wankan, sai da na wanke fuskata sannan na fito. “Ka shiga.” “Habibty jira ni dan Allah.” “Tom.” Na faɗa, shi kuma ya shiga cikin banɗakin, ya yi wankan shi ya fito ina nan zuane, sai da ya gama shiryawa sannan ya ce. “Habibyu, nasan kinsan samu da rashi duk na Allah ne, haka kuma Allah maji roƙo ne, nasan yanda kika dage akan addu’a, nima kuma na dage Habibty, duk wasu ‘yan uwa da abokan arziƙi suka dage, Habibty Allah yana ji yana gani kuma zai amsa, sanar dake cikin Laila bawai nuna miki farin ciki na bane, ko son ɓata miki rai. Na faɗa miki ne Habibty sabida yana da kyau na sanar dake tun da wuri kafin ki gani da idonki, dan Allah ki yi haƙuri ki kuma ci gaba da kai kukan ki ga ubangiji dan Allah, wallahi wannan cikin na Laila ba zai canja mata wani matsayi ba ko ya taɓa naki, Habibty wallahi har yau har gobe Laila tana cin albarkacin ki ne, tana zamane sabida kina zaune, a yau kikace ta tafi wallahi cikin dake jikinta bazai ruɗe ni ba, dan Allah karki sanya wannan damuwar a ranki kinji, bana so wani abu yazo ya dameki.” “Haba Habiby, idan banyi farin ciki da samun cikin nan ba me zanyi? Abinda kake so ne fa, kuma kake yi min kara a kai, ni dai dan Allah dan Annabi kar samuwar wannan cikin yasa ka sauya min dan Allah, zuciyata tana sonka tana kuma ƙaunarka, dan Allah karka guje ni ko juya min baya.” “In sha Allah Habibty.” Ya faɗa tare da tashi, ya riƙe hannuna muka fito tare, su Ra’is suna zaune a falo muka wuce su, sai da na raka shi har ya shiga mota, ya daɗe yana faɗamin kalamai masu sanyaya zuciya a cikin motar, sai da ya ga nagamsu sannan ya tada motarshi ya fita, ni kuma na juyo na yi cikin gida. Ina bakin ƙofar shiga part ɗin na ji an riƙo min bayan rigata, na tsaya ba tare da na waigo ba na fara ƙoƙarin ƙwace rigata. “Juya ce fa.” Na ji an faɗa, na yi murmushi ba tare da na jiyo ba. “Laila karki kuskura ki ce zaki ta da hankalinki, dan kinga mijinki yana rawar ƙafa akanta, kinsan dai juya ce ba haihuwa zata yi ba, ke kuwa da zarar Allah ya sauki wannan cikin naki lafiya to da kanta, zata bar gidan.” “Malama cika ni.” Na faɗa tare da waigowa, sai a lokacin ma naga ashe wasu ‘yan mata ne guda uku, sai kuma ita Lailan. “Anƙi a cika ɗin.” “Cika ni na ce.” “Ba za a cika ba fa.” Na yi murmushi na kalli Laila na ce. “Idan ba ta cika ba ke ta jawo wa, wannan cikin da kika gani bai isa ya canja ni daga matsayin da nake ba, kinsan da cewa zamana kike a gidan nan, a yau na ce sai kin bar gidan nan sai kin barshi.” “Ƙarya kike juya, kalle ni da kyau, ciki ne a jikina, haihuwa zanyi, bawai zama nake na ci na kasayar ba, dan haka Turaki sai ya zama nawa.” “To sai mene? Turaki fa namiji ne ko baki sani ba? Namiji tsamiya ne idsn yajiƙu ya ishe kuwa ya sha, ni na wuce matsayin da zan zauna na yi faɗa akan namiji wallahi.” “Daman ta ina zaki yi faɗa akan namiji? Kina juya baki ajiye masa komai ba? Dole ki ja da baya ki bawa uwar masu gida waje.” Hannu nasa na fisge rigata daga hannun wacca ta riƙe ni, aikuwa ta hantsila kamat zata faɗi ƙasa na matsa gefe ta buge da bango, aikuwa ta tashi ta yi kaina kamar zata dake ni, a lokacin kuma Lamrah da Ra’is suka buɗe ƙofar part ɗina. “Wai hayaniyar mece?” Lamrah ta faɗa, Ra’is kuma ya ce. “Kar ki kuskura ki yi gangancin kai hannu jikinta, wallahi sai na sassaɓa miki kammani idan kuma kina musu bisimillah.” Cike da rashin mutunci ta kai hannu zata dakeni, ai kuwa Ra’is ya riƙe hannunya tsinka mata mari, Laila dake gefe ta ce. “Wane ɗan iska ne kai da zaka shigo gidan matan aure, har ka daki mutane?” Lamrah ce ta danna wayarta ta kira lambar Turaki, sai kawai ji na yi ta ce. “Yaya Turaki idan bakayi nisa ba ka dawo, Laila da ‘yan uwanta zasu daki Anty Nana.” “Ka ji min munafuka, Laila wannan wace?” “Lamrah ce fa ‘yar gidan Daddy Isma’il, kinsan duk anyi musu asiri basa gane komai.” “Wai haka kike zama da ita tana yi miki rashin kunya? Gaskiyya bazata saɓu ba.” “To Ya za ta yi? Juya ce fa ita ba haihuwa, dolenta ta yi haƙuri dani uwar masu gida, Matar cushe uwar ‘ya’yan so.” “Ai ba cikin ba ji jira ki haifeshi lafiya, ban dake Laila ba ki da hankali, mata nawa ne suke mutuwa wajen haihuwa, ciki wahala shi ma kaɗai aiki ce, kizo ki haihu baki huta ba, amma kike cika baki kike neman yin rashin mutunci akai.” “Sai da uwarki ce ba zata haihu lafiya ba, jaka dake.” “Laila abinda kike yi kenan?” Muka ji muryar Turaki, gaba ɗaya ni banji buɗe gate ba bare kuma shigowarshi, sai kawai ganinsa muka yi. “Darling ba haka ba ne, zagina fa ta yi.” “Aina ta zage ki?” “Yaya Turaki wallahi ba haka ba ne, waccan dabadan mun fito ba fa da marin ta za ta yi, a yanzu ma sai da Yaya Ra’is ya mareta, kuma sai juya take ce mata.” “Ke dai Lamrah kinyi asara.” Laila ta faɗa tana tura baki gaba. “Laila na fuskanci har yanzu kanki rawa yake, har yanzu baki fahimci matsayi da muhimmancin matata ba ko? Dan kina ganinki da ciki ko? To kisani har kullum arxiƙinta kike ci, dan haka kije na sake ki saki ɗaya. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (26). “Ka sake ni kuma?” Laila ta faɗa a tsorace, ba ma ita ba ni kaina na tsorata, bansan cewar na kai wannan matsayin a wajen Turaki ba, bansan cewar zai iya aikata duk abinda yake faɗa ba sai yanzu, a take na ji wata sassanayr soyayyar Turaki ta mamaye zuciyata. Wata mata ce ta fito daga cikin part ɗin Laila, babba a ƙala zata kai shekara 35 ko fin haka, sai da ta ƙare mana kalllo baki ɗaya sannan ta ce. “Tabbas Turaku ka cika gwarzon namiji, ka kuma cika jarumi a cikin na jarumai, ka nuna asalin girma da daraja matarka, ka nuna cewar cikin sa Laila ta samu ba wani abu ba ne da zai ruɗe ka har ka hulaƙanta matarka, tabbas wanna shi ake kira da darajar mace. Ke Laila yanzu ya rage naki, sai ki sam cewar mijinki yana mutunta uwar gidansa, kuma akanta tsaf yake da ya rabu dake. Idan zaki kwantar da kai ki yi wa mijinki biyayya ki girmama masa uwar gida Bismillah, idan kuma baza ki yi ba kan ki, kawai ki sani cewa mijinki mutum ne na gari da yasan darajar iyalinsa, dan na tabbatar ko da kece akan daraja da mutuncinku tsaf zai yi haka, dan haka idan zaki yi biyayya lokaci ne, idan baza ki yi ba zai ƙure miki, ni da ina neman alfarma ɗaya wajen ka taimaka ka janye sakin nan.” “A’a Anty ba zan iya ba, ina son wannan sakin zamar mata jan kunne, idan har za ta gyara ta girma ma matata to sai ta dawo, idan kuma tana ganin bazata iya ba to taje kawai na haƙura, zan iya zama da matata a haka, ko da haihuwa ko babu.” Wasu irin hawaye ne suka biyo kuncina, tabbas Turaki ya girmama ni, ya yi mini matuƙar hallarci, idan na ce Turaki ba ɗan goyo da zani ba ne tabbas sai Allah Ya tuhume ni. “To kin ji dai Laila, idan zaki gyara ki gyara idan bazaki gyara ba shikenan.” Muryar Antynta ta ta katse ni, ta faɗin haka ra shige ciki, Turaki ya ce. “Bara na koma, idan na dawo sai mu yi magana.” Idonu na cike da hawaye na gyaɗa masa kai, ba tare da na yi magana ba, yana barin wajen muka juya zamu shiga ciki, ɗaya cikin ‘yan matan ta ce. “Chaɓ, Laila da aiki gabanki.” Lamrah ta riƙe hannuna muka shiga ciki, muna shiga na fashe da wani irin kuka kai wanke zuciya da ɓacin rai, ko ƙarya Turaki ya faɗa a wajen can ni kam ya gama yi min abinda ya da ce. “Anty Nana dan Allah ki daina kuka, yanzu abinda Yaya Turaki ya yi ai ya biya ki, duk rashin mutuncinta da ta yi a yanzu ta biya shi, dan Allah ki yi haƙuri.” Ra’is ma ya ce. “Dan Allah karki saka wannan damuwar a ranku kinji, ke ai baki da matsala tun da har mijinki zai iya sakin kishiyarki akan idonki, sabida ta yi miki rashin kunya, bayan tana ɗauke da cikinsa wanda ya daɗe yana nema, to tabbas wannan mijin ɗan halak ne, ya cika gwarzo kuma jarumin maza, Allah Ya ƙarawa Yaya Turaki arziƙi, lafiya da nisan kwana.” Cikin kuka na ce. “Amin…… Ra’is ba ina kuka dan wani abu ya dameni ba, ina kuka ne na zallan farin ciki wanda yake tafiya da dukkan wani ɓacin rai, tabbas Turaki ya biya ni, ya yi min abinda ba ni da wani nauyi akansa, sai dai shi ke da shi akaina, tabbas Turaki Namiji ne, gwarzo kuma madubin al’ummah.” Haka Lamrah da Ra’is suka ci gaba da tausar zuciyata, suna lallashi na da bani haƙuri har lokacin da su twins suka dawo, tun da suka dawo aka bar maganar, kasancewar sun da wayo da riƙe abu, kuma uwa uba suna da mugun surutu. Sai wajen yamma su Ra’is su ka tafi gida, Ra’is ma da twins ya tafi gidansa akan zai dawo dasu gobe tun da yau asabar ne, bayan sun tafi na tashi na shirya na gyara gida, dan na yi alƙwarin ko da Laila ko babu Laila zan kasance mai bawa Turaki farin ciki a kowanne lokaci, zan kasance masa sanyin idaniya. Sai da ya dawo ma nake jin labarin wai ashe Lailan ma bata gidan, na yi ta tausarsa ina faman bashi haƙuri akan ya janye sakin ya dawo da ita, sabida tana ɗauke da abinda yake so, cike da ɓacin rai ya ce. “Habibty wai tana ɗauke da abinda nake so, ni banganewa wannan zancen na ki ba, cikin jikinta mene? Dan tana da shi sai ta hulaƙanta ki? Wallahi da wannan cikin da su twins duk ɗaya nake jin su a raina, dan haka bazan taɓa bari wani ya hulaƙantaki ba in sha Allah Habibty.” Sai da Laila ta yo sati biyi cif a gidansu, sannan ya dawo da ita, dan a hakan ma nina sa baki sabida kirani da ta dinya yi a waya tana bani haƙuri, tun da ya dawo da ita ban haɗa ido da ita ba, part ɗinta ma tun da tazo gidan ban taɓa shiga ba, rayuwata nake hankali kwance ina kuma samawa mijina farin ciki, babu ruwan da ita kamar ma ba a hallice ta ba a gidan, haka nake rayuwa abuna kamar babu wata hallita a gidan sai ni. Ƙarar da waya ta ke yi ne ya tilasta min fitowa daga cikin kicin ɗin, ina zuwa na ɗauke ta akan kujera na ɗaga. “Hello good afternoon ma, muna magana da Mr’s Turaki mother of twins ne?” Yes! Nice is anything right?” “Calm down please, we want see you at school right now?” “Hello i don’t get you, what happens to my Babies?” “Plase come.” Tana faɗa ta kashe wayar, hankali a matuƙar tashe na koma cikin na kashe gas ɗin, na ɗau mayafi daga jaka na fice, a yanyin da na fita da mota kaɗai ya isa ya nuna mana ina cikin zallan tashin hankali, ikon Allah kaɗai ya kaini makarantarsu twins lafiya, ko gama parking banyi ba na fito, ina fitowa na nufi ofis ɗin principle ɗin hankalina a matuƙar tashe, sai dai ina shiga na ci karo da twins sun yi tsuru-tsuru, gafe kuma duk malamai ne a zaune, sai na ji wani sanyi ya ratsa ni, na yi musu sallama tare da samun waje na zauna. “Good afternoon.” Principle ɗin ta faɗa, na amsa mata da. “Afternoon.” “Waɗan nan ‘ya’yanki ko?” Ta faɗa cikin rashin wadatar hausa, na ce. “Eyh.” “To shekaransu nawane?” “Three going to four.” Ta ɗaga kai, sannan ta nuna min wani yaro ta ce. “Take a look, wannan yaron yana da shekara goma sa ɗaya ne.” Na yi saurin tare ta na ce. “Ma you can go with the english, zan gani.” Ganin hausar ta ta tana ƙoƙarin haifar min da ciwon kai. “Okay, wannan yaron da na nuna miki shekara shi goma sha ɗaya ne, amma yaranki suka yi masa duka suka zubar masa da haƙori guda shida, bayan malamarsu ta dake su, sun riƙe mata ciki tun ɗazu sai kuka take sunƙi cikawa.” Na kalli twins, sun haɗe rai kamar basu taɓa dariya ba, sai a lokacin na kula da gefen hijabin ɗaya ya yage a cikinsu, ɗayar kuma nata ya yi cuku-cuku alamun sun sha dambe, sai kuma ba kalli malamar tana zuane sai matse ido take, na kallesu na ce. “Me kuka yi mata?” Suka yi banza kamar ba su ji ni ba, cike da fushi na ce. “Ba daku nake magana ba?” Still suka sake yin shiru, har sai da raina ya ɓaci nasa hannu na dake su dukkansu, amma suka ƙi buɗe baki, sai da wani malami a gefe ya ce. “Ai wannan bakin da suka rufe shine ya matse ma ta ciki, da zarar sun buɗe bakin shikenan, taɓata musu raine shi ya sa, kuma duk tagwaye haka suke.” Tashi na yi na matsu kusa da su na riƙe musu hannu, cikin sanyi murya na ce. “My Babies, ku ƙyaleta malamar ku ce.” Hawaye ne ya fara zuba a idonsu. “Sorry kunji.” Sai a lokacin suka buɗe bakin, suna buɗewa suka fara kuka, ita kuma ta sauke wani dogon numfashi sannan ta buɗe idonta, alamun ciwon ya tafi, su kuma suka fara kuka. “Madam, amma sun taɓa yin irin wannan?” Na girgiza kai, na ce. “Ko da wasa.” Malamin dake gefe ya ce. “Dole akwai abinda aka yi musu, ba wai iya faɗan da suka yi ba.” “Daga suna faɗa na raba su, shine suka riƙen ciki.” Malamar ta faɗa. “Anty ce ta yi ta dukansu, har da gwara musu kai da bango.” Yaron da ake case ɗin akansa ya faɗa, wani irin zafi na ji a cikin zuciyata, jin wai ta dukansu ta dinga yi har da gwara musu kai da bango. “Me suka yi miki?” Malamin ya tambaya, sannan ya ce. “Principle daman na faɗa miki ana yawan kawo ƙarara malamar nan, akan tana dukan ‘ya’yan mutane, irin malaman nan ne masu rawar kai, da gigin gama secondary.” Legendspen 08129553971. SARTSE BOOK 3 Sayyid. (27). A take na rufe idona na ce basan zance ba a kan yarana ban da mutunci, da ƙyar aka lallaɓani na dawo gida tare dasu twins ɗin, gaba ɗaya raina ba daɗi na shigo gidan, in a shigowa naga motar da Turaki ya fita da ita, sai a lokacin na tuna ma ni ban sanar da shi fitar ba, ina ƙoƙarin shiga part ɗina na ji ya ce. “Ina kika je?” “Naje makarantar su twins ne, wai faɗa aka yi da su suka riƙewa malamar ciki, daman wannan abun da ake cewa tagwaye suna da shi gaskiyya ne? To ni dai gaskiyya akai su a karya musu nasu, kaga yanda suka ganawa yarinyar azaba.” “Ya naga fuskarsu a haka to? Dukansu aka yi?” “Waye ya dake su? Faɗa fa suka yi wai amma malamar ta dake su har da gwara musu kai a bango shine su kuma suka riƙe mata ciki, ko ba komai sun yi punishing ɗin ta, amma dai a cire musu.” “Ah, oh ni uwar magaji.” Laila ta faɗa tana fitowa, sai a lokacin ma na ganta na ga yanda cikin nata ya yi girma kamar yanzu zata haife shi. “Darling kabar ni ciki ina ta jira ka dawo ka ci gaba da matsan ƙafafu, waɗan nan ‘ya’yan naka suna takura min fiye da tsammani, Allah dai ya raya maka su, Daddyn Aiman da Aimana.” Ni sai da na kusa yin dariya sabida yanda naga take magana, tana wani bubbuɗewa kamar kaza zata saki ƙwai, na fara ƙoƙarin sa key na buɗe ƙofa, ta sake cewa. “A’a ko yaran nan duk baku iya gaisuwa ba ko? Ko baku sanni ba ne kuke kallona? To ni ce uwar Aiman da Aimana.” “Laila, mene kike yi haka?” “Au Laila, dan kana gaban matarka shine ba zaka ce cute Angel ɗin ba, nifa bazan ɗauke wannan abun ba gaskiyya Darling, idan muna ciki kace ni kaɗai kake gani da zarar mun fito ka mai dani wata banza, yanzu kagama cewa sai na haifa ma ‘ya’ya dozen, yanzu kuma ka zo kana kallona j Kamar yau kasan ina da ciki? Kai fa ka ce zaka dinga nuna min soyayya ako ina, ganin idon Nana bazai sa ka janye ba.” “Laila ki kama kanki, bana son wannan shirmen. Waɗan nan maganganun yaushe aka yi su ne, sharri kika fara ko me?” Na yi wani murmushi, na ce. “Habiby mene zaka damu kan ka, ni nasan mijina kuma na yarda da shi, dan haka duk wani abu da zata zo ta faɗa ba zai shiga kunnena ba, da maganar ta da haushin kare ina ga duk ɗaya ne.” “Maganar uwarki ce ta kare, lallai daman Darling ka yi gaskiyya da ka ce ba cikakkiyar lafiya ba ce da ita, kaima kan ka haƙuri kake da ita, na ga alama kam.” “Habibty shige ciki ki ƙyale ta.” Na buɗe ɗaki na ƙofa na shiga, muna shiga na cirewa twins kaya na haɗa musu ruwanka suka shiga toilet, ina fitowa falo na ji muryarta tana cewa. “Ai wallahi ka nuna min son zuciya, bakayin adalci a rayuwar gidanka, nice fa wacca zan haifa ma ‘ya’ya, ita juya ce ba ta haihuwa wace daraja da ita, amma ka nuna kafi sonta.” Ban bari nagama jin abinda ta ce ba, na koma ɗaki na kifa kaina da gwiwa na fashe da wani irin kuka, wanda ni kaɗai nasan irin yanda zan misalta shi, wani irin zugi nake ji akan zuciyata sabida zafin kalmar ‘Juya.’ Da ta faɗamin, na rasa me ya sa Laila take jifa ni da wannan kalmar, bata san irin zafin da nake ji ba idan ta kira ni da wannan sunan, ni ba shiga lamarinta nake ba, badamuwa na yi da ita ba? Ba sharri nake mata ko makirci ba, rayuwa ta nake rayuwar ta take, amma bata da aiki sai jifana da wannan kalmar ta Juya, haihuwa ba ita ta bawa kanta ba, bani na hana kaina ba, amma gaba ɗaya ta mai da abun gori. Na ɗaga hannu sama ina zubar da hawaye na ce. “Ya Allah, Kaine mai badawa, Kaine mai hanawa. Gidanka ba ya rashi, kuma taskarka ba ta ƙarewa. Ya Allah ga baiwarka nan, ya Allah na durƙusa a gabanKa, ina kuka da karyayyar zuciya ka dube ni da idanun rahama, Ya Ubangijina, mutane sun gaji da jirana, Ya Allah mijina ya yi haƙuri, ‘yan uwana sunyi ƙoƙari. Kunnuwana sun cika da jin gorin rashin haihuwa, idanuna sun gaji da ganin kallon tausayi da na ƙyama. Sun kira ni da juya, sun mayar da ni tamkar bishiyar da ba ta da amfani sai konewa. Ya Allah, ɗacin kalaman da nake haɗiya a kullum yana neman tarwatsa kirjina. Cikin nan nawa, wanda ya bushe ba tare da ya fito da rai ba, yana mini nauyi fiye da dutse saboda raɗaɗin da mutane suke jifa na da shi. Ya Allah ba zalunce ta ba, ban cuceta ba, ba ita ba wani ma ban cuta ba Allah, Allah banyi fushi ba dan ka bata ka hanani, banyi baƙin ciki ba Allah, amma ya Ubangiji, kada Ka bar ni a mace maras gado a bayan ƙasa. Kada Ka bar ni a matsayin wacce za a manta da sunanta da zarar ta koma cikin turɓaya. Ka san ba ni da kowa sai Kai, ba ni da madogara sai rahamarka. Idan laifukana ne suka toshe mini hanyar samun wannan baiwar, Ya Allah Ka yafe mini, Ka wanke ni. Kada Ka hukunta ni da laifin da zai sa in rayu cikin wannan ƙuncin. Ko da digon jini guda ɗaya ne Ka halitta a cikina, Ka sanya shi ya zama bishiyar da za ta rayu, Ka ba ni abin da zan rungume a kirjina na ji dumin abin da na Haifa, ko da hakan zai kasance silar cikar numfashina ne. Kada Ka bar maƙiyana su yi mini dariya, kada Ka bar waɗanda ke min gori su tabbata a kan maganarsu. Ka share mini wannan hawayen da ya zama abincina na rana da daddare. Ya Allah, Ka amsa mini, Ka ba ni tsuntsun da zai raya mini gida, domin Kai ne kadai mai jin kukan wanda kowa ya guje masa. Ya Allah ka sakawa mijina da aljanna, ka bashi ikon ci gaba da haƙuri da ni, Ya Allah mahaifiyata da ‘yan uwana ka ƙara musu lafiya da haƙurin zama da ni, Allah masoya na da suka damu da ni, ka ƙara musu lafiya da nisan kwana, Allah ka amsa amin.” Na shafa addu’a ta, na kwanta akan gado na ci gaba da raira kuka na a hankali, wanda ina yin shi yana rage min wani kaso na damuwar dake raina. Kamar daga sama na ji muryar Turaki yana kiran sunana. “Habibty, Habibty.” Cikin sauri na goge hawayen dake kwance a fuskata, na tashi zaune. “Habibty ki yi haƙuri dan Allah, abinda Laila take yi ba ta kyautawa, na rasa wacen irin macece ita.” “Bakomai, duk abinda take baya damuna, amma tabbas kalmar juya da take kira na da shi yana taɓa raina sosai wallahi.” “Ki yi haƙuri dan Allah, zan ɗau mataki sosai akai, bana son sake tura ta gida da ciki a wannan matakin, amma tabbas ta fara kaini bango.” Ihun su twins muka ji a falo, hakan yasa muka fito ba shiri, ina fita naga Laila ta riƙe hannunsu tana jan su. “Ke ina zaki kai min ‘ya’ya haka?” “Gidansu zasu bari, Aiman ya ce baya son bare a gidan ubansa?” “Waye Aiman?” Na faɗa ina mata kallon mamaki. “Ɗan da zan haifa mana, ko baki san namiji ba ne? To wallahi namiji ne kuma sai ya diro duniya ko mutuwa ne sai dai ki yi.” “Kinga Laila ba ni yaran nan.” Turaki ya faɗa yana matsowa inda take. “Wallahi bazan bada su ba, yau sai sun bar gidan nan.” “Laila ki ka ƙara taku ɗaya da yaran nan a sai kin bar gidan nan na faɗa miki.” “Aiman ne ya ce baya son bare.” “Waye Aiman, waye bare? Ɗan dake ciki ya faɗa miki, kuma ubansa ne ya ce masa su bare ne? To wallahi Laila yanda nake jin twins a raina ko shi Aiman ɗin bana jin sa haka, dan haka akan yaran nan kaɗai zaki iya rasa auren ki wallahi, tun da na fuskanci ke ba hankali ba ne dake, ke tsaya ki ji fa. Big Daddy ba ubana ba ne, idan na rabu dake babu abinda zai faru fa, na yi masa biyayyane na zaune dake, kuma kina cin albarkacin ita uwar twins ɗinsa, amma a yau ta ce a rabu dake sai na ƙarashe miki saki biyun da suka rage kin bar gidan nan.” “Akanta ‘ya’yan da ba naka ba shine zaka ce zaka rabu da uwar ‘ya’yanka, to bari na yi mata ɗan banzan duka sai ka gani.” Ta faɗa tana yiwa inda nake, cikin rashi sa’a ta zame da kafet ɗin falon nawa, ta faɗi ƙasa Tim, jini ya ɓalle mata da gudunsa, na tasake wani razanannen ihu. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (28). Da sauri na yo kanta, jinin da nagani ya yi matuƙar bani mamaki a kiɗime na ce. “Habibyu ɗauke ta mu tafi asibiti, jinin ya yi yawa fa.” Ɗaukan ta ya yi yasa ta a mota, muka nufi asibiti mafi kusa, muna shiga asibitin likitoci su karɓe mu aka shiga da ita ɗakin taimakaon gaggawa, tun iya nurses har babban likita yazo ya shiga da kansa, sai aka ɗauki wajen awa biyu sannan likitanya fito, a lokacin Turaki baya nan ya kalleni ya ce. “Ku same ni a ofis, idan ya dawo.” Na gyaɗa masa kai, yana shiga Turaki ya shigo na ce da shi. “Ya ce mu sameshi a ofis.” “To mu shiga.” Ya faɗa, ni ce na fara shiga sannan ya bi bayana. Bayan mun zauna likitan ya kalle mu ya ce. "Alhaji, mun gode wa Allah da Ya sa matarka ta tsira da rayuwarta, kuma aka samu nasarar ceto rayuwar jaririn tun kafin lokacinsa ya cika. Amma akwai wata gaskiya da ya kamata mu fuskanta game da lafiyar wannan yaron, wacce ta faru sakamakon faduwar da mahaifiyarsa yi lokacin yana ciki, har ya zama sanadin fitowar sa ba tare da lokacinsa ya yi ba. Lokacin da matarka ta fadi, mahaifarta ta sami matsala, wanda hakan ya sa jini da iskar oxygen da ke tafiya zuwa kwakwalwar jaririn suka yanke na wani lokaci kafin mu cire shi. Sannan kuma, jaririn ya sha ruwan mahaifa wanda ya ƙara toshe hanyoyin numfashinsa. Sakamakon rashin iskar oxygen da ƙwaƙwalwarsa ta yi na wasu mintuna, yaron ya sami matsalar da muke kira Cerebral Palsy Lalurar Shanyewar Kwakwalwa. Wannan ba cuta ce ta kwayoyin cuta infection ba, lahani ne da ya samu ɓangaren ƙwaƙwalwa da ke juya jiki.” “Innullahi wa’inna illahir raji’un.” Na faɗa, a take na ji kaina ya fara sara mun, ɗan da Laila ke ihu da hayagaga akansa ya zo da matsalal shanyewar ƙwaƙwalwa, kai Allah abuj tsoro ne. Na kalli yanda Turaki ya yi matuƙar shiga damuwa, yanayinsa ka ɗai zaka kalla kagane hakan, Likitan ya ci gaba da cewa. “Ga abubuwan da ya kamata ku sani kuma ku shirya musu, abu na farko shine Ba zai warke ba, amma za a iya taimaka masa. Wannan rauni ne na din-din-din a kwakwalwarsa. Ba shi da maganin da zai wanke shi ya ɓace gaba ɗaya. Sai dai za a riga ana ba shi magunguna da motsa jiki don rage zafin jiki da taurin tsoka. Abu na biyu kuma Yanayin Rayuwarsa. Yaron nan ba zai iya yin abubuwan da sauran yara suke yi cikin sauki ba. Akwai yauƙi da zai riga ya fito daga bakinsa, kuma yana iya samun matsala wajen hadiye abinci. Tsokokin jikinsa sun riga sun ɗaure, wanda hakan zai hana shi zama, rarrafe, ko tafiya da kansa. Gaba daya rayuwarsa za ta dogara ne a kan uwa. Sai kuma Zama a Asibiti, Ba za mu bar ku ku zauna a asibiti ba. Da zarar mun tabbatar numfashinsa ya daidaita kuma yana iya shan madara ta roba ko ta fida, za mu sallame ku ku koma gida. Jinyar wannan yaron a gida za a yi ta. Za ku ringa zuwa awo (clinic appointments) lokaci-lokaci kawai.” Yanzu kam a fili na ce. “Hasbunallahu wani’imal wakil, Likita yanzu shikenan haka zai dauwama kenan? Ya subahanallah.” “Zai yi komai amma a hankali, zai yi matuƙar jinkiri ne, sannan akwai Gargadi na Gaba. Saboda rashin karfin garkuwar jiki da matsalar haɗiya, zata iya kasancewa ya dinga yawan yin tari ko zazzaɓin sanyi (pneumonia). Ku kasance cikin shiri, domin kula da shi yana buƙatar hakuri, juriya, da sadaukarwa mai yawa daga gare ku." Sai a lokacin Turaki ya yi magana, muryarshi cike da sarewa ya ce. “Allah Ya bamu iko, Allah Ya bata haƙuri da juriyar iya jinyarsa.” “Amin.” Likitan ya faɗa, sannan ya ce. “Sai kuma matsala daga mahaifarta, babu tabbacin mahaifarta zata sake ɗaukan ciki, idan kuma ta dinga yi mata zafi a ƙarshe za a cire mahaifar baki ɗaya.” Ji na yi kaina ya sake sara min, wato kenan shi lalacewar mahaifa ba sai ka sha wani abu ba, idan Allah Yasa haka kawai sai ta sami matsala? Duk wani abu da Laila ke yi min sai na ji ya kau a zuciyata, tausayinta ya shiga ratsa jikina ta ko ina, tabbas Allah Abun tsorone. “Allah mun tuba Allah.” Na faɗa ina goge ƙwallar da ta fara zubo min a fuskata. Daga ofis ɗin Likitan Turaki ya kira gidansu ya sanar da su, haka ma gidansu Laila suma ya sanar da su, cikin ƙanƙanin lokaci asibitin ya cika ya batse da mutane, sai dai na hana shi sanar da kowa halin da jaririn yake ciki, har dare na tafi babu wanda ya sani, ina ganin wani kallo da ‘yan uwa Laila suke min, sai dai kawai na kawar da kai na yi kamar bangani ba. Sai da Laila ta kwana biyu a asibiti sannan ta farfaɗo, cikin ikon Allah mahaifarta ta bata sami matsala ba, amma da ta fuskancin halin da jaririn ta yake ciki ta yi kuka kamar ba gobe, haka Turaki ya sanar da Mommy abinda ya faru har ya ja faɗuwarsa, sai kawai ta ce. “Allah Ya kyauta.” Kwnana Laila biyar a asibiti aka sallamo su, bayanda ‘yan uwanta basu yi ba akan su tafi da ita ce ita a’a, sai ta zo gidan uban yaro ta yi gagarumin taron suna, da Turaki ya so hanta sabida lafiyar Jariri, amma na ce yabarta. Ranar suna Baby ya ci sunan Big Daddy, amma ana kiransa da Aiman, kamar yanda Laila ta faɗa ta yi gagarumin suna ita da ‘yan uwanta, dan babu Turaki babu abokansa sai ‘yan uwansa tsilli tsilli, a ranar sunan na ga Islaha, ta canja gaba ɗaya har ta sami mijin aure, wanu alhaji yana da mata ɗaya ita ce ta biyu, Alisha ma ta sake samun miji na biyu, daman tun bayan mutuwar aurenta bata sami miji ba, a lokacin na ce da Islaha. “Daman Alisha bata da aure? Naga ba a gidnaku take ba?” Ta gyaɗa kai sannan ta ce. “Seemah ma ai ba a gidansu take ba, kuma ita ma ba ta da aure, Big Daddy ne ya basu gida suke zaune ita da Alisha, kamar yanda na Yaya Turaki da Sardauna yake.” “Uhmm haka ne fa sai yanzu na tuna a gidanta ma kika zauna, amma ta ya akai Alisha bata taɓa kula da ke ba kuna gida ɗaya?” “To ai kamar yanda Yaya Turaki da Sardauna suke ba ruwan kowa da kowa to suma haka suke.” Na taɓe baki na ce. “Iko sai Allah.” A raina kuma na ce. ‘Wata wayewar dai ba amfani, ina dalili kuna ‘ya’ya mata ku bar gidan iyayenku kuje naku gidan ku zauna.’ Haka aka yi taron suna akwa watse, washe gari bayan anyi suna jibga jibgan raguna guda uku, Laila ta bi ‘yan uwanta suka tafi gida. Nama a farar leda aka ƙullo aka kawo min, na yi dariya na ajiye shi anan kan kujera, da almajiri na yazo amsar abincin rana na haɗa masa da shi akai ya tafi. Tafiyar Laila gida fa ya dawo dai dai, babu wata hayaniya babu damuwa komai ya yi tsit, Turaki da kan sa ya ce. “Habibty dama kar wannan fitinanniyar yarinyar ta dawo, wallahi nagaji da jin muryarta kamar kukan gyare.” Sai da na yi dariya sannan na ce. “Ai yanzu ta ci gida, uwar Aiman.” “Allah Sarki, ina tausayin Aiman wallahi babu yanda za ayi ya sami duk kulawar da aka ce a bashi daga wajen matar nan, da babu abinda ta ƙware da shi sai faman faɗa da hargowa.” “Allah zai kula da shi.” “Allah Yasa, gashi fa batasan matsalal da mahaifarta ta shiga ba, bazan iya faɗa mata ba gaskiyya.” “Eyh, rashin faɗar yana da matuƙar muhimmanci sosai da sosai kam.” “Allah kenan, tun farko abinda nake guje mata kenan, ina jiye mata ba ta yi wani dogon zama dake ba, kar ta je ta kwasarwa kanta haƙƙi amm taƙi, ta dinga isgili da gori, abinda Allah baya so kenan, shi ya sa ya yi mata sakayya tun da wuri, Allah Ya tsare mana imaninmu da zuciyoyinmu.” “Amin Habiby, amma wallahu na ji mata babu daɗi sosai da sosai, rashin haihuwa babban rashine.” “Wallahi hakane Habibty, amma ta wani fannin yanzu sai asami nustuwa da zaman lafiya, bakim kowa ya huta, duk da tana da guda ɗaya amma zata rage.” Bayan wasu kwanaku da tafiyar Laila, rayuwa me daɗi muke gudanarwa ni da Turaki, soyayya mi daɗi da tsayawa a rai, ninku kulawa da komai na soyayya Turaki sai da ya ninka min, a cikin kulawar soyayyar da yake ban ya ɗauke ni ya kaini Babban shagon NANA DAR, shagon da ya ji kayan siyarwa na mata, kama daga laces, atmafofi, shaddoji, mayafai, Hijabai, jaka da takami, turare, da duk wani kayan ado da ƙyale ƙyale na mata, ya kuma sanar da ni wajen nawa ne, da sunana da komau nawa ya buɗe shi, ranar na yi kukan farin ciki sosai da sosai. Tun safe ina kicin ina ta faman aiki, Turaki da su twins suna falo suna game, breakfast ɗin da nake yi ya yi nauyi yaki kammala da wuri har wajen ƙarfe sha ɗaya na safe, kncoking na ji anayi a ƙofar mu, ina cikin ɗin na ce. “Twins someone at the door.” Suka yi banza kamar basu ji ba, na sake kiransu, suka yi kamar basu ji ba, har na kira Turaki. “Habiby ana bugu.” “Game muke.” Ya faɗa, cike da takaicu na fito daga kicin ɗin, suk suna zuane sun gaye Tap a gaba suna game, ina mita na nufi ƙofar na buɗe, ina buɗewa idona suka yi karo da Sardauna. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (29). Yana sanye cikin wani farin yadi, ya canja kammani gaba ɗaya kamar ba shi ba. “Habibty waye anan, na jiki shiru.” Na ji muryar Turaki, gani wani irin murmushi da Sardauna yake min na ji ya fara ban tsoro, sai na ji ance. “Mu shiga.” Sai a lokacin na leƙa, na ga ashe ba shi kaɗai ba ne, na matsa musu tare da faɗin. “Ku shigo.” “Su waye.” Turaki ya tare ni, na sa hannu na nuna masa Sardauna da wanda yake shigowa. “Ah Doctor, Sardauna yaushe kuka dawo.” “jiya.” Wanda Turaki ya kira da Likita ya faɗa, waje suka samu suka zauna, na kalli twins na ce. “Oya muje ku yi breakfast.” Suka miƙe gaba ɗaya suka yi dinning, ni kuma na koma kicin na fara fito da abincin, har na gama jerawa sannan na zuba musu, ina cikin zubawa Turaki ya ce. “Habibty idan kin gama, meet me here.” “Okay.” Na faɗa tare da nufo inda suke, daga kusa da Turaki na zauna, sannna na ce. “Ina kwanan ku?” Likitan ne ya amsa da cewar. “Lafiya ƙalau, Yawwa Turaki i was saying, a haka dai gashi kamar mai cikakkiyar lafiya, zai yi magana zai yi aiki, zai yi tunani da lissafi. Amma da zarar ciwom ya tashi Sardauna yana komawa mahaukaci ne tubaran, ba shi da aiki sai kiran Sunan Nana, yana ganinta ta ko ina, yana surutai kuma wansa yaje inda yake yana dukansa, a taƙaice dai mahaukaci mai duka yake zama idan ciwon ya tashi.” Kallon Sardauna na yi, a haka dai gashinan mutum cikakke, amma na ji ana cewa a baɗani ba haka ba ne, wannan shine ake kira mahaukaci da riga kenan. “Raɗaɗin abinda matarsa Bilkisu ta yi masa ne, ya haɗu da zafin rashin Nana da ya yi ya haifar masa da brain damage, sannan a yanzu Sardauna baya iya tafiya ta da kai minti biyar, sakamakon ciwon da matarsa ta goga masa, anyi ƙoƙari sasai ganin an kashe ƙwayoyin ciwon, duk da a yanzu bai warke ba gaba ɗaya, amɓa ciwon ba shi da sauran illa ga lafiyarshi, sannan kuma wani ha zai goga ba, to a wannan ƙoƙarin ne kuma allulorin aka samu wata ta taɓa lafiyar ƙafarsa, ta haifar masa da hakan, saurin shi a tafiya ya ragu da kaso 60 cikin ɗari, kwata kwata tafiyar shi babu sauri, sannan babu tabbacin iya fitar da ‘ya’ya daga jikinsa, to waɗan nan abubuwan ne suka taru suka yi masa yawa suka haifar masa da brain damage, sai kuma ya kasance kamar akwai wani abu a ciki, to da na dawo da shi ne wadda take a matsayin mahaifiya wajen shi ta ce idan akwai haƙƙi bana kowa ba ne sai na Nana, a take na tuna sunan da yake kira kenan a duk lokacin da ciwon ya tashi, shine suka bamu address da na zo kuma naga ashe ma matarka ce.” “Hhhmmmm.” Turaki ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya, ni dai hankalina yana kan Sardauna, waɗan nan abubuwan da aka lissafa duka akanshi shi ɗaya, kai duniya ta kifa masa, Sardauna matashi ɗan wanka, mai ji da kai mai ji da kuɗi, mai tun ƙaho da fariya, shine ake nufin ya zama mahaukaci da riga? Kai innullahi wa’inna illahir raji’un, na yi tunanin abinda ya faru da Sardauna shine kaɗai hukuncin shi ashe akwai wani a gaba, ni dai a yanzu an zo matakin da zan yafewa Sardauna. Duk da shi ya cuce rayuwata amma Allah Ya kawo min Turaki ya kuna tsame ni daga duhun da Sardauna ya sani, bayan shi an yi min abubuwa da yawa, kuma na yafe me zai sa shi naƙi yafe na shi? “Habibty kin ji dai, kin ji komai da kunnenki, kin ji dukkan nin halin da aka ce yana ciki, nasan da kyakywar zuciya, ba wai zan miku daɗin baki ba ne, dan Sardauna ya kasance nawa ba, amma tabbas zan ji daɗi idan kika yafe masa, tabbas bai kyauta ba, ya cutar dake ya zalunce ki, kuma har yanzu kina kuka da wani daga cikin zaluncin da ya yi miki, amma ki sani Allah Ya yi miku wasu ni’imomi da dama daga baya, kuma hakan nan Allah Yana son bayi masu afuwa, ki yi tunani, ku yanke hukunci da zuciyarki.” “Hhhhm.” Nima na sauke wata ajiyar zuciya, tabbas nasan Sardauna ya yi min abubuwa da dama, amma kuma akwai alheri a cikin yafiyar. A take zuciyata ta dawo min da lokacin da ya ce. “Nana, kin sami labarin abin da na yi wa mahaifarki ko? To ba iya wannan ba... ki sa rai da shirin ganin abubuwa da yawa nan gaba Nana, waɗanda ma ba lallai kanki da rayuwarki su iya daukansu ba!” Wasu zafafan hawaye suka fara fitowa daga cikin idona, wani ɓari na zuciyata ya ƙara haƙaito min maganarsa da ya ce. “Na gode Nana... na gode da kika share mini kukan zuciya ta hanyar aura min mace mafi soyuwa a raina. Na gode da kika cika mini burina na aurar min da matar da nake so a cikin zuciyata." A takw kuma komai ya shiga dswo min kamar an kunna majigi. "Nana! Ba ke nake so ba. Ƙuciyar jikinki kawai nake so... wadda na riga da na gama mallaka gaba ɗaya. Nana, ban taɓa son na rayu da ke a matsayin macen da zan so ba, sai dai na rayu da ke a matsayin wadda zan killace ta, na hana ta kula kowa a duniya, saboda zazzafan kishin ki na ƙaddara da nake ji a rana, Nana." "Nana! A yanzu haka zan sauwaƙe miki, zan raba aurenmu. Amma kuma zan miki alfarma guda ɗaya, wadda ita ce zaki zauna a gidana a ƙarƙashin kula ta da ikona tun daga yau har ranar da zaki mutu, Nana. Tun da dai ke da kanki kika nuna idan babu ni ba zaki iya rayuwa ba. Kuma ko da na sake ki kika tafi, ai ba ki da kowa a duniyar nan, ba ki da inda zaki tafi... ‘yan uwa ne babu, ƙawaye babu, Nana! Ba ki da wata mamora ko amfani a rayuwa. Shi ya sa zan barki ki ci gaba da zama a nan tamkar baiwa, ba tare da kin faɗawa kowa cewar na sake ki ba. Gimbiya Bilki... ɗauko takarda ki rubuta mata takardar sakinta." Bansam lokacin da na fashe da kuka ba, wanda har sai da twins suka bar kan dinning suka yo kaina suna faɗin. “Maamah what happened?” Na goge hawayen, cikin muryar kuka na ce. “Bakomai, ku je ku ci gaba da cin abincin ku.” Na juya na kalli Turaki, na kalli likitan na kalli Sardauna, bakina na rawa na ce. “Na yafe masa, in sha Allah na yafe masa har cikin zuciyata, ina roƙon ubangiji ya sanyaya makwancin mahafina da ya rasu da baƙin cikin abinda Sardauna ya yi min.” “Ki yi haƙuri Habibty dan Allah, Likita ta yafe masa Allah Ya bashi lafiya.” “Amin amin.” Ya faɗa sannan suka tashi suka tafi, tun daga wannan lokacin na manta da Sardauna sa rayuwarsa, na riƙe mijina da ‘ya’yana muka ci gaba da rayuwa, ana cikin wannan yanayin ne Ra’is ya zo da maganar auren Lamrah, ta cikin whatsapp group na family ɗin mu muka fara magana, na zage ina ta voice note sai baloƙoƙo nake, na ɗauke ido na kamar Turaki baya wajen na ce. “Wallahi bazaka auri ‘yar wannan mutumin ba, nu kaina nan ba so nake ya ba, ji yake kaman ya cire ni daga gidan, ni da ba ɗan sa na cikinsa nake aure ba, bare kuma kai da zaka auri ‘yar cikinsa, wallahi Ra’is kabar maganar nan kafin ranka ya ɓaci, na ce ba za ayi ba.” Ina faɗin haka ma tura recording voice note ɗin, daman su Yaya Radiya duk suna ji sunce bazasu ce komai ba a tsakaninmu, ranar da na bawa ‘yan gidanmu labarin zuwa Sardauna da yafiyar da na yi masa Yaya Rumaisa tsinemin ne kawai ba ta yi ba, zagi da baƙar magana dai na sha shi, ƙarshe ta ce an janye yafiyar, ba ayi ta ba, idan ma na yafe su basu ya fe ba, kuma bazasu yafe ba. To da akazo wannan maganar ma kowa ya ce abinda na yanke shikenan, ni kuma na dage kan Ra’is ba zai auri Lamrah ba, badan bata sa tarbiya ba ko wani abu kawai halin mahaifinta. “Ranki ya daɗe a dinga yi ana haɗiyar yawo, kin rufe ido kamar ba kya ganina sai mahaifina kike kushewa, Lamrah fa ‘yar uwata ce amma kin rufe ido.” “Ba wai rufe ido bane, kafi kowa sanin halin Big Daddynku, ni bazan so ya tsani autan mu ba.” A daidai lokcin wayar Turaki ta fara ringing, ya nunu min ya ce. “Kinga Seemah akan layi, ‘yar halak.” Ya ɗaga yasa a buɗaɗɗiyar sifika. “Turaki kazo asibiti yanzu, hawan jini Big Daddy ya tashi.” Ta faɗa kana jin muryarta kasan ta sha kuka ta gode Allah. “Innullahi wa’inna illahir raji’un.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (30) “Turaki kazo asibiti yanzu, hawan jini Big Daddy ya tashi.” Ta faɗa kana jin muryarta kasan ta sha kuka ta gode Allah. “Innullahi wa’inna illahir raji’un.” Turaki ya faɗa tare da kashe wayar. “Habibty miƙo min key ɗina.” Da gudu na shiga ɗaki na ɗauko masa key na bashi ya fita, banyi garajen cewa zan bishi ba, dan nasan ma babu lallai ya ce zai tafi da ni, yana fita nasamu waje na zauna, na shiga tunanin daman yana da hawan jini? Ko da yake yawancin masu kuɗin nan ba a rasa su da hawan jini, ta shi na yi na shiga kicin zan ɗaura girki, sai dai ina kunna gas na ji, wani irin wari ya dake hancina, wanda ya haifar min da wani irin tashin zuciya marar daɗi, banyi aune ba na ji amai yana taso min, na yi ƙoƙarin fitowa na shiga toilet amma abu ya gagara haka na yi ta faman kwara shi anan, ina tsaka da aman na ji ana magana a falo na, ban iya amsawa ba aka shigo, duk da na yi tunanin ganin Anty Adizatu, tun da suka dawo daga kano take cemin zata zo zata zo, sai jiya da dddare take ce min yau zata shigo, har na bata location ɗin gidan. Da sauri ta shigo kicin ɗin tana faɗin. “Subhanallahi Nana me ya sane ki?” Na fara girgixa ma ta kai sabida jigarta da na yi, ta dafa min baya na ci gaba da kwara aman, sai da na gama sannan ta kama ni ta kaina toilet na wanke bakina, ita ta dawo ta gyara wajen. “Sannu Nana, me yake damunki?” Cikin muryarta dake ɗauke da gajiya na ce. “Wallahi lafiya nake, da shiga kicin na ɗaura girki shine na ji warin gas ɗin ya dake hancina ya haifar min da tashin zuciya.” Wani kallo naga tana yi min, wanda har sai da na ji na tsargu, sannan ta ce. “Al’ada fa?” “Bangane ba?” “Na ce yaushe rabon ki da period?” “Ni da yake wani lokacin sai ki ga ina tsallaken wata ɗai ɗai banayi, to ban wani fahimta ba.” “Last month kinyi?” Na girgiza kai. “Kina da test strip?” “Mene haka?.” Na tambayata cike da mamaki. “Abun gwada ciki.” “Me zai haɗa ni da shi?” Miƙewa ta yi, sannan ta ce. “Ina zuwa, kaman wani pharmacy nagani anan bakin layinku ko?” “Eyh pharmacy ne.” Na bata amsa ta fice, sai da ta fita kuma kaina ya kawo haske, yanzu idan aka ce ciki ne da ni fa? Kai Ya Allah, haka kawai na ji zuciyata ta yi sanyi, na nemi duk jirin da ɓacin ran na rasa, ina nan zaune ta shigo da shi a leda ta ce. “Ungo, je ki gwada.” “Ya ake gwadawa?.” “Idan kika sami fitsarin kadan a cikin wani ƙaramin abun da na tawo da shi daga pharmacy ɗin sai ki tsoma strip din, bayan kin cire  strip ɗin daga ledarsa, zaki tsoma alamar bakinsa inda aka yi kibiyar nan daga wajen da aka rubuta MAX a cikin fitsarin na tsayin daƙiƙa 5 zuwa 10. Sannan Kar ki nutsar da shi ya wuce layin MAX din. Daga nan Sai ki ɗauko shi ki a ijiye shi a kan wuri madaidanci na tsawon minti 3 zuwa 5.” “Tom, amma me zan gani ya zama akwai, me zan gani ya zama babu?” “Wai baki sani ba? Kina nufin baki taɓa amfani fa shi ba?” “To haihuwar nake?” Ta matso kusa da ni, sannan ta ce. “A jikin strip ɗin akwai layukan nan masu kalolin ruwan hoda, kin gansu ko?” Na gyaɗa ma ta kai alamar eyh, sannna ta ce. “Kinga layi biyu wannan yana nufin Akwai ciki Positive kenan, sannan ko da kinga layin na biyu ya fito da haske sosai bai nuna ja sosai ba, muddin yana da ɗan dishi-dishi, to akwai cikin. Amma idan kika ga layi ɗaya wannan yana nufin Babu ciki Negative kenan, layi guda ɗaya ne kawai na saman control line ke fitowa, kin gane.” “Eyh na gane, Allah Yasa ya zama possitive.” Na faɗa ina tashi, ta amsa da amin. Ina shiga toilet na yi dukkan abinda ta gwada min, cikin minti sha biyar da shiga ta na fashe da wani irin ihun murna sakamakon posstive da na gani, ina fitowa falo na durƙusa a ƙasa na yi wa Allah sujjadar godiya, na fashe da wani irin kukan farin ciki, wai yau ni Nana ke ɗauke da ciki, ashe zan haihu zan ga ‘ya’yana, bayan wannan uwar gwagwarmayar, bayan wannan uwar wahalal, na ɗaga hannuna sama na ce. “Ya Allah, ka bani masu albarka waɗan da zasu zama sanyin idaniya na, Ya Allah karka bani ‘ya’yan da bazasu bi umarnin ka ba, da bazasu yi koyi da annabinka ba, Allah ka albarka ce su, Ya Allah duk wata mace dake buƙatar haihuwa ka bata masu albarka.” Haka muka yi ta farin ciki ni da Anty Adiza, kafin ta tafi ta tabbatar min da muje asibiti wannan gwajin gida ne, sannan nasanar da Turaki komai amma idan zamu iya mu ɓoye shi har sai ya kai wani matakim girma, sai da ta ce Turaki na tuna wai ashe Big Daddy ba shi da lafiya yana asibiti, wallahi shaf na manta, sai bayan ta tafi na kira Turaki a waya, yana ɗagawa ya ce. “Habibty na yi fushi.” “Sorry Habiby, kana fita Anty Adiza tazo kuma zuwanta da wani kyakyawan albishir, wallahi duk shine ya sa na sha’afa, Ya jikin nasa?” “To da Sauƙi za a ce, amma likitocin sun tabbatar da Big Daddy ba zai ƙara tafiya ba, kuma manyan likitocin ne har guda uku da ƙasar waje, kinsan ashe shi gwamnati ta yi canciling visa ɗin shi ba shi da damar sake fita wata ƙasar.” “Ayyah Allah Ya bashi lafiya, zaka dawo yau ne?” “Eyh zan dawo me ya faru?” “A’a bakomai sai ka dawo.” “Yanzu ma Laila ta kira ni wai yau zata dawo.ɗ “To Allah Ya dawo da ita lafiya.” “Amin Habibty, ai yanzu ina jin ba za a sami matsala ba, sabida naga yanda jikinta ya fara sanyi da jinyar Aiman.” “Allah Sarki Aiman, Allah Ya bashi lafiya.” “Amin Habibty.” Jin ƙarar shigowar saƙo na yi a wayata, hakan yasa na ce da Turaki. “Tom Habiby sai ka dawo, Allah Ya bashi lafiya.” Ya amsa da amin tare da kashe wayar, sai da na duba wayar na ga ashe saƙon ma ta email aka turo shi, na shiga na duba na ga wai message ne daga wata babbar ƙungiyar NGO’s dake da babban rashe a ƙasar Chaina, sun turumin saƙon ne suna son na zama babbar wakiliyar su anan nigeria, ƙungiya ce da ke tallafawa mata marasa haihuwa, da kuɗaɗe, abinci, likitoci da zasu dinga duba su, sannan kuma suna tainakawa mata nakasassu, da kuɗaɗe, sutura, da likitocin da zasu dinga duba su, a taƙaice dai suna son na zama shugabar gidauniyar anan nigeria, banyi musu reply ba na ce sai Turaki ya zo ya yi min ƙarin bayani, duk da dsi banji ma sha’awar yi ba, sabida bana son na ɗaurawa raina abinda zai wahalal da ni.  Ina zaune na rasa abinda zanyi, na kira Hajiya mun gaisa, na kira Yaya Rumaisa da Yaya Radiya, na kira Yaya Ridwan na kira Ra’is, duka mun gaisa kowa sai ya tambayeni me ya faru sun ji muryata raɗau, sai da kawai na yi dariya na ce bakomai. Ana idar da sallah magariba na ji shigowar ‘yan uwan Laila, ba shiri na tashi na koma ciki, sabida kar ma na ji me suke cewa bare raina ya ɓaci. Har suka yi suka gama ina ciki ban ji me suka ce ba, su twins ma na hanasu fita compund su yi wasa na ce duk su yi a ɗaki, ba dan ran su ya so ba suka yi anan, wajen ƙarfe takwas Turaki ya dawo, kana ganinsa ka san a gajiye yake, sannu na yi masa sannan ba shiga na haɗa masa ruwan wanka, bayan ya yi ya ci abinci na tanbaye shi jikin Big daddy ya ce. “Habibty wai kin san yana halin wannan jinyar yake magana akan ki, wai ki yi masa alfarama ki yafe masa, ashe abinda ya ja faɗuwar ta shi Lamrah ce ta ce masa mugun halin sa yaja musu baƙin jini sunƙi auruwa, sannan ta faɗa masa kin hana ƙaninki aurenta, sabida mugun halinsa. Mama Amina ma ta ce Allah Ya isa abinda ya yi wa ‘ya’aynsa, ƙarshe ma ta bar masa gidan shine abinda ya faru ya ka shi ga faɗuwar, daman kowa ya gaji da halinsa ina jin Hajiya Falmata wai Allah Yasa ya mutu, ko zai bawa mazajen su damar da zasu juta kasuwanci suma, shima duk ya haɗa ya riƙe komai.” Duk jikina ya yi sanyi, na ce. “Habiby ba wai dan wani abu na hana Ra’is auren Lamrah ba, kawai ina tsoron halin mahaifinta ne kaga yanda ni kaina nake fama da shi.” “Hakane Habibty, amma ayi afuwa yanzu a halin da yake ciki ma me zai iya? Ki yi haƙuri dan Allah.” “Amaryarka ta dawo fa, sannan ina so gobe zanje asibiti naga likita dan Allah bana jin daɗi.” “Tom sai muje na kaiki, bari na je wajen amarya.” “Tom Alhaji.” Legendspen 08129553971. SARTSE BOOK 3 Sayyid. (31) RUFEWA. Tun da Turaki ya fita na tashi na shiga ɗakin sh twins na tarar har sunyi bacci, na gyara musu kwanciyarsu na lulluɓe su, na koma ɗaki na kwanta, daman ban saka ran dawowar sa ba sai da safe. Washe gari ma Turaki bai shigo ba har su twins suka tafi makaranta, sai wajen tara ya shigo bayan mun gaisa na nuna masa email din da aka yi min jiya, bayan ya gama karantawa sannan ya ce. “Habibty wannan babbar dama ce a gareki, aikin NGO’s da Chaina kinsan wannan ba ƙaramin aiki ba ne, kuma za a sami ci gaba da sauƙin abubuwa da yawa a ƙasar nan, masu fama da waɗan nan cuttukan zasu sami sauƙi da rangwami, in dai har wannan aikin ba zai kawo miki cikas a aikin da kuma shagonki ba to ina bayanki, amma ki yi shawara da ‘yan gidanku.” “Yan gidan mu kuma? Akwai wanda zanyi shawara da shi da ya wuce kai ne?” “Nufina ki sanar da su suma, ni dai ina goyan bayan yin wannan aikin Habibty sosai da sosai.” “Bari na shirya muje asibitin, daga nan sai na duba big Daddy na wuce gidan Hajiya kafin su twins su dawo, amma yanzu bari na shiga na ga Aiman.” “Toh shikenan Habibty.” Sai da na shirya har jakata na ɗauka sannan na shiga part ɗin, karo na farko da na shiga part ɗin Laila tun zuwanta gidan, a wani ya tsine take amsa gaisuwar tawa, na duba Aiman na fito abuna, ina fitowa na tarar da Turaki ya fito muka shiga mota muka je asibiti, tare da shi muka shiga ganin likitan, banji kunyarsa ba na ce. “Daman jiya ne bayan na yi amai haka da tashin zuciya na gwada test strip kuma ya ba ni possitve shine na ce zan zo nan a gwada ni da komai da komai.” “Kai Ma sha Allah congratulations Hajiya, amma yanzu kina likita ba zaki iya gwada kanki waɗan nan abubuwan ba.”  Na yi nurmushi na ce. “To ai mu ɓangaren Pharmacy ne ko?” “Duk da hakan dai, bari na haɗaki da nurse ta yi miki.” Juyawa na yi na kalli Turaki, na ga yanda ya haɗa hannaye biyu yana kallona, na yi murmushi na ce.  “Habiby nima jiya na gwada.” “Hhhhm.” “Allah fa.” A daidai lokacin kuma nurse ɗin da zata gwada ta shigo, muka fita na bata duk wani abu da yakamata, sakamakon asibitin ya nuna cikin wata biyu ne, sai kawai ganin Turaki mu ka yi ya zube a ƙasa yana sujjada tare da godiya ga Allah, ni kaina sai na ji wata ƙwalla a idona, karo na farko da na ga Turaki ya zubar da hawaye, tun bayan lokacin da nake ciwo a gidan Sardauna.  Daga nan muka wuce duba Big Daddy, lokacin da na ga yanda Big Daddy ya canja ya koma kamar wata hallitar ta daban sai da na tsorota, fuskarshi ta mammaule, can ys kumbura can ya sace,  ga bakinsa ya murguɗe, duk masu jinyar kallo ɗaya zaka yi musu ka san a gajiye suke, wasu ma ba dan Allah suke ba, dan su Hajiya Falamta da Maman Sardauna duk babu su a wajen. Cikin gurɗaɗɗiyar hausar sa ya ce. “Nana, ki yafe min dan Allah.” “Me ka yi min?” Na faɗa, dan ni na fara tsorata da kowa wai Nsns yafe masa. “Ina neman alfarma a wajenki, ki yi wa Allah ki bar ɗan uwanki ya auri yarinya ta, wallahi na tuba daga abubuwan da na aikata, na ƙyama ce ki sabida baki da arziƙi irin namu, wanda gashi a yanzu bai yi min komai ba, tin da bai hanani kwanciya jinya ba, na aikata son zuciya ga ‘yan uwana da ‘ya’yansu, sabida kawai ina ƙyamar ki na yi wa mijinki aure dan Allah ki yafe min.” “Ni ba abinda ka yi min, kuma in sha Allah Ra’is zai auri Lamrah, wannan kuma tskaninka da ‘yan uwanka da ‘ya’yansu babu abinda zai shafe ni.” “Nana, ni na bawa Sardauna shawarar Lalata miki mahaifa, ni na ɗora shi a kan tsarin da zai hanaki haihuwa, sabida bana so ki haifi ɗa ya fito a zuri’ar mu.” A take na ji wani hawaye ya zubo a idona, wani irin abun me zafi ya tsaya a raina, ba tare da na ji kunyar wani ko nauyi ba na ce. “Ko zan yafe maka komai wallahi bazan yafe wannan abun ba, sabida ka cutar da rayuwata.” Ina faɗin haka na fice, kwata kwata banji ma zan yafe wa wani Big Daddy ba, Turaki ya biyo ni yana kirana, na yi banza da shi dan wallahi bazsn yafe wa Big daddy ba, ai ba ubana ba ne. “Ki tsaya na kai ki gidan Hajiyar Mana.” “Zan hau mashin.” Na faɗa, dan kar ma mu shiga mota ya ce zai karanta min sharrinsu na ‘ya’ya maza yasa na yafe masa.  “Ba cewa zanyi ki yafe masa ba Habibty, ni kaina bazan bari ki yafe masa ba wallahi, kawai ki tsaya na kai ki.” Jin abinda ya faɗa ya sa na tsaya, ya ɗauko motar muka tafi, a gida ma ban faɗawa Hajiya ba sabida naga Lamrah tana shirin zam surikarta hakan zai iya ɓata ta, sai kawai na sanar da ita zance samun ciki da kuma aikin gidauniya da ƙasar Chaina, ina gidan Yaya Rumaisa ta zo itama na faɗa mata komai ciki da aikin, amma na ce ni banajin yin aikin. “Amma baki da hankali, to maza ki karɓa Nana, wannan aikin zai baki ɗaukaka ki zama wata a ƙasa, zaki sami lada, xa a girmamaki da iyayenki.” “Hakane kuma, kinga idan na shiga sai na shiga da niyar Allah Ya kai ladan ga Alhaji.” “Yawwa ko ke fa.” Da daddare Turaki ya zo ya ɗauke ni mu ka koma gida, nasanar da shi na amince da aikin, a daren muka tsara reply muka tura musu aka yi sa’a cikin daren suka dawo da amsa, suka sanar da ni zanyi baƙi ‘yan ƙasar zamu tattauna da su ds komai da komai. Tun daga wannan ranar ban sake zuwa asibiti ba kuma Turaki ma bai ce na je ba, a haka mu ka yi wannan zaman da ‘yan chaina ni da Turaki da Yaya Ridwan, aka ba da takardar contract nasa hannu a kai na shekara goma, sannan idan na ga da halin ƙarawa sai na ƙara, su suna son yi abun ne babu iyaka, ko da wani ya gaji wani ya ɗora.  Cikin ƙanƙanin lokaci muka fara gabatar da aikin gidauniyar, sabida irin rabo da ayyukan da gidauniyar ke yi cikin ƙanƙanin lokaci aka santa, abu kamar wasa na fara samun mabiya a shafina na facebook da instgaram har da X ma. Big daddy sai da  ya yi jinyar wata biyu a asibiti sannan aka dawo da shi gida, bayan an dawo da shi aka sanya bikin Ra’is da Lamrah, duka wannan dukiyar da Big Daddy yake ji da ita, yana ji yana gani aka mayar da kasuwanci da juya dukiyar ga ‘yan uwansa. Laila bata fuskanci ina da ciki ba, sai da cikin ya kai wata shida, sabida gaba ɗaya Laila ta canja ko ganin ta ma ba ayi, ba fita biki ba fita suna, tana ta faman jinyar Aiman, sabida wasu irin cututtuka da yake yi, daga wannan sai wannan, gaba ɗaya ta fita hayyacinta ta rame ta yi baƙi huluƙ, duk da tana da masu aiki har biyu, amma dai ita ce uwa jinya akanta take. Ranar da Allah Yasa ta ga cikin na shiga duba Aiman ne sabida rashin lafiyar da yake yi kwana biyu, tun da na shiga take kallona, har dai ta kasa haɗiye abinda ke ranta ta ce. “Nana ciki ne dake?” “Eyh, Laila.” Na bata amsa, ta sake kallona sannna ta ce. “Uhmmm sannu, ashe kina haihuwa.” “To gashinan dai kinga ni, samu da rashi ai na Allah ne.” “Nagani kam, yanzu gashi na samu yanda na gama cika baki, amma yazo da lalurar da ta zaunar da ni waje ɗaya, sai na ji daman ban haife shi ba.” “A’a Laila, kar ki ƙara tafka wani kuskuren dan Allah, ki yo haƙuri ki ci gaba da jinyar shi Allah Ya baki lada, ya kuma baki wasu a gaba.” “Amin na gode.” Daga haka na fita, a yanzu na rage zuwa wajen aiki dan ma ina tunanim ajiye aikim zanyi sabida yanda babban shagona na kayan sawa yake daɗa shahara a jihar jigawa dan ba ma iya dutse ba, tin da na fara aiki da wannan gidauniyar cinikin shagon nawa ya ƙara da kaso 50 cikin ɗari, kullum cikin order kaya ake shagon, ni da ba zama nake ba, amma kuma komai yana zuwa cikin waya ta, shiga da fitar kuɗi. Kuma ban kasance mai sa ido akai ba, tun da nasan masu kula da shagon suna ƙoƙari akai, kuma rashim sa idon da na yi musu shi yake ƙara musu amana, sannan na yarda da wani abu a tsarin rayuwa mussaman ta kasuwance, duk kularka sai ancuceka, dole sai wani ya yi kuɗi da kai, dan haka kasance mai adalci da kyautata mu’amala, ka kuma miƙawa Allah ragamar kula da komai.  Cikina yana wata takwas aka yi bikin Lamrah da Ra’is, bawani biki ne aka yi na shagali ba mussaman mu anamu gidan, amma ɓangarensu Mama Amina sunyi shagalinsu ba ruwansu da jinyar Big Daddy, sun yi gagarumim biki cikin gidan, dan ranar da aka kai amaryar ma da daddare sai da Mama Amina ta haɗa mana Family night, wai kowa yazo ya ci ya sha ya wuce gajiya, gaba ɗaya sai a shagalin bikin na ga Sardauna, ya canja gaba ɗaya, ya rame ya yi wani kala, kuma a yanzu baya tafiya da ƙafarsa sai a kaken guragu yake tafiya, yan dai miƙewa ya yi sallah, kuma zai iya zama a kujera, amma tafiya ce ba zai iya ba. Kasancewar suna da arziƙi suka siya masa wani irin keke mai rai da lafiya, wanda ba ruwanka da mai turaka kai za ka yi komai da kan ka. An cikin Family night ɗin aja jiyo hayaniya da Surutai a sama ɗakin Big Daddy, da sauri sauri muka nufi saman, muna shiga muka tarar da Sardauna zaune kan kekensa kusa da Big Daddy ɗin, yana kuka yana cewa. “Big Daddy bazan taɓa yafe maka ba, duk wani mugun abubuwa da kasa ni na aikata, kai ne kasa na zama mugu a cikin ahalin nan, kasan na dinga haɗa faɗa a tsakanin matan gidan, duk sabida kar azo yi maka magana akan kuɗaɗen da kake cinyewa, duk wani abu da ya faru da ni na sakayya kai ne ka ja min, na yi dana sanin kasancewa a tare da kai.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 3 Sayyid. (32) ƘARSHE. Gaba ɗaya ɗakin ya yi shiru, kowa yana bin Sardauna da ido, big Daddy kuma sai buga ƙafa yake shine abinda yasa muka ƙara, alamun yana som ya yi magana amma bakin rufe, sai zubar da hawaye yake, Sardauna ya ci gaba ea cewa. “A yanzu nasan gaskiyyar cewar ni ba ɗan wannan gida ba ne, ban da alaƙa ta kusa ko ta nesa daku, dukkanin abinda kuka yi min na gode, Allah Yasaka muku da alheri, kuma ina neman yafiyarku bisa ga haka. Duk wani abu naku da yake wajena na haɗe su na ajiye, zan tafi na je na yi rayuwa babu kowa babu komai, domin ita ce rayuwar da takamace ni, ba iya haƙƙin Nana bane akaina, akwai manya haƙƙi da yawa a kaina, na raba zumunci, na ƙulla shari kala kala, duk a bisa huɗubar wannan mutumin da yake kwance, ya kaini waje da yawa na shaida zir akan abina ban gani ba, kuma bansani ba, ta ina rayuwa zata bar mu? Ina neman afuwarku dan Allah, wannan shine ganinku da ni na ƙarshe a rayuwa ku yafe ni.” Gaba ɗaya jikin kowa ya yi sanyi, hawaye suka wanke fuskokin mutane, Mama ta ce.  “Sardauna ba ni na haife ka ba, amma ni ce na raine ka wajena ka girima ka taso, ko baka da alaƙa da wannan ahalin ni kana da alaƙa da ni, sabida nono na ka sha, dan haka ba zaka je ko ina ba kana tare da ni, tabbas ka aikata abubuwa da yawa amma rayuwa ta gaya ma gaskiyya kuma ka yi tuba irin tuban da Allah Yake so, dan Allah Sardauna ka zauna tare da ni.” Ya girgiza kai, ya ce. “Mama, kin soni, son da ko uwar da ta haife ni shi za ta yi min, kinyi ƙoƙari akaina baki taɓa nuna min ƙyama ba ko wani abu, amma na kasa miki sakayya mai kyau, bazan iya ci gaba da zama dake ba ina kallonki ina tuna mugayen abubuwan da na yi miki, tabbas a yanzu lokaci ne da zan girbi abinda na shuka.” Ba yanda ba ayi da Sardauna ba amma ya ce shi tafiya zai yi, ta dole aka ƙyale shi ya tafi. Haka muka koma gida gaba ɗaya jikinmu ya yi sanyi ƙalau, washe gari da safe kuma aka tashi da labarin mutuwar Big Daddy, zuciyarsa ta buga.  Bayan sati guda da mutuwar Big Daddy aka fara raba dukkanin wani abu na family da yake wajenshi, komai aka raba shi sai babban kamfinsu guda ɗaya shine aka bari aka ci gaba da juya shi, raywa kenan duk abinda ya daɗe yana ƙullawa ya ƙare, duniyar kuma ya tafi ya barta.  Bayan Shekara biyar.  Rayuwa ta sauya abubuwa da yawa sun faru, a cikin shekara biyar Allah Ya azurce ni da haihuwar yara maza guda biyu, mai sunan Alhaji ne farko wanda muke kiran shi Abhi, sai bayan shekara uku na haifi wani namijin da aka sanya sanya masa sunan mahaifin Turaki, wanda a yanzu yake da shekara biyu, Abhi kuma shekarar biyar, sai su Twins shekara takwas takwas. Aimam sai da ya yi shekara bakwai yana jinya sannan Allah Ya ɗauki ransa, mutuwar Aiman ta yi matuƙar taɓa Laila, wanda ta dinga abubuwa tana surutai har da cewa ni na kashe mata shi har sai da Turaki ya sake sakinta, wanda da ƙyar na sa shi ya yi dawo da ita, ya nuna mata cewar alfarmata ke riƙe da ita a gidan, wanda a lokacin ta yarda da hakan, ta yarda alfarmata ke riƙe da ita tun da ita a yanzu babu ɗa ba wani abu, ta dole ta fara biyayya a gareni, ni kuma na yarda a a raina Turaki jarumi ne a cikin jarumai, na yarda da shi fiye da zato, na yarda da shi da dukkan rayuwata. A zuwa wannan lokacin Gidauniyar mu ta kafu ta yi ƙarfi sosai da sosai, akaf arewacin nigeria babu inda ba a san da Mr’s Abubakar Turaki ba, shine sunan da nake amfani da shi a ko ina, har da kafafen sada zumunta da nake da tarihin mabiya, na mai da Hajiya aikin Hajji da kuɗi na kaina, na kuma kai Yaya Radiya da Yaya Rumaisa Umara hara sau biyu, Ra’is da Yaya Ridwan kam duk da kansu sukaje kuma suka kai Hajiya da sauran ‘yan gidan. Haka kasuwancina na buɗe manyan shagona a garuruwa daban daban, ciki har da kano da Abuja, kudaɗe nake samu ta hanyar kasuwancin gashi har empowerment matar gwamna ta ɗora ni akai na nawa mata jari, bisa irin ƙoƙari da gidauniyarmu take yi. Sardauna tun ranar da ya bar gidan Big Daddy ban sake sa shi a idona ba, na manta shi amma ba gaba ɗaya ba, ya zama wani tabo a rayuwata da bazai taɓa goguwa ba.  Bilkisu shekararta ukun a gidan yari aka fito da ita, bisa shiga da fita da iyayenta suka yi, sai dai ba ta yi doguwar rayuwa ba, cutar da ta shiga da ita da iya ta fito kuma ita ta yi ajalinta.  Tsakanina da ‘yan uwan Turaki sai son barka, ko ina ana sona ana kuma girmamani, Turaki ya zama bango a cikin familynsu yana gudanar da koamai cike da adalci. Gidanmu kam sai godiyar Allah, kowa ya zama wani, Allah Ya amsa addu’ar Alhaji duk ya ɗaukaka mu, ya yi mana arziƙin da muke taimakon al’umma, duk gidajen dake jikin namu mun siye su mun ginawa Hajiya babban gida, ‘yan uwan Alhaji duk sun zo suna borin kunya kamar yanda kowanne dangi  suke yi idan suka ga Allah Ya ɗaukaka waɗan da suks watsar. Tsakanina da al’umma kam na zama wata madubi da mata da yawa suke kallo suke koyi da ita, na tara ɗimbin masoya masu tarin yawa.  A cikin gidana kuwa na zama zinariya gimbiyar dake hask zuciyar Turaki, ni ce mai faɗa aji ni ce mai kula da shi da komai, wanda a ƙarshe dai sai da Laila ta nemi cikon saki ɗayan ta tafi, ta barni da mijina da ‘ya’yana guda huɗu.  Yau tun safe muke kicin ni da su Twins, kasancewar yau Turaki zai dawo daga tafiyar da ya yi, aiki muke ba kama ƙafar yaro mu ɗaura wancan mu sauke wancan. “Maamah, wai ba zaayi masa avocado ɗin ba jiya fa da muka yi waya da shi ya ce yana so.” Wani kallo na watsa mata sannan na ce. “Sauwama ki yi masa, tun safe muna aiki har yanzu bamu gama ba amma kina ƙara ɗauko mana wani daban.” “Haba Maamah dan Allah.” “Sai kuma ki yi.” “Yaya Twins Yaya Twins.” Abhi ya shigo yana magana. “Mene?” Sauwama ta faɗa tana tura baki sabida na ce ba za ayi Avacado ba, daman Sauwama ita ce mai zuciyar masifa.  “Ni bake ba.” Ya faɗa. “To fita daga nan.” Ba shiri ya fita dan yasan yanzu zata lugudeshi a banza, haka muka yi ta faman aiki sai wajen karfe shida muka kammala sannam muka jera komai a dinning, kowa ya shiga ya je ya shirya. Ƙarfe shid da mimti goma driver ya shigo daga ɗauko Turaki, na fito cikin shirina zan tare shi amma naga su twins ma sun ragani, na watsa musu harara na ce. “Ku shige ciki ku bar min miji.” Sauwama ta yi saurin cewa. “Maamah ki shige ciki, ki bar mana Papanmu.” Wani kallo na watsa mata sannan na ce. “Kuna hauka amma, wannan ai babu mai rabani da shi.” Sai a lokacin ya ce. “Har mutuwa kuwa Habibty na, ina sonki har abada.” “Mu baka son mu ko?” Abhi ya faɗa, Turaki ya ce. “Ya zaayi na ƙi Abhi na, kawai dai ita son nata na mussamman ne.” “To Allah Ya ƙara soyayya, ya barmu tare har abada.” Na yi saurin cewa Amin, ba tare da na tantance wacce ta yi maganar ba cikinsu twins. Wani irin daɗi na ji a raina, na tabbatar a yanzu duniya ta gama ba ni duk wani abu da nake buƙata, sai nake jin kamar babu wata mace dake da matsayina.  “Ya Allah ka tabbatarmin da Turaki a matsayin mijina har Aljannah.” “Amin Habibty.” "A cikin wannan rayuwar da na ratsa, na koyi abu guda ɗaya, kuma na koyar da abu guda ɗaya. Me na koya? Na koyi cewa dukkan abin da ka shuka, shi zaka girbe. Alkairi ba ya faɗuwa ƙasa banza, haka shi ma mugunta ba ta haifar ɗa mai ido. Me kuma na koyar? Na koyar da cewa, komai tsananin duhu, zafi, da matsin rayuwa, muddin ka miƙa al'amarinka ga Ubangiji, to tabbas komai zai wuce ya zama tarihi. Babu daren da ba zai waye ba. Alhamdulillah. Nan na kawo ƙarshen labarin littafin SARTSE. Godiya ta tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki, Mai kowa Mai komai, wanda IkonSa ne ya nuna mini wannan rana. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban halitta, Annabi Muhammad (SAW), tare da iyalansa da sahabbansa baki ɗaya. Na fara posting ɗin wannan littafi a ranar 8 ga watan Mayu, 2026, kuma cikin ikon Allah na kammala shi a yau 28 ga watan Yuni, 2026. Alhamdulillah! Bayan duk wani faɗi-tashi, daɗi da ƙuna, gashi tafiyar SARTSE ta zo muku cike da yaƙini da fatan alheri. Cikin nuna tsantsan farin ciki, ina mai tabbatar muku da cewa fatana bai yanke ba, kuma kyakkyawan tsammanin da na yi muku bai tashi a banza ba. Na gode sosai, na gode da yadda kuka karɓi wahalar da na ɗauki tsawon lokaci ina sassaƙa ta domin ku. Allah Ya saka muku da alheri, Ubangiji Ya haɗa mu a Aljanar Firdausi baki ɗaya, Amin. Bayan haka, kalmomin baki na ba za su taɓa iya bayyana irin soyayya da girmamawa da nake muku ba, masoyana na dandalin ArewaBooks da kuma WhatsApp. Kullum idan na tashi rubutu, kalaman ku na ƙarfafa gwiwa, likes ɗinku, da reviews ɗinku  sune suke zame mini fitilar da ke haske mini duhun daren tunani. Ba ku san darajar tattaunawar da muke yi a WhatsApp ba; kowane comment, kowace dariya, da kowane sharhi da kuke yi a kan sassan littafin nan, jini ne da ke gudu a jikina wanda yake ba ni ƙarfin ci gaba da rubutu ko da na gaji. SARTSE ba zai taɓa zama abin da yake ba a yau idan babu ku. Kun zama kwarin gwiwata, kun zama babban jigo na nasarata. Ganin yadda kuke bibiyata, kuna jirana, kuna nuna damuwarku a kan kowace haruffa da na rubuta, means a lot to me yana da matukar daraja a zuciyata. Ina muku alkawarin cewa muddin akwai rai da lafiya, Sayyid Legendspen ba zai fasa kawo muku labarai masu taɓa zuciya ba. Na gode da kuka kasance tare da ni tun daga farko har zuwa ƙarshe. Sai mun haɗu a littafi na gaba! Mu huta lafiya. Legendspen 08129553971