SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na ɗaya. 10:30am "Idan ka je bakin gate ɗin nan zan sauka." Na faɗawa me mashin ɗin da nake ciki, cikin dashashiyar muryata, yana ƙarasawa na sauka sabida nasan masu gadin gate ɗin bakin layin basa taɓa barin mashin ya shiga sai dai mota. "Gashi." Na faɗa ina miƙamai kuɗin na shi. "Ga canji." Na sa hannu na amsa sannan na shiga cikin layin, kamar wacca ke tausayin ƙasa haka nake tafiya, gaba ɗaya bana jindaɗin komai, ga tsoro da fargabar yadda zan sami gidan ya cika min zuciya, duk da naƙi bawa zuciyata damar yarda da maganganun da Sardauna ya faɗa min ɗazu a  asibiti, ko kuma wanda Dr Na’ima ta faɗa min bayan yabar asibitin, ko da wasa ma ban shirya yarda da ko ɗaya ba, hatta da sakin da ya ce ya yi min naƙi bawa zuciyata damar yarda. 'Ko ta ina Sardauna ma zai sake ni?.' Na tambayi kaina lokacin da nake tura Gate ɗin gidan namu. "Hajiya sannu da zuwa." "Yawwa." Na faɗa ina wucewa, har da ɗan gudu gudu na sabida tsoron kar Allah ya haɗani da Turaki, dan yanzu babu mutumin da nake jin tsanarsa kamar Turaki, duk wasu abubuwan shine sillarsu. Ina shiga cikin falon na kalli yadda yake, sai kawai na shige ɗaki na kwanta, amma gaba ɗaya bacci yaƙi zuwa idona. Ina nan kwance har wajen ƙarfe biyu na rana, sannan na ta shi na shiga toilet na ɗaura alwala na yi sallah, zama na yi kan daddumar da na yi sallah, maganganun Sardauna na jiya da ya yi min a asibiti suka shiga zarya a kunnena kamar yanzu yake faɗansu. “Hallau kisa ran ganin abubuwa da yawa Nana.” Da sauri na girgiza kaina tare da faɗin. “Zan zauna da kai Sardauna, zan zauna anan ɗin a haka, nasan wata rana zaka dawo gareni mijina.” Hannuna na kai cikin dirowar gefen gado zan ɗauki wayata, na ci karo da ƙwayoyin da Sardauna yake ba ni, waɗan da ya ce na gyaran mahaifa ne, ɗaukansu na yi na ƙura musu ido ina son na karanta, ko da banyi dogon karatu ba ai ina da ilimin da zan iya karanta turanci idan naganshi a rubuce, sai dai zuciyata ta hanani karantawa, gaba ɗaya taƙi gasgata ko kalma ɗaya da Sardauna ya faɗa. Ta shi na yi na shiga toilet na watsa su a masai na yi fuloshin ɗinsu, ba tare da na karanta ba bare ma nasan mene a jiki, ni dai na yi imani da cewa kunnena ya ji ba daidai ba, amma nasan Sardauna ba haka yake nufi ba. Sai wajen ƙarfe uku da rabi na tashi na shiga kicin, shayi na zuba sannan na ɗauko ragowa daga cikin cakes da na yi tun ranar da ‘yan uwan Bilkisu suka zo, na dawo falo na zauna na fara ci. Gaba ɗaya babu wani tastin haka nake cin cake ɗin, har nafima maida hankali ga shayin. ‘Nana, ki tabbatar kin mayar da hankalinki ga magungunan nan, suka ɗai ne wani bango da ya rage miki da zaki dafa ki iya miƙewa.” Maganar Dr Na’ima Daƙayyawa ta dawo kunnena, a hankali na miƙe na ɗauko magani na ɓalla na sha, bayan na kammala na sake dawowa na cure akan kujera, rayuwarmu ta baya da Sardauna ta shiga dawowomin a cikin kaina, hawaye masu ɗumi suka fara gangaro min a idona, cikin muryar kuka na fara magana. “Sardauna dan Allah ka dawo min, wallahi zan rayu da kai a kowanne yanayi, Sardauna kaine numfashina, kai ne nake so dan Allah Sardauna.” Wani irin yanayi ya ziyarci ne, na ji ina jin kaina wata fanko. “Au wai ta dawo Baby? Ni ina na sani ne.” Muryar Bilkisu ta isar min da saƙon cewa gata nan shigowa, sai dai ba ita kaɗai ba ce; ita da Sardaunana ne, Sardauna mutumin da na yi imanin zan rayu da shi amma gashi shi da wata hannunsa cikin nata, suna sanye da kaya iri ɗaya. “Marar zuciya, aikuwa ga ta.” Kallon Bilkisu na fara yi, wai Bilkisu da na aminta da ita sama da ‘yan uwana, amma ita ce tare da mijina, Bilkisu da na durƙusawa akan gwiwoyina sabida ta aure mijina, yau gashi ta aureshi ta fini iko da shi. “Ke mayya kallon me kike mana.” Sardauna ya faɗa a tsawace, da sauri na yi ƙasa da kaina. “Tsugunna a ƙasa! Muna tsaye kina tsaye.” Ya sake faɗa kamar zai dake ni, jikina har ɓari yake yi na zube a ƙasa, shi kuma suka zauna shi da Bilkisu, ta wani manne a jikinsa kamar zasu haɗe. “Baby ɗakin nan ƙauri.” Bilkisu ta faɗa tana yatsine hanci, tare da shafa masa ƙirji, wani irin zafi na ji a zuciyata na yadda take shafa masa ƙirjin. “Ke Nana!” Na ɗaga ido na yi masa wani kallo, mai isar da saƙon dake cikin zuciya cikin ƙanƙanin lokaci. “Ba zaki zauna min a gida haka kawai ba, Gimbiya ta ta ce dole ke ce zaki dinga yi mata duk wasu hidimomi na cikin gida.” Na sake kallonsa, sannan na ja da baya. “A’a ni wallahi.” Na faɗa ina miƙewa, shima ya miƙe tare da nufo ni. “Wane irin a’a ke wallahi.” “Ni bazan mata aiki ba, na tsane ki Bilkisu….” Ban ƙarasa ba na ji ya tsinka min wani azababben mari, wanda sai da na ga wasu taurari suna yawo a sama. “Nana wallahi zaki bar min gida, akan Bilksu ba abinda bazan miki ba, ki sani Bilkisu ita ce zaɓina, ita ce farin ciki na, kuma ita ce daidai da ni.” “Kenan ni ba zaɓin ka ba ce Sardauna? Ko da nasan ni ba daidai da kai ba ce, amma ai ka zaɓe ni kuma ka so ni harka aure ni.” “Ke dabba! Rufe bakinki anan, idan jahilci ya hanaki fahimtar aurenki ya yi sabida wata manufarsa to ni na fito ƙarara na faɗa miki.” “Maimaita ma ta dai, na faɗa mata ƙuruciyar jikinta na aura, shi ya sa na bata gata a farko sabida kar ƙurucuyar ta barta, amma da yake rainon wahala ce, ta saba da wahala ta ce ita ba ta son ma’aiki, ba ta son gas ba ta son waye, shi ya sa na barta da kayan jakanta tun da jakar ce.” Kuka na fashe da shi, tare da tsugunnawa a ƙasa na kama ƙafarsa. “Dan Allah Sardauna ka daina faɗar wannan maganar, nasan ba kana faɗa bane har ranka dan Allah Sardauna ka daina.” Da ƙarfi ya janye ƙafarsa, sannan ya ce. “Nana baki san Sardauna ba, baki san komai daga Sardauna ba, Nana abinda nasani akanki shine ke ta wace, da aure babu aure, zaki dauwama a ƙarƙashina.” “Ni Baby kawai ka faɗa mata abinda zaka faɗa mata mu tafi, waɗan nan maganganun wallahi soyayya suke nunawa kawai.” Bilkisu ta faɗa tana cuna baki gaba. “Never Bilkisu, wannan ƙasƙantaciyar yarinyar har abada, a yanzu zata zauna a gidan nan a matsayin ‘yar aiki ne.” Yana faɗin haka ya shige cikin part ɗinsu, da yake duk ta ƙofa ɗaya ne, shiga ko fita duk ta nan ne, itama ta bi bayansa suka barni kwance a ƙasa ina faman kuka. Sai da na yi mai isata har ya fara samin ciwon kai, sannan na kwashi jiki na yi cikin ɗakina na, a ƙasa na zauna na ɗora kaina akan gadon na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya, yadda nake yinsa da ƙarfi da hawaye sai nake jin kamar yanzu na fara kuka a rayuwata. Sai da idona ya fara dishi dishi sabida kukan da na sha sannan na yi shiru, na ƙurawa waje guda idanu, ina faman tunanin yadda rayuwa ta juyemin. Ni nasan Sardauna duk abinda yake yi ba har cikin zuciyarsa yake yin sa ba, iya fatar bakine yake faɗa kuma nasani. Sharrin muguwar mace ya haɗu da shi “Bilkisu ba ki yi min adalci ba.” Na faɗa a raina sannan na tashi na yi shiga cikin toilet. Ina nan zaune na sake jiyo muryar Sardauna a falo na, jikina har ɓari yake, sai da na kusa faɗuwa tsabagen sauri na fito falon. Ina zuwa na tsugunna akan gwiwoyina tare da faɗin. “Ga ni.” Zama ya yi akan kujera, ya kalle ni sannan ya ce. “Nana! Yanzu kin fi ƙarfin ki yi min girki ni da matata a gidan? Nana duk adalcin da na yi miki, na barki ki zauna a gidana, da ci, da sha, da suttura, amma Nana sakayyar yi min girki ne ba zan samu ba?” Gaba ɗaya kalaman Sardauna suka kashe min jiki ta ko ina, na rasa me yake min daɗi, na rasa me ya shiga kunnena a ɗazu har na iya cewa bazan yi ma sa girki ba. “Nana! Kinsan Bilkisu ba za ta so girkinki ba, ni kaina bansan zan iya son girkin ba, bayan na auri Bilkisu, amma na rasa masifar da tasa na kasa gamsuwa da girkin Bilkisu Nana, ko rabon ki hulaƙanta ni ne ya ja haka, ni bansani ba, Nana bansan cewar zaki iya fatali da abinda naso ba, Nana bansan zan iya neman alfarmar girki a wajenki ba ki ƙi yi mini Nana, Nana ki duba hallarcin da na yi miki.” Ƙwalla ta zuba a idona na sa hannu na goge, cikin muryar kuka na fara magana. “Ba haka ba ne Sardauna, zan yi maka girki a kullum, ko da sau goma kake so ba zan gaji ba, zan yi maka Allah, amma kar ka ce naje ɓangaren Bilkisu na yi acan.” “To Nana nan zan zo na ci? Ke fa a yanzu ba mata ta ba ce Nana, ba muharramata ba ce.” “Ka yi haƙuri zan yi maka, zan je ɓangaren na ta na yi maka, amma dan Allah ka daina faɗin wannan kalmar Sarduna dan Allah, ni taka ce har Abada, kai nawa ne dan Allah.” “Good girl.” Ya faɗa yana miƙewa. “ina jiranki ki zo ki yi min na dare yanzu.” Yana faɗin haka ya fice, miƙewa na yi na bi bayanshi, sai kuma na dawo na shiga ban ɗaki na wanke fuskata sannan na yi part ɗin na su. Dukkansu suna cikin ɗaki, wajen shiru ga ledoji nan duk an barsu a ƙasa, kan dinning ɗin na kalla wata farar jallop idona ya sauka akai, ga ta nan cikin faranti, da alama loma ɗaya ya yi ya ajiye, kuma ba a kwashe kayan ba. Kai tsaye cikin kicin ɗin na shiga, shima kayan da aka yi aikin da su duk ba a wanke ba, ga tukunyar ma ta yi wani baƙi. “Ikon Allah.” Na faɗa ina nufar gas ɗin, wata tukunyar na ɗauko na yi amfani da ita, da sauri da sauri nake komai kamar ɓarawon da yake sata yana tsoron akama shi, bana son na yi wani abu da zai sanar da masu gidan cewar ina nan. Jollop ɗin taliya na shiga haɗa musu, dan ma dai komai na buƙata akwai shi a kicin ɗin, motsu motsu na ji a falon sai da gabana ya faɗi, duk tsoro ya kamani. Bilkisu ta shigo kicin ɗin tana sanye da wata ‘yar iskar riga dukkan jikinta a bayyane, kanta babu ɗan kwali bare hula. “Me kike dafa mana.” Banza na yi da ita kamar ban ji me ta ce ba. “Ba dake nake ba.” Nasake yi mata banza na ci gaba da abinda nake, domin wata muguwar tsanar Bilkisu ke ci min rai, gaba ɗaya ta ɗauke min hankalin mijina, ni duk wanda ya ce zai shiga tsakanina da Sardauna ya raba ni da shi, to ko waye natsaneshi kuma bazan iya ɓoye mai ba. “Dan uwarki ba dake nake ba, shegiya ballagaza jaka marar kishin kai.” “Bilkisu ki fita a hurimina kafin na nuna miki zallan hauka.” Na faɗa ina ci gaba da aikin da nake yi, ta yi wata shu’umar dariya, sannan ta ce. “Nana bazan yi kishi dake ba, sabida nafi ƙarfin hakan, amma wallahi sai na gasa miki tsakuwa a hannu.” Tana faɗin haka ta fice, na sake goge ƙwallar da ta fito min a idona, wani motsi motsin na ji a falon, da kuma wani irin haukatacen nishi. Gabana ya faɗi ya bada wani ‘Dum.’ Legengdpen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na biyu. Sautin nishin yana bugun kunnuwana, kamar ana ƙwanƙwasa guduma, haka cikin ƙwaƙwalwata kamar ana buga kwano, ƙirjina ya shiga wani irin bugu da sauri da sauri, kaina ya fara juya da sauri na dafe bango. “Ah! Sardauna da sonka zan mutu.” Bilkisu ta faɗa cikin wata iriyar murya mai cike da kissa, da sauri na dafe kaina da faɗin. “Innullahi wa’inna illahir raji’un.” Gaba ɗaya na ƙasa ƙarasa girkin, sai da na ji ya fara ƙauri na yi saurin kashe wutar gas ɗin, gaba ɗaya so nake na fice daga cikin ɓangaren ko zanji sauƙin abinda nake ji a cikin zuciyata, domin wani irin tuƙuƙin azaba nake ji kamar ana soke min zuciyar da wuƙa. Kamar me lamɓo haka na ke bin hanyar da za ta sadani da ƙofar ficewa, bana ko kallon gabana na ƙurawa ƙasa ido ina tafiya. “Ba ta gyara wajen ba Baby.” Bilkisu ta yi maganar da ta tilastamin tsayawa. “Keeee.” Ya faɗa cikin wata iriyar murya, na tsaya ba tare da ɗaga kai ba. “Zo.” A hankali na tako ina kallon ƙasa, na zagayo daga bayan kujerar, yana zaune tana kansa. “Baby ɗaga ni.” Ya faɗa ni dai tun da na kallesu sau ɗaya ban sake kallonsu ba. “Nana bance dake zaki gyara mata gida ba.” Na girgiza kai sannan na ce. “Ba zan ba.” “Ni kike faɗawa haka?” “Baby kawai ta tafi gidan ubanta mana.” “Bilkisu da zan iya da tuni na sallamata ta tafi, bazan iya jurar gani tana mu’amala da wani ɗa namijin ba ne Bilkisu, bazan iya ba.” Hannu tasa ta fara shafa masa fuska, sannan ta ce. “To ka tursasata mana.” “Nana! Nana! Sau nawa na kira sunanki.” Bakina na rawa na ce. “Bib.. bib.. biyu.” “Kar ki bari na kira na ukun, domin bazan kira shi da alheri ba.” Yana gama faɗin haka ya jawota jikinsa ya ci gaba sa sumbatarta, wani zafi na ji ya mamaye rayuwata gaba ɗaya, take na fara zufa, cikina ya bada wani sauti. ‘Ƙululululuwww.” Da sauri na ta shi harda tuntuɓe na fice daga part ɗin na yi nawa, ina zuwa na faɗa kan kujera na fashe da wani irin kuka me tsuma zuciya, yinsa nake kamar raina zai fita, har ji nake gara na mutu da wannan baƙar ranar, wai mijina da nake so na yi imanin zan rayu da shi, na bashi yarda da dukkan amanata, shi nake yake mu’amalal aure da wata a gaban idona, wani irin cin mutunci ne wannan? Kuka na nake yi marar iyaka, sai da na yi mai isata sannan na tashi na yi alwala na yi sallah, ina kan daddumar da na yi sallah na ji motsin su a harabar gidan, da alamim fita za su yi. Suna fita na tashi na shiga ɓangaren nasu, kicin ɗin na shiga abincin da na dafa gashinan an ɗiba an bar ragowar a tukunya, ba a gyara komai ba na kicin ɗin ba. Kwashe su na yi na haɗe sannam na shiga gyara inda zan gyara, wanke wanke ne dai ban yi ba dan ko a nawa ɓangaren ba yi nake ba, sawa nake ayi min bare kuma a ɓangaren kishiya. Ina gamawa da kicin ɗin na dawo falon, shima na gyara duk abinda ya kamata na tattara idan zan tattara na fice zuwa nawa ɓangaren. Kicin ɗina na shiga na ganshi fes da shi, na ɗaura farar shinkafa akan gas, haka kawai na ji nima akan gas ɗin zanyi girkin. Ina gamawa na buɗe freeza na ɗauko miya na ɗumama, daga nan na dawo falo na zauna a ƙasa ina ci, bugu na ji a ƙofa na yi banza dan a tunani sune, sai da na ji ana cewa. “Nana buɗe Turaki ne.” Wani dogon tsaki na ja, a raina na ce. ‘Wannan uban me zai yi min? Duk wata matsala tsakanina da Sardauna shine ya asassata.’ “Saƙo ne Hajiya ta bada a kawo miki, gashinan a bakin ƙofa.” Yana faɗin haka ya wuce ni kuma na tashi, buɗe ƙofar na yi naga leda ce na ɗauka na shigo ciki, bushashen kifi ne da yawa a ciki. “Allah Sarki Hajiya, Allah Ya ƙara miki lafiya da nisan kwana.” Na faɗa a raina, Hajiya tasan yadda nake matuƙar ƙaunar bushashen kifi shine ta bada akawo min, rabona da shi tun kafin na auri Sardauna, shekara uku kenan. Ina nan zaune har bayan magariba shiru basu dawo ba, anan na yi i’sha ma amma basu dawo ba, ganin ƙarfe tara ta wuce na tashi na shige ɗakina na kwanta. ****** Ƙarar bugun ƙofar ɗakin bacci na ce ta tayar da ni, a hankali na buɗe ido tare da faɗin. “Waye?” “Nana zo ki buɗe ƙofar nan.” A zabure na tashi zaune daga kwanciyar, na sauƙo. “Shige muje.” Ya faɗa bayan na buɗe ƙofar, yana nuna min hannu, ba musu na bi hanyar na fice kamar munafuka, tun kafin na ƙarasa na jiyo sautin muryarta tana faɗin. “Bazan iya ba wallahi, haba Baby ka ce wannan ka ce wannan, ni ban iya kayan fulawa ba wallahi. Tun 8 nake kicin ina fama ƙwaɓa abu, na gama kuma ka ce wai ya yi baƙi, ba jaka ba ce ni da zan dinga yi ma girke girke.” “Baby it’s okay, gatanan ai.” Ya faɗa bayan mun ƙaraso ɗakin, kallona ta yi sannan ta ɗauke kai. “Ka yi yadda za ka yi da ita, gashinan goma saura, kuma sha biyu nake da class dan haka ni zan fice, ta yi min girkin rana.” Tana faɗin haka ta fice ta barmu ni da shi a falon, ni kuwa zallan mamaki ya cikani. ‘Ina Bilkisu ce min ta yi aiki take, to yanzu kuma ta ce lectures, ji shigar jikinta a haka za ta tafi makarantar? Ni da nake sanya hijabi ance ana kishina?.’ ‘Dole ya yi kishinki mana Nana, ita fa a yanzu amarya ce kome take so yi mata zaayi, kin san Sardauna yana sonki kuma zai dawo gareki.’ Wani ɓari daga zuciyata ya katsemin tunanin da nake ta wannan amsar. “Nana!” Ya kira sunana, na ɗaga kai na kalleshi ba tare da na amsa ba, a raina ina addu’ar Allah ya sa Sardauna ya faɗa min abu mai daɗi. “Nana kin zaɓi na dinga zama da yunwa?” Da sauri na girgiza kaina, wani tausayinsa ya ratsamin zuciya. “Nana! Daga yau kin daina girki a ɓangarenki, sai dai ki dinga yi anan kema kina ci.” “Tom.” “Sannan Nana zaki dawo da rayuwa anan ɓangaren gaba ɗaya, sabida Bilkisu tana makaranta ba ko yaushe zata dinga zama ba, idan ta dawo daga makaranta ke kuma sai ki tafi ɓangarenki ki zauna! Sabida kayan da suke nan sunfi naki daraja da tsada, can iya kayanki ne tun da na kwashe nawa, amma nan akwai nata akwai nawa, akwai gwala-gwalanta da sarƙoƙi.” “Tom.” “Yawwa Nana, yanzu asama min abinda zanci ina jiranki.” Ta shi na yi na nufi kicin ɗin, kwaɓin samosar da ta yi na ɗauka na ci gaba da shafawa, cikin ƙanƙanin lokaci na kammala na haɗa na kawo masa, bayan ya amsa na kalleshi, wani irin tausayinsa ya ratsa min zuciya, Allah Ya sani ina son Sardauna da dukkan rayuwata, ina tausayinsa da dukkan numfashina. “Allah Ya ƙara maka arziƙi da wadata.” Na faɗa a raina sannan na fice, gaba ɗaya tunanin irin yadda Sardauna da Bilkisu suka dinga yaudarata ya shiga zarya a kaina, har nake hasaso abubuwan da bansan da su ba, amma da yake zuciyata ta mutu akan Sardauna ta shiga bani uzurruka masu ƙarfi akan Sardauna har na kasa gani ko da laifi ɗaya. Tun daga wannan rana na ɗauki alƙwalin duk wani abu da zan faranta ran Sardauna shine zanyi, wanda zai baƙanta ransa ba zanyi ba, na rage rayuwa a ɓangarena gaba ɗaya da zarar Bilkisu ta fita zan dawo nan na zauna, wani lokacin ma yana bacci take fita, sai na je na yi masa girkin yake tashi ya ci ya shirya ya fita, ni zan gyara idan suka ɓata amma banda ɗakin baccinsu daban bazan iya shiga ba, amma ko ina nakan gyara, na yi girkin rana na ci ni kaɗai, dan Bilkisu kullum sai biyar da rabi take dawowa, shi kuma sai gab da magariba, gashi gaba ɗaya ya daina wannan fitar majalisar da ya dawo ta dawo zasu shige ciki sai kuma da safe. Turaki kuwa bansake bari na haɗu da shi ba, dan ba inda ma nake fita, wayata ma gaba ɗaya na tarkata ta na ajiyeta, babu wani abu da nake yi a yanzu, kullum ina cikin ɗaki. ********* Yau takama Asabar, tun da Sardauna ya sake aure ya daina fita ranar asabar sai yamma, ita kuma ba ta zuwa makaranta asabar da lahadi, tun safe na shiga ɓamgarensu yin ayyukana na kullum, dan tunda na yi shawara da zuciyata na yanke zan dage tuƙuru na yi duk abinda Sardauna zai so ko zai ji daɗi, nasan idan ya ga ina yi masa biyayya tabbas zai dawo da kallon sa yake yi min na sanyin idaniyansa. Aiki nake tuƙuru ganin na yi musu cake da shayin na’a na’a, nasan Sardauna zai ya ba kuma zai ji daɗi sosai da sosai, kamar daga sama na ji muryar Bilkisu. “Me yake ƙauri ne haka?” Ta faɗa tana shigowa kicin ɗin, kallona ta yi sannan ta ce. “Yanzu dan baƙin ciki Nana me kike babbakamin haka? Kayan nawa zaki lalata muguwa? Baby!” Da mamaki nake kallonta, ko me ta gani ya yi kama da za’a lalata oho mata? Jikinsa har rawa yake ya shigo cikin kicin ɗin, da sauri na tsugunna ƙasa tare da faɗin. “Ina kwana?” “Baby kaga abinda take yi, so take talalata mini oven.” Bilkisu ta tare masa numfashi ba tare da ta bashi damar amsamin ba,ban daddara ba na sake cewa. “Ina kwana?” “Ke dalla bama son surutu, abinda ake magana akai kenan?” Bilkisu ta ƙara faɗa, yayin da Sardauna ya kau da kai kamar bai jini ba, ko bai gani ba. “Muje na nuna miki wani abu.” Ya faɗa yana riƙe mata hannu, ta saki wani ihun. “Ah! Baby ai bazan iya tafiya ba, jikina ciwo.” Ɗaukarta ya yi a hannu kamar wata jaririya ya fice da ita, ƙwalla ta fara zirara daga idanuna, baƙin ciki da takaici suka haɗu suka ƙunsu a zuciyata. “Allah ka sakawa Sardauna akan abinda Bilkisu ta yi masa, Allah ka bi masa haƙƙinsa.” Na faɗa ina share ƙwallar da ta fito daga idona, na ci gaba da aikina tare da hira da zuciyata, kalaman Sardauna suka shiga dawo min a kunnena kamar yanzu ya faɗesu. “Nana ina so ki ci gaba da yi min uziri akan komai na rayuwa.” “Allah Sarki mijina, ina sonka, Allah Ya kare ka, Allah Ya dawo min da kai, Allah Ya yi maka arziƙi marar iyaka, ina sonka Sardauna.” Daga nan na ci gaba da abinda nake yi, har na kammala ban sake jin wani motsin Sardauna ko Bilkisu ba, ina gama na fito da su zuwa kan dinning ɗin Bilkisu na ajiye, bayan na ɗebi nawa da zanci na yi nawa ɓangaren. Ina shiga na zauna akan kujera, ban wani iya ci yadda yakamata ba na hau gyaran ɓangaren nawa, sai a lokacin tunanin nawa kayan ɗakin na can gidanmu na farko ya faɗo min, ko suna ina oho? Da dai Sardauna ya ce za a bada su, ko an bayar Allah masani. Tun daga can ɓangaren nasu na ji ana ta ƙwalamin kira. “Kee! Kee Nana!” Jikina har ɓari yake na fita zuwa falon nasu, suna zaune akan dinning suna cin abincin, wani tausayin Sardauna ne ya faɗo min a rai, tabbas da nice da bazan bar Sardauna ya zauna haka ba, ni da kaima zan bashi komai a baki, wani haushin Bilkisu ya kamani kan abinda take yi, gaba ɗaya ba ta iya biyayyar aure ba, iyayenta basu wani ba ta tarbiya ba. “Zo nan.” Sardauna ya faɗa, a hankali na taka zuwa inda suke. “Mene wannan kika dafa? Bilkisu ta ce ba ta iya ci ba.” “Duk abun babu taste Baby.” Kallon Bilkisu da ta yi maganar na yi, ni a yanzu haushinta da nake ji gaba ɗaya na yadda kwata kwata ba ta iya kula da Sardauna ba, abun ta gaba ɗaya babu biyayyar aure, kuma nasan Sardauna ba wai sonta yafi ba, kawai ita amarya ce. “Nana! Na yi wata shawara, ganin a yanzu ni dake babu aure a tskaaninmu, kuma bake ce matar gidan ba dan haka dole zan banbantaku da matar gidan ta dole.” “Tom.” “Nana, duk wasu kayan ɗaki zaki cire na cikin ɗakinki, amma za abar na ɗakina sabida idan maganannun yayunki sun zo sai ki nuna musu na ɗakina, sannam zaki bar kujerun amma Nana inda ke kaɗai ce ban lamunce miki zama akansu ba, ɗakin ki zaki bar katifa kawai, kayanki kuma zaki barsu a akwati a ƙasa, ɗakin zai zama daga katifa sai akwati, idan kinyi baƙi sai ki kaisu nawa ɗakin kuma ba kowa bama, ku ƙaraci zamanku a falo, kin jini?” Na gyaɗa kai sannan na ce. “Eyh na ji.” “Yawwa, daman kayan duka mallakina ne, dan haka za afita da su a yau.” “Sannan ba zaiyu ace ni matar gida ina sa kaya na kece raini ba, ita tama tana sawa dole asan yadda za’ayi.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na uku. Kallon Bilkisu na yi, bansan me ya sa ita nake jin haushin duk abinda ta yi ba, amma Sardauna kome zai faɗa ina yi masa uziri, a yanzu haka nasan bayin kansa ba ne, kuma nasan ba zaiyi haka dan ya cutar da ni ba. “Kike kallona da idanu kamar mayya.” Bilkisu ta faɗa a tsawace, na watsa mata harar sannan na ce. “Bazan yi ba, wallahi ba zan zauna babu sutturu ba.” “Lallai yarinyar nan wuyanki ya yi kauri, to wallahi Allah sai kin sauya shigarki, Baby ka ji fa.” “Baby, ba ta da wasu kaya masu tsada, kinsan dai daga inda ta fito dan haka bana ganin hakan zai dameki.” Cuno baki ta yi gaba, sannan ta ce. “Zuciyana tashi take idan na ganta fa, yanzu haka ma amai nake ji.” “Tashi ki bar wajen nan, ki fitar da kayanki daga sif yanzu, ki sauke katifar ma.” Ba musu na tashi na nufi ɓangarena na barsu anan, ina shiga na samu waje na zauna. “Wai shin me ya sa Sardauna yake min haka ne?” Na tambayi kaina, sai kuma wani tunani ya faɗo min. Sardauna ɗan Adam ne, ajizi me yawan laifi ina ganin bai kamata na zargeshi ba, tunda tabbaa a baya Sardauna yana sona kuma ya nuna min soyayya, dan haka dole ni ce na yi abinda ya ja Sardauna yake min haka tabbas? “Amma me na yi masa?” Na tambayi kaina, can kuma na girgiza kaina. “Nima bansaniba, amma tabbas duk abinda ya ja haka laifi na ne dole, dole ma.” Shiru na yi, na shiga kiciniya da ƙwaƙwalwata ko zan iya tuna wani abu da na yi wa Sarauna, sai dai na garara tuna komai, sai ma ƙoƙarin tunawa da Dr Na’ima Daƙayyawa da na yi, tabbas ta faɗa min wani abu, amma gaba ɗaya na kasa tuna abinda ta faɗa min, haka na yi ta faman kwance kwance da ɗaure ɗaure a cikin ƙwaƙwalwata amma nakasa tuna komai. “Nana!” Na ji andaka min wata razananniyar ƙara, azabure na juya na kalleshi. “Abinda na ce miki kenan? Kin raina ni ko?” “A’a.” Na faɗa ina jijjiga kai, ya matso a fusace yana wuci kamar zaki. “Wallahi Nana sai na ɓaɓɓarar dake, idan baki daina min wannan haukan da kika gada ba, shashasha da ba tasan ciwon kanta ba.” Yana faɗin haka ya ɗaukeni da wani azababben marin da sai da naga taurari sun gifta. “Ka yi haƙuri zanyi.” “Ina ma da lokacin jiranki kenan? Masu kwashe kayan suna waje suna jira, shine zaki wani ce na yi haƙuri? Na ƙi.” Ya faɗa yana nufar sip ɗin, a fuskata na ji ana watsomin kayan wasu kuma na zubewa a ƙasa, yana watsarwa yana faman faɗa, ni dai ina tsaye na zubawa Sarautar Allah ido. “Wallahi idan baki sauke katifar ba, idan suka zo har ita zasu haɗa, sai kina kwana a ƙasa daman anan kika saba.”’ Da sauri na juya, na yi ƙasa da matashin da kuma bargo da zanin gado, na fara kiciniyar sauke katifar sai dai gaba ɗaya tafi ƙarfina ko kusa ko alama, da dukkan ƙarfina nake ɗaga katifar ina yi ina nishi, amma ko jikin Sardauna, waya ma ya tsaya yana dannawa bayan ya gama zubar min da kayan ƙasa, har da sarkoƙi na da ɗan kunne duk ya watso su ƙasa. “Ku shigo ku kwashe kayan.” Ya faɗa bayan an ɗaga wayar da ya buga, sannan ya juyo ya kalleni. “Karki sauke, wallahi da ita zasu tafi.” Ƙara dagewa na yi da dukkan ƙarfina, cikin ikon Allah na yi wani irin nishi kamar mai naƙuda na ɗage katifar, cikin rashin sa’a ƙasan siket ɗina ya harɗe da katakwayen gadon, ina tafiya na ji kamar an janyoni bayan an maka ni da karagar gadon, na buge goshi na, hannuna kuma ya yi wata karciya mai azabar zugi, wadda sai da na saki ƙaramin ihu, daidai lokacin kuma suka shigo na miƙe ba tare da na ci gaba da jin zafin faɗuwar ba ko karcewar, ganin samarin guda huɗu kuma uku ne suke ƙoƙarin ɗaukan sif ɗin, ɗayan yana tsaye ya sa na yi masa magana. “Bawan Allah, dan Allah kama min na sauke katifar nan.” “Tom Hajiya.” Ya faɗa yana matsowa, ya fara kamawa ta gefen da yake nima na kama ta gefen da nake, daƙyar muka iya matsar da ita, cikin rashin sa’a jikina ya gogi na bawan Allah ba tare da sanin junanmu ba. “Fita daga nan!” Sardauna ya faɗa a tsawace, jikina ya ɗau karkarwa na nufi hanyar fita. “Ba ke ba, shi! Ke ai yau sai na ci ubanki tun da ke jaka ka ce bakisan darajar kanki ba, ki zauna kina haɗa jiki da namiji? Baki da hankali ne?” “Bawan Allah ka yi haƙuri ba da saninmu ba ne.” Sardauna ya matso kusa da shi a fusace, ya sa hannu ya kama masa kwalar riga. “Ai daman kai ɗan iska ne, ka saba taɓa matan mutane shine zaka ce ba da saninka ba, to wallahil azim da tsautsayi wani abu ya sake haɗa ka da jikinta sai na yi ƙararka a kotu, kuma ka fice min anan.” Yadda Sardauna ya yi maganar sai da ya tsorata mu baki ɗaya, idanunsa sunyi wani ja suna fitar da ƙwalla, bakinsa sai karkarwa yake haka ma hannunsa, ba musu ya fice yabar ɗakin daidai lokacin waɗanda suka fita da sif ɗin farko suka dawo. “Shige toilet.” Ya faɗa yana nuna min hanyar toilet ɗin, jikina na ɓari ma nufi toilet ɗin na kulle ƙofa, sai da na sauke ajiyar zuciya bayan na shiga toilet ɗin, dan tabbas na tsorata da yanayin Sardauna da nagani. Ina cikin toilet ɗin ina jin hayaniyarsu na fita da kayan sai kuma can na ji muryar Bilkisu tana cewa. “Baby me kake yi anan?” “Ina jira su kwashe kayan mana, ko baki gani ba ne.” “Baby ina ruwanka, kabarsu da ita mana.” “Kina ganin har wani yana taɓa mata jiki, daman ‘yar iska ce tana sane, wallahi yau sai na ci uban Nana.” Ya faɗa muryarshi na tashi da ƙarfi. ‘Oh ni na shiga uku.’ Na faɗa a cikin raina. “Baby tana ina ne yanzu? To zo ta yi mana girki kasan dai zamu fita ko?” “Ni bana jin fita yau, Bikisu wani zafi nake ji a zuciyata, bansan me ya sa na ke yi wa wannan banzar yarinyar wannan kishin ba, Bilkisu bansan ƙaddarar da ta haɗani da Nana ba, na faɗa miki tun ranar da na fara ganinta nake jin kishinta, Bilkisu har yau babu wani abu da ya ragu na kishin da nake mata sai wani da ya ƙaru.” “Baby take it izi, uban kishin kawai zaka ci ka sallama mistiyaciyar gidan ubanta.” “Ai da zan iya da tuni ta tafi wallahi, sabida na tsaneta har zuciyata, amma yadda kishinta yake addabar rayuwa ta Bilkisu bazan iya gangancin turata gida ba, ta dai zauna anan a killacen.” “Yanzu baza mu fitan ba?” “Eyh Bilkisu mu zauna, lets have romantic moments.” “Ni bana so, fita zanyi.” “To kiji Bilkisu ba matsala, i will stay at home.” Daga nan bansake jin muryarta ba, ina tunanin dai ta fice, a raina na ce. “Bazata iya ba, jaka ba zata iya yi masa biyayyar aure ba, ta cuceni da nasan haka take da ban aura mai ita ba wallahi sheɗaniya.” Sai da na kusa minti talatin sannan ya buga min ƙofar, kamar jira nake na buɗe dan nagaji da wannan zaman a toilet, ina fitowa naga ɗakin ya yi wayam kamar ba shi ba. “Ke kalleni.” Na ɗaga kai na kalleshi, sai kuma na sauke su. “A tsaye zaki tsaya ina tsaye?” Na yi saurin durƙusawa ƙasa. “Ke mene ya sa ke baki da hankali ne? Nana bakisan darajar kanki ba ne?” Na girgiza kai sannan na ce. “Nasani.” “To amma kike bari maza suke taɓaki, Nana kinsan yadda naji zafi, wallahi ji na yi kamar ansoki zuciyata da mashi.” Wani tausayinsa da na daɗe banji irinsa ba ne ya tasomin, sai na ji gaba ɗaya na rasa ƙwarin jikina. Ya taku inda nake, sannan ya ce. “Nana bansan masifar da takaini ba, bansan ƙaddarar da ta ɗauramin kishinki ba fiye da komai, Nana wani abun kika yi min? Nana yadda nake kishin ko Bilkisu da nake so bana mata wannan kishin, Bilkisu ita ce macen da nake so,na kuma zaɓi yin rayuwa da ita amma ko kaso ɗaya cikin ɗari na kishin da nake miki Nana banayi mata, Nana ina son wannan yazo ƙarshe, duk ranar da nasa wasu mazan suzo gidan nan, to ki dinga ɓoye kanki har su tafi, Nana ko bana nan ina jin zafi a lokacin da kike kusa da wani namijin, duk wata haɗuwarku da Turaki ina jin zafin a zuciyata ko da bana kusa, dan haka na rabaki Nana, da kowa har ‘yan uwanki Nana.” “Tom in sha Allah.” “Baby i’m out.” Muryar Bilkisu ta karaɗe ɗakin. “Okay take care my love.” Ɗaga kai na yi na kalli yadda take sanyi da wani mitsitsin gyale kamar soson wanka, amma ko a idon Sardauna. “Allah mai iko.” Na faɗa a raina shi kuma ya fice, bayan ya fita na hau gyara kayana ina ninkewa ina sanya su cikin akwati har na kammala, na jere akwatin agefe na yi shimfiɗa akan katifa ta na ɗaura matashi na, si naga ɗakin ya yi kyau sosai a hakan ma, daman nasan Sardauna bazai taɓa wani abu da zai cuceni ba ko kaɗan. “Allah Sarki Sardaunana, Allah Ya ƙara maka arziƙi, lafiya da nisan kwana.” ********* “Nana! Nana!” Na ji kiransa, ba shiri na miƙe ba tare da na amsa ba dan ya hanani amsa masa kira ina daga nesa. “Gani.” “Sama min abinci.”’ Kicin ɗin ɓangarensu na nufa, dan dama shi yana falo na ne bai shiga daga nasu cikin ba, jallop ɗin taliya na yi masa sauƙaƙaƙƙa na kawo masa, daga nan na koma ɗaki na kwanta. Ba ni na tashi ba sai gab da magariba, ina tashi na shiga toilet na yi alwala na zo na yi sallah, ina idarwa na ji motsin Bilkisu. ‘An dawo kenan?.’ Na faɗa a raina. Kasancewar basu wani fiya cin abinci da daddare a gida ba ya sa ban fiya girkin dare ba, tin da suka yi aure duk dare sai an fita ba a zama, yau ma kamar kullum naji ficewarsu. Zaman kaɗaici ya isheni na ɗauki wayata na kunnata, ni tun da na fuskanci Sardauna baya son na yi harka da waya ta fice a raina kwata kwata, ta na gama kunnuwa na ga message ya shigo wayata na Yaya Radiya. Ban tsaya dubawa na kirata, ji na yi ina son jin muryarta sosai, bugu ɗaya ta ɗauka. “Rawasiya yau a gari?” Na yi murmushi sannan na ce. “Wallahi Yaya, ya gida, yasu Hajiya?” “Kowa lafiya, Hajiya ma taje gida ziyara.” “Allah Sarki ita kaɗai?” “Ita da Ra’is.” “Ohky, yanzu na kunna wayar naga message ɗinki.” “Nana wajen kwana nawa da tura miki message ɗin sai yau kika kunna wayar?” “Kinsan ni ban cika wani amfani da waya ba.” “Kai Nana yakamata kanki ya buɗe, yanzu muna zamanin da ake samun wayewa da abubuwa dayawa ta waya, zaki ga halin da rayuwa take ciki.” “Uhm, ni dai Yaya barni kawai.” “Shi ya sa kanki yake kullum a duhu, ya amaryarki da mai gidan.” “Suna nan ƙalau kam.” “To ma sha Allah, ba dai wani abu ko?” “Babu Yaya, tana can sashenta ina nawa.” “Hakane kuma, bari na ƙyaleki kar mara mutuncin nan ya shigo.” Na yi dariya sannan na ce. “Ai sun ma fita.” “Shi da wa?” “Bilkisu mana.” “Lallai ne, Allah ya sa sai yana adalci a tsakaninku.” “Yanayi fa Yaya.” “Haka ake son ji, am Nana kinje wajen likitan da Rumaisa ta haɗaki da ita?” Shiru na yi ina son tunawa, tabbas Yaya Rumaisa ta haɗani da wata mata likita, to amma naje wajen na ta ko banje ba, ni duk na manta gaba ɗaya. “Kinje?” “A’a banje ba, amma ina sa ran zuwa, kina da lambar likitan ki ban?” “Eyh ina da ita, Dr Na’ima Daƙayyawa zan tura miki sai ku yi magana da ita, mussaman akan rashin haihuwar.” “Tom Yaya na gode, ina yaran?” “Sun tafi makarantar dare, ƙawarki Malaika ta sake haihuwa ma, amma tana can kanon.” “Allah Sarki zan kirata in sha Allah, ya wajensu Hajja.” “Tana nan tana abinda ta ga dama, wancan satin taje gidan Rumaisa ta yi mata rashin arziƙi wai ta roƙi mijinta kuɗi, wai daman Alhaji ne ki ciyar da ita, tun da ya rasu muka kwashe kayan shagon muka bawa wasu marasa mutunci suke mata rashin arziƙi, haka ta yi ta bara kamar almajira.” “Ikon Allah, ina ‘ya’ya da jikokin nata masu arziƙin da take magana fa?” “Nana kema kinsan babu mai jurar rigimar Hajja sai shi Alhajin.” “Hakane kam, Allah Ya jiƙanshi da rahama.” “Amin sai anjima.” Ta faɗa tare da kashe wayar, na yi shiru ina ƙoƙarin tuna wani abu, amma gaba ɗaya kamar antokaremin shi da wani abu a cikin ƙwaƙwalwata. ‘Ƙilinnn.’ Wayata ta yi Ƙarar shigowar saƙo, ɗauka na yi na duba lambar ce a jiki ansa Dr Na’ima Daƙayyawa. A take wani abu ya dawo kaina, muryar matar ta shiga amsa kuwa a kunnena. “Kin kyauta da kika sha abinda zai hanaku ɗaukan ciki.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na huɗu. Hayaniyar shigowar su ce ta ɗauke min hankali daga tunanin da na fara, na kalli inda suke hannayensu riƙe da ledoji, haka suka wuce ni kamar basu ganni ba. Tashi na yi daga zaman da nake akan kafet na yi cikin ɗakina, ban idda zama ba na ji muryar Bilkisu na kira sunana, banza na yi da ita har ta ƙaraso cikin ɗakin. “Ki zo ki ɗaura min ruwan zafi.” Kallonta na yi sama da ƙasa sannan na ce. “Bazan ɗaura ba.” “Ni kike cewa bazaki ɗaura ba?” “Uwa ta ce ke Bilkisu? Wallahi Bilkisu na yi danasanin aurawa Sardauna ke, tunda ke baki san darajar miji ba.” Dariya ta fashe da ita, sai da ta yi mai isarta sannan ta fara tafa hannu tana faɗin. “Au, ashe ma zan kula da miji, ashe bani da hankali irinki, Nana ki duba bautar da kika yi wa Sardauna me ta amfane ki da shi, banda shiga halaka, ni dai Sardauna wallahi sai dai na ja shi a ƙasa ba dai ya jani ba.” Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tsayamin a maƙoshi, cike da wani mugun takaici nake kallonta, ina jin kamar na rufe ta da duka. “Ba zaki zo ki ɗauramin ba?” “Bazanyi ba.” Ficewa ta yi a fusace, tana fita na bi ƙofar na sanya mata Sakata, na dawo na zauna akan katifa, ina ji Saradauna yana ta faman bugu amma naƙi buɗewa har ya haƙura, sama sama na fara jin muryarta tana magana. “Ka fasa ƙofar mana Baby, ka ci ubanta wallahi.” “Kina gani taƙi buɗewa, ni hannu zafi yake min idan ina buga ƙofar.” “Baby wallahi zuciyata tashi take, gashi kana gani sau uku ina dafa ruwan zafin ina sha amma baya ya zama, kawai nata nake sha’awar sha.” “To ya zanyi Baby?” “Dole fa ta buɗe, wallahi bazan iya bacci ba.” “Nana! Nana.” Ya faɗa yana buga ƙofar da ƙarfi, amma na yi kunnen uwar shegu da shi. “Idan baki buɗe ba Allah sai na dake ki Nana.” Tashi na yi na zo gab da ƙofar sannan na ce. “Wallahi bazan buɗe ba.” Ina faɗin haka na koma na kwanta, dan mugun haushin Bilkisu nake ji, tun suna bugawa har suka haƙura, ni kuma bacci ya yi gaba da ni. ********* Washe gari tun asuba na ta shi na yi sallah amma naƙi fita, gaba ɗaya sai na ji ma nafi sha’awar zaman cikin ɗakin kawai akan fitar, sai wajen ƙarfe bakwai sannan na fita zuwa falonsu, duk basu ta shi ba, dan dama ba tashi suke da wuri ba sai su kai goma suna bacci, mussama jiya da basu samu bacci sosai ba, dan na tashi cikin dare na ji surutun Bilkisu. 09:30am Tun da na gama yi musu abun abinda zan yi musu na dawo ɗakina na zauna, gaba ɗaya ji nake Sardauna ma ya fice min a rai, gaba ɗaya hankalina ya koma gida, gwanda na koma gidan mu naje na zauna acan ba zan iya zaman nan ba. “Nana.” Na ji ya kira sunana, na ɗaga kai na kalleshi sannan na amsa. “Na’am.” “Me kike son zama? Har ni zaki hulaƙanta jiya?” Shiru na yi masa ba tare da na tanka ba, ganin ba zance komai ba ya sa shi cewa. “Kibiyo ni.” Ba musu na tashi na bishi falon har wajen dinning, bayan ya zauna ne ya ce da ni. “Ki yi serving ɗinta.” “No Baby, ta fara haɗa min custard.” Bilkisu ta faɗa, kallonta na yi kawai na nufi kicin ɗin, ina shiga na fara haɗa custard ɗin na jiyo muryarta. “Nifa bazan iya ba, ace magana ɗaya ayi ta maimaita, jiya har wajen biyu na dare ana abu ɗaya.” “To ai kece kika ƙi fahimta Bilkisu.” “Ba abinda zan fahimta Baby, duka duka yaushe muka yi auren? Watan mu nawa sannan ka ce na haihu yanzu? Ashe ma haihuwa nazo yi duniya.” Ji na yi gabana ya buga da ƙarfi, cikine da Bilkisu daga zuwanta, amma kamar ita bata son cikin, shin bata san shine dalilin da ya sa aka aureta ba? Ƙasa ƙasa na ji yana magana alamar rarrashinta yake. “Bilkisu ina so haihuwa, ina son yara Allah ma ya sani, dan Allah ki jira mu fara tara ko uku ne sai ki yi planing ɗin, yanzu fa wannan ya riga da ya samu.” “Wallahi Baby ba zan haihu yanzu ba, kawai zubar dashi zanje ayi.” “Karki kuskura Bilkisu, ina son abuna, ina son ‘ya’yana ko Nana zan bawa ta kula dasu, zata iya zama mai rainonsu idan wahalace ba kya so, zata iya karɓarsu tun daga ranar da kika haifesu dan Allah.” “Baza ka gane ba, ka jira mana kamar nan da 5 years mun gama amarcinmu sai mu haifi ɗaya, bayan wata 5 years ɗin mu ƙara wani, yara biyu ba su isa ba?” “Basu isa ba Bilkisu, ina son yara, ‘ya’yana. Bilkisu ke ce macen da nake so dan haka ‘ya’yanki dole su kasance ababen so.” “Baby ni dai bazan haihu yanzu ba.” Ajiyar zuciya na sauke, sannan na juya ga custard ɗin na sauke shi, babban bowl na ɗauka na zuba mata sannan na fita, hannunshi na kan hannunta yana magana. “To tun da wannan ya zo ki bari a haifeshi shi.” “Wai yaushe na yi auren?” Ta faɗa a fusace tana ƙwace hannunta. “Sannan ace na haihu? To me na mora a rayuwar aure ne?” “Bilkisu ribar soyayya aure, kuma na aureki, ribar aure haihuwa.” “Nasani Sardauna, amma ban shirya zama uwa ba a yanzu gaskiyya.” “Allah ne fa ya baki a yanzu Bilkisu.” “Ke malama kin tsare mu da idanu, ajiye ki yi gaba.” Ba musu na ajiye mata na koma falo na zauna, ina ta jinsu sama sama, yana ta faman binta da magiya, amma taƙi saurarensa gaba ɗaya, ina zaune a kan capet ta shigo falon tana waya, a hankali take maganar cike da rashin tsoro. “Kinga, ni ki zo kawai muje azubar da cikin nan yanzu, wallahi bazan iya ba, wahalal dakon ciki ga ta haihu, bada ni ba, na haihu na yi me ma?” Shiru ta yi alamun ta cikin wayar tana magana, sai can ta ce. “Ki ƙyale banza, wai daga aure sai haihuwa, ni an faɗa masa ina son yara ne, ni na yi kama da wacca za ta yi wahalal yara for god sake?” Zallan mamaki ne yake shirin kashe ni daga zaune, yanzu Bilkisu cikin Sardauna zata zubar? Sardauna take cewa banza? Kai innullahi wa’inna illahir raji’un. “Ke ni na faɗa masa ma bazan iya ɗaukan wannan abun ba.” Na ji ta sake faɗa, ni kam duk abin duniya ya isheni, ga mamaki yan shirin hallaka ni. “Tana nan banzar, ai baza ta tafi ba wai har da cewa zata kula da yaran.” Ɗaga kai na yi na kalleta, tana zaune akan kujera tana kallona ido da ido. “Za ta iya mana, ba jaka ba ce.” Ta faɗa tana fashewa da dariya, har da ƙyaƙyatawa. “Ke ni ban shiryawa haihuwa ba, na ma yi sakaci daban yi planing ba tun farko, amma wallahi Yaya sai an zubar da cikin nan, idan na shiryawa haihuwar na haihu.” Ta sake yin shiru, sai kuma ta ce. “Tam Allah Ya kaimu sai kin zo, bari na shirya.” Tana faɗin haka ta miƙe ta yi ciki, ni dai ina nan zaune cike da mamaki, na ganin abinda yafi ƙarfina, tun ina saka ran zata fito na yi mata faɗa akan abinda take shirin yi har nagaji da zama, sai da ta kusa awa ɗaya da shiga sannan Yayarta ta zo. Ba ta kai ga shigowa ba ma, Bilkisun ta tare ta a hanya suka fice. Tun daga suka fita abun ya dameni, wani tausayin Sardauna ya tsayamin a rai, yanzu jaririn da Sardauna ke so? haihuwar da akanta aka yi min kishiya? ita ce Bilkisu zata je ta zubar? Har da ƙwallata ta tausayin Sardauna. Ba ita ta dawo ba sai bayan wajen ƙarfe huɗu, a yanayinta babu wata wahala da tasha, sai dai yadda yayarta ta ke mata sannu, yasa na tabbatar cewa ta aikata abinda take so ta ga dama. “Allah Yasa ka maka Sardauna na.” Na faɗa a raina ina kallon su, su kam kamar ba su kula dani ba. “Yanzu Bilkisu sai ki kula, karki sake ɗaukan ciki yawan zubarwar nan zai iya haifar da matsala.” “Nifa Yaya gani nake a juyar da mahaifar nan.” “A’a Bilkisu karki yi haka, wata rana zaki nema, mussaman ke da har yanzu Sardauna bai shiga hannunki ba, kince fa har yanzu yafi son wacca abar akan ki.” “Ai Yaya Sardauna mai sauƙi ne, wallahi sai ya shiga hannu, sai yadda na yi da shi, bare kuma waccan shegiyar da shi kansa ma yaƙi yarda cewar sonta yake.” “Nasani shigar Sardauna hannu abu ne mai sauƙi kam, dan duk faɗin gidanmu babu wacca mijinta baya hannu, kuma ba za a fara akan ki ba, kinsan ko zanyi yawo tsirara sai na ga ya shiga hannunki.” “Nasani Yaya, ko Mama da kanta ta karya miki kallabi, malaman da kika sani ko rabin su ba ta sani ba.” “Daman ai haka ne Bilkis, ka koya wa mutum abu ya zo ya fika ido, ke ma wata rana sai na karya miki kallabi nan.” Ni dai ina tsaye ina mamakin su, su Bilkisu wane iri mutane ne haka da babu Allah a ransu ko kaɗan? “Amma ina ganin me zai hana duk ajuyar muku da mahaifar tare ke da shi?” Wani kallo naga Bilkisun ta yi mata sannan ta ce. “Namiji ana juyar masa da mahaifa ne?” “A’a, amma akwai ƙwayoyin da zai yi amafani dasu sparm ɗinsa ba zai taɓa haifar da ɗa ba.” “Ina sonki Yaya, Allah Yabar min ke haka za’ayi.” Jin abubuwan nasu zasu iya haukata ƙwaƙwalwata ya sa na tashi na shige ɗaki, ina ta faman tunani. ‘Wannan wace irin rayuwa ce muke ciki haka? Me ya sa Bilkisu babu Allah a ranta?.’ Ban sake fita ba sai gab da magariba, har lokacin tana ɓangare na, kallo na ta yi sama da ƙasa sannan ta ce. “Ke banza.” “Bilkisu ki fita daga sabgar rayuwata, bana shiga sha’aninki dan haka ki fita daga nawa, amma dole na faɗa miki cewar baki da wayo kuma baki kyautawa kanki ba indai har kika zubarwa da Sardauna ciki, babu abinda yake so shi da iyayensa sai haihuwa, akan hakan fa ya auro ki.” “Ke dallah rufe min baki, me ya sa baki da hankali ne? Dan ya ce miki a gidansu ance ana son ya haihu shine zaki yarda? Ko da yake idan baki yarda ba ai baki cika mahaukaciya ba Nana, to na faɗa miki komai shirin Sardauna ne da ni, babu wata maganar haihuwa da aka yi masa, yana son ya yi amfani da wautarki ne ganin kin bashi damar ƙara aure da kanki, sannan ya ɗora ki akan keken nema masa aure da kanki, Nana wallahi kin rako mata, ko ni da kike tunanin na ce miki a gida ance na fitar da miji da gaske nake? To duk plan ɗinsa ne sabida a ƙara mayar da ke me ƙaramar ƙwaƙwalwa.” Da wani irin mamaki nake kallonta, me take so ta ce? Tana nufin komai tsarawa suka yi, ta ina zan yarda? Mene hujjarta da zan yarda da abinda ta faɗa, kukan da Sardauna ya dinga yi min a gidan nan fa duk na ƙarya ne ko me? “Nana idan baki yarda ba kanki, amma ki tabbatar komai shiri ne, ai duk jahilcinki kin iya hausa kin ita karatu kuma kinsan lokaci.” Ta faɗa tana matsowa inda nake. “Kalli, wannan message ɗin ranar da kika zo gidan mu ne zuwa na farko ya yi min wannan message ɗin.” ‘Ga banzar nan shigowa.’ Shine abinda ke rubuce a cikin message ɗin, wani abu ne na ji ya dirga a zuciyata, na dafe kaina da sauri tare da maimaita innullahi wa’ina illahir raji’un. “Sannan kinga, lokacin da kike kirana ya yi min wani message ɗin ya ce banzar na kira karki ɗauka. To Nana ki sani tun ranar da kuka dawo unguwar nan muka haɗu da Sardauna, kuma a ranar muka ƙulla soyayya abun mu, babu wata majalisa da yake zuwa sai wajena, babu wani da ya yi masa zancen haihuwa a gida, haka nima babu wanda ya ce da ni na yi aure a gida sai Sardauna, idan zaki farka ki farka idan ba zaki farka ba karki farka, amma dai Sardauna baya sonki, kamar yadda ya faɗa miki ya aure ki ne sabida wata manufar da shi kaɗai ya barwa kansa sani, amma baya sonki, sai da a zaman da kuka yi ya fara sha’awarki ba wai sonki ba, kuma ya dinga biyan buƙatarsa, daga nan kuma ya koma kishinki Nana, wannan kishin da yake miki shine baƙin cikina, yanda Sardauna yake kishinki ko ni da yake so baya kishi, Nana kuma ina baƙin ciki da hakan.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na biyar. Wani irin jiri na ji yana ɗibana ina daga zaune, ji nake kamar na kife ƙasa sabida abun da nake ji, wai Sardauna da ya zo yana kuka a ka faɗa ta yana cewa na sama masa mafita, ashe yana gefe yana zagina, yana ce da ni banza, yana ce da ni jaka, anya na yarda da wannan abun na Bilkisu, akan mema zan yarda da abinda ta faɗa, Bilkisu da ba Allah a ranta, ciki fa ta zubar me za ta faɗan na yarda? Sardauna dai yana sona, ni na sani. Recording ɗin voice note da ya yi mata a whatsapp ta shiga kunnawa a kunnena, ga sautin muryarsa nan ɓaro ɓaro. "Wallahi Baby, da na yi sha'awar yarinyar bayan na aureta, amma yanzu kwata kwata na daina sha'awarta, kuma daman ba dan sha'awarta na aureta ba, dan banyi niyar komai ya shiga tsakanina da ita ba, kawai kishinta nake wanda bansan daga ina yake ba." Sai kuma ta tsayar ta kunna wani. "Kinga ne Baby, yarinyar 'yar talakawa ce ta ƙarshe, har ƙyanƙyamin haɗa jiki nake da ita, doh dai tana da kyau, amma ba ta da wani diri ko wani abu, kishinta nake." Ta ƙarar tsayawar, sannan ta fara magana. "Wannan kishin a ko da yaushe sai ya faɗe shi, shi ya sa nake baƙin ciki da shi Nana." Tana faɗin haka ta ƙara kunna wani. "Ai na hana ta karatu, ya za’ayi na barta ta yi karatu? Ta fita tana haɗa jiki da wasu mazan, baby baza ki gane kishin da nake mata ba, kuma ni bana ma son naga ta zama wata a rayuwar nan, gwanda ta dauwama a ƙarƙashina." Shima ta tsayar dashi anan, gaba ɗaya jikina karkarwa yake, zuciyata ta fara wani irin zafi. "Duk na raba ta dasu har da uwarta ma, akwai wani shegen yayanta ma nake so na sa mata tsanarsa, wallahi ni kawai na buɗe ido na kalleta a gaba na shine kawai abinda nake jin daɗi, ko naga tana abu kamar za ta yi kuka, hawayen fuskarta suna burgeni, ta iya kalal tsoro, shi ya sa bazan saketa ba, bansan yadda zanyi ba idan na buɗe ido naga banganta a gabana ba." Shima ta tsayar dashi a wajen, sanna ta kama min ka haɓa ta ɗago da kaina. "Nana ni na bashi shawarar ya sake ki kuma ya barki a gidan zaune, ina mugun son Sardauna dan haka duk abinda zai bashi farin ciki zan nemeshi, amma ba zan zauna na haihu ba Nana, ke kuwa idan zaki farka ki farka, ki san zaman me zaki yi a gidannan, zaman bauta ne zaki yi wa Sardauna da ni matarsa, wacca yake so yake gani, amma ki sani Sardauna ya aureki da wata manufa ce da yabarwa kansa sani, sannan ki sani a cikin tarkon Sardauna zaki dauwama har abada Nana." A fusace na miƙe, dishi dishi nake gani amma hakan bai hanani cafkar wuyan Bilkisu ba, na riƙe shi iya ƙarfina, sannan na ce. "Wallahi Bilkisu ƙarya kike." Wata dariya ta saki sannan ta ce. "Mene nake ƙarya Nana?" "Bazan dauwama a tarkon Sardauna ba har abada, ke ce zaki yi dauwama kuma wallahi sai kinyi danasanin abinda kika yi." "Ni na yi miki kama da wacca namiji zai dauɗe? An gaya miki iyayena sakarkaru ne irin naki? Ko an faɗa miki basu san darajata ba?" Bansan lokacin da na yi tsallen albarka na sake kama wuyanta ba, na tsinka mata zazzafan marin da ni kaina sai da na ji zugi a hannuna. "Ni kika mara? Wallahi Nana yau sai naga gatanki." Ta kawo hannu za ta dake ni, na riƙe shi tare da hulli da hannunta, zuciyata tana wani irin tafarfasa dan bansan me ya sa ta tafasa har haka ba, ta ƙara yowa kaina na sake tare ta. Nan fa kokawa ta ɓarke, tana dukana da dukkan ƙarfinta, nima ina dukanta da dukkan fusata ta, abu kamar wasa faɗa ya yi ƙarfi, ƙaramin abinda Bilkisu take tunanin za ta gama da shi cikin ƙanƙanin lokaci ya turje mata, dan duk yadda taso kakkaɓeni abu ya gagara, sai da muka yi juna jina jina sannan muka rabu. Na koma ɗaki na zauna, gaba ɗaya zama da Sardauna ɗin ma ya fita a raina, gwanda na tafi gidanmu duk abinda zai faru ya faru, duk da nasan ba zan iya zama a gida babu Sardauna ba amma abubuwan da Bilkisu ta nuna ya yi matuƙar kiɗima ni, duk yadda zuciyata ke son yi wa Sardauna uzuri amma na kasa dan ba zan iya ba, har sai da ya haifar min da azababben ciwon kai me jiri, ta dole na kwanta ba dan raina ya so ba ko kaɗan ba. Har yamma Sardauna bai dawo ba, kuma bansake fita ba, ina zaune a ɗakina har magariba sannan ya dawo, ina jin ya dawo na tashi na fita so nake ma ayi komai ya ƙare, idan sakin da yake iƙirarin ya yi min na gaske ne ya faɗa min na kama hanya na yi gidanmu. A fusace na fita falon sai dai ina yin ido biyu da shi na ji duk wani abu me nauyi da yake ƙirjina ya tafi, wani irin sanyi ya ratsamin jikina, soyayya da tausayin Sardauna suka dirga a zuciyata, sai na ji na manta da komai da Bilkisu ta faɗa, daman nasan maƙaryaciya ce me zai kaini yarda da abinda ta faɗa ma. "Sannu da zuwa." Ya buɗe baki da niyar magana Bilkisu ta tare shi ta hanyar cewa. "Yau sai yarinyar nan ta bar gidan nan wallahi." Tana faɗin haka ta yi ɗakinta shi kuma ya bi bayanta, tashi na yi daga durƙushen na koma ɗakina na sa key na kulle, can su ƙarata amma ba zan bar gidan nan ba. Na yi matuƙar mamakin ganin bai zo ya yi min bugu ba, hakan ya sa na yi kwanciya ta hankalina kwance. Washe gari ma da na tashi na je na yi duk ayyukana da nasa ba na dawo ɗaki na zauna, sai dai ina zama kalaman Bilkisu na jiya suka shiga dawowa kunnuwana kamar an kunna recodin. "me ya sa baki da hankali ne? Dan ya ce miki a gidansu ance ana son ya haihu shine zaki yarda? Ko da yake idan baki yarda ba ai baki cika mahaukaciya ba Nana, to na faɗa miki komai shirin Sardauna ne da ni, babu wata maganar haihuwa da aka yi masa, yana son ya yi amfani da wautarki ne ganin kin bashi damar ƙara aure da kan ki, sannan ya ɗora ki akan keken nema masa aure da kanki, Nana wallahi kin rako mata, ko ni da kike tunanin na ce miki a gida ance na fitar da miji da gaske nake? To duk plan ɗinsa ne sabida a ƙara mayar da ke mai ƙaramar ƙwaƙwalwa." Tsam! Haka na ji zubar sassanyan ruwan a jikina, ban kai ga gama tantance ko mene ba, na ji an ɗauke ni da wani azababben mari, da sauri na riƙe kuncina tare da ƙwalla uwar ƙara. "Ahhhhhhhhhhhhh." Idanuna har wani dishi dishi suke, amma a haka na iya ganesu yana tsaye kiƙam, ita kuma ta dafa kafaɗarsa, hannunta riƙe da jug da alama ita ce mai watsa ruwan sanyin, shi kuma ya ɗaure fuska. 'wai ni ce yau Sardauna yake mari, wannan wace irin rayuwa ce?' "Na faɗa miki ki fita sabgar mata ta da abinda ke cikinta amma kin ƙi ko, wallahi Nana ina jiye miki ranar da zanyi miki Ɗan bara uban duka a gidannan, jaka kucaka." Wani irin abu ya toshe mini ƙirji, na ji kamar na faɗi ko zan samu faɗuwar ta zama sanadiyar da zan rasa rayuwata baki ɗaya, rayuwar da ba ta da wani amfani, a yanzu ba wai juya min baya da sardauna ya yi ba ne yake damuna ba, takaicin da danasin biyewa Sardauna da na yi, na zaɓe shi na watsar da 'yan uwana, na zaɓe shi na watsar da kowa, tabbas namiji ba Ɗan goyo ba ne, kuma duk wacca ta ɗauki miji uba zata mutu marainiya. "Na faɗa miki dai, jaka ballagazar da bata da ilimi." Ya faɗa yana barin wajen, a take na tuna lokacin da Sardauna ya ce dani. "Nana, ina da arziƙin da zan riƙe ki, bake kaɗai ba har da gidanku, muna da arziƙin da bazamu taɓa talauci ba, Nana a cikin gidan nan zaki zama kamar sarauniya ne, Nana bana son karatun boko nan, Nana bana son cuɗanya da maza, ina miki so mai tsanani, ina miki kishi mai zafi Nana dan Allah dan Annabi ki haƙura da karatun." Wasu zafafan hawayene suka biyo kuncina, a fili na furta. "Allah Yana ji Yana gani." "Kutumar uban can, Baby ta zageka, wai kaine shege!" Ni ban ma san tana wajen ba, dan ban kula da ita ba sai da na ji ta yi wannan maganar, ban kai ga gama kallonta ba na ji saukar wani marin a kunci na, tare da sa ƙafa ya kwarfeni na zube a ƙasa ya shiga duka na hannu da ƙafa, tun ina ihu da ƙara har sauti ya daina fita. Sai da ya yi min lilis sannan ya ce. "Nana! Akan cikin jikin Bilkisu wallahi zan iya kashe ki, muguwa mai mugun nufi, Nana natsaneki, bana sonki. Ke tsaya kiji na faɗa miki wani abu, kinsan dalilin da ya sa na aureki? Kafin na fara kishinki Turaki na fara kishi, tun muna yara nake kishin Turaki, kuma na yi alƙwarin bazan taɓa barin shi ya sami wani abu mai kyau ba, a ranar da naganki zuciyata ta raya min ke ce irin tsarin macen da Turaki yake so, domin kowa ya san burin Turaki da irin macen da yake son auren, ina ganinki na hangi Turaki a tare da ke, Nana da zuciyata tana son Turaki da alheri to da na kawo shi wajenki da kaina ya ganki, dan kece macen da Turaki yake mafarkin samu a rayuwa, amma da yake kishin shi zuciyata take sai ta kawar da wannan tunanin, na tafi da sa ran bazan sake ganin ki ba, amma ƙaddara ta haɗani dake a karo na biyu, tun a wannan lokacin na yi tunanin cewa ƙaddarar da ta haɗani dake a karo na biyu to tabbas za ta iya haɗaki da Turaki, kuma wallahi bana son Turaki ya same mace irinki, sabida zuciyata ba zata iya ɗauka ba, da kaina na shirya zuwa unguwarku wanna shine karo na uku da naganki." Wani irin abu naji yana shiga da fita a cikin zuciyata, kamar ana caka mashi ana cirewa, haka nake jin shiga da fitar abun a cikin zuciyata. Har rawa idanuna suke yi daga ciki, na ɗaga kai na kalli Sardauna dan babu magana ɗaya da nake iya ganewa, kawai dai ina jinsu ne amma bana gane komai ciki. "Nana! Tun daga lokacin na yi alƙwarin haramtaki ga Turaki, sai daga baya nagane ba iya Turaki nake son haramtawa ke ba kowa ne, ni dai nasan babu masifar da zata sa na haɗa iri da talakawa, shi ya sa na yardarwa zuciyata cewa sha'awarki ce ta kamani bayan na aureki, Nana ke mayya ce, Nana kin kama min kurwa, amma Nana kisa a ranki ban taɓa sonki ba kuma bazan so ki ba." "Yanzu Sardauna komai da ka faɗa min ƙarya ne?" Na faɗa muryata na rawa, ya kalli ni ya tuntsire da dariya. "Nana mene kike son tabbatarwa? Fushin da na ce miki Hajiya ta yi akan aurenki? To ƙarya na yi miki? Ko maganar ƙarin aure? Itama ƙarya ce. Nana na faɗa miki cewa ki aka ran ganin abubuwa da yawa, waɗanda ƙwaƙwalwarki ba za ta iya ɗauka ba." "Sardauna ka cuceni, ka cutar da zuciyata, ka azabtar da rayuwata, Allah Ya da samin son ka wanda bansan dalilin haka ba, ka yi min rai dan girman Allah Sardauna, ka ce min wasa kake min, Sardauna zuciyata ba zata iya ɗaukan rashinka ba Sardauna, bazan taɓa iya wa ba Wallahi Sardauna dan Allah." "Nana komai dana faɗa miki gaskiyya ne, babu abinda yake ƙarya sannan kisani na sake ki, kina zaune anan ba a matsayin matar aure ba, kina zaune a matsayin 'yar aiki ne, Nana bazaki taɓa haihuwa ba a rayuwarki, na yi miki abinda bazaki taɓa mantawa dani ba a rayuwa har Abada." Kalaman Sardauna suka shigo kunnena tamkar saukar ardu. Banko ƙofar da suka ya yi shida Bilkisu su ka barni a parlon, ya zama mafarin juyawar duniyata. Nan take na ji iskar ɗakin ta yi mini zafi tamkar wuta, na rasa ta ina zan shaki numfashi. Na ji ƙirjina yana wani irin matsewa kamar ana ɗaure shi da igiya, na sa hannu na dafe ƙasa  ina nishi sama-sama. Parlon ya fara juya mini, labulaye da kujeru suka fara juyawa, suna matso wa gaba na kamar za su danne ni. Na dafe tsakar kaina da hannu biyu saboda wani mugun duka da na ji kaina yana yi, ɗas! ɗas! tamkar jijiyoyin kaina za su tsage su fito waje. Zafin da nake ji a cikin kaina ya canza mini tunani, na zube a ƙasa na fara juyi. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na shida. Tuna baya…. Bayan Sardauna ya fita daga ɗakin asibitin ya bar ni da wannan sabuwar barazanar ta cewa na shirya ganin abubuwan da kaina bazai iya ɗauka ba, Dr. Na’ima ta dawo ɗakin riƙe da takardun binciken lafiyata. Ta zauna a gefena, ta dubi yadda nake ta faman kuka, ina ganinta na ce da ita. “Dr, don Allah ki ce masa ya yi mini haƙuri, na san ransa ne ya ɓaci... Sardauna mutumin kirki ne, laifi na ne da na takura masa...” Ta sauke nannauyan numfashi, ta katse ni ta hanyar dawo da fuskata daidai tata, ta ce. "Nana, ki saurare ni da kyau. Mutanen da yawa suna kallonki a matsayin wawa ko dolowa da ba ta da zuciya, domin duk wulaƙancin da mutumin nan yake miki, har yanzu ƙoƙarin kare shi kike yi kina masa uzuri. Amma a matsayina ta likita, na san ke ba haka ba ce, wata irin soyayya kike masa wacce ke maƙale a ƙwaƙwalwarki, ba a zuciya ba!" Na kurawa Dr. Na'ima Daƙayyawa ido, ina jiyo muryarta tamkar daga sama. Ta ci gaba da cewa. "A ilimin likitanci, akwai abin da muke kira Obversive Obsession (ko Limerence). Cutar haukan son abu ce da take kama sinadaran ƙwaƙwalwa. Mutumin da yake ɗauke da wannan rashin lafiyar, ƙwaƙwalwarsa tana daina nuna masa gaskiyar abin da idonsa yake gani, ma'ana ba zuciyarki ke son Sardauna ba ƙwaƙwalwarki ce. Duk lokacin da Sardauna zai cutar da ke, Kina masa uzuri marar iyaka ne domin idan ƙwaƙwalwarki ta amince Sardauna azzalumi ne, to gaba ɗaya za ki iya haukacewa, domin ƙwalƙwalwarki ce ke son shi, har takan mantar da zuciyarki sharrikansa!" Da sauri na buɗe idona na kalli silin, ina sake jiyowa ƙarar buga ƙofar da Sardauna da Bilkisu su ka yi, tabbas waɗannan sune kalaman da Dr Na’ima Daƙayyawa ta faɗa min a lokacin da nake asibiti, kuma waɗannan sune abubuwanda zuciyata take yaƙi da ƙwaƙwalwata akan su, duk lokacin da na so tuna so sai kaina ya fara azababben ciwo. "Nana! Ba ke nake so ba. Ƙuciyar jikinki kawai nake so... wadda na riga da na gama mallaka gaba ɗaya. Nana, ban taɓa son na rayu da ke a matsayin macen da zan so ba, sai dai na rayu da ke a matsayin wadda zan killace ta. Na hana ta kula kowa a duniya, saboda zazzafan kishinki na ƙaddara da nake ji a raina." Kalaman Sardauna suka shiga zarya suma a kunnuwa na. "Nana! A yanzu haka zan sauwaƙe miki, zan raba aurenmu. Amma kuma zan miki alfarma guda ɗaya, wadda ita ce zaki zauna a gidana a ƙarƙashin kula ta da ikona tun daga yau har ranar da zaki mutu, Nana. Tun da dai ke da kanki kika nuna idan babu ni ba zaki iya rayuwa ba. Kuma ko da na sake ki kika tafi, ai ba ki da kowa a duniyar nan, ba ki da inda zaki tafi... 'yan uwa ne babu, ƙawaye babu, Nana! Ba ki da wata mamora ko amfani a rayuwa. Shi ya sa zan barki ki ci gaba da zama a nan tamkar baiwa, ba tare da kin faɗawa kowa cewar na sake ki ba. Gimbiya Bilki... ɗauko takarda ki rubuta mata takardar sakinta." Da sauri na buɗe idona, tare da ƙwala uwar ƙara, idanuna su ka yi duhu dunɗum, na sake zubewa a ƙasa. ********* 05:15am Lokacin da na buɗe idona, na ji parlon ya yi tsit, sannan ɗaukacin zafin da radaɗin ciwon kan na ji sun ɗauke ɗif. Na miƙe zaune ina kallon ƙofofin ɗakin, sai na ga Sardauna yana zaune a kan kujerar dining yana mini murmushi, nima yi murmushi na ƙarasa gurinsa. "Mijina ashe ka tashi? Bari na haɗa maka shayin yau da wuri karka makara." Na faɗa cikin sanyin murya sannan na shiga kicin ɗin, Sardauna yana son cake dan haka shi zanyi masa yadda zai ji daɗi bana son abinda zai ɓata masa rai. ina ƙoƙarin fara ƙwaɓa butter da ƙwai, sai ga Bilkisu ta shigo kicin ɗin tana sanye da kayan barci. Ta kalle ni ta ɓata fuska. 'Ke doluwa! Me kike yi a kicin ɗin mutane da asusuba haka?' Na juyo na kalle ta cikin kwanciyar hankali fuskata ɗauke da murmushi, sannan na ce. "A'a Amarya Sardauna ne ya ce yana buƙatar abun breakfast da wuri, shi ya sa nake ƙoƙarin gama masa da wuri kafin ya fita masallaci." Kallon tsoro da mamaki ta jifeni da shi sannan ta ce. "Ke a ina kika ga Sardaunan?" Leƙawa na yi ta jikin kofar kicin ɗin, na ganshi nan zaune daram a kan dining yana jirana, sannan na juyo na ce mata. "Gashi nan zaune a kan dining." "Mahaukaciya!" Ta faɗa cikin fargaba tare da ficewa da gudu daga kicin ɗin. Ni kuwa ko a jikina, Allah-Allah nake na ga na gama gasa cake ɗin kafin mijina ya fita masallaci. Na farko yana gasuwa na fito da shi da zafinsa, na juye a cikin faranti na yi kan dining ɗin da sauri. "Mijina ka yi haƙuri na daɗe gashi," Na faɗa ina ajiye kwanon a gabansa, wannan murmushin na sa kawai ya sake yi mini ba tare da ya ɗaga hannu ya taɓa cake ɗin ba. Na karyar da kaina gefe cikin shagwaɓa sannan na ce, "Ka ci don Allah mijina..." Ina cikin wannan magiyar, sai na ji an tura ƙofar parlon da ƙarfi. Sardauna ne ya fito sanye da jallabiya ta barci, idon sa har rufewa suke alamun yanzu ya tashi daga barcin. Gabana ne ya yi bada tas! Na kalli Sardaunan da ya fito daga ɗaki, sannan na juya na kalli Sardaunan da ke zaune a gabana a kan dining yana mini murmushi, sai dai naga babu shi. Sardauna ya ƙaraso cikin parlon da hanzari, ya dubi plate ɗin cake ɗin dake kan tebur yana tururi, ya dubi kujerar dining ɗin da take wayam babu kowa sai iska, sannan ya juyo ya kalle ni yadda nake tsaye jikina yana rawa. “Nana... me kike yi a nan?" Ya tambaya muryar shi da alamun bacci, na miƙa hannuna na nuna masa kujerar da babu kowa. “Nana menene? Waye zaiyi breakfast yanzu koma kin kwanta, mu tafiya ma zamuyi.” Ba musu na shiga ɗaki zan kwanta, sai dai ina shiga na ci karo da shi. “Kaima kwanciyar zaka yi?” Ya gyaɗa min kai alamar eyh. “To kwanta, akan katifa zaka kwanta?” Na tambayeshi, sai da ya yi murmushi sannan ya ce. “Eyh.” “Nima na kwanta anan?” Ya girgiza kai tare da nuna min ƙasa, ba musu na kwanta a ƙasan, ina kwanciya bacci ya yi gaba da ni. Ba ni na farka ba sai wajen ƙarfe sha biyu saura, lokacin da na tashi banga Sardauna akan katifar ba, na tashi na fito falo ina dubashi ina faɗin. “Sardauna ina kashiga? Kana ina?” Idona ya kai kan agogon ɗakin, ƙarfe sha ɗaya da arba’in da huɗu, murmushi na yi tare da cewa. “Bai tashe ni ba, ya tafi ofis.” Ɗakinsa na nufa na ɓangaren Bilkisu, ina zuwa na fitar da kayansa waɗanda ba su da wanki, nasan Sardauna idan ya dawo ya ga na yi masa wanki zai ji daɗi sosai da sosai. Ina ɗaukowa na fita harabar gidan ta baya, inda yake ɓangarenmu ba tare da Turaki ba, na shiga wankina, tun ina yi a hankali har na fara da sauri da sauri, ba ni na idda wankin ba sai ƙarfe uku, ina gamawa na shanyasu na dawo ɗaki. Wanka na yi na shirya cikin doguwar rigar atamfa na yi kyau abuna, na tsantsara make-up na dawo na zauna, Allah Allah nake ƙarfe biyar ta gota na shiga kicin na haɗawa Sardauna girkin dare, yau tuwon shinkafa zan masa da miyar agushi, sai farfesun naman rago, nasan Sardauna yana mugun ƙaunar tuwon shinkafa. Har biyar Bilkisu ba ta dawo ba kuma ni ban nemeta ba, ina yin sallar la’asar na shiga kicin na hau haɗa masa abinci, tuwon shinkafa da lafiyayyiyar miyar agushi, wacca ta ji nama sosai da sosai, ina sauke na yi masa farfesun da yake so. Sai gab da magariba na kammala komai na ajiye akan dinning, na dawo falo ina zaman jira Sardauna ya shigo. Har aka yi isha’i babu Sardauna babu alamunsa, hakan ya sa na ta shi ma shiga ɗaki na ɗauko wayata, sai dai ina fitowa na ganshi zaune akan kujera yana sakar mini murmushi. “Ka dawo?” Na faɗa ina ƙarasowa, ya gyaɗa kai kawai sannan na ce. “Muje ka ci abinci sai ka yi wanka, yau tuwo na yi maka, sannan na yi ma wanki da yawa, zaka ci tuwon ai ko?” Ya gyaɗa kai kawai ya wuce dinning ɗin. “Ka yi magana dan Allah.” “Zan ci mana Nana.” Wani sanyi na ji a raina, tare da ƙarasawa wajen dinning ɗin. “Zo ka zauna.” Na faɗa ina kaɗe mai kujerar da ba ta yi datti ba, ya ƙaraso ya zauna. Na buɗe plast ɗin na sama tuwon, sannan na ɗau bowl na zuba mai miyar sai kuma na ɗau wani na sa mai farfesun, na miƙa mai cokali ina faɗin. 'Mijina gashi ka ci, nasan kana jin yunwa,' Na fada ina murmushi. Ya miko hannunsa zai amshi cokalin. Dai dai lokaci iska ta kaɗa labulen tagar ɗakin, Sai na ga cokalin da na tura gabansa yana nan a ajiye daram a kan kwanon abincin da har yanzu tururi ke tashi a ciki, babu alamun an taɓa shi, iskar daƙin ce kawai take kaɗe labulen da ke bayan kujerar tasa wacca babu kowa. Na waigo gefe na ƙara waigawa ina kallon ko ina, amma babu Sardauna babu alamarsa. “Sardauna wanene ya shigo ne?” Na faɗa muryata tana na rawa, ina jiran naji takun takalmansa ko sautin muryarsa. Amma shiru. Parlon ya yi mini tsit tamkar maƙabarta, sai sautin agogon bango dake ta faman duka ɗik-ɗik-ɗik wanda yake sake jaddada mini cewa ni kaɗai ce a cikin ƙatoton gidan. Wasu zafafan hawayene masu raɗaɗi da na daɗe ban ji irinsu ba suka ɓallo mini. Gidan ya dawo min na gaskiya wanda babu kowa sai ni kaɗai, babu Sardauna babu Bilkisu, na kalli cokalin dake kwance a kan kwanon tuwon, na kalli kujerar da take wayam babu kowa babu alamun an zauna a a kanta. Gwiwata ta gaza ɗaukana, na zube a ƙasa gaban kujerarun dinning ɗin da suke babu kowa, na fara karce fentin jikin teburin ina wani irin kuka mai cin rai. Kuka nake yi na tsantsar kaɗaici da wulaƙancin da aka yi mini. “Sardauna don Allah ka fito... don Allah karka yi mini haka. Idan laifi na yi maka ka dake ni amma kada ka ɓuye mini...” Na riƙa magana ina kuka, ina shafa iskar dake kan kujerar ko zan taɓa ko da jallabiyarsa ce, na juyar da kaina ina kuka, ina share idona da gefen rigata. Sai can, na sake ɗaga kaina na kalli saman kujerar. Kamar ko da yaushe, sai na ga ya sake bayyana zaune a kai, fuskar sa ɗauke da wannan sanyayyan murmushin nasa, ya miko hannunsa tamkar yana ƙoƙarin share mini hawayena. Cikin sauri na tsayar da kukan, na saki wani irin murmushin jin daɗi ina goge fuskata da sauri, na ce. “Haba mijina... daman wasa kake mini ka ɓuya a bayan labule? Dubi yadda ka sa na yi kuka. Maza dan Allah amshi cokalin ga tuwon yana hucewa...” Na ɗauki cokalin na sake miƙa wa iska, fuskata cike da hawaye amma bakina yana ta faman murmushi.. ta shi ya yi daga kan kujerar ya shiga ɗakin bacci, ba musu na bi bayanshi zuwa ɗakin. Kamar jiya haka ya kwanta akan katifar ni kuma na kwanta a ƙasa, na jima ina kallonsa kafin bacci ya ɗaukeni. ******** Washe gari ma kusan haka ce ta faru, na ganshi sai kuma ya ɓace, gashi gaba ɗaya abincin da nake dafa masa baya iya ci, sai dai na bawa me gadi da safe, gaba ɗaya na damu da hakan. Me ya sa Sardauna baya cin abincin da nake masa? Girkin ne baya masa daɗi ko wani abu ne daban? Ni ce ban iya kula da shi ba? Ko abincin ne ban iya ba shi ba? Ya rage yawan magana kwana biyu kamar ma dai ba shi da lafiya, ko a gida aka ƙara takura masa? Gashi Bilkisu ta zubar da cikin jikinta. Gaba ɗaya babu wani abu da nake fama da shi a kaina sai waɗannan, ta ina zan samawa Sardauna na farin ciki? Gaba ɗaya ba ya yin abu cikin walwala da kuzari abinci ma ya daina ci. ‘Dole na nemawa Sardauna farin ciki da walwala, bazaiyu na barshi a cikin damuwa ba.’ Na faɗa a raina ina tashi, gaba ɗaya gidan ya yi ƙura yana buƙatar gyara, agogo na kalla naga huɗu saura, da sauran lokaci kafin na shiga kicin dan haka zan iya gyara ko ina na gidan ya yi kyau. Ta ɗakinsa na ɓangarena na fara, ina shiga naga kayan wankin da na zube masa akan gado, har yau bai shigar da su sif ba, zama na yi a gefen gadon na shiga ninkesu, sai kuma na yi tunanin gwanda na gogesu Sardauna zaifi jindaɗi idan ya gansu a goge, duk da banda lokaci amma zan iya ƙoƙartawa. Kwaso kayan na yi na zube su a falo, sanna na jona dutsen na fara gugar, sai da na goge kala goma sannan na ta shi na shiga kicin. Cous-cous da miyar kaza zan yi masa abincin da yafi so. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na bakwai. Tun da na shiga kicin ɗin ban fito ba sai da cous-cous ɗin ya yi, sannan na shiga haɗa miyar, shima ban fito ba sai da na ga ta kammala, sannan na kwashe zuwa dinning na dawo na ci gaba da gugu ta, sai da na kai ƙarfe tara ina guga ban ji shigowar Sardauna ba, ina nan zaune har sha ɗaya sannan na haƙura na shiga ɗaki, na yi mamakin ganin shi a kwance yana bacci, na gyara mai bargo na lulluɓe shi nima na kwanta a gafe. Haka na yi ta rayuwa da Sardauna ina rasa gane kansa gaba ɗaya, kullum tunani da burina shine na ga yadda zan yi wani abu da zai burge Sardauna ko ya ƙara masa soyayyata a ransa. ********* Yau tun safe na ta shi, bayan nagama haɗa masa abun breakfast kamar kullum, na shiga banɗaki na haɗa masa ruwan zafi na wanka me zafi daidai yadda yake so, na dawo ɗakin yana kwance akan katifa. “Ruwan zafin yana ciki.” Na faɗa muryata a hankali, ya ɗago ya kalleni sannan ya ce. “Tom Nana.” Yana faɗin haka ya tashi ya shige toilet ɗin, ni kuma na zauna kan katifar ina zaman jiran fitowarsa, kusan awa ɗaya babu Sardauna babu dalilinsa, a hankali na tashi na ƙarasa bakin ƙofar banɗakin ina faɗin. “Baka fito ba fa, ka yi shiru.” Buɗe ƙofar banɗakin na yi, sai da wayam babu kowa a ciki, ga ruwa da sabulu babu alamar an taɓa. “Sardauna kana ina ne?” Na faɗa daga cikin baɗakin. “Kana ina ne wai?” Na faɗa ina fitowa ɗakin, shima wayam babu shi, fita na yi daga nan ɗakin na yi ɗakin gadonsa, kayan da na cire masa suna nan inda na ajiyesu. “Ina kashiga wai? Baka san kayan ba fa. Sardauna.” Na fara ɗaga labulaye ina dubawa amma babu shi kwata kwata a cikin gidan, ɓangaren Bikisu na nufa ina faɗin. “Nan ka shigo ne?” Ganin ɓangaren na yi ya yi wani dusu-dusu, alamar ba a gyara shi. “Ya salam Amarya, ya aka yi kika bar ɗakin naki haka ya yi datti, yi haƙuri kwana biyu bana shigowa bari na gyara miki.” Na faɗa ina ƙoƙarin fara kwashe kayan da suke zube a ƙasa, na hau gyara falon sannan na ɗauki abun shara na fara sharewa, bayan na gama na shiga ɗakin gadonsu, nan ma na shiga gyarawa tun daga kan gadon su da yake kaca kaca da kayan baccinsu, har zuwa sif da take baje baje da kaya a ƙasa, sai da na ɗauki kusan awa a cikin ɗakin sannan na fito, na shiga ɗakinsa na nan shima na hau gyarashi, ina cikin gyaran na ji ya shigo, na waigo fuskata ɗauke da murmushi. “Har ka shirya?” Ya gyaɗa kai sannan ya ce. “Eyh na shirya.” “Me za a dafa ma?” “Bakomai Nana.” Na haɗe rai kamar zanyi kuka sannan na ce. “Dan Allah me zan dafa ma.” “Babu komai, ko dafa abinda kike so.” “To muje na raka ka.” Na faɗa ina karɓar jakar hannunsa, haka muka fito harabar gidan muna hira cike da soyayya, har ya shiga mota ya tafi sannan na dawo, wani kallo naga mai gadi yana yi min wanda ya nemi ɓata min rai, amma kuma kawai na shige ciki na barshi. Ina shiga falon, na sauke nannauyan numfashi ina mai farin ciki, na kalli jakar Sardauna dake hannuna, wadda a idona take kyakkyawa baƙa mai tsada. “Ashe ma ban bashi jakar ba? Allah Sarki.” Na faɗa ina nufar kan kujera domin na ajiye ta, ina ta faman murmushin jindaɗi, wanda nasan yana da nasaba da yadda yau na raka Sardauna har ya hau mota. “Allah ya dawo min dakai lafiya, bari na adana maka jakar a nan.” Ina cikin ƙoƙarin ɗora jakar a kan kujera, sai na ji hannuna ya yi mini shafal kamar ban ɗauki komai ba, sai kuma na ji wata ƙara kamar ana buga ƙarfe ya na tashi. ‘Ƙal! Ƙal! Ƙal! sautin ya yi matuƙar ba ni tsoro, ya daki kunnuwa na wanda ya sa na ji tsakar kaina ya sara ya bada wani sautin ɗas! A take na ji wani irin abu kamar an fasa mini jijiyar kaina, jiri ya kwashe ni na daƙiƙa guda, idona ya buɗe fes, ɗaukacin hasken dake cikin ɗaki na ga ya ɗauke ya koma duhu, ɗakin babu wani abu mai kyau ko shauƙi, na dawo cikin ainihin zahirina na ɓacin rai. Na dubi hannuna na dama dake rawa, gaba ɗaya jikina ya ɗauki ƙarƙarwa, numfashi na ya maƙale min a makogwarona saboda tsantsar firgici. Ashe babu wata jakar Sardauna a hannuna! Wani kwanon ƙarfe ne a hannuna shi ne na ɗauko nake yawo da shi ina cewa jakar mijina ce. Shi ne ya suɓuce a hannuna ya faɗi ƙasa yake ta faman ƙara irin haka da ta firgita ni. Na ja da baya da gudu ina ihu, na buɗe idona na kalli falon da na ɗauki sa'o'i ina gyarawa. Wani uban firgici ya sake kama ni, na fasa wani ihu ina ja da baya jikina ya ci gaba da rawa, hannayena suna wani karkarwa kamar an watsamin ruwan sanyi a lokacin hunturu. Falon wayam yake kuma babu wani gyara da na yi masa, har da datti ma a ɗakin. Labulayen ma sun yi datti, kamar an daɗe ba a sauya su ba, kujerun ma duk kaya a baje a kansu, sunyi datti da ƙura sosai. Ganin abubuwan sunfi ƙarfin hankali ya sa na ruga da gudu na tura ƙofar ɗakin barcin Sardauna da Bilkisu wanda na gyara shi ɗazu, yananan kaca-kaca, ya yi wani irin datti kamar bola, babu alamar an taɓa gurin. “Mijina! Sardauna! Sardauna kana ina? Ka fito don Allah.” Na riƙa fadin haka ina duba ɗaki-ɗaki, ina neman sa a firgice tamkar wata zaburarriya, na dawo tsakar falon na zube a ƙasa, na takure jikina guri guda, na sa kaina a tsakanin gwiwata na fara wani irin kuka mai cin rai da raɗaɗi. Kuka nake yi, zuciyata cike da wani matsanancin tsoro, domin ji nake a jikina kamar Sardauna baya nan a tare da ni, kamar ya yi nesa da ni, na ɗauki kusan minti talatin a haka ina kuka mai ban tausayi, jikina duka ya jike da gumi, fuskata ta yi nasha nasha da hawaye. Sai can, na ɗaga kaina da ƙyar ina numfashi sama-sama. Na kalli kofar falon. Kamar ko da yaushe, sai na ganshi yana shigowa sanye da fararen kayansa, yana takowa har inda nake tsugune ina kuka, ya sakar mini sanyayyan murmushin sa, tare da miƙo min hannu bayan ya ƙara so inda nake. “Nana ta... yi haƙuri wasa nake miki ai kinsan ba zan iya tafiya na barki ba. Tashi maza ki share gurin nan karki ɓata min rai.” Ya faɗa cikin muryarsa a sanyaye, a take na ji dukkan ɗaukacin tsoro da firgicin dake jikina ya tafi gaba ɗaya tamkar an sanya min ruwan sanyi! Na saki wani sanyayyan murmushi, na goge hawayena da sauri sannan na ce. “Haba mijina... ashe kana nan baka tafi ba? Ka ga iskar nan ko? Har ta kusa firgita ni ta sa na kusa fasa kwanon ƙarfen nan, na amaryark. Bari na kwashe dattin na shi na shiga kicin yanzu...” Na miƙe da sauri ina murmushi, na ɗauki tsohon kwanon ƙarfen na ƙara matse shi a ƙirjina tamkar kaya mai daraja, na nufi kicin ina rera waƙa ta soyayya, na manta gaba ɗaya da cewa ɗazu na yi kuka. Ina shiga kicin ɗin na ajiye kwanon, na fara kici kicin sama masa abinci, sai dai ban kai ga sama masa na ya shigo. “Nana kin ɓata min rai, a gaskiyya bazan ɓoye miki ba, shine dalilin da ya sa na ɓoya baki ganni ba.” Ƙwalla ce ta ziraro a idona, na kalleshi sannan na ce. “Ka yi haƙuri mijina.” “Nana sai na hukuntaki, amma bansan wane hukunci zan miki ba.” “Ka yi mini ko wanne hukunci, indai zaka daina fushi da ni.” “Ki zaɓi hukunci da kanki Nana.” Tsugunnawa na yi a ƙasa na ce. “Zanyi kamun kunne, ko tsallen kwaɗo.” “To ki yi duka.” Ba musu na tsugunna ƙasa na kama kunnena, sai da na yi kusan minti biyar sannan na juye na koma tsallen kwaɗo, na kai na kawo, na kai na kawo sai dai na yi sama da sau ashirin, sannan na nemi Sardauna ko ƙasa ko sama na rasa, ta dole na koma kan kujera na kwanta,ina fama haki. ********* Ƙarfe 03:30 na dare wani azababben ciwon kai ya matsamin, da ƙyar nake iya fitar da numfashi kaina yana wani irin juyewa, zufa tana ta zubomin tamkar wacca aka ajiye a gaban tandar gasa gurasa, a hankali na miƙe ina faɗin. “Sardauna na… ta shi kaina yana ciwo zan mutu.” Sai dai na ji shiru, kamar ba tare da Sardauna nake kwance ba. “Kaina dan Allah ka tashi.” Na sake faɗa ina zubar da hawaye, amma Sardauna bai iya cewa komai ba. A take kaina ya bada wani ƙara. ‘Ƙau!’ Na ga ɗakin yana juya min kamar hajijiya. A hankali na tashi tsaye amma ɗakin yana wani ƙasa yana juyawa. “Wayyo kaina, Sardauna ka tashi gidan nan faɗuwa, kar ya faɗo ma dan Allah.” Ina ƙarasa miƙewa na ji an janyo ni ƙasa an buga ni da tiles. “Wayyo! Wayyo! Zan mutu.” Ji na yi anja ƙafata ta baya, sai kuma dariya ta fara fitowa ta ko ina, muryar Sardauna ta kare ɗe ko ina. “Wayyo Sardauna kabar ni dan Allah, ka ƙyale ni dan Allah zan mutu.” “Ba zan barki ba Nana, wasan soyayya za mu yi.” “Ka daina jana to dan Allah.” Na faɗa muryata cike da ƙara, amma kamar umarnin na ƙara ba shi akan ya jan nawa. Daƙyar na samu ya daina jana, na daddafa na miƙe ina miƙewa na ji an bugamin ƙarfe akai. Da sauri na zabura na miƙe daga baccin da nake, zufa ta cikani kamar wacca ta yi tsaren gudu, haka nake sauke ajiyar zuciya akai akai. Gefe na duba naga babu Sardauna, na fara kiran sunansa. “Sardauna! Sardauna!” Amma na ji shiru, sai da na kusa awa ɗaya a zauna sannan na sake kwanciya, ina kwantawa na sake zabura sabida ina rufe idona na ga ƙarfe yana tunkaro ni. Zama na yi na haɗe jikina waje guda ina kuka ƙasa ƙasa ina kiran sunan Sardauna, amma shiru babu amsa. Ni da na farko ƙarfe biyu amma har aka fara kiran asubahi ina zaune. Sai da na yi sallah sannan na dawo na sake kwanciya, zuciyata cike da tsoro da firgici. ********** Ƙarfw takwas da rabi daidai na farka, sabida ƙwaƙwalwata ta riga da ta saba da wannan lokacin na haɗawa Sardauna abun breakfast kafin ya fita, haka na miƙi na nufi toilet na wanke fuska na fito na yi kitchen. Ina tsaka da aiki na ji yana kiran sunana. “Nana! Nana.” Na waiga sannan na ce. “Na’am.” “Nana faten wake zaki min fa.” Duba girkin da nake yi nai, wanda ya kusa kammala, amma haka na sauke shi na maida zuwa faten waken, ko da nagama na kawo masa kan dinning sai yaƙi fitowa ya ci, ya kwanta akan gado yaƙi juyowa ma ya kalleni. “Sardauna na fa gama abincin.” Na faɗa ina kai hannu na taɓa shi, ya girgiza kai alamar a’ah. “Na daɗe ne?” Ya gyaɗa kai, na sanyayar da muryata sannan na ce. “Ka yi haƙuri ka ji.” “A’a.” Ya faɗa ba tare da ya waigo ba, kamar zan yi kuka na ce. “Ba zan sake ba Sardauna.” Ya ƙara girgiza kai, sannan ya ce. “Ki je bacci zanyi, anjima zan ci.” Miƙewa na yi na fito falo daidai lokacin kuma na ji ana buga ƙofar part falon nawa. “Waye?” “Nana Yaya Radiya ce ki buɗe.” Wani irim tsoro da fargaba ne suka kamani, ga Sardauna a gida baya son ya ga kowa ya zo wajena, gashi kuma Yaya Radiya ta zo kuma ya ce baya son hayaniya. Ƙara buga ƙofar akayi sannam ta ce. “Wai bazaki buɗe ba ne?” “Zan buɗe, ina zuwa abu nake ajiyewa.” Na faɗa tare da nufar ƙofar, daidai lokacin Sardauna ya kira sunana. “Nana.” Na waigo na kalleshi, sannan na ce. “Na’am.” “Zo.” Ya faɗa yana yi min alama da hannu, fasa ƙarasawa na buɗe ƙofar na yi, na juya wajensa. “Kar ku yi hayaniya bacci zanyi.” “Tom.” Na faɗa shi kuma ya koma ciki, na nufi ƙofar na buɗe. Kallona ta yi sama da ƙasa sannan ta ce. “Da uban me ya hanaki buɗewa?” Legendspen 08129553971. SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na takwas. Sosa ƙeya ta na yi, sannan na ce. “Bokomai Yaya, ina kwashe abu ne fa a ƙasa ke da wa?” “Ni kaɗai.” Ta faɗa tan zama. “Sannu da zuwa Yaya.” “Yawwa sannu, ya gidan?” “Lafiya ƙalau Yaya.” Na faɗa ina zama kusa da ita. “Mijinki yana nan? Tare muke da Ra’is kuma ya ce bazai shigo ba sai mijinki baya nan.” “Yana ciki amma bacci yake yi, ya shigo mana.” “Bari na gaya masa.” Ta faɗa tana miƙewa, bayan ta fita nima na koma na ƙara jan ƙofar ɗakin da Sardauna ya shiga sabida kar su yi surutu da ƙarfi ya tashe shi. Ban daɗe da zama ba suka shigo ita da Ra’is, fuskarsa a haɗe kamar zai daki wani. “Ra’is kai kuma lafiya?” Zama ya yi akan kujera, sannan ya ce. “Ai na ɗauka zan tarar da shi mijin naki anan ne.” Murmushi na yi sannan na ce. “Ka dai yi magana a hankali, bacci yake kuma bana so ya tashi yanzu.” “Kya ji dashi, muma ba zama ya kawo mu ba.” Yaya Radiya ta faɗa, ni kuma na miƙe ina cewa. “Bara na kawo muku abinci.” “Da kin barshi dai.” Sai da na shiga na ɗauko musu kayan snacks da nake da shi na kawo musu, sannan na zauna. Sai da Yaya Radiya ta kalleni sosai sannan ta ce. “Ni zuwa fa na yi nai miki faɗa, amma kuma Nana yanayin ki ya nuna damuwa sosai da sosai.” Kallon jikina na yi sannan na ce. “Ba wata damuwa wallahi Yaya, me kike gani.” “Kinyi zuru-zuru, idonunki sunyi ja, ƙasan su kuma ya yi baƙi! Nana kamar wacca ke kuka ko yaushe.” Yaya Radiya ta faɗa, na buɗe baki zanyi magana Ra’is ya tare ni da cewa. “Ta yi wani kala ma, kamar a tsorace take.” Sai da na kalleshi na yi murmushi sannan na ce. “Ko ɗaya fa, ina zaune zaman lafiya.” “Ina amaryarki?” Yaya Radiya ta faɗa, shiru na yi sai can na ce. “Tana nan, ni dake ba shiga al’amuranta nake ba, na kwana biyu banganta ba ma.” Matsowa kusa dani ta yi, tare da kama hannuna. “Nana, idan kina da wata damuwa ko matsala dan Allah ki faɗa mana, Nana mune ‘yan uwanki, Nana mune dolenki, Nana duk wani daɗi da ɗa namiji zai baki wallahi a baki ne Nana, a iya fatar baki ne Nana, ba zai kai ‘yan uwa a wajenki ba, Nana munyi kuskure a baya, munyi kuskure mai girma da mu ka yi shawarar fita daga dukkan al’amarinki, muka ƙyale ki, muka sallamawa miji ke, tabbas a yanzu mun gane babban kuskuren da muka aikata.” Daidai lokacin wayar Yaya Radiya ta fara ringing, ɗaukota ta yi daga jaka tana duba, sannan ta ɗaga tare fa faɗin. “Rumaisa.” Kasancewar wayar na Hands-free yasa ake jin muryar Yaya Rumaisan. “Yaya Radiya kun ƙarasa? Sai yanzu na fito daga theater.” “Eyh Rumaisa! Ga mu a gidan.” “Yawwa tho Yaya, bata wayar.” Miƙamin wayar ta yi nasa hannu na amsa, ina amsar wayar na ji ashe ɗazu Yaya Radiya rarrashi na take, yanzu ne aka zo kan gaɓar maganar. “Rawasiyya.” Ta faɗa a fusace, ita daman kullum zuciyarta a kusa take. “Na’am!” Na faɗa muryata na rawa. “Ke dan uwarki ki buɗe baki ki yi min magana, kafin kisa na ƙaraso gidan na yi miki ɗan banzan duka.” “Na’am!” Na sake faɗa. “Nana! Nana! Sau nawa na kira sunanki?” “Biyu.” Na faɗa kamar zan fashe da kuka. “To wallahi karki bari na kira na ukun, da bazan kirashi da ko ɗigon alheri ba, idan ada munyi sakaci mun barki da wancan mahaukacin mijin naki, to yanzu mun farga, ba zamu barki da shi ba zamu dage ta ƙarfi ta tsiya akanki, idan ba ya ƙaunar zaman lafiya, to nina fishi, idan tashin hankali yake so ni nafi shi.” Ni gaba ɗaya ma bangane akan me take magana ba, kawai masifa, ƙara da hayaniya nake ji. “Rumaisa, ai bamu kai ga faɗa mata sharaɗan da muka zo da shi ba.” Yaya Radiya ta faɗa bayan ta ƙarɓi wayar. “To kuma dai kuka sani, ni dai a yanda nake jin zuciyata hakan nan ko Sardaunan tsaf zan iya marin mitsiyaci.” “Ki yi haƙuri ki dinga kai zuciya nesa.” “Ai da haƙurin ake cutar mutane, Yaya idan ba zaki iya faɗa mata ba ni fa yanzu zan iya zuwa.” “Kina da matsala Rumaisa, duk ki rikita komai.” Katse wayarta ta yi ba tare da ta bawa Yaya Radiya amsa ba. Kallona Yaya Radiya ta sake yi sannan ta ce. “Nana! A baya kamar yadda na faɗa miki munyi sakaci akan ki, mun barwa namiji ragamar komai sabida idan ya yi mana rashin arziƙi muna haƙura, sannan kema da anyi abu zaki ruɗe ki fara kuka, to Nana a yanzu ya ƙare munje matakin da ko sakin ki zai yi to sai dai ya sake ki Nana.” “Saki Yaya?” Na faɗa idona yana tara ƙwalla, Ra’is ya matso kusa dani sannan ya ce. “A’a fa, bawai cewa akayi ya sake ki ba, tana nufin idan ya nuna rashin arziƙin da yasa ba, ke kuma ki dinga cewa ke Sardauna kaza ke Sardauna kaza, to mu dai duk hukunci da muka yanke shi zamu aiwatar, ya rage nake ki yi convencing nasa ya yarda ko kar ya yarda, Nana ba mu ce ki yi wa mijinki rashin mutunci ba, ko ki ƙi yi masa biyayya, a’a muna so dai mu faɗa miki Miji biyayya ake masa, saɓanin ke da kikewa miji bauta Nana.” Yaya Radiya ta ƙara da cewa. “Nana ni ba ruwana ma da kome za ki yi masa, amma akwai wasu haƙoƙƙi naki dake kansa, ki sani ba wai iya shi ka ɗai yake haƙƙi akanki ba, dan haka dole shima ya fitar miki da haƙƙinki Nana, dan abun na shi ba hankali ba nutsuwa a ciki.” Na yi shiru ina kallonsu, ni babu wani haƙƙi da nake nema a wajen Sardauna, bayan ci da sha da suttura, kuma yana yi min dan haka ni ba abinda nake buƙata daban. “Nana ko ki so, ko karki so mu dai sai inda ƙarfinmu ya tsaya, ko anfi mu kuɗi ba afi mu zuciya ba.” Wani banzan kallo na yi wa Ra’is, gaba ɗaya babu abinda ya kawo su gidannan banda su zo su haɗa min fitina su tafi su barni, na ce musu ina buƙatar wani abu ne? Ko na ce musu baya ye min abinda ya kamata? Kawai neman haddasa min fitina a gidan aurena. “Nana ina so ki buɗe kunne ki saurari duk abinda zan faɗa miki.” “Tom Yaya.” “Nana, dole ki ci gaba da karatu wallahil azim! Kinji ma na rantse miki ko da ci gaba da karatun zai zama sanadiyar mutuwar auren naki baki ɗaya Nana.” A tsorace na ɗago kai na kalleta, ƙwalla ta fara zirara a idona. “Yaya bangane ba?” “Ban buƙaci ki gane ba Nana, amma dai ko ta yane dole ki faɗa masa karatunki burin mahaifinmu ne, dan haka dole sai kin cika shi Nana, nauyi ne a kanki. Idan shi bai san darajar iyaye ba, to mu mun sani Nana.” “Yaya ai ya ce zamu tafi Turai, kuma zanyi karatun acan wallahi.” Ra’is ne ya ce. “Turan bogi? Ko Turan gangan? Nana Sardauna yana amfani da wautar ki ne kawai yana kiɗima ki.” “Ba haka ba ne Ra’is, Sardauna baya ƙarya bai taɓa yi min ƙarya ba.” Na tare shi, muryata na rawa har na fara zubar da hawaye, Yaya Radiya ta ce. “Idan ya yi miki ƙaryar fitowa zaiyi ya ce Nana na yi miki ƙarya? Nana wai akanki aka fara sone? Ko akanki aka fara aure? Duk kinbi kin kiɗime akan wani mutum ɗaya.” “Ni dai Yaya dan Allah abar maganar karatun nan, tun da ya ce zanyi a gaba zanyi.” “Idan kuma lokaci ya ƙure miki fa? Nana kinsan ‘yan ajinku yanzu sune ɗaliban ƙarshen shekara, sune zasu gama digira a wannan shekarar da muke ciki, wannan wane irin zalunci ne Sardauna ya yi miki, karatun da kika ci shekarar farko ya datse miki, amma ke sabida kinfi kowa wauta kike ganin zai barki ki yi a gaba?” A fusace na ce da Ra’is. “Kai Ra’is ka kama bakinki, mijin nawa kake faɗawa waɗan nan maganganun.” “Na faɗa ki dake ni.” Shima ya faɗa a fusace. “Ya isa haka!” Yaya Radiya ta daka tsawa, sannan ta ce. “Ra’is ka yi min shiru, Ke kuma Nana maganar karatu an gama ta nan da sati ɗaya zan sake zuwa kuma duk hukuncin da yayanke dole ki sanar da ni, idan ya ce Eyh to shikenn, idan ya ce A’a to nima zaki ga A’a. Wallahi Nana sai na tafi dake gida, kin gama auren Sardauna har abada.” Da sauri na girgiza kai, ina kuka na fara cewa. “A’a Yaya, ni dai a’a bana so, bana son karatun gaskiyya, mijina nake so ni dai.” “Ke kuma kika sani Nana, sannan magana ta biyu.” ‘Ta biyu kuma?’ Na faɗa a zuciyata, a take ƙwaƙwalwata ta nuna min cewa zuwa suka yi kawai su rabani da Sardauna. “Idan shi ba ɗauki iyayensa da daraja ba, ba ya zuwa wajensu ko kuma su iyayensa basu ɗauke shi da daraja ba, ba sa nemansa to mu mun ɗauke ki da daraja, kema kuma dole ki ɗauke mu da daraja Nana. Bazai yu ace ki dinga tafiya shariban magariban ba, ba zuwa gida ba waya da gida, Nana ya kau, dole ya barki ki dinga zuwa gida, dole ya barki ki yi mu’amala da iyaye da ‘yan uwa.” “Yaya wai duk wannan nemene ne?” “Na ubanki ne.” Na ji muryar Yaya Rumaisa, ‘shikenan yanzu zata har gitsa gidan, sardauna dake bacci ya ce baya son hayaniya ma sai ta tashe shi.’ “Yanzu Yaya zama ku ka yi a gabanta tana muku wannan shirmen, baza ku tsitsinka mata mari ba?” “Yi haƙuri Rumaisa ƙaraso.” Yaya Radiya ta faɗa. “Ni bazan ƙara so ba, ku faɗa mata abinda zaku faɗa mata mu tafi, idan kuma shi mijin na ta zamu jira ya dawo sai mu jira.” “Ai ta ce yana ciki.” Ra’is ya faɗa. “Anya kuwa? Yanzu fa na tambayi mai gadi ya ce bayanan.” “To mu dai ta ce mana yana ciki.” “Bata so ku zauna ne, shi ya sa zata ce yana ciki sabida ku tafi, to wallahi Nana ko a gabansa ne sai mun faɗi abinda muke son faɗa, da wannan zaman zalunci ya ƙare Nana, Sardauna mugun namiji ne, azzalumi ne wallahi.” “Ba haka ba…” “Rufe min baki, kafin na ƙaraso na yi ƙasa ƙasa dake anan wajen.” Yaya Rumaisa ta tare ni a tsawace. “Yanzu dai yana nan ko baya nan?” Yaya Radiya ta tambaya, Ra’is ya bata amsa da cewa. “Baya ciki mana, da yana ciki da tuni bai zo ya ce zai yi wa mutane rashin arziƙi ba.”’ “Shine dai.” Yaya Radiya ta faɗa. “Uhm, ni ina mamaki yanda aka yi Sardauna ya fito daga babban gida irin Ta Ambo family amma yake abu na ƙananan mutane, ji ko haɗi basu da shi da Turaki.” Yaya Rumaisa ta faɗa, sannan ta ƙara cewa. “Nana duk abinda muka faɗa idan kinji kanki, idan ba kiji ba shima kanki, a yanzu zamu baki time ki sanar dashi komai, shima idan ya amince kanshi, idan bai amince ba kanshi, Nana ba akanki aka fara zawarci ba, sannan ba akanki za a ƙare ba, dan haka ke idan kina kunya ko tsoro mu ba ma yi.” Tana faɗin haka ta sai kai ta fice, Yaya Radiya da Ra’is ma suka miƙe. “Gashinan dai mun faɗa miki duk wani abu da zamu faɗa miki, sauran ya rage naki Nana, idan kin zaɓi auren naku ya ƙare sabida tsoro shikenan, idan zaki ƙwaci haƙƙinki ku daidaita kuma shikenan.” Tana faɗin haka suka fice ita da Ra’is, na bi bayansu sai dai ban ƙarasa fita ba na ji muryar Turaki. “Au wai dukanku ne kuka zo kenan, ina Hajiyar tamu?” Yaya Radiya da ta fita yanzu ne ta ce da shi. “A’a ba ita mu kaɗai ne.” “Kwana biyun ban samu shigowa ba, ɗazu nan na dawo.” “Aikuwa tana ta cigiyarka.” Yaya Radiya ta sake faɗa, har da zan juya sai na ji Yaya Rumaisa ta ce. “Ɗan uwanka ba shi da kirki.” Da sauri na matso jikin ta ga na ji me zai ce, bayan na ɗage labule ina kallonsu tar. Murmushi ya yi sannan ya ce. “Ya zaayi sai haƙuri, ya dawo ne?” “To ita dai ta ce yana ciki, amma Rumaisa ta ce me gadi ya ce mata bayanan.” Yaya Radiya ta faɗa, gani na yi ya wani tsuke fuska, sannan ya ce. “Ita Nana cewa ta yi Sardauna yana gidan?” “Eyh haka ta ce, wai bacci yake ma kar mu yi hayaniya.” Wani kallo na ga ya yi musu, irin na tana ɓoye muku gaskiyya ɗin nan,sannan ya ce. “Gaskiyya fa Sardauna baya nan.” “Uhm daman Yaya na faɗa miki bata so ku zauna ne sabida kar ya dawo ya same ku, tunda tsoronsa take.” Yaya Rumaisa ta faɗa tana taɓe baki. “Ba fa haka bane, Sardauna ya kusa sati uku ma baya ƙasar nan shi da Amaryarsa Bilkisu.” Legendspen 08129553971. SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na tara. “Baya ƙasar kuma?” Yaya Radiya ta tambaya, ya gyaɗa musu kai sannan ya ce. “Eyh tabbas, Sardauna da Bilkisu sun je indiya horney moon, sabida sati uku da suka wuce aka kirani daga airport ɗin Delhi wai na manta jaka a airport, na ce gaskiyya ba ni bane, sabida sun ga sunan Ta’Ambo, kuma duk family ɗinmu nafi kowa shiga indiya shi ya sa suka yi tunanin tawa ce, sai da na yi tambaya anan aka ce Sardauna da matarsa ne.” Wani kallo na watsawa Turaki ta tagar da nake, daman Sardauna ya sha faɗamin cewa Turaki maƙaryaci ne, ‘wai ni zai cewa Sardauna baya ƙasar ma baki ɗaya, ni da na kwanatar da shi a ɗaki kafin zuwan su Yaya Radiya, har zuwansu ya yi min magana ya ce da ni, kar su yi hayaniya shine zai ce baya ƙasar?’ Lallai Turaki maƙaryaci kake.’ A take na ji wata tsanar Turaki da ɗarso a zuciyata, Sardauna a ko yaushe yana faɗamin gaskiyya, daman ya ce maƙaryaci ne. “To ita a yanzu haka ya barta a gidan ita kaɗai kenan?” Na jiyo muryar Yaya Radiya na tambaya, Yaya Rumaisa ta bata amsa. “Gashi kuwa kin gani, shine zata ɓoye mana.” “To Yaya mu tafi da ita kawai mana.” Ra’is ya faɗa, gabana ya wani buga ƙarfi. “A’a Ra’is abun duk bai kai haka ba, karku damu zan shiga wajen nata anjima.” “Toh shikenan mun gode.” Yaya Rumaisa ta faɗa, ni kuma na koma ɗakin da na bar Sardauna, ina shiga na ganshi zaune kan gado, ya haɗe fuskarsa kamar bai taɓa dariya ba. Nasan ya ji duk abinda su Yaya Radiya suka faɗa gaba ɗaya. Ƙarasawa na yi na zauna a ƙasa, shi kuma yana kan gadon. “Sardauna ka yi haƙuri, sai da na faɗa musu kana barci su yi magana a hankali amma su ka ƙi.” Miƙewa ya yi ya barni a wajen ba tare da ya ce dani ƙala ba, nima na miƙe ina faɗin. “Ka yi haƙuri Sardauna dan Allah.” Banza ya yi da ni ya ci gaba da tafiya, na tashi na bi bayansa ina faɗin. “Sardauna ka yi hakuri, ba nice na ce su zo ba, kuma duk abinda suka faɗa babu wanda zan ɗauka a ciki, ni bazanyi karatun ba tun da baka so, ba zanyi komai ba sai wanda kake so.” Zama ya yi a kan kujera yan juya min baya, na ƙaraso ina ba shi hakuri, ya ɗaga min hannu tare da cewa. “Karki ƙaraso nan.” “Ka yi haƙuri dan Allah.” Shiru ya yi baice komai ba, nima na ja na tsaya, sai kawai na ji shasheƙar kukansa. Hankalina ya yi matuƙar tashi, na ƙarasa da sauri tare da faɗin. “Sardauna! Ka yi haƙuri dan Allah, ka yi haƙuri.” Idanunsa sun cika da hawaye, cikin muryar kuka ya fara magana. “Nana! ‘Yan uwanki sun ci mutuncina, su ɗin mutanen banza ne.” “A’a ka yi haƙuri Sardauna dan Allah.” “Nana so suke su raba mu.” “A’a bazasu iya ba wallahi.” “Nana wai zasu tafi dake.” Ni gaba ɗaya kukan da yake yi ya ɗaga min hankali sosai da sosai, na rasa me yake min daɗi! Kawai nima na fara kukan ina girgiza kai ina faɗin. “Sardauna ka yi haƙuri, ba zasu raba mu ba.” Kamar daga sama na ji muryar Turaki yana faɗin. “Nana! Nana! Ke da wa haka?” Juyowa na yi na kalleshi, sannan na ce. “Sardauna ne yake kuka wai akan abinda su Yaya Rumaisa suka faɗa.” “Wane Sardaunan? Yana ina?” “Gashinan.” Na faɗa ina nuna masa inda Sardauna yake, sai dai wayam bayanan, na ƙara fashewa da kuka me tsuma zuciya, sannan na ce. “Gashinan ka ja ya tafi, ya ce baya so kadinga zuwa nan.” Na faɗa ina miƙewa, na shiga neman Sardauna ina faɗin. “Sardauna kana ina? Ka daina ɓoyewa, ka yi haƙuri dan Allah.” Shi kuma Turaki yana bina duk inda na yi, haka na gama zagaye gidan gaba ɗaya babu Sardauna ko kaɗan, na dawo na zauna akan kafet na haɗa kai da gwiwa, na shiga rera kukana ina faɗin. “Sardauna ka yi haƙuri, ni bazanyi karatun ba, mijina ka daina ɓoyewa dan Allah ka fito “Nana!” Na ji Turaki ya kirani da wata sassanyar muryarsa, a hankali na ɗaga kai na kalleshi, da sauri na ɗauke kaina sabida wani kwarjini da naga ya yi min. “Ki yi haƙuri Nana, zai dawo kinji.” “Ɓoyewa ya yi sabida ya ga kazo, amma kafin kazo muna ta magana da shi lafiya lafiya.” “Eyh Nana! Bari yanzu zan tafi kinji, ki samu ki kwanta kafin ya dawo.” “A’a bana jin barci.” Na faɗa ina girgiza kaina, shima ya girgiza na shi kan. “A’a Nana kije ki gwada kwanciya kinji, zaki yi barcin.” Ba musu na miƙe na yi cikin ɗaki, ya biyo ni a baya har sai da na kwanata sannan ya fice. ********* 04:57 Ina nan zaune akan kujera, na cure waje ɗaya hankalina gaba ɗaya baya jikina, Allah Allah nake biyar ta gota na shiga kicin na yi wa Sardauna girki, nasan na ɓata masa rai dan tun da ya fice lokacin da Turaki ya shigo bai sake dawowa ba. A hankali nake fitar da ƙwalla daga idona ina gogeta, ina kuma addu’ar Allah ya dawo min da Sardauna cikin ƙoshin lafiya, idona na kai kan agogon bango na ga biyar ɗin har ta gota, na miƙe na shiga cikin. Ina kiciniyar kunna gawayi sabida nasan idan Sardauna ya ga a gawayi na yi girki zaifi jin daɗi ya yafe min, na ji an turu ƙofar fallon, na miƙe a raina ina addu’ar Allah Ya sa Sardauna ne. Sai dai ina buɗe ƙofa naga Turaki shi da wani mutumi, kallonsu na tsaya ina yi idanuna cike fal da tambaya. “Sannu! Ni abokin Sardauna ne na zo wajen shi ne yana nan?” Mutumin dake tare da Turaki ya faɗa, jin ya ce abokin Sardauna ne ya sa na washe masa baki da faɗin. “Ya fita amma yanzu zai dawo.” “Tom, zan iya shigowa?” “Shigo mana.” Na faɗa ina gyara masa hanya, suka shigo tare da Turaki suka zauna akan kujera. “Bara na kawo muku ruwa.” “Tom.” Ya faɗa, ni kuma na wuce, ruwa da lemon na kawo musu na ajiye sannan na koma cikin, ina cikin aikin na ji muryar Turaki yana faɗin. “Nana, me kike yi anan ne?” “Sardauna nake yi wa girki, nasan yanzu zai dawo.” Na bashi amsa ina daga can kicin ɗin. “Ina so na ɗan yi miki wasu tambayoyi kafin ya zo.” Mutumin dake tare da Turaki ya faɗa. “Tom, ina zuwa.” Na faɗa tare da rufe tukunyar dake kan kurfotin na fito, zama na yi a kujerar dake nesa da su sanna na ce. “Ga ni.” Zama ya gyara sannan ya ce. “Tun yaushe Sardauna ya fita?” “Bayan ‘yan gidanmu sun tafi.” “Daman wannan lokacin yake fita ko yaushe?” Na girgiza kai sannan na ce. “Kwana biyu ba shi da taƙamemen lokacin fita, bare kuma na dawowa, ya kan fita anytime ya dawo anytime.” “To baki ga wani canji game da shi ba?” Shiru na yi ina kallonsa, sai Turaki ya ce. “Babban Yayanmu ne, ya kan je gidan kowa lokaci zuwa lokaci ya yi wa iyalensa wannan tambayar, likita ne.” “Yana yawan fushi, kuma ya rage magana, wani lokacin ma bana ganin fitarsa ko shigowa.” “To amaryarsa fa?” “Na kwana biyu banganta ba?” “Kin taɓa tambayarsa tana ina?” Na girgiza kai, sannna na ce. “A’a bantaɓa ba.” “Okay, yanzu kowanne girki kika yi masa yana ci?” Na girgiza kai, a take na fara ƙwalla. “Faɗamin mana Nana, me ya sa ki kuka?” “Bakomai.” “Kin tabbata, ki bani amsar tambayar da na yi miki.” Sai da na goge ƙwallar idona, sannan na ce. “A’a ba kowanne ba, wani lokacin sai na nemeshi na rasa gaba ɗaya.” Shiru ɗakin ya yi na kusan mintina biyar, sai can ya miƙe tare da cewa. “Muje ko, Nana ki gaida shi idan ya zo.” “Tam zai ji.” Suka miƙe a tare suka fice, basu kai ga fita ba na ji Turaki yana cewa. “Likita mene matsalal?” “Muje wajen me gadin, shima mu tambayeshi.” Suna faɗin haka suka fice, gabana ya faɗi. Allah Yasa ba wani abu ya sami Sardauna ba. Haka na koma kicin na ƙarashe aikina, har dare Sardauna bai dawo ba, haka na gaji da jira na yi bacci. Ina kwance na takure a kan gado, na matse ƙafafuna guda biyu zuwa ƙirjina, na naɗe dukkan jikina wuri guda tamkar jaririn da ke ciki, kamar wata me jin sanyi, amma doguwar rigar atamfar dake jikina ta riga ta jiƙe sharkaf da gumi, duk da sanyi da iskar fankar da ke kaɗawa a saman silin. Barci bai yi wani nisa a cikin idanuwana ba, asali ma ba barci ba ne, wani irin lalluɓi ne na kasala da dabarar guje wa ɗaci da radaɗin rashin dawowar Sardauna da ke damun ƙwaƙwalwata. Kwatsam, sai duhun dakin ya canza launi. A cikin ɓarawon barcin, na sami kaina a tsaye a tsakiyar wani makeken fili maras iyaka. Gari ya yi baƙi ƙirin. Ina tafe ina waige-waige, sai na ji ƙafafuna sun yi min nauyi kamar an ƙulla musu datsen ƙarfe. Can na jiyo wani irin taku da sauri da sauri yana nufo inda nake. Ɗas! Ɗas! Ɗas! Na yi wani irin juyi da sauri domin na gudu, amma numfashina ya tsaya. Wata ƙatuwar inuwa mai tsayin gaske ta bayyana a gabana, fuskarta ba ta fito fili ba, amma duka idanuwanta guda biyu suna ɗauke da wani irin farin haske mai ban tsoro da juyar da hankali. Kafin na buɗe baki na yi kuka, sai na ji an sa hannu an taɓo wuyana. Hannun ya matse min wuyana da ƙarfin tsiya. Na buɗe baki ina neman iskar da zan shaƙa amma na rasa, a take kaina ya fara juyawa, ina ji dukkan jikina yana neman rabewa ya ɗauke daga duniyar. “Wannan shi ne ainihin zafin da na ji sanda yayyunki marasa amfani suka zo suna farfaɗamin magana marar daɗi, ke kuma kika tsaya kika sauraresu.” Sautin muryarsa ya dakar min kunne. “Muddin kika sake kuskure, irin wannan ko makamincinsa Nana, zan iya lahanta rayuwarki ba tare da kowa ya sani ba!” "Haba...!" Wata uwar zabura na yi, na daka tsalle na tashi zaune a kan katifar ina haki. Murya ta maƙale a maƙogwaro, numfashina yana fita da sauri sauri ga kuma kuka me ƙarfi da nake yi tamkar wadda ta sheƙo tseren gudu na tsawon sa'o'i. Na dafe ƙirjina da hannuna na dama, ina jin yadda zuciyata take bugawa da wani irin ƙarfi ɗas-ɗas-ɗas tamkar tana shirin fasowa daga ƙirjina ta fito fili. Gumin da ke fita a goshina yana tsiyaya har kan idanuna, ya gauraye da ƙwallan da suka cika mini idanu ba tare da ta sani ba. Na duba hagu, na duba dama cikin duhun ɗakin, ina ta rarraba idanu duka a firgice. Fuuuuu... Kwatsam, sai iskar mai ƙarfi ta bugo ta cikin taga, ta daki dogon labulen ɗakin. Labulen ya hure ya ɗaga sama, ya siffatu a cikin duhun daren tamkar tsayin Sardauna, yana sanye da fararen kaya ya naɗe hannuwansa biyu a ƙirji yana kallona. Idanuna suka ƙara firfitowa waje, na buɗe baki ina faman rawar jiki. A lokacin, tunani da firgitar da ke raina suka haɗe min da gani-ganin tsoro. Labulen ya daina zama labule a idanuna; Sardauna ne! Yana tsaye a kaina cikin wannan fararen kayan nasa, yana kallona da fuskarsa wadda ta yi baƙi, ya daure ta cike da fushi, yana zazzare min idanu kamar yadda yake yi min a kullum. Kowane sauti da iskar ke fitarwa yayin da take kaɗa labulen, ina jin sa tamkar sautin muryarsa Sardauna ce, yana faɗa cike da ɓacin rai, yana magana da tsawa mai firgitarwa “Muddin kika sake... zan lahanta ki... muddin kika sake...” "Haka ne... don Allah kayi haƙuri Sardauna.” Na faɗa muryarta na rawa, sabida na tsorota sosai da abinda Sardauna yake shirin yi, ganin yana matso ni ya sa na yi saurin janye ƙafafuna da sauri na koma can ƙuryar bango na laɓe, wata iska mai ƙara ta shiga kururuwa, na sanya hannuwana guda biyu na danne kunnuwana da ƙarfi don kada na sake jiyo sautin muryar tasa da ke fita ta cikin iskar gidan. Na rufe idanunta dunɗum ina kuka, amma duka a banza, sabida ban fasa jin abinda nake ji ba. Da ƙarfi aka bankaɗe ƙofar ɗakin. “Nana! Nana!” Na ɗaga kai na kalli Turaki, na juyar da kai naga Sardauna. “Ka fita Turaki, baya son ganinka dan Allah.” “Waye baya son ganina? Me ke damunki?” “Ka fita.” Legendspen 08129553971. SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na goma. Shigowa ya ci gaba da yi cikin ɗakin, ni kuma na miƙe da sauri na nufi inda Sardauna yake, sai dai ina miƙewa na ji komai ya ɗauke, ya tsaya cak babu hayaniya, babu ƙarar iska. Sai muryar Turaki yana faɗin. “Nana ina zaki? Nana tsaya.” Kallonsa na yi na fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya, na tsugunna akan katifar ina kuka. “Ki yi shiru, ki yi haƙuri Nana kinji.” Banza na yi da shi na ci gaba da kukan nawa. “Nana me ya sami ɗakin naki? Ina kayan furnitures ɗin, ina sip da bed?” Kukana na ci gaba ban ce mai komai ba, ya matso gab dani kamar zai taɓa ni, sannan ya ce. “Ki yi haƙuri, Sardauna yanzu nan ya fita ya ce dani na zo na kula dake kina kuka, Bilkisu ce ba lafiya.” Na ɗago kaina na kalleshi, sannan na ce. “Me yake damunta? Ai ta zubar masa da cikin nasa, kuma bai sani ba.” “Eyh! Yanzu yake samun labari.” Kuka na ƙara fashewa da shi, sannan na fara magana cikin kukan. “Sai da na yi mata faɗa, amma ta ce wai Sardauna ya sake ni, ya ce na zauma ne anan sabida ya killaceni, ba ya so kowanne namiji ya zo kusa dani, kuma ƙarya take ko?” Ya gyaɗa kai, yana goge ƙwalla a idonsa, sannan ya ce. “Eyh Nana! Eyh! Ƙarya take.” “Ni nasan Sardauna bazai sakeni ba, kuma da yake min waɗannan abubuwan ai nice na yi masa lefi da bana haihuwa ko? Kuma wai Dr Na’ima ta ce wai ina shan ƙwayoyin da zasu hanani ɗaukan ciki, itama nasan ƙarya take sabida wanda Sardauna yake ban na gyaran mahaifane.” Ji na yi ya yi shiru, na ɗago na kalleshi sai na ga yana kuka. “Kukan me kake yi? Wani abu ne ya faru da Sardauna?” Ya girgiza kai, cikin kuka ya fara magana. “Babu abinda ya faru da shi.” “Yanzu da yaushe zai dawo, yanzu fa naga yana ta yi min faɗa akan abinda su Yaya Radiya suka ce.” “Zan bashi haƙuri kinji, yanzu ki samu ki kwanta.” Na girgiza kai, sannan na ce. “Sai ya dawo.” “Ai shi ya ce wai lallai ki yi bacci.” “Bana son na kwanta ya sake zuwa.” “Bazai zo ba fa Nana, ya fita ki kwanta sannan kike yin addu’a dan Allah.” “Tom.” Na faɗa ina kwanta, ya matso sannan ya ce. “Ai ya ce na tambayeki ina gadon.” “Shi fa ya ce wai bazan zauna da kayan gado ba, sabida ni yanzu ba matarsa ba ce, kuma bazan haɗa kai da matarsa ba, shine ya siyar dasu.” “To yanzu ki rufe ido, duk abinda na faɗa miki ki maimaita.” “Tom.” Na faɗa tare da rufe idon, nan ya karanto min addu’o’in kwanciya bacci ina maimaitawa, har ya gama sannan na ji yana tofa min ajiki, sannan ya tashi ya fice, ina rufe idona na kwanta. Hasken ranar da ya biyo tagar ɗakin ne ya daki idona, ba shiri na buɗe idona da sauri na miƙe zaune. Ji na na yi wata falau kamar ba abinda ke damuna, sai dai ganin hasken ranar da na yi ya tunasar dani cewar safiya ta yi, gari ya yi haske kuma ban kaiwa Sardauna komai ba, ƙila ma ya fita. Ba shiri na miƙe na fito falon ina kiran sunan Sardauna, sai dai babu shi babu alamunsa. Daidai lokacin aka tura ƙofa aka shigo, Turaki ne ya shigo fuskarsa ɗauke da fara’a. “A’a Nana an tashi?” Na sunkuyar da kaina, sannan na gyaɗa shi sama alamar ‘Eyh.’ Ya ƙarasa shigowa sannan ya ce. “Nana ina kwana?” “Ina kwana?” Nima na faɗa, bai amsa ba ya ce. “Yau kin makara, Sardauna sai a wajena ya yi breakfast, na faɗa masa baki da lafiya ne shi ya sa bai tashe ki ba.” “Har ya fita?” Na tambaya, ya ce min. “Eyh mn, kema ga naki.” “A’a, yanzu zan dafa nima.” “Ai shi ya ce kici, kuma ya ce wai ba kya ja da dukkan abinda ya faɗa.” Karɓa na yi na nufi kan dinning ɗin, shi kuma ya juya, sai da ya kai ƙofa sannan ya ce. “Ya jikin naki?” “Da sauƙi, Alhamdulillah.” “Allah Yasa kaffara ne.” “Amin.” Sai da ya fita, sannan na ce. “Kowanne jiki yake nufi? Oho.” Buɗe plate ɗin na yi naga soyayyen dankali da plantain, sai kuma ƙwai. A kufin kuma daman ɗumin da na ji ya sa nasan shayi ne, sai dai ina buɗe na ga coffe ne. Kamar wasa na fara ci, aikuwa sai da na ci da yawa sosai, sannan na shiga ɗaki na sha maganina, na dawo kan kujera na zauna. Tabbas nasan jiya da daddare na yi wata firgita, kuma Turaki ya shigo, amma sai dai na manta duk wani abu da ya ce dani ko na ce dashi, na kusa minti talatin ina faman tunane-tunane, amma na kasa tuna komai. Wajen ƙarfe biyu, bayan na iddar da sallar azahar ina zaune akan daddumar da na yi sallah, na ji murya a falona, yinƙurin miƙewa na fara yi, sai dai kafin na miƙi an shigo ɗakin. Na yi matuƙar mamakin ganin Sister Seemah a gidana, matar da gaba ɗaya sau biyu na ganta a rayuwata, shima a zuwa family meetings ne nake ganinta. “Sannu da zuwa, ina yini?” Na faɗa a dabarbarce, wani kallo na ga tana bin ɗakin nawa da shi, bayan ta gama ta sauke idonta a kaina, sannan ta ce. “Lafiya ƙalau, ya gida?” “Lafiya, ya su Momy.” “Lafiya, ke haka ɗakin gadon naki yake? Ina kayan da iyayenku suka yi miki?” Cikin rawar baki na ce. “Mun barsu acan gidanmu na da.” “Ina kuma wanda shi Sardauna ya yi miki da zaki dawo nan?” “Suna wancan ɗakin, nan ba ɗakin bacci ba ne.” “Uhm, biyo ni falo.” Ta faɗa tana ficewa, ba musu na bi bayanta zuwa falo, ta zauna akan kujera ta yi ɗaiɗai. “Bari na kawo miki ruwa.” Na faɗa ina nufar hanyar ɗakin Sardauna. “A’a barshi, ina shi Sardaunan kira shi mu yi magana.” “Ya fita.” “Tun yaushe?” “Ɗazu da safe.” “Kin tabbata?” “Eyh.” “Bilkisu fa?” “Na kwana biyu ban ganta ba.” Miƙewa ta yi sannan ta ce. “Idan yazo ki ce mai nazo” Tana faɗin haka ta fice, na bita zan rakata sai dai na hango su tare da Turaki, suna magana. Kasancewar glass din taga ta a rufe yake ban iya jiyo me suke cewa ba, na dawo na zauna. Ba afi mintuna biyar ba sai ga Turaki nan ya shigo. “Nana, ashe sister Seemah ce tazo.” “Eyh.” Na bashi amsa a daƙile, zama ya yi aka kujera sannan ya zaro wayarsa. “Nana kinga Sardauna yana kira na.” Ya faɗa yana sa wayar a kunne. “Hello Sardauna.” Sai kuma ya yi shiru, wajen sakan talatin sannan ya ce. “Ta tashi tun ɗazu, na kai mata ma abincin ta ci, yanzu Sister Seemah ma ta tafi.” Ya sake yin shiru, sai ya ce. “Ina?” Ya ƙara yin shiru, sannan ya ce. “Na kai ta gidan big daddy, ta yi me to?” Gabana ne ya faɗi, me zaayi a gidan big daddyn? Ba haihuwa ba ce, na ga ya auro Bilkisu. “Kasan Nana fa ba lallai ta fita ba, amma zan jarraba.” Yana faɗin haka ya katse wayar, sannna ya kalleni. “Ya ce na kaiki gidan Big Daddy.” Na girgiza kai sanna na ce. “A’a bai ce na fita ba.” “To yanzu ya faɗa min.” “Ni bazan fita ba.” “Na faɗa mai?” Na gyaɗa kai, na ce. “Eyh.” “Shikenan karki je, kunfi kusa.” Yana faɗi haka ya miƙe ya fice, ni kuma na shiga tunani kala kala, daman yadda naga Sister Seemah nan, nasan ba mutunci a idonta, ga shi kuma ance wai naje gidan Big Daddy. ‘Ni dai na shiga uku ni Nana, duk Bilkisu ta ja min, ta cuceni da ta zubar da cikin nan.’ Na faɗa a raina. Gaba ɗaya gidan ya daina yi min daɗi, duniyar ta tsaya cak, wani irin zafi ya gaureyi gidan gaba ɗaya, na miƙe na fara zagaye gidan gaba ɗaya, na shiga can na fita can, na shiga can na fita can. Daidai matattakalal da zata sadani da falo ƙafa ta ta gurɗe, wani zafi ya ratsa ƙashina. Ina tsugunnawa a ƙasa na ji kaina ya fara juyawa, idanuna suka buɗe tar, suka fara haskamin lokacin da muka shigo falon nida Sardauna, har zuwa lokacin da Bilkisu ta ce kar na zauna mata akan kujera, komai ya dawo min fes, harda sakin da Sardauna ya yi min. “Tabbas Sardauna ya sake ni, innullahi wa’ina illahir raji’un.” Sai a yanzu nake jin zafi sakin da ya yi min, sai a yanzu nake ganin hulaƙancin da Sardauna ya yi min ta hanyar sanya Bilkisu ta rubuta min saki. “Amma zaman me nake yi a gidan?” Na tambayeki kaina, da sauri na miƙe na shiga duba ko ina, ina neman Sardauna, amma babu shi babu Bilki. Ɗakina na shiga na ga babu wata sip babu gado, zama na yi akan kujera na fara tunanin yaushe rabona da Sardauna ne? Kamar fa Sardauna da Bilkisu sun daɗe ba sa gidannan, ni kaɗai ce a cikin gidan, ni kaɗaice ke shirme na. “Ya salam.” Na faɗa, sabida wani sarawa da na ji kaina ya yi, a take jiri ya ɗebeni, na riƙe kan nawa da na ji yana wani irin sarawa. Sai da na ɗauki kusan mintina goma sha biyar ina cikin wannan halin, sai can na ji kan ya tsagaita da sarawar da yake, a lokacin kuma na ƙara tabbatar da cewa babu Sardauna babu Bilkisu a cikin gidan nan, Sardauna ya sake ni, yabar gidan shi da matarsa, ya barni a ƙasƙance, ya barni ina zaune kamar mabaraciya. Sai a yanzu na tuna kallon da me gadi yake yi min a ranar da na fita raka Sardauna mota, domin kuwa ni kaɗai ce na fita ina shirmena, Sardauna baya nan, haka ma girkin da nake yi nake ganin ba yaci, ni kaɗai na kewa kaina bana ganin Sardauna bana ganin kowa, na taɓo ne kawai nake ganin abubuwa a haka. Wani irin matsanancin kuka na saki wanda ya haifar min da wani irin ciwon kai, me jiri da hajijiya, ɗakin ya fara juyamin na fara ganin dishi dishi. “Wai ni Sardauna ya saka? Ni Sardauna ya hulaƙanta.” Abinda ke yi min yawo a cikin raina kenan, yanzu duk soyayya da biyayyar da na yi wa Sardauna ta tashi a banza kenan, babu wata riba a duniya? “Innullahi wa’inna illahir raji’un.” Abinda na faɗa kenan, sai kum na tuna da kalaman Bilkisu, na yanda Sardauna ya dinga amfani da wauta ta yana sani ina zuwa wajenta, ina kiranta a waya, tana hulaƙanta ni duk da sanin…… kai na ne ya ɗauke lokacin da kalmar ba zaki taɓa haihuwa ba ta shiga kunne na. Na miƙe a zabure, sai dai kuma jirin da nake ji ya kayar da ni. “Ya Hayyu Ya Qayyum.” Na faɗa tare da fashewa da wata iriyar razananniya ƙara, na fara kuka. Sai da na yi na gaji sannan na dawo falo, tunani nake ta ina zan fara komawa gida? Me zance da mutanen gidanmu? Mutumin da na zaɓa sama dasu, sama da kowa ya sake ni? Mutumin da nake yiwa soyayyar da tafi ta kowa ya lalatamin mahaifa? Innullahi wa’ina illahir raji’un. “Allah Kasheni na huta ni Nana.” Na faɗa ina fashewa da wani irin zazzafan kukan, gaba ɗaya bana jin komai sai zafi, duniyar ta hirgitsemin. Yau ni Nana da na ce Sardauna ne ni, Sardauna ne abun so da ƙauna, yau ni Sardauna zai hulaƙanta. Sallamar Turaki na ji yana shigowa, da sauri ya yo kaina yana faɗin. “Ke mene? Me ya faru kuma?” Miƙewa na yi da niyar tafiya na barshi, amma wata juwa ta ɗebeni na zube a ƙasa, cikin sa’a na ji na faɗa a ƙirjinsa. Ni dai nasan sai da ya haɗa da gudu kafin ya tareni, sabida yadda nake nesa da shi. “Ki yi haƙuri Nana, yanzu zan kai ki gida.” Sama sama na ji muryarshi ya faɗa, ni daman neman hanyar da za a kaini gidan ma nake, dan bani da idon da zan taka na nufi gida, na ce wai Sardauna ya sake ni, wai ƙuruciyata ya aura, wai so yake ya raba ni da ɗan uwansa, ya killaceni ga wasu mazan. Ɗauka ta ya yi a hannu kamar ya ɗauki jaririya, ya taka ya nufi hanyar fita. Fitar tamu ta yi daidai da parking ɗin motarsu Sardauna. Da wata iriyar hayagaga ya fito daga motar yana faɗin. “Gidan ubanwa zaka kai ta, shege kwarto.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na sha ɗaya. “Bansani ba!” Turaki ya faɗa, muryarsa cikin tsawar da ta daki kunnuwana, na yi matuƙar mamakin jin bana sha’awar ko ganin Sardauna ne. “Sauke ta!” Ya faɗa yana matsowa, jin takunsa ya sa na ƙara matse Turaki, na kwanta a jikinsa. “Ka sauke ta.” “Sardauna bazan sauke ta ba, Sardauna kai mugu ne, me son zuciya, azzalumi. Baka san kowa ba, baka son komai ba sai kan ka Sardauna, ka cuci yarinyar mutane ka hulaƙanta, ka lalata mata rayuwa da ƙana nan shekaru, ka tafi ka barta, baka nemi ya take ba, baka nemi lafiyarta ba, ka sake ta a ranar da ta gama fafutukar nema ma aure, to abubuwan da ka yi mata sun haɗu sun yi mata yawan da su ka haifar mata da desprission, and the worst one, ka cuci Nana, ka lalata rayuwarta, anma ka sani Allah baya bacci. Sardauma ina mamakin yadda aka yi ka kasance jinin Ta Ambo, babu mugu a cikinmu, babu azzalumi kuma babu macuci, ka jirayi hukunci ubangiji, amma ina tabbatar maka Nana, tabar gidanka har abada.” “Turaki, wallahil azim ka sauke yarinyar nan kafin na yi ƙasa ƙasa da kai anan.” Sardauna ya faɗa, muryarsa cike da ƙara. “Baby kabar mai tsiyarsa ya tafi da ita mana, kai ba ya rage ma aiki ba ne.” “Bilkisu wannan ba abinda ya shafeki ba ne, ki wuce ciki.” Ya faɗa, sannan ya fara takowa yana faɗin. “Turaki ka ajiye ta.” “Wallahi Sardauna ka ƙaraso nan sai na fasa ma kai da bindigir nan, idiot da bai san kansa ba.” Gaba na ne ya faɗi, a raina na ce. ‘Bindinga! Turaki mene haɗinsa da bindinga kuma?.’ Shiru na ji babu alamun motsin Sardauna, da alama ya tsorata. Turaki ya taka a hankali ya buɗe gidan baya na motarsa ya kwantar da ni, sannan ya zagaya ya shiga ta gaba ya tada motar, yana fara tafiya na ji zuciyata tana wani irin tsinkewa, zanyi nesa da Sardauna, zanyi nesa da farin cikin raina. Me gadi ya buɗe gate, Turaki ya cinna hancin motar ta sa waje muka fice, muna fita na ji wani abu ya ɗauke a kaina, kamar an cire min wani nannauyin dutsen da aka ɗoramin a kaina. “Shikenan, shikenan na bar gidan, na bar ganin Sardauna, zan koma gida, shin zan iya rayuwa babu Sardauna? Shin za iya zama a cikin gidan da ba zanji motsi ko muryar Sardauna ba? Ina son Sardauna, so marar iyaka, ina ƙaunar Sardauna, Allah Ka so shi, Ka kula dashi ako da yaushe, Ya Allah.” Na faɗa tare da runtse idona na rufe, a hankali yake tuƙinsa kamar ko yaushe, sai dai yau saɓanin waƙoƙin nanaye karatun qur’ani ya sanya, a hankali har muka ƙarasa gidanmu. Sai da ya buɗe ya fito, sannan ya zagayo ya ce. “Nana zaki iya fitowa ko na ɗauke ki.” Na gyaɗa masa kai alamar eyh zan iya, ya buɗe min na fito ina dafe da shi, a hankali muka taka har zuwa cikin tsakar gidan, ina shiga idona ya sauka akan hajiya tana daka a turmi, wani irin abu na ji ya tokaremin maƙoshi, yanzu uwata na bari na zaɓi miji, gashi kan aje ko ina na kwashe kasona, namiji ɗan kunama. “A’a Abubakar lafiya? Me ya sami Nanan?” “Hajiya ba komai, ciwon kaine ki yi haƙuri.” Yaya Radiya ta yaye labule, tana ganin mu ta fito zuwa inda muke ta riƙe ni, tana faɗin. “Innullahi, sannu Nana, Abubuakar me ya faru?” “Bakomai ku yi haƙuri ta shiga ta kwanta, tana buƙatar hutawa.” Kama hannuna Yaya Radiya ta yi ta shiga dani ɗaki ta kwantar, sannan ta fito. “Abubakar me ya same ta ne?” Hajiya ta ƙara tambayar Turaki. “Hajiya, nima ban gama sanin komai akai ba, amma nasan tabbas Sardauna ya saki Nana, kuma ba yau ba, ba jiya ba, ina kyautata zaton tun ranar da ya ƙara aure ne ma ya sake ta, sai dai bai bata damar barin gidan ba, shi kuma yasa ƙafa da matarshi suka bar ƙasar ma baki ɗaya, zuwan da su Ra’is su ka yi, sun tambayi Nana Sardauna yana nan ko baya nan, ta ce da su yana nan, ba wai ta faɗa ba ne sabida ba ta so su zauna ko zo gidan ba, a’a Nana ta kamu da wata cuta ce da ake kira da Psychotic Depression a hausance zamu iya kiranta da haukan baƙin Ciki, ta yanda aka yi nasani, a ranar da na tarar da su Ra’is a gidan, a lokacin sai na yi tunanin Nana tana ɓoye musu gaskiyyar Sardauna ya yi tafiya ne da Amaryarsa, sabida kar su ga baƙinsa, sai da ga baya na fahimce cewar itama Nana batasan ya yi tafiyar ba, a lokacin da na je ɓangarensu na tarar da Nana tana magana da iska, a matsayin Sardauna, na yi matuƙar tsorata da yanayin nata, na kuma yi tunanin tana sane take yi, sai daga baya na ga irin firgita da take yi, sai na yi tunanin ko ta shiga trauma ne. Hakan ya sa na kira wani likitan family ɗin mu ya zo, a ‘yan ƙananan tambayoyin da ya yi wa Nana ya gane tana fama da wannan cutar, Trauma-Induced Illusion, tana jin raɗaɗin ganin abun da babu shi. Sai na tambayeshi me yake kawo wannan cutar, sabida naga ba normal trauma ko despression dana sani bane, sai ya ce dani cutar tana samuwa ne a lokacin da ka yi wani babban rashi na abinda kake matuƙar ƙauna, mafi akasari mata su kanyi idan sun rasa mazajensu, wasu kuma idan sun rasa ‘ya’yan da suke ƙauna, zuciyarsu zata kasa haƙuri ta shiga tsananin damuwa da baƙin ciki wanda ake kira Severe Depression, wadda idan ta kai maƙura, ƙwaƙwalwa take zautuwa ta haifar da Illusions wato Rudaɗɗen gani da Hallucinations ma’ana ganin abubuwan da babu su. Mutumin da ke ɗauke da ita yana cire alaƙa da mutanen gaskiya, ya koma rayuwa a cikin duniyar ƙarya da ƙwaƙwalwarsa ta gina masa domin ya tsira da rayuwarsa. A daren ranar kuma Nana ta sake wata firgirta wanda anan ne samu wasu imformations daga wajenta, inda ta ce Sardauna ya kwashe kayan gadonta ya siyar, sabida baza su daidai ta da matarsa ba tunda ita ya sake ta, sannan Dr Na’ima ta ce ta sha abinda ya zubar mata da mahaifa. Duk ta faɗa min waɗannan bayanan ne ba tare da tasan ta faɗa ba, a lokacin na fahimci cewar zuciyarta ba zata iya ɗaukan rashin Sardauna ba ne, shine ƙwaƙwalwarta ta shigar da ita Psychotic Depression. “To amma abinda bangane ba, ita a yanzu tasan ya sake ta?” Na ji muryar Ra’is yana tambaya. “Ta sani, amma kuma ba ta yarda da hakan ba.” “To amma shi likitan me ya ce maganin cutar? Kuma zata warke ne ko ba zata warke ba?” Yaya Radiya ta tambaya. “Za ta warke sosai, akwai magunguna guda biyu da ya sa na siya waɗanda a yanzu suna cikin mota ta, kowanne da bayaninsa, dole ne a sanya Nana ta riƙa shan waɗan nan ƙwayoyin na tsawon watanni, a ciki akwai Antidepressants.” Yaya Radiya ta ce. “Nasan Antidepressants, Magungunan kashe baƙin ciki a cikin ƙwaƙwalwa, kuma su kanyi ƙoƙarin dawo da farin ciki a ƙwaƙwalwar mutum.” “Eyh tabbas shi, sai kuma, Antipsychotics Maganin da ke kashe wannan ruɗin gani da jiyowa (Illusions), su sa ta daina ganin inuwar Sardauna. Sannan dole sai anyi zaman rarrashi da tattaunawa, za a riƙa koya mata yadda za ta yarda cewa Sardauna ya tafi, kuma ba shi ne ƙarshen rayuwarta ba. Sannan dole kowa ya zama mai goyon baya da kuma nuna mata ƙauna, domin nuna mata tsantsar ƙauna, kulawa, da goyan baya, da kuma daina barinta ita kaɗai cikin duhu. Wannan kulawar ita ce za ta sa ƙwaƙwalwarta ta gane cewa ashe zata iya samun farin ciki ko da babu Sardauna a rayuwarta.” “Yanzu Sardauna ya saki Nana? Saki nawa?” Hajiya ta faɗa, kamar me kuka take, Turaki ya ce. “Babu wanda ya sani sai abinda ta faɗa, amma nasan a yanzu dai ta gama iddarta, aiki ne akan kowa da kowa na ganin ya so ta, ya jawo ta jikinsa, ta yadda zata samu nutsuwa sosai da sosai.” “Amma Allah Ya isa tsakaninmu da Sardauna, Allah Ya isa, Allah Ya yi mana sakayya.” Yaya Radiya ta faɗa tana kuka. “Idan har ya cutar da Nana, wallahil azim ko zanyi yawo ba kaya a garin nan sai na ƙwato mata haƙƙinta.” Muryar Yaya Ridwan ta daki kunnuwana. “A’a Ridwan, ku barshi da Allah, duniya ce.” Hajiya ta faɗa, a yanzu kam na tabbatar kuka take yi, domin yadda muryarta ke rawa. “Ki yi haƙuri Hajiya, amma tabbas idan har ya cutar da ita, suna da damar da za su yi shari’ah da shi, sai dai Ridwan kasa a ranka ba lallai ba ne ka sami adalcin da kake so, a yanzu ƙasar mu ta juye zuwa wani irin yanayi, adadin alfarmar da kake da ita, adadin adalcin da zaka samu, Sardauna yasan mutane fiye da zaton ka, ko ni da nake ma’aikacin tsaro, Sardauna ya fini shige da fice, ta fini ido a wajen manya.” “Nima abinda na gani kenan.” Hajiya ta faɗa. “Ki yi haƙuri Hajiya dan Allah, ki daina kuka.” Yaya Radiya ta faɗa, tana rarrashin hajiya. “Haba Radiya, yanzu yadda yarinyar nan take son yaron nan, son da bata iya ɓoyewa ko a gabanmu iyayenta, mahaifinku da kansa ya jaddadamin Nana tana son mijinta, amma ace sakkayyar da zai mata kenan, dole na yi kuka domin tausayin da nake yi wa Nana, bazai barni na yi shiru ba.” “Hajiya Nana fa ba kuka take so ba, sai kun ƙwarara zuciyarku, kun tausasheta, kun nuna mata taku soyayyar, har asamu ƙwaƙwalwarta ta dawo daidai.” Turaki ya faɗa, sai na ji muryar Yaya Ridwan. “Yanzu mahaifar da ya zubar mata da ita fa? Ya riga ya cuceta? Tun ganin farko da shi na ji bai yi min ba, na yi duk ƙoƙarina akan Nana, amma taƙi, abinda na guda kenan. Duk cikin ‘yan uwana duk wacca ta tashi aure sai na ji a jikina, na nusar da Alhaji lokacin aurensu Yaya Radiya ya gaza fahimta, na nusar da shi a lamarin Nana ya gaza fahimta, a yanzu haƙƙin Nana akaina na ƙwato mata ‘yancinta a wajen azzalumin Sardauna.” “Yaya Ridwan ka yi haƙuri dan Allah, komai zai zo da sauƙi.” Ra’is ya faɗa, shima na ji kamar yana kuka. “Innullahi wa’inna illahir raji’un, Allah Kasakamin, Allah ka bi min haƙƙin na, Allah ka cire min son Sardauna, Allah na gaji, na gaji da son Sardauna, Allah kai ka jarabceni, ka yaye min, Allah na tuba Ya ubangiji, idan wani laifi na yi ka jarabce ni da son Sardauna har haka, Allah ka yafe min, Allah ka yaye min, Allah na tuba Allah, Allah ba dan ni da halina ba.” Na fashe da wani irin kuka, ina jin zafi a zuciyata wadda a yanzu take laluben neman uzirin da zata bawa Sardauna, duk wannan abun da ake magana, duk wannan abu da aka yi banji ko kaso ɗaya na son da nakewa Sardauna ba ya ragu, na gaji nima nasan na gaji da son Sardauna. Bansan kukan da nake yi ya fito fili ba sai da na ji Yaya Radiya na magana. “Nana, ke yi haƙuri dan Allah, komai zai wuce.” “Yaya bazai wuce ba, Yaya Sardauna ya cutar da son da nake yi masa, Yaya ya zalunci ne, ina zan saka raina, Yaya.” Matsowa ta yi ta rungume ni, tana fitar da hawaye a hankali. “Ki yi shiru, ki yi haƙuri.. Nana ki sa a ranki kamar baki rasa komai ba Nana, Sardauna ki ɗauka wata guguwace da ta zo ta tsaya, kuma ta wuce. Nana baki rasa komai ba, kina da Allah, kina da uwa, kina da ‘yan uwa masu sonki Nana, wallahi addu’ar da Hajiya ke raba dare tana yi ce Allah Ya amsa, Nana baki sani ba a kwana biyun nan babu wanda yake cikakken bacci a gidan nan, hatta da Ridwan da Ra’is, duk farkawar da zamu yi Ridwan zamu gane, yana sallah ko ya idar, har muna tunanin ma baya bacci, Nana kisa a ranki rabuwar ki da Sardauna shine alherin da yafi zamanki da shi. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na sha biyu. A hankali na kalli Yaya Radiya, jin ta ce wai duk ‘yan gidanmu basa bacci a kaina, suna raba dare suna addu’a akaina, amma ni ina can ina faman yiwa Sardauna addu’ar Allah Ya yi masa arziƙi duniya da lahira? “Kaicona ni Nana, kaico da ni da na zaɓi namiji sama da uwa da uba, kaico da ni da na zaɓi miji na bar ‘yan uwa, Allah na tuba Allah, Allah ka yafe ni, Allah ka kawo min sauƙi, ka cire min Sardauna, Allah ka mantar da ni Sardauna.” Na faɗa ina kuka, Yaya Radiya ra rungume ni a jikinta, itama ta fashe da wani irin kuka, mai cin rai. Sai da muka yi muka gode Allah sannan ta ci gaba da rarrashi na, har dare. Da ƙyar na samu bacci ya ɗaukeni, bayan Yaya Radiya ta kunna min karatun qur’ani ina ji. Ina jin sanda suka yi wa da Yaya Rumaisa tana ta lailaye lailayen ashar, tana jawa Sardauna da iyayensa tsinuwa, shi kuwa Yaya Ridwan har Turaki ya tafi bai sa ran zai ƙyale Sardauna ba. Cikin dare na yi wata iriyar firgita da ta tsora ta Yaya Radiya da Hajiya, ina kiran sunan Sardauna ina ba shi haƙuri da ce masa zan dawo, bazan zauna ba. Ra’is ya sha kuka a lokacin haka Hajiya da Yaya Radiya, duk jikin su ya yi sanyi da al’amarin nawa. Washe gari, haka na tashi shiru shiru, bana ko son jin sautin muryar kowa, bana son ganin haske ko kaɗan, nafi son na zauna a ɗaki a saki labule,Hajiya ta ce na zauna a ɗakin, amna ba za a saki labulen ba. Ƙarfe bakwai da rabi Yaya Rumaisa ta shigo ita da mijinta. Ina ɗaki na fara jiyo hayaniyarta. “Yanzu ranar da muka je ma ya sake ta kenan?” “Ke ance miki fa har idda ta kammala.” Yaya Radiya ta faɗa. “A’a fa Yaya baku da tabbaci, yakamata kuji komai daga wajenta, domin kiyaye haƙƙin shari’ah da adalci.” Mijin Yaya Rumaisa ya faɗa, Yaya Radiya ta ce “Ba lallai, ba zaima lallai ba ta faɗa, kuma ba a son a takura mata.” A raina na ce. ‘Mene zai sa naƙi faɗan komai, a yanzu zuciyata kwata kwata ba ta son Sardauna, amma ƙwaƙwalwata ta gaza goge min tunaninsa, kullum ta tsakar kaina nake jin sautin muryarsa, ta tsakar kaina nake jin numfashinsa.” “To ke ki gwada zuwa, amma ki san Mood din da zaki yi mata magana da shi.” Naji mijin na ta ya faɗa, ba afi minti ɗaya ba ta shigo, kallo ɗaya na yi mata na sauke kaina ƙasa, ta ƙaraso ta zauna tare da kama hannuna. Ta buɗe baki za ta yi magana na ce. “Ada ban yardarwa zuciyata komai ba, ban yarda da cewar wai Sardauna zai saki ni ba, amma dagaske ya sake ni, tun ranar da ya ƙara aure, a daren ya bawa Bilkisu damar rubutamin saki ɗaya, bayan ta rubuta ta nuna min nagani sai kuma ta yayyaga takarda ta watsomin a jikina, sabida ba ya son kowa ya sani. Yaya kinsan me?” Na faɗa ina ƙara kama hannunta, ta girgiza kai sannan ta ce. “Sai kin faɗa Nana.” “Yaya ashe zancen ki gaskiyya ne, Sardauna da Bilkisu masoya ne, wai ya yi amfani da wauta ta ne dan nema masa aure, daman Yaya ni wawiya ce?” Na faɗa ina murmushi, sabida kwata kwata banji zafin kalmar ba, ta girgiza kai tana hawaye ta ce. “Nana ke ba wawiya ba ce, ke yarinya ce ƙarama da Allah Ya jarabta da muguwar soyayya ta mugun namiji.” Sai ta yi shiru ta ja numfashi, sannan ta ɗora. “Idan suna kallonki matsayin wawiya, Nana babu wawaye sai shi da ita, Nana sun manta cewa Allah baya bacci! Sun mata cewar akwai wata shari’ar bayan ta nan, Nana sun mata cewar zaman ba ɗaya ba ne, ki yi haƙuri Nana, ina mai tabbatar miki rayuwar zata gyaru fiye da baya, Nana wannan wata babbar dama ce da ubangiji ya baki, wadda za ki ɗaura rayuwarki a wane tsari na daban, wani tsari wanda zai kai ki ga ci gaba, Nana bijahi Annabi Muhammadu sai kin sami abinda yafi Sardauna.” Na yi shiru ina kallonta har ta gama, sannan na ce. “Yaya ya ce ba ni da wani amfani a duniya, Yaya wai ya lalatamin mahaifa bazan taɓa haihuwa ba, Yaya bazan ga ‘ya’yan cikina ba fa.” “Zaki gani Nana, ai baki da haƙƙin Sardauna ko guda ɗaya, Nana baki cuceshi ba, kuma kinsan Allah baya bacci, baya barin wani da wani ya ji daɗi.” “Yaya ai banda haƙƙinsa ko? Ban taɓa cutar da shi ba wallahi, Yaya ko da wasa ban taɓa yin wani abu da zai cutar da Sardauna ba, Yaya da zuciya ɗaya nake zaune da shi, ina son sa wallahi.” “Na sani Nana, zaki sami wani sa yafi shi, zaki sami wani da zaki zo fin son da kika yi wa Sardauna.” “Yaya nasan bazan samu ba, ni zuciyata ma ba zata ƙara son wani ba, Yaya akan Sardauna na fara soyayya, kuma akansa zan ƙare.” “Ba haka ba ne Nana, dan kin rasa wani mutumi guda ɗaya a rayuwarki ba hakan yana nufin kin rasa komai ba Nana, wallahi na yi miki alƙwari sabida ina da tabbacin a gaba zaki sami wanda yafi Sardauna komai, ko da Nana baki sami wanda yafi Sardauna kuɗi ba, zaki sami wanda ya shi ilimi da nagarta, wanda yafi shi halin ƙwarai. Nana ba fa wai samun miji mai kuɗi ba ne dacewa a duniya Nana, kinga mijina wani kuɗi ne da shi na azo a gani?” Na girgiza kai, sannan ta ce. “Nana me na rasa? Me ‘ya’yana suka rasa?” Na girgiza kai na ce. “Babu.” “To Nana, Allah ba sona yafi ba akan ki, Nana ba fin ki na yi wani abu ba, dan haka kisa a ranki yadda na samu kema zaki samu, dukkanmu zamu rayu cikin farin ciki, addu’ar iyayen mu za ta yi tasiri akan mu Nana, kin tuna har Allah ya ɗauki Alhaji da albarka a bakinsa. Nana ki yi haƙuri ki ɗauki dangana, Allah Yana ji kuma yana gani, kuma zai miki sakayya, zai baki abinda yafi wanda kika rasa.” “Hhm, Allah Yasa, amma Yaya bana maraba da kowa a rayuwata, Yaya bana son na ƙara son wani namiji ko guda ɗaya.” “Ki yi haƙuri kin ji Nana, Allah zai mantar dake Sardauna cikin sauƙi, zamu dage, zaki dage da addu’a, Allah baya bacci Nana. Za a je a kwashe duk wani abu naki a ƙanƙanin lokaci, tunda kinyo iddar ki kin gama Nana.” “Shikenan Yaya.” Na faɗa tare da komawa kan katifa na kwanta, ita kuma ta tashi ta fita, duk abinda muka tattatuna ta juye musu, kowa ya jajanta, Hajiya ta ce. “Lallai lallai aje akwashe kayan, kuma a tafi da ita Nanan duk abinda ke na ta a ɗauke, wallahi bana fatan ko a lahira na sake haɗa ido da wannan yaron ko wani mai kama da shi.” “Shikenan Hajiya, bari na kira Ridwan mu haɗu mu tafi gaba ɗaya.” Yaya Rumaisa ta faɗa, shi kuma mijinta ya ce. “To Hajiya Allah ubangiji ya tsare gaba, Allah Ya bata lafiya ni zan wuce ofis.” “To an gode, Allah Ya tsare.” “Amin amin.” Ya faɗa, ni kuma na sake runtse idona, a take hoton Sardauna ya bayyana, yana zaune shi da Bilkisu suna cin rayuwarsu suna farin ciki, buɗe ba ki na yi da zummar na ce. Allah Ya ƙara maka lafiya mijina, sai kuma na juyewa ta hanyar cewa. “Allah Ya saka min, Allah Ya bi min haƙƙina.” Na faɗa tare da fashewa da wani irin kuka, a hankali nake raira kukana sabida bana so wani cikin ‘yan uwana ya ji ina kuka, nasan basa son kukana, dan haka dole nima na dinga sirranta damuwata. Daga wannan kukan barci ya yi gaba da ni, bani na farka ba sai gab da kiran azahar na ƙarfe biyu, ina miƙewa na ji kaina yana sarawa, a hankali na tashi zaune, sama sama naki jin maganar mutanen gidan namu, amma ban mai da hankali kai ba na tashi na fito, dukkansu suna seat room har da Maman Amir maƙwafciyarmu sai kuma Mamansu Amina aminu da Fauziyya. A yanzu nasan gaba ɗaya Yelwawa ya ɗauka aure na ya mutu, wani abu na ji ya ratsamin tsakar kaina, wanda ya yi koƙarin haifar min da jirin da zai iya kadani a bakin ban ɗaki. “Nana me kike yi haka, tangal tangal ɗin fa?” Yaya Radiya ta faɗa, bango na dafa sannan na ce. “Alwala zanyi.” “To amma tangal tangal ɗin fa?” “Kaina ne na ji yana sarawa.” “Ki tsugunna anan, idan ya lafa sai ki ki yi abinda za ki yi anan ki ɗaura alwalan.” “Tom.” Kawai na ce na tsugunna, ita kuma ta shiga kicin. Na daɗe a tsugunne sannan na ɗaura alwalan na koma ɗaki, a zaune na samu na yi sallar, na daɗe a sujjada ina kawai Allah kukana, ina roƙonsa da ya mantar da ni Sardauna ya cire min shi a raina, Allah Ya bani lafiya, ya kuma bani dangana.” Ina idarwa na koma na takure a gefe, tunanin da ya fara zuwa raina shine, yanzu me mutane suke cewa akaina, wasu suna can sun zagi na, wasu suna cewa na yi auren kuɗi gashi nan abinda na gani, ba kowa ba ne zai san asalin gaskiyyar zaman da na yi da Sardauna ba, wani ma ko ya sani bazai yarda ba. ‘Kai! Innullahi wa’inna illahir raji’un.’ Na faɗa tare da fashewa da wani irin kuka, sai na ji bana sha’awar ƙara fita ko da tsakar gidane, bana son haɗa ido da kowanne mutum a duniya, nasan kowa zagi na yake, wasu suna can suna aibata ni, na ɗaukowa kaina abun magana, gaba ɗaya na ji na tsani kowa, na tsani komai. Wani irin zafi na fara ji, wanda ya haifar min sa gumi ta ko ina, ɗakin ya fara juyemin, da sauri na miƙe tsaye sabida bana son na ga irin abinda nake gani a gidan Sardauna, bana son wannan yanayin yana haifar min da damuwa, da ƙarfi na saki wani razanannen ihu ganin wata dunƙulalliyar iska ta nufo ni, sama sama na ji ana cewa. “Ke nutsu, mene?” Kuka na sake fashewa da shi, sai na ji an rungumo ni, sai a lokacin na ji ɗif komai ya tsaya. Yaya Radiya ta fara bubbuga min bayana tana faɗin. “Nutsu Nana, ki nutsu kinji, babu komai.” Buɗe idona na yi kasancewar ɗazu a rufe yake, na sauke shi akan Hajiya dake zubar da hawaye, sai kuma Mamansu Amina aminu, da sauri na ɗauke kai na juyar da shi gefe. “Zauna kinji.” Yaya Radiya ta faɗa, tana zaunar da ni kan gadon. Ni a jikina nake jin yadda idanuna suka yi ja, su ka yi zuru zuru. Na kauda kaina daga kallon kowa na kifa kai a katifa. “Me ya faru?” Muryar Yaya Ridwan ta karaɗe ɗakin. “Firgita ta yi.” Yaya Radiya ta bashi amsa. “Hajiya ki daina kuka dan girman Allah.” “Dole fa na yi kuka, ace idanuna suna kallon ‘yata a wannan yanayin kamar na hauka, kuma ka ce kar na yi kuka, dariya kake so na yi? Ridwan dariya zanyi? To na fara dariyar ka ji daɗi? Kasan radaɗin da uwa take ji a duk lokacin da ta ga ɗanta cikin yanayin jinya? Wallahi ina jin ina ma Allah Ya ɗauke wannan yanayin daga kan Nana ya dawo da shi kaina.” Ta ƙarashe maganar tana ci gaba da kuka, duk suka yi kanta suna bata baki. “Hajiya ki yi haƙuri dan Allah, a yanzu fa sai kun daure zuciyarku, kun ƙwararata akan yarinyar nan.” Mamman Amir ta faɗa ita ma muryarta kamar ta fashe da kuka, Mamansu Amina aminu ce ta ce. “Wannan yaro ubangiji ya haɗa shi da daidai shi, ubangiji ya yi miki sakayya Nana.” Da Amin na ji sun amsa gaba ɗayansu, ni abinda basu sani ba ko muryar ɗayansu bana son ji, bana son jin ko motsin wani, nafi son na ji ko ina ya yi shiru, babu motsi ko numfashi wani. Legendspen 08129553971. SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na sha uku. Sai da suka gama addu’oin su suka fita na samu damar sauke wani numfashi da ya tsayamin a maƙoshi, ina son na rufe idona ina tsoron ganin Sardauna. “Nana ki kwanta.” Na girgiza kai sannan na ce. “A’a Yaya, bazan kwanta ba.” “Nana baki yi addu’a ba, Nana ki dage da sauraron karatun Qur’ani yana matuƙar wanke zuciya ki kuma ci gaba da haƙuri da addu’a Nana, kinji.” “Tom Yaya.” Na faɗa, ita kuma ta miƙe ta ɗauko waya ta kunna min ƙir’ar Sudais, ta fita ta barni, a hankali na fara samun nutsuwa na ji ciwon kan na sauka, har kuma bacci ya ɗauke ni, wanda ban tashi ba sai gab da magariba, lokacin na ji muryar Turaki yana magana. “Ai ba a yanzu za a yi mata wata maganar makaranta ba, Hajiya nake ganin kamar a ƙyaleta zuwa ta samu nustuwa sosai, tabbas rayuwarta zata gyaru zata ingantu, amma dole sai anyi mata haƙuri.” “Tom shikenan Abubuakar, na gode sosai da kulawarka, Allah Ya yi maka albarka.” “Amin Hajiya, tana ciki ko?” Ji na yi gabana ya faɗi, bana ko son ganin Turaki a rayuwata, da sauri na rufe idona na juyar da kai, da sallamarsa ya shigo a bakinsa. Maimakon da ya ga ni kwance ya juya amna sai ya ƙara shigowa. Jin shin na yi shiru wajen minti goma, shi bai fita ba, shi bai yi magana ba, kamar na buɗe baki na ce. “Turaki lafiya.” Sai dai na yi shiru, ganin baida niyar tafiya ya sa na jiyo na buɗe ido na kalleshi, yana zaune ya ƙuramin ido ko ƙiftawa ba ya yi, a raina na ce. “Turaki ko maye sai haka.” Sai dai ina faɗin kalmar ‘Maye.’ Abinda ya zo kaina shine ranar da Sardauna ya ce da ni. “Nana ke mayya ce, ke mayya ce kin kamani.” Ƙwalla ce ta fara fita daga idona, wacca ban masan tana fita ba sai da na ji Turaki ya ce. “To shi kuma wannan ɗin na mene?” Da sauri na goge ƙwallar, sannan na ta shi zaune tare da faɗin. “Ina yini?” Shiru ya yi bai amsa ba, zai zare waya da ya yi ya fara dannawa, ina sane wannan ne karo na uku da na gaidashi bai amsa ba, a raina na ce. ‘Indai gaisuwa ce ka yi da Nana ‘yar halak, bazan sake gaida ka ba.’ “Kina shan magungunan naki?” Na ji ya faɗa, cikon wani amon muryar kamar ba daga bakinsa ta fito ba, sai dai na jiyo na kalleshi, sannan na gyaɗa kai. “Yanzu mene yake damunki?” “Bakomai.” Na faɗ a fili, a raina kuma na ce waɗan nan idanun naka masu kama da na miji, Allah Ya gani tun da bana son ƙwayar idon Turaki, bare kuma yanzu da idan ya zubamin su nake jin kamar ana gasa naman jikina ne. “Nana!” Ya kira sunana a hankali, na waigo na kalleshi. “Kin san Sarauniya Victoria da Yarima Albert na Ƙasar Birtaniya?.” Na girgiza kai, ba tare da na ce. “A’a ba.” “Duk irin soyayyarki ba kya bibiyan labaran soyayya mafi shahara a duniya?” “Uhm.” “To tsaya ki ji, Sarauniya Victoria tana mugun son mijinta, Yarima Albert. Lokacin da ya rasu a shekarar 1861, Victoria ta shiga tsananin baƙin ciki ta yadda ta kwashe shekaru da dama tana sanya baƙaƙen kaya kaɗai, sabida tsabagen jimami da kaɗuwa. Kuma kinsan ta ci gaba da rayuwa ingantacciya daga baya.” Na ɗago na kalleshi, ni banga wani abu me daɗi ba a game da wannan maganar da ya faɗa ba. “Duk da wannan babban rashin nasa da ta yi, Victoria ba ta mance da nauyin da ke kansa na shugabanci ba. Ta ci gaba da gudanar da mulkin da aka kira da "Victorian Era" lokacin da ƙasar Birtaniya ta samu ci gaban masana'antu, fannin kimiyya, siyasa, da kuma faɗaɗa tasirinta a duniya. Ta gina manyan gine-gine na tunawa da shi kamar Albert Hall, kuma ta zama madubin dogaro ga kasarta har zuwa karshen rayuwarta.” “Ta kyauta.” Na faɗa domin son kawar da zancen, ya yi shiru yana kallona, sai kuma ya nisa ya ce. “Nana, bakowanne rashi ba ne ƙarshen rayuwa ba, a duk rashin ba komai ake wa kuka ba illa sabo, Nana sabo yana da daɗi yana da ɗaci idan aka zo rabuwa, amma wani lokacin ka kan zaɓarwa kanka mafita, ka rabu da abinda kake mutuwar so, ba wai dan baka so ko wani abu, sai dan tsira da lafiyarka, da ta ahalinka.” “Kana ganin zan iya zama wata anan gaba? Kana tunanin zan iya yin abinda zai amfane ni ya amfani wasu? Sardauna ya ce ba ni da wani sauran amfani.” Na faɗa ina zubar da ƙwalla, cikin kiɗima ya fara “Nana ba haka ba ne, kece kike da sauran amfani, kece kike da sauran mamora. Nana ke fa yarinya ce mai ƙarancin shekaru, Nana zaki iya aikata abinda yafi na Sardauna sanuwa, Nana kinsan ta yadda aka gina Taj Mahal, babban ginin soyayya na duniya?” Na girgiza kai alamar a’ah, ina zubar da hawaye. “Sarki Shah Jahan yana tsananin ƙaunar matarsa, Mumtaz Mahal, ta yadda takan bishi har fagen yaƙi, tana bashi shawara akan komai, Mulki da al’amuran rayuwa. Lokacin da ta rasu tana haihuwar ɗansu na 14 a shekarar 1631, sarkin ya shiga tsananin damuwa da kaɗaici da keɓewa. Amma kinsan wani abu da ya yi?” Na girgiza kai, shi kuma ya ce. “Domin ya tabbatar da cewa soyayyarsu ba ta mutu ba, ya mayar da baƙin cikinsa zuwa ga fasaha da ginin da babu kamarsa. Ya dauki shekaru fiye da 20 yana gina Taj Mahal, wannan katafaren gini na duwatsu wanda a yau yake daya daga cikin abubuwan al'ajabi na duniya (Seven Wonders of the World). Ya ci gaba da gudanar da daularsa tare da barin babban tarihi na gine-gine da fasaha wanda har yau Indiya ke alfahari da shi. Kinga kuwa idan ƙunci ya yi yawa, zaki iya sarrafashi ya hanyar mayar da shi wani babban abu.” “Su waɗan nan ɗin suna da dama, suna da gata, suna da arziƙi, ni kuma fa maraniyace ni.” “Nana kema kina da gata, kina da Allah, kina da uwa, kina ‘yan uwa, Nana kina da ni, komai zaki samu, da ni da ‘yan uwanki a shiye muke wajen ganin mun baki gudummawa ɗari bisa ɗari cikin dukkan abubuwan da kika saka a gaba Nana.” Na yi shiru ina kallonsa, ina son yarda da maganarsa, amma kuma ƙwaƙwalwata tana tunasar dani inda BaHaushe ya ce. ‘Ba’a ɓari a kwashe duka.” “Eyh Nana, BaHaushe kam ya yi gaskiyya, ba a ɓarar da abu akwashe duka, amma ke ai baki ɓarar da komai ba, kina da haƙƙin Sardauna ne? Kin taɓa zaluntarsa, shine ya yi ɓarin kuma shine ba zai kwashe duka ba.” Shiru na yi ina kallonsa, na buɗe baki da niyar sake yin magana sai na ji ya ce. “Nana, sai kin yi koƙari wajen kawar da duk wani tunani marar kyau daga rayuwar ki Nana, sai kin gayyato farin ciki kema a kanki, Nana ko dan ki faranta Hajiyarki, ki sa ta daina wannan kukan da take Nana.” “Shikenan, zanyi na gode.” Tashi ya yi ya fice, ya barni da wani dogon tunani. ‘Yanzu ta wacca hanya zan zama wata? Idan na zama watar ma, amfanin me zanyi wa wani a duniya, ni fa duk bana son komai, Sardauna ya gama da rayuwata kamar yadda ya faɗa, ya gama da ƙuruciyar tawa kamar yadda ya faɗa. Amma me ya sa zaka yi min haka Sardauna, me na yi maka da girma haka dan Allah?” Na tambayi kaina kamar wani zai ban amsa, na fashe da kukana mai tsuma zuciya, ina yinsa a hankali ina jan hanci, sai da na yi na gaji, sannan na kwanta. Ban fita ba sai gab da magariba, bayan na iddar da sallah na zauna akan babbar tabarmar tsakar gida da Hajiya ke shimfiɗawa dukkan dare, na takure a gefe ina jin hirar da suke yi sama sama, a gefe na ni kuma ina tuna cewa, da ace Alhaji yana duniya da yanzu yana tare da ni, yana ta rarrashina, yana nuna tausayawa yana tawo min da abubuwa daga shago. Ra’is ne ya shigo hannu sa riƙe da leda, kusa da Hajiya ya zauna suka fara ƙus-ƙus ɗinsu, Yaya Radiya tana wajen girki, a hankali na ce. “Ra’is mene a ledar nan.” “Awara.” Ya faɗa yana ci gaba da hirarsa da Hajiya, sai na ji gaba ɗaya na tsargu, sun ware sun barni, daman abinda nake gudu kenan. Na fashe da kukan da yasa duka suka maido da hankalinsu kaina. “Me yaru?” Hajiya ta faɗa. “Kar kazo kusa dani, kar kazo, daman abinda nake gudu kenan duk zaku ƙyamaceni, duk zaku dinga gudun.” “Subahanallahi, Nana waya ƙyamace ki? waya guje ki.” “Hajiya yanda kuka haɗe kai da Ra’is ai dole ta ji ba daɗi, ko ni da nake nan Allah Allah nake na fito na zo inda take.” Yaya Radiya ta faɗa daga kicin, ni kuma na ce. “Allah Yajiƙan Abbanah, nasan da yana raye da yanzu yana tare da ni.” “Nana gari banza ma da rigima da kishi kike, bare kuma yanzu.” Hajiya ta faɗa, shi kuma Ra’is ya ce. “Daman fa ke na siyawa awaran na tsaya ina faɗa ma Hajiya magana ne.” Hannun nasa na amshi awaran, ko ina ya samu oho, mu nan ba ma wata awara idan ka ganta to Anty Adiza ce ta yi wa Hajiya. “Nana tashi ki shiga ciki kici.” “Sabida me Hajiya?” Yaya Radiya ta tambayi Hajiya. “Yanzu Ra’is yake faɗamin yaga wancan ɗan yaron a waje.” “Wane yaro kuma?” “Tsohon mijinta.” Ji na yi gaba na ya faɗi, wai Sardauna ake kira da tsohon mijina, kai rayuwa. “Sardauna wai? Me ya zo yi anan?” Yaya Radiya ta faɗa, Ra’is ya bata amsar cewa. “Nima bansani ba, bai ma kula na gansa ba.” “Maza kira Ridwan a waya ka ce masa yazo.” Ni da kawai da ido nake binsu, wani ɓari na zuciyata amma addu’a yake Allah Yasa zuwa ya yi ya basu haƙuri a mayar da auren mu. “Ki shiga ko.” Hajiya ta faɗa, ba musu na koma ɗakin amma ina tsaye wajen labule ina leƙe, Allah Allah nake ya shigo na kalleshi, nasani na yi matuƙar kewarsa fiye da tsammani na, wani irin sauyin bugu na ji a zuciyata, jikina ya yi sanyi gaba ɗaya, kaina ya fara koƙarin saramin. Daidai lokacin da muryarsa ta fara shigowa gidan, na ji zuciyata ta yi wani irin bugu da ƙarfi, a take na shiga tuna maganganun cin mutunci da Sardauna ya yi min, na shiga tuna ƙasƙastaccen sakin da ya yi min, na tuna komai na hulaƙancin Sardauna, sai naji wani haushi ya mamaye rayuwar tawa, sai na ji ina son na ji da me ya zo, sai na ji ina son bashi amsa daidai dashi, ƙasƙantattun ‘yan uwana da yake cewa ba ni dasu, yanzu gasu nan. Amsa sallanar tasa na ji Hajiya ta yi, bai kai ga ƙarasa shigowa ba, Ra’is ya ce. “Malam me kazo yi nan, ka fita duk wani abu bama buƙata, idan ma takardar ƙarashen saki ce ka faɗa a baki ya wadatar.” “Kai ƙaramin yaro bani hanya na wuce, nazo na tafiya da Nana.” “Ka tafi da ita ina?” Yaya Radiya ta faɗa, ya bata amsa kansa tsaye. “Gidana, bazan iya jure rashin ganinta ba, ds rayuwarta anan ba, yarinya ta saba sa rayuwar hutu da jindaɗi me kuke dashi anan da zaku bata?” Wani ƙululun abune ya tsaya mina a maƙoshi, lallai yau zan nunawa Sardauna cewar ba shi da hankali. “Ta na ina? Ta fito mu tafi.” “Ku tafi gidan ubanwa wai, me ya sa baka da hankaline, zo ka fice mana a gida kafin na yi ma rashin mutunci.” Yaya Radiya ta faɗa a fusace. “Gida! Ina gida anan? Kango dai to bazan fita ba sai da Nana, ba dan Nana ba me zai kawo ni wannam wajen, me zai shigo dani wannan wajen? Daman haka kike so, kina zaune kina zawarci a gida kina zaga umguwa itama ta na yi ko?” “Ya isa haka Sardauna!” Na faɗa cikin wata matsananciyar fusata. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na sha huɗu. “Ya isa haka Sarduana.” Na faɗa cikin wata iriyar fusata, na taku inda yake daga baya baya na ce. “Ko da yake kango, yafi asararren gidanka Rana, Sardauna me ake yi da arziƙi irin naka wanda ba shi da wata rana? Sardauna wallahi da gida irin naka gwanda zama a bola, da zama da irin auren ka gwanda daumawa a zawarci.” “Nana! Ki biyo ni muje, karki bari su wure miki kunne su rabamu.” “Ta bika kuje ina da wane aure? Ko zaman dadiro kake so ku yi marar tarbiya.” Hajiya ta faɗa a fusace, daidai lokacin kuma Ya Ridwan ya shigo, sai ji kawai Sardauna ya yi an cakumi wuyanshi an hau duka, ta ko ina. “A’a Ridwan ƙyale shi, karka dake shi haka.” Hajiya ta faɗa, Yaya Radiya da Ra’is suka yi kan Yaya Ridwan suna kiciniyar ƙwace Sardauna, da ƙyar suka iya fusgar Sardauna a hannun Yaya Ridwan. “Ka fice kabar mana gida, karka sake zuwa inda muke, yarinya ce kana ganin ka cuceta to kaje dan kanka, kaje dan halinka, kuma wallahi ko a yanzu nasan kaji a jikinka.” Kallon shi Sardauna ya yi, sannan ya mayar da kallonshi kaina. “Nana kina gani ko? Nana na sha faɗa miki ‘yan uwanki ba son mu suke tare ba…” “Hold on Malam!” Na faɗa a tsawace, sannan na taku inda yake. “Sardauna idan kana tunanin makircin ka zai sake tasiri akaina, to wallahi ka yi ƙarya. Sardauna ko da zan mutu da sonka sai dai na mutu, amma ka sani na rabu da kai har abada, kuma ko da gangan kasake yinƙurin taɓa wani cikin ‘yan uwana, sai na karta maka rashin mutunci wanda baka yi tunani ba.” “Ƙarya kike faɗa Nana, ba abinda zaki iya yi min, Nana nine naki yau da gobe har abada.” Jikina ya yi sanyi, na ji zuciyata na ƙoƙarin bijiromin da wani tunani daban, na yi saurin ɗauke kaina daga kallonsa, ƙwalla ta taru a idona. “Nana na sani, kina sona, ina sonki, ƙaddara ta afka mana, ki yi haƙuri ki dawo wajena, na yi miki alƙawarin baki farin ciki fiye da na ko yaushe.” Ji na yi zuciya ta na rawa, nasan tsaf idan Sardauna ya ci gaba da maimaita waɗan nan kalaman zan sake komawa gidan jiya, na yi saurin kauda kaina, tare da cewa. “Sardauna, wallahi ko maza sun ƙare a duniya, bazan sake komawa gareka ba, natsaneka mugu.” Yaya Ridwan ne ya kama kwallar rigar Sardauna, sannan ya ce. “Ka fitar mana anan.” Ba musu Sardauna ya miƙe ya fice, yana fita na tsugunna a ƙasa na fashe da wani irin kuka mai sanya jiri a lokaci ɗaya, kowa ya dare ya yi banza da ni. Sai da na yi mai isata sannan na shiga ɗaki na kwanta, ina jinsu suna magana sama sama, Hajiya ta dage sosai akan lallai gobe sai anje an kwaso kayana, a raina na ce. ‘Hajiya baki san bani da komai ba kenan?.’ Jin Yaya Ridwan yana magana ya sa na mai da hankalina kansu. “Hajiya zamuje gobe, duk wani abu nata zamu ɗauke shi.” “Yawwa Ridwan, bana son wani abu ya sake haɗa mu da yaron nan, kana ji yanda yake farfaɗa mana baƙaƙen maganganu a kan idonmu.” “Hajiya ai ba shi da tarbiya kwata kwata, ki yi haƙuri kin manta da wannan abun dan Allah.” Yaya Radiya ta faɗa, Hajiya ta sake cewa. “Bazan iya kwantar da hankali na ba, sai na ga yaron nan ya rabu da yarinyar nan, ya ƙyale mata rayuwarta, mu yi jinyarta ta warke ta koma yadda take.” “Hajiya Nana zata warke, komai zai wuce, zai zama labari in sha Allah.” “Allah Yasa.” Na faɗa daga inda nake, dan nima na ƙosa na ga komai ya wuce, na ƙosa na ga komai ya zama kanar ba ayi ba. Yau tun da na kwanta banyi wannan firgitar ba, har asuba. Ni kaina na ji daɗi sosai kuma alamun na fara warkewa, dan a tsorace nake da wannan yanayin da nake ciki. Wajen ƙarfe 12 na rana Yaya Rumaisa ta zo, muka haɗu mu uko sai Ra’is da Yaya Ridwan su kuma a mashin ɗin Yaya Ridwan muka nufi gidan, bayan kuma manyan motoci ne guda biyu da za a kwashen kayan, sai samarin da zasu ɗauki kayan. Tun da muka nufi unguwar na ji gabana yana wani irin faɗuwa, sai na ji ina tsoron shiga unguwar, ina tsoron haɗa ido da Sardauna, motar da muke ciki ce ta fara shiga gidan, sai mashin ɗinsu Yaya Ridwan sai kuma manyan motocin guda biyu. Kamar me tsoron taka ƙasa haka nake fitowa daga motar, gabana yana wani irin faɗuwa a duk lokacin da na yi taku zan shiga cikin part ɗin, mun kusa minti goma sha biyar muna bugu sannan aka zo aka buɗe. Bilkisu ce cikin wata iriyar shiga, ta watsa mana wani kallo da yafi harara ciwo sannan shige. Shiga mu ka yi gaba ɗayanmu, Yaya Rumaisa ta kalle ni ta ce. “Kujerunku suna ina? Ai wannan basu ba ne asalin naki?” Shiru na yi nama rasa me zance, sai da ta ƙara cewa. “Ba magana nake miki ba?” “Sune, waɗan can da zamu canja gida ya bar su acan.” “Da zaku dawo gidan ya siya waɗan nan?” Yaya Radiya ta tambaya, na gyaɗa kai sama alamar eyh. “To shi ya sani, mu dai su zamu kwasa.” Yaya Rumaisa ta faɗa, sannan ta ce da masu kwasar kayan. “Ku fara da waɗan nan.” Ta nuna musu kujerun, sannan ta sake kallona. “Wanne ne ɗakin gadonki?” Nasa hannu na nuna mata nawa, na ce. “Shine wancan, amma babu kayan gado anan sai a wancan, shi ya ce na dinga kai mutane.” Shiga suka yi, na bi bayansu ɗakin komai da akwai amma babu komai a sip ɗin, zallan zalunci ne kawai na Sardauna ya sa ya ce na ajiye kayana a akwaiti. “Ina mai ɓallewar? Ya zo ya fara ɓalle waɗan nan.” Ta saki faɗa, Yaya Radiya ta ce. “Kayan sawarki fa?” “Suna wancan ɗakin.” Ta fice ba ta ce dani komai ba, na bu bayanta zuwa ɗakin. Ina shigowa ta kalleni ta ce. “Nana kinyi zaman azaba, ga ɗaki can guda da kaya complete amma kinzo nan kin ƙare kamar almajira, Allah Ya wadaran Sardauna.” Na yi mamakim tsintar kaina da cewa Amin, ta matsa ta fara jawo akwatin tana fita dasu. Sai da ta fito falo ta ce da Yaya Rumaisa. “Katifa ɗaya muka kawo ta da ita, ɗaya zamu ɗauka.” “To me zamu yi da kayansa daman, kayan tsiya. Waɗan nan ma daga nan kasuwar katakwaye zamu kaisu a siyar, mu canja mata wasu ko a ajiye mata kuɗin, da ba zamu shigar da irin masifa cikin gidan ba.” Wata uwar ƙara ce ta taso daga ɗakin Bilkisu, wata shegiyar waƙar Ado gwanja aka ƙure uwar volume, me shiga tsakiyar kai. Yaya Radiya ce ta ce. “Ke wannam kishiya take kwai sheɗaniya.” Yaya Rumaisa ta ce. “Ni kam na ji daɗin aurenta da Sardauna, wannan kina ganinta kinga sheɗaniya, zasu goge juna ne.” “Amma fa akwai kazanta, ji wani wari da gidan yake.” Yaya Radiya ta faɗa, tana toshe hanci. Muna tsaye a falon suka kwashe kujerun tas, sannan Yaya Rumaisa ta ja su ɗakin gadon, nan ma ta sa su fara kwance kayan kafin su fara fita dasu. “Sai kuma kicin ɗinki, shima ba abinda kika ɗauko acan?” Na gyaɗa kai sannan na ce. “Mun tawo da kurfoti.” “Mene kurfoti?” Yaya Rumaisa ta faɗa, na ce. “Abin girkin gawayi.” “Au, Nana da gawayi kike girki?” Na gyaɗa kai, ta watsamin uwar harara sannan ta ce. “Na gaisheki uwar asararru, wallahi Nana kinyi asara.” Yaya Rumaisa ta faɗa, Yaya Radiya ta ce. “Nana anyi bautar aure.” “Anyi fa.” Ra’is ya faɗa yana dariya, sai na tuna lokacin da Anty Adiza ta zo, take cemin miji biyayya ake masa ba bauta ba, yanzu yau gashinan gaskiyyarta ta fito, duk na matsu ta dawo daga Kano, gidanta ma zanje na yi ko sati ne. “An gama kwance kayan gadon.” Ɗaya daga cikin masu aikin ya faɗa. “Yawwa to, ku fara fito dasu, suma ku sanya a wancan motar.” Yaya Rumaisa ta faɗa, sannan ta ce. “Muje muga kicin ɗin.” Daidai lokacin kuma muka ga Bilkisu ta fito ta nufi ƙofa, ƙawayenta ne guda biyu suka shigo, suna shigowa suka tsuntsire da wata shegiyar dariyar da bamu san dalilinta ba. Kicin ɗin muka shiga, muna shiga Yaya Rumaisa ta ce. “Allah Ya tsareni fasawa ‘yar mutane kai.” “A’a Rumaisa ki kama kan ki, mu yi abinda zamu yi mu kama gabanmu.” “To amma Yaya ki ji iskancin da suke yi.” “Barsu su yi, ɗa namiji ne fa, ana zaune zai yi mata fin abinda ya yi wa Nana.” “Hakane kuma.” Ta faɗa suka fara kwashe kayan, Ra’is ne ya shigo yana faɗin. “Ga Sardauna can, zasu fara faɗa da Yaya Ridwan.” “Ya salam.” Yaya Radiya ta faɗa tana ficewa, Yaya Rumaisa kuma tsayawa ta yi tama faɗin. “Ki barsa ya ci kutumar ubansa, daman shi ya sa na ce kar ya shigo masa gida ya tsaya daga parking space, barshi ai Sardauna ko me yake haɗiya Ridwan yafi ƙarfinsa.” Ni dai ina tsaye bance komai ba, ta kalleni ta ce. “Zaki ta yani ko sai na danna miki zagi.” “Yaya bara naje dai.” Na faɗa tare da ficewa, ina zuwa na ji hayagagar Sardauna yana faɗin. “Get out from my house.” Shi kuma Yaya Ridwan ya ƙame yana faɗin. “Bazan fita ba, dalili ne ya kawo ni, kuma duk wani abu da yake na ‘yar uwata sai mun ɗauke shi.” “Ita ta ce muku tana da wani abu anan ne?” Yaya Radiya ce ta ce. “Ridwan, matsa gefe ka cika shi.” Ba musu Yaya Ridwan ya cika Sardauna ya matsa gefe, Yaya Radiya ta ƙarasa kusa da Sardaunan ta ce. “Mun zo mu kwashi kayanta ne, tun da dai kasan da muka kawo bata ita kaɗai tsilau muka kawo maka ba.” Ya buɗe baki zai yi magana idanunsa suka sauka akaina, ina tsaye na harɗe a jikin ƙofa ina kallonsa ido cikin ido, tunani ɗaya ke yawo a raina, mene abun so a sardauna, wannan mummunan farin? Ko wannan fuskar tsofaffin? ‘Allah Ya isa.’ Na faɗa a raina, tare da kawar da kaina gefe. “Gatanan ku tambayeta idan da wani abu wanda kuka kawo ta dashi gidan nan?” “Eyh ta ce babu kasiyar, me zuciyar mitsiyata, ka siyar. Amma wallahi kasani yanda kasiyar ka yi amfani da kuɗin kai kaɗai a cikin ka muma sai mun kwashi na ka kayan da ka sanya mun tafi dasu, ai ba ziƙau muka kawo ta ba.” Yaya Rumaisa dake bakin ƙofa ta faɗa. “And who the hell you think you’re? Ni Sardauna zako cewa me zuciyar mitsiyata? Me kuke da shi? Ina da arziƙim da zan siya duk maƙwaɗaitan danginku, ina da arziƙin da zan siye ki na siye talakan mijinki.” Wata muguwar dariya ƙawayen Bilkisu suka saki, ita kuma ta tako kamar wata jaɓa, ta ƙaraso inda yake. “My Baby, ka daina asarar miyan bakinka wajen musayar da mitsiyata.” “Wallahi yanzu zan tattaka ki anan, naga uban da ya tsaya miki.” Ra’is ya faɗa yana wuci kamar mayunwacin zaki, Yaya Rumaisa ta tako a hankali ta ƙaraso inda Sardauna yake. “Haka dai, fariya. Sardauna na kira ka da me zuciyar mitsiyata, ba ta mitsiyatan bace? Arziƙi irin naka Sardauna dashi gwanda babu, gwanda rayuwa cikin talauci. Arziƙin na baki na fatar baki, arziƙin da bazaka iya morawa kanka bare wani naka, Allah ya wadaran arziƙinka Sardauna. Kuma wallahil azim kayane duka sai mun kwashe waɗanda suke haƙƙinta, kuma daga nan sai kasuwar katakwaye muje mu siyar dasu domin bazamu bar kayan tsiya a cikin gidanmu ba, amma dai Sardauna ko wuta kake fesarwa duk wani abu da yake irin wanda muka sanyawa Nana sai mun ɗauke shi.” Tana faɗin haka ta juya ta yi ciki, cikin rashi sa’a ta yi gaba sa wata ƙawar Bilkisu ta hankaɗata cikin ɗakin, aikuwa su ka yi kan Yaya Rumaisa sa hayagaga, sai dai kafin su ƙarasa Ra’is ya sa hannu ya fisgo ɗaya baya ta faɗi ƙasa shaɓar. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na sha biyar. Shaɓar haka ta faɗi ƙasa, Bilkisu ta buɗe baki ta lailayo wani uban ashar, wanda kafin ta rufe baki Yaya Rumaisa ta mayar mata da shi, sannan ta ƙara da cewa. “Idan tijara da rashin arziƙi kuke ji dashi, to wallahi munfi ku.” Tana faɗin haka ta shige ciki, Yaya Ridwan ma ya shigo muka jera a tare muka shige, haka duk sanda za a fito da kaya Yaya Ridwan yana bayan masu fita da su. A haka aka gama kwashe komai aka sanya a mota, Bilkisu da tawagar ƙawayenta dasu kaga anfi ƙarfinsu sai suka ja jiki suka koma ɓangarensu. Ni dai ina tsaye a falo ana kai komo wajen kwashe komai da yake da sunan nawa a gidan, a raina ina ta nanata. “Shikenan nabar sardauna, na barshi har abada.” Sai wajen ƙarfe 4 aka gama kwashe duk wani abu nawa, sannan muka sa kai muka tafi, fitar da nasan ita ce ta ƙarshe, nasan har abada babu abinda zai sake dawo da ni gidan Sardauna, nasan tsakanina da Sardauna komai ya ƙare, soyayyar da nunawa Sardauna bata amfani ne da komai ba, sai wahala. Ni da Ra’is ne muka yi gida a mashin ɗin Yaya Ridwan, sai mota ɗaya me ɗauke da kayan kicin da kayan sawa na, da wasu abubuwan. Ɗayar kuma su Yaya Radiya da Yaya Rumaisa da Ya Ridwan suka nufi kasuwar katakwaye, sabida Yaya Rumaisa ta rantse ta kuma rantsewa ba za a shiga da kayan Sardauna cikin gidanmu ba. Tun da muka shiga unguwarmu idon mutane ya yo kanmu, gaba ɗaya na tsargu ganin irin kallo da ake bin mu da shi, da motar da muka kwaso kayan aciki. Har muka tsaya a ƙofar gida ina jin idanun mutane akaina. Da gudu gudu na shiga cikin gidan, ina shiga na fashe da wani irin kuka, idanun mutane da nagani ya kiɗima ni, yanzu nasan babu wata ake maganarta kaf yelwawa sai ni. “Nana me ya faru kuma?” Hajiya ta faɗa, ban kai ga bata amsa ba Ra’is ya shigo. “Hajiya ba abinda ya faru, kawai rigima ce irinta ta.” “Hajiya baki ga yadda mutane suke kallonmu ba, ba kiji yadda ake zunɗen mu ba Hajiya.” “To Nana kan ki farau ko ƙarau? Mene a ciki dan mutane sunyi zancen ki?” “Nima shine abinda nagani Hajiya.” Ra’is ya faɗa, yana ƙoƙarin fara shigowa da kayan da mu ka tawo dasu. “Ina sauran suke?” “Wai sun tafi kasuwar katakwaye.” Na faɗa, bayan na zauna akan dakalin ƙofar ɗakin Hajiya. “Me za su yi acan?” “Kayan zasu siyar.” “Sabida me?” Ban bata amsa ba Ra’is da ya sake shigowa ya ce. “Hajiya duk ya siyar mata da asalin kayan da aka kaita da su, sai waɗan nan aka ɗeba shine Yaya Rumaisa ta ce ba za akawo su nan ba siyarwa zaayi, ba ta son duk wani abu nasa a gidan.” “Eyh to, hakan ma ya yi.” Ni dai na zauna jigun ban iya cewa ko ƙala ba, da ido nake bin Ra’is da kayan da yake shigowa da su, har ya gama sannan ya zauna yana faɗin. “Hajiya a zuba min abinci.” “Karka zauna, zuba da kanka ni bayi zan shiga.” Hajiya ta faɗa, ba musu ya miƙe ya shiga kicin ya zubu. “Zaki ce?” “A’a.” Na ce da shi, na zauna na co gaba da tagumi na. Ina nan zaune shi yana gefe yana cin abinci Hajiya ta fito, ta shiga ɗaki ta shirya ta sake dawowa tsakar gidan. “Hajiya kinsan me?” Ra’is ya faɗa. “Daman zama na yi ka faɗa min abinda ya faru.” “Hajiya kinga rashin arziƙi kuwa? Wai amaryarsa har da wani ɗebu ƙawayenta su yi mana rashin mutunci.” “Dan Allah fa? Kai amma waɗan nan ‘ya’ya ba su yi ba.” Hajiya ta faɗa tana ta fa hannaye, ni kuwa kallonsu nake ina mamakin yadda suke zama kamar ƙawaye, suna hira. “Kinsan kuma ƙazama ce, gidan har wani wari yake.” “Can su ƙarata Ra’is, mu dai ga tamu anan, babu wani abu da ya shafemu da gida, dan haka su yi abinda suka ga dama.” “Ki faɗa masa dai Hajiya, sai gulma da ƙananan magana kamar wata mace.” “Ke kuma sai nunƙufurci.” Tashi na yi, na shige ɗaki na barsu suna ta mai da yadda aka yi, Hajiya kamar a gabanta akayi komai haka yake ba ta labari. Ina cikin ɗaki a zaune na ji sallamar ƙawata Malaika, duk daɗewar da akayi ba zan iya manta muryar Malaika ba, nasan dai jaje ta zo yi min amma kuma bana son wannan abun nawa ya yaɗu. Suna gama gaisawa da Hajiya ta ce da ita. “Ki shiga tana ciki.” Da sauri na rufe idona, na yi baje baje kamar me dogon bacci, amma dake Malaika uwar naci ce sai da ta tasheni, a hankali na buɗe idona na sauke su akanta, na sakar mata murmushi tare da faɗin. “Malaika.” “Nana.” Ta faɗa tana zama, na sake wani mumushin sannan na ce. “Yaushe a gari?” “Ɗazu na faɗa miki, ake sanar da ni abinda ya faru na ce wallahi bazan zauna ba, sai nazo na ga ƙawatah, Nana ashe abinda Sardauna ya yi miki kenan, Allah Ubangiji ya gamashi da daidai shi mitsiyaci.” Na yi murmushi, sannan na ce. “Wallahi fa.” “Ai tun yadda naga hotonansu suna yawo a kafafen sada zumunta na ce wannan tsohuwar soyayya ce, tun lokacin naso fargar dake amma naga kamar idonki a toshe yake.” “Wallahi Malaika ba iya idona ba, gaba ɗaya ma a toshe nake, na yi rayuwa a cikin duhun rayuwa, sai yanzu nake ganin haske.” “Allah Sarki ƙawatah, mun yi magana da Fauziyya da Amina tuntuni, amma ganin kamar ba kya buƙatarmu ya sa muka ƙyale ki, ace Nana a gidan miji ko waya ba kya ɗagawa, wane irin aure ne wannan?” “Ba zaki gane ba ne Malaika, sai dai kawai na ce Allah kar ya ɗorawa wani irin ƙaddarar soyayyar Sardauna da ya ɗoramin, amma kinsan wani abu?” Ta girgiza kai, na ce. “Wallahi Malaika ko ɗigon son Sardauna yanzu babu a raina, ina jin kamar ada ma ba son Sardauma na yi ba, wani abu ne kawai da Allah Ya ƙaga, a ɗazu da naga Sardauna sai na ji matuƙar haushin kaina, da na so sardauna, Malaika a gidan Sardauna ban sami wani abu na mussaman ba, wanda babu a wani wajen, kullum rayuwata daga kicin sai zaman falo, kinsan a gidan Sardauna ko firjin ban isa na kunna ba, tabbas Allah ne Ya ƙaddara min rayuwa a gidan Sardauna, kuma nasan na so Sardauna son dan bantaɓa yi wa wata hallita ba, a lokacin da son Sardauna ya tashi barin zuciyata, sai ya busar da zuciyar ta ƙame ƙam, babu wani abu da nake so ko marari, wallahi Malaika na haƙura da rayuwar gaba ɗaya, na haƙura da komai na sallama.” “Nana, kar ki ce zaki cire tsammani daga rahamar ubangiji, Nana akwai tarin alheri da suke a gaba, Nana rayuwar yanzu aka fara ta, akwai saura a gaba in sha Allah, kuma zaayi nasara, dole a yanzu kina cikin halin da zuciyarki ke buƙatar lallashi, kulawa da dogon haƙuri, amma tabbas Nana komai zai wuce, Wallahi zaki ga kamar ba ayi komai ba.” “Bana jin rayuwata da ta gutsire fatsa fatsa, zata sake haɗuwa waje ɗaya, akwai mutanen da basu da wata sa’a a rayuwa, ni dai ina fatan bana cikinsu.” “In sha Allahu Nana, ba kya ciki.” Sallamar su Yaya Rumaisa ce ta katse mana maganar da muke yi, muka tashi muka fito gaba ɗayanmu, mu ka tarar Hajiya na yi musu sannu da dawowa. Sai da suka zauna Yaya Radiya ta ce. “Hajiya kayan gado fa sun yi kasuwa, har miliyan ɗaya da dari huɗu.” A raina na ce. ‘Aikuwa ba su yi daraja ba, domin sardauna ya kashe sama da miliyan uku akan waɗan nan kayan, kuma ba wani amfani aka yi da su ba.’ “Ni Yaya bai dame ni ba, ai ɗan fariya ne zai yi abinda yafi wannan.” Yaya Rumaisa ta faɗa, Hajiya ta ce. “Me za ku yi da kuɗin ne yanzu, ni dai a mayar masa kar yazo ya yi wa mutane tashin hankali, yaron nan ba ɗan arziƙi ba ne.” “Ya daɗe bai yi ba Hajiya.” Yaya Rumaisa ta faɗa tana miƙewa ta nufi cikin kicin. “Hajiya ina abincin?” “Yana cikin seat room.” “Ni yanzu Hajiya da cewa na yi asiya wasu kayan katakon a ajiye mata, ko sabida gaba.” “Ni a’a, bana son kayan katako, ni bana son na ji anyi wata magana ta aure, bazan yi ba, bazan sake aure ba.” “Ke dallah rufe min baki, kar ki yi auren ke kika sani, ɗazu wani shegen kallo wancan mitsiyacin ya yi miki duk jikinki ya yi sanyi.” Yaya Rumaisa ta faɗa tana fitowa daga seat room ɗin, hannunta riƙe da plast ɗin abincin. “Rumaisa ce miki aka yi yarinyar nan tana buƙatar tsawa ne? Ko hayaniya, ki zo ki tarkata ki bar min gida.” “Hajiya ai Nana bata buƙatar wani rarrashi, maganin da Turaki ya kawo mata masu ƙarfine, kuma sun yi mata aiki da wuri, yanzu zallan iskanci ne.” Tashi na yi na shige ɗaki, jin surutun nasu zai sanya min wani ciwon kai na daban, ina shiga Malaika ta biyo ni, sai dai bamu kai ga magana ba Turaki ya yi sallama. “Waye ya zo?” Malaika ta faɗa, ban jiyo ba na bata amsa “Turaki ne, cousin ɗin Sardauna.” “Shi kuma lafiya?” “Eyh lafiya ƙalau.” “Nana bari na wuce to, gobe dai zan tafi amma zan sake shigowa.” “Shikenan Malaika, ki gaida su Mama na gode.” Fitar ya yi daidai da shigowar Turaki, wani irin abu na ji ya fara yawo a cikin zuciyata, na kasa jiyo na kalleshi ko na yi masa magana. Legendspen 08129553971 Sorry for the short page. SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na sha shida. “Nana, ya jikin?” Na ji ya faɗa, ni kuma gaba ɗaya na rasa me ya sa bana son na waigo na kalleshi. “Me kike a tsaye ne? Ko jikin ne?” Na girgiza kai, sannan na zauna. “Da sauƙi Alhamdulillah.” “Gashinann kam na gani.” Na yi murmushi ba tare da na bari mun haɗa ido ba, haka kawai na ji yau ina jin nauyinsa fiye da ko yaushe. “Nana.” Ya kira sunana, na amsa ciki ciki. “Ɗago ki kalle ni mana.” Na ɗago amma ban kalleshi ba. “Yanzu mene tsarinki na gaba?” Ba shiri na ɗago na kalleshi, Turaki irin mutanen nan masu yawan gashin gishi, kuma tana sa shape mai kyau, fuskarsa ba fara bace irinta Sardauna, hasken mu zau iya zuwa ɗaya dashi, yana da yawan gashin ido, waɗan da suka ƙarawa idanunsa kyau, Sardauna ya fishi dogon hanci, duk da shima Turaki na shi yana da tsaye daidai yadda ake so, yana da wani siririn gashin baki, da ya zagayo ta gefen bakinsa ya haɗe da gemunsa da bai cika yawa ba, Turaki yana da wani ɓoyayyen kyau da a kallo ɗaya ba zaka ganshi ba, sai ka yi masa kallon nutsuwa, saɓanin Sardauna da a kallo ɗaya zaki ga kyansa, sai kuma daga baya kiga ashe zallan fari ne, Turaki yana da baiwar gashi ta ko ina, saɓanin Sardauna da babu, ko a kansa ma wasu farare ne ƙananu. A yanayin jiki, Turaki yana da kyan jiki duk da hakan ya samu nasaba ne da motsa jiki da yake yi sosai. “Kin gama?” Na ji muryarsa a kunnena, ba tare da na yi magana ba na ɗago na kalleshi. “Na faɗi wata magana ne ta daban? Da na cancanci irin wannan kallon?” Na girgiza kai, sannan na ce. “Ni bani da wani tsari.” “Ko me ya sa?” Kauda kaina na yi gefe, sannan na fara magana. “Me zan tsara? Zama da Sardauna ne na tsara kuma bai tafi daidai ba, dukkanin rayuwata a kan haka na tsarata, ba aje ko ina ba tsarin ya wargatse, kaga kenan matsalal daga nice, idan na tsara abu zai wargaje, kaga bazan ƙara tsara wani ba bare ya wargaje raina ya ɓaci, na sake shiga wata damuwar ta daban.” Tun da na fara magana Turaki bai tsayar da ni ba, sai dai kawai ya gyaɗa kai alamar eyh, ko ya yi murmushi, a lokacin na fahimci wani ɗan banbanci tskaanin sa da Sardauna, kwata kwata Sardauna baya iya sauraro na ko da na minti biyu ne, ba zan taɓa magana ya gyaɗa kai alamar eyh ko ya ji ba, sai dai ya katseni ya kawo na shi Hujjar. “Eyh kamar fa gaskiyya kika faɗa Nana, kinga idan har kin tsara rayuwa da Sardauna kuma tsarin bai tafi daidai ba, zata iya kasancewa maganarki gaskiyya ce, amma kuma wani ya taɓa tsara miki wani abu kin bi tsarin kinga yadda aka kaya?” Na girgiza kai alamar a’a, sai kuma na ce. “Alhaji ya tsaramin na yi karatu kafin na yi aure, sai dai banyi tsarin ba, bare naga ya aikinsa, amma farko da na fara zuwa makaranta na yi nasara a shekarata ta farko.” “To kinga idan haka ne, maganar ki tana kan gaskiyya, dan haka ki gwada bawa wani ragamar tsara miki wani abun sai ki gwada.” “Idan ba a dace ba fa?” “A dai gwada ɗin.” “Shikenan, zanyi shawara.” Na faɗa tare da kwanciya akan gado, shi kuma ya tashi ya fice, yana fita na sauke wata ajiyar zucoya me nauyi, gaba ɗaya idan Turaki yana waje ji nake ya cika wajen, ga idanunsa idan suna yawo akaina, tsaf zasu haifar min da ciwon kai, su ka ɗai hukunci ne. Tunani na fara, nasan dai kowa tsarin da zai ce zai ɗorani akai shine, karatu. Babu babbar cutar da Sardauna ya yi min kamar ta karatu, ya daƙile min shi a shekarar farko, ya kuma rabu da ni a shekarar da ‘yan ajinmu suke gab da kammalawa. Kamar raɗa haka na ji an raɗamin kalmar. ‘Nana bazaki taɓa haihuwa ba fa.’ Wata ƙwalla na ji tana neman zubamin a idona. Idan zan zauna na lissada cutar da Sardauna ya yi min to tabbas zan sake komawa cikin damuwar da na fita, ya zama dole na mayar da hankali akan lafiyata, da kuma sauran rayuwar da ta rage min gaba, haka kawai sai na ji ina buƙatar waya, sannan ina buƙatar na koma wajen Dr Na’ima ko zan samu a ɗorani akan wani maganin na daban. Ina jinsu har Turaki ya ci abincinsa ya tashi ya tafi, ba su yi magana kwata kwata a kaina ba, sai na ji duk banji daɗi ba kuma, kwanciyar da na yi ban tashi ba sai da Yaya Rumaisa ta tashi ne, ina buɗe ido na ganta tsaye a kaina. “Ke tashi tafiya zanyi, magana nake so mu yi dake.” Tashi na yi na zauna, ina kallonta daga tsayen da take. “Nana, Nana, sau nawa na kira sunanki?” Ita sarar ta kenan ta kira ta ce wai sau nawa ta kira ka, bayan tafi kowa sanin sau nawa ta kira ka. “Biyu.” Na bata amsa, ta gyaɗa kai sannan ta ce. “Kar ki bari na kira na ukun, dan bazan kira shi da alheri ba, muddin kika ci gaba da zama kina sawa kan ki damuwa, kina wannan kuke-kuken har gida zan zo na tafi dake, wallahi acan ɓaɓɓala ki zanyi, idan yaso zuciyarki ko ƙwaƙwalarki su yi bindiga.” Komawa na yi na kwanta ba tare da na ce mata komai ba. “Ji dai nasan kinji, aiki da shi kuma umarni ne.” Tana faɗin haka ta fice, a raina na ce. ‘Kai wannan mata Allah Ya kawo mata sauƙi.’ Na koma bacci na, wanda ban tashi ba sai bayan magariba, shima tun da na yi sallah na ci abinci na koma na kwanta, sai dai da na shiga ɗaki babu abinda yake dawo min sai maganganun Turaki, sauti muryarsa kamar wanda ya tashi daga bacci, yanayin yadda yake fitar da magana kamar ba bakinsa ke motsawa ba, d ƙyar na samu na iya bacci. Washe gari da safe, na tashi da ƙwarin jiki abu kamar wasa Hajiya na kicin, Yaya Radiya na ɗaki tana shiri makaranta na fito tsakar gida, na ɗau tsintsiya na fara shara, Hajiya daga kicin take cewa. “Ki bar aiki nan Nana.” “Hajiya zanyi, ni yanzu na warke fa.” Ba dan ranta ya so ba ta barni na yi aikin nan, ni kuma na fuskancin zaman da nake yi a kaɗaici tsaf zai mayar da ni halin da na shiga a baya, dole sai na dage na fito na yi dukkan abinda zan iya wanda zai sa na kasance cikin mutane. Mussaman jiya da na ɗauki aron wayar Yaya Radiy, na duba facebook naga abubuwan da ake so masu cuta irin tawa su ƙauracewa, ciki har da zaman shiru da kaɗaici. Ina gama sharar na shiga kicin ta ya Hajiya haɗa abun da zaayi breakfast dashi, muna aikin muna taɓa hira sama sama, har na ce da ita yau ni ce zan yi girkin rana. “Nana da haka kike yi, ai da babu wata damuwa da zaki sake shiga. Na ji daɗi kuma na yi matuƙar godewa ubangiji da yasanya miki dangana haka Nana, yanzu abinda ya rage miki shine tashin dare, Nana gidan kowa yana tashi da daddare kece kaɗai ba kya tashi.” “Hajiya ai bansani ba, kudinga tashi na mana.” “Tom in sha Allah.” Ta faɗa, Ra’is ne ya leƙo kicin ɗin yana faɗin. “Hajiya ke dawa kike magana?” “Ba a sani ba, na gulai.” Dariya ya yi sannan ya ce. “Ɓatan hanya kika yi kenan?” “Bansaniba.” Na bashi amsa, ina ɗaukan kulal da muka gama fankr muka sanya a ciki. “Hajiya wai ta taɓa girki a gidan nan kuwa?” “Yau na farko.” Na ji Hajiya fa faɗa, a raina na ce. ‘Hajiya zaki lalata ɗanki ya zama namiji me tsegumi.’ Ko da aka zauna yin breakfast ɗin, na saki jikina muka ci tare mu ka yi hira tare, har kowanne ya gama ya tafi makaranta, aka barni daga ni sai Hajiya. Ina zaune ɗaki wajen ƙarfe sha biyu na rana, ina faman dakun jiran Turaki na ji dame ya zo, amma shiru. Sallamar Anty Adiza na jiyo, na yi matuƙar farin ciki na fita na rungumeta ina murna, itama fuskarta fal da fara’a ta tare ni tana faɗin. “Hajiya Nana.” “Sannu da zuwa.” Na faɗa ina jan ta ciki, mu ka ƙarasa Seat room da Hajiya ke zaune, muna shiga na kawo mata ruwa na ajiye mata, sannan na dawo na zauna a lokacin sun gama gaisawa da Hajiya, ta kalleni sannnan ta ce. “Hajiya ai jikin na ta kam ya yi sauƙi, ba kamar Yadda Yaya Radiya take faɗan ba.” “Kai ai yanzu Alhamdulillah kam, jikin duk ya yi sauƙi sai dai firgita da take yi da dadaddare, kuma itama ba ko yaushe ba.” Kallon Hajiya na yi, ni ban masan ina wata firgita ba, sai yanzu da ta faɗa. “Kai ma sha Allah, Allah Ya ƙara lafiya, shi kuma Sardauna Allah Ya yi masa abinda ya dace da shi.” “Amin dai kam.” Daga nan aka shiga taɓa hira, Anty Adiza na ta bani shawarara yadda zan manta da Sardauna na gina wata sabuwar rayuwar, abinda na ga sun kasa fahimta shine. Sardauna ya riga ya shiga rayuwata, shigar da bazan taɓa iya mantawa dashi ba, ko zan manta ma ba ta ruwan sanyi ba. Ana hira na tashi naje na ɗaura girki, wainar masa da miyar taushe nake yi, na fara ɗaura miyar ne kafin kwaɓin wainar ya tashi. Ƙarfe 2 saura Yaya Radiya ta dawo, lokacin ma na yi nisa a soya masar, nan aka haɗu da Anty Adiza ana ta hira anan ƙara bani shawarwarin da idan na ɗauka zaayi matuƙar da cewa. Sai yamma Anty Adiza ta tafi, duk suna zuane a tsakar gida ni kuma ina ɗaki, ina jiran zuwan Turaki, ina so na ji da me ya zo kuma, har magariba Turaki bazai zo ba, sai kawai na tsinci kaina da shiga damuwa, duk dan yaga na ƙosa akan yazo na ji me ya yanke shine yaƙi zuwa, abu kamar wasa dare ya yi har muka kwanta bacci. Washe gari ma irin jiya na tashi, duk wasu ayyukan gida da ni aka yi su, haka ma girkin rana ni na yi shi, Turaki dai har zuwa dare shiru, washe gari ma Turaki bazai zo ba, cikin dabara na tambaya Hajiya ko sunyi waya ta ce ita ba su yi ba. Sai da Turaki ya kwana huɗu sannan ya zo, zuwan na shi ya haifar min da wani irin fushi da jin haushinsa, ina zaune a tsakar gida amma ba haɗe rai na cure waje ɗaya, so nake ya yi min magana amma kamar bai kula da ni ba, abinda ya ƙara tafasa zuciyata dan ya ga na damu yazo shine zai yi min hulaƙancin ya yi da ‘yar halak. Kamar daga sama na ji muryar Hajiya na faɗin. “Nana kamar ke ce mai tambayar Abubakar kwana biyu ko?” Wata iriyar kunya ta lulluɓe ni, ba shiri na miƙe na yi cikin ɗaki, ina ji Ra’is ya tun tsire da dariya, Hajiya ta sake cewa. “Ni kam kamar haka ta ce min, bata ganinsa kwana biyu.” “To ina ga maganar da muka yi da ita ne, na ce ta yi shawara ta ga me ya da ce, to da alama ta yi shawarar.” “Ina jin haka ne.” Hajiya ta faɗa shi kuma ya tashi ya shigo, ina jin shigowarsa na yi sauri na rufe ido na, ji nake kanar ƙasa ta tsage na shige ciki sabida kunya, sai da ya zauna akan gadon sannan ya ce. “Nana.” A raina na ce yana son kiran sunan nan kamar shi ya raɗa, ya sake maimaitawa amma ba amsa ba. “Kunya ta kike ji, karki damu nima fa yayanki ne, dan kinyu cigiyata ai ba wani abu ba ne, Nana nima hankalina yana nan, yana kanki, kawai da yana da kyau na dinga baki space sabida gudun takura ko matsi.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na sha bakwai. Na ɗago na kalleshi, sai na ji maganganunsa sun yi min daɗi, sun rage min gajeren fushin da na yi. “Nifa daman akan maganar mu ne.” Na faɗa, kamar zanyi kuka. “To daman kince zaki yi shawara, shine baki space ɗin da nake magana akai daman.” “Eyh na yi.” “To me kika yanke?” “Na bada damar ayi min tsarin.” “To Alhamdullilah, duk da dai nasan tsarin da zaayi ba zai wuce kan karatu ba, ni dai shine nawa tsarin nasan su Hajiya ma duk shine, amma zaayi magana da kowanne sai aji.” “Tom.” Na faɗa, tare kau da kai. “Shikenan?” Ya faɗa, sai da na jiyo na kalleshi sannan na ce. “Shikenan me?” “Kin gama na tafi?” “Dame?” “Ganina mana, naga ranar nan kin daɗe kina kallona.” Kau da kaina na yi, a raina na ce na kalli me? Lallai Turaki. “Nana yaushe rabon ki da ki fita?” “An daɗe.” Na faɗa ba tare da na waigo ba. “To kishirya gobe zamu je unguwa.” “A’a, ni ba inda zani.” “Tom, sai da safe.” Ya faɗa tare da ficewa, ni kum na kwanta akan katifa, duk jikina ya yi sanyi, tsorona kar da ace Turaki cewa zai yi yana sona? Ni ai ban shiryawa wata soyayya ba, bama zan ƙara ba, kuma Turaki da Sardauma ya tsana, ai ba ma zai yu ba. A daren suka gama magana da su Hajiya akan makaranta, a cewar Turaki za a kaini kano a nema min wata pravite university, sabida karatun yafi zuwar min da sauri, amma Hajiya ta nuna bata so, Yaya Radiya da Ra’is suka nuna sona son hakan, ko ba komai nima zan shaƙi sabuwar iskar rayuwa, nima kuma sai na ji hakan yana da kyau, ko ba komai zan zanji daɗin garin kano, domin na gaji da duste iyakar gajiya, amma har Turaki ya tafi ba a gama tsayar da magana ba. Bayan ya fita Hajiya ta ce da Yaya Radiya. “Idan an kaita kano gidan wa zata zauna? Wa take dashi a kano?” “Hajiya ai suna da hostel, wajen zaman ɗalibai, idan kuma bata so ko gidansu Adiza ne ai ba zasu qi zaman na ta ba, Hajiya ita makarantar kuɗin nan, karatun su yafi sauƙi wanda zata yi anan shekara huɗu, can bazai fi biyu da rabi ba.” “To Allah Ya zaɓa abinda yake alheri.” Ina ɗaki na amsa da amin, ni sai na ji ma nafi son na tafi kano ɗin, dutse da jigawa sun isheni gaba ɗaya, idan naje kano zamanta da wani Sardauna gaba ɗaya. Bayan wata ɗaya. Duk wasu shirye shiye na tafiya kano sunyi nisa, Turaki ne da Yaya Ridwan suke komai, tun da ga zuwa kano da shirye shirye na nan, ni ko sunan makarantar ma bansani ba, sai lokacin da aka zo yi min maganar wani course nake so, na ce da shi kowanne ma ina so, a yau saura kwana uku tafiyar ta wa, sabida komai yazo ne akan gaɓa. Lokacin da aka fara nema min addmission makarantar har sun gama badawa, sai da aka yi amfani da masu gidan rana, sannan aka sami addmission ɗin, acewar Ra’is tskanin kuɗin a ƙalla naira miliyan biyu da rabi, na yi ta mamaki a lokacin da nake tare da Sardauna me ya taɓa yi min na miliyan ɗaya, sarƙa ce ya siya kuma ita ma ba tafi dubu ɗari uku ba, sai motar da ban taɓa hawa ba. Tunjiya naje gidan Anty Adiza, ta haɗani da ƙanneta duk ta ban lambarsu, suma ta tura musu tawa, ta so na zauna a gidansu amma aka ce Turaki har kuɗin Hostel ya biya, Yaya Rumaisa kwana na yi a gidanta, ta yi min faɗa sosai da sosai. Muna zaune a tsakar gida Ra’is ya shigo, hannusa riƙe da leda ya miƙo min. “Na waye?” “Naki ne mana.” Hannu nasa na amsa, ina buɗewa na ga kwalin waya iphone. “Waye ya ce ka kawomin?” “Turaki mana, idan ba shi ba waye zai kawo miki?” “Hhm.” Na faɗa a raina, rabo na da Turaki tun ranar da ya ce zamu fita gobe na ce bana so, ban sake sa shi a idona ba, ko ya zo sai dai ya zauna a tsakar gida, gashi ban taɓa yin sa’a ya same ni a tsakar gida ba, wani lokacin ma idan ina tskaar gida sai dai na ji Ra’is ya cewa Hajiya. “Yaya Abubuakar yana gaisheki.” Ita kuma ta ce. “Bazai shigo ba ne?” Duk na wani damu, damuwar da bansan ta mece ba, ni dai nasan ba son shi nake ba, ba kuma wani abu zanyi masa ba, amma ko bakomai a ƙalla dai na ganshi na ji. Kwaroroto muka ji a harabarmu ta waje, muryar Hajja ce sai da gaban kowa ya faɗi, rabon mu da Hajja anfi wata biyar, dan tu kafin na dawo gida. “To Allah ubangiji ya sa lafiya?” Hajiya ta faɗa, kowa ya amsa da amin. Ta na shigowa ta fara sabo sababi. “Wallahi Allah Ya isa tsakanina dake.” Ta faɗa tana nuna Hajiya, gaba ɗaya Hajiya ta kiɗime tana faɗin. “Hajja lafiya?” “Burinki ki raba min kan yara? Burinki ki raba min zuri’a, to wallahi ta Allah ba ta ki ba, mai mugun nufi.” “Hajja ki yi haƙuri dan Allah.” Hajiya ta faɗa, wani ƙululin takaci ya tsaya min a maƙoshi na haƙurin da Hajiya ke bata, Yaya Ridwan ya miƙe ya fice. “Ka fice mana, ɗan marasa tarbiya, yanu ace yarinya ta kaso aure, ta wulaƙanta miji da iyayensa, amma ku kasa faɗamin, ko wani a zuri’a ta dole sai kin raba min kan jikoki?” “Hajja ki yi haƙuri dan Allah.” “Karki ƙara bani haƙuri na faɗa miki, yanzu sai jiya da na tura yara gidan aka ce wai bata nan an sake ta, sabida tana kwasar kayan abinci tana kawo miki, yanzu ɗan gidan rufin asirin da ta samu tana dandalal ariziƙi, har muma mukaje mu dandala shine sai da kika guntile auren, ke wace irin uwa ce ne?” Ɗakina ta shi na shige, banda lokacin jin wannan zancen marar kai, a barni kawai da abinda ke damuna ma kawai, ina shiga na tura ƙofa, na daina jin sautin maganar ko ɗis. Bansake sanin yadda suka yi ba, sai da na sake fitowa lokacin kam ta gama sababinta ta tafi. Abu kamar wasa ban ga Turaki ba, har yau da takama ranar tafiyata kano, na yi shirina na haɗe komai da komai nawa, Yaya Radiya ma taso ta bini muje, kuma lokacin ya haɗe mata da zuwa asibiti, sabida yanzu ta fara zuwa. Sai wajen ƙarfe sha biyu na rana Turaki ya shigo, lokacin ina tsakar gida na gama fusata, ganin irin shanyawar da ya yi mana. Bayan sun gaisa da su Hajiya da kowa da kowa ya kalli ni sannan ya ce. “Yan makaranta an gama shiryawa?” Na ce. “Uhm.” Hajiya ta ce. “Ridwan ɗin ma ya ce wai ya fasa zuwa yau ko?” “Eyh Hajiya, da yake nima akwai wani course da zanyi anan kanon, na shekara ɗaya amma dai muna nisa da ita, to na ce da shi idan ƙarshen wata nan ya yi, sai na turu azo a ɗauke ku baki ɗaya kuje.” “Toh shikenan, Allah Ya tsare hanya, Nana dan Allah a kula, a kula, a riƙe dukkan abinda na faɗa miki da ‘yan uwanki, Allah Ya bada karatu mai albarka.” Jikina duk ya yi sanyi, ba miƙe na ce. “Hajiya in sha Allah.” “Kar da ki yi kuka to, ki kama kayan ky fitar da shi, Allah Ya tsare hanya.” “Amin amin.” Na faɗa tare da ƙarasawa, shima ya ƙara so wajen kayan ya ɗauka nima na ɗauka. Hajiya har sai da taga tashin motarmu sannan ta koma ciki, muna tafe na kwantar da kaina a jikin gilashin motar, ina faman tunani a hankali a hankali, sautin waƙa yana tashi kaɗan kaɗan, a haka muka fara tafiya. Sai da muka yi nisa da tafiya, sannan ya ce. “Nana.” “Na’am.” Na amsa tare da kallonsa. “Kinga yadda rayuwa take sauyawa ko? Kinga yanda komai yake juyewa saɓanin tsarin da muka shirya ko? Babu wani abu tabbatacce face mulkin ubangiji. Nana ki yi tunanin, ko da wasa kin taɓa kawo tunanin zaki bar dutse ki tawo har kano karatu? Nana kin taɓa kawo za ace yau gani gaki a mota har ni zan kai ki?” Na girgiza kai, a raina na ce. “Ban taɓa tunanin akwai ranar da zata zo ba, wadda zanji ko ɗigon son Sardauna babu a zuciyata.” “Nana.” Ya sake kiran sunana, na ɗago ba tare da na amsa ba. “Ina so dukkan abinda ya faru dake a baya, kisa shi kamar bai faru ba, kisa shi kamar mafarkine Nana, ki fuskanci gaba, ki mayar da hankali akan abinda kika sa gaba, Nana karatun nan zai amfane ki, Nana zaki cikawa Alhaji burinsa.” “In sha Allah zanyi, in sha Allahu. Na gode maka da irin ƙoƙarin akaina, babu abinda zan biyaka da shi sai dai addu’a, Allah Ya yi maka abinda ya zato bai taɓa zata ba, yanda kake ƙoƙari akan na cika burin mahaifina da ya rasu akai, ina fatan Allah Ya cika maka buri kan ka.” “Amin Nana, daga cikin burika na akwai son na ga kin zama wata a rayuwa, Nana ba wai ina kula dake ba dan natsani Sardauna ko wani abu ba, Nana kawai ina som nuna miki a duniya akwai na banza ko nagari, haka a family ɗinmu Nana, ina son tabbatar miki ba kowa ba ne na banza.” Na yi murmushi, sannan na ce. “Nasani sosai da sosai.” “Nana baki sani ba, sannan muguntar da Sardauna yake son ya yi miki ita, Nana in sha Allah zata zama alheri, daƙile miki wancan karatun da kika yi zai zama alheri in sha Allah, Nana wannan babban course ne aka baki, course din da a nigeria ba kowa yake yi ba, ba a ko ina ake yi ba, Nana medicine and surgery ne, Nana nasan zaki mayar da hankali, Nana nasan zaki zama wata anan gaba.” Wani irin abu na ji ya ratsamin zuciya, ya samu waje ya yi ƙabe ƙabe, sai dai abun bai dameni ba, sai ma wani sanyi da yake sa zuciyata. Na kalli Turaki da wani irin kallon da ni kaina bansan fassarar sa ba, sai na ji kamar ya fiye min komai kima a duniyata, sai nake jin kamar shi kaɗai ne mutumin kirki. “Na gode, kuma in sha Allah zan zama abar alfahari ga jihar jigawa, zan zama ‘yar da kowacce mace zata kala ta ji daɗi.” “Allah Ya amince mana Nana.” Na ce. “Amin.” Daga nan ya mayar da hankali ga waƙoƙin soyayyarsa, waɗan da ni kaina nake jin tashi su a zuciyata, Turaki bai da tarkacen waƙoƙi, gaba ɗaya basu fi goma ba, su ka ɗai ne suke maimaita kansu, amma tabbas duk cikinsu babu ta banza. A haka har muka shigo cikin birnin kano, babban birni mai tarin abubuwa daban daban, ɗaya daga cikin birane mafiya a kyawu a ƙasar nageriya, kano ta dabo tumbin giwa, ko da me ka zo an fika, me dala da gauran dutse, garin masoya Annabi. Sai da muka tsaya a wani wajen cin abinci, muka ci abinci sannan mu ka yi sallar la’asar, sannan muka koma mota muka ci gaba da tafiya, tun daga ginin makarantar zaka san makarantar ba ta kowa ba ce, sai ‘ya’yan waɗan da suka ci suka ta da kai, wajen parking ya nufa ya yi parking, sannan ya ce. “Ki bar kayan anan, muje mu gama da cikin school ɗin kafin muje hostel ɗin.” “Tom.” Kawai na ce, tare da ɓalle murfin motar, muka nufi cikin school ɗin. ‘Yan mata da samari ne kowa cikin irin shigar da yake so, kowa yana budirin gabansa ba ruwan wani da wani, da ido nake bin su da kallo dukkansu, har muka ƙarasa ofis ɗin da zamu, da harshen turanci suka yi magana da Turaki, har suka gama sannan me ofis ɗin ya bani wani hoto ya ce. “Ki yi scaning wannan ta whatsapp, link ne da zai kaiki group ɗin da ‘yan ajinku suke, sannan wannan kuma shine map ɗin school ɗin gaba ɗaya, dashi zaki dinga amfani kina neman venue ɗin da za ku yi lectures.” Ya faɗa, yana nuna min wata takarda, sannan ya ce. “Wannan kuma shine time table ɗinki, duk sauran abubuwa anyi miki, ga file ɗinki nan already har documention anyi, wannan kuma key ne na ɗakinku ku uku ne, kowacce bedrom ɗinta daban.” Na sa hannu na amshi duka, a raina na ce. “Shegiya naira.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na sha takwas. A raina na ce. “Shegiya Naira.” Bayan tuna uwar wahalal da muka sha a FUD tsakanin screening da documention, anan kuma dake lamarin na farar takardar ne gashi wai komai anyi mana. “Thank you.” Na faɗa bayan na amshi komai da komai, Turaki ya miƙe muka fice, sai da muka je wajen motar muka shiga ciki wajen hostels ɗin, a bakin hostel ɗin ya tsayar da motar muka ɗauki kayan da zamu ɗauka muka fara shiga, maza da mata ne kowa yana kai koma, shi ya sa Turaki bai yi tunanin ya tsaya ya barni ba, sai da mukaje ɗakin ne na yi knocking aka buɗe, wata farar yarinya ce sanye da riga da wando ta buɗe ƙofar. Tana buɗewa ta koma na yi saurin ce mata. “Minti ɗaya.” Ta tsaya ba tare da ta waigo ba. “Zan iya shigowa da brother na, ya taya ni shiga da kayana?” “Mene a ciki.” Ta faɗa, tare shigewa cikin na ta ɗakin, juyawa na yi na ce da shi. “Ka shigo.” Ya taku yana jan ghanna most go ɗin, da take cike da kayan abinci, taliya sai shinkafa da wake. Sai kuma fulawa. Ɗakin nawa muka buɗe, akwai komai a ciki gado, sip, har da fulo, ya ajiye jakar sannan ya fita, ni kuma na buɗe n fito da gas ɗin da kayan girki, lokacin ya ƙara shigowa ya ce da ni. “Ashe kowa kicin ɗinsa da banɗakin sa daban.” Na ce. “Eyh, ƙila waɗan nan ƙofofin guda biyu da suke a rufe sune.” “Zaku huta a wajen nan, ga Ac na gani.” Na yi murmushi, sanna na ce. “Ai wannan makarantar ta ‘ya’yan manya ce.” “Eyb gaskiyya kam, ai ta yi miki ko?” Na gyɗa kai, sannan na ce. “Ta yi sosai, ban taɓa hasashen kaina a irin wannan makarantar ba.” “Haka Allah Yake tsarin shi Nana, kinsan me nake so ki kula da shi?” Na girgiza kai, alamar a’ah. “Nana tarbiyarki da ta ‘yan makarantar nan ba iri ɗaya ba ce, akwai abubuwan da a addinan ce suke haram, amma a wajen ‘ya’yan masu kuɗi sun halastashi, Nana kamar anan zaki ga namiji a cikin mata, mace a cikin maza suna hira suna taɓa jiki, Nana sa waɗan nan ƙana nan kayan, duk ki kulasa da su, kinga duk abinda ya faru Hajiya ni zata ga laifi, Nana ta bani amanarki, ni kuma na baki amanar kanki da kanki.” Na yi shiru ina kallon Turaki, na rasa me ya sa a yanzu nake jin shi sama da komai a rayuwata, idan na ce duk abinda ya faɗa zan haɗa shi da Sardauna to zanga Sardauna ma ba mutum ba ne, Sardauna bai taɓa magana yana kwantar da murya ba, sai dai idan zalunci ya shirya yi. A take ma tuna lokacin da yazo yana kuka akan zai ƙara aure, na yi murmushi. “Kina ji na Nana?” Muryar Turaki ta katsemin tunanin da nake yi, na gyaɗa masa kai sannan na ce. “Eyh, na karɓi amana, kuma in sha Allah zan kiyaye komai.” “Yawwa Nana, Allah ubangiji Ya albarka ci rayuwarki duniya da lahira.” “Amin na gode.” “Nana.” Ya sake kiran sunana, na rasa me ya sa sunana ba ya yiwa Turaki wahalal faɗa, sai ya kira sau ɗari a rana ɗaya. “Nana.” Ya sake kira, na ce. “Na’am.” “Kin saita wayarki?” Na girgiza kai, ya ce. “Me ya sa?” “Bansan yadda zan kunna iphone ba, kuma ban masam tawa na ce ko a’a.” Ya yi dariya sannan ya ce. “Bangane baki san taki ba ce ko a’a?” Na cuna baki gaba, na ce. “To aina zan sani? Bayan Ra’is ne ya kawo.” “Bai ce miki inji ni ba?” “To da ya ce inji ka, ai ni nama manta kammaninka, gaba ɗaya ka daina bari mu haɗu, ko ina ɗaki ka daina shigowa, idan ina tsakar gida sai ka aiko Ra’is ka ce masa wai ya zo ya duba ma ina nan? Idam ya duba sai ya ce wai kana gaida Hajiya ba zaka shigo ba, ai duk nagane wayonka.” Ya yi dariya, sannan ya ce. “Kin ce fa ba kya son gani na.” “Ni a yaushe?” Na faɗa kamar zanyi kuka, ya tuntsire da dariya har da tsugunnawa ƙasa sannan ya ce. “Da na ce miki zamu fita mana.” “Ba dai dariya ba, ka ci gaba.” Na faɗa ina miƙewa, shima ya miƙe yana faɗin. “Yi haƙuri Nana, ba dariya nake miki ba.” “Me kake min to? Har da tsugunnawa ƙasa kana dariya ko?” “To na daina, kawo wayar a saita ta.” Jakata na buɗe na fito da kwalin wayar na bashi, yasa hannu biyu ya amsa har da durƙusawa sannan ya ce. “An gode ranki ya daɗe.” Na yi masa wani sassanyan kallo, haka kawai na ji dama Turaki na fara sani kafin Sardauna, dama ban san Sardauna ba, sai Turaki. “Zo ki ga.” Ya faɗa yana nunan wayar, na matsa kusa da shi daga gefe ina zuro kai cikin wayar. “Ko sabida gaba, kinga yanda ake opreating iphone.” Ya faɗa yana nuna min, ina kallon ko ina har ya kammala, sannan ya ce. “Akwai sim ai?” Na ce. “Eyh gashi.” “Ɗauko to, amma yanzu zanyi amfani da wife na buɗe miki icloud.” Na miƙe na ɗauko na dawo, shi kum ya ci gaba. Har ya kammala sannan ya sa sim ɗin. “Waɗan ne apps zan ɗauko miki, ko zaki iya?” “A’a ɗauko whatsapp.” Na faɗa, ina ci gaba da zura kai, sabida na ga yadda ake yi. “Dame kum?” Ya tambaya, na ce. “Shi kaɗai.” “Ba instagram, ba facebook, ba twitter?” Na gyaɗa kai kawai, ya kalli ne sosai sannan ya ce. “Me ya sa?” “Ance duk macen dake yin waɗan nan ‘yar iska ce.” “Auzubillahi Nana, wa ya faɗa miki? To wannan ba gaskiyya ba ne, a rayuwar da muke ciki Nana dole mace sai da social media, anan zaki samu tarin abubuwa da zasu taimake ki su taimaku rayuwarki, harkar ilimi, lafiya, har da kula da miji.” Na yi shiru ina tunani, amma fa Sardauna ya ce duka ‘yan iska ne a ciki, amma kuma Yaya Radiya da Yaya Rumaisa duk suna yi, kuma shima yanayi, to kenan ƙarya yake yi? Cike da gajiyawa na ce. “Wai Sardauna ƙarya nawa zai yi min?” Wani ɓari na zuciyata ya ce. “Ba adadi, daman ba ya ce ki ci gaba da sa’ido ba, zaki yi ta ganin abubuwan da baki yi tunani ba.” “Allah Ya kyauta.” Na faɗa, sai kuma a lokacin na tuna da Turaki, na yi sauri na ɗaga kai na kalleshi, yana zaune ya zuba min ido yana kallo. Sai na ji wata iriyar kunyar shi ta kamani, a gabansa nake zancen Sardauna. “Nana.” Ya kira sunana, na ɗaga kai ba tare da na iya ce mai komai ba, sabida wata kunyarsa da na ji a dirga a raina. “Babu wani hadisi ko ruwaya a addini da ya ce kar da abar mace ta yi social media, a addinance kenan, sannan a zamanance ma babu wani abu da ya ce macen dake social media ‘yar iska ce, Nana a yanzu muna cikin zamanin da a dole ma sai mace ta yi amfani da kafar sadarwa, kuma Nana ko ‘yan iskan ma akwai su tumuli a whatsapp, akwai su a ko ina, sai dai kawai ki mutunta kanki, kisan abinda zaki yi, Nanan sardauna kuma, duk wani abu da ya faɗa miki a baya, ya yi amfani ne da yarintar ki ya ɗoraki akan wasu tsarika na a ra’ayinsa, amma a sannu a hankali zaki gane komai, zaki gane kowacce gaskiyya.” “Tom, in sha Allah.” “Yanzu idan kika nutsu, sai ki sauke duk wani app da kike so, ki mutunta kanki tin daga sunan da zaki buɗe, hoton dp da kuma bio.” “Tom, zanyi in sha Allahu.” “Idan facebook kika buɗe, duk wani abu da kike buƙatar sani ko ƙarin haske kina rubutawa zaki samu, idan twitter ne, ki yi searching gidajen jarido da manyan bloggers na gida da na ƙetare, haka instagram, Allah Ya tsare mu da tsarewarsa.” Na amsa da amin, daidai lokacin kuma shi ya tashi. “Zan wuce, zan kiraki zuwa anjima.” Tashi na yi na rakoshi har wajen mota, sai da ya shiga na dawo ɗakina, na hau jera kayana a cikin sif, bayan na kammala na ɗauki na cikin kicin na shiga jera su a can, sannan na duba ban ɗakina, komai da ya fito fes, kuma ya tsaru, tsarin ya burgeni sosai da sosai, sai da aka yi sallar magariba sannan na shiga kicin ɗin, na dafa farar taliya na ci da miyar da Hajiya ta yi min, wacca ta soyu da naman kaza sosai, na ci na gode Allah na koma gefe, bayan wayata ta cika na cire ta. Wayar Hajiya na fara kira, bugu ɗaya ta ɗauka sai da Ra’is ne ya ɗauka tare da faɗin. “Tana sallah.” “Ku sai yanzu kuke sallah?” Na faɗa ina dariya, shima ya yi dariyar tare da faɗin. “Mutanen kano.” “Na’am mutanen dutse.” Na yi dariya sannan na ce. “Na samu kam, Ra’is ya zafi?” “Gashinan ana zubawa, duk muna tsakar gida.” “Sannunku, ka ganni nan cikin rahamar ubangiji, Ra’is Ac, kicin ɗina daban, toilet ma haka, ga firinji, Ra’is wuta 24/7.” “Ah Nana kin sami duniya.” Na sake wata dariyar, sannan na ce. “Na samu kam, saura lahira.” “To Allah Ya bamu tare, ga Hajiyar da idar.” “Tom, bata.” Na faɗa, ya miƙa mata ta karɓa tare da faɗin. “Nana.” “Na’am Hajiya, ina wuni?” “Lafiya ƙalau Nana, ya makarantar?” “Hajiya komai lafiya, ina Yaya Radiya?” “Tana can zaure, Samir ne ya zo, kin san ‘yar nan ya dage wai a ɗaura auren nan, ta tare bayan ta kammala karatun.” “Toopa, Hajiya yaushe aka yi wannan maganar daga tawowa ta.” “Yanzu nan zuwansa.” “Allah ya zaɓa abinda yafi alheri.” “Amin, ina shi Abubakar ɗin?” “Hajiya ai tun da ya kawo nu ya tafi, nan nu kaɗaice, sai maƙwaftana, suma ɗaya na gani.” “To Nana, ki kula kinji.” “Tom Hajiya, sai da safe.” Na faɗa, itama ta amsa da Allah Ya tashe mu lafiya, na kashe wayar tawa na ajiyeta, ina kwanciya na ji wayar tana ƙara, ina dubawa naga ansa Turaki a jiki. ‘Ko yaushe na yi saving lambar oho? Ko akan layin tazo.’ Na faɗa tare da ɗagawa. Cikin amon muryarsa ya yi sallama, na amsa masa cike da ladabi, bayan mun gaisa ya ce da ni. “Ya zaman?” “Gashinan dai, na yi girki na ce.” “Baki leƙa ko ina ba?” “Eyh, ban leƙa ba.” “Ai da kin ɗan leƙa, kin san fa zama waje ɗaya ba naki ba ne, yakamata ki duba wata cikin masu hankali da ƙoƙarin ajinku, ki yi ƙawance da ita.” “Tom, zan duba.” “Yawwa Nana, kunyi waya da gida?” “Eyh, munyi.” “Yawwa daman ina so na ce miki, a kullum ko da sau biyu ne ki dinga waya dasu, duk da yanzu farko farko ne, amma idan aka yi nisa nasan abubuwa za su yi miki yawa, sai ki dinga ƙoƙartawa kina kiransu ko da sau ɗaya ne a rana, yin hakan yana da muhimmanci kinji?” Na gyaɗa kai kamar yana gabana, sannan na ce. “Eyh, na ji.” “Yawwa Nana, albarka da suke sa miki a duk lokacin da kuka yi waya, daɗine da ita.” “Hakane.” Na faɗa, a raina ina tunanin babu wani haɗi ko ɗaya a tsaknin Sardauna da Turaki, halayensu mabambamta ne, Turaki yana da haƙuri, kawaici da nutsuwa, Turaki mutum ne mai haƙurin sauraro, idan zan shafe awa guda ina surutu ba zai taɓa gajiya ba, kuma bazai daƙile ni ba, ko tsayarwa, zai ta sauraro na har na kammala, sannan ya yi magana, tabbas wannan halin na Turaki ya yi min sosai da sosai, saɓanin Sardauna da ba ya iya sauraronka ko na minti ɗaya ne, ya yi ta cewa. “Tsaya ki saurareni, baza kiji me zance miki ba, ni rufemin baki.” Tun a farkon fara soyayyarmu haka yake, kuma ban taɓa ganin hakan a matsayin wani abu ba, sai a yanzu da na samu wanda zai saurareni. “Kina jina?” Na ce. “Eyh.” “Ki shirya gani nan zan zo yanzu.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na sha tara. “Na’am.” Na faɗa, ya sake maimaitawa. “Ki shirya, gani nan zuwa.” “Tom.” Na faɗa tare da miƙewa, wata doguwar rigar abaya na sanya, na ɗauki gyalenta da ƙaramar jaka na saka, sai takalmi da nasa flat. Fuskata na kalla a mudubi na ga tana wani irin maiƙo, ba shiri na cire kayan na shiga toilet na yi wanka, bayan na fito ma shirya na mayar da kayan, na shafa hoda sama sama, da man leɓe. Ina tsaka da goga man leɓen ya kira ni a waya, ina ɗagawa ya ce. “Ina inda na ajiye mota ta ɗazu.” “Tom, gani nan.” Na faɗa, tare da ɗaukan jakata na fito, kullr ɗakin nawa na yi da mukulli nasa mukullin a jaka, daidai lokacin wata ta fito daga ɗaya ɗakin itama tana kullewa, ganin kamar ba ta kula da ni ba ya sa na ce mata. “Excuse me.” Ta tsaya, ba ta ce komai ba. “Sunana Nana, kuma ni ce mazauniyar ɗakin nan.” Na ƙarashe ina nuna mata ɗakin. “Oh You’re welcome, sunana Afra.” “Thank you Afra.” “Nice to meet you.” Ta faɗa tare da ficewa, nima na fice. Kamar ɗazu ‘yan mata da samari nata hada hadarsu, kowa tare da ƙawayenta, ba ruwan wasu da wasu. Tsaye na ganshi ya jingina da motarsa, ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallona, fuskarsa ɗauke da wani sassanya murmushi. Haka kawai sai na ni ya yi min kyau, a raina na ce. ‘Nifa kamar son Turaki nake.’ Dariya na yiwa kaina ni kaɗai, kamar wata sabon kamu. “Me ya faru ake dariya, aban gulma.” Na kalleshi na ce. “Gulma kana namiji?” “Ai idan na yi dake ba gulma ba ne.” “To mene?” Na faɗa daidai lokacin da na shiga motar, sai da ya ga na shiga sannan shima ya buɗe ya shigo. “Labari kika samu, ki kawo mina matsayina na wanda yafi kusa dake.” Na yi masa wani irin kallo, shi kuma ya ɗaga kai, sannan ya ce. “Eyh mana, anan kano wa kike da shi?” “Allah.” Na faɗa tare da yin dariya, shima ya yi dariyar sannan ya ce. “Ai ako ina ma Allah ne.” “To kagani.” “A’a ban gani ba tunda baki faɗan ba.” Ya faɗa daidai lokacin da ya sa motar akan babban titi. “Wai me zan faɗa ma?” “Na ga wasu ‘yan mata, gaskiyya akwai kyawawa a school ɗin nan.” Haka kawai na ji maganar ta yi min baƙi, har sai da na yi shiru na ‘yan mintuna, sannan na ce. “Nima na gani, yanzu ma wacce ke kusa da ɗakina, kamar ba ‘yar nigeria ba.” Ya yi murmushi, sannan ya ce. “Amma ai duk kinfi su kyau, kufa fulanin adamawa ne.” Na yi dariya, sannan na ce. “Hajiya dai, mu ai ‘ya’yan Alhaji ne.” “Ai Hajiya ɗin ma ‘ya’yanta ne, kinga ke da Ra’is da Ridwan kunfi kowa kyau a gidan nan, har Hajiya ma kunfi kyau, duk da bansan Alhaji ba.” “Allah Sarki, shima yana da nashi kyan, sabida irin kammaninsa ne da Yaya Ridwan.” “Ay, to shima kyakyawa ne.” Na gyara zama na kalleshi, sannan na ce. “Tsakanin Ra’is da Yaya Ridwan waya fi kyau?” “Ridwan.” “Tsakanin nida Ra’is fa?” “Ke.” “To tsakanin ni da Yaya Ridwan fa?” Ya yi dariya, sannan ya ce. “Ai nasan wayonki, to Ridwan.” Na haɗe rai, sannan na ce. “Amma ake cewa nafi shi kyau.” “Ni bangani ba.” Ya faɗa yana parking motarsa, daidai wani waje wai Frosty pop, wajen ya yi haske ga ɗaukan ido, a raina na ce. “Su kuma kanawa ba a rabasu da ƙyale ƙyale.” “Fito mana.” Ya faɗa yana buɗe min ƙofa, nasa ƙafa na fito muka nufi cikin wajen, sai da muka shiga naga ashe banga komai daga waje ba, wajen shan ice cream ne mai rai da lafiya, shima wajen mutane sai hada hada suke, lallai na yarda kano ta ninka jigawa a wayan jama’a, ko ina ko gota mutane kaca kaca. Ina tsaye ya siya mana muka samu waje muka zauna, muna sha muna hira. A wannan zaman na fuskancin Turaki yana son gulma kamar Hajiyar mu ce ta haifeshi, da ya waiga ya ga mutane sunyi abu zai yi ƙasa da kansa ya ce. “Nana… kalli na bayan mu, karki kallesu direct ki ɗanyi kamar abu kike dubawa.” Ni dariya ma ya bani, yanda yake ƙasa da kai da yanda yake ƙasa da murya. “Nana wai me ya sa kike shiru? Nifa bana so kike shirun nan, shi ya sa nake miki gulmar mutane sabida musami abin faɗa, bana son kina wannan shirun, sai naga kamar kina da damuwa.” “Ni bani da wata damuwa, kawai yanayin wajen nake mamaki.” “Mamakin me?” “Acan bamu da irin wajaje haka.” “Muna da su Nana, kawai ba tsarinki ba ne, may be a gida baki sami damar zuwa wajen ba, sannan kuma mijinki na farko bai da wannan ra’ayin.” “Amma wajen ya burgeni.” “Shi ya sa Nana ake son ma’aurata su dace da yanayi halaiyar juna, ko da ba halayensu sun kasance duka iri ɗaya ba, ɗaya yasan halin ɗaya ya kuma ko yi zama da wannan halin.” “Hakane kam.” Na faɗa, daga nan muka ci gaba da hira, kamar yadda yake ɗauko zancen na baya na ya kawo min, haka nake ɗauko zancen na bayansa na kawo masa, yanayin ya yi min daɗi sai na ji kamar ma kar mu rabu, kamar mu dauwama a haka, idan a baya aka ce min bayan na rabu da Sardauna zan ga rayuwa irin haka bazan taɓa yarda ba, idan aka ce min zanyi farin ciki ina tare da wani namiji bayan Sardauna bazan yarda ba, dukkanin farin cikina na ɗorashi ga Sardauna. Tara da rabi daidai, ya sauke ni a bakin hostel ɗinmu, bai tafi ba sai da yaga shigata sannan ya shiga tashi motar ya tafi, ina shiga ɗaki na canja kaya na kwanta, sai dai ina rufe idona babu abinda nake ganin sai sassanyan murmushi Turaki. A haka na yi baci da murmushi a fuskata, babu abinda nake tunawa sai Turaki. Washe gari da safe, bayan na yi wanka na dafa wata taliyar na ci, sabida bani da wasu isassun kayan shayi, bayan na shirya ne na kira Hajiya a waya muka gaisa, sannan na kira Yaya Ridwan shima muka gaisa, bayan nan na kira Yaya Rumaisa ita ma mu ka gaisa, Anty Adiza kuma na ce sai na dawo, ina son ma na bawa Turaki addresss ɗin gidansu ya kaini ko cikin weekend ne. Da map ɗin na duba ajin da zamuyi lectures wanda ke jikin time table ɗita, group ɗin ma tun jiya Turaki ya yi min joining, amma naga a rufe yake Admin ne kawai zai iya magana a ciki. Ajin babu wasu hayaniyar ɗalibai, bamu fi mu talatin ba, malamin yana daga sama kowa yana zaune tsilli-tsilli. Cikin saukaƙaƙen turanci malamin yake bayani, wanda muke ganin a jikin computer da take gaban kowa, awa ɗaya da minti sha biyar daidai ya yi ya fita, ina duba wayata naga ashe Turaki ya yi min message daidai lokacin da na shiga ajin, ina fitowa daga ajin na kira wayarshi, bugu ɗaya ya katse ua kirani, ina ɗagawa ya ce. “Har an fito?” “Eyh an fito.” “Sai yaushe kuma?” “Bayan awa ɗaya.” “Tom, Allah Ya bada sa’a, kunyi waya da su Hajiya?” “Eyh, munyi.” “Tom Allah Ya yi albarka, nima meeting zamu shiga, idan muka fito zan kiraki, idan baki shiga ajin ba.” “Tom, Allah Ya bada sa’a.” Na faɗa tare da kashe wayar, wani waje nagani mai inuwa ga korayen ciyayi masu daɗin kallo, ga kuma kujeru da mutane tsilli-tsilli, nufar wajwn na yi na sami wata kujera na zauna, ganin kowa da waya a hannunsa yasa nima na ɗauko tawa na fara dannawa, rasa abinda zanyi da ita na yi, sai kuma shawarar gwada amfani da facebook ta faɗomin, na shiga wajen searching na rubutu, zawarawa, sai kuma na goge, na rubuta yaya ake samun taimako akan karatu, shima na goge, mutuwar aure a yau, shima na goge, na yi shiru ina tunanin me zan rubuta, sai can na yi tunanin rubuta matsalal rashin haihuwa, ina rubutawa naga sun watso min bayanai, posting ma mutane kala kala, kowa da kalal nashi bayanin da irin maganin da yake rubutawa a nema, na maida hankalina gaba ɗaya ina dubawa, na karanta wannan n karanta wancan, na shiga wannan comment ɗin na fita na shiga wannan, na samu ilimi mai tarin yawa a wannan posting ɗin da comment da na duba, idan kuwa hakane lallai Sardauna ya daɗe yana cuta ta, na rasa exprience nasanin abubuwa da yawa, yanzu da ace tun asali mahaifar tawa bace ƙwari ai da ina bibiyar nan akwai tarin magungunan da zanyi amfani da su, ina cikin dubawa ma naga wani group wai shi mu gyara kan mu mata, ba shiri na yi joining, na ci ga ba da dubawa, na ga wani ma sirrin ‘ya mace, shima na faɗa, nasan ba za a rasa group na banza da na gari ba, duk wanda naga abinda ake yi bai yi min ba sai na fita, haka naga wani ma magani a gomar yaro, duk na dinga shiga ina duba abubuwa da yawa, har lokacin shiga ɗaya lectures ɗin ya yi, na tashi na shiga. Shima wannan cikin sauƙaƙen turancin yake komai, shi ta awa ɗaya da rabi ya yi, kuma abinda ya ƙara burgeni yadda komai ake magana akai sai an sami samfirin shi an gwada muku komai. A haka aka tashi na koma ɗakina, na watsa ruwa na kwanta, ba ni na tashi ba sai wajen huɗu, ina yin sallah na shiga kicin na dafa farar shinkafa, a yanzu duk na koyi ƙiwar yin girki gaba ɗaya. Sai da na ci abincin na duba waya ta na ga she Turaki ya kira ina bacci, ina shirin bin kiran na shi ya ki rani, abinda yaban mamaki bai fara yi min maganar kin ɗaga kira ba, sai ya fara ce min. “Ya karatun?” Na ce. “Alhamdulillah.” “An dawo ko ana can?” “Na dawo, yanzu ma na tashi daga bacci, naga kiranka ina son kira kuma ka kira.” “Sai yanzu kike cin abinci? Karfe hudu fa?” “Lokacin da na dawo bana jin yunwa.” “A’a kar ki yi wasa da abinci.” “Tom, in sha Allah.” “Ɗazu ma Ra’is ya ce min wai Hajiya ta ce ya tura miki kuɗi, zaki yi siya kayan shayi ko? Me ya sa nj bazaki faɗan baki da kayan shayi ba?” Na yi shiru, ni dai nasan banyi wata magana da Hajiya ko Ra’is ba, amma kuma ya aka yi suka yi masa maganar. “Eyh Nana.” “Nifa banyi magana dasu ba, sai dai idan sune suka tuna ba a sa kayan shayi ba anan, shine Hajiyar ta ce masa ya turamin.” “To amma baki faɗan ba tun farko, ko da yake laifi na ne da ban bibiyi kayan abincin ba ki yi haƙuri.” “Haƙuri kuma?” “Eyh mana.” Na yi shiru ni bansan me zan ce masa ba, “Kinyi shiru.” “Bakomai fa.” “Ya karatun ana ganewa.” “Sosai da sosai.” “Yawwa hakan nake son ji, kinsan wani abu?” Na ce “a’a.” “Shikenan tun da baki sani ba.” Na yi dariya, muka shiga hirarmu. A kullum sai munyi waya da Turaki sama da sau biyar, duk da ba kullum yake zuwa ba, amma a kullum ji nake kamar ina tare da shi, ya siyo min duk wasu kayan buƙata, ya ƙara ɗaukana sau ɗaya munje wani wajen daban, kwana biyu aikin da yazo yi ya ɗan sa shi a gaba, amma ko da yaushe muna tare a waya, a yanzu ji nake kamar ba zan iya ƙwakƙwaran awa guda ba tare da na ji mostin Turaki ba. Yau tun safe na shirya zuwa gidansu Anty Adiza, na kira Turaki ya ce da ni yana aiki amma zai yi min Bolt ya tura min, ina zaune bayan na gama shiryawa aka kirani a waya, wai me mota ne yana wajen gate ɗin Hsotel, ko da na fita naga motar sai da nasa ki baki, wannan makekiyar motar ake haya da ita? Kai kano ko da me kazo anfi ka. Shiga motar na yi muka fara tafiya, tunda muka hau babban titi na ji gabana yana wani irin faɗuwa, wadda na rasa dalilin hakan. Muna tsyawa a danja kamar ance Nana kalli hagu, na ganshi a cikin mota, yana sanye da farin men lace kamar ko yaushe. “Innullahi wa’inna illahir raji’un.” Na faɗa ina ƙoƙarin kawar da kaina gefe. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na sha ashirin. Ƙasa na yi da kaina, na yi saurin zuge gilashin motar, a raina ina addu’ar Allah kar ya haɗa ni ido biyu da Sardauna, a gefe guda kuma ina mamakin mene ya kawo shi kano, kuma shi kaɗai ba Bilkisu? Cikin sa’a danjar ta saki muka wuce ungwuar su, Hotoro GRA sunanta, unguwa ce ta masu kuɗi sabida gaba ɗaya manyan gidaje ne a ciki, har ƙofar gidan ya kai ni; ina sauka ya kira Turaki a waya ya faɗa masa, shi ya tura masa kuɗin ni kuma na shiga gidan, na yi matuƙar mamakin yadda mutanen gidan su ka tarbe ni, kamar sun sanni kafin yanzu, haka yara ma Anty Nana, Anty Nana. Na ji daɗi sosai kuma naga karamci a gidansu Anty Adiza, abinci a kawo wannan a ɗauke wancan, sai yamma Turaki ya zo ta ɗaukeni, kafin mu koma Hostel ma wani wajen mu kaje. Haka Rayuwata ta fara tafiya a jami’ar Maryam Abacha komai yana tafiya yadda yakamata, sai dai har yanzu banyi ƙawa ba bayan wata guda ɗaya, karatun ma tare muke yi da Turaki, wani lokacin ma muje ɗakin karatu tare, ya koya min aikin da aka bayar, mun zama wasu irin abokai masu shaƙuwa sosai da sosai, hira babu wacca ba ma yi, yasan abinda nake so nasan wanda yake so, nasan abinda baya so kuma ina ƙoƙarin akai, haka shima. A duk tsawon zaman mu da Turaki sau ɗaya saɓani ya taɓa haɗamu, kuma shi mana ni ce na kawo shi. Yau ta kama Juma’a, Turaki ya je dutse tun farkon sati, sakamakon wani kiran gaggawa da ya ce ana yi masa a gida, kuma tun da ya je sau biyu mu ka yi waya, kuma a duka lokacin sai na ji muryarshi wani iri kamar kuka yake, ko kuka zai yi, gaba ɗaya na shiga damuwa. Tun bayan massallaci ban sami fitowa daga cikin hostel ba, ina ɗaki a zaune na rasa me ke damuna, ina kewar ganin Turaki sosai da sosai. Babbar ƙofar falon mu na ji ana bugawa, na miƙe na fito na buɗe, wasu yara na gani a bakin ƙofar, dan dai dukkansu na girme su, kallona suka yi sannann ɗaya ta ce. “Ace da Nana tana da baƙo a waje, yana jira.” “Baƙo?” Na faɗa a raina, sai kuma na ce. “Ko Turaki ne ya dawo.” Komawa na yi ciki na ɗauki mayafi na ɗaura a saman doguwar rigar abayata na fito, fuskata fal da fara’a, kowa ya ganni yasan ina cikin farin ciki. A haka na tako zuwa harabar wajen, idona na kan inda Turaki yake ajiye mota, sai dai wayam babu motar, da mamaki na waiga gefe, sai dai bangan shi ba, na ƙara waigawa ɗaya gefen sai dai abinda idona suka gane min yaban mamaki, Sardauna ne a tsaye na ja wani irin tsaki, me wannan yake yi min anan kuma? Takowa na ga yana yi zuwa inda nake, na haɗe rai kamar ban taɓa fara’a ba, har ya ƙaraso. “Nana Student.” Ya faɗa bayan ya ƙaraso, kallo ɗaya na yi masa na ɗauke ido, ina mamakin a raina ta yadda aka yi na neme son Sardauna ko guda ɗaya na rasa a cikin a zuciyata. “Ya aka yi?” Na faɗa idona ƙyam akansa, ya yi min wani irin kallo sannan ya ce. “Ni kike cewa haka? Nana Sardauna ne fa.” “Nagane mana, shine nake tambaya me kazo yi wajena?” “Ba damar nazo wajen ki? Yau na fara zuwa wajenki a makarantar nan? Nana ai na daɗe ina bibiyarki, har yawon karuwanci da wancan ɗan iskan yake jan ki, amma dai koma mene shi kam na yi maganinsa, sai dai wani ba shi ba.” “Bangane ka yi maganinsa ba?” “Nana, na sha faɗa miki ke tawa ce ni kaɗai, kuma a haka zaki ɗauwama, a yanzu haka nasa katanga me ƙarfi tsakaninki da yaron can Turaki.” “Me ka yi masa?” Dariya ya yi, sannan ya ce. “Karki fusata, kawai dai na faɗa miki nasa babbar katanga a tsakaninku, kuma ki sani a ƙarƙashin ikona kike rayuwa a cikin makarantarnan, wallahi Nana babu inda zaki je a rayuwarki, sai inda na tsara miki.” “Sardauna da yake kai ka halliceni, dole ka ce na rayu a inda ka tsara min, to idan kana mafarki ka farka, a yanzu ba Nana da kasani bace a baya, Nanan dake gaban ka wata ce daban, wacca mugun so bai rufe mata ido ba, ba wacca take kasa bambamce tsakanin fari da baƙi ba, Nanan dake gaban ka, Nana ce mai ilimin rayuwa, Nana ce me dakakkiyar zuciya, Nana ce me rayuwa a cikin soyayyya, kamar yadda nabar cikin mahaifiyata wallahi Sardauna na barka har abada.” “Shut up, ki daina waɗan nan bazanyen maganganun da suke ɓata min rai, Nana kinsan yadda na yi alƙwarin raba ki da Turaki ba zai tashi a banza ba, Nana yadda natsani Turaki banko tsaneki haka ba, Nana duk abinda na yi miki zallan tsanar Turaki ce ta shafe ki, shi ya sa na yi miki dukkan abinda na yi miki.” “Sardauna wannan tsakaninka da ubangiji ne, ni dai Nana ko ƙanin ubana ne kai bazan taɓa yafe ma ba, bare kuma ba ƙanin ubana kake ba, dan haka ka matsa min anan, kuma ko sau ɗaya karka ƙara nufo inda nake.” “A yau naso a canja miki hostel a makarantar nan sai an canja miki a ƙasa da awa ɗaya, sai nasa an kaiki idan sai yadda na yi dake, Nana a rayuwar nan kuɗi ne ke juya komai.” “Hhm, a wajen marasa tunani da basu san kimar kansu ba kenan, Sardauna ko ada da ka aureni ai ba kuɗi muka bi ba, tun da nake da kai mene ka taɓa yi da kuɗi ka bani ko bawa gidanmu? Sardauna ko ada ai banci kuɗin na ka da kake magana akai ba, dan haka baka isa ka kalleni ka ce kuɗi ne ke juyawa komai ba Sardauna.” “Bakin ki ya buɗe Nana.” “Bai buɗe ba, yana kan buɗewa dai, kuma ka ki ya yi ranar da bakina zai buɗe Sardauna, na yi imanin a ranar sai na faɗa maka maganar da zata dauma a tare da kai tana maka ciwo.” “Baki da shi Nana, baki da shi wallahi, baki da abinda zaki faɗa min ya dauwama yana min ciwo, Nana na yi miki abinda har abada ba zai goge a rayuwarki ba.” “Wallahi ƙarya kake Sardauna, mene bai zai goge ba, kana tunanin a yanzu ina iya tunawa da kai a rayuwata? To wallahi ka yaudari kanka, ni dai Nana bana fatan Allah Ya kawo min ranar da zan tuna da kai a duniya, kasan da cewa ina danasin sonka da na yi a rayuwata? Sardauna me kake da shi da za a so? Ba kyan fuska, ba na hali, babu kyakyawar mu’amala, yanda rayuwarka take ɓaƙa, zuciyarka ma haka take baƙa, ka cikata da ƙiyayyar wanda baisan kana yi ba, kuma wallahi Turaki kainuwane dashen Allah, babu yadda zaka iya da shi Sardauna, ya zamar maka ciwon ido.” “Nana ashe wautarki zata buɗe ta zama furuci kenan, ko kuma baƙin cikin abinda na yi miki ne ya taru a zuciyarki?” Na yi wata dariya, sannan na ce. “Wauta ta? Ko wautarka? Sardauna ai kanka kafi cuta a auren Bilkisu ba ni ba, haihuwa ce kake magana akai ko? Sardauna ko ɗigon haƙƙinka banda shi, kuma tun ina cikin gidanka, ubangiji Ya fara yi min sakayya, haihuwa ba? Kai ka haihun? Ko zaka haihun ne? Ba ta ɓarar da cikin ba? Ta ƙara ɗaukan wani? Me ka bani na sha? Maganin lalata mahaifa, amma kasan a yanzu na hau kan maganin gyara, tunda ba ubanginji ba ne Ya Lalata ɗan adam ne ya lalata, dan haka ɗan adam ɗin da ya lalata ya yi mata maganin gyara, amma kaifa? A yanzu kasan me yake damunka? Kasan me yake yawo a jikinka? Duk lalacewarka matarka tafi ka, to kaje kaji da ita.” Ina kaiwa nan na juya na koma cikin hostel na barshi a wajen, ina shiga na zauna akan gadona na fara wani irin kuka mai taɓa zuciya, me Sardauna kuma yake nema a wajena, me zan yi wa Sardauna, me ya sa bazai ƙyale ni ba, me ya je ya yi wa Turaki da yake cewa ya yi mana katangar ƙarfe a tsakani, me ya sa Sardauna yake azzalumin namiji ne? Me ya sa yake haka? Wayata na ɗauka na shiga buga lambar Turaki, sai dai har ta ƙaraci bugunta bai ɗauka ba, na sake kira shima bai ɗauka ba, kawai na yanke shawarar yi masa text message, na rubuta masa. “Salam, me yake faruwa ka barni anan cikin damuwa? Me kake ɓoye min? To Sardauna yazo yanzu, ya ce ya yi mana katangar ƙarfe a tsakani, sai ka daina ɓoye min ka fito ka faɗa min.” Ina tura masa ko minti biyar ba ayi ba ya kirani, ina ɗagawa na ce. “Ashe da duk kana ganin kiran nawa baka ɗauka?” “Ba haka ba ne Nana, yanzu na fito daga ɗaki na ga wayar text ɗinki na fara gani, sai kuma na duba naga missed calls ɗin, me ya faru me ya ce miki?” “Ya ce min ya yi mana katangar ƙarfe a tsakani.” “Nana ƙarya yake, aina yasan kina nan?” “Ya ce ya daɗe yana bibiyar mu, kuma kaima ya ti maganinka.” Shiru ya yi na ‘yan mintina, sai can ya ce. “Kenan shine, ya je ya haɗa abinda ke faruwa a gida, shi ya kunna wannan tashin hankalin, me yake damun Sardauna ne, me ya sa yake haka?” “Nima ban san masa ba, amma mene ya yi, wace huta ya kunna?” “Nana ina ta ɓoye miki ne, sabida karatun da zaki shiga, kuma ina ta ƙoƙari akan abubuwan ne, Nana na sake bibuyar duk wani abu da ya faru, kuma in sha Allahu komai zai zo da sauƙi, tun daga kan zaluncin da ya yi miki, har ɓata sunanki da ya yi a family, ya ja kowa da kowa ya tsaneki.” Shiru na yi, a raina na ce. ‘Yanzu Sardauna har cikin ‘yan uwasa ya je ya ɓatani?.’ “Eyh Nana, lokacin da zai ƙara aure ya ɓata ki sosai a cikin ‘yan uwa da iyaye, amma na yi miki alƙwarin zan tsaya tsayin daka wajen ganin na dawo miki da kimarki da martabarki, Nana ki bini wannan bashin.” “Hhhm, wace martaba.. wace kima? Kima da martaba ta sun tafi kenan har abada, tun da babu wani abu da zan iya tsinanawa a rayuwar nan, har abada fa bani da damar da zan iya haihuwa, tabbas Sardauna ya yi min Sartse me raɗaɗi a zuciya, wanda zai dauwama har abada yana bina, kaicon rayuwata.” cikin tausasawa ya fara magana, muryarsa da take da banbanci da ta Sardauna nesa ba kusa ba, muryar da babu sautin yaudara ko ƙarya a ciki, zallar murya mai cike da kwarjini. “Nana, abubuwa da yawa su kan lalace, wasu su fashe fatsa fatsa, kuma a iya gyarasu har su fi baya kyau da ƙarko. Ni Abubakar Turaki na yi miki wannan alƙwarin, Nana zaki ji daɗi, zaki san menene rayuwar aure, zaki yi farin ciki ki yi alfahari na har abada.” “To wace katanga ya yi mana?” “Nana ya sami hotona ni dake anan kano, ya yaɗa su a ‘yan uwa, sannan ya sa wata yarinya ta kunno wuta wai sona take yi, aure na zata yi, sai kuka take ma iyayenta, a rasa gane kan yarinyar, ta dage matuƙa akan ra’ayinta wai ta daɗe da tana sona kuma aurena take so, ya yi amfani da waɗancan hotonan ya nuna bibiyarki nake yi a wajen a yanzu, Sardauna ya ɓatamin suna a cikin ‘yan uwa Nana, Sardauna ya zubar min da mutucina, shi ya sa na shiga damuwa sosai da sosai, ga babban abu ma yarinyar, Nana ban taɓa sonta ba, kuma nasan ita ma haka.” Legendspen 08128553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na ashirin da ɗaya. Gaba ɗaya jikina ya yi wani irin sanyi kamar an watsa min ruwa, na so ace Turaki yana gabana, sabida na yi kuka akan idonsa, wani abu na ji yana sama da ƙasa a ƙirjina, zazzafan abu me nauyi, ina zan sa kaina? “Nana! Nana.” Na ji yana kiran sunana ta cikin wayar, na yi saurin goge hawayen dake fuskata na ce. “Na’am.” “Kar ki yi kuka kinji, ko mai zai zo da sauƙi.” “Na rasa me ya sa ƙaddara ta take zuwa da zafi, na gama da ta gidan Sardauna, yanzu wannan shima tun kafin komai ya yi daidai zai a samu tsaiku.” Bansan ina maganar a fili ba, sai da na ji ya ce. “Ba haka ba ne Nana, komai da kike gani Allah ya tsara shi, bisa tsarin shi, kuma Allah Baya taɓa ɗaurawa rai abinda bazai iya ba, duk wata jarrabawa da kika ga Allah Ya ɗauro miki Nana yasan zaki iya ne, ki yi haƙuri ki mai da hankali ga karatunki, zan dawo in a satinan kuma zan maida ke can hotoro gidan ‘yan uwanku, tun da nima course ɗin nawa yazo ƙarshe Nana. A yanzu an ci kusan wata tara, kema shekarun naki sun fara tafiya na makaranta. “Eyh, yanzu jarabawar zango karatu na farko za mu yi a shekara ta biyu, daman haka bambamcin su pravite ɗin yake?” “Eyh Nana, shekara biyu da wani abun zakiyi.” “Yanzu yaushe zaka zo?” “Nana, ina so mu yi magana da yarinyar ne ta fahimci ni.” “Me ya sa ba zaka aureta ba?” Ya yi shiru na ‘yan mintuna, sai can ya ce. “Dalilai da yawa.” “Waɗan ne dalilai.” “Nana abu na farko bana son ta, kuma a yanzu na sake samun wani dalilin, ita ma ba sona take ba, ada na yi tunanin ko sabida biyayya zan aureta, ammma a yanzu na ji bazan iya ba Nana.” ‘Kai Sardauna annamimi ne.’ Na faɗa a raina a fili kuma na ce. “To, Allah Ya zaɓa abinda yafi alheri.” “Amin Nana, ki yi karatu sosai kinji.” “Tom in sha Allah.” Muna gama waya na kira Yaya Rumaisa muka gaisa, sai dai ban faɗa musu komai ba, har Ra’is ma da muka yi waya. Tun daga wannan rana bansake haɗuwa da Sardauna ba, kuma ban bi ta kansa ba, mussaman a yanzu da exam ta kawo kai, na maida hankali ga karatu na sosai da sosai, muna magana da Turaki lokaci zuwa lokaci, amma kullum ya kance abubuwan sai addu’a. Yau na shirya zuwa gidan ƙawata Malaika, ganin mun kusa gama exam, kuma muna gama exam gida zan tafi, dan tun da nazo banje ba, hutun da muke yi gaba ɗaya sati ɗaya kwana uku ne, amma dai a wannan lokacin na ce ko kwana ɗaya sai na je gida. Ta whatsapp ta turamin location, kasancewar a yanzu nasan garin kano ba laifi, na ɗau mota na tafi unguwar da take Shardaɗa Quaters, ita ma dai unguwa ce ta masu kuɗi, haka gidan ma da kyansa, mun yi hira sosai da sosai, ni kaina na ji daɗin zuwa gidan mussaman da ta kalle ni ta ce. “Nana kinga yanda kika canja, kin koma rainon madara rarrafen kafet.” Na yi dariya, sannan na ce. “To Malaika, rayuwa ce shiru, ko magana sai ka yini ba ka yi ba.” “Ai fa, duk ‘ya’yan masu kuɗin nan ‘yan iska ne, basa kula kowa.” Ai kuwa kamar ta soso mun inda yake min ƙaiƙayi na gyara zama na ce. “Kinga ɗakinmu part uku ne, to wacca ƙofarta take kallon tawa ce kawai muka taɓa magana ita ma ina ga baifi sau biyu zuwa uku ba, ita waccan ta tsakiyar mu bamu taɓa magana ba, hana ƙarya dai munyi ranar da na fara zuwa.” “Lallai Nana, haka kike zaman shiru?” “Daga ni sai Turaki, yazo, ya kira ni a waya shikenan.” “Waye Turaki?” “Wannan cousin ɗin Sardauna fa.” “Aouh, nagane shi kuna tare kenan?” “Sosai ma.” Ta yi dariya sannan ta ce. “Allah Ya tabbatar mana da alheri, rabon ki sake komawa familyn su Sardauna ne.” Na yi murmushi kawai, ni nasan abinda yake faruwa kawai, daga nan muka shiga hira kala kala, sai wajen dare sannan na tafi, ina zuwa muka yi waya da Turaki yake sanar dani gobe yana hanya, ba ƙaramin daɗi na ji ba da zuwansa. Kasancewar a yanzu bama lectures tun da an fara jarrabawa, mu ‘yan dept ɗin mune ma bamu fara ba sai sati na sama, hakan ya sa yanzu bana ta shi da wuri, wajen ƙarfe sha biyu na rana kiran sa ya tashe ni, na ɗaga wayar ina faɗin. “Salamu alaikum.” “Bacci kike?” Na ce. “Eyh.” “Gani a harabarku.” Ba shiri na miƙe, tare da faɗin. “Ina zuwa.” A gurguje na watsa ruwa na shirya na fita, yana inda yake parking ɗinsa tun da ya kawo ni, anan yake tsayawa, ya yi wani irin kyau mai sanyi, sai na ga kamar wani sabo dal aka fitar daga kwali. Fuskarsa har wani sheƙi take na daban, har na ƙaraso kusa da shi ina kallonsa. “Na canja?” Ya faɗa yana murmushi, nima na yi murmushin sannan na ce. “Sosai kam.” “Kema kin canja, kinyi kumatu, wane mai kike shafawa naga kin fara haske.” “Caro Ac.” Na faɗa tare da tuntsirewa da dariya, shima ya tuntsire da dariya, ina son kasancewa da Turaki sabida indai ina tare da shi ina jin dukkan damuwata ta goge, na kan ji zallar farin ciki ya mamaye ni. “Ya exam.” “Monday zan fara, kuma ina son naje gida wannan hutun.” “Hutun zai kai sati ne?” Na girgiza kai, sannna na ce. “A’a, kwana uku ina ga, Alhamis za ayi final, monday adawo, amma ni tun talata zanyi tawa final ɗin.” “Eyh zaki iya zuwa, ko sati ne ki yi, shi karatun yaushe zamu fara?” “Ko gobe ko?” Na faɗa da alamar tambaya. “To hakan ya yi, bari na je na yi wanka, zuwa yamma may be na dawo.” “May be?” Na faɗa, ina yi masa wani kallo, ya yi dariya sannan ya ce. “Tom, da yamma zan dawo.” “Better.” Na faɗa tare da matsawa daga jikin motar, shi kuma ya shiga, sai da yabar harbar ni kuma na shiga, ina gab da shiga na ga kamar mutum a laɓe yana kallona, na yi kamar bangani ba, sai dai nasa ƙafa kamar zan shiga ciki na yi wata iriyar juyowa, Musa me bawa fulawa ruwa ne a makatanta, hannusa riƙe da waya yana yi min video, a take ƙwaƙwalwata ta haskomin shine idon Sardauna, jikinsa na rawa ya juya zai gudu na ce. “Na ganka, kuma sai na yi reporting ɗinka yanzu nan.” Ba shiri ya dawo tare da faɗin. “Dan Allah ki yi haƙuri, wallahi zan rasa aikina.” Na yi masa wani banzan kallo sannan na ce. “Kana tsoron rasa aikin ka, kake ɗaukan ɗaliban makaranta a video.” “Ki yi haƙuri, Yayanki ne ya sa ni, ya ce baya so tarbiyarki ta ɓaci.” “Wane Yayan nawa?” Na faɗa da alamar tambaya ƙarara. “Wanda ya zo wajenki wata rana, wani fari sosai, me yawan sa fararen kaya.” A take nagane Sardauna, na ce. “Ta ya ya ce ma shi Yaya na ne ka yarda?” “Yana nuna min hotonan ku tare, ya ce duk ranar da wani yazo wajenki, na yi video zai zo ya amsa yaban kudaɗe masu yawa, ranar farko ma dubu ɗari biyu yaban.” “Akan kuɗi, to ba Yayana ba ne, ba ɗan uwana ba ne, ban da wata alaƙaa da shi, dan haka zan kai ƙararka.” “Ki yi haƙuri.” Na tsaya ina kallonsa na daƙika, sai kuma na yi wata shawara. “Zan ƙyaleka, amma kuma za ka yi min wani aiki.” “Zanyi wallahi.” “Daga yanzu kullum ka kira shi ka ce masa mutane daban daban suna zuwa wajena, wata rana ma har mutum uku su kanzo wajena.” “Tom, zan yi wallahi.” “Idan baka yi ba, kaga nima na yi recording ɗinka, zan kai wajen hukumar makaranta.” “Innullahi, ki yi haƙuri, wallahi duka zanyi.” Ya rage naka, na faɗa tare da shigewa ciki, sai da na zauna na fara tunani, me Sardauna yake nufi dani Nana, me ya sa yake min haka, wace masifa ce wannan. Har yamma jikina ba ƙwari, ko da Turaki yazo ma ba wani shiri na yi na mussamaan ba, mu ka fita, yau wajen wasa muka je wai shi SKY PARK sai dai akwai nisa sosai sa sosai, amma na ji daɗin zuwa wajen sosai, na ƙara samun lokuta masu daɗi tare da Turaki, washe gari ya zo makaranta mu ka fara karatu a libarary tare, ina yi yanayi, yana min bayanin wasu da hausa yan da zan ƙara ganewa, sai yamma ya tafi ni kuma na koma ɗaki, ko a ɗaki na ci gaba da maimaitawa a cikin salon da ya yi min, abun farin ciki washe gari da naje ɗakin jarabawa, wasu tambayoyin da na tuna wani lokaci ko wani abu da ya yi min a lokacin da muke karanta wajen, sai na ji komai ya dawo min fes a kaina, haka na ƙare jarabawar nan zuciyata fal da soyayya, har na fito na dawo ɗaki. Ina shiga ɗaki na kirashi, na shaida masa komai, ya ce gobe ma haka zamu sake, aikuwa hakan muka yi duk wata jarrabawa a haka muke karatunta kuma da an shiga ɗakin jarabawa zata dawo min fes, har na samu na kammala jarabawa ta, a ranar na wuce dutse. Ina sauka daga mashin a ƙofar gida Ra’is ga fito da gudu kamar zai rugume ni, yana murna da kiran sunana, ‘ya’yan Yaya Radiya ma suka fito suna tsalle suna murna, wani irin daɗi na ji ya ratsani, ganin yanda ake murna da zuwa na. Ra’is ya ɗauki akwatin muka shiga ciki, a tsakar gida muka tadda Hajiya gab da bakin ƙofa tana tsaye, bakinta a washe, ina ganinta wani daɗin ya ƙara ratsani, na rugumeta tare da faɗin. “Hajiyata.” Cike da farin ciki ita ma ra rumgumo ni tana faɗin. “Nana sannu, sannu da zuwa.” Daga nan muka yi seat room, muna zama na ce. “Ina Yaya?” “Kin manta ta yi aure.” Ra’is ya faɗa, na girgiza kai na ce. “Ni ba wanda ya faɗamin, nasan dai ta sami aiki.” “To ai sai bayan anyi auren ne, waɗan nan ma sabida makatanta suke zaune, amma ana hutu suke komawa, sai ya ƙare su dawo. Suna shiga junior za a sukoma can.” “Allah Sarki, ai kuwa gobe ina gidanta.” Na faɗa, Hajiya ta ce. “Hutu kuka samu ne?” “Eyh Hajiya, hutun ma na kwana uku ne, amma sai na yi sati anan nikam.” “Eyh gaskiyya dai kam, yakamata ki zaga ‘yan uwa har su Hajja ma.” “Ra’is ya makarantar?” “Yanzu zamu shiga final year.” “Ma sha Allah, yanzu sai kun shekara kenan?” “Eyh.” “To ai duk a shekara ɗaya zamu gama kenan?” “Eyh, ai ku karatun naku ne gudunsa ya yi yawa.” “Tare kuke da Abubukar ne?” “A’a yana can kano dai.” “Aiy to.” Hajiya ta faɗa, Ra’is ya ce. “Ya kika ga kanon?” “Kai Ra’is ba haɗi chaɓ.” Ya yi dariya, sannan ya ce. “Ai can zayi service.” “Yakamata dai kaga kano, Hajiya naje gidansu Anty adiza wajen sau biyar.” “Har biyar ‘yar nan?” “Eyh, Hajiya mutaneb arziƙine na gaske.” “Ma sha Allah, ai daga ganinta kinsa daga gidan manyan mutane take.” “Sosai Hajiya.” Daga nan muka shiga hira kala kala, na basu wancan labarin, su bani nasu, har yamma muna haka, Yaya Ridwan ya dawo anan nake samun labari shima ya sami aiki, kuma wai duka shi da Yaya Radiya Turaki ya sama musu, kai ni ba abinda zance da Turaki sai godiya, ya yi namijin koƙari akaina da ‘yan uwana. Washe gari na shirya fara zuwa ziyara, na zaga ‘yan uwa, sabida bawani dogon zama zanyi ba, ranar farko na fara ta gidan Yaya Rumaisa, na ji daɗin zuwa itama ta ji daɗin yanda ta ganni, ta yi ta yabon kyan da na yi, ta kuma sanar dani sunyi magama da Dr Na’ima Daƙayyawa ta sanar da ita labari mai daɗi sosai da sosai, na kalleta sannan na ce. “Yaya wane labari ne wannan?” Ta yi murmushi sannna ta ce. “Su Hajiya duk basu faɗa miki ba?” Na ce. “Eyh fa.” Ta ce. “To ki godewa Allah Nana, mahaifarki za ta iya ɗaukar ɗa, amma kuma bawai da ssauri ba, kuma ba wai lallai duk zasu da rai ba, amma tabbas Nana mahaifarki zata haifar da ɗa, Allah Ya duba zuciyarki ya ga baki nufin kowa da sharri.” “Alhamdulillah Yaya, gaskiyya na ji daɗi, kuma na yi wa Allah godiya.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na ashirin da biyu. “Akwai wasu magunguna da aka kawo miki kwanaki, kina amfani da su ko?” “Eyh Yaya inayi.” “To ai akwai wasu guda biyu da ta ce za a ƙara miki dasu, yanzu zan yi waya da ita sai a kawo kafin ki koma.” “Tom Yaya, amma na ji daɗi wallahi.” “Ai daman Nana na faɗa miki, a yanda baki da haƙƙin Sardauna, Allah bazai ba shi damar cutar dake ba.” “Kinsan yazo makaranta, amma na yi mai kaca kaca, sai kuma satin da zamu fara jarabawa na kama mai bawa fulawa ruwa yana min video idan Turaki yazo yana tura masa.” “Lallai Sardauna masifa yake nema, wallahi Nana da badan wani abu ba, wallahi sai nasa anyiwa Sardauna kaca kaca da hulaƙanci.” “Ki barshi kawai Yaya.” “Ai na barshi, sabida Allah da bazai barshi ba wallahi.” Na ce. “In sha Allah.” Daga nan, muka ci gaba da hira, sai yamma na tafi gidan Anty Adiza itama mun sha hira sosai, ta faɗamin yanda ‘yan gidansu suka ji daɗin zuwana, nima na yi mata godiya da karamcin da suka yi min, har dare ina can sai da mu ka gaisa da mijinta wanda na daɗe ma ni bangansa ba, daga nan na dawo gida. Washe gari na fara ta gidan Yaya Radiya, ita ma na yini a can muka sha hirar yaushe gamu, sai kuma na ji gidan Hajja da Hajiya ta takura, ban wani jima ba na dawo gida. Washe gari na je gidansu Fauziyya da Amina aminu, suma mun sha hira kowacce ta yaba da canjin dana samu, a haka na dawo gida na cinye hutu. Ina komawa makaranta muka sake shiga karatu ka’in dana’in, muna tsaka da karatu Turaki ya kammala course ɗin ya tafi, amma yana ƙoƙarin zuwa duk bayan sati biyu, zancen aurensa dai abu yana ta kankama, dan a yanzu na sa shi ya yi min alƙawarin bazai ɓoye min komai ba, duk da ina jin ba daɗi, amma na faɗa masa zan kasance kai bashi ƙwarin gwiwa akan komai. Hakan ya sa ya daina ɓoyemin, kuma abun mamakin shine yanda yarinyar take iƙirarin tana son sa amma har yau taƙi bare magana ta haɗasu ko ta minti ɗaya ce, iyaye da ‘yan uwa kam sun dage akan maganar, ni kuma na ƙarfafashi akan ya yi musu biyayya. Sardauna dai ban sake bari na haɗu da shi ba, yana garin baya garin ni bansan masa ba, sannan ban sake haɗa ido da mai bawa fulawa ruwa ba, karatu na nake yi a hankali cike da nutsuwa, a lokacin da muka kammala aji na biyu, zamu shiga na uku aka sanyawa Turaki ranar aure da matar Islaha, ranar na yi yinin ɓacin rai da damuwa, duk da Turaki bai taɓa ce da ni Nana ina sonki ba, amma ni dai nasan zuciyata ta kamo da son Turaki, so mai girma, wannan son a cikin zuciyata nake jin shi tare da bugun numfashi na, ba wai a cikin kwanyar kaina ko ƙwaƙwalwata ba. Wata uku aka sanya komai da komai, a ranar ban iya kiran Turaki ba, kuma ban iya ɗaga kiran da ya yi min ba, duk yadda nake danne zuciyata nake ƙarfafa mai gwiwa, a wannan karon na kasa ƙarfafa tawa zuciyar, sai washe gari ya kirani, ba yadda na yi na ɗaga wayar. “Nana.” Ya kira sunana, ban amsa ba na ce. “Salamu alaikum.” Ya masa da. “Wa’alaiki salam, Nana.” “Na’am.” Na amsa cikin sanyi murya. “Ki yi haƙuri.” “Da me?” “Da abinda ya faru Nana, ba a sona ba ne kinsan komai.” A take lokacin da Sardauna zai auri Bilkisu ya ce da ni ba a son ransa ba ne ya dawo min tarwai. ‘Me ya sa duk maza suke hakane?.’ Na tambaya a zuciyata, sai dai ya bani amsa a fili, ya ce. “Nana, ba duka maza ba ne ɗaya, kowa daban yake. Kanar yadda kowacce mace take daban, halinta daban, kammanninta daban, haka maza suke, a baya Sardauna ya yaudareki da cewa ba da son ba ya yi aure, nima a yanzu na faɗa miki, nasani Nana abubuwan zasu ke zuwar miki wasu kala dabab, amma ki yarda da ni sa zuciya ɗaya da gaske nake miki Nana.” ‘Sardauna ya kashe min zuciya, ta hanyar da bana iya yarda da kowanne irin kalaman soyayya, ta hanyar da duk wasu kalamai zanji su a ƙarya.’ “Nana ba ƙarya nake ba, Ni Abubukar Turaki gaskiyya nake faɗa.” “Yaushe ne auren?” “Nana na faɗa miki wata uku ne.” “Allah Yasanya alheri ango.” “Ango Nana ba.” Ya faɗa yana dariya, na ce. “A’a, angon islaha dai.” “Idan ba Nana ba sai rijiya.” Na yi wata dariyar takaici, a lokacin na tuna nima fa haka na ce. “Idan ba Sardauna ba sai rijiya.” A fii na ce. “Allah Sarki.” “Me ya faru?” Ya tambaya, na ce. “Bokomai.” “Kin haƙura?” “Dame wai?” “Komai ma.” “Eyh, na haƙura.” “Da zuciya nawa?” Sai da na yi dariya sosai, sannan na ce. “Dubu.” Shima ya yi dariyar ya ce. “Ai baki haƙura ba, da zuciya ɗaya shine kin haƙura.” “To da rabin zuciya ma.” “Uhm, wai kwana biyu babu wani update ne a makaranatar ku?” Sai da na yi dariya, sannan na ce. “Babu ko ɗaya.” “Ina wannan me jan idanun?” “Tana nan.” “Ta sake yin aljanun?” Dariya na saki, sannan na ce. “Daman kana nan ta yi?” “Ina nan mana, kawai ta zubewa mutane a ƙasa.” Na yi dariya sannan na ce. “Bata sake ba.” “Amma dai ba kya kulata, kar ta goga miki ta ja min masifa.” “Suma Allah ne ya ɗora musu.” “A’a Nana, sau nawa ina ganinta anan wajen, har da daddare ma wani lokacin haka take fitowa ko ɗankwali babu, ai ina nuna miki ko?” “Eyh.” “To kinga, ya zaayi ki ce haka, gashi kullum fuskarta da kwalliya, kuma duk kayan kiran mutanen ɓoye ne, har da daddare fa ba ta wanke fuskarta, wa ya yake sallah ne?” Na yi dariya, sabida yanda ya ƙare maganar, sai da na yi sasai sannan na ce. “Ni bansani ba, amma ranar ta ce idan ta yi wannan attach ɗin da kwalliya sai lokacin da take al’ada ne, ba ta yin sallah shine take wannam gayun.” “Kinga kuwa dole sheɗanu su kamata, ga najasa a jikinta, ga ta ƙara wata najasar, kuma wannan ma ai ba tarbiyar addinin musulunci ba ne Nana, ki duba fa yanzu duk wata ta ganta a wannan shigar tasan a yanayin da take, baga maza ba, ba ga mata ba.” “To haka dai ta faɗa, ya zaayi mata to?” “Allah Ya tsare mana ku.” Na ce. “Amin.” Daga nan muka shiga hirar mu, sai sa muka daɗe muna magana sannan muka ƙare wayar, muna gamawa na tashi ma shiga kicin na haɗa abinci na fito na ci, ina gamawa na shirya na fita zaga makaranta, kamar yadda nake y lokaci zuwa lokaci. Ina tafe ina ganin mutane rukuni rukuni, suna fira abunsu, har kuwa nagano yarinyar da mukayi zancen da Turaki, ta ci uwar gashin dokin, fuskarta tasha uwar kwalliya ga gashin ido firi firi, tana sanye da wata biri da wando, a raina na ce. ‘Yau an shiga al’ardar kenan.’ Na wuce, kafin na kai bakin massallaci kuwa na ji ana ta ihu, wai ta zube a ƙasa aljanun sun zo, ai kuwa har Allah Allah nake na koma ɗaki na kira Turaki, bugu ɗaya ya ɗauka tare da faɗin. “Ita kika gani?” Na yi dariya na ce. “Aikuwa yanzu naga ta zube tana aljanun.” “To fa, da ma ina nan.” “Me zaka yi mata?” “Riƙe ta zan yi na yi ta tsinkawa aljanun mari.” “Allah Yayafe maka.” Na faɗa tare da kashe wayata, gaba ɗaya kwana biyu zaman makaranatar ya isheni, na matso ma a gama jarabawa ayi hutu, ko Turaki ya zo. Sai dai ya yi sati uku sannan ya zo kano, ranar na ji daɗi sosai da sosai, dan mun zagaya gari irin zagayen da muka daɗe ba mu yi ba, sati ya yi cif kullum sai mun fita, Sardauna sai da ya sa na ji daɗin da bansan akwai a duniya ba, bansan akwai farin ciki a duniya irin wanda nake ciki ba yanzu, daga nan dawowa ɗaya ya yi bai kuma sake ba, ɗaurin auren shi ya zo, tabbas a bikin na shi babu wasu shagulgula da aka yi, dan yanzu ina social media ina ganin komai, amaryar da ƙawayenta dai sunyi nasu amma baije ko ɗaya ba, haka kuma family sunyi sai a ranar ne ya je daga nan bai sake zuwa ba, amma hakan bai hanani jin haushin sa ba, mussaman yanda naga yana ta dariya a hotonan. A haka aka gama biki amarya ta tare, ranar da bacci sai ɓarawo ya kwashe ni, ni ba kuka bani ba damuwa ba, ina zaune jigum na takure waje ɗaya, na rasa abinda yake min daɗi. Kasancewar ɗaurin auren Juma’a aka yi masa, washe gari asabar bamu da makaranta, da safe ina zaune a ɗakina na ji ana bugawa, abinda ba a taɓa yi min ba a tarihin zamana a wannan hostel ɗin ba, shine buga ƙofa. Tashi na yi ina faɗin. “Waye?” Aka ƙara bugawa, nasa hannu na buɗe. Ina buɗewa naga Sardauna da sauri na yi ƙoƙarin turawa amma yasa hannu ya riƙe ƙofar, da sauri na yi ƙoƙarin shiga kicin amma ya tare ƙofar tare da faɗin. “Ke nutsu!” Na tsaya, ina kallonsa. “Nutsu na ce miki.” Na kalleshi, sannan na ce. “Me kake yi min anan, fita.” Ya yi dariya, sannan ya ce. “Nana bakomai, ki fahimce ni dan Allah.” “Na fahimce akan me Sardauan?” “Nasan kina sona Nana, na sani, amma Turaki ya shiga tsakaninmu. A yanzu Turaki to ya yi aure, kinga kizo mu mai da aurennu, Nana zan baki duk wani ‘yanci a rayuwa, Nana ki taimakamin na yi na dama da gaske.” “Wane ‘yanci nake nema, ni bana son sake rayuwa da kai Sardauna.” “Nana badan ni ba, ba dan halina ba, wallahi na yi na dama Nana.” “Ni dai ka rabu da ni dan Allah Sardauna, bana son sake ganinka, bana son dake haɗa hanya kowani abu da kai, Sardauna ka riga da ka wuce a rayuwata, ka barni na yi tunkari gaba da abinda take tafe dashi dan Allah, karka sake mayar da ni ruwa, karka mayar da ni rana.” “Nana ba Turaki ba ne? Ba Turaki ba ne, to ya yo aure, ya auri wacca yake so kamar yadda nima a baya na aure wacce nake so na barki, bana son ki sake shiga damuwa, Nana na yi nadama na tuba kinji.” Na girgiza kai, sannan na ce. “Turaki ba wacca yake so ya aura ba.” “Nana me ya sa bazaki waye ba, mene amfanin iliminki, ni da wane salo nazo miki, har kin manta, shinr kika sake yarda da wani salon, Nana kin manta da halin mu maza, Nana na sani na cutar dake a rayuwa, nasani ban kyauta miki ba, dan Allah Nana ki yi haƙuri, mu mayar da aurenmu, Nana kece zaɓin rai na, kece nake so, Nana na tuba bazan sake ba, Nana kin soni tun da ƙuruciyarki, Nana kar da ki tauye zuciyarki.” Legendspen 08129553971. SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na ashirin da uku. Shiru na yi ina kallon Sardauna, tabbas shima da irin salon da yazo kenan lokacin da zai auri Bilkisu, idan haka ne Turaki ma da hakan ya yi amfani kenan, me ya sa ni bazanyi hankali ba ne? Ya sake karyar da muryar sannan ya ce. “Nana, nine na lalata miki mahaifa, Nana ni zan iya ci gaba da zama dake ba tare da na yi miki gorin haihuwa ba, Nana nagane duk wani abu da na yi, na kasance mugu, marar imani, marar adalci Nana, amma wallahi na tuba, dan Allah kar ki auri Turaki Nana, ki zaɓe ni, zan zauna dake, bazan ƙara aikata miki wani abu daban.” Na yi shiru, jikina duk ya yi sanyi, ina ƙoƙarin na tuna zuciyata na ji ko akwai guntuwar soyayyar Sardauna, sai dai babu ko ɗis, kamar ba ta san wani Sardauna ba. “Nana, kin same, nimijinki da kike yiwa girki kala kala, kike bashi a baki, Nana kike kai mini ruwan wanka, Nana kike cire min takalmi, ki yi min wanki, ki yi min guga, ni Sardauna ɗan gatanki Nana, duk wannan ya kau, a yau ni zan haɗawa kaina ruwan wanka, Nana abinci sai wanda me aiki ta dafa Nana, wanke da guga sai na kai, Nana a dawo lafiya irin naki na soyayya bana samu, Nana ki yi wa Allah ki barni na ji da wannan, kar ki ƙaramin wani a lokacin da zan ganki ke da Turaki a matsayin mata da miji Nana, Nana bazan iya ɗauka ba, Nana dan Allah ki dawo gareni, zan baki duk wani abu da kike so.” “Ko ban auri Turaki ba, bazan koma wajenka ba Sardauna, sabida kuskure mafi muni da zan sake yi a rayuwata shine sake komawa hannunka, Sardauna biyayyar da na yi maka daman ba zaka sake samun wacca za ta yi maka wannan ba, a lokacin da nake tsaka da yi maka kake ganina na a matsayin banza marar daraja to a yanzu nafi ƙarfin wannan banzar, ni Nana zan zauna na rayu da wanda nake so, na auri wanda nake so, rabuwar da ka yi da ni ya zamemin alherin da ban taɓa zata zo ba, Sardauna idan Allah Ya yi Turaki mijina ne baka isa hakana ba, haka sabida kai bazan qi auren Turaki ba, sabida a yanzu ina sonsa kuma shine daidai da rayuwata, sabida shi ba azzalumin miji ba ne, Turaki ko mata huɗu zai ajiye ina da kyakyawan yaqinin cewa Turaki zai yi adalci.” “Nana!” Ya kira sunana da wata irin tsawa, wacca sai da na firgita, ya fara magana a fusace. “Nana ki auri duka mazan duniya, amma karku kuskura ki auri Turaki.” “Wallahi Sardauna baka isa ka bani zaɓin zaɓar miji ba, haifa ta ka yi?” “Ina jiye miki abinda zai je ya dawo a lokacin da kika auri Turaki.” “Sardauna ba abinda ka isa ka yi min sai wanda Allah Ya tsaramin, sabida haka bana jin tsoro ki shakkar ka.” “Lallai Nana, ki sani a lokacin da kika shiga gidan Turaki da mutun uku zaki yi yaqi, za ki yi da ni, ki yi da kishiyarki, ki yi da danginmu, sabida yands na ɓata ki a ‘yan uwa babu wanda zai so ki.” “Ai ba soyayyarsu nake nema ba ta mijina nake nema, dan haka ka fitar min anan.” “Nana, ni Fahad Ta’ambo nafi ƙarfin na yi miki barazana wallahi, duk abinda na faɗa miki sai ya faru.” Yana faɗin haka ya fice, a lokacin duk saura ‘yan ɗakinmu sun fito sabida yadda suka ji muna haniya, yana fita na fashe da wani irin kuka da sauri suka shigo, suna tambayata. “Nana lafiya? Waye shi? Mene ya yi miki?” Ina kuka na ce da su. “My ex Husband.” “Me ya zo ya yi miki? Na ji yana wani magana aure ne baya so ki sake?” Na gyaɗa kai ba tare da na yi magana ba. “Aikuwa bai isa ba, pls taks it essay Nana, Allah ya baki miji na gari, kina ganin wannan kinsan ba mutumin arziƙi ba ne.” Ni da ke cewa basu da mutunci ashe bata kama ba ne, dan yau yini suka yi a ɗakina suna faman ban haƙuri da rarrashi. Ko da muka yi waya da Turaki ban sanar dashi komai ba, na ɓoye mai sabida ni kaina so nake sai na yi shawara da ‘yan uwnaa akan maganar, domin kamar akwai hatsari a auren Turaki dan Sardauna ba mutumin arziƙi ba ne. Tun daga wannan ranar bansake sa Sardauna a idona ba, Turaki kuma sati da ya zagayo yazo, anan yake ce dani har yau fa yarinyar bata tsaya sunyi ko da magana ɗaya ba, sai na ji kamar na faɗa masa abinda Sardauna ya faɗa, amma sai kwai na ƙyale. Bayan shekara ɗaya. Rayuwa ta shuɗa abubuwa da dama sunja, a yanzu mun shiga shekara ƙarshe a makaranta, kuma zango na ƙarshe gaba ɗaya bai fi sati bitu ya rage mana, mu fara jarabawar ƙarshe, a yanzu na saba da makaranta, makaranta ta sabani, ‘yan ɗakinmu mun fara gaisawa da su, mun saba dan wani lokacin mu kan zauna a falo mu taɓa hira, Turaki dai duk wannan sati biyun sai ya zo, bai tama gajiyawa ba, matarsa kam ya ce yau da gobe ta sa ta fara yi masa magana, amma sama sama, ko girki mai aiki ce ke yi. Haka zan ta lallaɓa shi da nuna masa ya ci gaba da haƙuri da ita, ya matsa na yi nagama karatu, duk da bai ce min yana so na gama karatu ya aureni ba, amma yana cemin ya matso na kammala karatun nan. Yaya Ridwan ma ya sami matar aure, an sa mai rana. Ra’is ma ‘yan watanni kaɗan da suka wuce ya kammala na shi karatun, a yanzu haka ma service yake anan kanon, Yaya Radiya ta haihu a sabon auren nan da ta yi, ta haifi namiji. Sardauna dai duk tsahon lokaci nan ban sake sa shi a ido ba, gaba ɗaya ma cire shi a rayuwata na sake mantawa da shi kamar yadda na yi a baya. Har mantawa ma nake da shi a rayuwata. A yanzu an san fuskaata a makarantar mu daga ɗalibai har malamai sabida yanda nake dagewa a ajinmu, ina cikin ɗalibai guda goma masu hazaƙa a cikin ajin. Sabida yanda na cire komai a raina na durfafi karatu abuna. Mussaman yanzu da jarrabawarmu ta ƙarato, Turaki ma ya ce ba zai sake zuwa ba sai gradution ɗina, su Yaya Radiya sa kowa ma sun ce sai lokacin graduation ɗina, dake a wannan hutun na samu na kwana biyu a gida. Cikin ikon Allah, mu ka fara jarabawarmu ta ƙarshe, a cikin sati biyu muka kammala ta gaba ɗaya, ranar kammalawarmu ‘yan gidanmu duk sun zo har da Hajiya ma, na yi farin ciki na yi kuka sosai da sosai, a lokacin da aka bani certificate ɗina, cikin muryar kuka nake magana. “Alhaji… Alhaji dama ace kana raye yau, kaga ‘yar autarka ta kammala abinda kake so, Alhaji na yi karatun boko da kake so, Alhaji a yau na zama mai riƙe ta kwalin degree.” Babu wanda bai yi kuka ba, mussaman waɗan da suka san wannan shine babban burin mahaifina a kaina, tabbas Turaki ya yi min abinda ba zan taɓa mantawa dashi ba, ya riƙe hannu ya kai ni ga matakin nasara tabbas ya cancani kowace irin sadaukarwa daga gareni. Haka aka ga ma taro a makaranta, daga nan duka muka wucw gidansu Anty Adiza, su Hajiya ba suzo da shirin Kwana ba, amma irin karamci na ‘yan gidansu Anty Adiza sai da suka sa su kwana, Yaya Ridwan da Ra’is hotel suka kama, daman shi Ra’is yana nan yana service ɗinsa. Washe gari muka shirya muka kama hanyar dutse, a raina na yi ban kwana da kano, nasan babu lallai na sake dawowa, ko da zan dawo bazan sake irin wannan zaman ba kusan shekara uku. Amma tabbas na ji daɗin zaman kano fiye da yanda duk zan kwatanta. A haka muka ƙaraso dutse, har gida Turaki ya kawo mu, ana cikin shiga da kaya ya ce da ni. “Nana, ina so mu yi magana.” “To ka shigo ciki mana.” Ya girgiza kai, sannan ya ce. “Daga wajen nan ma, zan wuce gidane.” Dawowa na yi na jingina da jigin motar, ya kalleni ido cikin ido sannan ya ce. “Nana, a rayuwata na kasance mutun mai wani irin tsari, Allah da ya halliceni ya sanya min soyayyar yarinyar da bansan da ita ba, kowa da yake tare dani yasan da wannan soyayyar, Nana.” Na ɗago na kalleshi. “A lokacin da naganki a tare da sardauna a matsayin miji da mata, a kullum addu’a ta ita ce, Allah Ya bani mace mai irin yanayi, ɗabi’a, kamanni, da halaiyarki, hakan shi ya sani nazo gidanku ko Allah zai sa na yi sa’a na sami ƙanwarki, sai naga ashe kece auta. Nana duk yadda zanyi na ɗauke ido na daga kanki, amma Nana na kasa, sabida haka na yi nesa da gidan. A lokacin da nasami labari a wajensu Yaya Radiya kince Sardauna yana nan, a lokacin ban kawo komai a raina ba, sai da na ga halin da kike ciki, Nana na sha wahala, na yi fatan Allah Ya cire miki ciwon nan, a surutan ki na fuskancin komai da Sardauna ya yi miki, Nana na yi alƙwari da burika akanki, kuma Nana na fara cikawa, Nana dan Allah ina son ki aure ni Nana, ina sonki, ina yi miki so mai girma, so na gaskiyya da babu algus a ciki, Nana so guda ɗaya da ba shi da sirki.” Na yi shiru ina sauraren Turaki, tabbas nima nasan ina son Turaki, son da ya goge Sardauna a rayuwata, sai dai ina tsoron sharrin Sardauna, ina tsoron makircin Sardauna. “Nana ki je gida, ki yi tunani.” “Tom.” Na faɗa tare da shiga gida, duka ‘yan gidanmu suna ɗaki banda Hajiya da take tsakar gida. “Nana lafiya?” Ra’is ya tambaya, sai da na zauna na ce. “Ra’is Turaki ne ya ce yana son aure na.” “Kai Alhamdulillah Nana na yi miki murna.” Yaya Rumaisa ta faɗa, Yaya Radiya ma ta ce. “Daman nasani, Nana Allah Ya sanya alheri.” Na yi shiru, kamar kar na faɗa musu komai sai sai kuma suna buƙatar sani domin bani shawara. “Sardauna ya sake zuwa hostel ɗinmu.” Suka juyo su kalleni, na fara basu labari tun daga farko har ƙarshe. lon ya yi shiru, kowa yana saurarena har na kai aya, ina direwa Yaya Rumaisa ta cafe da cewa. “Nifa shi ya sa bana son shiga al’amuran Nana wallahi, yarinyar nan gaba ɗaya bata da lissafi ko kaɗan, idan ba ki sake aure ba dauwama zaki yi a haka, da baƙin ciki da wancan mistiyacin ta dasa miki?” “Ni bama wannan ba, Sardauna da kansa ya ce ba ke yake so ba, ƙuruciyarki yake so kuma ya samu, ya ce yana matuƙar kishinki fiye da kowace halitta a duniya, kuma wannan gaskiyya ne domin ko da mukaje ɗauko ki a gida, ina ganin kallon da yake yi wa Ridwan akan ya taɓaki, kallo ne me cike da kishi, haka ranar da mukaje kwashe kayanki, kinsan dalilin da yasa ya daki wancan mai motar?” Na girgiza kai alamar bansaniba, Yaya Radiya ta gyara zama sannan ta ce. “Sabida da muka zo shiga jikinki ya gogi nasa, ku duka baku sani ba, a lokacin ina ganin yadda Sardauna ya runtse ido, hakan ya nuna Sardauna yaba matuƙar kishinki fiye da yadda kike tunani, to kina tunanin idan ya ji kinyi aure ya zaiyi?” “Baƙin ciki ne zai kashe mitsiyaci.” Ra’is dake tsaye ya faɗa, sannan ya ce. “Ta wani ɓangaren ma, kinsan Sardauna ya tsani Yaya Turaki, a yanda kika faɗa mana ya ce ya tsani ya ga ya mallaki abu Yaya Turaki ya mallaki mai kama da shi, ki tuna gida ɗaya suke da Yaya Turaki, ki hango tashin hankali da rayuwarshi zata shiga idan ya buɗe ido ya ganki a matsayin matar Yaya Turaki Nana.” “Duk wata tsoratarwarsa ta banza ce Nana, idan kina son Turaki to ki so shi, idan zaki iya aurensa ki aure shi Nana.” Yaya Ridwan ya faɗa, na kalleshi sannan na ce. “Yaya kai ya ka gani, a lokacin Sardauna kaga abinda bangani ba.” “Nana a ta Turaki mutumin arziƙi ne, amma Sardauna sheɗani ne, sheɗan ɗin da zai iya wargaza muku zaman lafiya da soyayyarku. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na ashirin da huɗu. “To kawai dai ta amince ma sa kenan?” Ra’is ya faɗa, Yaya Rumaisa ta ce. “Bawai dan abun hannu ba, ko yana kyautatawa gidan nan ba, kawai duba da halaiyya da kamalarsa,ni dai ina ganin Nana ki amince ma sa.” Ra’is ma ya ce. “Nima dai.” “Kai ai ko kowa ce bai amince ba, kai kam zaka amince, kai da uban ɗakin ka.” Yaya Radiya ta faɗa tana dariya, sannan ta ƙara cewa. “Nima dai haka Nana, ga Ridwan ma, saura kuma Hajiya.” “Tom, Allah Ya tabbatar da alheri.” Kowa ya amsa da amin, haka muka yini a gida, sai dare sannan suka fara tafiya, ina son sanarwar da Hajiya kuma ina jin nauyi, ashe ɗan iya ya fesa ma ta, sai da kowa ya tafi sannan ta shigo ɗakin. “Nana ta shi mu yi magana.” Ba musu na tashi zaune, na zuba mata idanu. “Ra’is ya faɗan komai da kuma shawarar da suka baki, tabbas Nana Abubakar ya cika yaron ƙwarai, bani da wani abu na daban da zan faɗa miki sabida ‘yan uwanki sun ruga ni, sai dai na ce Allah Ya sanya muku alheri, ku kuma Allah ya haɗa kawunanku.” Na amsa da amin, sannan na koma na kwanta, washe gari da safe na dinga saka ran kiran Turaki amma na ji shiru, har zuwa yamma shiru. Daman Turaki akwai lafiyar bawa mutun space, zai baka ishashen lokacin da zaka yi tunani ba tare da ya takure ka ba. Har zuwa dare bai kira ba kuma bai zo ba, hakan yasa na yanke shawarar kiran da kai na kawai. Bayan na yi shirin bacci na, na hau kan gado na kira shi a waya, bugu ɗaya kuwa ya ɗauka, ya yi shiru nima na yi shiru, kusan mintuna biyar sannan ya ce. “Ba zaki iya magana ba ne?” Aikuwa kamar jira nake na fara kuka, kukan da ya ɗaga masa hankali ya fara faɗin. “Nana lafiya? Me ya faru ne?” Cikin kukan na ce. “Daga cewa zaka kira ni shine shiru, kwana da kwanaki.” “Ki yi hakuri Nana, na baki ishashen lokacine ki yi tunani, bana son na raba miki hankali Nana.” “Ina nake da nutsuwar da har zanyi tunani, bayan baka nan.” “Ki yi hakuri to, bazan sake ba.” “Yaushe zaka zo?” “Nana akwai labari ne? Kin gama shawarar.” Na ce. “Uhm.” “To Alhamdulillah, me kika yanke?” Na yi shiru, wata kunyarsa ta lulluɓe ni. “Eyh, Nana.” “Na amince.” “Kin amince da auren namu?” Na gyaɗa kai kamar ya gani na, sannan na ce. “Eyh.” “Na ji daɗi Nana, na kuma gode sosai da sosai, Allah Ya bani ikon faranta miki har ƙarshen numfashina.” A raina na ce. ‘Amin.’ A fili kuma na yi shiru. “Nana tunda kin amince, zanje na sami Big Daddy da wannan zancen, nasa baza su amince ba amma ina da hujjar da zata kare ni.” “Wace hujja ce?” “Sister Seemah, ranar da ta zo gidanki ni na kawo ta, bayan na kai mata likita ya yi mata bayanin komai, har da Dr Na’ima sai da na nema.” Na yi shiru ina tuna lokacin, lallai Turaki ya daɗe yana sadaukarwa a kaina. A fil na ce. “Allah Ya bada sa’a.” “Amin na gode.” Daga nan muka katse wayar, na zauna ina tunanin yadda rayuwa take tafiya, na yanda abubuwa suke ta canjawa, a wancan lokacin na shiga wannan gidan a matsayin matar Sardauna yanzu kuma zan koma a matsayin matar Turaki, wannan shi ake kira da juyin waina. Tun da na dawo bansa ƙafa na fita ko ina ba, gashi tsarin karatunmu na MBBS babu wani aikin bautar ƙasa kowanni abu, sai zuwa asibiti koyarwa ayi shekara guda, gaba ɗaya zaman gidan ya isheni, kamar acan yawo nake. Sai da Turaki ya yi sati guda sannan yazo, ko dai bai fito ƙarara ya faɗa min cewar akwai matsala ba, amma yanayin sa duk ya nuna haka, yanda yake magana yana nuna damuwa da ɓacin rai. “Habibty.” Ya kira suna na, na ɗaga kai na kalleshi, sai kuma ya kasa magana. “Ko zamu haƙura ne.” Na faɗa dan ganin yanda yanayinsa zai yi, aikuwa ya ɗago da wata iriyar fusata. “Mene haka kuma? Wane irin magana ne wannan? Kina ganin zan iya rabuwa dake akan wani ƙaramin abu? Yanzu idan kece haƙura za ki yi dani kenan?” Na girgiza kai sannan na ce. “A’a, kawai bazan juri ganin ka a damuwa ba, bazan so alherin da ka yi min ya zama sakayyar sanya ka a damuwa.” “Habibty ba wata damuwa, ƙaramin issue ne, kinsan Mamana ba ta da matsala ba ta da damuwa, ta ƙarɓi abun. ‘Yan gidanmu ma haka, amma su ‘yan gidansu Sardauna suna son su mai da abun wani kala daban, suna so su nuna ni na raba muku aure da Sardauna, Habibty kinsan me?” Na girgiza kai ina kallonsa, ya ce. “Na rasa inda Sardauna ya sami hotona ni dake, a yanzu hoton ya yaɗa shi a cikin ‘yan uwa, ya ce wai cin amanarsa muka yi ni dake, tun kina da aurensa nake bibiyarki, hakan ne ya ja ma ya sake ki.” “To su sun yarda?” “Kinsan Sardauna akwai tsari, ya iya tsara zance da shirya ƙarya, wasu dayawa sun yarda wasu kuma kwata kwata basu yarda ba, amma…” Ya yi shiru, na ce. “Amma me?” “Habibty, masu yarda sun fi yawa.” Hhhhmm, na sauke numfashi, a raina na ce. ‘Allah ka tsinewa Sardauna, wannan wane irin makirin mutum ne haka?.’ “Nana ni al’amuran Sardauna suna ban mamaki, ƙaramin abu ya mayar dashi babba, da sanina ban taɓa yi wa Sardauna wani abu da zai cutar dashi ba, amma ya ɗauki tsanar duniya ya ɗoramin.” “Ka bari kawai, ni zan faɗa ma Sardauna ya tsaneka, amma bata halinsa za a duba, yanzu abinda yake gabanmu shi kawai zamuyi.” “Nana, yanzu gobe zanje Abuja wajen Granny, za mu yi magana da ita, Big Daddy ya ce, ko mene ya faru tsakanina da ke, a lokacin aurenku da Sardauna mu da Allah, amma a yanzu tun da babu auren Sardauna kan ki a addinance zan iya aurenki, kuma su baza su ja da faɗar ubangiji ba, sai dai baza su kawo abinda zai raba kan zaman lafiyar ahalinsu ba. To Habibty idan kika duba wannan zance nasa, aure na dake duk ba matsala ba ne, amma baza su so a wargaza musu zaman lafiyar gida ba.” “Eyh nagane, amma yanzu idan ka je Abuja ɗin me zaka ce da ita?” “Nana tasan maganar tuntuni, ina tunanin idan ta ce da su ta amince babu wanda zai ƙara ja da maganar a cikin familyn.” “To dan Allah ka tafi yau, kasan Sardauna mugun mutum ne, wallahi idan ya fuskanci baka da wani abu sai ita, tsaf zaka sameshi a gidan.” Ya yi dariya, sannan ya ce. “Nana kin fahimci Sardauna gaba ɗaya.” “Uhm, to kasan aina ya sami hotonmu?” Ya girgiza kai, na ce. “Duk motsinmu yana bibiya, na taɓa kama mai bawa fulawa ruwa na hostel ɗinmu yana mana video ni dakai.” “Kai! Habibty, amma baki faɗan ba?” “Na yi tunanin na magance matsalal, ashe da saura.” “Lallai Sardauna, ina ga fa yanzu zan bi flight zuwa Abujan nan.” “Eyh, sannan duk yadda aka yi ka sanar da ni.” “Tom, Habibty.” Ya faɗa tare da tashi, nima na tashi na bi shi har ya shiga mota, sai da ya shiga motar na ce. “Kuma yanzu ƙarfe nawa zaka isa?” “Kafin biyar?” “To Allah Ya tsare, Allah Ya kai ka lafiya.” “Amin Habibity, na gode.” Yana faɗin haka ya ta da motar ni kuma na koma ciki, na shiga kicin na ɗaura girki. Wani abu da na koya a gidansu Anty Adiza shi zanyi wai sunasa Alkubus, da miyar taushe ko ganye a cikinsa. Ina shiga na auni fulawa na sama ta yest,gishiri da ɗan suger, na kwaɓa shi da ruwan ɗumi na rufe shi na ajiye, daidai lokacin almajirin mu da na aika ya kawo min kayan da na aike shi siya, yana tsayw na haɗa masa kayan ya tafi kai markaɗe. “Nana, yau me zaki dafa mana ne, tuwo zaki yi ko masa?” Hajiya ta faɗa tana fitowa daga ɗaki, na ce. “A’a, wani abu ne na ‘yan kano.” “Ke wai komai sai kece na ‘yan kano, na ‘yan kano, mu nan bamu da kayan fulawa ne?” Na yi dariya sannan na ce. “To acan na fara gani Hajiya.” “Allah Yasa ma ya yi daɗi, ba tsarabe, tsaraben su ba ne.” “Zai ma yi.” Na faɗa tare da komawa kicin ɗin, sai wajen karfe shida na kammala komai, daidai lokacin kuma na ɗauki waya na kira Turaki, amma bai ɗaga ba. Sai bayan anyi magriba sannan ya kira ni a waya, ina ɗagawa muka gaisa, sai dai na ji muryashi ba daɗi. “Me ya faru kuma?” “Habibty kinsan wani abu?” Na ce. “A’a, sai ka faɗa.” “Kinsan Sardauna jiya ya bar gidan nan.” “Toopa.” “Amma dai ta ce, wai zata duba al’amarin, ina ga yau zan sake dawowa.” “A’a ka bari dai ka kwana, ka sake kwantar mata da kai, ka yi mata bayani sosai ƙila a samu a dace.” “Habibty kenan, Allah Yasa.” “Amin-amin.” Na faɗa, daga nan muka taɓa hira, ina kwantar masa da hankali, ina nuna masa komai zai zo da sauƙi, sai dai ni kaina ina tsoron ɓata ni da Sardauna ya yi a ‘yan uwansu, a haka zan shiga gidan idan komai ya daidaita, ana yi min wani gani na daban? Duk sai na ji jikina ma ya yi sanyi, al’amrin ma ya fita a kaina baki ɗaya. Har Turaki ya dawo daga Abuja, babu wata ƙwaƙwarar magana daga Granny, haka ya dawo jikinsa ba ƙwari, Sardauna ya shiga ko ina, ya fita ya ga ya daƙile al’amarin. Ni da kaina nake tausayin Turaki, dan yana cikin wani hali, duk inda zai bi Sardauna ya bi ya toshe, duk hanyar da yasa ƙafa, sai ya ga Sardauna a wajen, ya zame masa annoba, ya zame masa ƙarfin ƙafa, a kullum iƙirarinsa shine ba zai barshi ya auri Nana ba, yaje ya auri duk matan duniya amma banda Nana. Ni ko tun da na dawo ban sake sa Sardauna a idona ba, kuma ban damu ba, ganin zaman yana ta ja ne yasa na yi magana da Turaki akan na fara zuwa asibitin koyarwa, tun da dai ko munyi auren dai zanje. Cikin kwanaki kaɗan aka sami asibitin aka yi komai na fara zuwa. Tun zuwa na asibitin Allah Ya haɗani da wani likita Dr Aliyu, matashine baifi sa’an su Turaki ba, kuma ba shi da aure. Tun zuwana asibitin yake shige min, tun bana ba shu fuska har na fara bashi fuska sabida na fuskanci shima yana da kyawawan ɗabi’u. Yana taimakamin sosai wajen ayyukana, yana nuna min abinda zanyi da wanda ya shige min duhu, ba ruwanshi da hayaniya mutum ne shiru shiru, duk da bansan asalin sa ba amma nasaan daga babban gida yake, kuma ya sami tarbiya ta mutunci, dan wata rana har gida yakan dawo da ni a motarsa. A kwana a tashi na ci wata huɗu a asibiti, ba auren Turaki ba zancen auren, kullum abubuwa ƙara cakuɗewa suke, duk wata hanya Sardauna ya bi ya hana, Sardauna ya cika shu’umi, kuma mugun mutu, ni a yanzu gaba ɗaya al’amarin ma ya fara fita a kaina, ba wai dan na daina son Turaki ba, sai zallan tausayinsa dake cin raina, gaba ɗaya ya fita hayyacinsa, abubuwan sun masa yawa kuma ya kasa saduda, a kullum cemin yake. “Habibty, duk tsanani duk wuya, ina tsaye akan al’amarin nan, indai ubangiji ya tsara akwai aure a tsakaninmu, to zan aureki. Wani ƙi da duk wani abu na mutane bazai sa na janye ra’ayina ba Habibty.” Ni kuma hakan yakan haifar min da tausayinsa a cikin zuciyata, har ba kanji gwanda ma mu haƙura, mu janye zancen auren. Mussaman a yanzu da Dr Aliyu ya shigo rayuwata, sai nake jin kamar shine mijin da zan aura, tabbas nasan banda wahalal faɗawa soyayya, shi ya sa babu wahala nake shan azaba a soyayya, amma tabbas a matsain nan da Turaki yake ciki, tausayinsa zai haifar min da gagarumar soyayyar Dr Aliyu, ko dan Turaki ya huta, sai dai kuma idan na yi haka burin Sardauna ya cika a kaina. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na ashirin da biyar. Cikin ƙanƙanin lokaci muka fara sabawa da Dr Aliyu, har gida ma suka san shi, duk da bai sami karɓuwa a wajen ‘yan gida ba, amma ni dai ya yi min, ya kan ɗebemin kewa sosai. Mussaman a yanzu da idan na kira Turaki bama samun dogon lokaci muna waya, sai kawai na kira Dr Aliyu, sai mu shafe awa guda ko fin haka muna waya dashi, haka a asibiti duk lokacin break muna tare. Yawan zuwan da yake yi ne ya sa Hajiya ta yi min magana a kansa, na ce mata a asibitinmu yake, sai kuma ta tambayeni Turaki na ce mata yana nan. “Nana, idan wani abu ne ya faru ya kamata ki sanar da mu.” Na ce. “Hajiya ba komai fa, shi wannan a asibiti yake, kuma yanzu muna samun lokaci tare da shi sosai, saɓanin Turaki da yanzu al’amuran kamar ansa hannu, sai mu daɗe ba mu yi doguwar magana ba.” “To Nana ki yi masa uziri mana, kinfa san abinda yake faruwa, da kanki kika ce akan ki yana fama da ‘yan uwansa.” “Hajiya, nifa ba wai son sa na daina ba ko auren sa na fasa, kawai na duba mana mafita a tsakanin ni dashi, bazan so ya ci gaba da kasancewa cikin matsala ba akaina, kuma wannan ai Hajiya ba cewa ya yi yana sona ba ko.” “Nana kenan, yanzu ke kina nufin baki fahimci soyayya ce a tsakanin ku ba ko me?” “Ni ban fahimta ba.” “Shikenan Nana, amma dai karki zama mace mai sonkai, da rashin uzuri. Kinsan dai abubuwan dayawa da yaron nan Abubakar ya sadaukar akan ki, ke da kan ki kinsan har yanzu yana fama da abubuwa duk sabida ke, amma kina son ki nuna bazaki iya yi masa haƙuri ba.” “Nifa Hajiya duk baku gane komai ba ne, amma ba haka nake nufi ba.” “Ni dai tunatarwa na yi miki.” Tashi na yi na shige ɗaki, gaba ɗaya maganganun Hajiya sun tsaya min a rai, kuma gaskiyya ta faɗamin sai dai ni ina cikin nau’in mata masu son soyayya da kulawa, a yanzu Turaki duk ya janye daga gaisuwa shikenan, idan kuma ya haƙura zai yi wa iyayensa biyayyane fa, nima ai gwanda na haƙura dashi kaman zaifi. Daidai lokacin kuma kiranshi ya shigo, na ɗaga tare da faɗin. “Salamu alaikum.” “Amin wa’alaiki salam, Habibty ya kike?” “Ina lafiya ya kake?” “Nima lafiya, ya su Hajiya.” “Duka suna lafiya.” “To Ma sha Allah, Habibty ina ƙara baki haƙuri akan yanda abubuwa suka canja, nima ba a so na ba ne, na ɗan ja baya ne sabida wasu dalilai, kuma in sha Allahu a gaba zaki fuskance su.” “Ba matsala, amma dan Allah Turaki idan ka fasa aure na ne ka faɗamin.” “Habibty mene haka wai? Na fasa aurenki kuma? Kina tunanin zan fasa aurenki akan wani abu? Dan Allah ki daina wannan zancen.” “Shikenan na daina, yanzu yaushe zaka shigo?” “In sha Allah zanzo.” “Ai kullum haka kake cewa.” “Nasani, amma zan zo.” “Tom.” Kawai na faɗa tare da kashe wayar, ni gaba ɗaya yanzu babu wani shauƙi a tattare da shi, anya ba daina sona mutumin nan ya yi ba. Ban kai ga amsa tambayar da na yi wa kaina ba kira ya shigo wayata, ina dubawa naga Dr Aliyu. Shima raina ba daɗi na ɗauka da faɗin. “Hello Dakta.” “Nana, ya gida?” “Lafiya ƙalau.” “Me yake damunki ne?” “Babu komai mai ka ji?” “Haba Nana, gashinan muryarki ta nuna damuwa.” Tashi na yi zaune daga kwanciyar da nake, na ce. “Kawai raina ne ba daɗi.” “Ayyah! Ki yi haƙuri kin ji ko, Gobe zaki shigo ko?” “Eyh, in sha Allah.” “To ko zan iya ganinki kafin ki shiga dan Allah, magana ce nake so mu yi mai muhimmanci.” “Tom shikenan, babu damuwa Allah Yakaimu.” “Amin Nana.” Daga nan muka ɗan taɓa hira, amma da yake raima duk ba daɗi ban wani jin daɗin hirara ba. Washe gari, ina zuwa asibiti na wuce ofis ɗinsa na same shi, duk na matsu na ji me zai cemin. Bayan na zauna ya kalli ni ya ce. “Nana.” Na ce. “Na’am.” “Nana, tun a zamana dake baki taɓa tambayar wani abu game da ni ba, rayuwata, iyayena da ‘yan uwana, ina da aure ko babu?” Na yi shiru, nasan tabbas ban taɓa amma ganina ai tun da zama ne na lokaci kamar babu buƙatar wannan. “Kinyi shiru?” “Eyh gaskiyya ban taɓa ba.” “To me ya sa? Nana kinsan yanda na ɗauke ki kuwa?” Ji na yi gabana ya yi wani irin bugu dum, na ɗago na kalleshi, ya gyaɗa min kai, sannan ya ce. “Nana na ɗauke ki da wani irin muhimmanci tun ranar da na fara ganinki, Nana tun bayan rasuwar matata Amina, bansake kallon wata mace da irin kallon da nake miki ba.” Na ɗago na sake kallonshi da wani irin tausayi. ‘Matarshi mutuwa ta yi kenan?.’ Na faɗa a raina, sai dai ya ban amsa da cewa. “Eyh Nana, Amina ita ce macen da na fara so tun muna makaranta, munyi soyayya mai daɗi, kuma munyi aure duk da mun fuskanci ƙalubale da dama, amma Nana hakan baisa mun janye soyayyar da muke wa junanmu ba, har Allah Ya nufe mu ga aure, mun fara rayuwa cikin soyayya Nana har Allah ya albarka ce mu da samun juna biyu, da gani har ita munyi murna, munyi farin ciki. Sai dai bamu san wannan juna biyun shine zai zama ƙarshen farin ciki a tsakanina da ita, lokacin da Allah Ya nufe da haihuwa lokacin ne kuma Allah Ya amshe ta a lokacin haihuwar, ta mutu ta barni da jarariya, wacca na mayarwa da sunanata. Nana tun a lokacin ban sake jin wata mace ba, bansake ganin wata mace ba, sai a yanzu da na ganki, Nana na kamu da soyayyarki me zafi, ki taimakamin Nana, wallahi ina sonki, Nana ko yanzu kike so zan aureki, Nana ba wasa nake miki ba.” Na yi shiru, jikina duk ya mutu, wani irin tausayinsa ya ratsa zuciyata, mutuwar mata a lokacin haihuwa tabbas abube mai tsayawa a rai. “Nana.” Ya kira sunana, na ɗaga kai na kalleshi, ya ce. “Nana ko kina da wanda kike so ne? Nana ko banyi miki ba?” Na girgiza kai, sannan na ce. “Ba haka ba ne, nima na taɓa aure, amma Allah bai nufi auren da kasancewa na har abada ba, duk da ba haka na so ba, amma Allah bai nufa ba, na yi shekara uku da watanni.” “Nana, ni ke nake so, nasan gidanku, nasan tarbiyar gidanku, Nana duk wani abu da ya faru a rayuwarki ta baya, ya riga da ya faru, sanin shi a gareni ba zai canja komai ba, Nana dagaske nake sonki, Nana ko a satinan ne a ɗaura mana aure.” Na girgiza kai alamar a’a, kafin na yi magana ya ce. “Nana, ba aiki ba ne, ni zan dage wajen sama miki aiki, Nana ina da ilimin addini, ina da na zamani,ina da wayewa, nasan abinda yake mai kyau nasan mara kyau Nana.” “Ba haka ba ne, akwai wanda a yanzu yake nuna yana sona, kuma shina aurena zai yi, sai dai yana da matsala ta ahalinsa.” Ya yi shiru na kusan mintina goma, sannan ya ce. “Nana, bazan tursasaki ba, ba kuma zanm raba miki soyayyarki ba, amma Nana ina sonki da gaske da zuciyata, Nana ki tausayamin, ki yi tunani a kaina, Nana ko ba ni ba ki duba yarinya ta ƙarama dake cikin halin maraicin rashi uwa, Nana nasan zaki kula da ita, zaki so ta tamkar yadda mahaifiyarta za ta yi Nana.” Wani ƙarin tausayin naji ya lulluɓe ni, tabbas ina son Turaki, amma ni kaina zan so masa zaman lafiya da iyayensa, na duba Dr Aliyu, da yarinyarsa, suna matuƙar buƙata ta a rayuwarsu. “Nana, dan Allah ki duba, bana son na takura miki, amma bana son na yi sanyi na rasa ki Nana, dan Allah.” “Shikenan, zanyi shawara.” Na faɗa, sabida zuciyata gaba ɗaya a cakuɗe take. “Shikenan Nana, na gode.” Na tashi na fito, kai tsaye gida ma na nufa dan bazan iya zama cikin asibitin ba, sabida wani irin nauyi nake ji a zuciyata, dole na yi tunani na yi shawarar. Sai dai ko da naje gida kasa maganar na yi da Hajiya, ga Ra’is bayanan, ga Yaya Ridwan babu fuskar ma da zamuyi wannan maganar da shi, Yaya Rumaisa kuma ba a maganar arziƙi da ita, gwanda Yaya Radiya ma. Haka na yini raina ba daɗi gaba ɗaya, sai dai a wannan yinin Dr Aliyu ya kirani sama da sau biyar ya ce wai ina lafiya, kar na takura kaina, kar na damu, na yi tunani a nutse, Turaki kam ko da na kira shi na ce yaushe zai zo sai ya ce idan zai zo zai yi min magana, har dare ina faman tunanin da narasa mafita, haka na kudirci niyar tashi cikin dare na yi sallah, dab da zan kwanta na saita alam ya tashi ne ƙarfe uku da rabi na dare, sannan na kwanta. Ƙarfe uku da rabi alam ɗin ya fara ƙara, na kusa minyi sha biyar a kwance kafin na tashi da ƙyar, gaba ɗaya ban iya tashi cikin dare ba, shi ya sa yau ɗin ma nakasa, ba ƙaramin mamaki na yi ba ganin Hajiya a tskar gida tana sallah. “Allah Ka bani ikon tashin daren nan nima.” Na faɗa ina nufar bayi, sai da na ɗaura alwala na fito, na leƙa ɗakin Yaya Ridwan ta taga na ganshi shima zaune kan abun sallah, na ce. “Ikon Allah, ana ta ibada ina ta bacci, dole ma abubuwa sun caɓemin.” Ɗakina na dawo na ɗauki abun sallah na shimfiɗa na tayar da sallah, sai da na yi raka shida, sannan na ta fara addu’a, sai da na yi addu’a sosai da sosai, sannan na koma bacci na, sai dai ban daɗe da kwanciya ba aka yi sallar asuba. Gari na wayewa na sake samun kiran Dr Aliyu, na ɗaga tare da faɗin. “Ina kwana.” “Lafiya ƙalau Nana, kintashi lafiya?” “Lafiya ƙalau Alhamdulillah, Ya gida, Ya little? Sunan da na ji yana cewa da ‘yar sa.” “Kinganta yanzu nake son tashinta, yau zaki shigo?” Na ce. “A’a.” “Me ya sa? Ko na takura miki?” “Ba haka ba ne, kawai sai gobe.” “To ni kam bazan iya, zan zo na ganki idan kin amince.” “Tom, Allah Ya kawo ka.” “Amin, zan gwada naga idan zan iya jira a tashi daga asibiti, idan bazan iya ba kam zaki ganni da yamma.” Na yi dariya sosai, sannan na ce. “Tom, sai ka zo.” “Yawwa Nana, na gode sosai.” Komawa na yi na kwanta bayan ya kashe wayar, gaba ɗaya tunani nake yi na yadda zan iya rabuwa da Turaki, idan na ɗauki Dr Aliyu. Gaskiyya ina son Turaki duk da kwana biyu ba mu yi wata magana mai tsawo ba, amma wani irin kewarsa nake yi sosai da sosai, shi kuma Dr Aliyu tausayinsa kawai na ke yi, amma kuma a yanzu kullum yana raina, mussaman jiya da yau da safe, shi ka ɗai nake yi tunawa. ‘Yanzu Nana, duk sadaukarwar Turaki zata tashi a banza? Nana ki yi tuani?.’ Na ji zuciyata ta tambayeni, a gaskiyya na bawa Dr Aliyu haƙuri na jira Turaki. ‘Amma jiran har yaushe?.’ Wani ɓari na zuciyata ya sake tambayata. Haka dai na yi ta faman tunani na rasa matsaya guda ɗaya, har yamma ina ta faman tunani, har Hajiya ta tambayeni me ya sa yau ban fita na na ce bana jin daɗi, wajen ƙarfe huɗu Dr Aliyu ya kirani, ina ɗagawa ya ce. “Nana, gani a waje.” “Tom ina zuwa.” Na faɗa tare da miƙewa, gyale na ɗauka na yafa na fice, bayan na ɗan gyara fuskata. A tsyae na sameshi daga jikin bango yana kallon ƙofar gidanmu, na sakar masa murmushi tare da faɗin. “Har an tashi?” Ya girgiza kai, ya ce. “A’a fa, banza iya jira ba ne, sai naga kyakywar fuskar da ta ƙwamushe mun rayuwa gaba ɗaya, Nana gaskiyya kin kamani, kin kamani, na rasa inda zan sa raina sai inda kika ajiye ni.” Na yi wani irin murmush, daban san daga inda ya fito ba, na buɗe baki da niyar magana na ji ƙarar tsayawar mota, ina waigawa na ga Turaki ta cikn mota yana kallona, Wani irin abu na ji ya tsargamin har tsakar kaina. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na ashirin da shida. Juyawa na yi na kalli Dr Aliyu, na ga kamar bai kula da shi ba, na sake juyawa na kalli Turaki sai na ga ya sake wani murmushin, ya ja motarsa ya yi gaba. Sai a lokacin ya ce. “Ko wannan ne?” Na gyaɗa kai, ba tare da na ce komai ba. “Ayyah, amma ya naga ya juya, ko ya haƙura ya barmin ne?” Na yi shiru kawai, danni gabana wani irin faɗuwa yake yi, ya Turaki zai tafi ba zai tsaya ya yi min magana ba. “Nana na ga kin damu sosai?” “Ai ka ga ba zai ji daɗi ba.” “Hakane kam Nana, amma na fuskanci mutumin nan ƙafa zai min a wajenki, dole na ƙara zubawa fulawata ruwan soyayya.” Na yi murmushin da iyakarsa fatar baki. “Haba Nana, ki kalleni mana, ko na tafi?” Na ce. “A’a.” “Amma hankalinki fa yana kasan gaba ɗaya Nana, kin manta dani.” “Ba haka ba ne, ya yi min abubuwa dayawa a rayuwa, ko da zan rabu dashi bai kamata ta haka ba.” “To ai ya rage miki aiki Nana, kawai ki ƙyaleshi.” Na girgiza kai alamar a’ah, ban jin zan iya fa. Duk hankalina ya yi na kira Turaki na ji me zai ce, haka Dr Aliyu ya yi ta surutansa ya tafi, ina shiga gida na kira wayar Turaki amma bai ɗauka ba, na kira shi yafi sau talatin amma bai ɗauka ba, daga baya ma sai ta koma sa user busy, haka na yini ina faman kiran Turaki amma shiru, har washe gari ma wayar Turaki ba ta shiga, na kusa sati ina faman kiran wayar ba ta shiga, na yanke shwarar kiran Ra’is na tambayeshi ko suna magana. Ina kiran sa ya ɗaga, bayan mun gaisa na ce. “Ra’is yaushe zaka dawo?” “Mun kusa gamawa, ya aka yi?” “Bakomai Ra’is, kuna waya da Turaki dai ko?” “Eyh, ɗazu da safe ma ya kira ni, munyi magana sosai har kudi ya tura min.” “To ma sha Allah, sai anjima.” “Lafiya dai ko?” “Eyh lafiya.” Na faɗa tare da kashe wayar, a lokacin na sake buga wayarta shi ma bata shiga, zuwa dare ma kuwa na ji suna waya da Hajiya a wayar Yaya Ridwan, a hankali dai na fuskanci daman Turaki neman hanyar rabuwa yake dani sai kuma wancan abun ya faru, shine ya samu hanya. A hankali na fara haƙura da Turaki na ci gaba da bawa Dr Aliyu dama har ya kan zo gida yanzu, duk da su Hajiya sun fuskanci na yi sabon saurayi amma babu wanda ya ce min komai, nima ganin haka ya sa na saki jiki da shi, ranar nan ma da na kira Yaya Rumaisa sai ta ce. “Allah Ya sanya alheri.” Ganin haka ya sa na fara ture Turaki ta ƙarfi a zuciyata na ɗauko Dr Aliyu na fara sanya shi, a kullum idan na je asibiti muna tare, safe rana, har gida yake dawo da ni, mun saba dashi ba laifi, sai dai har yanzu bai taɓa bani little munyi magana ba duk da irin takura masa da nake yi akan haka amma ya gagara. A kwana a tashi har muka ci wata uku, Ra’is ya dawo an fara cuku-cukun nema masa aiki wanda Turaki ne yake yi, duk da bama tare, yazo gida wajen sau biyu kuma ko kallona ba ya yi, hakan ya ƙara tabbatar min da cewar Turaki daman neman hanyar rabuwa yake da ni shine ya samu, ranar da ya fara yin banza da ni haka na shiga ɗaki na yi ta kuka, sai da Ra’is ya shigo ya sameni ina kukan. “Nana lafiya?” “Ra’is kalli Turaki kamar bai sanni ba.” “Ya sanki mana, kawai ya ƙyale ki ne sabida kin nuna a yanzu ba kya buƙatarsa.” “Shi ya fara nuna haka, amma ai a yanzu ko kallona ya yi dai.” “Kina da rigima Nana, idan ya kalli ki kice ya kalleki, yanzu bai kalleki ba kin ce bai kalleki ba, mene haka Nana?” “Tashi ka fita.” Na faɗa a fusace, ba musu ya miƙe ya yi waje, yana fita na koma na kwanta na ci gaba da rera kukana, daga nan bacci ya ɗauke ni, ko sallar ma ban tashi ba, daman ban saba ba, tun dai bai fi sau biyu na ta shi ba. Watan mu biyu muna soyayya da Dr Aliyu, a zuwa yanzu na gama yankewa shi zan aura, yanda Turaki ya fita sabgana nima na fita na shi, dan a yanzu har gidan ya kan zo amma ko kallona ba ya yi, sai dai ni da zarar yazo idan na shiga ɗaki bana iya fita ko aina har sai ya tafi, sai dai wani ƙwaƙwaran uzuri. Dr Aliyu kam na gama fahimtar halayensa mutum ne mai kyan hali da nagarta, son kowa ƙin wanda ya rasa, na gama mallaka masa rayuwata sai dai har yanzu a iya baki na ke jin sonsa babu a zuciyata, amma a haka na yanke zan aureshi, ko sabida yarinyarsa wadda ya ce a yanzu tana wajen dangin Mamanta, kallonshi na yi yana sanye da milk din yadi yasa hula coffe, waya yake dannawa ni kuma na zuba masa ido a cikin motar da muke. “Nana, yanzu yaushe ya kamata ayi maganar aurenmu, nifa bana son jan lokaci, ko wancan mutumin bai janye ba ne?” Ya yi maganar lokacin da ya gama danna wayarsa ya sanya ta a aljihu, na kau da idona daga kallonsa na ce. “Ko yaushe kawai ka yi magana, Turaki kam ai tuntuni ya janye.” “Ki ce ya barmin mallakina, daman ke tawa ce.” Na yi murmushi kawai, shi kuna ya sake cewa. “Maganar gaskiyya Nana, bana son auren nan ya ɗau lokaci, dan haka zan sanar da Hajiyata, idan ta amince ma zan kawo mata ke, ku gaisa. Nana ina son ko kasance kamar ‘ya da uwa, ko fahimci juna, Nana Hajiyata ba ta da wata matsala, kuma naga kema baki da matsala.” “In sha Allah, zan zauna da ita, na yi mata biyyayya, dan itama ta wa Hajiyar ce.” “Hakane Nana, na gode sosai da sosai.” “Badamuwa, little kuma zata sami uwa wacca zata kula da ita, in sha Allah ba zata taɓa kukan maraici ba.” Ya yi wani murmushi, me nuna tsantsar jin daɗi. “Nana, bansan a wane sahun mutane masu nasara zan sanya kaina ba, domin tabbas samunki ba ƙaramar sa’a ba ce.” “Kaima haka ai.” Na faɗa kaina yana ƙasa. “yanzu idan kin shiga sai ki yi maganar da ‘yan gida, ranar da muka je muka gaida Hajiyata, sai muje gida yayunki ko?” “Eyh hakan ya yi, amma akwai bikin Yaya Ridwan da za ayi nan da sati ɗaya, ko zamu jira a kammala.” “To Nana, hakan ma ya yi, amma yaushe aka sa bikin baki sanar dani ba.” “Eyh da yake abun lokaci ɗaya yazo, jiya ma aka sanya lokacin auren, amma tuntuni anyi musu enagagement.” “To, Allah Yasanya alheri.” Na amsa da amin, bayan mun gama hira na koma gida, ɗaurin auren ne ya zo ba shiri gaba ɗaya, ko kayan da ake kawai ma sai ranar ɗaurin auren aka ce za a kai. Gaba ɗaya gidan namu ya fara kacamewa sa hada hada, duk munyi bizi da shirye shirye, su Yaya Rumaisa kullum sai sunje kasuwa, ita da Yaya Radiya, Hajiya tasa an kaiwa Hajja komai na kayan abinci wanda za ta yi taron bikinta da su, duk da shagon Alhaji aka ɗeba, shagon da a yanzu ya zama plazar siyar da kayan abinci. Ranar da Ra’is ya kai mata kayan sai ga ta da kyautar dubu biyu ta bashi, kuma ta yi ta sawa auren albarka, sabida abanta kayan abinci. Shirye shiye sunyi nisa sosai da sosai, mu anan ɗaurin auren ne kawai za ayi sai yini da Hajiya za ta yi ranar, su acan ne zasu yi dinner da sauran abubuwa, mu dai munce ba zamu komai ba, namu na ranar asabar ya wadatar, munyi ɗinki kala ɗaya wajen guda uku, bayan shaddarar da zamu sa da safe wacca mukayi iri ɗaya har ango da Ra’is da yaransu Yaya Radiya da Yaya Rumaisa. Tun ranar alhamis suka fara bikinsu, amma mu nan gida ba mu yi komai ba sai ranar da aka yi ɗaurin auren, gidan ya cika ya batse da mutane, har Dr Aliyu sai da ya zo, a ranar ya takura na gabatar da shi ga ‘yan gidan, duk sun amsheshi amma ba yadda suka yi wa Turaki ba, haka aka yi shagali aka watse, kowa ya tafi aka barmu a gida. Washe gari lahadi su Yaya Rumaisa ma suka wuce, aka bar mu da gani sai Hajiya da Ra’is, a raina na ce. ‘Yanzu da na yi aure, shikena za abar hajiya da Ra’is, shima da ya yi aure sai abar ta ita kaɗai. Daman haka rayuwa take.’ Ranar monday Dr Aliyu ya ce da ni ranar laraba na shirya zuwa gidansu, amma na faɗawa su Hajiya, idan da yarinya ma ko yaro me wayo a haɗani da shi, na yi dariya sosai a lokacin na ce. “Wannan ai sai kace an nuna maka rashin yarda.” Shima ya yi dariyar bai ce komai ba, a ranar nasanar da Hajiya ta ce. ‘Allah Ya kaimu.’ Daga nan ba ta sake ta da zancen ba, a haka ranar laraba tazo na shirya zuwa gidansu Dr Aliyu, doguwar riga na sanya ta atamfa, na ɗau babban mayafi na sanya abuna, na fito a babbar mace. Hajiya na tsakar gida na ce da ita zan tafi. ‘Adawo lafiya.’ Ta faɗa kawai ta ci gaba da abinda take, in fitowa na shiga motarshi muka nufi unguwarsu, tun da muka shiga unguwar nani gabana yana faɗuwa, ya kalleni ya ga yanda nake rufe ido ya ce. “Nana, ki daina wani jin tsoro, Hajiya ba abinda za ta yi miki.” “Ba tsoro nake ji ba, kawai ji na yi gabana yana faɗuwa, bugun zuciyata yana daɗa ƙarfi.” “To duk kinsa tsoronta a ranki, Hajiya fa tana da sauƙin kai fiye da tsammaninki.” Na yi shiru kawai, ya ci gaba da tuƙinsa har muka ƙarasa gidan, da kanshi ya buɗe gate ɗin sannan ya dawo ya shiga da motar, ko da ya yi fakin kasa fitowa na yi. “Wai Nana duk mene haka? Kina tunanin zata dake ki ne?” Na girgiza kai, sannan na ce. “A’a.” “To kuma, ki fito.” Fitowa na yi, ta rufe motar muka fara tafiya, gaba ɗaya kamar ina tausayin ƙasa haka nake taka ƙafar, buga ƙofar falon ya yi amma sai ya ganta a buɗe, ya murɗa ya shiga nima na bi bayanshi. Babban falo ne mai girma, a gyare tsaf yake, ya ji kayan alatu na more rayuwa, an narkar da dukiya, ga wata makekiyar TV na ƙara. “Zauna, bari na yi magana da ita.” Ya faɗa tare da shigowa, na samu waje na zauna na zubawa hanyar da yabi ido, kusan minti uku ya fito, a bayanshi wa zangani idan ba Sardauna ba. A gigice na miƙe tsaye tare da faɗin. “Hasbunallahu wani’imal wakil.” Dukkansu suka saki wani murmushi a lokaci ɗaya,Dr Aliyu ya kalli Sardauna ya ce. “Abokina ga Assigment ɗinka nan, na kammala.” “Wel done abokina.” Sardauna ya faɗa yana ƙarasowa inda nake, na yi hanyar fita da gudu ya ce. “Tsaya Nana, ko kinfita ma baki da hanyar guduwa.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na ashirin da bakwai. “Sardauna me na yi maka ne? Me ya sa kake min hak? Wane zalunci ne wannan?” Na faɗa, ina goge ƙwallar da ta fara zubo min daga ido, ya yi murmushi sannan ya ce. “Nana, ni Sardauna shu’umin namiji ne wanda baki isa ki tsira daga komata ba, Nana bana sonki ma na bibiyi rayuwarki bare kuma yanzu da na yi imanin cewa ina sonki, duk yadda zanyi yaƙi da zuciyata na yi na kasa Nana, ta dole na yarda ina sonki bisa tsautsayi, na ce miki ba zaki auri Turaki ba, kin na ce kin yi kunnen uwar shegu ko?” Ya ƙarashe maganar da wata irin tsawa, wacca ta ƙara firgitani. “Duk wata hanya da Turaki zai bi ya aureki, sai da na bi na toshe ta, amma ya nace sabida shi maye ne ko, wallahi Nana har abada idan ban mallake ki ba, babu wani namiji da zai mallaki.” “Allah Ya isa Sardauna, Allah Ya saka min, mugu.” Ya yi dariya, sannan ya ce. “Lokacin da kika fara zuwa asibitin koyarwa, Dr Aliyu da kansa ya ganki, ya sanar da ni ya ganki, na ce ya dinga bibiyarmin ke, daga baya na yi tunanin na yi amfani da shi nasa shi ya tursasaki korar Turaki da kanki, ko za a samu ya ƙyaleki, duk wani tarihin shi da ya faɗa miki ƙirƙirarren labari ne daga ni Nana, na sa shi ya yaudaro zuciyarki kuma ya yi.” Cikin murya kuka na ce. “Wallahi Sardauna na tsaneka, na tsaneka fiye da kowacce hallita a duniya, kai ba mutum ba ne dabban ne wallahi.” Ya yi wata shu’umar dariya, sannan ya ce. “Ai Nana indai akan ki dauwama baki auri kowa ba ne, to zanyi duk abinda yafi wannan Nana, dan haka ki yi wa kan ki faɗa ki ci gaba da zama a haka, ko kuma ki dawo mu mayar da aurenmu, domin daga yanzu duk wani namiji da zai zo wajenki, kisa a ranki ni na turu shi.” “Har abada Sardauna, har abada bazan sake zaman aure da kai ba wallahi, kuma kana zaune zanyi auri ko ba Turaki ba zanyi aure.” “Nana, na gama dake a ‘yan uwa, na hulaƙantaki, na ɓarar miki da duk wani mutunci, to wallahi ina sanar dake idan kika matsa yadda na yi miki a cikin ‘yan uwana, haka zanyi miki a duniya gaba ɗaya Nana.” “Allah Yafi ka Sardauna, Allah Yafi ka.” “Wato bakin ki ya yi tsauri kenan? To ki ci gaba, a yanzu dai na gama da maganar Aliyu, sai kuma wani idan ya sake zuwa.” Daidai lokacin kuma Dr Aliyu ya sake shigowa, na ɗaga kai na kalleshu, wata tsanarshi sabuwa ta dirga a rayuwata, na ji na tsaneshi fiye da kowa da fiye da komai. Ya taku zuwa inda nake ya ce. “Nana! Na yarda ke wawiya ce, ba yarda baki da zurfin tunani a rayuwa, ke ina saurayi kamar ni ina auren bazawara irinki da ko haihuwa ba zata yi ba?” “Allah Ya tsinema Aliyu, Allah Ya hulaƙanta ka.” Ya yi dariya, sannan ya ce. “Kije kiji da abubuwan da suka yi wa rayuwarki dabaibayi, Nana ki sani gaba ɗaya rayuwarki a tafi hannun Sardauna take, sai yanda ya yi dake, kuma yanda ya yi miki alƙwarin bazaki auro ba, to ki haƙura ba zaki auro ba, gwanda ma kije ku yi zaman dadiro ke da shi.” A fusace na ɗago na ce. “Kaga zaman dadiro akan uwarka, ɗan mitsiyata wanda bai gaji arziƙi ba, Allah Ya hulaƙanta ka shege.” A fusace ya kai hannu zai mareni, Sardauna ya riƙe mai hannu da faɗin. “A’a, ina sonta fa Dr.” “Bakajin abinda ta ce?” “Wannan yarinyar bakinta da na kare ai duk ɗaya ne.” Tsaki yaja ya fice, ni kuma na miƙe tare da faɗin. “Sardauna abind baka sani ba, Bilkisu ta sama ƙwayar lalata sperm, kuma shekara da shekaru kana sha, kaga kuwa kaima kai da haihuwa har abada.” Ina faɗin haka na fice a guje, wani irin jiri nake ji har biyi biyu nake gani, daƙyar nake iya haɗa hanya har na fito bakin titi, sai dai ina fitowa bakin titi na ga mota ta tsaya a gabana, na ja baya da sauri zan gudu aka ce. “Nana shigo.” Muryar Ra’is ce, na ɗaga kai na kalli motar shi da Turaki ne a ciki, ba kunya na buɗe bayan na shiga, ina shiga yaja motar ya fara tafiya, na haɗe kaina sa gwiwa na fara kuka, babu wanda ya yi min magana har muka isa gida, muna zuwa na buɗe motar na shiga, sai dai ina shiga gidan naga Yaya Radiya, Yaya Rumaisa da Yaya Ridwan da Hajiya dukkansu a zaune kamar jiran shigowa ta suke, tsayawa na yi na fara binsu da kallo. “Zaki shigo ne ko sai na zo na janyo ki.” Yaya Radiya ta faɗa a tsawace, ba musu na taku na shigo na zauna a gefe na takure, daidai lokacin Ra’is da Turaki suka shigo, sai da suka zauna Hajiya ta fara magana. “Gashinan, daman hausawa sunce. ‘Wanda bai godewa Allah ba, zai gode azabarsa.’ Ke yanzu Allah Ya dube ki ya kawo miki miji, amma kika butulce masa ko? Yanzu me kika jiyo?.” Na yi shiru ina kallonsu, kenan sun san abinda ya faru dani? “Aini ban so Hajiya kika sa suka bita ba, da kin barta acan ko yayanka namanta Sardaunan zai yi ya yi, jaka da bata san ciwon kanta ba.” Ɗago wa na yi na kalli Yaya Rumaisa, ni fa bangane ba aina su kasan abinda ta faru, me suke nufi ne. “Nana.” Yaya Ridwan ya kira sunana, na ɗaga kai na kalleshi. “Me ya sa ba zaki yi hankali ba, a yanzu fa kinfi shekara ashirin fa, ko yanda muka karɓi saurayin naki ba zai sa ki yi hankali ba ki rabu da shi Nana?” Gaba ɗaya jikina ya yi sanyi, ya ƙara cewa. “Shi, yasan komai, tun ranar daga yaga saurayin naki ya gane abokin Sardauna ne, ya same ni da maganar na ce zan yi miki magana, amma ya ce bazaki gane ba a lokacin, Yaya Rumaisa ta ce a ƙyaleki idan ya yi miki abinda zaki yi hankali kya nutsu dan dole.” Na ɗaga ido na kalli Turaki, ya yi murmushi sannan ya ce. “Nana, ko a lokacin da na ganki da Aliyu, banji koamai ba, domin nasan Sardauna ya turoshi, amininsa ne, halayensu ɗaya, sai dai shi ba ya zama nan kwata kwata, sai da ya sami wannan aikin a asibitinku, a lokacin naga dacewar na rabaku amma nasan bazaki fahimt ba shi ya sa na ƙyale miki shi, amma komai da kuke yi ina bibiya, har wayarki na yi Tracking, tun da ya ce zaku je gaida Hajiyarsa nasan shirin sune, hakan ya sa na ce da Hajiya kina fita faɗamin, duka muna bin bayanku nida Ra’is, duk abinda suka faɗa miki muna sauraro.” Wata kunta ta rufe ni, ban yarda bani da hankali ba sai yau, duk jikina ya ƙara mutuwa. “Ku yi haƙuri dan girman Allah.” Na faɗa, Hajiya ta ce. “Ai kin riga da kin karɓi sakamakon ki wajen Sardauna, idan zaki yi hankali sai ki yi, idan ba zaki yi ba sai ki yi ta yi abinda kika ga dama.” “Hajiya ayi haƙuri, daman nima akwai abinda nake son faɗa.” Wani irin bugu na ji ƙirjina ya yi, ‘kar dai ya ce ya fasa aurena, na shiga uku.’ “Dalilin da ya sa na janye mata ƙafa kwanakin baya, su Big Daddy ne suke gudanar da bincikesun, kuma suka buƙaci na ja baya, a yanzu kuma sun kammala, idan ta amince ko daren yau zasu iya zuwa a ɗaura auren, sauran abubuwan ayi daga baya. “To ai wannan nata ne, tun da ta yi ƙarfin da zata zaɓi wanda take so ta aura.” Na girgaza kai sannan na ce. “A’a, Hajiya ku yi haƙuri dan Allah.” “Ai Nana ba zancen haƙuri, yanzu ki faɗa kina son na shi ko kina da wani da kike so?.” Yaya Radiya ta faɗa, na girgiza kai, na yi shiru. “Hajiya ku yi mata haƙuri dan Allah.” Turaki ya faɗa, Ra’is ya ce. “Ayi haƙuri.” “Ni a ganina a turu su kawai, amma sai zuwa gobe, sabida nima zanje na sami kawunan mu na faɗa musu.” Yaya Ridwan ta faɗa, Turaki ya miƙe tare da faɗin. “To Allah Yakaimu da rai da lafiya.” Da amin suka amsa Ra’is ya miƙe ya bishi, ni kuma na tashi zan shige ɗaki. “Dawo dan ubanki.” Yaya Rumaisa ta faɗa, ba musu na dawo na zauna. “Nana ki godewa Allah, kinsame mai sonki, amma shine kike wannam haukan.” “Yaya ku yi haƙuri, wallahi nima bansan haka za ta faru ba.” “Ke Nana yanzu sharrin Sardauna wannene baki sani ba?” “Wallahi ban taɓa tunanin abun nasa ya kai haka ba.” “Ai yanzu kinsani.” Na yi shiru, gaba ɗaya jikina ba daɗi. Basu wani daɗe ba kowacce ta tafi gida, na koma ɗaki na zauna, na yi ta kuka har dare. A ranar Yaya Ridwan yaje gidansu Hajja duka su ka yi magana, da yake yanzu sun fara fahimtar juna damu sabida ana kai musu kayan abinci duk ƙwarshen wata. Washe garin tun safe aka fara shirye shiryen tarbar su, ƙarfe huɗu na sha biyu na rana daidai suka zo, mu muna cikin gida su suna cam baranda, daga ni sai Hajiya, sai Ra’is a cikin gida, can kuma Yaya Ridwan da ƙannen Alhaji guda biyu. Bayan kusan minti talatin da zuwansu, Yaya Ridwan ya shigo fuskarsa ɗauke da fara’a, bai kai ga magana ba sauran suka shigo. “To, Alhamdulillah an ɗaura auren Rawasiya da Abubakar, yaro ya bada sadaki naira dubu ɗari biyar gasu nan, sai mu yi musu fatan Allah Ya kauda fitina yasa gidan zamana.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na ashirin da takwas. “To, Alhamdulillah an ɗaura auren Rawasiya da Abubakar, yaro ya bada sadaki naira dubu ɗari biyar gasu nan, sai mu yi musu fatan Allah Ya kauda fitina yasa gidan zamana.” Da Amin kowa ya amsa, ni kam ji na yi jikina ya yi wani iri. ‘Yau ni Nana na zama matar Turaki? Yau na tsira daga duk wani sharrin Sardauna.’ Ji na yi kamar na kira Sardauna a waya na faɗa masa, na ce da shi na yi aure ya mutu. “Nana lafiya?” Ra’is ya tambaya, na girgiza kai sannan na ce. “Bakomai, me ya faru?” “Naga duk kinyi wani kala, kaman ba kya son auren?” “Ni na faɗa ma Ra’is, kawai ina tunanin abinda ya faru jiya, Ra’is ina jin kamar na kasance mace mai son zuciya, Ra’is bana iya yin uziri a rayuwata, Turaki bai cancanci abinda na yi ba, duk wani faɗi tashi akaina yake, bai kamata ace na kasance a haka ba.” “Alhamdullilah, Nana kin fahimci gaskiyya, kowa fushi yake dake sabida abinda kika yi, Turaki shine ya shiga ya fita, ya tsaya tsayin daka a kanki, Allah ne ya yi, amma Turaki ne sillar kasancewarki a matsayin da kike, kinsan Sardauna, kinsan hatsabibancinsa amma Nana kinyi kunnen uwar shegu, me ya ce miki da kika yarda da shi haka?” “Wallahi bansan abinda ya shiga kaina ba, kawai ya ce da ni matarsa ta mutu, da ‘yar sa ƙarama.” “Yanzu abinda suka yi miki zai saki ki yi hankali ai, Nana sannan kina sakaci da ibada, kawai sallar ibada kike, babu ruwanki da wasu azkhar tashin dare da komai, Nana duk gidan nan babu wanda baya tashin dare sai ke, kuma ke da yakamata kifi kowa tashin, Nana ba wai gori zan miki ba, ko faɗa miki baƙar magana, Nana tun tashina matsalolin ki kawai nake gani ana fama dasu a gidan nan, Yaya Radiya da Yaya Rumaisa a tashi na matsala ɗaya aka fuskanta, lokacin aurensu sai sakin Yaya Radiya, Nana ke fa, daga wannan sai wannan, ba a gama da wannan ba a shiga wannan, kinfi kowa yawan matsaloli cikin gidan nan, amma kuma kinfi kowa sakaci a cikin gidan nan, kullum al’amuranki caɓewa suke, baya baya suke, amma kin kasa ganewa.” Na yi shiru, tabbas kalaman Ra’is dukkansu gaskiyya ne, nafi kowa yawan matsaloli a gidanmu, duk yayuna matsalolina suke fama dasu, amma na kasa hankali. “Ra’is, tabbas gaskiyya ka faɗamin, kuma in sha Allah zan gyara.” “Allah Ya gyara mana, a yanzu dai duk wata matsala da barazanar Sardauna ta ƙare, idan kika mayar da hankali da ibada, Allah zai dafa miki, ku zauna da mijinki, ki yi masa biyayya, na tabbatar a yanzu zakiji daɗin aure.” “In sha Allah Ra’is, na gode sosai da sosai.” ********** Tun da Ra’is ya fita daga ɗaki, ina zaune ina faman tunanin yanda zan gyara tsakanina da ubangiji, dan tabbas wata galabar da Sardauna yake samu akaina rashin ibada da sakaci na ne, ai Sardauna ba ubangiji ba ne, kuma baifi ƙarfim ubangiji ba, dan haka tabbas idan na gyara Allah zai gyaramin. Yaya Radiya ce ta kirani a waya, bayan na ɗaga ta fara min nasiha mai ratsa jiki, akan yanda zanyi haƙuri da rayuwa, na kuma miƙa al’amura na ga Allah, duk suka kashe min jiki gaba ɗaya, na yi kuma niyar in sha Allah zan dage da ibada. Gaba ɗaya Turaki bai kirani a waya ba, kuma da alamu ma bai buɗe black list ɗina da ya yi ba, duk na bi na damu, gashi yaƙi zuwa gidan, na yi nadamar abinda na aikata na kuma tuba akan kuskurena, daren ranar haka na yi ta kaiwa Allah kukana, sai da na yi asuba sannan na kwanta. Kiran wayar Turaki ne ya farkar dani daga baccin da na koma bayan na yi asuba, na ji daɗi a raina na yi wa Allah godiya sannan na ɗaga kiran. “Assalamu alaikum warrahmatullah.” “Wa’alaika salam, ina kwana?” Na faɗa, ya amsa da. “Lafiya ƙalau Alhamdulillah, ya kwanan amarya.” Na yi murmushi, sannan na ce. “Alhamdulillah.” Ya yi shiru, sai can kuma ya ce. “Nana.” “Na’am.” Na amsa masa, ni kaina ina da abin faɗa amma ina jira ya yi maganar. “Nana, ina so ki sani Allah ne ya ɗoramin sonki, tun bansan ki ba, Nana tun ban taɓa ganinki ba nake jin ina sonki, na kasa haƙuri da lamuranki, bana so na takura miki a rayuwa, Nana ban aureki dan na takura miki ba, sai dan ina jin kamar bazaki samu kulawar da ta dace a ko ina ba, Nana zan kula dake da dukkan iyawata, dan Allah ki yi haƙuri dani, ina yi miki wata soyayya da ni kaina bansan girmanta ba, a ranar da na ganki da Aliyu na ji duniya ta gaba ɗaya ta tsaya, duk da nasan shirin Sardauna ne, amma hakan naka sa nutsuwa, sai da na sami ‘yan gidanku da zancen, Nana kowa ya zuba miki ido, kowa ya yi miki shiru ya barki da halinki, amma kin kasa ganewa.” “Ka yi haƙuri Turaki, ni kaina bansan abinda ya faru dani ba, amma wallahi na yi nadama, nagane kuskurena, ka yi haƙuri dan Allah Mijina.” Ya yi dariya mai sauti, sannan ya ce. “Naji daɗin kirana da haka, Nana har yanzu na kasa yardarwa zuciyata cewar kin zama matata, ko sai na ganki cikin gida Nana?” “Me ya sa ka kasa yarda?” “Nana kina da daraja a idona, kina da matuƙar girma a rayuwata, sai nake jin kamar wahalal da nasha ta yi kaɗan, a irin girmanki a rayuwata.” “Uhm, to ai babu wanda yake son wahala a rayuwarshi.” “Hakane kam, yanzu yaushe suka sanya tarewar taki?” Na yi shiru, sabida bansan abinda suka tsara ba. “Nana.” Ya kira sunana. Na amsa a hankali, ya ce. “Naso na kaiki gida daban, amma sunqi amincewa, Nana gida ɗaya zaki zauna da ni isalaha.” “Ai bakomai ba ne, kowa zamansa daban ko?” “Eyh Nana.” “To, ai wannan ba matsala ba ne.” “Nana, karki ji wani abu dan zaki zauna tare da Sardauna, ni za kasamce garkuwarki Nana.”’ “Nasani, indai kana tare da ni babu wani abu da zai same ni, na gode sosai da sosai, ina kuma baka haƙuri akan abinda ya faru Mijina.” “Habibty bansan kowanne suna sai mijina.” “Tom, in sha Allah.” Na faɗa, daga nan muka yi hirar da zamuyi muka kammala. Sati ɗaya da ɗaurin aure suka kawo kaya, akwati shida Turaki ya yi masu kyau, waɗan da suka cika da kaya, duk da na ce babu wani shagali da zanyi amma Turaki ya dage, hakan yasa na ce zamuyi walima rana ɗaya a gida, kuma a ranar zan tare, ya dage akan sai an kama event anyi walimar acan, shima da ‘yan uwansa zasu zo. Su Hajiya ne suka sanya lokacin tarewar sati uku bayan kawo kayan. Ranar littinin ɗin farkon satin da zan tare, muna zaune a gida wasu ‘yan mata guda biyu suka shigo, kallo ɗaya na yi musu naganesu, nasan fuskarsu a family meeting din su Turaki, amma kuma bansan daga ina suke ba, nasan dai ba ƙannen Sardauna ba ne tun da su na san su. Bayan mun gaisa da su, Hajiya ta bamu waje ɗaya cikinsu ta ce. “Ni sunana Fatima, wannan Hajara. Kuma mu ƙannen Turaki ne.” Na yi murmushi, sannan na ce. “Daman nasan fuskarku amma bansan sunanku ba.” “Eyh, daman mun zo ne mu gaida ke, Yaya Turakin ma baisan munzo ba, sannan akwai wani abu da muke son sanar dake.” Na kallesu da wani irin kallo mai ban tsoro, sannan na ce. “Allah Yasa lafiya.” “Eyh, lafiyar zamu ce, amma dai gaskiyya da damuwa.” Gabana ne ya faɗi sosai, na ce. “To ku faɗan mana.” “Mu dai a gaskiyya tsakaninmu dake babu matsala ko wata damuwa, yadda muke son yayan mu, muna som abinda yake so, dan haka wallahi mu dai muna sonki, so na gaskiyya, haka ma Momynmu, duk ta matso akawo mata ke. Amma matsalal ita ce gidansu Sardauna, sun shirya miki tare da wasu daga family, duk an sanya musu tsanarki, sun shirya miki rashin mutunci da yawa, abinda ya sa muka zo faɗa miki sabida karki yi tunanin mu bama sonki lo hajiyarmu, wallahi suna sonki, zasu yi ta zuwa gidanki suna cewa ƙannen Yaya Turaki ne suna miki rashin mutunci, eyh dukkansu ƙannensa ne amma mune asalin ƙannensa na jini, babbar yayarmu mace tana Spain acan take aure, sai Yaya Abida ita tana Abuja, sai Yaya Turaki sai mu ‘yan biyu, bayan mu babu kowa, dan Allah kar su zo su yi miki wani kice zaki dinga jin haushin yaya Turaki, ko kice bama sonki.” Kallon wacca ta yi maganar na yi, sannan na ce. “Allah Yafi su, kuma ko da ban sami soyayyarsu ba, indai nasami ta mijina da ‘yan uwansa ai na gama mai wuyar.” “Naji daɗin fahimtar da kika yi, sannan wallahi suma ‘yan uwanmu ba haka suke ba, suna da mutunci da mutunta mutane, kawai Yaya Sardauna ne ya yi musu zuga ta gaske, dan Allah ki fahimce su, mu ƙananu ne a family, ba mu da bakin da zamu ce zamu tare miki idan anyi miki abu, amma tabbas muna sonki, kuma Momyn mu zata ji da komai, amma akwai abinda ba lallai muma mu san anyi ba.” “Hajara na zauna da Sardauna tun kafin yanzu, nasan halayensa tsaf, na shiga familynku a farko na fahimci halayenku, dan haka zanyi haƙuri na karɓi soyayayr mijina kaɗai.” “Wannan gashi, Momy ce ta ce akawo miki, amma dan Allah karki faɗa ma Yaya Turaki mun faɗa miki wannan maganar, kawai ki ce gaida ki muka yi.” “Tom in sha Allah.” Na faɗa ina karɓar abinda suka bani, daidai lokacin suka miƙe zasu tafi, sai da na rakasu har waje kasamcewar driver ne ya kawo su. Ina komawa gida na shiga ɗakin Hajiya na bata abinda suka bani na fito. Daman Sardauna ya ce zai ɓatani, amma Allah Yafi shi, kuma nima ba zan zauna ba, bayan addu’a dole na haɗa da gishirin zama, ba dai Turaki ne baya so ya ganni da shi ba, sai na yi abinda bakin ciki zai kashe shi, wannan shine alƙwarina.” Satin biki ya shigo, aka fara shirye shirye a gida, kuɗin kayan katakon Sardauna aka ɗauka, aka yi cikon da zaayi aka siyo wasu, abubuwan kicin ma an canja wasu da yawa, na sha gyara kamar wadda za ta yi aure na farko. Ranar juma’a ta kama ranar da zan tare a gidan Turaki, ranar da nake ganinta mafi muhimmanci a gareni, ranar da zan dake shiga gidan aure a karo na biyu. Tun safe ‘yan uwa suka cika gida, ana ta shige da fice, wasu ƙawayena da yawa sun zo mussaman tun da akwai walimar da zaayi, kuma fita za ayi, kowa sai fatan alheri yake min tare da fatan Allah Yasa gidan zama ne. Ƙarfe huɗu motoci suka fara layi a ƙofar gidanmu, mutane suka fara tururuwar shiga ama tafiya wajen walimar, a wannan tafiyar kam sai da aka tsantsar min kwalliya, na yi kyau abuna muka tafi, a motar da Turaki yazo da ita. Babban wajen biki ne da ya amsa sunansa, ya kuma cika ya batse da ‘yan uwa da abokan arziƙi, ‘yan gidan su Turaki suna ta kai koma, da wasu da nake kyautata zaton ‘yan uwan Momynsu ne. Muna zaune wajen da aka tanadar mana, Turaki ta riƙe hannuna ƙam kamar yana tsoron wani abu zai tafi dani, daidai lokacin kuma Sardauna da wasu mata suka shigo cikin Hall ɗin. Legendspen 08129553971. SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na ashirin da tara Gabana ne na ji yana wani irin bugu, kar da a ce rashin mutuncin Sardauna ne zai fara tun yanzu, sai dak ban ga alama ba sabida ‘yan matan da ya kawo gefe guda suka zauna, wani irin kallo na ga ya watsa mana, daidai lokacin ni kuma na kwanta a kafaɗar Turaki, ina ganin yanda ya wani rintse ido, Turaki kuma ya ce. “Karki wani tsoro, ba abinda ya isa ya yi.” Na yi murmushi, sannan na ce. “In sha Allah.” Haka aka ta shi daga wajen walimah, daga nan aka wuce dani gidansu Turaki, duk da momynsa na wajen amma sai da muka je, anan na ƙara tabbatarwa duk mutanen dake wajen ‘yan uwan momynsa ne ba wai familyn Ta ambo ba, Sardauna dai ya gama da ni a family ɗin Ta ambo. Na samu karɓa ta mutunci a wajensu, kowacce nan nan take dani, su ka yi min duk wata nasiha da takamata, daga nan aka wuce dani Takur Site C. Lokacin da aka zo shiga gidan sai da na ji numfashi na ya tsaya, yau gani a gidan da na ce na fita daga har abada, nasake dawowa amma da igiyar wani akaina ba ta asalin mijin ba, shin zama a gidannan dole ne? Ban bari na ɗaga ido na kalli part ɗin Sardauna ba, sabida zuciyata baza ta iya ɗauka ba, wani irin rawa take yi kamar zata fasa ƙirjin ta fito waje, a haka muka shiga cikin gidan, aka nemi ɓarin uwar gida aka fara shiga da ni, sai dai fa ɓangaren fal yake da mutane, wata cikin ‘yan uwan Momy ce ta ce. “Kunga ku wuce da ita na ta part ɗin, idan yazo shi ya haɗasu kawai.” Ba musu aka wuce dani, part ɗin da ke gab da na Sardauna, a raina na ce. ‘Me ya sa sai nan? Wannan wajen fa har motsin Bilkisu zan iya ji, indai ina ɗakin bacci na ne, innullahi wa’ina illahir raji’un.’ Yanda suka kawo ni haka suka fara tafiya, aka barni daga ni sai su Hajara, sai kuma Maman kaduna wacca itama daga family Momy take, sabida sunga take taken su islaha da ‘yan uwanta. Ana zaune zaman shiru wajen awa ɗaya sannan Turaki ya shigo, shi kaɗai ba gayyar abokai, yana shigowa suka yi min sallama suka fice. Ɓangaren namu ya yi shiru, da gani sai Turaki sai islaha, dukkanmu muna zaune akan kujera, ni ina zaune a guda ɗaya su kuma suna zaune a ɗaya su biyu, wannan yanayin shiga tuno min nawa lokacin, a ranar da Sardauna ya sake ni, a ranar da Sardauna ya yi min hulaƙancin da bai zataɓa gogewa a raina ba. Na yi shiru sanyin ɗakin haifar min da shiga wani irin yanayi, ina koƙarin fara rufe idona na ji muryar Turaki. “To da farko dai mu yi wa Annabi Salati.” Buɗe idona na yi na fara salatin, bayan munyi ya fara magana. “Alhamdulillah bi ni’imatihi, dole mu godewa Allah da ni’imar da ya yi mana, mussamman ni’imar musulunci. A yau cikin matuƙar farin ciki nake tara ku a wajen nan, ina mai alfahari da ku a duka ku biyun, Isalaha.” Ya kira sunanta, ta ɗaga kai ta kalleshi, sannan ya ce. “A shekaru ke ce Babba, haka ma a zaman gidan nan ke ce Babba.” “A’a, karka haɗani da tsohuwar guzuma, ko da nake babba, ita aurenta nawa? Ai ba wannan ba ne auren ta na farko, ta yi ta fito, nifa?” “Islaha, mene haka?” Ya tare ta, ta kalleshi tana wani jijjiga ƙafa, sannan ta ce. “Ai gaskiyya ce ma faɗa.” “Ko da gaskiyyar kika faɗa, amma ai addini ne ya ce duk wacca aka shigo aka tarar ita ce gaba, dan haka ba dole na baki girmanki.” Ni dai ina kallonsu da ido, ban tanka musu ba, danni maganar ta ma ba ta yi min zafi ba, mussaman aka haɗa ta da wacca Bilkisu ta yi min a wancan lokacin. “Nana.” Ya kira sunana, na ɗaga kai na kalleshi ya sakar min wani murmushi, sannan ya ce. “A shekaru islaha ta girme ki, ko da bawani da yawa ba ne, haka a zaman gida ma nan kika zo ki tarar da ita, ina roƙon ki da ki mutunta ta, ki ba ta giman da duk ya kamata, nasan ki baki da matsala da rayuwa.” Na buɗe baki da niyar magana ta tare ni, ta hanyar cewa. “Ni matsala nake da ita da rayuwa kenan? Daga gidan uban wa kike? Waye mahaifinki? Mene suna ahalinku? Wane matakin karatu kike da shi, just common degree, ke ni ba sa’ar ki ba ce. Ni banga amganin haɗani dake a waje ɗaya ba.” Na yi murmushi kawai, na kalli Turaki da ya yi wani kala, a take tausayinsa ya lulluɓe ni, na ce. “In sha Allahu ba zaka sameni da wata matsala ba, zan kasance me biyayya a gareka, zan kasance mai duk wani ƙoƙari wajen sanya ka farin ciki Mijina.” Wani dogon tsaki ta ja ji kake. ‘Mitchewwwwwwwww.’ Tare da ta shi ta fice, har ta kai ƙofa sannan ta ce. “Bazawarar arziƙi dai kwana uku ake mata, amma kishiyar waje bamu sani ba.” “Ka yi haƙuri, kar ka damu da komai, nasan daman zan tarar da abinda ya fi wanan.” Na faɗa ina komawa kusa da shi, ya yi murmushin da iyakarsa fatar baki, sannan ya ce. “Nana, islaha daman an aurota ne dan ta zama tsaiku a zaman aurenmu ni dake, bansan me ya sa ba, amma ina jin kamar na sake ta a yanzu, Nana ban shirya zama da abinda zai dame ni ba akan ki, Nana ina sonki, son da zan iya ɓatawa da kowa akanki.” Da sauri na girgiza kai, sannan na ce. “A’ah, karka fara dan Allah! Dan hakan wani baƙin jinin zai ƙara jamin daga zuwa na ka saketa. Tin da mun san manufarta sai mu ci maganin zama da ita.” “Shikenan Nana, Allah Ya yi miki albarka, mu tashi mu shiga ciki.” Na miƙe shima ya miƙe muka shiga ɗaki, muna shiga ya yi toilet ni kuma na tsaya ina ƙarewa ɗakin kallon, Ɗakin Turaki ma ya tsaro abunsa, komai ya dace da inda aka sanya shi, shawarar fita zuwa nawa ɗakin na yanke, naje na yi alwala na canja kaya dan wannan rigar ta isheni. Ina shirin buɗe ƙofar na ji an ce. “Ina zaki?” Sai da na waigo na kalleshi sannan na ce. “Zanje can na yi alwala, na canja kaya.” “Ba tare zamu ba?” Na girgiza kai na ce. “Ai yanzu zan dawo.” “Tom. Nima bara na canja.” Ina faɗin haka na fice na nufi nawa ɗakin, toilet na nufa na fara watsa ruwa, bayan na gama na yi alwala na fito, sif ɗita na buɗe zan ɗauko riga. Sai dai ina buɗe sif ɗin na ji murya sama sama, a hankali na saita kunnena, hayaniya ce kamar ta Sardauna, da sauri ma rufe sif ɗin na yi baya, sai dai na daina jin hayaniyar, kenan idan na buɗe sif ɗin shi nake jin maganarsu? Iko sai Allah. Ban mai da hankali ba na sanya riga ta na fito, ina shiga ɗakin ya ce. “Yanzu nake shirin bin bayanki, sa kaya kamar ba za a dawo ba?” “Sai da na yi wanka.” Na faɗa ina ƙarasa shigowa. “Shine kika yi ke kaɗai? Maimakon nazo na yi miki?” Na yi ƙasa da kaina, sannan na ce. “Kai ma ai ka kaɗai ka yi.” Matsowa ya yi kusa dani, ya dafamin ka faɗa. “Nana kinji ha daɗi? Ki yi haƙuri dan Allah.” Na girgiza kai, sannan na ce. “A’a, ba haka ba ne.” “Bana son ace darenki na farko a gidana na yi miki abinda zaki ji ba daɗi, Nana ina sonki.” “Nima ina sonka, kuma bana jin zan iya jin haushinka.” “Allah Yasa Habibty, mu yi sallah.” Ya faɗa yana miƙewa, nima na miƙe na shimfiɗa abun sallah muka tayar, ko da muka idar ya yi mana addu’a, sannan ya shiga jeramin irin girman soyayyar da yake min, irin yanda yake jina a zuciyarsa, duk wasu kalmomi da Turaki yake faɗa ina jinsu a cikin zuciyata. Washe gari. Ƙoƙarin miƙewa nake daga kan gadon, ya yi saurin matsowa kusa da ni. “Habibty na Good morning.” Na kawar da kaina gefe ba tare da na amsa ba. “Ta so Habibty.” Ya faɗa yana ƙoƙarin kamani. “Na ɗaga ki?” Na girgiza kai alamar a’ah, amma kamar ce masa na yi Turaki sama da ni, ya ɗaukeni ya yi sama dani, bai sauke ni ko ina ba sai a toilet, daman ya gama haɗa ruwan wankansa. Ƙoƙarin cire min kaya ya fara, na riƙe tare da faɗin. “Zanyi da kaina.” “A’a bazaki iya ba Habibty, bari na yi miki.” Duk yanda naso da Turaki amma ya gagara ƙyaleni, sai da ya saɓe ni tas. Haka ya sake ɗaukoni zuwa ɗakin, ya ajiye ni a gaban mudubi, na girgiza kai tare da cewa. “Ai ba nan zan shirya ba.” “Au, namanta Habibty bari na kai ki can.” “A’a dan Allah, zan iya zuwa.” “To taso.” Ya faɗa, na fara koƙarin miƙewa sai dai ban kai ga miƙewar ba ya sunkuce ni, ya yi waje. “Ka sauke ni na je da kaina.” Na faɗa bayan mun fito. “Ai sai na kaiki fa.” Ina ƙoƙarin ya sauke ni, shi kuma yana tafiya muka yi kiciɓus da Islaha, wani banzan kallo ta watsa mana, ta yi gaba. Muma mu ka wuce zuwa ɗakin nawa. “Kabarni na shirya da kaina dan Allah.” Na faɗa bayan ya sauke ni, ya girgixa kai tare da cewa. “A’a fa.” “Ni dai a’a.” “To wane kaya zan ɗauko miki?” “Kowanne, amma kabarni na shirya.” Ɗauko min kayan ya yi ya ajiye min, sannan ya ce. “Na jiraki ko zaki same ni?” “Aina?” “Dinning mana.” “Ohky, gani nan.” Na faɗa, shi kuma ya fice. Sai da na shirya tsaf, sannan na fito zuwa ɗinning ɗin yana zaune yana danna waya, yana ganina ya sakar min murmushi, nima na mayarsa. Sai da na zauna sannan na ce masa. “Ina take?” “Ta ce ba nan zata yi ba.” “To waye ya yi girkin?” “Ni mana my love, idan ban miki girki ba wa zanyi wa?” Na yi dariya, tare da girgiza kai. “Bari na zuba miki, ki ce girkin mijinki.” Ya faɗa yaba miƙewa ya fara zubawa, soyayyen da dankali ne, sai soyayyen ƙwai a gefe, sai wata miyar attaruhu da ya yi, sannan ya zubamin tea. “Gashinan ranki ya daɗe.” Na yi murmushi, sannan na ce. “Tom Mijina.” “Ɗan aiki ba.” Na girgiza kai, na ce. “Ni ba abakina ba.” “To ni a baki na, Habibty akanki komai ma a kira ni.” Fara cin dankali na yi, ina jin daɗinsa tare da shayin, sai da na ci da yawa, sannan na ɗauke hannu. “Kin ƙoshi?” “Eyh, ya yi daɗi.” “Abinda zan miki gobe ma, sai yafi na yau daɗi.” “Gobe ai da kaina zanyi.” “Kai Habibty, indai ina nan kisa a ranki ni zan miki breakfast.” Wani sanyi na ji a raina, tabbas Turaki ya cika masoyin na haƙiƙa, ina ma ace rayuwar ta tsaya a haka, bana fatan wani abu ya shigo rayuwata da Turaki wanda zai kawo mana tsaiko. Gani na yi ya fara kwashe kayan abincin, na yi saurin tare shi da cewa. “A’a bari na ɗauke.” Banza ya yi min ya kwashe kayan ya nufi kicin, na miƙe na kwashe ragowar na bishi kicin ɗin. “Kina son wahalal da kan ki Habibty.” “Bawami wahalal da kai.” “To ya ne.” Ya faɗa yana nufar sink, na yi saurin cewa. “Me zaka yi?” “Wanke kwanakun da muka ɓata mana.” “No…” Ya tare ni, tare da cewa. “Karki ɓata yawon bakin ki.” Matsawa na yi kusa dashi, na fara ta ya shi wanke kwanunka, haka muka wanke su muna hira yana hanani amma na na ce, daga kicin ɗin muka koma ɗaki muka zauna. “Habibty.” “Na’am.” “Yau waƙa zan miki.” “Waƙa kuma?” “Eyh, wacce kike so?” “Wacce ka rera da kanka?” Ya yi dariya sannan ya ce. “Ba wacca na rera, sai dai wacca wani ya rera.” “Tom.” “Habibty, wane mawaƙi ne yafi iya waƙa.” Na girgiza kai, sannan na ce. “Ni ban wani cika sauraron waƙa ba.” “Sai kallo?” Na girgiza kai shima. “To sai me?” “Nifa ba komai?” “Habibty babu wani abu na nishaɗi da kike yi?” “Nishaɗi?” Na maimaita kalmar, a raina na ce. ‘Babu, nishaɗi na ɗaya, kula da Sardauna.” Legendspen 08129553971. SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na talatin. Cikin sanyin Ac da ke ratsa ɗakin, ina zaune a kan kujera mai laushi, na takure waje guda ina kallon dukkan motsinsa. Hasken daƙin ya kasance mai sanyaya idanu, wanda ya ƙara wa fuskarsa wani irin kyau da kwarjini na daban. Yana tsaye a tsakiyar ɗakin, riƙe da remote ɗin Ac a hannunsa tamkar abun magana na makirofon, yana bin sautin waƙar da ke tashi a hankali. Idanunsa suna kaina, cike da wani irin murmushi mai taɓa zuciya, yana girgiza jikinsa kaɗan-kaɗan cikin ƙwarewa da kazar-kazar. Muryarsa tana fita a hankali, yana haɗa ido da ni yayin da yake rera waƙar. “In dai akan ki ne na yi nisa dan ba kiran da zan amsa.” Wani irin daɗi na ji ya mamaye mini dukkan jikina. Na lumshe idona ina jin yadda kalmar “na yi nisa” take ratsa kowacce jijiya ta jikina. Ina buɗe idona, na ga yana takowa zuwa inda nake, har yanzu idanunsa suna narke a cikin nawa, muryarsa tana daɗa zurfi. “Tilas ganin mu tilas barin mu ƙaunarki tun da nai nisa.” Wani gajeren kallo na jefa masa, wanda na san ya isa ya gaya masa dukkan abinda da ke ɓoye a raina na soyayyarsa. Na gyara zama, ina jin yadda shauƙin soyayya yake neman huda kowane sashi na jikina. Kalamomin da yake faɗa na kowanne baiti ba a iya baitin waƙa nake jin su ba, jin su nake tamkar suna bin jinina ne suna zazzaga a cikin zuciyata. Murmushi ya suɓuce mini, na kasa ɓoye farin cikin da yake shirin fito mini da hawayen daɗi. Shi ma ganin murmushina, sai ya fashe da wata daddaɗar dariya wacca ta bayyana kyakkyawan hakoransa, ya miƙa mini hannu tamkar yana roko na na karɓe shi. Yana daɗa matsowa kusa da ni, har ina iya jiyo hucin numfashinsa, ya tsaya daidai gabana sannan ya cike baiti na gaba cikin wani irin salon mai ratsa zuciya. “Sam ba batun na fasa ko za a ce mini in ba da rai fansa.” A lokacin da ya fadi kalmar “Rai fansa”, sai na ji wani irin shock ya ratsa ɗaukacin gangar jikina. Nima na fashe da dariyar. A daren nan, babu abin da zuciyata take gani sai shi, babu abin da nake ji sai kalaman sa, na sake tabbatar wa kaina cewa, babu wani abu a duniya da zai iya raba ni da shi na har abada. “Habibty ta yi daɗi?” Ya tambaya yana matsowa kusa da ni, na gyaɗa kai sama sannan na ce. “Mijina ka iya waƙa, kaman kaine ka rera, ina jin duk baitin waƙar nan da ka faɗa a zuciyata, ina jin kamar dan ni da kai aka yi waƙar nan.” Ya yi murmushi tare da rungumo ni jikinsa, ya fara magana yana shafamin bayana. “Habibty, ina jin kamar dan ke kaɗai aka hallice ni, bana son ko da rana guda ta zo wacca zanyi nesa da ke, ina sonki, Nana dan Allah ki so ni.” “Ina sonka mana, wallahi Ina sonka.” “Nasani, nima ina sonki.” Wani daɗi na ji, na sa hannu na ƙara matse shi a jikina, ina fatan Allah Ya dauwamar damu a haka. Haka mu ka yini a gidan muna tare, komai a tare muke yi, ina kwance a jikinsa naƙi na matsa kwata kwata, shi kuma yana shafa min kai ya ce. “Habibty.” “Na’am.” “Ranar da kika ganni me kika fara ji a kaina?” Na yi shiru, ina son tuna yaushe na fara ganin Turaki a raina. “Uhmm?” “Yaushe ma na fara ganinka?” “Kin manta?” Na gyaɗa kai, ya ce. “A family meeting.” “Oh! Banji komai ba.” “Ki faɗan gaskiyya, haushina kika ji ko? Sabida na yi faɗa da Sardauna ko?” Na yi dariya, sannan na ce. “Eyh gaskiyya dai, tun kafin lokaci ma ina jin haushin abinda kake yi wa Turaki, gashi ranar ka ja Sardauna ya kusa dukana.” “Ni bani na ja ba, daman da zafin zuciyasa. Ni kuma ranar da na fara ganinki, na ji duniyata ta tsaya gaba ɗaya, a lokacin ji na yi numfashi na yana shirin fita, a raina na ce. ‘Wannan kyakyawar hallitar daga ina haka? Nasan dai a family ɗin mu ma babu irin ta.’ Nana da aka ce min matar Sardauna ce na ji kamar zanyi kuka, har ma fara tunanin kamar Sardauna yafi ni sa’a a duniyar nan. Ashe nima sa’ar tana tare da ni.” Tunda ya fara maganar har ya ƙare ina kallonsa, yanayin yanda yake magana kaɗai yana sa naji kamar nice nafi kowa sa’a a duniya, sa’ar samun Turaki. Yinin wannan ranar haka muka yi shi cikin soyayya, a lokacin nake ƙara tabbatar da mene aure da bambamce bambamcensa, Turaki ya ɗoarani a tsanin da zangane menene aure, ribar aure, farin cikin dake cikinsa. Washe gari ma haka muka sha soyayyarmu a ɗaki, ko waje ban fito ba haka ma Turaki, dan Sallah ma shike jan mu, ranar kwana na uku, tun yamma Islaha take sintiri a ɗakinmu, gaba ɗaya ta kafa ta tsare har zama take yi, ana magariba na shirya na bar mata ɗakin ita da Turakin, su ci duk abinda zasu ci. Ina shiga ɗaki na kwanta akan gadon na rufe idona, ji nake kamar na yi nisa da Turaki, kamar na yi nisa da rayuwata, ji na yi an turu ƙofar ɗakin nawa an shigo. “Habibty ya zaki tawo.” Da sauri na mayar da ƙwallar dake ƙoƙarin fitowa daga idona, na miƙe zaune na kalle shi na ce. “Ai naga uwar gida ta shigo ne, bana son na zauna kaga ta ja maka ɓacin rai.” “Amma Habibty ai kya tsaya mu yi sallama ko.” “Sai ka ce waɗan da zasu rabu?” “To wai kwana nawa za a raba?” “Duk yanda ka tsara, tun da taƙi bada damar a zauna kowa aji raayinsa.” “Bana son na yi nisa dake, sai nake jin kamar zanyi nisa da farin cikina.” Na yi murmushi, sannan na ce. “Ai ba nisa zamuyi ba, gida ɗaya fa muke.” “Gida ɗaya ai ba ɗaki ɗaya ba ne.” Duk irin nauyi da zafi da nake ji a raina, nice na dage ina kokarin tura Turaki ɗakin matarsa, da ƙyar nasamu ya tafi, yana tafiya na kwanta duk raina na daɗi, cikin ikon Allah na farka cikin dare, na yi na fila ta raka’a biyu na roƙi Allah kwanciyar hankali da dauwammen farin ciki a gidan aurena.” Washe gari da kaina na tashi na haɗa breakfast na yi dukkan aikina, ina tsaka da jere plast akan dinning Turaki ya shigo, ina kallonsa na ji wani abu ya tsaya min a rai. “Habibty i missed you.” Ya faɗa yana jawo jikinsa. “I missed you, jiya a falo na kwana Habibty, gashi banda damar zuwa wajenki.” “Falo kuma?” “Bari Habibty.” Ya faɗa tare da ɗaukana zuwa ɗaki, bai dirini ko ina ba sai kan gado, yana ƙoƙarin cire riga ta banke ƙofar ɗakin ta shigo. “Maci amana, azzalumi wallahi sai na kai ƙarar ka wajen su big Daddy, ranar kwanan nawa ka biyo wannan barbaɗaɗɗiyar matar da kuka gama barbaɗewa a titi.” Rigarsa ya fara mayarwa, sai da ya gama sannan ya ce. “Islaha, karki kuskura ki ƙara faɗa min irin wannan maganar? Da na ɗauko kwanan naki na kawo mata dare na biyo? Ko kuma ke kin sauke min haƙƙina na kanki a daren jiya? Ki je ki sanar dasu Islaha, idan suka matsamin sai na sauwaƙe miki gaba ɗaya ma kowa ya huta, tun yaushe na miki haƙuri? Dutse ne ni ko me?” Wani irin kuka ta fashe da shi, wanda kana jinsa kasan na kissa ne, tana yinsa tana gunji ta fara magana. “Su Big Daddy kake zagi, sun takura maka sun aura maka ni, sai ka sauwaƙe min, sabida ka ɗauko kwana na ka kawo wannan ‘yar mitsiyatan.” “Islahaaaaaa.” Ya faɗa a fusace, tare da yin kanta. Na yi saurin riƙe hannushi tare da faɗin. “Kar ka ji haushi, kar ka fusata Mijina, ka yi haƙuri.” Wata irin runguma na ji ya yi min, ya matseni da tsananin ƙarfinsa, sai da ya kusa minti goma a haka sannan ya cika ni. “Habibty ki yi haƙuri.” Na yi murmushi, sannan na ce. “Bakomai fa, muma bamu kyauta mata ba, da har zaka shigo wajena a lokacinta.” “Habibty dare ne fa na ta, safiya ai ba tata ba ce.”’ “Idan ka yi haƙuri, yau ko gobe xaka dawo nan, muje na zuba ma break fast.” Na faɗa tare da kama hannunsa, muka nufi ƙofa. “Shegiya, ‘yar mitsiyata.” Ta faɗa tana riƙe min hannu, na fusge hannuna ba tare da na ce mata komai ba. Muna tafe tana bin mu abaya tana sirfa ruwan rashin arziƙi, ni dai ban tanka mata ba, haka shima bai tanka mata ba, har muka isa kan dinning muka fara cin abincin. Sai da muka gama, har kicin muka shiga muka wanke kayan da muka ɓata, sannan ya miƙe tare da faɗin. “Bari na je na shirya, yau zan leƙa ofis.” Gyaɗa masa kai na yi, ya fice ni kuma na shiga ɗaki. Ina shiga ɗaki na ɗau wayata na shiga whatsapp, group ɗin gidanmu na shiga na ga an ɗanyi magana, na fara bibiyar chat ɗin nasu sai da na gama sannan na yi musu sallama, ina yi Ra’is ya yi min reply da. “Amarya mai capacity.” Na tura masa emojin dariya, sannan na ce. “Autan Hajiya, ya gida da mutan gidan.” “Nana an fara jin daɗin aure.” Abinda na ga Yaya Radiya ta turu, na tura emojin kunya sannan na ce. “Yaya ina kwana?” A lokacin Ra’is ya dawo min da amsar. “Hajiya na lafiya, ina Yaya Turakin?” “Yanzu zai fita.” Na bashi amsa, ya turumin da cewa. “Yau zanje interview nima.” Na tura masa emojin tsalle, na ce. “A ina ne?” “Wani sabon company ne, na abokin Yaya Turaki, ya ce min baya son kaini na family ɗinsu sabida Sardauna.” Na gyaɗa kai kamar yana ganina, sannan na ce. “Hakan ya yi kam, Allah ya bada sa’a.” “Amin.” Ya faɗa, na duba naga sauran duk basa online, sai Yaya Ridwan shi kuma baima buɗe message ɗin ba, ta pravite na yi masa sallama, na ce. “Assalamu alaikum, Yaya Ridwan ina kwana, ya gida, ya mai jiki, Allah Ya ƙara lafiya.” Ina tura masa ya yi min reply, ya ce. “Wslm, Nana Alhamdulillah, mai jiki da sauƙi, ya me gidan naki, Nana ayi haƙuri da rayuwa.” Har cikin raina na ji daɗin amsar, yana yawan cemana mu yi haƙuri da rayuwa, idan ya faɗa sai na ji kamar Alhaji ne ya faɗa, dan shima ako yaushe cewa yake ayo haƙuro da rayuwa. “In sha Allah Yaya, Allah Ya ƙara lafiya, sai anjima.” Ina tura masa na kashe data, na tashi na fito falo, na tarar da Turaki yana fitowa. “Sai yanzu?” “Na sake wanka ne.” “Muje na raka ka to.” Na faɗa, tare da amsar jakar tasa mu ka yi waje. Daidai lokacin kuma Bilkisu ta fito daga ɓangarensu, tana sanye da wata doguwar riga lace, ta san wani farin mayafi a kafaɗa, ta bayanta kitsom attach duk ya zubo, mota ta fara ƙoƙarin buɗewa, kallo ɗaya na yi wa motar na ɗauke kai, motar da aka ce an siya min ita ce wacca matarsa ke hawa, na kalli Turaki da yake buɗe motarshi, na ce. “Da yaushe zaka dawo?” Kafin yaban amsa, aka buɗe ɓarin su Sardauna, ya fito da ɗan gudu gudunsa yana faɗin. “Bilkisu, kin manta abincinki.” Hannu tasa ta amsa, tare da faɗin. “Oh, ina ta sauri wallahi, thank you.” “Yaushe kike so na dawo?” Turaki ya faɗa, na kalleshi sannan na matsa kusa da kunneshi na ce. “Karfe sha biyu na rana.” Ya yi dariya, sannan ya ce. “Sha biyu me aka yi kuma? Ai sai dai na dawo araound 2 na ci abinci na koma.” “To kaga ga Islaha nan ba ruwana.” Na faɗa ina dariya, shima dariyar ya yi ya ce. “Sai kin ji kira daga sama.” Ƙarar tashin motar Bilkisu ne ya tsayar mana da maganar da muke yi, shima Turaki ya shiga tashi motar, na miƙa masa jakar tare da faɗin. “Allah Ya tsare hanya Mijina, a tawo min da tsaraba.” Ya ɗago min hannu, tare da cewa. “Me zan tawo miki dashi?” “Kayan daɗi.” “Tom idan na dawo, zan baki.” Na yi dariya na matsa gefe, ya tada motar tashi shima ya fice, ban kalli inda Sardauna yake ba na yi ciki. “Ke tsaya.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na talatin da ɗaya. Banza na yi masa kamar ban ji ba, na shige part ɗin, bansan Sardauna ba shi da hankali ba sai da na ga ya shigo yana kiran sunana. “Nana, Nana, Nana.” Ban kai ga tsayawa ba, naga Islaha ta fito har wani gudu gudu take yi, jikin ta na rawa ta fara magana. “Yaya ina kwana?” “Lafiya.” Ya faɗa tare da nufo inda nake, cikin ƙaraji na fara magana. “Sardauna, karka kuskura kazo inda nake, me ua sa baka da hankali? Bakasan ni matar aure ba ce.” Ya saki wani shu’umin murmushi, wanda ada nake kallonsa a matsayin, murmushin soyayya, ya taku inda nake sannan ya ce. “Nana, ke a ganinki yanzu ke matar aure ce, matar wani ba Sardauna ba, wallahi Nana ƙarya kike, baki isa zama mallakin Turaki ba, mene rana ta, mene amfanin abun da na ƙulla, Nana ni Sardauna bazan taɓa barinki ki rayu cikin salama ba.” “Sardauna ubangiji ne kai? Wa waye kal hallita a duniya? Dan haka babu abinda ka isa ka yi wanda Allah bai tsara shi ba, ka ji da abinda ke damunka Sardauna, kana pretending kana zaune da matarka lafiya, bayan ta mayar da kai bawa, Sardauna gatan da ka samu a wajena ka raina, shine kake biya a yanzu.” “Ke rufe min baki.” Tsaki na ja na bar masa wajen, dan bazan iya tsayawa na ci gab da magana da Sardauna ba, sabida ba ma muharrami na ba ne, babu wata magana a tskanina da shi. Ban kai cikin ɗaki ba na ji yana cewa. “Ke, kina matsa musu kuwa? Na faɗa miki ko da minti ɗaya kar da ki kuskura ki barsu su zauna lafiya, ki yi tada musu hankali ta yanda zasu ji auren ya fita akansu, na faɗa miki ranar da Turaki ya saki Nana, ranar zan tsaya miki kema ya sake ki, kuma a ranar da kika fita daga iddah, muma za a ɗaura namu auren.” “Tom Yaya, zan ƙara dagewa.” Mutuwar tsaye na yi, gaba ɗaya abun yana neman juyar min da guntun tunani na, na kasa gane me maganar Sardauna take nufi. ‘A ranar da Turaki ya saki Nana, a ranar zan tsaya miki ya sake ki, kuma kina gama iddah muma za a ɗaura namu auren?.’ Me kenan? Ita Islaha tana zaman ne anan bisa Umarnin Sardauna, tana zama ne na tayar mana da hankali mu ji auren ya ishemu, sai ni na ce Turaki ya sake ni, idan ya sake ni sai itama Sardauna ya sa shi ya sake ta, sai su yi aure, kenan son shi take, shine yake amfani da son da take masa, yasa take aikata wannan shirmen? Haka na yi ta faman saƙe saƙe, da kwance kwance kamar wata ƙaramar yarinyar, ina kuma mamakin islaha, ‘ina iliminta ya shiga, ina wayewarta, da har zata zauna namiji ya haukata ta haka, ashe akwai wacca ta fini hauka a soyayya? kai Sardauna mitsiyaci ne. Ina nan zaune akan kujera na kasa tashi, ni tsoron Sardauna ma nake yi a yanzu, al’amuransa kamar wanda baisan Allah ba, kamar wanda bai san kalmar shahada ba, babu ɗigon imani a ransa, abinda yake so shi yake yi? Tashi na yi na shiga kicin, na ɗora jollop ɗin taliya, girki na yi kamar ranar girki na ce, danni a yanzu ina ga kamar babu wani bambamci tsakanin ranar girki na da ba tawa ba, tun da ita Islahan ma ba hankali ne bane da ita, banga abinda za ta yi ya dameni ba. Ƙarfe ɗaya da kwata Turaki ya shigo gidan, tun bayan fitar Sardauna banji motsin Islaha ba sai a lokacin ta fito tana mai sannu da zuwa, ya amsa fuskarsa a sake sai na ji wani ba daɗi, maimakon na yi masa sannu da zuwan sai na coge ina kallonsa. “Hajjaju.” Ya faɗa yana kallona, na yi gefe da kaina kamar ba nice na ce ba abinda zai dameni da islaha tun ba hankali na ne da ita. Matsowa ya yi tare da kama hannu, na fara koƙarin cirewa ya ce. “Me ya faru?” “Bakomai.” “Faɗa min mana Habibty.” “Goyani zaka yi.” “Goyo da tsakar ranar nan, kinsan yunwar da na kwaso kuwa Habibty.” “Nima yunwar nake ji, amma ta goyo.” “Cewa zaki yi ke dai rigima kike ji, to hau na goyaki, idan kuma mun faɗi tare ay shkkenan.” “Uhm.” Na faɗa ina cuno baki gaba. “To mene kuma ai goyakin zanyi.” “Na fasa.” “A’a baki isa ba.” “Allah na fasa.” Na faɗa ina nufar wajen dinning, ya biyo ni yana cewa. “Sai fa na goyaki.” “Ka zauna ka ci abincin ka, ka koma ofis.” “Yawwa Habibtyna.” Ya zauna na zuba masa abincin, bai kai ko laumar farko ba Islaha ta dawo tana faɗin. “Wai ni mene matsayina a gidan nan ne? Yau fa girki na ne, shine zaka zo nan kana cin abinci.” Sai da ya turo abincin da ya ɗebo bakinsa, sannan ya ce. “Yi haƙuri, yunwa ta dawo dani.” “Ai kafin ka kawo ta ba dawowar kake ba.” “Yi haƙuri dai.” Ya faɗa yana mai da hankali ga abincin, ni kuwa ina kallonsa da ido, zuciyata cike da tausayinsa, a raina ina tunanin irin mugun halin Sardauna, duk ya matsawa rayuwar bawan Allah, ya hana shi zaman lafiyac ya ƙaƙaba masa abubuwa ko ta ina, yanzu wannan Islahan kawai ya sakota a rayuwar Turaki, ba son ta yake ba, ba son shi take ba, kai Allah Ya raba mu da zalunci. “Habibty, abinci ya yi daɗi.” Maganar shi ta dawo da ni daga tunanin da nake yi, na yi murmushi na ce. “Ka ci dayawa.” Daidai lokacin aka tura ƙofar aka shigo, wasu matane manya su uku suka shigo, Turaki na ganinsu ya mayar da kai ga abincinsa. “Baza ku yi min asara ba.” Ya faɗa ƙasa ƙasa, cikin wata iriyar izzah su ka yi sallamar, na miƙe na nufi wajensu tare da faɗin. “Sannunku da zuwa.” Sai dai su ka yi min banza kamar babu wata hallita a wajen, na buɗe baki zan ƙara ce musu sannu da zuwa, Islaha ta fito idonta ya yi ja jir kamar wacca ta shi kuka, sai jan hanci take. “Kun gani ko, see.” Ɗaya cikinsu ta faɗa tana nuna Islaha, ni dai ganin haka ya sa na matsa na koma wajen mijina, shi kuma daidai lokacin ya gama cin abinci ya taso. “Sannunku da zuwa.” Ya faɗa bayan ya ƙara so. “Ashe ka ganmu.” Wata ta faɗa a cikinsu, ya yi murmushi sannan ya ce. “Na ƙarasa cin abinci ne.” Islaha ce ta fara magana cikin kuka, tana yi tana jan majina. “Anty gaba ɗaya ya daina ko kulani, ya daina magana dani, yau fa ranar kwana na ne, amma a falo ya kwanta, da safe na kamashi a ɗakinta suna cire kaya, ya yi breakfast wajenta, yanzu ma gashi ya bar ofis ya dawo, na ce masa ya dinga adalci ya mare ni, ita kuma tana zugashi, har da ce min ‘yar marasa kamun kai, miji ya ce baya sona na zuana.” Ban gama tattare hankalina daga ɗimbin mamakin da na shiga ba, na ji an ɗauke ni da wani azababben mari mai sa jiri, a take na fara ganin dishi dishi, sai dai ban gama jin raɗaɗin shigar marin ba na ji sautin wani marin. ‘Tas.’ “Nusaiba karki kuskura ki ce ko da wasa zaki taɓa matata, karki kuskura wallahi ba ki da hankali ne.” “Turaki ni ka mara akan yarinyar nan? Akan mace?” “Na mareki Nusaiba, an faɗa miki gidana banzan gida ne da zaku zo ku yi abinda kuke so har da dukan matata, to wallahi baku isa ba.” “Kai marar kunya, banza da baisan kansa ba, baisan darajar kansa ba, dan ka auro wannan tsohuwar karuwar taka shine duk zaka bi ka ruɗe.” “Anty Alisha kar ki sake kiran matata karuwa, you know something? Duk ku fitar min daga gida har da ita Islahan, ba ƙanwarku ba ce? To ku ɗauke ta ku tafi nagaji.” “How dare you’re Turaki, akan wannan yarinyar zaka ce a ɗauki Islaha, wallahi baka isa ba Turaki ka yo kaɗan, kuma zalunci da kake yi wa Islaha sai mun ɗau fansa, sai ka amsa kira agaban hukuma, tun da mu family ne me displine, amma kaje ka ɗauko wata banza zata wargatsa mana cikin gida, to wallahi ba ta isa ba.” Ta ƙarasa maganar tana ga kawo inda nake, sai da tazo gab sannan ta cakumi kwalata, ta fara jijigani, cikin zafin nama Turaki ya matso ya yi wurgi da hannunta, ya fara magana cikin ƙara. “Ku bari na ce da ku, ku tafi ku bar min gida, bana son zuwanku.” “Nusaiba, Alisha, kuzo mu tafi.” “Yaya ya ce fa nabi ku fa, kar ku tafi ya dake ni.” “Kar ya fasa dukan naki, gaki gashinan.” Suna faɗin haka suka fice, nima na yi cikin ɗaki da gudu, ina shiga na faɗa kan gado na fara kuka, sai da na yi mai isata sannan na yi shiru, ina ɗagowa zaune ma ganshi yana zuane akan kujerar dake gefen gadonmu, ya zuba min idanu yana kallona, sunkuyar da kaina na sake yi, ya yi saurin matsowa kusa da ni. “Habibty.” Ya kira sunana, na yi shiru ban amsa ba. “Habibty ki yi haƙuri dan Allah, ni na ja miki har aka dake ki, ki yi haƙuri dan Allah.” Na girgiza kai, na ce. “Ni ce naja maka saɓani da ‘yan uwanka, ni ce na shigo rayuwarka da tarin matsaloli.” “A’a ba haka bane Habibtyna, ki yi haƙuri abar wannan maganar dan Allah, dan annabi, ko a kaina ne ki rama marin.” Na girgiza kai, sannan na ce. “Bakomai fa, ya wuce, ka tashi ka koma.” “Na koma aina? Ai ina tare dake ofis ya tashi.” “A’a ka koma kar ka zauna a gida.” “Tom, tashi mu tafi tare.” “Ina?” “Wani waje.” “Ko sati banyi fa, ba inda zani.” “Aiko yau aka kawo ki sai mun fita, zaki shirya ko na shirya ki?” “A’a zan shirya.” Na faɗa ina miƙewa, shima ya fita yana cewa. “Bara na canja kaya.” Doguwar riga na ɗauka nasa, bayan na fito daga wankan na ɗauki mayafinta nasa, bayan na yi wa fuskata light care, daga powder sai man baki, na ɗau jakada takalmi na, nasa wayata a jaka na fito falo, zama na yi akan kujera dan bazanje ɗakinsa ba ya ƙara ja mana wani abun, ina zaune naga Islaha ta fito daga ɗakinta, wayata ce ta fara ƙara na yi saurin ciro ta daga jakar na duba. “Hello Ra’is.” Na faɗa bayan na ɗaga wayar, daga can ɓarin ya amsa da. “Yaya Nana ya gida?” Tun da na auri Turaki Ra’is ya koma ce min Yaya Nana. “Lafiya ƙalau, ya su Hajiya.” “Kowa lafiya, wai daman su Hajja ne suka ce a tambayeki yaushe zasu zo?” “Too Ra’is yaushe kake gani, yanzu dai fita zamu yi dashi dan ma na shirya, amma idan naga yanayin gidan gobe sai na ce su zo.” “To Allah Yakaimu, komai da lafiya a gidan?” “Lafiya ƙalau Ra’is.” “To ma sha Allah, sai anjima.” Ya faɗa yana kashe wayar, ina ɗaga kaina na ga Turaki a tsaye. “Ra’is ne kenan?” “Eyh shine.” “Taso mu tafi.” “Ni sai dai ka goyani.” “Yanda kika ce ai haka za ayi ranki ya daɗe, hau.” Ya faɗa yana tsugunnawa, na yi dariya sannan na ce. “Bazaka karye ba?” “Habibty ko irinki goma bazasu karya ni ba.” Ya faɗa yana cacumata ya ɗorani a bayansa, ai kuwa ya ɗauke ni cas muka fice, ina dariya, shima yana dariya. “To ka sauke ni anan?” “Ai har mota, ko munje ma a baya zan shiga dake, duk wacca ta ganni tasan mijin Hajiya ne.” “Ko mijin ta ce ba.” Na faɗa ina dariya, shima ya yi dariyar sannan ya ce. “A’a kan ta ce ne ni.” Na sake wata dariyar, daidai lokacin muka fito ɗaga part ɗinmu, a lokacin kuma Sardauna yake fitowa daga cikin motarsa, wani irin bugu na ji ƙirjina ya bada. ‘Fat… fafat.” Shi kuwa Turaki ko ajikinsa ya taka zuwa wajen motar. “Ai baki da nauyi Habibty.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na talatin da biyu. Wata uwar ƙarar hon ce ta cika harabar gidan, wadda ta firgita mu har Turaki ya yi ƙoƙarin watsar dani ƙasa, sai da ya yi zafin nama ya tare ni na faɗa jikinsa. “Sannu.” Na faɗa ina ƙoƙarin miƙewa, ya riƙe ni tare da kashe min ido ɗaya. “Baki da nauyi Habibty.” “Na ji, amma tashi kana ƙasa fa, kayanka zasu ɓaci.” “Sai na canja wasu.” “Mu kuma mu ɓata lokaci.” “Na ji ni dai.” Duk yadda naso Turaki ya cika ni mutashi yaƙi, sai da muka kusa minti goma a zube a ƙasa, sannan muka tashi. “Juya naga bayanka.” Na faɗa ina koƙarin juyashi, ya juya naga duk ƙasa ta ɓata wajen. “Gaskiyya sai ka canja su.” “Tom ranki ya daɗe.” Ya faɗa tare da nufar cikin, ni kuma na koma jikin motar na tsaya, har ga Allah ni nama manta an hallici wani Sardauna a wajen, sai da na ɗaga kaina, kawai na ganshi ya zuba min idanu kamar zai cinye ni, na kau da kaina gefe tare da ɗauko waya ta na fara dannawa, ina tsaye Turaki ya dawo cikin wasu kayan, na buɗe mota na shiga shima ya buɗe ya shiga muka bar gidan. Kwata kwata Turaki bai min maganar Sardauna ba, haka nima bance mai komai, tun rana da muka fita bamu muka dawo ba sai bayan biyar, duk wani babban wajen shaƙatawa dake dutse sai da muka zaga shi, mu ka dawo a gidan gajiya ligib, kasancewar yamma ce kuma a ƙoshe muke ya sa bamu nemi abinci ba, ba mu yi girki ba. Wajen ƙarfe takwas na dare Turaki ya shigo, ina zaune inda dannawa waya, dan kwana biyu ma fahimci danna waya, akwai dadi ga ɗebe kewa. “Habibty ta shi.” Na miƙe ina faɗin. “Lafiya?” “Gidan Big Daddy zamu.” “Toopa.” Na faɗa, sannan na nufi sif na ɗauko mayafi na yafa na fito, Islaha na tsaye a falo shima yana tsaye, ina zuwa suka yi waje duka. Har da sauri na naje na buɗe gidan baya na zauna, na barta a gaban ta ci uban da zata ci. Tafiyar ta kasance shiru, babu wanda ke ce da ɗan uwansa komai, har muka ƙarasa gidan. Bansan zaman Babba ba ne, sai da na ga ‘yan gidansu Turaki dukkansu, da kuma ‘yan gidansu Islaha, a raina na ce. “Oh su mu saniyar ware.” Da sallama muka shiga duka, nuna shiga islaha ta yi ɓarin da ‘yan gidansu k zaune, ni kuma na yi kusa da ƙannen Turaki na zauna, babu wanda ya ce komai sai da Big Daddy ya zo, Big Daddyn dai ban taɓa sanin shine Big Daddy ba sai a yanzu, daman a wajen family meeting nake ganinsu, to kuma ni banda tabbacin waye wani Big Daddu sai yau. Bayan ya zauna ne, ya fara magana. “Abubakar! Abubakar! Abubakar.” Ya kira sunan Turaki sau uku, ba iya Turaki ba, ni kaina sai da na ji gabana ya faɗi sabida irin kiran da ya yi masa. “Na’am.” Turaki ya faɗa kansa a ƙasa. “Kan ka aka fara auren dangi?” Ya girgiza kai. “Kan ka aka fara haɗa mata biyu?” Ya sake girgiza kai. “Kan ka aka fara haɗa mata a dangi da wata a waje?” Nan ma ya girgiza kai. “To me ya sa naka zai zo daban? A kan mata ka sa hannu kamari Alisha, ka mari Nusaiba, ka mari Islaha, ka mari Rufaida, dukka akan mace. Bayan zalunci da kake yi wa Islaha a cikin gidan.” “Big Daddy wallahi ba haka ba ne, abinda suka faɗa duka ba haka ba ne.” “To idan ba haka ba ne yane? Ƙaryata ni zaka yi? Idan ka ƙaryata Alisha da take babba kaf cikin ku nima ƙaryata ni zaka yi?” Mamansu Islaha ta faɗa, sannan ta ƙara da cewa. “Ban da jaraba irin ta Islaha, ina so a wannan? Ina son a wannan da ya gama bin matar aure?” “Haba Hajiya Falmata, wannan wace irin magana ce ai kya jira manya su sasanta tun da a gabansu ake.” Momy ta faɗa, Hajiya Falmata ta tare ta cikin matuƙar fusata. “Ni rufe min baki, ai daman ko mene bazaki goyi bayan gaskiyya ba, zaki ɗauki ɗanki ne.” “Ku bari mana, mene amfanin zuwa nan da kuka yi? Dan a fahimci juna ne fa.” Matar Big Daddy, Mama Amina ta faɗa. Big Daddy ya ja numfashi sannan ya ce. “Islaha mene ƙorafin ki?” “Ƙorafi kuma?” “Falmata ki yi min shiru.” Big Daddy katse ta sannan ya sake cewa. “Islaha mene ƙofarinki?” Cikin muryar kuka ta fara magana. “Baya zama ya yi hira dani, Baya cin abincina, baya kwana a tare dani sai dai a wani ɗaki daban, ranar kwanana ma na kama shi a ɗakinta.” “Shine ƙorafin?” Ta gyaɗa kai, sannan ya juya ga Turaki ya ce. “Abubakar, matarka Islaha ta kawo ƙararka bisa waɗan nan abubuwan da ta lissafi, ko mene dalilinka na yin haka?” Sai da ya yi kusan minti biyar, sannan ya ce. “Big Daddy, Mom, Mama da sauran mutane ina neman afuwarku bisa abinda baki na zai furta, amma kamawa ta yi, bana so ku ɗauki kalamai na a matsayin rashin tarbiya ko wani abu na daban, maganar zama hira da Islaha, taƙi bani haɗin kai kwata kwata, ko ds muka yi aure ba ta taɓa zama mun yi magana da ita ba, ban taɓa zuwa na tarar ta yi min girki ba, tun auren mu har rana mai kamar ta yau, Islaha bata taɓa sauke haƙƙin aure guda ɗaya nawa akanta ba, hannu Islaha ba ta taɓa bari na kama mata ba, bansan irin auren da take yi dani ba, bansan matsayin aurena da ita a yanzu ba, ko magana na ke yi mata bata tsayawa, haka zan ta binta ina magana amma ko kallo ban ishe ta ba.” “Toopah!” Mama Amina ta faɗa, Big Daddy ya ce. “Islaha haka ne?” “A’a, nice nake binsa yana hulaƙantani, idan namasa girki ba ya ci, idan ina masa magana baya kulani.” “Me ya sa baki taɓa kawo ƙara ba? Kuma a yanzu ma da kila lissafa ƙorafinki baki faɗe su ba?” “Haba, a dinga adalci mana. Shi an yarda da zancensa ita na ta an ƙaryata.” Hajiya Falmata ta faɗa, Big Daddy ya ce. “Aina kika ji na ce ƙarya take, shi gaskiyya yake?” “To idan ma haka ne, marin da ya yi wa ‘ya’yana duka fa?” “Zaki iya yin shiru, wallahi idan kika kaini bango zan cire hannuna alamarin na barshi da ita, ko sakinta ne ya yi.” “To ya sake ta mana, idan ya sake ta sai me? Mene a ciki? Kanta zawarci farau? Matar da yake rawar ƙafa a kai ma bazawara ce.” “Ni A’a, Mommy kar ya sakeni dan Allah, kar ya sake ni.” Islaha ta faɗa tana kuka, ni dai ina zaune ina binsu da na mujiya, ɗakin ya kacame baki ɗaya, Big Daddy ya yi shiru, sai dai Mama Amina ta bashi haƙuri sannan ya sake magana. “Kar na sake jin bakin wani, idan ba magana aka yi da shi ba, Islaha mene gaskiyyar abinda ya faɗa, alamu sun nuna shike da gaskiyya.” “Ni ban iya girki ba, kuma bai kirani ɗakinsa ba.” “Zaki rantse da Allah? Sau nawa ina zuwa ɗakin ki?” Turaki ya katse ta, kawai ta saki kuka, Big Daddy ya ce. “Abubakar me ya sa ka daki Alisha, da Nusaiba, da Islaha, Hajara.” “Daddy, Nusaiba kawai na mara, itama sabida ta mari mata ta ba tare da ta yi mata komai ba, daga ta tashi tana musu sannu da zuwa, tasa hannu ta ɗauke ta da mari.” “Nusaiba.” Big Daddy ya kira ta. “Me ya kai ki marin matarsa?” “Rashin kunya ta yi min.” “Ba ta girmeki ba? Gidan ta fa kika je.” “Ni dai wannan zaman ba shi da wani amfani, zaman zalunci ne, ku tashi mu tafi.” Hajiya Falmata ta faɗa tana miƙewa, sauran ‘ya’yan nata suka miƙe, Big Daddy ya ce. “Abubakar, ya za ayi da Islaha?” “Tabi su kawai.” Mommy ta ce. “A’a Turaki, kuje idan Allah Yaso zaku sasanta idan abun ya gagara, kawai ka dawo da ita.” “Shikenan Mommy.” Ya faɗa yana miƙewa, su ma su ka miƙe duka muka fice, motarmu muka shiga suma suka shiga tasu, a yanzu ma bayan motar na shiga na zauna, ita kuma ta sake zama a gaba. Muna tsaka da tafiya Turaki ya ce. “Habibty, ya asibitin?” “One month ya rage, ban ma san yaushe zan koma ba.” “Monday ya yi ko?” “Eyh ya yi.” Na faɗa, sabida bana so aja hirar, zai zama kamar cin fuska ga Islaha, wacca ta rakuɓe kamar ba ita a motar, a raina na ce. “Kina wahalal da rayuwarki, babu abinda zai sa Sardauna ya aureki, mussaman a yanzu da ya zama mijin ta ce.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na talatin da uku. A haka muka ƙarasa gidan, ya koma ɗakin Islaha bansan yanda suka yi ba, ni dai fatana kawai kwana na ya dawo, cikin ikon Allah ya dawo muka ci gaba da rayuwa cikin farin ciki da kwanciyar hankali, Monday ta zagayo na koma asibiti, Turaki ke kai ni na dawo da kaina, tun da na koma sau ɗaya na haɗu da Dr Aliyu, ko kallon arziƙi bai samu daga wajena ba, kuma bansake bi takan shi ba, haka ma Sardauna idan zan ganshi sai dai safiya, amma lokacin dawowa ta bana ganinshi. Haka rayuwa ta fara tafiya a cikin gidan Turaki, hankali na kwance bani da wata damuwa, Islaha ta fita daga sha’anina, nima na fita daga na ta, Sardauna ko kaɗan bana ganinshi, Bilkisu ce ma kulluk da safe sai mun haɗu amma ko kallon banza ba ta yi min bare na arziƙi, ita rayuwarta kawai take kullum tana waje, ta san ƙana nan kaya ta fita ta dawo a lokacin da ta so, masu aiki ne da ita sunfi kala biyar, hatta girki suke yi. Turaki kam soyayya kullum da sabuwar da yake zuwa da ita, kulawa ma ta daban, ba ruwansa da idon kowa, nuna min soyayya yake, a zamana na wata ɗaya zuwa biyu naga soyayya daga ‘yan gidansu na ga bambamci da zaman gidan Sardauna. Yau ce rana ta ta ƙarshe a asibiti tun sha biyu naga ma komai na tawo gida, ina tunanin na zarce gidanmu, ina tunanin na wuce gidana kawai, ƙarshe na yanke hukuncin wucewa gidana. Kasancewar a ƙafa na shigo layin yasa na bi ta ƙofa maimakon gate, rana ta take ta buɗe iya ƙarfinta, haka na shigo part ɗina, ina shiga na yi ɗakina na shiga toilet na watsa ruwa, na fito na buɗe sif zan ɗauki kaya, sai da na ji sautin magana ƙasa ƙasa, har zan rufe na ji ance. “Islaha, idan baki raba auren nan ba sai dai mu yi ta rayuwa a haka ni dake.” Muryarta ƙasa ƙasa na ji ta ce. “Yaya Sardauna na rasa hanyar da zan raba auren nan, kaima ka yi shiru ka barni, bana so na ɗauki ciki muna rayuwa a haka, da wane ido zan kalli jama’a, Turaki dai ba abinda zai sa ya amshi cikin nan.” “Nima ba zan ba shi ba, zan riƙe abuna, ki yi ƙoƙari ki raba auren a satin nan, mu samu a ɗaura namu, nima na gaji da zama da Bilkisu, ina son na sake ta amma ko ido bana iya haɗawa da ita, sai rashin mutuncin da ta ga dama take yi min, na girki, ba sannu da zuwa, ba zama a gida kullum tana wayo atiti, sai dare. Gashi ta cika gida da masu aiki kuma duk ni nake biya, gashi taƙi ta haihu kullum tana yawon kwararo.” “Idan ka aureni komai zai kau, kasan yanda nake son ka, kasan alƙawarinka akaina.” “Islaha, aikin ki shine ki yi ta tada tarzoma a tsakanin zaman Nana da Turaki, naga har wata soyayyar munafurci suke yi, ranar nan sun kusa sa zyciyata ta buga, idan har baki kunna musu matsala ba, zan rabu dake na nemi wata hanyar, kuma zance cikin dake jikinki ba nawa ba ne, zance wani abu bai taɓa haɗani da ke ba, tun da ba hujja gareki ba.” “Yaya Sardauna, zan yi, zan shiga zan fita, zan haɗa da ‘yan uwa ayi ta kunna mata bala’i, har sai zaman gidan ya isheta ta fita dan kanta.” “Idan kika yi haka ni kuma ba zaki yi sati ba sai na raba aureki da Turaki na aureki.” Da sauri na saki sif ɗin, tare da faɗin. “Islaha sai dai ke ki bar min gidan nan, amma zama da Turaki da izinin manzan Allah yanzu na fara, kai kuma ba kishi ba, wallahi sai na ƙona ma zuciya.” Na faɗa tare da dawowa kan gado na zauna, na zuba uban tagumi na rasa abin yi, al amarin Sardauna na daban ne, dole na dage kai da fata, tin da alhamdulillah tun shigowa ta gidan nan kullum Turaki sai y tashe ni sallar dare, sia da fa, kaina da shi da iyaye da ‘yan uwa nakr roƙo, tun da na yi aure na manta da Sardauna, dan aganina ga tarin buƙatu me zai sa na kama suna Sardauna a gaban ubangiji. Ji na yi wata ƙaras. ‘Tas.. tas.. tas.’ Kamar ana fasa abu, da gudu na fito falon na ga Islaha tana faman duka Tv ɗina da taɓarya. “Tanan kika biyo?” Na faɗa tare da shiga cikin camera a wayata na fara mata hoto da video, a fili na ce wannan faɗan da ilimi za ayi shi, zaku san Nana ta yi karatu me tsada, sai da na gama ɗaukan tsaf sannan na fito falon na kalleta na kawar da kai, sai da na ji kan kujera na zauna sannan na ce. “Ashe ciwon hauka ne ya tashi? Muna zaune da mahaukata.” “Uwarki ce mahaukaciya.” Na saki wata dariya sannan na ce. “Au Falmata, na ga ni kuwa ta dinga hauka agaban big Daddy.” “Allah Ya tsine miki Nana, wallahi yau sai naga gatanki.” Na miƙe tsaye sannan na ce. “Ashe zaki gatana, bayan ubangijin da ya hallice ni, Islaha bazan yarda ke riƙaƙƙiya ba ce sai kin fasa duk wani abu na nan, kinje kin fasa na ɗakin ki, shine zan tabbatar da arziƙin ku sai naga tsakanin ni dake wace za a fara canjawa wasu.” “Ƙarya kike ‘yar mitsayata, zan je na fasa nawa ki gani cikin ƙasa da awa 24 sai an canja min komai.” A raina na ce. ‘Tafi jaka.’ A fili kuma na ce. “Ni kuma a ƙasa da awa biyar zan a canja min komai nawa, shege kafasa muje zuwa.” Ai kuwa ta tafi da gudu ta yi ɓangarenta, ni kuwa na bita a baya na laɓe ta can na fara ɗaukanta hoto da video irin ba a san ina ɗauka ba, ina gamawa na yi cikin ɗakina, na ɗau number Lamrah ‘yar gidan Big Daddy ce, zuwan ƙarshe da ƙannen Turaki su ka yi har ita suka zo. Ina kira ta ɗauka, na fara magana cikin muryar kuka. “Lamrah, dan Allah kuna da driver available, na kira gidansu Mommy duk wayarsu is’nt reachable, na kira Turaki akashe, kisa driver yaje gidan ya ce musu su taimaka su zo nan, ba lafiya wallahi Islaha sai fashe fashe take ita ka ɗai, ta fasa kayan ɓangarena ta je tana fasa nata shigowa daga asibiti kenan, yanzu ina toilet na kulle kaina, tsoro duk ya cikani, dan Allah Lamrah da wuri.” “Innullahi wa’inna illahir raji’un, yanzu ke kina ina?” “Toilet.” “Mama! Mama.” Naji tana faɗa, da kuma sautin gudu alamar guda ta yi, ta cikin wayar na ji Mama amina na cewa. “Lamrah kin ɗaga hankali mene?” “Yanzu Anty Nana ta kirani, wai a taimaka mata Islaha sai fashe fashe take a gidan, ta kira number su Mommy ba ta shiga, Yaya Turaki ma haka.” “Subhanallahi, fashe fashen me? Ɗauko min gyalena.” Katse wayar na yi, duk sai na ji ba daɗi na ruɗa mutane, amma gwanda na nunawa Isalaha makirci, idan sharri take ji, ni kuma zan nuna mata na koyo ilimin rayuwa nasan yanda zan sa reshe ya juye da mujiya cikin ƙanƙanin lokaci, sai ta bar gidan, shi kuma Sardauna sai mu fafata da shi, wanda ya fasa Allah Ya tsinema uwarsa. Daga nan na koma ɓangaren Islaha, na tsaya ta bakin taga na ce. “Ai baki yi musu kaca kaca ba, kamar nawa, ko kina tsoron kar kuɗin gidanku ya ƙare akan siyan kayan ne.” “Ai arziƙi ba zai ƙare a gidan Ta ambo ba, sai dai ku naku da ba asan inda suke ba.” “Gashinan nagani.” Na faɗa tare da barin wajen, ina shiga ɗakina na ji alamun shigowa, kusan a tare motoci biyun suka yi parking, ina jin sun shigo na fito da gudu, na faɗa jikin Mama Amina ina kuka. “Nana nutsu, faɗamin mene?” Kuka nake wiwi, ina nuna musu ɓangaren Islaha, aikuwa suna leƙawa suka ganta riƙe da taɓarya tana make make. “Ke islaha! Kin yi hauka ne?” Mommy ta faɗa, a tsorace ta saki abun hannunta, nasan a ranta mamakin yanda aka yi suka zo take, ni kuwa na ce baki ga komai ba, nima fa macece, kissa da kisisina ai sai dai na koya wa wani, zama da Sardauna na shekara uku ai sai dai na zama malamr koyar da makirci. “Me ya shiga kanki haka?” Mama Amina ta faɗa, Lamrah kuma ta yo kaina tana faɗin. “Anty Nana ki daina kuka, gamu munxo ba abinda zai faru.” Fitowa Islaha ta yi zuwa falona, idonta ya sauka a kaina da nake ta kuka. “Kunga kamar ta yi hauka, ni bana so ta fasan kayana.” Na faɗa ina kuka, a fusace Islaha ta ce. “Uwar ki ce ta yi hauka.” Da sauri na tashi zan gudu, Lamrah ma ta kwasa gudu, a lokacin kuma Turaki ya shigo. “Innullahi me yake faruwa?” Jin muryarshi ya sa na tsaya. “Me ya faru, Islaha mene haka? Nana waye ya yi abun nan?” “Gatanan.” Mama Amina ta faɗa tana nuna Islaha, ya matso zai yi kusa da ita, Mommy ta ce. “A’a, kar ka je kusa da ita fa, tsaya daga inda take.” “Haba Mommy, me ta yi ne? Hauka ne?” Ya faɗa yana nufar ta. “Na ce karka je.” “Haba Mommy.” Ya faɗa yana ƙarasawa kusa da ita, ya riƙe mata hannu wani ƙululun abu ya tsaya min a zuciya, shine har ds riƙe mata hannu ku? Na faɗa ina maka mai harara. “Islaha me ya sa kika yi haka?” Kuka ta fashe da shi, sannnan ta ce. “Ka rabu dani.” Ta faɗa tana ƙwace jikinta. “Me ya sa kika yi abinda kika yi.” “Na yi ɗin, wallahi idan baka saki Nana ba, sai na yi abinda yafi haka.” “Babu Nana da zai saka sai da ya sake ki dan ubanki.” Mama Amina ta faɗa, sannan ta ƙara cewa. “Ni abun nan yafi ƙarfina, ka kira uwarta ta zo taga abinda ta yi, sabida idan an faɗa ba yarda za su yi ba,kayan can da ta fasa nata ne, na Nana kuwa sai anbiyata.” “Ni abun ma mamaki yake ban, kamar me bori, ka yi mata wani abu ne? Ko ke Nana kin mata.” “Ni dai ban mata komai ba, tun safe na tafi asibiti, dawowa ta kuma na gata tafi to daga part ɗin Sardauna, kamar acan abun ya faru, ina shiga ɗaki ko zama banyi ba na ji ana fashe fashe, da na yi tunanin iya nawa zata fasa sabida na kula ta mu yi faɗa yasa na ce bazan kulata ba, zan dai ɗauke ta a hoto sabida hujja kar ta ƙarya tani, bayan na ɗauke ta na ga abin ya wuce misali, ta koma na ta ɓangaren, shine na fara gwada lambobinku amma basa shiga, ta Lamrah ce kawai ta tafi.” Na bada wannan bayanin kamar an wajen bincike, Islaha ta yi min wani kallo, sannan ta ce. “Uban kine ya kai ni ɗakin Sardauna, ko naje ai Yayana ne, kuma ba abinda muka yi.” “To ni na ce kunyi wani abu ne? Kawai kin tsargu.” “Ku tsaya ni bangane komai ba.” Mommy ta faɗa, Mama Amina ta ce. “Ke da kika dawo kinga fitowarta daga part ɗin Sardauna, bakisan komai ba kika shige ɗaki, kafin ki yi wani abu kika ji ana fashe fashe.” Na gyaɗa kai na ce. “Eyh.” “Ƙarya take, ko da na fito daga part ɗin Sardauna na kusa minti talatin kafin na fara fashe fashen.” Isalaha ta faɗa, a fusace Mommy ta ce. “Au, har amsawa kike kinyi fashe fashen, sabida ba wanda ya isa dake?” Mama Amina ta ce. “Kawai a kira gidansu, a kira kowa ya zo gani a haka, Abubakar idan ka ga dama ka ɗau duk matakin da yakamata, tun da iskancin na ta ya fara yawa.” Waya yasa ya kira Mama Falmata ya ce akwa matsala a gida, ita kuma Mama Amina ta kira Big Daddy. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na talatin da huɗu. Cikin ƙanƙanin lokaci su Hajiya Falmata suka iso gidan, da ita da Alisha da Nusaiba, kowa yazo yaga abinda Islaha ta yi sai ya tsaya yana kallonta, har Big Daddy yazo. Cikin faɗa ya fara mata magana. “Islaha wannan wane irin shirmene? Me kika aikata haka?” “Big Daddy, ita ce ta sani.” “Ita wa? Mahaifiyar taki kowa?” Ya faɗa cike da faɗa, domin ransa ya yi matuƙar ɓaci, Hajiya Falmata ma cikin fushi ta ce. “Kamar ya ni na sata, banda hankali ne zan sa ta ta yi asara?” “Ita matarsa ita ce ta ce idan na isa na farfasa kayan.” “Ke kuma mahaukaciya ko?” Ya tambayeta, Mama Amina ta ce. “Ƙarya ma take, so take ta shafa mata kashin kaza a fuska. Yanda kika ɓata kanki a family ita ma ki ɓata ta, ko abinda Sardauna yake faɗa a kanta, a zuwan su Lamrah duk sunce ƙarya ne.” “Wallahi Mama ƙarya ne, gasu Hajara nan, tana sa kyauta, tana da mutunci, gidansu suna da mutunci, tana son ‘yan uwa.” Wani irin nauyi na ji, da haka Sardauna ya yi ta ɓatani, ya hananu fita cikin ‘yan uwansa da nawa, kowa yana mun kallon mai mugun hali, dan na tuna a wancan zuwan da su Hajara suka yi, shima sun zo da wata yarinta ta ce, wai da tsorona ma take yi, a raina na ce. ‘Allah Ya isa Sardauna, ba shi anan, amma duk masifar shi ya tsarata.’ Big Daddy ya ce. “Islaha a karo na ƙarshe mene dalilinki na yin wannan ɗanyen aikin?” Ta yi shiru ba ta ce komai ba. “Ba magana ake yi miki ba Isalaha, zan cire kaina fa.” Hajiya Falmata ta faɗa, dan ita kanta ta fusata da abinda ‘yar ta ta yi, cikin kuka ta ce. “Sun ware ni, ko magana ba sa yi da ni har ita Nanan, ko zama mu yi magana ba sa yi.” “Kin basu fuska ne?” Big Daddy ya faɗa, Hajiya Falmata ta sake magana a fusace. “To dan uwarki dan basa baki fuska dole ne? Uwarki ce ita ko ubanki, ke daman akwai wata fuska sa ake so a wajen kishiya? Sabida ke baki da hankali shine zaki hau fashe fashe, kowa yazo ya yi miki kallon mahaukaciya ko?” “Mommy, ki daina mata faɗa, ahaan da me zata ji please.” Alisha ta faɗa tana matsawa kusa da ita, ta riƙe ta fara shafa mata baya, a raina na ce. ‘Ahaaan da me zata ji, da ubanta.’ Na yi ɗariya ta a ciki na haɗiye a bata. “Abubuakar!” Big Daddy ya kira Turaki, ya ɗaga kai tare da amsawa. “Ka sa akwashe duka kayan nan, acanja wasu a daren nan, ni zan bada kuɗin duka, Islaha kar nasake jin irin wannan ta taso.” Yana faɗin haka ya fice, ni dai wannan mutumi akwai nuna wariya, ga izza da ta ƙama, tun da ake zuwa gidansa bai taɓa kama suna na ba, gashi har yau ma da yazo namu gidan. ‘Canka ƙarata.’ Na faɗa a raina, ni yanzu ai wargi ce daidai da ƙugun kowa, akan Turaki zan iya tashin kowa. Kama hannu Islaha suka yi suka shige ciki, ni kuma na miƙe kamar wacca ta yi kuka, Mommy ta ce. “Nana.” Na ƙarasa kusa da ita, tare da zama a ƙasa. “Ki yi haƙuri da dukkkan abubuwan da suke faruwa kinji.” “Bakomai Mommy, nasan komai zai wuce da yardar Allah.” “Allah Ya yi miki albarka, Allah Ya kaɗe duk wata fitina.” Na ce. “Amin.” Turaki ya kira masu kwashe kaya duk suka zo suka fita dasu, bayan tafiyar su Mommy duk akazo akan canja su, ni dai tun da na shige ɗaki ban fito ba, takaicin abinda Turaki ya yi wa Bilkisu a gaban mutane ya fara ƙoƙarin riƙeta duk yabi ya dameni a raina, ai kuwa ina na zaune ya shigo, yana shigowa na miƙe na yi toilet. “Habibty sai da kika ganni, please ki yi sauri.” “Idan zaka tafi ka tafi, ba inda zan fito.” “Subhanallahi, Habibty me ya faru?” “Komai ma, wai kaje kana koƙarin kama hannun Islaha a gaban mutane, kai ga me mata, sai ka tafi kaje ka kama hannun nata.” “Haba Habibty, ki yi haƙuri ki fito zan faɗa miki dalilina.” “Wane dalili? Faɗa min ina nan?” “Haba Matar Turaki, Amaryar Turaki, Nanan Hajiya da Alhaji, ‘yar gatan su Yaya Ridwan, Yaya a wajen Abokina Ra’is, jikar Hajja ba da kanki asare.” “Bazan bada ba, kuma bazan fito ba.” Na faɗa, ina wuci.” “Yi haƙuri ranki ya daɗe.” “Bazan fito ba fa.” Takowa ya yi zuwa bakin ƙofar, ya fara magana. “Habibty kina jin na, ki fito idan na faɗa miki dalilina, idan na faɗa miki baki gamsu ba sai ki koma.” “Wato na koma ko?” Na faɗa tare da buɗe ƙofar na fito, na ja na coge a bakim ƙofar toilet ɗin na ce. “Ina jinka?” “Nana, Islaha fa mata tace, ya zaayi na ganta a wannan condition ɗin na tsaya baya baya.” “To sai ka je kana wani kama mata hannu, har ta wani fisgewa.” “Ki yi haƙuri Nana, baran sake ba.” “Ai zaka sake wallahi.” “A’a Sarauniyar mata bazan sake ba.” “Ni fa bazan haƙura ba, kawai ka koma ka ci gaba da kama mata hannu.” Tsugunnawa ya yi a ƙasa ya haɗe hannayensa, ya ce. “Nana ki yi min rai, na tuba bazan sake ba.” “Uhmm.” “Kinji My Love.” “Uhmm.” “Bari na yi frog jump, idan na yi tsallen ƙwaɗo zaki haƙura ko?” “Eyh zan haƙura.” “Haba Habibty.” Na haɗe rai, na ce. “Bazaka yi ba kenan?” “A’a zanyi, da gudu ma.” Ya fara ƙoƙarin yi, na yi sauri na ce. “Bana so, ni kawai bazan haƙura ba.” “A’a sai kin haƙura Habibty.” Na juya zan shiga toilet ɗin, ya yi saurin riƙo ni ta baya. “Haba Habibty na, ki yi min rai, fushinki babban uƙuba ce a gareni.” “A’a Islaha ce.” “Habibty.” “Ni kaina ciwo yake, ka tafi zan kwanta.” “Na tafi ina? Zo mu kwanta tare.” “Nifa yau bazan kwanta da kai ba, kaje wajen Islaha kawai.” “Ni Abubukar yau na ɗaukowa kaina abinda ya girmeni.” “Uhm.” “Xo kiga.” Ya faɗa yana kama hannu, ya jawo ni zuwa falo, komai na ɗakin an canja shi kuma ya yi kyau fiye da baya, gwanin burgewa. “Habibty kinga.” “Waye ya yi selecting kayan nan?” “Sun yi kyau?” “Sosai ma.” “A wajen na cewa wata yarinya ta yi min selecting kayan, amaryata zan canjawa, ina son waɗan da zasu burgeta.” Na haɗe rai, na ce. “Kai ko ina mata kakewa magana?” “A’a Habibty, sabida ke ne?” “Uhm, ni yunwa nake ji, kuma banyi girki ba.” “Tom Habibty, bari na zo muje ko?” “Tom, amma ka yi wa Islaha magana, ta ce ana ware ta.” “Habibty, ba turin jeka ka mutu kika yi min ba ko?” Sai da na yi dariya, sannan na ce. “Allah, kaga yakamata ai.” “To bara na mata magana, sai na shirya.” Ya faɗa yana shiga part ɗin nata, wajen minti biyar sannan ya fito. “Ta ce ba zata ba.” “Ita tasani.” Na faɗa, shima ya yi ciki ya shirya, sai da ya fito naje na ɗauko mayafina, muka fita hannun shi a cikin nawa. Daidai lokacin da muka fita Bilkisu tana fitowa daga motarta, Sardauna ya tsaya a bakim ƙofar part ɗinsu ya haɗe rai, bai ko kula da mu ba ya fara faɗa. “Bilkisu, na gaji da wannan abun naki? Idan kika fita sai lokacin da kika ga dama zaki dawo? Ba kya zama gida kwata kwata, kullum kina yawo, babu wani haƙƙina da kike saukewa.” “Kin tsyaa jin gulmar wasu ko?” Turaki ya faɗa, na kalleshi na ce. “Kaifa ka ce na dinga samo ma gulma.” “Ni, a ina?” Na yi dariyar da ta jawo hankali su Sardauna, sannan na ce. “Ranan nan mana ko kamanta?” “Kai Habibty ba ayi haka ba fa.” Ƙamewa na yi a inda nake, ya kalleni ya ce. “Lafiya.” “Bazan iya takawa ba” Na faɗa ina cuno baki gaba. “Me ya sa? Ko na ɗauke ki?” Na gyaɗa kai, aikuwa ya yi sama dani caf, muka ƙarasa. “Malam ka matsamin hanya na wuce.” Bilkisu ta faɗa, Sardauna ya ce. “Ki koma inda kika fito.” “Sardauna wallahi ba inda zani, kana tsaye kana kallon matar mutane, duk surutun da kake yi a ciki ba isa ba, ka yi ta kiran sunan ta idan kana bacci, bai ishe ka ba sai ka fito kana kallonta.” “Bilkisu Allah ba zaki shiga ba.” Daidai lokacin Turaki ya sakani a mota, sai da ya matso kusa dani ya ce. “Habibty ba kyau gulma.” “Ni gulma nake?” “Kunneki yana wajensu, ba kyau gaskiyya.” Shiru na yi masa, ya zagayo ta shigo ya kunna motar muka fice, tun da muka fara tafiya bai ce min ƙala ba, nima bance mai ba, haka muka fara tafiya, sai da muka yi nisa ya ce. “Habibty zamu canja gida.” “Na kalleshi, sannan na ce. “Gida kuma?” “Eyh Habibty, bana jin daɗin kusanci ki da Sardauna, tsakani da Allah ina kishi, kuma hankalina baya kwanciya.” “Bangane baya kwanciy ba?” “Kina ji matar sa ta ce idan yana bacci sunanki yake kira.” “To sai me? Idan mun tashi daga gidan zai daina ne?” “Idan yana ganinki yana jin daɗi a ransa, ni kuma ina kishinki Habibty, kuma nasan yana miki magana ko da ba kya kulashi.” “Ni kuma zan so mu zauna a gidan nan, ko sabida naga yanda Sardauna zai girbe duk abinda ya shuka, kasan Islaha zamansa take a gidan nan, duk wani tashin hankali namu shi yake kunno mana, sai kuma Allah Ya haɗa shi da ƙaddarar Bilkisu, baka ganin abinda take masa, ta mai da shi sallamamme, duk wani abu shi yake yi, ita tana yawon a kwararo?” “Habibty nasani, amma bana son gana kuna haɗa hanya, idan kika ganshi fa yanayinki sauyawa yake.” “Ni ba wani abu da yake sauya a jikina.” “Ba kya so kenan?” “Idan ka dage ba yanda zanyi, amma zan so zama anan ɗin, sabida akwai aikin da na ɗauka.” “Wane aiki ne Habibty.” Na yi shiru, sabida bana son faɗa masa, dan na yi ɗauki aikin sai na kashe Sardauna da baƙin ciki da kishi da takaici, sannan sai na tona masa asiri shi da Islaha, amma ban san fahimtar da Turaki zai min ba idan na faɗa masa. “Eyh Habibty.” Na kalleshi sannan na ce. “Zamanka da Islaha tana cutar da kai, tana cutar damu, ina so da kanta ta faɗi abinda ya kawo ta da zaman da take, yanzu idan kabiye ta abinda take tsaf zata raba muku zumunci, ni kuma abinda bana so kenan?” Sai da na faɗa na ga ƙwarewata a raina na ce. ‘Lallai ba haushe ya yi gaskiya da ya ce, wanda aka mara ya yi hankali yafi wanda aka haifa dashi.’ “Habibty, kina ganin bazaki samu a matsala ba?” “Babu wata matsala Mijina.” “Allah Yasa.” ************ Zama gidanmu ya dawo wani salo na daban, tun da na gama zuwa asibiti kullum ina cikin gida, sau tari da yawa na kanji maganar Sardauna da Islaha, duk wani zargi na yana neman ya tabbata, da Sardauna yake ce da Turaki mazina ci, shine mazinacin kenan? Ita Islaha bata tsoron kowa idon ya rufe da ruɗin Sardauna? Ya mayar da ita kamar matarsa, kuma yaƙi aurenta alhalin da igiyar wani ta aure akanta? Bilkisu kuwa ta mayar da shi shanyayye, ranar ina jin su suna ta faman faɗa, ita ta gaji da abinda yake mata shima yana cewa ya gaji da abinda take masa, zama gaba ɗaya yaƙi daɗi, shi ba ta bashi duk wani abu na aure, ko ɗaki ɗaya a yanzu basa kwana, ita kullum tafi ta sai dare, weekend ne kawai take zama a gida, bayan nan kullum tana kwararo, shi kuma ya gaza ɗaukan mataki akanta, sai da ya yi mata magana da baki, kuma tai ta hayayyaƙo masa, ba shi da damar yin wani abu, kamar tsoronta yake ji, sai yanda ta ce da shi zai yi, ga haihuwa kuma shiru, babu ita babu alamanta. Lallai Sardauna ka fara ganin rayuwa. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na talatin da biyar Bayan wata uku. Kamar yanda dare yake wanzuwa ya koma safiya, safiya ta wanzu ta koma dare, haka rayuwata take juyawa abubuwa duk suka canja, a yanzu ma haka take, zaman mu ya canja gaba ɗaya na gidan, tsakanina da Islaha ba magana ba komai, sai mu shafe sati biyu ko uku banganta ba, haka tsakaninta da Turaki, shima sai ya shafe kwana nawa bai sata a ido ba, idan ma ya je tana kwance take masa magana, ranar kwananta haka zai kwanta a falo sabida ba ta barin shi ya shiga ɗakin, girki kam daman ba yi take ba, kullum nice ke yi, duk rashin zaman da muke da ita amma rashin ganin na ta ya ɗan dameni, ni tsorona ka da ace irin ciwon da na yi a baya ta shiga, shine duk abinda ya ɗaga min hankali. A hankali nake takawo na fito falon, yau ma bata nan, haka kawai na yanke shawarar shiga part ɗin ta na je ko lafiya dai, danni bazan iya zaman nan haka ba, shirun na ta ya yi yawa, kuma idan wani abu ya sameta dole da laifi na a ciki. Na nufi hanyar part ɗin na ta na ji an buɗe ƙofa, Turaki ya shigo da sallama, da mamaki na juya gareshi tare da faɗin. “Welcome.” “Thank you Habibty, ina zaki?” Na girgiza kai, sannan na ce. “No fitowa kawai falo na yi, ya aka yi ka dawo da wuri.” “Albishirinki?” “Goro.” Na faɗa ina kallonsa, shima yana kallona ya ce. “Tukwicin me za a ban?” “Me kake so?” “Anything special, me girma sosai.” “To faɗamin.” “A’a, sai kin ce zaki ban.” “Zan baka.” Na faɗa daidai lokacin kuma wayata ta fara ringing, ina dubawa naga sunan Ra’is, ina kallo na ce. “Habibi kasan me?” “Sai kin faɗa.” “Wai Ra’is ne zai kawo min yarinyar da zai aura, wai har anyi magana, na ce ya kawomin ita sai na yi mata duka, Ra’is ɗin nawa yake?” “Dagaske yake fa, jiya anyi magana kuma da wuri za ayi abun, yarinyar tana Ss2 amma wai za ta yi exam wannan shekarar, gaba ɗaya abun ba zaifi 6 month ba.” Wayar na ɗaga tare da faɗin. “Kai Ra’is mene, ba dai shirmen zaka ci gaba da min ba ko?” “Mitcheww, Matar Yaya Ridwan ta haifi twins yanzu suna asibiti.” “Wayyo Allah, dagaske kake Ra’is?” “Gaske nake mana.” Yana faɗin haka ya kashe, na kalli Turaki na ce. “Shine albishir ɗin?” “Me ya ce miki?” “Matar Yaya Ridwan ta haifi twins.” “Wow Ma sha Allah, yaushe?” “Yanzu wai, to mene naka albishiri ɗin?” “Baki faɗi abinda zaki bani ba.” “Me zan baka to, koma mene zan baka.” “Ungo.” Ya faɗa yana miƙomin takarda, na sa hannu na amsa ya ce. “Duba.” Na buɗe na fara dubawa, idona ya cika da ƙwalla a lokacin da naga Upper aiki ce, a babban asibitin dake birnin Dutse. “Ya Allah, na gode sosai mijina, Allah Ya yi maka sakayya da gidan Aljanna.” “Amin Habibty na.” Ya faɗa yana matsowa kusa da ni, ya rungume ni a jikinsa ya ce. “Habibty karki yi kuka dan Allah, bana son zubar hawayenki dan Allah.” “Na farin ciki ne Habiby, na gode maka, na godewa Allah da ya bani miji kamar kai, tun da ka shigo rayuwata, alheri kawai kake kawo min, kana cika min duk wani burin mahaifina, na gode sosai da sosai.” “Nima na godewa Allah da mata kamar ke, Habibty samunki wata baiwa ce da Allah ya yi min, ina sonki ako yaushe.” “Nima haka Habibi.” “Muje ki ban abinci, muje asibitin.” “Tom.” Na faɗa tare da jan shi zuwa dinning, na zuba masa ya ci, sannna na shiga ɗaki. Ina zuwa na zauna a kan gado, gaba ɗaya sai na ji na damu. ‘Anya kuwa na warke? Anya kuwa zan haihu? Ya Allah.’ Na faɗa a take na ji hawaye sun fara zuba a idona, sai da na yi kusa minti goma sannan na tashi na shiga ban ɗaki na watsa ruwa. Ina fitowa na ganshi tsaye a bakin ɗakin. “Habibty.” Ya kira sunana, na amsa da. “Naam Habiby.” “Na ji kamar kinyi kuka?” Na girgiza kai, sannan na ce. “Me zai sani kuka?” “Zo mu zauna.” Ya faɗa yana nuna min gefen gadon, na matso na zauna shima ya zauna. “Habibty, da haihuwa ko ba haihuwa, ni zan zauna dake, ban aure ki dan wata buƙata ba, Nana na aureki dan ina sonki, ko kin haihu, ko baki haihu ba zan zauna dake, dan Allah karki damu kanki.” Na girgiza kai, sannan na ce. “Nasani, na gode.” “Ki ta shi ki shirya muje.” Tashi na yi na sanya doguwar riga muka fice, gaba ɗaya na manta da zancen zuwa wajen Islaha da na yi, mu ka fice zuwa asibiti. Asibitin ya cika da ‘yan uwa da abokan arziƙi daga ‘yan uwanmu har na matarsa, su Yaya Radiya kowa yazo, Ra’is kamar shi aka yi wa haihuwa, ina shiga na karɓi ‘ya’yan duka a lokaci ɗaya, wani irin son sa ya ratsa zuciyata a lokaci ɗaya na ji kamar ni ce na haifesu, a take na ji ƙwalla na ƙoƙarin fitowa daga idona, da sauri na goge sai dai idon mutane ya riga ya gani. “Nana.” Yaya Radiya ta kira ni, na ɗaga kai na kalleta na ce. “Yaya ‘ya’yan masu kyau.” “Nana.” Ta sake kirana, na ce. “Na’am.” “Kar ki bari wani abu ya ɗarsu a zuciyarki dan Allah, ki dage da addu’a Allah ya zai baki haihuwa, gaba ɗaya yaushe kika yi auren ba a shekera ba Nana, kuma likita da kanta ta ce mahaifarki ta warke, dan Allah karki bari wani abu ya dameki dan Allah.” “Yaya ba komai fa.” “Ɗazu ma kafin mu fito sai da ta yi kuka, na ce mata ta yi haƙuri komai zai wuce, Allah zai bata in sha Allah.” Turaki ya faɗa, yana matsowa inda nake, na ce. “Kallesu.”’ “Na gansu Habibty, kuna kama wallahi.” “Nima haka na ce, sun yi kama da babbansu, kuma daman ita da babbansu take kama.” Yaya Rumaisa ta faɗa, a lokacin Yaya Ridwan ya ce. “Nana.” “Na’am Yaya.” “Nana.” “Na’am.” “Ki tafi dasu na bar miki su duka.” Ji na yi kamar saukar aradu a kaina, nasan Yaya Ridwan ba ya taɓa maganar wasa, na kalleshi kafin na yi magana Yaya Radiya ta ce. “Mahaifiyarsu fa?” “A’a, daman tun kafin mu yi aure ya ce da ni ‘ya’yan mu na farko na ƙanwarsa ne, kuma na amince amma dai a barsu har zuwa na yayesu ko?” Ta faɗa tana daga inda take, Yaya Rumaisa ta ce. “A’a Muhibba, ana jin wannan maganar an san ba a son ranki ba ne, kuma ɗaukan ɗan fari a bada shi abu ne mai matuƙar taɓa zuciya, ni dai a tawa shawarar ku riƙe, idan Allah Ya baku wasa a gaba sai ku bata, idan kuma Allah Ya basu shikenan.” Turaki ya ce. “A’a, ba za ayi haka ba, tun da har sun bada gaskiyya muna so, ko Habibty?” Ni dai tuni hawaye suka wanke min fuska, wace irin ƙauna Yaya Ridwan yake min, har ya sanar da matarsa cewar ‘ya’yansa na farko na wane? “Yaya, muma Allah zai bamu wasu, kuma idan muka bata ba faɗuwa ba ne, sabida a wajenta kamar a wajenmu suke.” Muhibba ta faɗa, ni kam wani irin tausayinta ya ratsani, ni da bani na haifesu ba amma ji nake bana son a rabani dasu bare kuma ita da ta haifi kayanta, na ce. “Yaya, na gode da wannan kyautar da ka yi min, na gode sosai da soyayya, Allah Ya yi sakayya da Aljanna, Anty Muhibba na gode sosai da karamci, na gode matuƙa, kuma ina son su, so mai girma, amma kafin na so kaina na dubaki, Anty Muhibba ni da bani na haifesu ba a yanzu ji nake ba zan iya rabuwa dasu ba, bare kuma ke da kika haifesu.” “Nana indai kina so ki amsa, babu komai a zuciyata, tun kafin yanzu na riga da nasan da haka, har iyayena sun sani, kuma sun goyi bayan hakan.” “Na gode Anty Muhibba, na gode.” Na faɗa ina zubar da hawaye, Turaki ya ƙara matsowa kusa dani ya ce. “Habibty, mun gode, mu tafi dasu ko? “A’a ku jira aji ta bakin Hajiya.” Ra’is ya faɗa, a lokacin kuma ‘yan uwan Muhibba suka shigo, da ƙyar na iya basu yaran, wata cikin ‘yan uwan Muhibba ce ta ce. “A shawarce dai abar yaran nan su sha nonon mahaifiyarsu, lokacin yaye su kuma wajen ita wacca aka bawa.” Akan shwararta aka zauna, sai yamma mu ka tafi na ce dashi mu fara zuwa gidan Hajiya, aikuwa mun sha faɗa, muna faɗa mata ta ce. “Wannan ai fun ƙarfi ne, kuma zai zo ya sameni, kawai yarinya daga haihuwa sai ka ɗauki ‘ya’ya ka yi sadakarsu, sabida shi yafi kowa son ‘yar uwarsa, to ban lamunta ba, ba da yawo na ba.” Turaki ya fara lallaɓata, ni kam na sa ƙafa na yi waje, na shiga cikin mota na zauna, sai daga baya can ya fito, muka wuce gidan Momy, itama da muka bata labari ta ce. “A’a, ni ban taɓa ganin inda aka yi kyautar ‘ya’yan fari ba, da ace tana da wasu ne, sai a ɗauke waɗan nan, amma wannan daga zuwansu sai a baku, ku kuma ku ce kun ansa, ku canja shawara gaskiyya, kuma ku yi haƙuri dudu yaushe kuka yi auren? Kuma kun ce likitoci sun tabbatar mahaifarta ta warke zata ɗauki ciki, to ku yi haƙuri kawai.” Ni dai duk gida biyun ba wanda na ji daɗin zuwansa, haka na lallaɓa na tawo gida duk raina ba daɗi, naga samu na ga rashi, haka Turaki ya yi ta rarrashina. Washe gari ma tun safe muka je asibitin, na ɗauki ‘ya’yan na riƙe su ina kallonsu, haka Turaki ya barni a asibitin ya tafi ofis, ni har na ware ma sunan da zan sanya musu idan an bani su, tun da duka mata ne zan sanya musu, Qudrah da Sauwamah, sunayen sunyi min daɗi, su Yaya Radiya duk anan suka zo suka same ni, har da Ra’is. Tun da aka yi haihuwar ban sami zama ba kwata kwata, shi ya sa ban bi takan Islaha ba, haka na yi ta yawo tsakanin asbiti, kwananta uku aka sallameta suka koma gidansu, nan ma haka na yi ta sintiri har aka yi suna, ranar suna suka cin Sunan Hajiya da kuma Maman Muhibba, amma za a kira su da Qudrah da Sauwama sunan da na zaɓa musu, kuma Yaya Ridwan yana nan akan bakansa na bani su, bayan an yayesu, nima nida Turaki muna nan akan bakanmu na amsar su. Sai bayan anyi suna da ‘yan kwanaki sannan nasami nutsuwa, hankali na ya dawo gida, a lokacin na tuna da Islaha, tin da aka yi haihuwa ban ganta ba sai dai motsinta, Turaki ya na dawo na sa shi a gaba akan lallai sai mun je mun ganta. “Habity me ya sa kika takura? Ranar kwanta fa ina zuwa.” “Ina tsoron kar ta kamu da irin ciwon da na yi, shirun na ta ya yi yawa.” “Habibty ina ganinta fa, har ɗaki nake shiga na yi mata magana, tana amsa min amma dai kullum tana kwance kamar ruwa.” Na matso kusa da shi, sai da na kama hannunsa sannan na ce. “To ka ji, kullum ace mutum yana kwance ai kasan ba lafiya ba, ka taimaka muje dan Allah.” “Habibty muje.” Na tashi, shima ya tashi muka nufu ɓarin na ta, daman ba a samunta a falo kai tsaye muka yi ɗakin gadonta!nan ma bata nan, na kalle shi na ce. “Tana ina?” “Ko tana wancan ɗakin.” Ya faɗa, mun juya da niyar fita muka je tana buɗe toilet, muka waigo gaba ɗayan mu, ta fito ba tare da ta kula da mu ba. “Islaha.” Na faɗa ina motsowa, ta ɗaga kai a tsorace, tana ganinmu ta juya zata shige ciki a tsoroace, sai dai garin juyin da za ta yi idona ya sauka akan babban cikin dake jikinta, wanda kana ganinsa ya kai wajej wata huɗu, a tsorace na ce. “Islaha.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na talatin da shida. Da sauri ta juya zata shiga banɗaki, cikin rashin sa’a sansti ya kwashe ta ta nemi zubewa a ƙasa, cikin zafin nama Turaki ya yi wani irin tsalle ya tare ta, ta faɗa jikinsa. Nima da sauri na ƙasa wajen ina faɗin. “Sannu, Sannu Ishala.” Ita kam gaba ɗaya hankalinta baya garemu, burinta ta ɓoye cikin jikinta wanda ni na riga na gani, amma Turaki kam nasan bai kula ba. “Islaha, me yake faruwa da ke ne? Me ya sa kika zama haka? Mene abun gudu a tare damu?” Ya jera mata tambayoyi, kallona ta yi muka haɗa ido, wani irin tausayinta na ji ya ratsamin zuciya, na girgiza kai sannan na ce. “Kaje kawai, bari na yi magana da ita.” “Kina ganin ba matsala Habibty?” “Eyh babu Habiby, just go.” Ya miƙe ya fice, yana fita na kalle ta na ce. “Islaha ki yi haƙuri, ki faɗa min me ya ke faruwa, karki ɗaukeni a matsayin kishiya Islaha, ki faɗa min komai, zan taimake ki da zuciya ɗaya.” Kuka ta fara yi wanda nasan hakan alama ce ta karyewar zuciya, kuma zai bata damar faɗar abubuwa da yawa, waɗan da zasu sa zuciyarta ta yi sauƙi. “Nana ki yi haƙuri dan Allah, duk abinda ya faru akwai haƙƙinki a ciki, ni da ‘ ‘yan uwana a kullum bamu da aiki sai kira ki da karuwa, a kullum mune ke cewa da auren Yaya Sardauna akanki, kinje kuna abinda bai kamata ba da Yaya Turaki, wanda ko a zuciyar mu mun san ba haka ba, kawai mun faɗa a dangi ne sabida mu ɓata ki a dangi. Kafin aje ko ina sharri da ƙagin da muka yi miki ya fara bibiyar mu.” Ta yi shiru, ta fara kuka. “Islaha, ki yi haƙuri, ki ci gaba da faɗa min abinda ke zuciyarki, tabbas zai baki sauƙi sosai da sosai.” “Nana zan faɗa miki asalin gaskiyya daga farko, wallahi ban taɓa son Yaya Turaki ba, ban taɓa son zama da shi ba, tun da na dawo daga Abroad zuciyata ta kamu da son Yaya Sardauna, sai dai shi bai taɓa kallona a matsayin mace ba, ina zuwa gidansu sabida shi, ina masa girki, ina kiran shi a waya, amma Nana lokaci ɗaya ya yi aure, kuma ya aure ki.” “Nana tun daga wannan lokacin na tsane ki, na tsaneki tsana mafi girma a raina, kuma na yi alƙwarin ta kowanne hali sai na raba ku, zuwanki na farko family meeting, ni ce na kira Yaya Sardauna a waya na ce masa kun keɓance ke da Yaya Turaki, anan naga asalin son da yake miki, na ci gaba da tsanarki a zuciyata, cikin ikon wata rana Yaya Sardauna ya kira ni a waya, ranar na ji daɗi na yi farin ciki da ban taɓa yin sa ba, sai dai da ya kira ma aiki ya bani, wai akan na ɓata ki a ‘yan uwa, ni kam na ji daɗi tun da nasan tunda ya ce a ɓata ki, ya daina sonki, daga nan na ɗauki aikin ɓata ki a family, ni ce har gidan granny, har shaida na bayar akan naganki ke da Yaya Turaki a hotel. Nana duk wata tsana da ‘yan uwa suka yi miki nice na kunnata.” Nan ma ta ƙarashe tana kuka, gaba ɗaya jikina ya yi evening. ‘Ni Nana na haɗu da ƙaddarar rayuwa, yanzu ta yanda Sardauna ya raba ni da ‘yan uwansa kenan? Shi ya sa da ina gidan babu wata da ta taɓa zuwa, Allah Ya saka min.’ Islaha ta ci gaba da magana. “Amma ko yanzu zaki godewa Allah, tun da naga duk ‘yan uwa sun fara sakin jiki dake, sun daina tsanarki, sai dai Big Daddy shi kuma mutum ne mai magana ɗaya, amma with time zai fahimci komai. Nana ba iya nan aka tsaya ba, bayan aurenku ya mutu na dinga jiran Yaya Sardauna amma shiru, sai da suka ɗauki shekara da auren su da Bilkisu, sannan ya nemeni a waya, a lokacin ma haka na sake jin daɗi, kuma a lokacin ya yi min alƙawarin zai aure ni, amma da sharaɗi. Sharaɗin shine na je na ce ina son Yaya Turaki, na kuma dage akan ina son sa, har sai na aure shi, idan aka yi auren kar na bari komai ya haɗa mu da shi, na zauna sabida indai ya aureni ke kmua ba zaki aure shi ba. A yanda alƙwarin mu yake da Yaya Sardauna zanyi zaman wata uku ne anan, to daga baya zai sa ya sakeni sai shi ya aureni, wannan alƙwarin ya yi min. Amma cikin wata na biyu ya ce wai kin dage sai kin aure shi, sabida haka na zauna, bayan kunyi auren sai na dinga ta yar miki da hankali har sai kin ji zaman gidan ya isheki, daga ranar da Yaya Turaki ya sake ki, nima a ranar zai sa ya sake ni, sabida santsin soyayyar fa ya ɗebe ni, na sake amincewa. Nana babban kuskuren da na yi shine bawa Sardauna kaina, na mallaka masa kaina alhalin da igiyar auren wani akaina, Nana tsakanina da Sardauna ya zama kamar miji na, girki da banayi anan, to ina yi na ba shi, zanje duk lokacin daya buƙace ni, yanzu gashi ya yi min Sartse mafi rauni a rayuwata, Nana ciki ne da ni na Sardauna, Nana na shiga uku, na rasa abinda zanyi a rayuwata, Ƙazafin da na yi miki gashi ina kwashewa, Nana ina zan sa raina.” “Ki yi haƙuri Islaha, ni dai idan akwai haƙƙina akanki na yafe miki duniya da lahira Islaha, amma haƙƙin Turaki yana nan fal a kanki, ga zunubin zina da aure Islaha me ya kai ki?” “Sharrin da daɗin baki na mayaudari Sardauna, Nana na biye masa na yi dukkan abinda yake so.” “To yanzu yasan da haka?” Na tambayeta, ta girgiza kai alamr a’ah, na ce. “Kar ki bari ya sani, duk da yana son ‘ya’ya amma bana jin zai so ɗan da ba ta hanyar aure aka same shi ba, Islaha zai bi duk yanda zai bi wallahi ya zubar da shi, idan kika matsa zai lalata miki mahaifa kamar yanda ya yi min.” Cikin muryar kuka ta ce. “Nasani, nasan hatsabibancin Sardauna, shi ya sa na ɓoye kaina a ɗaki, kuma anan na ƙara tabbatar da baya sona, duk wannan tsahon lokacin bai taɓa nemana ba da ya jini shiru.” “Ai ba yi tunanin halin da kike ciki ba, amma ki zauna a haka, ni zan kula dake kuma zan fahimtar da Habiby, ta yanda zai gane ko ba a yanzu ba, dan Allah karki wani sa damuwa a ranki Islaha, Sardauna ba irin mutanen da za a damu akan su ba ne, Sardauna mugu ne, azzalumi ne, mai son kansa ne, kuma in sha Allahu zai ga sakkaya.” “Na gode Nana,na gode.” “Bakomai islaha.” Na faɗa tare da tashi, na je na zuba mata abinci da tea na kawo mata, sai da ta ci ta kwanta sannan, na koma ɗakin Wajen Habiby. “Habibty kin daɗe, duk hankali ya gaza kwanciya.” Na yi murmushin yaƙe, wanda iyakar saman leɓe, na ce. “Ba ta da lafiya ne sosai da sosai.” “Shine kika daɗe wajenta, almost an hour.” “To mene amfanin zaman mu waje ɗaya, idan ɗaya bai tsaya akan ɗaya ba a lokacin da yake ɓuƙata.” “Zuciyarki na da kyau Habibty, yanzu an gama kula da itan?” Na ce. “Eyh, an gama.” “To nima a zo a kula da ni.” Na ɗan haɗe rai, sannan na ce. “Nima bana wani jin daɗi.” “To Habibty asibiti ne akanki.” *********** Har Allah Allah nake gari yawaye na sallami Turaki ya fita, ina son na sami lokaci na zauna ni kaɗai ma yi dogon tunani, shi kansa ya fuskanci yau Allah Allah nake ya fita, da ƙyar na samu ya fita, yana fita na samu waje na zauna, na fara haɗa abubuwan da suka shafi Sardauna, abinda ya yi min da Islaha, basu da kamanceceniya, amma duk su na da suna ɗaya, mugunta. Har ta wani ɓari ma sai nake ganin kamar nawa ya fi sauƙi, ko da yake duk ɗaya, ni ya hanani haihuwa ita kuma ya bata cikin a waje. ‘Allah Katsine ma Sardauna.’ Na faɗa ina miƙewa, na ɗau wayata na kira Anty Muhibba matar Yaya Ridwan na ji lafiyar ‘ya’yana, danni ni dai na yi shawarar ko na ce munyi shawara da Turaki akan sai mun amshi yaran nan, tun da ba roƙa muka yi ba akan bamu. Kyauta ce aka yi mana, kuma bamu sani ba ko wannan ita ce kyautar da Allah zai bamu, idan muka qi amsa kuma muka rasa baki ɗaya fa. Bugu ɗaya ta ɗauka, muryata a sake na ce. “Anty Muhibba ina kwana?” “Lafiya ƙalau Maman twins, ya gida.” “Lafiya ƙalau, ina Yayana da ‘ya’yana?” “Yayanki gashi nan yana miki rainon ‘ya’ya.” “Allah Sarki babban Yaya, a miƙamin gaisuwa da godiya, ace maman twins ta gode.” “Tom zasu ji in sha Allah, sai anjima.” “Aji ma lafiya.” Na faɗa tare da kashe wayar, na yi ɓangaren Islaha, ganin abinci da na ajiye mata na breakfast ba ta ci ba ya sa na ce. “Islaha, karki bawa damuwa damar na kasa miki rayuwa, a yanzu fa bake kaɗai ba ce.” “Nana duk bakina babu daɗi.” “Ki yi haƙuri, ina tunani yau zamuje mu ga likita, amma zamu jira sai shima ya fita.” “Tom shikenan.” Ta faɗa tana fara kai abincin bakinta, haka muka yi ta jiran fitar Sardauna kamar wasu munafukai, ai kuwa yana fita muna muka fice, mu kaje asibiti ala duba ta aka yi mata scanining duk da lokacin da yakamata ta fara zuwa ya shiga. Muna gamawa da asibitin muka yi gidan, cikin sa’a babu wanda ya ganmu, haka muka ci gaba da rayuwa a cikin gidan, tsakanina da Islaha kulawa ce ta bada shawarwari, sai dai har yanzu na rasa ta hanyar da zan sanar da Turaki hakan sabida bana son abun da zai dame shi, amma kuma nasan dole ne na sanar da shi, Islaha kam wani lokacin Sardauna yakan kira ta ya ce ta zo, sai ta ce ba zata zo ba ta daina fita, tun da ma ya kira sau biyu bai ƙara kira ba, bai kuma nemeta ba, ni kam a yanzu nasan babu komai a zuciya sai mummunar tsanar Sardauna, har wani lokacin na kan zauna na yi ta mamakin yanda zazzafar soyayya ta ta koma ƙiyayya me zafi har haka, Twins muna ta shrin karɓarsu kam, an fara shiryr shiryen yanda zan za ayi musu ɗaki da kayan wasa, wata ɗaya da samun offer ta na fara aiki, a ranar kuma Turaki ya siya min mota, ranar kam na yi kuka na gode Allah, har gida na je na nuwa su Hajiya da gidansu Yaya Radiya da Yaya Rumaisa, kuma tar muke zuwa da shi yana nuna min yanda ake driving, wajen aikin da na fara zuwa a babban asibitin jiha ne, inda nake a ciki, babban aiki babban matsayi, babban ofis. A ranar da na fara shiga ofis ɗin ma sai sa na yi kuka, mussaman da na tuna, yau ni Nana ni ce anan, duk a sanadiyar Turaki tabbas na yarda aure dace ne, aurena na farko ya zama sanadiyar rugujewar dukkan mafarkai ne, sai kuma aurena na biyu ya zama sillar dawowar dukkan wani mafarkina, ya kuma tabbatar da su a rayuwar zahiri, wannan shine ake kira da NAMIJI GARKUWA. ********** Ƙarfe huɗu daidai na fito daga ofis ɗina na shiga mota ta na nufi gida, naso na biya ta gidan Hajiya sabida shirye shiyen auren Ra’is da muke, amma kawai na ji nafi buƙatar na tafi nawa gidan na huta, ga cikin Islaha a yanzu ya kai kusan wata biyar dan ya fito sosai, ina kuka tunanin ta hanyar da zan sanar da Turaki komai akan cikin, dan yakamata yasan komai kuma a ɗauki matakin da yakamata akai, tin da a yanzu cikin ya yi girman da Sardauna bai isa ya yi wani abu akai ba. Parking ɗin mota ta na yi a harabar gidan, na yi mamakin ganin motar da Turaki ya fita da ita. ‘Su Habiby yau an dawo da wuri kenan?.’ Na faɗa ina shiga ciki, sai da ƙamewa na yi ganin Turaki zaune akam kujera Islaha na tsugunne a gabansa tana kuka. “Habiby.” Legendspen 08129553971. SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na talatin da bakwai. “Habiby.” Na faɗa ina shigowa, wani kallo ya yi min wanda yasa jikina ya fara rawa, Turaki ko harara bai taɓa yi min ba, yau gashi ya yi min wannan kallon. “Ka yi haƙuri dan Allah, bana son na faɗa ma ne ya tayar maka da hankali.” “Yanzu da na gani fa? Me ya sa kika ɓoye min abu kamar wannan?” “Bansan ta yanda zaka ji abun ba, bana son abinda zai ɓata ma rai ko kaɗan Habiby.” “Ni ina zaune a gidana kenan a matsayin shashasha, matata tana ɗauke da cikin wani bansaniba, sabida ni ban da tunani, kwana da kwanaki bana ganinta amma nakasa damuwa na sauke haƙƙinta na je na duba ta sai a yau? Da ta mutu fa? Da wane ido zan kalli ubangijina?” “Ba laifin ka bane, namu ne ni da ita, ita ta ɓoye kanta da kuma shawarata, ka yi haƙuri.” Na faɗa ina zama kusa da shi. “Haba Nana, Haba Nana.” Wani irin abu na ji ya daki zuciyata, tin kafin mu yi aure da Turaki bai taɓa kirana da Nana ba, har muka yi aure, yau gashi ya kira da ni Nana, tabbas ko mene ya ɓata ran Turaki. “Yau ɗin ma baki tsara za a faɗan ba, sai da Allah Ya tsara kenan? Har na gama abinda zan yi na fita na ce dole sai na duba naga yarinyar nan, ina zuwa naganta da ƙaton ciki, ciki fa Nana, kuma a gidana, yarinyar da babu abu ɗaya da ya taɓa haɗani da ita, kinsan tana da ciki, kuma ciki na Sardauna amma kika ɓoye Nana, kina so ki rufa asirin Sardauna kenan? Tsohon mijinki, daman ya ce zako iya yi masa rainon yara shine yanzu kika fara.” “Ya isa haka Turaki!” Na faɗa a fusace, tare da miƙewa. “Nifa wannan abun da na yi ba na yi ba ne dan kaina ko wani abu, na yi ne dan na rufa muku asiri, amma shine zaka dinga faɗamin waɗan nan maganganun? Mene alaƙa ta da ita da cikinta? Duk wani abu da na yi dan na rufa asirinta ne na kuma kare ta, amma shine duk baka ga ni ba, to gata gaka, ku yi duk abinda zaku yi na tsame hannuna.” Ina gama faɗin haka na tashi na yi ciki, Islaha ta biyo ni tana faɗin. “Nana, dan Allah ki yi haƙuri ki tsaya, dan girman Allah. “Islaha tsakaninki da ɗan uwanki ne, ni ai bare ce daman, dan haka ku yi duk abinda zaku yi, ni gidanmu ma zan tafi.” “Ya salam.” Ta faɗa tare da komawa wajen Turaki, bansan me ta je tana ce masa ba, ni kam dai na fara zuba kayana a akwati, wannan cin mutuncin na Turaki har ina? Dan na shiga abu, shishigina uban wa ya sani? Haka na yi ta mita ina haɗa kayana, sai da na cika akwati dam, na sauke ta akan gado na ɗauki jakata da mukullin mota ta. “Nana.” Na ji ya kira suna na. “Ka ban hanya na wuce, Turaki bazan zauna ba ko cewa zaka yi na zauna, dan haka karka wahalal da kanka, laifi na ne da na shiga abun ‘yan uwa, bayan na manta ni bare ce.” “Kan ki kike kira da bare a wajena? Nana kinsan girman ki a zuciyata? Kinsan matsayinki a rayuwata? Nana kinfi ƙarfin rabin rai, sai dai dukkak rayuwar.” “Ba ƙaramar yarinya ba ce ni, da zan tsaya ka yi min daɗi baki, ka riga da ka nuna min matsayina, har da cewa zan rufe asirin tsohon mijina, daman so kake ka yi min gori kenan? Ka ce ina da tsohon miji? To bani na ɗaurawa kaina ba Allah Ya ɗoramin, dan haka ba zan ji ba daɗi ba da ƙaddarar ubangiji.” “Ya salam, Nana dan Allah ki yi haƙuri, ki tsaya ki fahimce ni dan Allah.” “Turaki ka bani hanya na wuce.” “Nana ba inda zaki.” Ai Nanan nan da ya faɗa ya ƙara ɗugunzumani, na ce. “Wallahi yau gidanmu zan kwana.” “Na ce ba inda zaki fa.” “Ni kuma na ce walllahi sai na tafi, ka zauna kai da ‘yar uwarka ku cinye juna, ni tafiya zanyi.” “To jeki.” Ya faɗa yana matsamin hanya, jikina ya yi sanyi, a hankali nake ɗaga ƙafa har na fito falo, ji na yi zuciyata na tsinkewa, ina zan iya zama babu Turaki? Amma dai gwanda na tafi na nuna masa muhimmancina, haka na fito jikina a sanyaye na shiga mota, sai dai ina shiga mota na ga Sardauna yana kallona, yana wani irin murmushi, sai na ji kunya ta rufe ni, haka na ja mota na yi gida. Ina shiga gida na fashe da kuka har da burgima a ƙasa, hankalin Hajiya ya yi matuƙar tashi, amma da takula da akwatina sai ta gane abinda ya faru. “Nana Allah Yasa ba ƙaddarar aure aure Allah Ya ɗora miki ba.” Ni kam kuka na nake ta ko ina, har Ra’is ya shigo gida, shima hankalinshi ya yi matuƙar tashi. Haka na gaji da kukana na kwanta, abu kamar wasa har yamma Turaki bai kira ba, har dare bai kira ba, abu kamar wasa kwana ɗaya kwana biyu, duk hankalina ya tashi na shiga damuwa, gashi Hajiya ma ta ce bai kira ta ba, Ra’is ma haka, ranar da n cika kwana na uku Ra’is ya kira shi amma sai ya ce da shi zai zo, anan na ƙara tabbatarwa Turaki ya daina sona, dan sai da na yi sati guda a gida sannan ya zo, ranar na ci kuka na gode Allah, da ya faɗawa su Hajiya kowa ya ga laifina, aka zauna aka yi min faɗa, buɗar baki na na ce. “Ni Hajiya kawai ya rubuta min takarda ta, wallahi ba sona yake ba.” Kowa sai da ya yi mamakin abunda na faɗa, ciki har da ni kaina. “Nana, kina cikin hankalinki?” Ra’is ya faɗa, Hajiya ta ce. “Ba ta dashi, ana ganin kamar ta yi hankali ashe ba ta yi ba.” “Hajiya bari na fa ya yi na yi sati guda anan.” “To bake kika buƙata ba?” Na yi shiru, ni dai raina ya ɓaci daga baya da aka lallaɓa muka koma, na yi mamakin rashin ganin Islaha, na ce da shi. “Tana ina?” “Tana gidansu.” “Me ya sa?” “Ki zauna ki fahimce ni Nana, na saki Islaha, saki ɗaya kuma ta koma gida, amma ba tare da Sardauna yasan komai ba, hasali ma ‘yan gidansu basu san komai ba, tana gidan Sister Seemah, kuma komai zaizo da sauƙi in sha Allah.” “Allah Yasa.” Na faɗa, daga nan muka ci gaba da zamanmu, komai ya fara wucewa a tsakaninmu, na mai da hankali ga aikina, da kuma kula da mijina, ƙarfe 9 Turaki yake fita, ni kuma sai 10, kuma ƙarfe 4 nake dawowa, aiki baya taɓa ɗauke hankalina daga mijina. Yau takama Weekend, kuma a lissafina saura wata biyu cif a kawo min ‘yan biyu na, fitowa na yi compund na ce da me gadi yaje can ya taromin yara anan, zanyi Sadaka, sabida jiya na yi wani kyakywan mafarki, wai ni da Turaki da yara guda huɗu muna wasa, maza biyu mata biyu, mafarkin ya faranta min rai sosai, shi ya sa nasa aka samo min sabbabbin ‘yan dari bibbiyu na yi sadakar dasu, ina zaune a ɗakin na ji yara sun fara magana a compound, na sanya Hijabina na fito. Ina zuwa naga duk sun hau layi na fara raba musu, yara suna amsa suna murna da addu’ar Allah Yajiƙan iyaye ya biya dukkan buƙata. Ina cikin yin sadakar na ji an buɗe ɓarin su Sardauna, Bilkisu ta fito a fusace. “Wane mitsiyacin ne ya tara mana yara anan, sabida ya hana mu baccin rana.” Na yi banza da ita na ci gaba da Sadakata, har na kammala sannan na juya na kalleta. “A’a Bilkisu ana ganinki daman?” “Ba aganina, ke wai tsaya, kin manta na ce miki ni ba sa’ar ki ba ce, kula ki da na yi a baya ma ƙaddara ce, kuma ko a yanzu ma baki kai na kulaki ba.” Bance mata komai ba ma juya na shiga, ban kai ga shiga ba na ji Sardauna ya fito yana faɗin. “Bilkisu ban kuɗi na.” “Wane kuɗi?” “Gashinan wanda kika yi transfer 2 millon zuwa account ɗinki.” Dawowa na yi na tsaya ina kallonsu, daman jiya na ji suna faɗa sama sama, amma ban mai da hankali na ji ba, danni yanzu tausayin Sardauna nake lokacin da zai ga Islaha da cikinsa na shege. “Haba wallahi bazan bayar ba, yaushe rabon da kaban kuɗi.” “Na daina baki, Bilkisu faɗa min amfanin ki guda ɗaya a gidan nan, haka kawai sai na yi ta ɗaukan kuɗi ina baki?” “To ni dai na cinye.” Ta faɗa tana ƙoƙarin shiga ciki, ai kuwa ya sa hannu ya yi baya da ita, ta faɗi ƙasa shaɓar. “Baby ni ka watsar?” “Na watsar, idan baki dawo min da kuɗi ba wallahi Bilkisu sai na ɓaɓɓallaki.” “Wallahi bazan dawo dasu ba.” Ta faɗa tana miƙewa, ni kuwa na dawo kan matattakala ta ake takawa idan za a buga ƙofar part ɗin mu na zauna, ina kallonsu. Ta ƙara yin ƙurin shiga ciki, ya sake jawo zai watsar ta riƙe, ya sa hannu ya kifa mata mari. “Kutumar uba, ka mareni?” Ta faɗa, shi kuma ya ce. “An mara, ki dawo min da kuɗina na faɗa miki.” “Wallahi ka mari kuɗinka.” Aikuwa Sardauna kamar jira yake ya fara dukanta har da bugun ta da ƙafa, tun tana ihu har ta fara ramawa, ta na yi tana zaginsa shi kuma yana ramawa, ni dai ina zaune ina kallonsu kamar TV, faɗa ya kaure, Sardauna yana dukan Bilkisu, Bilkisu na ramawa, ni banyi dariya ba amma na bisa da idona, abun ta kai har Sardauna a fincikewa Bilkisu kitson gashin doki guda ɗaya dake kanta. “Sardauna, ni ka yi wa haka, ni ka daka ka cirewa kitso?” Ai kuwa ta yi wani kukan kura ta ɗauki wani katako a gefe ta hau fasa masa masa glass ɗin motarsa, ta daki wannan ɓarin ta daki wannan ɓarin, aikuwa shima ya yi kanta ya sake wurgi da ita ta faɗi zuwa ɓangaren da nake, ai kuwa na miƙe ina ƙoƙarin shiga ɓangarena, ganin abun ya zama kamar faɗan arna da musulmai. Ta ƙara miƙewa tana faɗin. “Wallahi Sardauna naci kuɗi, kuma sai ka yi kashin wasu ma.” “Wallahi Bilkisu sai kin bani kuɗina.” Ya sake yowa kanta kamar sabon mahaukaci, ai kuwa na yi saurin buɗe ƙofa ta na shiga, na ce. “Bilkisu shigo.” Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na talatin da takwas. “Bilkisu shigo.” Ta yi wani irin tsalle za ta shigo, amma Sardauna ya riƙe mata ƙafa, ya yi wani kukan kura ya yo kaina, ba shiri na dannawa ƙofa ta key na dawo ta window ina kallonsu, jin bana wani jin su yasa na zuge glass din window, ai kuwa ina buɗewa na ji yana cewa. “Bilkisu idan baki dawo min da kuɗina ba sai na yi ƙararki wallahi.” “Au, ka gama yi min wannan dukan akan shegia 2m shine zaka yi ƙarata, wallahi Sardauna ko wuta kake fesarwa na ci kuɗin nan, kuma sai ka yi danasanin duka na.” “Bilkisu, idan akwai wanda zai yi dana sani to kece, dan sai kin biya kuɗin nan, kuma duk wani abu da nake miki a gidan nan wallahi na daina, sai dai ki zaɓa idan zama zama, idan gidanku to ki tafi.” Yana faɗin haka ya shige part ɗinsu, ta zauna a dandaryar ƙasa ta rusa wani irin kuka da na ji yana taɓa min zuciya, ba shiri na buɗe ƙofa na fito, a hankali na ƙarasa inda take, na ce. “Bilkisu, ki yi haƙuri ki daina kuka, mu je na yi miki dressing ɗin jikin ki.” Kukan ta ci gaba da yi, ta miƙe muka shigo ɓangarena, wannan shine karo na farko da ta taka ƙafa a ɓangaren, zaunar da ita na yi kan kujera, sannan na ce. “Ina zuwa.” Ta gyaɗa kai, ba tare da ta ce komai ba, naje na ɗauko na fara gyara mata wajen da ya tashi a fuskarta, na goge inda zan goge mata sannan na bata amfikulus ta sha. “Zaki iya zuwa, ko na raka ki?” “A’a Nana, dan Allah ɗan barni na huta anan, kaina ciwo yake.” “Tom.” Na faɗa tare da miƙewa na barta ta kwanta, na shiga kicin nasan lokacin dawowar Turaki cin na rana ya yi, ina tsaka da aikin na ji parking dinsa, a daidai lokacin ina kan yanka salat, sai da na gama sannan na fito falon na buɗe mai. “Yau me kullewa ce kenan Habibty.” Na yi dariya na ce. “Shigo.” Ya shigo, hankalinsa bai kai kan Bilkisu dake kwance akan kujera ba, ya ce. “Habibty Yunwa.” “Ya salam, Habiby kasan yau banyi girki ba, duk bana jindaɗi.” “Tom Habibty, wannan ƙamshin kuma na mene?” “Turaren wuta ne.” “Habity kinsan bana wasa da ciki ko?” “Tom zauna na zuba ma.” Ya zauna na shiga kicin na fara fito da food plast ɗin, bayan na ajiye na zuba masa farar shinkafa da farar doya, sai miya. “Habibty nama fa?” “Allah yau ba nama, ance illah fa ya ke yi.” “Ni dai Habibty ko kisa yake sai na ci.” Ƙarasa zuba masa na yi na miƙa masa, ya kalleni sosai sannan ya ce. “Wai dagaske dai ba naman?” “Babu fa, sai dai soyayye.” “Ni bari na ci haka, banga kin zuba ba?” “Ka ci ina zuwa.” Na faɗa tare da komawa can inda Bilkisu take, tana kwance amma idonta biyu, sai da na zauna sannan na ce. “Na zuba miki abinci?” Ta girgiza kai alamar a’ah, na sake cewa. “Kin ji daɗin jikin?” Ta gyaɗa kai alamar eyh. “To ki gwada cin abincin zaki ji daɗi.” “Habibty ke dawa kike magana anan ne?” Muryar Turaki ta katse ta daga bani amsa. “Ina zuwa.” Na faɗa masa, sannan na sake cewa. “Na kawo miki ki ci ko? Zaki ji daɗi sosai.” “Tom, Nana na gode.” Ta faɗa, ni kuma na miƙe zuwa inda yake. “Dawa na ji kina magana?” Ya sake tambaya, sai da na zauna sannan na ce. “Bilkisu ce.” “Wace Bilkisu?” “Matar Sardauna.” “Sunanta Bilkisu kenan? Me ya faru?” “Bakomai fa, ka ci abinci bari nazo.” Na faɗa ina miƙewa tsaye, na zuba mata abincin a plate na kai mata, da ƙyar ta samu ta tusa abincin, ba ta wani ci sosai ba ta ajiye. “Nana bari na koma, amma ina tsoron sake haɗuwa da shi.” “To Bilkisu ki sanar a gida mana, su yi masa magana.” Girgiza kai ta yi, sannna ta ce. “Bazan iya ba Nana, ai wannan abun kunya ne a gidanmu na ce miji ua dake ni, Nana Mahaifiyata da Yayata bazasu taɓa yafe min ba.” “Ai ba daɗi irin haka, amma idan abun ya zama babba ai ina ganin sanarwar yafi alheri.” “Baza ki gane ba Nana.” Ta faɗa tana miƙewa, adaddafe ta fita, ni kuma na koma wajem Turaki. “Habibty duk kin samin abinci kaɗan, gashinan sai da na ƙara.” Zama na yi ba tare da na bashi amsar sa ba, ya kalli ni ya ce. “Habibty why are you so worried, me ya faru? Ke da wa kike magana?” “Hhhm, Habiby Bilkisu matar Sardauna ce, faɗa su ka yi ɗazu a compound sosai, har da duka.” “Toopa, me ya haɗa su?” “Na ji kamar yana cewa wai kuɗi ta ɗaukar masa 2m, shine ya dake ta, ita kuma ta ce ya daki kuɗinsa, ba kaga dukan da ya yi mata ba, shine na ɗauko ta na shigo da ita nan, na yi mata dressing, shine ta ci abinci yanzu.” “Ke Habibty ina rabaki da shiga al’amarin mutane nan! Ba ita ce ta yi miki wannan wulaƙancin ba, Habibty ki rage shiga abinda ba ruwanki dai.” “Tom amma yakamata na ƙyale shi ya yi mata rauni?” “Ina ruwanki? Sunfi kusa Habibty.” “A’a Habiby.” “Daman bakisan na ji haushi akan na Islaha ba ko? Yarinyar da aka turu ta raba aurenmu, kika yi wa wannan gatan, sannan ga wannan ma. Ke ina ruwanki dasu, sunfi kusa.” “Abar maganar kawai Habiby, amma ni kam bazan iya jure ganin wani cikin damuwa ba.” “Ko da waɗan da suka saki ke a damuwar ne?” “Mu kyautata zuciya, muma sai Allah Ya kyautata mana.” “Hakane Habibty, tashi mu je muga ‘ya’yanmu, kafin na koma ofis.” “Daman ina son zuwa gida, ni har yanzu na rasa me zanyiwa Ra’is, gaba ɗaya saura 2weeks.” “Ni kaina Habibty, Ra’is ya wuce komai.” Tashi mu ka yi, na tashi na shiga ɗaki na shirya muka fice, bamu wani daɗe gidan Yaya Ridwan ba muka tafi, ya sauke ni gida shi kuma ya wuce, na yi mamakin ganin yanda Hajiya ta shiga busy, wai ita bikin auta, sai kawai na kalli yanda take hada hada, na tintsire da dariya. “Nana kizo ki tafi ki bar min gida, tun da yanzu kin zama abinda kika zama.” Na yi dariya na ce. “Hajiya, yanzu ba kya jin kunya, zaki aurar da ɗan auta amma sai waya kike kina cewa mutane su zo.” “Ke Nana, idan ban godewa Allah ba me zanyi? Allah Ya ja kwana na aurar da ‘ya’yana duka, dole na yi farin ciki Nana, na so ace mahaifinku yana raye ma, da mun yi farin ciki a tare, amma yanzun ma Alhamdulillah Kam.” “Hakane kam.” Na faɗa, sai can dare Turaki yazo ya ɗaukeni muka koma gida, daga wannan rana bansake bin takan Bilkisu ba, haka ma Sardauna sai dai wannan fitar safiyar da yake yanzu ba ta yi, dan da ina ganinta kafin na fita ofis, idan ina kicin, amma yanzu har na fita ma ina ganin motarta, kuma wata rana ina dawowa nake ganin dawowarta. Ana haka satin bikin Ra’is yazo, aka shiga hidimar biki, bayan na yi shawarar ƙarshe na haɗa masa kayan abincin da zasu yi masa shekara ko fin haka a gidan, da yake mu dangin ango ne ba mu fara bikin ba sai ranar juma’a, washe gari asabar kuma aka ɗaura auren Ra’is aka kai masa amaryarsa, gida ya zama saura Hajiya ita kaɗai. Dukkanmu muka koma gidajennu, aka bar Hajiya kaɗai. Wajen ƙarfe takwas na dare Turaki yazo ya ɗauke ni, kasancewar garin yanayin sanyi ne, kai tsaye gida muka yo. Tun da muka shiga harabar gidan muke jin hayaniya, sai da Turaki ya kalle ni sannan ya ce. “Habibty, ba ruwanki dasu.” “Kasan dai bazan shigar musu part ba ko?” “Yawwa, mu kaɗa kai mu wuce abun mu, su kashe kansu, alhaki ne ke bin su.” “Tom.” Na faɗa, tare da buɗe ƙofar na fita shima ya fito, daidai lokacin Bilkisu ta buɗe ƙofar part ɗin ta ta fito da gudu Sardauna ya biyo ta, it kuna ta yi kan mu tana faɗin. “Ku taimakamin dan Allah.” Turaki ya janyo ni jikinsa ya riƙe ni katamau, Bilkisu ta fara ƙoƙarin ɓoyewa a bayan mu. “Bilkisu wallahi yau sai kinyi danasanin abinda kika yi? Kuma wallahi sai kin cinye abincin nan, idan maganin mutuwa kika zuba a ciki wallahi sai dai ke ki mutu.” Ƙoƙarin jana Turaki ya fara, amma na tsaya. “Habibty tawo mana.” Na girgiza kai, ya sake cewa. “Ki tawo ki ƙyalesu, tsakaninsu ne sunfi kusa.” “Dan Allah karku barni da shi.” Ta faɗa tana riƙe ni. “Bilkisu me kike so mu yi masa, mu ce kar ya dake ki? Mutumin da yake jira wani abu ya haɗamu da shi ya ci mana mutunci? Babu ruwana.” Turaki ya faɗa, Sardauna ya ce. “Akwai mitsiyacin da ya isa ya shiga tsakanina da iyalina? Ka matsa daga nan kafin na haɗa daku.” “A’a abinda ba ka isa ba kenan.” Turaki ya faɗa, Sardauna ya sake cewa. “Bilkisu wallahil azim sai kin cinye abincin nan.” “Wallahi, ni bansan ma wani abu ba.” “Raina min hankali zaki yi? Da kina yin girki a gidan? Amma yau kika dage sai kinyi, tun da kika dage na fara shakku akan ki, ina ta zagaye kawai ma ga kin barbaɗa abu a leda, Wallahi duk bin malaminki nafi ƙarfinki Bilkisu.” Ji na yi ƙirjina ya yi wani irin buga, kamata ya yi tana masa barbaɗe a abinci, shine ya yi mata haka, lallai. “Habibty, kinga mu ƙyale su mu shige ciki, daman duk wanda ya siya rariya yasan zata zubda ruwa, kuma Habibty Allah baya barin haƙƙin wani akan wani, wanda duk ya cutar da zuciya irin taki Allah bazai barsa ba, na gode Allah da yake nuna miki wasu abubuwan akan idonki, ina matuƙar ƙauna da alfaharin kasancewa a kusa dake Habibty, tabbas na yi matuƙar dacen samun mace irinki da ta suɓuce a hannun wawa, ina ji dake ina ƙaunarki, dan haka a matsayina na mijinki, mutum ɗaya da ya isa ya saki ya kuma hanaki, na umarce ki Habibty da ki shige mu yi ciki.” Ji na yi jikina ya yi wani irin sanyi, zuciyata ta yi wani irin haske, wani irin jindaɗi ya shige ni, na kama hannunsa da ya miƙomin na fara tafiya, ai kuwa Sardauna ya yi wani irin ihu ya kama Turaki yana ƙoƙarin yin baya da shi, Turaki ya kwace, ya ɗaga rigarsa ya fito da bindigarsa ya ce. “Wallahi Sardauna ka matso nan sai na fasa kanka da bindiga, idan kuma kana musu ka matso, kasan Allah na harbeka na harbe banza, a dokance zan ce ɗan ta’adda ne kai, a addinance ma rayuwar azzalumi irinka bata da rana, fasaqi, mai zina da matar aure, shima kisa ne ya rataya akansa, dan haka na kasheka, na kashe banza wallahi.” Tsit ka ji ba motsin Sardauna, sai faman mamatso baki yake yi, yana son ya faɗi magana kuma ya kasa, babu abinda ya girgiza shi jin kalmar zina da matar aure, ko ba a faɗa ba yasan ansa abinda yake faruwa tsakaninsa da islaha, Bilkisu ce ta ce. “Duk abin kunyar da kake cewa na yi, na kamani ina yi maka barbaɗe a abinci, bai kai naka abun kunyar ba, zina da matar aure? Sardauna me zai sa na wahalal da kaina wajen mallalke? Kai da nasan ba wani lasting zaka yi a duniyar ba? Na gode Allah da na zubar da mahaifata, ban ɗauki cikinka na tsahon wannan lokacin ba, da zunubin ka na zina ya shafi ‘ya’yana, sharrin da ka ƙullawa Nana da mijinta a wancan lokacin shine ya dawo kanka, nasan Sardauna ba kaga komai ba a rayuwa, nasan nan gaba sai ka kwashe duk wani abu da ka shuka.” Kamar jira yake kuwa ya kai mata duka, Turaki ya jani mu ka yi ciki abunmu, ni duk kaina ma ya ɗaure, Bilkisu ta zubar da mahaifarta, amma kuma shi bata lalata masa nasa ba kamar yanda ta faɗa, tin da ga Islaha da cikinsa. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na talatin da tara. “Habibty kin ji wani abu ko?” Turaki ya tambayeni, na gyaɗa kai sannan na ce. “Habiby abubuwa duk basu yi daɗi ba.” “Ki kwantar da hankalinki, kaɗan Sardauna ya gani, in sha Allah komai sai ya girbe.” “Ko a yanzu ma ai ya girbe, Allah Ya tsare mana imaninmu.” “Amin Habibty, ki yi wanka mu kwanta da wuri, duk gajiyar biki kin gaji.” “Kaga ma mun manta jakar kayan ma a mota.” “Ma ɗauka da safe, idan sun gama tashin hankalin.” Na shiga ɗaki na watsa ruwa, na fito na dawo na zuana akan gado, na shiga tunanin yanda Sardauna ya yi amfani da Bilkisu suka yaudareni, suka ci amanata, yanzu gashi ba aje ko ina ba, duk a ƙasa da shekara biyar komai ya caɓe, mai hankali dole ya fahimci duniya babu tabbas a cikinta, ka shuka abun alheri kawai. Ina zaune Turaki ya shigo, sai da ya zauna kusa dani ya ce. “Habibty wai damuwar su Sardauna?” Na girgiza kai, sannan na ce. “A’a, ina tunanin yanda rayuwa take, yanzu amana ta zama ba komai ba, mutumin da aka aminta dashi sama da komai, shine mutumin da zai tura ka rana.” “Habibty me ya faru? Waye ya ci amanar wani?” “Anan dai babu, amma abinda yake faruwa a rayuwa kenan yanzu, mutane babu amana.” “Hakane Habibty, shi ya sa ake cewa ka koyi yanda zaka riƙe sirrinka, sannan kasa waɗan da zaka raba damuwarka dasu.” “Amma kasan me? Habibi wani abun fa baka da yanda zaka yi, dole sai ka raba shi da wani, kuma mutane ba’a gane na gaskiyya ko na banza a ido.” “Hakane, amma kuma ai Allah baya barin haƙƙin wani, yanzu ke akan ki baka ga izina ba? Yanzu waɗan da suka yaudareki suka ci amanarki, suka cutar dake, suna rayuwar daɗi ne ko akasin haka?” “Hakane kuma, Allah Ya bamu wucewa lafiya.” “Amin Habibty.” Ya faɗa tare da janyoni jikinsa, mu ka kwanta. Washe gari da safe ma wani sabon faɗan ne ya tashe mu, ta window na leƙasu dan shi Turaki ko akansa, kamar ma baisan suna yi ba. Sardauna sai fitowa da Bilkisu kayanta yake, ita kuma tana mayarwa, a raina na ce. “Sardauna ya haɗu da daidai shi a rayuwa.” Ina aiki ina gulma, haka na gama haɗa breakfast na kawo wa Turaki, mu ka yi breakfast ya fita, ni kuma na hau shirin ofis. Ƙarfe sha ɗaya daidai na fito daga part ɗina, ina ƙoƙarin shiga mota na ji ana kira. “Nana! Nana.” Na waiga naga Sardauna, na buɗe mota zan shiga ya riƙe murfin motar. “Nana tsaya mu yi magana dan Allah.” “Sardauna wace magana? Mene alaƙa ta dakai? So kake mijina ya zo yaga ina magana da kai, ranshi ya ɓaci?” “Nana dan Allah ki saurareni, Nana wallahi tun fitar ki daga rayuwata abubuwa suka canja min, rayuwa nake amma kwata kwata bana jin daɗin komai Nana, ki yi wa Allah ki dawo mu zauna.” “Mu zauna kuma? Ka fara haukane? Da aure na zan dawo mu zauna? Kowa Islaha ce?” “Nana, kin san ina sonki, ƙaddara ce ta rabani dake, kuma nasan kema kina sona.” “Eyh kam, ada na so ka Sardauna, son hauka wanda babu hankali a ciki, amma yanzu kam, babu.” “Nana ki fahimce ni., kiji abinda ke zuciyata?” “Wace fahimta?” “Nana, a duk ranar da naganki da Turaki ina jin zafi a zuciya, zuciyata tana ƙuna.” “Wallahi Sardauna da ina da yadda zanyi ido biyu da zuciyar taka sai na sa mashi na cake ta, ko ta ƙarfi ne na fito da ita, na yayyanka ta na watsawa karnuka ita, dan dabbobi ne suka da ce da ita, Sardauna na tsaneka bana son ko haɗa ido da kai, Sardauna wallahi ina danasin mai girma idan na tuna wai a baya naso mutum mai kama da kai, kuma idan baka matsamin daga nan ba, sai na take ka da motar nan wallahi.” Ina gama faɗin haka na buɗe motar na shige, ya yi saurin riƙe murfin motar. “Nana Sardauna ne fa.” “Mitchewwwww.” Na ja wani dogon tsaki na fisgi murfin mota ta na rufe. Mai gadi ya buɗe min na yi waje. Ni ko sha’awar ganin Sardauna bana yi wallahi, natsani ganin Sardauna ko kaɗan. In shiga asibiti na je wajen Dr Halim, likitar da take duba ni akan mahaifafa, ina shiga na sameta zaune tana duba files. “Good morning Ma.” Na faɗa ina zama, “Morning Nana, Ya mai gidan?” “Yana lafiya kam, Dr akwai wani bayani ne?” “Eyh Nana, kamar yanda aka faɗa miki a baya cewar mahaifarki ta warke dagaske ne, sai dai haihuwr ce shiru har yanzu Allah bai kawo ba.” Na yi shiru, jikina duk ya mutu, ina son haihuwa, ina son naga ‘ya’yana, nasan Turaki ma haka, kawai soyayya ta ce ta rufe masa ido, baya ganin hakan, amma tabbas nasan zai damu. “Dr Nana, karki sa wata damuwa a ranki dan Allah, haihuwa nufin ubamgiji ne, wasu sai su shekara goma da aure sannan su haihu, wasu ma fin haka, ki yi haƙuri kawai ki dage da addu’a, mussaman ke da aka cutar dake, Allah baya barin haƙƙin wani akan wani.” “Shikenan Dr Na gode sosai.” Na faɗa tare da ficewa na koma namu ofis ɗin, haka na yi aikin duk jikina babu daɗi babu kuzari, ko da mu ka yi waya da Turaki na ce masa kar yadawo cin abincin rana dan ina ofis, daman yawanci juma’a da asabar da lahadi ne yake dawowa kullum, sauran ranaku sai ya tambayeni ina gida ko ofis, sai da ya tambayeni me ke damuna na ce masa bakomai. A haka na tashi na dawo gida, ina shiga gida na watsa ruwa na kwanta sabida wani irin yanayi da nake ji, ji nake kamar fa ni bazan haihu ba, ba zan ga ‘ya’yana ba. “Allah ka sakamin nagani, Allah ka ƙara sakamin, bazan iya yafewa Sardauna ba.” Na faɗa ina zubar da hawaye, ina nan kwance har yamma ta yi, na shiga kicin. A sauƙaƙe ma dafa masa taliya na dawo ɗakin na zauna, ko da ya shigo ma ban ji shi ba har sai da yazo ɗakin da nake kwance. “Habibty lafiya wai? Tun ɗaxu na jiki wani kala, ko an miki wani abu?” Na girgiza kai, bance komai ba. “Tell me Habibty, wani abu ne, ko nine?” “A’a kawai munyi magana da Dr Halim ne, ta cr haihuwar har yanzu Allah bai bamu ba, amma mahaifar tana lafiya.” “To sai me? Dan Allah bai bamu ha shine kike fushi? Allah kikewa haka, ko me? Nana baki gode da ni’imar ‘yan uwa masu ƙaunarki da ya yi miki ba, kin manta ɗan uwanki ya baki kyautar yara har rai biyu a ranar da aka haifa masa? An faɗa mik baya son su ne da ya baki? Ba zaki yi wa Allah godiya da wannan ni’imar ba? Haba Habibty, ‘ya’yan Ridwan ɗin baki ɗaukansu a matsayin ‘ya’yanki? Kinga Habibty idan kin san bazaki so yaran nan ba kamar ke kika haifesu to kar mu ɗauko su, ni dai Allah Ya gani ina son su, ina jinsu a raina kamar nawa ‘ya’yan, ina sonki dan haka ina son duk wani abu sa ya fito daga wajenki Habibty.” Na share hawayen dake idona, sannan na ce. “Ina son su, kuma na godewa Allah, amma nasan kaima kana son kaga na ka ‘ya’yan.” “Ni na faɗa miki Habibty? Waɗan nan yaran guda biyu kaɗai idan Allah Ya raya mana sun ishemu, duniya da lahira, kuma ni bazan taɓa yi musu wani kallo wanda bana ‘ya’yan cikina ba, ni dai ta wajena ba za asami wani matsala ba.” “Nima haka nasani, nasani kuma in sha Allah bazan sake damuwa akai ba.” “Yaww Habibty, dan Allah karki damu, wallahi bana son abinda zai dame ki, ko kaɗan bana son naga wani canji yanayi a tare dake Habibty, ki kasance mai godiyar Allah ako da yaushe.” “Dole na godewa Allah ko da iya baiwar miji irinka da ya yi min.” Wani irin bugu muka ji ana yi wa ƙofar mu wanda ya sa muka fito a guje. “Nana! Nana! Nana!.” Kallon Turaki na yi, na ce. “Kamar fa muryar Sardauna?” “Shine, neman uban me yake miki?” “Leƙa da kanka, ji yanda yake abu kamar mahaukaci.” Buɗe ƙofar ya yi, Sardauna ya yi wani tsalli ya shigo, yana zuwa ya zube a ƙasa ya fara cewa. “Nana, Nana, ki taimakamin dan Allah, zan rasa raina, wallahi Nana ko minti ɗaya bana iya yi sau na kira sunanki, idan naganki zuciyata wani bugu take yi da ƙarfi.” Ni gaba ɗaya ma tsoro ya bani, na fara ja da baya, ya yi ƙoƙarin riƙe min ƙafa, na ƙwalla ƙara tarw da faɗin. “Habiby.” Turaki ya yi kaina, yana cewa da Sardauna. “Karka firgita min mata, ka fita anan.” “Nana dan Allah.” “Ka fita na ce ma.” Turaki ya sake faɗa, ni kuma na ƙara ruƙunƙumeshi ina faɗin. “Habiby dan Allah ya fita, ni tsoro yake ban, kar ya dake ni.” “Akan me zai dake ki, Sardauna fitar mana.” “Nana wait, ki taimaka dan Allah, wallahi ina sonki, ki yi haƙuri dan Allah.” “Karka ƙara cewa kana son matata, tun da baka da hankali.” Turaki ya faɗa tare da jan shi, ya dinga jan Sardauna har sai da ya fita da shi, yana fita dashi ya dawo ciki ya rungume ni, ni kuwa na fashe da kuka, har ga Allah abun Sardauna yanzu tsoro yake ban, mussaman ɗazu da naga idanunsa suna wani irin ja, gashi yanzu ma yazo nan, ni ko wani makircin ma ya shirya tin da shi lamarinsa babu Allah. “Habibty ki yi haƙuri, zanyi maganinsa.” “Nifa tsoro yake ban, ɗazu m zanje asibiti ya dinga riƙe murfin motar, kar dai wani makircin yake son saƙe ƙulla mana.” “To Habibty duk makircinsa ai sai da ya haƙura damu, a yanzu fa mun riga da munyi aure kuma babu wani abu da ya isa ya raba mu, ko ƙaddara bana fatan ta rabamu Habibty.” “Ni dai duk tsoro nake, ko gida zan koma, ko mutashi kawai mu bar masa nan?” “Idan kina so Habibty sai mu bar masa.” Ya faɗa daidai lokacin wayarsa ta fara ringing, ya zaro daga aljihu, ya kalle ni sannan ya ce. “Big Daddy.” Wani irin bugu na ji a ƙirjina, mai kuma ya ce mu yi? Wane sharri ya ƙulla mana, tabbas tashinmu daga nan shine alheri. “Habibty kinga Big Daddy.” “Nagani, ka ɗaga.” Ɗagawa ya yi, ya sata a hands-free Big Daddy ya ce. “Abubakar kana ina? Hajiyata ba lafiya yanzu zasu tawo daga abuja, ka shirya kaje ka ɗauko su, idan jikinta ya yi tsanani ku kaita asibiti, idan ya yi very worst ka faɗa min yanzu ku shirya ku tawo nan.” “Tom Big Daddy, bari naje waye ya tawo da ita?” “Usman ne.” “Tom.” Ya faɗa yana miƙewa, nima na miƙe na ce. “Muje tare, bazan iya zama anan ni kaɗai ba.” “Okay sa mayafi.” Na buɗe sif na ɗau mayafi muka fita, Sardauna yana tsaye yana kai kawo a parking spaces mu ka shiga mota muka fice, daidai lokacin da muka isa airport daidai lokacin jirginsu ya sauka, muka sa ta a mota muka wuce asibiti, jikin na ta baiyi tsananin da za ace har an tafi wata ƙasar ba, sai da kuma al’amuran sa masu kuɗi ba gane kansu ake ba, abinda bai kai ya kawo ba zasu ce sunje turai ganin likita. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na arba’in. Sai wajen ƙarfe sha biyu da kwata muka bar asibitin mu ka dawo gida, sai a lokacin Turaki ya ɗan sanar da waɗan da yakamata ya sanar, washe gari ma na yi mana breakfast muka ci, sannan mu ka tafi asibitin, daga asibitin ya wuce ofis ya barni, kasancewar ‘yan gidansu Turaki ne a wajen jinyar sai kuma ‘yan uwan Sardauna ya sa ban wani damu ba, ƙarfe sha ɗaya nima na wuce ofis. Wajen ƙarfe biyu na tashi daga ofis ɗin na yi gida, ina zuwa na dafa musu doya da miya na shirya na yi asibitin, lokacin da zan fita na ga Bilkisu ma ta shirya cikin ‘yar iskar shigarta ta fita, a raina na ce. ‘Mai hali baya fasa halinsa.’ A mota ta naje asibitin, ina shiga ɗakin na tarar da Mommy, Mama Amina, da Mamansu Sardauna sai sister seemah, har da su Islaha, gaisuwar gaba ɗaya na yi musu na ce. ‘Ina yinin ku?.’ Waɗan da suka amsa sun amsa, waɗan da basu amsa ba sun yi banza, ina zama Mama Amina ta ce. “Sannu da ƙoƙari Nana, tun jiya kuke hidima asibitinan, Allah Ya saka da alheri.” Na yi ƙasa da kaina bance komai ba, Sister Seemah ta ce. “Ai Mama Nana kam ba daga nan ba, a yanzu zamu ce ta canja, tana da kirki tana da son mutane, ba kamar baya ba.” “Ai ina ga a bayan dama ce ba ta samu ba.” Lamrah ta gidan Big Daddy, ƙanwar Sister Seemah ta faɗa. Sister Seemah ta tare ta. “Waya sa da ke?” “Bakowa Sister, kawai yanzu abun nata ya zama abun burgewa, har son zuwa gidan ta nake.” “Ai kya so zuwa gidanta, tun da sa’ar ku ce.” Mama Amina ta faɗa, sai a lokacin Momy ta ce. “Sa’ar su ce mana, dan Nana a shekaru ban jin ta haura 22.” “Kunzo kun dame da zancen wata banza a waje, sai wani yabon ta kuke.” Mamansu Sardauna ta faɗa, a take Hajiya Falmata ta cafe da cewar. “Abinda nagani kenan, yarinyar da bata kai ba sun zo sunsa zancen ta a gaba, ita wacca ma tana ta wani washe baki an yabi surikarta, sabida rashin kara da ta ido.” Mamansu su Sardauna ta ce. “Ai ni Hajiya Falmata, wallahi matar nan mamaki take ban, tun da ta amince ɗan ta ya auri ‘yar iska, ko da yake shi ya ɓata ta, wai amma yanzu su Amina sabida basu da kunya sun manta yanda muka zauna muka tsaya tsayin daka akan kar aka sake kawo mana wannan yarinyar cikin family, shine yanzu suka zo suke yabonta.” Mama Amina ta ce. “Ai ba a sanin halin mutum sai an zauna da shi, anan da kowa ya yi tunanin Nana yarinya ce marar mutunci marar tarbiya, duba da ko shiga ‘yan uwa ba ta yi, ba ta zuwa gaida iyaye, ga miji yana ta ƙofarinta, amma a yanzu da ta yi wani auren gashinan duk halinta yana fitowa, kunga kenan idan aka yi duba za a ce daga Sardauna ne, tun ga amaryarsa ta yanzu nan, babu inda take zuwa.” “Kya faɗa mana, kuna zaune da matar da ta yi iskancin da ƙanin mijinta, bayan da aure akan ta, sabida ba kwason gaskiyya, shi Turakin yana sakar muku abun duniya.” Mamansu Sardauna ta faɗa, Sister Seemah ta ce. “Haba Momies mene haka? Me Turaki yake da shi? Dan Allah a iya baki, ƙage da ƙazafa babu kyau, akwai abubuwan da idan aka ce za a baje su ba kowa bane zai iya ɗauka, Nana ce ake magana akai, da bata da zumuncin, bata son ‘yan uwan mijinta, a yanzu kuma ta canja, shikenan.” “Ke rufe mana baki, tun da baki da kunyar da zaki iya shiru idan iyayenki na magana muma muna da bakin da zamuyi magana.” “Kar ki yi min rashin kunya Alisha.” “Ke ba daɗi kika sa baki a maganar iyaye?” “Yanzu jinyar Hajiyar zakuyi ko yada magana?” Mommy ta faɗa, daga nan kuma aka yi shiru, kowa ya ja gefe ya ci gaba da abinda yake, Hajiya Falmata da Mamansu Sardauna suna ta haɗe kai suna hira ƙasa ƙasa, ni dai ina zaune jira nake kawai Turaki ya zo ya ɗaukeni mu tafi, dan zaman ba daɗi ba kwata kwata, ana haka Sardauna ya shigo, yana shigowa na kauda kai na yi gefe, ya shigo suka gaggaisa. Sister Seemah ta ce. “Bross mu yi magana.” Ta faɗa tana ta shi yabi ta suka fita, sai da suka kwashe kusan mintuna goma sannan suka dawo, yana ta haɗa gumi, a raina na ce. ‘Allah yasa ta faɗa masa cewar Islaha na da cikinsa, ko za a samu zuciyarsa ta buga.’ Sai wajen bakwai Turaki yazo, yana zuwa na matsa kusa da shi na ce masa. “Dan Allah mu tafi da wuri.” Ya gyaɗa min kai kawai na koma na zauna, ba mu muka tafi ba sai bayan takwas duk na gaji, muna zuwa gida na kwanta ban ma kula shi ba, duk yanda Turaki ya kaɗa ya raya naƙi kulashi, gaba ɗaya bana jin daɗi. Washe gari kam shi na bawa abincin ya kai, ni naƙi zuwa. Ko da na tashi daga asibiti ma ni banje ba, gida na dawo. A ranar kam naga zallan ɓacin ran Turaki, ina zaune a falo ya shigo, sallamar ma a zuci ya yi ya wuce ni, na miƙe ina faɗin. “Sannu da zuwa.” Ya yi banza ya shige ciki, na bi shi ina faɗin. “Me ya faru Habiby?” “Habibty kin kyauta? Kakata, mahaifiyar Abbana, abinda kika yi kin kyauta, ace daga jiya anyi miki abinda bai miki daɗi ba shine zaki ƙi komawa.” “Ka yi haƙuri dan Allah.” “Haƙurin me? Tun da abinda kika zaɓa ai shikenan.” Jikina ya yi sanyi, na fara kuka amma Turaki ya yi banza da ni ya wuce ɗaki. Ba shiri na tashi na bishi ɗaki. “Habiby, dan Allah ka tsaya ka saurareni.” “Habibty me zan ce miki? Me zanyi miki, kin yi fushi kin daina zuwa ba shikenan ba, so kike na tursasaki?” “A’a, ba zaka tursasa ni ba, yau ɗin ne bana jin daɗi kwata kwata, dan Allah ka yi haƙuri.” “Habibty dan Allah je ki, jeki ɗakinki.” “Ni kake cewa na tafi?” “Jeki.” Kuka na fashe da shi na fice, ina zuwa ɗaki na kwanta akan gado na fara kuka, haka na sha kuka na bacci ya ɗaukeni, ba Turaki ba alamarsa. Washe gari ma da safe banji shi ba, wannan ne karo na farko da muka raba ɗaki da Turaki, inda ba wajen Islaha za shi ba a wancan lokacin. Na yi kuka har nagaji, amma Sardauna bai lallaɓe ni ba, haka ko breakfast baiyi ba ya fita, kiran duniya na kira shi yaƙi dagawa, haka na je asibiti duk jikina ba daɗi. Ƙarfe biyu na dawo gida na yi musu girki, uku saura na fita na tafi asibitin, ina zuwa na ci karo da Sister Seemah a bakin asibitin, bayan mun gaisa ta ce. “Daman yau ba kowa, daga ita sai mijinki.” “Allah sarki bari na shiga.” Na faɗa, tare da shiga ciki. Ina shiga na ji muryar Granny ta na cewa. “Abubakar, a jikina ina jin bazan tashi ba, ina soka saurareni, a yau zan baka wani labari? Wanda ya kasance tarihin gidanku gaba ɗaya, sai dai ina so ya zama sirri tsakanina da kai.” *Asalin Ta’Ambo Family* Alhaji Abubakar Umar Ta’Ambo, babban ɗan kasuwa ne daga jihar kano, tun yana matashin yaro ya dawo jihar jigawa bayan an raba yta da kano, inda ya ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancinsa anan jihar jigawa. Sannu a hankali kasuwancin Alhaji Abubakar ya fara girma, ya zama babba ɗan kasuwa, mafi shara a jihar jigawa. Anan ne Allah Ya haɗa shi da Maimuna, Maimuna yarinya ce matashiya mai tsananin kyau, kyan da ya tara mata samari masu ɗimbin yawa, ranar da Alhaji Abubakar ya fara ganin Maimuna wata rana alhamis ce, sun shigo kasuwa ita da ‘yan uwanta, suna tafe suna hira idon Alhaji Abubakar ya kai kansu, ba shiri ya taso daga cikin shagonsu ya tare su yana faɗin. “ ‘Yan mata barkanku da rana, me ake buƙata?” Maimuna ce ta yi masa wani kallon sheƙeƙe, sannan ta ce. “Malam! Kaga munzo inda kake ne? Da zaka tambayemu me muke buƙata?” Ya rausayar da kai, ya ce. “Ayi haƙuri yallaɓia, muna son mu rage muku shiga rana ne?” “Da muka ce maka muna buƙata?” “Ku yi haƙuri ku shiga shagona, ni zan sanya a nema mu ko me kuke buƙata acikin kasuwar nan.” Da ƙyar Alhaji Abubakar ya lallaɓa su Maimuna suka shiga shagonsa, bayan yasa ancika su da kayan ciye ciye da shaye shaye. Tun daga wannan lokacin soyayya ta ƙullu a tsakanin Alhaji Abubakar da Maimuna, soyayyar da ba ta yi wani tsayi ba suka yi aure. Bayan aurensu Allah ya ƙara sanyawa dukiyarsa albarka, inda Alhaji Abubakar Ta Ambo ya zama ɗan kasuwa mafi shahara a jihar jigawa. Har ta kai ya fara tara masu yi masa hidima, da masu kula da shi a gida. Sai da suka shekara uku da aure Allah Yabasu Haihuwar farko, inda suka sanyawa ɗan suna Isma’il (Big Daddy) bayan shekara uku kuma suka samu haihuwar wani namijin wanda aka sanya masa suna Musa, bayan shi kuma sai ‘yan biyu Hassan da Hussaini, bayan su kuma suka sake haifar mata guda biyu, daga nan Allah bai ƙara basu haihuwa ba. Kasuwancin gidan Ta Ambo ya ci gaba da haɓaƙa, har ta kai sun fara fita ƙasahen ƙetare, Maimuna ita kaɗai ce matar Alhaji Abubakar Ta Ambo, ita ce mai kula da komai, mai zuba izzah da Sarauta, dan jin kanta take kamar matar Sarki. A Ɓari guda Hamisu yakasance Ɗa a wajen mai kula da lafiyar Alhaji Abubakar da iyalansa Malam Audu, duk da kasancewarsa yaro matashi wanda bai huce sa’anin ‘yan biyu ba, amma yana da kyakyawar zuciya, gaskiyya da riƙon Amana, wanda kuma ya gaje su ne daga wajen mahaifinsa Malam Audu, wanda ya kasance amintacce, amini ga Alhaji Abubakar Ta Ambo, har zuwa lokacin da ya rasu, tun daga wannan lokacin Hamisu ya zama kamar ɗan gidan, ya kasance aboki ga ‘yan biyu tun da daman sa’a yake a wajensu. Isma’il yana da shekara 23 ya yi aure, inda ya auri matarsa Amina, sai kuma Musa da matarsa Falmata, bayan shi kuma sai matan guda biyu suka yi aure lokaci ɗaya, aka bar gidan daga ‘yan biyu sai Hamisu, su ka ɗai suke dabdalalsu da dukiyar Alhaji Abubakar Ta Ambo, duk da Isma’il ne ke kula da komai na fannin kasuwanci tare da Alhaji Abubakar, su ‘yan biyu suna rayuwar hutawa ne kawai. Shekarar Isma’il ɗaya da aure Allah Ya albarka ci matarsa da haihuwa, sai dai ta ‘ya mace ce wacce aka sanyawa suna Seemah, bayan ita Allah Yasake azurt su da wata macen, a lokacin kuma aka sanya auren ‘yan biyu da kuma Hamisu. Hassan da matarsa Khadija (Mommy) wacce ta kasance ‘yar ƙawar Hajiya Maimuna, Hussaina kuma da Nafisa (Maman Sardauna), sai kuma Hamisu da matarsa Hafsa wacce ta kasance daga danginsu, kowa gida daban aka bashi ya zauna, amma shi Hamisu yana zaune ne a gidan Alhaji Abubakar aka bashi part ɗin shi daban, mai girma. Wannan abun ya yi matuƙar tsayawa aran Hafsa, idan ta tabbatarwa da kanta ana kallonsu ne a matsayin bayi a gidan, duk da part ɗin da aka basu ya kasance babba mai girma, amma ba ta ga haka ba, tana zaune a gidan ne amma ta ciki na ciki. Ita ta fara samun ciki, a tsakanin su ukun da aka aura a lokaci ɗaya, kowa ya yi murna. Sai da cikinta ya yi wata uku cif sannan Khadija ma ta sami ciki, ya rage saura Nafisa kawai. Hajiya Nafisa ta shaƙi takaici, ganin duk suna da ciki amma ita babu, gashi Hajiya Maimuna irin surikan nan ne masu mita, kullum sai ta yi mita kan ita ciki shiru, duk waɗan da suka yi aure tare sun sami ciki, haka ma Hajiya Amina bata tsira ba a kullum sai ta yi mata mitar ta haifi ‘ya’ya mata ajere. Hakama Hajiya Falmata da ta yi Alisha, bayan an haifi Seemah, sai ya zama Seemah ce jika babba daga gidan Big Daddy, sai kuma gidan Abbah Musa da Alisha, sai kuma cikin da Hajiya Khadija take da shi, Lokacin da cikin Hafsa ya kai wata takwas, ranar wata juma’a, ranar da ta bazata taɓa mantuwa na a tarihin gidan Ta Ambo, da misalin ƙarfe huɗu na dare, ‘yan fashi suka shigo gidan, Hajiya Maimuna da Alhaji Abubakar suna bacci suka ji ihun ma’aikatan gidan. Cikin ƙankanin lokaci duk wani da yake gidan ya gurfana a gaban ‘yan bindigan, har da Hafsat dake ɗauke da tsohon ciki, anan ‘yan bindigar suka buƙaci aba su tsabar kuɗi naira miliyan ɗari biyu, kasancewar babu wannan adadin cash ɗin yasa aka hau jayayya da su, cike da rashin imani wani cikinsu ya kaiwa Alhaji Abubakar harbe, inda Hamisu ya yi ƙoƙari wajen tsaretar da Alhaji Abubakar sai dai shi Harsashen ya same shi, wanda ya yi ajalinsa a take, abinda ya yi fusata Alhaji Abubakar ya miƙe tsaye, wani cikin ‘yan bindigar ya harbeshi har lahira. Legendspen 08129553971 SARTSE BOOK 2 (Sayyid legendspen) Shafi na arba’in da ɗaya. End of Book 2 Ƙarshen littafi na biyu. Wannan hari shi ya yi sanadiyar mutuwar Alhaji Abubakar Ta Ambo da kuma Hamisu, idan mituwar Hamisu ta tsaya a zuciyar matarsa wacca ke ganin da gangan suka tsaya jayya da ‘yan taadda akan wannan kuɗin har ya yi sanadiyar mutuwar mijinta. Washe gari jihar jigawa ta tashi da alhinin wannan rashi na babban ɗan kasuwa da yaronsa da aka yi, miliyoyin mutane sun gigita da rasuwar, wasu suna ganin mai taimaka musu ya tafi. Kwanaki kaɗan ‘ya’yansa suka mai da hankali kan kasuwanci, kowanne da ɓarin da ya ɗauka. Big Daddy ya kasance shine babba, shine ke jan ragamar komai na gidan, shine mai faɗa a ji, duk abinda ya faɗa ta zauna a cikin gidan. Ana wannan yanayi ne Hafsat ta tashi haihuwa, inda kowa ya tsaya akanta da ƙarfi da lokacinsa, cikin ikon Allah ta sauka, ta sami ɗa namiji sai dai ita ba ta yi rai ba, kowa ya kuka da rashin Hafsat, ba Hamisu ba Hafsat sai kyakyawan ɗa da suka bari, wanda bayan yanke shawara akabawa Nafisa shi, tun da ita ce babu ciki a tare da ita, idan aka sanyawa yaro sunan mahaifinsa Hamisu, amma Nafisa ta canja suna zuwa Fahad, bayan wata uku kuma Mommy ta haifi na ta ɗan, inda shi kuma yaci sunan Alhaji Abubakar, a lokacin nr Hajiya Maimuna ta sanya musu sunaye, Hamisu Sardauna, shi kuma Abubakar Turaki. Bayan haihuwar su Sardauna, kuma Allah ya ci gaba da ba kowa haihuwar ‘ya’ya maza da mata. Tun tasawowar Sardauna ba shi da maƙiyi sama da Turaki, kamar yasan da cewar Turaki ne asalin ɗam gidan ba shi ba, duk da babu wani mutum da ya taɓa nuna bambamci a tsakaninsu, dan cikin ‘ya’yan babu wanda yasani, duk a lokacin Seemah da Alisha ne kawai, suma kuma duk basu kai shekara biyar ba, babu wanda ya iya tunawa abinda ya faru. A daidai lokacin Hajiya Maimuna ta ce da Turaki. “Wannna shine taƙaitaccen tarihinku, ina so ka riƙe wannan a matsayin wani sirri mai girma, kuma kabar shi a zuciyarka, kasani Sardauna ba shi da alaƙa ta jini da wannan gida na Ta Ambo, Sardauna ba kowa ba ne sai ɗan riƙo. Na roƙe ka da ka riƙe wannan, na faɗa ma ne a matsayinka ja babban jika.” Da sauri na yi baya sabida ji da na yi kaina yana wani irin sara min. ‘Yanzu ace Sardauna ba ɗan asalin gidan nan ba ne? Ɗan ma’aikatan gidan ne? Dole! Ai wannan fariya da ɗagawa da yake yi, wannan cin mutunci da cin zarafi, sun isa su tabbatar.’ A take na tuna lokacin da Sardauna ya ce da ni. “Nana ku talakawa ne ma rasa gata, na tsani talaka, natsani talauci, bana son rayuwa da shi, bansan yanda aka yi kina talaka ba kika shiga zuciyata ba.” Na zauna akam kujera na dafe kaina, a fili na ce. “Ashe ni Nana nafi Sardaun gata? Sardauna dai ba shi da alaƙa da wannan gidan? Ya zaiyi idan ya ji wannan magana? Kai innullahi abubuwa sun caɓewa Sardauna, sun juye masa gaba ɗaya.” Ji na yi an buɗe ƙofa an fito, Turaki idonsa sun yi jawur. Kana ganinsa kasan ya sha kuka, ya ɗaga kai ya kalle ni. “Nana, kinji?” Na gyaɗa kai sama, ya girgiza min kai ya ce. “Nana sirri dan Allah, ya zama da gani sai ke.” Ban iya ce mai komai ba na miƙe na shiga ciki, ina zuwa na ajiye mata abincin na fito, a lokacin yana zaune a falon. “Habibty.” Na ɗago na kalleshi, ya ce. “Ki yi haƙuri da abinda na yi miki, raina ne ya sosu.” “Bakomai Habiby, nima ina ƙara baka haƙuri akan abinda na yi.” Daidai lokacin kuma Hajiya Falmata da iyalanta suka shigo, na matsa musu hanya suka shige, har sun yi gaba Alisha ta dawo ta kallemu sannn ta ce. “Wai me kuke nufi? Kulluk aganku ku biyu ina Islahan? Ko dubiyar ma ka hanata ne, sabida ka ɓata ta a cikin ‘yan uwa?” Hajiya Falmata da ta dawo ita ma ta ce. “Na yi alƙwarin bazan ƙara zuwa gidanka ba, amma tabbaa kaje ka kawo min ‘yata yanzu.” “ ‘Yar taku tana wajena ne? Ku tambayeta man…” Na yi sauri na rufe masa baki, jin yana shirin ɓallo ruwa, wanu kallo na yi masa wamda zai sa shi ya tuna Islaha bata nan, tana zaune a gidan Sisiter Seemah a sirrance, amma ina Alisha ta ce. “Bangane ba, kana nufin Islaha ba ta gidanka? To tana ina? Lallaima.”’ “Ke cika mishi baki, shashasha marar tarbiya, zai yi magana kin wami rufe masa baki, wallahi idan wani abu ya sami ɗiyata sai na kai ki prison.” Turaki ya ƙwace bakinsa, a fusace ya ce. “Ki kaita prison? Ashe kuwa za aje prison da yawa, ‘yar ki tana nan da tarin abun kunyar da ta aikata, kuje ku tambayi Sister Seemah, yarinyar ku tana wajensa, kuma ku sani abinda ke jikinta, bazan taɓa amsa ba.” “Bangane ba, tana wajen Seemah, kan babbar uba.” “Kuje ku nemeta a wajenta, kar wanda ya ƙara haɗani da ita, nasake ta tuntuni.” Yana gama faɗin haka ya ja hannu muka fice, muna fita na ce. “Me ya sa ka yi haka? Ba ance za a rufa asirin komai ba, me ya sa ka watsa?” Sai da muka shiga mota ya ce. “Habibty, Sardauna fa ba ɗan familynmu ba ne, amma yazo sai ƙoƙarin raba mana kai yake, duk wata fitina shi yake tado da ita, kanmu gaba ɗaya ya rabu duk a sanadin mutum ɗaya, yanzu wannan dole aiki na ne na haɗa kanmu waje, nine fa jika babba namiji, wannan nauyi na ne, haƙƙine a kaina, bazan bari wani daga waje yazo ya tarwatsa mu ba.” Na kalli Turaki kallo na tsanaki, yanda idonsa ya yi ja, yana fitar da ƙwalla ya yi matuƙar bani tausayi, tabbas a yanzu aikine akn Turaki ya haɗa kan ‘yan uwansu waje guda, amma ba sai ya biyo ta haka ba, na ja numfashi sannan na ce. “Habiby, tabbas wannan aikin ka ne, kuma sai ka dage akai, ka yi duk wani ƙoƙari da zaka iya akan hakan, amma kuma komai ta masalaha ake bi, kowanne abu kafin a aikata shi, sai anyi masa dogon zama, dogon nazari. An nazarce mai zai je ya dawo, sharri ne ko alheri, idan duka ne wanne yafi sharri yafi yawa ko alheri? Duk yakamata ayi masa wannan nazarin, ni Nana na yi alƙwarin zan tsaya da kai, zan kasance mai taimakonka ta kowanne fanni, komai tsanani komai wuya.” Ya sakar min wani murmushi, ya kama hannu ya ce. “Na gode Habibty, na gode da shawarwarinki, ma gode da. Kasancewa a tare da ni.” “Babu godiya a tsakanin mu habiby, haƙƙi ne akan kowacce mace ta gari ta kasance a tare da mijinta komai tsanani komai wuya, yin haka shine zai baki riba a duniya da kuma lahira.” Ya sake wani murmushin ya jawo ni jikinsa, daidai lokacin wayarsa ta fara ringing, ya ɗauka yana faɗin. “Sister Seemha.” Na gyaɗa masa kai, ya ɗaga kiran tare da sa wayar a buɗaɗɗiyar speaker. “Turaki kana ina? Me ka cewa waɗan can mutanen?” “Ina asibiti, yanzu zamu tafi gida.” “To ka jirani yanzu zan zo nan, ayi komai ya ƙare.” “A’a kar ayi asibiti, gwanda a nemi wani wajen da bazaiyu akan wani daban ba muje muna ɗaga hankalin kakarmu a asibiti, har wani abu yasake samunta.” “To kazo gidanmu, nima zamu wuce can, suma zance su je can, har da shi Sardaunan.” “Tom.” Ya faɗa tare da kashe wayar, yaja motar muka nufi hanyar, ni dai Allah Ya ganu banso ayi komai a haka ba, abi ta masalaha, yanzu me Sardauna zai ji da shi, cikin shege ko kuma rashin asali, ko da yake ba rashin asali ba, ya zai ji idan yagane shi ba ɗan asalin gidan da yake taƙama da arziƙinsu ba ne, ya zaiji idan yaji bashi da ko sile a ciki? Too jama’a, munzo iyakar littafi na biyu, ga dai Sardauna ba ɗan familyn Ta ambo ba ne, ga cikin da ya yi wa Islaha, shine familyn Ta ambo zasu ci gaba da riƙe Sardauna? Ko zasu sallameshi ni? Wai Nana zata samu haihuwa kuwa? Mu haɗu a littafi na Uku da zai fara zuwa ranar 20 ga wata june a arewapen, 22 a whatsapp. Legendspen 08129553971