*SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 FUTURE WRITERS ASSOCITION (FUWA) Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Gaisuwar SARTSE zuwa gareku Iyalan Fam. Alherin Allah Ya kai muku a duk inda kuke.  Shafi na ɗaya     (01) Labarin Sartse ƙirƙirarren Labari ne, ban a rubuta shi dan cin zarafin wani ko wata ba, idan akwai wanda ya yi shige sa yanayin labarinsa muna neman yafiyarsa akan hakan. Haƙƙin Mallaka nawane ni kaɗai.  Kamar ko yaushe Book one zai kasance Free, Two da Three kuma zasu a paid, akan ƙaramin farashi.  Shimfiɗa *Jihar Jigawa , Nageriya.* Jihar Jigawa tana daya daga cikin jihohin da aka kirkira a karkashin mulkin soja na Janar Ibrahim Badamasi Babangida a ranar 27 ga watan Agusta, 1991. An ciro jihar ne daga tsohuwar Jihar Kano, inda aka ba ta sunan "Jigawa" wanda ke nufin kasa mai tudu ko yashi, yanayin kasar da ya shahara a yankin. Jihar ta kunshi hadakar manyan masarautu guda biyar (5) masu tsohon tarihi, wadanda suka hada da: Hadejia, Kazaure, Gumel, Ringim, da kuma Dutse. Wannan ya sa jihar ta zama matattarar al'adu daban-daban na Hausawa da Fulani da kuma Mangawa. Ana yi wa jihar lakabi da Sabuwar Duniya saboda burin da aka sa a gaba na gina ta a matsayin jiha mai dogaro da kanta ta fuskar noma da kasuwanci. *ƙaramar Hukumar Dutse*  Dutse birni ne mai dadadden tarihi a kasar Hausa. Asalin sunan garin ya fito ne daga manyan duwatsu da suka mamaye yankin. Kafin kafuwar jihar Jigawa a shekarar 1991, Dutse tana karkashin jihar Kano ne kuma tana daya daga cikin tsofaffin gundumomi masu daraja. Birnin na da sarauta mai karfi wato Masarautar Dutse, inda sarkin garin ake kiransa da "Sarkin Dutse." Tarihi ya nuna cewa mutanen farko sun zauna ne a kusa da wadannan duwatsun domin samun kariya daga makiya a lokacin yake-yake. Yanayin Girman Garin a Taswirar Nigeria Dutse tana nan a Arewa maso Gabashin Najeriya. Haka A taswirar jihar Jigawa, Dutse tana tsakiya zuwa kudancin jihar. Ba birni ne mai matukar fadi kamar Kano ko Kaduna ba, amma yana bunkasa cikin sauri sakamakon zama babban birnin jiha. Yanayin garin akwai zafi sosai a lokacin rani, sannan akwai hunturu mai ratsa jiki saboda duwatsu da kuma kusa da hamada. Haka a bangaren Sana'ar Mutanen Garin Mutanen Dutse galibi Hausawa ne da Fulani, don haka sana'o'insu sun hada da • Noma: Shi ne babban jigo, musamman noman gero, dawa, wake, da kuma shinkafa a wuraren da akwai ruwa. • Kiwon Dabbobi: Ganin cewa akwai Fulani sosai a yankin, kiwon shanu da awaki sana'a ce mai matukar muhimmanci. • Kasuwanci: Akwai manyan kasuwanni inda ake hada-hadar amfanin gona. • Aikin Gwamnati: Kasancewar sa babban birnin jiha, akwai ma'aikata da dalibai da dama (musamman saboda Jami'ar Tarayya ta Dutse - FUD). Takur Site unguwa ce da ke zaman kanta a cikin birnin Dutse, wacce ta yi fice wajen tsari da kyawun gine-gine. Unguwar tana cike da manyan gidaje na zamani wadanda aka gina su da faffadan fili. Galibi gidajen suna dauke da fulawa da korayen bishiyoyi da ke kara wa unguwar kyan gani. Sannan Mafiya yawan mutanen da ke zaune a nan ma'aikata ne, manyan jami'an gwamnati, da kuma malaman jami'a. Wannan ya sa za ka iske mutanen cikinta masu ilimi ne da sanin ya kamata. Babban abin da ya bambanta Takur da sauran anguwanni shi ne shiru. Babu hayaniyar yara a titi, babu kade-kade, kuma babu cinkoson mashina. Daga karar fankar sai kukan tsuntsaye; hakan ya sa ta zama gurin da mutum zai iya hutuwa cikin natsuwa. Sannan Tana da tituna masu kyau da hasken wutar lantarki wanda ya fi na sauran sassan garin tabbas saboda kasancewarta unguwar manya. Da misalin karfe 05:40 na yamma.  Wani irin azababben zafi nake ji yana shiga jikina, kamar ana tafasa ni a cikin tandar gurasa. Kicin ɗin gaba ɗaya ya ɗumame yana fitar da wani irin wuci, sakamakon girkin da nake a kurfoti guda biyu.  "Wayyo Allah!."  Na faɗa a fili bayan na juya ga miyar da take tafasa akan ɗayan kurfotin, tsumma na ɗauka na sauke ta ƙasa na fara juyata.  "Maggi bai ji ba! A'a ya ji Sardauna baya son maggi ya yi yawa." Na faɗa a dabarbarce, ina mai sa hannu na taɓa wayata, allon wayar ya kawo haske na yi tozali da kyakyawan hotona ni da mijina a ranar ɗaurin aurenmu, a fili na furta.  "Ina sonka mijina, ina ƙaunarka, Allah Ya kula mini da kai."  Ina faɗin haka na maida kallona ga agogon, shida da rabi daidai. Nasan kowanne lokaci zai iya shigowa, ƙaurin gurasar da nake gasawa ne ya daki hancina, ba shiri na miƙe tsaye na sa hannu a kan kaskon da nake gasawa da niyar juyawa, sai dai cikin rashin sa'a na kama dandarrayar kasakon maimakon gusar, wani irin zafi ya ratsani har tsakar kaina, na yi baya da sauri ina faɗin.  "Wayyo Allahna."  Ƙwalla ta cika min ido sakamakon raɗaɗin zafin da nake ji a 'yan yatsuna, ga kuma zafi da turirin da yake tashi daga cikin kicin ɗin.  Sake komawa na yi  na kama gurasar a hankali na juya. Bayan na juya na ƙara ɗaukan wani curi ɗaya na ɗorashin akan abinda nake murzawa da shi na fara murzawa ina faɗaɗashi, har sai da ya yi falai falai, sannan na cire takan kaskon na ɗora wannan, daga nan na koma kan miyar na ɗauko plast mai kyau na juye ta a ciki gaba ɗaya, da niyar idan ya ci ya rage ni sai na ci. Domin azababben ƙamshinta da ya cika mini hanci ya cire mini sha'awarta na lokacin, bayan na juye na ɗauki plast ɗin na fito daga kicin ɗin zuwa makaken falona na alfarma da ya ƙawato da kayan ado masu kyau da tsari.  Ɓangaren dinning na nufa, shi kansa abin tsayawa ka kalla ne, domin ni kaina lokaci zuwa lokaci na kan tsaya na kalli gidana da irin ƙoƙarin da iyayena suka yi wajen cika shi da kayan alfarma, bayan ƙoƙarin da Mijina Sardauna ya yi na gina makeken gida a anguwar Takur. Ina ajiyewa na koma kicin ɗin na juya gurasar dake kan wuta, sannan na fara ƙoƙarin juye wutar dake cikin kurfotin da na sauke miya a cikin wani bukitin ƙarfe, sabida bana son kashe wutar a cikin kicin ɗin toka ta ɓata minin aikin da na yi, bayan na juye na ɗauki Bukitin na fita bayan gidan ta ƙaramar ƙofar kicin, ƙaramin famfon na nufa na tara bokitin da wutar garwashin a ciki, bayan ruwan ya taru na zubar da iya ruwan da ya yi sanyi a bakin rariya, da sauri na koma kicin na sauke gurasar da ke kai na ɗauki ta ƙarshen na fara murzawa, bayan ta yi faɗi na ɗora ta akan kaskon, daga nan na koma na shanya gawayen da na kashe ɗazu a ƙasa, sannan na dawo kicin ɗin.  Daidai lokacin da motarsa ta fara horn, da sauri na dawo falo na buɗe taga na fara kallonsa, tun daga parking ɗin har fitowarsa, yanayin yadda yake tafiya ma kaɗai abin a tsaya a kallani.  "Wayyo Mijina, Allah Ya ƙara maka arziƙi, lafiya da nisan kwana."  Na faɗa a raina, ina ja da baya.  Ƙamshin turarensa ne ya fara dukkan hancina kafin sassanyar muryarsa ta daki dodon kunne na.  "Sannu da zuwa."  Na faɗa kamar zan durƙusa ma sa, tsabagen biyayya da ƙauna.  "Yawwa! Sannu da gida."  Ya faɗa yana miƙo mini jakar hannunsa, na russuna na amsa, ya ƙara ciro hulal kansa ya miƙa mini kana ya sami kujera ya zauna, ɗakinsa na nufa zan ajiye cikin kakausar muryarsa ya ce.  "Ranki ya daɗe takalmin fa."  Murmushi na saki sannan na ce.  "Ina shirin fara shiga da waɗannan ne."  "Ko dai kin barni na cire?."  Na dawo kusa dashi, na tsugunna na cire masa takalmin, bayan na cire na kwaɓe mai safar sannan na ɗauka na shiga dasu cikin ɗakinsa, komai a mazauninsa na ajiye su na ƙara gyara inda na ga kamar bai gyaru ba a ɗakin sannan na shiga toilet na haɗa masa ruwan zafi daidai yadda nasan yana so.  A inda na barshi na sameshi yana danna wayarsa. Sai da na gyara muryata yadda zata fito da zaƙi sannan na ce.  "Ruwan wanka ya zama ready."  Ajiye wayar ya yi ya miƙi zuwa ɗakin.  "Ki jera mini abinci kafin na fito."  Ya faɗa cikin kakkausar muryarsa sannan ya shige ciki. Ina nan tsaye sai da naga ya yi kusan minti biyar a ciki sannan na sauke wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya, jin shi shiru ya bani ya bani tabbacin ruwan ya yi masa daidai.  Kitchen na koma na shiga haɗo kayan abinci, a hankali a hankali na jera komai akan dinning ɗin bayan na gama na shiga nawa toilet ɗin nima na watsa ruwa a gaggauce na fito daga bayin na hau shiryawa.  "Nana! Nana! Nana!!."  Na ji muryarshi, ba shiri na zura Hijabi na fito. "Na'am! Gani."  "Kina jina ina ta faman kiranki."  Ya faɗa yana zama akan dinning.  "Yanzu na fito daga wanka ne."  Na bashi amsa.  "Okay i see, zuba mini."  Ya faɗa hankalinsa yana kan wayarsa. Plate na ɗauko na saka masa Gurasar guda uku, sannan na ɗauki bowl na zuba masa miyar, sannan na ƙara ɗaukan wani bowl ɗin na saka masa farfesun tsokar rago, sai kuma kofi na zuba masa lemon citta da ya sa na yi masa. Sai da nagama gaba ɗaya sannan na ce.  "Gashinnan."  Wayarsa ya ajiye ya fara cin abinci, ganin ya fara cin abincin yasa na koma ɗaki na ci gaba da shiri na, sai da na taje dogon gashina sannan na fara shiri, sauƙaƙƙiyar kwalliya na yi, sannan na ɗauko doguwar rigar abaya na saka, bayan na feshi jikina da haɗin turarruka.  Ko da na fito falon  ban ganshi akan dinning ɗin ba, sai da na ƙarasa shigowa falon na hango sa acan kan kujera yana yana faman danna waya, kan dinning ɗin na nufa na zauna, buɗe plast na yi zansa gurasar sai sai guda ɗaya na gani, murmushi na yi a raina na ce.  "Yau yallaɓai anji daɗin girkin kenan."  Na ɗauki ɗayar nasa a plate ɗin da ya gama ci, na buɗe plast ɗin miyar zan zuba sai dai fa sam babu miyar a ciki ya shanye, karo na farko cikin abubuwan da Sardauna yake yi mini na ji babu daɗi, buɗe plast ɗin da farfesun naman ragon yake ciki na yi shima dai babu.  "Me ya faru haka?."  Na tambayi kaina, dan nasan dai Sardauna bazai taɓa cinye duka wa'yannan ba, dole wani wajen ya kai ko ya kai kitchen.  "Ka kai ragowar kicin ne?."  Na tambaye shi, muryata na rawa kamar wacca ta yi tsaren gudu, ko dayake ba shakka tsare na yi, domin na yi tsere da zuciyata kafin bakina ya iya fito da wanann tambayar.  "Ban ɗauke komai ba, ai aikin ne ko?."  Zama na yi akan dinning ɗin, gaba ɗaya raina babu daɗi na rasa abinda ke mini daɗi. Muryar shi na juyo ya na cewa.  "Me kike yi anan ne?."  Na goge ƙwallar da ta fito daga ido na ce.  "Babu komai?."  "To tawo nan mana."  "Abincin zan ci."  Na faɗa ba tare da na taso ɗin ba.  "Tom."  Kawai ya faɗa ya ci gaba da abinda yake, na tashi na shiga cikin kicin ɗin, ban masan me zan iya dafawa ba wanda zansa a cikina, ga yatsu na sai wani irin zugi suke yi mini kamar wacca na taɓa attaruhu.  Haka nagama zagaye na a cikin kicin ɗin na fito zuwa falo, na bude firij na ɗakko biredi na dawo kan dining na haɗa da ragowar romon farfesun naman na ci.  Bayan na kammala na ɗauke komai na kai kicin, na gyara wajen tsaf sannan na nufo shi zan zauna na huce gajiyar da take cin jikina. Sai dai ban kai ga ƙarasowa ba idanuna suka sauka kan abinda yake yi, ya zuge zif ɗin ɗaya daga cikin fulallukan kujera yana fito da katifar ciki yana gutsirawa a hankali, kamar ƙaramin yaro yana wasa, sai da na haɗiye wani abu a raina sannan na ce. "Sardauna! Kujerar kake yagawa fa?"  Na fada ina kallon katifar da yake gutsirawa, gabana yana faɗuwa ganin yadda yake ɓarnatar da kayan gidan namu. Kallona ya yi sannan ya kalli abinda ya watsar.   "To kin barni nan ni kaɗai, ba dole na yi duk abinda zanyi ba dan ma banyi miki kuka ba."  Murmushi na yi sannan na zauna kusa dashi da faɗin. "Abinci fa na ci." Cuno baki ya yi kamar ƙaramin yaro zaiyi kuka sannan ya ce.  "To kuma sai ki bar mijin ki da yake sonki fiye da komai shi ka ɗai, babu abokin ta ya shi zama."  "To ai gani nan nazo."  Na faɗa ina shafa masa kai, ai kuwa ya kwanto akan cinyata.  "Daman kaina ƙaiƙayi yake, ki gyara mini."  Ya faɗa bayan ya kwanto, tare da  janyo wayarsa ya fara dannawa, wani irin nauyi na ji kamar an ɗoramin dutse, kamar da gangan ya sakar mini nauyinsa, na fara shafa masa kansa, ina jin dumin gashinsa a tafukan hannuna. "'Nana." Ya kira sunana a hankali, idonsa har yanzu yana kan wayarsa.  "'Na ga yadda kika yi shiru ɗazu da kika ga na cinye Gurasa, Ko dai kin fara gajiya ne da yi mini girki ne, ko gajiya da zama dani a cikin gidan? Rayuwar aure fa bauta da soyayya ne! Na ɗauka kin fi kowa sanin cewa duk abin da yake nawa, naki ne... har da yunwar ki.'" Na haɗiye miyau me ɗaci da ya tsaya mini a maƙwogaro, na yi ƙoƙarin yin murmushi duk da raɗaɗin da yatsuna suke mini na ƙunar da na yi ɗazu na ce.  "'Haba Sardauna! Kai fa mijina ne, ni kuma matarka ce mai ƙaunarka, ai na ji daɗi ma da ka cinye abincin, hakan na nufin girkin ya yi daɗi kuma hakane burina." Ya ɗaga idonsa ya kalle ni, wani kallo mai wuyar fassara sannan ya ce.  "Yauwa. Domin idan kika fara ƙorafi a kan abinci, zan fara tunanin ko ni ɗin ne ba kya so... ko kuwa kin fara manta yadda iyayenki su ka gaya miki yadda mace ta gari take zama da mijinta?"  Ƙarar wayata ne ya katse mini maganar da na yi niyar yi, na kai hannu zan ɗauka amma Sardauna ya riga ni.  "Wake kiranki a daren nan?" Murmushi na yi sannan na ce.  "Bansaniba wallahi, amma bani na ɗaga."  Sardauna bai ba ni wayar ba, sai ma juyawa da ya yi ya fuskanci allon wayar, hasken ya haska kwayar idonsa da ta canza launi lokaci guda. Ya dade yana kallon sunan dake kan allon wayar kafin ya dago ya kalle ni, wani irin kallo nasa da yake mini wanda ni kaina bana gane me yake nufi dashi, sai kuma ya saki wani irin murmushi kana ya ce.  "Daga gida ne..."  Ya fada muryarsa na rawa kaɗan.   "Radiya ce."  Ya kama sunan babbar Yayarmu kai tsaye, sannan ya ce. "Me take nema gunki a wannan lokacin?" Ban kai ga ba shi amsa ba, ya danna maɓallin kin amsa kiran (Reject). Ya ajiye wayar a kan kirjinsa, ya kara gyara kwanciyarsa a cinyata yana kallon silin din dakin. "Ita taƙi zaman aure, tana so ta hanaki kula da miji ko bawa mijinki lokacinki. Nana, kin san ina son ki ko? Kuma kin san ba na son kowa ya shiga tsakaninmu. Wannan gidan namu ne mu biyu, duk wanda zai kawo mana rarrabuwa, ko da kuwa danginki ne, to ba ya son mu." Wani irin nauyi na ji ya ƙara danne ni, ba nauyin Sardauna ba, nauyin kalaman da ya jefo mini ne. Ya kama hannuna da ya kone dazu, ya matse shi a hankali sannan ya ce.  "Gobe me zamu karya dashi? Ni bana son cin biredi abinci nake son ci very special, ba irin wanda muka saba ci ba."  Na yi murmushi muryata na rawa sannan na ce.  "Tom Mijina na me kake so?."  "Zaɓi yana wajenki, amma dai abu na daban, ko zan sami Vento cake wanda zan fita dashi ofis?."  Na gyaɗa kai sannan na ce.  "Zaka samu mana." Bansan ashe ƙwalla ta fito daga idona ba, sai ji na yi ya kai hannu gefen idona ya goge hawayen da yatsansa, sannan ya kai yatsan bakinsa ya ɗanɗana.  "Hawayenki suna da ɗanɗanon gishiri, Nana. Kada ki sake kuka... domin kukan mace a gidan miji, alama ce ta rashin godiya ga Allah ko kuma raina kulawar da miji yake ba ta." Washe gari. Gaba ɗaya jikina babu daɗi haka na tashi, bayan na yi sallar asuba na shiga kicin, ba tare da sanin ainahin abu na daban da Sardauna yake maganarsa ba. Sai da na ƙarewa kicin ɗin kallon sannan basira ta faɗo mini, na tsugunna gaban kurfoti bayan na zuba gawaye na fara ƙoƙarin kunna wuta, sai dai da na kunna hutar iska take kaɗe ta, abu kamar wasa na kusa minti sha biyar a gaban huta amma taƙi kunnuwa.  Miƙewa na yi na nufi kan gas ɗina yau kawai zanyi girki akansa, ina kunnawa na ɗora tea kafin na ɗakko fulawa na shiga kwaɓa Fanke, amma wannan mai attaruhu da albasa da maggi ne a ciki, banda tabbaci amma nasan Sardauna bai taɓa cin wannan ba, nima na ko yi sarrafa fulawane a wajen Anty Hadiza matar Isah Nadabo dake ita 'yar kano ce kuma a kanon ma ƙwararriya ce a harkar sarrafa fulawa. Bayan kwaɓa na rufe shi na shiga juye tea din a flask sannan na ɗakko kasko na ɗora akan gas ɗin na zuba mai.  Ina ƙoƙarin fara saka fanke a cikin mai ya shigo kicin ɗin, har ƙasa na tsugunna ina gaida shi kamar zan yi masa sujjada. "Ina kwana, an tashi lafiya?."  Kallona ya yi sai kawai na ji ya ce. "Me yasa baki da tausayi ne Nana, me yasa imaninki yake raguwa a ko da yaushe?."  Gabana yashiga faɗuwa, ƙirjina ya fara dukan uku uku, bansan tausayin da ya kaini kunna gas ba, duk da ba wani amfani nake dashi ba, sai na yi sati biyu banyi girki akai ba, hasali ma shi ke amfanin da shi wajen dafa ruwan wanka, ko tea idan yana sauri.  "Ka yi hakuri dan Allah, gawayin ne yaƙi kamawa gaba ɗaya, na kusa minti goma ina kunnawa amma yaƙi kamawa."  "Mitchewww."  Ya ja wani uban tsaki, sannam ya ce.  "Minti goma kacal? Ba zaki iya minti goma wajen kunnawa hutar da zaki yi wa mijinki girki ba? Nana bansan yaushe rashin imaninki ya kai haka ba, tabbas 'yan uwnaki zawara suna fara ɗoraki a turbar da suka bi suka kashe aurensu."  Hawaye na ji ya fara gangaro mini daga ido, cikin sanyi murya na ce.  "Ka yi hakuri dan Allah, nasan kana son fita da wuri kar na ɓata maka lokaci, amma in sha Allahu bazan sake amfani dashi ba har Abada."  Na faɗa muryata na rawa, alamun kuka ya fara cin ƙarfi na.  "Kuka kuma? Nana me yasa kike son azabtar da zuciyata da hawayenki ne? Nifa mijinki ne mai sonki fiye da komai a duniya, Nana kawai ina guje miki bin hanyar da 'yan uwnaki suka bi." Shiru na yi bance komai ba, sai shashaƙar kuka da nake yi.  "Nana! Goge hawayen nan ki ci gaba da abinda kike amma bana son almubazaranci, kinsan yadda rayuwa ta yi tsada, ko da yake ba sai na faɗa miki ba, gidanku ka ɗai ya isheki ishara."  Legendspen 08129553981 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na biyu     (02) Goge hawayen na shiga yi, na rasa me yake mini daɗi, Allah Ya gani ina mugun so da ƙaunar mijina, kamae yadda shima na tabbatar yana sona, to me zai sa na tsaya akan gas ina ɓata masa rai. Tashi na yi na je na kashe Gas ɗin sannan na ce.  "Ka yi hakuri dan Allah, idan ban tausaya maka ba wazan tausayawa a duniya? Wa nake dashi da zan zo bayan kai?"  "Nana ai naga alamun kamar ana son shiga tsakanin mu a hure miki kunne."  Ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushin da nake kallo a matsayin soyayya mai girma, sannan ya ƙara cewa.  "Nana ina son na nemi alfarma a wajenki guda ɗaya."  Na gyaɗa masa kai sannan na ce.  "Ina sauraronka."  "Nana duk runtsi duk wuya ka da ki bari wani ya shiga tsakanin ki da mijinki, ina faɗa miki hakane a matsayina na mijinki, mai ƙaunarki."  Cike da farin ciki da gamsuwa da soyayyarsa na ce.  "Tom in sha Allah, yanzu kaje ka yi wanka zan kunna wutar gawayin na soya na kawo ma."  "Tom ki yi sauri kinsan dai fita nake son yi."  Ya faɗa yana juyawa ya fice, ni kuma na kulle ko ina na kicin din na fara ƙoƙarin kunna wutar.  Gaba ɗaya kicin ɗin ya turniƙe da hayaƙi wanda ya tsaya mini a maƙwogarona na fara tari babu ƙaƙƙautawa, ba shiri na tsugguna a ƙasa na fara kakari, ina jin kamar hanjin cikina zai fito waje, da ƙyar na iya tashi na fara buɗe kokafin bayan na ga wutar ta kama. Idona fal da ƙwallar da ta taru sabida hayaƙi na tashi na ɗakko farantin silba na shiga firfita wutar har takama.  Na sakko da kaskon daga kan gas din na ɗora akan kurfotin, ina yi ina firfitawa har man ya yi zafi na fara sanya fanken ina soyawa. Kusan minti talatin sannan komai ya kammala na juye a filas na fito falo, yana zaune kan kujera ɗaure da tawul ɗin wanka.  Kan Dining na nufa na ajiye plast ɗin, sannan na koma Kicin na ɗakko kufuna da faranti na dawo na jera akan dining sannan na dawo cikin falon.  "Komai ya kammala."  Na faɗa ina ƙoƙarin zama sabida sandarewa da na ji bayana ya yi, sakamakon durƙushen da na yi na soyawa fanken, kallona ya yi sanan ya ce. "Ni ai ban kammala ba! Ko ni zan shirya kaina ne?."  Murmushin yaƙe na yi sannan na ce.  "Aha ba dai! Ya zaayi ka shirya kanka ni ina nan, mene amfanina?." "Babu kam, idan har ba zaki yi mini biyayya ki faranta rai ba, babu."  "Mene haka?."  Na faɗa arazane sakamakon abinda nagani, sosa ƙeya ya fara yi sannan ya ce.  "To na buɗe zan shirya tun da naga kina kicin, kuma ni banga kayan da suka yi mini ba shine sai na fito dasu duka."  Yanayin yadda ya yi magana ya yi matuƙar burgeni, ya kuma goge mini dukkanin ɓacin ran da sheɗan yake son san ya mini.  Na yi murmushi ina matsowa sannan na ce.  "Ai da ka jirani, amma bari na duba maka nina san wa'yanda zasu yi maka kyau."  Na tsugunna a ƙasa na fara kwashe kayan da ya zuzubar a ƙasa ina zuba su kan gadon, sai da nagama kwashe su tsaf sannan na ce.  "Bari naga wanda zaifi maka kyau."  "Hon!."  Na ji sassanyar muryarsa ta kira sunan ds na tabbatar sai soyayya ta yi daɗi yake kiranshi.  "Naam Hon!." Na amsa masa nima cikin tawa sassanyar muryar da nasan ba ta yi ko rabin tasa a daɗi da sanyi ba, abu guda ɗaya da nake ƙara yararwa kaina shine. Sardauna Mijina ba tsarar aure na ba ne, Sardauna ba aji na ba ne, Sardauna yafi ni komai, ko naƙi ko na so Sardauna alfarma ya yi mini ya aureni, sabida yana sona.  "Kayan nan kamar ba'a taɓa gogesu ba ko?."  Ya faɗa yana taɓa kayan a yamutse kamar ba na sa ba. Da mamaki na kalleshi, sannan na kalli kayan, inda sardauna yake kai wanki da guga ba ƙaramin waje ba ne a Duste, idan suka yi maka wanki zaka rantse kayan ba a taɓa sa su ba, gasu nan suna sheƙi amma yake cewa kamar ba'a taɓa gogewe ba, 'ko ya fara ciwon ido ne?' "Ko?"  Ya sake faɗa, sai da na yi murmushi sannan na ce . "Wai Hon me ka gani ne?" "Duk sunyi wani sikwizin, kamar an ƙwato su daga bakin kura."  Na yi dariya ganin yadda yake taɓe hanci, kamar yana riƙe da kashi.  "To ai duk kaine ka yi musu haka."  Na faɗa ina ci gaba da duba kayan.  "To ai bansan zasu yi haka ba, yanzu haka zan dinga fita kamar almajiri?."  Ya faɗa kamar zaiyi kuka, gaba ɗaya naji nustuwata tana shirin barin gangar jikina, a ruɗe na ce.  "A'a Hon! Ya zaayi ka fita a haka? Zan bawa Madu ya kai wajen guga a sake gogewa, tun da kaga mu nan bama amfani da abu mai jan huta, mussaman dutsen guga, Tv, hita, da kukin gas, wani lokacin ma cewa kake a kashe fanka sabida Mita kuɗin wuta da wahala."  "To ya zaayi idan abu yakama dole ayi, ki yi amfani da dutsen kawai ki gogesu, amma kafin na dawo fa dan Allah Hon."  Haka kawai sai naji jikina ya yi wani iri, Miji na da nake so, nake ƙauna sama da komai shine zai dinga haɗani da Allah akan na yi masa guga, guga dai abar banza.  "Haba Hon! Haba Haba! Kafin ka dawo angama in sha Allah."  Na faɗa ina miƙa masa wani light bulun yadin.  "Kaga wannan bai yi sikwizin sosai ba."  Karɓa ya yi yasa, ni kuma na ɗau mataji na hau taje masa gashi, sai da gashim ya yi kyau sannan na sa masa hularsa, na fesa masa turare muka fito.  "Nifa na makara gaskiyya, na yi birek fas a ofis kawai."  Ya faɗa yana niyar ficewa.  "Haba Hon, ka tsaya dan Allah." "Hon it is almus 10:30, na makara sosai fa, ki ajiye min idan na dawo na ci." Bai jira amsa ta ba ya fice, yunwar da nake ji tun ta daren jiya da kuma ƙarin ta yau da safe ya sa na nufin kan dinning ɗin na fara cin abincina, bayam na kammala na kwashe koma na kai kicin, sannan na shiga ayyukana.  Ban ni na kammala komai ba sai wajen ƙarfe tara da rabi, Sardauna ya kawo mun masu aiki har guda huɗu amma ina sallamarsu, Allah Ya gani ina tausayin mijina bana so na ga yana ta kashe kuɗi a aikin banza, shi ya sa da ya kawo nake sallamarta, amma sai ya sake kawo wa, wai ance yawan aiki yana sa mace ta tsufa shi kuma bai son ma tsufa, sai da na yi da gaske kafin na fahimtar dashi cewar na haka ba ne.    Ina zama kan kujera bacci ɓarawo ya yi gaba dani ba tare da sani na ba. 'Gur! Gur! Gur!' Cikin bacci nake jiyo kukan wayata, ba shiri na buɗe ido na kai hannu na ɗauka, sunan Fauziyya ya bayyana akan Skirin ɗin wayar, bude ido na na yi gaba daya na ƙarewa wayar kallo, ina son ɗauka ina jin tsoron Sardauna ya rabani da kula ƙawaye, haka wayar ta ƙaraci kukanta ta gama kiran ya katse, sai a lokacin na duba naga wannan shine kira na bakwai da ta yi mini.  "Ko mutuwa aka yi?."  Na tambayi kaina, ba shiri na fara kokarin buɗe wayar na kira ta, sai dai ban kai ga kiran ba na ta kiran ta sake shigowa, ɗagawa na yi da faɗin.  "Salamu alaikum, Fauziyya."  Na faɗa murya ta ƙasa ƙasa.  "Nana ina kika saka wayarki, ina ta kira?."  "Wallahi bacci nake Fauziyya, Ya kike?." "Ina lafiya, matar nan gaskiyya kina hutawa abunki. Sardauna ya tsaya miki." Na yi murmushi mai nuna jindaɗi, sannan na ce.  "Wallahi tun da ya fita kawai na kwanta."  "Ai haka ake so, kin ga nazo bayan ku ne gidan yayar mijina shine na ce ko kina gida na biyo, kuma gashi na samu tabbaci."  Dum! Dum! Na ji gabana ya shiga faɗuwa, Sardauna baya sona da kowacce ƙawa, bai taɓa ce mini kar da ƙawayena su zo, amma ya fito ya nuna baya son ina kula su, ba ma iya su ba kowa ba ya so, ni kuma duk wani abu dai zai ɓata ran Sardauna bana maraba dashi.  "Kinyi shiru?"  Muryar Fauziyya ta dawo dani daga tunanin da na fara.  "Dan zaki zo gidana sai kin tambayeni? Kawai ki tawo, amma da wuri dan Allah kafin huɗu zai zo mu fita."  "Ah to ko ba sai na zo ba."  "Kai! Ya zaayi kive haka, kizo mana dan Allah."  "Toh shikennan yanzu zaki ganni."  Daga haka ta katse kiran, na miƙe na shiga ɗakina na ɗaura alwala na gabatar da sallah azahar ganin karfe ɗaya  ta yi, ina idarwa na shiga kicin na ɗora taliya jollop, sanin cewa zata iya zuwa a kowanne lokaci yasa na yi amfani da gas na ɗora girkin. Ina fitowa daga Kicin ɗin, na koma ɗakin Sardauna na fara haɗe kayan ina ninke su, daniyar idan ta tafi sai na goge su tunda mu nan bama rasa wuta kwata kwata. Ina cikin ninke kayan na ji sallama a falo, Allah Ya gani bana maraba da dukkan abinda zai ɓata ran mijina, na yarda da Allah, na yarda da cewar ina son Sardauna sama da komai.  Hakan ya sa bana farin ciki da zuwan Fauziyya, ƙaramin tsaki naja sannan na miƙe na fito, sai na zo dab da falon sannan na janyo murmushin yaƙi na sanya shi a fuskata. Itama fuskarta ɗauke da murmushin ta tare ni da cewa.  "Ƙawatah, ƙawar yarinta, ƙawar girma."  Na yi dariya na zauna akan kujera ina faɗin.  "Tawo mana."  Zama ta yi tana ƙare mini kallo. "kin canja gaba ɗaya abinki, kinsami aljannar duniya."   Na yi dariya da faɗin. "Alhamdulillah wallahi, bara na kawo miki ruwa kafin mu ci abinci."  "A'a yana ji ba sanyi a wannan zafin?."  Ta faɗa bayan na kawo mata ruwan, na yi murmushi sannan na ce.  "Kinga ni mura nake, shi kuma kwata kwata ba ya shan sanyi." Sai bayan na faɗa na yi mamakin yadda na iya shirya ƙarya a lokaci guda, na tuna lokacin da muka yi magana da Sardauna akan firjin.  "Nana! A gidanku babu firinji, baki sa ba shan sanyi ba, sabida yanayin unguwar ku ma zafi ake yi, dan haka anan ma ba zai zama wani abu ba dan na ce ba zaki dinga kunna firinji ba, sabida yanayin jan wutarsa."  Allah Ya gani ina tausayin mijina, ko bai ce ba nasam yadda kuɗin wuta yake anguwar masu kuɗi, shi ya sa ma yana faɗin haka, na ce Babu matsala.  Kicin na shiga na zuba mana abinci, na kawo mana falo jallop ɗin taliya da ta ji naman kaji zaƙwa zaƙwa, haka mu ka zauna muka ci, muna ci muna hira ko ba komai na ji matuƙar daɗin zuwanta. Bansan cewar ina zama kaɗaici ba sai da tazo, bansan cewa zaman da nake ni kaɗai ba, a ƙuntace nake ba sai da ta zo.  Muna tsaka da cin abincin aka yi sallar la'asar, hakam yasa muka gaggauta muka ci mu ka yi sallah, bayan mun idar ne Fauziyya ta ce.  "Gidanki ya yi kyau sosai, arziƙi da wadata faca-faca, sai dai ke din duk kina zaune babu wani kuzari kamar ba matar da take auren wanda take so ba?."  Murmushi na yi mata sanan na ce.  "Wanda nake so sama da komai ma a rayuwata, Fauziyya kinsan yanayin rayuwar auren, dole fa mace ta yi sanyi duk rawar jiki da kanta."  "Hakane kuma wallahi, to yanzu ya maganar wannan?" Ta faɗa tana nunan cikinta da ya tasa, na yi dariya sannan na ce.  "Yana hanya." "Kun fa kawo shekara biyu da aure ko?"  Na gyaɗa kai.  "Ikon Allah, kuma bai fara miki magana akai ba?"  "Bai fara ba gsky, ai yansan komai lokaci ne." "Da gaskiyyarku shi ya sa fa auren mai ilimi wayayye yake da daɗi, yanzu da irin mazajenmu timawan ƙauye ne, ai da yanzu andame ki da magana, ko shi bai yi ba 'yan uwansa sai sunyi."  A raina na ce. "Gaskiyya dai kam." Dan ko da wasa Sardauna bai taɓa yi mini maganar ciko ko haihuwa ba, ko zancen yara ma.  "Kinga har hudu da kwara, bara nazo na huce." Fauziyya ta faɗa tana miƙewa, nima na miƙi mu ka nufi waje na rakata, ina dawo wa hankali na ya yi kan gugar Sardauna, ba shiri na shiga ɗakin na dumbuzo kayan wajen Set goma na fito falo na jona dutsen gugar bayan na shimfiɗa darduma na zauna na fara gugar.  Kusan awa ɗaya da fara gugar ya shigo cikin gidan, haka kwai na ji gabana yana faɗuwa, duba da ko cikakken set bakwai bam goge masa ba, amma bayana ya ƙage, gashi ban ɗora masa girki ba. Jikina na rawa na kashe dutsen na miƙi na shiga kitchen.  Dame zanji kunna wuta? Ko tunanin abinda zan dafa masa? Ga kayansa da na bari a falo.  Ina jin ya shigo falon na fito da sauri tare da faɗin.  "Barka da dawowa."  Wani mugun kallo na ga ya watsamin, mai ɗauke da harara ya shige ɗakinsa. Dum! Daram! Haka na ji gabana ya buga. A fili na furta.  "Innullahi wainna illahir raji'un."  Na nufi ɗakim da ya shiga, yana zaune gefen gado ya haɗe rai, fuskar kamar bai taɓa murmushi ba.  "Sannu da zuwa dan Allah."  Na faɗa bakina yana karkarwa.  "Mitchew."  Ya ja tsaki yana ƙoƙarin cire takalminsa, da sauri na ƙaraso na tsugunna zan kama takalmin ina faɗin.  "Kawo na cire ma, wallahi kaina yake ciwo na kwanta, sai wajen huɗu na tashi." Wani kallon ya ƙara watsamin, sannan ya fara cire takalminsa, na kai hannu zan cire masa ya janye ƙafarsa tare da taƙemim ɗan yatsa. Na ƙwalla uwar ƙara tare da riƙe hannun da yake mini wani irin zugi kamar na sakawa ciwo gishiri. Yatsun da basu gama warkewa daga ƙonuwar jiya ba, gashi sun sha taku.  Miƙewa na ga ya yi ya shige ban ɗaki abunsa, ya buga ƙofar hakan ya ƙara tabbatar mini da cewa yana cikim fushi mai tsanani.  "Wayyo Allahna." Na faɗa idanuna na zubar da hawayen da bana raɗaɗin da hannuna yake ba, na raɗaɗin fushin da mijina yake yi dani.  "Me ya sa na kasance haka? Me ya sa na kasance sakarar da batasan abinda take ba? Me ya sa na kasance butulu mai manta alheri? Mutumin da yake sona, amma na zaɓi kullum na ɓata masa rai? Tir dani! Tirr da halayena."  Abinda nake faɗa a raina kenan, wani ɓari daga zuciyata da yake matuƙar ƙaunar Sardauna ya ce dani.  "Maza ki ƙara ɓata masa rai da baza kije ki yi masa girki ba."  Kamar mahaukaciya sabuwar kamu haka na miƙe na fice zuwa kicin, idanuna na zubar da hawaye na fara ƙoƙarin kunna wuta, hayaƙi ya turniƙe kicin ɗin, amma banaji bana gani. Legendspen. *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na uku     (03) A gurguje cikin ƙasa da minti ashirin na haɗa cus-cus da mayar ganye, wacca sai da na kwashe tsawo minti na goma ina tunanin mai zan dafa,  haka nake, a ko yaushe burina na ga na dafawa Sardauna abu na daban.  Albarkacin miyar ganyen da nagani a firiza ya gajarta mun tunanin da nake yi. Fuskarsa ka ɗai na kalla na ji gabana ya faɗi har na kusa yin tuntuɓe.  Ajiye masa plast ɗin abincin na yi akan dinning sannan na shiga ɗakinsa na buɗe ƙaramin firinji dake ɗakin na ɗakko ruwan sanyi na fito dashi, daman anan kawai ake samun ruwan sanyi sai kuma firiza ya ce ita firiza sabida kar kaji kifi ko abinci ya lalace baya son asara, shi kuma na ɗakinsa ƙarami ne ba zai ja wuta ba.  Ko da na fito falon yana zaune kan dinning din ya fara zuba abincin, na ajiye masa ruwan da faɗin.  "Kawo na zuba..." Ya kuwa gallamin uwar harara, ba shiri na cika mai cikolin na yi baya, da idonsa ya kalli kayan da nake gogewa sannam ya ɗauke kai.  Ba shiri na matsa daga wajen na dawo kan kayan na hau gogewa jikina yana ɓari haka nake gugar.  Ina nan zaune ya gama cin abincin ya tashi ya shige ɗaki, ba shi ya fito ba sai da aka yi sallar isha, yana tafiya massallaci na kashe dutsen na tashi na ɗaura alwala na yi magariba na yi isha. Sannan na kwashe kayan da na goge na shiga ɗakin na sanya su a sif, na sake ɗebu ragowar na dawo falon.  Sai da na yi nisa a gugar wajen ƙarfe goma na dare sannan ya shigo, bai kalleni bare na sa ran zai mini magana ya huce ɗaki, haka nai ta guga ta har wajen ƙarfe sha biyu da rabi na dare sannan na kamalla. Na ɗauki kayan zan kai su ɗakin sai jin ƙofa na yi a kulle, wani irin abu ya tsaya mini a raina, tabbas nasan na kai mijina bango har ya iya kullen ƙofa, tabbas ban kyauta ba, ban kyautawa kaina ba. Na daɗe a falon sai wajen ɗaya sannan na shiga ɗakina na kwanta, sai dai baccin da na yi ya kasance marar daɗi kwata kwata.  A tsakanin karfe ɗaya zuwa biyar da rabi na dare, na farka ya kai sau shida.  Yau kam tun asuba na shiga kicin, na hau haɗa masa abincim safe, cikin sa'a na kammala komai kafin ƙarfe bakwai.  Ina tsaka da jera masa dinning ɗin ya fito cikin shirinsa, kallo ɗaya ya yi min ya ɗauke kai ya nufi ƙofa zai fita.  "Baka karya ba."  "Bazan karya ba, ai bakya sona Nana, kin gaji da yi mini biyayya, kin daina jin maganata."  Ya faɗa yana tsareni da kaifaffun idanunsa, jikina yana ɓari na fara cewa.  "Wallahi a'a ba haka ba ne." "To ya ne? Har ƙarya fa kika yi mini jiya, wai bacci kikayi, bayan ƙawayen da na hanaki mu'amala dasu ne suka zo suka zuga ki. Nana dan ina sonki bazan juri abinda kike mini ba, kina ƙaskantar dani, kina nuna banda daraja banda mutunci. Nana a kaf faɗin duniyar nan ko iyayen da suka haifeki basu kaini sonki ba, Nana kinsani, ina sonki, ina kyautata miki, ina baki duk wani haƙƙinki, amma Nana me kike sakamini dashi? Mene abu ɗaya?" Na yi shiru, gaba ɗaya jikina ya yi wani irin sanyi, wani sabon tausayin mijina ya lulluɓe ni, a hankali na fara magana, idona cike da hawaye.  "Ka yi hakuri dan girman Allah, wallahi bazan sake ba, sai da na ce mata kar ta zo amma taƙi."  Sai yanzu na fara mamakin kaina, yadda aka yi na zama maƙaryaciya lokaci ɗaya, duk dan na faranta masa.  "To bance duka kike goge lambobi su ba?."  "Na goge fa, ai kana ganin wayar babu lambar kowa sai taka da ta 'yan gida, to idan suka kirani ne nake ganesu."  "Bani wayar."  Ya faɗa yana takawo cikin falon, fuskarsa a haɗe kamar zai dake ni, hannuna har karkarwa suke yayin da nake kokarin mika masa wayar, ya sa hannu ya fusgeta da ƙarfinsa. Daidai lokacin saƙo ya shigo wayar ji kake. 'ɗilim.' ƙarar shigowarsa.  "Waya turu miki saƙo?."  Ya tambaye ni, cikin muryar kuka na ce.  "Nima bansani ba."  Wayar ya danna ya bude saƙon, ya ƙura ma wayar ido yana motsa baki, idanunsa na yawo akan sikirin ɗin wayar, wanda yake daidai da ƙaƙƙarfan bugun da zuciyata ke yi.  "Mitcheww."  ya ja tsaki, ya danna maddanin gogewa ya goge saƙon.  "Ina so ki ciro mini layin nan yanzun nan."  Ya faɗa yana miƙomini wayar, da rawar jiki na amsa na fara ƙoƙarin cire layin, yana kallona da idanunsa har na cire na miƙa masa, ya karɓa ya sa a aljihu, kana ya zauna akan kujera, ya runtse idanunsa kusan mintina biyu sannan ya buɗe su, ni dai ina tsugunne ina kallonsa, ƙaunarsa da tausayinsa suna cika mini zuciya, ina son mijina,ina tausayinsa.  "Hon! Matso ki zauna."  Sassanayar muryarsa da tafi ruwan ƙanƙara sanyi ta doki kunnunwana, ba shiri na miƙi na matso kusa da shi na zauna, ya sa hannuwansa ya kama nawa, a hankali ya fara matsa su.  "Nana, kin san me ya sa nake yin haka?"  Ya tambaya, muryarsa tana fitowa da wani irin sanyi mai ratsa zuciya. Ya kura mini ido, idanunsa da suke daidai da kwayar idona suka sanya na ji wani irin mugun tausayinsa. "Domin ba na son kowa ya shiga tsakaninmu. Ke tawa ce ni kaɗai, Nana. Idan kika bari waɗancan kawayen naki da 'yan uwanki suka ci gaba da shigo miki da ra'ayoyinsu, za su lalata mana wannan kyakkyawar rayuwar da muke yi." Na gyaɗa kai, hawaye na wanke fuskata na ce.  "Na gane Hon. Nagode da kake kare ni, nagode da kake nuna mini gaskiya." "Yauwa Nana. Don haka, tunda yanzu babu layin a wayar, babu wani abu da zai dinga raba miki hankali. Ina so ki maida hankalinki gaba daya a kaina da kuma wannan gidan. Kuma ina so yau ki goge sauran kayan da suka rage." Ya sumbaci tafin hannuna, wanda har yanzu yake zugi saboda kunar jiya da kuma takewar da ya yi mini ɗazo. Amma kalaman sa sun sanya na manta da raɗaɗin. Na gyada masa kai cikin sauri na ce.  "Yanzu yanzu ma, kana fita zan ƙarasa." "Tashi ki je ki soma, ni kuma zan karya da kaina." Na miƙe ina jin kamar an dora mini wani sabon nauyi, amma nauyin da nake ganinsa a matsayin Ladan Bautar Aure, da kuma tukwici ga soyayyar da ake nuna mini. Kai tsaye na shige ɗakinsa na fito da ragowar kayan gaba ɗaya.  Ina tsaka da guguwar bayan fitar sardauna naji ana sallama, gabana har faɗuwa yake yayin da na tashi zuwa buɗe kofar. Ra'is!  "Ra'is lafiya?."  Na faɗa baki na yana rawa, ya kalleni cike da bacin rai, sannan ya ce.  "Alhaji bashi da lafiya, ya ce yana son ganinki, yana son magana dake amma kin ƙi, Yaya ta kira ki a waya kin ƙi ɗauka, anyi miki test message akan baba yana cikin halin jinya, amma kin gani baki ce komai ba, yanzu da safe an kiraki ma wayar akashe, sai kuma yanzu kika yi message a wayar mijinki kika wai ke ma baki da lafiya. Nana me yake damunki ne? Dan kinyi aure a gidan hali shine kika tsani 'yan uwanki?."  Tun da Ra'is yake magana ƙirjina yake bugawa, duk wata kalma da yake faɗa guda daya tamkar ana doramin dutse a kirjina ne, fuskata cike da hawaye na ce.  "Wallahi Ra'is ba haka ba ne, bansan Baba bashi da lafiya ba, kuma Sar...."  "Ta ina zaki san ba shi da lafiya, kin zaɓi miji mai abun duniya akan 'yan uwanki da iyayenki, wallahi Nana kin bawa kowa kunya ciki hardani, wahala da Alhaji da Hajiya suka sha akan aurenki basu sha ta akan kowa ba, Nana kinsan tunda kika ajiye karatun da Alhaji ya ci buri akanki bai ƙara lafiya ba. Wallahi Nana daba dan Baba ya takura ba babu abinda zai kawo ni gidanki babu shi, kuma idan kinga dama ki je ki ganshi idan baki ga dama ba kar ki zo, amma ki kwana da sanin duk wani abu da yasami mahaifinmu ba zamu taɓa yafe miki ba."  Yana faɗin haka ya juya zai tafi, cikin muryar kuka na ce.  "Ra'is! Dan Allah tsaya."  Tsayawa ya yi ba tare da ya juyo ba, na tako inda yake sannan na ce.  "Dan Allah kira mini Alhajin, na yi magana da shi dan Allah."  Kallona ya yi sannan ya ce.  "Ki yi magana dashi? Kina nufin bazaki zo ba?."  "A'a Ra'is zan zo, amma dan Allah na fara jin muryarsa kafin nazo."  Murmushin takaici Ra'is ya yi sannan ya sa hannu a aljihu ya zaro wayarsa, ya danna kiran sannan ya miƙo mini. Hannuna har rawa yake yayin da na amshi wayar, ana ɗagawa na fara magana.  "Ba..Baba!"  Na fada, daga can bangaren Yaya Radiya ta ce.  "Bara a miƙa masa."  "Yaya ki yi hakuri, wallahi bansan komai ba akai, wayar ta hannun Mijina."  "Mijinki kuma? Amma saƙon da kika turu dazu ai kece kika rubuta."  Yaya Radiya ta fada, ban kai ga bata amsa ba ta sake cewa.  "Ga Alhajin."  "Alhaji ina kwana, Ya jikin naka?."  Na faɗa cikin rawar murya.  "Rawasiya kina lafiya?."  Ya tambaya muryarshi cike da alamun rashin lafiya, wani abu ya tsaya min a rai, yana cikin halin rashin lafiya amma tambaya ta yake ina lafiya? Ina son Sardauna sosai, amma tabbas bai kai ko rabin soyayyar da nake yi wa Alhaji ba.  "Alhaji lafiya kalau, ya jikin naka?"  "Nana yaushe zaki zo?" "Baba anjima zan zo, yana dawowa zan faɗa masa ko da daddare ne sai nazo, ko gobe da safe."  "Toh shikenan! Ubangiji Ya yi miki albarka."  "Amin Baba, Allah Ya baka lafiya."  "Amin amin Nana."  Ya faɗa yana mikawa Yaya Radiya wayar.  "Nana ki samu ki shigo dan Allah."  Yaya Radiya ta fada, duk jikina ya yi sanyi na ce.  "In sha Allah Yaya." Daga nan na katse kiran na bawa Ra'is wayarsa, ya kaɗa kai zai tafi.  "Ra'is, baka shigo ba! Baka sha ko ruwa ba."  Murmushi ya yi sannan ya ce.  "A'a ba komai, zan wuce kawai sai kinzo."  Yana faɗin haka ya fice, ni kuma na koma ɗaki na zauna kan kujera, kamar wacca aka haskawa majigi haka rayuwata ta baya ta shiga tariyo wa a idanuna.  ****** Asalin labarina.  Da farko sunana Rawasiya Alqasim Babuga wacca kowa ya sani da Nana, sunan da na zaɓawa kaina kenan, tun ta sowa ta ni macece marar son hananiya ko kaɗan, bana son abun da zai dame ni a rayuwa ko ya ne, abun da nasa a gabana shi nake yi, shi nake so.  Mahaifina Alhaji Alqasim sannanne a anguwarmu dama gari gaba daya, kasancewarsa dan siyasa mai aƙidar riƙau. Sannan ɗan kwangila ne da yake da kamfaninsa wanda yake karbar ayyukan daga 'yan siyasa da ma sauran mutanen gari. Mahafiyyata Sailuba haifaffiyar jihar Adamawa yola ce, irin kyawawan fulanin nan ne na Yola, a lokacin da mahaifina yake tashin aikin kwangila da kuma siyasarsa Allah Ya haɗashi da ita, bayan shimfiɗa kyakyawar soyayya kuma suka yi aure, inda mahaifina ya dawo da ita unguwar Federal Low-cost dake dutsen jihar jigawa. Unguwa mai kyau da daɗin zama, unguwar da ta kasance ta masu matsakaicin hali, akwai manyan gidaje da kuma ƙananan, akwai hadaƙar masu kuɗi da talakawa.  Zaman tsarkakkiyar soyayya ya ginu tsakanin Mammanmu da Abbanmu da muke kira da Alhaji da Hajiya, tun haihuwarsu ta farko Alhaji ya zo da wani tsari, babbar Yayarmu sunanta Radiya, bayan yan shekaru aka sake haifi wata aka saka mata Rumaisa, bayan ita kuma sai namiji da aka sa masa Ridwan, a lokacin Alhajinmu yana tsaka da siyasa da samun kudi ya dauƙesu gaba ɗaya suka sauke farali, a lokacin ina ciki sai bayan sun dawo da aka haifeni inda aka samin Rawasiya, ban kai shekara ba dukkanmu Alhaji ya kwashe mu zuwa aikin Hajji, wanda bayan dawowarmu daga aikin Hajji karyar arziki ta sami mahaifina.  A lokacin ina da wata goma sha ɗaya a duniya, wannan lamarin ya afku, inda mahaifina da alhalina suka shiga matsanancin tashin hankali na rayuwa, duk arzikin mahaifina ya kare a yadda nasamu labari wani lokacin gidanmu suna iya kwana ba tare da suncu abinci ba, ana haka mahaifiyata ta shawaraci Alhaji da ya sayar da gidansa na Federal low-cost ya nemi wani karamin mu koma can ragowar kudin ya sa su a kasuwa, haka kuwa aka yi mahaifina ya siyar da gidansa na Federal Low-cost ya nemi matsakaicin gida a unguwar Yelwawa, inda suka dawo nan, gida mai dauke da dakuna uku, Na Alhaji (Baba) daban, na Hajiya (Umma) daban, Yaya Radiya da Yaya Rumaisa daya, shi kuma Yaya Ridwan tun da shine karami yana kwana dakin Hajiya, ni kuma ina karama.  Daga Amana Academy makaranta mai zaman kanta aka dawo da yan gidanmu zuwa Government Day School Yelwawa, canji rayuwa ya yi wa gidanmu ƙawanya, ni kam basan duk dadin da aka sha ba lokacin da Alhaji yake Alhaji bare nasan yadda aka shiga lokacin da ya dawo Hajijiya, wannan ya sanya Alhaji yake matukar so da tausayina, kasancewar gatan da yayuna suka samu a lokacin da suke kamar ni bansame shi ba, Alhaji ya fara zuwa kasuwar Laraba da take ci Mako Mako yana siyar da kayan abinci, sauran ranakun kuma yake zama a shagon da ya bude shima na awon kayan abinci a gida. Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na huɗu     (04) Shekarata uku a duniya, Hajiya ta sake samun ciki wanda shine cikin autanmu Ra’is a zuwa wannan lokacin Alhaji ya fara samun rufin asiri, duk wani ci da suttura na masu rufin asiri baya gagararmu, haka karatu babu wanda bamayi, na zamani da na addini, bayan haihuwar Ra’is sai Alhaji Yasa aka shigo da shagon waje zuwa cikin gida, bayan ya sami wani babban shago a bakin titi, tabbas ance haihuwar Ra’is ta zo da alheri sosai domin akwai wasu cikin yaran da Alhaji yake biyawa kudin karatu da ‘yan buƙatun rayuwa lokacin da yake amsa sunan Alhaji, wani cikinsu mai suna Isah Nadabo da ya zama babban mutum shine ya siyawa Alhaji Shagon a bakin titi, bayan ya cika masa shi da kayan siyarwa, sannan wani kuma ya cika mana gida da kayan abinci.  Tun daga lokacin haihuwar Ra’is bamu sake zama da rashi ba a gidan, muna zaune cikin rufin asirin ubangiji, haka kuma muna samun tsayayyiyar tarbiya daga wajen mahaifiyarmu Hajiya, domin Hajiya macece mai tsayawa kan tarbiyar yara. A bangaren kyau, dukkanmu irin kyawunta mu ka yi mussaman mu matan da mu ka yi har farinta, Yaya Ridwan da Ra’is da suka dan dakko duhun Alhaji, sai suka fi mu kyau ma, sabida ba suyi duhu dilik ba, sannan ba suyi haske fatau ba, sun yi black beauty ne, ko na ce Brown, ga sumarsu irin ta fulani, wacca duk muka ɗebo daga Hajiya, dan mu matan ma babu wacca gashinta bai kai gadon baya ba, kasancewar nafi su Yaya Rumaisa ƙanƙanta sai akafi ganin kyawuna akansu, kuma ni kaɗai ce na yo dara dara idanu irin na Alhaji, shi ya sa aka fi ganin kyawuna akansu. Sai da fa duk gidan kowa ya kwana da sanin cewa Yaya Ridwan yafi kowa kyau dan shi kama yake da larabawan Dubai. Yaya Radiya tana da matuƙar sauƙin kai, hakuri da kawar da kai akan abu, saɓanin Yaya Rumaisa Al-jarabatu, sunan da kowa ke kiranta dashi, bata neman sauki a rayuwatar ko kaɗan, rigima bata ta ba sai ta shiga ta yi kane kane, sai ka rantse ta tace. Yaya Ridwan kam, ɗan kurma dinfa kenan. Babu ruwanshi da abunda ba a sashi ba, wanda aka sa shi mai sai ya yi kamar bai ji ba, sai ya yini a gidan amma bai ce da kowa ƙala ba, ko abokai ba shi da su kullum yana cikin daki, sai ya yini a daki bai fito ba idan ba massallaci ba. Ni kuma ina cikin wasu nauyin mutane da ba agane kansu, idan naso zanyi surutu sai na addabi kowa, idan kuwa banso ba buɗe baki ma wahala yake mini, duk da cewa inda hakuri da kawar da kai, surutun nawa ma sai da ‘yan gidanmu nake yi idan na ga damar, abun da ba asani ba dai bazan shiga ba, sannan kwata kwata ba na cikin nau’in mutane marasa kunya, sannan duk abinda naga zai wahalal dani ina yi tattarashi gefe na watsar ko na tattara rayuwata na yi gaba. Haka ma Ra’is bai da hayaniya shima ko kaɗan duk cikinmu dai Yaya Rumaisa ce ta fita zakka, dan idan taso jarabarta kowa sai ya kula ta, Yaya Ridwan ne kawai ba ya kulata.  Kasancewar sunana Rawasiya yasa ‘yan makarantar daren mu suke tsokanta, yau su ce Rawasiya, gobe Gabashiya, jibi har shamiƙantun sai su ce min, gaba daya na zama abar tsokana a unguwar, shi ya sa na tattara sunan na watsar na koma Nana, indai aka ce dani Rawasiya to a gidane ko ‘yan uwa. Lokacin da na shiga FUD STAFF SCHOOL J S 1, idan ‘yan ajinmu suka ji suna yayuna sai su yi ta tambayata me ya sa sunana bai fara daga Ra ba, amma na yayuna duka Ra, kasancewar dukkanmu muka shiga makatantar, Yaya Radiya da Rumaisa suna J s 3, Ridwan J s 2, ni kuma J s 1, Ra’is ne kawai babu, sai na ce musu ni ba ‘yar gidan ba ce. Wata rana da Yaya Rumaisa ta zo ajinnu ta ce da ni Rawasiya nan ‘yan ajin suka ɗauka Rawasiya shamiƙatin, amma da yake ban bada fuska ba akan sunan sai Nana yafi zama a bakin nasu. Sanda muka shiga Aji na biyu lokacin su Yaya Radiya sun shiga Siniya, a lokacin Yaya Ridwan ne kawai, ‘yan matan makaranta tin daga ‘yan ajinmu har na ajinsu kowacce sai ta zo ta ce dani tana son Yayana, kaf makarantar yafi kowa yawan masoya, ga halinshi na rashin son magana ya kara ja masa farin jini a makarantar. Lokacin da zan shiga Siniya ne lokacin da muka yi saukar Al-kur’ani ni da Yaya Radiya, Yaya Rumaisa, Yaya Ridwan, ban da Ra’is sabida mun yi masa nisa sosai a karatu mussaman na addini.  Alhaji yana da burin mu yi karatu me zurfi, amma Allah bai nufi hakan ba, domin yaya Radiya tana shiga Aji 3 na babbar sakandire, Yaya Hadi dan gidan babbar yayarsu Alhaji ya ce yana son aurenta, babu yadda Alhaji ya iya haka ya sa ya aminta, sabida bai isa ya tunkari Hajjansa da maganar yana so ta yi karatu ba, ko da wani ne a waje ya ce yana sonta bare kuma Yaya Hadi jikan da tafi so a rayuwarta.  Tabbas Hajjansu Alhaji macece mai mugun son zuciya da sabon abun duniya, an ce sanda Alhaji yana da arziki babu wanda take so sama da shi, amma tun da ya sami karayar arziki ta watsar dashi da iyalansa, ta kama wanda yake da shi, gashi ba ta wani cika son Hajiyarmu ba, har wani suna take kiranta dashi wai Fulanin tashi ko Fulanin jeji ne, ni ban wani sani ba, tun da ba cika shiga sha’aninta na yi ba, domin nida Ra’is ta tsanemu har ce mana take masu farar ƙafa wai mune muka yi sanadiyar talaucewar ɗanta, wani lokacin ma ta ce ubanmu idan tana jin tsiyarta.  Shi ya sa ma mu a famili mu ka zama ware, muna gefe sai ayi abubuwa nawa ba muje ba, wani ma bamu sani ba, wani ko mun sani ba zama bu, da idan ba muje ba Hajiya na ta kura mana daga baya kuma ta kyalemu, tunda da zuwan da rashin zuwan ba tsira zamuyi da zagi ba, har gwanda bamu je ba ma zagin a bayan idanun mu ne.  Allah Ya haɗa jini Yaya Hadi Yaya Radiya tun da ita ma tana son abunta, ita ma Yaya Rumaisa ana haka saurayinta mai sunan Alhaji ya fito, ita ta turoshi ba ita ta turoshi ba Allah masani, dan da ya ce sai ta gama karatu amma rana tsaka ya sake maganar, hakan ya sa Alhaji ya amince zai aurar dasu tare da dora burinsa a kaina, ko ba komai ina da karancin shekaru a lokacin.  Ba mu dade da yin biki sauka ba aka sanya ranar aurensu duka su biyun, dan Hajja ta ce babu amfanin karatun da zasu yi. Haka ya sa aka sanya auren nasu, sai dai duk wannan baloƙoƙon da ta yi da aka tashi bikin babu kobo da ta bayar duk Alhaji ne da kudinsa ya yi, sai kuma yaransa da yake tare da shi Isah Nadabo har wannan lokacin, wanda ya siya maa shago a bakin titi ya cika masa shi da kaya, shine ya dauki nauyin yin kayan daki na duka su biyun.  Haka aka zo lokacin biki Alhaji da Hajiya sunyi hidima dai gwargwado, hidimar da babu wanda ya yi tunanin zasu iya irinta, dan bayan angama biki ma sai da Hajja ta kira Alhaji ta ce wai aina ya sami kudi, sai ya ce da ita ‘yan uwan Hajiya ne suka yi, maimakon ta gode musu ko ta yaba musu sai ta hau aibatasu, wai basu dauke ta da daraja ba da bazasu kawo gudumawa wajenta ba sai dai su ba wa ‘yarsu, abu kamar wasa sa ga Hajjan a gidanmu ta zo ta yi wa Hajiya tas, sannan kuma wai tafito da ragowar gudumawar sai dai Hajiya ta ce jiya ta haɗe komai anyiwa Yaya da Radiya da Rumaisa gara an kai musu, abu kamar shafar iska sai ga Hajja a gidan Yaya Rumaisa ba ta je gidan Yaya Radiya ba sabida tasan jikanta ne zai ci komai, sa ta je gidan Yaya Rumaisa, haka ta dinga jidar kayan garar abun haushi a gaban dangin mijin Yaya Rumaisa, har da kukanta sai sune suka rarrashe ta bayan Hajjan ta tafi.  A da Alhaji baya ɓoyewa Hajja komai amma yau da gobe tafi karfin wasa, a hankali ya gane Hajja ba ta yi dashi dan ba zai ce ba ta kaunarsa ba tun da babu uwar da zata haifi ɗa ta ce ba ta son shi, shi ya sa ya boye mata Isah Nadabo, mutumin da ya taimaka masa wanda ya rike amana ya dawo yana sakawa Alhaji da fin abinda ya yi masa, dan tsaf Hajja zata sa shi a gaba yakirashi ta kuma sa shi ya bata maƙudan kudaden da ba lallai gobe ya sake tun karar Alhaji, kuma ta dinga iƙirarin tsine masa idan yaƙi, a haka ma duk sati sai ta aika an amsar mata shinkafa da wake har dasu mai da maggi da kudi a shagon nasa, wani lokacin ma sai ta zo da kanta tai ta jidar indomi da madara, wani abun ma bata san shi ba kawai mugun hali ne, dan akwai lokacin da ta dauki Izel na wanke bandaki ta tafi dashi ta dauka abun sha ne ta sha, dakyar ta miƙe dan ta yi jinyar wajem wata biyu, maimakon ta yi hankali sai ta ce ita yanzu ta fara. Haka take rufe ido ta yi ta jidar kaya duk sanda tazo, akwai ma lokacin da ta fado daga kan kanta, dake shagon akewaye yake anyi gini tsakanin inda  kayan suke da inda mutane zasu tsaya, sai da fridge da kayan ruwa sune daga waje, shagon yana da girma da fadi, to garin haurowa ta tsallaka ciki ne ta dawo kasa ta fadi, nan ma sai da ta yi jinya, amma dake matar nan babu Allah a ranta sai ta ci gaba da zuwa. A kullum burina shine na yi karatu mai zurfi, na zama wata ko da a iya Dutse ne, na taimaki iyayena da ‘yan uwana, ina son ganin na yi wa Alhaji wani abu da zai ji dadinshi a rayuwa, mahaifina da mahaifiyata suna da buri akaina na ganin cewa na yi karatun boko mai zurfi, kuma ni kaina haka sabida na fahimci idan banyi karatu mai zurfi ba, babu inda zani.  Haka rayuwa take ta tafiya, yau fari gobe baƙi. Yayuna suna gidan aurensu kuma kowacce babu abinda zamu ce da Allah sai godiya, dan kowacce da ka ganta zaka san tana cikin rufin asiri, a hankali rayuwa tana gangarawa inan da burin na karatu mai zurfi, sai dai bansan me kaddara ta tsara mini ba. 09:30pm.  Zaune muke a tsakar gida ana dan taɓa hira, ni da Hajiya da Ra’is, ko na ce Hajiya da Ra’is da ni da ido kawai nake binsu, bansan me ke damauna ba amma gaba ɗaya tun yamma banajin daɗi, gaba ɗaya ji na nake wata sukuku. Yaya Ridwan kam yana can daki yana faman game, dan yanzu game ya siya da ake yi a tv da wani abu na rikewa a hannu wai shi Handle, in ji Ra’is.  Alhaji ya shigo bakinsa dauke da sallama, da sauri na miƙe ina faɗin.  “Sannu da zuwa, babanmu.”  Ya sakar mini murmushi sannan ya ce.  “Yawwa.”  Bayan ya zauna ne Ra’is da Hajiya suka yi masa sannu da zuwa, Hajiya ta miƙe ɗakko masa abinci, Ra’is da Hajiya Aminan juna ne, ko da yaushe tare zaki gansu, dan Ra’is ina ga ko a waje baida wasu abokan kirki, kullum suna zaune da Hajiyya hirar su ba ta ƙarewa, karasa me suke cewa, yanzun ma tare suka nufi kitchen din ɗauko ma Alhaji abinci.  Bayan Alhaji ya gama cin abincine ya ce.  “Rawasiya ga saƙonki.”  Ya faɗa yana miƙamin leda, nasan saƙon bai wuce maset da kalkuketa ba, dan su na ce masa ina so ɗazu da safe, sai kuma biskit na makarantar gobe, kafin na gama buɗewa Ra’is ya ce.  “Hajiya nima ina so littafi nawa sun cika, sannan rulata ta karye.”  Dariya na yi masa sannan na ce.  “Ai Hajiya ba ta da shago.”  “Barshi dai ya faɗa mata, ina ga kantin zata bini ta karɓa masa.”  Alhaji ya faɗa, Hajiya kuma ta ce.  “Ina ni ina binka kanti, kawai dai a kawo masa.”  “Wannan ya yi bacci ne?”  Alhaji ya faɗa yana nuna ɗakinsu Ya Ridwan.  “Yana ciki yana faman sana’ar.”  Hajiya ta faɗa, sannan ta ƙara da cewa.  “Wai ni kuwa Alhaji yaushe yaron nan zai fara zaman kantin nan ne? Ya kamata ya fara rage ma wasu abubuwan da wannan zaman asarar da yake.” Murmushi Alhaji ya yi sannan ya ce.  “Yaron da yake shirin shiga jami’a, ina yake da lokacin zaman kanti?” “Ni kuwa ansama masa Addmision din ne? Bai ma faɗan yadda suka yi da bawan Allah nan ba.”  Hajiya ta faɗa sai da Ahaji ya sha ruwa sannan ya ce.  “Ai Isah Nadabon ma ya zo waje na ɗazu, har yake yi mini maganar ita Rawasiya.”  Da sauri na katseshi da cewa. “Alhaji Nana dai.”  Banza ya yi dani ya ci gaba da cewa.  “Yana tambaya wai aure zata yi itama ko sai ta yi karatu, na ce dashi sai ta yi karatu, to wai da ya nuna sha’awar shi ne akan yana son aurenta, sabida ya na son ya yi tafiya ta shekara biyu kuma shi kanshi zaifi son ace ya tafi tare da iyali ne.” Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na biyar     (05) Tunda Alhaji ya fara magana gabana yake faduwa, aure kuma? Ni ba auren ba ma wallahi kwata kwata bana son mutum ya girmeni sosai, gaba daya shekara ta sha bakwai, Isah Nadabo a yanzu ya kai wajen talatin, ni nafi son yaro dan shawalwali, wanda baifi 26 ba haka, maganar Hajiya ce ta katse min tunanin da na shiga da na tana cewa.  "To Alhaji kamar Isah Nadabo ai yafi ƙarfin haka a wajenmu ko, da an bashi."  "Kai Hajiya!"  Na faɗa a raina, Alhaji ne ya ce da ita. "A'a dai, ai bama za ayi haka ba ita yarinyar ba ta da zaɓi ne?"  "Ai shikenan dai, Allah Ya bata na gari."  Alhaji ya ce. "Amin." Ni dai nan zaune bance ko ƙala ba, amma naji dadi gaskiyya, na auri Isah Nadabo na ce na auri wa, ƙanin babane ko me? Babba dashi da ace ya yi aure a shekara goma sha wani abun da yanzu yana da yarinya kamar ni, kowacce ta girmi ni ma. Gashi wani baki ma, ni Allah Ya gani ina son dan gayu dan zamani, shi kam kallo daya zaki yi ma Isah Nadabo kinsan mutum ne mara walwala, kansa a kulle yake.  Daga wannan rana ba a sake wata magana da ta shafi Isah Nadabo ba, kuma nima na ji daɗin haka, haka na ci gaba da rayuwa ina 'yan matancina a gida har zuwa ranar da ƙaddarar Yallaɓaina ta faɗa mini.  Ranar wata lahadi bayan sallar magariba na fito daga gida ina shirin tafiya makarantar dare da nake zuwa, wacca gaba daya banfi a sati biyu da fara zuwanta ba. Tafiya nake kamar ko yaushe cikin nutsuwa,kamar ance ɗaga idonki.  Kyakyawan matashin saurayi, mai kyakyawan yanayi da kyakyawar shiga, fuskarsa fara ce sosai yana da tarin kwantacciyar suma. Gaba ɗaya kammaninsa ba sa yanayi da na 'yan nigeria sabida yanayin idonsa har wani walƙiya suke mai daukan ido, hancinshi mai matsakaicin tsini haka bakinsa, wani kyakyawan gashin baki ya yi masa ƙawayan ya gangaro gefe da gefe ya haɗe da ɗan ƙaramin gemunsa.  "Ya Hayyu Ya Qayyum!"  Abinda na faɗa a raina, sannan na ce. "Wasu kamar sune suka hallicci kansu, sabida tsabar tsagwaran kyau, ina ganin Yaya Ridwan yafi kowa kyau ashe mummunane a gaban wannan."  A hankali ya fara ta kawo yana tun karo ni, wani irin "Dif! Dif!" Na ji ƙirjina yana bugawa, ƙafafuna suka fara karkarwa, ƙwalla ta taro a idona sakamakon matsanancin bugun da zuciyata take mai ƙarfi. A lokacin da ya matso gab da ni, sai da na ji numfashina ya ɗauke na daƙiƙa. "Salamu alaikum."  Wata sassanyar murya mai yanayi da busar sarewa ta shiga kunnena, bayan sassanya ƙamshin turarensa ya cika min rayuwa gaba ɗaya.   "Ina wuni?."  Na tsinci kaina da faɗa har da durƙusawa, ya yi murmushi sannan ya ce.   "Gidan can zan aiki ki."  Ya faɗa yana nuna min gida dake kallon namu, na juya na kalli gidan sannaan na ce.  "Toh!"  "Nan ne gidan Alhaji Hadi ko?" Ya tambaya, ni kuwa jikina har ɓari yake amsa tare da gyaɗa kai.  "Eyh! Nan ne."  "Ki shiga ki ji yana nan? Idan yana nan ki ce masa Fahad Ta'ambo ne, wanda su ka zauna tare a jirgi daga Dubai zuwa Nigeriya, ya yi mantuwar ne a cikin jakata shine na zo kawo masa."  Tun da ya fara magana gabana yake faɗuwa har ya ƙarashe. Yana gamawa kamar wacca aka umarta na fara tafiya, ban tsaya ba sai da na shiga gidan, bayan na isar da saƙon Alhaji Hadi ya ce dani yana zuwa, na dawo na faɗa masa ya yi min godiya, amma maimakon na kama hanyar makarantar sai na dawo gida, gaba daya ji na nake wani sukuku, unguwar ta yi min faɗi, ƙamshi turarensa ne ka dai yake yawo a kwanyar kaina, sai kuma maganarsa tun daga farko hat karshe, ban manta ko kalma daya ba.  "Ki shiga ki ji yana nan? Idan yana nan ki ce masa Fahad Ta'ambo ne, wanda su ka zauna tare a jirgi daga Dubai zuwa Nigeriya, ya yi mantuwar ne a cikin jakata shine na zo kawo masa."  Abinda na fada kenan da safe bayan na buɗe idona, da sauri na daki kaina tare da faɗin.  "Rawasiya wake-up, me yake damunki ne haka?"  Miƙewa na yi tare da nufar banɗaki na wanke baki na na fito zuwa tsakar gida, sai da ƙamshin turarensa har yanzu yana yawo a hancin na,  yanayin da na ji jiya yana nan kamar yanzu yazo unguwar.  Haka kwana daya ya wuce ina jin wannan yanayin a tare da ni, kwana na biyu ya wuce, sai da na yi sati sannan na ji yanayin ya fara raguwa, sai da na ɗau tsawon wata guda ina fama, kafin manta amma kuma har lokacin kammaninsa da sunan sa suna nan a kwakwalwata, domin a kallo daya kwakwalwata ta dauƙi hoton sa, wanda ya tsaya a a zuciya. Ranar da Allah Ya nufa zan sake ganinsa ranar wata laraba da yamma, lokacin Hajiya ta aiki ni gidan wata ƙawarta a fagoji, banson zuwa fagoji kwata kwata, ni ba ma fagoji ba gaba daya ban fiya son zuwa wani waje nesa ko kusa ba. Daidai bakin titin Rasheed shekoni special hospital mashin din da nake kai  ya tsaya, me mashin ɗin ya tsaya yana duba mashin ɗin ni kuma na sauka ina jiranshi.   A jiki na naji ido na yawo a kaina baya ga matsananciyar faduwar gaba da naji. Ina kai idona bakin asibitin na ganshi tsaye ya harɗe hannusa a ka faɗa yana kallona. Da sauri na sunkuyar da kaina ƙasa ina faɗin.  "Wayyo Allah."  Dan wani irin ƙarfaffan bugu zuciyata ta yi lokacin da muka haɗa ido dashi.  "Sannunki."  Na ji muryarsa dab da ni sai dai na kasa ɗagowa, idanuna suka kai kan ƙafarsa, takalminsa ma kaɗai abun tsayawa a kalla ne.  "Kamar ke ce ta unguwarsu Alhaji Hadi ko?"  Da sauri na gyaɗa kai, tare da faɗin.  "Eyh! Ni ce."  "Lol, me kike yi anan?"  "Mashin ne ya sami matsala, amma gashinan ya gama dubawa."  Ya kalli mashin din sannan ya kalli ni.  "Kuma a wancan unguwar kike?"  Ya faɗa yana baya da hannu alamun can. Na gyaɗa kai tare da cewa.  "Eyh! Yalwawa."  "Uhm! I see."  Ya faɗa yana shafa gashin bakinsa daga tsakiya zuwa gefe sannan ya ja shi zuwa ƙasa.  "Mu tafi ko?"  Mai mashin ɗin ya faɗa, na juya zan hau mashin ɗin sai na ji ya ce.  "Na ce ki tafi?"  Ba shiri na tsaya kaina a ƙasa.  "You're eager to go, kin gaji ko?" Ya faɗa cikin wani irin yanayi na fushi, da sauri na girgiza kai sannan na ce.  "A'a, bangaji ba.... Me mashin ɗin."  Kallon me masahin ɗin ya yi sannan ya ce.  "Malam ka jira."  "Alhaji sana'a fa nake, idan na ajiyeta wasu zan ɗauka."  Hannu Ya sa a aljihu ya zari kuɗi 'yan dubu dubu da a ƙalla sun kai guda goma ko sha, ya miƙa masa. Ba shiri me mashin ɗin ya amsa tare da matsawa gefe ya zauna, a raina na ce.  'Yanzu mu dai babu yaren da muke ganewa sai na kuɗi."  "So ba zaki tambayi sunana ba?."  Ya faɗa yana kafe ni da idanun da nake jin su tamkar na zaki sabida kaifi.  "Ka yi hakuri ai naga ranan ka faɗa min."  "Ni... when?"  "Da ka ce na cewa Alhaji Hadi Fahad Ta'ambo ne."  Shiru ya yi yana kallona na kusan minti biyar sannan ya ce.  "So kin ma riƙe sunana, shine da kika ganni kika yi kamar baki sanni ba ko? Na gode."  "Ba haka ba ne, ban kula da kai ba."  Na faɗa murya ƙasa ƙasa.  "Amma ni na kula da ke?"  "Ka yi haƙuri."  "It's fine, you can go. Na gode."  Shiru kamar an shuka ni a wajen na kasa matsawa.  "You can go fa."  "Ka yi haƙuri."  "Kije kawai."  Ya faɗa yana barin wajen, sai da ya shiga cikin motarsa sannan na iya matsawa zuwa ga mai mashin ɗin, ya ɗauke ni muka ci gaba da tafiya.  Gaba ɗaya hankali na ba yaga hanya, na tafi tunanin wannan mutumin, komai na shi burgeni yake, ya iya magana. Amma abinda ya bani mamaki shine kwata kwata banji ya tambaye ni sunana ba, ko da yake mene alaƙarshi da sunana da zai tambaya, kamar daga sama na ji ana cewa.  "Mun kusa wuce jakshon ɗin fa."  Na kalli me mashin ɗin na kalli hanya, sannan na ce.  "Wannan layin zaka shiga."  ******** 08:30pm Kamar wancan lokacin na farko da na haɗu da Fahad Ta'ambo na kasa mantawa da komai na shi, to yau ma haka. Tun dawowa ta na ƙure a ɗaki ina zaune ni kaɗai ina maimaita duk wata kalma guda ɗaya da ya faɗa a cikin zuciyata.  Hajiya ce ta leƙo tare da faɗin.  "Rawasiya me kike yi a ɗaki ne, bazaki ci abinci ba ne?"  "A'a Hajiya na ci acan, duk gjiya ce wallahi ke ci na."  "Mene abin gajiya a zuwa Fagoji? Sai ka ce yau kika fara?"  "Bazaki gane ba Hajiya."  Na faɗa ina juya baya.  "Eyh, bazan gane wannan karatun sangartarba."  Ta faɗa tare da ficewa, ni dai daren nan haka na ƙarar dashi a ɗaki ina ta hango kammanin kyakyawan matashi Fahad Ta'ambo.  Washe gari ma dai da mafarkin kyakyawar fuskarsa na tashi, ni dai ban taɓa soyayya ba, amma nasan yanayin da nake ji game da Fahad na san yanayi ne na soyayya. A gurguje na yi shirin makaranta na fito tsakar gida na ɗauki abin kari na na yi, bayan na karya na amshi kuɗin makaranta wajen Alhaji na nufi makaranta.  FUD STAFF SCHOOL 11:30am.  Tun da aka fita break ban matsa ko ina ba daga kan bencina, duk ƙawayena su Fauziya Tasi'u su Malaika sun fita sun dawo amma sun tarar dani anan zaune. Malika safwan ce ta zauna kusa dani tana faɗin.  "Nana meke dumunki ne haka? Tun ɗazu kina zaune sai faman murmushi kike?"  "Murmushi?" Na faɗa da alamun tambaya.  "Au baki ma san kina murnushin ba, sai dake malamar soyayya."  Ta faɗa tana dariya, na kalleta na ga yanayin ta ko a jikinta, daman Malika irin wayayyun 'ya'yan nan ne, dan a yanzu haka ma tana da saurayi abunta, idan anyi magana sai ta ce 'idan basu yi min aure ba, jiƙani zasu yi su sha?.' A yanzu haka har cikin Malamai tana da saurayi, sabida wayewarta ma Malaika Arora ake ce ma ta.  "Ni Malaika ban faɗa wata soyayya ba."  Na faɗa bakina yana rawa, kallona ta yi sannan ta ce.  "Mai da karuwa 'yar iska."  Tana faɗin haka ta juya ta shiga sabgoginta ta barni da faman tunani.  "Ya zaayi ace na faɗa soyayya, faɗawar da har wani zai iya ganewa, ko da yake a wayewa da gogewa irinta Malika ba abun mamaki ba ne dan tasan haka, amma ta ya zaayi na fara soyayya da mutumin da ko sunana bai ta ɓa tambaya."  Haka na yini sukuku, har washe gari ma hakan, sai da aka sake ɗaukan sati ina cikin wannan yanayin kafin na ji na dawo daidai, sai dai a cikin wannan satin fa duk ƙawaye na sun yarda da maganar Malaika kan na faɗa soyayya. Ni kam tsakanina dasu sai da ido, daga baya ne ma na fara biye musu har wata rana suka ce wai sai na zayyane musu kammanin mutumin, da na rufe idona kawai sai na ganshi ya harɗe hannu yana kallona.  Duk yadda na kai ga gaya musu cewar yadda na fasalta musu shi, haka yake a gaske sun ƙi yarda, dan daga masu cewa jaruman indiya nake fasaltawa, sai mai cewa larabawan Dubai ne, ni kam daga ranar ban sake biye musu ba.  A lissafina ranar da na cika kwana goma da haɗuwa da Fahad Ta'ambo na sake ganinsa, sai dai abun da ya yi matuƙar bani mamaki shine inda na gansa, daga can gaban gate ɗin makarantarmu, da sauri na juya baya sai dai naga idanun ƙawaye na akansa. Fauziya ta yi saurin matsowa kusa dani sannan ta ce.  "Ke Rawasiya! Wannan ai shine sak mutumin da kika fasalta mana, ko shine?"  Na gyaɗa mata kai, gaba ɗaya na rasa nutsuwa ta, kamar ko da yaushe. Da zarar ya ɗor ƙawayar idonsa a kaina, shikenan na rasa nutsuwata.  "Gaskiyya ƙarya kike Rawasiya."  Mailaka ta faɗa a saitin kunnena.  "Kina ganin yadda yake kollonta, zaki ce ƙarya ne."  Amina Aminu ta faɗa..  "Wannan ai yafi ƙarfinki Rawasiya, bama haɗi wallahi." Na ji muryar Malika ta faɗa, a take Amina Aminu ta cafe da cewa.  "Ni ban ma yarda ba, gashi dai gani nake da idona, amma na kasa gasgatawa."  "Kinsan kuwa wane ne Fahad Ta'ambo?"  Malaika ta faɗa, daidai kuma lokacin ya fara takawo kusa da mu, ni kam gaba ɗaya sai na ji maganganunsu sun tsayan a raina, ni kaina nasan tabbas wannan saurayin yafi ƙarfina, bazan taɓa samun wannan saurayin ba domin kuwa duk wani abu da ake nema ya haɗa. Kyau, kuɗi, Nasaba, gayu, ilimi da duk wani abu da 'ya mace ke nema wajen datattacen Namiji.  Gaba ɗaya daskarewa na yi na kasa motsi, kar na yaudari kaina Fahad ba tsarar aure na ba ne.  "Yau ba magana ne, kin wane tsari ni da ido kamar yau kika fara kallona?"  Ya faɗa daidai lokacin da ya iso, gaba ɗaya yau sai na rasa wannan yanayin da nake ji idan yana gabana, jikina sanyi ƙalau na ce da shi.  "Ina wuni?"  Kallona ya yi sannan ya kalli ƙawayena ya ce.  "Baki da lafiya ne?"  "A'a, ina da lafiya."  Na faɗa ina kallonsa. "Uhm."  Ya faɗa yana taɓe baki irin bai damu ba. Ganin na yi shiru kusan minti biyar, kuma ban tafi ba ya sa shi cewa.  "Ina so mu yi magana ranki ya daɗe, naga yau a saurauniyar ki kike."  Bin shi kawai na yi a baya, ƙawaye na dai suna bina da na mujiya. Har mu ka ƙarasaa bakin motarsa ina jin idanunsu akaina.  "Me yake damunki?" Ya faɗa yana kallona, girgiza kai na na yi sannan na ce.  "Bakomai"  "ƙawayenki ne?" Na ɗaga sannan na ce.  "Wai sun ce idan kai saurayi na ne yaudarata zaka yi ba zaka taɓa aurena ba. Sabida kafi ƙarfina."  "To ke me kika gani?"  Ba tare da wani lissafi ba na ce.  "Da gaske suke."  Ya yi murmushi sannan ya ce.  "Rawasiya daman ni na ce saurayinki ne?"  Na gwalalo ido waje sannan na ce.  "Kasan suna na? Aina?"  "Taambayar da na yi miki kenan?" Na girgiza kai sannan na ce.  "A'a da a'a."  "Mene a'a da a'a?"  Ya tambayeni yana kallona.  "Da ka ce tambayar da ka yi min kenan shine a'a ta farko, a'a ta biyu da ka ce daman ka ce kai saurayi na ne?"  Murmushi ya yi sannan ya ce.  "You're very funny, I love it girl."  Na yi murmushi sannan ya ce.  "Baki tambayeni me nake yi anan ba?" A raina na ce.  "Duk inda nake ganinka da na taɓa tambayarka me kake yi a wajen?"  "Sabida yau wajenki na zo shi ya sa na tambayeki."  Na ji muryarshi ta katse min tunani na.  "Shekararka nawa?" Na tsince kaina da tambayarsa, sai da ya ƙare min kallo sannan ya ce.  "Ashirin da shida."  Wani daɗi na ji ya ratsani, irin mijin da nake so.  "Ke fa?"  Na ji ya tambaya.  "Goma sha bakwai da rabi."  "Ko ba rabi ba?."  Ya tambaya yana dariya. "Yau na ganka da sauƙin kai, daman haka kake?"  Na tambayeshi, sai dai ya yi dariya sannan ya ce.  "Au da da zafin kai nake zuwa kenan?"  "ƙawayena bari na tafi."  Na faɗa ina nuna masa su, nan take ya haɗe rai ya dawo asalin Ta'ambo da nasani.  "Je ki."  Ya faɗa cikin wani irin amon murya, ba shiri na tsaya na kasa tafiya.  "Je ki mana."  Ya faɗa yanzu muryarsa da alamun fusata.  "Ka yi haƙuri." "What do you do? Kin nuna sun fini amfani da muhimmanci to sai me?"  Gaba ɗaya jikina ya fara rawa, duk na rikice lokaci ɗaya, bakina har rawa yake na ƙara cewa.  "Ba haka ba ne fa." Legendspen 08*SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na shida     (06) Bai ko kalleni ba ya shige mota ya tafi, na kusa minti biyu a tsaye sannan na juya ga su Malaika.  “Ku zo mu tafi.”  “Wallahi Nana ban yarda saurayinki ba ne sai yanzu.”  Fauziyya ta faɗa bayan sun ƙaraso inda nake.  “Ni har yanzu ma mamaki nake, kinsan su waye familyn Ta Ambo kuwa? Kaf jihar jigawa suna cikin manyan masu kuɗi guda biyar,  ‘yan kasuwa ne na gaske masu arziƙi, duk a turai suke rayuwarsu baki ɗaya, wannan ma kina ganinshi kinsan ba rayuwar nan ba ne, gashi duk ‘ya’yan attajirai suke aure.” Tin da Malaika ta fara magana har ta dire idanuna na kanta, domin nasan gaskiyya take faɗa zalla ma kuwa.  “Idan kuwa hakane tabbas wannan yafi ƙarfinki Nana, ina baki shawarar karki ɗaurawa kanki abinda bazai ɗaure ba, kizo ki sha wahala a banza.”  Fauziyya ta faɗa tana dafa ka faɗa ta, ni basu san abinda ke damuna ba wannan ba ne, fushin da ya yi ya tafi ya barni yafi komai ɗaga min hankali.  ‘Yanzu yaushe zan sake ganinsa?’  Na tambayi kaina sai dai ba mai bani amsa, tsoro na ɗaya kar ya yi dogon fushi, fata na dai Allah Ya kawo shi da wuri, sai dai fatan ba ai amso ba dan haka aka yi sati ɗaya babu shi babu alamunsa, duk na damu gashi ni irin mutanen na ce da ba su iya faɗar damuwarsu wa wani ba, sai dai na bar abu a zuciyata ya yi ta cina, ni kam sai dai aga ina ta rama duk na zagwanye. Haka kuwa aka yi na yi ta faman rashin lafiya a tsaye babu zazzaɓi sai ciwon kai sama sama, tari da kuma ɗacin maƙwogwaro, haka na yi ta fama sati ɗaya sati biyu har sati uku, hankali Hajiya da Alhaji duka ya tashi, kowa yasan akwai abinda ke damuna amma nakasa faɗa.  Haka su Malaika ko da yaushe sai sun tambayeni saurayina, kuma a ko yaushe sai sun nusar dani cewar yafi ƙarfina, tun ban fiya sa abun a rai ba har na yardarwa kaina Fahad yafi ƙarfina, har na fara jin cewa ya gane yafi ƙarfina ne shi ya sa ya tafi bai sake zuwa ba. Abu kamar wasa Fahad ya yi wata ɗaya, ya yi wata biyu, ya yi wata uku. Ta dole na haƙura da Fahad na fara tunanin cireshi a raina, sai dai hakan ya gagara duk ranar da na fita da sa ran ganinsa nake fita, haka zan ta ganin masu kama da shi a hanya.  Wata ranar juma’a cikin wata na huɗu da rabuwarmu da shi, ranar ma daƙyar na iya fita makaranta sai da Hajiya ta yi min jan ido sannan ma na fita, ko a cikin aji ma haka Malaika ta isheni da surutu.  “Daman na faɗa miki Fahad ba tsarar aurenki ba ne, bikin Cousin brother ɗinsa ake yi yanzu haka komai a Abuja aka yi sai jiya su ka dawo Jigawa ɗaurin aure zaayi yau ɗinnan sai kuma wani event ɗin anan dutse da zaayi gobe Asabar, ‘yar gidan ministan man fetur yake aure.”  “To yanzu ni mene alaƙa da hakan?.”  Na faɗa ina kallonta, wayarta ta zaro ta shiga dubawa, tana faɗin bari ki ga. Duk cikinmu daman ita kaɗaice mai waya, duk tafi mu waye sabida gidansu tsantsar ‘yan boko ne gaske.  “Kinganshi.”  Ta faɗa tana miƙomini wayar, idanuna suka saukan akan kyakyawar fuskarsa. Yana sanye da wani baƙin men lace da aka yi masa babbar rigar, yasa baƙar hula da baƙin takalmi haka baƙin agogo, wayanda suka ƙara haska farar fatarsa.  Ji nai zuciyata ta yi wani irin bugu da ƙarfi, na yi saurin runtse idona sai ga ƙwalla zir zir. ‘Ashe haka na yi kewarsa? Ashe haka nake son sa?.’ Na shiga tambayar kaina.  “Ke mene haka? Lallai iska na wahalal da mai kayan kara, chaɓ.”  Na ji muryar Malaika na faɗa, ban ko kulata ba na miƙa mata wayarta, na kifa kaina da benci na shiga kuka a hankali marar sauti.  Ina wannan yanayin har aka tashi, na ɗakko jakata na fito banko tsaya su ba, sai dai ina fitowa bakin gate na ji ƙirjina ya fara wani irin bugu, na shiga waige waige.  “Me kuma kike dubawa ne?”  Fauziyya ta faɗa, ban ko kula ta ba nasake waigawa. Yau daga can nesa ya tsaya, dan bana iya hango fuskarsa sosai sai dai na tabbatar da shi ne, baƙaƙen kaya ne a jikinsa sai dai na yau yadi ne, kuma motar ta sa yau ma baƙa ce. Basan lokacin da na fara ɗaga ƙafafuna ba ina bin hanya zuwa inda yake sai da na daina jiyo hayaniyar ‘yan makaranta sannan na waiga baya, ashe na yi nisa ma.  Haka na ci gaba da takawa har inda yake, bansan na yi kewarsa ba sai da na ƙaraso inda yake, na yi ƙasa da kaina na fara zubar da hawaye.  “Nana! Nana ɗago mana.”  Ya faɗa cikin sassanyar muryarsa, kasa ɗagowa na yi sai da yaji shasheƙar kuka ne, sannan ya ce. “Subhanallahi! Nana kuka kuma?”  Ɗagowa na yi na kalleshi, idanuna ne suka sanar dashi halin da zuciya da gangar jikina suke ciki. A hankali ya ce.  “I’m sorry Nana, kwana biyu da haɗuwar na tafi chaina, and daman zuwan da na yi nazo ma faɗa miki tafiyar ne, last week na dawo kuma Abuja na sauka sabida bikin brother na Aliyu, jiya muka dawo nan kuma jirgin dare ne, yau ko breakfast banyi ba na tawo nan, tun 9 nake wajen nan gashi har 12:30.”  Gaba ɗaya sai na ji wa’yannan ƙwayoyin kalmomin da ya faɗa sun goge duka wani ɗaci da ɓacin raina na wattanni, kalmar da ya faɗa ta. ‘Ko breakfast banyi ba na tawo nan, tun 9 nake wajen nan gashi har 12:30.’ Ta haifar min da wani zazzafan tausayinsa a cikin zuciyata, sai na ji dama nima banyi breakfast ba na tawo.  “Nana! Ki yi haƙuri dan Allah, baran sake irin haka ba.”  Sai da na ja numfashi sannan na ce.  “Na yi ta rashin lafiya sosai, har da low Bp.”  Ya gwalalo ido waje cike fa mamaki ya ce.  “Low Bp Nana? Akan me?”  “Ka tafi kana ta fushi da ni, gash bansake ganinka ba wajen kwana ɗari da uku.”  “Nana duk akaina haka? Ki yi haƙuri bansan zaki damu ba kwata kwata wallahi.”  “Uhm.” Na faɗa tare da niyar waigawa baya, sai dai da sauri na dakatar da hakan sabida bana son ma ganin ko sunan ko ba sa nan dan duk halin da na shiga sune suka ja min.  “Kawayenki?”  Ya tambaya, da sauri na girgiza kai sannan na ce.  “A’a basu ba?.”  Ya yi murmushi sannan ya ce.  “Suna nan tsaye.”  “Uhm su yi ta tsayawar, kasan me suke cewa?”  “A’a sai kin faɗa.” “Wai daman kaima kasan ba tsarana ba ne, shi ya sa ka daina zuwa.”  “Nana bana son sake jin wannan maganar abarta dan Allah.”  “Tom.” Na faɗa tare da fara wasa da yatsuna.  “Kizo na kaiki gida.”  “Yanzu ka dawo daga can ɗin gaba ɗaya kenan?” “A’a, zanyi one week anan sannan na je na yi 3weeks acan, shikenan.”  Tun daga wannan ranar kullum sai Fahad Ta’ambo ya zo wajena, soyayya da shaƙuwa ta shiga tsakanina da shi ba tare da kowa ya sani a gida ba, har ya yi satinsa ya koma.  Bayan tafiyarshi ma, munyi waya sau ɗaya a wayar Hajiya da na ɗauka na kirashi, sai kuma wata rana da na je gidan Yaya Radiya.  Ranar da ya cika sati uku cif ranar ya dawo kuwa, da na kirashi a wayar Hajiya ya ce dani ya dawo kuma zai zo har ƙofar gidanmu. Tun da ya sanar da na shiga tashin hankali, dan ko a hirar mu ta ƙarshe da Alhaji sai da ya tunasar dani akan course ɗin da yake so na karanta da kuma amfaninsa.  Afujajan na fice gidansu Amina Aminu, dan a cikin ƙwayenmu ta ɗan fi sirri, Fauziyya ma bata da matsala sai da yawan surutu marar amfani. Tana zaune a tsakar gida tana daka na shigo. Kallo ɗaya ta yi min ta gane ba lafiya ba.  “Nana me ya faru?”  “Muje soro dan Allah.”  Na faɗa ina fitowa, ta tashi ta biyo bayana.  “Amin wai Fahad ne zai zo kuma wai gidanmu.”  Na faɗa kamar zanyi kuka.  “To ke mene a ciki, ba son shi kike ba kuma duk wanda ya ce zai zo gidanku ai aure ne zai kawo shi, ji dai Abdul ɗin Fauziyya yanzu har magana ta tsaya.” “Ba haka ba Amina, kinsan ko ranan Alhaji ya ce da ni so yake na karanci ko Mass communication ko Law.”  “Kai Nana, Fahad ai me ilimi ne kuma da wayewa, kina tunanin zai iya hanaki karatun boko? Gaskiyya ba alama.”  “Nufinki zai ce zai jira nagama karatu? Mussamam Law wajen shekara goma.”  “Alhaji ba zai iya bari ki yi karatun a gidan mijinki ba, yanzu fa ke damuwarki kawai Alhaji ne, kuma idan kika matsa tsaf zai barki ki yi a gidan mijinki.”  Daga haka tai ta bani shawarwari kala kala, daga nan na koma gida na fara shiri. Ina zaune cikin ɗaki Hajiya ta shigo.  “Hajiya ina zaki?”  Na faɗa ganin irin shirin da ta yi.  “Ki shirya ki taso muje, Hajjace zata tsallaka titi mashin ya bugeta ta yi tsagewar ƙashi.”  “Allah Ya bata lafiya, amma ba inda zani.”  Na faɗa ina kwanciya.  “Bazaki tashi ba?”  “Uhm”  Na faɗa tare da rufe idona, haka ta ƙaraci faɗan ta ta fita, tana fita na miƙe tsaye tare da daka uban tsalle ina faɗin.  “Alhamdu Lillah.”  Ban ɓata lokaci ba na hau shiryawa, ƙarfe 05:30 daidai na ji yaro ya shigo wai ana kiran Nana a waje. A raina na ce. ‘Yanzu da Hajiya tana nan haka zaiyi mini chaɓ?.’  Ina shirin fita na ga Yaya Ridwan ya fito, kallo ɗaya ya yi min ya ɗauke kai ya fice. Nasan dai bazai taɓa yi masa magana ba dan ba halinsa ba ne, amma kallon da ya yi min tabbas ya bani tsoro.  Da yake gidan namu yana da girman compound kafin ka kai ga shiga cikin gidan ya sa na sauke anan, wajen yana da faɗi dan har mota biyu zasu iya tsayawa.  Tun da mike tsaye yake ƙare min kallo sai can ya ce.  “Na ga ma fa ke yarinya ce, anya za a aurar dake yanzu?.”  Na yo dariya sannan na ce.  “To ka jira na girma kawai, kafin nan na ƙarasa karatu na.”  “Ina bazai yu ba, ki girma kuma? Ai ba amfani.”  “Mene ba amfani?”  “Girman mana, bakisan mace tana ƙarama tafi daɗin zama ba, shi kanshi miji yafi son ya aureki kina ƙarama.”  Na yi dariya sannan na ce.  “Alhaji dai ya ce Karatu zanyi.”  “Dagaske ko wasa?”  Ya faɗa da alamar damuwa, ni kuma kai tsaye na faɗa masa gaskiyya.  “Kuma ba zai taɓa bari ki yi aure ba, sai kinyi karatun?”  “A’a zai iya bari na na yi mana idan mijin zai barni.”  “Nana!”  Ya kira sunana cikin wani irin yanayi.  “Na’am!”  “Nana, ina sonki dagaske, kuma aurenki nake son yi, bazan iya rayuwa ina kallonki a haka ba a matsayin matata ba, Nana ina da mugun kishi akanki sosai wallahi.”  Gaba ɗaya na ji tsigar jikina ta tashi, daidai lokacin kuma Yaya Ridwan ya shigo, kallo ɗaya ya yi mana ya ɗauke kai ya shige ciki.  “Nana wannam yayanki ne?”  “Eyh shi nake bi.”  “Okay, amma baya ganin mutane ne?”  Sai da na yi dariya sannan na ce.  “Ai haka yake, shi ko Abban mu ya gani a hanya ko Hajiya zai iya ɗauke kai.”  “Uhm.”  Ya faɗa yana zaro wayarsa, sannan ya ce.  “To yanzu mene mafita?”  “Game da me?”  “Kin manta?”  “A’a ban manta ba, amma maganganun da muka yi da yawa bansan akan wacce kake magana ba.”  “Zancen aure, Nana kina sona?”  Wani irin abu na ji a zuciyata, “wai ina sonsa?”  “Eyh Nana?”  Sai da na ɗago na kalleshi sannan na ce.  “Mugun so ma?”  Ya yi dariya sannan ya ce.  “Wane iri ne mugun son?”  Ƙasa na yi da kaina na fara wasa da yatsuna.  “Nana akwai wata matsala a gida, bansan ta yadda zan samu iyayena da maganar ina sonki ba, sabida mu family ɗin mu gaba ɗaya Rich Family suke aure.”  Gabana ne ya faɗi, maganarsu Malaika ta fito da suke cewa yafi ƙarfina, a Royal family suke aure ko ‘ya’yan manya.  “Nana wannan ba matsala ba ne, ni zanyi ƙoƙari da gida kema ina so ki yi koƙari anaku gidan ki tabbatar Abbanku ya ce zai miki aure.”  Shiru na yi gaba ɗaya jikina ya yi sanyi, ta ina zan fara tunkarar Abba da zancen ya yi min aure?  “Kinyi shiru, wannam fa aiki ne babba muka ɗauka Nana, kina sona ina sonki, kuma kowa akwai matsala a ɓangarensa, naki ɓangaren ba yanzu za su yi miki aure ba, nawa ɓangaren ‘ya’yan masu kuɗi suke su.”  “Yanzu ni ta ina zan fara, wannan aikin babbane.” Na faɗa kamar zanyi kuka.  “Ta ina da zan fara, look Nana idan bakya sona ne ki fito ki faɗan.”  “Ina sonka mana.”  “Banga alama ba.”  Ya faɗa tare da kaɗa kai zai fice.  “Ka yi haƙuri dan Allah, zan yi musu magana Allah.” Banza ya yi ya sa kai ya fice.  “Shikenan na sake ɓata masa rai.”  Na faɗa tare da juyowa idanuna suka faɗa cikin na Yaya Ridwan, yana tsaye yana kallona.  Legendspen 08129553971 129*SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na bakwai     (07) A hankali na shiga takawa zuwa cikin gidan, yana tsaye yana kallona har na shige, kamar daga sama na ji muryarsa.  “Wane wannan?”  Shiru na yi bance ko ƙala ba, a fusace ya sake magana.  “Ba dake nake ba?”  Bakina na rawa na ce.  “Saurayina ne?”  Ya yi dariya sannan ya ce.  “Ba shine Sardauna ba? Fahad Ta ambo.”  “Fahad Ta ambo.”  Na faɗa kaina a ƙasa.  “Nana.”  Ya kira sunana amma yanzu muryarshi a hankali, na ɗago kai na kalleshi.  “Zo nan?”  Ya faɗa yana nuna kusa dashi, kamar mai ciwon jiki haka na taka na je.  “Kinsan waye shi? Su ɗin masu kuɗi ne sosai kuma kinsan duk irin waɗan nan masu kuɗin ba wani kirki ba ne dasu, kaɗan ne masu mutunci.”  “Nasani.”  Na faɗa a hankali, ya kalleni sannan ya ce.  “Nana ki sani kefa macece, rayuwarki tana da daraja ga iyayenki da ‘yan uwanki, ba wai dan baku da kuɗi yana nufin ku ɗin baku da daraja ba, nasani muna cikin wani zamani wanda duk mai wani abu shine mutum, amma duk da haka kada ka ta ɓa bari darajarka ta ragu ko ki nuna baki da ita, karki ta ɓa sa wa ranki alfarma zai yi miki ko yake yi miki, ke macece kuma mai daraja. Dan haka ka da nasake ganin abinda ya faru yanzu ya faru.” Yana faɗin haka ya shige ɗaki, ya barni ina faman tunani, me ya gani? Me yake magana akai?.  Abu kamar wasa Fahad shiru, sati ɗaya sati biyu, idan na kirashi a wayar Hajiya ba ya ɗagawa, ta Malaika kam daman ya ja min kunne ya ce a wayar Hajiya kawai ya lamunce na kirashi.  Sai da aka yi sati uku baya ɗaga wayata kuma ba ya kirana, duk na bi na damu kuma na yi alƙwarin zanyi masa biyayya akan komai ya sani, tun da harshi ya ɗauki jahadin yi wa iyayensa magana akan yana son auren wacca ba ta kai ba, ni to me ya sa bazanyi ba.  Wata ranar laraba da yamma ina zaune a ɗaki na ɗauki wayar Hajiya na sake gwada lambarsa, ina kira ya katse ya kirani. Na ji wani mugun daɗi a raina, ina ɗagawa ya ce da ni.  “Ina bayan gidanku.”  Ba shiri na miƙi na zura hijabi na yi waje, Hajiya na tsakar gida tana kaɗa miya na ce da ita.  “Zani gidansu Amina.”  “Da yamman nan?”  “Eyh.” Ina faɗin haka na fice zuwa bayan layi, yana jingine jikin farar motarsa, yana sanye da light blue ɗin shadda, ina ganin fuskarsa na ji wani sanyi ya mamaye zuciyata, wata irin nutsuwa ta shigeni, duk wata fargabar da nake ji ta tafi.  “Yanzu ma kin daina damuwa idan ban nemeki ba.” Ya faɗa yana ƙare min kallo.  “Waya faɗa ma, wallahi na damu sosai da sosai.” “Ban yarda ba, gashinan har wata ƙiba kika yi.” “Ƙiba kuma?”  “Eyh, ya maganar mu? Me kika yanke?”  “Zanyi magana da Alhaji ta yadda zai fahimta.”  “Good girl.”  Ya faɗa yana buɗe motarsa, ya ɗauko leda ya miƙamin. Hannu nasa na amsa sannan na ce.  “Na mene?”  “Naki ne, na yi magana da Daddy ya amince amma Mom ce abun sai addu’a.”  Wani irin tausayinsa na ji ya ratsani, nasan irin wannan abun tabbas da wahala.  “Allah Ya sa ta amince itama.”  “Nana na sha wahala akan lamarinki, sai na ji kamar zan haƙura sai na ji bazan iya ba, amma ke  babu ruwanki ɓata min rai kawai kike, maimakon ki nuna sakayyar soyayya amma naga babu abinda kike so sai ɓacin raina.”  A tsorace na ce.  “Ya zaayi naso ɓacin ranka?”  “Gashi ina gani.”  Da irin waɗannan abubuwan Fahad ya dinga amfani yana cusa min tausayinsa da wata iriyar soyayyarsa mai girma, wanda a kullum gani nake yana shan wahala a kaina, sai da fa na kasa tarar Alhaji ko Hajiya da maganar, duk son da nakewa Fahad bana jin ya kai tausayin da nake yi wa Alhaji ba.  Shi kuma a kullum faɗa min irin tashin hankali da suke yi da mahaifiyarsa da ‘yan uwansa a kaina, har cewa ya yi dani ya daina shiga sabgar sister ɗinshi, a ranar na yanke shawarar tunkarar Alhaji akan maganar.  09:15pm.  Alhaji na zaune a ɗakinsa ya bayan ya yi wanka yana sauraren radio na shigo cikin ɗakin.  “Barka da hutawa Alhaji.”  “Nana barka dai, akwai abinda kike buƙata ne? Ko kin shirya sanar dani damuwar da na ce tana damunki kike ɓoyewa.” Gyaɗa kai na yi sannan na fara magana cikin rawar baki.  “Alhaji daman.. daman wani ne..”  Alhaji irin mutanen nan ne masu sauraron mutane, zai iya kwashe awa guda yana saurarenka ba zai katse ka ba, sannan kuma ba zai yanke ma hukuncin ba har sai ka kammala.  “Wani ne.. tun da daɗewa ya ce wai yana so ya turo iyayensa wajenka.”  Murmushi Alhaji ya yi sannan ya ce.  “Su yi mini me?”  “Wai yana sona zai aureni, kuma na faɗa masa kai bazaka aurar dani ba sai na yi karatu me zurfi na zama maaikaciya, ya ce wai ya ji ya gani zai barni na yi karatu duk wani waje da nake so.”  “Shi ɗin waye?”  “Sunansa Fahad Ta ambo.”  Wani murmushi Alhaji ya ƙarayi sannan ya ce.  “To ke me kika yanke, auren ko karatu Nana?”  Na yi shiru na rasa me zance. Allah Ya sani ina son Fahad ina tausayin halin da yake ciki a kaina, kuma bana son rasa shi, sannan kuma ina son cika burin mahaifina, amma kuma abu guda ɗaya da nake gani shine auren tun da Fahad zai barni na ci gaba da karatuna, domin a maganar mu ta ƙarshe da shi ya ce da ni.  ‘Idan kika ga zaiƙi sai ki faɗa masa ni zan barki ki ci gaba da karatun naki.’  “Nana”  Alhaji ya kira suna na.  “Na baki kwana biyu kije ki yi shawara, duk hukuncin da kika yanke zan amsa tare da nawa sharaɗin akai.”  “Na gode Alhaji.”  Na faɗa tare da tashi na fice, ko da na shiga ɗaki na kwanta abubuwa suka yi ta faɗomin a rai, na saƙa wancan na kwance wancan.  “Kalli su Yaya Radiya, da Rumaisa sunyi aure kuma suna cikin rufin asiri, ga Rumaisa nan ma ta koma makaranta tana karantar harkar lafiya, ke me kike jira zaki zauna wani zama idan kika gama karatun girma ya kama ki tsaf sai ki rasa mijin auren.”  Zancen zucin da na wayi gari da shi kenan, haka na yi ta abubuwa komai sukuku, dan ma yanzu ba makaranta muke zuwa ba WAEC zamu fara nan da sati biyu, shi ya sa bamu cika wani zuwa ba. Bayan Alhaji ya fita na shirya na lallaɓa Hajiya akan ina son zuwa gidan Yaya Rumaisa da Yaya Radiya duka a rana ɗaya.  “Wai me zakije ki yi musu duka su biyun a rana ɗaya?” Hajiya ta tambaya cike da mamaki, ganin tana neman hanane ya sa na ce.  “Alhaji ne fa ya ce na je dukkansu mu yi magana dasu.”  Kuɗi ta ɗauka ta bani tare da cewa.  “Kuma karki yi yamma.”  Ta gidan Yaya Rumaisa na fara, tun da shi yafi nisa, akan gidan Yaya Radiya. Shi ya sa na fara zuwa gidan Yaya Rumaisa, yanayin da na sameta ya yi matuƙar burgeni, ta yi ƙiba abunta duk da karatun da take yi ga yaranta kyawawa guda biyu Afra da Affan. Bayan mun gaisa ne na kalleta sannan na ce.  “Yaya shawara nazo nema wajenki.”  “Ina saurarenki.”  Sai da na ɗan yi jim sannan na ce.  “Nasami Miji kuma dagaske aure na yake so ya yi, sannan ya yi min alƙwarin bari na na ci gaba da karatu da nuna masa Alhaji yana son karatun.”  “Rawasiya, kinyi magana da Alhaji.”  “Na yi, shi ya ce na yi shawara.”  Yaya Rumaisa ta gyara zama, ta kalli ni cikin idanu tare da kamo hannuna, sannan ta numfasa ta fara magana cike da nutsuwa.  “Nana zan gaya miki abubuwan da suke cikin aure na daɗi da rashin daɗi, idan na faɗa miki sai ki yi tunani da kanki, ki ga wanne kika zaɓa.”  “Tom Yaya.”  “Nana, aure ba kawai canza gida ba ne ko samun wanda zai riƙa lura da ke. Aure ibada ne, kuma makaranta ce da ba a yaye ɗalibi har sai mutuwa ta raba. Idan kika ga mace a cikin jin daɗin gidam aure, to dole akwai matakan da ta bi waɗanda suka kai ta ga wannan matsayin jindaɗin. Nana abinda zaki fara sani a farkom farko shine, mene ne Aure kuma yaya Rayuwarsa take? Aure haɗaka ce ta rayuka biyu. Manzon Allah (SAW) ya ce a cikin Hadisin Al-Baihaqi Idan bawa ya yi aure, to tabbas ya cika rabin addininsa.... Don haka, rayuwar aure tana buƙatar haƙuri da juriya. Za ki ga daɗi, za ki ga wuya. Amma mabuɗin shi ne Biyayya da Fahimta. Sannan kisani akwai Abubuwan da ake so Mace mai aure ta yi, duk da suna da yawa amma bari na baki wasu daga ciki. Nana na farko akwai Biyayya. Ki sani Nana, biyayyar miji tana kai mace Aljanna. Amma fa muddin bai sanya ki saɓon Allah ba. Na biyu akwai Kwalliya da Tsafta, Nana ki zama kullum idon mijinki yana ganin abin da zai faru da shi, hancinsa ya riƙa shaƙar ƙamshi mai daɗi. Sannan kuma akwai riƙe sirri. Kada ki yarda sirrin gidanki ya fita waje, koda ga mu ‘yan uwanki ne, muddin ba neman shawara ta lalura ba ne. Bayan wayannan akwai abubuwan da ba a so Mace ta yi. Misali Gasar Iko, Kada ki riƙa nuna wa mijinki ke ma kina da iko kamar sa. Shi ne shugaban gida, don haka ki ba shi matsayinsa. Sannan Yawan ƙorafi Kada ki zama mace mai yawan gunaguni a kan kowane ƙaramin abu. Sai kuma wani abu da muke yawan yi shine ƙaryata Alkhairi. Manzon Allah (SAW) ya nuna cewa yawancin mata suna shiga wuta saboda rashin godiya ga mazajensu. Don haka, ko kaɗan ne ya yi miki, ki ce 'Na gode'." Ta ɗago ta kalleni yadda jikina ya yi sanyi, sannan ta ce.  “Nana aure kala biyu ne, ko na ce zaman aure kala biyu ne, na farko akwai farin cikin aure idan aka yi dace. Nana, idan kika samu miji na gari, miji mai tsoron Allah kamar nawa, to za ki ji kamar kina Aljanna a duniya. Za ki samu abokin shawara, wanda zai kiyaye miki mutuncinki, ya kare miki rayuwarki, kuma ya zama silar ƙarin kusancinki da Allah. Za ki ji wani sanyi a zuciyarki wanda ba shi da misali. Na biyun kuma shine akasin haka Idan ba a yi dace ba, Idan kuma aka samu rashin da ce wanda Allah Ya kare mu, to aure yakan koma kurkuku. Idan miji ya zama mara tsoron Allah, mai son kansa kawai, to zai riƙa amfani da ikon da Allah ya ba shi yana zaluntar mace. Zai iya raba ta da mutuncinta, ya raba ta da danginta, ya kuma mayar da ita tamkar baiwa a gidansa. Shi ya sa nake ba ki shawara Nana; Kada ki yi gaggawar aure don kawai kina son yin sa, ki yi shi don kin samu wanda ya dace, kuma ki tabbatar ba za ki daina karatun ki ba domin ilimi shi ne gatanki." Jikina ya yi sanyi, ya mutu baki ɗaya. Tabbas duk wata shawara da nake nema nasame ta wajen Yaya Rumaisa, kuma dole na zauna na yi zurfun tunani akai sosai da sosai.  “Nana karki yanke hukunci cikin gaggawa, ki sami lokaco ki nutsu, ki duba halayen saurayin naki Nana ki ga nagartacce ne ko akasin haka.”  “Shikenan Yaya Na gode sosai.”  Daga nan na yi mata sallama na wuce gida, ban ma je gidan Yaya Radiya ba, ko da Hajiya ta tambayi ya na dawo da wuri sai na ce da ita.  “Iya gidan Yaya Rumaisa na je.”  Da ta cika ni da tambayar ya take ya gidan, kawai na tashi ma shige ɗaki. Kwata kwata ma bana son magana, so nake na nutsu na saurari zuciyata me take ce min, me ta hanga a tare da Fahad, sai dai fa ko mene ina matuƙar ƙaunar Fahad, rabuwa da shi da wuya.  Legendpen 08129553971 553*SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na takwas     (08) Har dare ban iya ce da kowa komai ba, shiru kamar wacca ba ta da lafiya. Haka na kwana ina faman tunani har washe gari, gaba ɗaya ba mu haɗu da Alhaji ba shima kuma bai neme ni ba, har zuwa yamma lokacim da nasan Sardauna zai zo, Hijabi kawai na sanya na fita dan bana jin zan iya wata kwalliya a yanayin da nake, sai dai tambayar da nake yi wa kaina. ‘Wai shin me ya dame ni?.’  Kallo ɗaya Sardauna ya yi min ya gane yanayin da nake ciki, tambayar farko da ya yi min.  “Abban bai amince ba ne?.”  “A’a ya ce na je na yi tunani akan aure ko karatu?”  “To Nana me kike jira? Kinsan abinda na yi fama da shi yanzu kafin na fito?”  A hankali na buɗe baki na ce.  “Jiya da daddare muka yi maganar da shi, jira nake ya dawo na ce mai na amince.”  Ya yi wani murmushi sannan ya ce.  “Ko ke fa Hon.”  Nima na yi murmushi.  “Kinsan sunana?”  Na ɗago kai na kalleshi, ya gyaɗa mun kai.  “Wane suna?”  “Ban taɓa ji kin kira ba, shi ya sa na tambaya ko kin sani?”  Sai da na yi murmushi sannan na ce.  “Ya zaayi na kira sunan ka, ai babu ladabi.”  “To ai akwai sunan da nake so ki dinga faɗan.”  “Wannene?”  “SARDAUNA!” Har cikin raina na ji daɗin sunan, sai da na maimaita a raina sannan na ce.  “Sunan ya yi daɗi.”  “Ina som sunan &akata ce ta samin shi, shi ya sa na ce shine sunan da mata zata dinga kira na, kuma a yanzu naga komai ya kusa kammala, shi ya sa na faɗa miki dan nima Mom ta fara amincewa.”  “Kai Alhamdulillah.”  Na faɗa a fili, shi kuma ya ce.  “Yanzu saura ke da Abba.”  Daga nan muka ɗan taɓa hira sannan ya tafi, abu ɗaya da na kasa sabawa da shi, shine duk sansa Sardauna ya zo wajena zai tafi sai na ji ba daɗi, nifa ko ba zamuyi magana ba ya dinga kallona da ido kaɗai ina kallonsa abun farin ciki ne. Daga nan gidansu Amina na shiga, abun mamaki na tarar da Fauziyya da Malaika duka a gidan.  “Da banzo ba da ba zama a nemeni ba kenan?” Na faɗa ina kallonsu.  “To banza mun zo gidan naku aka ce kin fita, sai da muka zo Amina ta ce wai Fahad ne ya zo.”  “Eyh daga can nake.”  Na faɗa ina zama.  “Dagaske dai auren naki zai yi?”  Fauziyya ta tambaya, na kalleta sannan na ce.  “Eyh wallahi, a yanzu ma ‘yan gidansu so suke su zo, Alhaji ne har yanzu bai gama amincewa ba.”  “Kai ma sha Allah, muna da shagali a gabanmu, amma ya zancen karatunki?”  Amina ta tambaya, kafin na bata amsa Malaika ta bata amsa da cewa.  “Ke wai kin san gidan da zata shiga, to ƙila ma a ƙasar waje zata ƙarashe karatun na ta.”  “Kai Mailaka! Wai masu kuɗin gaske ne?”  Amina ta tambayeta.  “Wanne masu kuɗi kika sani kaf Jigawa?”  “Gidan gwamna.” Amina ta bata amsa.  “Ai gwamna kuɗin jama’a ne, wannan magana ake kan masu kuɗin kan su, yarinya kin yi da ce za ki shiga cikin manyan mata masu aji.”  Ni dai jinsu nake har suka kammala hirar, na dawo gida. A bakin ƙofa na ga Yaya Ridwan yana kallona, ban kai ga shiga gidan ba na ji muryarsa na faɗin.  “Na ƙara ganin kin tsaya da wani ɗan iskan sai na ci uwarki.”  Daga haka ya shige nima na shige ciki, sai dare sannan Alhaji ya dawo, sai da na jira ya kammala komai ya shiga ciki sannan na shiga ɗakin na sa.  “Alhaji Barka da dare.”  “Barka dai Nana.”  Ya amsa yana saurarena, sai dai na yu shiru na kasa magana.  “Nana ya aka yi? Kin yi shwarar ne?”  Na gyaɗa kai a hankali, ba tare da na yi maganar ba.  “Faɗi mana, ki yi magana ina sauraren kinji.”  “Al Haji.. da ma.. Daman Alhaji na gama ne.”  Na faɗa a rarrabe, ya ɗago kai ya kalleni sannan ya mayar da kansa ga abinda yake.  “Kinga me?”  A hankali na ce.  “Shwarar.”  Muryar na ba ta fito sasai ba.  “Tom me kika yanke, ina saurare.”  “Auren.”  Ya ɗago kai ya kalleni kusan minti biyar sannan ya mai da kai ƙasa.  “Wannan ita ce shawarar taki?”  “Eyh Abba.”  Abba ya sauke numfashi bayan ya gama sauraro na, ya kalle ni da idanuwan da suka nuna damuwa amma kuma cike da soyayya, sannan ya fara magana "Nana, na ji abin da kika zaɓa. Kuma a matsayina na mahaifinki, ba zan taɓa tilasta miki abin da zuciyarki ba ta so ba, domin aure ya fi ƙarfin dole. To amma, kafin mu kai ga mataki na gaba, akwai wasu abubuwa da nake so ki sani, kuma akwai sharuɗɗan da zan gina aurenki a kansu nasan kinsan Aure, Nana, ba wasa ba ne. Mutuncinki shi ne mabuɗin darajarki a gidan miji. Ina so ki sani cewa kowace mace ita ce take gina mutuncinta ko ta ruguza shi. Ki zama mai hakuri, mai biyayya, kuma mai kiyaye sirrin mijinki. Amma kuma, ki sani cewa Allah ya ba ki daraja a matsayinki na mace, kada ki bari wani ya take miki mutunci. Kamar yadda kika sani, burina ne ki karanta ilimin likitanci ko wani fanni da zai amfani al'umma. Tunda kin zaɓi aure yanzu, to zan bar ki ki yi auren, amma a kan sharɗi guda Lallai sai kin ci gaba da karatunki a gidan mijinki. Ba zan yarda ilimin ki ya tsaya a nan ba. Ilimi shi ne gatanki, shi ne haskenki, kuma shi ne zai ba ki ‘yanci koda bayan raina. Sannan, ina so in ga wanda ya sace zuciyar ‘yata har ta zaɓi barin karatu a yanzu. Dole ne in ganshi, in tattauna da shi, kuma in fahimci wane ne shi, daga wane gida yake, kuma wane irin hali yake da shi. Ba zan ba da ke ga mutumin da ban yarda da asalin sa da addininsa ba." Gaba ɗaya jikina ya yi sanyi, soyayyar da mahaifina yake yi min babba ce ba ƙarama ba, kuma in sha Allahi sai na cika masa wannan burin nasa, nasan Sardauna yana sona kuma zai so abinda nake so.  “Abba na yi maka alkwarin zan tsaya kai da fata akan karatuna, zan zama ‘yar da zaka yi alfahari da ita.”  Na faɗa muryata tana fitar da wani irin sauti, kamar mai kuka. Alhaji ya yi murmushi sannan ya ce.  “A kullum ina alfahari dake da dukkan ‘yan uwanki Nana, Allah Ya yi miki albarka.” “Amin Abba.”  Na faɗa tare da ta shi na fice, ko da naje ɗaki ban wani iya bacci sosai ba, bawai ina cikin yanayin farin ciki ba ne da amincewar Abba ba, ba wai kuma ina cikin damuwa ba ne, kawai wata iriyar soyayyar Alhaji ce ke ratsa zuciyata, ina son Abbana so mai girma. Washe gari.  A wayar Hajiya na kira Sardauna na faɗa masa yadda muka yi da Alhaji, maimakon naji farin ciki a muryar Sardauna sai tsoro.  “Hon ina jin tsora gaskiyya, ba zan iya tunkararsa ba sai dai kawai na turu.”  “Alhaji fa ba shi da matsala, kuma ba wani abu zai ce da kai ba kawai tattaunawa zakuyi ku yi hira da shi.”  “A’a Honey pls.”  Nasan dole aiki ne babba akaina, na lallaɓa Sardauna ya zo wajen Alhaji, cikin sanyin murya na ce dashi.  “Ko zaka zo yau mu haɗu.”  “So kike na zo ki haɗani da shi?”  “A’a magana zamu yi da kai.”  “Tam zan zo.”  Ya faɗa tare da kashe wayar, haka na mayarwa da Hajiya a barta, ni dai gaba ɗaya wani sukuku haka nake, tunanin yadda zan fara fahimtar da Sardauna muhimmamcin zuwa wajen Alhaji kawai nake.  Ra’is ne ya buɗe labulen ɗakin.  “Wai daman baki mutu ba?”   Na watsa mai harara sannan na ce.  “Sakar mini labule ka fita.”  “Naƙiya, wai me kike yi a ɗaki kwana biyu?”  “Ra’is ka sakar min labule ka fita kafin na yi ma rashin mutunci.”  “Karki fasa.”  Ya faɗa yana shigowa ya zauna gefen gadon ɗakin.  “Wai na ji aure zaki yi?”  A razane na juyo na kalleshi sannan na ce.  “Waya faɗa maka?” “Duk abinda ake ɓoyewa ai mun sani, mun yi waya da Yaya Rumaisa ta faɗan, sannan ta ce na zo na baki shawara.”  Shiru na yi ban ce komai ba, shi kuma ya ɗora da cewa.  “Wallahi indai saurayinki yana sonki, kin yarda da soyayyar da yake miki, to ki yi aurenki me zaki zauna ki yi a gidan? Ke mace fa, ba ‘yar zama ba ce, akwai lokacin da mace take samin samari cike har da na aure, da ta yi wasa ta ƙara girma shikenan zasu tsiyaye kamar hawaye su tafi.”  Kallon Ra’is na yi a raina na ce.  “Shi kuma kalal tashi shawarar kenan.” A fili kuma na ce.  “Alhaji yana so na yi karatu”  “To ai a gidan mijin ma zaki iya ci gaba da abinki, wannan fa a ganina ba matsala ba ce.”  Haka Ra’is ya yi ta bani nasa shawarwarin, bayan ya tafi na zauna na haɗe komai na cakuɗa a kwalwalwata, na yi ta faman kwashewa da ɗebewa har zuwa yamma.  Wajen ƙarfe biyar na tashi na fito tsakar gida lokacin Hajiya na shara, kallona ta yi sannan ta ce.  “Kwana biyu iskancin zaman ɗaki kika ɗaukarwa kanki ko Nana?”  “A’a Hajiya, bani da lafiya ne fa.” “Baki da lafiya shine bazaki sanar ba.”  Yaya Ridwan ne ya leƙo daga ɗakinsa sannan ya ce.  “Hajiya ƙyaleta kawai.”  Ni a raina na rasa me yasa Yaya Ridwan baya sona da Sardauna, ina tuna lokacin bikin su Yaya Radiya duk da bai yi magana ba amma yanayinsa ya nuna yana farin ciki da hakan, amma ni ya fito ya nuna baya farin ciki da hakan, dan ko jiya da daddare sai da ya sake min magana akan Sardauna.  Wayar Hajiya na ɗauka na shiga ɗaki, ina shiga na kira wayar Sardauna, ya katse bai ɗaga ba can kuma ya yi min text.  “Ki fito.” Abinda ya rubuta kenan, na rasa me yasa duk lokacin da Sardauna ya shigo unguwarmu sai na ji a jikina.  “Ina zaki ke da ba lafiya?” Hajiya ta faɗa ganin ina shirin fita. “Abu zan amso a waje.”  “Wajen wa a waje?” “Ɗan ajinmu ne.”  Sai da ta kalleni sossi sannan ta ce.  “Idan kinga dama ki zauna a wajen.” Sannan ta ci gaba da abunda take, ni kuma na fice.  Yau a barandarmu na sameshi, ya tsaya ya harɗe hannunsa a ka faɗa. Kamar ko yaushe dai cikin kyakyawar shiga yake.  “Ke baki damu bama da kiran da Alhajin yake min ko?”  Abinda ya fara faɗa kenan, bayan na ƙaraso inda yake. Na rasa me ya sa Sardauna yake ce min ni bandamu ba, ko so yake ya ga damuwar ƙarara a fuskata?  “Ba fa wani abu ba ne Allah.”  Na faɗa bayan na ƙaraso inda yake.  “Nana ajikina nake jin Abba bazai ban aurenki ba, ni dai idan kina da wata hanyar kawai ki faɗan.” “Wace irim hanya?”  “Wacca zamu bi a fasa zuwa wajensa.”  “Maganar makaranta kawai zai yi ma fa, Alhaji ba zai janye maganar karatu ba fa, kuma Alhaji idan yana ce akan magana babu mai sauye sai Hajjansa ita kaɗai.”  “Wace Hajja?”  “Kakarmu fa.”  “Aina take?”  “Dutse Gadawur.”  “Kina ganin ba zanje na gaishe ta ba yau, sai na ce mata nine saurayinki?”  Taɓe baki na yi tare da cewa.  “Ni ban wani cika shiga al’amuranta ba, hasali ma ba ta son mu.”  Murmushi ya yi sannan ya ce.  “Zata so ku, bani address kawai.”  Ba shi cikakken address na yi na gidan, bai wani jima ba ya tafi, na shiga gida. Ina kallon wani irin kallo da Yaya Ridwan yake min, ni narasa na mene haka?.  Ko da dare da Alhaji ya dawo bai yi min maganar ba, sai ma sanar damu da ya yi ansa bikin Isah Nadabo sati biyu, ya sami mata a jihar kano.  Na ji daɗi sosai a raina tare da yi masa fatan alheri, nasan dai bikine zamu sha dan a gidanmu zaayi komai daga farko har ƙarshe, dan iyayensa  ba anan suke ba ‘yan Gumel ne.  Kwata kwata ba muyi magana da Sardauna ba har washe gari, sai da safe ya kirani muka sha soyayya kuma a yanayinssa babu wannan fargabar, nima kuma ban tambayeshi ba.  Wajen ƙarfe tara da rabi, ina zaune bakin rariya ina wanke wanke, Hajiya na ɗakin Alhaji yana shiryawa, Ra’is kuma na sharar tsakar gida muka jiyo baloƙoƙon Hajja.  Gabana ya yanke ya faɗi. ‘Me ya kawo matar nan gidan nan kuma?.’ Na faɗa a raina, sabida daman a tsarin Hajja sai ta gama baloƙoƙo kafin take shigowa gidan. Hajiya da Alhaji duk sun fito tsakar gida suna jiran ta shigo, ita kuma tana can ta tagar ɗakinsu Yaya Ridwan ta baranda tana faman yi masa sababi.  “Ni dai kaf zuri’a ta a kanku a gama tabbatattu, ga dai farin jini Allah Ya yi muku amma sai baƙar zuciya, wacca nasan wajen uwarku kuka gado, yo daman fulanin jeji ina zuciyar arziƙi a tare da su, Allah Ya kyauta dai.”  Abinda ta shigo da shi cikin tsakar gidan kenan a bakinta, Alhaji ne ya fara tarar da faɗin.  “Hajja Barka da safiya, sannu da zuwa.”  “Yawwa sannu.”  Ta faɗa tana kauda ido, Hajiya ma ta ce.  “Hajja sannu da zuwa, ina kwana.”  “Lafiya.”  Ta amsa a daƙile, Ra’is ma ya ce.  “Sannu da zuwa.”  Banza ta yi da shi, nima na ce.  “Sannu da zuwa.”  Aikuwa ta washe haƙora tare da faɗin.  “ ‘yar arziƙi ke nake ta baza idanun ganin, kinsan idanun ba kowanne ke da kyau ba, gashi ke ba zuwa kike ba uwar mai mugun nufi ta hanaki.” “Ikon Allah sai kallo, yau rikicin tsufan nan ya kawo ta kenan.”  Ra’is ya faɗa yana daga inda yake, ni kaina nasan rikicin tsufa ne, dan ina ga ma Yaya Radiya take magana akai, tin da ita ce ta auri jikan da take so.  “Kina ina ne, matso na shafiki, na shafi arziƙi.”  Ta sake faɗa, kamar wacca ƙwai ya fashewa a ciki haka na taka na je idan take.  “Sannu mai ƙashin arziƙi! Sannu ‘yar nan.”  Ta faɗa tana riƙe hannu, sannan ta juya ga Alhaji.  “Sannu tabbatacce, kai yanzu ace yarinyar nan tana da wanda yake sonta daga gidan arziƙi irin haka kamar gidan Ta ambo, amma ka ɓoye min, sai yaron da kansa ya nemeni ya kawo min kayan arziƙi, ka ji tsoron Allah.” Legendspen 08129553971 971*SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na tara     (09) Da ido kowa yake kallonta, dan babu wanda yasan ma suna saurayin nawa bare familinsa a tsakanin Alhaji da Ra’is da suka san maganar, bare Hajiya da batasan komai a kai ba.  “Hajja wane yaro kike magana a kai?”  Alhaji ya tambaya, dan shi tunaninsa ko Isah Nadabo zata ce, shine ta ce Ta ambo, dan dai dukkansu sunsan Familin Ta ambo ba ƙaramin ahali ba ne. “Ka ce haka mana, wallahi zama da wannan matar ta shafa maka mugun abu, shi ya sa na gwammaci na ƙyale mata kai ka je ka ƙarata daman ba wata tsiyar kake ban ba, to yanzu gashi ɗan gidan arziƙi yana son yarinyar Gawasiya take kowa, mai dai sunan Mutanen can, jiya da daddare yazo gidana ya cika shi da abun arziƙi sannan ya cika mini ƙugu da sulalla. Dan haka abinda nazo na faɗa ma shine, idan kana nan da wannan mummunan ra ayin naka na sai yara sunyi karatun yawudu da nasara ta ka sauke shi akan yarinyar nan, dan na yi mata miji na ce ya tura maka iyayensa ko sati yake so ka fito da kuɗi, kema ki fito da kuɗin shanu, aje a aurar da ita.”  Ta ƙarashe maganar tana kallon Hajiya, ƙasa Hajiya ta yi da kai ba tare da ta ce ko ƙala ba.  “Magana nake da kai fa.”  Cike da ladabi da girmamawa Alhaji ya ce.  “Hajja bangane kan zancen ba.”  “Baka gane ba, mene baka gane ba, ke yi masa bayani.”  Da sauri na kalle ta na ce.  “Wane bayani kuma?”  “Yaron da yake son ki.”  Gaba ɗaya idanuna sun cika da ruwa na rasa me zance.  “Ko kema bakya son sa? ‘yai mai baƙin hali.” Gaba ɗaya Hajja ta rikita gidan, kowa ya kasa gane inda ta nufa, kuma taƙi ta yi bayani yadda za’a gane sai faman cewa take.  “Ni dai na faɗa ma zai tura iyayensa.”  Da ta gama banbamin ta tafi, Hajiya ta kalleni bayan Alhaji ya fita rakata ta ce.  “Wane yake zuwa wajenki?”  Ra’is ya yi saurin cewa. “Akwai saurayinta da yake zuwa wajenta wanda har Alhaji yasan maganar ya ce yana son ganinsa.”  “To shine ɗan gidan da Hajja take faɗa?”  Girgiza kai ya yi sannan ya ce.  “Wannan ne kuma bansaniba.”  “Dake nake.”  Hajiya ta faɗa tana kallona, na gyaɗa kai kamar ƙadangariya sannan na ce.  “Eyh… eyh, a gidan Ta Ambo yake.”  “Aina ya san Hajja? Har yasan gidanta?”  “Ya tambayeni yana son ya je ya gaida ‘yan uwanmu ne na ce masa na Hajiya ba anan suke ba, na Alhaji ne anan.”  “Shi baki faɗa masa halinta ba.”  “Bansan ma zai gane gidanta ba, kuma na ce mai ma bata son mu.”  Daidai lokacin Alhaji ya shigo, sai da ya ƙare min kallo sannan ya ce.  “Yaron da yake zuwa wajenki ɗan gidan Ta  Ambo ne?”  “Eyh Alhaji.”  “Shine kika ce masa ya je ya sami mahaifiyata, ya bata abun duniya?” Da sauri na girgiza kai sannan na ce.  “Wallahi A’a.”  “To Lallai kisa shi yazo.”  Daga haka ya juya ga fice, ni kuma na yi cikin ɗaki.  A ranar na sake sanar da Sardauna saƙon Alhaji, cikin wayo da dabara ya dinga tambayata abubuwam da Alhaji yake so akaina, nan na sanar dashi zance karatu, kuma yana son nasami miji mai ilimi da tarbiya.  Bayan Magariba Alhaji ya dawo, sabida zuwan Sardauna, wanda bai zo ba sai ƙarfe takwas. A tsakar gida suka zauna mu kuma duka muna cikin ɗakin gaba ɗayanmu, amma hankalina gaba ɗaya yana kan su Sardauna da Alhaji. Yadda Sardauna yake magana da Alhaji cikin ladabi da nuna tsantsar tarbiya ya burge mu duka da muke cikin ɗakin, Hajiya, Ra’is da Ni.  Yadda yake nunawa Alhaji zallar soyayyarsa ga karatu da burin na zama wani ya haifar da soyayyarsa mai girma a zuciyar Alhaji, haka kuma yadda yake magana da Alhaji kamar yana karɓar Umarni wajen mahaifinsa ya nuna tsantsar tarbiyarsa.   “Ma sha Allah, ubangiji Allah Ya sanya albarka a taraiyyarku, ya albarkace ku da zuri’a ta gari.”  Alhaji ya faɗa, daga cikin ɗakin na ji wani daɗi ya ratsani har cikin zuciyata.  “Ka sanar da magabatan naka, sai su zo Allah Yasanya alheri.”  Maganar Alhaji ta ƙarshe kenan, bayan Sardauna ya tafi Alhaji ya haɗa mu gaba ɗaya har da Yaya Ridwan.  “A gaskiyya na yaba da irin nutsuwa da tarbiyar yaron nan da Nana ta kawo, dan haka na bashi damar ya turu magabatan nasa.”  “Gaskiyya ne Alhaji, ni kaina daga cikin ɗaki na tsinci nitsuwa a cikin muryarsa, Allah Ubangiji yasanya alheri.”  “Amin Amin.”  Farin ciki ya cika rayuwata gaba ɗaya, bacci rabi da rabi na yi shi. Gari na wayewa ko takwas ban bari ta cika ba na je gidansu Amina na sanar da ita, ƙawayena sai murna suke.  Kwana biyu a tsakani ‘yan uwa Sardauna suka zo gidanmu aka tsayar da rana wata uku, lokacin na kammala jarabarwata.  Lisaafi ya canja, abubuwa sun ɗau harama, ni da ƙawayena babu zama. Kowa ya ganni yasan wanda nake so zan aura, Su Yaya Rumaisa da Yaya Radiya da Ra’is kowa farin ciki yake ta ya ni, idan ka cire Ridwan da na kasa gane kansa, ko sakarwa Sardauna fuska ba ya yi, idan muna tare zai zo ya wuce sau ɗari bai isa ya kalleshi ba, Hajiya ta ce mu dinga taɗi a cikin ɗakinsu amma Yaya Ridwan ya ce ban isa ba, gaba ɗaya gani nake ya tsani Sardauna.  A cikin wannan lokacin ne auren Isah Nadabo yazo da matarsa Adizatu ‘yar jihar kano, biki ne aka yi shi na alfarma daidai zamani, kuma mun halarci komai na bikin tun daga farko har ƙarshe, kano ne kawai ba mu je ba, Amma Alhaji, Yaya Ridwan, da Ra’is duk sun je. Tun da Sardauna ya ji na ce masa matar Isah Nadabo  ‘yar kano ce Sardauna ya dame ni akan naje ta koyan girkin kano, yadda ake sarrafa fulawa ayi gurasa da su cincin.  Ni ban fiya shigewa mutane ba, amma akan sardauna sai da na shigewa Anty Aadiza, daman ba ta da wata matsala tana son mu ta ɗauke mu ƙannen miji, ta ɗauki Hajiya Uwar miji, dan ko da aka kawo ta daga kano hannun Hajiya aka miƙa ta. A hankali ta fara koyan sarrafa fulawa mussamman da na faɗa mata wanda zan aura ne ya ce yana so.  Hajja ba ta cika zuwa gidanmu ba, tun da Sardauna ya kan je ya kai mata kuɗaɗe da kayyaki har gida lokaci zuwa lokaci. Shi ya sa ta ƙyalemu mu ci tsiyarmu.  Kwance tashi ba wuya a wajen Allah, har muka kammala jarabarwamu, inda bayan sati biyu aka ɗaura mana aure da Sardauna, biki ne aka yi shi na garari, masu kuɗine ke hada hada ta ko ina a wajen events ɗin da familin su Sardauna suka shirya. A cikin raina babu abinda nake ƙauna da tsumaye irin a gama wannan kiɗe kiɗen akaini gidan Sarduna, inda zan samu soyayya mai daɗi.  Daga wajen taron aka wuce da ni gidana na Takur, tun ina cikin mota nake mamakin irin girman gidan, da aka fito da ni kuma sai na fara mamakin irin tsaruwar gidan.  Haka aka shiga dani cikin gidan, kowanne ɗaki a tsare yake kuma sannan a cike yake da kaya.  “Allah Sarki Alhaji da Hajiya, Allah Ya ƙara muku arziƙi, lafiya da nisan kwana.”  Na faɗa a raina lokacin da aka shiga dani ɗakin gadona, nan masu kawo ni suka zauna suna ta faman yi min nasiha, nikam gani nake kawai ƙari suke domin Abinda Alhaji da Hajiya suka faɗa min, bana jin zan sake samun nasihar da ta wuce wannan, haka ma ‘yan uwana. Yaya Ridwan ma ganin dai dagaske za a kaini ɗakin aure ya zo ya same ni da yau da safe, ya yi min nasiha mai ratsa jiki. Akwai kalma da ya faɗan guda ɗaya wacca har yanzu tana nan daram a kunnuwana.  “Nana ba tsanar saurayinki na yi ba, da ki kaga ina miki haka, Nana ina matuƙar kishin ‘yan uwana mata, bana son naga wani abu zai wahalal da su.”  Wannan kalmar kishin ta tsaya min sosai a zuciyata, nasa hannu na goge ƙwallar da ta fito daga idona.  Haka aka tafi aka barni da ƙawayena, suma ba su wani daɗe ba Sardauna da abokansa suka zo suka tafi da su, aka barni daga ni sai Sardauna.  “Nana!”  Ya kira sunana a hankali, nima na amsa masa a hankali.  “A yau sai mu gode Allah da ya cika mana burinmu, ya nuna mana wannan ranar ga ni ga ki a matsayin miji da mata, tabbas ina cikin farin ciki da hakan Nana, ina farin ciki marar misaltuwa.”  Ya ƙarasa maganar tare da tasowa zuwa inda nake, yasa hannu ya yaye lulluɓin fuskata, ya kalli fuskta da take sheƙi, ya sa hannu ya jawo ni jikinsa.  “Nana kina jin sauti bugun zuciyata.”  Na ɗaga kai tare da cewa.  “Ina ji.”  “Nana ki saurare abinda zan faɗa daga zuciyata bawai bakina ba, ina matuƙar ƙaunarki Nana, ƙaunar da nima bansan irin ta ba, ina jinki cikin jini da tsokar jikina, ina son ganin walwalrki Nana, ina jin wani irin shauƙi idan na ganni ga ki.” Kalaman Sardauna suka kashen jiki, suka haifar min da wani irin yanayi mai daɗi, tabbas Nana na yi sa’ar miji, na yi da ce da miji na gari.  “Nana.”  Ya faɗa yana matseni a jikinsa.  “Kina jin yadda nake ji?”  “Uhm.”  “Kina jin kamar ki cinye ni, na koma jikinki gaba ɗaya?”  “Uhm.”  Haka Sardauna ya yi ta yi min kalamai masu nuna zallar soyayya da shauƙin ƙauna, mun kusa awa ɗaya a wannan yanayin sannan ya ce da ni.  “Nana ta shi ki yi alwala mu yi sallah, mu miƙa godiyarmu ga Allah.”  A hankali na tashi daga jikinsa na nufi toilet na ɗaura alwala, bayan na idar na fito shima ya shiga ya ɗaura tashi alwala daga nan ya ja mu mu ka yi sallah, tare da addu’o’i na neman albarkar aure.  Daga nan muka ci nama da lemo sannan ya kalli ni.  “Kin gaji ko?”  “A’a.”  “Ta shi ki canja kaya ki zo mu kwanta.”  Daga nan ya tashi ya fice, nima na tashi na sauya kaya zuwa na barci, bayan na sauya na zauna ina jiranshi. ‘Yan mintina kaɗan shima ya shigo cikin shirinsa na bacci.  “Wai baki kwanta ba? Sannu Nana.”  Ya faɗa yana hawa kan gadon.  “Matso kusa.”  Ya faɗa tare da jawo ni, ya rugume ni jikinsa a hankali bacci mai daɗi ya ɗauke mu. A raina ina faɗin haka ake aure? Haka rayuwar take da daɗi?  Kiran sallar asuba ne ya tashe ni na buɗe idona, idan da sabo na saba dan dama shine daidai lokacin tashinmu. Ina matsawa daga jikinsa ya buɗe ido. “Come on Nana.”  Ya faɗa cikin magagin bacci.  “Kiran sallah ake.”  Na faɗa a hankali.  “I know, matso!”  Ya faɗa yana kamo ni, ba shiri na koma na kwanta ya sake rungume ni bacci ya sake ɗibansa, ni kam idona biyu ina ta faman saƙe saƙe. Ba shi ya farka ba sai 6:30.  “Honey! Baki san irin gajiyar dake jikina ba.”  Ya faɗa yana kamo hannuna, na yi murmushi sannan na ce.  “Ina kwana.”  “Mu fara sallah mana.”  Toilet na shiga, sai kawai na ga shima ya biyo ni.  “Mu fara yin wanka, sai mu yi sallah.”  Abu kamar wasa  Sardauna ya ce tare zamuyi wanka, haka kuwa akayin, daga nan mu ka yi alwala mu ka gabatar da sallah.  Bayan mun gaisa ne ya ce.  “Ya kwanan sabon gida?”  Na yi murmushi sannan na ce. “Da godiya.”  “Nana i really love you, i love you smile please keep it.”  Muna zaune muna hira ya hanani tashi naga shiga kicin,  sai da aka yi masa waya sannan ya tashi, can ya shigo yana cewa. “Je ki haɗa mana breakfast.”  Na tashi na fita, wani babban kwando nagani ya ajiye akan centre table na ɗauka na kai kan dinning sannam na shiga kicin. Ba ƙaramin mamakin irin girman kicin ɗin na yi ba, dan zai iya fin girman wani ɗakin a gidanmu, amma duk da haka an zuba kaya masu yawa a ciki.  Da kansa ya zagaya dani ko ina na gidan, ya nuna ko ina har da ɗayan part ɗin, da kuma ɗakinsa na nan.  Sai can yamma sannan ‘yan uwana suka yi min zuwan nan da suke yi, da daddare ma cikin irin yanayin jiya muka sake kwana da Sardauna.  Har tsawon kwana goma da aurenmu muna zaman jin daɗi da soyayya da Sardauna ina samun soyayya da kulawa a wajen Sardauna, yana riritani kamar jaririya, ko ƙwai da ake tsoron fashewarsa.  Ranar juma’a su Malaika, Amina da Fauziyya suka shirya zuwa, tun safe nake rawar jiki da zuwansu, na faɗawa Sardauna ya kai sau goma, tun yana kulani har yafara min banza, haka har ya tafi ofis, girki wajen kala uku na yi musu sabida murnar zuwansu.  Wajen ƙarfe ɗaya suka zo, har wani tsalle na yi da na gansu, suma cike da farin ciki suka tarbeni suna murnar ganina cikin farin ciki, bayan sun zauna na shiga yi musu safarar abun sha, lemo kala kala na gora da na kwalli, sannan kuma wa’yanda na yi da kaina.  “Oh my, Nana kinga yanda kike glowing.” Malaika ta faɗa tana kashen ido.  “Nana duk waɗannan abun shan namu ne mu kaɗai, duniya sabuwa.”  Amina aminu ta faɗa, na yi dariya sannan na ce.  “Ku yara ashe haka aure yake da daɗi? Haka ake rayuwar auren, ai wallahi aure yafi komai daɗi idan kuka sami irin mijina. A shawarce karku ce zaku zauna, wallahi kuna komawa gida ku ce sai anyi muku aure.”  Legendspen 08129553961 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na goma     (10) Dariya suka kece da ita sannan Malaika ta ce.  "Yarinya ta ji daɗin aure."  Ni kuwa na ce.  "Ba dole ba? Mene wanda nake so mijina ba ya yi min, a zaman nan namu sau uku yana fita dane manyan wajen cin abinci, gaskiyya  duk wacca ta yi dacen miji ta yi riba."  Haka muka yi ta shan hirar mu muna dariya, wajen ƙarfe biyar Sardauna ya kirani a waya, a gabansu na ɗauka ya ce dani yana son na yi masa cous-cous da miyar kaza. Ina gama wayar na kallesu sannan na ce.  "Bara na shiga kicin."  "Kaga matar aure." Suka faɗa suna dariya, suna nan zaune na shiga kicin na fara haɗa masa girki, sai dai sanda na duba friza ɗaukar kaza babu kaza, sai a lokacin na tuna gaba ɗaya na yi amfani da ita, waya na ɗauka na kirashi sai dai bai ɗauka ba. Sai kawai na ɗora cous-cous ɗin. Ina cikin Kicin ɗin Fauziya ta sanar da ni cewar zasu tafi, haka na fito falon mu ka sake taɓa hira kafin su ka tafi, Naira dubu biyar na basu na ce su hau mota, ni kuma na dawo kan girki na.  Ashe Sardauna ya kira ni ban kula ba ina kicin wayar na falo, ganin lokaci zai ƙure sai kawai na ɗora miyar na yi masa ta nama, amadadin kaza tun da duk nama sunansa nama.  Bandaɗe da gama abincin ba ya shigo, da murna ta kamar ko yaushe na je na tare shi, na yi tsalle na faɗa jikinsa ya rungumoni yana faɗin.  "Hon yau bana jindaɗi."  "Meke damunka?" Na tambaya ina amsar jakarsa hannunsa, zama ya yi kan kujera tare da miƙamin ƙafarsa na fara cire masa takalmi.  "Wane mistiyacin yaro ne a family, ya dawo ƙasar shine yake neman yi min rashin kunya."  Ya faɗa yana taɓe baki, sai duk na ji ba daɗi. "Ka yi haƙuri ka ƙyaleshi kawai."  "No! Turaki bai isa na ƙyaleshi ba, dole na ɗau mataki zan nuna masa ni ba sa'ansa ba ne."  "Kai Sardauna shi Turaki?"  Tambayar da na fara yi kenan, kallona ya yi sannan ya ce.  "Granny ce ta sama na sunan dukkanmu, sa'a na ne, kusan lokaci ɗaya aka haife mu da shi, amma na girmeshi. But seriously Nana tun ina ƙarami bana son yaron nan, abokin dabi na ne, komai na yi sai ya ce zaiyi, natsani na ganshi da abuna ma gaba ɗaya."  "Ka daina faɗin haka Hon, ba a cewa antsani musulmi, mussaman shi da yake ɗan uwanka."  "Ƙyale wannan maganar Hon! Yunwa nake ji." Ya faɗa yana tashi zuwa wajen dinning, nima na ta shi na shiga da takalmi da jakarsa ɗaki.  "Me ya sa ma bazan yi biyyar aure ba, bayan Yaya Rumaisa da kanta ta ce Biyayya na ƙara soyayya kuma gashi ina gani, ni ina mamakin matan da basa yi wa mazajensu biyayya. Me suke nema a duniyar?."  Na faɗa bayan na ajiye kayan, sannan na fito falon yana zaune kan kujerar dinning yana jirana. Plate na fara ajiye mai sannan na buɗe cous-cous ɗin na fara zuba mai, sai bayan na gama na buɗe miyar na fara zubawa.  "What is this?"  Ya katseni.  "Abincin."  Na faɗa muryata na rawa, leƙa miyar ya yi sannan ya kalleni.  "Bance miki chicken nake so ba, me ya sa naga beef?"  "Ahm. Daman kazan ne babu, da na duba sai naga saura nama shi ya sa na yi na nama"  "Me ya sa baki sanar dani ba?"  "Na kiraka baka ɗauki wayar ba."  "Ban kiraki ba bayan nan? Me ya sa baki ɗauka ba, sabida kina can ƙawayenki sun zo ko? Ni ban isa na sa ki abu ba? Ban isa na ce ga abinda nake so ba ni da gidana?"  Ya yi maganar cike da tsawa kamar zai dake ni.  "A'a ba haka ba ne, ka yi haƙuri wallai gobe zanyi."  "Dalla malama rufemin baki, shashasha marar hankali, abinda zaki fara yi min kenan? To wallahi Nana baki isa ba."  Yana gama faɗin haka ya yi fatali da abincin ya yi waje, wani irin zafi na ji ya mamayeni, kamar ba wacca take cikin Ac ba, jikina gaba ɗaya ya fara rawa ba shiri na tsugguna ƙasa na fara raira kuka, sai da na yi kusan minti talatin ina kuka na babu mai rarrashina sannan na tashi daga baya na shiga kwashe kayan, sannan na gyara wajen na koma kan kujera na zauna. Ba Sardauna ya shigo ba sai wajen ƙarfe tara, kallo ɗaya ya yi min ya ɗauke kai, da sauri na tashi ina faɗin.  "Dan Allah ka yi haƙuri."  Ɗauke kai ya yi ya shige ɗakinsa, ya tura ƙofar ya murɗa mukulli, haka na yi ta faman bugu amma bai buɗe ba, sai wajen ƙarfe 12:30 na je na kwanta ganin Sardauna bazai buɗe ba.  Wannam shine karo na farko da muka sami saɓani da Sardauna tun zuwana, wannan ta kasance baƙar Rana a wajena domin naga abubuwa kala kala, ko baccin kirki ban iya ba.  Washe gari da safe tun da na yi sallar asuba ban koma ba, na shiga kicin haɗa masa abincin kari mai kyau da lafiya, sabida ina son na burgesa kuma ya yafe ni. Gurasar da na koya wajen Anty  Adiza na yi masa da miyar farfesun naman rago, na juye a plast na kawo kan dinnig ɗin. Na shirya na dawo falon na zauna jiranshi, bai fito ba sai ƙarfe tara kasancewar yau Asabar ne kuma babu aiki.  "Ina kwana?"  Kallona ya yi sannan ya kalli dinning ɗin, ya nufi wajen ba tare da ya ce da ni komai ba. Na bi bayanshi ina kuka ina faɗin.  "Dan Allah ka yi haƙuri, wallahi bazan sake ba dan Allah." "Uhm." Ya faɗa yana zama kan kujerar, ya fara zuba abincinsa, in tsaye akansa ina faman zubar hawaye amma ya yi banza dani kamar bai san ina wajen ba, har ya kammala sannan ya kalleni.  "Ki biyo ni."  Ba shiri na bi bayanshi zuwa falo, ya zauna akan kujera ni kuma na zauna a ƙasa, sai da aka kusa minti biyar sannan ya ce.  "Nana!"  "Naam."  Na amsa masa. "Nana wanene ni a wajenki?"  "Mijina."  Ya kalle ni sannan ya ce.  "Shine matsayina a wajenki?"  "Eyh."  "Nana"  Ya sake kiran sunana, na sake amsa masa.  "Nana,  ina so ki canja min matsayi daga na mijin da kika ba ni. Ina so ki bani matsayin da yafi kowanne matsayi a wajenki, ki bani matsayin Uwa, Uba, dangi, Nana ina so ki ɗauke hankalinki daga komai daga kowa ki mayar dashi kaina, Nana ni kaɗai. Nana irin son da nake yi miki bana so naga kina mu'amala da kowa a duniya, Nana ina jin kishin akan kowa ciki har da 'yan uwanki, Nana ko da mace naga kina magana ina jin zafi a cikin raina, ina jin duniya ta yi min zafi. Nana zaki iya yi min wata alfarma?"  "Eyh zan iya."  "Nana ina so ki cire kowa a rayuwarki, ki cire komai sai ni Nana, ni kaɗai zaki gani, ni ka ɗai zaki ji."  "Na yi maka alƙwarin."  "Ta shi ki zauna anan."  Ya faɗa yana nuna min kusa da shi, na miƙi na zauna ya kama hannuna.  "Nana ni mijinki ne, mai sonki! Da ya sadaukar da dubban farin ciki dan ya rayu dake, Nana ina son sakayya mai girma dan Allah."  Da irin waɗannan kalaman Sardauna, ya dinga dasa zazzafan tausayinsa a zuciyata, har na ji babu wani a rayuwata sai Sardauna.  Daga nan komai ya dawo daidai tsakanina da  Sardauna, muka ci gaba da rayuwa cikin soyayya da farin ciki. Sardauna yana yawan magana akan ayyukan gida sun yi min yawa, hakan yasa ya kawo 'yar aiki me ta ya ni aiki, a farko mun fara zama tare da ita tana ta ya ni aiki, amma daga baya na fara fuskantar abubuwa sun fara yi wa Sardauna yawa, mussaman yadda wata rana ya fara magana akan yawan kuɗin wuta da aka kawo masa bill. Hakan ya sa na sallami 'yar aikin, da ya yi magana na ce masa bana son yana yawan kashe kuɗi, amma bayan kwanaki ya sake dawo da ita na sake sallamarta, a haka ya kawo har guda uku ina sallamarsu, daga baya ya daina kawo wa.  Haka mu ka ci gaba da rayuwa cikin so da ƙaunar juna, Sardauna yana riritani tamkar ƙwai akan cokali wanda ake tsoron faɗuwarsa. Ina rayuwa ta cikin farin ciki kowa yana ta ya ni murna, na je gida sau biyu sannan na je gidan yayuna sau ɗai ɗai, suma sun zo baki ɗaya har da Ra'is amma banda Yaya Ridwan.   Ranar wata juma'a bayan ya dawo, yake sanar dani wai ƙarshen wannan satin ranar Lahadi suna da baban family meeting, kuma ana buƙatar kowa yaje har da iyalansa.  Tun da Sardauna ya faɗan na fara tunani, danni ban taɓa haɗuwa da 'yan uwansa ba tun lokacin biki, sai dai 'yan gidansu da ya kaini sau ɗaya. Hajiyarsa mutuniyar arziƙi da ƙannensa duk ba su da matsala, amma fa wannan ya ce wai babban famili meeting, duka 'yan uwansa zasu je.  Washe gari na kira Yaya Rumaisa a waya na faɗa mata bayan ya fita, nan ta bani shawarar irin yadda zan shirya, yadda zan kama kaina a cikinsu, da sauran abubuwa. Ranar Sunday tun safe, na fara shirina amma ina yin komai cikin nutsuwa sabida kar ya ga rawar kaima, kamar yadda Yaya Rumaisa ta faɗa. Bayan munyi breakfast ya ce dani.  "Ki shirya muje da wuri, zan ajiye ki sai na fita zuwa 12:00 ake farawa, zan dawo kafin lokacin."  Tashi na yi na shiga ɗaki, na ƙarasa shirina daga nan na dawo falo lokacin shima ya gama shiryawa.  FADA AREA 09:30am.  Babban gidane na gaske da ya ji kayan more rayuwa, mutane ne tsilli tsilli cikin gidan sabida basu gama hallara ba, yana gaba ina binsa a baya ya yiwa wayanda ya ga dama magana, ya yi banza da wayanda ya ga dama, har ya kaini inda Hajiyarsu take tare da 'yan uwansu. Dukkansu na gaishesu kamar yadda na ga ya yi, suna ta samin albarka kowacce fuskarta washe da fara'a.  Bayan mun gaisa ne na koma gefe na zauna a babban falon inda naga Lubna ƙanwarsa ta zauna, shi kuma ya tashi ya fice. Kowa sabgar gabansa yake masu danna waya na dannawa masu hira na taɓawa cikin harshen turanci, ba ruwan kowa da ni, hakan ya sa nima na ja waya ta na fara dannawa, nan ga message ɗin Amina Aminu cewar an fara cire WAEC, sun cire tasu a cafe kuma sun sami 8 credit, sannan an fara registration ɗin Jamb. Na yi mata reply da cewar Okay idan ya shigo zan faɗa masa sai ya ciro min.  "Salamu alaikum." Da sauri na ɗaga kai sabida yadda na ji muryar kamar ta Sardauna sai da ba shi ba ne, wannan wani matashin ne daban shima ɗan gayu amma Sardauna yafi shi kyau nesa ba kusa ba.  "Uncle Turaki Welcome."  Na ji muryar wata yarinya ta faɗa tana nufo sa.  "Dotti, how are you."  Ya faɗa cikin wani irim ƙwarewar turanci, kamar ma bai iya hausa ba, a raina na ce.  "Wannan shine TURAKIN? Duk rashin girman SARDAUNA da nake gani, sai naga wannan yafi ƙanƙantar jiki."  Na faɗa a cikin raina, ƙarasowa ya yi inda iyayensu suke ya fara gaishesu cike da girmamawa, ya ɗan fi Sardauna sakin fuska amma Sardauna yafi shi komai na duniya, haka kawai sai na ji bai yi min ba sabida yadda suke da mijina. Daga nan ya juyo inda sauran yayunsu suke suka ya fara gaishesu, yadda yake ɗan wasa da su Sardauna duk ba ya haka, dan ko da yazo daga Ina wuninku, Ya iyalai shikenan ya tashi ya fice. Amma shi gashinan sai hira suke har da wasa da yaransu, suma sai jan shi suke da hira mafi akasarin hiran na su ma cikin harshen turanci suke.  A raina na ce. "Su waɗannan sun maida turanci yaren uwarsu da ubansu, ba ga yaran ba ga iyayensu ba." Daga nan kuma ya juyo inda muke nan kowa ya fara gaisheshi, nima na gaisheshi ya amsa ba tare da ya kula da ni baƙuwa ba ce a cikinsu. Wata da na ji suna cewa Sister Seemah ta ce. "Blood meet your Amarya." Ta faɗ tana nuno ni, gaba na ne na ji yana faɗawa sabida irin kallo daya ke min, sai da ya kalleni tas sannam ya dawo inda nake.  "Daga ina?"  Ya tambayeta, Sister Seemah ce ta matso sannan ta ce.  "Sardauna's Wife."  Kallona ya sake yi tare da jijjiga kai, sannan ya ce.  "Matar ƙanina kenan? Me sunanta?"  "Nana." Lubna ta faɗa.  "Sannu Amaryarmu, sunana Turaki yayan mijinki Sardauna, kuma babban abokinsa."  Na yi murmushi sannan na sake cewa.  "Ina kwana?"  "Lafiya ƙalau, ina ɗan uwan nawa?"  "Yanzu ya fita zai dawo." Na faɗa a raina na fara mamakin me ya sa to basa mutunci da Sardauna, amma shi ga shi anan yana sakar min fuska har da cewa matar ƙaninsa.  "Okay zan jirashi a main falo, ya gidan?"  "Lafiya lau."  "To Allah Ya sanya alheri, Allah Ya bada zaman lafiya."  Na buɗe baki da niyar cewa Amin, muryar Sardauna ta cika ɗakin.  "Malam matsa daga kusa da matata."  Legendspen 08129553971. *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na sha ɗaya.     (11) "Kai yaro gyara bakin ka."  Turaki ya faɗa yana kallon Sardauna.  "Ni kake cewa yaro?" Sardauna ya faɗa yana ƙarasowa wajen.  "Relax boy."  Turaki ya sake faɗa, hannu Sardauna ya sa ya fisgo ni na faɗi ƙasa, da sauri Matar da na ji suna cewa Hajiya Maama ta shi tana faɗin.  "Sardauna bita a hankali, ba ita a lamarinku." "Maama me ya sa zai zo kusa da iyalina, mene haɗin shi da ita."  "Shut up malam, bansan har yarintarka ta kai haka ba, na yi tunanin duk wani abu da yake tsakaninmu zai ƙare a tsakaninmu ba sai ya shafi iyalanmu ba, amma na fuskanci har yanzu da yarinta a kanka."  Cike da wani irin fushi Sardauna ya yo kansa, Hajiya Maama ta ce.  "Dakata Sardauna, anan kaine baka da gaskiyya. Duk wani abu da yake between you guy's ku tsayar da shi iya ku biyu, karku sanya familinku." "But she is not our family she is mine, my family, so ya yi baya da ita."  "Sardauna karɓi wannan, ka ce she is not our family she is yours?"  Wata dattijuwar mata ta faɗa, ni mamakina ma yadda aka yi ta iya turanci har haka.  "Dada wasa yake."  Turaki ya faɗa, sai a lokacin na fuskancin yafi Sardauna wayo ne.  "No let him, allow him to say his mind."  "Dada wasa nake."  Sardauna ya faɗa.  "Are you kidding your parents?"  "Wannam tsohuwa da mita take." Na faɗa a raina.  "Kar nasake jin irin wannan."  Ta faɗa tare da komawa ciki, ni kuma na tashi zaune, Sardauna ya fice sauran kowa ya koma ya zauna. Haka su ka yi ta fira har zuwa 12 iyayensu maza su ka shigo suka tattauna abinda zasu tattauna daga nan aka ci gaba da hirarrakin su, banda Sardauna da ya fice. Duk lokacin da na ɗaga kai sai na ga munyi ido huɗu da Turaki, wani lokacin ya yi min murmushi wani lokacin kuma ya yi kamar bai ganni ba.  Haka aka gama zama kowa ya watse ya tafi, Sardauna ko a mota baice dani ƙala ba, bare kuma da aka koma gida. Nima dai ban ce masa ci kanka ba haka shima bai ce min ba, sai zuwa dare bayan ya sake dawowa na yi masa sannu da zuwa, sai da ya kallani sannan ya ce.  "Aini yanzu dole na kama kaina, nasan matsayina tun da kin raina ni bakya so na."  Bakina har rawa yake na fara magana.  "Wallahi ba haka ba ne, shi da kan shi ya yi min magana kuma ni bansan shi ba."  "Waye? Kar dai ki ce min yaron can, bana so! karki sake maganarsa a gidana, ni ba akan shi nake magana ba, akan ƙyale ni da kika yi." "Ba ƙyaleka na yi ba wallahi Allah.."  "To me kika yi?"  "Bakomai, kawai bana so ma cika takura ma a yadda kake ranka babu daɗi."  Jawoni ya yi kusa da shi, sannan ya ce.  "Ni na taɓa ce miki kina takura min?"  "A'a ba ka ce ba."  "To me ya sa kika yi wannan tunanin?"  Na yi shiru na rasa amsar da zan bashi. "Uhm? Magana nake."  "Kawai."  Kawai me?"  Ya faɗa yana miƙewa tare da ni zuwa ɗaki, ya ajiye ni kan gado ya hawo.  "Ina tambayarki?"  "Ba kowa."  "Tom."  Ya faɗa yana matseni a jikinsa, tun zamana a gidansa kusan wata huɗu yau ce rana ta farko da wani abu na aure ya shiga tsakanina da shi. sardauna ya zauna da nine kaiwa yana kallona kuma yana ba ni kula, sai a wannan ranar nagane aure da wata wahalal shi da ake faɗa.  Tun daga wannan lokacin zamanmu da Sardauna ya canja taku, da ba ya nuna sha'awarsa a kaina, amm yanzu kullum ne, ɗaiɗaikon rana kune yake fashi. Tun ina jin wahala da azaba har komai ya wuce. Irin azabar da na sha a ranar ta mantar da ni zance jarabawa ta sai da aka kwana biyu sannan na tuna, shima sakamakon wayar da muka yi da Ra'is yake ce min na ba shi number exam card ɗina zai duba min, Jamb kuma na yi wa mijina magana ya yi min Regostration.  Da dadare bayan ya dawo na faɗa masa amma dai ya yi banza da ni kamar bai ji ba, haka aka kwana ɗaya aka kwana biyu shiru bai sake min maganar ba, a kwana na uku na yanke shawarar ƙara tun kararsa da maganar, sai dai a lokacin ma banza ya yi da ni.  Washe gari Ra'is ya zo mun da sakamakona na WAEC da NECO na yi ta murna ganin result ɗin, ya ce da ni wai Abba ya fara tambaya akan wai na yi rijistar JAMB ko banyi ba, kar su rufe.  Lokaci na farko da na fara yi wa wani na gidanmu ƙarya akan al'amuran gidan aure.  "Ra'is ban masa maganar ba, kwana biyu suna aiki a kamfaninsu ne, bai ma cika dawowa da wuri ba, amma in sha Allah zan faɗa masa."  "Tom yakamata dai gaskiyya, kinsan su Jamb ba wani dogon lokaci suke badawa ba fa."  "Nasani sosai, ina Yaya Ridwan?"  "Yana nan."  "Baice ka gaisheni ba? Shi fa bai taɓa zuwa ba. Kuma ya je duk  gidansu Yaya Radiya."  "To ai su yayunsa ne, ke kuma ƙanwarsa ce. Yaya Radiya ma tana gida."  "Zuwa ta yi?" "Eyh, ta kwana biyu ma."  "Tafiya mijin na ta ya yi?"  "A'a saɓani suka samu da shi, wai yana da wata matar a waje."  "Mata a waje? Yau she ya yi auren ba mu sani ba?"  "Bawai matar aure ba, abokiyar iskanci."  Kama baki na yi sannan na ce. "Lallai chaɓ." "Jiya kuma Hajja ta zo ta sauke kwandon rashin mutuncinta tsaf a gidan."  "Da aka yi mata me? Ita kuma." "Wai ai Yaya ce ba tasan mene darajar miji ba shi ya sa ya fita ya nemi wata."  Na yi matuƙar mamakin jin wannan abun, ko da yake a son zuciya irin na Hajja inda za a bata kuɗi ta bataƙi ko kisa aka yi ba ta ce, wanda ya mutum shi ya taso ya kashe wanda ya yi kisan. "Ita ta sani, yanzu mai Alhaji ya ce?"  "Ita Yaya ta ce ba zata koma ba, haka kawai ya kwaso wata cutar ya goga mata."  "Wallahi Allah da gaskiyyarta, kuma ko ya ce zai daina ba lallai ya daina ba tun da daman ba mutunci ne da shi ba."  Na faɗa daman ni tun da ba gaisawa ma muke da shi ba.  "Haka Yaya Ridwan ya faɗa, ya ce ko kotu ne sai anje an raba auren."  "Uhm, ni kaɗai ce Yaya Ridwan ba ya so."  Kallona Ra'is ya yi sannan ya ce.  "Waya faɗa miki haka?"  "Ra'is alamunsa na gani, kana ganin ko Allah Ya sanya alheri bai yi min ba, kai ko gidana bai taɓa zuwa ba, farkon aure na da na kirashi da ya ɗaga ya ji ni ce sai ya katse."  "Kinsan halinsa dai."  Ra'is ya faɗa yana miƙewa. "Ni zan tafi."  "Tsaya na baka abu ka kaiwa Hajiya." Na faɗa ina shigewa ɗaki, na ɗauko wata leda da daman na ajiyeya na ba shi ya tafi sannan shima na bashi dubu bakwai, wanda shine kuɗina gaba ɗaya.  Ko da Sardauna ya dawo sai da ya tambayeni waye ya zo? Na yi mamaki sosai na yadda akayi ya sani, shi ba camera ce da shi ba amma ya sani, ko da na ce masa Ra'is ne bai wani saki fuska ba. Bayan ya ci abinci na ɗauko masa takardar da Ra'is ɗin ya ciro ya kawo min, buɗar bakinsa sai cewa ya yi.  "Kun dage dai sai kin yi karatun ko?"  "Alhaji yana so kasani kaima."  "Uhm."  Ya faɗa ya ci gaba da danna wayarsa, ni kuma na zauna ina wasa da ƙafarsa. Sai da aka kwana biyar da maganar sannan Sardauna ya kai ni wajen Rijsitar jamb, shima sai da na sake masa magana sannan ya kai ni.  Masu kuɗi basu da al'adar zuwa gidan mutane, amma kuma suna da kirki idan anje musu, duk ranar da mukaje gidan Hajiyarsu kamar zata cinye ni sabida kulawa ita da ƙannensa, haka idan na kiranta a waya shima kamar zata goyani, duk mutan gidansu suna sona sosai idan na je musu, sau ɗaya ƙanwarsa Lubna ta zo shima daga lectures ta dawo shine ta biyo.  Haka lokacin zana jarabarwar Jamb ya zo Sardauna ya kai ni na yi, idan na sami maki 189 na ji daɗi sosai domin zan sami Addmission a FUD, haka a gida kowa ya ji daɗi ya yi murna.  A lamarin Yaya Radiya kam, ta dage ba zata koma ba, haka Yaya Ridwan ma domin sun binciko asali ba iya wannan abun ba ne ya baro ta gidan, bayan neman mata harda shaye shaye yake yi, shima dalilin da ya sa su ka gano wata rana ne yazo gidan namu a buge ya yi wa musu tijara da hau na ƙarshe, ya ci musu mutunci sai da Ra'is da Yaya Ridwan suka fita dashi. Amma da Hajja ta zo yin ta ta tijirar sai cewa ta yi an dake shi an ji masa rauni. A yanzu Alhaji ya daina damuwa da abubuwan Hajja tsakanin shi da ita sai dai tom, amma ya faɗa mata a wannan maganar ba yadda ya iya tun da yarinya da 'yan uwanta sun dage akan ba zata koma ba. Sardauna ya ɗan san maganar tsilli tsilli ban saki jiki na faɗa mai komai ba, tun da naga kamar bai son maganar. Da kan sa ya kaini gidan Anty Adiza har sau biyu a cewarsa duk ranar da na je ina samu sabon ilimin sarrafa fulawa.  Kwance ta shi ba wuya a wajen Allah har aka zo lokacin da jami'a ta fara raba Addmission, kuma ina cikin mutanen da suka samu a lokacin farko. Alhaji bai taɓa zuwa gidana ba sai a lokacin ya zo ya yi wa Sardauna godiya akai, daga nan na fara shirye shiryen makaranta sai dai har zuwa wannan lokacin babu ciki a jikina, tun ina ɓoyewa har abim ya fara damuna, har na fara sanar da Sardauna amma sai ya ce shi haka yake so, da ya ga dai na fara damuwa da al'amarin bisa ga auren Malaika da akayi bayan namu, ta tafi jihar kano kuma a yanzu ta sanar da ni cikinta ya shiga watan haihuwa. Hakan ya sa na sake damuwa, sai shima ya fara nuna damuwarsa, yake kuma kwantar min da hankali. Da dai ya ga abun namu ba ƙarami ba ne sai ya ce na shirya zai kai ni naga likita. Rasheed shekoni special hospital ya kaini, asibiti da na yi ma sa gani na biyu a rayuwata, lokacin da mai mashin ya tsaya gyara. Kai tsahe wajem likitan muka je wanda daga yanayinsu kasan abokinsa sa ne, bayan ya yi masa bayani likitan ya sa na kwanta akan wani gado anan ya yi dube duben da zai yi sannan ya ce na koma na zauna.  Kusan mintina goma sha biyar, sannan ya fara bayani. "Madam mahaifar ta yi ƙanƙanta ne da ɗaukan ciki, amma kuma yau da gobe ya sa ta fara girma, idan kika yi haƙuri kuma kin zuwa ganin likita in sha Allah za ta buɗe."  "To wane magani za'a ba ni."  "A'a babu magani fa."  "A'a a bata wannan pils din mana."  Sardauna ya faɗa, wani kallo na ga Dr ya yi masa sannan ya ce.  "Ai zai yi mata ƙarfi, sai dai a dinga ba ta sha sau daya ko biyu a wata."  "Eyh hakan ma ya yi."  Sardauna ya faɗa, sannan ya dafa ni yana faɗin.  "Nana ki daina damuwa kin ji ko, rashim haihuwar ba matsala ba ne."  Na gyaɗa masa kai, sannan ya ce.  "Ki jirani a mota."  Na miƙe na fice na barsu a cikin ofis ɗin, ina fitowa waya ta ta hau ruri, ina dubawa na ga sunan Ra'is na ɗaga da faɗin.  "Ra'is ya aka yi?"  "An raba auren Yaya Radiya fa."  Gaba ɗaya sai na ji wani iri, Allah ya gani ina matuƙar tsoron mutuwar aure a rayuwata.  "Yaushe?"  "Shekaran jiya Hajiyarsa ta zo ta yi wa Hajiya rashin arziƙi. Yaya Ridwan ya sa 'yan sanda suka kamata, amma a ranar aka sake ta shine ɗazu ya aiko da takardar."  "Ka ce tashin hankali aka yi kenan? Allah Ya tsare gaba zan shigo in sha Allah."  "Amin amin, ya shirin makaranta?"  "Ranar monday zamu fara lectures."  "Allah Ya sa albarka."  "Amin amin."  Daga haka na katse wayar na shiga mota na jira Sardauna, sai da ya ɗau wajen mintina ashirin sannan ya fito, a hanya nake sanar da shi mutuwar auren Yaya Radiya, ya tausaya har muka koma gida.  Ranar Monday ranar da zan fara lectures Sardauna ya tashi baya jindaɗi kwata kwata, ta dole na haƙura da makarantar ban je, sabida bai samu kansa ba sai wajen sha biyu na rana. Haka washe gari ma ya tashi da irin ciwon, gaba ɗaya na ruɗe kamar shafar aljanu, duk asuba idan ya fara juye juye bai nutsuwa sai rana ta fito, kusan sati biyu a haka, ta dole na haƙura da makarantar sabida lafiyar mijina tafi min komai a duniya, har da ni kaina.  Legendspen 08129553971. *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na sha biyu.     (12) Abu kamar wasa ciwon Sardauna yana ta tsananta har lectures ɗin mu ta yi nisa, tun da ina bibiyar al’amarin makarantar ta waya har wasu malaman suna shirn fara yin test.  Tun ban damu da lamarin makarantar ba har na fara damuwa, mussaman da Baba ya kan kirani ya ce min ya karatu, gashi har Ra’is ya aiko ya kawo min dubu ashirin wai na ƙara kuɗin makaranata kar a bar mijina da wahala, ranar har da ƙwallata, da Sardauna ya dawo na yi masa maganar sai ya ce da ni, lafiyarsa zan sa a gaba sama da komai, daga ba ya na ce masa ai har lectures ɗin 12 muna yi har 2 wata ma 4 ce dan haka idan ya fita zan iya zuwa, ya daɗe yana kallona kafin ya ce ya amince.  Daga nan na fara zuwa, amma duk wata lectures ta ƙarfe takwas ko goma babu ni a ciki, cikin ikon Allah kuma ciwon na shi ya fara baya daga nan na samo damar hallartar ta ƙarfe goma amma dai banda ta takwas. Tabbas yanayin makarantar ta burgeni, kuma ina jindaɗin zuwa makarantar sannan na mayar da hankali akan karatun sosai, dan dana ta shi cikin masu ƙoƙarin ajin na shiga ana damawa da ni.  Kwance ta shi babu wuya a wajen Allah, mu ka cinye zangon karatu na farko, bayan munyi jarrabawa muka sami hutu na sati biyu, a lokacin ne naje gida Alhaji yana ta farin ciki da alfahari da ni da karatun, Sardauna kam ya sha albarka kamar Alhaji zai ari baki, ita ma Yaya Radiya Addmission za a sama ta a makarantar lafiya, washe gari na je gidansu, Hajiyarsa da Lubna gwanin sha’awa sai kuma na tarar da babbar yayarsa ta England ta zo jiya Sister Noor suke ce da ita, dake su lamarinsu kamar ‘yan chochi kowa Sister ce, kamar baki!  Sardauna na fita TURAKI ya shigo, wanda rabona da shi tun ranar Family meeting ɗin da suka yi wanda ba asake wani ba sai bayan wata shida kuma da dukkan alamu wata shidan ya kusa dan na ji Sister Noor tana cewa tana nan za ayi.  Yana ganina ya washe min baki tare da faɗin.  “Matar ƙani.”  Kaina a ƙasa na ce.  “Ina kwana?”  “Lafiya ƙalau ya kike ya gida?”  “Alhamdulillah.”  Daga nan ya shige wajen Hajiya, ita ma bai daɗe ba ya fito ya yi wajen Sister Noor, ita ce suka daɗe suna hira kusan awa ɗaya, har ya tafi Sardauna bai dawo ba. Bayan Sardauna ya ɗaukeni da yamma daga nam ya kai ni gidan Anty Adiza sai wajen tara ya dawo ya ɗauke ni.  A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah har muka cinye hutunmu muka koma makaranta, abubuwa suka ci gaba da gudana ba mu daɗe da komawa ba sakamakon jarabawar mu ya fito idan na sami 3.67cgp, na yi murna sosai kowa ma ya yi murna banda Sardauna, kuma na yi alƙwarin ƙara dagewa na sami sama da haka a wannan zagon, inda zan sami CGPA mai kyau.  Zancen ciki dai har yanzu shiru kamar an shuka dusa, magani dai ina sha sau biyu a wata wani lokacin ma Sardauna ya kan ce min na sha sau uku a wata ko zan samu cikin ya zo da wuri.  Wannan karon bansami zuwa Family meeting ɗinsu Sardauna ba sabida ina da test har biyu a ranar, dan mun kusa fara jarrabawar zango na biyu, daman haka karatun yake da zarar zangon ya fara zaka ga yazo ƙarshe. Lokacin jarrabawa da ya zo Sardauna ya tsiromin da wani abu, baya bari na na yi karatu kwata kwata, ya ta takuramin ayi ta abu ɗaya ba gajiya, gashi kuma ya ce dani yana so a rage amfani da kayan wuta sabida jan kuɗi, ya ce a daina amfani da dutsen guga da abin girki, na ce to daga baya ya ce adaina kumna ac sai dai fanka, duk da yanayin zafi na amince sabida tausayin da na ke yi masa. Wata rana bayan ya dawo ya ce wai na daina amfani da firinji kuma iya nawa, anan ne na so na ce wani abu sabida yanayin zafin da ake yi na gari amma ya ce da ni. "Nana! A gidanku babu firinji, baki sa ba shan sanyi ba, sabida yanayin unguwar ku ma zafi ake yi, dan haka anan ma ba zai zama wani abu ba dan na ce ba zaki dinga kunna firinji ba, sabida yanayin jan wutarsa." Tun daga wannan lokaci bansake gigin kunna firji ba da duk wani abu mai jan wuta, haka na yi ta fam da karatu ga wasu ƙarin wahalhalu da Sardauna ya fito da su, duk da ni ban taɓa ganin su da idon wahala ba, sai na bautar aure.  Cikin ikon Allah muka kammala jarrabawarmu, mu ka sami hoto na wata biyu, a wannna lokacin komai ya dawo daidai tsaƙani da Sardauna duk da bai janye wasu dokokin na sa ba, amma yanzu mun kan zauna mu yi hira, mu kan yi ‘yan wasannin mu da muka saba yi a baya.  Kwancw ta shi ba wuya a wajen Allah muka cinye wata biyu na hutu a kafara shirye shiryen komawa makaranta sai dai Sardauna ya fito min ƙarara ya ce da ni bazan koma makaranta ba, na yi tunanin a wannan lokacin ne ba zan koma ba shi ya sa ban damu da hakan ba. Amma ganin har an kusa cin tsakiyar zango na sake yi masa magana sai ya ce da ni gaba ɗaya karatun ne ba zan ci gaba, wata ƙara na ƙwalla tare da zubewa a ƙasa, abun mamaki sai ga jini yana zuba bayan faɗuwar da na yi, ko da muka je asibiti sai aka ce ɓari na yi. Na yi danasanin faɗuwar amma kuma na ji ɗaɗin cewar yanzu mahaifata ta yi ƙwari zata iya ɗaukan ciki.  Bayan na dawo gida na yi ƙaramar jinya na warke, mu ka ci gaba da Sardauna inda ya ce shi fa a’a Boko Haram, ba zam ci gaba. Na yi kuka sosai na nuna masa damuwata amma Sardauna ya ce a’a, ranar da abun ya yi ƙamari sardauna ya zaunar dani ya yi ta yi min bayani amma na nuna masa ni a’a Abbana yana son karatun nan gashi na fara har na cinye shekarar farko ga shi course mai kyau ma aka bani. Amma sardauna ya fara yi mini magiya yana haɗani da Allah.  “Dan Allah ka barni, tun da na fara kamar yau ne zan kammala.”  Na faɗa ina goge ƙwallar da ta fito daga idona, ya kama hannun tare da faɗin.  “Sakko nan.”  Na sakko na zauna, hannunsa yana cikin nawa ya fara magana.  "Nana, ina da arziƙin da zan riƙe ki bake kaɗai ba har da gidanku, muna da arziƙin da bazamu taɓa talauci ba, Nana a cikin gidan nan zaki zama kamar sarauniya ne, Nana bana son karatun boko nan, Nana bana son cuɗanya da maza, ina miki so mai tsanani, ina miki kishi mai zafi Nana dan Allah dan Annabi ki haƙura da karatun." Gaba ɗaya jikina ya yi sanyi, maganganunsa gaskiyya ne dole akwai kishi a hakan, kuma ni ina son sa bana son abinda zai dameshi amma Alhaji fa?.  “Sardauna Alhaji fa? Na yi Yaya da shi?”  Wani murmushi ya sakar min, ganin ya fara nasara a kaina tin da har na fara tunanin yadda zaayi da Alhaji.  “Honey! Idan kin amince Alhaji ma zai amince ba zai zama mai wahala ba.”  Shiru na yi, ta ɓari ɗaya ina jin son mijina yana rura zuciyata, ta ɓari ɗaya kuma ina tausayin Abbana na yadda yake jindaɗin karatun nan da nake yi.  “Kin ji dan Allah My love.”  “Shikenan zan sake tunani.”  “No wane tunani, kawai ki amince idan ba haka ba shikenan zan barki ki yi karatun, nima sai na tafi can America na ƙaro karatuna bayan shekara bakwai sai na dawo.”  Kamar saukar aradu haka na ji maganar tasa, ya tafi ya yo shekara bakwai ya barni, ina zan sa raina?  “A’a shikenan na haƙura.”  Na faɗa amma har cikin raina ban so ba kuma banji daɗin haka ba. Allah Ya gani ina son karatuna, kuma ina tausayina Alhaji, ban ma san yanayin da zai shiga ba idan na sanar da shi hakan.  “Amma ya na ga kamar kin damu.”  Kallonsa na yi sannan na ce.  “Bansan ya Alhaji zai yi ba idan ya ji hakan.”  “Ba zai ji komai ba, ai yasan nine mijinki a yanzu nike da iko akanki, shi sai dai mu yi masa biyayya, kuma ai mun yi masa tunda kin fara karatun.”  “Uhm.”  Kawai na faɗa, dan bansan wani abu da zan iya ƙara cewa ba, ni gaba ɗaya ma kaina ciwo yake min, hutu nake buƙata.  “Je ki kwanta.”  Kamar mai jira na miƙe na nufi ɗaki na kwanta, sai dai gaba ɗaya bacci ya ƙaura ce min, na rasa abin yi kwata kwata, waya ta na ɗauka na shiga rubutawa Ra’is message ta whatsapp, na yi sa’a koma yan kai.  “Salam, Ra’is ina cikin damuwa Sardauna ya hanani komawa makaranta.”  Na tura masa, cikin ƙasa da mintuna biyu ya dawo min da amsa.  “Ki yi min ƙarin bayani, bangane abinda kike mufi ba.”  “Na ce ma Sardauna ya ce bazan ci gaba da zuwa FUD ba.” Na tura masa, can ya dawo min da amsa.  “Shi ya isa? Sai da kika yi wannan nisan?”  “Ra’is gaba ɗaya na rasa abinda yake min daɗi gashi result ɗin mu ya fita ɗazu har na duba.”  “Me kika samu?” “CGPA ɗina 3.84.” “Shine zai hanaki, kina da second class offer? Dole a san abun yi.” “Mene shawararka?”  “Zan yi magana da Yaya Ridwan.”  “Kasan ba zai shiga al’amura na ba.” “Me ya sa zai shiga mana, zaki ji duk yadda muka yi.”  “To karka kirani kamun magana kawai ta nan.”  “Me kike kalla haka a wayar, da dukkan nutsuwarki?”  Sardauna ya faɗa yana zama kan gadon, yaƙe na yi masa da baki sannan na ce.  “Da Ra’is muka yi magana.”  “Me kuka ce? Ko shawara kika nema wajensa?”  Na gyaɗa kai ba tare da na ce komai ba.  “Okay kin kyauta, ba ni wayar ki kwanta.”  Ba musu na miƙa masa wayar, na kwanta kamar yadda ya ce.  Washe gari da na ta shi na ga wayar a gefen drower na ɗauka na kunna data, ina shirin duba saƙon Ra’is sai dai babu lambarsa a wajen an goge ta, alamun Sardauna ya ga chat ɗin mu kenan ya goge?  Ajiye wayar na yi na fita zuwa kicin, bayan na haɗa komai na breakfast na ajiye masa, sannan na shiga toilet zan yi wanka, ina banɗakin na ji rurin wayata alamun ana kira, sai da na fito sannan na ga lambar Hajiya ce ke kiran, na yi tunanin zata iya kasamcewa Ra’is shi ya sa ban bi kiran ba na jira ya gama ya fita.  Sai bayan ya fice na dawo na bi wayar, Hajiya ta ɗauka bayan mun gaisa ta ce daman Ra’is ne kuma ya fita, na ce to idan ya dawo ya kirani. Daidai lokacin aka fara knocking ƙofa.  “Hajiya ina zuwa, an bugo.”  “To Nana sai anjima, Allah Ya yi miki albarka.”  “Amin amin.”  Na faɗa ina nufar ƙofar, Ra’is na gani na matsa masa ya shigo.  “Ina wayarki?” “Ga ta na miƙa masa.”  Dubawa ya yi ya ga babu lambarsa, sannan ya miƙa min ta sa.  “Karanta.”  Karɓa na yi na duba message ɗin da aka tura masa da lambata.  “Ka fita sabgar gidana, zan yi komai da kaina.”  “Ra’is na duba da safe na ga ko ka tura min saƙo na ga babu lambarka gaba ɗaya.”  “Na kira da safe naga ta na sa failed, mijinki ya duba wayarki kenan?”  “Da alama kam.”  “Lallai mutumin nan, Nana mun yi magana da Yaya Ridwan, ya ce tun farko abin da ya guda kenan, amma dai tabbas mijinki ba isa ya hanaki karatun nan ba.”  Zama na yi akan kujera, sannan na ce.  “Ra’is ni wallahi duk tsorona Alhaji, da halin da zai shiga.”  “Nana ko ba dan Alhaji ba, ko dan gobenki maza ba kowa ke da tabbas ba, yanzu ji dai Yaya Radiya, yanzu da ta yi karatun ta tun farko da yanzu an nema mata aiki.”  “Wallahi hakane Ra’is, duk jikina ya yi sanyi amma zan sake lallaɓashi nima.”  “Tom shikenan, mu dinga waya a wayar Hajiya.”  Ya faɗa tare da tashi ya tafi, da Sardauna ya dawo sai ya hau banbami, faɗa na ba gaira ba dalili ya ma ƙi bari mu yi wata magana da shi, na rasa aina ya sami labarin zuwan Ra’is ko CCTV ce da shi da bansan yana da ita ba? Wani ɓari na zuciyata ya ce mai gadi, da sauri na dakatar da wannan tunanin, sabida zato zunubi ne.  Kwata kwata Sardauna ya daina fahimta ta, ya daina zama da ni, ya daina magana da ni, faɗa ta ko ina? Na sanar da Ra’is halin da ake ciki ya ce da ni wai tsoratarwa ce amma idan ya ga na dage akan matsayata dole zai sakko tun da yana sona.  Abu dai sai gaba yake, har ta kai Yaya Radiya da Yaya Rumaisa sun san da maganar kuma babu wacca taban shawara akan na amincewa Sardauna akan ajiye karatuna, kuma na tabbatar dukkansu akan gaskiyya ne. Sardauna ya zuba min ido ni da ‘yan uwana akan harkar karatun da suka na ce sai na yi.  Ra’is ya ce da ni yau Yaya Ridwan zai sami Sardauna su yi magana, amma abinda ya ban mamaki yanda Sardauna ya shigo gidan yana wuci kamar zaki.  “Nana! Dole yau ki zaɓa ko ni, ko ‘yan uwanki da suke son ki yi karatun boko?”  Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na sha uku.     (13) (Not edit) "Bangane ba Sardauna! Bangane ba?"  Na faɗa ina miƙewa.  "Na ce ki zaɓa 'yan uwanki ko ni?"  Wani abu na ji ya daki zuciyata, bansan haka nake ba sai yanzu, nasan dai ina son 'yan uwana amma bansan zan iya zaɓarsu akan Sardauna ba sai yanzu.  " 'Yan uwana mana."  Ya kalle ni sosai sannan ya ce.  "Nana 'yan uwanki?"  "Ina son su, suna sona Sardauna."  "Ni bana sonki Nana? Bana sonki? Wannan shine sakayar soyayyar da zaki yi min?"  "Sardauna ina sonka! Ina sonka, matsayin miji kake da shi a wajena mutum mai daraja a rayuwata sama da kowa, amma tabbas 'yan uwana abun so ne, kaima kana da su kana son su, kuma na zaka juri na yi wani abu mara kyau akam su ba."  Zama ya yi akan kujera, sannan ya ce.  "Nana ni mijinki ne, dole na yi kishinki sun san dalilin da ya sa bana son ki yi karatun? Sabida ina da kishi mussaman na ki, ban taɓa kishin wata mace a duniya ba sama da ke, Nana wallahi har cikin zuciyata nake kishinki bazan iya jurar gani kina fita kullum ba, bazan iya ba. Amma idan sun dage shikenan Nana zan sauwaƙe miki kije ki yi karatun acan, dan dama na fuskanci so suke su raba mu, zan bar musu." Ban taɓa tunanin jin wannam kalmar daga bakin Sardauna ba ko a mafarki, sai da na ji gabana ya yi wani irim faɗuwa. Na ɗaga kai na kalleshi amma na kasa magana, kawai na tsinci kaina da shigewa ɗaki na barshi s wajen.  "Rabuwa da ni Sardauna akan karatu? Tabbaa Sardauna baya son karatun nan, kuma hujjarsa ɗaya ita ce kishi, amma ai abinda kake so shi kake kishi, tabbas yana sona, nasake tunani."  Haka na yi ta ƙulle ƙulle da kwance kwance a cikin raina har wayewar gari, bayan na kammala masa abun karyawa ya ci na koma ɗaki, kasanxewar yau weekend ne bai fita sai rana kuma na ji yana cewa wai yau Big Daddy zai dawo, ko waye hakan oho masa.  Ina zaune cikin ɗaki bayan na sanar da Yaya Radiya yadda muka yi da shi, tana ta mamakin yadda aka yi baya son karatu har haka, kuma gasu gidan 'yan boko? Ni kaina abun ya ɗaure min kai sosai da sosai. 'yanzu Sardauna ya sake ni ina na kama ni Nana, zan iya rayuwa ba na jin numfashim Sardauna a kusa da ni kuwa?.'  Irin tambayoyin da nai ta jefawa kaina kenan har zuwa yamma, ko ayyukan gidan bansami damar yi ba sai da yamman, ina cikin aikin su Yaya Radiya da Yaya Ridwan da Ra'is suka zo, nasan akan maganar ne sabida ba sa so Alhaji ya san da maganar, ni kam Allah Ya gani karatun ya sauka daga kaina, amma an sauke min shi haka na ji, kalmar saki ta girgizani.  "Wai dagaske kike sakinki ya ce zai yi?"  Yaya Radiya ta faɗa cike da ruɗewa, bayan na gama gaya mata abinda ya ce da ni.  "Wallahi Yaya, sai na ji gaba ɗayan na tsorata."  "Kuma kina ganin dagaske yake?"  Ra'is ya tambaya.  "To nima bana ce ba, amma fa yau ko magana ba mu yi da shi ba, kawai ya ce duk abinda na yanke ya yi daidai."  "Amma mijin nan naki ɗan iska ne, bai da mutunci." Ra'is ya faɗa, na watsa mai harara, sannan na ce.  "Bana ciki da iskanci."  "Ridwan mene abun yi yanzu?"  Yaya Radiya ta tambayeshi.  "Ya bata zaɓi biyu, ko ta yarda da karatun ta rabu da shi, ko ta zaɓeshi ta rabu da karatun farin cikin iyayenta, tun a farkon mu'amalal su Nana ita ce ta bada kanta, na faɗa karta ta sawa ranta wai alfarma zai yi mata kowani abu. A gani na farko da na yi musu tare na gane soyayyarshi ta yi wa Nana mugun kamu, sannan ta bada kanta, ta zubar da darajarta, ina mugun jin kishin wannan abun? Ƙin kulashi ko shiga al'amuran da naƙi yi ba wai son shi ne bana yi ba, a'a zallan kishi ne bazan iya jurar gani tana ƙasƙantar da kanta ba, a matsayina na ɗan uwanta, jininta Nana kina tunanin wai idan muna yi wa samarinku wani abun haushi ne ko tsana? Tun a lokacin abinda na guda mata kenan, amma bata gane ba, a yanzu idan ta takura wallahi tsaf zai iya sakinta, ya mayar da ita ƙaramar bazawara ya cuceta."  Wani irim tsoro ne ya ratsani, ace Sardauna zai iya sakina, bana fatan wannan ranar wallahi na haƙura da karatun, ba zan ba chaɓ.  "To yanzu mene abun yi? Shikenan duk wani burin Alhaji ya tashi a banza, shikenan?"  Yaya Radiya ta faɗa, ni kam a raina ma ce. "Alhaji zai fahimta, zuciyar Alhaji tana da ƙwari zata iya ɗaukan hakan, ni kam bazan iya ɗaukan ƙaddarar rashin Sardauna ba."  "Nana me kika yanke?"  Yaya Radiya ta tambayeni.  "Na haƙura wallahi, na fasa karatun bazan iya ba." Na faɗa ina zubar da zafafan hawaye, ni kaina nasan ba abinda ke cikin zuciyata ba ne, amma bani da wani abun yi da ya wuce wannan.  "Kin haƙura da karatun fa Nana?" Ra'is ya faɗa, na gyaɗa kai sannan na ce.  "Ra'is ya zanyi, tunda ba ya so kuma ya riga da ya aureni ba yadda zan iya." "To sai me dan ya rabu da ke? Sai me?"  "Ra'is ba zan iya ɗaukan ƙaddarar rabuwa da Sardauna ba, zuciyata tana da rauni."  "Amma ai zaki iya ɗaukan ƙaddarar rashin mahaifinki ko?"  Yaya Radiya ta faɗa tana miƙewa, Yaya Ridwan ya ce.  "Abinda na faɗa muku kenan, tana yi masa mugun son da mu kammu ba ta ganin a matsayinta mutane, idan aka haɗa mu da shi."  "Nana namiji kina tare da iyayenki ma ya kuka ƙare, bare kuma kin ce kin zaɓeshi akan kowa da komai, ban ce ki kashe aurenki ba, kuma bazan baki shawara akam hakan ba, amma ko ya ne ki nuna masa iyayenki na da daraja a wajensa."  Yaya Radiya ta faɗa tana miƙewa, duka suka miƙe Yaya Ridwan ya kalle ni sannan ya ce. "Nana, Allah Ya shiga al'amirinki ya kawo miki mafita, da haske amma tabbas kina cikin duhun soyayya, ina guje miki lokacin da Sardauna zai fama miki SARTSEN da ya yi miki, dan tabbas Sardauna ya yi miki SARTSE a zuciya, ba zan miki baki ba, amma tabbas bazaku kwashe ƙalau da shi ba."  "Shikuma Allah Ya isa tsakaninmu da shi, dan tabbas ya cutar dake, wallahi Allah sai ya saka mana."  Ra'is ya faɗa, daidai lokacin Sardauna ya shigo fuskarsa ɗauke da murmushi, sai da ya ƙaraso inda suke sannan ya ce.  "Kunji kunya, dam girmanku kunzo kuna son kashe mata aure, mussamman ke."  Ya faɗa yana nuna Yaya Radiya, sannan ya ce.  "Kin kashe naki auren shine zaki kashe mata nata, ki zauna ke ba aure ita ba aure kuna yawo a unguwa daga nan ku ɓige da bin maz..."  Bai ƙarasa ba Yaya Ridwan ya sa hannu ya bige masa baki, har sai da jini ya fito, sannnan ya kama kwalarsa ya fara magana ya na wuci.  "Malam ka kama kanka, ka iya bakinka kafin na zubar ma da haƙwara wallahi Allah, ita dai da ka juyarwa da tunani ka je can, amma wallahi baka isa ka ce zaka gayawa wani magana ba a wajen nan."  Sardauna ya yi murmushi sannan ya ce.  "Na ji na juyar mata da ƙwaƙwalwar, ku yi abinda zaku yi idan zaku iya karatu ne wallahi ba za ta yi ba, dan na fusknci kai dayyus ne bakasan kishin kanka ba, bare kasan na wani, kuma ku fice mim daga gida, kar nasake ganin ƙafar wani cikinku, dabbobi."  Hawayene suka fara zubowa daga cikin idanuna masu ɗumi, gaba ɗaya na rasa abinda ke mim daɗi, me ma ya sa suka zo, me ya sa Yaya Ridwan zai dake shi?.  "Ba zamu sake zuwar ma gida ba, duk da cewa 'yar uwarmu na cikin gidan."  Yaya Radiya ta faɗa tana ficewa, Ra'is da Yaya Ridwan suka bi bayanta, nima na bisu da gudu ina faɗin. "Yaya ku tsaya dan girman Allah."  Amma babu wanda ya jiyo cikinsu, haka suka kaɗa kai suka tafi su ka barni ina faman zubar da hawaye. Ko da na dawo falon Sardauna baya nan , ban kuma nemeshi ba na shige ɗaki na hau kiran layinsu amma babu wanda ya ɗauka, har wajen ƙarfe goma babu Sardauna babu alamunshi, haka na kwanta bacci. Washe gari da safe ban iya ta shi da wuri ba, sabida ban samu bacci da wuri ba, karar bugun ƙofar da ake yi min ce ta tashe ni.  "Hon! Buɗe ƙofa."  Ƙafafuna na sauke daga kan gadon sannan na nufi ƙofar na buɗe, ban ko kalleshi ba na yi hanyar ban ɗaki.  "Ina zaki?"  "Wanke fuska zan yi."  "Okay ki yi sauri."  Bayan na wanke fuskar na ɗaura alwala na fito, kasancewar lokacin bana sallah ya ƙara ba ni damar mimiƙewa ina baccin.  "Zo.. ina da wani abu na baza ta."  Ya faɗa yana kama hannuna muka fito falo.  "Muje mu fara breakfast to."  Ya faɗa yana nuna min wajen dinning, da mamaki na kalli wajen sannan na ce.  "Waye ya yi girkin?" "Hon ai na iya girki sosai, muje ki ji."  Na nufi dinning ɗin, ya ja min kujera na zauna ya shiga zuba min, gasashen biride da ƙwai sai kuma shayin Na'a na'a. Komai ya yi daɗi sosai haka na ci ina mamakin yadda aka yi duk zaman nan Sardauna bai taɓa ce min ya iya girki ba.  Ina cikin ci ya tashi. "Hon ina zuwa." Ya faɗa tare da barin wajen, kusan minti uku sannan ya dawo hannun sa riƙe da wani ƙaramin kwali mai kyau.  "Hon, canki mene anan?"  Na yi murmushi sannan na ce.  "Mene?"  "Kin bani gari?" "Uhm na baka."  Aikuwa ya buɗe kwalin, kyakyawar sarƙa ta bayyana wacca aka yi ta da zinare sai sheƙi take.  "Hon naki ne."  "Wow, na gode."  Na faɗa bakina ya kasa rufuwa, ɗauka ya yi ya gwada min a wuyan, aikuwa ta yi kyau ta hau ɗas da ita kamat a wuyan nawa aka ƙera ta.  "Na gode."  Na sake faɗa.  "Akwai wani ta so." Ya faɗa yana kama hannuna.  "Hau na goyaki."  Ya faɗa yana sunkuyawa, aikuwa na hau ya ɗaukeni zuwa waje, bai sauke ni na  sai a harabar gidan.  "Kinga."  Ya faɗa yana nuna min wata ash ɗin mota. "Wow ta yi kyau wata ka sake siya."  "Eyh, amma wa ke, ta kice Hon."  "Ni.. tawa?"  Na faɗa cike da ruɗewa, ban taɓa hango kaina da mota ba a rayuwata, amma sai ga shi yau Sardauna ya bani, kai ina son Sardauna.  "Ko ba kya so?"  Na yi murmushi, sannan na ce.  "Na gode mijina, na gode Allah Ya biya ka da aljanna, Allah Ya ƙara maka arziƙi duniya da lahira."  "Amin Honey, na gode da soyayyarki a gareni, na gode sosai da sosai, muje ciki mu yi magana."  "Tom."  Na faɗa tare da binshi ciki, ya zauna akan kujera ya jawo ni kusa da shi, ya kura min idanu cike da wani irin tausayi na mussaman, ya fara magana cikin sanyin muryar tamkar mai shirin yin kuka.  "Nana, kin san me ya sa nake yin dukkan waɗannan abubuwan? Kin san dalilin da ya sa nake ƙoƙarin killace ki? Saboda Kishi ne, Nana. Kishinki nake yi fiye da yadda kike tunani. Duk lokacin da kika fita kika tafi wannan karatun na wahala, zuciyata ba ta samun natsuwa. Ina ganin kamar kowane namiji da kika bi ta gabansa, kallon sha'awa yake miki. Ba zan iya jure ganin wani namiji ya kalli kyakkyawar fuskarki ba, ko ya ji muryarki." Ya sauke numfashi, ya ɗago ya kalleni tare da matse hannuna dake cikin nasa.  "Wannan karatun na nan... Nana, wahala kike sha a banza. Kalle ki, yadda kika rame, yadda kika fita a hayyacinki saboda shiriritar malaman nan da ba sa ma san abin da suke koyarwa. Nana nasan ba kya gane komai, lokacinki kawainkike ɓatarwa, ni kuma bana son naga kina shan wahala. Shin darajar matar Sardauna Ta Ambo ita ce ta riƙa bin layin motar haya ko ta riƙa shiga aji ana cakuɗawa da ita? A'a, Nana. Matsayinki ya fi haka." Ya kamo hannuna ya ɗaura a kan saitin zuciyarsa, sannan ya cigaba "Nana, kalle ni cikin idanuwa na. Kin ga wannan motar? kin ga wannan zinaren? Duk ba komai ba ne a wurina idan aka kwatanta da darajarki. Ina son ki zama sarauniyar da ba ta taka ƙasa, sarauniyar da duniya za ta kalla ta san tana ƙarƙashin inuwar Sardauna Ta ambo. Nana a yanzu ina so na baki umarni, umarnin da nake son ki bi, ki je ki sami Alhaji. Ki gaya masa cikin lallashi cewa kin fasa wannan karatun na wahala. Ba wai kin daina ba ne, a'a ki gaya masa cewa ni Sardauna zan tafi ƙarin karatu a Turai, kuma na yanke shawarar tafiya da ke can. A can za ki yi karatu a manyan makarantun duniya, inda ba za ki sha rana ba, ba za ki fuskanci cin mutuncin malamai ba. Ba zaki yi karatu a wahala ba, can ne ya dace da matsayin matar Sardauna. Amma yanzu, kin daina ɓata lokaci a nan. Ki gaya masa kin gaji da wannan, kin fi son ki huta kafin mu tsallaka can ƙasar waje." "Nana, kina tunanin zan yaudare ki ne? Ni ne fa masoyinki. Idan ba ki bi maganata ba, za mu rasa wannan damar ta tafiya can tare, Nana ki amince da ni, sama da kowa, dan babu mai ƙaunarki kamar ni." Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na sha huɗu.     (14)  Na yi shiru har ya kammala, tabbas komai Sardauna yake faɗan gaskiyya ne, bai taɓa yi min ƙarya ba, kuma nasan bazai yaudareni ba, tun da da zai yaudareni ai da bai aure ni ba. Na buɗe baki yi zan yi magana wayarsa ta fara ringing, ya ɗaga yana faɗin.  “Sister Memah, ya sauka?”  Da ke wayar tana handsfree na ji ta ce da shi.  “Yeah! Kuma yana zama maganarku kai da Turaki ya fara, an sanar da shi faɗan da kuka yi last time a company, ya ce duka yana nemanku.” “My god! Big Daddy akwai faɗa yanzu shikenan zan kira anjima thanks you.”  Ya faɗa tare da kashe wayar, sannan ya juyo ya kalleni.  “Ina saurarenki.” A hankali na fara magana, cike kulawa da soyayya.  “Na yarda da kai Sardauna, na yarda baza ka taɓar cutar da ni ba, na baka ragamar rayuwata gaba ɗaya, zan yi amfani da ƙarfina da lokacina wajen sama maka farin ciki, zanje na sami Alhajin.”  Ban ƙarasa ba na ji ya rungumo ni jikinsa, tare da faɗin.  “Good girl, tare zamuje umara this year in sha Allah, i love you Nana.”  “Love you More Hon.”  Daga nan muka shiga lamarin soyayya, yinin ranar Sardauna kamar zai mayar da ni ciki, haka yake kula da ni, ko girki ba mu yi ba fita muka yi muka ci daga nan muka biya shopping duka a sabuwar motata, har ya fara nuna yadda ake tuƙi.  Gaba ɗaya na manta da wani abu ya faru jiya tsakanin Sardauna da ‘yan gidanmu, hankalina yana kan mijina ban nemesu ba, suma basu nemeni ba. Haka kusan sati guda sannan Sardauna ya ce da ni gobe zan je gidan.  ****** Shi ya sauke ni, amma bai shiga gidan ba ya tafi ya ce da ni idan ya dawo zai shigo,  shiga ta gidan na tarar da Yaya Ridwan zai fito.  “Ina yini?” “Lafiya.” Ya amsa bai ko kalleni ba, haka na shiga gidan jikina ba ƙwari, Hajiya ce a tsakar gidan tana ganina ta washe baki da faɗin.  “Zuwa ba sanarwa.”  Na durƙusa kasa na ce.  “Hajiya ina yini?”  “Lafiya ƙalau Nana, ya gida da me gidan” “Lafiya ƙalau Hajiya.”  Na amsa tare da shigewa cikin falonta, sai bayan na zauna ne na ce.  “Hajiya ina Yaya Radiya, da Ra’is?” “Radiya ta je makaranta wai za ta yi screening, Ra’is kuma yanzu na aiki shi siyo salat, baki ga Ridwan ba ne?”  “Mun gaisa Hajiya, kinsan halinsa.”  Murmushi ta yi tare da faɗin.  “Bari na sauke miyar nan.”  Ina nan zaune Ra’is ya shigo daga siyo salat, bai nuna mamakin ganina ba kuma bai nuna ɓacin rai ba, bayan mun gaisa Hajiya ta zuba mana abinci muka ci abinci, bayan Hajiya ta tashi ne Ra’is ya ce.  “Ya zancen makarantar?”  “Bawani labari Ra’is a yanzu har an fara jarrabawar zango na farko ma, na zo ne kawai na faɗawa Alhaji na ji abinda zai ce.”  “Allah Ya kyauta.”  “Me ya faru?”  Hajiya da ta shigo ta faɗa.  “Mijinta je ya hanata komawa makaranta, gashi har an fara jarrabawa.”  “Innullahi wa’inna illahir raji’un, garin ya? Me ya faru?”  “Wallahi Hajiya haka kawai, har Yaya Ridwan ya masa magana da Yaya Radiya ƙarshe ya yi mana rashin arziƙi.” “Hajiya Yaya Ridwan fa fasa masa baki ya yi.”  Na faɗa kamar zanyi kuka, da mamaki ta kalleni.  “A yaushe a ka yi haka?”  “An kwana biyu.”  “Amma babu labari.”  “Ai ni na yi tunanin ma sun faɗa muku, ni kuma gudun ɓacin ran Alhaji yasa mana na ja baya da zuwa.”  “Amma bai kyauta ba, to yana da wani dalili ne?”  “Eyh Hajiya, yana da dalilinsa mai ƙarfi ma, kuma ya ce da ni ƙarshen shekara zamu tafi turai, zai sama mini wata makarantar acan.”  “Tom Allah yasa, yawwa Nana ina fatan dai ba haɗa baki kukayi da mijinki ba, kika sha wani abu da zai hanaki ɗaukan ciki ba ko? Abun shiru ya yi yawa.”  “Eyh Hajiya ba abinda nake sha, nama je asibiti an bani magani ina sha.”  “To Allah Ya duba lamarin.”  Na amsa da Amin, sai yamma Yaya Radiya ta dawo, ko da na faɗa mata sai ta ce ita babu ruwanta da al’amurana. Yaya Ridwan kam bai ma sake kulani ba, sai yamma Alhaji ya dawo wanda daman ya saba dawowa a wannan lokacin sai ya koma gab da magriba.  Ya yi murnar  ganina sosai da sosai, mun gaisa dashi bayan ya shiga ɗaki na bi bayanshi, na iske shi yana duba wasu takardu. Na zauna a ƙasa, jikina duk babu daɗi haka nake ji na, bayan na zauna na fara wasa da yatsun hannuna yayin da zuciyata ke bugawa da sauri. Alhaji ya kalleni cike da kulawa, sannan ya ce.  “Nana, lafiya na gan kin biyo ni? Ko Akwai wata damuwa ne?" Cikin rawar murya na fara magana.   "Alhaji... dama... maganar karatuna ce. Na zo ne na roke ka alfarma." Alhaji ya gyara zama, fuskarsa cike da mamaki.  "Ina jinki Nana. Mene ne ya faru?" “Hon, idan kika je har kuka zaki yi masa, sannan karki kuskura ki nuna masa ni na tursasaki.”  Kalaman Sardauna suka dawo raɗau a kunnena, a hankali na fara fitar da ƙwalla daga idona, muryata ta fara rawa.   "Alhaji, don Allah ka yafe min, amma gaskiya na gaji. Karatun nan na nan... naga kamar wahala kawai nake sha, kuma gaskiya ba na gane komai. Kullum ina cikin fargaba, gashi kuma kishin Sardauna ya sanya ba na samun natsuwa. Yana yawan nuna min yadda yake damuwa idan na fita cikin maza a makaranta."  "Nana, me kike fada haka? Karatun da kika dage a kai shi ne yanzu kike cewa kin gaji? Ko Sardaunan ne ya hana ki?" Na tuna da  kashedin Sardauna, aikuwa na yi saurin kare shi.  “A'a Alhaji, ba shi ya sanya ni ba. Tausayina ne yake ji, sannan kuma yana da kishi sosai. Shi kansa yana so na yi karatu, amma ya ce ba zai bari na sake yin wannan wahalar ta nan gida nigeriya ba. Alhaji, Sardauna ya riga ya kammala shirinsa na tafiya Turai domin ƙarin karatu, kuma ya ce da ni zai tafi. Ya ce a can ne zan yi karatu mai kyau, a cikin nutsuwa da daraja, inda babu wanda zai rika kallo na ko ya shiga rayuwata." Na ƙara narkar da murya.  "Don Allah Alhaji, ka bar ni na ajiye wannan na nan. Na yi maka alkawari zan yi a can idan mun tafi. Shi Sardauna ya fi son na huta yanzu, na shirya wa tafiyar mu ta can gaba. Gani nake idan na nace akan wannan, zan ɓata masa rai, kuma ba na so na saɓa masa tunda kishinsa ne ya sanya shi yake son ya kiyaye ni." Shiru Alhaji ya yi na kusan minti biyar, har sai da na ɗago na kalleshi sannan ya ce.  “Kina ganin baki takura ba?”  “Ta takura Alhaji.”  Ra’is ya faɗa yana shigowa, sannan ya sake maimaita abinda ya faɗa.  “Alhaji wallahi duk abinda ta faɗa karanta ma ta ya yi, baya son ta yi karatun kwata kwata, tun kafin yanzu ta faɗa mana kuma har can muka je muka same shi dukan mu, dan ya fahimce mu amma ya yi mana barazanar sakinta idan muka takura.”  Alhaji ya ɗago y kalleni, yadda nake kuka ya bashi tausayi.  “Barazanar saki ya yi miki?”  Da sauri na girgiza kai na ce.  “A’a ƙarya yake Alhaji.”  “Ke dai kike ƙarya, amma dai ba ni ba.”  “Ra’is, ka tabbatar da abinda ka faɗa?” “Na tabbatar Alhaji.”  “Nana yanzu kin zaɓi miji akan kowa naki?”  “A’a Alhaji, bana so ya sake ni wallahi, Alhaji bana son ya rabu dani, ina son sa bazan iya jure rashin sa ba.”  Shiru ɗakin ya yi kusan minti goma, sannam Alhaji ya ce.  “Shikenan Nana je ki, Allah Ya yi miki albarka.”  Na miƙe tare da amsawa da Amin, haka na dawo falo na ci gaba da kukana, Hajiya dai ba ta ce dani komai ba haka Yaya Radiya, sai gab da magriba Sardauna ya kirani a waya ya ce da ni ya dawo.  “Ba zaka shigo ba?” Na faɗa masa muryata ba ƙwari, ya kashe wayar ya shigo, da Hajiya kawai suka gaisa tun da Alhaji ya koma, Ra’is yabi shi shago, Yaya Ridwan kam ko kallo bai ishe shi ba bare Yaya Radiya ta bata ma fito ba.  Ko da muka koma Sardauna bai tambayeni yadda muka yi da Alhaji ba, nima bansanr da shi ba. Sai washe gari yake sanar da ni, Wai Big Daddy ya basu gida shi da Turaki kuma gidan guda ɗaya ne amma part biyu ne kuma ya ce dole mu koma can, shima Turakin dole ya zauna acan idan ya yi aure. Ni bai dameni ba ko a jikina hankalina na bai kan komawa gidan, tunanin Alhaji kawai nake yi, bayan kwana biyu da na kira Hajiya take sanar da ni baya jindaɗi, gaba ɗaya na shiga damuwa ta dole na sa Sardauna ya kaini gida, na yi ta yiwa Alhaji kuka.  Sai da na yi zuwa uku a jinyar ta shi, har Allah Yasa ya warke, tun zuwan da ‘yan uwana suka yi gidana babu wanda ya sake zuwa har yau sai da Ra’is ya zo sanar da ni rashin lafiyar Alhaji.  Mun ci gaba da zuwa wajen Dr Ɗan Adala, yana ɗorani akan magani amma har yanzu haihuwa shiru, Sardauna yana ta shirye shiryen komawarmu sabon gida, ya hana duk wasu ƙawayena zuwa, ‘yan uwana kam dama ba wanda zai zo ko baice ba, gashi bana fita ko ina daga gida sai gida.  Bani da wani abu da nake yi sai kula da mijina, a kullum burina na yi abinda zaj faranta masa, son shi nake kamar raina, bana son duk wani abu da zai ɓata masa rai. Uwa uba ma tausayinsa da kullum ke cika min zuciya, wata rana bayan anyi refeiling ɗin gas yake sanar da ni kusan dubu saba’in aka yi ya gaji ga kuma yana son ƙara abubuwa na sabon gida, kamar wasa na ce da shi ko zai siyo min gawayi da abun girki na gawayi, ba arufa sati ba sai gashi da buhun gawayi biyu da kurfoti.  Rana ɗaya Hajja ta zo gidana tun daga ranar ba ta sake zuwa ba, sabida ya yi mata nisa gidan. Ranar da ta zo na ga tashin hankali wajen Hajja, har sao da ta fasa min plast ɗin ruwan zafi guda ɗaya, sabida fitina ta dinga yi kin kamar ƙaramar yarinya, kifin gwangwani ta ci ta ci har sai da ta yi amai, ƙarshe ta ci wai mai ƙarni na ba ta kamar ba ita ta zaɓa ba, kwana uku ta yi amma ji na yi kamar shekara uku ta yi. Sai da Sardauna ya zo da police dog gidan ta tafi, wai ita zaman jego za ta yi min tun da naƙi haihuwa. Amma tun da ta ga karen ta kwashe tsunmokaranta tafi Tunda ta tafi ba ta sake zuwa ba har yau. Ina zaune a gida na alfarma da ya ji kayan more  rayuwa amma dani da wadda ke zaune a gidan ƙasa na ƙauye marabar mu kaɗan ce.  Wannan shine asalin labarin.  Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na sha biyar.     (15) Ci gaba. Babu abinda na iya yi har Sardauna ya dawo, ina zaune jigum kamar wacca aka yi wa mutuwa.  “Honey! Me ya faru na ganki so sad?”  Tashi na yi na faɗa jikinsa na fara hawaye, gaba ɗaya ya rikice yana faman tambayata.  “Honey ki faɗa min mana.” Cikin muryar kuka na ce.  “Alhaji ne ba shi da lafiya sosai.” “Ya salam Honey, me yake damunshi haka?”  “Nima bansaniba wallahi.”  “Wa ya faɗa miki?”  “Ra’is, kuma Yaya Radiya ta kirani ban ɗauka ba, ashe faɗamin zata yi, sai yanzu da Ra’is yazo.”  “Ki kwantar da hankali kin ji, gobe zan kai ki.”  Ya faɗa yana zaunar da ni akan kujera. “Ki yi haƙuri kin ji, nima yanzu akwai wani abu da ya taso min.”  “Mene?”  “Big Daddy, bai kyauta min ba, ta dole sai ya haɗani da wancan yaron, ya sami duka labarin abubuwan da suke faruwa, a yanzu ya bamu gida ni da wancan yaron Turaki, ya ce dole mu koma can da iyalan mu mu zauna, gidan part biyu ne wai sabida faɗan da muke yi.”  “To ai nasani, wani abun ya sake faruwa?” “Eyh ya ce a cikin satinan zamu koma.” “Yanzu barin gidan nan zamu yi?”  “Eyh. Haka ya ke so kuma nan da next week.” “To shi Turakin yana da aure ne?”  “Ina yake da aure, yana can sai lalata da ‘ya’yan mutane.”  “Lalata kuma?”  Na faɗa a tsorace. “Eyh mn! Hon ace mutum ya yi wannan girman babu iyali ai kuwa sai dai idan lalata yake da yaran mutane, shekara talatin da ɗaya fa.”  “Talatin da ɗaya!”  Na faɗa cike da mamaki, ya gyaɗa sannan ya ce.  “To kinga kuwa.”  Ni ba zancen turakin yaban mamaki da tsoro ba, illah Sardauna, rufe idona na yi a take na tuna lokacin da na tambaye Sardauna shekarunsa, lokacin da ya zo makarantarmu. Ya ce da ni ashirin da biyar, har na ce irin mijin da nake so kenan, kuma ance shida Turaki ko kwana biyu ne a tsakaninsu ‘shin Sardauna ƙarya ya yi min a wancan lokacin? Sardauna zai iya yi min ƙarya kenan? Ko dai wasa yake min? Gaba ɗaya na ji jikina ya yi sanyi, ina so na tambayeshi amma bana buƙatar ɓacin ransa, ko ya ga kamar ban yarda da shi ba.  “Yau bazaki kwanta ba ne?”  “Uhm uhm zan kwanta mana.”  “Na yi tunanin dan Alhaji bai da lafiya ba zaki yi bacci ba, zaki zauna ki yi ta yi masa addu’a.”  Wani iri na ji a raina, gaba ɗaya a al’amurana ban iya tashi cikin dare na yi addu’a ba, idan ka ga na yi addu’a to bayan kowacce sallar farilla ce, tabbas mahaifina yana buƙatar hakan daga gareni.  “Eyh zan jira ƙarfe ɗaya na yi sallah.” Dawowa ya yi ya zauna daga miƙewar da ya yi sannan ya ce.  “Dagaske?”  “Eyh dagaske.”  “To ai yanzi akwai tazara sosai zuwa ƙarfe ɗaya, ki tashi mu shiga ciki idan kin yi bacci ni sai na tashi ki ƙarfe ɗayan.”  Ta shi na yi nabi bayanshi zuwa ɗakin, ko a ɗakin ma na daɗe a zaune har sai da ya ƙara cewa na kwanta zai tashe ni sannan na kwanta.  Ƙarar alam ce ta tashi ni, wanda na saita ƙarfe biyar daidai na asuba. ‘Sardauna ya manta.’ Na faɗa a raina ina saukowa, a gurguje na shiga banɗaki na ɗaura alwala na fara yin nafila kafin na gabatar da asuba, cikin hanzari na haɗa masa abin kari sabida ina son na fita da wuri, duk hankalina yana wajen Alhaji gaba ɗaya, ji nake a jikina kamar ni ce sillar kwanciyarshi wannan rashin lafiyar.  Haka Sardauna ya yi ta jan lokaci, ba shi ya fito ba sai sha biyu da kwata, kuma a hakan ma bai yi breakfast, har ƙwalla sai da na yi.  “Am sorry Hon, na ɗan duba wani abu ne shi ya sa na makara, yanzu ma ban ƙarasa ba amma ki zubamin breakfast ɗin na yi ke sai kije ki ƙarasa mayar da takardun kafin na kammala.”  Jikina duk babu daɗi, haka na je kan dinning na zuba masa farfesun naman rago da na yi sai kuma doya da miyar kaza da na dafa, sabida ina son tafarwa da Alhaji kuma nasan zaifi son dafaffiyar doya maimakon soyayyiya. Ina zuba masa ma nufi ɗakin, takardune duk ya zubar dasu a ƙasa, haka na shiga haɗasu ina zuba su a jakar da suke, ina yi ina ɗan duba wasu. Kwatsam idona ya faɗa kan wata takardar CV ɗinsa, date of birth na fara cikin karo da shi 11/08/1994.  ‘Ya tabbata dai Sardauna ba shekarunsa 25 ba?.’ Abinda na fara tambayar kaina kenan. ‘Amma me ya sa ya ɓoyemin, tabbas ƙarancin shekarunsa suna daga cikin abubuwan da suka sa na far son Sardauna.’ Na sake faɗa a raina, ƙwalla na ji ta fara zurara daga idona. ‘Ashe Sardauna zai iya yi min ƙarya? Kai ba zai yi min ba sai dai idan a lokacin ni ce na ji ba daidai ba, kunnuwana sun yaudareni.’  Haka na kwashe takardun ina ta saƙe saƙe a raina, ba mune mu ka bar gidan ba sai ƙarfe ɗaya da kwata, ni da na shirya tun tara. Kallon plast ɗin hannuna Sardauna ya yi sannan ya ce.  “Na mene wannan?”  “Ragowar doyar da na dafa ce, ban iya ci ba duk bakina ba daɗi, shi nake son tafiya ko Alhaji zai iya ci.”  “Shine kika bani kaɗan ni ko?”  “A’a ba haka ba ne?.”  “Ke kika sani.”  Ya faɗa yana shigewa motar, nima na shiga har mukaje gida baice dani ko ƙala ba, haka bai ce dani na gaida me jiki ba, amma na yi masa uziri ko ya yi mantuwa ko idan yazo ɗaukana zai shigo. Da sallama na shiga cikin gidan, mutanen gidanmu suna falon Hajiya duk sun yi zugum zugum, hankali a tashe na shiga ɗakin. Yanayin da naga Alhaji ya yi matuƙar tsorata ni,  yana kwance kamar marar numfashi, baya ko motsi.  Jikin Hajiya na faɗa ina faɗin.  “Yana ganshi a haka Hajiya?” Hajiya kuka take dannewa, ba ta iya ba ni amsa ba sai Yaya Radiya ce ta ce da ni.  “Haka kawai muka ga jikin nasa ya yi?”  Kusa da shi na matsa ina faɗin.  “Alhaji.. alhaji.” Yana kallona da ido amma bazai iya magana ba, Ra’is ya ce da ni.  “Ba zai iya magana ba fa.”  “Ina Yaya Ridwan baku tafi asibiti ba?.”  “Nana ki nutsu dan Allah.” Yaya Rumaisa ta faɗa, kowa fuska cike da hawaye.  Tashi na yi na janyo plast ɗin da na zo da shi.  “Alhaji dan Allah ka ci doyar nan.”  “Zo ki ba shi.” Ra’is ya faɗa, na matso kusa da shi na buɗe plast ɗin na ɗauki doyar na mammatse ta nasa masa a baki, a hankali ya cinye ta na ƙara samasa wata, sannan na ɗauki farfesun zan ba shi Yaya Rumaisa ta ce.  “Kar ki ba shi akwai maggi, ki ba shi iya doyar.”  Daidai lokacin Yaya Ridwan ya shigo ɗakin.  “Ga motar an samo.”  A raina na ce. ‘Yanzu mota ce ta hana akai mahaifina asibiti a lokacin da yakamata? Mene amfanin motocin da suke gidana? Ina ranar motar da Sarduna ya bani wacca ba na ko amfani da ita.” “Rid..wan.”  Alhaji ya faɗa a hankali, da sauri duka muka kalleshi, ya yi masa alamu yazo da hannu, sannan ya yi yawa Yaya Radiya da Yaya Rumaisa, ni da Ra’is daman muna kusa da shi, ɗai ɗai yake kallonmu sai da ya gama kallonmu duka sannan ya ce.  “Kaine Babba, kaine babansu Ridwan… ba ni na baka wannan nauyin ba Allah ne ya baka, ina mai rashim jindaɗin cewar zan tafi na barka da nauyi a kanka, Ridwan ka yafe min.”   Gaba ɗaya jikin mu ya yi sanyi kowa ƙwalla yake matsewa.  “Ku yi haƙuri kar ku yi kuka, ku haɗe kan ku ka zama tsintsiya ɗaya, ga mahaifiyarku nan, a tsahon rayuwata da ita babu komai sai alheri da kyautatawa, ku ci gaba da yi mata biyayya har ƙarshen numfashinku.”  Sannan ya nuna ni, ni da Ra’is.  “Sune ƙanana, ku yi musu afuwa, ku dinga haƙuri da su, mussaman Nana.”  Ya nuna ni, sannan ya ce.  “Tana sonku, ku yi mata afuwa kar ku taɓa fushi da ita, karku watsar da al’amuranta ƙaramar ku ce, ba ta da wani gata sai na Allah sai na ku.”  “Alhaji ka taso a kai ka asibitin dan Allah.” Hajiya ta faɗa tana kuka, ya girgiza kai yana sauke ajiyar zuciya sannan ya ce. “Na gode, na gode miki. Allah Na gode maka da rayuwa da ka bani, Allah ga Amanar ‘ya’yana da matata, Allah ga Amanarsu nan, Allah ka kula su, ka zame musu gata a duk inda suke ka kare su Ya Allah.”  Gaba ɗaya ɗakin ya yi shiru baka jin komai sai shasheƙar kuka, ya sa hannu ya nuna Yaya Radiya ta matso kusa da shi.  “Ki yi haƙuri, ki miƙa al’amuranki ga Allah Yana gani, kuma zai kawo miki mafita, ke ce babba Allah ne gatanku, ki haɗe kanku dan Allah, karki bari wani abu ya tarwatsa ku.”  “Alhaji ka yi ƙoƙari akanmu tun haihuwar mu har zuwa yau, ka cika mahaifini na gari, ka tsaya akanmu ka kula da mu, mun gode maka alhaji mun gode maka, ko a yanzu rayuwa ta tsaya Alhaji ka cika gwarzon uba, Alhaji mun gode maka.”  Yaya Radiya ta faɗa tana fitar da wani irin kuka mai taɓa zuciya, ya yi murmushi sannan ya nuna Yaya Rumaisa, itama ta matso kusa.  “Ki dinga dannar zuciyarki, ki dinga haƙuri da ‘yan uwanki dan Allah, ki yi wa mijinki biyayya, Allah Ya yi miki albarka ya haɗa kawunanku, ku ya fe min dan Allah.”  Cikin kuka itama ta fara magana.  “Alhaji muna sonka, mun kuma gode maka da dukkan abinda ka yi mana, Alherin Allah Ya tabbata a gareka Alhaji, Mun gode mun gode.”  Ya matse hannun Yaya Ridwan dake cikin nasa, sannan ya ce.  “Haƙuri! Haƙuri! Haƙuri dan Allah, Ridwan ban so na barka maka nauyin akanka ba, amma nasani Allah Ya na gani, kuma zai shiga al’amuranka zai buɗa maka yabaka ikon kula da ‘yan uwanka, a ko da yaushe albarka ta tana tare da ku.”  Yaya Ridwan kuka kawai yake bai iya cewa komai ba, Alhaji ya kalleni ya ce.  “Nana! Ki kasance mai karɓar ƙaddara kowace iri, Nana rayuwarki tana cike da ƙalubale da yawa, Nana karki yi wa Allah butulci, karki koka, ki yi haƙuri ki sa a ranki komai zai wuce Nana, komai da komai zai zama labari.”  Rungume shi na yi na ci gaba da rera kukan da nake yi.  “Ka kasance mai biyayya, mai kyautatawa ‘yan uwa, kasa a ranka Allah ne gatanKa sune gatanka, Ra’is ka yi haƙuri a duk irin rayuwar da ka tsinci kanka, Allah yana gani ka ji.”  Shima Ra’is ɗin kuka ya fashe da shi,  kowa kuka.  “Na gode miki, Na gode miki Allah Ya yi miki albarka, ya baki haƙurin rashi.”  Hajiya dai ba ta iya cewa komai ba sai faman ƙwalla da take.  “Allah ko a yanzu Alhamdulillah, Allah na gode maka, na ƙara gode maka, zan kasance mai gode maka Ya Allah, Tammat bi hamdillah Allah.”  Daidai lokacin Isah Nadabi ya shigo ɗakin, ganin dukkanmu muna kuka ya sa shi cewa.  “Me ya faru dan Allah, Ridwan ya baku tafi asibitin ba?”  Cikin Kuka Yaya Ridwan ya ce.  “Ya ce kar aje asibitin.”  Matsowa ya yi ya kama hannun Alhaji sannan ya ce.  “Alhaji akai ka asibiti dan Allah.”  “A’ah Isah, tsaya ka ji.” Alhaji ya faɗa murya a wahalce, ya riƙe hannunsa sannan ya ce.  “Allah Yasa ka maka da mafificin alheri, ubangiji ya raya maka zuri’arka, Allah Ya dauwamarma da suttura, ɗawainiyar da ka yi akaina ubangiji ya mayar maKa, na gode.”  “Alhaji ka bari dan Allah, Ridwan kama shi dan Allah.”  “A’ah! A’ah! Dan Allah ku barni.” “Me ya sa, Alhaji?”  “Ka barni, na ƙarasa rayuwata a cikin iyalina.”  Bai kai ga yi masa magana ba tari ta sarƙeshi, yanayi yana haɗawa da kalmar shahada. Gaba ɗaya muka zagaye shi muna kuka, a hankali har muka ji ya daina kakarin.  Gaba ɗaya duniyar ta tsaya mana cak, Isah Nadabo ne ya fara ɗaga hannuna yana faɗin.  “Alhaji Alhaji, innullahi wa’inna illahir raji’un.”  Ina daga zaune na ji wani irin jiri ya ɗebeni, aikuwa na kifi ƙasa kif.  Legendspen 08129553971. https://chat.whatsapp.com/DPr8Zlw33HeAkt3hhxIPYv?mode=gi_t *Munyi nisa a Arewapen, ta wannan link ɗin ko username Legendspen* https://www.arewapen.com/book?id=69d7e87dfc259651b7635bff *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu) Shafi na sha shida. (16) Sama sama nake jin hayaniyar mutane, a hankali na fara buɗe idona, dishi dishi nake gani kafin idon ya buɗe tarwar. A take komai da ya faru ya shiga dawomin kamar an haskan majigi. "Alhaji!" Na faɗa ina koƙarin ta shi, hannuna na ji an riƙe tare da faɗin. "Nana! Nustu ki nutsu." Muryar Sardauna ce, na ɗaga ido na kalleshi tare da faɗin. "Alhaji!" Ya riƙe ni tare da girgizamin kai, sannan ya ce. "Alhaji is no more Nana, Alhaji ya tafi ki yi haƙuri." Wani irin kuka na saki me raɗaɗi da taɓa zuciya tare da faɗin. "Innullahi wainna illahir raji'un, na rasa Alhaji na rasa gata na rasa komai, dan Allah ka mayar dani gida ka mayar da ni." "A'a Nana ba zaki koma yanzu ba, sai kin warke." Miƙewa na fara ƙoƙarin yi tare da faɗin. "Na warke Sardauna ka barni na tafi, na je na ga mahaifina, dan Allah." Kallon agogon hannunsa ya yi sannan ya ce. "Ƙarfe uku da rabi za ayi jana izarsa, kuma a yanzu uku da arba'in Nana, an kaishi gidansa na gaskiyya, ki yi haƙuri ki ɗauki rashi, ki karɓi ƙaddara Nana, ni zan zame miki gatan da kika rasa Nana, dan Allah." Kuka na ci gaba da yi, ni kaɗai nasan irin  yanayin da nake ji, ina jin kamar na fitar da zuciyata daga cikin jikina, ina jin zafi kamar an watsamin gishiri a jikin ciwo, raɗaɗi kawai nake ji da wani irin zafi yana ratsani, na gaji na rasa me zanyi, ba kuka ba, ba ihu ba, na gaji da rayuwar ma, na gaji. "Nana ki yi haƙuri dan Allah, ki yi haƙuri kinji." Ya faɗa yana jawoni jikinsa, na kwanta ina kuka mai tsuma zuciya, shi kuma yana shafa bayana. A hankali na fara sauke ajiyar zuciya. "Nana! Kina jina, Allah Yana jarabtar bayinsa ta kowanne fanni, Allah Ya jarabce ki da rasa mahaifi a yanzu, amma kuma ya yi miki sakayya da ni Nana, Nana ina son ki ɗauke ni a matsayin duk wani abu da kika rasa Nana, zan zame ki bango, zan zame miki inuwa Nana." Haka Sardauna ya yi ta lallaɓani da zafafan kalamai masu saukar da nutsuwa, amma gaba ɗaya a hankalina baya tare da ni, burina na ga 'yan uwana, ko zan tabbatar cewa Alhaji bai mutu ba, dan tabbas na hana zuciyata yarda da ko kalma ɗaya kan faɗin rasuwar Alhaji. Ba mu muka bar aaibiti ba sai bayan biyar, hannu maƙale da kanula sabida ba a gamin allura ba, har da ƙarin ruwa. Jama'ar da na gani a kwanar layinmu suka dawo min da kuka na sabo, so ake a tabbatar min na rasa mahaifina, na rasa Alhaji ina zan sa rayuwata. Yanayin fakin ɗin motar shi na fito, ban ko tsaya ba duk kiran sunana da yake yi. Da gudu na shiga cikin gida idon kowa ya yo kaina. "Wayyo! Wayyo!." Na ji muryar Hajja, wani takaici ya cikani na fara tafiya zuwa ɗakin Hajiya sai dai kawai na ji wani jirin na ɗibana, kan ka ce me na sake zuɓewa a ƙasa sumammiya. Sanyi da na ji a fuskata ne ya sa na buɗe idona, Maman walid wata maƙwafciyar mu na gani a kaina tana shafan ruwan, can na jiyo muryar Sardauna yana faɗin. "Ba yadda likitan baiyi ba, amma ta dage sai na kawo ta." "Da ba kawo ta ba, yanzu gashi ta sake zubewa." Banma tantance me muryar ba na ce da Maman Walid. "ina Hajiya? "Tana ciki Nana." "Kamani dan Allah." Na faɗa ina ƙoƙarin tashi, ta kamani ta shiga dani ciki, anan na tarar da har da mutane da yawa a  cikin ɗakin, har da Mamansu Amina Aminu da Fauziya. "Nan da zafi, a fita da ita wancan ɗakin ta sha iska mana." Wata maƙwafciyarmu ta faɗa, Maman Walid ta sake riƙeni zuwa ɗakin da yake seat room, ɗakin yana da faɗi kuma ba komai a ciki carpet shi ya sa yake da iska.  A cikin ɗakin na ga mutane da yawa har da ƙwayena da su Yaya Radiya kowa ya yi zungwi zungwi, haka nima na zauna a raina ina ta nanata kalmar. 'Alhaji is no more.' Da Sardauna ya faɗa min, haka na zauna har dare ban nemi Sardauna ba, sai wajen tara sannan ya sa aka kirani, ko da na je ban wani saki baki na yi mai magana ba, shima kuma bai daɗe ba ya ce da ni zai tafi sai gobe zai zo. Haka na koma ciki, jigun jigun ba magana ba ci ba sha, sai washe gari ne ma nasami damar shan shayi da safe, Sardauna da sassafe ya zo har da wasu daga 'yan uwansa wayanda daman jiya sun zo su Big Daddy ma duk ance da su aka yi sallar Alhaji shine dai babu shi, sabida zuwansa kenan ya gani a kwance ya ɗaukeni zuwa asibiti, da yamma su Hajiyarsa da su lubna suka zo har da su Sister Seemah. Ranar kwana uku ya ƙara tabbatar mana da cewa Alhaji ya tafi babu dawowa, haka muka yi haƙuri muka amshi rashin Alhaji. Washe gari ranar kwana na huɗu kowa ya watse gida daga mu sai mu sai 'yan uwan Hajiya da suka zo, sai Anty Adiza matar Isa Nadabo da bata koma ba tun da ta zo, a ranar muka ƙara tabbatar da rashi musamman da muka kasance muka ɗai, ranar kwana na shida Turaki ya zo ya yi min gaisuwa, baya ƙasar sai jiya da daddare ya dawo, ya yi min gaisuwa sosai da sosai, da zai tafi ya ce na haɗashi  da 'yan uwana maza, sanin halin Yaya Ridwan yasa ban ma haɗasu ba sai Ra'is na nema, bayan sun gaisa ya yi masa gaisuwa ya karɓi lambar Ra'is sannan ya bawa Ra'is ta shi, ya kuma sanar da shi akan cewa bayan anyi kwana bakwa ya tuntuɓeshi. Ranar bakwai aka sake zaman addu'a, da dare kowa ya watse aka sake barin mu daga mu sai mu sai Anty Adiza da take kamar 'yar gida, 'yan uwan Hajiya ma sun tafi, su Hajja kam tun ranar da aka yi rasuwa suka tafi gida akan cewa suma zasuyi nasu zaman makokin acan, bayan sun jidi kayan abinci a shago tun da ga nan Isa Nadabo ya karɓe mukkullin shagon. Ranar bakwai Sardauna ya tambayeni yaushe zan dawo na ce da shi sai na tambayi Hajiya, bai tankan ba ya tafi na koma cikin gidan, a zuwa yanzu mun karɓi rashin Alhaji, mun ci gaba da wasu abubuwan har magana da cin abinci, mu kan ɗan zauna mu tattauna wasu abubuwan. "Yaya, ɗazu mutumin nan ya kirani da kansa." Ra'is ya faɗa, na kalleshi na ce. "Wane mutumi?" "Wanda kika haɗani da shi ranar nan." "Aouho, me ya ce da kai?" "Waye ne?" Hajiya ta tambaya. "Wani ɗan uwan Sardauna ne." "Me ya ce ma?" Yaya Radiya ta tambayeshi, sai sa ya gyara zama sannan ya ce. “Da farko ya ce dani a wane aji nake, na ce da shi yanzu na shiga level 1 a FUD Sai ya tambayeni sauran fa, na ce masa Yaya Radiya tana shekara ra biyu a Health, sai Yaya Rumaisa da za ta gama, har ya tambayeni wace babba na ce Yaya Radiya, na ce ai ita ba ta fara karatun ba sai bayan aurenta ya mutu, sannan na ce da shi Yaya Ridwan ya shiga 400 level a FUD sai ya tambayeni Reg ɗina nawa nw na faɗa masa da na Yaya Radiya da na Yaya Ridwan to yanzu duk ya yi budget kuɗin har kowa ya kammala wai zai kama miliyan ɗaya da duby ɗari biyu, sai ya ce ba tura mai acc zamana anan na tura mai na Yaya Radiya, yanzu ya tura min recipt ya sa miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar, sannan ya ce duk wani abu na karatu ko nawa ko na Yaya Radiya ko Yaya Ridwan a sanar da shi in sha Allah.” Ba ƙaramin mamakin jin abinda Turaki ya yi na yi ba, cike da mamaki na ce. “Shi Turakin?” “Shi dai wanda kika haɗani da shi.” “Mene alaƙarsu da mijinki?” Hajiya ta tambaya. “Kamar ɗan wa da ƙani suke, amma dai gaskiyya Hajiya a iya sani na basa mutunci da Sardauna, hasali ma abokan faɗan ne basa ga maciji kuma nasan Sardauna bai san maganar ba.” “Kuma kika faɗa masa wallahi Nana sai ranki ya ɓaci.” Yaya Radiya ta faɗa, sannan ta ce. “Wannan mijin naki bai da hali, shi kaɗaine bai sallaci Alhaji ba.” “To ba suna asibiti ba ke kuma.” Hajiya ta faɗa. “Haba Hajiya, ƙarfe biyar fa aka yi sallar Alhaji kuma ya sani, ina ganin ko da yana kaita zai iya dawowa.” “Ƙarfe biyar kuma?” Na faɗa a fili, a raina kuma ina tuna lokacin da Sardauna ya ce da ni ƙarfe huɗu da rabi za ayi, kuma yanzu huɗu da arba’in. “Eyh mn biyar aka yi wa Alhaji Sallah, kowa ya sani wani abun ne?” Yaya Radiya ta tambayeni, na girgiza kai sannan na ce. “A’a ba komai, kawai gani nake babu rabom ganawarmu, amma da na fito lokacin da na farka ai da zan same shi.” “Zaki samu mana, ina Dutse clinic ina gidan nan ko minti biyar ba zaku yi ba.” A raina na ce me ya sa Sardauna yake son fara yi min ƙarya? Mutuwar mahaifina ce ta goge damuwar ƙaryar shekarun da ya yi mini, ga shi kuma yanzu ya sake min wata, ya san mene ganawa da mahaifi kuwa, anya ya sani? “Yanzu ya za ayi da wannan kuɗin?” Muryar Yaya Radiya ta katseni, sai na ji Hajiya na cewa. “Idan makarantar zasu yarda kowa aje a biya nasa gaba ɗaya kar ya kammala, idan kuma basu amince ba za a iya kaisu banki a ajiye idan lokacin biyan ya yi sai a dinga ɗauka ana yi.” Daga haka aka yanke shawara, ni dai an barni da tunani kala biyu a raina, yaushe Sardauna ya fara yi min ƙarya ko me ya sa ya fara? Washe gari na shirya komawa gida ni da Yaya Rumaisa, bayan Hajiya da Yaya Radiya sun yi mana faɗa sosai, kuma an gargaɗe ni akan kar na sake na sanar da Sardauna abinda Turaki ya yi tin da na ce ba sa shiri, da suna shiri ne ma za a sa shi ya yi masa godiya. Ko da na kira Sardauna na ce da shi yazo ya ɗaukeni sai ya ce da ni yana aiki na tawo kawai, haka na sami mashin na hau har gida. Gidan gaba ɗaya ya yi ƙura ya yi datti, ba wani zauna na ba na hau gyaran gida, ina cikin yi Sardauna ya dawo. Bai nuna wani farin ciki da dawowa ta ba ko kuma irin alamun ya yi kewata ba, sai ma sanar da ni da ya yi a cikin satin nan zamu koma sabon gidanmu dake Takur Site C wanda yanzu muke a A, ganin haka ya sa na dakatar da wasu ayyukan sabida wasu abubuwan duk kwashe su zamuyi, Sardauna bai duba halin rashi da nake ciki ba, haka ya yi ta fama, sannan kuma ya ƙara matsamin akan shan magunguna wai akwai abu da yake shirin faruwa. Ranar juma’a da yamma muka ta shi daga gidanmu na Takur Site A muka koma Takur site C, babban gidane mai ɓangare biyu, kowanne ɓangare ɗaya yafi gidanmu na site A, namu ne a hannun hagu na Turaki a hannun dama, muna shiga na ce da Sardauna. “Wai to shi Turaki shi da wa zai zauna? “Yaran mutane zai ci gaba kawowa yana abinda ya saba da su.” Ada ina yarda haka Turaki yake, amma yanzu kam bana yarda kwata kwata. Gidan ya yi kyau ya tsaru sosai da sosai, komai sabo ne a cikin gidan, kowanne ɓangare sai ya ɗauki mata uku a wadace. Abubuwan da muka tawo dasu basu da yawa, daga abin gawayi sai kayana da wasu kayan kicin ɗin. Ranar da muka koma da wani irin ciwon ciki na kwana, gaba ɗaya cikina ya wani irin murɗawa ta wajen marata, na sha matuƙar azaba har sai da jini ya fita daga jikina, Sardauna ya kaini asibiti wajen Dr Ɗan Adala, tambayar farko da ya yi min sau nawa nake amafani da magunguna, na ce da shi har sau biyar a wata na yi. A take ya ce na dakatar da shan maganin ba lallai ya yi wa mahaifata aiki ba, za a duban wani maganin nan gaba ko daga Turai ne sai akawo min, daga nan muka dawo gida. “Nana, ki daina damuwa da rashin haihuwar nan, gaba ɗaya ba mu shekara biyu da aure ba, wasu su kan shekara goma da aure ba haihuwa, dan haka ki daina damun kanki kin ji dan Allah, ke na ki so Nana, ba wai Baby daga jikinki ba, dudu nawa kike, Nana ko kinsan bana so tsufa. Nana girma bazai taɓa yi miki kyau ba.” Ga masu tambaya, Littafin Sartse Book one ne kaɗai Free wanda kuma mun kusa kammalashi, Book Two & Three. Kuma na kuɗi ne, domin sabuwar tafiya ce; sabuwar rayuwa ce da za ta girgiza ku. Komai zai sauya,Book one gaba ɗaya shimfiɗa ce, dan bamu fara tafiyar ba, Book 2 da 3 shine ainahin labarin. Kuna iya fara biyan kudin littafinku tun daga yau, kafin mu kammala Book One. • Account Details: • Account No: 8165383931 • Bank: Opay • Name: Sani Muhammad Lawan • Farashi: • Naira Dari Bakwai (700) kacal. Akwai giveaway na lokaci-zuwa-lokaci wanda muke yin ragin zuwa N500 ga mutane 20 na farko da suka fara biyan kuɗinsu. Garaɓasa ce ta iya mutane 20 ɗin farko, kar ku bari ku rasa. Masu VIP kuma babu tsarin VIP sai dai arewapen, da ake saka page 5 zuwa 6 kullum. Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na sha bakwai.     (17) Na ɗaga kai na kalleshi, ban gane inda kalamsa suka nufa ba kwata kwata. 'Tsufa bazai min kyau ba? To ai dole na nutsu fa ko? In da rai ko ba lafiya ai sai na tsufa, kuma ni Allah Ya gani ina son ganin 'ya'yana, amma ya zanyi da shi tun da ba ya so? Me zan so bayan abinda yake so?.'  "Shikenan, Allah Ya nuna mana lokacin."  "Amin Nanaty, me kike shiryamana na a sabon gidan nan?"  Na yi dariya sannan na ce.  "Me zan shirya mana kuwa?" "Sabuwar rayuwa mana Nana, sabuwar soyayya, sabuwar kulawa, ina ganin kamar kina rage tausayina, ada Nana kina tausayina sosai kin damu da ni da damuwata, amma yanzu sai nake ganin kamar ba haka ba ne Nana, ada abinci har abaki kike ban, amma yanzu kin barni na ci da kaina, me ya sa Nana?"  "Bakomai wallahi, kawai kutuwar Alhaji ce har yanzu ba ta gama sakina ba, ina jin rashin sa a cikin zuciyata sosai."  "Nana, Allan da yafi bamu Alhaji yafi mu son shi kuma ya amshi abunsa, ba yadda zamu iya, Nana wasu fa uwa da uba Allah Yake ɗauke musu rana guda lokaci ɗaya, su ce me? Allah Ya ce ku kasance masi godiya ni kuma zan ƙara muku, ko gode masa da ni'imar da ya yi muku Nana, zai ƙara muku wata."  Jawoshi na yi jikina na rungumeshi, sannan na ce.  "Hakane, Allah Alhamdulillah, ko kai da Allah Ya bani wata ni'imace da zan gode masa akai, ina sonka, ina ƙaunarka."  "Nima haka Nana, ina sonki! Ina ƙaunarki."  "Allah Yabar mu tare Mijina." "Amin matata."  Tun daga wannan lokaci na fara rage damuwa akan rashin haihuwa, na yarda da Sardauna na kuma amince da shi, na kuma yi alƙwarin ninka tausayi da soyayyar da nake yi masa.  Washe gari, tun asuba da na tashi na shiga haɗa ma Sardauna lafiyayen abinci, wanda rabona da na yi masa ƙayataccen abincin tun kafin rasuwar Alhaji.  Ina tsaka da aikin a cikin dabarar yi masa cupcake ta faɗomin, ba tare da wani dogon tunani ba na haɗa cake, ina wancan aikin ina wancan, wajen ƙarfe bakwai na fito na shiga ɗakinsa, yana kwance kan gado na shigo toilet na haɗa masa ruwan wanka sannan na fito, a hankali na zauna a gefen gadon sabida kar ma tashe shi, na kai hannuna kan sumar kansa na fara shafawa, da sauri ya buɗe idonsa ya sauke su akaina, ya sakar min murmushi sannan ya ce.  "Nanaty."  "Na'am, aje ayi wanka breakfast ya zama ready."  "Tom ɗago ni."  Ya faɗa yana miƙamin hannunsa, na kama tare da ja amma kamar banja ba.  "Ƙara dagewa." Ya faɗa, na kuwa sa duka ƙarfina na ƙara ja sai da na ji hannuna ya yi ƙas amma kamar bashi na ja ba.  "Raguwa."  Ya faɗa yana jawoni kansa, ai kuwa kamar takarda na faɗo, ya zame ya barni kwance ya shige toilet ɗin, sif na buɗe na ɗauko masa kaya na koma kicin na ci gaba da aikina, kusan mintuna ashirin na ji maganarsa a gab da kicin ɗin. "Baki gama breakfast ɗin ba ne?"  "A'a na gama gashi can a dinning bara na zo na baka."  "To me kike yi anan?"  Fitowa na yi sannan na ce.  "Girki nake ma."  "Me kike dafawa, kuma me zna yi da shi?"  "Cake ne na tafiya ofis."  "Awwww, thank you daman rabona da cake tun kina sona, gashi na ga alamar kin dawo da sona." "Wai na daina sonka."  Na faɗa ina ƙarasawa wajen dinning ɗin, shima yazo ya zauna na fara zuba mai.  "Wow, ni Sardauna mijin Nana, dama haka kike min kullum."  Na yi dariya sannan na ce.  "To me nake ma ai haka nake ma, kai dai kawai ka ci."  Haka kuwa ya ci sosai da sosai, daidai lokacin na juye masa cake ɗin da na gama decorating ɗinsa  a cikin ƙaramin box."  Sai da na rakashi har parking space, namu yana gefe na Turaki yana gefe, lallai fa ta dole sai sunyi zumunci domin kusancin gidan ya yi yawa, ko ƙara aka yi sai anji.  "Wannan yaron yana nan kenan?"  Ya faɗa yana shiga mota, sai na ga ya shiga sannan na juya na koma ciki na fara ayyukan, na gyara inda nake son gyarawa na goge ko ina sannan na dawo na zauna. Waya ta na ɗauka na fara dannawa, ga wayar dai amma babu layi babu wani abu da zanyi da ita, haka na gama juyata na ajiye, ga Tv babu damar yin kallo, daman gidan babu zafi  amma gaba ɗaya na ji ya isheni, kamar na yi kuka haka nake ji duk gidan ya yi min zafi.  Ganin zaman ba zai kai min ba na tashi na fara zagaye ko ina, na leƙa can na leƙa can daga baya na dawo bakin taga ina kallon gidan tanan. Turaki na ga ya fito daga ɓangarensa cikin shirinsa na ofis bai ma kalli ina ɓangaren mu yake ba ya shiga mota shima ya fice.  "Shikenan yanzu ni kaɗai ce a gidan, na shigo ni Nana."  Ɗakina na koma na zauna, amma zaman ba daɗi, na dawo falo ba daɗi, haka na yi ta zagaye zagaye har yamma. Ina xaune a falo na ji magana da motsin abubuwa, na buɗe taga na leƙa kayan gado da kujeru ne ake shiga dasu ɓangaren Turaki a raina na ce. "Gwanda ka yi auren, ko na sami abokiyar zama da ta ya hira."  Ina tsaye ta taga suka gama shi dasu, shi kuma yana basu umarnin inda zasu jera, har suka kammala suka tafi shima ya bisu, dambun cous-cous da miyar kaza na yi wa Sardauna, sannan na yi masa lemon abarba, tun biyar da rabi nake sa ran ganinsa amma ba shi ya shigo ba sai bayan magariba, yanayin dana ganshi kaɗai ya sani farin ciki, sabida na ganshi fuskarsa a washe.  "Ssnnu da zuwa."  Na faɗa ina amsar jakar hannunsa. "Yawwa, sannu da gida matata."  Tsugunnawa na yi na shiga cire mai takalmin ƙafarsa sannan na kwasa na shiga ciki, bayan na fito ne na ce.  "Wanka ko abinci?"  "Abincin dai sabida ina so na sake fita yanzu."  "Tom muje na baka."  Na faɗa ina nufar dinning ɗin shi kuma ya biyo ni a baya, ya yi farin ciki ganin abincin amma kuma farin cikin dake cikin wayarss yafi yawa, ina jin kamar na tambayeshi me yake gani a wayar sai kuma na ƙyaleshi, nasan ko mene alheri ne dai.  Ina son yi masa magana akan zaman da na yi yau ba daɗi amma bai bani damar hakan ba, har ya kammala cin abincin sannan ya ce.  "Haɗamin ruwan wankan."  Na tashi na shige ɗakin na haɗa masa, bayan ya fito ya shirya sosai ya yi kyau kamar ko yaushe.  "Nana, zancen dinner ɗin abokina ne, na ga kamar kin damu."  Na yi murmushi sannan na ce.  "Allah Ya tsare zaka yi dare ne?"  "Bazan wuce goma ba ina ga."  "Tom adawo lafiya, amma dan Allah ko Tv ne zan iya kunnawa zaman ni kaɗai ba daɗi wallahi."  Kallona ya yi baice komai ba ya fice, sai na ji kamar ban kyauta ba, na dawo na zauna kan kujera tare da haɗa uban tagumi, bayan na yi sallar isha na dawo na sake zama, tun ina sa tan ganin Sardauna ƙarfe goma har sha ɗaya shiru, ta dole na bawa baccin da yake fisgata damar ɗaukana.  Cikin bacci na na ji ana cewa. "Anan kika kwanta? Tashi Nana tun da ba zaki iya jirana na dawo mu yi magana ba."  A hankali na buɗe idona na kalleshi, cikin muryar bacci na ce.  "Ka dawo?"  "Eyh, tashi kije ki kwanta."  Miƙewa na yi na nufi ɗaki na kwanata, ba tare da nasan asalin daidai lokacin da Sardauna ya dawo ba.  Washe gari ma kamar jiya haka na tashi na shiga kicin, wani abu daban nasake haɗawa Sardauna, sanna na ɗauko wasu cikin cake ɗin jiya nasake docorating ɗinsu da icing suger, yau ko da naje ɗakinsa ma ya shirya da kansa, sai da wayarsa na kare a kunnesa yana magana.  "Breakfast ya zama ready." Gyaɗamin kai kawai ya yi alamun ya ji, ni kuma na shiga nawa ɗakin na shirya, bayan na fito na sameshi akan dinning yana danna waya.  "Ina kwana?"  "lafiya ƙalau Nana."  Zama na yi na fara zuba masa abin breakfast ɗin, bayan na zuba mai nima na zuba, sai a lokacin ya kashe wayar ya fara ci.  "Nana!"  Ya kira sunana a hankali, na ɗago kai tare da cewa.  "Na'am."  "Kince bakya jin daɗin zama ke kaɗai ko?"  "Ba banajin daɗi ba ne, kawai bansaba da gidan ba ne."  "Hakuri ake yi Nana, yau da gobe  zaki saba, amma tun da kina so na baki damar amfani da TV ɗin shikenan?"  "Eyh shikenan, sai kuma zancen sabon sim ɗin da ka ce zaka bani, ina son na dinga jin lafiyar Hajiya, kuma nasan itama zata nemeni, ya kamata na sanar dasu mun canja gida."  "Eyh, to da wannan kam."  Ya faɗa yana cire bayan cover wayarsa, ya ciro min sabon sim card sannan ya ce.  "Gashi, amma Nana bana son na ga lambar kowa sai ta Hajiya ita kaɗai, sai kuma tawa."  "Tom in sha Allah, na gode."  Daga nan ya ƙarasa abinda zai yi ya fita, bayan ya fita na sim ɗin na kira Hajiya muka gaisa nake sanar da ita muncan gida, umarni ne daga familynsu kan rashin zaman daɗi da suke da Turaki gidan ma guda ɗaya ne mu da shi.  Daga nan muka gaisa da su Yaya Radiya da su Ra'is, daga nan muka yi sallama na kashe wayar, haka kawai na ji zuciyata na ingizani akan na je na haɗa kayan Sardauna na wanke su, ba tare da na yi wani ja'in ja da zuciyata ba na ɗauka na shiga toilet na hau wanki, tun wajen sha biyu har uku na rana ina wanki, sannan na shan ya su na dawo na ɗaura girki, gaba ɗaya har na dare na yi. Bayan na ci na yi wanka na zo na kwanta na huta gajiya. Cikin barci na ji kamar ana bugu ƙofar tawa, buɗe da idona na yi tare da faɗin.  "Waye?"  "Ni ce."  Na ji muryar wata mata, tashi na yi zan nufi ƙofar sai dai idona ya kai kan waya ta na ga agogon wayar ya nuna ƙarfe 06:16, gaba na ne ya faɗi afili na ce.  "Ya ubangiji kasa ba baƙuwa na yi ba, a daidai wannan lokacin da Sardauna zai dawo ba." Ƙara bugu ƙofar a ka yi na fita ina faɗin.  "ina zuwa."  Na faɗa ina ƙarasawa wajen ƙofar, a hankali na buɗe gabana yana faɗuwa, aikuwa baƙuwar ce sai sai bansanta ba, murmushu ta yi min sannan ta ce.  "Sannu!"  "Yawwa sannu, shigo mana."  Na faɗa ina matsa mata ƙofar, ta shigo cikin falon.  "Ina wuni." Na faɗa ganin ta girmeni sosai ma.  "Yawwa Sunana Bilkisu, anan baya nake, na ga an kawo amarya kuma ina yawan cewa zan shigo Allah Bai nufa ba sai yau da na zagayo gidan kisto."  Ta faɗa tana nuna hannunta baya alamun kwatancen inda take, na yi mata wani murmushi mai wuyar fassara, domin ni kaɗai nasan irin bugun da zuciyata take, lokacin dawowar Sardauna ne yanzu, kowanne lokaci zai iya shigowa, gashi baya ƙaunar ya ga wata ƙawa ta kusa ko ta nesa ta zo wajena.  "Zauna mana to."  Na faɗa ina nuna mata kujera, ta yi min wani irin murmushi sannan ta ce.  "Ai sauri ma nake, amma zan dawo."  Ban kai ga buɗe baki ba na ji horm ɗin Sardauna, wanda yake yi daidai lokacin da zai kashe motarsa, wanda yake yinsa domin sanar dani ya dawo.  "Mai gidan ne ya dawo?" Ta tambaya ne, na yi murmushi sannan na ce.  "Eyh shine."  "Ayyah to kinga kuwa ba sai na zauna ba, amma in sha Allahu zan dawo." Ta faɗa tana juyawa zata fita, daidai lokacin kuma shi ya shigo. Kamar ana buga ganga haka na ji zuciyata na bugawa, da sauri na runtse idona sannan na buɗe.  "Sannu da zuwa."  Na faɗa ina ƙarasowa inda yake, ga mamakina ya sa hannu ya komo ni tare da faɗin.  "Nanaty baƙi ne damu?" Ya faɗa yana shigewa ciki, na bi bayanshi ina faɗin.  "Ina zuwa."  "Uhmm." Ta faɗa tare da zama, ni kuma na bishi ciki.  "Sannu da zuwa."  Nasake faɗa ina ajiye jakarsa a ma'ajiyinta.  "Yawwa"  Ya amsa yana zama kan gado, tsugunnawa na yi tare da fara cire mai takalmi ina faɗin.  "Wallahi bansanta ba, yanzu ta shigo wai anan baya take."  Kallona ya yi tare da kamo hannuna "To mene a ciki? Ai hakan yana da kyau sosai da sosai, ke fa kika ce min zaman ke ɗai ba ya yi miki daɗi kuma daman ka yi ta zama a waje bakasan kowa ba? Ta shi kije ku gaisa."  Da wani irin yanayin mamaki nake kallon Sardauna. 'Sardauna dai? yau shi ke barin wata tazo gidan nan, har da cewa ayi ta zama a waje ba asan kowa ba, Sardauna da ya tsani ganin baƙo a gidan?'  "Ki tashi mana."  Muryarsa ta katse min tunanin da nake, na miƙe na nufi falon.  "Ki yi haƙuri na bar ki."  "A'a babu komai fa, ai mai gidan ne ya dawo, bari na zo na wuce amma zan dawo."  "Tom shi kenan na gode sosai da sosai, nima idan na samu fita zan shigo gidan naku in sha Allah." Na faɗa ina rakata waje, a gurguje na dawo haɗa masa ruwan wanka sai na tarar yana toilet ɗin ma. Na fito na dawo na jera masa abinci akan dinning, bayan na fito masa da jallabiyar da zai sanya na ajiye mai kan gado, nima na tafi ɗakina na gabatar da magariba na dawo falon.  ***** "Ko ka kirani na yi serving ɗinka."  Na faɗa ina zama kan dinning ɗin.  "Ah bakomai, har baƙuwar ta tafi?"  Ya tambaya, na gyaɗa masa kai sannan na ce.  "Ta tafi wai amma zata dawo, ni ba ma so nake ta dawo ba, nasan kai baka fiya son mutane suna zuwar mana ba. Zan ma taka mata burki."  "Nina faɗa miki? kawai dai akwai waɗanda ban yarda dasu ba ne." Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na sha takwas.     (18) "Su waye baka yarda da su ba?"  "Nana kenan? Ni wannan ma duk da ba wani kallo na yi mata ba amma tabbas tafi ƙawayenki da yayyunki da yawa kalal nutsuwa."  Haka kawai na ji ta kwantamin a raina sakamakon abinda Sardauna ya faɗa, daman kuma tabbas zaman ni kaɗai ɗin ya isheni na gaji da zaman.  "To yanzu ba matsala kenan?"  "Eyh! Ba matsala kam amma dai ba ko yaushe anyhow ba gaskiyya kinsan tsarina."  "Tom shikenan na gode."  Na faɗa ina ci gaba da cin abincin, shima ya ci gaba da ci bayan mun kammala ya kalleni sannan ya ce. "Na yi wasu abokai anan baya, suna da majalisa ina tunanin zan fara zama ina rage dare kafin mu saba da yanayin unguwar."  "Eyh hakan yana da kyau kam gaskiyya, Allah Ya taimaka."  Na faɗa shi kuma ya tashi ya shiga ɗaki, can ya fito bayan ya ƙara gyarawa ya fice.  Daga wannan rana kullum Sardauna sai ya fita majalisar nan, baya dawo sai  goma ta gota tun bana jindaɗin zaman har nasaba, Bilkisu kam ba ta sake zuwa ba tun ranar ba gaba ɗaya na damu, har na fara tuanin ko sardauna ne ya dakatar da ita sai kuma na tuna kwata kwata basu haɗu ba tin da ya shiga ɗaki bai fito ba sai da ta tafi. Sai da aka yi sati biyu sannan ta sake zuwa, ranar na yi murna kamar na cinye ta, haka itama ta dinga biya min mun hira sosai kuma na ji daɗin zama da ita sosai da sosai, tun daga wannan lokacin ta fara zuwa duk da ba ko yaushe ba,  babban abin daɗin Sardauna bai taɓa yi min ƙorafi akan zuwa na ta ba, duk da wani lokacin su kan haɗu.  Na yi mata maganar rashin haihuwata, ta ƙara ƙarfafamim gwiwa tare da ba nj hakuri akan hakan, da cewa na dage da addu'a, babban abinda ya burgeni da Bilkisu shine karatunta ta ti degree a yanzu ma ta ɗaura masters sannan tana yin aiki, mace mai ilimi daban ce, komai na ta gwanin ban sha'awa akwai tsari, ban taɓa zuwa gidansu ba, amma ina yawan  ce mata zanje idan na fita.  A ɓangaren Turaki har yanzu auren shiru, sai dai kawai na ji mostintsa idan ina falo amma bai taɓa shigowa ba kuma ko a waje bamu taɓa haɗuwa ba, da muka yi magana da Ra'is ta wayar Hajiya ya ce da ni wai Turakin nema yake nemansa a waya lokaci zuwa lokaci ya ji lafiyarsa da ta mutanen gidan.  A tsakanina da Sardauna abubuwa suna tafiya yadda suke, kawai dai kwana biyu ya ƙulla sabuwar abota da wayarsa da kuma zuwa majalisa, wanda a yanzu ya ɗan rage bai cika fita kullum ba.  Yau tum safe na kammala aikina, dan mu yi da Bilkisu zan koya ma ta yadda ake Samosa wrap, ta ce tana so kuma ta ga ina yi yawan yi tasan dole maza suna so.  Ina tsaka da aikin gida ta shigo, daman ta ce yau gudun wajen aiki za ta yi, murmushi na sake sannan na ce.  "Har kin ta so?"  "Na dai gudu, ai yau sai na koyi abin Samosar nan, har da wasu kayan fulawar tunda nima na kusa aure."  Murmushi na sakar mata sannan na ce.  "Ke ce muna da shan biki."  "Ke ba wanda nake kulawa, kawai ma faɗa ne."  "Wai damam ina ta so na tambayeki me ya sa bakya kula maza ne, ba ayi miki zancen aure a gida?"  "To Nana ai aurw lokacine, bazan iya biyewa namiji ba inda ba na aure ba, dan ba duka ba ne suke da kirki, yanzu zai yi miki SARTSE a rayuwarki indai namiji ne."  "Amma nikam Alhamdulillah wallahi, miji dai na yi da ce."  Na faɗa ina shiga cikin kicin, bayana ta biyo tana faɗin.  "Ga alamu nan dai, muma idan mun sami irin nakun sai mu aura, amma wa'yanan samarin shawon ba dani ba."  Na tuntsire da dariya sannan na ce.  "Lallai fa Samarin Shawo."  Haka muka shiga ina yi tana kallo tana 'yan tamnayoyinta har muka kammala. Daga nan muka dawo falo muka shiga hira tana nan har yamma sannan ta tafi.  Haka rayuwata ta yi ta tafiya, yau daɗi gobe akasin haka, abubuwa suna tafiya wasu yadda aka tsara wasu kuma ba yadda aka tsara ba, tsakanina da Sardauna kullum sabuwar soyayya, sabuwar biyayya, a kullum Sardauna yana farin ciki tare da yin alfahari da ni. Yana yawan ce min.  "Nana kin yi min komai a rayuwa, Allah Ya bani ikon faranta miki rai."  Ni kuma a kullum duk wata sabuwar na'uin biyayya yi wa Sardauna nake, wani abu ni a kaina na kan ji kamar ya zarci hankali, dan a yanzu takai idan Sardauna yana kan kujera ni a ƙasa nake zama, sai ya dage min nake zama akan kujerar ko na ga ya sauko ƙasa.  08:30pm.  Zauna nake a falo, hankalina yana kan wayata dan nasan Sardauna yanzu ba lokacin dawowarsa ba ne.  "Hon!"  Kamar daga sama na ji muryarsa.  "Kawo min abinci."  Ya faɗa yana nufar kan gadon, a tsorace na tashi gabana ya na faɗuwa, me ya sami Sardaunana haka?  A yanayinsa ma kamar cusa abincin yake dan kamar baya jindaɗi.  "Me ya faru dan Allah."  "Bakomai."  Ya faɗa yana ci gaba da abincin, yana cikin ci ya tashi ya shige ɗakinsa, ba shiri nima na bishi ciki amma kafin na je ya kulle ɗakinsa.  "Innullahi wa'inna illahir raji'un, me ya faru dan Allah, Ya Allah Ka kawo wa Sardauna na sauƙi."  Na faɗa ina komawa falon, sai dai gaba ɗaya na rasa abinda zan yi tunaninma na kasa, halin da Sardauna yake ciki ya dameni, Whatsapp na duba naga Bilkisu na online, na tura mata message " 'yar uwa da matsala." Na haɗa mata da emoji na kuka, cikin ƙasa da minti ta dawo min sa amsa.  "Sisi me ya faru?"  "Sardauna ne ya dawo gida da damuwa."  "Me yake damunshi?"  "Bai faɗan ba wallahi." "To me kike da baki tambayeshi ba, Nana kije ki tambayeshi mana, a shawarar da nake baki a kullum ina faɗa miki ki mayar da damuwar mijinki taki."  "Ya kulle ɗakin."  "Toopa, gaskiyya wannan babbar matsala ce, ko dai zuwan da na yi ɗazu ne?"  "Anya kuwa, Sardauna baya son mutane su zo amma ke bai taɓa min magana akanki ba."  "Ikon Allah."  Ta haɗo da emoji na mamaki.  "Yanzu mene abin yi?"  "Abin yi kije ki tambayeshi mene, ki yi amfani da duk wani ikon da ƙarfinki wajen ganin kin magana ce mai damuwar tasa."  "Na gode 'yar uwa."  Daga nan na kashe data ta na kwanta, ina ta faman saƙe saƙe har bacci ya ɗaukeni, washe gari da safe bayan na yi duk wani abu da nasaba, amma Sardauna har wajen ƙarfe tara bai fito ba, ina nan zaune akan a falo ya fito da shirinsa, da sauri na tashi tare da faɗin.  "Ina kwana?"  "Lafiya, ya kike?"  "Alhamdu Lillah, ga abin breakfast nan."  "Nana bazan iya cin abinci ba, ina cikin damuwa ki yi haƙuri."  "Me yake damunka dan Allah, ka faɗa min ka ji."  "Nana ina cikin damuwa kawai, ki yi haƙuri."  "Yanzu akwai damuwar da bazaka faɗan ba a matsayina na matarka dan Allah?"  "Ba haka ba ne Nana, ki yi haƙuri zuwa na dawo kinji." Yana faɗin haka ya fice, ya barni tsaye kamar wacca aka dasa, na kusa minti goma sannan na sami waje na zauna, haka na shiga damuwa gaba ɗaya ko breakfast ɗin nima ban iya ba, sai wajen sha biyu na rana na iya sa abu a bakina, daga nan na dawo kan kujera na ci gaba da zaman damuwa, sai ƙarfe biyu Bilkisu tazo bayan ta dawo daga ofis, ta yi mamakin ganin yadda na rame ma fige duk a iya rana ɗaya.  "Nana haka kika damu da Sardauna? Duk akansa kin wani canja hala ji fa?"  "Bazaki gane ba Bilkisu, wallahi ina son mutumin nan sama da kowa, sama da komai a wannan rayuwar, bana so na ga wani abu guda ɗaya da zai dami Sardauna a duniya, bana son shi wallahi."  "Lallai Nana, to yanzu me ya ce miki yana damunsa?"  "Ya ce sai ya dawo."  "Allah Ya sa alheri ne, Allah Ya sauƙaƙa al'amuran."  "Amin amin."  Haka tai ta yi bani shwarwrin hamyoyin da zan bi na yi maganin damuwar tasa da yanda zan kwantar mai da hankali, na nuna komai zai zo da sauƙi, sai yamma ta tafi kamar ko yaushe.  Tana tafiya na yi wanka na gyara gidan, bayan na yi sauƙaƙƙen abinci na dawo na zauna, ina nan zaune na ji hayaniyar mutane. Labule na ɗaga na buɗe Turaki na gani yau ma kaya ake shigo masa da shi, da alama yau ya dawo dan dama na ji alamun baya gidan, komawa na yi na zauna akan kujera na ci gaba da tunanin yadda zanyi kwantarwa da Sardauna hankali yana dawowa.  Sai wajen tara sannan ya shigo gidan, babu damuwar a fuskarsa kamar jiya, amma bayan na shiga ɗaki na fito na ganshi ya haɗa lai da gwiwa, da sauri na ƙaraso inda yake tare da cewa. "Sardaunana, jarumina, Honey me ya faru?"  "Nana! Bansan ta inda zan fara yi miki bayani ba, amma tabbas akwai matsala."  "Wace irin matsala ce haka dan Allah?" "Nana su Big Daddy da Hajiya ta sun matsamin wai suna ganin jikokinsu na wajena, wai shirun ya yi yawa, Nana duk bayanin da yakamata na yi musu, amma su kasa fahimta, faɗi kawai suke duk inda matsalal take na nemo to na yi maganinta, Nana na shiga damuwa matuƙa na rasa abinda zan yi shi ya sa kika ga na damu kwana."  Shiru na yi nima kaina na rasa abinda zan faɗa, matsalal daga ina take, me ya kawo duka wannan zancen?  "Kinji abun wani kala ko?"  Na gyaɗa kai, sannan na ce.  "Yanzu mene abun da za ayi?"  "Ni kaina bansaniba, ina ta faman tunani."  "Allah Ya sauƙaƙa mana."  "Amin Honey nah."  Haka muka zauna jigun jigun gaba ɗaya na rasa abinda ke mun daɗi, me ya kai 'yan uwan Sardauna wannan zancen? Su da suke wayayyu, 'yan boko masu ilimi, amma zasu zo da wannan zancen?  "Kar ki sakawa ranki damuwa kinji Hon, komai zai zo da sauƙi."  "Nasani." Na faɗa tare da yi masa murmushin yaƙe, sai yanzu na ji ina ma ina da halin kiran su Hajiya na faɗa musu, gaba ɗaya rabona da su an kusa wata guda, Sardauna duk ya hanani.  Ko da muka je bacci ma haka kowa ya kwanta, ransa babu daɗi, ni barcin ma rabi da rabi na yi, Sardauna ne daman shi duk girman damuwa ba ta hanashi bacci, ni kuwa ko ya damuwa take mussamman ta al'amarin Sardauna to ba ni da wata nutsuwa akai.  *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na sha tara.     (19) Gaba ɗaya Sardauna ba walwala ya yi komai har ya fice, a yanzu ba ni da kowa na kusa sai Bilkisu ita kaɗai nake magana da ita, itama sabida mijina ya zaɓe ta, kiranta na yi a waya duk da nasan tana wajen aiki, har ta ƙaraci ringing ɗinta ba ta ɗauka ba, sai da na kira sau uku sannan ta ɗauka.  "Hello Nana, ya aka yi ina ofis ne."  "Bilkisu akwai matsala ne babba ba ƙarama ba."  "Ta mece? Me yake damun Sardaunan?"  "Matsalal daga gidansu take, akan zancen haihuwa ne."  "To ai Nana ba ke ce me matsalal ba ko? Kamar kince min kin taɓa ɓari ko?"  "Eyh na taɓa, nice me matsalal, wai mahaifata ƙarama ce, shi ya sa jariran basu fiya zama ba."  "Innullahi yanzu Nana mene abun yi?"  "Wallahi Bilkisu bansaniba, duk na shiga damuwa, mussamman ganin Sardauna da na yi a yanayin damuwa."  "Ai ba daɗi irin haka, ki lallaɓashi ki ji ko akwai wafa mafita da yake gani, yau bazan shigo ba sabida zani unguwa amma zan zo a satinan."  Daga haka ta kashe wayarta ta barni cike da damuwa. Ina nan zaune na rasa abinda ke min daɗi, kawai na kira Ra'is bayan mun gaisa na ce da shi.  "Ra'is akwai matsala a gidana."  "Ta mece ba dai mijinki ba."  "Shine Ra'is." "Lallai Nana, ke kenan bamu da amfani sai matsala ta taso tsakaninki da mijinki shine mule da rana, ba kyajin kunya sai ki tunkare mu idan kuma kuna cikin soyayya babu 'yan iska sama damu ko? To wallahi kisani babu wanda zai ƙara shiga al'amuranki tsakaninki da mijinki tun da kin zaɓi mutumin da ya haɗu dake ta haƙwaranki talatin da uku, kin bar wacca ta raini ki a cikinta har kika fito duniya, ta yi ɗawainiya dake, kin bar wayanda suka raine ki, su ka so ki, su ka bakk farin ciki, su ka tsoraci kukanki Nana, duk akan wani mutumi guda ɗaya, ki je rayuwar duniya ce."  Yana gama magana ya kashe wayarsa, kuka na fashe da shi, tabbas nasan maganarsa gaskiyya ce, kuma ya faɗa min abinea nake buƙatar a tinasar da ni, amma ya zanyi da Sardauna Allan da ya hallice ni shi ya sanya mini soyayyarsa.  Daga wannan lokacin na ƙudiri aniyar bazan sake kiran kowa a gidanmu akan damuwa ba sai dak gaisuwa kawai.  Bayan sati biyu.  Tun lokacin da maganar nan ta fito gidanmu ya canja daga gidan farin ciki zuwa damuwa, daga gidan walwala zuwa na ƙunci, babu wani abu ɓai daɗi a gidan, kullum muna neman mafita amna taƙi samuwa, ta ɓangaren gida kullum Sardauna matsanta masa ake yi, an hana shi sakat. A yanzu Sardauna har baya son zuwa gidan Hajiyarsu ko Family House, kullum daga gida sai Majalisa yanzu ma da mota yake fita majalisar, ni kam bana iya komai banda tunanin mafita. A ko yaushe cikin saƙe saƙe nake, na yi baƙi na rame gaba ɗaya na fita hayyacina.  Gashi Bilkisu ba ta sake zuwa ba, tun ranar da na faɗa mata matsalal ta ce zata zo a cikin satin, idan ma na kira ta sai ta ce ba ta gari ma baki ɗaya.  Jiya da muka haɗu da Turaki sai da ya tsareni da tambayar me yake damuna, me ya faru tsakanina da Sardauna, amma na ce da shi komai lafiya. Daga ƙarshe ma ya fara yi min nasihohi masu ratsa zuciya akam haƙuri da rayuwar aure, sannan ya dinga jaddadamin na dinga yi wa mijina biyayya, har sai da na yi mamakin me ya sa ya yi haka. Da na dawo ɗaki ma na yi ta faman tunani maganganun Turaki me suke nufi, yanayin maganar kaman faɗa da nasiha yake min daga baya kuma ya dawo shawara.  "Allah Ya sa alheri ne."  Na faɗa, sai kuma can na yi tunanin ko akan maganar da ta ɓullo ne ta haihuwa shi ya sa.  "Innullahi wa'inna illahir raji'un, ya zan yi ni Nana?" Na tambaye kaina tare da fashewa da kuka, sai da na yi mai isata na ta shi na shiga ɗaki, zaman gidanma ya isheni tun da na zo gidan ban taɓa fita ba ko sau ɗaya, a yanzu an kai wata uku zuwa huɗu amma ban taɓa fita ba ko gida ban je ba.  Kwanciya na yi akan gadon na shiga tunanin rayuwa, da irin abubuwan da Sardauna ya saukar akaina, gashi kuma yana ƙara fuskantar wasu.  "Lallai Sardauna ya cika sadauki, Allah Ka ƙara mai lafiya da arziƙi, Allah Ka ƙarawa Sardaunana haƙuri da juriya akan abubuwanda suke tun karoshi, Allah Ka sani ina son bawan nan naka, Allah Ka so shi, ka yarda da shi, ka amince masa akan duk abinda ya sa gaba."  Cikin ikon Allah wani bacci ya ɗaukeni, wanda kiran sallar magariba ne ya tayar da ni, ina tashi na ɗaura alwala na yi sallah, dan yanzu Sarduna a waje yake magariba, idan aka yi isha kuma ya fita, tara da rabi zuwa goma yake dawowa.  Ina idar da sallah na shiga haɗa masa abinci akan dinning, ina cikin haɗawa ya shigo, fuskarsa kamar kullum amma yau ma tafi raunana, ajiye abinda nake na yi tare da tawowa inda yake.  "Sannu da zuwa Mijina."  "Yawwa Nana."  "Ya ofis?" "Nana rayuwa babu daɗi, abubuwa duk sun kacame."  "Innullahi wa inna illahir raji'un, me aka sake cewa kuma?"  "Mene ma ba a ce ba Nana, mene ba a ce ba? Kinsan yau kwanakin da Big Daddy yaban zasu ƙare gashi babu wata mafita da muka samu."  "Ya baka kwanaki ne?"  Na tambaya cike da mamaki, ya gyaɗa kai kusan minti biyar sannan ya ce.  "Big Daddy ya ban 10days akan na fitar da mafita, na ce ya ƙara min zuwa sati biyu to kinga yau anyi sati biyun."  Hawaye na ji suna gangaromin a fuskata, da sauri na gogesu sabida kar Sardauna ya gani, ni da zan ƙarfafa masa gwiwa bai kamata na raunana ba.  "Nana bansan abinda Big Daddy zai ce ba."  "Ni kaina kwana biyu na dage da addu'a sosai da sosai, abinda nake gudu kenan tun farko akan rashin haihuwar nan ka ce kai ba komai, yanzu ga shi komai ya juye."  "Nana ni kaina matsamin aka yi a gida, shi ya sa kuma wallahi nauyinki nake ji Nana, ina jin kunyar yi miki magana akan haihuwa Nana."  "Nasani, duk wannan matsi da takurar da muka shiga akan haihuwa ba ra ayinka ba ne, na kasance me yi maka uziri a ko yaushe Sardauna, ina sonka son da na yarda da kai fiye da kowa fiye da komai, na yi imanin har abada ba zaka taɓa cutar da zuciyata ba Sardauna."  Na kama hannunsa, ya ɗago ya kalle ni. Idanuwansa fal da damuwar da ta dame ni.  "A ko da yaushe ina miƙawa ubangiji Amanarka Sardauna, ina miƙawa Allah ragamar kula da kai, nasani Allah zai amss addu'a ta, ba zai taɓa ɗoramin abinda zaifi ƙarfinka ba, a ko da yaushe ina sonka zan kasance mai sonka Sardauna har numfashi na ƙarshe." Ji na yi ya jawo ni jikinsa ya rugumeni tare da faɗin.  "Nana, bani da wata kalma guda ɗaya da zan iya godewa kan alherin soyayyarki agareni, Nana nasami damarmaki masu yawa sanadiyar soyayyarki, na gode Nana, nima ina sonki." Haka mu ka yi ta lallaɓar juna, ina ƙara nunawa Sardauna girman soyayyarsa a zuciyata, har na samu ya ci abinci ya shirya ya fita Majalisa.  Sai goma ya dawo gida, ina nan inda ya barni ina ta faman saƙe saƙe dan yanzu babu abinda na ƙware da shi kamar damuwa, ina saƙa wancan na since wancan.  "Honey baki yi bacci ba?"  Ya faɗa yana zama.  "Ban yi ba tukunna, har ka dawo?" "Eyh na dawo Honey, kin ga." Ya faɗa yana buɗe ledar da ya shigo ita, kwalin wayar iphone, ya miƙomin.  "Nana take."  Na sa hannu na amsa ina mai jindaɗi.  "Buɗe mana."  Na fara kici kicin buɗewa, iphone 16normal ce pink kala mai kyau.  "Na gode sosai mijina, Allah Ya ƙara arziƙi lafiya da wadata."  "Amin My love."  Ya faɗa tare da ɗaukana zuwa ɗaki.  Washe gari Sardauna bai fita ko ina ba, muna gida gashi ba weekend ba, da na tambayeshi sai ya ce.  "Bana som fita ofis, zan haɗu da Big Daddy. Kuma kinga yau kwana goma sha huɗu ta cika."  Kamo hannunsa na yi, sannan na ce.  "Wane irim hukunci kake tunani kake tunanin zai yanke?"  "Nima bansani ba, amma bana son ya bani hukunci mai tsauri Nana."  "Duk tsaurinsa bai zai yanke ma hukuncin da zaka rasa rayuwarka ba, Sardauna nasan ba zai yanke ma hukuncin da zai cutar da lafiyarka ba, to ina ganin duk wani hukunci da ya biyo bayan wannan mao sauƙi ne a wajena da kai, ni zan ta ya ka karɓar kowanne irim hukunci ne Mijina."  "Na gode Nana, Na gode amma bana son wani hukunci da zai cutar da rayuwarmu, ko wani hukunci da zai sa mu yi abinda ba zamu ji daɗi ba, Nana ke nake so ke kaɗai a duniya, ban damu da 'ya'ya ko rashin su ba Nana, amma tabbas ina jin ba daɗi idan na ga Hajiya ta a cikin halin damuwa, na kan ji zafi idan na ga Alhajina a cikin damuwa, duk akan yara."  "A kullum kaine mai cemin haihuwa da rashinta duk na Allah ne, akan wannan na tashi, akan shi na ɗaura yarda ta, kuma nasan suma sun san da haka, dan haka nasan ba zasu yanke maka hukuncin da zaka kasa ɗauka ba."  "Nana ki yi haƙuri, na yi miki laifi mai girma."  A tsorace na ce.  "Wane irin laifi kuma?" "Nana, na sanar da Hajiya asalin matsalal rashin haihuwarmu, a tunani za ta fahimta ko ta yi mana uziri, kuma nasan ta sanar da Big Daddy."  Shiru na yi na rasa me zance, yanzu tun da sun san matsalal daga wajena ne zasu iya cewa ya sakeni? A fili na furta.  "Innullahi wa inna illahir raji'un."  "Nana calm down kin ji, ko mai zai zo da sauƙi, kece mai faɗin haka."  Gaba ɗaya na tsorata idan babu Sardauna ina zan sa rayuwata ni Nana, ina zan kalla na ji daɗi, ta ina zan iya numfashi bayan babi Sardauna a kusa da ni, na shiga uku ni Nana.  "Ki nutsu ba zasu yanke hukunci mai kamar wanda kike tunani ba in sha Allah."  Cikin muryar kuka na fara magana.  "Wallahi cewa zasu yi ka sake ni wallahi, me ya sa  ka faɗa musu haka?"  "Nana baza su ce haka ba kwata kwata, in sha Allahu." "Sardauna."  Na faɗa tare da tsugunnawa a ƙasa. "Na'am Nana."  "Dan Allah, dan Annabi da girman iyayenka Sardauna kar ka sake ni, ko mene zai faru, wallahi ina sonka, ina sonka ban da wanda nake so bayan kai, Sardauna idan ka rabu dani bani da wata rana a rayuwata, ka yi min alƙwari dan Allah."  "Tashi Nana, tashi ki zauna."  Ya faɗa yana kamoni na zauna.  "Nana, ina sonki fiye da yadda kike tunani, na yi yaƙi mai girma kafin na aureki, sabida haka zan yi wani yaƙin akan na rayu da ke."  "Tabbas Sardauna idan ba kai ni gawa ce."  "Nasani Nana."  "Sardauna kai ne dalilin da yasa nake numfashi, Sardauna kai ne dalilin da murmushi yakw fitowa a fuskata, ka tausayamin dan Allah."  Rumgume ni Sardauna ya yi sannan ya ce. "Nana, na yi miki alƙwarin duk tsanani dui wuya ba zan taɓa rabuwa dake ba, ko da ke ce kika buƙaci haka, Nana wallahi ina yi miki kishin da bazan iya numfashi ba muddin na ga wani namiji a tare dake, ko da ɗan gidanku ne, Nana a ƙarƙashin ikona zaki rayu, anan zaki mutu na yi miƙi alƙwarin hakan Nana."  Duk wasu kalamam Sardauna daɗi suke mim a rayuwa, babban buri na shine na rayu na kuma mutu a ƙarƙashin auren Sardauna. Yinin ranar bai fita ba sai dare, haka washe gari ma wai duk akan big Daddy, sai da ya kwana uki a gida sannan ya yanke shawarar zai fita, shima dai duk a tsorace yake. Ni kuma wani tausayinsa ne yake taɓa min zuciya, Allah Ya gani bana son wani abu da zai dami mijina ko kaɗan, bayan ya fita na yi ayyukana na kwanta bacci.  ***** 06:30pm Yamma ce mai cike da sanyi, ina zaune a falo ina jiran dawowar Sardauna. Tun safe bayan ya fita na ji zuciyata tana bugawa, wani irin nauyi nake ji wanda na kasa fassara shi.  Ko da na yi bacci wani irin mafarki na yi marar daɗi, amma abinda ya kwantar min da hankali shine ba Sardauna ba ne a mafarkin ni ce, ni kuma nasan ina zaune anan babu wani abu da zai sameni, duk da a mafarkin ganina na yi ina kuka a zaune a falon nan, amma yanayin kujeruj falon su sauya kuɓa duk hotona na da suke falon babu su, nasan dai wannan duk mafarki ne.  Ina zaune ina ta faman addu'a Allah Ya sa alherine, duk da al'amuran gidansu Sardaina sun dame ni sosai da sosai, gashi rabon Bilkisu da gidan nan an kwana biyu, sai dai ta waya da muke magana. Ina jin ƙarar motarsa, na tashi da sauri don na tarbe shi kamar yadda na saba. Ina buɗe ƙofar, na gan shi tsaye, amma yanayin da na ganshi ya sanya na sandare a wajen. Sardauna ne, amma ba wannan Sardaunan mai takama da izza ba. Idanunsa sun yi jajir, fuskarsa ta kumbura alamar ya sha kuka, har lokacin hawaye suna zirara a kumatunsa. Legendspen 08129553971 Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na ashirin.     (20) "Sardauna! Me ya faru? Me ya faru da kai?" Na faɗa muryata tana rawa, hankalina ya gama tashi. Bai ce mini komai ba, ya ƙaraso cikin falon ya zube a kan kujera, ya rufe fuskarsa a cikin tafin hannunsa, kuka yake yi mai taba zuciya, yana girgiza kai tamkar wanda aka yi wa rasuwa. Ban san lokacin da nima hawaye suka fara wanke mini fuska ba, na durƙusa a gabansa na kamo hannunsa. "Don Allah Sardauna ka yi magana, ka tsoratar da ni. Ko wani ne ya rasu a gidan?" Ya ɗago idanunsa waɗanda suka rine suka yi ja, ya kalle ni da wani irin tausayi, sannan ya fara magana cikin muryarsa wadda ta dashe sabida da kuka. "Nana... gara ma mutuwa ta ɗauke ni na huta da wannan mummunar kaddarar. Nana, Big Daddy da Hajiya sun sanya ni a gaba sun ce lallai sai na ƙara aure. Wai saboda har yanzu shiru ba ki samu juna biyu ba. Kuma matsalal daga gareki take Nana, su kuma ba za su iya jure  hakan ba, tun da ba asan zuwa lokacin da mahaifar taki za ta yi ƙwari ba Nana, ina cikin damuwa gwanda mutuwa ta ɗaukeni da wannan abun." Wani irin jiri na ji ya kwashe ni, na ji numfashina yana shirin ɗaukewa. Aure? Sardauna zai ƙara aure? "Sun ce... sun ce idan ban yi ba, to za su cire ni daga cikin komai na gidan. Nana, na yi kuka, na roƙe su, na ce musu ke kaɗai kika isa ki zama uwar 'ya'yana, ke kaɗai nake so Nana ke  kaɗai nasani a cikin duka matan duniya amma sun ƙi saurare na. Wai ko dai na sake ki ko kuma na yarda na ƙara aure, idan lokacin da suka ba ni ya cika to za su aura mini wata ko wace." Ya sake fashewa da wani sabon kukan, ya jawo ni ya rungume ni yana kuka a kafaɗata, ni kuwa kamar mutun-Mutumi haka nake jina, ba na gane komai. "Nana, ba zan iya rabuwa da ke ba, amma kuma ba zan iya saɓa wa magabata na ba. Ina son ki Nana, amma kaddara tana shirin raba mana farin ciki." Nima kukan nake yi kamar raina zai fita. Ganin yadda Sardauna yake zubar da hawaye saboda ni, ganin yadda yake nuna mini yana cikin matsanancin hali, sai na ji duk duniya ba ni da masoyi kamarsa. Na ji tausayinsa ya mamaye mini zuciya, har na manta da zafin kishin da yake shirin shiga rayuwata. "Ka yi haƙuri Sardauna,"  na faɗa cikin dasasshiyar murya.  "Idan har hakan shi ne zai kawo maka kwanciyar hankali a gida, to ka bi maganar su. Ba na son ka shiga matsala da iyayenka saboda ni." A daidai wannan lokacin, na lura da wani ɗan gajeren murmushi da ya gifta a fuskarsa ba tare da na fuskanci ma'anarsa ba. Sai na ga ya ɗago ya kalleni, ya sake murmushin.  "Nana kina da hankali? Kinsan me kike cewa? Na je na yi auren haka kike cewa Nana wa zan aura, wa na sani? Kin taɓa ganina da wata mace? Kin taɓa kamani da wata mace? Nana ba kya kishina ne ko me?"  Da sauri na girgiza kai sannan na ce.  "A'a ba haka ba ne, amma ina ganin bamu da wata mafita a yanzu da ta kai hakan, babu ita dole ne mu yi biyayya, idan muna son kasancewa tare."  Kuka ya sake fashewa da shi, tare da tashi ya shige cikin ɗaki. Yana tashi na bi bayanshi har zuwa cikin ɗakin, nasan dole a yanzu ni zan tausashi Sardauna, tabbas yana cikin damuwa mai girma nina sani. Zama na yi akan gadon kamar yadda ya yi.  "Kai daina tagumin nan dan Allah."  "Hhhm! Nana idan banyi tagumi ba me zanyi? Ina da abun yi ne? Wai baki ji abinda na ce miki ba aure fa, aure suka ce na sake nan da two weeks ko zasu bani wacca suka ga dama kuma na sake ki."  "Nasan sun yi fushine, amma ka bi komai a hankali nasan Hajiya za ta sake fahimta dan Allah." "Nana kina nufin na je na yi musu wani bayani? Kina tunanin akwai abinda ban faɗa musu ba? Nana kin raina girman soyayyarki a zuciyata ne?"  "Ko kaɗan ba haka nake nufi ba wallahi, ina nufin mu nutsu mu sami mafita a hankali."  "Kina da mafita? Dan Allah Nana na faɗa min."  "A yanzu dai babu, amma dole na yi tunani na sami mafita domin matsalalka matsala ta ce."  "Allah Ya bamu mafita Nana, ki yi haƙuri kin ji ko?"  "Dame? Me ka yi min haka? Kai zan bawa haƙuri Sardauna."  ****** Washe gari Sardauna bai fita ko ina ba, yana gida gaba ɗaya babu abinda yake iya zuwa, ni ke ta ɗawainiya da shi kamar ƙaramin yaro, kuka kuwa ya yi yafi a ƙirga. Gaba ɗaya bai bani wata dama da zan yi wani tunani ba, gashi a yadda ƙwaƙwalwata ta toshe ina buƙatar isashen hutu kafin na yi tunani, nasan matsala ta babba ce amma har yanzu naƙi yardarwa kaina matsalar babba ce, gani nake akan Sardauna komai zan iya yi.  Sai wajen ƙarfe biyar sannan ya shirya ya fita, bai daɗe da fita ba na kira wayar Bilkisu, ina kira ta ɗauka, cikin muryata dake cike da damuwa na fara magana. "Sister kin daina zuwa kwata kwata, abubuwa duk sun caɓe mini."  "Ba haka ba ne Nana, nima ayyuka sunyi min yawa ga wata matsala da ta fara kunnomin kai a gida."  "Ya salam, ni kaina abubuwam sunyi yawa daga gidansu Sardauna."  "Nana tun da gidansu Sardauna ne ai da sauƙi, nifa akan kaina nake magana, Nana kinsan Abbanmu ya bani sati ɗaya na fito da mijin aure ko ya auramin wani abokinsa, Nana dattijo ne ya kai kusan shekara 70, gashi kinsan ni babu wanda nake kulawa, Nana ina cikin damuwa."  "Allah Sarki 'yar uwa, muma makamanciyar matsalalki muke fuskanta."  "Bangane ba?"  "Gidansu Sardauna sun matsa mishi akan ya ƙara aure."  "Saboda me to?"  "Rashin haihuwa mana."  "Nana kika ce kin yi ɓari har sau biyu, kuma kince mahaifarki ce ba ta yi ƙanƙanta ko?"  "Hakane."  "To ai zaki haihu Nana, ki yi musu bayani mana."  "Bilkisu ba zaki gane ba, a yanzu dole Sardauna sai ya ƙara aure ko kuma ya sake ni."  Na faɗa ina fashewa da wani irin Kuka, bana son kalmar sakinan ko kaɗan a rayuwata. "Idan har haka ne mafita Nana ki amince masa, tun da kina son sa, kina son farin cikinsa, farin cikin iyayensa ai shine nashi, Nana ke kika ce kina son Sardauna sama da kowa sama sa komai, to ki nuna masa a wannan lokacin, ki nuna masa soyayya ki dage ki danne ki barshi ya yi auren."  "To ai ba anan matsalal take ba."  "Nana ga Momy nan mu yi magana anjima."  Ta faɗa tana kashe wayarta, bayan wayar ta mutu ta barni cikim tunani. 'Idan da gaske nake son Sardauna yanzu ne lokacin da zan nuna masa soyayyar ta hanayar ƙarfafa masa gwiwa kenan? To amma Sardauna baya kula mata ba ruwansa.'  Wani ɓari daga zuciyata ya ce da ni. 'Ko a wajen aikinsa ba zai rasa ba, ko a 'yan uwansu.'  'A 'yan uwansu fa?' Na tambayi kaina.  'Kai a'a gaskiyya a gari kawai ya nema ya aura, zanyi haƙuri zanyi biyyaya in sha Allah.' Wannan ita ce shawarar da na yanke akan Sardauna, ita ce mafita guda ɗaya da nake ganin za ta fiye mana daga ni har shi. Sai wajen ƙarfe tara ya dawo, ina zaune a falo ya shigo.  "Sannu da gida Honey."  "Yawwa sannu da dawowa."  Na amsa masa, kasancewar ba shigar ofis ba ce yasa ban cire mai takalmi ko wani abu ba.  "Ga abinci."  "Honey ba ni da nutsuwar cin abinci, ni kaɗai nasan abinda nake tun kara Honey, ni kaɗai nasan abinda nake ji.Hon ina cikin damuwa, ina cikin tashin hankali, rayuwa ta yi min baƙi mutuncina yana watangarirya."  "Ka yi haƙuri, komai ya yi tsanani sauƙi yana tafe, a yanzu na yi tunani kuma na fitar da wata shawara da nake ganin kamar ita ce mafita Hon."  "Mecece? faɗamin dan Allah."  "Hon, rayuwa tana bamu zaɓi da dama, wani abun da muka tsara da kanmu, wasu kuma sukan afku ba tare da muntsara su ba, kamar yadda bamu taɓa tsara zamu san juna ba kafin nan, haka bamu taɓa tsara zamanmu zai zo da wata tangarɗa ba bayan munsan juna, Honey ubangiji ne ya dasamin sonka a zuciyata, na yi imani da Allah na yi imani da soyayyar da kake min Hon, dan haka ni dai a ganina kawai ƙara auren ne mafita agaremu dukkanmu. Duk son da nake yi maka, duk ƙaunar da nake yi miki ba ta da wani amfani a ranar da narasa ka, a ranar da nazama ba mallakinka ba, duk wata iriyar soyayyarka da nake ji ba ta wata rana. Idan har ina son ka me zai sa ba zan so ma farin ciki ba? Me zai sa bazan so ma ladan biyayya ga iyaye ba? Menene wata riba a duniya da ta wuce ta biyayya ga iyaye Sardauna?"  "Nana wai kina nufin kema kin amince na ƙara aure?" Wani irin zafi nake ji a zuciyata a duk lokacin da Sardauna ya ambaci ƙara aure, amma ya zanyi ƙaddara ta riga fata, dole ne na goyi bayansa akan yiwa iyayensa biyayya.  "Na goyi bayan ka yi biyayya ne Sardauna, domin kasami rabauta da tsira a duniya."  "Nana bazan iya ba, bazan iya ba, bazan iya ba wallahi, na yi miki kishiya fa Nana, wa zan aura to? Wa nasani ma bayan ke?"  "Ka duba zaka samu in sha Allah."  "Cikani."  Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa.  "Ka fahimce ni dan Allah, idan fa baka yi auren ba rasani zaka yi, zasu ce ka sake ni."  "Nana su faɗa, ai ba lallai ba ne na yi musu biyayya."  "A'a Sardauna, idan ka neman albarka dole ka yi wa iyayenka biyayya, ni dai ka fahimce ni."  "Nana kenan, wace kalal fahimta zan miki? Zancen ki anan babu abinda yake nunawa sai zallar rashi Kishina, Nana kalamanki tsaf zasu yi wa zuciyata Sartse mai raɗaɗi."  Kuka ne ya ci ƙarfina, ni a yanzu ai angama yi wa zuciyata Sartse gaba ɗaya, domin duk lokacin da na ji a raina wai Sardauna zai ƙara aure sai na ji wani raɗaɗi daga cikin zuciyata mai haɗe da ya ji, amma yana iya? Dole na so farin cikin mijina sama da komai a wannan rayuwar.  "Ka yi haƙuri Sardauna."  Na faɗa ina jawo shi jikina, ya rungume ni iya ƙarfinsa kamar zai mayar da ni jikinsa, ina jin yadda yake shasheƙar kuka.  "Ka yi haƙuri ka ji." "Ya zanyi Nana?"  "Ka yi tunani ta ina ka haɗu da ni, har ka tun kare ni, nasan zaka samu zaka samu wacca zaka iya aura."  "Nana bana so su bani a dangi, bana so su ce na rabu dake Nana, bazan iya ba."  "A waje zaka samu."  "Hhhm, Nana kenan."  ******* Har dare Sardauna ya kasa fahimta ta, ya kasa fahimtar inda zance na yake son nufa, a haka muka haƙura mu ka kwanata, sai dai fa ni bacci yaƙi zuwa idona, tunani nake anya zan iya kasadar barin wata kusa da Sardauna, babban abinda yafi bani mamaki, ban ji mahaukacin zafi a cikin zuciyata ba akan zancen ƙarin auren, zafin da fi ji shine na rabuwa da ni, ko dan maganar sake ta shigo ita ce ta cire min raɗaɗin kishin? Amma kwata kwata ban ji ina mugun kishi ba, ko a baya ma bana iya tuna kishin da na yi akan Sardauna ba.  Ƙarfe uku na dare na tashi, bayan na yi nafila raka'a biyu na yi addu'o sosai, sannan na dawo na kwanta, sai a lokacin bacci ya ɗauke ni.  Washe gari ma haka muka tashi da Sardauna yanayin babj daɗi, na yi masa bayani yafi sau cikin carbi amma amsa ɗaya yake ba ni.  "Honey bazan iya ba, Honey ban da ita."  Ya koma kamar wani ƙaramin yaro ba abinda yake iya ganewa, abinda ya ƙaramin tausayin Sardauna kenan, gaba ɗaya ji nake duk ni ce na ja masa komai ma, ko kuma na ji dama akaina waɗannnan abubuwan suke faruwa ba akan Sardauna ba, domin duk damuwar sardauna guda ɗaya, sau dubu nake jinta a zuciyata.  Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na ashirin da ɗaya.     (21) Da ƙyar na iya lallaɓa Sardauna ya fita ofis, amma da ya ce wai bazai iya fita ba sabida kowa ya ganshi zai san yana cikin damuwa. Sai da na yi masa daɗin baki sosai na nuna masa babu wanda zai gane yana cikin damuwa, sannan ya fita.  Tun bayan tafiyar Sardauna na shiga aikina na kullum, amma sai dai na yau zuciyata tafi nuna min wa Sardauna zai aura, wani irin zama zamuyi shin zai so ta kamar yadda ya so ni, ko ma zaifi sonta, za ta yi masa biyayya irin yadda nake yi? Ko za tafi ni? Dole fa na dinga raba mata kwana da Sardauna, duk da hakan bai dameni ba amma tabbas ina jin ba daɗi.  Har yamma ina ta faman tunani, da kuma tsoron me Sardauna zai dawo da shi, zai sami matar ne ko sai gobe? "Ya Allah ka sa wannan auren ya zama ƙarshen duk wata wahala, da wani tashin hankali."  Knocking na ji ana yi min, na tashi a raina ina addu'ar Allah Ya sa Bilkisu ce, sai ina buɗewa na ga Turaki.  "Ina wuni?"  "Lafiya ƙalau Nana."  Ya faɗa yana kallona, ganin shirun ya yi yawa na ce.  "Bayan nan."  "Nana komai lafiya a gidanki?"  "Lafiya ƙalau."  "Kinje wajensu Hajiya?"  "Na je."  "Amma Ra'is ya ce kin fi watanni baki je ba, me ya sa?"  "Ina zuwa."  "Nana yakamata kije ki yi magana da Hajiya, ki faɗa mata duk wata matsala da take damunki."  Yana faɗin haka ya juya ya shige ɓangarensa, haka na dawo ciki duk jikina babu daɗi, ni shikenan kullum rayuwata a babu daɗi, zaman ba daɗi, gidan ba daɗi, ni narasa wace irin rayuwar aure ma nake yi.  Waya ta na ɗauka na kira Hajiya, na yi sa'a kira ɗaya ta ɗauka. Bayan mun gaisa nake ce mata bani da lafiya ne kwana biyu.  "Me yake damunki?"  "Hajiya na yi ɓari ne." "Allah Ya ƙara lafiya." "Amin Hajiya, ya mutan gidan?"  "Nana kowa yana lafiya, Ra'is ya ce kun yu waya kwanaki, Nana duk wanda na ce ya zo gidanki sai ya ce bazai zo ba mijinki, sai  da wancan ɗan Albarkan Turaki ya zo na yi masa magana, nasan yanzu ma shi ya yi miki magana ko?"  "Eyh Hajiya shine."  "Nana ki dinga addu'a kin ji."  "In sha Allah Hajiya."  ***** Wayar da na yi da Hajiya ta rage min wani abu daga cikin damuwar da nake ciki, yamma lis sai ga Bilkisu ta zo itama a kiɗime, al'amarin mahaifinta ya ta azzara akan auren da ya ce  zai yi mata.  Itama gaba ɗaya ta yi wani sukuku, ta fita hayyacinta.  "Bilkisu to ke ki duba cikin masu zuwa wajenki mana." Na faɗa dan dai nasan Bilkisu ba zata taɓa rasa masu zuwa wajenta ba, domin dai tana da kyanta yadda yakamata, ga ilimi kuma yar gayu ce sosai da sosai.  "Nana bazaki gane ba kwata kwata, duk masu zuwa wajena ba na aure ba ne, burinsu na basu haɗin kai su ɓarar mun da mutunci su cuceni." "Ya salam, Allah Ya tsare ki." "Amin amin, ku yanzu kun sami matsaya?"  "Eyh mun samu, aure kawai Sardauna zai ƙara kamar yadda suka umarta." "Allah Sarki Nana gaskiyya kinyi namijin ƙoƙari Allah Ya baki haihuwar nan."  "Amin Bilkisu, Allah Ya kawo miki mafita."  Itama ta ce Amin, nan muka zauna kowa na jajantawa kowa har Sardauna ya dawo ya sameta, sai bayan ya dawo ta tafi.  A yanayin Sardauna na yau dai babu wata sabuwar matsalal, kuma na ji daɗin hakan sosai da sosai, haka washe gari ma babu wata matsalal. Al'amuran kamar sun sauƙaƙa wajen kwana biyar, sai ranar kwana na huɗu Sardauna ya dawo cikin tashin hankali, Hajiyarsa ta ce lallai lallai ya sake ni idan har bai fito da mata ba cikin kwana biyu, a kiɗime na ce.  "To baka ce musu kana dubawa ba ne?"  "Nana wa zan duba, har yanzu fa ban ga wata da na ji zan iya haɗa ta dake ba, Nana mata basu da kama ko kaɗan, bazan iya auren wacca zata hulaƙanta ki ba ko kaɗan Nana."  "Kar ka damu Sardauna, ni zan iya zama da kowace muddin kana nan kuma kana ganina a matsayin da kake ganina yanzu, Sardauna ka auri duk wacca ta yi maka."  "Nana anya kuwa kina kishi na?"  Kallonshi na yi, sannan na kalli ƙasa.  "Tayar maka da hankali shine kishi? Sardauna indai sai na ɗaga maka hankali na saka a damuwa bayan wacca kake ciki shine kishi to ni bana kishi, hasali ma babu zuciya a tare da ni, ina sonka a kowanne irin hali, zan ci gaba da sonka a kowanne irin yanayi Sardauna."  "Nana bana jin zan iya neman wacca zan aura, ina neman alfarma a wajenki guda ɗaya dan Allah."  Ya faɗa yan goge ƙwallar da take idonsa, bai bari na yi magana ba ya tsugguna a gabana, tare da riƙe min hannuna.  "Nana! Dan Allah, dan girman ma'aiki ki ta ya ni duba wacca zan aura, Nana kowa kika kawo indai kin aminta da ita to zan aura Nana, dan ke zan yi auren kuma ina so ki nema min waccan zan aura da kanki da hannunki Nana."  Wani irin nauyi na ji ya danne ni kamar an ɗauramin gungumen dutse. Tabbas wannan alfarmar da Sardauna ya nema a wajena da girma take, ta ina zan fara?  "Nana dan Allah, mutuncina da darajata duk suna hannunki a yanzu ki tallafa min Nana."  "Ka tashi zaune dan Allah."  "Nana ki yi min wannan alfarmar dan Allah."  "Tom na yi ka tashi zaune ka ji." "Na gode Nana." Ya faɗa tare da zama kan kujerar, ya ƙureni da ido sannan ya ce.  "Nana!"  "Na'am."  "Na ga kin rame kamar bakya cin abinci?"  Kallon jikina na yi, ni banga wata rama ba amma tabbas nasan a jikina ina jina falai falai kamar wata takarda.  "Nana kamar ba kya cikin ni'imar aure, matar Ta Ambo ce a haka Nana?" "Ba wata rama da na yi fa, kawai strees ne." "Name?"  "Abubuwan da suka dagule mana, komai ya rincaɓe."  "Nana ai komai yazo ƙarshe ko? Komai zai yu sauƙi tunda a yanzu za ayi auren kuma ai shikenan ko?"  "Eyh shikenan in sha Allah."  "Yawwa Nanaty, zan ci abinci."  Tashi na yi ma nufi wajen dinnig ɗin, shi kuma yana biye da ni a baya, alkubus da miyar taushe ne na yi, ya zauna ya ci sosai nima kuma ya matsamin sai na ce, yadda ya ci haka na ce. Ko majalisar ma baije ba ya kwashe ne muka yi ɗaki, duk ranar da Sardauna ya ɗaukeni da kansa ina shan wahala har nagane, shi ya sa bana so ya ɗaukeni nafi son mu tafi ƙafa da ƙafa.  Tun daga wannan lokaci Sardauna ya sani a wata duniyar ta daban, kullum aikina tunanin wace za ta da ce da Sardauna, dan ya zama dole na nema masa a ƙasa da kwana ukun da ya ambata. Ƙawayena Malaika ta yi aure tana kano, Fauziya ta yi aure, Amina Aminu ma ta yi aurenta daman su kenan, Yaya Radiya kuma Yayata ce babu aure a tsakaninsu, Anty Adiza kuma matar aure ce, ni kuma su kaɗai ne mutanen da nasani, sai dai ko Bilkisu ita kuma aure ne ba ta so a yanzu.  "Ni fa ina ganin can yaje danginsu ya nema, zai fi mana sauƙi."  Na faɗa a fili kamar ina magana da wani ko wata, ko da ya dawo ma baiyi min maganar ba kuma nima bance komai ba, washe gari ma haka na yi ta faman tunani, sai gab da yamma na shirya naje gidan kitso wanda daman na tambayeshi, tun zuwana unguwar gidan kitson kawai nake zuwa shima sai na yi wata nawa banje ba. A hanya na yi ya kallon 'yan mata ko akwai wacce za ta da ce da Sardauna, amma bansamu ba. Haka a gidan kitson ina zaune ina kallon mutane sai hira suke, a ɗauko gulmar waccan a sauke a ɗauki ta waccan har layi yazo kaina ni dai ban tanka musu ba.  "Baiwar Allah a wane gida kike?"  Wata mata ta tambayeni.  "Nan baya."  "Ina ne baya ko ba anan kike ba?" Wata daban ta yi tambayar. "Eyh ina Takur Site C ne."  "Eyh kam da dan nisa gaskiyya, amarya ce?"  "A'a na shekara biyu."  "Allah Sarki Allah Ya sanya alheri."  "Amin."  Na faɗa daga nan ban sake ce musu komai ba har aka gama yi min na tashi na tafi, a raina na ce.  "Ina fita zaku hau yi dani."  Illai kuwa ko ƙarasa fita ban yi ba na ji muryar wata ta ce.  "Wai ita matan Takur sai wani shan ƙamshi ake."  Murmushi na yi na ƙarasa ficewa ta, ba su san ɗimbin damuwar dake damuna ba ne shi ya sa ma suke wannan zancen.  Har na ƙaraso gidana ina kallon 'yan mata hanya sai dai Allah bai sa na ga wadda zata da ce da mijina ba, haka na dawo gida shiru. Nan dai na yanke shawarar tamnbayarshi na ji ko akwai wata yarinya da yake burgeshi haka, ko yake yawan ganinta.  Banyi masa maganar adawowarsa ta farko ba, sai da ya dawo daga Majalisa sannan na ce.  "Na yi tunani a iya matan da nasani, amma kafin nan kai babu wata yarinya da ka sani ko kake ganin tana da hankali."  "Nana bayan ke bansan kowa ba." "Ko a wajen aikinku, ko a family?" "Nana bayan ke bansan kowa ba."  "Ka na ji, ko a unguwarku da kuna ƙanana?"  "Nana unguwar da na taso ba irin Yalwawa ba ce, Unguwa ce da ba ruwan kowa da kowa, unguwa ce ta masu arziƙi babu talaka ko ɗaya a unguwar dan haka babu 'yar wanda nasani Nana, ba kamar ku ba cike da yara wani gidan na cin wani gidan, yara su shiga wancan gidan su fita wancan, mu duk ba haka muke ba." A maganar sai na ji kamar gori, na yi mishi murmushin yaƙe sannan na ce.  "Ba haka nake nufi ba ranka ya daɗe, irin ko a makaranta haka?"  "Nana, zaki yi min ko bazaki yi ba? Idan bazaki yi ba just tell me, ba sai kina haɗani da ƙazamar rayuwa marar daraja ba, rayuwata ba irin wannan ba ce Nana. Ina ga har yanzu bakisan su waye Familyn mu ba Nana." "Ka yi haƙuri, baka fahimce ni ba."  "A'a ba wani ban fahimce ki ba Nana."  "Ka yi haƙuri."  Ta shi ya yi ya shige ɗaki ba tare da ya ce dani ko ƙala ba. 'Oh ni yau me yake damun Sardauna ne?.' Na tambayi kaina a zuci.  Washe gari ma haka ya tashi yana faman cicin magani ko breakfast ma cewa ya yi wai ba zai ci ba.  "Dan Allah me ya faru?"  "Nana kinfi kowa sanin duk abinda ya faru." "Bansan sani ba, bansan wani abu da ya faru wanda yasa ka canja baki ɗaya." "Hhm! Nana sai na fito fili na faɗa miki cewar ki nemo min aure?" "Ai akan wannan maganar muke kai kuma ina kan dubawa."  "Su wa kika duba?"  "Duk cikin ƙawayena kowacca ta yi aure."  "Duka babu marar aure kenan?"  "A na kusa dai babu, shi ya sa nake so kara faɗa tunanina don bincikawa."  "Nana yau ne fa ranar ta ƙarshe da Hajiya ta bani."  "Nasani kuma in sha Allah yau komai ƙare."  "Nana ki yi duk abinda kike tunanin zaki iya, dan Allah."  "In sha Allah, to muje ka yi breakfast ɗin."  Muka nufi dinning ɗin, muna cikin breakfast ɗin Sardauna ya ce.  "Nana! Ko zan samu ki wanken kayana ko guda biyu ne, na ji daɗin wancan da kika yi min."  'Ashe Sardauna ya kula na yi masa wanki? Amma ko a ido bai taɓa nuna min ba, ko da yake gashi yanzu ya faɗa.' Murmushi na yi masa sannan na ce.  "Babu damuwa, ko ban yi yau zanyi gobe." "Me ya sa sai gobe." "Idan ba mafita na samu akan wannan maganar ba bani da nutsuwar da zan iya yin wankin da zai burgeka ya yi maka kyau."  "To shikenan, Allah Ya yi miki albarka Nanaty."  "Amin amin."  Tin fitar Sardauna nake tunanin inda za a sami mafitar ƙarshe, kwatsam Bilkisu ta kirani a waya, bayan na ɗaga muka gaisa na ce da ita.  "Ya Abban naku?"  "Nana ya ƙaramin one week ɗazu, na ji daɗi sosai wallahi Nana zan duba yanzu duk wanda yazo zan bashi fuska."  "Ma sha Allah Bilkisu, Allah Ya kawo na gari." "Amin Nana, na gode miki da nuna kulawa, zan je ofis mu yi magana anjima."  Bayan ta kashe wayar kawai tunanin haɗa ta da Sardauna ya faɗomin.  "Zaman Sardauna da Bilkisu zai yi ɗaya kuwa? Tsakanina da Bilkisu akwai fahimtar juna, akwai soyayya to amma Sardauna fa?"  Legendspen 08129553971. *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na ashirin da biyu.     (22) ‘Sardauna baya son karatu? Bilkisu har aiki take yi, shin Bilkisu za ta iya barin aikinta sabida Sardauna, ko kuwa Sardauna zai iya haƙura ta yi aiki, ya ce kuma yana da kishi ba zai iya jurar matan shi na yawo a titi ba suna cakuɗuwa da maza, amma tabbas Bilkisu za ta dace da zamanmu a wannan ƙadamin, tun da itama mahaifinta ya bata lokaci kamar yadda Hajiyar Sardauna da Big Daddy suka ba shi?’  “To Nana hakan ba matsala?” Na ji wani ɓari na zuciyata ya faɗa a fili kamar wani daga wajene ya faɗa. ‘Sardauna yana sona, kuma Bilkisu tana sa ilimi zata zauna da ni da Sardauna lafiya, ni bani da wata matsala indai Sardauna na nan kuma yana kallona a matsayin mata ina ƙarƙashen inuwar aurensa.’  Waya ta na ɗauka na kira Bilkisu amma ba ta ɗauka ba, ƙila bata ƙarasa ofis ba sai kawai na tura mata text.  “Bilkisu dan Allah ki kirani, akwai mafitar da nake tunani wacca za ta kawo ƙarshen komai in sha Allah.”  Na tura mata tare da emoji na kuka da na roƙo, ina turawa na nemi lambar Yaya Rumaisa dan tabbas sai na sanar da wani nawa. Bugu ɗaya ta ɗauka tare da faɗin.  “Manya yau a gari?” “Ina wuni Yaya?”  “Lafiya ƙalau Nana, ya gidan?” “Alhamdullah Yaya, dan Allah wata magana zan faɗa miki amma bana son Hajiya ko wani ya sani.”  “Wace magana ce haka Nana?”  “Ki yi min alƙwari dan Allah.” “Nana ya za ayi na yi alƙwari akan abinda bansani ba?” “Dan Allah ki yi min, ba wani abu ba ne na cutarwa kawai labari zan baki.” “Shikenan Nana na yi miki.”  Na sauke ajiyar zuciya sannan na ce.  “Zan ƙarawa Sardauna aure.”  “Bangane abinda kike nufi ba.”  “Yaya a gidansu aka bashi zaɓi guda biyu, tun da ni bana haihuwa mahaifata ba ta gama ƙwari ba ko ya sake ni su aura masa wata ko kuma ya ƙara aure.”  “Ke bana son rashin hankali, uban waye ya ce miki ba kya haihuwa?”  Ta faɗa cikin jarababbiyar muryarta. “Munje asibiti sabida na yi ɓari har sau biyu, shine aka ce ba ta yi ƙwari ba.”  “To da zai sake auren shine ke zaki ƙara masa?”  “Yaya ya bani zaɓi ne akan na nema masa matar.”  “Wannan shine kuskure na biyu da zaki yi a rayuwarki da Sardauna, na farko kin zaɓi miji sama da kowa, sai da ya raba ki da ‘yan uwanki da duk wasu mutane a kusa dake shine zai ƙara aure? Nana wai uban me kike sha?”  “Yaya Umarni ne daga gida, shi ya sa ma ya bani damar zaɓa masa wadda zai aura.”  “Lallai Nana mahaukaciya ce ke? Dan mun yi alƙwarin bazamu sake shiga al’amuran gidanki ba, amma dai sai na zo har gidan na ci ubanki na ci uban mijin, banza marar hankali wace yarinyar kika zaɓa masa?”  “Wata maƙwafciyar mu ce.” “Jaka! Nana bansan ki lalace ba sai yanzu.”  Tana faɗin haka ta katse kiranta, ni nama manta da halin faɗa irin na ta har na kira ta, gashi ta zageni ta zage mijin nawa gaba ɗaya, ita daman bata da haƙuri ba abinda ta iya sai faɗa a rayuwarta.  “Mitcheww.”  Na ja tsaki na kwanta akan kujera, banda rainin hankali irin Yaya Rumaisa mutumin da baya son auren ƙarshe ma yaban zaɓi shine za ta ce wai ya rabani da kowa shine zai ƙara aure. Duk sai da na yi danasanin kiranta, daman ita ba a fiya yin abun arziƙi a kwashe duka da ita ba, haka na yi ta faman ɓacin rai har yamma, yau indomie na yi wa Sardauna dan ba abinda zan iya sabida wani irin ciwon kai da na tashi dashi bayan na kwanta da yamma.  Fuskarsa babu yabo babu fallasa haka ya shigo cikin gidan.  “Sannu da zuwa.” Bai amsa ba ya ajiye jakarsa, yanayin da nake ji ma bazan iya tashi na bishi ba, yanda ya shiga ɗakin haka ya fito.  “Baki da lafiya ne?”  “Jiri nake ji.” “Sannu, bama ki yi girki ba kenan?” “Na yi.” “Bari na ci.”  “Tom, akwai magana.”  “An samu?” Na gyaɗa masa kai. “Faɗamin to.”  “Ka fara cin abincin.”  “A’a faɗan.”  Sai da na tashi zaune na riƙe hannunsa.  “Kasan dai bazan zaɓa ma abinda zai cutar da ka ba, dan Allah ina son ka amshi zaɓin da na yi maka da hannu biyu biyu, kuma kasa a ranka alheri ce a garemu duka.” “Nana duk jikina ya yi sanyi, wace ki faɗamin dan Allah.”  “Bilkisu! Wannan ƙawar ta wa ta kake ɗan ganinta.”  Shiru ya yi sai kuma can ya ce.  “Wata fara haka?”  “Eyh ita.”  “Anya Nana?”  “Dan Allah karka ce a’a.”  “Nana zan yi shawara.” “Tom, amma da matsala guda fa?”  “Kinji ko? Wace matsalal?”  “Tana aiki.”  “Wane kalal aiki kuma?”  “Aikin Ofis, kuma ka ce ba zaka iya jure ganin matarka na cakuɗuwa da maza ba, shine nake so dan Allah ka yi haƙuri ka barta.”  “Nana sai na yi tunani gaskiyya, bari na ci abincin.”  Yana faɗin haka ya tashi ya nufi dinning ɗin, da kanshi ya zuba ya ce kuma bai yi magana akan indomie ɗin ba, ko da yaga ban jindaɗi ne?  ********* Yau Sardauna bai fita majalisa ba, da na tambayeshi sai ya ce bani da lafiya dole ya yi jinyata kuma gashi yana son ya yi tunanin akan al’amarin nan. Haka dai na yi bacci na barshi yana faman tunane tunane.  Washe gari bayan munyi breakfast zai fita ya ce da ni. “Nana na yi tunani duba da yanayin da muke ciki na matsi Hajiya da Big Daddy na amince zan barta ta yi aikin na ta, amma gaskiyya bana so.”  Har cikin raina na ji daɗi.  “Alhamdulillah, Allah Ya sa albarka, yanzu sai na yi mata magana nasan zata amince itama.”  “Wannan ya rage naki.”  Ya faɗa yana ficewa, ni kuma na koma kan kujera na zauna, na ɗau wayata na fara kiran lambar Bilkisu, amma bata ɗauka ba, gashi message ɗin na jiya ma ba ta dawo da amsa ba. Sake kiranta na yi har ta gama ƙarar ta ba ta ɗauka ba, haka na ajiye wayar da tunanin an jima zan sake kiranta idan ba ta kirani ba. Har yamma ba ta kirani ba kuma nasake kira ba ta ɗauka ba, na yi ta addu’ar Allah Ya sa lafiya dai. Da ddaddare na faɗawa Sardauna na ce ya bani wayarsa na kira ta sai ya ce na sake kiranta dai. Ina kira kuwa ta ɗauka.  “Nana ki yi haƙuri, yau na yi busy da yawa wallahi, ina ta ganin kiranki ban sami zama ba.” “Ayyah ba komai Bilkisu, ya gida ya aikin?”  “Alhamdullilah, ya mai gidan?” “Lafiya ƙalau, na ce ya ake ciki da maganar Abban naku an da ce kuwa?”  “Tun da ya ƙaramin sati ɗaya bamu sake maganar ba, kuma kamar naga saƙonki ko? Kince kin sami mafita?”  “Eyh Bilkisu na samu wacca nake ganin za ta yi amfani wa ni dake.”  “Nana ai matsalal mu ba ta da alaƙa da juna.”  “Eyh Bilkisu sai dai kamanceceniya, Abbanku ya matsa miki, nima Hajiyar Sardauna ta matsa me zai hana Bilkisu mu haɗu a rufawa juna asiri, ki auri Mijina.”  “Nana kina da hankali? Kinsan abinda kike faɗa kuwa? Na auri mijinki Sardauna?”  “Is for the best Bilkisu Please.” “Nana bazan iya ba, a yadda kike son mijinki na shiga ciki? Ki rufan asiri Nana.”  “Bilkisu ke ce last hope ɗina, aure na ma tangarɗa yake ki taimaka.”  “Lallai Nana, dan Allah ina so ki a ranki bamu taɓa wannan maganar ba dan Allah.”  Tana gama faɗin haka ta kashe wayar, na kalli Sardauna da yake zaune yana sauroro.  “Nana akawai wata bayan ita?”  Na girgiza kai sannan na ce.  “Ita kaɗai ce.”  “Nana to ya za ayi?”  “Ita ɗin dai, nasan za ta fahimta in sha Allah.”  “Nana banga alama ba, ki na ji ta ce yadda kike son mijinki ba za ta iya shiga tsakaninku ba.”  “Hhhm, idan ba ta shiga ba rasa ka zanyi gaba ɗaya.” “Nana ki daina wannan tunanin ba zaki taɓa rasani ba, Nana a yadda nake jin ki a rayuwata idan babu ke nima ai babu ni.”  “Nima nasan ba zan rasa ka ba, amma biyayya ga iyaye dole ce idan muna neman albarka a rayuwa.”  “Nana bari na je gidan Hajiya na gara kiranta yanzu.”  “Tom Allah Ya tsare hanya.”  “Amin Ya Allah.”  Ya faɗa yana tashi, yana fita na sake kiranta a waya amma bata ɗauka ba, message na hau rubuta mata.  ‘Salam, Bilkisu dan Allah ki fahimceni, ina so ki aure mijina Sardauna sabida ki tsira daga auren dole da zaayi miki, shima ya tsira daga auren dolen da za ayi masa ki fahimta dan Allah.’  Na tura mata amma har Sardauna ya dawo ba ta yi min reply ba, washe gari da safe ma na sake tura mata wani amma shima ba ta ce dani komai ba.  “Honey ya kuka yi da yarinyar?”  Kallonsa na yi sannan na ci gaba da haɗa mai tea ɗin, sai da na gama sannan na ce.  “Ba ta sake cewa komai ba, amma dai zan ƙoƙarta zan sake magana da ita.”  “Shikenan Nana, nasan zaki iya, Allah Ya yi miki albarka.”  “Amin Amin.”  Bayan mun kammala breakfast ya tafi, na dawo na ci gaba da kiran wayar Bilkisu amma bata ɗauka ba, ganin ba zata ɗauka ba na shiga fito da wankin kayan Sardauna na hau yi, da ƙarfi nake dirza kayan sabida ina son su fita su yi haske yanda zai ji daɗi, sai wajen la’asar na gama wankin na shanya su s abun shanyar mun na bayan kitchen, ina dawo na ga missed call ɗin Bilkisu, jikina har ɓari yake na ɗau wayar na kira ta, ina kira ta ɗauka, cikin rawar baki na fara magana.  “Bilkisu!”  “Na’am Nana.”  “Bilkisu kinga messages ɗina?”  “Nagani Nana, ni bansan abinda zance miki ba shi ya sa ma ban miki reply ba, kina magana kamar wata ‘yar ƙwaya.”  “Hhm Bilkisu ba zaki gane ba ne, amma dan Allah ki taimaka, ki taimakeni ki taimaki mijina.”  “Nana babu wata hanyar taimako da zan ia yi miki bayan wannan? Gaskiyya wannan abun yafi ƙarfina, ki barni da matsalal Abbana kawai.”  “Bilkisu dan Allah ki biyo ta gidana mu yi magana.” “Nana bana jin zan sake zuwa gidanki, tun abinda kike son ƙullamin kenan? Ace na zo gidanki na aure miki miji, duniya ta yi ta zagina.” “Haba Bilkisu ya zaki ce haka? Dan Allah kizo ko ba zaki aureshi ba nasan akwai shawarar da zaki ban.”  Shiru ta ɗanyi na ‘yan mintina sannan ta ce.  “Shikenan, bari na zo yanzu.”  “Tom Bilkisu na gode sosai.” “Sai na zo.” Ta faɗa tana kashe wayar, na koma na zauna. ‘A halin da Bilkisu take ciki na yi tunanin zata amshi wannan tayin hannu biyu biyu? Ko dan mafita da take nema, amma taƙi! Lallai Bilkisu ta cika mutuniyar arziƙi.’  Ta shi na yi na duba kayan Sardauna dana wanke, na fara kawahe waɗanda suka bushe na shiga dasu ciki, ina fitowa itama ta shigo ɗakin, ban bari ta zauna ba na fara mata magana.  “Haba Bilkisu, ahalin da kike ciki na yi tunanin wannan mafita ce a garemu duka?”  “Nana mafita ce mana, amma da ace wani ne ba mijinki ba, Nana da wane ido zan kalli duniya? Da wani ido zan kalli mutane zan kalli makwafta, zan kalli ‘yan uwanki, ace ina ƙawarki na zo na auri mijinki, zagin da zan sha Nana ba ƙarami ba ne, Nana tsinuwa zan sha a bakin jama’a, ta yanda babu yadda zaayi na kare kaina, tun da gani a gidan naki, Nana a dinga duba ana saran gatari.”  “Bilkisu mu zauna.” Na faɗa ina kama mata hannu, zaman ta yi sannan na ce.  “Ina ruwanmu da surutun wani? Waye zai sani? Waye zai san mi dake ƙawayene, Bilkisu ko sun sani mene a ciki? Ba dai mu muna zaune ba, nasani Bilkisu zaki zauna tare dani cikin aminci, mu kula da mijinmu, to ina ruwanmu da zancen mutane? Su yi ta yi kar su daina.”  “Idan ke kunnenki zai iya jurewa, to ni nawa ba zai ya jurewa ba. Nana bakisan mene bakin mutane ba, idan suka sa ka agaba wallahi duk wata albarka dai ka nemeta ka rasa, Nana idan ke kin fahimta ina ‘yan uwanki zasu fahimta?”  “Kishiya ce fa Bilkisu! Kuma ba Kaina farau ba ko karau? Mijina ne kaɗai ya taɓa ƙara aure?”  Hannuna ta kama sannan ta ce.  “Nana, ki yi haƙuri abar wannan maganar, kamar zata fi amfani Nana, idan duk na ce na ji nagani shi mijin naki fa? Yana sona? Zai soni? Zaman alfama Nana bazan iya ba dan Allah.”  “Salamu alaikun.”  Muyar Sarauna ta ratsa ɗakin, ban maji ko warn ɗinsa ba, kawai sallamarsa na ji.”  “Sannu da zuwa.”  “Yawwa sannu.”  “Sannu da zuwa.”  Bilkisu ta faɗa kanta yana ƙasa.  “Yawwa sannu.” Yana amsawa ya shige cikin ɗakin, bai ƙara sa shigewa ba Bilkisu ta miƙe tare da faɗin.  “Nana, zan tafi.”  “Bilkisu bamu gama magana ba.”  “Nana ni dai nagama yanke hukuncina.”  Tana faɗin haka ta fice, hannuna na ɗora a goshine tare da faɗin.  “Hhhm, Ya Allah.”  Ɗakin da ya shiga na bi shi, ina zuwa na tarar da shi zauna a kan gado, idanunsa sunyi jawur alamun ya ci kuka ya gode Allah.  Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na ashirin da uku.     (23) “Ya salam! Me ya faru Sardauna?”  Wasu hawayen ne suka fara fitowa daga idanunsa, waɗanda suka ƙara ɗagamin hankali, ya riƙe hannu.  “Nana nagaji, ina danne zuciyata ina sonki, bana son abinda zai cuceki, amma Hajiya ta dage wai tana son ganin jikokinta, Nana ko zuwa gidan Hajiya bana son yi, bana so na ji an soke ki ko anci mutunciki, Nana bana son zaluntarki, bana son cutar da zuciyarki, bazan iya ƙara aure ba kwata kwata, karki ga yadda ake zancen nan a family house kamar akaina aka fara shekara uku da aure ba haihuwa. Hon haihuwar nan dole ne?.” Wani irim tausayinsa neya ratsamin zuciyata, sai na ji dama ni ce nake shiga wannan matsin ba Sardauna ba, dama nice nake wannan kukan ba Sardauna ba, bazan iya jure ganin hawayen Sardauna ba, suma azabatar da rayuwata.  “Ka yi haƙuri, haihuwa ba dole ba ce, amma tabbas a idon iyayenmu gani suke dole ne, Sardauna a yanzu ma da ka zo maganar muke da Bilkisu amma taƙi fahimta ta duk da nasan zata fahimta in sha Allah. Ina tunanin idan ka yarda zanje gidansu gobe mu sake magana da ita.  “Hon ina cikin damuwa, ina cikin tashin hankali, rayuwa ta yi min baƙi mutuncina yana watangarirya. Na yarda ki je da kanki, kisan yadda zaki yi da ita ta amince, Hon ki durƙusa mata a ƙafa, ko ni naje na durƙusa mata kawai Hon, da mutuncina ya zube a idon duniya, gwanda na yi haka, ko menene zan iya yi mata wallahi indai zata aureni.”  “Ya zaayi kaje ka durƙusa mata? Haba dai. Ka barni da kaina zanje gobe, zan yi magana da ita ta yadda dole zata amince, ka sa haƙuri a ranka dan Allah.” “Nana idan ba ta amince ba ina cikin tashin hankali, ni dake Nana bamu da wata mafita.”  Ji na yi kamar na tashi a cikin daren na je gidansu Bilkisu amma ba hali, daƙyar na lallaɓa Sardauna ya nutsu amma bai iya cin abinci ba, haka muka kwanta duk ranmu ba daɗi. Washe gari lokaci ɗaya muka fita dashi, ya yi ofis ni kuma na yi gidansu Bilkisu ta hanyar kwantancen da ta yi min tun kwanaki. A bakin gate ɗin na tarar da wata mata mai kama da Bilkisu na shirin fita, ƙasa na tsugunna tare da faɗin.  “Ina kwana?”  “Lafiya.”  Ta amsamin a daƙile, sannan ta ce.  “Wa kike nema.” “Bilkisu.” “Tana ciki.” Ta faɗa tare da hucewa, na kusa minti biyar a tsaye ina faman tunanin ta yadda zan fara da Bilkisu, bana son ta tirjemin kamar yadda ta yi jiya. A hankali na tura ƙofar falon na shiga, zaune na tarar da su 'yan mata ne sun kai su biyar da alamu ma wasu ƙawayenta dan ba 'yan gidansu ba ne, duk da nima wannan ne zuwa na na farko gidansu. cikin wani irin yanayi kamar na isgili haka ta tarbeni.  "A'a Nana kina ƙaraso."  Na yi mata murmushi sannan na ce.  "Eyh wlhi, ya gida?"  "Muna lafiya."  Zama na yi sannan na kalli sauran matan dake ɗakin, sannan na ce.  "Sannunku."  Bansaniba ko sun amsa ko basu amsa ba, nidai abinda ke gabana shine kaɗai ke damuna.  Gaba ɗaya tunanin maganganun da muka yi da  Sardauna ya cika min ƙwakwalwa, bana iya tuna komai sai muryarsa.  'Nana nagaji, ina danne zuciyata ina sonki, bana son abinda zai cuceki, amma Hajiya ta dage wai tana son ganin jikokinta, Nana ko zuwa gidan Hajiya bana son yi, bana so na ji an soke ki ko anci mutunciki, Nana bana son zaluntarki, bana son cutar sa zuciyarki, bazan iya ƙara aure ba kwata kwata, karki ga yadda ake zancen nan a family house kamar akaina aka fara shekara uku da aure ba haihuwa. Hon haihuwar nan dole ne?.' "Allah Sarki Mijina."  Na faɗa a zuciyata, a fili sai kuma na kalli Bilkisu na ce.  "Dan Allah magana nake so mu yi dake, ina son mu shiga daga ciki."  Dariya ta yi ita da mutanen nan nata sannan ta ce.  "Haba Nana kamar ba wise ba."  Ɗaya cikin ƙawayen ta ce.  "Baiwar Allah kizo ki ganmu tare sannan ki ce wai ta tashi ku shiga ciki a wane dalili?"  Baki sake nake kallon ikon Allah.  "Nana waɗannan ƙawayena ne duk wani sirri zan iya yi dasu, dan haka ki faɗi abinda zaki faɗa."  Ji nai na yi wani irin muzanta, kamar bata san maganar da zamuyi ba, to ma wai 'ƙawayenta ƙawayena ne?, ko da ƙawaye na ne kowacce magana yakamata na yi a gabansu?. "Hon ina cikin damuwa, ina cikin tashin hankali, rayuwa ta yi min baƙi mutuncina yana tangarirya Hon, na yarda amma ki je da kanki kisan yadda zaki yi da ita ta amince, Hon ki durƙusa mata a ƙafa, ko ni naje na durƙusa mata kawai Hon, da mutuncina ya zube a idon duniya, gwanda na yi haka."  Kalaman Sardauna suka dawo kunnuwa kamar yanzu yake faɗinsu.  "Bazan taɓa bari ka hulaƙanta ba in sha Allah Mijina."  Na faɗa, sannan na kalleta tare da tasowa zuwa inda take, na sanya gwiwoyina a ƙasa sannan na ce.  "Maganar mu ta jiya, ki taimaka ki auri mijina."  Wata shegiyar dariya na ji ƙawayen na ta sun kice da ita, kamar daman jira suke na yi magana. “Bilkisu wannan mahaukaciya ce?” Ɗaya cikin ƙawayenta ta faɗa, tana wata irin dariya.  “Bana ce ba, ni yadda nasanta lafiya ƙalau take, amma daga jiya zuwa yau gaba ɗaya ta canja.”  “Bilkisu kinsan komai, wannan abun mafita ce gani da ke.”  “Nana ki saurareni, na gama magana fa wai ma idan aure ne macece zata nema masa aure? Ke awa da zaki nema masa aure, ba zai zo da kansa ba? Kinga kenan kece kika aureni bashi ba.”  “Ba haka ba ne Bilkisu, kusancin dake tsakanina dake ne yaja haka, amma da kin bashi dama zai zo da kansa Bilkisu.” “Ke amma kin rako mata wallahi, bantaɓa ganin ballagaza marar kishin kai ba irinki, mijin naki kike yawo da shi a haka? Kina neman a aure shi? Sannu Saratu ba ki yi wa kanki tanadi ba wallahi, bama alfahari dake.”  Wani irin ɗaci na ji ya tsayamin a maƙogwaro zuciyata ta fara wani irin raɗaɗi. ‘Ko Bilkisu ta kawo waɗannan ƙawayen na ta suci mutunci na ne?.’ Na tambayi kaina, ban kai ga samun amsa ba na ji wata ta ce.  “Ni yau na fara ganin asara irin wannan ba, amma dai duk da yadda aka yi mijinne baya sonta, shine ya bata dama ta kawo mai wata ko ya rabu da ita.”  Suka tuntsire da dariya, Bilkisu ta ce.  “Ba fa haka ba ne, ni bansan mene asalin matsalal ba kamar haihuwa ne ba ta yi.” Wani zafi na ji a zuciyata, wai Bilkisu ke hulaƙantani, tana shela da ni haka, kamar ba ta san komai ba.  “Ai kuwa babbar matsala ce, dole ta fito ta nema masa aure kafin ya kaɗata, dan ba kowa zai iya jurar mace daga ci sai kashi ba.”  Ƙwalla na ji tana zirara daga idona, a fili na furta.  “Ya Allah Ka na ji ka na gani.”  “Nana idan zaki tashi ki tashi, babu abinda zai sa na auri mijinki, gwanda ma ke nemi wata mafitar.”  “Ji ta ballagaza.” Wannan ita ce maganar da tafi ƙonamin rai, ba shiri na miƙe a raina na ƙudiri cewar zan nemawa Sardauna wata ba dole sai Bilkisu ba, tun da daman ba sonta yake ba.  “Na gode Bilkisu.”  “To Nanan Sardauna, ki gaida gida sannan ki canja shawara.” Bilkisu ta faɗa, wata cikin ƙawayen ta ce.  “Ki canja tunani kam, kuma a dage a rage ci tun da ba haihuwa za ayi ba.”  Ban kai ga ƙarasa fita ba, na ji sun kece da wata irin dariya, haka na tawo ina haɗa hanya sakamakon matsanancin jirin da nake ji, fuskata ta jiƙe shargab da hawaye, wannan cin mutuncin har ina? Lallai Bilkisu.  A haka na shigo cikin gidan, daidai lokacin da Turaki ya fito daga ɓangarensa, da sauri na yi ƙasa da kaina sabida kar ya ga fuskata. Ba ni da damar yin sauri sabida jirin da nake ji, hakan yasa na tafi a hankali.  “Nana!”  Ya kira sunana, ta dole na tsaya ba tare da na juyo ba.  “Kuna waya da Hajiyarki?”  Na gyaɗa kai, ba tare da na yi magana ba.  “Good.” Ya faɗa tare da fara tafiya, jan hanci na yi tare da wata shasheƙa da ta ƙwacemin ba tare da na shirya ma ta ba ya sa shi dawowa.  “Nana! Meke damunki? Kuka kike?” “A’a.”  “Ƙarya zaki yi min, Sardauna ne ba lafiya?”  “A’a.”  “To me ya sa ki Kuka?”  Ya faɗa yana matsowa inda nake, girgiza kai na yi bance komai ba.  “Me ya saki Kuka!”  Ya faɗa a tsawace. “Ba komai, ka yi haƙuri, zan faɗa ma.”  “Haƙurin me Nana? Me ya ta ɓa ki haka?”  “Ka yi haƙuri, zan faɗa ma.”  Na sake maimaitawa gaba ɗaya na ruɗe. “Nana kina da damuwa ne? Duk kin ruɗe kin fita hayyacinki, are you okay?”  “Yes! I’m okay.”  “Hhhm.”  Kawai ya faɗa tare da sa kai ya fice, ni kuwa har da harɗe ƙafa sabida sauri na shige ciki, ina shiga na faɗa kan kujera na fashe da kuka, mai tsuma zuciya. Kuka nake yi mai ƙarfi har sai da na fara jin ɗaci a maƙwogarona. Kukan da ya haifarmin da wani ciwon kan wanda ya haɗe da jirin da nake ji gaba ɗaya na ji duniyar ta fara yi min zafi, abubuwan sun har gitsemin sama ta juye ƙasa.  Daƙyar wani wahalallen bacci ya ɗaukeni marar daɗi, ina yi ina firgita, ina zabura kamar wacca za a taɓa, cikin barci na fara jin hayaniya sama sama. A hankali na buɗe idanuna sa suke jawur, wani irin sarawa na ji kaina ya yi, amma a haka na dafe kan na miƙe sabida jin kamar cacar baki. A hankali na leƙa ta window Sardauna da Turaki ne.  “Turaki ina so ka sani, ni Sardauna na yi maka nisan da har abada ba zaka taɓa kamoni ba, Turaki duk abinda zaka yi tsakaninka da ni sai da ido. Kasani abinda Sardauna ya taɓa har abada ya yi maka nisa.”  Turaki ya saki wani murmushi, sannan ya dafa kafaɗar Sardauna ya ce.  “Alfahari da fariya na ƙarya kake yaro, ni lokacin da zan zauna na yi wannan maganar marar amfani ma ban da shi, sannan ina tunasar da kai cewar Ajuri zuwa rafi, wata rana tulu zai fashi. Shashasha.”  Yana faɗin haka ya wuce yabar Sardaunar a wajen, da sauri na koma kan kujera na kwanta, na rasa mene asalin wannam faɗan dake tsakanin Sardauna da Turaki. Da ƙarfi ya saki ƙofar bayan ya shigo, na runtse idona sabida wani irin bugu da na ji zuciyata ta yi.  “Nana! Nana! Nana!”  Na buɗe idanuna na kalleshi.  “Me kike yi a kwance.” “Bakomai.”  Na faɗa ina miƙewa zaune.  “Me ya shigo da wannan ɗan iskan bangarena?” “Waye?”  “Karki rainan hankali mana, waye banda Turaki.”  “Bai shigo ba.”  “To aina ya ganki?”  “A parking space ne, bayan na dawo daga gidansu Bilkisu.”  “Hhm, har ni zai cewa wai na dinga yin adalci, me kika ce masa?”  “Babu abinda na ce masa, to me kake yi min da zan faɗa masa?”  “Nasan mike, nasani ko kin yi min wani sharri.”  “Uhm.”  Kawai na faɗa tare da sake komawa na kwanta, kallona ya yi sai kuma ya sha jinin jikinsa.  “To kawai yana ganina ya wani hau yi min magana, ni da ba shiga sha’aninsa nake ba, tun muna yara Turaki yake son shiga rayuwata, yana baƙin ciki da ni a rayuwarsa, ni kuma ko magana ma bana son naga ta haɗani da shi, ina kishin naga nasan abu Turaki ya san shi, shi ya sa ma duk family na bar masa, na ja rayuwa ta na yi gefe, ranar da na ga ya yi miki magana a family meeting wallahi Nana ji na yi kamar an watsamin tafasheshen ruwan zafi a zuciyata, na ji zafi fiye da yadda kike tsamanni.” “Hhhm, to yanzu ni me zai haɗani da shi da har zan hau yi masa magana akanka.”  “Ki yi haƙuri to.”  Ya faɗa yana kama hannuna.  “Bakomai.”  “Ya kuka yi?”  Tashi na yi zaune duk da jirin da nake ji yana ɗibana, na kalleshi sannan na ce.  “Akwai matsala fa.”  “Wace irin matsala?”  “Babu wani nau’in rashin mutunci da kasani da Bilkisu ba ta yi min ba, ta inda ta shiga ba tanan take fita ba, abun babu daɗin ji.”  “Ita Bilkisun?”  “Ita fa, ni kaina har mamaki na yi, kamar ba ta sanni ba.”  “Innullahi wa’inna illahir raji’un, to yanzu Hon ya zaayi?”  “Ina ganin kamar a ƙyaleta a nemi wata kawai.”  “A nemi wata kuma Hon?”  “Eyh a nemi wata, tun da ita ba yarda za ta yi ba.”  “Nana haka zamuyi ta zagaye mutane muna faɗa musu matsalalmu, suna ƙin amincewa shikenan mun tonawa kanmu asiri?”  “To ya kake gani zaayi? Mene mafita a ganinka?”  Shiru ya yi na tsahon mintina sannan ya ce.  “Ni fa da har ta kwantamin a rai, Nana ki sake komawa.”  Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na ashirin da huɗu.     (24) “A sake komawa? Wajenta kenan?”  “Eyh Nana, aganina a sake komawa mai nema ai yana tare da samu, kuma muke nema bai kamata mu yi zuciya ba Nana.” Shiru na yi ina faman tunani, tabbas zancen Sardauna gaskiyya ne, wanda yake nema ba ya taɓa fushi amma tabbas abinda Bilkisu ta yi min abu ne da yake nuna zallan rashin mutunci, amma ya zanyi tun da Sardauna yana so.  “Shikenan gobe zan sake zuwa ko?”  “Yawwa Nana, ki bi duk wata hanya da zaki bi kinji ‘yar Aljanata.”  “Ina son gobe zanje asibiti, ina yawan jin jiri da ciwon kai sosai.”  Na faɗa ina lumshe idona.  “Okay tom daga gidan nasu sai ki je asibitin, da mota zaki fita?”  Na girgiza masa kai tare da cewa.  “A’a.”  “Tom, me aka dafa mana?” Na girgiza kai.  “Banyi komai ba, amma muna da gurasa.” “To aban na sha da tea.”  “Tam.” Na faɗa tare da miƙewa, anan falon na kawo masa ya ci bai ji dinning ɗin ba. Bayan ya gama ci na kwanatar da kaina akan cinyarsa.  “Yaushe zanje na gaida Hajiya.”  “Wace Hajiyar? Taki ko tawa?”  “Duka biyun.”  “A’a Hajiya ta dai ba yanzu ba, yadda take wannan fushin, sai da Hajiyarki, ita ma ba yanzu ba.”  “Sai yaushe?” “Mu gama da abinda yake gabanmu Nana.”  “Eyh hakan kam gaskiyya.”’ “Yawwa ko ke fa.”  “Ya zancen tafiyarmu Turai? Gashi kuma Maulidi ya tawo ka ce Umarar Maulidi zamu.”  “Nana, turai ba yanzu ba dan Big Daddy ma ya hana, sai dai Umarar.”  “Shikenan yanzu an fasa?” “Ko za a je ba kusa ba.”  “Shikenan yanzu karatuna fa, gashi ‘yan anjimu on 11 this month zasu yi resuming level 300 zasu shiga.”  “To Nana ya zaayi? Haka Allah Ya ƙaddara amma ki kwnatar da hankalinki kin ji Nana.” “Alhaji ya mutu da burin na yi karatu, akwai alƙwarinshi akaina fa.”  “Nana mene haka wai? Da matsalal da take gabanmu zamuji ko kuma da wacca kike shirin kunno mana?”  “Ni ba matsala nake son kunnowa ba.” Na faɗa ina goge ƙwallar dake idona, ban ƙara ko minti biyar ba na tashi na shige ɗaki na kwanta, ina jinsa har ya shigo ya gama gyaran muryarsa ban ce ko ƙala ba, ya jawoni jikinsa.  “Nana nah, me na yi?”  “Babu komai.” “Bangane ba komai ba, gashinan kina wani yi min banza.” “Ni ba banza nake ma ba, kaina ke ciwo ne.”  “Tom, na ƙyaleki kike so ki ce ko?”  “Jiri nake ji.”  “Uhm, shikenan.”  Yana faɗin haka ya cikana ya juya ya kwanta, haka kawai yau na ji ni bana wani marmarinsa ko magana ma ban son yi da shi.  “Bazaki kulani ba ko?”  Matsowa na yi kusa da shi sannan na ce.  “Ka yi haƙuri.”  “Nana kullum baki da aiki sai ayi haƙuri, amma kuma ko an haƙura ba kya fasawa.”  “In sha Allah za a gyara.”  Daga haka ya muka kwanta.  ****** Yau ma kamar jiya tare muka fita da Sardauna, na yi gidansu Bilkisu ya yi ofis, yau ma na ɗan jima a ƙofar gidan kafin na shiga, ko dame zata zo yau oho? Sai da na ƙarewa gidan kallon, su Bilkisu sun fi mu kuɗi sosai da sosai ko unguwar da suke ma kaɗai ya isa tabbatar min, ga gidan masu ya tsaru da tsaruwarshi. A hankali na tura ƙofar falon na shiga sai dai babu kowa a ciki, haka na tura kai na shiga tare da yin sallama, sai da na yi sau biyar sannan aka amsa min.  “Nana! Me ya dawo dake kuma? Kar dai ki ce baki haƙura da wannan zancen ba.”  “Bilkisu kenan, ai kya tsaya mu gaisa.”  “Tom zauna mana.”  Na sami waje na zauna ita ma ta zauna.  “Ina ina saurarenki.”  “Bilkisu dagaske kike akan maganar da kika faɗan?”  “Wace magana?” “Ta wajen mahaifinki.”  “Nana zan miki ƙarya ne?”  “To amma me ya sa baki amshi mafitar da nazo da ita ba.”  “Nana! Wai ta ya zan auri wanda baya sona? Da auren mijinki da auren wanda Abbana zai ban duk ɗaya ne tun da duk ba sona suke ba.”  “Bilkisu baki bawa Sardauna dama ba ne, amma yana sonki kuma zai nuna miki soyayya, Bilkisu dan Allah ki gwada ba shi dama.”  “Wace kalal dama?” “Ya zo ku yi magana, ko tattauna ko fahimci juna.” Shiru ta yi sai kuma can ta ce.  “Shikenan ya zo yau.”  Har cikim zuciyata na ji daɗi, kuma na kasa ɓoye jindaɗina.  “Na gode miki sosai Bilkisu.” “Karki gode min Nana, dan ba cewa na yi na amince zan aure shi ba.”  “Nasan ma zaki amice, daga hakan in sha Allah.”  Na ɗan zauna a gidan nasu har wajen ƙarfe goma sannan na ta shi na nufi asibiti, dan har zanje wajen Dr Ɗan Adala, kawai na yanke shawarar zuwa asibiti mafi kusa.  Duk da kasancewarsa asibitin gwamnati amma ma’aikatan ciki sun kasance masu matuƙar kirki, tun daga zamana har layi yazo kaina ban ji sun hantari wani ko wata ba.  “Wacece Nana.” “Ni ce.”  Na faɗa ina miƙewa.  “Ki shiga ciki.” Godiya na yi mata sannan na ta shi na shiga Likitar babbar Macece mai mutunci, Dr Na’ima Daƙayyawa. Shine sunan da naga an rubuta a jikin tag ɗin ta, kallo ɗaya ta yi min ta ce da ni.  “Mrs Ta ambo, gaba ɗaya shekarunki nawa? Me yake damunki da zai haifar miki da Low Bp a wannan ƙarancin shekarunki?”  “Low Bp Dr.”  Na faɗa a hankali, ta gyaɗa min kai sannan ta ce.  “Yeah! Low Bp ma’ana jininki ya yi ƙasa fiye da tsammani, ya kamata ki cire duk wata damuwa a ranki, ke yarinya ce ƙarama. Baki kai matsayin da abu zai dameki ba.”  “Yanzu mene abun yi?” “Ki cire duk wata damuwa a ranki, ki miƙa al’amuranki ga Allah, komai ya yi farko yana da ƙarshe.”  “Tom.” “Matsalal gidan aure ce ko? Ki yi haƙuri muma dukkanmu haƙuri muke, rayuwar gaba ɗaya haƙuri ake da ita, kin ji?”  “Tam na gode, amma dan Allah likita na tambayeki.”  “Allah Ya sa Nasani.”  “Zuwa shekara nawa ne mahaifar mace take yin ƙwarin da zata ɗauke ciki?”  “Bangane ba.” “Ina nufin zuwa shekara nawa mace take iya fara ɗaukan ciki?”  “Shekarun da ta girma mana.”  “To wasu da mahaifarsu ba ta da ƙwari fa?”  “Mrs Ta Ambo am sorry bangane abinda kike son faɗa ba, can you please open your mind and talk?”  “Shikenan zan dawo wata rana.”  Na faɗa tare da tashi.  “Okay Allah ya ƙara lafiya.”  Har na fita na dawo, “Dan Allah zan iya samin numberki?” Kati ta ɗauko mai ɗauke da sunanta address ɗinta da lambar wayarta ta ba ne, na amsa tare da yi mata godiya na fice.  Kai tsaye gida na dawo, bayan na sha magunguna da aka bani na kwanta bacci ya ɗauke ni wanda ban tashi na sai gab da la’asar, a gurguje na yi ayyukana na gama, yau Sardauna zai je gidansu Bilkisu Allah Ya sa su fahimci juna, ayi ayi auren nan kowa ya huta da ko zan sami nutsuwa jina na ya dawo daidai.  Lokacin da ya saba dawowa ya dawo, da farin ciki na tarbeshi kamar yadda nasaba yi masa a farko, da mamaki yake kallona, har ya kasa ɓoye mamakinsa ya ce da ni.  “Nana me ya faru?”  “Ka fara wanka ka shirya sai mu yi magana.”  “A’a kinsan ni bana son irin wannan kawai ki faɗa min.”  “Bilkisu ta ce dai ta yarda ka je ku yi magana ku fahimci juna.” “Ma sha Allah, na gode miki matata abar alfaharina, Allah Ya biyaki.”  “Amin amin, yanzu je ka yi wanka ka shirya sai ka tafi.”  “Tom, yadda kika ce haka za ayi Hajajju, ko tare zamu je.” Ya faɗa yana shigewa ɗaki, na yi dariya sannam na ce.  “Ni wa? A’a dai.”  Ina zaune a falon ya fara kirani, na tashi na shiga.  “Ya baka gama shirin ba?”  “Ke zaki shirya ni.”  Dariya na yi tare da buɗe sip ɗin ta sa na ɗauko masa wani men lace milk clour. A yanzu Sardauna ba shi da kayan da suka fi men lace, tsaf ya shirya ya yi kyau, sannan na bashi lambarta ya tafi, bayan na yi masa addu’a. Ina jin ya tayar da motarsa wani abu sa soki zuciyata mai zafi da raɗaɗi, zuciyata ta fara bugu da ƙarfi numfashina ya kasa daidaituwa. Kowane bugu na zuciyata kamar guduma yake dukan ƙirjina.  08:00pm Na dubi agogon falon, ƙarfe takwas na dare. A yanzu nasan Sardauna ya ƙarasa gidansu Bilkisu, tun da ba wani nisa ba ne damu, wataƙila suna zaune a kan kujera ɗaya, ko kuma yana kallon fuskarta da wannan idanunsa masu sa mutum ya mance kansa. Na tashi na fara kai da komowa a tsakar falon da ya yi mini faɗi da yawa kamar yau na fara zama ni kaɗai, na ji gidan ya yi mini tsit. Na kalli kaina a madubi, idanuna sun kumbura, fuskata ta yi jawur saboda kukan da na sha tun ɗazu bayan fitar Sardauna wanda bansan ma na mene ba? ‘Yanzu haka ko me yake gaya mata?’ Zuciyata ta tambaye ni. Wani abu mai zafi ya taso mini daga can ƙasan makogwaro. Na runtse idona, sai na ga hoton Sardauna ya bayyana a raina yana yi mata wannan murmushin nasa mai bayyana kyawawan haƙoransa. Wannan murmushin da na ɗauka nawa ne ni kaɗai. Wataƙila ma yanzu ya manta da kukan da ya rinka yi mini a baya a kafaɗata. Wataƙila ya mance da ni da rayuwata ma, ya mance da duk fafutuka ta akan auren nan. Na matse hannayena da ƙarfi har sai da ƙasusuwan yatsuna suka yi ƙara ‘Ƙas’. Wani irin zafi mai cin zuciya ba tare da hayaki ya fito ba, na ji ya ratsamin zuciya. Na ji tamkar an matse mini maƙoshi, iskar ɗakin gadon ta daina isata. Na nufi taga na janye labulen, ina kallon waje ko zan ga hasken motarsa, amma duhu kawai nake gani. Shin ta fi ni kyau ne? Na sake tambayar kaina cikin damuwa. Shin ita ma zai koya mata yadda yake son abincinsa? Ko kuwa ita ma zai rinka cewa kishinta yake yi shi ya sa yake son killace ta? Kowane tunani yana soka mini wani sabon mashi a rai. Na tsinci kaina da fara zargin kaina. Wataƙila da na dage akan karatuna, da hankalina ba zai rinka karkata ga wannan kishin da yake neman haukatani ba. Na tuna yadda Sardauna ya rinka yaudara ta da kalamansa , yadda ya rinka nuna mini cewa ni ce tauraruwarsa ta har abada. Amma yanzu, tauraruwar wata tana shirin fitowa a sararin samaniyar rayuwarsa. Na koma na zube a kan dadduma, na takure waje ɗaya, ina jin yadda ɗakin yake juya mini. Duk dukiyar da Sardauna ya zuba mini a wannan gidan, duk motar da ya saya mini da zinaren da ya ba ni, a wannan daren na ji ba su da wani amfani. Domin dukiyar ba za ta iya siyan natsuwar zuciyata ba. Wani sabon kukan ya sake kufce mini. Kukan da ba na rarrashi ba ne, kukan da yake nuna cewa yanzu na shiga tarkon da ba ni da tabbas idan zan fito lafiya. Ni da kaina na ba shi izinin tafiya zance, ni da kaina na ce ya bi maganar iyayensa, amma a yanzu, na gane cewa sadaukarwar mace ga namiji babban kuskure ne. Agogon wayata ya buga ƙarfe goma. Shuru har yanzu bai dawo ba. Kowane minti ɗaya jin sa nake tamkar shekara guda. Zuciyata ta ci gaba da saƙa mini abubuwa daban-daban. Shin yanzu sun daidaita? Ko har an tsayar da ranar auren? Na dafe kaina, ina jin tamkar zai rabe gida biyu.  Kishin Sardauna ya riga ya zama wani baƙin lillibi da ya rufe mini dukkan farin cikina, ya bar ni a cikin duhun fargaba da rashin tabbas na abin da gobe za ta zo da shi. Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na ashirin da biyar.     (25) “Sardauna ba zai dawo ba ne?”  Na tambayi kaina ganin har ƙarfe sha ɗaya da kwata, tabbas nasan a yanzu sun sasanta kansu, ƙila ma sun tsayar da ranar aurensu, yanzu burin Hajiyar zai cika.  Sai sha ɗaya da arba’in Sardauna ya shigo ɗakin da nake, daga yanayin yadda yake magana zaka san fuskarsa fal take da fara’a kamar wanda aka yi wa bishara da gidan al’janna.  “Nana! Kina ina?”  Ya faɗa yana kunna hasken ɗakin, da sauri na runtse idona da.  “Oh My, wai kinyi bacci?”  Daidai lokacin wayarsa ta fara ƙara alamun kira na shigowa. “Salamu alaikum.” Ya faɗa cikin amon muryarsa.  “Alhamdulillah yanzu nake shiga gidan, ya na barki.”  Wani irin abu na ji ya doki zuciyata fiye da wanda na ji ɗazu, ita ce ta kirashi kenan?  “Na gode sosai da kulawarki agareni.” “Har kulawa ta bashi kenan?.”  Na tambayi kaina, dariyar da yake ce da ita ce ta katsen tunanin da nake.  “Ai nagani, shine abinda ya ƙara burgeni da ke, idan zan dawo a ƙara yi min.” Ji na yi dama na mutu, dama na mutu da wannan baƙar ranar da nake ganin, kamar kunnuwana ba daidai suke ba, yau Sardauna ke waya da wata mace a gabana, akan idona, me ta yi masa da ya sa ta burgesa? Ƙila ma Samosar da na koya mata ne. ‘Na shiga uku ni Nana.’  Har ya kamalla wayar ina kwance ban buɗe idona ba, kusan minti ashirin yana wayar, sannan ya sake yi min magana.  “Nana tashi mana.”  Hannu yasa a jikina ya fara taɓani, ta dole na buɗe ido, amm sai na ji bana ma son ganinshi, na mayar dasu na rufe.  “Nana na dawo.”  “Har ka dawo.”  Na faɗa ina tashi.  “Har ne ma?” “Sannu da zuwa.”  “Yawwa.”  “Nana baki tambayi yadda muka yi da ita ba”  Murmushi na yi masa wanda yafi kuka ciwo, sannan na ce.  “Tun da naga ka daɗe ai nasan kun fahimci juna.”  “Eyh hakane kam, Nana na gode miki sosai.”  “Da na yi me?” Hannuna ya kama sannan ya ce.  “Da kika yi komai ma, Nana a yanzu an kai matakin nasara kar ki bari sheɗan ya shiga zuciyarki, ya lalata miki komai, ya ɓarar miki da ladanki.”  “In sha Allah.”  “Koma ki kwanta to.”  Ba musu na kwanta abuna, zuciyata gaba ɗaya babu daɗi, amma nasan ta bakin Sardauna ne sheɗan ne yake son ya shiga zuciyata ya haifar min da wani abu wanda zai ɓarar da lada na duka.  Abu Kamar wasa Sardauna da Bilkisu, kullum sai Sardauna ya je gidansu Bilkisu sai bayan sha ɗaya yake dawowa, gashi sai su kai ƙarfe ɗaya na dare suna waya, haka da safe kafin ya fita ma sai sun yi waya, duk abin ya dameni yadda sardauna ya fara janye lokacinsa daga kaina. A haka ma tun ba ayi auren ba, ina kuma ga idan anyi auren? Tsakanina da Bilkisu ko ta waya ba ma gaisawa ba ta sake cemin komai ba, ko kiranta na yi a waya ma bata ɗauka, gaba ɗaya na damu kamar na yi gangancin haɗa shi da ita, wani lokacin idan na zauna ina tunani sai na ji kamar ma Sardauna ko Bilkisu wani na son wani kafin yanzu, amma idan na tuna irin yadda na shiga na fita akan Bilkisu da Sardauna sai naga kowa da ta shi matsalal, yadda muka yi da Bilkisu da kuma yadda muka yi da Sardauna, sai na ji kawai Allah ne ya haɗa jininsu a lokaci ɗaya.  ******** Tun safe Anty Adiza ta kirani a waya akan yau za ta zo, na ji daɗin zuwan ta sosai, haka ma Sardauna da na faɗa masa, sai da ya ce kar na kuskura na yi mata zancem ƙarin aurensa. Wajen ƙarfe ɗaya ta ƙara so, na tarbeta da murna itama haka, bayan mun gaisa ne tasha ruwa ta kalleni sannan ta ce.  “Nana duk kin rame, kamar mara lafiya ji yanayin jikinki ko kina da hawan jini ne?”  Na girgiza kai sannan na ce.  “Na dai yi Low Bp kwanaki, bayan rasuwar Alhaji.”  Domin yanzu na zama mashahuriyar maƙaryaciya akan al’amuran Sardauna, har uwata ma ƙarya nake mata.  “Ayyah Allah Sarki, amma da kin mai da hankali akan ganyayyaki da sun ƙara jini sosai Nana.”  “Tom shikenan Anty Adiza zan maida hankali in sha Allah.”  “Nana.”  Ta sake kiran sunana, na ɗago na kalleta.  “Munyi magana da Yaya Radiya, akan wasu abubuwan dake faruwa, Nana wai menene asalin matsalalki?”  “Nifa ba ni da wata matsala, bansan me suke magana a kai ba.”  “Nana duk wanda ya ganki yasan da damuwa a tare dake, ga shi ba inda kike zuwa.”  “Mijina ba ya son fita, indai ba wani ƙwaƙwaran uziri ba.”  “Hhm, Me yaja miki Low Bp.”  “Tun rasuwar Alhaji ne.”  Anty Adiza wayayyiya ce, tasan ta yadda zata kama mutum ta dole, wasu irin tambayoyi ta dinga watsomin har sai da na yi suɓul da baka na ce da ita Sardauna ne zai ƙara aure, murmushi ta yi sannan ta ce.  “Nana kenan, bayan nan fa.” “Babu komai Allah.”  Matsowa ta yi kusa dani ta kama hannu, ta fara magana cikim tausasawa. “Nana karki kasance sokuwa, karki kasance shashasha! Daga lokacin da miji ya fuskanci kin shashantar da kanki a kansa, zai mai dake marar amfani, zai mai da ke tsanin da zai taka ya hau kowane mataki, Nana ba a ce babu soyayya ba, ba a ce soyayya ga miji ƙarya ba ce, amma Nana ki mutunta kanki, muma duka Nana ai muna son mazajenmu, so ba ƙarami ba Nana, amma muna mutunta kanmu ta yadda suma zasu mutantamu, Nana babu mijin da ya isa ya zo sama da ‘yan uwa ko iyaye, kowa matsayinsa daban. Ki farka daga wannan baccin da kike Nana, kisan idan kika tunkara karki zauna ki lalace a haka.”  “Shikenan Anty Adiza, na gode sosai kuma in sha Allah zan gyara.”  “Shikenan Nana Allah Ya sa gyara mana.”  “Amin amin .”  Kalamanta duk sun shige ne ba ƙarya, kuma a iya hasashen da na yi gaskiyya ta faɗa min, amma ni har yanzu banga mafarkin da nake yi akan Sardauna ba, matsala ɗaya ce rashin zuwa gida kuma in sha Allah zan dinga zuwa. Bata jira Sardauna ya dawo ba ta tafi sabida tabar yaronta a wajen masu aiki, ba ta daɗe ta tafiya ba na sake gwada lambar Bilkisu amma ba ta tafiya.  “Allah Ka sa wannan baiwar taka tana lafiya.”  Na faɗa a raina tare da ƙudiri niyar idan Sardauna ya dawo zan tambayeshi, sannan na ce idan ya je ya haɗani da ita.  Ba Sardauna ya shigo ba sai bayan magariba, shima a gurguje ya shigo ya shirya ya fita ko abinci bai ci ba, sai bayan goma ya sake dawowa, hannayen shi riƙe da leda da alama shopping ya yi.  “Nana ga wannan, Bilkisu ce ta ce akawo miki.”  Karɓa na yi sannan na ce.  “An gode.”  “Munje shopping ne, kinsan an sanya ranar aurenmu wata ɗaya, shine muka je siyayya.”  Kamar ansoka mini mashi haka na ji shigar maganarsa, amma sai na kauda kai tare da cewa.  “Allah Ya nuna mana.”  “Amin Nana.”  Miƙewa na yi da niyar shiga ɗaki na kwanta, Sardauna yasa hannu ya jawo ni kusa da shi, ya riƙe hannayena duka biyun da ƙarfi, riƙon da ya yi min ya haifar min da nutsuwar dole, shi kuma ya zuba min idanuwansa waɗanda suka riga canza launi zuwa yanayin tausayi da damuwa, sannan ya fara magana cikin muryar sa mai amo ta daɗi.  "Nana... kin san irin son da nake miki, kuma kin san cewa wannan lamarin ba zaɓina ba ne, kaddara ce ta iyaye. Amma abin da ya fi komai burgeni ya haifar min da nutsuwar da ta bani damar sauke haƙƙin da nake shirin ɗauka shi ne yadda kika nuna min tsantsar girma da biyayya kika amince da wannan auren. Nana, wannan babban Aikin Lada ne kika ɗauko wa kanki." Ya gyara zama, ya ƙara matse hannuna. "Nana, yanzu an riga da an sa rana, komai ya fara ɗaukan harama, kuma hausawa sunce aski idan yazo ƙarshe yafi ƙaiƙayi. Ina so ki sani, Shaiɗan ba zai bar ki ba. Zai rinƙa hura miki wutar kishi a zuciya don ya rusa miki ladan da kika fara nema. Kar ki bari Shaiɗan ya yi nasara a kanki. Ki duba yadda kika jure har zuwa yanzu, don Allah Nana ki daure ki ƙarasa wannan jihadin da kika fara." Ya ɗanyi shiru kamar mai tunani, sannan ya ci gaba. "Idan aka kawo matar nan, ina so ki nuna mata cewa ke mace ce ta gari, uwar gida mai daraja. Ina so ki sanya ta ta yi miki biyayya kamar yadda kike mini, amma ta hanyar nuna mata ke ce babba. Ki zama uwa a gare ta, ki koya mata yadda ake girmama ni. Idan kika yi hakan, Nana, kin gama mallakar zuciyata har abada, kuma kin tabbatar wa duniya cewa ke ba mace ba ce irin ta sauran mata masu kishin hauka." "Ina so ki nuna mata girmana da darajata a gidan nan, ta yadda ita ma za ta bi sawun ki wajen yi mini hidima. Ta hakan ne kishi ba zai taɓa samun gurbin zama a tsakaninku ba. Nana, shin za ki iya yi mini wannan alfarma ta ƙarshe? Ki zama jagora a gare ta, ki kuma kare ladanki daga sharrin Shaiɗan?" Wani irin sanyi na ji ya ratsa zuciyata, soyayya da tausayin Sardauna suka sake lulluɓe ɓargo da fatar jikina, cike da tausasawa nima na fara magana. “In sha Allah Sardauna, ni zan kasance mai biyayya da tausayawa a gareka har ƙarshen numfashina, Sardauna na yi niyar yaƙi da kowanne irin sheɗani da zai zo ya shiga rayuwata, zan yi haƙuri zan zauna da amaryar ko da ba ta son zama da ni, zan nuna mata girmanka da soyayyarka.” Ya sa hannu ya rungumo ni jikinsa, sannan ya ce.  “Na gode Nanata, Allah Ya yi miki albarka.”  Na amsa da amin, ina rugume da shi. Ban sami damar yi masa maganar rashin ɗaukan wayata da Bilkisu take ba, tun da gashi har abu ta bada akawo min. Tun daga wannan rana bansake bari sheɗan ya samin wani tunani na kishi ba ko wani abu mai kama da hakan, shirye shiryen biki suna ta ƙaratowa, Sardauna ya yi matuƙar busy abubuwa kawai yake shiryawa na auren, lefe akwati set uku ya yi mata, ni kuma ya yi min set ɗaya. Ranar da aka kai kayan gidansu Bilkisu ya kama ɗaurin auren saura sati biyu cif, amma shagulgulan bikin sauran kwama takwas afara a yadda Sardauna yake faɗan. Har da wasu Events da za ayi a Abuja ma, ɗaurin auren ma acan zaayi sabida Bilkisu na da ‘yan uwa acan, ni dai nawa na yi fatan alheri ne kawai.  Lokacin da bikin ya rage saura kwanaki biyu a fara Sardauna ya umarce ni da na je gida na faɗawa su Hajiya, idan zan iya ma na kwana ɗaya acan. Na ji daɗi sosai sabida ina son na zaga ‘yan uwa da na daɗe bangani ba, duk da ya ja kunnena sosai akan kar na faɗi wasu abubuwan.  Da kanshi ya kaini har gida, bayan ya shiga sun gaisa da Hajiya sannan ya tafi, gidan bakowa sai Hajiya Yaya Radiya tana makaranta, Ra’is da Yaya Ridwan ma haka, yaran Yaya Radiya ma sun tafi makaranta. Hakan ya bamu damar zantawa da Hajiya sosai da sosai, har na faɗa mata auren da zaiyi, sai dai na ɓoye mata cewar Bilkisu ƙawata ce, na ce a familyn ɗinsu take, ta yi aure ne ya mutu.  Yaya Ridwan ne ya fara dawowa, amma bai nuna ko ya ganni ba, ya shige ɗaki sai kuma Yaya Radiya, ita ce ma muka tattauna muka yi hira sosai, sai Ra’is da ya dawo. Da daddare Sardauna ya kirani na ce da shi zan kwana anan ɗin, ya kashe wayarsa na tare da ya ce min komai ba.  Washe gari na je gidan Yaya Rumaisa, ta yi mamakin ganina a gidan nata dan tun da na yi aure bai fi sau biyu na je ba, shima duk kafin rasuwar Alhaji ne, amma tun da Alhaji ya rasu banje ba. Muna cikin hira ta ce dani.  “Shashasha, wannan yarinyar ce zaki ce mijinki ba sonta yake ba tuntuni?”  Ta faɗa tana nuna min hoton Sardauna da Bilkisu a cikin mota wanda Bilkisun ta ɗauka da kanta, na yi murmushi sannan na ce.  “Yaya ai sun amshi ƙaddara ne, sabida dukkansu ƙaddararsu iri ɗaya ce, amma aina kika sami hotonan?”  “Nana baki da hankali, a yanzu babu wasu couples da suke trending a social media kamarsu. ko wane shafi kika duba hoton su nr, mutane suna ta posting suna cewa Sardauna Ta ambo, ya sami matar da yake so, wasu a comment sai ƙare miki zagi suke, har da masu cewa ‘yar mitsiyata.” “Hhm Yaya Wannan tunanin su ne, tun da dai muna zaune da mijina lafiya ai shikenan, duk abinda mutane zasu ce su yi ta faɗa,ni dai ina son mijina shima yana sona, ba shikenan ba.”  “Ke Nana kalle ni, wallahi Allah Sardauna baya sonki, ke ni yanzu na fahimci Sardauna auren manufa ya yi dake.”  Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na ashirin da shida.     (26) “Yaya bana son irin wannan maganar, ai daman na san kwata kwata ba kya son Sardauna.”  Na faɗa a fusace. “Ke dalla malama rufe min baki kafin na yi ƙasa ƙasa dake anan, rashin kunya zaki yi min akan Sardaunan?”  “Ni ba rashin kunya zan miki ba, amma kema kinsan ai abinda kika faɗa bai kamata ba, miji na ne fa.” “Au mijinki ko? To mene amfanin aure irin na Sardauna?”  “Yaya wai mene haka?”  “Duka na zaki yi Nana? Duka na zaki yi?”  Ta faɗa tana miƙewa, ganin tashin hankalin na ta ya yi yawa na miƙe da cewa.  “Ni kinga tafiya ta.”  Har n kai gab da ƙofa ta kira sunana.  “Nana!”  Na juyo na kalleta, ta yi min alama da hannu sannan ta ce.  “Zo.” Dawowa na yi na zauna, itama ta zauna kusan minti biyar  Yaya Rumaisa ta gyara zama, ta dubi ni, wadda idanuna suka yi jawur saboda riƙon da ta yi min kaɗai ya karyan zuciya da kuma fargabar abinda zata ce min. Ta nisa, sannan ta ƙara kama hannun na ta matse shi sosai, cikin muryar tausasawa ta fara magana. "Nana, ki nutsu kar kice zaki yi kuka ki saurare ni da kyau. Rayuwa ba soyayya ce kawai ba, kuma zaman gidan miji ba hauka ba ne. Ina kallon yadda kika lallace akan Sardauna, kina neman mayar da shi tamkar abin bautarki. To ki buɗe kunnenki ki ji; Iyaye daban, Miji daban." "Kar ki taɓa kuskuren nuna wa miji ya fi iyayenki a gare ki. Iyayenki sune tushenki, sune suka san ki kafin Sardauna ya san ki. Namiji, komai son da yake miki, idan lokaci ya yi zai iya juya miki baya, amma iyaye ba sa taɓa watsar da ɗiyarsu. Idan kika ɗaukaka miji sama da iyaye, to ranar da zai watsar da ke, ba za ki sami wurin komawa ba." Ta gyara zama ta ci gaba, "Nana, musamman yanzu da za a yi miki kishiya, kada ki kuskura ki shashantar da kanki. Wannan biye-biye da lallaɓawa da kike yi masa, ki rage shi. Namiji idan ya ga kina rawar ƙafa a kansa da yawa, to wulakanta ki zai yi. Ki kame kanki, ki mutunta kanki a mace. Mace mai mutunci ita ce wadda take da sirrin kanta, ba wadda take zama tamkar tsumma a gaban miji ba." "Kada ki bari kishi ya sa ki zama mahaukaciya, kuma kada ki bari soyayya ta sa ki zama doluwa. Ki zauna a matsayinki na Uwar Gida mai daraja. Ki yi masa hidimarsa na matsayin miji, amma ki bar wa zuciyarki sauran sararin numfashi. Idan kika bayar da komai na rayuwarki ga Sardauna, ranar da waccan matar ta shigo, za ki tarar ba ki da ragowar komai na kanki." "Ki tashi, ki gyara kanki, ki daina wannan kukan banza. Namiji girmama shi ake yi, ba bauta masa ake yi ba. Idan kika mutunta kanki, shi ma zai mutunta ki. Amma idan kika zama tamkar tabarma a gabansa, to kowa ma takawa zai rinka yi ya hucewa." ******* Ko da na dawo gidan Hajiya ban faɗa mata yadda muka yi da Yaya Rumaisa ba, na barwa raina da niyar in sha Allah zan ɗau matakin gyara, tsakanina da Sardauna soyayya ce da kulawa babu bautawar da kowa yake tunani, tun ina saka ran zai zo ya ɗauke ni har na kira sa, gaba ɗaya hayaniya ce a inda yake shi ya sa ban wani ji mai yake cewa sosai ba, na katse kiran na yi masa text akan ina jiranshi, amma amsar da ya dawo min da ita ta nemo ta jefani cikin ruɗani.  “Nana ba zan iya zuwa ba, Daddynsu Bilkisu ne ba lafiya tun safe ina asibiti!”  Tunawa na yi lokacin da Alhaji ba shi da lafiya, Sardauna bai ko shigi gidan nan ba sai da ya dawo. ‘Wai anya maganar da ake faɗa min ba gaskiyya ba ce? Bai ci ace na buɗe idona na yi tunani a kai ba?.’ Na tambayi zuciyata, amma da yake tafi ni mutuwa akan Sardauna sai ta ɓoye hakan, ta shiga lissafomin uzurirrika kala kala da zasu kare Sardauna, ina shirin tafiya Ra’is ya shigo yana faɗin.  “Hajiya ga Yaya Turaki nan.”  Mamaki ya kamani wai Yaya Turaki, to me yake yi anan.  “Bari na ɗan gyara wajen kafin ya shigo.”  Hajiya ta faɗa tana ɗan kwashe kayan dake wajen, sannan ta sa Yaya Radiya fa ɗauko mata dadduma ta shmfiɗa mai.  “Ke daskarewar uban me kika yi anan? Ba yanzu zai zo ba ne?.”  Yaya Radiya da zata shiga ɗaki ta tambayeni.  “Tafiya zanyi, yana wajen aiki ne.”  Daidai lokacin kuma Turaki ya shigo, shi da Ra’is kamar wasu abokai haka suka shigo suna dariya, ni abun ma mamaki ya ban, ashe akwai sauran mamaki ganin yadda Turaki ya saba da ‘yan gidanmu har da tsokanar Yaya Radiya.  “Ina yini?”  Na faɗa ganin kamar ma bai kula da ni ba.  “Amaryarmu kina nan kenan?.”  “Eyh! Ta nan tafiya ma za ta yi kuma bai zo ba.”  Hajiya ta bashi amsa, tana miƙewa zuwa kicin. Ƙila ma shi ya gyara musu gidan, dan naga Hajiya wani plast da cokali ta ɗauko masu kyau ta kawo ta ajiye a gabansa, ba tare da wata magana ba ya buɗe ya fara cin tuwon, yana ci Hajiyar tana taɓashi da hira, duk da bai da yawan magana amma su kam yana magana da su, kamar yadda yake yi da ‘yan uwansa.  “Hajiya ni zan tafi kawai.”  “Wai ba zai zo ba, to shikenan ina zuwa.”  “A’a ta jira mana mu tafi tare, ai gida ɗaya zamu.”  Ban tanka masa ba na kom ɗaki na zauna, na tarar da Yaya Radiya tana dannawa waya.  “Wai Yaya yaushe wannan mutumin ya saba zuwa gidan nan haka?”  “Tun rasuwar Alhaji, mene?”  “A’a bakomai.”  “Ai yafi mijinki hankali da nutsuwa.”  “Ku ana fara magana sai ku hau sukar mijina.”  Na faɗa ina cuna baki gaba. “To ai mijin naki ne ba halin arziƙi.”  “Bawani nan, ni kuwa ina Hajja ne?”  “Tana nan tana tijara wai sai an siyar da gidan nan.”  “Anyi mata uban me?”  “Oho mata, sai da Ridwan ya tsinkawa yaron da ya rakota mari sannan suka bar gidan, kuma kinsan yaron da akasa a shagon Alhaji Ridwan ne ya ɗauke shi to yaja masa kunne akan bata komai, shine fa duk take rashin arziƙi.”  “Uhm, aniyar ta can ta bita, yanzu Yaya yaushe zaku gama makaranta?”  “Nan da sati biyu zamu fara jarrabawa, ke ‘yan ajinku yanzu ƙila sun shiga shekarar ƙarshe ko?”  “A’a, za dai su shiga, zango uku ya rage musu gaba ɗaya.”  “Ai gashinan kin cuci kanki, ke ba karatun anan ba ke ba tafiya turan ba, kinbiyewa jirgin ƙarya.”  “Nana fio ku tafi.”  Hajiya ta faɗa tana yayen labulen ɗakin.  “Tom Hajiya.” Na faɗa tare da miƙewa, lokacin da na fito ma baya gidan, na kalli Hajiya na ce. “Hajiya ya zanyi da Sardauna?”  “Mene da Sardaunan?”  “Idan ya ji labarin Turaki ne ya dawo da ni, bazai ji daɗi ba.” “To Nana a daren nan tafi a ƙafa.”  Tana faɗin haka ta shige ɗaki tabarni, ba shiri na yi waje na bishi har ya shiga mota abunsa. A hankali na buɗe motar na shiga, wayarsa yake dannawa sai kuma waƙa tana tashi ƙasa ƙasa, yadda baza ta taɓa damunka ba, kashe wayar ya yi ya ajiye ta akan cinyarsa ya ta da motar ya tana tafiya a hankali cikin nutsuwa.  “Ina zaki irga masoya na ki sanyo da ni, ki duba kanki ana kallona majunoni, ni kuma na ce indai kai naki ne ban faɗi ba, saƙo ya bayyana ne tun da ga zuciya..”  Yana tuƙi yana bin waƙarsa kamar shi ya raira abarsa, ni dai bance ko ƙala ba, sai ma tuna tuƙin Sardauna da na yi kamar za a tashi sama, ga uban waƙoƙin turanci wai na wata Ariana grande, kullum su zaka yi ta ji yana ƙurewa.  “Kin shiga raina, kin zauna dan kin sami guri, na ji kiranki na amsa kuma na zo da wuri, ke ce farko kuma kece ƙarshe, bishiyar nan tai girma wadda kikai mini dashi. Matar ƙani.”  Ya faɗa yana kallona, na juyo na kalleshi sannan na ce.  “Na’am.”  “Na ga kun fara hankali ke da mijinki, tun da ta fara barin ki ki zo gida.”  Na yi murmushi sannan na ce.  “Uhm.”  Ban san me yasa ba, amma ni wani irin nauyin shi nake ji sosai, ku sunansa bana iya faɗa.  “Yanzu saura makaranta ko?”  “Eyh in sha Allah.”  “Tom Allah Ya taimaka ya bada sa’a.”  “Amin amin.”  Daga haka bai ƙara cemin komai ba, ya mai da hankalinshi kan tuƙi ya ci gaba da bin waƙarsa.  “Ke kika ce zaki rayu da ni, so wanda bai gamuwa.” A raina na ji dama sardauna ne yake da wannan yanayin, ina son waƙoƙin soyayya, mussaman ace ni da mijina ina yi masa yanayin min.  ********* Sai ƙarfe tara da arba’in muka shigo gidan, kusan minti talatin muna tafiya a hanya, tafiya kamar ta barin gari sabida yadda yake tuƙi, amma kwata kwata ban ji na takura ba, ko dan waƙoƙin da yake sawa suna haifar min da shauƙin da yake sani hasasomu ni da Sardauna.  Yana tsaye a bakin ƙofarmu, waya a kare a kunnensa da alama ma waya yake, gabana na ji ya tsanamta faɗuwa, na shiga maimaita Hasbunallahu wani’imal wakil, shi kam Turaki ko a kansa ya ƙarasa wajensa ya yi parking mota.  Ganin kamar bazan fita ba ya sa shi buɗewa zai fita, ba shiri na sa ƙafa na fito, gabana yana wani irin bugawa dum dum dum, kamar ana buga ganga. A hankali nake takawa kamar wacca ke tsoron taka ƙasa, idona yana a ƙasa bana son ma ɗagasu na kalli Sardauna.  “Ɗaga kai ki kalleni.”  Ya faɗa a tsawace, sannan ya juya ga Turaki dake shirin buɗe bangarensa.  “Kai uban me ya haɗaka da matata?”  “Tambayeta.”  Turaki ya faɗa yana ƙoƙarin shiga, wani irin tsalle Sardauna ya yi ya cakumo Turaki ya yi baya da shi.  “Uban me ya haɗaka da ita, na ce uban me ya haɗaka da ita?”  “Cika min riga kafin na yi ƙasa ƙasa da kai anan.”  “Ni zaka yi ƙasa ƙasa da shi, kar ka fasa Turaki uban me ya haɗaka da matata?”  “Na ce ka tambayeta mana,  ko ita bata da baki ne? Idan bakasan darajarta ba ka barta ta na tafiya a titi da tsohon dare, ni nasan darajarta a matsayinta na mace, ko ba ita ba naga mace na tafiya a hanya cikin dare ni mai iya taimaka mata na kai ta gidane, bare kuma ita da nasan gida ɗaya zamu je.”  A fakaice dai Turaki ya rufa asirin cewa daga gida ga ɗaukoni, ya sauƙaƙa min sosai.  “Daga yau… ba kai… ba wani abu nawa… Turaki ba kai ba matata, ko a jeji kaganta ba kai ba ita.. na faɗa ma.”  Idanun Sardauna nake kalla yadda suka rini suka koma jawur, ga wasu jijiyon kansa da suka fito raɗau. “To cikani, kuma matarka ce na ɗauko a mota ta, tana gaba ina gab…”  Kuɓus! Haka Sardauna ya make bakin Turaki, sannan ya saki wata ƙara kamar sabon Mahaukaci.   “Turaki akan iyalina wallahi zan iya kashe ka, ka fita sabgarta.”  Riƙe bakinshi Turaki ya yi da yake jini, a hankali ya taka ya buɗe ƙofarsa, sai da ya gama shiga sannan ya leƙo da kai.  “Kuma har ƙanshin Turarenra na ji.”  Yana faɗin haka ya tura ƙofarshi ta shige, da gudu Sardauna ya bi shi yana knocking.  “Turaki ka buɗe ƙofar nan na kakkarya ka.”  Da wani ƙarfi yake buga ƙofar yana kiran sunan Turaki.  “Wallahi Abubukar yau sai na raba hannunka da gangar jikinka, ka buɗe na faɗa maka.”  Can ta wajen window Turaki ya ƙara leƙowa. “Ga fuskarta mai kyau, ta iya murmushi.”  Da gudu Sardauna ya dawo wajen tagar, yana faɗin. “Abubakar zakaci kutumar ubanka wallahi, karuwa ɗan iska, me bin matan mutane.”  “Matarka dai akwai kyau ma sha Allah.” Turaki ya faɗa daga wajen ƙofa, ni dai ina daga tsaye, na fuskanci Turaki dai haukata Sardauna yake son yi, kamar daga sama na ji yana cewa.  “Uban me kike yi anan? Sai na zo na ɓaɓɓallaki, shashasha.”  Ba shiri na shige ciki, ya yo kaina yana faɗin.  “Wato Nana ke baki da hankali ko? Da zaki shiga motar wani namiji da ba mijinki ba, Nana ko yayanki uwa ɗaya uba ɗaya ai bazaki shiga mota tare da shi ba, shine zaki shiga da wancan ƙasurgumin ɗan iskan ko? Wallahi Nana yau sai kinji a jikinki.”  Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na ashirin da bakwai.     (27) Ina shiga ciki na yi cikin ɗakina na kulle ƙofa nasa Sakata, yadda yake wannan saman ai tsaf ya kamani sai ya ɓallani.  "Nana buɗe min ƙofa."  "Ka yi haƙuri dan Allah."  "Na ce ki buɗen ƙofa zaki zauna kina cewa na yi haƙuri?" "Karka dake ni dan Allah."  "Bazaki buɗe min ba Nana, na buɗe da kaina sai na ɓaɓɓallaki."  Ba shiri na taso na buɗe ƙofar, na maƙale a jikin bango. Da iya ƙarfin shi ya kamo hannuna ya matse shi sosai, idanunsa har wani hayaƙi ne yake fitowa daga cikinsu.  "Nana! Nana! Nana! Me ya sa kika shiga motar ɗan iskan can? Me ya sa ?"  "Bakomai ka yi haƙuri dan Allah." "Har wani murmushi kika yi masa? Har ƙamshin turaranki ya ji, ya kama miki hannu ko?"  Da sauri na girgiza kai.  "A'a wallahi, ko kallona bai yi ba."  "Ni zaki yi wa ƙarya, sai na make ki."  Da sauri na runtse idona tare da maƙalewa a wajen ɗaya.  "Ka yi haƙuri dan Allah."  "Me ya yi miki?"  "Bakomai wallahi."  "Bazaki faɗan ba sai na sumar dake?"  "Zan faɗa ma, zan faɗa ma wallahi."  "To faɗamin."  "Babu abinda ya yi min kawai ce min ya yi wai ni da kai mun fara hankali tun da har ina zuwa gida, sai kuma ya ce yanzu saura na makaranta na ce mai tom."  "Uban mene haɗinshi da ke da har zai ce miki saura makaranta, shi uban me ya kaishi unguwar Talakawan nan? Nana daga yau har Abada kar na sake ganin magana guda ɗaya ta haɗaki da Turaki, kin jini?"  "Eyh! Na ji ka." "Shi kuma sai na ɗau mummunan mataki akansa."  Yana faɗin haka ya fice zuwa ɗakinsa ya barni anan, sai da na yi kuka na na gode Allah sannan na yi wanka na kwanta, dan yanzu Sardauna ba ko yaushe muke kwana tare ba.  Washe gari na tashi da ciwon kai sabida kukan da na yi daren jiya, adaddafena haɗa masa shayi da soyayayyen biredi ya ci, har ya fita ya dawo ya kalleni.  "Nana Har abada bake ba Turaki."  "Tom."  Ya sa kai ya fice, nasan dai asibitin su Bilkisu zai tafi, wai ashe ma ƙanin babanta ne ba shi da lafiya shine duk ya ruɗe, bai fi awa ɗaya sa fita ba ya kirani a waya wai 'yan uwan Bilkisu zasu su yi mata jere acan part ɗin, ban ce masa komai ba bayan tom, ni a yanzu kalaman Yaya Rumaisa nake son zama na baje su a faranti na yi musu filla filla. Amma bansami damar hakan ba sabida kiran da Sardauna ya sake yi min akan lallai na yi wa 'yan uwan Bilkisu abun taɓawa. Ta dole na tashi na shiga kwaɓa musu cup cake, bayan na yi na haɗa musu sa cincin, sabida bana son abun da zai wahalal da ni. Wajen ƙarfe biyu na ji motoci suna shigowa nasan sune, hakan ya sa na ƙara gyara jikina na fito. Manyan matane masu kyau, gayu da ilimi, kowacce tafiya take cike da izza, sai na ji ma na raina kaina abun da na yi musu. Kowacce ta shigo zata ɗibi iska daga gabas ta watsa yamma, sai na zama kamar wata 'yar aiki, dan ba wadda tabi ta kaina, hakam yasa na tattare jikina na koma ɗaki, sai da suka kammala na ji wata na cewa.  "Ba mutane a gidan ne?"  Fitowa na yi, tare da faɗin.  "Gani."  "Ke kamar ba kya ganin mutane ne?" Murmushi na yi sannan na ce.  "Na gaisheku tun zuwanku, ganin kamar ba ku kula dani ba ya sa na shige nawa part ɗin."  "Ke 'yar talakawa 'yar mitsiyatan Yelwawa, ki iya bakinki nan baki ga mai kama da wacca zaki gayawa magana ba."  Wani irin ɓacin rai na ji ya ziyarce ni, wannan da ta yi maganar ba manta ta ba, ita ce ta ce danj ballagaza a lokacin da na je wajen Bilkisu, cike da ɓacin rai na ce.  "Ko da na ke 'yar mitsiyatan Yelwawan na sami ilimi da tarbiyar da nasan na girmama baƙo a duk inda ya same ni, kuma a 'yar mitsiyatan Yelwawan nake da ƙimae da 'yar masu kuɗin Takur zata nemeni da kanta."  "Ya isa."  Wata mata ta daka tsawa, sannan ta nuna yarinyar da ta yi maganar.  "Subisha baku kyauta ba, Nana ki yi haƙuri."  Na yi mata murmushi, sannan na ce.  "Bakomai Anty, har zaku wuce ne?"  "Eyh, zamu wuce sai kuma mun dawo kawo amarya."  "Allah Ubangiji ya kawo ku lafiya, ga Snacks da ya ce ayi muku."  Na faɗa ina shigewa kicin, box uku na yi na snacks ɗin na ɗauko na kawo musu, tare da faɗin.  "Gashi an gode, Allah Ya sanya alheri."  "Amin amin, ku ɗauka mu tafi."  Suna fita na koma ɗaki na kwanta, dan ni yanzu gidan ma gaba ɗaya ya daina min daɗi, na ƙagu ayi auren nan a gama hankalin Sardauna ya dawo jikinsa.  Washe gari ta kama rana littinin, ranar suka yi football match, tsakanin familyn Ta Ambo da na su Bilkisu, ba Sardauna ya shigo gida ba sai wajen ɗaya saura na dare, lokacin har na yi bacci na farka.  "Honey! Duk na yi busy al'amuran aure da wahala."  Iaa daga kwancen na yi mishi murmushi, sannan na ce.  "Sannu ko na yi ma tausa?" "Mene tausa Nan?" "Massage." "Uhm, ai kema kin gaji Nana."  "Idan kana so ai sai na yi ma." "Ki huta kawai Sarauniyar mata Nana, uwar gidan Sardauna Ta ambo."  Wani daɗi na ji kamar na jawo shi ma haɗiyeshi, washe gari Talata suka yi wani party, tsakanin 'yan gidan Ta ambo da 'yan gidasu Bilkisu, ina daga gida amma nasan su kansu 'yan uwa Sardauna sun fi farin da auren Bilkisu akan nawa, ranar kam sai bacci na yi na ƙyale Sardauna, dan ban san lokacin da ya dawo ba.  Ranar Laraba suka tafi Abuja, zasu dawo ranar juma'a bayan anyi ɗaurin aure, duk irin hidimar da Sardauna ke ciki ba cikakken awa sai ya kirani.  "Nana karki kula Turaki, karki kula wani namijn, ko su Ra'is." Shine kaɗai abinda yake faɗa da zarar ya kirani, na kira Hajiya awaya na ce mata dan Allah Yaya Radiya ta zo ta yani zama, a yanayin ina buƙatar wani a kusa da ni, Hajiya ta ce sai dai ta dinga zuwa tana yini idan dare ya yi sai ta tafi, ta dole na amince da hakan.  A zuwan da Yaya Radiya take yi, ta kan ɗan bani 'yan shawarwari akan yadda zan rayu da kishiyata, ba kowanne al'amuranta zan shiga ba har Sardaunan ma, na dinga kama kaina akansa a gabanta, na ja mutuncina. Haka dai ta dinga ba ni shawarwari.  Ranar juma'a ƙarfe ɗaya aka ɗaura auren SARDAUNA DA BILKISU, a babban masallacin birnin tarayya na Abuja. Duk da Yaya Radiya da Yaya Rumaisa suna nan hakan bai hanani zubar da hawaye ba, Sardauna dai ya zama ba nawa ba ni kaɗai, ya zama namu mu biyu da wata, ɗakin Sardauna ya zama ba sirrina ni kaɗai ba, ya zama sirrinmu mu biyu, na yi kuka kamar raina zai fita daga baya kuma na haƙura na fawawwala komai.  A daren juma'ar su ka dawo, amma Sardauna bai shigo, arzƙina ɗaya ina jin motsin Turaki dan baije Abuja ba kwata kwata, sai washe gari asabar Sarduana ya shigo, shima a gurguje ya zo yana shirye shiyen tafiya dinner ta yau. Bai ko tsaya ya ji yana ke ba, ya na rayu bayan tafiyarshi, ta dole na haƙura na sallama Sardauna, Allah Ya kaimu a gama bikin.  Anyi gagarumar dinner ta gani ta faɗa, wacca gaba ɗaya jihar jigawa ta ɗauka, ko ina kaduba sune suke yawo, Malaika daga kano ta kira layina, ina ɗagaqa ta fara magana kamar zata hau ni da faɗa.  "Nana ashe tun can da Sardauna ba sonki yake ba kika aureshi? Yanzu gashi duniya ta shaida a yanzu yake auren matar so."  Wani ƙululun abu ne ua tsayamin a raina, na fashe da wani irin kuka sannan na kashe wayar gaba ɗaya, mutane daman har jira suke wani abu ya faru su hau turama salan su ɗaga ma hankali, haka na yini ina kuka babu me rarrashina, ni dai har na yi bacci banga Sardauna ba, banji ɗuriyarsa ba. Haka na tashi da wani irin ciwon kai mai azaba, ko breakfast ban iya ba na watsa ruwa da ƙyar na kira Sardauna a waya akan banda lafiya, amma bai ɗauka ba sai na kira Yaya Rumaisa na sanar da ita, ba ta ce min komai ba rta kashe wayarta, can sai na ga ta turumin text da wata lamba DR NA'IMA DAƘAYYAWA. Tabbas a yanzu nake ƙoƙarin gano gaskiyyar cewa 'yan uwa 'yan uwa ne, duk daɗin da namiji yake baki bai ko rabi 'yan uwa ba, duk da irin fushin da suke da ni, bai hana su zuwa gidana ba lokacin da nake cikin matsala, haka bai hana su ba ni taimako ba a lokacin da na buƙata. Lambar na kira bugu ɗaya aka ɗauka.  "Salamu alaikum, ina kwana?"  "Lafiya ƙalau Alhamdulillah."  Ta amsa muryarta a sake, sai da na gyara murya sannan na ce.  "Ni ce wata da na taɓa zuwa wajenki, har kika yi min faɗa akan Low Bp, sannan na fara yi miki maganar haihuwa."  "Oh! Mr's Ta Ambo Right?"  "Eyh ni ce."  "Okay, me ya sake faruwa?"  "Daman yau ne na tashi da ciwon kai da jiri sosai. Ko zama na yi jiri nake ji, shine na kira sister ɗina  kuma sai taban numberki."  "Ayyah! To mene matsalal Kina cikin damuwa ne ko?."  Sai kuma ta fara magana  cikin sanyin murya.  "Tun a wancan lokacin na faɗa miki sakamakon gwajin jinin da muka yi miki ya nuna cewa hawan jinin ki ya yi ƙasa sosai, wato Low BP. Kuma shi ne yake kawo miki wannan yawan jiri da matsanancin ciwon kai da kike ji." Ji na yi idanuna sun sake yin nauyi,  na sauke wayar daga kunnena na kalle ta, ban ce uffan ba na sake mayar da wayar kunnena a cikin raina nake jin kamkar wani sabon nauyi ya sake danna mini ƙirji. "Nana, ke fa yarinya ce ƙarama, mai ƙarancin shekaru." Likitar ta ci gaba da magana, muryarta cike da gargaɗi.  "A wannan ƙanƙanun shekarun naki, bai kamata kina yawo da Low BP irin wannan ba. Illar da zai yi miki yana da yawa; zai iya sanya ki yawan suma, ya raunana miki jiki, kuma yana iya shafar yadda jini yake kwarara zuwa ga ƙwakwalwarki da zuciyarki. Me yake damunki ne?" Tambayarta ta na ji kamar ta soka mini mashi a zuciya. Me yake damuna? Sardauna ne... auren da zai ƙara ne... kishin da yake shirin cinye mini rayuwa ne.  Watsar da ni da ya yi. Amma sai na tsinci kaina da girgiza kai kamar ta na gani na, hawaye guda ɗaya ya subuce mini a kumatu. "Dole ne ki rage saka damuwa a ranki, Nana," ta faɗa cikin muryar lallashi. "Mata da yawa ba su sani ba, amma damuwa ita ce babbar makashiyar mace. Ki janye kanki daga duk abin da zai ɗaga miki hankali, ki huta, kuma ki rinka cin abinci mai gina jiki. Idan ba ki kula da kanki ba, babu wanda zai kula da ke ba, kin ji ni?" "Eyh na ji."  "Yawwa." Sai kuma ta sauya salon maganar zuwa wani batu da ya fi komai fasa mini zuciya. "Sannan akwai zancen rashin haihuwar da ku Ika zo da shi a wancan zuwan. Ina so idan za ta yiwu, yau ko kuma gobe da safe ki daure ki zo asibiti mu ƙarasa dukkan gwaje-gwajen da suka kamata. Dole ne mu gano tushen matsalar da wurin da take, domin mu san matakin da za mu ɗauka, nasan yana ɗaya daga abunuwan da suke saki damuwa." Kalmar 'Rashin haihuw_ar' ta daki kunnena tamkar tsawa. Na ji wani irin jiri ya sake kwasata a kan kujerar. Rashin haihuwa shi ne dalilin da Sardauna ya dogara da shi zai kawo mini kishiya. Shi ne silar da iyayensa suka matsa masa. A take na ji dukkan gidan yana juya mini, maganganun Yaya Rumaisa na cewa na ajiye soyayyar Sardauna gefe na kula da kaina suka dawo mini daki-daki. "Zan zo Likita... zan zo gobe Insha Allah," na faɗa cikin dasasshiyar murya, ina ƙoƙarin haɗiye kukan da yake shirin kufce mini. Legendspen 08129553971 *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu)  Shafi na ashirin da takwas.     (28) Tun bayan gama wayarmu da Dr Na’ima na rasa me yake min daɗi, ta shi na yi na shiga ɗaki na ɗauko drugs ɗina na kwanaki na dawo falo, fridge na buɗe na samu ragowar cake na zo na zauna na tura shi da tea kamar ina cin ganyen darbejiya haka na tura shi, ina gamawa na ɗauki drugs ɗin na sha, ciki har da nasa bacci.  Banyi ƙwaƙwaran minti sha biyar da shan maganin ba bacci ya ɗauke ni, sai dai kuma banyi nisa da baccin ba na ji muryar Sardauna akaina, a hankali na buɗe ido.  Dishi dishi na fara ganinsa, sai kuma can naganshi tar.  “Wayyo Allah.”  Na faɗa yayin da nake ƙoƙarin miƙewa zaune.  “Nanaty mene yake damunki?”  Girgiza masa kai na yi kawai, ba tare da na ce mai komai ba.  “Ki yi haƙuri Nana dan Allah.”  Na sake girgiza kai, hawaye suka shiga zarya a a fuskata.  “Ya salam! Nana mene dan Allah.”  “Yanzu shikenan sabida zaka ƙara aure ka manta da ni? Ka watsar da ni ka manta akwai wata mata Nana a duniya?”  Ya kamo hannu ya matse su, sannan ya ce. “Nana har abada. Babu abinda zan samu na manta da ke, na manta da hallacinki, ki yi haƙuri dan Allah.”  Ya sa hannu ya fara gogen hawayen, na kauda kai gefe na ci gaba da zubar da abuna. “Nana dan Allah ki yi haƙuri, ki tuna yau fa wannan babin zai ƙare, zamu shiga sabon babi, sabuwar rayuwa, sabon zama Nana, ki bari mu mori wannan lokacin a matsayin na ƙarshe tsakanina da ke.”  Na ɗago na kalleshi, alamun bangane na ƙarshen da ya ce ba. “Nana! Daga yau mun gama zama matsayin ni dake mu biyu kawai, mun zama uku, mun ƙara yawa Nana. Zanyi kewar hakan sosai da sosai.”  Na ji wani irin tausayin Sardauna, son sa ya sakw mamaye guntun ɓacin ran da nake ji, na kama hannunshi cike da soyayya.  “Sardauna ko mu ɗari ne a gidannan, ni taka ce kai nawa ne har abada.”  Ya yi murmushi, ya sa hannu ya ɗaukeni muka yi cikin ɗaki, muna shiga ya mai da hasken zuwa Dum light.  Ɗakin ya yi duhu, ƙanshin turaren wuta na  ɗan kullum ya cika kowane lungu da saƙon ɗakin, yana tashi a hankali. Sardauna yana zaune a gefen gadon, yayin da ni kuma ya kwantar da ni akan gadon, amma na ɗora kaina a kan cinyarsa, yana wasa da gashin kaina cikin wani irin salo mai cire wa mace kowace irin damuwa. Ya sauko da fuskarsa daidai tawa, idanunsa cike da wani irin kallo mai narka zuciya, ya kawo bakinsa dai dai kunnena ya raɗa mini  cikin sanyayya muryarsa.  “Nana... kin san wani abu? Duk duniya babu macen da nake gani na ji numfashina ya tsaya sai ke. Wannan auren da za a yi, kaddara ce kawai ta iyaye, amma babu wata mace da za ta taɓa samun ko da rabin matsayin da kika taka a zuciyata ne. Son da nake miki, ya wuce tunanin kowa.” Na ɗago idona na kalle shi, ina jin yadda duminsa jikinsa yake ratsa ni. Murmushi ya yi, ya sumbaci goshina sannan ya hawo kan gadon, ya kishingiɗe a jikin manyan matashin gadonmu, yayin da ya jawo ni  jikinsa na kwanta luf, na ɗora kaina a kan ƙirjinsa, jikinsa ɗumi, ina jin yadda bugun zuciyarsa yake harbawa a hankali. Hannunsa ɗaya yana yawo a cikin gashin kaina, yana rarraba su a hankali, yayin da ɗayan hannunsa kuma yake shafa lallausan kumatuna da bayan yatsunsa. “Kishinki nake yi, Nana. Kishinki nake yi ko da da iskar daren nan ne da take taɓa fatarki. Wani lokacin idan na rufe idona na tuna cewa nan gaba kaɗan zan rinka raba kwananki, har hakan yana sanya ni tsoro da fargaba. Na san ranar da ba zan kwana tare dake ba, ba zan iya baccin kirki ba, domin jikina ya riga ya saba da numfashinki da zazzafan duminki, Nana.” Hannuna na hagu na ɗora a kan fuskarsa, ina shafa sajen sa da ya sha gyara, ina jin yadda dukkan jikina yake ɓari saboda kalamansa. Ya kama hannun nawa, ya zura yatsunsa a cikin nawa ya matse su da ƙarfi, sannan ya ce.  “Har yanzu ba zan taɓa mance ranar farko da na ganki ba. Nana kinsan ba ranar da na zo umguwarku na fara ganinki ba?”  Ya ƙarashe maganar yana kallon cikin idona, wanda zallan mamaki ya bayyana.  “Kin tuna wata rana da kuka je Manpower ke da Alhaji da wannan yayan naki a wajen taron nan? Kina sanye da fararen kaya, a lokacin kallo ɗaya na yi miki na ɗauke kai, amma Nana wata magana da kika yi ta ja hankalina gareki, haka kawai na ji ƙuruciyarki ta burgeni, kin iya tsokana, kin iya dariya, kin iya fari sa ido, sannan kin iya shiru. Fuskarki kamar ta jirirai da basu san komai ba sai rigima Nana, tafiyarki ta kamun kai da yadda kike kallon ƙasa, shi ne abun da ya fara sace mini zuciya. Na so na ƙyaleki amma sai na ji bazan iya ba, tun daga nan na fara bibiyarki, yadda kike rayuwa da komai Nana, a hankali kika fara shiga raina, har ta kai ko ina gida na kan iya tuna wasu ɗabi’unki na yarinta.“  Ya ƙara matso da ni jikinsa, yana shafa fuskata cikin soyayya, “Nana bansan ina son ki ko kishinki ba, sai ranar da kika nuna kin zaɓi ƙawayenki a kaina, Nana ranar duniya ta tsayamin zafi, na ji wani irin zafi a raina, a ranar na ji a raina ina so ki zama mallaki na nine kaɗai Nana.”  Ya rage tsayin muryarsa ta koma kamar raɗa, ya sumbaci gefen wuyana wanda ya sanya wani irin sanyi mai daɗi ya ratsa mini dukkan jikina, sai kuma ya ce.  “Ranar da na ji zai kin zama mallaki na ni kaɗai, ranar da nazo da hotonki family meeting, kowa yana gani ana bawa wancan mitsiyacin yaron Sardauna kallon da ya yi wa hoton, kallo ne mai nuna sha’awa, na ji wani zafi a zuciyata, kuma na ƙudirci cewar sai na kareki daga dukkan sharrinsa, sai na haramta masa ke har Abada Nana,ke tawa ce ni kaɗai, daga yau har abada Nana.”  Na ɗago idona waɗanda suka riga suka yi ja saboda shauƙin ƙauma, na kalli cikin kwayar idanunsa. Ya ƙara matse ni a jikinsa, yana shaƙat ƙanshin jikina tamkar wanda ke tsoron za a ƙwace masa ni. Murmushi ya yi, ya sumbaci lips ɗina a hankali.  “Nana sai bayan na aureki na ji ina da burin mallakarki har abada, sai dai ƙuruciyarki da take burgeni kin dage sai kin kawar da ita Nana.”  A hankali na ɗan zame jikina, sannan na ce. “Ƙuruciyata kake so ba ni ba?” “Nana ko bake nake so ba, ke tawa ce har Abada Nana, mallakar da na yi miki ta har abada ce, me yake kawo kishi Nana?”  “Sone.”  “To ina yi miki kishin da babu wata hallita da nake yi wa irin shi, abu mafi girma a zuciyata shine tsanar Turaki, to Nana kishin da nake yi miki ya zarci tsanar Turaki sau ba adadi a zuciyata.”  Na ji wani sabon shauƙi ya lilluɓe ni, kalaman sa kamar zuma suke malala a cikin jyjiyoyin jikina. Duk wata fargabar kishiya da nake ji ta gushe a wannan daren, na ji tamkar ni kaɗai ce mace a duniya. “Don haka nake so ki kwantar da hankalinki, uwar gidana. Kewarki da zan rinka yi, ita ce zata riƙa addabar rayuwata a kowane minti. Babu wata mace da ta isa ta maye gurbinki.” A  cikin tsantsar daɗin baki da zafafan kalaman Sardauna, na mika masa dukkan ragamar rayuwata, har ina jin cewa ko da duniya zata tashi, wannan mutumin Sardauna nawa ne ni kaɗai. *********** 06:30pm Zaune yake gefen gadon, ni kuma ina tsaye na gama sanya masa babbar rigarsa, haka hulal ma da kaina na yi masa karinta, ya fito fes kamar ango a daren aurenshi na farko. Duk wani jiri da ciwon kai da nake ji ɗazu, yanzu babu shi.  Muna nan zaune masu kawo amarya suka shigo, kallon kaina na yi a mudubi, na yi kyau na gaji da haɗuwa, lace ɗina dark blue ne da touch ɗin golden, ya yi matuƙar amsar jikina. Ɗikin doguwar rigar ya kwanta a jikina ɗas, na yi ɗaurina mai kyau na ɗora ƙaramin blue mayafi akaina ma zagayoshi ta ka faɗa, kunnena da hannu ɗankun zinare da Sardauna ya siya min ne. Sallama da na ji ana yi a ɓangarena, ya sa na fita zuwa falon, iyayen amarya ne da ita amaryar. Cike da ladabi na tare su tare da basu mazauni.  “To Uwar gida ga amarya mun kawo miki, muna fatan zaku zauna lafiya da juna.”  Na yi murmushina na ko yaushe, sannan na ce. “Ni da Bilkisu kamar ‘yan uwa muke, in sha Allahu babu abinda zai biyo baya sai ɗimbin alheri, ‘yar uwa barka da shigowa.”  “Ma sha Allah, gaskiyya Nana munji daɗi sosai na yadda kika karramamu, Allah Ya yi albarka.@  “Amin na gode sosai.”  Daga haka suka miƙe nima na miƙe suka fice zuwa part ɗinta, na dawo na sameshi zaune gefen gadon.  “Amarya ta zo.”  “Ina sonki Nana.”  Kallonshi na yi, a raina ina jin daɗi. ‘Me yafi wannan daɗi? Mijinki yana ƙara aure amma babu abinda yake ce miki sai yana sonki. Shin a matan duniya akwai wacca tafi ni sa’a kuwa? Ni Nanan Sardauna.’ “Ina sonka Sardauna, ina tare da kai komai runtsi komai wuya Sardauna, Allah Ya baka ikon yin adalci mijina.” “Nana!”  “Na’am.”  “Bilkisu ta ce min ba za ta iya girki a gawayi ba, amma na amince mata tunda daman kece kika zaɓi yin amfani da shi, sannan ta ce ba zata rayu ba Ac, ba Iron, ba fridge ba, shima na amince mata, duba da adalaci ke baki saba da su ba, ita kuma ta saba, tun da a addini ma ance idan ka auri mace ka ba ta abinda take ciki a gida, ko wanda ya fishi, idan ba zaka iya ba kar ka aureta, shi ya sa Nana, ke kuma ko da na hanaki wannan Nana nasan na baki fin abinda yafi na gidanku ko?.”  “Sardauna! Ni ba duk wani ƙyale ƙyalen duniya nake buƙata ba a zama na da kai, Sardauna kai kawai nake so, kai nake buƙata, kai ne zan rayu da shi Sardauna.”  Rungumo ni ya yi jikinsa, sannan ya ce.  “Nana girmanki da kimarki a idona abune da bazasu taɓa taɓuwa ba, Nana zan iya yaƙi da kowa akanki, Nana ina so a yadda kike yi min uziri a yanzu ki ci gaba da yimin har ƙarshe Nana, ina sonki ina sonki ina sonki.”  “Ina sonka nima sosai da sosai, yawwa gobe zanje asibiti akan ciwon kaina.”  “Tom Nana, Allah Ya kaimu.”  “Amin amin.”  “Ƙarfe tara ta yi Nana bara na je wajen amarya, ki shiryawa zuwana, da akwai magana Nana.”  “Tom Allah Ya tsare, amma ina kazar?”  “Nana tana mota, yanzu zan shigo da ita, akwai taki akwai ta ta Nana.”  “Tom Ango.”  Ya sa kai ya fice, ni kuma na zauna a gefen gado. ‘Idan ace haka Sardauna zai nuna min soyayya, ya auri mata dubu mana, ni dai Allah Ya sallameni wallahi, na yi da ce da Sardauna, na yi da ce da miji na arziƙi, Allah Ya barmin Sardauna  na. Dan na yi imani Sardauna ya cika jarumin maza, ya cika miji, wai ni shin idan ban bautawa mijina na me zan masa, ni na daina zuwa wajen su Yaya Rumaisa, tun da na fuskanci kamar basu san me suke faɗa ba, ina dalili ace wai biyayy zan masa ba bauta ba, Mitcheww.”  Na ja tsaki tare da tashi na fito falo, ina nan zaune har wajen goma Sardauna bai dawo ba, a raina na ce ko Sardauna ya je siyo kaza ya yi dare ne bai dawo ba? Ganin goma da kwata ya sa na ɗaga labule sai dai ga motarsa Nana.  “A’a ina ya yi ne? Ko yana can wajen Bilkisun?”  Na faɗa cike da mamaki, daidai lokacin kuma na ji sautin takunsa, komawa na yi na zauna akam kujera daidai lokacin kuma ya shigo.  “Nana!”  “Na’am.”  “Ta so muje ko?”  “Zuwa ina?”  “Ɗakin Bilkisu mana? Ko kin manta.”  “Na yi tunanin nan za ta zo.”  Na faɗa ina miƙewa.  “Ki kijiki ta zo ta yi miki me?” “Bakomai.”  Yana gaba ina binsa a baya muka shiga ɓangaren nata, ya ji kaya na alfarma, kina gani kinsan ‘yar masu hali ce a gidan. Da sallama a bakina na shiga, tana zaune kamar ba amarya ba, ta mimmiƙe tana danna waya, ɗaki ga Ac ga fanka abunta.  “Hajiya Bilkisu amarya.”  Na faɗa ina washe baki da niyar zama akan kujera.  “Ke dakata! Kar ki kuskura ki zauna min akan kujera.”  Kallon ta na yi baki a sake, na kalli Sardauna da ya zauna yana danna waya.  “A tsaye zan zauna?”  “Nana zauna a ƙasa.”  Sardauna ya faɗa, mamaki kamar ya kashe ni.  “Ki zauna Nana.”  Ba musu kamar umarnin ubangiji na zauna.  “Nana!”  Sardauna ya kira sunana, na ɗaga kai na kalleshi.  “Nana! Na gode da aura min mace mafi soyuwa a raina, na gode da aura min mace da nake son ta a zuciyata.” https://chat.whatsapp.com/FaQD2pS03r12pfKIb7jQMb?mode=gi_t (Wannan shine sabon group ɗin mu) *Munyi nisa a Arewapen, ta wannan link ɗin ko username Legendspen* https://www.arewapen.com/book?id=69d7e87dfc259651b7635bff *SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu) Shafi na ashirin da tara.     (29) END OF BOOK ONE. (Ƙarshen littafi na ɗaya) Kamar saukar aradu haka na ji maganganun Sardauna suna dukan gangar jikina. Gaba ɗaya na ji duniyar ta yi mini tsit, kalaman sa suka baibaye mini tunani na, jiri na ji yana neman kwasata. "Na gode Nana... na gode da kika share mini kukan zuciya ta hanyar aura min mace mafi soyuwa a raina. Na gode da kika cika mini burina na aurar min da matar da nake so a cikin zuciyata." Waɗannan kalaman na Sardauna su ne suka daki kunnena ta baya. Na ji tamkar an tsire min zuciya da mashi mai zafi. Na ɗago raunanun idanuna da suka riga suka yi jaƙaɓ da hawaye, suna mini wani irin zazzafan zafi, na kalli fuskarsa. Fuskarsa daban da waccan da na sani a baya, Sardaunan Nana, babu sauran ɗigon tausayi ko ƙauna, sai tsantsar wulaƙanci da ya bayyana a cikinta. Na juya na kalli fuskar Bilkisu, wadda ke tsaye tana kallona tamkar tana kallon dabba. A daidai lokacin, na fara kokawa da zuciyata ta ina ƙoƙarin ƙaryata abun da kunnena ya ce ya ji. A raina na ce, 'Ba Sardauna na ba ne... mafarki nake yi... Sardaunana ba zai mini haka ba.' Cikin taƙama da jiji da kai, Bilkisu ta saki wata daddaɗar dariya mai cike da baƙar baƙantawa, ta kalle ni ta ce. "Kanki ya ɗauke wuta ko, Nana? Ke yarinya ce marar wayo, marar ilimi da tunani!" "Bilkisu, yi shiru!" Sardauna ya dakatar da ita. A lokacin, wani ɗigon fatan alheri ya ɗarso a zuciyata. Na rinƙa jiran abinda Sardauna zai ƙara cewa. A cikin raina addu’a nake yi, 'Ya Allah... Allah Ka sa cewa zai yi ƙarya take yi... Allah Ya sa cewa zai yi shi nawa ne.' Amma sai na ga ya tako a hankali, ya tsaya daidai inda nake, ya zuba mini idanun sa da babu alamar tausayi a cikinsu, ya ce. "Nana! Ba ke nake so ba. Ƙuciyar jikinki kawai nake so... wadda na riga da na gama mallaka gaba ɗaya. Nana, ban taɓa son na rayu da ke a matsayin macen da zan so ba, sai dai na rayu da ke a matsayin wadda zan killace ta, na hana ta kula kowa a duniya, saboda zazzafan kishin ki na ƙaddara da nake ji a rana, Nana." Ɗum...! Haka na ji kaina ya ɗauki wani irin zafi, wani baƙin abu mai nauyi ya daki ƙarƙashin ƙirgina, ya tare mini numfashi. Jikina gaba ɗaya ya daina aiki, ya saki tamkar gawa. Kafin na dawo cikin hayacina, muryar Bilkisu ta sake dukan kunne na. Wani irin masifaffen jiri ne ya ɗebeni, na ji ɗakin yana neman kayar da ni. Cikin tsananin razana da gigicewa,na lallaɓa na dafa gefen kujerar da ke kusa da ni, jikina gaba ɗaya yana wani irin karkarwa kamar wacca za a zarewa rai, bakina yana ɓari na fara faɗin. "Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un...! Don Allah... don girman Allah Sardauna karka sake ni! Don girman Allah karka yi mini haka!" Cikin rashin tabbas da ƙasƙanci na zube a ƙasa, na rarrafa ina jan gwiwoyina na matsa daidai wajen ƙafafunsa, na sa hannuna duka biyu waɗanda ke rawa tamkar ana jijigasu, na ƙanƙame ƙafarsa da ƙarfi, hawaye masu zafi suka wanke mini fuska. "Sardauna...! Sardauna ka yi wa Allah, ka yi wa Ma'aiki karka sake ni! Ina sonka... ina sonka da dukan rayuwata! Ban san yadda zan yi ba, ban san yadda zan rayu ba idan babu kai a rayuwata... Don Allah Sardauna, karka watsar da ni...!" Cike da ƙyama, ya janye ƙafarsa da ƙarfi daga kankamewar da na yi masa, wanda hakan ya sanya na kusan kifa fuskata da ƙasa. Ya ja wani uban tsaki mai tsayi, ya dube ni da waɗancan idanun nasa da suka riga suka zama tamkar na dabba mai cutarwa, sannan ya ce. "Ke dallah malama, sake ni! Ubanki ma ai kin rasa shi kuma kin rayu, balle kuma ni da kika ganni da haƙoranki talatin da uku! Nana, na gaji da zama da ke... zama marar amfani da riba. Ke ba haihuwa za ki iya yi ba, ba za ki iya samar mini da ‘ya’ya ba, kuma ke ba karatu gare ki ba balle a ce za ki zama wata abar alfahari a nan gaba!" Na daskare a wurin. Idanuna suka ƙafe a kan kafaɗarsa, wani irin masifaffen sanyi mai daskarar da jini ya ratsa daukacin gangar jikina. Nan take, wani irin sauti mai amo Ƙuuuuuuu...! ya shiga ruri a cikin kunnuwana, yana toshe mini kowane sashi na jiyya. Zuciyata ta fara wani irin juyi na takaici da nadama. Sardauna... Sardaunan da ya zama silar ajiye karatuna tun bayan gama Aji na Farko a jami'a, domin kawai ya ce kishina yake yi ba ya son maza su kalle ni, yau shi ne yake tsaye a gabana yana yi mini gorin rashin karatu? A daidai lokacin da abokan karatuna suke gab da shiga shekarar ƙarshe ta kammalawa, yau ga ni nan daskare a ƙasa, ina karɓar kaskanci a matsayin jahila marar amfani. "Hahahaha...! Ana bikin duniya, akan yi na ƙiyama! Ga ki nan don Allah, shashasha da ba ta san darajar kanta ba. Miji zai sake ki, amma kina wani durƙusawa a ƙasa kina masa magiya da kuka! Gaskiya Nana, ke jahila ce ta ƙarshe, tabbas!" Muryar Bilkisu, mai cike da dafin da ya fi na kowane maciji ɓarna, ita ta dawo da ni daga wancan zancen zucin da nake yi. Ina nan a durƙushe, amma ɗakin gaba ɗaya jiri yake mini, ganina yana neman gaba ɗaya ya canza launi ya koma baƙi. Hawaye masu zafi suka wanke mini fuska, amma saboda tsananin son Sardauna da ya riga ya zama jinin jikina, ban ji kunya ko tsoron sake kaskantar da kaina ba. Da ƙyar, cikin rawar jiki da karkarwa, na sake rarrafawa a kan gwiwoyina zuwa daidai inda yake tsaye, na sake sa hannuna duka biyu na ƙanƙame ƙafarsa, muryata tana fita kaɗan kaɗan. "Don Allah... don Allah Sardauna karka sake ni! Zan zauna da kai a kowane yanayi... ko da a haka ne. Ba zan nemi abinci ba, ba zan nemi abin sha ba, ba zan sake neman suttura ba! Ko magana ba zan rinka yi maka ba, ba zan sake takura maka ka kalle ni a matsayin mace ba... don Allah muddin dai ina cikin gidan nan da sunanka, zan jure kowane irin wulaƙanci...!" Ya kalle ni na tsawon daƙiƙa guda, fuskar nan tasa babu alamar imani ko ɗigon tausayi, ya ce. "Nana, ba zan iya ci gaba da zama da ke a haka ba. Daman ƙuruciyarki na aura, kuma a yanzu gashi ta riga ta tafi, kin rage daɗi. Nana, ba ke nake so ba... ƙuruciyarki nake so, kuma da ita nake son na rayu, ba da ke ba, Nana! Zan dai bar ki ki ci gaba da zama a ɓangaren can na gidan, ba tare da rashin abinci, abin sha, ko suttura ba. Amma kuma babu wanda zai san na sake ki a duniyar nan... har abada!" Na yi shiru, tabbas ina son Sardauna, so mai girma da zafi, son da ya riga ya zama jinin jikina. Idan har zan zauna a gidan nan ƙarƙashin ikonsa, to wallahi zan zauna, matuƙar dai ina numfashi a inuwar gidansa. “Saki nawa za a rubuta?” Muryar Bilkisu ta katse mini tunani, tana tambayarsa cikin isa. “Ɗaya.” “Ɗaya kuma?” Ta tambaya a gatsine, cike da rashin gamsuwa. Shi kuma ya dube ta, ya ba ta amsa a tsawace tamkar zai rufeta da duka. “Eyh ɗaya! Ki rubuta: Ni Fahad Ta’ambo (Sardauna) na saki Nana saki ɗaya.” Ba musu ta ɗauki biron ta rubuta. Ni kam wani irin baƙin abu mai ɗaci na ji ya tsaya mini a wuya, ya toshe mini ƙofofin numfashi. Saki mafi ƙasƙanci da walakanci a rayuwar mace, shi ne kishiyarki ta rubuta miki saki da hannunta! Ni Nana na shiga uku! Rayuwata ta gama lalacewa! “Nuna mata ta gani!” Sardauna ya ba ta umarni cikin ko-in-kula. Ta sa takardar daidai saitin fuskata, ta nuna mini rubutun da ya wargaza mini dukkan sauran darajata. Sannan ya kalli takardar, ya ce. “To yaga, saboda ba na so kowa ya gani.” Ba musu Bilkisu ta cire takardar, ta yaga ta guntu-guntu ta watso min a fuskata tamkar almajira. “A tashi a tafi!” Ba shiri na yunƙura zan miƙe, sai dai kafin gwiwoyina su ɗauki nauyin jikina, na ji ɗakin gaba ɗaya ya kife da ni. Wani duhu mai nauyi ya lullube idanuna, na zube a kasa sumamma... ******** Ɗum... ɗum... ɗum...! Haka nake jin kaina yana mini wani irin duka kamar an buga guduma. A hankali na fara Ƙoƙarin buɗe idona, amma wani zazzafan raɗaɗi ya sara mini a tsakiyar kaina ya sanya na sake rufe idon da sauri, ina dafe gashin kaina. Muryoyin mutane na jiyo a kaina sama sama. “Dr. Na’ima, zan bar wannan case ɗin a hannunki don Allah. Referral ne daga wajen wani abokina, to ba ya ƙasar a yanzu, ki kula da ita sosai.” “Ni fuskar patient ɗin tamkar na sani, amma bari ta tashi tukunna.” Sai da na kwashe kusan mintuna talatin ina nishi, sannan na iya buɗe idona gaba ɗaya. A hankali na sauke su a kan kyakkyawar fuskar Dr. Na’ima Daƙayyawa, wadda ke sanye da farar rigar likitoci tana duba wani file. “Mrs. Ta’ambo, is that you?” Na gyaɗa mata kai a hankali, hawaye guda ɗaya mai zafi ya fito daga gefen idona. Ta taso kusa da ni, ta zauna a gefen gadon asibitin. “Duk abin da nake fada miki a baya, ba kya ji ko? Ki godewa Allah da yasa yanzu BP ɗin ya dawo daidai, amma kina da babbar damuwa a ranki.” Na girgiza kaina na kasa cewa uffan, bakina ya yi mini nauyi tamkar an daure shi. Ta zuba mini idanu na tsawon dakika, sai can kuma ta ce. “Kin kyauta abin da kika yi wa mahaifarki? Na shan abubuwan da za su hana ki daukar ciki?” "Ban gane abin da kika fada ba fa..." Na fada cikin kiɗima, kaina ya sake ɗaukar wani irin sabon jiri. Ji nake yi kamar akan garwashin wuta nake kwance ba a kan gadon asibiti ba. "Abin da kika shuka da hannunki ne ya dawo miki yanzu.” Ta faɗa tana yi mini wani irin kallo na zargi da takaici. "Wallahi ban gane abin da kike nufi ba! Abin da na sani, rayuwata ban taɓa shan wani abu da zai hana ni ɗaukar ciki ba! Hasali ma akwai wani likita da nake zuwa wajensa tun can baya, kullum yana duba ni yana ce mini mahaifata ta fara ƙwari, kuma bai taɓa yi mini irin wannan zancen ba!" "Uhm... shi wane ne wannan likitan?" "Sunansa Dakta Ɗan Adala... kuma abokin miji na ne." Fuskar Dr. Na’ima ta canza gaba daya, ta matso da fuskarta tana kalleni, "Kina nufin da kanki ba ki taɓa shan wani abu ba da zai hana ki ɗaukar ciki ba, wanda gashi yanzu ya haifar miki da mummunar lalacewar mahaifa? Kuma wannan lalacewar tuntuni ta faru, ba yanzu ba." "Wallahi-Allah ban taɓa sha ba! Ban taɓa sani ba!" Na fada ina kuka, kaina yana wani irin juya mini, jiri yana ɗibana duk da cewa a zaune nake. Hannuna ta kama ta damƙe shi da ƙarfi, sannan ta ce. “Mrs. Ta’ambo, ki nutsu... ki saurare ni da kyau." Kallonta na yi, babbar mace wadda na san tabbas ta haife ni, ta haife har Yayatama. "To..." Na fada ina saurarenta da dukkan guntuwar nutsuwar da ke tare da ni. "Mijinki... ya kuke da shi? Ina nufin yanayin zamantakewar aurenku na cikin gida?" Sai da na goge hawayen idona da gefen rigata sannan na ce. “Komai daidai yake... yana nuna mini soyayya ta daban." "Bai taɓa nuna miki bacin rai ko damuwa a kan rashin haihuwa ba?" "Eyh... bai taɓa ba. Shi da abokinsa Dakta Ɗan Adala ma sune kusan kullum suke kwantar mini da hankali, suke ce mini lokaci ne bai yi ba. Sai dai daga baya-bayan nan ne ya fara nuna damuwa a fili, har abin ya kai shi ga ƙara aure." "Hhmm... auren soyayya kuka yi ko na haɗin gida?" Ta tambaya tana girgiza kai. Sai da na kalleta da kyau sannan na ce. “Na soyayya ne." "To akwai babbar matsala gaskiya! Tabbas, ko da saninki ko akasin haka, amma an daɗe ana baki kwayar da ke hana ɗaukar ciki, kuma da alamu kin daɗe kina amfani da ita a asirce har aka kai ga wannan matakin na cewa mahaifarki ta mutu!" Wani muguwan shock ne ya daki zuciyata...! Dakta Ɗan Adala? Magungunan da yake ba ni yana cewa na "Kwarin Mahaifa" ne? Sardauna ne ke karbo mini? Kafin na gama hada wannan mummunan lissafin a kwakwalwata, aka buɗe ƙofar ɗakin asibitin Sardauna ya shigo, fuskarsa ɗauke da wani irin murmushi. A hankali ya tako cikin ɗakin tamkar babu abin da ya faru. Dr. Na’ima na ganinsa ta miƙe tsaye, ta dube shi cikin ɓacin rai ta ce. “Idan ka gama da ita, meet me in my office.” “Okay,” ya amsa mata cikin ko-in-kula, ita kuma ta fice ta ja musu kofar. Ɗakin ya rage daga ni sai shi. Ya tsaya daidai saitin gadon, ya zuba mini idanunsa da na daɗe ina bai wa amana. “Nana... kallon me kike mini?” Wata irin azabbariyar tsana, mai ɗaci da zafi, ita na ji ta dirga ta mamaye kowane sashi na zuciyata a lokaci guda. Tsanarsa ta daki jinin jikina. Ya duka daidai fuskata, ya rage murya yadda ni kaɗai zan ji, ya ce. “Nana, kin sami labarin abin da na yi wa mahaifarki ko? To ba iya wannan ba... ki sa rai da shirin ganin abubuwa da yawa nan gaba Nana, waɗanda ma ba lallai kanki da rayuwarki su iya daukansu ba!” KARSHE EN LITTTAFI NA FARKO END OF BOOK ONE. Jama’a wannan bakomai ba ne illa shimfiɗa, littafi na ɗaya ya shimfiɗa mana hanyar da zamu kwarara doguwar tafiya. Ga dai Sardauna ya saki Nana, shin zata zauna a gidan ko tafiya zatayi? Ga kuma Turaki a gefe. Ku hanzarta ku biya kuɗinku ku karanta, na tabbatar muku babu nadama a cikin wannan tafiyar. *Littafin Sartse na kuɗi ne 700 a whatsapp ake posting, ku tura kuɗin karatu ta wannan acc ɗin 8104743474 opay Hafsat muhammad lawan, shaidar biya ko tuntuɓa ta wannan lambar.* 08129553971