Compiled By Umar Dalha Funtua. Copied By Zulyheart Rano [10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* ```Wannan page din sadaukarwa ne ga MARYAMERHABDUL (KWAISEH), fatan Alhairi na ke maki a dukkan rayuwar ki, Ubangiji ya kareki daga sharrin makiya da masu yi maki hassada, Wallahi Allah ina kaunarki har cikin raina, Allah ya kara maki basira da kafin k'wak'walwa. Ina yinki sosai marubuciyar DUHUN DIMINA```😍😍 _*MY BESTY KHADIJAH S MUHAMMAD, HMMMM BA SAI NA FADA MAKI IRIN SON DA NAKE MAKI BA, DON KE DIN SHAIDA CE*_💞 *27* Wani sansanyar ajiyar zuciya ya sauke, tare da lumshe ido ya buɗe su fes a inda yake, sosai ya ke jin dadi na kewaya duk ilahirin jikinsa a fili ya furta "Alhamdulillah! Na sauka a kasar haihuwata Nigeria kasar mu ta gado." Duba ya kai ga agogon da ke manne a hannunsa, in da ya nuna masa karfe biyar harda mintina, sanye yake cikin kananun kaya wanda suka amshi jikinsa, ya yi kyau a ɗan zaman da ya yi na kwanaki bakwai a can, ji ya ke kamar ya yi tsuntsu ya gansa gabanta, babu abin da yake buk'ata a wannan lokaci sai ganin kyakkyawar fuskarta da daddaɗar muryarta, murmushi ya sauke ma kyau a fili ya ce *I LOVE YOU AMEESHA* Muryar direban su ne ya sa shi dawowa da hankalinsa sa kan shi, murmushi ya saki tare da fadin "Har ka iso?" "Eh! Yallaɓai." "Madallah! Mu je kawai." Shigowa ya yi cikin motar, sannan direban ya ja, mintina ƙalilan suka isa gidan, a parking space direba ya faka motar sannan ya fita, da sallama ya shiga falon "Assalamu Alaikum!" Mummy da ke kai komo tsakanin falo da kicin ta amsa masa "Wa'alaikumus salam! Barka da isowa NAJEEB." Murmushi ya saki yana ci gaba da takawa har inda Mummy take, ya ce "Yawwa Mummy na, *I miss you* ." " *I miss you too my son*" Mummy ta faɗa cikin jin daɗi. Zama ya yi akan kujera ya soma gaidata, da kulawa ta amsa tana tambayarsa yadda ya baro garin "Ka ga kar ka zauna surutu, ga dukkan alamu akwai yunwa a tattare da kai, don haka tashi ka yi wanka sai ka zauna cin abincin." "Wallahi kamar kinsan na yi missing ɗin abincin ki mai daɗi, bari na fito wanka sai na zauna." Ya yi maganar yana soma tafiya. "Najeeb! Mummy ta kira sunan sa. Dawowa ya yi yana faɗin " gani mum." "Ka bar wankan nan, bari na hada maka kawai ka je da shi gidan ka, tunda yau kwana biyu kenan da aka kai maka amarya kuma ba ka nan." Kallon Mummy ya yi mamaki kwance a fuskarsa ya ce "Mummy Ameesha ta tare ne?" Girgizar kai ta yi ta ce ya zauna, zama ya yi duk jikinsa ya yi sanyi, nusiha Mummy ta fara yi mu mai tsuma jiki "Kana ji ko Najeeb! Ina so ka yadda da komai na duniya sai da Allah ya tsara shi, ka yadda wani ba zai taɓa auran matar wani ba, haka duk inda ka kai ga son abu matukar ba Alhairi ba ne bazaka taba samunsa ba, ka yadda Ameesha ba matarka ba ce, Rufaida ce matarka ina son ka yi hakuri da canjin da ka samu." Mummy ta dakata tana kallon wani yanayi Najeeb ya shiga, sai ta ga ya saki murmushi ya ce "Mummy na fahimci inda nusihar ki ta dosa, wallahi na yadda da kaddara kuma insha Allahu ba zan bijirewa ikon Allah ba." "Yawwa ɗan albarka, Allah ya yi maka albashi ya baka zuri'a dayyaba." "Amin." Ya amsa cikin ɗan dariya, duk da zuciyarsa tana kuna da rashin Ameesha, sai dai hakan ba zai hana shi kula da Rufaida ba domin kuwa ita ce farkon masoyiyar sa. "Mummy haɗa min in tafi." Najeeb ya yi maganar yana mik'ewa tsaye. Tashi Mummy ta yi tare da nufa kicin ɗin, sai da ta haɗa masa komai sannan ta kawo masa, tana faɗin ƙasa Rufaida ta ci abinci da yawa, domin na kulla bata son cin abinci." Da yake tunda aka kai Rufaida kullum sai Mummy ta aika mata da abincin. "Insha Allahu Mummy zan sanyata." "Yawwa to ka gaidata, idan ka huta ko zuwa jibi ne sai ka kawo min ita." Don lokaci ɗaya Mummy ta ji son Rufaida, domin dai Allah ya yita da nutsuwa ga kunya. ****** Dr yana fita gida ya nufa, lokacin da ya shiga falon babu kowa, don haka bedroom ɗinsa ya shiga, shirin wanka ya yi cikin sauri sauri, bai wani jima da shiga ba ya fito, shiryawa ya soma yi cikin wasu kananan kaya wanda suka karbi jikinsa, sosai kayan sun yi masa kyau jikinsa yana fitar da wani sansanyar kamshi mai sanya nutsuwa a jikin dan Adam. Rigar kalar ja ce an yi mata rubutu da kalar golden *Special one* sunan dake manne a jikin rigar kenan, ya yin da wandon kuma baƙi ne, wayoyinsa ya kwasa tare da key ya yi waje, har ga Allah ya manta da wata Aneesa, don burinsa kawai ya yi arba da Ameesha farin cikinsa, motsin da ya ji shi yasa shi saurin waigawa Gabansa ya yi mummunan faduwa ganin yadda fuskar Aneesa ya kumbura, cikin sassarfa ya k'arasa inda take yana faɗin "Anee lafiya?" Ya yi maganar yana kai hannu jikinta. Harara ta watsa masa tare da kaucewa don bata son hannunsa ya sauka jikinta, juyar da kai gefe ta yi ranta yana tafarfasa ji take kamar zuciyarta zata faso waje muryarsa ta kuma shiga kunnenta "Tambayar ki fa nake yi, ni yanzu bani da yancin taɓa jikinki kenan?" Da masifa ta kalleshi ta ja tsaki tare da tabe baki ta ce "Ina ruwan ka da lafiyata, maganar taɓa jiki kuma ai ina ga ka yi sabuwa sai ka je ka ci gaba da taɓa nata na bar mata, yanzun ma wajenta ka nufa ko? Wai don Allah Hamma dama haka kake ko kuwa dai zumudin amarya yasa haka?" Cikin kunar rai ta k'arasa maganar. Murmushi ya saki ya ce "Bari na dawo zan baki amsa, amma Please ki daure ki bar kuka haka, ki dubi yadda kika koma fa? "Ina ruwanka da yadda na koma? Duk yadda na zama ai ina ga ba matsalar ka ba ce ko?" "To ki daure ki ci abinci, kar ulsa ta kamaki." "Ba ulsa ce zata kamani ba typoid zaka ce, kaga Hamma bana son *kankamba cirani ba miji a tafi ba ciki a dawo da goyon* ba zan ci ɗinba." A fusace ta dire maganar. Girgiza kai ya yi cikin takaici da halin Anee, karin maganar ta ta karshe ce ta bashi dariya, har ya kusa yin dariyar sai ya yi saurin kumshe dariyar don kar ya kuma kular da ita sai kawai ya fita, tana ganin ya nufi fita ta ruga ɗaki da gudu bedroom ɗinta tare da sakin wani kukan. Shi kuma yana fita motarsa ya shiga tare da bata wuta cikin gwaninta da kwarewa yake juya kan motar, har ya isa unguwar su Ameesha, farin ciki ke kwarara zuciyarsa har ya ɗan gana da get din yana hon maigadi ya buɗe masa, shi kuma ya cusa hancin motar cikin gidan yana gaida maigadin. A parking space ya faka motar ya fito, jingina ya yi tare da harde hannunsa a kirjinsa yana tasbihi ga Allah, a hankali ya zame hannunsa ya zaro wayarsa ya yi dailling Number ɗin ta, Lokacin wayar tana hannun Meena don ita ke amfani da shi, ganin Number din babu suna sai ta yi kamar kar ta ɗauka, har tana daf da katsewa sannan ta dauka "Hello." "Assalamu Alaikum! Dr ya faɗa yana gyara tsayuwa. Amsawa Meena ta yi tana dan zaro ido jin muryar kamar ta Dr. Maganar sa ce ta dawo da ita daga tunanin da ta faɗa. "Meena Dr ne gani a cikin gida, ki yi min iso a wajen Ummi." "To." Meena ta amsa tana nufa bangaren Ummi, a falo ta samu Ummi Ameesha ta yi filo da cinyar Ummi ɗin, zama ta yi kusa da Ummi sannan ta ce "Ummi Dr ne fa yazo! Murmushi ta saki tare da shafa kan Ameesha ta ce "Barkan shi da zuwa, a kawo shi nan bari in koma bedroom ɗina." Ta Kai karshen maganar tana mik'ewa. Meena ma hannun Meesha ta ja tana fadin "Mu je ki shirya tarbar Dr ga shi can a harabar gida." Tana maganar ne suna tafiya, suna shiga bedroom din Ameesha, Meena ta fara gyara mata kwalliyar fuskarta, domin bata wani dade da yin wanka ba, ko kayan jikinta bata canza ba domin dai doguwar riga ce baka, wacce ta sha adon duwatsu, sosai rigar ta yi mata kyau dankwalin rigar kuma aka yi mata rolling ɗinsa akanta sosai ta yi kyau. Turaruka masu sanyin kamshi Meena ta feshe mata jiki da shi, kai masha Allah gaskiya Ameesha ta haɗu iya haɗawa, takalmi ta dauko mata shima baƙi, Meesha sai murmushi take yi don ita kanta tasan ta haɗu balle kuma shi ogan ya ganta. Sosai Meena ke kula da lamarin Meesha, duk wani abu da tasan Meesha tana yi a lokacin da take cikin tunanin ta, shi take mata. (Allah ka hadamu da kawaye na kwarai ameen). Rike mata hannu ta yi har suka shiga falon, tunda Dr ya daura idonsa kan Ameesha ya kasa saukewa, domin ba karamin kyau ta masa ba, sai yaga kamar yau ce ranar da ya soma ganinta. Ita ma Ameesha ganin yadda ya kafeta da ido fuskarsa da murmushi i it din ma ta sakar masa, kallon su Meena ta tsaya yi domin sun bala'in burgeta, Meesha tana isa inda Dr yake sai ko ta faɗa jikin sa tana faɗin *"SWEETY ASMAD?"* Domin ta rike yadda ya ce mata rannan, sai dai ita da sigar tambaya take maganar. _Nafee Ankerh korafi_☹ _*YAR MUTAN RANO*_ [10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* My Wattpad username *ZulayheartRano89* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* _*Wannan page din sadaukarwa ne ga NAFEESA ANKERH (mr korafi) na sadaukar maki da shi ki yi yadda zaki yi dashi idan ma kika ce kar kowa ya karanta wannan ikon ki ne, ni dai kawai a barnin in inke yin typing a time da na samu dama hhhhhhhhh!, Fatan Alhairi a gareki Zulayheart Rano tana yinki sosai*_ 😍😍 *28* Daddaɗar muryarta ne ya ratsa kunnuwansa, musamman yadda ta faɗin sunan sai ya ji ta saukar masa da kasala, dadingushi kuma yadda ta lafe a jikinsa, sai wani feeling wanda tunda yake da Meesha duk fadawa jikinsa da ta keyi, bai taɓa jin irin saba, gyara mata zama ya yi a maimakon da da yake zameta daga jikinsa ya ce "My Meesha ya ki ke?" Bata ce komai ba sai lumshe ido da ta yi, fuskarta har yanzu da murmushi, Meena kam tsayawa ta yi tana kare masu kallo don yadda Dr ya yi ko wanda bai san SO bane ya gansu to zai iya shaida su ɗin masoyan junane, murmushin farin ciki ta yi a ranta tana faɗin "Alhamdulillah! Ashe Dr ma yana son Meesha Amma wannan abu ya min daɗi." Ganin hankalin Dr yana ga Ameesha bai masan da wata Meena ba sai ta ɗan gyaran murya ta ce "Dr ina wuni! An daura aure lafiya?" Wata kunya ce ta kamashi, don da farko yaga lokacin da suka shigo tare da Meena ɗin, amma tunda Meesha ta matsa inda yake sai ya manta da komai ya maida hankalinsa kan Ameesha. "Lafiya lau Meena ya kuke?" "Duk muna lafiya." Ta bashi amsa tana tafiya. Meena tana wucewa ya maida hankali kan Meesha da ke ta daddana wayar Dr ɗin. Ya ce "My Meesha zaki bini gidanmu?" Da sauri ta daga kai alamar "eh!" Murmushi ya yi ya ce "to bari Abba ya dawo, sai na kaiki wajen Nenne ku gaisa." Ya ida maganar dai dai da zuwan Meena, abin motsa baki ta shiryo masa. "Thanks Meena sannu da k'ok'ari." "Your are welcome!" Ta faɗa tana tafiya. Shi Dr tunda Ameesha ta wanzu kusa da shi sai ya nemi yunwa ya rasa, don kasancewarta kusa da shi ba karamin farin ciki ne a gare shi ba. Kallon ta ya yi tana ci gaba da danna wayarsa, cikin zuciyarsa fadi yake "Ina ma ace Ameesha tana cikin tunanin ta aka daura masu aure! Lallai yasan da ace tana tunanin ta, to yau da abin ya fi masa jin dadi, amma a haka ma yana farin ciki, yana godiya ga Allah." Dr ya manta da komai ya dauki lokacin da kacokan ya dankawa Ameesha, sam ya manta a gidan surukai yake, soyayya kawai yake nuna mata irin mai tsayawa arai dinnan, ya yin da ita kuma ta wani lafe a jikinsa kamar wani ya ce zai raba su, bai tashi farga ba sai da ya ji kiran sallar magriba, ɗago da ita ya yi yana faɗin "Meesha time for prayer, zan je masallaci." Da kallo take binsa don bata fahimci inda maganar sa ta dosa ba, ganin zata bata masa lokaci har ya rasa jam'i yasa ya kira Meena yana sanar mata to zo ta tafi da Meesha, babu bata lokaci sai gata, da wayau Dr ya samu ya guje mata. **** Aneesa kam tana shiga dakin wani sabon kuka ta fashe da shi, zuciyarta tana wani irin zafi tana jin kishin Dr fiye da komai, zata iya yin komai don ta hana Dr zama da amaryar sa, yadda take kukan Ni kaina sai da na tausaya mata, don *kishiya ko ta kashin dankali ne babu daɗi* balle wacce aka auro don ku zauna a karkashin inuwar mutum ɗaya. Ganin kukan ba shi ne solution ba sai ta jawo wayarta tare da dannawa Rukky kira, bugu biyu kuwa Rukky ta amsa "Hello k'awata!" Rukky ta faɗa tana gyara wayar a kunnenta. Shiru Aneesa ta yi har sai da Rukky ta yi magana sau uku kana ta iya sauke nannauyan ajiyar zuciya ta ce "K'awata babu lafiya fa!" Zaro ido Rukky ta yi kamar Aneesa tana kallonta baki har yana rawa ta ce "Mai ya faru? Da ga jin muryar ki nasan babu lafiya faɗa min mai ya sameki?" "Dr ya yi aure." Ta yi maganar cikin rawan murya. "Aure! Kan uban... Rukky ta mulmulo wani katon ashar, ke Aneesa anya kuwa kin san me kika faɗa min?" "Ce maki na yi Dr ya yi aure." Wannan karon tare da hawaye maganar ta k'arasa fitowa. "Amma kuwa an yi mara mutunci, yanzu don Allah duk son da kike masa shi ne zai saka maki da kishiya? Lallai na yarda da ake cewa *namiji dan kunama* to ke yanzu wane mataki kika ɗauka?" "Hmmmm! Wane mataki zan ɗauka kuwa, Nenne ce fa da bakinta ta sanar min da maganar, abin takaici ma wai har yau kwana biyu da ɗaurin auren fa, saboda ranin hankali wai bai san an yi masa auren ba, ki ji fa kamar shi ɗin yaro ne da za'a masa dole." Mtsss Rukky ta ja tsaki ta ce "Kina nufin haka zaki zuba masa ido?" "To ya zan yi Rukky? Kuka kawai nake yi, amma mutumin nan haka ya tsallakeni ya yi tafiyar sa wajen ta." "Allah ke Aneesa wani time gaki kamar wayayya ashe ba haka ba ne. To bari ki ji wallahi da Ni ce ke sam bazan damu da lamarin sa ba, balle har in damu da lamarin aurensa, domin kuwa kamar wata dama na samu in yi yadda na ga dama da rayuwata." Rukky ta yi shiru don jin me Aneesa zata faɗa. "In fita harkar Asmad hmmmm! Gaskiya wannan ne da kamar wuya gurguwa da auren nesa, kince na samu dama ban gane nufin ki ba? Wacce irin dama kenan?" Aneesa ta yi tambayar cike da rashin fahimta. "Dallah ke wallahi kina da matsala fa." "Gidan haya ce Ni." Aneesa ta bata amsa cikin jin haushi da maganar Rukky din. "Ki bari zan shigo Kano rana ita yau, wannan maganar tafi gaban yinta a waya, fatan kina ci gaba da shan mugungun nan?" "Suna nan ina sha, duk da dai zubar da ciki bai min rana ba, ina gudun na tsufa da wuri, sai gashi tun ba aje ko ina ba an samu matsala." "Karki damu fa komai zai warware, matuk'ar dai muka bishiyoyi a sannu, ki tattara lamarinsa ki watsar nan da sati biyu, zaki ga canji ita ɗin banza." "Kai wallahi Rukky bana jin zan iya barin ma wata Hamma, domin shi ɗin ba fa irin sauran mazan da kika sani bane, bazan iya barin Hamma." "To na ji karki rabu da shi amma ki ɗauki shawarata ki rika tada masa hankali sam karki raga masa sam." "Tabbas haka zan yi ko dan na kwatowa kaina yanci, zan nuna masa ainahin Aneesa." ta bata amsa cikin tabbatar mata da zata iya aika abin da ya fi haka. ```(Allah ka shirya mu Ubangiji kasa mufi karfin zukatanmu, Allah ka rabamu da aikin danasani, Aneesa kin yi asara tunda dai ke har kullum idan kika samu matsala kawa kike fara sanarwa, duk shawarar da ta baki shi kike dauka wata rana da idonki zaki yi hawaye. Allah ya tsaremu ya tsare mana imanin mu.)``` Karfe takwas da mintina Dr ya koma gida, domin sai da ya biya wajen Hafiz a falo ya samu Aneesa zaune ko sallamar da ya yi kin amsawa ta yi sai hararar da ta rika zabga masa, murmushi kawai ya yi ya wuce bedroom ɗinsa ya canza kaya sannan ya kuma dawowa falon harlau dai tana zaune wajenta ya nufa ya zauna tare da faɗin. "Sannu da gida kanwata." Cikin tsokana ya yi maganar. Turo baki ta yi ta juyar da kai gefe, don haushi yake bata "Allah sarki kanwata fushin ne har yanzu Allah dai ya huci zuciyarki!" Shiru ta masa har lokacin, ko juyo da kai taki yi "Ina dai kara bada hak'uri adaure ayi min koda magana ne kila ko baki sanyi." Cikin sigar lallashi yake maganar. "To ina ruwan biri da gada! Nifa wallahi bana son sanabe kai Hamma kana tunanin akwai sauran abin da zaka faɗa min!" A fusace ta dire maganar. "Yi hakuri yanzu dai kawo karshen ci abinci?" "Bana jin yunwa?" Ta bashi amsa a takaice. "Ban gane mai kike nufi ba, rabon ki fa da abici tun safe baki tsoron wani ciwon ya kamaki?" "Eh! Ta bashi amsa kai tsaye. Gyada kai ya yi ya ce "da da kyau gashi kuma nima ɗin yunwa nake ji ya za'ayi da ni?" Ya yi tambayar yana kashe mata ido ɗaya. Karamin tsaki taja ta ce "kai da ka je gidan amarya kuma mai zai sa kazo kana tambayata abinci?" Cike da tsiwa ta ƙarashe tambayarsa. Mik'ewa ya yi sannan ya saki Murmushi mai birgewa ya ce "Saboda naki na saba ci, amma wallahi yammata kin haɗu fa, aikinki yana kyau ina son irin wannan tsiwar, ya yi maganar yana kai hannu kan bakinta. Kuka Aneesa ta fashe da shi cikin kunar rai da maganar shi, don a nata tunanin ya maidata wata mara lissafi ne, bai san irin mugun kishin sa da take ji bane shi yasa. Amma a fili sai ta ce "Hamma dama don ka riƙa walak'antani ka yi aure? Tun kafin amaryar ta tare har ka soma faɗa min magana, har ka fara nuna baka damu da damuwa ta ba?" Ta yi maganar tana mik'ewa tare da soma tafiya. Cikin zafin nama ya rikota ta faɗa jikinsa gam ya riketa, hannu saya tare da ɗago fuskarta ya ce "Sam ba shi ne dalilin aurena ba Aneesa ki yi hakuri kar kisa wannan a ranki har ya zame Mali matsala, insha Allahu ni ASMAD na dauki maki alk'awari ba zan taɓa walak'antaki ba." Cikin sanyin murya wacce a ke kwantarwa da mutum hankali ya ke maganar. Sun ɓuro baki Aneesa ta yi ba tare da ta ce komai ba. Mu je in haɗa maki te... _*YAR MUTAN RANO*_ [10/8, 8:08 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* My Wattpad username *ZulayheartRano89* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* *29* "Mu je in haɗa maki tea please don bani son ki kwana da yunwa." "A'a bana sha nifa." Cike da shagwaɓa ta k'arasa maganar. "Haba dai My Anee ki dai daure kishi, ko kina son in shiga damuwa ce?" Dan juya kai ta yi alamar a'a. "Ok zauna bani five minutes bana son ki wahalar min da kanki." Ya ida maganar yana zaunarta a kan kujera kamar wata kwai. Har ya kama hanya sai ya dawo ya sa hannunsa cikin nata ya marairaice fuska ya ce "My Anee wai har yanzu ban baki ajiya bane?" "Wane ajiyar?" Ta tambaya tana binsa da kallon rashin fahimta. "To menene na zaro ido kuma? Nufi na fa shi ne har yanzu baki dauke da cikina?" Wani irin faduwar gaba ta ji da jin da tambayar da Dr ya mata, ba karamin firgita ta yi ba, amma sai ta dake ta ce "A'a Hamman har yanzu bani da komai." A tsorace ta bashi amsa. Murmushi ya saki tare da safa gefen fuskarta ya ce "Karki damu my Anee zan kokarta yau din nan in baki ajiya, ina son yara ko nawa kika haifa ina sonsu, su Nenne ma zasu sosu kema kin san irin son da Nennena kewa yara, Please Aneesa ki haifa min yara." Cikin sanyin murya ya gama maganar. "To Hamman Allah ya bamu masu albarka, amma ina tsoron haihuwa akwai wahala." "Babu wani wahala fa, kuma zan yi maki addu'a Allah ya baki mai sauki My Anee." Cikin kwarin gwiwa ya yi mata maganar. Daga kai ta yi alamar "to" fuskarta ɗauke da murmushi. Shi kuma Dr ya nufi kicin ɗin ransa fes yana addu'a Allah ya ba Aneesar sa ciki, burinsa bai wuce ganin Aneesa ta dauke da cikinsa ba. Bangaren Aneesa kuwa, wani farin ciki ne ya rufe ta, musamman yadda Dr ke lallaɓata tabbas ko yanzu tasan tana da wani matsayi a wajen sa, sai dai da wuya ta iya yadda ta zauna da cikinsa domin dai ita fa bata jin zata iya yadda da ciki har ta haihu don bata son ta tsufa da wuri. Duk da ta yadda da halayyar sa da tausayin sa, da wani ne da ko sauraron ta ba zai tsaya ya yi ba, amma Dr mai kyawun hali bai ko duba rashin mutuncin da ta masa ba sai lallashinta yake yi. Ko minti biyar ɗin bai cika ba ya dawo hannunsa dauke da cup din tea da bread, da kansa ya bata har sai da ta koshi, da kasan ya gyara komai na kicin ɗin da falo sannan suka nufi bedroom ɗinsa, wannan rana dai Aneesa a jikin Dr ta kwana, duk da dai yaso ya kwana wajen bincike asbitin da za'a kai Ameesha, amma ganin yadda Aneesa ta rukungume shi yasa ya hakura. Washe gari karfe bakwai Dr ya gama kammala shirin sa, har a lokacin Yar Mulkin tana ta sheka bacci, tunda yasan dama akwai sauran dramar jiya sai kawai ya fita da nufi zai biya gidan Nenne ya yi break. ******* Ko da Dr ya isa asbitin bai samu zama ba don wata mata aka kawo haihuwa ranga ranga don haka cs ya shiga yi mata domin ceto ranta da na abin da ke cikinta. Ya yi nasarar ciro mata yarta lafiyayya katuwa itama matar ta samu lafiya. Ko da ya fito haka ya ci gaba da kula da sauran mutanen da zai duba, bai samu kansa ba sai karfe biyu. Sallah ya yi sannan ya jawo laptop ɗinsa akan ya soma binciken da yake son yi. Yana son ya samu cikakkiyar information akan asbitin da zai kai domin duba lafiyar Ameesha. *AS-SALAM INTERNATIONAL HOSPITAL* shi ne sunan asbitin da Abban Ameesha ya faɗa masa sunan, binciken ya soma cikin nutsuwa, sai ga wayar Hafiz ya shigo, ɗauka ya yi cikin sauri magana suka yi sannan ya katse kiran. Sosai ya duk'ufa neman abin da yake son sani, domin kuwa gaba daya tafiyar tasu bata wuce satin sama. Hamdala ya yi tare da sauke nannauyan ajiyar zuciya alokacin da ya soma karo da abin da yake muradin gani, dan haka sai kawai ya tattara kayansa don zuwa gida domin dai ya gaji kuma yana son ya yi komai a nutse. Gidan Nenne ya nufa domin ɗazun da safe bai wani zauna suka yi hira ba, sai da ya biya sahad store, lokacin da ya yi karo da inda suka soma haɗuwa da Ameesha wani irin yanayi ya tsinci kansa, sai yaga kamar alokacin abin ke faruwa, tausayin Ameesha na halin da ta samu kanta a ciki ya kuma baibaye shi. Jiki a sanyaye ya yo masu shopping ɗin sannan ya ɗauki hanya, mintina ƙalilan ya isa gidan, parking ya yi a parking space sannan ya kwashi ledojin da ya saya guda biyu ya yi ciki da su, ya yin da ya bar wanda zai kai wa Aneesa a mota. Cikin falon ya shiga bakinsa dauke da sallama, Nenne dake zaune a falon ta amsa masa. Dan waro ido ya yi ganin wacce ke zaune kusa da ita, kafin ya gama mamaki har ta iso inda yake, jikinsa ta faɗa kamar kullum tare da ɗago kai tana kallonsa bakinta na faɗin "Sweety Asmad! Yar yaji tsigar jikinsa ya tashi, jin Ameesha a jikinsa a yan kwanakin nan yana sashi shiga wani hali, da kyar ya iya dai dai ta nutsuwarsa sannan ya ce "Princess yaushe kika zo?" Yana maganar ne yana dan janye ta daga jikinsa, don kunyar Nenne ya ji. Da ido ta bishi har suka dan gana ga kujera, zama ya yi ya zaunar ta gefen sa. "Ina yini Nenne!" Asmad ya soma gaidata. "Lafiya lau ya aiki?" "Alhamdulillah! Ya bata amsa yana lumshe ido alamar gajiya. "Nenne wa ya kawo Ameesha?" "Ni ce naje gidan sai ta ce zata biyoni, sai na taho da ita." "Ameesha rigima bata yadda da kowa sai ni, yau kuma ta yadda da Nennena." Ya yi maganar cikin farin ciki. "Aikuwa da ka ganta tun da muka iso take bacci yanzu ba'a daɗe ba ta tashi." "Eh! Ai dama tunda wannan matsalar ta samu a gare ta yawan bacci ne da ita, fatan ta ci abinci?" "Eh! Amma fa da kyar da alama bata son cin abinci kam." "Shi kenan tunda ta ci, dama biyowa na yi mu gaisa daga office nake." "Madallah! Ai ka kyauta, bari a haɗa maka abinci kamar kana tare da yunwa." Nenne ta yi maganar tana mik'ewa. Ameesha kam tana ma'kale jikinsa ko k'wak'waran motsi taki yi, lumshe ido kawai ta yi, a hankali ya juyo da fuskarsa gareta ya ce "Princess! Shiru ta masa sai dan buɗe ido da ta yi. "Tashi kije ki kwanta kamar baki gama bacci ba ko?" Ma'kale kafada ta yi ma'ana bazata jeba. Hannu ya kai saman goshinta don yaga kamar batta jin dadi, aiko sai ya ji zafi zauu da sauri ya janye hannunsa yana furta "Ya ilahi! Meesha baki da lafiya ne? A rude ya ke maganar, dai dai da zuwan Nenne. "Lafiya kuwa?" Nenne ta tambaya. "Zazzaɓi ne ya kama Meesha." Ya bata amsa. "Subhanallah! Zazzaɓi kuma? Sannu Ameesha Allah ya sauwaka, bari na kawo mata magani." Nenne ta dire maganar tana nufa bedroom ɗinta. Dr da kansa ya bata maganin zazzaɓin, tana gama sha ta soma rufe ido zata kwanta, amma Dr ya hanata sai ta yi minti goma bayan dasha sannan ta zame ta kwanta, kallonta ya yi cikin tausayi ya ce "Sorry Meesha insha Allahu cikin kwanakin nan zaki warke ki koma kamar yadda kuke a da." Karshen maganar tasa sai da ta shi faduwar gaba, domin tuni Ameesha a watannin baya. Girgiza kai Nenne ta yi ta ce "Allah ya bada nasara Ubangiji ya sa a yi cikin nasara, hakika tana cikin yanayi a ce mutum ko ciwo yake yi bai san yadda zai faɗa ba! Kai Allah ya bata lafiya." "Ameen." Ya amsa yana jawo ture ɗin abinci. Sosai ya ci abinci ya koshi, yana kammalawa ya, ya zame Ameesha tare da gyara mata kwanciya, yana addu'ar Allah ya bata lafiya cikin zuciyarsa. "Nenne zan wuce gida." "To Allah ya kiyaye hanya, Ubangiji ya yi albarka ka gaida Aneesa." "Amin Nenne zata ji." Ya amsa yana tafiya. Ko da ya isa gida wanka ya faɗa sannan ya sanya kananun kaya, don kamar yanayin na zafi zafi ne, falo ya koma inda Aneesa ke zaune, kusa da ita ya zauna yana fadin "Na shigo banji motsin ki ba?" "Na dan kwanta ne, motsin ka yasa na fito." "Ki daina kwanciyar yamma babu kyau." "Na daina." ta bashi amsa tana shigewa jikinsa. Remort ɗin TV ya dauka yana canza tasha, alokacin shida da minti goma "oh my Anee na manta akwai kayan za'kin da na shigo maki da su suna mota." Gyara kwanciya ta yi ta ce "Anjima ka dauko, ina son Jin dumin mijina." Murmushi mai sauti Dr ya yi yana shafa gashin kanta Sannan ya ce "Da gaskiyar ki yammata." Shi dai Dr biye mata kawai yake amma tunanin sa yana ga Ameesha musamman yadda ya barota yana son ya kira waya amma baya son ɓata ran Aneesa. Haka dai ya biye mata suka yi ta hiransu har aka kira yi magriba sannan Dr ya nufi masallaci, ita ma ta nufi bedroom ɗinta. Da dare suna zaune hira suke cikin kwanciyar hankali wayar Dr ta soma ruri da sauri ya dauka Banji mai aka ce masa ba, kawai cewa ya yi "gani nan zuwa." Daga haka ya kashe wayar. "Bari inje gidan Nenne bazan jima ba zan dawo." Yana maganar ne yana tafiya. Cikin mintina ƙalilan ya isa gidan ko kyakkyawan parking bai yi ba ya kutsa falon. A tsaye ya samu Nenne "Lafiya kuwa?" Ya tambaya. "Da sauki amma dai jikin nata sai a hankali yanzu zazzabin ya dawo sabo." Bai gama jin maganar da take faɗa masa ba ya kutsa bedroom din Nenne, kusan a tare suka shiga shi da Nennen. Can a kan gado ya ga Ameesha kwance rufe da bargo, da sauri ya matsa yana yaye mata bargon, tare da ɗago ta yama manta da wata Nenne rungu... ```don Allah Fans KU yi hakuri da rashin ganin post kullum hakan yana faruwa dalilin bana samun isasshen lokaci, yanzu bana jin dadi ina barar addu'ar ku ``` _*YAR MUTAN RANO*_ [10/8, 8:08 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* My Wattpad username *ZulayheartRano89* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* ``` Wannan page din kyauta na baki RUFAIDA OMAR fatan Alhairi a gareki da zuri'arki baki daya, Zulayheart Rano tana yinki sosai Allah ya kara maki basira da kaifin k'wak'walwa na fasihiyar marubuciya mai baiwar fikira da Nagarta``` *30* Tsam ya rungume ta cikin jikinsa, yana kallon yadda take fusgar numfashi da kyar! Duk tausayinta ya cika shi. ɗago da kai ya yi ya ce "Nenne bani ruwa da towel a goge mata jiki zafin zai ragu." Yana maganar ne yana kuma tallabar ta. "To." Nenne ta amsa tare da fita. Cikin sakan ashirin har ta kawo masa ruwan, koda ta ba shi fita ta yi don ta ba shi waje. Yana ganin Nenne ta fita sai ya yi saurin kwantar da ita, ya zame rigar ta cikin nutsuwa yake bin jikinta da jikakken towel din yana manna mata, jikin dai har lokacin da zafi amma numfashi ya daidai ta. Rasa yadda zai yi da ita ya yi, domin shi a wannan lokaci ya manta shi fa Dr ne, sai zuwa can wata basira ta fado masa cikin sauri ya kuma rungumota ya cusata a jikinsa ya soma murza mata baya ahankali, ya yi kusan minti sha biyar kafin ya ji zafin jikin ya koma daidai. A lokacin kuwa har bacci ya yi gaba da Ameesha, a hankali ya zame jikinsa ya gyara mata kwanciya. Fita ya yi ya dauko first aid kit ɗinsa, allura ya haɗa ya yi mata. Ya zauna a gefenta yana kallonta fuskarsa ɗauke da damuwa, sosai yake jin Ameesha a zuciyarsa baya k'aunar koda 'kuda ne ya sauka jikinta balle aje ga batun ciwo. "Sannu Asmad har ta samu bacci kenan?" Muryar Nenne ya ji. "Eh! Ta samu yanzu." Dr ya bata amsa. "To ya kamata dai ka tafi gida, domin dare yana kara yi fa, yanzu tara harda rabi." Ta dire maganar tana kallonsa. Jikinsa sam babu kwari ya mike yana faɗin, "To Nenne sai da safe duk yadda ake ciki da safe sai ki sanar min, duk da nayi mata allurar saukar da zazzabi." Cikin sanyin murya ya yi maganar. "Allah ya kaimu, insha Allahu za ta samu sauki zuwa safen ma." Cikin karfafa masa gwiwa ta yi maganar. Fita Dr. ya yi badan ya so tafiyar ba. Da tunanin Ameesha ya isa gida, ko da ya shiga cikin falon babu kowa don haka bai tsaya ba sai ya nufi bedroom ɗinta. Kwance ya same ta kallo ɗaya zaka mata kasan ba bacci take ba, zama ya yi kusa da ita yana faɗin "Madam har kin kwanta?" Wani mugun kallo ta aika masa da shi tare da juya masa baya, mamaki ya kama Dr. ganin dai lafiya lau suka rabu ɗazun amma yanzu har ta ɗauki fushi "Wai lafiyar ki kuwa?" Ya kuma mata magana. Tsaki ta ja mai karfi ta ce, "Ina ruwan ka da lafiyata? Ba wajen amaryarka ka je ba? Ita wato ka damu da damuwarta? Amma ni da yake baka kaunata baka damu da halin da zan shiga ba, ai shi yasa ka yi tafiyar ka sai yanzu kake dawowa anya ma kuwa Hamman kana tsoron Allah?" Murmushi mai ciwo ya yi ya ce, "Ki yi hakuri duk yadda kike tunani ba haka bane, amma ki yi hakuri." Daga haka yasa kai ya fita. Domin dai zafin karshen maganar Aneesa basu da maraba da saukar tafasasshen ruwa a jikinsa, ya barta mata dakin ne don karda zuciya ta sashi aikata mummunan aiki. Amma tabbas maganar ta ta bata ransa, duk iya kokarin da yake akanta bata gani, yana lallaɓata ne ba dan komai ba sai su Nenne amma yau har ta iya bude baki tana fada mishi *Yana tsoron Allah kuwa*. Ajiyar zuciya ya sauke a fili ya furta, "Aneesa kenan kinci daraja ɗaya amma karki bari laifin ki ya kara girma, domin dai akwai babban laifin da kika aikata min mafi muni amma na barki ne har zuwa lokacin da zan baki mamaki. Dafe kai ya yi da ya tuna lokacin da ya yi arba da Aneesa ta zubar masa da cikinsa, tsab! Yasan tana da ciki amma sai bai nuna mata ba, shi ne da ta tashi ta zubar da shi zai nuna mata bata da wayyo rakata kawai ya ke. Tashi ya yi zuciyarsa sam babu daɗi ya nufi toilet, ruwan sanyi ya sakarwa kansa, ya yi kusan minti sha biyar kafin ya fito, sallaya ya shimfiɗa domin dai ya dauro alwalarsa. Tada sallah ya yi, sai da ya gabatar da ishsha a ya yi shafa'i da wuturi, addu'oi sosai ya yi na nemarwa Ameesha lafiya kafin daga bisani ya tashi tare da cire jallabiyar jikinsa ya jawo laptop ɗinsa don ya ci gaba da binciken da ya soma. Bar mu waiwayi NAJEEB da amaryar sa. Kasancewar yau week end, Najeeb ne zaune a k'aton falon gidansa, daga shi sai singileti da gajeren wando, hannunsa cup din fresh milk ne yake kurba. Rufaida ce ta fito cikin kyakkyawar shirinta na atamfa riga da siket sosai kayan suka mata kyau, fuskarta ta sha kwalliya, jikinta sai fitar da sansanyar kamshi yake. Fuskarta ɗauke da murmushi mai birgewa ta nufi Najeeb ɗin rankwafawa ta yi dai dai fuskarsa ta ce"Ranka ya dade barka da hutawa." Cikin sanyin murya ta yi maganar. Ɗago kansa ya yi cikin nashi murmushi ya ce "Barkammu dai gimbiya, kin yi kyau" "Na gode! Ta faɗa tana zama a kasan carfet tare da lankwashe ƙafafunta. "Kamar kina son yin magana ko?" Ya dire maganar idonsa a kanta Murmushi dai ta kuma yi tana wasa da yatsun hannunta ba tare da ta ce komai ba. "Rufaida! Ya ambaci sunanta cikin wata irin murya. Saurin ɗago da kai ta yi jin yadda ya kira sunan. "Na'am." Shi ne abin da ta iya faɗa. "Me yasa kike min haka bayan kinsan mun zama daya Ni mijinki ne, ke matata ce, ki daina ɓoye min komai duk abin da kike bukata ki sanar min insha Allahu zan yi kokarin yi maki." Gyada kai ta yi ta ce "Babu komai fa Ranka ya daɗe." "No! Rufaida tell me your problem." "Sadda kai ta yi ta ce dama cewa zan yi ka kaini gidanmu ina son ganin Mamana." Cikin kunya ta k'arasa maganar, don sosai take son ganin family ɗinta tunda aka kawota babu wanda ya zo. "Oh! Baby dama don wannan ne kika kasa faɗa min? To bari na yi wanka sai mu je har gidan Mummy." Cikin sakin fuska ya ke maganar. Wani farin ciki ne ya rufe Rufaida har bata san time ɗin da ta rungume Najeeb ba, tana zuba masa godiya cikin tsantsan jin dadi. "Na gode *hubby*." Ta faɗa tana kara hugging ɗinsa. "You are welcome my baby, Amma fa sunan can da kina ambata ya min daɗi ki rika kirana da shi ina son sunan." Kunya ce ta kama Rufaida, da sauri ta sake shi ta na nemar hanyar guduwa, har ta kusa shiga koriɗo wanda zai sadaka da ɗakunan baccinsu ya ce "Baby ki haɗa min ruwan wanka gani nan zuwa." "To." Ta amsa tare da shigewa. Murmushi ya yi tare da girgiza kai, cikin farin ciki da samun Rufaida matsayin mata sam ita bata fushi, yana alfahari samun ta matsayin mata, shi yasa tun da Mummy ta yi masa bayanin aurensa da Rufaida, komai bai ji ba na takaici ko da nasani, domin dai Rufaida ma masoyiyar sa ce, yasan ya so Ameesha so na gaskiya amma tunda Allah baiyi nufin ita matarsa ba ce ya yadda da kaddara, ya kuma rungumi matarsa yana addu'ar dorewar zaman lafiya a aurensa. Da taimakon Rufaida ya kammala shiryawa, cikin wasu riga da wando wanda suka amshi jikinsa, sansanyar kamshi turare ke fita daga ko wane lungu na jikinsa, keys ɗin mota ya ɗauka yana faɗin "Madam mu je ko?" Murmushi ta saki tare da daga kai alamar "to." "Ka yi kyau hubby." Cikin muryarta mai sanyi ta yi maganar. "Na gode." Shi ne abin da Najeeb ya faɗa yana ci gaba da tafiya. Sai da suka biya wani babban kanti ya sayawa iyayen Rufaida tsaraba wacce zata kai masu, domin ko ya basu kuɗi ba amsa zasu yi ba, shi yasa ya sai masu kawai, tare suka shiga bayan ya gaida da Mamanta sai ya koma mota inda zai jirata, sai Maman ta yi farin ciki da ganin yartata don da gani hankalinta a kwance yake duba da irin kyaun da ta yi. Bata wani jima sosai ba ta yi masu sallama, zata ta fi "Hajiya ki yiwa mijinki godiya, mun gode Allah ya saka da Alhairi, don Allah Hajiya ki kula da auranki duk abin da zaki gani ki rika hakuri kin ji ko?"Maman Rufaida ke mata nusiha, da yake bata faɗan sunan Rufaida sai dai ta ce mata Hajiya, don sunan k'anwar mahaifiyar ta aka sanya mata. "Insha Allahu Mama zan yi yadda kika ce, mu dai a ci gaba da yi mana addu'a." "Addu'a kam ana yi sai dai a kara kaimi, Allah ya kai ku gida lafiya." Da haka suka yi sallama, ji ta yi kamar kar ta tafi, a mota ta same shi yana zaune yana latsa wayarsa kamshin turare ta ya sanar shi isowarta. Ɗago da kai ya yi tare da aje wayar ya ce "Har kin fito?" Ya yi tambayar idonsa a kan ta. "Eh! Ta bashi amsa tana bude kofar motar. "Mama ta ce ayi maka godiya." A hankali ta yi furucin. "No ba sai sun gode min ba domin suma iyayena ne." Cikin kulawa ya bata amsa. Murmushi ta yi don ta ji dadin furucin sa, da haka suka isa gidan Mummy, sosai Mummy ta ji dadin zuwan Rufaida sai nan nan take da ita, tana son Rufaida har cikin ranta domin Allah ya yota da nutsuwa ga hankali uwa uba kuma kunya. Nan Najeeb ya barta akan bayan magriba zai zo ya dauketa su koma gida. *** Tashi ya yi cikin sauri tare da kallon agogon da ke manne jikin bangon daki "subhanallah! Ya furta a fili ganin har bakwai da minti sha biyar, ya makara sosai sakamakon kwanan da ya yi wajen binciken asbitin da zai kai Ameesha, tun tun sha biyu yake aikin bai samu kansa ba sai karfe huɗu, bayan ya kammala alwala ya dauro ya soma gabatar da sallah sai da ya yi asbah kafin bacci ya dauke shi, da azama ya isa toilet din shaf shaf ya yi wankan ya fito ya soma shiryawa. Bai jima ba ya kammala shirinsa, falon ya fita hannunsa dauke da wayoyinsa, babu kowa a falon da alama ma dai matar gidan bata tashi ba, don haka sai ya nufi bedroom ɗinta yana tura kofar ta buɗe can ya hangota cikin bargo tana sharar bacci ta, takawa ya yi har bakin gadon ya zauna tare da ambaton sunan ta "Aneesa! Ya yi maganar yana dana buga kafadarta ta, ido ta buɗe cike da mayen bacci ta ba ta ce komai ba sai kallonsa da ta yi. "Kin yi sallah kuwa?" Ya tambaye ta tare da tsare ta da ido. Doguwar Hamma ta yi tare da girgiza kai alamar a'a, "ok tashi ki yi gari ya waye ras har bakwai da rabi, zuwa yanzu ya kamata ki gyara halinki ki daina wasa da ibadanki." Harara ta bi shi da ita don haushi yake bata, sam ta tsani ko da ganinsa tashi ta yi bata ko ce masa komai ba, yana zaune har ta fito sannan ya tashi tsaye yana faɗin "To nikam na tafi office sai na dawo." Bata ce masa kala ba ta tayar da sallar ta. Girgiza kai ya yi tare da fita, cikin zuciyarsa yana mamakin halin Aneesa. Duk da yasan ya yi latti amma hakan bai hana shi biyawa gidan Nenne ba, domin duba lafiyar Ameesha da jiki, sallama ya yi cikin falon ya ji shiru, a zuciyarsa yana tunanin kila suna ɗakin Nenne don haka sai ya nufi haryar motsin da ya ji a dining ne ya sashi lekawa zaune ya ganta a dining din tana juya cokali cikin cup Murmushi ya saki yana faɗin " *Heartbeat* kina nan ke kaɗai?" Ya ida maganar yana zama a daya daga kujeran dining din. Itama murmushi ta yi ta ce "Sweety Asmad! Shi ne kaɗai kalmar da Ameesha ke iya faɗa. Siririn dariya ya yi yana kallonta cikin wani yanayi mai wuyar fassara ya buɗe baki zai yi magana kenan ya ji muryar Nenne "Maganar wa nakeji kamar ta Asmad?" Nenne ta yi maganar tana zama a dining din. "Wallahi ni ne Nennena, na biyo duba jikin Ameesha ne." "Ah! Ai jiki ya yi sauki ka ganta nan." Ta dire maganar tana kallon Ameesha da har yanzu take juya tea din. Mamaki ya kama Nenne ta ce "A'a Ameesha wa ya haɗa maki tea din?" "Au bake kika haɗa mata ba? Nima nazo naga tana juya abinda, madallah! Ashe Heartbeat ta Fara hada shayi da kanta." Cikin murmushi ya ida maganar. "A'a bani na haɗa mata ba don na shiga ciki, ai haka ake so sauki ya rika samuwa." Nenne tana maganar ne tana haɗawa Dr tea, a lokacin kuma Ameesha ta daga kofin tea din tare da kaiwa bakinta da sauri ta furzo shi tare da bata rai, da kallo suka bita da mamaki, ba su gama mamakin ba sai suka ga ta mika hannu tare da dauko cup din da Nenne ta haɗawa Dr tea ta kai... _*YAR MUTAN RANO*_ [10/8, 8:14 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* My Wattpad username *ZulayheartRano89* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* ``` wannan page din kyauta na baki ZEETY MUM HANAN ki yi yadda zaki da shi domin jin dadin ki, ki daɗe ki yi karko uwargida sarautar mata, Allah ya kara maki lafiya da basira Ubangiji ya raya mana su Hanan rayuwa mai inganci ``` _*Hazika kuma Hamshaqiya fasihiya duk ke kaɗai kika amsa wannan sunan BESTYNA Khadija s Muhammad ke ɗin ta daban ce, fadan matsayin a wajena ba zai yiwu ba, sai ina kara tabbatar maki da Ina jinki har cikin jinina, Allah ya k'ara tsare min ke a duk inda kike amin ina jin dadin littafin LAFIN WA? Wannan Nagartacciyar marubuciya kina ɓarar da ilimi a cikin sa Allah ya kara basira*_ *31* Bakinta da ta kurba sai ta saki murmushi tana kallon Dr, su dai mamaki kawai suke na Ameesha sai zuwa can Dr ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Heartbeat bani tea na in sha sauri nake yi." Ko kallonsa bata yi ba sai ci gaba da shan kayanta ta yi. Murmushi Nenne ta yi ta ce "kai ka dauki nata kasha tunda ta dauki naka." Ɗauka ya yi yana faɗin "wai Nenne Ameesha ta haɗa tea da kanta amma sai ta dauke wanda kika haɗa min, bayan nawa bai kai kaurin nata ba." Ya ida maganar ya kai cup bakinsa, da sauri ya zubar da wanda ya kurba tare da aje cup din. Kallonsa Nenne ta yi ta ce " Lafiya kuwa menene ka zubo da shi? "Nenne tea din fa ɗaci yake saboda tsabar sugar da ta cika." Cikin dariya da mamakin yadda Ameesha ta iya wayon haka ya ida maganar. "Au ho! Wato shi yasa ta kasa sha kenan? Ikon Allah wannan abu da mamaki fa." "Yo ai bazai sha wu ba kam, hakan da ta yi ba karamin daɗi ya yi ba, domin in sha Allahu da alamar nasara." "To Allah ya taimaka, bari na hada maka wani yaushe ne tafiyar taku?" "Jibi ne zamu tafi, kawai Nenne ki bar shi idan na tsaya sha zan yi latti." "Allah ya kaimu, fatan ka sanar da Aneesa?" "A'a ban sanar mata ba." "Sam haka bai kamata ba, idan ka koma ka sanar mata, Asmad ka kasance mai adalci tsakanin matanka fa." "In sha Allahu zan kasance Nenne, walllahi abin ne ya ɗan shige min, amma yau da na koma zan sanar da ita." Ya dire maganar yana k'ok'arin tafiya. "Allah ya baka iko amma ka dai daure ka sha sai ka ji dadin tafiyar." Sam Dr ba ya son musu da Nennensa shi yasa ya zauna. Zuwa wannan lokacin tuni har Ameesha ta shanye tea din Dr har ta dire cup. Nenne tana gama haɗa masa ta mike zata bar dining Dr ya ce "Nenne inaga kamar fa gara ki sanarwa da Aneesa maganar tafiyar mu zai fi." Ya kai karshen maganar yana kurɓar tea. Komawa Nenne ta yi ta zauna tare da zubawa Asmad ido, kamar tana son gano wani abu, zuwa can kuma sai ta girgiza kai ta ce "Me ya sa ni zan sanar mata, kai ba zaka iya bane?" "No! Ba wai bazan iya faɗa mata bane, kawai ina ga idan kika sanar mata zaifi." "To shi kenan, zuwa anjima zan sa direba ya daukota sai in sanar mata, amma anya kuwa kuna zaman lafiya da Aneesa?" "Me kika gani Nenne? lafiya lau muke zaman mu fa." Dr ya bata amsa. "To ai shi kenan." Ta yi maganar tana mik'ewa, ta fita daga dining room din. Shi kuma Dr yana ganin Nenne ta basu waje, sai ya kai duban sa kan Ameesha ya ce "Allah ke Heartbeat ko wato kin iya mugunta, shi ne kika dauke nawa bayan kin cikawa naki sugar ko?" Dan murmushi ta yi tare da kallonsa, zuwa can kuma sai ta fara hamma alamar bacci "Oh! Lallai ma Heartbeat wato bacci ma za ki yi ko?" Ita dai Ameesha bata ce masa komai ba, duk maganar da yake, sai ma k'ok'arin tashi don taje ta kwanta take yi, dakatar da ita ya yi ta hanyar rike mata hannu daya, bai sakar mata ba har sai da ya kammala break kafin ya mike Yana rike da hannunta har cikin bed room din Nenne, kwantar da ita ya yi yana faɗin "A tashi lafiya Yar Ummi." Lumshe ido ta yi batare da ta yi magana ba. Yana fita falo ya samu Nenne zaune tana karatun littattafin hisnul-muslim, dubanta ta kai ga Asmad ta ce "A'a Asmad dama baka tafi ba?" "Eh! Dama Ameesha ce take jin bacci shi ne na kai ta bedroom, na barta har ta fara baccin." Ya bata amsa yana sosa kai. Harara ta zabga masa ta ce "Ya yi kyau, amma bana son wannan shashancin." "Yi hakuri Nennena." Dr ya yi magana cikin shagwaɓa. Murmushi ta yi ta ce "To na hak'ura Allah ya taimaka." "Amin." Dr ya amsa daga haka ya fita zuciyarsa fes, ko da ya isa office aiki sosai ya yi, da zai koma gida bai biya gidan Nenne ba domin dai yasan matukar ya je ba zai je wajen Aneesa a kan lokaci ba. Don haka sai kawai ya wuce gida. A falo ya samu Gimbiyar kwance da waya a hannunta, ko sallamar da ya yi bata amsa ba, bai nuna ya ji haushi ba domin so yake su yi magana ta fahimta, don haka sai ya isa inda take kwanciya ya zauna yana faɗin "Wai Aneesa har yanzu fushin ne?" Ko ɗago kai ta kalleshi ba ta yi, sai ma ɗan matsar da jikinta da ta yi, tana taɓe baki, murmushi ya yi tare da jawota jikinsa yana fadin "Gaskiya na gaji da fushin nan zuwa yanzu ya kamata a sarara min." "Wa yake fushi da kai?" Ta yi tambayar kamar bata fahimci inda ya dosa ba " Ke ce kike fushi da ni Aneesa." "A kan me zan yi fushi da kai?" Ta yi maganar cike da rainin hankali. "Ok shi kenan tunda baki fushi da ni, yanzu dai tashi mu yi wata magana dake mai muhimmanci." "Kunne ke jin magana don haka ina jinka." "A'a kinga ki tashi kawai kamar yadda na bukata, don ba maganar wasa za mu yi ba." Cikin daure fuska ya yi maganar. "Mtsss" taja ƙaramin tsaki a zuciyarta tare da tashi ta zauna "ina jinka." Ta faɗa cikin karamin murya. Ya bude baku zai yi magana ta yi saurin katse shi "Dazun Nenne take sanar min da tafiyar ka Egypt, da gaske tafiyar zaka yi ka barni?" Ta kai karshen maganar tana gyara zama, sam fuska babu walwala. "Eh! In sha Allah jibi ne tafiyar." "Ni kuma a ina za'a barni kenan? Ko tare zamu tafi? Tsare shi ta yi da idanunta. "A'a ita ɗaya zamu tafi, ita ma ɗin don lalura ce, in sha Allah zan rika dawowa ganinki har lokacin da zata samu sauki. "Asmad kenan! Allah ya bata lafiya, amma dai a rika yin adalci." Zuciyarta wani irin zafi da raɗaɗi take yi. "Kar ki damu my Anee zan rika yi." Cikin farin cikin yadda abin ya tsaya a haka yake yi, tabbas yasan badan Nenne ta faɗa mata maganar da kanta ba, lallai da ba karamin daru Aneesa zata masa ba. "Sai ki yi min list ɗin duk wani abu da zaki buk'ata." "Hmm! Sai anjima zan yi, ina godiya." A takaice ta bashi amsa. "Ok ari na ɗan watsa ruwa zafi nake ji, sai na fita na samo mana abin da zamu ci nasan yanzu hutu kike yi babu ruwan ki da girki." Cikin zolaya ya karasa maganar yana tafiya. "Hmmmm! Shi ne kaɗai abin da Aneesa ta iya faɗa, lokacin da taga Dr ya shige dakinsa, wani irin takaici ne ya rufe ta. "Lallai Asmad kenan zai kai matarsa Egypt! Duk da dai rashin lafiya ne, amma ai sam bai kyauta min ba, har yaushe ni da ya fara aura ko Abuja bai taɓa zuwa da ni ba, amma ita zai tafi har Egypt Wai don neman lafiyar ta, ko wane irin ciwo ke damunta oho! To koma dai hutun amarci zasu je, no! Ta ba kanta amsa dai dai da zubowar hawayen da suka cika idonta. Kuka sosai take yi, a haka har Dr ya fito ya sameta, bai yi mamakin yadda yaga tana hawaye ba, don sa rai ya san ta da bakin kishi, babu mamaki akan maganar tafiyarsa take kuka. Lallashinta ya yi da kyar ta yi shiru, sannan ya shiga kicin da kansa ya dafa masu indomie, ya juyo a plet sannan ya fito falon, ko da ya kawo cewa ta yi bata ci sai da kyar ya rarrasheta ta yadda zata ci, a baki ya rika bata har ta koshi. "Madam har kin koshi kenan?" "Eh! Ta bashi amsa a takaice. "Ok sai bacci ko?" "Uhmmm." Ta ce tana mik'ewa "To Allah ya bamu Alhairi." Cikin kosawa da maganar ta ce "Amin" tare da tafiya. Da kallo ya bi bayanta har ta shige,, sannan ya sauke nannauyan ajiyar zuciya, plet ya dauka yafara cin abincin don sosai ya ke jin yunwa, tas ya cinye ya kora da fresh milk, kallo ya kunna don yana son kallon news, karfe goma ya kashe komai na falon sannan ya nufi makwancinsa, sai da ya leka Aneesa ya ga ta yi bacci kafin ya wuce. Yana shiga dakin ya yi shirin kwanciya, yana addu'an samun nasarar tafiyar su. A bangaren Aneesa kuwa tana kallon lokacin da Dr ya shiga ɗakinta, kuka take yi amma jin shigowar sa , sai ta yi kamar tana bacci, don bata bukatar ganinsa so take ta yi kuka sosai don ta samu sassauci a zuciyarta, tana jin fitarsa ta kuma sakin wani sabon kukan kwana ta yi tana tsiyayar da hawaye, da ta tuno da maganar tafiyarsa sai hankalinta ya kara tashi, bata taɓa sanin tana wa Dr mahaukacin so ba sai yau, kishinsa ta ke fiye da tunani. Tunda ya dawo sallar asuba bacci ya koma bai farka ba sai bakwai saura, sai da ya gama shiryawa ya fita falo bai samu Madam a falo sai ya shiga bedroom, kwance ya sameta jikinta rufe ruf da bargo bacci take yi, kallo ɗaya zaka mata kasan ba baccin jin dadi bane. Girgiza kai ya yi tare da soma tashin ta a hankali har ta bude ido. "Tashi ki yi sallah Please." Sai da ta yi doguwar mik'a kana ta sauka cikin daure fuska kamar wacce bata taɓa dariya, alwala ta yo sannan ta tayar da sallar har ta kammala yana zaune, tana idarwa ta koma kan gado tare da jan blanket. "Barka da safiya Madam, tunda ni dai bani da matsayin da za'a gaisar da ni." "Sorry wallahi bacci ne a idona, ina kwana an tashi lafiya?" Ta ida maganar tata tana lumshe ido, domin dai sosai take jin bacci don sai kusan karfe huɗu da rabi kafin bacci ɓarawo ya dauketa. "Lafiya lau." Shi abin da ya iya faɗa, cikin takaici sosai yake mamakin halin Aneesa, wani time sai ta zama kamar mai tambotsai, haka dai ya fita jiki a saɓule ga wata irin yunwa da yake ji shi yanzu har kunyar zuwa gidan Nenne ya ke tunda har ta soma zargin basu zaman lafiya da Aneesa. Badon ransa ya so ba ya dafa shayi zalla da bread da shi ya yi break ya fita, office ya wuce kai tsaye, bayan ya kammala da duba marasa lafiya sai ya jawo wayarsa ya kira Hafiz bai fi minti goma ba sai ga shi ya iso asbitin. Bayan sun gaisa Dr ya gyara zama ya ce "Gobe ne fa tafiya." "Eh! Ai jiya bayan na tashi aiki sai da na biya gidan Nenne ita ke sanar min, ina maku addu'ar samun nasara da lafiya." "Muna godiya da addu'a, ai gaskiya ina gano nasara domin Dr Ansar ya yi matukar k'ok'ari, tun daga information na asbitin da ya bani na ji na yadda, sannan na kuma bincike sosai asbitin *AS-SALAM INTERNATIONAL HOSPITAL* ya kware wajen iya kula da masu ciwo." "Ai wannan asbitin ya fi haka Allah dai ya bada nasara, yanzu gobe ku kaɗai zaku tafi kenan?" "Eh! Sai su Nenne da su Abba su biyo bayanmu." "Hakan zai fi kyau, nima in sha Allah idan aka dan kwana biyu zan zo." "Allah ya kawo ka lafiya" Hira sosai suka yi har wajen karfe uku kana suka bar office don zuwa gidan Abban Ameesha. Bayan sun gaisa ne Abba ke kara tambayarsa yadda tafiyar zata kasance, nan dai suka tattauna da Abban yana ta masu fatan alheri da samun nasara daga karshe ya yi sallama da Abba akan sai gobe. Yau ta kasance ranar asabar kuma ranar ne da su Dr zasu tafi Egypt tun wuri ya tashi domin dai jirgin karfe takwas zasu bi ya yi wanka tsab ya shirya cikin wasu kananan kaya wanda suka matukar amshi jikinsa, sai baza kamshin turare ya ke yi falo ya fita hannunsa dauke da karamin jakar da ya shirya kayansa kai tsaye bed in Aneesa ya nufa da sallama. A zaune ya sameta ta zuba uban tagumi, cikin sauri ya matsa inda take ya na faɗin "Lafiya kuwa?" "Lafiya lau mai ka gani?" "Naga kin haɗa kai da gwiwa ne alamar damuwa zalla." Murmushi ta kakalo ta ce "Babu komai fa Hamman, har ka shirya kenan?" "Eh! Na shirya ki yi mana addu'a." Cikin murmushi ya yi maganar. "Allah ya tsare hanya." "Amin ya amsa yana kallon agogonsa tare da tafiya. "Hamman..." Sai kuma ta yi shiru. Dawowa ya yi ya zauna kusa da ita yana faɗin "Menene Aneesa fadi maganar ki ina ji." "Don Allah ka barni in tafi Adamawa." Murya na rawa ta dire maganar. Girgiza kai ya yi ya ce "Ba zai kije Adamawa ba, amma dauko gyalen ki in kaiki gidan Nenne." "Please Hamman." "Bana son musu ki yi yadda na ce kawai." Haka nan ta tashi badon ranta ya so ba, gyale ta dauka suka fita. _*YAR MUTAN RANO*_ [10/8, 8:15 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* My Wattpad username *ZulayheartRano89* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* ```Sadaukarwa ga AMRAH AUWAL MASHI (Princess Amrah) na sadaukar maki da wannan page din kyauta domin jin dadin ki, Allah ya kara basira da kaifin k'wak'walwa, ki ci gaba da suburbuɗo mana AMRAH NAKE SO muna jin dadin buk ɗin sosai, ina gaida RAZ``` _*I hearttttt You My Besty irin har abada dinnan.*_💞 *32* Tsayuwar motarsu ta yi dai dai da zuwan motarsu Abban Ameesha, cikin sauri Dr ya faka motar ya fito, kai tsaye wajen su Abba ya nufa, cikin fara'a Abba ya fito tare da mikawa Dr hannu sukai musabaha, ya yi da Dr ya tsuguna yana gaida Ummi da Abba cikin kunya. Wasu motar ce suka kuma shigowa, yaya Jaheed ne da matarsa sai ta ya Abdul da Meena, duk fitowa suka yi suka nufi inda Alhaji Taheer ya ke. Sai a lokacin Haydar ya fito daga cikin motar su Abba, gaisuwar mutunci suka yi da Dr sannan suka kama hanyar falon, wanda tuni Aneesa ta shiga tana zaune a falon tare da Nenne suna dan taɓa hira. Sallamar Dr ce ta katse masu hiran "Nenne ga su Abban Ameesha sun iso fa." Dr ya yi maganar bayan sun gama gaisawa. "Je ka dakin Bobbo ka sanar masa, bari na shigo da su Hajiya Halimar." Nenne ta ida maganar tana mik'ewa. Daret Dr bed room na Bobbo ya shiga ya sanar masa da zuwan su Alhajin, a tare suka fito fara'a sosai Bobbo ya saki suka gaggaisa da Alhaji Taheer, don tuni sun shiga falon. "Nenne ina Meesha ne?" Meena ce ta yi tambayar don tun shigowar ta bata ganta ba. "Twin's din Ummi har kin gaza hakuri kenan? To tashi tana cikin bedroom." Cikin dariya Nenne ta yi maganar. Ai tun kafin Nenne ta rufe baki har Meena ta nufi bedroom din. Su dinma dariya suka yi, suna jin dadin yadda Meena da Meesha suke rayuwa, sam babu hassada balle bakin ciki. Dr kallon agogon hannunsa ya yi yana faɗin "Abba time yana tafiya fa, 7:45 AM yanzu kuma 8:15 AM jirgin zai tashi." "To mai muke jira? Ya ci gaba "ai inaga gara mu tashi mu tafi kar mu makara." Abba ya gama maganar dai dai da fitowar Meena da Meesha. Murmushi Abba ya saki ganin Ameesha. Ita kam wajen Nenne ta nufa ta zauna, sai kallon su Ummi take yi, ido Aneesa ta zubawa Ameesha tana kallon kyau irin na Ameesha sai yau ta yi mata kollon sosai. Sanye take da wani hadaddiyar doguwar riga kalar pink da white, fuskarta ta sha kwalliya daga inda Aneesa ke zaune tana jiyo sansanyar kamshi turaren da ke jikin Ameesha a jiyar zuciya ta sauke a ranta ta ce "Dole Hamman ka riƙa yin rawan kai." Shi kuwa Dr tunda yaga Ameesha ta fito sai ya maida hankalinsa kacokan kan Ameesha yana kallon irin kyau da ta yi, yana jinjina k'ok'ari irin na Meena don yasan aikinta ne wannan. Sosai ya shagala har ya manta a wajen da yake sai da ya ji muryar Alhaji Taheer yana faɗin "Dr ka tashi mana lokaci fa yana tafiya." "To." Dr ya faɗa yana mik'ewa. Gaba daya suma suka mik'e, daret wajen motoci suka nufa kusan duk bakin su dauke da addu'ar samun nasara, kai tsaye babban filin saukar jirgin saman suka ɗauki hanya, cikin mintina ƙalilan suka isa airport. Ba su wani daɗe ba, suka gama duk wani shiga da fita har komai ya kammala, sai jiran a fara kiran fasinjoji Dr ne ya dubi Abba ya ce "Abba zamu tafi a yi mana addu'an samun nasara." Cikin ladabi ya yi maganar. "Allah ya taimaka Dr in sha Allah za'a samu nasara, nan da kwana huɗu zamu zo, Allah dai yasa a yi cikin a." Cikin kwantar da hankali Abba ya yi maganar. "Allah ya kawo ku lafiya Abba." Dr ya yi maganar dai dai lokacin da aka fara kiran fasinjoji. Addu'a kawai su Ummi suke yi har da hawaye, musamman yadda ita Ameesha bata wani damu da abin da ake ba, ita dai tunda taga da Dr zasu tafi sai ko tada hankali bata yi ba, Dr yana daga masu hannu har suka shiga cikin jirgin. Meena wani sabon kukan ta fashe da shi a fili take faɗin "Allah kaba Ameesha lafiya, Ubangiji ka yaye mata wannan lalura." Ta ida maganar wasu hawaye suna zubowa. "Amin." Su Ummi suka amsa, suna wajen har sai da jirgin ya tashi tukun suka dauki hanyar gida. Dr kuwa ko da suka shiga jirgin zama suka yi, ya dauko wani littafi yana karantawa, jingine Ameesha take da jikinsa har bacci ya kwashe ta, ko da yaga haka sai ya gyara mata kwanciyar, yana shafa sumar kanta wanda yasha gyara sosai Meena ta gyara mata sumar sai kyalli take, tafiya ce mai tsawo suka yi kafin suka isa Egypt. Lokacin da jirgin ya sauka a *INTERNATIONAL AIRPORT CAIRO* Dr Asmad kallon agogon hannunsa ya yi yaga karfe biyu saura mintina goma sha biyar, akalla sunyi awa biyar da minti ashirin da biyu suna tafiya, yana rike da hannunta suka fito daga jirgin motar da zata ɗauke su a wajen suka sameta, da yake Dr sun yi musayar pic da Dr Ansar basu yi wahalar gane juna ba. Gaisawa suka yi cikin farin ciki kamar sun daɗe da sanin juna sannan Dr Ansar ya umurce su da su hau mota, suna shiga direba ya ja bai zame da su ko ina ba sai *Steigenberger Hotel El-Tahrir* dake cikin birnin CAIRO, sosai hotel din ya yiwa Dr kyau repretion suka shiga inda aka basu makilin dakin, Dr Ansar har dakin ya raka su "Dr ku zauna anan idan ku ka huta ku ka ci abinci zuwa 6:30 direba zai zo daukar ku." Cikin turanci yake maganar. Gyada kai Dr Asmad ya yi tare da cewa "To muna godiya Dr." Murmushi kawai Dr Ansar ya yi ya ja masu kofar ya wuce. Ciki Dr ya shiga inda ya samu Ameesha kwance akan kujera three sitter, idonta lumshe kamar mai jin bacci zama ya yi kusa da ita yana faɗin "Heartbeat kina Jin yunwa ko? Sorry yanzu za'a kawo mana abinci, tashi ki yi wanka." Ya ida maganar yana latsa wayarsa lambar Nenne ya kira. "Hello Nennena fatan kina lafiya?" "Lafiya lau Asmad kun sauka lafiya?" "Alhamdulillah lafiya muka sauka, gamu a hotel ma." " Masha Allah! Na ji dadin jin haka, Allah yasa ayi wannan aiki a sa'a ina autar Ummi?" "Ga ta nan tana jinki Nenne." "To ai shi kenan Allah ya taimaka." "Amin." Dr ya amsa sannan suka yi sallama. Number Abba ya Kira, nan ma sun daɗe suna hira kafin su kai sallama. Ya kira Hafiz Yana sanar masa sun sauka, ya dai yi waya da mutane da yawa. Ameesha dai buɗe ido ta yi tana kallon sa, bata da alamar tashi, murmushi ya sakar mata tare da sa hannu ya dagota ta faɗa jikinsa, tsam ya rungume ta yana sunsunar wuyar ta, wata duniya Dr ya shiga mai cike da nishaɗi, kwankwasa kofar da ake ne yasa shi dawowa nutsuwarsa, kwantar da ita ya yi sannan ya nufi kofar tare da buɗewa. Abinci ne aka kawo masu, amsa ya yi ya shiga da shi, ajewa ya yi kan dining din dake falon ya matsa inda take kwance cak ya dauketa kamar wata baby bai zame ko ina da ita ba sai toilet, d kansa ya cire mata kayan jikinta ya mata wanka sannan ya fito da ita, shirya ta ya yi, kafin shi ma ya shiga. Ko da ya fito shiryawa ya yi cikin kaya marasa nauyi, kamar yadda ya sawa Ameesha itama, sallar azahar suka gabatar, rike da hannunta suka nufi falon ya zaunar da ita, abinci ya soma bata sai shagwaɓe masa take a haka har ta koshi bayan ta koshi ya fara ci shima, ko da suka gama toilet ya kaita ya wanke mata baki da suka fito basu zame ko ina ba sai kan gado. Rungume Ameesha Dr ya yi kamar wani ya ce zai raba su, a haka bacci ya dauketa mai dadi farin ciki ne ya mamaye Dr ganin yau gashi ga Ameesha a gado ɗaya yana rungume da ita, hamdala ya yiwa Allah yana fatan Allah ya nuna masa ranar da zasu kasance tare tana cikin hankalinta, kara manna ta da jikinsa ya yi kafin shima bacci ya kwashe shi. Ba su farka ba sai shida saura minti goma, da sauri ya sauka a gadon, tashin ta ya fara yi, da kyar ta iya bude ido don har a time ɗin bacci ne a idonta. Alwala ya yi ya taimaka mata ta yi sannan suka gabatar da la'asar, falo suka koma ya kunna masu t.v suna kallo, karfe shida da minti sha biyar Dr Ansar ya kira wayar Dr yana sanar masa da su sauka kasa motar asibiti tana zuwa, tashi ya yi ya canza kayan dake jikinsu kafin ya ja hannunta suka sauka. Ko zaman minti biyar basu yiba sai ga motar ta iso, shiga motar suka yi sai asbitin *AS-SALAM INTERNATIONAL HOSPITAL*, cikin mintina ƙalilan suka shiga asbitin babba ne sosai iya haɗawa ya hadu, duk da girman asbitin amma babu wasu mutane dai ɗai ɗaiku, domin dokar asbitin mutane basa zama, ana yin parking kafin su fito har Dr Ansar da wasu likitoci sun iso wajen motar. Cikin girmamawa da mutunta juna suka tarbe su, cikin asbitin suka shiga, bayan kara gaisawa ne Dr Ansar ya bukaci Dr Asmad ya yi masa bayanin ciwon Ameesha, take ya fito masa da duk wani fayal da ya shafi ciwon, amsa ya yi ya duba, sannan ya dubi Dr Asmad ya ce "Wannan ciwon yana da saukin warkewa a wajen mu amma da yaddar Allah, yanzu zamu fara mata gwaje gwaje sai musan matsayin da zamu taka." "Allah ya taimaka ya bamu sa'a." Dr ya faɗa yana ji cikin zuciyarsa kamar Ameesha ta samu lafiya, Dr Ansar yana gaba su na binsa a baya tare da wasu Nurse har wani daki mai cike da na'urori wani riga aka ba Ameesha ta sanya, da taimakon Dr ta sanya wajen shiga da ita ciki sam taki yadda a dole sai da Dr aka shiga, abin da yasa aka bar Asmad shiga don shima ya kasance likita ne kuma Dr Ansar yasan matsayin Ameesha a wajen Dr Asmad shi ne dalilin barinsa shiga ciki, wasu na'urori aka sanya mata akai ya yin da Dr Ansar ya koma wajen computer dake nuna cikin kan Ameesha. Dr Asmad da wasu manyan likitoci suna kallon computer. Dai dai kan wani abu, wani ɗan alama ya tsaya sai mutum ya zuba ido da kyau zai iya fahimtar menene a wajen, juyowa Dr Ansar ya yi yana kallon sauran likitocin ya tsaida kansa a kan Dr Asmad. Ya ce *Wai wallahi na gaji ku yi hakuri da wannan i hearttttt you all SANGARTA FANS* _*YAR MUTAN RANO*_ [10/8, 8:15 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* My Wattpad username *ZulayheartRano89* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* *33* "Dr ka kula da menene a wajen ca." Ya yi tambayar idon akan Asmad. Dr Asmad bai kalli Dr Ansar ba idonsa yana kan computer yana nazarin abin dake k'wak'walwar Ameesha, kusan minti biyu tukun ya sauke a jiyar zuciya ya ce "Dr duk iya nazari na ban gane ko menene ba." Har a lokacin yana kallon computer. Murmushi kawai Dr Ansar ya yi yana zomming na pic na photo, sai ga wajen ya fito fes, zaro ido Dr Asmad ya yi cike da mamaki ya ce "Da fatan yanzu ka ga komai?" Ya yi maganar yana ci gaba da daddana wa. "Yes! Dr na ga komai har na gane abin da ke wajen." "Me ka gani kenan?" "Jini ne kwance a wajen, ga shi nan." Dr ya yi maganar yana nuna cikin computer. "Tabbas jini ne ka duba da kyau yana motsa wa daf yake da gangarawa cikin k'wak'walwar ta, kuma da zarar ya ida shiga babu tantama haukace wa zata yi." "What! Dr ya faɗa da karfi. "Yes! Abin da na faɗa ma gaskiya ne, domin wannan ciwon da kake gani ba karamin illa garshi ba, AMNESIA babban cuta kenan sosai yake mai da mutane mahaukata amma ita nata da sauki kawai manta baya ta yi sakamakon wannan jinin dake cikin k'wak'walwar ta, amma da zarar an cire shi tunaninta zai dawo, sai na yi mamaki da duk fayal din da ka kawo babu mai makamancin irin wannan, mu kuma a binciken farko mun gano asalin inda matsalar ta ɓullo." Jinjina kai Dr ya yi yana kara yadda da kudurar Ubangiji, ya yadda da ci gaban kasashen duniya wanda har zuwa yanzu Nigeria bata da kashi biyu bisa uku cikin masu ci gaba ba, cikin lokaci ƙalilan har an gano ciwon da aka yi kusan wata uku ana fama, ya tabbata da kudi na sayan lafiya da Abban Ameesha ko nawa zai iya sawa ya saya mata, sai dai shi lafiya wani kyauta ne daga Allah madaukakin sarki, yau ga shi cikin karfin ikonsa ya kawo su idan zata samu waraka _(Allah ka kara mana imani da tsoronka, Ubangiji kara mana son Annabi Muhammad.)_ "To Dr yanzu yaushe za'a shiga da ita don wanke jinin, bana son ya gangara gaskiya." "Kar ka damu bari mu shiga office sai mu tattauna maganar, yanzu bari mu ci gaba da bincike ko zamu gano wani abun." Yana maganar ne yana bubbuga kafadar Dr Asmad. Dr Asmad bai kuma magana ba, sai ci gaba da kallon computer, Sun dauki time cikin wajen kafin Dr Ansar yasa suka koma office don ba suga komai ba, wani daki yasa a kai Ameesha allura ya umurci nuser su kuma suka fita. Dr ne zaune shi da Dr Ansar wanda keta rubuce rubuce, kusan minti biyar sannan ya ɗago da kai yana kallon Dr Asmad "Tunda an yi saurin gano matsalar zuwa gobe sai a yi mata aiki ma'ana a wanke jinin dake cikin k'wak'walwar ta." "Eh! Haka ma ya yi don burina da na iyayenta bai wuce ganin ta dawo normal ba." "In sha Allah zata koma dai dai duk da aikin babban ne, dole sai an hada da addu'a." Cikin karfafa masa gwiwa Dr Ansar ya dire maganar. "Kullum addu'a ana yin sa sai dai akara." "Nan zata zauna gobe da karfe biyar na yamma za'a shiga da ita tiyata." "To! Shi ne abin da Dr ya iya faɗa, zuciyarsa cike da tunanin samun nasara ko akasinta, sun daɗe shi da Dr Ansar kafin suka nufi dakin da Ameesha take, tana kwance kamar tana bacci sai dai ba bacci take yi ba allurar da aka mata ne ke aiki a jikinta. Wajenta Dr ya nufa zama ya yi tare da ɗaura hannunsa a kan fuskarta yana shafa wa a hankali "Kar ka damu fa Dr in sha Allah sauki zai zo." Maganar Dr Ansar kenan da ya yiwa Dr Asmad. Murmushi ya yi ya ce "Babu komai Dr a wannan shi ne burinmu, saboda zan yi kewarta ta ne daga yanzu har ranar da za'a fito da ita." A ɗan raunane ya dire maganar. "True love kenan kada ka damu da wannan, domin kana da matsayi a wajena zaka iya ganinta duk time da kaso." "Na gode da karamci, amma da gaske Dr ba zan dawo sai bayan an yi mata aiki, domin nasan zata samu kulawa yadda ya kamata." Ya kai karshen maganar yana mik'ewa tsaye. Sosai Dr Ansar ya ji dadin irin yabon da ya samu daga Dr Asmad, wata nuser yasa ta zauna da Ameesha su kuma suka fita, Dr Ansar da kansa ya kai Dr Asmad hotel ɗin da ya sauka, sai da ya ga shigarsa dakin kafin ya yi masa sallama. Ko da ya shiga falon zubawa ya yi akan kujera yana sauke numfashi, ya yi farin ciki sosai da zuwan sa garin, domin yadda yake ta ganin nasara a kan komai, rigar jikinsa ya cire tare da dauko wayarsa sam ya manta da wata aba wai ita waya Number Bobbo ya Soma kira suka gaisa yana tambayarsa yadda jikin nata yake "Da sauki Bobbo na barta a asbiti." "To madallah! Allah ya kara lafiya." "Amin." Dr ya amsa sannan Bobbo ya mik'awa Nenne wayar, sun gaisa take tambayarsa jikin Ameesha. "Ai Nenne Alhamdulillah! Nasara ta samu har an gano matsalar a gabana akai komai, nan yaba Nenne labarin komai da ya faru. Sosai ta ji dadi sai addu'a take zuba masu shi da Dr Ansar. "Tun da ka ce gobe za'a mata aiki zuwa jibi zamu taho, ai bamu san abin haka yake ba." "Allah ya kawo lafiya, da karfe biyar zasu shiga, kila har ku iso kafin ta farka." "In sha Allah muna zuwa, yanzu dai ka sanar da mahaifin Ameesha domin ya samu kwanciyar hankali." "Yanzu zan sanar masa, ina Aneesa?" "Tana ɓangarena yanzu karfe biyu na dare ne, ka bari da asbah sai ka kirata, ko dama ba ku yi waya ba ne?" Cikin mintinan da ba su fi uku ba Nenne ta yi masa maganar. "A'a Nenne mun yi waya da ita ɗazun." Ya ba Nenne amsa. "To shi kenan Allah ya taimaka ya bada nasara." "Amin." Ya amsa sannan suka yi sallama. Wayar Alhaji Taheer ya kira, bayan sun gaisa yake masa bayanin komai, sosai Abba ya ji dadin wannan bayani, suna gama wayar ya tashi ya dauro alwalarsa kamar yadda Nenne da Bobbo suka suka yi duk addu'ar tasu akan samun nasara aikin da za'a yi mata ne. Shi ma Dr toilet ya shiga sai da ya yi wanka ya dauro alwala jallabiya ya sa, kafin ya tayar da sallah, ya daɗe yana addu'a, sai kusan huɗu bacci ya kwashe shi. Bacci sosai Dr ya yi bai farka ba sai karfe tara na safe, da sauri cikin takaicin irin baccin da ya yi har ya rasa sallah aka lokaci yake, toilet ya shiga ya sake wanka tare da alwala, sallah ya gabatar kafin ya kira yan hotel ɗin ya sanar masu abin da yake buk'ata, wayarsa ya dauka ya danna Number Aneesa, lokacin tana kwance cike da tunaninsa sai ta ji karan wayarta dauka ta yi tare da karawa a kunne "Hello Assalamu Alaikum my Anee!" Dr ya yi maganar lokaci ɗaya. Lumshe ido ta yi ta buɗe don jin muryar Dr ta yi ta kara daɗi, har wata kasala ta saukarwa Aneesa, shiru ta yi masa "To me kuma na yi da aka ɗauki waya magana dani ya gagara?" Cikin sanyin murya ya mata tambayar. Turo baki ta yi kamar yana ganin ta ta ce "Babu komai fa gani na yi ka manta da ni!" Dan wari ido ya yi waje ya ce "Ke kullum cikin korafi yanzu don Allah wa ya faɗa maki na manta da ke, Ni ban yi korafin kin kirana da ba ki yi ba amma ke ki ke min?" "Babu." ta bashi amsa a takaice. Ajiyar zuciya ya sauke, cikin ransa ya ce "ina jiran ganin ranar da Aneesa zata yi hankali." Amma a fili sai ya ce "My Anee gaisuwa ma yau ya gagareki balle ki tambayeni mai jiki?" Harara ta wurgawa wayar kamar dai Dr na kallonta ta ce "To ina kwana ya mai jikin?" Daga jin yadda ta yi maganar yasan ta ji haushin maganar sa. Dariya ya yi ya ce "Lafiya lau Aneesa mai jiki ta ji sauki." Hira suka shiga irin ta mata da miji har kusan sha daya sannan suka yi sallama, an kawo masa abinci tuni amma wayar da ya ke da Aneesa ya hana shi ci, har sai da suka gama ko da ya gama cin abincin zama ya yi yana kallo har bacci ya kwashe shi. Ko da ya tashi wanka ya yi tare da sallah, bayan ya ci abinci ya shiga yawon zaga gari domin dai zaman ya ishe shi, bai koma masaukin sa ba sai karfe biyar, a dai dai lokacin kuma aka shiga da Ameesha dakin tiyata, inda suka kwashe kusan awa uku ana yi, basu fito ba sai takwas na dare. Fuskar Dr Ansar kaɗai zaka kalla ka fahimci halin da yake ciki na farin ciki, domin dai ya ji a jikinsa aikin zai yi kyau, don ko kadan ba'a samu matsala a lokacin yin aikin ba, Dr na zaune akan sallaya don tun da ya shiga dakin dukufa ya yi addu'a da samun nasara, wayarsa ce ta fara ringing Yana dubawa yaga sunan Dr Ansar ai da sauri ya dauka. "Alhamdulillah! Dr Asmad ya faɗa da murya mai cike da zallar farin ciki, domin albishir din Dr Ansar ya yi masa na har sun fito daga aikin, suna gamawa ya kira su Abba ya sanar masu, su ɗin ma sosai suka yi farin ciki. Daga Dr har su Nenne su Ummi da Abba kwana salloli da addu'a suka yi, Dr kam bai rintsa ba sai da ya yi sallar asuba nannauyan bacci ya kwashe shi, karar wayarsa ce ta tashe shi daga bacci cikin baccin ya ɗauki wayar Muryar da ya ji ne ta shi saurin tashi. "Assalamu Alaikum Abba har kun iso ne?" "Eh! Gamu nan a airport muna jiranka." "To Abba gani nan zuwa yanzu in sha Allah." Dr ya yi maganar yana tashi, mamaki sosai ya yina irin baccin da ya yi, sai a lokacin ya duba agogo yaga har karfe biyu na rana, shaf shaf ya yi wanka ya shirya daret airport ɗin ya nufa, cikin lokaci ƙalilan suka hadu Abba ne da Ummi sai Bobbo da Nenne, sosai Dr ya yi farin ciki da ganin su, bayan sun gaisa sai Nenne ke tambayarsa "Ameesha ta farka kuwa?" "A'a Nenne ya ce sai nan da awa biyu." Gaba daya suka hada baki wajen faɗin "Allah ya tabbatar da Alhairi, yasa an yi a sa'a." "Amin." Ya amsa sannan suka shiga mota zuwa hotel su dan huta kafin su je asbitin. Sosai suka huta don har abinci da salloli suka yi, sai suka dunguma zuwa asbitin. Tun a farkon shiga Abba ya fara yabawa da tsarin asbitin don komai na ciki mai inganci ne da kyau Fitowar su daga mota ta yi dai dai da zuwan Dr Ansar, yana ganin su Dr Asmad sai ya yi saurin k'arasawa, musabaha suka yi da Dr ya gaida su Abba, sannan suka shiga cikin asbitin daret dakin da Ameesha take suka nufa Dr Ansar yana kara faɗa masu yadda komai ya wakana, sun ji dadi burinsu su karasa inda Ameesha don su ga halin da take. Wani daki ne mai kyau sosai kamar ba dakin asbiti ba suka shiga, Dr Ansar da Dr Asmad ne a gaba sai Abba da Bobbo dake biye da su a baya, wajen gadon suka yi burki tana kwance kamar gawa don babu inda ke motsi a jikinta addu'oi suka fara tofa mata suna addu'ar Allah ya bata lafiya "Dr zuwa yaushe zata farka?" Dr ya yi tambayar. "Nan da minti talatin zuwa awa daya." Dr Ansar ya bashi amsa yana kallon agogonsa. "Ok Allah ya kaimu." Duk suka faɗa. Sannan suka fita daga dakin aka bar Nenne da Ummi, Nenne ce ta matsa tare da riko hannun Meesha tana mata addu'a, Ummi kam kasa matsawa ta yi sai dai ita dinma addu'a take yi mata daga inda take zaune. Dr Asmad ne tare da su Abba, yana tsugune gaban su kansa a kasa magana yake son yi amma ya kasa. "Asmad kamar kana son yin magana ko?" Abba ya tambaya. Dan sosa kai ya yi ya ce "Amm dama Abba cewa zan yi ko da Ameesha ta farfaɗo karku sanar mata da matsayin ni mijinta ne." "Me ya sa za yi haka? Kasan dai dole zata san da maganar ko?" Bobbo ya yi saurin jeho masa tambayar. "Eh! Bobbo ina son sanar mata da kaina ne, ina rokon alfarma." "To ai shi kenan tunda kai ka bukaci haka." Abba ya bashi amsa. Daga haka suka shiga hiransu da ciye ciyen. Cikin dakin kuwa Nenne tana rike da hannun Meesha sai taga hannun ya soma motsi.... ```Tofa jama'a ga dai Meesha nan ta fara motsi alamar ta farka shin a wane yanayi zata farfaɗo? To wai idan ta farfaɗo ta ji maganar aurenta da Dr kuna ganin zata yadda? Ya Dr zai kasance bayan farfaɗowar Ameesha? Duk da wannan amsar yana ga Zulayheart Yar gidan Haruna, ku biyoni a hankali zan warware maku komai da yadda Allah, i hearttttt Your My fans``` _*Yar mutan Rano*_ [10/8, 8:15 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* My Wattpad username *ZulayheartRano89* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* ```Har abada bazan manta da Alhairin ku a gareni ba, tabbas ba dan kuba wallahi da yanzu babu sauran maganar labarin SANGARTA, amma kasancewar ku a wajena yasa ku ku ka assasani har labarin ya kawo yanzu, ina kara godiya a gareku Allah ya saka maku da mafificin Alhairin sa ameen da ku nake KHADIJAH S MUHAMMAD ( Bestyna) & BADEEYAR ADAM (Beauty Queen) Allah ya barmu da k'aunar juna``` *Dedicated to LAIFIN WA & SANGARTA FANS* ina son ki sosai😍😍😍 *34* Da sauri Nenne ta kara damke hannun, cikin zuciyarta tana tasbihi ga Allah a haka duk jikin Ameesha suka fara motsi "Alhamdulillah!" Nenne tafa murya a bayyane. Ummi da sai a lokacin ta kula da sauri ta matso tana faɗin "Kamar tana motsi ko?" "Eh! Bari a kira Dr." Nenne ta yi maganar tana mik'ewa. "A'a zauna kawai bari na kira shi." Ummi ta dire maganar tana fita daga dakin ranta fes. Lokacin da Ummi ta sanar masu duk sun ji dadi, suna addu'ar Allah yasa ta warke kenan, babu kamar Dr da ya ji maganar kamar anyi masa bushara da aljanna, sujada ya yiwa Allah don nuna jin dadin sa, ji ya yi kamar ya ri ga kowa ganin Ameeshar sa, sai dai yana kunyar su Ummi, lokacin da ya dawo tunaninsa wayam yaga wajen ma'ana har su Abba sun tafi ganin Ameesha kenan? Ya yi maganar shi ma yana nufa dakin. Su kam su Abba kusan a tare suka shiga, kan gadon duk suka nufa tare da zuba mata ido, "Dr ashe ta farka?" Abba ya tambaya. "Eh! Ta farka yanzu, sai dai akwai buk'ata ta samu hutu." "Ku yi hakuri ku dan bani waje." Dr ya yi maganar yana nufa wajen gadon, ya soma duba ta ganin numfashin ta ya dawo normal, sai dai bata buɗe ido ba, ganin haka da Dr Ansar ya yi sai ya ce "Kin farka?" A hankali ta soma buɗe ido har ta bude su duka, ta daura idonta akan na Dr Ansar tana masa wani irin kallo na mamaki, sam Dr bai damu da haka ba. farin ciki ne ya kama Abba da su Nenne ai da sauri suka shiga ɗakin, ganin an turo kofar yasa Ameesha saurin daga kai tana kallon masu shigowa bata ce komai ba sai lumshe ido da ta yi "Alhamdulillah! Autar Ummi." Ummi ta yi maganar cikin farin ciki. A karo na biyu ta kuma buɗe ido ta zuba su kan fuskar Ummi, ko kadan bakinta bai motsa da sunan magana ba. Gaba daya suka fita sai Nenne kawai aka bari a daki, Nenne bata yi musu ba domin babu mamaki Ameesha ta farka tana bukatar wani abu babu kowa. A inda suke Dr ya same su "Abba ina son magana da ku a office." Dr Ansar ya yi maganar yana tafiya, bayan sa suka bi Ummi da Abba da Bobbo, sai Dr Asmad da ya bisu a baya. A hankali likitan ya zare farin gilashin da ke fuskarshi, lokaci d'aya kuma ya tattara hankalinshi a kan Su Abba da suke zaune su ma hankalinsu a kanshi. "Ita cutar Amnesia cuta ce da take samuwa ta hanyar duk wani abu da zai taba Kwakwalwa sannan a rasa hankali gabadaya, musamman idan kai ya bugu sosai. Lokacin da mutum zai dawo hankalinshi sai ya manta dukkan wasu abubuwa da suka faru da shi. Wannan ita ce ake kira Amnesia." Ya tsahirta hade da kallon su Abba kafin ya ci gaba. "Cutar ta kasu kashi - kashi, amma kashin da ya fi shahara shi ne: *Anterograde* da *Retrograde* Antrograde: ita mutum baya iya tuna abinda ya faru da shi nan take, yanzu zai yi abu, yanzu kuma zai manta ya yi." "Subhanallah! Abba ya fad'a cikin jimami Likitan ya ci gaba " Retrograde kuwa, mutum ya kan manta komai ne na baya, sai dai ya dora sabon tunani." "Allah mai iko" Abbah ya kuma fad'a. "Cutar ba ta da magani da ake sha don a warke, sai dai ko a magance wani ciwo da aka ji a lokacin da tsautsayin ya faru. Kuma ba a yi mata aiki, ma'ana a yanka mutum don kwashe cutar. Dabaru kawai ake amfani dasu wajen magance ta, shi ne tunawa mutum duk abu muhimmi da ya faru da shi, yin wani abu a gabanshi wanda ya saba yi, ci ko shan wani favourite food na shi, sanya kida ko amfani da wani abu me kamshi da ya sani." Ya dan tsahirta yana duban Asmad da ya yi shiru kamar bai taba jin bayanin cutar ba sai yau. " Don haka da ma na fada maku, koda kun kawo ta zamu yi amfani da wasu hanyoyi ne don jaraba sa'armu, wanda ba lallai ne kuma ayi nasara ba. Kuma yanzu haka da su din muka yi amfani, inda muka yi nasara Kwakwalwarta ta cafki sauti guda daya, a yanayin yadda ta tashi, muna da tabbacin dawowar tunaninta, amma dai sai a hankali za ta rika tuna wasu abubuwan, abu d'aya zaku yi shi ne, tuna mata duk wani da kuka san tana yi lokacin da take da lafiya, ko kawo abinda kuka san tana so lokacin da take da lafiya.... "To in sha Allah zamu yi kokari Allah ya saka da Alhairi." Abba ne ya yi maganar cikin dakiyar zuciya. Daga wannan bayanin suka yi sallama da Dr Ansar, cikin mutunci. Sai da suka leka dakin da Ameesha take, ganin tana bacci yasa suka fita don komawa masaukinsu don su huta, tunanin Abba shi ne da me za'a fara tuni ga Ameesha. DR bai tsaya jira su Abba ba, ya koma hotel zuciyarsa tana takaicin rashin sa bo da Ameesha kafin ta samu ciwon, domin da ace ya saba da ita da kansa zai rika tuna mata har ta koma dai dai, tunanin Meena ce ta fado masa a fili ya furta "Dole ana bukatar Meena a wannan lokacin, domin tafi kowa sanin abin da Ameesha ke aikatawa da wanda ta fi so, matsalar bata a kusa da daga yau ta fara..." Da sauri ya juyo, ganin Abba ne ya dafa shi sai ya saki murmushi. "Tunanin me kake yi haka sai sambatu kake yi?" Abba ya yi tambayar yana rike da kafadar Dr Asmad. "Babu komai fa Abba." "Ka kwantar da hankalinka ka ji ko? Mu je ciki ka samu ko abinci ka ci, dubi yadda ka koma lokaci ɗaya?" "Bana jin yunwa Abba." Dr ya bashi amsa. "No! Mu je dai ban yadda da kai ba." Cikin murmushi Abba ya dire maganar. Babu yadda Dr ya iya haka nan ya bi su Abba ciki. Shigar su dakin ba jimawa wayar Abba ya soma ruri, daukowa ya yi yana mamakin ganin Number Jaheed kuma da Number kasar CAIRO "Ikon Allah." Ya furta yana kara wayar a kunnensa. "Kuna airport fa ka ce? To sai ku dauko mota ta kawo ku, Steigenberger Hotel El-Tahrir muna ciki yanzu haka." Daga haka ya kashe wayar. Ummi ta bishi da kallo ta ce "Su waye ke airport?" "Su Jaheed mana, wai sun kasa jure rashin ganin Ameesha, shi ne suka biyo mu." Murmushi Ummi ta yi a zuciyarta ta ce "ikon Allah soyayyar yan'uwa jini daya ba wasa ba." Amma a fili sai ta ce "To ai shi kenan tunda sun iso sun kyauta." "Sun kyauta kuwa, amma da sun yi shawara baza su taho yanzu." Cikin faɗa Abba ya dire maganar yana shiga toilet. Mintina ƙalilan suka kira Ummi suna sanar mata ga su cikin hotel ɗin, kusan a tare suka fita harabar hotel ɗin, Dr ma da yake ya ji wayar da suke har ya ri ga su zuwa, rungume juna sukai da Jaheed yana tambayarsa jikin Ameesha. "Alhamdulillah! Dr ya bashi amsa, tare da kai dubansa ga Meena ya ce "Madallah dake kawarmu wallahi kamar dai kin san muna da buk'atar ki a dai dai wannan lokacin." Murmushi Meena ta yi ta ce "Kuma sai gani, na kasa jure rashin ganin Ameesha na kwana biyu." "Kamar yadda ita dinma yanzu taimakon ki take buk'ata, yanzu dai mu shiga ku samu ku ci abinci ku dan huta sai mu je wajen ta." "Ina ai babu maganar hutu kawai a kaimu muga autar Ummi." Ya Jaheed ya yi maganar. "To ai sai ku je mu kam zamu huta dawowar mu kenan." Abba ne ya yi masu maganar cikin fara'a. To Abba suka amsa suna shiga cikin mota. "Ke Meena da kin zauna ki huta, don yanayin jikinki fa." "A'a Ummi zan iya zuwa, ina son ganin Meesha sosai ne nayi missing ɗin ta." "To ai shi kenan a dawo lafiya." Har a lokacin da suka isa asibitin Ameesha bacci take yi, don haka zama suka yi bayan sun gaisa da Nenne, tare da tambayar ta mai jiki. "Da sauki tun ɗazun da ta farka ta koma bacci har yanzu bata tashi ba." "Allah yasa ta tashi cikin nasara." Ya Jaheed ya faɗa. "Amin." Nenne ta amsa tana faɗin "Oh! Ni yarsu, sannu Meena da k'ok'ari ko nauyin jikinki baki ji?" Murmushi ta yi ta ce "Allah Nenne akan Meesha har mantawa nakeyi da wani nauyin jiki." "Ai naga alama, Allah ya bar kaunar juna kin cika kawa ta gari, samun irin ki sai an tona." Meena dai murmushi ta yi , tana zaune a ɗakin burinta bai wuce ganin Meesha ta farka, a lokacin kuwa su ya Jaheed da matarsa Badiyyah da mijin Meena Abdul hotel suka koma Meena da Dr sai Nenne kadai ke asibitin. Sai da Meesha ta share awanni uku tana bacci kafin ta tashi, idonta kyar akan Meena tana kallonta, murmushi Meena ta yi ta ce "Yes Meena ce Besty friend dinki a gaban ki, ya jikin?" Ameesha shiru ta yi tana kallon Meena kamar mai son tuno wani, amma ta kasa, ita kam Meena buɗe jaka ta yi ta ciro kwalbar turare wani Meesha tafi kauna da so sunan turaren *Obsessed* a duniya shi ne turaren Meena. Mik'awa Meesha ta yi cikin murmushi ta ce "Ga tsaraba na kawo maki, nasan zaki yi farin ciki." Amsa Meesha ta yi tana jijjuya... _*YAR MUTAN RANO*_ [10/8, 8:16 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* My Wattpad username *ZulayheartRano89* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* *35* So take ta tuna wani abu, sai dai sam k'wak'walwa ta ta kasa tunowa, Meena ta kula da haka sai kawai cikin sauri ta ce "Kin manta ranar da muka je sahad, kika ga turaren har ki ka ɗauka! Duba sunan ki gani Obsessed sunansa." "Meena Obsessed! Ameesha ta maimaita sunan da wata irin murya. "Yes! Shi fatan kin tuna?" A hankali lokacin da ta saya turaren ya fara dawo mata, sai dai ta kasa tuna wani abu bayan shi, kanta ne ya yi wani irin sarawa "Wash! Ta furta a fili "Mu je ki yi wanka kafin Abba ya zo." "Abbana? Ina Abba yake Ummi fa?" "Duk za ki gansu, yanzu dai ta shi ki yi wanka." Da kanta ta yi wanka, ta shirya cikin doguwar rigar atamfa, sosai kayan sun yi mata kyau, Nenne ta haɗa mata shayi domin babu abinci cikin dakin, Dr Asmad ya tafi kawowa. "Na gode! Ta faɗa tana kai cup bakinta, tas ta shanye tana aje cup din ta furta "Alhamdulillah!" Murmushin nasara Nenne ta yi, domin kuwa tabbas ta yadda Ameesha ta fara samun lafiya, tunda gashi har tana abubuwa da kanta. "Ga wayar ki Ummi zata yi magana da ke." Meena ce ta yi maganar tana mik'awa Meesha wayar. Amsar wayar ta yi tana kallon ta, sai kuma ta ɗago kai ta zubawa Meena ido, kafin ta yi magana sai jin sallamar su Abba suka yi, cikin masu amsawa har da Ameesha, wacce ta yi saurin tashi tsaye tana faɗin "Abbana ina Ummi?" Ta kai karshen maganar tana fadawa jikinsa, don sam bata kula da Ummi ba balle su ya Jaheed. "Kai masha Allah autar Ummi ta samu sauki, ga Ummin ki da su Jaheed." Abba ya faɗa yana dagota. Kallon su ta yi tana ganin Ummi da sauri ta nufeta ta rungume ta cikin zallar farin ciki Duk sun ji dadin ganin yadda ta koma, hira suka shiga yi ita dai Ameesha tana jin su, bata furta komai ba domin bata fahimtar inda hiran tasa gaba, a haka Dr Asmad ya yi sallama lokacin idonta a lumshe yake, jin sallamar sa yasa ta yi saurin bude ido domin dai take ta dauki muryar sa. Fes ta sauke idonta akan fuskarsa, wani kallo suka wa junansu mai cike da ma'anoni daban daban, murmushi Dr ya saki tare da fadin "Princess kin tashi?" Wani kasala ta saukar mata jin muryar sa, bata iya bashi amsa ba sai lumshe ido da tayi tare da buɗewa. Kana kallon Dr zaka iya fahimtar yana cikin zallar farin ciki, da kansa ya zuba mata abincin ya mika mata, amsa ta yi har a time ɗin bata daina kallonsa ba. Haka dai a hankali sauki ke samuwa ga Ameesha har aka yi kwana uku, a lokacin Dr Ansar ya ce zai sallame su, tunda zuwa yanzu ta fara tuna wasu abubuwan a hankali zata tuna komai. Suna zaune dukan su, kanta yana saman cinyar Nenne ta yi kamar tana bacci, su kam dama hira suke zumbur kamar an tsikare ta ta mik'e tana waige-waige "Ummi Ina Najeeb?" "Najeeb kuma? Wanne Najeeb ɗin?" "Ummi Najeeb mana yaron Alhaji Mansur abokin Abba?" Ameesha ta fada tana gyara zama. "Autar Ummi Najeeb yana Nigeria fa, nan muna CAIRO ne." "Cairo kuma? To mai ya kawo mu?" "Baki da lafiya ne aka kawo ki." "Bani da lafiya? To mai ya sameni? To amma Ummi ai ko a ina nake ya kamata yazo, ya zama shi zan fara gani, tunda har Abba ya soma maganar aurenmu da shi." Shiru suka yi suna sauraron maganar ta, cike da mamaki Meena ce ta yi karfin halin yin magana "Meesha ya sunana?" "Haba wannan wane irin tambaya ne? Meena mai kika mai dani?" "Yi hakuri k'awata zaki iya lissafo min duk mutanen dake dakin nan?" Harara ta watsawa Meena ta ce "Eh! Duk na sansu *Ummina, Meena k'awata, ga Abbana* ke duk na sanku na tuna komai. "Kin tuna komai fa kika ce?" "Eh! Ta bata amsa kai tsaye. "A ranar da Abba ya kai ki school, bayan kin fito lacca zaki koma me ya faru da ke a hanya?" Meena ta yi saurin jefa mata tambaya. "Na fito daga school na je tsallaka titi naji karan wani abu, to nidai daga haka ban kuma sanin komai ba sai yanzu." "Gud k'awata ta koma normal Alhamdulillah! "Amma wadinnnan ne ban san ko su waye ba. Ta nuna su Nenne da Bobbo "Karki damu suma kin sansu domin su ɗin suna da matukar muhimmanci a rayuwar ki, a hankali zaki san matsayin su a gareki." Ummi ta bata amsa. Shafa kanta Nenne ta yi ta ce " karki damu 'yata, ki kwantar da hankalinki." Gyada kai ta yi tana gyara kwanciya, sallamar Dr ne yasa ta buɗe ido, da mamaki take kallonsa bakinta har yana rawa ta ce "Dr! "Na'am Princess ya jikin naki?" Harara ta aika masa tare da fadin "Ni kam lafiyata lau." "Au to yi hakuri lafiyar ki lau, Allah ya kara mana lafiya." Ko kafin ta yi magana ya riga ta "Abba Dr Ansar fa ya bamu sallama, ko yanzu zamu iya barin asibitin tunda an samu nasara." "Kai madallah! Yanzu to sai mu hada kayanmu, mu koma hotel zuwa gobe sai mu koma Nigeria." Duk sun yi na'am da maganar Abba, don haka cikin sauri suka haɗa kayan su, hotel suka koma Ameesha sai zubawa Abba shagwaɓa take a hanya, shi kam biye mata yake domin dai yana cikin farin cikin dawowar ta dai dai. Suna isa kowa ya shiga dakinsa, Ameesha kam cewa ta yi inda Nenne take nan zata zauna, domin kuwa lokaci ɗaya Allah ya daura mata son Nenne saboda ta kula Nenne tana da kyawun hali. Suna shiga akan kujera ta zube tana furta "Wash! Kallonta Nenne ta yi ta ce "Lafiya?" "Lafiya lau Nennena." Da sauri Dr ya kalleta jin yadda ta ce wai Nennenta. "To ai shi kenan yanzu dai bari na yi wanka, sai mu fita harabar hotel mu dan sha iska, wallahi na gaji da zaman waje daya." Nenne ce mai maganar tana shiga bedroom. "A fito lafiya Nennena." Meesha ta faɗa tana gyara kwanciya, wayarta ta jawo dan kallon wayar ta yi, cikin phone ta shiga tana duba kiran da kai mata a hankali take sauke Number har ta isa kan wanda take tunanin lambar Dr ne. Ta ɗan yi mamaki ganin 23 /june /2018, kenan a yadda Meena ta faɗa mata ta yi wata kusan uku tare da ciwon tunda yau dai 7/ August /2018, ikon Allah lallai Allah yana kaunata. Cikin zuciyarta take maganar. Fita ta yi ta shiga contact, number din Ni'eema ta gani, murmushi ta yi tare da danna mata ki, ringing biyu ta dauka "Meena ko Meesha?" Shi ne farkon tambayar da ta yi. Murmushi Meesha ta yi ta ce "Meesha ce fatan kina lafiya?" Cike da mamaki Ni'eema ta amsa "Lafiya lau ya jikin?" Da yake Meena ta sanar mata da ciwon Meesha ɗin, kuma lokaci zuwa lokaci takan kira ta tambayi jikin Ameesha, shi yasa yanzu ta cika da mamakin ganin kiran Meesha. "Na warke fa nikam, ina Fasmir da Yumna?" "Duk suna lafiya, in sha Allah gobe zamu zo gaida ki." "Bamu dawo ba, muna Egypt yanzu haka, amma gobe zamu dawo da yaddar Allah." "Allah ya dawo da ku lafiya." Hira suka ci gaba da yi, ya yin da Dr ya zubawa Ameesha ido, shi dai a duniya tana matukar burgeshi, duk wani abu da zata yi kyau yake mata, yana jin sonta kota ina babu ma kamar yanzu da ya yi wani irin sabo da dumin jikinta. Muryar Nenne ce ta dawo da shi daga tunanin da ya lula "Wayar ce dai har yanzu bata kare ba?" "Eh! Nenne da wata k'awata muke yi, wai gobe zata zo gaidani shi ne na ce mata bamu dawo ba." "Ayya gaskiya tana da kirki." "Sosai kam Ni'eema keda kirki, yawwa Nenne tunda kin fito bari na cewa Abba mu zaga gari tunda gobe zamu tafi." "Babu inda zaki." Dr ne ya yi maganar yana ci gaba da danna wayarsa. Wani irin juyowa Ameesha ta yi ta ce "Kai kuma a suwa da zaka hana ni fita *Ji shiga uku takabar suruki*,To sai naje ɗin. Meesha ta faɗa tana fita daga dakin. Nenne kam harara ta aika masa da shi ta ce "Ina ruwan ko? Kana ganin yarinyar an samu da kyar Allah ya taimaka shi ne zaka ɓullo da wata maganar? "Allah ya baku hakuri ne..." Wai typing da wahala Yaseen. _*YAR MUTAN RANO*_ [10/8, 8:16 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* My Wattpad username *ZulayheartRano89* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* Dedicated to _*RAHEENAT MAMOUDOU (HEENART)*_ ```Betsy Allah ya baki lafiya, jin ciwon ki nake kamar a jikina yake 😭😭 sosai na yi missing ɗin ki, Allah yasa kaffara ne```👏 *36* Nenne bata ce masa komai ba, sai ma zama da ta yi tana jiran zuwan Ameesha, bata fi minti biyar ba ta dawo da ganin yadda ta turo baki zaka san da magana, kusa da Nenne ta zauna cikin zallar SANGARTAR da ta saba. " 'Yata lafiya kuwa?" "Ba Abba bane wai inzo in tambayi Dr, idan ya bari sai mu tafi." Cike da shagwaɓa har da dira kafa kamar wata karamar yarinya ta ida maganar. Wani irin murmushi Dr ya saki don tabbas ya ji dadin maganar Abba, ya kuma bashi wani matsayin na musamman, domin ya cika suruki na gaske. Sosai ta cika da mamakin furucin Abba da ya ce sai da izinin Dr zata fita, to wani matsayi Dr ke da shi a wajenta da har Abba zai fadi wannan maganar?" Tambayar ta yiwa kanta wanda bata da amsar sa, ko kafin ta lalubo amsa sai jin maganar Nenne ta yi. "To kai ka ji abin da ta ce ko?" Babu alamar dariya Nenne ta masa tambaya. "Eh! Na ji Nenne a dawo lafiya, mu je nima ina son k'ara ganin garin." Kusan a tare suka fito, domin su Meena ma yawon zaga garin zasu je, haka suka fita suna hira Ummi da Nenne suna taɓa hira, Meena da Meesha ma haka, sai su Jaheed da Dr, sun zaga gari sosai har sayayya suka yi, Dr ma ya sayawa Aneesa tsaraba domin ya faranta mata, washe gari jirjin karfe takwas suka bi. *NIGERIA* ko da jirgin su ya sauka kowa gidan sa ya nufa, Dr dai kin bin su Nenne ya yi domin cewa ya yi sai ya kai Ameesha har gida, Allah ya sani baya son rabuwa da ita don dai ya zama dole ne. Yana cikin gidan sai wajen karfe shida ya fita, a lokacin tuni Aneesa ta shirya masa lafiyayyen girki, shi kadai take jira ganin har shida ta yi sai ranta ya soma ɓaci domin ta yi amanna yana tare da Ameesha shi yasa ya manta da ita. Sallama ya yi tare da shiga cikin falon, Aneesa dake zaune ta watsa masa wani irin kallo tare da dauke kai "My Anne mai nayi kuma daga dawowata?" Ya yi maganar tare da hugging ɗinta. Bata fuska ta yi ta turo baki, tana mutsu-mutsu so take ta zame jikinta daga rikon da ya mata "Sorry na yi laifi ko? Amma fa ba laifi na yi ba, kinsa tare da mara lafiya nake dole tana da buk'atar kulawa." Kuka ta fashe masa da shi tana faɗin. "Ai Ni bana buk'atar kulawa tunda har ka tafi kusan kwana goma." Da shashsheka take maganar. Gyara rikonta ya yi ya ce "Please ki yi hakuri bazan kuma ba, kin ji matata farin cikina?" "Babu komai ya wuce." "Da gaske?" "Eh! Mu je ka yi wanka sai ka ci abinci." "Yawwa matata yar albarka." Aneesa ta taimaka masa ya yi wanka, jallabiya ya zira lokacin ana kiran sallar magriba, masallacin kofar gidan ya je lokacin da ya dawo bai taras da ita a falo ba, don haka sai ya nufi bedroom ɗinta, zaune ya ganta gaban dressing mirror tana fesa turare, shakar kamshin ya yi yana rungume ta jikinsa. "My Anne kin yi kyau." "Na gode." Ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi. "Ranka ya daɗe mu je ka ci abinci." "No! Barni in gama shakar kamshin matata." "Please." Ta faɗa kamar zata yi kuka. Sakinta ya yi ya riƙe hannunta, a haka suka isa dining room din. Da kanta take ciyar da shi har ya koshi, falo suka koma, ranar dai sosai Dr ya cika da mamakin canzawar Aneesa. Washe gari tun wuri Dr ya shirya domin ziyartar asbiti, bai biya ko ina ba, domin baya son ya yi latti ya dai turawa Ameesha text message na barka da safiya, karfe takwas a asbiti ta yi masa da yake sun san ya dawo komai a gyare ya taras, aiki sosai Dr ya yi har bai samu kansa ba sai biyun rana. **** "Sannu My Ruffy har yanzu amai ɗin bai tsaya ba?" "Eh! Ta bashi amsa tana mai da numfashi, domin dai sosai ta galabaita, da kansa ya gyara wajen ya canza mata kaya, yana rike da ita har suka isa wajen motarsa, taimaka mata ya yi ta shiga, sannun da yake jero mata tunda ga bedroom ɗinta har nan sun kai hamsin. Tsabar tausayin ta ke damunsa sosai, ba su yi wata tafiya mai nisa ba suka shiga wani karamin asbiti mai kyau, parking ya yi tare da riketa har cikin office din Dr, domin ya yi masa waya tun kafin su taho. Dr Auyo sosai ya tausayawa Rufaida ganin halin da take ciki, tambayoyi ya fara mata tana bashi amsa, inda daga karshe ya kira Nurse tare da umurtanta da ta dibi jinin Rufaida da fitsarinta domin a yi test, ba'a wani dade ba ta dawo da result ɗin. Gama karanta result ɗin ya yi fuskarsa ɗauke da murmushi, hannu ya mik'awa Najeeb yana faɗin "Congratulations! Sir Allah ya inganta, Madam na dauke da juna biyu na sati biyar." Wani irin farin ciki ne ya kama Najeeb, wanda har bai san lokacin da ya rungume Rufaida ba, ita kam kasa ta yi da kai cike da kunya, Najeeb fa ya manta a gaban Dr yake, da Dr Auyo da yaga haka sai ya fita ya bar masu office din. Najeeb kuwa rungume Rufaida ya yi a jikinsa, yana gwada mata tsantsan farin ciki da murna na cikin dake jikinta, lokacin da ya ɗago bai ga Dr Auyo ba murmushi ya yi don yasan shi da kunya. Mik'ewa ya yi ya leka waje inda ya ga Dr na magana da wasu, Nurse ya sanya ta yi masa magana, bai jima ba ya shigo, bakin Najeeb sam yaki rufuwa ya ce "Dr da alama cikin zai bata wahala musamman ta yawan aman dake damunta, ko akwai maganin da za'a bata?" "Eh! Akwai wani magani da mai ciki take amfani da shi sunan sa *Ancloxine tablet* sosai yake tsayar ma masu ciki amai matukar dai ya amshe ta, kasan laulayi ne kowa da irin yadda ya ke yi." Dr Auyo ya yi masa bayanin cikin kwantar da hankali. "To Dr muna godiya sosai Allah ya bar zumunci." "Amin." Dr ya amsa ya na mika masa takaddan da ya rubuta sunan maganin. Daga haka suka yi sallama, ko da suka fita ba su nufi gidan su ba sai kawai ya nufi gidan Mummy da ita. A falo suka samu Mummy tana ganin Rufaida ta mik'e cikin sauri tare da kulawa tana kamo hannunta fadi take 'yata Barka da zuwa, kune a wannan lokacin?" Rufaida dai da kyar ta iya gaida Mummy sai wani sinne kai take ala dole tana kunya. Shi kam uban tafiyar sai washe baki yake kamar gonar audiga "Daga ina kuke?" Mummy ta tsinka shirun da falon ya yi na yan sakonni. "Asbiti na kaita bata jin dadi." "Ayya sannu'yata, ashe shi yasa na ganki a haka sannu Allah ya baki lafiya, mai yake damunta?" ta yi maganar tana kallon Najeeb. Mika mata takaddan ya yi yana murmushi, "Alhamdulillah! Ta furta murya a bayyane, zuciyarta cike da farin ciki. Sosai Mummy ta nuna farin cikinta, sai ririta Rufaida take sam bata son wani abu ya daga hankalinta, Najeeb dai gidan Mummy ya bar Rufaida da niyyar bayan magriba zai dawo ya dauketa. **** Zaune suke cikin bedroom na Ameesha, Meena da Meesha ne suke hira, sannu a hankali har suka iso kan Dr, Meena sai fadan Alhairin sa da kirkinsa take yi. Meesha tana sauraron. Nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗaura idonta a fuskar Meena ta ce "Wai wa ya bama Dr Asmad damar shigowa gidan nan har cikin falo ne, ranar da zamu fita zaga gari a CAIRO wai Abba har da cewa in tambayi Dr na dade ina mamakin maganar fa?" "Meesha kenan Dr ai yana da matsayin da kike da shi a gidan nan, ke kusan ya fiki ma." Zaro ido ta yi jin maganar Meena ta ce "Haba dai duka yaushe yasan nan gidan da har zai taka matsayin da nake ? Kema wallahi faɗa kawai kike yi." "Allah da gaske Dr yana da matsayin da na sanar maki, wallahi da zaki san irin taimakon da ya yi wa rayuwar ki tabbas da sai kin ninka akan son da kike masa a da, Dr Asmad wani jigo ne a rayuwar ki." "Hmmmm! Bana fahimtar bayanin ki fa, yi min dalla-dalla don nafi ganewa." "Zan yi maki bayani amma ba yanzu ba." Meena tana gama fadin haka ta mik'e tare da fita daga bedroom din. Cikin zallar jin dadi ya dauki hanyar gidan su Ameesha burinsa kawai ya ganta ko hankalinsa zai kwanta, lokacin da ya isa kofar gidan hon ya yiwa maigadin gidan da sauri ya wangale masa get, ciki ya cusa hancin motar a parking space ya yi parking, wayarsa ya kwasa sannan ya fita daga motar cikin kwanciyar hankali yake takusa mai firgita yan mata, hannunsa na juya keys din motarsa, kamar an ce ya dubi gefen haggunsa sai ko idon sa ya sauka kanta, cike da mamaki ya kara bude ido yana kallonta tabbas ita din ce, tsaye da wani mutum idan har ba gizo idonsa ke masa har murmushi ya hango kwance a kan kyakkyawar fuskanta. Wani irin tashin hankali ya ziyarce shi, kishinta da sonta suka rufe masa ido har bai san lokacin da ya isa inda take ba, bai jira komai ba ya finciki hannunta, a firgice take kallonsa ganin kamar ba a hayyacinsa ya ke ba yasa ta yi shiru, shi kam bai zame ko ina da ita ba sai cikin falo jefata kan kujera ya yi sai huci ya ke yi. "Baki da hankali ne zaki je ki tsaya gaban wani kato har kina masa murmushi?" A kausashe yake maganar. Harara ta jefa masa ta ce "ikon Allah kai a suwa kuma *kare da gudun layya*? Ina ruwan ka sani? Bana son shishshigi ban shiga rayuwar ka ba, don haka kaima karka shiga rayuwata, baka isa ka rabani da samarina ba." Cikin karaji ta dire maganar. Murmushin takaici ya yi ya ce "Ni kike tambaya matsayina a gareki? Tabbas kuwa nike da matsayi da iko dake." Dariyar rainin hankali ta masa ta ce, "kenan kaine Abba? Don nasan babu mai iko dani kamar Abba, idan ko kai ba Abbana bane waye kai?" "Mijinki ne ni." Ya bata amsa kai tsaye. Wani irin ihu Meesha ta yi cike da tashin hankali ta ce"..." _*YAR MUTAN RANO*_ [10/8, 8:17 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* My Wattpad username *ZulayheartRano89* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* ```Wannan page din Sadaukarwa ne ga KHADIJA BEE BEEN MASOYA uwar Ilham mata a wajen Hafiz, uwargida kike kinfi amarya 😉 Hajiya ki daɗe ki karko ki yi shekaru irin na dabino, Allah ya ja zamanin ta Masoya mai Masoya da yawa, wannan kirarin duk domin ki ne ke ɗaya Հմʆαίհզ ɾզησ tαηα ψίηKi ιяσи ѕσѕαι ∂ιи иαи😍😍😍``` *37* "Miji? Mijin wa kenan?" "Mijin Maryerm Taheer Ameesha, don haka ina kara gargadin ki da ki shiga hankalinki wallahi idan ba haka sai kin gane kuranki." Yana gama faɗa mata haka ya juya fuuu ya bar gidan ma gaba ɗaya domin ransa ya ɓaci da kallon Ameesha da wani. Ita kam Meesha duniyar mamaki ta shi da jin furucin Dr "Wai mijina! To ta ya har ya zama mijina da har yake ikirari?" A bayyane take wannan tambayar da sauri ganin bata da amsa, sai ta nufi bedroom din Ummi domin samun amsoshin tambayoyin ta. Ko sallama bata yi ba ta shige cikin dakin, Ummi dake zaune tana linke kayan da aka gogo mata sai ganin Ameesha ta yi a yam a kanta kamar wacce aka jeho. "Oh! Ni Halima ke kam Auta zanga ranar da zaki yi hankali, lafiya kika shigo min daki a wannan yanayin?" Kukan shagwaɓa ta fashe da shi ta zube a wajen "Ke nifa bana son rashin hankali, daga tambaya sai ki kama kuka, naga alamar ke kullum SANGARTAR ki gaba take, idan ba zaki bani amsa ba tashi ki fita." Mik'ewa ta yi tare da ficewa, a cewar ta Ummi ta kara bata mata rai, girgiza kai Ummi ta yi tare da fadin "Allah ya shirya min ke Ameesha." Ta gama maganar tana ci gaba da abin da take yi. Ameesha kam bedroom ɗinta ta shige inda ta ci gaba da kukanta, wani tunani ta yi wanda yasa ta yi saurin mik'ewa sai alokacin maganganun Meena ke dawo mata *"Meesha kenan Dr ai yana da matsayin da kike da shi a gidan nan, ke kusan ya fiki ma."* *"Allah da gaske Dr yana da matsayin da na sanar maki, wallahi da zaki san irin taimakon da ya yi wa rayuwar ki to tabbas da babu raini har abada tsakanin ku, kuma sai soyayyar da kike masa ta karu, Asmad wani jigo ne a rayuwar ki* "JIGO? ta yi tambayar a bayyane, "kenan jigo na nufin mijina ne? Ta ya ya zama mijina? Me yasa daga ranar da na tuna komai zuwa yau ban fahimta ba?" Wa zan tara da wandinnan tarin tambayoyin? "Abba." Shi ne amsa da wata zuciyar ta bata amsa. Wani sabon kuka ta fashe da shi, wata zuciyar tana farin cikin samun Dr matsayin miji, wata zuciyar kuma tana alhini, a haka bacci ya yi awon gaba da ita. Dr kan ransa a matukar ɓace ya bar gidan, zuciyarsa wani irin zafi take masa, bai san son da yake wa Ameesha ya zarta har haka ba, ji yake kamar zuciyarsa zata faso, kasa zuwa gidansa ya yi sai ya dauki hanyar gidan Nenne, idonsa jawur kamar garwashin. Ko parking Mai kyau bai tsaya ya yi ba, ya fita daga motar cikin kai tsaye falo ya shi da wani irin sauri, sallama ma kasawa ya yi sai zubewa da ya yi akan kujera. Bobbo da Nenne a tare suka ɗago da kai suna kallon Asmad wanda yake dafe kansa da hannu bibbiyu "Lafiya?" Nenne ta yi masa tambaya. "Babu komai." Ya basu amsa yana a yadda yake. "Kai karka faɗa min zancen banza, ya ana tambayarka kana faɗa mana babu komai bayan ga a yanayin da ka shigo? A fusace Bobbo ya dire maganar. "So nake Maryerm ta tare cikin satin nan." Jikinsa ko alamar motsi baiyi ba ya yi maganar. "Maryerm ta tare anya kana cikin nutsuwarka kuwa Asmad?" "Eh! Nenne ina cikin hankalina." "To bazata tare a satin nan ba ka ji na faɗa maka, tashi ka bamu waje shashasha kawai." Cikin faɗa Bobbo yake maganar. Sai a lokacin ya dago kansa tare da bude ido sa, wanda suke masa nauyi, hankalinsu ya tashi da ganin yadda Asmad ya koma. Dafa kansa Nenne ta yi tana faɗin "Asmad ka riƙa hakuri da duniya saurin fushi yana kawo dana sani, riƙa maimaita inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, zaka samu sassauci." Gyada kai ya yi cikin zuciyarsa yana maimaita inna lillahi, a hankali ya ji zafin zuciyarsa yana ragu wa, su kam kallonsa kawai su ke yi, ganin an kira magriba sai Bobbo ya fita Masallaci, Nenne dai bata matsa ko ina ba har sai da ta ji abin da yasa ɗanta ɗaya tillo damuwa. "Ina jinka Asmad ɗina mai ya sameka haka?" "Nenne wai na je gidan su Ameesha shi ne na ganta da wani a tsaye, wallahil azeem Nenne raina ya mugun ɓaci har dai na kasa danne kishina na yi mata magana Allah Nenne baki ji amsar da ta bani ba." Cikin takaici ya gama maganar. "To ka yi hakuri, Ameesha dai matarka ce, komai dadewa zata tare gidan ka, da kanka zaka koya mata yadda zata soka kuma bana tunanin tasan kai miji ne a gare ta, na tabbatar da saurayi ne yazo wajen ta Hajiya Halima ba zata barta ba, babu mamaki cikin masu zuwa dubata ne. saurin fushi yanzu ba naka bane kaji ko?" "To amma Nenne sai ta saka shi gaba har tana masa murmushi?" "Ka dai yi hakuri na ce, tashi ka je ka yi sallah lokaci na tafiya." Kai ya gyada alamar ya gamsu da bayanin Nenne ****** A gajiye Alhaji Taheer ya shiga gida, yau ko bedroom ɗinsa bai nufa ba, a babban falo ya yada zango, yana furta "Wash! "Sannu da dawowa Alhaji ya aikin?" Ummi ta yi maganar tana mika masa sassanyan ruwa. "Aikin Alhamdulillah! Wallahi na gaji sosai, duk na kosa in dawo." Abba ya yi maganar bayan ya gama shan ruwan. "Ai gaka ka dawo hankali ya kwanta." Cikin murmushi ta fada. "Lallai kuwa Halima tunda na yi tozali da ke hankalina ya kwanta." "Hmmm! Alhaji kenan." Ummi ta, ka yi wanka lokacin sallah ya gabato go." "Mu je uwargida kuma amarya." Cike da farin ciki Abba ya fita Masallaci, ko da ya dawo a falo ya yada zango, Ummi ce ta fito cikin kwalliyar ta, kusa da Alhaji Taheer ta zauna tana faɗin "Alhaji an dawo?". "Eh! Na dawo." Ya bata amsa. "Abinci na jiranka." "Ok wai ina yaran gidan ne? Uwata fa tunda na dawo ban ji motsinta ba?" "Rigimammiya Ameesha ɗazun ta shigo wai zata tambayeni, na ce akan me shi ne ta fara kukan sangarta bata ce min komai ba ta fita, to nidai daga haka ban kuma ganin ta ba." "Kuka?" Abba ya tambaya cikin mamaki. "Eh! Alhaji Ummi ta tabbatar masa. Wayarsa ya jawo Number Ameesha ya kira ringing biyu ta dauka muryar irin ta mai bacci. "Subhanallah! Uwata lafiya kuwa?" Shagwaɓe fuska ta yi kamar zata yi kuka ta ce "Abba Dr ne." "Dr kuma me ya faru da Dr?" A rude yake mata tambayar. Wannan karan bata yi magana ba sai kuka da ta fashe da shi mai tsuma zuciya, hankalin Abba ba karamin tashi ya yi ba da jin kukan Ameesha don haka cikin sauri ya ce "Sauko ina falo kin jiko ki daina kuka haka nan." Ummi dai zubawa sarautar Allah ido ta yi har zuwa lokacin da Meesha ta sauko, kusa da Abba ta zauna tare da ɗaura kanta a kafadar Abban, har a time ɗin idonta na hawaye, saurin sa hannu ya yi yana share mata. "Sorry uwata ki bar kuka me ya samu Dr?" "Abba da gaske wai Dr Asmad mijina ne?" "Wa ya faɗa maki?" Abba ya yi tambayar yana dan bubbuga kafadar ta. "Shi da kansa ya faɗa min." "To kuma shi ne abin tada hankali uwata?" Cin kwanta da hankali Abba ke Magana. Wasu hawaye ne suka kuma zubowa ta ce "Abba ta ya har ya zama mijina bayan Bama son junanmu?" Murmushi Abba ya yi cikin nutsuwar da lallama ya warware mata komai, babu abin da Abba ya boye mata, kuka sosai Meesha ta yi domin jin yadda Alhaji Mansur ya kirata mahaukaciya sannan ya yiwa Abban ta walak'anci, sosai ta yaba da mutuncin Dr da na Bobbo domin sune silar samun nutsuwar mahaifinta, sai dai bata so yadda auren ya zama kamar na hadi ba, taso taji labarin Dr da kansa ya ce yana sonta ba wai mahaifinsa ya nemi a ɗaura ba kamar yadda ta ji Abba ya fada Wani irin zabura ta yi ta ce "Abba Dr Asmad shi ne mijina? Abba shi ne fa wanda ya mareni a sahad." Wani irin zabura Alhaji Taheer ya yi cikin tashin hankali ya ce what..?" _Nima Yar mutan Rano tsawar da Abba ya yi ce tasani jifa da wayata, Ni kam har na firgita da yanayin Abban Ameesha🤔 wai to mai yake shiri cewa ne? Kardai ku manta Abba ya dau alkawarin duk ranar da ya yi ido hudu da wanda ya mari Ameesha sai ya hukunta shi._ _To kuma yanzu wane hukunci zaiwa Dr Asmad? ku biyoni don jin yadda zata kaya_ *Allah ya baki lafiya bestyna Khadija s Muhammad please kusa min ita a addu'a👏* _*YAR MUTAN RANO*_ [10/8, 8:17 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* My Wattpad username *ZulayheartRano89* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* *38* "Au dama Dr Asmad ne ya yi maki wannan walak'ancin?" "Eh! Abbana." Meesha ta bashi tabbaci. "Ai ko sai na nuna masa kurakuransa tunda ya taɓa min uwata." "Yawwa Abba wallahi ka nuna masa kurakuransa, har yau idan na tuna marin raina yakan ɓaci, kuma fa shi ne sanadin da na daina zuwa sahad yanzu." "Yi hakuri 'yar Abbanta tabbas Dr bai kyauta ba, don haka zan dau mataki, tashi ki ci abinci." "Bari na je na yi wanka tashina daga bacci kenan ko wanke baki ban yi ba." "A fito lafiya, amma don Allah Mamina a daina baccin yamma." Dariya sosai Ameesha ta yi jin yadda Abba ya yi maganar, kamar wani marayan yaro "Na daina in sha Allah." "Allah ya yi albarka, je ki fito ina nan tare za mu yi dinner." Amsawa ta yi tana tattaka matakalar benen. A jiyar zuciya Ummi ta saki, domin tun ɗazun ta suma da jin maganganun Abba da 'yarsa, gyara zama ta yi tare da maida hankali kan Alhaji Taheer ta ce "Alhaji da gaske mataki zaka ɗauka kan Dr Asmad?" "Me kika gani?" "Na ji kana tabbatarwa da Auta ne, to wallahi Allah tun wuri ka sake tunani, wannan SANGARTAR da kake nunawa Auta sam ba abin arziki ba, kai yanzu ko shawara aka baka sai ka ɗauka Alhaji?" Cikin sanyi take maganar. Murmushi ya yi irin tasu ta manya ya ce "Haba Halima! Ai karen hauka bai cijeni ba, da har zan ce zan ɗauki mataki akan Dr Asmad, ba Dr ba wallahi ko wanine babu abin da zan masa, kin san menene hikimar amsa mata zan dau mataki?" Girgiza kai Ummi ta yi idonta na kan fuskar Alhaji Taheer. "Saboda yanzu uwata ta zama hukuma sai da lallashi, yanzu da ace ba haka na ce mata sanin kanki ne da yanzu bata bar kuka ba, to kin ji dalilin amsa mata, ai kaf duniya uwata bata da wani miji sama da Dr Asmad." Murmushin nasara Ummi ta yi ta ce "Madallah! Da maigidana abin alfahari na, tunanin ka abin sone ga kowa, Allah ya tabbatar da Alhairi." "Hhhhhhhhh! Tunanina? Ko tunaninki? Ai yanzu duk wani abu da nake aiwatarwa ke ce SILAH, a da bana gane karatun da ki ke min amma yanzu Alhamdulillah! Allah ya maki albarka." "Amin." Ummi ta amsa sannan suka ci gaba da hira, a haka Meesha ta same su, kai tsaye dining suka nufa domin yin dinner, sai a time ɗin Haydar ya dawo gida. Bayan sun gama cin abinci, Ameesha suka ci gaba da hira ita da Abba rabi duk nusiha ne, ta yadda zata kula da Dr, domin cikin hikima da basira Abba ya tabbatar mata da aurenta da Dr babu fashi, domin dai Dr Alhairi ne a gare su. Bayan duk ta gama jin bayanin Abba, sai ta mik'e cikin zallar SANGARTAR ta fashe da kuka, harda bubbuga kafa kamar dai wata karamar yarinya, da gudu ta kwasa ta yi sama cikin fushi. Duk yadda Abba yaso ya shawo kanta abin ya gagara sai kawai ya barta. Da niyyar da safe zai lallasheta **** Yanzu dai zaman Dr da Aneesa sai madallah, domin tana kokarin yi masa duk wani biyayya, wannan duk aikin Rukky ne, a cewar ta ta haka ne zata samu Dr a hannu kafin Ameesha tazo. Dr kansa ya ji dadin haka, domin ranar suna zaune bayan sun gama love dinsu, Aneesa tana jikinsa sai shagwaɓa take zuba masa, sai ya ɗago da fuskarta ya manna mata kiss ya ce "My Anne don Allah Yanzu baki jin dadin zaman da muke yi?" Wani murmushi ne ya bayyana akan fuskarta ta ce "Ni kam ke ji, yanzu ko da yaushe ina tare da mijina mu yi bacci tare mu ci abinci tare, kana nuna min soyayya komai duk wani hakki nawa kana kokarin saukewa, nikam a duniya mai ta kai min wannan daɗi? Wallahi Hamman ba bi shi." "To kinga wallahi kaf duniya zaman lafiya ya fi komai, don haka Please mu zauna lafiya da juna ko da abokiyar zamanki ta zo a daure a rika kai zuciya nesa." Wani irin faduwar gaba ta ji da ya ambato abokiyar zama, ita da har ta manta da wata matarsa, sai yanzu da ya tuna mata, da kyar ta iya tattaro nutsuwarta ta ce "Karka damu Hamman baza'a samu matsala ba da yaddar Allah." "Allah ya maki albarka matata." "Amin." Ta amsa tana sauka daga jikinsa, toilet ta faɗa sai da ta sha kukanta kafin ta yi wanka ta fito, tana fitowa ya shiga ko kafin ya fito, har ta gama shafe-shafenta ta kwanta kamar mai bacci, alhalin kan ba bacci take ba kishi ne ya motsa. Magana ya yi mata, tunda ya ji ta yi shiru sai kawai ya kwanta a bayanta, tare da rungumota jikinsa a haka bacci ya yi awon gaba da shi. Ta daɗe tana takaici kafin bacci ya kwashe ta. Da asbah kusan a tare suka farka, Dr toilet ya shiga ya dauro alwala sannan ya wuce masallaci, Aneesa kam bedroom ɗinta ta koma, sallah ta gabatar sannan ta koma bacci, sam ta ji bazata iya haɗa masa abin break ba, domin da takaicin sa ta kwana. Bayan ya dawo masallaci, karatun Alkur'ani ya yi, ko da ya kammala sai ya dan kwanta domin dai ba zai fita office da wuri ba, nannauyan bacci ya kwashe shi, bai farka ba sai 9:30 shi din ma wata mahaukaciyar yunwa ta tayar da shi. Wanka ya yi ya yi shirin fita, falo ya fita babu kowa ya duba dining babu komai akan dining din, sai ya nufi bedroom a kwance ya hango ta ta yi dai dai tana ci gaba da sharar bacci. Cikin takaici ya girgiza kai tare da fita daga gidan gaba daya, gidan Nenne ya nufa don yasan can suna da komai, bayan sun gaisa ne ya ce "Nenne yunwa ta biyo dani nan gidan fa." "Yunwa ina Aneesar?" Nenne ta tambaya cike da mamaki. "Wallahi Nenne bacci take yi kamar dai bata jin dadin jikinta ne." Ya ɓoye don kar Nenne ta fahimci wani abu. "Allah ya bata lafiya." Shi ne abin da Nenne ta faɗa tana nufa dining, mintina ƙalilan Nenne ta kawo masa break, yana ci suna hira har suka sauka kan na Ameesha gyara zama Nenne ta yi tana fuskantar Dr ta ce "Wai kuwa Asmad ka koma gidansu Ameesha?" "Ban koma ba Nenne." Kai tsaye ya bata amsa. "Menene dalili?" "Bana son ta kuma bata min rai." "Kai bana son shashanci, ko ka manta matarka ce Ameesha, dole sai kana mantawa da wasu abubuwan kuma ai ɗan Adam ajazi ne, tana da hakki akan ka, don haka ya zama wajibi ka kula da hakkin ta." "To Nenne in sha Allah, yau zan biya idan na dawo." Yana maganar ne bayan ya mik'e tsaye. "Allah ya yi albarka." Daga haka Dr ya bar gidan, ko da ya isa office bai wani jima ba, domin babu wani aiki tunda ranar ta ƙkasance asabar ne, da ya bar asbiti, wani mall ya biya ya yiwa Ameesha shopping don yasan ta da shan kayan zaki, yana fita diret gidan Alhaji Taheer ya nufa, ya yi hon maigadi ya buɗe masa, ya faka motar sannan ya daga waya ya kira number ɗinta. Lokacin tana zaune ta yi nisa cikin tunaninsa, sai yanzu take dana sanin abin da ta masa ga shi rabon ta da shi tun ranar da ya bar gidan cikin zuciya babu mamaki ma fushi ya yi da ita. Wayar ta ce dake kusa da ita ta fara ruri, a zabura ta kalli wayar, har murza ido ta yi don son ta gasgata abin da ta gani tabbas Number Dr Asmad ne, cikin sanyin jiki ta ɗauki wayar tare da karawa a kunne "Assalamu Alaikum." Ta furta cikin siririyar murya. Daga ɓangaren Dr sai da ya saki ajiyar zuciya jin muryar Ameesha "Wa'alaikumus salam, ki fito ina jiran ki domin sauri nake." Abin da ya faɗa kenan ya kashe wayar. Jiki a sanyaye ta mik'e ta kudirta sai ta ba Dr haushi tunda haka yake faɗa mata, sai da ta gyara fuskarta, ta nufi bedroom din Ummi, sanar mata ta yi da zuwan Dr ya ce "Yana jirana." "To ki shigo da shi falo mana, ke kamar wata mara wayau ki ke." Ummi ta faɗa cikin takaici. "To." Ta amsa tana nufa waje. Jingine yake jikin motarsa, ya zubawa hanyar da Ameesha zata fito ido, can yaga ta nufo wajensa cikin takunta mai daukar hankali, sosai ta tafi da hankalinsa har bai san time da ta iso wajen ba, sai jin sansanyar kamshi turarenta da ya gauraye wajen, dogo da kai ya yi tare da zuba mata ido. "Sannu da zuwa." Ta faɗa tana kauda kai gefe. "Yawwa." Ya amsa a dakile, shiru ne ya ratsa na yan dakiku, sannan yasa hannu cikin mota ya dauko mata ledar da ya shigo mata da shi, yana tambayarta "Ga wannan ki yi amfani da shi, baki jin komai a jikinki ko?" "Eh!" Ta bashi amsa. Bata da niyyar amsan ledar. "Princess ke fa nake mik'awa?" "No! Dr ka barshi kawai na gode." Da mamaki ya kalleta, cikin zuciyarsa ya ce "lallai yarinyar nan, Ni kikawa laifi amma kuma ke kike jin haushi na, aikam sai kin gane kuranki. A fili kam sai ya ce "amsa ki kaiwa Meena, tunda ke baki buk'ata." Babu musu ta amsa, Dr dai kuma kallonta ya yi ya ce "Dama nazo dubaki ne tunda babu matsala zan wuce." Ya ida maganar yana buɗe kofar motar "Ina son zuwa gidan Nenne." "Allah ya dawo da ke lafiya, amma ki sani karki kuskura ki tuka mota da kanki." Yana maganar ne yana kunna motar, ko kafin Ameesha ta yi magana sai ganin motar Abba suka yi. Cikin sauri Dr ya fito yana gaida Abba cikin yanayi me nuna alamar jin kunya, Abba ya amsa cikin sakin fuska yana tambayarsa su Bobbo "Duk suna lafiya." Dr ya bashi amsa, kanshi a kasa. "Naji daɗin zuwanka domin tun jiya naso kiranka, akan ka fara shiri uwata ta tare a ɗakinta, zamanta haka babu amfani, kamar yaushe kake ganin zata tare ɗin?" Shiru Dr ya yi, har yanzu kanshi a kasa, bai nuna alamar zai yi magana ba. Duk dai a zuciyarshi Sosai ya ji dadin maganar Abba, don dama haka yake so kuma ga damar ta samu. "Ko akwai matsala ne?" Abba ya tambaya gani shirun ya yi yawa Har yanzu kanshi a kasa yake, yayin da ya kai hannunshi yana shafo kanshi "To Abba, amma akwai wasu yan gyare-gyaren da zan yiwa bangaren ta, nan da sati biyu zafi kyau." Cikin ladabi ya yi maganar. "Allah ya kaimu." Daga haka suka yi sallama. _*YAR MUTAN RANO*_ [10/8, 8:17 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga khadija s Muhammad My Besty* *39* Gida kai tsaye Dr ya nufa, bayan ya kira Hafiz ya sanar masa, yadda suka yi da Abba, cikin kwanakin sam Dr baya samun zama domin aikin da akewa sashin Ameesha, suma a bangaren Nenne da Ummi abin haka yake, Ameesha tana ta shan gyara, wata mata aka dauko mata musamman domin ta gyara ta. Shirye-shiryen biki ya kankama yau saura kwana biyu tarewa, duka gidajen biyu cike yake da mutane wanda suka zo domin taya su murna, sosai Dr ya yi bajinta wajen haɗa mata akwatina. Aneesa kam idan hankalinta ya yi dubu to fa a tashe yake, musamman da taga irin kuɗin da Dr ya kashe wa Ameesha, duk sai ta ji ta raina kanta. Cikin tashin hankali ta dauki waya ta danna Number din Rukky ringing biyu ta dauka "Hello Rukky! Aneesa ta faɗa cike da tashin hankali. "K'awata lafiya kuwa na ji muryar ki a haka?" "Babu lafiya kam domin jibi matar Hamman zata tare, kin ga irin kuɗin da yake kashe mata kuwa?" "Ina zan sani ina Adamawa kina Kano?" Rukky ta faɗa. "Wallahi kuwa Rukky, wallahi ina cikin tashin hankali, Please ki bani shawara." "Kin ga Aneesa kwantar da hankalinki, ki bari ta tare sai asan yadda za'a yi, amma ki fito fili ki nuna masa fushinki." "Hmmmm! Rukky kenan wai kina ganin Hamman yana wani damuwa ne idan yaga ina fushi?" "Ko baya damuwa ki nuna masa." "To shi kenan zan jaraba, zaki ji komai." Daga haka suka yi sallama, ita kam Aneesa ta ci gaba da kai komo tana neman mafita. Wow gaskiya bangaren da za'a sanya Ameesha ya haɗu sosai, tuni aka kawo kanya daki an daka komai sai jiran zuwan amarya, Dr kam cike yake da farin ciki, ko yaushe fuskarsa ɗauke da murmushi. Dinner kawai suka shirya, wanda za'a yi ranar tarewar, Dr ya yi gayyata sosai musamman abokansa da abokan aikinsa na kasashe daban daban, ciki har da Dr Ansar wanda ya taso takanas don hidimar bikin Dr Asmad, ya samu tarba mai kyau daga Hafiz domin shi ne ma masaukin baki, kuma babban abokin ango. Abba, Bobbo da Dr, sai Hafiz angon wata dakakkiyar shadda suka yi, zanenta iri ɗaya da ta su ya Jaheed sai dai kalar ya bambanta, karfe uku aka tashi daga walimar da Bobbo ya haɗa don farin cikin Auren Asmad Nenne da Bobbo suka zaunar da Dr suna masa nasiha akan ya riki matansa cikin amana da adalci "Kana jina ko Asmad? Ina so ka sanya hakuri da juriya da kai zuciya nesa a cikin zamantakewar ku, ka kasance mai adalci tsakanin matanka, ka zama tsayayye namiji mai mulkar da adalci." "In sha Allah Babbo zan yi amfani da duk abin da ka faɗa min." "Allah ya maka albarka, Ubangiji ya baka zuri'a dayyaba." "Amin." Dr ya amsa. Ita ma Nenne haka ta yi masa nasiha mai tsuma zuciya, kafin suka sallame shi. Komawa cikin abokansa ya yi inda aka ci gaba da harkoki. Ameesha da Dr Asmad yau ranar ta kasance ranar farin ciki ne a gare su, kallon fuskarsu kawai zai baka tabbacin haka, sanye take ciki wani rantsattsen lacce mara nauyi, wanda ya yi mugun amsar jikinta fuskar nan ta sha meka'up har wani kyalli take, duk inda ta gifta sai kamshin turarenta ke tashi, kawaye ta duk sun halarci taron tarewar ta, ciki har da Ni'eema sosai Ameesha ta yi farin cikin ganin ta. Liyafa sosai aka hada, an ci kuma an sha, an dauki hotuna domin tarihi kai abin dai gwanin sha'awa cikin lafiya da salama aka gudanar da taron, karfe biyar Abba da kansa ya kai Ameesha gida Dr bayan tarin nasihar da tasha a wajen Ummi da Abba, kuka sosai ta yi har idonta ya yi jawur. Ko time da Abba yasata cikin ɗakinta sai da ya kuma mata nasiha, mai sanyaya zuciya, kafin ya yi mata sallama, shiru ta yi zaune cikin dakin ita ɗaya hawaye suna zubowa daga cikin idonta, maganar Abba ta karshe ita ta kuma sanyaya mata jiki *"Uwata ki sani ni da kaina na kawoki gidan aurenki, duk ranar da kika fita daga gidan nan da sunan ya ji karki kuskura ki nufo gidana, domin nan shi ne gidanki marufar asirin ki, mutuwa kaɗai nake fatan ta rabaki da gidan nan, Allah ya maki albarka."* Cikin murya mai kamar ta kuka ya gama maganar, don taga lokacin da yasa hannu ya share hawaye. A fili ta furta "In sha Allah Abba zan yi maka biyayya." Ta yi maganar tana share wasu hawaye da suka zubo. Sai kuma ta tuno nasihar Ummi, kamar yanzu take mata maganar "Ameesha ki kula da jinsa, ganinsa, da kuma dandanon mijinki, *1 karki bari ya ji wani abu da daga hankalinsa, ko ta tsaftar jikinki, jikinki ya kasance ko yaushe cikin kamshi na turaruka, haka falonki da ɗakunan baccinku, bakinki da duk wani lungu da sako na jikinki* *2 ma'ana karki bari yaga wani abu da zai bata ransa akanki, musamman ta bangaren gidanki ko jikinki* *1 karki kasance kullum cikin girka masa abinci kala ɗaya, a'a ko wacce rana ki yi masa kaloli daban-daban kuma ba guda ɗaya ya ba ki yi hakuri da biyayya, karki kuskura ki bijirewa umarninsa domin aljannarki tana karkashin kafarsa, duk maganar da zaki yi masa ta zama cikin tsusasa murya da nutsuwa, in sha Allah matukar kika lazumci yin haka zaki ci ribar zaman aure.* Tana cikin wannan tunanin ne ta jiyo motsin mutane kamar a falo, ko kafin ta yi wani kwaukwarar motsi har sun shigo bedroom din, muryar Aunty Saude k'anwar Ummi ta ji, ai da sauri ta daga gyalen ta sauka a gadon tana faɗin "Sannu Aunty dama yanzu nake tunanin ni kadai a gidan har tsoro ya fara kamani." "Nima Aunty Halima ta sanyamu zuwa, don ta ce bata son abarki ke ɗaya, nan da wasu awanni idan zaku je dinner zamu koma." "Ai kam na gode wa Ummina." Hira suka shiga yi da Aunty Saude har lokacin da Dr ya bugo mata waya akan ta shirya, mai mata kwalliya zata shigo don yi mata "To." Ta amsa tana gyara kwanciya. Mintina ƙalilan ta ji sallama, lokacin Meena da wasu daga cikin kawayenta sun iso gidan, wanka Meesha ta sake sannan tare da dauro alwala, tana cikin sallah mai mata kwalliya ta iso, bayan ta isar Aunty Teena ta tsantsara mata kwalliya sosai Meesha ta yi kyau, gama kwalliyar babu dadewa motocin su Dr ya iso, cikin rakiyar Meena ta isa wajen motar da Dr ke ciki, cikin sanyin murya ta yi sallama tare da shiga, amsawa ya yi cikin kasalalliyar murya yana lumshe ido, domin kamashin turaren ta ya kashe masa jiki, Meesha kam kasa ta yi da kanta don ji ta yi a takure take. A haka suka isa wajen, lokacin wajen ya cika sosai da dan adam, suna zuwa aka soma gudanar da shagalin. Sosai dinner ta yi kyau, anci an sha, Aneesa ma an halarci wajen dinner, sosai ta yi kokarin danne kishinta har aka tashi, karfe goma aka tashi gida Dr da Ameesha kawai suka nufi gidan Rike da hannunta Dr yake har cikin bedroom ɗinta, akan gadon ta ya yi mata masauki, yana faɗin "Heartbeat ki zauna ki huta ina zuwa." Ya yi maganar yana buɗe gyalen ta. Saurin rintse ido ta yi, domin yadda yake mata wani irin kallo, da kyar ta iya daga kai ta amsa, domin gaba daya jinta take kamar a daure, murmushi ya saki sannan ya bar dakin. Mota ya dauka bai dade da fita ba ya dawo, hannunsa dauke da manyan ledoji, falon Ameesha ya shiga ya aje, sannan ya nufi bangaren Aneesa, a falo ya iskota ta zuba uban tagumi, zama ya yi kusa da ita yana faɗin "My Anne baki kwanta ba?" "Yanzu nake son kwanciyar." Ta bashi amsa tana mik'ewa. "Ok ga wannan bari." Ya yi maganar yana mik'a mata." Ko kallonsa bata tsaya yi ba, ta yi shigewarta idonta taf da hawaye, tsaye Dr ya yi cikin mamaki halin Aneesa, sai kuma ya nufi bedroom ɗinta tunawa da ya yi da Ameesha ita ɗaya. A kan gado ya ga ta zube tana aikin kuka, da kyar ya lallasheta ya nufi bangaren Ameesha, tana ganin ya fita ta kuma sakin wani kukan, Dr kam ko da ya koma bed din Ameesha a kwance ya sameta. "Heartbeat ba dai har kin yi bacci ba?" "Zan yi dai." Ta bashi amsa. "Oya tashi ba zaki kwanta da yunwa ba." "Dr nifa na koshi." "No! Maryam tashi ki ci." Tashi ta yi tana turo baki, falo ya koma ya dauko plet, juye masu lafiyayyen kasashen kaji ya yi, ya tsiyaya masu fresh milk a glass cup, lallaɓata ya yi ta ci kadan ta ce ta koshi "Je ki yi brosh sai ki kwanta nasan kin gaji da yawa." "To." Ta amsa tana mik'ewa, bata jima ba ta fito kwanciya ta yi tana addu'ar bacci, bata daɗe da kwanciya ba bacci ya kwashe ta. Murmushi Dr ya yi ganin har bacci ya kwashe Ameesha, lallai bata da wuyar bacci, sai a lokacin ya soma ci, sai da ya koshi sannan ya tattara kayan ya kai kicin, dawowa ya yi yana tofe ta da addu'a ya rufe ta da bargo tare da kara mata gudun AC sannan ya fita. *YAR MUTAN RANO* [10/8, 8:17 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga khadija s Muhammad My Besty* *40* Bedroom ɗinsa ya nufa, sai da ya soma rage kayan jikinsa sannan ya faɗa toilet ruwa ya watsawa jikinsa, bayan ya fito ya gabatar da sallah, jikinsa ya shafe da mai tare da feshe ko ina da turarr, kayan bacci ya sanya sai ya bi lafin gado bakin sa dauke da addu'a, bai wani dade ba bacci ya yi a won gaba da shi, mai cike da mafarkin Ameesha. Kiran sallar asuba ya farkar da shi, mika ya yi tare da addu'a kana ya nufi toilet ya dauro alwala, bai ta yar da sallah ba sai da ya je dakin Ameesha wacce ke sharar bacci, a hankali ya matsa inda take tare da kai lallausan hannunsa fuskarta yana mata waiwayi. Buɗe idonta ta yi mai cike da bacci, ta zuba su bisa fuskar Dr. "Lokacin sallah ya yi tashi ki yi." Mika ta yi tare da hamma alamar dai bacci bai isheta ba, ta amsa da "To." Yana zaune har ta shiga ta fito, sannan ya jasu sallah suna idarwa Ameesha ta sanyaya murya ta ce "Ina kwana Dr!" "Lafiya lau Heartbeat fatan kin tashi lafiya ya sabon waje?" Murmushi ta yi kanta a kasa ta ce "Alhamdulillah!" "Madallah! Yanzu dai nasan kina da buk'atar hutu, je ki kwanta ki huta zuwa anjima." Mik'ewa ta yi ta nufi gadon, shima Dr gadon ya nufa ya kwanta cikin hikima ya jawota jikinsa tare da rungumota, kamar zai mai da ta ciki duk da son jiki irin na Ameesha amma ganin yadda Dr ya cusata jikinsa sai ta fara k'ok'ari janye jikinta, shi kuma ya ki barinta, gajiya ta yi ta barshi a haka bacci ya kwashe su. Basu farka ba sai karfe tara, Dr ne ya soma tashi sannan Ameesha bed ɗinsa ya nufa don yin wanka, shaf shaf Dr ya yi wanka ya fita, kai tsaye bangaren Aneesa ya nufa. A hakimce ya ganta zaune kan kujera, ko sallamar da ya yi kin amsa masa ta yi "Kin tashi lafiya?" Banza ta kuma masa, bai yi zuciya ba ya kuma faɗin "Kin yi break ne?" Mtsss ta ja tsaki ta ce "Ina ruwanka da break ɗin na? Kai dai ba kana can tare da matarka ba, kaga kenan rashin yin break na ba matsalar ka ba ce." Tana dire maganar ta yi shigewarta bedroom. Tsayawa kawai Dr ya yi yana kallon Aneesa, tun yana mamakin halinta zuwa yanzu har ya daina, nannauyan ajiyar zuciya ya sauke tare da kaɗa kai ya fita. Mota ya ɗauka ya fita, don nemo masu abin da za su ci, bai ta de ba ya dawo, wannan karon ma falonta ya shiga, mika mata tek away din ya yi ba tare da ya ce komai ba ya fita, yana jin lokacin da ja tsaki. A bangaren Ameesha bayan Dr ya fita itama toilet ta shiga wanka ta sillo daure da towel gaban madubi ta yi masauki, duk ilahirin jikinta ta shafe da mai kafin ta nufi wordrop da niyyar dauko kayanta, sai jin sallamar Dr ta yi take wani irin kunya ta kamata, motsi ma kasawa ta yi don kunya. "Heartbeat baki gama shiryawa ba?" Shiru ta yi ta kasa ko da ɗago kai. Ganin taki magana yasa ya karasa inda take yana faɗin "Kinga Wallahi yunwa nake ji fa kuma nasan kema haka Please bari na shirya ki." Ya yi maganar yana sa hannu cikin wordrop ɗin, kaya ya dauko mata riga da siket da pant and bra, aje su ya yi kan gado tare da riko hannunta. "Please Dr ka barni zan iya sawa fa." A hankali ta yi maganar. "No! Bana so ki wahala bari na shirya ki kawai." "Please.. " Ko sauraron maganar ta bai yi ba, sai ma fara sanya mata pant da bra, tsaf ya shirya ta har yana shafa mata hoda, ita kam sai turo baki take har da kukan sangarta, hannunta ya ja sai falo a dining ya yi mata masauki, don ya yi masu tek away, tsaf ya shirya masu komai a kan dining. Da kansa ya zuba mata komai sannan ya soma bata shi ma yana ci, suna ci suna soyayyar su har suka gama, tashi Ameesha ta yi tare da kwashe duk wani kaya da suka bata ta yi kicin da su, bata fito ba sai da ta wanke tare da gyara kicin ɗin. Dr na zaune shi kadai a falon yana jiran ta fito amma ya ji shiru sai kawai ya bita kicin ɗin, zaro ido ya yi cikin mamaki ya ce "Heartbeat aikin me kike yi kuma?" Murmushi ta saki ta ce "Dr gyara kicin nake yi." "Me yasa baki kirani ba?" "In kiraka ka yi min me?" Da mamaki ta yi tambayar. "Aikin mana." ya bata amsa. "Hmmm! Dr kenan ai wannan ba irin aikinka bane nawa ne don haka na hutace ka." Yadda take maganar kawai abin birgewa ce. Domin har kasala ta saukarwa Dr. "Ni dai ban yadda da wayonki ba, Heartbeat kullum nafi so ki rika hutawa kinji ko?" Ya yi maganar yana jan hancinta. Dariya suka yi gaba daya, ta ce "Na daina Dr." "Yawwa autar Ummi mu je mu gaida Aneesa." "To." Ta amsa tana tafiya. Yana rike da hannunta suka yi sallama a falon Aneesa, Aneesa wacce ke zaune ta buga uban tagumi saurin ɗago da kai ta yi, tana amsawa cikin murmushin karfin hali ganin Dr da Ameesha. Ji ta yi kamar ta tashi ta shake Ameesha, wani irin kishin Dr ke a zalzalar ta, da kyar ta yi control ɗin kanta ta tattaro nutsuwarta ta furta masu "Sannun ku da zuwa." "Yawwa." Yawwa Dr ya amsa . Yana zama a kan kujera Ameesha kuwa a kasa kusa da kafar Dr. "Hamman ina kwana?" "Lafiya lau My Anee ya kika tashi?" "Lafiya lau." "Ina kwana?" Ameesha ta faɗa cikin sanyin murya. "Lafiya." Shi ne amsar da Aneesar ta bata, bayan ta dauki kusan minti biyar kafin ta amsa tana aika mata harara. Gyaran murya Dr ya yi, wanda yasa duk suka nutsu tare da maida hankali kansa, godiya ya soma yi ga Allah da ya nuna masa wannan rana, sannan ya soma masu nusiha cikin kwantar da murya akan su zauna lafiya da junansu baya son tashin hankali. Shiru suka masa har ya gama sannan ya tambaye su ko da mai wata matsala "Babu." Ameesha ta ba shi amsa. Aneesa kam banza ta masa sai jijjiga kai da hura hanci take yi, ko kallon inda suke bata yi ba. "Don Allah ku zauna lafiya, matuk'ar kuka zauna lafiya to kwanciyar hankalina ne, haka in akasin zaman lafiya ta samu wallahi tashin hankalina ne, ku rika kai zuciya nesa ku yi koyi da kishin matan Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama." "Allah ya bamu iko." Cikin siririyar murya ta yi maganar. Aneesa kam ka sa cewa komai ta yi domin, ji ta yi wani kuka yana shirin zuwa mata, tana son Dr son da batawa kanta tana matukar kishinsa wanda har take jin kamar ba zata iya takwara zuciyarta ba, don haka ganin ya gama sai ta mik'e kamar dai wata kububuwa ta yi shigewarta bedroom Ameesha kam hamma ta saki, don ta gaji da zaman, kallonta Dr ya yi ya ce "Ya dai autar Ummi bacci ko?" Kai ta gyaɗa alamar "eh." "Ok tashi mu je ki kwanta." Ya yi maganar yana k'ok'arin tashi tsaye. " *Wai Auta*! Aneesa ta maimaita sunan, wato ma ita ce Auta, sai wani narkewa ta ke masa, hmmmm! Zan yi maganin ku daga ke har shi, ganin yana niyyar tafiya yasa Aneesa ta ce "Hamman ina son zuwa gidan Nenne, domin yau yan Adamawa zasu koma zan je masu sallama." Ta yi maganar ne tana maida kwallar da suke niyyar zubowa. "Allah ya kiyaye hanya." Ya yi maganar yana mik'ewa tsaye rike da hannun Ameesha. Kallonsa ta yi cikin wani irin yanayi, hankalinta ya tashi ganin yadda Dr ya mata, don haka suna fita ta saki wani irin kuka mai cin rai, tana bakin ciki da Auren Dr ta kula son da Dr kewa Ameesha ko kwansa baya mata, lallai sai ta mik'e tsaye domin ta samowa kanta yanci. Dr kam suna fita daga falon ɗaga Ameesha ya yi sama tare da rungumeta, ita kuma sai ciccila kafa take alamar ya sauketa, bai sauketa ba sai ma ci gaba da tafiya da ya yi har suka shiga falonta, a nan ma bai sauketa ba sai juyata da yake kamar wata yar baby. Kukan sangarta ta fashe masa da shi, ko hawaye babu tana ta bubbuga masa kirji "Lalala autar Ummi an ya kuwa kina cin abinci?" "Ni dai ka saukeni gaskiya Dr." "Allah ba zan saukeki ba, tambayarki nake kina cin abinci kuwa?" "Ina ci sosai ma, amma m e ka gani Dr?" "Sam baki da nauyi kamar na ɗauki yar shila." "Ni dai saukeni." Ta yi maganar tana turo baki. Bai sauketa ba sai da ya gama shilla sama, sannan ya direta a kan kujera sai dariya suke yi abin su, kara rungumota jikinsa ya yi yana sinsinar sumar kanta, hannunsa na wasa da sassan jikinta jikin Ameesha duk ya gama saki da salon wasannin da Dr yake mata, a haka bacci ya kwashe su kar'ar wayar Dr e ta farkar da su. Sunan Nenne ya gani a kan screen ɗin wayar, da sauri ya daga tare da sallama. Bayan sun gaisa take tambayarsa ina Ameesha. "Gata nan Nenne bari na bata." Da yake ta tashi har ta bude ido. Mika mata wayar ya yi yana faɗin "Nenne ce ke son magana da ke." Amsa ta yi ta soma gaidata cikin kunya da ladabi har da tsugunawa, abin da ya kara mata daraja a idon Dr kenan " 'yata kin tashi lafiya ya bak'on waje?" "Lafiya lau Nenne." "Madallah! Fatan babu wata matsala?" "Eh! Nenne babu komai." "In har da matsala ki sanar min kin ji ko?" "In sha Allah! Ameesha ta amsa cikin ladabi. Da haka suka yi sallama ta mik'awa Dr wayarsa suka ci gaba da magana da Nenne, ita kam bedroom ta nufa don yin sallah. Zata tayar da sallar kenan Dr ya shigo "Wai har kin yi alwalar?" "Eh! Zan tayar da sallah." "Ok jirani na yi alwala." Yana maganar ne yana shiga toilet. Bayan sun idar suka ci abincin da Dr Asmad ya fita ya sayo masu, sai suka ci gaba da hira har magriba, wannan lokaci Dr ba a gida ya yi sallar ba domin masallaci ya je, bayan ya idar da sallah ya nufi gidan Nenne don ɗauko Aneesa kuma ya gaisa da bakin gidan, bai su shigo gida ba sai bayan ishsha. Ko a mota Aneesa sai cika take tana batsewa, domin da cewa ta yi gidan Nenne zata kwana, da kyar lallabota ta biyo shi, ko da Dr ya bata take away din da ya yo masu kin karba ta yi, har sai da taga ya nuna ɓacin ransa. Ita kam Ameesha bayan ta idar da sallar ishsha zama ta yi tare da ɗaukar littafin addu'oi tana karantawa, sallamar Dr ce ta sanyata ɗago kai. "Sannu da dawowa! Ta yi maganar tana amsan kayan da ya shigo da su. "Yawwa ya zaman kadaici?" Murmushi ta yi kawai ta kai kayan ma'ajinsu. Ruwa ta kawo masa mai sanyi, tas ya shanye ruwan ya aje cup din, zama kusa da shi ta yi tana faɗin "Dr ka daɗe a masallaci." "Ki bari kawai na biya gidan Nenne ne bayan an idar da sallar, kin san Aneesa tana can." "Ok ya Nenne da Bobbo?" "Duk suna lafiya, ga abinci nan na shigo da shi nasan kina jin yunwa ko?" "An gode, amma fa ni Dr bana wani jin yunwa." "Ji beta don Allah wai bata jin yunwa, ko dai baki son cin abinci? Shi yasa kullum baki kiba." Ya yi maganar yana jan kumatunta. Dariya ta yi tare da daukan kayan ta nufi dining room da su "Na gama haɗawa fa Dr." "Ok bari na yi wanka tukun. Ya bata amsa yana tafiya, bai jima da shiga ba ya fito cikin wasu rigar bacci mai kalar milk, tana ganin sa da kayan ta kauda kai dining suka nufa sai da suka koshi Dr ya suri Ameesha bai zame ko ina da ita ba sai kan fadeden gadonsu, da sauri ta tashi zaune "Lafiya kuwa?" Cikin mamaki Dr ya yi tambayar. "Wanka zan yi kuma ban yi brosh ba." "Mu je na yi maki." Zaro ido ta yi, cikin sauri ta ce "A'a." "Please mana My heartbeat." "Don Allah dai Dr ka yi hakuri." "Na hak'ura idan kin gama wankan ki dauro alwala." Ya yi maganar bayan ya aje mata kayan bacci a kan gado. "To." Ta amsa tana shiga toilet, ganin ya fita, ko da ta gama wankan daure da towel ta fito, ganin babu Dr a bed din ta yi saurin isa gaban mirror ta shafe jikinta da mai da turare, jikinta sai fitar da sansanyar kamshi turarenta yake, wajen gadon ta nufa don sanya rigar baccin, "Inna lillahi! Ta furta a fili ganin irin kayan da Dr ya aje mata, sai juya su take tana tunanin ta yadda zata sanya, a haka Dr ya shigo "A'a ya baki shirya ba?" "Dr wannan kayan..." "Mai suka yi?" "Ummh! Ban iya sanyata." "Ok kawo na sanya maki." Ya yi maganar yana nufarta." "Sorry Dr Please." "No! Kawo kawai zan sanya maki." "A'A ka bari zan sa amma ka fita." "Ba zan fita ba, ki je toilet ki sa kina bata min time fa." Ganin ya hada ransa yasa ta nufi toilet, sa kayan ta yi ta tsaya tana k'arewa kanta kallo "Woww." Ta furta ganin yadda kayan suka yi mata kyau, sai dai bata jin zata iya fita a haka don sam kayan basu da maraba da tsirara, riga da wando ne da kadan rigar ta wuce cinya, shi kam wandon har gara babu kalar milk ne, komai a bayyane yake. Dr kam yana zaune yana jiran ta fito ya ji shiru, don haka sai ya nufi toilet din Yana faɗin "Heartbeat ki fito ina jiran ki fa. " Da ya ji shiru sai ya tura kofar, nan take ya bude tsaye ya ganta ta rintsa ido. Kallonta ya yi sosai tare da sakin ajiyar zuciya, hannunta ya riko dogon hijab ya sa mata, kana suka tayar da sallar bayan sun idar ya dafe kanta ya karanto addu'ar da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya umurci ko wane ango ya yiwa amayarsa, yana gama mata addu'oi tare da bata tatacciyar Madara, sannan ya soma tambayarta game da addinin ta, sosai Ameesha ke bashi amsa, ya ji dadin yadda Ameesha ke ba shi amsa, cire mata hijab din ya yi ya ce ta kwanta. Kwanciyarta babu dadewa shi ma Dr ya hau gadon tare da kashe hasken bed room din, da yake tuni ya kashe duk wani kayan wutan falo, bacci ya soma daukarta kenan ta ji mutum a jikinta, sosai hankalinta ya tashi duk iya kokarin ta na gujewa Dr abin ya faskara, sai ma ji ta yi yana karanta addu'ar saduwa da iyali, tsabar azabar da taji yasata sakar masa kuka ganin abin ba mai k'arewa ba, Dr ma bai san tana yi ba ya dauki dogon lokaci kafin ya maida Ameesha cikakkiyar mace, wahala kam ta duniya ta sha shi, albarka kuwa Dr har ba zai iya fadi adadin wanda ya sanyawa Ameesha ba. Don sosai ya ji dadin yadda ya sameta, Aneesa Yar uwarsa ce kuma tabbas shi ya soma saninta, amma Ameesha ta daban ce ba zai iya haɗa matsayin ta da ko wacce mace a zuciyarsa ba. _To sannu Ameesha sangartacciya, yau dai duk ta sangarta ta kare domin kema kin shiga sahun matan aure, Allah ya bada zuri'a dayyaba_ 😍💖💓💗 *YAR MUTAN RANO* [10/8, 8:17 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga khadija s Muhammad My Besty* *Wow gaskiya ina godiya sosai masoya, bani da bakin da zan iya kwatanta farin ciki da nake ciki, sai dai nace Allah ya saka da mafificin Alhairi, ina alfahari da ku😍😍* ```Khadija S Muhammad & Badeeyar Adam (beauty queen) hakika ku ɗin na daban ne, babu abin da zance akan ku, sai Allah ya saka maku da Alhairin sa ya bar mana zumunci har karshen rayuwa. (Aneesa tana gaisuwa lol)``` _*Sorry sister SHAMSHIYA SALIS wallahi na yi missing contact naki, na yi ta jira ko zan ga maganar ki na ji shiru, amma jiya nasa mu Number insha Allah zaki ganni yau*_ *41* Ya yi kusan minti biyar a zaune, rungume da Ameesha wacce ke ta sakin ajiyar zuciya, kallonta ya yi cikin tausayawa ya kaima goshinta sumba, tabbas ya jinjina mata don sosai ta yi kokarin amsan lalurar sa, bai so tun yanzu ya nuna mata haka ba so ya yi sai ta ɗan kwana biyu amma sam a daren jiya kasa control ɗin kansa ya yi, gyara mata zama a jikinsa ya yi yana faɗin "Allah ya maki albarka Maryerm hakika kin cika yar halas." Jin Dr ya yi sama da ita yasa ta kuma rintse ido don bata son su yi ido hudu, bai zame ko ina da ita ba sai toilet inda ya haɗa mata ruwa masu dan karen zafi, Ameesha batai aune ba sai jinta ta yi cikin wannan ruwan, ai da karfi ta saki k'ara saboda yadda ta ji shigar ruwan jikinta, sam Dr bai damu ba sai ma ci gaba da buɗe mata kafa yadda ruwan zai shiga da kyau yake yi, tun tana mugun jin zafi har ta soma jin dadin sa. Sai da ya sanya ta cikin ruwan zafi sau uku, sannan ya barta. "Heartbeat ki yi wankan tsarki ina zuwa." Dr ya yi maganar yana fita. "To." Ameesha ta amsa idonta a rufe don taki yadda su hada ido. Fita ya yi ya cire zanen gado ya canza wani, sannan ya koma toilet ya ɗauko Ameesha akan gado ya yi mata masauki, fita falo ya yi bai wani jima ba ya dawo hannunsa dauke da cup din shayi. "A'a wai har kin kwanta?" "Dr bacci nake ji." "Ok tashi ki sha tea sai ki sha magani kin ji ko?" "To." Ta amsa tana tashi zaune. "A'a wai lafiya kuwa, shi idon yau an daina buɗe shi ne?" Yana maganar ne yana mik'a mata cup. Turo baki ta yi cikin shagwaɓa, bata ce komai ba haka ya shiga bata tea a baki ido na rufe kamar makauniya, bata wani sha da yawa ba ta ce ta koshi, magani ya balla ya bata yana shafa mata gadon baya ya ji ta saki gyatsa, babu jimawa bacci ya yi gaba da ita. Gyara mata kwanciya ya yi ya rufe ta da blanket, kafin ya nufi toilet ya tsarkake jikinsa, lokacin karfe uku na dare sallaya ya shimfida ya shiga nunawa Allah farin cikin sa tare da gode ma Allah da ya ba shi Ameesha matsayin mata, yana mai addu'a da babban murya Allah yasa kwallonsa ya shiga raga. Ya daɗe zaune yana addu'oi kafin ya kwanta rungume da ita a jikinsa, bacci mai dadi ya ɗauke shi, yadda jikin Ameesha ke kadawa ne ya farkar da shi a gigice a lokacin karfe shida an dade da isar da asbah, kallon ta ya yi a dimauce jikinta babu inda baya rawa haƙora ta sai haduwa suke da juna, saboda zafin zazzaɓi, magani ya ballo ya bata da kyar ta iya hadiyewa, sannan ya goge mata jiki da ruwan sanyi da towel, sosai zafin jikin ya ragu har bacci ya dauketa, sai lokacin ya samu nutsuwa har ya yi sallar asuba. Bai koma bacci ba sai zama da ya yi yana jiran ya ga tashin ta, yana ta zaune har ya soma gyangyadi bai sannan lokacin da wani nannauyan bacci ya dauke shi ba, sun sha bacci inda Ameesha ta soma farkawa karfe tara, yanzu kam jikin da sauki sai dai jinta take fayau da ita kamar iska zai dauketa. Shiga toilet ta yi tare da haɗa ruwa, sai da ta kuma zama cikin sa ta yi wanka hadi da alwala, har zuwa lokacin Dr bai farka ba sallah ta yi, sannan ta tsantsara kwalliya cikin wata jar atamfa dikin riga da siket, sosai kayan suka amshi jikinta, feshe ko ina na jikinta ta yi da daddaɗar turarenta mai sanyin kamshi ta yi, har ta zauna sai kawai ta tashi ta nufi bedroom ɗinta, don tasan Dr ba barinta zai yi ba. Tana shiga ta haye gado tare da jan blanket, wayarta ta ɗauko ta yi dailling Number Meena, ringing biyu Meena ta dauka "Hello Meesha amarya ya garin?" "Lafiya lau wallahi, shi ne tunda ku ka aje Ni babu wanda ya kuma lekowa?" "Ki bari kawai k'awata, wallahi ko jiya naso zuwa sai Ya Abdul ya hanani." "Shi yasa nake fushi, ai na gane ashe duk kun koda na bar gidan ne ku huta." "Haba Meesha wani irin magana ce wannan, karki manta amarya ki ke dole a bar ku ku sha soyayya, anata dirzan amarci." "Kai Meena wa ye ya faɗa maki? Ko kin manta Dr ustaz ne?" "Ummh raba ni da yari auran sarki, kin ga yanzu ma awo zan tafi kika tsayar dani, Ummi ta ce in daina bari sai rana ta take kafin in tafi." "Masu maza bari na barki, don bacci nake ji sai anjima, amma Please yaushe zaki zo?" "Don Allah ki barni da maganar zuwan nan, inda yayanki ya barni cikin satin sama zan shigo." "Satin sama?" Ameesha ta tambaya cikin sauri. "Eh! "Allah ya kaimu." Daga haka suka yi sallama. Bayan sun gama hira bacci ya dauki Ameesha duk da yunwar da take ji. Cikin bedroom ɗin Dr farkawa ya yi tare da mika bakinsa dauke da addu'a, kara bude ido ya yi ganin babu Ameesha, murmushi ya saki a zuciyarsa yasan guduwa ta yi, tashi tsaye ya yi yana tafiya har wani layi yake domin yunwa yake ji. Kai tsaye bedroom ɗinta ya shiga, kwance ya hangota ta rufe da bargo, girgiza kai ya yi ya fita, ɓangaren Aneesa ya yi zaune a falo ya sameta tana aikin latsa waya. Ko dubansa bata yi ba, sai ma ci gaba da abin da take ta yi "My Anee baki ganni ba ne?" "Ina kallonka me zan yi ma?" Ta ba shi amsa cikin ko in kula. "Ko arzikin gaisuwa ba zan samu ba?" "Kamar baka ko ya min ba." "Ok kawo min break." "Break wani irin break kuma?" Ta mai tambayar cike da rainin hankali. "Kina nufin baki yi break ba? Kuma ai a kwanakin nan da zamu yi ke ya kamata ki rika yi mana abinci." Wani irin tashi tsaye ta yi tana hankada masa harara "Lallai Dr Asmad sannu, wato kai ka je ka kwana da mace, sai ni da yake shashasha ce sai na yi maku girki ku tashi ku ci ko? To wallahi baki isa ba, ba a haifi matar da zan bauta wa haka ba, can ka je kasa ta yi ma girki." Da zallar masifa take maganar. Girgiza kai Dr ya yi domin gaba daya maganar Aneesa ta gama daga masa hankali, yarinya karama kamar Aneesa ke faɗa masa magana yadda ta ga dama, Allah ya taimaketa ba ya da agenda ta duka mace wallahi da sai ta gane kurenta, kada kai ya yi kawai ya mike cikin ɓacin rai ya dubeta "Kina nufi bazaki girka ba ko?" "Eh! Ta faɗa da babban murya. "Gud." Shi ne abin da ya faɗa ya bar mata falon. Mtsss ta rakashi da dogon tsaki. Nutsuwarsa ya tattaro lokacin da ya shiga bedroom din Ameesha, ganin ta buɗe ido yasa shi sakin murmushi cikin sauri ya k'arasa inda take ya na faɗin "Cutie har kin tashi?" "Eh" ta ba shi amsa fuskarta ɗauke da murmushi. "Ok bari na yi wanka shaf-shaf in nemo mana abin da za mu ci, nasan kina tare da yunwa ko sorry." "To." Ta amsa tana sauka. A tare suka shiga bedroom nasa, ganin ya shiga toilet yasa ta fita, kai tsaye hanyar kicin ta yi, sai da ta haɗa duk abin da take buk'ata ta sannan ta soma aikin ta cikin gwarewa, nan da nan kamshi ya cika kicin ɗin break ta haɗa masu lafiyayye. Bata son abincin siya sam, da tasan haka da tuni ta gama haɗa masu. A nutse take aikinta saura kadan ta kammala, sam bata ji motsin shigowar sa ba sai ji ta yi an rungumota ta baya, sosai ta tsorata har ta bude baki zata zuba ihu ya yi saurin rufe mata baki yana faɗin "Cutie shi ne ki ka taho kicin kina aiki alhalin baki da lafiya kuma na ce maki zan fita in sayo mana me yasa?" "Sorry beby wallahi gani na yi duk wannan kame kamen ba zai kaimu ba, kuma gashi time ya yi nisa yanzu fa sha daya ake nema." Ta yi maganar tana shigewa jikinsa. Shafa kanta ya yi tare da bata sumba a kumatu ya ce "Kar ki damu cutie na baki uzuri, amma daga yau sai kin yi sati kafin ki fara girki." "Yawwa na gode beby, bari na kwashe wancan dankalin kar ya kone." "No! Zauna anan ya yi maganar yana zaunarta a kan kujera." Da kansa ya kwashe dankalin ya gyara kicin ɗin. Ameesha na zaune tana kallonsa har ya gama, taimaka masa ta yi da ɗaukar food plaks din, a kan dining suka shirya komai. Dr da kansa ya rika bata a baki har ta koshi, haka Ameesha itama ta rika ba Dr a baki har ya koshi, sun ci sun koshi cikin zallar soyayya da k'aunar juna, wata irin nutsuwa ce ke saukarwa Dr a duk lokacin da yaga Meesha cikin farin ciki, ko bayan sun kammala yin break da kan sa ya kai kayan kicin, Ameesha ta taimaka suka gyara komai suka san ya shi ma'ajinsu sannan suka bar kicin ɗin. "Kin ga bari na fita yanzu bazan daɗe ba." "Ina zaka je beby?" "Zan je asbiti kuma zan biya gidan Nenne." "A dawo lafiya Allah ya tsare hanya." "Amin cutie Ina godiya da addu'a." Har wajen motar ta taraka shi, sai da taga fitar da kafin ta koma ciki, kwanciya ta yi akan kujera. Dr kam yana fita asbiti ya soma zuwa, cikin sauri sauri ya gama duba wanda suke kwance, domin ba aiki ya zo ba bayan ya gama ne suka shiga motarsa shi da Hafiz lokacin karfe sha biyu da kusan rabi, suna tafe suna tattauna yadda bikin Hafiz din zai kasance har suka isa gidan Bobbo. A parking space ya faka motar suka shiga ciki bakunan su dauke da sallama. Nenne dake fitowa daga kicin ta amsa tana faɗin "A'a ku kuma daga ina haka?" "Daga asbiti." Suka bata amsa. Zama suka yi akan kujera suna gaidata. Cikin sakin fuska ta amsa tana tambayarsa Ameesha da Aneesa. "Duk suna lafiya." Ya bata amsa. "Madallah! A rika hakuri dai da zaman tare, domin in aka rasa hakuri matsala tana yawan faruwa." "In sha Allah Nenne za'a rika hakurin." Asmad ya bata tabbaci, suna dai zaune a gidan har ɗaya da mintina, sannan Hafiz ya masa sallama don yana da wasu aiki da zai yi, raka shi ya yi kafin ya koma cikin gidan don yana da magana da Nenne, don haka ko da ya koma ciki zama ya yi a kasa kusa da kafafunta, murmushi ta yi don tasan da magana wai gawa ta rike mai wanka, ya yi minti uku kafin ya dubi Nenne wacce ke zaune ya ce "Ummh." Sai kuma ya yi. "Asmad akwai magana a bakin ka, faɗa min domin ni ce mahaifiyar ka nafi kowa sanin halin ka." "Ehmm! Dama cewa zan yi inda an yi abinci a gidan nan, a rika kai mana har Ameesha ta yi sati guda ta amshi girki." Ya karasa maganar yana sosa kai. Tsira masa ido ta yi kamar mai son gano wani abu, sai zuwa can ta ce "Ita Aneesa aikin me take yi?" "Ehmm Ummh! Dama bata da lafiya ne, ba zata iya yin wani girki ba." Dr ya shirgo karya. Duk a zaton Nenne ciki ne da Aneesa. Don haka cikin murna ta ce "Masha Allah! Na yi farin ciki, gaskiya bai kamata kam ta shiga kicin ba musamman kila ba mai son kamshin abinci bane, ka riƙa lallaɓata Allah ya inganta, an ri ga da an kammala abincin bari nasa Larai ta haɗa maku kawai, da yamma direba zai kawo na dare." Nenne ta yi maganar tana mik'ewa don zuwa kicin. "Hmmmm! DR ya sauke a jiyar zuciya kawai, shi dai ba maganar cikin Aneesa ba ce matsalar sa, tunda ta amince zata basu abincin shi kenan. [10/8, 8:17 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga khadija s Muhammad My Besty* *42* Da taimakon ma'aikatan gidan ya shirya kulolin a mota, sannan ya yiwa Nenne sallama, kai tsaye gida ya nufa a lokacin karfe biyu saura mintina. Bayan ya yi fakin ya kwashe kayan zuwa bangaren Ameesha, yana buɗe kofar Ameesha da ke zaune a falon ta yi saurin tashi tana amsar kayan da ya shigo da su. "Sannu da dawowa baby." Ta yi maganar tana shirya kayan a kan dining. "Yawwa Cutie na barki ke kaɗai ko?" Dr ya yi tambayar yana kai hannunsa kugunta. Bata yi magana ba har sai da ta gama abin da take sannan ta juyo. "Baby na yi kewarka sosai." A shagwaɓe ta yi maganar tana rungumeshi. "Na fiki kewarki Cutie na na kosa na dawo gida na yi arba da kyakkyawar fuskarki." Yana maganar ne yana sinsinar wuyar ta. "An ya kuwa baby?" "Sosai kuwa." Ya tabbatar mata da haka. Ko kafin ta yi magana ya yi saurin faɗin "Mu je ki ci abinci sai ki bani labarin missing dina da kika yi." Zaunar da ita ya yi a dining din sannan ya ɗauki plet ya cika da abinci "Ina zuwa Cutie zan kaima Aneesa abinci, karki fara ci fa don tare za mu ci." Yana maganar yana tafiya. "To! Kawai Ameesha ta amsa. Kamar ko da yaushe yanzu ma kofar ta abude take shiga cikin falon kawai Dr ya yi bakinsa dauke da sallama, ko ɗago kai ta kalleshi bata yi ba sai ma ɗaukar remote control ta yi tana kara maganar t.v Murmushi kawai ya yi lamarin Aneesa sai dai addu'a, kullum abin gaba yake ba ya sauki kusa da ita ya isa tare da aje plet ɗin ya ce "Ga abinci nan ki ci my Anee don nasan kina tare da yunwa." Yana gama faɗa ya sa kai zai fice. Cak! Dr ya tsaya jin maganar da Aneesa ke yi. "Zo ka ɗauki abincin ka bana ci, ko an ce ma ni mayunwaciya ce?" Ta kai karshen maganar tana watsa masa harara. Takowa ya yi a hankali har inda take zaune ya sassauta murya ya ce "Look Aneesa ya kamata kisan da wa kike magana, domin na fi kowa sanin ke ba mayunwaciya ba ce, amma hakkin ciyar da ke yana kaina don haka ga abinci nan na kawo maki, ko kici ko ki zubar ruwanki." Gama maganar sa ya yi dai dai da soma tafiyarsa. Mtsww! Aneesa ta ja tsaki bayan fitar Dr daga falon, gaba daya haushinsa take ji, ko birgeta ba ya yi yanzu. Yana takaicin halin Aneesa sam bata da halin kwarai ita kenan kullum cikin masifa, kai Allah ya kyauta, sai da ya daidaita nutsuwarsa kafin ya shiga falon, inda ya bar Ameesha zaune a nan ya sameta tana aikin Game a wayarsa. "Sorry Cutie na barki ke kaɗai ko?" A je wayar ta yi tana sakar masa murmushi bata iya cewa komai ba, saboda wani irin kallo da Dr ke aika mata, take wani irin kasala ta saukar mata, zama Dr ya yi bayan ya zuba masu abinci kan cinyarsa ya yi mata mazauni da kan sa ya rika bata har sai da ta koshi, sannan ita ma ta shiga ba shi, suna yi suna zuba soyayyar su har suka kammala, kwashe kayan Meesha ta yi ta kai kicin, sannan ta gyara inda ya ɓaci Dr kallonta kawai yake cikin wani irin shaukin soyayya, ya yadda yana son Ameesha so irin wanda bai taɓa yiwa wata ba, bai san time da ta iso wajensa ba sai jinta ya yi ta shige jikinsa. "I love you Meesha." Dr ya faɗa yana kara shigar ta jikinsa "I love you too." Ameesha ta ba shi amsa, wani irin tashi zaune ya yi wannan shi ne karon farko da ya ji Ameesha ta furta tana sonsa ita ma. "Kina so na yaushe kika fara so na?" Dr ya yi tambayarsa da mamaki. Babu kunya ta ce "Tun ranar farko da muka soma haɗuwa a sahad store na fara sonka Dr." "Kina nufin a lokacin ɗaya muka yi *MUSAYAR ZUCIYA*? (Littafin Hajja). "Kwarai kuwa sai zuciyoyinmu ta soma mana *BAHAGGON TUNANI* (littafin Badeeyar beauty queen). "Ba shakka *SANGARTAR* ki ta taka muhimmiyar rawa wajen hanamu mallakar juna tun tuni." Ya yi maganar yana lakace mata hanci. Turo baki ta yi ta ce "To amma duk *LAIFIN WA?* (Littafin Khadija S Muhammad). "Dukkan mu muna da laifi tunda mun kasa bayyana soyayyar mu a fili, sai faɗa da muke da juna sam bama jituwa, lallai Allah shi kadai yasan abinda ya ɓoye cikin tarayyar mu." Ya dire maganar yana manna mata kiss a kumatu. "Allah ya bamu hak'urin zama da juna lafiya. Ameesha ta faɗa tana kara shigewa jikinsa idonta lumshe kamar mai jin bacci. "Amin." Ya amsa yana ci gaba da wasa da jikinta a haka bacci ya kwashe su, ba su farka ba sai bayan la'asar, Dr ya fara farkawa ya sauke idonsa kan agogon da ke manne a bangon falo, da sauri ya tashi zaune ganin lokacin sallah ya gota. Tashin Ameesha ya soma yi tana farkawa suka shige bedroom Dr niyyar wanka ya yi, don har ya ɗaura towel a kugunsa ya zubawa Ameesha ido ganin tana niyyar kwanciya "Tashi mu yi wanka mana Cutie time na tafiya fa." "No! A fito lafiya zan yi nawa." "Ba ki yin wankan kenan?" Kai ta gyaɗa tana gyara kwanciya, Dr bai ce komai ba ganin ta rufe ido, ai da sauri ya sureta bai zame da ita ko ina ba sai cikin toilet cikin kwamin wanka ya sakata, yana sanya ta ta mik'e zaune jinta cikin ruwa tsundum kallonsa ta yi a shagwaɓe ta ce "Please Dr me haka?" "Soyayya ce haka." Ya bata amsa yana shiga cikin kwamin shi ma. Shiru Ameesha ta yi masa tana jinsa ya gama cire mata kayan jikinta wanka ya mata tas yana yi yana love wanda Meesha ko kallonsa taki balle ta taimaka masa, a haka ma ya ji dadi yana gama mata ta daura alwala cikin towel ya nadeta da kaita bedroom, cikin sauri ya kammala wankan ya yo alwala ko da ya fito ya sameta har ta gama shafe jikinta da mai ɗaya daga cikin jallabiyar Dr Ameesha ta san ya suka gabatar da sallah. Bayan sun idar Dr ya je ɗakinta kaya ya kwaso mata wanda zata saka, three kwatan wando da karamar top mai hannun bes, tana kwance Dr ya gama mata komai har shiya ta, ya feshe mata jiki da turaruka masu sanyin kamshi, woww gaskiya Ameesha ta yi kyau, Dr ma cikin kananan kaya ya shirya three kwata da singileti, sosai kayan suka amshi jikinsu, falo suka koma inda suka kunna tv suna kallon tashar Bollywood. Karfe shida saura direban gidan Nenne ya kawo masu abinci, Dr da kan sa ya fita ya kwaso, a dining suka shirya komai [10/8, 8:18 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © _*ZULAYHEART RANO*_ *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* *43* Haka Ameesha ta sha kukanta daga karshe ta lallashi kanta, a three sitter ta kwanta tana mai ambaton sunan Allah a hankali wata nutsuwa ke saukar mata. Dr kuwa ko da ya shiga bangaren Aneesa kwance ya sameta kamar ko da yaushe tana aikin latsa waya, ko kallo Dr bai isheta ba balle ya samu arzikin sannu da zuwa. Zama ya yi tare da bismillah yana faɗin "my Anee barka da hutawa." Bata amsa ba sai dan dagowar da ta yi ta kallaceshi, kamar wacce aka tsikara kuma sai ta mik'e tare da shigewarta bedroom. Girgiza kai kawai Dr ya yi shima ya shiga bedroom ɗinsa, kayan jikinsa ya rage sannan ya nufi toilet alwalarsa ya dauro ya zira jallabiya sannan ya nufi masallaci, bai shigo gidan ba sai bayan ishsha da tek away ya shigo da su, a dining ya aje ledojin babu kowa a falon hakan ya nuna Aneesa bata fito ba, bai bi ta kanta ba don yasan masifa take nema da shi shi kam ba zai biye mata ba. Leda ɗaya ya ɗauka ya nufi bangaren Ameesha, kamar yadda ya zata kuwa a falo ya sameta tana zaune ta buga uban tagumi jin an bude kofa yasa ta yi saurin ɗagowa ido hudu suka yi da Dr wani irin lallausan murmushi ta sakar masa, sai da gabansa ya fadi da yadda yaga idanunta sun kumbura a lamar ta sha kuka, "Cutie lafiya kuwa kalli idonki fa?" "Babu komai fa baby." Ameesha ta ba shi amsa tana amsan ledar da ya shigo da ita. "An ya kuwa Cutie?" "Allah nifa baby babu wani abu." A shagwaɓe ta yi maganar. "Ok tun da babu komai ai shi kenan, amma Please abar kukan haka nan ya isa." "Na daina." "Promise?"Dr ya fada yana kallonta. Murmushi ta saki ta ce "Yes promise." "Ga abinci nan ki ci sai ki kwanta, karki manta da addu'a fatan kin yi sallah?" "Eh na yi." Ameesha ta bashi amsa. Fita Dr ya yi yana mata sai da safe, bayan fitar Dr abincin ta jawo hankali ta soma ci, duk da dai turawa kawai take sam bata wani jin dadin sa, bata ci da yawa ba ta ture shi gefe tare da hamdala ga Allah. Dr kam ko da ya koma falon Aneesa bata fito ba, don haka sai ya ɗauki leda daya ya nufi bedroom ɗinta akwance bisa gado ya sameta, cikin nutsuwa ya zauna a bakin gadon yana kallonta a hankali ya furta "My Anee." Sarai tasan da shigowar sa sai ta ɗauke kai, jin yadda ya ambaci sunanta sai da wani abu ya tsirga mata tun daga tsakar kai har yan yatsun kafarta, amsawa ta yi ba tare da ta tashi ba. "Tashi mu yi magana." Fuska babu walwala ya yi maganar. Tashi ta yi tare da kauda kai gefe taki ko da kallonsa, murmushi ya yi ya ce "Aneesa faɗa min laifin da na yi maki kike fushi dani?" Ya ida maganar yana kafeta da ido. Shiru ta yi kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce "Ni baka min komai ba." "Ban yi maki komai ba kike fushi da ni Aneesa?" Cike da mamaki yake tambayarta. "Eh gaskiya na faɗa maka babu abin da ka yi min." Ta faɗa tana mik'ewa. Sam Dr baya son jan magana don haka sai ya ce "Shi kenan tunda kika ce haka, amma nasan mutum haka kawai bazai fara fushi ba tare da an yi masa komai ba." "Ni dai Hamman na faɗa maka baka min komai ba." "Ok dawo ki zauna, kila babu abin da kika ci ga abinci nan idan kin gama ina jiranki a bedroom." To kawai ta amsa tana shigewa bedroom, ruwan sanyi ta sakarwa kanta zafin da zuciyarta take ta ɗan ragu ko yanzu tasan tana da matsayi a idon Dr tunda har ya yi mata magana cikin tausasa murya, duk da tarin rashin mutuncin da ta yi masa, bayan ta fito ta zauna ta ci ta koshi da yake ta yi sallah sai kawai ta koma toilet ta kuskure baki, rigar bacci ta zura ta nufi dakin Dr. Lokacin Dr na zaune cikin tunanin halin da Ameesha ke ciki, kalkalo murmushi ya yi ya ce "Barka da zuwa My Anee." "Hmm! Barkammu dai Hamman." Tana gama faɗin haka ta yi kwanciyar a kan gadon, wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyarta don ganin ta a kwance a gadon Hamman ɗinta. Dan ɗago kai ya yi ya ce "Daga zuwa sai kwanciya? Ko dan hira baki taya mijinki." Kunya ce ta kamata don haka sai ta sauka daga gadon ta nufi inda yake zaune, kusa da kafafunsa ta zauna. Murmushi ya saki sannan suka soma hira irin ta mata da miji, idan ka ga yadda Aneesa ta saki jiki sai murmushi take yi ba ka taɓa cewa ita ce. Tsakanin miji da mata sai Allah nan take suka ɗinke, dama dai Aneesa kishin Dr ke damunta. Gari na wayewa Aneesa da kanta ta shiga kicin ta haɗawa Dr break, bai fita ba sai da ya yi shirin zuwa office break din ya yi kafin ya yi mata sallama, yana fita bangaren Ameesha ya yi don ganin yadda ta kwana. ***** Ameesha kam ganin bacci yaki zuwa mata sai ta mik'e alwala ta dauro mai kyau ta shiga nafilfili, ba ita ta bar sallayar ba sai bayan ta yi asbah sannan bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita. Dr na shiga falon yaga bai ganta ba sai ya nufi bedroom ɗinta, amfani ya yi da fitilar wayarsa ya haska daki don gulob ɗin akashe yake, can ya hangota karshen gado a kwance kallo ɗaya zaka mata kasan sam bata jin dadin baccin, musamman yadda ta wani ta kure waje daya. A hankali Dr ke takawa har ya isa gadon, tsayawa ya yi yana kallon gadon, ko alama bai yamutse ba a gyare yake tsaf shi kansa dakin wani irin kamashi yake fitarwa, haka kan gadon lumshe ido ya yi ya buɗe sannan ya hau gadon bayan ya cire takalmarsa, kusa da kanta ya zauna a hankali yake shafa gefen fuskarta yana magana a kunnenta "Cutie tashi gari ya waye fa." Buɗe ido ta yi jin muryar Dr fes ta sauke idonta cikin nashi murmushi ta sakar masa tana kokarin tashi duk da idonta fal bacci. "Baby yaushe ka shigo?" "Yanzu ban dade ba Cutie kina ta bacci, kamar ba ki yi kewata kamar yadda na yi taki ba?" Yana maganar ne yana jawota jikinsa. "Baby kenan kewarka da nayi ba zai fadu ba, nasan wanda ka yi ko kwatan nawa bai kai ba domin kana da Sister Aneesa kusa da kai." Cikin turo baki ta gama maganar. "Da gaske kin yi kewata?" Sauri ta daga kai, alamar "eh!" Tana tuna yadda bacci ya kwasheta a daren jiya. "Idan na dawo zaki gwada min irin kewata da kika yi, yanzu dai tashi ki yi break don gari ya gama wayewa, zan tafi office duk abin da kike buk'ata ki sanar min." Mik'ewa ta yi tare da jawo hijjab ɗinta dake kusa ta sanya, tana faɗin "a dawo lafiya Allah ya tsare ya bada sa a." Maganar ta ta dire lokacin da suka isa kofar falo." Murmushi ya yi yana amsa addu'ar ta tare da manna mata kiss a goshi, sannan ya tafi. Ciki ta koma sai da ta gama haɗa break ɗin ta, doya kawai ta soya da kwai sai ruwan shayi, bata zauna ba sai da ta gyara ko ina na bangaren, sannan ta shiga wanka shiryawa ta yi cikin wasu riga da siket wanda suka yi mata kyau jikinta ta feshe da turare sannan ta koma ta fara break. Karfe goma da rabi ta gama, duk ranta babu dadi kasantuwarta ita ɗaya a gidan, hijjab ta dauka bayan ta sanya ta fita daret bangaren Aneesa ta shiga, duk da Aneesa na zaune a falon amma ko ɗagowa ta kalli Ameesha ba ta yi ba. Sai cewa ta yi "Lafiya da safen nan? Murmushin yake kawai Ameesha ta yi ta ce " lafiya lau gaisarki kawai na zo yi." "Na gode da gaisuwa, tunda kin ganni lafiya ai sai ki tashi." Ta dire maganar tana aika mata harara ta mike tare da barin mata falon ta yi shigewarta bedroom. Shiru Meesha ta yi tana kara mamakin halin Aneesa, girgiza kai ta yi tare da tashi ko alama bata nuna wani damuwa ba. Tana komawa bangaren ta wayarta ta soma ringing, cikin sauri ta dauka da sallama, Dr ne ke tambayarta lafiyar ta, ita kuma ta tabbatar masa tana cikin koshin lafiya. Bayan sun gama wayar Meena ya shigo inda take shaida mata zata zo anjima, wani irin murna Ameesha ta yi, ai da sauri ta shiga kicin ta haɗa mata lafiyayyen abinci, hira suka sha sosai don yini Meena ta yi mata, da zata tafi kamar kar su rabu haka Ameesha ta ji. Haka rayuwa ke tafiya kwanaki suna zama makonni haka makonni ke komawa watanni, su Ameesha zuwa yanzu watan ta biyu kenan a gidan Dr tana samun duk wani jin dadi a wajen Dr sam baya kaunar ganin ɓacin ranta, ta yadda da irin soyayyar da Dr ke mata, duk da Aneesa tana yi mata abubuwa marasa daɗi amma ita sam bata damu ba, don ita da zuciya daya ta dauketa. Ranar safiyar wata Alhamis Dr ne kwance ya yin da Ameesha ta yi filo da faffadar kirjinsa sai wasa take da suman dake kwance luf a kirjinsa bayan sun gama shan love dinsu, wayar Ameesha ce ta soma ringing Dr wanda hannunsa yafi kusa da wayar ya mika mata, ganin Number din Meena yasa ta yi saurin ɗauka, wani irin kara ta saki irin na marna ta na faɗin "Yaushe? To gamu zuwa da Dr." Tana aje wayar ta ce "baby tashi ka yi wanka mu je gidan su Ummi Meena ta haihu." "Kai Masha Allah! Abin farin ciki Allah ya raya, ya nuna min lokacin da Cutie zata haifa min yara." "Amin." Ta amsa tana saurin rufe fuska. "Kunya kike ji ne Cutie? Ki bar Jin kunya ina son yara ko nawa zaki haifa ba zan taɓa gajiya da ke ba please Maryam karki sha wani abu don hana daukar ciki." Da muryar tausayi ya gama maganar. Tausayin Dr ne ya kama Meesha ta ce "in sha Allah babu abin da zan sha Allah ya bamu masu albarka." "Ameen matata yar albarka." Yana gama fadi ya shige toilet, itama ɗakinta ta wuce ta shiga wanka bata jima ba ta fito kai tsaye kicin ta nufa ta sama masu abin break kunun gyada ta dama sai ta soya doya da dankalin turawa, komai ta jera a dining bayan ta gyara kicin ɗin fes baka taɓa cewa an yi aiki a ciki. Kai tsaye bedroom ɗinsa ta nufa, a kwance ta same shi yana game a wayarsa, kan gadon ta hau tare da amshe sayar ta ce "baby break is ready." A shagwaɓe ta yi maganar. Tashi ya yi yana murmushi ya ce "An gaida Cutie mu je mu gama har an soma kira na." Yana rike da hannunta suka isa, a natse suka kammala break ɗin kwashe kayan ta yi ta kai kicen sai da ta wanke ta gyara komai kafin ta dauki gyalen ta. Bangaren Aneesa suka shiga suka mata sallama. Cikin farin ciki Ameesha ta shiga gidansu, har bangaren Meena Ameesha ta kai Dr da kanta ta shiga bedroom ta ɗauko masa jaririn tukeke da shi tubarkallah ta kaiwa Dr, sosai Dr ya rike dan a hannu kamar kar ya rabu da shi, domin Allah ya yi Dr Asmad da san yara, sai da ya yiwa su Ummi barka kafin ya tafi da cewa idan ya dawo aiki zai biya ya dauketa. Rayuwar farin ciki Ameesha ta yi a gidan su, kaf yan'uwanta sai da ta gansu sun nuna irin kewarta da suka yi babu ma kamar Haydar da yamma Dr ya dauketa suka tafi gida, sai dai fa Ameesha da ciwon kai ta koma, tun tana daurewa har Dr ya fahimta hankali tashe yake tambayarta "Cutie lafiya kuwa?" Da kyar ta ce "kaina ke ciwo." "Ayya sannu." Ya yi maganar da muryar tausayi sannan ya nufi inda yake aje magani don ya bata ta sha yana cikin duba maganin sai ga wani ya fado da sauri ya kai hannu ya dauko yana gama karantawa ya furta " *Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!* Ni Ameesha zata ciwa amana?" Da sauri ya dafe kansa dake barazanar rabewa biyu. Tofa Dr me ka gani ne haka, har kake furta irin wannan maganar ga Cutie din ka Ameesha? Ku biyo alkalamin Zulayheart Rano don jin yadda zata kaya don koni bana ce ga abin da ya gani ba . *Don Allah ku yi min addu'a wallahi bani da lafiya sosai*👏🏻 _*YAR MUTAN RANO*_ [10/8, 8:18 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © _*ZULAYHEART RANO*_ *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* _Ina dai bada hak'urin rashin ganin post kullum wallahi dai abubuwa ne sai a hankali amma zan fara k'ok'ari ina typing ɗin. Matsalar baku yi comment._ *44* Zama ya yi kansa na wani irin sarawa, juya kwalin maganin yake yana karawa ya yi kusan minti biyar a wajen sannan ya ɗauki maganin ciwon kan ya fita falo inda Ameesha take, mika mata ya yi bayan ya yi kokarin danne zuciyarsa. Amsa Ameesha ta yi sam bata kula da yanayin da yake ciki ba tunda idanunta a rufe suke, sai dai ta yi mamakin ganin ya mika mata maganin ba tare da ya bare ba, bai saba yi mata haka ba sannan kuma babu ruwa. "Baby baka bare min maganin ba kuma baka kawo min ruwa ba." A shagwaɓe ta gama maganar, da muryar ciwo. Dan tsaki Dr ya ja zuciyarsa cike da haushinta ya ce "sai na kawo maki ruwa za ki sha maganin? Ashe kam yau ba za ki sha ba." Yana gama faɗin haka ya yi shigewarsa bedroom. Kan Ameesha ya daure da maganar da Dr "me haka ke nufi?" Tambayar da ta yiwa kanta kenan hankali tashe, sai ma ta ji ciwon kan ya ware, jiki a sanyaye ta nufi dakin sa tana faɗin "baby wai yau ba zaka min wanka bane tunda ka ki bani ruwan na maganin to na fasa sha." Tana maganar hawaye suna barazanar zubowa. Mtsww Dr ya ja tsakin da ya yi sanadin daukewar numfashin Ameesha na sakonni, sai kuma ta tsinkayo muryarsa yana magana cikin muryar da bata taba sanin Dr na da irin ta ba "Ke bana son damuwa, ki barni na huta kina neman takurani fa Ameesha je ki waje bana buk'atar ki kusa dani." A zafafe ya ke maganar. "Ameesha." Ta maimaita yadda Dr ya kira sunan ta kai tsaye, saurin toshe kunne ta yi tana ambaton sunan Allah a fili. Wasu hawaye suna zubowa daga idonta jikinta ya yi sanyi kalau take ciwon kan ya dawo sabo, da kyar ta bude baki ta ce "Baby me kake nufi da maganar da na ji, shin ba kunnena suka ji.." hannun da ya daga mata yasa ta yi shiru da sauri. "Za ki fita ko ni na bar maki daki?" Tambayar ya yi yana daukan wayarsa. Kallonsa ta yi sai ta ga kamar ba Dr Asmad da ta sani ba ne wannan don shi ko da yaushe fuskarsa ɗauke da murmushi yake, saɓanin wannan da ya wani murtuke kamar wanda baisa wani abu dariya ba, da sauri ta fita tana kara fashewa da kuka. Dr na ganin ta fita ya furzar da wani iska mai zafi, zuciyarsa cike da takaicin matan nasa yanzu duk so da tattalin da yake wa Ameesha da wannan zata saka masa, shi ko me yake wa matansa da suka zaɓi su musguna masa ta hanya mafi muni, Aneesa ta zubar masa da ciki bata tsaya iya nan ba ta ci gaba da shan magungunan hana daukar ciki, sam bai damu ba shi ne itama Ameesha zata bullo da haka me ya yi masu da zafi da basu kaunar hada jini da shi? Wannan tambayar shi ya ci gaba da yiwa kan sa sai dai ya rasa amsansu. Ameesha kuwa tana shiga bedroom din ta kuka ta ci gaba da yi, duk iya tunanin ta ta kasa tuna laifin da ta aikatawa Dr mafi muni da har ya jefa ta cikin wannan mawuyacin halin, kwana ta yi idonta na hawaye sam bata rintsa ba yadda taga dare haka ta ga rana, shi ma bangaren Dr da kyar wani wahalallen bacci ya kashe shi ko da asbah sallah kawai ya yi ya koma baccinsa. Ameesha tana idar da sallah ta shiga kicin ta fara shiryawa Dr abin break tana yi tana hawaye a haka ta kammala, sannan ta gyara kicin ɗin da falo, kafin ta yi wanka sai da ta gyara bedroom ɗinta ta turareshi da turare, wanka ta shiga bayan ta cika ruwan wankan da turaruka masu sanyin kamshi, bata wani jima ba ta fito simple dressing ta yi top da wani three kwantan wado ta sanya ta raba gashinta gida biyu da reboom kalar rigar ta, jikinta sai kamshi yake fitarwa kallo ɗaya zaka mata kasan tana cikin damuwa musamman yadda idanuwanta suka kumbura sosai. Jiki a mace ta nufi dakin Dr. Ta kai hannu da niyyar buɗewa sai ta ga an buɗe kofar, baya ta ja tana faɗin "Barka da safiya." Bai amsa ba sai ma hanyar wucewa da ya lalubo, ganin da gaske zai wuce sai ta yi saurin riko hannunsa tana faɗin "mai na yi maka baby kake fushi da ni tun jiya ga shi kuma yanzu gaisuwata ma kaki amsawa?" Zame hannunsa ya yi daga rikon ba tare da ya furta komai ba. Wasu sabbin hawaye suka zubo daga idonta murya na rawa ta ce "Na kammala break please ka tsaya ka yi." Sai yanzu ya yi magana shi ma a takaice ya ce "bana buk'ata." Daga haka ya yi wucewar sa, inda ya bar Ameesha zaune cikin kuka ta kasa ko da tashi a inda take, duk iya tunanin ta bata gano laifin da tawa Dr ba, haka dai ta kasance cikin hawaye har bayan la'asar da kyar ta iya yin break shi ma sai da ta ji tana shirin hallaka kanta, tana zuba idon ganin Dr amma sai ta ji shiru, duk da tasan yau ba ita keda shi ba amma ya saba zuwa ya yi mata sallama yau kam shiru har bayan magriba. Sabon kuka ta fashe da shi tana tir da halinta tunda ta kasance mai sabawa mijinta har ya dau fushi da ita mai tsanani, sam ta manta da wai ana cin abinci don rabonta da shi tun na safe ta nemi yunwar ta rasa, alwala ta dauro tazo ta zube gaban Ubangijinta ta ci gaba da kai kukanta bata gushe ba har sai da ta yi sallar asuba sannan nannauyan bacci ya kwashe akan sallayar. Duk da ya ji zafin abinda da yake ganin Ameesha ta ha'ince shi da shi, wani gefen na zuciyarsa tana jin haushin yadda Ameesha ta kasance daga dare zuwa safe, kukanta ya tsaya masa a rai sosai, har ya ji kamar ya je ya lallasheta sai dai ya zama dole ya nuna mata kurenta. Aneesa ma tunda taga Dr da ya dawo office yau bai je sallama da Ameesha kamar yadda ya saba ba sai ta yi tunanin kila ba'a gidan ta kwana ba, ci gaba ta yi da kulawa da Dr tana son ta bashi dukkan wani farin ciki. Sosai ya yi kokarin biye mata ko dan ya sauke hakkinta da ke kanshi, duk da hankali da tunanin sa suna ga Ameesha ba. **** Najeeb ne keta kai komo tsakanin repretion da kofar dakin haihuwa, gefe guda kuma Mumynsa ce da alama Rufaida ce a dakin don yadda Najeeb ke zarya hankali a tashe. "Haba Najeeb ka kwantar da hankalinka insha Allahu lafiya zata sauka." Da taushin murya take masa kalaman. "Na kwantar Mumy Allah ya sauketa lafiya." Amin Mumy ta amsa tana ci gaba da kwantar masa da hankali, minti talatin tsakani wata Nurse ta fito dauke da jaririya cikin towel mai laushi da kyau, mikawa Mumy ta yi tana faɗin "Hajiya ga baby girl nan Madam ta sauka." "Alhamdulillah!" Suka hada baki wajen fada, Najeeb kuɗi ya zaro ya mikawa Nurse din ya ce ga goron albishir nan. Amsa ta yi tana godiya Mumy ta cika da murnar samun jika yarinya kyakkyawa da ita, ko kunya Najeeb bai ji ba ya amshi yarsa yana kiss da addu'oi. Babu jimawa aka fito da Rufaida zuwa dakin hutu tunda lafiya ta haihu sai gajiya. Cikin dakin bayan Mumy ta haɗa mata shayi mai zafi ta sha, sai Najeeb ya kuma rungumar yarsa ya bata zamzam da zuma kafin ya soma yi mata huduba, Mumy ta kalleshi ta ce "huduba kake mata?" "Eh Mumy na yi mata huduba da *Maryam*. _Littel Ameesha_." Murmushi Mumy ta yi ta ce "Allah ya raya Maryam cikin musulunci." Domin dai tasa irin son da Najeeb ke yiwa Ameesha. Ita kanta Rufaida bata ji haushin sunan da ya sanya wa jaririyar ba, sai ma addu'a da take yiwa yarta, babu dadewa jama'a suka cika asibitin don taya su murna. **** Wasa wasa dai har Dr ya fita dakin Aneesa bai saurari Ameesha ba, yau take sa ran zata karbi Dr kuma ta yi alkawarin sai ta daidaita tsakanin ta da Dr kuma sai tasan laifin da ta yi masa domin a kwanaki biyun nan ita kadai tasan a hankali da ta yi su. Mikewarta kenan daga kujera zata nufi kicin domin uku da kwata ta yi sai ta ji ana buga kofarta, da mamaki ta isa kofar tana faɗin "waye?" Muryar da ta ji ya sanya ta buɗewa tana kallonta baki bude. Aneesa kam wani kallo ta watsawa Ameesha tare da jan siririyar tsaki ta ce "Hamman ne ya ce in kawo maki wannan lemon ki sanya masa a firij don ke kike da shi." Har ba za ta amsa ba, domin bata taɓa ganin haka ba sai kuma ta Murmushi wanda ya tsaya iya labba tasa hannu ta amsa tare da shigewa ciki. [10/8, 8:18 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © _*ZULAYHEART RANO*_ *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* *45* A firij din kicin ta sanya sannan ta fara aikinta hankali kwance, tafashen nama ta ɗaura baya ta wanke, yana fara taushi ta sauke sannan ta haɗa masa kayan hadi lokacin an shiga sallar la'asar don haka ita ɗin ma bedroom ta shiga ta gabatar da sallar, bayan ta idar ta koma ta ci gaba da aikinta, dambun shinkafa ta yi masa sai farfesun naman rago da sansanyan abin sha. Karfe biyar saura ta kammala aikin ta jera komai akan dining bayan ta gyara kicin ta wanke duk kayan da ta yi amfani da shi. Falo ta koma ta kara gyara duk inda ya kamata ta turare shi da turaruka masu kamshi da daɗi gaba daya gidan ya cika da kamshin abincin tare da na turare, cikin sauri ta faɗa toilet don ganin lokacin shigowar Dr ya kusa, wanka ta yo ta mulke jikinta da mayuka masu kamshi cikin wata riga ta shirya wanda iyakar sa cinya, santala santalan cinyoyinta duk sun bayyana sosai ta yi kyau duk da ba wani make up ta yi a fuska ba. A falo ta zauna tare da daura kafa daya kan daya tana canza tashoshin t.v. kamar a mafarki ta soma jiyo fitinan nan kamshin turaren Dr wanda ya yi sanadin da ta lumshe ido wani irin feeling ya saukar mata, tana jiyo takunshi ta yi saurin tashi tare da nufa kofar. Dr na buɗewa Ameesha ta faɗa jikinsa tare da kamkame shi, cikin siririyar murya ta ke faɗin "baby sannu da dawowa." Bai amsa ba sai k'ok'arin yaki ce ta daga jikinsa ya fara, ita kuma ta ki sakin sai ma kukan sangarta da da fara yi masa, sam ya kasa tankwara zuciyarsa akan kar ya sauka daga fushin da yake da ita, daukarta cak! Ya yi ya k'arasa shiga falon da ita. Sam Ameesha ta ki barin kukan kuma ta ki dagawa daga jikinsa, shafa sumar kanta ya soma yi cikin wani irin salo ya kasa magana sai zuwa can ya ce "haba Cutie kukan ya isa haka kar ki bata min kwalliya ga yi ko gani ban yi ba." Da taushin murya ya yi maganar. Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyarta ta kara lafewa a kirjinsa tana ci gaba da shashsheka. "Ba na ce kukan ya isa ba?" Wannan karon adan hasale ya yi maganar. "Ni dai ba zan yi shiru ba sai ka faɗa min laifin da na yi maka kake yin fushi da ni?" Da shagwaɓaɓɓiyar murya ta yi maganar. Kiss ya yi mata a kumatu ya ce "wannan maganar ya wuce tuni na bar yin fushi dake, domin ba zan iya ba duk kuwa da girman laifinki." "Laifi na wallahi ban san na yi maka laifi ba baby ka yi hakuri ka yafe min in sha Allah bazan kara ba." "Kin yi min laifi Cutie wanda yasa har na kasa ɓoye fushi na." "To ka yi hakuri ka yafen." "Na hakura Allah ya yafe mu baki daya." Amin ta amsa tana ɓalle masa botirar rigarsa, kwashe kayan ta yi ta kai masa bedroom sannan ta haɗa masa ruwan wanka, ita ta taimaka masa ya yi wankan ya shirya sannan suka fita falo. Ameesha da kanta ta rika ciyar da Dr har ya koshi, kwashe kayan ta yi takai kicin sannan suka koma kan three sitter, soyayyar su su ke Ameesha ta kuma narkewa a jikin Dr ta yi kasa da murya ta ce "baby wai wane laifi na yi maka da ka kira shi mafi muni? Ina son sanin laifi na domin gujewa sake aikata maka irinsa nan gaba." Shafa kanta Dr ya yi cikin soyayyar ta da ta yi masa yawa ya ce "ki bar tuna min Cutie wannan fa ya wuce kuma bana fatan na kara kamaki da makamancin sa, a wajen ki ba babban laifi bane domin ban san manufar ki ta yin haka ba, amma ni a wajena babban laifi ne Maryerm." Ya ɗan takata da maganar sa, jin ya yi shiru sai ta ɗago kai ta kalleshi ta ce "in sha Allah bani kumawa amma ina son jin sunan laifin." "Hmmmm! Dr ya saki ajiyar zuciya ya ce "Maryerm kina shan maganin hana daukar ciki saboda karki wahala ko?" Wani irin zabura Ameesha ta yi murya na rawa ta ce "Maganin hana daukar ciki baby?" "Yes Ameesha da idona na gansu ranar da kanki ke ciwo na je dauko maki magani ." Ya dakata da maganar yana kallon Ameesha, saurin mayar da hawayen ta ta yi sai dai duk da haka mamakin maganar Dr bai bar fuskarta ba, ta dai kasa magana don bata da kalmar kare kanta tunda ya gani da idonsa kuma cikin kayanta. Ya zama dole ta amsa laifin duk da dai ba ita ta aikata ba, hasalima bata taɓa koda tunanin shan irin maganin ba, Wasu hawaye masu zafi suka sauko saman fuskarta muryarta na rawa ta ce "Na yi kuskure in sha Allah makamancin haka ba zai kuma faruwa ba ka yafe min." Kara rungumar ta ya yi yana hura mata iska a kunne ya ce "ya isa haka kukan, kar ki kara sha." Da kyar ya lallasheta ta yi shiru har bacci ya kwashe ta anan a jikinsa. Shiru Dr ya yi yana kallon yadda Ameesha ke saukar da numfashi duk da baccin ba na daɗi ba ne, amma ta yi kyau a cikin baccin. Sam baya kaunar damuwarta balle akai ga yin kuka. Sun ci gaba da gudanar da rayuwar su, yau saura kwana ɗaya sunan Meena tun safe Meesha ta soma shiri domin kwana zata yi a gidan, in da Allah ya taimaketa ba ita keda Dr ba, karfe goma ta kammala shirinta ta dauki karamin kit ɗinta da ta sanya kaya kala uku a ciki sai kayan kwalliya, Number din Dr ta soma laluba don ta sanar masa ta shirya. Dr dake asbiti ya tabbatar mata da ga shi nan zuwa nan da mintina ashirin. Bai wani jima ba ya iso, ganin kit gabanta ya sa shi zaro ido da mamaki "Cutie wannan kayan fa?" "Da su zan tafi." Ta bashi amsa cikin shagwaɓa. "Kuma har haka? Ina laifin kala ɗaya gobe zan zo ɗaukar ki fa?" "Gobe fa baby? Ba sai jibi ba?" "A'a ki dawo gobe plea.." Bata bari ya gama rufe baki ba ta yi saurin sanya bakinta cikin nashi tana yi masa wani shu'umin kallo mai kashewa lafiyayyen namiji jiki, sun dau kusan minti goma a haka kafin ta fara k'ok'arin zare bakinta daga na shi, shi kuma Dr ya ce bai san wannan ba bai barta ba sai da ya samu nutsuwa don kansa. Su ka shiga mai da numfashi jiki a mace Dr ya mike bai iya cewa komai ba sai daukar mata kit da ya yi ya kai mota sannan ya ce ta fito su je. basu nufi mota ba sai suka nufi bangaren Aneesa kusan a tare suka yi sallama. Aneesa dake zaune a falon da kyar ta iya amsawa tana jifan Ameesha da wani irin kallo, ita kam murmushi ta yi tana zama a kasa kusa da kafar Dr. Dr ya kai dubansa ga Aneesa dake ci gaba da danna waya ya ce "Fatan kin shirya?" Ya mutsa fuska ta yi ta ce "Hamman na ce maka bani da lafiya fa, ba zan iya zuwa ko ina ba." Ran Dr ya ɗan ɓaci da maganar Aneesa ya aika mata wani kallo da yasa ta sunkuyar da kai kasa, ya ce "minti biyar na baki ki fito ina jiran ki." Daga haka ya mike. Ameesha ta bi bayan sa, da yake ranar zai koma ɗakin Aneesa sai Ameesha ta zauna a gaba. Cikin turo baki Aneesa ta isa wajen bata yiwa kowa magana ba ta shiga motar sannan Dr ya ja suka tafi. Bai zame ko ina da su ba sai gidan su Ameesha farin ciki sosai ya kama Ameesha, a parking space ya yi parking suka sanya Dr a tsakiya part din Meena suka shiga, har yan'uwanta sun fara zuwa Ameesha ta shiga cikin bedroom ɗin tana sanarwa da Meena zuwansu tare da Dr da Aneesa, cikin farin ciki ta fito da jaririn a hannu kamar kullum Dr ta mik'awa Yaron sannan suka gaisa, rungumar yaron Dr ya yi baya kaunar rabuwa da yaro, haka Aneesa ta ji zallar soyayyar Yaron ta ji tana son itama ta samu nata dan. Sakin fuska ta yi sosai akai ta harkar arziki, domin Dr nan ya barsu da niyyar idan ya dawo zai dauketa. Ummi da Abba sun ji dadin yadda Aneesa ta zo barka kuma har ta saki jiki hakan ya nuna suna zaman lafiya, karfe biyu Dr ya zo ya ɗauki Aneesa ya yin da aka bar Ameesha, ba su wuce gida ba sai da suka biya gidan Nenne a can suka k'arasa wuni sai yamma suka koma. Ameesha kam bayan tafiyar su Dr sai ta kwashi kayanta ta koma bangaren Ummi, Abba dake zaune yana karanta jarida ya bi Ameesha da kallo ganinta da kaya. "Uwata wannan kayan fa?" Turo baki ta yi ta ce "Kaya na ne Abba." "Shi ne kuma kika shiryo a cikin akwati?" "Eh! Abba ai kwana biyu zan yi." Wannan karon da sakin fuska ta yi maganar. "A'a uwata ki koma ɗakin mijinki gobe tunda ba wani abu za'a yi ba idan an gama sunan." "Abba ai shi ya ce na yi kwana biyu ka tambaye shi ka ji." "Ko shi ya ce gobe zaki koma." "Don Allah Abba ka yi hakuri wallahi shi ya bani kwana biyu Please Abbana." Ameesha ta k'arasa maganar tare da hawaye. "Je ki zamu yi magana da Asmad ɗin wannan ai shashanci ne." Ita dai tunda taga Abba ya barta da sauri ta haura sama, fes ta samu ɗakin kamar akwai mutum a ciki sai da ya gama zagaye dakin sannan ta shirya kayanta cikin wardrop, kwanciya ta yi tana tuna rayuwar ta na baya ga dimbin kewar Dr haka ta kwana, washegarin suna Yaro ya ci sunan Alhaji Abubakar suna masa lakabi da *(Sahal)* Aneesa da Nenne ma sun zo haka Ni'eema da mijinta Muhammad da yaransu Irfan da Yumna, ba su bar gidan ba sai daf da magriba. Washegarin suna sai bayan magriba Dr ya zo ya ɗauki Ameesha, domin ranar ta amshi girki, ji ta yi kamar karta bar gidan su, domin a kwanaki biyu da ta yi ta ji bata son rabuwa da gida. A gajiye ta k'arasa falon a kan kujera ta zube tana faɗin wash! Kallonta Dr ya yi yana faɗin "Autar Ummi kin gaji kenan?" "Allah baby na gaji sosai." Ki je ki watsa ruwa sai na samo mana abinci." "A'a baby nikam bana son cin komai sai abu mai sanyi zan sha." Sam Dr bai wani damu ba domin yasan sai da suka koshi a gidan su Ummi kafin suka fito, don haka sai ya nufi bedroom ɗinsa itama tashi ta yi ta nufi nata, wanka ta shiga bata daɗe ba ta fito karamar riga ta sanya wanda kusan komai nata a bayyane suke, domin zafi take ji daret firij ta nufa babu komai sai five alive din da Aneesa ta kawo ta ajewa Dr ranan, ɗauka ta yi ta fara sha har tana lumshe ido don ya yi mata daɗi sosai musamman irin sanyin da ya yi. Sai dai me kurɓanta na uku ta soma rasa hankalinta take ta tsinci kanta a wani yanayi da bata taba samun kanta ciki ba felling take ji sosai babu abin da take buk'ata sai Dr wata irin buk'ata take ji mai tsanani. Da kyar ta iya kai kanta falo haka da irin wannan ta nufi dakin Dr bata jin zata iya barin Dr ya fito. Fitowar Dr kenan daga toilet daure da towel, ya ga Ameesha ta zube a jikinsa da sauri ya taro ta yana girgiza ta "Cutie lafiya me ya faru da ke?" Kara shigewa jikinsa ta yi ta tana hawaye ta kasa faɗin abin da yake damunta, take Dr ya soma fahimtar abin da Ameesha ke ciki don haka sai ya haɗe bakinsu waje daya amma duk da haka bata bar hawaye ba, bai tsaya komai ba ya sureta sai kan gado yana kwantar ta a hankali ya shiga shafar duk ilahirin jikinta ya yi nisa, Ameesha tana jin dadin abin da yake mata Dr daga Ameesha sai ko idonsa ya sauka akan magani sak irin wanda ya gani ranan a ɗakinta, da sauri cikin takaici ya turo ta kasa daga gadon, wani irin zafi zuciyarsa ke masa. Sam bata ji zafin faduwar da ta yi ba, ita kawai buk'atar ta ta biya, don haka ta tashi ta hau gadon tana son shigewa jikinsa, rungumar sa ta yi tana faɗin "baby wake up please Dr wake up." Tana maganar tana ci gaba da shafata, cak ya dauketa daga jikinsa ya daka mata wani tsawa, wanda ya yi sanadin nutsuwarta. "Ke Ameesha karki takura ni, Ni zaki mai da shashasha wanda bai san abin da yake ba?" Hawaye na tsiyaya daga idonta take kallonsa bata san me ta yi masa ba, bai ji tausayinta ba amma yana mata masifa murya a raunane ta ce "ka yi hakuri Dr ban san laifin da na yi maka ba, don Allah ka yi min aikin gafara ka taimaka min kar na shiga wani hali." "Rufe min baki kin iya debo min bukata amma ni ba zaki yi min abin da nake so ba? Da bakin ki kika ce kin bar shan maganin amma dubi wannan ki gani." Ya jefa mata maganin. Dauka ta yi duk da bata cikin nutsuwa haka bai hana ta shiga wani rudun ba. Saurin toshe baki ta yi ta ce " Dr don Allah ka yi haku..." Bai bari ta gama maganar ba ya yi saurin katse ta "Fitar min a gida ki je gidan ku Maryam, bana son ganin ki na tsaneki." Yana gama faɗin haka ya shige toilet. Durkushewa Ameesha ta yi tare da rushewa da wani sabon kukan, maganar Dr ta karshe ta mugun girgiza ta, ga halin da take ciki ga maganar Dr. Jan jikinta ta yi da kyar tana hawaye ki cikin ta shiga Allah yasa ta ga da lemon tsami shi ta dauka cikin sauri ta yanka ta soma sha, domin ta rage sha'awa. Tana gama sha ta nufi bedroom canza kayanta ta yi ta dauki dogon hijabi tana tafiya tana cije baki ga hawaye a haka ta fita get tana tunanin ina zata nufa. *I love You fisibilillahi my fan's* 😘 *YAR MUTAN RANO* [10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* _*Masoya abin alfahari, duk inda nake bani manta masoyana Allah ya barmu tare da ku*_ *Ina yan TEAM NAJEEB MANSUR?* *Jinjina yake maku da fatan Alhairi* *Ina yan TEAM DR ASMAD ABUBAKAR (ɗan fullo)?* *Dr ya ce yana godiya sosai da k'aunar da kuke masa, ku ta ya shi da addu'ar samun farin cikinsa* *22* "Madallah! Ni ɗimma zuwan da na yi don mu k'ara shawarta yadda bikin zai kasance." Wani irin farin ciki ne ya ziyarci Mummy da jin batun Alhajin "Abba da gaske ka yadda in aure Ameesha?" Najeeb ya yi maganar jikinsa har yana rawa. Daga kan Najeeb ɗin Alhaji Mansur ya yi ya ce "Haba Najeeb duk duniya bani da burin da ya wuce in faranta maka, don haka na yadda da auranka da Ameesha, don Alhaji Taheer bai cancanci haka daga gareni ba." Don farin ciki ai Najeeb bai masan lokacin da ya rungume Abban nasa ba, ya soma zuba masa godiya kamar zai ari baki. Ita kanta Mummy farin ciki hana ta magana ya yi, amma da gani kasan tana cikin tsantsan farin ciki. Shi ma Alhaji Mansur ganin yadda suka samu farin ciki sai shima ya ji abin ya masa daɗi. "Ya maganar gidan naka?" Alhaji Mansur ya dawo dashi daga duniyar mamakin da ya shiga. "Em! Um! Abba na gama sai yan abin da ba'a rasa ba." "To ai shi kenan, tunda ka kammala komai, motar da na saya maku kai da matarka suna hanya insha Allahu." "Mun gode Abba Allah ya saka da Alhairi Ubangiji ya kara budi." "Amin Najeeb." A ranar dai haka gidan Alhaji Mansur ya kasance cikin farin ciki da kwanciyar hankali. *************************** "Ki bari kawai Rukky, ai wato ranar yana fita nima na yi fice wata, wani lafiyayyen asbiti na shiga mutanen sun iya aiki fa!" "Allah Hajiya yanzu cikin ya zube kenan?" "Tun yaushe na sa aka zubar da shege, duk da dai na ci wahala wajen fitarsa, ban da yawo da hankalina da wani likita ya yi, da yaga ruwan kudi sai kawai ya yadda, ke harfa harka muka kulla da shi sai dai ina tsoro, gashi jinin har yanzu yaki tsayawa." "Tsoro! Wani irin tsoro, ke Wallahi ki saki jiki ki fantama har duniya ta sanki, ke kenan kullum zaune cikin gida, shi kuma jini ki samu magani dole ya tsaya ko baya k'aunar Allah." "Eh! Ina tsoro duk da dai guy din ya haɗu, ko da ya ke bai kai Hamma Asmad ba, tom zan koma asbitin zuwa gobe, kuma dai ina tsoron abin da zai je ya dawo, don wallahi Hamma ba saurara min zai yi ba." Mtsss Rukky taja tsaki ta ce "Amma ke banza ce, fitowa fili zaki yi ki faɗa masa? Wai halan ke ba mace ba ce, da har bazaki iya yin abin ki cin sirri ba?" "Zan duba Rukky nima ina muradin saurayin, duk yadda muka yi zaki ji labari." "Yawwa yar gari, sai ki tanaji magungunan hana daukar ciki, da na tsayar da jini don kar a samu matsala, tunda shi Dr ya zo hannu bana jin zai samu salama a kwanakin nan." Da haka suka yi sallama, wani jin dadi ya kama Aneesa akan shawarar da Rukky ta bata. Ta mike da zumar fita falo sai ga Dr ya shigo bed din. Da sauri ta matsa inda ya ke tana faɗin "Hamma na shiga bed dinka ban ganka ba?" "Na fita tun asbah sai yanzu na shigo, fatan kin tashi lafiya?" "Lafiya lau, ina fatan kaima haka?" "Alhamdulillah! Sai kewarki da nake ji, Please Anee har yanzu jinin bai tsaya ba?" Kara shigewa jikinsa ta yi ta daura kanta a kirjinsa ta wani kashe murya ta ce "Bai tsaya ba, nima na rasa yadda zan yi Hamma." "Ok bari na kawo maki wani magani, insha Allahu zai tsaya don wallahi ina shiga wani hali, da kyar nake control ɗin kaina." "Kawo na sha nima ina son ya tsaya ɗin." Jin yadda ta ke kara shiga jikinsa duk sai hankalinsa ya tashi, karfin hali kawai ya yi ya mik'e, don yasan babu wani abu da zai samu a wajen ta. Yana fita taja siririn tsaki ta ce "Jini kam ya tsaya kawai bana son kana tumurmusa na ne a banza." Dai dai nan ya shigo tare da mika mata maganin. Amsa ta yi tana godiya. "Ki sha biyu yanzu zuwa anjima sai ki kuma shan biyu, zai tsaya ko wane irin jini ne." To ta amsa tare da bude firij ɗin bedroom ɗinta tare da dauko goran swan water, ta balli maganin. "Bari naje na shirya zuwa asbiti, na so makara yau kam." Asmad ya yi maganar yana tafiya. Aneesa dai karya ta yiwa Asmad akan haka kawai taga jinin ya ɓalle mata tunda ga jin mestiretion, alhalin kuma karya ne tun jinin da ta zubar da ciki ne yaki tsayawa. ************************** Yau biki sauran kwana huɗu, duk wani shiri sun kammala hattana kayan daki Alhaji Taheer ya saya mata na gani na faɗa, kai da gani kasan an kashe kudi wajen sayen su. Ita dai Amarya Ameesha bata ma san me yake gudana ba, da Meena kawai ake shawara, duk da Meena ba wani daɗi take ji ba, ciki ne da ita sai wahalar da ita yake, haka take daurewa. Suna zaune a falo dukka family na Alhaji Taheer, tattaunawa suke na bikin Ya Jaheed ya gyara zama tare da maida hankali kan Abba ya ce "Wai Abba yanzu idan aka daura auren Auta tarewa zata yi?" "Mai zai hana Jaheed?" "Abba ya kamata dai ka duba halin da take ciki, ka bar maganar tarewa har zuwa lokacin da zata samu lafiya." "A'a Jaheed ka barta ta tare, ai kwanaki kaɗan ya rage su tafi." "To Abba ai shi kenan." "Bari na mike don muna da meeting yau, kai Jaheed akwai wasu kaya da zasu shigo yau sai kaje ka kula da komai." Abba ya yi maganar yana fita, suma tashi suka yi don dama rana ta yi sosai. Ummi dai dake gefe shiru ta yi tana sauraron su, a zuciyarta tana alhinin rabuwa da autar ta, sai dai tana mata addu'a da fatar samun lafiya. ******** Zaune cikin ofishin sa, waya ce yake yi da gani kasan mai muhimmanci ci ne "No! Hafiz wallahi na cire raina daga Ameesha, duk da ina mugun sonta, kuma na tabbatar ko mutuwa na yi to sonta ne dalili amma kar wannan ya dameka." "Yawwa abokina, kasa aranka in har matarka ce tofa babu makawa sai ka aureta." "Insha Allahu na dauki shawarar ka, Allah dai ya kara rufa mana asiri." Daga haka suka yi sallama. A haka Dr Asmad ya gama aikinsa ya wuce gida, duk da zuciyarsa tana mararin ganin Ameesha amma haka ya daure don yasan kwanaki biyu ya rage ta matar wani. Addu'a ya je mata da fatan alheri, a duk inda ta samu kanta, ko da ya fita ba gidansa ya nufa ba, gidan iyayensa ya nufa, don ya kwashi gaisuwa. *Gidan Alhaji Taheer* Ummi ce tsaye a farfajiyar gidan, tana kallon yadda baki 'yan biki ke ta hada - hada, yayin da wasu suke isowq ma a lokacin. Kasancewar kwana biyu ne ya rage kacal daurin auran Ameesha. Duk wanda yasan Ummi da kuma yadda ya karancin halayyar dan Adam, to cikin kankanen lokaci zai gane Ummi na tattare da damuwa. Ta ja wani siririn tsaki hade da daga kafafunta da suka yi mata nauyi, ta shige kuryar dakinta, inda ta yada zango a kan gadonta. Namma tsakin ta rika ja, duk lokacin da ta dakko tunanin ta hade direwa. Da za a dure tsakin da Ummi ta yi yau a buhu, ba abun mamaki ba ne don ya cika buhu da rabi. Tana daga kwancen ta amsa sallamar da aka yi, ba tare da ta dago kai ta kalli me sallamar ba. " Tun da na shigo gidan nan na fahimci kina cikin damuwa. Wai duk tunanin rabuwa da Ameeshan ne tun yanzu? Aunty Saude k'anwar Ummi ta yi tambayar tana zama kusa da ita. "Bari kawai, har da hakan ma wallahi, ina tunanin ya zaman yarinyar nan zai kasance, ita ba wata me koshin lafiya, wallahi naso ace magani aka fara neman mata fiye da maganar aure. Har yanzu mune muke kidanmu da kuma rawarmu, don gidan su Angon nan har yanzu tsinkensu bai shigo gidan nan da sunan maganar aure ba." Ta karasa maganar tata hade mikewa zaune, cikin jimami tana kallon Aunty Saude. A jiyar zuciya Aunty Saude ta sauke ta ce "Ki bar tunanin nan kar ya haifar maki da wata matsala, tunda Alhaji ya yi niyyar auren nan na tabbata ko da ba zasu kawo komai ba tofa sai anyi shi, ita dai Ameesha addu'o kawai zaki rika yi mata." "Insha Allahu zan yi. "Amma anya kuwa Aunty gidan mazan nan suna son auren kuwa...? _Ku yi hakuri da wannan Please._ _*YAR MUTAN RANO*_ [10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* *23* "To ni ina zan sani masu, abu daya dai na sani shi ne sun bata min rai." Cikin takaici Ummi ta k'arasa maganar. "A dai kara hakuri Aunty." "Yo ai hak'uri ya zama dole, tashi ki je wajen autar kila tana bukatar wani abun." "To Aunty" shi ne abin da Aunty Saude ta faɗa tana mik'ewa. *********** Asmad ne kwance a daki sai juye juye ya ke yi, tunda garin Allah ya waye sallah kawai ya yi, sam baya jin dadin jikinsa tunanin rabuwa da abar sonsa Ameesha shi ya haddasa masa wannan zazzafar zazzaɓin, duk da ya sha magani amma babu wani sauki. "Sannu Hamma ya jikin?" Aneesa ce ta yi maganar tana zama a bakin gadon. "Da sauki." Asmad ya yi maganar cikin karamar murya. "Allah ya kara sauki, ko za'a sanarwa su Nenne ne?" "No! Ba sai kin sanar masu ba, kar hankalinsu ya tashi, ai na samu sauki zuwa anjima zan fita." "Allah ya kara lafiya." "Amin! Haɗa min ruwan wanka kila ko na kara samun kwarin jikin." Ya dire maganar yana tashi zaune. Cikin kankanin lokaci har ta gama haɗa masa ruwan, sannan ta fito tana faɗin "Hamma na gama!" "Na gode, ɗan taimaka min." Da taimakon Aneesa ya yi wankan, har ya shirya babu laifi ya ɗan samu kwarin jikin, tunda har falo ya fito ya kunna t.v . *Yau saura kwana daya biki* Zaune a falo Ameesha ce da Meena, Meena ke gyara mata gashinta wanda suka je aka wanke, shi ne kaɗai abin da Ummi ta yadda akawa Meesha don ta ce yarta bata da lafiya abarta har zuwa lokacin da zata sami sauki sai a yi shagalin auren. Meena ta kalli Meesha ta ce "Meesha gobe iwar haka kin zama amaryar Najeeb." "Amaryar Najeeb?" Meesha ta tambaya. "Eh! Gobe zaki tafi ki barmu, zan yi kewa." Wannan karon Meesha shiru ta yi kamar mai tunanin wani abu, haka Meena ta ci gaba da mata hira amma taki amsawa. "Alhaji wai kuwa kana ga yaron nan na son Auta?" "Wannan wacce irin tambaya ce?" "Allah ya baka hak'uri, amma ni sam tsarin auren nan bai min ba." "To ni kuma ya min." Abba ya kai karshen maganar yana barin wajen. "Allah ya kyauta, amma wannan abin ban taɓa ganin ko jin irinsa ba." ** Yau kam jikin Dr ya yi sauki don har fita ya yi asbitin su, sai da ya kammala da duba marasa lafiya tunkun ya koma office, duk da yau din ta kasance Lahadi ne, babu aiki amma shi Asmad ya saba ya je don duba marasa lafiya. Office ya koma, ya zauna tare da janyo laptop dinsa, wani bincike yake yi akan wata ciwon, wayarsa dake gefe ta soma kara, ɗan tsaki ya ja don bai so a katse masa aikin da yake, sunan Hafiz ya gani . Hannu yakai tare da ɗaukar wayar ya kara a kunne "Hello Dr kana jina?" "Eh! Dr ya amsa a takaice. "Dama zan ce maka ne zaka samu zuwa wajen daurin auran kuwa?" "Daurin auran wa?" Ya yi tambayar. "Auren Ameesha mana." "Oh! Wai yau ne auren?" "Eh! Mana hala baka duba katin da Jaheed ya kawo mana ba?" "Gaskiya dai ban duba ba, kuma yanzu ina wani aiki ne, bani ma a gida ina office don haka ba zan samu zuwa ba, amma ko zuwa gobe zan je na yi masa Allah sanya Alhairi." "To ai shi kenan, nima ɗin da kashe aikin zan yi muje tunda haka ne to mu bari sai goben." "Allah ya kaimu." Dr ya faɗa yana kashe wayarsa. Ko da ya gama wayar, tagumi ya zuba idonsa taf da kwallah, zuciyarsa wani mugun zafi take, musamman da ya ji yau auren farin cikinsa, a fili ya furta *"Shi kenan ni kuma na rasa farin cikina daga yau har zuwa ranar da zan koma ga mahaliccina."* A dole barin aikin ya yi don wani sabon zazzaɓin ne ya kuma saukar masa. Da taimakon addu'a ya isa gidansu. Ko kyakkyawan fakin ba yi ba, ya fita daga motar. Ko sallama kasawa ya yi sai zubewa da ya yi akan kujera, dage da kansa Nenne dake zaune a falon ganin shigowar Asmad ɗin a wannan yanayin yasata saurin mik'ewa tana ambaton sunan Allah. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Asmad lafiya?" Da kyar ya iya furta "Nenne bani da lafiya ne." "Subhanallah me ya same ka? Daga ina kake?" A hargitse Nenne kewa Asmad ɗin tambaya. Cije leɓe ya yi ya ce "Daga office nake, wayyo Nenne kaina ciwo ya ke." Hankalin Nenne ya mugun tashi da ciwon Asmad ɗin, wayarta ta dauka ta kira Bobbo tana sanar masa da halin da ake ciki. Ai cikin sauri Bobbo ya iso gidan yana, shi ma ya tsorata da yadda Asmad ɗin ya ke. Wayarsa yasa ya kira wani Dr abokin Asmad ɗin, cikin kankanin lokaci ya iso, duba shi ya yi sosai sannan ya masa allura ya bashi magani, babu jimawa bacci ya kwashe shi. Kallon su Bobbo ya yi ya ce "Ku kwantar da hankalinku damuwa ce ta haifar masa da zazzaɓin, amma insha Allah sanda zai farka zai ji sauki ." Godiya sosai suka masa sannan ya tafi. (To Asmad Allah ya baka lafiya da sauran musulmai baki daya.) *Wajen daurin auran* Jama'a ne dankam a kofar gidan Alhaji Taheer, duk inda ka duba motocine ga sunan birjik manya na Alfarma, kallo ɗaya zakawa Abba kasan yana cikin farin ciki da wannan rana. Su ya Jaheed ma sun hallara, fuskokinsu cike da farin ciki, dangin Ango kawai ake jira a daura auren. Tun 12 aka sa lokacin auren gashi har 12:30 da yawan mutane har sun fara kosawa, shi kansa Abba mamakin rashin zuwan su Alhajin yake. Wani mutum dake gefe ya buɗe baki sosai tare da fadin "Kai wallahi mukam mun gaji da wannan jiran, zamu wuce don muna da aikin yi..." Tun kafin ya gama rufe baki sai ga wani mutum, da gani kasan dan jagaliya ne don yadda ya burgago mashing ɗinsa cikin mutane mai cikakken hankali ba zai iya yin haka ba. Kai tsaye wajen da su ya Jaheed suke ya nufa tare da mika masu zungureriyar takadda mai cike da rubutu, da rashin sani ya Jaheed ya kalli mutumin ya ce "Kai wannan fa daga ina?" "Kai ma ba kazo daurin auran ba ne?" Ya yi maganar cikin muryar su irin ta yan dabar. "Eh! Ya Jaheed ya bashi amsa. "To ka bawa uban amaryan, don ni ba sanin sa na yi ba." Yana gama faɗin haka ya ja mashin dinsa ya bar wajen. Da kallo suka raka shi, juya takaddan ya Jaheed yake sannan ya nufi inda su Abba suke, zuwa wannan lokacin jikin Abba ya jike sharkaf da zufa. Zuwa lokaci Alhaji Taheer da abokinsa Alhaji Usman sun yanke shawarar a daura auren, har an soma gabatar da yadda ake auren. Maganar Jaheed ce ta dawo da shi "Abba gashi wani ya kawo wai abaka." Jaheed ya yi maganar yana mik'a masa takaddan. Hannu Abba ya mika cikin faduwar gaba, ya ce "Daga ina kuma ina mutumin?" Ya yi maganar yana juya takaddan. "Yana bani ya wu ce." "To aje wajenka har a gama daurin auran." "A'a Alhaji ya kamata abude wannan takarda don sanin me ta kunsa, mu je daga waje." Alhaji Usman ya yi maganar. Babu musu Abba ya yadda, sai da suka fita can nesa da jama'a suka tsaya, sannan Abba ya bama ya Jaheed umarnin ya karanta, take ko ya buɗe ya karanta masu. Hankalin Abba ba karamin tashi ya yi da jin abin da takardar ta kunsa ba, nazari ya yi kamar na minti biyu da ya ce "Mu je kawai Alhaji a daura auren, ka zama wakilin amarya ni zan zama wakilin ango." Aiko haka aka yi cikin karamin lokaci aka daura auren, ana gama ɗaura auren Abba ya saki ajiyar zuciya take wata ni'ima ta saukar masa, hankalinsa ya kwanta. Sai dai kuma a waje mutane duk sun cika da mamakin yadda aka canza akalar daurin auran kamar yadda suka gani a kati, haka dai suka gama haɗa hadar su Abba kam yana gama sallamar manyan bakin da ya gayyata cikin gida ya shiga, falonsa ya shiga tare da cire babbar rigarsa wayarsa ya ɗauka ya kira Ummi lokacin tana cikin jama'a babu wayar a kusa da ita sai Aunty Saude ta kawo mata. Tana duba Number din ta yi saurin ɗauka "Ki sameni a falona." Shi ne kaɗai abin da Abba ya faɗa ya kashe wayar, ya soma sintiri cikin dakin, yana jan tsaki. A haka Ummi ta isa falon bakinta dauke da sallama. "Lafiya Alhaji?" ta faɗa bayan ta kammala karantar halin da ya ke ciki. "Babu lafiya Halima." Ya bata amsa a takaice. "Me ya faru? Ta kuma masa tambayar hankali tashe. "Babu lafiya." "Ba'a daura auren ba ne?" "An daura sai dai an samu canji." "Wani irin canji kuma Alhaji?" "Canjin ango aka samu." "Ango kuma? To dawa aka ɗaura auren?" "Da ..." _Ku biyo ni don jin dawa aka daura auren, ni ce dai_ _*YAR MUTAN RANO*_ [10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* *24* Zama ya yi akan kujera, don duk wannan maganar da suke yi a tsaye ya ke ya ce "Wato Halima da mutuncina da komai aka so tozartani, babu komai domin Allah ya kawo canji mafi Alhairi." "Alhaji ka fara maganar kuma yanzu ka dauko wata, wacce ban fahimci komai daga ciki ba." "Haba menene abin saurin tambaya kuma? Ai gani gaki dole ne kisan komai da ke faruwa, Alhaji Mansur ya bani mamaki matuka ya dasa min bakin ciki a zuciyata." Tagumi Ummi ta yi tare da zuba masa ido tana kallonsa,har zuwa wannan lokacin bata gane inda maganarsa tasa gaba ba. Ganin ta kosa ta san komai sai Abba ya mika mata takaddan ya ce karanta wannan. Cikin sauri tasa hannu ta amsa tare da buɗewa ga abinda sakon ya kunsa. *Malam Alhaji Taheer kenan, nasan ya zuwa yanzu kun riga da kun hallara wajen daurin aure ko? To kar kayi mamakin rashin ganina da jama'ata, don tuni aka daura auren Najeeb da matarsa lafiyayya, na faɗa maka maganar gaskiya shi ne ka nema wa mahaukaciyar yarka miji dai dai ita, amma fa ba dai Najeeb nawa ba, don shi lafiyayye ne kuma lafiyayyen mata zai aura.* *Wato tun lokacin da ya kamata ka yi maganar zaka hada su aure ba ka yi ba sai da yarka ta haukace tukun ka ɓullo da maganar don kana son rabuwa da ita, sai ni kuma ka kwaso ka kawo min gida to ba zai yuwu ba, nima bani haɗa zuri'a da mara hankali, don haka ka sama mata miji dai dai da rashin hankalinta, in yaso sai su yi ta haifo maka jikoki marasa hankali sako daga ni ALHAJI MANSUR.* "inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Shi ne kalmar da Ummi ke maimaitawa a fili. "Ai dama wallahi jikina ya bani, an so shirya mana walak'anci baccin haka ta ya za'a ki kawo kayan da gidan ango suke kawowa? Tun farko abin da na guda kenan sai gashi ya afku yanzu Alhaji ya kenan za'a yi?" Ta ci gaba "amma wallahi Alhaji Mansur ya bani kunya ban yi tunanin haka daga gareshi ba." "Sosai kuwa, domin ko ni lokacin da wasikar ta same ni, gaskiya na yi mamaki don har kiran wayarsa na yi ya kuma tabbatar min da shi ya aikota." "To ai shi kenan, tunda haka ne yanzu ya za'a yi kenan?" "Kamar ya fa?" Abba ya tambaya. "Game da ɗaurin auren mana. Ummi ta bashi amsa. Nannauyan ajiyar zuciya ya sauke, tare da muskutawa ya ce "Bayan Jaheed ya gama karantawa kuma na kira Mansur ya kuma tabbatar min da shi ya aiko da takadan." "Shi ne Alhaji Usman ya ce sam haka ba zai yiwu ba, in samu wani ko da a cikin ya'yan yan'uwana ne a daura da shi, nan ma naga ba wata mafita kada a samu cin mutuncin da yafi na Mansur, sai ga wani mutum ya nufo inda muke tsaye, shi ne fa ya tambaya me yake faruwa take muka sanar sa, sai ya ce n ba damuwa a daura ɗansa duk da a farko na so bijirewa amma sai Alhaji Usman ya hana, nan take na amince amma fa can kasan zuciyata ina tunanin abin da zai je ya dawo." "Take mahaifinsa ya biya kudin sadaki dubu hamsin kawai na amsa, don irin halarci da ya min duk da ban san kalar ɗan nasa ba, sai dai ina fatan ya kasance mutumin kwarai. "Ɗazun aka daura auren *ASMAD ABUBAKAR DA MARYAM TAHEER* "Masha Allah Alhaji Allah ya tabbatar da Alhairi, Ubangiji yasa haka shi ne mafi Alhairi a garemu da ita baki daya." "Amin." Abba ya amsa "Yanzu dai ki tashi ki je ki ci gaba da sallamar baki zuwa anjima sai mu kara shawartawa, ni ɗimma da sauran mutanen da zan sallama." Da to Ummi ta amsa tana fita daga falon, a zuciyarta tana Allah wadai da halin Alhaji Mansur. A daya bangaren kuma tana addu'a Allah yasa wanda Ameesha ya zame mata bango wajen jin gina. Haka dai a kai ta gudanar da biki har zuwa lokacin da bakin kusa suka tafi sai wanda suka zo daga nesa. ****** "Najeeb ne zaune a wata farfajiya duk da iskar dake kadawa amma shi Najeeb, jin iskar ya ke kamar hucin wuta, kallo ɗaya zaka masa kasan yana cikin muguwar damuwa." Tsaki ya ja mai karfi tare da jawo wayarsa, a gogon wayar ya kalla karfe 2:01a gogon kasar Faransa dai dai da agogo Nigeria karfe goma sha biyu. Wani murmushi ya saki a fili ya furta "Alhamdulillah! Yau Ameesha ta zama tawa." "Ya so da Abbansa bai turo shi garin nan ba, musamman da yau ne ranar da ta kasance ranar farin ciki a rayuwarsa, amma sai Abbansa ya turo shi akan wasu kaya wanda shi bai ga wani amfanin su ba." Mtsss ya ja tsaki. Hankalin Alhaji Mansur kwance yana zaune akan kujerar falonsa, waya kawai yake amsawa daga abokan arzikinsa suna masa murnar daurin auran, Mummy ce ta k'araso falon cikin farin ciki bayan ta zauna ne ta ce "Sannu Alhaji an daura aure lafiya?" "Yawwa Hajiya lafiya lau." "To yanzu Alhaji ina za'a kai yarinyar kasantuwarta mara lafiya, kaga dole tana bukatar masu kula da ita, inda zai yiwu kawai a kawo ta nan har ta samu lafiya." "Wa ki ke nufi ne?" "Matar Najeeb mana Ameesha." "A'a gyara magana dai, ai matar Najeeb sunanta *RUFAIDA*." Wani zabura Mummy ta yi ta ce "Ban gane Rufaida ba, ina ce Ameesha ce yar gidan Alhaji Taheer?" "Haba Hajiya ya ki ke son maida hannun agogo baya? kin san tuni na ce bana son auren nan ke da ɗan ki kuka na ce sai an yi, to da naga na rasa hanyar da zan bi don hanawa shi ne ai na tura Najeeb ɗin kasar Faransa da sunan ya kular min da wasu kaya, na yi haka ne don in samu in cika burina, to kuma Alhamdulillah don buri ya cika..." "Alhaji an ya kana cikin hankalinka kuwa? Wai kasan abin da kake faɗa ma kuwa?" "Ras na sani, ce wa na yi da Rufaida aka daura auren ba da wannan mara hankalin yar Taheer ba, don ina son ake haifa min jikoki masu hankali ba mahaukata ba." Ya ida maganar cikin izzah. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Amma kam wallahil azeem Alhaji baka da imani, dama saboda ka tauye hakkin yaron nan ne ka tura shi can kasar? Allah sai ya maku hisabi da shi." Harara kawai ya ke ta aika mata da shi sannan ya ce "Kin gama zagina? To wallahi bari ki ji, ke kin yi kaɗan in zartar da hukunci ki ce zaki bijire min, ai tun farko sai da na ce bana son auren kuka na ce, don haka sai na bullo maku ta yadda baku tunani." "Hmmmm! Wannan kuma matsalar ka ce, amma sam baka wa Najeeb da Alhaji Taheer adalci ba, kuma insha Allahu zaka ga abin da ka aikata masu." "Ke wallahi ki yi a hankali akan wannan auren kina iya rasa na ki aurn." Yana gama faɗin haka ya tashi tare da barin mata wajen. Kuka Mummy ta fashe da shi domin kuwa abin ya ɓata ranta sosai, addu'a take Allah ya sawa Najeeb dangana akan Ameesha. ******* Dr dai har yanzu sam jikin babu daɗi domin dai ya kasa cire tunanin Ameesha a zuciyarsa, Nenne ce ta shigo bedroom ɗin hannunta rike da cup, kallon Asmad ɗin ta yi ta ce "Tashi kasha wannan shayin kana ciwo babu cin abinci!" Girgiza za kai ya yi ya ce "A'a Nenne bana jin dadin bakina ne, ki bar shi zuwa anjima zan sha." "Ka daure dai ko kaɗan ne ka sha ka ji ko?" Sam Asmad baya k'aunar yiwa Nennensa musu don haka sai ya tashi zaune tare da karbar cup din, kurba biyu ya yi ya ce ya koshi ya aje cup din. "Ka kira Aneesa ka sanar mata baka da lafiya?" "A'a Nenne." "Tom ya kamata dai ka sanar mata, don karta ji shiru." "To." ya amsa yana gyara kwanciya. Girgiza kai Nenne ta yi kawai, wayar Asmad dake kan dressing mirror ta dauki kara, Nenne ce ta dauko wayar tare da mika masa. Ganin Number din Bobbo ne yasa shi ɗauka tare da yin sallama. "Assalamu Alaikum! Bobbo an wuni lafiya?" Daga ɗaya bangaren Bobbo ya amsa "Lafiya lau Asmad ya jikin naka?" "Da sauki ." Asmad ya bashi amsa. "Allah ya kara lafiya." "Amin." Ina ji Asmad. "Ka daure ka shirya zaka rakani wani waje." Gaban Dr ya yi muguwar faduwa da sauri ya ce "To Bobbo gani nan zuwa." "Eh! Yanzu bari na shirya." "Kai dawa kake magana? Har na ji kana ce wa kuna zuwa, kai da baka da lafiya?" Nenne ta yi tambayar tare da tsare Dr da ido. "Nenne inji Bobbo wai in shirya zamu fita." "A haka zaka fita kai da ba daɗi kake ji ba?" "Ai zan iya tafiya." Dr ya yi maganar cikin karfin hali. "Ok" kawai Nenne ta iya fada, cikin zuciyarta kuwa cike da mamaki ta ke fadi "oh! Dama don budurwarka tana aure shi ne har da yin ciwo? Lallai ba karamin so Asmad kewa wannan budurwar ba, da a ce tun-tuni tasan kallar son da Asmad kewa wannan budurwa kenan, to da tasan yadda ta yi har Asmad ɗin ya sameta, to an baro shiri tun rani, yanzu kam addu'a zata ke masa Allah ya daura masa hakuri da dangana." Domin dai ɗazun da Hafiz ya zo Ne ta ji hiranmu. Shi ma Dr Nenne tana fita ya tashi ya shiga toilet, bai wani jima ba ya fito sam jikinsa babu kwari a haka ya fita falon ya samu Bobbo da Nenne "Ya jikin naka? Bobbo ya kuma tambaya. "Da sauki." "Zaka iya tafiyar ma kuwa?" "Eh! Zan iya." Asmad ya baya Bobbo amsa. "To shi kenan mu tafi ko?" "Eh! Kawai Asmad ɗin ya faɗa yana soma tafiya. Cikin motar Bobbo suka shiga, Dr yasa hannu zai buɗe kenan sai ga Hafiz ya shigo, Bobbo ya yi murmushi ya ce "Dama dai yanzu nake shirin kiranka ina ce ma mu haɗu a can." "A'a kuma sai gani tanan." "Ka kyauta, shiga mu je kawai." Shi Hafiz ya yi kamar yadda Bobbo ya bukata, sannan direba ya soma jan su. Mamaki sosai ya kama Dr ganin sun nufi unguwar su Ameesha, bai gama yin mamakin ba sai da ya ga sun shiga cikin gidan. "To wai mai Bobbo da Hafiz suke nufi, sun dauko shi zuwa gidan su Ameesha bayan yau aka daura aurenta da wani, ko dai basu san sanadin ta ne ɗazun ciwo ya kama shi ba?" Ya yi wa kansa tambayar da babu amsa. A parking space direba ya faka sannan suka fita dai dai lokacin da ya Jaheed ke fitowa ganin Dr a da sauri ya k'arasa wajen, "a'a Dr Barka da zuwa ku zo lafiya?" "Lafiya lau, an daura auren lafiya? Please ka yi hakuri wallahi yau ban wuni da lafiya ba ne." Dr ya yi maganar cikin sanyin murya. "Haba Dr wallahi karka damu ai ciwo ya fi gaban wasa." " Yi mana iso wajen Alhaji mana! Bobbo ya katse masu jiran da su ke yi. Babu jimawa ya Jaheed ya dawo yana sanar masu da Abba ya ce su shiga, babban falo aka yi masu masauki zallar farin ciki ne ke tattare da Abba, duk sun zazzauna sannan Bobbo suka kara gaisawa da Bobbo. Mamaki ya kama Abba ganin Dr tare Allhaji Abubakar ɗin "A'a Dr yau kaine a gidan namu?" "Eh! Abba." Dr ya amsa masa cikin girmamawa. "Ashe kun ma san juna! To ai shi ne ɗan nawa." "Eh! Mun san juna don shi yake kula da lafiyar yartawa." Domin dai Abba ya yi masa bayanin ciwon Ameesha ɗin. "To ai shi kenan ma faduwa tazo dai dai da zama." "Kai madallah! Wallahi wannan abu ya yi sai fatan Allah ya sama abin albarka,domin dai Dr mutumin kirki ne." Duk wannan maganar suna yin tane bayan fitar su Asmad. "Alhaji kun zo tafiya da ita ɗin?" Abba ya tambaya. Murmushi kwance a fuskar Bobbo ya ce a'a ya zo dai ya gaidaka ne, har yanzu bai san abin da ke faruwa ba." "To ai shi kenan." "Yanzu abin da za'a yi kawai shi ne, Hafiz zai ɗauki ita Ameesha don shi Asmad gida zai tafi in ya so sai dai ya zo gida ya ganta ina ganin haka zai fi ko?" "To ni ai bani da wani zaɓi da ya wuce yadda ka ce, fatan alheri zan yi masu da nasara, zuwa karshen sati za su tafi Egypt inda za'a duba Ameesha din." "Allah ya kaimu, muna godiya da karamci Allah ya saka da Alhairi." Haka su Bobbo da Abba suka yi ta hiransu. Bangaren Asmad kuwa can lambun gidan suka koma shi da Hafiz da ya Jaheed hira suke, amma shi Dr daga eh sai a'a kawai ya ke faɗa, so yake ya tambayi ankai Ameesha ko ba'a kai ta ba amma ya kasa. Da ya gaji sai ya mik'e yana faɗin "Ni kam na gaji da zaman nan, bari na tafi gida insha magani." "Ayya to sannu Allah ya kara sauki." Suka hada baki wajen faɗa. "Mu je sai na sauke ka a gidan." Ya Jaheed ya yi maganar yana tashi. "Hafiz kai ba yanzu zaka tafi ba?" "Eh! Zan jira Bobbo sai mu tafi." Hafiz ya bashi amsa. "Ok." Dr ya faɗa yana tafiya. "Allah ya kara sauki *angon Amee...* Wani irin juyowa Dr ya yi cikin wani irin yanayi ya ce.... *YAR MUTAN RANO* [10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* *Na baki kyautar wannan shafin ki yi yadda za ki yi da shi, UMMYN YUSRAH ke ɗin ta daban ce, Ubangiji ya bar k'auna Allah ya raya mana su Yusrah bisa sunna.* ```Ina miko godiya a gareku masoya wannan buk ɗin hakika ina jin dadin yadda kuke gwada min k'aunar da kikewa wannan buk Rabbi ya barmu tare, ina sonku masoya```😍😍😍😍 *LAIFIN WA? & SANGARTA FANS* Ina yinku irin sosai ɗin nan, musamman yadda kuke comment.😘😘😘 *I hearttttt you my besty KHADIJAH S MUHAMMAD*💞 *25* Sallama ya yi tare da shiga cikin falon, shirun da ya ji shi ya bashi damar sanin babu kowa a falon, don haka sai kawai ya kama hanyar bedroom ɗinsa, kasancewar tun a hanya ya ga an shiga sallah sai shima ya wu ce toilet ya dauro alwala, ba zai iya zuwa masallaci ba, don haka cikin bed din ya tada sallarsa, yana zaune har aka kirayi ishsha aka shiga, bayan ya idar da sallar sai ya koma falo yana mamakin rashin jin motsin Aneesa a gidan. Bai zame ko ina ba sai bed ɗinta, yana tura kofar ta buɗe can kuryar gado ya ganta ta kudundune cikin bargo, duba ɗaya zaka mata ka tabbatar babu lafiya. Ganin Dr ai da sauri ta ya ki ce bargon ta nufe shi da dan sassarfa, jikinsa ta faɗa ragafff, saurin tallafeta ya yi yana faɗin "Subhanallah! My Anee mai ya sameki?" Ɗago jajayen idanunta ta yi wanda kallo ɗaya zaka mata kasan ta ci kuka "Hamma daga ina kake?" Ta yi tambayar dai dai da zubowar hawayen da ta ma'kale. "Ina gidansu Nenne tun safe bana jin dadi." Ya bata amsa yana gyara mata zama a jikinsa. "Sorry Hamma ai ban san kana gidansu Nenne ba da nazo, hankalina ya tashi da rashin ganinka na kira wayarka duk baka ɗauka ba!" "Ban kula ba da yake wayoyin duk suna silent ne." "Please Hamma karka kuma tafiya ka daɗe, ko baka da lafiya ka dawo gida zan fi son haka." "An gama Madam." Dr ya yi maganar tare da ɗan sakin murmushi. "Mu je falo ka ci abinci." Aneesa ta yi maganar tana tashi. Tashi ya yi tana rike da hannunsa suka nufi dining inda ta shirya masa abinci ****** "Kai Alhamdulillah! Wallahi Alhaji na yi matukar farin ciki da jin wannan maganar, Allah ya amsa addu'a ta, ya haɗa Auta da miji na kwarai mai cikar mutunci da hankali." Cikin tsantsan farin ciki Ummi ke wannan maganar. Shima ɗin Abba zama ya gyara ya ce "ai wato Hajiya wani hani daga Allah baiwa ce, kin ga yanzu babu wanda ya yi zaton haka, amma gashi Allah mai rahama da jin kai ya yi mana canji na Alhairi, addu'ar zaman lafiya kawai zamu ke yi masu." "Haka ne Alhaji Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a dayyaba." "Amin." Abba ya amsa. Suna cikin hiran ne Meesha da Meena suka shigo, Meena zama ta yi a kasa tana gaida su Ummi ya yin da Meesha ta je kan kujerar ta yi kwanciyar ta, ko kallon su Ummi bata yi ba. "Meena kin kuwa san dawa aka daura auren Auta?" Ummi ta tambaya. "A'a Ummi" Meena ta bata amsa. "Ai kin san Dr da yake dubata ko?" Cikin sauri Meena ta amsa da "Eh!" "To da shi aka daura auren, bayan rashin mutunci da Alhaji Mansur ya yi mana." Ummi ta k'arasa maganar cikin takaici. Wani farin ciki ne ya ziyarci Meena jin da Dr aka daura auren Ameesha, wannan abu yana daga cikin burin Meesha sai gashi dama ya samu, sai dai kash Meesha bata san wainar da ake to yawa ba." "Amma fa Ummi na yi farin ciki sosai Ubangiji ya sa hakane mafi Alhairi." "Ameen." Ummi ta amsa. Tashi Meena ta yi tana faɗin "Ummi bari na tafi sai da safe." "Allah ya tashemu lafiya." Bayan tafiyar Meena, Ummi ta umarci Meesha ta shiga bedroom ɗinta. Kin tashi ta yi sai ma kallon Ummi da ta ke yi "Uwata ta shi ki shiga ciki ki yi sallah sai ki kwanta." Abba ne ya yi maganar yana da ga inda ya ke zaune. Tashi ta yi tana turo ƙaramin bakinta, mamaki ya kama Ummi ta ce "Ikon Allah ko dai yarinyar nan da abun da ta ke bukata ne?" "Babu komai rabu da ita, yanzu zata wuce." "To Allah ya kyauta." Ummi ta yi maganar bayan wucewar Ameesha. **** Da mamaki sosai Nenne ta ke kallo Bobbo jin maganar da yake faɗa mata. Wani jin dadi wanda rabonta da shi tun ranar haihuwar Asmad sai yau da ta ji wannan labari ta kuma jin irinsa. "Alhaji dama ka taɓa zuwa nema masa aure ne?" Nenne ta yi tambayar cikin mamaki. Girgiza kai ya yi ya ce "a'a ko ɗaya kawai zuwa wajen ɗaurin auren na yi, dama kafin na tafi sai da muka tattauna da Hafiz, yake sanar min halin da ake ciki, na tausaya ma Asmad sosai haka na tafi wajen ɗaurin auren bani da cikakken nutsuwa, bayan mun je sai baƙon lamari ya bullo, ganin uban yarinyar yana gaf da shiga wani hali sai kawai na yake shawarar a daura da Asmad ɗin, cikin karamin lokaci aka daura." Bobbo ya dire maganar murmushi kwance a fuskarsa. "Masha Allah! Allah ya tabbatar da Alhairi, na yi farin ciki sosai." "Ameen." Bobbo ya amsa. "Amma fa har yanzu Asmad ɗin bai sani ba." "Hhh! Ka ce *Auren bazatta* ka yi masa?" "Sosai kuwa." "To ai shi kenan, muna godiya da hakan, sai yaushe kuma zata tare?" "Sai bayan sun dawo daga Egypt tukun, don ana son a kaita don duba lafiyarta." "To Allah ya taimaka, amma ni dai gobe zan je ganinta." "Allah ya kaimu." ***** DR ne zaune a bakin gadonsa hannunsa a kan haɓarsa, tunda garin Allah ya wu ye sallah kawai ya yi ya zauna ya soma tunanin Meesha, duk lokacin da ya tuna ya rasata bugun zuciyarsa ke ƙaruwar, ƙaramin tsaki ya ja tare da cusa hannunsa cikin sumarsa. Ƙaran wayarsa ta dawo da shi cikin nutsuwarsa, kallon wayar ya yi tare da sa hannu ya dauka "Assalamu Alaikum Nenne ina kwana?" "Wa'alaikumus salam Asmad lafiya lau ya ƙarfin jikin?" "Alhamdulillah! Na samu sauki sosai, har masallaci na je." "Madallah! Allah ya kara sauki, ina son anjima kazo kai da Aneesa." "Ameen! Insha Allahu zamu zo." Daga haka su ka yi sallama, Dr kwanciya ya yi tare da lumshe ido cikin wani yanayi mai wuyar fassara, a haka bacci ya dauke shi bai farka ba sai ƙarfe tara. Yana tashi toilet ya nufa wanka ya yi yana fitowa ya shirya cikin wani riga da wando kayan sun amshi jikinsa, ya yi kyau sosai falo ya fita inda ya ke tunanin Aneesa na ciki, ilai kuwa tana zaune a falon cikin kwalliyar ta mai kyau, tana ganin Dr ta saki murmushi ta ce "Hamma ka yi kyau." Murmushi ya mayar mata shi ma sannan ya amsa da "na gode." "Mu je ka yi break kar ka makara." Aneesa ta yi maganar tana fara tafiya. Bin ta a baya ya yi har kan dining din ya zauna ta zuba masa abin da ta haɗa, sannan ita dinma ta zauna "Ki yi break fa yanzu fita za mu yi mu je gidan su Nenne ." Yana maganar ne yana ci gaba da cin abincinsa. "To." Aneesa ta amsa kirjinta yana bugawa, haka kawai ta ji hankalinta ya tashi. Sam jikinta babu kwari ta kammala break ɗin, gyale ta dauko suka kama hanya. Suna shiga mota aka soma kiran Dr ana sanar masa akwai mara lafiya emergency, don haka cikin sauri ya k'arasa da su gidan, lokacin da suka isa gidan Bobbo ya fita, a gaggauce Dr ya gaida Nenne ya fita. Bayan fitar Dr ne Nenne ta gyara zama tare da kallon Aneesa, "Aneesa! Nenne ta kira sunanta. "Na'am Nenne." Cikin nutsuwa ta amsa. "Kina jina ko? Duk abin da zan sanar maki ki yi haquri domin ya zama dole ki sa ni, ki yi haquri ki dau dangana." Gyada kai ta yi har yanzu kanta a kasa yake. "Aneesa jiya aka daura auren Asmad, amma aurensa ba yana nufin cin mutuncin ki bane, babu wani cin zarafi tsakanin ki da Hamma ɗinki, in har wani abu ya biyo baya ki sanar min." Nenne ta fada cikin karfafawa Aneesa gwiwa. Girgiza kai Aneesa ta ke yi cikin mummunan faduwar gaba, hankalinta ya yi mugun tashi da jin maganar Nenne, addu'a take Allah yasa ba gaske ne abin da ta ji Nenne ta faɗa ba, a fili ta bayyana "No! Ba haka bane." Ta yi furucin cikin tashin hankali. "Karki tada hankali ki hakuri Aneesa." Da sauri Aneesa ta tattaro nutsuwarta, ta tuna a gaban Nenne take, murmushi ta yi wanda da gani kasan gara kuka da shi "To Nenne Allah ya sa Alhairi." Allah kaɗai yasan ta yadda Aneesa ta haɗa wadannan kalmomin. "Allah ya maki albarka ya zaunar da ku lafiya." "Ameen." Kawai Aneesa ta amsa, sai ta mik'e kamar wacce aka tsikara. "Ina kuma zaki je?" "Umm Nenne dama zan yi baki ne, shi ne zan koma in dafa masu abinci." "To ai shi kenan, amma da naso ki wuni mana tunda baƙi ne sai kin kuma zuwa." Sam Aneesa bata wani tsaya sauraron abin da Nenne ke faɗa ba, kawai ta sa kanta ta yi waje. _*YAR MUTAN RANO*_ [10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* _*wannan shafin sadaukarwa ne gareki AYSHA WARIZI ki yi yadda za ki yi da shi in yaso ma ki hana kowa ya karanta, indai gaisuwa ta ta sameki Alhamdulillah ina maki fatan Alhairi da nasara a rayuwar ki*_ *Hak'uri nake baku akan rashin ganin post ɗina kullum, hakan nada nasaba da halin da na tsinci kaina, ku taya ni da addu'a Please.* *Masu kirana da masu yi min text message ina godiya da kulawa, Allah ya bar zumunci* ```Nafee Ankerh korafi```☹ *One in town my Besty, ke kam kin zama jinin jikina k'aunar da nake maki daga Allah ne, Allah ya barmu tare har karshen rayuwa*😍😍 *26* Sallama ya yi tare da karasawa tsakiyar falon, abin da ya bashi mamaki shi ne yadda bai ji an amsa masa ba, duk da akwai mutum a falon bai damu ba don haka sai ya taka zuwa kan kujera tare da furta "wash! Madam na gaji fa." Ko daga kai bata yi ba balle yasa ran zata masa magana, Zama ya yi kusan na minti uku yana kallonta tare nazari halin da ta ke ciki, a iya tunaninsa bai mata wani abu wanda har ya bata ranta ba, hasalima cikin farin ciki suka fita har ya barta gidan Nenne. Tashi ya yi daga inda yake ya matsa kusa da ita yana faɗin "My Anee me na yi ne? Ya yi tambayar yana kai hannunsa jikinta. Da sauri ta janye jikinta tare da watsa masa wani mugun kallo na tsana zallah Ta ce "Kar ka taɓa min jiki Hamma. Da kyar ta hado kalmar domin yadda zuciyarta ke wani irin tafasa, ji take kamar ta shakeshi ta huta. Da mamaki ya ke kallonta ya ce "Aneesa me ya faru? Me na yi maki da har zan kai hannuna jikinki ki goce?" Buɗe ido ta yi tana kallonsa da mamaki mai cike da takaici "wato baka san me ka yi min ba, lallai ma Asmad ɗin nan ka mugun raina min hankali." A zuciyarta ta ke wannan maganar amma a fili sai cewa ta yi. "Ba kai min komai." A takaice ta yi maganar. "A'a Aneesa ban yi maki komai ba ki ke fushi da ni, dole akwai dalili Please me ya faru?" Wannan tambayar tasa na rainin hankali ta bata ranta fiye da jin labarin aurensa, kwafa kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba, sai ma mik'ewa da ta yi da niyyar shiga bedroom ɗinta. Da sauri ya janyo ta ta faɗa jikinsa, hannu yasa ya rungume ta tsam kamar wani zai rabasu. Kokarin fisge jikinta take tana faɗin "Please Hamma ka barni wallahi na tsaneka ni zaka ciwa amana, me kuma zaka faɗa min?" Bai damu da maganganun da take faɗa masa ba, shi dai burinsa ya ji laifin da ya aikata mata har ta dauki zafi haka. "Aneesa ki nutsuwa ki faɗa min abin da na yi maki don ban san laifina ba." Kuka ta rushe masa da shi ta ce "Hamma ashe kaima kana cikin masu karya da cin amana, Hamma menene bana yi maka da zaka saka min da kishiya?" Da karfi ta k'arasa maganar. Shi fa maganar ta ma dariya ta sashi amma sai ya dake ganin yadda ta ke kwararar da hawaye "anya kina cikin hankalinki kuwa? An yi maki kishiya? Kuma wa ya faɗa maki? Dariya ta yi duk da akwai hawaye a idonta, domin dai maganar Hamman ɗinta ya bata mamaki "wato wa ya faɗa maki an yi maki kishiya?" A fili, ta maimaita kalmar ta ce "Nenne ce ta sanar min kuma kasan dai ba zata min karya ba, ashe dama jiya kana can tare da Amarya ne shi ne da ka dawo ka shirga min karyar baka da lafiya hmmmm! Hamma kenan, yanzu ma kazo ka tsara ni ne bayan ka je wajen matarka, wallahi Hamma na tsaneka." Ta k'arasa maganar tare da rugawa da gudu ta shiga bedroom ɗinta. Sororo Dr ya yi maganar Aneesa suna masa yawo a kunne "Aure kuma Nenne ta fada mata?" Ya yiwa kansa tambayar da babu amsa. Jagaf ya zauna akan kujera tare da dafe kansa, shi yama rasa tunanin da zai yi, wayarsa ce ta fara ruri don neman a gaji, jiki a saɓule ya kai hannu tare da dauko wayar ganin Number din Hafiz yasa shi ɗauka. "Ango! Hafiz ya faɗa daga ɓangarensa. Buɗe ido ya yi tare da gyara wayar a kunnensa ya ce "Kai fa sai a hankali, wani irin Ango kuma?" "Ango ka ke mana ko ka manta?" Hafiz ya k'arasa maganar cikin dariya. Mtss ya ja tsaki ya ce "Kai wallahi ka faye zolaya da yawa fa, angon Aneesa ba." "A'a na Ameesha dai." Hafiz ya faɗa. "Da a ce haka zata faru da nafi kowa murna, amma kash sai dai Ameesha ta min nisa tana karkashin wani." Cikin zuciyarsa ya ke maganar. Amma a fili sai ya ce "Please bar maganar nan karka sa na shiga wani ha..." Tun bai gama maganar ba Hafiz ya yi saurin katseshi da fadin "Kai abokina kana nufin har yanzu baka san an daura auren ka da Ameesha ba?" Wani irin mik'ewa ya yi daga zaunen da yake ya ce "Me ka ce?" "Yes an daura auren ka da Ameesha." Hafiz ya yi maganar kai tsaye. "Please bana son haka, idan wasa kake min ka daina Ameesha dai ina sonta so na gaskiya, amma na hak'ura da ita." A zafafe Asmad ya k'arasa maganar. "Haba Dr ya ina faɗa maka maganar gaskiya kana karyata ni, ka je ka tambayi Bobbo ko Nenne zasu sanar ma shekaran jiya da kai aka daura auren Ameesha." Yana gama faɗin haka ya kashe wayarsa. Da kallo Dr ya bi wayarsa, cikin zuciyarsa yana mamaki da tunanin maganar Aneesa da ta Hafiz, Aneesa ta ce Nenne ta sanar mata, shi kuma Hafiz ya ce ya tambayi Nenne, abin da ya daure masa kai shi ne "ɗazun da zai dawo gida sai da ya biya ta gidan don ya ɗauko Aneesa a tunanin sa tana can gidan, kuma bai ji Nenne ta sanar masa da makamanciyar wannan maganar ba, kai shi kam bai yadda da wannan maganar ba." "Yanzu me abin yi?" Ya yi wa kansa tambaya. "Ka fara zuwa ka lallashi Aneesa tukun." Wata zuciyar ta bashi amsa. "A'a kar ka je domin kuwa a yadda ta ɗauki fushin nan ko ka je bata sauraron ka." Wata zuciyar ta yi saurin tunasar da shi. "To mai zan yi, menene mafita?" A fili ya yi maganar. "Wajen Nenne da Bobbo." Wani bangare na zuciyarsa ta bashi amsa. "Yes! Sosai ya ji ya yi na'am da shawarar da zuciyarsa ta bashi. Cikin kwarin gwiwa ya mik'e yana fita motarsa ya ɗauka tare da bata wuta sai gidansu Nenne. Ko tsayawa kyakkyawan fakin bai yi ba, ya fita daga motar, cikin gida ya nufa da sassarfa a wannan gaɓar sallama ma ta gagareshi da Nenne ya yi karo ta fito daga hanyar kicin. Kallonsa ta yi tare da girgiza kai ta ce "Lafiya kuwa?" "Lafiya lau Nenne." Ya bata amsa. "An ya kuwa lafiya, kalli fa ta yadda ka shigo?" Sosa kai ya fara da keys din hannunsa ya ce "Allah Nenne babu komai, dama dai tambayar ki zan yi?" "Tambaya?" Wacce irin tambaya kuma? Ko da yake zauna in ji me ke tafe da kai?" Zama ya yi tare da lankwashe ƙafafunsa ya sun kuyar da kai, sai dai me tambayar da ya ke niyyar yi ta ki fitowa. Ita dai Nenne zuba masa ido ta yi tana sauraron abin da zai ce, ganin ya yi shiru sai ta gyara zama ta ce "Asmad wai kuwa ka je gidansu Ameesha kuwa?" Ɗago da kai ya yi yana kallonta ya ce "Gidansu Ameesha? Me zan je yi mata bayan yanzu tana inuwar wani, ko kin manta na ce an daura auren ta da wani?" "A'a ban manta ba, sai dai yana da kyau ka lek'a domin duba a wani hali ta ke, saboda wannan ɗin ya rataya a wuyar ka ne." Da amaki ƙarara a fuskarsa yake kallon Nenne bakinsa har yana rawa ya ce "Ya rataya a wuyana? Nenne ban gane nufin ki ba?" "Eh! Haka nake nufi, yau kwana biyu da Ameesha ta zama a karkashin inuwar ka, ma'ana dai Maryerm Taheer wato Ameesha ta zama mata a gare ka." Kallon Mahaifiyarsa ya yi a karo na barkatai, ganin yadda ta dire maganar sam babu alamar wasa ya sa shi ya yadda, ai da sauri ya tashi tare da yin sujada ga Allah don nuna farin ciki, yana ɗagowa ya zubawa Nenne ido kallo ɗaya zaka masa kasance wa yana cikin zallar farin ciki, musamman yadda fuskarsa ta nuna. Kasa furta komai ya yi sai wani fara'a da murmushin da ke k'arasawa fuskarsa kyau ya yi, cikin zuciyarsa kam godiya ya ke ga Allah. Muryar Nenne ya ji tana faɗin "Kaga yanzu dai ka tashi ka je gidan nasu domin duba wani hali take ciki." "To." Tare da mik'ewa yana faɗin Nenne sai na dawo. _*YAR MUTAN RANO*_ [10/8, 8:00 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)* *SANGARTA* © *ZULAIHEART RANO* *_Bismillahir Rahmanir Rahim._* *_Allah ina rokon ka don karfin ikon ka, kabani iko kamar Yadda na fara rubuta littafin nan lafiya Allah kasa in kammala rubutawashi lafiya_* *1* Zaune yake cikin kasaitaccen falonsa wanda aka tsara su da manya-manyan kujeru ne na alfarma. Kallo daya zaka yiwa falon ka san ba karamin dukiya aka narka ba. shi kansa kafet din falon ba duka gidaje ake samun irinsa ba sai gidan wane da wane. Hannunsa ya mika tare da dauko jaridar Leadership daga kan wani kyakykyawan teburin dake kusa dashi, ya bude tare da soma karantawa. Cikin wata irin tafiya take taka steps din tana saukowa fuskarta dauke da murmushi, jikinta sanye da wata rigar bacci wandda bata gama rufe mata cinyoyi ba, kanta ko dankwali babu. Kai tsaye wajensa ta nufa. Shi ma tunda ya hangota fara'ar fuskarsa ta karu. Bata zame ko'ina ba sai inda yake zaune, ta zauna tare da dora kanta saman kafadarsa, cikin shagwab'a tace "Abbana barka da safiya" Murmushi ya yi yace "Barka dai uwata, fatan kin tashi lafiya?" Dariya ta yi tace " Lafiya lau Abbana." "Madallah, fatan babu wata matsala?" Ya yi tambayar yana kallonta. "Innalillahi.... Ni Halimatu! ke kuma Amesha kina daukan maganata kuwa? sau nawa ina maki maganar ki daina fitowa a haka?" Maganarta da suka ji kamar daga sama ne ya hana ta ba Abban nata amsar tambayarsa, duk suka juyo ga mai maganar. Turo baki tayi tare da kunkunai "To ni Ummi wai shikenan mutum ba zai sake ba shi da gidannsu?" Dakuwa Ummin ta watsa mata tare da daure fuska tace "za ki tashi kije ki suturta jikin ki kosai na bata maki rai?" Ganin fuskar Ummin ba wasa yasa ta mikewa cikin takaici. Abbanta yace "Haba Hajiya! me yasa kullum sai kin rika takurawa Yarinyar nan ne? Ko baki san har yanzu karamar Yarinya take ba?" Wani takaici ya rufe Ummi ta ji kamar ta gaurawa mijin nata mari "Haba Alhaji, ta yaya zaka ce kar na yiwa Ameesha fada in ta yi ba dai dai ba? Yarinyar nan fa kullum kara girma take yi amma babu hankali a tare da ita. Ji fa irin kayan da take fitowa falo dasu, by mistake ayi bako ta fito haka ai kunya zamu ji....." Ya dakatar da ita da hannu "Look! Hajiya ban son dogon turanci, gida dai nawa ne kuma Ameesha gidan ubanta take, don haka babu mai takura mata. Ke kullum baki da abokiyar fada sai yar cikinnki? wallahi wani in ya shigo sai ya yi tunanin bake kika haife taba, musamman da kullum fada kike mata. Kuma kina maganar bako, ai ba mai shigowa falon nan sai da izini. Gidan nan duk muharramanta ne, basai ta rika sa kaya masu nauyi ba." Takaici ya rufe Hajiya, Wanda har ta kasa furta komai, sai aje masa cup din coffee din tayi ta nufi bedroom dinta. Tabbas ta san duk wani abu da Ameesha takeyi da izinin mahaifinta, don shine baya kaunar a fadi laifin Yarinyar. Allah ya sani ina iya bakin kokari na wajen bama Yarinyar tarbiyya, amma taki daukan duk wani nasiha ta, ta fada a ranta. Ameesha tana shiga bedroom dinta toilet ta zarce ta sallo wanka. Tana fitowa ta zauna gaban dressing mirror ta soma tsantsara kwalliya. Tana gamawa ta shirya cikin wata bakar doguwar riga, mai masifar kyau, tayi rolling dankwali a kanta. Iya kyau dai kam Ameesha tayi, kamar a sace a gudu. Kyakykyawa ce sosai yar shekara goma sha takwas. fara ce amma ba sosai ba. Ta samo asali da kyau ne wajen mahaifiyarta, komai nata irin na mahaifiyar ne. *MARYAM TAHIR* kenan inkiya kuma Amesha Yarinya yar gatan Abbanta. Wayoyinta ta kwasa daga kan gado ta sanya takalminta mai kyau, sannan ta fita falon don yunwa take ji sosai. wani murmushi ta saki ganin har a lokacin Abbanta na zaune a falon "Wow! Babyna kinyi kyau." Abban ya fada yana nuna farin ciki. Dan turo baki tayi ta ce "Na gode Abban Ameesha. Abba so fa nakeyi naje saloon a wanke min kai" Cike da shagwab'a ta karasa maganar. "Ok babu damuwa my baby. Yanzu dai je ki fara yin break don nasan kina jin yunwa. In kin gama sai ki tafi." "Abba nifa ba kudi a hannuna, ka ban kudin da zanyi amfani da shi" "Sai dai kije da ATM Card don banda wasu kudi masu yawa a gida" Ya bata amsa a lokacin da yake kokarin mayar da hankalinsa ga jaridar da ke hannunsa. "No Abba, Gaskiya ba zan iya bin layin ATM ba, mutum yaje ya yi ta tsayuwa" Ta yi maganar kamar zata yi kuka a daidai lokacin da Hajiya Halima mahaifiyar Ameesha ta iso inda suke. "Yawwa Hajiya muna da bukatar kudi in kina da su a hannu" Alhaji Tahir ya fada, yana rufe jaridar. "Wani irin kudi kuma Alhaji?" Hajiya ta tambaya cikin nuna rashin fahimta "Baby ce zata saloon kuma wajena babu kudi a gida, ki bata 30 thousand naira kila su ishe ta" Zaro ido Ummi tayi tace "Alhaji dubu talatin fa kace! Da su zata wajen saloon din?" "Eh, saboda zata biya ta yiwo shopping. ko kuma dai bata fifty zaifi" Jinjina kai tayi tare da cewa' "Ai bani da su" "Zan maida maki kudinki Hajiya" Juyawa tayi ta nufi bedroom dinta, tana Kara mamakin halin mijin nata. Ameesha kam sai da ta kammala break din tsaf, kana ta baro dining tabke din. Wajen Abban ta taje tace "Abbana na gama" "Ok je ki amshi kudin wajen Umminki, 50k ne ai zasu ishe ki ko? Sai ki siyo yan abubuwan bukata da abinda ya rage." Daga kai tayi kafin ta nufi bedroom din Ummin. Ta yi Sallama ta shiga. Hajiya Halima dake zaune ta amsa. "Ummi ki ban kudi inji Abba" Ameesha ta fada. Girgiza kai Ummi ta yi tace "Allah ya shirya min ke Ameesha, wai yaushe zaki hankali ne?" Ta karasa maganar tana mika mata kudin. Amsa tayi tare da yin waje. tana zuwa ta aje masa kudin a kusa da shi. Cikin muryar kuka ta ce " Abba ba na son kudin nan" Hankalin sa ya tashi da ganin hawayen tilon diyarsa mace, yace "Uwata me ya faru?" Jikinsa har wani rawa yake. "Ba Ummi bace bayan ta ban kudin tace Wai Allah ya shirya ni.........." *_Yawan Comment dinku zai sa ni cigaba..._* *_Yar Mutan Rano._* [10/8, 8:00 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)* *SANGARTA* © *ZULAIHEART RANO* *2* Zaro ido ya yi yace "Me Hajiya take nufi da wannan kalmar? Tana nufin ke ba shiryayya bace?" a zafafe yake maganar. "To Nima fa Abba abin da ya ban haushi kenan, ita Ummi kullum bata son taga ina farin ciki, sai tayi dalilin sani cikin damuwa" Ameesha tayi maganar tana cigaba da matsar kwalla. "Yi hakuri yar Abba tashi kije zan sami Hajiyar yanzu, sai ta fada min dalilin ce maki hakan, oya je ki wanke fuskarki" Ummi ce ta fito daga bedroom dinta, ganin Ameesha na kuka yasa ta mamaki tace "ke lafiyar ki kuwa?" "Wani irin tambaya ce haka Hajiya, kefa kika sa Yarinyar nan kuka, amma yanzu kina tambayar ta" cikin fad'a ya kara sa maganar. Dan murmushi Ummi tayi tace "Haba Alhaji ka daina saurin daukar fushi a kan lamarin Ameesha, in banda kaima kana biye mata, har yaushe zata ce na sata kuka ka yadda? Ko da yake tunda *Sangarta* na damunta, dole tayi kuka don nace Allah ya shirya min ita" "Yawwa kinji ba, me kalmar Allah ya shirya ta yake nufi?Gaskiya ni ban son haka, duk mai son zaman lafiya to karya tab'a min uwata."ya yi maganar cikin fushi. Jinjina kai Ummi tayi tace"Allah ya baka hakuri Alhaji, amma maganar neman shirin Ameesha wajen Allah yanzu na fara fada" tana gama fadi haka ta yi kicin. "'Yar Abba tashi kije ki wanke fuskarki, sai kizo ki tafi ko?" "Nifa Abba kamar na fasa zuwa" Ameesha tayi maganar tana cigaba da latsa wayar ta. Don dama duk maganar da Abbanta da Umminta suke tana jin su, ko kallon su bata yi ba har suka gama. "Haba yar'lele mai zaisa ki fasa, tashi maza kije ko kina son na kaiki da kaina ne?" "A'a Abba da kaina zanje." "Ok wane motar zaki fita da shi?" "Abba sabuwar motar ka zan hau yau, wannan wanda aka kawo last week, *Bugatti vogron* dinka" ta bashi amsa tana hawa down step. Fada da fara'ar sa ya yi yace "To maza ki fito kizo ki dauko key, sai ki tafi yar Abbanta." ya karasa maganar yana girgiza kai. Da sallama ya shigo falon tare da tsugunawa, ya soma gaida mahaifin nashi. Fuska sake ya amsa da "Lafiya Lau Jaheed ya ka tashi" dukar da kai kasa ya yi yana amsawa. Hajiya Halima ce ta fito daga kicin fuska dauke da fara'a tace"Lallai Jaheed yau Kayi nannauyan bacci, har sha daya kafin ka fito?" Dan murmushi ya yi yace "Wallahi Ummi jiya da zazzabi na Kwana yanzu ma da kyar na tashi" "ayya Sannu Allah ya kawo sauki, tashi kayi break sai kasha magani, shi yasa banga ka fito da wuri ba, gashi yau kuna da aiki." cikin tausayawa dan nata take maganar. "Abba na dauko key din Sai na dawo." muryan Ameesha ya cika falon. "OK yar Abba a dawo lafiya" "Ke ina zaki yanzu a wannan lokacin har da daukan mota?" Jaheed ya tambaya ransa a b'ace"Yaya saloon zanje fa daga nan zan biya nayi shopping" cikin shagwaba ta yi maganar. Harara Alhaji Tahir ya zabga masa yace"Kai nikam ban son fi'ili ina ruwan ka da inda zata je, kawai ka sawa Yarinya ido sai faman tambayar ta kakeyi" "Yi hakuri Abba bada wani manufa nayi Mata tambayar ba." "Kudai kuka sani kuma, amma uwata da shen Allah ne." Ummi ta jinjina kai cikin ranta tace"Lallai lamarin Alhaji kara gaba yake" Ameesha ta matsa inda Abban ta yake ta manna masa kiss a kumatu tace"Abbana ina sonka sosai, sai na dawo." murmushi ya saki yace "A dawo lafiya uwata Allah ya tsare, ki rika kula don kin San akwai Wanda suka sa maki ido." "Insha Allah Abba." ta yi maganar tana fita daga falon. Mamaki sosai ya rufe Ummi, da irin maganar Alhaji Tahir din, jaheed ya bude baki zayyi magana suka hada ido da Ummi, yana ganin kallon da Ummin tayi masa ya gane nufinta, don haka sai ya yi shiru. Ameesha kam tayi tafiyar ta. *ASALIN LABARIN* AMEESHA diya ce wajen Alhaji Tahir da Hajiya Halima,Yarinya ce yar gata wajen mahaifinta, Alhaji Tahir haifaffan garin kano ne, cikin karamar hukumar bicci, yana da matar aure d'aya da ya'yan sa biyar,Hajiya Halima itace matar sa, Kuma ita ce ta haifa masa duk ya'yan sa, suna zaune cikin garin kano a unguwar Tudun Yola dan kasuwa ne babba Allah ya bashi tarin dukiya. Don yana da manya manya shaguna a kantin Kwari da singa duk dake garin kano,Babban dansa shine Muh'd Mujahideen, wanda suke kira Jaheed, sai AbdulMalik, Umar Faruk, sai Aliyu Haidar, sai Auta Maryam Wacce suke kira Ameesha, Allah ya daurawa Alhaji Tahir son Ameesha, yana kaunar ta sosai don tace Sunan mahaifiyar sa, Kuma ta kasance ita daya ce ya mace da Allah ya azurta shi da ita, Baya kaunar bacin ranta, lokacin da take karama duk rashin kunyar da tayi maka, baka isa ko kallon banza Kayi mata ba, balle akai ga maganar duka ko zagi, to a ranar ba zaman lafiya don an tab'a masa 'yar lelensa, haka yasha zuwa makarantar akan an daketa ya zabgawa malaman rashin Mutunci, Ameesha tun tana karama abin da tayi niyya shi takeyi, babu daman wani ya yi magana sai Alhaji Tahir ya soma, yana cewa an sawa yarsa ido, Koda kuwa Ummi ce da yayyin ta sukai magana Kan abin da take haka yake rufe ido ya yi ta ruwan masifa, *Sangarta* kala kala Ameesha keyi, babu mai magana. wannan Abu yana bawa Hajiya Halima haushi, sai dai bata da yadda zatayi da ya wuce Addu'a. Har zuwa lokacin da ta girman ta bata rage ko Abu daya daga Halayyar ta ba, sai ma rashin Mutuncin ta dake karuwa a kullu yaumin. *** Fitowar ta kenan daga cikin Shahad store, inda tayo shopping din duk wani Abu da take so, idonta sanye da wani kwamemen glass, Kallo daya zaka yi mata kasan babu mutunci a tattare da ita. Musamman yadda take wani irin taku cikin isa da tak'ama. Hannu tasa tare da zame glass din idonta, tana kallon motar da aka faka kusa da ta ta motar. Jinjina kai ta yi tana mamakin wanda ya faka motar don ya tare mata hanyar fita, tsayawa ta yi jikin motar tana jiran ganin fitowar ko ma waye mai motar, don ta nuna masa ba'a mata haka, Yau zata nuna ma duk Wanda ya yi mata wannan aikin rashin Mutunci. Tafiya yake cikin nutsuwa, wayar sa makale a kunnen sa, da gani kasan waya yake yi, isa ya yi wajen motar sa tare da budewa, zai shiga ciki kenan maganarta ta hana shi shiga. "Kai Malam me kake ji dashi da har zakayi min crossing din hanya, sannan kazo ka wuce ba tare da ka ban hakuri ba?" Dago da kyakykyawan fuskar sa ya yi, ya sauke idon sa Kan fuskar ta, take ya ji wani yanayi ya shige sa wanda bai tab'a jin sa ba. Kallon beauty face din ta yake babu kakkautawa. Ran Ameesha ya baci matukar da irin kallon da yake mata, sannan ta yi magana bai amsa mata ba, don haka sai ta daga hannunta tare da kaiwa fuskarsa mari. Saurin gocewa ya yi bata same shiba, ransa ne ya baci har Shima bai San Sanda ya daga hannu tare da gwaura mata wani lafiyayyen mari. cikin sanyanyar murya yace" Ke dabba, mahaukaciyar ina ce da har zaki daga hannu da sunan marina?" Bude ido ta yi cike da mamakin marin da ya mata, a iya saninta rabon da wani ya mareta tun tana primary 3, Shima malamin Sanadin dukan da ya mata ya bar koyarwa a school din, cikin sauri ta zaro wayar ta tare da dailing number din Abbanta cikin kuka ta soma zayyane masa abin da ya faru...... " *_Yar mutan rano_* [10/8, 8:01 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)* *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *3* "Wa ye shi a Nigeria da har zai daga hannu ya mareki?" Alhaji Taheer ya yi tambayar a zafafe. Hawaye suka kuma zubo wa a idon Ameesha, don ba karamin shigar ta marin ya yi ba. Murya a sanyaye tace "Abba badan ko wa bane hasalima wani kaskantaccen mutum ne, wanda ba shi da ko sisi, motar da yake hawa ko kyauta aka bani bazan iya hawanta ba." "Maza dauko min number din motarsa, zanyi maganin kowaye." Dago kan da Ameesha ta yi sai taga wayam babu motar mutumin, wani karin takaici ya rufeta, a zafafe tace "Abba ya wuce ban san ma lokacin da ya wuce ba." "Maza ki dawo gida, ko nazo na dauke ki ne? " " No Abba ba sai kazo ba yanzu zan taho." Ameesha ta yi maganar tana shiga motar, a ranta ta kudurta bata kuma zuwa *Sahad store* ba domin wajen ya zama mata wajen jin kunya. Cikin gida kuwa Abba sai kai komo yake, yana ta jan tsaki, don hankalin sa ya tashi da jin maganar marin Ameesha, Hajiya Halima ta fito daga kicin tare da kallon mai gidan nata, cikin kulawa tace "Alhaji lafiya kuwa?" Tsaki yaja tare da hararan Hajiyar yace "Yo ina fa lafiya, an samu wani dan iskan ya maran min yarinya a banza." Mamaki ya kama Hajiyar tace "Alhaji mari Ameesha aka mara kowa? " " Inada wata 'yar ce bayan Uwata? Ya cigaba kinga Hajiya karki kuma 'bata min rai, dama fa na kula tun farko baki so fitan yarinyar nan ba, don haka burin ki ya cika tunda an wulakanta min ita a waje." Girgiza kai Ummi ta yi tace "Amma Alhaji kana bani mamaki, in ka fad'i wata maganar, ta ya zakace wai ina son a wulakanta Ameesha?kar fa ka mata ni na haifeta, kuma banki ace Ameesha tafi ko wace ya mace nutsuwa ba, na tabbata Ameesha rashin kunya ta yi wa duk wanda ya mareta, amma kai ba ka yi bincike ba, sai ka yanke hukunci ka daura laifi akan mutum, gaskiya haka ba kyau. Daga mata hannu ya yi alamar ta yi masa shiru, dai dai da shigowar Ameesha, jikin Abba ta fad'a tare da sakin wani sabon kukan. Bubbuga bayanta Abba ya soma alamar rarrashi "Yi hakuri uwata karki bar wannan ya dame ki, insha Allah zan dau mummunan mataki akan koma waye, shi duk randa Allah ya had'a mu." "Da dai kabi komai a hankali zaifi, amma wannan maganar da kake ba shine dai dai ba." Hajiya Halima ta yi maganar tana zama kan kujera. "ke Ummi kinga kuwa irin wulakacin da ya min?kike cewa a bi komai a hankali, wallahi Abba karka bi a hankali." "To uwar rashin kunya, duk wannan abin da kuke yi wata rana sai kunyi nadama kuma ma mara amfani." "Nifa wallahi Hajiya ban son irin maganar da kike yi, ke kullum baki mana fatan Alhairi sai mugun baki, to ta Allah ba ta kiba." "Gaskiya ce baku so ni kuma dole sai na fad'a." "Ki rike gaskiyar ki bamu so din" "Yawwa Abba ina son duk lokacin da kuka had'ui, karka saurara masa ka nuna masa ni din yar gatan ka ce." "An gama Uwata maza jeki daki ki dan watsa ruwa ko zakiji sanyi." "To Abba sai nayi sallah zan fito, don a hanyata ta dawowa naji an kira." "A fito lafiya diyar Abba." Murmushi Ummin Ameesha ta yi, don wannan halin na Ameesha kadai ke burgeta, duk abin da take da zaran taji an kira sallah, bata bari lokaci ya wuce. Kusa da Ummin ta matsa tace "Ummi yau me kika dafa ne?" "Tuwon shinkafa ne miyar wake." "Wow Ummi kinyi abin da nake son ci." Da fa kanta Ummin ta yi tace "To ga yacan a dining komai is ready." "Ok bari na fito." Ameesha tayi maganar yayin da take taka matakalar benan don hayewa sama. Farin ciki ne ya kama Alhaji Taheer mahaifin Ameesha ganin yadda suka yi magana cikin walwala da farin ciki. Shigarta bedroom din ke da wuya sai ta wurgar da Jakarta dake hannunta (hand bag) tare da cire gyalen da ta yafa, Kai tsaye toilet ta nufa ta sakarwa kanta ruwan sanyi, kila ko ta samu sassaucin abin da take ji a zuciyar ta, ta jima sosai sannan ta fito bayan ta dauro alwala, zanen da take sallah ta dauko tare da hijjab dinta sannan ta tayar da sallar. Bayan ta idar da sallar, ta shirya cikin wani wando da riga wanda suka mata matukar kyau, wandon pencil ne kalar pink, rigar kuma body top ne kalar white, sun amshi jikinta, ta yi pakin kanta da ribbon kalar wandon ta, tsaf ta feshe jikin ta da turaruka masu kamshi. Masha Allah, Gaskiya Allah ya yi halitta don Ameesha kam babu inda Allah ya rage ta, ta fannin halatta kyakkyawa ce wato (First Class) a jin farko, gata doguwa, bata da Kiba ko kadan, amma fa akwai ta da hips and braest, komai cif. ******************************** Cikin kwarewa yake driven motar, fuskar sa dauke da wani special smile, haka kawai in ya tuna Ameesha yake jin zuciyar sa fes, sai dai wani bangare na zuciyar sa tana fama da rad'ad'i tare da dana sanin marin da ya mata. A fili ya furta "Shi is very beautiful girl, duk wanda ya samu wannan matsayin mata lallai ya more." Wayarsa ce ta soma ruri a lamar tana neman agaji, da sauri ya dauki wayar ganin mai kiran yasa shi sakin murmushi, picking ya yi tare da karawa a kunne "Hello Allah hokke sabbugo Nannena, mid'o a nyalli jam, noi sare? " (" Allah ya baki tsawon rai Nannena, fatan kina lafiya ya gida?) " Jamni tawon Asmad mid'o yela wala billare fere kam.... " (" lafiya Lau Asmad fatan kaima baka da matsala?) " A'a Nanne wala ko d'ume, jottama mid'o lawol Wartugo sare." ("a'a Nanne babu matsalar komai, yanzu haka ina hanyata ta dawowa gida") "Allah wadde jam amma a hakkilina lawol anani naa barkantejo.... " (" Allah ya dawo min da kai lafiya Amma ka kula da kyau kaji dan Albarka.") Murmushi ya yi lokacin da ya kammala waya da mahaifiyar nasa,yana jin farin cikin yadda Nannen shi ke bashi kula, cikin mintina k'alilan ya isa unguwar su, bakin wani makeken get naga ya nufa, hon ya yi cikin sauri mai gadin ya wangale masa get din, wow masha Allah wannan rantsatsen gida haka, gida ne babba ginin zamani, Kai da ganin gidan kasan an kashi kudi, da ka shigo gidan da dakin maigadi zaka soma karo, gefen dama kuma, wani dan dakine aka gina da alama na generator ne, sai wasu flowers da aka daddasa masu kyau, su suka kuma sa gidan ya had'u, gefe guda kuma parking space ne, motoci jere a ciki masu dan banzan kyau. Sai mutum yayi dan tafiya kafin yasa da kansa da ainahin cikin gidan. A parking space ya faka motar sa, sannan ya fito tare da d'aukan laidar da ya yi sayayya a Shahad din, kofar babban falon gidan ya shiga bakin sa dauke da sallama, wata kyakkyawan macece wacce bazata wuce shekaru 40 zuwa 42 zaune cikin hadadden falon, babban falo ne wanda aka kawata sa da wasu manya manyan kujeru na alfarma, ga wani carpet mai shegen kyau wanda ya fito da ainahin kyaun falon, kalarsa da kujerun d'aya, wato brown color, haka ma labulen, babban plasma TV ne manne a bangon falon. Kallo daya zakiyi wa matar kasan bafulatana ce, fara ce fuskar ta kunshe da annuri, macece mai riko da Addini don hannunta rike yake da wani littafin Addu'oi tana karantawa, jin sallamar dan nata yasa tayi saurin d'agowa fuska d'auke da murmushi ta amsa masa sallamar. Inda take zaune ya 'karasa, zama ya yi kusa da kafarta tare da lank'washe 'kafarsa, ya soma gaidata, shafa kansa tayi tace "Ja66ama Asmad, awartii Jam... " (barka da zuwa Asmad ka dawo lafiya?) " Jamni tawon Nanne, sai welo minanata... " (lafiya Lau Nanne sai dai ina jin matukar yunwa). " Ta damu mitimmini nyamdu.... "(karka damu akwai abinci, ban dade da gamawa ba.) " Yawwa Nanne 6ewaddina aam sudu aam, hiddeko mi wurta yiwugo..." (Yawwa Nanne a kawo min bedroom dina yanzu, kafin na fito wanka.) "To ha ladidi waddine.... " (bari ladidi ta kawo maka.) " A'a Nanne miyid'a 6ingel d'o nastimi sudu aam, toi aneesa ko'o huwata, hokku moo ne o wadda..." ( "a'a Nanne ban son wannan Yarinyar tana shigar min bedroom, ki dai Ba Aneesa ita aikin me takeyi?) " To yahu hami hokka aneesa man waddine..." ("To jeka Aneesa zata kawo maka.") "Yawwa Nanne hanju wad'i miyid'i Ma..." ("Yawwa Nanne shi yasa nake Kara sonki." Asmad ya yi maganar yana Mika mata, d'aya daga cikin ledar da ya shigo da shi, amsa ta yi tare da sanya masa Albarka, shi kuma ya fita tare da nufa 'bangaren sa. _*Yar Mutan Rano*_ [10/8, 8:01 PM] Zulayheart Rano: [4/15, 4:00 PM] Zulaiha Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* *(NWA)* *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Please fans kuyi hakuri anyi mistake a pagen ɗin jiya amma gashi yanzu na gyara da fatan zakuyi min afuwa,ku cigaba da bibiyar littafi* *Nice dai Zulayheart Rano* *4* Asmad na wucewa Nanne ta soma 'kwalawa Aneesa kira, cikin sanyin murya ta amsa da "Na' am Nanne ga ni" Aneesa ta fada lokacin da ta isa wajen Nannen. "Yawwa yi sauri ki hada wa Hammanki Asmad abinci, ki kai masa bangaren sa." Murmushi ta saki jin Nanne ta ambaci Asmad. "To Nanne." Ta yi maganar tana nufa hanyar kicin din, cikin kankanin lokaci har ta shirya masa duk wani abu da suka dafa ta nufi, bangaren da shi, a k'ofar falon ta tsaya tana sallama, Asmad dake fitowa daga toilet ya amsa, tare da buɗe mata ya dan matsa ta ida shiga bedroom ɗin. Kallon sa ta yi cikin wani irin shauki, bayan ta aje tire ɗin tace "Hamman Asmad Sannu da dawowa" "Yawwa." ya amsa yana goge kanshi da karamin towel. Tsayawa ta yi tana kallon sa, a rayuwarta tana mugun son Asmad sai dai tasan, ta makaro don bata cikin irin matan da Asmad yake so, domin duk wani hanya da zata bi don shawo hankalinsa ta yi amma a banza. "Ke tunanin me kike yi da bazaki wuce ba, kin wani sani gaba kina kallo kamar na zamar maki bak'o?" Dan murmushi ta yi ta ce "Lah yi hakuri Hamman, dama so nake nace maka ina son zuwa wajen saloon." "Anjima ki amsa kudi a wajen Nanne, jeki ina son gama shiryawa." Jiki a sanyaye Aneesa ta bar ɗakin, ba don ranta ya so ba. Aneesa 'yar k'anwar Nanne ce ta zo daga Adamawa, da yake dama duk sanda ta samu hutun school to anan kano gidan su Asmad take yin hutun ta. Kamar ko yaushe wannan karon ma hutu ta samu, Aneesa budurwa ce kyakkyawar gaske, tana da dan jiki sai dai bata da tsawo, shekarun ta Ashirin da haihuwa, a fuska mutumiyar kirki ce sak, amma akwai ɓoyayyen hali a tattare da ita, tun tasowanta take son Asmad din, sai dai shi bata tata yake ba. Falon Nanne ta koma, a inda ta barta na ta sameta, kasa tayi da murya tace "Nanne inji Hamman wai ki bani kudi anjima zani saloon." "Ba dai yau ba, sai gobe don yanzu kam yamma ta soma yi." "To Nanne." Aneesa ta yi maganar cikin sanyi. cikin kwanciyar hankali, Asmad ya gama shirin sa, sosai ya yi kyau, domin Asmad kyakkyawan bafulatanin garin Adamawa ne. *Asmad Abubakar ɗan Fullo* shi ne cikakken sunan sa, mahaifinsa Alhaji Abubakar da mahaiyarsa Hajiya Binta duk haifaffun garin Adamawa ne, kasuwan ci ya kawo mahaifinsa kano. Allah ya ba Alhaji Abubakar dukiya, sosai ɗa ɗaya Allah ya basu shine Asmad, ya taso cikin gata ta ko wane fanni, sai dai ya samu ingantaciyar tarbiya, duk da kasancewar sa shi ɗaya Allah ya ba iyayen sa, akwai shi da nutsuwa da hankali, shekaran sa ashirin da takwas da haihuwa, Nanne takasance mece ce mai hankali da tunani, ko da yaushe fuskar ta a sake take, mace ce masaniyar Alkur'ani mai girma, Kuma mai aiki da shi, shi yasa sam bata yadda aka ɓata Asmad da wasu munanan d'abi'u ba, amma fa dai-dai da minti ɗaya in ka zauna da su zaka fahimci tsananin son da Nanne ke masa, don bata iya ɓoye son Asmad a gaban kowa, duk da kasance warta bafulatana. Asmad Abubakar ɗan Fullo, babban likita ne wanda duk faɗin garin kano aka san da shi, kawarrene a kan aikin sa, yana aiki a babban asbitin kano. ********************************** Juyi tayi akan makaɗeɗan gadon ta, tare da kai hannu ta dauki wayar ta dake neman a gaji, idonta fal da bacci ta dubi screen din sunan wacce ta gani ne yasata ɗaukar wayar tare karawa a kunne "Hello k'awata." Ameesha ta yi maganar tana lumshe ido Daga ɗaya ɓangaren a ka amsa "Meesha kina ina ne haka? gani a hospital, tun dazun kin san Dr ɗin da aka ce mana zai zo yi mana practical 8:30 zai shigo lab gashi yanzu 8:20." Ya mutsa baki Ameesha tayi, kamar wacce ke mata maganar tana kusa da ita tace "Kinsan Allah Meena na manta da maganar zuwan wani asbiti, yanzu haka da kikeji da gani cikin blanket nake, wayar ki ta tasheni daga bacci." "Haba Meesha please ki tashi yanzu kiyi sauri ki shirya, kinsan fa irin mutanen nan basa tsayawa jira, kina gani hatta manyan malaman makarantar suna mugun bashi girma." Tsaki taja tace "to uwar tsugudidi gani nan zuwa, tunda naga kina son takura ni." Ta karasa maganar tana tashi zaune, Meena kam murmushi tayi, tana mamakin halin Meesha. Toilet ta faɗa saida ta salle jikinta sannan ta fito, Kai tsaye gaban dress mirror ta nufa, inda kayan kwalliyar ta suke, zama ta yi ta tsantsara kwalliyar ta mai kyau, ta feshe jikinta da turaruka, shiryawa tayi cikin wani doguwar riga kalar blau da ratsin golden, sosai rigar ta k'arbi jikinta, gyale ta yawa fari, sannan ta ɗauki key na motarta, a hankali cikin ta kunta ta soma taka stair ɗin. Har ta sauka babban falon, Abba da Ummi ne kaɗai a falon suna zaune, hira suke yi, ganin Ameesha ta fito sai Abba ya washe baki yana fad'in "uwata an tashi?" "Na tashi Abba Asbiti zan shiga, ina kwana? " " Lafiya Lau Uwata fatan kin tashi lafiya? " " Lafiya lau. " " Ummi ina kwana? " " Lafiya Ameesha, kin tashi lafiya? " " Lafiya lau. "ta yi maganar ta na tafiya. " a'a uwata ba zakiyi break bane? " " Abba sauri nake yi, zanyi in na shiga." "OK Allah ya bada sa'a." "Ameen." ta amsa tana cigaba da tafiya. Tana fita daga falon kai tsaye inda motocin gidan suke ta nufa, wata zafafaffiyar mota ta dauka, cikin kwarewa taba motar wuta, duk wanda yaga Ameesha cikin motar sai ya kalleta, don motar ta mugun da cewa da ita. Kai tsaye Asbitin ta nufa, don suna practical ne a Asbitin Malam Aminu dake kano, Ameesha tana karantar Accident prevention and safety,Yau ce ranar da zasu fara practical d'in kuma da alama Dr da zai yi masu practical ɗin bashi da sauki, musamman in mutum ya yi duba da yadda Meena take mata magana. Tana shiga daret ta nufi inda aka tana da don aje motoci, anan ta faka tata hand bag ɗinta ta ɗauka tare da ciro wayar ta, layin Meena ta soma kira, ringing biyu ta Meena ta dauka. "Hello Meesha ya kin iso kuwa? " " Eh gani cikin Asbitin kina ta wajen ina? " " Please kiyi sauri ina wajen lab yanzu mutumin nan zai shiga, kuma yace koda minti biyu ya riga shiga bazai bar kowa ya shiga ba." Kashe wayar kawai Ameesha tayi tare da nufa inda Meena take, Meena tana ganin Ameesha tace "Wallahi Meesha kin kwafsa, yanzu ya shiga muje Allah yasa ya barmu." Tsaki kawai tayi suka nufi hanyar shiga lab ɗin, gaban Ameesha ne ya faɗi ganin wasu yan class ɗin su a tsaye, suna isa wajen Ameesha ta cusa kai cikin lab ɗinn cikin dakewar zuciya. Yana tsaye yana masu bayanin kansa sai ganin Ameesha ya yi ta shigo lab ɗin, k'ara bude ido ya yi da kyau ya tabbatar da ita ce dai wacce suka hadu jiya ta masa rashin kunya. Haɗa rai ya yi kamar bai taɓa dariya ba, dama fa shi ɗin ba gwanin dariyar bane, ko da yaushe fuskar sa a haɗe kamar ta sa............." *Tofa ke Ameeshan Abba da wa Allah ya haɗa ki? Sai kun biyoni don jin ko waye.* _*Yar Mutan Rano*_ [10/8, 8:01 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* *(NWA)* *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *5* "Heeee." ya daka mata wata irin tsawa, da yasa Meena rugawa waje, don Meena fa akwai tsoro. "Get out side." "Sorry sir! Wallahi makara dai ko mukayi." Ameesha ta yi maganar ta na ci gaba da tafiya. "Baki ba ki ji abinda na ceba ne? ki fita min a lab, tun kafin na shigo ai na faɗa maku doka ta, don haka yi waje ba karatun kike so ba, da har zaki ce Wai makara ku ka yi noises nonsense kawai." Cikin daure fuska ya ke maganar, in ba kana cikin lab ɗin ba, sai ka rantse da Allah ka ce ba shi ya ke maganar ba, don ko kallon inda take bai yi ba. Cikin sauri Ameesha ta d'ago da kai, jin yadda ya zageta karaf suka had'a ido da shi, don dama duk maganar da su ke yi ba ta kalle , Shi ba tana ganin shi, sai ta saki wani malalacin tsaki tare da juyawa. Gaba d'aya yan lab ɗin sakin baki suka yi tare da bin ta da kallo. Dai dai lokacin da za ta fita taji ya na faɗa masu sunan sa. Wato *Asmad Abubakar ɗan Fullo* Yace amma anfi sanin sa da *Dr ɗan Fullo* Maimaita sunan Ameesha ta yi a zuciyar ta wato *"Asmad Abubakar ɗan Fullo* lallai zaka gane kuranka." Ta k'arasa maganar tana fita daga lab ɗin. In da Meena ke zaune ta nufa ranta a matukar ɓace, kallon ta Meena tayi tare da fashewa da dariya tace "Kai Meesha wannan irin abu haka, kinga yadda kika yi kuwa kamar fulawar da ta samu yis da rana? " Meena ta kai Karshen maganar tana ci gaba da dariyar ta. Wani malalacin kallo Meesha ta watsawa Meena ta ce " Ke fa Meena baki da kirki me nayi da har kike cewa wata fulawa da ta sami yis da rana? Ke bama wannan ba wai tsoron mutumin can kikaji ne?" "Sosai ma kina jin irin tsawar da ya zabga mana, kamar an busa algaita taf ai wallahi ya firgita ni, amma ke naga ko a Jikinki ?" "Kwarai kuwa ko a jikina, dama ina neman sa, kuma ga shi yau Allah ya haɗa ni da shi, don haka wallahi sai na rama marin da yamin jiya." ta kai K'arshen maganar tana huci. Cikin rashin fahimta Meena ta ce "ban gane ba Meesha dama kin san shi ne?" Sweet ta ɗauko cikin jakarta tare da jefawa cikin baki ta ce "Jiya muka haɗu a Sahad naje yin shopping, shi ne fa ya yi min crossing hanya don nayi masa magana sai ya mareni." Mamaki ya kama Meena, don haka sai kawai ta zubawa Ameesha ido tana kallon ta, zuwa can tace "Amma Meesha da zaki yadda in na baki shawara, wallahi ki bar mutumin nan, don baki da yadda za ki yi ki rama........." Hararar da Ameesha ta jefeta da ita, shi ne ya hanata k'arasa maganar da take yi. "Meena kenan kin manta halina ne hala?" "A'a shawara dai na ke baki." "To bani son shawarar rik'e kayan ki, amma ramuwa kuwa babu fashi." Meena ta buɗe baki da niyyar magana, Ameesha ta yi saurin katse ta tace "Please karki ce min komai, tashi muje nayi break don ban yi ba na fito, wallahi da nasan wannan nonsense ɗin mutumin ne, to ba zan fito ba sai na yi break d'ina." Tashi Meena ta yi suka kama hanyar inda Rastaurants d'in da Ameesha ke cin abinci. Dai dai lokacin da suka dawo shi kuma ya ke fitowa daga lab ɗin, harara Ameesha ta cilla masa, sai ko akayi sa'a ya gani, girgiza kai kawai ya yi ya nufi inda motarsa take, hannunsa rike da bag d'in laptop ɗin sa. Don tsakanin lab ɗin da office ɗinsa da tazara, don haka cikin motarsa ya d'auki hanyar da zata sada shi ga office nashi. Waje su Ameesha suka samu suka zauna "ta ciro hand out ɗin tana dubawa, don suna da test idan sun koma school, ita ma Meena karatun take yi." Karfe ɗaya da rabi suka bar Asibitin ,daga nan school suka nufa don suna da test,ba su fito ba sai biyu da arba'in da biyar, lokacin da suka fito a gaji suke bama kamar Ameesha da gaba d'aya bacci takeji, don haka suna fitowa bata tsaya komai ba ta nufi motarta, Allah yasa ma sun gama da laccan yau, burin Ameesha ta isa gida, sai da ta sauke Meena sannan ta wuce. ************************************ Zaune yake cikin kayataccen office d'in sa, iya had'uwa ofis d'in ya yi komai na ciki kalar brown ne da milk, katon table ne a gabansa mai d'auka da file na mutanen da zai duba. gefen dama wani dan gadone irin na duba marasa lafiya, gefen haggu kuma, karamin firij ne mai kyau, ga wani lallausan kafet da ke shimfide a tsakiyar ofis d'in, kai masha Allah komai na ofis d'in abin sha'awa ne. Kallo d'aya zaki yi masa kasan yana cikin damuwa, don kuwa hannunsa ne cushe cikin tsakiyar kyakkyawan sumar sa dake kwance luf da shi, don yana samun gyara sosai, tsaki kawai yake jerowa a fili, duk motsin da zaiyi sai fuskar Yarinyar can ta bayyana ya rasa dalili. Dan murmushi ya saki wanda iya karsa leb'e, da ya tuno yadda take magana d'azun, bai tab'a ganin Yarinyar ba sai jiya, amma kuma tunda suka had'u sai matsala ake samu, kamar wasu dai wanda suke jin haushin juna, shifa Yarinyar burgeshi take, musamman in tana rashin kunya. Wayarsa ya jawo, wacce ke kusa da shi ya soma dialing number "Hello ku turo su yanzu in duba su, don ina son fita." Iya abin da ya fad'a kenan ya datse kiran. Mintina k'alilan ya kammala da duba jama'ar da zai duba, gajiya ya yi sosai ya k'osa ya dan gana da gida, kila in ya sakarwa kansa ruwa zai samu sauki Motarsa ya ɗauka kai tsaye gida ya nufa, a babban falo ya iske Nanne da Bobbo, duk'awa ya yi tare da gaisar da iyayen nasa, baki Alhaji Abubakar ya washe cikin jin dadin ganin ɗan nasa, shima Asmad din farin cikin ganin mahaifin nasa ya rufe shi. Cikin ladabi yace "Baffa awarti jam! noi kugal?" ("Bobbo ka lafiya ya aiki?") "Jam kolon asmad, noi kugal ma ambo?" ("lafiya lau Asmad, kai ma ya naka aikin?") “Yettore jaumirawo Bobbo, wallahi hande kam mi somi siutare tan mi mari haje hande". ("Alhamdulillah Bobbo wallahi yau kam a gajiye nake hutu kawai nake bukata.") " Na alari naa jotta to ad'onno mari debbo ni nanon non noo, alari jotta no awarti d'oo o hakkan noo ma diyam yiwugo be yamdu jamun" ("Kaji ba ka gaji ai da kana da mata duk da haka bata faru ba, kaga yanzu yadda ka dawo d'in nan zata baka ruwan wanka da lafiyyen abinci.") Murmushi Asmad ya yi don yasan dama dole ne Bobbo ya masa maganar aure, burin sa kenan har kullum. "Asmad mosii tan, nane maa o andino ko baffa wi'ata hala bangal tan haje mako" A'a a bangal kam ai wakkati on ,bo ammi aam d'on wad'ana amm komi yid'i fuu, gamman na saito mi banyi. ("Kai Babbo shi fa aure lokaci ne, kuma Bobbo na tana yi min komai da nake so, don haka ba zanyi wani aure ba.") Aa bangal kam dole a bangan, mid'o rufini maa gite taan dikka a fudda taskugo. ('a'a aure kam yinsa zakayi ina dai rakakane, amma tun yanzu gara ka soma shiri.") Tab minkam bangal na jotta gam milarai momi yid'i, amma mid'o d'abbita be hakkilo harmi heba momi yid'i. ("taf ni kam Bobbo har yanzu ban ga matar da tayi min ba, zan dai ci gaba da bincika har na samu.") denden ammi wad'i hunduko der hala man.("in ma baka samu ba ni zan zaba maka wacce ta dace da kai, kuma nasan zakayi farin ciki da zab'ina.") Owii! Sai a nan Nanne ta sa baki tace. Allah subune ko lati hairu, ummu ayaha ayama yamdu maa ta fewa "Allah ya kawo tagari Asmad, tashi kaje kayi wanka abinci na jiran ka." Yana tashi ko bangaren sa bai kai ba, Bobbo ya dubi Nanne ya ce "na yanke wani shawara game da auren yaron nan, don banga yana da niyyar yin auren ba, amma zan tuntub'i Alhaji Bashir don inji ko ya Amince." "Kai Alhaji wa zaka had'a da Asmad d'in? Nifa bani son azo rayuwaka suna b'aci fa?" "Kar dai ki damu insha Allah Alhairi nake hangowa don haka ki taya mu da Addu'a, kuma had'in da zanyi kema zakiyi farin ciki." "Allah ya taimaka, nasan Asmad bashi da matsala, zanyi masu Addu'an fatan Alhairi." ******************* Alhaji Mansur ne tsaye a falon shi, cikin wani irin yanayi, me wuyar fassarawa. Da alama, ya kai karshen tunani ne amma bai samo mafita ba. Ya yi amfani da hannunshi na hagu wajen kwankwasar kanshi, sai kuma ya nufi window ( taga) falon ya yaye labulen ya leka tare da kwada ma Najeeb kira iya karfin shi. Sai da yaga fitowar Najeeb ɗin, sannan ya sake labulen ya koma ya tsaya kamar ya hadiyi tabarya. "Ka san Ameesha?" Alhaji Mansur ya faɗa bayan Najeeb ya zauna. Ido da baki Najeeb ya bude sannan ya ce... _*Yar Mutan Rano*_ [10/8, 8:01 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* *(NWA)* *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* ``` Gaba ɗaya littafin nan naki ne my Cittah wato KHADIJAH A MUHAMMAD Allah ya bar k'auna ,inajinki har a zuciyata Kema kisa a ranki Zulayheart taki ce.``` *6* " Bayan Najeeb ya rufe budadden bakin shi tun sa'adda ya ji sunan Ameesha a bakin mahaifinshi. Sai ya ce " Na san ta. Akwai wani abu ne? Ko ba yar gidan Alhaji Taheer ba?" Shi ma Najeeb ya rufe maganar ta shi da tambayar mahaifin na shi. "Eh itaa, to ka bude kunne ka jini da kyau." Gyara zama Najeeb ya yi, tare da mai da hankalin sa kan Abban nashi. Sannan Alhaji Mansur ya ci gaba da maganar sa "Kana jina ko Najeeb? so nake daga yau zuwa satin sama masu zuwa ka tabbatar ka cusa kanka gareta,so nakeyi nayi amfani da wannan damar don cimma burina." Najeeb da kallo ya bi mahaifin nasa, don kwata kwata bai gane inda yasa gaba ba, kamar Alhaji Mansur yasan tunanin da Najeeb ya fad'a, don haka sai ya ce "So nake kaje wajen ta da batun soyayya, ka san yadda zaka yi har ta soka wannan shi ne abin da nake umurtanka." Zaro ido ya yi baki na rawa ya ce "Abba kasan fa Yarinyar nan ba wata kunya ce da ita ba, kuma dai da kyar zata amince min don ba mutunci ne da ita ba." Tun kafin ya kai karshen maganar Alhaji ke aika masa da wani mugun harara, wanda har ya firgita Najeeb din, cikin fushi ya soma magana "Kai kam Najeeb anyi shashasha, yanzu kai a matsayin ka ka ce baka iya tsara wannan 'yar Yarinyar? To bari kaji dole sai kayi abin da na sanya ka." Girgiza kai kawai ya yi, yana mamakin halin mahaifin nasa sosai. "To naji Abba amma in ta amince ya zanyi da Rufaidat, kasan dai ita nake so." Mtsww Alhaji Mansur ya ja wata doguwar tsaki, don takaici "Kai fa Najeeb da alama kana son raina min hankali, ina ruwana da maganar Rufaida indai bukata ta zata biya, daga baya kasan yadda za'ayi da ita." "Amma Abba baka tunanin a samu matsala, Yarinyar nan fa da wuya ta soni, kuma nima dai ba wani sonta nake yi ba. " " Bani son rashin ta ido, kana jina koh? Maganar da ma fada maka dole ne kayi amafini da ita don abin da nake son yi kai zakayi Alfahari da shi ba ni ba." " Yi hakuri Abba zan yi yadda kake so insha Allah." Cikin ladabi Najeeb ya k'arasa maganar. "Yawwa d'an Albarka haka nake so." Alhaji Mansur ya yi maganar cikin farin ciki. Mik'ewa Najeeb ya yi yana mamakin halin mahaifin na shi. Bayan fitar Najeeb, sai Alhaji Mansur ya manna bayan shi da kujera haka ya sauke wani numfashi me kauri. Ya kai hannunshi yana shafa goshin shi, wannan ita ce hanya daya tilo da yake ganin zai yi amfani da ita don cikar wani buri na shi da ya dade a zuciyarshi. Idan har wannan buri na shi ya cika, bai san irin kalar munan da zai yi ba. Zumbur!Kamar Wanda ya tuna wani abu haka ya tashi, ya dauki key din motar shi ya nufi waje. ***************** Nanne ce zaune a bedroom din Bobbo, magana yake fad'a mata kuma ga dukkan alamu maganar nada muhimmanci, cikin nutsuwa ta ce "Amma kana ganin bamu shiga hakkin Yarinyar ba?" "Maganar shiga hakki bata taso ba, tun da asalin maganar ba daga wajen mu take ba, abin da nake so kawai shi ne in samu Asmad din ya yadda." "Kai ma Alhaji kasan bashi da matsala kuma yana kokarin yin biyayya, kar kayi tunanin haka, Ubangiji Allah ya sa haka shi ne Alhairi." "Amin." Bobbo ya yi maganar cikin jin dadi. " Yawwa da na manta Aneesa fa sun kusa komawa makaranta, don haka zata koma gida." " Yaushe zata koma din?" " Ranar Asabar zata koma." "To Allah ya kaimu." "Bobbo ya mike tare da fadin bari na leka wajen masu aikin gidan can." A tare suka fita zuwa falon, suna shiga Shima Asmad na fitowa daga bedroom din sa, sauri yake yi don dama har ya fita mantawa ya yi shi ne ya dawo. "Bobbo barka da rana. " Asmad ya fada cike da ladabi. " Lafiya lau Asmad har ka dawo ne?" Bobbo ya amsa cike da kulawa. "Eh amma yanzu zan koma, dama na danyi mantuwa ne." Asmad ya karasa maganar yana nufa hanyar waje. Najeeb ne a bangaren sa, ya na faman aikin kai kawo gaba daya kansa ya kulle ya rasa tunani d'aya da zaiyi. " shi damuwar sa Rufaida shin taya zata dauki maganar in har ta samu labari?" Ya yiwa kansa tambayar da bashi da amsa, zuciyar sa tace " kawai kayiwa mahaifin ka biyayya tunda umurni ya baka." Najeeb dai ya kasance d'ane mai biyayya sam baya tsallake maganar mahaifansa, don haka da sauri ya nufi toilet, wanka ya yo kana ya shirya cikin kananan kaya wanda suka amshi jikinsa, ya fashe jikinsa da turare mai sanyi kamshi, key na motarsa ya d'auka sannan ya yi waje." Sai da ya isa bangaren mahaifiyar sa, bayan ya gaida ta sannan ya nufi parking space. Tunda ya tada motar ya ke tunanin ta ina zai fara ne? Shi dai bai tab'a zuwa wajen wata budurwa da sunan soyayya ba Sai Rufaida, to yau gashi da rana tsaka Abban sa ya daura masa aiki, babban matsalar ma ita ce bashi ya ga Yarinyar yana so ba, da a ce shi ya ganta yana so to da da sauki, amma wannan umurnin da wuya in za'a ci nasara. Rasa inda zai nufa yayi don haka kawai sai ya tsayar da shawarar zuwa makarantar su. Bai zame ko ina ba sai makarantar su Ameesha, don yana tunanin tana school din, tunda yanzu sha d'aya ne na safe, parking ya yi a kusa da kofar makarantar yana jiran ganin fitowar Ameesha. Najeeb na zaman jiran ganin Ameesha, ita kuwa tana Asbitin da take practical, suna zaune a karkashin wata itaciyar mangwaro hira suke ta sha da kawayenta. Hira sukeyi hankali kwance, ita da Meena ce sai wasu 'yan class d'in su biyu, d'aya daga cikin wacce suke zaune ta kalle su gaba d'aya ta ce kunsan me?" ta ci gaba nifa wallahi Dr dan fullo burgeni da zai soni wallahi da na more..... " Tun kan takai karshen maganar ta yi saurin katseta. " Kina da aiki wannan mara mutunci ne zaki wani ce kina son sa? Taf lallai da babban aiki a gaban ki." "Kai Meesha ke dai naga alamar ba zaku sha inuwa d'aya da Dr dan fullo ba, ko da yaushe akayi maganar sa sai ki soma wani hakikance wa." Salmah ce ta yi maganar, a dan hasale, d'aya daga cikin wacce suke zaune a wajen. " Allah ya baku Hak'uri, ni fa bani da matsala, amma na fada maki gaskiya tun wuri ki cire shi a ranki Kar ya zame maki wata wahalar, ni shi yasa nake Alfahari da kaina domin kuwa Allah bai doro min san maza ba ko kadan." Hango Dr dan fullo tayi yana parking motarsa, taja wani dogon tsaki wanda yasa duk suka maida hankalin su kanta "Meesha lafiya kike tsaki?" " wancen dan rainin hankali ne kalleshi fa, yadda yake wani tafiya yana tak'ama, gaskiya Dr bai hadu ba." Dariyar rainin hankali kawai Meena tayi, don tasan Meesha fad'a kawai ta yi, ko mara ido ya shafa Dr dan fullo yasan, hadadden guy ne, balle kuma masu ido matashi mai jini ajika, gashi kuma billion naira. " Tashi muje kawai tunda yau bamu da lacca, muje gida daga nan ma zan biya na gaida Ummi." Meena ta k'arasa maganar tana mik'ewa, su dai sauran shiru sukayi suna mamakin yadda Ameesha take raina Dr dan fullo. Najeeb dai na zaune a kofar school har sha biyu da rabi, baiga alamar wata Ameesha zata fito ba, don haka sai kawai yaja motarsa da niyyar anjima zai kai mata ziyara gidan su. ************************************ Bobbo ya gyara zama tare da maida hankalin sa kan Nanne dake zaune kusa da shi. "Yawwa kina jina ko mun gama komai da Alhaji Bashir, sannan su Baffa ma sun shiga maganar, komai anyi na yadda auren zai tafi babu gargada." Nanne ta dubi mai gidan nata, cikin sakin fuska da kulawa tace " Masha Allah Ubangiji ya tabbatar da Alhairi, sai dai har yanzu baka sanar dani wa ka zab'awa Asmad din matsayin matar aure ba." Duk da taji ya ambaci Sunan Alhaji Bashir, amma tana son gasgata hasashen ta. " yanzu zaki sani kuma zakiyi farin ciki da zabina ba kowa ba ce illa.......... " _*Yar Mutan Rano*_ [10/8, 8:01 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* *(NWA)* *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* ``` sadaukarwa ga KHADIJA S MUHAMMAD my Cittah``` *7* Nanne ɗan murmushi ta saki, tana mamakin yadda mai gidan nata yake farin cikin sanar mata da maganar, ita ma nan take taji ta kosa ya sanar mata zabin da akayi wa Asmad din ta. "Aneesa na masa zaɓi, don nasan ita ce kadai zata iya zama da shi cikin mutunci." Kara gyara zama Nanne tayi, da jin zaɓin da aka yiwa Asmad, wani kyakkyawan murmushi ta saki, wannan shi ne burin da ta jima da shi a ranta, sai dai tayi shiru ne don kar ta shiga hakkin su, sai ga shi mijinta mai dogon tunani, shima ya yi irin nata nazarin." Murmushi ta kuma sakewa a karo na biyu, wannan karon bakinta yak'i rufuwa, cikin jin dadi tace " Allah ya sa Albarka cikin wannan haɗin, Ubangiji ya kade fitina, Allah ya basu zama lafiya da zuri'a tagari." " Allahumma amin, Hajiyar Asmad ga dukkan alamun dai wannan maganar ta yau tayi maki daɗi?" " Sosai kuwa Alhaji, ai wannan abin farin ciki ne, Allah ya tabbatar da Alhairin sa." Haka suka ci gaba da hiran su, cikin jin daɗi. ************************* Ameesha ce zaune cikin falon su, waya ce a hannunta da alama game takeyi ko chat, Haidar ne wato Yayanta wanda take bi mawa ya shigo falon da sallama. Tayi saurin ɗago da kai ta ce "Yawwa Ya Haidar, wallahi tun ɗazun zaman jiran ka nake." Harara ya banka mata cikin daure fuska, Allah ya yo Haidar da iya haɗa fuska, baya k'aunar raini ko kaɗan, balle kuma Ameesha da ta rawan kai. " Kai Ya Haidar daga magana sai ka soma min harara to na fasa." Zama ya yi yana faɗin " Kin yiwa kanki, tashi ki kawo min abinci." "Kai don Allah nifa game nakeyi, kuma ina tashi zasu cinye ni." A shagwabe Ameesha ta k'arasa maganar. "Ba zaki tashi ba kenan?" Ganin mugun kallon da yake watsa mata yasa ta mike, komai sai da ta haɗo masa sannan ta aje masa a gaba, komawa tayi kan kujera ta lafe, cike da jin takaicin yadda Haidar din ya mata. " Yawwa k'anwata kin san me? Zo kiji? " Haidar ne ya yi maganar, wannan karon fuskar sa a sake, kamar ba shi ba. Banza ta masa tare da ci gaba da buga game ɗin. " Meesha my lovely sister zo kiji please? " Kallon inda yake ta yi tare da turo k'aramin bakinta ta ce " Ba yanzu ka gama min masifa ba, kuma kaki tsayawa kaji abin da zan ce." " Oh! Sorry my sister, faɗi inji mai kike so? " Murmushi ta saki ta ce " Dama so nake in ce maka laptop ɗina ya lalace, jiya da zan dawo daga school." " Yanzu ya kike son a yi?" " Abba nake jira ya dawo, sai in amshi kudi sai ka sayo min sabo, tunda wancen ya tashi aiki." " Je ki ɗauko." ya yi maganar yana aje plet ɗin. Ta mike da zumar tafiya, sai taji sallama a kofar falo, amsawa ta yi tare da tambayar "waye? Dai dai sanda ta isa kofar. Ganin mai bawa fulawar gidan ruwa yasa ta ce " Lafiya kuwa? " " Lafiya lau Hajiya dama bak'one ya ce a kira ki." " Bak'o?" Tayi tambayar tana kallon wanda ke tsaye gabanta. "Eh Hajiya." "To ina zuwa." Shi ne iyakar abin da Ameesha ta faɗa, mamaki sosai ya rufeta, ita ai bata yi magana da wani akan yazo gidan suba "to waye wannan" ta yiwa kanta tambayar da babu amsa. Bedroom ɗin Ummi ta nufa, don ko takan Haidar bata yi ba, akan sallaya ta samu Ummin, zama tayi gabanta tare da rika hannunta ta ce " Ummi kinji wai wani yazo nema na? " Shafa Addu'an Ummi ta yi ta ce" To ya baki tafi ba? " To ni ai Ummi ban San shi ba, kuma ai da nasan da zuwan shi zai kira wayata." Ameesha ta yi maganar ranta a ɗan ba ce. "Haba Ummin Abba ba'a haka, tashi ki ɗauko gyalen ki, kije kiga ko waye daga nan ki hada masa abin sha kin ji ko?" Daga kai Meesha ta yi, badon ranta ya so ba, amma tunda Ummi ta bata dama bari taje, ji take kamar ba ita ba, tunda take bata taɓa zuwa harabar gidan su da sunanan tsayuwa da wani ba. Amma yau gashi wani ya tako har gidan su, tana jinjinawa ko waye wannan da kokari. Ko ruwa bata ɗauka ba, ta nufi wajen dama jikinta fes yake, fuskar ta shafe yake da powder. Cikin nutsuwa ta ke tafiyar, jikinta ko ina iska ke kada ta, tunda nesa ta soma shakar daddar turaren sa, tsaye yake ya jingina bayan sa jikin motar, waya ce a hannunsa da alama waya yake, can nesa da shi ta tsaya, tana kallon sa. Bai san ta iso ba har sai da yaji kamshin turarenta ya cika wajen, a hankali cikin nutsuwa ya juyo da fuskar sa zuwa gareta, fuskar nan tashi ɗauke da murmushi " Barka da zuwa Gimbiya sarautar mata." Shi ne abin da ya faɗa, yana kallon Ameesha, dan tabe baki tayi cikin jin kai ta ce " bawan Allah ban gane ka ba, daga ina kuma wajen wa kazo? " Murmushin dai ya kuma yi ya ce " Haba Ameesha baki dai gane niba, da farko dai sunana *Najeeb Mansur* dan Alhaji Mansur abokin Abban ki." Zaro ido tayi cike da mamaki ta ce " oh! Sannu da zuwa Najeeb ya Alhaji da Momi? " Ameesha ta tambaya fuskar ta ba yabo ba fallasa. " Lafiya lau Ameesha, zakiyi mamakin gani na a gidan ku ko? To wannan ba'a bin mamaki bane domin kuwa mai son ɗan tsuntsu shi ke binsa da jifa, gaskiyar magana dai nazo maki da wata magana ne mai muhimmanci, sai dai tunda baki san da zuwa na ba, ina son ki bani lokacin da zan dawo mu tattauna." Kallon sa take tunda ya soma magana, Najeeb dai kyakkyawa ne son kowa kin wanda ya rasa, da ganin sa kasan da nutsuwa a tattare da shi, sannan kalaman da ya yi amfani da su wajen yi mata magana sunyi mata dadi. Amma sai ta basar tace " No nikam bani da wani time, don kullum ina school yau ma kayi sa'a ne ka iskoni a gidan." " Haba princess Meesha ki taimaka, matukar baki bani dama na fayyace maki abin da ke raina ba, tom zan iya shiga wani hali, kiyi hak'uri ki bani dama? " Da muryan tausayi ya k'arasa maganar. Yadda ya yi maganar har ya kusan bata dariya ya yi, amma sai tayi saurin fuskewa ta ce " kana iya dawowa nan da two weeks." Zaro ido ya yi a ɗan firgice ya ce " Haba princess ina laifin two days, wallahi two weeks ya min yawa." Ta gaji da jin maganar, tana son ko mawa cikin gida don haka ta ce " to one week ya yi? Don ina da test a school, a cikin week din nan." "Allah ya kaimu amma ba haka naso ba, sai dai kuma tunda princess ce ta zaba bani da yadda zanyi." Har ta kama hanya zata tafi ya ce " princess baki bani phone number ɗin ki ba please ki bani? " Wayarsa ta amsa tasa masa numbers ɗinta sannan ta wuce. Shi kuma a nashi ɓangaren wani nannauyan ajiyar zuciya ya sauke, da ya gama da wannan, don yasan tunda ya samu number ɗinta ya yi mai wuya. Maimakon ya yi farin ciki da ya samu ta ɗan Amince da shi, sai takaici ya rufe shi, don yasan abin da zai aikata ba abin kirki bane, tunda yaudara ce zaiyi, takaici sosai da tausayin ta suka rufe shi. A gefe ɗaya kuma yana yaba kyaunta da nutsuwarta, tabbas da a ce bashi da Rufaidat tofa zai iya auren ta, sai dai shi yanzu Rufaida kawai yake kallo a matsayin mace. Ko da yake jan motar haka ya yi ta tunanin abin da zai aikata, Allah ya sani umurni zai cika ba yin kansa bane. ********************************* Zama ya yi kusa da Nanne ya ce (o jod'i haa kombii Nanne! owi "Nannena da alama yau dai kina tare da farin ciki?" ("Nanne aam ko fe'i hande banta ad'on seyi? ") " Sosai kuwa Asmad tunda burina ya kusa cika." ( "sosai mid'on seye gam heje aam badake hubugo Asmad." ) Dariya ya yi wanda ya kuma fito da asalin kyaun shi ya ce ( o jali ha wad'ega mako beddi wartugo dendenta owi) " Nannena kenan, hala saudiyya zaki kuma zuwa? " (" Nannena aam d'oo kaam makka na alorata? ") " A'a ba saudiyya bane mafarkina na son Asmad dina yayi aure shi yake shirin tabbata." (' a'a na maka sam miyahata koid'ol aam on badake wartugo gonga Asmad aam badake bangugo. ") " Kai Nannena yo nida ko budurwa bani da ita kike maganar aure?" ("Kai Nanne aam min mowala ko berajo awolwinta hala banga?") " Ai uba nagari tuni ya samar maka da mata yar kirki."( "ai dottijo gonga hebani maa debbo jabdubo") " Nanne kina nufin Bobbo ya samar min mata? Oh! Shet." ( "Tani wiaam bobbo aam subani aam debbo? Or toskiyam") Asmad ya yi maganar cikin wani irin yanayi. (Asmad wi'ika der mettam beram) " Eh ya zabar maka kuma mata yar kirki, wacce kai kanka zakayi Alfahari." (" E of subani Maa debbo kand'o bema to'o larima ko an alarima saito a mani moo") Nanne ta yi maganar cikin kwantar da hankali. (Nanne wii banjin don wallina moo hakkilo.) " wacce mai sa'ar Bobbo ya zaba mata ni a matsayin mijin aure? " (" mard'o sa'a to be bobbo subani aam?") " Aneesa." Nanne ta faɗa babu shamaki. (Nanne not moo) Wani irin zabura Asmad ya yi bakin sa na rawa ya ce "What........?" (Asmad haftii hunduko mako don wama owi "d'ume........?") _*Yar Mutan Rano*_ [10/8, 8:02 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* *(NWA)* *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* ``` Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah``` *8* Kallon Asmad din Nanne ta yi don ganin irin zaburar da ya yi ta ce " lafiya kuwa Asmad? Ko zaɓin ne bayyi maka ba? " Saurin dai dai ta nutsuwar sa ya yi, da ya tuna fa a gaban Nanne yake. Yace " Haba Nannena ta ya zan ce zaɓin ku bayyi miba? Kawai dai gani nayi kamar Aneesar bazata yadda da hadin ba. " Murmushi Nanne ta yi cikin jin daɗi, da samun Asmad ɗin matsayin da don bai taɓa jayayya da duk wani umurnin su ba, Koda hakan bayyi masa ba amsa ya ke ba tare da ya nuna ɓacin ransa ba. " Haba karka damu ai Aneesa 'Yar'uwar ka ce, kuma da amincewar mahaifin ta hakan zata faru, don haka kayi hak'uri da zaɓin insha Allah zakayi Alfahari da shi." Gyada kai kawai ya iya yi "ya mike ransa a dan bace" don bai so wannan zaɓin ba, to amma tunda Bobbo sa ya masa ya zama dole ya yi biyayya. Kai tsaye yana fita daga falon Nanne, ɓangaren sa ya shiga kan kujeran dake falonsa ya faɗa yana ambaton Allah, da ya kawo masa ɗauki cikin wannan bak'on lamarin da ya kunno masa kai, abin da ko Mafarki bai taɓa tunanin gani ba. Amma yau sai gashi ido buɗe yaji kuma ya gani, da sauri ya mik'e tunawar da ya yi yana da shiga *CS* a dai dai wannan lokacin. Bedroom ɗin sa ya shiga, ruwa ya watsawa jikinsa, bayan ya fito ya shirya cikin kananan kaya riga da wando, bai koma falon Nanne ba sai ya nufi motarsa, ba kuma don wannan maganar ce ta hana shi komawar ba, a'a ganin da ya yi lokacin ya kusa, har ya buɗe mota zai shiga sai kawai ya fasa, ya zama dole yaje yawa Nannen sa sallama, ba haka ya saba yi ba. Asmad kenan yaro mai neman Albarkan iyayen sa. *********************************** Ameesha na shiga cikin falo, bedroom ɗin Ummi ta zame, wannan karon Ummin ta idar da abin da takeyi "Ummi na dawo " Cewar Ameesha tana zama abakin gadon ɗakin Ummi. " Madallah! sannu da dawowa, har ya tafi ne? " " Eh Ummi." Ta bata amsa a takaice. Dan juyo wa Ummin ta yi ta kalli Ameesha, ganin ta kwanta sai Ummin ta girgiza kai, a ranta ta ce " Allah ya shirya min ke Ameesha, Yarinya kullum ciki zurfin ciki. Da Abban tane da yanzu ta soma bashi duk labarin abin da ya faru, amma ji yanzu ko ta sanar min yadda su ka yi. " " Ummi wai kinsan waye yazo wajena? " Ameesha ta yi maganar tana ci gaba da latsa wayarta. " Ta ina zan sani Ameesha, nida ko falo ban lek'a ba har kika dawo. " " Najeeb Yaron Alhaji Mansur abokin Abba." Ameesha ta yi maganar ba tare da ta ɗago kai ba. Dan ware ido Ummi ta yi cikin mamakin jin abin da Ameesha ta faɗa "Najeeb kuma? To mai ya ce maki? " " Ya ce zai dawo na bashi rana, shi ne na bashi." " Allah ya tabbatar da Alhairi." Shi ne kaɗai abin da Ummi ta iya faɗi, don zuwan Najeeb wajen Ameesha ya bata mamaki, sai dai kuma bata tashi hankalin ta ba, don tasan Najeeb yaro ne nutsatse bashi da wata matsala. "Tashi muje kicin kin San yau Abban ki zai dawo." Ummi tayi maganar tana kallon Ameesha, ɗan turo baki tayi tace " Allah Ummi in mutum ya shiga kicin duk sai ya fito da gajiya." " Allah ya shirya ki, ke kam ban san irin ki ba, amma in aka dafa kin iya bude baki ki ci? Zanga wanda zai rik'awa mijinki abinci." " Ai Ummi na iya kawai shiga kicin din ne bana so a koda yaushe. " " To kuma dai wannan ke kika sani, tunda baki zuwa ki gyara min bed ɗin akwai turaren wuta." Ummi ta karasa maganar tana fita. ********************************* Alhaji Mansur ne zaune tare da abokin sa Alhaji Kabiru, hira sukeyi hankali kwace, daga gani kasan abokan juna koma a kira su da aminan juna, Alhaji Kabiru ya muskuta tare da gyara zama ya ce "Wai kuwa Alhaji ina maganar da mukeyi da kai waccen lokacin? " " Tana nan koba ta Alhaji Taheer ba? Ai tuni har na soma aiwatar da k'udurina, kaima kasan bana wasa ta ɓangaren kuɗi, kasan Allah Alhaji sai nayiwa Taheer walak'anci, duk kuɗin da mutumin nan yake samu, amma don na ce ya bani contena ɗaya na shinkafar,da aka shigo masa da ita, shi ne ya ke neman wulak'antani, wallahi abin da zan masa sai ya fi wanda ya min. " " Ai na tura Najeeb wajen 'yarsa kasan yafi sonta da kowa cikin ya'yansa? Da ita zanyi amfani. Jinjina kai Alhaji Kabiru ya yi yana yabawa da karfin hali irin na abokin sa. ********************************** Fitowar ta daga toilet kenan ta ji wayarta kirar Infinix dake kan drissing mirror tana riging don neman agaji, a hankali ta matsa wajen wayar ta zurawa number ɗin ido tana kallo, a zuwan ko zata gane mai numbers ɗin gani har yana shirin tsikewa bata gane lambar ba, yasa takai zara zaran yatsunta tare da ɗaukar wayar ta kara a kunne ba tare da tayi magana ba. " Assalamu Alaikum." Ya yi maganar cikin nutsuwa. Shiru ta yi ba tare da ta amsa ba, sai ma tunanin mai muryan da ta faɗa yi. " Hello." ya kuma faɗi a karo na biyu. Cikin siririyar murya ta ce "Hello wake magana please? " Ajiyar zuciya ya sake a hankali, har yana lumshe ido ya ce " Najeeb ne." Dan murmushi Ameesha tayi tare da faɗin " Oh! Sorry Najeeb wallahi ban ɗau muryan ka bane, ya Momi? " " Tana lafiya." ya bata amsa. "Kina gida ne in shigo yanzu? " Girgiza kai ta yi kamar yana ganin ta da kyar ta buɗe baki ta ce " A'a " " Haba princess kiyi hakuri, wallahi ina son ganin ki a wannan lokacin." Mtsssw taja tsaki ta ce " Please wai Najeeb mai kake nufi ne? " Wata mayaudarin dariya ya yi ya ce " Ki bani dama nazo yanzu sai in fayyace maki abin da ke raina." Kosawa da maganar tayi shine yasa ta ce masa "sai yazo." da haka su ka yi sallama. Minti goma sha biyar ya kawo shi gidan, wayarta ya kira yana sanar mata da zuwan sa, tana zuwa kadai ta iya ce masa. Waya ta ɗaga ta kira Mai ba fulawa ruwa, ce masa tayi ya kaishi falon baki, Allah ya yo Ameesha da son kwalliya koda yaushe cikin gayu take, matsalar dai tafi sa kananun kaya, Yau ma kamar ko da yaushe cikin gayunta take na doguwar riga wacce tayi mugun amsan jikinta, fuskar ta tasha kwalliya sosai tayi kyau, turare ta kuma fesawa sannan ta nufi fita. Koda ta fita a bedroom din Ummi ta yada zango, kallonta Ummin tayi ta saki murmushi ta ce " Autana sai ina haka? " Dan ya mutsa baki ta yi ta ce " Najeeb ne yazo yanzu." " Ji sakarci shi ne kuma kika shigo nan? maimakon ki wuce babu kyau fa wulakanci Ameesha." " Zuwa nayi kawai in gaya maki, amma yanzu zan tafi." "Yawwa 'yar Albarka tashi ki tafi masa da ruwa." "To." shi ne kaɗai abin da Ameesha ta faɗa ta mike. Yau ɗin ma haka ta fita ba tare da ta ɗauko masa ruwan ba, shiga falon tayi da sallama ta samu waje ta zauna, ba tare da ta ce masa ta tafasa a sauke ba. Kallon ta ya yi da murmushi ya ce " princess da alama yau sarautar ta motsa." Ko ɗaga kai bata yi ba balle ya samu arzikin magana. " Shiru ya ɗan ratsa na mintuna, yana jiran ta yi magana, taki sai latsa wayarta da takeyi, ganin shirun ya yi yawa yasa ya ce " Ameesha? " Ɗago da kai tayi ta kalleshi bata ce komai ba. " Kin san me ke tafe dani?" Girgiza kai ta yi, alamar a'a. " Karki yi mamaki in nace maki maganar soyayya ce ta kawo ni wajen ki." " What.... " ta faɗa tare da ɗago kai ta watsa masa wani harara ta kuma bude baki ta ce......... _*Yar Mutan Rano*_ [10/8, 8:02 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* *(NWA)* *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* ``` Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah``` *9* Girgiza kai ta yi tace " Ayya Najeeb ai Ameesha bata soyayya, don bata iya wa da kayan takaicin da ke cikin soyayya." Kasak'e ya yi yana kallonta, tare da mamakin furucin ta, in har hasashen da yake yi gaskiya ne, kenan Ameesha bata tab'a soyayya ba. "Kayi hakuri Najeeb gaskiya ba zan iya amince maka ba, don ban son in jefa zuciya ta cikin halaka, shi yasa ko kadan bana ɓata wa kaina lokaci." Tana gama faɗin haka ta yi waje. Nannauyan ajiyar zuciya ya sauke, ganin ta tashi tafita, tabbas sai ya yi da gaske hak'an sa zai cimma ruwa, da wannan tunanin ya tashi jiki a sanyaye. Ameesha na barin falon bak'in bedroom dinta ta shiga, hankalin ta ya tashi b'ata tab'a soyayya ba, haka kuma bata jin zata iya soyayya da wani, wayarta ta jawo ta dan nawa Meena kawarta kira. Bayan sun gaisa ne Ameesha ke sanar mata da yadda sukayi da Najeeb din. Daga bangaren Meena ajiyar zuciya ta sauke ta ce " Bai kamata kiyi saurin fada masa haka ba, kamata ya yi ki zauna kiyi dogon tunani akan maganar, musamman dai kin ga Najeeb ba wai mutumin banza ba ne." " shi yasa na kira ki ai yanzu ya kike ganin za'a yi? " " OK mu haɗu a school gobe. " Daga haka sukayi sallama. Bayan sunyi sallama ne, ta mike ta koma falo jin alamar shigowar Abbanta, ai ko shi ɗin ne yana zaune ga yayyenta suma a zaune kusa dashi, da sauri ta karasa tana fad'in " oyo-yo Abbana welcome back." Murmushin jin daɗi ya yi ya ce " Thanks my daughter ya gida? " " Lafiya lau Abba, gaskiya nayi kewarka fa." Ta karasa maganar cikin shagwaba. " Zo zauna uwata, ayi min Afuwa nima ina can tunanin rashin ki kusa dani ya dameni." Sai da ta zauna kusa da Abbanta, sannan ta gaida yayyenta, wanda suke zaune cikin jin daɗin ganin Abban nasu, a tare suka amsa cikin kulawa don suna matukar son Ameesha sosai, kasancewar ta ita ɗaya ce mace cikin su. "Wai Abba waye naga kun tsaya da shi ɗazun da ka shigo? " Jaheed ne ya yi tambayar. " Najeeb ɗin ne kuma yau baka sani ba? " Alhaji Taheer ya yi tambayar fuskar sa cike da mamaki. Dan rufe baki Jaheed ya yi cikin dan mamaki ya ce " badai Najeeb din Alhaji Mansur ba? Allah Abba ban gane shi ba, naga ya canza." " Aiko shi ɗin ne, nima nayi mamakin ganin sa a gidan." "yo Alhaji wajen Ameesha yake zuwa, Yau shi ne zuwansa na biyu. " Ummi dake zuwa falon ta yi maganar. Ai Ameesha tana jin maganar Ummin ta kwasa a guje tayi stair, bata zama ko ina ba Sai bedroom ɗinta. Da kallo suka rakata, Jaheed ya dan kada kai take ya fahimci in da maganar Ummi ta dosa, Kai kusan dukkan su sun fahimta, amma shi Jaheed tuni ya fahimci zuwan Najeeb din, don yasan ba abin da zai kawo shi wajen Ameesha sai soyayya. Mikewa su ka yi gaba daya jin an soma kiraye kirayen sallar magriba. Bayan an idar da sallar ne suka dawo falon, don cin abinci wannan al'adar su ce, da safe da dare tare ake cin abinci a dining. Suna gama cin abinci duk suka mike zasu tafi "Kai Jaheed da Abdul ku tsaya, ku kuma kuna iya tafiya." Alhaji Taheer ya yi maganar ba tare da ya ɗago ba, Ameesha ta mike zata wuce "A'a uwata ke zauna, ai yau hira zamuyi da ke wacce muka daɗe ba muyi ba." Zama tayi tare da jingina jikinta da kujera, lumshe ido tayi "ba don Abbanta bane babu abinda zai hana ta wuce wa, don so take ta kebe waje ɗaya, don ta yi dogon tunani akan maganar ta da Najeeb." "Wai ku kuwa sai yaushe zaku girma? Zuwa wannan lokacin yaci a ce kuna da mata, kai fa Jaheed shekaran ka talatin (30) kai Abdul kana da ashirin da takwas (28) shekarun ku kullum k'ara ja yake, me kuka nema kuka rasa? " Shiru su ka yi suna sauraren mahaifin nasu, ci gaba da magana ya yi " Duk kuna da aikin yin ku, kuna da karfin da zaku rike matan ku da ya'yan ku, to ku buɗe kunne kujini da kyau, na baku nan da sati biyu ku kawo min matan da zaku aura ko ya'yan waye ku tashi kuban waje." Jaheed ya kuma sadda kansa k'asa ya ce " Yi hakuri Abba wallahi dama tun satin da ya gabata, Abban Baderyeet yake ta ce min yana son ganin ka, to jira nayi zuwa da safe sai inyi maka bayani." "Masha Allah kai amma naji daɗi da jin wannan furucin, insha Allah gobe zan tura su, Alhaji Isa da Alhaji Mansur don su tambayo." "Kai fa? " " Dan murmushi ya yi ya ce Abba nima mun dai dai ta, da Meena dama jira nake ka dawo sai in sanar maka." Meena kawar Ameesha ita yake nufi. To Alhamdulillah tunda hakane Allah ya sa Alhairi, duk gobe za'aje nema maku auren." Farin ciki ne ya rufe Ummi da Ameesha, Ummi fatan Alhairi kawai takeyi a zuciyar ta, don sosai taji daɗin wannan maganar. Da haka kowa ya wu ce, aka bar Ameesha da Abba da Ummi, wanda suke hira. ************************************ Bayan sati ɗaya komai ya dai dai ta, na maganar auren su Jaheed har an tsayar da ranar auren, wata biyu masu zuwa. Kuma ya zuwa wannan lokacin, tuni an daɗe da sanya ranar auren Asmad da Aneesa, farin ciki wajen Aneesa ba'a magana, don wannan shi ne burinta ta mallaki Asmad a matsayin mijin aure, shi kuwa a nashi bangaren ba haushi ba haufi, wato kadaran kada han. Ta fannin Ameesha kuwa, duk da dumbin shawarwarin da Aneesa ta bata, har yanzu bata yadda da Najeeb ɗin ba, sai ma garashi take kamar ball a fili, koda yaushe cikin zuwa gidan su yake, don Abban shi ya takura shi yana son jin gamsashshiyar amsa. Yau ma kamar kullum, Najeeb din ne zaune a gaban Ameesha, yana ci gaba da jaddada mata irin son da yake mata. " Zan yadda da buk'atar ka amma sai kayi min Alkawarin ba zaka ci amanata ba, ba zaka sa zuciya ta cikin damuwa ba, don kai kaɗai ta fara niyyar amincewa, sai dai ban baka wani babban waje ba, amma matukar kayi min Alkawari to ni kuma zan soma son da ban taɓa yiwa wani ba." Kallon ta yayi gaban sa na dukan uku uku, da jin furucin ta lokaci ɗaya tunani kala uku ya yi cikin second goma, na farko ji ya yi zuciyar sa tana gargadin sa da karya cuci yar mutane, na biyu yana tunanin yadda zata kaya tsakanin sa da mahaifinsa, na uku kuwa shine take yaji zuciyar sa ta kamu da son Ameesha so na gaskiya ba irin wanda Abbansa ya turosa yi ba. To kuma in haka ta faru tabbas akwai matsala babba. Dago da kai ya yi ya dubi Ameesha dake ci gaba da matsa wayarta cikin sanyin murya ya ce " ki yadda da ni princess, bada yaudara nazo gareki ba, da son gaskiya nazo wajen ki." "Indai Alkawari ne nayi maki, ni Najeeb bazan ci amanar ki ba." Gyada kai ta yi ta ce "Tom Allah ya sa haka, amma matukar dai ka yaudareni bazan taɓa yafe maka ba." Wani farin ciki ya mamaye Najeeb don jin daɗin furucin Ameesha. Soyayya suke gudanarwa, abin gwanin ban sha'awa hatta cikin gidan su Ameesha kowa yasan da maganar, Abba ya yi farin ciki sosai da jin wannan maganar, don yasan karfafa zumunci zaiyi da abokin nashi. ********************************** Wata mahaukaciyar dariya Alhaji Mansur ya saki don jin Najeeb ɗin ya ce ai Ameesha ta amince, har ma Alhaji Taheer ɗin. " Wayyo Taheer na kusa tarwatsa maka farin cikin ka, na kusa sanya maka takaici." Girgiza kai Najeeb ya yi cikin takaici da dana sanin biye wa mahaifin nashi buɗe baki ya yi yace "Abba............" _*Yar Mutan Rano*_ [10/8, 8:02 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* *(NWA)* *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah* *10* "Abba gaskiya abin da kake son aikatawa bashi da kyau, ka dubi girman amintar dake tsakanin ku da Abban Ameesha, amma Abba yau har kai kake son yin amfani da ɗiyar sa don cimma wani buri na..." Wata muguwar tsawa ya daka masa, ransa a matuk'ar ɓace ya katse Najeeb cikin sauri. "Kai Najeeb har ka kai matsayin da zaka zauna kana min wa'azi? To bari ka ji Allah yasa Masallaci ne kai ,ba malami ba tashi kabani waje tun ban tsinka maka mari ba." Tashi Najeeb ɗin ya yi yana faɗin " Allah ya huci zuciyar ka Abbana." Dogon tsaki Alhaji Mansur ya ja tare da shigewa bedroom ɗinsa. Najeeb na fita bangaren Mominsa ya shiga, zama ya yi a falon tare da dafe kai, don kwata kwata tunanin sa ya kulle ,da yana da yadda zai yi tofa lallai da ya hana mahaifinsa aiwatar da wannan mummunan aikin. Sai dai bashi da wannan damar don mahaifinsa ya kasance mutum ne mai mugun ra'ayi, duk abin da ya yi niyya tofa sai ya cimma biyan buk'atar sa. Haka Najeeb ya kasance cikin tunane tunanen yadda zata kaya, shi dai yasan a wannan gaɓar tabbas ya kamu da don Ameesha so kuma na gaskiya, bawai na yaudara ba. ************************************** (" Asmad noi haa jotta minanai ad'on wolwa hala yahugo Adamawa da yald'e bangal d'on badita lutti burai sati tatii.") " Asmad har yanzu ban ji kana maganar zuwa Adamawa ba, ga lokaci nata gabatowa yaufa kwata kwata bai fi sati uku bikin ba amma, baka ko maganar zuwa." (Nanne wii Asmad binni.) ce kewa Asmad maganar. (O wo'ini jode mako dendenta o lorni hakkilo mako do Nenne owii.) Gyara zama ya yi tare da maida hankalinsa kacokan kan Nanne yace (" To Nenne jotta saito miyahi Adamawa? Minna mi anda tomi andino da miyahino miwarti.") Yo Nanne wai a haka har Adamawa zanje, ni ai ban yi wannan tunanin ba, da tuni naje ai." (Nenne d'oiliti moo) Harara ta yi masa cikin wasa,ta ce ( "Nananam 6ingel, jotta ad'on numa na saito a yahi ha Aneesa maan? To dei on narrata be mako?" )" Kuji min yaro , yanzu kai kana tunanin ba sai kaje wajen Aneesa ba? To kenan ta ya zaku fahimci juna?" (" Allah Nenne sina gam awolwi mii tammai saito miyahi, amma jotta de a hirliti aam der satii do miyahan.") " Allah Nanne ban da yanzu da kika yi maganar ban san sai naje ba, amma tunda haka ne insha Allah cikin satin nan zan yi k'ok'arin shiga." (" Yawwa barkantejo yahu Allah wanne barka.") Yawwa ɗan kirki ka k'ok'arta ka shiga ɗin Allah ya yi albarka." ("Amin") "Amin Nanne." (Asmad noti d'on lara agogo jungo mako.) ya amsa yana kallon agogon hannunsa. ("Nanne hami yaha Asibiti gammi d'on momi wanni *CS* o badeke fintugo.") "Nanne bari na tafi asibiti don akwai wacce nayi wa *CS* to ta kusa farkawa." ("Allah wallu Nenne wii.") "Allah ya taimaka." Nanne ta faɗa. Mintina goma suka kai shi asibitin, a parking space ya paka motar sa, wasu takaddu ya kai hannu zai ɗauko kamar ance ya ɗago kai, sai kuwa idon sa ya sauka akan su. Kara buɗe ido ya yi sosai, tabbas itan ce suke hira da saurayi da alama tana jin daɗin hiran musamman yadda take ta sakin murmushi, kana kallon su zaka gane su ɗin masoya ne, shi duk gani ganin da yake mata bai taɓa koda ganin tayi murmushi ba, amma gashi yau har dariya take, ji ya yi ransa ya sosu da ganin da ya mata haka. _*( A'a ikon Allah, kuji shiga uku takabar suruki, inji Kamala Minna, in ba shiga uku ba ina ruwan Asmad da Ameesha? To ko dai ko dai..... bari nayi shiru don ban tabbatar ba.)*_ A fusace ya fita daga motar cikin zuciyarsa yana dana sanin zuwan sa asibiti a dai dai wannan lokacin, tabbas da yasan irin wannan gamon zai yi gaskiya babu abin da zai kawo shi. Office ɗin sa ya shiga, sam bai samu sukuni ba a wannan rana, don hoton su kawai yake gani kota ina, tsaki kam har ya yi babu adadi. Haka dai ya yi ta duba majinyatan nashi, duk don ya manta dasu amma ina kamar ma yanzu suke zaunen haka yake gani. Su kam bama su san ya na yi ba, don hiran su suke sha irin ta masoya, Najeeb ne ya kawowa Ameesha ziyara har asibitin, karkashin wata bishiya suka zauna sai hira suke zubawa, sosai Ameesha ta kamu da yawa, bata k'aunar abin da zai raba ta da Najeeb don tana masa wani irin so ne. Sun daɗe suna hiran kafin su ka yi sallama, shi ma badon sun so rabuwa da juna ba, Najeeb ya soma wucewa ita kuma ta kuma shiga ciki inda Meena ke jiranta "Kai Meesha hala da ba zaku rabu da juna ba ne ? Kin shanyani Bros Abdul sai kirana yake." "Ki bari kawai Meena wallahi in Ina tare da Najeeb bana k'aunar abin da zai gifta da sunan katse mana jin daɗin mu." " Yana da kyau haka, yanzu dai tashi muje lokaci kan ya tafi sosai." Meena ta k'arasa maganar tana ɗaukar jakarta, Meesha ma jakarta ta ɗauka sannan suka nufi inda motar Ameesha ya ke, suna zuwa shima Asmad na zuwa don shi ɗin ma gida zashi ya gaji da takaicin da yake tunawa " Dr sai gobe." Meena ce mai maganar,ita Madam ko kallon sa bata yi ba tayi shigewarta mota. Murmushi ya yi ya ce " Allah ya kaimu." Tsaki taja tare da bama motar wuta ta juyo ta kalli Meena ta ce "Ke kam kin fiye cusa kai ba k'warjini, wannan miskilin kikewa magana?" " Babu wani cusa kai, yanzu ke fisbilillah ya da ce mu wuce ba tare da munyi sallama da shi ba?" " Yo Ina ruwan biri da gada?" Tayi maganar tana watsa hannu irin ko a jikina Gyada kai Meena tayi cikin zuciyarta ta ce "Allah ya shirya min ke." Meesha kam bata kuma magana ba,don wayarta ta ɗauko ta kunna wak'a ,ita ma shiru ta yi har suka iso kofar gidan su Meena , buɗe kofa Meena ta yi ta ce " To ta Najeeb! jikam sai gobe in Allah ya kaimu." " Allah ya kaimu, don Allah ki zomin da han out ɗin nan na Chemistry, don gobe school zamu shiga kuma test jibi." " Ok zan fito maki da shi ɗin." Meena ta kai karshen maganar tana nufa get ɗin gidan su. Meena tana wu ce wa, sai ta soma duba wasu takaddun ta ,duk ta duba motar babu ,da sauri ta kira Meena ta ce bata gansu ba, fitowa Meena ta yi ta ce "ki koma asibiti, muje ina raka ki." "No Meena koma gida kawai bari na koma asibitin." Ta ida maganar tana juya kan motar ,gudu take yi kai tsaye asibitin ta shiga don babu tantama a cen ta zubar, addu'a takeyi Allah yasa ta gani. Tana shiga ta faka motar cikin sauri sauri ta fita , cikin ta shiga ta dudduba amma bata gani ba, bayan ta gama duba duk inda take saran ganin takaddun amma bata gani ba. Sai kawai ta dawo gurin motar jiki a mace, ji take kamar ta kwanta ta yi ta birgima da ƙafafuwanta kamar dai yadda yara suke yi idan abu ya ɓata masu rai sosai. Ta kai hannu jiki a mace da niyyar buɗe motar sai ta ji magana kamar daga sama. " Lafiya ki ka dawo?" Ta juyo kamar ta k'wala ihu, rasa abin da zata ce ta yi,sai ta zuba ma sa ido game da langaɓar da kai gefe hawayen da ta ke ɓoyewa , suka ziraro. Mamaki ya kama Asmad,duk irin tsiwarta,yau kuma ita ce ta koma haka. Sai kawai ya yi murmushin da yake k'arawa fuskarsa kyau , buɗe wani file ya yi ya zaro takardun tare da mik'a mata. _*Yar Mutan Rano*_ [10/8, 8:05 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* *(NWA)* *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* ``` ina matukar taya ki murna my sweet sister BILKISU BILYAMIN Ubangiji Allah yasa kifi haka Allah ya kara baiwar fasaha da kaifin brain``` *Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah* *11* A hankali cikin mutuwar jiki ta kai hannu ta amsa. " Na gode" Ameesha ta yi maganar cikin wani irin voice. Murmushin nan ne dai kwance a fuskar sa " no need " Ya bata amsa, yana juya kai, bai wani bata lokaci ba ya tada motarsa don dama jiranta ya tsaya yi, kuma tunda ta dawo har ta amshi abin ta mai zai tsaya yi. Fuskar nan tata yake gani kota ina, yanayin da ta shiga dazun yake mamaki, da wannan tunanin ya kama hanyar gidan su. Ameesha kuwa bayan wucewar sa, da kallo ta raka motar har sai da ya kulewa ganin ta sannan ta saki wani sansanyan ajiyar zuciya a fili ta furta " Allah na gode maka." Motarta ta koma, zuciyar ta cike da tunanin Dr dan fullo, da irin taimakon da ya mata a wannan rana, da wannan tunanin ta isa gida. Parking ta yi tare da zaro hand back din ta, cikin rashin kwarin jiki ta nufi hanyar shiga falo, dan juyowar da zata yi sai ko idonta ya sauka kan motar Najeeb dake aje a parking space, siririn tsaki taja ranta ya dan sosu da ganin motar. Falo ta shiga ko sallama bata samu ikon yi ba sai ma zubewa da ta yi a kujeran falon ta furta " Wash! " Ummi dake fitowa daga kicin ta zubawa Ameesha ido, da mamaki ta ke kallonta don duk wanda ya ga Ameesha yasan ba a cikin nutsuwa take ba. " Lafiya kuwa Auta? " Ummi ta karasa tambayar tana nufa inda Ameesha ta ke. Wani murmushi ta k'ak'alo wanda iya karsa lebe, don tun kallon da Asmad ya mata Jikinta ke mace. " Ummi lafiya lau fa, kawai gajiya ce." Ta bata amsa tare da maida hankali kan Ummi. Zama Hajiya Halima tayi tare da riko hannun Ameesha, don ko kadan bata kaunar damuwar Ameesha. " Anya kuwa Ameesha? Jifa yadda kika koma kodai baki da lafiya ne? " Girgiza kai tayi alamar a'a. " Are your sure?" "Sure Ummi." " OK tashi kije kiyi wanka, sai ki ci abinci, ga Najeeb can yana jiran ki." "To " kawai ta amsa tana mikewa. A toilet ma dai da Ameesha ta shiga, duk tunanin Asmad din ne a zuciyar ta, ruwa ta watsa tana fitowa ta shirya, Yau simple dress tayi, don riga da siket ta sanya na atamfa, powder ta mursa sai lipstick da ta shafa, ya zuwa wannan lokacin miss call a wayarta sun haurawa ashirin, a fusace ta dauki wayar " Hello." ta fada bayan ta Kara wayar a kunne. Banji mai aka ce mata ba Sai ce wa ta yi, ai nasan da zuwan ka amma yau sai dai ka daga min Kafa don ina da bukatar in samu nutsuwa." Fadin haka keda wuya ta yanke kiran, tare da jifa da wayar rai a bace, tafiya ta soma yi don sauka falo, domin tasan matukar bata sauka falon ba to Ummi sai ta daga hankalin ta. Najeeb kuwa tunda ya ga Ameesha ta datse kiran, yasan da matsala, shi kuma baya son tambaya don haka sai ya fito daga falon bakin da yake, jikin sa a sanyaye yana Addu'a Allah yasa ba shi ya bata mata rai ba. Koda ta kammala da cin abinci sama ta koma, tana shiga taji karar wayarta, da sauri ta karasa tare da d'auka, suna nan Meena ta gani akan screen din. " Ya Meesha wai kuwa kinga takardun? " Ajiyar zuciya ta ja ta ce " Eh Meena na gani a asbiti." " Masha Allah, wallahi tun dazun tunani kawai nake yi fa." " Ki bari kawai Meena zamu hadu a school akwai labari." " Allah k'awata? " " Allah kuwa." " Dan fara bani labari mana kin san ni da son jin labari." " No maganar bata yuwuwa a waya, ki dai bari har mu hadu din zai fi." "To ai shi kenan." Meena ta fada. Daga haka sukayi sallama. ************************* Koda Asmad ya shiga gidan, bangaren sa ya soma shiga ruwa ya watsa sannan ya nufi babban falo, da sallama ya shiga. Nenne da wata ne kadai suke zaune a falo, amsa masa sallamar su ka yi, ya ida shiga yana fadin "Nenne barka da yammaci, Adda sannu da zuwa. " " Yawwa Asmad an dawo? Ya aikin ya kuma masu jiki? " " Aiki Alhamdulillah! Masu jiki da sauki. " Zamewa kasa ya yi tare da gaida Addan, cikin sakin fuska ta amsa, bakuwa ce tazo daga adamawa matar Yayar Nennen Asmad, ta zo ne kan maganar bikin Asmad din. Amsawa ta yi cikin farin ciki ta ce " Asmad ango ya shirye shirye? " Dukar da kai kasa ya yi cikin kunya bai ce komai ba, sai ma tashi da ya yi ya nufi kicin don yana jin yunwa, koda ya dibi abincin bai zauna a falo ba sai bangaren sa da ya nufa, don gaba d'aya kunyar Nenne da Adda ya ke ji. Bayan ya kammala cin abinci ne ya koma cikin bedroom din sa, zama ya yi a bakin gadon sa, hannun sa ya kai saman sumarsa ya na shafawa a hankali, a hankali ya furzar da wani irin iska mai zafi, dai dai da soma ringing din wayarsa, juyo da kai ya yi ya dubi wayar sunan da ya gani ne yasa shi dan jan tsaki. Bai dauki wayar ba sai ci gaba da tunanin sa kawai ya yi, fuskar Ameesha ce ke masa gizo, ya rasa fahimtar yadda ya ke ji game da ita. **************************** Zaune suke a karkashin wata bashiya, saurin dago da kai Meena ta yi bayan ta gama jin labarin da Meesha ta ba, baki bude don tsananin mamaki ta ce "Meesha Dr dan fullo fa kika ce? yaushe kuka dai dai ta da shi? " " ki bari kawai amma wallahi jiya nayi matukar mamaki, da ya bani takardun nan, kinsan Allah daga jiya zuwa yau sai naji cikin kashi dari na haushin da nake ji nashi, ashirin da biyar sun fita." Murmushi Meena ta yi cikin dai mamakin maganar nata ta ce " Kuma ina maganar rama Mari aka barta? " " Tana nan sai na rama komai dadewa. " Taba Meena amsa tare da gyara zama. " Amma nifa gani nake kamar gaba kadan zaku zama masoya, musamman yadda kuke hakan alamar soyayya ce." Harara Meesha ta watsa wa Meena ta ce " Allah ya kyauta waye zai yi soyayya da wannan mutumin, kema kin san na wu ce da ajinsa." Dariyar rainin hankali ta yi ta ce " Lallai Meesha ke Wai kina ganin kin fi Dr dan fullo aji ne? To wallahi bari kiji duk fa inda kike tunanin sa ya fi haka. " Tsaki kawai ta yi tare da tashi tsaye. Itama Meena ganin haka sai ta mike, suka kama hanyar su da yake daman sun riga da sun gama laccan ranar. Yau dai sauran kwana bakwai bikin su Yaya Jaheed da Yaya Abdul Malik, shirye shiryen bikin ake ta yi kota ina, tuni gidan Alhaji Taheer ya cika da mutane domin wannan shine karon farko da zai fara auraswa, su Ameesha kam babu zama, sai kai komo ake musamman da Ya Abdul din Meena zai aura. Kudin da Abban ta ya bata kawai don shagalin biki, dubu dari uku ne, a ce warsa baya son ta nemi komai ta rasa har a gama bikin. Suna kwance a dakin Meena, bayan sun dawo daga shopping don a gajiye suke likis, wayar Ameesha ce ta soma ruri alamar neman agaji dan dago da kai tayi a hankali ta dubi fuskar wayar, Sunan da ta gani ne yasa ta sakin murmushi. Cikin sauri ta dauki wayar " Hello." Ta fada cikin sansanyar murya. Daga bangaren Najeeb din lumshe ido ya yi, cikin jin dadin muryar da ya ratsa masa kunnuwa. " Baby son ki na neman hallaka ni fa." Murmushi mai sauti ta yi ta ce " Kamar yadda naka ke wahalar dani." "Kina ina ne haka? " " Gani gidan su Meena." " OK bari na zo don ina son ganin beauty face naki." " Allah ya kawo ka lafiya." ta fada tana gyara kwanciya. "Please Meesha ga number din Dr ki tura masa da text din bikin." Maganar da Meena ta fada kenan wanda yasa Meesha saurin tashi zaune wani harara ta watsawa ta ta ce..." _*Yar Mutan Rano* [10/8, 8:06 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* *(NWA)* *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah* *12* Ta ce " A haba dai Meena kema kinsan haka ba zai yuwu ba, sai dai ki kawo wayar ki in yi masa da naki." Murmushi Meena taja ta ce " To ai ga wayar nan kusa da ke ki yi masa, nidai burina Allah ya sa ya zo, don shima satin sama ne bikin sa." Wani mummunan faduwar gaba ya zuyarci Ameesha lokaci guda, tare da wani irin sarawa da kanta ya yi, ji taji kamar Meena ta watsa mata ruwan zafi " Da gaske auren sa ya kusa? " Tayi tambayar hankali a dan tashe. Mamaki ya kama Meena ganin yadda ta tashi hankalin ta lokaci daya, tabbas tasan wacece Ameesha ta kuma san halinta tsaf, a wannan karon ma akwai tunanin da take a kan Ameesha da Dr dan fullo. Saurin kawar da tunanin ta yi tace " Allah kuwa lokacin da ake maganar a asbiti kina ina? " Da sauri ta wayan ce don kar Meena ta gane ta ce " Oh! Wallahi kam na manta, Allah ya sanya Alhairi." " To ai yanzu na tuna maki don haka sai ki shirya masa abin gudummawa." Tsaki kawai Meesha ta ja tare da gyara kwanciya,bayan ta tura masa text din, zuciyar ta na wani irin zafi da maganar da Meena ta fada mata, har tana mamakin kanta na jin faduwar gaba da taji maganar auren sa. Haka akayi ta shagalin bikin, anyi lafiya kuma an tashi lafiya, Meena gidan su Ameesha aka kaita bangaren da Yaya Abdul ya gina, ya yin da ita kuma matar Yaya Jaheed take gidan da ya gina a sabuwar gwandu, Dr dan fullo ya yi kokari wajen halartan bikin. Tun kafin a gama bikin Ameesha ke Fama da wani zazzafan jiwon kai, da zazzabi daurewa ta tayi har aka gama bikin, Yau dai abin yana nema ya yi yawa don har ta kai ga ta kwanta jikinta ko ina rawa yake hakoran ta sai haduwa suke da juna. Hajiya Halima ce ta haura saman Ameesha, ganin har rana tayi sosai bata fito ba gashi suna da school, don haka sai ta ce bari ta leka ta ga ko lafiya " Inna Lillahi wa Inna ilaihin Raju'un! Shine abin da ta fada tare da saurin karasawa bakin gadon da take kwance. " Auta lafiya meke damunki? " Da kyar ta iya faɗin " Zazzabi" Hankali tashe ta dauki wayar Ameesha dake kusa da ita ta soma kiran layin Yaya Abdul. Minti uku kacal sai gashi sun iso tare da Meena, suma hankalin su ya tashi da ganin jikin Ameesha "Kira Dr don jikin nata sam babu dadi." " Ummi asbiti ya kamata muje fa, kalli yadda ta ke? " " Eh ina ga zuwa asbitin zai fi." " Gaskiya kam Ummi." " Je ka fitar da mota, bari mu fito da ita. " Ita dai Ameesha bata ma San abin da su ke yi ba, don yadda take jin jikin nata. Ummi da Meena suka taimaka mata har zuwa wajen mota. ******************************* Asmad ne zaune shi da abokan su, suna ta tsara yadda bakin zai kasance, shi dai shiru ya masu ko ta tafasa a sauke bai ce ba, tunanin sa na kan Ameesha wacce yau kusan kwana uku bai ganta ba. A takaice dai tun ranar daurin auren Meena da ya ganta, kuma yasan itan bata gan shi ba, don a lokacin tana tare da wasu ne sun ɗibo kayan da zasuyi amfani da shi a wajen walima. Ba karamin kyau ta yi masa ba, kyau na gaske har yake ganin kaf matan duniya babu kamar ta, take ya hasaso kyau Aneesa don ita ma fa ba baya ba wajen kyau, amma sai ya ga Meesha ta fita sau dubu, matsala daya gareta shi ne jin kai, koda ya ke wannan jin kan da takeyi shi yake kara mata kwarjini. " Ango lafiya kuwa irin wannan dogon tunani? In ka kwantar da hankalin ka kwana nawa ya rage? " Wani daga cikin abokan sa ne yake magana. Girgiza kai ya yi tare da bude baki da niyyar magana sai ringing na wayar sa ya hana shi, dan tsaki yaja tare da ciro wayar ya danna tare da karawa a kunne muryan da ya ji ne ya sa shi saurin tashi tsaye. " bata da lafiya kuna ina yanzu? " " Inna Lillahi! " ya kuma fada a rude. " Ina zakaje kuma? " " Sorry Hafiz nemana ake, wata ce bata da lafiya an kaita asbitin mu, kuma tunda suka nemeni abin ya dan girma, don haka zan wuce in na gama komai zan dawo. " Yana gama faɗin haka ya fita daga falon. " Allah ya bata lafiya." suka hada baki wajen faɗa Kai tsaye asbiti ya nufa, cikin sauri sauri ya faɗa motarsa, emergency room ya nufa da sassarfa, don nan aka shiga da ita ko office bai nufa ba, haka kuma bai tsaya duba jama'ar da ke waje ba, nurse ya samu a kanta sun ɗaura mata dirif na ruwa. Kallon ta ya yi cikin mamaki ganin yadda ta koma, daga ganin da ya mata zuwa yau. Koda ya kai hannu jikinta ya yaji mugun zafi, take yasa wata daga cikin nurse din ta hada masa allura, wacce ke saurin saukar da zazzabi, hankali sa a tashe yake da ganin Ameesha a matsayin mara lafiya. Cikin ikon Allah ba'afi minti goma ba sai zafin jikin ya ragu, sai a sannan ya samu dan nutsuwa har ya fita, yana fita Ummi ta yi saurin ta sowa tana tambayar sa jikin Ameesha. Kallon Ummi ya yi take ya gane ita din ce mahaifiyar Ameesha, don muguwar kamar da su ka yi. Murmushi ya saki mai kwantar wa da mutum hankali ya ce " Karki damu Hajiya ta samu sauki don yanzu ma bacci takeyi, Kuma zazzabin ya sauka, insha Allah sanda zata farka zata koma normal, gajiyar da tayi na aikace aikace ne wanda bata sababa shi ya haifar mata da zazzabin . " (Hmmm abin mamaki su Ameesha *SANGARTA* na damunki, daga aikin biki sai ciwo? Kodai kodai damuwar wani akasa a zuciya? ) Bayanin da ya mata ne yasa hankalin ta dan kwanciya, sai a lokacin ta samu damar kiran Alhaji Taheer tana sanar masa da rashin lafiyar Ameeshan. Sosai hankalin sa ya tashi don haka cikin sauri ya dauki hanyar hanyar ko mawa kano don yana garin Abuja, jirgi ma yabi don yana sauri. Ameesha yar gata cikin lokaci kalilan har asbiti ya cika da mutane, Najeeb ma ya zo hankalin sa a tashe, domin fa yanzu Allah ya jarabci Najeeb da mugun son Ameesha, wanda har yake mamakin yadda son nata ya shige shi sosai. Sai bayan la'asar ta farka, lokacin Alhaji Taheer ya daɗe da bayyana a asbitin, koda ta farka tuni zazzabin ya sauka, amma ganin Alhaji Taheer sai ta wani kuma narkewa. " Sannu Uwata ina ke maki ciwo? Me kike so? Mai zaki ci? " Alhaji Taheer ya ke jero mata wandinnan tambayoyin. Girgiza kai ta yi tace " Ni dai Abba bani son komai, bacci nakeji kawai." " Haba Uwata ki daure ki ci wani abun mana? " Allah ya yo Ameesha bata son jan zan ce, don haka sai ta ce " To Abba." Asmad shigowarsa kenan ya ji Abban Ameesha na lalla6ata, a zuciyar sa ya jinjina girman son da mahaifan ta suke mata. "lallai dole ki yi *SANGARTA* har rashin kunya ta samu wajen zama. " Babyn Ummi ya k'arfin jiki? " Najeeb ne ya ke magana idon sa akan Ameesha. Murmushi ta saki tare da lumshe ido, ta buɗe ta ɗaura idon ta kan fuskar Najeeb ɗin a hankali ta furta " Jiki da sauki." " Allah ya k'ara sauki." Ya fada. Wani takaici ne ya rufe Asmad, ganin yadda ta saki jiki da Najeeb ɗin, har take masa murmushin da ba kowa ya kamata ya gani ba. Don haka cikin sauri tun kafin zuciyar sa ta buga kawai sai ya masu sallama. Don duk wani abu da take buk'ata ya gama, sai dai bai gaji da ganin kyakkyawan fuskar ta ba, amma sakamakon ganin Najeeb sai da ya yi dana sanin zuwan sa asbitin, duk sai yaji ya tsani Najeeb ɗin. Asmad ne zaune da tare da Nenne da Bobbo a babban falon gidan su, hira su ke yi cikin kwanciyar hankali, Bobbo ne ya kira shi don su tattauna wani muhimmin abu, al'adar su sai sun fara hira kafin ya gabatar da abin da ya hada su. To yau ma kamar kullum suna zaune, a babban falon gidan , domin kuwa tuni gidan ya soma amsar baki daga waje daban daban, kasancewar yau saura kwana biyu ɗaura aure, Yan Adamawa tuni suka bayyana, muskutawa ya yi tare da gyara zama, sannan ya kai hannu ya bude wata jaka dake kusa da shi. Wasu takardu ya kwaso cikin jakar tare da mik'awa Asmad ɗin, hannu biyu yasa tare da amsa cikin rashin fahimta " Buɗe ka gani Asmad, yau kam alkawarin da na ɗauka Allah ya bani iko na cika shi." Buɗe takardun ya fara cikin wani irin mamaki ya mik'e tsaye baki na rawa ya ce " Bobbo na ga takardan asibiti ne?" " Eh Asmad! Sune takardun asibitin dana gina maka ba tare da saninka ba , dama na ce sai lokacin da za'a ɗaura aurenka zaka san da shi." " Masha Allah! Ina matuk'ar godiya Bobbona, Allah ya saka maka da Alhairi ." Farin ciki ya cika Nenne da irin kyautar da mai gidanta ya ba ɗan nasu guda ɗaya da Allah ya basu. Sai sanyawa abin albarka take yi Farin ciki hana shi magana ya yi, sai kallon Bobbo ya ke, wayar sa ce ta dawo da shi daga tunanin da ya lula number ɗin da ya gani ne yasa shi ɗauka tare da karawa a kunne, cikin zuciyarsa faɗi ya ke yar matsala Saurin fita daga falon ya yi yana faɗin me...?" _*Yar Mutan Rano*_ [10/8, 8:06 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* *(NWA)* *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah* *13* " Lafiya kuwa?" Daga can ɓangaren Aneesa ta ce " Hamma ina yini?" "Lafiya." Ya yi maganar fuskar sa ba yabo ba fallasa. " Ehm daman..." Sai kuma ta yi shiru. " Aneesa ina jinki akwai matsala ne?" Dan murmushi ta yi ta ce "Dama so nake na ce muna da buk'atar kuɗi, wanda zamu yi amfani da shi." "Ok" Shi ne kaɗai abin da Asmad ya faɗa ya katse kiran. Aneesa kuwa sororo ta tsaya da waya a hannu, tana mamakin Asmad ɗin , sai kuma ta saki murmushi da ta tuna kwana kaɗan ya rage su kasance matsayin miji da mata, tana alfaharin kasance wa da Asmad a matsayin miji. Da wannan tunanin ɓacin ran da ya ɗan sa mata ya gushe. Asmad kuwa falon ya koma inda iyayen sa suke, zama ya yi tare da kallon Bobbo ya ce " To Bobbo yau she za'a buɗe asibitin?" Asmad ya yi tambayar yana kallon Alhaji Abubakar. " Ranar ɗaurin Aure ina kamar zai fi." Bobbo ya bashi amsa. " A'a ko dai washe gari, don kasan fa kafin a dawo gida za'a daɗe a hanya." Nenne ta faɗa. " Tom a barshi haka ɗin, tunda muna da buk'atar mutane." Allah ya sa albarka ya taimaka, Ubangiji ya ida nufi ka kula da kyau Asmad ka taimaki bayin Allah, domin kaima Allah ya taimake ka ." "Insha Allah Nennena zanyi yadda kika umurta, kudai ci gaba da yi mana addu'a." Kullum muna yi maku Allah ya yi albarka. ******************************** " Abba wai ni kam sai yaushe za'a sallame ni?" "Ina zan sani uwata? Ki bari dai har ki kara samun sauki." "Nidai gaskiya na gaji, shi mutumin nan tunda ya aje mutum babu wanda ya kuma ganin shi." Ameesha ta karasa maganar kamar zata yi kuka. Harara Ummi ta watsa mata ta ce "To ai ko yanzu kina iya tashi ki wuce, tunda ke kamar karamar yarinya ki ke ji." "A'a Hajiya me kuma na harara? Baki ganin ba lafiya ne da ita ba?" Kai Alhaji sai kayi ta goyon bayan Ameesha, duk maganar da taga dama shi take yi, yanzu don Allah ina laifin yaron nan?" Dan murmushi yaja ya ce "To naji amma dai lallaɓata ya kamata kiyi." Su Alhaji Mansur ne su ka yi sallama, shi da matarsa fara'a sosai Alhaji Taheer ya saki da ganin abokin nasa. " Sannu da zuwa Alhaji ku ne a wannan lokacin?" Faɗa ɗa murmushi Alhaji Mansur ya yi ya ce " wallahi mune muka ce yau dai tunda mun samu lokaci bari muzo mu duba mai jiki." " Masha Allah ai mai jiki ma ta samu sauki sosai." Zama su ka yi kafin aka hau gaggaisawa, Ameesha dai kanta a kasa ta kasa ko da kallon su, wani karin haushi ya rufe Alhaji Mansur, ganin yadda ya tasa Ameesha a gaba sai *sangarta* take masa ga uban kaya da ya zuba a ɗakin na kwaɗayi, kamar ba asibiti ba " yanzu da nine bani lafiya sai dai yazo gaishe ni, zanyi maganin ka" ( "Kai dai Alhaji Mansur hassada ta yi maka yawa, baka san hassada kan meshi ya ke komawa ba? Ubangiji ka rabamu da hassada don bata yi ba a rayuwa") Hajiya Salaha wato mahaifiyar Najeeb ita ce ta kalli Ameesha da murmushi ta ce "Daughter ya jikin?" "Da sauki." Ta bata amsa. Sun ɗan daɗe a asibitin kafin su ka yi sallama. Asmad ne zaune ya jingina bayansa a kujerar da ke office ɗin sa , zuwan sa kenan daga gida, tunanin Ameesha ne ya addabe shi har ya kasa jurewa , yana son ya bata sallama sai dai kuma bai gaji da ganin ta ba. Sannan yana jin haushin yadda yake ganin ta tare da Najeeb, domin ko da yaushe yana shigowa asibitin sai dai baya zuwa ɗakin da take, da yake ɗakin nata na musamman ne, ya kula kuma Najeeb ko da yaushe yana cikin asibitin. Tsaki yaja a karo na barkatai ya faɗa a fili " Ya zama dole na sallame ta domin gobe ne zan tafi Adamawa don jibi daura aure, kuma idan na bar asibitin a yau ni da kaina ban san ranar da zan dawo ba." Da wannan tunanin ya mik'e ya nufi hanyar ɗakin da take, tun da ya doshi wajen ya hango motar Najeeb, sai ya ji wani kululun bak'in ciki ya tokareshi a zuciya , tabbas yasan yana cikin ɗakin yasa ta a gaba tana masa murmushi. A kofar shiga ɗakin ya haɗu da Meena gaisuwar mutunci su ka yi ta ce " Dr mukam yau she za'a bamu sallama? Mun gaji da zaman asibitin nan fa?" Murmushi ya yi ya ce " Yanzu zan baku sallama ku kwantar da hankalin ku, bari na shiga na kuma dubata." Ya ida maganar yana shiga ɗakin . Sai da suka gaisa da Ummi da Abba sannan ya dubi inda take kwance. Najeeb ne zaune kusa da Ameesha suna hira kasa kasa,sai ka saurara da kyau za ka ji abin da suke faɗa, wani kallon ya yi wa Najeeb mai cike da ma'anoni daban daban, Malam ɗan bani waje zanyi aiki." " Tom" Najeeb ya faɗa tare da tashi ya ce " Babyn Ummi ina tunanin na tafi, idan an sallame ki tom sai nazo gida." Gyada kai tayi kawai, don tunda taga Dr ɗan fullo ya shigo ta rasa nutsuwa, don haka sai ta kasa masa magana. Bayan fitar Najeeb ɗin sai Dr ɗan fullo ya watsawa wa Ameesha harara ,wanda akayi sa'a tagani " Ashe daman rashin lafiyar karya ki ke yi?" " Bangane ba?" Tayi tambayar tana murguɗa baki. "Ai dama ba zaki gane ba, tunda fa kinsa wannan k'aton a gaba kina masa dariya taya za ki gane?" Mamakin maganar nasa take yi, don bata fahimci me yake nufi ba... Bata gama tunanin ba sai ta kuma tsinkayar maganar sa " Bari na sallame ki don nan asibiti ne ba gidan love ba, don naga alamar ke baki da ta ido, a gaban iyayen ki sai ki zauna kina wa wani k'ato murmushi, ku ala dole ga masoya ko? To kuje gida can kuyi soyayyar." Yana maganar tana aika masa harara, cikin zallar rashin kunya. Yana gama faɗin haka ya mik'a mata takaddan da ya rubuta mata sallamar, sannan ya yi sallama da su Ummi ya yi gaba, ita kam banda juya maganar da ya faɗa mata babu abin da ta ke yi, gaba daya ta kasa gane inda maganar ta dosa . " Auta ya ce ya sallame ki ko?" " Eh Ummi ga takardan da ya bani." " Ok to bari mu tafi kenan, dama ɗazun na rage wasu kayan." Dan danan suka tattara kayan su suka koma gida. Yau dai rana bata karya a yau asabar aka ɗaura auren Asmad da Aneesa wanda dubban jama'ar Adamawa suka shaida, shi dai ango a nashi fannin babu kuka babu dariya, baya farin ciki kuma baya bak'in ciki. Yana cikin abokan sa sai harkan bikin suke. Aneesa kuwa yau babban burinta ya cika, tunda yau ta kasance matsayin matar *Asmad Abubakar ɗan fullo* ta zama matar Dr ɗan fullo kyakkyawan matashi mai ji da kyau da kuɗi,kai ita kam babu wacce ta kaita sa'a. Ana gama ɗaura aure suka kamo hanyar kano, inda abokan sa suka shirya masa dinner a cikin wani haɗaɗen hall mai suna *Zamani* . Basu isa gida ba sai bayan magriba, don haka wanka kawai su ka yi ta yi tare da salloli, sannan suka soma shiri don karfe goma za'a fara tafiya. Sosai amarya ta yi kyau na ban mamaki, take aka fara haska bikin cikin gidajen Talabijin, a dai dai lokacin Ameesha ne zaune da Abbanta yana lallaɓata akan ta sha yogurt ɗin da ya shigo mata da shi, don kwata kwata bata son cin abinci TV Abbanta ya kunna ya kamo tashar liberty , dai dai sanda ake nuno shagalin bikin. Sam Ameesha hankalin ta bashi kan tv ɗin sai da Abbanta ya ce "A'a uwata wannan ba shi ne likitan da ya duba ki ba ?" Gabanta ya yi wani irin faduwa da jin maganar Abba, saurin ɗago kai ta yi tare da watsa idonta akan TV ɗin Dr ɗan fullo ne da wata sun yi mugun kyau, gashi sun da ce da junansu. "wai dama da gaske aure zai yi?" Gyada kai ta yi da kyar ta buɗe baki ta ce " eh shi ne" tana gama faɗin haka ta yi saurin mik'ewa tare da nufa bedroom ɗin ta hankalinta a mugun tashe. Ko da ta shiga bed room ɗinta,kuka ta fashe da shi irin mai ban tausayi, wani irin zafi ta ke ji a zuciyarta, ta rasa me ke mata daɗi ta ji takaicin auren Dr tana nan tana fama da ciwon sonsa, ashe yana da wacce yake gashi har an ɗaura aure suna can cikin farin ciki, ita kuma tana fama da ɓaci rai Ta sha kukan ta inda daga karshe ta rarrashi kanta, Amma ko da safe da ciwon kai ta tashi, don kar ta ɗaga hankalin su Ummi sai kawai ta cije. Ganin bata iya direvin mota ya sa ta amsa kudi wajen Ummi, sannan ta fita ko tsayawa jiran Meena bata yi ba *** *** *** Kai na gaji Yaseen Please kuyi min addu'a am not feeling fine 👏 _*Yar Mutun Rano*_ [10/8, 8:06 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* *(NWA)* *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah* *14* Tsaye ya ke a kofar gidan hannayen sa rungume a kirjin sa, ya zubawa get ɗin gidan idanu, burinsa bai wu ce yaga ta fito ba , gefe ɗaya kuma yana tunanin yadda zata kaya, rabon sa da zuwa wajen ta yau kusan wata biyu kenan. Yanzu ma nazari ya yi ya ga dai tabbas bata cancanci irin wannan hukuncin daga gare shi ba, sosai ya lula duniyar tunani,sai jin Muryar ta ya yi ta na faɗin " Barka da zuwa, yau a gari, ashe talaka na ganin ku?" Ju yowa ya yi tare da sauke idonsa a fuskarta, wanda ke ɗaure kamar bata taɓa sanin wani abu wai shi murmushi ba balle dariya ba, take ya ji gaban sa ya faɗi da yanayin ta, da kyar ya dage tare da tattaro nutsuwar sa ya buɗe bakin sa da ya masa nauyi ya ce " Ki yi *Rufaida* wallahi abubuwa ne su ka yi min yawa." (Fatan masu karatu basu manta da Rufaida ba, asalin budurwar Najeeb?") " Har suka hana ka ɗaukan wayata?" Ta yi saurin jefa masa tambaya, har yanzu bata ko kalli inda ya ke ba. "No Ruffy ba shi ne yasa ba ." " Ok ganin dama ne kenan? Ashe haka k'auna take komawa? Wallahi Najeeb ka bani mamaki ban taɓa tunanin haka daga gare ka ba" "Kiyi hakuri Ruffy na yi kuskure, amma insha Allah haka ba zai kuma faruwa ba." " Hmmmm Najeeb kenan ai bana jin akwai abin da zaka gaya min in yadda." "Haba Please Ruffy ki fahimce ni, kin fi kowa sani halina fa, Please ki yafe ni." Da kyar ya lallaɓata ta yadda, da abin da ya ke faɗa mata. "Fatar kin yafe min?" " Ba komai Najeeb amma tabbas kasani a damuwa, har nake tunanin na aikata maka ka dai dai ba." " Baki min komai ba, kuma gani yanzu nazo fitar da ke." Ya karasa maganar cikin murmushi. Itama murmushi ta saki ta ce " Tom nayi farin ciki, amma fa Najeeb ina ga lokaci ya yi da zaka gabatar da kan ka a wajen Abbana." " Karki damu na kusa shiga,so nake na kammala wasu abubuwa." "Allah ya tabbatar da Alhairi." Haka Najeeb da Rufaida suka kasance cikin hira irin ta masoya. Sam Rufaida Allah ya yi ta bata da fushi, ko da yaushe fuskantar a sake take bama idan tana tare da Najeeb manta duk wani damuwa ta ke yi. Shi kuma Najeeb gefe ɗaya tunanin Ameesha ne ya addabi zuciyarsa, tabbas yana don Ameesha sai dai kuma yana alhinin rabuwa da Rufaida. Ameesha kuwa ko da ta fita a gida, ta yi tafiya mai dan nisa bata samu adai dai ta ba, ga jikinta na ci gaba da ciwo, kan wani ɗan dakali ta zauna tare da zubawa hanyar ido, duk wanda ya ganta ba zai ce ita ce Ameesha yar Abba ba, gaba ɗaya ta canza ta koma wata silet. Tana zaune dai a wajen, tana kuma hango nafef ɗin amma ta kasa yadda zata tsayar da su,don bata saba ba, sunkuyar da kai k'asa ta yi wasu siraran hawaye suka zubo, hak'ik'a tana son Najeeb sai dai kuma bata jin sa kamar yadda take jin Asmad a zuciyarta, ta rasa gane wani irin abu take ji ɗin game da shi... Firgigit ta yi saurin ɗagowa da kai sakamakon jin hon na mota a gaban ta. Kallon mai motar ta yi cikin rashin sani, murmushi ta cikin motar ta yi wanda suka amshi fuskarta, cikin Muryar ta mai sanyi ta ce " In ba za ki damu ba muje na rage maki hanya?" Lokaci ɗaya Ameesha ta ji tana son matashiyar matar, da bazata wuce shekara ashirin da biyu zuwa da uku ba Saurin share hawayen ta yi , don kar ta fahimci halin da ta ke ciki. " School fa zani." Ameesha ta bata amsa. " Wane school ɗin? don nima can na nufa." "B.U.K" Ameesha ta bata amsa. " Ok shiga muje , nima can zan shiga ina da laccan safe ne." Shiga motar Ameesha ta yi , ta zauna tana mai ambaton Allah a zuciya. " Sunana Khadija Yaseer amma an fi sanina da *Ni'eema* fatan zamu zama kawaye? Murmushi ta saki ta ce " Insha Allah ni kuma Maryam Taheer wacce a ka fi sani da *Ameesha*." "Masha Allah Ameesha Allah ya bamu ikon zama da juna cikin amana, ina da aure da yara biyu asali mu yan Kaduna ne aiki ya dawo da mijina nan, in zan tafi makaranta ina yawan ganin ki da wata cikin mota kuna tafiya" Murmushi ta saki don tana jin daɗin hiran da su ke yi ,gefe guda kuma tana mamaki da Ni'eema ta ce tana da yara biyu, don ba mai kallonta ya ce ta yi aure bare kuma a ce da yara, saurin kawar da tunanin ta yi ta ce " Eh matar yayana ce , kuma kawata tare muke tafiya yau bata da laccan safe, ni bani da aure tare da iyayena na ke." Da wannan hirar suka isa school ɗin, har a zuciya Ameesha ta ji tana son Ni'eema, har musayan number su ka yi da ita . Da yake Ni'eema tana 300 level ne, Ameesha kuma na 200 level. ********************************* Can kuma wajen ango da amarya an sha shagali sosai ko dinner sai biyun dare aka tashi, washe gari kuma aka buɗe asibitin Ango Asmad mai suna *A&A* special hospital asibitin da ya samu kwararrun likitoci. Sai muyi fatan alheri ga wannan gudunmawa ga al'umma wanda Asmad da Alhaji Abubakar suka samar. Amarya Aneesa buri ya cika fata ga Asmad matsayin miji da mata, sosai Asmad ɗin ya ke k'ok'arin sauke duk wani nauyi na Aneesa da ke kansa, duk wani tana jin farin ciki ya na bata, shi yasa cikin kwanaki kaɗan ta murje ta yi kyau sosai. Meena ce ta haura saman Ameesha, ta kalli ta a tsorace cikin mamaki ta ce "Meesha anya kina da lafiya kuwa?" "Me ki ka gani? "Meesha ki kalli yadda ki ka koma, baki magana baki cin abinci, baki da walwala ko yau she kina cikin daki ki zauna ki yi shiru, why why Meesha?" Hawayen da take makalewa suka zubo, bata damu da share su ba ta kalli Meena ta re da sakin wani murmushi mai kama da kuka ta ce " Meena ta ya zan samu farin ciki? Bayan farin cikin nawa baya tare da ni, ta ya zan yi walwala? bayan abokin walwalar tawa ba ta ni ya ke ba." "Ba zan ɓoye maki ba Meena, wallahi ina cikin wani hali mawuyaci, Meena ke ce kaɗai zan iya faɗawa damuwa ta." Meena shiru ta yi zuciyar ta cike da tausayin kawarta ta cikin sanyin murya ta ce " Meesha faɗa min insha Allah zan yi kokarin sama maki mafita." Murmushin takaici ta yi ta ce " Kar kiyi mamaki inda na ce maki Allah ya jarabceni da son Dr Asm..." _*Yar Mutan Rano*_ [10/8, 8:06 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* *(NWA)* *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah* _*AYSHA WAZIRI kina raina har na rasa bakin da zan ya beki, amma duk da haka Allah ya tsare ki a duk inda kike ya kare ki da sharrin mahassada and kuma ba zan manta da ke ba i heart you*_ *Fans Ina jin korafin ku, amma Please kuyi hakuri wallahi harkoki ne suka yi min yawa amma insha Allah zan yi kokari na rika yi maku post a kai akai, don farin cikin ku shi ne namu, in babu ku tofa muma babu mu, a dai ci gaba da hakuri, tare da bin Yar Mutan Rano sannu a hankali* jin jina ga surbajo novel👍 ``` My Besty taki salon ta daban ce, Yaseen ina mugun yinki```😍😍 *15* Mamaki karara ne a fuskar Meena, ido kawai ta zuba tana kallon ta, tsawon minti biyar sannan a hankali ta saki ajiyar zuciya ta ce "Meesha me ki ke nufi? Shi Najeeb kuma ya za ki yi da shi?" "Shi ma ina son sa, Meena ba zan ɓoye maki ba ina son Dr ɗan fullo har cikin zuciyata,so fa ba na wasa ba, wallahi kar ki so kiga halin da na shiga da jin maganar auren sa." " Kar ki damu da auren sa, ki sa a ranki in mijinki ne zaki aure shi ko da yaushe ne, amma abin da yake bani mamaki yadda kika ce shi ma Najeeb kina son sa." " Eh ina son Najeeb saboda yana da halayya masu kyau, amma so ɗaya tak yana ga Dr Asmad." "To Allah ya zaɓa mafi alheri." "Amma Please Meesha ki yi kokarin danne son sa a zuciyar ki kar ki bari ya sani, ki ci gaba da dauriya har ya furta maki da kansa yana son ki." Murmushin takaici ta yi ta ce "Haba Meena kema kin san halina, ba zan taɓa bari ya sani ba ko da kuwa son na sa zai zama ajali..." Saurin toshe mata baki Meena ta yi ta ce " Please bar maganar ajali insha Allah zaki auri Dr ke dai ki ci gaba da addu'a ni ma zan ta ya ki, ba ri na kawo maki abinci." "Ko kar ki kawo na koshi." Harara Meena ta jefa mata cikin wasa ta ce "Ai ko ya zama dole ki ci abinci, don baki zama da yunwa." Ta ida maganar tana sauka daga gadon, Meesha kam gyara kwanciya ta yi tare da lumshe ido. Gidan ango Asmad kuwa ana ta shan angonci, zaune ya ke a babban falon gidan daga shi sai singlet da gajeren wando, laptop din sa ya ke matsawa, zuciyar sa cike da tunanin Ameesha wacce ya kwana biyu bai ganta ba, inda so samu ne yau ya leka asibiti don babu mamaki ta na ciki a yanzu haka, sai dai ya san halin yar matsala wato Aneesa, tana iya hana shi fita. Lokacin da ya ke tunanin, tana tsaye a bakin koriɗo ta zuba masa ido, cikin wani irin shaukin so. Ita dai Allah ya jarabeta da son wannan bawan Allah, cikin kwalliya ta ke kai da gani kaga amarya, kai tsaye wajen sa ta nufa da zuwa bata jira komai ba tasa hannu tare da zare laptop din, ta wani narke fuska kamar za ta yi kuka ta ce " Haba Hamma aikin me kake ta yi ne har yanzu, ya ci fa a ce kana samun hutu" Kallon ta ya yi tare da ɗan sakin murmushi ya ce "Ban da abin ki ina hutu a wajen Dr? Ke dai kawai kin rasa abin korafi, yanzu ma tashi zan yi in shiga asibiti don duba petient ɗina." Saurin ɓata rai ta yi ta ce "Haba dai tun yanzu zaka soma fita, ina laifin ka yi one week a gida?" "Ba zai yiwu ba ne Anee da na yi hakan, yanzu dai tashi muje ki haɗa min ruwan wanka,in yi shaf shaf." Ba don ranta ya so ba ta mik'e, shi kuma ya saki murmushi kawai ya kashe laptop din.cikin sauri sauri ya kammala da shiryawa, sam Aneesa ta ki saki rai ita a dole kar ya fita. A haka ta rako shi wajen motarsa " Please Hamma kar ka daɗe." " Ba zan daɗe ba My Anee." Ya faɗa cikin tabbatar da abin da ke ransa. " Allah ya tsare hanya ya dawo da kai lafiya." Ta faɗa tana rufe masa kofar motar "Allah ya sa" shi ma ya faɗa yana ba motar wuta. ********************************** "Najeeb! Alhaji Taheer ya kira sunan sa cikin murya ta nutsuwa. Najeeb da ke zaune gaban Abban Ameesha ya amsa cikin ladabi. "Kasan abin da yasa na kira ka?" Alhaji Taheer ya tambaya. Girgiza kai ya yi ta re da faɗin "a'a Abba." " Yawwa to akan maganar ka da Auta ne, shin da gaske ka ke sonta ko kuwa?" Dukar da kai ya yi , cikin sanyin murya ya ce " Eh Abba." Murmushi ya saki ya ce "Allah ya yi maka albarka, na gode sosai, insha Allah zamu zauna da Mahaifin ka domin tattauna maganar, saboda bani son aja maganar." "To Abba na gode." Najeeb ya faɗa. "Dama shi ne dalilin kiran tashi ka ta fi." ********* ******** ******* ****** Ko da Asmad ya fita kai tsaye gidan su Nenne ya nufa, don ya kwashi gaisuwa a babban falo ya same su, sallama ya yi su, su ka amsa masa cikin kulawa. ("Nenne a nyalli jam? Bobbo a nyalli jam?) "Nenne ina yini? Bobbo an yini lafiya? " ("Jam kolon Asmad noi Aneesa?")" Lafiya lau Asmad ya Aneesa? " ("O jamo kolon,owi mi hofnna mon.") " Tana lafiya, har ta ce a gaida ku. " (" Min notii Allah wadbarka.") " Muna amsawa Allah ya yi Albarka. " ("Ameen Asmad noti.") " Amin." Asmad ya amsa (" Wala damuwa fere Kam?) "Babu dai wata matsalar ko? " (" Wala ko d'ume Bobbo,minastan noo asibiti on miwi hami yalta mihofna on") " Babu komai Bobbo, dama zan shiga asbiti ne na ce bari na biyo don na gaida ku. " ("To usoko Allah barkid'in ummu dillu de jam kam da alari kanko fere mako a accimo ha sare useni jogumo amana ta awada ko a wasmititta Yesu.") " To masha Allah tunda lafiya, ka tashi ka tafi kaga dai ita d'aya ka bari a gida, abin da dai nake kara jaddada maka shi ne ka rike amanar Yarinyar nan, kar ka yadda wani abu ya shiga tsakanin ku na sabani, har ya sa ka aikata dana sani. " ("Insha Allah mi mi hakkilan Bobbo.") " Insha Allah Bobbo zan kiyaye. " ("To Allah wallu") " To Allah ya taimaka. " (O lari agogo jungo mako dendenta o ummii.) Agogon hannun sa ya kalla tare da mikewa. (" Nenne minkam mi salan.")" Nenne nikam na ta fi. " ("Allah hoinu lawol a yaltan naa to ad'on qarya?") " Allah ya tsare hanya, zaka biyo ne in ka dawo? " ("Kai gonga miyaltata Nenne mi salan sare on.") " Kai gaskiya Nenne da kamar wuya, don ina tunanin gida zan wu ce. " "(To Allah karu.") " To Allah ya tsare. " ("Nonnon Asmad wurti sare man odon der seyo.") Da haka Asmad ya fita a gidan cikin farin ciki da annashuwa. Yana parking motarsa a parking space, ya fito nurse na Asibitin sai masa barka da zuwa suke tare da ta ya shi murnar aure, fuska a sake ya ke amsa masu har ya isa kusa da ofishin sa. Yasa hannu zai buɗe kofar kenan ya hango ta, zuba mata ido ya yi cikin wani irin yanayi, sai ya ga ta rame ta ɗan kara tsawo, da yaga suna shirin haɗa ido sai ya yi saurin fuskewa Wani irin daɗi ya ziyarci zuciyar Ameesha, ganin Dr yau a asibiti, ji ta yi duk wata damuwar ta ta ragu. Amma a zahiri sai ta kuma haɗa rai kamar zata ce wayyo Allah. " Da gani ansan ango ka ke musamman yadda goshi ke kyalli." Tayi maganar cikin zuciyarta, tare da saurin maida kwallar ta don kar ya gane . "Barka da zuwa Dr." Ameesha ta yi maganar a hankali, cikin nutsuwa. Dan juyo da kai ya yi ya kalleta ya ce " Yawwa ." Bata ce komai ba sai ci gaba da tafiyar ta ta yi, har ta ɗan gota shi ya ce " Ke ina son magana da ke?" Juyowa ta yi tare da murguɗa baki ta ce " Ba sunana ke ba Maryam Taheer sunana." "Nice name." ya faɗa a zuciyar sa, amma a fili sai ya ce "Oh! Ai ban ma san sunan ki ba, to Maryam ina neman ki." Ya ida maganar ya na shiga ofis ɗin, ita ma Ameesha binsa ta yi, kujera ya nuna mata ya ce "Zauna." Ba musu ta zauna tare da duk'ar da kai k'asa. Shi kuwa wasu file ya dauka yana dubawa, tsawon minti biyar babu wanda ya yi magana, ita Ameesha ci gaba da wasa da zoben hannun ta ta yi. "Wai Maryam baki da labarin na yi aure ne? Asmad ya yi maganar ya na ci gaba da abin da yake yi. Wani mummunan faduwar gaba ya ziyarci Ameesha, da jin maganar sa duk da ta sani amma sai ta ji na yanzu ya fi ranar da ta soma jin maganar ta da hankali. Amma sai ta yi saurin da kewa ta ce "To kuma me hadina da auran ka?" Ta yi maganar tana hararan sa. "Oh! Ashe fa ba ruwan ki da aurena? Amma ai yana da kyau ko murna ki ta ya ni." Wani kallo ta watsa masa wanda ya kasa fahimtar ma'anar sa. Yau dai yana son ya ga shin Ameesha ta na sonsa, in tana sonsa zai tabbatar ,don haka sai ya tashi daga kujerarsa ya matsa inda ta ke, hannun ta ya rik'o ya ce "Maryam me yasa ki ke min rashin kunya baki ganin girma na, kullum kallon tsana ki ke min?" Juyar da kai ta yi murya na rawa ta ce "Please Dr ka sakar min hannu, sauri na keyi fa Ummi na jirana." "Zan barki amma sai kin bani amsar tambayar da na yi maki." "Babu komai." Ameesha ta ba shi amsa, dai dai da zubowar hawayen da ta e ɓoyewa, hankalinsa ya tashi da ganin hawayen Ameesha, don haka cikin sauri ya ce " Iya sani na na taɓa marin ki a Sahad store, kuma shi ɗin ma wallahi ke ki ka jawo, domin kuwa in da ban mareki ba, to fa babu shakka ni zaki mara, amma ki yi hakuri ga fuska ta ki rama marin." Maimakon hawayen su tsagaita sai k'ara tsiyaya suke, a kan fuskar ta tama kasa furta komai, don abin da ta ke son ji daga gare shi bai furta mata ba, duk da tasan da kamar wuya ta samu wannan tsadadden kalmar daga gare shi. Asmad kuwa zuba mata ido ya yi yana kallon ikon Allah, zuwa can yasa hannu cikin aljihu ya cire hankacif na shi ta re da mika mata. "Sorry Maryam ki bar kuka, ga shi ki share hawayen ki." Ya kai karshen maganar yana mik'a mata. Amsa tayi tare da goge hawayen da hankerchief ɗin da ya mika mata, sai ya kuma jan hannunta kamar dai wata karamar yarinya, zuwa kan doguwar kujerar da ke office din, ya zaunar da ita sannan shi ma ya zama . Sanyaya murya ya yi ya ce... _*Yar Mutan Rano*_ [10/8, 8:06 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah* *Alhamdulillah Ina godiya da Allah ya kawo mu wannan lokaci, ina son in dakata da typing wannan littafin har sai Allah ya kaimu bayan sallah lafiya, ina wa ɗauka cin musulmai murnar zuwan wannan wata mai alfarma Allah ya sada mu da Alhairin da ke ciki Ubangiji ka bamu rabauta da falalar da ke wannan wata na Ramadan* _*Har lau dai korafi baya karewa? To duk kuyi hakuri Yar Mutan Rano tana kara ce wa kuyi hakuri ku kara akan na da, insha Allah bayan sallah ba za ku yi korafin rashin typing ba*_ i heart you irin totallyn ɗin nan😍😍 *16* Nannauyan ajiyar zuciya ya sauke, tare da zubawa Ameesha ido cikin wani irin yanayin da shi kaɗai ke gane wa, cikin taushin murya ya ce "Magana ta tasa ki kuka?" Girgiza kai ta yi , ba tare da ta ce komai ba. "No Maryam in muna magana ki rika buɗe baki Please." "Ni fa Dr ba maganar ka ta sani kuka ba." A shagwaɓe ta karasa maganar. Ji ya yi ta bala'in burgeshi,yana ɗaya daga cikin abin da yasa yake sonta kenan. "To me ya saki kuka in ba maganar ba, na ce baki min Allah ya sanya Alhairin Aure na ba, sai na ga kin fara kuka ko?" Harara ta watsa masa ta ce "Ni fa kaina ke ciwo shi ne kawai." "Hmm Maryam kenan kina da saurin daukar zafi, nifa banga abin tada hankali ba cikin abin nan, in ki ka bi a hankali to komai zai ta fi yadda ki ke mafarkin samu." Ya yi maganar ta re da kashe mata ido ɗaya. Saurin ɗago da kai ta yi tana kallon sa, tare da mamakin maganar da ya faɗa "kenan ya san tana sonsa?" Ta yi saurin kawar da tunanin don ta san ba haka ya ke nufi ba. Mik'ewa ta yi tare da ɗaukar jakarta, ta kuma kallon kyakkyawar fuskasa ta ce "Dr ni kam zan wu ce don yamma na yi." Wani tsadadden murmushi ya bata, wanda ya kara wa fuskarsa kyau ya ce "To Princess sai yaushe kenan?" "Gobe school zan shiga zuwa sai jibi." "Ok Allah ya kaimu, mu je na saukeki ko kin zo da mota ne?" Wani irin daɗi ya ziyarci zuciyar ta , amma sai ta fuske ta ce "A'a Dr ka barni kawai na hau nafef." Ta ida maganar tana tafiya. "Maryam." Ya kira sunan ta da wani irin murya. Cak Meesha ta tsaya ba tare da ta juyo ba, don yadda ya ambaci sunan sai ta ji kamar duniya babu wanda ya iya fadar sunan kamar shi. "Mu je na ce maki ko?" Ya yi maganar yana daukan key. "Dr ai baka duba petient na ka ba?" "Dama ba su nazo gani ba, da abin da ya kawo ni, kuma na gani hankalina ya kwanta." Yana bata amsa ne yana rufe kofar, a tare suke jerawa sun yi mugun da ce wa da juna, don duk wanda ya gansu sai ya yi tunanin miji da mata ne a haka har zuwa inda motarsa ya ke , buɗe mata kofa ya yi ta shiga sannan shima ya zaga. Yana shiga wayar sa ta soma ringing, da sauri ya dauko don ganin me kiran ɗan murmushi ya saki tare da karawa a kunne "Hello My Anee ya aka yi?" Ameesha na jin haka tasan tabbas da matarsa ya ke waya, nan take sai ta ji hankalin ta ya tashi. Maganar shi ta kuma tsinkaya ya na faɗin "Haba Anee gani nan a hanyar dawowa, bani minti talatin." Ya faɗa tare da kashe wayar. Juyo da fuska ya yi yana kallon Ameesha ya ce "Kinji matata tana kirana wai na daɗe?" Karamin tsaki ta ja ,ba ta ce masa komai ba, don gaba daya haushin shi da kishin sa suka rufe ta. Shi ma shiru ya mata ya ci gaba da tukin sa, Ameesha tana nuna masa hanya har suka isa unguwar, a dai dai get din gidan ya faka, kallon sa ta yi ta ce "Na gode Dr sai da safe." Harara ya mata ya ce "Kuma shi kenan iya sallamar da za mu yi?" Dan ware ido ta yi cikin mamaki ta ce "Dr wani irin sallama za mu yi wacce ta fi wannan?" Har yanzu fuskarta ɗauke da mamaki. Dan sosa keya ya yi ya ce " To ai naga har kin fita ne, ko fa Number din ki bani da?" "Hmmmm! ta furta da da dai wannan yanayin mamaki ta ce "bani wayar ka nasa ma kafin Abba ya zo ya same ni." Mik'a mata ya yi ta amsa cikin sauri sauri ta sanya masa, sannan ta nufi get din Asmad na kallonta har ta shige cikin gidan sannan ya saki ajiyar zuciya a fili ya furta "Allah ka mallaka min Maryam matsayin mata amin." Ya kai karshen maganar yana ta yar da motarsa. ******** ********** ******* Ko da Ameesha ta shiga gidansu da ɗoki ta k'arasa falon, ganin motar Yaya Jaheed ta san shi ɗin ne ya zo, sallama ta doka tare da shiga, wani murmushi ta saki ganin sa zaune a falon da matarsa. Ai da sauri ta isa inda suke tana faɗin "barka da zuwa Yaya" murmushi ya saki cikin jin daɗi ya amsa mata maganar ta. "A'a Ameesha autar Ummi sai yanzu aka shigo?" Matar Ya Jaheed ne ta yi maganar. Matsawa kusa da ita ta yi ta ce "Aunty ina yini?" "Lafiya ya makarantar?" "Alhamdulillah." Ameesha ta bata amsa tana nufa hanyar stair. Har ta soma taka matakalar ta tuna bata wa Ummi sannu da gida ba don haka sai ta sauka, bedroom din Ummi ta shiga bakin ta ɗauke da sallama. Hajiya Halima da ke buɗe k'ofar toilet ta amsa mata cike da kulawa. "Auta kin dawo?" "Eh na dawo Ummi." "To sannu da dawowa,je kiyi wanka abinci yana jiran ki." "Ummi nifa a koshe na ke, wanka kawai zan yi." "Ke abin da na ce kenan je ki yi, naga yanzu kwata kwata baki k'aunar cin abinci ko?" Ummi ta k'arasa maganar tana hararan Ameesha. Shagwaɓe fuska ta yi ta ce "Allah Ummi ina ci fa, kawai yau na koshi ne." "To je ki yi wankan." "Yawwa Ummina." Ameesha ta faɗa tana fita daga bedroom din. Bayan ta yi wanka ne ta koma falo inda su Ya Jaheed da matarsa suke, tana zama Meena ta shigo hira suka ci gaba da yi. ******* "Alhaji wato kasan abin da yasa na nemeka a wannan rana?" Alhaji Taheer ya yi maganar yana aje cup din da ya sha ruwa. "Sai ka faɗa Alhaji." Alhaji Mansur ya yi maganar cikin ɗan murmushi irin na ya ke. "Dama kan maganar Najeeb ne da Ameesha, na ga soyayyar ta su kullum kara gaba ta ke , shi ne na ce gara asan matsaya." Wani mummunan faduwar gaba ya ziyarci Alhaji Mansur ya ce "Na shiga uku ni Mansur, kenan burina ba zai cika ba? To wallahi ba zai yiwu ba dole sai na cika abin da na yi niyya, Taheer ba ka isa ba ba zai yiwu." Amma a fili sai ya kakalo ya ke ya ce "Yo Alhaji ban da abin ka ai kana iya zartar da hukuncin auren su gaba ɗaya, babu abin da zance sai fatan alheri." Sosai Alhaji Taheer ya yi farin ciki da jin furucin Alhaji Mansur ɗin, don haka sai ya ce "To zamu zauna nan da kwana kaɗan don asa rana." "Allah ya kaimu." Da wannan hirar suka ci gaba da hirar duniya, sun daɗe sosai ka ɗin su ka yi sallama ko wa ya kama hanyar gidan sa. Lokacin da Meesha da Najeeb suka samu wannan labarin ba karamin daɗi su ka ji ba, babu kamar Meesha da ta ke murna zata huta da tunanin Dr ɗan fullo, tunda zata auri wanda ta ke so. ******* "Um um Abba yau fa kai zaka kaini school." Meesha ta yi maganar tana zama kusa da Alhaji Taheer ɗin. Murmushi ya saki tare da shafa kanta ya ce "Duk yadda ki ka ce haka za'a yi uwata, dama muna da meeting da su Alhaji Mansur, in na sauke ki sai na wu ce." "Yawwa Abbana! Shi yasa na ke kara sonka." Ta kai karshen maganar tana kiss ɗinsa a kumatu. Murmushi ya yi cike da farin cikin yadda Ameesha ta yi. Ummi da ke gefe ta ce "Alhaji kenan kullum dai kai ke kara shagwaɓa yarinyar nan." " Haba Hajiya dole na shagwaɓa yarinyar nan, ita fa kaɗai gareni gata da sunan Mamana." "To Allah ya k'ara taimakawa." Tana faɗan maganar dai dai da zuwan Ameesha "Ummi sai mun dawo." "Allah ya dawo da ku lafiya." Rike da hannun Abba su ka fita inda motar ta ke, har ta buɗe sai kuma ta rufe ta soma tafiya "Auta ina zaki kuma?" "Abba zan yi sallama da Ummi ne." Ta bashi amsa tana tafiya, kafin Alhaji Taheer ya yi yunkurin yin magana har ta yi nisa. Ita kanta ta rasa me yasa ta ji tana son k'ara ganin ummin, shi yasa kawai ta fasa shiga har sai ta gano Ummi ɗin. Ummi da ke zaune ta yi mamakin ganin Ameesha ta dawo "A'a ya kika dawo kuma?" "Ummi ganin ki na dawo yi." Ta bata amsa tana zama, kallo ɗaya zaka mata kasan jikin ta ya yi sanyi. "Anya kuwa Auta lafiyar ki?" "Lafiya lau na ke Ummi." Ta bata amsa tana kwanciya a jikin Ummin. "To kuma na ga kin dawo?" "Eh zan tafi ban son rabuwa da ke ne fa?" "To fasa zuwa kawai." "A'a Ummi zan tafi." Ta faɗa tana mik'ewa. Tana tafiya tana ɗagawa Ummi hannu har ta fita, a motar ta samu Abba yana waya, shiga ta yi ta zauna. Sai da ya kammala da wayar sannan ya juyo inda Ameesha ta ke "Uwata sai yanzu ki ka fito?" "Abba ina fa wajen Ummi ne." Kamar zata yi kuka ta ida maganar. Bai ce komai ba ya ja motar. Suka tafi a kofar makarantar ya ajeta shi kuma ya wuce. ******** Zaune da wayarsa a hannu,sai juya wayar ya ke Number din ta ya ke son kira sai dai kuma yana tunanin abin da zai ce mata, da kyar ya yi shahada ya danna kira. Ameesha da ke tafiya har ta kusa shiga class ta ji wayarta na ringing, cirowa ta yi daga cikin jakarta ta duba Number din, sai taga bata sani ba har zata maida jaka sai dai ta ɗauka. Wani irin faduwar gaba ya ziyarce su lokaci ɗaya, Ameesha shiru ta yi bayan ta yi sallama, shi ma a nashi ɓangaren haka ya yi bayan amsa mata sallamar. Kusan minti biyar sannan ta yi k'arfin halin ce wa " Hello wa ke magana?" Sai da ya dai dai ta nutsuwar sa kafin ya ce "Haba Princess nine fa?" Murmushi ta saki mai kyau, amma sai ta yi kamar bata gane shi ba ta ce "Ban gane ka ba ai..." Tun kan ta ida maganar har ya katse, ɗan dariya ta yi da ganin ya kashe wayar. Shi kam tsaki ya ja da maganar da Meesha ta faɗa masa "wai wa ye?" Wannan abu ya bashi haushi. Ita kam ko a jikinta class ta shiga, bar fito lacca ba sai karfe uku, yau Meena bata shigo ba haka kuma kawarta Ni'eema bata zo ba. Don haka sai kawai ta kama hanyar fita don ta hau nafef, a hankali cikin nutsuwa take tafiya har ta fita wajen makarantar ta hau titi da niyyar tsallakawa sai ji ka ke kiii. Mota ta banke ta sai da ta daga ta sama sannan ta faɗi k'asa. Kafin mutane su yi yunkurin ceto ranta har mai motar ya gudu, da sauri mutanen suka ɗauke ta zuwa asibiti don wajen basu da nisa da police station, da taimakon yan sandan aka amshe ta a asibitin Malam Aminu Accident and emergency room aka nufa da ita don ceto ranta, Allah yasa cikin wanda su ka kaita asibitin akwai wanda ya ɗauki wayarta, duba contact ɗinta ya yi yaga Number din Abbanta da sauri ya kira, lokacin Abba suna zaune da Alhaji Mansur sai hira su ke yi , ya ji karan wayarsa yana dubawa ya ga Number ɗin Ameesha murmushi ya yi ya kara a kunne yana faɗin "Auta sai yanzu kuka fit...? Bai gama rufe baki ba sai jin, mai kiran ya ce "kaine Abbanta ko to tana asibiti ta samu haɗarin mota, tana asibitin Malam Aminu Kano." A kiɗime Alhaji Taheer ya mika hankalinsa ya yi mugun tashi, su Alhaji Mansur har suna haɗa baki wajen tambayar me ya faru? "Ameesha ce wai mota ta bige ta tana asibitin Malam Aminu Kano." Yana basu amsar ne yana tafiya. Ko da Abba ya isa asibitin kasa nutsuwa ya yi, da ba'a barsu ganin ta ba, sosai ya yi wa wanda suka kai Ameesha asibitin sannan ya kira Ummi yana sanar mata, kuka ta fara ta na cewa "Allah sarki Auta dama shi yasa ɗazun ta kasa tafiya? Wayyo Allah ka tashi kafadar Auta." Kan ka ce me har asibitin ya cika da mutane, sai dai duk wani taimako da ake wa Ameesha bata farka ba, kusan awa uku kenan manyan likitoci suka duk'ufa akan ta, kowa aiki yake abin mamaki babu wani ciwo da yake jikinta sai wani kusa da kanta, amma yadda numfashin ya ɗauke shi ne abin tsoro. Asmad na zaune sai hira suke shi da Aneesa cikin farin ciki, sai jin wayarsa ya yi yana ringing, Dan tsaki yaja tare da kara wayar a kunne. Jin abin da ake faɗa masa a wayarta sa shi saurin mik'ewa "Please Aneesa bari na je asibiti akwai babban matsala." Bai ko tsaya jiran me zata ce ba kawai ya yi gaba. Cikin sauri ya auri motarsa, ko parking me kyau bai tsaya yi ba ya tunkari emergency room din. Haka kawai ya ji hankalinsa ya tashi, da taimakon addu'a ya isa gaban gadon "inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un". Shi ne abin da Asmad ya faɗa ya yin da ya yi arba da Ameesha. "Princess me ya faru da ke? Dazun fa mu ka yi waya da ke?" A rude ya ke maganar jikinsa har rawa ya ke. Da sauri cikin kwarewa ya soma bata nashi taimakon, duk sauran likitocin gefe suka koma suna kallon sa, ya dai ki manin awa ɗaya kafin ya samu numfashin ya dawo dai dai, wani dogon ajiyar zuciya ya ja tare da hamdala ga Allah. Suma sauran likitocin sun yi farin ciki sosai,kuma sun yaba da aikin Asmad ɗin. Da kansa ya gungura ta zuwa ɗakin hutu. Su Abba ma har hankalinsu ya ɗan kwanta da jin an samu numfashin ya dawo. Sai da ta yi awa uku tana bacci kafin ta farka, lokacin ɗakin daga Ummi sai Meena da Abba. Meena ce ta kulla da Ameesha ta farka "Ummi kalli bestyna ta farka." Meena ta yi maganar cike da jin dadi, tare da nufa waje ɗin kiran Dr domin ya ce in ta farka a yi saurin sanar masa, murmushin farin ciki ne ya mamaye su Abba, har suna rufe rigen matsawa inda ta ke "sannu Auta ya jikin?" Da wani Irin kallo Ameesha ta bisu ina rashin sani, sun yi mamakin irin kallon sannan kuma bata yi magana da Kowa ba. Dai dai da zuwan Dr ɗan fullo. Kallon Ameesha ya yi ya ce "Princess kin tashi ina ke maki ciwo?" Abin mamaki sai suka ji ta ce "Princess kin tashi ina ke maki ciwo?" Dan Zaria ido ya yi tare da murmushi ya ce "Haba Princess kuma da tsokana ki ka tashi?" Itama ma ta ce "Haba Princess da tsokana ki ka tashi?" Mamaki ya kama su da yadda Ameesha ta ke, don zuwa yanzu sun fahimci Ameesha fa ba wasa ta ke ba. "To me hakan ke nufi?" Dr Asmad ya wa kansa tambayar da babu amsa. _*Yar Mutan Rano*_ [10/8, 8:06 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad my Besty* _*Ina taya dukkan Musulmai murnar sallah, Allah ya amsa ibadunmu Ubangiji ya sa muna cikin yantattu da wadinda aka yiwa gafara Allahumma amin*_ _ina cigiyar Baseera Sabo Nadabo! Please baiwar Allah ina kika shiga haka?_ *My Besty ke kam dama ta dabance, a lokuta da dama har rasa kalmar da zanyi amfani da ita yayin nuna maki zallar farin ciki da kulawar da kike min nake yi, amma duk da haka ina maki fatan alheri, Allah ya baki miji na gari Ubangiji ya nuna min auran ki muzo mu kwashi shokiiii* ``` Happy sallah Uncle HASSAN ATK & Uncle HUSSAIN ATK``` inji Sweet *SAFWAN* fatan kunyi sallah lafiya Allah ya maimaita mana na baɗinbaɗaɗa *17* Zuru Ameesha ta yi tana kallon sa. Shima Asmad ɗin zuba mata ido ya yi cikin wani irin yanayi. A hankali ya girgiza kai, a zuciyar sa yace " *Lossing memory?* " Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un. Ashe maganar a bayyane ya yi ta sai jin muryar Meena ya yi ta ce "What Dr Meesha tayi lossing memory? Hasbinallahu wani'imal walkil, Inna lillahi! Haɗa rai ya yi yace " Please Meena kiyi shiru domin ban tabbatar ba." Faɗin haka ke da wuya, sai ya nufi kofa da niyyar fita, zuciyar sa cike da tausayin halin da ta tsinci kanta a cikin. Bai ko kalli su Abba ba, ya ce " Alhaji bari na ɗauko wani abu a office." Ita ma Ameesha maimaitawa ta yi, tana mik'ewa tsaye da sauri ta isa inda Asmad yake tayi saurin rik'o hannunsa ta kankame, sai kuma ta bata fuska. "Cike da mamaki, haɗe da mutuwar jiki, Alhaji ya bi Ameesha da kallo, saboda yadda yaga ta kamkame hannayen likitan. Wannan bakon al'amari ne a rayuwar." A hankali Dr ɗan fullo ya zame hannayen sa daga rikon da ta yi masa, ya zaunar da ita bisa gadon ya kalleta zuciyar sa a karye kamar zai zubar mata da hawaye "Zauna ina zuwa kin ji ko? Ya faɗa a hankali cikin dakin fuka. Ita dai kallon da ta yi wannan karon bata yi magana ba. Wani murmushi ya saki, aiko sai ita dinma ta yi murmushin, kallon su Abba ya yi ya kuma maida kallon sa kanta, in har ya fahimta dai dai to Ameesha yunwa take ji, don haka sai ya ce "Meena taimaka mana da tea please! Dr Asmad ya faɗa. To kawai Meena ta amsa sannan ta soma haɗawa, cikin kankanin lokaci ta mika masa, shi kuma ya mikawa Meesha, ita dai Ameesha zubawa cup din ido tayi tana kallo don bata san ya zata yi da shi ba. Kamo hannunta ya yi yasa mata cup din ya ce "Princess sha tea kina jin yunwa ko? Cup din ta rike sannan ta maimaita abin da ya faɗa ɗin. Ita bata sha ba kuma bata aje ba. Wani tunanin ya yi sai ya ce "Meena haɗa wani tea din ki zauna kusa da ita, sannan ki fara sha." Yadda ya ce kuwa haka ta yi tana sanya cup din sai itama Ameesha ta kai baki, ta kurba sai ta aje shi a baki ta kasa haɗiyewa, don bata masan haɗiyewar ake yi ba. "Meena ki kuma kurba sai ki hadiye ta gani." Dr ɗan fullo ya yi maganar. Cikin ikon Allah kuwa sai Ameesha ta yi yadda Meena ta yi har saida ta shanye tas ta saki gyatsa. Sai ga zufa ya soma keto mata. Murmushi ya yi irin mai nuna farin ciki. Ji yowa ya yi ga su Ummi wanda suka yi jugum, suna kallon ikon Allah. "Alhaji ku sameni a office yanzu." "To" suka amsa, shi kuma ya nufi fita, ai kuwa sai Meesha ta mike ita a dole binsa zata yi, ita fa a nata tunanin duk inda Dr ɗan fullo ya yi shi zata yi. "Jira ni yanzu zan dawo." Still dai ta maimaita yadda ya ce, ganin tana don bata lokacin sa ga Aneesa tana ta kiransa sai kawai ya yi tunanin yin mata allurar bacci. Wani dogon ajiyar zuciya ya sauke, tare da kuma duban Ameesha wacce ta zuba masa ido. Bai ɓata lokaci ba ya haɗa allura kawai ya yi mata, cikin zuciyar sa yana addu'ar Allah yasa ta farka lafiya ba tare da wannan lalura ba. "Lafiya kuwa Dr me hakan ke nufi?" Muryar Alhaji Taheer kenan. "No Abba kayi hak'uri ku dai sameni a office dina, nayi mata allurar ne don tana bukatar hutu." "Tom Allah ya bata lafiya! Amma Please Dr ka taimaka kar wani abu ya sameta wallahi ita ɗaya ke gareni." "Ku kwantar da hankalin ku insha Allah komai zai zo da sauki." Yana gama faɗin haka ya yi waje domin shi kansa yana da buk'atar ya samu nutsuwa har ya yi tunanin matsalar Ameesha. Yana fita Ummi ta matsa inda Abba yake, sam bata cikin nutsuwa don gaba daya ta canza sosai hankalinta ya tashi da ganin yadda Ameesha ta koma, musamman maimaita maganar da ta yi a ɗazun abin ya tsaya mata a rai. "Alhaji wallahi ina tsoron kar wani ciwon ya samu Ameesha, gani nake fa kamar hauka take yi fa! "Inna lillahi! Ya yi saurin faɗa a zuciyar sa, don shi ɗin ma ya yi tunanin haka, domin kuwa yaji Dr ɗazun ya ce lossing memory, kenan ta manta komai? Kai ina hakan ba zai faru ba. Amma a fili sai ya ce "karki damu kiyi addu'a Hajiya babu wani abu da zai faru face da sanin Allah, don haka kawai kiyi hakuri ki barwa Allah." "Na bar masa, amma gaskiya dai na firgita da wannan lamarin. Alhaji Mansur dake gefe yana sauraron su, in ka kalli fuskarsa sai ka yi tunanin zallar tausayin Ameesha ya ke, amma ina a cikin zuciyar sa sai cewa ya yi "Allah na gode maka da haka ta faru, na samu hanyar raba ta da ɗana kenan, kai kuma Taheer sai a yi ta fama da biyan kudin magani tunda yartaka ta haukace." Ya karasa maganar tare da sakin wani mugun murmushi. ******************** A office Abba ne da Ummi zaune suna sauraron bayanin Dr, gyara zama ya yi cikin nutsuwa ya soma yi masu bayani yadda ciwon Ameesha ya ke. *"Wato Alhaji gaskiya dai Ameesha ta samu matsala sakamakon bigewar mota, kuma dai gaskiya matsalar ta babba ce don ta samu ciwon nan da ake kira da mantau a turance kuma lossing memory amma asalin sunan ciwon (AMNESIA), shi wannan cuta ana samun ta ne musamman ga hatsarin mota, in kan mutum ya bugu cuta dai ta jikin k'wak'walwa.* *Sannan kuma ita wannan cuta kala biyu ce, 1- akwai wanda in mutum ya kamu da ita zai manta komai na baya sannan kuma ko magana ka gama faɗa masa ba zai taɓa rikewa ba, kai ko hotonsa ya gani ba zay iya shaida ko shi ne ajiki ba, ko ya sha ruwa ko abinci zai iya mantawa yaga kamar bai ci ba.* *2- shi na biyun yafi sauki, shi ne wanda zaka ga mutum ya manta komai na rayuwar sa na baya, amma kuma duk abin da aka faɗa masa ko aka koya masa zai fahimta har ya aiwatar, kamar dai yadda ita Ameesha ta keyi a halin yanzu.* Dr ɗan fullo ya dire maganar sa cikin jimami, musamman yadda Ummi ke tsiyayar da hawaye, shi kansa Alhaji karfin hali kawai yake, amma ko kadan bashi a nutsuwar sa, jin irin ciwon dake damun yar tasa ba karamin daga hankalin sa ya yi ba. "Babu komai Dr mun yadda da kaddara! Allah ya bata lafiya shi ne kawai addu'ar mu, amma Dr ita cutar bata da magani ne? In tana da kuma taya ake maganceta?" "Tana da magani sai dai gaskiya bamu da kayan aikin ta anan Nigeria, amma dai in har mai lalurar ya ga irin abin da ya haddasa masa shiga tashi musamman in ya firgita to yana iya dawowa dai dai, sai kuma a rika tunawa mutum irin abin da yake aikatawa a rayuwarsa ta baya shi ɗin ma zai taimaka wajen dawo da tunanin mai lalurar ." "Tom yanzu Dr ya kake ganin zamu yi?" Ummi ta yi tambayar hawaye na zuba. "Ki kwantar da hankalin ki Hajiya, kar da wannan ciwon yasa ki a damuwa insha Allah zata dawo dai dai, don zamu ci gaba da bincike tare da addu'a har Allah ya bata lafiya." "Allah ya bata lafiya." Iya abin da Alhaji Taheer ya iya fadi kenan ya mik'e. "Zan baku sallama gobe don allurar bacci nayi mata, sai cikin dare zata farka daga bacci, zuwa safe kuma sai ku tafi gida, domin dai bata da wani ciwo sai matsalar nan, sai ku tafi gida a ci gaba da addu'a da yawan ziyartar asibitin k'wak'walwa ko za'a da ce." Daga haka suka fita daga ofis ɗin. Shi ma Dr tattara kayan sa ya yi ya tafi gida domin dai Aneesa ta addabe shi da kira. Ko da suka koma dakin kowa zama ya yi, tare da buga uban tagumi suka yi jugum kowa da kallar tunanin sa. Ameesha kam bacci take sosai bata farka ba sai kusan huɗu da rabi na dare, har a lokacin suna zaune babu wanda ya rintsa, ita ɗaya suke jira su ga farkawar ta ko da ta bude ido bata kalli inda su Ummi suke ba, sai ma lumshe ido ta kuma yi. A wannan dare babu wanda ya rintsa, har gari ya waye, tunda sassafe Dr ɗan fullo ya diro Asibiti don ganin yadda Ameesha ta kwana, sanda ya shiga bata farka ba don haka sai ya koma ofis. Bata farka ba sai takwas, batawa kowa magana ba amma idonta a buɗe ya ke. ganin ta farka sai Abba da kansa ya je ya kira Dr. Tare suka shigo da Abban, ya yi wa Ummi sannu tun kan ya gama rufe baki har Ameesha ta diro daga gadon ta rungu... _*Yar Mutan Rano*_ [10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* _*Gaskiya dai bani da bakin da zan ce wani abu domin kuwa masoya wannan littafin kun gama min komai, ko da yaushe ina samun sakonnin ku masu text message da masu kirana ta waya, fatan alheri nake maku ina jin dadin addu'oin ku, masu korafi kuyi hakuri wannan Nobel fa yanzu aka fara matukar dai kuna bina a hankali zaku fahimci komai, AMEESHA ma tana godiya da addu'ar ku.*_ *18* Rike masa hannu ta yi gam, sai zarrare ido take kamar wacce taga wani abin tsora. Dr ɗan fullo kuwa kunya ce ta kamashi da sauri ya ja hannunta zuwa bakin gadon yana faɗin "Princess kin tashi? Barka da safiya! Shiru ta yi ta dai zuba masa ido tana kallon bakin sa, murmushi ya saki don ya fuskanci halin da take ciki. Mai da duban sa kan su Ummi ya yi ya ce "Hajiya Princess fa yunwa take ji, matukar kuka ga ta natsu bata maimaita magana abu biyu ne ko dai yunwa ko kuma bata jin dadi." "Insha Allah zamu kula, bari a bata shayi tunda babu abinci mai ɗan nauyi." Ummi ta yi maganar tana kokarin jawo flask. Sai ko ga sallamar yayyinta gaba daya, Ya Jaheed ne a gaba sauran suna binsa a baya. Kallo ɗaya ya yi masu ya shaida su ɗin yan'uwan tane musamman muguwar kamar da suke yi. Ita kuwa da kallo Ameesha ta bisu kamar idon zai fado, zuwa can kuma sai ta lumshe ido. "Autar Ummi sannu ya jikin?" Abdul ya yi tambayar yana matsawa kusa da gadon. Bata buɗe ido ba, amma ta maimaita abin da ya faɗa. Hawaye ne yake tsiyaya daga idanuwansu, suna matukar tausaya yar'uwar tasu wai Ameesha autar Ummi ce cikin wannan halin, lallai ikon Allah ya fi gaban wasa. Kuka sosai Abdul ya yi domin dai dama shi ne abokin kaftawarta to kuma yanzu ga yadda Ubangiji ya maidata. "Kunga bafa kuka za ku yi ba, ku yi mata addu'a ne." Ummi ta kai karshen maganar cikin kulawa ci gaba da fifitawa Ameesha shayi. Share hawayen su su ka yi sannan suka soma gaida iyayen nasu, Ya Jaheed ya mikawa Dr ɗan fullo hannu suka gaisa "Dr ya mai jiki?" "To jiki Alhamdulillah sai godiyar Allah." "Allah ya bata lafiya!" "Amin." Dr ya amsa yana mikawa Ummi takardar sallama domin Abba ya fita daga dakin ya ce zuciyarsa zata iya bugawa matukar dai yana kallon Ameesha a irin wannan yanayin, ko a jiya da kyar ya kawo safe don yadda zuciyarsa ke masa wani irin zafi. Ummi kam amsa ta yi tana masa godiya, lokacin shayi ya ɗan huce. "Auta amsa ki sha! Tayi maganar tana mika mata cup din amma fir taki amsa, juyin duniya amma ta ki, Abdul ne ya je ya kira Dr. Tare suka dawo da shi, yana zuwa ya amsa ya kai bakin sa sannan ya mika mata yana faɗin . "Amsa Princess ki sha kin ji?" Babu musu ta amsa tare da kaiwa baki kamar yadda Asmad ɗin ya ce. Kafin ta gama sha har sun gama kwashe kayan su daga ɗakin. Wajen tafiya gida ma da kyar aka lallaɓa ta, don tirjewa ta yi ita fa adole babu inda zata je sai tare da Asmad, to shi dinma yana alhinin rabuwa da ita, sai dai bai nuna ba don karda su yi tunanin wani abun. "Please Dr ko zaka taimaka mana ne ka kasance gida?" Muryar ya Jaheed kenan. "No babu damuwa, domin ni ma gida zan ta fi." Dr ya ba shi amsa. "Mun gode sosai Allah ya bar zumunci." Ya ida maganar yana nufa inda su Ummi su ke. "Ummi Dr ya ce zai kai ta gidan tunda kinga fa bata yadda da kowa sai shi." "Kar ka damu mudai mu yi fatan Allah ya bata lafiya." Ummi ta ida maganar tana kamo hannunta. Fisge hannun ta yi. Ganin haka sai Dr ya iso wajen ya kamo hannunta a hankali suka nufi inda motarsa ya ke. Suma su Ya Jaheed suka nufi mota, babu wani bata lokaci suka isa gida har falo ya kaita, lokacin Meena ta gama haɗa break ɗin da za'a kai Asibiti, tana ganin Ameesha ta yi saurin aje flask ɗin hannunta tana faɗin " A'a Meesha har kun dawo? Dr ina kwana" Murmushi ya yi itama Meesha ta yi murmushin ya ce " Kin san da yake bata da wani ciwo shi yasa." "To sannu Dr da k'ok'ari mun gode sosai." Dai dai da shigowar su Abba. Kallon agogon hannun sa ya yi ya ce " Ni kam bari na tafi gida, Ummi kusata ta yi wanka don ta ji daɗin jikinta. Amma sai dai a sami wanda zai koya mata" Da sauri Ameesha ta fadi yadda ya ce. Dan murmushi Ummi ta yi tana kara godiya ga Dr sannan taja hannunta zuwa bedroom ɗinta tana faɗin "Mu je kiyi wanka yana jiran ki a falo." Kamar ta san abin Ummi ta ke nufi sai ko ta ci gaba da tafiya. Yana ganin sun tafi ya yi sallama da su Ya Jaheed sannan ya nufi fita. Ko da ya shiga lokacin goma saura don haka gidansu ya nufa, domin dai yasan Aneesa bata tashi ba don haka gara kawai ya tafi can ɗin, dama jiya bai samu zuwa ba. ************************* Da sallama ya shiga falon Nenne da Bobbo ne suke zaune a falon suna hira, da alama yau Bobbo ba zai fita da wuri ba. (Ha leddi o rongini o hofni saro mako.) Har kasa ya tsuguna yana gaida iyayensa. (Der fertare be notani moo.) Cikin sakin fuska suka amsa masa. (" Nanne nyami mo noi Aneesa waldi.") "Ya Aneesa ta kwana?" Nenne ta yi tambayar. ("O jamo kolon. Kenya minani odon wi'a o waran hamon.") "Lafiya lau ta kwana, jiya na ji tana faɗin zata zo nan gidan." (Usoko! Allah waddu mo jam.") "Madallah! Allah ya kawo ta lafiya." ("Ameen" o noti Nenne welo minanta fa!) "Ameen ya amsa. " Ummi yunwa nake ji fa! ("To hami hauta ne nyamdu man gam minin maa jotta min hasiti.") "To bari na hada maka, muma da yake yanzu muka gama yin break ɗin. ("Haba Asmad noi a wurtata sare a hasiti? Bobbo wolwi der mettam beram.") "Haba Asmad ya zaka fito gida ba tare da ka tsaya ka yi break?" Bobbo ya yi maganar cikin ɗan faɗa faɗa. ("A'a Bobbo daga jamdi jego mi wurti sare gam mid'o mari nyoudo, mi yahi milari noi o waldi, den mi yalti en hofni dira wali didi mi warai.") "A'a Bobbo ai tun shida na fita don ina da wata mara lafiya, na je duba jikin ne shi ne na biyo nan mu gaisa tunda jiya ban leko ba." ("Towo jotta minanai hala, mi tamma daga sare a wani a darai a hasiti, Allah wasu barka.") "Aiho yanzu na ji magana, ai nayi tunanin daga gida kake shi ne baka tsaya ka karya ba, Allah ya yi albarka." ( Hokkilo don wali Asmad nyamata kasitari mako ha o timmini, o warti falo ha Nenne en wonii.) Cike da kwanciyar hankali Asmad ya ke yin break ɗinsa har saida ya kammala, falon ya dawo inda su Nenne suke (" Nenne mi hiran sare.") "Nennezan na k'arasa gida! ("Allah hore jam, hofnu Aneesa.") "To Allah ya kaika lafiya ka gaida Aneesa." ("O nanan insha Allah." Asmad jabi moo.) "Za ta ji insha Allah." Asmad ya bata amsa yana fita. Lokacin da ya je gida a falo ya iske Aneesa da sauri ta tashi tana faɗin "Hamma daga ina kake? "Daga Asibiti nake don akwai mara lafiyar da na je dubawa." Ya bata amsa yana zama a kujerar da ke kusa da ita. Gyada kai kawai ta yi, haka kawai ta ji sam bata so ya fita ɗin ba, domin ita har ga Allah tana tsoron ganin sa da yammata balle kuma ya ce zai kara aure, bata k'aunar ganin wannan lokacin. "Aneesa tashi ki haɗa min ruwan wanka, kin yi break?" Da kai ta amsa masa don dai jinta ya yi sanyi. "Ok mu je in yi wanka, kema ki yi ko kin fasa zuwa gidan su Nenne ɗin? "Lah! Hamma zan je, naga baka yi min maganar ba ne." "Ok to ai yanzu na yi maki sai ki shirya har na faɗawa Nenne zuwanki." Daɗi ya rufe Aneesa da jin zata je gidan Nenne, aiko cikin saura ta shirya, shi ma a lokacin Asmad ya gama shirin sa jerawa suka yi har mota. *Gidan Alhaji Mansur* "Kai Najeeb kana jina? Bai jira amsar da Najeeb ɗin zai bashi ba sai ya daura a maganarsa. "Kana jina ko! Kai aiwatar da abu daya da nake so, sai abu na biyu, ina tunanin baka manta da maganar babu aure tsakanin ka da wancen mahaukaciyar yariyar ba?" "Abba wacece mahaukaciya?" "Kai bana son shashanci Wancen yarinyar da bata da wani aiki sai SANGARTA. Uban wa ya sani ko haɗa baki suka yi da likitan har ya ce ta samu ciwon mantuwa, don nasan halin Taheer tsaf ba zai bari a ce Yar shi ta haukace ba nikam nasan hauka take yi sam bata aikin masu hankali." "Abba yanzu baka tausayin halin da Ameesha ta samu kanta? Wallahi duk wani mai imani in har yaga yadda Ameesha ta koma zai tausa..." Tun kun kafin ya gama rufe baki Alhaji Mansur ya sauke masa wasu mahaukatan mari har biyu, wanda suka yi mugun shigan Najeeb. _*Yar Mutan Rano*_ [10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* *Saboda yadda ki ke son wannan Nobel din yasa na baki kyautar wannan page din na yau, MARYAM BINTU hakika kin cancanci fiye da haka, amma ki yi haquri da wannan, fatana Allah albarkaci rayuwarki Ubangiji ya rabani da sharrin makiya, YAR MUTAN RANO tana k'aunar ki har cikin ranta.* ```Masu korafin in bude groups, don Allah ku yi hakuri ba sai na buɗe group daban ba, a kawai groups na yan'uwana da yawa, irin su UMMYN YUSRAH NOVEL, MARYAM MUKHTAR FAN GROUP, da dai sauransu duk ina post a ciki, ba sai na buɗe ba, ina godiya da shawarwari Allah ya barmu da k'aunar juna.``` *19* Sadda kai k'asa Najeeb ya yi, cikin zuciyarsa yana mai tsantsan jin takaici da halin mahaifinsa. Muryar Alhaji Mansur ya ji yana faɗin "tashi ka bani waje shashashan banza kawai, kuma dole ka yi yadda na ke so , ko kuma wallahi ranka ya yi mummunan ɓaci." Jiki a sanyaye ya mike bai nufi inda sashin sa yake ba, sai ya nufi wajen motarsa ya ɗauka, cikin nutsuwa ya tashi motar bai zame ko ina ba sai gidan Alhaji Taheer. Ya yi parking sannan ya k'arasa cikin gidan. A babban falo ya samu su Abba zaune suna hira da Ummi, gefe guda kuma Ameesha ce ke kwance akan three sitter. Cikin sakin fuska Abba ya amsa masa sallamar da ya yi. Tsugunawa ya yi har kasa ya ce "Ina kwana Abba ya mai jiki?" "Lafiya lau Najeeb mai jiki ta ji sauki, ya su Alhajin?" "Yana lafiya ya ce a gaida ku! "Muna amsawa." Kansa ya kuma saddawa da alama magana ya ke son yi. Abba ya fahimci haka "Kamar kana son yin magana ko?" Alhaji Taheer ya tambaya. "Eh! Abba. Ya bashi amsa "Ok ina jinka." Ya ida maganar yana maida hankalinsa shi. "Ehm uum! Dama kan maganar Ameesha ne, Abba don Allah karka fasa bani ita, wallahi zan iya aurenta a ko wane hali take." Murmushi Abba ya yi cikin jin daɗi da maganar Najeeb ɗin, don har cikin zuciyarsa yana tunanin yadda lamarin zai kasance, musamman daga halin da Ameesha ta samu kanta a ci, amma yanzu Alhamdulillah tunda ga Najeeb yana jaddada masa son da ya kewa Ameesha ɗin. "Haba karka damu da wannan insha Allah Ameesha taka ce, bata da wani miji da ya wuce kai." "Na gode Abba." Ya yi furucin cike da jin dadi. Kallon agogon hannunsa ya yi tare da mik'ewa, don tuni Ummi ta bar falon "Najeeb zan fita! In ka koma ka gaida su Hajiyar." Ya kai karshen maganar yana fita. Shi kuma matsawa kusa da ita ya yi ya ce "Meesha ya jikin?" Idonta biyu amma in ba ka duba da kyau ba sai ka ce bacci ta ke yi, ko da ya yi maganar tana jinsa amma da yake yan maimaita maganar basu kusa ko ɗago kai ta kalleshi bata yi ba, domin dai wannan muryar bata saba jin taba, ita kuma so take ta ji irin wanda ta saba ji. Haka ya gaji da magana ya tafi. Yana fita Meena ta shigo falon, ganin ta ita ɗaya a kwance sai ta matsa tana faɗin "Meesha ke ce kawai a falon?" Bata yi magana ba sai buɗe dara daran idonta da ta yi tana kallon Meena ɗin. Gyara zama Meena ta yi tare da sanya game a wayar Ameesha, kuma shi ne game din da Ameesha ta fi so akan ko wanne. Zuba wa wayar ido ta yi tana kallon yadda Meena ke buga game ɗin, har wani murmushi ta ke yi alamar abin ya mata daɗi, ganin haka sai itama Meena ta ji dadi. "In baki kema ki buga?" Bata fahimci me Meena ta ke nufi ba, don haka sai ta ci gaba da kallon wayar, mika mata wayar ta yi , amma sai ta bata rai, cikin sauri ta kamo hannun Meena ta daura akan wayar alamar dai ta ci gaba da bugawa . Da ta fahimci nufin ta sai kawai ta ci gaba da bugawar, haka suka kasance cikin farin ciki, domin dai a duniya Meena tana son farin cikin Meesha. ************************* Aneesa ce zaune a can kuryar gado, ta zabga uban tagumi kai da gani kasan cikin tunani take, can dai ta sauke tagumin tare da jawo wayarta dake dan nesa da ita. Number ta lalubo sannan ta danna kira ringing biyu aka daga wayar. "Hello k'awata gaskiya fa ina cikin wani mawuyacin hali." Ta yi maganar ciki rashin nutsuwa. Daga ɗaya bangaren ta amsa "Anee mai ya sameki?" "Ki bari kawai wallahi ina cikin matsala." "Ke nifa bani son wannan abin na, ki yi min magana sak bana don kwana kwana." Ajiyar zuciya Aneesa ta sauke ta ce "Kinga wai fa ciki ne da ni, kuma ke kinsan bana son haihuwa a irin wannan lokacin." Mtsss Rukky ta ja tsaki, ta ce "Amma wallahi Aneesa har kin bani haushi, yanzu don Allah saboda cikin ne ki ka tada hankalin ki?" "Dole in tada hankalina duka yaushe aka yi auren? Wata fa na uku kenan, shi ne har zan samu ciki?" Ta ci-gaba "Gaskiya dai ban shirya haihuwa ba, kuma bana kaunar cikin nan wallahi, yanzu ya ki ke ganin za'a yi?" "Gaskiya nima dai ban baki goyon bayan haihuwa yanzu ba, don mazan yanzu da kun haihu suke daina ya yin ki, musamman irin su Dr da yanzu suke ganiyar tashen su. Akwai hanya amma da fatar bai san da cikin ba?" "Eh! Gaskiya dai bana tunanin yasan da shi, domin da ya sani da kansa zai sanarmin don dai yana da son yara sosai." "Gud! Haka yana da kyau, kina ji kawai ki shirya ki je asibiti sai a zubar da shi, tunda bai wani girma ya... "Ke! Aneesa ta yi saurin katseta, ta ce "nifa nan babu inda na sani." "Dallah! Ke wallahi baki haɗu ba, ga asbitoci nan da yawa a gari, ki bari in ya fita kema ki fita abinki, kafin ya dawo kin gama komai, kuma ai nan layinku naga wani asbiti ki gwada zuwa, ke kam wani lokacin kamar wacce bata waye ba." "Tom shi kenan, zan gwada ɗin. Zaki ji kirana a kowane lokaci." "Yawwa ko ke fa! Amma ki yi kokari don matukar ya fahimci kina da ciki to fa sai kin haifa masa, musamman da shi fa a gidansu shi kadai ya taso, zai so ganin jinin sa." "Karki damu an gama." "Sosai Aneesa ta yi na'am da shawarar Rukky, don ita fa bata son ta rasa Dr Asmad ne, kar ta haihu ya je ya sake auro wata, ita kuma ya daina ya yinta, tana wa Dr wani irin so ne ba na wasa ba." *( Hmmmm Aneesa kenan, wannan sam ba shawarar arziki ba ce, Allah ya baki kyauta mafi daraja amma saboda wani banzar hujjar ki ki ce baki so? Ina ji ye maki zuwan ranar nadama)* Aiko cikin zuciyarta ta kudurci niyyar gobe yana fita, itama zata kama kanta. *ASBITIN MALAM AMINU KANO* Asmad ne zaune ya zuba wani uban tagumi, tunanin Ameesha kawai ya ke yi, shi bai taɓa tunanin sonta ya kama shi haka ba, sai da wannan ciwon ya kamata, ya ji daɗin kasancewar su a asbitin, yana son Ameesha so mai tsanani amma ya rasa hanyar da zai bi don ganin ya mallaketa. Masifar sonta yake don ko motsi ya yi sai ya tuna ta, musamman murmushinta, kallonta, dariyarta, uwa uba kuma *SANGARTA* da take yi, kai komai nata yana burgeshi. Wayarsa ya jawo ya soma buɗe pic din da ya mata lokacin da take asbiti, wasu tana bacci wasu kuma idonta biyu, wani kuma tana murmushi, yana kallon pic din yana murmushi tare da girgiza kai a fili ya furta *Princess kin haɗu iya haɗawa, Allah ya mallaka min ke matsayin matar aure* _Don Allah ku yi hakuri da wannan, wallahi shi din ma da kyar na tafa shi_ ``` I hearttttt you all my fans```😍😍 _*YAR MUTAN RANO*_ [10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* *I love you all SANGARTA FANS* 😍😍😍😍 Dedicated to *SHAMSHIYA SALIS* _*Na yi mamaki sosai a lokacin da na samu labarin harda SHAMSHIYA SALIS, cikin masu bibiyar wannan Nobel din. Gaisuwa ta musamman tare da fatar alheri a gareki* *20* Sosai ya maida hankali wajen kallon pic din Ameesha, sai ko dayar wayarsa ta soma ruri, sunan wanda yaga yana kiranne yasa shi ɗauka tare da karawa a kunne "Hello abokina ya garin?" "Lafiya lau! Aka bashi amsa daga ɗaya bangaren. "Kana ina ne?" Dr ya tambaya. "Gani zan shigo asbiti, shi ne na ce bari na kira ko ka fita?" Dan dariya Dr Asmad ya yi ya ce "Ina office ka shigo kawai." "To! Ya amsa ta re da kashe wayar. Minti biyar tsakani sai ko yaji norking ɗin kofar office din. "Yes shigo mana!" Babu bata lokaci ya shigo, a tare suka sakarwa juna murmushi, tare da gaisawa. "Kai wallahi na yi farin ciki da ganin ka Hafiz, domin dai ina da bukatar shawarar ka." Wanda aka kira da Hafiz zama ya yi tare da fuskantar Dr ɗan fullo, yana sauraron maganar da ya ke masa. A jiyar zuciya Dr ya sauke yana ci gaba da kallon pic din Ameesha. "Dr ka fara magana kuma ka yi shiru, wai me ya faru ne?" Murmushi ya yi ya ce "Haba Hafiz, babu fa wani abu na damuwa, shawara kawai nake nema a wajen ka." "Ok ina sauraron ka!" Gyara zama ya yi tare da maida hankali kan Hafiz din ya ce "Wato maganar dai ita ce, kasan wannan yarinyar dana taɓa baka labarin ta, wacce muka haɗu a shahad store har na mareta?" "Yes! Na gane ta, amma ban san yarinyar ba." Hafiz ya bashi amsa. "Ok mun kuma haɗuwa da ita, har ma na zama mata Malami ta fannin karatu, duk da dai a da ba wani shiri muke ba, amma a yan kwanakin can kafin ta samu ciwo mun fara dai dai tawa, tun ranar farko da na ganta nake jin sonta, har zuwa yau ina jin kishin in ganta da wani saurayin balle inga tana masa murmushi, kai a takaice dai ina mugun sonta so irin mai tsanani ɗin nan, wallahi sonta ya hanani sukuni, ko yaushe cikin tunanin ta nake, duk wannan abin bata masan ina yi ba, na yi dogon tunani ya kamata in sanar mata, sai dai an samu matsala, domin ranar da nake niyyar bayyana mata kudirina sai Allah ya gifto da wani iftila'i ." Dr ya yi shiru da maganar sa yana mai tsantsan tausayin Ameesha. "Ina jinka ." Hafiz ya faɗa. "Eh iftila'i domin dai ta samu ciwon mantau, ma'ana ta manta komai na rayuwar ta na baya, ina sonta tare da tausaya mata, ina burin ta zama matata, amma na rasa ta yadda zan yi wa su Nenne bayani." Jinjina kai Hafiz ya yi ya ce "duk ta su Nenne mai sauki ne, matsalar tana ga ita yarinyar domin a yanzu komai zaka faɗa mata ba zata gane ba, hasalima bata sanka..." "No! Hafiz wallahi tun ranar da ta samu ciwon babu wanda ta yadda da shi kamar ni, domin da kyar nake guje mata har kunya ta rika bani a gaban iyayenta." "Simple ai ma maganar ta zo cikin sauki, domin kuwa basai ka tsaya bata time dinka ba, kaje ka faɗawa iyayenta kana sonta fakat." A jiyar zuciya ya sauke ya ce "toh! Zan gwada amma ina kunya." "Ka tsaya kunya sai dai kaji labarin aurenta." "Kuma fa haka ne, wannan saurayin nata kamar zai cinyeta ɗanya ko yaushe cikin rawan kai yake." Dr ya k'arasa maganar yana kwashe wayoyinsa. Dariya Hafiz ya yi ya ce "to ita kuma Aneesa fa?" "Ina sonta, amma son Ameesha ya fi nata a zuciyata." Dr ya bashi amsa. "Allah ya tabbatar da Alhairi, ya baka ikon yin adalci in ka auri Ameeshar taka." "Ameen" ya amsa " tashi ka rakani ma in dubo ta! Haka suka fita a office din tare don zuwa gidan. ************************** Tun daga nesa ya soma kwallah mata kira, cikin sauri ta fito daga bedroom ɗinta tana faɗin "gani Alhaji Allah yasa lafiya?" Wata muguwar harara ya cilla mata, zuciyarsa na tafarfasa ya ce "Wallahi keda danki ku fita idona, ida ba haka ba wallahil Azeem sai na mugun bata ranku." "Allah ya baka hakuri Alhaji, amma ban san laifin da muka yi ba?" "Au tambayata ma kike to? To bari ki ji domin nasan ke ce kike zuga Najeeb har yake min rashin mutunci son ransa ko? Wallahi zan yi maku walak'anci sosai a gidan nan." "Allah dai ya baka hakuri, amma ban san laifin da ake tuhumar mu da shi ba." Ta yi maganar cikin sanyin murya. "Wai kamar ni ina matsayin mahaifin Najeeb, har zan gindaya masa sharɗa amma ya yi burus da ita, yanzu kawai ina ofis sai ga kiran Taheer yana sanar min wai ya tsayar da ranar auren Najeeb da wannan mahaukaciyar yar tashi, ko uban wa ya ce masa zan haɗa zuri'a da mahaukaciya?" Wani murmushi ya kubce ma Mummy, ta ce "kai masha Allah da wannan hukunci, amma na yi farin ci..." Bata ko gama maganar ba, sai ji ka ke kau Alhaji Mansur ya dauketa da mari ya daura da fadin "Amma ke shashasha ce, ai shi yasa na ce ke kika zuga shi har yake min yadda ya so, to wallahi baki isa ba matukar dai ina numfashi babu wani maganar aure tsakanin su." Yana gama faɗin haka ya yi bedroom ɗinsa tare da buga kofar ji kake yi bom. Mummy kam nata dawowa daga zafin marin ta girgiza kai, a zuciyarta ta tir da halin mai gidanta. ************************** Ummi ce ta tasa Ameesha a gaba don ta ci abinci, amma fir taki ci sai ma juya wa Ummi baya da ta yi, a haka Abba ya fito ganin ta juya baya ya sashi saurin matsawa dining din ya ce "A'a Hajiya lafiya kuwa uwata ta juya wa dining din baya?" Share hawayen da suka soma sauka akan fuskarta ta yi ta ce "Alhaji ya zan yi mata? Tun ɗazun nake fama da ita kan ta ci amma fir ta ki, ina tunanin akwai abin da ta ke so, sai dai bata iya faɗa min." "Ki bar yi mata kuka insha Allah, Auta zata sami lafiya yanzu haka nasa mu labarin wani asbiti a kasar Egypt insha Allah nan da karshen wata lokacin anyi aurenta da Najeeb zasu ta fi." "Aure! Tayi saurin faɗa tare da ɗago kai, jin ya ambaci aure. "Eh! Aure zan yi mata domin kuwa ina ga shi ne kawai mafita, nan da kwana ashirin da biyar biki. "Allah ya kaimu." Ummi ta yi maganar jiki a sanyaye. Abba yana shirin magana sai ga Abdul ya shigo, ya gaida iyayen sa tare da kallon Ameesha ya ce "Sis kina dining ne kuna hira da Abba! Sai kuma ya maida hankali kan su Abba ya ce "Abba Dr ne fa ya zo ganin Ameesha!" Washe baki Abba da Ummi suka yi a lokaci guda da sauri Abba ya ce "Shigo da shi maza." Da sallama suka shiga falon Abba da Ummi wanda suka komo falon suka amsa masa, a kasa suka zauna shi da Hafiz din suna gaida su da tambayar mai jiki. Ameesha da ke zaune tana jin muryar Dr Asmad da sauri ta taso daga inda take, wani kyakkyawan murmushi ne kwance a fuskarta, shi dai Asmad sai ganin ta ya yi kusa da shi zaune tare da rike masa hannu tana zazzare ido. Murmushi ya sakar mata ya ce "Autar Ummi babu magana sai zama kawai?" Cikin muryarta mai sanyi ta maimaita abin da ya faɗa, shi dai Hafiz kallonsu kawai ya ke yi sun yi mugun da ce wa, gefe ɗaya kuma yana tausayin halin da Ameesha ta samu kanta. Ummi ta yi murmushin takaici ta " Kai Auta wato ɗazun duk kin wani share maganar mu, har abinci kin ki ci amma daga ganin Dr ki sake, to Allah yasa yazo da allura!" Bata rai ta yi, don dai bata son allura sam. Shi kam Dr hankalinsa ne ya tashi jin Ameesha bata ci abinci ba, da sauri ya ce "Ummi ina abincin?" "Yana dining table taki ta ci, tun ɗazun nake fama da ita." "To Ummi a kawo mata nan kila ta ci!" Dr ya yi maganar yana kallon Ameesha. Haka kuwa aka yi, inda suke zaune Ummi ta kawo abinci, Dr Asmad da kansa ya dauki abincin ya mikawa Meesha ya ce "Oya fara ci! Jijjuya kai ta yi alamar a'a. Bata rai ya yi ya ce " ok baki ci dai ko? To babu inda zan je da ke dama nazo ɗaukar ki ne, ko ba zaki bini ba...? Ai tun kafin ya ida maganar ta dauki cokalin tana juya wa alamar dai zata ci, sai dai ta kasa don ta saba Ummi ke bata. Ummi ce ta matso wajen ta ce " Bari na bata! Domin bata iya ci da kanta." *SANGARTA* na damun ```MARYERM TAHEER```. inji Yar Mutan Rano. Ummi ta ida maganar tana kama hannun Meesha, aiko babu musu ta bi Ummi har dining, Ummi na bata tana ci, don Dr ya ce zai ta fi da ita. A falo kuwa Abba ne zaune ya maida hankali kan maganar da suke da Dr. "Alhaji dama ce wa na yi, ya kamata a fita da Ameesha waje domin dai tunda an yi anan babu wani canji sai kawai a fita da ita." Murmushi Abba ya yi ya ce "Tuni na yi wannan tunanin har ma nasa mu bayani game da wani asbiti dake Egypt, to insha Allah end of this month zasu ta fi, don ina son su ta fi da mijinta n..." Wani irin zabura Dr Asmad ya yi jin Abba ya ce mijinta. "Mijinta" Ya yi maganar har jikinsa yana rawa. *KUYI HAKURI DA WANNAN PLEASE*🙏 _*YAR MUTAN RANO*_ [10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* © *ZULAYHEART RANO* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* *Page din yau naki ne Badeeyar Adam (Beauty Queen), na baki page din kyauta, dubun gaisuwa inji DR ASMAD DA AMEESHA lol, Allah ya kara maki lafiya mai amfani*😍😍😍 _*Besty Najeeb ya ce yana godiya da son da kike masa zai zo har gida ya kwashi gaisuwa lol*_😻😻😻 ```TEAM NAJEEB MANSUR``` *21* Kallonsa Alhaji Taheer ya yi cike da mamakin yadda hankalinsa ya tashi lokaci ɗaya. "Dr lafiya kuwa?" Abba ya tambaya. Gyara zama Dr Asmad ya yi tare da dafe kirjinsa, wanda ke harbawa da sauri da sauri ya kakalo murmushin da iya kacinsa leɓe ya ce "Babu komai Abba, gani dai na yi a condition din da Ameesha ta ke bai kamata a yi maganar aurenta ba!" Murmushi Abba ya yi ya ce "Nima sai da na faɗawa Najeeb haka, amma ya ce shi fa a haka yake sonta, zan aura masa ita in Allah yasa zata samu lafiya sai ta samu a ɗakinta." "Allah yasa haka shi ne mafi alheri." Dr ya yi maganar cikin karfin hali. Daga haka suka mik'e tare da faɗin "Abba mu kam zamu ta fi gida, dama mun biyo duba Ameesha ne." "Mun gode sosai Allah ya shi albarka, ka gaida iyayen ka." "Za su ji." Ya yi maganar yana fara tafiya. Ameesha da ke cin abinci tana ganin Dr ya mike da nu fi tafiya, ai da sauri ta mik'e tare da nufar su. "Auta! Don Allah ki dawo ki gama cin abincin ki, ina kuma kika nufa?" Ina ai sam bata masan me Ummi ke faɗa ba, har saida ta ɗan gana da inda Dr yake, kansa ta faɗa tare da sakin kuka. Sosai hankalinsa ya tashi da jin kukanta, saurin birkitota gabansa ya yi yana tambayar ta lafiya? Shiru ta yi masa sai hawayen da ke zuba daga idonta, jan hannunta ya yi suka fita waje a can bayan gidan ya nufa da ita inda aka shirya wasu fararen kujeru domin shan iska, zaunar da ita ya yi shima ya zauna akan wacce ke fuskantar ta. Zuba mata ido ya yi har na sakonni sannan ya sauka daga kujerarsa ya tsuguna a gaban ta, hannunsa ya zira cikin aljihu ya zaro kyakkyawan hankerchief ɗin sa ya soma share mata hawaye yana faɗin "Me ya sanya ki kuka Princess?" Shiru ta masa, ya kuma faɗin "Ko baki son in tafi ne?" Da sauri ta daga kai alamar "eh! Murmushi ya yi irin wanda ake yiwa masoyin gaskiya "Oh! Princess rigima." "Zaki bini gidanmu?" Nan ma da sauri ta amsa. "Gud sai kin ce Sweety Asmad!" Cikin daddaɗan murya ta ce *"SWEETY ASMAD?"* Ta yi maganar cikin sigar tambaya. Wani irin yar Dr ya ji a jikinsa musamman yadda ta ambaci sunan, sai ya ji ina ma zai dauwama yana mai jin muryar Ameesha, nan da nan sai ya ji damuwa ta ziyarci zuciyarsa da ya tuna da maganar Abba na ɗazun. Kara kallonta ya yi ya ce "Ki daina kuka insha Allah zan zo in tafi da ke, amma fa ba yau ba sai na Kuma zuwa kin ji, kuma in dai baki cin abinci ba zan je da ke ba, ki rika cin abinci kinji ko?" Da sauri ta daga kai alamar dai "to! "Yawwa tashi mu je karki kara kuka ki zauna a falo." Ai ko babu musu ta mike suka nu fi cikin gidan, a kofar falo suka yi karo da Hafiz "Sorry abokina mun bata lokacin ka ko?" Murmushi ya yi kawai ya ce "No! Babu komai tunda dai ka lallasheta." Kallon kofar Dr ya yi sai ko ya ga Ameesha tsaye tana kallonsu, murmushi ya sakar mata tare da daga mata hannu alamar bye. Ita ɗimma daga masa hannu ta yi har sai da taga fitar motarsu tukun ta shiga cikin falon. ************************** Cikin wani irin yanayi Asmad ya isa gidansu Nenne, ko sallama ya kasa da dai yana cikin muguwar damuwa, babu kowa a falon don haka sai ya zube akan kujera tare da lumshe ido. Nenne ce ta fito daga bedroom ɗinta, hannunta rike da waya tana dannawa da alama wata Number take nima. Kara bude ido ta yi ganin Asmad ɗin zaune a falon, da sauri ta k'arasa tana faɗin. "Asmad lafiya kuwa, yau she ka shigo?" Kasa magana ya yi kuma bai buɗe ido ba, har sai da Nenne ta kuma tambayarsa. Da kyar cikin damuwa ya ce"Nenne na rasa Ameesha don Allah ki taimaka min!" Da rashin fahimta Nenne ke kallonsa ta ce "Ameesha ko Aneesa?" "Ameesha dai Nenne." Asmad ya bata amsa. "Wacece kuma Ameesha, a ina take?" Sai a lokacin ya ɗan dawo nutsuwarsa jin tambayar da Nenne ke masa. Buɗe idonsa da yake yi jajir ya yi ya ce "Nenne Ameesha budurwa ta ce aurenta zan yi. Kallon mamaki Nenne ke bin Asmad da shi ta ce "Ita kuma Aneesa fa? "Ai ita matarsa ne, kuma yana da damar yin mata hudu." Kafin ya yi yunkurin bata amsa ne suka ji maganar a bayansu. Da sauri Ummi ta juya tana kallon Alhaji Abubakar ɗin. "Alhaji ka ji abin da ya ce kuwa?" "Sosai na ji, koba ce wa ya yi zai kara aure ba?" "Eh! Haka ya ce." "To na bashi goyan baya Allah ya tabbatar da Alhairi, yar wacece?" "Alhaji ka ce kana goyon bayan shi fa, duka duka yaushe ya yi auren?" "Look! Hajiya ya kamata ki fahimci halin da yaron nan ya ke ciki." Shiru Nenne ta yi, don ta san duk wani bayanin da zatawa Bobbo ba fahimta zai yi ba, amma sam bata son Asmad ya kuma aure a yanzu. Muryar Bobbo ta ji yana kuma tambayarsa yar wacece? "Bobbo ina sonta sosai amma kuma yanzu da na je gurin mahaifinta ya ce ya mata miji, Bobbo wallahi idan na rasata zan shiga wani hali." Cikin karaya ya ida maganar. "Kar ka sa damuwa a zuciyarka, ka yadda samu da rashi duk na Allah ne, kuma in har matar ka ce sai ka aureta, ina son farin cikin ka kamar yadda kake son na mu." Wani daɗi ne ya rufe shi, duk da dai yasan Ameesha ta yi masa nisa, sai dai zai ci gaba da addu'a kamar yadda Bobbo ya bukata. A haka Bobbo ya yi ta kwantar masa da hankali, sannan ya yi sallama da su ya ta fi zuciyarsa wasai. *GIDAN ALHAJI MANSUR* Mommy da Najeeb suna ta shirye shiryen aure, kuɗi sosai Mummy take kashewa Wajen haɗawa Ameesha kaya, kamar kullum yau ma zaune suke suna lissafin abin da basu saya ba. "Kasan menene Najeeb?" Mummy ta tambaya. "A'a" Mummy ya bata amsa. "Yawwa so nake a kammala duka kayan kafin satin sama, don satin da zamu shiga lokaci ya kure." "Eh! Mummy hakan yana da kyau, dama gidan an gama komai sai saukar Alkur'ani da nake so a yi." "Madallah! Allah ya tabbatar da Alhairi." Alhaji Mansur ne ya shigo falon, fuska sake kamar wanda aka wa bushara da aljanna, zama ya yi akan kujera tare da kallon Mummy ya ce "Kuna nan sai shawara ku ke yi da ɗanki, kun wareni a gefe!" "Abba ina wuni?" Najeeb ya yi maganar yana tsugunawa. Sosai ya saki fuska yayin amsawa. A jiyar zuciya Mummy ta sauke don jin yau Alhajin da yan mutunci aka shigo ta ce "Haba Alhaji kana ranmu fa! "Haka dai kika ce, maganar mai kuke tattaunawa?" "Maganar yadda auren Najeeb zai kasance mu ke yi." Ta ba shi amsa cike da jimamin yadda zai dauki maganar. Wani irin zabura Alhaji Mansur ya yi ya ce... *A dai kara hakuri da ni Please, Zulayheart Rano tana tsananin kaunar ku gaba ɗaya.* _*YAR MUTAN RANO*_ *SANGARTA* © _*ZULAYHEART RANO*_ *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* ```Wannan shafin na ku ne ku kadai yan jahata babban birnin Nijeriya wato RANO a duk inda kuke ina alfahari da ku ina jin duk wani dan Rano jinina ne, Allah ya barmu da kaunar juna``` _*Happy birthday Ramlat Ar Manga wish you many many year's in your life*_😍😍😘 *46* Tunanin inda zata nufa take, sam bata jin zata iya komawa gidansu tasan sarai halin Abba tunda Asmad ya shiga rayuwar ta ya rage sake mata sai Asmad ɗin, yanzu idan ta tunkare shi tabbas tasan ba zata taɓa samun mafaka ba, kila ma a daren nan ya dawo da ita hukuncin Ya Jaheed ma yafi daga mata hankali babu makawa Ummi fushi zata yi da ita, hannu tasa a ka ta fashe da wani kuka a fili ta furta "oh! Ni Maryerm ina zan nufa?" Take wata zuciyar ta bata amsa gidan Nenne. Bata tsaya komai ba ta yi na'am da shawarar zuciyarta domin shi ne mafita, da kyar ta kai kanta bakin titi domin cikin layin babu wani masu abin hawa, ta dade sosai kafin ta iya taran dan keke napep, duk da ko kwabo babu a hannunta haka ta shiga ko ciniki ba su yi ba, domin yadda kanta ke mugun sarawa bata jin zata iya magana. Tafiyar mintina ta kaisu gidan "ka yi hakuri bari a kawo maka kuɗi." Ta yi maganar da kyar tana nufa get din. Kwankwasawa ta yi cikin rashin kuzari, maigadin ya fito cikin sauri ganin Ameesha ya yi saurin tsugunawa yana gaidata, bata iya amsawa ba sai ce masa ta yi "ya amso dari biyar a cikin gida ya bama mai napep ɗin." Cikin kankanin lokaci ya isa cikin gidan sallama ya yi a kofar falon Nenne da Bobbo ne zaune suna hira, kafin Nenne ta amsa har Bobbo ya amsa bayan sun gaisa ya ce "Hajiya dama matar Alhaji karami ne ta ce a amshi dari biyar a kai wa dan adaidaita." Bobbo ya ɗauki dari biyar din ya mika masa ya yin da Nenne ta cika da mamakin wai matar Asmad ce ta zo kuma ta sanya a amshi kuɗin napep, ko kafin ta gama mamakin sai jin sallamar Ameesha ta yi cikin wahalalliyar murya, da sauri ta isa gareta ganin tana niyyar faduwa kasa. "Subhanallah! Ameesha ke ce da daren nan ina Asmad ɗin?" A kidime Nenne ta jero mata tambayar. "Nenne zan sha ruwa." Ta furta da kyar." Bobbo ne ya mikawa Nenne goran ruwan Faro da ya siyaya ɗazun, ɓalle murfin ta yi ta shiga bata ruwan har sai da ta shanye kafin ta saki goran tare da ajiyar zuciya. "Maryam sannu dama baki da lafiya ne?" "Eh!" Ta bata amsa. "Kuma dan rashin hankali irin na Asmad sai ya barki kika fito a wannan yanayin?" A fadace Bobbo ya yi maganar. Ganin jikin nata ya fara zafi sai Nenne ta ce "Alhaji ko zaka kira Asmad ba ne? Don jikinta kara zafi yake." Zazzafan zazzaɓi ne ya rufeta, cikin muryar da bata fita ta ce "a'a Bobbo karka kira shi ba sai ya duba ni ba, idan akwai pracitamol a bani." "Ki dai bari a kira shi don kina da buk'atar taimako." Nenne ta yi saurin katse ta. Kuka ta sanya tana faɗin kar a kira shi, take Bobbo ya fasa tare da tsare Ameesha da ido "Anya kuwa lafiya Maryerm?" Kanta a kasa ta ce "lafiya lau Bobbo, bana jin dadi ne na fito kuma bai san ina rashin lafiyar ba." "Kan ji shashanci kuma shi ne kika fito baki tunanin zai iya shiga wani halin idan?" "A yi hakuri Bobbo da safe a kira shi." Ganin kamar ba cikin nutsuwa take ba yasa Bobbo amincewa. da taimakon Nenne suka shiga ciki, ruwan wanka Nenne ta haɗa mata sai da ta taimaka mata wajen shiga toilet din kafin ta bata waje. Bata jima ba ta fito ko tsayawa sanya kaya bata yi ba ta kwanta, gaba daya jikinta ya kuma gashewa da dumi, bargo ta ja ta rufe jikinta hakoranta sai haduwa suke da juna, a haka Nenne ta shigo ta sameta "Tashi ki sha tea sai ki sha magani." Kaɗan ta kurba ta watsa maganin kafin ta koma ta kwanta. A haka suka kwana Ameesha bata jin dadi, zazzaɓin ya sauka sai ciwon da gaɓoɓinta ke yi, sam Nenne bata rintsa ba domin tausayin halin da Ameesha ke ciki, tabbas tasan ba lafiya ya kawo ta gidan cikin daren ba, amma duk tambayar da ta yi mata amsa daya take bata shi ne "Babu komai." Ta ta gaji da tambayar sai ta yi shiru, ta kudiri a zuciyarta in har Dr wani abu ya yiwa Ameesha tazo gidan zai ga ɓacin rai ganin idonsa. **** Tun bayan tafiyar Ameesha Dr ya kasa samun nutsuwa sai zarya yake a dakin shi kaɗai, tsaki ya yi shi har bai san yawan su ba, daga karshe komawa toilet ya yi ya sakarwa kansa ruwa ko zai samu sauki a zuciyarsa. Bayan ya fita kayan bacci ya sanya ya kwanta sai juyi yake zuciyarsa tana tuno masa yadda Ameesha ke kuka tana rokonsa, mtsww ya ja tsaki tare da juyawa da kyar bacci ɓarawo ya samu nasarar ɗaukan shi, kallo ɗaya zaka masa kasan baya cikin nutsuwarsa. "Hmmmm! Rukky wallahi bazan ɓoye maki ba ina cikin damuwa." Aneesa ce ke maganar cikin waya bayan ta kule a bedroom ɗinta. Daga ɗaya bangaren Rukky ta ce "kina da matsala Aneesa, yanzu baki ga canji ba ne da kika kai maganin? Ko dai baki sanya inda zai gansa ba?" Mtsww Aneesa ta saki tsaki ta ce "Ni Ko na sanya inda zai gani domin na farko sai da suka yi kwana huɗu basa magana, da kyar ta samu suka daidaita yau kuma abin ya kara gaba ina jin koranta ya yi don naga ta fita." Hehehe! Rukky ta saki dariyar keta, ta ce "Kina wuta Anee, kinga yanzu saura kiris Dr ya zama naki ke kaɗai, idan kin dage gaba kadan komai zai daidaita." Cike da murna ta kammala maganar. Hmmmm! Kawai ta iya faɗa suka yi sallama, tana aje wayar ta buga uban tagumi, a yanzu sam hankalin ya kasa kwanciya. Washegari da safe sai da ya yi wanka, ruwan zafi kawai ya ɗaura tea ya haɗa bayan ya gama sha ya yi shirin zuwa office, sama sama suka gaisa da Aneesa ya tambayi ko da matsala, ta tabbatar masa babu sannan ya wuce domin akwai masu jiran sa a office din. *Bangaren Ameesha* Kamar ciwon na jiran Bobbo ya fita ya dawo sabo, dalilin break ɗin da Nenne ta kawo mata, tunda ta ci hankalinta ya kasa kwanciya sai yunkuri take amma aman yaki fitowa, haka ta wuni aikin abu daya da Nenne ta yi mata maganar Asmad sai ta kuma fashewa da kuka, shi yasa ta zuba mata ido. Karfe uku ya taso daga office daret gidan Nenne ya wuce, har yanzu dai ba a cikin nutsuwarsa ya ke ba musamman yadda ya yi parking motar zai nuna maka haka, cikin falon ya shiga bakinsa dauke da sallama. Nenne dake zaune duk abin duniya ya dameta ta saki ajiyar zuciya ganin Asmad ɗin, ta tabbata zata samu rangwame cikin damuwarta, amsawa ta yi da sakin fuska. "Barka da yammaci Nennena fatan kin wuni lafiya?" "Barkammu Asmad lafiya lau ya Aneesa da Ameesha." "Duk suna lafiya." Ya bata amsa fuska babu walwala. "Asmad lafiya kuwa?" "Ummh Nenne me kika gani?" Ya yi tambayar bayan ya kalkalo murmushi dole. "Babu shakka yau na san babu lafiya a gidanka, domin kallo ɗaya mutum zai yi ya fahimci haka kamar yadda nima na fahimta, me yake faruwa a gidanka?" Tambayar ta yi fuska ba alamar wasa. "Babu komai Nenne kawai bana jin dadi ne." Ya bata amsa yana shirin mik'ewa. Murmushin takaici ta yi ta ce "Na ji lafiya lau ina Ameesha?" Dawowa ya yi baya ba tare da ya shirya ba sai jinsa ya yi yana shirin faduwa, bai iya magana ba sai dafe kansa ya yi dake barazanar tsagewa. "Tambayarka na yi ina Ameesha?" Cikin tsawa ta yi maganar wanda har Ameesha dake bacci sai da ta farka. "Ku gafarceni Nenne jiya mun sami matsala da ita da dare har na ce mata ta tafi gidansu..." "Kun sami matsala? Asmad dama kana daya daga cikin mazajen nan masu rasa hankulansu idan mayensu sun yi masu laifi? Ka bani mamaki ka tozarta mu a idon duniya, matarka ta aure ka kora da dare don kun samu matsala ko? Ya yi kyau tashi ka bani waje." Da zallar faɗa wanda tunda yake da ita bai taɓa sanin tana da fada ba sai yau ta dire maganar tana nufa hanyar bedroom. Duk yadda Asmad yaso tsayar da Nenne abin ya ci tura domin yadda ta haɗa girar sama da ta kasa, lallai yasan ya batawa mahaifiyarsa rai tunda har ta dau zafi da shi. Jiki a sanyaye ya fita daga falon, haushin Ameesha ya kuma darsuwa a ransa tunda akanta har Nenne ta yi fushi da shi irin wanda bata taɓa yi ba, bayan kuma kowa ya ji yasan ita ke da laifi. Mtsww ya ja tsaki yana bama motar wuta. Nenne na ganin Dr ya fita ta ɗauki wayarta layin Hafiz abokin Dr ta kira, ringing biyu ya dauka cikin ladabi ya gaidata kafin ta sanar masa tana son ya zo gidanta ya duba Ameesha amma kar ya sanar da Dr, cikin mintinan da basu gaza talatin ba ya isa gidan, bayan sun gaisa ta kaishi daki inda Meesha ke kwance. Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗan saki murmushi domin kamar hasashen da yake ya tabbata. Don haka sai ya shiga mata tambayoyi sannan ya amshi fitsarin ta ya kuma debi jininta. Kallon Nenne ya yi yana faɗin "Nenne bari na je lab a yi test bazan jima ba." "A dawo lafiya." Nenne ta faɗa cikin sakin fuska. A kalla Dr Hafiz ya yi kusan awa kafin ya dawo fuska cike da fara'a mai tsanani. Mika mata farar takadda ya yi yana faɗin" masha Allah Nenne Meesha na dauke da ci..." 😓 *Ba sai kun faɗa ba walle nima nasan ina da matsala sosai, na rasa abin da yasa nake jin kiwar typing gashi abin ya zo gangara, ku kara hakuri dai kaɗan ya rage in sha Allah.* Ina son ki har cikin raina my fan's😘😘 *YAR MUTAN RANO* *SANGARTA* © _*ZULAYHEART RANO*_ *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* *47* "Masha Allah! Nenne Meesha na dauke da ciki har na wata daya da kwanaki." Wani irin farin ciki ne ya ziyarci Nenne wanda rabonta da jin irin wannan farin cikin tun lokacin cikin Asmad "Alhamdulillah! Ta furta a bayyane fuska cike da zallar farin ciki. "Sannu da k'ok'ari Hafiz na gode da wannan kyakkyawan albishir ɗin." Meesha kam tana gama jin bayanin Dr Hafiz sai wasu hawaye na farin ciki suka soma zubowa daga idonta, hakika wannan rana ta zame mata na farin ciki domin daga wannan rana ta fita daga zargin da Dr ke mata, tana son ganin farin cikin da Dr zai yi idan ya ji tana dauke da cikinsa, gaba daya sakin baki suka yi suna kallonta don hawayen da take ba na wasa bane "haba Ameesha ke da zaki yi farin ciki sai kuma ki ke hawaye?" Hafiz ne ya yi maganar cikin sigar lallashi. Murmushi ta yi kanta a kasa, bata jin zata iya sanar da kowa sirrinta da mijinta, don haka sai kawai ta ce "Babu komai fa Hafiz farin ciki ne kawai." Ta dire maganar tana sinne kai cikin filo. Murmushi suka yi gaba daya, sannan Dr Hafiz ya mik'e yana faɗin "Nenne zan k'arasa gida anjima zan kawo mata wasu magunguna." "Allah ya kaimu." Nenne ta faɗa da murmushi. Bayan tafiyar Dr Hafiz sai Nenne ta tsare Ameesha akan sai ta faɗi abin da take so. "Nenne ni fa bana jin cin komai." "A'a Ameesha kin ga ki daure ki faɗa min bana son zama da yunwa balle kuma ba ke daya ba ce yanzu." "Zan rika ci Nenne faten dankalin turawa nake so." "Yawwa Yar Nenne haka nake so." Nenne ta yi maganar tana mik'ewa, da kanta ta shiga kicin ɗin ta soma haɗawa Meesha abin da ta ce tana so, faten ta yi mata mai ruwa ruwa yadda zata ji daɗin sha har da alayyahu ta yanka ciki da hanta, lokacin da ta shiga har bacci ya soma daukar Meesha, don haka cikin hikima da dabara ta tashe ta. "Sannu da k'ok'ari Nenne." Ameesha ta yi maganar tana tashi daga kwanciya. "Yawwa ta shi ki sha da zafinsa." Ruwa ta bata ta kuskure baki sannan ta bata abaki, ba ta wani ci da yawa ba ta ce ta koshi. Duk yadda Nenne taso ta kara dole ta barta, toilet ta nufa ta sakarwa kanta ruwa masu dan zafi don ta ji dadin jikinta, bayan ta fito kayan jikinta ta mai da domin bata da kaya a gidan, Nenne ne ta shigo ta kalli Ameesha ta ce "Har kin fito?" "Eh" Nenne sai dai "bani da kayan sawa." A shagwaɓe ta yi maganar. "Kuma fa bari na kira Asmad ya kawo maki." To kawai ta amsa tana ci gaba da wasa da zaren rigarta. Tana kallon Nenne ta fita tana waya. Ba a fi minti talatin ba, tana kwance kewar jikin Dr take tana son ta ji dumin jikinsa, Kamar daga sama ta ji sallamar sa murya ciki ciki, da sauri ta tashi zaune tana amsa sallamar "Sannu da zuwa baby." Ta faɗa tana kallonsa. "Yawwa." ya amsa a takaice fuska babu walwala. "Ga kayanki nan da kika sanya na kawo maki, dama na kula tuni baki son zama da ni shi ne dalilin ki na shan magani, tunda ba ki son zama dani me ya kawo ki gidan iyayena?" Ya kai karshen maganar yana daka mata tsawa. Tun kan ya gama maganar, hawaye ya soma wanke mata fuska domin maganar sa yana daga mata hankali, murya na rawa ta ce" Ka yi hakuri ba da wata manufa nazo nan gidan ba, kuma wallahi laifin da kake tuhumata da shi bani da masaniya..." Hannun da ya daga mata ne ya sanya ta yi shiru da maganar ta amma hawayen basu tsaya ba. "Kinga ki yi min shiru ai kin sire min Ameesha yadda na daukeki kin bani kunya, sai an yi magana ki farawa mutane kukan SANGARTA." Mtsww ya ja tsaki kafin ya bar mata dakin. Ragaf ta faɗa kan gadon ta saki sabon kuka sam bata son irin abin da Dr yake mata, duk da yanzu tasan Allah ya wanketa to amma ai muggan kalamai Dr bai daina furta mata ba, haka ta ci gaba da kukan har bata san lokacin da Nenne ta shigo ba sai jin muryar ta ta yi "Ameesha lafiya kike kuka?" Hankali tashe ta yi tambayar. Saurin share hawaye ta yi ta kalkalo murmushi ta ce "kaina ke min ciwo Nenne kamar zai rabe biyu." "Allah ya baki lafiya, fatan kin sha magani?" Ta yi tambayar badan ta yadda da abin da Meesha ta faɗa ba. "Eh na sha." Ameesha ta bata amsa. "Ki bar kuka zai daina." Nenne ta k'arasa maganar tana fita, cikin zuciyarta tana sanyawa Meesha albarka ta tabbata Ameesha suruka ce ta kwarai tunda har tana iya ɓoye matsalar ta da mijinta, kwafa ta yi a ranta ita kadai tasan abin da zata yiwa Dr. Ameesha na ganin Nenne ta fita ta kuma sakin wani kukan, tana tausayin kanta da hukuncin Dr. Asmad kuwa yana fita gidan su Hafiz ya yiwa tsinke, har ya karya kwana zai shiga layin ya tuna kila Hafiz din baya gida, don haka sai ya dauko wayarsa ya kira layinsa, ringing biyu ya dauka bayan sun gaisa ne yake tambayarsa Allah yasa yana gida "Eh ina gida ban jima da shigowa ba." "Ok gani nan zuwa." Yana gama faɗin haka ya katse wayar. Yana fakin motar ya kara kiransa, minti biyu kacal Hafiz ya fito musabaha suka yi kamar yadda suka saba sannan Hafiz ya kalli Asmad da kyau ya ce "mu shiga daga ciki mana abokina?" "A'a ba sai mun shiga ba, sam na rasa jin dadi na gaba daya bana cikin nutsuwa." Da damuwa Asmad ya gama maganar. " Subhanallah! Dr me yake faruwa haka? Mu shiga ciki zai fi." Ciki suka shiga a falo suka yada zango, ruwa mai sanyi Hafiz ya kawo masa bayan ya sha sannan ya soma magana "Wato Hafiz Aneesa da Ameesha suna neman caza min k'wak'walwa, ko kasan duk tsayin lokacin da muka dauka da Aneesa maganin hana daukar ciki take sha?" "Maganin hana daukar ciki?" Da mamaki Hafiz ya yi tambayar. "Sosai kuwa ina tabbatar maka har cikina Aneesa ta zubar wanda take tunanin ban sani ba." "Zubar da ciki?" "Sosai kuwa." Dr ya tabbatar masa. "Inna lillahi! Wannan wacce irin masifa ce? Kuma kana sane baka dau mataki ba" "Ban ɗauka ba sai yanzu nake son ɗauka akansu duka, domin Ameesha ma sau biyu ina ganin maganin a bangaren ta." "Au har Ameesha din ma?" Hafiz ya yi saurin katse shi. "Tabbas, na farko ranar da ta dawo daga gidansu, na biyu shekaran jiya da dare, wallahi bazan ɓoye maka ba na Ameesha ya fi bani haushi domin yadda na dauketa ba haka ta ɗauke Ni ba, abin haushi kuma tana gaya min bata taɓa sha ba ka ji wani rainin wayau bayan na gani da idona..." "Amma Dr ka binciki na Ameesha kuwa? Ban ji ajikina Meesha zata ma haka ba... Idan har Aneesa ka sameta da laifin dumu dumu Ameesha fa? Bana jin zata iya aikata maka makamancin haka..." Mtsww Dr ya ja tsaki "ya Ina sanar maka abu kana neman karyatani...? "Ka taɓa ganin ta da maganin a hannu tana sha?" Hafiz ya yo saurin jeho masa tambaya. "Look Hafiz bana son irin wannan tambayar please." "Am sorry to say Dr Asmad amma wallahi na yi rantsuwa Ameesha ba zata iya abin da kake tunani ba, shin ina hankalinka ya ke da baka bincika ba? Shin menene na saurin sanya zargi cikin rayuwar aurenku? Ina mai baka shawara ka je ka yi bincike domin tabbatar da abin dake wakana a gidanka." Wannan karan a zafafe Hafiz ya gama maganar. "Bincike! Hmmmm ai ba sai na yi bincike ba, domin amsar a fili take na gani da idona, kuma ba sharri na yi mata ba, don haka Hafiz sai anjima." Yana direba maganar ya mike da niyyar barin falon. "Ka je Dr amma ka yi gaggawar daina wannan fushin tun kafin ta kai ka ga dana sani." Bai fasa tafiyar ba sai da ya kai kofa kafin ya juyo ya kalli Hafiz ya ci gaba da tafiyarsa. Tafiya yake a mota maganganun Hafiz na yi masa yawo a k'wak'walwa, ya rasa ta ina zai fara matsalar sam Nenne bata sakar masa fuska balle ya je can ya samu mafita, to kuma idan ya je sangartacciya tana can haka zata sanya shi gaba da kuka mtsww ya ja tsaki a karo na barkatai. **** Haka kwanaki ke tafiya yau watan Ameesha uku a gidan Nenne, tattali Nenne ke bama Ameesha sam bata barin ta da damuwa, ita dinma tana jin dadin zama da Nenne domin tana samun kula a wajenta har wata kiba Ameesha ta yi, ba lallai ne mutum ya kula tana da ciki ba, bata neman abu ta rasa duk kankantar sa Ummi da Abba sau uku suna zuwa duba ta, sun yi farin ciki da jin Autar su na dauke da ciki Ummi har tana tsokanarta "Oh! Autar Ummi yanzu kuma dole a rage sangarta domin kin kusa zama uwa." "A'a Hajiya Halima Ameesha ai sangarta ba zai barta ba yar gatan Abba da Nenne da Bobbo ne fa, ta ya zata daina sangarta." Gaba daya suka saki dariya Abba ya ce "Faɗa mata dai ai ba a canzawa tuwo suna sangarta kuwa uwata yanzu ta fara ko a gaban kanwata ko kanina (yaron Meesha ko yarta Abba ke nufi.) Kar ki fasa komai uwata. Murmushi ta yi bayan ta gama tunawa. Dr ya yi na cin duniya Nenne ta bari Ameesha ta koma amma ta ki yarda, da taga zai dameta sai ta soma haɗe girar sama da ta kasa idan ta kasa gaisuwa ma da kyar yake samun ta amsa balle ya samu damar ganin Ameesha, har ya ɗan zama abin tausayi. Duk wannan abin da ake yi Aneesa bata taɓa sanin Ameesha tana gidan Nenne ba, domin ita bata wani damu da zuwa gidan ba kuma ko taje bata dadewa take tafiya, Ameesha kuma kullum cikin bedroom take sai kuma garden in tana son shan iska take zuwa. A gaggauce ya yi parking motarsa ko tsayawa rufe motar da kyau bai yi ba, domin har ya je asbiti ya yi mantuwa shi ne dalilin dawowarsa, kai tsaye bangaren Aneesa ya yi, yana tura kofar ta buɗe kutsa kai cikin falon ya yi duk sallamar sa bai samu an amsa ba, yasan har matar gidan shi yasa bai damu ba ya yi wucewar sa bedroom ɗinsa, ya ɗauko file har zai fita sai ya fasa don yana son ya sanar mata da ta shirya idan ya dawo su je gidan Nenne, abin da kunnuwan sa suka soma jiyo masa ne yasa shi daskarewa... *YAR MUTAN RANO* *SANGARTA* © _*ZULAYHEART RANO*_ *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* *48* Da kyar ya janyo numfashin sa kafin ya gyara tsayuwa yana ci gaba da sauraren maganar Aneesa "Rukky wallahi bazan ɓoye maki ba ina cikin damuwa wacce ta amsa suna damuwa, ɗazun bayan Dr ya fita na sai nima na fita domin dama ina son komawa wajen Dr ya dubani, a halin da ake ciki so nake na samu ciki amma kin san ne Dr Ashrab yake faɗa min?" Daga can bangaren Rukky ta amsa da "A'a." Aneesa ta ci gaba cikin raunin murya "cewa ya yi mahaifata ta yi rauni dalilin magungunan da na rika sha ba za ta iya rike ciki ba." Wannan karon da kuka mai sauti ta gama maganar. "Ki yi hakuri Anee kuma ai wannan ba wani abin damuwa ba ne da har za ki rika tada hankalin ki..." "Dole na tada hankali Rukky duk ke ce silar shigata duk wata matsala, yanzu ga abin da ya faru na yi nadamar bi yewa shawarar ki..." Tana gama faɗin haka bata jira jin me Rukky za ta faɗa ba ta kashe wayar. Tana ci gaba da kuka. Dr dake tsaye ya share zufar da ya tsatsatsafo masa "Lallai ina cikin masifa da jalala, Aneesa kin cuci kanki yanzu ga abin da ya faru dole ya dau mataki kan Ameesha, domin ba zai taba bari ta yi wa kanta illa irin ta Aneesa ba." Ransa a matukar ɓace ya bar kofar, sai da ya shiga mota kafin ya kirata bayan ya danne duk wani abu dake ransa. Ringing biyu ta dauka cikin muryar kuka "Hello Hamman." Shi ne abin da ta iya faɗa. "Aneesa lafiya kuwa na ji muryar ki kamar wacce ta yi kuka?" "Lafiya lau sai dai ciwon kai ne ya dameni, amma nasha magani." "Ok dama na kira ne in sanar maki ki sameni a asbiti yanzu." "To." Ta amsa jiki a sanyaye. Cikin mintinan da ba zasu gaza talatin ba Aneesa ta gama shiryawa, doguwar riga ta sanya ta yafa babban gyale, wayarta kawai ta rike a hannu sannan ta nufi asibitin Dr Asmad, bata dauki mota ba sai fita ta yi ta hau a dai dai ta. Mitina goma ta isa asibitin daret ofishin Dr ta nufa nocking ta yi daga ciki Dr ya bata umarnin ta shiga, shiga ta yi tare da yi masa sannu sannan ta zauna suna fuskantar juna. Sun yi kusan minti biyar a haka idon Dr a kan fuskar Aneesa yana kallonta da nazarin yadda zai fara mata magana. A jiyar zuciya ya yi tare da ambaton sunanta "Aneesa." A ɗan razane ta amsa da "na'am." Muryarta na rawa. "Lafiya kuwa?" Ya jefa mata tambaya." "Lafiya lau Hamman." "Ok dama ina son in duba ki ne..." "Duba Ni Dr? Ai lafiya ta lau." Ta yi saurin katse shi. "Eh na san lafiyar ki lau amma ya zama dole na duba ki Aneesa saboda har yanzu tun bayan aurenmu ban ji alamar ko da ɓatan wata kin yi ba, kin ga ya kamata na duba ki domin gane ko akwai wata matsala." "No! Dr ka barni kawai lafiya lau nake ciki kuma Allah ne bai kawo ba, mu ci gaba da addu'a har Allah ya kawo." Ta dire maganar tana kokarin mai da hawayen ta. "Na san lafiyar ki lau Aneesa amma ki bari na duba ki." Da kyar ya shawo kanta har aka yi mata komai, jikin Aneesa ban da tsuma babu abin da yake don tsabar farga, ta sa a ranta matukar Dr ya gane gaskiya zamanta ya kare a gidansa nan da nan sai zazzafan zazzaɓi ya saukar mata. Taimakon gaggawa Dr ya bata sannan bacci ya dauketa. Dr Asmad na zaune ya zuba mata ido cike da takaicin halinta Nurse ta yi nocking, jiki babu kwari ya bata umurnin shigowa, mika masa result ɗin da aka yi wa Aneesa test ta yi. Zuciyarsa ta tsinke lokacin da ya yi karo da irin bayanin da Aneesa kewa kawarta a waya ce ya tabbata, sosai ya yi takaici da ganin sakamakon haka. A dana takaddun ya yi don baya son ta san ya san sanadin rashin lafiyar mahaifarta. Bayan ta farka tea ya Bata da magunguna lokacin biyar har da rabi don haka suka nufi gida, duk yadda ta so ta karanci wani abu game da shi abin bai yiyu ba, ganin har sun shiga gida da kansa ya haɗa mata ruwan wanka da abinci, suna zaune a falon Aneesa ta yi kasa da kai ta ce "Hamman wai me ke damuna ne, har yanzu baka ce min komai ba?" Murmushi ya tattaro don baya son ta ji komai, ya ce "Haba Anee me kike son sa ni bayan wanda kika sa ni kuma?" "Wanda na sa ni Hamman?" A razane ta yi tambayar. "No! Ke kina da saurin daukar zafi, bana son ki tayar da hankali domin baki da matsalar komai kuma rashin samun ciki lokaci ne, da zarar lokacin ya yi za ki samu ki kwantar da hankalin ki kin ji Anee." Da sigar lallashi ya yi maganar. Ganin yadda ya yi maganar yana lallashinta sai ta ɗan saki jiki. Haka dai rayuwa take tafiya musamman ta bangaren Aneesa da yanzu damuwarta ta ɗan ragu. Yau dai Dr ya dau aniyar komai rintsi sai ya ga matarsa, domin a halin da yake ciki baya jin zai iya kwana a yau ba tare da ya yi arba da Ameesha ba, don haka cikin sauri ya yi wanka ya shirya cikin kananan kaya jeans da T-shirt kayan sun yi masa kyau sosai sai zuba kamshin turare ya ke. Key ɗin motarsa ya ɗauka sannan ya fita daret gidan Nenne ya nufa yana addu'ar Allah yasa Nenne bata gidan, ko sallama bai yi ba ya shiga falon. "Hee ya dai?" Nenne ta yi maganar ganin yana niyyar bude kofar. Dan sosa keya ya yi cikin jin kunya kafin ya dawo baya tare da zama kasa kusa da Nenne yana faɗin "ina wuni Nennena?" "Lafiya lau." Ta amsa tana jifansa da kallon tuhuma. Kara kasa ya yi da kai ya ce "don Allah Nenne ki yi hakuri ki barni na ga Ameesha please." "Ka ga Ameesha? Sai yanzu kasan da zamanta?" "Hakuri nake kara baki." "To ban amsa hakuri, tashi ka bani waje." Da fada ta yi maganar. Kin tashi ya yi ya zauna sai magiya ya ke mata amma ta ki ko da kallonsa. **** Watan cikin Ameesha biyar kenan, har ya fito ya yi mata das da shi gwanin sha'awa, jikinta ya murje sosai ya yi kyau irin ta masu ciki, sanye take cikin doguwar riga wanda suka amshi jikinta ta yi matukar kyau da ka ganta kasan bata da matsala, cikin nutsuwa take takawa har ta fita falon ganin Nenne sai ta shagwaɓe fuska, sam bata kula da wani Dr ba duk kamshin turaren sa ya cika falon hakan bai sa ta yi tunanin shi ne a ciki ba. Don haka sai ta ce "Nenne ashe kina falo shine ba ki tasheni ba gashi har an gama dadin kowa." "Wayyo mantawa na yi Autar Ummi." Turo baki ta yi tana zama kusa da Nenne. Dr kuwa tunda Ameesha ta fito ya zuba mata ido kamar wani mai son gano wani abu, ya cika da mamakin yadda ta sauya, idan ma ba gizo idonsa ke masa ba sai ya ce ciki ne da ita. Sosai ya lula duniyar tunani, muryar Nenne ce ta sanya shi juyowa "Tashi Autar Ummi ki ɗauko abinci ba ki ci komai ba fa." "Nenne na koshi ne." "Oya tashi bana son musu je dauko, kuma fa abin da kike so ne na yi maki." Ai da sauri Ameesha ta tashi ta nufi kicin, da kallo Dr ya bi ta kamar wani maye har yana hadiyan miyau ya ke har ta shiga "ba za ka tashi ka tafi bane dare na yi fa." Nenne ta tsinka masa tunani. "Eh, Nenne yanzu zan tafi dama." Ya dire maganar yana sosa keya. "Mik'ewa tsaye Nenne ta yi tare da nufa hanyar bangaren Bobbo tana faɗin "ka gaida Aneesa." "Za ta ji." Ya bata amsa yana dan sakin murmushi, yana ganin ta shige ya nufi hanyar kicin, Ameesha ta bude firij zata ɗauki C-way Apple sai ji ta yi an rungumota bude baki ta yi tana niyyar kurma ihu, Dr ya yi saurin toshe mata baki ya rada mata cikin kunne "Cutie ni ne fa yi shiru." Wani irin yanayi ta shiga da jin muryar Dr, duk da sai ta soma kokarin kwace kanta, amma sam ta kasa. Ganin ta ɗan nutsu ne ya sanya Dr sanyaya murya ya ce "Wai Cutie ba za ki koma gidana bane?" Ya yi maganar yana sassauta rikon da ya mata, wasu hawaye ne suka taru a cikin idonta, ganin haka Dr ya girgiza kai alamar kar ta bari su fito. Murya na rawa ta ce "Please baby ka yi hakuri ka yafe min..." Saurin sanya bakinsa ya yi cikin nata, don ba ya son ya ji abin da zata faɗa sai da ya tabbatar ta samu nutsuwa ya sakin bakin "Kar ki kuma cewa komai Cutie kin ji na yafe maki." Murmushi ta yi har tana kara rungumarsa ta manna masa kiss a kumatu. Hannu ya kai saman cikinta yana taɓawa a hankali ya ce"Cutie wannan menene?" Cikin kunya ta sadda kai kasa ta kasa furta komai. Ganin yadda ya yi ya sa ya yi sujadar shukur a fili ya bayyana "Alhamdulillah! Cutie dama kina dauke da cikina kika bari har zargi ya shiga tsakanin mu? Me yasa baki fargar da ni ba?" "Baby kai ne ka ki saurarata, kuma ni ma ban san da shi ba sai da Hafiz ya dubani." "Hafiz? Kina nufin yasan da cikin?" "Eh." Ta amsa tana murmushi. Kara matseta ya yi yana kara jin kaunarta yana shigarsa "I love You Maryerm." "I love You to Dr Asmad." Ameesha ta yi maganar cikin murya mai sanyi. Sun daɗe rungume da juna kafin Dr ya ce "Baby mu je ki ci abinci bana son ki bar min yarinya da yunwa." Daukar ta ya yi daga ita har kayan sam ya manta da wata Nenne a kan dining ya yi mata masauki. Da kansa ya rika ciyar da ita har ta koshi, bedroom ya kaita lokacin karfe goma har da mintina "Cutie zan tafi ko za ki bini?" Zaro ido ta yi waje ta ce "Ina zan bika baby?" "Gidanmu mana." Girgiza kai ta yi da sauri ta ce "a'a Allah ya kaika lafiya ina nan." "Please mana Cutie." Ya yi maganar yana jawota jikinsa, kafin ta yi wani yunkurin har Dr ya soma fitar ta nutsuwarta domin sako yake bata da zafi zafi. Sun dau lokaci a haka sannan Dr ya sassauta mata rikon bayan ya samu nutsuwa, kwantar da ita ya yi tare da lulluɓa mata blanket yana fadin "Cutie ki kular min da kanki da babyna ina son ku." "Kar ka damu baby za ka sameni yadda kake so." Kiss ya manna mata a kumatu sannan ya gyara mata sumar kanta da ta barbaje ya ce "Sai da safe." "Amin baby Allah ya kiyaye hanya." Idonta a lumshe ta yi maganar sam sai ta ji bata kaunar tafiyar Dr, tana jin ya buɗe kofa ya fita ta saki ajiyar zuciya tashi ta yi ta nufi toilet sai da ta yi wanka sannan ta gyara jikinta ta kwanta bakinta ɗauke da addu'a. A daren da Dr ya koma gida yake sanar da Aneesa cikin dake jikin Ameesha, da farko ta shiga shock amma da ta tuna duk abin da ya faru ita ta jawo sai kawai ta taya Dr murna, sai dai ta ji haushin yadda Dr ya mai da maganar cikin Ameesha wani babban lamari, baya magana daya sai ya yi maganar cikin, musamman ya dauketa ya kaita ta duba Ameesha a ranar kam da bakin ciki ta kwana don sai ta ga kamar Meesha na yi mata wani irin kallo na rainin wayau don tana da ciki ga wani uban sangarta da ya fi na baya, Dr da Nenne sai biye mata suke, nadamar abin da ta aikata ne ya shige ta sosai tabbas tasan ta yi kuskure mai tsanani da yanzu tarairayar da ake wa Ameesha a bayan tata yake. Yau juma'a kuma a yau Dr yake muradin matarsa ta koma gidansa, shi ya sanya tun biyu ya baro office, Allah ya sa Bobbo na gida don haka bayan sun gaisa sai Dr ya yi kasa da kai cikin ladabi ya ce "Bobbo don Allah a taimaka min a bani Ameesha." Harara Nenne ta aika masa da ita. Shi kam Bobbo murmushi ya yi ya ce "haba Asmad ai Ameesha matarka ce don haka ko yanzu kana iya tasa ta gaba ku koma gidanku." "A'a Alhaji sai ta haihu zata koma." Na yi ta yi saurin katse Bobbo. "A yi hakuri dai Hajiya." Sam Nenne ta ki yarda da kyar suka shawo kanta da sharadin duk abin da ya samu Ameesha za su ji a jikinsu. Take Dr ya amsa zuciyarsa cike da farin ciki. Bobbo da Nenne faɗa sosai da nusiha suka yi masu Ameesha sai aikin kuka take sam bata son rabuwa da Nenne, amma ya zata yi dole ta koma gidan aurenta ko a mota sai sharan hawaye take Dr na aikin lallashi, da kansa ya dauketa bayan ya yi fakin motar su a falo ya yi mata masauki "Cutie KE fa yau amarya ce, bari na samo maki wani abin ki yi wanka kafin na dawo." "A dawo lafiya." Ta yi maganar cike da kulawa. Da farin ciki Dr ya bar bangaren, tana ganin ya fita ta nufi bedroom ɗinsa duk inda ta kai hannu sai ta ji k'ura don haka cikin sauri ta soma tsaftace bangaren nata, duk watannin da ta yi bata gidan yadda ta tafi ta barshi haka ta dawo ta taras. Cikin lokaci ƙalilan har ta gyare ko ina na bangaren ta turare shi da turaruka masu sanyin kamshi, sai dai ta mugun gajiya shi yasa ta zube a falo ta kasa ko da motsin kirki, a haka Dr ya sameta. Sosai ya cika da mamakin aikin da ta yi, faɗa ya soma mata akan ba ya son tana wahalar da kanta, ban da murmushi babu abin da take, shi ya taimaka mata ta yi wanka ta shirya cikin rigar bacci, shi ma wanka ya yo ba yan ya kammala shiryawa cikin kayan bacci sai ya soma ciyar ta har sai da suka koshi, wanke baki suka yi kafin suka kwanta a wannan rana sun nunawa juna zallar sosai da kewar da suka yi na juna, ba su samu kansu ba sai daf da asbah sannan bacci mai nauyi ya ɗauke su. Rayuwa mai daɗi ake a gidan Dr Asmad, zuwa yanzu dai Aneesa ta rage zafin da ta dauka da Meesha domin yanzu har zuwa take bangaren Ameesha su gaisa. Hankalin Dr akwance ba ya da wata mata, babban burinsa shi ne yaga Ameesha ta sauka lafiya don cikinta ya shiga watan haihuwa kuma ko da yaushe tana iya zuwa. Kamar kullum suna zaune suna hira duk da yau Dr ba a bangaren ta yake ba ya zo mata sallama ne, duk hiran da suke dauriya kawai ta ke domin tun safe take jin alamar ciwo sai dai ba ya wani matsa mata shi yasa ba ta damu ba amma yanzu abin yana neman ya yi yawa, Dr ya kula da halin da take ciki tun shigowar sa zama ya yi tare da riko hannunta ya ce "Cutie an ya yau kam lafiya?" "Me ka gani baby?" "Komai ma na gani haihuwa ce gata nan." "Hmmmm! Baby kenan wai haihuwa ce to ina kaga haihuwar?" "Wajen autar Ummi." "A'a ni kam babu wata haihuwa haba haihuwar kamar wani shan ruwa Allah babu komai." Gyada kai Dr ya yi badan ya yadda da maganar ta ba, mik'ewa ya yi don ya sanar da Aneesa halin da ake ciki kar ta ji shiru, yana fita jikin Ameesha ya hau tsuma ciwo wanda tun da take bata taɓa ko da jin irinsa ba ya taso mata gadan gadan, ji take mutuwa zata yi zufa kawai ke karyo mata ko ta ina sunan Allah kadai take iya ambato, a haka Dr da Aneesa suka sameta da sauri Aneesa ta matsa tana yi mata sannu wannan shi ne karon farko da Aneesa ta ji tausayin Ameesha. Da sauri Dr ya kwaso kayan aiki nan ya shiga bata taimako yana yi yana addu'a, aiko cikin nasara sai ga kan jaririya ya fita. "Alhamdulillah! Suka faɗa kusan a tare. Murna wajen Dr ba a magana da kansa ya gyara yarinyar da uwarta, Aneesa kuma ta gyara wajen tsaf babu mai cewa a wajen aka haihu, sai tashin kamshi wajen ke yi. Shayi mai kauri Dr ya haɗa mata sannan ya yi mata allurai, Aneesa kam na rungume da babyn wani irin soyayyar babyn na shigarta har sai ta ji bata kaunar a raba su. Sai da Ameesha ta huta sannan ta yi wanka, bayan ta fito ta shirya kai ka ce ba ita ce ta haihu ba don yadda ta yi kyau abinta, Aneesa matsawa ta yi kusa da ita tana faɗin"Ameesha amshi yarki ta ji duminki ki ji nata ta haka ne zata taso da soyayyar ki tare da tausayinki. Murmushi Ameesha ta yi ta ce "Dama babban burina in haifi mace, ya kasance ke ce mace ta farko da zata fara rungumarta kuma Allah ya amshi addu'ata domin ke ce uwarta Aneesa har gaban abada bana son yarinyar nan tasan ni ce na haifeta." Ta gama maganar daidai da shigowar Dr daga shi har Aneesa mutuwar tsaye suka yi da jin kalaman Ameesha, Aneesa kasa motsi ta yi sai Dr ne ya yi karfin halin cewa "ke kina da hankali kuwa yarinyar tawa za ki yi min kyauta da ita dawa kuka yi shawara to wallahi ba ki is..." To fa! Yau fa ake yinta. Ga Ameesha daga haihuwa ta yi kyauta da yarinya shi kuma Dr Asmad ya ce bai san wannan ba, ya kuke ganin zata kaya? Ku bi Yar Mutan Rano a hankali don ta warware maku, a yi hakuri kaɗan ya rage in sha Allah. I hearttttt You fisibilillahi😘 *YAR MUTAN RANO* *SANGARTA* © _*ZULAYHEART RANO*_ *SADAUKARWA* *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* _*Wow Masha Allah hakika na ji dadin comment ɗin ku, hakika ya sanya Ni nishaɗi ku ci gaba da ina son comment dinku hakan ya nuna min kuna bibiyar labarin sosai, masu korafin cewa Ameesha ta yi wauta da ta yi wa Aneesa kyautar 'yarta ku sa ni cewa ba wauta Ameesha ta yi ba, domin rama Alhairi ga mai sharri ba illah ne ba, ko ni zan iya fiye da abin da ta aikata.*_ *49* "Yau kuma sangartar ne da wauta ya fado kanmu ni da ɗiyata?" Turo baki Ameesha ta yi ta ce "Babu wani wauta ni dai wannan maganar har cikin zuciyata na yi ta ko bayan babu raina Aneesa zata riki 'yar na..." Saurin rufe mata baki Dr ya yi cikin sauri ya ce " ki bar yi min wannan mummunar fatan in sha Allah babu maganar mutuwa yanzu sai kin haifa min 'ya'ya goma sha biyar." Zaro ido ta yi ta ce "Sha biyar? Tab sannu baby ai mutuwa ta Allah ce idan lokaci ya yi babu makawa." Kasa furta komai ya yi sai kallonta yana matukar mamakin maganar ta. Wani kallo ta aika masa da shi wanda ya sanya jikinsa mutuwa murus, shi sai yaga kamar ba Ameeshar sa ba, duk lokacin da suka hada ido sai yaga murmushi ne kwance a fuskar ta wanda ya kara fito da zallar kyaunta, "Cutie kin yi kyau da shayarwa fa." Ya yi sauri kawar da wan can maganar."Babu wani kyau ni kuma zafi nake ji baby." "Kwantar da hankalinki ki saba tukun, idan na fita zan shigo maki da magunguna wanda za su rage maki zafin." "Tom kafin na saba da aiki, ka fadawa Nenne kuwa?" "Eh! Har da su Ummi sai dai na manta ban fadawa Meena ba." "Ok bari na kira ta har da k'awata Ni'eema Allah yasa tana gari." Ta ida maganar tana lalubo wayar. Amsan babyn ya yi a hannunta, tare da zuba mata ido "Cutie Wai yarinyar nan da wa take kama?" "Yo Ina zan iya bambance wa kasan jarirai rikida ne da su, amma kamar tana kama da Autar Ummi." Ta karasa maganar cikin sigar tsokana. "A'a da Autan Nenne ta ke kama Malama." Dariya suka sake gaba daya kafin su yi wata maganar Aneesa ta yi sallama, hannunta rike da plet na farfesun kayan ciki. "Ki fara cin wannan kafin na yi maki girki." Amsa Ameesha ta yi tana faɗin"Na gode." Idonta akan Aneesa don gani ta yi kamar ta yi kuka. Sai dai bata yi magana ba ta soma shan farfesun suna dan taɓa hira. Kwantar da jaririyar Dr ya yi ya fita. "Wai Yar'uwa kuka ki ka yi ko?" Ameesha ta yi tambayar tana ci gaba da shan farfesun ta. "A'a ban yi kuka ba mai kika gani?" "No! Ban ga komai ba, amma yana da kyau komai a rika fawwalawa Allah shi zai kawo karshen damuwa." "In sha Allah ina godiya." Tabbas Ameesha ta yi gaskiya domin ba karamin kuka Aneesa ta yi ba, nadama sosai ya shige t da yanzu ita Dr ya fara yi wa hidima, tana ji Dr har kyautar sabuwar mota ya yi wa Ameesha dalilin haihuwa, lallai ta cutar da kanta. Cikin hiransu sosai Aneesa ta fahimci wasu daga cikin halayyar Ameesha kuma ta tabbata mutum ce ita mai sanyin hali da cikakken imani, tana yi wa 'yarta fatan ta dauki halinta na karamci. Mik'ewa ta yi tana faɗin kin ga "bari na je na dafa maki abu mai dan nauyi yadda baby zata samu ta koshi. Tana mik'ewa Meena tana yin sallama, sai da suka gaisa kafin ta fita. Fitar ta babu jimawa Dr ne ya shigo hannunsa dauke da ledoji irin ta pamarcy Ameesha ya mik'awa yana faɗa mata yadda zata yi amfani da shi, sannan ya amshi yariyar a hannun Meena har tana tsokanarsa "Oh! Yau ga ɗiyar sangartacciya Ameesha a hannun Dr! Dariya ya yi ya ce "Meena kar ki ta do min baya yanzu dai ita kanta ta shaida ta girma sangarta sai a barwa yara. Harara kawai Ameesha ke aika masu, Meena fita ta yi ta bar Dr dauke da 'yarsa yana mata addu'a bayan ya gama ya dubeta tare da ya ce "Cutie kin ga kyautar da Allah ya yi mana wanda babu mai iya bamu sai Ubangiji sai mu godewa Allah." "Alhamdulillah! Ta furta cikin sanyin murya. "Yanzu wani suna kike son a sanya mata?" "Bani da zaɓi bari Aneesa ta shigo." "Ok." Ya amsa yana ci gaba da kallon yarsa. Cikin kananun lokaci har ta kammala girkin da taimakon Meena cikin babban tire suka shiryo. Da sallama ta shiga dakin ta aje tana faɗin "Hamman Baban baby Sannu da hutawa, Yar'uwa sannu." Yawwa suka amsa a tare, zuba mata abincin ta yi ta mikawa Ameesha. Dr ya dubi Aneesa cikin kulawa ya ce "Uwar 'ya wane suna za a sanyawa ɗiyar taki?" "A'a tambayi Yar'uwa duk wanda ta zaba ya yi min." "A'a zaɓa dai Yar'uwa na baki dama." "Tom ina godiya da wannan dama a sanya mata sunan Nennena." Dariya Dr ya yi ya ce "Babban BURINA kenan to Allah ya raya mana FATIMA BINTA." Take ya yi mata huduba ya kalli Aneesa yana faɗin. "To kuma ya lakabin ta?" "*(Miemie)*." Zamu rika ce mata. Ameesha dai tana gefe sai murmushi take dokawa, yau abin masha Allah daɗi yake mata tana fatan Allah ya dauwamar da su cikin farin ciki mai dorewa. Babu jimawa Nenne suka iso kamar haɗin baki su Ummi ma suka zo, gida ya cika da murna babu kamar Nenne da ta samu takwara. Haka suka ci gaba da zama kullum gidan cike da masu zuwa barka, har ranar suna ya zagayo inda aka yi gagarumin taro wanda ya amsa sunan sa, an ci an sha an yi komai cikin kwanciyar hankali, su Nenne sun taka muhimmiyar rawa haka ma Hafiz da yan gidan su sun yi hidima sosai wa Ameesha da yarta. Bangaren gidan su Ameesha ma sosai aka yi hidima. Ba a bar Aneesa a baya ba ta yi bajinta sosai wanda ya ba wa kowa mamaki ciki har da Dr, domin akwati guda ta yi ma Ameesha da diyarta. Haka dai taro ya tashi lafiya Ameesha ta ci gaba da kula da Miemie yarinya mai kama da ubanta sak, idan kaga Miemie a wajen Ameesha to abinci aka kawota ta ci amma wajen Aneesa take wuni komai ita ke mata, zaman su abin burgewa da sha'awa. Yanzu watan Miemie biyu ta yi wayau sosai abinta gwanin sha'awa gata tubarkallah. Sai dai fa Allah ya yi Miemie da shegen rigima, kullum kuka har asbiti suka je aka tabbatar lafiyar ta lau, sosai kukanta haushi yake ba Ameesha, Aneesa kaɗai ke iya lallashinta. **** Kaiwa kawai yake yana komowa a cikin katafaren falonsa , hannunsa rike da waya yana kiran amininsa Alhaji Mamman "Hello ina jiran ka cikin gidana dake bayan gari." Daga haka ya katse wayar yana jero tsaki marasa adadi, ban abin da yake so a yanzu sai dai ya samu mafita domin kullum tsanar Alhaji Taheer gaba yake a zuciyarsa. Ba a jima ba Alhaji Mamman ya iso, gaisawa suka yi ya bashi ruwa don tsabar tashin hankali kasa ce masa komai ya yi sai girgiza kai da yake irin dai yana cikin muguwar damuwa Alhaji Mamman ya muskuta tare da cewa "Wai Alhaji Mansur ya maganar ka da Alhaji Taheer ne?" A jiyar zuciya ya sauke mai karfi kafin ya yi karfin halin cewa"Yo wane amsa zan baka ai Ni kam Taheer ya zame min ciwon ido na rasa ya zan yi da shi, wannan shashashan da matarsa ta haihu ko shawara dani baiyi ba ta sanyawa 'yarsa sunan mahaukaciyar yar Taheer wannan abu ya min ciwo amma akwai shirin da nake masu." " Gaskiya dai ka dage don kullum abin gaba yake kayan da ake shigo masa da shi har sun haura na da, ga yar tashi ma ta haihu ba kaga irin dukiyar da suka kashe ba." "Kai dai zuba ido ka yi kallo kidnapped ɗinsa zan sa ayi, kila ko tanan ma samu rabonmu." "Wannan gaskiya ne, yin haka shi ya fi maka." Haka dai suka ci gaba da hira Alhaji Mansur yana ci gaba da bayyana munanan manufofin sa akan Alhaji Taheer. Kwanci tashi babu wuya wajen Allah har Miemie ta yi shekara a duniya, yarinya mai shegen wayau tasan kowa na gidan, bata saba da Meesha da Dr ba kamar Aneesa komai Momma haka take faɗawa Aneesa, Ameesha kuma Mami Dr Kuma Daddy, tun tana da wata bakwai a duniya ta soma tafiya magana kuwa kamar wacce ta hadiyi rediyo, wani lokacin har mamakin wayanta suke yi. Meesha ce kwance idonta lumshe kamar mai bacci, Miemie ta kwaso da gudu ta faɗa kanta tana faɗin "Mami tashi." "Oh! Allah Miemie ke kam ba ki son na huta idan na tashi mai zan yi maki?" Aneesa dake zaune a falon ta saki dariya tana faɗin " ke kuwa Yar'uwa tashi mana ki ji me zata faɗa maki." Ta shi ta yi zaune hannunta dafe da goshinta, ta ce "wallahi kaina ciwo yake." "Ayya sannu." "Yawwa ina za ku je ne haka?" Da sauri Miemie ta ce cikin Hausar ta mara fita "gitan Nenne ta mu je." "Shi ne ko ku faɗa min na shirya?" "A'a yi zamanki wannan baccin da ya sarface ki a kwanakin nan bana jin zai barki zuwa unguwa." "Hmmmm! Ki dai bari Yar'uwa wallahi kamar mai cutar bacci haka nake jina, sam na rasa gane kaina ɗazun indomie zan dafa daga daura ruwan zafi kafin ya yi zafi na dawo falo wallahi bacci ya dauke ni, in da Allah ya rufa min asiri ruwan bai kai ga kone wa ba na farka." Murmushi Aneesa ta yi ta ce "Bari Hamman ya zo ya kamata ya duba ki wannan sleeping ɗin ba na lafiya ba ne." Zaro ido ta yi ta ce "A'a nikam lau nake bacci ne kawai Allah ya kawo bari ma ki ga na tashi." "Za ki ga lafiya Yar'uwa mu dai Ni da babyna mun ce Allah ya inganta." Tana dire maganar ta suri Miemie suka fice, ya yin da suka bar Ameesha cikin mamaki. Bata bar mamaki ba har zuwan Dr bayan ya gama cin abinci ya fara tambayarta ko me ke damunta, a sanyaye ta ce "ɗazun Aneesa ta yi wata magana kamar nufin ta ciki ne dani." "To kuma shi ne abin damuwa?" "Haba beby ciki tun yanzu wallahi haihuwa da wahala duka yaushe na haifi Miemie?" "Kwantar da hankalin ki Cutie Yi addu'a Allah ya baki nagari, domin ciki ya tabbata a gareki har na wata biyu." Kara zare ido ta yi da jin maganar Dr ta ciki? Ai ni sam ban ji wani alamomi ba sai bacci kamar wata mai cuta." "Baccin shi ne alamar da ya kamata ki gane, nikam tun bai kai wata ba na fahimci ajiya ta don wannan karon ban yi sake ba." Fuska dauke da murmushi mai nuna zallar farin ciki da jin dadi Dr ya dire maganar. Ameesha kam kasa cewa komai ta yi sai kallon Dr da take yi. Mu je zuwa dai an zo final in sha Allah. *YAR MUTAN RANO* [10/27, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA* ® _*ZULAYHEART RANO*_ *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* *50* Haka ta wuni sukuku har su Aneesa suka dawo, a falo suka sameta kwance Miemie da sauri ta faɗa kanta tana faɗin "Mami min dawo." "Sannu da dawowa 'yar Momma ya Nenne?" "Lafiya lau tana gaidaki." Aneesa ta bata amsa. "Ina amsawa." Ta amsa a takaice "Wai har yanzu ciwon kan ne?" "A'a me kika gani?" "Babu komai kawai na ga kamar ba ki cikin nutsuwa?" "Ki bar kawai wallahi ɗazun bayan fitar ku Dr ya tabbatar min ina da ciki har tsawon wata biyu." "Shi ne abin tashin hankalin?" "Eh mana duka shekarar Miemie daya fa gaskiya ba haka na so ba." "Hmmm! Yar'uwa kenan wallahi wannan ba abin damuwa ba ne ki bar tada hankali ki yi addu'a Allah ya sauke ki lafiya, idan ta Miemie ne ba abin damuwa ba ne saboda Miemie tana cin komai tana tafiya kuma bata damu da nono ba." "To ya zan yi dole ai na hakura Allah ya bamu masu albarka, Miemie kuma yanzu zan hado mata sauran kayanta dake dakina ku karata can, dama kun saba Allah ya raya maki ita." "Yar'uwa kina nufin kin yaye Miemie kenan?" "Eh, ta koma dakin Momman ta dama tun da ta zo duniya take ɗiyar Momma to yau Allah to yau Allah ya tabbatar." Ameesha ta gama maganar tana mik'ewa tsaye. Rasa abin da zata faɗa Aneesa ta yi don sosai abin ya bata mamaki, wato kyautar da Ameesha ta yi mata na Miemie tun ranar da ta fado duniya gaske ne? Lallai ta jinjina da karamci irin nata da zallar farin ciki da murna ta ce "Na gode sosai Ameesha Ubangiji Allah ya baki abin da kike nema duniya da lahira, wallahi da ana samun kishiya irin ki da ko wacce mace zata so a yi mata kishiya hakika ke kin bambanta da sauran mata, na cutar da ke Ameesha na mugunawa rayuwar ki amma duk da haka ke kullum da Alhairi kike nufina, a zatona tun da kin kasance shagwaɓaɓɓa idan kika auri Hamman za ki iya raba ni da shi ko dan salon SANGARTAR ki ashe abin ba haka ba ne, ki yafe min don Allah." "Na yafe maki Allah ya yafe mana baki daya." Ameesha ta faɗa fuska sake. "Na gode Allah ya saka da mafificin Alhairi, Ubangiji ya biya maki buk'atar ki ya sauke ki lafiya." Murmushi kawai Ameesha ta yi ta amsa amin "Allah ya ci gaba da bamu hak'urin zama da juna da zuciya daya." "Amin" suka amsa tare. Sannan ta nufi bedroom kaf kayan Miemie ta kwashe ta kai bangaren Aneesa, farin cikin da Aneesa ta shiga a ranar baya misaltuwa. Ko da Dr ya dawo ya samu labari dariya kawai ya yi ya ce "Allah ya taya ta riko, Ameesha na lura dama kamar baki damu da Miemie ba?" "Haba beby wannan wacce irin magana ce? Miemie fa 'yata ce bana jin duk duniya akwai wanda ya kaini sonta, amma ka duba hidimar da Aneesa ke yi wa Miemie wallahi ta cancanci kyautar Miemie, na bata da zuciya daya Allah ya kara haɗe kanmu." Rungumota jikinsa ya yi yana jin wani sabon soyayyar ta a zuciyarsa, bai taɓa ganin mai sanyin hali irin ta Ameesha ba, wallahi a time ɗin da suka fara haɗuwa da Ameesha a sahad bai taɓa tunanin tana da sanyin hali da tunani ba sai da ya mallaketa, kara matseta ya yi jikinsa ya ce "ina sonki matata so irin wanda bazai misaltu ba Allah ya yi maki albarka." "Nima ina sonka Dr Asmad Abubakar My fullo, Ina jinka har cikin zuciyata uban 'yayana, kullum fatana shi ne in faranta maka." Daɗi sosai ya rufe Dr jin kalaman da take faɗa masa, shi sai ya ji a duniya ya fi kowa sa'a. Sun daɗe a haka rungume da juna kafin Ameesha ta lankwashe murya tana faɗin "Beby wankan fa kalli time ga yi baka lek'a Aneesa da Miemie ba." "Oh! Wallahi har na manta, idan ina tare da ke manta kowa nake yi mu je ki yi min My wife." "An gama mijin mace biyu." Ta gama maganar da dariya. "Baki karya na autar Ummi ni ne mijin mace biyu Aneesa da Ameesha Baban Fatimah (Miemie)." Dariya sosai maganar Dr ya ba Ameesha don haka har suka shiga toilet din tana dariya. Sun ci gaba da gudanar da rayuwar su cikin jin dadi da kwanciyar hankali, har Allah ya sanya Ameesha ta shiga watan haihuwar ta, ranar wata Alhamis ta tashi da nakuda ga shi Dr baya gida, Aneesa ce ke ta taimaka mata amma fa sosai ta sha wahala fiye ma  da haihuwar Miemie sannan  ta haifi lafiyayyun yaranta biyu mace da namiji, tsaf Aneesa ta wanke yaran tare da shirya su cikin kayan sanyi masu taushi da kyau. Lokacin da Dr ya ya dawo Ameesha tana toilet, ido ya daura akan gadon ya ci karo da jarirai har biyu kwance akan gadon, matsawa ya yi fuska ɗauke da mamakin yadda Ameesha har ta haihu bai sani ba, karan buɗe kofar da ya ji ya sanya ya juya wayam ya ga cikinta baki buɗe yake kallonta, ita kam murmushi kawai take aika mas, doguwar a jiyar zuciya ya sauke yana faɗin "Cutie haihuwa kika yi shi ne ko ki sanar min in tari baby's ɗina da kaina?" "Sorry baby bayan fitarka babu jimawa sai nakuda, ni na hana Aneesa kiranka don can dinma aiki ka ke yi, kuma ka ga da sauki sosai tun da na sauka lafiya." "Madallah amma ban so yarana suka fito duniya bana kusa ba." Ya dire maganar yana isa bakin gadon. "Ai k'anwar ka ta amsheka domin ta yi aiki sosai Allah ya saka mata da Alhairi." "Amin.*" Dr ya amsa sosai ya cika da farin ciki kamar wannan ne karon farko da aka taba masa haihuwa, daukar yaran ya yi cikin zallar soyayyar su da kaunarsu, sai kiss yake masu take yama yaransa huduba da sunan Ummi da Abba. Wannan abu ya yi wa Ameesha daɗi, mutane sai tururuwar zuwa barka suke har ranar suna, an yi lafiya an gama lafiya, yara suna amsa HIBBAN DA HIBBA, Ameesha zaune tana shayar da Hibba ya yin da Hibban ke kwance  Miemie ta shigo da gudu ta k'arasa bakin gadon tare da kaima Hibban raruma a dole daukarsa za ta yi, da sauri Ameesha ta janye Hibban ɗin tare da kaima Miemie duka ba na wasa ba. Kuka ta saki aiko cikin sauri Aneesa ta shigo tana faɗin "Subhanallah Miemie me ya faru? Yar'uwa me ya sameta?" Harara Ameesha ta banka masu ta ce "Allah Yar'uwa ki faɗawa yarki ta kiyayi min yara yanzu fa Babana yana kwance shi ne ta zo zata daukar min shi bige mata hannu na yi." "Sorry yarinyata kin ji rabu da Mami kawai don zata ɗauki Hibban mu tafi unguwa  shi ne ki ta dokeki? Babu komai in kika kwantar da hankalin ki yanzu zamu bar maki gidan kuma ba bu inda zamu da Hibban ɗin." Ta karasa maganar tana daukar Miemie. "Hhh! Ku gaida su duk inda ku ka je za ku dawo ku samemu, Allah wannan yarinyar taki tana fama da sangarta." "Hmm! Yar'uwa yanzu duk SANGARTAR Miemie ta kai ki?" "Ta ma fini ki tambayi Ummi ki ji." "Umm ki faɗawa wasu amma mukam mun sa ni don haka sai mun dawo." "A dawo lafiya." Ameesha ta faɗa tana kwantar da Hibban ɗin. Fitar su Aneesa gidan Nenne suka fara zuwa sun daɗe a can bayan la'asar suka fita dan zuwa gida, suna cikin mota Miemie ta ce "Mommana ice-cream." "Ok mu je gida akwai." "A'a Mommana ni dai ice-cream ki ciya min yanju." "Kai Miemie kin fiye rigima mu je." Kwana ta yi ta shiga wani super market ice-cream din ta saya mata robobi biyar sannan suka nufi wajen biyan kudi Aneesa tana biyan kudin Miemie ta fice ba tare da ta sa ni ba, ta gama biyan kudin ta duba bata ga yarinya ba cikin sauri ta fita wajen mota, sai dai me babu Miemie take hankalinta ya tashi ta koma ciki tana sanar da ma'aikatan wajen ba taga yarinya ba, su ma nan suka fara duba wa amma duban duniya babu Miemie babu alamar ta, tuni Aneesa ta barke da sabon kuka dama tuni ta fara, zaman dir shan ta yi a wajen ita sai an nemo mata yarta, duk lallashin da suka mata ta ki yadda. Da kyar ta yadda ta nufi tafiya wanda sam ta kasa yin direban da kanta ga uban jiri idonta ya kumbura sun tun saboda kuka har bata iya buɗe su, babban tunaninta ta yadda zata tun kari Ameesha da Dr ita kuwa mai zata ce masu, sai sabon kuka a haka suka isa gidan da kyar ta shiga bangaren Ameesha hawaye na shatata, Ameesha tana jijjiga Hibba ta koma bacci sai ganin Aneesa ta yi sosai hankalinta ya tashi musamman yadda idonta suka koma, da sauri ta kwantar da Hibba ta nufi wajen Aneesa tana tambayarta menene. "Yar'uwa Miemie! Miemie Yar'uwa." Shi ne kawai abin da take faɗa. " Miemie! Me ya sameta?" Wasu sabbin hawaye suka zubo daga idonta ta ce "a wajen sayan ice-cream ban ganta ba." "Baki ganta ba? Miemie ɗin?" A dan firgice ta yi maganar. " Eh, ta faɗa murya a dashe, Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un shi ne kalmar da Ameesha ke maimaitawa har ta ɗan samu nutsuwa waya ta dauko ta soma kiran layin Dr lokacin har ya shigo cikin gida, ɗauka ya yi ya ce "To gani nan har za a fara min waya." Cikin dariya ya gama maganar. Ba iya cewa komai ba sai kashe wayar ta yi har ya isa shigowa. "What! Dr ya fada da ya gama jin labarin da Ameesha ke ba shi tashin hankali sosai Dr ya shiga da jin ba a ga Miemie ba, a fusace ya nufi Aneesa tare da shako wuyarta tare da sakar mata wasu lafiyayyun maruka biyu wanda suka yi sanadin daukewar numfashin ta ya daura da faɗin "wallahi matuk'ar baki nemo min yarinya ba duk abin da na yi maki ke kika ja, tun farko irin haka na guda amma Ameesha kika na ce sai an bata dama mata da ba imani ne da ita ba ta ya zata iya kula da yar wata, da kanki Ameesha kika zubar min da ciki sannan kika ci gaba da shan magunguna har kika yi wa kanki illa, wannan ba matsala ba ce domin ko yanzu Allah ya nuna maki ishara ni, ki fito min da yarinya tun ban yi maki lahani ba." Da kyar Ameesha ta samu Dr ya saki Aneesa sai huci yake, Aneesa kam sam shakan da Dr ya yi mata bai dameta ba sai ciwon rashin Miemie, tana zaune a wajen hatta motsi kasawa ta yi sai kallinsu ita kadai ta san halin da take ciki, cikin lokaci kadan har maganar batan Miemie ya karede jama'a, Abba tuni ya kai sanarwa gidajen rediyo da talabijin har cikin jaridu, Dr kam sam ya rasa nutsuwa duk cikin su Ameesha ce kawai mai dauriya amma Aneesa kam bata da aiki sai kuka da sambatu, bata taɓa damuwa da bakaken maganganun Dr ba bata da wani buri sai na ganin Miemie kusa da ita, har aka kwana shiru babu labari. Nan fa hankula ya kara tashi aka duk'ufa addu'oi. **** "Hahaha." Dariya Alhaji Mansur kenan lokacin da su mugu suka kawo masa Miemie, kallon yarinyar ya yi ya ce "tabbas wannan jinin Alhaji Taheer ne, don haka da ita zan yi amfani wajen cimma burina." "Kai Alhajina gaskiya kasan kan tsiya yanzu wannan yar yarinyar ka sanya aka dauko maka na san dole hankalinsu ya tashi, kuma ko nawa ake bukata za su kawo." "Sosai kuwa ai na yi bincike ne akan son da suke mata, kuma idan muka dauko Alhaji Taheer akwai matsala amma kaga wannan bata sammu ba mu dinma bamu santa ba. "Ka yi farar dabara" tafawa suka yi cikin jin dadi. Number din Alhaji Taheer ya ba mugu ya ce maza ya kira shi ya faɗa masa ga jikarsa sun kama sai ya bada miliyan ashirin za su bada ita "yau kwanan ta nawa ma." "Eh Alheji kwanan ta uku, gaskiya a yi ayi domin gaba daya ta damemu da sangarta kuma ka ce mu rika bata komai, haka jiya ta ishemu da surutun tsiya sai da bobo ya kai ma bakinta duka." "Du me? Waye  ya baku izinin duka? To kar ku kara." "An gama oga." Ya fadi maganar yana dan nawa Alhaji Taheer kira. Lokacin yana zaune a cikin gida abin duniya ya dameshi sam ya rasa tunani daya sai jin kar'ar wayarsa ya yi, da sauri ya dauka ganin sabuwar Number Yana Addu'a Allah yasa sun ga Miemie ne, maganar da ya ji ya firgita shi amma cikin dakiya ya ce "Ku fadi in da za a kawo kuɗin nan da awa daya zan turo amma don Allah karku yi mata komai." Faɗa masa suka yi kafin ya yi wata maganar har sun katse layin. Dr ya kira yana faɗa masa yadda suka ce "Abba karka yi saurin tura masa kuɗin nan fa ka bari a yi bincike." "A'a zan tura Asmad zan iya kashe ko nawa in dai  Fatima zata fito mu ci gaba da addu'a." Cikin kankanin lokaci har su Nenne da Bobbo sun isa gidan Asmad su Ummi da Abba ma haka har da Meena. Kudi Alhaji Mansur ya mika ma su mugu ya sayo masu abin sha, aiko ya sayo har da kayan maye sun sha sun yi ta tutul, Miemie sai wasa take yi abin ta bata damu ba da ta gaji da zaman falon ta fita, suna kallonta don sun san babu mai shigowa gidan tunda akwai mai gadi kuma ba zai barta ta fita ba, kuma ma dai ai Miemie bata da wayan da zata gudu fitarta ya yi  daidai da zuwan Najeeb tare da Littel Ameesha sun zo gaida Abbansa domin kwana uku kenan yana zuwa gidan baya samunsa shi ne ya yake shawarar zuwa nan gidan domin duba shi, ido hudu suka yi da Miemie duk da bai taɓa ganin yarinyar ba sai jiya a Arewa 24 ana cigiyar sa sunanta makale da sunan Dr Asmad ya shaidata, da sauri ya rikota yana dube-dube don kar wasu su ganshi a hankali ya ce "ke ce Miemie?" Kai ta gyaɗa ta ce "ka kaini wajen Mommana..." *YAR MUTAN RANO* [10/27, 8:08 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*                                     ©     _*ZULAYHEART RANO*_ *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty* *LAST* _*Masha Allah! Alhamdulillah Ina matuk'ar godiya ga Allah da ya nuna min wannan rana da na kammala wannan littafi, ina cikin farin ciki mara misaltuwa*_ GODIYA *GODIYA MAI TARIN YAWA GA* *My Besty Khadija S Muhammad, hakika ina alfaharin samun ki a matsayin amintacciya, domin kuwa duk wani abu da aka gani cikin wannan labari ke ce silar shigarsa banza gaji da gode maki ba, Allah ta'ala ya saka maki da mafificin Alhairi ya bar mana zumunci har ya'ya da jikoki Allahumma amin.* ```JINJINA GA Ummyn Yusrah fan's group Bilkisu Bilyamin Novel's 3 Star Hausa Novel's Surbajo Hausa Novel's group Láifin wa? And sangarta fan's Khalisat Haydar Hausa Novel's Zama na amana 2 Hassan ATK Hussain ATK Umar Dalhat Kamala Minna Khadijah S Muhammad Fa'eeza S Muhammad Ummu Sayyid Ummyn Yusrah Amrah Auwal mashi (Princess Amrah) Ramlat Ar Manga (My me Dambu) Nafeesa Musa Ankerh``` Da sauran wanda ban lissafo ba. ```I hearttttt you my daughter Badeeyar Adam (beauty queen)```       *51* Daukarta ya yi ba tare da ya ce komai ba ya nufi motarsa, ciki ya sanya su suna ci gaba da wasa da Littel Ameesha kai tsaye gidan su ya kaita, Rufaida kanta ta yi mamakin ganin Miemie har ta kasa hak'uri ta ce "Honey wannan kamar yarinyar da ake cigiya ko?" "Eh! Ya amsa mata a takaice. "Please ki yi mata wanka ki canza mata kaya sai mu kaita gidan su." "Gidan su honey baka tsoro ace kai ka saceta?" "Ai Gara ace ni ne na saceta akan akama wanda ya saceta ɗin, amma duk da haka ya zama dole iyayenta su san wanda ya saceta." Ya gama magana tana dage kai wanda ke tsananin yi masa ciwo, tir yake da halin mahaifinsa na son abin duniya, wato ashe Abba zai iya hada kai a yi kidnapped din jikar amininsa? Lallai duniya tazo karshe Allah ya rabamu da son zuciya. Cikin kananun lokaci har Rufaida ta tsaftace Miemie ta shiryata cikin wata kyakkyawan doguwar riga mai kyau da tsada sosai yarinyar ta yi kyau da yake har kitson kanta ta canza mata sai ta fito fes, suna rike da hannun juna ita da Littel suka shiga mota, sai da suka biya suka ɗauki mommy sannan suka dauki hanya a tsanaki yake tuki har  suka isa unguwar. Horn ya yi a kofar gidan mai gadi ya buɗe masa  parking ya yi yana hamdala da ganin motar Abban Ameesha a gidan, hakan ya nuna cewa yana cikin gidan kenan, bayan ya faka motar bai fita ba sai ya ce "Littel da Miemie su fita, sai da yaga sun yi nisa har sun kai kofar falon Aneesa sannan suka fito daga cikin motar, kowa ya ga fuskar Najeeb yasan akwai damuwa "Ka ga Najeeb ka cire wannan damuwar kar wani cutar ta shigeka." Mommy ta yi maganar cikin sigar lallashi. "To mommy ya amsa yana kalkalo murmushi iri wanda iyakar sa laɓɓa. Suna kallon yaran suka fito daga ɗaya bangaren suka nufi ɗayan. Duk suna zaune sai ganin Miemie ta shigo rike da hannun Littel, da mamaki suke kallonta sun kasa motsi, kallo ɗaya zaka masu ka tabbatar sun cikin farin cikin ganinta, babu ma kamar Aneesa har rige rigen zuwa daukarta ake wani irin mik'ewa Aneesa ta yi da gudu ta nufi Miemie wacce ta saki hannun Littel ta nufi Aneesa tana faɗin "oyo-yo Momma." "Oyo-yo 2 My baby I miss you, daga ina kike? Wa Ye suka dauke ki Miemie?" Aneesa ta jero mata tambayoyin cikin sauri. "Watu mutane tuka ta ni a motarsu wai za su kaini wajen Daddy shi kenan na tena ka nin ku." Cikin maganarta ta yi maganar. Kafin ta yi wata magana sai jin sallamar su Najeeb suka yi. Gaba daya suka ɗago da mamaki suna amsawa. Ciki suka shiga aka gaisa Ameesha cike da ɓacin rai tana shirin yi wa Najeeb rashin mutunci, wato shi ya ɗauki mata yarinya ya barsu cikin matsala da tashin hankali, shima a bangaren Dr haka abin yake hanya yake nema da zai nuna wa Najeeb kurensa, sai yanzu ya tuna shi wannan saurayin Ameesha ne na da wanda suka yi zaman asbiti lokacin, maganar Najeeb ce ta dawo da su hsnkalinsu"Abba a yi hakuri ga Miemie nan ɗazun Allah ya sanya muka ganta, bana son kowa ya ce komai sai kun je gidan da muka samu Miemie daga nan sai ku san matakin da za ku dauka, amma ina rokon alfarma Abba kar ka ji kunyar wanda ya aikata hakan. Duk sun yi na'am da maganarsa don haka gaba daya suka ɗauki mota don zuwa gidan motoci uku suka nufi gidan Aneesa rungume da Miemie kamar wani ya ce zai raba su. Can bangaren kuwa ba su tashi farga babu Miemie ba sai da suka ga ta yi kusan awa bata shigo, nan fa hankalin su ya tashi duk gidan an duba babu Miemie sun tambayi mai gadi ya ce babu wanda ya shigo, domin Najeeb ya bashi kuɗi masu yawa ya ce kar ya faɗawa Alhaji Mansur ya shigo, ai ko ya ce babu wanda ya shigo, ya sanya su mugu su daure shi kenan aka fara horn, da sauri ya je ya bude don a tunaninsa Najeeb ne ya dawo, su mugu sun yi tunanin Yan sanda ne don haka da gudu suka biya. Mamaki matuka ya kama su gaba daya, Alhaji Taheer cikin fara'a ya fito yana faɗin "a'a Alhaji har kun riga mu isowa kenan? Lallai na yadda da soyayyar ka a gareni." Dabur cewa Alhaji Mansur ya yi zai fara kame kame Najeeb ya yi saurin cewa "Ina mai bakin cikin sanar maku da mahaifina Alhaji Mansur ya sanya a dauke Miemie domin kwadayin abin duniya." Doguwar salati jama'ar wajen suka dauka "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un." "Kai Najeeb bana son shashanci Yanzu ka rasa wanda za ka yi wa sharri sai mahaifinka?? Wannan wacce irin rayuwa ce Allah ya kawo mu da 'ya'ya basa kaunar iyayensu??"" "ABBA ya yi maganar cikin tashin hankali. "Sam Alhaji a zamanin yanzu kafin ka samu yaro mai biyayya wa iyayen sa kamar Najeeb da wahala wallahi duk abin da ya faɗa maka gaskiya ne, wannan kadan kenan daga cikin halin Mansur inda har baka ji tsoro ba wallahi shi ya sanya wasu marasa imani suka bige Ameesha har ta samu wannan lalurar." Wannan karon har kusan faduwa Abba ya yi don firgici, mutumin da ka yadda da shi shi ke ha'intar ka? Lallai mutum ba abin yadda ba ne, kallon Alhaji Mansur ya yi wanda ya yi tsiru-tsiru kunyar duniya ta rufe shi bai taba tunanin yana da kunya irin ta yau ba ji ya yi uwa kasa ta nitse ya faɗa ciki ko ya huta da kunya da nadama, yau kaɗai na ya ji ya tsani irin halinsa. "Babu komai Alhaji duk abin da ka yi ka yi wa kanka, Allah ya sani da zuciya daya na daukeka amma tun da haka ne babu komai, har cikin zuciyata na yafe ma duk abin da ka yi min, kuma ina rokonku da ku yafe masa kunshi? Kai Jaheed ɗauko jakar kuɗin nan ka bashi miliyan biyar a ciki yi tun da domin kuɗi ya yi." Cikin sauri Jaheed ya cika umurnin Abba nusiha sosai Abba ya yi wa Najeeb wanda ya sanyaya masa jiki sannan suka juya, su ma su Najeeb motarsu suka shiga sai dai ya kasa jan motar sai Rufaida ta ja. Su Abba na fita su mugu suka fito, Alhaji Mansur har zai fara kaso suka kwace kudin babu tausayi babu tsoro yana kallo suka wuce da shi, kuka sosai ya yi ya rasa aboki mai taimakonsa sannan kudin da aka bashi sun kwace wayyo tarin nadama da dana sani suka masa yawa take kansa ya fara wani irin sarawa. Da kyar ya iya jan motarsa zuwa gida, kwana biyu ciwo ya kwantar da shi, da kyar da lallashi Mummy ta samu Najeeb ya kai shi asbiti. Gwajin farko aka ce ciwon zuciya da hawan jini wanda suka masa mummunan kama, domin zuciyarsa kumbura ta yi haka jikinsa ya fara kumburi. Allah ka bamu ikon aikat kyakkyawa, ba irin halin Alhaji Mansur ba na zallar cin amana da bakin ciki tare da hassada, ga dai yadda ya kare nan Bangaren su Ameesha ma Alhamdulillah komai ya wuce, ta ci gaba da shayar da su Hibban da Hibba yara masu kyau da wayau sun yi tula-tula gwanin sha'awa *BAYAN SHEKARA GOMA* Alhamdulillah! Gidan Dr arziki ya ci uban na da don yanzu ya zama katafaren mai kuɗi k'aton gida ya gina masu, haka ya mallaki asbitoci har uku wanda ya sanya masu suna *A'A specal hospital* (Asmad Abubakar) duk a cikin garin Kano, duk inda ka zaga maganar sa ake Dr Asmad, ya yi suna fiye da tunani, yanzu yaransa biyar duk da su twins *Fatimah (Miemie), sai su Hibban da Hibba, sai mai sunan Meena wacce suke kira (Besty) sai yanzu da take goyon mai sunan Bobbo suna masa lakabi da (Aryan)* gaba da yara yan gata da ko wanne fanni ga tarbiyya da nutsuwa. Miemie da Sahal yaron Meena suka shigo cikin falon bakin su ɗauke da sallama, Ameesha da ke zaune ita da Dr tana shayar da Aryan ta amsa "Mami Daddy sannunku da hutawa." Suka hada baki wajen fada. "Yawwa Abbana da Nennena an dawo daga school ɗin?" Da yake school daya suke da Sahal yau sai ya biyo direban Miemie wai zai gaida Ameesha "Eh Daddy Mommana bata da lafiya tana can sai juyi take yi." Miemie ta gama maganar tana hawaye. Kusan a tare suka tashi Ameesha saɓe da Aryan falon Aneesa suka shiga inda suka sameta kwance kamar yadda Miemie ta faɗa, da sauri Dr ya matsa kusa da Aneesa yana faɗin "sannu Aneesa me yake damunki?" "Cikina." Ta yi maganar da kyar. Cikin tausayi Ameesha ke mata sannu, shi kuma Dr ya dauko kayan aiki gwaje gwaje ya soma mata cikin kwarewa, Yana gamawa ya saki murmushi ya ce "Masha Allah! Miemie kin kusa yin kani Momma na da cikin wata biyu da kwanaki." Tsalle Miemie ta soma na jin dadi, ita ma Meesha farin ciki ne ya kamata har da hawaye ta rika godiya ga Allah, ya yin da Aneesa idonta ke fitar da hawaye duk na farin ciki." Sai ku bar kuka shi yasa tun tuni ban faɗa maku ba gashi yanzu ya nuna da kansa a bar kuka a yi murna Allah ya inganta. Aiko murna sosai suka yi daga lokacin Aneesa ta daina aikin komai sai da ta huta tattali da kula Dr na yi mata daidai gorgodo har Allah ya sauketa lafiya in da ta haifi santaleliyar budurwa mai kama da Dr kar kusa kuga farin cikin da family ɗin Dr suka shiga, ranar suna yarinya ta ci sunan Maryerm Aneesa da kanta ta zaɓi sunan da aka sanyawa 'yarta suna kiranta da *(IFTIHAL)*. DUK WANDA YA GA ZURI'AR DR ASMAD SAI SUN BURGESHI, DOMIN MATAN BIYU SUN HADA KAN YA'YANSU BAKA TABA CEWA YA'YAN KISHIYOYI NE, DON TUNI IFTIHAL TA KOMA BANGAREN AMEESHA, FARIN CIKI KE WANZUWA A KO WANE RANA A GIDAN DR ASMAD. To muna sai mu ce Allah ya bamu farin ciki da kwanciyar hankali. TAMMAT ALHAMDULILLAH Anan na kawo karshen wannan littafi Mai suna sangarta, Alhairin dake ciki Allah ya sadamu da shi kuskuren da ke ciki Allah ya yafe mana. Godiya gare ku masoya abin tunkaho abin alfahari, Allah ya barmu da ku har gaban abada Amin.🤩🤩 Tukuici ga my Besty Khadija S Muhammad, bana gajiya da yabon ki wallahi, domin karamcin ki a gareni ba ya faduwa sai dai na ce Allah ya biya bukatu na Alhairi.😘 SAI MUN HADU A WANI *Ni ce ta ku har kullum* *ZULAYHEART HARUNA RANO* *ZULAYHEART RANO* *UWAR FAWZAN*💞