4 SUMAYYAH ABDULKADIR Babbangoro2015@yahoo.com Takorikabara@gmail.com SADAUKARWA Sadaukarwa ne ga duk makaranta littattafan TAKORI. Wadanda na sani da wadanda ban sani ba, Allah ya hada mu cikin alherin sa, har zuwa ranar da muka daina numfashi. DON TUNAWA DA Domin tunawa dake marigayiya Kakata kuma Goggo na HAJ. HAWWA ABUBAKAR WALI (Haj. Mai Mage ). You are evergreen in my memory Allah ya kai haske da rahma kabarin ki. TUNASARWA Ban yarda a kwafi wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba ko karanta shi a rediyo ba tareda iznina ba, hakan zai kaimu ga tsayawa gaban hukuma, wadanda bansan inda kuke ba kuma zamu hadu a kotun Allah ranar da bawa bashi da abin biyan hakkin dan uwansa sai kyawawan Ayyukansa. Takori FATAN ALKHAIRI Fatan alkahairi gareku makaranta na da jimirin bin littattafaina ina yi muku fatan alkhairi a duk inda kuke, nagode madallah da yabawarku. . JINJINA Littafin SANADIN KENAN! Ya jinjina miki AUNTY ZULAIHA ZUBAIR (Mrs late Tafidan Kano Hakimin Kura, SANADIN KENAN! Ya jinjina miki saboda gudummuwarki gareshi. Aunty Zulaiha Madallah Allah ya kara lafiya da nisan kwana. SANADIN KENAN 4 Su Jalan sunyi mamakin daular da suka ga 'yar uwarsuHauwa a ciki. Don a saninsu mijin ta bashi da komai har ya rasu, bayan gidan da suke ciki.Da mahaifiyarta ta tambaye ta murmushi ta yi, tace"SANADIN ilmin Amina ne". Ranar litinin ita ce ranar da Amina za ta tare a gidan mijinta. Kamin ranar ta kimtsa komai nata. Har Goggo na yi mata fadan ta ajiye tsofaffin kayan sawarta, ta fiya tsumulmula. Amina tayi murmushi ta ce, "Goggo ki bar min su. Akowanne canjin rayuwa da na samu ina son in ke sanyayadda nake a baya in memory, kada in shagala, in manta da yadda na taso". Goggo ta tabe baki, "Ai falsafa nan ta ganki ta barki". Manyan motoci biyar Akilu ya kawo Shira, aka kwaso gaba daya dangin Amina manya da yara da matan Baffanninta kai har da wadanda ba dangin Iya babu na Baba aka dura su sai gidan Gwamnati. Su Aisata kuwa motoci ne na alfarma daga maigirma Gwamna guda uku don su kadai jamaar Sierraleone. A cikin gari kuwa dukkan abokan arzikin Goggo, Inna Zulai ita ce kan gaba, su Talatu masu aikin Goggo abu nasu maganin a kwabe su. Makotan Goggo na unguwar da suka baro da na sabuwar unguwa duk haka aka kwashe su Government House. Sai a wannan lokacin mutane da yawa suka san waye ya auri Dr. Amina. Masu mamaki sun yi, masu gulma sun yi amma masu fatan alkhairi sun fi yawa kasancewar mahaifiyarta mutum ce wadda ta ke zaune lafiya da kowa, kuma ma'abociyar alheri, masoyanta sun rinjayi makiyanta. Aka bude wa duka 'yan kawo amaryar guest house aka ce ango ya ce su zauna su huta har tsayin kwana uku. Murna a gurin 'yan Shira abin sai ya ba ka dariya. Shi kuwa ya sa aka yi ta cika su da liyafa iri-iri, sai da ya kure hadamar kowa, abinci suna gani amma sun kasa ci saboda koshi. Sun manta da wata Amina wadda aka kai 'upstairs' shagalinsu kawai suke yi. Yan Sierraleone kuwa downstairs aka bude musu tareda alummar Hajiyan Jikas. Koda suka sada Amina da dakin aurenta basu ma zauna sun kwana ba suka koma gidan Goggo a motocin da suka kawo su, bayan an gabatar dasu ga Hajiyan Ji-kas. Anty Laila ba ta kasar, ta je umrah, wannan karon da gaske Saudiyyan ta je ba Dubai bamusamman don ta yi addu'a Allahya ba ta haihuwa tunda likitoci sun kasa tsinana mata komai a Dubai, sai cin kudinta a banza, ta ga gara ta koma ga Allah don ta ji rade-radin Ma'arouf yana neman aure. Hankalinta in yayi dubunnai to ya tashi, sai dai duk kwakkwafinta an kasa gano mata wa zai aura saboda ba’a sa a (media) ba, yau satinta daya a can kuma sati biyu za ta yi. Hajiyan Ji-kas da jama'arta da suka karbi amarya daga hannun danginta na uwa da uba suna nan a downstairs, washegari za su koma Ji-kas, Hajiya kuma Lagos za ta wuce. Amina tana kusa da Hajiya lullube cikin laffaya, ta ki yarda ta zauna a dakinta da ke upstairs,self-content ne kamar duka dakunan wanda ke kallon na mai gidan, na Laila kuma yana nesa da nata sai dai duk cikin tafkeken falo daya suke. Hajiya da 'yan uwanta da kishiyarta Lami hira suke, har dare ya soma yi. Hajiya ta lura Amina ta fara gyangyadi, ga dare ya yi wajen karfe goma sha daya na dare, ta ce, "Tashi haka Amina, mu je in raka ki dakinki dare ya yi". Amina ta turo baki cikin shagwaba, yadda ta ke yi wa Goggonta don ba ta bambanta Hajiya da Goggo, tana fadin, "Don Allah Hajiya ki bar ni in kwana cikin mutane. Ni wallahi tsoro nake ji gidan yana da girma sosai, na yi miki alkawarin gobe zan koma". Hajiya ta rasa yadda za ta yi da ita don ba ta so ta takura mata ta koma kukan nan da ta yi musu sanda suka banbaro ta daga jikin Goggonta. Kafin ta bata amsa ma Amina ta gyara waje a gadon ta yi kwanciyarta, barci ya sure ta. **** Sanda angon ya shigo gidan, karfe goma sha biyu na dare ya yi. Wajen Hajiya ya fara dosa da takunsa mara amo, wanda yake yi cikin nutsuwa, ya shiga ne don ya yi mata sai da safe ya wuce wurin amarya. Duk jama'ar dakin sun yi bacci, wasu a gado wasu a kasa, Hajiya ce kadai ido biyu, makure ta ke a can kusurwar dakin kan sallaya tana lazimi, ba komai Hajiya Saude ke roka ba daga wurin Ubangijinta face nema wa danta Ma'arouf dacewa a cikin wannan auren da zuri'a dayyiba, Allah ya kare mata shi daga duk mai nufinsa da sharri, ya ba shi alherin da ke tare da Amina ya nesanta shi daga rashin alhairanta. Ya sanya ta zamo marufar asirinsa kamar Aisha, ya kade dukkannin fitintinu daga cikin aurensu. Jin murda kofarsa da sallamarsa ya sanya ta yi fatiha ta shafa. Bai shigo ba saboda mutane, daga bakin kofar ya tsaya rike da marikin kofar. Hajiya ta amsa sallamarsa fuskarta cike da yalwa. Ya ce, "Hajiya ba ki kwanta ba?" "Yanzu dai nake shiri, don gobe sammako za mu yi, zan je ganin Ameena a makaranta (an kai Ameena wata makarantar kwana ta yara 'yan firamare a Lagos) sannan na wuce Jikas". "Ai booking din naki na rana ne Hajiya, ba sai kin yi sammako ba". "A'ah, gara dai in yin don ta ji dadi". Ya juya zai fita, "Allah ya ba mu alkhairi Hajiya". "Amin. Ga Aminar a nan ma bacci ya dauke ta". Cak! ya tsaya kamar bai ji daidai ba. Hajiya ta yi murmushi. "Na yi-na yi ta zauna a dakinta ta ki, wai tsoro take ji, abu kuma da gajiya ba ta san sanda bacci ya dauke ta ba". Saura kadan ya ce, Taso ta Hajiya, wannan wane irin abu ne? An taba yin haka?Amarya a ranar aurenta ta kwana da 'yan biki? To ni kuma fa? Hajiya kin daina sona da alama........!". Dariya ta kusa kwace wa Hajiya Saude ganin ya kasa tafiya, ya kuma kasa magana. Sannan ya kasa juyowa. Ta yi niyyar tashinta wata zuciyar ta ce, 'kyale ta yau daya dai ta huta da gajiyar biki, yadda Maarouf yake rawar kafar nan da kyar zai barta ta runtsa, gobe mu bar muku gidanku ku karata'. "Ka ce sai da safe kuma ka tsaya, ko in taso ta ne?" Ya yi gaba yana fadin, "A'ah, Allah ya ba mu alkhairi". Hajiya ta ce, "Amin". Washegari da safe su Hajiya suka yi shiri suka wuce. Bayan ta raka Amina dakinta ta yi mata nasihohi a kan ta zauna lafiya da Laila, ta yi hakuri da ita kamar zamansu na baya. Ta yi musu addu'a suka tafi. Gida ya saura 'yan Shira a sassan baki suna ta sha'aninsu. Ba wanda ya damu da ya zo inda amaryar ta ke ban da Ramma matar Baffa Bilya, ita kam ta zo taya Amina hira. His Excellency bai shigo gidan ba saboda ayyuka masu yawa da suka tsare shi a office. Tunda aka fara hidimar auren bai dauki hutu ba sai yau. Wajejen karfe uku na yamma ya samu ya kira Amina a waya. "Shirya kayanki da abubuwan amfaninki da za su yi miki kwana bakwai, za mu tafi Abuja". Amina ta ajiye wayarta a gefe, twna mita cikin ranta, wace irin tafiya ce saboda Allah daga kawo ta jiya ko 'yan biki ba su watse ba? Sai kuma su nemesu a gidan su rasa? Abin da ta ke fadi a ranta kenan. Bata san shi yan bikin yakeson gujewa ba. Sun isheshi sun dameshi, yana son samun privacy hakannan da matarsa. Rabon da ya ganta tun kafin daurin aure. Hakan kuma bai hana ta bin umarninsa ba, ta samu babbar jaka ta shirya duk abin da ta san za ta bukata. Ya fi karfin ya yi hukunci, ta ce, a'ah! Ya fi karfin komai a gare ta!! Ya sake kiranta a karo na biyu bayan ta idar da sallar la'asar. A gurguje yake fadin, "Ki fito, direbana yana bakin falon karshe yana jiranki, zai taho da ke filin jirgi. Ba za mu hadu ba sai a jirgi, ina tare da jama'a sosai. Ina rokon kada hakan ya bata ranki, sai kin yi hakuri Amina, yanayin rayuwar tawa kenan. Are you o.k?" Ta gyada kai kamar yana ganinta. "I'm o.k, zan fito yanzu". Da kanta ta turo jakar tata waje, bayan ta nade jikinta cikin wata lallausar laffaya fara mai ratsin shudi mai hasken sararin samaniya. Ta feshe jikinta da turaruka masu sanyin kamshi. Kamin ta isa downstairs wani ma'aikacin gidan ya zo don fita da jakarta, direban na jiransu ya karbi jakar ya sanya a bayan motar kirar 'porsche' ta shiga suka kama hanya tare da security dinta mace a gidan gaban motar. A takaice Ma'arouf da Amina, ba su hadu ba sai a first class seats na jirgin Azman mai zuwa Abuja daga Bauchi. Kar ki so ki tona zuciyar kowannensu a yayin da suka yi arba da juna domin ba za ki iya kididdige adadin farin cikin da ke cikinta ba.A lokacin da Amina ta zauna a kujerar dake daf dataangon nata. Karo na farko a tarihin rayuwarsu da ya kama hannunta ya rike cikin nasa. Ji tayi tamkar magnet ya manne hanuwan nasu. Kanta ta sunkuyar,ta kasa hada ido da shi, tana mai karbar sababbin sakonnin farin-cikin dake shigowa zuciyarta, ba ta iya ta dube shi ba, amma wata rahma taji ta sauka aruhin ta. Shi kuwa ajiyar zuciya ya ke saukewa da sauri-da-sauri, cikin ransa yana godiya ga mai tsarkin mulki, da ya nuna masa wannan ranar, wanda ya mallaka masaAminar nan da ya dadeyana so da kauna lokaci mai tsawo ba don isarsa ko mulkinsa ba. Sun sauka a hotel din TRANSCORP HILTON da misalin karfe takwas na daren ranar. Gajiya ba ta bar Amina ta tsinana komai ba. Ta yi alwala ta yi sallar magriba da isha da ta riske su a hanya, a nan kan sallayar barci mai nauyi ya dauke ta. Ta bude ido ne ta ganta tsakiyar wani ni'imtaccen gado, rufe ruf da lallausar (duvet).Da ta kara bude idon, ta juya sosai, a can gefe bisa wata yar kujera da dan tebir a gaban kujerar Ma'arouf ne yake cin abinci. Sanye yake da karamar t/shirt deep-bluesamfurin DKNY da bakin dogon wando samfurin Armani. Sosai yayi mata kyau irin na ranar nan data ganshi cikin kananan kaya, yau fiye da waccan ranar saboda harda hasken amarci tareda shi.Yayi wani fresh dashi (wanke hannu ka taba) inji zuciyar Amina. Suka kalli juna na 'yan sakanni tana daga kwance cikin duvet din, kafin ya ture tebir din duka ya taso ya tako har inda ta kekwance, tsayawa yayi akanta ya kama kallonta kamar a lokacin ya taba ganinta, gashin kanta da ya sha gyaran Aunty Jalan ya kwanta akan filon ya baje sai sheki yake, da Amina ta kasa jure kallon sai ta lumshe idanunta, siririyar fatar bakinta ta nuna alamar dan murmushi, hakan ne ya baiwa Maarouf damar sunkuyawa ya sumbaci saman idanun nata dake lumshe, ya tafi da gaggawa ya iso kan karan hancinta, kamin yacigaba da mikawa a urunce ya iso tausasan labbanta, anan ya ja birki yayi mata sumba mai tsayi da zurfi. Amina ta tsinci kanta cikin wata duniya da bata taba tsintar kanta a ciki ba. Shi da kansa ya tuna Amina babu komai a cikin ta, ya dakata, sannan ya mike tsaye, hannun damansa ya mika mata ta kama cikin jin wata irin kunyarshi da bata taba ji a rayuwarta ba. Tsaye ya mikar da ita ya shiga warware laffayar jikinta, ya saura doguwar rigar robar data bi fatar jikinta ta kwanta kalar (sky-blue). Gigicewa Maarouf yayi, wata irin gigicewa da bai taba yi akan diya mace ba. Yau ne ya ga zahirin Amina diyar Goggo Hawwa, ashe ba karamar ajiya Ubangiji yayi masa ba wadda bai taba tsammani ba??? Tsarki ya tabbata ga wanda ya halicci wannan sura!. Ya cigaba da kissing dinta ta koina sannan ya rungumeta tsan-tsan a jikinsa kamar mai tsoron kada wani abu yaratsa ta tsakaninsu. Sun dauki dogon lokaci a haka cikin sauraron bugun zuciyar junansu, kukan da akuyar cikin Amina ta soma yi ne ya ankarar da shi. Gabadaya ya dauketa bai dire ta koina ba sai a tebirin cin abincin. A baki Maaroufya ke baiwaAmina abincin wanda a rayuwarta bata taba cin mai dadi da dandanonsa ba, tun tana jin kunya tana sunkuyar da kai har ta ware ta ci sosai, sai mamakin Maarouf takeyi soyayyarshi na kara kama zuciyarta, sai da ta tabbatar masa ta koshi sannan ya kyaleta ta shiga wanka, misalin karfe goma na daren ranar mai dumbin tarihi a garesu. Ince zan tsaya wassafo muku wannan ranar da alamuran da suka wakana cikinta sai biro na yakare, takarduna su cika taf! Ba tare da na gama ba, idan ya kare yaya zanyi in kawo muku karashen labarin? Dr. Amina Mas'ud Shira,ta kira daren farkon ta da night of AMEENAH! Wato ita Aminar kadai ta san me ke cikin abinta. Abin sirri ne, sirrin ma ba dan kadan ba. Sirrin Maarouf da Amina. Gane hakan dana yi ne yasa na soma ja da baya a hankali da birona da tarinfull-scaps dina har na fice daga TRANSCORP HILTON (murmushi). ***** Sun mori (honey moon) na tsayin kwana bakwai yadda ya kamata a wannan hotel wanda babu na biyunshi a Nigeria. Sun kara fahimtar juna, so da kaunar junansu ya kara habaka da shaharar da a da, bai yi ba. Sun dinke zukatan junansu cikin na juna sun zama daya. Kowanne ya shiga tababar yadda zai rayu, rayuwa mai inganci ba tare da dan uwansa ba. A Transcorp suka ajiye tarihin. A can suka baro shi kamar kar su baro, Ma'arouf Ji-kas ya yarda Allah ya sako Amina cikin rayuwarsa SANADIN tashi Ameenar ne don ta gyara ta, ta maye mashi gurbin Aisha, ta wanzar da farin ciki a rayuwarsa wanda ya rasa tun gushewar Aisha. Ta wanke bakin cikin Laila Ji-kas da yake kwana yana tashi da shi. Ta kawo sauyi mai albarka daga rayuwar kadaicin da ya tsinci kansa a ciki tun bayan rashinAisha. Ita din ALHERI ce, kuma AMANA a gare shi (sunan wasu littattafan Takori). Isowarsu gida ke da wuya tun kafin su isa dakin barcinsu wani mai share-share ya sanar da Ogan nasa, Anty Laila ta dawo. Fuskarsa ba ta sauya ba, haka komai nasa bai canza ba. Amma Dr. Amina ta ji faduwar gaba matuka. Sai jin tausasan yatsun Ma'arouf ta yi cikin nata, ya rike ta gam ya ja ta sun fara taka matattakalar (upstairs) tare. **** LAILAH JI-KAS Lailah na zaune cikin daya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun falon, ta dora kafa daya kan daya ta harde, ta ci ado da kayan Larabawa na kece raini har ta gaji. Remote din talabijin ne a hannunta tana sauya tasoshi. Ta dago kai a yangace kamar yadda yake a al'adarta ta dubi masu shigowa ba tareda ta amsa sallamar da suka yi ba. Sosai ta saki baki tana kallonsu, Ma'arouf ba zai taba kama macen da ba tashi ba. Wannan na nufin...... wannan na nufin....likitar Ameena wannan 'yar rainin hankalin ya aura??? An tabbatar mata Ma'arouf ya yi aure tana Saudiyyah, amma ba ta taba kawo Amina ba ce. Ta dauka iyakarta kenan sun rabu tunda Ameena ta warke. To yaushe aka kulla soyayyar wadda har ta kai ga aure tana gidan bata sani ba??? Ta tambayi kanta, bata kuma samu amsa daga kowanne sashe na zuciyarta ba. Har suka zauna a kujera guda hannunsu na cikin na juna, Amina dai a tsorace ta ke ganin kallon kura ta ga nama da Laila ke mata. ta kawo karfin zuciya ta sanya wa ranta, tana murmushi, ta ce, "Anty Laila, ina wuni? An dawo lafiya?" Shiru ta yi mata ba ta amsa ba, har yanzu ba ta dauke ido a kansu ba, irin kallon nan na kun ci AMANATA. "Wuce dakinki Amina ki huta, zan yi magana da ita". Amina ta mike ta nufi dakin nata. Ba ta kai ga isa ba ta ji an shako ta ta baya, an yi mata wani wawan naushi a wuya, an maka mata wani irin abu a tsakar kanta da ya fi kama da kofin gilashi. Fasashshiyar Kwalba! Ta yi gaba luuu! Ta fadi a kofar dakin nata, tana jin sanda Ma'arouf ya yi magana da karfin gaske da iyakacin sautinsa, "Lailaaa! Kina hauka ne? Kisa? Wallahi in ta mutu a bakin aurenki!". Ya yi kokarin buga waya don kiran likita, amma ya kasa. Ya kuma kasa isa ga Aminan ya bata wani taimako saboda gigicewa. Hannunsa sai rawa yake yi, haka ilahirin jikinsa, wayar na subucewa yana sake dauko ta. Ita kanta Laila ta dan tsorata da ganin yawan jinin Amina da ke malala a kasa daga tsakiyar kanta, sai mazari ta ke yiamma ta maze, yadda take jin zuciyarta zata iya kashe Aminan kamar yadda ya fada in yaso itama a kasheta. Ya samu ya lalubo lambar Dr. Isma'el (personal doctor) dinsa,jikinsa na cigaba da mazaridon kuwa Laila ta shammace shi, sanda tayi wuf ta mike bai ankara ba balle isar ta ga Amina kamar walkiya. ".....Ka zo maza-maza har upstairs Isma'el.......". Babu tambayar ba'asi Dr. Isma'el ya amsa da; "Ga ni nanzuwa ranka ya dade". Ya isa inda Amina take a kwance a kofar dakinta magashiyyan ya ciccibe ta ya kwantar a doguwar kujerar falon, bai damu da jinin da ya bi ya bata masa jiki ba. Ya soma yi mata firfitababu alamun numfashi a tare da ita. Bai kara bi ta kan Laila ba wadda ke tsaye a kansa tana kuka. Kukan da bai san maanar sa ba. "Allah ya sa ban yi kisa ba zuciya ce, na shiga uku Ma'arouf ka yafe ni...". Abinda take fadi kenan cikin rishin kuka. Ko kallonta bai yi ba, firfita kawai yake wa Amina da gefen babban rigarsa idanunsa sun kada sun yi jazur. Abubuwa da yawa yake kissimawa a ransa da zasu faru da shi idan ya rasa Amina. A haka likitan ya iske su, bayan Ma'arouf ya ba da umarnin a shigo da shi. Da kayan aikinsa yake tafe don haka a take ya fara bai wa Amina taimakon gaggawa, har ta farfado. Ya cire kwalbar data nitse cikin kanta yayi dressing din wajen da ke fidda jinin, ya tsayar da gudunsa ya rufe da plasta. Ya dubi Ma'arouf da Laila mai kuka kashirban, Ma'arouf din ya ki ko kallonta hankalinsa da kulawarsa duk suna kan Ismael dake aiki kan Amina wadda ke kwance ido rufe. Nan ya gano bakin zaren, ya dubi Ma'arouf ya ce, "Garin yaya? Yaya haka your Excellency? Wane ne da wannan danyen aikin? Wannan kan dole sai an je asibiti an yi hotonsa don mai yiwuwa akwai (Internal injury) na kwalbar, da nake addu'ar Allah ya sa bai taba kwakwalwarta ba". Laila ta kara gigicewa, daidai da karuwar fushin Ma'arouf a kanta, ya ce da Doctor din, "Je ka ka zo da (nurses) ku tafi da ita a ba ta duk kulawar da ta dace". Cikin dan lokaci Dr. Isma'el ya yi waya asibitin cikin gidan, nurses biyu suka zo suka tafi da Amina. Aka barshi daga shi sai Laila a falon. Ya zauna cikin kujera ya tallabi fuskarsa da hannu bibbiyu cikin damuwa. Laila ta tsugunna a gabansa, ta kama kafafunsa tana kuka. "Tunda ba ta mutu ba, don Allah kar ka sake ni, wallahi zuciya ce na tuba, zan zauna lafiya da ita insha Allahu". Janye kafafunsa yayi, daga rikon da ta yi musu. Bai saki fuskarsa ba har yanzu, haka fushinsa bai sauka ba. Da kyar ya yi mata magana cikin muryar bada umarni, "Hada kayanki Akilu ya kai ki gida Ji-kas sai na neme ki". Laila ta rushe da kuka, "Na roke ka da Allah da manzonSa ka bar ni a dakina, in dai Amina ce na yi maka alkawarin za mu zauna lafiya". Zuciyarsa ta so ta fara sanyi, sabida irin kukan da ta ke yi mai nuna nadamarta a fili. Amma ya yi rantsuwa cikin zuciyarsa sai ta je gida ko da bai sake ta ba. "Hakuri na daya ne Laila, ki je gida sai na neme ki, amma ban sake ki ba, in kuma ki ka kara yi min musuraina zai kara baci, shiga ki tattaro kayanki". Ba yadda ta iya, ta juya ta yi dakin nata tana share hawaye. Hankalinta a matukar tashe. Shi kuma ya kira Akilu a waya, "Zo maza, za ka kai matar gidan nan Ji-kas". Ta gabansa Laila ta wuce tanna jan akwatinta, ta yi lullubi da wadataccen mayafi, wanda a da ba ta amfani da irin shi sai raka-ni-gantali. Ta dube shi cikin ido da idanun neman afuwa, ya kauda kai don ba ya son ya ba wa tausayin da ke son rinjayar fushinsa dama ya yi tasiri. Wannan karon ya yi aniyar daidaita mata sahu in har tana son ci gaba da zama da shi, to dole ta bar duk abin da ba ya so ta kuma zauna lafiya da zabin ransa. Ba ita dake cin alfarmar zabin iyaye ba. Zaman hakurin da yake yi da ita inda tana da hankali adalci ne ya yi mata. Yaushe ta fara sonshi so na gaskiya da har ta san ta yi kishi a kansa? Kishin ma na jahilai da rashin imani. Bayan tafiyarta ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai safah da marwah yake yi, yana son jin halin da Amina ke ciki wayar Dr. Isma'el na kashe alamar yana bakin aiki. Shi ba abun ya fita da kansa ya je asibitin ba. Ya daure ya shiga (master-bedroom) dinsa ya yi wanka da alwala, ya yi sallah nafila ya roki Allah matsalar Amina ta zo da sauki. Yana kan sallayar bai sauka ba bayan awa daya, sai ga kiran Dr. Isma'el. Da mugun sauri ya amsa wayar. "Ya ya Isma'eel, is she o.k?" "Eh, toh, shes conscious now,amma mun samuinternal injury, bayan na wajen, dole zaayi (minor-surgery) akwai bukatar ka sanya hannu, zan kawo maka takardun yanzu kayi signing. Amma ranka ya dade ya kamata a dinga kula a kuma dinga tsawatarwa iyali idan sun aikata ba daidai ba irin wannan, this issheer rudeness,don dai matsalar ta cikin gida ce, amma da ba za mu barta ta tsaya a haka ba". "Kada ka damu Isma'el, it's o.k, za a kiyaye zaa dau mataki. Yanzu ina Aminan? Ya ya yanayin jikin nata?" "Alhamdulillahi ta farfado, amma za mu rike ta har muyi aikin ya warke, bari in kawo takardun maza". Har Dr. Ismael ya iso gumi kawai yakeyi a zaune. Bai san yana son Amina har haka ba sai yanzu da take cikin wani hali da yake ji da zai yiwu da ya maido da ciwon jikinsa. Laila zata dandana kudarta yadda gobe ko da kyauta aka ce ta kwatanta rashin hankali irin wannan cikin gidannan bazata soma ba. Ya yiwa Ismael umarnin shigowa, ya kawo takardun har inda yake cikin girmamawa, ya karba ya rattaba hannu. Mintuna talatin suka dauka suna zare kwalbar data nitse cikin kan Amina amma alhamdulillahi bai tabi kwakwalwar ta ba. Karfe takwas na dare sukayi waya da Ismael ya tabbatar masa zai iya zuwa ya ganta yanzu. Asibitin nan cikin gidan gwamnati yake don haka akwai tsaro sosai. Amina na kwance lamoo!A gado, bayanta jingine da filo, ta sha katuwar plasta a ka. Maarouf ya murdo kofar ya shigo, idanunsu suka sarke dana juna, sun dauki lokaci suna kallon juna kafin hawaye ya cicciko idon Ameena. Ya karasa jikin gadon ya kama hannun ta ya ja farar kujera ya zauna a saitin kanta. Zaiyi magana ta kai tafin hannunta ta rufe masa baki ta san hakuri ne zai bata akan laifin da ba nasa ba. Don Allah kada ka sake ta na ji sauki wallahi na ji sauki. Kaima ka yi laifi da tuntuni baka fada mata ba, da bazata dauki alamarin da zafi haka ba. Ido ya zuba mata ya kasa cewa komai, wace irin mutum ce Amina?Wace irin kyakkyawar zuciya gareta? Yake tambayar kansa. Me kike so yanzu? Me zaki iya ci? Ya kawar da maganar data yi masa don bashi da amsar da zai bata, babu bayanin da zai yi mata ta fahimci irin zaman auren da yake yi da Laila Jikas wanda babu emotion ko affection a cikin sa da har zaa zauna ana tattauna muhimman alamura da suka shafi rayuwar juna, zaman auren kawai akeyi don ya zama dole. Amma yau an zo wani limit da yake jin wannan mugun zaman ya kare, babu wanda ya isa ya tankwara zuciyarsa ta sake zama da Laila har ita Aminar kuwa. Bashi da sauran abin nema a wata diya mace, duk abinda ya rasa a Aisha ya sameshi a tareda Amina har ma fiye da ita, ko baayi haka ba ya yanke shawarar kawo karshen zaman nasu don yiwa kansa da ita kanta adalci, yana tsoron kada ya tashi ranar Alqiyama da shanyayyen barin jiki. Zai bi hadisin Manzo (SAW) wanda yace; Ku auri abinda yayi muku dadi daga mataye daga dai-dai har hurhudu, idan kunji tsoron bazaku iya adalci ba to ku zauna da daya. (Bukhari). Ba abinda nake so, Goggo kawai nake so a dauko min don Allah! Ya dan fiddo ido damuwarsa ta karu kina so a tayar mata da hankali Amina? Ba kankanin abu ke tada hankalin Goggo ba, tanada juriya,idan bata zo ba bazan iya cin komai ba. Bai yi musu ba wannan karon, ya fiddo waya yana magana da daya daga cikin direbobinsa tunda Akilu ya tafi da Laila Ji-kas. Amina na ganin Goggo ta shigo sai kuka, Maarouf yayi kasa da kai ya russuna ya gaida Goggon ya fita, zuciyarsa cike da damuwa, kukan Amina na tada tsigogin jikinsa.Ga nauyin Hajiya Hawwa da yazo ya baibayeshi, ace matarsa ce ta aikata wannan taaddancin yana zaune ma ai sai aga sakacinsa. Ba kuma yadda zaiyi ya hana Amina fadawa Goggonta tunda ta riga tazo. Cikin nutsuwa Hajiya Hawwa ta zauna a kujerar da Maarouf ya tashi, ko hankalinta ya tashi babu alamun hakan akan kamilalliyar fuskarta. Ta kai hannu ta dafa kafadun Amina don an nade kan da bandeji. Yi hakuri daina kukan ki gayamin me ya faru daku? Kunyi hatsari ne a hanyar Abujan? Amina ta girgiza kai Goggo ai na gaya miki, Anty Laila ce, kofin gilashi ta kwantsa mini aka. Goggo ta girgiza kai babu mummunan rauni to? Akwai Goggo amma an cire kiyi hakuri, nasan zai dauki mataki Hajiyarsa ma haka, Allah ya kiyaye gaba Allah ya baki lafiya. Tun yaushe rabon ki da abinci? Wallahi Goggo tun a Abuja don a jirgi ma ban ci komai ba. Ni sai da na ganki ma na ji yunwa. Goggo tayi murmushi bansan yaushe zaki girma ba Amina, me kikeso ki ci? meat-pie da cakezobo da kunun ayarki murmushi Goggo ta sake yi ta ciro wayarta daga purse din hannunta ta kira Ilya ta gaya masa Amina na asibiti wai zata ci meatpie da cake, zobo da kunun Ayansu, ya jajanta ya kuma tabbatarwa Goggo yanzu zai kawo dama yana cikin gari. Cikin dan lokaci Ilya ya kawo cikin bokiti, Amina ta shiga ci hannu baka hannu kwarya. Ya tambayi Goggo abinda ya faru ta sanar dashi. Ilya ya shiga tsokanarta“raguwa kawai, mai tsoron kishiya don me baki bude kwanji kin rama ba? Amina bata kula shi ba, a ranta fadi take baka san Anty Lailah ba, (shes super warrrior) labarinta kake ji ina ni ina gwada yar kashi da ita ta karairayani a banza! Sai da ta koshi ta rufe ragowar tace. Goggo na ragewa Baban Ameena wannan, nasan shima tunda muka dawo bai ci komai ba, baki ga yadda yake cikin damuwa ba har ya fini damuwa”.Goggo tace to Amina! Ilya ya kama haba yana kallonta bakinsa fal magana amma bai furta ba, sai taji kunya ta rufe fuska tana dariya. Goggo tace ah toh mutum yayi rashin kunyarsa ya nade kayarsa shikadai ba! Ilya yace wallahi kuwa Goggo, oh! Su Ameena dadi miji ta galla masa harara. A daren Maarouf na shirin kwanciya, hankalinsa ya kwanta ganin Amina ta samu sauki kiran wayarta ya shigo. Ya mika hannu ya dauko wayar daga inda take ajiye gefen gadon sa ya manna a kunnensa ya makale da kafadar sa yana kakkabe shimfidar gadon da dukkan hannayensa biyu zai kwanta. Yaya akayi my patient? Bakiyi bacci ba har yanzu? Nayi zaton tun dazu kinyi bacci a cinyar goggo kina bukatar hutu. Amina tace ni bana kan cinyarta, gata can ma a gefe sallah take yi. Yaya zan iya runtsawa alhalin nasan baka ci komai ba? murmushi yayi, zuciyarsa na yi masa wani irin dadi tunda kin samu sauki sai naji na koshi, babu yunwa a tare da ni Amina gashi ni kuma bazan iya bacci ba baka ci komai ba wallahi mai dafa min abincin ya kwanta already, bazan iya kiransa yanzu ba, amma nayi miki alkawarin zan sha tea inada kettle da lipton da Zuma a dakina bana shan sukari. Na rage maka abinda naci, zaka iya cin cimar gidanmu? murmushin sa ya fadada why not? Zobo, Cake, da meat pie din Goggo ko? tayi smiling tareda kara manne wayar a kunnenta ta lumshe idanunta. Yadda suke maganar goggo dake gefe bisa sallaya bata jin su. A ina ka sani? Wa ya gaya maka? Ya kada kafada kamar tana ganinsa ina ruwanki? Babanki Turaki bai hana ki bin kwakkwafi ba? Ta zarce da murmushin zuwa dariya kamar inyi tsuntsuwa ta sama inzo in ganka. Maarouf yaji zuciyarsa ta dauke shi ta cilla shi wata hamada mai cike da koramu na madara da Zuma sabida jin dadin kalaman Amina. Sai ji tayi ya kashe wayarsa. Ta ciro wayar daga kunnenta ta duba sosai, ya kashe. Ta shiga mamakin me yasa ya kashe toh? Ko kalaman data fada ne suka bata masa rai? To amma me tace na bacin rai din? Ta daga ido ta dubi agogon dakin karfe goma sha biyu na dare. Idanunta suka soye ta kasa bacci sai kissime-kissime take yi a ranta na abinda ya sanya rabin ranta kashe mata waya. Ji tayi ana knocking kofarsu, lokacin goggo tayi sujjadah, ta dauka nurses ne don haka daga kwancen tace Yes!. Ya bayyana a dakin mutum biyu da suka rako shi suka tsaya daga waje, wanda bata taba kawowa ranta gani a lokacin bane, Maarouf Ji-kas ne. Cikin matsanancin mamaki da alajabi, so, kauna, da bayyanannen farin ciki take kallon sa. Ya daga mata gira ya karaso gaban gadon nata ya mika mata hannu. Gani, bani abincin. Shudin wandon jeans da farar shirt mai rubutun marks&spencer ne a jikinsa. Sassanyan kamshinturaren (givenchy) ya bakunci hancinta. Rufe ido tayi tana hailala don ta dauka bacci ne ya dauketa take mafarkin sa, saboda yadda zuciyarta ta dokantu da son ganinsa a lokacin. Shine ya bayyana a mafarkin ta. bude idonki, ba mafarki kike ba, nima na kasa baccin. Ya russuna daidai kanta ya fada mata cikin kunnuwanta. Da sauri Amina ta bude ido tana nuna masa Goggo dake sallah. Yayi dariya ya sumbaci bakinta zuwa wuyan ta sannan ya ja kujerar goggon ya zauna. Amina tayi suman zaune tana kallonsa a marairaice alamar rokon kada ya sake. Yace Ok? To ina kayan dadin da kika cin? Ta mike zaune ta dauko masa bokitin data ci ta rage daga kan locker ta mika masa. Ya karba ya bude ya soma ci. Ta sauko daga gadon ta isa ga firji ta bude ta dauko sassanyan zobo da kunun Aya wanda baa bude robar su ba da yake Goggo da sababbin robobi takeyi ta kawo masa. Zuwa dawowar ta mazauninta yaci meat pie ya kai hudu. Da kansa ya bude robar kunun ya soma kwankwada, sanyin kunun da gardinsa da ya ratsa shi ba irin na kowanne ordinary kunun Aya bane, wannan na professional Haj.Hawwa ne. Daga shi har ita shiru sukayi yana ci yana sha sai da yayi kat! Yayi gyatsa yayi hamdala, da gaske ya azabtu da yunwar ashe. Shi kansa yayi mamakin yadda ya ci snacksdinnan da yawa, kunun Aya roba biyu zobo roba daya.Godiya ga Amina, wadda ta damu da cikin mijinta, wani abu da bai kara samu ba tunda ya rasa Aisha. Ko ya ci ko bai ci ba ba ruwan wani.Daga ido yayi yana kallonta da wata irin siga data sanyata sakin murmushi. Ta russunar da idanun ta. Amina ta kawar da robobin daidai sanda Goggo ta shafa adduar ta ta juyo don ganin abinda nurse ke yi har yanzu a dakin, sai ta ga angon Amina da Aminarsa, suna hirar da bata san me suke cewa ba. Fuskokinsu dab da na juna, tana kwance a gadon asibiti yana zaune a kujerar mai dubiya. Kallodaya zakayi musu ka fahimci dab suke da su hadiye juna in suna iyawa. Hajiya Hawwa ta mirgina kai tayi murmushi. Jikin su ne ya basu Goggo ta idar da sallahr ta. Mai yiwuwa tana kallonsu. Sai tsinkayota sukayi a bakin kofa zata fice. Da sauri Maarouf ya ja baya ya ce Goggo, don Allah kuyi hakuri,ta kirawo ni ne inci abinci. Goggo bata juyo ba tace kuma kuyi hakuri, ai da baka kirawo ni ba ka yi jinyar da kanka Yallabai yayi dariya yace don Allah Goggo ki dawo, wallahi na tafi. Bata tanka shi ba ta fice.Shi da Amina suka sa dariya ya bi bayan Goggo ya rufo mata kofar. Kwanan Goggo uku a asibitin gidan gwamnati tana jinyar Amina, kaida ne Maarouf ya zo duba jikin nata sau uku a rana, da safe kafin ya shiga ofis, da rana in ya dawo da kuma da daddare kafin ya shiga barci, tun Goggo Hauwa na jin kunyar surukin nata har ta sake dashi, ta lura yanada saukin kai matuka kuma bai aje Amina nan kusa a zuciyarsa ba, don haka bata iya jure ganin su tare yana shigowa zasu gaisa ta nemi wurin fakewa don Maarouf ba ya jin kunyar kama Amina a gabanta da nuna mata kulawa mai nuna soyayyar sa gareta ba kadan bace. Goggo ta kasance koyaushe cikin godewa Allah akan hakan, ta kuma amince wani jinkirin alheri ne, inta tuno yadda ta matsawa Amina akan aure ashe kyakkyawan rabon ta na gaba. Goggo kan daga hannu ta godewa Ubangijin ta. **** Yana sane ya kashe wayoyinsa tsawon kwana uku don ya san dole za a neme shi kan batun Laila. Ba ya zuwa ko'ina a kwanaki ukun nan, wakilai yake turawa. Daga (office) sai gida manne da Aminarsa. Hajiya da ta gaji da nemansa sai ta kira layin Amina, ta ce ta hada ta da shi. Ba yadda zai yi don yana zaune a wajen. Ya karbi wayar ya soma gaida Hajiya cikin ladabi, ba ta bari sun gama gaisawar ba ta jefo masa tambayar da take dauke da ita. "Me ya hada ka da Laila? Ta zo wajena ban barta ta karasa wajen iyayenta ba. Nayi-nayi ta gaya min me ya faru ta ki. Sai kuka ta ke tana fadin in nema mata afuwa a wajenku". Da ba Hajiya ba ce kashe wayarsa zai yi, amma wannan ita ce mace mai daraja ta farko a gare shi. Ya gaya mata duk abin da ya faru, a yau kuma ya bude baki ya sanar da ita irin zaman da yake yi da ita tun aurensu. Ya ce, saboda rashin kaunarta da tausayinta ga Ameena ya dauko Dr. Amina ya kawo gidan. Don haka ita ce SANADIN aurensa da Amina ko ta ina aka je aka dawo. Da ta bi yadda yake so su rayu shi da ita da tilon yar sa, shi da ba mai ra'ayin kara aure ba ne. To ta kwashi wasu dabi'u da halaye na kawayen banza da matan bariki ta daura wa kanta. Shi kam, ya gama aurenta zai aiko mata da takardarta don ko ta ce za ta canza ba zai iya adalci tsakaninta da Amina ba, kuma Annabi (S.A.W) ya ce a zauna da daya, in ba za a iya adalci ba. A karshe ya ce, "Hajiya ki barta ta tafi gidansu, yanzu ne ta san ke mutum ce da za ta amfane ta? Ta taba zuwa har inda ki ke haka siddan ta gaishe ki tunda na aure ta? A matsayin ki na wadda ta haifa mata miji? Ta taba jin kan abin da na haifa a lokacin da take bukatar Uwa mai tausaya mata? Ta taba nuna min kauna ta hakika ban da ta in na ba ta kudi? Laila ba matar zama ba ce Hajiya, don Allah kada ki takura ni in maido ta ta fita daga raina gaba daya. Ki barta ta je gida don Allah na sake ta saki daya......". "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel... Ma'arouf ni za ka bai wa aiken saki? Ka yi min adalci kenan? In don ta ni ne duk abin da ta yi min na yafe mata, na yi mata uzuri tunda ta yi nadama kuma ta kara jaddada min ba za ta sake duk abin da ba ka so ba, za kuma ta zauna da Amina lafiya. To na yafe mata duniya da lahira, ko tsoron surutu ba ka yi a ce don ka yi aure ka saki uwargidanka? Ce ne ka maida ita maza-maza tun wani bai ji ba bayan ni". "Sai ta ji na sake ta Hajiya wallahi sai ta ji, ba ni ita a wayar". Tunda ya rantse jikin Hajiya ya kara yin la'asar, ba ya rantsuwa koda wasa, tabbas yau an kure hakurinsa, ita kanta ta san halin Laila ba mutuniyar kirki bace, ita ma dattaku ne kawai a matsayinta na uwa gyara ne nata ba bin bayan daya ba. Tunda kuma ya rantse ba za ta so shi da kaffara ba. Lailan ta kuma sabule mata da a yau ta ji bata kaunar jikarta tilo a duniya;Amina diyar Aisha.Daga bakin da bazai yi mata karya ba. A sanyaye ta mika wa Laila wayar wadda ke zaune gabanta dirshan tana tikar kuka, tana kuma jin duk abinda suke tattaunawa tana mai yarda da kuskurenta. "Ma'arouf don Allah ka yi hakuri na tuba, na bi Allah na bi ka......" "Na sake ki saki daya. Kije gida kawai. Allah ya hada kowannenmu da Alherinsa. Wayyo Allah Maarouf ka yimin rai, ina son ka, ina kake so insa raina.....??? Sai a lokacin ta lura ya dade da kashe wayar hannunsa. Hajiya ta rasa kuzari, ta kasa yin komai akai, a karshe da Laila ta yi kuka ta gaji ta umarce ta data yi hakuri taje gidan nasu kawai kafin tayi tunanin yadda zata shawo kansa. **** An sallami Amina ta koma gida amma baa kwance bandejin kanta ba, Amina zata iya rantsuwa cewa ciwon nan a jikin ta yake amma Maarouf ne yake jin zafin sa. Har dakinta nurse ke zuwa tayi mata dressing din ciwon kullum. Sai kasancewarsu su kadai cikin makeken gidan mai rassa daban-daban ya zama wata hanya ta kara dankon soyayya da fahintar juna, aminci da kauna mai karfi a tsakaninsu. Amina ya zamanto bata da damuwa, koyaushe idanMaarouf ya shiga office zama take ta kira Goggonta da yan uwanta na gida dana kauye dana Sierraleone su sha hira ko ta tura mota a dauko su su wuni tare, duk wanda ke da nasaba da Amina komai kankantar ta to kuwa yana shan inuwar data ke ciki, wannan a fili yake, hannunta a bude yake kullum cikin bayarwa take da yiwa alummar data shafe ta hanyar cin abinci. Hatta Yayanta Hafiz kuma tsohon masoyinta Amina tasa Maarouf ya dauke shi daga kamfanin mtn da yake aiki ya maida shi bankin GT. In ma tanada damuwa to na rashin practising aikinta ne.Ta taba yiwa Maarouf zancen tanaso ta koma aiki don bata iya zama waje daya ba ta komai ba, kuma ba ta son tsoma hannunta cikin siyasa. "Ina matar Jikasda zuwa aiki? Kin taba jin wata matar gwamna na aiki a Nigeria? Ko zan amince da komawarki asibiti sai ranar da bani da nauyin kowa a kaina muka bar wannan gidan na aro muka koma gidana na Fati Mu'azu". Dole Amina ta hakura ba don ta so ba, ta maida hankali ga bautar aurenta, domin neman dacewa wajen Ubangiji, don a duniya kam ta yarda ta gama dacewa. Alfarmar auren miji na gari irin Ma'arouf Habibu Ji-kas ba karamin dace ba ne. Ta kowanne fanni da diya mace ke buri. Duk da an ce kowanne dan Adam tara yake bai cika goma ba, a wurinta ita nata mijin ya cika har ya wuce ya isa goma sha tara!!!Matsalarta da Maarouf bazai wuce yawan tafiye-tafiye ba wanda ba yadda zatayi da hakan yanayin rayuwarsa kenan a haka ta ganshi ta aure shi, ba kuma kowacce tafiya ce yake iya yi da ita ba wata tafiyar bata bukatar rakiyar ta. Kullum Tana kitchen,safe, rana da dare tana girka masa abinda zai ci da hannunta, tafi gamsuwa da hakan, bata ga amfanin ta ba in zata harde kafa a gefe gardi ya shigo ya shiryawa mijinta abin ci ya gama kalle kwalliyar ta ta gefen ido,ta fannin His Excellencyfadar farin cikinsa da hakan bazai misaltu ba. Kullum zaka ganta da littafi da biro tana tsara time-table na abinda zata dafawa maigidan nata, ko ka ganta gaban talbijin tana murdo tasoshin girke-girke na kasashen duniya tana jotting. ***** Laila ta isa gidansu yamma lis almajiri dauke da katuwar akwatunta, mahaifinta ta fara arba dashi a kofar gida ya shimfida tabarma yana kishingide yana sauraron radio, tun daga nesa ya hango ta tana tafe amma ya sawa ransa ba ita bace mai kama da ita ce, ina Laila ina tafiyar kasa da dirkeken akwati haka kamar mai barin gari? Bai tabbatar itace ba saida ta tsugunna a gabanshi tana gaishe shi tana share hawaye da gefen gyalenta. Muryarta ba ta fita sosai saboda kukan da ta ci. Dagaci ya ce, Laila ce? Ta ce cikin dusasshiyar murya, Ni ce Baba. Ya ce, Lafiya kwaram-kwaram da yammacin nan kamar korarriya? Da farko Laila ta so ta boye wa mahaifinta gaskiyar cewa, Maarouf ya sake ta, sai kuma ta yi tunanin gara ta gaya masa ko ba komai Maarouf na ganin girmansa idan ya nemi alfarmar ya maida ta dakinta zai yi masa. Don haka ta bude baki ta ce, na dade a garin nan, ina gidan mahaifiyarsa, mun samu sabani ne. Jiya kuma ya sake ni. Amma saki daya ne. Don Allah Baba ka je ka ba shi hakuri. Dagaci ya gyada kai cikin matsanancin takaici, Ya yi kyau. Na tabbata halin naki na tsiya da ki ke shukawa a gidan da giggiwarki ce ta ishe shi. Ga gidan nan tunda zamansa ki ke shaawa kafada daya da uwarki sai ki shiga ki yi ta zama ki ji in zaman gidan dadi ne. Amma ni ko sawuna ba zai taka inda Maarouf yake ba balle in wani ba shi hakuri alhalin ban san me ki ka shuka masa ba. Haka siddan yaron nan yaron kirki ba zai sallamo ki ba, da ma ina jin wai-wai a kan wulakancin da ki ke wa yan uwanki saboda Allah ya rufa miki asiri. Duniya ta fi bagaruwa iya jima Laila, ga gidan nan ki zauna haka kawai ba za ki zo ki daga min hankali ba ina zaman-zamana lafiya. Ya nuna mata hanyar cikin gida, ya ce, Wuce ciki. Sabon kuka Laila ta sakar wa Babanta, fadi ta ke, Wallahi ba abin da na yi masa Baba, sabon aure ya yi shi ya sa ya sake ni. Maigari ya ce, Yanzu na ji magana. Ya yi sabon aure kin yi masa tashin hankali ko? Saboda gidanku ba mata uku ris ki ka tashi ki ka gani ba. To madallah wuce ciki na ce ki gama idda ki auri wanda ba shi da mata. Kada in kifta ido in bude in sake ganinki a wajen nan duka za ki sha wallahi. Tana kuka ta ja akwatinta mai tayoyi ta shige cikin gidansu kamar ta dora hannu a ka ta zabga ihu. Matan gidan uku duka suna tsakar gida har mahaifiyarta, kowacce da sabgar da ta ke yi. Mahaifiyarta ce mai girki, don haka talgen tuwo ta ke yi, mai bi mata Larai tana tankaden garin kuka. Sai amarya Laminde ita kuma tirken awaki ta ke sharewa. Ga kannenta nan matasa da kanana kowa abin da yake yi daban. Jin karar akwatunta duksuka juyo suka dubi hanyar shigowarta. Babar Laila Inna Saade ta washe baki amma ganin yanayin Lailan sai gabanta ya fadi ta bar abin da ta ke yi ta shige daki, ta fi so ko ma mene ne ta ji shi a daki ita kadai ba gaban wadannan masu son ganin hanjin nata ba. Kai tsaye kuwa Laila dakin mahaifiyar tata ta wuce. Ta jefar da akwatin gefe ta samu waje ta hada kai da gwiwa ta ci gaba da kuka. Inna Saa ta ce, Ke lafiya? Mutuwa aka yi? Laila ba ta amsa ba sai hadiyar zuciya. Tambayar duniyar nan Innar ta yi Laila ta ki gaya mata komai har ta fusata ta fita ta kyale ta. Kishiyoyin kuwa abin nema ya samu tattaunawa suka shiga yi tsakanin Larai da Laminde. Wannan akwatin dai ko saki ko yaji. In ji Larai. Laminde ta ce, Ko kuma an nado mata dankaren duka ba, an koro ta. Ahayye! Ita dai Inna Saa ba ta tanka musu ba ta wuce murhunta ta ci gaba da tukin tuwonta zuciyarta a jagule. A daren ranar Laila ba ta runtsa ba sabida cizon sauro, ga Innarta ta hada ta shimfida da kananan yayanta sun jike ta sharkaf da fitsari. Bargon da ta kwanta a kai kuwa jinsa ta ke kamar karzuwa saboda kaushinsa a fatar jikinta. Wancan zuwan da ta yi da Maarouf ya dage sai ta kwana biyu karbar matar gwamna Inna Saade ta yi mata, gadon audiga ta bar mata ta kwana ita ta kwana a kasa da yake an san bakuntar arziki ta zo. Sai yanzu ta shiga nadamar rashin gyarawa Innarta daki a lokacin da ita ta ke cikin kololuwar daular rayuwa. Washegari da safe kuwa koko da dumamen tuwo Innar ta dangwara mata a gabanta ko uffan ba ta ce mata ba, cike da haushin ta ki gaya mata abin da ya kawo ta ta barta da kishiyoyi suna yada mata habaici. Shi ma Dagaci bai yi wa kowa zancen Laila ba ya ja bakinsa ya yi shiru, harkokinsa kawai yake yi. Sai da Laila ta kwana uku a gidansu ganin ba wanda ya zo biko, sannan Maigari ya gaya wa uwarta sakinta aka yi. Hadiyar zuciya ne kawai Inna Saade ba ta yi ba, amma ta fashe da kuka mai karfi wanda ya janyo hankalin abokan zamanta suka zo kofar dakinta suna tambayar ko lafiya? Ko kula su Inna Saa ba ta yi ba, amma maigidansu ya gaya musu Laila aure ya mutu don shi a wurinsa duk an zama daya. A fili suka jajanta suka wuce dakunansu farin ciki fal zuciyarsu suna labarta wa yayansu har wadanda ke gidan miji sun aika musu. Yan uwan Laila, Asiya da Sadiya in ban da Allah ya kara ba abin da suke yi, ba za su taba manta wulakancin da ta yi musu da za a yi (swearing in ceremony) na mijinta ba, suka ce za su zo ta ce ba ta gayyatar gayyar naayya. Wani cikin gidansu bai taba taka muhallin da ta ke ba, hatta uwar da ta haife ta, to juyayin me za su taya ta don yau ta ga juyin rayuwa? Da ma an ce ka taka duniya a sannu domin ba matabbaciya ba ce. Kwanan Laila biyar a gidansu ko kofar dakinsu ba ta iya fitowa saboda habaicin su Laminde da dariyar ketar kannenta da yayyenta maza. Kuka ta yi shi har ta gode Allah, nadama kuwa ba irin wadda ba ta yi ba. Ranar da ta cika kwana bakwai Inna Saade ta soma tila mata wanke-wanke da wankin kayan fitsarin kannenta da girkin gida in ya zagayo kanta, ta ce ba zai yiwu kina kwance a daki ina dafo abinci ina kawo miki alhalin kin fi ni karfi ba. Ai shi zaman gida cudarni in cude ka ne ba irin gidan miji ba, shi ya sa ki ka ga ko mu da muke kauye lallaba aurenmu muke balle mai auren gwamna ta ce sai abin da ta ke so za ta yi? Haka Laila ta ci gaba da rayuwa a gidansu cikin wani hali na tagayyara da fita hayyaci. Gaba daya ta zuge ta fita hayyacinta, fatar jikinta ta canza kala hatta gashin kanta ya san uwar dakinsa ta samu gigitaccen sauyin rayuwa na farat daya. Ba irin kiran da ba ta yi wa Maarouf a waya, ba ya dauka sai ta koma yi masa sako (text) ko karantawa ba ya yi yake gogewa. Ga lokaci na tafiya tsoronta Allah tsoronta lokacin cikar iddarta. Babban abin da ya kada ta hatta Hajiya Saude ba ta kara waiwayarta ba, kuma tana da labarin ya zo Ji-Kas har sau biyu a bakin kaninta mai bi mata. Haka Laila ta rungumi kaddara ta maida alamarinta ga Allah. Kullum ta yi sallah sai ta roki Allah ya juyo mata da hankalin Maarouf, in hakan ba za ta yiwu ba tana rokon sa ya fiddo mata wani mijin cikin gaggawa mafi alkhairi a gare ta, ta yi aure ta huta da masifar gidan ubanta. ***** A wannan satin Ameena karama ta zo hutun (third-term) daga makarantar da Babanta ya kai ta a Lagos. Ta tadda Antinta a upstairs’ tare da Babanta a gida daya kuma daki daya. Ta kuwa hau murna ba yar kadan ba. Kullum tana manne da Antin nata ko tsakiyar iyayen nata biyu tana sakin hira. Farin ciki ya cika ta ta rasa inda za ta sanya kanta don farin ciki. Amina ta roki Maarouf da ya shirya musu zuwa Ji-Kas ita da Little za su je su yi wa Hajiya kwana uku. Ya ce, Ni kuma fa? Haka za ku bar ni ni daya kamar maye Amina da Amina? Kwana uku kamar kiftawar ido ne Your Excellency, na kwana biyu ban ga Hajiya ba, Ameena ma tana ta zancenta. Nayi-nayi ka dawo da Anty Laila ai ka ki saboda irin haka, mai mata daya fa aka ce aminin gwauro ne. Nan da nan ya yi fuska, Kin jawo wa kanki fasa zuwa Ji-kas din, na kuma gane ba kya kishina ko kadan Amina. Ai sai ki dawo da Lailar tunda igiyar aurenta ai tana hannunki. Na tuba, na bi Allah na bi ka, ba nufina kenan ba. Kawai na ga ya kamata zuwa yanzu a ce ka huce daga fushin da ka ke yi da ita, amma tunda hakan shi ne decision dinka ba ni da say Baban Ameena. Da kyar ta shawo kansa ya sauko daga fushin nasa. Wannan ta sha faruwa ba sau daya ba, ba sau biyu ba tun barin Laila gidan da dawowar Amina daga jinya a asibitin da Laila ta yi mata sanadin minor-surgery a cikin kai. Idan Maarouf ya ce ba ta kishinsa a kan Laila hankalinta yana tashi. Domin da bacin rai yake fada, ko uwar da ta haife shi tunda ya nuna mata ba ya son zancen komen Laila ta daina yi masa sai ita? A nata bangaren Amina ba rashin kishi ba ne, ba dai ta son zama kwarkwata fidda mai giji, ba ta so a ce a kanta wani ya shiga wani hali ko kankani, zuciyarta mai kyau ce maabociyar imani, idan akwai abin da ta ke kishi a duniya, to Maarouf Ji-Kas ne!Kishi kuwa wanda ko a tarihi babu irinsa. Amma na musulunci. Ta kudire a zuciyarta ba za ta kyale shi ba, in dai ta samu faraga ta ganinshi cikin nishadi za ta ambato neman alfarmarta na a mayar da Laila ba don halinta ba. Tunda Annabi mai tsira da aminci ya ce, Imanin dayanku ba ya cika har sai ya so wa dan uwansa abin da yake so wa kansa. Tana so wa kanta Maarouf tana so wa kanta rayuwa da shi. Ta tsaya ma tana cewa tana sonshi bata baki ne, don haka tana kishin abinta. Sai dai ba za ta bari kishin ya dakusar da kaifin imaninta ba. **** Sun isa Ji-kas lafiya ana kiraye-kirayen sallar magriba. Hajiya tana alwala sai ji ta yi Little ta dafe ta ta baya. Ta ce, Ho! yar nema, ni kada ki karasa ni. Little Ameena na dariya ta ce da karfi, Hajiyan Ji-kas!. Ta ce, Ni Saudatu sunana, ubanki ne Ji-Kas! Amina da kishiyar Hajiyan suka yi dariya, Hajiya da jikanyarta kullum suka hadu sai sun ba da dariya. Amina ta nemi buta ita ma ta yi alwala suka bi jamin sallar magariba daga masallaci. Hajiya ta rasa ina ta-ka-sa-ka, ina ta-ka-a-je da surukarta, inda duk ta mika hannu kwano ta ke janyowa cike da abincin da makota ke kawo mata da wanda mai aikinta ta dafa mata, fadi ta ke, Zabi wanda za ki ci Dr. Amina, kin san nan kauye ne ba ma cin cima kala daya. Zabi duk wanda ki ke so. Amina ta yi murmushi ta zabi burabuskon gero da miyar taushe wanda aka dafa wa Hajiya. Hira suke sosai kamar uwa da yarta yawanci duk a kan abin da ya shafi Maarouf ne da siyasarshi. Ana haka Amina ta sako zancen Laila, Hajiya ba za ki roki Baban Ameena ya maida Anty Laila ba? Saura kadan fa ta kare iddarta. Bana so su rabu kwata-kwata a dalilina. Hajiya ta girgiza kai, Ko kusa, kada ki kara sanya wa ranki da ke cikin dalilan rabuwarsu. An samu sabanin halayya tsakanin Maarouf da Laila, mun ganganda (rushing) wajen tabbatar da aure a tsakaninsu ba tare da binciken halayya ba, inda za ki san ba ke ce sanadi ba hatta iyayenta da yan uwanta ba sa jin dadinta, sanda tana gidan yaron nan. Sawun barawo naki alamarin ya taka don haka ki daina damun kanki. Zan tsaya kan ya maida ta din amma ba yanzu ba, sai ta kara tarbiyyantuwa. Don labari yana zuwar min kala-kala tana can nadamar rayuwa ta ishe ta duk surfen gidansu da sanwar gidansu ita ta ke yinta, kin ga ko ai Laila in mai hankali ce dole ta shiga karatun ta-nutsu. Amina ta langabar da kai, Ni tsorona Hajiya kada iddar ta kare wani ya fito ya aure ta. Hajiya ta ce, To ba shi kenan ba?Allah ya hada kowa da rabonsa. Ni yanzu na daina gaggawa a kan aure Aminatu. Dole Amina ta yi shiru don ta fahimci daga Hajiyar har danta sun hau doki guda, ba za ta iya sauko da su ba, sai ranar da Allah ya nufa. Da za su kwanta ta canza zuwa kayan barci masu kauri ta daura zanin atamfa a kai, ta kakkabe wa Hajiya gado, kayan da ta tara tsibi guda ba ninki bayan ba masu dauda ba ne, ta ninke mata su ta shirya mata a sif, lungu da saqo na dakin Amina ta bi ta kakkale shi tana mamakin wace irin mai aiki ce Tambai da a kicin da dahuwar abinci kawai ta ke aiki? To daga ita har Hajiyar sun kwana biyu ba za su iya wannan (neatness) din ba. Ta sawa ranta alkawarin zuwa Ji-Kas akai-akai da kula da Hajiya kamar yadda za ta kula da Goggo, ta wanke mata bayi kal sai sheki da tashin kamshi yake kamar ba bayan gida ba. Ta kuma koya wa Tambai yadda ake wankin bayi na zamani ta gane sosai. Hajiyar sai albarka ta ke sanya mata har suka kwanta barci. Washegari ita ta yi wa Hajiya girkin rana da na dare. Har zuwa ranar da za su taho ita ke yi wa Hajiya girki da shara da gyaran bangarenta. Babu abinda Maarouf bai sanya mata ba na saukaka rayuwa, amma ba sa samun kulawa yadda ya kamata sakamakon Tambai din ta kwana biyu, kuma girman kauye ce. A kwana ukku da Amina ta yi Hajiya Saude gani ta yi sassanta ya dawo sabo kal. Ta yi kewar su ba kadan ba bayan komawarsu Bauchi. Kowa na gidan ya yi kewar Amina don mutum ce mai saukin kai da dadin muamala duk yayan Baba Liman sun saba da ita. **** WATA SABUWA Bayan Little ta koma makaranta da sati biyu aka bugowa Babanta waya daga ofishin shugabar makarantarsu cewa ba ta da lafiya. A take ya tsallake abin da ke gabansa ya shirya musu tafiya Lagos shi da Amina. A Clinic din makarantar suka riske ta a kwance ana kula da ita. Ya karasa jikin gadon jikin sa na kyarma ya dafa kanta ya tambaye ta me ke damunta? Cikin sassanyar muryarta take masa bayani. Daddy watarana in na zauna ba na iya tashi tsaye sai an daga ni. Hankalin Amina da na Maarouf ya yi mummunan tashi. Ameena little ta cigaba da cewa, Cikin kashin kafata in na tsugunna sai in ji kamar zai tsage, sannan kafafuna suna karkarwa in na dade a tsaye. A take Amina ta janyo ta ta soma dudduba ta, to babu kayan aiki a tare da ita, don haka ta nemi izinin Maarouf na son yin magana da Dr. Turaki. Shi ya kira shi da kansa ya hada su. Amina ta gaya masa matsalar da ta biyo bayan warkewar Ameena. Suka yi magana irin tasu ta likitoci. Ta mika wa Maarouf wayar ya ce da shi su zo da ita asibiti a duba ta sosai. Makaranta ta ba da izni suka taho da Ameena Bauchi. To a binciken su shi da Amina da sauran likitocin bangaren su na ATBU Teaching Hospital sun gano matsala babba a tare da Ameena. Sun gano cewa kashin kafarta na hagu bai gama yin kwari ba, yana bukatar wani irin gashin wanda ba su da injin yinsa sai a waje. Dr. Usman ya ce ya san wani asibitin da suke irin wannan aikin a Vienna (Austria) wadanda sukawarkar da EFCC Lamido Nasir (Babban Goro) da kuma wani a Jeddah (Saudi-Arabia). Maarouf ya zabi na Jeddah, ko ba komai bai karya (patriotism) dinsa na yin alaka da kasashen Turai ba. Ya soma yi musu shirin tafiya Jidda shi da Amina da Ameena. Ranar wata asabar jirgin KLM ya daga dasu zuwa Saudi-Arabia. Madinatul-Munawwara suka wuce kai tsaye don fara yin umrah musamman akan Allah ya basu saar abin da suka zo nema, daga Madina suka wuto Makkah suka yi cikakkiyar umrah, duk adduoinsu a kan lafiyar Ameena ne na neman nasara a kan aikin da za a yi mata. Sannan suka isa asibitin da suka zo a Jeddah (Solayman Faqeeh) aka fara yi wa Ameena(Radiotherapy)na musamman. Amina ta ja gefe tana kuka fuskarta cikin mayafinta kawai saboda tausayin Ameena. Yarinya karama tana shan azabar da bata misaltuwa a yan kananan shekarunta da basu kai goma ba. A duk lokacin da ta ga ana yi wa Little therapy din nan ba ta iya daurewa sai ta yi hawaye kamar ba likita ba. A karan-kanta yanzu in zaa bata trillion ba abinda zata iya kara iya yiwa Ameena. Ba don komai ba sai don tausayi da sarewa. Daga ita har ubanta tausayinsu take ji har batasan wa tafi tausayi ba tsakanin yar da ubanta. Amina keda ciwon a jikinta amma zata iya rantsuwa Maarouf zai fi so a dawo da ciwon jikinsa in har zata samu lafiya. Tana ganin yadda baya iya barci tun saukar su a Saudi. A makkah da madinah a masallaci yake kwana. Anan jeddah kuwa bisa dardumarsa. Da gaske Allah ba ya hada maka komai a rayuwa, in ya baka wannan sai ya jarrabeka da wancan, shi kuma Maarouf Ji-kas ga ta inda allah yake jarrabarsa (ciwon Da). Ganin halin da take kasancewa in sunzo asibitin tare sai Maarouf ya daina zuwa asibitin da ita, ya gwammace ya zo shi da wadanda suka rako su (securities) dinsa. A hotel din da suka sauka (Aljamjoum) yake baro ta ya zo asibitin da masu tsaron lafiyarsa. Ba su fara samun nutsuwa ba sai da manyan likitocin na asibitin (Doctoor Solayman Faqeeh) suka tabbatar musu kafafun Ameena sun samu waraka cikin yardar Ubangiji, amma zai iya yiwuwa wani lokacin ta yi fama da dan ciwon kafa kadan-kadan, da zarar ta yi complain din hakan sun rubuta magungunan da za’a bata ta dinga sha a take ciwon zai daina. Sai a lokacin ne Maarouf da Amina suka samu lokacin junansu, aka biya bashin soyayyar da aka ci kwana da kwanaki wanda tashin hankalin ciwon Amina ya mantar dasu. Sun yi honey-moonmai tsayawa a zucci fiye da na farkon aurensu a Transcorp. Wata guda da rabi suka kwashe a Saudi-Arabia sannan suka tattaro suka dawo gida Nigeria. Daga airport kai tsaye direban da ya kwaso su Ji-kas ya wuce da su. Maarouf bai kwana ba ya koma Bauchi su kuwa suna tare da Hajiya har tsayin kwana uku. A nan ne Amina ke yi mata bayanin matsalar da ta fidda su Jeddah. Hajiya Saude ta ce, Kai! Wato dan Adam har ya mutu ba zai huta da kaddarorinsa ba, Allah ka kara mana lafiya bakidaya, Allah ya kara miki lafiya mai dorewa Amina. Da suka koma Bauchi da wata daya aka mayar da Ameena makaranta bayan ta kara samun kyakkyawar kulawa a hannun Antynta. **** Watarana Amina na gyaran tsofaffin takardun ta na makarantar sakandire wani karamin littafi ya fado, ta dauka ta goge shi tana dubawa, a ciki ta ga lambar waya a kasa an rubuta Hafsa Datti. A take ta tuno kawarta ta makaranta Hafsa. Murmushi tayi tareda yin hamdala ta roki Allah ya sa ta samu Hafsa a wannan lambar wayar, bazata taba mancewa da Hafsa ba, ta dade tana fado mata a rai batasan ya zatayi ta riske ta ba, abinda ta sani kawai shine a Abuja take. Da gudu ta dauko wayarta ta shigar da lambobin. Sai da ta gama abincin ranan His Excellency ta shirya komai a inda yake cin abincin tayi wanka ta kintsa a lokacin bai dawo daga office ba ta harde a hakimar kujerar falon ta ta soma kiran lambar. Kira na daya, na biyu ta ji lambar ta shiga, ta fara ruri. Addua kawai take Allah ya hada ta da Hafsa Datti a wannan gabar na rayuwarta. Wata mutum daya cikin masoyan ta na hakika da bazata manta gudummuwar da suka bata a rayuwarta ba. Sannan tana bukatar aboki bayan yan uwa da dangi, aboki saanta wanda zata ke tattauna wasu alamuran dashi bayan Goggo. Assalamu Alaykum. Taji muryar wata kamilalliyar dattijuwa ta amsa. Amin waalaikumus-salam . Ina yi ni? lafiya lau yammata, daga ina? Ban dau muryar ba kuma bansan lambar ba. Sunana Amina Masud, daga Bauchi nake magana, ni kawar Hafsa ce da mukayi makarantar sakandire tare. Don Allah ko zan iya samun magana da ita? Allah sarki, Amina ke ce! Yau Allah ya hada Hafsa da Aminar ta. Kullum tana zancen ki, tana rokon Alla ya sada ku watarana kun rabu ba tareda karbar adireshin juna ba kullum cikin zancen take. Allah Rahim, ni mahaifiyarta ce, zan turo miki lambarta yanzu. Bata kasar nan tana aure a kasar Russia. Yanzu na gama magana da ita. Amina tayi godiya sosai dadi fal ranta. A take maman ta turo mata lambar Hafsa ta kasar Russia. Amina ta kira Hafsa Sunana Dr. Amina Masud Shira. Tsalle Hafsa tayi ta dire akan mijinta. Amina! Dr. Amina? Ashe Allah ya cika buri? Ya cika Hafsa. Im a proffessional physiotherapist, married to Maarouf Ji-Kas. Maarouf Ji-kas wanne? Hafsa ta tambaya cikin mamaki. Murmushi Amina ta yi, ta daga ido tana kallon sa yana shigowa, idanunsu suka sarke dana juna bayan ya zare farin gilashin sa. Babbar rigarshi ya cire ya jefeta da shi ya wuce bedroomyana fadinnaji ana cewa Maarouf Ji-kas, ke da waye? murmushi tayi, tace wanda kika sani, I think shikadai ne me wannan sunan a Arewa. Yaya bayan saduwa? Mama ta gayamin kina Russia. Yaranki nawa? Don nasan bakya son karatu, Hafsa tayi ajiyar zuciya. Amina, tun farko na fahimci ke yar baiwa ce kuma mai saa a rayuwa, kina daga cikin mutanen dake cimma burirrikan rayuwarsu yadda sukayi fata. Na jinjina miki, na kuma sara miki ta yadda kika yi nasarar auren mutum irin Maarouf Habibu Ji-kas. Na sanshi a jaridu tun yana dan majalisa, na san sanda matarsa tayi accident ta rasu ta barshi da ya ba lafiya. Kada dai ince SANADIN KENAN? Bakin Amina dai ya kasa rabo da murmushin SANADIN KENAN Hafsa, paralysed Amina. Kuma alhamdulillah ta samu lafiya. Baki bani amsar tambayoyi na ba. Hafsa ta yi murmushi Eh, karatu kam bana son sa amma Baban Iman bai kyaleni ba saida nayi shi anan Russia na karanta (education) yanzun haka (lecturing) nake university din dana yi. Shi maaikacin embassy ne kwanannan zamuzo hutu zan iskoki a Bauchi insha Allah idan zamu samu ganin Her Excellency da sauki Ta karashe cikin dariya. Amina tace Hafsa ho! Kina nan yadda na sanki. Nace yarana nawa? Hafsa ta yi murmushi Iman, Imam da Amina, nayi miki takwara don kar in manta dake. Hawayen kauna suka cicciko idanun Amina. Bansan kin dauke ni da muhimmanci har haka ba Hafsa da ban kai wannan lokacin ban binciko ki ba ko da da taimakon Yallabai ne. Nagode Hafsa, ki shafa min kansu, ina duban hanyar ku zuwa Bauchi, gaisuwa ta musamman ga Mahmoud. A bedroom ta iske shi ya fito daga wanka kenan ruwa yana bin fresh fatar jikinsa. Kafin Maarouf ya juyo sai yaji Amina ta rungume shi ta baya. Sosai take cikin farin cikin da ya dade bai ganta ciki ba, sai ya taya ta farin cikin ta hanyar datafi kowacce sanya farin cikin. Sun farantawa juna yadda ya kamata da soyayya mai tsayawa a zuci. Suna kwance take bashi labarin samun Hafsa, ga mamakinta sai taga ya dakata yana yi mata kallo na rashin gamsuwa da labarin nata. Amina bana son ki da kawa, bana so. Gaban Amina ya fadi meyasa Maarouf? “Abinda nakeso ki tambaye ni kenan. Muna zaman mu lafiya nida ke, banida matsala dake ta kowanne fanni haka kema, in ma akwai muna tattauna ta a junanmu mu magance ta ba tareda kowa ya ji ba, amma kinyi aminiya duk sirrin aurenmu zai zama a kunnenta. Kada ki dauka wayon ku daya ita budadden ido gareta tarbiyyar turai, ina tsoron ta canza maki tunani. Amina ta kwantar da kai bisa kirjin mijinta jikinta yayi sanyi. believe me Maarouf Hafsa ta gari ce, ba yau na santa ba. Amma ka fada min abinda zan kiyaye a kawancena da ita insha Allah zan kiyaye. kinyi alkawari? wallahi nayi, in ma kace in rabu da ita kwata-kwata zan yi hakan amma zan kasance cikin kewar ta. Murmushi yayi wato dai bazaki iya rabuwa da ita din ba kenan shine zaki yimin wayo, irin wayon ku na likitoci da kikayo course wajen su Turaki. murmushi tayi mai sauti ni kam na rasa me Baban nan nawa yake maka daka sako shi gaba, don baka san yadda yake son ka ba, ga yi maka campaign a fakaice, ga wanke laifin ka, ga-ga...... alherin Turaki mai yawa ne akan ka. Dariya ta bashi sosai ya bubbugi bayanta kin ganki! To shikenan, albarkacin ki an daga kujerarsa daga yau daga matsayin commissioner zuwa na SSG. Kuma ke zakiyi masa wannan albishir din.Wata sumba da Amina tayi super ta mannawa Maarouf dinta,ta tabbatar masa tafi malamin nata godewa. Saboda kunyarta mai yawa ce,sau-tari sai ta kai zuciya nesa take iya kissing dinsa. Bata bashi bashi damar yin commenting ba domin ta rufe bakinsa gabadaya da tausasan labbanta. Sai a washegari ne da yake cikin nutsuwar sa yayi mata conclusion na zancen Hafsa Datti. Yace ya amince suyi kawancen su amma, bai yarda ba bai amince ba,not in anyway, tayi zancen sa kowanne iri ne da Hafsa. Su cigaba da magance abinda ya shafe su a tsakaninsu yadda suka faro. Ko Goggo ta zama thirdparty. Amina ta amince da umarnin mijinta,ko dama can kullum cikin umarnin sa take. Zata iya sadaukar da komai akan Maarouf Jikas. Wani kwayan mutum guda daya da ruhinta ke so, zuciyarta ke kauna, gangar jikinta ke bege. Allah kuma ya dauko yaya bata ba tareda tsimi ko dabararta ba. Yaya kuwa zaayi bazata zamto mai biyayya ga umarninsa ba? Da son duk abinda yake so tana so ko bata so,in cewa yayi ta gutsuro masa naman jikinta, shell do so willingly, without feeling any hurt,balle wannan kankanuwar biyayya? Wadda ko da bai fada ba ai tanada hankalin kanta. A abubuwa da dama sunna da raayi daya.Itama ba mai raayin hakan bace. Bazata taba iyatona sirrin sa ga kowa ba koda kuwa ga GOGGON data haife ta. Don haka da gudu ta amince da sharadin sa akan alaqarta da Hafsa Datti. Da safe kafin ya fita suna karya kumallo, a bisa dining-table mara tsayisosaisuke zaune na zallar gilashi (raw glass) kowanne kujerarsa daban tana fuskantar ta dan uwansa, amma can a karkashin table din kafafunsu harde suke dana juna.Ya dauki wayarsa dake gefe ya kira Turaki. Amina na jin sanda Dr. Turaki yace breakfast nakeyi Yaa Maulaya yanzu zan fito, ai takwas din bata idasa cika ba ni bani na kira ka ba, ina sane sai 8:30 zamu fito. yar ka ke son magana da kai Ya mikawa Amina. Murmushi tayi sosai ta karba Assalamu Alaykum my humble consultant amin waalaikumus-salam a daughter like no other, mun tashi lafiya? sai godiyar Allah! Yaa Maulaya ne yace inyi albishir da sabuwar kujera ta SSG. Zaayi taron kaddamar da kujerar rana ita yau. Allah ya taya ku riko bakidaya. Bata tsaya taji reaction dinsa ba ta mikawa Maarouf wayar. Tana ji Maarouf na cewa to menene abin kuka? You deserve it ne. What are friends for? Beside, kai ne SANADIN haduwa ta da alkahairin dana ke tare dashi a yanzu. Kai ka tsaya da hikimarka da zuciyarka daya saida na mallake ta, na samu kwanciyar hankali kuma kuka samu. Zan iya hakura da kujerar bakidaya na bar maka na zama mataimakin ka in ana yin hakan. Im rest assured zaka shugabanci alumma da gaskiya da amana. Don haka naga ba kujerar data kamace ka sai ta SSG. Daga ni har ita bamu cancanci godiyar ka ba. Ya kashe wayar sa. Da wannan amina da Hafsa suka cigaba da zumuncin su ba dare ba rana, zumunci mai tsafta da sanin ciwon kai. Amina na lallaba Hafsa ta koma makaranta ta yo Doctorate Degree ranar da suka dawo gida Nigeria zaiyi mata amfani. Hafsa na kara koyar da ita dabarun sace zuciyar miji ta hanyoyi masu kyau da maana. Ta bar ganin Maarouf baida raayin aure-aure komai dalili takeyi don haka ta tsaya ta kafa kanta yadda ya kamata yadda ko wata ta shigo saidai ta biyo bayanta. Dr. Zainab Turaki ta kira Amina karo na farko da suka taba gaisawa tayi mata godiya akan kujerar Dr. Turaki. Ta bawa manyan yayanta maza biyu Aadil da Aabid wayar sunyi mata godiya. Amina taji dadi sosai, da wannan sabo ya fara shiga tsakaninsu suke gaisawa sosai don Zainab ta iya takunta bata zaqewa, respect ne da girmamawa tsakaninta da Amina kawai. Anyi liyafar kaddamar da kujerar SSG, taro na farko na siyasa da Amina ta halarta, suka dumfaro dakin taron itada maigidan ta His Excellency Maarouf Habibu Ji-kas. Tana sanye da kyakkyawar doguwar riga ruwan makuba kirar Dammam ta zagaye fuskarta da mayafin abayar. Takalmin kafarta mai tsayi sosai, ta kama hannun Maarouf ta rike na rashin sabo. Kowa ya mike tsaye don nuna girmamawa yayin da suka shigo dakin taron na ( ) saida suka zauna sannan kowa ya zauna. Ga Gwamnan da maidakinsa Dr. Amina nanike dashi, ga mataimakinsa Prof. Bugaje da mai dakinsaZarah, sannan maigirma SSG da mai dakinsa Dr. Zainab da yaran su biyu. A haka aka fara gudanar da liyafar yadda aka tsara bayan mai gabatarwa ya gabatar da abinda ya tara su. Anyi vedio anyi hotuna iri-iri, yan jarida sun samu babban (cover story) yau kowa ya ga matar Ji-kas da yake boyewaba Laila Ji-kas ba. Kowa kuma ya bude baki sai masha-Allah. A haka taron ya tashi. Litinin na zagayowa Dr. Usman Turaki ya shiga sabon ofishinsa. Suka cigaba da gudanar da administration dinsu cikin ilmi da sanin makamar mulki. Talakawa na gamsuwa domin babu handama da cikin mulkinsu sai tsananin jin kai ga alummar su da bullo da hanyoyin kyautata musu. Kullum tunanin su shine, ta yaya zasu kyautata rayuwar alummar jihar su a fannonin rayuwa daban-daban? Ta yaya zasu ciyar da matasa gaba don sune shuwagabannin gobe. Ta yaya alummar karkara zasuji dadin rayuwarsu acan inda suke ba tareda gudowa maraya ba? Ta yaya zaa inganta lafiyar kananan yara daga ciwuwwukan zamani da suka addabe su? Ta yaya zaa samar da ingantattun mgunguna kyauta ga asibitocin gwamnati? Ta yaya malamin makaranta zaiji dadi ya san babu career mai daraja da kima irin tasa? Ta yaya? Ta yaya? Ta yaya Bauchi zata kere sauran jihohin arewacin Nigeria saanninta a fannonin ilmi, kiwon lafiya, infrastructure, aikin yi (employment) sanaoin dogara da kaida sauran alamuran cigaban rayuwa. Sunan Jikas na kara yin fice a tsakanin gwamnonin Nigeria yan uwansa. He is ranked asthe best governor inthe North on initiating stabilisation and developmentdaga shugaban kasa na lokacin wanda suke karkashin jamiyya daya. Anyi wannan taron karramawar a birnin tarayya Abuja inda shugaban kasa ya karrama shi, yayi kira ga gwamnonin arewa dana kudu yan jamiyyarsu (Northern People Congress) da aka fi sani da (NPC)kan suyi koyi dashi a hadu a ciyar da Nigeria gaba, jamiyyar su ta kara karbuwa a wurin alumma duk da cewa itace kan gaba. Amina ta halarci wannan taron karramawar, karkashin rakiyar Hafsa da mai gidanta Mahmoud wadanda suka kawo mata ziyara daidai lokacin daga birnin Belarus din kasar Russia.Tana gefen damansa inda duk ya sanya kafa nan take mayar da tata. Ta shiga cikin jerin matan gwamnonin Nigeria dake karkashin (Northern People Congress). Dukkansu kuma tafi su zati da ilhama wanda tsarkin riko da addini ke haifarwa mai shi. Sannan kuma jikinta a lullube cikin abayat kirar Oman kai kace daga can tazo ba don kalar fatar jikinta ba. Lokacin da Ilya ya murdo wa Goggo da Kaka abinda ke faruwa a Birnin Tarayya daidai wannan lokacin (live) a makekiyar plasma din falon Goggon, Goggo Hauwa ta gane Aminanta ce can kusa da matar shugaban kasa, ga Maarouf kamar ya maida ita ciki don kulawa, ya kasa boyewa duniya soyayyar da yake yi mata sabida tsohon cikin dake tareda ita, sai tasa kuka tana yi tana karawa tana yiwa Allah godiya.Kaka da Ilya na rarrashin ta. Ilya na fadin; dariya ai zakiyi Goggo ba kuka ba, kece SANADI. Shi kansa Ilyafarin-ciki kamar yayi yaya. A ganin Hajiya Hawwa, wani farin cikin yafi gaban ayi masa murmushi ko dariya, sai dai kukan. .....Alhamdulillah Alaa niimatihi. Shine abinda Goggo ke ambato har ba adadi. ***** WAIWAYE Laila ta cika iddarta, ba da jimawa ba zawarawa suka soma damun Dagaci da aike, ciki kuwa har da tsohon (fiance) dinta Mahdi maaikaci a gidan rediyon Jigawa. Dagaci ya zaunar da ita a wani marece ita da mahaifiyarta, ya ce. Laila, yau wata uku kenan da gama iddarki, babu Maarouf babu aikensa, ga manema Allah ya ba ki tun gama iddarki, don haka na ba ki sati biyu ki fidda gwani a cikinsu, in kuma za ki bi shawarata to ki zabi Mahdi, da sabon gini gwanda yabe. An sanshi, an san asalinsa, ke kika jawo ya janye auren ki a wancan lokacin, amma ya rage naki. Ni dai na ba ki sati biyu ki kawo min mijin aure cikin mutum hudun nan da suka addabe ni. Kin san ni sarai bana son rainin hankali, ba don addini ne ya ba ki wannan yancin ba da sai dai ki ji na daura miki aure. Laila na share hawaye ta tashi ta bar wajen, mahaifiyarta ta yi tsaki ta ce, Halin mutum ya ja masa ya ishi mutane da koke-koke. Amma abin ki da mahaifiya, can cikin zuciyarta tausayin ta take ji, koda bata amfanuwa da komai a zaman Laila gidan Jikas,tana yi mata fatan komawa. Mahdi tsohon saurayin Laila ne, har an sa musu ranar aure, ya aiko ya karbi kayanshi ya ce ya fasa, a sabili da har lokacin da aka yi musu baikon Laila ba ta daina sauraron sauran samarinta ba, shi kuma ga shi da kishi, ya yi ya yi ta bari ta ki, shi ya sa ya aiko ya ce ya fasa, ya karbi kayansa. Iyayenta duka a lokacin babu wanda ya ga laifinsa don su ma shaida ne, sun kuma tsawatar mata a lokacin ta ki ji sabida giggiwarta. Don haka yanzu da ya dawo ya ce zai aure ta a bazawararta shi ko auren fari bai yi ba, duk suka hadu suka yi naam da shi. Amma har kwanakin da Baban ya diba mata suka cika Laila ta ki cewa uffan. Har kullum tunaninta na ba ta cewa, Maarouf zai dawo gare ta ko ba dade ko ba-jima. To amma haka za ta yi ta zama tana jiran tsammanin warabbuka? (inji Mairon ABARI YA HUCE) Don haka ta yanke wa zuciyarta zuwa kai tsaye har inda Maarouf yake ta roke shi gafara, ta gaya masa ta yi nadama za ta rayu da shi da duk abin da ya yi mata umarni, yake kuma son ya rayu tare da shi. Don ta lura Hajiya Saude a wannan karon duk kawaicinta sai abin da Dan nata yake so za ta bi. Ta yi shiri tsaf ta ce da mahaifiyarta za ta je Gwaram wajen wata tsohuwar aminiyarta, Innar ba ta hana ta ba, don ta san yadda suke da Hannatun. Amma data samu rayuwa yadda take so ai watsar da Hannatun tayi,Lailah kenan. Tana zuwa tasha ta yi shatar karamar mota har Bauchi don bata son bata lokaci, tasan lokacin da yake dawowa daga ofis zata isa in a karamar motarta ne da yake akwai isassun kudi a tareda ita. Sojojin da ke gadin gidan gwamnatin duk sun san fuskar Laila a matsayin matar mai girma gwamna, babu kuma wanda ya san ya sake ta a cikinsu sun dauka tafiya tayi kamar yadda ta saba duk da cewa wannan karon ta dade fiyeda tsammani, ko kuma sun samu sabani ne a dalilin sabon auren da yayi, don haka sun yi mamakin ganin a yadda ta zo yau da motar da ta kawo ta, sai suka ki yarda su barta ta shiga, suka ce ta jira sai sun yi bincike tukunna. Waya suka yi ta bugawa har suka samu yin magana da Amina. Suka fada mata ko wace ce ta zo, kuma wai tana son a barta ta shigo. Amina ta yi musu iznin su barta ta shigo su kawo ta har downstairs. A dakin Amina na da aka sauki Laila. Ta zuba uban tagumi, ta tsura wa hoton Maarouf da Amina da yarsu Ameena ido, suna manne da juna sun yi kyau, sun yi kyan har sun gaji. Katon hoto ne da ya kusan cinye bango guda, sun dauke shi ne a hotel dinsu na birnin Jeddah bayan Amina ta samu lafiyar kafafunta a karo na biyu. Duniya juyi!. Laila ta ce a zuciyarta, da ta tuna yadda ta ke zuba mulki a gidan nan rana daya duniya ta yi mata gwatson mage. Amina ta hambare gwamnatinta, ta maida ta kauye. Tsanar Amina ta kara ninkuwa a zuciyar Laila, ji ta ke da da hali da ta danne ta da filo ta mutu ta huta. Amma ta yi amanna da cewa in har tana son ci gaba da zama da Maarouf dole ta koyi kissa wadda ada bata iya ba, take abubuwanta keke-da-keke, dole ta yakice wa kanta kishin Amina, ko ta ki ko ta so. Ta tusawa ranta kaunar wannan gawa ta ki ramin yar tasa. Ta nisa, ta ja dogon numfashi, daidai lokacin da mai aiki ta shigo da trolleydin abincin rana, ta jere mata su a diningta gaishe ta ta fita. Babu wani girmamawa ko jin tsoro irin yadda suke mata a baya, kamar ma ba su ji dadin ganinta ba, sun tuno yadda ta ke cin zarafinsu ne ga shi yau ita da su an zama daya. Sai da umarni za a ga uwargidan gwamna mai mutumta su da karrama su. Har gara ma su, sun fi ta tsafta da kyan gani a yadda ta koma din nan. Maarouf ya fito daga wanka, bayan shigowarsa cin abincin rana.Amina na jiransa a gefen gado ta mike tana tsane masa jiki da karamin towel, ta fiddo masa kayan da zai sanya bayan ta feshe su da turarensa. Dawowarsa kenan daga ofis ya shiga wankan ya fito. Sai da ta gama taimaka masa ya shirya ya janyo ta jikinsa yana fada mata, I have a green great giant surprise for you. Ki shirya wani kauye za mu je. Ta kwantar da kai a kirjinsa tana shakar kamshinbath-gel din da yayi wanka dashi,sannan ta ce, Kana da baki your excellency, ka fara (attending) dinsu sannan mu tafi. Ya dago fuskarta da tafukan hannayensa biyu ya soma (kissing) dinta lightly cikin wata irin siga har sai da dukkaninsu suka soma fitanutsuwarsu, sannan Amina ta yi karfin halin janyewa ta ce, Da gaske kana da baki, I would like you to attend to them first, sai mu je duk inda za mu. Harararta ya yi, sannan yayi tsaki yana saka rigarsa Wadanne irin baki ne zan je inda suke alhalin ban san ko su waye ba? Ka yi hakuri dai ka je, ka sani ba zan kawo wadanda za su cuce ka har sassan nan ba, haka (securities) din da ke cike da gidan nan, don Allah ka je. Da mamakinta ya ce, Suna ina? Ai sai ki wuce mu je tare in dodanni ne su fara cinye ki, haka kawai za ki tura ni wajen wadanda ban sani ba, ban san me ya kawo su ba?. Dariya Amina ta yi ta yi gaba ta zura takalminta marar tsayin dunduniya, Na yarda, wuce mu je. Ni a gaba kai a baya. Har ya zauna a kan kujerar hutawar da Amina ta fiya zama a kai lokacin aikinta a gidan bai gane Lailah ba, wadda kanta ke sunkuye. A sabili da abubuwa da yawa ya kasa gane ta. Na farko dai ta yi duhu tunda babu mayukan nan masu tsada na shafe-shafe. Na biyu ta yi lullubi wanda a da ba ta yi, sannan sitturun jikinta duk sun kode. Yana zama Amina ta kama hanyar fita, amma sai ta ji ya riko hannunta ta baya. Juyowa ta yi ta dube shi da idanuwan nan nata masu kama da zaiba don sheki da kyalli, ta girgiza masa kai alamar ya barta ta tafi. Ita ma tata zuciyar fal da wani irin kishi da bata san tana da shi ba, jin ta tayi ta rikide kamar ba ita batamkar wata mai (multi-personality disorder)amma ta yi kokarin hadiye shi. Ta yi magana ba tareda ta yarda sun hada idanu ba. Anty Laila ce ta zo ganinka. Da haka ta kwace hannunta ta fice. Laila ta sauko daga kan kujera ta rarrafo gabansa ta zube ta rushe da wani irin kuka. Mikewa tsaye ya yi da hanzari. Zan fita in zuwa ki ka yi ki tada min hankali. Me aka yi? Haka kawai ki zo min gida ki rusa kuka bayan ba wanda ya mutu cikin gidan? Laila ta tabbatar in ya fita kyakkyawar damar da ta samu ta ganinsa ta kubuce mata, don ba ta isa ta ganshi a ofis ba ko wani waje, ta yi saurin kama kafarsa ta rike ta soma jero masa ban hakuri masu nuna tsantsar nadamarta. Tana rokonsa ya yi mata alfarma cikin irin dimbin alfarmominsa ga alumma ya maida ita dakinta, ta yi alkawarin zai same ta mai biyayya a gare shi da zama lafiya da abokiyar zamanta, da kula da yar sa, da guje wa duk abin da ya furta ba ya so. Sai da ta dasa aya ya janye kafarsa ya koma gefe ya zauna. Ya sarke hannayensa cikin na juna ya tallafi habar sa dasu. Ya dube ta sosai tana faman share ruwan idanunta. A nitse ya soma yi mata magana irin wadda bai taba gaya mata ba, ba ta kuma taba zaton yana kunshe da su a zuciyarsa ba. Ta ya ya zan iya kuma ci gaba da zama da ke Laila? Ba kya girmama mahaifiya ta, ba ki damu da ita ba, ba kya kaunar abin da na haifa ko da da tausayi ne, ba kya tausaya min ba kya bani hakkin aure yadda ya kamata alhalin kinsan banida wata matar bayan ke kuma ni ba mazinaci bane, ba kya mutunta aurenki harkar neman kudi kawai ki ka sa a gaba. Idan na ce ba na son abu ke kuma a lokacin za ki nuna min yanzu ki ka fara sonsa, kin maida ni bankin karbar kudi ba mijin aure ba. Tunda na aure ki ba ki taba girka min abin da zan ci da hannunki, ba ki taba kula da alamarina ba sai alamuran kawaye da buga-bugar karbar kudin siyasa ne kawai a gabanki. Na bi kowacce hanya don in zauna lafiya da ke na kasa billewa. Na yi aure don in samu nutsuwa da karin zuria kin nuna ke mai iya aikata kisan gilla ce a kan hakan. Ta ina zaman aure zai ci gaba da irin wannan matar a ganinki Lailah? Ki yi hakuri ki rungumi kaddarar da Allah ya rubuto mana, ta cewa za mu rayu tare na wucin gadi ne amma kowannenmu da tabbataccen abokin rayuwarsa wanda zai samu nutsuwa a tare da shi. Na yi alkawarin zan yi muku komai na rayuwa ke da mijin da Allah ya ba ki, amma aure a tsakaninmu ya kare. Don ba zan so in tashi a ranar lahira da shanyayyen barin jiki ba na rashin yin adalci a tsakaninki da matata. Laila Im sorry, ki duba (account) dinki zuwa gobe za ki tadda sakona. Na barki lafiya. Ya fice da hanzari ya bar Laila durkushe tana gursheken kuka. Baya so ya bar tausayin da ya tsirga a zuciyarsa ya yi tasiri. A ganin sa hakan da ya yi shi ne daidai, kuma shi ya fi dacewa da rayuwar kowannensu. Laila ba kaunarsa ta ke ba, kudinsa da kyale-kyalen rayuwar da ke tare da shi ta ke hange. Ya yarda da hakan, yana so ita ma ta yarda. Ya yi alkawarin ba ta su (kudi da kyale-kyalen) amma ban da Maarouf da gangar jikinsa. Haka Laila ta baro gidan gwamnati wutsiya a zage amma zuciyarta a dake. Ta tabbata ta bar gidan da mai shi har abada. Ta auna kalamansa a sikeli na hankali da tunani babu wanda ba ta amince gaskiya ya fada ba. Abu daya ne ba ta amince ba da Maarouf ya ce ba ta sonsa, kudinsa ta ke so. Ta amince farkon zuwansa rayuwarta da gaske kudin ta ke so, amma ban da yanzu. Ita kanta ba ta san hakan ba sai da ya bar rayuwarta kwata-kwata. Ta amince ta hakura da Maarouf har abada, za ta je ta gina sabuwar rayuwa ta manta da shi da duk abin da ya shafe shi, tunda ba shi ne autan maza ba. A washegarin ranar ta samu (alert) na zunzurutun kudi naira miliyan goma shha biyar cikin asusunta. Amma ga mamakinta ta kasa yin farin ciki da su. Yanzu ne ta gane cewa, SO YA FI KUDI, amma tata soyayyar ta zo (at a wrong time). Da a ce ta san (account number) dinsa mayar masa da su za ta yi. A ranar ta tabbatar wa mahaifinta ta zabi Mahdi a matsayin mijin aure. Ta yi aniyar gyara zuciyarta ta koyi yin komai saboda Allah, ta daura aniyar yin amfani da damarta a lokacin da ta zo mata ba za ta kara wasa da ita ba, ta koyi girmama iyayen miji da yan uwanta da duk dan Adam din da rayuwa ta hada su tare. Za ta koyi daukar duniya da sauki ta rage (high taste) domin ba ya amfanar da kai komai. Ubangiji ya dankwafar da shaidan ne saboda girman kansa. Ta yarda da duk laifuffukanta da Maarouf ya zano, wadanda ba za su bari ya iya ci gaba da rayuwar aure da ita ba. Tana rokon Allah ya sa yadda ta yi aniyar gyara halayen nan nata halayen su gyaru a rayuwar aurenta na gaba. Zuciyarta ta gyaru ta koma yin komai saboda Allah. **** An daura auren Laila da Mahdi ranar wata asabar. Da sati ya zagayo ta yi walima ta tare a gidansa da ke cikin garin Dutse. Kudin da Maarouf ya ba ta da su ta yi amfani ta yi wa kanta komai ta kuma taimaka wa Mahdi ya kara gyara gidan ya fito fes! Ta sayi mota ta ja jari ta koma makarantar da Maarouf ke ta goranta mata. Komai na Maarouf ya zama bygone a gare ta, ba ta ko son tuno rayuwarsu ta baya, ta dumfari sabuwar rayuwarta da ikhlasi. **** Hannunta kawai yake ja har zuwa falo na karshe, wanda daga shi za su tadda motocin da zasu shiga da masu mara musu baya. A nan ne ta daddage ta kwace hannunta ganin ba shi da damuwa don maaikatansa sun gansu a hakan. Wani irin kallo ya bi ta da shi wanda ita kadai ta san maanar sa. Ya lura a cike take idanunta sun juye kamar ba ita ba. Wannan balai har ina? Yana zaman-zamansa ta daukeshi ta kaishi yanzu kuma zata yi masaprotestmara dalili, shi meye laifinsa? Bayan fitowarsa daga wajen Laila yazo ya sametadon su tafi inda yace zasu tafi, budar bakinta sai cewa tayi ita ba inda zata, su tafi shi da Anty Lailah. Da farko abin haushi ya bashi sai kuma ya koma bashi dariya. Ya fincikota yana fadin wallahi sai kin je, bana niyyar fita in fasa kan wani abu marasa tushe da madafa. Shine ya janyo ta tana turjewa amma karfin ba daya ba, a haka suka fito. Inda ta gode Allah basu hadu da kowanne maaikaci ba. Suka fada mota yana dama tana hagu, mai tsaron lafiyarsa a gaba (securities) suka biyo su a baya. Sai da suka dauki hanyar barin gari ta ji ya ce da direban Shira za su je. Suna tafe ba mai magana da dan uwansa, hadiyar zuciya kawai takeyi alhalin ba kuka tayi ba. Yayi banza da ita yana amfani da wayar hannunsa har suka isa. A can bayan gari tsakiyar gonaki Amina ta ga an yi parking a daidai wani katon gate. Motocin suka tsaya, a nan duk suka firfito. Sanye ta ke cikin riga da zani na atamfa ta yi lullubi da wadataccen mayafi launin adon atamfar jikinta. Ta yi kyau kamar koyaushe. Don ita ba sai ta bata lokaci wajen yin kwalliya ba, kullum kyakkyawa ce ahalittar Ubangiji mara yawan kyalekyale. Kowanne kalar kaya ta sanya karbarta suke su amsheta su dace da zubin halittarta. Physiotherapist Amina Masud kenan. Masu gadin gidan suka bude wawakeken gate din. Nan Amina ta yi arba da kasaitaccen gidan gona na kiwon tsuntsayen gida, amma tantabaru farare sun fi yawa. Bude baki ta yi tana kallonsa bakinta kamar zai tsage, ya wani kawar da fuska ya tamke ta, ta karasa inda yake ta manta ba su kadai bane ta kamo hannunsa, ta russuna saitin kunensa tace Maarouf Jikas! Im dying for you, my heart is itching da tamkewar fuskarka. Waiwayawa yayi da sauri don ba ahankali ta fada ba, babu wanda hankalinsa yake kansu cikin yan rakiyar nasu sun yi gefe sun samar da space sosai a tsakaninsu. Yayi ajiyar zuciya. Kai wannan yarinyar sai a barta. Ya kwace hannunsa ta kara rikowa ..... na tuba, na bi Allah na bi ka! Tayi conclusion da marairaice idanunta cikin nasa. Bashi da katabus a duk lokacin da ta kira yi sunansa na ainihi, wanda ba kasafai take yi ba tun sanda ta fahimci fadar hakan na sanya shi a wani hali, tafi cewa (Your Excellency)a gaban kowa don ya zauna lafiya. Sai in sun kebe ne take kiranshi da duk yadda taga dama. A take ya sassauto, hannunta dake cikin nashi ya bi da kallo yana murmushi infront of them Ameenah? Hawaye suka cicciko idanunta kayi hakuri in nayi laifi, bazan iya sakin hannun bane. Ta fada cikin emotion (shauki). Da gaske ya bata a very big giant surprise kamar yadda yace which she didnt expect. Tantabarunta ne fa sukayi wannan bunkasar. A mahaifar mahaifinta SHIRA. Sai ya kara damke hannun nata sosai cikin tafin hannunshi, ya jata suka shiga zagaye gidan gonar lungu da sako. Sun kasa cewa juna uffan zuciyoyi kawai ke aiki, farin cikin Amina heighteneda lokacin da ta gane dukyawan tantabarun da ke ciki nata ne suka hayayyafa. Sai da suka gama shirunsuka tsaya cikin dakin tantabarun suna fuskantar juna, ta mika hannu ta kamo aure daya ta dora akan tafukanta, suka tashi firrr!Suka koma tukwanensu alamun sun manta da ita, dada ne bazasu tashi ba. Zama zasuyi sai ta maida su da kanta. Ta dubeshi ya dubeta ya daga mata kafada alamun ita ta jawo sai sukayi dariya, anan ya gaya mata cewa duka wannan gidan gonar nata ne, mallakinta ne. Ya hayo kwararru a kiwon tsuntsayen gida ne suna kiwata mata su. Tunda yanzu bata da lokacin hakan. Tantabarunta da ya amsa ne suka yi wannan albarkar bayan nan kuma ya kwaso nata na gida da iznin Goggo ya hade. Surprise din da ya ce zai mata kenan. Tukuici ne ya ba ta for bringing happiness to his life, for her sacrifice to hisdaughters life(na kawo farin ciki a rayuwarsa da ta yi, da sadaukarwarta kan rayuwar diyarsa). To sai ta rasa me zata ce masa. Shi kuma me ya kawo cikin tata rayuwar? Contentment, love,affection, devotion, family tie, and everything!Ita bata da abinda zata bayar tukwicin, banda mallaka masa kanta da komai nata wanda dama nasa ne. Kawai sai ji ya yi ta yi azama ta rungume shi tsam-tsam tana hawaye. Ubangijin da Ya halicceta Shi Ya sanya mata kaunar tantabarun mahaifinta. Kwarai ta ke sonsu, ta maida su wani bangare na rayuwarta. Su ne kadai take kalla ta tuna ya bar mata wani abu na rayuwarsa. Ta dade tana tunanin yadda za ta habaka kiwonta yau ga Maarouf ya cika mata burinta, ya hutar da ita, kuma a kasar mahaifinta (Shira). Damka mata takardun gidan gonar ya yi, ya gabatar mata da maaikatanta, ya kuma gaya musu ita da su cewa, yanzu hakkin kula da gidan gonar da hakkin mallakarsa ya koma karkashin ikonta. **** Shekaru uku kenan da auren Maarouf da Amina, tana goyon danta na biyu mai sunan Baban Maarouf wato Habib da suke kira ABBA. Wanda ya biyo bayan danta na fari Masud. (Hanif). Maarouf na gab da sauka daga kujerarsa don haka komai ya cakude musu, ba ya samun zama ko kadan, suna yawon kamfen gari-gari don neman samun kara hayewa gwamnatin Bauchi a karo na biyu. Sosai suke kewar sa a gidan musamman Hanif da yayi mugun sabo da mahaifinsa. Hatta wanka in yana gida shi yake masa. Abba dan maman sa Hanif dan Abbansa.Kullum haka rayuwarsu take cike da soyayya tatacciya kamar Zuma. Sabuwa take komawa a ledar ta, kullum cikin mararin junansu suke. To komai yayi farko zaiyi karshe. Yau shekarunsu hudu ba wata uku akan karagar mulki. Tenure tazo karshe sai fafutukar yadda zaayi a cigaba. Kai ya dau zafi komai ya cushe musu babu lokacin iyali ko kadan. A irin wadannan lokutan Amina na yiwa mijinta uzuri, bata damunsa, bata nanike masa, bata binshi da korafin rashin zamansa a gida. Mayar da hankali take kan ibada da rainon yayanta tana kuma binsa da kyakkyawar addua. **** A daya gefen tsohon kwamishinansa na kananan hukumomi da mai ba shi shawara kan ci gaban karkara da ya sauke sun dade da fito da sabuwar jamiyyar adawa (opposition party) da suka sanya wa suna NRC (Northern Region Congress) sun fito da karfinsu suna yakar (NPC) ta karkashin kasa da ta duk sauran hanyoyin da zasu iya. Tsohon kwamishinan Abdallah Ganjuwa da tsohon mai bada shawarar Yushau Saminu sun tsaya neman kujerar gwamna da ta mataimakinsa. Lokacin da Maarouf ya samu wannan labarin daga bakin Turaki da sauran kwamishinoninsa a dakinsu na zartarwa bai yi mamaki ba, in kanna siyasa ba abinda bazaka gani ba, sun ci gaba da kulla wadda za ta fishshe su ne kawai ba su sanya su a lissafinsu ba balle har su dame su. Amma abin mamaki abin da kuma yaa kada yan hanjinsu shi ne yadda alummar jihar da dama suka soma karkata zuwa (NRC). Lokacin da aka yi (primary election) Maarouf ne ya ci, a can su kuma Abdallah ne ya ci. Allah kadai ya san irin kulle-kullen da suke yi wa (NPC) har da bin bokaye da yin kazafi iri-iri gare su. A cewarsu, mabiya jamiyyar (NPC) masu ruwa da tsaki dukkansu sumumu-kasau ne, wai macijin sari-ka-noke, kasancewarsu tsofaffin jiga-jigan jamiyyar suka rinka fidda sharri kala-kala da suka shirya musamman da rahotanni na karya da alkawurra iri-iri masu ban mamaki ga alummar jihar. Da yawa an karkata gare su tunda Maarouf din ai dan Adam ne kamar kowa dole a wani fannin yana da kasawa. Duk da kokarin su Ilya na shiga birni da kauye suna karyata zargin da ake yi wa jamiyyarsu da kare gwamnatinsu an ce wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi, Abdallah da Yushau ba rana daya suka fito ba, kwanton bauna suka yi wa (NPC) suka rarake kasansu kamaryadda suka ci alwashi. Sannan bokayensu sun dade suna shiri a kan wannan lokacin kan Maarouf da magoya bayansa. Lokacin da zabe ya matso ya zama ko lokacin gidansa ba ya da shi, ya shiga damuwa. Yadda ya shiga damuwa haka iyalinsa, hatta Abba da ake goyo ya san rayuwar gidansu ta sauya. Amina sai ta kwashe sati guda cur bata sanya Maarouf a idanunta ba. Hakan baya damun ta addua kawai take ba dare ba rana, idan mulkin nan alkhairi ne a gareshi Allah ya maimaita masa, in babu alkahairi tana rokon ubangiji ya fitar dashi daga ransa ya huta suma su huta. Ranar zabe duk suna (polling unit) na mazabarsu shi da iyalinsa, Amina rike da hannun Hanifa Abba yana kwance a kafafunta, anyi-anyi a karbe shi ya ki sai kuka yake yi, ta zauna don ta shayar dashi ya ki yarda ya kama nonon sun rasa abinda ke damunsa, Dr. Turaki ne yayi nasarar karbar sa ya fita daga wajen dashi, Amina ta rasa abin da zatayi ta rasa me ke mata dadi kawai sai ta tsugunna ta soma kuka. A cikin tawagar harda Goggo, Kaka Maryama, Inna zulai, Dr. Zainab Turaki da nata iyalin, Ilya da iyalinsa, yaransa biyu shima, Hajiya Saude wadda aka fi sani da Hajiyan Ji-kas, Alhaji Mansur da daukacin iyalinsa, Uwa uba mahaifin da ya haifeshi Mallam Habibu, Dr. Umar Bolori da family din gidansu duka, da duk wani makusancinsa suna tattare a rumfa guda anan suka jefa kuriunsu. Aka taru akan Amina ana lallashin ta wadda baa san kukan me take ba, ita kanta bata san kukan me take yi ba ko me ya sanya ta kukan, ta san danta lafiyarshi kalau yanada damuwa ne irin ta kananan yara ga iyayensu har suka dawo gida, amma da tayi tsam da zuciyarta sai ta fahimci Maarouf take tausayawa, tausayi mai dumbin yawa domin jikinta ya gama bata zaben nan basu da nasara. Suka dawo gida suka zauna gaban radio. Aka tafka zabe aka gamaa karo na biyu, Maarouf Habibu Ji-qas ya fadi. Wato ya sha kaye daga abokin karawarsa Abdallah Ganjuwa. A lokacin da zuciyarsa ta afu ga son ci gaba da kujerarsa!!! Bai san yana son mulkin har haka ba, sai lokacin da kafafen yada labarai suka bayyana an kayar da shi. Kayarwa daga abokin takarar da bai taba zato ba. Ya shiga damuwa ba yar kadan ba, Amina dake gefe ta kashe radion, ta shiga karfafa masa gwiwa tana tunatar da shi muhimmancin yarda da kaddara mai dadi ce ko mara dadi, tana ankarar da shi tarin niimomin Ubangiji a gareshi, kada ya butulce, ta cigaba da tuna masa; sanda ya bashi mulkin nan fa ba kokarin sa bane ko na magoya bayansa, ya gode maSa, ya karbi sauyin da hannu bibbiyu. Ya bude ido yana kallon ta,wani irin kallo mai tsayi da zurfi, a zuciyarsa yana fadin ko da ke kadai na tsira zan iya rayuwa a duk inda na tsinci kaina. Sabo ne turken wawa!!! A fili ya rinka maimaita kalmar Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Har sau uku. Wata irin nutsuwa ta zo masa. Ya runtse idonsa ya bude su a kanta, ya mika mata tafukan hannayensa biyu ta kama ta mikar dashi tsaye. Toilet ya nufa ya dauro alwala ya tada sallah. Amina ta mara masa baya ta hanyar janyo hijabinta ta bishi sallahr. Sosai suka samu nutsuwa, da gaske ne samun mata ta gari shine cikar rabin addini. He thank ALLAH for this blessing, yana rokonsa ya tashe su tare har a gidan aljannah. Ya kwantarda kai a kafadunta, ta rike shi sosai a jikinta. Tuni ya manta da komai. **** SAUYIN RAYUWA Suna ji suna gani ranar wata asabar suka tattara suka fito daga gidan gwamnati, Amina kullum cikin kwantar wa da maigidanta Maarouf hankali ta ke har ya ware ya saba da sabuwar rayuwarsa. Suka share gidansa na Fati Muazu, sabuwar rayuwa ta fara. Ameena little ta gamaprimary a shekarar. Mahaifinta ya kai ta makarantar sakandire ta kwana ta Nigerian Turkish dake Kanoaka sanya ta a J.S.S 1. A shekarar ne kuma Amina ta kara haihuwar yarta mace mai kama da ita a komai. Ta roki Maarouf alfarmar ya sanya mata sunan kakarta da ta rasu a wannan shekarar, mahaifiyar Goggo, wato Maryama, suna kiranta Maryam. Amina ta koma bakin aikinta a asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa (ATBU Teaching Hospital), da taimakon Dr. Turaki. Maarouf ya koma (contract) din gine-ginensa, saidai samun kwangilar gine-ginen ya ja baya ba kamar da ba, tunda gwamnatin dake bada kwangilar ba tasu bace. Sauyin rayuwar da suka samu za su iya cewa mai yawa ne. Abin da za a ce shi ne ba sojoji babu bodyguards da masu take baya, babu (security), babu maids rututu da sauransu, bayan wannan babu ta inda rayuwarsu ta canza ba su nemi komai sun rasa ba sai mulki da abin da ke zagaye da shi. Bayan barinsu gidan gwamnati Ilya ya zama babban yaron Maarouf shi ke kula da harkokin gidansa kuma ya yanka albashi yana ba shi duk wata duk da bai kai wanda yake karba lokacin da ana gwamnati ba, cike da godiya da kyakkyawar zuciya yake zaune da uban gidansa. A tsayin shekaru uku na zaman su gidan Maarouf na Fati Muazu Links, Amina ta sake haihuwa, wannan karon ma diya mace ta haifa. Maarouf ya yi mata kuhtbah da sunan mahaifiyarsa, wato Saudatu. Shekarunsu biyar kenan da aure yayansu hudu, maza biyu mata biyu da babbar Yayarsu Ameena, wadda ke zana jarrabawar kammala karamar sakandire a wannan shekarar daga Nigerian Turkish. **** GASKIYA DOKIN KARFE! Shekaru uku kenan da kafuwar sabuwar gwamnatin (NRC) a jihar Bauchin Yakubu, tun kafin a kawo wannan lokacin talakawan jihar suk soma dandana kudarsu a hannun sabon gwamna Abdallah Ganjuwa. Hatta ruwan sha da na amfani ya gagare su, wutar lantarki sai a yi wata ba a kyallaro musu ita ba, jinkirin albashin maaikata da sauransu. Wannan kadan ne in aka yi laakari da yadda rashin tsaro ya bi ya addabi jihar, sata, sane, kwace da fashi da makami, hanyar Bauchi ba ta biyuwa saboda yan fashi da suka mamaye ta kuma gwamnatin ta kasa yin komai akai, haka kebantattun unguwanni basa shiguwa, babu wani kokari dagagwamnatin jihar ta kasa yin komai sai sata da itama ta sanya a gaba. A yadda talakawa suke tunzure da sabuwar gwamnatinsu da da-na-sani wajen zabenta la-shakka da lokacin mulkin soja ne, sai sun yi mata juyin mulki. Allah-Allah suke ta gama cin-zalinta ta kara gaba su dawo da gwamnatinsu mai adalci. Ko da wannan (rumours) ya shiga kunnen Maarouf tsaki ya yi, ya ce, ina! Siyasa ya gama ta, ba ya fatanta, ba ya sake kwadayinta. Matasan Bauchi wadanda suka san sun amafana ne karkashin (Maarouf Foundation) har suka tsaya a kan diga-digansu sun ci alwashin sake tsayar da tsohon gwamnansu duk da ya bayyana raayinsa na ba ya shaawa, ba ya bukata. Ilya ne ja-gabansu suka yi tattaki suka tadda Baba da Alhaji Mansur da kokon bararsu na su shawo musu kan Engineer Maarouf ya yarda da kyakkyawan kudirinsu su sake tsayar da shi takara a karo na biyu. Baba da Alhaji Mansur suka sanya shi a gaba a wani yammaci, su billo ta nan ya billo ta can wajen nuna ba ya raayi, siyasa sai ta neman aljannah ce ta rage masa. Su kuma suna fadin jihadi zai yi in ya koma ya ceto alummarsa daga hannun wannan azzalumin shugaba. Haka yana ki yana komai matasan Bauchi suka yi gangami suka sai masa (form) na tsayawa takarar gwamna a karo na biyu. Ilya ne shugaban kamfen a birni da kauyuka, ya tsaya wa kamfen din da jikinsa, lafiyarsa da aljihunsa, ba su samu kwanciyar hankali ba sai da suka maida shi kan kujerarsa ta gwamnan Bauchi a karo na biyu. Amina ta hakura da aikin asibitinta a karo na biyu ita ma, Maarouf ya bude mata asibitin kula da masu lalurar shanyewar barin jiki nata na kanta, ta ci gaba da kula da Goggonta da yan uwanta. A dalilinta sai da dukkan danginta suka baro kauyen Shira suka dawo maraya, ta sama musu abin yi. Wadanda ba sa son zaman marayar sun samu abin yi mai karfi a kauyen, Hassan dan Baffa Bilya na cikin wadanda ba sa son zaman marayar shi da iyalinsa, shi ta nada wa alhakin kula da gidan gonarta na tantabaru da tsuntsayen gida da ke Shira. A wani hutu da Maarouf ya dauka na karshen shekara Amina ta jajibeshi suka yi Sierra Leone tare. Ya ga tarba ta mutumci da karramawa daga dangin Amina. Yaran duka har Amina karama sun ji dadin hutun su a Sierra Leone sabida basu taba fita daga cikin Africa ba saboda patriotism din mahaifinsu. Gara Amina little taje Saudiyyah sau uku. Maarouf da Amina suna adduar Allah ya basu tsawon rai su cika barinsu akan Aadil (babban dan Dr. Turaki) da little Amina, wanda ke ajin farko a jamia yana karantar medicine. Rayuwar Maarouf da Amina ta ci gaba da yin albarka cikin niimomin Ubangiji masu yawa, sun tara iyali masu albarka. Suka ci gaba da cin gwamnatinsu cikin kwanciyar hankali da burin neman kujerar da ta fi wannan a can gaba idan mai duka ya yarje masu da lafiya da nisan kwana. **** Masha Allah laquwwata illa billah. Nan na kawo karshen littafin SANADIN KENAN 1, 2, 3&4, sai mun hadu a littafina na gaba mai suna:- AUREN KWANGILA. Taku har kullum. Sumayyah Abdulkadir Takori. DANDANO DAGA AUREN KWANGILA! N isawa AbdulAziz yayi, ya sauke numfashi mai nauyi, Ishma, wata musiba ce ta tunkaro ni nake so ka taimaka min. Nikuma nayi maka alkawarin yi maka duk abinda kake so a duniya, zan kuma dinga raba albashina biyu ina turo maka rabi har ka gama karatun ka ka tsaya da kafafunka. Maganganun sounds funnya kwakwalwar Ismael Dakata. Daga ji ba abin alkhairi Yayan zai nema ba tunda har sai ya biya laada. Ni kuwa me zan yi maka da har sai ka biya ni Yaya Azeez? Gaya min ko me kake so in yi maka kawai in har na alkahairi ne zanyi. Zan iya fansar da raina don in cece ka. Amma wace irin musiba ce wannan da iyayenmu bazasu iya yi maka maganin ta ba sai ni? Su suke son jefa ni cikinta ai Ismael subhanallah! Please Yaya kada ka sake fadin haka, nayi amanna bazasu taba jefa ka a musiba ba sai alkhairi ga rayuwarka. Yanzu dai me kake so inyi? A shirye nake da in taimaka in har zai tafiyar da damuwar ka. Wallahi ba sai ka bani komai ba zanyi, nima ka sanya ni cikin damuwa matuka Abdulaziz ya canza rikon wayarsa daga kunnen dama zuwa hagu, ya juya ya tabbatar babu kowa a cikin dakin kuma babu motsin kowa daga waje. So nake ka bugo waya wa Mammah, ka ce mata ka dade kana son Hafsat, don Allah a baka aurenta, ka kasa maida hankali kan karatun ka saboda soyayyar ta, ka ce sonta kake tun tana yarinya, ka nuna mata irin wani abu zai iya samun ka dinnan idan baka samu aurenta very soon ba, sauran kalaman ka tsara abinka ai kai ba yaro bane tunda na baka topic din, ka gane? Mamaki ya gama kashe Ismael a tsaye, sai da ya lalubi kujera ya zauna Yaya wace Hafsat din? Ta gidanku mana? kana nufin Suhaana? nifa Ishma sunannakinnata ba duka na rike ba, kuna kiranta da sunaye barkatai, I dont know! Ta wajen Mammah dai . Don Allah Yaya muyi magana ta fahimta, Hafsat-Suhaana Addar Mammah? A ginshire Abdulaziz ya rausaya da kai Eh, ita, don naji Baba Azumi ma ta ce mata Addar. Dariya ta kama Ismael amma ya gimtse, yanzu ya gano bakin zaren duk da bai gayamasa ba. Mamakin Yayan nasa ya kama shi matuka, amma tunda bai fito fili ya gaya masa dalilin bukatar tashi gareshi ba, bari ya bishi a hakan. Yaya akan me to? Akan me zanyi hakan? Akan me zan yaudari Mammah inyi wasa da hankalinta akan abin da ba haka yake a zuciyata ba? Yaya Hafsat mai martaba ce a wajen Mammah damu bakidaya da muka rayu tare muka san wacece ita, wace irin martaba Allah ya yi mata. Kasancewar ta ba jinin mu ba, baya nufin bama kaunarta ko don kaunar da mahaifiyarmu ke mata. Yarinya ce ta gari, amana a hannun mahaifiyarmu, ta yaya kake tunanin zan iya playinggame akanta? To akan me ma? AbdulAziz ya hadiyi miyau, jin makoshinsa ya bushe kyamas, ga dukkan alamu bazai samu nasara a plan 1 ba, amma dai bari ya cigaba da turzawa tunda Ismael dai a kasan sa yake. Akan duk kaunar da kuke mata bata kai wadda ke tsakanina daku ba......!!! AUREN KWANGILA! Yana zuwa bada jimawa ba, goron sabuwar shekara Insha Allah. Tare da SUMAYYAH ABDULKADIR. Nuwamba, 2018