*SAKAYYAH Book 3 PAGE 1* Na *Aysha Aliyu Garkuwa* *Sanarwa! Sanarwa!! Sanarwa!!!* *PART OF OUR DESTINY* *Shin ko kunsan shahararriyar marubuciyar nan me suna *FATYMASARDAUNA* marubuciyar *SHU’UMIN NAMIJI* *SOORAJ* *LAYLERH MALEEK* *MAJNOON* ta sake kawo muku sabo kuma dadd’an littafinta dake cike da tarin zazzafar soyayya me gigita hankali, sadaukarwa, k’addara, da kuma hamshakiyar Kaunar dake gudana acikin jinin jikin mazaje guda biyu da suka kasance y’an uwan juna, duk acikin littafin nata me suna *PART OF OUR DESTINY* kada ku sake abaku labari domin samun karantawa da kuma shiga cikin group din marubuciyar zaku biya 500 ne kacal ta wannan account number din 2268498748 Fatima Abubakar UBA bank, ko ku tuntub’eta ta WhatsApp number dinta kamar haka 07069917168. Kada ku Bari abaku labarin wannan littafi me suna *PART OF OUR DESTINY* littafine dake cike da tarin zazzafar soyayya.... Ahankali ya kwantar da ita kan cikinsa, tare da yi mata pillow da ƙirjinsa, sai kuma ya jawo blanket ya ɗan rufe su. ahankali ya haɗa tafin hannunsa waje ɗaya tare da karanta addu'oin bacci _Falaƙi, 3 Nasi 3, Ƙulhuwa 3, Ayatulkursiyyu, 1 kana ya haɗa da Amanarrasulu1 Laƙadja'akum_ yanayi yana hura hucin numfashi nai cikin tafukan hannunsa. Cikin kulawa ya shafa mata kana. Yayi kansa shima ya shafa ajikinsa yana mai lumshe Idanunsa, hakanan yake jin wani irin farin ciki wanda tunda yake a iya tsawon rayuwarsa bai taɓa riskan labarin da yasa shi farin ciki da jin daɗi ba kamar wannan labarin ba, ko labarin kasancewar su Didi iyayensa baisa shi farin ciki kamar wannan labarin cikin nasa ba, ya rasa ya aka yi labarin ya kasance masa baƙon lamari abin yazo masa abazata, sabodaai kawo hakan a ransa da sauriba, shi ganima yake ai Khausar ɗin ƙaramace. Haka ya kwana cikin tsananin jin daɗi da farin ciki kusan a zaune ya kwana da zaran ta motsa zai gyara mata kwanciya. A gefen Hajiya Bunayya ma ita ma haka ta kwana da azabebben ƙaiƙayin dake addabar rayuwarta Rayuwa tayi mata ƙunci haka ta kwana ƙaiƙayi ya hanata kataɓus. Ana kiran Sallar Asbah ta fara sauƙe numfashi saboda jin ya fara lafawa, kamar abin Jaraba ƙaiƙayin ya daina wunin ranan haka tayi tana rama bacci da bata samu ta yi shi a daran ba. Ana kiran Sallar Maghriba ƙaiƙayin na Assalamu alaikum yana sake dawowa haka wannan ranan ma haja ta kwana ƙaiƙayi, gaba ɗaya ta rasa inda zata sa kanta jin ƙaiƙayin ya gallaza mata yasa ta haɗa ruwan zafi da gishiri ta cika Baho da ruwan ɗumi da gishiri ta shiga cikin. Numfashi wahala ta fara sauƙewa jin abin ya fara lafawa, Sai kuma tayi saurin sunkuyar da kanta jin yadda wasu abubuwa caccakarya a wurin. Ido ya kuma fiddawa sosai saboda ganin wasu ƙananan tsutsotsi masu baƙin baki suna fita ta gabanta asaman ruwa bisa alamu sune suke sa mata ƙaiƙayin kuma suke hanata bacci. Shiyasa idan ta shiga ruwan zafi sai take jin sauƙi idan ta fita kuwa ko awa ɗaya bazai kai ba zai da meta.. Haka dai take fama da wannan rayuwar da zaran dare yayi tayi sallama da kwanciyar hankali da bacci sai kuma safiya. Haka ta rayu tsawon Makonni biyar tana fama da wannan azabebben ƙaiƙayin da bai nuna alamun akwai sauƙi ko sassauci ba. A gefen Samira Sani ma ita baki ɗaya rayuwa ta sake yi mata ƙunci da duhu abin ba a cewa komai. Morocco Acan gefen su Khausar kuwa rayuwa tayi daɗi Khausar na samun kulawa na musamman daga gefen uwar mijinta da kuma Kakar Mijinta Niyna kana da Innayi. Hadimanta nayi mata komai daya kama na rayuwa har zuwa yanzu bata iya wani cin abinci amma ko yaushe cikin Hidima suke mata haka Didi nayi mata komai na sungullan rayuwa takowa mata wannan ta kawo mata wancan, amma bata iya cin komai yau tsawon kwana goma shabiyar da jin labarin Khausar nada ciki, wanda haka yayi dai-da cika wata biyu kenan da cikin yayi. Kwance take akan 3sitter yayinda tayi pillow da cinyarsa. Cikin sanyi ya shafa kumatunta tare da juyiwa ya kalli plate ɗin abincinta kwata-kwata ko cakali shida mai kyau bata yiba. Cikin takaicin rashin cin abinci ya shafa cikinta dake lafe kamar bata da komai cike da damuwa yace. “Minha”. A hankali ta ɗan ɗago kanta ta kalleshi jin yadda ya kirata da alamun damu cikin kula yace. “Rashun cin abinci kinnan yana damuna, ina ga zan kira Momy in faɗa mata matsalar rashin cin abinci nan koda shawarar da zata bamu”. Ware manyan Idanunta dake lumshe kamar na mejin bacci tayi tare da cewa. “Momy kuma?”. Kai ya jinjina mata, cikin sauri tace. “Bana ce maka mubar maganar faɗa wa Momy nan ba”. Yana shafa gashinta yace. “Gsky ni dai inaga gwara mu gaya mata wata ƙil kiga mun samu mafita?”. Kai ta girgiza tare da cunno bakinta gaba tace. “Kenan me zaka ce mata?”. Kallonta yayi tare da tallafo kanta ya juyo da ita suna fuskantar juna cikin sassauta murya yace. “Ce mata sanyu Minha bata cin abinci ni kuma rashin cin na damuna”. Lumshe Idanunta tayi tare da buɗe su akansa cikin yanayin irin mata masu fama da laulayi tace. “ Idan tace maka me ya hanani cin abinci ke zaka ce mata?”. Matsota yayi sosai kana yace. “Ce mata zanyi kina da cikine kuma yana hana ki cin abinci?”. Zare idanu tayi kamar wacce tayi wani laifi sai kuma ta kife kanta akan ƙirjinsa. Lallausan murmushi ya saki kasancewar tun washe garin ranan da akace tana da ciki yace zai faɗa wa Momy amma fir taƙi yarda wai tana kunya, sosai ta sake mannuwa ajikinsa kana ta manna kanta da faffaɗan ƙirjinsa cike da kasala tace. “Nikam Yah Mu'allim Ina kunya taya zaka faɗawa Momy wannan magana Taya zaka faɗa wa Momy cewa ina da ciki Fisabilillahi yanzu sai ka iya faɗa?”. Murmushi yayi tare da cewa. ”Toh mene cikin nan fa halartacce ne, cikine mai gata mai daraja gashi da mahaifinsa na rasa kunyar me kikeji?”. Kallonsa tayi da mamaki sai kuma ta langwaɓar da kai tace. “Yanzu Yah Mu'allim baza kaji kunyar cewa Momy ina da ciki ba?”. Idanunsa ya buɗe tare da karkata mata kai kana yace. “Toh me aciki?,me abin kunya aciki don kina da ciki?”. Wani kallo ta masa mai tattare da shauƙi da yanayi na musamman ahankali ta motsa laɓɓanta kamar mai raɗa tace. “Yanda aka samu cikin shine abin kunya kowa fa yasan me muka yi”. Ta ida maganar tana rufe fuskarta janyota jikinsa yayi tare da rungume ta kana yayi murmushi tare da faɗin. “Toh shikenan tunda baki so, Sarkin kunya zanga yanda zakiyi kuma idan munje Auren su Dr Jameel ai zata ga cikin kafin nan”. Cikin sauri ta girgiza masa kai tare da narke fuska sai kuma ta janyo hannunsa ta ɗaura akan cikinta tace. “Toh ai cikin baya wani girma". Yana ƙunshe dariyarsa yace. “Ai kafin nan zai ƙaru tunda zuwa lokacin ya cika wata uku tunda kinga an ƙara wata biyu a asalin date ɗin kinga har zai shiga wata na huɗu ma kafin nan”. Kanta ta ɗan jujjuya sai kuma ta tsirawa sajensa dake ƙyalli Ido tace. “Ha'a sai dai-dai lokacin Auren yayi zamu tafi ne?”. Kai ya girgiza tare da cewa. “A'a sai bikin ya rage saura sati zamu tafi kinga kafin nan cikin ya cika wata uku har ya shiga na huɗu ma”. Ganin yanda ta narkar da fuskarta ne yasa ya janyonta jikinsa ya sake rungumeta cikin tura baki tace. “Nikam gaskiya ina jin kunya wallahi”. Sosai ta bashi dariya amma baiyi ba yace. “Uyumm idan kina jin kunya ki riƙa cin abinci”. Narai-narai tayi da idanu tare da faɗin. “Yah Mu'allim toh bana jin yunwa kaga kuma yanzu nasha fruit Alhamdulillah na ƙoshi”. Janyota yayi ya rungumeta daga haka bacci ya ɗauke su. Acan ɓangaren Amina kuwa yanzu baki ɗaya rayuwa tayi mata ƙunci gani take kamar rayuwarta yazo gangara. Cikin sauƙe numfashi ta kalli Uncle Naseer Dake gefenta kana tace. “Uncle Naseer bani da lafiya”. Wani kallo ya mata sai kuma tayi murmushi tare da faɗin. “Ba wani nan lafiyarki ƙalau”. Cikin sanyi da kasala daya gama baibaye rayuwarta ta fesar da numfashi kana tace. “Allah da gaske bani da lafiya Ni nasan yanda nake ji ajikina”. Yana ɗan latsa wayarsa yace. “Kada ki damu”. Araunane tace. “Ji nake kamar zan mutu”. A wannan karon ma murmushi yayi yana gyara zamansa yace. “Baza ki mutu ba yarinya ki kwantar da hankalinki”. Kanta ta jinginar da jikin kushin tare da cewa. “Uncle Naseer to yaushe zamu tafi gida naga Auren Addah Asiya ya matso du-du-du saura wata ɗaya da sati ɗaya”. Juyawa yayi ya kalleta sai kuma ya ɗaga kansa sama alamar tunani yana sauke kansa ƙasa yace. “Auren saura sati ɗaya zamu tafi kinga yanzu kenan saura 1month zamu tafi”. Cikin sanyi ta gyaɗa kai tare da faɗin. “Shikenan Toh Allah ya kaimu”. Kafin yace wani abu wayarsa ta hau ruri ahankali ya miƙe ya fita tare da picking call ɗin. Daga ɗaya bangaren akace. “Ranka yadaɗe nan Veazer ka na komawa India zai fita”. Cike da farin Yace. “Alhamdulillah Nagode bari zuwa anjima zan kiraka”. Kana ya katse wayar tare da komawa Falon ya zauna gefen Amina ahankali ta ɗago Idanunta ta kallesa tare da cewa. “Uncle Naseer ya batun tafiyarmu Indi'a ne?”. Still da murmushi afuskarsa yace. “Sai mun dawo bikin Asiya”. Cikin sanyi tace. “Toh Allah ya kaimu”. Acan gefen Hajiya Bunayya kuwa rayuwa tayi mata tsanani abubuwan ta kullum gaba-gaba yake da safe zuwa rana zata yini cikin kwanciyar hankali sai dai da dare yana yi bata da kwanciyar hankali zuwa yanzu ƙyanƙyamin kanta da kanta ta keyi. Cikin sauƙe numfashi ta kalli Hajiya Lami Idanunta cike da ruwan hawaye tace. “Na lura ko ɗana Sulaiman ƙyamar zama kusa dani yake yi sannan Lamiɗo koda abinci na kai masa sai yace in tattara in fita dashi shi ya ƙoshi. Hankalina ya tashi Hajiya Lami kaddai mugun abinda naje yiwa Khausar ya dawo kaina ya addabi rayuwata? Ji nake kamar ƙaiƙayin yasa gabana ya haɗe da bayana”. Zare idanu Hajiya Lami tayi cikin yanayin tashin hankali tace. “Mun shiga ukun mu Hajiya Bunayya wannan wani irin abu muke fuskanta a rayuwar ki kalli haka Samira fa yanzu yanda ta bushe ta rame duk ta lalace sannan nima bana bacci dana kwanta da daddare sai muggan mafarkai na rasa yanda zanyi da rayuwarta” Cike da damuwa Hajiya Bunayya ta girgiza kai tare da cewa. “Ke koni?,Auren Asiya sai matsowa yake gashi Lamiɗo ko zama kusa dani muyi maganar Auren nan baya yarda sai kyara da hantara ina ga baƙin jinin da Boka yace Khausar za tayi ya tabbata nice nayi shi”. Cikin mamaki Hajiya Lami ta tallafe kuncin ta tana sauraron masifar daya riskesu lokacin ɗaya duniya tayi musu atishawar kaji. Hajiya Bunayya kuwa da damuwa ta cigaba da cewa. “Ƴaƴana ma duk sun fita harƙana dama Asiya ita tun can ba shiga harƙana take ba. Kuma abin mamaki itace take ɗan daurewa tana zama kusa dani shekaran juya da taga ina ta fama da ƙaiƙayin nan ina zirya da sintiri shine ta faɗa wa Lamiɗo aje asibiti koda ta faɗa masa ma cewa yayi shi bazai samu damar kaina ba inje in Kai kaina idan na kuɗine in faɗa masa ko nawa ne magana ta ƙare”. Tallafe kunci Hajiya Lami tayi kana tace. “Ohhh Mukam munga ta kanmu wannan al'amari wacce irin Musifa da fitinace ta Kunno mana kai”. Kafin Hajiya Bunayya tace wani abu Asiya ta fito daga cikin Bedroom ɗin ta kana ta zauna gefen su tare da girgiza kanta sai kuma ta kallesu ahankali ta sunkuyar da kanta Idanunta na cika da ruwan hawaye murya cike da rauni tace. “Umma ku koma ga Allah ku nemi gafarar waɗanda kuka cutar sai kuga Allah ya kawo muku sauƙi wannan ishara ne Ubangiji yai muku Allah ya soku da Rahma ne daya kama ku tunda ranku baku mutu ba dan haka kunemi yafiyar wa'anda kuka cutar tun kafin lokaci ya ƙure muku”. Kallonta suke tunda ta fara magana har ta dasa aya basu katse taba kamar yadda suka sqba. Karo na farko a rayuwar su da suka ji jikinsu ya mutu akan abinda suke aikatawa kana kalaman ta ya ratsa su. Ganin yanda jikinsu yayi sanyi alamar nadama tare dasu yasa cike da girmamawa matsayinsu na iyaye taci gaba dayi musu nasiyya mai ratsa jiki kana ta nuna musu kuskuren su da basu shawarar su nemi gafarar waɗanda suka cutar kana su nemi yafiyar Allah da yardarsa... Morocco bangaren Khausar sosai al'amura ke tafiya yau ya kama Auren Asma'u da Dr Jameel saura mako biyu haka Auren Asiya da Zakariyya da kuma Yah Aliyu da Dija saura mako biyu Cif-cif sukuma a shirye-shiryen su saura Mako ɗaya su tafi Nigeria. Ahankali ta ɗaga kanta tare da zubawa ƙofar falonta Ido jin sanyayyan kamshin turaren Moddibo wanda da alama ya dade da dawowa harma ya shiga side ɗin sa yayi wanka kai tsaye gefenta ya nufa ya ya kwanta kana ya ɗaura kansa kan cinyarta kasancewar tana kan 3sitter sai kuma yasa hannunsa ya shafa cikinta kafin ahankali ya maida hannunsa kan cikinta yace. “Baby ya kake kana lafiya?”. Murmushi Khausar tayi amma bata ce komai ba. Sake manna kansa da cikin yayi tare da cewa. “Meimei ta baka abinci Kaci?”. Still shiru tayi sai kuma ya ɗago ya kalleta tare da cewa. “Kinci abinci ko?”. Kai ta gyaɗa masa tare da faɗin. “Eh wallahi da gaske naci”. Cikin tsira mata idanu yace. “Da gaske?,Me kika ci?”. Kai ta gyaɗa kana tace. “Nayi wainar Fulawa kuma naci guda uku”. Kai ya jinjina tare da faɗin. “Masha Allah Alhamdulillah haka yayi kyau ai naga cikin ya ɗan tashi”. A hankali ta ɗan ɗaura hannunta bisa sajenshi tana shafawa a hankali tace. “Yau ina ka tafi tunda safe baka dawo ba”. Saman hannunta ya shafa tare da cewa. “Mun fita ne da Dr Jameel da Zakariyya kinsa ya dawo tun shekaran jiya sunje sun nuna min gidansu an tsara musu komai masha Allah. Dan su bikin saura kwana goma ma zasuyi gaba”. Cikin sauri ta kallesa sai kuma ta langwaɓar da kai tace. ”Toh muma mu tafi dasu mana Yah Mu'allim”. Kai ya girgiza tare da faɗin. ”Tafiyarsu da ban tamu da ban”. Sake marairaice murya tayi tace. “Allah mu tafi dasu na ƙagu naga Raudat nayi kewar Momyna sosai”. Cikin kwantar mata da hankali yace. “In sha Allah zakije ki ganta”. Kallonsa tayi sai kuma ta make kafaɗa tace. “Ni dai wallahi da zamu tafi tare nafi so". Yana gyara kwanciyarsa yace. “Suɗin ma ina ga zance su haƙura kawai mu tafi tare, tunda saura sati ɗaya zamu je gwara su haƙura mu tafi”. Cikin sauƙe ajiyar zuciya tace. “Toh Allah yasa su haƙura mu tafi". “Ameen”. Sai kuma yayi saurin miƙewa daga jikinta jin wayarsa na ruri ɗagawa yayi ta kalli screen ɗin, sunan Sheikh Jabeer ya bayyana da murmushi afuskarsa ya dauka tare da cewa. “Kaka”. Daga ɗaya bangaren Sheikh Jabeer dake zaune cikin falonsa A'ish ɗin sa na zaune gefe ya saki murmushi tare da cewa. “Na'am Jikalle Barka da yamma”. Moddibo na gyarawa Khausar zama ajikinsa yace. “Barka dai ya gida?". Ahankali Sheykh yace. “Lafiya lau”. Ya ƙare mgnar yana gyara zama yace. “Kwanaki munyi magana da kai akan ɓatan Jameel da plate number motar ɗin da muke magana akai?”. Kai Moddibo ya gyaɗa tare da faɗin. “Hakane”. Anutse Sheikh Jabeer yace. “Masha Allah idan ban manta ba cikin mutanenku akwai wacce tasan number motocin da ake zargin suna yawan binbiyarku gab da ɓacewan Jameel ”. Kai Moddibo ya jinjina yana mai tuno J dinsa yace. “Eh Khausar ce ma ”. Cikin sauƙe ajiyar zuciya Sheikh Jabeer ya gyara zamansa tare da faɗin. “Toh ba matsala idan har yanzu tana riƙe da number ka turo min saboda akwai ƙungiyar da Tabital Fulani suka kama a Taraba. Wanda an kamasu da motoci tawaga guda kusan guda goma wanda gaskiya muke zaton motoci ne da suke harkan Kidnapping dasu saboda a dokar adaji aka kama su da kuma makamai kana da tarin kuɗaɗe". Numfashi Moddibo ya fesar kana yace. “Toh shikenan In sha Allah bari muyi maganar da ita”. Bayan ya katse wayar ya maida kallonsa gare ta ahankali ya riƙe hannayenta cikin nasa cikin natsuwa ta zuba masa ido. Cikin fesar da numfashi yace. “Minha batun number motar nan da Asma'u tace kin riƙe,har yanzu kina riƙe dashi akan ki?”. Kai ta gyaɗa cikin tabbatar tace. “Tabbas kuwa har abada bazan manta number motar nan ba saboda na ganta alokuta uku maban-banta na ganshi a Jauro Yaya. Na ganshi a bakin Makarantar mu. Sannan ranan da muka yi rabuwa ta ƙarshe da Yah Jameel na ganshi yana bibiyarmu”. Numfashi ya fesar tare da faɗin. “Yanzu zaki iya faɗa min?”. Kai ta gyaɗa mishi. Ganin hakane yasa ya ɗauki wayarsa ya danna kan number Sheikh Jabeer ya shiga wajen text yace. “Gashi sa”. Karɓa tayi ta rubuta number motar da komai da komai harda collor ta miƙa masa number ya tsirawa idanu sai kuma ya kalleta yace. “Kin tabbatar shine dai-dai?”. Kai ta gyaɗa tare da cewa. “Na tabbata shine babu shakka ko Haufi ko yanzu na rufe Idanuna ina kallon number motar”. Kai ya jinjina kana yace. “Ok ba laifi”. Ba ɓata lokacin ya yiwa Sheikh Jabeer sending. Ahankali ya maida hannunsa kan cikin nata wanda zuwa yanzu ya fara bayyana kallonta yayi tare da langwaɓar da kai yace. “Minha yunwa nake ji mai zan samu?”. Tana lunshe Idanunta cikin nasa tace. “Mekake so?". Muryansa cike da kasala ya sake narkewa jikinta tare da cewa. “Me kika yi min?”. Manyan Idanunta ta juya sai kuma ta sakar masa da murmushi tare da cewa. “Nayi maka abinda kake so?”. Ɗan ware idanunsa yayi yana cigaba da shafa cikinta yace. “Mene?”. Langwaɓar da kai tayi tace. “Nayi dambu a tunanina zan iya ci sai kuma naji bazan iya ciba”. Wani kallo ya mata me cike da tarin tausayi da jin ƙai yace. “Ke kuma me yake miki daɗi In banda Fakala ba”. Da sauri ta sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta tare da cewa. “Kai Yah Mu'allim”. Kai ya jinjina kana yace. “Ehem sai an jima da daddare zaki ce min kina son pakala”. Marairaice fuska tayi kana tace. “Ni dai wallahi kabar faɗa min haka kar kayi min sharri”. Idanunsa ya buɗe kanta tare da faɗin. “Sharrine ma?,Toh bari zan kama kine?”. Murmushi tayi tare da faɗawa jikinsa amma bata ce komai ba. AnanTaraba shirye-shiryen biki ya kankama tuni aka fara gyara amare an killace su. Momy da kanta je gyara Asma'u Asiya ita ke mata Dilke sai wani ƙyalli suke sunyi kyau gwanin ban sha'awa soyayyar ta da Dr Jameel ɗin ta kuwa na tafiya hakama su Asiya. Yau ya kama Auren saura kwana goma wanda ya rage saura kwana uku Moddibo su taho da Angwaye da ƴan ɗaurin Aure. Yau tun safe Ummi da kanta da Asma'u suka tafi gidansu Innayi kasancewar key na hannunta Ummi da kanta ta shiga Side ɗin Moddibo da kanta ta gyara masa ta killace Asma'u kuwa gefen Innayi ta gyara ta killace ko ina yayi gonin ban sha'awa. Ga kuma sabbin part guda biyu da ake ƙenƙesa sabon gini, na alfarma wanda tuni an gama komai nasu, wanda bisa shawarar inanayi aka tsara da umarnin Abualeey tare jagorancin Abban Jameel abune na kuɗi shiyasa tuni an gamsu wanda nanne masauƙinsu in sun iso. Morocco Khausar ce kwance akan kujerar bisa alamu da Momy take waya cike da farin ciki ta gyara kwanciyarta tare da cewa. “Momy In sha Allah mun kusa zuwa". Murmushi Momy tayi kana tace. “Toh Khausar me kike so in shirya miki idan kin zo. Ga Raudhat baki ɗaya lissafinta da tunani Adda Khausy ta kusa daeowa. da an taɓa ta sai tace sai Addah Khausy tazo, wanka ma ƙinyi tayi yau wai sai Addah Khausy tazo tayi mata”. Dariya Khausar ta sanya tare da faɗin. “Yau mun bonu kafin inzo ai datti zai kashe ki Raudat ”. Ta ƙare faɗin haka jin muryan Raudat ta amshi wayar Raudat kuwa itama cikin dariya tace. “Addah Khausy datti bazai kashe niba fa zan riƙa fesa turare sannan insa humran Momy saboda nayi kamshi sai kinzo ki min wanka”. Dariya suka sanya Dukansu daga nan suka cigaba da hira. Suna gama waya dasu Momy ga Mamaki ta sai ga kiran Hajja Nana ya shigo tana ɗagawa tace. “My Kakus”. Baki Hajja Nana ta taɓe tare da faɗin. “Ƴar tselen Uwa tunda muka dawo sau ɗaya mukayi waya dake baki sake kirana ba”. Murmushi tayi tare da cewa. “Kai Hajja Nana kuma abin harda Sherri ne? kin manta cewa garin ku babu network in baku kuka kira ba baya shiga, kullum fa kina raina”. Dariya Hajja Nana tayi tare da faɗin. “A yayi kyau yaushe zaku zo?”. Cikin sauri tace. “Next week”. Cikin so da ƙauna Hajjaj Nana tace. “Yau da kaina na ɗibo ƙafana har bidhiyar ƙare zancenka saboda inji Labarin Ƴar jikata dan nayi kewarki ina so in San yaushe zakuzo”. Khausar na murmushi me ɗauke da ƙaunar Kakar tata tace. “In sha Allah nan da kwana uku dai muna cikin Nigeria”. Kai Hajja Nana ta gyaɗa tare da faɗin. “Toh Allah Ubangiji ya kawo ku kafiya”. Bayan ta gama wayar ne ta miƙe ahankali kasancewar tun safe bata leƙa Didi ba kallon jikinta tayi ganin dogon riga ce budadde da mayafinsa babba yasa ta sauƙa falonta ta wuce Side ɗin Didi. Tana shiga Falon ta samu Didi zaune da ahlinta, Modibbo Sai Zakariyya da Dr Jameel, Sai kuma Lalla Khadijah da Lalla Salma da Hafsat wanda ga duk kan alama sunzo tafiya bikin ne Didi na ganinta ta miƙa mata hannu idanunta akan cikinta,. Sai lokacin itama ta kalli cikin ta ga Mamaki ta sai taga cikin nata har ya tura rigar ta kaɗan cikin jin kunya ta zauna gefen Didi cike da kulawa Didi tace. “Barka da yamma?”. Kai ta gyaɗa tare da cewa. “Yawwa Barka dai Didi”. Didi na gyara zama tace. “Yau tun safe nake ta zuba ido zan ganki ban ganki ba ki shigo ba, nace Rahama taje ta du baki data dawo sai tace kina bacci”. Tana kallon Moddibo tace. „Eh Didi ina bacci ban daɗe da tashi ba shine nayi wanka sai kuma na ɗanyi waya da Momy na Momy tace in gaishe ki ma”. Fuska a sake Didi tace. “Ina amsa wa Masha Allah fatan suna lafiya?". Kai ta gyaɗa tare da faɗin. “Lafiya ƙalau”. Ita kuwa Khausar kallonta ta mayar kan Lalla Khadijah da Lalla Salma da Hafsat cike da girmamawa ta gaishesu cikin sakin fuska suka amsa mata suna tambayar jiki. Kallonta ta mayar kan Didi jin tana cewa. “Khausar ya shirye-shiryen tafiya?”. Dariya Khausar ta sanya tare da faɗin. “Aini har na gama shirya wa ma”. Ahankali Moddibo ya ɗago Idanunsa ya kalleta kana yace. “Toh da kika gama shirin ma ai ke ba zuwa zakiyi ba”. Zare idanunta tayi sai kuma ta kwaɓe fuska ahankali ta maida kallonta kan Didi dake murmushi tace. “Didi kiji fa abinda yake cewa". Ɗan dariya Didi tayi ganin yanda ta kwaɓe fuska yasa tace. “Rabu dashi waya isa ya hana ki zuwa Mamana ai kece agaba idan baki zoba amaren ma baza su zoba”. Ware idanu Dr Jameel yayi tare da sanya dariya yace. “Anya kuwa Didi wannan zai saɓu dan bata jeba ace Amare baza su zoba ai ita ta zauna gidan mijinta mu muje mu ɗauko Matan mu". Cikin murmushi Zakariyya cewa. “Gaskiya dai kam”. Dariya Didi ta sanya kana tace. “A'a Zakariyya har kaima wato zama da Jameelu ya dawo da kai mai surutu da baki”. Dariya Lalla Khadijah ta sanya tare da faɗin. “Aikam Didi Hausawa sunce zama da maɗaukin kanwa shi ke kawo farin kai". Dariya suka sanya Lalla Hafsat ta karɓe da cewa. “Aikam dai ko kurma ne ya zauna da Dr Jameel Sai ya koyi magana". Zakariyya kuwa ƙeya ya sosa tare da sunkuyar da kai... Ɗago kansu sukayi atare tare da kallon Ibraahim dake shigowa cikin mamaki suka haɗa bakin cewa. “A'a Ibraahim kuma”. Kai ya gyaɗa tare da buɗawa Rahama hannu wacce ta nufo kansa da gudu da murmushi afuskarsa yace. “Surprise dama bazata na shirya muku Yah Jameel ba jiya muna waya kana zaton bazan zoba, har kana fushi”. Ya ƙare maganar tare da ƙarasawa gefen Lalla Khadijah ya zauna kana ya ɗaura kansa kan kafadarta Dr Jameel cikin murmushi yace. “Aikam da har nayi fushi da kai”. Jujjuya idanu yayi yace. “Amma dai yanzu ka huce ko?”. Kai Dr Jameel ya gyaɗa tare da cewa. “A na huce tunda kazo”. Lalla Salma ce tace. “Toh dama taya za'a yi Auren Yayun ka har biyu baka nan ai dole saida babban ƙanin ango za'a ɗaura Aure”. Dariya yayi tare da faɗin. “Aikuwa dai Lalla Salma kin gane”... Haka dai suka cigaba da hiransu. Ana gobe zasu tafi da misalin karfe goma na dare Moddibo ne kwance a gefen Khausar yana romance ɗin ta tare da shafa cikinta ahankali ya ɗago Idanunsa ya kalleta tare da cewa. “Gobe idan munje Nigeria gidan Innayi zamu sauƙa” . Idanunta dake shanye kamar na mai jin bacci ta buɗe tare da tura baki tace. “Yah Mu'allim gidan ku kuma? Nikam dai inje gidan Momyna ”. Da sauri ya ware idanunsa tare da dafe ƙirjinsa kana yace. “Na isa ki tafi kibarni da waye idan kin tafi gidan Momy?”. Cikin tura baki tace. “In barka da Innayin ka mana”. Kissing ɗin goshinta yayi tare da cewa. “Innayi zata bani abinda kike bani ne Minha? Innayi bazata bani abinda kike bani ba Minha sabida duk duniya babu wanda yake bani abinda kike bani fa Minha ya za'a yi kice dan ina tare da wasu za kiyi nesa dani ai bazan iya jura ba”. Ahankali ta fesar da numfashi tare da cewa. “Kai Yah Mu'allim Kuma fa kasan nayi missing na Momy”. Tafin hannunta ya riƙe cikin nasa yana matsawa yace. “Nayi miki alƙwari idan munje kullum zan na kaiki ki wuni amma kwana bazan barki ba. Babyna ma bazai iya ba saboda yana son ɗumin jikin Abbansa”. Ta buɗe baki da niyar magana ta fasa jin wayarsa na ruri ahankali ya miƙe tare da janyota jikinsa yana shafa bayanta ganin number Sheikh Jabeer yasa ya dauka muryansa can ƙasa yace. “Kai baka san dare yayi bane?". Ware idanu Sheikh Jabeer yayi tare da cewa. “Ƙaniyarka ne ni kake faɗawa dare yayi?” Cikin kwaɓe fuska Modibbo yace. “Toh Amman dai kasan inada iyali ko?”. Wani irin murmushin mai cike da tuna baya Sheykh Jabeer yayi tare da cewa. “Hmmm yaro man kaza da kake cemin bansan dare yayi bane shin baka san cewa duk abinda ɗanyen ganye ya sani ya kuma ganiba bushesh-she ya riga saba". Murmushi Moddibo yayi tare da cewa. “Can maka dai da karin maganar ka Ni ban fahimci me keke nufi ba". Dariya Sheikh Jabeer yayi kana yace. “Ai baza ka fahimta ba, amma dai kasani duk abinda kake tunanin kasan shi na fika sanin shi kai abayana kake”. Moddibo kuwa hannu ya cusa cikin sumar kan Khausar yace. “Toh naji Ni dai yanzu ka faɗa min me yake tafe da kai ina da abinyi”. Cikin so na kaka da jika Sheykh Jabeer yace “Eh Ya maka kyau. Dama akan batun number motar da kuka turo min ne tun jiya nayita kiranka baka ɗauka ba bansan me kake ba”. Cikin sauri Moddibo ya dai-daita nutsuwarsa tare da cewa. “Kuma banga Miss call ɗin ba”. Cikin fesar da numfashi Sheik Jabeer yace. “An samu motar cikin motocin da aka kamo sannan acikin mutanen ana so gane su waye ke amfani da motar dan mutanen kusan su ashirin da biyar aka kama. Toh muna so mu gane su waye ke amfani da wannan motar sannan su waye suka sace Jameel suka kashe sa”. Cikin fesar da numfashi da kuma rauni Moddibo yace. “Alhamdulillah in Sha Allahu Jinin J bazai tafi abanza ba”. Kai Sheikh Jabeer ya jinjina tare da faɗin. “Yanzu shine abinda muke so tunda har ita mai ɗakin ka ta gansu tasan Fuskarsu tunda jibi kuna hanya idan kun iso kafin ku wuce sai munje kun gan su”. Cikin sauri Moddibo ya runtse idanunsa yace. “Yah Sheikh bana son ganinsu”. Ahankali Sheikh Jabeer yace. ”Meyesa?”. Araunane ya girgizar kai tare da cewa. “Bana son ganin waɗanda suka kashe min J idan na gansu bansan me zanyi musu ba, kar nazo nima nayi abinda bashi bane, bansan mai zan musu ba, na tabbatar dai in na zan ga wanda ya kashe J. Bazan iya barinshi arayeba zan iya yi musu komai”. Cike da nutsuwa da dattako Sheikh Jabeer yace. “In sha Allah babu abinda zaka musu dole zaku zo ku gansu ”. Idanunsa na tara hawaye yace. “Bazan gansu ba bazan iya ba har abada bana ƙaunar ganinsu. Babu wa'anda na tsani gani a duniya sama dasu”. Ahankali Khausar ta miƙe ta zauna Sheikh Jabeer kuwa ahankali yace. “Toh ba laifi ku dai ku shirya idan kun zo sai kun biya nan”. Kai ya gyaɗa tare da katse kiran sai kuma ya maida kallonsa kan Khausar cike da rauni lokaci ɗaya mutuwar Jameel ya dawo masa sabo idanunsa muryansa cike da sanyi da kuma rauni yace. “Kinji fa waifa cewa yayi inje in Kalli waɗanda suka kashe min J. Ina zan iya kallonsu?”. Hannunta tasa ta tallafo kansa tare sa ɗaura aƙirjinta kana tace. “Yah Mu'allim zamuje ko domin mu tabbatar da cewa suɗin ne suka kashe sa sannan mu tabbatar da cewa suɗinne an kamasu, sannan ayi musu hukunci dai-dai da laifinsu. Ni na tabbatar muddin na gansu wallahi zan gane su da Izinin Ubangiji”. Araunane ya girgiza kai tare da cewa. “Muje kuma Minha?, Minha bazan iya ganin suba fa”. Kansa ta tallafe tana ɗan shafa bayansa alamar kontar da hankali tace. “Yah Mu'allim zamu iya zamu iya ganinsu kodan ahukuntasu abinsa cutar damu da sukayi”. Zuciyarsa na ƙuna yace. “Minha zan iya musu abinda basuyi tunani bafa”. Sake tallafo kansa tayi tare da cewa. “Yah Mu'allim babu abinda zaka musu hukumane za tayi aiki akansu kamar yanda Shari'a ta tsara”. Ta ida maganar tana shafa kansa ganin yanda mutuwar Jameel ya dawo masa sabo ahankali ta haɗe lips ɗin su waje ɗaya wani gauron numfashi ya saki tare da janyo jikinsa ya fara shafa sassan jikinta ahankali ya ɗago kai ya kalleta tare da yin murmushi kana yayi ƙasa da rigar baccin jikinta muryansa ashaƙe yace. “Minha kina ganin gaba ɗaya abin nan sai sake girma suke”. Shanyayyun idanunta ta ɗago ta kallesa tare da sakin murmushi hannunta na shafa kansa tace. “Yah Mu'allim ba dole su sake girma ba gaba ɗaya ka buwaye su ka gigita su sannan ka hanasu nutsuwa da kwanciyar hankali ”. Hancinta ya lakace yace. “Ba dole ba waɗan'nan kayan marmarin ai ba'a barinsu Minha suna da matsayi babba dama rashin samun hannu ne shiyasa basa girma sosai yanzu kuma kinga sun samu”. Dariya tayi haka tayi ta yi masa abubuwan da suka mantar dashi damuwa da kuncin daya shiga haka suka kwana cikin farin ciki... Ranan dasu tafi Misalin 12:00pm jirginsu ya tashi daga kasar Morocco zuwa Nigeria. Kasancewar Private Jet ne shida Khausar suna First class daga can ƙarshe Zakariyya,Dr Jameel, Abualeey, Galadima, Waziri, suma na cikin First class daga gaba sai Innayi kana Didi, Lalla Khadijah da Lalla Hafsat duk suna baya. Misalin ƙarfe biyar dai-dai jirginsu ya sauka a Adamawa kai tsaye motoci suka zo suka ɗauke su daga Airport zuwa fadan Mai martaba sarki Jabeer Nuruddeen Bubayaro. Kyakkyawan masauki na musamman aka basu anan suka kwana bayan anyi musu tarbar na mutuntaka Didi takasance ga Mahaifiyarta da Mahaifinta sannan ga Ummi Kakarta Ummei Jakadiyarsu. Washe gari da safe Misalin ƙarfe bakwai na safe Sheikh Jabeer da kansa ya wuce Masauƙin da aka bawa Moddibo da Khausar yana shiga ya samu Moddibo na haɗa mata tea. Juyawa Moddibo yayi ya kallesa tare da faɗin. “Wai ya kake shigo mana haka ba neman izini”. Kallonsa Sheikh Jabeer yayi tare da cewa. “Ka manta nan Fada tace ba Fadar kuba da zaka ce sai na nemi izini”. Murmushi Moddibo yayi yana mikawa Khausar tea ɗin yace. “Toh me kake nema da sanyi safiyar nan da kazo mana?”. Sheikh Jabeer na gyara tsayuwar sa yace. “Tashi zakuyi mu tafi inda zamuje”. Langwaɓar da kai Moddibo yayi tare da faɗin. “Ni bazan jeba”. Cikin sauri Khausar tace. “Kayi haƙuri Yah Mu'allim muje”. “Gwara kam ki faɗa mishi muje mu tabbatar dan kada aɗaurawa wasu laifin da bana su ba”. Haka dai suka ta lallaɓa Moddibo har ya amince suna fita sai ga Amintaccen Hadimin Sheikh Jabeer ya ɗauke su a mota suka tafi kurkukun dake cikin Yola suna isa bisa sirri akayi musu jagora da iso, aka wuce da ciki. Duna shiga Khausar tayi saurin komawa bayan Modibbo tare da riƙe hannunsa gama, cikin rawan jiki ta ɗago hannunta tana nuna wasu ƙattun mutum biyu da babu alamun imani tare dasu, shiyasa aka ɗan waresu gefe suna zaune sai kuzurai suke. Cikin tashin hankali gami da tsanarsu ta fashe da kuka murya narawa tace. “Ga sunan wallahi Yah Mu'allim sune, sukayi ta bin motarmu da Yah Jameel randa aka sace shi, kuma sune suka je Jauro Yaya sannan kuma sune suka je bakin Makarantar. Wallahi tallahi sune suka bibiye mu aranan da muka rabu da Yah Jameel na ƙarshe har da muka tsaya a suma suka tsaya”. Cikin Tsananin tsana takaici da ƙunar rai Modibbo ke binsu da wani irin kallo mai nuna jin zafin illar da sukayi mishi. Shi kuwa Sheikh Jabeer nan take yasa aka killace su waje na musamman da kansa ya tsananta bincike Matsayin sa na SS mai zaman kansa wanda yasan kansa da aikinsa da ƙirewa. Bisa jagorancin Jalal yasa aka musu ɗan banzan bugun da ya karya ƙarfin zuciyarsu. Kana yacewa su Modibbo su shiga. Cikin tsaresu da ido ya nuna musu Khausar tare da cewa. “Kunsanta?”. Agalabaice suka ce. “Eh mun santa itama an bamu kwangilar kashe ta”. Aruɗe ta zare ido kana ta ɗaura hannunta aƙirji tace. “Kasheni kuma nima? me nayi muku”. Kai Sheikh Jabeer ya jinjina kana ya nuna Moddibo dake binsu da wani irin kallon tsana gaba ɗaya jikinsa rawa yake shi kuwa Sheikh Jabeer cikin sanin makamar aikinsa yace. “Wannan fa kun san shi”. Kai na farkon ya gyaɗa tare da faɗin. “Eh ai dama shi tare aka bamu kwangilar karshe sa da Malam Jameel”. Zama sheikh Jabeer ya gyara tare da faɗin. “Waya baku kwangilar kashe su? Sannan akan me zaku kashe su?”. Ɗayan da yafi galabaitane ya ɗago fuskarsa da duk halittarsa ta canza saboda azabebben bugu da ya sha yace. “Mu mutanen garin dake gefen Jauro Yaya ne, kuma manyanmu ne suka bamu kwangilar karshe su". Akai Khausar ta ɗaura hannu tare da faɗin. “Ai kune ma na gani a Jauro Yaya ”. Cikin tsawa Sheikh Jabeer yace. “Me ya kaiku Jauro Yaya kuma?”. Na farkon ne ya karɓi zancen da cewa. “Mu muka kashe Garkuwan Rugar Jauro Yaya Umaru”. Wani irin raunataccen kuka ne ya kubcewa Khausar yayinda gaba ɗaya jikinta ya ɗauki rawa. Jalal kuwa a hankali ya gyara riƙon da yayiwa wayarsa saboda video'nda yake yi musu. Zama Sheikh Jabeer ya gyara tare da ci gaba dayi musu tambayoyi. Shi kuwa Moddibo gaba ɗaya ilahirin jikinsa rawa yake ji yake duniyar tayi masa ƙunci ji yake tamkar ya fisge bindigar dake hannun Sheikh Jabeer ya kashe su kowama ya huta”. Amma ya kasa motsa wa saboda Khausar dake rungume dashi ita ta hana shi motsi. Dayan ne ya karɓi maganar da cewa. Kamar haka uuna ɗaya daga cikin mutanen dake Maƙoftaka da Rugar Jauro Yaya wanda sun kasance arna ne sannan manyan sune suka bamu umarnin su kashe Garkuwan Rugar Jauro Yaya saboda shine yake shiga cikin Sabgoginmu yana hana mu Kidnapping yanda suke a yankin, dan da in sun sato mutane a nan cikin tsaunukan dake zagaye dasune suke zuwa su ɓoye mutane, sai an biya su kuɗi wanda in za'a samu mutane a wurin kai tsaye cewa za'ayi Fulani wurin ne suke satosu. saboda haka ne in sunje sunyi kidnapped shi yake hana su sakewa, kuma basu isa su ɗauki dabbobi yanda suke so saboda kasancewar mutum mai sa ido da kuma Jarumta”. Cikin tafarfasan zuciya Sheikh Jabeer ya dasa masa bindiga akansa kana yace. “Shi kuma Malam Jameel meya muku?,”. Cikin haki da fusgar numfashi yace. “Shima Malam Jameel manyan mune suka bamu kwangilar kashe sa Saboda shine mutum na farko daya buwayi al'ummar mu da wa'azi wanda yake zama sanadin da matasanmu da yawa suke Musulunta shiyasa manyan mu suka bamu umarni shi da Moddibo mu haɗa su mu kashe su shine abinda zai fi mana sauƙi da kwanciyar hankali idan ba haka ba zasu janye mana ra'ayi da tunanin matasan mu”. Dafe kai Sheikh Jabeer yayi tare da cewa. “Innalillahi wa'inna alaihi raji'un”. Cikin tashin hankali Moddibo ya dafe kansa tare da faɗin. “Hasbunallahu wani'imal wakin". Sai kuma ya koma ya zauna yana dafe kansa da hannun ɗaya yayinda ɗaya hannun kuma ke tallabe da Khausar cikin kaɗuwa yace. “Ana zaton wuta amaƙera sai gata a masaƙa ina zaton kashe J akayi tunda aka kamasa na tabbatar cewa magautane acikin kashe sa amma duk atunanina akwai sa hannun ɗaya daga cikin Yadikkonsa ashe babu su Astagfirullah Allah na tuba ka yafe min da zargin da Nai ta yiwa Hajia Turai da Karima Allah na tuba”. Cike da rauni da tausayinsa Khausar ke zubda hawaye, shi kuwa Modibbo cikin rauni ya cigaba da cewa. “Manzon Allah (S.A.W)da kansa yace _Azzhana zhambu Walau kana haƙƙun_ sai naje na nemi yafiya da gafarar Hajiya Karima saboda duk tunanina ko ita ko Hajiya Turai akwai sa hannun ɗaya daga cikinsu aɓacewan J ashe suma ba abinda suka sani waɗan nan kafiran maƙiya Allah da Manzonsa suka sa aka kashe min J ɗina”. Sosai Sheikh Jabeer yasa aka azabtar dasu suka faɗi duk laifinsu daga nan aka tura su waje na daban aka killace su domin jiran yanke musu hukunci. Jalal kuwa nan take ya tura Modibbo video da yayi musu na cikekken bayanansu da sukayi. Sheykh Jabeer kuwa da kansa ya tara su Abualeey yayi musu cikekken bayanin, ya ƙara da cewa, sai yazo ɗaurin auren su Dr Jameel shi da kansa zai yiwa Ummi da Abban Jameel dukkan bayani. Aranan ƙarfe goma dai-dai na safe suka kama hanyar tafiya Membila da rakiyar motoci na musamman. Ƙarfe huɗu dai dai ya musu acikin garin Gembilan... By *GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH Book 3 PAGE 2* Na *Aysha Aliyu Garkuwa* KAZAURE COLLEGE OF NURSING SCIENCES (KCONS) Lafiya Uwar jiki, Kuma sai da lafiya ake morar rayuwa. Kazaure College Of Nursing Sciences (KCONS) ta kawo muku ingantaccen tsarin koyar da jinya da unguwar zoma, mun himmatu wajen samar da kwararrun ma'aikatan jinya da unguwar zoma a fadin Nigeria da ma matakin duniya baki daya, a KCONS mun tanadar muku kwararrun malamai, ingantaccen yanayi da tsarin koyo da koyarwa kai harma da tsarin e-learning, ka zalika akwai tabbataccen tsaro a dakunan kwanan dalibai maza da mata, bugu da kari kudin makaranta dai-dai aljuhu ne, KCONS munanan a lamba 5 layin fadar sarki dake kan hanyar kano zuwa daura a Kazaure jahar Jigawa, za'a iya samummu a shafikanmu na facebook da instagram @KCONsciences domin bayani, za'a iya tuntubanrmu a wadannan lambobin, 07066542055, 08035298851, ko shafin mu na yanan gizo @ http://kcons.edu.ng/admission KCON sciences kan turbar aiki da kwarewa muka shahara. https://chat.whatsapp.com/HCji7xLpR1VEJGYcZJMP6k Ajere-Ajere motocinsu suka fara shiga harabar gidan Innayi. Moddibo kuwa sassayan numfashi ya fesar a hankali ransa cike da mamakin, shin meyesa Abban Jameel yace su sauƙa anan duk da yasan cewa ba wasu wadatattun ɗakuna bane a gidan, kasancewar daga ɗakin Innayi sai Side ɗin sa dake da 2 bedroom sai single room a bakin ƙofar falon, yace wa Abba su sauƙa a hotel daya musu booking Amma yace a'a yaƙi masa musu ne, saboda bai san mai ya shirya ba duk da yafi tunanin Abba yace hakane ko sai sunci abinci kafin su tafi Masauƙinsu. Akuma dai-dai lokacin motocinsu sukayi Parking a farfajiyar gidan. Daga can waje kuma cikin sassarfa Haiydar da Bashir suka nufo gidan wanda har sun dauki hanyar komawa gida kasancewar sun jira su basu zoba sai kuma suka hango motocin su. Acan harabar cikin gida kuwa cike da matsanancin mamaki da al'ajabi Moddibo ke bin baki ɗaya ilahirin gidan da kallo wanda aka tsara shi yayi masifar kyau wasu dan ƙara dan ƙaran Side ne akayi su guda biyu wa ɗan da kusan komai nasu irin nasa ne sai dai basu da wadatan flowers kamar nashi cikin fesar da numfashi da mamakin dake kwance saman fuskarsa ya ziro ƙafarsa na dama kafin ahankali ya gama fito da gangar jikinsa daga motar, hannunsa na riƙe cikin na Khausar still Idanunsa na bin harabar gidan da kallo. Akuma dai-dai lokacin Idanunsa suka sauƙa kan Abban Jameel, Lamiɗo da Malam Ahmad suna sauƙa daga kan barandar ɗaya daga cikin Sabon Side biyu da aka gina still da mamaki ya maida kallonsa kan Innayi data fito daga Motar da suke. Murmushi Innayi tayi ganin kallon mamakin da yake bin gidan dashi kana tace. “Bismillah ku shiga side ɗinka”. Kallon yaushe akayi wannan ginin yayi mata, fahimtar kallon da yake mata yasa ta jinjina masa kai tare da cewa. “Tun kwanaki ai aka fara ginin saboda sanin cewa zamu zo Auren su Jameel, kana lokaci zuwa lokaci zamu buƙaci zuwa nan tunda ni da kai dai ba zamu manta garin Membila ba”. Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kana yayi murmushin gefen baki sosai yaji daɗin hakan saboda bawai ya tsani garin Membila bane saboda ya samu nasa garin, kawai dai Membila ta fita a ransa ne saboda rasa amininsa, Amman duk da haka yasan gari Membila garine wanda yake da tarihi arayuwarsa yana jin Membila na cikin garin da yake tamkar tsagin jikinsa, ya sani bazai manta garin arayuwarsa ba, ko ina yaje a duniya watara zata faɗo masa arai kuma dole zai buƙaci jin yana son zuwa cikin garin. Anutse Didi ta fito kana Lalla Khadijah, Lalla Hafsat, Sai Rahama tana fita ta nufi gefen Khausar fuskarta ɗauke da murmushi tace. “Woww Lalla Khausar haka garinku yake daɗi?,Masha Allah kina jin weather Mai daɗi haka Masha Allah i like it”. Murmushi Khausar tayi kana ta gyaɗa mata kai da faɗin. “Aikuwa zaki sha sanyi”. Idanu Rahama ta lumshe sai kuma ta buɗe tace. “Aikam akwai sanyi kam, duk da muma A Morocco ana mana sanyi but time to time ne amma bai kai wannan ba sanyin nan daban ne”. Ta ƙarashe maganar tana ƙanƙame jikinta waje ɗaya jin yanda sanyi ke ratsata. Kallon Khausar dake ɗan lumshe idanu Didi tayi kana ta maida kallonta kan Moddibo cike da kulawa tace. “Aleeyu ku shiga ciki yarinyar ta gaji da zaman motar nan ”. Kai ta gyaɗa Tare da cewa. “Toh”. Sai kuma ya damƙe hannun Khausar cikin nasa tare da ɗan janyota jikinsa suka nufi Side ɗin sa. Gaba Innayi tayi tana mai cewa. “Didi, Lalla Khadijah Lalla Hafsat Bismillah”. Kai suka gyaɗa tare da bin bayanta suka nufi ɗaya daga cikin Side ɗin. Akuma dai-dai lokacin Ummi ta fito daga Side ɗin fuskarta ɗauke da farin ciki da mamakin ganinsu tace. “Masha Allah sannunku da zuwa, sai yanzu kuka iso, da naji ku shiru-shiru har nake cewa barin tafi wata ƙil zaku kai dare”. Ta ida maganar tare da rungumar Didi itama Didi rungumeta tayi tana cewa. “Masha Allah fatan mun sameku lafiya”. Kai Ummi ta gyaɗa tare da riƙo hannun Lalla Hafsat tace. “Alhamdullah. Bismillah mu shiga daga ciki”. Cike da farin ciki suka bi bayanta... Abban Jameel kuwa shi yayi wa Abualeey, Waziri, Galadima, Baffan Zakariyya, Dr Jameel Zakariyya jagora zuwa Side ɗin da suka fito ko wanne yana ɗauke da 3bedroom manya,-manya wanda aka shirya su da kaya na alfarma da kawa ɗaya daga cikin ɗakunan Dr Jameel, Zakariyya da Ibraahim ne aciki. Sai kuma na biyun Abualeey ne da Waziri, Sai kuma Baffan Zakariyya, Galadima. Acan Side ɗin su Ummi kuwa Didi da Rahama ta nunawa ɗakin farko inda zasu zauna kana bedroom ɗin gaba ta kai Lalla Khadijah, Lalla Hafsat,da Niyna. Sai da ko wannensu yayi wanka kana suka canza kaya zuwa mai ɗan nauyi amma ba can ba saboda yanayin sanyin garin kafin suka gabatar da sallolin suka ɗan huta tare da taɓa hira sai kuma suka fito Falo Ummi da kanta tayi musu iso zuwa dining. Didi na murmushi ta shaƙi sanyayyar Iskar garin da kuma wanda bishiyoyi da flowers ɗin gidan ke kaɗawa tace. “Kai Alhamdulillah Masha Allah weather garin nan akwai daɗi ”. Murmushi Ummi tayi tare da cewa. “Aikam sai dai akwai sanyi”. Sai kuma tayi serving ɗin su da lifiyayyan abinci iri iri na alfarma da suka musu. Akuma dai-dai lokacin Haiydar da Bashir suka shigo bayan sun fito daga ɓangaren su Abualeey Haiydar na bin Falon da kallo yace. “Ummi ina Addah Khausy?”. Ɗan Murmushi Ummi tayi tare da faɗin. “Tana side ɗin Moddibo”. Cikin sassarfa ya juya da niyyar fita sai kuma yayi saurin juyawa ya kalli Didi cikin girmama ya ɗan rusunar da kanshi yace. “Ayyah Didi kuyi haƙuri na manta bamu gaisa ba ina yininku fatan kunzo lafiya?”. Dariya tayi tare da faɗin. “A' lafiya lau anyi kewar ƴar uwa ko?”. Dariya yayi tare da kama hannun Bashir da yake gaida su daga nan suka ficewa kai tsaye Side ɗin Moddibo suka nufa. Acan Side ɗin Mazan ma haka ya kasance Abban Jameel da kansa yagabatar musu da abinci na alfarma da girmamawa sosai Abualeey suka jinjina mutunci da karramawarsu... Haiydar da Bashir kuwa tun daga kan step ɗin Side ɗin Moddibo suke ƙwalawa Khausar kira suna cewa. “Addah Khausy! Addah Khausy!!, Addah, Khausy!!!”. A kuma dai-dai lokacin Khausar da Moddibo ne tsaye Dining hannunsa na cikin nata cikin taushi ya ranƙofa kanta tare da sassauta murya yace. “Me zaki ci?”. Kanta ta langwaɓar tare da tsirawa jerin abincin dake dining ɗin ido lumshe idanunta tayi tare da fara buɗe womers ɗin cikin yanayin jin sanyi ta motsa laɓɓanta tare da cewa. “Ga nan tuwo miyan kuka kasa min kaɗan zanci ”. Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da faɗin. “Masha Allah zauna toh bari na zuba miki”. Da dan sauri ta juya jin Bashir da Haiydar na cewa Addah Khausy Addah Khausy hannunta dake cikin nasa ta janye ta juya cikin sassarfa ta nufi ƙofan anufinta tayi gudu. Da wani irin sauri Moddibo ya riƙo tsintsiyar hannunta yace. “Kiyi haƙuri Minha na tuba dan Allah kada kiyi gudu”. Ɗan ware idanunta tayi tare da faɗin. “Su Bashir da Haiydar ne fa”. Kafin ta ƙarasa suka ƙara so cikin falon tare da rungumeta shima Bashir cikin sauri ya rungumeta ta gefen Haiydar. Murmushi Moddibo yayi tare da harɗe hannunsa aƙirji yana kallonsu da tattausan murmushi bisa kekkyawar fuskarsa. Khausar kuwa kallon Bashir tayi tare da cewa. „Bashir ina Asma'u?”. Murmushi yayi kana yace. “Ba tazo ba wai ita kunya Amarya baza ta zo ba”. Dariya mai tauri ta sanya tare da faɗin. “Don Allah yanzu baza tazo ba haka zata min kenan?”. Kai ya gyaɗa tare da cewa. “Wallahi fa taƙi zuwa tun safe taƙi zuwa ayi shara da ita wai Ummi tayi haƙuri”. Dariya Khausar ta sanya tace. “Lallai dai kam”. Haiydar kuma hannunshi yasa cikin nata. Cikin mamaki ta kamo hannun tare da kallon faratunsa hararansa tayi tare da cewa. “Me haka zaka wani tare farce kamar mace?”. Cikin lingwaɓar da kai yace. “Na gaza koyan yanke wa nefa, Mommy kuma tace in dai bazan koyaba bazata yanke minba”. Murmushi tayi tare dasa hannunta ɗaya ta dungure ƙeyarsa tare da cewa. “Shine daga isowata zaka haɗani da aikin yankewa” Ta ƙareshe mgnar tana jawosu suka zauna bisa kujerun Dinnin table ɗin. Moddibo kuwa a kujerar dake fuskantar Khausar ɗin ya zauna, yana maiyi mata wani arin amintaccen kallo ya fahimci akwai tsananin shaƙuwa da so tsakaninta da Haiydar duk da yawan faɗan da suke a da. Anan sukaci abinci tare. Kana sukayi ta hira kiran sallan Magrib ne yasa duk mazan sunka tafi masallaci. Kana basu dawoba saida sukayi sallan Isha sannan suka dawo nan kuma suka sake dasa sabon hira. Hakama Abban Jameel dasu Abualeey. Suma su Didi da Ummi haka ta kasance a wurinsu. Misalin sha ɗaya su Lamiɗo suka yiwa su Abualeey saida safe kana suka tafi. Su kuma duk sukayi shirin bacci suka kwanta. Ummi dake tare da Malam Ahmad ta nufi sashen Khausar tana faɗin. “Bari in je in jawo su Haiydar dan na lura su yau in zasu samu a nan zasu kwana”. Kai ya jinjina mata tare da jingina jikin motarsu ya tsaya jiran fitowarta. Ummi na shiga ta kalli Haiydar dake zaune gefen Khausar tace. “Ku tasa mu tafi”. Da sauri Khausar ta miƙe tare da cewa. “Toh Ummi bari in ɗauko mayafina mu tafi”. Juyawa Ummi tayi jin Moddibo na cewa. “Ina zaki je?". Idanunta ta narkar kana tace. “Zanje gida mana”. Yana tsuke fuska yace. “Da Izinin wa?". Murmushi Ummi tayi tare da kallon Haiydar da Bashir tace. “Haiydar kuzo mu tafi dare yayi mu barsu su huta”. Saurin kallon Ummi Khausar tayi tace. “Ayyah Ummi dan Allah ku jirani ya za'a kuma ace bazan jeba don Allah kayi haƙuri”. “Da Izinin wa?”. Ya maimaita tambayar yana mai tsuke fuska. Kamar za tayi kuka tace. “Da Izinin ka mana”. Kai tsaye yace. “Toh ban bada Izini ba”. Ummi kam hannun Haiydar da Bashir taja suka fice. Sai da suka sauƙe Haiydar agida kafin suka wuce. Haiydar na shiga Falon Momy ya shiga da sauri ya zauna gabanta kan lallausan Darduma da take bisa alamu shafi da witri tayi. yayin da ta jingina kanta jikin kushin cike da matsanancin farin ciki yace. “Momy". Cikin tsira nasa ido ta gyara zamanta tare da cewa. “Na'am”. Murmushin fuskarsa ya faɗaɗa tare da faɗin. “Kin ga yanda Addah Khausy ta dawo kuwa Momy?”. Kai Momy ta girgiza kana tace. “A'a ya ta dawo?”. Zama ya gyara yace. “Wallahi idan kika ganta zakice Balarabiya ce Masha Allah Subhanallah, tayi wani irin fari mai masifar kyau farinta har wani ƙelli takeyi”. Ɗan ware idanu Momy tayi tare da faɗin. “Allah ko?”. Kai ya gyaɗa yace. “Wallahi fa”. Daga nan suka cigaba da hira. Acan ɓangaren su Moddibo kuwa cikin tura baki Khausar tace. “Haka kawai ahanani zuwa gidan mu yanzu Fisabilillahi muna ƙasa ɗaya gari ɗaya ace bazan ga Momyna ba?”. Kansa ya ɗaura bisa kafaɗarsa yace. “Na isa? Ai ban isa in hana ki ganin Momyn kiba? waya isa ya raba uwa da ɗa? ban isa in ra Baki da Momy ba. Kawai dai nima bana so ara bani da ɗana akusa dani ne shiyasa”. Cunno baki tayi tana kallonsa cike da shagwaɓa hanci ya lakace mata kana ya cigaba da cewa. “Kuma ina so ki huta nasan in kunje hira zaku tayi baza ki huta ba kiyi haƙuri ki kwanta kiyi bacci ki huta gobe da kaina zan kai ki muje mu gaida Momy”. Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa. “Da sassafe”. Kai ya gyaɗa cikin tabbatar wa yace. “In sha Allah in dai mun karya”. Lallausan murmushi ta sakar mishi tare da riƙe tafin hannunsa tace. “Toh shikenan”. Bedroom suka wuce sosai tsarin ɗakin yayi kyau komai yayi yanda ake buƙata kana agyare tsaf-tsaf sai tashin ƙamshin roomfteshner yake, zama tayi kan gadon tare da jingina kanta da jikin gadon. Moddibo kuwa gefenta ya zauna yana ɗan matsa mata ƙafafun yace. “Kinga tafiyar nan da akayi mai ɗan tsawo sai nake ga kamar ƙafarki ta kumbura”. Idanunta dake lumshe ta ɗan buɗe ta kalli ƙafan sai kuma ta gyaɗa masa kai tace. “Eh dama Ni haka nake in dai na ɗanyi tafiya mai tsawo amota Normal haka yake min, zuwa safiya zaka ga ya watse”. Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da faɗin. “Kuma ahaka kike so ki tafi kije ki zauna ba kiyi bacci ba”. Ya ƙare maganar yana jan yatsun ƙafar tata tare da ɗan mammatsa mata su, sassayan numfashi ta fesar tare da muskutawa, da sauri ya ɗan tallabota tare da gyara mata kwanciyar saboda ganin duk ta sake alamun bacci mai nauyi takeji. Ahaka ya cigaba dayi mata massage suna hira jefi-jefi har bacci ya ɗauketa. janyota jikinsa yayi ya haɗa hannunsa waje ɗaya ya tofa musu addu'a ajikinsa ya fara shafawa kana ya shafa mata. Washe gari bayan sun kammala breakfast da duk wani abu da za suyi Kai tsaye sashen su Didi suka shiga bakinsu ɗauke da sallama suka shiga bayan sun gaigaisa Moddibo ya kalli Didi tare da cewa. “Didi zamu je wurin Momy”. Kai Didi ta gyaɗa kana tace “Ok sai munzo muma yanzu Ummin Jameel zata zo mu taho tare”. Kai ya gyaɗa yana ɗan matsa hannun Khausar yace. “Toh shikenan sai kun zo”. Daga nan suka miƙe suka fito da kansa ya shiga mazaunin driver, kana ta shiga gefen mai zaman banza, cikin nitsuwa yaja suka tafi anutse yake driving yana Jin wani yanayi na daban. Titinan garin ya zubawa ido lokaci ɗaya kuma tunanin J ɗinsa ya faɗo masa sai kuma yake tuna Lokuta da dama Idan yana tuƙi J na gefensa ko kuma J na tuƙi shi yana gefensa jikinsa ne yayi sanyi, tafin hannunta ya riƙo tare da mannawa kan cikinta yayi shiru kwayar idanunsa na tsats-tsafo da ruwan hawaye. Tuni ta fahimci yanayin da yake ciki cikin sanyi da rauni tace. “Allah ya jiƙan Yah Jameel Allah ya mishi Rahma Allah ya gafarta masa” Araunane yace. “Ameen Ya Allah Minha”. Tana matsa hannunsa dake cikin nata tace. “Yah Jameel yanzu baya buƙatar kukan nu addu'ar mu yake buƙata”. Cikin ƙoƙarin hana hawayen sa zuba yace. “Nima haka nakeso ina ta ƙoƙarin hana zuciyata da Idanuna kuka akan J sai dai muyi ta mishi addu'a Amman wasu lokutan ina gaza hana kaina hawaye a kanshi saboda nayi rashine da har yau ban samu madadinsa ba”. Cikin tausasawa tace. “Na sani Yah Mu'allim to Amman Allah ya fimu sonshi, kuma dama shi ya bamu shi dan haka addu'a kawai zamuyi ya mishi”. Cikin sanyi yace. “In sha Allah za muyi masa”. A kuma Dai-dai lokacin mai gadi ya buɗe musu gate ɗin gidan Lamiɗo Parking yayi kana suka fita da sauri ta nufi harabar gidan da nufin gudu, saurin riƙo hannunta yayi cikin tsira mata idanu ya langwaɓar da kai yace. “Kar kiyi gudu mana wai ke bakya jin tsoron ki faɗine”. Kai ta ta gyaɗa tace. “Toh ai sauri nake inje inga Momy". Sake langwaɓar da kai yayi yace. “Ai zaki ganta Minha ba sai kinyi gudu ba tun da gaki cikin gidan”. Ko gama rufe baki baiyi ba ta hango Raudat riƙe da Comb da kifiya bisa alamu kitso zata tafi. Da sassarfa ta nufeta tana kiranta, Ita kuwa Raudat jin muryar Adda Khausy tane yasa ta ɗago kanta aiko ganinta ne yasa ta buga tsalle cike da matsanancin farin ciki tace. “Addah Khausy”. Da wani irin sauri Khausar ta janye hannunta dake cikin nasa ta ruga da gudu. Atsorace ya sanya tafin hannunsa biyu ya dafe kansa kana ya motsa laɓɓansa tare da faɗin. “Ya Salam ki daina gudun nan”. Ina bata saurareshi ba da gudu ta rungume Raudat Raudat kuwa tsalle ta riƙa yi ajikinta tana cewa. “Oyoyo! Oyoyo Addah Khausy!, Mommy Addah Khausy!! Tazo Addah Khausy!!!,Oyoyo”. Cike da matsanancin farin ciki Khausar ta ɗaga ta sama ta riƙa juyawa da ita a tsakiyar gida wanda hakan ne yasa baki ɗaya mutanen gida suka san cewa Khausar tazo. Dai-dai lokacin kuma Haiydar ya fito daga ɗakinsa. Da gudu Sulaiman ma ya fito daga sashen Hajiya Bunayya atare suka rungumeta suna faɗin. “Oyoyo Addah Khausy ”. Khausar kuwa cike da matsanancin farin ciki take jujjuyawa atsakiyarsu ruggume da Raudat tsam a jikinta. Jin sowarsunw yasa Momy dake zaune falonta ta miƙe da sauri ta fito jin sautin muryansu na tashi cak ta tsaya ta riƙe ƙafan Falon tare da tsirawa Khausar idanu tana kallonta cike da so, ƙauna, bege, kewa irin na uwa da yarta. Khausar kuwa sai juyawa take dasu tana ƙyalƙyala dariya sai kuma tayi saurin sake su ta nufi Momy tana gudu tare da faɗin. “Oyoyo Momyna”. Runtse idanunsa yayi sai kuma ya ɗan ɗaga saitin muryansa yace. “Dan Allah Momy kice mata ta daina gudun nan zata yiwa kanta Illah fa”. Murmushi Momy tayi tare da kallon Khausar kallo ɗaya ta mata ta fahimci tana da ciki wanda har ya ɗan tasa ga wani irin kyau da tayi sai ƙelli take zubawa ga ɗan cikinta daya turo gwanin kyau ya zauna a jikinta cib da cib sai ƙugunta da ya ƙara faɗi. Cikin sauri da bege Minti ta rungumeta asanda ta isa gareta sau kuna tace. “Ke meyesa bakya girmane. Khausar wannan guje-guje har yanzu baki barshi ba”. Murmushi tayi tare da sake Momy sai kuma ta sake rungumeta kana ta sake ta ta kuma sake rungumeta ɗan turata Momy tayi tare da faɗin. “Ni matsa ahanya Bismillah Moddibo shigo". Sai alokacin Haiydar ya miƙawa Moddibo hannu kana yace. “Yah Moddibo Bismillah mu shiga”. Kai Moddibo ya gyaɗa suka shiga bayan sun zauna a falo Momy da kanta ta kawo musu Drinks da Snacks da ruwa ta ajiye musu agabansu. Raudat kam cike da farin ciki ta kwanta kan Khausar tana ta nuƙurƙusata, ahankali Moddibo ya riƙo tafin hannunta yace. “Kiyi haƙuri Aunty Raudiy adaina danne Adda Khausy kar aji mata ciwo”. Cikin jin daɗi Momy ta kawar da kanta jin yanda yake mata magana cike da kulawa sai kuma ta miƙe tace. “Bismillah kusha ruwa bari nazo ”. Ta ƙarashe maganar tana fita kai tsaye bedroom ɗin ta ta wuce. Acan ɓangaren Hajiya Bunayya kuwa a dai-dai lokacin zaune take aruwan zafi idanu ta tsirawa ruwan tana kallon ƙananun tsutsotsin farare masu jajayen kai wanda ga duk kan alamu sune suke addabar ta da jarabar ƙaiƙayi wanda zuwa yanzu tsakaninta dubaranta da gabanta ya wawake tuni sun fafeta ta kashin ta da gabanta ya haɗe saboda masifar ƙaiƙayi da yanda suke cinta taje asibiti har ta gode Allah abanza kana ta kira matar data haɗa su da Boka Gillaw. Taje ta faɗawa Boka Gillaw ga abinda yake faruwa yace wannan sakamakon aikin su suke girba babu abinda zai iya kada su sake kiransa, dama shi ya gaya musu idan buƙata ta biya su biya kuɗi idan kuma bai biya ba shikenan suji da kansu. Matar ta tambaye shi mai zai basu amma yace babu abinda zai basu wannan Sakayyar sune babu wanda ya isa ya kawar da Sakayyar zunubansu ne ya sauka akan su Babu ruwansa suji da kansu shima yaji da kansa. Tuno waɗanan maganganun ne yasa ta fashe da marayan kuka mai cike da nadama mara amfani, tana cikin kukan ta jiyo sautin muryoyi ana cewa Oyoyo Addah Khausy ahankali ta juye ruwan tana kallon tsutsotsin masu masifar gudu da ƙaiƙayi dole sai ta shiga ruwan ɗumin ne take ɗan jin sauƙi. Tana fitowa daga Bathroom ɗin ta zaune gefen Amina dake kwance kan gadon wacce ta rame ta zama wata halitta daban kamar ƙwarangwal tana nan tamkar wacce babu numfashi ajikinta kuka ta fashe dashi tare da cewa. “Amina kinga Sakayyar abinda mukayi ko. Ubangiji ya kama mu tun a duniya Allah ya kamu da Sakayyar tarin zunubanmu Amina ya zamuyi?”. Araunane Amina ta ɗago kanta cikin muryanta da baki ɗaya ya koma na wata halitta ta kalleta duk ta disashe baki ɗaya kamanninta da siffofinta ya fara zama na maciji ne ko menene dai ho da kyar ta buɗe bakinta tace. “Umma munemi gafarar wa'anda muka cutar tun kafin dare ya mana ”. Cikin rauni da zubda hawaye Hajiya Bunayya tace. “Dole ma mune mi gafarsu su yafe mana nasani wannan Sakayyar abinda nata yiwa wannan baiwar Allah ne, da abinda nayi wa ƴarta da kuma yanda nayi ta zubar mata da ciki sannan nasa aka kashe Ramadan yanzu shine Allah ya jarabceni da wannan abin”. Kuka sosai Amina ta fashe dashi tana ji kamar adawo mata da lokacin baya ta gyara kuskurenta. Ita ma Hajiya Bunayya kuka ta fashe dashi Asiya ce ta shigo ta zauna gefen su ta shiga rera kuka cikin rauni da tausayinsu tace. “Umma ku nemi gafarar Momyn Khausar da Khausar duk wanda ku kasan kun cutar kunemi gafarar su Allah gafururrur rahim ne shima zai yafe muku sai kuma ku nemi gafarar Allah akan shirka da kuka yi Allah ya yafe muku ”. Cikin raunin Murya da shesh-sheƙa Amina ta gyaɗa mata kai tare da faɗin. “In sha Allah zamu nema amma Addah Asiya ki taya mu basu haƙuri ”. Kai Asiya ta gyaɗa tare da cewa. „In sha Allah yanzu ma mukayi waya da Samira Sani take cemin itama jiya baki ɗaya Momyn ta kwana tayi tana ta ihu acikin gida gaba ɗaya tazama kamar mahaukaciya, ita tana jin tsoro yanzu zata dawo nan ma”. Atsorace Hajiya Bunayya ta dafe kuncinta tace. “Yau sun shiga ukunsy Hajiya Lami fa ta haukacene”. Cikin sanyi da zubda hawaye Asiya tace. “Haka dai alamu suka nuna Umma Allah ya yaye muku ya dubeku da idon Rahama”. Cikin rauni da tarin tsoro Hajiya Bunayya tace. “Ameen”. Amina kam sai hawaye take tana nadama da danasanin abinda ta aikata. Acan Falon Momyn kuwa bayan Moddibo yasha ruwa kana yaci Snacks da Drinks Momy ta fito suka gaisa bayan sun gaisa ta kallesa da kulawa tace. “Ina su Didi kuma?”. Sake sunkuyar da kansa yayi tare da cewa. “Momy su Didi suna gida amma sunce zasu ɗan fito zuwa azahar, sannan zasu fara ta gidan su Ummu kafin suzo”. Dai-dai lokacin kuma Asma'u ta shigo Falon bakinta ɗauke da sallama kasancewar Haiydar ya kirata ya sanar mata Khausar tazo gida. Khausar na ganinta ta miƙe da tsalle kana ta haɗa da gudu suka rungume juna da Asma'u suka fara juyawa atsakiyaar Falon. Cikin tsuke fuska Moddibo ya kalli Asma'u tare da faɗin. “Asmau me haka ki sake ta?”. Ahankali Asma'u ta sunkuyar da kanta ƙasa sai kuma ta saki Khausar ta tsugunna gefen Moddibo cike da ladabi tace. “Yah Moddibo sannu da zuwa Ina yini”. “Lafiya”. Ya faɗa yana ɗan sake Fuskara sai kuma yace. “Ke baki ga yanayin yanda ƙawar taki take bane kike mata irin wannan rungumar?”. Dariyar dake cinta ta danne ganin yanda Khausar ta Cunno baki kana tace. “Yah Moddibo ayi haƙuri”. Yana murmushi yace. “In sha Allah yanzu dai akiyaye”. Kai ta gyaɗa tare da miƙewa ta riƙe hannun Khausar suka nufi bedroom ɗin ta. Ganin haka yasa ya miƙe tare da cewa. “Momy bari in fita dan su Dr Jameel na jirana zamuje gida Abban Jameel ”. Mommy na gyara mayafinta tace. “Ayyah ai nima Jameel ɗin nan ina so akawo minshi in ganshi Haiydar yata bani labarinsa”. Cike da girmamawa yace. “In sha Allahu Momy za'a kawo miki shi”. Murmushi tayi tare da faɗin. “Toh ka gaishe su”. Amsawa yayi kana ya fita. A dai-dai lokacin kuma Didi, Lalla Khadijah, Lalla Hafsat, Suna gidan Ummin Jameel duk sun gaisa da ƴan Uwanta wanda suka fara taruwa saboda bikin bayan sun gama suka fito zuwa gidansu Momyn Khausar. Suna shiga Falon dai-dai lokacin Asma'u da Khausar na kitchen Khausar har mamakin kanta take saboda ƙosai da kunun gyaɗan da taci da safe, kana yanzu kuma Asma'u da kanta ta tuƙa mata tuwan Semovita da miyar ɗanyen kuɓewa aƙaramin dining Dake kitchen ɗin suke zaune. Khausar kam ta kasa daina mamakin kanta yanda take cin tuwon sosai kallon Asma'u da itama tayi wani irin kyau na ban mamaki tayi ta fito a asalin amarya tace. “Wallahi Asma'u har mamakin kaina na keyi rabona da abinci hakafa nafi wata huɗu”. Murmushi Asma'u tayi tare da cewa. “Ikon Allah baby ɗan albarka yasan yazo garinsu kenan”. Murmushi Khausar tayi tare da sunkuyar da kanta ta ɗan kalli cikin, dai-dai lokacin kuma suka jiyo sallamarsu Didi sun shigo gidan cikin wani irin... By *GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH Book 3 PAGE 3* NA *Aysha Aliyu Garkuwa* KAZAURE COLLEGE OF NURSING SCIENCES (KCONS) Lafiya Uwar jiki, Kuma sai da lafiya ake morar rayuwa. Kazaure College Of Nursing Sciences (KCONS) ta kawo muku ingantaccen tsarin koyar da jinya da unguwar zoma, mun himmatu wajen samar da kwararrun ma'aikatan jinya da unguwar zoma a fadin Nigeria da ma matakin duniya baki daya, a KCONS mun tanadar muku kwararrun malamai, ingantaccen yanayi da tsarin koyo da koyarwa kai harma da tsarin e-learning, ka zalika akwai tabbataccen tsaro a dakunan kwanan dalibai maza da mata, bugu da kari kudin makaranta dai-dai aljuhu, KCONS munanan a lamba 5 layin fadar sarki dake kan hanyar kano zuwa daura a Kazaure jahar Jigawa, za'a iya samummu a shafikanmu na facebook da instagram @KCONsciences domin bayani, za'a iya tuntubanrmu a wadannan lambobin, 07066542055, 08035298851, ko shafin mu na yanan gizo @ http://kcons.edu.ng/admission KCON sciences kan turbar aiki da kwarewa muka shahara. Zare idanu Asma'u ta miƙe tare da kallon Khausar tace. “Kamar su Didi ce suka shigo?”. Kai Khausar ta gyaɗa tare da cewa. “Ehem sune ya akayi?”. Yarfe hannu tayi sai kuma ta girgiza kai kana tace. “Wayyo Allah nikam zan fita ta ƙofar kitchen bana zaton zan iya haɗa ido da ita”. Dariya ce taso kufcewa Khausar amma sai ta daure bata yiba tace. “Meyesa?”. Cikin sauƙe ajiyar zuciya Asma'u ta ɗan kalli ƙofar tare da faɗin. “Wallahi kunyar su nake ji”. Baki sake Khausar ke kallonta kafin tace. “Dallah tafi daga nan muje ki gaishesu idan yaso sai mu tafi gidan Ummi tunda su suna nan”. Kai ta gyaɗa tare da faɗin. “Toh shikenan ”. Kana suka fito Falon Khausar ce agaba Asma'u na biye da ita cike da kunya. Didi na kallon Asma'u ta miƙa mata hannu tare da faɗin. “A'a ɗiyata ƴar Albarka Masha Allah fatan mun same ku lafiya?”. Kai Asma'u ta gyaɗa batare data kalleta ba kana ta gaishesu ɗaya bayan ɗaya. Anutse Khausar da cikinta ya ƙara bayyana dabida samun cin wadataceccen abinci ta juya jin Lalla Hafsat na cewa. “Ƙanwata ya dai an samu anci abinci kuwa?”. Murmushi Momy tayi tana kallon Lalla Hafsat tace. “Dama bata ci abinci ko?”. Kai Didi ta gyaɗa cike da tausayi tace. “Ina kuwa take cin abinci sai dai tai ta shan fruits”. Mommy na kallon Khausar dake sunne kai kana tace. “Ikon Allah nan kuwa tunda tazo cikinta bai huta ba haba ashe shiyasa take ta ci ba sausauci”. Asma'u ce ta karɓi zancen da cewa. “Yanzu ma tuwo da miyar kuɓewa tana ɗa a kitchen kamar me”. Khausar kuwa ɗan hararan Asma'u tayi. Didi kam da mamaki ta kalli Khausar tare da faɗin. “Ikon Allah Alhamdulillah ai haka akeso”. Murmushi Lalla Khadijah tayi kana tace. “Ai dama wani cikin hakane in Kaje unguwa sai kiga Kaci abinci idan kuma agidanka ne ba zaka iya ba”. Ahankali Khausar ta sake kasa da kanta cike da kunya wani irin masifeffen kunya ne ya mamaye ta jin yanda ake ta maganar tana da ciki. Batare data ɗago kanta ba ta riƙe hannun Asma'u tare da cewa. “Mu tafi”. Miƙewa Asma'u tayi kana suka shiga bedroom ɗin Khausar ta dauko mayafinta kallonta Momy tayi tare da cewa. “Ina zaki je?". Tana ƙoƙarin gyara mayafinta tace. “Zamuje gidan Ummi ne”. “Toh kin tambayi mijinki ne?". Cewar Momy. Murmushi Didi tayi kana tace. “A Babu Matsala ai taje tunda ziyara ne”. Miƙewa sukayi suka fita kai tsaye Side ɗin Hajiya Bunayya suka shiga bakinsu ɗauke da sallama. Falon shiru ba kowa sake sallama Khausar tayi da ɗan ƙarfu. Asiya dake bedroom ɗin tun ɗazu suna kukane tashin hankali d suke cikine ya hanata fitowa, jiyo muryar Khausar ɗin ne yasa tayi saurin miƙewa ta fito idanunta cike da hawaye ga kumburar da sukatu Khausar ta rungumeta tare da cewa. “Oyoyo Khausar sannu da zuwa fatan kunzo lafiya? ya gida yasu Didi da kowa da kowa?". Khausar na sake ruggume ta tace. “Duk lafiya lau". Ta ƙare maganar tana kallon idanunta da Fuskanta da suka kumbura alamar taci kuka da damuwa tace. “Addah Asiya lafiya kuwa?”. Ɗan Murmushi tayi tare da cewa. “Lafiya lau Khausar ”. Kai Khausar ta girgiza tana nazartan yanayinta tace. “Amma Addah Asiya kamar kuka kika yi fa dan Allah ki faɗa min dakuwarki na tabbatar akwai abinda ke damunki”. Araunane Asiya ta maida hawayen dake ƙoƙarin zubo mata tace. “Amina da Umma ce babu lafiya shiyasa hankalina yake tashe”. Da damuwa Khausar ta kalli Asma'u da itama ita take kallo kana tace. “Subhanallah me ya sami Aminan?”. Ahankali Asiya tace. “Bata da lafiya ne”. Da sauri Khausar ta ɗan kalli Falon tare da cewa. “Toh Ina take?”. Bedroom ɗin Hajiya Bunayya ta nuna mata tare da faɗin. “Tana ciki”. Cike da kulawa da tarin tausayi tace. “Toh mu shiga mana”. Kai Asiya ta gyaɗa kana tayi gaba Khausar da Asma'u na biye da ita. Suna shiga Idanunsu ya sauƙa kan Hajiya Bunayya dake zaune gefen gado tana sharɓan Kuka cikin sauri Khausar ta ƙarasa shiga kana ta zauna gefen Amina ta riƙo hannunta acikin nata cikin raunin ganin halin da Amina ke ciki tace. “Innalillahi wa'inna alaihi raji'un Amina meyesa meki?,me yake damunki?,Ya ilahi ya mujibud da'awati ya hayyu ya ƙayyum meye haka yake damunki?”. Ƙasa furta komai Amina tayi sai hawaye dake ambaliya saman fuskarta kallonta ta mayar kan Asiya kana ta cigaba da faɗin. “Addah Asiya meke damunta?”. Kai Asiya ta girgiza tare da cewa. “Muma bamu san meke damun Amina ba”. Muryanta na rawa tace. “Yaushe taxo to?”. Kai Asiya ta girgiza tare da faɗin. “Abin sai ahankali Khausar am”. Cikin matsanancin Kuka Amina ta damƙe hannun Khausar dake cikin nata kana muryanta cike da rauni tace. “Khausar ki yafemin”. Da sauri Khausar tace. “Ni kuma me kikayi min”. Cikin rawan murya Amina tace. “Ai ba abinda ban mikiba na cutar dake arayuwa Khausar ki yafemin”. Cikin sauri Khausar ta girgiza mata kai Idanunta na zubda hawaye. Hannunta ta ɗaura akan bakinta ta datake wani irin zaro harshe waje kana tace. “Ba kiyi min komai ba Amina ki daina kuka Allah Ubangiji ya yaye miki abinda yake damunki Allah ya baki lafiya Amina”. Kallonta ta mayar kan Hajiya Bunayya jin yanda shesh-sheƙa kukanta ke tashi tace. “Ummu kema kina kuka toh ita kuma ya zata yi aike zaki ƙarfafa mata guwwa!”. Amaimakon tayi magana sai ta zame ƙasa ta gurfana gwiwoyinta gaban Khausar tare da riƙe hannunta cikin wata raunatacciyar murya mai sanya tausayi tace. “Khausar ki yafe min nasan na cutar dake a rayuwata na cutar da mahaifiyar ki nasan kin sani na cutar daku”. Ahankali Khausar ta cije gefen bakinta kana ta jujjuya kanta still hawaye na bin fuskarta tace. “Bakomai Umma Allah ya yafe mana”. Kuka sosai Hajiya Bunayya ta fashe dashi tare da cewa. “Khausar na cutar daku da cutarwa mafi muni azaman da mukayi nasan ke kina zargina ”. Kai Khausar ta girgiza tare da faɗin. “Astagfirullah ai nima zargi nake Umma Allah ya yafe min kan zargin dana miki saboda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce. _Azzannah Zhambu Walau kana haƙƙun_”. Araunane Hajiya Bunayya ta girgiza kai tare da cewa. “Ba zargi bane Khausar dagaske ne tunanin ki akaina, ina cutar daku gashi Allah ya muku Sakayyah alokacin da bakuyi tunani ba ba kuma san ina yiba. Allah yayi muku Sakayyah alokacin da banyi Aune ba don Allah Khausar ki roƙamin gafarar wurin Momynki ku yafemin”. Asma'u kuwa cikin yanayin tsoro take kallon Amina data kasa tantance yanayin da take ciki. Hajiya Bunayya kuwa cikin tarin nadama ta cigaba da faɗin. “Kiga yanda Allah ya jarabceni kiga yanda Amina ta dawo kiga abinda Naseer ya mana Naseer yaje ya cutar min da yarinya. Jiya da yamma yazo ya wurgar mana da ita ya tafi ko shigowa cikin gidan nan baiyi ba. Ya juya ya tafi yau ya tafi Indi'a yabar mu da jidali Uwarsa da Ubansa sai binmu sukayi da rashin mutunci”. Nan ra kwashe duk labarin da Amina ta basu na macijin da yake fitowa yasha nononta da yadda ta kasa faɗawa kowa da kuma yadda yake hanata faɗa ta kara da cewa. “Ashema shine yake juyawa ya zama macijin yayi ta shan nononta sai jiyan duk yake gaya mata ya aureta ne dan tayi tsafi da ita ya samu biyan buƙatar rayuwar duniyar sa, yanzu kuma buƙatarsa ya biya ya haɗota da takardar saki uku yazo ya wurgar mana da ita”. Hawayen da yaƙi tsayawa Khausar ta share tare da faɗin. “Innalillahi wa'inna alaihi raji'un Uncle Naseer”. Sai Kuma ta juya ta kalli Asma'u da itama ita take kallo Asma'u kuwa cikin sanin muguwar ɗabi'arsa tace. “Hmmmm Uncle Naseer zaiyi abinda yafi haka ma”. Hajiya Bunayya kuwa cigaba da cewa. “Khausar nasan Sakayyar abinda nayi miki ne nayi muku sihiri na biku da bita da ƙulli”. Daga nan ta tsinke da surutai duk wani abu data aikata musu saida ta faɗa. Khausar kam baki ɗaya ilahirin jikinta rawa ya fara cikin tsananin kiɗima mamaki da al'ajabi gami sa tsoro. Duk da cewa tana zarginta bata taɓa tunanin abin nata yakai haka ba. Hajiya Bunayya kuwa miƙewa tsaye tayi sai kuma ta durƙusa tana ƙoƙarin naɗa zaninta tace. “Khausar kiga yanda tsutsotsi suke cina yanda na dawo”. Cikin sauri Khausar ta riƙe hannunta tare da cewa. “Innalillahi wa'inna alaihi raji'un Umma kada ki nuna min Ummu kiyi addu'a Allah ya yaye miki kuma in Sha Allahu nima zan miki addu'a nikam na yafe miki”. Idanunta ta mayar kan Amina kana tace. “Amina Allah ya baki lafiya Ubangiji ya yaye miki zan faɗa wa Yah Moddibo ya miki addu'a Allah yaye miki kuma zan sa Dr Jameel zai zo ya duba ku in Sha Allahu Allah yaye muku ya baku lafiya mai amfani mai albarka Allah ya yafe muku shurkar da kukayi”. Da karfi Hajiya Bunayya ta fisge hannunta dake cikin na Khausar kana tace. “Um-um Khausar ki bari in nuna Miki abinda ke cina kiga *Sakayya* data diromin”. Cikin sauri Khausar ta girgiza kai tare da cewa. “A'a Umma basai kin nuna min ba wannan bai kamata ba ai”. Ta ƙarashe maganar hawaye na cigaba da kwaranya daga idanunta ganin ta da Amina ke wani irin numfashi tana hura yayin da take zazzaro harshenta waje tana kaɗawa kamar yanda maciji keyi”. Asiya kuwa ta gaza cewa komai sau wani irin kuka mai cike da ƙuna da ƙuncin zuciya da take yi tamkar ranta zai fita. Asma'u kuwa cikin yanayin tsoro ganin abinda Amina keyi ta shiga jan hannun Khausar dake zaune tana cewa. “Khausar mu tafi”. Cikin dashewar murya da rauni Amina ta kalli Asma'u tare da faɗin. “Ayyah Asma'u am ki barni in nemi yafiyarta”. Kai Khausar ta girgiza cikin sake jin tsoron Allah da tsoron hakkin mutum tace. “Amina wallahi na yafe miki duniya da lahira”. Cikin sauƙe ajiyar zuciya tace. “Toh kicewa Momynki ma ta yafemana”. Kai Khausar ta gyaɗa tare da cewa. “In sha Allah Momy zata yafe muku Momy kam ma bata riƙe ku ba”. Asma'u kam.da ƙarfi taja hannun Khausar suka fita daga bedroom Khausar kam wani irin tsoro gami da mamakine ya mamaye mata zuciya ganin yanda rayuwa ta juye dasu suna fitowa compound ɗin gidan Samira Sani da Hajiya Lami na shigawo. Samira na ganin Khausar ta nufeta tare da fashewa da kuka kana ta rike hannunta tare da cewa. “Khausar! kece haka?”. Cikin sanyin jiki Khausar ta gyaɗa mata kai tare da faɗin. “Eh nice Samira ya gida” Ta ida maganar tana kawar da kai gefe saboda wani irin masifeffen wari da take ji Samira kuwa cikin rauni tace. “Khausar ki yafe mana Khausar dubi yanda Allah ya dawo dani”. Idanunta ta mayar kan cikin Khausar daya fara tashi kasancewar rigar jikinta lafaffiya ce cikin sanyi ta cigaba da cewa. “Ayyah Khausar dubi yanda Allah ya miki gata arayuwa sabida kin bishi, mukuma dubi yanda Allah ya mayar mana da mugayen aiyukabmu damu”. Hajiya Lami dake gefe wacce duk yanda Samira taso gudu ta barta batare data biyo taba sai da ta manne ta biyota ta fashe da wani irin dariya mai firgitarwa kana ta tafe hannu tare da faɗin. “Iyyeee sukam ai sunbi Allah sun samu yanda suke so mu da muka bi Bokaye baga nan sakamakon mu yanda ya dawo ba Itama Hajiya Bunayya Stuliya ta ruɓe tsutsotsi na zuba ke kuma gaki nan kinata Yoyon ruwa mai ɗoyi Ni kuma gani nan gani nan dai Ni ba mai hankali ba niba mara hankali ba”. Cikin zubda hawaye Samira tace. “Dan Allah Momy ki daina surutan nan”. Ta wani zare idanu tana kallon Samira tace. “Wani irin surutai zan daina ai gaskiya nake faɗa abinda muka aikata ne yoh tunda ma Allah ya ɓallomin waɗanan sutura akwai wanda ya isa ya hanani zubasune ai nice nan mai tona asirinmu”. Bisa alamu dai yadda take maganganu ƙwaƙwalwarta ya fara taɓuwa ne ta dawo sha tara sha tara haka hankalin ya zama tara da indagi. Khausar kam baki ɗaya ilahirin jikinta rawa ya fara Allah ya sani tana masifar tsoron Mahaukaciya ga kuma Hajiya Lami dake nan atsaye ƙam kaman ƙiran Samudawa ga tsawo ga jiki da uban zuguda. Asma'u kam cikin sauri taja hannunta suka fita dai-dai lokacin Haiydar da Bashir suka zo akan mashin Bashir ya goyi Asma'u kana Haiydar ya goyi Khausar suka nufi gidan Ummi. Suna isa Falon Ummi suka gaishe da Goggonayen Asma'u ƙannen Malam Ahmad da ƴan uwan Ummu kana suka wuce bedroom ɗin Asma'u... Suna zama dai-dai lokacin kira ya shigo wayar Khausar ahankali ta ɗaga ganin sunan Moddibo yasa tayi picking. Daga ɗaya ɓangaren ta tsinkayo sanyayyar muryansa na cewa. “Minha”. Cikin sanyi ta gyara zamanta murya cike da rauni tace. “Na'am Yah Mu'allim”. Cike da kulawa yace. “Lafiya kuwa ya naji kinyi sanyi”. Kai ta girgiza tare da cewa. “Bakomai Yah Mu'allim?” Da damuwa yace. “Ina kike yanzu?”. Ahankali ta ɗan lumshe Idanunta tare da cewa. “Ina gidan Ummi ”. Ɗan tsuke fuska yayi kana yace. “Minha meyesa kike son yawo ne?. Toma tukun meyasa da zakije baki kirani kin faɗa min ba”. Still asanyaye tace. “Yah Mu'allim kayi haƙuri nida Asma'u muka taho kuma Haiydar ne ya kawo mu”. Da sauri ya zare idanunsa yace. “Ya za'a yi Haiydar ya kawo? ki akan me ya kawo ki?”. Numfashi ta fesar tare da faɗin. “Akan Mashin ya kawo ni”. Cikin bada umarni yace. “Bana so kada ki sake hawa Mashin banaso”. Kai ta gyaɗa tace. “Yah Mu'allim kayi haƙuri bazan sake ba”. Ahankali ya sassauta muryansa tare da gyara zamansa acikin mota yana kallon Dr Jameel da Zakariyya yace. “Tukunna ma yanzu menene matsalar ki naji duk kinyi sanyi”. Muryanta na rawa irin na wanda ke gan da zubda hawaye tace. “Yah Mu'allim Amina da Umma ce basu da lafiya sai kaga yanda suka dawo”. Cikin rashin fahimta ya shafa sajensa tare da faɗin. “Wacece Amina?”. Cikin sauri tace. “Yah Mu'allim ya za'a yi kace min wacece Amina ka manta Amina?”. Ɗan shiru yayi sai kuma yace. “Gaskiya na manta ta”. Tana jinginar da kanta jikin gadon Asma'u tace. “Wannan wacce muke zuwa makaranta tare Yah Mu'allim ya za'a yi kace baka santa ba”. Numfashi ya fesar tare da cewa. “Ok na tuna ta”. Cikin sauƙe numfashi tace. “Wallahi bata da lafiya”. Ba yabo ba fallasa yace. “Ayyah Allah yaye musu”. “Ameen” Ta amsa sai kuma tace. “Ayyah Yah Mu'allim kayi ta musu addu'a Allah ya basu lafiya”. Kai ya gyaɗa tare da faɗin. “Toh Allah Ubangiji ya yaye musu ya basu lafiya”. Ahankali ta gyara zamanta kana tace. “Kuma inso samu ne dan Allah kasa Dr Jameel yazo ya duba su da jiki”. Yana lumshe Idanunsa yace. “Yanzu dai tukunna muyi Abin dake gabanmu Ni naji gaba ɗaya kinyi sanyi shine matsalata”. Cikin tabbatarwa tace. “Wallahi lafiya ta lau kawai dai jikin sune”. Kai ya gyaɗa kana yace. “Ok toh Allah ya basu lafiya in Sha Allahu za'a yi musu addu'a kuma Dr Jameel zai zo ya duba su hankalinki ya kwanta”. Kamar yana gabanta ta gyaɗa masa kai. Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa. “Toh yanzu bari muna zuwa dan Dr Jameel ma yana son ganin Asma'u”. Kai ta gyaɗa kana sukayi sallama. Ba daɗewa suka isa a waya Moddibo ya kirata tare tare da sanar mata sunzo yana dakin Bashir kana Asma'u kuma ta samu Dr Jameel a mota. Acan ɗakin Bashir kuwa cike da tarin kulawa taysayawa Moddibo ya jawota jikinshi tare dayi mata sahihin rugguma, sai kuma yasa hannunsa duka biyu ya tallabo kanta wani irin amintaccen lasa tayi lips inta duka biyu sai kuma ya fara yi mata wani irin amintaccen kiss mai saukar da nitsuwa salama da mantar da ita duk damuwar dake tare da ita. Hannunta tasa bisa sajenshi tana ɗan jujjuya yatsunta, mirginata yayi a kan jikinshi tare da gyara kwanciyarsa bisa tattausar katifar Bashir dake zuwa amintaccen ƙamshi da watar tsabta. Hannunshi ya cusa cikin rigartan tare da fara shafa cikinta. Cikin tarin farin ciki ya zare harshensa daga bakinta tare da kallonta itanma shi take kallo cikin zare ido saboda jin yadda cikinta ke wutsul-wutsul, da sauri ta fara nannaɗe rigar ta tare da turashi sama cikin ya bayyana a fili, ido suka zubawa cikin baki ɗayansu, sai kuma tayi saurin kamo tattausan rafin hannunsa tana mai ɗaurawa akan dai-dai inda cikin ke wutsulniya tare da cewa. “Yah Salam Yah Mu'allim kaji yadda yake ta motsi irin motsin da Dr Jameel yake cewa zan fara ji da zaran ya shiga wata na huɗu”. Cikin tsananin farin ciki mara musaltuwa ya sunkuyo kan cikin tare da fara manna ma hot kiss tako wani sashin na cikin bisa alamu jin daɗin ya hanashi mgn, ita kuwa Khausar hannunta ta cusa cikin sumar kanshi tana cakuɗawa. Sai kuma ta lunshe udanunta saboda jin sautin muryansa yana rero addu'o'in na musamman na kariya yana tofawa cikin tare dasa mishi albarka. Murmushin takeso ciki da jin daɗi tana mai ƙara shafa sajenshi da tuni ta fara rabashi sa nitsuwarsa. Da sauri ta buɗe idanunta jin ya naɗe rigarta har sama har caɓɓullenta sun bayyana faresa, wanda zuwa yanzu sun gama cika sunyi tamtsam-tamtsan dasu gwanin kyau. Shyyyht taja wani irin amintaccen numfashi lokacin da taji ya manna sassayan tongue ɗinsa bisa kan caɓɓullenta na dama kana yayiwa hannunsa na hagu masauƙi a kan na hagunta. Wani irin amintaccen kana fitinennen salon sa bazata iya ƙi ko bujurewa ba ya fara yi mata, tuni ta fara amsar saƙonninsa tare da maida masa amsar da tasa ya zare rigarta ya dire gefe kana ya zare tasa rigar cin mancewa da inda suke ya fara ida nufinsa sosai ta amshi baƙocinsa gami dayi masa kekkyawar tarbar da tashi sambatu da sanya mata albarka da yiwa J ɗinshi Addu'a. Bayan kamar 50 minutes ne ya sahirta mata tare da jawota jikinshi yayi mata kekyawan rugguma cikin sauƙe numfashi yace. “Kai Minha Vidaa kwaɗayi yanzu a ɗakin Bashir ma, baki barniba saida kika tsotse min ɗan ruwan jiki”. Cike da kunya tace. “Yah Mu'allim banda sharri fa, ba kai bane ka fara”. Da sauri yace. “A'a ni kawai gaisawa nayi da Babyna nasa mata albarka, ke kuma kwaɗayi irin rabonki da abin daɗinki tun a marocco, shine kakayi ta min kuka a waya to nazo na baki hankali ya kwanta ko”. Cikin zazzafan shaƙuwa tace. “Zan rama ai”. Cikin yin murmushi yace. “Ƴar al'barka matar aljanna ai uwar ƴaƴana gari na tuba kada arama”. Cikin kwaɓe fuska tace. “Toh Amman zaka tura Dr Jameel ya duba su Umma ko?”. Ganin yadda duk tai sanyi ne da alamun sosai abin ya bugeta cikin sanyi ya, rika kwantar mata da hankali har ta saki fuskarta kana cikin sanyi ta gyara zama tare da zayyane Moddibo duk abinda ke faruwa. Kansa ya girgiza tare da cewa. “Ai dama haka rayuwa take Minha Duk wanda ya saki Allah ya kama wani yana tare da wahala mabayyani. Fatanmu Allah yaye musu zan sashe addu'a kuma batun asibiti yanda kika ce ɗin nan zaiyi wuya ai maganin asibiti ya musu aiki sai dai suyi na Islamic sannan kuma a dage da addu'a kana ki yafe musu domin Ubangiji yana son masu yafiya kinji Minha tunda dai Allah ya rufa min asiri basu samu damar lalatamin duniyar jin daɗinaba abu ya komai kansu ai ni sai dai ince Alhamdulillah yanzu da ace suhirinsu yaci ai da bamuji wannan daɗin da mukajiyar da juna yanzu”. Cikin yin ƙasa da kai tace. “Uhmmm da tuni ka sakeni dai ka koroni Nigeria na dawo da ƙafa”. Cikin gsky da gaskiya yace. “Wannan kuma duk rintsu duk wuya bazai taba faruwaba in sha Allah, da haka ta faru ina mai roƙon Allah gwara in mutu kiyi takabana, shima kuma in Allah ya bani dama kafin in mutu sai na roƙi alfarma na bar Miki watsiyar ko bayan raina kada ki sake aure dan bana son wani ɗa na miji yaji abinda nakeji a jikinki bana son ko wani ɗa na miji ya kallemin abinda nake gani inji daɗi kayan marmarina nawa ne ni ɗaya. Har abada babu wani mai mallakarsa, tunda J ya sadaukar min dashi, dama shi kaɗai ne a duniya na iya yakicewa abin sona na sadaukar mushi dake”. Cikin wani irin amintaccen so ƙauna da kuma ganin wutar kishinta a ranshi da idanunsa tace. “Ni kuwa alfarma ɗaya nakeso in zan samu”. Da sauri yace. “Faɗi inji in zaki samu”. Cikin tsananin bayyanar tsananin sonshi da kishinsa murya na rawa tace. “Ni iyakar in ina rayene kaɗai bani son inga wata ya mace ta raɓeka, ta ganka a suffar da in na ganka a haka nakejin cewa duk duniya ba macen da ta kaini dace, kana na tabbatar muddin nasan zakayiwa wata ɗiya mace abinda kakemin a duk dare da muke kasance a muhalli ɗaya na sani zan mutu wlh zuciyata zata buga na mutu”. Wani irin amintaccen numfashi mai tafe da murmushin mai cike da tsananin farin ciki ya saki saboda fahimtar kalamanta da ganin tsananin so da kishinsa cikin kwayar idanunta, sai kuma tayi saurin kallonta jin ta saki sassayan kuka murya na rawa taci gaba da cewa. “Amman idan har rigaka barin duniya ni na amince Yah Mu'allim kayi aure saboda nasan zamanka ba mace, zai cutar da kai sabida nasan mijina inƙarman namijine ma buƙaci, Amman indai ina raye kada ka haɗani da wata nayi alkawarin zan ɗauki dukkan buƙatar ka don mallakar ka ni ɗaya, shiyasa nakeso kayi min alkawarin bazaka haɗani da ko wacce ya maceba a fagen mallakarka”. Cikin sanyi yasa rafin hannunsa bisa kuncinta yana share mata hawaye sai kuma ya ɗaga mata girarsa ɗaya cikin sahihiyar murya yace. “Sai nayi nazari zan baki amsa sarkin”. Cikin rauni tace. “Sai kayi nazari kuma ni yanzu nakeso kayi min alkawarin”. Cikin kauda mgnar yace. “Da fari ki yafewa su Umma tunda basu samu damar rabaki da mijinki ba, muna nan tare zanyi ta baki abin daɗinki”. Ya ƙare maganar cikin son kauda tunaninta da waccar mgnar alkawarin. Kai ta gyaɗa kafin tace. “Ai dama Ni na yafe musu Yah Mu'allim Kuma zan faɗawa Momyna ma ta yafe musu”. Cikin son sama mata nitsuwa da sassauta zazzafan kishinta daya motso yace. “Toh yanzu ki kwantar da hankalinki in Sha Allahu zasu samu lafiya ai babu abinda yafi ƙarfin Allah”. Kai ta gyada tare da faɗin. “Hakane”. Haka dai ya cigaba da kwantar mata da hankali da kauda mgnin ta. Acan ɓangaren Dr Zakariyya kuwa shima yana tare da Asiyansa. Bayan Sallar la'asar Moddibo ya maida Khausar gidan Momy. Akuma dai-dai lokacin Didi dasu Lalla Khadijah Lalla Hafsat suka tafi hakan ya bawa Khausar daman ke ɓancewa da Momynta kasancewar kowa ya watse cikin sauƙe numfashi Khausar ta kalli Momy tare da cewa. “Momy ashe Amina da Umma basu da lafiya?”. Zama Momy ta gyara tare da faɗin. “Ke dai bari Khausar Rayuwar Nan abin tsoro ne jiya-jiyan nan Naseer yazo ya kwantar da Amina a ƙofar gida abakin gate fa ko ciki bai shigoba ya juya barta”. Da sauri Khausar ta dafe ƙirjinta Momy kam cikin sanyi ta cigaba da cewa. “Babu ma wanda yasan ya kawo ta Haiydar ne ya dawo ya ganta akwance da Ghana Masgo ɗin ta da yake tana iya magana ne shine tace shi ya kawo ta ya ajiyeta ya juya ya tafi kuma taji yana waya kan cewa yau zai koma Indi'a kuma ma ya tashi ya tafi”. Zuwa lokacin kam hawaye sunƙi tsayawa akan kuncinta. Cikin sauƙe numfashi Momy ta cigaba da faɗin. “Koda Lamiɗo yaje wajen Mahaifinsa sai cewa yayi ina ruwansa tunda shi da Naseer ƴan Uwa ai shine bare a ciki, kar a wani sashi a ciki, kar kiga yanda Amina ta dawo Khausar Rayuwar Nan wanda bai ji tsoron Allah ba ya wahala Kinga dai wannan ya ishe ki ishara”. Khausar na zubda hawaye ta gyaɗa kai tare da faɗin. “Momy da naje duba su sunata bani hakuri tare da faɗe-faɗe abubuwan da nake faɗa Miki ina zargin Umma ita da bakinta tayi ta min faɗe-faɗe Hajiya Lami kam naga kamar ma ta haukace”. Cikin sanyi da al'amarin Momy tace. “Hmmm sosai ma tayi ta ife-ife daga bisani mijinta yazo ya ɗauketa yace gata ɗaya zaiyi mata ya Kaita gidan mahaukata. daƙyar aka samu aka ɗauke ta aka fitar da ita ƴarta ma cewa tayi tana tsoronta. Lamiɗo kuwa kullum binshi nake yakai su asibiti yaƙi ance kuma ya ɗaga Auren Asiya tun da ga jikin Mahaifiyarta da ƴar uwarta ba lafiya yace babu wanda ya isa ya hana suje can su ƙarata da zunubin su”. Cikin jimami Khausar ta tallafe kuncinta tare da cewa. “Kai Rayuwar Nan Allah dai yasa mu cika da imani” . Cikin sanyi jiki Momy tace. “Amin ya Allah, haka rayuwa take dan kayi abu a ɓoye Allah na ganin ka gashi yau yaya da kanta ta fito take ta faɗamin abubuwan da tayi ta min da bakinta, wai harda cewa ita ta kashe min Ramadan nace a'a ni karya ɓatamin gawar ɗa, dan dama tunda yayiwa wannan haɗarin garin gwaje-gwajen aga kanshi bai buga aka gane cewa yana da cutar brean Cancer. A lokacin ma sunce ya cinye kaso biyu cikin uku kanshi shiyasa ko mgnin basu bashi ba. Ni nasan kuma Abbanku ma ya sani kune dai bamu faɗawaba.” Cikin zubda wa Khausar tace. “Allah Sarki Ramadan Allah ya jiƙanshi”. Cikin sanyi Momy tace. “Amin ya Allah kinga ni dai na yafe mata kema ki yafe mata”. Tana shafa cikinta tace. “Na yafe mata Mommy, kuma in sha Allah duk randa na haifi mai kama da Ramadan tun asibiti zan bakishi ya meye Miki madadin Ramadan ɗinmu ki raineshi”. Murmushin jin daɗin Momy tayi tare da cewa. “Allah ya sauƙeƙi lfy Khausar am ki raini abinki da kanki Mamana”. Cikin kunya ta ce “Amin ya Allah”. Sai kuma ta kalli Momy jin tana cewa. “Wata nawa ne yanzu”. Kai ta ɗan sunkuyar tare da cewa. “Wata uku ne ya shiga na huɗu”. Kai Momy ta jinjina. A wannan ranan haka Momy da Khausar suka yi yammacin suna hira. Da daddare bayan an idar da Sallar Isha'i Moddibo yazo ɗaukarta. Bayan Moddibo yazo suna hira Momy ta kalli Khausar tare da cewa. “Khausar kawo masa abinci”. Kai Khausar ta gyaɗa kana ta miƙe ta shiga kitchen ta kawo masa. Gabanshi ta zauna tare da matso da warmars ɗin. Tuƙeƙƙen tuwon shinkafa da miyar kase wanda yaji man shanu, da kifi haɗi da nama. A plate ta zuba masa mai ɗan yawa kana ta ajiye masa agabansa tare da sa kishi sassayan kunun ayan da Momy tayiwa su Didi cika cup ɗin tayi kana ta koma bisa kujerar. Gyara zamansa tare da cewa. “Toh saƙƙo muci”. Kai ta girgiza tare da shafa cikinta tace. “Um-um ai na ƙoshi”. Ɗan ware idanunsa yayi tare da faɗin. “Kin tabbatar?”. Cikin gaskiya da gaskiya tace. “Wallahi naci Yah Mu'allim”. Kai ya girgiza yana mai tsirawa cikinta idanu yace. “Ban yarda ba”. Raudat dake shigowa ta kallesa tare da cewa. “Wallahi taci da yawa Yah Moddibo Addah Khausy yau tunda tazo sai tuwo take ta ci”. Cikin mamaki ya kalleta tare da faɗin. “Da gaske?”. Daidai lokacin kuma Momy ta fito daga bedroom ɗin ta cikin shiri wanda da alamu Side ɗin Lamiɗo zata tafi, cikin yin ƙasa da Moddibo ya kalleta kana yace. “Momy wai dagaske taci abinci?”. Murmushi Momy tayi tare da gyaɗa masa kai tace. “Wuuuu ai Khausar yau ko Gara nan ya barta acin abinci ai daga safe zuwa yanzu taci abinci ya kai sau bakwai”. Cikin mamaki yace. “Ikon Allah Momy bata cin abinci a gida fa”. Momy na ƙoƙarin fita tace. “Aikam haka su Didi suka faɗa amma nan kam tana ciki inaga duk yunwar data tara take sauƙewa”. Cikin farin cikin daya kasa ɓoyewa yace. “Alhamdulillahi”. Bayan fitan Momy yafara cin abinci suna ɗan taɓa hira. Suna cikin hirar Momy ta dawowa zuwa wannan lokacin already Moddibo ya gana cin abincin har Khausar ta kwashe kayan kallon Khausar yayi tare da cewa. “Toh mu tafi dare yana yi momy zamu tafi dare yayi”. Ya ƙare maganar yana kallon Momy. Ɗan murmushi Momy tayi tare da faɗin. “Toh Allah ya bamu Alkhairi”. Kallon Khausar dake zaune yayi kana yace. “Minha mu tafi ko?”. Kallonsa tayi tare da faɗin. “Ba anan zan kwana ba?”. Yi yayi kamar bai jita ba sake langwaɓar da murya tayi cike da shagwaɓa tace. “Ayyah ka barni in kwana mana”. Still yi yayi kamar bai jita ba ya ma Mai da kallonsa kan Momy yace. “Momy zamu tafi dare yayi”. Kai Momy ta gyada tare da faɗin. “Allaj ya bamu Alkhairi ku gaida su Didi”. Cikin sauri da lumshe ido Khausar tace. “Dan Allah kabarni in kwana mana”. Juyawa yayi ya kalleta kana ya kalli Momy da tayi shiru alamar tana son ƴartata ta kwana. Har ga Allah baison barinta ta kwana amma ganin yanda Momy tayi shiru tana Murmushi yasa shi kallon Khausar data langwaɓar da kai da kuma yanda akace tana cin abinci yasa shi fesar da numfashi tare da faɗin. “Shikenan zo muje ki rakani”. Da sauri ta ɗan ware idanunta tace. “Kenan ka barni in kwana?”. Kai ta gyaɗa tare da faɗin. “Eh ba damuwa amma muje in Baki saƙo amota”. Cike da farin ciki tace. “toh”. Kana ta miƙe tabi bayansa. Cikin tsananin jin daɗi momy ta rakasu da ido domin ta samu cikekkiyar gamsuwa akan mutumunci da kulawar Modibbo da iyayensa akan ɗiyar tata. Mazaunin Driver ya zauna yayin da ta zauna gefen mai zaman banza janyota jikinsa yayi kana ya ɗaura hannunsa akan cikinta tare da faɗin. “Minha bana son barinki ki kwana awani waje batare dani ba amma yanda kika nuna agaban Momy ba yanda zanyi”. Cikin sanyi tace “Kayi haƙuri Yah Mu'allim nayi kewar Momyne”. Cikin lumshe idanu yace. “Shikenan ba komai”. Ya ƙarashe maganar yana ɗaura hannunsa akan cikinta ahankali tace. “Kayi haƙuri ”. Kai ya girgiza tare da cewa. “Bakomai”. Cikinta yake shafawa kafin ya buɗe tafin hannunsa ya karanta _Ƙulhuwa³ Falaƙi³ Naasi³ Ayatulkursiyyu¹ Amanarrasulu ¹ Laƙadja'akum¹_ ya shafa mata cikinta tare da faɗin. “Toh Allah ya kare ki ya kare min Babyna saboda banason Maƙwabtakanki da Hajiya Bunayya tsoronta na keji akan abinda tace ta miki”. Kai ta girgiza tana sake lafewa jikinsa tace. “Bakomai in Sha Allahu ba abinda zai samemu tunfa addu'o'inka na tare damu”. Cikin sanyi yace. “Dan Allah Minha kada ki kwanta bakiyi alwala ba kuma kiyi addu'a Kinga Bama tare bare inyi miki”. Cikin shaƙar ƙamshin jikinsa tace. “In sha Allah zan yi kuma Momy nayi min yadda kake min”. Cikin jin gamsuwa yace. “Ayyah Mommy Allah ya bar mana su ”. Amin. tace tana shafa sajenshi. Bayan sun sake taɓa hira ya rakata har ƙofan Falon Momy sai da ta shiga kana ta juya ya koma. Ita kuwa Momy hannun Khausar ta kalla. Ummmmm tace saboda ganin ba wani saƙo kawai so yake ya kebe da matarsa fahimta haka ya sata mgnar. “Uhmmm kaddai in shiga haƙƙinshi shi da matarsa”. Sai kuma ta kalli Khausar dake matsar da Raudat gefe tare da kwantawa kusa da Momy tana cewa. “Yau dai ke zaki koma gefe ni zan kwanta kusa da Mommy na”. Murmushi Momy tayi tare da cewa. “Je kiyi alwala tukun”. Toh tace kana taje tayi alwala kana tazo ta kwanta nan sukayi ta hira. Washe gari bayan an idar da Sallar Asbah duk su Abualeey sun koma gida. Moddibo kuwa karatun ƙur'ani ya fara daga bisani yayi Azkhar. Takwas dai ya miƙe ya nufi gida. Har ya nufi bedroom ɗinda sai kuma ya fasa key ɗin motarsq dake kan Dinnin table ta ɗauka, kana ya fito kai tsaye mota ya shiga. Tare da nufan gidan Momy haka nan yake ji yayi mugun missing ɗin ta ji yake kamar ya ɗauki wasu kwanaki bai ji ɗumin baby nai ba. Yana Parking motar aharabar gidan ya hango Haiydar da Bashir wanda yanzu ya dawo gidan da kwana saboda baƙin da suka cika gidansu. Suna ganinsa suka isa wajensa tare da cewa. “Yah Moddibo Barka da safiya”. Cikin sakin fuska yace. “Yawwa Haiydar Barka dai”. Su Haiydar ne sukayi nasa jagora zuwa Falon Lamiɗo bayan sun gaisa Lamiɗo yace. “Nima yanzu nake shirin zuwa wajensu Abualeey”. Anutse Moddibo ya ɗan sunkuyar da kansa ƙasa tare da cewa “Ayyah ai suna na tare da Abban Jameel ma da Malam Ahmad”. Kai Lamiɗo ya gyaɗa tare da kallon su Haiydar kana yace. “Ku isa dashi”. Kai suka gyaɗa tare da fita kana ya miƙe yabi bayansu. Dai-dai lokacin kuma Momy na kitchen. Yayin da Khausar ke kwance kan 3sitter. Suna isa bakin Falon Haiydar ya kalli Moddibo tare da faɗin. “Yah Moddibo ka shiga ”. Kai ya gyaɗa kana yace . “Ok”. Sai kuma ya kalli Bashir tare da cewa. “Ina zakujo”. Cikin shaƙuwa Bashir yace. “Adda Asma'u ce ta matsa mana da kira wai muje mu amso mata ɗinkunanta”. Kai jinjina musu, daga nan ya nufi cikin ɗakin. Kana suka juya da alamu aikan zasu tafi. Ahankali Moddibo ya shiga Falon bakinsa ɗauke da sallama. A hankali ya lumshe idanunsa kana ya buɗesu sabida hango Khausar kwance bisa 3 sitter. Falon shiru ba kowa sai sassayan ƙamshi da sautin TV can ƙasa da ake addu'o'in azkar. A hankali idanunsa suka suke yawo a kanta tana bacci cikin kwanciyar hankali wanda ga duk kan alamu tana jin dadin bacci.. Sai kuma plate dake gabanta da cup wanda ke da guntun tea a ciki sai plate ɗin dake da alamun indomei ne taci a ciki kafin tayi baccin. Anutse ya ƙara sa tsakiyar Falon tare da zama agefenta daga ƙasa ahankali ya ɗaura hannunsa dai-dai kan fuskarsa kana yasa babban yatsansa kan gashin girarta ya kwantar. Ahankali ta fara jin alamunsa akusa da ita yayin da take zuƙan ƙamshinsa ahankali ta buɗe ido ta kallesa fuskar ya shafa cikin wata sanyayyar murya yace. “Barka da safiya me kyau ko Babu kwalliya”. Idanunta ta sake lumshe jin yanda sautin muryansa ya ratsa ainihin ƙoƙon zuciyarta. Moddibo kuwa ahankali ya kamo tafin hannunta tare da ɗaurawa asajensa kana ya motsa laɓɓansa tare da cewa. “Na kasa juriya rai kin ka kwana tun jiya”. Da wani irin sauri Khausar ta damƙe hannunsa dake cikin nata jin wani irin nutsuwa da farin ciki. cikin nutsuwa da zaƙin muryansa ya cigaba da faɗin. “Ko rufe ido nayi kece kaɗai nake gaaaani kin wadaci zuciyata ba wacce zata rarrafo”. Hannunsa ya mayar kan lips ɗin ta yana shafawa ya cigaba da cewa. “Tattalinki zan kamar ya ƙwai”. Cikin jin daɗi ta matso da kanta ta ɗaura asaman tafin hannunsa cikin tarin ƙaunarta ya kashe mata ido ɗaya tare da cewa. “Duk abinda kin kaso akwai, babu wacce zata ji da kai gareni dan ni ina da Gimbiya”. Da hannu ta nuna kanta alamar Ni ya gyaɗa mata kai yana shafa sumar kanta yace. “In kiraki Layla ne ko Majnuniya”. Ahankali ta ɗan mike tana jin wani irin farin ciki da nutsuwa yayin da wani irin ƙaunarsa ke fusganta ganin yanda ta kwanto jikinsa ya sanya shi kuma ahankali ya janyota tare da rungumeta tare da man.... By *GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH Book 3 PAGE 4* NA *Aysha Aliyu Garkuwa* Tallah !! Tallah !! Shahararriyar Marubuciyar nan Ikilima Adam (kyauta daga Allah) wacce ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *Kanwata* *kaikajawa kanka , *Rai daya janzaki*. Yau na sake dawowa domin Domin tallata muku Littafaina mai Suna *(RUDANI )* Da kuma *Makauniyar Shari'a* littafine mai kunshe da Butulci , cin amana ,zagon Kasa , soyayya irin ta gani kasheni , aminci da saura n su basai n'a cika Ku da surutu ba Hausawa sukace Gani yakori ji. Karku Manta *Makauniyar Shari'a* sabon littafi ne mai bibiyar Ma'anar sunan sa. Ya zarce duk littafai na , na baya. RUDANI littafine mai cike da Rudani da ban Al'ajabi , duk wacce kika fi buƙata zaki biya kudin sa Naira ɗari biyar kacal. Farashin kowannen su Naira Dari biyar ne 500 kacal Domin Karin bayani Ku tuntubeni a lambata kamar haka (09069080725 ko Kuma + 22953726162 ) wacce Bata shirya Siya ba kada mu batawa juna lokaci. Domin aikawa da kudi kai tsaye . 3115484026 ikilima Adam first bank Turo shaidar biya akan wannan 09069080725 sai najiku. Ahankali ya shaƙi ƙamashin jikinta tare da kallon plate da cup dake gabanta wanda da alama akwai abinda taci kafin ta bin ba ba kwanta. A dai-dai lokacin kuma Momy ta fito daga Kitchen idanunta suka sauƙa akan Moddibo dake zaune a hannun kujeran Khausar na zaune gefensa ta manna kanta da kafaɗarsa yayin da hannunsa ɗaya ke bayanta yana shafawa ganin haka yasa Momy saurin komawa kitchen. Ahankali Moddibo ya ɗago kansa tare da kallon ƙofar Falon jin sautin muryan da ko agigin bacci ya farka zai gane ta muryan Hajja Nana. Khausar kuwa cikin yanayin baccin da take ji ta buɗe idanunta ta kalli Hajja Nana sai kuma ta maida idanunta kan Moddibo ahankali ta sake maida idanunta kan Hajja Nana tare da cewa. “Da sassafen nan?Wannan wani irin sammako kika yi?”. Cikin sauri Hajja Nana ta kallesu tare da faɗin. “Toh ƴar nema wato karota ma kike yi?,Ni ina nan tunda kuka zo na gaza bacci ina ta begenki ina son ganin ki shiyasa ana fitowa masallaci nace wa Baffa Liman da Abba su kawoni amma shine kike cewa nayi sammako toh ai ba gidanki naje ba sai ki bari idan gidanki naje kiyi min iyaka da zuwa”. Murmushi Moddibo yayi kana yace. “Toh ki zauna mana kina tsaye”. Kai ta gyaɗa tare da ƙarasawa tsakiyar falon madadin ta zauna kan kushin sai ta zame ƙasa ta zauna tare da kamo ƙafafuwan Khausar ta fara jan yatsun sai kuma ta maida idanunta kan cikinta cikin mamaki ta riƙe haɓa tare da faɗin. “Ohhh Allah mai iko, Allah mai kyauta da daɗi”. Sai kuma ta maida kallonta kan Moddibo. Moddibo kuwa kansa ya ɗan jujjuya kana ya juya ƙwayar idanunsa sai kuma ya sanya hannunsa na dama ya shafa sajensa ya fahimci kallon cikin Khausar yasa take yi masa kallon irin sannu. Jarabebbe mayatacce har ka ɗirka mata ciki? fahimtar hakan yasa ya kauda kansa. Hajja Nana kam ganin yanda ya jujjuya idanunsa yasa ta jinjina kai tare da faɗin. “Hmmm Allah Ubangiji ya shirye ka ke kuma Allah ya sauƙeki lafiya”. Cike da kunya Khausar ta sake manna kanta da kafaɗan Moddibo kana ta motsa laɓɓanta ta furta. “Ameen”. Cikin ɗan ɗaga sautin murya Moddibo yace. “Amin Amin Ameen ya Allah, Allah ya amsa addu'ar ki mun gode da addu'a”. Kallonsa tayi tana mamakin yanda zamani ya sauya sukam a zamaninsu ko kusa da makamancin wannan ba'a yi ga yadda ya wani ƙwaƙumeta a farkon surka. Momy dake kitchen kuwa jiyo kaman muryan Hajja Nana yasa ta leƙo. Ganin tabbas Hajja Nana ce yasa cikin sauri ta fito tare da cewa. “A'a Hajja Nana, dama naji kamar Muryar ki na dan kasa kunne ashe dai ke ɗin ce”. Murmushi Hajja Nana tayi kana tace. “Wallahi fa tun randa mukayi waya kika cemin tazo nake ta son zuwa washe garin ranan kuma Mashin ɗin Abba ya samu matsala shine malam Liman yace na bari sai yasa mai a mota kafin muzo, tunda zai zo ya marabci su Abualeey yanzu ma tare muke suna falo da Lamiɗo”. Kai Momy ta gyada tare da faɗin. “Kai Masha Allah sannun ku da zuwa. Ahankali Moddibo ya juya da naiyyar gaisheta Sai ya ga har ta shige kitchen Momy kuwa already ta gama haɗa breakfast Sultan Cheaps ta soya wanda yaji Vegetables da naman rago mai laushi sai kuma Ƙosai data soya wanda keta tururi wanda Khausar ce tace tana so sai kuma Koko wanda duk zaɓin Khausar ne sai kuma tea dake ƙamshin Kanunfari, Citta Na'a'na'a ta fito dasu. Anutse. Moddibo ya sunkuyar da kansa kana yace. “Momy Barka da safiya". Cike da kulawa tace. “Barka dai Moddibo ka iso?”. Kai ya gyaɗa tare da faɗin. “Eh Momy ina kwana”. “Lafiya lau Alhamdulillah ya gida”. Kallonta ta mayar kan Khausar tace. “Ki tashi ki samu ku abinci kuci”. Juyawa Khausar tayi tare da kallon Momy kana tace. “Momy kinyi min ƙosan?”. Kai Momy ta gyaɗa cike da tarin ƙaunarta tace. “Nayi miki mana ai dole na inyi miki”. Hajja Nana dake cigaba da matsawa Khausar Kafa tayi dariya tare da faɗin. “Aikam dole kiyi mata naga abin na musamman ne”. Baki Khausar ta ɗan tura tare da hararan Hajja Nana kana ta ɗan janye jikinta daga na Moddibo wanda shi har ga Allah yama manta Momy na wajen jin ta ɗan matsa ne yasa ya kalleta. Ganin yana kallonta yasa ta juya mishi ido alamar yaga Momy na nan. Fahimtar hakan yasa ya gyara zama sai kuma ya zame ya zauna akan tattausan Carpet ɗin ya zamana suna fuskantar juna yayin da Hajja Nana ke gefensu. Kulan farkon ta jawo ta buɗe idanunta suka sauƙa akan ƙosan dake zuba wani irin tururi da ƙamshi ajiyar zuciya mai sanyi ta sauƙe irin yanda duk wata mai ciki keji asanda ta samu abinda take so. Flaks din dake gefe ta jawo ta buɗe sai taga tea. Fuska ta kwaɓe kamar za tayi kuka tace. “Momy kunun fa?”. Momy na ƙoƙarin janyo Flaks din gabanta tace. “Gashi nan ki buɗe mana ki gani ke kina da ci da zuci”. Ɗan Murmushi tayi kana ta buɗe tare da cewa. “Kai Momy Ubangiji Allah yabar min ke Allah ya miki Albarka Ubangiji ya miki sakayya da gidan Aljanna”. Murmushi momy tayi tare da faɗin. “Ameen ya Allah Mamana”. Murmushi Hajja Nana dake gefe tayi kana ta kalli Khausar sai kuma ta kalli Momy ahankali tace. “Ubangiji Allah ya rabaku lafiya”. Cikin sanyi Khausar tace. “Ameen”. Moddibo kuwa fuskarsa ɗauke da murmushi ya gyara zama tare da cewa. “Ameen ya Allah aini ina ga yau tukuici na musamman zan banki tunda kika zo kike mana addu'a da fatan Alkhairi ”. Baki Hajja Nana ta taɓe tare da cewa. “Allah yasa dagaske kake”. Cikin tabbatar wa yace. “Dagaske nake mana ai ina ga ke tare zamu tafi dake kiyi ta mana addu'ar nan sannan kiyi ta kula mana da ita”. Ɗan zare idanu Hajja Nana tayi kana ta hararesa tace. “Kunyi ƙarya nikam bazan zama mai aikin kuba kuda gacan innare kuna tare da ita ai magana ta ƙare duk kular da kuke buƙata zaku samu”. Kai ta jinjina kana tayi Murmushi tare da faɗin. “Aikam itama munzo dasu jiya ma take cewa tana son zuwa wajen ki sai Khausar ke cewa ai kema zaki zo shiyasa bata jeba”. Ɗan gyara zama Hajja Nana tayi tare da faɗin. “Aikam toh shikenan”. Khausar kuwa ƙosai ta zuba kusan guda goma kana ta zuba Kokan sai kuma ta zuba wa Moddibo Sultan Cheaps da Perpe Chicken mug ta ɗauka ta haɗa masa tea mai kauri. Hajja Nana ma ƙosan Khausar ta zuba mata tana kallon ƙosan da yayi kyau a ido ta kalli Momy tace. “Ƙosan ya isa haka, asamin shayi sai ahaɗa min da biredi”. Kai Momy ta gyaɗa kana ta miƙe ta ɗauko Bread Mai yanka-yanka Karɓa Hajja Nana tayi ta shiga haɗa breading, ƙosai da tea tana sha. Khausar kuwa Ƙosai da Kokon ta shiga sha cikin tsananin mararin abin. Ahankali ta gutsiri Ƙosan da cikin tsakiyarsa ke ɗauke da diddigin nama kana ta kuma kurɓan kokon daya sha kayan ƙamshi yawun bakinta sai tsinkewa yake saboda yanda ya mata masifar daɗi. Moddibo kam cike da mamaki yake kallon yanda Khausar ke cin ƙosai da Koko tsakaninta da Allah. Hajja Nana dake kai biredi da Ƙosai baki ta kalli Moddibo daya zubawa Khausar idanu yana cew. “Ni mamaki nake bata cin abinci fa agida”. Murmushi Hajja Nana tayi tana kallon yanda Khausar ke shan Koko tsakaninta da Allah tace. “Ai dama haka wani yake in dai yana da ciki baici agidansa amma da zaran yaje unguwa zai ci abinci”. Kansa ya girgiza tare da cewa. “To ai can ko munje gidan Lalla Khadijah bata cin abinci amma kinga tunda muka zo nan cin abinci fa takeyi”. Momy dake fita zata kaiwa Abba da Man Liman nasu tayi Murmushi tare da faɗin. “Sosai ma kam tunda aka zo nan abinci take ci babu kama hannun yaro taci ta ƙara ɗayan daren ma munyi hira mun gama tace min yunwa take ji sai da naje na dama mata Quaker oats tasha kafin tayi bacci”. Cike da farin Moddibo ke sakin murmushi yana kallon Khausar dake ɗan Cunno baki gaba Momy kuwa idanunta akan Hajja Nana ta cigaba da cewa. “Sannan da safe kafin ta kwanta plate da kuka zo kuka samu shima indomei taci tasha tea kafin ta kwanta tayi bacci anan gashi yanzu ma tana ta ɗurawa”. Langwaɓar da kai Khausar tayi tare da faɗin. “Toh Momy yunwa nake ji na daɗe bana cin abinci fa”. Dariya Momy tayi kana tace. “Keee dama haka kike da cin abinci nayi mamaki ma da akace wai ciki ya hanaki cin abinci. Don banyi tunanin akwai abinda zai hana ki cin abinci ba, tunda ke ciwo ma baya hana ki cin abinci”. Kanta ta sunkuyar ƙasa ta cigaba da cin ƙosanta kallonta Moddibo yayi ganin ta gama cinye duk ƙosan hannu tasa ta sake janyo kular ɗan ware idanunsa yayi tare da faɗin. “Minha bazai Miki yawa ba?”. Kallonsa tayi sai kuma ta girgiza kai tace. “Um-um kaɗan zan ƙara naji cikina ya ƙoshi amma bakina bai gaji dashi ba”. Yana rufe kulan yace. “Toh ki bari sai anjima”. Marairaice fuska tayi ganin haka yasa Momy cewa. “Ki bari na rage Miki ƙullu a fridge idan kina so anjima zan sake soya miki ”. Gyatsa tayi kana ta gyaɗa kai tare da faɗin. “Toh shikenan”. Ta ida maganar tana jingina bayanta da jikin kujera. Ahankali Moddibo ya matsa kusa da kujeran da take ya ɗan jawota jikinsa tare da cewa. “Zo, Zo zonan kada ki kwanta, ki ɗan zauna tukun mu samu abincin yabi jikinki”. Ya faɗa yana manna kanta da kafaɗarsa yayin da hannunsa ɗaya ke kan cikinta yana shafawa shi kuma yana cigaba da cin abinci da hannunsa na dama. Ahaka suka gama cin abinci suna taɓa hira jefi-jefi. Suna gama cin abinci Momy ta shigo idanunta akan Khausar tace. “Toh tashi ki tattare wurin”. Kai ta gyaɗa tare da faɗin. “Toh”. Kana ta yunƙura zata miƙe. Ahankali Moddibo ya kalli Momy kana yace. “Momy bari na tattare”. Ɗan ware idanu Momy tayi kana tace. “Ta isa tana zaune ka tattare mata kwanika”. Cikin sanyi yace. “Momy toh ta gaji ne kuma ta cika cikinta da yawa bata son motsi”. Kai Momy ta girgiza tare da faɗin. “Aikuwa dole tayi motsi maza tashi ki tattare su”. Ta ƙare maganar tana kallon Khausar. Hajja Nana dake kallonsu ta ɗan taɓe baki tace. “Kai dai kai dai kam wannan akwai ka da tsirfa iri-iri yo in Mai ciki bata motsa jiki ba mai za tayi!? Ko kaine zakayi mata naƙudar”. Ɗan hararan Hajja Nana Khausar tayi sai kuma ta kalli Momy tare da cewa. “Nima fa bance yayi ba shi yace zaiyi”. Ta ƙarashe maganar tana kwashe kwanukan ta kai kitchen kana ta dawo ta zauna bayan ta dawo sun zauna Momy suka gaisa da Hajja Nana bayan sun gaisa suna cigaba da hira. Asiya ta shigo cikin sassarfa kamar an jefota cikin yanayin tashin hankali tace. “Momy dan Allah kizo kiga Ummana baki ɗaya yau tunda gari ya waye atsaye take bata zauna ba kona minti ɗaya fa gaba ɗaya yau jikinta ya tashi!”. Da damuwa Momy ta miƙe cikin sauri tabi bayan Asiya suka nufi Side ɗin Hajiya Bunayya. Khausar kam ahankali ta juya ta kalli Hajja Nana itama Hajja Nana kallonta tayi sai kuma ta juya ta kalli Moddibo cikin sanyi tace. “Yah Mu'allim nace maka batun jikin Umma da Amina ayi musu addu'a sannan ka turo Dr Jameel yazo ya duba su amma Yah Mu'allim har yanzu baka ce komai akai ba”. Ahankali Moddibo ya dafe kansa da hannunsa na hagu yace. “Wallahi na manta, koyie haƙuri mantawa na keyi Minha”. Kamar za tayi kuka tace. “Yanzu fa kaji abinda Asiya tace”. Hajja Nana da batasan meke faruwa ba ta kalli Khausar tare da cewa. “Meke damunta?”. Cikin rauni Khausar tayi ƙasa da kanta kana ta kwashe labarin duk yanda ta faɗawa Moddibo ta faɗawa Hajja Nana. Ajiyar zuciya Hajja Nana ta sauƙe tare da jinjina kanta tace. “Ai dama haka duniya take idan kace tukunyar wani bazai tafasa ba naka ko ɗumi bazai yiba arayuwa ka taka ahankali kada ka shiga hurumin da bana kaba duk lokacin daka shiga hurumin da bana kaba sai ka samu abinda zai shiga huruminka”. Araunane Khausar ta risinar da kanta Hajja Nana kuwa cikin jimami ta cigaba da faɗin. “Ya hanaka zaune ya hana ka tsaye yanzu wa gari ya waya ita wancan ta haukace ƴarta ta zama mai wari ita gata nan ƴarta ta zama wata halitta daban gashi ita kuma yanzu ƴarta tazo tana cewa tunda gari ya waye bata zauna ba ta isa ta zauna tsutsotsi na cinta”. Ahankali Khausar ta rausayar da kanta hawaye na kwaranyowa daga idanunta tace. “Hajja Nana Ni tausayi suke bani musamman Amina tana bani tausayi gaba ɗaya sai kinga yanda ta dawo ita ma Umman na ban tausayi bata isa ta zauna bafa Hajja Nana wlh ko jiya data shigo nan mu gaisa tsutsotsin har bin ƙafarta suke yi sai in taji kiga tana ta buge-bugen ƙafart kamar itama so suke su haukatata gaba ɗaya ”. Cikin sauƙe numfashi Hajja Nana ta gyara zama tare da cewa. “Dama haka duniya take”. Still idanunta na zubda hawaye ta kalli Moddibo tare da faɗin. “Ni dai ina so a samar mata magani ayi mata addu'a ane ma mata sauƙi awajen Allah”. Acan Side ɗin Hajiya Bunayya kuwa Momy na shiga ta sameta atsaye sai bubbuga ƙafa take saboda yanda tsutsotsin ke cinta yayin da Amina ke gefenta tana zazzaro harshenta waje. Da sauri Momy ta ƙarasa wajenta ta riƙe hannunta kana tace. “Yaya ki zauna mana”. Kai ta girgiza cikin tarin damuwa tace. “Ina Momyn Khausar bazan iya zamaba idan na zauna ji nake har cikin hanjina tsutsotsin suke ci suna gigitani na rasa yanda zanyi na cutar dake arayuwa gashi nima yanzu na samu abinda yake cutar dani na rasa yanda zanyi a rayuwata”. Cike da tarin tausayinta Momy ta girgiza kai tare da faɗin. “Bakomai in sha Allah zaki samu lafiya”. Kai ta girgiza tana cigaba da buga ƙafarta kana tace. “A'a nikam nasan na nemowa kaina abinda yafi ƙarfina Momyn Khausar ki yafe min ki cewa Khausar ta yafe min”. Cikin sauri momy ta juya tare da faɗin. “Ki kwantar da hankalinki Yaya bari naje na kira Lamiɗo yazo ya kai ki asibiti ”. Ta ida maganar tare da nufar Side ɗin Lamiɗo. Cikin kiɗima tace. “Wallahi Lamiɗo Yaya ce babu lafiya gaba ɗaya ta kasa zaune ta kasa tsaye ta kiɗime ta gigice ga Amina ma ita ma baki ɗaya yau jikinta nata abin ya sake motsa wa”. Anutse Lamiɗo ya juya ya kalleta kana yace. “Hmmm shine baki ɗaya kika gigice haka?, Mutanen dake suka cutar Sakayyah ce ta sauƙa akan su shine zaki gigice haka?”. Kai ta girgiza kana tace. “Nikam basu cutar dani ba kuma koda sun cutar dani na yafe musu Duniya da lahira”. Gyaran murya Man Liman yayi tare da cewa. “Wayene ba lafiya?”. Zama Momy tayi muryanta ɗauke da damuwa tace. “Uwar gidata ce babu lafiya Baffa Liman jinyan kuma ya kiɗima mu”. Kai ya jinjina yace. “Toh kunje asibiti ne?”. Kai ta gyaɗa tare da cewa. “Munje asibiti. Likitocin da kansu sunce bana asibitinba ne na gidane sai kaga yarinyar mijin da aka Aura mata ne bisa duk kan alamu tsafi yayi da ita ita kuma Yayan dai baza ka tantance ba”. Zama Lamiɗo ya gyara kana yace. “Ki daina cewa ba za'a tantance ba ki fito kice sihiri tayi Miki keda Khausar ya dawo kanta haka zaki faɗa masa ki fito fili ki faɗa masa abinda ta miki Saboda ko baki faɗa ba Allah ya sani kuma taga Sakayyar abinda ta aikata”. Kai Momy ke girgiza masa shikam cikin tsanar Muguwar ɗabi'ar Hajiya Bunayya ya cigaba da cewa. “Ita kuma Amina dama ai ƙulle ƙulle sukayi Ni kaina tsoron Al'amarin Naseer nake yi suka nuna dole-dole sai Naseer ya auri Amina yaje yayi tsafi da ita ya dawo da ita me zance musu su suka jawa kansu jiki magayi. Ai dama sai dana ce duk abinda ya faru babu Ni aciki ba hannuna bare ƙafata aciki”. Cike da nutsuwa Man Liman ya kalli lamiɗo tare da faɗin. “A'a Lamiɗo baza ayi haka ba ai ita rayuwa rai da lafiya ita ake bibiya ake duban Lamarinsu kuma komai lalacewan Amina jinin kace tsatsonka ce kana Hajiya Bunayya komai lalacewan ta Matarka ce Uwar ƴaƴan kace”. Da sauri ya girgiza kai yace. “Uwar ƴaƴana ne babu yanda na iya amma Ni na saketa na saki Hajiya Bunayya tun wata ɗaya daya wuce Ni yanzu babu alaƙa tsakanina da ita na barta dai ta sauna a gida nane albarkacin Asiya da Sulaiman, taje can rayuwarta da ban rayuwata da ban”. Mommy kam kallonsa take cike da matsanancin mamaki jin cewa ya saki Hajiya Bunayya ko kaɗan batayi farin cikin jin haka ba sai ma damuwarta ɗaya karu. Man Liman kuwa cike da nutsuwa yace. “Ai baza ayi haka ba yanzu idan babu matsala kayi min jagora muje in gansu Babu abinda yafi ƙarfin Ubangiji zanyi musu abinda Allah Ubangiji ya sanar dani”. Kai Lamiɗo ya girgiza kana yace. “Baffa Liman ka barsu baka san su bane” Cikin rauni Momy ta kallesa kana tace. “Dan Allah Lamiɗo kayi haƙuri ka taushi zuciyarka”. Ahankali Lamiɗo ya ɗago ya kalleta kana ta girgiza kai ganin yanda ta tashi hankalinta yace. “Kina jifa da bakinta tace ita tayi sihiri ta kashe Ramadan ”. Cikin sauri Momy tace. “Innalillahi wa'inna alaihi raji'un yanzu kai Lamiɗo sai ka yarda ita tayi sihiri ta kashe Ramadan?”. Kai ya gyaɗa tare da faɗin. “Ehem ita ta faɗa da bakinta ai ”. Cikin sauƙe numfashi ta kalli Man Liman ta kalli Lamiɗo tace. “Amma ka manta tun lokacin da Ramadan yayi accident an gaya mana cewa yana da brein Cancer tun lokacin daya karye ka manta cewa Likita ya faɗa mana kuma ko kai kanka kasan cewa ciwon kan da Ramadan yayi dare ɗayane sannan kuma an tabbatar mana da cewa ciwon ne ya kashe sa”. Kai Abba dake gefe ya jinjina Momy kuwa cikin rauni ta cigaba da faɗin. “Ko Sihiri da tace tayi Ni banyi Imani Sihirinta da tayi shi ya kashe min ɗana ba imma shine ya kashesa tsakaninta da Ubangijinta kuma ko cikina da take cewa ita tayi sihiri ya zube wallahi bata isa tayi Sihiri cikina ya zube ba face dama Allah ya ƙadarta waɗanan cikin bazan haifesu su taka doron ƙasa ba, shine kaɗai amma Ni bata isa ta kashe min ɗa ba bata isa zubar min da ciki ba wa'adin sa ne yayi”. Cikin sanyi ta ƙare maganar tana mai zubda hawaye ta cigaba da cewa. “Kuma ai ita in tayi zalunci mu bai kamata mu saka mata da zaluncin ba sai mu barta da Allah shi yasa Sakayyar da zaiyi mana”. Jikin Lamiɗo ne yayi sanyi jin abinda ta faɗa sai kuma ya kalli Man Liman dake cewa. “Kayi haƙuri muje mu dubata”. Ahankali Yah Abba ya gyara zamansa tare dasa baki acikin tattaunawar su yace. “Ayyah Lamiɗo ayi haƙuri adubasu ai rai da lafiya ake dubawa”. Kai ya gyada tare da cewa. “Shikenan”. Momy ce ta fara miƙewa ta fita Lamiɗo na biye da ita sai kuma Man Liman da Yah Abba Abaya. Suna shiga falon Hajiya Bunayya suka sameta atsaye sai bubbuga ƙafanta take tana tsalle ga ƴan mili-milin tsutsotsin nan na bin ƙafafunta yayin da Amina ke kwance kan 3sitter tana karkata kanta tare da zaro harshenta Man Liman na ganinta yace. “Innalillahi wa'inna alaihi raji'un”. Juyawa yayi ya kalli Hajiya Bunayya kana ya kalli Amina sai kuma ya sake juyawa ya kalli Momy tare da faɗin. “Momyn Khausar akwai Zam-zam?”. Kai ta gyaɗa tace. “Eh akwai”. Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da faɗin. “Toh ki temako min dashi”. Da sauri tace. “Toh”. Kana cikin hanzari taje ta dauko Zam-zam Babban gora ta kawo karɓa yayi kana yace. “Allah yasa kuna da ganyen Magarya ko ɗanye ko bushesh-she amma idan akwai ɗanye anfi buƙatar shi”. Ajiyar zuciya Momy ta sauke kana tace. “Alhamdulillah akwai ɗanye abayan window na adan kwai bishiyarsa”. Cikin sauke numfashi yace. “Toh Alhamdulillah aje atsinko akawo min”. Cikin sauri ta juya taje ta tsinko ganyen Magarya ta kawo masa tana kawowa ya karɓa kallon Asiya dake kuka yayi kana yace. “Asiya idan akwai sabon roba mai haske ki kawo min”. Cikin sauri tace. “Toh”. Kana ta shiga kitchen ta ɗauko roba mai ɗan girma karɓa yayi yasa rabin Zam-zam ɗin aciki zama yayi ya Tofa Ayatul Shifaa gaba ɗaya aciki idan ya gama tofawa yasa ganyen Magarya guda bakwai aciki kallon Asiya yayi yace ta kawo masa karamin kofi cikin minti ɗaya ta kawo kofin ruwan addu'ar ya ɗebo ya bawa Amina yace. “Karɓi kishi”. Akarkace Amina ta miƙe tare da kauda kai gefe. Cikin tausasa murya ya sake cewa. “Karɓi kisha”. Still juyawa tayi alamar bazata shaba. Kallon Lamiɗo Man Liman yayi tare da cewa. ”A danneta Abata tasha”. Cikin takaici Lamiɗo ya girgiza kai kana yace. “Ta karɓa tasha sai adanneta ai jiki magayi lafiyarta ne ko lafiyanmu”. Man Liman na gyara alkyabbarsa yace. “Ayi haƙuri Abata ai sihirin da aka yi mata ne an haɗa mai tafiya da siffar maciji bayin kanta bane bazata sha ɗinba”. Cikin rauni Asiya ta kalli Lamiɗo tace. “Ayyah Abba don Allah Abata ”. Ta ƙare maganar tare da karban kofin ta matsa kusa da Amina. Amina na ƙoƙarin ture kofin Lamiɗo yayi saurin kama hannayenta kana ya rike kanta Asiya ta ɗura mata ruwan Tofi da ganyen Magaryan tasha mai ɗan yawa amma sauran ya zube. Ahankali ta fara yin gyatsa lokaci ɗaya jikinta ya saki ta koma ta kwanta kan kujeran atake bacci ya ɗauke ta. Tana yin Bacci Man Liman ya sauƙe ajiyar zuciya yace. “Alhamdulillah tunda har tayi bacci in Allah yaso ya yarda zata rabu da abinda ke tare da ita amma wannan yaron da kuka Aura mata ya cika taƙadirin Jahili makirin mutum mushirki”. Kai Lamiɗo ya girgiza tare kana yace. “Su suka siyawa kansu”. Cikin kuka da nadama Hajiya Bunayya ta durƙusa gaban Man Liman tace. “Dan Allah nima ataimaka min mana abani abinda zansha inji sauƙi atemaka min”. Kai Man Liman ya gyada yace. “Ba matsala in Sha Allahu”. Sai Kuma ya tsiyayi ruwan Zam-zam daban akofi yasa ganyen Magarya aciki yayi mata Tofi kana ya bata yace ta taune ganyen Magarya Zam-zam ɗin shi kai ta gyaɗa kana tayi kamar yanda yace tana gama yi taji kamar fitsari take ji cikin sauri ta nufi bedroom ɗin ta ta wuce Bathroom. Man Liman kuwa kallon Asiya yayi tare da cewa. “Idan ta farka wannan ruwan daya rage ta samu tayi wanka dashi awajen da babu najasa”. Kai Asiya ta gyaɗa tare da faɗin. “Toh In Sha Allahu”. Yana kallon Aminan dake bacci yace. “Kuma in sha Allah akwai tofin da zan mata amma da Zam-zam ɗin ne sai dai zai ɗauke Ni tsawon kwana biyu in sha Allah idan anyi shi in zamu zo daurin Auren su Jameelu zamu zo dashi da izinin Ubangiji zata samu sauki”. Kai Asiya ta gyaɗa kafin cikin sanyi tace “Umman mufa?”. Ɗan gyara tsayuwar sa yayi kana yace. “Toh bamu san mai Ubangiji zaiyi ba amma itama in sha Allah muna kyautata zaton Allah zai bata lafiya”. Cikin sanyi da ɗan jin nutsuwa tace. “Allah yasa mun gode”. Nan Lamiɗo da Man Liman da Yah Abba suka fita. Momy kuwa cikin jin sassauci tace. “Alhamdulillah Amina ta samu sauki”. Kai Asiya ta gyaɗa. Momy kuwa ganin Hajiya Bunayya ta tafi daki yasa tayi zaton sauki ta samu tana kallon Asiya tace. “Barin tafi ina da baƙi kinsan Hajja Nana nacan” Cikin ƙaunarta da sake jinjina kyawun halinta Asiya tace. “Toh Mun gode”. Lamiɗo Man Liman da Yah Abba kuwa Side ɗin Lamiɗo suka koma... Momy na shiga falon Moddibo ya mike kana yace. “Toh Momy Ni zan wuce”. Kai ta gyaɗa tare da cewa. “Toh mun gode”. Khausar kuwa cikin sanyi ta kallesa kana tace. “Dan Allah Yah Mu'allim kada ka manta Dr Jameel yazo ya duba Umma”. Kai ya gyaɗa kana yace. “In sha Allahu bazan manta ba Minha baza ki rakani bane”. Kanta ta langwaɓar tare da ƙyafta ƙwayar idanunta ciki nasa sai kuma ta daura hannunta na dama kan ƙafarta tace. “Ayyah kayi haƙuri baki ɗaya Ƙafafuna rawa suke”. Lallausan murmushi ya sakar mata tare da motsa laɓɓansa cikin ƙasa da murya yanda ita kaɗai zata ji yace. “Toh sai nazo da daddare”. Kallonsa tayi da sauri tace. “Me kuma za kazo yi da daddare?”. Yana ɗan lumshe Idanunsa cikin nata yace. “Bakyaso in kawo Dr Jameel ɗin ne?”. Ahankali tace. “Ina so mana”. Kai ya gyaɗa yana gyara tsayuwar sa yace. “Toh idan nazo kuma ki shirya zamu tafi tare”. Langwaɓar da kai tayi tare da faɗin. “Ayyah Yah Mu'allim ka barni in kwana mana”. Kai ya girgiza tare da faɗin. “Bazan iya ba dole fa yau zamu tafi muje mu kwana tare”. Sake langwaɓar da kai tayi tare da marairaice fuska tace. “Dan Allah Yah Mu'allim ”. Cikin sauri ya ɗan tsuke fuska yace. “Kada ma ki haɗani da Allah ki cuceni”. Shiru tayi ganin kallon da Momy ke mata me nuni da alamun gargaɗi. Shi kuwa Modibbo Hajja Nana ya kalla jin tana cewa. “Idan Allah ya kaimu gobe ko jibi in ba matsala zamu tafi jahar Gombe muje kaga asalin masarautar su Khausar kuna mahaifarta”. Cikin murmushi Khausar tace. “Gobe dai zaifi dan Allah Yan Mu'allim kace gobe”. Kai ya jinjina cike da jin yana son yaje yaga Masarautar su yace. “Allah ya kaimu goben in ya samu in kuma bai samuba sai jibi, za dai muje kafin ayi bikin”. Amin suka amsa kana shi kuma ya juya fita. Yana isa gida kai tsaye Side ɗin su Dr Jameel ya shiga nan yasa masu suna ta maganar abinda za'a yi kasancewar yau saura kwana huɗu ne ɗaurin Auren kasancewar yau ya kasance Litinin. Talata Laraba Alhamis juma'a za'a ɗaura Auren. Nan dai suka cigaba da hiransu. Acan gidansu Asma'u ma shirye shiryen biki ya kankama. Alhamdulillah washe gare suka tafi Gombe. Harda Dr Jameel da Lallai Khadijah da Rahma harda Didi da Innayi da Galadima suka je dan ya gabatar da masarautar su. Kwana su biyu suka dawo Gembilan. Alhamdulillah zuwa yanzu Amina ta fara samun sauyi dan yanzu ta daina zare harshenta. Hajia Bunayya kuwa abu kam sai gaba gaba. Samira Sani kuwa jin Amina ta samu sauƙine da yadda akayi yasa itama ta zo ta kokawa Momyn kuma Alhamdulillah yau dasuka dawo daga Gombe. Man Liman yayi mata tofi, ya bata ya bawa Amina. Alhamdulillah cikin kuɗirar Ubangiji kafin zuwa la'asar Samira ta fahimci zuban ruwan nan ya ragu sosai. Amina kuwa sosai itama mummurɗewa da jikinta keyi ya fara raguwa. Nan ya sake yi musu tofi cikin zam-zam ɗin na wasu keɓantattun ayoyi da sauri kamar haka. *Al-araf ayata 117, 118, 119, 120, 121 da kuma 122. Sai Suratul Yunus daga ayata 79, 80, 81, 82, Sai kuma suratul Ta-ha aya ta 65 66, 67, 68, 69, 70, Sai kuma suratul al-Kafurune gaba ɗayanta, da kuma suratul al-ikhlas dukanta sai suratul al-falaq itama dua da kuma suratul An-nas itama dukanta da forko zaki samu zam-zam ki zuba mai yawa a tsabtacecen mazubi ko roba ko kwarya, ki tabbatar zam-zam ɗin zai ishe ki sha da kuma yin wanka, sai zuba a robar kana kisa kanyen magariyar guda bakwai an fison ɗanye Amman busheshenma ba matsala zaki daka guda bakwai in ɗanyen nema ki daka bakwai, sai ki zuba a Zam-zam ɗin kana ki karanta ayoyin Alkur'ani mai tsarkin dana lissafa Miki da surorin ki ɗan motsashi zakiga ya ɗan buga kumfa sai ki ɗiba a cup wanda zakisha ki ƙoshi kuyi gyatsa, sai ki zauna bisa yaƙini da niyar Allah ya yaye Miki matsalarki ko wacce iri yace Sihiri, ko tsafi, Sammu, ko kambun baka, ko cutar da ba'a gane kantaba ko sharrin iska. Kisha koyi hamdala kana ki ɗauki sauran na cikin robar ki samu sarkakekken wurin da babu najasa kiyi niya da duk matsalarki kiyi wanka. Wlh da izinin Ubangiji zakiji sauƙi ki samu sauyi anaso na farko dai kiyishi da Zam-zam inda hali duk bayan wata shida ko shekara ɗaya kiyi kiyiwa yaranki da mijinki dan makarine mai girma in ba hali saboda tsadar da Zam-zam keyi in kinyi na forkon da Zam-zam to na biyu kiyi da ruwan sama na uku da duk ruwan da ya sauwaƙa gareki, inda hali ko yaushe da Zam-zam in ba hali ayi na forkon da Zam-zam in bai samuba ayi da ruwan sama na roƙon da na biyun da na ukun, kiyishi maƙo maƙo ko wata wata ana dai son duk bayan wata shida ko shekara ɗaya kiyi, yar uwa ko ɗanki, ƴarki mijinki ƙanwarki ƴaƴan yar uwa ki ko ɗan uwa duk inda kukaga yaro ko yarinya sun cika rashin ji gagara rawan kai gardama da alamun kwaucewa hanya kuyi masu yanada matuƙar fa'ida da falala, sadakace fisabilillahi idan kinji daɗinshi kiyi niya kiyiwa Mahaifiyata Fatima Dedde na ƙu'huwa ƙafa uku da fatan Allah ya jiƙanta ya kai haske da ni'ima Qabarinta. Ni kuma inada wata buƙata mai girma da falala da daraja a wurin Allah kuyi min addu'a kisa yaranki suyi min addu'a kice su roƙawa Aysha Aliyu Muhammad Garkuwa Allah ya biya mata buƙatarta akan alkhairi, ya raya mata ƴaƴanta Muhammad Jabeer da Maimuna Ikhram da Ibraahim ya shirye su ya basu ilimi mai amfani da albarka yasa su zama abin alfahari ga Musulunci da Musulmai mazan ya basu mata na gari da zuraya ɗaiyi ba, macen ya bata miji na gari da zuri'a ɗaiyiba, kana Allah ya bani wasu ƴaƴan masu albarka da nisan kwana tagwaye inyiwa Deddena takwara da Babana in samu Aliyu Haiydar da Fatima Khausar in samu auta A'isha takwarar kakata mafi soyuwa* Man Lima da Hajja Nana ma bayan sunyi sallar la'asar da Baffa Liman da Yah Abba suka kama hanyar komawa Jauro Yaya. Acan ɓangaren Hajiya Bunayya ma tunda tasha wannan ruwan tofin sai tsutsotsin suka yawaita fita yayin da suke cinta da gasken gaske sai dai tana shiga ruwan ɗumi zai lafa amma bazai wuce awa biyu zuwa uku ba zai sake dawowa haka tayi wannan yinin ranan zunibi da sakayyan aikinta na bibiyarta. Daddare bayan sallar Isha'i Moddibo ne da Dr Jameel zaune afalon Hajiya Bunayya tana zaune Sai murtsukuku take yi akan kujeran jin yanda tsutsotsin ke cinta yayin da Amina ke zaune gefenta bisa duk kan alamu Alhamdulillah ta fara samun sauƙi har nishinma duk ta daina . Anutse Dr Jameel ya kalli Hajiya Bunayya kana yace. “Akwai tests ɗin da za'a Miki. Sai kiyi ƙoƙari kije asibitu aduba ki acan”. Cikin sanyi tace . “Nagode Nagode Dr Jameel Allah ya saka da Alkhairi ”. Kai ya gyaɗa tare da cewa. “Bakomai”. Kana suka miƙe suka fita dai-dai lokacin kuma Dr Zakariyya da Asiya ne zaune amota suna hira fitowa su Dr Jameel ne yasa Asiya yiwa Dr Zakariyya sallama ta fita kana Dr Jameel ya shiga Motar. Moddibo kuwa bayan Khausar dake shiga Side ɗin Momy ya nufa yana shiga falon yaga ba kowa sai Raudat dake kallon Catoon yace. “Raudy ina Addah Khausy?”. Hankalinta na kan kallon tace. “Tana ɗakinta”. Kai ya gyaɗa tare da cewa. “Momy fa?”. Still idanunta na kan tv tace. “Tana gidan Ummin Jameel Yah Haiydar ya kaita”. Kai ya gyaɗa kana ya shiga ɗakin Khausar zaune ya sameta agaban Weldrop ɗin ta gabanta littafaine tana ta duddubawa. Da mamaki ta kallesa kana tace. “Yah Mu'allim har nan kuma?”. Kai ya gyaɗa kana yace. “Eh ai gidan mune”. Kai ta gyaɗa hannunta na kan littafin tace. “Eh nasani ai yanzu in Momy tazo ta same mufa?”. Murmushi yayi tare da shafa sajensa kana yace. “Eh dai-dai kenan idan Momy tazo ta ganni zata san ina buƙatar matata zata kora min ke mu tafi tun da ke yanzu kin iya gardama da taurin kai ”. Kanta ta langwaɓar tare da cewa. “Ayyah Yah Mu'allim ba gardama da taurin kai bane kaga idan mun koma kafin na sake ganin Momy fa zai daɗe ”. Yana gyara zamansa gefenta yace. “Amma Ni bakya jin tausayina tunda muka zo fa kike bari na ina rayuwa Ni kadai kamar Maraya Babu kowa kusa dani”. Kallonsa tayi tace. “Yah Mu'allim aima mun kusa komawa dai kayi haƙuri kwana nawa ya rage”. Ta ƙare maganar tana cigaba da dudduba littattafan sai kuma ta ajiyesu ta gefensa kallon yanda ta hargitsa Littattafan yayi kana yace. “Me kike nema?”. Tana cigaba da abinda take tace. “Wani littafi na nake nema?”. Da mamaki yace. “Littafi kuma?”. Kai ta gyaɗa tare da cewa. “Eh”. Kamar mai raɗa ya sake matsawa kusa da ita yace. “Toh me zakiyi dashi?”. Kanta na kan tulin littattafan tace. “Wani abu ne aciki?". Da mamaki yace. “Wani abu ne kuma aciki?,ki bari gobe sai ki duba”. Kai ta girgiza tare da faɗin. “Ina so ne in tabbatar yana nan ko baya nan saboda da nazo na samu Raudat tana wasa takarduna da jakar makarantana ta bubbuɗe min ban sani ba ko ta jefar min da littafin ”. Cikin mamakin yanda take neman littafin yace “Toh littafin na wani Subjects ne?”. Tana ɗan tura baki tace. “Um-um fa littafin bana karatu bane?”. Yana ɗan ƙara matsota yace. “Ikon Allah toh littafin na menene?”. Ya ƙare maganar yana dudduba littattafan data tutturo gefensa yayin da take sake zaro na cikin jakar ganin basu cikine yasa ta jawo durowan ƙasan Weldrop ɗin tare da cewa. ”Toh ban sani ba bari in duba ko suna cikin nan ne”. Dai-dai lokacin yaga wani note Book An rubuta *SPECIAL MAN* da manyan baƙi Aransa ya maimaita Special Man ahankali ya jawo littafin yana ɗan jujjuyawa Khausar kuwa baki ɗaya hankalin ta na cikin durowan Weldrop ɗin. Ahankali ya buɗe shafin farko na littafin. ga mamakinsa sai yaga Drawing ɗin hoton fuskarsa ne rauɗau ba abinda aka bari har sajensa. Cikin tarin wani irin mamaki al,ajabi da kuma kaɗuwa ya kalli gefen shafin. A gefen kuwa Drawing ɗin fuskarsa ne acikin aji hannunsa na kan Black board kamar yana rubutu cikin sauri ya kalli rubutun da akayi da kalo wanda akayi musu design yanda ya kasance na musamman haka sunansa ya kasance na Musamman _Aliyu Youseef Mohammed Mouley (Moddibo)_ da mamaki ya kalli inda aka rubuta sunansa anyi zanen ❤️ sai kuma ya maida idanunsa inda akayi Drawing ɗin fuskarsa yaga date and time ɗin da akayi rubutun Drawings ɗin. Idanunsa ya jujjuya ya kalleta amma baki ɗaya hankalinta na kan tarin himilin sauran littafan. Kallonsa ya mayar kan date ɗin idan har baiyi kuskure ba toh shekaru huɗu kenan ranan dasu Khausar suka fara zuwa SS3 cikin mamaki da wani irin yanayi ya buɗe page ɗin gaba sai yaga Drawing ɗin Fuskarsa ne amma ba'a fitar da fuskan sosai ba sai sajensa aƙasan ta rubuta. _One's if I remember your face, my actionable will be change to cool, is your Breed brightly my heart always yo be sunshine , i really love you with deep voice. Uncle Aliyu Youssef Mouldy (Modibbo)_ Ahankali ya motsa laɓɓansa ya furta. “Ya salam”. Wani irin amintaccen numfashi ya fesar saboda jin kalaman suna Barka duk kan lakar jikinsa. Fahimtar da yayi baki ɗaya littafin kamar akansa yake magana haka nan yaji wani abu yana sauƙa tun daga ƙwaƙwalwar kansa har zuwa babban yatsarsa a iya shafi biyu daya buɗe ya fuskanci gaba ɗaya Khausar ta rayune da soyayyar shi acikin zuciyarta shi kansa baisan meyesa ba ya dai tsinci kansa da naɗe takardan yasa cikin aljihunsa. tare juyawa yayi mata wani amintaccen rugguma yana mai kallonta yace. “Wai wani littafi kike nema ne?” Batare data kallesa ba tace. “Wani Littafina ne na musamman, nasan da wuya in Raudat bata ɓatar min da shiba dan haka taɓatar min da ɗan uwanshi da Nai ta rubutawa tun daga JSS one to 3”. Kai ya gyaɗa kana yace. “Ko dai Diary kine?”. Kai ta gyaɗa kana tace. “Kusan haka amma shi babban littafine ai yama fi Diary daraja awajena”. Gira daya ya dage tare da faɗin. “Toh tashi mu tafi da safe sai muzo na tayaki dubawa”. Kai ta langwaɓar kana tace. “Allah ina so ba mamaki yanzu Raudat ta ɓatar min dashi. In dai ta baddashi wlh sai na daketa dan yana tunamin abubuwa da yawa a rayuwata”. Kai ya girgiza tare da faɗin. “In sha Allah ma bai ɓata ba kada ki damu kizo mu tafi da safe za'a zo mu duba”. Ya ƙare maganar da ƙaguwar so yake ya ga su ƙeɓe daga shi sai ita. Kai ta girgiza tana cigaba da hautsina littattafan tace. “Um-um.ni dai ina son gani ”. Fuska ya tsuke tare da cewa. “Mu tafi nace ko?”. Ganin yanda ya tsuke fuska yasa ta gyaɗa kai tare da faɗin. “Toh”. Kana tattare littafan ta mayar cikin drawer. Hannunta ya jawo ya riƙe kana ya kalli gyalen jikinta ganin babu laifi yasa yace. “Mu tafi toh”. Suna fita motarsu Dr Jameel na fita agidan motarsu suka shiga kana suka tafi gida. Suna shiga Falonsu ya rufe ƙofan kana ya ɓalle botir ɗin wuyan rigarsa ya zare ya ajiye kana ya jawota jikinsa ya rungumeta ajikinsa cikin sanyi ya kai bakinsa saitin kunnenta kana ya shiga raɗa mata abinda ta rubuta yana cewa. “ _One's if I remember your face, my actionable will be change to cool, is your Breed brightly my heart always you be sunshine , i really love you with deep voice Aliyu Youssef Mouldy (Modibbo)_” Cikin sauri ta ɗaga ido ta kallesa tare da wani irin fiddo idanun duka tamkar zasu faɗo ƙasa, ido ɗaya ya kashe mata kana yace. “Tukuocin soyayyar da kike min nake son baki a daren yau”. Baki ta tura tare da kwaɓe fuska kana tace. “Waye ɗin?”. Ido ya kashe mata tare da cewa. “Keɗin mana”. Ɗan ware idanunta tayi akansa kana tace. “Kamarya tukuicin soyayyar da nake maka kuma?”. Ta ƙare maganar cikin kunya da son waskewa. Cikin wani irin yanayi yace. “Shekara nawa kika yi kina dakon soyayyata azuciyarki?”. Kallonsa tayi da mamaki sai kuma ta lumshe Idanunta tace. “Kamarya kuma nayi dakon soyayyar ka azuciyata?”. Murmushi yayi tare da cewa. “Littafin da kike nema yana hannuna fa?” Still kallonsa tayi tace. “Wani littafi kuma?”. Ɗan murmushi yayi kana ya hura mata sanyayyar iskan bakinsa yace. “Littafinki da kike nema”. Littafin ya zaro acikin rigarsa ya nuna mata cikin mamaki ta kallesa kafin tace. “Yaushe ka ganshi?”. Dariya yayi tare da cewa. “Tun ɗazu har na karanta shi ma”. Da sauri ta kife kanta akan ƙirjinsa cike da kunya murmushi yayi kana ya shiga tura yatsunsa ƙasan ƙafarta jin haka yasa ta ɗaura ƙafanta kan rumfar ƙafansa. A hankali ya fara tafiya da ita har suka isa bedroom. Cikin sanyi ya kwantar da ita akan gado. Kana yayi kissing ɗin goshinta da lips ɗin ta ahankali ya fara cire mata rigarta cikin wata kasalalliyar murya yace. “Khausar da shin da gaske kina min soyayyar da baza ki iya furta min ita abaki ba Khausar?Meyesa baza ki faɗa min ba inji sanyi raina sai kiyita dakon soyayyata tsawon shekaru meyesa baki faɗa min ba meyesa baki nuna min ba? Da gaske kece kika rubuta littafin nan”. Ahankali taja numfashi mai tsawo hannunta na cikin sumar kansa tana shafawa kana manyan yatsunta guda biyu na kan sajensa tace. “Ni ba ni na rubuta ba. Haka kawai ka'ida basona kake ba kalen ince ina sonka ka kashe ni?”. Cikin sauƙe numfashi ya gyara ta ajikinsa tare da cewa. “Wayace miki bana sonki? Minha”. Idanunta ta lumshe zuciyarta na bugawa tace. “Nasan baka soma kuma nima ba nice na rubutaba”. Yana shafa sumar kanta yace. “To amma tunda ke kina sona ai da kin faɗa min munyi ta cutar da juna tsawon lokaci?,bamu sani ba”. Muryan cike da sanyi ta ɗan cije gefen bakinta tace. ”Ni dai bance ina son wanda baisona”. Saurin girgiza mata kai yayi tare da faɗin. “Ki daina cewa bana sonki Minha”. Sai kuma ya shiga romance ɗin ta yana shafa saman Breast ɗin ya cigaba da cewa. “Kinsan dalilin zamana aƙasan nan kuwa? Naƙi na koma Jami'atul Madina nayi aikin dana samune saboda ke tun lokacin dana fara sauke idanuna akan ki Allah ya jarabceni da sonki na soki alokacin da bakisan kanki ba Minha”. Da wani irin sauri mai nuni da zallan farin ciki Khausar ta tallofo kansa tana kissing ɗin dogon hancinsa cikin kasala da shauƙi kana da yanayin da yake ji yaci gaba da cewa. “Sanadinki na zauna anan nasoki soyayyar da bazan iya yiwa kaina ba duk Drawing da kike yi na ki wasa ne ni duk wani motsin da kikayi a duniya idan na dawo sai nayi Drawing ɗin sa na ajiye babu abinda yake sani farin cikin gani a duniya kamar fure da kuma ke saboda furanni kansu kin fisu kyau sai dai suna ɗebi min kyewar rashin ganinki ne, kana suna cike min gurbin kallonki”. Cikin mamaki Khausar ta ɗago ta kallesa ido cikin ido tace. “Yah Mu'allim kenan kana sona da gaske?”. Kai ya jinjina tare da faɗin. “Minha ina sonki son da bansan adadinsa ba nayi Miki son da ba yiwa kowacce ƴa mace irinsa a duniya ba”. Sai kuma ya miƙe da sauri, ya buɗe durowar dake jikin gadonshi, wasu manyan takardu masu kana da kalandu ya ja, a kan kadon ya zubasu. Da sauri ta zubawa na forkon idanu. Sai kuma ta kalleshi domin ta tuno yanayin da suka kasance a cikin mota a ranar daya rage mata hanya. Da sauri yaja mata na ƙasashi. Wani irin murmushin ne ya subce mata ganin zanenta tana rawa a gaban motarsu ranar da suka haɗu gidan Ummi. Baki ta turo ganin na ƙasanshi ranar da take kakkaɓe ɗan kwali ne sai kuma wani da bazata manceba na ranar data fara ganinshine da ta tsaya tana kallonshi harda karkata wuya ranar da ta fara zuwa JSS one kenan sai kuma wanda ta diƙo kan bishiyar ranar da suka zo da Asma'u sai wanda suka haɗu a rugar Jauro yaya. Ya Salam sai kuma wasu wanda bisa alamun nashine da Yah Jameel. Kawai sai ta faɗa jikinsa. Ture takardun yayi tare da ruggumeta da kyau. Kanta ta kwanta ajikinsa tana jin yanda hannunsa ke yawo a sassan jikinta tace. “Amma kuma Yah Mu'allim kullum dukana kake yi ya za'a yi na yarda dagaske cewa kana sona”. Yana sakin ajiyar zuciya yace. “Dole ne yasa nake Miki wannan yanayin saboda na fahimci kamar J yana sonki so kuma irin na aure”. Saurin kallonsa tayi ya jinjina mata kai yana cigaba da cewa. “A duniya ban taɓa son abu J yaƙi shiba. Kana J bai taɓa son abu naƙi shiba sai nazo na fahimci akan mace ma zamuyi tarayya akan soyayya kuma hakan zai zame mana masufa a amintakarmun shiyasa nasawa raina hantarar ki da nisantarki da ƙin kasancewa kusa dake saboda in yakice ki azuciyata J ya mallake ki dan nayi alkawarin mace bata isa ta shiga tsakanin amintakarmu ba”. Idanunta ta lumshe tana jin wani irin ƙaunarsa na huda duk wani magudanan jinin jikinta ahankali ya cigaba da cewa. “Abinda J ya faɗa min kenan a voice ɗin sa na ƙarshe yace min ya fahimci ina sonki yamin voice da ace alokacin yana raye zance J ai kaima kana sonta amma tun a voice ɗin yace min kana tunanin kamar ina son Khausar ko? Shiyasa kake hantararta dan ka yakiceta a zuciyarka. Wai sabida zaka bar min ita ko?. To ni ba sonta nake ina taya ka son abinda kake sone A.J ka Aureta dan naga zanenta da kayi a takardu, in su ka ɓoyesu shin zaka ita ɓoye na zuciyarta da ƙwaƙwalwar kane, AJ. Ka aureta. abinda J ya faɗa min Kenan ”. Duk da nasan ya faɗane kawai Amman J ya soki Minha ya soki irin so na aure ashe ya gane ina sonki”. Idanu ta tsira masa kana tace. “Dagaske Yah Mu'allim?”. Kai ya gyaɗa tare da cewa. “Sosai ma”. Daga nan ya cigaba da romance ɗin ta ya dauki Kimanin minti arba'in da biyar akanta kafin ya jawota ya rungumeta yana sa mata albarka tare da cewa. “Alhamdulillah ashe son da nake baso bane soyayya ce?”. Tana sauƙe Ajiyar zuciya tace. “Kamar ya?”. Murmushi yayi tare da faɗin. “Eh so na gefe ɗaya shi ake cewa so amma tunda kema kina sona kinga soyayya ce”. Sake shiga jikinsa tayi kana tace. “Dagaske Yah Mu'allim maganar daka ke faɗa?". Cikin tabbarwa yace. “Ki daina kokonto Minha Vidaa Ana uhubbuki kubban axeem”. Wani irin farin cikine mara misaltawa ya mamaye gaba ɗaya ilahirin zuciyarta. Awannan daren haka suka kwana cikin farin ciki da kwanciyar hankali... Alhamdulillah haka rayuwa ta cigaba da tafiya ranan Alhamis akayi walima ranan juma'a aka ɗaura auren. Malam Liman da yazo ɗaurin Aure ya kawowa Amina da Samira magani da yayi alƙawar kamar yanda ya faɗa zuwa yanzu Alhamdulillah jikinu da sauƙi amma dan Amina har abinci takeci. Samira kuwa ruwan ya rage zuba sosai a wuni haifi sau uku zai zuboba. Hajiya Bunayya kam abin nata babu sauƙi kullum gaba-gaba yake. A ranan jumma'a akayi Dinner mai rai da lafi. Alhamdulillah ranar Litinin sufa dawo Adamawa da amarensu Zakariya da Aseeya Asma'u Da Dr Jameel Dija Yah Ali Su Didi sunje har falon bappa Jimeta. Washe gari talata jirginsu ya ɗaga zuwa Morocco. Misalin ƙarfe 2:00pm suka sauƙa acikin Morocco anan suka samu motoci daga Masarautar Mouley na jiransu suka shish-shiga kana suka tafi motocin ajere ajere suke tafiya a sai da sukayi nisa Khausar taga motarsu ta fita cikin sauran tawagar motocin ahankali ta kalli Moddibo dake gefenta kana tace. “Yah Mu'allim ya naga su sunyi can mu munyi nan?”. Yana ɗan shafa cikinta yace. “Gida zamu tafi”. Idanunta ta zare kana ta langwaɓar da kai tace. “Yah Mu'allim gida kuma? Baza muje inga gidansu ba? Ai kamata inyiwa Asma'u rakiya aminiyata fa”. Kai ya gyaɗa tare da cewa. “Za kije amma ba yau ba sai kin huta”. Kai ta gyaɗa direct motarsu Masarautar Mouley ta nufa. Yayin da Amare aka wuce dasu gidajen su batare da rakiyan kowa ba daga Nigeria kasancewar ga Didi da Innayi sun sai Goggo Asma'u ta wadatar dan a cewarsu ai Asiya ga Khausar dijama ga Khausar ga Yah Abbanta. Khausar kuwa suna isa abinci suka ci kasancewar an shirya musu komai kana ko wanne yayi wanka ya kwanta dan huce gajiya. Bayan kwana biyu Moddibo ne zaune akan sallaya gabansa ɗauke da starm da Kur'ani ke kai, bayan ya dawo daga sallar Asbah yayin da Khausar ke gefensa ahankali ta ɗago kanta jin ringing ɗin wayarta kallon Moddibo tayi kasancewar ya fita kusa da wayar da ido ta mishi alamar ya dai wake kira?. Juyawa yayi kana ya kalli screen ɗin wayar sai kuma ya kalleta yace. “Asma'u ce”. Da ɗan sauri ta miƙe ta karɓi wayar tare da amsawa takai kunnenta tare da cewa. “Hello Besty na kiyi haƙuri laifin yayanki ne. Yah Mu'allim ne ya hanani zuwa wai in barku ku gurji amarc... Sai kuma tayi shiru ba tare da ta ƙarasa mgnar ba, sabida jin muryan Asma'u a disashe kana yayi sanyi alamun taci kuka ta godewa Allah cikin raunin murya tace. “Khausar”. Da damuwa Khausar ta ɗan jingina bayanta da kafaɗar Moddibo kana tace. “Subhanallah Asma'u meke faruwa”. Cikin rauni da zubda hawaye Asma'u tace. “Khausar zan mutu dan Allah ki cewa Yah Mudibbo kuzo ki ɗaukenu, wannan mutumin mungu ne ya kasheni ”. Dariya mai sauti Khausar ta fashe dashi har tana ɗan bubbuga kanta da jikin kafaɗar Moddibo kana tace. “Ya kashe ki kuma kike magana?”..... By *GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH Book 3 PAGE 5* NA *Aysha Aliyu Garkuwa* *WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA* _Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu...Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_ _Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 08069423567 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci...._ 🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida, Cikin dariya sosai ta ƙarshe Maganar, sai kuma tayi saurin sa tafin hannunta na dama ta rufe bakinta, sabida jin yanda muryan Asma'u ya fito tana shesh-sheƙa. Tare da saki sanyayyan kuka tana cewa. “Dariya ma kike min Khausar?,Baki san halin da nake ciki bane wallahi zai kashe ni fa!”. Da sauri Khausar ta gyara zamanta cike da tausaya wa tace. ”Kiyi haƙuri My Besty babu abinda zai kashe ki in Sha Allahu, wahala ce dai anshata kuma in sha Allah baza amaimaita irin taba”. Sai kuma ta kalli Moddibo da idanunsa ke lumshe yana motsa laɓɓansa amma bisa duk kan alamu yana sauraron tattaunawar wa tasu tace. “Kin manta nima lokacin haka kike ta min dariya idan kin tuna alokacin har ce miki nayi kema kwana nawa ya rage Miki amma kika cigaba da dariyar ki”. Araunane Asma'u taja dogon numfashi tare da cewa. “Baza ki gane bane Khausar Ni ba maganar dariya nake Miki ba Ni dai yanzu dan Allah ki daina yimin dariya,yanzu ina Yah Moddibo yake ki bashi wayar”. Cikin tausayinta da kuma yanda take jin shesh-sheƙan kukanta Khausar tace. “Menene? me zaki ce masa?”. Asanyaye Asma'u tace. “Ni dai dan Allah ki bashi wayar”. Kai Khausar ta gyaɗa tare da cewa. “Toh”. Kana ta sanya wa Moddibo wayar akunnensa. Ahankali ya juya ya kalleta kana ya ɗaura hannunsa akan nata ya riƙe wayar. Asma'u kuwa da muryanta ya gama dishewa da kuka tace. “Yah Moddibo”. Ahankali ya ɗan runtse idanunsa yana mai jin tausayinta, rauninta, damuwarta, domin jinta yake tamkar jininsa tsatsonsa yana jinta tamkar yanda yake jin Rahama Aransa, cikin sanyi da tausasawa yace. “Na'am Asma'u me ya faru? Me yake damunki?”. Kuka ta fashe dashi cikin dashewar murya tace. “Yah Moddibo bani da lafiya ni dan Allah kazo ka ɗaukeni”. Cikin fesar da numfashi Moddibo ya ɗan gyara zamansa tare da cewa. “Kiyi haƙuri Asma'u, Kwantar da hankalinki ki daina kukan ki faɗa min meke damunki!?,Mene matsalar ki?”. Cikin son danne kukan dake taso mata tace. “Bani da lafiya zazzaɓi nake ji ƙafafuna, bayana, kaina, duk ciwo suke min”. Ahankali yace. “Toh kiyi haƙuri Yi shiru yanzu me kike so?”. Tana shesh-sheƙan kuka tace. “So nake ka kawo min Khausar kuma kaima kazo”. Kai ya gyaɗa tare da faɗin. “Toh kiyi shiru in Sha Allahu zan kawo miki ita”. Cikin muryanta da bai fita sosai tace. “Yanzu fa?”. Kai ya gyaɗa mata kamar tana gabansa yace. “Eh in Sha Allahu yanzu”. Ya ƙarashe maganar yana mai jin matsanancin tausayinta kasancewar yasan wanene Dr Jameel mutum ne mai shegen fitina kana yasaba neman mata ya saba ko yaushe rayuwarsa da mata sannan yasan tunda sukayi maganar Aurensa da Asma'u ya daina neman mata, tun lokacin yake fama da Azumi yasan ya tara fitinar da tafi ƙarfinsa shi kansa shiyasa yake jin tausayinta dan ya san ya mata wawan riƙone. Cikin sanyi ya fesar da numfashi kana ya cigaba da cewa. “Kiyi haƙuri ki share hawayenki kuma ki daina kuka, kukan da kike yi zai sa kiki zazzaɓi da ciwon kai”. Kai ta gyaɗa kamar yana ganinta ta share hawayenta tare da cewa. “Toh ka bawa Khausar ”. ”Toh”. Yace kana ya miƙawa Khausar wayan tare da faɗin. “Tashi, tashi ki shirya mu tafi”. Khausar kuwa cikin sanyi da tarin tausayin aminiyar nata tace. “Asma'u kiyi haƙuri ganin nan zuwa ki daina kukan dan Allah ”. Ba tare data tsaida kukan nata ba tace . “Nikam dan Allah kizo kuma idan akwai magani ki kawo min”. Murmushi Khausar tayi kana ta kalli Moddibo da fuskarsa ta nuna damuwa numfashi ta fesar tare da cewa. “Kamar ya in kawo kiki magani Asma'u!,Keda kike tare da Likita?,Ai ke kece gidan magani”. Sabon kuka ta fashe dashi kana tace. “Baza ki gane bane yanzu ma yamin allurai sannan yaban magunguna kuma duk nasha”. Ajiyar zuciya Khausar ta sauke tare da cewa. “Toh kiyi haƙuri in Sha Allahu zaki ji sauƙi ”. Kai ta gyaɗa tare da katse kiran kana ta mike suka fito. A Corridor sukayi kiciɓis da Innayi wacce bisa alamu taje ta gaida Didi ce ta dawo cike da kulawa ta kallesu kana tace. “Lafiya ina zaku je?”. Kallon Khausar Moddibo yayi kana cikin sauri yace. “Zamu je tayi Anti nytel ne”. Kai Innayi ta gyaɗa tare da cewa. “Toh shikenan amma da sassafe haka?”. Yana kallon Khausar data ɗan lumshe Idanunta yace. “Eh”. Kai ta jinjina kana tace “Ok kuma naga wancan zuwan nata da daddare kuka je wannan kuma da sassafe?”. Yana riƙe hannun Khausar acikin nasa suka nufi hanyar fita kana yace. “Eh”. Kai ta gyada tare da shigewa ta nugi kitchen. Nan ta samu Hadimai da already sun fara girki. Dr Jameel ne zaune dafe da kansa fuskarsa ɗauke da Murmushi. Cikin kasala da alamun rashin wadataccen bacci ya muƙe a saɓule jin ana knowking ɗin ƙofar. A hankali ya buɗe ƙofar ganin Khausar ce agaba yasa ya ɗan ja baya cikin sauri Khausar ta wuce cikin falon tare da cewa. “Barka da safiya Dr”. Fuskarsa ɗauke da ƙayataccen Murmushi yace. “Barka dai Bestynmu”. Sai kuma yayi saurin juyawa tare da rungume Moddibo cikin matsanancin farin ciki yace. “Ka gama min komai Aminina kuma ɗan uwana ka bani abinda ban taɓa samun irinsa ba arayuwata ta duniya”. Ya lumshe idanunsa yana tuna irin garar daya kwasa awajen Asma'u kana ya cigaba da faɗin. “Dukk biye-biyen neman Matana ban taɓa samun gamsuwa, nutsuwa, da kwanciyar hankali ba kamar akan wannan ƙanwar taka kagama min komai” Ɗan tsuke fuska Moddibo yayi kana yasa hannunsa na dama ya make ƙeyensa tare da rike ƙunnensa yace. “Ka kuwa san abinda kake faɗa?,”. Still fuska ɗauke da murmushi Dr Jameel ya gyaɗa masa kai tare da cewa. “Na sani mana, nasan me nake faɗa kawai dai na rasa ta ya zan nuna farin cikina ne. Ji nake kamar in kira Ummi in sa mata albarka saboda ta bani abu mafi daraja da daɗin samuwa arayuwar duniya”. Zare idanu Moddibo yayi kana yace. “Baka da hankali fa”. Kai Dr Jameel ya gyaɗa yana lumshe idanunsa kana har zuwa lokacin fuskar na ɗauke da Murmushi yace. “Sosai ma bani da hankali, Wallahi bani da ishesh-shen hankali saboda tun jiya da hankalina ya tafi cikin gajimare har yanzu bai dawo ba. Ni kaɗai nasan irin daɗi da shaukin dana kasance”. Da ɗan ƙarfi Moddibo ya matsa kunnensa wanda yasa Dr Jameel sakin ƙaramin ƙara. Moddibo kuwa yana cigaba da matsa kunnensa yace. “Shine ka azabtar min da ƙanwata da fitinar da baka kasheta ba na tsawon watanni ko? shine yanzu dare ɗaya zaka sauke akanta ko?”. Langwaɓar da kai Dr Jameel yayi tare da cewa. “Ƙanwar taka ce tafi zuma daɗi baki ɗaya ta gigitani ta gigita min lissafi duk ta rikitani”. Ƙeyensa Moddibo ya kuma makewa da karfi kana ya wuce cikin falon. Da sauri Khausar da tuni tayi ciki, ta juya ta kallesu kana tace. “Dr ina Asma'u take?”. Da hannu ya nuna mata Corridor da bedroom ɗin su yake. Da sassarfa ta wuce. Moddibo kuwa zama yayi akan kujeran kana Dr Jameel ya zauna gefensa. Asma'u kuwa cikin yanayin baccin daya fara ɗibarta ta fara jiyo sautin muryan Khausar cikin sauri ta yunƙura da niyyar tashi. Da sauri Khausar ta tura ƙofa ta shiga Asma'u kuwa da wani irin sauri ta runtse idanunta kana ta koma ta zauna tare da sakin ƙara tana yarfe hannunta. Cikin sauri Khausar ta matsa ta zauna kusa da ita kana ta riƙe hannunta tare da cewa. ”Allah sarki Asmeeyn Ummi an girma”. Harara Asma'u ta galla mata da kumburarrun idanunta tace. “Wani an girma?,An dai zalinceni!, Kawai ai wannan zalincine ba girma ba”. Murmushi Khausar tayi wanda ya bayyanar da hoƙoranta tace. “Kema kiji abinda ake ji, kiji abinda ko wacce ƴa mace take ji fatan mu dai Ubangiji Allah yayiwa iyayenmu albarka ya kuma saka musu da mafi kyawun sakamako da tarbiyyan da suka bamu Ubangiji Allah ya bamu zaman lafiya a gidajen aurenmu”. Cikin shesh-sheƙa Asma'u tace. “Ameen ya Allah amma Ni dai wallahi tare zamu tafi”. Zare idanu Khausar tayi tare da cewa. “Tare zamu tafi?,Na isa? A,a ni kam ba isa in ɗauke wa Dr Mata ba”. Ɗan hararanta Asma'u tayi kana tace. “Idan ke baki isa ba Yah Moddibo ya isa?”. Sai kuma ta fara yunkurin miƙewa tana cewa. “Ina Yah Moddibo?”. Ganin yanda take ciccije bakinta yasa Khausar faɗin. “Ki zauna mana bakya jin zafi ne”. Tana goge hawayen fuskarta tace. “Ai nasha magunguna na fara jin yana raguwa sosai yanzu”. Kai Khausar ta gyada tare da cewa. “Toh yanzu ina zaki je”. Tana cije gefen lip inta na ƙasa tace “Zanje wajen Yah Moddibo”. Dariya Khausar ta sanya tare da faɗin. “Iyeee wai ke bakya jin kunya ne?” Hararanta Asma'u tayi kana tace “Eh ɗin bana ji,Ke lokacin da aka miki kunya kika ji?,Ina gaban su Ummi kika je kika rinka Zuba taɓara son ranki”. Dariya Khausar ta sake fashewa dashi ganin yanda Asma'u ke wani ciccije baki alamar har yanzu bata gama warware ba tace. “Eh amma ai agaban mata nayi ba Maza ba”. Shiru Asma'u tayi kana ta fara ƙoƙarin miƙewa har ta mike ta fara tafiya miƙewa Khausar tayi tabi bayanta tare da riƙe hannunta ahaka suka fito falon kallonsu Moddibo yayi ganin yanda Asma'u ke tafiyar yasa ya sunkuyar da kansa ƙasa ya kalli gefe tare da cewa. “Asmeeyn Ummi kin fito?,”. Cikin da shashshiyar muryanta tace. “Eh Yah Moddibo ”. Akuma dai-dai lokacin suka ƙarasa cikin falon zama sukayi akan 2sitter ahankali Asma'u ta zame ta kwanta kana ta ɗaura kanta akan cinyar Khausar. Ahankali Khausar ta gyara zamanta kana ta tallafo kanta. Moddibo kuwa ba tare da ta kuma sallonta yace. “Asmeey zaki danne Baby fa”. Murmushi Asma'u tayi duk da yanayin da take ciki saboda ya bata dariya ta lura Yah Moddibo yana masifar tattalin cikin nan juyawa Asma'u tayi ta kalli tudun cikin Khausar hannunta na dama tasa kan kitchen tare da cewa. “Baby kayi haƙuri nima yau ina buƙatar cinyar Mamynka”. Murmushi Khausar tayi kana tace. “Yama isa tun kafin ya fito,ai tare ya ganmu ma”. Ahankali Moddibo ya shafa sajensa yace. “Adai barshi kar ta kura mishi”. Dr Jameel dake Murmushi ya kalli Moddibo yace. “Iyeee komai yaya dai yau zai bari ayi tattalin Umminsa”. Murmushi suka baki ɗaya kafin Moddibo ya kalli Asma'u yace. “Ya jikin?”. Asanyaye tace. “Da sauƙi Yah Moddibo ”. Kallonsa ya mayar kan Dr Jameel tare da cewa. “Ya baki magunguna ko? Kuma kinci abinci?” Kai ta girgiza tana ɗan lumshe Idanunta tace. “A'a banci ba”. Shiru yayi kafin yace. “Toh yanzu me zaki ci insa akawo Miki daga gida?. Cikin sauƙe numfashi Khausar tace. “A'a bari in shiga kitchen in girka mata”. Da sauri Moddibo ya girgiza kai tare da faɗin. “A'a bana so”. Kai ta langwaɓar tare da cewa. “Yah Mu'allim zan iya mana agida ma ina shiga inyi girki ” Cikin sauƙe numfashi yace. “Toh shikenan”. Asma'u kuwa miƙewa tayi tare da cewa. “Toh mu tafi kitchen ɗin tare” Kai Khausar ta girgiza tare da cewa. “A'a ke kam ki wuce bedroom ki kwanta naga kamar bacci kike ji”. “A'a muje dai”. Cewar Asma'u tana lumshe Idanunta. Numfashi Khausar ta fesar tare da kallon yanda take lumshe idanu tace .“A'a ke dai kije kiyi baccin”. Ahankali tace. “Toh”. Hannunta Khausar ta riƙe suka wuce bedroom ɗin kwanciya Asma'u tayi kana Khausar ta zauna gefenta tace. “Amma kinyi amfani da Ruwan ɗumi sosai?”. Kai Asma'u ta gyada tare da cewa. “Eh ya sassani kuma ya ban magunguna sannan yamin allurai kuma ya shafa min wani ma a wurin Alhamdulillah naji sauƙi sosai yanzu ɗazun fa ko numfashi nayi zafi nake ji kamar raina ake zarewa”. Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe kana tace. “Toh ba komai yanzu dai bari na miki abinda zaki ɗan ci mai zan dafa Miki?”. Idanunta ta juya tare da taune lips ɗin ta tace. “Nikam ma bana jin yunwa”. Cike da kulawa Khausar ta dafa kafaɗarta tace. “A'a ki dai fadi me kike so adafa miki?”. Rau-rau tayi da idanuna tare da cewa. “Nifa bana jin kwaɗayin komai”. Shiru Khausar tayi na tsawon minti ɗaya alamar tunani kafin ta mike tace. “Bari dai naje kitchen in ga abinda zan Miki. Ko dai in gasa Miki nama? Dan nasan ki”. Tana gyara kwanciyarta tace. “Eh”. Kai Khausar ta gyaɗa tare da wucewa kitchen. Kallon Moddibo Dr Jameel yayi kana yace. “Yanzu kusan 1month fa kenan da Khausar taje anti nytel ya kamata ace gobe ko jibi ku samu ta sake zuwa”. Cike da gamsuwa Moddibo ya gyara zamansa yace. “Eh nima dama gobe ko jibi nake so muje,dama tun bayan 2weeks ma naso muje toh ya kama bikin nanne da muka tafi amma in sha Allah gobe ma zan kawo ta”. Kai ya jinjina kana yace. “Toh Allah ya kaimu”. “Ameen”. Ya amsa kana suka cigaba da hira... A gefen Khausar kuwa cikin sauri sauri ta gasawa Asma'u nama mai ɗan romo-romo sai tashin ƙamshi yake kana ta dafa Cous-cous da yaji Carrot da grean beans daya ƙawata kyawunsa gashi yayi wasar-wasar abin sha'awa sai kuma tayi miyar hanta da yayi kyau sosai bayan ta gama ta zuba a Warmer kasancewar duka ayyukane masu sauƙin yi ta ɗauki na Moddibo da Dr Jameel ta kai musu Falo kana ta koma ta ɗauki nasu ta wuce bedroom ɗin Asma'u. Tana shiga ta samu Asma'u na bacci jin alamun tana jin yunwa yasa ta zauna a tsakiyar ɗakin kana ta zuba a plate ta fara ci. Tana cikin ci ta ɗago kanta ta kalli Asma'u jin alamun Asma'u tayi motsi. Asma'u kuwa cikin baccinta taji kamar sautin ƙaran cokali tare da yunwar daya murɗeta ne ta mike ta zauna. Dan ɗan murmusu tayi sai kuma ta miƙe ta zauna. Khausar dake kallonta tace. “Ya dai”. Cike da farin ciki ta shafa cinyoyinta kana tace. “Zafin ya tafi fa”. Ajiyar zuciya Khausar tayi tare da kai spoon ɗin bakinta tace. “Haba dai”. Cikin tabbatarwa ta gyada mata kai sai kuma ta sakin sanyayyar ajiyar zuciya tace. “Wlh kuwa”. Ta ƙare maganar tana gyara zamanta. “Masha Allah magunguna sun kama aikinsu”. Cewar Khausar na Murmushi. Asma'u kam cikin jin daɗi tace. “Wlh kam". Warmer Khausar ta janyo tana ƙara musu abincin tace. “Toh saƙƙo muci abinci”. Kai ta gyada kana ahankali ta saƙƙo ta zauna suka fara cin abinci bayan sun gana Khausar tace. “Akwai magungunan da zaki sha yanzu ne?”. Kai ta girgiza tare da cewa. “A'a sai bayan Azahar zan sake shan wasu”. Tana tattara plate ɗin waje ɗaya tace. “Toh shikenan”. Daga nan sukaci gaba da hira. Wunin ranan dai haka Khausar ta yini agidan Asma'u koda Moddibo yace su tafi cewa tayi yayi haƙuri sai bayan Sallar Isha'i yazo ɗaukar ta. Tsaye suke a abakin gate kallon Asma'u Khausar tayi tare da cewa. “In sha Allah daga nan zamu wuce gidan Addah Asiya”. Cikin sanyin Asma'u tace. “Wallahi nima ina son zuwa”. Dr Jameel da baki ɗaya nutsuwarsa ke kanta tace. “Ki bari idan kin sake warware wa in Sha Allahu zan kai ki”. Langwaɓar da kai tayi tare da cewa. “Toh ba ance kwanan nan zasu tafi ba?” Kai Khausar ta girgiza tace. “A'a ance dai kwanan nan zasu koma kuma naji ance anan zai gama hutunsa”. Kai Asma'u ta gyada tare da cewa. “Toh shikenan In sha Allahu kafin su tafi zamu sake zuwa mu wunin mata ko?”. Kai Khausar ta gyaɗa tare da faɗin. “Eh in sha Allah”. Daga nan sukayi sallama suka fita. Suna fita kai tsaye gidan Asiya suka nufa. Dai-dai lokacin kuma Asiya ce da Dr Zakariyya ke zaune a falo suna hira jin ana knowking yasa Dr Zakariyya miƙewa ya buɗe. Khausar ce agaba Asiya na ganinta ta miƙe da gudu taje ta rungumeta Moddibo kuwa cikin Murmushi yace. “Addah Asiya abi ahankali”. Murmushi tayi kana ta riƙe hannun Khausar tare da cewa. “Adda Khausy tun shekaran jiya nake ta zuba ido ina so in ganki ban ganki ba”. Cunno Baki Khausar tare da kallon Moddibo da suke magana da Dr Zakariyya tace. “Yah Mu'allim ne ai”. Murmushi Moddibo yayi kana ya marairaice fuska yace. “Komai dai Ni ko wani laifi nawa ne komai ace Yah Mu'allim toh naji na ɗauki laifina”. Cikin narke fuska tace. “Ato ai kasan hakane”. Murmushi yayi. Asiya kuwa kitchen ta shiga ta kawo musu abubuwan motsa baki taɓa ka lashe. Khausar ce dai ta ɗanci Amman shi Modibbo ko ruwa bai sheba. Bayan sun gama hira kusan karfe goma na dare sukayi musu sallama suka tafi. Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya Khausar na samun kulawar Uwar mijinta da danginsa Innayi ma na iya bakin ƙoƙarin ta kana suna waya da Momy, Ummu, Hajja Nana, akai-akai hakama Aunty Ruƙayya da Aunty Hajara. Bayan sati Uku Asma'u da Khausar suka je gidan Asiya suka yini mata bayan sati ɗaya da zuwa su Asiya da Dr Zakariyya suka koma Indi'a... Washe garin ranan da suka tafi a Nigeria Amina ce zaune a falo yayin da Hajiya Bunayya ke tsaye tana bubbuga ƙafa tare dasa hannunta tana bubbuga mazaunanta jin yanda masifaffun tsutsotsin nan ke addabar rayuwarta wanda da ƙanane suke fita yanzu kuma manya ne Amina kuwa Alhamdulillah bisa ga duk kan alamu jikinta yayi sauƙi sosai kasancewar har ta fara maida ƴar ƙibanta alamun ta samu sauƙi sosai-sosai. Ahankali ta tallafe haɓarta tana kallon Mahaifiyarta ta zuwa yanzu ta fahimci tsutsotsin nan sun haukata mata mahaifiya saboda ko yaushe ƙoƙari take ta cire zaninta ta yasar ita take ƙoƙarin hanawa kamar dai yanda yanzu ma take ƙoƙarin cirewa. Cikin sauri Amina ta miƙe cikin rauni da zubda hawaye tace. “Dan Allah Umma kada ki cire zanin”. Alalace ta juya ta harareta tare da cewa. “Kada in cire zani in zauna kenan su cinyeni ke kin san abinda nake ji kuwa? baki ga tsutsotsin nan yanda suke cina ba ko kuma dan ke kin samu lafiya bake kike shan azaba yasa zakice haka, ai dacan da kike zazzaro harshe waya ce ki daina”. Ta ƙare maganar tana kwayewa Amina ɗuwawunta tare da cigaba da faɗin. “Ki ga fa”. Cikin sauri Amina ta runtse idanunta kana tace. “Innalillahi wa'inna alaihi raji'un”. Ganin manya-manyan tsutsotsin dake cin Mahaifiyarta cikin matsanancin tashin hankali ta saki ihu dai-dai lokacin da Lamiɗo ya hau Farandar falonta saboda yanda Amina tayi ta kuka daren jiya akan cewa ya kai Hajiya Bunayya asibiti cikin sauri ya karaso Falon yayin da Momy ke biye dashi abaya ganin haka yasa Momy saurin ɗaukan zanin ta daura mata. Ga mamakinsu sai suka ga Hajiya Bunayya ta fara buge-buge tare da ɗaga hannu zata daki Momy cikin sauri Lamiɗo ya kamo hannayenta ya riƙe. Dariya ta fara ƙyalƙyalawa alamun hauka ta tabbata tuburan ziraran. Kuka sosai Amina ta fashe dashi. Dai dai lokacin Haiydar da Sulaiman suka shigo ganin haka yasa Sulaiman rungume Haiydar suka fashe da kuka cikin rauni da shesh-sheƙa Sulaiman yace. “Haiydar kaga Ummana yanda ta koma”. Shiru yayi ganin yanda take ƙoƙarin ƙwace hannunta Momy kuwa duk da yanda take ƙoƙarin kawo mata duka sai da ta jawo zanin ta ɗaura mata ta baya. Wani irin abu ta fara kamar rawa kamar tsalle alamun dai hauka Muraran ziraran. Kai Lamiɗo ya girgiza tare da juyawa ya kalli Gimbiya Dadu da tazo wacce hayaniyar dake faruwa ne yasa taxo tana shigowa taga Hajiya Bunayya keyi ta saki ƙara ta faɗi awajen atake a wurin ɓarinta ɗai ya shanye tun, kafin aɗagata ɓarin jikin ta ya mace. Cikin gigita da Kiɗima Lamiɗo ya kalli Haiydar kana yace. “Haiydar jeka kira min bappanka”. Cikin rawan jiki Haiydar ya juya ya fita yaje ya kirasa. Hajiya Bunayya kuwa ƙoƙarin duka take kai masa ɗankwalin kanta ya since ya ɗaure hannunta. Dai-dai lokacin da ƙanin nashi ya shigo cikin tashin hankali Lamiɗo yace. “Yusuf ka ɗauki Hajiya Bunayya ka Kaita Sycatry na cikin Taraba”. Cike da damuwa yace. “Innalillahi wa'inna alaihi raji'un Sycatry kuma?”. Araunane Lamiɗo ya kalli Hajiya Bunayya dake wani irin fusga tana ƙyalƙyala dariya yace. “Toh ya zamuyi Yusuf?Bata da wani amfani daya wuce mu Kaita Sycatry dama arayuwa duk abinda mutum zai yi yabi ahankali”. Kuka sosai Bashir keyi tamkar ransa zai fita Lamiɗo kuwa cikin sanyi ya cigaba da cewa. “Gashi tun ba aje ko ina ba Ubangiji Allah ya haɗa mata sakamakon aikin ta ya liƙa mata su atsakiyar kanta sun zame mata matsala, muma sun zame mana matsala tun da komai yaya zukatanmu nada Imani zamuji tausayinta”. Cikin azabebben kuka Amina ta kalli Lamiɗo tare da faɗin. “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Ummana yanzu Sycatry za'a kai ta?”. Cikin sauƙe zazzafan ajiyar zuciya yace. “Yanzu Amina anan za'a barta tayi ta hauka?,Mutane suna kallonta tana since zani idan mun barta anan cikin gari zata shiga tayi ta yawo tana bayyana tsaraici kinga ai baiyi ba”. Cikin matsanancin kuka da shesh-sheƙa Amina ta gyada kanta tare da faɗin. “Hakane kam Abba”. Alh Yusuf kuwa janta yayi ya sata a mota. Lamiɗo kuwa sai alokacin yaje ya ɗaga Gimbiya Dadu da tuni ta sume. Cikin kiɗima ya Kaita asibiti, inda duk binciken da akayi likitoci suka tabbatar masa da cewa ta kamu da ciwon ɓarin jiki awanna ranan dai haka suka yini a asibiti koda ta farfaɗo gefen bakinta ya karkace tana magana yawu na zuba cikin zubda yawu da magana irin na wanda suka samu shanyewar ɓarin jiki tace. “Ohhh nima dai ga karshena nayi ta cin ƴaƴan mutane ina ta zubar da cikin ƴaƴan mutane idan naga ɗan da yamin maiƙo in lashe in naga mai ciki inlamushe”. Cikin sauri da matsanancin mamaki da tashin hankali Lamiɗo ya rufe mata baki tare da cewa. “Dadu Ki daina faɗan haka dan Allah ki dai na faɗa ”. Bakinta na tsulalar da yawu tace. “Ai dole in faɗa ayyukana ne in ban faɗesu ba ya zanyi. Ni na aikata kana ganin kamar zargina mutane suke da suke cewa Ni mayyace. Tabbas ni mayyace da gaske amma kai Allah ya tsare ka da ƴan Uwanka dama nida ƴar uwata siya mukayi bawai tsatson mu bane”. Araunane Lamiɗo yace. “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un hasbunallahu wani'imal wakin”. Haka yaita addu'oi wai ko zai samu ta bar tone-tone ta kama addu'a amman a banza. Washe gari da safe aka sallamosu a asibiti suka dawo gida saboda Likitoci since babu abinda zasu iya mata dole yasa Lamiɗo ya nemo masu aiki wanda zasu riƙa kula da ita. Yayin da Hajiya Bunayya da Hajiya Lami ke can asibiti suna can suna buga wash-shagare wallensu a haukace. A kuma dai-dai wannan ranan Khausar ce zaune a falonta kunnenta maƙale da waya tana hawaye cikin rauni tace. “Yanzu Momy haka Umma da Hajiya Lami suka dawo? Ita ma Gimbiya Dadu haka ta dawo?”. Cikin sanyi da damuwa Momy tace. “Wlh Khausar am ai rayuwar nan mu bita a sannu”. Cikin zubda hawaye Khausar ta gyara zamanta tare da cewa. “Dama Momy ina faɗa Miki kallon da Gimbiya Dadu take yimin yana ban tsoro kullum cikin kareta kike”. Ajiyar zuciya Momy ta sauke kana tace. “Toh Khausar baka da tabbaci ka isa ka tuhumi mutum ne? ba kiji Manzon Allah (S.A.W.)yace _Azzhana zhambu Walau kana haƙƙun_ ai zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya amma yanzu da taxo ta faɗa da bakinta ai taga *SAKAYYAR ta*”. Kai Khausar ta jinjina tare da faɗin. “Allah ya rufa mana asiri ya kare mu”. Dai-dai lokacin Moddibo ya shigo ganin tana hawaye yasa yayi saurin shigowa ciki, tare da zama a gabanta kana ya sanya hannunsa ya share mata hawaye. Yana mai kallonta, sai kuma ta ɗan sauƙe ajiyan zuciya, ganin yanda ya zuba mata idanu yasa tace. “Toh Momy sai anjima”. Kana suka katse kiran. Ahankali ya janyota jikinsa ya ɗaura hannunsa akan cikinta yana shafawa saboda yanzu cikin yashiga wata na biyar zuwa na shida haka yasa cikin ya ɗan bayyana ya girma yayi ɗas a jikinta gwanin ban sha'awa ganin yanayin fuskarsa yasa tace. “Ya akayi Yah Mu'allim?”. Fuska ya narkar da damuwa atare dashi yace. “Minha kuka fa kike yi ya za'a yi kintam bayeni ya akayi?”. Asanyaye ta bashi labarin da Momy ta bata ta faɗa mata sai abinda take ga sirrinsu ne bai kamata ya saniba ta ɗan sakaya. Jikinsa ya sake janyota ya rungumeta kana yace. “Mu godewa Allah, Allah ya sake tsarkake zuciyanmu Allah ya hanamu samun damar da zamu cutar da wani, Allah ya hana wani ma samun damar da zai cutar damu. Cikin sanyi da rauni ta gyara zamanta ajikinsa tare da cewa. “Ameen” Yana shafa gadon bayanta yace. “Kuma ki daina damuwar nan ki riƙa yi musu addu'a Ubangiji Allah ya gafarta musu”. Tana ɗan lumshe Idanunta tace. “In sha Allahu ”. Sake janyota jikinsa yayi, bakinsa ya kai saitin kunnenta cikin wata kasalalliyar murya mai cike da shauƙi da bege yace. “Minha babu matsala ban takura ki bako?”. Cikin lumshe idanu da yanda hannunsa ke yawo a sassan jikinta ta fesar da wani sanyayyan numfashi tana sake shiga jikinsa tace. “Ya zanyi Yah Mu'allim tunda kana da buƙata?Kuma dole in ɗauke buƙatar ka tunda bana so wata ta raɓeka”. Ya tsarsa manuniya da babba yasa ya kamo tsinin hancinta ya jijjiga tare da cewa. “Kishi! Kishi!! Kishi!!!”. Cikin Cunno baki ta langwaɓar da kai kana tace. “Toh ba dole inyi kishi ba, Idan banyi kishin kaba waye zai yi kishinka a duniya”. Sai kuma ta marairaice fuska tace. “Ka ƙi kayi min al'ƙwarin baza kayi min kishiya ba”. Jawota jikinsa yayi ya rungumeta kana ya haɗe bakinsu waje ɗaya daga nan yashiga sarrafa ta cike da bege da tarin ƙaunarta... Bayan wani ɗan lokacin Alhamdulillah yanzu cikinta ya cika wata bakwai Cif-cif. Ahankali take sauka kan tsep ɗin sauƙa Falon Didi. Didi dake zaune tayi saurin miƙewa hangota da tayi kana ta riƙe hannunta cike da kulawa tace. “Ba nace miki sauƙan nan idan yana wahalar dake ki bari ba?,Idan kina son ganina ki riƙa kirana in zo ba”. Murmushi tayi tare da faɗin. “Toh ai Didi Likita ma da kansa yace na riƙa motsa jiki na zaman bazai yiba”. Kai Didi ta jinjina tare da cewa. “Haka ne kam ƴata zo ki zauna me kike so in dafa Miki?”. Murmushi tayi kana ta maida kallonta kan Moddibo da Ibraahim dake shigowa cikin langwaɓar da kai Ibraahim yace. “Toh koma menene za'a dafa adafa dani”. Dariya Didi tayi tare da cewa. “Wannan ba naku bane ”. Murmushi Moddibo yayi tare da shiga Falon kana ya zauna agaban Khausar tare da janyo ƙafarta ya ɗaura akan cinyarsa yana ɗan jan yatsunta sai kuma ya maida kallonsa kan Didi yace. “Didi kalli ƙafafun tan nan kamar kumbura sukayi?”. Juyawa Didi tayi ta kalli ƙafafun kana tace. “Eh nima naga kamar kumbura sukayi amma Dr Eshaa tace bakomai dan tun shekaran jiya da naga kumburin na kirata tazo ta duba ta tace bakomai wannan Normal ne mafi akasari wasu na fuskantar haka daga ciki wata Bakwai kuma kaga kumburin bamai yawa bane”. Ajiyar zuciya ya sauƙe yana cigaba da matsa ƙafafun yace. “Toh shikenan ”. Didi kuwa Kitchen ta shiga ta ɗauko Pride rice da yaji Vegetables da naman zabbi sai Perpersoup ɗin Kifi da yaji kayan ƙamshi ta kawo fitowa dasu tayi da plate guda biyu ta zubawa Khausar kana tasa mata kifin agefe. Kana ta zuba aɗaya plate ɗin tasa spoon biyu aciki ta ajiye atsakanin Moddibo da Ibraahim. Daidai lokacin Rahama ta fito daga ɗakinta ware idanunta tayi tare da cewa. “Didi anyi Babu Ni ko?”. Murmushi Didi tayi kana tace. “Na isa ƴar Autana bata ciba ɗauko plate kizo ki ɗibi na ki”. Kai ta gyaɗa kana ta juya ta shiga kitchen ta ɗauko plate tazo ta zuba suka fara ci suna hira... Yayinda hadimai keta zuryan aikace-aikacen yau da kullum. A haka rayuwa ta cigaba da tafiya Alhamdulillah Khausar na samun wadatacciyar kulawa daga wajen tako wani sashin, sosai rayuwa take tafiya zuwa yanzu cikinta ya cika wata tara Cif-cif amma dai na ƙuda har yanzu bai zoba kuma. Cikin kulawa Asma'u da tazo mata yini, ta zuba mata ganin ta yunƙura ta nufi bedroom cikin sauri Asma'u tace. “me kike so in kawo Miki?”. Kai ta girgiza tare da faɗin. “Bakomai kawai ina so in shiga bathroom ne yau tunda gari ya waye fitsari da yaƙi ƙarewa nake tayi”. Ɗan zare idanu Asma'u tayi tare da cewa. “Fitsari kuma?,Kin fa ɗawa Dr?”. Kai ta girgiza kana tace. “A'a ban faɗa masa ba bakomai ai”. Cikin cikin kulawa Asma'u tace. “Toh bari in tai maka Miki?”. Ƴar dariya Khausar tayi tare da faɗin. ”Laaa da kin bari babu inda ke min ciwo fa”. Cike shaƙuwa Asma'u ta gyaɗa kai tace. “Toh shikenan ”. Khausar kuwa ban ɗakin tashiga. Asma'u kuwa wayarta ta dauka tare da kiran Dr Jameel yana ɗauka tace. “Hello Dr”. Daga ɗaya ɓangaren cike da begenta yace. ”Na'am dear ya akayi?”. Cikin sauƙe numfashi da da kulawa tace. “Kaga tun daga ɗaxun da muka zo zuwa yanzu bai wuce awa ɗaya zuwa biyu ba ko?”... Kai ya gyaɗa mata tare da faɗin. “Eh”. Numfashi ta fesar tare da cewa. “Toh wallahi daga lokacin zuwa yanzu Khausar ina ga tashiga ban ɗaki tayi fitsari ya kai sau biyar nace ta faɗa maka tace wai babu matsala kawai yau yawan fitsari ne take fama dashi”. Da mamaki yace. “Ha'a ikon Allah kuma tace ba abinda yake mata ciwo?”. Kai ta gyaɗa tare da faɗin. “Eh”. Cikin sanin makamar aiki da yanayin masu ciki yace. “Alamun na ƙuda ne yana iya tashi ko yaushe”. Cikin sauƙe numfashi tace. “Kuma fa tace babu abinda yake mata ciwo”. Ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin. “Eh ba komai bari idan ta fito sai ki haɗa Ni da ita”. Kai ta gyada kana ta katse wayar, jim kaɗan Khausar ta fito. Tana fitowa Moddibo na shigowa kasancewar Dr Jameel ya kirasa ya faɗa masa yana shiga ya kama hannunta ya zaunar da ita akan kujera kana ya zauna aƙasan lallausan Darduma tare da k... By *GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH Book 3 PAGE 6* NA *Aysha Aliyu Garkuwa* *Dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn, masu cewa wai sun goda suga number'n nayine, ko kuma a'a bari dai in na shirya zan sake miki mgn, ko kuma yanzu dai kuɗin bai cikaba tukun sai sun cika, ko kuma a wanne gari kike, kai munyi nisa, toh in ba iyayiba ai duk nisan state da kike ba ruwan mota ba inda bazai kai mikiba, nake turawa ƴan ƙasashen wajema. Kuyiwa Allah da Manzonsa in dai in kinsan Baki shirya sayan kaya ba ku daina min mgnar ku bari sai kun shirya,kada kizo ki ɓata min lokaci a banza, wlh ni na tsani harkar karanta, duk bayani na gamayi in dai saya zakiyi ga kuɗin kaya ga account no ga numberta ai sai ki biya kawai kafin kimin mgn. Tunda dai ga alamominshi da duk illar da yakeyi na faɗi in kina dashi faƙat in babu kada ki wani zo kice min bayani dan ko kinzo iya bayanin da zan miki kenan* Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha'awa. Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni'ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al'ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban lissafa. Sune manyan alamomin infection. Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi. Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni'ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya, zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa. KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni'imomin ki, da sha'awarki, duk kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA'AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau, duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha'awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor's suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic infection ne yar uwa. INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai Maganin na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi'izinillahi ta'ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma'ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya'ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER'N na 08069423567 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA'AURATA. A kan ƙafafunsa ya durƙusa ya zama na kansa na dai-dai kan cikinta ahankali ya dafa cikin, cikin amintacciyar murya mai ɗauke da nutsuwa da tarin kulawa ya fara yi mata addu'a na tsawon minti bakwai sai kuma ya ɗago ya kalleta ita ɗin ma shi take kallo muryansa ɗauke da Amintaccen kulawa da jin ƙai yace. “Minha Viddaa meke damunki?”. Numfashi ta fesar kana ta girgiza kai tare da cewa. “Bakomai fa”. Juyawa yayi ya kalli Asma'u dake kallon Khausar cike da tausayi yace. “Asma'u menene matsalar ta?”. Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da faɗin. “Yah Moddibo daga zuwa na zuwa yanzu fa tashiga ban ɗaki yakai ƙafa bakwai tana fitsari”. Da sauri ya kalleta kana yace. “Ba abinda yake Miki ciwo?”. Kai ta gyaɗa tare da cewa. “Yah Mu'allim nifa ba abinda ke min ciwo”. Da damuwa asaman fuskarsa yace. “Toh ba abinda kikeji?”. Kai ta gyaɗa tare da cewa. “Wallahi ba abinda ke min ciwo”. Yana cigaba da massage ɗin ƙafanta yace. “Yanzu kuma Dr Jameel ya kirani yace muje asibiti”. Langwaɓar da kai tayi tare d cewa. “Nifa ba abinda ke yimin ciwo Yah Mu'allim ai da akwai zan faɗa muku amma wallahi babu?”. Numfashi ya fesar kana yace. “Toh amma dai bari na sanarwar Didi halin da ake ciki”. Ganin yanda ya damu yasa ta gyaɗa masa kai tace. “Toh shikenan ba laifi kaje ka faɗawa Didi”. Dai-dai lokacin kuma wayar Asma'u ta hau ruri ahankali Asma'u ta ɗauka ganin Ummi yasa tayi saurin Picking ta kai kunnenta suka gaisa da Ummi sai kuma taji kamar muryan Momy tana gyara zamanta tace. “A'a Ummu ina kike?”. Murmushi Ummi tayi tare da cewa. “Ina gidan Momyn Khausar ne na kwana biyu banji labarinta bane shine nazo kuma dana zo ma muke ta hiranku sai nace bari in kira ku inji Labarin ku”. Murmushi Asma'u tayi kana tace. “Nima kuma yau ina gidan Khausar ce ki bawa Momy wayar”. Wayar Ummi ta bawa Momy suka gaisa Ahankali momy tace. “Ya dai Asma'u ya jikin Ƙawar taki lafiya ko?”. Kallon Khausar dake lumshe Idanu Asma'u tayi tare da cewa. “Momy lafiya lau sai dai yau tunda gari ya waye take ta yawan fitsari dai take tayi banfi awa biyu da zuwaba fa, amma tayi fitsari yakai sau bakwai”. Ahankali Momy tace. “Ikon Allah toh kuje asibiti mana”. Tana gyara zaman wayar akunnenta tace. “Eh na kira Dr na faɗa masa yace dai yanzu babu wata matsala tunda Babu abinda yake mata ciwo amma Yah Moddibo yace zai je ya faɗawa Didi yaji mai zata ce”. Cikin sauƙe Ajiyar zuciya da fargaba irin na duk wata Uwa ke shiga idan ƴarta na fama da ƙaratowan naƙudan tsohon ciki tace. “Ikon Allah toh bata wayar”. Wayar Asma'u ta miƙa mata karɓa Khausar tayi tare da faɗin. “Momy ya gajiya?”. Cikin sanyi Momy tace. “Lafiya lau Khausar meke ke damunki?”. Langwaɓar da kai tayi tace. “Momy Nifa ba abinda ke yimin ciwo”. Ahankali tace. “Toh amma kuma iya fitsarin kike?”. Kai ta gyada kana ta ɗaura hannunta ɗaya akan cikin tace. “Eh fitsarin ne kawai sai dai yanzu dana shiga ina ganin har da wani ruwa yake fito min”. “Ok ki faɗawa Dr toh”. Cewar Momy suka katse kiran. Dai-dai lokacin kuma Moddibo ya shigo bayansa Didi,Niyna Innayi ce ke biye dashi abaya cikin sauri Didi ta zauna kusa da ita hakan yasa Asma'u ta ɗan matsa gefe tace. “Ɗiyata me yake damunki?,Ba abinda yake Miki ciwo?”. Kai ta girgiza tare da faɗin. “A'a abinda yake min ciwo”. Cike da kulawa Didi tace. “Duk da haka dai mu tafi asibiti”. Kai Khausar ta gyaɗa. Nan take suka tafi asibiti kafin su isa ma Already an shirya komai. Suna isa aka karɓesu aka shirya komai kana akayi duk kan abinda ya kama na gwaje-gwaje. Bayan an gama gwaje-gwaje Dr Jameel ya fito zuwa lokacin kuma ruwan dake zuban nan zubansa ya ƙaru sosai shigowa yayi kana ya kalli Niyna ya kalli Didi kallonsa Didi tayi kana ta miƙe tabi bayansa zuwa office ɗin sa tace. “Jameel ya akayi?”. Ƙofan ya ɗan tura tare da zama kan kujera kana ta zauna gefe sai kuma Moddibo dake biye dasu yazo ya zauna gefen Didi gyaran murya Dr Jameel yayi tare da kallon Didi yace. “Kinga Didi tun cikin nan yana da wata bakwai munyi Sikaynin komai lafiya sannan ko kwanan nan bai daɗe ba still munyi Sikaynin komai lafiya”. Cikin bugawar zuciya Moddibo ke kallonsa cikin sauƙe numfashi ya cigaba da cewa. “Kuma ko yanzu ma Alhamdulillah zaman yaro lafiya to Amma kuma kinga yanzu ruwa yana ta zuba mata kuma ba alamun naƙuda tare da ita”. Numfashi Didi ta sauƙe tare da cewa. “A wannan Normal ne in dai wannan ne ruwan zaƙine”. Kai Dr Jameel ya jinjina kana yace. “Eh nima ina ga kamar Normal ne?”. Cike da gamsuwa ta gyaɗa masa kai tare da faɗin. “Eh dan nima wani lokaci yana kai kusan sati kafin naƙuda yazo ya tashi idan na ƙuda ya tashi kuma baya wuce awa ɗaya ko biyu shikenan na haihu”. Cikin rauni da tarin tausayi Moddibo ya juya ya kalleta yace. “Didi Amma ba matsala?”. Kai ta gyada tare da cewa. “In sha Allahu ba matsala wannan ana ce mishi zaƙi zaƙine yake zuba”. Numfashi Dr Jameel ya fesar kana yace. “For now dai zaƙine yake zuba amma yanzu zaku tafi gida, tunda ba haihuwar bane amma kullum da daddare kafin ku kwanta azo in duba ta saboda kada ruwan ya canza ya zama wanda yaro ke rayuwa a cikine ke zuba, amma for now ba matsala”. Hararansa Moddibo yayi tare da faɗin. “Toh munji”. Murmushi Dr Jameel yayi tare da cewa. “Ha'a Yayanmu laifin me nayi kuma?”. Murmushi Didi tayi daga nan dai suka tattara suka koma gida. Haka Khausar suka yini da Asma'u sai dai har zuwa lokacin ruwan nata zuba sai dai ba sosai yake zuba ba, da daddare bayan sunje asibiti Dr Eshaa ce ta duba ta tace in sha Allah babu wata matsalar komai kuma ba haihuwa bace... Kwance Khausar take agefen Moddibo yayin da hannunsa ke kan cikinta yana tofa mata addu'oi. Ahankali ta juya ta kallesa tare da cewa. “Yah Mu'allim!”. Idanunsa dake lumshe ya buɗe kana yace. “Na'am Minha ya akayi?meke damunki meke kiki ciwo”. Ya ƙare maganar cikin tsananin kulawa, tausayi, jin ƙai. Kai ta girgiza tare da faɗin. “Babu abinda ke yimin ciwo amma Yah Mu'allim dan Allah don darajar Annabi ka cewa Momyna tazo mana”. Cikin sauri ya miƙe ya zauna ya kalleta tare da cewa. “Meyesa kika ce haka Minha?”. Kai ta girgiza asanyaye tace. “Ni dai kawai nafi so Momyna tazo ina son ganinta kaga bata taɓa zuwa ba kuma ina so in na haihu tazo kaga ga abin na zuba kuma Dr Jameel yace in sha Allah nan da sati ɗaya zan haihu kaga ai tazo yafi”. Kai ya jinjina kana yace. “Amma dai ba abinda yake Miki ciwo ko?”. Tana riƙe tafin hannunsa acikin nata tace. “Um bakomai kawai ina so Momyna tazo kuma dan Allah in zata zo taxo min da Raudhat in yaso in na haihu kafin suna Hajja Nana ma tazo kaji ko Yah Mu'allim”. Cikin sanyi yace. “An gama Minha in Sha Allahu Momy za tazo”. Cikin jin daɗi tace. “Yaushe za'a faɗa mata?”. Kallon haɗeɗɗen agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa yayi ganin 10pm yayi ya sanya shi sauƙe numfashi yace. “Kinga karfe goma tayi sai gobe zan faɗa mata”. Marairaice fuska tayi tare da cewa. “Um-um Yah Mu'allim a faɗa mata yanzu mana”. Kai ya girgiza kana yace. “Minha idan na faɗa mata yanzu kinga dai lafiyarki lau, toh Amman in taji zatayi zaton baki da lafiya ne karshe muzo mu hanata bacci”. Idanunta ta narkar acikin nasa tare da cewa.. “A'a Yah Mu'allim baza ta tsorata ba ai zanyi waya da ita zata fahimta”. Sake kallon agogo yayi yace. “Mu dai bari har sai da safe”. Kamar za tayi kuka tace. “Ni dai Um-um mu faɗa mata yanzu”. Ganin yanda ta damu yasa yace. “Toh shikenan”. Ya ƙarashe Maganar tare da ɗaukar wayarsa yayi dearlin number mommy. A can Nigeria kuwa dai-dai lokacin Momy ce tare da Amina zaune a falonta cikin sanyi Amina tace. “Momy kinji ɗazu an kirani ko?”. Kai Momy ta gyaɗa tare da cewa. “Eh Amina naji". Cikin fesar da numfashi da kuma yanda nutsuwa da nadama ya baibaye rayuwarta tace. “Kin san waye ne ya kirani”. Cikin sanyi gami da rauni ta gyara zamanta tare da faɗin. “Baban Samira Sani ne fa yazo wajena”. Da mamaki Momy tace. “Kai haba dai?”. Araunane ta gyaɗa kanta tare da cewa. “Wallahi”. Ajiyar zuciya Momy ta sauke tace. “Lafiya dai?”. Kanta ta sunkuyar ƙasa idanunta na ciko da ruwan hawaye tace. “Wai cewa yayi yana sona zai Aureni”. Shiru Momy tayi kana ta ronƙofar da kanta kafin sai kuma ta ɗago kanta ta kalleta. Amina kuwa cikin sanyi ta cigaba da cewa. “Momy nikam kuma da zama hakan nan tunda ya sanni kawai zan Aureshi kawai yafi min tunda tuntuni na gama iddah kuma babu wanda yake zuwa wajena”. Cike da tausayinta Momy tace. “In dai har kin gamsu kinga zaki Aureshi ai babu laifi, tunda dama mun sanshi mutum ne mai mutunci da kamala da daraja”. Tana wasa da yatsun hannunta tace. “Hakane kam Momy kuma ma kinga ya bada hujjan cewa zamu zauna cikin aminci, tunda dama nida Samira mun saba zanje in zauna in maye mata gurbin Mahaifiyarta sannan kuma muyita mata addu'a Allah ya fito mata da mijin Aure na Alkhairi ”. Kai Momy ta jinjina cike da gamsuwa tace. “Toh shikenan Amina Allah ya tabbatar da abinda yafi Alkhairi ”. Ahankali tace. “Dama shine nace bari na faɗa Miki saboda ki faɗawa Abbana, nikam na yarda shiɗin in Aureshi dama Momy Ni yanzu waye zai kalleni ya Aureni in ba tsohon ba?”. Cikin kwantar mata da hankali Momy ta ɗan muskuta tare da cewa. “Bakomai Amina in Sha Allahu zan faɗawa Abbanku Allah kuma ya sanya Alkhairi kuma ai mutum ne mai mutunci”. Cikin sanyi Amina tace. “Ameen ya Allah”. Suna cikin hiran ne kira ya shigo wayarta da mamaki tace. “Toh Moddibo kuma”. Sai kuma ta amsa kiran ta kai kunnenta tare da faɗin. “Assalamu Alaikum ”. Anutse Moddibo yace. “Wa'alaikum Salam Barka da dare Momy kina bacci na tashe ki ko?”. Murmushi tayi tare da faɗin. “A'a idona biyu muna hira da Amina ce ma”. Kai ya gyaɗa yana shafa cikin Khausar yace. “Masha Allah”. Sai kuma yayi shiru cike da kulawa tace. “Lafiya kuwa Moddibo?,Me yake faruwa faɗa min mana?”. Kansa ya sunkuyar ƙasa tare da ɗagowa ya kalli Khausar sai kuma ya maida hankalinsa kan wayar yace. “Momy Khausar ce kin san yau tun da safe”. Sai kuma yayi shiru ya rasa ta ina zai fadi maganar. Ganin haka ne yasa Khausar ta karɓi wayar tasa akunnenta tare da faɗin. “Momy”. Cikin sauƙe ajiyar zuciya Momy tace. “Na'am Mamana lafiya kuwa?”. Murmushi tayi tare da cewa. “Lafiya lau Momy?”. Tana ɗan jingina da jikin kushin momy tace. ”Toh me yake faruwa?”. Tana gyara zamanta tace. “Bakomai fa Momy kinga yau munje asibiti an duba ance ba matsalar komai, kuma in sha Allahu nan da sati ɗaya ko kwana biyar zan haihu shiyasa nake so ki tambayi Abba in ya barki kizo”. Da damuwa Momy tace . “Amma dai kin tabbatar Babu komai”. Idanunta ta lumshe tare da buɗe su akansa tace. “Allah Momy ba komai kawai dai ina so kizo ne kuma dan Allah Momy kizo da Raudhat yanzu ki tura mana hoton Passport ɗinki amiki booking”. Murmushi Momy tayi tare da cewa. “Da gaggawa haka Mamana?,Ba dai abinda kike ji?”. Kai ta gyaɗa tare da faɗin. “Bafa abinda nake ji” Cikin ɗan radaɗine Mommy tace. “Ok toh shikenan zan faɗawa Abbanku idan ya amince zanzo, tunda ga Amina da sauƙi zata zauna da ƙannen ku kafin mu dawo”. Tana ɗan lumshe Idanunta tace. “Toh shikenan Momy ina Aminan?,Ki bata mu gaisa”. Momy na ƙoƙarin miƙa wa Amina wayar tace. “Gata nan”. Jin Amina ta karɓi wayar Khausar tace. “Amina ina yini”. Asanyaye Amina tace. “Lafiya Khausar ya gida ya labarin Addah Asiya ”. Khausar na jinginar da kanta kafadarta Moddibo tace. “Munyi waya ma tace kwanan nan zasu zo hutu akwai bikin abokinsa da za'a yi zasu zo”. Ahankali Amina ta gyara zaman wayar akunnenta tare da cewa. “Allah ya kawo su lafiya ya jiki?”. “Alhamdulillah”. Cewar Khausar tana lunshe idanu. Cike da kulawa Amina tace. “Toh Allah ya raba lafiya”. Daga nan sukayi sallama. Nan take Momy ta mike taje ta faɗawa Lamiɗo ba gardama Lamiɗo ya amince tare da yi mata fatan Alkhairi kana ya fara yi mata booking ɗin tafiya cikin ikon Allah ya ga nan da kwana huɗu akwai jirgin da zai tashi daga Abuja zuwa Morocco direct cikin Rabat zai sauƙa nan take yayi mata komai da komai a online kasancewar ranan juma'a ce kuma jirginsu zai tashi ranan Laraba Ranan Lahadi da yamma Khausar da Moddibo ne zaune a Falon Didi suna hira Ahankali ta yunƙura ta miƙe jin kamar tana jin fitsari ta nufi bedroom ɗin Rahama cak ta tsaya tare da juyawa ta kalli Didi dake cewa. “Ha'a lafiya?”. Ganin wani ruwa daya tsinko mata yake bin ƙafafunta cikin sauri Moddibo ya matso kusa dasu tare da cewa. “Lafiya?”. Kallon Didi tayi kana ta kalli Innayi sai kuma ta maida kallonta kan Moddibo da damuwa ya bayyana asaman fuskarsa Ahankali tace. “Nima ban sani ba”. Cikin wani irin yanayi Moddibo yace. “Ya salam”. Ganin yanda ruwan ke gudu akasa cikin sauri Didi tace. “Ɗaukwta mu tafi asibiti” Da sauri ya ɗauketa ya sata Amota Didi na gidan gaba tare da Ibraahim dake mazaunin Driver sai kuma Moddibo dake rungume da Khausar baya. Sai kuma ɗaya motar da hadimai ne aciki sai Innayi da Niyna da kuma jakadiya direct suka nufi asibiti. Bayan anyi mata gwaje-gwaje bayan wani lokaci Dr Eshaa ta fito tare da Kiran Didi bayanta Didi tabi cikin sauri Moddibo yabi bayanta yana cewa. “Dr Lafiya meke faruwa?”. Zama tayi akan kujeranta tare da kallon Moddibo sai kuma ta kalli Didi tace. “Toh gaskiya da farko dai ba muyi tunanin haihuwar Nan zai zo da gardama haka ba saboda komai naga da baby lafiya lau Toh amma kuma daga ɗazu zuwa yanzu ruwan da yaro yake rayuwa aciki ne yake zubowa wanda kwata-kwata naƙuda bai tashi ba bare ta iya haihuwa dole sai an nata C'S”. Cikin sauri gami da wani irin azabebben bugawan zuciya Moddibo ya dafe kansa tare da cewa. “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Theater Kuma?". Cikin sauri da son kwantar masa da hankali Dr Eshaa tace. “Bakomai fa ai Theater ba wani abu na tashin hankali ko kiɗima bane”. Still hannunsa na dafe da kansa yace. ”Allah ko?”. Kai ta jinjina cikin tabbarwa tace. “In sha Allahu bakomai babu abinda zai faru sai alkhairi wasu ma da yawa basu bari suyi naƙuda kawai sai ayi musu Theater”. Cikin sauri da damuwa Didi tace. “Toh yanzu yaushe za'a Theater?”. Juyawa tayi ta kalli agogon hannunta kana ta maida kallonta kan Dr Jameel dake shigowa cikin sauƙe numfashi ya gyara tsayuwar sa tare da cewa. “Gaskiya Theater zai kai kamar ƙarfe biyu na ranan gobe za'a yi”. Cikin Jimami Didi tace. “Toh amma ba matsala zuwa goben ko?”. Kai ya gyaɗa yana gyara zaman farin glass ɗin idanunsa tare da cewa. “Eh in Sha Allahu bakomai saboda ba wani ciwo take jiba ruwan ne dai kuma already kafin lokacin zai ɗan ƙara sa zubowa ne gaba ɗaya zai kuma iya riƙe yaron”. Still da damuwa atare da ita tace. “Allah ya kaimu lokacin”. Sai kuma ya ƙarasa gefen Moddibo ya dafa kafadarsa ganin kamar duk ya rikice cike da kulawa ya ɗan bubbuga tare da cewa. “Eh in Sha Allahu ba komai sai alkhairi ”. Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace. “Toh amma babu matsala zan iya sanar mata C's za'a yi mata ”. Kai Dr Jameel ya gyada tare da cewa. “Of Cause ya kamata ka faɗa mata sannan ka kwantar mata da hankali. Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da fita kana ya ciro wayarsa tare da dearlin number Mommy Jin ta ɗaga yasa cikin sanyi yace. “Momy yaushe Jirginku zai taso?”. Ahankali tace. “Yanzu ma ina Abuja idan Allah ya kaimu gobe Jirginmu 9:00 zai tashi”. Cike da girmamawa yace. “Toh Momy Allah ya kaimu”. Da ɗan damuwa atare da ita tace. “Lafiya dai Babana”. Kai ya gyaɗa kana yace. “Lafiya lau dama naƙudan ne ya tashi kuma ance”. Sai kuma yayi shiru shin ya faɗa mata C's za'ayi wa ɗiyarta, Sai kuma ya katse mgnar sabida tunanin kada ya faɗa mata ya tsinka mata zuciya tare da tayar mata da hankali da sauri Momy tace. “Ance me?”. Da sauri yace. “A'a ance ba matsala in Sha Allahu yanzu haka ma muna asibiti”. Anutse tace. “Masha Allah yanzu ina Khausar ɗin?”. Yana gyara tsayuwar sa yace. “Ni ina office ɗin Dr ita kuma tana ɗakin da aka kwantar da ita tare da Innayi da Niyna Ni kuma ina tare da Didi”. Cikin sauke numfashi tace. “Toh abawa Didi”. Miƙa wa Didi wayar yayi Didi tace. “Maman Khausar ”. Cikin sanyi Momy ta gyaea zaman wayar akunnenta tare da cewa. “Na'am ya gida ya yara?”. “Lafiya lau Alhamdulillah ya hanya”. Cewar Didi Momy kuwa Ahankali tace. “Ya jikin ƴar taki”. Didi na kallon Moddibo da idanunsa ke lumshe kana ta maida hankalinta kan wayar tare da faɗin. “Ba damuwa Maman Khausar in Sha Allahu ki kwantar da hankalinki gobe kina isowa Mai gidanki ko Amarya na bisa hanya”. Cikin jin karfin gwiwa tace. “Toh Allah ya kaimu rai da lafiya ”. Cikin kwantar mata da hankali Didi tace. “Kiyita mata addu'a Allah ya kawo mata da sauƙi”. Kai Momy ta jinjina tare da cewa. “In sha Allahu ina mata kuma zan cigaba dayi mata”. Daga nan sukayi sallama bayan sun fito office ɗin Dr Jameel Moddibo ya wuce ɗakin da Khausar ke ciki. Yana shiga ya hangota kwance akan gado tayi shiru Ahankali ya ƙara sa ciki kana ya riƙo hannunta tare da cewa. “Minha”. Idanunta ta ɗago ta kallesa kana tace. “Na'am”. Yana matsa hannunta dake cikin nasa yace. “Minha Me yake Miki ciwo?”. Ajiyar zuciya ta sauƙe kana ta jujjuya masa kai tare da cewa. “Babu inda yake min ciwo Yah Mu'allim ”. Ahankali ya zauna bakin gadon tare da janyo hannunta ya daura kan cinyarsa kana ya cire pillow ya ɗaura kanta akan cinyarsa yace. “Minha naƙuda akwai zafi ko?”. Idanunta ta zuba masa sai kuma ta girgiza kai tare da cewa. “To ai ban fara bama Yah Mu'allim bare inji?”. Murmushin karfin hali yayi kana yasa ya tsansa yana kwantar da gashin girarta tare da faɗin. “Toh ai ma bazan bari kiyi naƙudan ba”. Cikin sauri tace. “Toh ai Yah Mu'allim ance dole sai mutum yayi naƙuda kafin ya haihu”. Cikin rauni da rawar murya ta ƙare maganar lokacin ɗaya tsoro da fargaba ya mamaye mata zuciya. Cikin sauri ya tallafota kanta tare da manna mata kiss agoshi yace. “Bakomai kinga yanzu muka gama magana da Dr Eshaa ai kinsan Momy ma Theater akayi mata a haihuwar Ramadan da Raudhat ko?”. Cikin sauri ta gyaɗa masa kai tare da cewa. “Eh”. Yana shafa kanta yace. “Momy bata taɓa faɗa Miki cewa ba wahala ba?”. Cikin lumshe idanu ta fesar da sanyayyar numfashi tare da faɗin. “Haka dai take cewa haihuwa yafi Theater wuya”. Sake janyota jikinsa yayi kana yace. “Toh shiyasa na zaba Miki mai sauƙi Minha ayi C's kawai lafiya lau kar wani abu ya samu Babynmu ya cutar dashi”. Da sauri ta ɗaura hannunta akan cikin ta shafa tare da cewa. “Yah Mu'allim”. Cike da tsantsan so da kulawa yace. “Na'am amma dai ai Baby lafiyarsa lau kina jin motsinsa?” Dai-dai lokacin tayi saurin kamo hannunsa ta ɗaura akan cikin tace. “Kaji yanzu ma yana motsi ko?”. Kai ya jinjina tare da cewa. “Tabbas naji Allah ya mishi albarka ya kawo shi kafiya”. Kallonsa tayi cikin sanyi ta langwaɓar da kanta kana tace. “Amma Yah Mu'allim ai Theater ma da zafi”. Ɗan ware idanunsa yayi cikin son kwantar mata da hankali yace. “Inji waye ba wani wuya munyi magana da Dr Eshaa, tace ayi Miki Theater kin san itama tana sonki bata so ki wahala, kuma itama Didi tace ayi kiki Theater yafi sauƙi”. Dai-dai lokacin Didi ta shigo tana shiga ta riƙe hannunta tare da kallonta tace. “Kada kiji tsoron Theater ba komai ɗiyata ai kinga Lalla Hafsat ma, haihuwar Hakeem ɗin ta Theater akayi mata kuma gashi nan lafiya lau itama lafiya lau kuma bayan shi duk yaranta da kanta take haifarsu”. Shiru tayi tare da lumshe idanunta. Cikin jin sanyi tace Didi taci gaba da cewa. “Ki kwantar da hankalinki in Allah ya kaimu gobe za'a yi Miki Theater”. Idanunta ta lumshe tare da cewa. “Toh Allah ya kaimu bisa rai da lafiya ”. Sai kuma ta maida kallonta kan Didi tace. “An faɗa wa Momy na”. Kai ya jinjina yace. “Eh an faɗa mata gobe-gobe ma tana hanya in Sha Allahu yanzu ma haka tana Abuja kafin a shiga dake Theater jirginsu zai iso”. Ahankali tace. “Toh Allah ya kawo ta lafiya”. Ameen ya amsa dai-dai lokacin kuma Dr Jameel da Dr Eshaa suka shigo. Khausar na kallon Dr Jameel tace. “Dr kuma zamu koma gida ne ko kuma zamu yita zama anan ne?”. Hannunsa na cikin aljihu yace. “Eh zaku zauna anan saboda ki kasance cikin kulawarmu”. Kai ta jinjina cikin gamsuwa. Dai-dai lokacin Asma'u kuma ta shigo, ganin Khausar ɗin zaune ras ana hira da itane yasata saki ajiyan zuciya tare da zama gefenta. Daga nan sukaci gaba da hira kamarsu saboda bata jin komai. *Masu son Maganin infection da maganin mata, ku marmatso wannan account no in ne naku ta ciki zaku turo kuɗin ku 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, Sai ki turo shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER'N na 08069423567. akwai sabbin kaya masu zafi suna nan Available ki turo kuɗinki a saki cikin lissafi. Kayanen mata masu zafi sadidan daga Chadi akwaisu Garukan daka, gumbunan, Tsumummuka, cida Ciccibi Abodi cida kaza ci da jan nama kwanon ƙasaitacciyar mace butar sirri, furar mata, gumbar madara Gumbar kolli mai ƙyallin al'khairi gumbar uku al'khairi, gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, gumbar riɗi, garin maɗi garin melɗamhi garin ilanwaddihi garin mallaka, tsumin riɗi tsumin tsirtai tsumin kinfi budurwa, tsumin riɗi, tsumin ta baje Sabaya, haɗin sabon budurci 40k matsin maliƙi mai masifar matse mace matsin daɗi har maɗiga, mai ɗan kare kyau. Kullacar sirri al'ajabu shu'umar Humra, da duk sauran kayan ƙamshi. Haɗin amarya budurwa ko bazawara haɗin mai jego ko uwar gida, akwaisu Available set ɗinmu hawa hawane akwai manya akwai ƙananan, ƙanan daga 40k ne 35k 30k 25k 20k 15k 10k 5k shine ƙarami haɗina na karshe sai kuma haɗin kwanon ƙasaitacciyar shi 7k ne shine ƙarshen haɗina kenan... Manyan set ɗin kuma daga 50k 60k 70k 80k 90k 100k ke zaki faɗi haɗin nawa kikeso anyi miki kana kimin bayanin yadda kikeso da matsalarki ni kuwa nasan abinda zan haɗa miki, ina araha kam amman ina hana bashi* By *GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH Book 3 PAGE 7* NA *Aysha Aliyu Garkuwa* *Masu son Maganin infection da maganin mata, ku marmatso wannan account no in ne naku ta ciki zaku turo kuɗin ku 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, Sai ki turo shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER'N na 08069423567. akwai sabbin kaya masu zafi suna nan bisa hanya, ki turo kuɗinki a saki cikin lissafi. Kayanen mata masu zafi sadidan daga Chadi akwaisu Garukan daka, gumbunan, Tsumummuka, cida Ciccibi Abodi cida kaza ci da jan nama kwanon ƙasaitacciyar mace biyar sirri, furar mata, gumbar madara Gumbar kolli mai ƙyallin al'khairi gumbar uku al'khairi, gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, gumbar riɗi, garin maɗi garin melɗamhi garin ilanwaddihi garin mallaka, tsumin riɗi tsumin tsirtai tsumin kinfi budurwa, tsumin riɗi, tsumin ta baje Sabaya, matsin maliƙi mai masifar matse mace matsin daɗi har maɗiga, mai ɗan kare kyau. Kullacar sirri al'ajabu shu'umar Humra, da duk sauran kan ƙamshi. Haɗin amarya budurwa ko bazawara haɗin mai jego ko uwar gida, akwaisu Available set ɗinmu hawa hawane akwai manya akwai ƙananan, ƙanan daga 40k ne 35k 30k 25k 20k 15k 10k shine ƙarami haɗina na karshe sai kuma haɗin kwanon ƙasaitacciyar mace shi 7k ne shine ƙarshen haɗina kenan... Manyan set ɗin kuma daga 50k 60k 70k 80k 90k 100k ke zaki faɗi haɗin nawa kikeso anyi miki kana kimin bayanin yadda kikeso da matsalarki ni kuwa nasan abinda zan haɗa miki, ina araha kam amman ina hana bashi* Haka dai yinin ranan Didi suka yini da ita kana suka kwana Asma'u kuwa sai da Dr Jameel ya gama duty inda suka tafi tare da barin Dr Esha. Washe gari da sassafe Asma'u ta zo hannunta riƙe da wani madaidaicin Basket Dake ɗauke da Warmer masu kyau bisa ga duk kan alama abinci ne tayi kana kafadarta maƙake da waya ta ƙara sa shiga ɗakin alamar waya take yi sai kuma tace. “Eh Ummi gata nan ma yanzu na shigo”. Ta ƙare maganar tare da miƙa wa Khausar wayar kana ta ajiye Basket ɗin hannunta tana mai gaida Moddibo dake magana da Dr Jameel. Khausar kuwa cikin sanyi tace. “Ummi” Cike da kulawa Ummi tace. “Khausar lafiya dai kike jin jikin ki ba abinda yake Miki ciwo?”. Kai ta gyaɗa kamar tana gabanta tare da cewa. “Ummi ba abinda. Yake min ciwo fa”. Cikin jin sanyi da tausayinta Ummi tace. “Toh Allah ya rabaku lafiya ”. Tana ɗan lumshe Idanunta ta gyara zamanta tare da cewa. “Ameen ya Allah Ummu kuyi min addu'a”. “In sha Allahu muna miki kuma zamu ci gaba daya miki yanzu ma mukayi waya da Momynki tace min yanzun jirginsu zai tashi”. Juyawa Khausar tayi ta kalli agogon wayanta tare da cewa. “Yanzu ma ai sun tashi tun da gashi har tara da rabi kuma tara dai-dai ma jirginsu ya tashi”. Cikin sauƙe numfashi Ummi tace. “Toh Allah ya kawo su lafiya”. Ameen ta amsa suna cikin waya da Ummi taga kiran Hajja Nana ya shigo ta wayarta cikin sauri ta miƙa wa Asma'u wayarta kana tayi picking nata takai kunnenta atake muryan Hajja Nana ya ratsa kunnenta tana cewa. “Khausar”. Ahankali Khausar tace. “Na'am”. Cike da so irin na Kaka da Jika Hajja Nana tace. “Ya jikin naki?”. Tana ɗan lumshe Idanunta ta gyara zamanta tare da cewa. “Da sauƙi”. Cikin sauke ajiyar zuciya Hajja Nana tace. “Jiya mukayi waya da Momy take cewa baki jin daɗiba ma tana kan hanya zata zo”. Kai ta gyaɗa tana kallon Asma'u dake cire warmers cikin Basket tace. “Eh lafiya lau ba abinda ke damuna Hajja Nana amma wai ance Theater za'a min”. Cikin son kwantar mata da hankali kana da son sama mata nutsuwa tace. “A'a kada ki damu ki kwantar da hankalinki ai Theater ba abinda yake yi nima in Sha Allahu da izinin Ubangiji zanyi ƙoƙari in zo”. Murmushin tayi cikin jin daɗi ta gyara zamanta tare da cewa. “Allah ya kawo min ke lafiya Allah yasa ki same ni araye”. Cikin rashin walwala Hajja Nana tace. “Wani irin magana ne wannan in Sha Allahu ma araye zan sameki kar ki karya min zuciya”. Murmushi tayi tare da faɗin. “Toh Allah ya kawo ki lafiya”. Ameen ya Allah ta amsa kana sukayi sallama. Kallonta ta mayar kan Moddibo dake riƙe da hannunta cikin rauni yace. “Kina so ki karya min zuciya ko Minha? wani irin kalma ne kike faɗa haka”. Ɗaya hannunta ta ɗaura akan nasa tare da cewa. “Bakomai Yah Mu'allim”. Dr Jameel kuwa kallon Asma'u dake tsaye gefensa yayi wacce tunda ta cire Warmers cikin Basket bata zauna ba yace. “Toh ki zauna mana”. Ahankali tace . “Toh bari in sa mata abinci”. Idanunsa ya zare tare da cewa. “Dear wa yace Miki idan za'a yiwa mutum Theater yana cin abinci ai baza taci abinci ba sai bayan an fito da ita”. Kallonsa Khausar yau cikin langwaɓar da kai tace. “Kuma wallahi yunwa nake ji Dr”. Idanunsa akan Asma'u yace. “Ki ƙara haƙuri in Sha Allahu ana fito dake ba daɗewa zaki samu ki ɗanci wani abu”. Rau-rau tayi da Idanunta tare da faɗin. “Toh shikenan”. Bayan zuwan Asma'u ba daɗewa Niyna da Innayi suka iso wanda hakan yasa Didi ta samu ta koma gida tayi wanka ta sake shiryawa. 12:30pm dai-dai suka fito da niyyar komawa Asibitin wanda kuma yayi dai-dai da Jirginsu Ummu ya kusa sauƙa hakan yasa tace da Ibraahim dake driving ya wuce da ita Airport kana sai motar Hadimai dake biye dasu wanda sun kai huɗu motar Ajere-Ajere suke tafiya motar Hadimai ɗaya agaba saina su Didi sai kuma sauran ukun abaya ƙarfe 1:05pm dai-dai suka shiga cikin airport Akuma dai-dai lokacin jirginsu Momy yayi Landing. Bayan Fasinjoji sun fiffito Momy ta fito hannunta riƙe da Raudhat yayinda wani yaro daga cikin ma'aikatan wurin ke gabanta da troling su. A hankali take tafiya tana ɗan jujjuya ido alamar tana neman ta inda zataga fuskantar da ta sani, sai kuma tayi saurin juyawa jin Raudhat na cewa. “Oyoyo Didi Yah Ibraahim Oyoyo”. Murmushi Momy tayi kana tace. “A'a gasu can ma”. Ibraahim kuwa sunkuyawa yayi tare da buɗewa Raudhat hannu da gudu tajeta ta rungumesa tare da cewa. “Ina Addah Khausy?”. Yana ɗan Sharking ɗin hannunsa acikin nata yace. “Addah Khausy na asibiti”. Cike da zumuɗin son ganinta tace. “Toh mu tafi inganta ina son ganinta ”. Miƙewa yayi tana riƙe hannunta yace. “Toh shikenan ”. Cikin sassarfa Didi ta rungume Momy tare da cewa. “Momyn Khausar Barka da zuwa”. Fuska ɗauke da Murmushi Momy tace. “Barka dai ya mai jikin?”. Suna tafiya Didi tace. “A'a Alhamdulillah mai jiki tana can anata hira da ita amma yanzu nan da minti arba'in za'a shiga da ita sai muyi ƙoƙari mu tafi asibiti kafin a shiga da ita”. Momy ta gyaɗa kai tare da cewa. “Toh shikenan”. Daga nan suka shiga motoci Madadin su wuce gida kai tsaye asibiti aka wuce dasu. Dai-dai lokacin kuma Lalla Khadijah da Rahma ne da Asma'u ke tare da Khausar, cikin kulawa Lalla Khadijah ke kallon Khausar ɗin jin yadda tayi mgnar a yunwace. “Ayyah Rahma kije ki tambayi Dr Jameel, zan iya shan tea ne”. Cikin kula Rahama tace. “Ai ɗazuma naje Lalla Khausar cewa yayi ki ɗan ƙara haƙuri”. Gyara zama Lalla Khadijah tayi tare da cewa. “Kiyi haƙuri ko Khausar ba komai zuwa yamma dai zaki samu kici wani abu”. Ɗan kwaɓe fuska tayi tare da kallon Asma'u dake cewa. “Toh ni bari inje in kira Dr suzo su shiga suyi mata mana ta samu taci abinci”. Ta ƙare maganar tana fita. Su Momy kuwa da Didi tafe suke suna hirarsu, duk da dai duk karfin hali suke. Raudat kuwa sai surutu take zubawa Ibraahim. Acan asibitin kuwa lokacin da Asma'u take ta kira Dr zuwa lokacin 1:30pm yayi, haka yasa suka fara shirya komai, nan da nan suka gama shirya komai da komai na asibiti kasancewar ƙarfe 2:00 dai-dai za'a shiga da ita ahankali Dr Eshaa ta shiga ɗakin hannunta riƙe da wani riga da hula irin wanda ake sawa idan za'a shiga da mutum ɗakin C's miƙa mata rigar tayi tare da cewa. “Gashi zakisa wannan ɗin”. Kai Khausar ta gyaɗa tare da karɓa kana ta juya ta kalli Moddibo cike da tarin ƙaunarta da kuma tausayinta Moddibo yace. “Insa Miki ne?”. Langwaɓar da kanta tayi tana rau-rau da Idanunta tace. “Nikam tsoro nake ji zuciyata bugawa take Yah Mu'allim”. Kamota yayi kana ya ruggumota jikinsa cikin wata amintacciyar murya mai cike da jin ƙai da tausayi yace. “Bakomai Minha, ba abinda zai sameki sai alkhairi kinji ko Minha”. Ya ƙarashe Maganar cikin sanyi haka nan yake jin jikinsa ya mutu kana zuciyarsa na tsinkewa ya rasa mai yake masa daɗi a duniya. Ganin haka yasa Dr Jameel da Dr Eshaa juyawa suka fita Ahankali Asma'u ta yunƙura da niyyar fita da sauri Khausar ta riƙo tsintsiyar hannunta tare da cewa. “Asmeey ina zaki je?,Ki tsaya mana”. Cikin rauni da karyewar zuciya Asma'u ta kalleta kana tace. “Khausar abinda kike faɗa yana tayar min da hankali ance Miki bakomai a Theater Nan Amma sai wasu maganganu kike masu tarwatsa lissafi da hargitsa mana nitsuwa”. Araunane ta sunkuyar da kanta tare da cewa. “Toh ya za muyi da abinda Ubangiji ya tsara mana Asma'u”. Cikin ƙarfafa mata gwiwa tace. “In sha Allahu Alkhairi Ubangiji ya rubuta mana”. Kallonsu tayi sai kuma tace. “Hmmm Allah yasa”. Asanyaye Asma'u tace. “Ameen”. Shiru ɗakin yayi na wasu mintuna katse shirun Khausar tayi ta hanyar cewa. “Gashi kuma har yanzu Momyna bata zoba”. Kallon time Asma'u tayi tare da faɗin. “Ai zata zo kafin a shiga dake in Sha Allahu yanzu naji Didi na waya da Innayi tana cewa sun taho asibiti”. Sake jingina bayanta da jikin Moddibo tayi kana tace. “Allah ya kawo su lafiya ta ganni inganta koda ma na karshene waya sani!?”. Cikin sauri Moddibo ya sake janyota jikinsa ya rungumeta haka nan yaji wani irin rauni tausayi jin ƙai baisan lokacin da shesh-sheƙan kuka ke taso masa daga ƙasa ba yace. “Minha meyesa?”. Kai ta girgiza tare da cewa. “Bakomai fa Yah Mu'allim”. Haka yaita rarrashinta tare da kwantar mata da hankali yace. “Bakomai Minha babu abinda zai sameki sai alkhairi lafiya za'a shiga dake afito dake lafiya”. Ɗan Murmushi tayi tare da cewa. “Ameen Yah Mu'allim in Sha Allahu ya Mu'allim na daina damuwa amma ina neman yafiyarka iya tsawon rayuwar da mukayi tare tun daga makaranta har zuwa dana kasance ƙarƙashin Inuwar Aurenka idan akwai abinda nayi maka ka yafe min kayi min aikin gafara”. Cikin sauri ya sake ƙanƙameta ajikinsa kana yace. “Babu abinda kika yimin Minha. Ni kuma me zakiyi kin aduniya Ni babu abinda kika yimin kuma koma akwai na yafe miki duniya da kiyama”. Kanta ta sake mannawa da ƙirjinsa tare da cewa. “Nagode Yah Mu'allim”. Ahankali Dr Eshaa ta sake turo ƙofar ta shigo tare da kallon Moddibo tace. “Asa mata rigar yanzu fa sauran minti goma a shiga da ita kunga har 1:50 yayi”. Kai ya gyaɗa kana ya cire mata rigar jikinta ya zira mata na asibitin sai kuma ya tsugunna ya zare mata skintied dake jikinta ya cire ya ɗaura akan gadon da take kwance ya riƙo hannunta yayin da ƙafanta ke sanye cikin wani takalmin roba mai taushi Ahankali ya kama gashin kanta ya nannaɗe kana ya tura acikin hular rigar sai kuma ya sakar mata da lallausan murmushi yace. “Kin kuwa ga yanda kika yi kyau cikin kayan nan kuwa?”. Murmushi tayi tare da cewa. “Hmmm”. Matsowa jikinta yayi tare da tallafo kanta ya manna da ƙirjinsa kana ya mata kiss agoshi yace. “Kinyi kyau sosai tare dani za'a shiga ayi Theater dake kinji Minha”. Kai ta gyaɗa tare da faɗin. “Toh Yah Mu'allim”. Yana ɗan janta jiki yace. “Ana Miki Theater za'a cire mana ɗan mu kina gani muna hira”. Saurin kallonsa tayi sai kuma ta zaro idanunta tace. “Yah Mu'allim wani irin Theater ne ina kallo”. Yana matsa hannunta acikin nasa yace. “Kawai za'a Miki alluran kashe zafi ne sai ayi Theater kina ji kina gani muna kuma hirarmu Yah Mu'allim ɗinki a kusa dake”. Cikin sauri ta girgiza masa kai idanunta na tara hawaye tace. “Um-um nikam bana son wannan Yah Mu'allim a cire min hankalina kawai ayi min Theater”. Ganin alamar hankalinta ya fara tashi ya sassauta murya tare da cewa. “Haka kike so?”. Kai ta gyaɗa dai-dai lokacin Dr Jameel ya karaso yace. “Bakyaso amiki kina kallo?Idan kina so na sai a jawo Mirror a sama Anuna Miki kina kallo”. Da sauri ta runtse idanunta tare da manna kanta a dantsen hannun Moddibo tace. “Nikam ina tsoro nice zan tsaya har acire ɗa ajikina?,Nikam bana so wallahi Dr Jameel kawai dai ayi min alluran da zai cire min hankalina gwara ayi min shi ina bacci in na farfaɗo in ganni da yaro na”. Moddibo na shafa bayanta ya kalli Dr Jameel tare da cewa. “Ayi mata yanda take so” Kai Dr Jameel ya Jinjina kana yace. “Toh shikenan ba matsala haka za'a yi mata” Fita sukayi dai-dai lokacin kuma su Momy suka shigo cikin sassarfa taje ta rungume Momy. Momy kuwa cikin sauri ta lumshe Idanunta jin hawaye na tsats-tsafowa cikin sanyi da rauni tace. “Ubangiji Allah ya rabaku lafiya Khausar Allah yasa ayi aikin nan cikin lafiya akan alkhairi Allah ya fitar dake lafiya ". Araunane ta kalli Momy tare da faɗin. “Ameen ya Allah Momy Allah ya amsa kiyita min Addu'a Momyna kiya femin idan akwai abinda na taɓa yi Miki na cutar wa ko ɓacin rai”. Da ɗan sauri Momy ta mari kumatunta kadan kana tace. “Me kikayi min?,Ni babu abinda kika yimin Mamana Ubangiji Allah ya fito miki dashi da sauƙi”. “Ameen ya Allah” ta faɗa tare da sakin Momy jin muryan Raudhat wacce suka shigo da Ibraahim da sauri ta risina ta rungumo Raudat cike da farin cikin ganinta Raudat tace. “Oyoyo Addah Khausy ”. Rungumeta Khausar tayi tana Murmushi cike da farin ciki Raudat ta cigaba da cewa. “Addah Khausy wannan kayan fa”. Kallon jinkinta tayi sai kuma tace. “Raudat Theater za'a yimin”. Cikin rashin fahimta Raudat tace. “Addah Khausy menene kuma Thearter?” Ɗan murmushi tayi tare da cewa. “Abinda aka yiwa Momy lokacin haihuwar ku keda Ramadan”. Jim tayi sai kuma tace. “Toh Addah Khausy Allah ya kawo miki sauƙi da lafiya” Cikin sanyi da rauni tace. “Ameen ya hayyu ya ƙayyum”. Moddibo kuwa Ahankali ya kamo hannunta ya tsayar da ita sai kuma ya juyo da ita gaban Momy yace. “Momy ayi mana addu'a Allah ya fito damu lafiya ”. Ahankali Momy tace. “Ameen ya Allah Moddibo”. Ahankali Khausar ta sake janye hannunta ta rungume Momy sai kuma ta rungume Didi Dr Eshaa ce ta ƙaraso tare da cewa. “Lokaci yayi fa kizo mu tafi Khausar”. Cikin sanyi ta kamo hannun Asma'u. Ita kuwa Asma'u tuni take zubda hawaye hakanne yasa ta kauda kanta gefe tare da ruggumeta. Ganin hakane yasa Modibbo ya kamo hannun Khausar ɗin suka juya suka nufi cikin ɗakin. Anutse Khausar ta juya ta fara tafiya Ahankali tana waiwayen su cikin ƙarfin hali Momy tace. “Mene kike tafiya haka kamar Kazar da ƙwai ya fashewa aciki, kiyi maza kishiga ayi Miki minti nawa kin fito hankalin ki kwance Mamana kike tafiya kina sanɗa”. Juyawa tayi ta kalli Momy cikin sanyi da langwaɓar da kai tace. “Momy ba sanɗa nake bafa yunwa nake ji shiyasa bani da ƙarfi”. Jin haka yasa Moddibo ya sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa. “Shikenan toh tunda yunwa kike ji”. Ya ida maganar tare da tsugunnawa ya ɗauke ta cak kamar Baby ya rungumeta. Raudat dake kallonsu ne ta sanya dariya kana ta buga tsalle tare da faɗin. ”Iyeeee Addah Khausy kin lale kinji daɗin ki Yah Moddibo ya ɗaga ki”. Ibraahim dake bayanta ya matsa kusa da ita tare da ɗagata sama kana yace. “Toh kema kiji daɗi an ɗaga ki”. Cike da farin ciki ta riƙa ƙyalƙyala dariya tana cewa. “Addah khausy Bye bye sai kin fito”. Juyawa Khausar tayi ta kalleta kana tace. “Toh Raudy na”. Su Momy kuwa shiru kawai sukayi tare da rakasu da ido. Suna shiga ɗakin direct kan gado Moddibo ya kwantar da ita Dr Jameel kuwa gefen kanta ya tsaya yana Murmushi yace. “Mrs Mouley Ya kike?”. Idanunta akan Moddibo tace. “Lafiya”. Yana kallon Norse biyu dake tsaye gefe hannunsa riƙe da wani ɗan tiren silver yace. “Ina yake Miki ciwo?”. Baki ta Cunno gaba still idanunta na kan Moddibo tace. “Nifa babu inda yake min ciwo”. Murmushi yayi tare da faɗin. ”Masha Allah”. Sai kuma ya matsa kusa da Dr Eshaa ya miƙa mata alluran yace. “Gashi kiyi mata”. Karɓa Dr Eshaa tayi kana tayi mata. Dr Jameel kam sake matsawa kusa da ita yayi tare da cewa. “Mrs Mouley me kike ji yanzu?”. Cikin wani irin yanayi data fara tsintar kanta ta lumshe Idanunta tare da cewa. “Wani irin bacci mai daɗi nake ji Yah Mu'allim ”. Ta ƙare maganar tana sauƙe sassayan numfashi. “Masha Allah”. Cewar Moddibo yana matsa hannunta cikin nasa. Dr Jameel kam Murmushi yayi kana yace. “Asha bacci lafiya”. Ahankali tace. “Toh”. Sai kuma ta sake lumshe Idanunta tare da buɗe su ta kalli Moddibo sai kuma ta juya ta kalli Dr Jameel Ahankali ta sake kallon Dr Eshaa. Cikin wani irin murya na magagin bacci tace. “Dr Eshaa”. Cike da kulawa tace. “Na'am Mrs Mouley”. Cikin yanayin baccin dake fusgar idanunta tace. “Bacci nake ji”. Murmushi tayi tare da cewa. “Toh gaki ga Mijinki akusa dake kiyi bacci”. Ɗan jujjuya idanunta tayi tare da faɗin. “Ta ina yake?”. Da hannu ta nuna mata gefenta kana tace. “Ba gashinan kusa dake ba”. Ƙyafƙyafta idanunta dake cike da bacci tayi tace. “Ina yake ban ganshi ba bacci nake ji”. Dai-dai lokacin kuma alluran ya gama fara aiki ajikinta ta narke idanunta suka tafi luuuuu. Moddibo kuwa Ahankali ya ɗan sun kuyo kanta tare da faɗin. “Minha! Minha!! Minha!!!”. Yi tayi kamar zata buɗe idanunta kuma ta kasa kasancewar alluran ya gama game jikinta ya saki sai kuma ta buɗe idanunta cikin magagin bacci tace. “Yah Mu'allimmmmm”. Shikenan kuma sai bacci. Sake sunkuya kanta yayi tare da cewa. “Minha”. Dr Jameel dake kallonsa yace. “Kai ka daina ma kiranta allura ya fara aiki ajikinta bari muzo mu fara aikin mu”. Momy kuwa toilet dake cikin ɗakin da aka kwantar da Khausar ta shiga tayi alwala kana tayi sallar Azahar kasancewar su Didi already sun idar. Momy kuwa koda ta idar addu'a ta shiga yiwa Khausar kan Allah ya fito da ita lafiya haka ma su Didi, Innayi, Niyna ke tayi. Ahankali Moddibo ya juya ya kalli Dr Jameel tare da cewa. “Wai da kai za'a yi Theater ne?Dr Eshaa baza ta iya bane?”. Kai Dr Jameel ya jinjina kana yace. “Zata iya amma dole sai da taimakona”. Ya ƙare maganar yana kallon Norse biyu dake tsaye. Cikin sanyi Moddibo yace. “Toh shikenan”. Ahankali Dr Eshaa ta zuge zip Dake gaban rigar yanda baza aga al'amuran ta ba sai cikinta daya bayyana a fili, cike da kwarewa suka fara Thearter cikin abinda bazai gaxa minti goma sha biyar zuwa ashirin ba suka cire yaro fari ƙall kyakkyawan jariri gwanin ban sha'awa. Dr Jameel na ɗago shi ya cilla ihu Yararai-yararain alamar lafiyayyan yaro cikin sauri Dr Eshaa ta miƙa hannu zata karɓe shi sai kuma tayi saurin ja baya tana Murmushi ganin yanda Moddibo ya buɗe rigarsa ya tallafi yaron ya manna shi da jikinsa. Murmushi Dr Jameel yayi tare da yin ƙasa da murya a hankali yace “Wai kai ma ka zama Likita ne?”. Cikin matsanancin farin ciki da wani irin azabebben ƙaunar yaron daya mamaye ilahirin jikinsa yace. “Ba dole ba”. Dariya Dr Jameel yayi tare da faɗin. “Aikam toh yanzu dai a bawa Likitarmu ta gyarashi tukunna”. Moddibo na sake ƙanƙame shi jikinsa yace. “Wani gyarawa sai na kaiwa Didi ta ganshi”. Dr Jameel na saka hanglove acikin wani ɗan silver dake riƙe hannun Norse's dake tsaye yace. “Zaka kaisa amma ka bari agyara shi tukunna”. Kai Moddibo ya gyada tare da miƙawa Dr Eshaa jaririn ta amsa tare da miƙawa Norse's ɗin karɓa sukayi kana suka je suka fara gyara jaririn. Su kuwa Dr da Dr Eshaa nan take suka cigaba da aiki bayan sun gyara sun gama komai suka sa mata plaster kasancewar ba ɗinki bane atake suka ƙarasa mata komai kana suka balle wani abu daga jikin gadon ya zama dai-dai yanda suke buƙata, kana Norse's ɗinsu suka fara tura gadon yayinda ƙarin ruwan ke maƙe a hannunta. Cikin sauri Moddibo ya matso ta gefenta ganin kamar ta buɗe Idanunta sai kuma tayi saurin rufe su Ahankali yabi bayan gadon. Dr Eshaa kuwa juyawa tayi ta koma bayan Norse's ɗin dake gyara jaririn karbansa tayi ta cigaba da gyara shi da kanta... Su kuma suna fita kai tsaye wajen Didi da Momy suka nufa. Momy, Didi, Innayi, Niyna kuwa cikin sauri suka mike hangosu ta window da sukayi Norse's kuwa dakin hutu suka nufa kafin su shiga ma sun buɗe musu ƙofa kawai shiga sukayi. Akuma dai-dai lokacin Lalla Khadijah da Rahama suka shigo harabar Asibitin wanda dama sunje sun saukowa Khausar da Baby abin buƙatarsu ne. Khausar kuwa Ahankali ta sake buɗe idanunta sai kuma tayi sauri ta rufe ganin kamar Mutanen da Kai suke tsaye bada ƙafafunsu ba kasancewar har zuwa lokacin alluran bai gama sake taba Ahankali ta sake buɗe idanun tana ɗan jujjuya kanta Ahankali. Cikin wani irin matsanancin ƙaunarta da matsayin mai girma da take dashi a zuciyarsa ya matsa daf da ita ya riƙe hannunta cikin wata sanyayyar murya mai cike da aminci da sadaukarwa yace. “Minha”. Idanunta ta sake buɗe wa sai kuma ta sake rufe wa. Norse's ɗin kuwa zaman gadon suka gyara kana suka gyara mata ɗaurin ruwan dake jikinta kana suka juya suka fita. Kujeran dake gefenta ta wajen kafafunta Momy ta zauna. Moddibo kuwa kujeran dake gabanta daf da kanta ya zauna yayin da Asma'u Rahama, Lalla Khadijah suka ɗaya gefenta. Ibraahim kuwa bayan Moddibo yake tsaye Niynah da Innayi kuwa zaune suke bisa carpet dake shinfiɗe. Fuskarsu ko wannensu ɗauke da matsanancin farin ciki. Anutse Moddibo ya ɗaura hannunsa na hagu akan gashin girarta yana ɗan kwantarwa yayin da yake motsa laɓɓansa yana mata addu'a. Didi kuwa cikin sauri ta nufi waje jin Dr Eshaa na cewa. “Didi ga mai gida ya ƙara so”. Cikin sauri da matsanancin farin ciki Didi ta karɓesa kana tace. “Masha Allah Fatabarakallahu Fi Ahsanil Khaliƙin Masha Allah”. Sai kuma ta rungumesa Momy kam baki ɗaya hankalinta na kan ƴar ta. Da sauri Rahama taje ta karɓi Yaron ta zuba masa idanu tana kallon baiwar kyau da Allah ya zuba masa yaro ɓulɓul dashi fari ƙal. Rungumesa tayi tana cewa. “Alhamdulilah Alhamdulillah nayi yaro Ni zan riƙa masa wanka ina rainonsa”. Murmushi duk sukayi kana Innayi ta karɓesa ta kalla tare da miƙawa Lalle Khadijah cikin matsanancin farin ciki take masa addu'oi. Cikin matsanancin farin ciki Asma'u ta leka fuskar yaron tare da shafa kansa tace. “Baby ka wahalar mana da Maminka bazan ɗauke kaba har sai taci abinci tukunna”. Dariya suka sanya Kana Niyna ta karbi yaron sai kuma duk suka koma suka zauna akan Lallausan Darduma Asma'u kam gefenta ta koma ta zauna. Ibraahim ne ya amshi yaron tare da rugumeshi tsam a jiki yace. “Welcome to the world *Keyan*. “. Ma'ana King kenan. Murmushi Didi tayi tare da cewa. “In sha Allah kuwa”. Khausar kuwa Ahankali ta motsa laɓɓanta a hankali murya can ƙasa tace. “Yah Salam, Yah Mu'allim”. Kasancewar da sunansa ta tafi kana kuma bayan sunan Allah data kira da sunansa ta fara farfaɗo wa. Da sauri ya sunkuya kanta yace. “Na'am Minha” Still idanunta na lumshe tace. “Yah Mu'allim”. Ahankali ya sake sunkuyar da kansa daf nata har suna shaƙan numfashin juna yace. “Na'am Minha”. Hannunta ta yunƙura kamar zata ɗaga sai kuma taji ta kasa fuska ta narke tare da cewa. “Yah Mu'allim ka ɗaga min hannuna”. Dai-dai lokacin Dr Jameel ya shigo cikin sauri yace. “Kada ka ɗaga mata hannunta ka bari sai ta ɗaga da kanta” Kallonta Moddibo yayi cike da tausayi sai kuma ya gyaɗa masa kai yace. “Ki ɗaga hannunki mana Minha ai zaki iya”. Idanunta ta rufe kana ta sake buɗe su cikin narkewan murya da sanyi tace. “Yah Mu'allim ta ina kake?”. Cikin tsira mata idanu yace. “Gani nan Minha gani kusa dake”. Rufe idanunta tayi ta buɗe tare da cewa. “Ina Momy”. Cikin sauri Momy tace. “Gani nan Mamana gani nan kusa dake ki kwantar da hankalinki”. Ƙyafƙyafta idanunta tayi tare da cewa. “Yah Mu'allim ka zauna daidai mana meyesa kake zaune da kan ka?”. Da mamaki yace. “Zaune da kai kuma?”. Murmushi Dr Jameel ya masa kana ya masa alamar alluran ne bai sake taba har yanzu. Muskutawa yayi tare da faɗin. “Toh Minha na gyara”. Motsa idanunta tayi tare da cewa. “Toh”. Sai kuma ta buɗe idanunta ji tayi kamar alluran ya fara saketa ahankali ta ɗago hannunta sai kuma tayi saurin sakewa tace. “Yah Mu'allim ka tayani in ɗaga hannu na mana”. Kai ya girgiza tare da cewa. “Ki ɗaga da kanki mana”. Momy kam na zaune gefenta ta tsira mata Idanu. Didi kuwa wayane maƙale kunnenta cikin jin daɗi da girmamawa tace. “Alhamdullilah Abokinka, Amininka, Jikanka Kuma Sarki mai Jiran gado ya fito duniya”. Abualeey dake zaune cikin Fada ya gyara zamansa cike da matsanancin farin ciki yace. ”Masha Allah Alhamdulillah Allah ya raya mana shi bisa Imani”. Cike da jin daɗi tace. “Ameen”. Kana ya katse kiran. Abualeey kuwa cikin jin daɗi ya juya ya kalli Waziri, Galadima da sauran fadawa yace. “Alhamdulillah an cirewa Matar Aleeyu ɗa namiji lafiya lau ”. Cikin sauri da jin daɗi Galadima yace. “Alhamdulillah”. Waziri kuwa juyawa yayi kana yayi Sujudur Shukur tare da cewa. “Alhamdulillah abu duk yanda ake fata haka ya tabbata magauta basu sami yanda suke soba”. Kai Abualeey ya jinjina kana yace. “Idan munyi sallar la'asar sai muje asibiti Mu duba ta”. Amsawa sukayi daga nan suka ci-gaba da zaman fada. Agefen Khausar kuwa zuwa yanzu ƙarfin jikinta ya fara dawowa Sai dai har yanzu alluran bai gama saketa ba bisa duk alamu maganar da take Sambatune. Ahankali ta ɗago hannunta kana ta ɗaura kan cikinta ta shafa ɗagowa tayi ta kalli Moddibo tare da cewa. “Yah Mu'allim”. Kallon hannunta yayi tare da faɗin. “Na'am Minha”. Idanunta alumshe tace. “Ina cikina”. Juyawa yayi ya kalli Kyakkyawan Jaririn dake hannun Ibraahim yace. “An cire mana Baby”. Idanunta ta rufe kana tayi Murmushi tare da cewa. “Yah Mu'allim”. Hannunsa ya ɗaura kanta tare da faɗin. “Na'am” Tana shafa cikin tace. “Ka ganshi?”. Kai ya gyaɗa tare da cewa. “Eh na ganshi?” Murmushi tayi kana tace. “Momy na ta ganshi?” Kai ta gyaɗa tare da faɗin. “Eh”. Murmushi ta sake yi still tana shafa cikin tace. “Didi da Asma'u fa su ganshi?” Kai ya sake gyaɗa wa tare da cewa. “Kowa ya ganshi”. Baki ta tura gaba cike da shagwaɓa kamar za tayi kuka fuskanta ta shafa kana yace. “Minha ya akayi”. Fuska ta sake narkarwa cikin mayen allurar tace. “Yanzu shikenan kowa ya rigani ganin ɗana”. Murmushi yayi kana Didi ma tayi Murmushi Asma'u kam dariya tayi tare da cewa. “Aikam dai kece karshen kallo duk mun riga ki”. Baki ta Cunno gaba. Didi kuwa sake matsawa kusa da ita tayi kana tace. “Kiyi haƙuri Ɗiyata In sha Allahu zakiga ɗan ki”. Sake narke fuskarta tayi tare da cewa. “Hmmmm”. Sai kuma ta jinjina kanta tare da juya kanta gefe tace. “Yah Mu'allim”. Ahankali yace. “Na'am”. Lallausan Murmushi ta saki tare da cewa. “Yah Mu'allim ina sonka”. Kansa ya sunkuyar ƙasa tare da sakin Murmushi kana ya ɗago ya manna mata kiss agoshi. Ahankali ta cigaba da kiransa. “Yah Mu'allim! Yah Mu'allim!! Yah Mu'allim!!!”. Duk kiransa da take yi yana amsawa. Cikin sanyin murya da shagwaɓa ta cigaba da cewa. “Ina sonka! Ina sonka!!,Ina sonka!!!Yah Mu'allim Kasan ina sonka ko?”. Dariya Asma'u ta sanya tare da cewa. “Dan Allah kar ki dame mu ai mun san kina sonshi”. Ta ƙare maganar tare da ciro wayarta tana mata video Khausar kuwa jin abinda Asma'u ta faɗa yasa ta Cunno baki gaba har lau kuma cikin mayen take. Moddibo kuwa wani Amintaccen Murmushi mai cike da jin daɗi gami da shauƙi ya saki Sambatu take yi amma yana masifar jin daɗin su. Aƙage da kuma shauƙi yace. “Na sani Minha?”. Sake Cunno baki tayi tace. “Yah Mu'allim kaima kana sona?”. Tafin hannunta ya matsa tare da cewa. “Ina sonki Minha Ina sonki ina sonki Minha”. Cike da kunya Didi ta koma kan Darduman ta zauna. Momy dake zaune gefensu kuwa sunkuyar da kanta ƙasa tayi. Lalla Khadijah Rahama Asma'u Dr Jameel kam Murmushi kawai suke suna sake jaddada ƙauna da shaƙuwar dake tsakanin su sun lura Moddibo yama mance da suna wajen. Khausar kuwa cikin Sambatu da azabebben ƙaunarsa tace. “Ina matuƙar Ƙaunarka Yah Mu'allim tun ina JSS one fa nake sonka kasan kafi duk malaman makarantar mu kyau ko ina ka sani ko?”. Cikin jin daɗin gami da farin ciki yace. “Uhmmm”. Cikin narkekkiyar murya tace. “Da gaske fa kafi duk mazan duniya kyau, sajenka mai kyau, ai kasan ina son sajenka ko Habibeeey”. Lallausan Murmushin mai cike da farin ciki yayi tare da cewa. “Yesss na sani”. Cikin tsokana Ibraahim yace. “Toh ashe fa tsohuwar soyayyace, ashe nima sai in fara aje saje”. Murmushi sukayi baki ɗaya, Asma'u kuwa gefen Dr Jameel daya riƙo hannunta yaja ta ɗan matso still tanayiwa Khausar video. Ita kuwa Khausar Jujjuya kai tayi tare da tura baki sai kuma tace. “Ina sonka har rainafa, kuma ina tsoron kayi min kishiya bana son rayuwa da kai da kishiya Yah Mu'allim kayi min alƙwarin baza kayi min kishiya ba, kuma ka ƙi kayi min alƙwari Yah Mu'allim”. Gashin girarta ya shafa kana ya kwantar kanta ya sunkuya ya kai bakinsa saitin kunnenta ya raɗa mata. “Minha aike ta musamman ce arayuwata koda wata mace takasance kusa dani Babu wata mace da zata kai ki matsayi da daraja akusa dani”. Idanunta ta buɗe ta kallesa kana cikin wata sanyayyar murya mai cike da shauƙi da bege ta ƙyafƙyafta idanunta tare da cewa. “Yah Mu'allim ina son ka”. Murmushi yayi kana yace. “Naji”. Kanta ta juya ɗaya gefen tare da cewa. “Didi?,Didi!!”. Didi dake gefe tace. “Na'am Khausar ” Baki ta tura kana ta marairaice fuska tare da cewa. “Didi ki faɗa masa ina son shi Dan Allah kar ya yimin Kishiya”. Murmushi Didi tayi kana tace. “Shikenan ɗiyata kwantar da hankalinki kin ji”. Sake tura bakinta tayi tace. “Ina Momyna?,”. Kallon Momy Didi tayi tare da cewa. “Gata nan”. Ɗan buɗe idanunta tayi tace. “Momy ki matso ta nan mana”. Miƙewa Momy tayi kana ta matsa kusa da kanta ta tsaya jin alamun ta kusa da ita tace. “Momy”. Anutse Momy tace. “Na'am”. Tana ɗan Murmushi tace. “Momy kinga Babyna?”. Kai Momy ta gyaɗa tace. “Eh”. Kwanciyanta ta gyara tare da cewa. “Momy kinga yaro na ko?,Didi tace namiji ne?”. Kai Momy ta gyada kana tace. “Eh”. Murmushi ta saki tare da faɗin. “Momy dawa yake kama?”. Murmushi Momy tayi tare da juyawa ta kalli Jaririn dake hannun Niyna kana ta juya ta kalleta tare da cewa. “Da Ramadan yake kama Khausar”. Wani Amintaccen Murmushi ta saki mai cike da jin daɗi kana tace. “Alhamdulillah Momy na samu mai kama da Ramadan". Kai Momy ta jinjina tace. “Sosai ma”. Fuskarta ta shafa tare da faɗin. “Momy Kyakkyawa ne kenan?”. Ta ƙarashe Maganar da alamar tambaya kana da Murmushi afuskarta. Kai Momy ta gyada tare da cewa. “Kyakykyawane Mamana ɗan ki kamar Balarabe”. Tana Murmushi tace. “Ai tunda aka ce da Ramadan yake kama nasan kyakkyawane Momy”. Sai kuma ta Maida idanunta kan Moddibo tace. “Yah Mu'allim kaji wai ɗan mu da Ramadan yake kama, kyakkyawane ko?”. Kai ya jinjina kana yace. “Kyakykyawa ne yama fiki kyau ai?”. Baki ta tura gaba tace. “Ni dai bai fini kyauba”. Murmushi yayi yace. “Toh naji bai fiki kyau ba Rigimatu, ki Kwantar da hankalinki”. Asma'u kam sai dariya suke mata. Haka ta cigaba da surutu da Sambatu har kusan karfe huɗu zuwa lokacin already alluran ya gama saketa ta dawo hayyacinta. Kallon Moddibo tayi tare da cewa. “Yah Mu'allim zan tashi zaune”. Sumar kansa ya shafa tare da cewa. “Toh ki taushi ki zauna mana”. Fuska ta narke tare da cewa. “Ka tayani”. Cikin yi mata kallo mai haɗe da zazzafan yanayi yace. “Toh ki tashi ki zauna mana ai likitoci sun hana in tayaki, ki tashi da kan ki mana”. Baki ta tura tayi ta ƙorafi misalin 4:15 ta mike ta zauna da kanta kasancewar ta tashi ta zauna da kanta yasa Dr cewa Moddibo ya tallafa mata amaida ta ɗaki ta taka da ƙafanta. Da ƙafanta ta taka aka canza mata ɗaki wanda akwai step agabansu suna komawa ɗaki Asma'u ta zauna ta gabanta Moddibo kuma nata bayanta. Kallon Dr Jameel Asma'u tayi tare da cewa. “Dr”. Yana gyara abin karfen gadon yace. “Na'am my Dear”. Kai ta langwaɓar tare da faɗin. “In bata abinci?” Kai ya dafe kana yayi Murmushi tare da cewa. “Kai ke dai baki ɗaya na lura bama ta ɗan mu kike ba ta Ƙawarki kikeyi”. Dariya Momy tayi kana tace. “Da gaskiyar ta wa yake ta ɗan ku”. Murmushi Moddibo yayi tare da faɗin. “Momy harda kema bata ɗan mu kike ba wato ta ita kike ” Cikin sauri Dr Eshaa tace. “To ai har kaima bata ɗan ka kake ba ta ita kake tunda ka ɗauke sa aɗaki baka sake ɗaukar saba kana riƙe da hannunta yanzu dai lokacin sallar la'asar yayi atafi ayi Sallah. Zuwa biyar a ɗan asa mata abinci. Cheaps kaɗan da tea rabin cup”. To sukace kana su tafi masallaci, su kuwa matan sukayi salla a nan. Sai ƙarfe biyar dai-dai Asma'u ta ɗan sa mata cheabis ɗan kaɗan sai tea rabin cup, kamar dai yadda sukace mata. Bisa jagoranci likitoci ta matsa ta riƙa bata taɓa ci. Moddibo kuwa kanta ya riƙa shafawa tare da cewa. “Minha kinga muje muyi alwala muyi sallah na roki Allah ya baki lafiya ya raya mana ɗanmu”. Lallausan murmushi ta sakar masa kana ta gyaɗa kai shi kuma ya zauna gefe, nan dai ta gama ci, kana ta ɗan gyara manta. Dai-dai lokacin kuma Abualeey suka iso, bisa jagorancin Ibraahim m suka nufi dakinta dai-dai lokacin da suka shiga a kuma dai-dai lokacin Khausar ta fara wani irin.... By *GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH Book 3 PAGE 8* NA *Aysha Aliyu Garkuwa* *GARKUWAR* taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya* Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara. Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida. Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 08069423567 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so. 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida. GARKUWAR MA'AURATA Tana wani sassayan tari, wanda take ta son danneshi, cikin sauri suka ƙara sa cikin ɗakin da sauri Dr Jameel yace. “Ha'a ya dai?”. Momy ce ta ɗago kanta tare da cewa. “Kamar ƙwaruwa tayi”. Cikin tsoro gami da damuwa Moddibo ya kalli Dr Jameel kana yace. “Jifa tari take ba matsala ko?”. Kai Dr Jameel ya girgiza tare da faɗin. “A'a ba matsala bari nasa akawo mata wani magani tasha tarin zai bari”. Ya ƙare maganar tare da kiran Line-line dake cikin wayar ya kira Pharmacy ya faɗa musu su kawo maganin jim kaɗan Norse ta kawo maganin karɓa yayi ya bata tasha cikin ikon Allah atake tarin ya bari. Sai alokacin ta samu nutsuwa numfashi ta fesar kana ta maida kallonta kan Abualeey tare da cewa. “Abu ina yini”. Cike da kulawa yace. “Lafiya lau ya jiki?”. Ahankali tace. “Da sauƙi ”. Kai ya gyaɗa tare da faɗin. “Masha Allah Allah ya raya abinda aka samu”. Karɓan Jaririn yayi tare dasa mishi albarka kana ya miƙawa Waziri da Galadima dai-dai lokacin kuma kira ya shigo wayar Khausar Momy anutse ta duba ganin sunan Hajja Nana yasa ta ɗauka muryanta cike da farin ciki tace. “Hajja Nana Alhamdulillah anyi Theater ancire ɗa namiji”. Cikin jin daɗi da sauke ajiyar zuciya Hajja Nana tace. “Alhamdulillah amma tana lafiya ko?”. ”Eh lafiya lau gata nan ma”. Cewar Momy na miƙa wa Khausar wayar karɓa Khausar tayi suka gaisa cike da farin ciki Hajja Nana tace. “Ƴar tsele da zaki kasheni azaune”. Murmushi Khausar tayi cikin rashin jin karfin jikinta tace. “Yaushe zaki zo?”. Fuska ɗauke da farin ciki Hajja Nana tace. “Kwanan nan in sha Allah kafin ayi suna”. Murmushi Khausar tayi tare da maida kallonta kan Moddibo da idanunsa ke kan Jaririn tace. “Ayiwa Hajja Nana shiri in Sha Allahu tana kan hanya zata zo”. Kai ya gyaɗa mata tare da cewa. “In sha Allahu”. Akuma dai-dai lokacin Dija da Yah Aliyu suka shigo Murmushi Khausar tayi tare da cewa. “Dija”. Cike da farin ciki Dija tace. “Na'am Khausar ai mu bamu sani ba Khausar baku faɗa mana ba”. Still da Murmushi afuskarta tace. “Kiyi haƙuri Dija gaba ɗaya abin ne yazo min atsorace”. Dariya Yah Ali yayi tare da faɗin. “Raguwa gaba ɗaya kin gigice kin gigita bayin Allah”. Langwaɓar da kai tayi kana tace. “Hmmm ba dole inji tsoro ba Yah Ali abinda ance wasu da yawa idan an musu kafin afito dasu ta can suke wucewa”. Murmushi yayi tare da cewa. “A'a ke kam in Sha Allahu kina nan sai kin kawo wasu ƙannensa goma sha ɗaya sun zama Dozen”. Idanunta ta zaro tare da faɗin. “Goma sha ɗaya”. Baki ɗaya ɗakin suka sanya dariya. Raudat dake zaune gefen Asma'u ta ƙyalkyale da dariya kana tace. “Addah khausy idan kika haifi Dozen sai ki bani biyun saman na riƙa kulawa dasu kar suyi Miki yawa ai Yah Moddibo zaku bani ko?”. Ta ƙare maganar tana kallon Moddibo kai Moddibo ya gyaɗa yana Murmushi. A ranan haka suka yini suna kula da ita. Bayan sunyi kwana uku aka sallame ta suka koma gida. Haka Didi da Momy suka cigaba da kula da ita suna bata kulawa na musamman... Washe gari da safe Misalin ƙarfe 7:30 Asma'u ta zo zaune ta samu Lalla Khadijah, Rahama, na zaune kan lallausan Darduma Yayin da Didi,Momy,Innayi ke zaune gefe ɗaya Hajja Nana kuwa na gefen Khausar da Moddibo dake riƙe da Jaririn yana masa addu'a kana su kuma suna hira. Ahankali Asma'u ta ɗago fuskarta ɗauke da Murmushi ta miƙa wa Khausar wayarta tare da cewa. “Kalli wani special abu dana ajiye Miki wanda nake da yaƙinin sai kinyi min kyauta na musamman”. Ɗan ware idanu Khausar tayi tana kallon Rahama dake cewa. “Aikuwa dai Addah Asmeey muma dake gefe muna sa ran samun khauta”. Dariya Khausar ta sanya kana tace. “Aikam dai zanso gani”. Ta ƙare maganar tana playing video Da sauri ta zaro Idanunta waje ganinta kwance kan gado tana surutai. Moddibo kuwa wani Amintaccen Murmushi ya saki ganin yanda ta zaro Idanunta waje sai kuma tayi saurin ɗaga kanta cike da kunya jin yanda suka ƙyalƙyale da dariya cikin tura baki ta kalli Asma'u tare da cewa. “Asma'u Ni ko?,Aikuwa kin ci bashi sai na rama”. Ta ƙare maganar cike da kunya ganin yanda suke maimaita maganar. Asma'u kuwa Gwalo Asma'u tayi mata tare da cewa. “Aikuwa sai dai ki rame yarinya dama can abinda ke Ranki kika faɗa”. Khausar kuwa juyawa tayi jin Hajja Nana na cewa. “Yoh ai gaskiya Asma'u ta faɗa ke da wannan mijin naki duk ba kunya ne daku idan ke baki cikin hayyacin ki kika faɗa ai shi yana sane bare keɗin ma kina sane”. Rau-rau da idanu Khausar tayi ta shiga bubbuga ƙafa daga zaune tace. “Didi kiji fa abinda Hajja Nana ke faɗa wai bani da kunya”. Murmushi Didi tayi tare da faɗin. “Rabu da Hajja Nana am Khausar ɗina kina da kunya sosai ai bada sanin ki kikayi ba”. Momy kam Murmushi kawai takeyi. Daidai lokacin Jakadiya ta shigo tare da sanarwa Didi tayi baƙi ƴan Barka. Miƙewa Didi tayi kana tace. “Toh ganan zuwa”. Sai kuma ta kalli Momy dake cewa. “Mu tafi”. Atare Didi Momy Innayi,Niyna suka fice. Kallon Rahamah kalla Khadijah tayi kana tace. “Rahama muje ki tayani haɗa Alawar Madara da gullisuwa tun jiya naso yi kuma ina zirga-zirga”. Murmushi Rahama tayi tare da miƙewa Lalla Khadijah kuwa har taje ƙofa ta juya ta kalli kana tace. “Ƙanwata kema zo muje”. Kai Asma'u ta gyaɗa tare da miƙewa suka fita. Falon ya rage daga Khausar, Moddibo sai Hajja Nana da itama ta miƙe ta fita falon. Cikin shagwaɓa Khausar ta kalli Moddibo tare da narke fuska kana ta tura baki tace. “Yah Mu'allim”. Murmushi yayi kana ya kwantar da jaririn ya janyota jikinsa bakinsa ya kai saitin kunnenta yace “Na'am Minha Viddaaaa ya akayi?”. Ya ƙarashe yana jan sunan. Cike da shagwaɓa tace. “Jifa yanda na saki baki naita faɗan magana gabansu Momy da Didi kuma baka hanani ba”. Murmushi yayi yana shafa bayanta yace. “Ya za'a yi in hanaki fallasa min sirrin dake Ranki?,Taya kike tunanin bakina zai iya dakatar da zinaren kalaman da suke fitowa daga bakinki suna ratsa kogon zuciyata?,Kin kuwa san farin ciki da shaukin dana kasance alokacin?”. Ya fesar da sanyayyan numfashi mai cike da zallan so da shauƙi yace. “A lokacin ji nake tamkar ina yawo a gajimare ji nake tamkar nafi Mazan duniya Sa'a da samun Nagartacciyan mace irin ki kin nuna min so tun baki san menene so ba shin mai zanyi in biyaki”. Cikin wani irin yanayi na musamman tace. “Ka ƙaunaceni ka kuma soni fiye da yanda nake son kaina kada ka haɗa ni da kowa atare da kai idan kayi min haka kaga yimin komai Yah Mu'allim”. Ahankali ya ɗago kanta tare da ɗaura lips ɗin sa asaman nata yashiga kissing ɗin ta... Alhamdulillah zuwa yanzu jikinta yayi ƙwari bazama ace Thearter aka mata ba kullum Asma'u da Dija anan suke yini ana I gobe suna Dr Zakariyya, Asiya Hajja Nana, Abban Jameel, Lalla Hafsat suka zo. Hajja Nana da Innayi ce zaune da Khausar aɗaki yayin da Innayi ta zuba mata abinci ta bata taci Momy kuma na riƙe da jiriri tayi masa wankan Yamma ta saka shi cikin wasu fararen kayan sanyu masu masifar taushi pink and white collar. Anutse Moddibo ya shigo ya same su Kai tsaye bakin gadon ya wuce gefenta ya zauna. Kallonsa hajja Nana tayi tare da cewa. “Wai kai kam baka jin kunya ne?”. Juyawa yayi ya kalleta kana yace. “Kin iso da sa ido ko? Idon ki be iya gani bakinki yayi shiru ko?”. Hararansa tayi tare da faɗin. “Ba dole ba idan bani nake taka maka birki ba babu mai taka maka birki”. Kallonta yayi tare da cewa. “Toh sai kiyi mugani in birkin zai taku”. Anutse Khausar ta kallesa kana ta kalli Hajja Nana tace. “Yah Mu'allim rabu da ita”. Murmushi yayi tare da cewa. “Aima na rabu da ita?”. Khausar kuwa nutsuwarta ta tattara kana tace. “Yah Mu'allim gashi har gobe suna in Allah ya kaimu”. Kai ya gyaɗa kana yace. “Eh”. Ahankali ta langwaɓar da kai tare da cewa. “Kuma banji ka faɗa min sunan yaron ba”. Murmushi yayi kana yace. “Kuma tun a asibiti kafin ayi mishi wanka na masa huɗu ba tun kafin ki farfaɗo”. Murmushi tayi kana ahankali tace. “Kuma Yah Mu'allim baka faɗa min ba". Juyawa yayi ya kalli Asma'u kana ya kalli Asiya dake cewa. “Ai dai kam bamu san sunan yaro ba gashi har gobe Suna”. Didi kam ido ta zuba mishi tana kallonsa Momy kuwa sunkuyar da kanta ƙasa tayi tana sawa Jaririn safan hannu tace. “Toh menene sunan”. Sunkuyar da kansa ƙasa yayi kana ya motsa laɓɓansa tare da cewa. “Sunan shi Jameel”. Cikin tsananin jin daɗi Asma'u ta kallesa tare da cewa. “Allah sarki Yah Moddibo Ubangiji Allah ya saka da Alkhairi Allah yabar zumunci ayyah Yah Jameel ɗina Allah ya raya shi Allah ya mishi Albarka”. Murmushi yayi tare da cewa. “Ameen ya Allah Asma'u, Allah yasa ya biyo halin takwaransa”. Ya ƙare maganar yana Murmushi. Innayi ce ta amshi zancen da cewa. “Naji Ibraahim kuna na kiranshi da *Keyan*”. Kai Modibbo ya jinjina tare da cewa. “Eh laƙanin kenan. Amman asalin sunan Jameel, Allah ya raya mana shi yayi nagarta irin ta mai sunanshi”. Cikin tsananin jin daɗi Asma'u tace. “Ameen ya hayyu ya ƙayyum ”. Khausar na Murmushi tace. “Ameen ya Allah yasa ya biyo halin takwaransa Allah yasa yayi Ilimin takwaransa”. Cikin jin daɗi Didi tace. “Ka kyauta Babana Allah Ubangiji ya raya mana Jameelu”. “Ameen ya hayyu ya ƙayyum ”. Cikin tuno da Jameel Hajja Nana tace. “Ameen ya Allah ai Jameelu mutumin kirki ne”. Asma'u kuwa cikin sauri ta ɗauki waya tare da kiran Ummi Ummi na ɗauka tace. “Ummi albishir”. Daga ɗaya ɓangaren Ummu tace. “Goro”. Cike da farin ciki Asma'u tace. “Yah Jameel ya samu takwara”. Murmushi Ummi tayi tare da faɗin. “Hmmm Asma'u kenan kece baki sani ba amma ainin tun ranan Aliyu ya faɗa min” Murmushi Asma'u tayi kana tace. “Ummi shine baki faɗa min ba ranan muna hira ina cewa Ala'andi wani suna za'a sawa yaron kikayi shiru ashe duk kin sani”. Murmushi tayi tare da cewa. “Na sani mana tun ranan ya faɗa min”. Murmushi Moddibo yayi tare da cewa. “Ai TOH na rigaki yin albishir ɗin”. Dariya ta sanya tace. “Wallahi Yah Moddibo Ina sauri in rigaka ashe ka rigani”. Haka sukayi yinin ranan anata shirye-shiryen suna, nan washe gari suna akayi raɗin suna da hidindimu kamar yanda al'adan masarauta take. Bayan sallar la'asar manyan Fada ne a zaune saboda Aranar Abualeey yake son yin Murabus ya barwa Moddibo sarauta. Bayan an zauna an cika a Fada anyi komai an taru Sarkin Al'adun Fada ne ya juya ya kalli Moddibo dake cikin wani irin shiga na alfarma da kawa da yayi masifar fitar da ainihin kyawunsa da ƙwarjinsa kana yace. “Alhamdulillah kamar yanda al'adun Fada take sarki yana da dama da iko da zai yi Murabus tun yana da rayuwarsa ya danƙa Mulki a hannun ɗan sa da yake ganin zai iya gadon mulkinsa kana zai iya kula da Masarauta yanda ya kamata dan haka Sarki Youseef Mohammed Aliyu Mouley ma yayi alƙawari zai maida Sarauta ahannun ɗan sa Aleeyu Youseef Mohammed Aliyu Mouley”. Cikin jin daɗi Manyan cikin Fada da Manyan Masarautu na gefe-gefe wanda baki ɗaya sun san da Maganar an samu sa hannunsu tun watanni hudu da suka wuce kowa cikin jin daɗi da farin ciki yake faɗin Alhamdulillah. Cike da girmamawa Sarkin Fada ya juya ya kalli Moddibo tare da cigaba da cewa. “Kuma a wannan ranane za'a ƙara wa Sarki Aleeyu Youseef Mohammed Aliyu Mouley mata kamar yanda atsarin Masarauta sarki bai kasancewa da mace ɗaya sai an masa biyu aranan da za'a danƙa mulki a hannunsa”. Cikin sauri Moddibo ya ɗaga kansa ya kallesu sai kuma ya saki wani Murmushi dashi kaɗai yasan ma'anar sa juyawa yayi ya kalli Abualeey dake cikin matsanancin farin ciki kana ya kalli Sarkin Fada tare da cewa. “Ina son magana da mahaifina”. Kai Sarkin Fada ya gyaɗa kana yace. “Toh shikenan ba damuwa”. Kana suka shiga ɗakin Sirri Shida Abualeey, Waziri, Galadima Wambai Garkuwa... A dai-dai lokacin kuma acikin gida Khausar ce cikin shiga ta alfarma sanye take cikin wani lafiyayyan Abaya Pinch colour mai masifar taushi da santsi da yasha duwatsu kana ta ɗaura Alkyabba ta Masarauta fari ƙall mai masifar taushi wanda al'ada ce ta Masarauta wanda ranan da za'a naɗa mijinka a Masarauta zaka sa. Shima Jaririn sanye yake cikin shiga na alfarma wasu picnh colour kayane tausasa kana aka daura masa ƙaramin Alkyabba fari irin na jarirai. Sai hotuna suke ta ɗauka dasu Lalla, Khadijah Lalla, Hafsat Asiya, Asma'u, Dija, Rahama, Raudat Asma'u kuwa kai tsaye take turawa cikin group ɗin su na class mate ɗin su da suka gama makaranta. Nan da nan cikin group ɗin ya kace me da surutu kala-kala kowa na tofa albarkacin bakinsa wata ƙawarsu wacce lokacin da suke makaranta bencinsu ke kusa da nasu Khausar mai suna Hawwa Idris ne tace. “Ikon Allah wai Khausar ce haka🤔 girma yazo rawan kai ya gudu?”. Tayi typing da emotion na mamaki dariya Asma'u ta tura mata tare da cewa. “Gashi kuwa kinga zahiri” Cikin Mamaki tayi voice dan gani take typing ɗin bai mata sauri kana tace. “Masha Allah shiyasa akace arayuwa kada ka taɓa wulakanta mutum domin baka san baiwar da Allah ya mishi ba wai yau Khausar ce matar Sarkin Morocco kuma Malam Moddibo?”. Hoton dariya Asma'u ta sake tura musu tare da faɗin. “Aikam ikon Ubangiji yafi gaban haka?”. Wata mai suna Jidda ce tace. “Aikuwa dai muma Allah yasamu Adamshin ku Asma'u ku kam kunji daɗin rayuwarku”. Murmushin Samira Sani ta turo tare da cewa. “Uhmmm kuma ku godewa Allah a yadda kuke ɗin”. Da sauri Khadijah Sule tace. “Sosai ma kam Samira am”. Amin kuwa cikin sanyi da nadama tace. “Alhamdulillah ai in Allah ya baka lfy ka gode masa”. Haka dai suka cigaba da hira acikin group ɗin kowa na faɗin albarkacin bakinsa. _Daga can gefe kuwa su ne Rafi'a,Tutus kitchen, Mom sayyeed&Noor Tatti Dija chiroma, ne da suka halarci wajen sunan ne suke ta Video da hotuna suna turawa cikin Group ɗin SAKAYYA Team Moddibo da Khausar kam baki yaƙi ruhuwa duk farin ciki ya cika su ganin irin gift da Khausar ta bayar akawo musu._ _Daga can gefe kuma ƴan karatun bati siddan na Allah ya isa kenan da basu biya kuɗi ba suke wiƙi-wiƙi da ido duk hakki ya hanasu sakewa da samun nitsuwa..._ Asma'u dake cigaba da hotuna da wayar Khausar wayar ya ɗauki suwwa ganin sunan Yah Mu'allim na yawo yasa da sauri ta nufi Khausar dake tsakiyar Didi da Momy suna hoto tayi saurin isa gareta kana ta tsugunna zata miƙa mata wayar kasancewar azaune suke haka yasa ta fito a hoton da yayi masifar kyau. Asma'u kuwa cikin raɗa takai bakinta kunnenta tace. “Gashi fa Yah Moddibo yana kiran ki”. “Mu gani”. Cewar Khausar tana karɓan wayar tare da kaiwa kunnenta tace. “Assalamu Alaikum Yah Mu'allim”. Cikin wani irin yanayin na musamman yace. “Minha kizo ki sameni aɗakina”. Kai ta gyaɗa tare da cewa. “Toh”. Sai kuma ta miƙe tare da rungume jaririn kai tsaye ta nufi sashen bakinta ɗauke da sallama ta shiga falon nan ta samu Dr Jameel, Dr Zakariyya, Ibraahim,Yah Ali, da Yah Abba da sauran yan uwansa. Yah Abba na ganinta yayi Murmushi tare da cewa. “Mai jego kin sha ƙamashi”. Murmushi tayi kana tace. “Ai dai kam”. Kallonta ta mayar kan Ibraahim tare da cewa. “Ibraahim Yah Mu'allim fa?”. Da hannu ya nuna mata bedroom ɗin kana yace. “Yana ciki”. Ahankali ta nufi bedroom ɗin kwance ta gansa akan gadon yana ganinta ya saki sanyayyar ajiyar zuciya tare da buɗe mata hannunsa. Cike da begensa ta zauna kusa dashi miƙewa yayi ya haɗa ta da jaririn ya rungumesu ahankali ya riƙa kissing ɗin goshinta zuwa wuyanta da kuma sassan jikinta baki ta ɗan tura tare da cewa. “Yah Mu'allim ka matsaneni kuma ɗanka ya matse min wajen Theater na”. Cikin sauri ya saketa kana ya karɓesa ya kwantar dashi tare da jawota jikinsa ya rungumeta sai kuma ya saki sanyayyar numfashi kana ya ruggumeta tsam cike da kulawa da kuma ganin yanayinsa ta shafo sajensa tare da cewa. “Yah Mu'allim lafiya meke faruwa?”. Kanta ya tallofo kana ya kalleta ido cikin ido da mamaki take kallonsa ganin yanda idanunsa suka kaɗa sukayi jawur dasu cike da kulawa tace. “Yah Mu'allim lafiya?”. Sunkuyar da kansa ƙasa yayi kana ya ɗago ya kalleta tare da cewa. “Minha na yiwa Abualeey laifi kuma har yayi fushi dani”. Cikin sauri ta zare idanunta tare da faɗin. “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Yah Mu'allim laifin me kayiwa Abualeey?”. Araunane yace. “Minha nayi mishi babban laifi naƙin bin Umarninsa”. Cikin tsoro da kaɗuwa tace. “Ya Ilahi Yah Mu'allim akan me baza kabi umarnin Abualeey ba?”. Langwaɓar da kansa yayi kan wuyansa yace. “Saboda kece ban bi Umarnin Abualeey ba!”. Cikin sanyi da rauni tace. “Ya Ilahi bana son jin wannan maganar sam maganar babu daɗin ji Yah Mu'allim Kabi Umarnin mahaifinka shine abinda ya dace kuma shine *SAKAYYAR* da zamuyi masa”. Cikin rauni da karyewar zuciya yace. “Bazan iya ba”. Cike da mamakin shin wani irin abu ne me nauyi da girma agaresa da yasa har ya yiwa mahaifinsa gardama tace. “Haba Yah Mu'allim ya za'a yi kace baza kayi abinda mahaifinka keso ba shin wani irin abu ne?”. Cikin sanyi ya kalleta kana ya lumshe Idanunsa tare da cewa. “Saboda yau yake so a bani mulkin Masarautar Mouley ahannuna”. Cikin sauri da jin daɗi kana da Jimamin yanayin da yake ciki tace. “Toh mene Yah Mu'allim mulkin ne baka son rikewa ko me meyesa zaka yi mishi gardama?Kuma ai nikam ma ina son mulkin nan meyesa baza ka karɓi Sarautar ba? Kawai ka karɓi mulkin shine abinda ya dace”. Kai ya jujjuya tare da juya ƙwayar idanunsa acikin nata kana ya riƙo hannunta acikin nasa tare da cewa. “Ba karɓan mulkin bane matsala Minha”. Cikin rashin fahimtar abinda ke damunsa tace. “Toh ka karɓi mulkin mana kayi mishi biyayya akai”. Hannunta ya damƙe kana yace. “Ki bari kiji ko menene”. Fuska ta tsuke tare da cewa. “Nikam babu abinda zanji Yah Mu'allim kawai kayi mishi biyayya akan abinda yake so ka karɓi mulki Allah ya tayaka riƙo ya baka ikon Adalci kai masa biyayya ka samu lada”. Cikin sanyi da rauni yace. “Cewa yayi an bani mulki bisa sharaɗin za'a bani Auren wata mata ya zama ina da mata biyu!”. Da wani irin sauri ta dafe ƙahon zuciyarta da yayi wani irin harbawa cikin rauni da fusgar magana tace. “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”. Atake jikinta ya fara rawa kar-kar-kar tamkar wacce aka watsawa ruwa ƙanƙara atsakiyar hunturun sanyi kana idanunta suka kaɗa sukayi jawur tamkar garwashin wuta lokaci ɗaya taji numfashinta na Up and down alamar yana shirin barin gangar jikinta jawota yayi ya riƙe ta da damuwa atare dashi yace. “Kee ki tsaya mana ki nutsu me haka!?”. Gaba ɗaya ta rikice numfashinta sai fusga yake alamun tana gab da suma saboda tsabar masifar kishi, cikin fusgar numfashi da ficewar hayyaci ta dafe ƙahon zuciyarta tare da cewa. “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Yah Mu'allim Aure kuma?,Wata matar za'a Aura maka?,ita?”. Sai kuma ta tsaya da Maganar jin numfashinta na shirin barin gangar jikinta alamar zata iya rasa numfashinta. Moddibo kuwa cikin matsanancin mamaki tsoro gami da ruɗu yake kallonta tabbas yasan tana da kishi amma bai taɓa tunanin kishinta yakai wannan matsayin ba. Cikin sauri ya rungumeta tare da riƙo hannayenta kana yana jijjiga fuskarta yace. “Khausar Khausar ki nutsu mana ki buɗe idanun ki dan Allah ki tsaya ki fahimci abinda zan faɗa miki”. Da ƙyar ta iya buɗe idanunta. Cikin sauri da tsoro ya sake tallafe Fuskarta ganin yanda ta zazzaro idanunta sukayi wani irin ja. Ahankali ya fara bubbuga kumatunta tare da cewa. “Dan Allah Minha ki nutsu kiji abinda zan faɗa Miki”. Cikin rauni murya da bugawar zuciya tace. “Yah Mu'allim yanzu mata zasu ƙara maka innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”. Sai kuma ta kife kanta akirjinsa ta saki marayan kuka mai masifan cin rai da zafi kukan data sakene ya temaka wajen daidaiton numfashinta ya tsaya. Ahankali ya tallafota jikinsa yace. “Minha shine laifin da nace Miki na yiwa Abualeey saboda nace masa, in dai har sai an ƙara min mata za'a bani mulkin, ni na yafe bana buƙatar mulki abawa Ibraahim nayi alƙwari zan rayu daga Ni sai ke sai kuma ɗan mu da kuma wa'anda zamu haifa nan gaba”. Khausar kam wani irin kuka mai tsuma zuciya da tsananin kishi take yi. Moddibo kuwa cikin gaskiya da gaskiya ya cigaba da cewa. “in dai akan mulkine zan yi Miki kishiya abawa Ibraahim in yaso a Aura mishi Mata huɗu a rana ɗaya, nayi alkawarin bazan yimiki kishiya a kan mulkiba Amman ban miki alkawarin cewa wai bazan Miki kishiyaba dan bansan ne Allah zai tsara a kanmuba a gaba”. Da sauri ta tashi kana ta buɗe Idanunta cikin rauni da shesh-sheƙa tace. “Mata fa kace zasu Aura maka”. Cikin kwantar mata da hankali yace. “Ba kiji mai nace Miki bane indai mulki ne na haƙura dashi a bawa Ibrahim abarni Ni in rayu dake da ɗana da abinda zaki haifa agaba”. Ahankali ta shiga sakin ajiyar zuciya Moddibo kuwa cike da tarin ƙaunarta ya cigaba da faɗin. “Na tabbar kun isheni farin ciki kun isheni jin daɗin rayuwa kun isheni komai batare da mulkin nan ba Ni na yarda zan kasancewa Ibraahim mai bada shawara abawa Ibraahim mulki shine abinda yafi min kwanciyar hankali hakan ya miki kinji daɗi akan haka”. Cikin matsanancin jin daɗi da farin ciki tace. “Na yarda in dai har Abualeey ya yarda Bama son mulkin mun bar musu mun yafe musu mulkinsu Mukam Bama so”. Akuma dai-dai lokacin Jaririn yasa kuka cikin sauri ta kallesa cikin shesh-sheƙan kuka tace. “Abu J ba ka jiba yana kuka shima baya so a yiwa Mimeeinsa kishiya”. Cikin sauri ya rungumota jikinsa kana ya haɗa da jaririn ya rungumesu tare da cewa. “Mu bar musu mulkinsu Minha ba ruwanmu suje can su ƙarata da mulkinsu, su riƙe abinsu abarmu haka mu cigaba da jin daɗi da kwanciyar hankali yafi mana”. Dai-dai lokacin Ibraahim yayi knowking kana ya sanar masa zuwan Momy da Didi. Suna shiga Didi ta kallesa Babu walwala atare da ita tace. “Yanzu Aleeyu ka kyauta kenan ɓacin ran da kasa Mahaifinka”. Cikin sauri ya mike kana ya tsugunna gaban Didi tare da cewa. “Didi dan Allah kuyi haƙuri”. Cikin sauri da rashin walwala Didi tace. “Shi ya gama yanke hukunci amatsayin sa na Mahaifin ka Sarautace an riga da an baka ita sai kayi abinda kaga zaka iya akai”. Da sauri cikin shesh-sheƙa Khausar tace. “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Didi yanzu kuma harda Mata za'a ƙara mishi?,”. Cikin tsuke fuska momy ta harareta tare da cewa. “Dan Allah rufe mana baki, sokuwar banza sokuwar wofi, in ba'a Aure ke aka Auro ki baza ki taya mijinki yanda zai yiwa iyayensa biyayya ba, sai ki tsaya sokonci kina kuka kina cewa an ƙara masa mata matar kashe ki zata yi, ko kuma akan ki zata zauna?”. Cikin rauni ta fashe da kuka kana ta jingina kanta da bakin gado cikin shesh-sheƙan tace. “Momy ba zaki gane bane bazan iya rayuwa da wata mace tare da Yah Mu'allim ba”. Ahankali Didi ta ɗagota kana ta dafa kafaɗarta tare da cewa. “Kiyi haƙuri Sarauta ce an bashi Mata kuma tunda yace baiso da ɗaya zai zauna shikenan tun da dama bawai shariya ɓace ta tsara haka, al'adace”. Ajiyar zuciya mai sanyi ta shiga saki tana jin nutsuwa na diran mata shi dai Moddibo kan sa na ƙasa Didi kuwa cikin kwantar mata da hankali ta cigaba da faɗin. “Allah da kansa ya basu Umarni suyi Huɗu, Uku, Biyu idan kuma ba zasuyi adalci ba suyi ɗaya tunda yace ba zai yi adalci ba laifi. Mahaifinsa ya yarda an bashi Sarauta batare da anƙara mashi mata ba”. Cike da matsanancin farin ciki ta mike ta rungume Didi kana tace. “Nagode Didi Ubangiji Allah ya miki Albarka”. Cikin sauri ta saki Didi kana ta tsugunna ta fuski Alƙibla tare da yin Sujudur Shukur ta godewa Allah kallonta ta mayar kan Moddibo dake Murmushi ta miƙa masa hannu tare da cewa. “Yah Mu'allim Alhamdulillah ”. Martanin Murmushi ya mayar mata yana mai jin wani irin nutsuwa na ratsa sassan jikinsa ganinta cikin farin ciki ahankali yace “Alhamdulillah” Murmushi Didi tayi tare da riƙe hannun momy kana ta kalli Moddibo tace. “Idan ka gama murnan ka tashi ka tafi Fada ana damƙa maka sarauta”. Kai ya gyaɗa tare da cewa. “Toh”. Momy kuwa kallon Khausar tayi kana tace. “Wuce mu tafi ” Ta ƙare maganar suna fita. Cikin sauri Khausar ta miƙe tare da faɗawa jikin Moddibo tayi masa wani Amintaccen runguma sai kuma ta tallafo kansa ta haɗe bakinsu ta shiga kissing ɗin sa ahankali ta zare harshenta cikin nasa tare da riƙe hannunsa Fuskarta ɗauke da maɗaukakin farin ciki tace. “Ina ƙaunarka Abu J My life is nothing without you”. Murmushi yayi kana ya lakace mata hanci tare da cewa. “Shikenan kuka ya ƙare ko?”. Dariya ta sanya tare da ɗaukan Jaririn tabi bayansu Momy da tuni suka fice kana shi kuma ya fita ya samu su Ibraahim suka wuce Fada. Aranan aka naɗa masa Sarautar Mouley kana aka ɗaura auren Rahama da saurayinta kana matar da za'a Aura masa aranan aka Aura wa Ibraahim ita Ibraahim kam. baki har kunne cikin jin daɗi da farin ciki aka gama Shagali da daddare aka kaiwa Ibraahim matarsa. Tun aranan Lalla Hafsat da wasu daga cikin baƙi suka tafi da Rahama kasan cewar ƙanin mijin Lallai Hafsat ne mijinta yasa aka wuce Mexico da ita baƙin suna kuma duk an watse lfy... Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Khausar na samun kulawa mai kyau. ranan da ta cika sati Uku Alhamdulillah Thearter yayi gwaɓi sosai suka je asibiti aka sake dubawa a ranan sukaje asibiti Alhamdulillah aka duba akace babu matsala yayi kyau saboda jikinta yana da kyau yaro yayi kuɓul-kuɓul gwanin sha'awa Masha Allah. A ranan da suka cika wata ɗaya da yammaci Khausar bayan ta fito daga wanka ta shirya cikin wani riga da skirt na less me kyau jikinta sai ƙamshi yake ɗan ta yayi kuɓul-kuɓul Masha Allah yayi ƙato gwanin ban sha'awa. Zaune suke Khausar Innayi da Hajja Nana suke a bedroom. Yayin da Momy da Raudat ke zaune Side ɗin Didi tana ta shirye-shiryen tafiya nan da kwana biyar masu zuwa. Ahankali Moddibo ya shigo bedroom ɗin hannunsa riƙe da Jaririn dake tsala kuka kusa da Khausar ya zauna kana ya ɗaura mata yaron akan cinyarta kai ya langwaɓar cikin wata amintacciyar murya me cike da kulawa tare da tsantsar soyayya yace.. “Minha yunwa fa yake ji”. Ashagwaɓe ta tura baki kana ta langwaɓar da kai tare da cewa. “Yah Mu'allim ɗazu fa yasha kuma sai yaita tsotseni”. Akasalance yace. “Ki ƙara mishi”. Fuska ta narkar tare da faɗin. “Toh tunda ya daina kuka a bari sai anjima”. Ahankali ya girgiza kai kana yace. “A'a ki bashi yanzu”. Miƙewa Innayi tayi tare da cewa. “Khausar bari inje inyi Miki ɗan wake naji kina cewa kina son ɗan wanke tunda kika haihu baki ciba”. Murmushi tayi kana tace. “Yawwa Innayi na ayi min shi yaji yaji yayi daɗi sosai sannan asa min da ƙwai da lemun tsami akai”. “Toh". Innayi ta amsa tare da ficewa. Hajja Nana kuwa ido ta zubawa Moddibo lokacin daya zuge zip ɗin rigar Khausar ta baya. Cikin Mamaki tace. “Ohhhh ikon Allah”. Ta faɗa asanda taga yayi ƙasa da wuyan rigar Nonon fito, kan yaron ya tallabe ya sawa yaron abakinsa. Ta cigaba da cewa. “Gwara ma ni in tattara mu koma in bar muku gidanku. hankalin mu ya kwanta wai nan kai Sarki ne guda". Juyawa yayi ya kalleta kana yace. “Toh ce Miki akayi Sarauta anayinsa atsakanin Iyalai ne? Ai sarauta iya kacinta Fada”. Cikin taɓe baki Hajja Nana tace. “Ohhh Allah ya kawo mu zamani ai kai ko A Fada idan zaka samu za kayi musu taɓara” Murmushi yayi yana shafa sajensa yace. “Toh Matatace fa,Ko ba matata bace? Sadaki fa na biya”. Hararansa tayi tare da cewa. “Ka biya ko aka biya maka?”. Dariya maganar nata ya bashi amma sai ya murmusa yace. “Eh koma dai menene Matatace ni wlh kin isheni da gorin biya min sadaki akayi dan haka ni yau zan biya nawa sadakin”. Ya ƙare maganar yana jan wayarshi tare da ƴan danne-danne. Dariya ta sanya tare da cewa. “Ohhh baki baya mutuwa ai da kai da ita duk bakin ku ɗaya ne”. Khausar Murmushi take musu tana cigaba da bawa yaron Nono. Sai kuma ta kalli wayarta jin sautin shigowar saƙo. Hannunta na hagu tasa ta ɗauki wayar tare da buɗe saƙon. Cikin tsananin mamaki ta zaro ido ganin alert ɗin 10 million da Modibbo ya tura nata da rubu a jiki. *Minha ga sadaki na*. Cikin kaɗuwa tace. “Yah Mu'allim 10 million fa ka turo min me sanyi dasu, million goma”. Sai kuma ta ƙare maganar da kallon Hajja Nana dake cewa. “Da gaske”. Cikin tsananin jin daɗi Khausar tace. “Wallahi kuwa gasu kin gani”. Ta ƙare maganar tana miƙa mata wayar da kuma yaron sai kuma ta ruggumeshi tana saki kishi sassayan kiss tako ina a jikinsa. Ganin yadda ta ruɗene yasa Hajja Nana yarda bawai dan ta fahimci rubutun alert ɗin ba. Haka tai ta murna tare da godiya, kukan da Keyan ya sakan ne yasa ta saki uban ta karɓi ɗan kana taci gaba da bashi Nono. Cikin dariya Hajja Nana tace. “Daga yau ka huta da gori, kuma dole a bani million ɗaya a ciki”. Murmushin yayi tare da cewa. “Kawo account inki in baki naki sadakin tunda jikarki na gudun kishi sai in haɗata dake”. Cikin dariya tace. “Yoh ina ni ina aure ai na gama aure kam”. Dariya sukayi baki ɗaya. Bayan ta gama bashi da kansa ya mayar da Nonon kana ta mike tare da faɗin. “Kizo muje ki gyara min Siff ɗina ya hargitse”. Kai ta gyaɗa kana tace. “Toh”. Tare da miƙewa tabi bayansa da kallo Hajja Nana ta bisu sai kuma ta saki Murmushi tare da ɗaukan Jaririn tana mishi wasa. Suna shiga tsakiyar bedroom ya jawota jikinsa ya rungumeta yana shaƙan ƙamshin Kwalaccan Sirri da Humran _Aunty Aysha Aliyu Garkuwa_ da tayi amfani dashi sosai ƙamshinta ke zautar dashi yana masifar son ya riƙa shaƙar ƙamshin jinta yana masifar gigita masa tunani cikin wata kasalalliyar murya me cike da shauƙi da fitina yace. “Minha yanzu dan Allah tsawon kwana nawa kika fara Sallah?”. Cikin lumshe idanu da yanda lallausan tafin hannunsa ke yawo asassan jikinta ta fesar da sanyayyan numfashi tare da cewa. “Yah Mu'allim nafi sati biyu da fara Sallah ”. Ɗan ware idanunsa yayi kana muryansa can ƙasan maƙoshi yace. “Kina tsoron kishiya kuma kina tsoron kyautatawa mijinki da ɗauke bukatarsa”. Ashagwaɓe ta ƙyafta ƙwayar Idanunta cikin nasa tace. “Yah Mu'allim nifaaaa” Da sauri ya sake ƙanƙameta yana sakin ajiyar zuciya yace. “Minha kin san dai ina da buƙata bazan iya jiran abinda Likitocin nan suka faɗa ba”. Cikin sanyi da ɗan tsoro tace. “Thearter na fa kada ya ɓalle”. Yana yawo da hannunsa aƙugunta yace. “Bazai ɓalle ba”. Ya ida maganar yana zama bakin gado kana ya zaunar da ita kan cinyarsa tare da zuge zip ɗin rigar ta yayi ƙasa dashi kana shima ya cire nashi blanket ya jawo ya rufe su tare da ɗaura bakinsa akan dogon hancinta yana tsotsa kana ya mayar kunnenta yana hura mata sanyayyar iskan bakinsa. Sai kuma ya tsaya jin tana cewa. “Yah Mu'allim ina tsoron Theater nafa”. Muryansa can ƙasan maƙoshi irin na wanda ke cikin tsananin buƙatuwa yace. “Na sani zan biki ahankali”. Bai jira jin Abinda zata ceba ya shiga sarrafa ta cike da bege da kuma shauƙi yayin da ya shiga Binta hankali cikin shagwaɓa da tsoro tace. “Wayyo Yah Mu'allim wajen Theater na zafi fa ina tsoro kar ka ɓalle min ɗinki?”. Cikin ficewar hayyaci yace. “Minhaaaaa bazan ɓalle Miki ba ki nutsu dan Allah”. Ita kam cigaba da zuba masa shagwaɓa da raki tayi tana cigaba dace masa wajen Theater ta sai da ya ɗauki kusan awa ɗaya akanta kafin ya janye jikinsa daga nata ya janyota jikinsa ya rungumeta yana sa mata albarka sai kuma yayi Murmushi yace. “Matsoraciya sai raki ɗinki ɗinki ɗinki sai raki da tsoro". Cikin sauƙe ajiyar zuciya tace. “Yah Mu'allim Allah tsoro nake ji kar ya ɓalle”. Yana shafa shafeffen cikinta yace. “Ba abinda zai ɓalla shi Minha”. Miƙewa sukayi suka shiga toilet sukayi wanka atare bayan sun fito suka fara jiyo muryan Raudat na cewa. “Assalamu alaikum. Addah khausy”. Da sauri Khausar ta ƙarasa jan Zip ɗin rigar ta ta nufi ƙofa kallonta Moddibo yayi tare da cewa.. “Kamar Raudat ko?”. Kai ta gyada kana tace. “Eh Itace kuma kamar Naji kukan Keyan”. atare suka fita yana gyara wuyar rigarsa yayin da take naɗe ƙasan rigarta. Suka fita falon idanunsa ya sauƙa kan Raudat dake rungume da jaririn. Ware idanu Moddibo yayi tare da faɗin. “Ya Salam Aunty Raudhiy yanzu ke aka bawa Yaron nan?”. Murmushi tayi tare da kallon fuskar Keyan tace. “Yah Moddibo ai na iya riƙewa bazan kada shiba”. Murmushi yayi tare da faɗin. “Aikam ba zaki kada shiba kawo shi nan”. Karbansa yayi ya bawa Khausar ta zauna tana bashi Nono suka zauna gefenta suna ta hira... Bayan kwana biyar Momy suka wuce Saudi ita da Hajjaj Nana dan Modibbo ya biya musu umra, bayan sun gama aikin umrarsu ne suka koma Nigeria bayan komawar su da sati ɗaya akayi. Auren Amina da Baban Samira Sani cikin ikon Allah mai gadin gidansu Samira yace yana sonta fahimtar yanayin da take ciki kuma zuwa yanzu Alhamdulillah jikinta yayi sauki arana ɗaya aka ɗaura Auren Babanta ya bashi gida da jari kana ya nemi wani sabon mai gadi. Haka suka tare abinsu Samira da maigadinsu. ita kuma Amina tana rayuwarta da tsoho. Hajiya Bunayya da Hajiya Lami kuwa na can Sycatry suna gallar rayuwarsu da girban abinda suka shuka. Haka dai Rayuwa ta cigaba da tafiya Khausar kam Alhamdulillah yaronta ya kai wata shida yayi ɓul-ɓul dashi yana zama kana yana wangale baki yana dariya sosai. A wannan lokaci kuma suka tafi aikin hajji, Ita da Modibbo da ɗan Jaririnsu da Hadimar dake kula dashi da kuma innayinsu, Asma'u da Dr Jameel, Asiya da Dr Zakariyya, Dija da Yah Ali, Yah Abba da matar daya aura wata biyu ɗaya wuce. Sai Didi da Innayi da Abu Ali, da kuma Ibrahim da matarsa. Watansu ɗaya a can suka dawo, bayan sun dawo da mako biyu suka je Mexico. Sosai Lalla Hafsat da Rahama sukayi daɗin sosai. Itama kanta Khausar Mexico tayi mata daɗi sosai. Makonsu uku suka dawo. Taraba. Nigeria Gembilan Yau ya kasance labari cikin ɓadda kama Uncle Naseer ya shigo cikin garin Gembila da niyyar kwashe Mahaifiyarsa da Mahaifinsa su koma Indi'a da zama. Cikin dare ya shiga cikin unguwar su da sauri ya buɗe musu mota tare da cewa Mamansa da Babansa. “Kuyi sauri kushi ga mu tafi”. Kai Maman ta gyaɗa kana tace. “Toh ai gwara ka kwashe mu mu tafi mu huta da jaraba da Sa idon mutanen gari da gulmace-gulmace”. Ta ƙarashe Maganar tana shiga motar. Shikam Uncle Naseer cikin sauri ya shiga motar yaja su. Suka fara tafiya suna gab da fita garin Gembilan motarsu tayi tambul ta riƙa juyawa tana bugawa da tsaunukan gefen titi kafin ta kama da wuta sukayi mugun ƙonewa sai ya Fuskarsu ce ta rage kana kuma b.... By *GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH Book 3 PAGE 9* NA *Aysha Aliyu Garkuwa* Uncle Naseer kuwa, daga ƙugunsa zuwa ƙafafunsa ya ƙone ƙurmus kana bai mutuba yayin da fuskarsa yayi baƙiƙƙirin yanayin halittar fuskarsa ta sauya tamkar an babbaka kare. Mamansa, Babansa kuwa atake rai yayi halinsa Uncle Naseer kuwa cikin ƴan kawo agajine suka daukesa suka kaisa asibitin cikin. Taraba. Daga ƙarshe dai dole Lamiɗo aka kira Lamiɗo kam lokacin da akace Uncle Naseer yayi hatsari sosai yayi mamaki kasancewar baisan zuwansa garin ba kana yayi mamaki da akace iyayensa sun mutu... Lokacin da Lamiɗo ya isa asibitin ya samu ina baki ɗaya Uncle Naseer babu abinda yake Banda jujjuya kai cikin tsananin azaba da Kiɗima sosai Lamiɗo ya tsorata da ganin yanda halittarsa ta sauya baki ɗaya jikinsa yayi sanyi ya sake jin tsoron Allah da kuma tsoron saɓawa Ubangiji. Uncle Naseer kuwa Cikin matsanancin kuka da radaɗin azabar daya game jikinsa ya kalli Lamiɗo kana ya riƙe hannunsa tare da cewa. “Na ƙulla sharri na kulla rashin imani na ƙulla shirka da riya da yawa gashi Allah ya kamani lokacin da banyi zato ba lokacin da nake tsaka da shirya makirci na zama abin tausayi kuma abin ƙonawa cikin wanan azabebuyar wuta”. Kai Lamiɗo ke girgiza wa cikin tsananin tausayi da son kwantar mishi da hankali Amman ina. Cikin ihu da kururuwa Uncle Naseer ya cigaba da cewa. “Gashi tun daga nan duniya Allah ya fara ƙonani da wuta ina ga naje lahira nayi tsafi na sadaukar da mutane da yawa nasha jini”. Kai Lamiɗo ya girgiza cikin sanyi da mamaki yace. “Babu amfanin wannan maganar Naseer kawai ka tuba zuwa ga Allah kayi ta Istigfari”. Cikin kururuwa da azaba Naseer ya girgiza kai tare da faɗin. “Bazam iya ba bana jin zan iya tuba Ni mushrikine na haɗa Allah da wani saboda duniya wayyo nashiga uku na lalace kaicona wayyo Ni wayyo kaina”. Kallonsa Lamiɗo yayi cikin mamaki yace. “Baka iya tuba kuma toh kana so ka mutu da zunubi ne?”. Kai kawai Uncle Naseer ke girgizawa ya gaza buɗe bakinsa ya nemi gafarar Ubangiji alamar Allah ya hana shi samun rahamar sa haka sai ya cigaba da surutai yana kururuwa tare da faɗe-faɗe da kuma abinda yake aikatawa cikin azaba da zugin da jikinsa ke masa yace. “Ni nake zama Maciji na tsotsa jinin Amina naso in kashe ta Allah bai ƙaddara ba kwananta yana gaba ita. Asirinta ya ruhu naso in cutar da ita Allah bai nufa ba amma laifin Mahaifiyarta su suka nuna kwaɗayin kuɗinsu ga yanda rayuwa ta zamo mini”. Ya ƙare maganar cikin tsananin kururuwa da firgita yayin da yake fisge-fusge yana zabura kana idanunsa suka zazzago cikin ihun azaba yace. “Ka gani ko zan mutu kuma in na mutu cikin wuta zan shiga kaga wutar da ake nuna min kalletafa sai ci take tamkar ba abinda zai kashenta”. Cikin rashin sanin madafa da tarin tsoron Allah Lamiɗo yace. “Naseer ka daina kururuwa ka tsaya kayi salati da istigfari”. Yana cigaba da ihu tare da firgita yace. “Inyi salati kana ganin wutar da ake nuna min cikin wutar nan wai za'a jefani? Kuma kace inyi shiru”. Haka dai ya ci gaba da tona wa kansa asiri ɗa'a fade-faɗe abubuwan d yake ganin, yinin wannan ranan ya mutu aka tattarasu dasu da iyayensa aka binnesa... A cikin wannan kwanakin kuwa Baffa Jimeta yace Hajja Nana ta tattara kayanta su koma Yola ya gaji da zamanta a Jauro Yaya haka ya ɗaukota ta dawo Adamawa da zama ba don ta soba, Amman bini-bini zatace ya kawota haka kuwa dole yake kawotan tai kwanaki azo a ɗauleta tana komawa bazata rufa wataba zatace a Kaita. Amina kuwa Alhamdulillah rayuwa ta cigaba da tafiya mata cikin kwanciyar hankali tana ta Istigfari tana zaune Lafiya da Mahaifin Samira wanda har ta samu ciki. Wata rana ta fito daga gidan Samira kasancewar basu da nisa tayi mata rakiya kasancewar aminaine har zuwa yanzu suna Aminanta kansu. Suna fitowa suka ga wani mahaukaci yara na binsa suna ta ihu yana cewa. “Nine dai Boka Kar'uzu na aikata shirka na ɓatar da mutane na shuka zunubai da yawa Ni nariƙa yiwa mutane Sihiri!”. Cikin tsananin mamaki da rawan jiki Samira ta kalli Amina tare da cewa. “Amina wanna Boka Kar'uzu ne fa”. Da sauri Amina ta dafe ƙirjinta tace. “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un wallahi Samira shine rayuwa ba tabbas duk wanda ya saki Allah ya kama waninsa ya shiga uku”. Cikin sanyi Samira tace. “Wallahi kuwa Allah ya yafe mana Ubangiji yajiƙanmu ya gafarta mana zunubanmu”. Cikin kaɗuwa da rauni Amina tace. “Ameen ya hayyu ya ƙayyum ”. Boka Kar'uzu kuwa cikin ihu irin na ƙazamai lalatattun mahaukata da ƙarshen su ya munana ya cigaba da ihu yana faɗe-faɗe yaje zai tsalle ke kwalta wata ƙatuwar Mota ta buge kansa atake yayi daga-daga akan kwaltan mai motar kuwa ko tsayawa baiyi ba ya gudu. Irin ƴan iskan samarin nan ne suka sa Shebir suka kwashe Jejjegen naman gawarsa suka tura aƙaton kwalbet da ruwa ke gudu ruwa yaja gawarsa ya wuce ya kai sa cikin Fadamar Gembila kifaye suka samu abinci. Haka dai Rayuwa ta cigaba gaba da tafiya mai aikata Alkhairi ya fuskanci Alkhairi mai aikata sharri ya fuskanci sharrinsa ra'anul aiyn... Morocco rayuwa ta cigaba da tafiya cikin daɗi da kwanciyar hankali Keyah yayi kuɓul-kuɓul dashi ya shiga wata na takwas har ya fara tsayuwa Moddibo ne zaune a tsakiyar falon Didi yayin da Keyah ke rarrafe cikin Murmushi Moddibo yace. “Iyeeee Toyi manga toy-toy Toyi manga toy-toy manga”. Yana ɗan tafa hannunsa Keyah kuwa ƙoƙarin miƙewa yake yana ƙyalƙyala dariya. Didi dake gefe tayi Murmushi tare da cewa. “Ohhh zai fa haukataku in baku nutsu ba fa”. Dariya Moddibo yayi kana yace. “Didi kin gani dai ya fara tsayuwa ko”. Kallon Keyah dake tsaye ya dafe jikin kujera tayi tare da faɗin. “Toh Barka tunda ya fara tsayiwa yayi kyau anyi Sa'a Barka”. Matar Ibraahim dake gefen Didi tayi Murmushi tare da cewa. “Wallahi kuwa Didi kallifa ya tsaya fa”. Sai kuma ta juya ta kalli Khausar tace. “Ba ina faɗa Miki ba shekaran jiya ya riƙe kujera ya tsaya ba. cewa kin dai ji baki yardaba tunda ba ki gani ba Lalla Khausar”. Murmushi Khausar tayi tare da cewa. “Ato yanzu kam na gani da idona Oum Keyah”. Cikin sauri Matar Ibraahim ta rungume Keyah tare da faɗin. “Allah ya raya mana kai da Imani Keyah”. Murmushi Moddibo yayi kana yace. “Ameen ya hayyu ya ƙayyum”. Miƙewa tayi ta ɗauki Keyah tana masa wasa ta nufi Side ɗin sa. Khausar kuwa Ahankali ta juya ta kalli Moddibo cikin sanyi tace. “Yah Mu'allim na kwana biyu banji labarin Asma'u ba tun ranan sunan Addah Asiya fa bamu sake haɗuwa ba”. Cike da kulawa Moddibo ya gyara zamansa yace. “Toh badamuwa in Sha Allahu da daddare zamu je”. Bayan Khausar sun idar da sallar Isha'i suka tafi gidan Asma'u afalon suka same su zaune Dr Jameel na zaune ƙasa Asma'u na saman kujera kallon Khausar Dr Jameel yayi tare da cewa. “Yawwa gwara ma da kika zo”. Cikin kula Khausar tace. “Toh meke faruwa?”. Ta ƙare maganar tana miƙawa Asma'u Keyah data miƙo hannu”. Karbansa Asma'u tayi cikin sanyi murya take masa wasa tare da cewa. “Keyah ɗan Albarka”. Wangale baki yayi yana ƙyalƙyala mata dariya ƙyal-ƙyal-ƙyal rungumesa tayi tare da sumbatar sa kana tace. “Allah ya maka albarka”. Khausar na Murmushin yanda Asma'u ke nunawa Keyah soyayya tace. “Ameen!”. Moddibo kuwa ido ya ɗan zubawa Asma'u dan ya lura kamar fuskantar na ɗan kumbere kaɗan more especially eyes ɗinta. Ajiyar zuciya Dr Jameel ya sauƙe kana yace. “Ki ganta nan wai ita tana ga bata da rabon haihuwa tunda duk gwaje-gwajen da za'a yi anyi lafiyanta ƙalau nima lafiyata lau, amma gashi har yanzu bata da ciki shine take ta kuka b'na faɗa mata lokacine, ta kwantar da hankalinta”. Cikin sanyi tayi Murmushi hawaye na zuba a idanunta tace. “Ka gani fa Addah Asiya ta haihu Dija ma ta haihu amma Ni har yanzu ko ɓatan wata ban taɓa yiba ina so in haifawa Keyah Mata”. Murmushi Khausar tayi tare da faɗin. “Ai zaki haifa masa lokacine fa Asma'u yaushe ma akayi Auren badan haihuwar wuri da ake yiba”. Lumshe Idanunta hawaye suka zubo kana ta taune lips ɗin ta na kasa tare da faɗin. “Hmmm Khausar yanzu fa kusan shekara biyu muke nema tunda mun cika shekara ɗaya da wasu watanni da yin Aure har na biyu muke nema”. Araunane taci gaba da cewa. “Khausar am har yanzu fa ban haihu ba ko ɓatan wata ban taɓa yiba kuma duk gwaje-gwajen da za'a yi anyi ance lafiyata lau shima Dr bashi da matalan komai”. Gyaran murya Moddibo yayi kana yace. “Kiyi haƙuri Asma'u lokacine idan ban manta ba Ummi ta faɗa mana sai da tayi shekara bakwai ana takwas ta samu cikin J ɗina. Tace mana a randa ta cika Shekara tara ta haifi Jameel dan haka kema ki kwantar da hankalinki, in sha Allahu Babu abinda zai faru sai alkhairi kinji ko My dear”. Ya ƙare maganar cikin kulawa a matsayinsa na babban yayanta. Kai ta gyaɗa tare da cewa. “Toh shikenan Yah Moddibo yana iya amma dai ku sani a addu'a Allah ya kawo min masu albarka ”. “In sha Allahu zakmu yita Miki addu'a ”. Sai kuma ta juya jin Khausar na cewa. “Kima kwantar da hankalinki daga Yaye in kawo Miki Keyah shikenan zan bar miki ɗanki”. Murmushi tayi tare da kallon Moddibo tace. “Allah dagaske Yah Moddibo zaku bani?”. Zamansa ya gyara tare da cewa. “Toh me aciki Asma'u ɗana ai ɗan kine, kuma ɗan Khausar ɗan kine”. Cikin jin daɗi tace. “Toh Allah ya raya mana shi da Imani ”. Atare suka amsa da Ameen ya hayyu ya ƙayyum. Haka dai ranan sukai ta hiransu suna bata ƙarfin guiwa sai karfe 12 suka tafi. Bayan wata biyar Khausar ta yaye Keyah kana ta kaiwa Asma'u kamar yanda ta mata alƙwari satinsa uku agidan Asma'u ya saba da yaye ya daina tambayar Nono. Inda ya zamana mafi akasarin zamansa a tsakanin su koda Moddibo ya matsa aje a ɗauko sa Khausar zata danne sa akan abarwa Asma'u. Bayan Yaye Keyah da wata Uku Allah ya sake baiwa Khausar wani cikin. Bayan shekara watannin tara da kwana tara ta haifan ɗa namiji aka sa masa sunan Abualeey Youseef ana kiransa da Ayman haka ranan sunansa aka ta biki da hidindimu bayan ta haihu da wata biyu matar Ibraahim ma ta haihu hakama Dija da Asiya da Matar Yah Abba duk sun haihuwa, Ameena ma ta haifi ƴan twagaye duka maza, Samira Sani ma ta haifi yarta mace Masha Allah itama Khausar ta kuma haihuwa Uwar ƴaƴa maza. Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya akwana a tashi asarar mai rai. Keyah yana da shekara takwas Ayman nada shekara shida sun girma sunyi kyau gwanin ban sha'awa sunyi kuɓul-kuɓul dasu zuwa lokacin ƴaƴan ta maza Uku Keyah, Ayman, Haiydar mai shekara huɗu daga nan bata sake haihuwa ba sai yanzu da take rainon ciki na huɗu wanda yama ɗan girma. Ahankali Khausar dake zaune a babban Falonsu na ƙasa ta ɗan ɗago kanta ganin yaran na sauƙowa daga matakalan Benin Keyah na gaba Ayman na biye dashi Jikinsu sanye da wani Gezner Fari ƙall ƙafafunsu sanye da half covel golden color na maza mai masifar kyau yayin da kansu ke dauke da hula Zhanna bukar blue mai ratsin fari daya dace da kayan jikinsu sosai sukayi nasifar kyau tamkar ka sace su ka gudu. Anutse Moddibo da shigowar sa kenan daga Fada ya durƙusa tare da buɗe musu hannayensa alamar suzu ya rungumesu. Da gudu yaran suka rungumesa. Sai kuma suka maida kallonsu kan Ibraahim kana suka haɗa baki wajen cewa. “Uncle Ibraahim mun gama”. Ibraahim dake riƙe da ƴa mace Kyakkyawa mai suna Mifra wacce bisa alamu ƴar sace da sauri Ayman yace. “Mifra Oyoyo zo?” Da sauri tazo ya rungumeta sai kuma suka kalli Moddibo dake cewa. “Ina zakuje?”. Keyah na Murmushin yace. “Zamu tafi gidan Ummina” Kasancewar da Ummi suke kiran Asma'u. Yana murmushi yace. “Toh ku gaida Ummin ku” ya ida mgnar yana kamo hannun Haiydar dake ƙoƙarin kwanciya a jikin Khausar yace. “Tashi kuje kaima”. Cikin lingwaɓar da kai yace to kama ya miƙe. Kai suka gyaɗa kana suka fice tare da nufar gidan Asma'u. Suna shiga gidan suka sameta kwance a falo ta lulluɓe jikinta da bargo tana rawan sanyi cikin sauri da kulawa Keyah ya ɗaura hannunsa kan Fuskarta tare da cewa. “Ummina meke damunki?”. Cikin alamun zazzaɓi da rawan jiki tace. “Zazzaɓi nake ji Keyah”. Da damuwa atare dashi yace. “Uncle ya sani?”. Kai ta girgiza tare da cewa. “Bai sani ba ɗazun ne ya fara min” Cikin sauri ya juya gudu kna yace. “Bari naje na faɗawa Uncle Ibraahim yazo ya ɗauke ki mu tafi asibiti”. Ya ƙare maganar yana fita dai-dai lokacin kuma Ibraahim ke reverse ɗin motar yana shirin fita cikin ɗan ɗaga murya yace. “Uncle Ibraahim ka tsaya”. Ahankali Ibrahim ya tsaya cikin damuwa Keyah yace. “Ummina bata da lafiya Uncle Ibraahim ka Kaita asibiti”. Kai ya gyada tare da cewa. “Toh”. Kana ya yayi Parking tare da zaro wayarsa ya kira Dr Jameel ya sanarmasa. Shi kuwa Keyan da gudu ya koma cikin gidan hannunta ya kamo tare da cewa. “Ummi tashi mu tafi asibiti”. Ahankali ta gyada kai tare da miƙewa ta gyara mayafinta. Kama ta tasasu a gaba duka fita. Tun suna mota ta kira Dr Jameel ta faɗa masa gasu ahanya Ibraahim ya kawo mata yara yanzu zai kawota asibitin nan yake cemata ai Ibraahim ɗin ya gaya mishi. Suna isa asibitin Dr Jameel da kansa ya karɓeta kana yayi mata duk gwaje-gwajen daya kamata nan yaga ashe tana da ciki har na tsawon uku batare da sun sani ba cike da farin ciki ya ɗagata sama ya riƙa juyata kafin ya sauƙeta cikin matsanancin farin ciki yace. “Sweetheart albishir”. Tana ɗan lumshe Idanunta tace. “Goro”. Wani kallo ya mata still fuskarsa ɗauke da Murmushi yace. “Wani kalla”. Ɗan ware idanunta tayi da kuma yanda zazzaɓin ya fara sauƙa tace. “Fari ƙall”. Sake rungumeta yayi kana yace. “Ciki ne fa dake Sweetheart?”. Cikin mamaki da wani irin farin ciki data kasa tantance yanayin da take ciki tace. “Ciki?da gaske?”. Kai ya gyaɗa mata tare da cewa. “Wallahi da gaske Sweetheart kina ɗauke da cikina ajikin cikin da muke muradi da mararin samu”. Ahankali tace. “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un?wata nawa?”. Cikin farin cikin daya kasa ɓoyuwa asaman fuskarsa yace. “Har wata uku fa”. Da wani irin sauri ta ɗauki waya ta kira Ummi Ummi na ɗagawa tace. “Ummi Ummi ina da ciki har na wata uku” Cike da matsanancin farin ciki da jin daɗi Ummi tace. ”Alhamdulillah³ nayi farin ciki Ubangiji Allah ya raba lafiya kice na kusa zuwa”. Murmushi Asma'u tayi kana tace. “Yawwa Ummi dama kin daɗe baki zoba tun sunan Ayman baki sake zuwa ba dan haka kima fara shiri kin kusa zuwa”. Kai Ummi ta gyaɗa tare da cewa. “Toh Allah yakai mu da lokacin rai da lafiya”. Ameen ta amsa tare da katse kiran ta kira Khausar ta sanar mata murnan da Khausar tayi ba a cewa komai. Ummi na gama waya da Asma'u ta kalli Bashir da Haiydar dake zaune gabanta wanda zuwa yanzu sun zama manyan Samari sun mallaki hankalin kansu. Wanda tuni an gama maganar Auren Raudat da Bashir. Haiydar kuma ya auri ƴar Aunty Ruƙayya. sosai sukayi farin ciki jin Asma'u nada ciki kana atake awajen suka kirata suka tayata murna... Zuwa yanzu kuwa Khausar ta haife cikinta, an samu ɗiya mace, ansa mata sunan Didi suna kiranta Eeman Bayan watanni Allah ya sauƙi Asma'u lafiya ta samu ƴa mace wacce taci sunan mahaifiyar Dr Jameel A'isha suna kiranta Ishmah. Anyi suna lafiya an gama Alhamdulillah Ummi da Mommy sunzo wajen suna. *BAYAN SHEKARU ASHIRIN* Alhamdulillah ƴaƴan su sun girma sun mallaki hankalin kansu an haɗa Auren Keyah da Ishmah ƴar Asma'u. Sai Ayman da Mifra ƴar Ibraahim. Alhamdulillah Raudat ma ta haifi ƴaƴanta mata biyu duk sun girma Hakeem ɗan Lalla Hafsat ya Auri Fatma ƴar Dija Haiydar kuma ya Auri Ruƙayya yarinyar Rahama. Alhamdulillah rayuwa ta cigaba da tafiya tamkar yanda ake buƙata. Bayan anyi biki an watse. Ahankali Khausar ta shirya cikin shiga ta alfarma sai baza ƙamshi take sanye take cikin wasu tausasan rigar bacci masu masifar kyau da santsi idan ka ganta zaka yi zaton yau akayi Aurenta duk da cewa sun Aurar da ƴaƴan su amma tana da kyakkyawan jiki wanda Babu wanda zai ce ita ta haifi wannan yaran ga autarma Eeman an zama manyan ƴan mata wacce ba abinda ya bari na mahaifiyarta har rawan kan. Anutse ta tura ƙofan bedroom ɗin ta ta shiga idanunta suka sauƙa akan Moddibo daya sake zama magidanci baza kayi zaton ya wuce 45years ba saboda kyawun jikinsa nutsuwa, jin daɗi kwanciyar hankali sun sake wanzuwa acikin rayuwarsu yana ganinta ya buɗe mata hannunsa anutse ta ƙara sa tsakiyan tare da faɗawa jikinsa ya mata wani Amintaccen runguma ahankali yake cusa yatsun ƙafansa aƙasan nata ganin haka yasa ta ɗaura ƙafafunta asaman rumfar ƙafansa anutse ya riƙa tafiya da ita har yaje bakin kofa yana isa ya rufe ƙofar saurin kallonsa tayi tare da cewa. “Yah Mu'allim ya zaka rufe ƙofa”. Goshinsu ya haɗe waje ɗaya still ƙafafunta na kan nasa yace. “Um Minha Vidaa (My life) rufe wa zamuyi saboda kada _Aysha Aliyu Garkuwa_ ta shigo ta samu abin rubutawa Fan's ɗinta”... Acan gidan Dr Jameel kuwa Asma'u ce zaune tare da ƴaƴanta wa'anda ta haifa bayan ta haifi Ishmah ƴaƴa maza guda biyu wanda ɗaya an yiwa Moddibo ta kwara suna kiransa da Moddibo sai takwaran Abban Jameel suna kiransa da Abba ahankali tace. “Yah Moddibo”. Anutse ya kalleta cike da girmamawa yace. “Na'am Ummina”. Tana gyara zamanta tace. “Yaushe zakaje Nigeria ne?”. Murmushi yayi tare da cewa. “Ummi kwanan nan dai nake son zuwa amma nafi son mu tafi da Abba idan ya gama exams ɗinsa”. Kai ta gyaɗa tare da faɗin. “Toh ba matsala nima dama nayi kewar Ummina idan yaso zamu tafi tare”. Dr Jameel dake gefe yai mata wani kallo mai cike da so kauna yace. “Nima ɗin dani za'a je saboda nayi kewar Abbana da Ummina”. Hira suka cigaba dayi mai cike da farin ciki da ƙaunar junansu... Acan bangaren Ibraahim rayuwa tayi musu daɗi da matarsa. Haka bangaren Asiya ma Alhamdulillah rayuwa na tafiya cikin farin ciki da kwanciyar hankali ɗan ta ya Auri ƴar Amina da suka haifa da tsohonta... Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya hankali ya kwanta ya kowanne ɓangaren... _TAMAT BIHAMDULILLAHI..._ Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Na godewa Allah daya bamu aron rai da lfy da lokaci da dama ya nuna mana forkon littafin nan lfy tare da aramana daman ganin ƙarshensa lfy dani daku masu karatu. Toh Alhamdulillah. Yah Allah mun gode maka, muna kuma neman yafiyarka da gafararka da rahamar ka, Yah Allah ka yafe min kurakuran dake cikin wannan littafin ka shafe zunubaina kayi min gafara da rahama da jinƙai dani da masu karatu. Abinda mai dai-dai Ya Allah ka haɗamu a kan ladan, ya Allah ka nuna mana forkon wanda zan fara lfy da ƙarshensa duk lfy, ya hayyu ya ƙayyum kasa al'ummar Annabi su amfana da alkhairan dake cikin littatafai na ka tsaresu da sharrin dake ciki. *Yafiya! Yafiya!! Yafiya!!!* *Ina mai neman yafiyarku makarantan littatafai na, mace ko namiji babba ko yaro wacce muka taɓa mgn da ita da wacce bamu taɓa mgn da ita, na kusa dani dana nesa. Wala Allah akwai abinda nai Miki ko nai maka ko cikin rashin sani ko ajizanci ko kuma yanayin gajiyawa da raunin ɗan adam ki kuma yanayin ɗan fusatan lissafi ko gaza danne fushi, Ka! Ku! Ki! Haƙuri ku yafe min, kuyi min azurun na fama da yawan jama'a, ni na yafewa duk wacce taimin abu cikin rashin sani, Amman wlh ban yafewa masu fitarmin littafina su tura a wasu groups ɗin ba domin misali ka bawa ɗan uwanka mutum ɗaya biyu wannan da banner da turawa a groups mutum dari ko sari biyu ko uku ku dari hudu ai wannan kai kankama kasan me sunanka madadin samun wani suyi Murmushin group a kuma kwashi zunubi* *Littafin Sakayya dai kowa ya sani na kuɗine, in ma kin ganshi a wani wurin to na satane kika karanta 1k ne kacal, 0661110170 GTBANK Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidar biyanki ta Whatsapp number na 09097853276. In tura Miki littafin complete Kisha karatun ki ba haƙin kowa a kanku* *Gareku masu son kayan mata ko turarukan wuta da kulacca da su Humra a wannan no ɗin ne zakuyi min mgn 08069423567 in kuma kuɗi zaki tura to ta account in na na Jaiz bank zaki tura. 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta Whatsapp number na na 08069423567, in haɗa Miki kayanki in tura Miki shi duk state da kike nama lfy fata lfy**WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA* _Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu...Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_ _Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 08069423567 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci...._ 🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,*GARKUWAR* taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya* Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara. Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida. Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 08069423567 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so. 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida. GARKUWAR MA'AURATA*Al'bishirunku Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA* NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA. Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su. Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki. Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!? Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu. Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki? Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu, Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan. Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya. Akwai daya bangaren wato *KAMSHI* Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia. Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 08069423567 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn. 🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA *(GARKUWAR MA'AURATA)**Dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn, masu cewa wai sun goda suga number'n nayine, ko kuma a'a bari dai in na shirya zan sake miki mgn, ko kuma yanzu dai kuɗin bai cikaba tukun sai sun cika, ko kuma a wanne gari kike, kai munyi nisa, toh in ba iyayiba ai duk nisan state da kike ba ruwan mota ba inda bazai kai mikiba, nake turawa ƴan ƙasashen wajema. Kuyiwa Allah da Manzonsa in dai in kinsan Baki shirya sayan kaya ba ku daina min mgnar ku bari sai kun shirya,kada kizo ki ɓata min lokaci a banza, wlh ni na tsani harkar karanta, duk bayani na gamayi in dai saya zakiyi ga kuɗin kaya ga account no ga numberta ai sai ki biya kawai kafin kimin mgn. Tunda dai ga alamominshi da duk illar da yakeyi na faɗi in kina dashi faƙat in babu kada ki wani zo kice min bayani dan ko kinzo iya bayanin da zan miki kenan* Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha'awa. Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni'ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al'ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban lissafa. Sune manyan alamomin infection. Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi. Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni'ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya, zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa. KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni'imomin ki, da sha'awarki, duk kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA'AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau, duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha'awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor's suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic infection ne yar uwa. INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai Maganin na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi'izinillahi ta'ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma'ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya'ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER'N na 08069423567 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA'AURATA.*Masu son Maganin infection da maganin mata, ku marmatso wannan account no in ne naku ta ciki zaku turo kuɗin ku 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, Sai ki turo shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER'N na 08069423567. akwai sabbin kaya masu zafi suna nan bisa hanya, ki turo kuɗinki a saki cikin lissafi. Kayanen mata masu zafi sadidan daga Chadi akwaisu Garukan daka, gumbunan, Tsumummuka, cida Ciccibi Abodi cida kaza ci da jan nama kwanon ƙasaitacciyar mace biyar sirri, furar mata, gumbar madara Gumbar kolli mai ƙyallin al'khairi gumbar uku al'khairi, gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, gumbar riɗi, garin maɗi garin melɗamhi garin ilanwaddihi garin mallaka, tsumin riɗi tsumin tsirtai tsumin kinfi budurwa, tsumin riɗi, tsumin ta baje Sabaya, matsin maliƙi mai masifar matse mace matsin daɗi har maɗiga, mai ɗan kare kyau. Kullacar sirri al'ajabu shu'umar Humra, da duk sauran kan ƙamshi. Haɗin amarya budurwa ko bazawara haɗin mai jego ko uwar gida, akwaisu Available set ɗinmu hawa hawane akwai manya akwai ƙananan, ƙanan daga 40k ne 35k 30k 25k 20k 15k 10k shine ƙarami haɗina na karshe sai kuma haɗin kwanon ƙasaitacciyar shi 7k ne shine ƙarshen haɗina kenan... Manyan set ɗin kuma daga 50k 60k 70k 80k 90k 100k ke zaki faɗi haɗin nawa kikeso anyi miki kana kimin bayanin yadda kikeso da matsalarki ni kuwa nasan abinda zan haɗa miki, ina araha kam amman ina hana bashi*