PROLOGUE Wani lokaci, mutum ba ya tsayawa gaban madubi ne don ganin fuskarsa kawai… yana tsayawa ne don yin hukunci da kansa. Kin taɓa tsayawa a hankali ki kalli kanki? Ba da ido na wucewa ba, amma da idon da ke neman aibi a kowane sashe na jiki—kamar duk abin da ke jikinki yana buƙatar gyara kafin a ce kin isa a kalle ki? Pimples da ke fuskarki su fara zama kamar sun fi ƙarfinki magana. Sauyin jiki ya fara zama kamar tambaya mai nauyi wadda ba ki da amsa. Wani ɓangare na zuciyarki yana tambaya: “Me yasa ni ban zama kamar su ba?” A waje kuwa, duniya na tafiya. Wasu suna dariya cikin sauƙi, suna tafiya da kwarin gwiwa, suna jin kamar komai yana musu daidai. Amma ke… kina jin kamar kowace ido da ta kalle ki tana ɗauke da hukunci a cikinta—ko da ba gaskiya ba ne. Kin taɓa jin bugun zuciya yana ƙaruwa idan kina tafiya kusa da mutane, hannunki a gaban hijabinki ba don ado ba, amma don ɓoye abin da kike jin zai jawo kallon da ba ki so? Kin taɓa jin kalma daga wani ta zama kamar dutse a zuciya? Kalma ɗaya kawai… amma ta iya canza yadda kike ganin kanki na tsawon lokaci. Har sai zuciya ta fara maimaita ta ko da babu wanda ke magana. Sannu a hankali, mutum zai fara zama mai kallo a rayuwarsa—ba mai rayuwa ba. Yana kallon kansa daga nesa, yana kwatanta kansa da kowa, yana rage kansa a duk inda ya ga wani ya fi haske. Wasu mutane suna kiran hakan “rauni.” Wasu kuma ba sa ganin shi ma. Amma ga wanda ke ciki… yana zama nauyi da ba a gani. Ni Abeedah… Na san wannan nauyin. Na san yadda kalma ɗaya za ta iya zama kamar tana bin mutum har cikin dare. Na san yadda mutum zai iya fara jin kamar ba shi da kyau, ba shi da ƙima, ba shi da wani abu da zai sa a tsaya a kalle shi sau biyu. Na san yadda hankali zai iya zama kurkuku—inda mutum kansa ne mai tsare kansa da tunanin wasu. Akwai waɗanda suka koyi ɓoye rauni da murmushi. Akwai waɗanda suka koyi yin dariya duk da zafin ciki. Amma akwai wasu—waɗanda komai ke shiga musu kai tsaye, su riƙe shi, su maimaita shi, har ya zama gaskiyarsu. Ba kowa ne yake neman soyayya kawai ba. Wasu suna neman a gan su ne. A yarda da su. A ce suna da muhimmanci. Amma abin da ke da ban tsoro shi ne—lokacin da wannan buƙata ta fara cin mutum fiye da yadda ya ke sarrafa ta, sai ta fara mayar da shi baƙo a cikin kansa. Ni ba cikakkiyar jaruma ba ce. Ba ni da labarin da aka riga aka rubuta da nasara. Ni ce sakamakon duk abin da na ji, duk abin da aka faɗa min, da duk abin da na fara gaskatawa game da kaina. Kuma wannan ba labarin kamala ba ne… Labarin ne na girma. Labarin ne na yadda zuciya ke karyewa a hankali, sannan ta fara neman hanyar sake haɗuwa. Idan ka bi wannan labari, ka shirya jin abin da ba a saba faɗa ba—domin wannan ba labarin kyawawan kalmomi ba ne...Labarin gaskiya ne!! Sometimes the hardest person to love is yourself... Ni Abeedah na fahimci hakan Story about self esteem and self love over coming challenges and learning to love yourself even though SOME TIMES THE HARDEST PERSON TO LOVE IS YOURSELF BUT YOU LEARN TO LOVE ANYWAYS... RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁 🍁 A love that grew in_silence Aheart that hoped to be chosen And a destiny that has been decided SADAUKARWA Ga duk wanda ya taɓa yin mafarki mai girma... amma rayuwa ta rubuta masa wani labari daban. Ga waɗanda suka rasa kansu suna ƙoƙarin zama abin daduniya take so su zama. Ga waɗanda suke yaƙi da insecurities,low self esteemow self worth,self love da self-doubt a kullum, duk da cewa suna nuna ƙarfin da ba su ji suna da shi ba. Ga duk wanda ya taɓa kallon madubi ya ga flaws kafin ya ga kyawunsa. Ga waɗanda suke ɗauke da ciwon da babu wanda ke gani.. The ones who laugh the loudest, yet cry in silence. The ones who keep saying "I'm fine" when their hearts are anything but fine. Rayuwa ba koyaushe take ba mu abin da muka nema ba. Sometimes the prayer remains unanswered. Sometimes the door remains closed. Sometimes the dream stays a dream. Kuma wani lokacin, abin da ya fi cutarwa ba rasa abin da kake so ba ne... It's losing yourself while chasing it. Wannan littafin ba wai game da perfect people ba ne. Yana magana ne game da real people. Mutanen da suke jin tsoro. Mutanen da suke kuskure. Mutanen da suke son a ƙaunace su. Mutanen da suke neman kansu a cikin duniya da ke sa su ji ba su isa ba. Idan ka taɓa jin cewa baka isa ba... Idan ka taɓa jin kamar kowa yana tafiya gaba yayin da kai ka tsaya a wuri ɗaya... Idan ka taɓa rasa wani ɓangare na kanka saboda neman karɓuwa daga wasu... Then this story is for you. May these pages remind you that your scars do not make you less beautiful. Your failures do not make you less worthy. And the dreams that never came true do not define the rest of your life. Because sometimes... the greatest journey is not finding love. It is finding yourself. — Autumn 17 RU'UYAA: The Dreams We Never Lived ✨🌹 ❤️📖✨ NOTE:Free pages zasu kasance a first person's point of view (1st POV) paid pages kuma narrative point of view SHIMFIƊA... OSLO, NORWAY... 05:30 P.M Garin yana cikin duhu mai nauyi. Ba duhun yamma kaɗai ba ne,wani irin duhu ne da yake sa komai ya yi kama da ba shi da rai. Sama ta lulluɓe Oslo da gajimare masu kauri, hasken fitilun titi kuwa ya narke cikin ɗigon ruwan sama kamar ƙananan fitilu da aka manta a tsakiyar ruwa. Ruwan ya ɗan tsagaita, amma ƙasa ta riga ta jiƙe. Mutane na ta gudu daga nan zuwa can, wasu suna neman mafaka a ƙarƙashin rumfuna, wasu kuma suna tsaye a kan gefen titin ba tare da sanin inda za su dosa ba. Hanyar kwalta ta yi sheƙi da ruwa, tana ɗaukar hasken manyan gine-ginen kamfanoni da gidajen da ke gefenta. Bishiyoyin gefen titi suna jijjiga a hankali saboda iska, kusa da su kuma akwai dogayen kujeru da ake zama domin hutu,amma yau babu wanda ya damu da zama. Kowa yana da abin da yake nema. Kowa yana da abin da yake ji. A kan manyan billboards da aka jera a wurin, ake hasko hotunan hatsarin jirgin saman da ya faru jiya da rana. Hotunan sun sake maimaituwa. Jirgi. Wuta. Hayaki. Taro. Kuka. Mutane da dama sun taru a wurin, idanunsu manne da allon. Wasu suna kuka a fili. Wasu kuma sun sunkuyar da kawunansu, kamar har yanzu hankalinsu bai amince da abin da ya faru ba. Wata mata ta riƙe baƙin cikinta da hannaye biyu tana kuka ba tare da ta damu da yayyafin ruwan da ke sauka a fuskarta ba. Hayaniyar jama'a ta gauraye da sautin motoci da iska. Amma a tsakiyar wannan hayaniyar akwai wata tsaye ...ba ta jin komai. Ta tsaya can nesa da taron... kamar kasancewa daga nesan zai sa tafita daga cikin jerin wa'yanda abin ya shafa Sanye take da baƙar coat, ƙaramin mayafi ya rufe kanta da wuyanta. Hannayenta sun zurfafa cikin aljihun coat ɗin, amma ba don sanyi ba. Saboda hannayenta sun kasa daina rawa, Idonta sun yi jajir,Ba wai saboda rashin barci ba,ba saboda sanyi ba. Saboda abin da ta gani a kan allon ya riga ya shiga inda babu ruwan sama da zai iya wanke shi. Ta kalli hoton jirgin na ɗan lokaci sai ta ɗauke idanunta, ta sake kallo,ta sake kau da su. Kamar idan ta ƙi kallon hoton, abin da yake nufi zai daina zama gaskiya. Amma gaskiya ba ta taɓa bukatar izinin mutum kafin ta karya shi. Numfashinta ya fara fita da sauri, gajere-gajere. Ƙirjinta na matsewa kamar an ɗaure shi da igiya. Sai ta juya ta fara tafiya Mataki ɗaya,na biyu,na uku kafin ta ƙara sauri,ba ta san inda take zuwa ba. Ta dai san cewa dole ta bar wurin dole ta bar waɗancan hotunan dole ta bar muryoyin mutane Dole ta gudu daga kalmar da babu wanda ya faɗa amma take ihu a kunnenta tun jiya ya tafi..a'a! hakan ba daidai bane...zai dawo..wasa yake da yace bazai dawo ba...wasa yake that most be it!!!amma ina yake??? Hawaye suka fara zubo mata,tun tana sharewa har ta fashe da kuka. Ta dafe ƙirjinta da hannu ɗaya, tana jin kamar an cire zuciyarta daga cikin kirjinta aka ajiye ta wani wuri da ba za ta iya kaiwa ba... numfashinta kamar irin na mai asthma Sanyin ruwan sama ya daki fuskarta,amma bai kai inda ciwon yake ba...ko kusa Domin akwai wasu ciwon da ba'a gani...da ba sa konewa a fata. Suna konewa a cikin mutum...babu halin sosawa bare kaji sauƙi Ta bi wata ƙaramar hanya da babu kowa a cikinta. Takalmanta suna taka ruwan da ya taru a kan interlock, amma ba ta ma lura da hakan ba. Hawayenta sun ƙi tsayawa,ta goge su,sabbi suka zo,ta sake gogewa. Sai wasu suka sake gangarowa.. Kamar zuciyarta ta yanke shawarar cewa babu abin da zai iya hana ta yin kuka...kukan girman rashinta... Har ta isa wani wuri mai natsuwa. Akwai wata babbar bishiya a wurin—cike take da ƙananan fararen furanni. Iskar sanyi na motsa rassanta a hankali, furannin suna zubewa ɗaya bayan ɗaya a ƙasa. A gabanta kuma akwai teku. An katange bakin tekun da ƙananan tubalin bango, ruwan yana bugawa a hankali yana ja da baya. Gaba da baya... batareda tsayawa ba.. tare da iska mai sanyin dake ratsa ƙasusuwa Kamar wani abu da yake ƙoƙarin komawa inda ya fito, amma ba zai iya ba. tsayawa tayi,ta kalli tekun... tana ji inama zata iya mayarda rayuwar ta baya koda na yan daƙiƙun daya kasance tare da ita ne... Daga nan sai ta kalli furannin da ke zubewa daga bishiyar ɗaya ya faɗi kusa da ƙafarta ta kalle shi na ƴan daƙiƙu. Farin furanni.... Sai wani abu ya karye a cikin ta,ta saki wani irin ihu da ya fito daga can cikin ƙirjinta,ta durƙusa tana matse hannayen ta tsakanin cinyoyinta,jikinta gaba ɗaya yana rawa. Hawayen da suka cika idanunta suka gangaro suka faɗa kan interlock ɗin. ɗis!! ɗis!! ɗis!!! Suna haɗuwa da ruwan sama har ba a iya bambance wanne ne na sama, wanne ne na zuciyarta. Ta ɗaga kanta zuwa sama.... Ta runtse idonta gunjin kuka na fita daga bakinta ''M... me... ya sa shi...?''muryarta ta karye...maƙogaronta ya tsuke,ta haɗiye iska. Amma iska ma ta gagara kawo mata sauƙi... ''Me ya sa shi...?!'' Ta sake maimaitawa, wannan karon da ƙarfi... kamar akwai wani gabanta sai kuka ya mamaye muryarta...ta fara sabbatu,duniyar ta yi mata ƙunci. Tekun da ke gabanta ya yi kama da ba shi da iyaka. Sama ta yi nisa. Ƙasa kuma ta yi kamar ba ta da ƙarfin riƙe ta. A wannan lokacin, ta ji kamar ita kaɗai ce ta rage a duniya. ''LUMINA...''Muryar ahankali kamar daga mafarki. ta daskare,hawayen da ke gudu a fuskarta suka tsaya na ɗan lokaci,numfashinta ya makale ta lumshe ido ta sake nutsuwa dan saurara. Sai ta sake jin muryar dako a cikin miliyoyan mutane zata gane...saboda shi kaɗai ke kiranta da wannan sunan... ''LUNA...'' Idonta ta buɗe da sauri ta miƙe tsaye. ''Kana ina?!'' ta furta da ƙarfi tare da fashewa da kuka ta juya gefe guda ba kowa....ta juya ɗayan nan ma ba kowa sai iska,sai teku...sai bishiyar sai hazo... Hazo mai kauri da duhu ya fara cika wurin a tsakiyarsa,akwai inuwa....inuwar mutum. A hankali take matsowa, ta tsaya cak,ba ta gudu ba...ba ta yi tunanin tsoro ba Domin zuciyarta ta riga ta gane abin da idanunta suke ƙoƙarin tabbatar mata. Inuwar ta ƙara bayyana...har ya fito daga cikin hazon... Idonta suka wani irin lumshe kafin suka sake buɗe wa a slow motion... ta sani dama...bazai barta ba... sanye yake da fararen kaya daga sama har ƙasa. Fararen kayan sun haɗu da hazon da ke kewaye da shi har ya zama kamar suna tare ne,idan babu hazon... shima babu shi... kyakkyawar fuskarsa ɗauke da murmushi...ba murmushin farin ciki ba...wani irin murmushi mai laushi, mai ciwo. Murmushin wanda yake kama da sallama.. ta rufe bakinta...idonta suka sake cika da hawaye...amma wannan karon?murmushi ne ya bayyana tare da hawayen. Domin na ɗan lokaci, zuciyarta ta manta da gaskiya....ta manta da jirgin...ta manta da hotunan...ta manta da duniya...abu mai muhimmanci a wannan lokacin? Suna tare ta ga gida....taga bugun zuciyar ta...ta ga abin da take so ta gani...ta matsa kusa da shi da sauri... Crossing the distance between them...ta riƙe hannunsa....dake da ɗumi...bakinta ya kasa rufuwa tana shafa shi ta ko ina dan ta tabbatar shi ɗin ne..cikin jini da nama... Wannan ɗumin data saba ji a duk sanda jikinsu ya haɗu..shi take ji a yanzu...ko kuma wataƙila zuciyarta ce ta yanke shawarar cewa dole ta ji ɗumin nasa...sai ta sake shi kamar ta tuna wani abu. Ta rungume shi.... kamar zata shigar da jikinta cikin nashi, ƙamshin shi na haifar mata da nutsuwar data manta akwai a duniyar nan... yayi wrapping hannayen sa a ƙaramin jikinta dake tsananin rawa kamar zai karye ta ruguje... ''Dan Allah...'' muryarta ta fita cikin kuka. ''Kazo mu tafi gida.'' Ta ƙara ƙanƙame shi... ''Nayi alƙawarin zan saurareka... zan kyautata maka.'' Ta ɗago fuskarta tana kallonsa. ''Ba zan sake yin wani abu da baka so ba.'' Hawaye suka gangaro daga gefen idonta. ''Just... let's go home, please...'' ya ɗaga hannunsa ya shafa kanta....tare da goge mata hawayenta,his touch like a feather sending warm and tingling sensation a duk ilahirin jikinta ta lumshe ido... hawayen wasu nabin wasu... Kamar wannan taɓawar kaɗai ta isa ta gyara duk abin da ya karye...sai muryarsa ta zo a hankali. ''No, LUMINA...'' Ta buɗe ido...suka shige cikin nashi masu duhu kamar ramin da baida ƙarshe bambancin kawai shine yanzu sun bada damar ganin abinda ke zuciyar shi...utter sadness.. ''It's too late.''ya furta kamar raɗa,murmushin fuskarsa bai gushe ba. ''Ai ke baki sona ko?'' girgiza kai tayi da sauri. ''A'a...'' ''Ba koda yaushe kin fi so in yi nesa dake ba?'' Ta ƙara girgiza kanta, kamar tana ƙoƙarin girgiza maganar daga cikin kanta. ''Ba haka bane... wallahi ba haka bane.'' '' kuma kin tsane ni!" Ta riƙo fuskarshi da tafukan hannayenta. '' ban tsaneka ba...Ina sonka.... fiye da yanda nake son kaina pls..'' Muryarta ta ragu...ta sake fashewa da kuka tana tsananin roƙon shi da idonta akan ya gane abinda take faɗa gaskiya ne... ''Ina sonka sosai.'' Zuciyarta ta buga da ƙarfi. ''Just... kazo mu tafi gida, dan Allah.'' Amma ya cire hannayenta a hankali daga fuskarshi... Ya ja baya...tazara ta fara shiga tsakaninsu...ɗaya daga cikin matakan da zuciya ta fi tsoro. ta kalle shi... fuskarta tashin hankali ɓaro ɓaro... ''LUNA...'' ya kira in a whisper tareda ƙara taku zuwa baya...hazo ya fara haɗiye ƙafafunsa...sai jikinsa...sai kafadunsa. Murmushin fuskarsa ne kawai ya rage a bayyane. ''... it's too late.''wannan sentence ɗin ya ƙara rufto da duniyar ta... Muryarsa ta fara nisa. ''Kada ki jirani.'' Ta yi yunƙurin matsawa kusa...kuka wiwiii! ''Marry again.'' ta girgiza kanta hawaye na yarfi daga fuskarta...ta daskare... kalmomin sun bugi ƙirjinta...taji duniyarta ta ruguje ta faɗa cikin duhu mara iyaka ''A'a...'' Ta fara bin shi. ''Kada ka tafi.'' ta roƙa da tsananin bege..'' we can make things work..'' Ya ci gaba da tafiya cikin hazon ''Akwai abubuwa da nake so na faɗa maka!'' Ta ƙara sauri. ''Ka jini, dan Allah!'' Hawayenta suka koma gudu... itama kanta ta fara gudun zuwa inda yake... ''Ka tsaya!'' Ya juya ya kalle ta. Murmushin nan har yanzu yana fuskarsa. ''Komai ya ƙare, LUNA.'' Muryarsa ta yi sanyi. ''Ba zamu iya cigaba da kasancewa tare ba.'' ''A'a!'' Ta kira sunansa... kamar mahaukaciya amma ya ɓace cikin hazon...babu sawun shi bare ta bishi... Ta yi gudu. Amma duk lokacin da ta yi ƙoƙarin kusantarsa, hazon ya ƙara shiga tsakaninsu. Kamar akwai wani abu da ya riga ya yanke igiyar da ke haɗa su. Ta miƙa hannu. ''Kada ka tafi!...'' Murya a raunace... ''Miss! Are you okay?'' Matar ta ji an girgiza kafaɗunta...da ƙarfi... tayi hiri hiri da jajayen idonta da suka ƙanƙance... kamar an watsa mata ruwan sanyi ...take kallon Baturen da ke gabanta Hannayensa suna kan kafaɗunta, fuskarsa cike da damuwa. Sai ta kalli gefensa...Hazo..., ɗayan gefen ma hazo...babu kowa ,ta kalli bayansa,babu farin kaya...babu murmushi..babu hannun da ta riƙe babu komai sai teku..sai bishiyar sai fararen furannin da ke ci gaba da zubewa ɗaya bayan ɗaya.. a hankali ta kalli hannunta...wannan hannun da take jin kamar har yanzu yana riƙe da nasa...babu komai.... sai iska. Kamar fitilar da aka kashe ba tare da an sanar da ita ba... ta gane....ba ta same shi ba...ba shi ne ya dawo ba...zuciyarta ce ta ƙi barinsa ya tafi. Ta sake kiran sunansa a cikin zuciyarta, amma wannan karon babu amsa....sai wani sabon ƙunci ya cika kirjinta...da kuma emptiness da babu mai cikawa...ƙafafunta suka kasa riƙe ta...ta saki mutumin....ta durƙusa a kan interlock ɗin...tayi sujuda. Kuka ya sake fashewa daga cikinta—amma yanzu ba kukan neman ya dawo ba ne....kuka ne na wanda ya fara fahimtar cewa babu abin da zai dawo...duk da zuciyarta taƙi yarda da hakan Ruwan sama ya fara sauka a hankali...ya bugi bayanta. Ya gangaro daga coat ɗinta,ya haɗu da hawayenta. Teku ya ci gaba da zuwa da dawowa. Gaba. Baya. Gaba. Baya. Amma matar ta tsaya a wurin. Kamar furannin bishiyar da ke zubewa kusa da ita— wasu abubuwa suna faɗuwa sau ɗaya ne kawai. Kuma ba komai ya isa ya mayar da su kan reshe ba... Ta tuna wata magana da aka taɓa faɗa mata a wannan lokacin '' ki darajta abinda kike dashi...kafin ki rasa shi...'' yanzu take ji inama ace ta saurara,babu adadin kalamai da zasu iya bayyana nadamarta... +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 1. ...Farko...🖋️ Turawa na cewa, “Be careful what you wish for.” — Ka yi hankali da abin da kake fatan samu. Na ji wannan karin magana ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba,amma duk da haka, ban taɓa tsaya wa na yi tunani a kai ba. Ban taɓa tsammanin akwai ranar da zan waiwaya baya in ce: “Inama ace na tsaya na yi tunani a kan wannan kalmar kafin na furta abin da na furta ...” Tun ina ƙarama, ban taɓa samun kyakkyawan tunani game da kaina ba. Abubuwa da yawa da suka faru da ni ne suka koya min ganin duniya da idon tsoro. Kullum ina cikin ƙoƙonto da shakku. Ban isa ba...ban kai ba....babu wanda ya damu da ni...ban cancanci a so ni ba...ban da kyau...ban iya ba Sai kuma tambayar da ta fi kowacce sanyaya min jiki: “Har abada, abubuwan da kike ta addu’a a kansu, za ki taɓa samu? Akwai wanda zai so ki? Idan fa kika ƙare rayuwarki ke kaɗai?” A daidai lokacin da nake cikin ruɗani da rashin yarda da kaina, lokacin da zuciyata ta karye ta tarwatse zuwa ƙananan pieces, sai ya zo. Kamar wata da ke haska sararin sama mai duhu, ya fara tattaro ragowar zuciyata yana gyara ta da soyayya mai ratsa zuciya da ɓargo. Na ɗauka shine nawa...na manta da wancan abin da na taɓa roƙa.. Na manta da abin da na faɗa cikin rashin sani, cikin rashin tunani, ba tare da na fahimci nauyin addu'ar da nake yi ba. Duk cikin rashin sani ne..da rashin wayo. Sunana ABEEDAH ABDUL WAHHAB Haifaffar garin Zamfara , amma yanzu muna zaune a Kano, a Kofar Mashi. Mu uku ne kawai a gidanmu—ni, Mama da ƙanwata Asma'u. Babanmu ya rasu tun muna ƙanana. Hakan yasa ba mu san shi sosai ba. Danginsa ko sau ɗaya basu taɓa leƙowa ba,ba taimako, ba tambayar halin da muke ciki... Mama ita kaɗai ta raine mu har muka girma ni shekaruna goma sha bakwai, Asma'u kuma goma sha shida. Amma idan ka kalle mu, abu na farko da za ka ɗauka shi ne Asma'u ce babba. Ba don shekarunta sun fi nawa ba, sai don Allah Ya yi mata ƙira da ke sa ta zama kamar babbar mace. Kyakkyawa ce kamar matar novel—ba wai kyakkyawa kawai ba, tana da kaifin basira, iya magana da kuma natsuwa. Ni kuwa? A ganina, babu wani abu da mutum zai kalla ya yaba,bani da cikar halitta kamar Asma'u...Fuska? Ba kyau. Ƙwaƙwalwa? Ba wani abu. Shape ɗina kamar 1 Hakan ya sa na zama insecure,har tafiya nake yi da hannuna a gaban hijabi..cikin shekaru goma sha bakwai na rayuwata, babu wanda ya taɓa tsayar da ni da sunan soyayya. Amma Asma'u? Tana da farin jini sosai duk da ba kulasu take ba,ba wai ina kishin Asma'u ba ne Allah Ya kiyaye. Na yarda ta fi ni kyau. Ta fi ni zubi da tsarin halitta. Amma... Me ya sa mutane ba sa ganina?ai ni ma mace ce ko?ni ma na cancanci a so ni ko? Dan kawai jikina bai girma ba ai ba kyaun halitta ake dubawa ba,kyaun hali dana zuciya shine jigo... Na tuna lokacin da nake JSS2. Akwai wani yaro da na taɓa rubuta wa letter saboda ina son shi,ba ƙaramin ƙwarin guiwa na tattaro ba wurin juye abinda zuciya ta ke ciki saman paper nan,amma da ya karanta, maimakon ya ba ni amsa cikin mutunci, sai ya zaɓi ya wulakanta ni a gaban kowa. Har yau, maganganunsa suna nan a raina. «“Ke yanzu, dan Allah baki ji wani abu ba a ranki? Kalle ki, dan Allah! Yanzu ke a tunanin ki ke mace ce? ƙirji kamar allo, baya kamar plate, fuska kamar ƙwarangal, baki da kyau, baki da shape, gashi kusan kullum ke kike ɗauko na ƙarshe a ajinku, amma shine za ki kalle ni ki ce kina sona? Gaskiya wannan shine mafi munin cin mutunci da wani ya taɓa yi min!”» Maganganunsa sun rusa ni fiye da zaton mai karatu,mutanen da ke zagaye da mu kuwa, dariya suke irinta ƙeta ɗin nan Ba su taɓa bari ko rana ɗaya ta wuce ba tare da sun tunatar da ni abin da ya faru ba...na yi kuka kamar raina zai fita...Mama da Asma'u sun yi ta lallashi da nasiha, amma komai ya zama kamar ana zuba ruwa a dutse. Ƙirjina har ciwo yake yi saboda yadda abin ya shiga zuciyata..na daina fita sosai. Domin daga lokacin da ɗaliban makarantarmu suka hango ni, shikenan. Tsokana za ta fara—ko ina, ko a gaban wa,ni kuma ban iya kare kaina,saboda ina ganina ƙasa dasu... Kusan kullum idan na fita, nakan dawo da hawaye a idona..daga nan na fara addu'a..na roƙi Allah Ya yi ni kamar sauran mata Ya ba ni abin da yake ba mata...na yi kuka...na yi sadaka...na yi magiya...amma babu abin da ya canja...saboda wasu lokuta zaka yi komai da komai da kake tunanin zai sa ka samu cikar burin ka amma sai kaga ba haka ba.. Zuciyata ta ƙara ƙuntata,abu kaɗan sai in fashe da kuka...idan na ga wasu mata ƙirji a cike, sai in kalle su ina tunanin: “Inama ace nima nawa haka suke...” Daga baya na fara saka bra,hakan ya ɗan ba ni ƙwarin gwiwa..amma da zarar na je makaranta, sai tsokanar ta dawo..suke kirana flat board Sun riga sun san cewa ba ciko na gaske ba ne...sai na daina sawa,baƙin cikina har zuba yake, musamman idan na kalli Asma'u. Alhamdulillah. Yarinyar kamar matar novel. Gashinta har tsakiyar baya,nakinta ƙarami. Hancinta kamar pencil. Idanunta manya masu kyau. Shape ɗinta mai ɗaukar hankali. Natsuwa. Iya magana. Kamar dai duk wani abu da ake bai wa matan novel, Asma'u tana da shi—over and over. amma tsawonmu kusan ɗaya. Ni ma doguwa ce, amma ba ni da ƙiba sosai. Wasu lokuta nakan ji kamar rashin ƙibata ma yana daga cikin dalilin da ya sa nake haka...gashina kuwa?taurin tsiya ne dashi,da ƙyar yake saukowa idan na yi kitso...wurin taje shi sai na kusa sakin fitsari. Fuskata ɗauke da wani special abu da ba kowa ke da shi ba, PIMPLES... Manya manyan pimples ne suka dabaibaye min fuska..duk abin da na yi na magance su da magungunan gida, sai dai su ƙara yawa. Na yi amfani da magungunan ƙyamis ma, amma maimakon su taimake ni, sai suka ƙara lalata min fuska ta hanyar barin tabo Wasu lokuta har kuka nake yi saboda waɗannan abubuwan..amma ban daina neman hanyar da ƙirjina zai girma ba...ko pimples ɗina su ragu...ko gashina ya yi tsawo...ko yanda zan zama kamar matar novel Mai shape da kyau ba Duk yanda na yi ƙoƙarin kada in haɗa kaina da Asma'u ko wata mace da ta fi ni kyau, na kasa...duk da na san hakan baƙin ciki kawai yake ƙara min. Na kan ɗauki kaina a matsayin mara godiyar Allah,ya kamata in gode masa saboda yadda Ya halicce ni,amma na kasa. Musamman idan na tuna yadda ake cin mutunci na saboda hakan.. Wata rana wasu 'yan matan ajinmu naji suna magana game da abubuwan da mace za ta iya yi idan tana son ƙirjinta, mazaunanta da hips ɗinta su ciko da sauri. Nan take na riƙe komai,na fara yi,ina yi ina addu'a. Ina kuma jin wani irin farin ciki idan na tuna cewa watakila ba da daɗewa ba ni ma zan zama “cikakkiyar mace”sai dai me?na yi na gama,babu abin da ya canja,sai ɗacin rai da na kwasa. Na sake faɗawa cikin ƙunci da damuwa,har sallar dare na fara yi, ina roƙon Allah duk yadda zan iya,amma abin ya ci tura,daga ƙarshe na haƙura da gwada komai...duk da ba duka ba, Ba wai na daina fatan samun abin da nake so ba ne,sai dai na fara tunanin cewa watakila babu abin da zai canja. Idan na saka hijabi, ba na iya sauke hannuna ƙasa,ina gudun kada a ga ƙirjina...kun dai san maza da kallon tsiya... Idan iska ta kaɗa hijabi, sai in gyara shi nan take don kada ya manne a jikina,don kada a ga bayana ya yi kamar plate..domin mutane haka suke faɗa,nima sai na yarda Amma duk da haka, ban tsira daga maganganunsu ba,wasu har suna kirana suke da mayya. Dalili? Idanuwana,ruwan toka ne, masu duhu, kuma shape ɗinsu yana kama da na mage. Mutane sun sha ganin mage da daddare mai irin wannan ido, don haka suka ƙara gasgata cewa ni mayya ce. Har wasu suke gargadin 'ya'yansu su nisance ni,lokacin da na shiga SS3, da farko babu ruwana,bayan yadda aka ci min mutunci a SS1 da SS2, na rasa ƙarfin guiwa. Ina tsoron shiga cikin mutane. Ina tsoron kada wani ya faɗi wata magana da za ta sa in yi kuka. Amma ban tsira ba. Ganin abin nasu gaba yake, ba baya, yasa na fara koyon tsayawa wa kaina. Ko da ba sosai ba. Akwai wani malami bayarrabe da ke kirana Abeedatuwo,wai shi ala dole sai yace Abeedatu Abin na ba ni haushi sosai,mutane suka lura,sai suka ɗauki sunan suka manna min shi,wasu ma har Abeedah ba sa cewa... Tuwo kawai. Ba a makaranta kaɗai ba,har gida abun ya biyo ni. Gidanmu gidan kara ne. Ɗaki ɗaya tak muke da shi, kuma dukkanmu tare muke kwana. Gidan haya ne. Mu talakawa ne—talakawa tuguf-tuguf. Ni nake aiki a wani hotel don in sama mana abin da za mu riƙe kanmu da shi. Mama ba ta son zuwa na wurin,amma babu yadda muka iya. Mama tana matuƙar ba ni tausayi. Ta tsufa, amma har yanzu burinta guda ne,ta ga mun zama wani abu a rayuwa. Duk da tsufarta, har yanzu tana son ta yi aiki a duk inda za a biya ta, don ta inganta rayuwarmu. Amma ba zan iya bari ta yi hakan ba. Shi ya sa nake aiki. Asma'u kuwa, tunda ta iya lalle da kitso, ita ma takan yi,a haka muke gudanar da rayuwarmu, cikin rufin asirin Allah. Aikin hotel ba shi da sauƙi,musamman idan ka haɗu da wasu customers marasa mutunci Shi yasa koyaushe nake tafiya da ƙaramin kwalbar turaren yaji dake ɓoye a jikina. Duk wani ɗan iska da ya nemi yi min rashin mutunci, sai ya ga tijara,an sha kai ƙara ta wurin manager saboda hakan,ya sha yi min faɗa da barazanar kora Amma bai taɓa aiwatar da hakan ba,saboda Allah Ya jefa wani irin ƙauna ta a zuciyarsa..ba ƙaunar soyayya ba. A'a. Irin ƙaunar da mutum zai yi wa ƙanwarsa. Akwai akwai wasu jigon mutane da bana so...Masu kuɗi. Ba wai na tsane su gaba ɗaya ba,amma kawai kasancewarsu kusa da ni yana iya sa haushi ya taso min...a ganina, suna ganin kansu kamar su suka fi kowa. Kamar kowa ƙasa da su ne. Kamar kowa bawansu ne. Suna da girman kai, jijji da kai da ɗagawa. Ni kuwa duk lokacin da Allah Ya kai ni aiki a ɗakin wani mai kuɗi, idan ransa yana dubu, sai na ji raina ya ɓaci. Amma babban abin da ya sa bana son masu kuɗi shi ne tunanina... A ganina, rayuwa tana zuwa musu da sauƙi. Duk abin da suke so suna samu saboda suna da kuɗi,ba sai sun sha wahala kamar mu talakawa ba,kuma a tunanina, ba su da tausayi ko kaɗan. Yau Lahadi ,gobe Monday,bayan sallar La'asar, Mama tana zaune a barandar ɗakinmu tana kallonmu. Asma'u kuma tana wanke uniforms ɗinmu,ni ina tsaye da madubi a hannu na ina kallon pimples ɗina. Haushi ya cika zuciyata kamar zan cije wani abu,amma me?na sauke ajiyar zuciya, sannan na ɗauki wata gora da na zuba ruwan shinkafa,na samu wuri na zauna.. “Asma'u, ɗan zo ki shafa min ruwan nan a kai!”na faɗa ina ci gaba da kallon madubi,ƙarshen kitsona na riƙe a hannu ina ja, ko zai sauko aƙalla ya ɗan wuce wuya. Amma shegen abun, saboda taurin kai, ya ƙi ƙara tsawo,can na ji Mama tana dariya. Ɗagowa na yi na kalleta, fuska ta kamar zan yi kuka. “Shine kike min dariya ko?” Na faɗa a shagwaɓe,rufe bakinta ta yi “A'a, wai gani nayi kina ja'in-ja da abun...” Sai ta sake tuntsirewa da dariya da dariya,Asma'u da ke shanyar hijabi saman igiya na tayata... na cika na yi fam Mama ta kalle ni. “Wai shi wannan ruwan shinkafar, aikin sa meye? Mene ne amfanin sa?”Cikin turo baki na ce, “An ce fa yana da Aminu acid!” Kafin in ƙarasa, Asma'u ta fashe da dariya. “Ke, tuwo! Amino acid ake cewa, ba Aminu acid ba!” tsaki na ja kamar bakina zai katse,ganin yadda suka maidani abun dariya ya ƙara ba ni haushi. “Ko uban me ake kiran shi! Shi Aminu acid ɗin yana sa gashi ya yi ƙarfi sannan yana haɓaka girman gashi!” Na faɗa a harzuƙe...Mama ta kalle ni da murmushi. “Ke da gashin ki yake nan kamar ƙirigi, har da comb kika karya mana tsabar yadda yake da tauri, shine kike neman wani ƙarfin gashi kuma?” Na daure fuska. “Idan gashin yayi tsawo zan sa masa relaxer! yayi kamar irin na indiyawa..” Wata irin muguwar dariya Asma'u ta saki har da riƙe ciki. “Waih! Sallar da ta wuce kin manta abin da relaxer ta yi miki kenan? Ta kwashe gashin ki kika koma kamar talle mai shayi! Black Indian!” Miƙewa na yi na bi ta da gudu...itama bata jira niba ta ɓoye bayan Mama su biyun suna dariya... “Ayi haƙuri Anty Tuwo!” Niko sai huci nake kamar wata zakanya. “cewa fa tayi ina kama da talle mai shayi!” Mama ta ɗaga gira. “Toh, ko shine surukin namu?” Wata irin ƙara na fasa, na faɗi ina birgima. Su kuma suka cigaba da dariya. Kafin daga ƙarshe Mama ta jawo ni jikinta. Asma'u ma ta rungumeni ta baya. Mama ta shafa bayana a hankali. “Ina roƙon Allah Ya nuna min ranar da za ki karɓi kanki yadda Allah Ya yi ki, Abeedah. Ya nuna min mijin da za ku aura ku biyun nan. Kuma ya nuna min ranar da Tuwo za ta girma ta dena shagwaɓa...” Ta faɗa cikin wani yanayi mai wuyar fassara. Na ji Asma'u ta ce, “Ameen.” Ni kuwa na yi shiru. Ban sani ba ko zan iya rayuwa wata rana ba tare da Mama da Asma'u ba. Ina matuƙar son rayuwarmu yadda take. Ba na son komai ya canja. Bana son komai ya yi yawa. Ko ya yi kaɗan. Ina son komai ya kasance yadda yake. A ganina, yawan abu yana sa mutum ya ɗauki ni'ima a matsayin abin da ba komai ba, har ya kasa ganin albarkar da Allah Ya ba shi. Amma idan abu bai yi yawa ba, sai mutum ya koyi tattali. Ya koyi godiya. Ya koyi ganin abin da yake da shi a matsayin ni'imar Allah. “Tuwo, ba ki ce Ameen ba!” Asma'u ta katse min tunani.... “Na ce a zuciyata munafuka.” Na amsa ina jan gashinta. Ta yi dariya. “Kada ki ɓaɓɓake min gashi, ni dai!” Mama ta girgiza kai. “Ku ɗaga ni kada ku ƙarasa ni!” Sakin gashin Asma'u na yi, na ƙara shigewa cikin jikin Mama na kwantar da kaina. Asma'u ta tashi ta ɗauko ruwan shinkafar, ta miƙa wa Mama, sannan ta koma ta cigaba da aikinta. Mama ta fara shafa min ruwan a gashina, tana yi min tausa a hankali. Na lumshe idanuwana. A wannan lokacin, zuciyata ta yi shiru. Kuma a cikin wannan shiru, na yi wata addu'a. Ba don ƙirji na ya girma ba. Ba don pimples ɗina su ɓace ba. Ba don gashina ya yi tsawo ba. Sai don wata rana Allah Ya kawo min ranar da zan amshi kaina yanda nake.'..babu abinda yakai karɓar kanka a yanda kake daɗi Ranar da zan kalli madubi ba tare da na tsani abin da nake gani ba. Ranar da zan iya tafiya ba tare da hannuna ya riƙe hijabi saboda tsoron maganganun mutane ba. Ranar da kalmomin mutane ba za su ƙara samun ikon karya ni ba. Ranar da zan iya cewa: “Wannan ni ce.” “Kuma ban da abin da zan gyara domin in cancanci a so ni.” Ban san cewa a wannan lokacin, ina addu'a ne ga wata rayuwar da ba zan taɓa iya hasashen yadda za ta zo ba. Ban san cewa wata rana zan waiwayi wannan ƙaramar yarinyar da ke kwance a cinyar mahaifiyarta, ina kallon ruwan shinkafa yana jika gashinta, sannan in fahimci ainihin ma'anar kalmar da ban taɓa ɗaukar muhimmancinta ba.* Be careful what you wish for. Domin wani lokaci... Allah yana amsa addu'arka. Amma amsar ba koyaushe take zuwa cikin irin yanayin da ka zata ba. +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 2. ...a mafalkina...🖋️ '' Albishirin ki tuwo " Mama ta furta tare da dakatawa da shafa min ruwan shinkafa a kai tashi zaune nayi ina kallon ta kafin in kalli Asma'u dake riƙe dariyar ta hmm...ban yarda da su biyun ba amma sai nace ''goro'' ina kallon Mama cike da ƙoƙonto, basarwa tayi tace '' Yau tuwon masara za'ayi da daddare!" zaro ido nayi baki sake ina kallon ta kafin kuma fuska ta,ta sauya kamar wadda ruwan sama sukayi ma duka, juyowa nayi na kalli Asma'u ta tuntsire da dariya ji nayi kamar in haukace '' Mama wane irin tuwon masara kuma?" na furta baki na rawa,na tsani tuwon masara a rayuwa gara tuwon dawa sau dubu tace '' tuwon masara dai da kika sani da miyar kuka!" dafe zuciya ta nayi kamar mai ciwon zuciya baƙin ciki na turnuƙe ni sosai fuuu na miƙe na shige ɗakin mu dake ɗauke da ledar da taga yaƙin duniya ta gode rabbi na kwanta saman gadon daya girme mu nida Asma'u ina risgar kuka,shekaran jiya da jiya duk wannan mugun abun mukaci shine kuma yanzu ma za'a dafa mana shi... share hawaye na nayi sai kuma na ƙara fashewa da kuka harda dukan gadon '' kada ki sabauta mana gado Dan Allah '' inji Asma'u tana cigaba da ayyukan ta... da daddare bayan sallar isha'i zaune muke cikin duhu kafin Mama ta shigo da fitila a hannun ta ɗayan hannun riƙe da plate ɗin tuwo, ajiyar zuciya na sauke lokacin da ta ajiye plate ɗin tsakiyar mu ta zauna hannu suka zura su biyu suna ci niko na zuba musu ido '' bazaki ciba?" Inji Asma'u,Mama ta kalle ni, saida na harare plate ɗin sannan na zura hannu muka cigaba da ci kuma ba ƙarya abincin yayi daɗi sosai daga ƙarshe har da janye plate ɗin nayi na iyarda cinyewa na siɗe taɓe baki mama tayi '' ai na ɗauka da yunwa kike shirin kwana..dama kince cikin ki yayi ƙato...'' idona kamar zasu faɗi hakane fa! bana so ciki na yayi ƙato wasu lokuta abincin ma bari nake saboda hakan, daidai nan aka kawo nepa da sauri na miƙe na isa gaban mirror dake maƙale da tsohuwar wardrobe ɗin mu daga gefe kuma ƙaramar TV tun kafin in ɗaga rigata naga yanda ciki na ya turo kamar me ciki, ihu na fasa Mama dai tayi zugum tana kallona kafin taja tsuki ta fita daga ɗakin daidai Asma'u data tafi wanke hannu ta shigo jawota nayi da ƙarfi na tsayar da ita gefe bata cemin komai ba sai ma tayani ɗaga rigarta da tayi fuska a tsuke... kallon cikinta nayi gashi nan a ɗame kamar bataci komai ba...waist ɗinta ɗan ƙarami hips ɗinta manya tsabar yanda waist ɗinta yake gani nake kamar idan mutum ya riƙe da ƙarfi karye wa zai yi ƙwace rigarta tayi ta wuce ta kunna tv ta zauna bakin gado tana kallo,na kalli kai na a cikin madubi kamar wacce akayi ma albishir da mutuwa kife kaina nayi a saman table ɗin kwalliyar mu ina furta kalmar turancin dana fi sani '' why!" Ina kukan daba hawaye amma ciwon danake ji da gaske ne ajiyar zuciya Asma'u ta sauke tana faɗin '' dama zaki kalli kanki yanda nake kallon ki,ina son yanda kike komai naki tuwo toh ke meyasa ba zaki karɓi kanki ba?" Sharply na juyo ina kallon ta da wani expression a fuska ta '' sauƙin faɗa ne dashi saboda bake kike fuskantar abinda nake fuskanta ba sannan bake kike jin yanda nake ji ba!" nayi maganar ina hararar ta,taɓe baki tayi kafin ta zare ɗan kwalinta gashinta ya fara walwalewa ya zuba har tsakiyar bayanta wani kuma ya zubo ta gaba sakin baki nayi ina kallon ta kafin na kalli nawa kan dake ɗauke da kitso all back '' why he!!!!" na sake furtawa ina dukan table ɗin bada ƙarfi ba '' why me ake cewa ba he ba,idan kika ce he kina nufin namiji kenan!" ɗago idona na nayi ina hararar ta'' to kun alijabe turatu uwar turai '' (queen Elizabeth) '' bafa kun alijabe ba elizabe...'' kafin ta iyar na ɗauki powder na jefe ta dashi ya same ta a goshi '' idan ina turanci kada ki ƙara gyara min!" shafa wurin dana jefeta tayi tare da faɗin '' mugunta dai ba kyau!" kafin ta mayar da hankali tana kallon Chinese drama ɗin da ake yi nima zuwa nayi na zauna kusa da ita muna kallo tare idan aka nuno wata ko wani mai gashi inyita santi,riƙo hannu na tayi ta ɗaura saman gashin ta ta kwantar da kanta saman cinyata '' ɗan shafa min kaina kinji!" tayi maganar a sheɗanan ce, kamar in ture kanta amma saboda yanda nake son gashi na kasa cike da jin haushi na dinga jan gashin muna kallo tare '' Tuwo xoki kwaso kayan da Asma'u ta shanya ruwa za'ayi!" Mama ta faɗa tana tattara kayan dake tsakar gida ta kai kitchen '' ga ninan tafe'' na bata amsa amma banida niyar tashi '' yaushe hadari ya taru? nasan yanzu zasuyi gaba da wutar su...'' Asma'u ta faɗa tana tashi daga jiki na,da takaici nace '' dan Allah kada kiyima mutane baki'' sannan na fita naje kwaso uniform Muna shigowa cikin ɗakin aka fara ruwa da mugun ƙarfi tule ma Asma'u kayan nayi a jiki ina faɗin'' ki lunke'' fara ninke kayan tayi na zauna kusa da ita mama a gefe muna kallo bayan na banko murya saboda ƙarfin ruwan baya bari aji magana...dama kuma dai ba turanci nake ji ba kawai kyaun mutanen da yanda suke tashi da kuma kayansu da gashin suke burgeni '' Tuwo rufe mana ƙofa feshi ake!" '' toh mama!" nayi amsa Batareda na tashi ba idona yaƙi barin TV'n duka mama ta kawo min nayi saurin tashi naje na rufe ƙofar ina turo baki dai dai ankawo wurin akshon (action) Asma'u tace '' ace kawai sai a ɗauke wuta?" '' ta Allah ba taki b..'' kafin in iyar yan nepa sun warce wutar su, faɗuwa wurin nayi ina shure shure ina birgima ɗauke ƙafafunta Asma'u tayi tana sheƙa dariya '' mama kin gani yarinyar nan baƙin bakine da ita wallahi!" nayi miƙe na hawo gado matsawa Asma'u tayi sanin tsaf zan kaimata duka cikin duhu mama tace '' kai banson shashanci fa!" tsawar da aka saki yasa muka ƙanƙameta,fitila ta lalubo ta kunna ta kalli Asma'u '' ke tashi kije ki ajiye kayan nan a closet!" kwasar kayan tayi tasa mana a wardrobe tsakiyar gadon na kwanta mama da Asma'u a gefe da gefe na bargo suka jawo kowa ya lulluɓe banda ni don na tabbar da wuri zan fara jin zafi ruwan suka ƙara ƙarfi sauka Asma'u tayi ta kashe tv da wuta ta dawo ta kwanta '' Mama Saida safe,tuwo sai da safe!" ''Allah ya bamu alkhair'' mama ta amsa '' Ameen '' mu biyu muka faɗa.... Bayan mun yi sallar asuba Asma'u ta shiga aiki kamar dai matar novel ta gaske tayi wannan tayi wancan,nidai na tsuguna bakin ƙofar ɗaki ina binta da kallo harda tagumi mama kuma tana kitchen tana haɗa kunu...kunu kawai mafa babu ƙosai...kai! zuciya ta kamar zata kama da wuta.. ɗauke idona nayi daga kallon su na koma tunanin mafalkin da nayi wai a cikin mafarkin,wani farin mutum mai baƙin gashi wanda bama ɗan Nigeria bane yake faɗa min yana sona...Ni Abeedahtuwo 😳 harda sunan shi ya faɗa min amma dai na manta sunan dan shima bana yan Nigeria bane...dogon tsuki naja..in bacin da kwashe kwashen mafalki nida ko airport ban taɓa zuwa ba...ban masan hanyar ba ta ina zan haɗu da bature? Kuma na tabbatar yana ganina zai juya yace anyi kuskure niba wannan na sani ba... 🙄! amma fa kalaman shi ɗin sun ratsa zuciya ta..duk da suma na manta su,wata rana nima dai insha Allah zan gano masoyina na gaskiya ..irin mazan novel ɗin nan masu tsananin kyau... murmushi mai kyau nayi harda rufe fuska ta kamar mai jin kunya... Dan kam mijin novel da nake tunanin samu sai dai a mafalki ko a littafin...shine yasa wasu lokutan nake share awa da awanni ina hasashen yanda rayuwa ta zata kasance idan na samu irin wannan soyayyar...inyi ta tsara abinda zuciya ta tayarda bazai taɓa faruwa dani ba..amma kuma ina da damar ƙirƙirar tawa duniyar a cikin ƙwaƙwalwa ta inda nice sarauniya...bani da wani aibu... sannan duk wani abunda nake burin samu akwai shi a can... '' Mama yaudai shinkafa zakiyi ko?" na tambaya daga inda nake '' infa tuwo zan yi bazaki ciba?" '' kai mama dan girman Rabbi karki kiɓa mana wannan mugun abun!!" nayi maganar cikin magiya ina haɗa hannayena,bata ce komai ba miƙewa nayi '' kada ki kuskura kizo nan babu takalma tunda ke bakijin ƙyanƙyamin taka wuri mai damshi!" takalmina na saka sannan nazo na tsaya daga gefe ina ƙara roƙonta kada tayi mana tuwon masara '' naji!" ta furta batareda ta kalle Ni ba '' thanks You Mama!" '' Tuwo bafa Thanks You ake cewa ba,thank you...idan kince thanks...ma yayi amma kada kice thanks da ƙara s daga ƙarshe kuma kice You a gaba mai makin exam zai faɗar dake!'' juya idona nayi kamar in kaima yarinyar can duka amma dai. ƙarasowa tayi ta ɗauki bokiti ta juye ruwan data tafasa ta wuce bayen mu na kara, ɗaki ta shiga ta ɗauko zanin ta sannan ta shige wanka kamar wadda ke canja fata saida muka gama kari sannan ta fito '' ai na ɗauka farar mace zamu gani bayan kin fito!" batareda ta kalleni ba tace '' toh ai saiki ajiye yanzu '' sannan ta shige ɗaki nan ma ta daɗe kafin ta fito cikin uniforms ɗin makarantar mu brown ɗin wando farar riga da hijabi kayan sun bala'in amsarta har suka fitar da shape ɗinta daya ke nan kamar irin na yar cartoon ɗin nan mema ne sunanta...uhm.. yawwa olsa ta cikin pirozin (frozen) haka shape ɗin Asma'u yake ƙirjinta cike kamar na yar cartoon ɗin nan,hakama hips ɗinta... gashinta ta taje kafin ta kitse shi kamar yanda olsa ɗin take kitse nata don makarantar mu idan tayi parking za'a ce acuci maza ne sannan ta shafawa idonta da shape ɗinsu yake kamar na ƙwai kwalli wani irin sihirtaccen kyau tayi ta ɗauko lip gloss tashafawa pink lips ɗinta da suke ƙanana kuma acike masu shape kamar na M daga sama,hancinta kamar pencil... ba ƙaramin kyau tayi ba wallahi '' wannan kallo haka kada a cinye ni nidai!" juya idona nayi "kinyi kama da akuyar da aka yima kwalliya '' na furta kafin na iyar da shanye kunu na na miƙe,nima ruwan na juye na shiga na ɗauki zane nima na shiga bayen zuwa tayi ta ɗauki kunun ta tana sha Mama tace '' shi zuwa makarantar har sai anyi kwalliya?" ƙasa da idon ta Asma'u tayi zuciyar ta na dukan uku uku jin idanun Mama na yawo akanta... Bayan minti goma na fito nima na shiga ɗaki na shirya cikin uniforms ɗina,naɗan riƙe rigata ta baya in gani ko akwai shape Babu abinda idona suka gani sai tulelen ciki da shafaffen ƙirji da ɗuwawu hips ɗin ma babu taɓe baki nayi kafin na kalli baƙin gashi na daya ke nan da mugun tauri tun kafin ma mutum ya taɓa..ya wani coge taƙi ma ya kwanta duk da anyi kitson sannan na kalli wuyana....yana da ramuka sannan da wani V shape a tsakiya sannan babu layi layin nan smooth yake,fuska ta cike da pimples musamman goshi na da haɓata da kuma kumatuna,hancina irin na Asma'u ne abu guda da muke dashi iri ɗaya Sai kuma na kalli girata kamar an aske hakama lashes ɗina wasu sunfi wasu tsawo suma dai kamar gashin kaina,daga ƙarshe na kalli ƙwayar idona da suke ash... mutane dayawa suna faɗin wai insa kontat glasses abun yake ko kanta leshi (contact lenses) amma naƙi...na farko ba muda kuɗi na biyu inason kalar idona...don yana tsorata mutane idanuna manya ne sosai shape ɗinsu kamar na mage, sun dace dani sosai... +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋 ️ RU'UYAA (The dreams we never lived) By Autumn 17 🍁🍁 3. ...na amsa tambaya a karon farko...🖋️ Fitowa nayi saye da farin hijabi na jakata ta ledar biki pink color riƙe da hannu na,ɗayan hannun kuma riƙe da jakar goyo mai zanen cartoon ɗin nan pirozin da farin hijab na miƙa ma Asma'u, ta samu jakar ne lokacin da sukayi wani spelling bee tayo na ɗaya sandals ɗina baƙaƙe dake kitchen na ɗauko na cire slippers ɗin dake ƙafafuna na saka,itama na dauko mata nata brown na bata '' yau kuma mutanen na kai kenan?" ta tambaya tana ajiye cup ɗin data sha kunu ciki '' ke kika sani!" na bata amsa takalmin kafarta ta cire tasa sandals ta saka hijabinta sannan muka tsaya gaban Mama dake ta kallon mu '' Mama mun tafi!" ƙullin zanenta ta kwance ta miƙo muna ɗari biyu '' Allah ya kiyaye '' Ameen na amsa ina yin gaba bayan na karɓe kuɗin '' bazata bani ba fa'' ta kai karata '' tuwo kiba Asma'u ɗari ki ɗauki ɗari!" juya idona nayi sannan nace '' toh '' biyo bayana Asma'u tayi, har ƙofa Mama ta rako mu tana faɗin '' banda biye biye,banda hawa bishiyar mangoro,kuyi addu'a kafin ku fita!" '' toh Mama '' muka amsa muna mata bye bye.kullum Mama sai tayi wannan maganar amma kuma kun sani babu yanda za'ayi mutum na secondary ace baiyi biye biye ba.. sannan wannan bishiyar mangoron bata da nisa da gidan mu kuma mafiyawanci nan muke haɗuwa da yan makarantar mu.. har yanzu da ya kasance karfe bakwai da rabi gari bai iyarda wartsake wa ba,kamar akwai hadari hadari don rana bata fito ba... dai dai bishiyar mangwaro muka kawo '' riƙe min!" na miƙa mata jakata amsa tayi nikuma na shiga tattare wando na, na hawo bishiyar na fara tsinko mana mangoro ina jefowa Asma'u na kamawa... can sai ga wasu yan mata kusan su biyar saye da irin uniforms ɗin mu sun iso wurin haka na dinga katso ma kowa da kowa...sai ga ƙananan yara wasu almajirai wasu yan makaranta suma sun taru kowa ma so yake ja Asma'u tayi ta tsaya gefe tana kallo dan tasan yau muda barin wurin sai wani ikon Allah wani mutumi ya iso wurin da tsumagiyar shi yayi cikin yaran aiko kowa ƙafa me naci ban baki ba, tuntuni yake magana amma mun ƙiji Ganin baba Iliya yana korar Mutane yasa na maƙe saman bishiya idan na sauko ya haɗa dani ban shirya ba…. ‘’ ki sauko ki tafi makaranta!” Baba iliya ya faɗa yana kallona ‘’ toh idan na sauko zaka buge ni?” Na tambaya a shagwaɓe ''ABEEDATU Allah ya shirye ki! Sauko bazan buge ki ba" a hankali na riƙe wani reshe daga bishiyar ‘’’ wiiiiyyyyy!” Na furta ina dariya tare da shilla ƙafafuna ina lilo cike da nishaɗi ‘’’ au..wasa ma kika tsaya yi ko?” Ya tambaya yana riƙe baki ‘’ yanzu zan sauko!” Na faɗa tare da sakin reshen na diro.. kuma fa tsaye nayi ban faɗi ba!...na kalli Baba iliya ina murmushi nace ‘’ nima nayi irin na yan chana…’’ Taɓe baki yayi yace ‘’’ tunda baki kare ba ai anci sa'a!” Sai na turo baki tare da yin gaba ina bubbuga ƙafafuna ƙasa ‘’ Allah ya shirye ki!” Ya sake faɗa… ina kawo wa wata kwana naga su Asma'u zaune su shida suna jirana,suna ganina suka kwashe da dariya nima sai na taya su...'' ya dake ki? Ameena ta tambaya girgiza kaina nayi '' ina zai dake ta ta zama mage da daddare ta hanashi bacci!" inji Aleeyah,juya idona nayi abinda ya zame min ɗabi'a idan Abinda mutum ke faɗa baida muhimmanci ko kuma abin situpit(stupid )ne hira mukeyi har muka isa makaranta daidai an gama assembly class muka wuce,nida su Aleeyah ajin mu ɗaya SS3D Asma'u kuma science take... Muna shiga mathematics na shigowa ji nayi kamar in fasa ihu,bani son makaranta amma kuma naƙi jinin mathematics da malamin da kuma mai koyar da subject ɗin '' Gooooood mooooooining sir!" muka gaidar dashi, kallon mu yayi cike da jin haushi kafin ya bamu izinin zama batareda ya amsa gaisuwar muba '' ku fito da mathematics note book ɗin ku,ku buɗe zuwa inda muka tsaya!" yayi maganar yana jinginar da zabgegiyar bulalar shi kusan rabi da kwata na aji sai rarrabar ido muke kuma nima ina cikin su... a inda nake zaune daga baya dan back bencher ce duk wuya duk runtsi babu Ni a gaba aji ya ɗau surutu tsawa ya daka mana tare da faɗin '' ba surutu nace kuyi ba ku nunamin littafin ku..'' kafin ya gama wayarshi tayi ringing kallon kallo muka shiga yi wasu na shewa wayanda keda note kenan,wasu sun fara sun shiga uku wasu kuma suna faɗin in ma kashe su za'a yi saidai akashe su...wasu har sunfara kuka suna yarfar da hannu,oh...ashe ban faɗa muku cewa makarantar mu makarantar mata bace? makarantar mata ce toh nidai daga inda nake zaune babu abinda ya dame ni nama ga nawar azo ayi dukan kowa yakama gabanshi bawai dan inason duka bane sai dai saboda bani kaɗai za'a daka ba, sannan wani irin daɗi nake ji ajiki na me haɗe da tsoro... '' Operation show me your note!" wata mai suna Hameeda ta faɗa tana sheƙewa da dariya itama fa bawai dan tanada note ɗin ba,ga hadari daya taru aji yayi duhu da haske da sauri muka fara yan dabaru masu ƙananan jakunkuna suka rage littafan su,sai su tusa jakar a bayan su idan malami na duka bazasu ji zafi ba..nima dai haka nayi Bayan wani lokaci sai gashi ya dawo da discipline master Wanda kafiri ne sunan shima gunta..amma tunda mu Hausawa ne kuma yan makaranta Mr Mugunta muke kiran shi, musamman ni...da muguwar fuskar shi da akoda yaushe murtuke take da kuma buɗaɗdiyar muryar shi yace '' idan kasan baka da note ka fito '' sai ga rabi da ƙwatar aji sun fito wasu harda hawayen su zan iya rantsewa naga lokacin da ya lashe bakinshi tsabar mugunta kafin yayo cikin mu bulala biyar biyar,duk inda ya samu zunta ma mutum ita yake, hankali na ya tashi amma kuma wannan daɗin ƙara ratsani yake musamman wasu idan aka dake su naga yanda suke faɗuwa ƙasa suna billiƙe billiƙe kamar tanar da aka zuba ma gishiri abun dariya yake bani wasu harda yar drama '' wayyo Mallam tsaya kar ka karye Ni....na bani na shiga uku.... wallahi Ni kaɗai mamata take dani.....dan Allah kayi haƙuri...mamata ki taimake ni.....'' haka dai lokacin da aka kawo kaina ba ƙarya nima bulalar ta shige ni wallahi ba ƙarya amma sai na dake lokacin da yagama zane mu wasu harda kukan su,shiko sai huci yake harda zufa yana cigaba da murmushi Bayan ya tafi kowa ya koma seat ɗinshi aka fara wani banzan ni nama manta sunan topic ɗin amma dai nasan akwai logic ciki...oh na tuna logarithm...har da wani graph Wai sai mu gano wata banzar X da Y can...har yayi ya gama wallahi komai ban gane ba yana fita aji ya kacame da surutu '' kai amma mutumin nan anyi tsinanne... wallahi bulalar da yayi min babu wadda ta shige ni sai ta ƙarshe dan ga ɗuwawu ya zunta min ita da ƙyar nake iya zama!" inji A'ishah class Captain,muka kwashe da dariya suma wasu sai ƙara tsine ma mr mugunta suke wani Malami ne ya leƙo '' wane subject kuke dashi yanzu?" '' I.R. S'' suka amsa tare gyaɗa kai yayi yana faɗin '' ku fito da littafin ku kafin yazo!" muka amsa da '' Yes sir '' amma babu wanda yayi hakan '' Macijin sari ka noƙe muke dashi fa!" Muneeba ta faɗa tana kallona, wannan sunan nice dakai na na raɗa masa shi me yasa? mutumin tsohon munafuki ne kuma na tsane shi...tantagaryar ɗan iska ne,na rantse ba sau ɗaya ina ganin shi a hotel ɗin danake aiki ba da yan mata daban daban suna iskancin su amma idan yazo gaban mu sai yayi tayi kamar na Allah yana jawo ayoyin Alkur'ani da hadisi yana fassarawa, yan mata da yawa harda ni ada yana burge su..sai da na gano waye shi Sannan nagane cewa kuskure ne...yan mata da yawa suna matuƙar macewa akan mutumin nan musamman saboda kyakkyawa ne gaskiya,ga ilimin addini ɗalibai sun yarda dashi basu kaɗai ba harda iyayen su,na rasa dalilin dayasa mutane irinshi ke ɓoyewa bayan addini suna cin amanar ɗalibai da iyayen su da kuma addini duka... ina tsaka da tunani ya shigo ajin yan mata suka fara gyare gyare, yanda ya tsuke fuska zakayi tsammanin mutumin kirki ne...naji daɗi sosai da Asma'u ta rabu dashi,nasan lokacin dayake magana da ita da zummar yana sonta sai ya dinga kiranta office ɗin shi... Allah yasa na gano hakan da wuri na kuma taka musu burki na rabasu kuma tayi min alƙawarin bazata sake ba,bansan ya zanyi ba idan wani abu ya faru da ita wani banza ballagazan namiji ya lalata rayuwar ta... lokacin harda zuge ta yake akan ni ina kishi da ita ne don tafini komai...abun ya baƙantamin rai sosai ya sani nima kuma nasani nidashi maƙiya ne na har abada bazamu taɓa shiryawa ba! '' me kike tunani?" naji muryarshi kusa dani dab da kunne na,da sauri na juya na kafe shi da idona da launin suke ƙara rinewa idan na tsani mutum,idan kuma inason mutum idona har wani ƙyalli suke idan nayi fushi ko kuma bana son in nuna emotions idona size ɗinsu ragewa yake kallon shi nake cike da tsanar data kasa ɓoyuwa a idona '' meye damuwarka?" na mayar mashi da tambayar haɗiye fushin shi yayi tare da faɗin ki maida hankali,komawa yayi gaban allo kowane sakan biyar sai ya kalle ni har yayi ya gama bance komai ba..yan matan ajinmu kuwa sai biloshing suke...bafa haka kalmar take ba amma aidai kungane ko? Bayan ya fita sai ga Civic ta shigo,nifa bana maida hankali idan ana karatu dan ba ganewa nake ba,amma yau topic ɗin da aka koyar damu yaja hankali na sosai,da farko waje nake kallo kamar koda yaushe ina tsarawa acikin raina yanda zanyi kyau idan inada wannan da wancan idan fuska ta babu pimples idan... idan... '' Our topic for today is SELF ESTEEM!!". Muryar malamar ta dawo dani daga tunani na, duk da bansan mai hakan ke nufi ba jinayi ina so insan ma'anar hakan yasa na mayarda hankali '' wa zai faɗa min me ake nufi da SELF ESTEEM?" ta tambaya tana kallon mu, mutane dayawa sun ɗaga hannu amma babu wanda ya cinki ansar da kyau..nuna ni tayi tareda faɗin '' meye ma'anar SELF ESTEEM?" kallon mutane nake ido waje kamar yanda suke kallo na,sun sani na sani bansan amsar ba,wasu har sun fara dariya, yawu na haɗiye kafin na miƙe ina kallon malamar da itama nitake kallo batareda tunani ba nace '' sef istim na nufin sanin darajar kai da kuma samun ƙwarin guiwa a duk abinda mutum yake...kamar dai ace yaƙini.. mutum yazama mai yaƙini akan kanshi!" na amsa da ina ina,ina shafa kunne na inda ake sa ɗan kunne idona ƙasa..duk sanda nake jin tsoro kaɗan haka nake ji nayi yan aji suna dariya,banji ba daɗi ba don abune dana saba dashi malamar ta kalle ni tareda ƙara faɗin '' shine amsar ki?" ta tambaya,gyaɗa kaina nayi alamar eh '' CLAP FOR HER!!!" ta faɗa da ƙarfi,sai kawai suka faramin tafi sakin baki nayi kafin na zauna na kasa yarda wai yau ni ake tafa mawa abinda bai taɓa faruwa ba tsawon shekaru goma sha bakwai na rayuwa ta, suma yan ajin mu sunyi mamaki don dai sun sani niɗin daƙiƙiya ce lambar ƙarshe ban taɓa daga hannu don amsa tambaya ba ban kuma taɓa amsawa daidai ba koda kuwa amsar a bayyane yake bayan wani lokaci malamar ta fara bayani da turanci - Self-esteem: It's how you feel about yourself, your worth, and your abilities. It's your internal evaluation of yourself.( self esteem shine yanda kake ji game da kanka da kuma yanda, amfanin ka,da kuma abunda zaka iya yi... yanda kake ji azuciyar ka dakuma yanda kake ɗaukar kanka... Sai kuma akwai low self esteem da high self esteem - Low self-esteem: You're kinda down on yourself, doubt your abilities, and might feel unworthy or not good enough. 😔( Shine tsaurarawa Kai, kokonton abinda zaka iyayi da wanda bazaka iya ba, sannan kake ji kamar baka cancanta ba ko bakada amfani ko baka kai ba.... - High self-esteem: You feel confident, capable, and worthy. You like who you are and trust your abilities. 💪 ( high self esteem,kanajin ƙwarin guiwa, zaka iya, ka cancanta...kana son kanka kamar yanda Allah yayi ka,baka neman wani ya yabe ka ko ya soka sannan kayarda da abinda zaka iyayi... misalin low self esteem= 😔 - Constantly comparing themselves to others ( haɗa kanka da Wasu) - Saying "I'm not good enough" or "I'm a failure" ( cewa ni ban isa ba kuma ban kai ba ta hanyar raina kai) - Avoiding challenges or new experiences due to fear of failure ( gujewa ƙalubale da sabon abu gudun kada a faɗi) - Needing constant validation from peers ( buƙatar mutane su yabe ka ko abokai) - Negative self-talk or self-criticism (Maganar da bata dace ba ko mara daɗi wa karan kanka) - Difficulty accepting compliments or praise ( wahalar yarda idan an yabe mutum) - Feeling like they're not worthy of love or respect ( ji kamar basu cancanci a girmama su ba ko a sosu..) tunda malamar tafara magana na nitsu bani kaɗai ba ma harda sauran yan aji... bamu taɓa bada hankali ga wani subject ko topic ba kamar yanda muka bada a wannan topic nake ji araina kenan bani kaɗai bace mai wannan sef istim ɗin? ke nan low self esteem ɗin kesa ina kushe halitta ta kuma ina haɗa kaina da Asma'u,low self esteem kesa inason in cire pimples daga fuskata sannan in zama me kyau don a yabe Ni? badon hakan shine abunda nake so daga ƙasan zuciya taba! tunani na ya katse lokacin da naji Malamar na faɗin '' nasan dayawa daga cikin ku abinda ke damun ku kenan,akwai abubuwa dayawa da zaku iya yi amma saboda kuna gudun kada a kushe ku ko kada ku faɗi sai ku ƙiyi...da yawa daga cikin ku kuna kallon kanku kamar munana ko idan jikin ku bai girma ba, dan baki da ƙaton ƙirji ko ƙaton ɗuwawu ko girman hips ko idan kina da wannan masu girma da suka girmi shekarunki sai ki dinga jin kunya.. kina gudun abinda mutane zasu ce...ya zama rayuwar ki gaba ɗaya ke burin ki ki burge mutane ko dai ki tsira daga maganganun su....idan har kina ji yanda kike bakya son kanki a haka,kina ji yanda mutane suke so ki kasance haka kema kike so ki kasance to kina da low self esteem!" tayi shiru tana kallon mu kamar tana ƙoƙarin gano idan mun fahimce ta tacigaba da faɗin '' ku kalle Ni,ku kalli fuskata duk pimples, shekaruna ashirin da bakwai amma wasun ku sunfini girman ƙirji da ɗuwawu da hips.. kin gane ni idan ina tafiya ina nuƙu nuƙu?" '' a'a'' muka bata amsa muna ƙara kallon ta da kyau yau nima naga wadda ta girme ni kuma take a shafe kamar ni hakan ba ƙaramin ɗaukaka sef istim ɗina yayi ba tacigaba da faɗin '' wasun ku suna tafiya suna nuƙu nuƙu cikin hijabi badan suna jin kunyar Allah ba sai dai saboda suna gudun maganganun mutane...ku dena kunyar yanda Allah ya halicce ku,kuso kanku yanda kuke... babu wata wacce tafi ki,you're beautiful a yanda kike bakya buƙatar saiwani ya faɗa maki... love your self! abinda wani yake tunani game dake ba damuwarki bane,abu me muhimmanci ya kika ɗauki kanki? kina da HIGH SELF ESTEEM OR LOW SELF ESTEEM shine kawai" ta ƙarashe maganar tana kwasar littafan ta miƙewa nayi tsaye na fara mata tafi haka ma sauran yan aji suka bini juyowa tayi ta kalle mu tana murmushi muma muna dariya '' muna sonki sosai malam Hafsah '' muka faɗa kusan atare dariya tayi tana mana bye bye tace'' nima ina son ku '' sannan ta fita..... +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋 ️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 4. ...laifina ne...🖋️ har aka tashi break ina tunanin abinda aka koyar da mu, shine karo na farko da akayi karatu naji na fahimta kuma naji abun ya taɓa zuciya ta,duk abinda ta faɗa ya shafe ni....sai dai taya zan zama mai high sef istim? abun yanada sauƙin faɗa amma aiwatarwar ne da wahala, nasan dacewa yanzu na rage nuƙu nuƙu cikin hijabi kamar yanda ta faɗa, amma har yanzu ina matuƙar jin kaina a takure musamman idan ina gaban maza ranar ina wucewa ta filin ƙwallo,akwai mata da yawa da suka wuce kafin ni kuma ko wace mace idan ta wuce mazan dake wurin sai sun bita da kallo suna maganganun da basu dace ba...ina zuwa naji wani na faɗin '' wannan kamar sandar sluka (snooker)... idan mutum ya rungumeta ciwon ƙirji zata sashi!" abun ya bala'in yimin zafi kunya ta rufeni lokacin da suka kwashe da dariya naji kamar ƙasa ta buɗe ta haɗiye ni,duk yanda naso in bashi martani kasawa nayi dole nabar wurin zuciya ta na tsananin zafi.. Numfashi na sauke ina kalle kalle, kwanakin nan Asma'u ta dena zuwa amsar kuɗin break ɗinta sai nata neman ta kafin inganta bayan da ba haka bane to Meya sauya? rashin amsa yasa na miƙe na fara neman ta na zagaye makarantar duka har bayan masallaci na tafi amma bangan ta ba '' Habeeba kinga Asma'u?" na tambaye yar ajinsu '' tana wurin Macijin sari ka noƙe !" tabarni tsaye a wurin da tsananin faɗuwar gaba! meya kai ta wurin ɗan iskan nan dan Allah? bata yimin alƙawarin bazata sake zuwa wurin shiba? kodai ƙarya take basu rabu ba? da wani irin sauri ƙafafuna suke tafiya har na shigo office ɗin shi,samun shi nayi tsaye dab da Asma'u dake maƙe da bango idonta sun fito tsabar tsoro hannun shi riƙe danata yana Magana cikin kashe murya '' I love you...kin san hakan kema bansan dalilin da yasa kike wahalar da zuciya ta ba ma'u...'' katse shi tayi a tsorace '' Abeeda tace...tace in dena...kulaka!" fushin dake cin shi ya danne yana ƙara matso ta kafin ya ɗaura hannunta a ƙirjinshi ƙoƙarin cire hannun take daga jikin shi ya riƙe da ƙarfi yana mata wani ɗan iskan kallo yace '' kina kuwa jin yanda zuciya ta ke bugu saboda soyayyar ki ma'u?" ɗago idonta tayi tana kallon shi kafin da sauri tayi ƙasa da su ya cigaba da faɗin '' yayar nan taki burinta ta raba mu dan taga kin fita kyau da zubi bake kika faɗa min cewa babu wanda ya taɓa cewa yana sonta ba?" gyaɗa kai Asma'u tayi... nikuwa naji wani irin abu ya soki zuciya ta,kenan Asma'u...kafin in gama tunanin naji yana sake faɗin '' kuma kikace akoda yaushe sai ta haɗa kanta dake ba?" nan ma kai ta gyaɗa..naji ƙafafuna sunyi sanyi... wannan sirri nane kuma abinda ya shafi rayuwar mu taya zata faɗa masa wannan? '' kishi take na faɗa miki baki so kiji idan mun rabu na tabbatar zata zo tace tana sona! kin san yan mata nawa kuwa keson mu'amala dani amma na zaɓe ki ma'u? ki saki jikin ki dani kinji!" yayi maganar yana ƙara jawo ta jikinshi duk da a tsorace take bata hanashi ba hakan ya tabbatar min dacewa maganganun shi sunyi tasiri akan ta, idona suka ɗau zafi cike da hawaye akan komai dana gani kuma naji '' Tsohon ɗan iska munafiki,dallah sake ta!" a wani irin firgice su biyun suka juyo suna kallona musamman ita, wani irin kallo nake binsu dashi su biyun amma dayake ɗan iska ne sai Kallon ta yayi yana faɗin '' Babe kinga ni ko? na faɗa maki kishi take dake!" '' Rufe ma mutane baki!!!" na daka mashi tsawa idona suka ƙara duhu..farin ciki ya rine, '' babu abinda ka iya sai lalata yaran mutane kawani riƙe ta a kwana kana cusa mata maganganu... wallahi tallahi idan har baka fita daga harkar Asma'u ba zan iya kashe ka nima daga baya a kashe ni!" zaro ido yayi yana kallona hannun shi dafe da bakin shi dan yagani a idona Abinda na faɗa ɗin da gaske nake... '' Abeeda ki den...'' kafin ta gama faɗar abinda zata faɗa na wanke fuskar ta da mari shock rubuce a fuskar ta take kallo na,ni kuma ina kallon ta cike da fushin cin amanar datayi min'' akan wannan ɗan iskan zaki gaya min magana har kike kira na Abee..''hawaye na sauka a idonta a tsawace tace '' eh! an kiraki Abeeda ba sunan ki bane? ina son shi shine yasa kika gan mu tare ki dena shiga rayuwa ta..da gaskiyar mutane kishi na kike kawai ba wani abu ba..so kike in rabu dashi don ke ki samu ki maƙale mashi kuma bazan rabu dashi ɗin ba!" ta fita daga office ɗin kamar zata tashi sama nabi bayanta da kallo... dariyar macijin sari ka noƙe ce ta dawo dani daga shock ɗin da har yanzu Ban dena jin shiba zagayowa yayi ya tsaya bayana ya ranƙwafo yana wani hura min iska a fuska '' huɗubata tayi aiki ko? yanzu zaki iya raba mu? ki sani sai na samu Abinda nake so daga ƙanwarki iya karki kallo don babu wani abinda zaki iya yi akai!" kasa cewa komai nayi tsabar yanda jiki na da zuciya ta suka min nauyi tureshi nayi daga hanya ta na fita ina layi hawaye suka ciko idona..da gudu na ruga na ɓoye bayan masallaci ina risgar kuka duk dacewa an koma aji...yau Asma'u da bakinta ke irin wannan maganar? ashe dama ƙarya take da tace zata rabu dashi? Kuma dama itama tun tuni tana gani na a matsayin mai kishi da ita har take faɗar sirrika na mawani banza can? zuciya ta ta karye fiye da zaton mai karatu har aka tashi short break ina kuka sai dai na canja wuri saboda masu zuwa wurin...sai lokacin Sallah na gama kukan idona sunyi luhu luhu sun ƙanƙance sunyi jawur.. alwala nayi na shiga Masallacin mukayi sallah da aka gama ban koma class ba sai lokacin tashi naje na ɗauki jakata ban jira kowa ba nayi gaba abuna...wata doguwar hanyar danake bi a duk sanda rayuwa tayi min zafi ko nake buƙatar kaɗaici nabi ina tafiya ina tunani zuciya ta na ƙara ƙuna a duk sanda na tuna abinda Asma'u ta faɗa min '' laifi nane!" na faɗa da shaƙaƙƙar murya ina goge hawayen da suka silalo min...da ace na iya son kaina a yanda nake ..da ace inada ƙwarin guiwa..da ace na gode Allah yanda yayi ni..da babu wanda zai faɗi maganar da zata sosai raina...hawaye kamar ruwa suke kwaranya daga idona sai dai nake sa bayan hannu na ina sharewa wurin ƙarfe uku da rabi nakai gida samunta nayi tsaye kusa da bishiyar mangoro tana jirana dan bazata iya shiga ita kaɗai ba... ina ƙarasowa ta miƙe muka cigaba da tafiya babu wanda yace uffan cikin mu har muka shiga ciki Muka iske Mama tsakar gida riƙe da hijabi fuskar ta ɗauke da damuwanmu muka tsaya kallonta jin tsayuwar mutum yasa ta juyo ganin mune ta sauke ajiyar zuciya '' ina kuka ts..'' kafin ta gama magana na saki jakata na ruga na rungumeta tareda fashewa da kuka mai ƙarfi ''Maamaaaa!" zuciyata na ƙara karyewa hankalin Mama ya tashi sosai hakama Asma'u ɗago Ni daga jikinta tayi duk ta daburce baiwar Allah'' meya faru yar Mama faɗa min!" take share min hawaye na da suka kasa tsayawa... wani irin rauni da baƙin ciki ke ɗawainiya da zuciya ta... Mama a ruɗe take tambaya ta cigaba da tambaya ta da ƙarfin hali irin na uwar data ga yarta cikin damuwa '' hum...dama wasu ne suka yi mata abinda suka saba!" da sauri Asma'u ta faɗa kanta tsaye hakan yasa na ƙara ɓoye fuskata a ƙirjinta, rungume ni tayi tana lallashina Muryar ta na rawa na tsani inji muryar Mama a irin haka, zuciya ta karaya take..duk da akwai sauran kuka cikina sai na haɗiye kawai Mama ta ɗagoni tana share min hawaye tace '' Abeeda dan Allah ki dena saka kanki a damuwa ki tuna cewa duk wannan abun lokaci ne sannan kyaun jiki dana sura suna ƙarewa banda na hali...ki zama mace me kyakkyawar zuciya shine Abu mafi muhimmanci!" gyaɗa kaina nayi kawai babu wanda ke ganewa ko kuma zai gane sai wanda ke cikin yanayin..... Asma'u daga gefe tayi tsaye bata ce komai ba yanayin ta ya nuna bata ji daɗin abinda ya faru ba mema ake kiran kalmar da turanci....uhmm.. Autumn: guilty ta kasa cewa komai.. riƙe hannayen mu Mama tayi ta shigar damu ɗakin mu dake ƙamshin tsintsiyar ƙamshi ta zaunar damu sannan ta fita matsowa tayi da niyar magana sai kuma me ta tuna oho ta matsa baya nasan maganganun macijin sari ka noƙe ke yawo a kanta... cire hijabina nayi tareda rigar uniform ɗin na ɗaura zane na zauna ƙasa bayana jingine da bango ido lumshe...bina da ido tayi,tasan maganganun ta ba ƙaramin...uhm..mema ake cema kalmar da turanci? yawwa... Autumn: emotional breakdown ...eh.. kalaman ta sun ruguza ɗan sef istim ɗin dana samu daga malama Hafsah..da ina da low sef istim...amma yanzu shima low ɗin ƙila ya koma kwata ko babu ma duka Kayan ta itama ta cire ta ɗaura zane ta zauna nesa dani tana wasa da yatsunta saboda wannan gilti ɗin datake ji..Mama ce ta shigo da plate ɗin shinkafa da miya ta ajiye.. da lafiya lafiya tashi zanyi inyita tsalle tsalle amma banda yau...baƙin ciki ne fal a raina abincin ma ya fita daga raina... '' matso ga shinkafar nadafa tuwo!" Mama ta faɗa itama dai har yanzu bata wartsake ba,na tsani inga Mama cikin damuwa badan naso ba na matso mu duka muka fara cin abincin bawai dan inajin daɗin abincin abakina ba nake ci... Bayan mungama miƙewa nayi na fita ruwan sanyi na ɗiba daga drum na shige bayi nayi wanka minti talatin na fito na wuce ɗaki Vaseline na ɗauka ina shafawa ahankali a hankali ina kallon kaina ta madubi Mama da Asma'u suka bini da ido, bayan na gama da wannan tsohuwar wardrobe ɗin mu na buɗe na ɗauki uniforms ɗin wurin aikin mu, baƙaƙen riga da wando da hijabi half sunna nidai nawa ya wuce ƙirji... ƙaramar singlet irin ta yara da pant pink color na ɗauka na matsa can gefe na saka kayan sannan na dawo na ɗauki hula fara itama na saka yau shiru nayi babu mita babu kompilen,kwalli na shafa a idona dayasa suka ƙara fitowa da kyau naɗan shafa man baki wanda ni gaba ɗaya kwalliya bata dame ni ba,a ganina ni ba mace bace ban kaiba shine yasa banayi ko lip gloss ɗin bana shafawa... duk da yanda nakeji na juyo da murmushi na kalli Mama nace '' Naga kinsa hijabi akwai inda zaki ne?" ajiyar zuciya ta sauke tace '' gidan Haule zanje ɗanta sale ne ya goce a ƙafa..'' '' subhanallahi! Garin yaya?" nida Asma'u muka tambaya '' wai an aikeshi shine kiken shi ya samu matsala wurin taka birki suka game da me mashin " ta bamu amsa cike da alhini '' bari idan anyi Sallah sai mu tafi tare daga nan in wuce wurin aiki!" na faɗa mata gyaɗa kai tayi nikuma na shiga neman wannan abun da ake laƙa ma mutum da suna a uniform mema ake kiranshi da turanci..uhmm... yawwa nem tag ( name tag) ganin shi nayi a ƙasan wardrobe na zuƙuna na ɗauka na kakkaɓe kafin na maƙala shi a gaban riga ta sunan dake jiki ' A.Tuwo' wato Abeeda tuwo juyowa nayi naga Asma'u ta kafe ni da ido rage girman idona nayi zuwa rabi...hakan yasa zuciyar Asma'u tsinkewa...tunda muke Abu irin wannan bai taɓa haɗamu ba...bana saurin warkewa daga gori...idan har aka goranta min akan abu ko kuma akayi anfani da ammm...mema ake kiranshi da turanci idan mutum na tsoron Abu...yawwa..insikiuritis (insecurities) toh yana matuƙar wahala in manta kuma bama dawowa daidai da koma wane ne yayi min hakan... Bayan la'asar tare muka fito mu duka muna tafiya muna hira hakan ba ƙaramin rage min abinda ke zuciya ta yayi ba..ina matuƙar son Mamar mu ita kaɗai Banda Asma'u...uhh... shike nan dai.. itama ina sonta amma yanzu nayi fushi da ita koda muka isa gidan Haule akwai mutane da yawa ga Saleh nan zaune da ɗauri a ƙafar shi,shima shekarun mu ɗaya,ana kiran hakan da turanci...?age mates! nida shi bamu shiri ko kaɗan duk dashi bai taɓa kushe niba amma yana hararata gaisuwa aka fara tsakanin manya kafin aka fara magana akan Asma'u don ita duk wanda yaganta saiya maganta,tayi ƙasa da kanta tana murmushi jin ana yaba kyaunta'' oh harda ke aka zo kenan?" ya buɗe idonshi daga jin murya ta,kuma fa bacci yake..zama nayi gefen mama nace '' daga jin murya ta sai ka buɗe ido?" gyara zaman shi yayi yace '' yo na sani ko zuwa kikayi ki ƙarasani?" murmushi nayi nace '' ai saida daddare zaka ga wata mage me irin idona to nice!" tuf tuf yayi tareda faɗin '' li'ilafi ƙuraysh,aniyar moɗa tabi randa!" mutanen dake sauraren mu sunata dariya banda Asma'u...nima dai dariyar nayi Mama ta miƙa gaisuwa nima na miƙa tawa da sauri yace '' ankarɓi ta Mama, ba'a karɓi ta Tuwo ba!" miƙewa nayi na taɓe baki tare da faɗin '' kadai ji dashi nan..ƙafarka ta karye kowa ya miƙo gaisuwa karɓa ake don ayi saurin tashi kai kana dawo ma mutane da gaisuwar su... toh nitawa karɓaɓɓace ehe!" nakai zauren gidan naji yana faɗin '' gocewa nayi fa ba karyewa ba!" aka saka dariya nima sai na murmusa... duk da bamu shiri da Saleh wallahi ina matuƙar ƙaunar shi fisabilillah Kuma shima yana ƙaunata idan muka samu Abu sai mun bawa juna.. kuma bama rabuwa da cacar baki sai dai idan bamu ga juna da sauri sauri na kawo bakin gate ɗin Maina granda hotel... gaidar da masu gadin nayi kamar koda yaushe sannan na shiga daga ciki,ƙaton hotel ne mai haɗe da restaurant,hotel ɗin ya haɗu ya gaji da haɗuwa dan 7 star hotel ne babba kenan ta ƙofar baya na shiga na gaida head chief ɗin mu ko hakane sunan ta koba haka ba oho... faɗa ta balbale nidashi wai nayi latti... tafiya ta nayi nabarta da ɓaɓatu cikin restaurant ɗin na shiga na samu abokan aiki na suna aiki nima sai na bisu ina karɓar order,Ina matuƙar son aiki na mafiyawanci duk ɓacin ran dana kwaso anan yake kwaranyewa idan na haɗu da abokan aiki... wurin a raye da surutun mutane ƙasa ƙasa ga hasken wannan globe ɗin me kama da sarƙa da ake kira da turanci uhmm.....candaliya ( Chandelier) ga sanyin ac da kuma Ƙamshin turaruka daban daban..duk da yau akwai sanyi dan Haryanzu rana bata fito ba,hakan bai hana a kunna ac ba tuntuni na lura da yanda wasu dake zaune a table No. 6 suke kallo na suna lasar baki suna maganganu amma ban bi takansu ba...kirana suke zasu bada order naƙi zuwa na jawo zainab nace '' ga wasu can kije ki karɓa '' tafiya tayi ni kuma na matsa zuwa ɗayan table ɗin Bayan mun gama karɓar order kowa yaje ya amso wanda ya karɓa, saboda zainab ta tafi toilet dole ni na karɓi order no.6...tura baron abincin nayi wanda ake kira da turance 🛒 cart... wannan na riƙe ba sai nayi tunani ba.. abubuwan da suka yi order shinkafa da mai da yaji,yajin cikin wata ƙaramar roba fara,sai salads da lemu, boza (burger)da tabarma (shawarma)da sauran su.. fuska a matuƙar ɗaure na isa gabansu na fara sauke musu abincin '' ji mana yan mata!" wani farin saurayi daka ganshi kaga bafulatani yayi maganar,sauran suna kallon kallo suna magana da ido,banza nayi dashi ina cigaba da sauke abincin '' kayan jikin ki sun burgeni! musamman daga ƙirji'' yayi maganar da shaƙiyanci, abokansa na taya shi ji nayi kunya ta fara rufe ni jikina yayi sanyi musamman danaga kamar mu ake kallo, naji kamar insa hannu in kare ƙirjina amma konayi hakan abanza hijabin ƙarami ne '' faɗa min bra size ɗinki in siya maki." plate ɗin dake hannuna na dire da ƙarfi jikina ya fara rawa kaɗan idona sukayi ja,na ɗago nakejin fushi na tasomin na kalleshi, sun ɗan tsorata kaɗan'' warin bakinka na damuna ko zaka iyayin shiru?" galala sukayi su dukan su.... mutanen wurin suka kwashe da dariya..wai an kunyata ɗan gaye a fusace ya riƙe hannu na '' dan ma kin samu a na maki magana? me zanyi da flat board like you? da mumm....'' kafin ya ƙarasa maganar na ɗauki cokali na cika shi da yaji na tura masa a baki... mutane suka hangame baki suna kallona shiko nan take idonshi suka yi jawur jijiyoyin wuyan shi suka miƙe...abokanshi suka kasa motsi salad plate na ɗauka na kife masa akai na kalli cikin idonshi'' Flat board? a haka sheɗaniyar zuciyar ka take ƙawata maka ni...kuma kake yimin magana! nafi ƙarfin ka!" na faɗa ina warce hannu na nabar wurin.. tari yafara da ƙarfi ,da sauri ƙawayenshi suka dinga bashi ruwa yana haɗiye wa saboda azaba... idonshi sunyi ja dayaga abun bazai ƙare ba ya wani kwasa da gudu kamar mahaukaci salad na reto akanshi mutane sai dariya suke ƙawayenshi suka ajiye mana kuɗin mu a table suka bar restaurant ɗin... +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma ₦800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 5. ... Bayan barina restaurant ɗin toilet na wuce na sha kuka sosai ina fitowa kuma akace manager na kirana..tsaye nake gaban shi yanata surfafa min bala'i akan abinda ya faru a restaurant yana magana akan wasu etik and etike (ethics and etiquette) '' taya za'ayi kima customer ir..." '' uban etik and etike manager...taya za'a yi kafaɗi irin haka? kasan abunda yayi min ne? idan ƙanwarka ce wani ya riƙe mata hannu yana mata maganganun banza zaka ce haka?..." nan nashiga sauke mashi bala'i ta inda nake shiga bata nan nake fita ba,dafe kanshi yayi kafin ya fara bani haƙuri... dan kuka nake kamar raina zai fita ina sheshsheƙa, zaunar dani yayi a ɗaya daga cikin kujerun dake office ɗin shi ya ɗauko ruwa ya miƙa min ya tsuguna gabana yana bani baki...bayan nasha ruwan na ɗan rage sheshsheƙa ya ƙara bani haƙuri sannan yace intafi hotel inyi aiki in bar restaurant ɗin gyaɗa kaina nayi na miƙe na fara tafiya '' na gode '' na faɗa sannan na iyarda fita, elevator na shiga ya ajiye ni a floor ɗin kitchen.. gani nayi chefs ɗin suna ta kai komo daga gani sauri suke suyi subawa kowa order shi '' ke zo ki ɗauki wannan abincin ki kai ma room no 207 !" wani daya juyo ya ganni yayi maganar yana nuna min cart ɗin da aka shirya komai ciki.. yatsine fuska nayi kafin na ƙarasa naja cart ɗin na shiga elevator na danna 2nd floor kafin ƙofar ta rufe sai ga Abeed ya shigo yana min murmushin shi mai kyau har saida dimple ɗinsa ya fito tsayawa yayi kusa dani hannunsa ɗauke da wani rufaffen plate '' yau ba magana name sake?" ƙin kallonshi nayi,yayi yar ƙaramar dariya, wani abu ya zaro daga aljihunshi ya miƙo min,saida na kalli abun dake ɗauke cikin ƙaramar kwalbar nace '' meye shi?" hannuna ya riƙe ya samun a tafi...yace '' sunan shi Usma grass root,ranar naji kina tambayar abinda zai sa gashin mutum ko girar mutum da eyelashes suyi tsawo su ciko da sauran su shine na kawo maki...amma kibi ahankali idan ya shiga ido akwai zafi sosai!" ya ƙarashe maganar yana kashe min ido, juya abun nayi a hannu na kafin na ƙara kallon shi nace '' ina ka samu?" '' siya nayi " ya bani amsar '' nawa?" na sake tambaya '' dubu sittin!" zaro ido nayi wannan albashi nane na wata uku,kuma shima haka '' ko baki so?" ya tambaya yana ɗage min gira '' girgiza kai na nayi...sai kuma nace '' meyasa zaka kashe kuɗi masu yawa don ni bayan kai ma ji da kanka kake?" murmushin gefen baki yayi min wanda bansan ma'anar shiba '' kada ki damu,kedai kiyi amfani dashi kawai!" '' meyasa kake kulani?" na tambaya hannu naɗe a ƙirji na juyo ina kallon shi,ya shafa ƙeyarshi'' son ki nake!" waro ido nayi da farko sai kuma na fara dariya kamar mahaukaciya harda ɗaura hannu akai...'' bana son wasa... me yasa kake kulani?" nayi tambayar fuska a tsuke, ajiyar zuciya ya sauke ya koma serious yace '' saboda kece the most authentic person Dana taɓa gani a rayuwa ta!" kallon shi nake cikin rashin fahimta bangane me yake nufi da wannan kalmar ba,gane hakan da yayi yasa ya fara min bayani,'' idan akace mutum authentic,ana nufin yana abu da gaske,baya ɓoye ɓoye,baya yin abu dan mutane su gani..da zuciya ɗaya yake abu!" yake juya ido kamar mace '' Oh..'' na furta ahankali, na faɗawa duniyar tunani da gaske ni...mema nene kalmar? aidai kunji Abinda ya faɗa ko da gaske ni haka nake? '' keep being yourself,zaki gani wata rana akwai wanda zai soki dan hakan kawai..zai soki a yanda kike batareda ya nemi ki canja wani abu game da kanki ba!" buɗewar elevator yasa yayi gaba batareda ya sake cewa komai ba,sanin idan na cigaba da tsayuwa elevator zata rufe dani a ciki yasa na fito ina tafiya a hankali ina tura cart ɗin da gaske akwai wanda zai soni a yanda nake batareda na zama mai kyau har na fitar hankali ba? naga yanzu mazan sun iskance idan har baki da wa'yannan kyaun zuciya bazai sa su kulaki ba! Na sauke ido tare da danna ƙaraurawar ɗakin na ɗari biyu da bakwai...da turanci aka amsa '' come in..'' taɓe baki nayi ina faɗin ' yan wulaƙancin ' a raina tura ƙofar nayi na shiga wani irin daddaɗan ƙamshi na dukar hancina da kuma sanyin Ac, ɗakin yayi min kyau sosai king size bed ne me ɗauke da jan zanen gado kamar wani ɗan tsafi sai dogon benci mai katifa..aidai kun gane shi irin wanda ake ajiye wa gaban gado ko? wanda masu kuɗi tsabar iyayi suke ajiyewa bayan bashida wani amfani Sai jan carpet me ratsin fari a gaban gadon,daga gefen dama na ɗakin idan an shigo TV ne sai wardrobe dake kallon ɗayan bangon daga Tsakiyar ɗakin akwai kujera zaman mutum biyu da table a gaba sai labule masu nauyi suma jajaye painting ɗakin kamar fari kamar yellow bansani ba sai toilet...ɗakin ya burgeni sosai duk da ba wannan ne karo na farko da nake shiga ɗakin hotel ba wani saurayi ne zaune a saman kujerar daga shi sai ƙaramin wandon da ko rabin cinyarsa bai kai ba,askin kanshi low cut kyakkyawa ne sosai ban taɓa ganin wani me kyau irin nashi ba duk rayuwata fuskar sa ɗauke take da manyan laɓɓa (full lips) hancinsa dogo mai kyau haka ma idanun shi farare masu ɗauke da ƙwaya hazel brown kamar zuma..yana da ƙaton jiki.. '' kutumelesi!" kalmar ta fito daga baki na batareda na shirya ba,amma wannan anyi babban ɗan iska! wane irin iskancine wannan? ji nayi na fara tafasa daga ciki ni kyaun shi bai wani burge Ni ba kokaɗan gefen wando na na taɓa naji turaren yajina na nan.. gyaɗa kai nayi tsaye daga bakin ƙofa '' ga abincin na kawo'' na faɗa batareda motsawa ba daga inda nake ba... ɗagowa yayi ya kalleni tareda sakar min Murmushi mai kashe zuciya sai dai ni tawa zuciyar bata mutu ba! ya tashi zaune yana shafa kuncin shi yace '' kece wacce ta cika ma wani baki da yaji ko?!" sai dana harare shi nace '' ko kaima kana so ayi maka fiye da nashi ne?" Naji kamar in share wannan banzan murmushin dake fuskar shi...taya ma ya sani? munafukai masu kwana da ido ɗaya a ko ina... '' to ƙaraso ciki mana...''ya share abinda na faɗa dogon numfashi naja tare da juya idona a kaikaice jin yanda zuciya ta take ingizani da inyi mashi wanka da turaren yaji amma sai na dake na tura cart ɗin har zuwa gabanshi na fara sauke abincin duk abunda nake inajin yanda idonshi ke yawo a jikina hakan ya ƙara hasala ni miƙewa nayi tareda ɗaura hannuna a ƙugu a matuƙar tsiwace nace '' wai Malam kallon bai isa haka ba? ko kai maye ne aniyar moɗa tabi randa!" Takaici duk ya isheni...bai dena kallo na ba sai ma kamar dariya nabashi '' meye sunan ki?" ya tambaya '' ba faɗin suna nazoyi anan ba!" na bashi amsa a zafafe '' sunana Ibrahim '' '' ban tambaye ka ba!" gyaɗa kanshi yayi yana riƙe dariyar shi, da alamu wannan ne karo na farko daya haɗu da masifaffiyar yarinyar da kyaun shi baisa ta rusuna ba lashe bakin shi yayi,'' zamu iya zama abokai?" yayi maganar yana miƙo hannu mugaisa '' sunana ba chidera ba dakake miƙo min hannun ka,nan kano ne garin hausawa idan kana buƙatar abokai mata katafi Lagos! !" nayi maganar ina sauke abu na ƙarshe dake saman cart ɗin na miƙe zan tafi ya riƙe hannu na..shima ya miƙe,ji nayi zuciya ta tana bugu da mugun ƙarfi, jan hannu na nayi a tsiwace nace'' dalla sake min hannu dan niba yar iska bace!" amma ko gezau sai ma ƙara riƙe hannun da yayi yana murmushi, tsoro naji ya saukar min irin wanda ban taɓa ji ba...na kuma san saboda ba kayane a jikinshi ƙwace hannu na nayi ina matsawa baya shima yana matsowa har muka dangane da window yayi min runfa da faffaɗan ƙirjinshi,naji numfashina nafita sama sama,ya saka idonshi cikin nawa Haryanzu da murmushi a fuskar shi '' ww...wai...mmm..meye..haka?" nayi maganar a tsorace ina damƙe turaren yaji na idan naga abu yaci tura in watsa masa inyi gaba, ahankali cikin raɗa ya matso da fuskar shi dab da tawa yana faɗin '' to waye ɗan iska?" Yawu na haɗiye ina nadamar abinda na faɗa.. '' banda amsa yanzu kam!" na kawar da fuskata gefe dan yanzu ba shine lokacin rashin kunya ba...yayi dariya daga ƙirjin shi tare da danne leɓenshi da fararen haƙoranshi... Hakan ya ƙara tsorata ni sai ƙoƙarin basarwa nake kamar bana jin tsoro amma ƙafafuna rawa suke..harda ɗan ƙaramin fitsari nayi a wando... murya na rawa nace '' nidai matsa min in wuce!" maƙe min kafaɗa yayi yana kallon idona.. pepper spray ɗina zan jawo yayi saurin ɗaura hannun shi mai bala'in laushi a nawa...ɗan ƙaramin sauti ya ƙwace min a razane nayi hiri hiri da ido...tawa ta same ni,yana kallon cikin idona da manyan nashi, da zurfaffar murya yace '' meye sunan ki?" zuciya ta kamar zata fita daga ƙirjina tsabar yanda take bugu...har so nayi in ture shi amma ina zan taɓa a jikin nashi daba kaya? Runtse idona nayi na ɗaura hannayena a ƙirjinshi ina turawa da duk ƙarfin da Allah yayi min amma bai ko matsa ba sai dariya da naji yana yi '' wato abun ya kai har da cin zarafi ko?" Ya tambaya murya ƙasan maƙoshi... buɗe idona nayi suka shige cikin nashi,da sauri na ɗauke su na mayar akan hannayena dake manne da ƙirjinshi...gefe da gefe...saman kan baƙin abun nan da maza da mata suna dashi...yawu na haɗiye zan janye hannu na ya riƙe.... saura kaɗan zuciyata ta fito ta baki ...murya na rawa nace '' n ...nifa...ka rabu..da..Ni...baka gani mayya bace...zan iya shanye maka..jini... ka barni in fita..toh!" wannan barazana ko ƙaramin yaro aka yiwa ita tsaf zai kwashe da dariya bare babban mutum...yake kallona kamar abinda na faɗa shine mafi girman wasa daya taɓa ji... '' oh.. Allah sarki...so you're a witch?" Ɗaure fuska nayi dan bana jin turanci can can...kuma ban gane abinda ya faɗa ba...sai na gyaɗa kai kawai ..na ɗauka ya rabu dani...ƙara matso ni yayi..nima na sake shigewa cikin bango..ƙafafuna manne da bangon...yanda yayi min runfa da jikinshi idan mutum ya shigo bama zai san da akwai ni a wurin ba... '' i surprisingly have a thing for witches with gray eyes...can I kiss you?" Batareda na fahimci abinda ya faɗa ba na shiga gyaɗa kai kamar ƙadangare nidai kawai ya barni in tafi...tsawon shekarun dana kwashe ina aiki a hotel ɗin nan ba'a taɓa rutsani har haka ba...sai dana haɗu da wannan kyakkyawan ɗan tashan...har lokacin idona sunƙi komawa dai dai..duk na gama tsora ta...na ɗauka nan ne ƙarshe yanzu kawai zai yi dariya ya juya ya koma wurin abincin shi amma a mamakina sai ya sauke yatsan shi saman laɓɓana yana kallon cikin idona wani irin abu naji yana min yawo tun daga tsakiyar kaina har yatsun ƙafafuna kuma naji kamar jikina ya mutu, karkace kanshi yayi tare da lumshe ido zai sumbace ni, wata irin gigitacciyar ƙara na saki,tare da buga mashi guiwata tsakanin ƙafafun shi na kwasa da gudu..nabar shi da durƙushewa ƙasa yana zagi da turanci...yau kallon fim ɗin China yayi min rana... Kamar makauniya naji naci karo da mutum ..kuma wannan mutum ɗin bai yi komai dan taro ni ba lokacin da nayi tangal tangal kafin ɗuwawuna su sha ƙasa runtse idona nayi saboda zafi, kafin na buɗe su ina kallon mutumin dake tsaye gabana,saye da ƙananan kaya riga mai dogon hannu ash color wando baƙi ya ɗan tattare shi daga ƙasa fuskar shi sakaye da face mask...sumar kanshi baƙa wulik ga wani sihirtaccen ƙamshi da yake zubawa...yana kallona da baƙaƙen idonshi kamar na maijin bacci da sauri na miƙe ina kallon shi a masife nace '' baka ganine? baka ga ka ture niba?idan wannan ramen dake fuskarka bai aiki,abunda xaka iyayi dan taimakon kanka da kowa ma shine ka zauna cikin ɗaki basai kazo kana bangaje mutane ba!'' na ɗanyi nadamar yanda na zage shi amma ban bashi haƙuri ba..sai ma nayi tsammanin yabani haƙuri amma sai cewa yayi '' Get.Out.of.My.Way!" yayi maganar da wata irin ƙatuwar murya idonshi suka ƙanƙance a kaina...daga yanayin maganar shi zaka san ba ɗan Nigeria bane ..abinda ya faɗa aiko wanda baije makaranta ba aka cema get out yasan abinda ake nufi gyara tsayuwata nayi gaban shi nace '' bazan matsa ba ka..!" ban gama sentence ɗina ba ya wani bangajeni gefe saura kaɗan in faɗi yayi tafiyar shi.. sakin baki nayi kafin naja wata gora dake saman wani cart ɗin abinci da aka aje a hanyar na saita bayan kanshi na jefe shi...sai ga ƙeya.. juyowa yayi yana kallona, hannu dunƙule kamar zai naushe ni gwalo nayi mashi na kwasa da gudu ina dariya aini ɗin bata wasa bace... ganin lokacin sallah yayi yasa na wuce masallaci bayan na shiga Baye nayi tsalki saboda yanda mutumin nan yasa nayi fitsari a wando,ana gama sallah na dawo na cigaba da aiki..sai ƙarfe tara shift ɗina ya ƙare har nayi sign out naga Macijin sari ka noƙe da wata mata zaune a wani table....jinayi haushi ya kamani dole inyi wani abu akan abinda ya faɗa min ɗazu tare suke saukowa daga stairs cikin shiga iri ɗaya baƙaƙen riguna da baƙar jacket a sama sai baƙin wando jeans suna zuba ƙamshi, har yanzu da face mask baƙi a fuskar shi Ibrahim kuma magana yake masa idonshi ya sauka akan tuwo data karɓi plate daga hannun wani waiter tana tafiya kamar bada gangan ba ta juye duk abinda ke cikin plate akan Macijin sari ka noƙe dake riƙe da hannun yarinyar da suke tare...daga gani yarinyar bazata wuce sa'ar Tuwo ba... tsayawa sukayi su biyun suna kallo... Macijin sari ka noƙe ya wani miƙe kamar wanda aka watsa ma ruwan sanyi '' Abeeda wannan wane irin rashin hankali ne?" kukan ƙarya Tuwo ta fara tana faɗin bada gangan bane amma ya zaƙe sai faɗa yake mata ganin irin kallon da mutanen wurin ke masa kamar na wani mara tausayi yasa ya shanye fushin shi sai kuma a fusace yabar restaurant ɗin yarinyar da yazo tare da ita ta matso wurin Abeeda '' Nagode!" ta raɗa ma Tuwo a kunne kafin ta bar wurin '' i like that girl!Ro..?" Ibrahim ya faɗa ma gayen dake kusa dashi amma koda ya juyo yaga wurin babu kowa... murmushi yayi yabi bayanshi.. Batareda wani damuwa ba nima nafita daga restaurant ɗin ina tafiya ina tsalle tsalle iskan hadarin na ƙara ratsani,ni tuni ma na mance da wannan mutumin da muka haɗu dashi a hotel '' hi kyakkyawa '' naji Muryar shi daga bayana da sauri na juyo ina kallon shi dan harabar hotel ɗin akwai haske sosai kamar rana..take na gane shi, haɗe rai nayi na juyo a masiface nace '' yawwa ɗazu dana shigo ɗakin ka shine zaka wani yimin runfa kana laguda ta ko? toh bari kaji niba yar iska bace idan wani abu ya sake haɗa mu ka taɓani sai na tsinka ma mari a fuska !" Ya shafa fuskar shi tare da matsowa dab dani ba shiri naja baya '' ai saida na tambaya idan zan iya sumbatar ki,kika ce eh remember?" ɗaure fuska nayi '' taya ni ban tuna ba?" '' not my fault if you have short memory!" ya kashe min ido...naji kamar in soka mashi yatsa cikin ido...naja tsuki ƙasa ƙasa zan bar wurin ya jawo ni ya rungume da ƙarfi da duk ƙarfin da Allah yayi min na gantsara mashi cizo a gefen wuya '' ahhh!!" ya sake ni tare da ja baya...da wannan damar nayi amfani zan gudu ya damƙo hijabina,ba shiri na ƙame ƙam... ''ki gudu mana!" Ya raɗa min a kunne..oh ni tuwo na shiga uku waye wannan mutumin wai? gabana sai faɗuwa yake...ƙamshin turaren sa ya dabaibaye ni kamar ni na shafa.. iska na haɗiye ina kalle kalle koda Allah zai sa wani ya kawo min ɗauki '' ashe ke vampire ce? a freaking vampire in a modern society!...'' sai yayi dariya tare da sakina ya zagayo gabana hannu a aljihu... Autumn: what an absolute moron! Abeedah: ashe kin gane...ji nayi kamar in naushi muguwar fuskar shi '' Meye sunan ki'' ya dawo dani daga duniyar tunanin dana shiga..ko kaɗan bai burgeni ba..na ɗage mashi kafaɗa '' nima ban sani ba!" na amsa ina ja baya..hannu ya miƙa zai ɗage min hijabi '' wai meye haka?" na faɗa murya a sama '' sunan ki nake so in gani...'' ''.sunana Khadijah!" Na faɗa mashi sunan daya faɗo raina...gyaɗa kanshi yayi ya zaro wayarshi daga aljihu ya miƙa min '' your digits!" Daga shi har wayar tashi binsu nayi da kallo ƙwaƙwalwa ta na loading a 360...tunda muka haɗu sai turanci yake ni kuma baji nake ba... '' lambar ki!" Ya ɗan waro min idonshi...ɗauke nawa nayi nasa mashi lambar da ban san kota waye ba..mufa bamu da waya..sai ta mama dake ringin sau ɗaya a shekaru masu yawa...har da saving na mashi cikin style ''Cardy..I like the sound of it..sai munyi waya..goodnight ..Khadija!'' ya sakar min Murmushi kafin yayi gaba ya barni tsaye... ajiyar zuciya na sauke tare da fashewa da dariya '' ace wacce zai kira ɗiyar soja ce...kuma babanta ya ɗauki wayar a wannan lokacin?" wata sabuwar dariya na kwashe da ita kafin nabar wurin kada ya dawo ya same ni koda na koma gida Mama na zaune a tsakiyar gida suna hira itada da Asma'u na kuma san ni suke jira '' salama alaikum '' nayi sallama na shiga '' wa'alaikumssalam '' Mama ta amsa da sauri nazo na faɗa jikinta '' Mama antaso!" '' maraba maraba!" Mama ta amsa min, miƙewa nayi na shiga kitchen na zubo abinci Batareda na cire hijabin ba nashiga ci.. su biyun suka kafeni da ido...''.akwai wani abu ne?" '' ina kika samu wannan turaren...ƙamshin sa irin na maza?" Mama ta ƙanƙantar da idon ta...sarƙewa nayi da abincin dake cike a bakina...da sauri Asma'u ta kawo min ruwa amma naƙi sha...kamar zan mutu amma kuma tunanin ƙaryar dazan sharara nake..mutumin nan ya gama dani wallahi Mama taƙi dena kallo na...sai dana gama tarin ido jawur nace '' zainab ta kawo..na yayanta ne...'' saida mama tayi min irin kallon da ban san ma'anar shiba ta gyaɗa kai.. ina tsaka dacin abinci aka fara ruwa ba sallama,da sauri muka faɗa ɗaki '' ruwa ba sallama ba iska". inji Asma'u Mama tace '' shikuma hadarin da yake nan baki gani ba ko?"...saida na cinye abincina tass sannan na ɗauki zane na fito waje rataya zanen nayi a bakin taga na kwaɓe uniforms ɗina ya rage daga Ni sai pant da singlet na shiga cikin ruwa...ina tsalle tsalle '' waini Allah yaushe Tuwo zata girma?" inji Mama tana shafa kan Asma'u dake saman cinyarta...sai wurin ƙarfe goma sannan na cire pant ɗin da singlet na ɗaura zani na shiga ɗaki ina rawar sanyi Mama ta bini da ido kasancewar fitilar da aka kunna yasa nake ganin inda nake saka ƙafa...wata doguwar riga rabin cinya nasa na saka pant na faɗa saman gado,Mama ta gyara ma Asma'u kwanciya sannan ta rufe mana ƙofa ta kwanta... matsawa nayi kusa da ita na riƙo hannunta '' ke wai yaushe zaki girma?" ta tambaya tana ƙwace hannun ta,turo baki nayi '' to Ni ban iya bacci saina riƙe wani abu!" tsuki taja ta juya min baya kawai sai na rungumeta tabaya...lumshe idona nayi inaji yanda ruwa ke dukan kwanon mu...har bacci yayi gaba dani har ma tsawon kwanaki nida Asma'u bamu dawo daidai ba da Mama tagane hakan ta tambaya sai cewa tayi '' Ni Na gaji da yanda Tuwo takeyi ta karɓi kanta yanda Allah yayi ta amma saita ta gwada kanta dani bana jin daɗi!" tayi maganar ne yanda duk mai saurare zai ɗauka abinda nakeyi ne bata so,amma a zahiri bataso in faɗama Mama abinda ya faru... murmushi nayi na miƙa ma Mama ruwan shinkafar dana ɗauko na zauna gabanta ta fara shafa min batareda tace komai game da abinda Asma'u ta faɗa ba...niko tunani kawai nake yaushe Asma'u ta iya makirci har haka? duk dan saboda wancan makirin mutumin ne ko dai dama haka take? haɗa ido mukayi ta sakar min harara lumshe ido na nayi... Asma'u ba haka take ba saboda mutumin nan ne na tabbatar... amma saidai akwai wani sashe na dake faɗa min dama haka take nice dai bansani ba...ture tunanin gefe nayi nace '' Mama ranar Lahadi zamuyi wanki ko?" '' Eh'' ta amsa '' daga nan sai kimin kitso in gani idan gashina ya ƙara tsawo!" jinayi Asma'u na faɗin '' gashin ki nanan yanda yake,tsawon nan dai bazai ƙaru ba!" kamar ba ita tayi maganar ba tacigaba da assignment ɗinta Wanda nima ina dashi amma bazanyi ba '' yau bazakije aiki ba?'' Mama ta tambaya girgiza kai nayi '' hutu nake '' na bata amsa ************ Yan kwanakin nan Asma'u ta sauya sosai a gida idan gaban Mama ne saita dinga yama ake cema kalmar a Turanci.... pretending! Sai ta dinga pretending kamar ina wani abun da bata so, a makaranta ta dena zuwa wuri na kuma a bayyane take kai kanta ga Macijin sari ka noƙe... sannan take ƙarayin komai dan tasani inji ba daɗi game da kaina...take ƙara nuna min abubuwan data fini dasu,tafini kyau, tafini gashi,ta fini ƙwaƙwalwa....kuma tayi sa'a don kuwa emotional break down ɗina ya dawo sabo fil kullum sai nayi kuka safe da rana da daddare kuma hakan ba ƙaramin faranta mata yake ba,duk dani ban fahimci hakan ba,na ɗauka duk dan saboda Macijin sari ka noƙe ne sai na ƙara himma wurin son nuna mata shi wane irin mutum ne amma bata koso taji.... +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma ₦800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 6. ...Jay D...🖊️ zaune muke a class ana shakaka ruwa kowa sai ƙoƙarin rufe jikinshi yake banda ni sanyin daɗi yake min ba kaɗan ba...ƙanƙame ni a kayi daga baya .tun kafin na juyo nasan ko wace ce...Jadeedah,babbar ƙawata, banyi muku magana akanta ba saboda mun samu saɓani da ita,aganina duk wanda ke ƙoƙarin shiga tsakani na da Asma'u to ya zama dole in rabu dashi... abinda take ƙoƙarin yi kenan tace wai, Asma'u tana kishi dani bayan ni nasan cewa ba haka bane..toh me zaisa ma tayi kishi dani bayan tana da duk wani abinda banda shi? shine yasa nida Jay D mukayi farraƙ.. '' kiyi haƙuri Bee...bazan sake ba kinji '' ƙin magana nayi hakan yasa ta ƙara ƙanƙame ni '' pls Bee..'' '' naji!" na faɗa mata batareda na kalleta ba sai kuma na juyo muna kallon juna riƙe hannunta nayi cikin nawa ina kallon kyakkyawar fuskar ta nace '' Jay D Ina matuƙar son ki,kinsan cewa bana abota da masu kuɗi amma ƙawance na dake daga Allah ne...kada ki shiga tsakani na da Asma'u..Ina matuƙar son ƙanwata!" gyaɗa kanta Jay D tayi tana sakar min murmushin ta me kyau har dimple ɗinta ya fito murmushi nima nayi '' kina Min kama da wani a wurin aiki...sunan shi Abeed '' na faɗa mata har yanzu hannu na cikin nata '' ai yau zan zo wurin aiki nima'' kallon ta nake ina tunani a raina meyasa suna da kuɗi amma suke aiki a restaurant? kasa haƙuri nayi saida na tambaye ta '' saboda kuɗin baban mune ba namu ba,baban mu baida matsala fa,har faɗa mana yake kowa yayi kuɗi da kanshi,kuɗinshi nashi ne ba namu ba..bla bla bla '' nikam na kasa Dena kallon Jay d ta ƙara da faɗin '' nima nafison haka bana so in dinga dogaro da kowa gara insan kuɗin nawa ne!" murmushi nayi na ja dogon hancin ta . daidai nan IRS ya shigo macijin sari ka noƙe ido muka haɗa yayi min wani banzan kallo yan matan ajin mu suka fara gyare gyare... irin nason ɗaukar hankalin mutum nan ya fara zagayen aji yana magana akan topics ɗin daya koyar kwanaki,komai ban tuna ba wallahi '' ke!" ya nuna ni bazato ba tsammani ɗagowa nayi na kalle shi '' meye janaba kuma meke kawo janaba?!" yayi maganar fuska a matuƙar tsuke waishi kada akawo mashi raini,ni kuwa nasan iskancin shine ya motsa shine yake tambaya ta wannan tambayar kuma wallahi bazan amsa ba kai tsaye nace '' ban sani ba!" tsawa ya daka min ya fara zagina yana aibata ni,yan ajin mu sukayi shiru wasu suna dariya abun yamin zafi ba kaɗan ba kasa magana nayi sai hawaye da suka jiƙe min fuska '' babu abinda ke cikin kanki sai iskanci daƙiƙiya kawai... Fuskar ki mummuna kiyi ƙoƙari kisa wani abu a wannan jakar ƙwaƙwalwar taki!" ya ƙarashe maganar yana nuna ni da yatsanshi... idona sukayi jawur ga yan ajin mu sai dariya suke kawai dan yace inada jakar ƙwaƙwalwa...'' haba Malam,a tunani na kai Malami kake koyar damu shin baka karanta acikin Alkur'ani ba inda Allah yace, Al-Hujurat 49:11 يَآأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا يَسۡخَرۡ قَوۡمࣱ مِّن قَوۡمٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُونُواْ خَيۡرࣰا مِّنۡهُمۡ وَلَا نِسَآءࣱ مِّن نِّسَآءٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُنَّ خَيۡرࣰا مِّنۡهُنَّۖ وَلَا تَلۡمِزُوٓاْ أَنفُسَكُمۡ وَلَا تَنَابَزُواْ بِٱلۡأَلۡقَٰبِۖ بِئۡسَ ٱلِٱسۡمُ ٱلۡفُسُوقُ بَعۡدَ ٱلۡإِيمَٰنِۚ وَمَن لَّمۡ يَتُبۡ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّٰلِمُونَ ";Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada waɗansu mutãne su yi izgili game da waɗansu mutãne, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (mãsu izgilin), kuma waɗansu mãtã kada su yi izgili game da waɗansu mãtã mai yiwuwa ne su kasancc mafĩfĩta daga gare su. Kuma kada ku aibanta kanku, kuma kada ku jẽfi jũna da miyãgun sunãye na laƙabõbĩ. Tir da sũna na fãsicci a bãyãn ĩmãni. Kuma wanda bai tũba ba, to, waɗannan sũ ne azzãlumai."; Shiru dukan su sukayi harda malamin sari ka noƙe,wankin babban bargo Jay D tayi musu ba tsoro...fita yayi daga ajin a fusace yan ajin mu suka zo suka fara bani haƙuri...harda jana sukayi wurin rumfar mama yam lokacin break suka siyama na kayan ƙwalama....nayi farin ciki sosai sannan nace na yafe musu,daga nan muka fara wasanni daban daban dama nikam ina son wasa ba kaɗan ba... a gurguje na shirya na wuce wurin aiki cike da farin ciki...amma bayan naba Mama labarin abinda ya faru a makaranta, Asma'u daga gefe batace uffan ba,nayi kewarta kuma nasan itama tayi kewata... Fuska a sake nake karɓar order '' ..da alamu yau kina cikin farin ciki?" Abeed dake gefe na ya faɗa, murmushi na me kyau nayi cike da nishaɗi nace '' yau Jay D zata zo aiki!" ''uhmm...Yau dai zanga wannan Jay D ɗin'' ya furta,yar ƙaramar dariya nayi daga ƙasan zuciya ta nace '' nifa mamaki nake wai baku taɓa haɗuwa ba duk da muna aiki tare!" Murmushi kawai yayi baice komai ba ya fara amsar table ɗin dake gaban shi nima ina kallon table ɗin dake gabana na haɗe fuska, wannan mutumin ne mema sunan shi..ɗan iskan nan daya taɓa rutsani a ɗaki? yawwa..wai Ibrahim...kamar koda yaushe ya kafe Ni da shegun idonshi kamar na akuya yana murmushi gefen shi kuma wannan mutumin ne wanda na jefa da gora saye da facemask yake kamar wani mai korona Virus, wayar shi a hannun yana latse latse, sai wani mai farin gashi,dukan su shigar su iri ɗaya ƙananan kaya riga da wando jeans baƙaƙe..gayen Nan me saye da face mask yasa p cap ƙamshin turaren sa se shiga hancina yake.. ... har zan wuce table ɗin su yace '' Pretty deejah baki karɓi order table ɗin muba ai!" dariya ya bani daya kirani da wannan sunan...wai firijin deejah...dakewa nayi nace '' ba hakane sunana ba!"wannan gayen mai farin kai ya ɗago ya kalleni kafin ya mayarda kanshi ƙasa,mai facemask kuma kamar bai san da mutane a wurin ba.. '' to meye sunan ki?" yayi tambayar da zolaya (flirtatiously) yana min kallon ƙasan ido.. naji kamar in shaƙo shi '' Malam nan wurin aiki nane ba wurin faɗar suna ba...idan ba abinci zaka ci ba ina da abun yi!" na faɗa a ƙule takaici na kawo min har maƙoshi farin gaye mai farin gashi ya fara magana da turanci yana kallo na...nayi tsaye ƙiƙam ina binshi kamar kurmar da bata ji kuma bata iya magana ba...ina fa nake ji?suyi magana da Hausa ala dole sai sun ba ƙwaƙwalwata wahala... juya hannu na nayi littafin riƙe da ɗayan hannun '' English no! Hausa Yes!" na faɗa ina zaro ido...yayi shiru, Ibrahim ɗin nan kuwa ya gimtse dariya..ban kalli sashen Shiba...nayi ƙoƙarin barin wurin sai kuma na dakata na sake tambaya '' me za'a kawo muku?" '' Shine kika ban wrong number ko?" ya jefo tambayar batareda ya amsa tawa ba...wai shi me yake damun shine? ga abinda na tambaye shi ga wanda yake magana akai... '' oh...ashe wrong number ne? ina fatan dai mijin wacce ka kira ya maka dukan tsiya!" na ƙarashe ina hararar shi''lumshe idonshi yayi ya sake buɗesu tare da faɗin '' sorry to burst your bubble,ai budurwa ce... besides Bruno anan...'' ya nuna min mai farin gashi '' zai shigar min!" ɗage kafaɗa nayi dan ban fahimci mai sentence ɗin shi na farko ke nufi ba..wannan sunan bruno yayi kama da sunan kare amma dai ban faɗi hakan a fili ba nayi tafiya ta, araina kuwa har naga abinda zan kawo musu,shi wannan ɗan wulaƙancin kamar bai san da mutane a wurin ba,ko ɗagowa bai yiba kitchen na shiga nace a haɗa tuwon dawa miyar kuka..duk da sunyi mamaki hakan bai hanasu haɗawa ba,plates uku kuwa..zama nayi har suka gama aka haɗo min tuwon dawa miyar kuka da ruwa...ɗaukar tray ɗin nayi ina tafiya a hankali tun daga nesa nake jin idonshi akaina...na rasa Uwar me yake nema na kawo wurin su ina tsaka da ajiye tray ɗin ta rugo da gudu '' Beeeee!!!! ''tayi tsalle ta haye ni trayn ya faɗi daga hannu na abincin ya juye musu a jiki nida Jay D muka faɗi ƙasa...suma da sauri suka miƙe saboda yanda miyar kukan ke basu ƙyama.... wurin kowa ya dawo da kallon shi akan mu...Jay D ta fara miƙewa tayi hiri hiri da ido kafin nima na miƙe Gayen nan mai farin gashi yake magana da Yaren da ban taɓa jiba...fuskarsa ba kyaun gani tsabar ɓacin rai... mai facemask kuwa kamar wanda ya shiga shock sai kallon kayan jikinshi yake... Khalil babu abinda ya samu nashi kayan..in wani abu sai gimtse dariya yake...nima nawa idon kamar zasu fito,harda yar zufa naji tana sauka a gadon baya na..na haɗiye yawu sanda mai saye da facemask ya watsa min wani shegen kallo har cikin ƙasusuwana.. ƙirjinsa na sama da ƙasa..kamar zai ƙona ni da idonshi...Jay D ta riƙe hannuna muka yi taku ɗaya baya .. wurin yayi shiru kowa mu yake kallo, ƙafafuna babu abinda suke sai rawa..zagayowa mai facemask yayi zai damƙo ni,da sauri Ibrahim da ɗayan gayen suka tare shi " Calmati Di caprio (kwantar da hankalin ka Di caprio)!"mai farin gashi ya furta da yaren da ban sani ba, Ibrahim na shafa ƙirjin gayen..ture su biyun yayi a tsananin fusace ya nuna ni da muryar shi kamar ana tuƙa tsohuwar mota yace ''Come faccio a calmarmi?! Ma è pazza?! Mi ha rovinato i vestiti, maledetta!(taya zan kwantar da hankalina? bata da hankali ne? ta ɓata min kaya..damn girl!) " Calmati! calmati!" kawai gayen mai farin kaya yake maimaitawa...shima Ibrahim yana taya bada haƙuri... ido na ya haɗu dana mai face mask...naga idon shi ya ƙara duhu..can kuma ya dunƙule hannunshi..sama da ƙasan ƙirjinshi na ƙaruwa kamar kallona kawai na ƙara kunna shi...da sauri na cire idona daga nashi na kalli Ibrahim da shima ni yake kallo..murya ba amo nace '' dan Allah kayi...'' '' SHUT UP!!!!" Mai facemask ya daka min tsawa sai dana kusa faɗuwa,Jay d ma ta tsorata da alamu ta ƙara ƙame ni... '' calm down Ro..'' da wani irin yanayin magana(accent )wanda bai yi kama da yanda masu turanci ke magana ba yace '' this is all your darn fault BRAHAM!'' Ibrahim ya gyaɗa kanshi da ban haƙuri a fuskar shi... nifa gayen ya fara ban haushi tuntuni sai haƙuri ake bashi amma yaƙi ya sake harara ta '' Abeedah mubar wurin nan...'' jay d ta raɗa min a kunne...gyaɗa kaina nayi muka fara ja baya a tare..mai facemask sai banbamin bala'i yake da shegen yaren su mara daɗin ji ido na sake haɗawa da Ibrahim '' in kawo maku wani sabon tuwon?" na waro mashi idona,dama ace abincin kan shi ya zube..amma naji daɗi daya zuba kan wannan mara mutuncin...ɗan zaro ido yayi sai ya girgiza kai yana nuna min gayen nan da idon shi...wata irin dariya na kwashe da ita ba shiri...kowa yake kallona a wurin kamar na haukace gane hakan yasa na miƙe da kyau tare da haɗa hannayena wuri guda '' yi haƙ...'' '' if you open that your dirty mouth again,I will slap you hard across the face!" yayi maganar a mugun fusace.. jim nayi ina ƙoƙarin fahimtar abinda yake nufi can ƙwaƙwalwata,ta tattaro bayanai da ƙyar...haɗe fuska nayi cin mutuncin yayi yawa'' baƙin ciki kake min ko? Allah ya bani baki wanda bai wari ba saina sa fes mas ba shi...'' kafin in gama naga ya wani harzuƙo mun bansan sanda na warto hannun Jay D muka kwasa da gudu ba sai kitchen bayan mun gama haki sai kuma muka rungume juna muna dariya '' ke Bee, wannan gabjejen mutumin idan ya same ki ai shemar dake zaiyi da bugu ɗaya!" '' yoni hauka nake da zan bari ya same ni?" na bata amsa mu biyun muna miƙewa tsaye ganin manager, fuskar shi a murtuke...kafin ya fara magana na fara kukan ƙarya '' Jay D bayana ji nake kamar ƙashin bayana ya karye!" nayi maganar ina juya mata baya da ƙifta ido '' yi haƙuri Bee laifi nane..'' ganin dramar mu manager ya ɗauka da gaske ne ya shiga bamu haƙuri daga nan ya bamu dubu biyar yace Jay D ta kaini kyamis yana fita muka ƙara rungume juna muna dariya sannan muka fita ta baya, a parking lot na hango Asma'u... da sauri muka isa wurin datake '' me kike yi anan?" Jay D ta tambaya nabi ta da ido,faɗawa jikina tayi murya kamar zatayi kuka '' dan Allah Tuwo kiyi haƙuri...'' kallon kallo mukayi nida Jay D shafa kanta nayi '' ba komai!" na faɗa ina ɗagota murmushin ta me kyau tayi min '' Mutafi mu hole da dubu biyar ɗin manager!" Jay D ta faɗa tana riƙo hannu na,har zamu bar wurin saiga Malam samin macijin sari ka noƙe ya shigo shida wata yarinya, hannun shi riƙe da ƙugunta,yana mata raɗa a kunne kafin kuma suka haɗe baki wuri guda kis,zaro ido mukayi mu biyu kafin mukalli Asma'u dake hawaye, lallashinta muka fara yi amma ina kukanta ƙara sauti yayi da ya jawo hankalin su akan mu... tsaye yayi wuri guda shima yana kallon mu idonshi kamar zasu faɗo firgici bayyane a fuskar shi musamman dayaga yanda Asma'u ke risgar kuka . takowa ya fara zai zo wurin mu ta tsere tabar wurin ,bin bayanta Jay D tayi kallon sama da ƙasa nayi mashi '' Sheɗanin banza ɗan iska!" na faɗa a fuskar shi kafin nima nabar wurin Asma'u kuka take kamar ranta zai fita lallashinta ba ƙaramin aiki bane, jan mu Jay D tayi zuwa wani wuri inda ake sayarda su abincin gefen hanya,irin su suya,ice cream da sauran su,wasu dubu biyar ta ƙara akan wanda manager ya bamu muka kwashi Gara suya ta siya mana ta dubu biyu da ice cream na dubu ɗaya da ɗari biyar kowa ɗaya, duk wani kayan maƙulashe saida Jay D ta siya mana daga ƙarshe sai wurin maghrib muka bar wurin bayan mun ƙara sayen suya ta dubu biyu muka wuce da ita gida.... Jadeedah ma ta wuce gida bayan ta bamu dubu biyu mu riƙe munyi mata godiya sosai... '' Tuwo kiyi haƙuri akan duk abinda na maki bazan sake ba insha Allah '' Asma'u ta faɗa tana shafa min ruwan shinkafa akai,yau akwai wuta, Mama tana tsakar gida tana kalkamta kaya dan akwai hadari.. '' nayi farin ciki..yanzu dai nasan kinga Abinda nake faɗi ko? Wannan yarinyar ba itace ta farko ba,ya kawo mata da yawa...bai dace dake ba!" gyaɗa kanta tayi hawayen ta na faɗowa a fuska ta da sauri ta goge su kada Mama ta gani... washegari jumu'a yasa Mama bata bamu ko kwabo ba,ina ta ture turen baki kamar ƙaramar yarinya taɓe baki Mama ta ɗauke ido '' Mama abincin jiya ya rage?" Asma'u ta tambaya '' a'a, shinkafar ma ta ƙare yau idan kun dawo sai dai ku sha garin kwaki'' Mama ta bata amsa jida nayi ance babu shinkafa yasa naji wani iri a zuciya ta '' yanzu tuwo zamu dinga kilma ko?" wani kallo Mama tayi min '' ai shima tuwon babu .. abincin ya ƙare duka!" kallon kallo mukayi nida Asma'u kuma fa wata baiyi nisa ba balle ince an kusa biyan mu albashi... '' kuyi sauri kada ku makara har rana ta fito '' Mama ta faɗa tana miƙo mana kunun mu karɓa nayi raina a cunkushe yanzu ya zamuyi? nasan buba me kayan masarufi bazai bamu bashi ba dan har yanzu akwai sauran bashin shi a kan mu..har na shanye kunun bansan na shanye ba tsabar yanda nayi nisa cikin tunani, ajiye cup ɗin nayi na goge baki itama Asma'u ta ajiye nata muka saka hijaban mu dake rataye a igiya jakunkunan mu a hannu '' mun tafi..'' miƙewa Mama tayi ta biyo mu da nasiha da addu'oi har bakin ƙofa '' a dawo lafiya.." yau Ban hawo bishiyar mangoro ba makaranta muka wuce daret babu wanda ke magana cikin mu,sanda muka isa an kusa gama assembly bada daɗewa ba muka shiga aji...abin da ya ƙara min baƙin ciki..Jay D bata zoba! dama ita doja ce ta bugawa a jarida lokacin break na cigaba da tunanin ya zanyi da abincin da babu a gida? shawara na yanke zan karɓi rabin albashi na hakan ya ɗan sanyaya min ruhi da gaske da muka dawo garin kwaki muka sha ba suga ba giɗa babu ƙuli... Kamar inyi kuka,muna gamawa muka ɗauki bucket gidan wani Alhaji babba muka tafi ɗibar ruwa, akwai layi dayawa dan haka muka shashance da wasa...sai wurin ƙarfe uku muka kawo bokiti guda guda Mama tana tayi mana faɗa...da muka koma layi ya rage da sauri muka ɗibi ruwan muka cika komai kafin na shirya na wuce wurin aiki bayan nayi wanka Sai dai me? an kore ni daga aikin ba bayani ba komai kuma an canja manager,duk yanda naso in ji dalilin korata babu wani takamammen bayani... albashin ma an hanani...a dai dai wannan gaɓar ji nayi rayuwa tayi min zafi, duk yanda naso in daure na kasa na fara surfa masifa....sabon manager'n yasa securities su fitar dani daga wurin wai ina damun customer ɗinsu... haka wa'yannan gaɓa gaɓan abubuwan suka saɓani a kafaɗa suka jefar dani waje kamar buhun shinkafa... zagi da Allah ya isa sai wanda na manta kafin na duƙe a wurin ina sharɓar kuka...ban ankara ba ashe har dare yayi miƙewa nayi na fara tafiya gani nayi kamar akwai wata mota a baya na amma ban kawo komai a raina ba har Saida na sha wata corner inda babu mutane sosai motar nan tasha gabana.... PAGE 7 A AREWA PEN +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 Free pages 7. ...Ya xanyi ... 🖊️ Tsayawa nayi zuciyata na duka da ƙarfi, ina jin labarai daban daban yanda aka sace yan mata ana yi musu fasadi kala kala? toh ko nima layi ya biyo ta kaina? jinayi tsoro ya shige ni musamman dana ga an buɗe motar su uku suka fito, duk da duhu ya sauko hakan bai hanani gane suba,gayen nan ne dana tura ma cokali ɗaya na barkono a baki tareda ƙawayenshi... juyawa nayi zan gudu yayi saurin cafko hannu na,ihu na fasa ina shilla ƙafafu dan ɗauke ni yayi kamar yar tsana ƙawayenshi na dariya suna tafi da shewa '' tsuntsu daga sama gasashshe!" ɗayan su ya faɗa hawaye suka wanke fuska ta zuciya ta na bugu da ƙarfi har cikin kunnuwa na...'' bani kika sakawa barkono abaki ba,yau zan rama ne then babu wanda zai sake kallon ki shiga cikin mutane sai ya mike wahala!" yayi maganar yana ƙoƙarin turani cikin motar su kuka nake da iya ƙarfi na dan ba ƙaramin matse ni yayi ba, '' Hakane guy, kayi mata abinda bazata sake iya fita cikin mutane ba!" inji abokinshi dake wasar hauru kamar anyi watsin masara kan titi '' Bara in buɗe maka ƙofa!" ɗayan dake tsaye kusa kusa yayi maganar shima yana buɗe mashi ƙofa '' kai daya kamata ka buɗe mashi ƙafafunta!" wanda yayi maganar da farko ya faɗa yana sheƙewa da dariya '' ataimake Ni... jama'a a taimaka... wayyo Allah na...na shiga uku...'' ganin ina ihu zan iya taro musu mutane yasa yayi saurin toshen min baki aɗan zafafe ya kalli ƙawayen nashi yace '' wai dalla kun barni da ita,ni kaɗai zan sha gara ne?" '' haka fa!" aboki 1 ya faɗa tareda matso wa ya kama ƙafafuna sai zillewa nake zuciya ta a ƙuntace,a kace a wannan zamani mace takai mutuncin ta gidan miji ya ta ƙare bare ace ta tafi fanƙo...? nasan idan wani abu ya same ni Mama zatayi kuka... sannan ta ɗaura ma kanta alhakin komai zata shiga damuwa sosai ƙara ƙarfin kuka na nayi duk da ya rufe min baki...samu sukayi suka turani cikin motar tare, gayen da nasa ma barkono a baki ya shigo shima..wani irin faɗuwa gabana ya shiga yi hawaye suka dena fita tashin hankali ya ziyarci ilahirin gangar jikina ganin yana zare belt da sauri sauri finciko ni yayi na gantsara masa cizo a hannu,yarfe hannun sa yayi kafin ya yarfa min mari '' shegiya mai baƙar zuciya!" ya zage ni a zafafe ya ƙara finciko hijabi na,riƙe hijabin nayi ina rushewa da sabon kuka daga sama aka buɗe ƙofar juyawa yayi don ganin waye wani irin naushi ya sauka a fuskar shi,kafin ya warke aka wani finciko shi daga motar, ana cigaba da naushin shi,maƙewa nayi a ƙarshen mota jiki na na tsuma tsoro na ya ninku dan gani nake bayan su sai ni a hankali iska ya dinga ɗaukar ƙamshin turaren shi zuwa hancina, Ibrahim ne ya leƙo cikin motar idon mu ya haɗu...'' Oh...kitten!" ya furta da mamaki a fuskar shi fashewa na sake yi da kuka fiye da wanda nayi a baya, sassanyan murmushin shi ya sakar min ya miƙo min hannun shi,a tsorace na kama ya taimaka min na fito daga motar '' Shhh... it's okay!" ya furta da sanyayyar murya hakan ya ƙara ma kuka na sauti... daga can gefe naga wannan gayen dake sa fes mas yana ta jibgar gayen dana zuba ma barkono a baki... wani irin sanyi naji araina ina furta Alhamdulillah dabadan Allah ya kawo suba da shike nan '' shiga mota in sauke ki gida!" maganar shi ta katse tunani na da sauri na zare hannu na daga nashi ina girgiza kai alamar a'a..dan sun taimake ni yanzu baya nufin zan sake faɗawa motar su,nasan kosu wane irin mutane ne?shima baya taɓa rutsani a ɗaki ba? gayen nan mai facemask ya ƙaraso inda muke,yana ganin nice ya min kallon uku saura kwata ya juya ya shige motar su,oho ko a slippers ɗina share fuska ta nayi hankalina ya koma gida me zan faɗa ma Mama? idan fa tashiga damuwa saboda wannan aikin da narasa ko tace zata fara zuwa neman aiki? a'a! Dole inyi wani abu tafiya nake da sauri sauri hankali na a ɗauke ban masan cewa ya biyoni ba '' su waye su?" muryar shi ta sauka a kunne na har saida na razana..sai kuma na tsaya juyowa nayi ina kallon shi, murmushi yayi min, shi bai gajiya da murmushi? Naji haushin sa ya kamani... '' ban san suba! ashe baka tafi ba? '' na tambaya bayan na amsa tashi tambayar '' raka ki zanyi!so ashe sunan ki Abeedah?"...ƙanƙantar da idona nayi '' oh..haka fa...na ɗauka Khadeejah ne!" ya miƙa hannu zai shafa fuskata,share hannunsa gefe nayi tare da ɓalla mashi harara..na juya na cigaba da tafiya '' ya akai kuka..'' katseni yayi da faɗin '' motar muce ta samu matsala daga wurin shine na sauko zan amsa waya naji ihu...so we came to your rescue!" na fahimci abinda ya faɗa daidai inda yasako turanci notikan kaina suka kwance na tsare sa da ido alamun ban gane ba '' nifa bana so anamin magana ana haɗawa da turanci!" nayi maganar da iya gaskiya ta,shafa ƙeyarshi yayi murmushin shi na ƙara faɗaɗa '' sorry..my bad!" guntun tsuki naja ƙasa ƙasa yanda bazaiji ba.. '' Na gode zaka iya tafiya '' na furta daga baya ina cigaba da tafiya jin an fara kiraye kirayen isha'i amma bai tafi ba ya cigaba da bibiya ta gyaran murya yayi yana faɗin '' zamu iya zama abokai '' daidai mun kawo wata kwana me duhu, ban amsa shiba na cigaba da tafiya caraf! ya riƙe hannu na na juyo zan sauke mashi kwandon rashin M na gacewa kusancin mu yayi yawa,duk da tsawona na koma yar ƙarama gabanshi,dai dai nan aka yado mu da Torchlight... '' ABEEDATU..??" a ɗan firgice na juyo,na haɗe fuska ganin maman su nusaiba munafukar anguwar mu, ta wani riƙe baki ido waje irin taga wani mugun abu..nasan sallallami take a ranta kallon maman su nusaiba Ibrahim yake ba alamun damuwa a fuskar shi kuma har yanzu riƙe yake da hannu '' Me ya faru?" na tambaya ina waro mata ruwan tokan idona tsoro ya bayyana a fuskar ta, na ƙwace hannu daga riƙon Ibrahim na matsa kusa da ita '' me kika gani?" na tambaya ina juya idona kamar ba mutum, girgiza kai tayi tana ƙifta ido tace '' b..bb..babu komai!" gyaɗa kaina nayi cikin ƙasa da murya nace '' Wallahi tallahi idan kika kuskura maganar nan ta fito musamman idan Mama taji...hmm'' kallon cikinta nayi duk da bansani ba ko tana da ciki ko bata dashi nace '' wannan abun bazaizo duniya ba zan hallaka shi tun cikin ciki!" jkinta ne ya fara tsuma ta dafe cikinta '' don Allah kiyi haƙuri na maki alƙawarin babu wanda zan faɗa mawa!" tayi maganar da magiya na jinjina kaina tare da nuna mata hanya kamar wata uwarta '' oya bita nan!" ta fara tafiya da sauri sauri har tana cin tuntuɓe ajiyar zuciya na sauke bayan tafiyarta Atleast nayi maganin ta idan ba haka ba zama a unguwar nan tsaf zai gagare mu dan ba abinda ta gani kaɗai zata faɗa ba harda wanda bata gani ba juyowa nayi wurin wannan Ibrahim ɗin ina mashi faɗa cikin duhu duk da ba wani ganin fuskar shi nake sosai ba '' woah!yanzu fa muka taimake ki!" yayi maganar yana matso ni '' na roƙe kune? in sunbaci ƙafafunku dan kun taimake Ni?'' da mamaki a fuskar sa ya kalleni sai kuma ya sauke ajiyar zuciya yace '' shike nan amma zamu iya zama..'' '' ba zamu iya ba!" na katse shi kafin ya iyar na ɗaura da faɗin '' ban san dalilin ka nason ƙulla alaƙa dani ba,ina roƙon ka daka rabu dani ,saboda kai saura kaɗan in zama abin faɗa a unguwar nan ka rabu dani dan Allah!" Ya kalli hannayena gira a ɗage kafin ya dawo da idonshi a fuska ta ..matsowa yayi kusa dani sosai numfashin sa na dukar fuska ta '' I don't give up easily kitten! Sai mun sake haɗuwa!" Daga nan ya juya yayi tafiyar shi, shiya San abinda yake nufi Allah yasa kada mu sake haɗuwa duk da wani sashe na zuciya ta yaƙi yace Ameen ga wannan addu'a... ina shiga gida duk wani abun daya faru ranar ya dinga dawo min ji nayi hawaye sun fara zirara daga ido na, jin sheshsheƙar kuka na shirin kama Ni yasa na ɓoye bayan ƙofar mu ta kara ina goge hawaye '' waye nan? Abeedah?" Mama da alamu yanzu tagama salla dan saye take da hijab ta tambaya hannunta riƙe da tasbih da sauri na shigo gidan na ajiye hijabi na a gaggauce na ɗauki buta kamar mejin kashi na faɗa toilet na toshe bakina da hannu na na duƙe ina kuka inajin Mama tana faɗin '' Allah ya shirye ki Abeedah '' dafe kaina nayi ya zanyi yanzu? na daɗe a bayen ina fitowa na ɗibi ruwa bucket na sake shigewa cikin duhun bayen wanka nake naji wani abu me ɗumi na bin ƙafafuna... lokacin haila tane dogon numfashi naja sannan na wanke ƙafafuna na iyarda wankan na fito samun mama nayi tsaye a tsakar gida tana jirana fuskar ta ɗauke da alamun tambaya,daidai nan aka dawo da nepa da ƙarfi tsakar gidan mu kamar rana Mama ta kalle ni da kyau da kyau,ƙasa nayi da kaina nakasa kallon ta '' wani abu ya faru ne Abeedah?" ta tambaya tana ɗaura hannun ta a kafaɗa ta ɗayan kuma ta ɗago haɓa ta tana kallon shatin marin dake kumatuna, Asma'u ta fito ta tsaya daga bakin ƙofa '' yimin magana Abeeda" mama ta furta muryar ta cike da damuwa fashewa nayi da kuka har da jan majina Hankalin Mama da Asma'u ya tashi matsowa tayi itama tana tambaya ta meya faru, Hawayen da na gani a fuskokinsu yasa na shanye kuka na'' wani yayi miki wani abu ne Abeedah? meyasa ki kayi wanka daga shigowa?waya taɓa ki? ina ganin shatin mari a fuskar ki ''Mama ta tambaya a tsorace tana ƙara dubani gaba da baya...ganin jini a rigar jikina yasa ta ja baya hawaye na wanke fuskar ta haka ma Asma'u '' A..aabeedah?" ta kira a rarrabe,da farko bansan mezan faɗa ba, dalilin wanka na da kuka na, ganin hankalin su ya tashi nace cikin Muryar kuka '' jini nane yazo ina tsaka da aiki shine mutane suke ta min dariya,na kunya ta Mama!!" bayani na yasa Mama sauke wani irin nannauyan ajiyar zuciya a bayyane ta miƙe tana ƙara kallo na sai kuma tace '' kin tabbata?" gyaɗa mata kai nayi amma kamar bata yarda ba'' muje in duba!" zaro ido Asma'u tayi nima haka murya na rawa Asma'u tace '' Mama me zaki duba?" kallon da Mama ta watsa mata yasa tayi shiru..ban faɗa muku ba ko? haka Mama take idan har bata yarda ba saita duba ba tun yau ba haka take mana tun muna yara..na ɗauka yanzu tunda mun girma zata dena ashe ba haka bane...wasu abubuwan basa canja wa a kunyace na shiga ɗakin itama ta shigo,kasa motsi nayi duk kunya ta kamani '' Mama wallahi ba abinda kike tunani bane '' '' me nake tunani?" ta tambaya tana min wani kallo ƙasa nayi da kaina kafin na kwanta ɗin,ɗage rigar tayi nikam na runtse idona..wani irin azababbiyar kunya na kamani dumƙe zanen gadon nayi a hannu na ina cije baki can naji tace '' shike nan!" miƙewa nayi zaune na kasa kallon ta '' ba wai nayi hakan bane dan in kunya taki ba,ko don Ban yarda dake ba,a'a ni uwace dole in tabbatar da lafiya da ingancin rayuwar ya'yana Abeeda...idan wani abu ya same ku bansan ya zanyi da kaina ba ku riƙe min Mutuncin kanku ina roƙon ku!" ta faɗa tana kallona da kuma Asma'u dake tsaye bakin ƙofa dukan mu kawunan mu ƙasa muka amsa da '' insha Allah !'' fita tayi zuwa tsakar gida tana tattara kayan dake nan takai su kitchen, wata doguwar rigar atampa da ta ƙoƙe na ɗauko nasa sannan na duba cikin kayan mu wani pad da aka taɓa bamu a makaranta na ɗauka tareda baƙin pant nasa na haye gado na kwanta...da ƙarfe biyun dare na farka nakasa komawa..sai tunani nake daban daban mezan cewa Mama? ya zamuyi da abinci daya kusa ƙarewa? abubuwa da yawa suka shamin kai da safe bayan sallar asuba nida kaina nayi share share na haɗa mana abun kari, Asma'u ta shirya zuwa makaranta amma ni? '' yau bazaki tafi makarantar ba?" Mama ta tambaya tana kallona '' ban jin daɗi Mama!" na bata amsar a gajarce '' Allah ya sawaƙe!" Asma'u ta faɗa na amsa da Ameen,bayan ta gama ta ɗauki jakarta da hijabi ta tafi makaranta wanke wanke nayi sannan na koma ɗaki,ji nayi fuska ta na ƙaiƙayi na sosa.. can naji ta ƙara fara ƙaiƙayi fiye da ɗazu na dinga sosawa kafin nayi amfani da ruwan gishiri na wanke fuska ta '' Abeeda ko zakiyiwa manager'n wurin aikin ku magana ya baki wani abu daga sallary'n ki kinga shima garin kwakin ya kusa ƙarewa!" Mama ta faɗa daga kitchen,dum! naji gabana ya faɗi murya na rawa nace '' ai basuyin haka Mama..jiya na tambaya'' nayi ƙaryar wani irin nauyi na sauka cikin zuciya ta kamar an ɗaura dutse '' Allah ya kyauta '' na amsa da 'Ameen ' tareda faɗawa saman gado inaji duniyar tayi min zafi ya zanyi ne? bada daɗewa ba Asma'u ta dawo kasancewar yau juma'a,tana murmushi ta shigo gidan '' Mama an taso!" ta faɗa tare da ɗaukar buta ta shiga toilet,'' sannu da zuwa'' Mama ta bata amsa daga inda take zaune nikam kwance nake saman gado na juya baya duk da ba bacci nake ba ga ƙaiƙayin fuska daya shamin kai shigowa tayi ta zauna bayan ta cire hijab tana murmushi tace '' Mama akwai wani spelling bee competition da za'ayi a makarantar mu kuma an zaɓe Ni!" Mama tayi dariya tace '' haba dai?" Itama Asma'u tana dariya ta bata amsa da '' Eh'' sannan ta ɗaura da faɗin '' akwai kyauta kuma,wanda yayi na ɗaya za'a bashi miliyan ɗaya da gida irin na yan gayu,na biyu dubu ɗari takwas da gida shima amma baikai na ɗaya ba,na uku da na huɗu suma. haka...mama wallahi duk gidan na huɗu shine mara kyau...nidai ban sonshi... kuma dubu ɗari biyu kawai za'a bashi'' juyowa nayi ina kallon ta da murmushi nace '' nikam da zan shiga gidan na huɗu nake so...'' katseni tayi da faɗin '' yo ke ana maganar masu ƙwaƙwalwa ina ke ina sako baki Tuwo?'' '' ba'a son wulaƙanci!" Mama dake sauraren mu ta faɗa tana ranƙwashin Asma'u '' Ouch!" Ta shafa wurin tare da turo baki juyar da kaina nayi ina kallon gadon mu hawaye suka ciko idona maganar ta tayi min zafi amma ya na iya? da gaskiyar ta...kuma ma wane abune na iya? meye amfani na?...ciwo zuciya ta tafara na lumshe ido na hakan yaba hawayen dake maƙale damar silalowa ban san meya faru ba amma dai nasan bacci ya kwashe ni..da ƙarfe biyar na farka kitchen nashiga na jiƙo gari ba suga nazo na zauna ƙarƙashin baranda inda su Mama Asma'u kwance a ƙafarta tana shafa gashinta,suna magana akan abinda ban sani ba kallon su nake su biyun kamar su sak kamar an tsaga kara an ajiye kawai Mama tafi Asma'u tsufa ne, itama gashinta har ya wuce wuyanta amma ƙila saboda tsufa bai kai yawan na Asma'u ba sannan duk furfura ta cikashi '' ya dai da kallo? kinga yan mata kyawawa biyu ko?" Asma'u tayi maganar tana ɗadɗage min gira da wani murmushi maƙale a fuskar ta ji nayi na kasa shan garin sai juya shi nake tashi zaune tayi tana kallon Mama tace '' wai ita wannan dawa take kama? kodai da baba take kama? Amma baba yana da kyau kuma kema Mama kina da kyau amma Abeeda... hideous!" sanin bana jin turanci yasa Asma'u ƙarasa maganar da turanci amma daga yanda take kallo na zan iya cewa na fahimci abinda take nufi '' kedai Asma'u Allah ya shirye ki.. Tuwo tana da kyau wallahi kawai dai itace bata ganin hakan!" Mama ta faɗa tana tashi daga wurin ta ɗauki buta tashige baye murmushi wanda ya ɓoye asalin zafin da zuciya ta take min nayi nace '' Asma'u zaki yarda dani cewa zaifi idan mutum na da kyakkyawar zuciya da mummunar fuska sama da ace yanada kyakkyawar fuska da mummunar zuciya!" dariya Asma'u tayi sosai '' pftt! babu wanda zai zaɓi hakan Tuwo,kowa yana so yayi kyau wa'yanda keda irin wannan tunanin.. they're losers! sun san basu da kyau shine suke fakewa da kyakkyawar zuciya bla bla bla.... kamar dai ke yanzu!'' Maganar ta kamar an daɓa min wuƙa a ƙahon zuciya..... +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17🍁🍁 8. ...🖊️ Daga ƙarshe dai Asma'u ta fito fili ta faɗa Ni,mummuna ce..haɗiye abinda ya tsayamin a maƙoshi nake ƙoƙarin yi amma na kasa '' wai kin ko kalli madubi duk yau? Ni sai naga kamar pimples ɗin...'' kafin ta kai ƙarshe da gudu na na isa ɗaki na tsaya gaban madubi hawaye masu yawa kamar ambaliya suka fara bin fuskata ashe ƙaiƙayin dana ke ji bahaka kawai bane..ƙurajen sun wani fito ɓula ɓula a gaba ɗaya fuskata babu inda babu su... musamman goshina sunyi daɓa daɓa faɗuwa nayi wurin na fashe da kuka '' meyasa? meyasa hakan ke faruwa dani..!! ada akwai inda babu su amma yanxu akwai su ko ina bazan taɓa magance su ba!" sosai nake kuka kamar raina zaifita shigowa Asma'u tayi tana kallo da murmushi tace '' nikam Alhamdulillah..sai Godiya!" takoma waje ta zauna cikin nishaɗi.. fara karanto min list zuciya ta tayi '' da farko kinyi addu'a ba'a karɓa ba,bakida shape bakida kyau ,baki zama me Godiya ba,bakida sef istim,an kore ki daga aiki ,cikin ki ƙatoto bakida gashi..dadai sauransu kuma fa kinyi addu'a! inaa sallar daren da kikayi? ina addu'oin da kikayi? ina sadaƙar da kika bada...amma har yanzu babu abinda ya canja sai ƙara lalacewa da abubuwa suke tuwo anya ma addu'ar kina karɓuwa? anya ma zaki samu Abinda kikayi addu'a akai kuwa? zaifi dacewa ma idan kin dena addu'ar da sallar daren duka dan ba amfani!" Wannan tunanin ya ƙara haifar min da wani ƙunci a zuciyata meyasa? meyasa duk wannan gaskiya ne..meyasa ko abu guda danayi addu'a da fatan samu ban samu ba? Tun ina jss nake ta addu'a akan kusan komai danake kuka akanshi yanzu amma babu abinda ya canja meyasa? Ga mutane da yawa ko rabin abinda nake basayi amma suna samun biyan buƙatar su...ji nayi daga yanxu bazan sake addu'ar ba idan har BAZAN samu Abinda nake so ba '' bazan sake yin addu'ar ba,ƙaramin ƙunci ha...'' '' kul Abeedah!" Mama ta katseni daga bakin ƙofa,ɗago jajayen idanuna nayi ina kallon ta taƙara so ciki ta zauna kusa dani '' ashe bakida hankali baki da wayo ban sani ba? shi Allah'n kike cewa bazaki sake yiwa addu'a ba? toh ai kanki kika yi mawa! shi Allah baya da buƙatar Addu'ar ki shashasha kawai!" nan Mama ta canja min ta dinga yi min faɗa ta inda take shiga bata nan take fita ba '' akan wani banzan kyau da wani banzan abinda kike sha'awa zaki kafirce ma abinda Allah Yayi miki? ya baki lafiya,ya baki gida ci da sha kina raye kina da uwa da ƙanwa amma akan wani ɗan ƙanƙanen abinda ƙila ma ba alkhair bane gareki kike nan kina faman kushe abinda yayi maki? wai Abeeda bakisan a yanda kike ɗin nan kinfi wasu ba? waya faɗa maki cewa pimples da rashin diri shike nuna asalin ƙimarki...'' shiru nayi ina kallon Mama ina ajiyar zuciya ina ma ace Mama zata fahimce Ni? abun... babu wanda yasan yanda ake ji sai wanda ke fuskantar hakan yanda nake ji na muzanta yanda mutane ke ƙara sani ina tsanar kaina yanda maganganun su ke tasiri akai na,,,inama ace inada sef istim... jawoni Mama tayi tana goge min fuska ta '' Mama...nima bada son raina nake haka ba,amma babu yanda zanyi zuciya ta baƙin ciki take a koda yaushe,koda nayi ƙoƙarin kada in kalli abinda banida shi,koda nayi ƙoƙarin inyi farin ciki da wanda nake dashi kasawa nake Mama, Babban dalili kuma shine nayi addu'ar,nayi sadaƙar,nayi roƙon amma...'' ƙara rushewa nayi da kuka zuciya ta na ƙaramin raɗaɗi rungume ni tayi tana shafa kaina '' babu abinda ya canja Mama, abubuwa sai ƙara lalacewa suke... Mama ji nake kamar duk sanda na fara addu'a akan wani abu da nake so,me makon ya ƙara kusanto ni sai nisa yake ƙarayi...bana so ina munana zato ga Allah,bana so in zama marar godiya gareshi amma...na kasa jurewa! zuciya ta akoda yaushe tana tunamin da cewa nayi addu'a amma har yanzu babu abinda ya canja sai ma ƙara ƙuntata da nake yi....'' na ƙarashe maganar ina kuka sosai... Babban abinda na fahimta game da kaina shine koda abubuwan da mutane suke yabawa bana buƙatarshi kuma bana sonshi,matsawar mutane sun yabe shi,ji nake kamar nima in sameshi koma menene shi bayan ni har ƙasan raina abun nan bashida wani amfani a gareni! bansan meyasa rayuwa ta ta ta'allaƙa da abinda mutane suke tunani ba ina so in zama duk wani abun da mutane suka yaba koda babu amfanin da hakan zai min gaba ɗaya jina nake kamar bani ba...kamar wata ce daban a jikina wacce maganganun mutane ke juyata son ransu,ni kuma ina daga gefe ina kallo kamar prisoner duk yanda naso infita daga wannan prison ɗin in zama ni...na kasa! '' Na fahimci abinda kike ji Abeedah!" ɗago kaina nayi ina kallon Mama itama ni take kallo ta fahimce Ni? bata ji aranta kamar niɗin me tsananin raki ce kawai ba? bata ji aranta kamar ni ina kokawa akan abunda bai kai ya kawo ba? bata ji aranta kamar abinda nake kuka akanshin situpit ne? Dan nida kaina ji nake idan da za'a tambaye ni takamammen abinda nake ma kukan shiru zanyi ..na farko saboda ban tabbatar ba idan abinda nake ma kukan ina sonshi da gaske,ina buƙatar shi... a ganina kawai ina da son mallakar abune koda bazai amfane niba.. mema ake cema kalmar da turanci? uhm.... yawwa 🍁🍁: Obsession! yawwa inada obsession akan abinda nake burin samu musamman idan nayi addu'a akai toh aganina dole in samu wannan abun na biyu kuma saboda inaga abun baikai yakawo ba amma shine nake nan ina wahalar da kaina...abun har kunya yake bani amma ya zanyi? zuciya ta tana son abinda take so lokuta da yawa nayi ƙoƙarin in sadaƙar in dena kokawa amma na kasa... '' na fahimci abinda kike ji Abeedah,ashekaru irin naki,yara masu tasowa kamar ki suna fama da irin wannan matsalolin wasu suna iya magana wasu basu iya magana,na san yanda kike ji Abeedah akwai wahala ganin kowa na cigaba yana samun abinda yake so kai kuma kana nan a'inda kake bakayi gaba ba sai ma baya! amma ki saurareni Abeedah, baki yi latti ba kina a inda ya dace ki kasance! Sannan addu'oin ki da kike gani kamar basu karɓuwa, Allah yaji kukan ki,ya karɓi addu'oin ki yana shirya maki wani gagarumin abune a bayan fage fiye da yanda kike tsammani kuma kika roƙa! kowa da kike gani a duniyar nan da tashi ƙaddara da jarabawa,ke wannan itace taki jarabawar dan haka kiyi ƙoƙari ki cinye kinji?" gyaɗa kaina nayi wani irin natsuwa na sauko min,ina matuƙar godiya ga Allah daya bani Mama da wata uwace da tuni ta kore yaranta ko tana faɗa musu cewa sun cika raki ko abin ba wani abu bane ko me suka sani game da hakan da suke wani damun mutane... Amma Mama? Ita ta daban ce,ta fahimce mu idan munzo da damuwar mu bata kore Mu tana saurarar mu sannan ta bamu shawara! amma Ni nakasa yarda da cewa abinda nake fuskanta jarabawa ce,a tunani na kafin a kira abu da jarabawa sai yakai matuƙa wurin wahala,kamar ace mutum baida gida,baida abinci,baida inda zaije ga rashin lafiya...da dai sauran bala'oa irin wannan, nikuma ɗan ƙaramin abune nake fuskanta..da gaske jarabawa ce hakan?... washegari asabar bayan sallar asuba muka zauna mu duka harda Mama mukayi muraji'ar hizb goma daga cikin ƙurani mai girma,duk cikin mu,Mama itace haddar ta take tass babu wani kuskuren harafi ko madda ba kamar nida Asma'u ba, har gara ma ni... da gari ya waye muka karya da kunu kamar kullum sannan muka kwaso kayan muna datti duka muka fara wanki bamu gama ba sai washe gari da yamma zaune muke mama na shafa min ruwan shinkafa akai Asma'u tana duba littafin ta na math '' Mama nima ina ga zan shiga spelling bee ɗin nan,ina so in sama mana sabon gida..!" nayi maganar ina wasa da gashin jiki na daya kwanta luf '' ke Abeedah rufa mana asiri,ba makarantar mu kaɗai bace ba fa! kin tabbata zaki iya hawa stage gaban camerori da wannan fuskar taki da pimples suka dabaibaye? ko kada kije wurin riƙe gaban hijabi kisa mu faɗi..'' Asma'u ta faɗa tare da ɗaukar buta ta shige baye na kasa fahimtar dalilin da yasa Asma'u take min haka.. '' Manta da Asma'u, Allah ya bada Sa'a amma nidai nafison gidan nan tuwo..'' ture tunanin Asma'u nayi daga raina sannan nace '' nima Mama amma muna buƙatar yalwataccen gida..'' batace komai ba Bayan ta gama madubi na ɗauka ina kallon fuska ta musamman girata da take nan kamar an aske da lashes ɗina da suke ƙara guntancewa, tuna wannan abun da Abeed ya bani nayi da sauri na miƙe na shiga ɗaki ina neman abun amma ban ganiba '' me kike nema?" Mama ta tambaya daga inda take '' wani ƙaramin kwalba me takarda green anyi wani rubutu da Larabci da turanci!" na bata amsar da damuwa ganin ban gani ba '' ki tambayi Asma'u naganta da wani ƙaramin kwalba bansan ko shine ba '' Asma'u na fitowa daga bayen na tambaye ta sai cewa tayi ta jefar... hawaye suka taru a idona '' ko kinyi amfani dashi babu abinda zai canja.. you're hideous!" ɗauke Asma'u da mari nayi kafin insani,Mama ta kalle mu a nutse amma bata ce komai ba ɗago kanta Asma'u tayi da mamaki tana kallona,jiki na narawa na nuna ta, hawaye maƙale da idona murya ƙasa nace '' meyasa kike min haka Asma'u? na yarda kin fini komai ni ban kaiki ba ata ko wane fanni meyasa kike ƙoƙarin ƙaramin damuwa akan wanda nake cike?" idanunta sunyi jawur ƙirjinta na sama da ƙasa cikin muryar dani kaɗai zanji abinda ta faɗa tace '' saboda ke mummuna ce ina matukar jin kunyar a gan mu tare!" bangaje ni tayi ta wuce ɗaki,bayanta nabi da kallo hawaye na zuba babu wani shamaki ɗauke fuskar ta Mama tayi... hijabi na najawo na fice daga gidan, ahankali nake tafiya ba tareda nasan inda zani ba, mutanen unguwar mu musamman yan makarantar sai magana suke min amma ban tanka kowa ba... zagayawa nayi na tafi gulbin dake bayan gidan mu nayi tsaye wurin hannu na rungume da ƙirjina ina kallon ruwan da suke kore shar... Ga wani dutse dayake kwance malale bishiyar kaiwa ta fito saman dutsen sannan wurin kwari ne inda ake fasa duwatsu... da yawan lokuta almajirai harda yaran unguwar mu suna zuwa wurin dan suyi wanka kuma fa ruwan datti ne dasu, mutum zai iya samun wasu ƙuraje ana kiransu da ƙazuwa... har kashi ake ciki ana zubar da shara amma hakan bai hana su iska sai kaɗa ruwan yake...suna baya a wani irin salo me sanyaya zuciya... amma ni? zuciya ta da yanayin da nake ci,bai bani damar godewa wannan yanayi ba... ina nan tsaye har hadari ya ɗan taru sannan daga can gefe shara ake ƙonewa wani farin hayaƙi ya game wurin rana ta faɗi,tunda natsaya wurin babu abinda nake sai hawaye kukan ma yaƙi zuwa Asma'u ta karya min zuciya fiye da yanda yaron nan yamin lokacin da na rubuta masa letter... shikenan duk abinda Mama ta faɗa min ɗazu yabi iska don dai na dawo yar gidan jiya '' meyasa nake mummuna? me yasa nima ban kasance kamar yanda nake addu'a akai ba? me yasa ban kasance kamar irin matan novels ɗin da nake karantawa ba? Akwai wanda zai taɓa sona a yanda nake...?" kuka me ƙarfe ya sarƙeni, zuciya ta na tsananin ƙuntata rufe fuska ta nayi da tafin hannuna ina risgar kuka hayaƙin dake wurin sai ƙaruwa yake amma ina ruwa na tunda ba Asthma nake da ita ba? ji nayi fuska ta tafara ƙaiƙayi sosa wa nake idona sunyi wani mahaukacin ja,dena kukan zahiri nayi saidai na zuci... da ƙyar na samu ƙaiƙayin ya tsaya kallon ruwan gulbin da ruwan suka ɗan dena motsi sai kuma na kalli ranar data kusa shigewa,gobe na tabbatar da sabon baƙin ciki zan tashi babu kokonto a wannan sake cikowa da hawaye idona sukayi hayaƙin nan ya ƙara zama me kauri harma ba'a ganin wanda ke ɗayan ɓangeren dan kamar hayaƙin ya zama labule ne daya raba wurin..mayarda kallona nayi akan ruwan gulbin jin ana kiraye kirayen salla '' Kitten!" lallausar muryar shi ta sauka a kunne na..juyowa nayi naga mutum na fitowa ta cikin hayaƙin nan hannayen shi cikin aljihu da murmushi a fuskar shi kamar kullum,idon mu ya haɗu,jinayi zuciya ta na bugu da sauri kunya ta rufe ni kamar ƙasa ta haɗiye ni da sauri nayi ƙasa da kaina, hawaye na zuba ina wasa da hannayena a ƙarƙashin hijabi na anya kuwa bazan fara saka bra ba duk da har cikin raina na tsani wannan abun ƙarasowa yayi ya tsaya daga gefe na ƙamshin shi na cika hancina duk daya biyo ta cikin hayaƙin amma beyi ƙauri ba Murmushin dake fuskar shi ya ɓace ganin yanda idona sukayi jawur, yamutse fuska yayi kafin cike da damuwa yace '' Are You okay?" jina yi tambayar taban haushi na ɗago da jajayen idona a ɗan tsiwace nace '' nayi maka kama da wacce ke lafiya?" ƙiftawa yayi sau dayawa sai kuma a sanyaye yace ''yi haƙuri.. faɗa min Meya faru?" share idona nayi batareda na kalleshi ba nace '' babu komai... kawai ina...babu komai!" na faɗa a dake gyaɗa kanshi yayi yana kallona da idon nan nashi dake sani ina rasa natsuwa ta... ban san yanda zan fasalta ba amma wani irin kallo yake bina dashi wanda nake ji har cikin ƙasusuwana... turo baki nayi inaja baya nace '' wai kai baka gajiya da kallo? bafa nasan kallo!'' yar ƙaramar dariya yayi yace '' ni kam ina son kallon ki ABEEDAH...'' ya kira sunana da wani irin salo da yasa na kalleshi da idona da sukayi ja ƙwayar idona ya ƙara zama dark ash colored...murnushin shi ya ƙara faɗi har ina ganin haƙoran shi..samun kaina nayi dajin kunya na juya da sauri nabar wurin '' Bamu gama magana ba kitten!" ya faɗa yana ɗaga murya banma jishi ba nikam... Shafa fuskarshi yayi.. '' My little kitten..🐈" ya furta kafin ya juya yabar wurin yana tafiya a nutse.... +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 9. ... Babban darasi...🖊️ tsaye nake a tsakiyar gida ina mayarda numfashi idona cikin na Mama data gama alwala, nayi ƙasa da nawa '' daga ina kike?" ta tambaya tana miƙa min butar '' gulbi '' na amsa mata ina wasa da hijabina Asma'u ce ta fito da tabarma ta shimfiɗa ta kabbarta sallah,duk da kamar akwai Magana bakin Mama batace komai ba... ta wuce ɗaki ta ɗauko hijabi tazo ta kabbarta sallah kitchen na shiga na ɗebo gari na zauna nasha bayan sun gama sallah sunyi azkar,kiran mu Mama tayi ta zaunar damu tana mana nasiha me ratsa zukata,sosai nasihar ta tashige ni kuma zanyi amfani da ita insha Allah... washegari koda muka isa makaranta munyi latti hakan yasa aka yi mana bulala biyar biyar, muka wuce aji kuma nida Asma'u bamuyi magana ba Jadeedah ta lura da yanayi na lokacin break ta matsa min da tambaya babu yanda na iya dole na faɗa mata abinda Asma'u ta faɗa min plus ankoreni daga aiki sannan abincin mu ya ƙare, tayi mamaki sosai da komai dana faɗa,jakarta ta jawo ta ciro kuɗi kusan dubu biyar ta bani amma ni Abeedatu bana son yama kalmar 🍁🍁: Favours bana son favours gani nake kamar daga baya mutum zai min gori akan hakan '' rance nake baki idan kin samu sai ki biyani!" tayi saurin faɗa dan tasan tsaf zanƙi amsa... kallon kuɗin nake ina saƙe saƙe a raina,hannu na ta jawo ta tura min kuɗin '' Idan ban taimake ki ba bansan wazan taimaka ba Bee me yasa har yanzu kin kasa sakin jikin ki dani ne?" girgiza kaina nayi amma nakasa cewa komai,daga ƙarshe sai canja topic nayi '' Spelling bee nake so zan shiga Jay!" riƙo hannu na tayi cike da murna kamar ita zata shiga muka doshi office ɗin'' baki san irin farin cikin da nayi da jin haka ba,awwn,Bee ta fara girma!" Ta ƙarashe tana dariya,wani irin kallon na watsa mata '' da ban girma ba?" ɗan waro idonta tayi sai tace '' a'a ba irin wannan girman ba,kin kuwa fahimci cewa wannan shine karo na farko da kikayi initiating babban abu irin wannan? Oh my God Bee kin fara yarda da kanki!" ta juyo tana jijjiga kafaɗuna fararen haƙoranta a waje,ɗauke idona nayi daga kallonta..ni ban kawo duk wannan a rai ba da gaskiyar ta fa.. murmushi ne ya wanzu a fuskata kafin kuma na fashe da dariya tana taya ni naji wani irin farin ciki ya mamaye zuciya ta..da gaskiyar Jay D '' you know what?" Sai ta matso kusa tare da riƙon hannu na '' I'm proud of you...ina nufin ina alfahari dake!" Tayi saurin yimin bayani ganin ina harararta, sai kuma ta rungume ni..da sauri naja baya ina ɗan ƙaramin tsuki '' such a buzz kill!" ta furta fuska a haɗe...ganin kamar bata ji daɗi ba yasa nayi dariya mai sauti sannan na matso na rungume ta '' ni ina abinda yafi alfahari dake!" ina jin sautin ƙirjinta a nawa tsabar yanda take tayani farin ciki... muka nufi office ɗin event master, saida malamin yayi min kallon sama da ƙasa ya taɓe baki kafin ya tambaye ni sunana bayan yayi min registering ya bani wata farar paper Godiya Jay tayi mashi nidai bance komai ba saboda yanda yake min wannan banzan kallon sai naji farin cikina ya ɗan ragu '' come on,kada ki bari ya ɓata maki rai..'' sai tayi ƙasa da murya ta raɗa min a kunne '' nan gaba zance ya kalli madubi kafin yayi fuskarshi haka,kin kuwa ga yanda yayi kama da birin da aka shafawa lip stick da eye shadow a ɗuwawu? Harda yar powder nan ta jarirai ma!" Kafin in iya hana kaina na fara ɓaɓɓakar dariya...samun Jay d kusa dani babban magani ne lokacin da aka koma aji wasu mutane..yan mata dai kamar likitoci suka sa aka taro masu yan matan ss3 dukan mu,suka zaunar damu aji ɗaya suna mana Magana akan menturechon 🍁🍁: Menstruation! Ke Oti ɗin nan kin cika iyayi 🙄🙄 🍁🍁: Autumn koma menene, ,yan da zamu kula da kan mu lokacin jinin haila,yan mata da yawa sunji kunya akan wannan topic ɗin,amma nidai na ƙaru..daga baya suka bamu audugar mata..ni nama manta da sunan masana'antar tasu abu me muhimmanci shine nasamu pad dama wanda nake amfani dashi ya kusa ƙarewa idona ne ya haɗu dana wani malami shima dai danginsu macijin sari ka noƙe..ɗauke idona nayi suka sauka akan Macijin sari ka noken shima kallo na yake..mamaki nayi wannan ai abinda ya shafi mata ne to me maza sukeyi a wurin? tsuki naja Batareda nasan danayi hakan ba..duk aka wani juyo ana kallo na fuskewa nayi kamar bansan ni ake kallo ba... bayan an kammala wannan bayane bayanen muka koma aji,kowa sai maganganu suke '' wai a canja pad duk bayan awa huɗu hauka ake?" Muhsina ta faɗa, A'ishah ta taya ta faɗin '' sun raina ma kansu wayo kuɗin haƙo su ake ko kyauta zasu bamu?" '' hmm..Ni wallahi idan nasa wannan abu wuni nake dashi ina naga kuɗin canjawa duk bayan awa huɗu?" Hafsa ta ƙara '' ku gara kuma kuna da kuɗin siya,nidai idan ba kyauta aka bamu ba saidai inyi amfani da tsumma ato '' inji Labeebah '' Amma dai kunsan kasancewa da wannan abun a jiki na tsawon lokaci yana da illa ko?" '' pftt!! To illa ta nawa kuma? ai saidai ɗan baƙari!" muhsina taba Fateema amsa nida Jay D muka bisu da ido bamu ce komai ba ana tashi daga makaranta motar su jay d tazo ɗaukar ta,duk yanda tayi in shigo su rage min hanya naƙi dole ta barni .shagon su Saleh na tafi har yanzu baiji sauƙi ba dan haka bai dawo duty ba .shinkafa tiya huɗu na auno mana na haɗa da wake da taliya sai kuma garin kwaki duk da yanda bana sonshi amma yana iya? Daga nan na haɗo da magunguna da kuma kayan miya sannan na bar wurin raina a sake..kuma har yanzu Ban biya buba mai kayan masarufi kuɗinshi ba da Mama ta tambaye ni inda na samu kuɗin ban ɓoye mata ba..gyaɗa kanta tayi fuska ba walwala.. Asma'u tayi mana shinkafa dafe duka da wake ta kumayi mugun daɗi bayan mun gama cin abincin wanka nayi na shirya cikin kayan aiki na nayi masu sallama na fita... zuciya ta cike da nauyi na fara zageye zagayen gari ina neman aiki ido rufe amma har lokacin tashi daga aiki na yayi ban samu ba kusan kullum haka nake abun ya zame min jiki harna ma manta da wata rana za'a iya kamani..a ɗayan ɓangeren kuma ina nan ina koyon wannan mugun spelling Bee ɗin,a gida Mama ke koya min dan dama tayi daga primary zuwa secondary a makaranta Jay D, Asma'u bata da aikin yi sai gwale ni amma bana bi takanta.. oh itama ashe harda ita cikin masu yin spelling bee ɗin... Jay D dai Saida ta ƙara nanata min cewa Asma'u kishi take dani amma har lokacin banyarda ba kuma bazan taɓa yarda ba..duk bata da wani uzuri nayimin abin da take min lokacin da wata ya ƙare Mama nata zuba ido inkawo albashi sai nuƙu nuƙu nake..turnuƙe ni tayi akan saina faɗa mata gaskiya,cikin hawaye na sanar da ita an kore ni aiki bata ji daɗin ɓoye matan da nayi ba... Daga nan itama ta shiga neman aiki haka ma Asma'u na tsawon lokaci babu wanda yazo neman kitso da lalle wurinta... gaba ɗaya sai abubuwan ƙunci suka ƙara yimin yawa, Mama na matuƙar ban tausayi ina kuma baƙin cikin ganin ta tana yawo gida gida neman aiki ban ƙarajin cewa niɗin mara amfani bace sai da na farko da daddare naji Mama na kuka saman sallaya tana koro addu'oi... ji nayi wani sabon ƙunci da baƙin ciki sun mamaye ni dama na lura kwanakin nan kamar ƙasan idonta yayi duhu sannan idonta sunyi ja,na ɗauka rashin baccine ashe ba haka ba... da safe ma da muka tashi ɗan abincin dana kawo ya ƙare babu komai har gari, muka koma talakawa talaf talaf kullum sai Mama ta bamu haƙuri akan gazawarta amma ni a ganina nice na gaza... da wannan dalilin ɗan iska Macijin sari ka noƙe yayi ƙoƙarin lalata Asma'u da alƙawarin zai biyata Alhamdulillah kafin yayi mata illa na ganoshi har office ɗin principal nakai ƙarar shi duk da nasan ba wani abu za'a yi ba dan baban shi ƙaramin ƙwaro ne a gomnati... na ƙara shiga tashin hankali bayan na fahimci abinda Asma'u ke shirin yi kenan.. rayuwar mu ta wani irin ƙuntata musamman ni...damuwar su itace damuwa ta,farin cikin su shine nawa naga nawar ayi ayi wannan spelling bee ɗin in samu kuɗin da gidan in fitardamu daga wannan ƙangin rayuwar... wata rana aka tara mu ake faɗa mana anfasa spelling bee ɗin..ji nayi duniyata ta faɗo ta ruguje duhu ya sake mamaye ni..ɗan spelling bee ɗin dana ƙwallafa rai akai... Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,ranar nasha kuka kamar raina zai fita amma duk da haka ban dena karatun spelling bee ɗin ba sannan mu dukan mu bamu dena neman aiki ba har na tsawon wata uku rayuwar mu ta cigaba da gudana cikin ciwon rashi..da ƙyar muke samu muna ci muna sha,ba sau guda ba ina kama Mama tana kuka hakan ba ƙaramin karya zuciya ta yake ba..kuma yakan ƙara tunamin dacewa na kasa sharema ƙanwata da mamata hawaye...gefe ɗaya kuma ga self esteem ɗina dake ƙara raunana ƙila ma ya ƙate tass yanzu dan kamar idon kowa ya dawo akaina ne ko a makaranta haka idan ana bada misali sai ayi dani,,,harda ji nayi wata me suna Saddiqa tana faɗin '' abuna kamar na ƙananan yara..ita ta kasa ganewa koni macece ko akasin hakan...'' kasa tsayawa nayi inji ta har ƙarshe dan kuka ne yaci ƙarfi na meyasa bazan iya jurewa ba in basar kamar ban damu ba? ko faɗa muke daga sanda aka zagi halitta ta shike nan an gama wannan faɗan sai kuka da misalin ƙarfe huɗu ina zaune a ƙarƙashin bishiyar mangoron nan na kusa da gida saman benci.. hannu na riƙe da spelling bee ina karantawa saye da uniforms ɗina Dan banso in koma gida, jinginar da kaina nayi na jawo jakata ina duba pen dan inyi ticking kalmomin da ban iyaba, na ɗauki pen ina maki har na gama mayarwa nayi na sake jinginar da kaina ina tunanin yauma haka zamu kwana ciki rabbana? ƙamshin turaren shi ne kamar kullum ya shiga hancina kafin naji zaman shi kusa dani idanun shi akaina..zuciya ta tashiga bugu da ƙarfi... wani irin zafi ya turnuƙe ni daga ciki har waje,na rasa dalilin dayasa nake jin haka a duk sanda yake kusa dani,ƙila saboda yana da kyau ne kuma ni ga yarda nake '' Kitten...'' ya kira ƙasan maƙoshi,matse ƙafafuna nayi da idona kafin na shiga buɗe su ahankali ganin shi nayi zaune kusa dani dama kuma nasan yana kusa dani ɗin '' Meye kuma wani kichin can?" na tambaya gira ɗage batareda ya dena kallona ba murmushin shi a faɗaɗe yace '' kitten..na nufin jinjirar mage...'' wani irin tashi zaune nayi da kyau ina hararar shi a ƙufule nace '' oh,wato ni kake haɗawa da mage ko? nayi maka kama da mage ne?" wani irin lumshe idanunsa yayi tareda tallafo gefe da gefen fuskarshi da hannayen shi yana bina da kallon ƙasan ido da yasa zuciya ta neman fitowa ta baki yace '' Eh mana, musamman idanun ki... da yanda kike min tsiwa kullum idan mun haɗu..i like your eyes.. they're beautiful!" Ƙifta idona nayi cike da jin haushi nace '' na faɗa maka ban jin turanci ka dena min turanci amma baka ji!" dariya kaɗan yayi sannan yace '' Allah ya gafarci ranki ya daɗe..bazan sake ba!" ɗauke kaina nayi daga kallon shi '' Abeedah...'' ya kira irin yanayi da ban fahimta ba, juyowa nayi idona suka shiga cikin nashi a wani irin kasalance yace '' ina son Idanun ki... suna da kyau sosai!" Naji kamar shock ya ziyarci ilahirin gangar jikina,kamar yanda mutum zaiji idan ya taɓa wayar nepa...banan kaɗai ba harda wani wurin da bazan iya faɗa ba...'' a'udhu billahi '' na faɗa cikin raina ina ɗauke kaina daga kallonshi,wanda shi a wurin shi a bune me wuyar aiwatar wa dan dai ya cigaba da kallo na '' toh ko cirewa zanyi in baka?" Yana wani shu'umin murmushi ya jinginar da bayanshi ga bishiyar '' gashi ban zo da kayan aiki ba da mun gwada...'' sakin baki nayi da abinda ya faɗa...na ɗauke ido na daga kallon shi... '' muzama ƙawaye mana!" ya sake furtawa a kasalance to ko bacci yake ji? Ko dai shegantaka ce irin ta maza yake ƙoƙarin gwadawa a kaina? Na kalle shi da takaici a fuskata kafin na maƙe kafaɗa '' Pls!" ya furta da murya me zurfi ya cigaba da faɗin '' ko nawa ne zan biya just pls '' miƙewa nayi na ɗauki jakata shima ya miƙe batareda na kalleshi ba nace '' matsalar masu kuɗi gani suke kamar zasu iya sayen kowa...'' kallo na yake da damuwa jin abinda na faɗa shiba haka yake nufi ba sam '' ki fahimce ni..'' '' shhh..!" na katse shi ta hanyar ɗaura hannu na a baki na,ragema idona girma nayi sannan na ƙara da faɗin ''bakada kuɗin da zaka saye ni KHALIL!" na juya na tafi Yabi bayanta da kallo'' hmm fiesty little kitten! we're tangled" ya furta word by word sai ya juya yabar wurin dana koma gida ganin Mama da Asma'u nayi suna dawowa daga inda ban sani ba na matsa na gaida Mama ta amsa da tambayar ina nake..kawai na faɗa mata ina zaune ƙasan bishiyar mangoro.... washegari da muka tafi makaranta a mugun mugun bazata aka kwashe mu yan spelling bee muka tafi kwampetishon..babu wanda ya shirya cikin mu sai Zufa muke wasu harda hawayen tsoro Asma'u taso ta dizgani gaban mutane amma hakan bai yiyu ba lokacin da muka isa mun ɗauka round round ne abun idan an zubar daku wannan round ɗin zaku iya shiga a wani round a wani sati amma ba haka bane, round guda ne makarantu biyar harda tamu... Sannan kowa kanshi zai amsa mawa ba kamar yanda muka tsamma ta ba tashin hankali mun shige shi, musamman ni, ganin anata zubar da mutane masu kwanya ina gani danake daƙiƙiya? lokacin da aka kawo kaina jikina ya hau ɓari dole aka tsallake ni aka yima wa'yanda suka shirya... mafiyawancin su ko point guda basu samu. da aka kawo kan Asma'u harda wani ɗan iskan kallo tayimin irin na ki kalla ki koya amma sai Asma'u tayi dumkun kum da aka tambaye ta sai rarrabar ido take, tama ƙasa magana ko tsoro take ji ne?.. nice ta ƙarshe kuma Alhamdulillah na samu point uku cikin biyar... ba ƙaramin mamaki kowa da kowa yayi ba harni kaina daga ƙarshe akayi announcing result,gidan nan dai da nayi burin samar mana na sameshi harda ƙarin dubu ɗari biyu... Wasu yara daga wata government school sukayo na ɗaya da na biyu sai wata yarinya itama tayo na na uku ni nayi na huɗu exactly position ɗin da nake so.... kuma fa ba mata kaɗai bane akwai maza yan makarantar mu sun tayani murna ba kaɗan ba banda Asma'u data yi kamar zatayi kuka har na tanadi maganar da zan faɗa mata amma ganin yanayin ta yasa nayi shiru nan gaban jama'a aka mallaka ma kowa mukullin gidan dayaci kuɗi cikin envelope nayi matuƙar farin ciki harda hawaye shikenan matsalar mu taƙare... da muka koma makaranta dubu ɗari aka barni dasu, dubu ɗari kuma wa'yanda muka tafi tareda su dasu malaman dasu ka kaimu suka raba... da gudu na isa gida na faɗa jikin Mama na fashe da kuka, lallashina ta fara duk da batasan dalilin kukan ba saida na huta daga kukan sannan na faɗa mata aiko ta faɗi tayi sujoodush shukoor bawai dan abinda naci ba, a'a karo na farko dana nuna cewa niba daƙiƙiya bace.. tayi murna sosai tamin addu'a Asma'u kuwa kamar xatayi kuka Mama ta ɗauka Saboda bataci bane ta dinga lallashinta amma dalilin wani abune daban... makullin gidan na miƙa mata ta karɓa ta ajiye tareda kuɗinu '' yaushe zamu koma gidan Mama?" jim tayi kafin tace a sanyaye '' yaushe kuke so mu koma?" '' ko ranar Lahadi haka '' na bata amsa '' Allah ya kaimu!" washegari da muka tafi makaranta harda assembly aka tara don a karramani yan ajin mu sun kasa yarda wai tuwo tayi na huɗu da addu'a suka bini, lokacin munyi sharholiya duk dan su tayani jin daɗi... ranar da muka koma gida bayan mun gama cin abincin mun huta muka shirya muka tafi unguwar da gidan yake, unguwar masu ƙaramin hali ce dai kamar tamu amma hanyoyin wannan unguwar sunfi na tsohuwar unguwar mu kyau,daɗi da ƙari bishiyar kashuna ( cashew nut) daidai ƙofar gidan mu har tayi mashi runfa kaɗan... sauke mu me mashin yayi daidai ƙofar gida Mama ta biyashi kafin ta buɗe ƙofar da mukullin,zauren gidan anyi cementi a ƙasa haka ma bangon anyi plaster.. tsakiyar gidan m haka,ɗakuna biyu ne suna kallon juna sai dakalin da aka sama tiles a tsakani Sai kitchen da baye sosai gidan ya burge Ni , Asma'u kuwa a ƙuntace take har lokacin, Mama nata yaba kyaun tsakar gidan...cikin ɗaki Munyi mamakin ganin akwai komai da muke buƙata sannan harda baye Akwai gado da wardrobe da dressing mirror harda TV a ɗaya daga ɗakunan, sannan tiles ne a ƙasa ɗakunan suna da faɗi sosai komai sak... saidai ɗakin da nida zamu zauna ba tv... sosai Mama take samin albarka, bayan mungama ganin gida muka koma... nan na gane cewa, wasu lokutan zama me ƙoƙari bai wadatar ba idan babu aiki tuƙuru sannan mutum ya zama me tawali'u sai ya fita daga kunya,girman kai da jiji da kai bashi da amfani kuma mafi girman darasin dana koya shine kawai mutum na zama abunda ya yardar ma kanshi ne,ni ba daƙiƙiya bace na zama hakan ne kawai dan nayarda niɗin daƙiƙiya ce da gaske... +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 10... Kada ki jira ni Mama...🖊️ Ɗauke da farin ciki muka koma gida muna hira cikin adaidaita sahu, saida muka fara biyawa wurin buba mai kayan masarufi Mama ta biya shi kuɗin daya ke binmu ... Duk wannan ran Asma'u a cunkushe bata ce uffan ba cikin hirar mu '' wai Asma'u lafiya kike kuwa?" Mama ta tambaye ta bayan mun shiga daga ciki,da basarwa tace '' lafiya kawai dai banji daɗi daban samu komai ba..'' ta faɗa a fili amma cikin zuciyarta ta ƙara da faɗin ' Tuwo kuma ta samu gida da kuɗi bayan ni ya kamata ace nasamu wannan...' Murmushin yaƙe ta sakar mana sannan ta rataya hijabin ta da igiya ta ɗauki buta ta wuce baye Mama ta bita da kallo, zuciyarta na rawa dan idan ta gane kamar Asma'u kishi take kawai,bataso ko kaɗan ɗaya daga cikin yayanta ya zama me baƙar zuciya kuma dai tayi ƙoƙari sosai wurin ganin ta basu tarbiyya me kyau... infact ita ta fahimci yanayin Abeedah dan ita bata ɓoye abu..amma Asma'u..? '' Ya Allah gani gare ka..kaji ƙaina!" Ta furta da karyayyar murya kafin itama ta wuce cikin ɗaki Nidai tuni ina kitchen wurin neman abinci,amma babu A hankali muka fara sanar ma da mutane zamu tashi zuwa wata unguwa daban,wasu suna ƙorafin ba'a faɗa musu da wuri ba,amma dai mutane dayawa sunzo taya mu murna... Washegari da muka tashi akwai hadari sosai garin yayi duhu, a gurguje muka shirya dan zuwa makaranta.. kallon Asma'u nayi daga inda nake zaune inasa socks ita kuma tana sa rigar sanyin saƙa brown color kamar wandon mu,gaba ɗaya babu walwala a kyakkyawar fuskar ta ji nake kamar daga ni har ita mun canja kamar bamu ba... Miƙewa nayi na matsa kusa da ita na tsaya bayanta,ta cikin madubi ta kalle ni sai kuma ta ɗauke idonta tana parking gashinta '' Asm na miki laifi ne?" na tambaya murya a sanyaye idona suka ciko da hawaye batare da ta kalle niba tace '' ni na faɗa maki hakan?" Girgiza kaina nayi kamar itace yaya nice ƙarama Hula ta ɗauka tasa, ta juyo muna fuskantar juna '' baki yimin komai ba Tuwo kawai ina buƙatar lokaci ne,idan komai ya daidaita zan dawo!" Ta faɗa idonta ƙasa kamar tana ɓoye wani abun datake jin tsoron kallon idonta zai fallasa, wuce ni zatayi nayi saurin riƙo hannun ta zuciya ta ba daɗi '' jinake kamar bamu ba...kamar mun canja mun dena farin ciki kamar da Asm,dan Allah mudawo kamar da!" Na roƙa a matuƙar raunace Kallon hannun mu tayi kafin ta kalli idona da suka ciko da hawaye ,a hankali ta zare hannunta '' wasu lokutan abubuwa basa taɓa kasancewa kamar da Abeedah,canji...dole mu karɓi canji! Baza mu iya komawa kamar da ba... A halin yanzu dai!" Ta bani amsar kai tsaye hannayen ta cikin aljihun wondo '' Meyasa?" Na tambaya hawaye na sauka a fuskata '' Ban sani ba nima '' ta amsa batare da ta kalli idona ba ta fita daga ɗakin tabarni tsaye na share hawaye ,nake ji kamar Asma'u ta tsane ni yanzu kamar tana jin haushi na, zuciya ta takarye bazan taɓa kasancewa cikin farin ciki ba idan Asma'u bata farin ciki Matsawa gaban madubi nayi da ƙyar na iya kallon fuskata kafin sauran sassan jikina na sauke ajiyar zuciya WASU LOKUTAN MAFI WUYAR WANDA ZAKA SO SHINE KANKA... Na kasa son kaina ,na kasa ganin ƙimar kaina bare har inyarda dani kyakkyawa ce ko zan iya yin wani abu babba A duk sanda naji kamar na fara iya koyon yanda zan rayu da kaina,sai ingane cewa ba hakan bane... Taya zan so kaina bayan banida kyau? Bayan bani da diri? Bayan babu abinda zan iya tsinana wa na azo a gani? Bayan mutane suna faɗamin kuma nima ina yarda da maganganun su? Na fahimci cewa idan dai har ina so in rayu da kaina dole in koyi yanda zan yarda da kaina kuma kada maganganun mutane suyi tasiri a zuciyata amma niɗin mai rauni ce, bazan iya ba!! Bazan taɓa iyawa ba! Wannan tunanin ya haifar da mummunan ciwo a zuciya ta babu yanda na iya '' Abeedah ki fito ki karya ku samu ku wuce kafin a fara ruwa!" Naji Muryar Mama daga kitchen,saida naja dogon numfashi sannan nace '' Toh Mama!'' nayi hakan ne kada taji murya tata canja Hula da rigar saƙar sanyi nasa sannan na ɗaura hijabi na sama na ɗauki jakar leda ta na fito sandals nasa sannan na shiga kitchen ɗin,duk da yanda Mama ke kallo na ban bari idon mu ya haɗu ba Ɗaukar kunu nayi na juye cikin wata gora na jefa cikin jaka na fito daga kitchen ɗin '' mama yau ayi ɗan wake '' Asma'u dake tsaye bakin ƙofa ta faɗa '' kina da garin ɗan waken ne?" Mama ta tambaye ta, girgiza kanta tayi '' ba'a kwai abubuwa ba? Ki kawo in kai niƙa'' '' ke kin cika rigima wallahi'' turo baki tayi nidai ina daga gefe ina kallo,tashi mama tayi ta ɗebo rogo da dawa da wake da sauran abubuwan ɗan wake ta zuba cikin buhu ta miƙama Asma'u ta karɓa,Mama ta bamu kuɗin break sannan muka tafi Haka muke tafiya babu wanda yace komai cikin mu...daga lokaci zuwa lokaci nakan kalli gefen datake amma ita ko kallo na bata yi ba...sai da mukayi tafiya mai nisa sannan muka iso wurin sani me niƙa... Ta ajiye niƙan kafin muka ɗauki hanyar makaranta...sai ƙoƙarin janta hira nake ita kuma tana ban amsa ƙire ƙire daga uhmm.. sai a'a ba ragi ba ƙari...dole na nayi shiru badan maso ba Tare muka shigo makarantar da Jay d data fito daga motar su fuska a murtuke...tana ganina ta sakar min murmushin nan nata me haske dake sa wanda ke kallon ta shima yaji kamar yayi murmushi '' Bee! Ina kwana!" Ta faɗa bayan ta ƙaraso ta zagayo hannun ta a wuya na,nima murmushi na sakar mata na amsawa cike da murna '' lafiya lau! Now is my nat!'' na faɗa wai ni ina ƙoƙarin yin turanci Asma'u ta saki dariya ta juyo ta kalle ni '' ke Ni ina mamakin yanda akai kika kawo SS3 yar gaisuwar ma da turanci shine kike nan kina akwaɓa...wai now is my nat... hahaha waya ga now is my nat!" '' To sai uban me dan bata faɗa da kyau ba? Su turawan ma ai ba duka ne suka iya turancin ba ko? Idan har kina ganin rashin iya turanci wani babban abu ne to kinyi kuskure '..ƙasashe da dama da suka cigaba kamar korea ta kudu, China da japan dukan su basu wani cika jin turanci ba da Yaren su suke magana...that didn't make them any less... Kuma ita ma Abeedah ai ta iya yarenta dan haka banga dalilin da zaisa ki wani dinga sa tana jin ba daɗi ba!" Jay d ta faɗa a fusace..nidai nayi ƙasa da kaina raina ba daɗi Tsuki Asma'u taja tare da faɗin '' Toh uwar shiga shara ba shanu..waya kasa dake balle ki ɗauka? Kega advocate ko to sannun ki! Ita bata da bakin magana sai ke aku...kin wani bi kin cika mutane da zance caaaa! Pls badake nake ba so mind your business!" Wani lallausan murmushi Jay d ta sakar ma Asma'u '' ke nifa na daɗe da halbo jirgin ki Asma'u!.." dakatawa Asma'u tayi itama Jay d saita tsaya nima haka... Asma'u take binta da wani banzan kallo daga sama har ƙasa '' The truth is you're jealous of ABEEDAH! Kina fakewa da duk wannan gatsen da kike mata kina ƙara ƙuntata mata.. sannan kina jin daɗin ganin Abeedah cikin ƙunci... wannan kyaun da kike dashi bai hanaki jin insecurities ba..bai hanaki kishi ba..kina tsoron kada wata rana Abeedah ta fiki... Kada adinga maganar ta fiye dake..kada a zaɓeta sama dake... Kina ji inama ace kece da idonta sabida yanda mutane ke son idonta amma basu iya tunkarar ta sufaɗa mata saidai su biyo ta wajenki...nasan komai Asma'u...nasan komai!" Asma'u tayi tsaye wurin kamar an ɗasa ta, ahankali na ɗago idona na kalli Asma'u kafin na kalli Jay d data yi maganar zuciya ta ɗebi Asma'u tayo kan Jay d zata dake ta,aiko Jay D ta riƙe hannun ta wanka mata mari... '' JADEEDAH!!'' na kira da ƙarfi ina riƙe Asma'u data sha mari,hankaɗe ni Asma'u tayi hawaye nabin fuskarta ta ƙara yin cikin Jay D su biyun suka fara faɗa..kafin kasani sai gasu ƙasa... mutanen dake wucewa sukayi tsaye suna kallon yanda yan matan ke tumurmusar juna a ƙasa... Ganin Jay D a saman Asma'u yasa na finciko ta..na bangaje ta gefe... Ina huci '' KI RABU DA ITA KI ƘYALE MU!!! Ni tayi wa laifi bake ba dan haka ki rabu damu!!" Jay d ta kalleni da hawaye a idon ta amma batace komai ba,ita tana ƙoƙarin ta tsaya min shine ni kuma zan Gara ta a gaban mutane...ta cije leɓenta kafin ta ɗauki jakarta da aka yasar gefe ta kakkaɓe tabar wurin Mutane sai magana suke suna ƙus ƙus Asma'u dake kwance ƙasa na kalla '' Asma'u..'' na kira ina riƙo hannun ta,fisge hannun ta tayi ta ture ni,na faɗi wurin zaune '' Dalla rabu dani...ai ƙawarki ta fini muhimmanci kina ganin abinda tayi min tsabar munafuncir shine zaki wani zo kina jana..baƙar munafuka!!" Ta faɗi duk wannan tana kallon cikin idona,nata idon sunyi jawur..kamar yanda nima nawan sukayi ja Uniforms ɗinta suka ɓaci..haka ma nawa...nabi bayanta da kallo tana tafe tana kakkaɓe uniforms ɗinta Mutane babu wanda yace min ko sannu, ahankali na miƙe na fara tafiya sai kuma naji ban kyauta da abinda nayi ma Jay D ba...da sauri na ƙarasa aji amma sai naga bata zauna seat ɗin mu ba,ta zauna a seat ɗin masu kuɗin ajin mu... Dama babu malami sai hira suke suna dariya ko kallon inda nake batayi ba,ajiye jakata nayi tare da ɗaura kaina akan benchi... Inaji sanda English ya shigo aka tashi aka gaishe shi amma banda Ni dana cigaba da zama na Izini ya basu akan su zauna sannan ya fara rubutu akan Allah kafin ya juyo yana kallon yan aji yace '' Our topic for today is..Comrehension...'' sai ya fara bayani akan zai kira mutum biyu suzo su karanta shafi biyu cikin text book..kowa shafi ɗaya Ya kira wata yarinya mai suna Jameelah Umar... yarinyar tana da kunya Sosai,take tafiya kamar wacce bata da laka..yan ajin mu taliya suke kiranta...haushin yanda take tafiya yaji '' ke dallah kiyi sauri kina wani tafiya kamar nazo gidan ku taɗi!" Nan da nan tayi ƙasa da kanta hawaye suka dinga fita da sauri da sauri kuma tayi tsaye wuri ɗaya ta kasa cigaba da tafiya yan aji sai kallo suke kowa ya nutsu '' ke zoki sa ƙafar ki a ƙasa!" Ya bata umarni yana nuna mata bakin ƙofa, yarinyar ta kasa motsi sai kukan ta daya ƙara ƙarfi tana sheshsheƙa tana sa hijabinta ta goge hawaye fuskarta tayi jawur Saboda fara ce bafulatana '' dan ubanki bakiji ko..idan na same ki wurin sai kin yaba ma aya zaƙinta!" Ya faɗa a harzuƙe tareda ɗaukar wata zungureriyar bulala ya ƙaraso inda take ji kake sha! sha! sha! Yana ta auna mata buloli ta ko ina yarinyar takai ƙasa tana shille shille kamar kifin da aka fitar daga ruwa tana faɗin '' dan Allah malam kayi haƙuri'' shiko kamar mara imani Saida taba kowa dake ajin tausayi wallahi '' tashi ki wuce ki zauna banza jaka!!" Ya faɗa yana huci harda share zufa..dukan sauran yan aji sun tsorata sanda ya ɗago da jajayen idonshi yana kallon su..sai kuma idonshi suka sauka akan Tuwo data ajiye kanta akan desk '' wacece ke mun kwana a aji?!" Ya tambaya yana huci kamar wannan shine mafi girman laifin da akayi mashi Da sauri na tashi zaune..idona sunyi ja dan dama duk wannan dramar da ake ni kuka na nake sharɓa... Hijabina nasa ina goge fuskata... '' Ke zonan!" Muryar shi kamar ana surhen ƙanzo ba daɗin ji ko kaɗan... Ahankali na tashi kaina ƙasa ina zuwa inda yake..sai bina suke da ido kamar na basu tausayi '' Gani!" Na faɗa tsaye a gabanshi..hararata yayi daga sama har ƙasa sannan ya miƙa min littafin '' karanta mana wannan shafin!" Zaro ido nayi bakina na motsi hakama jikina na ƙyarma...yanda yan ajinmu suke kallon kallo na tabbatar sun hangoni a ƙasa kamar yarinyar nan... '' Amsa mana!" Ya daka min tsawa..hawaye suka shiga rige rigen sauka a fuskata Karɓar littafin nayi sannan na juyo ina kallon su,shi kuma ya tsaya baya na..murya na rawa na shiga karatun da hausa '' Comfri henshon... T-hey..le'a' der and t- le'ad.. On' ce uupon a ti me,t..here was...'' ''.innalillahi wa inna ilaihi raji'una...ke dan ubanki turanci kike karantawa ko Hausa!!!" Yanda yayi maganar ba ƙaramin razana nayi ba..da sauri na juyo hakan yasa nidashi mun game dan kusa kusa dani yake... Da sauri nayi saurin matsawa baya suko yan aji suka yi wani '' Hah!!" Dan kawai jikin mu ya haɗu..toh ai dai bada gangan bane..sai ƙus ƙus suke '' laa wallahi Abeedah ta rungume malamin nan! '' ɗan iska laifin shine shifa ya wani tsaya bayanta..dama abinda yake son yi kenan! Nidai jikina babu abinda yake sai rawa ganin banzan kallon da yake jifa ta dashi sai kuma ya daka ma ajin tsawa '' Silence!!" Sukayi tsit...a fusace ya zari bulala yayo kaina na fara ja baya kuka na,na ƙara ƙarfi indai ni kaɗai za'a daka wallahi bana so ko kaɗan '' zonan!" Ya furta yana matsowa '' dan Allah kayi haƙuri...'' nidai sai jin saukar buloli na fara daga kowane sashe..sai ihu nake... Ina murje murje dan bulolin ba wasa... Sai da yayi min ligya kamar Jameelah sannan ya daka min tsawa yana faɗin '' tashi ki bar wurin nan sakarya daƙiƙiya!" Jiki ba daɗi na miƙe ina tafiya ina sharar hawaye.. Allah yasa matane mu babu namiji ko ɗaya bayan malamin Jay D na kalla kafin in isa seat ɗina ta ɗauke kanta... Ina zama aka fara ruwan sama da ƙarfi, huci mugun Mutumin ya saki kafin ya kwashe kayan shi yabar ajin mu '' a gaskiya mutumin nan ɗan iska ne,Ni dama tunda na fara ganin shi bai min ba wallahi!" Hameeda ta faɗa tana harare harare Sauran yan aji suka biye ta murya sama saboda ruwan basa bari aji abinda ake faɗa...nidai na cigaba da kuka na ,nayi tunanin Jay d zata zo ta lallashe Ni amma babu ita babu alamun ta Har sanda aka tashi break kuka nake sannan kuma ruwa basu dena sauka ba Masu sayar da abubuwan ciye ciye suka dawo barandar ajujuwan mu dan babu wanda yayi yunƙurin fita, idan malamai suka kama mutum ribiti suke mashi kamar sun samu jaki.... '' tuwo bani kuɗin tara na!" Naji Muryar Asma'u akai na..na ɗago kaina naja hijabi na zuwa gaba sannan na ciro kuɗin cikin Safa na miƙa mata..ta karɓa ta fita batareda tace komai ba... '' Abeedah kiyi haƙuri, wallahi sai Allah ya isar maki!" Inji A'ishah tana shafa baya na... '' Ni wallahi yanda malaman nan suke dukan mu ba imani kada suje su mana illa '' wata mai suna Afrah ta faɗa tana gyara glasses ɗinta Sai mutane suka fara bamu haƙuri nida Jameelah..nayi mamakin yanda basu zauna suna mana dariya ba,dan dai abin dariya wurin yan ajinmu baya kaɗan Da ƙyar na iya dena kukan.. sai kuma na kalli sashen Jay D na ganta tana ta raha da yan uwanta masu kuɗi sanda muka haɗa ido wani kallo tayi min kamar nida ita bamusan juna ba...naji kamar zuciyata tabar ƙirjina..sai nayi ƙoƙarin basarwa amma na kasa jiki ba ƙwari na miƙe na isa inda take '' Jay D...ina so muyi magana...dan Allah!" Sai sauran yara masu kuɗin suka kalle ni cike da rainin wayo amma banda ita,kawai ina son ƙawata ne... Ganin bata juyo ba kuma batace komai ba..ga mutane sai kallon mu suke yasa na fara jin kunya na kamani... Gani nayi ta miƙe ta fita waje sai nabi bayanta sauran kuma suka cigaba da harkokinsu wasu na gulmar mu '' Jay D...'' '' babu abinda ya rage da zamuyi magana akai Abeedah...kin ban kunya kin watsamin ƙasa a ido...nida nake ƙoƙarin yi maki faɗa tunda ke baki iyawa da kanki shine zaki dakamin tsawa a gaban mutane kina shatamin layi ko? Akan yarinyar da nake ƙoƙarin nuna maki ita wacece nake ƙoƙarin kare ki...ba matsala na fahimta jini yafi ruwa kauri kije keda ƙanwarki kawai nima sai in kama kaina...nasan matsayina yanzu ai!" Tayi maganar cike da ƙunar rai... Tana ƙifta ido kada ta fashe da kuka,ni na kasa riƙe nawa Kafin in yi magana '' me kuke anan shegu cikin ruwan nan salon ciwo ya kama yarinya taja ma iyayen ta bala'i zaku wuce ku koma aji koko?" Wani malami ne wanda ake kira da ƙashin miya yayi maganar.. mutumin sai tsawo kamar zanƙalalo ba ƙiba Shigewa Jay D tayi ina biye da ita kaina a ƙasa, ta koma ta cigaba da zama da group ɗin masu kuɗi tabarni ni kaɗai...sai naji kaɗaici ya dabaibaye ni da ƙunci da raɗaɗin zuciya musamman idan na juyo naga kowa tare da abokin shi....Ni kaɗaice zaune a nawa seat ɗin kamar wata dodo ashe ban san nan gaba wanda zan ɗanɗana sai yafi haka ba Ba'a Dena ruwa ba sai lokacin sallah, nan ma nayi ƙoƙarin yima Jay d magana amma sai ƙawayenta suka tafi da ita bansamu dama ba... kuma itama da kanta bata so tayi min magana...nasan abinda nayi mata ba ƙaramin jin zafi tayi ba kuma zata daɗe kafin ta sauko...amma dan Allah bazata iya dawowa mu cigaba da zama a seat ɗin mu ba? meyasa zata barni? dafe ƙirjina dake motsi da kuka nayi,tare da ɗauke idona gefe kada aga hawaye na Sai kawai nayi alwala na shige masallaci..bayan antashi makaranta ma tafiyar ta tayi tabarni, Asma'u kuma wai sun shiga wani debate da za'ayi tsakanin makarantar mu da wata private school...wata yar ajinsu ta faɗa min Sai kawai na tafi gida ni kaɗai duk ƙunci ya kamani... Sanda na shiga na iske Mama tana tuƙa tuwon masara... Tana ganin fuskata ta gimtse dariya '' A'a tuwo yau babu sallama? Baki ga takwaranki nake ba...?" Turo baki nayi inaji kamar in jefar da wani abu ko in gwara kaina da bango... Sai kawai na haɗiye ɗacin danake ji na shagwaɓe fuska nace '' Ni bazanci ba!" Ɗage kafaɗa tayi '' tuwo dai nan nayi meci yaci wanda bai ci ya bari....'' Innalillahi..duk sanda Mama ta faɗi wannan haushi nake ji kamar kamar.... Idona suka ciko da hawaye ƙirjina na sama da ƙasa...ina hura hanci... Fitowa tayi daga kitchen ɗin tana share gumi tace '' ina Asma'u?" Na hankaɗa labule na shige ɗaki ina faɗin '' wai debate suke a makaranta" '' toh niƙan data kai wa zai ɗauko?" Mama ta tambaya tana biyo bayana '' inta dawo sai taje ta ɗauko ai..'' '' a'a wallahi baza'a bar min niƙa awaki suyi wasa dashi ba maza canja kaya kije ki ɗauko min niƙa na!" Mama ta faɗa da bada umarni..hawaye na farayi zuciya a ƙuntace...nayi faɗa da Jay d, Asma'u bamu shiri..mama tayi tuwo....yanzu kuma inje in ɗauko niƙa ciki empty..kai! gaskiya ranar yau baƙinta yayi yawa Mama tatafi tabarni,zane na ɗaura na fito na ɗebi ruwa cikin bokiti na faɗa toilet nayi wanka... Bayan na fito nasa doguwar riga green color da hijabi ruwan toka da hula ita ma haka sai nasa takalmi nazo wurinta karɓar kuɗin niƙa Ɗari biyu mama ta miƙo min inata ture turen baki...bata kula niba '' ƙila ma in ɓace!" Na faɗa ina karɓar kuɗin '' Yoh in kin ɓace ai inada Asma'u tuwo..sai muyi addu'a Allah yasa duk inda kike kina lafiya!" Ta faɗa cikin halin ko in kula,maganarta tasa naji numfashina ya ɗauke,dama na sani babu wanda ke sona..toh mai zai sa a soni? me nake dashi? dariyar ƙunci na saki tare da sa ƙarshen hijabina ina goge hawayen da suka fara sauka '' dama nasan ba'a so na,amma fadar hakan a fili ya ƙara tsaurara ciwon a zuciya ta!" Mama ta kalle ni ido waje ganin ina hawaye sai kuma ta matso da nadama a fuskarta kafin tace wani abu nayi gaba ina faɗin '' kada ki jirani Mama dan baxan dawo ba!" ta biyo bayana tana lallashina amma bana ko jinta har na fita, mutane irin mu ba'a masu magana irin haka koda da wasa ne zamu iya jin ciwo mai tsanani,(could hurt harder than intended)kuma wannan maganar zata cigaba da zama damu,dama can bama kallon kanmu da ido mai kyau,wannan maganar sai ta ƙara ƙarfafa wancan zargin namu kawai Oti ki kiyayi abunda zaki faɗawa mutum koda da wasa ne,zai iya kasancewa a gareki ba komai bane amma su kuma wannan maganar zata zauna dasu tasa su dinga tunanin ta dare da rana suna masu tsananin baƙin ciki dan a gare su abunda aka faɗa ɗin gaskiya ne koba haka ba 🍁🍁: NOTED ABEEDAH 🥹 Ina tafe ina sharar hawaye,taya Mama zata faɗi haka! Ba daɗewa na kawo wurin sani me niƙa..kuɗin niƙan naira ɗari ne,na biya na ɗauki niƙan dake da bala'in nauyi..ga hanyar duk ruwa sun taru ba kyau duk inda mutum ya tsoma ƙafa sai ya taka kashi ko ya jefa ƙafa cikin kwata... Har yanzu kuma gari bai washe ba..kamar akwai hadari...kowane juyi sai mutum yaga gungun maza zaune idan mutum yazo wucewa su bishi da ido..kuma Allah ya gani hannu na dana sa ina tare hijabina tagaba ya fara ciwo ga ɗayan dana riƙe garin dashi shima ya gaji Ga yunwa data ƙara salsale min ciki..Ni Abeedahtuwo naga rayuwa wallahi! '' Yan mata ina zuwa ne!" Wani gaye dake tsaye bakin wata motar data ga duniya ta gode Allah tsakanin leɓenshi wani siririn karan taba...bakin nan yayi baƙi ƙirin haka ma idonshi sunyi ja...sai wasu banzayen ƙananan kaya daya ke saye dasu,cikin shi kamar na me ciki wata uku..yana wani shafawa nidai yayi min kama da ɗan iska wallahi... Kuma tunkaro ni yake yana jimana..yan mata me ruwan tokan ido...ji nayi kuka na shirin ƙwace min gashi babu mutane a hanyar fa... Na ƙara sauri inayi ina juyowa...da naga abun yaci tura sai kawai na saki garin na kwasa da gudu shima biye dani a tamanin '' wayyo Allah..mutane a taimake ni...kwarto!!!" Na faɗa da iya kar muryata ina ƙara ƙarfin gudu na... '' ke ki tsaya mana magana nake so muyi!" Wai Magana yake so muyi shine yake bina da gudu haka Haka muka dinga kwasar gudu kamar wasu mahaukata gashi na gaji, wallahi idan a tambaye ni bansan inda nake sa ƙafa ba Sai kwararo kwararo muke bi...Ni ban masan ko yana nan biye dani ba, kayan jikina duk sun ɓaci da jar laka saboda yanda slippers ɗina ke ɗibar lakar yana watsa ta sama zuwa ga kayana! Sulɓucewa nayi na faɗi ƙasa tim, fuska farko cikin wasu jajayen ruwan laka kaya na da jikina suka ɓaci...cikina ya bugu da ƙasa... slippers ɗina suka bar ƙafafuna...naji wani arnen ciwo yana ratsa Ni... Mutanen dake tsaye wurin suka juyo suna kallona suna magana ƙasa ƙasa '' Subhanallahi! Ashsha tashi tashi...'' wani mutumi ya faɗa tare da miƙar dani...sauran mutanen suka fara min sannu mafiyawancin su maza ne..naji kunya ta kama ni...da ƙyar nake iya tsayuwa '' sannu yan mata baki ji ciwo bako?" Wani mutum daban ya tambaya gyaɗa kai nayi ina sakin wani marayan kuka Sai kuma na shiga tafiya batareda na tanka masu maganganun suba..ko tambayoyin su Sai da nayi tafiya mai nisa na gane cewa ashe har na fito babban titi...inda akwai tituna da yawa sannan saman gada nake ina hango ƙasan gada...da gine gine daga nesa... Gaba da baya titi ne...babban titin jahar kano... Sai kuma rana ta ƙwalle da wani uban haske da zafi...ga sauran hadari ... Ban kosan inda nake ba.. Innalillahi wa inna ilaihi raji'una... Dama na faɗa ma mama ƙila ɓacewa zanyi amma wallahi dana ce bazan dawo ba da wasa nake ...wayyo Allah...na cigaba da kuka na ina tafiya daƙyar kaya na na ɗiga da ruwan datti..idona sunyi mahaukacin ja jan ajiyar zuciya kamar zan shiɗe Babu abinda yafi tada min hankali irin kasancewar bansan inda nake ba..kuma bansan inda zani ba...kuɗin dake hannuna sun faɗi ko takalmi babu a ƙafata Mutanen dake wuce wa saman gadar sai kallo na suke...kuma har lokacin hannu na banyi ƙasa dashi ba a ƙirji..ga tsoro daya cika ni kuma ban san ko ƙarfe nawa ba A nan gida mama ganin har ƙarfe huɗu kuma tuwo bata dawo ba, hankalin ta ya tashi ,kada dai ace Abeedah ta ɗauki maganar ta har zuci, zata shiga bayi taji sallamar Asma'u '' Salam alaikum!" A gaggauce Mama ta amsa sallamar tace '' Ma'u zoki bi man bayan Tuwo,tun ɗazu dana aikata ta ɗauko niƙa bata dawo ba..'' da damuwa a fuskarta tayi maganar Ajiye jakarta Asma'u tayi daga bakin kitchen '' ƙila baiyi niƙan ba sai yanzu yake yi ko ƙila mashin ɗin ya samu matsala...bari in tafi yanzu!" Ta faɗa tare da shiga kitchen tasha ruwa sannan ta fita Mama ta sauke ajiyar zuciya '' karfa ki jirani Mama baxan dawo ba!" Maganar tuwo ta maimaitu a ƙwaƙwalwarta gabanta ya faɗi... '' zaki dawo Abeedah kuma zan baki haƙuri..kidawo kawai!" Ta faɗa cikin ƙarfafa kai kafin ta shige baye zuciya da nauyi +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 Free pages 11. ... there's life in art...🖊️ Mama na Safa da marwa a tsakar gida Asma'u ta shigo kamar zatayi kuka Mama ta tsaya cak tana kallon ta, '' Mama wai yace tun ɗaxu ta bar wurin shi bayan ta karɓi niƙan...'' ta ƙarashe da hawaye '' Innalillahi wa inna ilaihi raji'una... ya Allah ina ɗiya ta tashiga ne..ka karemun ita..'' Mama ta faɗa tana ƙoƙarin riƙe kukanta.. idonta sunyi ja fuskar ta a ƙuntace kamar zuciyar ta... sai kuma ta shiga ɗaki ta ɗauko hijabinta ita da Asma'u suka fito daga gidan suka shiga neman tuwo..duk wanda ya gansu ya tambaye su, Mama take musu bayani da karyayyar murya cewa bata ga Tuwo ba sai su dinga taya ta nema... Ni kam cigaba nayi da zurarawa kuma har lokacin bansan takamammen inda nake ba,idan na tambayi mutane..sai suyi ta bani mabanbantan wurare wani yace airport road,wani yace ɗorayi.. wani yace..wani yace... Hawaye sai zuba suke daga idona ba tsayawa..ga yunwa ta fara ƙarar da ƙarfi na harda ƙishirwa '' wayyo Allah..ka kaini gida da wuri.. Mama ta damu nasani...dan Allah ko cikin addu'oin dana ke ne da baka amsa ba,ka amsa wannan na yafe sauran...'' na faɗa cikin kuka irin sosai sosai ɗin nan...kukan motocin nan dake wuce wa zut zut ba ƙaramin tayarmin da hankali suke ba..danji nake kamar zasu make ni... Zaune suke cikin wata baƙar mota me tinted glasses.. Khaleel a baya saye da riga blue da jeans shima blue...ga jacket black color daga gefen shi,hannun sa saye da silver wrist watch... Askin kanshi low cut lips ɗin shi kamar ya shafa lipstick Hannunshi riƙe da waya yana video call da wata baturiya cikin deep voice ɗinshi yace '' i missed you too Leona... Ji nake kamar inyi Fika fiki in ganni America!" Ya ƙarashe yana shafa kanshi haɗe da kashe mata ido '' Awwnn... Abraham i love You so much...'' ta faɗa tana blowing kiss...ya wani taune leɓenshi yana mata kallon ƙasa ƙasa Daga seat ɗin gaba driver ne saye da fararen uniforms..daga gefen shi kuma gayen nan ne..kamar koda yaushe saye yake da facemask... Sai baƙar T shirt mai dogon hannu an rubuta' VOID' da kuma jeans baƙi, ya ɗaura rigar sanyin saƙa baƙi asama...jet black hair ɗinshi ya zubo har saman girar shi..hunter eyes ɗinshi kafe akan littafin drawing dake hannunshi yana drawing ɗin wata mace...his vertiver scent filled the car kamar wanda yayi mugun abu yake ɓoyewa da ƙamshin turare tsabar ƙarfin turaren,ga wani mysterious aura emanating from him ... Ɗago idonshi yayi yaɗan kalli gaban motar can ya hangi wata yarinya na tafiya duk tayi daƙun daƙun sai kalle kalle take kamar tana ƙoƙarin tsallaka titi...ɗauke idonshi yayi ya mayar akan sketching pad dake cinyarsa ya cigaba da zanen shi... Khalil na dariya ya juyar da kanshi gefe..daidai Abeedah ta juyowa da fuskarta..his heart skipped,duk da baiga fuskar ta da kyau ba,zai iya rantsewa itace! '' za muyi magana anjima babe!" Ya faɗa cikin wayar yana gyara zaman shi ya taɓa gayen dake zaune a gaba '' ROM,waccan ba Abeedah bace?" Ya tambaya ido waje yana sake kallon bayan su dan har sun wuce ta da deep baritone voice ɗinshi yace '' why are you asking me?" ya dawo masa da tambayar batareda ya ɓamɓare idonsa daga sketch pad ɗin ba,Khalil ya fisge littafin '' come on don't be heartless!" Banza dashi Roman yayi yana kallon cinyarsa that was now empty,ya watsa ma Khalil wani banzan kallo as if he had stolen his life ''you have five...'' ya ɗago fararen yatsun shi guda biyar ya cigaba da faɗin ''just five seconds to return my book!" Ya ƙarashe his hunter eyes dangerously cold,cold enough to slice the air quietly Khalil ya ajiye masa littafinsa inda ya ɗauka for peace to reign '' Allah ya baka haƙuri!" Roman bai sake kallon Khalil ba ya cigaba da abinda yake Khalil ya Kalli driver'' Habu kayi U turn mu koma wurin yarinyar can!" '' toh oga!" Driver'n ya faɗa kafin ya canja hanya... Mayarda bayanshi Khalil yayi ya jingina da seat yana tapping ƙafafunsa restlessly Ina tsaka da tafiya naji anata wani peef peef da mota bayana..haushi naji ya ƙara ƙume ni wallahi..kamar in tsaya in zazzage musu abinda ke raina amma ban tsaya ɗin ba saboda rana ta faɗi kuma babu alamun zan kai gida da wuri...zuciya ta sai bugu take da ƙarfi idan fa ban isa ba? Idan fa ƙara ɓacewa nake batareda na sani ba? Hawaye na da suka tsaya suka shiga rige rigen saukowa da sauri... Sai kuma kuka ya biyo baya ga wannan banzar motar dake bina da peef peef kome na tsare musu ban sani ba ! Tsayawa nayi na rarume wani dutse na juyo a fusace na jefa a glass ɗin gaban motar duk baƙin ciki da tsoron da nake ji na sauke shi akan su '' dalla wai meye haka kun wani bikun ishe Ni da peef peef me na tsare muku ne eh? Duk wannan hanyar da aka bar muku bai ishe ku ba sai kunzo kuna cika min kunne da wani peef peef can...an san kuna da mota dalla ku matsa kuba mutane wuri....'' ina Magana hawayen takaici na zuba kamar pamfo na tsani wannan abun da masu mota suke su wani su dinga damun mutum da odar mota... ...'' amma yarinyar nan...'' Kallon da Khalil ya jefa mashi yasa driver Habu yayi shiru...buɗe motar yayi ya fito ya tsaya yana kallona da tambaya a fuskar shi '' Kitten!!" Ya kira da mamaki,nima ƙifta idona da suka yi ja kamar gauta nayi dan in tabbatar shine..shi ɗin ne amma me yake anan? '' what happened?" ya tambaya tsaye dab dani,share hawaye na nayi da magiya nace '' dan Allah ka kaini gida!" da sauri na tura hannu na cikin hijabina tare da matsar dashi daga jikina kunya ( shame and embarrassment) ya rufe ni..ya gani? meyake tunani? ko in tambaye shi? Nayi wannan tunani tare da ɗago idona dake ƙasa suka shige cikin nashi dake kallona kamar yana ƙoƙarin fahimtar abinda ya faru..ko dai yana duba wani abu daban ba😡 wannan tunanin yasa naji haushin sa ya cika ni '' toh ko a kawo maka kujera sai ka zauna ka kalle ni da kyau?" Nayi maganar a fusace,dan nidai a ƙwaƙwalwata ƙirjina yake kallo eh... 🍁🍁: ke Abeedah mutumin dake shirin taimakon ki? Abeedah: dan zai taimake ni sai ya gama kalle ni? 🍁🍁: bafa abunda yake kallo ba kenan Abeedah: toh nidai abunda raina ya ayyana min kenan 🍁🍁: your insecurities really run deep Abeedah:🙄🙄 koma me hakan ke nufi to gaskiya ne..ba zaki gane ba Autumn sai idan ke ce a wannan yanayin... juyawa nayi na fara tafiya bayan na faɗi hakan haushinsa na ƙara hauhawa a raina manta kawai dama koda yaushe ni ina sama ma kaina maslaha batareda kowa ya taimake ni ba,yanzu ma zan koma gida..Ni ɗin mai dogaro da kai ce yanzu ma zan dogara... jin an riƙo hannu na yasa na tsaya na juyo '' You have a fiery temper,yi haƙuri muje in kai ki gida!" zare hannu na nayi daga nashi ganin yana murmushin nashi sai kuma na wuce shi kamar motar mu ce da kanshi ya buɗe min ƙofar har zan shiga naji Muryar me fes mas yana faɗi cikin wata ƙatuwar murya mai cike da ban tsoro duk da muryarshi ba ɗaga ta yayi ba '' Are You kidding me? Does this look like a dumpster?" '' Rom,have some humanity in you...'' Khalil ya faɗa da rashin jin daɗi a murya shi,ni kam sai rarrabar ido nake tsakanin su, ƙwaƙwalwata na loading a 360 ina ƙoƙarin fahimtar mai suke cewa amma dai wannan mai fes mas ɗin na fahimci cewa mugun bawa ne wallahi,sai gardama suke, hankali na ya ƙara tashi ganin dare na yi '' idan taimako take buƙata,ka tarar mata abun hawa mana yakai ta har gida...akan me zata shigo tayi contaminating iskan cikin motar... '' aha! an faɗi magana da yaren da nake ji..wai kuma mugun bawa ne ya faɗa..dama yana jin Hausa? hausar ma irin ta kanawa..taɓ ɗi jam amma anyi ɗan gulma kuma sai na gano ma'anar wannan kalmar kntamineyt daya faɗa..kuma Oti kada kiyi ƙoƙarin gyaramin yanda ya faɗa na faɗa ehe ƙafafuna suka fara rawa da naga rana ta faɗi duka, hawaye suka fara sauka daga idona,na juyo na kalli Khalil,tattausan hannun shi ya kawo a fuskata yana share min hawaye,na daskare dan banyi tsammanin hakan ba '' don't worry kitten,zan kai ki gida yanzun nan!" gyaɗa kai nayi jiki a sanyaye '' pls Roman!" Khalil ya roƙa,wai ashe sunan mugun bawa Romo..Romon kaza? Romo bai sake cewa komai ba..hakan yasa Khalil sakin lallausan murmushi kafin ya taimaka min na shiga cikin motar sai shima ya shigo...kafin in zauna yayi saurin ɗaukar rigar dake wurin ya shimfiɗa min sosai yake kusa dani kamar zai rungume ni,ba ƙaramin takura nayi ba '' zauna!'' Ya matsa daga kusa dani sai lokacin na samu na saki numfashin da bansan na riƙe ba amma kafin in zauna direban ya figi motar da ƙarfi...sai gani daɓas akan cinyar khalil hannun shi a ƙirjina 😳😳...irin daga ni harshi ɗin ba muyi tsammanin abunda ya faru ba,saura kaɗan numfashi na yabar gangar jikina 🍁🍁: what the freaking pregnant duck!!!! Abeedah: ke dai tayani jimami ɗazu ina ƙorafin yana Kallona sai kuma ga hannunshi daɓe daɓe a wurin wayyo kunya!!! a bazata na faɗo saman shi.... Kai!!!..wani irin kunya ne ya dabaibaye ni irin wanda ban taɓa ji ba,naji kukana na shirin dawowa sabo..da sauri na miƙe daga jikinshi na zauna inda yayi min shimfiɗa hawaye na sauka a hankali ta coner idona naji inama ace ban shigo motar ba,har lokacin ina jin hannunsa a wurin duk dana sauka daga jikin shi,na kasa yarda da abinda ya faru,ya taɓani fa... '' ka dinga abu a hankali mana!" Yayi maganar wa driver '' yi haƙuri yallaɓai!" Ya furta '' kada ki damu bada daɗewa ba zaki koma gida!" jinjina kaina nayi ban yarda na kalle shi ba,ko me yake tunani a ranshi? '' me kike yi anan?" Ya sake tambaya,ko kaɗan bana son magana dashi da alamu shi bai ma san abinda yayi ba,sai dana ɗago na zabga mashi harara ina turo baki nace '' Mama tace in tafi..in ɗauko mata niƙa shine wani mutum me shan taba ya biyoni da gudu... Yasa na ɓace!'' na ƙarashe da goge fuskata da hijabi na Sosai fuskar Khalil ta nuna baiji daɗin abinda ya faru da niba,kawai sai naji hannun mutum a kafaɗa ta yana shafawa alamun lallashi '' it's okay...'' yafara da turanci..wani irin ɗagowa nayi na harare shi da jajayen ido na sai kuma na kaɓe hannun shi ina ji kamar zuciyata na kamawa da wuta,ai tunda ya taɓa ni duk da nasan bada gangan bane na dinga jin haushin sa kenan 🍁🍁: ai shine,akan me zai taɓa forbidden fruit 🍓 🤣 Abeedah: ni dai kada ki kaini inda ban jeba toh! 🍁🍁: 🤣🤣 '' lallashin ki nake fa!" ya rausayar da kanshi gefe,ji nayi kamar in make shi da shegun idon nan nashi kamar na akuya '' toh idan ana lallashin mutum sai akace a dinga taɓa shi?" duk da nayi ƙoƙarin kada in nuna fushi na kasa dannewa,ji nake kamar ana yayyafawa zuciyata fetur '' yeah.. that's how it's done!" yayi maganar murya ƙasa,bakin shi a washe dan ya fahimci ya ƙular dani sosai ɗauke kaina gefe nayi ban sake cewa komai ba shima sai yayi shiru Duk wannan maganganun da muke Romo fa yana jin mu amma kamar babu shi a wurin ko juyowa baiyi ba shi uban jiji da kai zan koya mashi hankali kuwa Da misalin ƙarfe shida da rabi muka iso anguwar mu, ganin mutane da yawa tsaye bakin ƙofar gida da Mama da Asma'u yasa gabana ya faɗi... Ina gani daga inda nake zaune Mama tasa ƙarshen hijabinta tana goge hawaye...Malam Hassan maƙobcin mu da maman Amal na bata haƙuri... Asma'u daga gefen ta itama dai alamun tayi kuka... '' inda mutane zaka tsaya!" Na faɗa cike da damuwa,motar na tsayawa na shiga ƙoƙarin buɗewa in fita amma na kasa,dole Khalil ne ya miƙo hannu ya buɗe min,da sauri na tare ƙirjina kada ya sake taɓawa bada gangan ba,tunda dai na dawo gida bazamu wanye lafiya ba Na fita da gudu kamar zan kife ina kiran '' Mama!! Mama!!" Mutanen suka fara rabewa suna bani hanya Mama ta miƙe da jajayen ido '' Abeedah..'' ta kira itama tana zuwa inda nake Asma'u biye da ita,muna cimma juna na faɗa jikinta tare da sakin kuka itako sai hamdala take Mutanen wurin na tayata...duk da wasu yan gulmar kayan jikina suke kallo da kuma motar dana fito daga ciki '' ina kika tafi Abeedah? Kin samu a damuwa!" Mama ta tambaya tana ɗagoni daga jikin ta..ina kuka na shiga faɗin abinda ya faru... saboda bana so mutane su fara cece kuce da yamaɗi ɗi anga Abeedah ta fito babbar mota Sai mutanen suka mayarda kallon su wurin Khalil dayayi tsaye wurin batareda sanin abinyi ba...ya sakar musu murmushi yana shafa kanshi '' ina yini...!!" Ya faɗa da murmushin kunya..sai suka fara amsawa suna sake yimashi godiya..matan kuwa duk da akwai masu aure sai duba shi suke dan da gaske ba ƙarya gayen ya haɗu nima na sani sakina Mama tayi sai Asma'u ta riƙe ni itama tana kallon Khalil Har ƙasa Mama ta kai tana kwararomashi godiya da ruwan addu'oi...ɗan zaro idonshi yayi awkwardly kafin shima yakai ƙasa yana amsa addu'oin ta yana sosa kai.... Slowly ya ɗago hunter eyes ɗinshi da suke blank babu wani expression a fuskar shi datake cikin mask... blankly yake kallon taron jama'ar wurin, idonshi akan Mama dake yi kamar zata mayarda Abeedah cikin cikinta ''Perché una madre ama sempre il proprio figlio,E ti amo allo stesso modo E ti amo allo stesso modo, qualunque tu sia Romano.(saboda uwa tana son ɗan ta,kuma nima ina sonka a duk yanda kake Romano)" maganar ta fara amsa kuwwa akanshi kamar alarm ɗin daya ƙi mutuwa... Driver ya jinginar da kanshi a glass Yana kallo shima,sosai abin ya ƙayatar dashi,a hankali mutane suka fara raguwa Sai Mama ta miƙe shima ya miƙe ya kalle ni '' Toh Mama sai gobe zan zo insha Allah!" Ya faɗa yana kallo na '' Allah ya kawo ka lafiya!" Mama ta bashi amsa da farin ciki Ya jinjina kanshi tare da kallo na da murmushi a fuskar shi '' Bye kitten!" Yayi min alama da bakin shi ..a karo na farko nima sai na sakar mashi murmushi ina mashi bye bye haushinsa ya ɗan ragu a raina ganin yanda ya girmama Mama Ya juya ya shige motar su har lokacin muna kallon juna sai da motar tabar wurin... mutanen suka watse muma muka shige gidan mu '' Asma'u ɗaura min ruwa a wuta in ma Abeedah wanka!" Zaro ido nayi jin abinda Mama ta faɗa ina kallon ta...sai na shagwaɓe fuska '' Mama kimin wanka kuma?" Nayi maganar rai ba daɗi '' Yoh ko kin wuce in maki wankan ne?'' '' gaskiya kam! Gabjejiya da ita zaki mata wanka?" Asma'u dake shigewa kitchen ta faɗa...Mama bata saurare muba,ta fara cire min hijabina da lakar ta bushe akai Sai tace inje baye in jirata..kaini Abeedahtuwo yaushe Mama zata dena wannan al'adar Tata?ƙila ma tunani take wani abu ya faru! Ina tsaka da wannan tunanin ta shigo riƙe da ruwan zafi...amma ban iyarda cire kayan ba,akwai yar ƙaramar singlet data tsaya rabin cikina da kuma pant Sai nayi ƙasa da kaina ganin yanda ciki na yayi flat naji inama ace ya cigaba da zama a haka... '' Mama dan Allah..babu abinda ya faru kuma zan iya yin wankan da kaina dan Allah!'' na roƙe ta da magiya...ta tsare ni da Ido na tsawon lokaci kamar me lissafin wani abu kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye min ruwan ta fita Asma'u tayi zaune tsakar gida zugum.. zuciyar tana kai kawo...waye gayen nan na ɗazu? Taga alamar da yayi ma Abeedah yace '' bye bye kitten '' dama sun san juna ne? Ina tasan zazzafan gaye haka.. kyakkyawa dashi son kowa ƙin wanda ya rasa...ita ya dace ace sun fara haɗuwa ba Abeedah ba! '' Me Asma'u ke tunani haka?" Inji mama dake fitowa daga ɗaki ta ɗauko tabar ma,jin anfara kiraye kirayen salla kuma ƙasan ma ta bushe '' babu komai...kawai ina tunanin...dabadan Allah ya kawo shi ba,da mai zai faru da tuwo!" Tayi ƙarya lafiya lau duk da wani sashe na maganar ta gaskiya ne amma ita babban tunanin ta,ya zata haɗu da guy ɗin...wallahi ta kamu da sonshi...' Abeedah ta san shi' Wani sashe na zuciyarta ya ayyana sai itama ta samu dabara,tasan yanda zatayi Bayan ta samu mafita ta miƙe da murmushi a fuskar ta,ta ɗauki buta tayi alwala dan yin Sallah Da ƙarfe bakwai mu duka muna zaune,kaina saman cinyar Mama dake shafa min ruwan shinkafa tana tambaya ta...kamar wata..uhmm... 🍁🍁: Detective Yauwa kamar detective,har nayi wanka lokacin na sauya kaya zuwa farar riga doguwa... Asma'u daga gefe tana rubutu a littafin ta '' Shi wannan waye shi? Wanda ya kawo ki gida!" Mama ta tambaya...sai Asma'u tayi cak da rubutun da take '' Oh... Khalil...sunan shi Ibrahim,a maina hotel muka haɗu yana ta so mu zama ƙawaye amma nidai naƙi yarda...'' Mama ta ɗanyi jim kafin tace '' meyasa baki yarda ba? Yana da wani aibu ne?" Girgiza kaina dake kan cinyarta nayi ina turo baki nace '' Mama fa suna da kuɗi..kuma nidai bana son masu kuɗi wallahi!" Mama batace komai ba ta cigaba da yimin abinda take '' kenan kun daɗe da sanin juna?" Asma'u ta tambaya daga gefe tana kallo na '' ban sanshi ba...'' '' yake kiran ki kitten kuma baku san juna ba?" Ta sake magana..na ɗan ɗago idona na kalleta " ya kira ni da kitten?taya ni banji ba sai ke mai kunne an uku ko?" sai tayi shiru Bayan sallar isha'i sosai ake kwararo sanyi kuma babu nepa....amma akwai taurari da wata ga iska mai daɗi yake share mana saurayen dake gantsarar mutum daga zaran ya zauna...Mama take sanar dani wai wayanda suka bamu kyautar gida sunzo sun kawo takardun gidan duk da su hankalin su ma baya jikin su alokacin..nemana shine gaban su,ta ƙarashe da faɗin '' na ɗaga batun komawa sabon gida sai sati na sama!" Idona har sun fara lumshewa nikam...cikin muryar bacci nace '' Allah ya kaimu!" Ta amsa da Ameen '' Mama yace zai sake zuwa gobe ko?" Na tambaya ina nufin Ibrahim '' haka yace!" Inji mama... lumshe idonta Asma'u tayi dajin daɗi aranta gobe zatayi shiga ta musamman dan jan hankalin shi Nidai daga Maganata ta ƙarshe ban sake cewa komai ba, da safe bayan munyi salla mun zauna har rana ta fito muka fito mama ta wuce kitchen ni kuma na fara sharar tsakar gida Asma'u tana wankin toilet ''.Mama naso ace gidan nan akwai bishiya cikin shi wallahi!" Nayi maganar ina tattare sharar mama ta taɓe baki '' dan ki dinga hawa ko?" Na ƙyalƙyace da dariya jin abinda ta faɗa Muka cigaba da hirar mu..nidai dama ba makaranta zanje ba...bayan munyi kari nayi wanka nasa riga da zane atamfa shuɗi..na ɗaura zanen wani gefe yafi wani tsawo..idan ina tafiya sai ƙafafuna su dinga kwarewa '' ke dai Allah ya miki magani..zanen ma baki iya ɗaurawa ba!" Mama dake zaune kitchen tana rigar shinkafa ta faɗa da alhini..nikam dan mutum bai iya ɗaura zane ba,a ganina ba wani abu bane amma mama ta dinga mita... Kuɗi taba Asma'u dake saye da baƙin hijab tace taje ta siyo kayan miya..karɓar kuɗin tayi tana faɗin '' ni zanyi miya!" Zuwa nayi na zauna bakin ƙofar kitchen ɗin '' Mama wai wannan abincin da ake faman yi na menene?" Mama ta ɗan kalleni '' na tarbar yaron arxiƙi ne,dabadan Allah ya kawo shiba da bansan inda kike ba Abeedatu!" Ta ƙarashe tana jinjina kai kamar tunanin rasa ni na haddasa ma zuciyarta babban ciwo Nayi murmushi'' ashe kina sona? Ba kince kina da Asma'u ba?" Na tambaya da hawaye a idona..duk da ba ciwo nake ji a zuciya ta ba '' wasa nake..dukan ku inason ku,idan wani abu ya faru da ɗayan ku Bansan yanda zanyi ba... Kiyi haƙuri idan abinda na faɗa yasa kinji ba daɗi!" Mama ta faɗa tana cigaba da aikinta Sosai naji ta ban tausayi...sai na share hawaye na na gyaɗa kai Har zanyi magana'' NEPA!!!" Na faɗa da ƙarfi tare da miƙewa daga bakin ƙofar kitchen ɗin ina taka rawa da maɗaukakin farin ciki a fuskata...Mama ta girgiza kanta da murmushi a tata fuskar itama Faɗawa ɗakin nayi na kunna tv nasa tashar yan china daidai ana fim ɗin kashi of lof ...( Ashes of love) Tun ina kallo har bacci ya ɗauke ni...da ƙarfe ɗaya mama ta tayardani inyi sallah,bayan na gama naci abinci Asma'u nake kallo data zage tana kwalliya tasa irin kaya na sosai tayi kyau kamar in sace ta in gudu...' idan fa yaga tafi ki kyau..ya Dena kula ki?' wannan tunanin yasa naji abincin da nake ci ya fita raina...ba lallai na faɗa ba..amma ina son shi..bawai sona soyayya ba a'a irin dai kamar idan kana da aboki...sai abokin ya haɗu da wani wanda yafika sai ya dena kula ka... irin ciwon da mutum zaiji a wannan lokacin shine nake ji a raina yanzu... '' Asma'u kina da kyau meye na kwalliya kuma? Ina zaki haka...'' Tayi murmushi tana kallona ta cikin madubi tace '' kishi kike ne? Babu inda zanje so calm your heart...'' jin amsarta ban sake cewa komai ba da gaskiyar ta,a karo na farko nayi kishi da ita. ba irin kishin dana kasa tantancewa akan ko ina jinshi ko bana jinshi ba.... wannan na tabbatar da kishin ta nake ji...kishin kyaun ta...inama ace nima ina da kyau har haka? Idan Khalil ya ganta zai dena kula ni? akwai lokuta da yawa da mutane suke Dena kula ni daga lokacin da suka ga Asma'u Har yanzu ban dena jin tsoron sake faruwar hakan ba..wai yaushe ma shi Khalil ɗin ya dame ni? Yaushe na damu dashi har haka? ' saboda shine namijin daya fara kulaki duk da munin ki!' zuciya ta tunatar dani '' ya dai? Da gaskiya ta kenan? Kina gudun kada yaga yar kyakkyawa ya dena kula ki ko?" Sai nayi ƙasa da kaina.. murmushi me kyau tayi kafin ta taso ta tsaya bayana.. numfashinta na dukan wuya na...muryarta da kaifi bakinta saitin kunne na tace '' ki tafi ki ɓoye...wani wuri kafin ya iso...ki hutar da kanki daga zama ' invisible ' idan ina a wuri! Babu wanda zai taɓa lura dake Abeedah...ke ɗin..zaki cigaba da zama a inuwata!...'' ko wace kalma daga bakin Asma'u tana yanka zuciya ta kamar wuƙa mai kaifi ko fiye da haka.. hawaye suka fara ƙone idona... zuciyata tayi nauyi...abincin dana ɗiba cikin cokali na kasa kaiwa baki Ɗis! ɗis! Hawayen suka fara sauka da mugun sauri...sai tasa hannun ta tana share min...da wani irin abu da bansan meye shi ba a muryar ta tace '' ba ina cutata maki bane..kawai ina faɗa maki gaskiya ne! Ke akoda yaushe kina faɗin..Gara mutum ya faɗa maki gaskiya komai ɗacinta abinda nake kenan Abeedah!!kada ki riƙe ni a zuci!" Ta ƙarashe maganar tana ja baya kamar batace komai ba '' d..d..da gaskiyar ki...zai fi..idan na bar wurin!" Na faɗa cike da rashin wayo..Ni Abeedahtuwo ban san sanda zan koyi tsaya ma kaina ba..kullum saidai inta yarda da abinda mutane suka faɗa min... ajiyar zuciya na sauke tareda ajiye abincin gefe na share hawaye na Ina nan zaune ina tunane tunane har ƙarfe huɗu sai mukayi sallar la'asar tare..bayan mun gama azkaar Mama tace '' har yanzu yaron nan bai zoba...kodai sun fasa xuwa ne?" Da sauri Asma'u tace '' kai Mama..taya zai fasa zuwa bayan yace zai zo? Ƙila Saida yamma..'' '' Allah yasa! Wai ina zaki da kika sha wanka haka?" Idon Asma'u suka fito jin tambayar mama zuciyarta na bugu tace '' Uhmm...dama..uhmm yau naso inje gidan su ƙawata rakkiya amma sai na fasa yanzu...'' na ɗago idona ina kallon ta jin ƙaryar data shuta amma bance komai ba Sai na miƙe '' Mama ina zuwa zanje gidan su sale... Tun ranar da muka tafi tare ban sake zuwa duba shi ba...'' na faɗa.. gaskiyar shine kawai ina so in tsere kafin su iso kamar yanda Asma'u ta faɗa Mama zatayi magana ta rigata faɗin '' gaskiya ya kamata ki tafi...kai zumunci baice haka ba Abeedatu...yaron nan abokin kine fa '' tayi maganar tana girgiza kai..sai Mama bata ce komai ba.. hijabi na na canja zuwa baƙi sannan na fita Ba gidan su sale na tafi ba...bayan gidan mu..inda gulbin nan mai koren ruwa na tafi na tsaya.. kamar hawaye na sun san cewa na kawo inda nake jin nafi samun sirri suka fara zuba ba ƙaƙƙautawa ban san dalilin da yasa kalaman Asma'u game da khalil suka yimin ciwo ba... Ina kallon ruwan ina kuka.. fuskata ta ɗanyi ja kamar idona...na daɗe a wurin duk lokacin da nayi niyar komawa sai wata zuciya ta kwaɓe ni daga ƙarshe na duƙa wurin ina dambe da zuciya ta kafin na samu ƙwarin guiwar miƙewa na fara barin wurin A hanya na gamu da sale dake tafiya da sandar guragu da guntun wando a jikinshi kamar zanyi dariya amma saina haɗe '' ke bakida mutunci ai..yayi..'' '' yi haƙuri..rayuwa ta shamin kai wallahi..yanzu ma gidan ku nayi sai gashi mun haɗe..'' na faɗa ina haɗa hannayena alamun ban haƙuri sai da ya harare Ni sannan yace '' Naji ance tashi zakuyi?" Gyaɗa kaina nayi '' amma sai wani sati..'' Ya ɗan kalleni kafin ya sauke ajiyar zuciya yana gungurawa yace '' toh Allah ya sada mu da alkhairi harna fara kewarki!" Sai nayi dariya jin yace yana kewata '' ni asuwa ɗan wake a hotel?" Yayi murmushi tare da faɗin '' bazaki gane ba...sai anjima'' daga nan yayi gaba Ban wani mayarda hankali akan yanayin shi daya sauya ba nayi gaba nima Ina kawowa wurin bishiyar mangoro naga yara da almajirai da zungureriyar sandar su suna takalar mangoron da yaƙi ya faɗo..gasu da yawa Suna gani na sukayo kaina cike da murna...sosai nake jin daɗin yanda suke min..nasan dacewa suna zuwa wurina ne kawai saboda wani abu da suke so...amma hakan bai hana naji daɗin cewa wani yana ganina da muhimmanci ba... Akwai wani karin magana na turawa da na riƙe 'it feels good to be wanted...' ma'ana akwai daɗi sanin cewa kai ma ana sonka Dan haka sai na yi gaba suna biye dani har muka iso wurin, takalmina na cire,na tattaro zane na dake shirin barin jikina Allah yasa yaran ƙanana ne ai,sai da nayi kalle kalle kafin na hawo bishiyar ina tsinko masu mango ɗin suna rububin kamawa ___ Zaune yake saman bonnet ɗin motar hannun shi riƙe da sketching pad...kayan jikinshi shadda baƙa fuskarshi sakaye da mask kamar kullum Jet black hair ɗinshi yake shimmering kamar mai yayi yawa a ciki hasken ranar yana bashi wani red glow....gashin ya zubo har saman girar shi..ƙamshin shi ya gauraye wurin duka... hannun shina motsi da pencil saman farar paper he was deeply focused ya fara jin hayaniyar yaran Slowly ya ɗago hunter eyes ɗinshi da suke kamar a lumshe yana kallon su...sai kuma ya hangi Abeedah dake faman jefo musu mangoro...sai data tabbatar kowa ya samu kafin ta fara saukowa yaran suka haɗu suna mata godiya..da murmushi a fuskarta take kallon su... Ɗauke idonshi yayi ya cigaba da drawing ɗinshi feeling so irritated da yanda yaran ke ihu Ya kalli zanen da yayi na ƙaramin yaro playing in a meadow cike da farin ciki da annashuwa ga wata mata a bayan shi tana ɗaura masa flowers a saman lallausan gashinsa “C’è vita nell’arte(There's life in art)” ya furta slowly.. +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 12. ...Ina ƙaunar ki...🖊️ Khalil ne zaune saman tabarmar da aka shimfiɗa masa tsakiyar gida..can gefe nesa dashi Mama zaune da hijabi har ƙasa.. Asma'u zaune kusa da ita babu hijabi ɗan kwalinta ma ya zame.. gashin ta ya bayyana sai wani kallo take bin Khalil dashi duk da kanshi na ƙasa '' to kaci abincin mana '' Mama ta faɗa da murmushi a fuskar ta...har taji ya kwanta mata a rai bayan hirar da sukayi yanzu '' Toh Mama..'' ya bata amsa tare da motsa hannun shi dan ya zuba abincin dake cikin kula,da sauri Asma'u ta tashi zaune zanen ta ya kware tana faɗin ''bari in zuba maka'' hannun ta ya sauka anashi dake riƙe da marfin idon Mama suka ƙanƙance ganin abinda Asma'u tayi Khalil ya ɗago idonshi suka sauka a nata dake kallon shi flirtatiously sai ya ɗauke hannun shi murmushin fuskar shi ya ragu.Mama batace komai ba sai ma ɗauke idonta da tayi kamar bataga abinda ya faru ba,stylishly Asma'u ta iyarda zame ɗan kwalinta sai yayi kamar bada gangan ba,iska ya fara kaɗa gashin ta, Khalil yayi wani wurin daban da idonshi sai Mama tace '' Abeedah ta tafi nan maƙota..ban san Meyasa bata dawo ba har yanzu...'' murmushin fuskar shi ya dawo,bayan Asma'u ta gama zuba abincin ta koma wurinta ta zauna..'' na gode..'' ya faɗa da cool voice ɗinshi daya ƙara kashe ma Asma'u zuciya,komai nashi kyau yake mata ƙamshin turaren sa babu kamar shi muryar shi mai daɗi fuskar shi mai kyau... The typical Every girls' dream... murmushi take zubawa foolishly Mama ta miƙe tare da faɗin 'ina zuwa',tayi ma Asma'u alamun ta biyota amma Asma'u tayi kamar bata fahimta ba Ahankali Khalil ke cin abincin idonshi na yawo ko ina banda wurin Asma'u data kafe shi da ido tana murmushi like a love struck fool'' abincin yayi daɗi? '' ta tambaya cike da murna politely yace '' Eh,yayi daɗi.Kitten ceta dafa?" Cikin nuna rashin fahimta tace '' waye haka kuma?" rashin jin daɗi bayyane a muryar ta dan ta gane Abeedah yake tambaya,ajiye abincin gefe yayi '' Abeedah The fiery kitten..My kitten?" Yanda Asma'u taji yana kiran Abdeedah da wani irin possessiveness kamar ita ɗin tashi ce yasa taji sense of dread ya lulluɓe ta,is he blind? Baya ganinta ne? tayi murmushin yaƙe tareda faɗin ''' pftt! Ai tuwo bata iya dafa abinci ba!gishiri da yaji take bankawa. Kuma abincin baya daɗi shine yasa Mama ta hanata dafa abinci a gida...'' tana Maganar da dariya tana share gashinta da iska yake jawowa zuwa fuskarta da salon jan hankali,sai yayi murmushi yana kallonta '' kyakkyawa..'' ya ayyana aranshi '' kina da kyau..'' Asma'u taji farin ciki ya lulluɓeta... after all he noticed, ta tabbatar bazai dinga neman Abeedah ba tunda dai tafi Abeedah'r kyau and he's not blind is he? ...farin ciki a fuskar ta ya kasa ɓoyuwa,sai kuma taji kunya ta kama ta...sai blushing take. Khalil bai sake kallon inda take ba after the compliment '' na gode'' ta faɗa dajin nauyi,ƙirjinta na tsananin bugu da ƙarfi,baice komai ba sukayi shiru Asma'u ganin idan ba batun Abeedah take mashi ba,bazai yi magana ba yasa ta dinga jan shi da hira, tana faɗa mashi abubuwa game da Abeedah amma tana sako kanta itama tana nuna mashi qualities ɗinta masu kyau,sosai Khalil ya mayarda hankali yana saurare turned out his kitten had exceeded his expectations '' Mutanen Unguwar mu sun ɗauka Abeedah mayyace saboda kalar idonta har suke faɗin idan da daddare kaga mage mai ido ruwan toka to Abeedah ce!!!" Yar ƙaramar dariya mai daɗin sauti Khalil yayi yana kallon Asma'u ya ɗan zaro ido '' really?" Jin ya mata turanci sai tayi murmushi ta mayar mashi da turanci '' of course..!" ____ Ahankali nake tafiya tunanuka sun toshe min ƙwaƙwalwa ban san yanda zanyi ba. daga nesa na hango wata ƙatuwar mota baƙa pake agaban gidan mu ga wani mutum zaune a sama saye da shadda baƙa,hannun shi riƙe da abinda na tabbatar ƙila biro ko pensir da kuma ƙaton littafin saman cinyarsa fuskar shi saye da face mask,tun kafin in ƙarasa na tabbatar da waye,bugun zuciya ta ya ƙara ƙarfi na tsaya cak ina tunanin ko in koma? Ko In cigaba da zuwa? bansan ya zanyi ba jiki na yayi sanyi, numfashi na ya fara fita da sauri sauri naji cinyoyina sun fara gumi 'ki tafi ki ɓoye wani wuri kafin yazo,ki hutar da kanki daga zama ' invisible 'idan ina a wuri...' Maganar Asma'u ta shiga yawo akai na sai na juya zan koma numfashi na na fita da zafi da sauri kuma... Har nayi taku biyu sai kuma na dakata ''Khalil bai taɓa damuna ba kuma ba zai taɓa damuna ba,idan har shima kamar sauran,zai Dena kula nine dan yaga wacce tafini kyau yayi da kyau '' na faɗi hakan cike da tabbatar wa wani irin ƙwarin guiwan daban taɓa jin irinshi ba yana zuwa min Sai naja dogon numfashi na saita yanayi na sannan na fara tafiya a hankali..sai naji ni ina nishaɗi,kamar an sauke wani ƙaton dutse dake hange da zuciya ta. na kalli kaina cike da rashin yarda wai yau nice ke tafiya batareda na saka hannu na gaban hijabi ba bayan nasan akwai wani namijin da zai iya kallo na yaga ƙirjina a shafe Ya Allah na kasa yarda da hakan tafiya nake uhm 🍁🍁: Freely ina tafiya freely ba damuwa ba fargaba Tun kafin in ƙaraso ƙamshim turarensa ya mamaye min hanci mai,ga iska mai sanyi rana ta zama ja dan wurin ƙarfe biyar da rabi ne Ɗan kusa da shi na tsaya ba sosai ba,ina ƙare mashi kallo,yasan da tsayuwata a wurin amma ban kai ya kalli sashena ba shi ɗan abunda bance ba '' to ko dai koroma bairo kake da ita?" nayi tambayar ina riƙe haɓa ido na har lokacin a kanshi,bai yi kamar yaji abinda na faɗa ba ya cigaba da zanen shi,har wata zuciya tana ayyana min ƙila kurma ne ko kuma Hausar ce bai fahimta ba amma ai ranar ƙatuwar Hausa ya sako ko? '' hala robar mai ka juye ma gashinka? naga yana ta ƙyalli kamar anyi hatsarin motar mai a ciki!" nan ma bai kulani ba kamar ni fatalwace da ba'a iya gani,ɗaura hannu na nayi a ƙuguna haushin sa ba cika ni da sauri,dan rainin wayo ko kallona bazai yiba ko? Toh wallahi yau sai ya magantu, Na matso kusa,pencil ɗin da yake amfani dashi saman farar paper na dungure na ɓata mashi zane, ya tsaya da abinda yake amma bai kalle ni ba nasan so yake yayi magana ko yayi min ihu amma tsabar jin kai ya hanashi sai kawai ya buɗe sabon shafi ya fara sabon drawing taune leɓena nayi na gyara tsayuwata kamar wadda ta samu aikin yi inata mashi magana amma yaƙi tankani '' in gani mai kake zanawa'' nayi maganar ina leƙa littafin amma sai yayi saurin rufewa batare da ya kalleni ba,kamar wanda akayi wa dole da garmahon Muryar shi yace '' Bar wurin nan!" na tsaya a ƙame kamar ƙanƙara ya juyo a hankali har idon mu ya haɗu, idonshi manya suna da tsananin duhu da kwarjini na ɗan ji shakku ya shige ni amma bazan tafi ba sai na matsa ina ƙara kallon shi da fes mas ɗinsa baƙi mai ƙwarangal,na tabbatar mummuna ne wallahi dan fararen mutanen nan basu wani cika kyau ba,bare shi da farin shi ya mugun ɓaci sai kawai na fashe da dariya...muryarshi ta bala'in ban dariya..kai abu kamar ana surfa ƙanzo a wannan lokacin ban damu da yanayin da hijabina yake ba ajikina ina jina Free ba'a takure ba kamar koda yaushe. ya ɗauke idonshi ya sake buɗe littafin shi yana cigaba da zane,da ƙyar na iya dena dariyar sannan nac '' dan Allah bari inga abinda ka zana, ko dai baka iya zanen bane shine baka so in gani?" nayi maganar ina miƙa hannu da niyar karɓar littafin yayi gefe dashi,yana kallon gaba bai kalli inda nake ba,taɓe baki nayi na kalli sumar shi naji kamar in taɓa,sai na saci kallon shi '' in taɓa sumar ka?'' batareda ya kalle ni ba yace '' try it and kiss your wrist goodbye...ki bar wurin nan!" Ya faɗa da deep baritone voice ɗinshi Turo baki nayi haɗe da sauke ajiyar zuciya ban fahimci turancin ba amma dai nasan try na nufin mutum ya gwada abu ko? sai dai yanayin muryar shi bai yi kama da abinda yake nufi ba kenan,na fara tafiya kaina a ƙasa,juyowa nayi naga yayi nisa cikin Abinda yake na rugo da gudu na damƙi sumar shi a hannuna na murza,shegen laushi ne ita, da wani daddaɗan ƙamshi dake tashi a mugun razane ya juyo amma har na saki na ƙara gaba da gudu ina dariya ya sauko daga saman motar yana huci yama kasa magana Na faɗo cikin gidan ina ta dariya kamar mahaukaciya sai nakai hannu na saitin hanci shinshina, na sake kwashewa da dariya Asma'u dake zaune dab da Khalil su biyun suka juyo suna kallo na da ganin yanda fuskar Asma'u tayi nasan bata ji daɗin dawowata ba. na kalli Khalil dake min murmushi amma ni ban mayar masa ba '' Ashe kin iya dariya kitten kullum idan mun haɗu kiyi ta hantara ta'' ya furta idon shi a kaina,tsuke fuska nayi na taɓe baki na ƙaraso ciki Yanda Asma'u ke kallona ya tabbatar min da cewa bata so in zauna a wurin sai kawai na wuce ciki ina faɗin '' Mama na dawo'' Mama ta fito saye da hijabi '' daga kije ki dubo mutum shiru kamar an aiki bawa garin su?" Na marairaice fuska '' Mama akwai abinci? Yunwa nake ji!" Girgiza kanta tayi '' baki ga kinyi baƙo ba?" juya idona nayi nace '' yunwa ta rufe min ido bana ji bana gani'' murmushin Khalil ya faɗaɗa '' Ka gani?ita tuwo kullum abinci kaɗai ne a gabanta.,duk da kazo duba ta ko gaishe ka batayi ba!'' ta faɗa da sauke ajiyar zuciya kamar nayi wani babban laifi '' shine yasa she's my kitten'' Asma'u taji haushi ya ƙumeta '' Babu abinci amma yanzu nake shirin yin tuwon masara...'' '' Innalillahi wa inna ilaihi raji'una...Allahuma ajirni fiy musibati wa akhlif ni khairan Minha ..Mama na roƙe ki dan girman rabbi kada ki mana wannan mugun abun..dan Allah!'' na zube a kan guiwowina na riƙe ƙafafun Mama ina mata magiya '' da miyar kuka zan haɗa!" '' hasbunallahu wani'imal wakeel... laa'ilaha illa anta subhanak inni kuntu minazzalimeen... Allah kana gani...dan Allah kada ka bari Mama ta yimana wannan mugun abun a gida...'' Mama tayi dariya kafin ta zare ƙafafunta tayi gaba na tashi ina binta...Mama dan Allah kada ki mana tuwo.' '' ki tafi ki gaishe da baƙon ki'' inji Mama bayan mun isa kitchen '' kice ma Asma'u tazo ina kiranta!" Ta ƙara,yawu na haɗe ƙafafuna suna min wani irin nauyi sai na bar ƙofar kitchen ɗin na fara zuwa inda suke,fuskar Asma'u kamar hadarin kaji na ƙara so wurin na zauna inda mama ta zauna ɗazu jin yanda har lokacin bai dena kallo naba yana murmushi yasa nace '' nifa bana son kallo!" '' I can't help it especially when I had heard many things about you !" Na ɗago idona dake ƙasa ina hararar shi kafin ince wani abu Asma'u da haushi ya kaimata maƙura ta saki wata banzar dariya tana faɗin '' ai tuwo bata jin turanci ko karatun turanci bata iya ba sai na hausa!" Tayi maganar dan ta tozarta nine,har zan bata amsa ya riga ni faɗin '' na sani,tunda tana jin Hausa hakan ma ya wadatar!" da jin haka fuskar Asma'u ta sake yin duhu sosai,kamar zatayi kuka,ina ta kallonshi kamar naga sabon halitta ya kashe min ido,na ɗauke idona da sauri '' wai kai baka gajiya da kallo ne?" Na ɓata fuska ina hararar shi...sai yayi murmushi '' a'a!" Ya amsa kai tsaye '' Asma'u!!" Mama ta kira daga kitchen tana kunbure kunbure ta amsa '' na'am?" Ta miƙe tana rangwaɗe rangwaɗe kamar zata karye kuma tafiyar tayi mata kyau wallahi,na dawo da idona kan kular abincin dake gefen shi,na ɗago idona suka haɗu da nashi '' ka ƙoshi?" murya ƙasa nayi tambayar ina kallon Mama da Asma'u '' hmm!" ya turo min kular da sauri na buɗe banko damu da zubawa cikin plate ba na zuba miya ciki na fara ci duk da shinkafar nada yawa Sai yayi ɗan guntun murmushi tare da turo min ruwan dake gabanshi da sauri na ɗauka na kwankwaɗa sannan na cigaba da sunƙar abincin loma loma kada su Mama su kamani,da ahankali ahankali ya fara jana hira ina amsa mashi sama sama '' yayarki, she's beautiful!" Ya furta da ɗan kallon gefen su Asma'u,juya idona nayi nace '' waye yayata Asma'u?" Yanda nayi maganar kishi na bai ɓoyu ba'' eh!" Ya furta yana karantar yanayi na abincin da nayi niyar kaiwa baki na ajiye inajin sauyin yanayi, raina ya ɓaci kuma bansan dalilin hakan ba na ɗauka na saba babu wanda zai yabi Asma'u inji ɗar,inji Ina ma ace nice,bawai ina fatan ta rasa nata kyaun ba sai dai da akwai ciwo babu wanda ke sani sai wanda ya ɗanɗana Ba kamar ɗazu da nake hannu baka hannu ƙwarya ba,yanzu a hankali nake ci...idona cikin nashi,na turo baki na da yayi shanana da mai nace a shagwaɓe ''ƙanwa ta ce fa!" Ɗan kauda kanshi yayi gefe,na mayarda hannu cikin kular,sai dai abincin ya ƙare batareda na ankara ba na ɗan zaro ido dan wallahi duk da yawan abincin nidai bansan inda yakai min ba,ji nake kamar banci ba '' well tana da kyau,dana ganta na ɗauka yayarki ce!'' ya faɗa yana kallona da murmushi ji nayi kamar in maka mashi kular dake hannu na ko in dagale bakin shi dake murmushi da cibi mai yatsu ko inyi ma kyakkyawar fuskar shi zane da wuƙa '' tana da kyau tana da kyau tana da kyau hayn!sau nawa zaka maimaita min?kaje ka faɗa mata mana ka dena cika min kunne!" na faɗa a harzuƙe ina huci '' kina kishi ne?" ya ɗan waro idonshi na akuya Kallon gefen da Asma'u take nayi idon mu ya haɗu muka wani sakar ma juna harara kafin na dawo da ido na wurin shi sai dai na kasa kallon fuskar shi nace '' eh ina kishi ka fahimta? ka dena goga min gishiri a ciwo!" Na faɗa da iyakar gaskiya ta dan bana ɓoye gaskiyar abinda ke raina Shiru ne ya biyo baya,bayan na faɗi abinda na faɗa ina wasa da kular abinci raina ba daɗi,'' You don't have to be'' ya fara muryar shi da sanyi,sai na ɗan kalle shi ya cigaba da faɗin '' kema kina da naki kyau,ba sai kinyi ƙoƙarin zama kamar ta ba,ke ta dabance kitten you're special the way you're, you're genuine'' Maganar shi taban mamaki sosai duk da babu abinda kalaman shi suka rage min, na juya idona dan ji nake kamar ya cika ko da surutu wallahi '' kin san me?" ya tambaya '' taya za'ayi in sani tunda ba cikin kan ka nake rayuwa ba?" na amsa da gatse '' nasan kina sona fa!" waro ido nayi baki sake na kalle shi,sai ya washe min fararen haƙoranshi '' nd you're blushing!" ya nuna min kumatu na wai sunyi ja,kauda kaina gefe nayi abun ya ban dariya wai ina son shi.. In kallon gefe naga Asma'u tsaye da kwanoni riƙe a hannunta tana wani irin hararata kamar zata kashe ni da idonta da alama taji abunda ya faɗa '' ashe ka iya karantar zuciya?" '' of course,kawai idan na kalli kyawawan idon ki zan san abinda kike tunani!" Abeedah: Oti meye tunanin ki game da gayen nan faka daka amsa da turanci 🍁: such a big flirt! haka fa,kawar da kaina gefe nayi '' ni bana son daɗin baki!'' '' It's not daɗin baki!" Sosai yaban dariya..kuma nayi mai isa ta ... '' Abincin baƙon ne kika cinye Abeedah?" Mama data fito daga kitchen ta furta tana kallo na '' Mama ya ƙoshi fa.gidansu kaza da ƙwai kawai ake'' '' kinci gidan ku!"Mama ta katseni da daƙuwa,idona suka ciko da hawaye.sai faɗa take min gaban Khalil da yayi ƙasa da kanshi yana dariya da ƙarfi na ajiye kular na miƙe tsaye hawaye na sauka da sauri sauri na wuce ɗaki zuciya ta kamar zata fashe...faɗawa nayi saman gado na fashe da kuka haƙƙun Khalil yabi Bayan Abeedah da kallo bayan ta shige ɗakin can kuma ya jiyo yanda take kuka da ƙarfi kamar an dake ta yaɗan yi tsuru da ido ashe abun har ya kai haka na ɗan lokacin da suka zauna yanzu ya fahimci Abeedah tana da soft and innocent heart Mama dake ta faman faɗa sai tayi shiru ta juyo tana ba Khalil haƙuri.. can na jiyo annakurin na faɗa mata ai shi yace inci...na juya idona da farko data na min faɗa meyasa bai ce hakan ba? Asma'u dake wanke wanke tana ta murmushi '' yayi mata da kyau...hmm!" Ta faɗa tana wanke kwanonin da sauri ganin magrib ta ƙarato yasa Khalil fara shirye shiryen tafiya kuma har lokacin kuka nake sosai ma Mama ta ɗan damu sai ta shigo tana lallashina da ƙyar na dena kukan tace in fito inyi sallama da Khalil Ta tashi ta fita,sukayi sallama da shi , Asma'u ta yafa mayafi wai zata rakashi '' wallahi idan baki tafi kin saka hijabi ba saina ɓata maki rai!" Mama ta faɗa da ɓacin rai a muryarta,na ƙyalƙyace da dariya daga cikin ɗakin jin abinda ya faru buguzun buguzun ta shigo ɗakin tana kumbure kumbure ta ɗauki guntun hijabi na na wurin aikin maina hotels ta saka Mama na ganin ta,ta korata ciki '' wuce ki zauna babu inda zaki!" Asma'u kamar an girgiza duniyar ta, hawaye suka ciko idonta '' Mam...'' '' na gaya maki,ki wuce ki zauna '' kamar zata haukace ta shigo ɗakin kuka wiwiii tayo kaina da sauri na miƙe daga saman gadon ina dariya sosai na fito daga ɗakin a guje na fita daga gidan Ina tsaka da magana da wata yar ajin mu Khalil ɗin ya fito,sallama yarinyar tayi min sannan ta tafi sai na ɗan kalle shi,sai kuma na ɗauke idona fuska haɗiye '' to muje ki rakani ko?" Ya furta da murmushi '' Ni nace dan zan raka ka na fito?" Na tambaya batareda na kalli inda yake ba '' wayyo Allah kitten kina Min wulaƙanci.. shikenan Allah na sama na kallo !" Yayi maganar tare da langaɓar da kai kamar ƙaramin yaron da aka zalunta.... rufe baki na nayi da hijabi ina dariya ƙasa ƙasa Nace '' ashe kaima ka san da wannan? Na ɗauka ya'yan talakawa kaɗai ke faɗan haka!" Ya shafa ƙeyarshi yace '' ɗazu dazamu zo naji wani yaro ya faɗi hakan!" '' shine kai kuma ka ara ka yafe?" Na furta cikin dariya muna tafiya gefe da gefe '' a'a sabon ilimi na koya!" Muka cigaba da hira sosai yake da sauƙin kai da daɗin kasancewa, muka isa motar tare da jingina muna cigaba da hira '' yanzu dai zamu iya zama ƙawaye ko?" Na juya idona nace '' a'a!" Ya ƙwalalo min manyan idonshi kamar mace yace '' to meyasa?" Na fashe da dariya sannan nace '' sai in ka dena kallo na...'' gemun shi da babu gemun ya shafa yace '' zan gwada!" Muna nan tsaye naga yana kalle kalle '' ina Rom?" '' wannan farin gayen mesa fes mas kamar me korona!" Ya gyaɗa kai murya sama nace '' yana can baya yana zuƙa kashi!" Khalil ya saki dariya nima ina taya shi, sai gani mukayi gayen ya raɓa mu ya shige cikin motar bai ko kalle mu ba, hannunshi riƙe da madubi da kuma abun aski na dakata da dariya ina kallon Khalil nace '' da alama fa yaji abinda nace!" Ɗage kafaɗarshi Khalil yayi,ya ɗan ranƙwafa yace '' Rome...Meya faru da sumar ka?" Batareda ya kalli Khalil ba yace '' mind your business!" Nidai mamaki ya kashe ni,wai dan na taɓa gashin shine yaje yayi aski taɓe baki nayi dama can mummuna ne yanzu duk da akwai fes mas a fuskar shi na tabbatar ya ƙara muni... '' ƙila ƙwarƙwata tasha mashi kai!" na raɗawa Khalil a kunne,ya dafe bakin shi yana cigaba da dariya Asma'u ta leƙo ta kira ni '' toh sai anjima!" na ɗaga mashi hannu kafin yace wani abu na bar wurin da murmushi a tawa fuskar Da Isha'i muna zaune tsakar gida saman tabarma dan babu wuta...sama ta ƙarayin duhu saboda hadari ga sanyayyar iskan dake kaɗawa kaina saman cinyar Mama Asma'u idonta sun kunbura saboda ba ƙaramin kuka tasha ba,nidai ko a slippers ɗina, tunanin Jay d nake Allah yasa idan naje makaranta mu shirya a haka har bacci ya ɗauke ni Mama ta kalli Asma'u dake wasa da yatsunta bayan Abeedah tayi bacci,jin idon Mama akanta yasa taja dogon numfashi tace '' wasu lokutan sai inga kamar kinfi son Abeedah...Meya sa?" Mama tayi matuƙar mamaki da abinda Asma'u ta faɗa sai ta girgiza kanta murya a sanyaye tace '' ban taɓa jin nafison ɗaya sama da ɗayanku ba Asma'u, abinda kikayi baki kyauta ba shine yasa...ban san dalilin ki nason fitarda tsiraici ba a gaban yaron nan abinda nasan ba ɗabi'arki bane meya faru?" Asma'u dake kuka ta ƙara yin ƙasa da kanta daga inda take zaune tana taunar lips ɗinta kamar tana weighing a ranta idan ta faɗi maganar dake bakinta ko a'a '' zaki iya faɗa min komai zan saurara!" Mama ta furta gently '' Mama...na kamu da sonshi...daga sanda na fara ganin shi ... Kawai ina so inja hankalin shine Mama..duk da nasan ba kyau!" Mama tayi jim bayan abinda Asma'u ta faɗa,sai kuma ta nuna ma Asma'u gefenta tazo ta zauna, slowly Asma'u ta isa wurin ta zauna Mama ta ɗaura hannunta a sumar Asma'un tana shafawa slowly '' na fahimta...bake kika ɗaurawa kanki ba....amma Asma'u ki saurare ni da kyau ba'a jan hankalin na miji da surar jiki,sai dai da halaye da ɗabi'u masu kyau mace mai ƙoƙarin jan hankalin na miji da surar jiki zata kai kanta ta baro ne kawai bana fatan hakan ta faru da kowa bare kuma akan ya'yana ina fatan kin fahimta?" Asma'u ta gyaɗa kanta tare da kwantawa a ɗayar cinyar Mama '' kiyi haƙuri bazan sake ba!" suna a haka har bacci ya ɗauke Asma'u,ajiyar zuciya Mama ta sauke,a hannu ɗaya akwai Abeedah ɗayan hannun kuma ga Asma'u '' ya Allah kada ka haɗamu da Abinda bazamu iya ba!" Ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya. ___ Kwanakin da suka biyo baya suka wuce kamar ba'a taɓa yinsu ba,a makaranta Jay d ta cigaba da share ni na kasance cikin tsananin kaɗaici kullum ina nan laƙe a duk inda nasan zata kasance amma bata kulani kuma itama tayi kewa ta Ranar Alhamis na tare ta na faɗa mata zamu tashi daga Unguwar mu cewa tayi '' yayi da kyau... Allah ya bada sa'a!" Ba ƙaramin ɗaci raina yayi ba na riƙe kukan dake cina ina tafiya ɗaya ɗaya ban tafi gida ba na wuce gulbi a wannan lokacin ne hawaye suka fara sauka akan fuska ta na samu na zauna saman dakalin da aka zagaye wurin dashi dan dama wurin ba ƙasa bane interlock ne sai aka zagaye gulbin da bulo saboda yara masu ƙiriniya Na zauna ina ta kuka kamar raina zai fita hadari ya fara haɗuwa amma akwai rana har lokacin '' Tuwo me ya faru?" Saleh ne ya zauna kusa dani ya jinginar da ƙarafun shi '' ƙawata ta dena kula ni bata sona!" Na bashi amsa ina mutsutstsukar fuska ta da hijabina '' me kika yi mata?" Ya sake tambaya '' yah dai da tambaya?" Na ɗago jajayen idona ina hararar shi,rufe bakinshi yayi yana dariya yace '' wai har na fara tunanin yanda zaki shawo kanta ne..amma tunda harara ta kike shikenan!'' Yayi maganar tare da riƙe ƙarafunshi zai tashi '' Toh kayi haƙuri!" Na furta ina sake sakin wasu hawaye ajiye ƙarafun yayi ya jawo jakata ya ɗauke pen da paper yayi rubutu a sama '' ungo nan!" Ya miƙo min paper..share fuska ta nayi sannan na karɓa,na tsare paper da ido ganin da turanci yayi rubutun na fara ƙoƙarin karantawa '' I was a hor rible frind..for' give mey....'' da Hausa nake karantawa Saleh da ya saki baki yana jin karatun ya kwashe da dariya harda faɗuwa ƙasa dakatawa nayi tare da ɗaure fuska wane irin iskancine wannan '' Abe...ed..ah...hahaha... Meye kike karantawa haka?" Ya faɗa cikin dariya Ganin babu wasa a tattare dani yasa ya tashi zaune yaja wani dogon numfashi yana ƙoƙarin riƙe dariyar shi yace '' ai ba haka ake karantawa ba kawo ki gani!" Ya amshi paper ya fara karantawa....har ya gama ina binshi da kallo kamar zan rufe shi da duka '' nifa ban iya turanci ba!" '' exactly!" Ya faɗa yana kallona '' idan kika karanta mata wannan taƙi yarda sai ki ɗan rungumeta kice..Kinga saboda ke har da turanci na koya kiyi haƙuri sai ki ɗan fara kuka kin gane ai?" '' kace kai ma ka iya markici har haka?" Na faɗa da annashuwa dan ji nake kamar an ɗauke wani ƙaton abun da ya danne min ƙirji..'' zama da maɗaukakin kanwa...'' '' shike Kawo farin Kai!" Na iyar mashi mukayi dariya tare,sai muka miƙe tare muna tafe muna hira har bakin ƙofa ya ajiye ni sosai nayi mashi godiya kafin na shige Ina gama cin abinci na shiga haddar rubutun Mama da Asma'u suka bini da ido daga lokaci zuwa lokaci Mama take yimin gyara kafin ta tambaye ni wa zan bawa haƙuri haka '' Jadeedah!" Bata matsa min da tambaya ba... Washegari lokacin MSS bayan an taru kafin malamin dazai gabatar da mss ɗin ya shigo na miƙe,dama nayi ma piripoper (prefects) magana wurin yayi tsit aka bini da ido naja dogon numfashi ina kallon inda Jay D take zaune da wasu masu kuɗin dake bina da kallon rainin wayo Na fara magana '' Jay D.. I'm so sorry...I was sace a hor'rible fri'end...'' da farko dana fara karanta abun da kyau sai sukayi shiru suna sauraro amma jin na fara karanta abun da Hausa yasa suka fashe da dariya naji kunya ta kamani.... '' kai kai! Duniya kana ganin abubuwa iri iri'' '' Horo'ribu'le fri'end..haha'' '' turanci take ko hausa?" '' Silence!" Headgirl dake tsaye tun daga lokacin dana fara karanta takardar haƙurin nawa ta faɗa tsit wurin yayi masu dariya suka daina duk da na rasa karsashi na cigaba '' Yo'u trey toh stand uu'f for Mey...boot I was un'gretful... I'm sorry...I missd you... for'gibe mey!" Na ƙarashe a kunyace kaina ƙasa da hawaye a idona Jadeedah ta taso daga inda take zaune har zuwa inda nake itama da hawaye a idon ta..ta riƙon hannu na '' nima nayi kewarki sosai Bee kada ki ƙara yimin abinda kika yimin kinji?" Ta faɗa tana rungume ni ƙam ''bazan sake ba!'' na bata amsa '' Ohhhh...masoya... soyayya ruwan zuma ce yara kusha...'' wurin ya kaure da wasu suna kiran mu wai Lailah da majanunu wasu suka hau table suna duka kamar sun samu ganga ta riƙo hannu na muka samu wani seat daban muka zauna '' iyye amma yaran nan anyi ja'irai!" Wani Malam Auwal ya leƙo hannunshi riƙe da zungureriyar bulala ɗayan kuma a haɓa... muryar shi kamar ta mata laƙabin da aka yi mashi shine ' yanga dot com ' tsabar yanda yake magana cike da yanga amma fa baƙin mugune na ƙarshe ma kuwa aka fara rububi wurin zama,shiru ya cika ajin.. prefects ɗin dake wurin suka yi ƙasa dan idan aka gansu punishment ɗin su zaifi na kowa ƙwafa yayi kafin ya bar wurin sai macijin sari ka noƙe ya shigo yan matan suka ƙara bada hankali na musamman wurin sauraren shi nidai a wannan lokacin Abu mai muhimmanci shine Jadeedah ta dawo.. naji ni a matsayin mutum a karon farko na tsawon lokacin da bama tare... Bayan an tashi break muna zaune nida Jay D ƙarƙashin bishiyar umbrella Jadeedah sai kallona take tana murmushi '' Meya faru?" Na tambaye ta ina juya idona...sai tayi murmushi tana kallon ɗan sululun dake riƙe a hannu na ta ɗauke idonta tana kallon nesa damu inda katangar take guntuwa muna hango mutanen dake wajen makarantar mu... masu aikin gyara hanya '' Faɗa min,ya kika ji sanda bama tare?" Ɗan sululun dake bakina na haɗe sannan nace daga ƙasan zuciya ta ina kallon ta '' ji nayi...kamar ni marainiya ce Jay D...ban san yanda rayuwa ta zata kasance ba idan babuke...'' taɓe baki tayi hmm.. Allah ko?" Alamun bata yarda ba...dukar wasa nayi mata a kafaɗa mu biyun muna dariya '' kin dai san ni abinda ke zuciya ta kaɗai nake faɗa Jay D bana ƙaryar abinda nake ji...'' '' Tuwo masu faɗar gaskiya sannun ki!" Wata mai suna Fadeelah daga C class ta katse ni tana zama kusa dani ta wani tsoma hannu cikin ɗan sululun...kuma sai da idon mu ya haɗu ta tura har guda biyar cikin baki....take na haɗe fuska tareda jaye kwano na...Jadeedah ta rufe baki tana danne dariya '' kinci rabon ki wallahi!" Na faɗa ina ƙoƙarin miƙewa '' Matsala ta da Abeedah rowa!" Hafsah daga SS2 ta furta itama ta kwashe fiye da rabin abunda ya rage '' kambuuu!!!!" Na zaro ido kafin in sani sauran wasu dake kusa sun zo sun warce kwanon daga hannu na suka daka wasoso kamar zanyi kuka ganin yanda suke tumurmusar juna yasa mu dake kallo muna ta dariya...duk sun ɓata hijaban su da manja kafin suka fara guje guje'' zo muje in siya maki wani!" Jadeedah ta riƙo hannu na muka bar wurin...'' ke baki faɗa min yanda kika ji...'' '' Oh Ni I felt empty ban san yanda zan iya fasaltawa ba su ɗin da nake tare dasu ko kaɗan bamu dace da juna ba,ba kamar ke ba Abeedah... I love you so much!" Ta ƙarashe tana jan kumatuna '' Innalillahi duk sai kin ƙara sa pimples sun fito min!" Na kaɓe hannunta daga fuskata...dariya tayi sai kuma ta shafa hannun a fuskar ta '' idan kina da pimples nima ya kamata ace ina dasu. ..'' '' pfft!! Akan me zaki so ki samu pimples akan kyakkyawar fuskar ki?" nayi tambaya ina kallon hannunta dake riƙe da nawa... zuciya ta na ƙara son Jadeedah sosai '' saboda ina so inyi kama dake...sosai! Ji nake inama ace gidan mu ɗaya..ke Bee kwanakin nan da nayi babu ke wata irin ƙaunar ki ke ɗawainiya dani!" '' wai ke sai kita magana kamar na miji...'' '' waya ce namiji kaɗai zai iya bayyana ƙauna Abeedah? Bawai ina ƙaunar ki..irin na banza ba...kawai ƙaunar ki daga Allah ne kin gane?" '' na gane!" Haka muka cigaba da hira...har aka koma aji ranar naci ɗan sululu har nayi rarraba dashi nida Jay D har aka tashi muna maƙale da juna,ban wani cika shiga motarsu ba amma ranar har gida aka sauke mu nida Asma'u.. Ban taɓa sanin ƙaunar da nake ma Jadeedah tana da yawa ba sai da mukayi faɗan nan kamar zuciya ta zata buga bana fatan ƙara kasancewa nesa da ita... Kamar yanda Mama ta faɗa ranar Lahadi muka koma sabon gidan mu,sosai muka share ko ina muka gyara...wasu Mutanen anguwar mu suka biyo suna tayamu gyara gidan,farin cikina baya misaltuwa a wannan ranar mama ɗakinta ita kaɗai,nida Asma'u ɗakin mu ɗaya sai wurin magrib gidan yayi shiru ya dawo daga mu sai mu...bayan Isha'i muna zaune a inda mukayi sallah nake kallon Mama data kafe wuri guda da ido... '' Mama ko bakison gidan nan ne?" Asma'u ta riga ni tambaya '' kawai dai...nayi kewar gidan mu ne!" Ta amsa a sauƙaƙe '' zaki saba ai!" Asma'u ta amsa mata..sai kuma ta matsa ta kwantar da kanta saman cinyar ta'' Mama tare zamu kwana anan ɗakin...'' na faɗa ina kwantawa a inda nake '' ɗakin kufa?" '' kin dai san bamu saba kwana daban daban bako?" Asma'u ta rigani faɗa.. girgiza kanta Mama tayi...mukayi shiru... A raina ina mamakin meyasa Jadeedah bata zoba? Daga ƙarshe dai tare da Mama muka kwana ranar Monday Jadeedah bata zo makaranta ba.hankali na ya tashi haka ma ranar talata Naji na ƙara shiga ƙunci... Ranar laraba ina zaune ƙarƙashin bishiyar da muke zama tare ina saƙe saƙe a raina 'idan fa kamar yanda yake faruwa a fim sai ka nemi abokin ka karasa ya tafi wani wuri bayan kunyi faɗa kun shirya nima abinda zai faru dani kenan?idan fa... '' BEEEE!!!! Wai Meye kike tunani haka?" Jadeedah dake zauna gefe na tana magana tuni amma banjiba ta jijjigani tana kiran sunana da ƙarfi na juyo na kalle ta kamar na kasa yarda da ita ce a gefe na..sai da na taɓa fuskar ta '' kece?" '' fatalwa ce!" Sai na saki dariya..inajin sanyi a raina...muka rungume juna '' ina kika shiga kwana biyu?" Sakin juna mukayi ta gyara zamanta ta riƙo hannuna '' wai Abba...haka kawai muna zaune zaman zaman mu wai...yayi mana visa zamu bar Nigeria!" faɗuwa gabana yayi.. '' ku bar Najeriya ku tafi ina?" Tana girgiza kai tace '' wai New Zealand! '' ''.oh...'' na faɗa inayin ƙasa da idona ta cigaba da faɗin '' amma kada ki damu,yanzu mu duka muka yi mashi yaji...muka dena mashi Magana daga ƙarshe dai ya yarda zamu cigaba da zama Nigeria amma shi zai tafi...nan gaba kaɗan wai muma zamu bishi!" '' nan gaba kaɗan zaku bar Nigeria...hakan bai sa naji hankali na ya kwanta ba Jay D..idan fa kuka tafi? Ya zanyi?" '' abu mai sauƙi zan saka ki a akwatina!" '' kina da Iskan bani ke nan?" '' ai ke babbar yarinya ce bakya buƙatar oxygen!" '' idan na margaya barzahu kenan!" Mukayi dariya '' hankali na ya tashi sosai...'' ''.nima inata kuka a ɗakina jin wai zamu bar tuwo a Nigeria!" Ta ƙarashe tana jan kumatuna.... +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma ₦800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 13. ...let me help you...🖊️ '' yaushe zaki zo gidan mu?" Na tambaya ina kopar mata notes ɗin da bata yiba,ɗauke kanta tayi daga kallon window ta dawo dashi a kaina '' kin san abinda nake tunani? Ta tambaya da murna a muryarta,na girgiza kaina batare da na ɗago daga littafin ba gyara zama tayi taɗan duƙo da fuskarta kusa da tawa tace '' idan fa kika zo gidan mu kikayi kwana biyu,nima inyi kwana biyu a gidan ku kamar sleep over?" sai da na gama rubuta layin da nake kafin na ɗago na kalleta '' ban fahimta ba" '' ina nufin Mu kwana a gidan mu yau da gobe da jibi wani sati sai mu kwana a gidan ku irin haka! shi ake kira sleepover!" Na bita da ido har tagama '' slif kobar?" Na tambaya ina ƙoƙarin rubutawa a bayan littafina tayi yar dariya tace '' sleep over ba koba ba,kuma kina nufin duk abinda na faɗa abinda kaɗai kika ji kenan!" ta ɗaure fuska '' a'a..ban taɓa zuwa gidan kuba..idan fa innarki bata so ana kawo mata mutane? Kuma bansan me zance ma Mama ba '' '' ba sai kin ƙara cewa komai ba!" Ta ɗaura yatsanta a bakina '' Indai Ummi kike magana akai well,bata da matsala kullum sai ta tambaye ni ina ƙawarki Abeedah? Yaushe zata kawo mana ziyara? Yau ma faɗa mata nayi ta shirya abinci na musamman dan dake zan dawo gida kuma zamu fara biyawa gidan ku ai ni zanyi wa Mama magana kin san ni da iya zuba zance!" ta gyara zama da Murmushi a fuskar ta kamar har tayi nasara ina son yanda Jadeedah take da ƙwarin guiwa da yarda da kai duk tace zata yi abu komai wahalar shi sai tayi duk yanda abu ya ɓaci tana da yanda zata ga abun cikin haske mai kyau Ita ɗin Uhmm 🍁: Optimist Jadeedah ofitamus (optimist)ce,bazata taɓa yarda taga baƙin abu ba sai dai farin shi acewarta abinda kake tunani kodai ya gina ka koya rusa ka... ma'ana idan tunanin ka mai kyau ne to abubuwa masu kyau zasu dinga faruwa dakai haka zalika idan gurɓataccen tunani kake dashi abubuwa marasa kyau kaɗai zasu dinga faruwa dakai tunanin ka kai yake cutarwa ba kowa ba kai zaka kasance a yanda ka ɗauki kanka '' kina jin abinda nake faɗa kuwa?" Jijjiganin datayi ya dawo dani '' eh inaji!" Na amsa duk da banji komai data faɗa ba kallon data yimin ya tabbatar da bata gamsu ba '' ina matuƙar ƙaunar ki Jadeedah Ahmad!" Ta sakar min Murmushi mai sanyaya rai '' ba kamar yanda nake ƙaunar kiba Abeedah Abdul wahhab...'' '' dan na kira sunan babanki kema sai kin kira nawa ko?" Na tambaya ina murmushi '' duk cikin son ne!" Ta bani amsa... '' har da wani littafin Hausa na siyo maki..'' Idona suna ƙyalli nace '' dan Allah?" '' sosai ma kuwa..kuma kin san abin burgewa?" Ta tambaya tana ɗaura hannunta a table '' sai kin faɗa!" '' jarumar baƙa ce...kuma bata da kyau, bata gane abubuwa bata da dogon gashi a taƙaice dai mummuna ce!" Sosai nayi dariya dayasa yan ajinmu kallo na,na tsani ina karatun littafi inji ance jaruma fara ce ga kyau kamar ita tayi kanta raina mummunan ɓaci yake! Kullum sai ata zuzuta kyaun jaruman da har za'a sa mai karatu tambayar kanshi mai yasa baya da irin abun da suke dashi Na fiso ace jarumar tana da wani abun da zai haɗa mu kamar dai ita baƙa nima baƙa babu malamin daya shigo yan aji aka taru.ana wasar police kama ɓarawo wasu kuma sunyi gungu suna hira wasu suna carafke idan munji malami na zuwa kowa ya dawo wurin shi a guje,ranar tayi daɗi kamar kada a tashi Sanda aka tashi,a mamakina sai ga Asma'u ta rugo ta rungume ni,na ƙame ƙam Jay D ta tsaya gefe jakar goyonta a hannu tana kallon mu Asma'u ta ɗago kanta ta kalle ni sai ta sake ni batareda tace komai ba Da murmushi a fuskar ta '' sannu Jadeedah '' ta gaishe ta '' Ni Jadeedah ko wata daban?" Ta tambaya tana kalle kalle sai kuma ta nuna kanta '' a'a ta bayanki!" Asma'u ta amsa tana juya ido '' I thought as much!" Jadeedah ta furta haɗe da taɓe baki '' nidai mu tafi...'' sai muka yi gaba Wurin fita daga get duk anbi an matse ma mutum kayan ciki,kamar idan munyi da ɗai ɗai baza a fitan ba wasu suna dukan juna suna gudu tare da faɗin '' na sha ta anjima'' wasu kuma suna ma juna bye bye wasu suna faɗin sai Monday hanyar da muke bi mutane ƙalilan ke bin hanyar ɗayan hanyar kusan rabin makarantar mu nan ne hanyar su '' sai Monday Jadeedah da Tuwo!" Wasu yan ajin mu su dayawa suka faɗa suna bin hanyar can '' sai Monday '' nida Jadeedah muka faɗa tare muna musu bye a hankali na juyo ina kallon hanyar nan dake cike da mutane,Mu hanyar mu yamma ne inda rana ke faɗuwa su kuma hanyar su gabas inda rana ke fitowa nake jin kaɗaici a duk sanda na juya naga mutane da yawa suna bin hanya guda mu kuma yan ƙalilan a tamu hanyar kamar inbi inda mutanen masu yawa kebi duk da nasan ba dukan mu bane uhm.. Autumn: destination Ba dukan mu bane zamu isa destineshon ɗaya ba duk da haka Jay D take jana da hira anan ne Asma'u tasan zan tafi gidansu tayi ƙasa da kanta tana sauke ajiyar zuciya... '' akwai matsala ne?'' na ɗan kalleta jin ajiyar zuciya'n data sauke '' babu'' ta bani amsa da murmushi sai ta shigo cikin hirar mu abinda bai faru ba da daɗewa ita da Jay D basu yi faɗa ba kamar yanda suka saba wannan babban canji ne gaskiya Muna kaiwa bakin hanya motarsu Jay D ta iso, ta buɗe mana ƙofa muka shiga a tare muka gaishe da Musa direba ya amsa da fara'a tare da faɗin '' yau Abeedah ce a motar mu gaske naga hadari ya taru!" Asma'u da Jay D suka yi dariya kafin tace '' ai baka san artabun da nasha ba kafin ta shigo shine yasa'' na taka ƙafarta tayi shiru murmushi yayi kafin ya fara tuƙi '' ɗan bani wayarka in kira Ummi'' miƙa mata wayar yayi Ta kira mamansu sukayi magana '' toh ba matsala me kike so a dafa kafin ku iso?" ta tambaya,Jay d ta kalle ni '' Bee me kike so kici?" Nida Asma'u muka bita da ido '' kawai adafa abinci mai daɗi'' ta ɗage kafaɗa suka ƙara magana kafin ta katse kiran daidai an kawo gidan mu godiya muka yiwa direba sannan Jay D ta faɗa mashi yazo ya ɗauke mu da ƙarfe shida da rabi Sallama mukayi muka shiga ciki muka iske Mama tana sharar tsakar gida Jin baƙuwar murya yasa bayan ta amsa ta miƙe tsaye har muka ɓullo daga zauren '' a'a a'a..maraba maraba da Jadeedahtu.. '' Jay D ta rufe fuskarta tana dariya kafin takai ƙasa ta gaishe da Mama Mama ta amsa tare da ɗago ta suna cigaba da gaisawa muka wuce ciki Mama ta rako Jay da har ɗakin mu sannan ta wuce kitchen Cire hijabinta Jay d tayi amma tana da hula akai kallonta nake dakyau da kyau Ni ban taɓa lura ba amma Jay D tana da wani irin kyau na daban uniform ba ƙaramin rage ta suke ba girar ta da hancin ta kamar zana su akayi idonta manya ƙwayar ciki fari sosai baƙin ciki baƙi wulik ga wani gashi daya kwanta a bayan wuyanta bakinta ɗan ƙarami amma ba pink bane kamar na Asma'u amma duk da haka ni idan za'a ce in zaɓi wanda yafi kyau cikin su biyun Jay D ce ban taɓa ganin ta babu hijab ba sai yau. Fuskarta kyakkyawa surar jikinta? ɗauke idona nayi daga kallonta sai kuma naji nauyin cire nawa hijabin kowa a cikin ɗakin yafini komai kunya kamani dana kalli ƙirjina ta cikin madubi '' Bee ki cire hijabin mana'' Jay D tayi rashe rashe saman gadon mu,ajiye jakata nayi na fara cire hijabin kamar a wata ƙasa ƙarshen hijabin yake Mama ta shigo da shinkafa da miya cikin plates harda cokula guda uku da ruwa da sauri Jay D ta tashi ta karɓa suna ma juna murmushi Asma'u dai bata ce komai ba sai kallo take Da ƙyar na samu na gama cire hijabin ƙirjina yayi min nauyi ajiye abincin tayi a tsakar ɗaki muka zauna a saikul kowa ya ɗauki cokali tana murmushi ta kai baki tana ta santi tun ina jin kunya har na saki jiki Kuma ma dukan mu mata ne ai ko? Eh hakane amma kasancewar mu mata bai hana ni jin abinda nake ji ba bayan mun gama cin abincin nakai mata ruwa a bayi ta shiga tayi wanka ni kuma na wuce ɗakin Mama Asma'u tunda Jadeedah ta cire hijabi take binta da kallo tana analyzing kowane curve na jikin Jadeedah dan ma sha Allah,ta tashi ta isa gaban madubi tana duba kanta duk da itama tana da nata amma na Jadeedah was on another level tsuki taja tabar gaban madubin ta koma ta kwanta Ina tsaka da magana da Mama naji Muryar Jay d'' Bee zoki ban kaya in sa!" na miƙe na fita zuwa ɗakin mu na tsaya daga gefen ta gaban wardrobe ɗina ban yarda na kalle taba na jawo wata doguwar rigar atamfa ja na miƙa mata '' na gode ƙawar!" Murmushi nayi, ta karɓa ta tsaya a wata yar kwana ta canja duk da maneji tayi dan kayan sun matse ta fiye da ƙima bayan ni har yawo nake cikin su gashinta dake naɗe cikin hijabi ta saki ya sauko har zuwa mazaunan ta baƙi wulik ko daga ido mutum yasan ba ƙaramin laushi ne dashi ba,na kafe ta da ido ko ƙiftawa banyi wannan shine karo na farko dana taɓa ganin gashin Jay D,kullum a makaranta daga fuska sai tafin hannun ta nake gani zan iya rantsewa ko ƙafarta ban taɓa gani ba Asma'u dake kallo daga gefe ta tashi zaune daga kwancen da take... '' kai...ashe haka gashin ki yake da tsawo?" Hannu tasa tana baza shi tace '' ji nake kamar insa almakashi in yanka da badan ummi dake hanani ba wallahi dana aske shi'' Na matsa inda take ina taɓawa nace '' ai ko dana sa bulala na miki raɗam..in zane ki yanda ko tafiya ba zaki iya yi ba!" Tayi dariya ''.dama ace idan mutum ya yanke gashin shi zai iya ba wani da kin bani ai!" Na faɗa mata ina auna tsawon,ita kam tayi sa'a ga kyau'n fuska na hali da kuma na jiki. Allah ya kashe ya bata.... Asma'u tazo itama tana taɓa sumar tana gyaɗa kai Jay D bata ce mata komai ba..'' Bee ki kamamin mana kalba biyu! Ko tsoro biyu irin na turawa!" Na nufi ƙofa '' bari inyi sauri inyi wanka sai inzo in miki!" Na ɗibi ruwa na wuce baye,na cika kofin wanka na juye a kaina ruwan na sauka zuwa sauran sassan jikina haɗe da hawayen da nake ta riƙewa a ɗaki Ina kallon jiki namusamman ƙirjina da har lokacin bai canja ba kamar yanda ƙirjin mace yake kasancewa idan ta fara fitar da uhm uhm ai kun gane ko? To nima haka nawa yake amma meyasa? na kalli gefe da gefe na da kuma bayana duk a shafe ba kamar nasu ba, nita dabance? Ko akwai inda nake yin ba daidai ba a addu'a ta? Meyasa nima bazan samu irin abinda suke dashi ba? Kafin in sani na shiga gwada kaina dasu na manta da maganar Malama Hafsah comparison is the thief of joy,ina ƙara tuna duk addu'oina na baya. na duƙe a wurin ina kuka ƙasa ƙasa ina jin na tsani kaina da kuma rayuwa ta ko kallon kaina bana son yi na daɗe a bayen kafin na fito Nayi alwala na shige ɗaki cike da jin kunya Asma'u ta tashi ta fita Jadeedah kuma sallah take a gaggauce na shirya cikin irin kayan dake jikin Jay d na kalli kaina a madubi ƙunci na ƙara turnuke ni da sauri na ɗauki hijabi nazo na tsaya gefen ta na kabbarta sallah Na daɗe ina addu'oi na riƙe hawaye na kada aga ina kuka a tambaye ni bani da amsa Bayan na gama na daɗe zaune a wurin, Jadeedah ta tafi ɗakin Mama sai da tayi sallama mama tabata izini sannan ta shiga kamar yanda ta faɗa kuwa ta tsara zance har mama ta yarda da In tafi gidan nasu in kwana data gayamin banyi mamaki ba Ta lura da yanayina amma bata tambaye ni mai ya faru ba ina son hakan game da ita tana da hankali bata matsamin da tambaya a irin wannan halin sai dai kawai inji tana zayyano min dalilin daya sani a yanayi...tana da 🍁: observation Tana da obzabeshon sosai...miƙar dani tayi muka isa bakin madubi na shiga gyara mata gashinta idona kafe a kanta naƙi yarda in kalli ƙasa da hakan Asma'u ta shigo itama ɗaure da towel dai duk sune nice a baya meyasa ni? naji kuka ya fara taso min saukar hannun Jay D a nawa yasa na fahimci abinda ke zuciya ta ya fara bayyana a fili,nayi ƙasa da idona hawaye na barazanar saukowa murza hannu na ta farayi,da ƙyar naja dogon numfashi na mayarda hawayen na sakar mata murmushin da yafi kuka ciwo itama ta mayar min da mai sanyi Bayan duk mun gama komai muna zaune muna hira aka dawo da nepa, dukan mu ɗakin Mama muka wuce, tv'n na kawowa da sauri nasa tashar yan china daidai ana fim ɗina ' waild fulawa '' ''.ashe kema kina kallon wannan series ɗin?" Jay d ta faɗa da murna '' sosai ma kuwa..kuma wannan mai sa baƙaƙen kaya mugun nan shi nafi so!" Na bata amsa '' bani mukashe!" Ta faɗa tana ɗaga hannunta...muka haɗe itama shi take so Asma'u ta taɓe baki '' Jadeedahtu gyaran gashin ki yayi kyau masha Allah" Mama ta faɗa tana kallon tsoro biyun dana yima Jay D fuskar ta kamar irin na yar tsana '' na gode..Bee tayi min!" Ta amsa Mama Muna nan zaune muna kallo har ƙarfe biyar sai lokacin na fara shirya kayana Mama ta kira Ni ɗakin ta tayi min nasiha kamar garin zan bari duka bazan dawo ba Maman mu kenan Da ƙarfe shida da rabi direba yazo ɗaukar mu,Mama harda yan kayan miya kamar su daddawa da su tafarnuwa su masoro ta bani in kaiwa maman su Jay D sosai Jay D tayi godiya Asma'u da Mama suka rako mu har bakin ƙofa, Asma'u kamar zatayi kuka Nima haka kamar bazamu sake haɗuwa ba '' sai Monday Mama!" Jay D tayi musu bye ta riƙo hannu na sai juyawa nake ina kallon su mama tana murmushi take mana bye Asma'u ta wuce ciki da gudu buɗe min ƙofa tayi na shiga,direba ya buɗe mata buut tasa kaya na sannan itama ta shiga tana cigaba dayi musu bye bye har muka bar wurin... Cikin mota inata sharar hawaye..itakam sai murmushi take...tafiyar minti arba'in muka kawo gidan su duk da dare ne bakina ya kasa rufuwa,idan na kalli makeken gidan dake gabana sai in kalli Jay D..ban taɓa tsammanin a irin wannan wurin take zama ba,na ɗauka ƙananan masu kuɗi ne ashe ashe Rufe min bakina tayi ganin yanda yake wangale Bayan ya paka gaban gidan muka fito na kalli ƙasan da tayis (tiles) ne malale a ƙasa A tsakiyar gidan ga shuke shuke nan ƙanana a gaban ƙofar kuma (entrance) fulawowine daga gefe da gefe da yar ƙaramar hanya a tsakiya sannan gidan sama da ƙasa ne sai wani ɗan ƙaramin gida a sama 🍁:attic Yauwa atika 🍁: ba Atika ba Attic '' koma meye...ai dai sun gane '' ƙofar shigar ma glass ne haka tagogi ƙofar glass ne dasu...sai wata kujera mai tsananin laushi, tsakiyar gidan yanada faɗi sosai kuma haske ta ko ina kamar rana ...lallausan hannunta naji a nawa '' mu tafi!" Ta riƙo hannu na,na kasa warkewa tura ƙofar tayi muka shiga da sallama daddaɗan ƙamshin abinci haɗe dana turare ya fara dukan hancin na haɗe da sassanyan A'c... Ma sha Allah na furta cikin raina dan ba ƙaramin haɗuwa gidan yayi ba... Ban taɓa ganin gidan da yayi min kyau ba irin nasu Jay D Har saman lallausar kujerar suta zaunar dani '' ina zuwa '' ta faɗa sannan ta haye sama da jakar kayana,na cigaba da kalle kalle kafin na mayarda kallona a TV'n ina kallon cartoons ɗin da ake nunawa MSA naji tafiyar su akan stes ɗin da sauri na miƙe tsaye Ganin maman su Jadeedah saye da baƙin hijabi har ƙasa Jadeedah maƙale a gefenta kamar wasu ƙawaye sosai suke kama duk da haka naji tayi min kwarjini ina wasa da ƙarshen hijabina zuciya tana bugu da ƙarfi..naji labari kuma na kalla a TV yanda maman su masu kuɗi ke cin mutuncin talaka kafin su koreshi..idan fa nima '' lale lale..barka da zuwan babbar ƙawar mu Abeedah...'' naɗan zaro ido jin abinda ta faɗa har suka ƙaraso inda nake nikam nayi tsaye baki sagam dan banyi tsammanin haka ba naji saukar hannun ta akan kafaɗa ta da sauri nakai ƙasa ina gaishe ta da fara'a ta amsa min..tana kallo na sosai '' Ma sha Allah.. kyakkyawa '' ta furta hakan ya ƙara ban mamaki sai nayi ƙasa da kaina ina murmushi kuma naji daɗin yabon da tayi min duk da nan da anjima kaɗan Zan koma gayawa kaina akasin hakan.. Jay D tana ta murmushi Zama mamansu tayi ta nuna min gefenta in zauna naɗan kalli Jay D data zauna ɗayan gefen sai nima na zauna ina cigaba da wasa da hijabina '' meyasa tuntuni baki zoba? Kusan kullum sai Jiddah ta bani labarin ki...'' na ɗan saci kallon Jay D data wani langaɓar da kanta gefe tana kallo '' ban saba yin nesa dasu Mama ba!" dajin amsa ta sai tayi dariya '' yar Mama kenan..'' nayi murmushi kawai ban ce komai ba '' Jidderh ai tace saboda ba kya son masu kɗine!" kallon Jay d nayi ta ɗauke kanta gefe,sai na dawo da idona kan Mamar su nayi ƙasa da kaina '' haka ne,amma duk wani ra'ayina game da su, Jadeedah ta canja shi koda ba duka ba..ita ɗin ta daban ce!bana son cin mutunci" Maman su take kallona har lokacin murmushin ta bai gushe ba '' No wonder jidderh ta laƙe maki, turned out she found a gem!" Nidai ban fahimci abinda ta faɗa ba nadai ga Jay d tana dariya kafin tace '' dan ma baku zauna tare bane,ina faɗa maki ba zaki so ku rabu ba!" nayi ƙasa da kaina ina sauraren su yanda take ta zuzuta ni a gaban maman su yasa na shiga tambayar kaina idan da gaske hakan nake kodai dan ni ƙawarta ce take faɗan hakan.... Can dai muka miƙe muka nufi dining abinci kala da iri harda na turawa duk na kasa sakin jiki duk da yanda mamansu take jana da hira abincin ma sama sama nake ci mamansu tace '' duk wannan abincin danke nefa kici iya cinki!"naɗan zaro ido dan ni? na gyaɗa kaina ina cigaba da cin abincin can Jay D ta tafi inda na zauna ta ɗauko sakon Mama ta miƙa ma mamansu..nayi mamakin farin cikin dana gani a fuskar ta akan ɗan wannan abun tana ta godiya... Daga nan ta tashi tabar wurin ya rage daga Ni sai Jay D '' kici abincin danke aka dafa fa'' ta sake maimata min kafin ta dinga jawo abincin kala kala tana zuba min..yanzu da babu mamansu a wajen na saki jiki ina ci kuma nafi jin daɗin abincin yanzu cewar dan ni aka dafa duk wannan yasa na ji kamar ni ta musamman ce... Abinda yayi saura na daga abincin muka kwashe muka kai kitchen nan ma abun kallo bai ƙare ba Muka saka abincin cikin fridge bayan mun kwashe shi a wani roba daban sannan mukayi wanke wanke Bayan mun gama tajani zuwa ɗakin ta mai kyau shima babu wani tarkace da yawa ƙasa kapet pitch da ash color ne gadon shimfiɗe da bedsheet fari pillow baƙaƙe da pitch sai wani ɗan ƙaramin table da aka saka ma pitch ɗin ƙyallen tebr shima pitch mai laushi daga gaban gadon..daga bayan gadon akwai taga da labulaye pitch da aka raba gefe da gefe sai madubi da kujerar gaban madubi da wardrobe harda wata yar shuka a gaban madubin...duk wannan a gefen hagu ne...a gefen dama wata farar ƙofar da zan iya cewa baye ne...da kuma madubi dogo har ƙasa.... sai wardrobe mai tsawo da faɗi... Ga A'c dake kunne...sai irin lantarkin nan da ake ajewa gefen gado.. nata popl (purple bed side lamp) Ta rufe ƙofar nidai na zama kamar bani ba duk na rasa ƙwarin jiki na ganina a haka yasa tace'' zo muyi salla muyi wanka mu kwanta '' na yarda da abinda ta faɗa dan har wani bacci nake ji bayan mun gama sallah ta haɗa min ruwa cikin wannan abin na masu kuɗi 🍁:Bath tub Da na shiga nayi mamakin ganin shi battob (bath tub) ɗin da kuma wani wuri da yake a sakaye da glass sai akwai wani irin shaya a sama...da tsakiya da kuma ƙasa...na saman yana zuba kamar rariya zai jiƙe mutum daga sama har ƙasa...na tsakiya kuma yana fisa ma mutum ruwa daga ƙirji zuwa ƙasan ciki...na ƙasa kuma daga ƙasan ciki zuwa ƙafafu.... Taɓe baki nayi kafin na cire doguwar rigar jikina ina juyo wa naci karo da madubi ya nuna min kaina daga sama har ƙasa zuciya ta tafara nauyi kafin idona suka fara ƙaiƙayi da sauri na ɗauke kallona na shiga cikin ruwan data haɗa min masu daddaɗan ƙamshi da ƙyar na gama wankan batare da bacci ya ɗauke ni ba saboda daɗin ruwan... Wani farin towel na ɗaura na fito babu kowa a ɗakin sai kayan bacci riga da wando masu hoton zaki da na gani saman gado da kuma paper an rubuta '' kisa wannan" ajiye paper nayi na ɗauki kayan ina dubawa kafin nasa ina tajan rigar daga gaba Na kalli ƙwayar idona da ash ɗin yayi duhu farin ciki yayi ja irin idan mutum yayi kuka Jay D ta shigo da irin kayan dake jikina tana dariya tace '' kinyi kyau fa '' ɗauke idona nayi daga kallonta kayan sun mata kyau suna ƙara nuna abinda bani dashi '' zaki shafa mai?'' '' da daddaren nan?" pink ɗin robar mai dake gaban madubin ta jawo mu biyun muna shafawa '' naga baki saki jiki ba...ko baki son gidan mu?" Da sauri na girgiza kai '' ba haka bane kawai ina kewar su mama ne kuma wannan shine karo na farko dana taɓa yin nesa dasu shine yasa '' na bata amsar da rabi gaskiya ne rabi kuma saboda kaina ne '' zaki saba ai shine yasa nake cewa kizo gidan mu da yanzu kin saba..abincin yayi daɗi?" '' yayi daɗi sosai...har naji ina kewar abincin daban ciba,idan na koma gida duk sanda zan tuna wannan lokacin sai na ranƙwashi kaina '' mukayi dariya naji raina ya ɗan saki... Barin gaban madubin tayi ni kuma na cigaba da shafa man..kafin na faɗa duniyar tunani '' it's not daɗin baki...'' Sai na saki dariya tuna yanda Khalil ya faɗi hakan'' kina ta blushing lafiyar ki kuwa ko saurayi kikayi?" Jay D ta tambaya ta baro saman gado tazo ta tsaya kusa dani da kallon tuhuma dariya na sake yi kafin nabar wurin na wuce saman gadonta na juya gefe ɗaya kashe wutar tayi take wannan popl ɗin lantarkin ya kawo ta hauro saman gadon '' faɗa min waye shi?" Ta tambaya da zolaya rufe fuska ta nayi da hannu na'' ba saurayi na bane bafa!" Sai na juya ina kallon ceiling itama ta kwanta a irin haka...'' sunan shi Ibrahim..amma nidai ina kiranshi Khalil '' ta zaburo ta juyo tareda tallafo fuskarta da hannayenta '' dan Allah..faɗa min yana da kyau? Ina kuka haɗu?" '' yana da kyau mana, sosai ma....''.nan na bata labarin yanda muka haɗu da Khalil da komai ma '' bari mu fara neman anko'' ta faɗa tana min cakulkuli....ina ta dariya '' sai kunyi soyayya kuma da alamu ke zaki fara kamuwa!" Tayi maganar da kwantawa gefe na tana haki sai dana ja dogon numfashi sannan nace '' bana tunanin haka daga haɗuwar mu kuma sai ki fara neman anko? Ni mema na sani game da soyayya?'' '' hmm..yanda ake kiss mana!"taban amsar maganar ƙarshe '' Innalillahi wa inna ilaihi raji'una..ke Jay d..'' '' malama ki dena yi kamar ke innocent ce duk littafan da kike karantawa kizo kina wani yi kamar ta Allah..'' ta maka min pillow'n dake gefenta '' toh ni ta sheɗan ce?" Na tambaya tsakanin dariya '' oho.. sai da safe;" '' Allah ya tashe mu da Alkhairi'' Daga nan babu wanda ya sake magana cikin mu sai dai ni ba bacci nake ba tunani nake nasan koda ace naji kamar ina son Khalil baso bane zai kasance kawai 🍁: Emotional dependency... Yauwa...zai kasance wannan kawai... saboda duk da bamu daɗe da haɗuwa ba shiɗin yana saurare na kuma bai taɓa... 🍁: judging Bai taɓa jojin ɗina ba duk da banyi abinda zai sa yayi hakan ba amma ina ji a raina shi na daban ne sai dai bazan iya sonshi ba na sani. maza da yawa sun faɗi abinda yake sa zuciya ta cikin ƙunci banda shi hakan zai sa inso kasancewa dashi wannan shine emotional dependency/, security duk da ban yi bayani da kyau ba... Waye zai soni a yanda nake? Mutane irina basa samun masoya wa'yanda zasu girmama su duk wanda ya aure su zai dinga ji kamar yayi musu babbar alfarma kuma zasu rayu cikin ƙunci da wulaƙanci...Hawaye suka fara sauka daga idona kafin na fara kuka ƙasa ƙasa dan na ɗauka Jay D tayi bacci '' meyasa kike kuka?" Tayi maganar tana juyowa sashe na,da hanzari na goge hawaye na '' b..ba kuka nake ba!" Amma muryata ta fallasa akasin hakan tashi zaune Jay D tayi, hannunta akaina '' Bee muyi magana '' runtse idona nayi ina taune leɓena kafin na tashi zaune ina share hawaye '' meyasa kike kuka?" Ta sake tambaya '' nayi kew...'' ''ba haka bane!" Ta katse ni..hakan yasa na ɗago idona suka shige cikin nata...ta riƙo hannu na '' naga yanda kike kallo na sanda ina gidan ku naga yanda idonki sukayi ja sanda kika fito daga wanka..naga yanda kike ƙoƙarin danne hawayen ki sanda kike gyara min gashi nasan yanda bakya son karanta littafai idan jarumar ciki tana da komai meyasa?" A wani irin slow hawaye na suke tsiyaya jin abinda take faɗa kafin suka fara fita da sauri sauri...ta matso kusa tare da riƙe hannu na ''kin tsani kanki saboda kina tunanin baki kai mace ba a yanayin halittar ki ba...! '' ta fáɗa a hankali bada hukunci ba sai da tabbatar wa ban taɓa faɗawa Jay D wani abu game da sef istim ɗina ba amma ta fahimta '' Ban san yanda zan yi ba...na kasa son kaina...ko wace rana ina ji na ƙara tsanar kaina ne... meyasa bazan zama kamar sauran matan ba? Meyasa addu'oi na basa faruwa? Meyasa nake a yanda nake? Meyasa baxan samu abinda nake so ba? Meyasa sai ni abubuwa ke ƙin yiwa aiki...kalle ni doguwa dani amma kamar ƙaramar yarinya kalli Asma'u na girme ta amma kamar itace yaya ta'' na faɗa ina rufe fuska ta da hannaye na...cikin kuka sosai Rungume ni Jay D tayi tana shafa bayana '' saboda keta dabance Abeedah, addu'oinki ba wai basa karɓuwa bane lokacine bai yi ba,ko me mutum xai yi idan har lokaci bai yiba,babu abunda zai faru...zaki sha mamaki idan lokaci yayi Allah ya fara baki abinda kike kuka akai yanzu'' Ta share min hawaye na,tana maganar a sanyaye '' ba lallai abinda kike roƙa ɗin a yanzu ya kasance alkhairi gare kiba,ƙila da yanzu kin zama mutuniyar banza..ƙila kuma Allah na shirya maki fiye da yanda kika roƙa ne ki dena ƙuntata kanki pls!" Nayi shiru ina sauraren ta '' na san yanda kike ji duk da, insecurities nada wuyar sha'ani amma kada ki bari hakan yayi sanadiyar dena farin cikin ki,kada ki tsayar da farin cikin ki wurin jiran abinda bai zoba har yanzu...nasan da wahala amma kiyi ƙoƙari ki dena kwatanta kanki da kowa... you're not them and they're not you!" ɗaura hannuna dake saman nata nayi ina kuka sosai '' amma Jay d ji nake kamar kowa yana yin gaba ni kaɗai ce a inda nake duk sanda naga wa'yanda suka fini nake ji wani irin nauyi a zuciya ta na dole nima sai na cimma su..'' tana gyaɗa kanta da damuwa sosai a fuskar ta tace '' na gane Bee,amma bakya buƙatar kiji haka...ba tserarra kuke ba, a rayuwa wasu suna samu da sauri wasu tsaka tsaki wasu kuma sai sunyi gwagwarmaya..abu mai muhimmanci shine a duk inda kake baka yi latti ba you're exactly where Allah wants you to be..nasan akwai wannan pressurize ɗin nason kamo wani but your time line isn't theirs and theirs isn't yours... kiyi rayuwar ki dai dai naki saurin,idan kika ce zaki yi rayuwar wasu...zaki cutar da kanki ne ki gajiyar da kanki kuma ki haddasa ma kanki ciwo a zuciya..ki kwantar da hankalin ki akwai Allah...!" '' ban san yanda zan kwantar da hankalina ba,koda yaushe zuciya ta rawa take kamar idan nayi tunani mai tsawo zan iya gano inda matsalar take...'' '' that's the problem! Babu matsala anan,zaki ji kamar idan kinyi tunani long enough you'll figure things out but in reality kina ƙara cusa kanki cikin damuwa ne kawai!" Mu biyun muka yi shiru,ta ƙara matsowa kusa dani, hannu na a nata '' let me help you,bakya buƙatar ki ɗauki komai ke kaɗai I'm here for you bee...ni zan taimake ki uhm?" ta miƙa hannu tana share min hawaye kafin ta rungume ni '' na gode!"... '' kina da kyau.. idan kika fahimci hakan zaki rayu cikin kwanciyar hankali da nutsuwa da wadatar zuci..rayuwar wasu ba taki bace Abeedah kowa da nasa lokacin uhm!" Na gyaɗa kaina bance komai ba +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 14. ... Anaam...🖊️ Washegari bayan munyi sallar asuba muna nan zaune muna tasbih har sai da rana ta fito mukayi salatul ishraq muka daɗa da karatun Alkur'ani na tsawon minti talatin Jay D sauka tayi dan haka da Qur'ani take karatu ni kuma hadda nayi da kai nake karantawa babu kuskure ko ɗaya Sai da ƙarfe bakwai sannan muka gama '' ina kwana Bee" ta gaishe ni duk data girme ni da wata ɗaya... Na faɗa saman gado ina kallon ceiling '' lafiya lau ya kike...?" Wani kallon tayi min kafin ta kwanta gefe tana jan kunne na tace '' cewa ake ina kwana,ni ƙanwar kice eh?" '' Haha toh bake kika ce ina kwana ba?sai in tambayi ya kike'' mukayi shiru na ɗan lokaci kafin na tashi zaune da yan kame kame nace '' jiya...Uhmm...kince zaki taimaka min taya?" Idonta dake lumshe ta buɗe kafin ta tashi zaune '' ta hanyar canja tunanin ki...'' Muka kafe juna da ido ta gyara zama haɗe da jan dogon numfashi '' zanyi ƙoƙarin yi maki bayani as best as I could...'' Na riƙe haɓa ina Kallonta gaba ɗaya ni abun ya fara ban haushi sannan zuciyata ta yarda da bazaiyi aiki ba,kuma ina jin hakan kamar wani babban nauyi ne aka ɗaura min a ƙirji '' kiyi tunanin...Uhmm ƙwaƙwalwar ki kamar gona Abeedah...kuma duk abinda kika shuka ai shi zai fito ko?" Ta tambaya '' ehemm!" Na faɗa da ƙatuwar murya cike da takaici '' oh...Kay....yi haƙuri kada ki haɗe ni!" Ta furta tana ɗaga hannu ido buɗe '' yanzu ki ɗauki tunanin ki a matsayin iri (seed)ace kuma kina so kiyi noman shinkafa amma sai kika ɗauki irin masara kika jefa cikin ƙasa yanzu me kika shuka?" Na juya idona bayan amsar a bayyane take tambaya irin wannan tana matuƙar ban haushi '' MASARA!!" '' kada ki fashe min dodon kunne akwai yanda za'ayi ki canja masara zuwa shinkafa?" Ta tambaya kamar malamar data kai ɗalibinta maƙura yanda baya da zaɓi sai dai ya bata amsar da take so Hmph! babu yanda za'ayi in bata amsar data ke son ji '' eh mana! Idan kika cire masarar kika mayar da irin shinkafa na!" “Exactly! Haka tunani yake. Babu yadda za’ayi in so in yi kuɗi amma a kullum tunanina yana cewa ba zai yiwu ba. Abin da nake so ya yi matching da tunanina da emotions ɗina. Akwai wasu signals da ƙwaƙwalwa ke turawa duk lokacin da mutum yake tunani—kamar signal na neman abin da yake tunani. Idan tunaninki kullum na baƙin ciki ne, abubuwa marasa kyau za su ci gaba da faruwa; idan farin ciki ne, abubuwa masu kyau za su biyo baya. Ƙwaƙwalwa ba ta bambance daidai da ba daidai ba, kawai umarni take bi. kina fahimta?” Ta dakata tana kallona, ganin na yi zugum, amma ban ma san ko na fahimta ba. Sai ta ci gaba, “A sauƙaƙe, Bee, ki sauya tunaninki daga negative zuwa positive. Idan kika canja tunaninki, komai zai canja.” Ta riƙo hannu na cikin nata '' ki gwada koda na sati ɗaya ne kiyi ta tunanin abu mai kyau kinji!" Hm...kamar abun yana da sauƙi taya zan yi tunanin abu mai kyau bayan babu wani abu mai kyau dake faruwa dani? Rayuwa ta a wani irin birkice take babu abinda nake ganewa kuma taya zan bar duk munanan abubuwan dake faruwa kamar babu komai? Bayan ni bana son haka kawai mutum ya kasance mai gaskiya da kowa da komai harda kanshi '' zan gwada!" Na faɗa bawai dan ina tunanin hakan zai yiwu ba... '' yauwa Bee... Allah ya taya ki!" '' Ameen!" Na amsa a taƙaice.... Sai ta sake ni ta shiga baye ta haɗa min ruwan zafi '' tafi kiyi wanka bari inje in gani idan an gama abun kari '' ta fita daga ɗakin ajiyar zuciya na sauke na shiga bayen raina a wani irin ban ma sani ba Kayan jikina na fara cirewa a gaban madubi na tsaya ina ƙare wa kaina kallo tun daga kaina dake ɗauke da shuku tsoron yayi tsaye a tsakiyar kaina tsabar taurin gashin gira ta kamar aske wa ake kullum gashin idona ma haka shegun pimples ɗin nan kamar ƙara kiransu nake sun dabaibaye min fuska babu wani wuri a fuskata da babu pimples, goshi,hanci,ƙarƙashin haɓa,kumatu da sauran wurare wasu sun mutu sunyi baƙi ash ɗin idona ya ƙara duhu Na kalli ƙirjina kamar in make wurin meyasa yake ban wahala har haka? Bayan abune da kowace mace ya kamata ace tana dashi meyasa nawa suke jan jiki wurin girma?kawai dan su ƙuntata min dan sun ga ina son su... Nayi ƙasa da idona zuwa sauran sassan jikin nawa ba gaba ba baya a haka Jay D ke faɗar in sauya tunani na zuwa fozitf.(positive) wai sun ɗauka akwai sauƙi ne? Suna tsammanin nima ina jin daɗin yanda nake? Wasu zasu iya kallon abinda bai masu ba(flaws)su ɗauke ido wasu kuma idan suka ga abinda bai musu ba(Flaws) hankalin su bazai kwanta ba har sai sun gyara baxan iya cigaba ba har sai na sauya wannan abin dake tattare dani(flaws)dan ni Abeedah ina cikin sahun mutane na biyu Sosai hawaye suke sauka daga idona kamar an buɗe pamfo nabar gaban madubin na shiga cikin ruwan data haɗa min nayi amfani da sabulan ta na ruwa nayi wanka sosai Harda kaina na wanke Bayan na fito na tsaya gaban madubi na shafa man da muka shafa jiya na ɗauki riga da skirt daga kayan dana zo dasu na saka.na fesa turarukanta ban shafa man bakin dana gani ba dan ina ɗaukar shi a matsayin kwalliya amma ni zan fara kwalliya ne idan na samu na gyara (flaws) ɗina... 🍁: Allah baya kuskure wurin halitta Abeedah... '' nasani ai...'' 🍁: TOH me kike ƙoƙarin canjawa? '' abinda na gama magana akai...'' '' baki da aibu you're flawless.mutane kawai su suke ganin aibun wani bayan basu ne sukayi halittar ba kiyi haƙuri ki zama mai ƙwarin guiwa mai self esteem da self lovenzaki gani kina da kyau kuma zaki karɓi kanki a yanda kike kuma zaki fi kasancewa cikin farin ciki...'' '' sauƙin faɗa ke dashi bake ce niba oti... baki san yanda ake jiba baki san irin kunyar da nake shiga ba baki san dararen da nake kasance wa ido biyu ba baki san irin gajiyar da nake yiba wurin tare gaban hijabi na ba idan ina tafiya bakisan irin faɗuwar gaban da ke riskata ba abduk sanda nazo wucewa inda akwai maza ba bakisan yanda na parka farin ciki na gefe ba ina jiran ranar da zan zama cikakkiyar mace lokacin kaɗai zan cigaba da farin ciki kada kiyi magana baki san yanda ake jiba ko kaɗan!!!!!'' '' lafiyar ki kuwa?" Jadeedah dake tsaya daga bakin ƙofa ta faɗa tana kallo na daga sama har ƙasa sai kuma ta dafe kumatun ta '' oh my Bee baki ga yanda kika yi kyau ba...'' tazo ta tsaya gefe na saye da rigar material kore sosai tayi kyau sai ƙamshi take murmushi nayi mata ''.na gode '' kwalli ta ɗauka tana ƙoƙarin shafa min '' a'a ni bana so..'' Bata jini ba sai data shafa min harda man bakin...ta tsaya baya na hannun ta a kafaɗu na,nikam ko kallon kaina banson yi '' kalli yanda kikayi kyau dan girman rabbi amma mata kullum da ido kamar tsohuwar mayya ɗago ki kalli kanki mana!" Ta faɗa da murna badan naso ba na kalli kaina ɗin nima nayi mamakin irin kyau'n da nayi sai dai duk da haka an fini kyau idona sai ƙyalli suke sun ƙara fitowa sak na mage ash ɗin ciki ya ƙara duhu turo baki nayi ina matsawa daga bayan ta '' ba kamar keba'' na bata amsar da basarwa kafin na matsa bakin taga ina kallon waje yau asabar koya su Mama suka ji babu ni? '' zaki canja '' '' mutafi mu karya!" saukowa nayi muka fita tare a dani muka iske maman su hakan yasa na kai har ƙasa na gaishe ta ta amsa da fara'a tana ta yabon kyau'n da nayi duk kunya ta kamani abin kari lafiyayye muka karya dashi bayan mun gama muka yi wanke wanke Maman su ta wuce ɗaki muka koma parlor nida Jay D inata kallon ko ina,sai ƙamshi ke tashi kuma ko ina tsab tsab... Bayan tv'n ta kawo...tashar yan china ta fara sawa ganin ba wani abun kirki ake ba ta kalle ni '' zaki kalli MSA?" Da rashin fahimta nace '' Meye MSA?" Ta miƙe daga inda muke zaune tana faɗin '' yan katun ne (cartoons) kuma yana da kyau wallahi.. yaran iyakar su shekarun mu suma amma da turanci ake magana '' canja setting ɗin Jay D tayi daga Netflix zuwa You tube ta dawo ta zauna kusa dani.tayi rubutu inda akwatin nan me cokali (, search 🔍 box) Sai ga shi ya fito da yawa Ta ɗauki ɗaya tasa muka fara kallo babu abinda nake ganewa ita take yimin bayani duk da haka sosai katun ɗin ya ƙayatar dani musamman yanda koda yaushe daga ƙarshe suna samun masoya da kuma yanda suke ƙawance da kuma komai da komai a cikin katun ɗin... Kafin in sani nima na fara son abun... Can ta tafi kitchen ta dawo mana da abubuwan ciye ciye bayan mun gama ta fita dani daga parlorn tana nuna min ko ina na gidan...muka zauna cikin lambun su muna wasa da fulawowi... Rayuwa a gidan su Jay D kamar wata duniya daban ne, lokaci na saurin wucewa,kafin kwanaki uku suka ƙare na koyi abubuwa da yawa harda yan kalmomin turanci sannan na gane ba duk masu kuɗi bane marasa mutunci ba kaɗan ba Jay D tayi ƙoƙarin ganar dani abinda take kira self love da self esteem (yanzu na iya faɗan kalmomin da kyau😅) Kuma na fara koya fata ta tayi kyau da haske ranar Monday bamu je makaranta ba da yamma na shirya komawa Jay d kamar zata yi kuka sai kallona take a marairaice...nima dai kamar zanyi kukan wani ƙaramin akwati maman su ta siyo min,aciki akwai kaya atamfa guda biyar sai materiyal kala uku da shadda suma kala uku turaruka kala uku da singilet kusan guda biyar irin masu tsayawa a rabin ciki da kuma fararen turarukan da ake amfani dasu idan an gama al'ada,da hijabai suma guda uku Duk ta bani inata godiya da addu'oi kamar zan kife ita dai sai murmushi take Bayan nan harda atamfofin da ba'a ɗinka ba da wasu turarukan na gida dana jiki ta bani in kaiwa Mama da ƙarfe biyar da rabi muna tsaye bakin mota idon Jay D sun ciko da hawaye ta rungume ni '' sai nazo Bee...dan Allah kizo makaranta gobe kinji?" Nima idona da hawaye na rungumet '' zan zo...'' muka rabu na kalli ranar data kusa faɗuwa sannan na kalli Jay D sosai nake jin kaɗaicinta kuma nima ina cikin shi taban tausayi kamar in jawo ta mu tafi tare na sake kallon ko ina na gidan musamman lambu da inda akwai pipe ɗazu da safe kamar bamu zo nan munyi wasa da ruwa ba... Bye bye mukayiwa juna ta buɗe min ƙofar na shiga sannan ta rufe motar ta fara tafiya tana tsaye a wurin dana barta na cigaba da kallon ta har saida muka fita daga gidan duka naji kamar an tona rami an barshi buɗe a cikin zuciya ta naja dogon numfashi kewarta na mamaye ni... nayi ƙasa da glass ɗin motar ina kallon ranar data zama ja,iska mai sanyi na kaɗawa dogayen bishiyoyi inuwar su tayi wani irin tsawo lokacin da muka kawo inda trapic inata kalle kalle ina kallon yaran nan masu sayar da abubuwa yanda suke gudu nan da can yanda suke magana da ɗaga murya da kuma yanda muryoyin mutane ke nesa nesa kowa yana ta harkar gaban shi wasu suna dariya wasu suna tsallaka titi kowa da nashi a rayuwa farin ciki zaɓi ne a duk yanda kake zaka iya zaɓar farin ciki ko akasin hakan...amma nidai Abeedah ban yarda ba Ƙarfe shida da minti goma muka kawo ƙofar gidan mu, ƙarƙashin bishiyar kaiwa direba ya paka..nake kallon yaran dake wasa a filin dake nesa kaɗan da gidan mu sai kuma na ƙara jin ina kewar Jay D,direba ya fito ya fara cire min kayana ya shigar min dasu har zaure fitowa nayi sanyin marece na duka na da ƙarfi '' na gode sosai '' yayi murmushi '' ba matsala '' sannan ya shige motar shi yabar wurin Na daɗe tsaye a wurin ina jin kewar Jay D sosai kafin na shiga gidan '' kewai Asma'u Matsala ta dake kin cika laƙaita.. mata kamar baki da jini a jiki mtschewww!" '' toh keda kike da jini ai da kinyi ke kaɗai!" '' kada dai kice zaki gayamin magana yanzu in gyara maki zama wallahi!" '' Toh kyanwa da ɓera... Bismillah marece yayi ko?" Muryar da take kamar ta Mama kamar bata Mama ba ta katse su biyun ko su waye? Akwatina na fara ja tare da buga sallama daidai ana dawo da wuta da ƙarfi '' wa'alaikumussalam '' nayi tsaye a wurin ina kallon matar data amsa min baki sake daidai nan Mama ta fito daga baye '' A'a Tuwo kin dawo...'' sakin akwatin nayi na isa na rungume Mama inaji kamar zanyi kuka Mama tana dariya tace '' ai na ɗauka kin manta damu...'' batareda na ɗago ba na girgiza kaina '' shin wai dama Abeedah ce? Na ɗauka ai wata baƙuwa ce akayi!" Inji inna Sarai ƙanwar Mama sai na saki Mama na isa wurinta ina murmushi kamar bakina zai cire gefenta na zauna '' wai kece?'' '' a'a bani bace uwarki ce...''ta bani amsa tana harara ta '' da gaskiyar ki ƙanwar uwa itama ai uwace...'' na faɗa ina dariya sosai nake jin farin ciki '' har yanzu kina nan da rashin kunyar ki ko?" Ta tambaya tana tiƙa ta....na turo baki...'' ina Anaam?" '' gani nan munafuka kike wani tambaya kamar kin damu!" Doguwar yarinyar mai zubin fulani ta amsa min da jin haushi a muryarta tana harara ta... Ban kalle ta ba..na isa wurin Asma'u dake kusa da ita na rungumeta '' nayi kewarki Asma'u '' '' nima '' ta bani amsa da jin daɗin daba ta nuna shi ba da daɗewa.... Bayan nan Mama taje ta zauna a baranda..Ni kuma na jawo akwatin da sauran abubuwan da Maman su Jay D ta bani na nuna mata..sai albarka take sawa...sai da na buɗe akwatin naga bandir ɗin dubu dubu guda biyu nayi mamaki sosai gashi niba waya ba balle in kira in yimata godiya dan nasan ita tasa su.... Asma'u da Anaam suna ta kallo baki sake dan komai dake cikin akwatin duk da sauƙin su a ido,kuɗin su idan mutum yaji sai ya riƙe baki nan nake ta basu labarin gidan girman shi da kuma kayan more rayuwar dake ciki da kuma yanda mamansu take kyautata min... '' kuma a haka yarinyar bata da girman kai ko nuna ita wata ce'' mama ta faɗa '' ai nima nayi mamaki ba kaɗan ba Allah dai ya barni da Jay D...'' '' Ameen...'' suka amsa... Anaam tabar wurin ta shige ciki tana kallo...tashi nayi nima na wuce kitchen na ɗaura ruwan zafi... sannan na dawo nace ma Asma'u ta ɗauki abinda take so....naba mama kuɗin... Da Isha'i ina ɗakin Mama kwance a cinyarta bayan na gama sallah nan take faɗa min ashe ranar dana tafi ranar suka zo da ƙarfe taran dare...auren Inna sarai ya mutu da mugun mijinta kuma yace shi bazai riƙe Anaam ba sai dai ta tafi da ita dama Mama ita kaɗaice dangin data rage mata shine yasa suka rankayo nan nidai naji daɗin kasancewar su damu duk da waccan Anaam ɗin yar rainin hankali ce kuma shekarun mu guda da ita mata kamar tabi iska amma sai shegen tsiwa... '' yanzu kenan mun dena kwana tare?" Na tambaya ina tashi zaune '' toh ko saman wani daga cikin mu zaki dinga kwantawa?" Inna sarai dake shigowa cikin ɗakin ta tambaya tare da zama bakin gado tana harara ta '' nidai da Mama ta na saba kwana!"nayi maganar ina turo baki '' TOH ai sai kixo ki ture ni daga saman gadon ki kwanta ko kuma ki shige cikin cikinta...'' Na miƙe tsaye ina buga ƙafafuna nayi ƙofa ina faɗin '' toh ki buɗemin cikinta ki gani in ban koma ba!" Ta ɗauki pillow ta jefe ni dashi nayi saurin kaucewa ina ƙunƙuni...Mama dai bata tanka mana ba...na wuce ɗakin mu, iske su nayi suna magana, suna gani na suka yi shiru kamar sunga munafuka..ban bi takansu ba na wuce na kwanta ina jin kewar Jay D..gashi banida waya da number ta dana kira ta '' Ibrahim yazo sanda baki nan..'' Naji muryar Asma'u banyi niyar tanka ta ba nayi shiru na cigaba da tunani na '' daga zuwa gidan masu kuɗi zaki ari halinsu ki yafe,wahala zaki sha wallahi..'' inji Anaam itama banyi niyar amsa mata ba amma kafin in iya hana kaina nace '' muryar ki tana jima kunnuwa na ciwo..shirun ki shine alkhairi pls'' Asma'u ta juyo dan kawai nace pls murmushin gefen baki nayi da basu gani ba...Anaam kuwa kamar zata kama da wuta... Asma'u ta ɗaura hannun ta a kafaɗar ta tana tausar ta can suji dashi '' nace Khalil yazo '' ta maimaita ganin na farko ban amsa ba '' ba kurma bace Ni!" Daga nan ban sake tanka masu ba tun ina jinsu sama sama har bacci ya ɗauke ni washegari Litinin bayan mun karya wanka nayi na fito ɗaure da zane saye da hijabi na shigo ɗaki nabar su zaune a baranda banda Anaam dake cikin ɗaki itama tana shiri share ta nayi na jawo uniform ɗina ina sawa na saka wando da singlet zan saka riga naji tana faɗin '' mace kamar na miji ba gaba ba baya tabɗi jam ni da ace na miji ce ko kyauta baxan karɓa ba!" Sosai maganarta ta dake ni amma nayi kamar ban jiba ita da Asma'u haka suke idan suka haɗu suyi ta yimin wulaƙanci suna ƙuntata ni dan kawai sun ga ina biye su ina nuna baƙin ciki na banda yanzu zama gidan su Jay D ya canja ni koda kaɗan ne '' ke idan ana harka da muta ne..ki dena shigowa...babban zagi ne ga jinsin mutane...'' ta tashi zaune daga kwancen da take '' kina nufin niba mutum bace? To wacece ni?" Na saka farar rigata da hula na fesa turare mai daɗin ƙamshi na juyo ina kallonta da idona dake a ƙanƙance na yan sakanni kafin na sauke ajiyar zuciya na zauna bakin gado ina sa safa nace '' yanzu ma da nake ƙoƙarin gano a wane sahu kike..idona har sun fara ciwo..dan ke dai ba mutum bace..sannan kiranki dabba..babban cin zarafi ne ga dabbobi!" Na miƙe nabar ɗakin da murmushi ganin fuskarta tabini da ido cikin rashin gasgata abinda kunnuwanta yaji ta saba yaɓa min magana sai dai inyi shiru ina kuka amma wai yau shine na bata amsa mai zafi...lallai '' Ke Anaam ki tashi ki shirya mu tafi makarantar su a miki rijistreshon!'' inna sarai ta leƙo ta faɗa ma Anaam dake kwance zuciyarta a maƙoshi saboda abinda Abeedah tayi Mata ''ni sai wani tam (term) zan shiga makaranta!" Tayi maganar tana juya baya kamar an jefo inna sarai ta wani irin tiƙe ta a baya da tafin hannu Anaam ta zabura kamar akuyar da aka zuba ma ruwan zafi tana soshe soshe fuska a kwaɓe '' idan ina magana kina magana sai na dinga saɓa maki dalla jeki yi wanka In ma haka zaki tafi da warin jiki ke kika sani!" Tana kaiwa nan tabar wurin..Anaam ta fara kuka ƙasa ƙasa kafin ta fito daga ɗakin sum sum ta wuce bayi '' Mama xan fara neman aiki fa...daga yau '' na faɗa ina karɓar kuɗin break '' aikin me kuma? Kuɗin da muke dasu sun isa ba saikin nemi aiki ba...'' Na girgiza kaina nace '' kuɗin zasu ƙare musamman yanzu da muka ƙaru sannan kuma ni bana son zama haka kawai..nafison ace ina da aiki...'' '' ke uwar son aiki...ai saiki tayi...Uhmm na manta ban faɗa maki ba...yaron nan.. Ibrahimu yazo...'' har zan fita na juyo '' waya kawo shi? Mema yazo yi?" '' wani yaro daga tsohuwar unguwar mu ya kawo shi...harda jikunkunan shinkafa dasu mai ya kawo mana..ya bada kuɗi duk da banso karɓa ba...'' na sosa gefen fuska ta ina tunani sai kuma na juya nace '' an gode amma Mama in faɗa min kike Dan kada in nemi aiki..gaskiya dai...'' '' wane mutum? ai tunda kika ce zaki nemi aiki ban isa in hanaki ba...''nayi dariya tare da fita daga ɗakin Na samu inna sarai zaune tare da Asma'u tana kama mata gashinta na zauna daga gefe ina kallonsu '' Nasan Tuwo ji take ina ma ace itace da wannan gashin ko?" Asma'u tayi maganar tana ɗage min gira da murmushin gefen baki '' wai ku har yanzu baku canja da wannan halin nason ƙuntata ma baiwar Allah bako?" Inna sarai ta dakata kaɗan '' ita dai take son ƙuntatawa kanta ba kowa ba...''Asma'u ta amsa ta..ina murmushi nace '' dana ga gashin Jay D na tabbatar da naki ashe sheƙar tsuntsaye ne,inna sarai gashin Jadeedah har mazaunai kuma baƙi wulik ga laushi ga ƙanshi mai daɗi ba irin na Asma'u ba da ake wata da watanni bai ga ruwa ba duk wari yabi ya ishe mutane'' Asma'u ta ƙwace kanta daga inna sarai tana kallona baki sake inna sarai tana ta dariya ''.kice kema kin koyo yaɓawa mutane magana'' Asma'u ta katse tada faɗi '' amma ai nan kike kina santi...'' '' dane kai bai waye ba amma yanzu da kaina ya waye ji nake kamar in ranƙwashi kaina dayake dai rashin sani yafi dare duhu...'' Asma'u take harara ta kamar idonta zai faɗi ta miƙe tabar wurin fuuu tare da jan tsaki na ɗauke kaina Ƙarfe bakwai da arba'in muka bar gidan mu huɗu harda Inna sarai da Anaam dake ta cin magani mu uku muna ta hira har muka kawo makaranta har anfara tare latti daƙyar aka bar mu muka wuce bayan inna sarai ta roƙa mana gafara kamar wasu fursunoni (prisoners) aji muka wuce su kuma suka tafi ofishin pirinsipal Math ne cikin ajin hakan yasa ko ina ya ɗau shiru kamar sunga mala'ikan mutuwa nima kaina dai tsoron mutumin nake nayi tsaye a wurin ina kallon Jay D da ita bata ma lura dani ba badaɗewa yan ajinmu suka taru da yawa a waje '' ehen meye ne?" Ya tambaya da ƙatuwar muryar shi yana kallon mu da jajayen idonshi '' anan ajin muke'' Hameeda ta faɗa cikin rashin damuwa dan ita dama bata tsoron duka ko kaɗan '' in roƙe ku ku shigo ne?" Ya tambaya da ɗaga murya da sauri sauri aka fara shiga aji Ni ban ankara ba jin tambayar da yayi yasa nace '' hakan ma dai dai ne!" Maganar ta sauka a kunnen shi yan aji ma sunji '' dan Ubanki zo nan!" Ya faɗa yana jawo hijabina ta baya saura kaɗan in faɗi na tashi tsaye da kyau ina ƙwalalo ido ''.maimaita abinda kika faɗa'' nayi tsuru da ido tsoro ya cika ni yan aji suka bimu da ido '' b...ba..n..ce komai ba...'' sai da yayi min kallon sama da ƙasa kafin idonshi ya sauka cikin nawa ya ja baya ''ke mayya ce?" Ya tambaya da rainin wayo '' a'a sunana Abeedah ba sumayya ba'' na bashi amsa nima da rainin wayo kafin yayi magana sai ga exam master ya faso kai aka tashi wurin gaishe shi hakan ya bani damar tserewa ya bamu izinin zama kafin ya shiga dogon zance akan waec dake ƙaratowa bayan ko rabin term ba'a kai ba yana ta zance har piriyod ɗin mas ya ƙare na gode mashi sosai...IRS...macijin sari ka noƙe ne ya shigo gaba... '' goooood morrrrrrni saaaa '' yan aji suka gaishe shi nidai miƙewa kaɗai nayi da wata yar iskar murya yace '' morning how' you?" '' fayyyn tank yuuu saaaa'' abu kamar suna waƙa zab ban takaici '' ku zauna '' ya faɗa da rubuta kwanan wata da sunan subject ɗin '' ba magana Bee?" Jay D ta faɗa murya ƙasa bayan mun zauna '' ban shirya amsar bulala da safen nan ba'' na bata amsa nima murya ƙasa ina jin haushin Mutumin nan har cikin raina...yan matan suka nutsu na girgiza kaina '' excuse me uncle saminu munyi sababbin baƙi'' Malam murtala ya faɗa tare da shigowa yayi ma baƙin alamun su shigo ciki,zamu sake tashi mu gaishe shi yace mu zauna macijin sari ka noƙe ya kafe baƙin da bamu san ko waye su ba da ido dan sun ɓoye bayan malam murtala '' class monitor?" Ya kira yana kalle kalle da sauri ta fito ta tsaya gaban shi '' ga baƙi idan malamin ku yazo sai ki nuna mashi su a sa sunan su a rijista '' ta gyaɗa kanta yayi ma macijin sari ka noƙe godiya sannan ya tafi Sai lokacin naga ashe Anaam ce da wata bafilatana kai!! da duk ajujuwan dake makarantar sai ajinmu za'a kawo ta Innalillahi na ɗaure fuska ganin yanda yake binta da ido ƙasa ƙasa yana lasar baki, saye take da riga da skirt da suka kama ƙugunta da mazaunan ta.. dan tana dasu ma sha Allah amma itama ƙirjinta kamar nawa..nata ya ɗanfi nawa girma.. farar fata,ƙaramar fuska manyan idanu da dogon hanci ƙaramin baki wanda kalar take pink gashinta irin na Asma'u. doguwa ce itama bata da ƙiba... Hijabinta fari zuwa guiwa hannunta riƙe da jakar leda da littafai a ciki fuskarta kamar zatayi kuka Ɗayar kuma dogon hijabin ta ruwan ƙasa ya ɓoye kayan dake jikinta har ƙasa yake kanta ƙasa.amma dai fara ce sosai kamar zabiya... '' zoku zauna!" Class monito ta faɗa tana nuna masu wuri....'' yarinyar can kyakkyawa'' Jay D ta faɗa a kunne na tana nufin Anaam '' sai shegen tsiwa '' na bata amsa '' kin santa ne?" Kafin in bata amsa naji yana faɗin '' baƙi su gabatar mana da kansu ko?" Anaam ta kalli macijin sari ka noƙe...sai ta ɗauke kanta da wata ƙaramar Muryar munafunci tace '' Sunana Sha'awanatu Is'haq Anaam '' Yan aji basu ce komai ba amma na tabbatar kowa da magana a bakin shi..ɗayar baƙuwar kuma da sanyayyar murya mai daɗin sauraro tace '' Safiyya Muhammad Diyaam''.ya ɗauke kallon shi daga Anaam zuwa Diyaam data mayarda kanta ƙasa bayan ta gama gabatarda kanta,Ma sha Allah kyakkyawa ce sosai tana da gashin gira baƙi mai yawa..ga gashi kwance a goshinta....itama bakinta ƙarami laɓɓanta jajaye '' Ma sha Allah Sha'awanatu da Safiyya..kuje ku zauna..'' yayi maganar yana nuna masu seat ɗin mu nida Jay D,da kuma wanda ke gefen mu,dama mukaɗai ne zaune mutum biyu.Anaam taci magani da idon mu ya haɗu..na ɗauke idona daga kallonta Seat ɗin gefenmu ta zauna hakan ba ƙaramin daɗi yayi min ba ,'' matsa mata ta zauna mana!" Inji macijin sari ka noƙe ni nayi nisa cikin tunani ita kuma yarinyar tayi min tsaye a kai maimakon tace in matsa wasu mutane dai...!! Jay D ta fara matsawa sai nima na matsa ta zauna a hankali tana ajiye jakarta mai hoton yan matan nan masu dogon gashi 🍁: Disney princesses Izini parinses...sosai jakar tayi min kyau amma ta Jay D da take baƙa tafi kyau Bata ce mana komai ba muma ba muyi mata magana ba yana koyarwa idonshi na yawo tsakanin Anaam da Diyaam shiɗan abinda ban ceba... '' na kawo mana abinci yau '' Jay D ta faɗa muna coper note daga allo '' har naji ina jin yunwa '' amsa mata... tayi murmushi '' ranar da kika tafi kamar inyi hauka...'' '' nima nayi kewarki s....'' '' Abeedah Abdul wahhab Jadeedah Ahmad ku tashi tsaye!" Inji macijin sari ka noƙe yan aji suka bimu da ido kamar basu san muba tsabar gulma da tsegumi Miƙewa mukayi muna cigaba da maganganun mu da rubutu a paper... Ya juyo yana kallon yan aji yana musu bayani sai sintiri yake a layin mu...kai!! Allah ya wadan naka ya lalace... Koda aka tashi break riƙe mu yayi wai zai mana test....sosai nake ji kamar in shaƙo mugu '' ku zauna '' ya faɗa Jadeedah harda godiya Bayan ya gama rubuta tambayoyin ya samu ya zauna saman desk ɗin wasu yan mata bayan ya Kore wacce bata da kyau a cikin su,ya ɗaura ƙafar shi inda ake zama ya wani buɗe ƙafafu zaman iskanci Duk wanda yaga yanda yayi zaman zai ɗauka nomal abune amma Ni Abeedahtuwo nasan akwai manufar hakan ... '' malam zan iya shigowa?'' Asma'u da bata san kowane malami bane ta nemi izini.. batareda ya kalli ko wacece ba yace '' shigo '' Anaam na ganin Asma'u ta wage baki tana murmushi Allah ya gani ita babu abinda ta gane ga yunwa dake cin hanjinta Asma'u na murmushi ta ƙarasa seat ɗin su Anaam '' Allah ya kawo min ɗauki.. dan Allah tayani rubutun nan dan ban gane ba kuma ban san amsar ba...'' sai ta matsa ma Asma'u ya kasance su huɗu ne a seat ɗin dukansu babu wanda yasan komai... '' ke kin matse mu!" Wadda ke ƙurya ta faɗa tana ya mutse fuska.. sharply Anaam ta kalle ta '' nasan babu abinda kika sani dan kin samu za'a taimake mu shine kike yimana baƙin ciki ko?" Ɗayar ta kalli yarinyar dake ƙurya fuska ba annuri tace '' kiyi shiru dalla...tana gamawa zata tafi ai...'' Asma'u ta fara rubuta amsar suna kwashewa...ɗago kanshi yayi daga wayarshi da yake latsawa suka sauka akan Asma'u... '' ke me kike yi a nan?" Ya tambaya da ƙarfi yana cin magani..sai lokacin Asma'u ta lura da shi '' n..na..t..nemi izini...'' tayi maganar a rarrabe '' zoki fita!" Ya faɗa a fusace yana hararar ta ta miƙe sum sum ta fita daga ajin ya fesar da numfashi mai zafi kafin ya koma ya zauna.... Na taɓe bak Juyowa inda sabuwar yarinyar nan take nayi naga rubutun mu iri ɗaya dukan mu a seat ɗin yanda take rubutun a nutse a kuma a hankali Na ɗauke idona na mayar akan nawa paper da Hausa nake rubuta amsoshin duk da kuwa zan iya kwafa wurin Jay D amma dai na fison inyi da kaina minti goma yaci cikin break ɗin mu sannan yace wai a zo a dinga submitting ɗaya bayan ɗaya matan suka yi tururuwa a gaban shi suna botsare botsare gaskiya basu da kamun kai Anaam ce ta ƙarshen kaiwa yake binta da wani matsiyacin kallon ƙasan ido kamar in sa biro in tsikare shegun idon nan nashi .. '' class monitor zoki taya ni ɗaukar wa'yannan papers ɗin'' yayi gaba yarinyar biye dashi '' ɗan iska '' na faɗa murya ƙasa.yana fita aka fara surut wasu suna gulmar Anaam akan yanda tayi magana da kuma yanda itace ta ƙarshe wurin kai paper ta ita kam ko ajikinta na kalli window naga ashe akwai hadari kaɗan sai kuma masu sayarda abubuwa mutane sun dabaibaye su Na juyo na kalli baƙuwa daidai itama ta juyo idon mu ya haɗu na zaro mata idona '' Innalillahi!'' ta faɗa dafe da ƙirji nida Jay D muka yi dariya '' Tuwo samin wannan a jakar ki dan Allah '' Anaam ta faɗa tana turo min littafanta '' salan jakar ta katse ko? ban sawa!" '' mtchewww... Matsala ta dake baki da mutunci..'' ta faɗa tana juya ido ta ƙara da faɗin '' ina ne ajin su Asma'u?" Share ta nayi... '' kin santa ne?" Jay D ta tambaya '' ɗiyar ƙanwar Maman muce...'' '' cousin ɗinki ce kenan?" '' koma me hakan ke nufi, eh '' Bata ce komai ba ta jawo wata jakata fito da babbar kula '' su Jadeedah me aka kawo yau kuma?" Habeeba ta tambaya miƙa masu kular tayi tace '' gashi dukan ku kuje kuci '' sai ga yan mata da yawa sun yo wurin seat ɗin mu,kafin habeeba ta karɓi kular wasu sun rigata a wani seat ɗin ƙarshen aji suka tafi duk mutanen dake ajin ƙalilan kaɗai ne basu tafi ba kan kasani sai gasu suna wasoso hannu baka hannu ƙwarya suna zage zage..wasu an ɓata masu hijabi '' me kika kawo masu?" Na tambaye ta '' kaza,zo muje wurin masallaci '' ta miƙe tare da ɗaukar jakar baƙuwar na ganin zamu wuce ta miƙe ta bamu hanya '' zo mu tafi..'' tayi maganar tana kallon yarinyar sai da taɗan yi jim na yan sakanni kafin ta ɗauki jakarta ta biyo mu '' Anaam mu tafi '' na kira ta ganin tayi zaune '' ai na ɗauka kin manta dani!" Ta faɗa da gatse ban tanka ta ba... ''.mun gode Jadeedah.. Allah yabar ƙauna!!" Yan ajin suka faɗa ta window... cike da jin daɗi '' Ameen '' Jay D ta amsa..hannunta riƙe da nawa.. Mu huɗu muka jero muna tafiya...'' ranar kina tafiya Deen ya dawo da daddare...'' ''.yayan ki?" Na tambaya duk da nasan shiɗin take nufi '' a'a ubana!" ta amsa dajin takaici kamar zata kaimin duka ''haha Jadeedahtu Jidderh ƙawar Bee...'' muka yi dariya nida ita Anaam taja tsaki '' ashe kice Jadeedah?" '' baki da kunnuwa ne? Baki ji abinda kowa yake kiranta ba?" '' kewai tuwo naga sai wani zaƙewa kike daga kinje gidan su kin dawo ita ɗiyar masu kuɗi ce ke ko da kike ɗiyar talakawa wahala zaki sha in gaya maki toh yayi'' zan bata amsa Jay D ta hanani hakan yasa nayi shiru ina jin haushi sosai... Yarinyar nan kuwa shiru tayi kamar babu ita a wurin..duk inda muka wuce sai ayita kallon har muka iso wurin masallacin ba kowa muka zauna saman dakali sai ga Asma'u tazo itama ta zauna tare da mu Anaam na ganinta ta fara zuba kamar pamfo Kular ta ciro ta ajiye tsakiyar mu sannan ta ɗauko ruwan gora ta wanke hannunta ta miƙa min,na wanke na miƙa ma baƙuwar yarinyar..saita girgiza kanta alamun bazata ci abincin ba..na ƙanƙantar da idona '' kina tsorata baiwar Allah '' Asma'u ta furta '' ni ba mayya bace bafa... kuma idan naba mutum abu dole ya karɓa'' na riƙon hannun ta na wanke mata tayi tsuru da ido... hannunta da laushi kamar auduga '' ji bala'i..ana dole ne?" Anaam tayi maganar share ta nayi na miƙa ma Asma'u ta wanke hannunta taba Anaam Nina buɗe kular wani irin dadɗaɗan ƙamshi ya ziyarci hancin mu lafiyayyen farfesun kaza ne daya ji haɗi... '' Bismillah '' Jay D ta faɗa masu kowa ya saka hannu banda baƙuwa..share ta nayi ganin yarinyar yar rainin hankali ce sai da Jay D tayi ta roƙon ta kafin tasa hannu na taɓe baki sosai kazar tayi daɗi '' na gode'' yarinyar ta faɗa da kaji maganar ta kasan yar fulani ce '' Meye sunan ki?" Asma'u ta tambaya tana kallon yarinyar daga sama har ƙasa duk da zaune take '' Diyaam '' ta furta a sauƙaƙe..oh..kawai Asma'u ta faɗa...bayan an koma break Jay D ta kwashi littafan ta ta arama yarinyar wai taje tayi note nidai na taɓe baki kawai '' baki ban littafin ba'' nayi maganar ina kallon waje '' na duba ban san inda ya faɗa ba..kodai Deen ya ɗauka?" '' tambaya ta kike?" Na amsa fuska ɗaure '' mamaki nake...'' ta faɗa hannu sama kamar me saranda (surrender) Lokacin da aka tashi mu biyar muka jera muna tafiya harda sabuwar yarinyar data ƙiyin magana kamar tana jin tsoro kuma duk mun fita tsawo...ƙila bazata wuce shekaru sha biyar ba.da muka fito bakin gate wata baƙar mota mai baƙin glass ke jiranta bye bye tayi mana sannan ta wuce na ɗauka salin alin zata tafi batare da tayi mana magana ba ganin abin kamar yana mata wuya su Jay D sai ɗaga mata hannu suke abun yaban haushi Muka cigaba da tafiyar mu muna hira kamar kullum.... '' Hamma ina yini...'' ta gaishe dashi bayan ta zauna cikin motar da ƙamshin turarenshi ya dabaibaye. batareda ya ɗago daga sketch pad ɗinshi ba yace '' ya makarantar?" '' Alhmadulillah..na gane karatu sosai.'' ta faɗa tana wasa da hannun ta.ya gyaɗa kanshi can kuma yace '' kinyi ƙawaye?" Ɗan shiru tayi kafin tace '' ban sani ba kosu ƙawaye nane...gasu can'' ta faɗa tana nuna mashi su Abeedah dake tsaye wurin mai sayarda yoghurt kallonsu yayi ta cikin glass ɗin daidai Abeedah na karɓar yagot ɗin da yake ƙarami wai kuma ɗari biyu..ta dinga balbale mai yoghurt da faɗa wai cutar su yake kawai, shiko ƙoƙarin bayani yake mata daga ƙarshe dai yoghurt ɗin ɗari takwas ya basu a Naira ɗari huɗu, Abeedah ta biya kuɗin taba kowa cikin su ɗaya ɗaya... Ɗauke idon shi yayi voice flat yace '' ki mayarda hankali akan karatun ki,kada ki dinga ƙawance da bad girls...they will badly influence you'' ganin zai ɗago daga drawing ɗin shi tayi saurin ɗauke idonta daga kallon shi tana gyaɗa kai batareda ta sake cewa komai ba.... +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁 🍁 15. ...Sofia Diyaam...🖊️ '' wayyo gayen yaban tausayi kin koga yanda kika sashi gaba kina ta mashi faɗa kamar wata uwar shi?" Anaam ce tayi wannan maganar tana juya yagot ɗin a hannun ta '' yayi tsaye kamar maraya.'' Jay D ta ƙara jefar da ledar yagot ɗin nayi ina tsotse ƙanƙarar nace '' kawai yana so yayi mana skam ne taya zai ce wannan abun ɗari biyu?'' Muna kawo wa bakin hanya motar su Jay D ta danno kai muka yiwa juna bye bye sannan ta shige mu kuma muka isa gida da ƙafa bayan Anaam ta gama shiriricewa a hanya Inna sarai muka samu zaune tsakar gida tana ta fama da itace sunƙi ruruwa hakan na nufin ba abinci jefar da jakarta Anaam tayi tana buga ƙafa a ƙasa '' wai mutum yaje makaranta ya dawo kuma ace ba'a gama abinci ba ni wall...'' take maganar da ƙunƙuni a sakalce kamar ƙaramar yarinya nida Asma'u duk da muma muna jin yunwar muka tsaya gefe muna shan dariya '' kizo ki buɗe baki hayaƙi ya dinga shiga kafin ki sani cikin ki ya cika dam!" Inna sarai ta faɗa '' kamar wata yar wiwi..'' Asma'u ta furta cikin dariya kafin nida ita muka wuce wurin mama Anaam ta zauna tsakar gida tana ta rusar kukan yunwa wai ƙatuwa da ita abun kunya... Abinci dai sai ƙarfe biyar ya dahu fuskar Anaam tayi ja saboda kuka cikin trey babba aka zubo abincin mu dukan mu harda su Mama muka zauna a baranda muna ci tare Anaam hannu baka hannu ƙwarya ni dariya ma take bani duk da zafin abincin kafin kowa yayi loma ɗaya ita takai ta uku kuma tanayi tana hararar mu kamar mun tare mata wani abu Sosai naji daɗin kasancewar mu tare a matsayin iyali ɗaya na gode Allah akan wannan bayan mun gama cin abincin aka ce Anaam tayi wanke wanke tasa ma mutane drama wai cikinta ciwo yake ta wuce ta kwanta inna sarai ta biyo ta cikin ɗaki da maburki Washegari da muka koma makaranta baƙuwar nan ta ƙara kamewa ko sanda aka tashi break da Jay D tace tazo muje waje ta girgiza kanta wai zata zauna a aji na gyaɗa kaina itako Jay D sai wani lallashin yarinyar take '' kika sani kota gurgunce ba zata iya tafiya ba kin zo kina damunta '' inji Anaam dake mayarda littafinta cikin jaka yarinyar bata ce komai ba kamar ma Anaam bata yi magana ba muka fita mu uku zuwa wurin da ake sayar da abubuwa Anaam sai so take tasa Jay D ta kashe kuɗinta ba gaira ba dalili itama Jay D biye mata take duk abinda Anaam ta nuna sai ta siya mata Kusan dubu ɗaya Jay D ta kashe ma Anaam bayan duk tsawon da muka kasance da ita ko ɗari biyar ban taɓa bari ta kashe min ba sosai Anaam taban kunya '' kedai Abeedah baki da yarda ace duk tsawon lokacin da kuka ɗauka tare baki yarda da Jadeedah bazata yi maki gori ba?" Jay D ta kalle ni kamar ta yarda da abinda Anaam ta faɗa kuma taji zafi da yanayin da take kallona na gane haka ina yan kame kame ta miƙe zata bar wurin Anaam take dariyar mugunta '' kedai anyi sheɗaniyar yarinya daga zuwa zaki raba ƙawaye...'' taɓe baki tayi tare da riƙe abubuwan da Jay D ta saya mata tace '' idan har zan iya raba abotar ku,kenan dama ba wani ƙarfi ne da ita ba? Abeedah ina matuƙar son kasancewa boss (villain) a kowane labari ki kula da ƙawarki dan kuna kyautata min baya nufin idan na tashi aiwatar da abinda ke zuciya ta zan kalli duk wannan'' tayi maganar tare da barin wurin '' shine yasa kike a bushe tsabar makirci( ☠️)'' na faɗa a ƙasan raina ina bin bayan Jay D data ɓace min cikin dandazon yan matan dake wasa...can na hango ta zaune a ƙarƙashin wata bishiya..na ƙarasa wurin da sauri..ina magana da sauri sauri '' kin san dai abinda ta faɗa ba haka bane..kin san kawai ni ina..'' '' baki yarda dani ba...'' ta kalle ni a karo na farko tunda na fara magana '' kema dai kin san ba haka bane ko? '' na zauna kusa da ita mu biyun mukayi shiru '' me ake nufi da kntamineyt(contaminate)?" Na tambaya bayan lokaci bata amsa da sauri ba sai data gama shan ƙamshi sannan tace '' gurɓatacce'' nayi jim ina ƙoƙarin fahimtar abinda yaron nan mai sa fes mas yake nufi ''kam bala'i!" Na furta ido waje, kenan yana nufin idan na shiga motar su zan gurɓata masu iska lallai '' Meye ne?" Ta tambaya tana zama da kyau '' kin san Khalil ɗin nan dana faɗa maki?" Ta gyaɗa kanta '' yana yawo da wani mai sa fes mas ranar dan kawai na faɗa cikin ruwan taɓo shine yake faɗa ma Khalil ɗin wai idan na shiga cikin motarsu zanyi kntamineyt (contaminate) iskan dake cikin motar'' ''.lallai wannan yaro bai da mutunci'' '' ai kin san shima,kin tuna yaron nan da tuwo da miyar kuka suka zubewa a jiki a maina hotels?" Ta gyaɗa kanta tana dariya sosai '' Muryar shi kamar ana surfa ƙanzo'' ta cigaba da dariya '' toh shine ai shi ɗan rainin wayo mugun bawa!'' sosai Jay D ke dariya harda riƙe ciki mukayi zaune nan muna ta hira har aka koma break '' sannu da aji '' ta gaishe da baƙuwa nidai zama na kawai nayi dan naga yarinyar akwai ji da kai kamar wata yar gidan sarauta... Bayan mun koma gida,da ƙarfe biyar na shirya cikin riga da zanen da Mama ta ɗaura min shi dan nidai ban iya ba nasa baƙin hijabi nayi masu sallama '' ina zaki haka?'' Inna sarai ta tambaya '' wai aiki zata tafi nema'' Mama ta bata amsa '' kowa na tafiya da takardun neman aiki ke zaki wani kwashi jiki buguzun buguzun ki tafi tsoron ki suke ji da zasu baki aiki?'' Inji Anaam kafin in amsa mata tace '' ko wannan fuskar taki da take kamar anyi azdent (accident)zasu kalla sai su baki aikin?'' Takalmin dake kusa da ƙafarta inna sarai ta ɗauka ta jefe ta dashi ta kuwa same ta a baki dafe bakin Anaam tayi ido ƙanƙance take faɗin '' laa! laa!laa!laa!laa!" Idonta suka ɗuri ruwa. Asma'u dake zaune daga bakin ƙofar kitchen ta fashe da dariya nima da raina ya sosu da maganganun ta sai dana dara '' ban san inda kika koyi maganganun dake sosa ma mutum rai ba Anaam kullum kika buɗe baki sai baƙar magana...'' tana buga ƙafafu ƙasa ta hankaɗa labule ta shige ɗaki tana kuka sosai na girgiza kai kafin na fita daga gidan wurin neman aiki,a takure nake tafiyar hannu na gaban hijabi amma har na zagaye restaurants ɗin dana ke gani a hanyar mu ta zuwa makaranta ban samu ko ɗaya da suka ɗauke niba acewarsu basa buƙatar ƙarin ma'aikata duk na gaji ana kiran sallar magrib na dawo gida dajin ban samu aiki ba Anaam tana ta yimin dariya ban wani damu ba Mama ta tausashe ni itama "gobe idan an tashi makaranta bazan dawo ba sai na fara neman aiki kinji'' gyaɗa kanta Mama tayi Da sassafe sai ga Jay D da ƙaramar jakar kayanta da waya da laptop dai a gidan mu ta shirya muka tafi makaranta tare hakan ba ƙaramin daɗi yayi min ba '' ba gobe ya kamata kizo fa?" '' oh ban sani ba..ko in tattara kaya na in koma ne?" '' da zaki tambaye ni da hakan yafi!" Anaam ta amsa batareda ta kalle taba jay d tace '' luckily bake aka tambaya ba,sai ki rufe wa mutane wannan ramin dake fuskar ki!" Nida Asma'u muka fashe da dariya '' kambu bakin nawa ne rame?" Tayi tambayar tana nuna kanta '' ƙato ma kuwa!" Jay d ta amsa hannu Anaam ta ɗaga zata kai mata duka da wani irin sauƙi kamar dama ta saba yin hakan Jay D ta damƙi hannun Anaam ta murɗe shi bayan Anaam ya haɗu da ƙirjinta ''fuskar Anaam tayi ja, idonta suka ciko da hawaye wannan shine mafi girman kuskure da zaki taɓa aikatawa yan mata!" Inji Jay D sannan ta ture ta nida Asma'u muke kallo da burgewa ashe akwai wanda ya iya faɗan chana a ƙasar mu Taja hannu na muka bar su biyun tsaye tana yarfar da hannunta Anaam take faɗin '' wallahi sai na rama,saina mata abinda ba zata manta dashi ba!" Asma'u ke kallon Anaam na yan seconds kafin ta riƙo hannun tana kallo amma batace komai ba... '' jiya nacewa Ummu tabarni inzo gidanku yau, kuma ta yarda da sauƙi'' ta furta tana ɗage kafaɗ nayi murmushi batareda nace komai ba da daɗewa bayan mun iso sannan Anaam ta shigo ajin ...ko ina suke tuntuni? Oho! nabi ledar dake hannunta da kallo kamar uniforms ne a ciki... '' Guuuuud mowwwwni ma!" Naji yan aji suna gaishe da malamar data shigo da sauri na miƙe daidai nan baƙuwa oh Diyaam ta shigo ajin saye da farin hijabi rabin guiwa jakarta rataye a kafaɗa '' ina kwana Abeedah '' ta faɗa da ƙaramin murmushi tana tsayawa kusa dani.nikam sai ƙifta ido nake wai ni take gaishewa na ɗauka ai bata sona kuma kamar bata ma taɓa yimin magana ba sai yau '' ana gaishe ki baki iya amsawa'' Jay D ta bugi kafaɗa ta da yar harara toh aini mamaki ne ya hanani amsawa '' ina kwana Jadeedah '' '' lafiya lau Sofia Diyaam'' tayi dariya da yanda Jay D ta amsa mata '' good morning how are you?" Malama Hafsah ta amsa mana tana rubuta sunan subjet ɗin a allo sai lokacin ma naga ashe itace '' fayyyn tannnk uuuu maaaa...'' tayi murmushi tare da bamu izinin zama '' kuyi haƙuri kwana da yawa ban zoba aiki ne ya shamin kai wa zai faɗa min ina muka tsaya last topic?" Ta tambaya tana bin mu da kallo '' Sef istim '' Asiya ta amsa mata ta sake sakin murmushi mai ƙayatarwa tace '' kuma kowa dai ya tuna abinda ake nufi da sef istim ko?'' muka haɗa baki wurin faɗin '' eh...'' '' good....da yanda hijaban ku suke ƙyalli na tabbatar kowa a ajin nan yana da high self esteem ko?" Da ƙarfi muka amsa da '' eh...!" '' very good..'' ta furta sai ta juya tana rubuta wani sabon topic a allo yan ajin mu suka nutsu tana rubutu muna bin ta da alama kowa yana cike da farin ciki ban sani ba ko malamar ce ko kuma dai abinda take koyarwa ne tunda ya shafe mu yasa muke sonta amma dai nasan muna sonta ajin har wani ƙamshin farin ciki yake '' Our topic for today is INFERIORITY COMPLEX '' na ajiye biro na tare da rufe littafin na gyara zama kamar yanda kowa yayi domin sauraren shi kuma wannan Meye shi? Tana zagaye ajin ta sake nuna ni '' ke ƙawata... meye inferiority complex?" Na miƙe tsaye ina rarrabar ido dan dai bansan meye shiba ina ta buɗe baki ina rufe wa,kowa ya kafe ni da ido,da alama suna tsammanin dan na amsa tambayar wancan karon, wannan karon ma na san amsar.naji wani irin nauyi ya saukar min su Jay D suna ta kallo na '' haha Malama kina tambayar tuwo da bata san komai ba? ai wannan da kike ganin ta kamar kwando haka ƙwaƙwalwarta take bata gane komai sai tsananin hangen nesa da son abinda wasu ke dashi Kullum sai ta haɗa kanta da Ma'u da duk wanni wanda ya fita kyau ga shegen kishin tsiya...'' Ji nayi numfashi na,na sama da ƙasa Anaam na shirin kunce min zane a kasuwa hawaye suka ciko idona gabana ya shiga faɗuwa,kuma abin nata harda sharri ajin yayi tsit aka kafe ni da ido Malama Hafsah ita ma idonta akai na, hawayen suka shiga saukowa ɗaya bayan ɗaya ganin yanda nake kuka ba shiri Jay D ta miƙe ji kake '' tas tas!" Ta wanke Anaam da maruka har guda biyu '' hah!" Yan aji suka ja ajiyar zuci suna rufe baki ido waje '' kam bala'i..me nayi maki kika mare ni'' Anaam ta furta hawaye suna sauka a fuskar ta '' tambaya kike? Da sanyin safiyar nan kike ƙoƙarin kurmantar damu da wannan ruɓaɓɓen ƙaton ramin da kike kira baki how dare you Kike ƙoƙarin muzanta Bee a gaban mutane? Abeedah ita ɗin she's someone da har abada bazaki taɓa kamowa ba a kowane fanni'' Jikin Jadeedah har tsuma yake yanda ta tsaya min yasa naji na ƙara ƙaunar ta inama ace nima zan iya kasancewa kamar ita? Yan aji kuwa sun shiga shok dan basu taɓa ganin Jadeedah tayi faɗa da kowa ba Malama Hafsah take bin mu ukun da kallo Anaam sai sharar hawaye take fuskar ta tayi ja nima idona sunyi ja Juyowa Jay D tayi tana fuskanta ta ta riƙo hannu na tareda zaunar dani Diyaam tayi saurin ɗauko ruwa daga jakarta ta miƙo min na karɓa ina sha da ƙyar abinda Anaam tayi min ba lallai in warke da wuri ba... Malama Hafsah ta nuna Anaam '' ke zonan!" fuska ba walwala sum sum Anaam ta miƙe tana sharar hawaye '' g..gani!" Ta furta tareda tsayawa gefen Malama Hafsah ''.meye sunan ki?" '' Anaam!" '' kin san abinda kika yi cin zarafi ne?'' Anaam da sauran yan aji suka zaro ido nidai na jinginar da kaina a kafaɗar Jay D na runtse ido zuciya ta na bugu da ƙarfi '' koda abinda kika faɗa gaskiya ne baki da haƙƙin cin zarafin ta a cikin mutane kije ki bata haƙuri yanzu!!" Kowa na ajin ya yarda da abinda Malama Hafsah ta faɗa Anaam taji kunya sosai abinda tayi niya bai yi aiki ba ta kalli seats ɗinsu Abeedah wani irin resentment na cika zuciyarta musamman saboda abinda Jay D tayi mata har sau biyu kuma duk saboda Abeedah yanzu kuma cin mutunci? Lallai Abeedah zata biya sosai ma kuma tasan yanda zata sata ta biya.... Da sauri ta iso wurin seat ɗinmu Jay D na harararta haka ma Diyaam '' Abdeedah dan Allah kiyi haƙuri bazan sake ba kinji '' ta faɗa da kuka amma Jay D kallo ɗaya ta yima Anaam ta fahimci ƙarya take nidai ban ɗago ba'' Kiyi haƙuri ƙawata kin ji...'' inji Malama Hafsah..gyaɗa kaina kawai nayi Taba Anaam izinin zama yan aji suka dinga kallon Anaam da wani irin kallo kamar kowa baiji daɗin abinda tayi ma Abdeedah ba tayi ƙasa da kanta cike dajin haushi Diyaam ta riƙe hannuna tana shafawa da hannunta mai laushi cike da damuwa '' Meye ma'anar inferiority complex?" Malama Hafsah ta sake tambaya tana dawowa akan topic ɗin yau ɗaga hannu Diyaam tayi hakan yasa na buɗe idona daga lumshen da suke ina kallonta..Malama Hafsah ta bata izini '' Inferiority complex kamar low self esteem ne shine haɗa kanka da wasu kana ji kamar sun fika da komai koda ba haka bane idan abu bai kai 100% kake ji kamar ka gaza kamar ka faɗi kake ƙin yin abu saboda kana ji kamar idan kayi faɗuwa ma zakayi ko bazai yiba Ko kuma ka dinga tunanin idan da ace wasu ne sukayi abun da ƙila ma sai yafi naka...'' Malama Hafsah ta kafe Diyaam da ido da babban murmushi a fuskar ta...'' wow...clap for her...a round of applause pls '' nan yan aji suka fara tafi da ƙarfi kamar zasu cire mana dodon kunne... Daga nan ta cigaba da bayani sosai na fahimci abinda take faɗa... Daga ƙarshe ta ƙara da faɗin '' ku dena haɗa kanku da kowa yan mata na...koda kunga wani abun da suka fiku dashi,wataƙila idan aka duba za'a ga kuma kuna da wani abu da kuka fisu dashi... sannan kowa da irin nashi halitta wanda kuke haɗa kanku dasu,ba zasu taɓa zama ku ba kuma,ku ma bazaku taɓa zama su ba...kamar yanda na faɗa a da...we all are unique in our own ways...idan kayi haƙuri ka so kanka a yanda kake.. zaka fi samun farin ciki sannan zaka fi samun kwanciyar hankali Haɗa kai da mutane shine abu na farko wurin sace farin ciki (comparison is the thief of joy) kun gane?" '' eh Malama Hafsah mun gane!" Suka faɗa da ƙarfi nidai ina ji amma ni baxan iya amsawa ba kamar can baya saboda Anaam ta gama ɓata min rai '' yauwa yan Matana sai mun sake haɗuwa...'' tayi maganar tare da fita daga ajin kamar ranar ma kowa suna ta hira nidai na ƙara riƙe Jay D na ɓoye fuska ta a gefen wuyanta ina cigaba da kuka na duk da dai ban riƙe Anaam a rai ba yan ajin mu suka dinga bani haƙuri suna zagin Anaam dan dama suna jin haushinta akan ranar data maƙale wa macijin sari ka noƙe murya '' badai kida ɗabi'a wallahi '' Anaam tayi zaune a wurin ta kasa motsi sai kunya dake ƙara lulluɓe ta kuma ba kowa take azawa laifi ba sai Abdeedah... Diyaam ta ɗauko cakulet daga jakarta ta riƙo hannu na ta ɗaura hakan yasa na ɗago kaina na kalle ta.da muryar Fulani tace '' gashi...Hamma na yana bani wannan duk sanda nake kuka.yace cakulet yana sa mutum yayi farin ciki saboda yana sa ƙwaƙwalwar mutum ta saki dopamine. zaki ji farin ciki..'' Na kalli ƙaton chocolate ɗin amma fa ban gane abinda take nufi da wani dokamin (dopamine) ba '' iyye Diyaam tana ƙoƙarin sace min ƙawa fa..'' inji Jay D da sauri tana zaro manyan idonta tace '' ba haka bane naga tana kuka shine yasa...'' '' haha wasa nake actually duk wanda ke son Bee nima ina son shi amma idan Bee tafi son shi sama dani zanji kishi...'' tayi maganar da gaskiyar ta tana kallo na da murmushi nima nayi mata murmushi... '' akwai wanda zan so sama da Jay D? Ƙaunar ki anan take rayuwa...''na nuna zuciya ta... Diyaam take kallo kafin tayi ƙasa da idonta '' na gode Dee 😊'' na faɗa da murmushi daga ƙasan raina gyaɗa kanta kawai tayi '' tuwo Kiyi haƙuri '' naji muryar Anaam '' ba komai..'' na amsa ba tare da na juya ba '' ada kina da ciwon kai ɗaya yanzu sun zama biyu kibi a hankali yarinyar nan she's a fake! Duk da dai naga kamar Asma'u ta canja kaɗan wannan yarinyar munafuka ce!" Jay d ta faɗa murya ƙasa nidai ban yarda da abinda ta faɗa ba chocolate ɗin na raba huɗu tsakanin mu Da aka tashi break muka tafi wurin da ake sayar da abubuwa Jay D da Dee sai kashe mana kuɗi suke Anaam itakam ba kunya take karɓa nikam nauyin karɓar abun mutum har lokacin yaƙi bari na dan haka nima da yan kuɗin da nake dasu nakan siya ma Jay D da Dee ɗin abubuwa daga ƙarshe dai tare muka ci komai Asma'u itama ta biyo mu,kaɗan kaɗan Dee take magana kamar tana jin kunya.Muryar Anaam tafi ta kowa... Kafin a koma break ta saki jiki damu, lokacin tashi muka fito a tare cikin nishaɗi sai da muka tsaya wurin mai yoghurt muka siya kamar jiya, Asma'u da Anaam suna cecekucen da suka saba,munyi tsaye daga gefe muna kallo Piff!!!!! Ƙarar motar da mukaji yasa mu uku kallon wurin.Motar su Diyaam ce ta iso '' Hamma yazo sai gobe '' tayi maganar a sanyaye tana mana bye bye '' sai gobe sofia Diyaam'' '' wai ke dole sai kin kira sunan biyu?" " ke kuma ko mai nayi sai kin lura?" Jay d ta amsa min tana wani juya ido kamar wacce shoking ɗin wuta yaja nayi dariya da wannan tunanin ina girgiza kaina Ta gaban mu motarsu Diyaam tabi ta wuce muna ta ɗaga mata hannu itama tayi ƙasa da glass ɗin wurin da take zaune tana ɗaga mana hannu sai lokacin muka ƙara lura da tsiraran mutane suka rage da kuma mu... '' kuzo mu tafi ina da aikin neman aiki''.nayi maganar ina yin gaba Anaam tayi sauri shan gabana...'' mubi waccan Hanyar da mutane da yawa ke bi dan Allah...'' '' a'a Anaami bamu san hanya ba...''inji Jay D '' wacece kuma Anaami? Anaam ba Anaami ba!" Anaam ta bata amsa '' Toh An'am...'' '' wai wane irin an'am kuma? Anaam ba An'am ba...'' Jadeedah ta cigaba da ɓata wa Anaam suna ita kuma ta zage sai gyara mata take daga ƙarshe tace '' kin san me? Ki kira ni da Sha'awanatu kawai!" Da murmushi Jay D ta jinjina kanta da muka sha kwana munyi mamakin ganin akwai mutane dayawa kamar lokacin ne aka tashi amma dai sunyi nesa damu ba sosai ba gudu mukayi muka cimma su kowa da abokinshi kai anawa lissafin koda ace baka da aboki idan dai har zaka yi tafiya cikin wannan gungun mutanen to bazaka ji kaɗaici ba nake ji kamar ace koda yaushe nan zamu dinga bi... Ana tafe ana hira mai ban dariya dalilin dayasa muka cimma su duk da lokacin da muka ɓata wai ashe faɗa akayi tsakanin prefects da'yan ss 2..Ni har mantawa nake a makarantar tamu ma akwai prefects Duk da tsawon tafiyar saboda akwai mutane sai naji ban gaji ba baki na ya kasa rufuwa sai murmushi nake hanyar tana da kyau sosai akwai bishiyoyi da kuma rafi da yawa daga gefe ɗaya kuma akwai shuke shuke suma su Jay d daga gani suna jin daɗin tafiyar tamu naji Jadeedah tana kiran sunan abun da '' adbenca(adventure)...kuma sai rana ta fara ɓoyewa cikin giragizai alamun hadari.... '' a'a su tuwo yau hanyar mu aka biyo?" Hameeda ta ɗaura hannunta a kafaɗa '' wallahi dama rashin abokin tafiya yasa ban taɓa biyowa ba'' na amsa mata '' Allah dai yasa kun san hanya kada ku ɓace!" Jameelah ta faɗa '' ai babu yanda za'ayi mu ɓace daga ƙarshe dole mu koma gida!" Jay D tayi maganar tana gyara sandals ɗinta...muka cigaba da tafiya cike da nishaɗi Sai da muka ƙara tafiya mai nisa sannan muka kawo wani wurin da Jay D ta kira '' kros rod (Cross roads)'' hanyoyi huɗu ne..gaba da baya..hagu da dama... ''.yanzu wace hanya zamu bi?" Asma'u tayi tambayar '' mubi inda mutane suka fi yawa!" Anaam ta amsa Sallama mukayiwa yan ajinmu dake bin wata hanyar daban mu kuma muka bi hanyar dama dan mutane sunfi yawa a wurin... Amma hanyar kamar daji ina mamakin waya'nda ke biyowa hanyar su kaɗai bayan tafiya mai tsawo sai gashi mun rage mu huɗu kawai babu wasu sai mu kuma abun ban tsoro? Bamu san inda muke ba ga Anaam ta fara kukan yunwa take ji muka ɓulla a wani wuri shiru mai manyan gine gine irin na gidan masu kuɗi ko ina shiru ''nidai mu koma gida gaskiya ko mu koma baya tunda bamu san hanya ba'' inji Anaam '' tun farko wama yace muzo wai?" Asma'u ta tambaya '' nice nan nace muzo damar abin ban jawo mutum ta ƙarfi da yaji ba...'' Anaam tayi maganar a harzuƙe daidai mun kawo gaban wani gida mai gate ruwan madara..suka fara cecekuce nidai duk da ban san inda muke ba, hankali na kwance kuma ban damu ba tunda bani kaɗai bace sannan na faɗa wa Mama xan tafi neman aiki idan an tashi daga makaranta dan haka banda damuwa Yi suke kamar zasu yi faɗa Jay D na faɗin su bari kafin itama ta biye su har da ita aka koma cacar bakin... A gaban gidan muka fara jin kukan kare sai suka mayar da faɗan su akan kare suna zaginshi harda mai gidan ma daya ajiye kare a gidan nidai na tsaya ina kallon su kamar na samu TV Ta ɗan ƙaramin ramin mukulli Muryar wani ke faɗin mubar wurin ko ya sakar mana kare harda haɗa mana da ashaar Anaam cikin zaƙewa tace '' idan baka sakar mana kare ba,baka haihu cikin uwarka da ubanka ba kai da karen na biku da gudu ba wando...'' Aiko mukaji alamun buɗe ƙofa kafin haushin kare idon mu suka wani irin buɗe ganin da gaske karen ya sako muna kowa cikin mu ya kwasa da gudu Anaam tana gudu tana kiran sunayen mu cikin kuka da hawaye kowa takan shi yake can nake jiyo baƙin mugun yana dariya... Ƙafa kawai nake sakawa ba tare da nasan ina nake ba sai da na juyo naga ashe nikaɗai baƙin mugun karen kibi sannan yama daina bina dan nayi mashi nisa sai ya juya ya koma sosai zuciya ta ke bugu da ƙarfi na tsaya tareda dafe guiwowina ina nishi kafin na miƙe na cigaba da tafiya ina mamakin ko ina sauran? Can na ɓulla bakin titi ƙarƙashin wata bishiya saman benci na zauna tare da ajiye jakata gefe ,na zare safa ta dan na jefa ƙafa cikin ruwan datti safar tayi baƙiƙirin Allah yasa akwai pamfo kusa kawai na wanke ƙafafuna na sha ruwa na wanke fuskata na dawo na zauna Ina cigaba da kalle kallen inda zasu ɓullo araina ina ƙara tsinewa wannan shegen karen minti biyar sai gasu sun iso muna ganin juna muka kwashe da dariya banda Anaam dake aiko min da harara suka zo suka zauna gefe na suna haki '' ga pamfo can kuje kusha ruwa ku wanke fuska...'' sukayi yanda na faɗa ɗin '' yunwa nake ji kuma bazan bar wurin nan ba sai na cika ciki na!" Inji Anaam '' toh wazai baki abinci?" Jay D ta tambaya '' Abeedah ki hawo wannan bishiyar ki katso mana lemu.'' dukan mu muka kalli bishiyar ta lemun tsami '' ni banma lura ba...'' miƙewa nayi na cire sandals ɗina ina tattare wando na,dukan mu bamu lura da baƙar motar data parka gefen mu ba har na hawo saman bencin na riƙo wani reshe na bishiyar Jay D na faɗin '' kibi a hankali '' muka ji ance '' Kitten" dukan mu muka juyo.... +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 16. ...hug you goodbye...🖊️ A tare dukan mu muka juyo muna kallon baƙar motar dake pake daga bayan mu,sannu sannu glass ɗin yayi ƙasa fuskar Khalil ta bayyana da murmushi kamar koda yaushe idonshi ke yawo tsakanin mu dukan mu samun kaina nayi da sakar mashi murmushi nima har cikin raina na gode Allah daya kawo shi saukowa nayi daga saman kujerar tareda ɗaukar jakata Anaam take faɗawa Jay D waye Khalil kamar ita dashi sun rayu tare... A tare muka isa wurin motar yayi mana alamar mu shigo bayan ya cire ma ƙofar mukulli su uku suka shiga baya da hannun shi yayi min alamar inzo in zauna gefen shi, na zagaya ɗayan gefen tare da buɗe ƙofar na shiga gaishe shi mukayi yake amsawa fuska sake sannan ya tayar da motar muka bar wurin ina ta satar kallon shi naga kamar ya canja duk da bansan a ina ya canja ɗin ba... '' me kukeyi anan?" ya tambaya a tare mukayi murmushi nida su bayan mun tuna biyo mu da kare yayi,banda Asma'u datayi shiru ta kafe wuri guda da ido..kamar Khalil take kallo ko ƙila tana kallon hanya ne '' Tuwo ce da baƙin yawo ta jawo mu har zuwa nan.. da badan Allah ya kawo kaba da shike nan mun ɓata...'' da sauri na juya na kalli Anaam datayi maganar tana fari da ido '' kiji tsoron Allah...'' Jay d ta riƙe baki '' da tsoron ki nake ji ai!'' ta amsa mata... ''munafuki baida kama...'' na furta..da yanda fuskar ta tayi ja na tabbatar taji zafin abinda na faɗa... '' ashe haka kike da yawo kitten?" Na ɓoye hannu na cikin hijabi na saboda sanyin AC'n dake feso min yana sanyaya kowane gaɓa na jiki na..na kalle shi sannan nace '' motsa jiki nada kyau wata rana ka ajiye mota kayi taku da ƙafa yawan zama nasa mutum ya gurgunce!" Yayi murmushi yana shafa gefen fuskar shi da hannu ɗaya amma fa ban sani ba koda gaske ne zama nasa mutum ya gurgunce '' Allah ko?" Ya tambaya ɗage kafaɗuna nayi '' ƙarya take kawai hasada ke damunta dan taga kana da mota itako sai dai duk tsawon tafiya ta daddale ta ƙasa..'' '' wai ke komai sai kin sa baki? Kina ban haushi kamar in shaƙe ki!'' Jay d tayi maganar da takaici tana hararar Anaam...matsawa daga kusa da ita Anaam tayi dan tun sanda Jay d ta murɗe mata hannu take ɗan shakkunta sai data matse Asma'u sannan tace '' to ki shaƙe ni mana...naga dai bakin naw...'' Yunƙurawa Jay D tayi kamar zata riƙo ta, Anaam ta saki ƙara tareda ƙanƙame Asma'u dukan mu ta bamu dariya harda Asma'u shidai Khalil murmushi kawai yayi ga tsoro ga rashin kunya... '' Asma'u dai tayi shiru Meya faru?" Jay d ce tayi maganar sai dukan mu hankalin mu ya koma kanta gyara zama tayi kamar a takure take sannan tace '' yunwa nake ji shine yasa...'' '' oh... gaske kika nutsu kamar wata ta arziƙi...'' ture Anaam daga jikinta Asma'u tayi tana hararar ta tace '' kin cika surutu ki dinga sakawa bakin ki linzami '' '' a'a sukun da nunus sakina zan sa'' Anaam tayi maganar a harzuƙe hakan ya bamu dariya Jay d ta ƙara da '' ki haɗa harda wasali bayan nunus sakina kinji...'' da alamu Anaam takai ƙarshe wurin ƙuluwa dan bata sake cewa komai ba motar tayi shiru bayan ƙamshin turare da kuma sanyin AC babu abinda ke tashi lura da yayi ina jin sanyi ya miƙa hannu ya kashe ta cikin madubi ya kalli fuskar Asma'u dama tuni shi take kallo idonsu ya haɗu da sauri ta ɗauke nata kunya na kamata '' tunda Asma' is hungry bara na kai ku wurin cin abinci mana...'' daga kallon waje na dawo da idona akanshi gaskiya nidai babban muradina a wannan lokacin shine in kai gida,na kalli Jay d data jingina da kujera na sake dawo da idona kanshi daidai mun kawo traffic ya juyo ya kalle ni idon mu ya haɗu ya ɗage min gira,da sauri na ɗauke kaina ina jan hijabina nace '' kadai kai mu gida...mun riga da muny...'' '' toh uwar baƙin ciki shi ɗan abincin na yan gayu da za'a kai mu muci kike mana baƙin ciki ko? Nasan gida tuwo aka kiɓa shine...'' '' Anaam kina bamu kunya...'' Asma'u ta katse ta,ta juyo da kyakkyawan murmushi tana kallon Khalil duk da yanda zuciyar ta ke lugude da lallausar murya tace '' a'a kabarshi kawai ya Khalil...idan mun koma gida zamu ci abinci..'' Taɓe baki Khalil yayi yana kallo na yace '' tsoro kuke zan sayarda kune?" Zaro idona nayi dake cikin nashi nace '' abinda kake tunanin yi kenan?" Shine ya fara ɗauke idonshi da faffaɗan murmushi a fuskarshi..nima sai nayi murmushin daidai nan aka bada hannu '' muje Asma' taci abinci da ƙawata a can...'' yayi maganar yana kallon Anaam data kusa yin bindiga..jin abinda ya faɗa Anaam ta washe baki... Asma'u tayi ƙasa da kanta tana blushing.. zuciyar ta na ƙara girma da soyayyar Khalil kamar an hura balon balon...the fact that yayi prioritizing ɗinta a wannan lokacin means a lot to her... Bayan wani lokaci muka kawo wani haɗaɗɗen wurin cin abinci, parking yayi muka fito biye dashi a baya sai bin ko ina muke da kallo banda Jay d, wurin ya haɗu sosai ba ƙarya lokacin da muka shiga daga ciki na gane cewa wajen ba komai bane idan an haɗa da cikin dizain ɗin wurin yana da ƙayatarwa sosai ga sassanyan ƙamshin da zai sa mutum yaji kamar kada yabar wurin kowa sai harkar gabanshi yake banda ƙarar cokula da kuma maganganun mutane ƙasa ƙasa babu abinda ke tashi ina kalle kalle na ban san sanda muka iso bakin wani tebur ba sai da Jay D ta zungure ni kallonta nayi kafin na kalli tebur ɗin idona ya sauka cikin na Romo daidai shima ya ɗago daga magana da baturiyar dake zaune daga gaban shi,gashinta kamar makaroni duk ya laulaye sannan guntu ne ko wuyanta bai wuce ba kalar gashin kamar zuma mai haske fatar ta fara kamar tayi wanka da gari kayan jikinta suda babu a wuri na duk ɗaya.. wandon ta ko rabin cinya bai kai ba..rigar jikinta da kaɗan ta wuce ƙirjinta sai wasu shegun akaifa zaƙo zaƙo kamar wacce zata ci mushe ta ɗanyi kyau fa amma, fuskar ta da kwalliya kaɗan... Amma dai abinda yafi ban mamaki shi ɗin...kamar koda yaushe saye da takunkumi da baƙaƙen kaya to kodai vampire ne idan ya cire takunkumin zai dinga zuƙewa mutane jini ne? Dama can daga abinda nake iya gani na fatar shi..farin shi ya ɓaci kamar zabaya (albino) zabayan ma sun fishi kala shi ɗin fari ne fat kamar takarda...harara na banka mashi ina murguɗa baki ɗauke idon shi yayi kamar ni ɗin ban cancanci ya kulani ba Dama ai ba neman kulawar shi nake ba hmp! Gashin shi daya aske kawai dan na taɓa har ya ƙara fitowa saboda babu hula akanshi gashin baƙi wulik Ina tsaka da wannan tunanin naga baturiyar nan ta tashi ta rungume Khalil tana faɗin '' Abraham awwnn...!!!" Shima sai ya ɗaura hannayen shi a ƙugunta ya rungumeta yana murmushi '' Leona..what a surprise...'' idona kamar zai faɗo haka ma su Jay D muka kalli juna kafin muka dawo da idon mu akan su shi kuma Romo kamar babu shi a wurin sai danna wayar shi yake... Oh ni Abeedahtuwo gaskiya ba ƙaramin mamaki abun yaban ba kaina ya shige cikin kwali...ja baya tayi har lokacin murmushin ta bai ɓace ba '' Innalillahi wa inna ilaihi raji'una..na shiga uku ni Anaami dama...''da sauri mu uku muka rufe mata baki kafin ta faɗi abinda ba shiba,idon mu waje sai lokacin Khalil ya lura damu haka ma baturiyar '' oh kuyi haƙuri ku zauna'' ya nuna mana kujerun da babu wanda ke zaune akai ashe ya manta damu tsabar wulaƙanci zama sukayi banda ni da nayi tsaye zuciyata na tafasa wannan ai wulaƙanci ne babu abinda nake banda hararar shida baturiyar data laƙe mashi kamar ƙadangare ƙwayar idonta shuɗi(blue) shafa ƙeyarshi yayi Jay d taja hannu na '' Bee ki zauna mana''girgiza kaina nayi kafin inyi magana da Muryar shi mai zurfi yace '' yi haƙuri kinji ƙawa tace daga America...'' juya idona nayi da abinda ya faɗa.' kallon da yake min ne yasa na sauke ajiyar zuciya tareda zama kusa da Jay d baturiya da Asma'u suka saka Khalil a tsakiya Anaam kusa da Romo da ganin yanda ta zauna kasan a takure take '' who're they?" Baturiyar tayi tambayar tana kallon mu duka sannan ta mayar da idonta a kanshi '' wai wancan abin dake kanta makaroni ne?" itama Anaam ta jefa tambayar da tabbacin baturiyar bata jin Hausa...dariya Jay d da Asma'u sukayi nidai nayi murmushi baturiyar take kallon mu tana ƙoƙarin fahimtar abinda Anaam ta faɗa'' ga wani jan abu can sama ko miya ce?'' '' what is she saying? Ko zagina take yi?" Baturiyar ta sake tambayar da alamun ɓacin rai to fa daga jin mutane suna magana da yake nima dai ba sanin abinda ta faɗa nayi ba '' relax Leon...cewa tayi gashin ki,bata taɓa ganin kamar shi ba.yayi mata kyau sosai...'' zaro ido su dake jin turanci sukayi nidai nayi tsuru da ido ban fahimta ba Anaam ta yamutse fuska zata sake magana da sauri na mintsine ta a ƙarƙashin tebur '' washhh! Tuwo mey haka?" Waiter ya iso teburin mu kafin inyi Magana ya fara gaishe damu kafin ya miƙa mana littafin abinci...Khalil yace kowa ya zaɓi abinda yake so... '' Rome ba magana ne?" bai yi kamar dashi ake maganar ba bale ma asa ran zai amsa ɗaukar kanshi na matuƙar ban haushi '' nima da muke zaune tare daga uhm sai uh uhm kamar kurma, seriously is he being charged for every word'' inji baturiyar duk da ni ba fahimta nayi ba karɓar odar mu waiter ɗin yayi,baturiyar ta mayarda hankalinta akan su Asma'u suna magana har da Anaam da ba wani turancin kirki ta iya ba nikam na shiga duniyar tunani sanda ina maina hotels sai dai ni in kai wa kostoma abinci amma yau ina zaune ni za'a kawo mawa abinda mamaki magana suke da baturiyar kamar sun san juna nidai nayi shiru jefi jefi Jay d ke tanka musu..Nasan saboda taga nayi shiru ne shine yasa itama take min kara murmushi nayi ina kallonta..har abada babu wanda zai taɓa zama kamar Jay d a wuri na '' ita wannan bata jin turanci ne?" Ta nuna ni sai kuma tayi ƙoƙarin magana da hausa tana ya mutse fuska da alamu tana ƙoƙarin gano kalmar da ya dace ne..ta zaro min manyan idonta '' ba English?...'' duk da naso in cije kada inyi dariya ko murmushi na kasa..na gyaɗa kaina ''Hausa..'' na bata amsa sai itama tayi murmushi tana kallon Khalil tace '' kyakkyawa ce ita...'' Anaam ta turo baki kafin tace da gurɓataccen turancin ta '' duk mu dake nan baki ga wanda zaki ce yana da kyau ba sai Tuwo...ouchh!! Taka ƙafarta Jay D tayi ni ban san abinda ta faɗa ba amma dai nasan ba abun kirki bane '' beauty is subjective to individuals my dear'' baturiyar ta furta Khalil ya gyaɗa kanshi bada daɗewa ba abinda muka yi order ya sauka '' Asma bakida lafiya ne kin yi shiru?" Ya tambaya da kulawa kallon shi Asma'u tayi ta ɗauke ido kumatun ta sukayi ja kaɗan murya na rawa tace '' a'a lafiya ta lau...kawai ina..uhm so in tafi gida...'' '' okay..'' Babu wanda ya ƙara magana suka fara cin abincin su ni na kasa cin abincin a gaban mutane da yawa.. musamman kuma da wannan ɗan rainin wayon da duk abinda ake bai ce ko ƙala ba...Anaam hannu baka hannu ƙwarya zar ban takaici kamar bata taɓa cin abinci ba... Jay d tana ci kamar irin na yan gayu... Asma'u kuwa wasa take da abincin ba wani ci take ba Baturiya da Khalil wani abinci sukayi oda..ni wallahi ƙyama abun yake ban kamar zanyi amai da sauri na ɗauke kaina kada suce nayi musu rashin mutunci... Bamu bar wurin ba sai wurin ƙarfe huɗu da rabi,Khalil yasa aka samin nawa abincin a take away dukan mu harda romo muka fito har hadari ya taru kamar ruwa zasu iya tsugewa a koda yaushe,shuke shike nan sai rawa suke da iska..ƙamshin ƙasa ya fara tashi wurin yayi duhu mutane wasu na shiga wasu na fita..naji wani irin mutuwar jiki ya ziyarce ni saboda wannan hadarin muka haɗa ido da Asma'u itama dai abinda ke raina shine a nata bamu taɓa daɗewa har haka bamu koma gida ba na juyo na kalli baturiya laƙame da Khalil kamar zata koma cikin shi suna magana suna dariya Romo yana tafiyar shi da ɗaiɗai hannu cikin aljihu duk shine a baya,juyawa Khalil yayi yana mashi magana da wani yaren daban fahimta ba '' ni na kawo sune da zan mayar dasu?" Ƙatuwar Muryar shi ta karaɗe wurin duk da bada hayani ta fito ba..gabana ya faɗi Ko kaɗan bana son zama inuwa ɗaya dashi taya zai mayar damu kuma?... '' Capri pls we have some catching up to do okay '' baturiyar ce ta faɗi hakan muka koma rarrabar ido dasu Jay d Anaam dake kusa da Asma'u tace '' Allah dai yasa ba wannan mai takunkumin'' ban iyarda jin abinda zata faɗa ba nayi gaba iska na kaɗa hijabina da sauri na tare jikina ta gaba da baya na tafi na tsaya wurin motar shi... a maimakon su iso sai naga ya tsaya ya nuna musu wata baƙar mota irin tashi mai baƙin glass duk da a ɗan kwai tazara tsakanin mu,naga yanda fuskokinsu suka canja da alamu suma basu so Jiki a saɓe sukayi mashi godiya, baturiyar tana yi musu bai bai suma sunayi mata suka wuce biye da Romo a baya Asma'u take ji kamar tayi kuka ko kaɗan bata so haɗa su da Roman da Khalil yayi ba,a nata lissafin da zatayi duk yanda zatayi ta zauna a gaba kusa da khalil amma yanzu duk wannan ya rushe taji hawaye sun cika idonta musamman data ga yanda Leona ta kanainaye Khalil wani irin pang of jealousy ke sukar zuciyar ta at the same time tana ji inama ace itace in place of Leona take bin bayan su da kallo iskan daya ɗan fara tasowa sai kaɗa gashin Leona yake, Khalil ya share mata gashin zuwa bayan kunnen ta suna murmushi kamar masoya ɗauke idonta Asma'u tayi ƙololon abinda ya tsaya mata a maƙoshi sai ƙara girma yake ta juya ta isa motar Roman suna isowa Khalil ya buɗe mata motar ta shiga tana dariya akan wani abu daya faɗa da alama basu ma lura Dani ba... sai daya rufe motar sannan idonshi ya sauka akaina ji nake kamar zanyi kuka '' kitten...'' turo baki nayi idona suka ciko da hawaye sai ya zagayo sashen da nake yana kallo na..ɗauke idona nayi ina ƙoƙarin danne kukan dake taso min '' kina buƙatar wani abu ne?" Ya tambaya bayan ya gama kallona sama da ƙasa '' m..meyasa kace ya mayar damu gida? Dama ka bari mun hau abun hawa da zai fi idan fa ya sauke mu a tsakiyar hanya..?" Nayi maganar ina kallon fuskar shi idona suna ƙyallin hawayen matsowa ya ƙarayi da murmushi a fuskar shi yace '' shine yasa zakiyi kuka?" Kwaɓe fuska nayi tare da kallon gefe '' akan me zanyi kuka?" '' that you're missing me already...'' ya bani amsa na taɓe baki wai kewar shi taɓ ɗi jam '' anyways kada ki damu Rome zai kai ku gida lafiya lau trust me yana da mutunci idan kin sanshi...'' wai yana da mutunci idan na san shi bai yi kama da masu mutunci ba wallahi buɗe motar yayi ya ɗauko jakunkunan mu ya riƙe '' mu tafi in raka ki'' badan naso ba muka jera muna tafiya nake ji kamar kada mu rabu nidai ko kaɗan wancan Romo'n bai yimin ba wallahi... mun kusa isa na miƙa hannu '' kawo jakunkunan budurwarka na jiranka...'' miƙo min jakunkunan yayi da murmushin zolaya '' ko kema kina so ki zama budurwata ne?" girgiza kaina nayi ina kallon jakunkunan naso in rataya jakar Jay D da Asma'u amma hakan na nufin hijabina zai mannu da jiki na za'a ga abinda nake ƙoƙarin ɓoye rashin shi sai kawai na riƙe jakunkunan a hannun haguna jakata data Anaam ana dama na ɗago fuskata a marairaice nace '' toh kazo muje sai idan ya sauke mu sai ku dawo ku ɗauki ɗayar motar dan Allah'' nan ma hawaye suka ƙara cika min ido na rasa dalilin hakan amma dai sahihin bayani shine bana son kasancewa inuwa ɗaya da Romo.... Shafa gefen fuskarshi yayi ya ranƙwafo murya ƙasa yace '' oh kitten..ki dai ce bakyason rabuwa dani...ko?" zaro idona dake cikin nashi nayi hawayen sai suka kwanta a ƙasa suna sheƙi amma basu zubo ba..baki na ya buɗe amma na kasa cewa komai... murmushi yayi ya ware hannayen shi tare da faɗin '' let me hug you goodbye...'' ya fara ƙoƙarin rungume ni kuwa da sauri naja baya kumatuna sukayi ja na kasa cewa komai na juya na bar wurin harda ɗan guduna ina jiyo dariyar shi mai daɗin sauraro daga baya na yana faɗar abinda banji da kyau ba sai da nakai wurin motar Romo sannan na juya na kalle shi har lokacin yana tsaye a wurin hadari ya ƙara tasowa farfajiyar restaurant ɗin ta ƙara duhu sassanyan iska na busowa bishiyoyin sai rausayawa suke da iskan dake kaɗa su yayyafi aka fara kaɗan kaɗan Rungume hannayeneshi yayi murmushin shi yaƙi ɓacewa sai kuma ya ɗaga min hannu na turo baki Ina ji kamar in bishi yana da kirki sosai... Ɗauke idona nayi na mayar akan motar da zan shiga baya na buɗe na same su zaune a takure wuri guda kamar waya'nda ke zaune saman garwashi kowa dai ya kama kanshi so nayi in zauna a baya amma duk sun mahe wurin Anaam harda faɗi ƙasa ƙasa '' ke kije ki zauna gaba kada ki takura mana anan...'' Asma'u ta gyaɗa kai alamun gamsuwa tana harara ta kamar na tare mata wani abu bana son rigima yasa na ajiye musu jakunkunan su..nabar ƙofar buɗe idan sunji haushi su rufe jiki a sanyaye na buɗe gaban na shiga shegen turaren nan nashi mai ƙarfi da wari kamar kashi ya cika min hanci ko kallona bai yiba sai ma wayar shi da yake daddannawa shiɗan rainin wando da Khalil ne da bazai yi mana haka ba... Rufe ƙofar nayi na takure waje ɗaya sai daya gama ɓata lokaci sannan ya miƙa farin hannun shi ya kunna motar ya gyara zaman shi ya fito da motar daga inda take pake dukan mu muka yi shiru da ƙyar muke numfashi kamar muna gudun ɓata mashi rai gaba ɗaya yanayin motar Ba rayuwa a ciki ba kamar ta Khalil ba dogon tsuki naja batareda na ankare ba amma duk da haka bai kalle ni ba Tsayawa yayi daidai inda Khalil ashe har lokacin yana tsaye a wurin na ɗauka ya koma motarsu... Sai daya gama shan ƙamshi sannan yayi ƙasa da glass ɗin fuska sake yace '' Rome dan Allah ka kaisu har ƙofar gida...Kitten tace wai sauke su zakayi a tsakiyar hanya.. don't do that...'' yayi maganar yana min murmushi nikam na turo baki batareda nasan nayi hakan ba murmushin shi ya faɗaɗa '' hmm sauke su tsakiyar hanya sounds epic'' dariya Khalil yayi yace '' ayi haƙuri...'' baice komai ba ya kalli bayan motar yana yi masu Jay D bye bye sannan ya ƙara kallona nima shi nake kallo '' ka fita daga cikin ruwa kada ka kamu da mura'' inji Asma'u sai ya gyaɗa kai batareda ya cire idonshi a nawa ba yaja baya sannu sannu glass ɗin ya fara yin sama tun ina hango shi har glass ɗin ya rufe duka naji kamar ina zaune a keji na ɗauke idona inajin wani abu a zuciya ta daban taɓa sanin meye shiba... Da ƙarfi ya figi motar muka fita daga wurin amma wani sashe na zuciya ta har lokacin bai dena son kasancewa tareda Khalil ba bata dena burin ina ma ace shine a maimakon wannan..ugh!! ƙara shigewa nayi cikin kujerar ganin uban gudun da yake shararawa kamar zai aika mu lahira suma a can baya sun ƙanƙame juna ido waje suna shinshino ƙamshin mutuwa..shi mugun hankalin shi kwance zuciyar shi zaune...runtse idona nayi ina karanto addu'oi ƙasa ƙasa wani irin wawan burki ya taka dayasa nayo gaba kaina ya haɗu da gaban motar naji zafi sosai suma daga baya goshin Anaam ya bugi bayan kujerar da nake zaune badan taso ba tayi gum da bakinta da jin zafi na ɗago ina kallon shi idona cike da hawaye ina murza wurin amma bai ko kalle inda nake ba bare ya bani haƙuri sai ma gabanshi da yake kallo hankali kwance kamar bai san abinda yayi ba 'Mugu kawai..' na faɗa ƙasan maƙoshi..gani nayi yana shafa sumar shi kamar yanda cikakkun mugayen mutane suke yi a cikin fim sai yayi baya ya jingina da kujerar ƙila yaji abinda na faɗa,hararar shi nayi kafin na kalli gaban mu ashe wurin tirafic muka kawo motoci da mashuna sun cika wurin..ruwa ake kamar da bakin ƙwarya...nake kallon wannan baƙin abun dake faman share ruwan dake zuba a gaban motar tashi Hannun rigar shi yaja...agogo mai bala'in kyau ya bayyana...yayi ƙasa da kanshi yana duba lokaci na lura da R-MAN da aka rubuta a farar fatarsa da wani handwriting mai bala'in kyau da baƙin bairo ƙila..daga gefe kuma hoton ƙwarangal irin na kai da ƙasusuwa ☠️ 🍁: Tattoo ne Ɗauke idona nayi ina cigaba da jin haushin shi..a can baya suma sunyi tsit nasan sun ga nawar ya sauke mu mufara nunfashi...wayar sace ta hau ringin daidai saura second talatin a bada hannu...sai da wayar ya kusa katsewa sannan ya ɗauka da wani yare aka rubuta sunan dake yawo a screen ɗin...da ƙatuwar muryar shi yace '' Halo...'' abinda kaɗai na iya fahimta kenan...daga nan ban sake jin komai ba dan ƙasa ƙasa yake maganar kamar munafuki... Ana bada hannu ya sake fisgar motar su Jay D da suka saki juna suka ƙara ƙanƙamewa...cire hannun shi yayi daga abun tuƙin ya ƙara ƙarfi AC'n bayan ya ga ina luƙunƙume kaina cikin hijabi tsabar mugunta... Bada jimawa ba ya kawo tsohuwar anguwar mu, lokacin har ya gama wayar...naɗan zaro ido amma nakasa cewa komai har ya paka ƙofar tsohon gidan mu da yanzu wasu ke haya ciki... batareda ya kalle niba yayi baya tare da faɗin '' come on Chop! chop! ...'' Yawu Anaam ta haɗiye ta buɗe baki tace '' b..ba na..nn ba..ane...'' bai motsa ba..nima ƙarfin hali nayi duk da so nake in sauka daga motar amma dai albarkacin littafan mu da zasu jiƙe nace '' mun can ja unguwa fa...'' Wayarshi ya kalla..bai kalli inda nake ba yace '' in fitar daku ne?'' wato shidai ala dole sai ya tabbatar min dashi Mugu ne ko? In ba mugunta ba taya zai sauke mu cikin ruwan nan? Tura ƙofar Asma'u tayi ta sauka suma su Jay d suka sauka sai dana gama hararar shi na buɗe ƙofar na sauke ƙafa guda na juyo '' Amma baka da mutunci wallahi ga motar nan an sauka ka cinye tayi maka maganin yunwar dare!'' na sauka tare da buga murfin motar da ƙarfi take ruwa suka fara jiƙani amma hakan bai kashe wutar dake cikin zuciya taba tada motarshi yayi yabar mu tsaye a wurin Anaam ta jefo min jakata '' yaron nan baida mutunci Saida ya Khalil yace ya kaimu har gida amma ji inda ya sauke mu'' babu yanda muka iya muka fara tafiya dan ko kuɗi bamu da bare mu samu abun hawa Allah ya taimake mu wani mai adaidaita sahu yayi mana lift har zuwa gida...muka rakashi da addu'oi...duk da dai mun ɗan jiƙe amma ba sosai ba... sallama mukayi muka shigo ciki inna sarai ta ɗage labulen ɗakin su saye da hijabi tana kallon mu cike da tuhuma gaisheta mukayi bata amsa ba ta shiga tambayar daga ina muke da sauri Asma'u da Anaam suka samu ƙarya suka faɗa..bata yarda damu ba amma bata musa ba ɗakin mu muka wuce zane na ɗauka na fito daga ɗakin zuwa baye bayan na gama wanka nayi alwala nazo nayi salla suma haka sukayi sai da muka zauna na tuna da abincin da Khalil yayi min take away '' hah ai sai dai ki hari gaba..ko in zaki iya kibi bayan wannan marar mutuncin dan dai abincin yana cikin motarshi a baya...'' inji Anaam '' kuma idan mun shigo dashi ai daya tona mana asiri..ina muka samu?" Asma'u ta ƙara... naji haushi sosai... '' ɗazu da kika rugo da gudu me yake faɗa maki hala?" Jay d tayi tambayar kowa ya tsare ni da ido '' cewa nayi dan Allah ya kaimu gida ko ya biyo kada wannan mara mutuncin ya mana ta'asa shine yace wai kawai bana son rabuwa dashi ne.'' na ƙarashe ina dariya...itama Jay d ta tayani '' ai dai abinda ake gudu ya faru kam...'' Anaam dake gaban madubi ta faɗa... Asma'u bata ce komai ba sai assignment ɗinta da take... Dawowa Anaam tayi ta zauna tare da mu,muna hira mu uku jefi jefi Asma'u ke sako baki...da ƙarfe bakwai da rabi ruwan saman suka tsaya... Bayan Isha'i na zubo mana shinkafa da miyar da aka dafa..Anaam tana ci tana yamutsar fuska ita ala dole abincin da Khalil ya siya mana yafi daɗi '' toh ko zaki nemo shi ya ƙara siya maki ne?" Asma'u tayi maganar tana ɗage gira '' kema kin san da ace nasan gidan su,da tuni na mayarda shi wurin zuwa na..'' '' uhm tsabar rashin kamun kai...'' hararata tayi tare da jan tsuki...Jay D ko Magana batayi sai lodawa take... Bayan mun gama cin abincin muka fito zuwa baranda,samun Mama mukayi da inna sarai zaune suna magana akan koma Meye fitowar mu ta katse musu zance kamar basa so muji abinda suke magana akai..zama nayi kusa da Mama Jay D ta zauna gefe na...Anaam ta wuce ta kai plate kitchen Asma'u a ɗayan gefen Mama..babu wuta amma...Jay d ta kunna laptop ɗinta..na lankaye jikina dana Mama ina rawar sanyi '' kuje kusa kayan sanyi mana..'' Mama ta faɗa...a tare muka girgiza kan mu alamun a'a...ta taɓe baki '' toh ai shikenan...'' '' Jadeedahtu ya kika ji da zama a gidan namu?" Mama ta mayar da hankalinta akan Jay d.. murmushi tayi da gaskiya tace '' ji nake kamar in cigaba da zama anan!" '' Allah ko?" Inna sarai furta...gyaɗa kanta Jay D tayi su Mama sukayi dariya '' yarinya baki da wayo bakisan daɗi ba...'' inji Anaam '' sannu ke mai wayo..'' inna sarai ta harare ta...nida Asma'u bamuce komai ba sai ƙara shigewa nake jikin Mama '' wai dai Abeedah ko ciki za'a mayar dake ne? Wannan abu haka..ko Asma'u bata da son jiki kamar ke!" '' Nima dai abinda na gani kenan mata kamar kyanwa...'' juya ido na nayi '' idan kashi banza ne kaza tayi mugani ma..'' '' idan fitsari banzane ake cewa...shima karin maganar sai an ciki gyara...'' tashi zaune nayi na jefa ma Anaam wani kallo'' eh sai an cini gyara...aini ba kamar wasu bane komai sai dai ayi irin na wasu...ni nawa daban nake dan haka ina sane nace kashi ehe!" '' hum! Abeedahtu kenan!" Inji Mama..tana shafa kai na...Anaam ta taɓe baki... laptop ɗin Jay D data fara magana ta katse mana ɗan cecekucen da mukeyi,wani fim ɗin Hausa tasa saboda su Mama '' dama kin sa mana fim ɗin chana...'' ''.ba'a sawa...'' Inji Anaam '' ke kiyi ma mutane shiru kinji ko!" Inna sarai ta tiƙi Anaam a tsakiyar baya...Anaam kamar zata haukace sai soshe soshe take bakin nan a gaba kamar daɓurin saniya...rufe bakina nayi ina dariya Daga nan muka yi shiru muna kallon fim ɗin,kallo da inna sarai da kwai takaici bata iyay' yin shiru daga ta dame mu da tambaya sai ta dinga faɗar abinda zai faru koda kowa ya sani...duk sanda ta faɗi wani abu ko tayi tambaya Anaam tafara sallallami kenan kamar ita tafi kowa jin haushi amma ina son yanda Jay D take mata bayanin komai dan dai da nice bazan iya ba wallahi... Bayan fim ɗin ya ƙare muka koma kallon fim ɗin China... Allah yasa bata dame mu da tambaye tambaye ba sosai sanyi ya sauko yana shiga cikin ƙasusuwan mu amma babu wanda ya shirya miƙewa..dukan mu mun bada hankali muna kallo...da ƙarfe goma muka yi ma su Mama sai da safe muka shige ciki... Hasken wayarta Jay d ta kunna muka gyara shimfiɗar mu kafin muka kwanta a tare...kowa da abun lulluɓinshi Nake jin annashuwa na ratsani saboda kasancewar mu a tare...Jay ma bata ɓoye jin daɗinta ba...hira muka shiga yi kafin da guda guda bacci yayi gaba damu... Da safe bayan munyi sallar asuba bamu tafi makaranta ba kamar yanda muka yi a gidan su Jay d sai da rana ta fito sannan muka tashi daga wurin da mukayi Sallah...a tare muka tafi ɗakin su Mama muka gaishe su..suka fi mayar da hankalinsu akan Jay d..bayan gaisuwa Mama tace kunu da ƙosai za'a yi Da sauri Asma'u ta ɗauki tsintsiya ta fara share tsakar gida..na faɗa kitchen na aza ruwan dama kunu...taune leɓenta Anaam tayi ganin mun barta da wankin wake '' yayi '' ta furta daga ƙarshe..wake ta auno ta zauna ta fara wanki tana gunguni '' bari in taya ki..'' Jay d tasa hannun ta su biyun suka cigaba da wanki suna hira kamar ƙawaye kamar babu rashin jituwa tsakanin su... Bayan sun gama tare suka kai niƙan,dama ƙullu nayi na sauke ruwan na juye sannan na ɗaura mai... Asma'u ta wuce ɗakin mu ta gyara ta share harda kunna tsintsiyar ƙamshi, a ɗakin su Mama ma tayi haka...ta share baranda sannan ta shimfiɗa tabarma...na ɗauka rana bazata fito ba amma sai naga ta ƙwalle kamar ƙarfe goma tayi lokacin... shigowa su Anaam sukayi suna dariya...ta kawo min ƙullun,albasa na fara yankawa na zuba sannan nasa magunguna da sauran su..bayan man yayi zafi na fara soyawa...bada daɗewa ba na gama na ɗauki kular ƙosan na ajiye inda zamu zauna na dawo na ɗauki kunun da kofuka... Su Mama suka fito suma,kowa ya zuba kunu da ƙosai daidai wanda zai iya ci...har Saida ma suka rage..dole aka bawa almajirai dake ta Bara... Kayan datti inna sarai ta kwaso ta watso mana mu wanke bamu da zaɓi dole muka haɗo da namu duka muka wanke...sannan muka yi wanke wanke..aikin tare mukeyi...da nishaɗi da annashuwa...wurin ƙarfe goma na fito ɗaki zan sha ruwa naji hayaniya a ƙofar gida..hijabina brown na jawo nasa sannan na leƙa,wasu yan mata ne su uku da duka duka bazasu wuce shekarun muba suke roƙon wani dogon yaro akan ya tayasu ɗaura lilo ga bishiyar kaiwar dake gaban gidan mu..shiko sai ƙamshi yake sha musu..ƙarasowa wurin nayi..suka kafe ni da ido saboda ƙwayar idona.. murmushi nayi musu sai muka gaisa...nake kallon igiyar dake riƙe da hannun ɗaya daga cikin yaran tace '' wai lilo muke son ɗaurawa a nan dafatan ba matsala?" Karɓar igiyar nayi daga hannun ta '' ba matsala bari in taya ku ɗaurawa...'' Wata daban ta riƙe baki ta kalli doguwar bishiyar sannan ta kalleni '' kin tabbata zaki iya kuwa?" Har nayi gaba nake faɗin '' ki kalle ni...'' namijin yayi tsaye daga gefe hannu naɗe a ƙirji irin yana jira yaga na kasa...na basu mamaki sanda na haye saman bishiyar batareda na sha wahala ba... ɗaura igiyar nayi a reshe mafi tsawo..na tabbatar ya ɗauru da kyau sannan na biyo igiyar na sauko dan tabbatar da ingancin ɗaurin... Suna tayi min godiya '' sunana Maryam..wannan Hibbatullah..sai Amatur Rahman..'' wacce na karɓi igiyar daga hannunta ta gabatar min da kansu...'' suna na Abeedah...'' Da jin haushi na mijin ya bar wurin nima na koma ciki...can wurin sha ɗaya gaban gidan mu ya cika da masu sonyin lilo manya da yara mafi yawancin su yan mata ne da ƙananan yara... Fitowa mukayi muma tunda bamu da aikin yi muka bi ayarin masu son yin lilon,ganin akwai layi yasa wasu daga cikin yan matan suka ja gefe wasu suna yar carafke dan ƙasar wurin mai laushi ce sosai wasu kuma suna a yu redi (are you ready) Masu carafke nabi..Jay d da Anaam kuma yan Are you ready.. Asma'u lilo...wurin ya zama wurin wasa nan da nan muka ƙara sanin mutane suma suka san mu,wasu ma maƙotan mune...sai suyita kallo na saboda kalar idona..nidai ban damu ba A karo na farko ina ƙare ma unguwar tamu kallo..unguwa ce mai kyau... akwai gidaje uku manne da namu daga gefen dama da hagu...a gidan ƙarshe can gefe akwai wata bishiyar dalbejiya inda masu saide saide ke yaɗa zango..sai nan gaban gidan mu kaɗan filin ƙwallo ne daga can gaba sosai akwai borehol da sauran su.. Kamar kada ranar ta ƙare saboda yanda muke nishaɗi...daga ƙarshe mun samu damar hawa lilon sai kuma muka taru duka mu manyan muna Are you ready...bakin Jay D ya kasa rufuwa Da ƙarfe ɗaya muka watse kowa ya tafi wurin salla '' to tunda kun dawo sai kuzo ku ɗaura abinda zakuci ko?" Turo baki Anaam tayi tana ƙunƙuni wai ba'a dafa abinci ba.babu wanda yabi ta kanta,Saida muka yi salla sannan muka dinga tunanin mai za'a dafa daga ƙarshe dai muka dafa taliya Jay d ta kira mamanta muka gaisa harda su Mama... Da yamma muka koma wurin wasa mutane kamar ɗazu yanzu ma sun taru..wata wasa daban mai nishaɗantarwa muka yi...filin ƙwallon nan duk yan maza masu guntun wando...sai ƙarƙashin bishiyar dalbejiyan nan mutane sun taru sun rufa akan masu sayar da abubuwa... Wurin magrib muka koma gida...nishaɗin da muka kwaso daga waje har lokacin yana tattare damu,yau akwai wuta hakan yasa bamuyi kallo da laptop ɗin Jay d ba...sauran ranakun da suka biyo baya farin cikin da muka tsinci kanmu a ciki baya misaltuwa da sauri ranakun suka wuce kamar basu taɓa kasancewa ba... Jay d ta koma gidan su muka dawo daga mu sai mu...wasannin da ake gaban gidan mu ba'a dena ba.... A nawa ɓangaren kuma na cigaba da neman aiki na, makaranta anyi sanarwa cewa wani sati zamu fara jarabawar wai mok (mock) kafin jarabawar ta gaskiya harda lesson akeyi...nima kuma na shiga musamman ajin da ake koyar da turanci...su Asma'u dasu Diyaam ma duk suna ciki... +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 17. ...Matsaloli...🖊️ Yau weekend,wurin ƙarfe goma Asma'u na zaune saman lilo ita kaɗai ba kamar sauran ranaku ba da mutane ke tururuwa yau daban ne ... saye da wandon jeans da riga sai hijabi peach color fuskarta fayau amma kyaunta bai ɓoyu ba..a hankali take shilla lilon tayi nisa cikin tunanin Khalil tana tsara an impossible future with him murmushi tayi tana lumshe ido ta fara shilla lilon da ƙarfi da nishaɗi tana sama da ƙasa ko tsoro bataji Da sassarfa yake tafiya hannunshi riƙe da baƙar leda,kayan jikinshi yadi baƙi yasha ruwa ya gaji takalmin ƙafarshi ma sun siɗe bai ankara da mutum a saman lilon ba...GBAM!! Ƙafafun Asma'u suka sauka a fuskar shi da ƙarfi har Saida yayi baya baya ya faɗi baƙar ledar hannun shi ta faɗi duk abubuwan dake ciki suka zube ya dafe gefen idonshi daya fashe yana zubar jini... Asma'u ta ƙanƙame lilon that was spiralling out of control a mugun tsorace ..sai jujjuyawa yake da ita yana haɗa tada bishiyar ta bugu ba kaɗan ba ihu kawai take... '' kamar Asma'u ce ke ihu ko?" Cewar inna sarai data fito daga ɗaki a gaggauce hannunta riƙe da hijabi, Anaam ma ta fito saye da gyale suka fita daga gidan a tare...nidai ina kwance a ɗakin mu..yau ranar tazo min a wani irin yanayin ƙunci da har bana son ko motsawa,kamar inyita kwanciya kada in tashi...bawai dan na mutu ba... jan bargo nayi na lulluɓe har zuwa kaina... Da ƙyar Mama sarai ta tsayar da lilon daga juyawa Asma'u ta ƙanƙame ta kamar tana gudun idan ta saki zata faɗi idonta a matuƙar firgice tana numfashi sama sama tambayar ta inna sarai take Meya faru amma ta kasa Magana sai juyawa tayi inda mutumin nan yake zaune..gaban rigar shi ya ɓaci da jini hannun shi ɗaya rufe da idonshi..su Inna sarai suka kalli inda take kallo '' Innalillahi wa inna ilaihi raji'una meya faru?" Anaam ta kafe gayen da ido inna sarai take sallallami,wurin shi suka isa Anaam ta duƙa tana tattaro mashi abubuwan shi.. Asma'u ta duƙa gaban shi fuskar ta ɗauke da rashin jin daɗi.. batare da tunanin komai ba ta kai hannun ta,ta cire nashi dake rufe da idon...har wurin ya kunbura idon ma yayi ja '' laahaula wala ƙuwwata illa billa...wai Meya faru ne?'' Murya na rawa Asma'u tace '' buge shi nayi ban san yana zuwa ba kayi haƙuri dan Allah...'' naɗan lokaci baice komai ba sai ƙoƙarin buɗe idon yake amma ya kasa..da sanyayyar murya yace '' ba komai...'' hakan yasa Asma'u ta ƙara jin bata kyauta ba..she felt guilty..'' tunda kina da fes ait bos ki kular mashi da ciwon mana...'' da sauri ya girgiza kanshi '' ki bar shi kawai sauri nake..'' '' A'a bawan Allah tunda ita tayi maka wannan ta'asar kabari ta gyara dama nos (nurse)take so ta zama...'' bai sake cewa komai ba cire hannun ta Asma'u tayi daga fuskarshi ya miƙe da ƙyar suka nufi cikin gidan sai da suka fara shiga sannan ya bisu..kujera Anaam ta ɗauko daga kitchen ta ajiye mashi a tsakar gida.. Asma'u ta shiga ɗaki ta ɗauko first aid box a gaggauce ta fara wanke mashi ciwon bayan ta share jinin da auduga kamar yanda aka koya musu a practical.. sannu Inna sarai da Anaam suke mashi every now and then Daga cikin ɗakin ina jin yanda suke ta yi mashi sannu suna ƙara bashi haƙuri harda Mama amma ban fita ba na cigaba da kwanciya ta...zuciya ta a ƙuntace na rasa inda zan sa kaina ji nake kamar in aske fatar jikina in sauya zuciya ta da komai nawa ko zan samu sauƙin abinda ke damu na...yaushe zan samu abin da na roƙa? Yaushe rayuwa ta zata sauya? Wayyo Allah na! siririn hawaye ne ya sauka daga idona nayi saurin share shi jin an ɗaga labule '' wai Abeedah yau lafiya kuwa?" Inna sarai ce take tambayar yi nayi kamar ina bacci ban tanka taba...a can tsakar gida Asma'u ta gama addressing ciwon ta manna mashi auduga da plaster with expertise...ta sauke ajiyar zuciya tana kallon fuskar shi,samu tayi shima ita yake kallo ta ɗauke idon ta tareda miƙewa ta kwashe abubuwan da tayi amfani dasu tana faɗin '' kabi a hankali kada ruwa ya taɓa wurin kaji...'' sai kawai ya gyaɗa kanshi ya nemi tafiya..inna sarai da Mama suka hanashi wai ya ɗan jira kaɗan..bai so yayi musu kawai sai ya zauna ɗin...Anaam ta jawo kujera ta zauna kusa dashi ta fara zuba kamar pamfo...shidai daga uhm sai uh uhm da murmushi a fuskar shi Daga lokaci zuwa lokaci idonshi ke kaiwa gefen da Asma'u take duk tayi sanyi..bayan wani lokaci ya miƙe cike da girmamawa yayi ma su Mama sallama..sosai suka ƙara bashi haƙuri akan abinda ya faru yace ba komai ya ɗauki ledar magungunan shi ya ƙara kallon Asma'u one last time da murmushi kafin ya fice... '' kamar in bishi...'' '' daga ganin mutum kamar ki bishi to ki bishi ɗin...'' turo baki Anaam tayi da abinda inna sarai ta faɗa... Ji nayi fuskata ta fara ƙaiƙayi ban wani damu ba na cigaba da kwanciya ta amma ƙaiƙayin ya cigaba...tashi zaune nayi na fara sosawa ƙaiƙayin ya ɗan rage na ƙara yin kwance ina kallon ceiling...nan bacci ya kwashe ni... '' Innalillahi Asma'u zoki ga fuskar Abeedah sama sama nake jiyo hayaniyar su hakan yasa na buɗe idona'' '' taɓ ɗi jam...'' Asma'u ta rufe baki tana jinjina kai faɗuwa gabana yayi da sauri na tafi gaban madubi take zuciyata ta tsuke kamar ana matse min ita da ƙarfi ƙirjina ya fara sama da ƙasa na kasa kuka sai raɗaɗin da zuciya ta take yi wasu manya manyan pimples ne suka ƙara fito min da yawa kamar an watso su a ƙarƙashin haɓa da goshi da hanci... '' wani abu kika sha hala?" Anaam ta tambaya tana duba ni nan da can. lumshe idona nayi hawaye suka fara silala kafin jikina ya fara rawa kuka na ya fara fita da sauri ...sukayi tsaye suna kallo na babu wanda ya lallashe ni '' wai Meye nake jin tashin kuka?" Inna sarai ta shigo cikin ɗakin..nuna mata ni Anaam tayi '' ƙuraje ne suka fito mata a fuska shine take kuka...'' inda nake inna sarai ta iso '' na gani...'' itama ta shiga duba fuskata daga gefe da gefe '' ƙila wani abu tasha ko ta shafa..'' ina ji suna cinke cinken abinda nayi dayasa fuskata ta lalace har haka ban buɗe idona ba ƙuncin dake raina baya misaltuwa meyasa ni kaɗaice ta daban? Meyasa kowa yana rayuwa cikin sauƙi da jin daɗi banda ni? Ƙara rushewa da kuka nayi inna Sarai take lallashina har da cewa zata taya ni tafiyar dasu hakan yaɗan rage min wani abu kaɗan ba mai yawa ba Asma'u da Anaam kallo kawai suka bini dashi '' ke baga jiki ba ke baga kyau ba..oh ni tuwo..wannan abu haka? gaki da shegen tsawo mutum tsaf zai ɗauka ke namiji ne..'' cewar Anaam, bayan tafiyar inna sarai Asma'u tayi wata yar iskar dariya mai ƙular da mutum ...ina jinsu amma ban tanka ba..toh mema zance? Da gaskiyar ta ai..nidai bani da Sa'a... Maganganun Jay d akan zama pozitif (positive) suka faɗo raina...wani siririn hawaye ya sulalo min..taya zan zama pozitif bayan abinda yake faruwa ba hasashen shi nake ba...da gaske ne? Taya zan mayar da duk wannan a bayan ƙwaƙwalwa ta in cigaba da rayuwa kamar babu abinda ke damuna? taya zanyi farin ciki bayan abinda zai sani farin cikin banda shi? Fita su Asma'u sukayi ya rage ni kaɗai cikin ɗakin... miƙewa nayi da jajayen idona na isa gaban madubi naja doguwar riga ta baya ina kallon ƙirjina kamar ƙara shafewa yake a kowace rana... cikina ma ƙato sannan ƙuguna da bayana duka a shafe..meyasa? Fuskata kam bana son kallo ba ƙaramin ɗacin rai hakan ke sani ba...gashin gira ta yanzu a ɗan kwai shi amma bai da yawa...gashin idona har yanzu baida tsawo..sai dogon wuya duk ƙasusuwa da nake fama dashi...niɗin dai mummuna ce ta ƙarshe ma... sakin rigar nayi ina tunani..akwai abinda nake ba daidai bane? Ko banda yaƙini ne kamar yanda ake cewa mutum yayi addu'a da yaƙini... ko akwai wani zunubin da nake aikatawa wanda yake hana addu'oi na karɓuwa? Wannan tambayoyin sun zama wani sashe na rayuwata..wanda har yanzu na kasa samun amsar su... Cike da baƙin ciki na baro gaban madubin nazo na zauna saman katifar mu..Anaam ta shigo tana magana da kanta ƙasa ƙasa ban ma san abinda take faɗa ba wurin kayanta ta nufa tana neman wani abu..bin bayanta nayi da kallo..tana da faffaɗan ƙugu mazaunan ta manya...juyowar data yi yabani damar ganin yanda ƙirjinta ya ƙara girma cikin yan kwanakin da sukayi a tare damu...da bahaka suke ba,ƙanana ne ko ganin su ba'ayi amma yanzu har sunyi wannan girman ban taɓa lura ba sai yanzu...ƙasa nayi da kaina zuciya tana barazanar tarwatse wa...murya na rawa nace ''...n..i..ta dabance?'' na rasa inda zan sa kaina gaba ɗaya duniyar tayi min faɗi ban san inda zan kama ba... Magana ta fara yimin da ba'a tana dariya...a ƙufule nace '' abinda kike min dariyar akai..yanda nake bani nayi kaina ba kuma bani na zaɓi zama hakan ba ki dena bana so bani nayi kaina ba bani na zaɓi hakan ba'' murya ta tafito kamar raɗa hawayen da nake ta riƙewa suna rige rigen wanke fuskata kamar an ɗaura min wani abu a maƙoshi na kasa numfashi da kyau...jikinta ne yayi sanyi...nadama bayyane a fuskar ta bata ce komai ba ta fita ta barni ni kaɗai... Washegari bayan mun gama kari inna sarai ta kawo wani abu da bansan Meye shiba ta kirani a tsakar gida Mama na zaune daga baranda tana kallo..shafa min shi ta fara yi tana faɗin zai tafiyar da pimples ɗin sosai naji daɗi amma daɗin da sauri ya gushe...idan fa baiyi aiki ba? Su Asma'u daga gefe suna kallo wurin awa ɗaya abin yayi a fuskata koda aka wanke na duba madubi babu abinda ya ragu...kuma nasa rai koda za'a wanke inga fuska ta ta dawo lafiya lau ashe dai ni wawuya ce dana yi tunanin hakan.... Aloe vera ta ƙara shafamin bayan minti shabiyar ta wanke..ina jin Asma'u na faɗin wannan abin ba aiki zai yi ba...ban bi takansu ba... Bayan lokaci itama aloe vera'r aka wanke ban damu kaina da duba madubi ba dan dai Nasan labarin gizo baya wuce ƙoƙi... Ranar haka ta wuce zuciya ta ɗauke da nauyin daya kasa sauka...na ƙuntata nake ji kamar duk nauyin duniyar ne a kafaɗu na babu abinda ke min daɗi...abun ya ƙara tsanani da washe gari aka tashi rana bata fito ba ko ina yayi shiru yaran dake taruwa a gaban gida yau ma basu fito ba,da kosu mutum ya gani ƙila yaji sanyi a ranshi Da ƙarfe goma na fita sayen pad duk a takure nake hannu na gaban hijabi,iska na kaɗawa a hankali faɗuwa gaba na yayi dana ga hanyar da zanbi in wuce akwai dandazon maza da yawa na taka burki ina ji kamar in koma amma ina matuƙar buƙatar pad ɗin...dogon numfashi naja zuciya tana dukan tara tara na cigaba da tafiya '' a'a kaga wata yar silandiyon nan tafe...'' wani daga cikin mazan ya nuna ni '' doguwa yar shafal shafal...inama zata saki hijabin sai mu auna....'' wani ya faɗa yana tsareni da shegun idonshi da suke ja Nidai cikin raina sai addu'a nake jikina duk yayi sanyi tsoro ya shige ni ta shi wani daga cikinsu yayi ina kawo wa daidai wurin su ya jera dani muna tafiya Innalillahi ji nayi kamar in zura da gudu..abokanshi sai shaƙiyanci suke mana...hankalina yayi mummunan tashi '' yan mata ya yau...'' Muryar shi kamar irin na riƙaƙƙun yan shaye shaye,ban amsa ba nayi sauri nayi gaba yana biye dani a baya iska yake kwashe min hijabi naji kamar inyi kuka ban ƙara shiga yanayi ba sai dana isa shagon naga nan ma akwai maza da yawa zaune a wurin...taya zance a bani pad yanzu? Allah yasa akwai mutane da yawa kafin ni...sai binmu suke da kallo... '' kaga wata mai idon mage...'' wani ya taɓa abokinshi yana nuna mashi ni.. ƙin kallon sashen su nayi babban burina a wannan lokacin shine inga na isa gida '' yan mata mai za'a baki?" Mai shagon ya tambaya da murmushi a fuskar shi...numfashina na riƙe ina tunanin abinda zan faɗa mashi batareda wa'yannan sunji ba biro idona ya hango min sai na ɗauka na rubuta saman kuɗin ' Pad'na miƙa mashi...karantawa yayi a ranshi cike da fahimta ya juya ya ɗauko yasa cikin baƙar leda... '' na gode...'' na faɗa da sassauci a raina. .'' yauwa...'' na ƙara gyara hijabina sannan na juya Zan fita '' kalla kalla idonta wallahi kamar na mage...'' wani daban yayi maganar da hanzari nabar wurin Wannan gayen da ya biyo ni yana nan tsaye muna haɗa ido ya sakar min wani murmushin dayasa naji cikina ya bada ƙuuu..gaba ɗaya zubin shi bai yi kama dana mutanen arziƙi ba... Wuce shi nayi ina tafiya da sauri...yana biye dani babu abinda nake faɗa sai Lailaha illa anta subhanak inni kuntu minazzalimeen '' yan mata ji mana..'' ya sha gabana saura kaɗan jikin mu ya haɗu.. nayi saurin ja baya '' Innalillahi wa inna ilaihi raji'una...'' na furta hawaye na ƙwace min wasu biyu daga cikin ƙawayen nashi suka zagaye ni suna maganganu ba daɗin saurare '' ni yanzu wa zai taimake ni?" Nayi ma kaina tambayar cikin raina..ina kallon su da idona da sukayi ja ash ɗin ya ƙara duhu '' ku kalli ƙwayar idonta kamar ruwan toka...'' '' eh lallai ba shakka hakane...'' '' daɗin ta na daban ne da alamu...'' suka kwashe da dariya ni kuwa babu abinda jiki na keyi banda rawa...na zama kamar tunkiya a tsakiyar kuraye..ban ƙara ruɗewa ba sai da naji ana jan hijabina daga baya... Na fashe da kuka '' wallahi ƙwayar idonta da shape ɗinsu ƙara tsumani suke.. '' Na shiga tashin hankali na tsorata sosai..fara matsoni suka yi dukan su babu mai kyau'n gani sai jajayen idanu... wani daga cikin su ya riƙe hannu na dana damƙe hijabina dashi..ihu na kurma gaba ɗaya na fice hayyacina na shiga wani irin yanayi da nima ban fahimta ba sakina yayi suka dafe kunnuwansu kafin kuma suka fara tserewa sakamakon ihun da nayi ya jawo hankalin wani mutum dake wucewa ...da sassarfa ya ƙaraso inda nake nikam na rufe idona sai ihu nake... '' baiwar Allah...'' mutumin ya kira da ƙarfi fuskarshi da damuwa..buɗe idona da suke rufe nayi...suka sauka akan fuskar shi...ido guda manne da plaster ɗayan kuma lafiya lau..''.kina lafiya?" Ya tambaye ni Girgiza mashi kaina nayi...duƙawa yayi ya ɗaukar min ledar pad ɗina data faɗi '' mu tafi in raka ki...'' ban Musa ba nayi gaba yana biye dani duk a ruɗe nake... babu abinda nake banda hawaye ina tafiya da sassarfa kamar zan kife..yana faɗin inbi a hankali... Jikin Mama na faɗa na rushe da kuka tana tambaya ta mai ya faru...inna sarai kuma ta fita zuwa ƙofar gida saboda sallamar da mutumin keyi...na tafi na barshi da pad... Anaam ma tazo ta zauna daga gefe haka ma Asma'u...hankalin Mama ya tashi.. sassauta kukan nayi na faɗa mata abinda ya faru...ta rungume ni tana shafa baya na...'' Allah yasa bawan Allah'n nan da Asma'u ta jiwa ciwo yana kusa shine ya ceceta..gashi har yanzu bamusan sunan Shiba...''.inna sarai ta faɗa da alhini... Anaam da Asma'u suke taywy Mama lallashina a haka har bacci ya ɗauke ni.... gaba ɗaya babu wanda yaji daɗin abinda ya faru... Ranar Monday da wuri muka isa makaranta har ma muka samu assembly kuma Diyaam da Jay D suma har sun iso...hakan yayi min daɗi '' uniform ɗin sunyi maki kyau..'' Murmushi Anaam tayi da jin Diyaam ta yabe ta '' na gode...'' '' Attention..'' Assembly pirifet ta ɗaga murya..hakan yasa yan SS 1 da 2 sun yi ƙasa da surutun da suke..kowa ya shiga layi..nice a baya gaba ɗaya dan wurin gyaran layi mun rabu sannan dama nafi son kasacewa a ƙarshe bana son kowa yana goga min jikin shi a baya bayan anyi addu'oi, national anthem da national pledge principal ta hawo saman dakalin ta fara magana akan jarabawar dake ƙaratowa... Tayi mana nasiha da kuma ƙarfafa mana guiwa da muyi karatu sosai Bayan tagama ezzam master (exam master) shima ya hawo bayan ya gama cika mu da surutu yake faɗin kuɗin waec da neco dubu saba'in da biyar...'' hmmm!!" Wurin ya ɗauka da surutu wasu kamar zasu dake shi jin uwayen kuɗin daya ambato ya ƙara da faɗin wani sati za'a fara mock exam ɗin...naji gabana ya faɗi...idan fa banci jarabawar ba? Idan fa na faɗi? Ƙasa nayi da idona na ɗaura hannu na a gaban goshi na saboda ranar data fito...gashi ko kuɗin wannan term ɗin bamu biya ba...kuma mu uku ne..kenan kusan dubu ɗari biyu da wani abu zamu biya...BALA'I!! Ji nayi zufa tana wanke ni daga ko wacce kusurwa ta jikina..jini ya janye daga fuska ta... Sai da suka gama yi mana gargaɗi akan mu da ake bi bashi muyi sauri mu biya idan ba haka ba,bamu ba rubuta jarabawa.. sannan aka sallame mu... Koda muka shiga aji sai alhini suke wasu suna faɗin baza su rubuta jarabawar ba dasu biya dubu saba'in da biyar Gara sun kama sana'a...ni kuwa nawa tunanin shine dole in ƙara ƙoƙari wurin neman aiki zama nayi ina cigaba da tunani naji wasu daga gefe na suna faɗin '' wai fa ba'a haɗa da kuɗin lesson ba...in an haɗa dasu dubu tamanin da biyu ne...'' da ƙarfi na juyo Wacce ke shan ruwa kusa da wacce tayi maganar ta fesar da ruwan ta window ido zare '' dubu tamanin da biyu? Kam bala'i da yake dai Allah yasa ba lesson ɗin nake ba...'' wacce ta fara magana da farko ta sheƙe da dariya '' dey play..yarinya ko kinyi lesson ɗin ko bakiyi ba dole sai kin biya...'' Ajin ya kacame da surutu kowa yana ƙorafin kuɗin sunyi yawa...ina zan sama mana kusan dubu ɗari biyu da arba'in da wani abu? ɗauke kaina nayi na koma kallon window..ina hango bishiyoyin da ganyayyakin su suke Kore shar...hasken rana na ƙarama kalar su haske,ga yara can ƙila yan SS 1 da 2 suna kai kawo wasu na shiga aji wasu na fita babu ruwansu da abinda ya shafe mu..mu yan SS 3...haka zalika babu wanda yasan abinda ke raina babu wanda yasan matsalolin dake damuna... Bana tunanin akwai abinda za'a faɗa idan dai ba kuɗin za'a kawo ba da zai canja min yanda nake ji a raina...oh Allah ni Abeedahtu tako wace fuska ina da matsala... '' Bee...'' Jay d ta jijjigani tana yaƙune fuska ta kasa fahimtar me nake tunani da har banji taba...'' me kike tunani haka?" Matsa mata nayi ta shiga ta zauna ƙamshin turaren ta yaɗan sa naji yar ƙaramar nutsuwa.. Diyaam ma ta zauna a nata gefen sai lokacin naga ashe Itama tasa uniform sosai tayi kyau farar fatar ta ko mutum bai taɓa ba zai san tana da laushi '' lesson ɗin da akace wai ko mutum bai yiba zai biya sannan ni ban san cewa ana biya ba wallahi..'' na faɗi rabin gaskiyar abinda nake tunani...juya idonta Jay d tayi '' dama suna abu kyautane?" Na girgiza kaina...na juyo gefen Diyaam '' Ma sha Allah Sofia Diyaam tayi kyau'' tayi murmushi batace komai ba... Daga nan malamin literature ya shigo ajin.. mayarda hankali mukayi akan abinda yake koyarwa musamman ni..a da bantaɓa jin ina buƙatar in mayarda hankali ba domin in fahimci karatu ba saboda na riga da na yarda cewa bazan gane ba..amma yau daban ne,ina so in fahimci abinda ake koyar damu...kuma ƙwaƙwalwa ta taƙi bani haɗin kai..amma na tilasta kaina..bayan ya tafi nasa Jay d da Diyaam suka ƙara yimin bayani... ''.you know what? Idan an tashi ki biyo ni gida mu dinga study session akan English da math.. kin ji?" Jay d tayi maganar tana kallo na...'' idan na biki,wazai nema min aiki?" Dogon numfashi taja.. Diyaam tabi mu da ido...'' zamu iya duk lokaci guda...ina nufin,idan mun fara mock,wasu ranaku zamu tafi gida da wuri sannan jarabawar Bama dole bace.. idan mun gama study session sai ki tafi neman aikin...'' gyaɗa kaina nayi da gamsuwa da abinda ta faɗa.... '' zamu iya farawa yau?idan an tashi tara'' '' idan kina so...'' murmushin jin daɗi nayi...daga nan muka cigaba da hira.. Diyaam ta bamu wani cakulet da muka tambaya ina ta samu saboda daɗin cakulet ɗin '' hamma na ya kawo Mani daya tafi ƙasar su...'' kallon ta mukayi dan bamu fahimci abinda take nufi da 'ƙasar su'' ba amma bamu yawaita tambaya ba Anaam itama ta shigo cikin hirar...bayan an tashi tara bamu fita ba,maka Jay d ta ɗauka tayi rubutu a gaban allo..sannan ta juyo ga sauran dake cikin ajin tace '' ina bada study session kyauta ga duk mai so zai iya shigowa... subjects ɗin da nake koyarwa math da English da literature..'' rabi da kwatan yan aji duk sukace suna so yan kaɗan kawai ne suka tafi wasa...Jay d ta tsaya gaban allo tana mana bayani da ƙwarewa da kuma haƙuri...yanda take bayanin ko wani malamin albarka.... Kuma ina fahimta dama tun farko matsalata ba rashin fahimta bane sai na fahimta na gane sosai amma kuma nan da ƙanƙanin lokaci sai in daburce idan an tambaye ni... Bayan an tashi makaranta mu yan SS 3 muka tsaya domin lesson ɗin....sai ƙarfe huɗu muka gama.. sallah muka fara yi sannan kowa ya kama gabanshi...yan ajin mu sai godiya suke ma Jay d..nida kaina naji ina alfahari da ita Wurin famfo muka tsaya mu biyar ɗin,muna wanke ƙafafun mu da suka ɓaci da ƙasa..nake kallon ranar data zama ja ta fara tafiya gida sai kuma makarantar mu data zama empty ba mutane da yawa duk sun fita...ajujuwan mu da wasu tagogi suke buɗe...ƙaraurawar dake maƙale da bishiya bata da mai bugata...da yan tsiraran mutane da suka rage...wasu suna wasa a hanyar su ta fita..wasu suna da yawa..wasu su kaɗai suke tafiya..ba kowa tare dasu... Wasu da murna da farin ciki a fuskokinsu wasu kuma... fuskokinsu ba walwala naji abu ya tsaya min a ƙasan ciki..kamar kada mu tafi...kamar mu koma aji...bana so in rabu dasu..na gode Allah daya sa bani kaɗai ce zanbi hanya ba da irin fanƙon (emptiness) da zanji sai ya ninka wanda nake ji a yanzu... '' mu tafi...'' Diyaam data gama wanke fuskarta ta faɗa...a tare muka jero muna tafiya suna hira nidai nayi shiru ina sauraren su... A bakin gate muka samu motocin su Jay d da Diyaam sun iso kafin muyi wata tafiya mai nisa... dolen mu muka yi musu bankwana suka shige motocin su,mu kuma muka cigaba da tafiya a ƙasa... Na juyo ina kallon wa'yanda ke bin hanyar nan da mutane da yawa ke bi...rana ta haska bayan su,mu kuma muna fuskantar ranar...ina cikin yanayi...ban san abinda kemin daɗi ba...har ji nake kamar in jawo gobe... Jay d..da Diyaam..su nake kewa duk da bamu daɗe da rabuwa ba...sai kuma damuwar data maƙale min a zuciya kamar baƙar tsutsa... (leech) Da muka koma gida babu wanda yayi maganar kuɗin makaranta...kawai muka yi wanka muka ci abinci..na fito bakin ƙofar gidan mu domin wasa da sauran dake wurin..abubuwa suna tafiya dai dai da farko su Asma'u ma suka fito suma..bada daɗewa ba mutane suka soma taruwa... Ina tsaka da lilo naji wata mai suna A'e tana faɗin '' fuskar ki Abeedah kamar anyi ƙunar baƙin wake...duk ta gwalje ta lalace...'' wa'yanda ke kewaye damu suka fashe da dariya...lilon dake shilla wa da ƙarfi... Ya rage tashi kamar farko...naji kamar an soki zuciyata da mashin da aka ɗosana cikin wuta.... '' wallahi kuwa da gaskiyar ki..da nice da irin fuskarta,da bana tunanin zan iya fitowa cikin mutane...'' inji Sumayya...sauka nayi daga lilon... Wata yarinya ta hawo..na ƙaraso inda suke '' cin fuska har a gabana baxaku iya bari in bar wurin ba?" Nayi maganar da ɗacin rai...da farko zaune suke sai suka miƙe '' wasa muke fa..ke baki iya ɗaukar wasa bane?" Haleema ɗaya daga cikinsu take min kallon rainin wayo... Haɗiye abinda ya tsaya min a wuya nayi...na kalli A'e '' Fuskata bata gwalje ta lalace ba A'e,ƙila rashin idon ne yasa kike ganin haka...ina nufin,mutum mai ido biyu yafi mai ido ɗaya...ki kalli kanki a madubi A'e...ƙila shima ɗayan idon naki ya fara samun matsala...'' sakin baki A'e tayi tana kallona suma sauran sukayi shiru Anaam ta matso kusa tana hararar su, wurin yayi tsit da wani iska mai nauyi na juyo na kalli Sumayya '' da yake ni bana kunyar fitowa da yanda fuskata take..ba sai nayi kwalliya mai yawa ba don ɓoye Fuskata da yake Allah ya rabani da yawo da fuskar da gefe guda fari gefe guda baƙi kamar anyi gobara tsabar bleaching...'' Sumayya ta zaro ido...da alamu mamaki take ya akayi na sani... '' haba Abeedah akan me zaki dinga zaginsu har haka ke baki san wasa ba..?" Aliya da batayi magana ba tuni ta furta..ganin yanda suka yi shiru kamar ruwa ya cinye su... dariyar da bata kai zuci ba nayi..ina danne baƙin ciki na...'' wasa?" na ɗago idona ina kallon su duka '' lokacin da suke wasar sun yi tunanin yanda zanji? Sunyi tunanin wani irin yanayi hakan zai jefa Ni? Sunyi tunanin wane irin tasiri hakan zai haifar a zuciya ta da rayuwa ta?..." Na dakata ina share hawayen da suka sauko min dukan su jikinsu yayi sanyi na cigaba da faɗin '' mafiyawancin mutane suna faɗin abinda yazo kansu ne batareda tunanin yanda wanda aka faɗawa maganar zaiji ba...a wurin su wasa ne..abin ayi dariya...amma wanda aka faɗa mawa? Baya mantawa! Wasu har su mutu wannan maganar tana kasancewa dasu ta rayu dasu....wasu maganar tana gina su wasu kuma ta rusa su... Akan mai zasuyi wasa da abinda bani na ɗaurawa kaina ba? Ita A'e da take da ido ɗaya,ita ta halicce kanta a haka? Meyasa bazatayi tunanin yanda zata jiba idan wani ya faɗi magana akan yanayin halittar ta? Bana son irin wannan wasannin!" Na ƙarashe maganar da gargaɗi ban jira cewar kowa ba na wuce ciki...kallo ya koma akan su A'e..da yawan su sun gamsu da abinda na faɗa...ai babu wanda zaice ba'a taɓa faɗa mashi wata maganar data tsaya mashi a rai ba ko? '' ku iya bakin ku idan ba haka ba wata rana zai saku a matsala...'' cewar Asma'u kafin ta wuce ciki...da nadama a muryarta A'e tace '' dan Allah Anaam ki bawa Abeedah haƙuri...'' suma sauran abinda suka faɗawa Anaam kenan.... +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 18. ... tawakkalin da nake so...🖊️ Da na shiga gidan,daurewa nayi na hana kaina kuka na danne baƙin cikina kuma na hana zuciya ta..tambayoyin da take rattafo min a duk sanda abubuwa suka kasance kamar haka... Dogon numfashi naja sannan na shige cikin gidan ina kallon tsakar gidan da ba kowa sai na wuce ɗakin Mama '' Ni babban abinda yafi damuna kuma yake ban tsoro saratu shine idan fa wata rana sukayi ƙoƙarin....'' ɗaga labulen da nayi ya katse Mama daga ƙarasa faɗar abinda take faɗa duka su biyun suka jiyo suna kallona kyakkyawar fuskar Mama dake ɗauke da damuwa tayi saurin canja wa zuwa mai walwala inna sarai take zarar ido...su biyun daka gansu kasan yaya da ƙanwa ne, nayi nadamar ɗaga labulen dama na bari na gama jin abinda zata faɗa amma kuma ata wani fannin Haramun ne laɓe aiko? na sassautawa kaina... '' Abeedah har kin dawo?" Inji inna sarai da alamun rashin gaskiya jinjina kaina kawai nayi...sai na shigo cikin ɗakin na zauna gefen Mama tareda kwantar da kaina saman cinyarta,ta ɗaura hannun ta saman goshina... '' Mama dan Allah ayi fate yau...'' '' wai fate,na bishi da gudu ba wando...!" Anaam ta hankaɗo labulen tana harara ta '' to uwar yan marasa kunya shi za'ayi bari in tashi ma kigani...'' kwantawa wurin Anaam tayi tana birgima ita ala dole baza'ayi fate ba '' yauwa inna sarai sai dake...'' na faɗa ina dariya da son ƙular da Anaam... '' ai sai dai in kwana da yunwa wallahi...'' '' cikin ki kona wani? Ke kika sani...'' miƙewa inna sarai tayi ta fita Anaam biye da ita...nikam na raka su da dariya '' Ya kike?" Mama ta tambaya da kulawa, mirginawa nayi ta yanda ina kallon fuskarta batareda na tashi daga jikinta ba...ita da Asma'u kamar an tsaga kara duk da Mama ta tsufa idan ka kalleta zaka gane ba ƙaramar kyakkyawar budurwa akayi ba lokacin yarinta '' dama banda lafiya ne?" Na mayar mata da tambayar tayi murmushi '' ba wannan rashin lafiyar nake tambaya ba Abeedah...ina nufin ya kike ji a ranki yanzu?" '' oh...'' sautin ya fito daga bakina ya nake ji yanzu? Babu komai bana farin ciki bana baƙin ciki a dai dai wannan lokaci ban san nan da anjima kaɗan ba '' babu abinda nake ji'' na mirgina na koma gefe...'' wani abu ya faru a waje?" Tambayar data yi yasa na juyo na kalli fuskar ta...'' na lura da sanda kika shigo...'' '' A'e ce tace wai Fuskata kamar anyi ƙunar baƙin wake...'' murya ba amo maganar ta fita '' hmm..ke kuma me kika faɗa mata?" '' nace ƙila idonta ne bai gani da kyau tunda ido ɗaya ne da ita...kuma na faɗa masu bana son wasan banza tunda sunce wai wasa suke niban iya ɗaukar wasa ba...Mama meyasa mutane basa tunani kafin su faɗi magana ne?" '' kowa da yanda yake Abeedah..ba zaki iya sa mutane suyi yanda kike so ba...'' ta fara sai na juyo ina kallon fuskar ta,ta cigaba da faɗin '' amma kina da damar zaɓin yanda zaki tunkari abinda suka faɗa ko sukayi....zaki iya kallon alkhairi ko gaskiyar dake cikin maganar su,sai Kiyi aiki da wannan,Kiyi farin ciki ki cigaba da rayuwar ki...ko ki kalli sharri da ƙaryar dake cikin maganganun su,sai ki bari hakan yayi tasiri a kanki sai ki kasance cikin baƙin ciki da damuwa da rashin karsashi....'' Ƙasa tayi da kanta idonta cikin nawa '' ina so koda yaushe ki kasance mai tunani mai kyau koda baki fahimci abinda ke faruwa ba..Kiyi tawakkali ki fuskanci gaba da ƙwarin guiwa da kuma yarda da cewa Allah ya isar maki abinda yayi shine daidai...'' gyaɗa kaina nayi duk da ban fahimci inda maganar tata ta dosa ba...naso inyi mata magana akan abinda naji suna magana akai itada inna sarai,kafin in tambaye ta naji inna sarai tana ƙwala min kira '' tashi ki tafi...'' Tashi nayi na fita daga ɗakin ina jujjuya maganganun ta amma na kasa fahimtar me take nufi... Anaam na fara gani a tsakiyar gida tana jajjagen kayan miya bakin na yayi tsawo kamar mazurari... Asma'u tana baye inna sarai a kitchen tana fita wuta..duk hayaƙi ya baɗe wurin ... '' xoki kula da wutar bari in wanke tsaki...'' tayi maganar idonta cike da hawaye hanci majina ba shiri na saki dariya '' gaskiya dai bari in wanke tsakin ke kyaji da wuta...'' '' ke uwar son banza ko?" Girgiza kaina nayi ina cigaba da dariya na shiga na ɗauki tsakin dake cikin ƙwarya... Ɗakin Mama Asma'u ta wuce bayan ta fito daga baye... ba kamar Abeedah ba nesa da Mama ta zauna tana binta da ido da alamun magana a bakinta '' ƙaraso nan...'' sai ta tashi ta isa inda Mama take,ta kwantar da kanta saman cinyar ta, zame ɗan kwalin kanta Mama tayi tana shafa gashin ta tace '' akwai abinda zaki faɗamin ne?" Asma'u tayi shiru na lokaci dan batasan inda zata fara ba kuma bata san me zata ce ba '' zaki iya faɗamin ko meye ne...ni Maman kice...'' mama ta ƙarfafa mata guiwa '' ina son Khalil...'' shiru ne ya biyo bayan maganarta hannun Mama dake motsi saman gashinta ya tsaya cak... hawaye Masu ɗumi suka silalo daga idon Asma'u...kafin kuka mai ƙarfi ya biyo baya jikin Mama yayi sanyi.haɗiye damuwarta tayi da taushin murya tace '' meyasa kike kuka?" Tashi zaune Asma'u tayi ta riƙo hannun Mama ta ɗaura saitin zuciyarta '' duk da yanda zuciya ta ke kiranshi...shiɗin burine da bazai taɓa kasancewa ba Mama...na tabbatar yana da masoya da yawa..kuma daga ƙarshe niɗin yarince kawai daga cikin wa'yannan ɗinbi jama'ar... I'm Just a girl part of the crowd...'' rasa abin faɗa Mama tayi kawai sai ta jawo Asma'u ta rungume ta tana shafa bayanta...'' akwai Allah Asma'u...ki cigaba da addu'a...'' ***** Bayan Isha'i dukan mu zaune muke saman baranda yau ma ba wuta sai fitilar da muka kunna daga gefe, akwai iska mai sanyi da taurari kaɗan kuma akwai hadari ,cikin wani ƙaton tire inna sarai ta zubo faten da cokula kowa ɗaya ɗaya muka zauna a cycle nida Asma'u gefe da gefen Mama..inna sarai da Anaam gefe ɗaya,ƙamshin faten mai sa yawun mutum su tsinke amma dai a ganina yayi yawa... '' kai wannan fate yayi mana yawa inna sarai...'' Asma'u ta rigani faɗa taɓe baki inna sarai tayi '' munanan daku wannan mai cikin zanen saita nemi ƙari shine yasa na ciko faranti....'' dukan mu muka yi dariya harda Mama tana harare harare tace'' ai dai lafiya ke ci.yanzu idan mutum baida lafiya ko kaza aka ajiye gaban shi sai dai yayi ta lasar baki..ku barni inci abinci na dan Allah...'' '' Ina bayan ki Sha'awanatu...'' Mama ta goyi bayanta,ajiye cokalin Anaam tayi taje ta wanko hannu ta dawo ta tsunbula ciki,kowa nashan fate da cokali ita da hannu take sha harda wani ' zuruf zuruf 'take...inna sarai ba abinda take sai aika mata harara faten yayi daɗi sosai bayan mun gama muka zauna a wurin Anaam tana bamu labarin garinsu mun sha dariya ba kaɗan ba...'' akwai wata yarinya mai suna Salame kusa da gidan mu suke wai ɗan ƙaramin bunsuru take goyawa a baya a matsayin jaririnta ko bari batayi ya taka ƙasa...ɗan bunsuru ko ya kafa tsuwa musamman idan tasa zane ta goye shi....'' '' Haahaa! kai.wai mutum da goyon bunsuru ina Lafiya..'' inji Mama... '' wallahi ko..ranar an ɗaura sanwa saman wuta,bunsuru garin kwaɗayi ya toye baki yana ta tsala ihu '' Inna sarai tayi maganar wurin dariya har saida ciki na yayi ciwo...kuma naji daɗin kasancewar mu tare a wannan lokacin..hakan ya rage min girman damuwa ta ba kaɗan ba.... Washegari da muka tafi makaranta,na iske Jay d da Diyaam har sun iso sannan ajin shiru,kusan kowa ya mayar da hankali yana rubutu akan wata farar paper wurin zaman mu muka isa nida Anaam muka gaishe da wa'yanda ke kusa kusa,farar paper nima ta miƙo min.. Diyaam kuma taba Anaam... '' me zan yi dashi?" Dakatawa tayi da rubutun ta '' ai dole sai da wannan su xasuyi amfani dashi wurin cika bayanan ki,suna, ranar da aka haife ki,me kike so ki zama da sauran su...'' '' oh...'' na furta a hankali...na dawo da idona kan paper,me nake so in zama? Ban taɓa tunani akan wannan ba tsawon rayuwa ta ban taɓa ganin wani abun daya birge ni ba naji ina so in zama sunana na rubuta da sauran abubuwan da aka buƙata na ajiye biron batareda na cika inda aka tambayi me muke so mu zama ba''.na gani...'' Diyaam ta ɗauki paper tana dubawa kafin ta ajiye tana nuna min '' nan baki sa komai ba...'' ɗagowa Jay d tayi '' baki fahimci bayanin da na maki bane?" Ɗage kafaɗuna nayi '' ban san me nake so in zama ba ban taɓa tunani akai ba...'' Suka kalli juna kamar na faɗi wani gagarumin abu'' nima ban san abinda nake so in zama ba...'' Jameelah dake zaune daga gaban mu ta juyo... Wasu ma daga cikin yan ajin mu sukace basu san abinda suke so su zama ba.. wasu kuma kawai suna rubutawa ne badan abinda suka rubuta ɗin shine burin suba...wasu kuma daga gida aka zaɓar masu abinda zasu zama... '' kuna buƙatar career counseling...'' Jay d ta furta tana kallon mu... Ta sake fita ta tsaya gaban allo ta shiga rubuta sunan abubuwan abinda mutum zai iya zama.. tana bayani akai... Daga nan waya'nda suka fahimta ko suka ji abin yayi musu sai su zaɓa...nidai har lokacin ban sani ba...bana son in shiga abinda bana ra'ayi... Wata yarinya daga can gefe...kowa na rubutu banda ita,ta mayarda kanta tana kallon waje..'' Amina kefa? Bazaki yi rubutun ba?" Hameeda ta tambayi yarinyar kowa ya mayar da hankali akanta ta sauke numfashi sannan tace '' idan akwai abinda nake so in zama ina so in zama ƙwararriya a fannin soyayya...wannan shine kawai...'' '' Oh abinda kaɗai ke ranki kenan?" '' aure kike so ko meye?...'' '' awwn...kamar saliha...'' Sai zolayar ta ake ita dai murmushi ne nata tafa hannayen ta Jay d tayi kowa ya mayar da hankalin shi wurin ta '' eh...akwai...zaki iya zama love coach..mai bawa mutane shawara fanin soyayya..amma meyasa kike so ki zama wannan?" Jay d ta tambaya... murmushin yarinyar ya ƙara faɗaɗa...'' saboda idan nayi aure in sace zuciyar mijina ni kaɗai bazai kalli wata mace ba.. kamar yanda yake faruwa a littafi.. yarinyar da suke so ita kaɗai suke gani...'' '' ayyiriririri!!!!!ohhhhhh!" Yan aji suka ɗauka Ameena ta rufe fuskarta da hijabin ta '' amma dai kin san wannan soyayyar sai a littafi ko?" wata yarinya ta miƙe saman wurin zamanta tana riƙe ƙugu '' yo dama fa? Mazan yanzu ko suna tafiya tare da matar su wata tazo wucewa sai sun bita dana mujiya na rasa uban me suke kallo...'' wata daban ta faɗa... '' kuma sai ayi ta zuzuta kyaun jaruman abu zar takaici..kai mutum gaka ga kamar ka..ana ƙarasa mutum najin ɗaci...'' Nake sauraren su ina tankaɗe da rairaya akan kowane bayani da suke faɗi abu ya zama muhawara kowa yana bada nashi fahimta akan soyayya wasu na ganin irin soyayyar da ake yi a littafi har abada baza'a taɓa irin ta a rayuwar gaske ba...wasu kuma suna ganin zai yiwu Hafsah tace '' ban sani ba koda gaske irin wannan soyayyar tana faruwa..amma ni...zan so in yarda da cewa,zata iya faruwa...tunda akwai Allah...kuma ina fatan samun irin wannan soyayyar ko fiye da haka...'' gungu mu kayi suna cigaba da hirar su akan soyayya nidai ina saurare amma a raina ba tun yau ba,nima ina fatan samun irin wannan soyayyar Jay d da Diyaam suma sun tofa albarkacin bakinsu...abu yayi ƙamari da har yan wani aji suna shigowa ajin mu dan ayi muhawarar dasu...wasu daga cikin masu zuwa littafan soyayya makaranta harda musaya suke...wannan yaba wancan wancan yaba wannan...nima na samu wani littafi Mai suna ' DA AKWAI CIWO CIKIN ZUCIYA TA...' Jay d ma ta ƙara min da wani na turanci tace '' tunda kin fara fahimtar turanci,karatun littafan turanci zai taimaka maki ki ƙara iyawa...'' duba littafin nayi... zanen cover wani namiji saye da baƙaƙen kaya irin na turawa da wata farar mata saye da baƙin gyale kamar hijabi ya riƙe fuskarta yana sumbatar goshinta sunan littafin ' HER SHIELD ' Shi kuma dizain ɗin littafin Hausar wata yarinya dafe da ƙirjinta da hawaye a fuskar ta...kamar ta karye fiye da yanda za'a iya gyarawa(broken beyond repair) Jefa su nayi cikin jakar leda ta,hirar yan ajin namu na man daɗi sosai kowa sai kare abinda ya yarda dashi yake... suna kawo hujjoji masu wahalar sharewa...amma dai na zaɓi in yarda da cewa,wannan soyayyar zata iya faruwa a gaskiya kuma daga wannan lokacin na ƙudiri aniyar nemo tawa... Sanda ake koyar damu lesson bayan an tashi,na mayar da hankali na ina ƙoƙarin fahimta,duk da ba duka na fahimta ba na fahimta to some extent... 🍁🍁: Naji su Abeedahtuwo kamar anyi turanci? Eh mana turanci nayi...baki ji nace yanzu ina fahimtar karatun ba kamar daba? ai kawai ku shirya daga yanzu ina magana ina haɗowa da turanci dan in ƙara ƙwarewa kuma a san na iya ehe... 🍁🍁:🤭 Sanda muka koma gida,muna gama cin abinci Kasancewar babu wani aiki da zanyi na shiga karatun littafan dana samo na fara dana turanci ina da saurin karatu sosai duk da wasu kalaman sai dai in tsallake dan ba iya karanta su nake ba,wani abun ma ban ganewa haushin daya cika ni yasa na ajiye na turanci na dawo karatun Hausa inda nafi ƙaimi...rayuwar jarumar abun tausayi wato ita ɗin kamar babu ta, babu wanda ke lura da ita,babu wanda ke ganin ta..ba wai dan ita fatalwa bace sai dai saboda kamar ita ɗin bata da muhimmanci baga iyalanta ba.baga sauran mutane ba ko ƙawaye bata da babu wanda ke son magana ko mu'amala da ita... Idan da ace rayuwa ta zata koma kamar haka? Allah ya raba ƙila mutuwa zanyi ya zanji idan zan wayi gari ace su Mama sun dena kulani babu Jay d a tare dani? Har dare ina abu guda kwanakin da suka biyo baya na ƙara tsoma kaina cikin labarin..dan an fara kawo wa wurin daɗi sannan a makaranta ina iyakar bakin ƙoƙari na kuma a duk sanda na samu lokaci ina cigaba da neman aiki na har yanzu bamu faɗi a gida ba kuɗin da ake nema mu biya a makaranta Jay d tana ƙara taimaka min itama a nata fannin rayuwa ta cigaba da tafiya..ina jin sauyi tattare dani kullum ina Cikin murmushi idan na tuna irin soyayyar da ake zubawa a cikin littafin da kuma yanda nake ƙudurin samo tawa soyayyar kowa dake tareda ni ya fahimci nishaɗi na...ko aiki nake nakan tsinci kaina da hasashen faɗawa soyayya da nawa namijin novel... A haka kwanaki suka cigaba da tafiya..har ranar da zamu fara mock ta iso...nayi karatu sosai a gida,a makaranta ma munyi tare da Jay d da Diyaam wasu kam sai ƙoƙarin shiga suke da littafi da pepopin da aka rubuta amsa akai tsaye muke a gaban block ɗin ajujuwan mu mu yan SS 3,sunaye aka fara kira daga A-Z aka bamu lambobi Nice lamba 25 a ajin farko Jay d lamba 113,a aji na biyu Diyaam lamba 305 a ajin kusa dana ƙarshe Anaam lamba 205 ajin su ɗaya da Diyaam Asma'u lamba 101 ajin su ɗaya da Jay d... Ana kiran mutum zai shige kowa da seat ɗinshi...mun sha gargaɗi har kunnen mu yayi ciwo malamai kuma sai zagaye mu suke..duk dai irin abubuwan nan da ake idan za'a rubuta jarabawa dan tabbatar da cewa ɗalibai basu samu damar satar amsa ba shi ake mana yanzu... Paper farko English ne....yawu na haɗiye ganin tambayoyin da suke hararata jikina yayi sanyi naji hankalina ya fara tashi..na ɗaga kaina naga kowa na rubutu banda ni '' ki tuna kada ki tsoro ta kija dogon numfashi idan baki fahimci tambayar ba ki tsallake ki amsa na gaba kada ki ɓata lokaci akan wanda baki sani ba...'' kalaman Jay d suka dawo min kamar lokacin take yinsu badan na yarda dacewa jan numfashin zaiyi wani abu ba naja ɗin na ɗauki biro na shiga rubutu... Wanda ban sani ba in tsallake nayi mamaki dana ga cewa ina amsa tambayoyin da sauƙi... to da yake dai nayi karatu..na ɗago kenan naga wasu suna fito da littafi daga cikin hijabin su.. wai suna duba amsa taɓe baki nayi dan Jay d tace babu amsa a cikin littafi na mayarda hankali na akan paper ta bada daɗewa ba mukaji ance '' KAI KU TASHI!!!" Sai da naji hanjina sun kaɗa da sauri na ɗago naga ashe waya'nda suka fito da littafi ne aka kama taɓ ɗi jam sun wulaƙanta gaskiya Da ƙarfe sha biyu muka gama jarabawar ko kaɗan bana son yanda aka wani zauna ana faɗar amsar da ba daidai ba da wacce ke daidai hakan na tayar min da hankali '' ya jarabawar?" Diyaam ta tambaya '' jarabawa da godiya Allah yasa munci...'' ''.haha..kada ki damu wannan ba itace mai muhimmancin ba gwaji ne kawai'' na gyaɗa kaina muka zauna ƙarƙashin bishiya bada daɗewa ba su Jay suka ƙaraso'' ya jarabawar?" Murmushi tayi min ta zauna kusa dani '' dama wannan jarabawa ce?'' tayi maganar da dariya nayi murmushi..itafa na manta...ashe yar baiwa ce.... Mutane da yawa suka taru a ƙarƙashin bishiyar muna hira,dayawa daga cikin mu sun damu da idan abinda suka rubuta daidai ne .. wa'yanda basu damu da sakamakon suba,suna burgeni cewa sukeyi abu mai muhimmanci da kansu suka rubuta sannan kuma sun yi iya ƙoƙarin su,sun barwa Allah saura irin wannan tawakkali shine zuciya ta take mutuwar son samu amma na kasa a koda yaushe Nasan da cewa akwai mutane da yawa da yanayin su yafi nawa ɓaci amma kullum suna rayuwa da murmushi da gode Allah..meyasa nima baxan zama kamar suba? '' kai dan Rabbi kuzo muyi wasa...'' Hameeda ta miƙe tsaye tana gyara rigarta...'' wace wasa zamuyi?" Wata daban ta tambaya '' kacha (catcher) ni zanyi...'' Hameeda ta amsa mata...da yawa muka yarda.. muka shigo cikin wasar...tayi daɗi kamar kada mu dena amma lokaci yayi saurin tafiya. da ƙarfe ɗaya muka baro makaranta Diyaam ta tafi motarsu tana mana bye bye mu kuma muka bi Jay D a tata motar...gidan su zamu saboda lesson ɗin data ce zata dinga koya min... Lokacin da muka iso Anaam bakinta ya kasa rufuwa sai santin girma da kyau'n gidan take itama Asma'u ta yaba... Da muka shiga ciki Anaam harda yin luuu kamar zata faɗi tsabar ita yar drama ce '' ashe Aljannar duniya kike rayuwa a ciki Jadeedah?" Inji Anaam tana kallon ko ina ido waje da alamu ba ƙaramin burgeta gidan yayi ba samun innarsu mukayi zaune a parlor dukan mu muka gaishe ta da girmamawa ta amsa mana da fara'a da sakin fuska... '' Umma karatu zamuyi kin san mun fara jarabawa...ina Deen?" '' Deen bai dawo ba su kuma ki sama masu abinci kafin ku fara...'' godiya muka yi mata Jay d taja mu zuwa ɗakinta Anaam ta ƙara ruɗewa da ganin kyaun ɗakin... Asma'u take kallon ko ina amma bata taɓa komai ba,ba kamar Anaam ba...hijabin mu muka cire, ɗaya bayan ɗaya mukayo alwala mukayi salla muka sake komawa ƙasa har kitchen ta jawo mu ta buɗe fridge akwai abinci daban daban tace kowa ya zaɓi abinda zaici Anaam ita tafi kowo ɗaukar kaso mai yawa.ta bamu kunya ba kaɗan ba bayan mun gama duk wannan nida Anaam muka zauna Jay d na koyar damu ita kuma Asma'u take kallo a ƙatuwar TV'n su Jay d tunda ita bata buƙatar a koyar da ita. Study session ɗin yayi min daɗi sai da aka kawo wurin math naji raina ya fara ɓaci..amma Alhmadulillah sauran subjects ɗin na fahimta...sai bayan la'asar muka koma gida ... Ranakun da suka biyo baya cike suke da wahala a wurina...kullum idan an tashi muke biyo Jay d gida don study session ɗin mu,bayan mun gama idan mun koma gida da wuri zan shirya in tafi neman aiki har sabon gari kasuwar kwari..da sauran wuraren da nake tsammanin zan samu aiki amma babu wani cigaba...ga jarabawar mu ta mock yanzu na fara jin wahalar ta har naga nawar mu gama... A gefe ɗaya kuma ina cigaba da karatun littafai na...ina ɗan ƙara iya turancin..duk kalmar da ban san ma'anar taba,nakan rubuta idan na haɗu da Jay d sai in tambayeta ma'anar kalmar... A duk sanda na tuna kuɗin da ake tsammanin mu biya sai naji hankalina ya tashi gabana ya faɗi...ban san inda zamu samu wa'yannan maƙodan kuɗaɗen ba...duk sanda nake tunanin na fara samun sararin shan iska daga matsalolina sai wata ƙatuwar matsala ta kunno kai ta sake tayarda wayan'can na bayan da nake tunanin ba zasu sake damu na ba... Zaune muke a parlon su Jay d muna kallon wani fim ɗin Hausa..dukan mu mun mayarda hankali ko ƙiftawa bama san yi... Takun da mukaji a matattakala yasa muka juyo ba shiri dan dai mun san mu kaɗai ne a gidan,Maman su Jay d ta fita mamaki ya hanani motsi ganin wanda ke wurin shima yayi tsaye yana min murmushi..saye da baƙin wandon Gucci da farar riga da slippers... '' Name sa...'' kafin ya iyar Anaam data sheƙo da gudu daga ɗakin Jay d tayo cikin shi ta bangaje shi dama ya kawo ƙarshen stairs ɗin faɗuwa yayi Itama garin ƙoƙarin taimaka mashi ta biyo shi suka faɗi tare ita a sama '' Ahhh!!!"miƙewa mukayi muka isa wurin su muna musu sannu Abeed yayi kwance fuskarshi a yamutse alamun yaji zafin faɗuwar hakan yasa ya kasa motsi ya buɗe ido yana kallon sama..da sauri Anaam ta miƙe tana rarrabar ido '' sannu Deen tashi...'' Jadeedah ta miƙa mashi hannu ya kama ya miƙe da ƙyar hannun shi dafe da ƙugu... ta taimaka mashi ya isa ya zauna saman kujera muka bi bayansu da sannu Anaam ta tsaya kusa da benen tana cizon yatsa da zarar ido... '' yauwa...wash Allah na...ta kusa karya Ni...'' ya furta yana lumshe ido tareda jingina da kujerar...mu uku muna fuskantar shi '' ni ban ma san kana nan ba...'' murmushi yayi yana kallona nima shi nake kallo na kasa yarda da cewa shine Deen ɗan uwan Jay d da take magana akai koda yaushe... '' Bee wannan shine yaya na da nake ta faɗa maki...Deen...'' ta juyo gefe na '' kina nufin Abeed ɗin da nake baki labari muna aiki tare?" haɗe girar ta tayi take kallon tsakanin nida shi shafa ƙeyarshi yayi '' yeah nine...'' nama rasa abin faɗa haka ma Jay d kamar bata san cewa shima a maina hotels yake aiki ba... '' haka kawai muka neme ki muka rasa...'' ya furta.na sauke numfashi nace '' ai korata sukayi ba bayani kuma ko suba ni notis wallahi...'' '' haba dai?" Ya gyara zaman shi njina kaina nayi muka cigaba da hira a hankali Anaam ta ƙaraso ta zauna daga gefen Asma'u ya juyo gefenta '' wannan yar fullo yar uwar kuce?" ƙasa da kanta Anaam tayi Abeed na mata kwarjini sai satar kallon shi take tunda ta zauna wurin yanzu kuma da yake kallonta ta kasa haɗa ido dashi '' eh baka ga kama ba wannan Asma'u kuma ƙanwa ta sai Jay d da nake ta faɗa maka ƙawata...'' mukayi dariya dukan mu banda Asma'u da Anaam da tayi ƙasa da kanta jin yanda Abeed ke kallonta...duk ta takura... '' Mu tafi gida...dare yafara yi...'' ta faɗa min tana turo baki '' ƙarfe biyar fa..yadai yar fullo? Tserewa kike ƙoƙarin yi baki ban haƙuri ba?" Ɗauke fuskar ta tayi tana ƙara zumɓuro baki gaba tana ƙunƙuni ya girgiza kanshi cigaba da azalzalar mu tayi akan mu tafi dole muka miƙe ba shiri '' bari in sauke ku...'' inji Abeed,Anaam kamar zata yi bindiga..dama dan yana wurin tace su tafi yanzu kuma shi zai sauke su gaskiya dai da sauri tace '' a'a ka barshi kawai,za muyi essa sais (exercise)...'' ɗage gira yayi tayi saurin ɗauke idonta '' nima bari inzo mu tafi...'' Jay d ta ruga sama da sauri ta ɗauko mayafi muka fito tare bayan Abeed ya ɗauki mukulli muna tafe muna hira..sai naga kamar ya ƙara girma ya ƙara zama wani kamili... Anaam itace a baya... Mu uku muka shiga baya...Anaam tana zuwa taga mun cika wurin ta nemi da in dawo gaba naƙi badan taso ba ta shiga gaba ta zauna,yanayin zaman naga kamar tana zaune saman garwashi sai hura hanci take... Tada motar Abeed yayi muka fita masu gadi na mana Allah ya kiyaye...nida Jay d muke ƙara yin revision akan abubuwan data koya mana a yau har muka kawo. godiya mukayi mashi,Jay d ta shigo ciki ta gaishe da Mama...kafin suka tafi... Bayan Isha'i muna kallo a ɗakin su Mama a ba zata Anaam tace '' inna wai kin san kuɗin waec ɗin mu..ina nufin kuɗin jarabawar mu ta ƙarewa..dubu tamanin da biyu!" Dafe ƙirji inna sarai tayi ido waje tace da ƙarfi '' Dubu tamanin da biyu? Ina za'a samu wayan nan kuɗin ma ku uku?" Tashi zaune nayi ina kallon fuskar Mama data canja damuwa ta mamaye ta a tashi guda.... Asma'u tace '' ai ke zaki zauna idan munyi graduating sai daga baya kiyi ko Abeedah wani dai daga cikin k..m'' '' sannun ki uwar yan son kai...!" Anaam take hararar Asma'u kamar idonta zai zubo...a sanyaye nace '' ina cigaba da neman aiki ai...'' '' toh wane aikin zasu biya ki koda dubu ashirin ne bale har yakai dubu tamanin faɗa min inji?" Anaam ta jefa min tambayar..na kasa bata amsa..kuma ma idan nace zan dinga tarawa ai lokaci ya ƙure '' gashi azumi ya kusa kenan bamu da kayan salla" Ita baƙin cikinta kenan babu wanda ya tanka ta daga ƙarshe muka kwanta kowa zuciya da ɗaci... Washegari bani da jarabawa yasa na shirya nake neman aiki daga restaurant zuwa restaurants harda hotels duk na gaji amma da yake ina tafiya ina ɗan imajinashon ɗin haɗuwa da saurayi kamar yanda yake faruwa a novel naji gajiyar bata wani durƙusar Dani ba...sai wurin ƙarfe biyar da rabi na koma gida a gajiye babu Sa'a Mama tace '' da kin bar neman aikin nan..wata rana kina zaune zaman ki aiki zai zo ya same ki...'' jinta kawai nayi badan na yarda da abinda ta faɗa ba '' yaushe ne azumi?" Na canja topic '' nan da kwana takwas..'' zaro ido nayi ashe har azumin ya ƙarato kusa kusa haka... Na sauke ajiyar zuciya...rayuwa ta cigaba da shillawa yau da farin ciki gobe da baƙin ciki...har yau ya rage azumi saura kwana biyu kacal...kuma yau muka gama jarabawar mock...sunce zasu bamu sakamako idan an dawo daga hutun azumi amma muyi karatu sosai dan cikin wannan hutun kalandar mu ta rubuta jarabawa zata fito... Bayan an watse daga assembly muka koma aji ana hirar ƙarshe dan wasu ba zasu dawo ba...wasu yan aiki ne kuma uwayen gidan su bazasu biya musu ba...wasu kuma aure xasuyi wasu basu da halin biya...muma mun faɗa cikin jerin wa'yanda basu da halin biya...Amma ni Abeedahtu baxan bari mu rasa wannan damar ta mallakar satifiket ba... zanyi iya ƙoƙarina dan ganin na samo kuɗin nan... Da ƙarfe sha biyu aka gargaɗa mu akan mu tafi gida makaranta ta rufe sai bayan azumi...mukayi bankwana da ƙawayen mu anan Jay d take gaya mana ashe banan ƙasar zasu yi azumi ba..umra zasu...a karo na farko naji ina ma ace nice ita...'' Allah ya dawo daku lafiya...'' na rungume ta..itama Diyaam tazo ta rungume mu...tace '' ki kawo min yashin Madina....'' '' ke dalla yan Najeriya ke kiranshi yashin Madina..babu wani yashin madina da ake sayarwa....'' inji Anaam,ta murguɗa min baki...Jay d tayi dariya '' kada ki damu zan kawo maki tsaraba...'' Daga nan muka rabu ta shige motar su mu kuma muka kama hanyar gida... Wasu yara su uku muka samu suna jiran Asma'u sunzo kitso da lalle...ajiye Jakarta tayi ya canja kaya zuwa wani tsohon zane da riga tazo ta zauna ta fara da ƙaramar nima wanka nayi ma canja kaya..na shiga kitchen abincin da yarage jiya tuwon masara miyar kuka badan naso ba na zuba ma kaina naci...bayan na gama na fita farautar aiki...yauma kamar kullum ba nasara..wai ni kodai wani ya jefe nine? Tsaki naja takaici na cika zuciya ta na dawo gida....Washe gari ban wahalar da kaina ba nayi zaune na gida...da yamma kuma dukan mu muka shiga gyaran gida saboda gobe azumi... Kowa na murna banda Anaam saboda za'a katse mata jin daɗi a nata cewar....unguwar duka babu abinda kowa ke magana akai sai azumi... Washegari aka tashi da azumi...Anaam ta dinga ɗirkar abinci kamar hakan zai sa kada taji yunwa sai gashi tun kafin a kai ko ina tayi lamo...daga lokaci zuwa lokaci take shiga baye ta jiƙo kanta da ruwan sanyi... nima dai yunwar bata yimin da daɗi ba wallahi naji kamar an yashe min ciki kamar banci komai ba...magana ma daƙyar nake yi.. Asma'u tana ta mana dariya..ita kamar ba azumi take ba sai nan da can take kazar kazar abunta... Da aka sha ruwa cup ɗaya na ruwan sanyi Anaam ta shanye tana sauke ajiyar zuciya nidai ruwan zafi na fara sha... muka yima juna Barka da shan ruwa...bakin Anaam ya buɗe choin choin choin... Bayan mun gama buɗa baki mukayi sallah anan saman baranda lokacin Isha'i muka wuce masallaci wurin sallar alkareji (taraweeh) masallacin ya cika sosai... Wuri muka samu muka tsaya...bayan sallar isha'i, round guda kaɗai akayi nida Anaam muka ɓuge da bacci dan mu muka fi kowa cika ciki sanda aka sha ruwa... '' Malamai sai ku tashi mu tafi ko?" Asma'u ta faɗa bayan taga ma jibgar mu wai ita tashe mu take..Anaam kamar zata kama da wuta...barinta wurin Asma'u tayi ta fice daga masallacin... Da muka isa gida,su mama na zaune saman baranda ga bandir ɗin kuɗi gaban su...ƙarasowa mukayi bayan munyi sallama sun amsa '' mama daga ina wa'yannan kuɗin?" Na tambaye ina jawo bokitin da aka jiƙa jolly juice ciki Anaam ta zauna gefe na muna sha tare... '' Jadeedahtu ce ta kawo...tace sauri suke zasu tafi airport jirgin su zai tashi..shine ta biyo kuyi bankwana...'' tiyarar da nake sha naji ta fitar min arai na ture gefe '' da yake ba rabon ku haɗu..ke kina masallaci lokacin kuma baku daɗe da fita ba...'' inji inna sarai... kawai na jinjina kaina Ina jin ba daɗi... '' Allah ya dawo dasu lafiya...'' Asma'u tayi addu'ar tare da shigewa ɗakin mu Da safe da ƙarfe goma na sake fita kamar koda yaushe ko Allah zai sa in dace..dan ji nake jiyan da ban fita ba nayi missing... amma kamar kullum daga masu cewa basa ɗaukar sabbabin ma'aikata sai masu cewa bani da qualifications...sai masu cewa in dawo nan gaba...raina yayi ɗaci har na kasa haɗiye ƙololon baƙin cikin dana keji...na samu wuri na zauna nasha kuka sannan na cigaba da tafiya A wani masallaci nayi sallar zuhr da Asr,ina zaune aka fara tafsir a cikin tafsirin shine malamin ke faɗin wata addu'a da idan mutum yayi ta zai samu biyan buƙata Addu'ar itace za'ayi raka'a biyu na sallar nafila...idan angama ko acikin sallar a fara neman gafara,a yabi Allah ayi ma Annabi salati....sai ace ' Laila illah Allahu Akbar... Lailaha illal lah wahdahu lasharikalah lahul mulk wa wahul hamd wahuwa ala kulli shai'in qadir... Lailaha illallah wala haula wala quwwata ilabillahil aliyul adheem...,lailaha illallahul adheemul haleem lailaha illallahu rabbul arshil adheem alhmadulillahi rabbul alaamin as'aluka muujibaati rahmatik,wa idhaami maghfiratik..wassalamata min kulli ithmin walghaniy matu min kulli birrin,la tadha'ali dhamban illa gafarta wala hamman illa farrajta wala haajatan hiya laka ridan illa qadaita bi rahmatika ya Ar hamurraahimin...'' ya ƙara da faɗin '' duk wanda yayi wannan addu'ar ya roƙi Allah da yaƙini Allah zai bashi..amma matsalar itace Mutanen mu basu da yaƙini kuma basu da haƙuri...'' ban zauna har ƙarshen tafsir ɗin ba amma dai na ƙudiri aniyar yin wannan addu'a sannan idan ma yaƙinin ne banda shi da gaske nayi alƙwarin zan yishi...zan yi iyakar ƙoƙarina kuma a watan Ramadan...bana tunanin addu'a ta zata ƙi amsuwa ga lailatul qadr da nake fake ko?... Asma'u ain't the villain,__ just a girl insecure Anaam ain't bad __ just sharp mouthed Jay D__ everyone needs a friend like her trust me 😇 Khalil__ girls are having a crushing crush on you ooo🤣 +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 19. ...bayan komai sai tawakkali...🖊️ Da wannan tunanin na isa unguwar mu da tafsir ke tashi ta kowane lungu da saƙo...wasu yara na gani kamar almajirai kwance a ƙarƙashin bishiya azumi ya musu dukan bala'i ga wasu suna wasa da lilo cikin nishaɗi da alamu basu azumi na kalli ranar data fara shigewa kalarta ya canja zuwa miyan goro na sauke ajiyar zuciya...da sallama na shiga gidan mu inna sarai dake tatar ƙullu ta amsa min '' har kin dawo kenan?" Gyaɗa kaina nayi ina kallon Anaam dake kwance tana kallon sama kanta saman cinyar Mama.. Asma'u daga zaune a bakin ƙofar ɗakin mu na cire hijabi na '' Mama ina yini...'' na gaisheta tareda kwantawa a ɗayan gefen na kwantar da kaina saman cinyarta kamar koda yaushe Anaam ta juya idonta tare da fitar da sauti na rashin jin daɗin kwantawar da nayi saman jikin Mama... '' lafiya lau...wai ba zaki dena wahalar da kanki ba?" Tana shafa kaina tayi maganar da dasashshiyar murya Asma'u tace '' kuma na tabbar yauma baki samu aikin ba...yanzu fitar da kikayi mai ta ƙara maki?" Murmushi nayi mai sauti batareda na amsa ba...fitar da nayi ta ƙare ni da koyon addu'ar biyan buƙata...daga ƙarshe nima zan samu cikar burina..hakan ba ƙaramin farantawa zuciya ta yayi ba... Taɓe baki Asma'u tayi ta ɗauke kanta...da ƙarfe biyar da rabi muka tashi taya inna sarai aikin haɗa abubuwan shan ruwa...Anaam ta tafi siyo ƙanƙara da tiyara... bada daɗewa ba aka sha ruwa... Sai da nayi addu'ar nan dana koya na ƙara koro duka buƙatuna sannan nasha ruwa... '' ɗazu dana tafi sayen tiyara baki ga wasu takalmi dana gani ba masu shegen kyau wallahi sun burgeni kuma sai na saye su insha Allah....'' '' nawa ne kuɗin?" Inna sarai ta tambayi Anaam...haɗiye ƙosan dake bakinta tayi sannan tace '' dubu biyar ne...'' ''kuuut! ana maganar ina za'a samu kuɗin jarabawa wa zai baki dubu biyar?" Asma'u ta zaro ido tana kallon Anaam...nima ita nake kallo taja tsuki sannan tace '' yanzu ni danayi maganar nace wani yaban kuɗi? Kuɗin jarabawa ba damuwa ta bane amma dai na tabbatar wa'yannan takalmi dana gani wallahi sai na mallake su....'' '' hada rantsuwa?" Ta kalli saitin da nake zaune da karsashi a muryar ta ''.ƙwarai kuwa Allah bazai bari inyi kaffara ba...'' na gyaɗa kaina '' yanzu ke Sha'awanatu ina zaki samu wa'yannan kuɗin?" Mama ta tambaye ta...tana murmushi tace '' wurin Allah mana gare shi nake nema shine yasa ma tun farko bance kowa ya bani ba....'' Babu wanda ya sake yin magana cikin mu... lokacin da muka tafi taraweeh ina jinta tana addu'a bayan gama sallah... Tsakiyar dare na tashi itama ta tashi don yin sallar dare '' yanzu takalmin kika tashi ki roƙa?" Da alamun jin haushi a muryarta tace '' koke ke bayarwa ne in koma ?" na girgiza kaina da ƙaramin murmushi muna tsaka da alwala sai ga Asma'u itama ta fito...tare muka gama muka shiga kowa ya tada sallar shi daban addu'ar dana koya a kowace sujuuda da tahiya da duk inda ake addu'a a salla sai na karanto ta sannan in roƙi Allah abinda nake so...ban taɓa jin ina kusa da cimma burina ba sama da yanzu '' Allah ka bani dubu biyar in saye takalmin nan wallahi sun mini kyau...ya al wahhabu ya al fattahu ya Ar razzaqu kaji ƙaina...'' Anaam ta cigaba da addu'ar ta nida Asma'u muka bita da ido ita kam ko a jikinta...maimakon tace Allah yasa mu samu kuɗin jarabawa...ina tsaka da wannan tunanin naji tace '' Allah ka kawo ma Abeedah aikin da take nema mu huta..kaba Asma'u abinda take so..ka dawo dasu Jadeedah lafiya kasa tayi min tsaraba...kasa muci jarabawar mu harda Diyaam...Ameen...'' daga nan ta miƙe tana yar waƙa..bata ko kalle mu ba ta koma ta kwanta abunta...banyi tsammanin Anaam ta damu dani har haka ba...da take koda yaushe nuna kamar jira take abu ya haɗa mu ta hayayyaƙo min,naji ɗumi ya sauka a zuciya ta game da ita Asma'u ma tayi mamaki... Daga wannan lokacin a kowane dare sai nayi sallar dare komai gajiyar da nayi komai baccin da nake ji...haka da rana ma nakan ƙara yawaita aikin lada.. wa'yannan suna bani tabbacin cewa addu'a ta zata amsu...duk da wasu lokutan ina shiga yanayi na damuwa da waswasi da sauri nake koɓar kaina daga wa'yannan tunanikan... Azumi yayi nisa har an kai na sha takwas yau...Anaam zaune take daga gaban ɗakin mu tana cin shinkafa da miya kasancewar bata azumi yau..sai washe mana baki take irin kun gani ƙwalelen ku...juya idona nayi..ni idan dai azumin Ramadan ne,mutum ko abinda yafi duniya daɗi zai ci bazai tayar min da hankali ba...sam sam... '' Abeedah naga kina haɗiyar yawu.. Bismillah to?" Inna sarai da itama abin yake bata haushi ta kaima Anaam duka a cinya '' bata so...gyandiya kawai...'' turo baki Anaam tayi '' kai Innalillahi Inna...'' Harzuƙo mata da inna sarai tayi yasa ta tashi da gudu ta bar wurin... Mama ta ɗaga labulen ɗaki ta fito '' Anaam zo ki tafi nan kasuwa ki siyo min abu...'' daga nesa Anaam ta cika bakinta da abinci tana karkaɗa kai...tsuki inna sarai taja muka cigaba da hirar yanda kwanakin farautar lailatul qadr ya ƙarato...farin ciki mai haɗe da faɗuwar gaba suke ziyarta ta a duk sanda aka yi maganar wannan dare...idan fa bana cikin waya'nda zasu ga daren? Tunanin sake jira har wata shekara kassara ni yake ... Anaam ta shiga ciki ba daɗewa ta fito saye da hijab pink rabin guiwa ta shafa ma idonta masu kyau kwalli ta shafa man baki... '' duk shirin zuwa kasuwar ne haka?" Asma'u ta zolaya Anaam na juya idon ta tace '' eh mana...dole in zama presentable...'' murmushi nayi dan na fahimci abinda take nufi da presentable... Ɗakin Mama ta shiga ta karɓi kuɗi tayi mana sallama sannan ta tafi bayan ta gama tsokanar mu... **** Tafiya Anaam take cikin nutsuwa da kamala kamar ba itace Anaam ɗin da koda yaushe take faɗa dasu Abeedah ba...duk da Mama ta bata kuɗin abin hawa ta zaɓi tayi tafiyar ƙasa..a cewar ta can garinsu suna tafiyar data fi wannan nisa da ƙafa wurin samo ruwa dan haka wannan ba komai bane....minti sha biyar ta ɗauka kafin ta isa kasuwar...ganin yanda mazan dake zaune daga baki baki suka kafe ta da ido yasa ta ƙara ɗaure fuska amma bata canja yanayin tafiyar taba... Wurin da ake sayarda kayan ƙamshi ta nufa..ta fadi abubuwan da take so mai wurin ya shiga auna mata..wani magidanci ne daga gefe sai kallon Anaam yake yana lasar baki kafin can ya kasa haƙura '' yan mata ji mana?" Yi Anaam tayi kamar bata ji shiba ya sake maimaitawa nan ma ta share shi..sauran dake zaune daga gefen shi sukayi hiri hiri da ido... '' yan mata salama alaikum...'' A ƙufule Anaam ta juyo tana ɓalla mashi harara tace '' wai Meye ne? Naci bashin kane? Baka da aikin yine? Ko tsaye nake a tsakiyar kanka ko na tare maka wani abu ...'' Rasa abin faɗa mutumin yayi ya girgiza kai jajayen idonshi waje '' ehm...kabi ka ishe ni da ji mana...hayn..bana son takura!" Ta ƙarashe maganar da finality a muryarta yanda bata bar wani ƙofar gardama ko cigaba da bibiyarta ba...ta juyo ta biya kuɗin ta karɓi kayanta tabar wurin tana huci...the guys were speechless...abokan mutumin suke dariya ƙasa ƙasa shiko kunya ta lulluɓe shi... Anaam tana tafiya tana bala'i duk da ba kowa tare da ita,mutane sai matsa mata suke ..a cikin azumin ma akwai wa'yanda ba zasu iya controlling kansu ba sai sunzo suna abubuwa irin wannan...taja dogon tsuki tare da kawar da kanta gefe..idonta ya sauka akan wani tsoho daya gama tsufa tuguf tuguf da ƙyar yake tafiya zai tsallaka titi...amma motoci sai shararowa suke da gudu suna tsorata shi...mutane kowa sai harkar gaban shi yake babu wanda ya kulashi...da sassarfa ta iso wurin tsohon ta gaishe shi da girmamawa '' tsallaka wa kake so kayi?'' '' eh amma motocin nan sun hana ni...'' Ɗaga kanta Anaam tayi tana kallon motocin dake zuwa kamar ana kwararo su dan babban titi ne mai hanya biyu wasu na zuwa wasu na tafiya.... numfashi taja ta riƙo hannun tsohon...da kulawa dan tsohon baida ƙiba kamar ayi iska ya tafi dashi...suka fara tafiya...motocin sai honking suke da ƙarfi...zuciyar Anaam ta dinga bugu da ƙarfi...tsohon kuma duk ya firgita jikin shi nata rawa idonshi sun fito kamar zasu faɗi...wasu daga cikin motocin kamar bazasu tsaya ba..kamar zasu bi takansu su wuce Da ƙyar Anaam ta tsallakar dasu zuwa ɗayan gefen inda akwai bishiya a wurin ta zaunar da tsohon saman benci...itama ta zauna tana sauke ajiyar zuciya...'' na gode sosai yar nan Allah shiyi albarka ya kawo miji na gari..yasa a gama da duniya lafiya...'' duk addu'oin da yake mata ta amsa da Amin banda addu'ar aure..not when she saw yanda babanta ke treating mamanta da sauran matan shi...not when she saw yanda babanta yayi neglecting duties ɗin da yake dashi akan ya'yan shi..Anaam bazata taɓa yin magana akan babanta ba..dan babu wani abin da yake dashi na faɗa na alkhairi...da ace ita keda zaɓi bazata taɓa yarda ta kasance yarshi ba...sai dai mutum baya zaɓan yanayin haihuwar shi.... Gani tayi tsohon zai miƙe ta kalle shi tare da faɗin '' kana buƙatar wani abu ne?" Yana cigaba da miƙewar yace '' zan yi sallah ne...'' '' to ka zauna bari in kawo maka ruwa...'' zama tsohon yayi Anaam ta miƙe tana kalle kalle.. can ta hangi pamfo harda masallacin da dafarko ma bata lura dashi ba...isa wurin tayi ta ɗauki buta ta cika mashi da ruwa ta ajiye gaban shi '' Allah shiyi albarka...'' yake maimaitawa kafin ya naɗe rigarshi data gama tsufa ta dagargaje ya fara alwala...Anaam ta tsugunna daga gefe tana kallon shi..amma a zahiri tayi nisa cikin tunani ne...bata roƙon Allah ya kawo ranar da zata sake komawa mahaifinta...kuma ta gode Allah da auren shi da mamarta ya mutu har abada... '' na gama...'' Muryar tsohon ta fito da ita daga tunanin data shiga ta iso inda yake ta taya shi miƙewa har bakin masallacin ta isar dashi..ta gyara mashi mat ɗin dake gaban wurin...ya dafa bangon wurin yana tafiya da ƙyar ya shiga Masallacin ita kuma ta tsaya daga waje tana kallon shi...daga baki baki ya tsaya da alamu nan zai yi sallar ya juyo one last time yace '' Allah ya raba ki da mummunar ƙaddara ya baki zuri'a na gari...wanda zai kula dake da ya'ya na gari da zasu kula dake kamar yanda kika kula Dani...'' Murmushi Anaam tayi tana amsa addu'ar farko sauran kuwa taɓ ɗi jam... Jin yanda idanun mutanen dake masallacin ke yawo a jikinta yasa ta bar wurin...yanayinta ba daɗi...wani makahon tsoho ta gani yana dungura sandar shi da robar Bara a hannunshi...ɗari uku ɗin da batayi amfani dasu ba wurin hawa abin hawa ta miƙa mashi bayan ta isa inda yake... Nan ma tasha godiya da addu'a ...ita dai nata murmushi...har tsohon yabar wurin tabi bayanshi da kallo...a niyarta shine Allah yaba su abinda suke nema ita dasu Abeedah kuma har abada kada ya ƙara haɗa fuskarta data babanta... Ta juyo kenan idonta ya sauka akan Abeed daya daɗe yana kallonta da burgewa...gabanta ya shiga faɗuwa..da sauri ta juya ta fara tafiya kamar zata tashi sams Shiga motar shi Abeed yayi ya biyo bayanta...a daidai saitin ta yayi ƙasa da glass ɗin shi '' yar fullo ba magana?" bata tanka shi ba sai sauri data ƙara..shi kuma ya cigaba da bibiyarta da mota...a fusace ta tsaya Tare Da Juyowa...sai dai ta kasa sauke masa tsiwar data yi niyar yi saboda yanda ya cika mata ido ..samun kanta tayi da jan tsaki ƙasa ƙasa... '' shigo in kai sauke ki...'' da sauri tace '' a'a kabarshi kawai ...zan ƙarasa da ƙafa...'' '' okay bari in sauko sai mu tafi tare...'' ganin yana shirin saukowa kuma dai ita bazata so a ganta tana tafiya da wani namiji ba yasa tayi saurin faɗin '' Allah ka tafi zan iya tafiya gida da kainaaa...'' taja kalmar ƙarshe a shagwaɓe batareda tasan tayi hakan ba... Jinginar da bayan shi Abeed yayi '' a'a sai dai ki shigo in sauke ki...'' ganin bazai bari ta tsere ba idan ba'a yi ɗaya cikin biyu ba yasa taja dogon numfashi ta shiga motar kawai badan taso ba... Abeed yaja motar suka bar wurin... through out jinta take kamar ta zauna saman allurai...zaman ma da rabin jiki tayi shi..rabin kuma a ɗage...yana lure da ita amma bai tanka ba sai can yace '' nayi kama da mugun mutum ne?" '' mugu ai bashi da kama,amma tambayar ta tabbatar min da mugunta kake shirin aiwatar wa...don't'' maganar ta fito daga bakinta ba shiri murmushin gefen baki Abeed yayi yana kallon hanya '' meye sunan ki...'' Haushin shi take ji sosai irin wa'yannan maganganun takaici suke bata take ganin su kamar ɓata lokaci kawai'' Anaam...'' '' Anaaam'' ya maimaita ƙasan maƙoshi..' bana son munafunci..' tayi maganar a ranta tana juya ido jin yanda ya kira sunan wai shi a san ya iya ...shiru ne ya biyo baya babu wanda ya sake cewa komai cikin su har suka iso...bakin ƙofar gidan su yayi parking...tayi ƙoƙarin buɗe motar taji ta gam...kallon shi tayi..shima ita yake kallo ta haɗe girar sama da ƙasa duk da kwarjinin da yake mata...well to hell with that Brown envelope ya ɗauko ya miƙa mata... tabi hannun shi da kallo amma bata karɓa ba kuma bata da alamun zata karɓa '' amsa..'' ya furta.. girgiza kanta tayi tace '' a'a ka barshi kawai...koma meye Inna bazatayi farin ciki ba ...'' '' sai kice Abeed yayan Jadeedah ya baki zasu fahimta...'' persistently Anaam taƙi..shi kuma yace idan bata karɓa ba bazai buɗe mata motar Ba ta gama tafasa da fushi ba yanda ta iya ta warce envelope ɗin daga hannun shi...'' AN GODE TOH...'' ta bashi dariya ba kaɗan ba... buɗe mata motar yayi da sauri ta tura zata sauka '' SHA'AWAH...'' dakatawa tayi daga ƙoƙarin saukar da take da jin sunan da ya kira ta dan ko a unguwar babu wanda yasan ainihin sunan ta ya akayi shi ya sani ta juyo ta ga ita yake kallo, murya ƙasa yace'' My wife!'' ba shiri Anaam ta sauka daga motar blushing furiously ta banko ƙofar... fuskarta tayi ja kumatun ta suka ɗau zafi...take tafiya kamar zata kife..sauke glass yayi ya sake faɗin '' in five years...'' Tsayawa tayi a zaure tana shafa kumatun ta,lokaci guda kuma haushin Abeed ya cika ranta kamar ita ɗin kaya ne dake jiran wani ya mallake su ko shine da gobe bale har yayi maganar shekaru biyar...dogon tsuki taja tare da buga sallama '' wa'alaikumussalam..mun ɗauka kin ɓata...'' Asma'u ce ta amsa mata sallamar tana tsantsame hijabin data gama wanke wa... da takaici Anaam tace '' tunda kun ɗauka ai sai ku ajiye...'' Asma'u bata tanka ba...Mama ta fito daga ɗakin '' kin dawo Sha'awanatu...'' jingina kanta kawai Anaam tayi ta miƙa ma Mama abubuwan data siyo... kula da envelope ɗin hannunta yasa Mama tambayar '' waya baki?" Zare hijabinta tayi ta zauna sannan tace '' ɗan uwan Jadeedah ne,shi ya dawo dani...'' Mama tace '' Allah sarki ashe bada shi aka tafi umrah'r ba?" Anaam bata tanka ba ta buɗe envelope ɗin kuɗi taga ni a ciki tayi frowning fuskarta ta zazzage kuɗin duka.. yan dubu dubu sababbi Asma'u na shanya hijabinta tace '' Uhmm... addu'ar ki ta karɓu da alamu ...'' Da gaskiyar Asma'u,addu'ar ta ta karɓu ta yanda bata yi tsammani ba.amma hakan bai mata daɗi ba,ajiyar zuciya ta sauke tana furta ' alhmadulillah ' ta nuna ma Mama kuɗin '' TOH kin gode ai '' tashi tayi ta wuce wurin inna sarai itama ta nuna mata... Fitowa nayi daga baye na wuce ɗakin mu,samun Anaam nayi kwance tana kallon ceiling hannunta saman goshinta tayi nisa cikin tunani abinda ban taɓa gani tattare da ita ba... kamar zan share ta sai kuma na zauna kusa da ita '' lafiyar ki kuwa?" '' me kika gani?" Ta tambaya tana harara ta..'' naga kinyi shiru...'' '' tadabburi nake..kada ki dame ni'' taban dariya da tace tadabburi take ...amma tunda tace kada in dame ta yasa ban cigaba da matsa mata ba...nima na shiga tawa duniyar tunanin har bacci ya ɗauke ni Har aka sha ruwa Anaam ba kamar kullum ba yau ko magana bata cika yiba...juyin duniya an tambaye ta tace ba komai... lokacin taraweeh bacci ta ɓuge dashi..sallar tahajjud ɗin ma batayi ba..washe gari nake gano ashe buƙatarta ta biya..na jinjina kaina bayan ta faɗa min yanda ta samu kuɗin..idan har tata buƙatar zata biya... surely...nima zan samu tawa ko? Duk da abinda nake roƙa yafi wanda ita take nema girma...duk da haka na ƙarawa kaina ƙwarin guiwa... Kwanaki goman da suka biyo baya na ƙara ƙaimi wurin ibada duk da yanda zuciya ta take a sage..banga alamun nasara ba..amma na ƙuduri aniyar yin kamar yanda Jay d ta faɗa min positive thinking a koda yaushe... Duk yan canjin dana samu a wurin sadaka suke ƙarewa...nakan shagaltar da kaina da ibada da roƙon abubuwan da nake buƙata...a rana ta ashirin da biyar nida Asma'u baƙon mu na wata yazo...ba ƙaramin baƙin ciki hakan ya haddasa mana ba.. amma banyi ƙasa a guiwa ba wurin cigaba da ibaduna...nake ƙoƙarin rufe idona daga rashin nasarar da nake gani tattare da yanayi na...nake convincing kaina cewa daga ƙarshe kafin ranar salla komai zai canja...akwai lokaci...amma nima Nasan zuciya ta abu daban take hanga....a yan kwanakin nan kuma mutane kusan kullum sai sun cika gidan mu wurin kitso da lalle..tun Asma'u nayi ita kaɗai har dai dan dole na nima na dinga taya ta badan naso ba...dan na tsani kitso da lalle Mutane sai suyita cewa sun fi son nawa suna ƙara sani a wahala...hakan bai yima Asma'u daɗi ba dan dai sana'ar tace...amma take ɗauke kai kamar bata damu ba.... Tun kafin sallar taxo Nasan da cewa bazatayi min daɗi ba...kamar kowa ce sallah da nake ɓoyewa in sha kuka na..wannan ma bazata kasance ta daban ba...da duk nayi ƙoƙarin kwantar wa da kaina hankali akan har yanzu akwai sauran lokaci da zuciya ta take ƙara karyewa....dan wani sashe na zuciya ta..ya riga da yasan gaskiyar ko kuma ya riga da ya zaɓi gaskiyar abinda zai faru.... Nakan yi murmushi a gaban kowa da kowa bayan daga ciki ...ina rushewa...nakan yi dariya bayan abinda kawai zuciya ta take so shine tayi kuka a fili...nakan nuna jarumta bayan niɗin mai rauni ce...nayi iyakar bakin ƙoƙarina wurin danne ɗaci da raɗaɗin dake mamaye da zuciya ta kamar baƙin hayaƙi mai kauri...kowa na rayuwa a irin yanayin da har abada Ni baxan taɓa iya alaƙantar hakan ba...nake ji kamar na zama fatalwar dake kallon komai amma bazata iya zama daga cikin komai ɗin ba sai dai kallo... Anaaam ma ta sayi takalmin data ke ta son siya har damu ta siya mawa tace '' ai na faɗa maki... Allah bazai ban kunya ba...'' nayi ƙasa da idona..da gaskiyar ta...murya ta na rawa numfashina na fita sama sama nace da dariyar da bata kai zuci ba '' haha haka fa...nima nan gaba ki haɗa dani cikin addu'ar ki....'' kwanakin suka zo suka wuce kamar basu taɓa wanzuwa ba...nake jina kamar kawai ina tafiya da rayuwa ne ba ruhi..na kuma fahimci cewa a tawa rayuwar ba fari sai dai baƙi da ruwan toka...only Black and gray...never white... Finally gobe sallah ... Zaune muke dukan mu saman baranda bayan sallar isha'i kowa na bayyana farin cikin kasancewar gobe sallah..jin su nake batareda nace komai ba...tun kafin ranar tazo...zaren farin cikina ya gama katsewa duka...na tabbatar baƙin cikin da zan kwasa gobe sai yafi wanda nake ji a yanzu da kuma wanda na kwasa a sauran kwanakin... Amma duk da haka... Sanda zamu kwanta...na daɗe ina kallon ceiling bayan an kashe wutar ɗakin.... nunfashina na fita a wahale.... idanu na sunyi ja amma ba hawaye ina ayyana wa a raina yanda zan ji da za'a ce gobe kawai zan tashi inga duk wani abu da nayi addu'a nayi kuka akai..ya zama.... Na juya gefe na idanu na buɗe ina sauraron bugun zuciya ta.. abinda nake ji hauhawa yake kawai...sallar ma baxan iya yiba saboda banda tsalki,ƙila niɗin...abinda nake fatan samu ɗin..har abada... Yawu na haɗiye tare da dafe ƙirjina...ban san tsawon yaushe na ɗauka ba kafin bacci ya sace ni Washegari da sassafe kowa ya tashi ana ta barka da sallah...su Asma'u murmushi har kunne...maneji nayi ina tayi musu murmushi da murnar yaƙe dan ko kaɗan babu wa'yannan a raina...daga ƙarshe dai tsorona ya kasance gaskiya...da ganin yanda iska ke kaɗawa da yanda sama take ɗauke da gajimare masu duhu zai tabbatar maka da akwai hadari...wannan yanayi yayi daidai da yanda nake ji a raina...sai dai ni a cikina,akwai tsawa harda walƙiya... Da ƙarfe tara daidai muka isa masallaci cikin tsofaffin kayan sallar mu..dukan mu babu wanda ya damu ,Allah yasa mu ba masu son abun duniya bane... Nayi zaune zugum na kasa gane yanayin da nake a ciki yanzu... Bayan abinda malamin dake wa'azi ya faɗa na cewa wasu lokutan mutum zai iya yin addu'a yaga kamar ba'a amsa ba...nan ko Allah ya amsa kuma yana shirya mashi gagarumin abu...sannan Allah na gwada wa'yanda yake so... murmushi mai ciwo na saki...ni Abeedah a suwa ɗan wake a hotel..mai ma nake yi da Allah zai soni? bayan ko gode mashi akan ni'imar shi na kasa yi sai hangen nesa... Badaɗewa liman ya iso aka tada sallah..bayan an gama naji inama ace su Asma'u basa tare dani dana bi doguwar hanya na saki kukan da nake dannewa..wata sallar batareda cikar burina ba...suna tafiya suna murmushi dukan su ba ƙaramin kyau sukayi ba...naji ina ma ace nice ɗaya daga cikinsu..ƙila in zama Anaam tafi kowa zama free spirited a gidan mu... 🍁: naji kina banko mana manya manyan turanci Abeedah... Abeedah: ina ƙoƙarin in ƙara ƙwarewa ne otum... A duk sanda suka sako ni cikin maganar su nakanyi iya ƙoƙarina wurin ɓoye sirrin dake raina... Muna komawa gida..na cire kayan sallar na saka kayan gida na shige ɗakin su Mama da ƙaryar ciwon kai...nayi kwance bacci ya ɗauke ni..a duk sanda nake cikin baƙin ciki,bacci shine hanyar da nake samun kaina... Nayi ƙoƙari sosai wurin ganin ban kalli madubi ba... Sai da ƙarfe ɗaya na tashi da kaina...kuma da gaske naji ni wasayau...badan ciwon zuciyar ya tafi ba...sai dai don na ƙara jefa shi a wani ramen dake zuciya ta..na cigaba da harkokin gaba na gida je da yawa suka kawo mana abinci...muma mun kai...yan tukuicin da muke samowa duk na bayarda nawa a sadaƙa...duk da zuciya tana faɗamin in cire rai in huta...na kasa... nake ji kamar ina ƙara bayarda sadaka...ina ƙara kusanto cikar burina... Bayan salla da kwana biyu na cigaba da neman aiki na...Mama tace in dena Allah zai kawo mafita amma baxan iya ba...zama babu aikin yi..zai iya sa tunani ya halakani... amma kamar ko yaushe ƙunshe da baƙin ciki nake dawowa ba cigaba..ga makaranta da aka kusa dawowa... Yau asabar da ƙarfe huɗu da rabi na fito daga wani restaurant bayan sun gama ɓata min lokaci sunsa nasa rai a samun aiki a wurin su..daga ƙarshe sai cewa sukayi sun fasa ɗaukata ba gaira ba sabar...tunda na fito gida restaurant ɗaya kawai na shiga kafin na iso nan...suka zaunar dani kuma yanzu shine tsabar wulaƙanci zasu ce bazasu ɗauke niba... Ba ƙaramin baƙin ciki naji ba..na cigaba da tafiya har na kawo ƙarƙashin wata bishiya da benci ba kowa a wurin gidaje ma sunyi nesa nesa..wurin na ɗauke da yashi mai laushi...ganyen bishiyar sai kaɗawa yake da iska yana bayarda sauti da kuma fitarda sanyi mai ratsa jiki.... ganyayyakin sun baje sosai sun hana rana shigowa wurin sosai...sai kaɗan kaɗan daga space ɗin da suka bari tsakaninsu....zama nayi a wurin na damƙe hijabina a cinyata...ina taune leɓena...kafin naja numfashi domin hana hawayen da suka taru a idona damar saukowa...komai da yake faruwa a rayuwa ta ya shiga playing kamar a tv...ban san na fara kuka ba sai da hawayen suka sauka a hannu na...nafara sheshsheƙa kafin kuka mai ƙarfi ya biyo baya...amma banida mai lallashina...na gaji da duniyar duka..a wannan gaɓar mutuwa shine yafi dacewa a tunani na...duk da dai ba hakan nake fata ba.... Na kasa fahimtar abinda yake faruwa dani... nake kuka kamar raina zai fita..inama ace mutum zai iya koke duka damuwowin shi... danayi Tsagaita kukan nayi ina kallon ba komai...ban san inda kalaman suka fito ba naji ina waƙa 🎶 Da akwai ciwo cikin zuciya ta... ....bamai faɗa bamai sani sai wanda ke ji..🎶 🎶Hawayena na zuba...zuciya da rauni.. .....Naso ace rayuwa ta,tazo da sauƙi Allahu ne mai magani shine wanda ke ji🎶 Sake fashewa nayi da kuka..na daɗe a wurin saida rana ta faɗi sannan na tashi na cigaba da tafiya...ana kiran magrib na iso gida... Mama duk ta damu...kowa sai tambayar abinda ya faru yake da ganin idona... Banyi ƙarya ba na faɗa masu abinda restaurant ɗin sukayi min na ƙara da faɗin '' baxan sake zuwa neman aiki ba..'' '' Duk abinda kika zaɓa..matsawar daidai ne muna bayan ki Abeedahtu..'' Inna sarai ce tayi maganar kowa ya gyaɗa kanshi Mama tana shafa kaina da ƙaramin murmushi a fuskar ta..na tabbar wani abu take tunani da yanda idonta ya kafe wuri guda... Muna zaune cikin shiru wayarta ta ɗau ƙara.. nida Asma'u mun yi mamaki.... wayar Mama tana ɗaukar wata da watanni kafin tayi ringing har mantawa ake da ita a gidan... Anaam ta miƙowa Mama wayar bayan ta ɗauka tasa a handsfree..kafin Mama ta fara magana wata murya daga ɗayan gefen ta katse ta da faɗi a mugun fusace kamar zai fasa screen '' a dana gaisuwar ki Ameenatu....baki tashi gaishe dani ba sai da na kira? Tunda Abdul wahhabu yabar duniya kika raba mu da ya'yan daya bari a baya..bayan kin san da dangin uba ake ado idan babu uba,yara mata ba maza ba balle kice zasu iya aurar da kansu...idan Kinga abinda kike shine dai dai ki cigaba ...'' '' ayi...'' katse kiran akayi daga can...Mama ta kafe wayar da ido fuskarta kamar an jaye jini firgici da tsoro ɓaro ɓaro...mu da mukaji abinda koma wane marar mutuncin ne ya faɗa... muka yi shiru kamar babu mu a wurin amma naji zafin kalaman da aka gayawa Mama... Inna sarai take kallon Mama da kulawa a idonta.. '' Mama wane marar...'' '' Na hane ki!" Mama ta katse Asma'u..sannan ta juyo gare mu '' ku tashi kuje kuyi sallah...'' jiki ba ƙwari muka fito daga ɗakin..nake jin sanyin yau akan fata ta.. yafi na koda yaushe kasancewa mai tsanani ba lallai dan hakan gaskiya bane sai dai saboda abinda ya faru a ciki... Bayan munci abinci muka sake komawa ɗakin Mama amma Inna sarai ta hana mu shiga tace muje mu kwanta kada mu dame Mama... Koda safiya ta waye muka tafi gaishe da Mama yanayinta bai zama kamar irin na koda yaushe ba..na tabbatar harda sunan baba da koma waye daga can ƙarshen ya kira yasa ta a yanayin da take...naga kamar idonta sunyi ja kaɗan... duk da haka bata bawa Kowa damar tambaya game da abinda muka ji ba...yanayinta yasa nima naji nawa yanayin ba daɗi...haka ma sauran Sai wurin yamma sannan naga kamar taɗan wartsake sai murmushi ya dawo a fuskar kowa...da ƙarfe huɗu da rabi muna zaune saman baranda mu duka iska na kaɗawa a hankali a hankali da sanyi mai sanyaya zuciya...kai na a saman cinyar Mama kamar koda yaushe Asma'u nayi ma Anaam kitso inna sarai na tsintar shinkafa muna hira da nishaɗi '' Assalamu Alaikum...masu gidan nan ana sayen gwanjo'' Muryar matar ta karaɗe ilahirin gidan '' waih...speaker!" Inji Anaam '' ke ba'a son wulaƙanci...'' inna sarai ta kwaɓe ta '' wa'alaikumussalam...ba'a saye...'' Asma'u ta ɗaga murya itama dan matar taji '' dan Allah a sammin baye...'' matar ta sake faɗa...kallon kallo mukayi...ko matar so take ta shigo ta gama gane mana gida? Koda yake ance fa wai idan mutum yazo gidan ku yace wai ku samma shi toilet kada ku yarda yan tsafi ne '' shigo...'' Mama ta katse ni... '' Abeedah jeki ɗiba mata ruwa...'' Na tashi na nufi inda ake ajiye ruwa..matar ta shigo suka gaisa dasu Mama a mutunce ta kawo kayanta wurin baranda can naji su suna ƙara gaishe gaishen yaushe rabo ashe sun san juna ''.ina yini..''.matar ta kalle ni da murmushin mutunci tace '' lafiya lau...Ameena wannan itace Abeedahtu ko?" Mama ta gyaɗa kai '' Ma sha Allahu... yarinya ta zama kyakkyawar budurwa...'' nayi murmushin kunya kafin na dawo na zauna inda na tashi ita kuma ta wuce baye... Inna sarai ta tafi kitchen ta juye shinkafar data gama tsincewa a cikin ruwan da suka tafasa... Ba daɗe Matar mai suna inna sabuwa ta fito daga baye...tazo ta zauna suka buɗe shafin hira...hmm kundai san yanda idan mamansu mutum suka haɗu da wani wanda suka sani ake shafe awa da awanni ana hira...nikam har abun ya fara cimin tuwo a ƙwarya... Da ƙarfe biyar da rabi abinci yayi..aka xubo sai da aka ta roƙon matar akan ta zauna taci tana bata so...kafin aka shawo kanta... nidai idan mutum yazo gida na...na bashi abinci yace bazai ciba bazan roƙe shi ba... Muna tsaka dacin abinci wayarta tayi ringing..lalubo wayar tayi daga kwagirinta dake ɗaure a ƙugunta ta amsa murya a sama...muna jin duk abinda ake faɗa...wai ana neman masu aiki guda biyar mata a gidan wasu masu kuɗi...zare hannu na nayi daga abincin ina sauraren wayar matar... jikina har tsuma yake dana ji ance albashi dubu hamsin...amma mutum zai dinga zama a can gidan masu kuɗin dawowa gida sau ɗaya a ƙarshen wata... Mama ta lura da yanda nake ɗoki yasa tayi min kallon gargaɗi...Anaaam ma ta lura dan haka bayan matar ta ajiye waya tana sake faɗawa Mama abinda aka faɗa duk da munji da sauri Anaaam tace '' Laa kin koga Abeedah tun tuni take ta neman aiki amma ba nasara...yanzu wannan dan Allah ba babbar dama bace?" Da sauri Asma'u tace '' na sani ko? Itama ta huta da biye biyen rana...'' Mama da inna sarai basu ce komai ba...sai da Inna sabuwa tayi ma Mama magana..hararar mu tayi sannan tace '' manta dasu sabuwa ... Abeedah aiki kaɗai ta taɓayi a restaurant...'' '' hakan ma ya wadatar...'' inna sabuwa ta katse Mama...Inna sarai Mama ta kalla tana neman ceto dan dai bata son inyi nesa da ita... duk inda ta ɓullo inna sabuwa sai ta toshe daga ƙarshe ta tabbatar mata data san shugabar ma'aikatan gidan sannan bani kaɗai bace akwai sauran mata...kuma zata sa matar ta saka min ido,makaranta ma zan cigaba da zuwa......badan Mama taso ba tayi saranda...kamar in zuba ruwa ƙasa in sha...ashe Allah yasan abinda yake tanadar min shine yasa ban samu aiki a duk inda na nema ba..oh Allah na gode maka... '' Congratulations.. Abeedahtu...yar wahala '' Anaaam ta faɗa tana juya ido...ni ban damu ba..sai murna nake '' za'a iya ba Abeedahtu advance payment na wata biyar...dan mu samu mu biya kuɗin makarantar mu?" Asma'u ta tambaya...jim inna sabuwa tayi kafin tace zata gwada tambaya...farin cikina ya ƙaru..inna sarai na tayani .... ...anan tace wai gobe goben nan da rana zamu tafi... Raina fes nace '' Allah ya kaimu '' Fuskar Mama dai ba fara'a...da daddare bini bini ta ɗago ta kalle ni... Har lokacin ban fahimci girman abinda nake shirin shiga ba sai da muka tafi ɗakin mu... bayan an kashe wuta...bayan zolaya da surutun su Asma'u yayi ƙasa..na kasance idona biyu a duhu..na fahimci cewa..gobe zan bar gidan mu...zan bar su Mama in tafi wani wurin da ban sani ba...ban san abinda yake jirana a can gefen ba...zan iya ɗauka? A duk sanda nake baƙin ciki na da koke koke na,su Mama na nan don kwantar min da hankali yanzu kuma zan tafi inda babu su..ya zanyi? Ban taɓa yin nesa dasu ba sai wannan karon...anya kuwa? ' tunani akan abinda zai faru a nan gaba yana haifar da anxiety..ciwon damuwa...' maganar Jay d take amsa kuwwa acikin kaina...sauƙina guda zan dinga haɗuwa dasu a makaranta banda Mama da inna sarai... numfashi na sauke na lumshe idona...ban san tsawon yaushe na ɗauka ba kafin bacci ya ɗauke ni... Da safe kamar akwai wani baƙin hadari dake maƙale a saman gidan mu..jikin kowa ya mutu babu mai magana daga uhm sai uhm Uhmm..sai bin juna da ido...ni kaina jikina ba ƙaramin mutuwa yayi ba...naji zuciya ta tayi nauyi...su ɗin iyalai nane..yanzu kuma zan rabu dasu in fara sabuwar rayuwa a wani wuri inda bani da tabbas... Kewar su nake tun kafin mu rabu...ido muka haɗa da Anaaam ta sakar min Murmushi mai kashe jiki..naji kamar zanyi kuka... Inna sarai ita take shirya min kayana cikin jaka tana min nasiha da wa'azi akan in kula da kaina, addini na da mutun cina... Su Asma'u jikin su yayi la'asar kamar ni...bayan mun gama sallar Azahar Mama ta kira ni ɗakinta...samun ta nayi zaune saman abun sallah tana tasbihi...na zauna kusa da ita ba kamar koda yaushe da nake kwantar da kaina a cinyarta ba.... wayarta ta miƙo min bayan ta gama tasbihin... Sannan ta fara magana '' bana buƙatar ince komai..Nasan kin san abinda yake dai dai da wanda ba daidai ba Abeedahtu..na yarda da tarbiyyar dana maki...amma duk da haka...ki kula da mutuncin ki..ki kiyaye Allah...kada ki bari duniya ta ruɗe ki..ko don Kinga bama kusa kice zakiyi wani abinda kin san ba zamu ji daɗi ba...'' ta juyo tana kallona daidai ina share hawaye ta cigaba da faɗin '' abu mai muhimmanci da nake so in faɗa maki shine,idan kin gaji...idan duniyar tayi maki zafi ..idan baki san inda zaki juya ki samu sanyi a ranki ba...kina da Mama Abeedah...ki dawo gida a koda yaushe ƙofar a buɗe take,kada ki manta da Mama dan Allah....'' Muryar ta take rawa..itama tana ƙoƙarin danne kukan da take ji Rungume ta nayi ina cigaba da nawa kukan...taya zan manta da Mama? '' Mama ga inna sabuwa nan...'' Asma'u ta ɗago labulen tana kallon mu...jaye ni daga jikinta Mama tayi ta miƙe ta fita.. Asma'u ta shigo ciki...sai ga Anaam ita ma...muka rungume juna...never in my life nayi tsammanin wannan ranar zata zo...kuma ban taɓa tsammanin ɗacin ta zai kai haka ba... Bayan wani lokaci inna sarai tace '' toh Abeedah ki fito ku tafi...'' jiki ba ƙwari na miƙe tare da ɗaukar hijabina baƙi dake saman gadon Mama nasa idona sunyi ja haka ma nasu Asma'u...ina fitowa Inna sarai ta rungume ni itama '' Allah yasa kin fara a sa'a Abeedahtu ya kaɗe bala'i da masifa daga afka maki...'' saki na tayi na isa inda Mama take tsaye da inna sabuwa itama na sake rungume ta '' Mamaaa....'' na kira da muryar kuka... ''.au Dena kuka Abeedahtu nan da ƙarshen wata ai zaki dawo...''.inna sabuwa take lallashina...ɗago ni daga jikinta Mama tayi tana shanye nata kukan...ta goge min hawaye na '' Allah ya tsare ya kare min ke Abeedah...'' aka amsa da Ameen Na ƙara kallon su Asma'u dake tsaye daga bakin ƙofar ɗakin mu kowa da hawaye a idon shi kafin na fita...wani sashe na zuciya ta maƙale da gidan mu...rana ta ɓoye bayan gajimare...tana ƙara sani a ƙunci... kamar inyi zamana kada in tafi... Nayi tsaye bakin ƙofa ina kallon motar da take kamar bus da aka faka gaban gidan mu ga wasu yara zaune a ciki suma... Su Inna sarai dasu Anaam suka fito...inna sarai riƙe da kayana..wani yaro daga gaban motar ya fito ya karɓa ya samin a bayan buut...share ƙwallar dake idonta inna sarai tayi ta taimaka min na shiga motar na zauna gaba gaba bakin taga...ina ƙarewa unguwar mu da kuma maƙotan mu kallo...yau zan bar abinda na sani...zuwa wanda ban sani ba... The future...my future is uncertain... Idona sukayi jawur kamar an zuba yaji ciki...ƙila wannan shine farkon abinda nake ta addu'a akai...dama wanda ban san dashi ba? Inna sabuwa ta fito bada daɗewa ba tare da Mama...sai godiya take mata.. sannan ta shigo motar..driver ya tada muka fara tafiya..su Asma'u suna yimin bye bye kafin Asma'u da Anaam suka rungume juna... fashewa nayi da kuka...zuciya ta tayi min nauyi... ...ina kallon gidan mu..da sabuwar anguwar mu...bishiyar nan dake ƙofar gidan mu da yaran dake wasa saman lilo wasu na faɗa....wasar da muke da yaran maƙwabta...muka wuce filin ƙwallon nan da koda yaushe yara da masu sayarda abubuwa suke cika wurin dan su kalli ƙwallo...nake kallon ƙananan shuke shuken nan da suka fara bushewa..su tafasa dasu sanga sanga...nake kallon makarantar almajiran nan da kuma ƙaton bohol ɗin da ake ɗibar ruwa duk da bamu taɓa zuwa wurin ba... Nake kallon wani ƙaton dutse da nake da burin hawa amma ban samu na hawo ba...yau gashi zan bar unguwar mu...gidan mu da kowa nawa...in fara rayuwa a wani sabon wuri...na shirya? Me yake jirana? yanzu babu Mama babu Jay D a kusa dani ya zanyi?... nake jin wani irin ƙaton abu ya tokare min a maƙoshi... musamman da muka hawo kan titi nake ta kallon waje..kamar ince a ajiye ni in koma gida taya zan rayu babu su Mama?... Lumshe idona nayi...ina addu'a a cikin raina koma meye ne a gaba Allah yabani ikon iyawa dashi sannan ya dafa min... +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 20. ...Ranar farko...🖊️ Gyara zama na nayi bayan na share hawaye na,na juyo ina kallon mutanen dake cikin motar,duka duka mu Ashirin ne, mafi yawanci daga shekaru sha bakwai zuwa Ashirin da biyu ne,sai wata yarinya ƙwaya ɗaya yar shekaru sha uku...kuma babu wanda yayi kama da ɗan ƙauye ...ganin kallon da suke bina dashi har wasu suna yan ƙus ƙus yasa na ɗauke idona daga kallon su... '' Hmm...anya kuwa yar wata zata samu aiki? Kun kuwa ga idon ta kamar na mayu...''juyowa nayi na kalli wacce tayi maganar daga yanda muryarta ke fita da kuma kallon rainin da take bina dashi na fahimci nayi sabuwar maƙiyyiya tun kafin in fara aiki amma ban ce komai ba suka mayarda ni abun hirar su amma ni ban damu ba ko kaɗan..har wani sashe na zuciya ta na fatan kada a ɗauke ni don in dawo gida in cigaba da rayuwa dasu Mama.... Ɗauke kaina nayi ina kallon window da abubuwan da muke wucewa da sauri,na ɗauka dukan mu wuri guda zamuyi aiki amma a mamakina sai naga munata tsayawa a gidaje ɗaya ɗaya har gida uku na masu kuɗi ana tafiya da mutum biyar a kowacce tsayawa...daga ƙarshe ya rage mu biyar,ni, yarinyar nan da bazata wuce shakaru sha uku ba,wata mai shekaru sha tara...da wata mai shekaru ashirin da biyu..da kuma cikin rashin Sa'a yarinyar data ce ba lallai in samu aiki ba Naji inama ace harda ita aka ajiye a wani gida daban... Wata unguwa muka kawo ta masu kuɗi, gine ginen wurin kamar a ƙasar waje, guntuwar gina kamar yanda turawa sukeyi,manya manyan gates.. tsakanin wani gida da wani akwai tazara...ƙasan wurin interlock ne sai bishiyoyi masu tsawo da korayen ganyayyaki ... korayen ciyayi da kuma wurin zama a ƙarƙashin ko wace bishiya..sannan kowane gida nada lamba...unguwar ta haɗu kuma ba ƙaramin tafiya dani tayi ba... Ina tsaka da kalle kalle naga mun kawo wani makeken gida kamar ƙaramar masarauta....bani kaɗai ba,har da sauran dake cikin motar duka muka saki baki da ido muna kallo...fa tabarakallahu Ahsanul khaliƙin baƙin gate ɗin da kanshi ya buɗe sai da muka yi yar tafiya mai tazara kafin muka kawo gaban wani ƙaramin sashe dake gefen ƙaton gidan...wata tsohuwar mata biye da ita matashiyar budurwa suka fito daga wannan sashen suka yo inda motar mu take.... '' Ku fito...'' inna sabuwa ta fara sauka sannan ɗaya bayan ɗaya muka fito yarinyar nan da ban san sunan ta ba ta tsaya dai dai ni take ƙare min kallon ƙasƙanci '' da nice ke da nayi zama na gudun rasa fuska...'' Miƙewa tsaye nayi na bangaje ta sai datayi tangal tangal kamar zata faɗi tayi saurin riƙe kujera fuskarta ɗauke da fushi take kallo na... Na tsaya bakin ƙofar na juyo ina kallon ta '' amma bake ce niba...sai ki adanawa kanki wannan shawarar...'' Na sauka daga motar bana son ko kaɗan mutane suna faɗa min nasu ra'ayi game da yanda ya kamata in tafiyar da rayuwata...ƙila da badan na kasance ina sauraren suba,da ban kasance mai yawan jin kanta a ƙasƙance ba... Gefen sauran na tsaya ake sauko mana da kayan mu,inna sabuwa da wannan matar kuma suka nufi babban gidan...tana bawa waccen matashiyar umarni data shigar damu ciki... Sai yanzu na samu damar kalle kalle da kyau...ƙasan gidan tyles ne,sai wani taskar ruwa a tsakiyar gidan a gaban babban gidan Ɗaya bayan ɗaya muka ɗauke kayan mu biye da Wannan matar data kai mu har ciki... A gidan tuni akwai ma’aikata kusan ashirin ko fiye... - Masu girki 4,uku yan ƙasar waje ɗaya na Nigeria - Masu tsaftace gida 4 - Masu kula da lambu 3 - Direbobi 4 - Manajan gida 2 Sai sauran masu yan gyare gyare,wanke wanke,share share..da sauran su wanda muma cikin su muke Aatika ta jagorance mu kai tsaye zuwa ƙofar ma’aikata da ke gefen babban gidan. Ƙofar ƙarfe ce mai keypad. Ta danna lambar, sai ƙofar ta buɗe da ƙarar beep. Da muka shiga, iska mai sanyi ya buge mu. Falon yalwatacce ne, kuma shiru ya mamaye wajen. Aka fara kai mu zuwa Basement ɗin Ma’aikata (Floor B1).inda a ciki akwai Ɗakin rajistar aiki,Ƙaramin tebur, babban littafin rajista, da kyamarar CCTV a kusurwa. Matar tace mana "Ku sa hannu a nan. Lokacin aikinku Litinin zuwa lahadi daga ƙarfe 7 na safe zuwa 7 na yamma."..na zaro ido kenan bamu da hutu? Suma sauran kusan abinda suke tunani kenan..daga nan taja mu zuwa ɗakin Akwai lockers guda 21, sauran shashidan suna ɗauke da sunayen masu su..mu da muke sabbabi za'a ɗauki sunayen mu..a cikin kowace loka akwai - uniforms guda huɗu,baƙaƙe ɗaya,ruwan toka, ruwan ƙasa da kuma farare... nake kallon komai kamar a mafalki ko fim daga nan taja mu zuwa ɗakin cin abinci.. inda akwai Dogon tebur, jarkokin ruwa, da firiji mai abinci "A nan za ku ci. Ba a saman gida ba." Kamar zan juya idona,dan Allah daga zuwan mu sai wannan? Meyasa baza'a fara bamu abinci a bamu wuri muyi salla ba? Daga nan taja mu inda Taswirar gidan Wannan shi ne abin da ya fi ba bani mamaki kamar wasu masu gano ma'adanan ƙasa harda taswira a gidan? "Za ku riƙa ɓacewa. Ku haddace wannan taswira." Yanda matar take magana business kawai ba fara'a..murya ƙamas ƙamas...cikin kamewa yasa naji kewar su Mama na tasomin kamar zanyi kuka Sai ta nuna sama dukan mu muka bi wurin da kallo "Gidan nan yana da bene shida. Idan kuka yi yawo ba tare da izini ba, CCTV za ta gan ku. Don haka kada ku yi yawo." Muka gyaɗa kai ina addu'ar Allah yasa wannan shine ƙarshe,fita tayi muna biye da ita benen dake tsakiyar parlorn muka hawo sai ga ɗakunan bacci harda doguwar kujera ƙwaya ɗaya gaban wani ɗaki ta tsaya kafin ta juyo kalle mu na tsawon lokaci sannan ta raba mu,ta haɗa nida yarinyar nan data tsane ni tace ɗakin mu ɗaya sauran ma ta nunawa kowa ɗakin shi... yarinyar nan na kalla naga ta sakar min wani mugun murmushi Jikina yayi sanyi idanfa ta dinga cuta ta kuma na kasa tsaya ma kaina ya zanyi? '' Oya...ku faɗa min sunayen ku...'' maganar matar ta katse ni daga tunanin dana shiga Ta nuna ni '' Abeedah...'' na faɗa a sanyaye,kafe ni tayi da ido tana duba ni bada hukunci ba sai dai kamar tana ƙoƙarin fahimtar wani abu...can ta gyaɗa kanta ta juya ga sauran Waleedah, yarinyar mai shekaru sha uku,Ayna'u yarinyar mai shekaru sha tara...sai Rahma yarinyar mai shekaru ashirin da biyu... muguwar nan sunan ta Hansa'u shekarun su ɗaya da Aina'u... Gyaɗa kanta matar tayi ta bamu shawara,ko nasiha take mana,ko faɗa ban fahimta ba '' duk wacce tayi ciki a gidan nan,gidan iyayen ta zata koma babu hanya biyu game da wannan!,ku shiga ciki kuyi wanka ku canja kaya..anjima za'a kai ku babban gida a gabatar daku.." Tabar mu tsaye a wurin ta wuce muka shiga kallon kallo gabana naji ya fara faɗuwa... Ture ni Hansa'u tayi ta shiga ɗakin mu nabi Bayan ta...babu tarkace da yawa a ciki...gadon nan mai hawan mutum uku,da wardrobe guda uku labule fari da kuma baye sai fanka da farin ƙwai ko TV babu ... Nake tunanin..akwai gado uku,kuma mu biyu ne waye na ukun? Baye na nufa Hansa'u ta sha gaba na '' ni zan fara shiga..'' tayi maganar da izza bana son faɗa shine yasa kawai naja baya..tayi ƙwafa sannan ta shige bayen ta ɓata lokaci kafin ta fito nima na shiga.. duk tayi ma bayen kaca kaca...ga kashi da tayi bata yi flushing ba baye duk ya gume...cikin ɗacin rai na tsaftace bayen sannan nayi amfani dashi.. Sanda na fito har an kawo mana kayan mu,naji daɗin hakan,na duba riga da wando marasa nauyi da singlet nasa,na ɗauki hijabina na kabbarta sallah Hansa'u tayi kwance saman gado tana latsa waya ƙila bata salla,ina nan zaune har Saida akayi maghrib...bayan mun gama,wata mata ko yarinya ce oho..tazo ta kira mu wurin cin abinci..kusan a tare mu sabbabin zuwa muka fito daga ɗakunan mu...lokacin ƙarfe bakwai da yan mintuna dan haka tsofaffin ma'aikatan sun dawo... suke bin mu da kallon dana kasa fassarawa..muna tafiya a tsorace muka iso dining ɗin,muka gaishe da waya'nda ke wurin wasu suka amsa ba yabo ba fallasa wasu kuma ko kallo bamu ishe suba... Matar farkon nan data shigo damu wurin tace muje kitchen mu zuba ma kanmu abinci...a sanyaye muka wuce kitchen ɗin muka zubo abincin muka dawo tace mu zauna a seats ɗin da babu wanda ke zaune saman su...mutane da yawa a wurin ransu bai so ba... Tace '' bari in fara da kaina...sunana Ateeka nice mataimakiyar shugabar ma'aikatan gidan nan... wa'yannan...'' ta nuna sauran tana gabatar mana dasu,yawansu yasa ban riƙe sunan kowa ba.. taci gaba da faɗin '' a gidan nan babu seniority,wani baya aikin wani...kada ku bari wani ya cutar da ku,kuma kada ku cutar da wani,amma duk da haka akwai girmama juna..wanda ya girme ka ya girme ka...'' Ta dakata tana kallon mu dan fahimtar ko mun fahimci abinda ta faɗa ko akasin haka ta ƙarashe maganar da faɗin '' akwai rules and regulations a gidan nan..za'a ba kowa copy ya ajiye idan mutum ya cika karye ƙa'ida zai bar gidan nan! Fatan zaku kiyaye?" '' Insha Allah '' muka amsa...nake ji gidan ya zama kamar kurkuku duk da har yanzu babu wani gagarumin abu daya faru...a hankali nake cin abinci na..ina jina duk a takure '' kuyi sauri ku gama mu tafi main house bayan sallar isha'i..'' muka jinjina kan mu tabar wurin... tsofaffin ma'aikatan suna cin abinci suna hira akan aikin su naji inama ace nima ba sabuwar ma'aikaciya bace...'' Ke!" ɗagowa nayi daga abincina ina kallon wacce ta kira ni da 'ke' hararata tayi...'' contact lenses kike sawa?" Sauran suka juyo suna kallona da sauri na fahimci abinda take nufi ganin kallon zargin da ake bina dashi...'' haka idona suke..'' '' ƙarya kike..maza tafi ki cire wannan abun daga mummunar fuskar ki...'' yarinyar maganganun ta na cin mutuncin ne..take naji idona sun ciko da hawaye kuma babu wanda ke mata magana... '' haba Fauziyya bai kama...'' '' Babu ruwanki Mama Asabe!" Fauziyyar ta katse matar da ɗaga murya, matar ta fara tsufa kuma insha Allah zata haifeta,sannan ta sake juyowa inda nake '' ba zaki tashi ba?" Da takaicin abinda tayi ma tsohuwar nace '' eh bazan Tashi ba,idan kin damu kizo ki cire da kanki...'' wurin yayi tsit da tension...nida fauziyya idon mu cikin na juna...naji cikina ya kaɗa..amma duk da haka...waya bata ikon cin mutun cina da kuma na tsohowar? Ina girmamawar da akace ana yiwa na gaba da kai? Ruwan dake gabanta ta ɗauka ta wanke fuskata dasu..naja dogon numfashi..dan banyi tsammani ba...da alama akwai wa'yanda suke jin daɗin abinda ke faruwa ciki harda Hansa'u '' Subhanallahi..''Mama Asabe ta koka...amma Fauziyya bata ko kalle taba.. ta miƙe tsaye tare da ranƙwafowa hannayenta dafe da table tana kallona da tsana a idonta tace . '' manta da abinda Ateeka ta faɗa...idan har baki shiga taitayin kiba na miki alƙwarin zama a gidan nan sai ya gagare ki!" Tsoron da ya kamani na haɗiye dole ne in koyi tsayawa kaina idan ba haka ba kowa zai dinga takani yanda yaga dama... '' Bismillah.. tsoron ki ake ne? Yanzu dai Madam Atika ta gama faɗar babu seniority ko...koda yake...'' murmushin gefen baki na saki batareda na iyarda abinda nayi niyar faɗi ba..gray eyes ɗina suka ƙara duhu abin ban tsoro...firgici ya bayyana a fuskar kowa dake wurin...na miƙe tsaye batare da na gama cin abincin ba na koma ɗakin mu daga lokacin dana rufe ƙofar duk wani jarumta ya rushe hawaye suka wanke fuska ta...(Su Abeedah masu super power ido🤣) '' kamar yarinyar nan is a bad omen, kunga idonta kuwa...ruwan toka?" Rasheedah ta faɗa tana aza hannu saman kai idonta kamar zasu faɗo '' kodai mayya ce?" Wata daban tayi maganar '' You're very stupid!" Fauziyya ta daka musu tsawa a fusace haushi da takaici ya ƙumeta...wannan sabuwar yarinyar tana ƙoƙarin zamar mata sartse a nama...dole ta koya mata hankali... Wurin yayi tsit da shiru mai nauyi babu wanda ya isa yayi magana ... ***** Wayata dake ringin na lalubo daga cikin komatsai na...lambar inna sarai ke yawo akan ƙaramin glass ɗin,kukan dana tsagaita naji yana neman dawomin sabo..ɗage kaina sama nayi ina jan numfashi sannan na amsa kiran '' Abeedah...'' lallausar Muryar Mama ta faso wayar bayan tayi sallama..damƙe baki na nayi ina haɗiye kuka na '' N...na..am...Mamaaaaa'' daga ƙarshe dai na saki kuka...da yanda take ta rattafo min tambayoyi naji ba daɗi dan nasan hankalin ta ya tashi su Inna Sarai suma suka yo kan wayar kowa na tambaya ta lafiya...zama nayi bakin gado bayan yunƙuri da yawa na samu na haɗiye kukan '' ..bba komai...nn..ayi kewar kune.mm... sosai kuma ....wann..an shine karo na farko dana yi nesa daku...'' na faɗa a rarrabe..daga cikin wayar naji mama ta sauke nannauyan ajiyar zuciya kafin ta fara lallashina..su Anaam da Asma'u muryoyin su,sun ƙara jefani a yanayi...mun ɓata lokaci muna waya kafin daga baya mukayi sallama,kalaman Mama na ƙarin ƙwarin guiwa sun sa naji sauƙi a raina..na shiga baye na wanke fuska ta... Bayan sallar isha'i,Madam Atika ce gaba muna biye da ita a baya mu biyar zuwa babban gidan...gaban babbar ƙofar mai Black and golden muka tsaya ta danna ƙaraurawa..wata na'ura ce tayo gaba kamar zata ɗauke mu hoto alamun scanning ɗin mu ake...kafin ƙofar ta buɗe... Sumar tsaye ni Abdeedah nayi da ganin haɗuwar wurin..ashe gidan su Jay d wasa ne idan an haɗa da wannan..bare tun kafin na shiga daga ciki na fahimci gidan hawa shida ne... Ga wani ƙaton bookshelf a wata kusurwar stairs ɗin,sai ƙaton bishiyar cherry blossom dake waje bishiyar tayi tsayi har ana hangowa ta window'n sama Kamar yanda nake kalle kalle kamar baƙauya haka sauran suma suke al'ajabi,wata yar coner Madam Atika ta nufa damu,isar mu wurin ta zaro ƙaramin kati ta nuna a ƙaramin glass fari maƙale da wurin.. take ya buɗe ashe elevator ce ... '' ko in ɗauke kune?" Maganar ta tasa munyi rububin shiga cikin elevator ta wuce damu first floor, take nuna mana abubuwa Floor B1, Sashen ma’aikata, wurin wanki, ɗakunan ajiya, da genetors room 2nd Floor: Babbar ƙofar shiga, babban falon baƙi, ɗakunan cin abinci biyu na musamman, da banɗakunan baƙi. Floor 1: Falon iyali, ɗakin TV, babban kicin, wurin karin kumallo, da tafkin iyo na cikin gida... - Floor 2: Ɗakunan baƙi guda biyar tare da ɗakin sallah. - Floor 3: Bangaren Alhazozan gidan da matayensu Kowacce sashe yana da ɗakin kwana da falo - Floor 4: sashen yaran gidan,samari da yan mata - Floor 5 (Rooftop): Gym, tafkin iyo na waje, wurin barbecue da lambu ... Lif yana aiki ne kawai da katin ma’aikata. Matakalar hawa kuma tana da ƙofofi biyu masu kama da juna. Har akwai wata doguwar hanya da idan ka bi ta sai ta kai ka wata doguwar hanyar daban. Tana nuna mana wurare tana bayani...muke binta kamar wasu mutum mutumi...taga ma bayani amma akwai sauran wurare da bata faɗi komai akai ba '' na kawai nuna maku inda zakuyi aiki ne,sauran wuraren baku ba yawace yawace ko taɓa wannan taɓa wancan..Na hane ku..ba ruwanku da shige shige..a duk sanda kuka haɗu da yan gida,ku kasance a mafi kyaun halayen ku...kun gane?'' '' eh mun gane!"amsar mu tazo da haɗa baki kamar yan primary'n dake amsa tambayar malamar su... Cikin elevator muka ƙara shiga muka iso kitchen ɗin a first floor,nan muka iske masu dafa abinci..turawa uku ɗan Najeriya ɗaya suna nan da can domin shirya abinci..magana tayi da shugaban wurin...ya kalle mu kafin ya isa wurin ƙaramar cupboard ya ɗauka wasu papers ya miƙa mana...karɓa mukayi muna karatun wuraren da zamu dinga kula dasu - Tafkin iyo na cikin gida(swimming pool): Goge tayal, cire ganyen da ya faɗa, da duba sinadaran ruwan kowane Asabar. - Wuraren cin abinci uku: Babban ɗakin cin abinci mai kujeru 20, na iyali, da na saman rufi... A tsaftace a gyara a canja table cloth a goge kujerun - Gidan kallon fim(movie room): Share kujeru da injin vacuum, goge remote, - Dakunan ajiyar kayan abinci biyu: Ɗaya na busassun kayan abinci, ɗaya kuma na abubuwan sha...a kowane ƙarshen mako,a duba aga abinda ya ƙare... A fitarda wanda ba'a buƙata - Ɗakin wasanni: Teburin billiards, PS5, da ƙaramin mashaya...a tabbatar komai a gyare kuma a kimtse... Ƙaton ɗakin taro a tsaftace bayan kowane kwana uku... Yawan aikin yasa naji kaina harya sara..nida ban taɓa yin aiki mai yawa har haka ba taya zan fara? Wai ma nan akwai wuraren da bamu sani ba sai nan gaba ''.kada ku damu...akwai duty roster..kowa zai san ranar aikin shi...'' ganin kamar mun shiga damuwa mutumin yayi ƙoƙarin kwantar mana da hankali... Ajiyar zuciya na sauke da ƙarfi daya sa kowa kallona kamar nayi laifi.... Munanan tsaye tsofaffin ma'aikatan suka shigo cikin uniforms ɗinsu ash,babu wacce tasa hijabi suka fara kwasar,abincin da aka dafa ba ƙarya ba sun kusan kai kala goma... Yanda suke sauri sauri kamar suna tsoron ɓatawa masu gidan rai...nake binsu da kallo...Madam Atika ta juyo tace '' ku shirya yanzu zamu je ku gaishe da mutan gida ..'' Dukan mu daka kalle mu zaka san ba daidai muke ba, duk jikin mu yayi sanyi...kafin nan Madam atika ta gabatar mana da masu girkin...ta fara da wasu masu kama da larabawa '' wannan shine Alexander laroi, Muhammad Salah...yan ƙasar turki...'' suka risina mana cikin girmamawa mukayi tsaye rashin sanin yanda zamu yi..kawai nima sai nayi musu yanda sukayi mana..sauran ma suka bini Ta nuna ɗayan baturen '' wannan shine Leonardo daga italy...'' '' Ciao ragazze, piacere di conoscervi (sannun ku yan mata,naji daɗin haɗuwa daku)'' kallon shi mukayi kamar yanda kurma ke kallon wanda ke magana dashi dan bai fahimta ba..batareda damuwa ba ya juya ya cigaba da girkin shi... '' sai Na'em...daga nan Kano!" Ya juyo da murmushi '' sannun ku...'' ''.yauwa sannu dai...'' muka amsa mashi '' mu tafi...'' Madam Atika tayi gaba muna biye da ita muna tunkaro dining...wurin yayi tsit ba'a ganin mutanen dake zaune wurin sakamakon irin wannan labulen da yake kamar zare da aka saukar... bangon wurin painting shi sky blue...wata chandelier babba daga sama...an jera abinci kala kala... ma'aikata tsaye daga bayan su duk wanda ke buƙatar wani abu da sauri ma'aikatan ke miƙa masu... '' ina zuwa...'' ta dakatar damu a wurin..ta isa ita kaɗai ta rusina da girmamawa ta nemi izini sannan ta jagorance mu zuwa wurin...muka tsaya a layi guda mu biyar ɗin muna fuskantar iyalan da suna da yawa sosai...wata dattijuwar matace zaune a farkon table ɗin,kallo guda mutum zai san itace mai faɗa aji a gabaki ɗaya gidan...daga gefenta dattijai ne da basu kaita tsufa ba,da alamu ya'yan tane daga babban cikin su zuwa ƙarami...daga gabansu a ɗayan gefen table ɗin kenan,suma wasu matane zaune cikin shigar alfarma da alamu matan sune...sai yan mata da samari..a kowane gefe... Madam Aatika ta fara gabatar mana dasu bayan mun gaishe su da ko kallo bamu ishe suba tsohuwar itace Hajjo shugabar gidan duka..duk abinda ta faɗa ya zauna babu ɗaya daga cikin ya'yan nata dake burin ɓata mata rai... Sai mutum na farko bayan ita shine Alhaji Mansir da matarshi Hajiya Ruƙayya,shine babban ɗan hajjo... ƴaƴan su huɗu,Huriyya,juwairiyya,Khadeeja da Jawaad... Sai Alhaji sulaiman da balarabar matarshi Hajiya Wareesha... ya'yan su biyar suma, Kareema,Nu'aymah,kulthum, Seraphina da Mukhtar Alhaji Hussein da matar shi Hafsah, da ya'yan su, Farzan,Abdul Jalal,Isa,Ayan da kuma Imam... Alhaji Kabeer da Hajiya Bushrah, da ya'yan su Mufeedah,Heedayah,Khaleesat, Jameelah Alhaji Sa'eed da Matar shi Hajiya Zeenatu ya'yan su, Armani,Arman,Aryan , da Aryana... Wa'yannan sune wa'yanda ke wurin a yanzu..akwai sauran da suke a ƙasar waje sai wanda ya rasu Alhaji Muhammad na biyu bayan Alhaji Mansir Ban sani ba kona riƙe sunan mutanen da aka faɗa mana,dan yanda suke kallon mu kamar bamu cancanci dasu kulamu ba ya soki zuciya ta...shine yasa bana son masu kuɗi...amma ƙaddara ta shilloni a hanyar su dole in haƙure '' ban taɓa sanin akwai baƙaƙen mutane masu idon mage ba ai...'' ɗaya daga cikin mazan ya faɗa da shaƙiyanci...sai sauran suka kalle ni,duk na jini a takure hannayena a gaban hijabina '' Atika kada yarinyar nan ta dinga shiga kitchen dan gudun contaminating abincin mu...'' inji ɗaya daga cikin yan matan '' Come on.. she's pretty...after all''inji Mukhtar yanda yake kallona yasa naji kamar ƙasa ta tsage in shiga...babu ladabi a kallon nashi ko kaɗan duh!🙄 har naji abincin ya fita daga raina...Atika pls take this dirty kids away...'' Dariya suka saka dacin mutuncin da yarinyar tayi muna musamman ni.....ƙasa nayi da idona hawaye suka taru a ciki..ta gefen ido naga Hansa'u namin dariya..na muzanta ƙwarai... Tsofaffin masu aikin suma a ɓoye suke min dariya kamar sunji daɗin abinda ya faru dani... Da sauri Atika ta jagorance mu,muka bar wurin tana bani shawara '' Kiyi kamar baki ji abinda suke faɗa ba..wata rana sai labari '' na gyaɗa kaina hawaye sun rufe ganina Muna shiga ɗakin mu Hansa'u ta fashe da dariyar ƙeta tana nuna ni da yatsa..ban bi takanta ba nayi tsaye dan ban san inda zan kwanta ba... Mama Asabe ta fito daga baye '' Meya faru?" Girgiza kaina nayi bana son faɗin ainahin abinda ya faru amma Hansa'u tayi saurin faɗa mata dan aci mutunci na...na fashe da kuka Ƙarasowa tayi ta rungume ni tana bani baki har na daina kukan... '' ni nake kwana a gadon ƙasa...ki kwanta a na biyu...'' '' wallahi bata isa ba...ni zan kwanta nan!" Hansa'u tayi tsalle ta dire akan bazata canja wuri ba...ganin kawai kamar Mama Asabe tana da sanyin hali...harda hawa tayi bake bake..a fusace Mama Asabe ta ɗauki wayar caji ta zabgawa Hansa'u a cinyarta dake kware ta saki ihu...dariya na fashe da ita tun daga ƙasan zuciya ta '' TOH sai ki buge ni...'' tayi maganar tana taɓune fuska duk munin ta ya ƙara bayyana..tana wani turo baki kamar mutum yayi amai.. '' wallahi idan baki sauka ba sai na ƙara maki...'' badan Hansa'u taso ba ta sauko tare da hararata ta haye gadon sama '' na gode sosai Mama Asabe...'' '' bakomai yar nan..Meye sunanki?" '' Abeedah...''na haye lallausan gadon ina rufe jikina da '' Allah ya tashe mu Abeedah'' na amsa da Amin takashe wutar, mukayi shiru ...sai Hansa'u dake ƙunƙuni...juyawa nayi ina kallon saman gadon Hansa'u.. maganar mutanen nan tana maimaituwa akaina...dan kawai suna da kuɗi,babu wanda ya basu damar cin zarafin mu marasa kuɗi...hawaye suke sauka ta gefen idona batarada na sani ba... na daɗe ina juye juye kafin bacci ya ɗauke ni... +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 21. ...an absolute witch...🖊️ Washegari da ƙarfe biyar na tashi naga Mama Asabe saman abun sallah , gaishe ta nayi ta amsa min da kulawa,na sauko na shiga baye...wanka nayi tare da alwala na mayar da kayan dana cire na fito daga bayen, wardrobe na buɗe na ɗauki hijabi ash nasa na kabbarta sallah gefen Mama Asabe..bayan na gama na sake ɗauko Qur'ani na fara muraji'a kamar yanda muke yi a gida...sai da hasken rana ya fara fitowa sannan na rufe Qur'anin na sake gaishe ta,ta amsa da murmushi... Na kalli tagar da labulen bai iyarda rufewa da kyau ba,hakan yabawa hasken rana damar shigowa...sai ɗakin ya kasance ba mai duhu ba sosai duk da dama can akwai wani ƙaramin globe kunne...nayi kewar su Mama...da sassarfa na ɗauko wayata daga wardrobe daga tsaye na shiga contact na kira number inna sarai..kamar ana jira aka ɗauka...nayi dariyar farin ciki muka gaisa da ita tabani Mama daga nan su Asma'u kafin mukayi sallama... Mayarda wayar nayi na isa wurin Hansa'u ina tayarda ita tayi sallah '' inke kike karɓar sallah'r kada ki amsa...'' ta juya kwanci kamar lokacin dare yayi... ''.kinga rabu da ita kawai...'' barin kusa da ita nayi,na zauna akan kujera ɗaya dake ɗakin bada daɗewa ba aka ƙwanƙwasa ƙofar na tashi na buɗe... yarinyar dake gabana ban isheta kallo ba ta turo min uniforms ba bayani ta ƙara gaba...oh ni Abeedah suba masu gida ba,suda jiji da kai... Rufe ƙofar nayi '' ga abinda ta bani...''na nuna ma Mama Asabe '' kije ki canja zuwa wannan ki ajiye wa wannan yarinyar ɗaya...'' Baye na shiga na canja kayan..nake kallon kaina a madubin dayake nuna sama har zuwa ƙasa...kayan ash wanda ya dace da kalar idona...kayan sunyi min girma musamman wandon amma naji daɗin kasancewar su masu girma...gefen aljihu harda sunana a rubuce kamar sanda ina aiki a maina hotels... Fitowa bayen nayi bayan na kimtsa kayan dana cire, wardrobe na nufa na ɗauki hula ruwan toka da hijabi rabin guiwa na ɗaura sama...na kafe kaina da kallo abu na taso min,da sauri nabar wurin na koma na zauna... koba komai yau ne ranar farko ya kamata in fara da murmushi '' Ma sha Allah,kinyi kyau...''. '' na gode..'' na duƙar da kaina a kunyace...tashi tayi daga inda take zaune..'' bari inyi wanka mu tafi kada mu makara..'' '' toh...'' **** ### **DOKA DA TSARI - NA YAN AIKI** **1. Lokacin Aiki Da Bacci** Lokacin tashi: 5;30 na safe. Dole ne a gama tsaftace gida kafin 7:00. - Lokacin bacci: 10:00 na dare. Ba tare da izini ba, ba za a iya fita daga sashe ba bayan wannan lokaci. - Ranar hutu: ƙarshen kowane wata na rana biyu.... cikkaken wata ɗaya a shekara **2. Ayyuka Na Gida** - Tsaftace ɗakunan girkin abinci, wankin kaya...da ban ɗakuna - An haramta shiga ɗakin Alhaji ko Hajiya ba tare da an knock ba. - Duk kayan da suka lalace dole ne a ba da rahoto nan take. 3. Ladabi Da Halaye - A amsa da "Eh Madam / Eh sir" cikin ladabi. - An haramta yin waya mai tsawo, kallon TV mai yawa, ko gayyatar abokai zuwa gida. - Dole ne a rika sanya uniform mai tsafta kowane lokaci. - An haramta ɗaukar wani abu na gida ba tare da izini ba. Ana kallon hakan a matsayin sata. **4. Sirri Na Gida - Abin da ya faru a cikin gida dole ne ya tsaya a cikin gida. Bayyana shi a waje laifi ne. - An haramta yin magana game da iyalin gidan ga maƙwabta ko a social media. 5 Albashi Da Hukunci - Albashi yana biya ranar 30 na kowane wata. - Zama a baya sau 3 ba tare da dalili ba = Rage albashi. - Yaudara, sata, ko rashin mutunci = Korewa nan take. -6 Muhimman Bayanai - Duk baƙon da ya zo dole ne a ba da rahoto ga Madam. - Idan kina rashin lafiya, sai a faɗa tun da wuri don a sami taimako. -Gidan yana da tsarin kamara CCTV don tsaro. Abi doka..a zauna lafiya... Wannan shine abinda mu sababbin zuwa muke karantawa a dining sanda muka zo karin kumallo tsofaffin ma'aikata har sun tafi harda Mama Asabe duk data makara hakan yasa ko karyawan bata yi ba... Hansa'u tasha faɗa wurin Madam Aatika dan ita taje ta tashe ta...hararata take kamar zata kashe ni ..share ta nayi na ajiye paper na fara cin abinda ke gabana.. suma sauran haka sukayi...bayan mun gama kowa ya wanke abinda ya lalata muka zauna dining cikin shiru dan bamusan abinda zamuyi ba Nake kallon waleeda, yarinyar ƙarama ce bata da jiki kuma bata da tsawo, uniforms ɗin sunyi mata yawa... murmushin kunya tayi min da idon mu ya haɗu '' shekarun ki nawa?" Na tambaya da mayar mata murmushi... '' sha uku...'' '' na ɗauka goma...'' '' nima haka...'' Aina'u ta furta cikin rashin yarda... waleeda bata samu damar yin magana ba,ɗaya daga cikin tsofaffin ma'aikatan ta shigo '' kuzo muje...'' Tashi mukayi muka bi bayanta zuwa babban gidan,har ahalin sun fara hallara domin karin kumallo... elevator muka shiga zuwa 4th floor...ɗakuna daban daban ta tura mu...'' a canja zanen gado,a share ɗaki ayi mopping, a wanke Baye a goge ko ina...kayan da sukayi datti a fito dasu zuwa ɗakin wanki...'' tana gama wannan bayanin tayi gaba...kallon lambar ɗakin dake gabana nayi room no 202...tura ƙofar nayi na shiga da sallama babu kowa ciki,na isa ɗakin,makeken gadon na nufa da kamar anyi dambe a sama na gyara na canja zanen gado,na tsince kayan dake ƙasa harda na ciki...na shiga Baye na wanke tass na goge ko ina na ƙyalli..fita nayi zuwa inda ake ajiye abubuwan shara na ɗauko na share ɗakin nayi mopping na fesa air freshener na kwashe labule sannan na fita na rufe ƙofar Na shiga ɗaki na gaba...shima nayi irin haka...a ɗaki na uku na zauna ƙasa ina hutawa kaɗan...wannan aikine mai sauƙi? Ko kaɗan! Har naji na gaji wasu sassa na jikina sun ɗau zafi... Minti biyar na miƙe na cigaba da gyara gyaren ɗakin, na gama na nufi ɗaki na gaba...zan tura in shiga naji ana magana '' aunty Muf...'' Maganar ta katse sakamakon saukar mari...na rufe baki na...'' ke dan ubanki ina magana kina magana ko? Nan gidan ubanki ne?" Banji amsar da wacce aka mara ta bayar ba sai sheshsheƙar kukanta Wata murya daban da wa'yannan biyun tace '' ai dan taga tana zaune cikin mune tana cin abinda muke ci ta kwana a irin inda muke kwana...ban san abinda kike tunani game dashi ba ..amma ki sani you're just a maid kuma bazaki taɓa canjawa daga yar aiki ba...tausayin ki dayaji ne kawai yasa ya sama maki wuri a nan.. nothing more!" Koma wacece tayi maganar tana gamawa tayo hanyar fita...da sauri na matsa na ɓoye a bayan wani abu kamar table dake wurin...har tazo ta wuce saye da kayan bacci...ta biyun ma tafito su biyun suna tafiya suna magana... Miƙewa nayi bayan sun shige elevator na shiga ɗakin bakina ɗauke da sallama..babu kowa ciki sai dai ƙarar saukar ruwa a Baye...kayan aikina na ajiye na shiga gyara ɗakin,ina jin tausayin koma wacece aka mara yanzu...har nayi na gama bata fito ba yasa na kwashe kayana na fita... Kitchen na koma a 1st floor,a can na samu da yawa daga cikin ma'aikatan suna kai komo...wurin Madam Aatika na tafi na faɗa mata na gama aikin da aka bani.. Ta gyaɗa kanta tare da nuna min wasu tsofaffin ma'aikata dake wanke wanke in taya su...yawu na haɗiye dan wanke wanken nada yawa kamar dutsen mareri...magana suke akan wani da ban san ko waye ba '' oh kinji cewa wani sati zai dawo?" Ɗayar ta kalli wacce suke aiki tare da murna a muryarta '' da gaske... Innalillahi daga ƙarshe nima dai zanga wannan kyakkyawan...har naji...'' Da sauri wacce tayi magana da farko ta rufe mata baki...tana mata alama da tayi shiru saboda ina wurin... '' kece wannan mara kunyar data tasar ma Fauziyya ko?...'' ɗage gira nayi tare da fuskantar su '' well,kidai bi a hankali, Fauziyya hatsabibiyar yarinya ce..'' ''.gashi tana da wanda ke ɗaure mata ƙugu a gidan nan...'' wacce batayi magana ba ta faɗa tare da tattare hannun rigar ta muka cigaba da wanke wanken suna hira akan samari da yan matan gidan... Sai wurin sha ɗaya muka gama wanke wanken...na gaji iya kar gajiya...fita sukayi daga kitchen ɗin na samu wuri na zauna saman ɗaya daga cikin kujerun dake kitchen ...ruwan goran dake gabana na shanye ina tunani... Ina kallon kitchen ɗin shima dai ba ƙaramin kuɗi aka kashe ba... '' yan mata...'' a hankali na juyo,ganin shi nayi tsaye daga bayana...gayen nan ne daya zage ni a dining jiya irin kallon nan na rashin ɗa'a yake bina dashi kamar jiya...da ɗan iskan murmushi a fuskar shi yana shafa ƙaramin gemon shi kamar na bunsuru...sauka nayi daga saman kujerar na matsa nesa dashi yake bin duk wani motsi nawa da idon rashin kunya,na buɗe baki zanyi magana kenan Hansa'u tashigo kitchen ɗin tana botsare botsaren ƙirji..cikin maƙe murya tace '' Abeedah,Mama Asabe na neman ki...'' take wani fari da ido...da ace kallo na kashe mutum data kashe ni,batareda na sake kallon kowa cikin su ba na fita daga kitchen ɗin... Bin bayan Abeedah yayi da kallo dirty things na yawo a kanshi,her gray eyes were a massive turn on for him.. idonshi suka ƙanƙance ya sake shafa fuskar shi... Hansa'u take kallon tsakanin ƙofar da Abeedah ta fita da kuma gayen da yayi tsaye yana bin ƙofar da kallo like a fool..tsuki taja a ranta...sai kuma ta fara takowa cikin jan hankali '' Barka dai yallaɓai...kana buƙatar wani abu ne...?" Kallon idonta da take jujjuyawa kamar na kwaɗo yayi...yaja dogon tsuki out loud..hakan ya soki zuciyar Hansa'u...ya zagaye ta zai fita sai kuma ya tsaya ya juyo ya ƙare mata kallo...the girl was curvy amma baƙa ce mummuna... however,zai iya maneji besides itama ai abinda take nema kenan ko... '' ki kawo red wine...22'' ya fice daga kitchen bayan faɗar hakan... Hansa'u ta ɗanyi jim tana tunanin Meye 22...nan ta fahimci ɗakin shi yake nufi...zaro ido tayi ta dafe kumatun ta...damn! She landed a jackpot ɗakin shifa ya kirata.... Sashen muna koma na, anan parlor naga da yawa cikin masu aiki sun dawo harda Fauziyya gaishe su nayi dayawa cikin su sun amsa harda tambaya ta ya ranar farko murmushi nayi '' ba sauƙi ko kaɗan...'' Na basu amsa sannan na wuce ɗakin mu,samun Mama Asabe nayi saman sallaya tana tasbihi da alamu salatul duha tayi..hijabina na cire na ɗan kwanta da niyar idan tagama inji kiran datake min... '' Abeedah ki tashi karfe biyu...'' naji ana jijjigani..buɗe idona nayi..lokaci guda na tashi zaune ina murza ido da sauri na faɗa Baye nayi alwala nazo nayi sallah...taya akayi nayi bacci har haka '' bacci lokacin aiki nasa a rage ma mutum albashi ki kiyaye...'' Mama Asabe dake jirana ta faɗa..gyaɗa kaina nayi dai dai nan Hansa'u ta shigo tana tafiya da ɗingishi..ƙila ƙafarta ta buge..amma kallon da Mama Asabe take yimata ya faɗi wani labari daban...well,ba ruwana da yima kowa hukunci... '' Mutafi Mama Asabe...'' na miƙe na ninke daddumar na mayar da hijabi na sannan muka fita zuwa babban gida.... kitchen muka shiga naga su Aina'u da Waleeda suna cikin wa'yanda ke jera abinci dining.. murmushi muka sakarwa juna kafin suka fita... Mama Asabe itama fita tayi daga kitchen ɗin da alamu tana da aikin yi... '' yarinya zoki ɗauki wannan salad ɗin ki kai musu a can...'' ɗaya daga cikin masu girkin ne yayi magana... numfashi naja..na ɗauki Salad ɗin na fita zuwa dining...ina ƙara matsowa ina jin hargagi na tashi ana yima wata faɗa '' stupid girl,kin ɓata min kaya dan baki san ciwon kuɗi ba...'' '' come on, ya'yan talakawan nan yan baƙin ciki ne...'' '' shine yasa bana so suna zuwa kusa Dani kada su goga min tsiya!" Wa'yannan sune maganganun dake tashi...dana matso kusa naga wata yarinya daga cikin ma'aikatan duƙe a saman guiwowinta..kuma fa duk manyan gidan na nan..a gaban su ake komai Zuciyata ta kusa faɗawa cikin ciki na sanda naga ashe waleeda ce yarinyar da ake yima wannan cin kashin... Sauran kuma sunyi tsaye kansu ƙasa... '' Seraphina..ya isa haka...'' hajiya Wareesha ta harare yar ta... '' But mom,kina ganin yanda dumb girl ɗin nan ta zubar min da juice on my expensive dress...'' ''.babu kuɗin sayen wani ne?" Hajiya Wareesha ta katse ta '' this is my favorite....'' '' come on sera, kibar shi kawai zan maki transfer ki sayi wani is that okay?'' Alhaji Sulaiman yayi ma yar tashi murmushi tare da zaro wayarshi yayi mata transfer ɗin Tasowa tayi daga inda take zaune tazo ta rungume shi '' thank you dad... you're the best..I love you...'' shafa doguwar sumar kanta yayi yana murmushi dan sosai yake son ta '' Hmmp! Dad nima fa ina buƙatar kuɗi...'' Khaleesat tayi maganar tana kallon mahaifinta Alhaji Kabeer...ɗaure fuska yayi shikam '' saboda wani yayi abu kema sai kin yi ko?" Turo baki tayi idonta ya ciko da hawaye ta juyo tana kallon hajjo dake kallon ya'yan nata da jikoki da murmushi a fuskar ta '' Hajjo kin gani ko?'' Tea'n dake hannunta hajjo ta karɓa da Muryar ta mai ɗauke da isa da izza tace '' zan baki kada ki damu...'' Da murna Khaleesat tayi godiya...sauran ma suka shiga ƙorafi akan akwai abubuwan da suke buƙata... Gaba ɗaya mutanen nan sun manta da baiwar Allah'r da suka sa tayi kneel down a guiwarta... Jiki a sanyaye na shigo wurin,ido na ya haɗu dana Waleeda..naji zuciya ta ta ƙara karyewa...salad ɗin na sauke a saman dining jiki ba ƙwari '' Oh Sera...ki kalli yarinyar nan mai fuska kamar anyi hatsari....'' Aryana ta faɗa tana dariya...sauran ma suka bita.... '' Ke,bana ce kada in sake ganin ki a wurin nan ba?" kamar sun samu TV dayawan su suke kallon dramar dake faruwa... ''Oh....ban jiba kenan...'' '' ke! Kina yar talakawa ƙasƙantacciya kina aiki ana faɗa kina faɗa?" Armani ta daki table ɗin ta miƙe tsaye tana nuna ni da hannunta kamar zata haɗiye ni '' Ni,ba ƙasƙantacciya bace! Kamar yanda kika faɗa aiki nake ana biya na..bawai kyauta ake bani kuɗin ba! Ke...'' Mama Asabe tayi saurin ƙarasowa ta jaye ni da sauri... mutanen dining ɗin suke bina da kallo... '' Dan Allah kuyi haƙuri,sabuwar zuwa ce bata san yanda abubuwa suke tafiya a gidan nan ba,ai mata afuwa zan mata bayani...'' '' a matsayin ta na yar aiki,tasan wannan idan masu gida suna magana,bai kamata ta amsa ba har sai an bata izini...'' Hajiya Bushrah ta katse Mama Asabe muryarta da zafi a ciki '' kuma idan ana magana ƙasa ya kamata tayi da kanta bata dinga kallon mutane ba cikin ido...'' Hajiya Ruƙayyah ta ƙara batareda ta kalli inda muke ba ... Sauran ma kowa sai zagin mu suke suna faɗin yanda ya kamata inyi a matsayi na na yar aiki... Zuciya ta tafasa takeyi musamman dana ga Mama Asabe ta zage tana bada haƙuri...dungura ta tayi akan in bada haƙuri...dogon numfashi naja badan naso ba na bada haƙurin wanda nayi nadamar badawa saboda yanda suke kallonq... Mama Asabe ta riƙa hannu na zamu bar wurin '' wayace ita zata iya tafi? Ta tsaya nan!"inji Mukhtar...sakin hannu na Mama Asabe tayi tana kallona da idonta alamun in kama kaina... Badan naso ba na dawo na tsaya... '' Oya zonan zoki dinga ɓanɓare fatar wannan grapes 🍇 ɗin...'' Heedayah ta nuna min wasu inibi dake tsakiyar table ɗin,sauran suna kaɗakai kamar wannan shine hukunci mafi tsauri...kallon ta nayi na ɗan zaro ido... '' Madam,bawai ina ƙin abinda kika sani bane,amma bakya gudun kada inyi contaminating ɗinsu?" Haɗe fuska tayi kafin tayi magana Seraphina ta rigata faɗin '' ba damuwar ki bane, besides babu wanda zai ci abinda kika taɓa..so just do as you're told!" Na kalli yarinyar da bazata wuce shekaru sha takwas ba yanda take bani oda kamar uwata...da yake suna da kuɗi ai dole suyi yanda suka ga dama... Zagayowa nayi na fara yi kamar yanda ta faɗa,ba abu bane mai sauƙi,sauran yan aikin suke kallona da tausayi..nima dai na fahimci wauta ta... Da ɗaya ɗaya manyan suka fara barin table ɗin ya rage saura samari da yan mata suna magana akan abubuwa kafin maganar su ta dawo akan mu yan aiki...suna zagin mu da ci mana mutunci... '' Ke!" Armani ta nuna waleeda da idonta sunyi jawur...a firgice waleeda ta kalle ta '' bar wurin nan!" Miƙewa tayi da sauri amma sai dai ƙafafunta sunyi tsami dan haka ta faɗi...taune leɓenta tayi kafin ta sake tashi tana ɗingishi ta bar wurin da hawaye a idonta... Tunda na tsaya wurin nake jin ido na yawo ajikina ɗagowa nayi idona ya sauka a cikin na Mukhtar dake kallona kamar tsohon maye...nake ji kamar in zube mashi plate ɗin inibin nan a jiki...amma ba dama... '' wannan yarinyar is too flat..dalla sai wani kallonta kake...bata da gaba bare baya...can you not disgrace us pls!" Seraphina ce tayi maganar kowa dake wurin suka kwashe da dariya...jikina ya fara rawa dan Nasan dani take...duka mazan suka juyo suna ƙare min kallo..da farko Mukhtar kaɗai ne...... A zahiri hankalina kwance yake..amma a baɗini ni kaɗai Nasan yanda nake ji... Jameelah tace'' da gaskiyar ki fa Sera...I wonder idan tayi aure mai mijinta zai taɓa yaji laushi...'' suka sake dariya...sauran yan aikin kuwa kansu na ƙasa bansan meye tunanin suba... '' come on, don't be dirty minded ...'' Ayaan ne yayi maganar yana latsa wayarshi '' na yarda she's flat like board...amma gray eyes ɗin nan..Are a big turn on don't you think?" Imam ya furta '' ka rigani furtawa ne ɗan uwa...'' suka kashe shida Mukhtar kamar mata... '' Awwn...kuka take fa...da alama kun tsallake iya ka!" Kareema ce ta faɗi hakan da nuna tausayin ƙarya... Ashe kuka nake? Ni ban ma sani ba sai da tayi maganar naga hawaye na sauka akan hannu na... '' yanzu ma ta fara..badai tana da baki ba? Bakin zai mutu kafin tabar gidan nan...haka wannan shegiyar yarinyar itama a da baso tayi ta botsare ba...yanzu ta isa ko kallon mu cikin ido tayi?" Cewar Mufeedah Haka suka cigaba da ci min mutunci...naji duniyar tayi min zafi...na wulaƙanta...raina har ɗaci yake...da ɗaya da ɗaya suka bar wurin," ki tabbatar a koda yaushe kina dining...safe,rana da dare...'' Seraphina dake ƙarshen fita ta faɗa... sauran ma'aikatan suka shiga gyara wurin... Aina'u ta matso kusa ta rungume ni tana bani haƙuri... ...da ƙarfe huɗu na koma sashen mu Mama Asabe tayi min nasiha da kuma nuna min illar biye musu '' yanzu dukansu zasu iya targeting ɗinki su dinga bullying ɗinki ... ki kiyaye kinji?" Kaina kawai na jinjina hawaye na rige rigen sauka a fuskata... Wurin ƙarfe biyar muka sake komawa bakin aiki,ɗakin Seraphina aka turani wai tana nema na... Batareda wani shayi ba na isa ɗakin da ya tsaru sosai...samun ta nayi kwance saman gado da bumshort da half cut... Baƙin gashinta ta raba shi gida biyu ya sauko har zuwa kafaɗarta...fararen ƙafafunta sun sha nail polish ita kanta yarinyar kyakkyawa ce daka ganta kaga jinin larabawa...in banda zuciyarta da take mummuna bata da aibu... '' Gani Madam Saratena...'' zabura tayi ta xauna dan kawai na kira ta da saratena..'' me kika kirani?" '' Madam Saratena!" Na maimaita badan ban iya kiran sunan ba sai dai dan hakan naga damar kiranta '' witch,sunana Seraphina ba Saratena ba...'' duk da ta gyara min yi nayi kamar baxan iya kiran sunan ba nacigaba da ɓatawa '' Oh my God! You know what..ki kira ni da Sarah!" Ta faɗa da ihu kamar zata dake ni '' toh Madam Sanah...'' da takaici ta nunamin bayenta...'' akwai kayan dana jiƙa a ciki...kije ki wanke...'' Bayen na wuce batareda nace komai ba..ta saki murmushin gefen baki...ban fahimci ma'anar hakan ba Saida na shiga na iske pants ɗin tane datayi jinin al'ada dasu suka gama ɓaci ta jiƙa na tsawon lokaci har sun fara wani arnen wari take so in wanke...ji nayi kamar zanyi amai '' kuma ki tabbatar sun fita bana son naga stain..'' ta faɗa daga waje like an absolute witch... Hijabina na cire na ɗaure hancina na shiga wanke wa amma duk yanda nayi ƙoƙarin ganin na wanke su da kyau sunƙi fita...daga ƙarshe na tsantsame su..na gyara bayen na fesa air freshener duk zufa ta wanke ni.tana gani na ta sheƙe da dariya harda riƙe ciki ..haushi yasa banyi wata wata ba na juye mata wankakkun pants ɗin a fuska.... '' Oh my Goooood...witch!!!" Ta saki ihu tana hankaɗe pants ɗin daga jikinta da ƙyanƙyami...dama can warin bai fita ba '' ewwww!!!!!!!"... +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17🍁🍁 22. ...Farzan...🖊️ Yawu na haɗiye ganin yanda Seraphina ke ihu kamar mahaukaciya...sai kuma ta miƙe tayo kaina tana huci...ja baya nayi da zufa tsakanin cinyoyi na,ƙafafuna sunyi sanyi...Fuskarta tayi ja da alamu idan ta cimman mari zan sha... Abu guda ne ke yawo a kaina a wannan lokaci...sakin bokitin dake hannu na nayi tare da sakin ihu na riƙe kaina....na jujjuyar da idona...gray ɗin ciki ya ɓace duka farin kawai ake gani...na cigaba da ihu ina jujjuya kai ina gurnani... Tsayawa Seraphina tayi ido waje tsoro ya bayyana a fuskarta...ƙirjinta ya fara sama da ƙasa....wani irin juyowa nayi inda take da ƙarfi kamar zombie na saki murmushin daba murmushi ba...irin wanda kesa mutum ya tsorata '' Oh... SERAPHINA....'' na fara matsota ina tafiya a murɗe kuma har lokacin idona basu koma daidai ba Ja baya ta shiga yi tana kalle kalle... na tabbata a wannan lokacin jinin ta ya hau kamar yanda jinin mutum zai hau idan yana kallon fim ɗin horor... '' s...stay ..'' kasa Magana tayi sai ihu data saki ta faɗa Baye ta rufe da mukulli.. da sauri na isa wurin ina buga ƙofar da ƙarfi ina kiran sunanta da Muryar tsoro..daga ciki take kiran innarta ta ceceta.... Ganin nayi nasarar ceton kaina,kada in cigaba da acting ta gano ƙarya ne in shiga uku yasa nabar pants ɗin nan na fita daga ɗakin a guje kamar wacce ke gudu daga abin tsoro...gaban wata ƙofa Ash na tsaya a ƙarshen hallway ɗin na fashe da dariya tuna yanda fuskarta ta kasance a wancan lokacin... dena dariyar na juyo ina kallon ƙatuwar ƙofar...kamar wani abu daga ciki na kira na ... meyasa wannan kaɗaice ƙofar da kalar ta yake daban da sauran ƙofofin? A maimakon numba, XXXX ukune rubuce a sama...matsawa nayi kamar wadda aka asirce na ɗaura tafin hannu na a sama ido waje baki sake..har zan tura ƙofar '' Wacece ke?" Firgita nayi na juyo da ƙarfi..ƙafata ta gurɗe na faɗi ƙasa zuciya tana tsananin bugu...kallon wanda ke gabana nayi..dogon gaye ne fari tass,sumar kanshi ja yana da ember eyes kamar na vampire,ga lips piercing da yan kunne da fuskar rashin mutunci...idonshi kamar na shaho,akwai wani tabo tsakanin girar shi...Muryar shi kamar ƙanzo...damtsen shi duk ya zane da tattoo yana ƙare min kallo... Rasa murya ta nayi...nake haɗiyar yawu'' mage ta cinye harshen kine?" Ya haɗe gira da irin kallon da yake min Nasan bai sona ko kaɗan,nayi mamakin hausa a bakin shin kamar jakin kano..da yake dai ɗan kano'n ne '' Uhmm... yar aiki ce Ni...UHM...zanyi aiki ne...'' ɗage gira yayi,idon shi a nawa,na haɗiye yawu ganin ya mayarda kallon shi a ƙofar na fara rarrafe zan bar wurin '' nace ki tafi ne?" Ya tambaya da daga murya...da sauri na zauna wurin ina matsa ƙafata...'' gwadawa nake in gani ko ƙafata lafiyar ta lau...kwanakin baya na faɗo daga bishiya...'' riƙe numfashina nayi da irin kallon da yake min..sai yayi ƙwafa yabar wurin... Ajiyar zuciya na sauke na miƙe tsaye da sauri na kama gabana...ina mamakin meye bayan wannan ƙatuwar ƙofar? sanda na shiga sashen mu ƙarfe shida da rabi,duka sauran ma'aikatan sun dawo harda su Fauziyya... wuri na samu a nan parlor na zauna ina tunanin waccan ƙofar..ina so in San meye a baya.. '' Sir Farzan ya dawo fake Fauxeey!" Rasheedah ta zauna kusa da Fauziyya dake latsa wayarta tana cin cingum ƙaras ƙaras...da yawa daga cikin ma'aikatan suka ɗago '' dan Allah?" Duk da badasu take ba suka tambaya suna dafe ƙirji ido waje '' sosai ma,ƙarya zan maku ne?"...girgiza kansu sukayi kafin suka cigaba da hira akan sauran biyun da zasu dawo ranar Monday..wanda Allah ya gani bana farin ciki da dawowarsu koma su waye su.... Aina'u da Waleeda suka zauna kusa dani muna yar hirar mu..duk da bamu san juna sosai ba,amma ai tare muka zoko? '' da yake Allah yasa ni ranar Monday makaranta zani...aikina zai ragu!" Na faɗa da jin sanyi a raina,zanje inga su Asma'u da Jay d...naga nawar Monday tazo '' wasu basa son aiki sai kawai son banza da kuma a biya su...hmm ba haka abubuwa ke faruwa anan gidan bafa...dole mutum yayi aiki ehe!" Fauziyya ce tayi maganar kuma nasan dani take '' kema dai kya faɗa,tun kafin aje ko ina,yar wata har tafara gajiya....'' Amrah ta goya mata baya.. dama naga alamun itama yarinyar wani kallo kallo take min sannan itace tasa min uniform a hannu batareda tayi min bayani ba... '' ɗazu ba kunan da kunga yanda Madam Seraphina da sauran yan uwanta suka ci mata mutunci...wai harda kiranta flat board...da gaskiyar sufa amma!" Dukan su dariya suka sa dajin abinda Habeeba ta faɗa...idona suka fara ƙaiƙayi hawaye suka taru ciki... Aina'u da Waleeda suka dafa hannu na alamun tausasawa... Koda basu tausashe niba ai dole in tausashi kaina... da gaskiyar su,ko acikin masu aikin bayan waleeda tunda ita ƙarama ce,nice wacce gaba ɗaya bata da shape kuma take da fuska mai pimples dayawa.... Tashi nayi na nufi ɗakin mu daga bayana ina jin yanda suke dariya suna shewa..suna ƙara kirana da sunayen cin mutunci... Rufe ƙofar nayi na faɗi zaune a baya na fashe da kuka mai cin rai...har Saida kaina ya fara ciwo..jin kiran Sallah na miƙe na isa bakin taga na kware labule da jajayen idona ina kallon tsakiyar gidan ba kowa...rana har ta faɗi..haske mai ɗan duhu ya sauka irin na maghrib sai bishiyoyin dake nan da can saboda iska dake kaɗa su...ji nake kamar ana matse min zuciya ta,kamar an ɗaura min abu mai nauyi... Barin bakin tagar nayi na shiga Baye nayi alwala nazo nayi sallah...can anjima kaɗan Mama Asabe ta shigo ɗakin takalli fuskata...da farko batace komai ba sai data gama sallah sannan ta juyo sashen da nake zaune ta tambaye ni mai ya faru...da naso in ɓoye mata,ban sani ba ko saboda yanda tayi tambayar a tausashe ne yasa na faɗa mata komai batare da na ɓoye yanda nake ji a duk sanda na kalli kaina ba ko idan aka yi magana akan yanda nake... Ta lallashe ni tare da faɗin zata taimaka min... murmushi kawai nayi..naji wa'yannan kalmomin fiye da a ƙirga daga ƙarshe babu abinda ke canjawa... Bayan Sallar Isha'i kamar yanda Seraphina tace ina tsaye sanda suke cin abincin su na dare...every now and then sai ance in miƙo wannan ko wancan...idan nayi ha daidai ba nasha faɗa... sauran ma'aikatan kawai suka zama by standers babu wanda ke wani abu sai Ni '' duh! Ke baki iya yin abu daidai ne?" Heedayah tayi maganar tana harara ta...naso in mayar mata da baƙar magana sai kawai nayi shiru..na ɗauki abinda take so ɗin na miƙa mata...take huci kamar tunkiya... '' ke miƙo min sushi...'' Mukhtar ne ya faɗi hakan yana min wani banzan kallo...na gama kalle table ɗin Ni banga wani abu ba can wai shi shi..'' ban san Shiba...SIR!" Na faɗa da takaicin kallon shi da baya ƙarewa Ayaan ne ya nuna min tsushi ɗin...abin yaban ƙazanta...dole sai dana zagaya na ɗauko tsushi ɗin nazo inda yake na miƙa mashi...amma sai cewa yayi in zuba mashi,na tsaya ta bayan shi ina tsaka da zubawa ya kwanto da kanshi ya gogi ƙirjina...zabura nayi badan nayi niyar hakan ba,tsushi ɗin dake hannu na ya zube mashi a jiki... '' Ahhh!!!" Ya saki ihu dan abin nada zafi... '' subhanallahi!!" Naja baya...mutan gidan kuwa suka hau yimashi sannu kafin lokaci guda manyan su da ƙananan su suka yimin caaa suna zagina ta uwa ta uba..naji kamar zuciya ta zata fashe... Damƙo hannu na Mukhtar yayi ya miƙe ya ware faffaɗan tafin hannun shi zai zabga min mari,na tsorata iya tsorata musamman dana san babu wanda zai taimake ni,wasu daga cikin tsofaffin ma'aikatan na basu tausayi..banda Fauziyya da take ji kamar ta zuba ruwa ƙasa ta sha... Runtse idona nayi hawaye na silalowa na sadaukar...sukuma sauran mutanen gani suke hakan daidai ne...jin marin bai sauka ba yasa na buɗe idona ɗaya bayan ɗaya...gayen nan dana haɗu dashi a wurin ƙofar nan ne... '' Ah,ya Farzan!!?" Kusan yan mata da samarin dake zaune a table ɗin suka kira da mamaki a muryoyinsu...sauke ma Mukhtar hannun shi yayi...sannan ya warware ɗayan hannun dake riƙe da nawa '' can you not be such an embarrassment?!" Ya ture Mukhtar...ya kalle ni,nayi ƙasa da kaina... Dunƙule hannun shi Mukhtar yayi yabar dining ɗin bayan ya jefa min kallon daya sa zuciya ta tsalle ta faɗa cikin cikina.. Wurin Hajjo ya isa ya gaisheta ta hanyar sumbatar goshinta '' ja'irin yaro,ai ban san ka tuna dani ba!" '' taya zan manta da tsohuwar nan mai yawan takuramin...'' wannan maganar da yayi ta dawo da peaceful atmosphere a dining ɗin...sauran suka shiga gaishe shi... Ya kalli Hajiya Hafsa Maman shi kenan ya sakar mata murmushi...gyaɗa kanta tayi da basarwa...ya gaishe da sauran Manyan dake table ɗin...Alhaji Hussein ya kalli yaron nashi da alfahari.. Fauziyya na kalla naga tana harara ta kamar zata kama da wuta,share hawaye na nayi nakasa motsi... Daga ƙarshe na tattaro ƙwarin guiwan da yayi min saura na ɗauki izini nabar wurin ban koma ɗaki ba,na tafi 5th floor bayan nayi amfani da katin ma'aikata daban daɗe da karɓa ba, ...sashe huɗu ne a wurin akwai wurin motsa jiki, swimming pool da barbecue da kuma wani abun da ban sani ba kamar asibiti...daga ƙarshe ƙarshe naga lambu da sauri na isa wurin na ɓoye tsakanin shuke shuken dake wurin da aka haskaka da yellow lights..na zauna ƙasa na sha kuka sosai... Bayan na gama nake zagaye wurin dayake ɗauke da fulawowi masu kyau..daga roses,lilies,sun flowers...tulips,da sauran su,harda wasu baƙaƙen roses na gani...ban taɓa sanin akwai ba...ko waye dasu? Saman wurin glass ne ana hango sama...na ɗaga kaina ina kallon taurari da makeken watan da suka fito...inama ace nima tauraruwa ce... Na daɗe wurin kafin na fito na nufi first floor kafin elevator ta rufe Mukhtar ya faɗo ciki... directly wurina yayo ya jawo ni da ƙarfi ya rungume... Innalillahi wa inna ilaihi raji'una...Ni Abeedatu na shiga tashin hankalin daban taɓa shiga irin shiba na kasa ƙwatar kaina..kuma sai ƙoƙarin zura hannun shi yake cikin riga ta yana faɗin '' sauran masu aikin abinda ake dasu kenan..kawai ki bada haɗin kai...'' Da ace hawaye na ƙarewa da nawa sun ƙare a wannan rana inata roƙonshi amma ko saurarena bai yiba... Har yayi sa'a wurin shafar cikina elevator ta kawo ƙasa ta buɗe,banyi wata wata ba na gantsara mashi cizo a kunne na kwasa da gudu na barshi da kururuwa... A guje na iso sashen mu,samun dayawa nayi cikin su zaune suna kallo... Fauziyya ta sha gabana hakan ya tsayar da guduna... ''.ke dan uw...'' hankaɗe ta nayi na haye sama da sauri dan gani nake kamar zai biyo ni..ɓoyewa nayi cikin bargo jikina na tsananin rawa...hawayen sun dena zuba sai tsoron daya rage a zuciya ta... Idona biyu har ƙarfe biyun dare bayan kowa yayi bacci..a wannan gaɓar tsoro ya gama kashe min jiki..dan duk sanda na rufe idona abinda yayi min kawai nake mafalki... Da safe da ƙarfe huɗu na tashi ban samu damar yin Bacci sosai ba amma kuma ban gaji ba ... Bayan nayi nafila nayi zaune wurin ina gudun abinda zaije ya dawo... Amma ga mamakina, normal akayi break fast yau babu wanda ya faɗa min wani abun cin mutunci sannan Mukhtar bai ko kalli sashen da nake zaune ba... Da ƙarfe tara aka tara mu duka yan aiki..aka rarraba mana ayukkan gyara gida wasu daga yan gidan zasu dawo daga tafiya... Wani ƙaton hall mu goma akayi assigning da gyarawa ciki harda Fauziyya da muƙarabanta sai harara ta suke..amma ni basu gabana Aiki muka shiga yina share wurin kuma fa ƙal wurin yake..bayan mun gama muka goge tagogi da kuma mopping ƙasar wurin sannan muka dinga jido kujeru muna ajiye wa a wurin..irin kujerun yan gayu da table Dukan mu muka yi kwance Rashe rashe a gaban wurin bayan mun gama aikin duka '' gaskiya naji daɗin wannan aikin duk da akwai gajiya...'' Aina'u ta faɗa tana Juyowa sashen da nake... '' nima,kamar kada mu gama..duk da wayan'can mugayen mutanen!" Fadeelah ɗaya daga cikin tsofaffin masu aikin kenan.. '' sauran ko wane aiki aka haɗasu dashi?"Nake mamaki Muna tsaka da hirar mu Fauziyya ta iso inda muke ba zato ba tsammani naji an jiƙe ni da ruwa...kafin ta finciko ni... '' ke dan ubanki jiya ina...'' ''.badai ubana ba sai naki!" Na katse tada takaicin zagin da take min...ƙawayenta sukayo gaba suka tarar min su uku suna bugu na...su Aina'u suka shigar min wurin ya kacame da faɗa.. sai hankaɗe kujeru muke '' Iyyeh!!!!" Malama Amina shugar Madam Aatika ta riƙe baki tare da gwalalo ido tana kallon mu...da sauri muka rabu kowa na huci... Da tsantsar ɓacin rai take tambayar mai ya faru...ba ɓata lokaci Mariya ɗaya daga cikin waya'nda basu yi faɗa ba ta faɗi abinda ya faru... '' ku bani katin ku na yan aiki.. '' tayi maganar a kausashe ba damar musu muka miƙa mata..muda bamu daɗe da karɓar namu ba gashi mun rasa Tunda party ɗin su Fauziyya ne masu laifi nasu katin sai nan da sati biyu mu kuma namu zamu karɓa bayan sati ɗaya...kafin nan ƙafafun mu sun gama karyewa da hawan stairs ... Sake gyara wurin mukayi kowa na hararar kowa Fauziyya tace '' zamu sake haɗuwa...'' ɗage kafaɗuna nayi a yanayin ko in kula...bayan mun rabu ina tsaka da tafiya a 4th floor naci karo da Mukhtar... murmushin mugunta ya sakar min...nake kallon shi ido waje kafin na juya da gudu shima biye dani.... Ban san inda nake sa ƙafa ba kuma ban san tsawon yaushe na ɗauka ina gudu a dogon hallway ba bayan na dinga tsallake stairs da biyu biyu sai jinayi na shige jikin mutum... Riƙe kafaɗuna yayi ya jani baya... fuskarshi a haɗe...Farzan ne...ina haki nace '' excercise nake!" bana tunanin akwai amfanin faɗin dalilin gudu na shine yasa na faɗi hakan... '' biyo ni...'' ya sake ni tare da yin gaba...babu yanda na iya dole na bishi ɗin..koba komai a idona kasancewa dashi yafi kasancewa da wannan mugun Mukhtar ɗin ko? Maimakon mu shiga elevator gani nayi munbi ta stairs...zaro ido nayi '' yallaɓai ba elevator zamu shiga ba?" '' ba excercise kike ba?" iska na haɗe ido waje...daga first floor har fifth floor muka kai da ƙafa.. sai kuma muka sake juyowa...duk na gaji ƙafafuna kamar ana sare min su...bayan mun kawo first floor muka sake komawa fifth floor sai dana roƙe shi sannan yabar ni zaune a cikin fulawowi yayi tafiyarshi.... '' Mugu...'' +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 23. ... Kitten...🖊️ Washegari Lahadi,da sassafe Mama Asabe ta kawo min wani haɗin da ban san ko a ina ta samu ba, Karɓa nayi na shanye koba komai meye ciki? Yau gaba ɗaya ma'aikata kamar jiya muka haɗu muna aiki kamar ba gobe. wani sashe mai ɗakuna uku da ya tsaru ya gaji da tsaruwa aka buɗe,kusan mu dayawa aka tura wurin gyara shi,bayan ko mutum ɗaya ya isa ya gyara ɗakin ya goge... A kitchen ma'aikatan sai gudu suke nan da can kamar kaji..su Seraphina da yan uwanta aka kwasa aka tafi wurin gyaran jiki hakan ya cecemu daga matsalolin su...wurin ƙarfe sha biyu wata mata mai jiki ta iso da wasu yan mata uku masu shegen jiji da kai,kowace fuska ta babbake tsabar bleaching...sai girman kai da ɗagawa...ashe ƙanwarsu Alhaji ce Hajiya safara'u da ake kira Hajiya Momma... Parlor ta zauna tarin ma'aikata suka yi kanta wasu na mata tausa,wasu suna cika gabanta da abun ci da abun sha amma sai ashar take ɗura masu...yan matan nan suma suka fara bada oda nan da can... nikam ɓoyewa nayi daga ganin su dan bana son raini... Gidan ya ƙara duhu bawai duhu na duhu da haske ba...duhun yanayi dan ni wa'yannan mutanen kallon matsala nake musu...sai data gama ci ta ƙoshi sannan ita da ya'yan ta suka haura sama...oh ashe kowacce cikin su tana da ɗaki a gidan... Kitchen na wuce ɗaya daga cikin ma'aikatan ya kirani,plate ya nuna min dake ɗauke da kayan ciye ciye na gida Nigeria da ƙasar waje yace in kai 3rd floor wanda shine ɓangaren Alhazozan da matayensu....wannan shine karo na farko da zan tafi wurin... Ɗaukar plate ɗin nayi nabi stairs fuska ba walwala..kusan stairs talatin da shida na taka kafin in iso makeken parlorn daya haɗu ya gama haɗuwa...komai na wurin golden ne harda kujerun,da labulayen...sai carpet ɗin daya kasance ja...daga tsakiya akwai ƙaramin table..sai TV... dispenser daga can gefe,da flowers da aka jera saman wani shafaffen faranti cike da ƙasa...wurin ya game da ƙamshin turarukan su da kuma air freshener... samun matan gidan nayi zaune suna hira kowa cikin shigar alfarma harda hajiya Momma dabata daɗe da zuwa ba... gaishe su nayi na ajiye abinda ke hannu na sun amsa gaisuwar ko akasin hakan? Ban sani ba... Nake jin idonsu na yawo a kaina ba dalili..ɗagowa nayi idona ya shige cikin na Hajiya Momma ta dafe ƙirji harda zabura ta zaro ƙananan idonta '' Innalillahi wa inna ilaihi raji'una...harda Mayu kuka koma ɗauka a matsayin masu aiki Ruqayyah? Duba min idon yarinyar nan...'' ƙara kafe ni sukayi da kaifafan idonsu nikam na rasa abunyi ko in tsuguna ko in tashi... '' Ba mayya bace Ni,haka idona suke...'' '' ƙarya kike..idan ke ba mayya bace contact lenses kike sawa kenan?" Kowa ya kafe ni da ido and I felt so helpless...daga cikin matan akwai wani kallo na musamman mai cike da tsana da nake ji har cikin ƙasusuwana da yasa gashin jikina miƙewa...na rasa sanin ko daga ina wannan kallon ke zuwa Ƙatuwar matar ta tashi ta damƙo hannuna ''buɗe min idon in duba da kyau in gani''...inji Hajiya Momma tana ƙoƙarin tale min ido ta tsoma hannu ciki...na shiga uku ni Abeedah..kuma babu ɗaya daga cikin mutanen wurin dake ƙoƙarin hanata...su wa'yannan mutanen ata yin abun mugunta gaban su babu mai hanawa dan basu ake yimawa ba... '' wallah...'' '' yimin shiru...'' ture ni ƙasa tayi ta zaune min ƙafafu ta riƙe hannayena..jajayen idonta abun tsoro..naji wasu daga cikin matan sun kwashe da dariya...abinda nayi ma Seraphina na sake maimaitawa Wannan harda cizonta nayi...da alamu sauran matan sun tsorata dan tashi sukayi daga inda suke zaune suka maƙe wuri guda jikinsu na rawa... Na dinga sakin ihu ina shille shille,na jefar da hijabina ina ɗage riga kamar zan cire itama na samu na canja muryata zuwa ta abun tsoro convincingly baiwar da ban san ina da ita ba...sai wannan lokacin Hajiya Momma tasha yagalgala daga gare ni...matar sai ihu take...Farzan ne ya shigo wurin ganina zaune saman ƙatuwar matar Hajiya Momma tace'' Farzanu ka taimake ni...'' taban dariya sosai...zuwa yayi ya ɗage ni ya fitardani daga parlorn muka shiga elevator tare...naso in cigaba da acting ɗina, fahimtar ya gano ni yasa na dawo daidai,ina rungume hannayena a ƙirji kafin ya tambaya na shiga mashi bayani da fuskar tausayi '' wai cewa tayi ni mayyace kuma so take ta tsiyayar min da ido...'' na gwalalo ido ina nuna mashi ƙwayar ciki da take dark gray... ɗauke idonshi yayi '' and you decided to turn into a maniac huh? You are more dangerous than you seem" gumi naji ya ɗan tsatstsafo min..na fahimci abinda ya faɗa amma ban san me yake nufi da..Uhmm.. 🍁: Maniac Ban san meyake nufi da maniac ba...amma sai na waske kada ya fahimci ban sani ba... '' Next time xan barki kisha duka ne,who knows nan gaba your gray eyes will have silver in them and that's it! You're a witch!"zaro ido nayi jin abinda ya faɗa wai zan koma mayya '' gashinki ma zai koma gray,at least a cikin littafai haka kamannin witches suke...'' da sauri na shafa kaina da hular ta faɗi,naji kunya ta kamani,na ɗago ido na slow naga ni yake kallo fuska a ɗinke gyaɗa kaina nayi kamar ƙadangare elevator ta buɗe a second floor..yai tafiyarshi nima na juya ina tafiya jiki a sanyaye..na kawo wurin wani ɗaki zan sha kwana naji an hankaɗa ni ciki an rufe ƙofar daga waje...duk yanda nake bubbuga ƙofar anƙi a buɗe '' shegiya nan ciki zaki mutu!" Muryar Fauziyya ce ba kuskure... cigaba da buga ƙofar nayi tsoro na kama ni...ɗakin babu ko ɗigon haske kuma babu taga bare iska ya shigo..kenan babu oxygen..idan babu oxygen mutuwa zanyi... Cigaba da buga ƙofar nayi numfashi ya fara min wahalar ja...ga uban zafi ga tarin ƙura..faɗuwa ƙasa nayi ina cigaba da buga ƙofar...na ɗauka mutuwa zanyi...idona sun fara rufewa naga an buɗe ƙofar wata yarinya da ban taɓa gani a gidan ba duk da buji buji nake ganin ta...ta shigo tana kiran sunana 04:00 Buɗe idona nayi na ganni a sashen mu Mama Asabe tayo kaina tana shafa goshina '' kin tashi?" Gyaɗa kaina nayi na tashi zaune...'' sannu kawo ki akayi wai kin suma...'' '' Fauziyya ta rufe ni a wani ɗaki mai duhu,ba wai na ganta bane amma naji muryarta tana faɗin in mutu...'' Mama Asabe ta kalleni da damuwa...'' dole mu faɗawa Madam..'' na jinjina kai ina tunani ai Fauziyya bata tsoron Madam Aatika sai da nayi sallah ina zaune aka kira Ni wai Madam na ƙasa tana jira...tashi nayi na tafi ƙasa ɗin na samu duk sauran ma'aikatan suma suna nan harda Fauziyya However ba Madam Aatika bace, Madam Amina.. Bayan na gaisheta ta tambaye ni meya faru? Ido na haɗa da Fauziyya take min alamun idan har na kira sunan ta zata kashe ni...ɗauke idona nayi daga kallonta Badan ina jin tsoronta ba na faɗi abinda ya faru amma ban kira sunan ta ba tunda bani da tabbaci... Madam Amina ta haye mu da faɗa tana ƙara gargaɗin mu akan irin wannan halayen...daga ƙarshe tace gobe kafin in tafi makaranta in haɗu da ita ..na jinjina kaina sannan ta tafi Zan koma sama Fauziyya ta biyoni '' kin yima kan ki adalci da baki kira sunana ba..'' Kallon ta nayi nace ''.idan kina tunanin tsoron ki ake...well,ke ce mafi yaudarar kai a gidan nan!'' Ɗage kafaɗa tayi baki kyaɓe tace '' kuma ina shawartar kida ki rabu da sir Farzan! Duk inda kika ganshi ki kauce daga wurin kin jini ko?" ta damƙi cinyar hannu na riƙo bana wasa ba..toni ina ruwana dashi? Cike da haushi na gatsa mata cizo kamar vampire ban sake cewa komai ba na barta da yarfin hannu... A ƙasan raina nake tunanin ko wace mai mutunci ce a gidan ta taimake ni? oho... Da daddare bayan na gama duk ayukkan daya dace nayi na sake hawa har 5th floor cikin lambu na shiga na tsaya daga gaban wurin ina kallon sama..duk da kuwa ance kada mu dinga yawo yau ba taurari saboda hadari daya taru... naji ina nishaɗi dana tuna gobe zan fita daga gidan nan a karo na farko tunda nazo...zama a gidan nan is quite suffocating babu wanda zai san da hakan sai wanda yake a ciki... Da ƙarfe goma lokacin aikin mu ya ƙare na sauko zan tafi sashen mu...na haɗu da Waleeda tayi min murmushi isa wurinta nayi ta riƙo hannuna muna tafiya tare muna hira '' da ace mutum zai iya rubuta ƙaddarar shi,da ban kasance a nan ba...'' ta faɗa min '' wata rana zamu girmi duk wannan ba zamu bautama wasu ba,sai dai a bauta mana!'' farin ciki nagani a fuskar ta sosai bayan nayi wannan maganar tace '' tunda kin faɗa...zan fara addu'a akan hakan...ada na ɗauka hakan kawai zai faru dani a mafalki duba da yanda rayuwata take lilo...you gave me hope...na gode..'' Jinjina kaina nayi ta rungume ni kafin mukayiwa juna sai da safe muka wuce ɗakunan mu Dana shiga ɗakin mu har Mama Asabe tayi bacci banda Hansa'u dake danna waya... gado na haye na rufa badaɗewa ba aka tsuge da ruwa '' ashe ni ake jira in ɗaura kaina a matashi...'' nayi murmushi da wannan tunanin... Da safe kamar jiya haka Mama Asabe ta sake bani irin wancan abun,naso inƙi sha tace ai yana ciko mace ya gyara ta...naji kamar inyi dariya amma bana so in ɓata mata ƙoƙari yasa na shanye abun...na miƙe na shirya cikin uniforms ɗina da suke a goge amma fa sun tsufa..ban damu ba dai .. Hula nasa ruwan toka,na shafa kwalli da turare mai daɗin ƙamshi...jakar leda ta na ɗauko ina duba komai da komai akwai a ciki... Duk da Nasan ba kowa bane zai dawo ranar da aka dawo duk da haka na kasa haƙura da tafiya wannan ranar...kawai ina so in bar gidan nan ne...waya tana ɗauko na kira gida bayan mun gaisa na faɗa ma su Asma'u suzo makaranta... Tare muka fito da Mama Asabe muka karya da sauran masu aiki a dining da babu abinda suke magana akai sai dawowar biyun nan a yau, cikin hirar tasu naji ana cewa ɗaya daga cikin biyun ɗan Italy ne..ko kaɗan banji ina so in ga suwaye ba... Kafin a gama breakfast ɗin nasha harara da baƙaƙen maganganu a kaikace amma ɗokin zuwa makaranta ya hanani jin baƙin ciki...sai ma nake mayar musu da maganganu masu kyau maimakon biye masu taɓaci... '' ke Abeedahtu ashe bakya sign-in..hakan zai iya zama matsala fa...'' Mama Asabe ta nuna min littafin ko sau ɗaya ban taɓa sign in ba ko sign out na manta duka '' zan kiyaye...'' na faɗa sannan nayi sign in na yau kafin na fito saye da hijabi daban dana makaranta.... Kitchen na tafi dani da wasu ma'aikatan muka shirya abinci a dining...koda yan gidan suka hallaro har mun gama...duk wanda yazo sai mun risina mun gaishe shi..saɓanin koda yaushe da nake jin haushin hakan yau harda murmushi..babu abinda ya dameni kawai ayi a gama in tafi makaranta... Harda hajiya Momma tazo...muna haɗa ido ta Harare ni da jajayen idonta murmushi nayi na sadda kai...yau hirar su ta ta'allaƙa akan mutane biyun da zasu dawo,yan matan kowa ka kalla zakaga fuskokinsu ɗauke da annuri nake mamakin waye wa'yannan? Kuma wane muƙami suke dashi a gidan da kowa ke maganar su..duk da samarin basa ɗoki kamar sauran.... Yau munci sa'a mu yan aiki cin mutuncin da aka saba yimana ya ragu sosai... Farzan ne na ƙarshen zama ya gaishe da manyan fuskar shi ba annuri dama kuma ba wani fara'a ne dashi ba..ban taɓa ganin yayi murmushi ko dariya ba.... Nayi nisa cikin tunani naji ance '' ke!" A firgice na kalli Khaleesat dake harara ta '' baki ji ana magana bane ko kin kurmance?" '' ai tunda tasa wa'yannan koɗaɗɗin kayan take jin kanta ya ƙara girma...aikin banza!" Jameelah ce tayi maganar tana harara ta '' dalla miƙo min ketch up!" Ɗaukar ketchup ɗin nayi na miƙa mata '' oh ni zan zuba kenan?" Danne takaicina nayi na buɗe abun na fara zubawa..sai ihu take min..bana son ɓata ranar farkon komawa makaranta yasa naja dogon numfashi bance komai ba '' Hajiya Momma meya faru da hannun ki haka?" Ayaan ya tambaya yana bin hannun ta da kallo '' wannan shegiyar yarinyar ce ta kusa illata Ni..'' ta nuna ni da mamaki kowa yake kallona Gabana ya faɗi idan fa aka Kore Ni? '' the girl is dangerous...ya kamata a kula da irin masu aikin da ake ɗaukowa!" Alhaji Sulaiman ne ya faɗi hakan... Itama Seraphina ta faɗi abinda nayi mata..kowa yayi min caaa! '' ayi haƙuri Madam bada gangan bane hakan bazai sake ba...'' '' matsiyaciya ai haka zaki faɗa...'' ji nayi idona sun fara ƙaiƙayi..na taune leɓena amma na kasa haƙura '' ka kuwa san abinda ake nufi da hakan?" Na kalli Arman da yayi maganar ido cikin ido...kusan pausing sukayi da abincin dake gaban su '' tsiya ba shine kasancewar mutum talaka ba,tsiya shine rashin wadatar zuci...rashin sanin darajar ɗan Adam! Dan kawai Allah ya baku kuɗi mu kuma ya ajiye mu a ƙarƙashin ku,ba finmu kuka yiba! Ba kuma dabarar kubace ta sa ya baku!'' '' wannan yarinyar ta cika shegen ji da kai da girman kai! Wai meyasa baza'a kore taba?" Hajiya Momma ta faɗa Mufeedah tace'' yarinyar da alamu mayyace ta cinye mu ta lashe shine yasa!" Ranar dai nasha faɗa da ɓacin rai nabar gidan bayan na haɗu da Madam Amina ta tura ni makaranta da wani daga cikin ma'aikatan gidan don a biya kuɗin makarantar mu...da alamu na samu advance payment ... Bayan mun isa makaranta mutumin ya biya kuɗin aka bani receipt guda uku,nawa, Asma'u da Anaam...nayi farin ciki sosai Nayi mashi godiya da muka fito filin makarantar kuɗi ya ciro daga aljihun yace idan an tashi in hawo abin hawa in dawo gida sannan ya tafi.... Makarantar na kalla hakukuwa da ciyayi sun girma sunyi tsawo... ganyayyakin bishiyoyi sun bushe sun faɗo... Murmushi nayi na isa wurin ƙaraurawa na buga ina dariya... mutane tsirara ne a makarantar ajin mu na wuce ba kowa... Zama nayi bakin taga bada daɗewa ba mutane suka taru....muka zauna muna hirar yaushe gamo kafin assembly prefect ta buga ƙaraurawa muka taru a assembly ground...inata kallon inda zan gasu Asma'u...kuma yan SS 3 ne kawai hutun su ya ƙare... Muhimman abubuwan daya kamata mu sani suka faɗa mana kafin suka samu kwasar desk daga office ɗin principal zuwa ajujuwan da zamu zana jarabawa ciki... Wurin ƙarfe goma duk yanayi na ya canja na fidda rai daga zuwan su Asma'u naji an rufe min ido daga baya...kafin in juyo ƙamshinta ya sanar dani wacece...Jay D Juyowa nayi tareda sakin ihu na rungumeta...itama ta ƙanƙame ni....'' wayyo Allah na Jay D...'' '' Bee...'' ta kira da farin ciki..naji baƙin cikina ya ragu sosai...muka rabu muna kallon juna...naga ta ƙara min kyau... '' Abeedah kin ga yanda kika ƙara kyau kikayi fresh kuwa?" Dariya nayi sosai '' ji wadda ke magana...'' '' da gaske nake...da muka dawo na tafi gidan baki nan...'' '' ina tsaraba ta?" Na miƙa hannu kamar na bata ajiya '' banyi tsammanin zaki zoba sai gobe!" '' Abeedatuwoooo!!!!!'' Anaam tayi tsalle ta haye ni...muka faɗi ƙasa Asma'u ta faɗo kan mu...Jay d ta tsaya daga gefe tana dariya... '' wash zaki karye ni!" Anaam na dariya tace '' duk cikin murna ne...'' tashi mukayi Muna kallon juna kafin muka sake rungumewa..naga duk sun canja suma sai faɗi suke na canja... Ƙarƙashin bishiya muka zauna muna hira nake basu labarin wurin aiki na duk da ban faɗa masu wahalar dake ciki ba...na ɗauki receipt na miƙa masu.... Farin cikin dana gani a fuskar su yasa na ajiye a raina zan jure komai a gidan nan har sai mun kai tsayawa da kan mu... Wasu daga cikin yan ajin mu suka ƙaraso ana hirar dasu cikin farin ciki da nishaɗi... '' ina Diyaam?" Na tambaya amma babu wanda yasan wani abu game da ita Lokacin tashi su Asma'u suka ce in biyo su mu tafi gida amma baxan iya ba saboda Madam Amina ta gargaɗe ni... Badan mun soba muka rabu bayan Jay d tabani lambar ta...yau gani ina bin hanyar da mutane da yawa ke bi amma bana farin ciki saboda babu su Jay d... Yau babu rana kun dai san yanda yanayi yake kasancewa idan rana bata fito ba kuma mutum na cikin baƙin ciki...nake ji kamar an ɗaura nauyin duniya a kafaɗa ta...da sauri nayi ƙoƙarin saita yanayi na...ranar ta kasance mai daɗi kuma zamu sake haɗuwa gobe...kada in bari rabuwar mu tasani a baƙin ciki ko? Da wannan tunanin farin ciki ya dawo min nake tafiya a hankali ina lura da abubuwan da tafiyar mu ta farko ban lura dasu ba Na ɗauka tafiya ƙasa mai sauƙi ne kuma zan isa gidan da wuri...da sauri na fahimci kuskure ne dan Saida na shafe awa biyu ina tafiya kafin na kawo ... Na ɗau lokaci ina kallon unguwar abinda ban samu damar yiba a karon farko...wurin nada kyau sosai... murmushi nayi sai kuma na fara tafiya da sauri na isa bakin gate...buɗe wa sukayi na shigo na gaishe da gayen dake wurin...sannan na wuce sashen mu Ma'aikatan na samu suna magana akan yanda ɗaya daga cikin biyun ya ƙara kyau da komai...a gajiye nake yasa bayan na gaishe su na wuce ɗakin mu...Mama Asabe bata nan..Baye na shiga nayi wanka na sauya kaya zuwa uniforms Brown da suka dace da kalar fatata na fesa turare kaɗan nayi sallah..har xan kwanta na canja shawara...sabon hijabi na ɗauka ash na fita daga ɗakin... kitchen ɗin mu na shiga na zubo abinci waleeda da Aina'u suka zauna gefe na muna hira suke faɗa min sunga ɗaya daga cikin biyu ɗin,amma na biyun yanzu da yamma zai dawo... Ina sauraren su har na gama muka wuce babban gidan tare...wurin Madam Amina na fara zuwa na gaisheta nayi mata godiya ta samin albarka Kowa daga cikin mu ya kama aiki...plate aka cika da kayan ciye ciye aka bamu mukai ma yan gidan a Movie room dukan su suna can... Ɗauka mukayi... muna ƙunƙuni akan hawan stairs... Aina'u take bamu labarin garin su yanda suke hawa bishiya da kuma wasannin da suke da tafiya rafi ɗibar ruwa wata rana wani Mutum ya biyo su suka saki tulukansu suka kwasa da gudu... Muna dariya nida waleeda har muka iso movie room ɗin,mun ɗauka harda yan mata..mazan kawai muka iske suna kallon fim ɗin iskanci....a tare jikin mu ya ɗau rawa...mukayi tsaye daga bakin ƙofa babu wanda keda niyar matsawa cikin mu '' anan zaku cigaba da tsayuwa ne?" Abdul Jalal yayi maganar da alamun jin haushi saurin suka bimu da kallon rashin ɗa'a...ƙarasawa mukayi a tsorace muka ajiye abubuwan dake hannun mu...da sauri muka fita daga wurin zuciyoyin mu na dukan tara tara musamman ni da nake jin idon Mukhtar akai na.... Bari na sukayi suka nufi 3rd floor Dan suna da aikin da suke a can suda sauran ma'aikata... kitchen na sake komawa... Leonardo ya nuna min sabon faranti da aka cika da wani abu da turanci yace '' ana kiran shi da 🦐🦐 shrimps..master yana son su shine yasa na dafa...ki ɗauka ki kai Room no 207...'' yayi min bayani ganin kallon da nake bin abun dashi ''.ka tabbatar bazasu cije ni ba?" Na zaro ido dan gani nake kamar suna da rai...sauran masu girkin suka sa dariya Naeem yace '' baki ga an soya suba? Koke idan aka soya ki zaki iya motsi...'' Harara na jefa mashi nace'' ko zaka gwada ne?" Matso ni ya shiga yi yana wasa wuƙa...da sauri na figi farantin na tsere daga kitchen ina jiyo dariyar su...Nima murmushi nayi... wannan shine karo na farko da mukayi magana mai tsawo... Stairs na fara hawa ƙafafuna suna tsananin ciwo saboda tafiyar da nayi a ƙasa...ƙwanƙwasa ƙofar nayi ina sauke ajiyar zuciya daga ƙarshe dai na kawo... '' Come in..'' murya mai zurfi ta amsa daga ciki..tura ƙofar nayi da sallama na wuce parlorn zuwa ɗakin bacci... ɗakin da muka gyara ne ɗazu duk da ba haske saboda labulayen masu nauyi da aka saki ƙamshin turare da air freshener ne ke tashi...ganin wanda keda muryar nayi kwance saman gado ya rufe daga ƙugunshi zuwa ƙasa da bargo faffaɗan bayan shi a buɗe...gabana ya faɗi sai kuma naji haushin sa ya cika ni... '' yallaɓai ga abincin ka!!"nayi maganar da takaici kamar in kife masa shrimps ɗin a jiki! da kasala ya nuna min table a gaban gadon yace '' ajiye nan...'' ƙarasawa nayi na ajiye ya sake faɗin ''kwashe labulen''...na matsa zan kwashe labulen ya yunƙura ya tashi zaune,sai nayi pausing Nabi bayanshi da kallo ƙatone sosai saye yake da baƙin jeans amma ba abinda ya dameni ba kenan..gani nayi ya nufi ƙofa...yawu na haɗiye garƙame ni zaiyi ne? Zuciyata ta fara abinda ta saba...tsoro yasa na dena motsi...ban san me yayi ma ƙofar ba na dai ga ya taɓa handle sound ɗin rufewa da mukulli ya shiga kunne na... Innalillahi... ya juyo Rufe idona nayi na kurma ihu kamar zan cire mashi dodon kunne...ganin yana tunkaro ni yasa na fashe da kuka ina roƙon shi akan ya rabu dani tsayawa yayi gabana yace '' what nonsense!" Ji nayi kamar muryar na taɓa jinta amma firgici ya hanani tantancewa... saukar tattausan hannun shi a nawa yasa a rikice na zare hannuna daga fuskata hawaye na sintiri kamar an buɗe pamfo zan fara roƙo... Zaro ido nayi ganin Khalil tsaye gabana fuskarshi a ɗaure... eventually mamaki ya bayyana a fuskar shi shima.... '' kitten?.." +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 24. ...a massive jerk!...🖊️ Faɗin mamakin dana shiga ɓata lokaci ne... never in my wildest dream nayi tsammanin ganin shi,hawaye na suka tsaya kamar anyi ruwa an ɗauke...share min hawaye na yake da damuwa a fuskar shi '' did I scare you?...'' Ture Hannunshi nayi daga fuskata wannan tambayar ta ƙara fusatani abu a zahiri yake tambaya? Na tashi tsaye shima ya miƙe yana kallona da alamun tambaya a kyakkyawar fuskar sai naga kamar ya ƙara kyau fiye da lokaci na ƙarshe da muka haɗu...'' me kike yi anan?" Hararar shi nayi da jajayen idona takaici na kamani...bai ga uniforms ɗin dake jikina bane? '' wasa nake ai ka gani!" nake ji kamar in kwaɗe shi yayi murmushi yana bina da kallon nan nashi da har yau ban san ma'anar shiba...zagaye shi nayi zan wuce ya riƙo hannu na ya rungume ni yana dariya...gwalalo ido nayi ƙirjina na gaba da baya... yace '' toh muyi wasan tare!" mamaki ya hanani motsi ko ƙoƙarin ƙwatar kaina..muna tsaye aka turo ƙofa da sauri muka rabu..ko ya rabu dani cikin rashin gaskiya...naji kunya ta lulluɓe ni kumatuna suka ɗau zafi... Da sauri nabi ta gefen koma waye zan fita..dai dai nan idona ya haɗu dana Farzan daya zuba hannayenshi cikin aljihu...kallon da yayi min yasa na ƙara jin ba daɗi... Da sauri sauri nake tafiyar banko kallon inda nake sa ƙafafuna ƙwaƙwalwa ta taƙi yin shiru jikina yaƙi yayi sanyi...ji nayi na haɗu da wani abu kamar bango nayi baya baya na faɗi,ƙamshin turaren nan da nake iya tantance mai shi ya daki ƙofar hancina tare da ƙarama zuciya ta gudu...da sauri na ɗago inga ko da gaske shine idonmu ya haɗu na brief second... Saye yake da baƙar riga,baƙin jeans ya ɗaura trench coat data tsaya daidai guiwar shi hannun shi soke cikin aljihu...gashin kanshi slickly combed, fuskarshi saye da face mask kamar koda yaushe,sai ya cigaba da tafiyar shi kamar ni ban cancanci ya tsaya yaga idan ina lafiya ba '' wai kai baka iya zama gentle man bane? ka ture ni ko ka taya ni tashi!" nayi maganar ina jifar shi da takalmi na kamar yanda na jefe shi a maina hotels, batareda ya juyo ba ya riƙe takalmin ta baya kamar dama yasan yana zuwa share shi nayi duk da yanda zuciya ta ke bugu na shiga kakkaɓe kayana, ganin bai tafi ba yasa na miƙe ina kallon shi Karkatar da kanshi gefe yayi '' I'm sorry..." Deep baritone voice ɗinsa ta sauka a kunne na,mamaki ne ya kusa gamawa dani a tsaye amma sai nayi saurin saita yanayi cike da basarwa na fara faɗin '' ah ai ya wuce kasan ni Abeedahtu ina da karam..'' '' that you didn't fall hard enough to shut that hole on your face!" Ya iyar tare da sakin takalmin yana bina da wani irin kallon dayasa naji kamar an watsa min ruwan ƙanƙara, har ina jin zufa tana sauka a bayan wuyana,wai bakina yake kira rame,naso in mayar mashi da magana amma idonshi sun ɗaure min baki har da ƙafa ma,sai kuma yayi ƙasa da idonshi.. nima nayi ƙasa ina kallon abinda yake kallon ashe fitsari na saki Da sauri nayi zaune ciki kunya na barazanar gamawa da rayuwata..meyasa zanyi fitsari a gaban shi batareda nama sani ba? girgiza kanshi yayi kafin ya bar hall ɗin,naji haushinsa ya cika zuciya ta '' what a massive jerk!" Lokaci guda kuma ƙwaƙwalwata ta fara aiki,nan ne gidan su?kuma ni yar aikin suce? ina Allah Allah kada in haɗu da wani na miƙe na fara tafiya duk ƙyanƙyami ya kamani,kamar wata mai yoyon fitsari? abun ya fito salin alin batareda na sani ba Sashen muna koma na wuce baye na wanke jiki har lokacin na kasa dena jin nauyin abinda ya faru ina tsaka da canja kaya Hansa'u ta shigo tana min kallo a ɗaɗɗage '' ke!'' Ban tanka ba taja tsuki '' Fauziyya tace bata so ta ganki a dining!" tana botsare botsare ta juya ta fita daga ɗakin.. lumshe idona nayi da ace akwai yanda zan tserewa zuwa wurin ai da tuni na dena... Alwala nayi bayan Mama Asabe ta fito nayi sallah ina zaune har sallar Isha'i...koda na second ne,naso inyi yanda Fauziyya ta faɗa ɗin sai dai albashina ba'a hannunta yake ba...jiki ba ƙwari na fita daga ɗakin Kamar kullum zaune suke suna hirar samarin gidan... precisely Khalil da Romo..wai wayafi kyau a cikinsu? Wasu na faɗar Romo wasu na faɗin Khalil Wuce sunayi zan fita naji an riƙo hannu na Fauziyya ce '' bana ce kada inga ƙafarki a wurin nan ba?" Juyowa sukayi suna kallon mu na fisge hannu na '' ki gafarce ni ranki shi daɗe,it must have slipped my mind!...'' Zagaye ta nayi na fita daga sashen...ina jiyo muryoyinsu wai nayi fiffike ina tashi sama da nisa... Kitchen na shiga,a maimakon in tafi dining,sai na tsaya a nan ina taya masu wanke wanke...na ɗauka na tsira sai da aka bani wani juice da aka haɗa da fruits wai in Kay dining....naji ina zufa amma babu damar musu yasa na karɓa... '' ya makaranta Ibraheem?" Alhaji Kabeer yayi tambayar yana kallon Khalil da yayi ƙasa da kanshi da girmamawa '' Alhmadulillah kawu...karatu da godiya...'' ya amsa yana zuba wani abinci a plate ɗin shi...yace '' naga hajjo ko kulani batayi ba...ina fatan ba'a shiga tsakanin muba?" Sai lokacin tsohuwar tayi murmushi da basarwa tace '' wazai shiga tsakanin mu kuma?'' ya ɗage kafaɗa...aka cigaba da hira cikin nishaɗi... Seraphina idonta buɗe tana jira taga inda zata ga Roman... '' Ya I.B ina Ya Rome?" Yan matan suka kalli sashen Khalil expectantly, daga sanda ta kira sunan shi light atmosphere ɗin ta ɓace fuskar Alhaji Hussein tayi duhu yaja dogon numfashi batareda yace komai ba... '' Ɗan iskan yaron ina zai zo ya gaishe da mutane? Baya girma ba...'' '' aunty don't curse him!" Seraphina ta faɗa tana turo baki...juya idonta Hajiya Momma tayi... sauran matan gidan basu ce komai ba haka ma hajjo samarin suma sunyi shiru...no one talks about Roman... '' come on...daga dawowa Sai faɗa .. just chill..." Khalil ya faɗa yana tura cokalin abinci cikin bakinshi hakan yaba su dariya...aka dawo yanayin murna da farin ciki... Shigowa Dining ɗin nayi ɗauke da farantin juice a hannu na...'' bani ɗaya nan!" Khalil ya ɗaga hannun shi kamar yaron dake tambaya a aji murmushin nan manne da fuskarshi... naji kamar in juya idona amma na cije na ajiye mashi ɗaya a gabanshi '' Thanks kitten...'' yanzu kam kasa haƙura nayi Saida na juya ido... '' na sani yarinyar nan mayyace! Daga zuwan ya Khalil harta yi bewitching ɗin shi!" Mufeedah ce tayi maganar tana huci kamar zata kama da wuta...yan aiki suka sadda kansu wasu suna dariya '' na shiga uku...me nayi Kum...'' '' rufe ma mutane baki munafuka!" Heedayah da itama da alamu taji haushin murmushin da Khalil yayi min Khalil yake kallon su batareda ya fahimci inda lamari ya dosa ba... '' duh she's so ug..'' '' SHUT UP!!" Farzan ya daka masu tsawar data sa suka firgita..nima da kaina sai da naji yan hanji na sun kaɗa '' bar yara suyi magana, yarinyar nan tunda tazo sai saɓani ake samu a gidan nan!" Hajiya Bushrah da alamu ban mata ba ko kaɗan '' come-on aunty kada ki faɗa min kema kin yarda da superstitions...'' '' babu maganar superstitions anan Farzan,kalli kai da kanka baka cika magana ba amma saboda wannan yarinyar kayi sentence mai tsawo. mai zamu kira wannan fisabilillahi?" Sauran suka gyaɗa kansu cike da goyon bayan abinda ta faɗa '' kuma fa yarinyar nan mahaukaciya ce...'' Hajiya Momma ta shiga faɗin abinda nayi mata harda ƙara gishiri da mai da yaji.. Seraphina ma ta faɗi nata labarin..sukayi min baƙin painti '' da gaske kitten ɗin tayi haka?" Khalil ya tambaya da mamaki yana kallona...ɗauke idona nayi nake ji kamar kamar.... '' ƙarya za'a yimaka Ibrahim?" ya girgiza kanshi...Hajjo batace komai ba...sai saurare da take...babu wani abu dazai bada damar sanin abinda take tunani... A hankali nake jin ƙamshin turaren shi tun daga nesa..sai nake ji yana ƙara kusantowa..kowa yayi tsit aka zuba ma hanyar shigowa Dining ɗin ido... Romo ne ya ɓullo hannun shi riƙe da plate nacin abinci...sakin baki nayi da naga babu face mask a fuskar shi...kamar irin mazan da nake karantawa a novel babu abinda yafi ɗaukar idona a kyakkyawar fuskar tashi sai hancin shi da yake dogo ƙofar hancin ƙarami nake tunanin taya yake numfashi? Gashin girar shi a cike..fuskarshi fara sosai kamar baida jini...laɓɓanshi jajaye marasa kauri...saye yake da dogon wandon roba da large black t shirt da za'a iya fitar da guda biyu a ciki gashinsa pinned with a butterfly hair clip Fuskarsa ba expression,bayan shi akwai wata mai aiki riƙe da wani plate daban a hannunta...jayewa kaɗan ɗin da yayi ya bani damar ganin ko wacece '' DIYAAM!!" Na kira da mamaki... Leƙo kanta tayi daga bayan shi taga waye ya kirata..da gaske ita ɗince... Wuce ni Yayi ya zauna a kan kujerar dake gefen Khalil... Diyaam ta ajiye plate ɗin dake hannunta ta tsaya gefe na...amma bata yimin magana ba...sai leƙa fuskar ta nake dan in tabbatar idan ita ɗin ce... Tsit wurin ya ɗauka, shikam ogan kamar baisan tension ɗin daya sauke a dining ba ya shiga cin abincin daya kawo wanda bai yi kama dana yan Nigeria ba ... Fuskar Seraphina tayi ja blushing take? '' toh mara kunya...mai idanu a tsakiyar kai, gaisuwar ma ba zamu samu ba kenan?" Hajiya Momma ce tayi maganar da takaici a muryar ta '' tsawon rai zaki samu idan an gaishe ji ɗin?!" He answered with a chilled voice Batareda ya ɗago daga kwanon shi ba,wurin ya sake yin shiru kamar anyi ruwa an ɗauke, Hajiya Momma zata sake magana seraphina ta riga '' Aunty ki...'' '' ke dalla rufemin baki! Shashar yarinya kina nan kina kare shi bayan shi bai masan dake ba!'' juya idonta Seraphina tayi,itako Hajiya Momma kamar zata kama da wuta Kowa a dining ɗin suka zuba ma Romo ido nikam nayi mamakin abinda ta faɗa..kuma batare da Khalil suka zoba? Meyasa kowa yake murna da Khalil amma ba Romo ba?da yake dai a gabana ya saki rashin kunya bari in kama kaina Da baƙin cikin halin ɗan nashi Alhaji Hussein yace '' Ibrahim ina fatan kana mayarda hankali a karatu baka biyewa mutanen banza kamar wasu ?" Daga ji kasan da wanda yake amma wanda ake maganar dan shi,bai motsa ba '' Kawu Rom baya bin mutanen banza,sannan shine yayi graduating a saman yan ajin su...'' Ɗauke kanshi Alhaji Hussein yayi Farzan yace '' da gaske?cuz he seems as dumb as fuck!!" Muryar shi ɗauke da gubar data kasa ɓoyuwa Cikin son daidaita yanayi Khalil yace '' come on,kada kabashi kunya a gaban budurwar shi mana!" '' wacece budurwar tashi?" Seraphina ce tayi tambayar idonta waje,sai kowa ya dawo da kallonshi akan Romo that was unbothered.. Farzan ma ya dakata da abincin da zai kai baki yana jiran amsar Khalil...nikam so nake in bar wurin nan ƙafafuna har sun fara ciwo..ina tsaka da tunanin uzurin da zan bada in bar wurin naji Khalil yace '' gata tsaye a bayana..." Ya nuna ni...lokaci guda kowa ya sauke idonshi akaina.... Shock rubuce a fuskokinsu...nima dai shock ɗin na shiga sai rarrabar ido nake... Mukhtar da Farzan ban san wanda yafi Zama shocked cikinsu ba... ''No way!!" ''Impossible'' '' wannan mummunar yarinyar ce budurwar ya Rom?'' Muryoyin suka faɗa a lokaci ɗaya... Seraphina,Huriyya... Jameelah da Khadeejah ne suka faɗi a dukan su sun tashi tsaye daga wurin zaman su Khalil yayi ƙasa da kanshi yana murmushi '' Ya Rome,da gaske wannan itace budurwarka?" Khadeejah tayi tambayar cautiously cike da tsoron amsar da zata biyo baya ..kowa ma amsar shi yake jira har dani '' Ask Google!" Batareda ya ɗago daga abincin shiba garmahon muryarshi ta amsa kuwwa a kunne na a karo na biyu,ƙafafuna kamar zasu zubar dani Damƙe tiren dake hannu na nayi..cikina ya ɗaure..zufar da ba'a gani ta wanke goshina mutumin nan zai sani a matsala dama can ba wani sona mutan gidan suke ba yanzu kuma wannan... Miƙewa yayi babu wani sauran bayani ya nemi fita daga wurin Alhaji Hussein da tunda yayi magana Roman bai ce ko ehm ba ya paka abincin shi gefe ya kalli ɗan nashi dake barin wurin ya miƙe '' Romano!" Kamar Romo bazai tsaya ba can kuma sai ya tsaya batareda ya juyo ba ... Alhaji Hussein kamar zai yi aman wuta ya nuna shi yace '' kai bazaka zama ɗa na gari ba? A matsayina na ubanka ba zaka girmama niba? Kaje wata ƙasa ka dawo bazaka iya gaishe niba... I'm your father!'' wurin yayi tsit kamar babu mai rai a wurin, mu masu aiki kan mu a ƙasa sai rarrabar ido muke '' My father....'' ya furta slowly kamar abun na bashi mamaki,sai ya juyo ta kafaɗarshi '' didn't see you there...PADRE!''... Voice cold as ice, idonshi da tsananin duhu ya cigaba da tafiyar shi +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 25. ...yar aiki ce...🖊️ Kamar anyi ruwa an ɗauke bayan tafiyar Romo daga wurin...ƙila kowa ya shiga shock da abinda ya faɗa.... '' kun gani ko..Allah ya wadan naka ya lalace!" Hajiya Momma ce ta faɗi hakan Hajiya Ruƙayyah ta taya ta da faɗin '' ai kam dai,bawai bana son yaro bane...amma gaba ɗaya hallayarsa abun tambaya ce!" '' Gaskiya Alhaji ya kamata ka ƙara sa ke...yaro yana nema ya gagareka...'' Inji Hajiya Wareesha '' nidai fatana wannan lokacin bazai dinga kwasowa mutane abun magana ba'' '' once a trouble maker always a trouble maker!" Farzan ya miƙe daga wurin zamanshi bayan ya faɗi hakan... '' kuyi mashi uzuri...rayuwa babu uwa akwai wahala sosai!" Hajiya Hafsah ta faɗa daga ƙarshe...Hajiya Momma na hura hanci tace '' Koda Fateemah aw Cora ɗin tana nan ai ba wani abun kirki zata aiwatar ba? Kai haɗa zuri'a da irin wa'yannan mutane dai masifa ne wallahi!" Miƙewa Hajjo tayi cikin shiru tabar wurin sauran manyan matan suka cigaba da magana akan wacce suke kira Cora ko Fateemah duk sunanta ne,kamar basuga cewa Hajjo tabar wurin ba,suma mazan suka bar wurin kusan a tare...amma Cora bai yi kama da sunan musulmai bako? Sai lokacin da suka bar wurin na lura cewa yan matan kamar zasu kashe ni da kallon da suke min...nayi ƙasa da kaina...Khalil ma yayi shiru kafin ya miƙe yabar wurin... '' Mtchewww! aikin banza...this guy is a bad luck! daga dawowar shi har gida yayi tsami!" Jawaad da bai cika magana ba idan ana cin abinci ya faɗa tareda dukan table ɗin kafin yabar wurin suma sauran suka zare jiki ɗaya bayan ɗaya sai da ya rage yan matan da mu masu aiki harda Diyaam Seraphina tayo kan DIYAAM '' Tass!" Ta ɗauketa da marin daya amsa ƙara a gaba ɗaya dining ɗin ƙirjinta na sama da ƙasa Ɗan kwalin Diyaam ya faɗi doguwar sumarta baƙa ta warware ta rufe rabin fuskarta.. hannun ta dafe da kuncinta... sakin baki nayi idona na kallon tsakanin su biyun... sauran suka sadda kansu,yan matan suke kallon mu kamar zasu kashe mu '' ba saida nace kada inga ƙafar ki a parlorn nan ba?" Murya na rawa Diyaam tace '' K...kit...haƙ..hamm..'' damƙo gashin Diyaam Seraphina tayi Heedayah tace '' ki haɗa min da shegiyar nan mai idon Mayu!" Kallonq Seraphina tayi kafin tace '' ki bari in gama da wannan annobar...'' Idon Diyaam suka fito.. jijiyoyin goshinta sukayi ruɗu ruɗu hannunta riƙe dana Seraphina '' Bana ce kada ki sake kiranshi da Hamma ba? Dan ubanki yaushe ya zama Hamman ki?'' ''.kiyi haƙuri dan Allah!" Diyaam ta faɗa tana kuka sosai.. idonta kamar jini..da ƙarfi Seraphina ta tureta ta faɗi goshinta ya haɗu da table take wurin yayi ja kasancewar ta fara... Tana huci ta juyo kaina..sauran yan matan suka miƙe kamar cin mutuncina yafi ƙayatarwa sama da Diyaam '' Ji nayi ya I.B ya kira ki budurwar ya Rome?" Matsawa na shiga yi tana matso Ni...'' hala baki ji bane da kyau kike tambayarta?" Jameelah ta ɗauki gorar ruwa ta harbo sashena..da sauri na duƙe gorar ta sauka akan Seraphina... '' Ahhh!!!!" Ta saki ƙara...ta juyo tana kallon Jameelah da fushi... '' what the hell!" '' oh bake nayi niyar jifa ba!" '' amma ni kika sama!" '' Duh! Ba laifina bane idan kin shigo tsakani....'' a fusace itama Seraphina ta ɗauki gorar ta jefawa Jameelah..ta sameta a goshi '' yanzu kema kin san yanda ake ji ai!" '' Guys calm down!" '' taya zanyi calming down wannan ugly duckling ɗin na ƙoƙarin shiga tsakanina da Ya Rome..bayan ni yake so!" Tayi maganar tana kallona '' excuse me...wane irin ke yake so? Huriyya take hararar Seraphina kamar idonta zai faɗi '' wasn't it obvious?'' Seraphina ta bata amsa '' delude yourself girl!" Faɗa ya koma tsakaninsu akan wake ƙoƙarin ƙwace Romo daga wa...ganin hankalin su baya kan mu na isa wurin Diyaam na taimaka mata ta miƙe salin alun muka bar dining hawayen da suka zuba daga idonta sun isa cika murfin hira koma abinda yafi hakan girma...katin ma'aikatan tayi swiping elevator ta buɗe muka shiga ciki..nesa na tsaya da ita ..ƙila bata so asan munsan juna...ina satar Kallon ta daga lokaci zuwa lokaci yarinyar fara ce sosai...yanzu ta dena kuka kanta a ƙasa... Sautin buɗewar elevator yasa ta ɗago ta fita ina biye da ita kuma ban san dalilin bibiyarta ɗin ba...ƙofar ɗakinta muka tsaya ta buɗe ƙofar na samu kaina da juyawa zan tafi '' Abeedah...'' ta kira sunan muryarta da taushi..Juyowa nayi ina rarrabar ido..ta nuna ɗakin '' mu shiga ciki...'' tayi gaba ina biye da ita abun ya ɗaure min kwanya...idan ita yar aikice meyasa take da ɗaki a cikin babban gida? Meyasa kuma Seraphina tayi mata yanda tayi mata...gefen gadonta ta zauna ta nuna min kusa da ita...nake jin ɗar ɗar..kafin daga ƙarshe na zauna ɗin ƙaramin locker dake gefenta ta buɗe ta ɗauko magani tana lura da ciwon data ji '' kawo in yimiki...'' na karɓa daga hannunta...bayan shuɗewar lokaci tace '' ashe kina ɗaya daga cikin sabbabin ma'aikatan da aka ɗauko...'' gyaɗa kaina kawai nayi..ban manta yanda ta share niba ɗazu da nayi mata magana '' oh...nima aiki nake a nan gidan..nasan kina tunanin yanda akai nake da ɗaki anan a maimakon sashen ma'aikata ko?" Jinjina kaina nayi tareda ajiye almakashi bayan na samata plaster a ciwon '' Hamma Roman ne ya kawo ni shekarun baya...ya ganni ne a gefen hanya bani da inda zani...ni na zaɓi in zama mai aiki a nan a maimakon in zauna ana ciyar dani kyauta...'' nayi mamakin jin wannan.. kuma na rasa abun faɗa gane hakan tace '' kin tafi makaranta jiya? Yasu Anaam da Jadeedah?" Murmushi nayi kafin na bata labarin abinda ya faru a jiya ɗin duk da ba wani abu mai yawa ne ya faru ɗin ba... Mun daɗe muna hira kafin na tashi na wuce sashen ma'aikata inda ake magana akaina...da gaskiya ta..abinda Khalil ya faɗa baƙin jini ya ƙara min..ina tafiya ana bina da baƙin ido kamar zasu sa in faɗi... Washegari da safe ban samu damar zuwa dining ba saboda wannan Hajiya Momma data tsare ni a ɗakinta da wanki kuma fa akwai laundry room wai ita bata so ana sama ta kaya a mashin kuma bata ga wanda ya dace data ba wannan aikin ba sai ni koda na gama ƙarfe sha ɗaya bazan iya zuwa makaranta ba...haushi kamar in cinna mata wuta..dataga alamun na ƙufula wani shegen murmushi ne maƙale a fuskarta..nakai bakin ƙofa na juyo na kalleta nace '' aljannu na suna tashi su daki wanda ya ɓata min rai...ko su haukatar da mutum... Hajiya gwaggo kibi a hankali...'' expression ɗin dake fuskarta was priceless Da sauri na fita daga ɗakin ina dariya... kitchen na tafi na iske sun haɗa wani abu a tray kamar biscuit da juice..da sauran abubuwa..kusan plate biyar ne... Hansa'u ceta shigo ta kwashi guda uku saura biyu Leonardo yace in bita dasu zuwa Movie room... Badan naso ba nabi bayan ta.. yarinyar is self absurd ...ji take kamar tafi kowa kyau da komai a gidan saboda kawai uniforms ɗin ta sun matse ta sun fito da surar jikin ta take ji kamar maxan gidan ba zasu iya haƙura ba harda su Romo da Khalil tana tafe tana juya mazaunai... abinda ya faru a Movie room ya ƙayatar dani fiye da komai a ranar... sanda muka shiga wurin da duhu amma ba mazan kaɗai bane yau harda matan...layi layi take bi tana miƙa masu suna ɗauka kowa hankalin shina akan TV nidai ina tsaye daga gefe... Bayan ta gama dana hannunta tazo ta karɓi nawa na juya Zan bar wurin saboda yanda Mukhtar ya dawo da hankalin shi akaina naji an bada tass Juyowa nayi da sauri naga Hansa'u riƙe da kuncinta Armani tsaye a gabanta '' BABBAR BALA'I!!! Ni kika mara?'' Hansa'u tayi maganar kamar zatayi kuka...'' ko zaki rama ne?'' Armani ta tambaya '' dalla fita kiba mutane wuri shegiya me kama da aljannu..'' Dariya aka saka... Fuuu Hansa'u tazo ta wuce ni tana cika tana batsewa..sanda muka fito kasa haƙura nayi na kwashe da dariya... Juyowa tayi da jajayen ido tayo kaina..na kwasawa da gudu da ita biye dani...ina gudu dariya na cina...ban tsaya ba sai dana kawo gaban wata ƙofa...koda na ɗago bayan na gama kama numfashi ganina nayi gaban ƙofar nan mai XXX.. na juyo naga babu Hansa'u...ni kullum idan ana bina sai na kai wani wuri idan na juya sai inga wa'yanda ke bina ɗin har sun daina... Miƙewa tsaye nayi da kyau na sake tabbatar da babu wanda ke ganina na matsa gaba na ɗaura hannu na akai zan tura... '' kina da ajiya a ciki ne?" Maganar ta sauka cikin kunne na a bazata yasa na juyo da ƙarfi losing balance nayi na faɗa jikinshi..yayi tsaye ƙiƙam kamar bishiya hannayen shi cikin aljihu...da sauri naja baya kamar na ɗosanu da wuta ido waje na kalli fuskar shi da take a matuƙar ɗaure... '' Uhmm...na manta da soso ne a ciki jiya dana gyara wurin...'' ƙaryar ta gamsar dani don haka shima dole ta gamsar dashi ko? amma ko kaɗan babu alamun hakan sai ɗauke idonshi da yayi daga kaina '' bar wurin nan!'' muryarshi ba wasa a ciki yasa na kama gabana Sai kuma na tsaya '' soson fa?" wai kada ya ɗauka ƙarya nake...bai ko kalle niba naga ya ciro mukulli daga aljihun shi...gwalalo ido nayi kenan shine da ɗakin..kuma na zage ina makaka ƙarya... Da sauri nabar wurin na tafi ɗakin Diyaam na ganta tana karatun jarabawa..zama nayi muka cigaba tare tana nunamin abinda ban sani ba....tana da ƙoƙari sosai... Washegari muka tafi makaranta amma ba tare ba...su Jay d suke tambayarta me yasa bata zoba ranar farko.. murmushi kawai tayi bata ce komai ba...nima ban faɗa masu cewa a gida guda muke aiki ba... Rayuwa ta cigaba da tafiya...har exam time table ɗin mu ya fito..a nan gidan su Khalil kuma dayawa daga mutanen gidan sunyi tafiya...harda Hajjo data tafi Makka... cikin Alhazozan daga Alhaji Hussein sai Alhaji Mansir suka rage Yan matan Seraphina, Heedayah Khadeejah da wasu da bansan sunan suba da kuma ya'yan Hajiya Momma kaɗai suka rage...suma samarin tsiraran su kawai ne a gidan duk sun tafi ƙasar waje karatu... Yau Alhamis ina zagaye ƙaton gidan dan babu aiki da yawa saboda raguwar mutanen gidan... kitchen na shiga na buɗe ƙofar bayan nan da koda yaushe take a rufe.. nayi mamakin ganin dogon swimming pool da bishiyoyi hagu da dama da kujeru farare masu taushi...daga can gaba green grass mai laushi... Iska da yanayin wurin na daban ne,kallon ruwan nayi da murmushi a fuska ta kafin nabar wurin na koma ciki na fara zagyena daga first floor... gidan kamar bada gaske ba saboda haɗuwarshi....daga first floor zuwa second floor har zuwa fifth floor...harda ɗakin motsa jiki na shiga na fito na duba sauran wurare a can ƙarshe naga wani ƙaramin matattakala, Da nahau matattakalar ya kawo ni a roof top dake kewaye da glasses harda wani swimming pool...da kujeru masu taushi da lema kamar dai Beach...gaban wurin na isa ina kallon ƙasa jiri naji yana ɗiba ta da sauri naja baya tare da dafe ƙirji... Zagaye wurin nayi ya tsaru sosai...zan bar wurin idona ya sauka akan Romo dake saye da rigar sanyin saƙa da baƙin jeans rigar tayi mashi yawa, ƙamshin shi ya mamaye wurin... hannun shi riƙe da plate ɗin katako da ake zuba paint 🎨 sama...ɗayan riƙe da brush...gaban shi allo da paper yana zane... Matsawa kusa nayi na tsaya daga ɗan nesa kaɗan dashi ina kallon painting ɗin ƙaramin yaro da bazai wuce shekaru biyar ba yana bibiyar bilbilaye a wurin dake kewaye da bishiyoyi da haki mai taushi..komai na wurin green ne,sai wata mata biye da yaron su biyun farin cikinsu a bayyane yake...daga yanayin zanen zaka gane da safe ne wurin ƙarfe tara ko makamancin haka rana ta fito amma bada ƙarfi ba... Daga ƙasa ya rubuta wani abun da ban san ma'anar shiba **(La cosa che ho perso**) abunda na rasa) Painting ɗin yayi min kyau sosai...'' idan kin gama kallo zaki iya tafiya!" Muryar shi ta sauka a kunne na,...Hausar shi idan dai mutum ba saurara yayi da kyau ba,zai ɗauka da yaren Italiya yake magana...abu na chakwakiya '' waya ce zanen ka nake kallo? ni aiki nazo yi... zanen ko kyau beyi ba... yaron daga gani bai jin magana...da nice Mamar dana kamashi na zane mashi jiki gobe bazai sake ba....fuskarshi kamar an taɓe alala kan titi kaɗan goge wannan abun..'' na ɗan matso gaba kaɗan amma cikin rashin Sa'a i tripped on absolute nothing, tafin hannayena suka damɓaru akan painting ɗin A wani irin slow na fara juyo da kaina ido waje na kalle shi,if looks could kill da ban zo ina baku labari ba,ƙasan idon shi har wani ja yayi tsabar takaici Da sauri na cire hannu na, zan matsa kuma na sake cin tuntuɓe da akwatin kalolin shi na damɓara hannayena a ƙirjinsa, ya wani irin zabura kafin plate ɗin painting ɗin ya sulɓuce daga hannun shi ya sauka saman yatsun ƙafafunshi dake saye cikin baƙaƙen slippers Da sauri yaja baya yana tsalle akan ƙafa guda yana faɗin '' LORD GIVE ME THE PATIENCE '' idon shi kafe a kaina,ni kam nayi tsaye baki sagam ina kallon shi,mutum kamar ba namiji ba ganin ya dena wannan tsalle tsallen yana takowa inda nake kamar dutse mai aman wuta,yasa na fara ja baya idona kamar zasu faɗo '' ehhmm..naji kamar ana kirana bari in tafi...'' a gaggauce nabar wurin gabana na faɗuwa kuma babu wanda ke kirana fa... __ Yau da wuri dukan mu muka gama aiki yasa mun taru a parlor muna kallon fim ɗin indiya kafin wata mai suna Nana ta canja tashar zuwa ta yan Italiya wai tana so ta koya don ta burge Romo...aiko sauran kamar mahaukata suma wai suna so su koya ɗin...aka bi aka ishemu da shegen Yaren mara daɗin sauraro... amma fim ɗin yayi kyau..kuma naji daɗin kasancewar mu tare ba tare da anyi faɗa da hantara ba... na kuma riƙe kalma ɗaya take..wai ragazze..nifa ina ganin so suke suce ragadada,wannan abun da ake haɗawa da nama ko? Oho..nidai idan na haɗu da Romo nan gaba zance mashi ragadada ake cewa ba ragazze ba..ehe! +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 26. ... Maraya ne...🖊️ Washegari da sassafe ina kitchen...coffee Leonardo ya miƙo min yace '' ki kai room no 207'' '' Kai bazata yi hausa ba wai?" Nayi maganar da hausa,tsare ni yayi da ido ƙwaƙwalwarsa na aiki a 360..karɓar coffee ɗin nayi ina tunanin yanda zan fara hawa stairs tunda sassafe naga Farzan ya shigo Parlorn ya nufi elevator da sauri na faɗa ciki tare dashi bayan elevator ta buɗe...saura kaɗan in mashi wanka da coffee ɗin yayi saurin kaucewa '' baki da nutsuwa!" na zaro ido nace '' ban taɓa jin wannan kalmar ba,akwai a dictionary?" ya ƙanƙantar da idon shi akai na can yace '' of course you're dumb bazaki San me hakan ke nufi ba!" turo baki nayi fuska a ɓace kafin in bashi amsa elevator ta buɗe yayi gaba yabar ni tsaye a wurin sai dana ga ƙofar zata sake rufewa nayi saurin fita samun Khalil nayi kwance saman blue carpet dake gaban gadon shi yana excercise...nuna min table yayi na ajiye coffee ɗin anan zan tafi naji yace '' zoki dafe min ƙafafuna kada ki bari suyi sama...'' Juyowa nayi idon mu ya haɗu...nake ji kamar in kwarara mashi coffee ɗin dana kawo...'' Uhmm..'' ya nuna min ƙafafun shi yana murmushin gefen baki Dawowa nayi na dafe mashi ƙafafun yana tashi daga kwance ya zauna sai ya koma..kuma baiyi zufa ba..ɗauke fuska ta nayi gefe dan idan ya ɗago fuskokin mu zasu kasance kusa kusa,hucin shi na sauka a gefen fuska ta... '' wai har yanzu baka gama ba?" Na tambaya bayan shuɗewar lokaci zuciya tana tafasa Rashin amsa daga gareshi yasa na juyo daidai ya taso fuskokin mu were inches a part...idon mu ya shige cikin na juna ..bugun zuciya ta ya sauya... lumshe idonshi yayi tare da karkatar da kanshi yana matso da fuskar shi saura kaɗan bakin mu ya haɗu nayi saurin miƙewa Dariya yayi yana kawarda kanshi gefe '' such a buzz kill...da kin tsaya mana...'' Hanyar fita nayi..wannan Khalil ɗin is a bad influence...'' oh haka fa...baka yi brush ba shine yasa!" ina jiyo dariyar shi na riƙa handle ɗin zan fita naji yace '' zoki jira inyi brush sai mu sake gwadawa...'' na buɗe ƙofar na juyo akan kafaɗuna nace '' Too bad..you missed!" Na fice da sauri, kumatuna suka yi ja..tunowa da haɗuwar mu ta farko yasa murmushi ya wanzu a fuskata Wurin tagar dake corridor na tafi na tsaya ina kallon tsakar gida,idona ya sauka akan Romo dake zaune saman wani baƙin mashin ƙato irin wanda masu gudun tsere suke hawa...shima yasa baƙaƙen kaya daga sama har ƙasa... hannunshi riƙe da helmet baƙi...ƙila yaji a jikin shi a na kallonshi ya juyo da baƙaƙen idonshi saitin da nake tsaye...duk da nisan da muke dashi sai da zuciya ta ta buga da ƙarfi...kallon shi bai daɗe ba ya ɗauke yasa helmet ɗin ya fice da gudu daga gidan kamar zai tafi lahira... Zan bar wurin ɗakin ƙofar Seraphina ya buɗe tana ganina fuskarta ta sauya '' ke zonan!'' ƙarasawa nayi gabanta ɗin ta nuna min ɗakinta '' wuce ki gyara min ɗaki...'' tana faɗar haka tayi gaba ta barni tsaye '' wuce ki gyara min ɗaki... ba'a gyarawa!" Na kwaikwaye ta amma dai daga ƙarshe banida zaɓi dole na shiga na gyara... Da ƙarfe goma duka yan gidan ne zaune a parlor harda su hajiyoyi,samari da yan matan da suka rage a gidan... Wasu mutane suka zo daga company'n kaya daban daban suna nunawa yan gidan kowa ya zaɓa...nake ji yan gidan na faɗin kayan designer ne limited edition... Kowa darjewa yake ya zaɓa...mu masu aiki ba'a barmu mun huta da guje guje zuwa nan da can ba... yau ma munci Sa'a hankali bai a kanmu da yawa hakan ya rage mana cin mutunci da alamu akwai taron da suke shiryawa ƙarshen mako Seraphina ta saka wata doguwar riga pink irin ta Disney princesses..ta saki gashinta tayi kyau sosai Hajiya Wareesha sai yaba kyaun yar tata take... sauran yan matan suke binta da kallon kishi... '' wow you look stunning in that dress phina!" Ayaan ne ya faɗi haka yana ɗaukar doughnut daga plate ɗin da aka ajiye masu '' na gode...'' ta faɗa da murmushi badiyya tace ''kinfi kama da malnourished akuya a cikin wannan rigar'' '' kidai faɗi gaskiya Badiyya, kin san a gidan nan babu kamar Phina...'' juya idonsu sauran sukayi jin maganar Hajiya Wareesha Hajiya Momma tace''la shakka tunda ita akayi ma wahayin kyau ba...mata duk ƙasusuwa kamar mai fama da kwashiorkor!" Da yawa daga cikin yan matan suka kwashe da dariya Nima na toshe bakina ina yi ƙasa ƙasa Seraphina kamar zatayi kuka da cin mutuncin data fuskanta... Sauran ma suka shiga gwada kaya yan mazan na zaɓen wacce tafi kyau...duk Seraphina tafi su samun points... Sukam ma'aikatan company'n sun zage sai ƙara nuna masu kaya suke...daga nan aka shiga zaɓen sarƙoƙi da awarwaro.. wata sarƙa na gani mai simple design tayi min kyau sosai Ɗaukar sarƙar seratena ta ajiye... Khalil ne yaxo ya zauna daga gefen da nake tsaye ya gaishe da matan gidan a girmame,kafin ya kalle ni with a smirk on his lips,na ɗauke kaina...such a big flirt he is yan matan suka zo suka zagaye shida sarƙoƙi suna tambayar shi wane zasu ɗauka...kamar shi mace ne da zai san wanda yafi kyau '' Uhmm... maybe ku tambaya su aunties...nida ba mace ba...'' '' Mufeedah tace '' ni ina so insa abinda ka zaɓa min ne kawai!" '' sannu yar iya...'' Mardiyya ta harare ta..abu ya kusan zama rikici sai da Hajiya Hafsah ta tsawatar Khalil ya shafa ƙeyarshi... sarƙar da nake ta kallo ya ɗauka ya duba...'' I'll take this..'' ya nuna ma staff ɗin har zasu karɓa su ajiye cikin kayan da yan gidan suka zaɓa yace subar shi kawai... '' Budurwar ka ka siya mawa?" Hajiya Bushrah ta tambaya... nayi mamakin jin yanada budurwa..'' nope... it's for some one else...'' '' Kai Khalil yanzu bayan Eden ɗin da aka sa muku rana kana da budurwa gefe?" Sauran yan matan suka tsaya cak...''sa rana...'' suka faɗa a tare...samarin suka kwashe da dariya ganin shocked expressiom ɗin yan matan wasun su kamar zasu yi kuka '' waih Allah yasa ya Rome baida budurwa what would I have done?" Seraphina ce tayi maganar tana ƙaramar dariya hannunta dafe da ƙirji... '' meyasa kika kira sunan shi...'' Arman ne ya faɗi haka '' saboda shima mutum ne ...'' ta juya idonta Khalil kam tunda aka faɗi maganar sa ranar shi yanayin shi ya sauya, muna haɗa ido yayi ƙasa da nashi.. weird Farzan ne ya iso wurin hannun shi riƙe da kofin tangaran yana shan shayi a ciki ya zauna gefen Khalil yana kallon bajakolin kayan dake wurin da murna rubuce a fuskarshi da kowa bai kasa lura ba '' did you hit a jackpot?" Khalil ya ɗage gira..kurɓar coffee ɗin shi yayi da murmushin mugunta yace '' abinda yafi jackpot na samu...akwai wani abu dake cimin tuwo a ƙwarya.. yau nayi maganin ab...'' kafin ya gama magana,babbar ƙofar shigowa parlorn ta buɗe dukan mu muka mayarda kan mu...muga waye zai shigo Ƙamshin shi ya fara isowa kafin shida kanshi ya ɓullo...Romo ne...he was disheveled...gashinshi ya ɓaci ga ƙananan tabo a gefen baki da kuncin shi...ya yagalgalu Kamar wanda aka ƙwato daga bakin zaki...wurin yayi tsit kamar an ɗauke ruwa..kowa yabi shi da kallo.. tafiya yake kamar yanda ya saba.. fuskarshi kamar hadari, sanda ya wuce ta gefena sai da gabana ya faɗi... Farzan ya furzar da shayin dake bakin shi yana kallon Roman hakan ya dawo da kowa daga suman zaunen da sukayi Take fuskar Farzan ta canja daga murna zuwa fushi...Romo bai shiga elevator ba ta stairs yake bi '' ya akayi ka dawo?" Yayi tambayar hannayenshi dunƙule daga gefenshi..mun sha mamaki musamman ni dama bai kamata ya dawo bane? '' oh... disappointed to see me?'' kofin shayin shi Farzan ya wurga ma Romo... Na gwalalo ido kowa ya rufe bakin shi amma kofin bai cimma Romo ba ya tsaya few steps ƙasan shi...shayin yayi staining wasu daga cikin dresses ɗin da kuma farin tiles ɗin Farzan kamar zai kama da wuta... coldly Romo yace ''Lord!you're such an embarrassment to the male gender a new born baby would have done better!" sai ya juyo yana kallon Farzan dake tafasa fuskarshi tayi ja,ember eyes ɗinsa kamar ƙyanƙyashen garwashi flatly Roman yace '' idan kaji zafi,akwai bango a kusa bang your head on it! har abada bazaka taɓa matakin dana taka ba.. never!" Ya juya yana tafiya kamar babu abinda ya dame shi a duniyar nan...nabi bayan shi da kallo wani irin abu na sauka a zuciya ta game dashi... Lokaci guda bayan tafiyar shi muka dawo da kallon mu akan Farzan '' Dude...abinda kayi kenan? You targeted Rome so kake ka kashe shi?" A fusace Farzan yace '' nayi baƙin cikin rashin mutuwar shi!" Babu wanda ya ga sanda ta tashi sai dai gani muka yi ta share Farzan da mari...'' ɗan uwanka kake ƙoƙarin kashewa Farzan? I brought you up better than this.. '' sosai ɓacin rai ya bayyana a fuskar Hajiya Hafsah Hannu ya cusa cikin gashin shi ya faɗa da ƙarfi '' SHIBA ƊAN UWANA BANE!!" daga haka yabar wurin..da sauri Khalil yabi bayan Romo riƙe da sarƙarshi...Hajiya Hafsah tayi tsaye a wurin kamar an ɗasa ta.. '' kada Kiyi fushi Hajiya...lamarin yara sai a hankali!" Hajiya Ruƙayyah ta tausasa '' kuma gashi Roman ɗin ya dawo gida lafiya lau kiyi haƙuri!" Hajiya Wareesha ta ƙara '' dama shegen yaron da taurin rai...mai zai same shi? Mtchewww! dama ace ya karya koda yan ƙasusuwa ne!" Hajiya Momma ta faɗi hakan Seraphina idonta suka ciko da hawaye ta haye sama da gudu tana kuka... Mukhtar yake murmushin ɓoye '' gaskiya Farzan ya ƙetare iyaka wannan lokaci...'' inji Jawaad '' ko? Nasan da cewa dukan mu Bama son Roman amma duk da haka shi jinin mune...idan Hajjo ko kawu mansir suka san cewa Farzan ya yi ƙoƙarin raunata Roman,zai fuskanci hukunci mai tsanani!" Inji Ayaan '' Toh magulmata saura inji wani ya faɗi abinda ya faru..'' Hajiya Zeenatu ta kacace su da faɗa .. Hajiya Hafsah ta fara barin wurin cike da kunya kafin samarin suka zare jiki ɗaya bayan ɗaya Suma ma'aikatan company'n sallamar su akayi..ya rage mu yan aiki muka shiga gyara wurin da aka ɓata Tsofaffin yan aikin suna hira tsakaninsu bada gangan ba na samu kaina da saurare '' da ace Yallaɓai Roman ne yayi ma yallaɓai Farzan ko wani daga cikin yan gidan haka,da sai inda ƙarfin hajiyoyin nan ya ƙare wurin ganin an hukunta shi!" Lateefa ta faɗa murya ƙasa Hajar tace '' ai matan gidan nan munafukai ne, maraicin uwa a gida irin haka masifa ne abi a sakoka gaba yallaɓai Roman yana ban tausayi wallahi!" '' Toh ba yana da uba ba?" karima tayi tambayar Suka ja tsaki kusan lokaci guda '' uban ai hoto ne kawai! shida babu duk ɗaya ne! " Ban iyarda sauraren maganganun suba na bar wurin tausayin Romo na kamani...tafiya nake banma san inda zani ba ko ɗakin shi ban sani ba da sai na shiga...ina wannan tunanin na kawo wurin wata corner a ƙarshen corridor naga wata ƙofa baƙa nan ma babu number sai XXXX uku Ina tsaka da tunanin ko nan ne ɗakin shi naga Khalil ya fito daga ciki...ɓoyewa nayi sai da naga tafiyar shi daga wurin da sauri na isa bakin ƙofar na ƙwanƙwasa babu amsa daga ciki Tura ƙofar nayi na shiga, parlor na ci karo dashi wanda painting ciki da kuma furnitures ɗin ruwan toka ne ƙamshin shi ya cika wurin..a ciki ɗakuna uku ne...ban san wane ne ɗakin shiba Na tsakiyar na nufa naji ƙofar gam..sai na koma na gefen dama ina tura ƙofar ta buɗe Leƙa kaina nayi na hange shi kwance saman gado yana kallon ceiling da alamu bacci yake duba da yanda ƙirjin shi ke sama da ƙasa... Na shiga yanayi tsakanin in ƙarasa ciki ko in koma...daga ƙarshe na shiga ..ina tafiya a hankali har na iso bakin makeken gadon shi daya kasance baƙi kamar sauran abubuwan dake ɗakin duk da kuwa labule a sauke yake hakan ya ƙarama ɗakin duhu..wai shi komai nashi baƙi Wurin kanshi na tsaya ina leƙa kyakkyawar fuskarshi... zuciya tana tsananin bugu da ƙarfi...saye yake da baƙar riga data ƙara ma fatarshi haske gashin shi ya tarwatse saman pillow'n..hannu na miƙa zan gyara mashi blanket saboda akwai sanyi sosai Buɗe idonshi yayi kamar zombie,na firgita..ya damƙo hannuna ya jawoni na faɗo gefenshi ya mulmula kaina...kamar sojan dake kwance a tanti amma yana lure kada a shammace shi da hari... zuciya ta takawo maƙoshi...idona suka fito kamar zasu faɗi ya sakar min nauyin shi ...yake kallona kamar zai yanka ni da idonshi.. fuskar shiba annuri '' what're you doing here?" Muryarshi bata ɓoye fushin da yake ƙoƙarin dannewa ba '' Uhmm......dubawa nake idan kana numfashi...na ɗauka ka mutu...'' that was an awful lie... fuskar shi ta ƙara duhu,hucinsa yake sauka a fuskata da mugun zafi,ya tsare ni da shegun idonshi kamar yana karantar abinda ke wakana a zuciya ta.. gashi na kasa numfashi saboda yanda yabi ya haye ni kamar nima gadon shine...shi ɗan abunda ban ce ba... +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 27. ... Gentle man Khalil...🖊️ Da wani irin chilly voice kamar ƙanƙara yace '' what has my breathing got to do with you?" yawu na haɗiye ban yi tsammanin wannan tambayar daga gare shi ba...'' get out! kada ki ƙara shigo min ɗaki!" sauka yayi daga sama na..sai lokacin sanyin Ac ya bugo min...amma bai kashe zafin da jikina ya ɗauka ba...da sauri na sauka daga gadon na nufi hanyar fita '' Ke!" Ya kira da rainin wayo tsayawa nayi nima ina tafasa nace '' k ta cikin ABCD?" shima dai sai da ya gama laguda ta shine zai wani dinga cin magani,ɗan iska kawai! Ƙanƙantar da idonshi yayi akaina...murya ba wasa yace '' don't ever...kada ki ƙara shiga harkata...and don't try to get close to me!" '' oh...da farko ai na ɗauka kai kurma ne!me zanyi dakai? Mutum kullum cikin haɗe fuska kamar hadari...Hmph!" Da ƙarfi na bugo ƙofar ina ƙunƙuni kuma naji haushin kaina...da har naji tausayin shi ashe baida mutunci..'' and don't try to get close to me...me zanyi da tsoho kamar shi!" haushinsa sai ƙara ruruwa yake a zuciya ta..samun farzan nayi tsaye ya tokare ƙafa ɗaya a baya hannun shi cikin aljihu yana kallona da ido masu duhu '' so...da gaske ne ke budurwar shi ce?"yake kallona sama da ƙasa baki tsuke Juya idona nayi '' meyasa ƙwayar idonka yake ja? Ko dai kai ma vampire ne?!" Na tambaya a maimakon amsa tashi tambayar '' answer the darn question I asked!" yayi maganar da rashin haƙuri yana hararata matsawa nesa dashi nayi '' damar abun banyi kama da Google ba!" na bashi amsa kafin na sheƙa da gudu ganin yana shirin damƙo ni Bin bayan Abeedah yayi da kallo... idonshi suka ƙanƙance, '' You look like her....kina kama da ita sosai!" yayi maganar yana jinjina kai hannun sa cikin aljihu,lokaci guda kwanar bakin shi tayi sama murmushin mugunta ya wanzu a fuskarshi... '' Perfect!" Ya furta da poisonous voice sannan yabar hall way... Ɗakin Diyaam na tafi na ganta tana ƙoƙarin kama sumarta amma abun yaci tura fuskarta tayi ja '' Oh Abeedah..zoki taya ni...'' ƙarasawa nayi na karɓi tsinken daga hannun ta nayi tsagu kafin na fara kitsawa '' wai ya kuke samun dogon gashine?" '' haka gashina yake..kona aske sai ya ƙara tsawo!" Na zaro ido aske gashi tab ɗi jam... '' Abeedah kin taɓa son wani...? Wanda kike addu'ar samu kuna tare a koda yaushe amma duk da haka yay miki nisa?" Leƙa fuskarta nayi jin tambayar data jefomin '' wani kike sone?" girgiza kanta tayi amma nidai ban yarda ba '' ko Romo kike so?" Dariya ta saki harda hawaye tace '' shi ina mashi kallon yaya ne kawai...ban taɓa jin hakan game dashi ba!" Na gyaɗa kaina '' ni ban taɓa soyayya ba...ban ma san yanda ake jiba...amma ina so inyi experiencing karayar zuciya!" Da sauri ta juyo tana bina da kallon ' baki da hankali' Nayi dariya nace '' na san abinda kike tunani amma da gaske nake...ina so in san yanda ake ji idan mutum ya rabu da masoyin shi!" Na sake maimaitawa '' Allah ya maki magani!'' '' Ameen...'' Bayan na fito daga ɗakin Diyaam sashen muna koma na ɗauko wayata na kira Jay d muna ta hira..daga nan na kira su Mama..na kwanta ina tunani...duk da yace in fita daga harkar shi ji nayi ina so in ƙara tsoma kaina a harkar tashi dan in bashi haushi...zai gane baya da wayo... Bayan sallar la'asar nida su Fauziyya muna kitchen muna aikin jidar abinci kusan kala shida da masu girki suka dafa muna kaiwa a parlorn baƙi...wasu maza ne su biyar suka zo daga gani ƙawayen su Khalil ne... suna hira tsakaninsu.. Romo ya hakimce a kujerar shi shi kaɗai riƙe da littafin drawing ɗinshi duk hirarrakin da ake bai ko ɗago ba kamar babu shi a wurin naji kamar in kwarara mashi juice ɗin dake hannuna ashe da rabon wani daban zanyi ma wanka da juice...sanda muka shigo wurin dariya suke akan wani abu da ɗaya daga cikin maxan ya faɗa Fauziyya gaba sai wata yarinya tsakani nice ta ƙarshen shigowa.... Kun dai san Fauziyya yanda take yauƙi tana botsare botsare..ba ƙaramin kunya ta bani ba...duk cikin ma'aikatan ni kaɗai ce kesa hijabi... Shigowar mu wurin yasa sunyi ƙasa da dariyar su suka kafe muda ido... particularly wani wanda yafi sauran baƙi naji idon shi akaina ɗagowa nayi daga juice ɗin dana tsare da ido gudun kada ya zuba dan an cika cups ɗin har baki idona ya sauka a cikin jajayen nashi...yana da kyau amma nidai mummuna ne a idona '' Sassannun ku ina yini!" Fauziyya ta gaishe su da yauƙi '' lafiya lau'' suka amsa da fara'a '' Biatris tana ta neman ka Rom...'' ɗaya daga cikin maxan ya ɗaura hannun shi a kafaɗar Romo '' in mata me?" Ya tambaya batareda ya ɗago daga abinda yake ba '' well sonka take kasani fa...'' bai amsa ba ya cigaba da harkar shi '' We have Romeo among us...'' wani daban ya faɗa Khalil yace '' who is not Romantic!'' duka suka saka dariya...gayen nan dai har yanzu Idon shi na akaina sanda idon mu ya haɗu ya lashe baki kamar maye... tuni naji na kama da wuta... Fauziyya take zuƙunne a gabansu tana zuba masu abincin..nida ɗayar yarinyar munja mun tsaya gefe Sai juya idona nake...su wa'yannan mutanen basu san su Dena kallon mutum ba '' I.B,wannan kyakkyawar mai idon mage fa?" Wani daban ya nuna ni da wani banzan murmushi a fuskar shi... murmushin Khalil ya ragu '' Nope Auwal..kitten is off limits!'' '' shegen kaya...kace kanka kaima reservation!" Sauran suka sa dariya '' Allah yasa mutum ya sarƙe da abinci!" Na ɗauka cikin raina nayi maganar..sai da naga kowa ya dawo da kallon shi akaina nayi tsuru tsuru da ido '' ke Abeedah baki da manners ko gaishe su bakiyi ba kuma kina musu mugun fata!" Fauziyya ce tayi maganar tana maƙe murya... '' bulo aka ɗaura maki a maƙoshi ne? Naji kina magana kamar akuyar da aka shaƙe!" Fuskar ta tayi ja da fushi..na juya idona ita tasani.. Bayan ta gama iya yinta ta miƙe nida ɗayar yarinyar dake riƙe da wannan shrimps ɗin muka matsa gaba...tana tura masu suna ɗiba ni kuma ina miƙa masu juice Da Romo na fara dan shi yafi kusa kusa...ƙin karɓa yayi kuma bai ko kalle niba,sai dana kalli mutanen wurin naga hankalin su baya kai na,na karkatar da tray ɗin ina so in zuba mashi juice a jiki ,da wabi irin murya that could freeze an entire town yace '' idan koda ɗigo ɗaya ya sauka akai na,sai ma maki tsirara a wurin nan!" yayi maganar hankali kwance kamar ba abun banza ya faɗa ba "Subhanallahi!!!!" na faɗa da ƙarfi haɗe da ja baya,juice ɗin yayi gaba zai zube,ƙafa ta ta daku da table ɗin dake wurin,kowa ya dawo da idonshi kaina na kusa faɗuwa har na Runtse ido naji saukar hannu a ƙugu na,kafin ƙamshin turaren Khalil ya cika hancina zuciyata na tsananin bugu na buɗe idona suka sauka cikin na Khalil dake kallona da kulawa, hannu na a kafaɗarshi, kamar daga ni sai shine a wurin...duk wani surutu da abinda mutanen wurin ke faɗa yayi nesa da kunne na as I got lost in his hazel eyes ''You'kay?'' ya sake tambaya a karo na ba adadi, da sauri na sake shi kunya tasa na kasa ɗago kaina,idon mutanen wurin sai yawo yake a kaina suna maganganun da bana ji saboda yanda kaina ya fara ɗaukar zafi,haka ma ƙasan idona,sai na ɗago na kalli Khalil idon mu ya haɗu,ban san meya faru ba kawai na fara hawaye kafin nasa hannuna na tare fuskata ina kuka sosai '' hey.. it's okay..'' ya faɗa gently yana matsowa kusa, da sauri naja baya zan bar wurin,wani irin azababben ciwon dayasa nayi losing balance zan faɗi naji ya ratsani a karo na biyu naji hannunsa zagaye da cikina ya riƙo ni gam kafin in kai ƙasa '' i got you...'' ya ɗago ni sannan ya riƙe kafaɗuna muka fara barin wurin,har lokacin ban dena kuka ba sai haƙuri yake bani,ina tafe ina ɗingishi wai harda tambaya ko ya ɗauke Ni...ina hauka ne? Su Seraphina su cinye ni ɗanya sashen shi muka wuce ya zaunar dani a ɗaya daga cikin kujerun dake parlorn ya wuce ɗakin shi sai gashi ya dawo da wani ointment,ya durƙusa gabana ya riƙo ƙafar '' ina ke ciwo?" kasa amsawa nayi sai sheshsheƙar kuka da nake kamar zan shiɗe,hawaye na ɗiga a hannunsa, a nutse ya ɗago ya kalle ni,ya riƙon fuskata yana share min hawayen '' ki dena kuka kin ji,idan ciwon yayi tsanani zan iya kai ki asibiti..'' da sauri na girgiza kaina, sannan na nuna mashi inda ke ciwon,cike da kulawa ya shafa ointment ɗin yana tausa wurin,duk da zafin da nake ji na hana kaina ihu,sai kuma na kafe shi da ido he looked so perfect, wannan shine gentleman ba ɗan iskan Roman ɗin nan ba... mtchewww... mugun banza ina wannan tunanin ya ɗago,idon mu ya sake haɗuwa, zuciya ta tafara bugu da ƙarfi,sai lokacin ma na lura da yanda muke kusa kusa sosai,for some seconds babu wanda ya ɗauke nashi sai kuma lokaci guda muka kauda kawunan mu gefe '' uhm, kina jin yunwa?" ya tambaya tare da miƙewa,na girgiza kaina..sai ya gyaɗa kanshi,ya kai ƙofar fita daga sashen,nabi bayan shi da kallo sai kuma ya dawo ya kunna min TV '' you can wait here till you get better!" yayi maganar yana kallo na, nayi ƙasa da kaina dan wani irin nauyin shi nake ji haka kawai... da ƙarfe biyar muka taru a wurin swimming pool muna tsame ganyayyakin da suka faɗa ciki...aikin yayi min daɗi Fauziyya take harara ta a kaikaice ban ankara ba ta jefani cikin swimming pool ɗin amma kafin in faɗa sai dana jawota mu biyun muka faɗa tare... Sauran suke bin mu da kallo...a mamakin mu sai gani mukayi suma sun afko ciki..daga aiki muka ɓuge da wasa... Diyaam tazo ta taya mu aiki na jawota muka shiga watsa ma juna ruwa babu wanda ke nutsewa cikin mu kenan dukan mu yan ruwa ne.... '' meyake faruwa anan?!" Su Seraphina ne suka iso wurin ɗaure da wasu ƙyallaye a ƙugu da breziya Innalillahi wa inna ilaihi raji'una kamar wasu kafurai... Da gudu muka fara fita daga swimming pool ɗin kamar kifaye ruwa na tsiyaya daga jikin mu Ƙin bari mu koma cikin gida sukayi wai mu tsaya nan sai mun bushe kuma fa akwai sanyi....babu wanda ya lura da akwai hadari cikin mu aka tsuge da ruwa suka wuce ciki suka barmu tsaye a waje Yaran nan mugaye ne na ƙarshe...wasun mu kamar zasu suma... Mukhtar ne ya buɗe wurin da wata mai aiki maƙale a jikinshi suna abinda suke...da sauri na runtse idona na rufe ma Waleeda da DIYAAM nasu ... Sauran ma they were shocked '' kubar wurin nan!" Ya faɗa cike da rashin kunya da gudu muka dinga wucewa ciki wasu daga cikin ma'aikatan muryoyinsu da ɗaci nidai ina ruwa na.... Sashen mu muka wuce muna dariya na samu Mama Asabe kwance tana bacci a karo na farko salin alin na canja kaya na zauna ina rawar sanyi...da ƙarfe tara muna babban gida a kitchen nida Diyaam muna wanke wanken daya ƙi ƙarewa tsabar yawa... Heedayah ce ta bamu wannan a matsayin punishment... '' yaran nan mugaye ne...'' na faɗa ina wanke wani ƙaton plate daya girmi hannu na Romo ne ya shigo kitchen ɗin DIYAAM ta gaishe shi ya gyaɗa kanshi kawai,take na tuna abinda ya faɗa a parlon nan idan ka ganshi kamar na Allah ashe iskanci ne cike da cikin shi, ɗauke idona nayi daga kallon shi wani cupboard ƙarami ya nufa ya zaro makulli daga aljihun shi ya buɗe ya ɗauki wani abu a cikin leda kamar lipton ya zuba ruwan zafi ya tsoma ciki ya koma can gefe wurin ɗauko cokali Cup ɗin kawai na matsar daga inda ya ajiye ina share wurin .yana zuwa ya ɗauki cup ya zubar da Lipton ɗin simply saboda na taɓa....nabi shi da kallon mamaki ya sake haɗa wani yayi gaba ''baya so ana taɓa mashi abu musamman abinci ko sha...'' '' kaji min wani rainin wayo...'' daga nan na ƙudiri aniyar koya mashi hankali wallahi Ranar juma'a da daddare mun aikatu ƙaton hall ɗin nan da muka share kwanakin baya muka koma muna laƙa ƙananan globes masu haske kalala...sai wasu manya manyan speaku da aka samu gogewa suma aka kai a can...abubuwan ciye ciye wa'yanda bazasu lalace ba da sauran su...ranar sai ƙarfe ɗaya mukayi bacci Washegari muka tashi da wuri muka cigaba daga inda muka tsaya su Seraphina ansha kwalliya kamar Disney princesses...sauran ma sun ɗau ado na kece raini amma matasan kaɗai suke abinsu su Hajiyoyin na sashen su babu wacce ta leƙo Samarin ma ba ƙarya da ƙarfe goma party ya kankama harda caterers akayi hayarin bayan wa'yanda ke dafa abinci a gida... ma'aikata sai nan da can muke bamu da lokacin hutu sai lokacin salla gida ya karaɗe da waƙe waƙe... Cikin hall ɗin kuwa mata da maza ne ake ci ana sha ana raye raye da wasanni..suma wa'yanda aka gayyato party'n ya'yan wasu ƙwari ne a gwamnati sai jiji da kai... Wurin ƙarfe huɗu na tafi kitchen aka turani ɗakin Mukhtar da drinks...tunda naji sunan shi Nasan ba Alkhairi zan tarar ba,ai kuwa dana shiga ban gan shiba sai da na ajiye plates ɗin zan juyo aka rungume ni ta baya ... ihu na saki yayi sauri toshe baki na ya jefani saman gado yayi tsalle zai faɗo sama na... bedside lamp na kwaɗa mashi ya faɗi gefe Jiki na ɓari nayi ƙofa yana biye dani a baya... '' ba zaki tsaya ba...ki tsaya nace!" Inaaaa ban ko jishiba sai dana fita daga gidan gaba ɗaya...na isa wurin motoci na shige cikin wata baƙar mota dake buɗe na ɓoye a baya jikina na tsuma...idan fa aka Kore Ni? ' sai ki koma gida,kina da Mama!' zuciya ta taban amsa...hawaye ne suka ciko idona dana tuna abinda Mama ta faɗa Bada daɗewa ba naji anbuɗe gaban motar an shiga..tsoro ya hanani ɗagowa a tunani Mukhtar ne ya biyo ni...ji nayi an tada motar kafin aka ƙara gaba...gabana ya shiga faɗuwa...motar waye na shiga Kuma da gudu ake tuƙa motar Innalillahi ni Abeedahtuwo...da ƙyar na ɗago daga duƙen da nake a baya inga ko waye...gabana ya faɗi da ƙamshin Romo ya daki hancina idona ya haɗu da ƙeyarshi ƙasa na sake yi da kaina zuciya tana dukan tara tara...bayan tafiya mai tsawo motar ta tsaya...ɗagowa nayi naga munkawo cikin wani wuri kamar daji mai ɗauke da fulawowi...fita yayi ya zagayo ya buɗe bayan motar idon mu ya haɗu...bai nuna alamun mamaki ko akasin haka ba, abubuwan painting shi dake baya ya ɗauka yabarni a wurin... Da sauri na buɗe ƙofa nabi bayanshi...haɗuwar wurin ya tafi da zuciya ta dama kuma ƙarfe huɗu da rabi tayi a lokacin....i couldn't believe he brought us to a meadow...duk yanda zan faɗi tsaruwar wurin bazai faɗu... ƙarƙashin wata bishiya mai ƙarancin hasken rana ya ajiye abubuwan shi,saye yake da farar riga da baƙin wando a karo na farko ya haɗa wata color daban da baƙi hair clip ya ciro daga aljihun shi ya tattare gashin shi ya ajiye abubuwan drawing ɗinshi ya shiga aiki.... Bai yimin magana ba,bai kalli inda nake ba nima na share shi kawai...ina wasa tsakanin fulawowin na manta da abinda ya faru tsakanina Mukhtar.... Bishiyar da yake a ƙarƙashi nake zagayewa da ɗan gudu gudu ina dariya...ga sassanyan iska dake kaɗawa ƙamshin furanni na tashi na ɗauka ƙarya ne idan ana nunawa a fim yanda suke shaƙar fulawa wai tana da ƙamshi sai yanzu na tabbatar ba ƙarya bane da gaske ne.... Ƙila ya manta dani ko sau ɗaya bai kalli inda nake ba... ciyayi da fulawa na kwasa a hannuna na watsa sama '' yeyyyy!!!!!" Na saki ƙara da nishaɗi..sai dai naji idanu akaina kamar zasu huda ni da sauri najuyo naga yana kallona kamar ya mangare ni Kallon drawing ɗinshi nayi naga ashe ciyayin dana watsa sama sun sauka akan painting ɗin '' oh! Yi haƙuri...'' matsowa nayi kusa ina cire hakukuwan amma painting ɗin ya ɓaci sosai ƙirjin shi sai sama da ƙasa yake '' Uhmm,ba wannan setting ɗin ka zana ba,idan ciyayi sun faɗa sama...ai duk cikin yanayin ne ko?" Na kalli hannu na daya ɓaci da kala naja baya da murmushin rashin gaskiya sai kuma na kwasa da gudu ina dariya sosai... Sabon page ya buɗe ya fara wani drawing ɗin daban ni kuma na cigaba da wasa nesa dashi...harda cire takalmi ƙasan wurin da taushi..kwantawa nayi ina mulmula..can na miƙe jin gurnanin wani abu kafin shuke shuken dake wurin suka fara motsi kamar wani gagarumin abu zai fito '' Ahhh!!!!!" Na saki ihu tareda yasar da hijabina gefe wani ƙaton ƙadangare ne yayi supa ya haye min saman kai Ba burki nayo cikin Romo daya bayarda duk hankalin shi wurin zanen shi...jin ihuna yasa ya juyo nikam sai kakkaɓe kaina nake ido rufe nayo cikin shi nida shi mukayi baya baya muka faɗi,cikin painting ɗin daya sha wahala kafin ya samu ya fito...idona ya sauka cikin nashi dake ɗauke da matsanancin fushi tureni yayi daga jikinshi ya tashi zaune da sauri Sakin baki yayi daya fahimci ashe kwance yake saman painting ɗin bayan rigarshi ya ɓaci da kala.. painting ɗin ya dame '' LORD GIVE THE PATIENCE!!!" Ya furta da ƙarfi...nafara ja baya...ya miƙe tsaye yana goga haƙoranshi ya nuna ni '' You!..." He was speechless sai hura hanci yaki jikinshi na rawa..na rakuɓe wuri guda duk kunya ta kamani Gaba yayi yabarni a wurin da sauri na ɗauki hijabina nasa bayan na kakkaɓe nabi bayanshi..ba takalmi...sai tafiya yake da sauri har lokacin temper ɗin shi yaƙi ya sauka... Muna ta tafiya cikin daji cikin shiru...'' yanzu fa idan akwai namun daji a wurin nan?" Na faɗa ina kallon ko ina '' ko akwai kura?" Nayi tambayar ina kallon gefen shi '' kasan hanya kuwa?" Na daɗa jefo tambayar bayan wani lokaci '' idan fa dare yayi? Idan fa namun daji suka cinye mu? Idan fa muka ɓace? Idan fa aka fara ruwa?...'' riƙe kumatuna nayi idona sun kasa tsayuwa wuri guda..sai tafiya muke gashi dare na ƙara yi Can naji kukan wani abu kamar kura Hannun shi na damƙa a tsorace...ƙwace hannun shi yake ƙoƙarin yi na ƙara damƙe shi...'' tsoro nake ji...'' '' idan fa bamu...'' '' One more word and I will chew your lips and spit them on the ground!!!" Daga ƙarshe dai ya fashe, tohhh kun dai gani na faɗa maku mutumin nan tantiri ne,wai zai cinye min baki kai!... da sauri na rufe bakina,ina kallon shi ido waje,ya kamata inyi nesa da mutumin nan tunda ba mutumin arziƙi bane,sai kawai na jinjina kaina amma ban saki hannun nashi ba...dajin tsit babu abinda ke tashi sai kukan tsuntsaye duhu kuma ya fara sauka.... 🍁🍁: baki sake shiba bakince zakiyi nesa dashi ba? Abeedah: cikin dajin zanyi nesa dashi inje ina? nasan hanya ne?😡 🍁🍁:🤭 Bayan wani lokaci na sake jin motsi cikin bishiyoyi kafin wani abu mai jajayen ido ya fito daga wurin....ido waje banko tsaya naga menene ba na saki ihu nayi tsalle na haye shi fuska ta ɓoye a gefen wuyanshi, hannuna dafe da idon shi '' ROMAN!!!!!!" +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 28. ...yayi fushi...🖊️ Bayan na saki wannan ihun daya kusa fasa mashi dodon kunne, wurin yayi tsit...bai riƙe niba hannayen sa toshe da kunnuwansa fuskarshi kamar hadari yana wasa haƙoranshi kamar yana ƙara masu kaifi dan ya cije ni..ɗagowa nayi idon mu ya haɗu...takaici da haushi na gani a ciki... '' Damn! It's just a rabbit,and here you're trying to destroy my ear drums!" turo baki nayi can kuma na fara kalle kalle idan da gaske hakan ne,wani farin zomo mai fato faton kunnuwa na gani riƙe da wani abu a hannun shi yana ci...'' shegen abu ya kusa bani hawan jini!" '' zaki sauka ko cigaba da kasancewa a haka zakiyi?" Oh...sai lokacin naga yanda na ƙanƙame shi kamar rayuwata ta dogara dashi...da sauri na sauke ƙafafuna daga ƙugunshi na warware hannayena daga wuyan shi... Ya juya ya cigaba da tafiya ina biye dashi kukan wannan abun kamar fara da sauran abubuwa duk ya cika dajin...na tabbar da yanda sama tayi duhu wurin ƙarfe shida da rabi ne.. '' Zom...ina nufin Romo ka tabbatar ka san hanya kuwa?'' bai kalle niba can yace '' ina fama da ciwon mantuwa ai ...'' Tsayawa nayi na rufe bakina '' Innalillahi shine ka kawo mu nan? Yanzu ya zamu kumo gida?" '' i didn't force you into my car did I?" '' ai da sai ka faɗamin in fita!" Ɗage kafaɗa yayi ya cigaba da tafiya...nikam ina tafiya gefen shi ina kallon nan da can sai nake ji kamar za'a iya kawo mana hari... Kafafuna duka sunyi ciwo..tsoro ya fara shigata da gaske amma mutumin nan ko a slippers ɗinshi... '' wai shekarun ka nawa?" na tambaya ina kallon shi '' none of your business!" Muryar shi ta fito da zurfi da kuma fushi...to daga tambaya? '' na faɗa maki.. don't try to get close to me baki ji ko?" ya sake faɗa..kallon space ɗin dake tsakanin mu nayi '' akwai taku uku tsakanina da kai,taya na matso kusa da kai?" na haɗe fuska nima wa zai dinga raina ma wayo? bai ce komai ba... badaɗewa ba muka iso ƙarƙashin bishiyar nan daya fara zanen shi nayi mamaki sosai... Kwashe abubuwan shi yayi nima na sako takalmi na yana gaba ina biye dashi ***** Tsaye Khalil yake a ƙarƙashin shower ruwan sanyi na dukan shi idonshi sunyi jawur..hannun shi ɗaya dogare da bango ɗaya dunƙule daga gefen shi, jijiyoyin kanshi sun miƙe..ƙirjinshi na sama da ƙasa...ya karya alƙawarin shi! Ya sake yin abinda ya riga da ya rantse bazai sake komawa ba...how was he so weak? Meyasa bai hana kanshi ba? Runtse idonshi yayi zuciyar shina tafasa... numfashin shina fita da zafi kashe ruwan yayi dan aƙalla yayi kusan awa ɗaya da rabi a wurin...kayan jikinshi ya fara cirewa ya jawo tawul cikin duhu dan bai kunna wuta..baya so yaga reflection ɗinshi... Bayan ya ɗaura clumsily ya fito daga bayen ko kaya bai saba ya faɗa saman gadon shi yaja blanket ya rufa yana rawar sanyi,'' Astaghfirullah'' ya furta da muryar rashin lafiya.... Mukhtar kuwa zaune yake a gaban madubi ya ɗauko first aid box yana kula da ciwon da Abeedah ta jima shi, every now and then he groans, bazai bar yarinyar nan ba,ko badaɗe ko bajima sai ya cimma burinshi...it was her fault! He got seduced kawai bayan ta kalle shi yanzu kuma sai ta hana shi? Impossible! da yafita don cigaba da party'n kowa sai tambayar shi yake mai ya same shi '' mind your business '' shine amsar...can ya zauna a wata kwana sai ga Hansa'u ta saci jiki ta zo wurin shi tana yauƙi..baƙaƙen uniforms ɗin jikinta sun matse ta sosai '' yallaɓai kana buƙatar wani abu ne?" ta tambaya in a slutty voice Kallonta yayi da takaici ya daka mata tsawa '' get out!" kamar wacce ta haɗu da zaki ta bar wurin da sauri kamar zata kife...shima tashi yayi ya fita daga gidan cikin motar shi... Tsaye take a ɗakinta ta kasa zaune ta kasa tsaye sai nan da can take...wurin ƙarfe goma ta leƙa window'n ɗakinta ta hangi motar Roman ta shigo cikin gidan...bayan yayi parking a parking lot gani tayi ya fito ya buɗe ƙofar baya ya ranƙwafa ya faɗi wani abu sai aka buɗe ɗayan side ɗin Abeedah ta fito Zallo zuciyar ta tayi daga ƙirji zuwa maƙogaro idonta zazzare..it can't be right? Da sauri ta koma bakin gado ta ɗauki wayarta ta shiga contacts wata lambar da bata kira ba in years ta zaƙulo sai da tayi kokonto na yan mintuna kafin ta danna layin... wayar ta kusa katsewa kafin a ɗauka '' I have got a job for you...'' ****** Ban san sanda muka shigo gidan ba dan bacci ya ɗauke ni naji ya buɗe ƙofar bayan yace '' ki fito ki kwanta nan ƙasa...i want to lock my car!" ina yabon shi sallah zai kasa alwala '' na gaji sosai kaɗan ɗauke ni ka kaini sashen mu...'' na miƙo hannuwa na kamar da gaske ina ƙoƙarin riƙo wuyanshi Ja baya yayi '' I'm too lazy to do that! Ki fito ko in rufe ki ciki.. '' da gaske yake fa hakan yasa na shafawa kaina lafiya na fito ƙafafuna sunyi tsami.. Allah yasa munyi salla a wani masallaci bakin hanya harda abinci ya siya min ashe yana ɗan da mutunci... Rufe ƙofar yayi,ina gaba yana biye dani baya har muka kawo sashen mu...na tsaya bakin ƙofar wurin har zai wuce nace '' Romo...'' Ɗage gira yayi hannayen shi cikin aljihu '' kai kaɗai zaka kwana a wannan ƙaton ɗakin naka?" '' so?" ya furta da rashin haƙuri '' bari in kwaso kayana inzo in taya ka...'' kallo ya ƙare min daga sama har ƙasa yace '' fitsarin kwance nake gudu...'' yayi gaba abinshi ya barni da sakin baki.. '' Goodnight Roman...'' na faɗa ina juya mashi hannu da murmushi a fuska ta ɗan dakatawa yayi ya juyo ya kalle ni ya gyaɗa kai kawai baice komai ba... Nayi tsaye har saida ya shige gidan su Sannan nima na nufi ɗakin mu.. zuciya ta da farin ciki da kuma tunanin shi...mai yasa nake tunanin shi? he's growing on me isn't he? Wanka nayi na canja kaya na kwanta murmushi yaƙi barin fuskata...sanda bacci ya ɗauke ni mafalkina cike yake da Romo a wurin da muka tafi da kuma wasu wuraren daban... kuma Nasan daga wannan lokacin baxan sake kallon shi iri ɗaya ba... Washegari mutum uku ne basu zo wurin kari ba,harda Mukhtar dasu Romo da Khalil...ko meya sa... Su Seraphina babu abinda suke magana akai sai party'n jiya...Farzan na lura da yanda yake kallona...ba irin kallon Mukhtar ba amma nashi kallon yafi tsoratar dani,ƙasa nayi da kaina... Yauma mun ci sa'a ba aci mutuncin mu sosai ba...wurin ƙarfe goma muka shiga lambu dan zaƙulo shukokin da suka mutu naji yanayin wurin ya bambanta dana koda yaushe rana taɗan hudo glass roof ta haska wurin kaɗan sai ƙamshin furanni dake tashi da kuma sanyayyar iska... Gloves muka sa a hannayen mu dan wasu daga cikin shuke shuken suna da guba...can sai ga Diyaam ta shigo itama...muka taru dasu waleeda da Aina'u muka zaɓi section ɗaya muna aiki akai suma sauran abinda sukayi kenan... ranar tayi min daɗi amma ban haɗu da Khalil ko Roman ba..meyasa? naji raina ya fara min ba daɗi... Ranar Monday muka tafi makaranta, su Asma'u suka zo da ɗan tamalele aiko gaba ɗaya yan ajin mu aka zagaye seat ɗin mu..an face kowa ya jira aci da guda guda amma haka yaran nan suka daka wasoso daga ƙarshe wasu basu samu ba,mu kuma hijaban mu sun ɓaci da manja...amma waya damu? abu mai muhimmanci shine muna tare kuma muna farin ciki... Jay d taxo da wayarta mukayi hotuna da video.. jarabawar mu zata fara ranar laraba..duk da ina farin ciki dan nayi karatu,hakan bai hana jikina sanyi ba daga lokaci zuwa lokaci... Yau ma da kaina na koma gidan, DIYAAM kuma dama tana da dreba... mutum na farko dana fara cin karo dashi bayan na wuce gate ɗin shine Roman... zuciya ta tafara bugu da ƙarfi...wani irin murna ta kamani..kafin in yanke hukuncin zuwa wurin shi ƙafafuna har sun kaini..zaune yake saman mashin ɗinshi kayan jikinshi baƙaƙe kamar ranar...ya riƙe helmet zai sa na tsaya gefen shi...na kai hannu na zan taɓa wani button akan hannun mashin ɗin ya juyar da kan..tare da kallona sau ɗaya ya ɗauke kai '' inzo muje?" Na tambaya da murmushi...'' no thanks!" Ya bani amsa yana tada mashin ɗin '' wayyo bafa damunka zanyi ba!" '' You look dirty...matsa kada ki shafa min!" turo baki nayi '' xan taya ka hira fa..'' na share abinda ya faɗa game da uniforms ɗina '' nace ina buƙatar abokin hira ne?" '' exactly! Nasan ba zaka iya faɗa ba shine yasa nake yimaka tayi...'' wani jan botin na latsa saman mashin ɗin ya fara tsuwa jar wuta na kawowa tana ɗaukewa '' bar wurin nan!..'' '' Bar wurin nan!" Muka faɗa a tare dan dama nasan abinda zaice kenan...ƙanƙantar da idonshi yayi..nayi dariya... helmet ɗin yasa na kunce igiyar daya gama ɗaurawa na tsere da gudu nabar wurin... Su Fauziyya na gani zaune suna kallo.. da gani na suka rakani da harara '' yar wata sai ƙoƙarin cusa kanta take a wurin masu gida... yallaɓai Roman babu abinda zai yi dake!" Rasheedah ta faɗi hakan...ban tanka ba na shige ɗaki.. Bayan na sauya kaya na koma ƙasa naci abinci na tafi babban gida nayi ƙananan ayyuka harda wanke ma seratena pants yarinyar ƙazama ce...yan matan zaune suke a ɗakinta suna hirar soyayya... Mufeedah tace '' ai idan kana son mutum zaka so ka kasance tareda shi koda yaushe sannan zaka ji kana farin ciki idan kuna tare kuma zaka so kaganshi cikin farin ciki da abubuwa da dama...'' '' toh magulmaciya mai kike saurare?" Jameelah ta jefeni da pillow '' abinda har abada bazata samu ba da wannan mummunar fuskar tata!" Khaleesat ta bata amsa '' da yake Allah ke bawa Kowa nashi rabo!" Ina jin yanda suke kirana in dawo su cimin mutunci na share su nayi gaba abina... Haɗuwa nayi da Farzan a hallway naga yana tunkaro ni...ji nayi gabana ya fara faɗuwa yana isowa inda nake baiyi wata wata ba ya rungume ni..na shiga shock...Roman yazo ya wuce mu kamar babu mu a wurin da sauri na ture Farzan da bai ko kalle niba bayan wucewar Roman...amma dai wannan gaye...fushi naji ya cika ƙirjina naja dogon numfashi na wuce ɗakin DIYAAM.. ganinta nayi tana karatun jarabawar mu..na zauna muka cigaba a tare duk da ba wani fahimta nake ba saboda abinda farzan yayi min da kuma Roman daya gan mu... Ina ɗakin Diyaam har lokacin sallah'r Isha'i sannan na wuce dining Samun su nayi suna magana akan wannan Fateemah Cora Maman Roman suna faɗan baƙaƙen maganganu akanta... musamman Hajiya Momma.. Hajiya Hafsah dai tayi shiru abunta da gani bata son hayaniya Can anjima Roman yazo wurin amma duk da haka basu dena maganar taba... dunƙule hannun shi yayi saman cinyar shi Hajiya Momma tace '' An apple doesn't fall far from the tree ai,wayasani shima abinda yake kenan...'' '' dayake jini yafi ruwa kauri ba!'' Hajiya Wareesha ce ta faɗi hakan... Slowly Roman yace '' da gaskiyar ki...i suggest kafin Kiyi magana akan wasu,ki fara duba naki ya'yan..after all we won't want you eating your words do we?" Ya ƙarashe yana kallon Mukhtar,Wurin yayi tsit bayan ya faɗi hakan... '' baka da kirki yaron nan! Baka san ka girmama na gaba da kai ba!" inji Hajiya Zeenatu '' unfortunately wannan kalmar 'girmamawa' babu ta acikin dictionary ɗina.. especially ga mutanen da basu girmama kansu ba first!" Ya miƙe tsaye yana kallon Hajiya Momma yace '' you talk big on morals...idan akan tarbiyya ne,baki kama ƙafarta ba...'' Hajiya Momma ta ƙwalalo ido dining yayi tsit Ya juya zai bar wurin ya ƙara da faɗin '' none of you are qualified to talk about her with your contaminated mouths!" Hajiya Momma kamar zata kama da wuta tsabar haushi da takaici... Farzan bai ce komai ba...suma sauran matan sai hura hanci suke naji Roman ya ƙara bani tausayi...rashin uwa ba ƙaramin abu bane ... amma ina take? ko tabar gidan ne? Da ƙarfe tara na yanke shawarar zuwa ɗakin Khalil in duba tunda kwana biyu ban ganshi ba... Tura ƙofar nayi na ganshi kwance saman gado rabin jikin shi rufe da bargo..ƙarasawa ciki nayi ɗakin ba haske sosai nake kallon fuskar shi datayi alamun rashin lafiya...ashe baida lafiya? wake kula dashi to? Buɗe ƙofar akayi,da sauri na juyo naga Roman ne ya shigo saye da kayan bacci baƙaƙe da takalmi masu laushi suma baƙaƙe hannunshi riƙe da plate...ƙarasowa yayi ya tsaya ɗayan gefen bai cemin komai ba ya yaye bargon ya taɓa gefen wuyan Khalil..sai ya tashi ya shiga Baye ya ɗebo ruwa cikin rober ya zauna gefen shi yana goge mashi goshi da kulawa...bayan lokaci kaɗan Khalil ya buɗe idonshi kafin ya yunƙura ya tashi zaune... abinda ke cikin robar ya fara ba Khalil a baki...sai ya mutse fuska yake alamun bai so...'' if you don't eat,taya zaka ji sauƙi?" Khalil yace '' wannan Italian recipe ɗin naka ne ba daɗi.. '' muryar shi da rashin lafiya...nake kallon su biyun yanda Roman keta ƙara cusa ma Khalil koma meye shi kuma yana ƙoƙarin kauda kanshi...daga ƙarshe dai sai daya shanye tass, Roman ya share mashi bakinshi sannan ya kwanta...ya gyara mashi blanket.. Ya tashi zai tafi Khalil ya riƙe hannun shi,ya juyo slowly yace '' thanks Rome...'' gyaɗa kanshi Roman yayi...ya nufi ƙofa..da alamu Khalil bai ganni ba yasa nima na fita cikin shiru Lokacin har Roman ya ɓace..naso inyi mashi magana amma ba dama... Washegari ban tafi makaranta ba dan Nasan babu abinda zamu yi... babban dalilina na zama gida kawai ina so in haɗu da Roman ne... Zagaye gidan na fara yi har na kawo wurin ƙofar XXX...babu kowa a corridor'n kuma ƙofar da alamu buɗe take yasa na tura na shiga...cikin sanɗa... ƙanshin turpentine (ruwan wanke brush) da zaitun da tsofaffin littattafai ya daki hancina...ƙanƙame jikina nayi cikin hijabi saboda sanyi Babban taga daga ƙasa zuwa rufi, gilashinsa fari ƙal . Hasken safiyar ya shiga ya faɗa akan wani ƙaramin akwati baƙi mai ratsin zinari mai bala'in kyau Baƙar kujera ta fata a tsakiya, . A kusa da ita akwai easel na itace, an fara painting akai amma ba'a gama ba Bangon dama duka shelves ne. Akwai 🖌️🖌️ painting brush ko wane size , sai wasu ƙananan drawers da diary ɗinsa a sama mai baƙin cover Bangon hagu kuwa... komai baƙi ne. Yana cike da zane-zanen da idan mutum ya kalla zai iya jin emotions da kuma ciwon da suke fuskanta A ƙasa akwai tabo-tabon paint. Ja, baki, blue. Kamar taswirar raunukansa.... Akwai wani rubutu da Yaren daban gane ba da alamu da baƙin painting aka yi shi da hannu Questo è il mio mondo... dove esisto da solo.`** (Wannan duniyata ce... inda nake wanzuwa ni kaɗai.) Ɗauko allon nayi daga inda yake na ajiye a gaban bangon glass ɗin nan na ɗauki brush da painting na cigaba daga inda yatsaya kamar wata ƙwararriya a harkar zane...daga ƙasa na rubuta sunana nayi signing Ja baya nayi na goge zufar data tsatstsafo min a goshi da murmushi a fuskata kamar na cinye lottery... sosai zanen yayi kyau a idona,ba wata yarinya bace yake drawing ni kuma na iyar mashi... ''WAYA CE KI TAƁA MUN?'' muryar shi ɗauke da fushi da sanyi mai illatarwa ta sauka a kunne na, a firgice na juyo hakan yasa plate ɗin dake kai yabar hannu na yayi sama kamar ana controlling ɗinshi ya sauka akan fuskar shi sannan yayi ƙasa ya ɓata rigar dake jikinshi kafin ya faɗi ƙasa ya baltsu a takalmin shi farare...nima garin Juyowa na rasa balance na faɗa cikin painting ɗin dana gama yi yanzu nida allon painting ɗin crashed on the floor...datse bakina nayi dan hana ƙarar data kawo maƙogwarona fita... Tsabar yanda ɗuwawuna suka sauka akan katakon da ƙarfin daya sa na ɗauka for a second baxan sake iya zama ba...ido waje ina numfashi sama sama Ƙafafuna buɗe gashi babu damar sosawa tsabar yanda yake kallona da takaici.. fuskarshi tayi ja..ƙirjin shina sama da ƙasa bakin shi a tsuke kamar yana hana kanshi magana Nuna ni yayi jikin shi na tsuma yace '' You...! Why does my painting have to pay the price for your clumsiness!" Sai ya koma shafa goshin shi kamar tsohon daya gaji da rashin jin jikokinshi Da ƙyar na miƙe tsaye nace '' ba kaine ka tsorata niba...'' idonshi ya sauka akan painting ɗin shi dana lalata '' Oh my God what have you done?'' ya ɗaura hannunshi saman kai..ya wuce ni zuwa allon dake kwance ƙasa....ya ɗauki brush ɗin daya karye sanda muka faɗi Da matsanancin fushi a fuskar shi ya miƙe yayi cikina samun kaina nayi daja baya zuciya ta na tsananin bugu....hancin shi har wani huci mai zafi yake fitar wa Hannu na ya damƙo yaja ni da ƙarfi ya fitar dani daga ɗakin....na juyo zan bashi haƙuri ya buga ƙofar da ƙarfi kamar zai ruguje gidan duka... Kin ƙetare iya ka...hajiyar su🤭 +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 29. ...tayi mashi magana...🖊️ Da sauri Roman ya isa wurin allon bai bi takan painting ɗin ba ya ɗauki brush ɗin daya karye yana kallo like it's the most precious thing in the world...idon shi turned blood shot numfashin shina fita da zafi..taune leɓenshi yayi feeling sick to the pit of his tummy... Wannan brush ɗin yana daga cikin memories ɗin da mahaifiyar shi tabar masa...shine farkon kyautar ta a gareshi bayan ya fara zane...she was the one who taught him painting..and now this clumsy girl... Miƙewa yayi ya gyara komai da komai a studio ɗin ya kashe wutar ya fito..ɗakin shi Ya shiga ya sauya kaya zuwa baƙaƙe daga sama har ƙasa ya tattare sumar shi into a bun ya fito... elevator ya shiga kafin ta rufe Farzan ya faɗo ciki... Roman bai kalle shiba...da wani smug face Farzan ya tsaya gefen Roman yana cin chewing gum yana ƙaras ƙaras... Wayar Farzan ce tayi ringing ya duba yaga Hajiya Hafsah ce.. ɗaukar wayar yayi yasa a speaker '' Hello Farzan,ina kake ne?" Slowly yace '' zan fita ne MAMA'' ya kalli sashen Roman daga cikin wayar Hajiya tace '' okay,ina fatan kaci abinci ko?" '' eh MAMA!" '' ka dawo da wuri... Allah ya tsare min kai!" Ya amsa da Ameen kafin ya katse kiran '' Ah! It's such a wonderful feeling to have a mother...amma wasu Mutane ba zasu fahimci hakan ba ko kaɗan...'' ya jinginar da kanshi da elevator da murmushi a fuskar shi, however Roman bai nuna kamar yaji abinda Farzan ya faɗa ba if anything he was aloof Hakan yaba Farzan haushi '' da yake yan wasu basu da ita ai baza su sani ba...'' dunƙule hannunshi Roman yayi zuciyar shina kaikawo... Farzan daya fahimci hakan ya tsaya da kyau '' what's wrong? Na tado da tsohon ciwo?" '' You are right it's a wonderful feeling having a mother...amma da irin uwar da kake da ita zama maraya is absolutely best...'' Roman ya amsa with a cold voice, batareda ya kalli Farzan ba sai kuma ya matso kusa dashi face flat bakinshi saitin kunnen Farzan yace '' come on,kayi saurin mantawa da baya do you need a recall?'' Dunƙule hannun shi yayi zai kaima Roman naushi.. Roman ya riƙe hannun ya juya sannan ya jefar da Farzan ta kafaɗar shi... Yakai zuƙunne gaban shi '' you're embarrassing yourself... weakling!" Tsallake shi yayi ya fita daga elevator yabar Farzan kwance a ƙasa groaning in pain... Parking lot ya isa bike ɗin shi ya hawo yau ko helmet ɗin bai saba ya fita da gudu... Khalil na zaune saman gadonshi saye da farar riga mai V neck ƙirjinshi slightly out yana kallon gefe yayi nisa cikin tunani wayarshi ta fara ringing ganin mamar shice ke kira ya ɗauka murya sanyaye '' ya kake Ibrahim?'' shiru yayi na lokaci kafin yace '' yaushe zaki zo?" '' i can't come akwai abubuwa da yawa...'' '' that need your attention..what about me? Ni bana buƙatar kulawar kone?" Ya iyar mata,shiru akayi daga can ɓangaren '' manta kawai...lafiya ta lau.. thanks for checking!" Ya katse kiran...tare da jinginar da kanshi...idonshi ya sauka akan ƙofar shi that was slightly ajar...gani yayi kamar akwai mutum a wurin....their eyes met...da sauri aka ja baya '' zo nan!" Ya faɗa da muryar shi mai zurfi...ƙifta idonta Diyaam tayi several times kafin ta tura ƙofar ta shiga ciki zuciyarta na lugude...kanta ƙasa tayi tsaye daga bakin ƙofa...saye take da jar atamfa ta ɗaura farin hijabi sama.. average in height extremely fair in complexion..wasa take da hannun ta nervously '' meyasa kike leƙe?" Taune jan leɓenta tayi murya na rawa da Fulani accent tace '' Uhmm..d..dama...ina neman...Ham..ma ne'' Khalil looking a bit disappointed yace '' forget it..na ɗauka kinzo ki duba ni ne...'' panicking Diyaam tace '' h..harda wannan..'' har lokacin bata ɗago kanta ba...'' hmm,are you sure gaskiya kike faɗa kuwa...You look suspicious...'' da sauri ta ɗago kanta ta waro manyan idanunta tace '' wallahi banyi komai ba...abinda ya kawo ni kenan...kayi haƙuri baxan sake ba...'' ta haɗa hannayenta alamun roƙo idonta na ƙyalli...this is the first time tunda tazo gidan nan cikin shekaru data taɓa magana da Khalil... '' Okay...zan yi haƙuri idan kin zauna tare dani,Kinga banda lafiya kuma kowa yabarni nikaɗai...'' ya faɗi hakan da wasa but he was deeply lonely... '' eh zan zauna...'' Murmushi yayi ya nuna mata gefen gadon shi '' zoki zauna anan...'' hesitantly taje ta zauna a ƙarshen gadon a maimakon inda ya nuna mata... '' meye sunan ki?'' ya tambaya suddenly finding the girl interesting'' D.. Diyaam!" ya ɗage gira '' kaɗai?" ta girgiza kanta '' Safiyyah Diyaam..'' '' oh DIYAAM na nufin ruwa ko?" Jinjina kanta tayi '' ranar da aka haife ki kenan ruwa ake yi a garin ku?" daji abinda ya faɗa tayi yar ƙaramar dariya mai daɗin sauti sai kuma fuskarta tayi ja sanda tagane kallonta yake '' eh... haka ne...baban mu yace, ranar da aka haife ni anyi ruwa sosai kuma dama ƙauyen mu,babu ruwa lokacin sai anyi tafiya mai nisa zuwa birni kafin a samu ruwa shine ranar da aka haifeni ana ta ruwa shine yan ƙauyen mu ke kirana DIYAAM...'' tayi mashi bayani a kunyace tana wasa da hannun ta '' I like the sound of it...amma xan kira ki Sofia..can I?" gyaɗa kanta Diyaam tayi feeling so happy at last tayi magana dashi,zuciyarta kamar baloon tsabar yanda take farin ciki ***" Bayan Roman ya Kore ni daga ɗakin zanen shi kasa komawa sashen mu ko ɗakin Diyaam nayi... lambu na tafi na zauna zuciya ta tayi nauyi kamar inyi kuka amma me zai sa inyi kuka? Laifina ne dana shigar masa wuri Batareda ya gayyace niba babu abinda yafi min ciwo irin fushin dana gani a fuskar sa...na daɗe zaune a wurin kafin na tafi kitchen...abincin ranar da aka dafa na karɓa na wuce dashi sashen Khalil sai dana ƙwanƙwasa ya bani izinin shigowa sannan na shigo..nayi mamakin ganin Diyaam a ciki suna hira ita da Khalil kamar ƙawaye...da yake ta daɗe gidan ƙila ƙawaye ne '' Oh kitten...'' Khalil ya kira murmushin shina ƙara faɗaɗa...nima murmushi nayi mashi na ƙaraso kusa dashi '' ya jikin ka?" '' naji sauƙi baki zo kin dubani ba...'' na zauna kusa da Diyaam '' nazo jiya kaine dai baka ganni ba...'' '' oh I must have missed...'' ya nuna min Diyaam '' kinga sabuwar ƙawata yar fullo..'' sadda kanta Diyaam tayi blush ya mamaye fuskar ta...ajiye mashi abincin nayi '' kyakkyawar ƙawa kake da ita!" Dariya yayi data fito daga ƙasan ƙirjinshi '' Are you jealous?" tsuke fuska nayi shi koda yaushe idan anyi magana sai yace jealous '' a'a...ga abinci nan kaci...'' gyaɗa kanshi yayi ya fara cin abincin..Diyaam ta tashi zata tafi nima zan bita yace mu zauna mu taya shi hira...zaman mukayi...nan ne yasan gobe zamu fara jarabawa..yace zai sa a ɗauke mana aiki har sai mun kai ƙarshen jarabawa...dan muyi karatu da kyau ya ƙara da faɗin '' plus..I want to spend lots of time with you!" Ya kashe min ido... Ɗauke kaina nayi gefe ina murmushi wannan Khalil ɗin... Da ƙarfe ɗaya muka bar ɗakin shi zuwa na Diyaam mukayi sallah kwantawa nayi saman gadonta ina kallon sama duk na damu da Roman '' meya faru ne duk kin damu?" naso in ɓoye mata amma sai kawai na faɗa mata abinda ya faru tsakanina da Roman...'' kada ki damu... eventually zai sauko...'' gyaɗa kaina nayi '' kin shirya ma gobe kuwa?" Ta tambaya tare da kwantawa kusa dani itama tana kallon ceiling '' gabana faɗuwa yake..duk da nayi karatu!" '' nima!"ta faɗa...littafan literature guda biyu ta ɗauko drama da prose ta bani prose ɗin ...muka shiga karatu... Har bacci ya ɗauke mu... Wurin ƙarfe uku na farko daga baccin nayi kwance ban motsa ba..can dai na sauka daga saman gadon na tsaya gaban full length madubin ta ina kallon kaina...abinda na daɗe banyi ba...ƙurajen fuskata sun rage sosai...gashin girata dayake kamar an aske ya taru yayi baƙi da kauri duk da ba sosai ba...gashin idona ma sun ƙara tsawo kaɗan...sai ƙirjina daya fara tasowa shima kaɗan... Cikina da yake ƙato yanzu ko ganin shi banayi ta cikin rigata dayake banci abinci ba...taune leɓena nayi ina danne murmushin dake ƙoƙarin wanzuwa a Fuskata...da gaske nice? Yar ƙaramar dariya nayi kafin na koma gaban madubi na ɗauko mashaci da tsinke ina kunce kaina a nan tsaye har na gama..na shace gashin..gani nayi ya ƙara tsawo da cika amma har yanzu bai da laushi sai taurin tsiya... '' tunda kin kunce ki shiga Baye ki wanke mana...'' ta cikin madubi na hangeta zaune daga bakin gado... '' kina da shampoo ne?" '' eh mana..'' Ajiye tsinke da mashacin nayi na shiga bayenta da yake a tsabtace nayi wanka na wanke kaina na tsane shi sannan na fito sai lokacin na gane ashe banda kaya a nan... wasu riga da wando palazo ta bani daga cikin kayanta harda singlet baƙa nasa na dawo gaban madubi ina goge gashina sosai reflection ɗina ya daɗaɗa min rai...ƙirjina ba kamar daba...ya ƙara girma nake ji kamar in rungume wani...da ace ina gida dana nuna masu Mama...dariya nayi da wannan tunanin sai kace wata marar kunya Bayan na gama busar da gashin Diyaam ta ɗauki wasu hair cream da oil ta zaunar dani akan kujerar dake gaban madubi ta shafa min su Sannan ta fara yimin kalaba '' tana sa gashi yayi tsawo!" Gyaɗa kaina nayi cike da godiya '' shekarunki nawa?'' '' shabiyar..'' '' ya kamata ki dinga kirana aunty Abeedah...'' '' Hahaha..to aunty Abeedah da shakaru nawa kika girme ni...'' '' biyu...'' na bata amsa ''a she ke tsohuwa ce?" Zaro ido nayi hakan ya bata dariya...wani ƙaramin littafi na gani na miƙa hannu na ɗauka..daga sama an rubuta abinda ke raina...kenan diary ne..har xan buɗe in karanta ta warce abinta '' ba'a karantawa mutum diary aunty Abeedah!" ta turo baki..she looked cute! '' oh ban sani ba...yi haƙuri aunty Safiyya Diyaam..inji Anaaam!" Muka yi dariya... Da daddare da muka tafi dining Khalil ma yazo da alamu ya gaji da zama ɗakin shi Munyi mamaki daya faɗa masu cewa ba zamu sake aiki ba saboda jarabawar da zamu rubuta har sai mun gama..hakan ya jawo cecekuce da kuma harara cike da tsana... Mukhtar ne yazo wurin shima..har lokacin bai warke ba .sai tambayar shi ake mai ya faru dashi '' wannan mahaukaciyar ce ta kusa kasheni!" Ya nuna ni kafin ya ƙirƙiro ƙarairayin sharri ya sauke akaina wai na kawo mashi kaina ɗakin shi dan yaƙi yarda shine na buga mashi bedside lamp akai..na tsere...dukansu harda ni kaina na shiga shock... miƙewa Hajiya Wareesha tayi ta juyo dani ta ware tafin hannun ta zata sauke min a fuska.. kamar iska Khalil ya tsaya gabana ya kare ni da jikinshi hakan yasa marin ya sauka akan bayanshi... Diyaam ta rufe baki idonta suka ciko da hawaye kamar yanda nawa ke tsiyaya Sauran ma'aikatan suka zaro ido...su Seraphina suma sun shiga shock da abinda Khalil yayi... ajiyar zuciya ya sauke ya sake ni yana kallon cikin idona yace '' are you okay Kitten?" naji kamar lokaci ya tsaya kamar babu kowa sai mu...my heart broke '' wallahi ƙarya yake min..'' '' shhh...na yarda dake!" Ya katseni ya juyo ga sauran '' Abeedah bazata taɓa yin hakan ba!'' Hajiya Wareesha ta kama da wuta '' yanzu Ibrahim ka gwammace ka goyi bayan yar waje sama da ɗan uwanka?" Fuska ba annuri Khalil ya kalleta '' I'm just supporting the truth aunty!" '' Kai wannan yarinya anyi annoba! daga zuwanta gidan nan an samu matsala yafi a ƙirga shegiya mayya!" Inji hajiya Ruƙayyah... '' ya kamata a koreta daga gidan nan kawai wannan shine maslaha!" Sharply Khalil ya juya ya kalli Hajiya Momma datayi maganar kafin yayi magana daga baki baki Muryar shi mai amo ta karaɗe wurin ''No body is firing her!" Maganar ta fito da wani irin absolute finality babu batun musu... juyawa mukayi...it was Roman! Fuskarshi tayi duhu ya ƙaraso wurin '' Toh marasa ta ido nuna mana cewa ka kai girma!" Hajiya Zeenatu ta miƙe tana nuna shi da cokalinta mai yatsu '' ai na faɗa yarinyar nan annoba ce..ji yanda ta haɗa faɗa bayan bata daɗe da kasancewa a gidan ba!" Hajiya Momma ta sake faɗa ... Nikam babu abinda nake sai kuka...abinda Mukhtar ya faɗa yayi min ciwo fiye da tunanin mai karatu... '' dan kaga Hajjo bata nan shine zaka faɗi hakan...mu muka haife Romano bakai ka haife muba! Yanzu xan kira securities su fitar da yarinyar nan!" tana faɗar haka ta ɗaga waya ta kira wasu mutane Few minutes later sai gasu sun shigo cikin baƙaƙen kaya...nuna masu ni tayi tace su fita dani... Khalil ya ƙara riƙe ni a jikinshi..nima ina ƙara ɓoyewa bayanshi...dining ɗin yayi duhu da da nauyi da tension ɗin dake maƙale da iska..yan mata da samari suna jira suga yanda zata kaya.. mafiyawanci idan da za'a yi ƙuri'a da zasu sa in bar gidan..Nima da badan Khalil da kuma Roman ba,da nayi tafiya ta.. ''.me kuke jira? Ku fita da ita!" Hajiya Momma ta faɗa... mutanen saye da baƙaƙen kaya sukayo kaina...mutum na farko daya miƙa hannu don fincikoni ganinshi mukayi kwance a ƙarshen bango..muka kalli Roman da yake tsaye kamar Boss na cikin TV .ya kalli su Hajiya Momma yace '' I said No one FIRES HER!" Da wani irin calmness yayi maganar emphasizing each word... Mutanen wurin we're shocked haka nida kaina abun yaban mamaki...aka shiga kallon kallo Sauran securities suka ja baya... Hajiya Momma ta sallame su da baƙin ciki ganin babu abinda zasu iya aiwatarwa..suka ɗauki ɗan uwansu daya kasa tashi suka tafi dashi '' mu muka haife ka bakai ka haife...'' '' KE DA WA?" Ya katse Hajiya Momma dake repeating sentence ɗinta, tayi shiru kunya na ɗiga daga jikinta,sai zarar ƙananan idonta take '' dake ki kasance uwata...Gara na mutu tun ina ciki!" Maganar ta sauka kamar bomb sauran matan suka zaro ido amma babu wanda ya isa yace komai...yan aikin sukayi ƙasa da kansu Fuskokin duka waya'nda ke wurin sukayi duhu... Seraphina take kallon mu cike da tsana ba ita kaɗai ba harda yan uwanta...da gudu tabar wurin tana kuka... Diyaam yadai?? 👀👀 +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️ RU'UYAA The dreams we never lived By Autumn 17 🍁🍁 30. ...son shi nake...🖊️ '' Come kitten...'' ya riƙo hannuna muka bar wurin Diyaam biye damu... zuciya tana tsananin ciwo... Jinginar da bayan shi akan seat ɗin shi farzan yayi yake binsu da kallo har suka ɓace da murmushin nasara a fuskar shi yabar wurin. su Hajiya Momma kamar maƙoshi zai faɗi tsabar yanda take ihu... Anan parlor'n shi Khalil ya zaunar dani Diyaam zaune a gefe na shi kuma ya zauna a kujerar dake kallon mu...su biyun sai lallashina suke da ƙyar na samu na dena kukan sai shaƙuwa... Ruwa ya zuba min a cup ya bani na amsa na shanye duka Diyaam ta riƙe hannu na tana shafawa nayi ƙasa da fuskata suddenly naji duk kunya ta kamani '' Are You blushing?" Ya tambaya sai ya zaro wayarshi daga aljihun shi '' kalli nan..'' hannuna nasa na rufe fuska ta bai barni ba har saida nayi dariya Diyaam na tayani daga nan yake bamu labarin zaman su Chicago yanda Roman abu kaɗan yake kaiwa mutane duka kamar Jackie Chan..hakan yasa ya dinga zuwa detention every now and '' ai yanzu yayi sanyi,da dane ko magana ba zai yiba...cikin mu zai yi da duka dukan mu!" Nida Diyaam mun sha dariya har sai da cikin mu yayi ciwo... da ƙarfe goma muka bar sashen shi,Diyaam ta wuce ɗakinta ni kuma na wuce namu sashen..samun Hansa'u nayi tsaye daga wurin gado na ina shigowa tayo kaina ta shaƙe min wuya ''shegiya wane irin tsafi kikayi amfani dashi wurin kama maxan gidan nan a tafin hannun ki...'' ƙoƙarin cire hannun ta nake daga wuyana amma abu yaci tura,fim ɗin Chinese ɗin da muke kallo ya faɗo raina yanda suke shure mutum idan an musu irin haka,ƙafata na ɗaga na sauke mata a ciki...taja baya harda faɗuwa ƙasa tana mulmula...da ƙyar na samu numfashina... Ta miƙe tsaye tana huci..nace '' idan kina neman tsafin da nake amfani dashi...'' idona na nuna mata ina juyasu '' wannan ne,kuma ke baki dasu...kin gane? Duk wanda ya kalla dole yaji ya ƙyasa!" Na bangaje ta daga gabana na haye gado na...bada daɗewa ba Mama Asabe ta shigo ta samu Hansa'u na kuka data tambaye ta cewa tayi '' ba ruwanki tsohuwa..'' baki Alaikum Mama Asabe ta haye nata gado ta kwanta tan sauke ajiyar zuciya sai kuma ta fara juye juye '' Mama Asabe lafiya kuwa?" Na leƙo kaina '' lafiya lau Abeedah ciki nane ba daidai ba'' '' oh... Allah ya kawo lafiya...'' '' Ameen...'' bayan wani lokaci nace '' abin nan naki yana aiki Mama Asabe na gode sosai Allah ya ƙaro arziƙi!" '' Ameen Ameen Abeedahtu..'' *** Washegari a gaggauce na shirya cikin uniforms ɗina, tunda ance ba zamu dinga aiki ba sai kawai na ɗauki littafina ina muraji'a... Da ƙarfe bakwai muka sauko zuwa dining ɗin mu wurin kari...Su Fauziyya, Hansa'u da sauran wasu daga cikin masu aikin sai hararata suke kamar na tare masu wani abu..babu abinda ya shamin kai ko kaɗan... '' Allah ya bada sa'a Abeedah yasa a rubuta a sa'a ba sai an maimaita ba!" Mama Asabe tayi min addu'ar.. waya'nda ba yan baƙin ciki ba suka amsa da Ameen Hansa'u taja tsuki tace '' Allah yasa daga waec har neco ɗin kiyi ta maimaitawa har ƙarshen rayuwar ki!" '' Ameen ya hayyu ya qayyum!" Su Fauziyya suka amsa da ƙarfi.. Naji ba daɗi amma sai na kauda kaina kawai...bada daɗewa ba na gama breakfast ɗin...Babban gida muka shiga tareda Mama Asabe dasu waleeda suka wuce wurin aiki Ni kuma na wuce sashen Khalil in duba shi... Da farko ƙofar ɗakin Roman na fara isa kamar in shiga kamar in ƙwanƙwasa daga ƙarshe na juya na bar wurin raina ba daɗi .. Sashen Khalil na tafi na ƙwanƙwasa ya bani izinin shiga...na ɗan waro ido ganin su biyun zaune a parlor...Roman saye da jajayen kaya..gashin shi ya pake sama da ƙasa..ba ƙaramin kyau yayi ba... hankalin shi a kan laptop yana aiki.. '' Oh kitten...'' murmushi nayi mashi yace in ƙaraso ciki...ya nuna min ɗayar kujerar dake daga gefen hagu shida Roman zaune a kujera ɗaya...na zauna ina satar kallon Roman da bai kalli inda nake ba... '' how are you today?" ya tambaye ni '' lafiya Lau,ya jikinka?" '' Alhmadulillah!" Na gyaɗa kaina...na ƙara satar kallon Roman...can ya ɗago ya kalli Khalil ya tura mashi laptop ɗin yace '' na gama yanzu zaka iya submitting ba dole sai kaje can ba!" Duba laptop ɗin Khalil yayi ya gyaɗa kanshi..Roman ya fita daga sashen..bai kalle niba...kenan yayi fushi dani... Khalil ma ya shiga nashi ɗakin,ina nan zaune ya fito riƙe da chocolate irin wanda Diyaam ta taɓa bamu ya miƙa min na karɓa ina kallon shi '' good luck with your exams!" Murmushin shi yasa naji nauyin da zuciya ta tayi ya rage...'' na gode!" Na amsa..sai na miƙe '' bari in tafi kada inyi latti!" '' driver zai kai ki?" Ya tambaya na girgiza kai, naga ya ɗauki wayar shi dake saman table da sauri nace '' a'a nafi son tafiya da ƙafa ne...'' '' really?" Ya ɗage min gira na gyaɗa kaina '' okay...'' Fitowa daga ɗakin shi nayi ina tafiya slow slow naci karo dasu Seraphina..wani tsinannen kallo suka wurga min su uku dayasa zuciya ta bugawa da ƙarfi... '' manta da cewa Ya Rome yace a rabu daku, wallahi sai zama a gidan nan ya gagari ku biyun!" Khaleesat ta faɗi hakan sauran basu cemin komai ba sukayi gaba...gabana ya shiga faɗuwa.. addu'a nayi na wuce ɗakin Diyaam itama ta shirya breakfast take yi ita kaɗai a ɗakinta '' Toh ni zan tafi idan kin gama sai ki iske ni..'' da sauri ta tashi tasa hijabinta tace '' bari inzo mu tafi...'' '' ke da mota zaki ni kuma da ƙafa zani...'' '' zan faɗawa Hamma sai mu tafi taren...'' '' a ƙafa?" Ta gyaɗa kanta... Jakarta ta ɗauka ta fito...ɗakin Roman muka tafi amma bai nan muka sake zuwa inda yake art..nan ma bai nan Sai da muka fita muka hange shi a parking lot,Diyaam gaba ina biye da ita... fatan zai kalleni ko sau ɗaya ne amma da muka isa har sukayi magana suka gama bai kalli sashe naba...irin chocolate ɗin da Khalil ya bani ya miƙa mata tare da faɗin '' Ace your exams papillon (butterfly)'' ta amsa da '' insha Allah Hamma...'' ya gyaɗa kanshi sannan muka bar wurin.. zuciyata na ci da wuta..kamar inyi kuka sai Juyowa nake ina kallon shi... Yau ko kyau'n anguwar ban gani ba...har muka iso makaranta raina ba daɗi kuma babu wanda yayi magana cikin mu... Wurin ƙarfe takwas su Jadeedah suka iso muka haɗu cikin farin ciki muna yima juna Allah ya bada sa'a.. wannan lokacin har an canja mana lambobi... Dukan mu ajujuwa daban daban muke...kafin mu shiga jarabawar sai dana raba mana chocolate ɗin da Khalil ya bani '' ina kika samu wannan chocolate ɗin Abeedah?" Jay d ta tambaya '' Khalil ya bani...'' zaro ido Asma'u tayi '' ina kika ganshi?" yanda idonta ke sparkling naso in gano wani abu kafin in amsa malam Nura ya gargaɗa mu zuwa ajujuwan mu... Tsaye mukayi a bakin ƙofa idan an kira mutum da number shi sai ya shiga aji...nice no 17... ana kira na faɗa ajin na samu wuri na zauna...kafin wani lokaci har kowa ya zauna...babu kowa a corridor'n... Ajin duk wanda ka kalla zaka ga fuskar shi ɗauke da damuwa sai yan ƙalilan...ajiye pencil da biro da cleaner nayi saman table ina addu'a zuciya ta fal da tsoro da ƙarfe goma za'a fara jarabawar,a tunani na kafin nan,fargaba da tsoro sun gama damu... Finally lokaci yayi aka shigo ana rarraba mana tambayoyin da amsa booklet bayan an gargaɗi masu ɗauke da takarda ko wani abu na satar amsa su fitar dashi... da ƙarfe goma da rabi exam ta kama zamu gama huɗu da rabi... numfashi naja kafin na jawo pencil ɗina na fara rubuta amsa bayan na cika duk bayanan da aka buƙata Malamai ne ke bi row by row suna karɓar kuɗin ɗalibai suna basu amsa...sanda naga hakan ba ƙaramin mamaki nayi ba sannan naji wani abu ya daki zuciya ta...idan anyi magana sai suce taimako suke bayan kuma babbar illa suke haifar wa na cin hanci da rashawa da kuma daƙile ɗalibai wurin karatun jarabawa... sanda suka tambaye ni idan ina so in biya ɗari biyar na girgiza kaina wani irin kallo suke bina dashi,bani kaɗai ba harda sauran wa'yanda suka ƙi... Da ƙarfe sha biyu da rabi muka gama objective aka bamu hutun awa ɗaya kafin a koma ayi essay... Ƙarƙashin bishiya muka zauna mu biyar... Asma'u ta sake tambaya ta ina na haɗu da Khalil '' wai ke ko son Khalil ɗin nan kike ne?" Anaam ta tambayi Asma'u tana riƙe haɓa... blushing Asma'u take kafin tace '' wai ma...ni nace ina son shi?" Jay d tana dariya tace '' to bagashi ba duk kin bi kin isheta da ina suka haɗu....'' '' in sonshi kike Gara ki faɗa tunda wuri!" Anaam take tura kafaɗar Asma'u da zolaya '' ba so ba ƙauna... mtschewww!" Tashi tayi tabar wurin bayan ta faɗi hakan... Sallah mukayi kafin muka sake komawa aji..nan ma an karɓi kuɗin mutane,nidai da kaina nayi wannan jarabawar kuma ina roƙon Allah yasa hakan ta kasance har ƙarshe...2:00 muka gaba paper essay aka zo oral test kuɗin wannan sashen yafi yawa har dubu ɗaya acewar malaman wai wannan yafi wahala... Wani abun mamaki harda invigilators aka haɗa baki ana biyan su...faɗin yanda nake jin ƙunci a zuciya ta game da hakan ɓata baki ne ... Da ƙarfe huɗu muka gama jarabawa...muda bamu biya kuɗi an bamu amsa ba,cewa suke mu jira ranar mathematics..dole muma mu shigo layi... nikam insha Allah har ƙarshe da kaina zanyi... Ƙarfe biyar da rabi muka isa gida nida Diyaam..muna tafe muna magana akan jarabawar duk da nidai nace kada ta faɗa min wanda ke daidai da wanda ba daidai ba gudun anxiety... Sashen mu na tafi ita kuma ta shige babban gida... Wanka nayi na canja kaya naci abinci cikin kwanciyar hankali... tunanin haɗuwa da Roman yasa bugun zuciya ta ya ƙaru kafin nishaɗi ya mamaye ilahirin jikina... Da sauri na gama cin abincin na shiga can ciki... sashen Khalil na fara zuwa na same shi yana kallon ƙwallo...yana ganina ya saki murmushi '' Oh.. kitten!" Murmushi nayi mai haɗe da dariya kullum haka yake cewa '' oh kitten..'' '' Oh Khalil..." Nima na faɗa tare da zama can ƙarshen kujerar dake gefen shi,shafa ƙeyarshi yayi '' ashe kaima kana ɓata lokaci haka? '' ɗage gira yayi nace '' wai mutum yayi ta guje guje cikin fili ana sharɓe shi yana faɗuwa...wai duk dan ya kamo waccan abun!" '' it's entertaining...'' ya ban amsa taɓe baki nayi nace '' ai nikam idan nayi aure mijina yace zai kalli wannan abun sai dai ya kwana waje!" Sosai yayi dariya...sai ya miƙo min remote yace '' to ki kalli abinda kike so..'' '' a'a ka barshi kawai tunda kallo kake...''bai saurare niba ya turo min remote ɗin...ɗauka nayi na canja zuwa YouTube na nemo MSA Ya ɗan zaro ido '' Cartoons kike kallo?" '' nayi girma da yawa?" ya girgiza kanshi sai muka mayarda hankalin mu muna kallon tare... '' ya exam?" Can ya tambaya..ai ko kamar an buɗe tap na fara bashi bayani yanda yan kaɗan cikin mu kaɗai sukayi jarabawar da kansu... Da kuma yanda ake karɓar kuɗi aba mutum amsa harda invigilators ɗin.. duk cikin bashi labarin ne na taso daga inda nake zaune na zauna gefenshi.. '' You did well,kada ki bada kuɗi a baki amsa, kiyi da kanki kinji?" gyaɗa kaina nayi ya sakar min murmushi na dawo da kallona akan tv'n dai dai an kawo wani wuri a cartoon ɗin, inda akwai wasu kaloli da yawa kamar hayaƙi suna bin sama..kalolin akwai green,pink,blue da sauran su... Sosai idona ke ƙyalli '' ya maki kyau ne?" Khalil daya lura da yanda nake kallon wurin ina zallo kamar zan shiga cikin TV'N ya tambaya '' sosai ma...akwai wuri irin haka da gaske?" gyaɗa kanshi yayi '' it's called Aurora..ko northern lights...'' '' Innalillahi ina so in tafi wurin...'' na faɗa cike da murna '' I'll take you some day...'' yaban amsa '' da gaske? amma ai babu a Nigeria...'' '' akwai a Norway...da Canada da sauran ƙasashe...'' '' xan yi farin ciki kuwa...'' na faɗa da gaskiya..ya ɗan matso yace '' kin san a US idan mutum yana farin ciki...they used to give a hug like this...'' ya matso zai rungume ni, pillow'n dana rungume na tura mashi na miƙe ina dariya nayi ƙofa '' idan ka kaini sai nima inyi maka...'' Shafa gefen fuskar shi yayi '' remember your words!" Ya faɗa daga bayana... Ƙofar ɗakin Roman na tafi na bubbuga amma ba'a buɗe ba kuma ba'a bani izinin shigowa ba...ƙila bai nan...studio ɗin shi na tafi nan ma bai nan Naji yanayi na ya koma na rashin farin ciki...wurin lambu na tafi a can na same shi ya ajiye painting tools ɗinshi yana painting Zuciya na zallo na ƙarasa wurin...'' Roman...kayi haƙuri..'' na riƙe gefen hannun rigar shi...mutumin nan ko gezau kamar bai san dani a wurin ba '' kaji...'' na ƙara jijjiga hannunshi ina turo baki...'' kaji Romeo...'' cije bakina nayi kada inyi dariya dana kira shi Romeo hannunshi dake shafa painting ya daskare '' Kaji..bazan sake ba!" '' Are You trying to annoy me,cuz it's working!" Ya faɗa sharply tare da Juyowa ya kalleni da fushi a idonshi '' a'a..'' '' to bar wurin nan!" Ya nuna min hanyar fita sakin hannun rigarshi nayi...sai kuma na lakato painting na shafa mashi a kumatu ba zato ba tsammani...sakin plate ɗin painting yayi ya fara tattare hannun rigar shi kamar zai kama da wuta da alamu..abinda yayi ma securities ɗin nan zai yimin...da gudu na juya na fita Daga nan ya dena yimin magana kona mashi bazai amsa ba,bazai kalle niba..duk nabi na damu.. fara'a ta ta ragu...su Jay d sun lura da wannan dan haka...ranar juma'a ta titsiye ni akan sai na faɗa mata abinda ya faru...cikin kuka na zayyane mata gidan su Khalil nake aiki...kuma yanzu...well ban sani ba ko sonshi nake amma dai baya min magana kuma hakan na sani a baƙin ciki... Rufe bakinta tayi bayan na gama kafin ta saki dariya hakan ya ƙara ƙular dani..tsagaitawa tayi ta fara lallashina sannan ta faɗamin abubuwan da zan yi dan ya kula ni..harda..bashi haushi, tambayar shi abubuwa marasa ma'ana...da flirting...nidai ban san ko wannan good ideas bane...but I was determined to try! masu cewa Roman ya fara son Abeedah..toh nidai na faɗa tun farko yarinyar tana da rawar kai..ga shi harta faɗa tun kan aje ko ina 🙆🤣 shi kuwa bamu masan abunda ke wakana a ranshi ba....tsabar kamun kai😏😏 +2349138091955 RU'UYAA…📖 ₦500 ne idan ya kammala zai koma 800 Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay Shaidar biya ta +2349138091955 Autumn writes 📖🖋️