[2/6, 5:50 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *Book 2* *By Mariam sani Riamcool* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* *Bismillahirrahmanirrahim* *Page* 62&63 _____________✍️Tana kaiwa nan taci gaba da wani kalar gurnani,shi kuma ya riƙe ƙanƙarar kam,tun tana iya motsi harta kai ga ta sulale ta faɗi sumammiya, yana ganin haka ya ɗauketa yasakata a mota,kai tsaye gida ya nufa da ita,gudu yaketa shararawa har yakai gida,yana yin parking ya saɓeta ya nufi part ɗin Mommy da ita,yana shiga ya iske babu kowa Falon,ajiyeta yayi kan 3 saeter ya ɗakko wayarshi yana lalubar number Jabir ya doka mashi kira, yana ɗagawa daga can ɓangaren banji abinda aka ce ba naji ya ce "kuyi sauri ku ƙaraso," bai jira abinda za'ace ba ya datse kiran yana haurawa sama wajen Mommy,yana zuwa ya sameta ita da Hameed da Hameeda zaune suna hira,kallonshi Mommy tayi tana faɗin "lafiya dai Son naga ka shigo a firgice?," Ta faɗa tana kafeshi da ido "Mommy koma dai miye zakiji zan faɗa miki amma dai ki taso muje," ya faɗa yana ficewa,ajiyar zuciya Mommy taja tana miƙewa suka safko ita dasu Hameeda,ita dai tun daga nesa take kallon mace kwance bisa kujera ga Nuraim tsaye bisa kanta,ga gabanta dake wani irin faɗuwa,ƙarasowa tayi har inda Raihana take tayi,saidai tana zuwa tayi turus tana kallonta, Nunata da yatsa tayi tana faɗin "Sajeeda, Wallahi wannan fuskar Sajeeda ce,Nuraim ina ka samo mani ƙanwata?," Ta faɗa tana mai fashewa da kuka sannan ta rungumo Raihana dake kwance, ɗagota Nuraima yayi yana faɗin "Mommy ki kwantar da hankalinki wannan ba ƙanwarki ba ce ki duba kiga wannan ita yarinya ce". "Nuraim wannan koba Sajeeda bace tabbas jininta ce ƴar ƴar uwata ce," Mommy ta faɗa tana sake ƙanƙame Raihana kamar wani zai ƙwace mata ita,da ƙyar Nuraim ya samu Mommy ta kwantar da hankalinta,suna nan zaune saiga Jabeer yayi Sallama,Ko gaisawa Nuraim bai bari sunyi da Jabeer ba ya tashi yana faɗin "Jabeer ina Baban yake ya banga kun shigo tare ba." Kallonshi Jabeer yayi yana faɗin "kai Man wannan zaucewa haka,yana waje ya tsay...," Kojin ƙarshen maganar Jabeer baiyi ba ya fice,tsaye ya sami Dattijon yasha fararen kaya,kallon idanun shi Nuraim yayi,saidai da sauri ya kauda don ganin wani abu na daban a tare dasu,gaisawa sukayi da Baban sannan yai mashi iso har ciki,yana zuwa Suka gaisa da Mommy sanan ya kafe Raihana da idanu,zama yayi yana furta "Innnalilahi wa'inna ilaihirraji'un, haƙiƙa an zalunci wannan baiwar Allah an mata baƙar Mallaka da baƙin iko,don Tabbas azzalumin Ruhi mai tattare da baƙin iko na tareda ita,wanda fitarshi a jikinta ba ƙaramar gwagwarmaya za'a sha ba," ya faɗa yana nuna tsantsar damuwa a fuskarshi Kallonshi Nuraim yayi yana faɗin "To yanzun Baba miye mafita? Ka faɗa mafitar yanda zata fita daga wannan hali,ni kuma koma miye zan san yadda zanyi ƙoƙari na taimaketa," ya ƙarashe zancen matuƙar damuwa a fuskarshi, "bazamu san miye mafita ba a yanzun sai naje na ƙara bincikawa sannan ina son wannan ƙanƙarar ka adanata sosai dan Ruhin zai iya ɗauketa,da wannan ƙanƙarar ce zamu samu mu tasgarar da baƙaƙen ikon dake tattare da ita" yana kaiwa nan ya miƙe,shima Nuraim da Jabeer miƙewa sukayi suka biyoshi, wasu ruwa ya miƙo ma Nuraim ya ce idan sun koma su shafa mata shi a goshi, godiya sosai Nuraim yayi mashi sannan babu yadda basuyi ba su maidashi ya ce a'a cikin minti ɗaya ma ya isa su ƙyaleshi kawai (Tom Baba Mutum ne kai ko Aljan🥺) haka suka ƙyaleshi,suka dawo,suna dawowa Nuraim ya zauna kusa da Raihana yana shafa mata ruwan a goshi, Mommy kam ta kafe Raihana da idanu tana kallonta,wani irin ƙaunar yarinyar ya kamata lokaci guda da kuma tausayinta, don ta fahimci akwai wata gagarumar matsala dake damunta Nuraim saida ya shafa mata ruwan har sau ukku a goshi sannan taja wata doguwar ajiyar zuciya ta buɗe idanunta,addu'a nake son nayi amma bakina yayi nauyi bazai iya furtawa ba,a hankali na dinga buɗe idanuna harna waresu duka akan Hamma,gabana ne yai wani irin faɗuwa lokaci guda,tashi nayi ina bin ko ina da kallo don gaba ɗaya na mance mai ya faru,nadai san naga Hamma a gurinda muka haɗu rannan,da sauri naga wata matashiyar budurwa sa'ata da Dattijuwa suna ƙarasowa wajena suna mani sannu,da kallo nabisu duka ina gaisheda su sannan na kalli Hamma, Murmushi ya sakar man nai saurin haɗe rai ina faɗin "nan kuma inane ka kawoni? na riga na faɗa maka kada ka cilla kanka a matsala ka ƙyaleni kawai." Kallona matar tayi tana faɗin "ƴata kiyi wanka kici abinci tukunna sai ya faɗa mana yadda akayi ya kawoki nan," Mommy ta faɗa tana sakin Murmushi, kaɗa mata kai nayi ina miƙewa,sannan wannan matashiyar budurwa ta miƙe tana Murmushi ta miƙo man hannu tana faɗin "sunana Hameeda ke kuma fa," Murmushi na sakar mata ina faɗin "Raihanatu," " wow nice name," ta faɗa tana rungumeni, Nuraim da yake ta kallonsu ya ce "wai Hameeda bazaki kaita tayi wankan bane kin tsareta da surutu," ya faɗa yana banka mata harara,sum_sum taja hannun Raihana suka haura sama ta kaita ɗakinta,niko da kallo nake bin ko ina ina mamakin yadda akayi na shigo gidannan,ga sai mamakin Matar da nagani nake don ganinta da nayi naji wata irin ƙaunarta ta mamayeni, naji ta tuna man da Mahaifiyata,gashi banji wani rashin yadda a tattare dasu ba,kai tsaye Toilet na faɗa nayi wanka tareda Alwalla ina fitowa na iske ta ajiye man abaya baƙa, Murmushi na saki,lotion ɗinta naje na shafa sanan na ɗan shafa powder wacce rabonda na shafata harna manta,lip gloss na ɗan shafa sai kwallin dana shafa ya fiddo da asalin kyawun idanuna,abayar na ɗauka na saka,tai man masifar kyau Wardrope ɗinta na buɗe na fitoda dogon Hijabi na zira na tada sallah,saidai azabar danake ji idan zanyi sallah naji ta yau ta linku fiyeda kullum,da ƙyar na samu na idata,ina gamawa na dinga sauke numfashi da ƙyar na samu na tashi mayafin abayar kawai na yafa na fito,a hankali nake bin step ɗin harna safko,tunda ta safko kowa ya kafeta da idanu don ganin haɗaɗɗiyar balarabiya ta fito sak,Nuraim kam ko ƙyaftawa baya son yi saida Jabeer ya take masa ƙafa sannan ya ɗago yana hararar Jabeer ɗin, Mommy kam a fakaice ta share hawaye don duk yadda ta kalli Raihana saita tuna mata da Sajeeda, murmushi ta ƙaƙalo tana faɗin "zo ki zauna kusa dani ƴata,nima Murmushin na mayar mata ina zama kusada ita, Hameed kam sai wani shisshige mata yake, kallon NURAIM da ya kafe Raihana da idanu kamar wani maye Mommy tayi tana faɗin "sai ka faɗa mana yadda akayi ka samo wannan baiwar Allah" Nan Nuraim ya zauna ya faɗa masu tun tsawon shekara biyu take zuwar masa a mafarki tana neman temakonsa takan faɗa mashi shi kaɗai ne zai iya temakonta,tun abun bai damunsa har yakai ga ya damesa don kullum ya kwanta sai ya ganta,haka ya ƙuduri aniyar temakonta,saidai ƙaunarta da ya kamu da ita ke bai faɗa masu ba, yaci gaba da faɗin "duk lokacin da naji zuciyata tayi zafi da rashin ganin inda take ballantana harna temaketa, kawai saina tsinci kaina ina tafiya a dokar daji,kwatsam wata rana ina tafiya a dokar daji naji an dakatar dani ana faɗin nazo a haɗa ƙarfi dani a taimaki wacce nake nema don tabbas Ruhina ne mai ƙarfin da zai iya tunkarar su,a hanzarce na juyo ina kallon farin Dattijon dake ta zuba man Murmushi,duk yadda nake tambayarsa akan ya faɗa man koshi wanene ƙiyawa yayi saidai kawai ya nuna man kogon da yake zama ya ce duk lokacin da nakeda buƙatar temakonshi to nazo a wannan kogon shima zai bada tashi gudummuwar,ban wani tsawwala tambayarsa ba, haka naci gaba da zuwa wajensa har Allah yasa na haɗu da ita," nan dai ya zauna ya basu labarin komai har izuwa yanzun tunda ya fara zancen zuciyata ta tsinke da lamarin ganin cikin ƙudurar Allah, Ubangiji ya kawo Mani mai taimakona lokacin da banyi tsammani ba a lokacin dana fidda rai daga rahamar Ubangiji,lokaci guda kuma naji wani abu na tsarga man zuciya gameda Hamma,wasu siraran hawaye ne suka biyo kuncina wanda na rasa na miye tsakanin tausayin kaina kona halin da Hamma zai shiga ne,hannu nasa na ɗauke su ina kallonshi nake faɗin "haƙiƙa kayi abinda bazan taɓa mancewa dakai ba har yazuwa ɗaukewar numfashina,ada nayi niyar dakatar dakai don ganin zaka saka kanka a haɗari,amma a yanzun zan ƙara ƙarfafa maka gwiwa akan ka tunkari azzaluman dake zaluntar bayin Allah ni kaina zanyi ƙoƙarin dakatar da ikon baƙin Ruhin dake cikin jikina zanyi ƙoƙarin sarrafa kaina," na faɗa ina jin wani raɗaɗin ɗaci a zuciyata Ajiyar zuciya Mommy da Nuraim suka sauke sannan Mommy ta kalleni tana faɗin "saidai ƴata muna son ki bamu tarihinki mu san koke wacece,dukda kamanninki da kuma yadda nake jinki sun tabbatar man da ko tantama banayi ke ɗiyar ƙanwata ce Sajeeda." Saurin ɗago fuskata nayi donjin abinda ta faɗa da mamaki nake faɗin "dama ke ce Yaya faɗimar da Ammi ke faɗin......✍️ *Ayi man afuwa yau nayi gajeren Typing,yau banda Isasshen Time ne amma insha Allah gobe zan ƙara maku shi* Wannan kenan *Comments, Share fisabilillah* Waɗannan su ne ƙwarin guiwata *By Mariam sani Riamcool* *08109554986* [2/6, 5:51 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *Book 2* *By Mariam sani Riamcool* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* *Bismillahirrahmanirrahim* *Page* 64&65 ___________✍️"Dama ke ce Yaya Faɗimar da Ammi ke yawan faɗi, ashe dama zan ga jinin Mahaifiyata? wanda mun riga mun daɗe da son neman sanin inda kuke," na faɗa ina faɗawa jikin Mommy na fashe da kukan farinciki,ɗago fuskata Mommy tayi tana faɗin "ya isa haka ƴata yanzun ba lokacin kuka bane lokaci ne da zakiyi farinciki da Allah ya haɗamu," Mommy ta faɗa tana bubbuga bayana, fuskata na ɗago ina share hawaye ina faɗin "Mommy dole nayi kukan farincikin ganinki,wanda ke ce a halin yanzun zaki maye man gurbin Mahaifiyata" kallonta Nuraim yayi yana sakin Murmushi yake faɗin "to Alhamdulillahi da Allah Ubangiji ya bayyanar mana daku cikin sauƙi,ashe dukma ana kusa,yanzun ina Ammin tamu take?." hawaye na sake sharewa ina faɗin "Ammi yanzun bata tare damu ta tafi ta barmu.....," "ina Sajeeda ta tafi? Kardai kice man Sajeeda mutuwa tayi don Allah,kada ki faɗa man kalmar da bazan iya ɗauka ba," Mommy ta faɗa a kiɗime,kallonta nayi wasu sabbin hawayen na saken bin kuncina, "ko zamu iya sanin tarihinki da abinda ya samu Ammi?," Hameed dake zaune ya faɗa,kallonshi nayi ina ɗaga masa kai sannan na ce, *WAIWAYE* "Asalin mahaifina ɗan Niger ne,mahaifansa Safiyya da Usman Toro sune suka haifi Abba,waɗanda dukkansu bazan iya kiransu dana kirki ba,saboda dukkansu sun kasance masu zubar da jinin Al'umma ta hanyar tsafi,saboda Juwala Safiyya itama ba ƙaramar matsafiya bace don tafi Toro iya tsafi saboda ƙwarewarta a tsafi ma yasa Toro auren Juwala,koda sukayi aure basu wani daɗe ba Allah ya azurta su da samun ɗansu na farko Baba Sa'adu,daganan kuma sai Baba Sharu daganan kuma sai ta samu ciki, wanda Toro a lokacinne ya ce zai ƙara aure,Juwala bata wani damu ba saboda ita ba wani miji bane a gabanta abinda tasa a gaba kawai shine harkarta ta tsafi,koda aka auro Aishatu itama dai ba wata ta kirkin Toro ya auro ba saboda itama cikin ƴan ƙungiyarsa ta tsafi ce ya auro,ga rashin imani a zuciyarta,haka dai Juwala da A'ishatu sukayita zaman doya da manja dan babu mai shiga harkar wani a haka dai Juwala ta haifi Baba Khabir bayan ta haifeshi ne ta ƙara samun wani cikin wanda itama ashe Aishatu na dashi,saida Aishatu ta haifi Baba Nazeer wato Modibbo,sannan itama Juwala ta sake haihuwar Abba Wanda aka raɗa ma suna Nuraddeen,da ganan kuma ta ƙara samun ciki wanda Toro ya ce shifa ya gaji da haihuwar da take masa hakanan wanda ya hassala zuciyar Juwala har takai ga sunyi gagarumin faɗa,wanda takai ga Toro sakin Juwala, daganan ne ita kuma Juwala tayi zuciya ta ce ko ƴaƴanta bazata sake waiwaya ba kamar yadda tabar cikin Mahaifiyarta ita kuma haka zata bar ƴaƴanta da Toro,wanda wannan abu ba ƙaramin farinciki yasa Aishatu ba,haka Juwala tai nesa da Toro taje taci gaba da rainon cikinta,har Allah yasa ta haifi ɗanta Baba Sule, lokacin itama Aishatu nada ciki,bayan watanni sai gashi Allah ya azurtata da ƴarta mace Saddeƙa,haka yaran Juwala suka tashi babu wani mai kula dasu don Aishatu bata wani shiga sha'aninsu Nuraddeen ne kaɗai ta ɗauka tamkar ɗanta wanda ya taso komai a wajenta yakeyi,hakan yasa sukayi muguwar shaƙuwa tsakanin Nuraddeen da kuma Modibbo wanda suka taso cikin ƙaunar junansu,wanda ko wanda suke ciki guda basa masa ƙaunar da Modibbo ke masa,hasali ma su basu wani damu da ƙanen nasu ba,kowa sha'anin gabansa yake,haka Toro yaci gaba da koyawa yaransa harkar tsafi,wanda Modibbo da Nuraddeen,suka feɗare masa suka ce sam su bazasu koyi tsafi ba,wanda Aishatu ta goyi bayansu,wanda da kanta ta saka su makarantar boko,suka ci gaba da karatu,saidai kuma ƴarta Saddiƙa tun tana ƙaramar yarinya ta kasance wata feɗararrar yarinya marar tausayi da Imani,wanda ta samu farin jini sosai a wajen Toro da kuma su Baba Sa'adu wanda a hankali suka fara koya mata harkar tsafi tun tana ƴar ƙaramarta,wanda ba ƙaramin ɗaci zuciyoyin su Nuraddeen da Modibbo sukayi ba ganin kalar gurɓatacciyar Rayuwar da ƴan uwansu Da Mahaifinsu suka ɗora masu ƙanwar tasu wanda babu yadda basuyi ba akan suga sun dakatar da ƙudirin Mahaifinsu,saidai abin yaci tura, Saddiƙa kuwa ganin Modibbo da Nuraddeen sun takura mata yasa tai masu wata muguwar tsana, wanda suma ko kaɗan basa jituwa da ita ko kaɗan,don ko Mahaifiyarta Aishatu ta gagara,kullum Aishatu cikin baƙincikin ganin halinda ƴarta ke ciki take, Saddiƙa kuwa kullum lamarin nata ta'azzara yake,haka su Sharu Khabir Sa'adu suka taso cikin gurɓatacciyar Rayuwa,wanda kowane a cikinsu burinsu bai wuce ace sun gaji Mahaifinsu ko Mahaifiyarsu Juwala,ganin Saddiƙa tai musu fintinkau a harkar tsafin yasa suka saduda,sai kuma Sharu ya biyo bayanta ganin hakane yasa Saddiƙa kula Sharu suna tsafikansu a tare,wanda har takai sun fara ajiye baƙaƙen Aljannu da kuma ƙananun Dodanni tsafi, lokacinne kuma Nuraddeen ya gaji da halayyar ƴan uwanshi ya tattara nashi ya nashi ya bar ƙasar Niger gaba ɗaya,wanda babu yadda baiyi da Modibbo ba su taho tare amma ya ƙiya,dole yasa shi barin ƙasar Niger ya komo Kano da zama wanda ya bazama neman ilimin boko dana Arabi, ganin zaman baiyi masa ne yasaka shi zuwa kasuwanni yana dako don ya samu ɗan abinda zai saka ma cikinsa,a haka har ya samu wani shago yana zama ana biyansa...........✍️ *Wannan kenan* Comments Share fisabilillah Wadannan su ne ƙwarin guiwata *By Mariam sani RIAMCOOL* *08209554986* [2/6, 5:51 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *Book 2* *By Mariam sani Riamcool* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* *Bismillahirrahmanirrahim* *Page* 66&67 ____________✍️ "Cikin hukuncin Ubangiji yana zama yana samun abinda zaici har ya dan dunga samun na kashewa,a haka yaci gaba da zama shago shima a hankali Allah ya bashi ikon nashi nakansa,yana nan Kano da zama yaji gaba ɗaya garin Kano ya fice masa a rai,dole yasa ya tattara yanashi_yanashi ya bar garin Kano ya koma Katsina da zama,nan ma ya buɗe shagon yana zama kuma yana karatunsa a Funtuwa,bayan ya kammala karatunsa ne a makarantarsu ya haɗu da Safara'u,suka ƙulla soyayya,har Allah Ubangiji ya bashi ikon aurenta,suka zauna anan Unguwar yari, saidai Safara'u tanada wani boɗaɗɗen hali wanda baza ka taɓa gane mata ba,sai ka zauna da ita,tunda Nuraddeen ya aureta ta fitineshi da masifa da jaraba,komai ya kawo mata bata godewa saidai rainuwa,gashi ta riga da ta rainashi bata jin maganarsa ko kaɗan,shi kuma gashi dama can bai iya masifa ba shiru_shiru yake,koda ta ishesa da masifa saidai kawai ya fice ya bar mata gidan, haka ya dinga rayuwar ƙunci da Safara'u, koda ta ishesa ya yanke hukuncin ƙara aure ko zai huta da jarabarta,haka ya shiga neman auren ƴar maƙwabcinsa Karime har aka bashi ita,ranar da Safara'u taji zai ƙara aure ba ƙaramin tashin hankali akayi ba don tayi rantsuwa ta maya ta ce duk ranarda aka kawo Karime sai an ɗauki gawarta haka aka ɗaura mashi aure da Karime yarinya nutsatstsiya bata da kwaramniya ko kaɗan,hakan yasa Nuraddeen jin daɗin zama da Karime,ana nan kwatsam wata rana saiga wata matashiyar budurwa ta shigo wujiga_wujiga tana neman temako,ganin halinda Matashiyar nan take ciki ne yasa Karime Temakonta,ta bata abinci da kuma masaukin da zata kwanta,koda Nuraddeen ya dawo saiga Safara'u ta fito tana masifar an kawo masu Aljana cikin gida an girke to wallahi kodai ta fita ko kuma ita ta tafi ta bar musu gidan, Nuraddeen da baisan kan zancen ba ya tambayi,Karime abinda ya faru,nan ta zauna ta faɗa masa kan temakon da tayi ne, Karime yasa ta kirawo masa budurwar,tunda ta fito ya kafeta da idanu,ganin tsantsar kyawu kamar Aljana don koshi kansa bai yarda da cewar Mutum bace yafi yarda da cewar Aljana ce,koda ta fito ya tambayi sunanta,cikin gurɓatacciyar hausarta ta ce masa sunanta Sajeeda kuma ita batada kowa iyayenta hatsari sukayi duk sun mutu gashi ita bata san kowa a Nigeria ba Sosai Nuraddeen da Karime suka ji tausayinta, Nuraddeen ya bata ɗaki guda a cikin gidansa donta zauna,saidai Safara'u tunda taga Sajeeda take jin wani uban haushinta,haka komai na gidan sai tace Sajeeda ita zatayi shi hatta da wankin kayanta Sajeeda keyi,saidai ita Sajeeda bata wani damu ba saboda tayi bautar da tafi wannan,koda Safara'u taga wannan bautar da take yi mata bata damuwa,sai tajanza ta dawo horata da yunwa da kuma gori da cin mutumci,Karime na gani ba halin yin magana don itama Safara'u bata raga mata ba,me gidanma kanshi ba wani taga masa tayi ba shiyasa kowa yake binta a sannu Tunda Sajeeda taga abinda Safara'u ke mata ta yanke hukuncin guduwa tabar gidan don bazata iya zama a gidan ba ko don horon yunwar da Safara'u ke mata,saidai da tazo guduwa saita fasa,don tasan ta gudu duk aikin da take yi zai dawo kan Karime,ga Karime ba lafiya gareta ba yanzun,hakan yasa ta haƙura da guduwar ta zauna,ana nan kwatsam sai ciki ya ɓullowa Karime wanda Safara'u taji zafi da haushin samunsa ta bazama bin bokaye da malamai,don ganin cikin jikin Karime ya zube amma sai Allah bai yarda ba,saidai Karime kullum cikin zubda jini take,wanda anyi maganin har an gaji ga kullum cikin ciwo take,haka cikin jikinta ya isa haihuwa amma shiru babu haihuwa har yakai shekara bata haihu ba,kullum cikin magani ake,ana haka wata rana saiga naƙuda ta taso gadan_gadan,koda Karime tazo haihuwa da tayi wani motsi sai gaɓar jikinta ta kare, koda akaga abinda ke faruwa aka yanke yi mata C S kawai,haka Nuraddeen da Sajeeda suna ji suna gani akayi mata tiyata,anyi nasarar fiddo jaririyar saidai abin mamaki itama kamar yadda mahaifiyarta ta kare itama haka Jaririyar gaɓɓan jikinta suka kare, haka Karime tasa aka kirawo mata Nuraddeen da kuma Sajeeda koda suka zo ta ɗauki hannayensu ta haɗa ta ce don Allah Nuraddeen yayi mata Alƙawarin auren Sajeeda don tasan ko bayan ba ranta Sajeeda ita ce zata maye masa gurbinta,ya temaka ya ɗaukar mata wannan Alƙawarin ko ba komai zata mutu cikin farinciki. Tunda Sajeeda taga yanayin da Karime take taketa faman kuka,bata ida shiga tashin hankali ba saida Karime ta ce ta auri Nuraddeen, taya zata auri Nuraddeen? mutumin da ko gaishesa tayi da ƙyar yake amsa mata,kuma gani take idan ta auri Nuraddeen kamar taci amanar Karime,kallonta Sajeeda tayi tana faɗin "don Allah Karime ki janye wannan alƙawarin don bazan iya cin amanarki ba na aurar miki miji," ta faɗa tana sakin kuka Murmushi Karime tayi mata tana faɗin "Sajeeda in har kina son na mutu cikin farinciki don Allah ku cika man ƙudirina ku auri junanku,don nasan ke kaɗaice Macen da Nuraddeen zai samu kwanciyar hankali,ki taimaka ki cika man wannan mafarkin nawa dana daɗe ina son ganin ya cika," Kama hannunta Nuraddeen yayi yana faɗin "Karimatu bama zaki mutu ba insha Allah,bana son kina wannan zancen," Kallonshi kawai tayi hawaye na bin kuncinta ta ƙara kamo hannun Sajeeda ta ɗora akan jaririyar ta ce ta bama Sajeeda ita halak malak in har ta rayu dukda tasan bama lallai itama ƴar ta rayu ba, kuka sosai Sajeeda tayi abinda Karime ke faɗa, Nuraddeen ma hankalinsa yayi masifar tashi,suna zaune haka suka dinga jin jikin Karime na bada sautin ƙas alamar karyewa,haka duk gaɓar da jikin Karime ta karye ta Jinjirar ma saita kare,babu abinda Karime ke faɗa in banda kiran sunan Allah da kalmar shahada,jaririyar kuwa tun tana kukan azaba har ta daina,haka Karime ta amsa kiran Mahaliccimmu,tana rasuwa itama Jinjirar ta rasu hauka ne kaɗai Nuraddeen da Sajeeda ke basuyi ba don Nuraddeen yama fi Sajeeda dangana,don ita suma ta dinga yi da ta farfaɗo sunan Karime take kira,suna ji suna gani aka kai Karime da ƴarta Makwancinsu Safara'u kuwa ganin taci ma ƙudirinta na ganin bayan Karime da abinda ta haifa hankalinta ya kwanta taci gaba da nishaɗi a ɓoye, a fili kuwa ta fito kamar tafi kowa shiga tashin hankali,don saida tayi sumar ƙarya tafi goma,haka aka gama zaman makoki Sajeeda kuwa kullum cikin kuka take duk ta fita hayyacinta,dagana saima Safara'u data dinga bin ƴan unguwarsu tana faɗin ai Sajeeda Mayya ce ita ce wacce ta cinye Karime da ƴarta,wai a ƙasarsuma saboda tsabar maitarta shiyasa aka korota ta taho Nigeria,gaba ɗaya Unguwar ta ɗauka da lalle Sajeeda Mayya ce shiyasa gatanan kamar Aljana,haka Sajeeda batada kingin shan ruwa cikin Unguwar data fito yara zasu dinga yi mata ihu da jifarta suna faɗin ga mayya nan ga mayya nan,ga matsatsin da take fuskanta ga Safara'u,anan kwatsam saiga Nuraddeen ya faɗa mata aurenta zaiyi don cika ma Matarsa ƙudirinta,itama Sajeeda bata wani ja ba,amma taci kuka kamar zata suƙe,koda Safara'u taji zai auri Sajeeda hankalinta ya tashi don saida tayi ɗan ƙaramin hauka,don saida ta kama Sajeeda tai mata shegen dukan da ko ɗan yatsanta bata iya ɗagawa,koda Nuraddeen ya dawo yaga ɗanyen hukuncin da ta ɗauka ya fusata shima yai mata shegen duka,abinda bai taɓa ba,kuma yai rantsuwa ya maya yace muddin ko kallon banza tayiwa Sajeeda Wallahi sai ya saketa, wannan hukuncin daya ɗauka ne yasa Safara'u shafama Sajeeda lafiya ta bari har akayi auren ranar da aka ɗaura auren Sajeeda tayi kuka Sosai na rashin iyayenta da kuma ƴar uwarta ita kanta ta rasa taƙamaiman abinda yasa ta baro ƴar uwarta ga ko kaɗan bata son ama kira sunan Abuja *Wayyo ni kaina labarinku Sajeeda da Nuraddeen ya fara taɓa man zuciya😓* Wannan kenan *Comments Share fisabilillah* Waɗannan su ne ƙwarin guiwata *By Mariam sani Riamcool* *08109554986* [2/6, 5:51 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *Book 2* *By Mariam sani Riamcool* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* *Bismillahirrahmanirrahim* *Page* 68&69 ______________✍️Zaman da Sajeeda take a gidan Nuraddeen zama ne na rashin jin daɗi ko kadan, dan ko kaɗan rayuwar gidan bata mata daɗi, Nuraddeen da ita da babunta duk ɗaya yake, shimfiɗa ce kaɗai ke haɗasu da ita, magana ma wannan sai da dalili take masa, Abinci kuwa sai Safara'u taga damar bata take ci, idan ko bata bata ba haka zata kwana da yunwa, duk tayi baƙi da rama ta fita hayyacinta, ga ciwo da takeyi daga tsai tsaye, ganin ciwon da Sajeeda keyi ne yasa Nuraddeen kaita Asibiti, koda ya kaita gwajin farko aka tabbatar masa da ciki ne a jikinta, wanda ba ƙaramin farin ciki yayi ba, cikin dake jikinta ne ya saka yake bata kulawa aiki ma ya hana Safara'u ta sakata, haka ya ɗauki son duniya ya azama cikin jikin Sajeeda tunda Safara'u ta fahimci Sajeeda nada ciki ta ƙudiri aniyar ganin bayanta, hakan yasa ta bazama bin bokaye da Malamai don ganin bayanta, kamar yadda tasa akayi ma Karime aiki, haka tasa akayiwa Sajeeda, cikin Sajeeda nada wata bakwai ta fara zubar da jini wanda hankalin Nuraddeen dana Sajeeda ya tashi, wanda ya bazama neman maganin gida don ya fahimci ƙullin Safara'u ne. Cikin hukuncin Allah sai gashi an dace an samu jinin ya tsaya, saidai Nuraddeen ya faɗa ma Sajeeda ta gwada ma Safara'u jinin bai tsaya ba,ita kam Safara'u ganin haƙarta ta cimma ruwa yasa ta zuba ido tana jiran mutuwar Sajeeda, A hankali kuma Arziƙin Nuraddeen ya dinga bunƙasa, tun yanada shago guda har yakai ga yana buɗe shaguna yana zuba yara a ciki, hakan yasa ya tashi daga Unguwar yari ya koma Sabon gidanshi daya gina me kyau, cikin jikin Sajeeda nada wata tara cif ta haifi ɗanta namiji, wanda Safara'u tayi matuƙar mamaki ganin Sajeeda bata mutu ba, ga Bokan da yayi mata aiki baya nan. Nuraddeen yayi matuƙar murna ganin Allah ya azurtasa da samun ɗa, kasancewar Sajeeda batada kowa ya saka basu wani taron suna ba, aka sakawa yaro suna Fauzan, sai kuma kulawar da ta samu daga Nuraddeen ta bar samunta ta koma ga Fauzan, ana haka hankalin Nuraddeen ya kuma karkata da son zuwa Niger, haka ya tattara su Sajeeda suka tafi Niger, tunda ya doso hanyar gidansu gabansa yaketa mummunar faɗuwa, Sajeeda ma gurinta hakan yake, Yadda yabar gidan haka ya samesa babu abinda ya canza, koda ya shiga ɗakin A'ishatu suka fara sauka, a bakinta yake jin mahaifinsa Toro ya mutu, wanda mutuwar ba ƙaramin razanasa tayi ba ganin yadda mahaifinsa ya mutu a gurɓatacciyar Rayuwa, saidai ya masa addu'a haka su Sajeeda sunyiwa ƴan gidan gaba ɗaya ta'aziyya wanda gidan yanzun ya ciki da zuri'ar su Baba Sa'adu. Tunda Saddiƙa taga Safara'u ta ɗora mummunan ƙudiri akanta saboda ba ƙaramar tsana Saddiƙa tayiwa Nuraddeen ba, a hankali ta dinga shiga jikin Sajeeda, wanda Sajeeda tunda taga Saddiƙa hankalinta bai kwanta da ita ba, hasalima ko haɗa ido sukayi da Saddiƙa sai idonta ya dinga zafi kamar za'a ƙwalƙwale mata shi haka take ji, sai dai ta nemi tsari wajen ubangiji Tunda su Baba Sa'adu da Sharu suka ga yadda Nuraddeen ya koma shikenan suka dinga masa Hassada babu kamar Sharu yafi kowa yiwa Nuraddeen Hassada dande shi tashi bata fito fili ba ta Sa'adu ne ta fito fili, Modibbo kuwa shima tunda Nuraddeen ya bar ƙasar shima ya ɗaga saidai Time to Time yakan zo ya duba gida ya koma, shi kam Nuraddeen ganin halinda ƴan uwansa suke ciki ne ya sakashi jin tausayinsu ganin ga tsafikan suna yi amma basa da dukiyar, haka ya tattaro iyalansa suka dawo,koda suka dawo ya fara ma ƴan Uwansa ginin ƙaton gida,da taimakon Ubangiji ya kammala musu ginin gidan haka yasa suka tattaro kayansu suka dawo nan da zama dukkansu ya basu jarin da zasu iya riƙe kansu,har Saddiƙa saida ta dawo ita da mijinta Tunda Saddiƙa ta dawo tazo ta dunga shigewa Sajeeda ga wani irin tsoronta da Sajeeda keyi komai tasakata shi take AIKATAWA, lokacin da Fauzan yakai 5 yrs ne Safara'u ta samu ciki wanda shima Nuraddeen yayi murna,hakan yasa Safara'u ta tsiri iskanci kala_kala Sharu ma tunda yaga Sajeeda yaji duk duniya babu Macen da yake so sama da ita hakan yasa ya tsiri zuwa gidan koda yaushe, a hankali ya fara bijoro ma Sajeeda da son kasancewa da ita, nan ta nuna masa sam bai isa ba kuma ta ƙudiri aniyar faɗa ma Nuraddeen saidai da tazo faɗa masa saita manta, ga Saddiƙa data tasota gaba,dan shigar da ita ƙungiyar tsafi saidai komai suka sakata aikata musu takan bijire masu hakan yasa suka dinga gana mata baƙar azaba kala_kala,sauƙinta guda koda yaushe bakinta bashi rabo da addu'a, Haka rayuwar taci gaba da tafiya har Safara'u ta haifi ƴarta ta farko Zulfa'u, sannan ta haifi Suhailat,wanda Nuraddeen ya tattara dukkan wata kulawa ya miƙata ga ƴaƴan Mama wato Safara'u Sajeeda kuwa kullum cikin azabar Saddiƙa take gashi ta kasa faɗawa kowa,to wama ke gareta da zata faɗawa damuwarta? shiyasa tai haƙuri ta maida dukkan lamurranta ga Allah ga koda yaushe da tunanin halunda ta baro ƴar uwarta take,ga Sharu da ya ƙara takura mata kullum idan yazo sai yayi yadda yayi ya taɓa mata jiki don shima yanzun ko kaɗan bata iya yi masa musu, kusantarta ne kaɗai ta hana yayi dukda tana bala'in jin tsoronsa, haka rayuwar taci gaba da tafiya, lokacinda Fauzan yake shekara goma Allah ya sake bama Sajeeda wani cikin, tunda cikinta yakai wata tara take munanan mafalkai akan cikin don tunda ta samu cikin kullum sai tayi mafalkin tana cikin jini da jinjira, ranar da zata haihu ne tai mafarkin jinjirai mata biyu a hannunta ga Saddiƙa da wani mutum wanda bata san koshi waye ba saboda wata kalar suffa yazo mata Saddiƙa ce kaɗai tazo a suffarta,koda mutumin yazo ya ɗauki jinjira ɗaya a hannun Sajeeda ya miƙawa Saddiƙa, yana miƙo mata Saddiƙa taci gaba da ƙyalƙyala wata sheɗaniyar dariya sannan ta ce ma Sajeeda tayi musayar Ruhi ta cireta daga ƙungiyar matsafa amma tabbas ƴarta ita ce wacce zata maye gurbinta, tana kaiwa nan Sajeeda ta farka da wani Azababbiyar naƙuda gashi Nuraddeen bayanan daga ita sai Fauzan, tada shi tayi yaje ya kirawo mata Mama,dukda tasan mawuyacin Abu ne tazo, Fauzan na fita ta dunga jin wata irin Shaɗaniyar dariya mai ban tsoro ga wulgawar baƙaƙen Abubuwa da take gani, tsurewa tayi waje guda dukkan wata addu'a da tazo bakinta ita takeyi,hakan yasa ta daina ganin abubuwan saidai dariyar da akeyi ne wacce kamar ta tsaga ɗakin ita ce ba'a daina ba,jin tahowar abu yasa ta kira sunan Allah haka ƴa ɗaya ta faɗo,sannan ta ƙara jin tahowar wata sunan Allah taci gaba da faɗi ƴar da tazo fitowa saita koma,ga dariyar da aketa ƙyalƙyalawa,da ƙyar ta samu ƴar ta faɗo wacce tana faɗowa ta tsaya ita ba sama ba sannan kuma ba ƙasa ba,ɗakinne yai ɗif na ƴan mintuna sannan kuma aka cigaba da tafi raf_raf wasu kalar halittu na fitowa suna gewaye jinjirar suna surutai ganin haka ne yasa Ammi wato Sajeeda ta rarrfo domin ɗauke ƴarta, wata sarƙa aka saka aka ɗaureta,wani irin kuka ne ya kufce mata tana roƙon su akan su ƙyale mata ƴa ita ta yarda su tsafa nata ruhin, haka tana kallo suka cigaba da surkullen tsafi da ƴarta,suna gamawa jinjirar ta canyara uban kuka,sannan suka ɓacce suna ɓaccewa Ammi ta rarrafo ta tallabi ƴarta tana kuka,ware idonta jinjirar tayi ta sauke su akan Ammi wanda zuciyar Ammi ba ƙaramin bugawa tayi ba ganin wasu kalar idanu dake da jinjirar, blue ne har wani walƙiya suke suna haskawa ga kafeta da ido jinjirar da tayi, hawaye na fitowa, Kuka Ammi ta fashe dashi tana faɗin "miye na aikatawa dangin Mahaifinku da zasu cutar dani har haka me yasa ni basu mallake ruhin nawa ba saike da babu haƙƙin kowa akanki, Saddiƙa kin cuceni dakeda azzalumin mutumin can wanda ke ɓoye kama wanda nasan tabbas shi ɗin jinin Nuraddeen ne?," tana kaiwa nan ta fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya wajen gudar ƴar ta nufa tana dubata kama suke Sosai data hannunta wacce babu abinda ya banbantasu ɗaukosu tayi ta rungumesu a ƙirji tana maijin tausayin halinda yaran zasu tashi,tashi tayi ta samu reza ta yanke musu cibi ta ɗan goggoge musu jiki sanna ta fito Falo tana fitowa taci karoda Fauzan yanata sharara bacci addu'a ta tofa masa ta gyara masa kwanciyarsa sannan ta dawo ta kwanta kusada jinjiran tana kwanciya wani kalar bacci mai nauyi ya ɗauketa sai waje asuba ta farka da addu'a ɗauke a bakinta ta tashi kallon yadda ruwan wanka ta shiga ta ɗora,saida ta gyara yaran da ɗakin sannan ta shiga tayi wanka ta gyara jikinta itama Fauzan ta tada yaje yai salla sannan ya dawo koda ya dawo yaga jinjiran ya tare wajensu babu abinda ke tadasa saida dalili Tunda akayi haihuwar sau ɗaya Mama tazo ta duba yaran wanda saida ta yaɓa baƙaƙen maganganu akan jinjirar da idonta ya banbanta,dan itama ganin farko saida ta tsorata da idon yarinyar,hakan yasa duk wanda yazo barka Ammi ke hanasa ɗaukar ɗayar jinjirar,haka zalika koda matan su Baba Sa'adu suka ga ƴar suka dinga faɗin lallai tayi gadon tsafi,daganan ko waccensu ta fara jan jiki daga Ammi, sai ran kwana shidda sannan Nuraddeen ya dawo,koda ya dawo yaga kyautar da Allah ya bashi yayi Matuƙar murna, haka yayiwa yaran huɗuba da *RAIHANATU* da kuma *RAHEENATU* haka Ammi taci gaba da rainon ƴaƴanta wanda tun suna yara suka fara fuskantar tsangwama daga wajensu Zulfa'u don Mama ta kitsa masu ko kaɗan basa shiga sabgar Fauzan,dan duk yadda yayi ya jawo su a jiki basa yadda su zo ko gunsu ga hantara da dukan da Mama ke masa wanda Ammi ko kaɗan bata ɗaga kai ta kalleta,shima Fauzan ɗin ganin ya fara hankali yasaka shi maida hankalinsa da kulawarsa akan ƙannensa waɗanda ya ɗauki son duniya ya aza masu, haka Abba duk cikin yaransa yafi nuna ƙaunarsu Raihana akan kowa Ana nan kuma saiga Abba ya ƙara auro bazawara Zainab wacce tunda tazo daga farko kamar babu ruwanta don duk yadda Mama tayi su haɗa kai da ita ta ƙiya don ko kaɗan babu ruwanta da kowa, a lokacin kuma Abba arziƙi ya bunƙasa hakan yasa ya dinga nunawa Ammi izaya kala _kala, abu kaɗan zatayi sai masifa da zaginta,tun yana zaginta har yakai ga yana dukanta,wanda cikin matansa ita ce ta zama Bora duk kyan jikin Ammi saida ya lalace da azabar gidan Nuraddeen,ga Sharu daya matsa mata akan ta amince ya kusanceta ko ya ƙaƙaba mata sharri, ana cikin haka saiga kuma ciki ya ƙara ɓullo mata,lokacinda su Raihana suke da Shekara biyu lokacinne kuma ta haifi Saddeeq, ga lamarin Raihana daya fara bata tsoro yarinya ƙarama saita dinga ambatar jini zata sha,duk ko ranar da ta ambaci hakan to lallai ranar bata cin komai ita a lallai jinin data ambata shi zava bata, a hankali kuma Fauzan ya fahimci shima abinda ke damun ƙanwar tasu wanda kullum cikin yi mata Addu'a yake, wanda Raihana tun tana yarinya take shiru__shiru saka makon Raheenatu da take ƴar masifa tun tana tatsitsiyarta,haka zalika ko faɗa aka yiwa Raihana tai zuciya sai mutum ya gayawa jikinsa.......✍️ *Wannan kenan* Comments, Share fisabililla Waɗannan su ne ƙwarin guiwata *By Mariam sani Riamcool* *08109554986* [2/6, 5:51 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *Book 2* *By Mariam sani Riamcool* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* *Bismillahirrahmanirrahim* *Page* 70&71 ___________✍️Shiyasa abin nawa yake bama Ammi tsoro,shiyasa tun ina ƙarama Ammi bata barina shiga yara don ko faɗa ya haɗani da yaro harya kai ga ya dokeni,to washe gari da gawar yaron za'a tashi,tunda Ammi taga hakan saita dinga hana ni shiga cikin yara, Ammi kuwa babu abinda ke ɓata mata rai irin yadda Sharu yake ƙara shishshige mata don tun yana taɓa mata jiki har yakai ga ta ƙarfi ya kusanceta,kuma yai mata gargaɗi mai tsauri akan muddin koda wasa ta sake ta tona masa asiri saiya kasheta ya ɓatar ya kuma yiwa yaranta mata fyaɗe,ta yadda babu wanda zai zargesa Wannan gargaɗin da Saharu yayi mata shiya hanata tona masa asiri,don tasan tabbas duk abinda Sharu ya faɗa tsaf zai iya don ko kaɗan babu zuciyar musulunci a tare dashi ana haka saiga kuma Abba zaiyi tafiya na tsawon shekara guda wanda dagashi sai Mama da yaranta sai Aunty Amarya suka tafi,tunda ya tafi Sharu ya mayar da Ammi kamar wata matarsa don duk lokacin daya so buƙata zaizo wajenta ya sauke wutar sha'awarsa akanta,Shiyasa koda yaushe cikin kuka take da dana sanin auren Abba,haka tun ina ƙarama na taso nake ganin kullum Mahaifiyata cikin zubarda hawaye take,ga dama tun ina ƙarama nake yawan mafarkin yadda nake shan jini da kuma yadda ake bani mutane ina kashewa, wanda wannan kisan idan nayi shi yake sakani cikin shauƙi, haka tunda aka sakani a makaranta nakan fuskanci kyara da kuma tsangwama don acewarsu kalar halittana yayi kama dana Mayu ko Aljannu wannan dalilinne yasa tunda na taso yara da manya ke faɗa mani kalmar mayya wanda a lokacin bansan ma'anar kalmar ba, wani lokacin nakanzo na tamabayi Ammi ta faɗa man ma'anar kalmar mayya saidai tayi murmushin takaici ta kalleni, tunda na fara wayo nake ganin mahaifiyata kullum cikin zubarda hawaye take,ga abinda naɗan fara lura dashi duk ranarda Baba Sharu yazo saiya koromu yace mu fito,daya fito muka shiga zamu iske Ammi na kuka hakan yasa na dinga tunanin ko idan ya shiga dukan Ammi yake shiyasa take kuka, nikam tun ranarda naga ya fito Ammi na kuka na yanke hukuncin da yazo saina laɓe naga miyake yiwa Ammi har take kuka don muddin na kamasa yana dukan Ammi to tabbas saina tanadi duwatsun da zan fasa masa kai dasu,haka washe gari yana dawowa na laɓe ina don inji ko dukanta yake saidai leƙawar da zanyi naci karo ya daɗe mata baki da hanci yana ta shaƙa mata wata Powder wacce yasa jikinta yai laƙwas wata uwar ƙara na ƙwalla wacce ta ankarar da Baba Sharu,ganin hakan ne yasa ya fisgoni ya ɗaga hannunsa da niyyar shararaman sai kuma ya fasa yana mai man gargaɗi akan muddin na faɗa ma wani abinda nagani to saiya saka wuƙa ya yankani ya bada jinina hakama Ammi saiya kasheta, wannan gargaɗin da yayi shine wanda ya tsoratar dani sosai,inaji ina gani ya fice,yana fita na fashe da kuka ina faɗawa jikin Ammi itama hannu tasa tana bubbuga bayana tana son yi man magana amma ta kasa ko kaɗan bata iya buɗe bakinta ji take da tazo yin magana kamar an saka mata zare da Allura an ɗinke, saidai tasan koma miye yanada nasaba da abinda Sharu ya zuba mata tabbas koda zata yafewa kowa duniya to bazata taɓa yafewa Sharu ba,koda Ya Fauzan yazo yaga halinda Ammi ta shiga na rashin magana,hankalinsa ya tashi ga babu abinda yafi ɗaga masa hankali irin kukan da yaga mahaifiyarmu nayi, hakan yasa ya dinga kiran Abba amma ko kaɗan baya samunsa dole yasa ya haƙura haka muka kwana da ita wanda da ƙyar Yaya Fauzan ya lallaɓamu mukayi bacci,shikam da Ammi babu wanda ya runtsa a ranar yanda suka ga rana haka suka ga dare,washe gari ma haka ta yini babu maga,ga wani uban aman jinin da take gundari_gundari,ga Abba ko kaɗan ba'a samun wayoyinsa, haka Ya Fauzan ya sanarda su Baba Sa'adu,amma babu wanda yabi takan abinda ya faɗa kowa ya kama harkar gabansa, haka muka zubawa sarautar Allah ido muna kallo kullum Ammi cikin ciwo take ga ƙafafuwanta dake mata ciwo ko kaɗan bata iya tashi babu magana bata kuma ita tashi,ranar da muka samu wayar Abba muka sanar masa shima babu wani alamar damuwa daya nuna saima cewa da yayi abari idan ya dawo ya neman mata magani,haka muka ƙyale muna kallon mahaifiyarmu cikin wannan hali, tunda abinnan ya faru bamu ƙara ganin Baba Sharu gidanba wanda tunin duniya tsani dukkan wani ɗan uwan Abba don a ganina sune Silar jefa Ammi cikin wannan hali,saidai muna cikin wannan halinne muka nemi Ammi bamu ganta ba, hankalimmu ya sake tashi wanda harda ƴan unguwa aka shiga cigiyarta hakama Abba ya sanya ana nemanta amma ƙasa ko sama har tsawo 3 Month babu Ammi,wanda duk wata kulawarmu ya koma akan ya Fauzan kullum shine yakan zauna ya rarrashemu ga Sadeeq shima da yake tada rigima akaisa wajen Ammi, rana guda aka tsinci gawar mace wacce aka cirewa kai da ƙafafuwa wacce akeda tabbacin ta Ammi ce ranan kowa saida ya shiga matsanancin tashin hankali wanda bazan iya misulta muku shi ba,muna ji muna gani aka kaita makwancinta,tun daga lokacin kuwa Ya Fauzan ya zamto shine ya maye mana gurbin Ammi,ga Abba tunda ya tafi saida ya share shekara da watanni sannan suka dawo shima Abba tunda ya dawo ya dinga bamu kulawa ta musamman dan saida ya rasa Sajeeda yake jin wata ƙaunarta da ƙaunar yaranta na musamman,hakan yasa koda yaushe ya kanzo ya tare wajemmu yana mai ɗebe man kewar Mahaifiyarmu,saidai wannan kulawar da yake bamu ita ce ta ƙara janyo ƙiyayyar ƴan Uwammu da kuma Matan Abba,wanda ko kaɗan tsakanimmu dasu bamu shiri, haka zalika ina girma lamarina na ƙara ta'azzara don tun mutane basu farga ba har suka fara ganewa cewar lallai duk wanda ya dokeni baya kwana duniyar, don ko a lokacin ni kaina na kashe mutanen da bansan adadinsu ba, tun Mahaifimmu na bamu kulawa har yakai ga ya sauya yaji kuma duk duniya babu waɗanda ya tsana sama damu,haka shima Ya Fauzan kwatsam aka nemesa aka rasa,wanda tun ana saka ran ganinsa har muka fidda,haka muka ci gaba da rayuwa mu kaɗai," nan na zauna na faɗa masu da ta yadda muka taso gidanmu harya kawowa auren biyan bashin da aka mana dukkansu shiru sukayi Mommy kuwa idan banda kuka babu abinda take yi jin irin jarabawar data samu ƴar uwarta wanda koma miye ita ce sanadi, Da ƙyar muka samu muka rarrashi Mommy tayi shiru, Hameeda ma kukan tausayin rayuwar da mukayi take, Nuraim ma ya ƙara jin wani karsashin ƙara son temakon Raihana,dukda zuciyarsa da take wani bugawa sakamakon jin Raihana nada aure......✍️ *Sakamakon rashin Comment yasa na maida wannan littafin na kuɗi duk wacce take son ci gaba da karantawa ta siya💁‍♀️* Wannan kenan *By Mariam sani Riamcool* *08109554986* [2/6, 5:51 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *Book 2* *By Mariam sani Riamcool* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* Happy New Year 2024 as we saw 2023. May God bless us with good health. May God open the doors of blessings for us. *So da na ce bazan yi a kyauta ba sai an biya za'a ci gaba da karantawa,sai kuma jiya naga kun janza kunyi man Comment,shiyasa zan cigaba a kyauta amma dan Allah ku dinga Comment in har bakuyi bazanji daɗin maku Typing ba dan Allah fans ku janza, ku dinga bamu ƙwarin gwiwa,mu munayi don mu nishaɗantar daku da faɗakarwa donmu faranta muku amma kukuma sai ku musguna mana ta hanyar ƙin yin Comment* *Bismillahirrahmanirrahim* *Page 72&73* ___________Duk yanda yaso danne abinda ke zuciyarsa kasawa yayi saboda,ace wacce ya daɗe da mafarkin son kasancewa da ita a rayuwa,wacce kullum yake cikin mafarkinta,wacce ya daɗe da cimma burin zama uwar ƴaƴansa tun a mafarkin da yake ganinta, ashe ma duk wannan abun da yake tanada aure shi kam ya zaiyi da zuciyarsa da take yunƙurin tarwatsewa, a hankali wasu siraran hawayen da baisan da zuwansu ba saidai yaji ɗuminsu a kuncinsa a hankali yasa hannu ya ɗaukesu Tunda ya lula duniyar tunani nake kallonsa harya zuwa lokacin da hawayen suka zubo masa ya share, zuciyata ce ta shiga kokwanto abinda yasaka shi hawayen,sharewa muka ci gaba da hira nida Hameeda da miƙewa Nuraim yayi ya ce "Mommy zan shiga ciki naɗan kwanta saboda kaina na ɗan sara man ," ya faɗa yana yamitsa fuska Kallonshi Mommy tayi tana faɗin "Son da so nake ka maida Raihana gida kaga saima kaga gidan daganan." "Hameed ya kaita ko Jabir Mommy ni bazan iya driving ba." Yana gama faɗa ya fice, kowa da kallo ya bisa Yana fita Part ɗinsa ya wuce a hankali ya zo danna door bell ɗin zai shiga saidai cak ya tsaya sakamakon jin maganar da Nafisa ke faɗi, "Shu'aibu Tabbas NURAIM ya ida gano wasu gurɓataccin ayyukan da nakeyi to bazan saurara masa ba wallahi saina kashesa na sadaukar da ruhinsa, Wannan ma abinda yasa na ƙyalesa barinsa nayi naga iya gudun ruwansa,kuma shima yayi yunƙurin tona mani asiri to tabbas saina kashesa naci zuciyarsa nasha jininsa,yanzun ma abinda yasa na raga masa ina son mallakar dukkan wasu Company sa, sannan na aiwatar da ƙudirina akansa, sannan wannan abokin nasa Jabir a yau nake son ku ɓatar man dashi idan da hali ma ina so ku kashesa ku ɓadda gawarsa, saboda na fahimci shine ke taimakawa Nuraim wajen gano miyagun ayyukana, ina son kuma Ku tasgara rayuwar matarsa Ni'imatu kuyi mata yankan,haka zalika yarinyar da kuka ce kunga Nuraim da ita itama da sun fito ku haɗa da ita ku kashe banza, wallahi yanda Nuraim ya fara shiga lammurrana saina mayar da Ahalinsa gawarwaki saina mayar da gidansu gidan zaman makoki,sannan munafukar Uwarsa dake bashi ƙwarin gwiwar bibiyata itama bazata sha ba,sannan shima Abdurrahim da kuka riga kuma kama kada ku barsa ya kubce maku so nake ku haɗa shi da wannan daɗaɗɗen Saurayi ku ƙara gana masu azaba," tana kaiwa nanan ta fashe da dariya tana jan dogon numfashi sannan tace "wallahi Nuraim saina tasgarar da rayuwarka tunda ka taɓoni". Shikam Nuraim suman tsaye yayi zuciyarsa na tafarfasa da zafi, da sauri ya juya zuwa Part ɗin Mommy don ya tsayar da Jabir dake yunƙurin tafiya shida Raihana, ko Sallama baiyi ba ya shiga Falon yana faɗin "Mommy ina Jabir da Raihana?." Kallonshi Mommy take tana faɗin "Son lafiya naga hankalinka a tashe meya faru? su Jabir kana fita shima ya fita da Raihana don mayarda ita," ta faɗa itama hankalinta a tashe Baiyi magana ba ya juya da sauri ya shiga Mota ya jata da gudun tsiya yana tunanin ta ina zai fara ga Abdurrahim gasu Jabir ga Ni'imatu, wani irin gudu yake shararawa kai kace zai tashi sama, saidai wata ƙatuwar Mota dayaga tana yo kansa gadan_gadan hankalinsa ya tashi, haka yaita ƙoƙarin kauce mata amma saida ta cimmasa da mugun gudu ta kawo ma motarsa karo wacce ta birkice da Nuraim daketa ambatar sunan Allah, motar na bige ta Nuraim ta wuce a tsiyace, Tun sanda su Raihana suka fito Jabir zai kaita wata mota ta dinga binsu ta baya sai daga baya Jabir ya lura da binsun da akeyi, gudu ya ƙara ma motarsa,saidai duk iya gudunsa saida suka cimma sa da wata motar tasha gabansa,da sauri ya taka birki yana ambatar sunan Allah, wani baƙin ƙaton mutum baƙi mummuna ya fito, yana zuwa ya buɗe yana fisgo ni da ƙarfi sannan ya ɗaga hannu ya sharara man marin da saida bakina ya fashe, sannan ya fiddo Jabir daga Motar yana saitasa da bindiga, dukkan waɗancan na cikin motar suka fito sannan ɗaya daga cikinsu ya matso yana bugawa Jabir ƙasan bindigarsa, wanda yasa tsakiyar kansa fashewa yana zubar da jini, nikam wannan jinin dana gani shine yasa kaina wani irin juyawa a hankali naji zuciyata na sauyawa tana komawa ya zuwa ta rashin imani, ji nake tsaf zan iya cin mutum a ɗanyensa, sannan na kora da jininsa, ga gangar jikina data fara janzawa ji nake kamar anyi man musayar wata, da sauri na gartsa wa mutumin nan cizo a hannu sannan na shaƙesa ina kafa masa wani cizon a wuya ina zuƙar jininsa ina jin wani manɗon daɗi da garɗi, da sauri wannan wani yazo yana fizgoni da ƙarfin tsiya, saidai ina juyowa dukkanninsu kowa ya tsorata, ganin yadda yanayin halittana ta fara janzawa yazuwa wata halittara ta ban ga haƙorana da baki da sukayi jage_ jage da jini.........✍️ *Wannan kenan Comment Share fisabilillah* Waɗannan su ne ƙwarin guiwata *By Riamcool* *08109554986* [2/6, 5:51 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *Book 2* *By Mariam sani Riamcool* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* *Bismillahirrahmanirrahim* *Page* 74&75 ___________✍️Da wata kalar murya mai fidda amo da sauti take faɗin "duk wanda yai ƙoƙarin taɓa man makamin fansata bazan taɓa ƙyalesa ba, ku tabbatar da dukkanku babu wanda zai tsira bare ya sha, wallahi dukkanku saina kashe ku, kamar yanda kuka so kashe man makamina, saidai ku zaɓi mutum guda wanda zan tura yakaiwa wacce ta aiko ku saƙo." dukkansu tsit sukayi jukunnan su duk sun jiƙe da zufa da fitsari ko wane jikinsa idan banda kyarma babu abinda jikinsa yake, Jabir kanshi shima matsanancin tsoro ya kamasa, lallai be yarda da Raihana mutum bace, ganin babu wanda yai magana a cikinsu yasa duk ta dinga binsu ɗaya bayan ɗaya tana zuƙe jinanansu, sai mutum ɗaya data bari shima tuni ya suma a wajen, ina gamawa naji wata juwa na neman yada ni ƙasa da sauri na dafe motar dake kusa dani ina ƙoƙarin amboton Allah amma zuciyata da bakina sun mani nauyin furtawa, a hankali na sulale ƙasa ina fashewa da kukan dana saba, ni kaina na kasa tantace wace kalar halitta ce ni da zan maida jinanan mutane ruwan shana, Jabir ne ya matso a ɗaɗɗare yana rarrashina da ƙyar na samu na miƙe ina ciro mayafin abayar na goge jinin daya ɓata man fuska da hannuwa, sannan na shiga motar Jabir yaja, yana parking a ƙofar gidan Alhaji Muttak'a na fito ina masa godiya na shige, Ina shigewa nayi saurin lulllub'e fuskana ina tafiya karo naji naci da mutum da sauri na juyo da fuskana, ina kallon Alhaji Muttak'a dana ɓata masa farar shadda da jini, shima a razane yake kallona da ƙyar ya haɗiye wani yawu daya tokare masa maƙoshi, sannan ya ce "Raihana kije na sakeki saki ukku ki gafarceni akan abinda nayi maki amma dan Allah dan annabi ina roƙonƙi da girman Allah da Manzonsa ki ƙyaleni da rayuwata da rayuwar iyalina, nasan tabbas ke ce kika kashe Aslam bana fatan ki ƙara ɗaukan rayuwan wani iyalin nawa,kinga kinsha jinin iyalina biyu to kinga kamar kinsha nawa ne, yanzun ki faɗa man dukkan abinda kike buƙata zan baki." ya faɗa yana fashewa da kukan daya daɗe da riƙewa wani banzan kallo na masa ina sakar masa wani Miskilin Murmushin daya saka ƴan hanjin cikinsa kaɗawa, kafin na kafesa da idanuna masu ƙara razana sa,tun zufa ta fara tsatsafo masa a jiki, saida na tabbatar ya razana sannan na kaɗa kaina ina wucesa, kai tsaye Side ɗina na wuce ina shiga na sauke wata nannauyar ajiyar zuciya sakin da Alhaji Muttak'a yai man ji nake kamar anyi man Albishir da gidan Aljanna, ji nake dukkan wani nauyin daya danne zuciyata ya ragu, wani kalar farinciki na tsinci kaina a ciki, saidai matsalar ɗaya ce yanzun "nikam ina zan dosa?," na tambayi kaina don bana son ƙara shiga cikin Al'umma ballantana na ɗauki rayuwan wani shiyasa zan nisanci mutane na koma a jeji da zama don hakan shine zai fiye mani Alkhairi *Nuraim* kuwa tunda motarsa ta birkice kansa ya bugu sosai har yai sanadiyar tsagewa jini na malala a hankali tsiraran mutanen dake wajen suka fara kawo temakon gaggawa wanda da ƙyar aka samu damar cirosa daga cikin motar babu alamar numfashi a tare dashi, ga kansa dake ta zubarda jini, da sauri aka ɗaukesa aka nufi asibiti dashi, kai tsaye Emergency room aka shiga dashi, wayar da aka zaro daga Aljihunsa aka fara duba Number ɗinda ya kira ta ƙarshe ita ce aka kira, lokacin Jabir yana tuƙi saida akai masa kusan 3 miss call sannan ya lura don kwata_kwata hankalinsa baya tare dashi, zaro wayan yayi yana dubawa yaga Number Nuraim da sauri ya danna kira, yana kira aka ɗauka yaji ana cewa mai wayar ne yai Accident idan ɗan uwansa ne yazo ana buƙatarsa, "Innnalilahi wa'inna ilaihirraji'un," shine abinda Jabir ke maimaitawa hankali a tashe yace su faɗa masa wane asibiti ne, nan suka faɗa masa, da sauri ya datse kiran gabansa idan banda dukan ukku_ukku babu abinda yake tabbas ko tantama baya yi wannan shirine aka shirya masu shida Nuraim shi an tura kashesa shi kuma Nuraim an haɗa masa hatsari, da hanzari ya nufi Hospital ɗin Kafin kace me su Mommy sun shigo suma hankalinsu ba'a kwance ba ciki kuwa harda Nafisat dake kukan munafurci, saidai tana ganin Jabir gabanta ya faɗi "to shi ya akayi wannan bai mutu ba? shida naso ace ya riga Nuraim mutuwa." ta tambayi kanta sun daɗe nan zaune kowa jirin_jirin zuciyoyin nata bugawa ba barema Mommy wacce dauriya kawai take Hameeda kuwa sarkin rashin dauriya tuni take kuka,ga wani babban tashin hankalinnasu anata kiran wayar Abdurrahim tana ringing amma ba'a ɗauka ba, Dada ce ta shigo da gudu daga ita sai bujen tsahhi na ciki, zane a hannu tanata sharɓan hawaye, Baba Salihu da Mama Sharifa nata rarrashinta, tana zuwa ta faɗa jikin Mommy ta sake fashewa da wani matsanancin kuka tana faɗin "Faɗima ki faɗa man me ya samu Nura ake faman ɓoye man kardai ki ce man mutuwa yayi," da sauri Mommy ta ɗagota itama hawayen nata na ƙoƙarin zubowa tai ƙoƙarin dannewa ta ce "Dada Nuraim ba mutuwa yayi ba hatsari ne yayi ki kwantar da hankalinki insha Allah zai tashi." Doctor ne ya fito yanata faman sharce zufa da hanzari Dada ta miƙe tana cewa "kai likita ya jikin Jikan nawa da sauƙi dai ko." wata zufar ya sake sharewa fuskarsa ɗauke da matsananciyar damuwa ya kalli Dada yana faɗin "Iya tabbas Allah shine ke rayawa kuma ya kashe wanda yaso babu abinda zance maku saidai haƙuri domin kuwa Allah........," bai ida ƙarasawa ba Dada tai tsallen ƴan bori ta cakumo kwalar likita tana falla masa mari sannan ta ce "kai likitan nasara ƙwalbatin ubanka nace, kada ka kuskura ka tunzura zuciyata na ci buhun ubanka yanzun, yoo dama ai munsan Allah shike rayawa kuma ya kashe wanda yaso, to kada ka kuskura ka ida hassala zuciyata yanzunnan nai maka abinda babu daɗi, harda wani cemin Iya, ka faɗa man wane ɗan tsako na taɓa ƙyanƙyashewa harda zaka kirani iya." ta faɗa tana sakin huci kamar wata kumurcin Maciji, Baba Salihu ne yazo ya dinga bama Dada baki da haƙuri harta saki likitan da ya fara jin azaba duk idanunsa sunyo waje saboda Dada ba ƙaramin shaƙarsa tayi ba, haƙuri su Mommy suka bashi, sannan ya ce su biyoshi Office don Dada bazata bari suyi magana a tsanake ba *Raheenatu* duƙe take tana kuka da wuƙa a hannunta ga Alhaji Bashir kwance cikin jini wata kalar ƙara ta ƙwalla tana girgiza kai,da sauri aka banko ɗakin ana shugowa saidai turus Hajiya Bilkisu tayi tana yadda Cup glas ɗin dake hannunta hankali a tashe ta kalli Raheenatu hawaye na zubowa take faɗin "Raheenatu kashe man miji kika yi, meya aikata miki da zaki kashesa? shan ƙwayar ki harya kai ga kisan kai, to wallahi yanda kika kashesa nima saina kasheki," ta faɗa tana nufo wajen Raheenatu a fusace wuƙar dake hannun Raheenatu ta amsa zata caka mata,kamar an wullo Sabreen tai saurin zuwa tasha gaban Hajiya Bilkisu tana riƙe hannunta ta ce "me kike shirin aikatawa ne? so kike kema a kasheki ne ki bari doka tayi aiki akanta." Wani kalar matsanancin kuka mai ban tausayi Raheenatu ta fashe dashi tana faɗin "wallahi bani ce na kashe miki Miji ba, taya kike tunanin zan kashesa? amma Allah ne shedata." a fusace Sabreen ta ɗaga hannu ta faska mata mari tana ƙara kai mata gula a ciki wacce tasa cikinta yin wani ƙugi tana duƙewa a wajen, kuka su Hajiya Bilkisu da Sabreen suke riris, tuni ƴan unguwar suka cika wajen da Police kowa da abinda yake faɗa donma Police sun tsawata wa mutanen dake ƙoƙarin kashe Rahinatu da bugu, tuni Police suka buga mata Ankwa a hannu suna tasa ƙeyarta ya zuwa Police Station ƴan Jarida da kuma mutane sai ɗaukarta hoto suke, wasu zafafan hawaye masu raɗaɗi da ɗacin zuciya ne suka sabko mata a kumatu tana sadda kanta ƙasa, "Hmmmm rayuwa kenan ashe duk yanda baka tunanin ƙaddara ita tana nan tana bibiyarka ko kaɗan banyi tunanin rayuwata zata juye daga mai kyau ba ta koma gurɓatacciya, saidai koma miya faru dani ta silar Mahaifimmu ne." ta faɗa zuciyarta na sake tafarfasa Hajiya Bilkisu kuwa tana can tana kukan munafurci da suman ƙarya, Sabreen ma kukan baikai har zuci ba tunda komai shirinsu ne, haka aka sallaci gawar Alhaji Bashir aka kaisa makwancinsa, Raheenatu kuwa tana hannu ƴan sanda suna gana mata azaba sunyi tambayar duniya ta faɗa masu me yasa ta kashesa amma sai tace Allah ne shedarta don komi zata ce masu bazasu yarda da ba ita ta kashe Alhaji Bashir ba, shiyasa tun ta jansa kala jikinta duk ya farfashe hannunta kuwa harya samu karaya, idanunta harsun rufe tsabar kumbura da sukayi . *Ɓangaren Jogu* Tsaye yake gaban wani ƙasungumin mummunan halitta mai ban tsoro,ga shima Naseer na kusada shi a zaune da wata kalar murya Jogu ke faɗin "dukda na hau karagar mulkin tsafi a yanzun banida wani ƙarfin ikon da zan iya dawo da mallakar da nayiwa waccan yarinya saboda baƙin ruhin Saddiƙa na a tareda ita, sannan ruhin wacce nake amfani dashi a halin yanzun Saddiƙa ta mayarwa da maishi,ka taimaka man da wani baƙin ikon da zaisa ya zamo kariya a garemu domin hana ɗaukar fansar Uwargijiya." wani kalar gurnani da nishi wannan baƙin Dodan yayi sannan ya dinga yin wani zance wanda ba'a ganewa, yana gamawa su Naseer suka dubesa a matsanancin tashin hankali suna cewa "ka taimaka ka bamu iko mu kuma munyi maka Alƙawarin kawo maka budurcin mace goma sannan jinin jinjirai goma sannan kawunan tsofi goma indai ka temakemu da baƙin ikonka...........✍️ Love U oll my fans😍 *Aci gaba da Comment ni kuma naci gaba da suɓurɓuɗo maku Typing* Wannan kenan *Comment share fisabilillah* Waɗannan su ne ƙwarin guiwata *By Riamcool* *08109554986* [2/6, 5:51 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *Book 2* *By Mariam sani Riamcool* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* *Bismillahirrahmanirrahim* *Page* 76&77 _____________✍️wani kalar dariya mai haɗe da gurnani mai tsoratarwa Dodan yayi, wannan ke nufin ya riga da ya amince zai basu baƙin ikon, wata ƙatuwar ajiyar zuciya suka saki gaba ɗayansu *London* Zulfa'u ce sanye da wani arnen white jeans daya kamata tsam duk a farfashe, da ƴar ɓingilalliyar Top wacce da kaɗan ta sauka a cibinta,ga gashin dokin data saka a kai ya wani zubo mata har ƙugunta,sai zaƙo_ zaƙon farcen kanti da aka saka mata a hannu sunsha pentin light pink color da kaganta kai bazaka ce tasan wata kalma ta musulunci ba ballantana har akirata da musulma , a hankali tasa hannunta ta buɗe ƙofar wajen ta shiga ciki haɗaɗɗen eatery ne,wanda wajen babu wasu mutane da yawa,yawancinsu duk turawa ne, tafiya take tana wani murguɗa ƙugu tana girgiza boobs ɗinta,wanda yaja hankalin turawan wajen, kai tsaye wajen wani guy choculate color ta wuce da pipe ɗin shisha dake riƙe a hannunsa yana taja yana fitarda hayaƙi ta hanci ta baki ga wasu ƴam mata suma duk a zaune suna jan shishar, tana zuwa ta faɗa jikin saurayin nan tana sumbatarsa, ta ce "How are You Sweet darling?, two day I missed U over, it is I come coved you," ta faɗa tana sakinsa wani kallo yai mata irinna ƴan iska ya ce mata "You know i'm not time always da zan dinga biye miki muna harka kullum kamar wasu dawakai." ya faɗa yana jan wani siririn tsaki wani ƙululun takaici ne ya kama Zulfa'u ganin irin wulaƙancin da Ma'aruf yayi mata gaban su Zeey da Billy, amma saita shanye, itama ta janyo pipe ɗin shisha tana ja,cikin ƴam matan babu wanda ya ce da ita ƙala ganin itama basu tanka ta ba, order Ma'aruf yayi musu suka ci suka sha sannan kowa ya kama gabanshi ya tafo da Zulfa'u dukda fushin da takeyi, haka ya rarrasheta domin yana son ya kashe arna da ita, kai tsaye wani haɗaɗden Hotel suka wuce,suna shiga suka faɗa Toilet sukayi wanka a tare sannan suka fito suka fara baɗalarsu,sun dade sannan Ma'aruf ya sararawa Zulfa'u shima don ta haɗa masa da kuka don ba ƙaramin azaba yake bata ba, saboda bata wani ƙware a harkar ba,duka zuwansu London ta haɗu da Ma'aruf suka fara Soyayya shima ɗan Nigeria ne, amma suna zaune shida Mamanshi da Babansa a London, haka Ma'aruf ya yaudari Zulfa'u harta yarda dashi ta bashi kanta yai amfani da ita, haka ya maida ita kamar wata matarsa,ita kam abinda yasa ta amince ganin yanada maƙuddan kuɗaɗe, shiyasa ta yadda ta buɗe masa gareji yana shiga ciki ya kwashi harka yanda yake so,daganan kuma ya haɗata da su Zee suma abokansa ne na kwalɓewa shi yasa suke adawa da Zulfa'u, kwance sukayi suna maida numfashi, saida Zulfa'u ta huta sannan tayi wanka ta fice gida Tunda ta shiga take jin kukan Mama ƙasa_ƙasa ida shiga ɗakin tayi kallon Mama tayi yadda ta shaƙe Suhailat tana faɗin "dan Ubanki ki faɗa man waye ya ɗibga miki ciki cikin samarinki masu jajayen kunnuwa kona shaƙeki ki mutu wallahi." Kuka sosai Suhailat keyi tana faɗin "Mama nima kaina bansan waye yayi man ciki ba wallahi saboda inada samarin da muke mu'amala dasu da dama,gashi yanzun cikin ya wuce 5 Month ballantana mu zubar dashi," gaban Zulfa'u ne ya faɗi itama fa ashe tana ɗauke da cikin Ma'aruf,kuma abinda yasa ta barshi don kawai ya aureta ne ko don albarkacin abinda zata haifa, to ashe itama Suhailat na dashi Sulalewa Mama tayi ta ce "shikenan Suhailat kin ida tona man asiri baya ga wanda Zainab ta tona man ashe dama muguwa itama yaudarata zata yi,na biyewa son zuciya na baro mijina cikin mawuyacin hali don kawai son abin duniya,gashi yanzun bani ga tsuntsu bani ga tarko, abinda naso su Raihana suyi cikin shege sai gashi kune kukayi, yanzun gashi haƙƙinsu dana Nuraddeen na bibiyata," haka Mama tayi_tayi Suhailat ta faɗa mata wanda yayi mata ciki amma ta ce itama bata sanshi ba, baƙin ciki goma da gomiya tara ya haɗe mata ga cikin shege ga Aunty Amarya ta yaudareta ta gudu da maƙuddan kuɗaɗe, haka ta zauna ta zurawa sarautar Allah ido, ana nan kuma itama saiga cikin Zulfa'u ya bayyana wanda saida Mama da kanta taje wajen Ma'aruf ta faɗa masa,kuma ya yadda da nashi ne,kuma ya ce aka zubar masa da ciki sai ya ɗaure su,idan ta haifa ta bashi ɗanshi kuma bazai taɓa aurenta ba,daganan ma ya rabu da ita *Raihana* tunda na zauna na fara haɗa kayana abinda kaɗai nake buƙata na ɗauka sai dai na rasa ina zan nufa shin a jejin zan tafi koko na tafi wajen Mommy nima naji ɗumin dangin Mahaifiyata,canza shawara nayi na nufi gidan Mommy dukda ba sosai nake gane hanya ba, haka na dinga Tafiya naci uwar tafiya ba kaɗan ba kafin na ƙarasa gidan da baƙar wahala,shiga nazo yi masu gadi suka hana,hakan yasaka ni neman waje na zauna don bazan iya jayayya da Mutum ba,zaune nayi ina jiran ko zanga Motar Nuraim yazo ko Hameed don na shiga amma shiru har 10:pm yayi shiru kakeji ga wajen daya yi tsit baka jin motsin komai can Asibiti kuwa ba ƙaramin artabu aka sha da Dada ba akan cewa itama fa lallai saita bi Office ɗin likita taji mike faruwa da Nuraim amma aka hanata, koda su Mommy suka shiga Doctor ya kallesu yayi masu ƴa ce "to Alhamdulillahi tunda mun samu damar ceto rayuwarsa yanzun mun riga munyi masa alluran bacci" godiya su Mommy sukayiwa Doctor sannan suka fito suna fitowa Nafisa ta zo tana kuka ta ce "ya mutu Mommy ko yana raye? dan Allah ki faɗa man wane hali yake ciki" "bai mutu ba Allah ya tseratar dashi daga sharrin miyagu ta faɗa tana bankawa Nafisa harara" gaban Nafisa ne ya faɗi "to taya suka gano nice na shirya komai? amma idan wannan baiyi ba ai akwai wani tarkon harke uwarsa bazan ƙyale ba" ta faɗa tana ficewa daga asibitin gaba ɗaya Jabir kuwa tun sadda yazo asibiti ya buɗe wayansa yaga message ɗin Nuraim ya faɗa masa duk abinda yaji daga bakin Nafisa shi yasa yaje ya ɗakko su Ni'imatu dasu Mommy, bai ɓoyewa Mommy komai ba ya faɗa mata koda Mommy taji hankalinta yayi masifar tashi jin har Abdurrahim yana hannunta,saida Jabir ya kwantar mata da hankali kan cewa zai san yanda za'ayi a cetosa daga hannunta,amma ya yanke shawarar su koma ɗaya daga cikin gidajen Nuraim wanda Nafisa bata ma san da zamansu ba ganin dare nayi yasa su Hameeda dasu Dada tahowa gida tunda suka tafo Hameeda taga Raihana zaune waje guda saboda hasken dake wajen yasaka ta ganeta nikam ina zaune ganin dare nata yi yasaka nama fidda rai da zuwan wani na gidan, tsayuwar Mota naji hakan yasaka ni saurin ɗagowa Hameeda ce tazo ta ce "Raihana mi kike yi anan?" "muje ciki zan faɗa miki abinda ya maidoni" shiga nai cikin Motar ina shiga wata tsohuwa tai tsimil ta ce "ke Hameeda a ina kika samo mana wannan Ajnar mai kama da Sajeeda?"Dada ta ƙarashe zancen da jin tsoro dan fa ita kallon Aljana take yiwa Raihana banza Hameeda tayi mata jikina ne yai sanyi jin abinda ta ce a sanyaye na gaida ita,amsa mani tayi tana yatsina fuska koda muka fito Hameeda ta jawo ni muka fito kai tsaye wani Part mu kayi,tareda tsohuwar nan muna shiga ta ƙara kallona tana faɗin "ke Hameeda gaskiya bazan zauna da Aljana a wuri ɗaya ba jata kuje can Part ɗin uwarki ku kwanta,ina dalili na kwana waje ɗaya da Aljana" cikin masifa Hameeda ta ce "wai ke Dada miye haka? daga ganin mutum kawai sai ki kirata da Aljana to koma Dodanniya ce babu inda zamu je nan zamu kwana kuma a tare dake" Hameeda ta faɗa tana gallawa Dada harara dan ta bata mugun haushi "Iye Hameeda yaushe idonki ya buɗe? har haka da zaki zauna kina mani masifa akan bare don ubanki ni sa'arki ce da zaki man masifa, kwana ne na ce bazan kwanta da Aljana ba, a toh" a fusace Hameeda ta ja hannuna muka shige bedroom ɗin Dada ta dannan mukulli ta rufe ta ce "wallahi saidai ki canza wani bedroom ɗin amma ba wannan ba" kallonta nayi sai naga dukkan abinda take yi kamar Raheenatu, girgiza kai nayi ina tunanin ko wane hali take, "wai ina Mommy ne naga munyo nan gurin?" na faɗa ina kallon Hameeda "tana Hospital wajen Hamma Nuraim" gabana ne yai muguwar faɗuwa da sauri na tambayeta "mi ya faru dashi Hameeda?" nan ta zauna ta faɗa man abinda ya faru dashi da kuma maƙasudin faruwan lamarin, zuciyata ce ta dinga man zafi da tafarfasa "tabbas Nafisa sai kin ɗanɗana kuɗarki tunda har kika zubar da jinin na musamman a wajena yanzu ne tsafina zaiyi amfani ga irinku azzalumai, saidai mu gwabza yaƙi a tsakanin nida ke" na faɗa ina sakin wani huci *Raheenatu* Raheenatu kam koda suka je kotu aka tabbatar da lallai ita ce wacce ta aikata kisan ba'a wani tsaya ja ba aka yanke mata hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan yari, sosai Raheenatu ta shiga matsanancin tashin hankali,sai dai koma miye tabarwa Allah shine zai mata sakayya Kai tsaye ɓangaren Mata suma ƴan ɗaurin rai da rai aka kaita gashinan kowa nata harkokin gabansu,wani ɗaki aka wullata a ciki tunda ta shiga take faman risgar kuka kamar ranta zai fita, tsawa taji an daka mata ana faɗin "ke dan Uwarki yi mana shiru anan" saurin ɗago fuskarta tayi tana kallon budurwa dake ta zuƙar sigari..✍️ wannan kenan *Comment,share fisabilillah* Waɗannan su ne ƙwarin guiwata *By Riamcool* *08109554986* [2/6, 5:51 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *Book 2* *By Mariam sani Riamcool* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* *Bismillahirrahmanirrahim* *Page* 7&&79 _______________✍️Saurin ɗago fuskarta tayi tana kallon budurwar daketa zuƙar tabar wiwi, zuwa budurwar tayi tana miƙo mata tabar wiwin dake hannunta ta ce "ke dalla ba'a mana kukan baƙin ciki a gidannan kawai idan zaki zo mu kwalɓe kizo a kwalɓe dake dan nan ɗakin na ƴan kwalɓewa ne,tunda kin riga kinzo baƙin ciki na miye kawai ki biye a hau yarima asha kiɗa" wani banzan kallo Raheenatu tayi mata ta ce "ke dalla Malama barni nayi kukan baƙinciki wataƙil daga wannan ba sake wani zanyi ba,ni bani buƙatar wiwi idan kina da Cocain Just give me,kinga idan na shaƙeta na wartsake sai inyi muku iskanci me digi,ke nima fa ba ƙaramar ƴar tasha ba ce kada ki kawo man yawa yanzun na dinga fatali dake don banida kyau ko kaɗan" wata kalar dariya Hajjo ta sheƙe da ita ta ce "buhun uban can kayyasa ki ce kema duk mune, a fagen iskanci kema ba'a barki a baya ba, to amma ke wane laifi kikayi ne da har aka kawo ki anan?" Kallonta Raheenatu tayi kawai tana girgiza kai "ta ce laifina bai shafeki ba babu buƙatar kiji" dafata Hajjo tayi ta ce "ni a ganina ciwon ƴa mace na ƴa mace ne bai kamata a ce kin ɓoye man abinda kika aikata ba tunda har an kawo ki anan ki faɗa man ni kuma indai case ɗinki baifi ƙarfina ba zan temaka na fitar dake duba da yanayin da kike ciki ya saka na tausaya miki,gashi kuma kema kamar ƴar hannu ce kamar ni ɗinnan" "Ko ɗaya ni ba ƴar hannu ba ce kamarke ni bana harkar banza,amma na daɗe da son fara karuwanci saidai ƙaddara ta riga da ta gibto dani tanan" "karki wani damu na faɗa miki indai case ɗinki baifi ƙarfina ba zan fitar dake amma ki faɗa man wane laifi ne kika aikata,indai laifinki sharri ne zan fitar dake in kuma kin aikata gaskiya bazan fitar dake ba" Kallonta Raheenatu tayi ta zauna ta bata labarin da yadda har akayi masu aure dasu Alhaji Bashir da kuma yanda tai rayuwa a gidan ta ci gaba da cewa "nidai tun lokacin da Sabreen tazo ta ce min naje Alhaji Bashir na kirana naje,saidai ina shiga na gansa an soka mishi wuƙa yana kirana nazo na fidda mishi ita hankali a tashe na nufi wajensa na fidda mishi ita,to shine har uwargidansa tazo" nan ta bata labarin duk yanda akayi Sosai Hajjo ta tausayawa Raheenatu jin abinda ya faru da ita, kallonta tayi ta ce "insha Allah zaki ko danke nima zani fita zan taya ki ɗaukar fansar abinda suka aikata miki, saidai da sharaɗi ɗaya in har kina son fita dole sai kin bada kanki,idan kin yarda zanyiwa Alhajina magana yau ma idan yaga dama tsaf zai fitar dake amma abi komai a tsari" dariya Raheenatu ta sheƙe da ita ta ce indai gareji ne zan bashi ya baje harka indai zai fitar dani, sabuwa nake dal yazo ya keta leda ya kwashi harka" dariya Hajjo tayi ta ce "ke da alamu kika shiga harkarmu saima kinfimu iskancin ai" dariya Raheenatu tayi ta ce "indai na shiga iskanci harna siyarwa saina siyar dashi,amma baki faɗa man sunanki ba" "Sunana Shafa'atu amma ana kirana da Hajjo motar bariki" Mai kayan harka ce ta shigo tana ɗura ashariya sannan ta dubi Hajjo ta ce "Motar bariki kindai faɗa ma wannan dokokinmmu na ɗakin nan" kallonta Hajjo tayi ta ce "ke ni na manta ma na faɗa mata maza faɗa mata mu fara bata training tun kafin ta shiga harka" Sigari mai kayan harka ta jawo tana zuƙa ta kalli Raheenatu ta ce "to ƙwailar cikimmu dokar wannan ɗakin da dare kafin mu kwanta dole sai munyi girgizar boobs da ɗuwawu sannan mu ƙa'idarmu bamu shan ƙwaya da kuma kingin kayan shaye_shaye, iyakarmu shan sigari da Wiwi wannan ko bommaly ya bamu award" "Indai wannan ne gidan kuka zo,amma fa batun hana ni shan Cocain bai taso ba ni hasali ma ban taɓa ko shan sigari ba, ku bar kowa yayi rayuwarshi yadda yaso" Hajjo ce ta zauna ta bama mai kayan harka labarin Raheenatu da kuma abinda ya kawota gidan yari Wata ashariya mai kayan harka ta ƙara jawowa ta ce "kutmar..... Keni har kinsa jinina tafasa bani address ɗin gidan nasaka su Bash suje suyi man maganin ƴan iska har sai sun fito da bakinsu sun faɗa sune suka aikata ba ke ba, sannan ke Hajjo babu abinda zai saka ta bada kanta a fiddota, wannan ma bai taso ba indai ina raye saina tsaya miki koma minene ni bazan taɓa barinki kiyi karuwanci ba saboda rayuwar karuwanci ba mafitarki ba ce, ki bar mutunciki ni nan zan tsaya miki sai inda ƙarfina ya ƙare, ki bari duk mu tafi a tare,ki ƙara haƙuri Allah yana tare da mai gaskiya daga yau ki ɗauke ni a matsayin yayarki sannan kayan shaye_shaye ma daga yau na haneki" "Allahu Akbar!!!" suka ji an ambata da ƙarfi juyawa sukayi suna kallon Shamsy wacce shugowarta kenan taji mai kayan harka na hana wata shiga harkar bariki, "Mai kayan harka ke ce yau kike ma wata faɗan shiga bariki? gsky nayi mamaki sosai kodai kema Allah ya shirye ki ne" Shamsy ta faɗa da mamaki "Ke waya faɗa miki kawai dai rayuwar ta ce ta bani tausayi,ganin zata ida rusa rayuwarta baya ga wacce aka rusa mata, shiyasa na hanata shiga bariki tazo tayi zamanta zan sata har makaranta taci gaba da karatu,har nayi mata aure,bazan taɓa bari tayi Rayuwa marar galihu ba" Cikin kwana biyun da Raheenatu tayi sosai take ganin kulawa wajen su Hajjo da mai kayan Harka don ko kaɗan basu son su ganta cikin damuwa gashi sun hanata shan komai, sun tura su Bash suyi bincike akan su Sabreen, saidai koda Bash suka je suka yi bincike suka gano Hajiya Bilkisu ce, suka faɗawa su Hajjo, tunda Hajjo suka ji ko su wanene suka ƙara ƙulla ɗammara cin uwar Hajiya Bilkisu don suma ita ce Silar jefasu cikin wannan hali dam sosai suke neman ɗaukar fansa a gunta **************** wani kalar nishi ke tashi a cikin rufaffen ɗakin mai cike da duhu,kwance take tana kuka ƙasa_ƙasa wanda muryanta ya riga daya dishe ko kaɗan baya fita, kullum cikin zubar da hawaye take wanda zubar da hawaye ya zame mata al'ada tunda aka dawo mata da ruhinta a gangar jikinta, gaba ɗaya duniyar taji yai mata nauyi kullum cikin roƙon Ubangiji take akan ya kawo mata Mutuwa ko zata samu salama, tabbas an zalunceta,an cuceta cutar da bazata taɓa yafewa waɗanda sukayi mata ita ba,dangin Miji sune asalin tarwatsa rayuwarta data yaranta,sune silar dukkan abinda ke faruwa da ita, da mugun ƙarfi taji an banko ɗakin an shigo an tsaya mata ƙiƙam a kanta,ji take duk duniya idan akwai halittar data ƙi jini da tsana mafi muni bai wuce wannan ba shine mafarin tarwatsa mata rayuwar ƴarta, da ƙarfi taji an damƙo gashin kanta ana wanka mata mari, sannan ya ƙara kwalfa mata wani marin wanda ya saka bakinta fashewa,cikin Muryarta marar fita sosai ta ce "Jogu insha Allah abinda kake bazaka taɓa gamawa da duniya lafiya ba kuma sai ka girbi abinda ka shuka naga ƙarshen Saddiƙa saura ƙarshenka,ka riƙe wannan a ranka ko badaɗe ko bajima sai ƴata ta ɗaukarwa Al'umma fansar abinda kuka aikata,hmmm aka faɗa maka Ruhin Saddiƙa kaɗaine a jikinta,to kasani fansa bisa fansa ce, ni ko a iya haka ma na Mutu tabbas zan tafi da farinciki" ta faɗa wani matsanancin Kuka na kufce mata Ƙara wanka mata wani marin yayi yana haɗa mata da shuri sannan ya janye zanen dake jikinta ya kunce zariyar Wandonshi yana kusantota,ja da baya da dinga yi harya ƙure mata, haka kamar wani dabba ya kusanceta ta baya saida yayi mata fata_fata sannan ya ƙyaleta, yana kallonta ya ce "Sajeeda aka faɗa miki don wani abu ko dan tsafi ya saka na kawoki nan, abinda yasa na kawoki nan kawai don na dinga amfani dake,gashi harna samu ƴa dake wanda dama matata bata haihuwa sanadinki naga jinina" yana gama faɗa ya maida Wandonshi ya fice yana jan ƙofar ɗakin ya rufeta Sosai Ammi ke kuka wai ita ce ƙaddara tazoma a haka,duk lokacin da Jogu ya kusanceta yakan fama mata raɗaɗin data daɗe dashi,duk lokacin data tuna ta haifi ƴa da Jogu ta ƙazamiyar hanya takan ƙara tsanarsa da kuma Nuraddeen, yanzu ma wane hali yarinyar take wace kalar rayuwa zata taso dukda tasan Jogu yana ma ƴar so na gaskiya bazai taɓa bari wani abu ya cutar da ita ba,shiyasa ya ɗauke ƴar daga wajenta bayan ta yayeta, ya kaita can ƙasar Turai ayi renonta, dukda ga ta tsatson data fito hakan bai hana Ammi ƙaunar ƴar ba,sosai take son ƴar da kuma tausayinta, a halin yanzun babu abinda take fata sama da mutuwa *Ɓangare guda kuwa* Tunda sassafe muka tashi nida Hameeda muka shirya girkin da zamu kai Asibiti, sanye nake da Atamfa ɗingi riga da siket waɗanda suka amshi jikina tsam sun fito dani caras,ga ɗaurin ɗan kwalin da Hameeda tayi man wanda daga tsakiya ta buɗe ta zubo man da dogon gashina, nayi kyau ba ƙarya sai zuba uban ƙamshi nake a hankali nake tafiyar,tunda na ƙaraso Dada ta kafeni da idanu tana kallona can kuma saita taɓe baki tana galla Mani harara Murmushi kawai nai mata ina ƙara gaisheta da ƙyar ta amsa mani tana yatsina fuska, Hameeda ce ta kalleni ta ce "wai kinga kuwa yanda kikayi kyau kamar wata Aljana, wallahi ke koni nan idan na ganki tsaf zance ba Mutum ba ce dan tsabar kyanki" Murmushi kawai nai mata ina shigewa Mota kusa da Dada sannan Hameeda ta shigo Driver yaja, Hameeda kuwa ta zage sai surutu take mana, Dada da haushi ya isheta ta sakarwa Hameeda dundu a baya tana faɗin "ke don Ubanki kiyiwa Mutane shiru ke kamar redio baki gajiya da surutu kin wani dage sai bama Aljana labari kike" "Dada da bakina fa baki hanani yin surutu wallahi Dada ki rage hassada don nasan wannan fushin da kikeyi bai wuce ganin Raihana du tafi jikokinki ba,kuma kina baƙincikin ta raɓe mu ne don karta ci arziƙi shiyasa, ke nifa Hamma Nuraim zansa ya aureta ayiwa jikarki kishiya da ita" Hameeda ta faɗa don ta ƙule Dada banza Dada tayi mata don tasan halin Hameeda halimsu ɗaya da Abdurrahim shiyasa bata cika takura masu ba, Da sallama ɗauke a bakunansu suka shiga zaune Nuraim yake Mommy nata fama dashi akan yasha koda tea ne amma ya ƙiya ga Nafisa zaune waje guda tana danna waya, jin Sallama yasaka Nuraim ɗago fuskarshi karaf idanunsu suka haɗe dana juna wanda ya saka zuciyoyinsu bugawa,da sauri ya janye idanunsa yana haɗe rai ya kauda fuskarsa,tunda Raihana ta shigo Nafisa take kallonta sosai gabanta ya faɗi ganin kyanta da kuma abubuwan data gani don duka wani sirrin tsafi na jikin Raihana tana ganinsa,tabbas idan ta ce zatai faɗa da Raihana a haka bazata kai labari ba, dole taje ta samo wasu ɗalasiman tsafin da zata fuskanceta..........✍️ A daure a dinga sharhi dan Allah *Masu sharhi ina godiya* *Mariyanbaba* *Mmn minister* *Gimbiyar oga* ina godiya da sharhinku Much love oll🥰❤️🙏 Wannan kenan *Comment,share fisabilillah* Waɗannan su ne ƙwarin guiwata *By Riamcool Hasken Royal star🌟✨💫* *08109554986* [2/6, 5:51 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *Book 2* *By Mariam sani Riamcool* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* *_Ayi man afuwa da jina shiru_* *Bismillahirrahmanirrahim* *Page* 80&81 ____________✍️ Wannan kallon da tayiwa Raihana ya tabbatar mata da Raihana ko wacece, shin anya ma koda ta ƙaro ɗalasiman tsafin zata iya fuskantar Raihana? saboda ganin hatsabiban ruhika da iko a tattare da ita, kallon Raihana ta ƙara yi a razane,karaf suka haɗa ido, kallonta nayi ina sakar mata wani shaiɗanin murmushi wanda ya saka ƴan hanjinta hautsinawa lokaci guda,tunda na shigo na ganta na fahimci ko ita ɗin wacece sosai naci alwashin ganin bayanta, wani hatsabibain Murmushi na ƙara sakar mata wanda yake mata nuni akwai haɗuwar gwabza yaƙi a tsakanina da ita, sosai Nafisa cikinta ya hautsina ganin lallai ta ce su fafata da Raihana to lallai rayuwanta na cikin masifaffen haɗari, dan kar a fahimci wani abu ya saka nai saurin gaida ita ina zama kusa da Hamma Nuraim na masa ya jiki ya amsa man babu yabo ba fallasa, taɓe bakina nayi nima ina kauda kaina gefe, sosai muke fira nida Mommy har take tambayana ina mai gidan nawa, Murmushi kawai nayi mata na ce "Mommy jiya ai ya sawwaƙe mun" sosai Nuraim ya kasa kunne don yaji ƙarin zance da mamaki Mommy ta kalleni tana faɗin kamar ya ya sawwaƙe miki ki faɗa yanda zan gane" "Ina nufin yai man saki ukku,yanzun babu wasu kingin igiyoyi a tsakanin mu" Sosai Nuraim yaji wani masifaffen daɗi ya ratsa zuciyarsa, nan take ya saki ran daya haɗe ya kalli Raihana yana faɗin "Alhamdulillahi da Allah ya rabaki da jalli jogan tshoho,ke karki wani damu nida kaina zan samar maki ɗan sawalwalin saurayi kamar ni ɗinnan" ya faɗa da sigar zolaya, dariya muka saka dukkammu harda Mommy,don itama tayi farincikin dawowar Raihana wajenta, Dada kam duk firar da suke ta kasa kunne tai ka saƙe tana ji taɓe baki tayi tana faɗin "yo dama Allah na tuba waye zai zauna da Aljana? ai ƙara ya saketa daya zauna da jarfa" wani bala'in haushin tsohuwar naji yadda take ta shiga Al'amurrana, sauya idanuna nayi ya zuwa kalar na Maciji yadda ita kaɗai zata ga sauyawarsu,kallonta nayi tazo dalla mani harara karaf muka haɗa ido da ita sosai Dada ta firgita hantar cikinta ta kaɗa wani kalar zufa taji yana keto mata, ƙara zare mata idanuwana nayi yadda zata ƙara tsorata,cikin Dada ne ya murɗa alamar zawo, da gudu ta miƙe ta shige bayi tana gudawa, sosai cikin Dada ke ƙara hautsinawa, hawaye ta share tana faɗin "oh ni Saude yau bakina marar faɗin Alkhairi ya jawo man, gashi wajen tsinanniyar masifata na taɓo Aljana" kowa mamaki yake yadda Dada ta rikice lokaci ɗaya yake, Hameeda kam sai dariya take tana faɗin dama gudawar ajali take uban kowa ya huta da masifarta, nima dariya ta bani yadda ta zuba da gudu amma wannan kadan nai mata, Fitowa Dada tayi tana sharfe zufa kowa sannu yake mata "Dada mi kika ci haka ya hautsina maki ciki"Nuraim ya faɗa yana ƙunshe dariyarsa, "Nura jaraba da masifa da kata'i duk sune naci" ta faɗa tana figar gyale don so take tabar ɗaki ko kaɗan bata son ƙara kallon Raihana, hanyar Toilet tayi wai fita zatayi duk ta ruɗe,saida tazo shiga taga ashe bayi ne "ke dan kut...... Nafisa taso ki maida ni gida" Dada ta faɗa tana ƙundumawa Nafisa ashariya Kowa dariyarsa ya riƙe,Nafisa ta taso tana ƙara kallona don tasan abinda na aikata, mamakin shu'umancin Raihana take,jiki a sanyaye ta taso Dada ta figi hannunta da sauri suka bar ɗakin, Nafisa na aje Dada ta fita ta lalubo wata Number tana kira, ana ɗagawa ta ce "ku saki Abdurrahim bana son wani abu ya sameshi" tana gama faɗa ta datse kiran tana sakin wata nannauyar ajiyar zuciya Sabreen ta kira tana ɗagawa ta ce "Sabreen akwai fa matsala ina buƙatar temakonki sosai" "haba Nafeesa ba ta'aziyya ba gaisuwa zaki ce akwai matsala" Sabreen ta faɗa cikin jin haushi haƙuri Nafisa ta bata ta ce dan Allah komi take tazo cikin satin tana buƙatar temakonta,nan take yanke Nafisa ta janye dukkan wani shirinta da ƙullinta akan su Nuraim da ƴan uwansa don tana ganin hakan shine zaisa su rabu da Raihana (tab kina ruwa Nafisa Raihana fa bata yafiya) Bayan kwana biyu sosai Nuraim ya warke ya samu sauƙi har an sallamo shi, zaune nake ina tunanin ta inda zani fara yaƙar azzalumai na kawo ƙarshen zalunci,takan wa zan fara,sosai nai zurfi cikin tunani,can kuma na tuna Abba, "shine wanda zan taimaka ya warke" na faɗa ina sakin murmushin jin daɗi tsaye yake yana kallonta ya harɗe hannuwansa a ƙirji yana ta zuba murmushi shi kaɗai, Sanye yake da T_shirt red wacce ta amshi fatar jikinsa sai wando jeans black, ga sumar kanshi da taci uban gyara sai ƙyalli take tana ƙamshi, sosai kayan jikinsa sukai masa kyau da ƙara haska Kyakkyawan fatar jikinsa, wani sassanyan ƙamshi ne ke fita ta jikinsa,a hankali ya tako ya zuwa bayanta hannu ya saka yana rufe mata Idanu ta baya nayi nisa a cikin tunani naji an rufe man ido ga wani sassanyan ƙamshi dake tashi dariya nayi na ce "Hamma nafa ganeka baka san ni tawa baiwar ba har ta baya ina ganin mutane"na faɗa ina dariya sakina yayi shima yana dariyar ya ce "kaji ƴar baiwar Mommy ki ce ke taki baiwar tana da yawa" ya faɗa yana dawowa kusa dani Juya masa fararen idanuna nayi ina dariya na ce "eh mana kaɗan daga cikin baiwata kenan" Yanda ta juya masa idanun sosai zuciyarsa ta wani tsinke yana dafe saitin Zuciyar *Abba* Sosai abin nashi yaƙi yin sauƙi kullum babu sauƙi,ga maganin ake amma yaƙi gaba yaƙi baya,kullum Sadeeq cikin damuwa da tashin hankali yake don gani yake koda wane lokaci zai iya rasa Abba wanda shi kaɗai ne ya rage masa a halin yanzun, gashi ji yake koda yaushe gabanshi na sake matsanancin faɗuwa, Zaune yake yayi zugum kusa da Abba yana share hawayen days saba zubar dasu a koda yaushe Sallamar Modibbo ce ta sake tsinkar masa da zuciya,a razane ya ɗago kansa yana kallon Modibbo ya gaishe dashi cikin ɗari_ɗari, gabansa na tsananta faɗuwa, mai makon Modibbo ya amsa masa sai kawai yai masa wani mugun kallo mai cike da gargaɗi,wanda ya ƙara tsinka zuciyar Sadeeq ɗin,ƙara makurewa yayi ga bango jikinsa na tsananta makyarkyata, kaɗa kansa Modibbo yayi kamar wani ƙadangare ya fita Wata nannauyan ajiyar zuciya Sadeeq ya saki yana tunanin mafita daga cikin wannan baƙin kurkukun gida mai cike da ruɗani,da abubuwan al'ajabi wanda koda yaushe cikin razana da ruɗani yake,koda yaushe rayuwanshi cikin fargaba take wanda daga shi har mahaifinsa yake gaɓar rayuwa ko mutuwa, sosai yake ƙara jin tsanar rayuwa cikin duniya ji yake da yana da iko da hali babu abinda zai hana shi yaƙar zalunci, ji yake dukkan wani tako ko fitar numafashinsa dai_dai yake da ƙara tunkarar ƙabarinsu muddin ya zauna gidannan mai cike da baƙaƙen lamurra *Raheenatu* sosai take shaƙatawarta gidan yari,ga ko wace kalar ƙwaya su harka sun hanata sha,ko ruwa zata sha sai sun duba shi a cewarsu gudun matsala, saidai iskanci da feɗarewa da suka ƙara koyawa Raheenatu,iskanci tayi yadda take so babu ubanda ya isa koda ɗan yatsa ya nuna mata, Zaune su Hajjo suke suna zuƙar sigari ko wace da karan sigari a hannu,kallonsu Raheenatu tayi ta buga uban tagumi tana kallonsu da ɗai_ɗai can kuma sai ta dage iya ƙarfinta ta kurma ihu Kallonta Hajjo tayi baki sake ta ce "Raheena lafiya, kodai kina da Aljannu? muyi maki raƙiyya yanzun"ta faɗa tana ƙara cuno baƙin bakinta Raheenatu ta ce "kusan hakan dan nidai yau idan ban sha ƙwaya ko Cocain ba zan tado tshohuwar ƙwayata,gsky baku min adalci ba haba dan Allah ku kun zauna kuna kwalɓewa da sigari nikam kun hanani shaƙar Cocain kullum saidai ku koya man girgiza boobs da ɗuwawu,haba dan Allah kuna yawa kuma wallahi" "Ke kinci Ubanki dan uwarki ba gata muke nuna miki ba, tarbiyya muke baki ƴar........" Kayan harka da danno ashariya taci gaba da cewa "idan bamu koya miki girgiza boobs da bombom ba tun yanzun ki faɗa mana yaushe zaki koya,ko so kike muyi maki aure kije kiyiwa miji tsaye dangangan babu wata ƴar girgizar jan hankali,kina tafiya babu wani juya bombom wanda zai ja hankalinshi,so kike yaje ya kalli na waje?"....✍️ Wannan kenan *Comment,share fisabilillah* Waɗannan su ne ƙwarin guiwata *By Riamcool Hasken Royal🌟✨💫✨ *08109554986* [2/6, 5:51 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* By *Mariam sani* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* *Bismillahirrahmanirrahim* *Page* 82&83 __________✍️ Sosai mai kayan harka taiwa Raheenatu tas, muƙui Raheenatu tana turo baki cikin gunani ta ce "tabɗijam dandai kawai kina ke mai kayan harka shiyasa na barki ki kayi man ashariya amma Alqur'an da bake ba ce da kafin ki ida na fasa maki baki,abinda yasa na kyaleki dandai ni kaina nasan kun taimaki rayuwata kun nuna man so" "magana kike ne" Hajjo ta tambayeta, yaƙe Raheenatu tayi ta ce a'a istigfari ne nake,shiyasa kika ga bakina na motsi" "Wai ku yaushe ne zamu fita daga nan muje ɗaukar fansa wajen waccan sheɗaniyar, sannan nifa Raheenatu ban yadda kanta ɗaya ba duba da yadda take son harkan karuwanci dana shaye_shaye shiyasa tun rannan na bugawa su ƴar ɗagwas suje wajen Malamina ya duba man lamarin Raheenatu,koda suka je ya duba ya ce asiri aka mata kuma zai karya shi,yanzun nake jiran akawo man magungunan hayaƙi dana wanka,dan asirin ya fita" mai kayan harka ta faɗa tana kallonsu Sosai kowa ke yaba mata da ƙoƙarin temakon data ke son yi Bayan kwana biyu su Hajjo sunyi magana da Alhazawansu akan fitarsu,dandanan aka gama shirye_shiryen fitowar su saboda suna tare da manyan ƴan siyasa wanda magana ɗaya za suyi case ya mutu,sun yanke hukunci indai suka fito direct gidan Hajiya Bilkisu za suyiwa tsinke,su fara cin ubanta dana Sabreen, Tunda dare suke shiye_shiryen fita ,haka suka gama shirinsu tsaf da safiya tayi fita dukkansu zasuyi, washe gari nayi aka ko fito dasu daga gidan yarin,wani sanyi da daɗi Raheenatu taji na ratsa dukkan wani sassa na jikinta,haƙiƙa bata da bakin da zata godewa su Hajjo da suka temaketa, faɗawa jikin Mai kayan harka tayi tana fashewa da kukan farinciki, ta ce "tabbas bani da bakin da zan iya gode maku bayan ƴar uwata kune mutane na farko da kuka fara ceto rayuwata daga halaka,ada na fidda tsammani da samun ƴancin rayuwa,ashe bawa baya fidda rai daga rahamar ubangiji,ngd ngd muku sosai" ta faɗa tana ƙara share hawaye Sosai jikinsu yai sanyi dukkansu murmushi mai kayan harka tayi ta ce "kada ki damu ƙanwata duk wanda ya taimaki wani shima Allah zai taimake sa ki ƙara haƙuri da yanayin rayuwa" ta faɗa tana mai sake rungume Raheenatu, Suna nan saiga mota dalleliya tazo ɗaukar su kai tsaye haɗaɗɗen gidan mai kayan harka suka wuce, suna shiga ciki ko ina wani haɗaɗden ƙamshi ke fitowa ga Abinci nan duk an jera musu a dinnig,dama tun da dare mai kayan harka ta kirawo ma'aikatanta su gyara mata gidan da kuma yi masu girki, wanka suka fara yi sannan suka ci abinci bayan sun huta ne mai kayan harka ta kallesu tana faɗin "da munyi niyyar gyarawa Hajiya Bilkisu zama,saidai itama fa ba ƙaramin lissafi gareta ba saboda itama ba ƙaramar hatsabibiya ba ce to dana duba na gani bai kamata muce zamuyi ma komai gaggawa ba, abinda ya dace dukkan wasu tsare_tsaren ayyukanta na sirri zamu sa ɗan leƙen asiri ya dinga bibiyar mana ita, daga baya zamu saka Alhaji na Madi ya haɗa ni da yaransa su aiwatar mana da aiki" sosai sukai na'am da shawararta *Raheenatu* kamar yadda nai niyar fara taimakon Abba kafin naje na tunkari azzalumai, haka na kwanta da ƙudirin son cimma burina, tafiya nake na dinga jin wani huci da gurnani a cikin wani tsohon gida wanda duk yana ta riga data rufesa, a hankali nake tunkara wajen ina keta itacen da ciyayi cikin ƙurgunmin daji mai cike da duhu da ban tsoro sosai nake ƙara himmar tafiya don son cimma ganin na iso gidan,saidai dana kusa cimmasa saiya ƙara nisantana, a hankali kuma dajin ya fara man amsa kuwa da wasu kalar maganganu masu tsawar gaske,wacce tasa hanjin cikina kaɗawa, wata kalar tsawa aka sake doka man da wani kalar yare wanda bani ganin mai mani wannan tsawar, wani kalar ihu naji an ƙara saki wanda ya saka ni runtse idona da ƙarfin gaske daga bisani kuma naji an kece da wata kalar sheɗaniyar dariya wacce ta sakani buɗe idona,saidai duhun dana gani ne ya saka na ƙare ware idona ina duban baƙar halittar dake tsaye gabana a hankali na fara kai dubana ga kwata_ kwatan takon ƙafafuwanshi harna gangaro ya zuwa jikinsa mai cike da gashina, dubana nakai da baƙar fusakarsa mai cike da tsoratarwa baƙa mummuna ga wasu kalar ƙahunna a tare dashi,wani miyau na haɗiye muƙut sannan na zagayesa zan wucesa saboda ganin ya tokare man hanyar da nake son bi na cimma gidan, wata kalar fisgo ni naji yayi da hannunsa mai cike da masifaffen zafi wata kalar ƙara na saki jin wani raɗaɗin zafi na ratsa ƙwaƙwalwata, Cikin kausasshiyar muryarsa mai fidda amon ban tsoro ya kalleni da idanunsa masu razanarwa yana faɗin "muddin kina son cimma gidancan sai baƙin ruhin dake tattare a cikin jikinki ya fita sannan ki shiga ko kuma mu ɗaure ruhin" Zuciyata ce tai man wani kalar zafi da tafarfasa cikin tsananin fushi na dube sa da kakkausar murya nace "ka kuwa san me kake faɗa akan na tunkari gidancan zan bari a cire ruhin fansata kada ku aikata man abinda zaku zalince ni da ku cire man shi ƙara na koma inda na fito dukda baƙar wahalar dana sha" na faɗa ina sakin wani hucin ɓacin rai ji nake zuciya kamar ta faso ƙirji ta fito dan tsananin ɓacin rai dariya aka kuma kecewa da ita daga bisani kuma aka dinga tafi ana faɗin "tabbas baƙin ruhi zaka dishe baka ida cika baƙin ƙudirinka akan *Juwala* ba jininta ita kaɗai zata kaikam yanzu zamu cireka a jikinta" kafin nayi wani wani yunƙuri baƙar halittar nan yai saurin watsa man wasu baƙaƙen ruwa yana surutai kala daban_daban wani kalar ihu da kururuwa nake na faɗi ƙasa ina tirje_tirje a hankali wani baƙin abu yake fita ta jikina daga bisani kuma nai laƙwas ina jiran tsammani, wasu ruwa y bani na karɓa nasha sannan yai man nuni dana miƙe jiki a sanyaye na miƙe yana tafe ina binsa a baya, tunda muka tunkaro tsohon gidan mai kamar ginin gidan sarauta gabana ke faɗuwa, a hankali wannan halittar ya ƙara janyo hannuna yana shiga dani ciki, muna shiga ciki wani kalar ƙura da yana be duk ya cike wajen, a hankali kuma naji wata waƙa mai amsa kuwa na tashi a cikin ɗakin daga bisani kuma naji shesheƙar kuka na tashi hakan ya saka ni tunkarar tshohon ɗakin ina mai ƙara jin tsananin tsoro........✍️ Ayi haƙuri da wannan yau na so nayi muku mai yawa wallahi,saidai idona dake man ruwa shi ya hana in muku mai yawa Wannan kenan *Comment, share fisabilillah* Waɗannan su ne ƙwarin guiwata *By Riamcool Hasken Royal star🌟✨💫✨💫* *08109554986* [2/6, 5:51 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *Book 2* *By Mariam sani Riamcool* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* *Bismillahirrahmanirrahim* *Page* 84&85 _____________✍️ Tunkarar ɗakin naci gaba da yi gabana na tsananta faɗuwa,a hankali na saka hannuna ina tura tsohuwar ƙofar ɗakin, waro idona na sake yi ganin mace tsohuwa ta sadda kanta ƙasa ƙafafuwanta ɗaure da sarƙa, a hankali nake jin fitar numfashinta, da wani kalar nishi da take yi, hannuwa ta miƙo man alamun nazo, dukkan wani tako ɗaya da zanyi dai_dai yake da bugawar zuciyata, wanda nake ji saboda bugawa tamkar zata faɗo, hannuna na miƙa mata da ƙarfin gaske ta riƙeshi kam sannan cikin muryanta mai daɗin sauraro take raira wata kalar waƙa mai daɗin sauraro wacce ta saka jikina tsima, daga bisani kuma tai tsit tana shesheƙar kuka,tana ƙara matsa hannuna, ƙara ɗago fuskata nayi ina kallonta a dai_dai lokacin itama ta ɗago da tata fuskar tana sakar mani murmushi, kallonta nake sosai ganin yadda take masifar kama da Abba har murmushin da tayi sai nake ganin tamkar Abba ne yayi shi "wacece ke" tambayar data fito daga bakina kenan ina sake dubanta, nuni tayi man dana zauna, zama nayi sannan ta ƙara matse hannuna kam tana kallona ta ce " Raihana ba zaki sanni ba saboda na kasance mai son zuciya,ni ɗin sam ba tagari ba ce,na kasance mai zaluntar al'umma, saboda son zuciyata nabar mijina da ƴaƴana, tabbas da ace na kasance tare da ƴaƴana da ko kaɗan bazan taɓa bari ki shiga wannan rayuwar ba" ta faɗa tana mai sake zubar da hawayen nadama Sosai Tsohuwar ta bani tausayi, hannuwana na saka ina share mata hawayen, zoben dake hannunta naga ta ciro ta kamo hannuna ta saka mani ta ce "Raihana ga wannan shine zobena, wato zoben JUWALA, kije ki riƙe zaiyi maki amfani sosai" "dama ke ce Juwala? Maman Abba, kina raye ne dan naga ke bakiyi kama da ruhi ba, yanayinki ya tabbatar mani da ɗaureki aka yi na tsawon shekaru" na faɗa ina sake kafeta da idona "Tabbas ni ba matatta bace ina raye ban mutu ba, saidai tsawon shekaru 20 na kasance ɗaure anan saboda wani gagarumin laifi dana aikata wanda aka yanke man shekara 20 a ma'adanan ruhika" "To amma me yasa kika gayyato ni anan" "saboda ina buƙatar na taimaki jinina sannan ina buƙatar ki taimaki Mahaifinki da ɗan uwanki saboda suna a hannu macucin Mutum azzalumi, wanda shine wanda ya lalata miki rayuwa,shine wanda ya sace mahaifiyarki yake azabtar da rayuwarta, Mahaifiyarki na raye tabbas ba Mutuwa tayi ba, a halin yanzun dukkan Alhakin ceton rayukansu suna a wuyanki, zoben dana baki shine zai baki damar tunkararsa,sannan ruhin Saddiƙa da aka cire maki shi zai ƙara taimaka miki" ko kaɗan banyi mamakin jin cewar Ammi na raye ba,saboda dama can ni ban yadda da mutuwa tayi ba, "amma ta ina zan gane mutumin da kika faɗa, waye shi? a cikin su Baba Sa'adu" "ko kaɗan baya cikin su Sa'adu, wanda kuka yarda dashi kuka aminta dashi,shine ya daɗe yana cin dunduniyarku,kuma ba kowa bane face Modibbo,shine Jogu ɗin da kika sani,wanda yake ɓoye maki murya da kuma fuska" cikin tsananin ruɗewa na tashi ina faɗin "Wallahi ba dai Modibbo ba ki sake tunani, nasan ko kaɗan Baba Modibbo bazai kasance mai zaluntar mu ba, saidai ciki na tabbata Sharu ko Sa'adu" "cikin daka tsawa ta ce tabbas kinyi wawan tunani,abinda na faɗa miki shine gaskiya, fitar da ita daganan ka mayar mata da baƙin ruhinta" ta faɗa da alamun ɓacin rai magana nazo yi mata amma wannan halittar ya daka man tsawa yana fizgoni ya jefar dani a wajen yana fesa mani wani turare, ruhin da aka cire shine ya dinga dawowa, har ya shige a jikina,niko sai burburwar azaba nake, zafin ranar da naji yana dukana shine ya saka ni ware idona a hankali harna buɗesu duka,miƙewa nayi da mamaki ganina kwance cikin dokar daji, "kenan dukkan abinda ya faru jiya da daddare da gaske ne?" na tambayi kaina da mamaki na ida miƙewa tsaye duban jikina nayi na ganni daga ni sai ƴar ɓigilar rigar bacci wacce na saka ta Hameeda, a hankali na buɗe bakina ina karanto wasu ɗalasiman tsafi waɗanda zasu mayar dani gida, ina gamawa na buɗe idona na ganni bedroom,murmushi na saki ina shigewa Toilet dan yin wanka da kuma Arwalla, ɓangaren Mommy da Hameeda sai sintiri suke saboda tunda Hameeda ta tashi bata ga Raihana a inda ta kwanta ba har tai sallar asuba ta koma bacci, koda ta tashi wajen 11:30 bata ganta ba, ga Nuraim ya fita Office an kira wayarshi bata shiga, Mommy ce ta kalli Hameeda ta ce "kodai ki ƙara zuwa ɗakin ki duba" da to Hameeda ta amsa tana hawan sama zuwa bedroom d'inta, tana shiga taji ƙaran ruwa hakan ya sakata sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, zama tayi bakin bed ɗin tana jiran fitowar Raihana, fitowa nayi ɗaure da towel, kallon Hameeda nayi dake zaune na sakar mata Murmushi, hararan wasa tayi min tana faɗin wai ina kika je ne? nake ta faman nemanki har hankalimmu ya tashi nida su Mommy" cikin yanayin damuwa na dubeta na ce mata zan faɗa mata inda naje, shiru tayi bata sake tambayana ba, cikin kayan da su Mommy suka siya man na ɗauko wata haɗaɗɗiyar gown baƙa mai kyau wacce taci adon white stone, na saka sosai tayi man kyau, lotion na ɗan murza da turaruka na saka Hijab ina kabbara Sallah, ina sallamewa istigfari kaɗai nayi ko salati banyi ba na miƙe,ina cire Hijab ɗin "amma me yasa baki Addu'a Raihanatu? Hameeda ta tambaye ni, kallonta nayi ban ɓoye mata komai ba na faɗa mata ƙwalla ta share ta ce "Raihana Allah ya fitar dake daga wannan halin, idan kin gama ki safko ƙasa kici abinci, kuma Hamma Nuraim ya ce ƙarfe 2:00 zai dawo zaku je wani wuri dashi da Mommy" da to na amsa mata na ce ta jira ni mu fita tare, gyara gashina nayi nai parking ɗinshi, ko powder ban shafa ba na ɗauki veil ɗin nayi roning ɗinshi, feshe jikina nayi da turaruka, ɓata fusaka Hameeda tayi ta ce "haba Raihana kalli fa ko Powder baki shafa ba naga baki son shafa powder,to gaskiya ki shafa" ta faɗa tana turo baki dariya nayi nace "to ƴar uwar Raheenatu" itama dariya tayi ta ce "ni kam naso naga Raheenatu ɗinnan" murmushi nayi na shafa powder da ɗan kwalli sai lip gloss,muka sabko Mommy muka samu zaune ta zuba tagumi, tana ganimmu ta saki wata nannauyan ajiyar zuciya, ta ce "Ƴar Mommy ina kika shige ne kika tayar mana da hankali" "Mommy yunwa nake ji idan na ci abinci zan faɗa maki" na faɗa ina mai nufar dinning nida Hameeda, sosai na zage na narƙi abinci har Hameeda na man dariyar mugun cin da nayi Mommy kam sosai take jin daɗin yadda Raihana ta ƙara sakewa da su yadda kasan tayi wasu shekaru a wajensu, don kullum tana maƙale jikin Mommy duk yadda Raihana bata da ɗimi ta zauna kusa da Mommy sai tayi mata surutu, Murmushi Mommy tayi ta ce "ƴar Mommy zo ki faɗa mana inda kika ɓuya muke ta nemanki" babu abinda na ɓoye mata na faɗa mata dukkan abinda ya faru dani harna gwada mata zoben dake hannuna, sosai Mommy ta shiga damuwa,kuma wani ɓangaren tayi farincikin jin cewar ƴar uwarta na raye, amma jin cewar hannun mugun mutumin da take shine yafi ɗagar mata da hankali , ganin damuwar data shiga shine ya saka ni kwantar mata da hankali akan cewar zan ceto rayuwarta insha Allah bayan munyi sallar Azahar sai ga Hamma Nuraim dashi da Abdurrahim sun shigo, jugum_jugum suka samemu suna tambayar mu abinda ya samemu mukayi sukuku, kamar yadda na faɗawa Mommy haka itama ta faɗa musu, kwantar mata da hankali sukayi ko cin Abinci Nuraim bai tsaya yi muka tafi wajen Baba......✍️ wanna kenan *Comment, Share fisabilillah* Waɗannan su ne ƙwarin guiwata *By Riamcool Hasken Royal star✨🌟💫✨💫* *08109554986* [2/6, 5:51 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *Book 2* *By Mariam sani Riamcool* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* *Bismillahirrahmanirrahim* *Page* 86&87 ____________Gudu yake shararawa sosai don tunda yaji abinda ya faru da Raihana yau hankalinsa ya sake tashi da lamarinta, babu abinda yake so sama da yaga Raihana ta fita daga cikin wannan rayuwan, da tunane_ tunane ya ratsa dajin yaci gaba da gudu nikam ina ganin ya shiga dajin kaina yai wani irin sara man a hankali na lumshe idona bacci na ɗaukana, kwanciyar Mommy ta ƙara gyarawa Raihana jikinta yai sanyi ƙalau, a haka har suka isa cikin ƙungurmin dajin parking Nuraim yayi ya fito, sannan Mommy ta fito, tana kallon inda suke, ganin Raihana na bacci yasashi ɗauko ruwa a hankali yana shafa mata a fuska, a hankali na dinga buɗe idona harna waresu duka akanshi, miƙewa nayi na kalleshi ina turo masa ɗan mitsilin bakina, dan haushin tadawar da yayi man naji, kafeni yai da ido yana ƙara haɗe ranshi, wai irin karma ta fara rainashi tun yanzun ƙara shima ya ɗan ja mata aji, da hannu yai mani alamar dana fito fitowa nayi ina ƙara jin haushin haɗe man ran da yayi, ƙara turo bakina nayi ina wucewa wajen Mommy, "ƴar Mommy lafiya dai ko, ko wani abun Hamman naki yayi maki?" Mommy ta tambaya da kulawa kallonshi nayi sannan na kalli Mommy na ce "Mommy babu abinda yai man kawai baccin ne ban ƙoshi dashi bane, kuma mamadin ya ɗan bubbuga man ƙafa amma saiya shafa man ruwan a fuska" na faɗa a ɗan shagwaɓe yanayin yanda tayi maganar yasa shi jin wani yar, ga ɗan bakinta da take turowa duk sai ta sakashi shiga cikin wani kalar yanayi, cikin kasalalliyar murya yace "muje Mommy" shiga gaba yayi muka dinga binshi wajen baka jin motsin komai saina tsuntsaye da kaɗawar ganyen itatuwa, haka muka dinga tafiya a ƙasa har muka iso wani kogo, wanda kallonshi da nayi saida ya saka kaina juyawa, Hamma Nuraim ne ya fara shiga, sannan muma muka shiga wani kalar ƙamshin turare ne wanda a take ya ƙara hautsina man kai, waje muka samu muka zauna ina ƙara ƙura ma Dattijon dana gani ido, da sauri na janye idona daga kansa, gabana na wani irin bugawa, sadda kaina ƙasa nayi na gaishesa a ladabce, amsa mani yayi da murmushi a fuskarsa bayan sun gama gaisawa dasu Mommy ne ya tashi yana ɗauko wani ɗan hannu mai kama da zoben da Juwala ta bani, miƙo manshi yayi ya umarceni dana saka shi, sannan ya ƙara dubana yana faɗin "wannan ɗan hannun shine mahaɗin zoben dake hannunki, sune lu'ulu'un dake ƙarawa kakarki Juwala ƙarfi, shiyasa ta baki su don yaƙar azzalumai, sune waɗanda zasu ƙara maki ƙarfi, a lokacin da zaki tunkari Azzalumai, nasan jiya ta faɗa miki wasu abubuwan wanda babu buƙatar faɗa miki su" girgiza masa kaina nayi ina faɗin "babu wani abu mai fa'ida wanda ta faɗa man hasalima so take na tunkari wanda babu ruwansa, wanda shine wanda ya mayewa Abba gurbin ƴan uwansa, ya nuna masa ƙauna wanda ko wanda suka fito ciki ɗaya basu nuna masa gwangwanin tashi ba" na faɗa irin ban ɗauki maganarta da mahimmanci ba, murmushin takaici yayi yana faɗin, "yaro man Kaza, wannan shi ake kira da sauran kuka wai an hana Maye sadaka, tabbas abinda Juwala ta faɗa miki shine gaskiya, ki tsaya ki ƙara tunani da kyau, idan kuma ba zaki yarda ba bari na gwada maki zahiri" ya faɗa yana ɗakko wata ƙwarya, girke man ita yayi ya umarceni dana wanke fuskata da ruwan dake ciki, babu musu nai abinda yace, umartana yayi dana runtse idonta in karanto wasu ɗalasimai nanma babu musu nai yadda ya ce ina karantowa, kamar an girke man TV haka naga Baba Modibbo, tafe yake cikin sauri harya tunkari wani ɗaki, yana shiga ɗakin ya wuce ya zuwa inda Sadeeq yake yana shaƙo masa kwalar riga sannan ya falla masa mari yana faɗin "muddin ka sake koda wasa ka ƙara yunƙurin shiga cikin ɗakincan to tabbas saina sadaukar da jininka ga Dodo, sannan Mahaifinka da yake kwance shima na ida ƙarasashi" ya faɗa yana nuna Abba dake kwance kamar gawa, jikin Sadeeq idan banda karkarwa babu abinda yake, hawaye kawai ke bin fuskarsa, ingizasa Modibbo yayi yana barin ɗakin cikin matsanancin ɓacin rai "ya zamar mani wajibi kafin wancan sheɗanin yaron ya gano Mahaifiyarsa na cikin gidannan na ɓatar dashi ko nai sadaukarwa dashi da ruɓaɓɓen Mahaifinsa" ya faɗa yana mai sake buɗe wani ɗaki wanda ya ƙargame da kwaɗo kamar koda yaushe zaune take ta kifa kanta tana kukan daya zame mata al'ada wanda koda yaushe cikin yinsa take,haka zalika bata san ranar daina shi ba,babu abinda take jira sama da Mutuwa tazo ta sameta, wanda dama ta riga da tasan babu ranar da zata samu wani wanda zai ceceta, wanda ta riga ta cire tsammani daga samun ƴantacciyyar rayuwa, kamar yadda ya saba fisgo mata gashi yauma hakan ta kasance,koda ya sake fuzgota saida ya faska mata maruka lafiyyayyu har ukku, sannan ya ɗakko wata igiya wacce yake ɗaureta da ita a duk lokacin da yake son azabtar da ita dira mata yayi ga ruwan ciki wanda ta sakin ƙarar azabar da bata fito ba saboda dishewar murya, ƙara shurinta yayi da ƙafa, sannan ya shaƙar mata maƙwallaton wuya ya ce "Sajeeda sau nawa zan hana ki karatun ƙur'ani a nan amma baki bari kinsan kuwa irin bala'in da kika jawo man? to wallahi yau sai kin kwana cikin azaba, yadda kike burin na kasheki bazan kasheki ba, har sai kinga yadda zanga bayan ƴaƴanki, haka zalika babban ɗanki Fauzan na ɓatar masa da hankali wanda koda sau dubu zai ganki bazai taɓa gane ki da ƴan uwansa ba, haka zalika yama manta da yayi rayuwa a tare daku, kin kuwa san yanda ya zama Young millionaire dan haka zan ƙara shigewa a jikinsa a matsayin nine Mahaifinsa kamar yanda na batar masa da hankali na tusa masa tunanin nine mahaifinsa" ya faɗa tana ƙyalkyacewa da wata sheɗaniyar dariya wacce tasa ni tuno da kalar dariyar Jogu, tabbas wannan ko tantama babu ita ce dariyar Jogu Fashewa da kukan tausayin kanta dana ƴaƴanta Ammi tayi tana faɗin "haƙiƙa Modibbo ba zaka taɓa gamawa da duniya lafiya ba kai munafiki ne mai fuska biyu insha Allah ba zaka samu nasara akan yarana ba, ni na faɗa maka da kai da mugun abokinka sai kunyi mutuwar wulaƙanci, ka faɗa man laifin mi na aikata maku da kai da kingin sheɗanun ƴan uwanka har kuka cutar dani, kuka tasgarar da rayuwar ƴaƴana, wane gagarumin laifi na aikata maka har haka" ta faɗa tana mai sake fashewa da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro wani Marin ya sake kifa mata sannan ya duƙa kusa da ita yana kallon fuskarta ya ce "Sajeeda nasara ta nawa na samu akan yaranki, kin manta dana riga na maida ƴarki matsafiya mai shan jini kamata mai kashe rai kamata, haka zalika ɗanki na samu nasarar mayar dashi ɗana, sannan Mijinki na saka ƴarki ta mayar dashi gawa, dan dashi da gawa basu da banbanci, na juyar ma ƴarki da tunanin ba zata taɓa gane cewa nine Jogu ba, ki sani abinda ya hana ni kasheki bai wuce haifar man ƴa da kikayi ba wato Husna" yana gama faɗa ya samu igiyar nan ya ɗaure mata Hannuwa a jikin ƙarafuna sannan haka ƙafafunta ya ɗauresu duk ya wani bankareta da ɗauri, wata zabgegiyar dorina ya ɗauko da kuma reza yana ɗebe mata rigar jikinta ɗaga zabgegiyar dorinar yayi yana sauke mata a fatar jikinta wanda duk guda idan yai mata saita shiɗe, haka yai mata ruɗu_ruɗu du shatin dorinar ya fito yai mata bororo, rezar ya ɗauko duk inda yai bororo sai yasa rezar ya zarga wajen yana baɗe shi da niƙaƙƙen yaji, haka yai mata wannan azabar sannan ya isa baɗe mata yajin a fuska yana dariya ya ce "wannan hukuncin karatun ƙur'ani da kikayi ne da kuma mugun fatan da kike man sannan fa kika ƙara man mugun fata ɗanki Sadeeq dake hannuna ki sani saina sadaukar dashi kinsan dai yana hannuna" ya faɗa yana mai kwance ɗaurin da yayi mata, yana kwanceta ta hau burburwa ƙasa tana mai ihu da neman ɗauki daga bisani kuma numfashinta ya tsaya cak wani uban ihu na saka ina mai buɗe idona "na rantse da Mahaliccin daya bisa mani numfashi Modibbo ba zan taɓa ƙyaleke ba kamar yadda ka azabtar da Mahaifiyata nima saina azabtar da kai kafin na zuƙe jininka, yanda kasa Mahaifiyata kuka kaima saina saka ka kuka kafin lokacin Mutuwarka, bana mantuwa bana Yafiya, ka cutar dani,bazan raga maka ba, Ammi karta mutu" na faɗa ina faɗawa jikin Mommy na fashe da wani kalar masifaffen kuka, wanda ni kaina ina jin raɗaɗi da ɗacin fitar dukkan wani hawaye nawa, da zai fita Nuraim da Mommy hankalinsu dukya tashi babu abinda suke idan banda lallashina, nikam idan banda kiran Ammi zata mutu babu abinda nake, da ƙyar aka samu nayi shiru amma hawayena basu tsaya ba Nuraim duk ya kara gigicewa ya zuba uban tagumi cikin damuwa ya kalleni ya ce "haba ƴar Mommy haƙuri zakiyi da dukkan jarbatar da kika ga ta sameki mamadin ki zauna kina kuka kiyi tazbihi ga Ubangiji ki nemi sauƙi a wajensa dukkan wani bawa da yanayin ƙaddararsa, wani tazo masa a mai sauƙi wani kuma akasin haka, ki sani dukkan wani mumini shi Ubangiji ke jarabta, kiyi haƙuri da yanayin ƙaddararki, insha Allah komai mai wucewa ne" ya faɗa yana jin kamar ya zubar mata da hawayen tausayi Kallonshi nayi nace "na yarda da ƙaddara shiyasa harna karɓeta Hamma, amma me mukayiwa Modibbo daya zaɓi ya cutar damu har haka, me yasa zai cutar man da Mahaifiya? baya ga lalata man rayuwa da yayi, shin wannan wace irin RUSHEWAR RAYUWA ce? yayi mana ya riga daya rusa mani rayuwa ya riga daya barmini tambarin tsafi, wallahi tallahi koda wajen ɗaukar fansa zan rasa numfashina bazan damu ba indai naga ƙarshen numfashin Jogu, ya cucemu ya zalincemu, me yasa zaiwa Ammi cikin shege? harta haifi ɗiya dashi, me yasa ko wane karen cikinsu ya kwaso wutar sha'awa sai yazo ya sauke akan Mahaifiyata, ni Raihana bana yafiya bana manta sharri" na faɗa hawayen takaici na ƙara bin kuncina Mommy kuwa itama hawayen ta share tana mai ƙara jin cewar duk laifinta ne saboda da bata rabo Sajeeda daga wajen iyayensu ba hakan bazata faru ba, aka soyayyar Haris ta zamo mai son zuciya, kuka Mommy ta fashe dashi tana faɗin "Sajeeda nice naja miki wanna rayuwar nice da laifi bazan yafewa kaina ba" tsaida kukan nawa nayi na rarashi Mommy dukda ban gane kan zancen da Mommy keyi ba, shiru tayi sannan na kalli Baba na ce "haƙika Juwala tayi gaskiya yanzun ne na ƙara ɗaura aniyar cin uwar Jogu in baɗeta da yaji wallahi idona idon Modibbo saina zuƙe jinin ɗan banza sannan inci naman jikinsa ɗanye".......✍️ Wannan kenan *Comment, share fisabilillah* Waɗannan su ne ƙwarin guiwata *By Riamcool Hasken Royal star✨💫🌟💫* *08109554986* [2/6, 5:51 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *Book 2* *By Mariam sani Riamcool* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_* _(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_ *Alk'alaminmu 'yancinmu* *Bismillahirrahmanirrahim* *Page* 88&89 ____________✍️ Wallahi idona idon Modibbo saina zuƙe jinin ɗan banza sannan inci naman jikinda ɗanye, yadda ka shayar da Mahaifiyata gubar azaba nima saina shayar dakai Jogu lokacinka ya ƙare yanzu nawa lokacin zai soma" na faɗa zuciyata na man wani raɗaɗin azaba kallona Baba yayi ya ce tabbas akwai tsafin Jogu a jikinki, wanda ya bama Dodon tsafi ya sadu dake, indai muna son wannan baƙin mallakar da yayiwa gangar jikinki da ruhinki ya fita ki ƙara ƙarfin fuskantarsa to tabbas sai an samu Namiji mai ƙarfin Ruhi ya kusanceki, idan ba haka ba ba zaki iya tunkararsa ba dukda akwai ruhin fansa a tare dake" gabana ne yai wani irin bada dummm jin cewar dole sai namiji ya kusanceni sannan tsafin Jogu zai fita a jikina, "amma Baba wane Namiji kake tunanin zai aureni? ya saka rayuwanshi a haɗari, dukda ni bani buƙatar aure amma ƙudiri da son cimma fansa yasa zanyi auren, amma a ina zan samu wanda zai iya temaka min bana tunanin akwai wanda zaiyi wanna jihadin" "nine zanyi wannan Jihadin a karo na biyu, nine na cancanci na ƙara taimakonki a karo na biyu, ki sani ɗaukar fansa ba taki bace ke kaɗai dole ne nima zan shigo ciki ayi yaƙin dani, in hardai tsafin Jogu zai fita ki ɗauki fansa to ni kuma Raihana zan aureki koda kuwa zan rasa numfashina a wajen ceton rayuwarki, Raihana tun ban san ke wacece a wajena ba na ɗauki aniyar temakonki, ballantana yanzun da nasan ke ɗin jinina ce, zan aureki dan ganin rayuwarki ta daidaita, koda zan rasa tawa rayuwar" maganganun Hamma Nuraim sukai man amsa kuwa a cikin kunnuwa, ɗago fuskana nayi wanda ya jiƙe sharkaf da hawayen tausayinsa, kallon Mommy nayi itama hawayen farinciki take ganin Abinda Nuraim zaiyi "Mommy Hamma Nuraim ya ceci rayuwana a karo na farko, amma dan Allah ki dakatar dashi a wannan karin tabbas zai saka kanshi a matsala muddin ya ce zai aure ni bana son sanadin temakona ya rasa tashi rayuwan" na faɗa ina sake zubar da ƙwallan tausan kaina da kuma Hamma "Ƴar Mommy insha Allah babu abinda zai sameku ke dashi yayi niyyar temakonki ki barshi ya temaki rayuwanki, kuma koda baice zai aureki ba ni ɗinnan zan saka ya aureki, dan haka kada in sake jin kince na dakatar dashi daga cetonki" Mommy ta faɗa tana sakar mani murmushin dole faɗawa jikinta nayi ina faɗin "haƙika Mommy bani da bakin da zan iya gode muku keda Hamma" shafa bayana Mommy tayi tana faɗin "ƴar Mommy ba buƙatar godiya a tsakanimmu idan kika faɗi hakan zan ɗauki kamar baki ɗaukeni a matsayin Sajeeda ba" ta faɗa da murmushi ɗauke a fuskarta "ungo nan Nuraim wannan ƙirin duk lokacin da zaka kusanci Raihana ka ɗaura shi,sanna wannan zoben shima ka saka shi a hannun haggunka, sannan waɗannan ruwan dana miƙo maka dasu ne zaka kama ruwa yau" Baba ya faɗa yana miƙowa Nuraim, Sosai Baba ya bamu abubuwan da zasu ƙara taimaka mana Tunda muka taho nai zurfi cikin tunanin yadda zan fara fuskantar Modibbo, da kuma matsayin auren da zaniyi, haka dai Mommy ta dinga bani baki tana ƙara kwantar man da hankali har muka iso gida, koda muka dawo da wani Matsanancin ciwon kai na dawo wanka kawai nayi na kwanta Koda Daddy ya dawo Mommy ta faɗa mashi komai babu abinda ta ɓoye masa, sosai yaji tausayin Raihana, nan suka yanke shawaran da an gama Sallah asubah za'a ɗaura auren, hakan kuwa ba ƙaramin daɗi yayiwa Mommy da Nuraim ba, Wani kalan huci da da ihu Nafisa ta saki lokaci guda tana sakin Madubin tsafin dake hannunta ya tarwatse, wani kalar ihu ta saki tana faɗin "shikenan ni Nafisa asirina ya tonu, me yasa take shiga harkana? na shiga Ukku nasan muddin ta aureshi harya kusanceta dukkan wani asirina zai tonu da baƙaken lamurran da nake aikatawa, dole nayiwa shugaba Magana kafin mai faruwa ta faru, wallahi muddin Raihana kika auri Nuraim sai nasan yadda nayi na rabaki da numfashinki, koda kuwa hakan na nufin zan rasa nawa numfashin saidai dukkammu mu rasa" ta faɗa da wani irin tashin hankali hatta jijiyoyin kanta sun fito sun mata ruɗu_ruɗu A hankali takai dubanta ƙasa ai bata san sadda ta ƙara sakin ihu ba ganin yadda madubin tsafinta ya tarwatse, duƙewa tayi Idanunta nan take suka ƙara rikiɗewa suna janza launi zuwa jajir dasu, nan take halittar jikinta itama ta fara sauyawa tana wani kalar gurnani kafin daga bisani ta ɓace ɓat, cikin bacci na dinga jin wani gurnani mai birkita lissafin mai sauraro, a hankali na buɗe idanuna, ina kallon baƙar halittar data tsaya man akai tana huci, zara_zaran farcinta ta miƙo da niyyar caka man su a maƙoshi, caraf na riƙe hannun ina ƙarewa halittar kallo, daga bisani kuma na fashe da wata sheɗaniyar dariya wacce tasa ɗakin girgiza da juyawa daga bisani kuma na haɗe rai kamar ban taɓa dariya ba "Nafisa kina tunanin zaki iya gwabzawa dani? kinyi kuskuren tunani, na rantse miki da Allah kamar yadda madubin tsafinki ya tarwatse haka kema rayuwanki data uban gidanki zata tarwatse, kafin ku koma da Mahaliccinku, sannan karma kiyi tunanin zaki iya zuwa ga mugun azzalumin Uban gidanki dan duk wata kafa da zaku haɗu da Ruhikanku nabi na toshe" na faɗa ina sake fashewa da dariya A hankali wannan halittar ta sauya ta dawo ainahin Nafisa, wani irin mugun kallo ta wurga mun tana ja da baya, daga bisani kuma ta ɓace, wata nannauyar ajiyar zuciya na saki ina sake jin zuciyata na man zafi da ƙuna, Tunda Nuraim ya shiga ya iske Nafisa duk ta fita hayyacinta, bai wani bi ta kanta ba ya shiga Toilet wanka yayi sannan ya kama ruwa da ruwan da Baba ya bashi, shirin bacci yayi yazo ya kwanta, wani yawun takaici Nafisa ta ƙara haɗiyewa tana binshi da mugun kallo, daga bisani kuma ta saki murmushin mafitar data samu na ta tsafashi kawai yanda hankalinsa zai bar jikinsa,ya fasa auren Raihana, wani miskilin Murmushi ta saki tana miƙewa, ta fito daga bedroom ɗin, wani ɗan ƙaramin ɗaki naga ta nufa tana shiga ta ɗauko wani turare tana shafe hannunta dashi, fitowa tayi ta nufi Bedroom ɗin Nuraim koda taje ta iske bacci ya kwashesa murmushin samun nasara tayi tana nufarsa da niyar shafa masa turaren a jikinsa, a hankali ta miƙa hannunta da niyyar shafa masa, da sauri ta janye hannun ganin wata narƙeƙiyar Macijiya tabi ta naɗe jikinsa ta ƙura mata idanunta masu mugun razanar da ita,cikin wata razananniyar murya macijiyar ke ambatar "Muddin Nafisa kika ce zaki tsayar man da ƙudirina na cimma fansa to na rantse miki da Mahaliccin daya busa man numfashi ko 2 minute ba zaki ƙara ba zan zuƙe baƙin jininki"........✍️ *Nidai ku ƙara haƙuri dani ba Time ne sosai shiysa ban muku dogon Typing ba wannan ma dan nayi Alƙawarin, yadda na kwana biyu banyi posting ba naso nayi muku mai yawa ayi haƙuri da wannan* Wannan kenan *Comment, Share fisabilillah* Waɗannan su ne ƙwarin guiwata *By Riamcool Hasken Royal star✨💫🌟 *09028190442* [2/6, 5:54 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *BOOK 2* *By Mariam sani Riamcool* *ROYAL STAR ✨💫WRITER'S ASSOCIATION* Bismillahirrahmanirrahim Page 90&91 ___________✍️ Macijiyan nan na gama magana a hankali ta girgije ta dawo Raihana, tana makawa Nafisa wata muguwar harara, mai hautsina ƴan hanjin mai kallonta girgiza kai kawai Raihana tayi tana wucewa tabar Nafisa sake da baki tana saƙe_saƙe a ranta Nikam koda na fito na kwanta inata saƙe_saƙe a raina, na ganin mafitar da zan samu kafin harna gama Iddah ayi auren, amma kafin na tunkari Modibbo zan ceto rayukan dake hannunsa, sannan zan warkar da Abba daga ƙangin azabar dana sakashi, a hankali na miƙe, na rufe idona, ina karanto wasu ɗalasimai wanda ni kaina bansan abinda nake faɗa ba, buɗe idona nayi na saukeshi a bisa wani rufaffen ɗaki wanda bakajin sautin komai idan banda sautin kuka dake tashi a hankali, a hankali na ɗaga ƙafata wacce nake jin tayi man nauyi, hannuna nakai ga kwaɗon ɗakin, da sauri na janye hannun jin wani abu na daban ya ziyarceni, share ɗakin nayi naci gaba da tafiya,harna isa ga wani sirɗaɗɗen lungu wanda ɗaki ɗaya ne tal a wajen, tunkarar ɗakin nayi, wanda nake da tabbacin cewar Abba na ciki, saidai ganin wasu kalar baƙaƙen halittu, na kai kawo a ɗakin ya tabbatar min da cewar gadin dakin suke Ƙara rufe idona nayi ina mai waɗansu surutai, waɗanda suka janyo hankulan halittunnan su kayo kaina, saidai kallon da nai musu da idona waɗanda suka ƙara komawa shuɗi ya sasu dakatawa, ratsasu nayi na kutsa kaina a cikin ɗakin Kamar yanda nayi tsammanin ganin Abba hakan kuwa ta kasance dan kwance yake, marabarsa ɗaya da gawa, shine numfashin da yake, shi kanshi numfashin da ƙyar yake fita, wasu hawaye masu raɗaɗi ne suka samu damar sauka a kuncina a hankali nasa hannuna na ɗauke su ina tunkarar inda yake, kallonsa na ƙara yi kai bama zaka ce wai Mutum bane, don dukkan wasu ƙasusuwa na jikinsa sun fito, ba zaka taɓa cewa akwai wata tsoka a jikinsa ba, "ni kaina nasan na ɗauki rayukan Al'umma da dama na tasgarar da rayukan mutane ba adadi, amma ban taɓa tunani zan illatar da rayuwarka ba Abba" na faɗa ina mai fashewa da kuka mai cin rai ɗaya kaina nayi nakai dubana ga Saddeeq wanda ya makure waje guda yana bacci, wanda baccin da gani ba'a kwanciyar hankali yayi sa ba, hannu nasa ina dafa shi, fasa zaiyi nai maza na rufe masa baki "shiii kayi shiru kawai Sadeeq banson kayi ihu nice Raihana" na faɗa ina mai janye hannuna daga bakinsa Faɗawa jikina yayi yana fashewa da kuka "Adda Raihana me yasa zaki tafi ki barni, me yasa baki bibiyi rayuwarmu ba?" ya faɗa yana mai sake fashewa da kuka "Ya isa Sadeeq, wannan kukan ba naka bane, ina dauriya da jarumtar taka take? kamar ba kai bane Jarumin dana sani mai dakakkiyar zuciya, kada ka bani kunya mana Sadeeq" na faɗa ina mai shafa kanshi ni kaina hawayen na zubo min "Adda Raihana don Allah duk yadda zaki ina son ki kuɓutar da Abba ya rayuwa a cikin salama kada ki bari Baba Modibbo yayi sadaukarwa dashi, Adda Raihana ni ban damu da tawa Rayuwar ba nafi damuwa data Mahaifimmu, saura 3 day ayi sadaukarwa dani wanda ni zan fanshi Abba yanzun ki ɗauke shi ku tafi don Allah" ya faɗa yana mai haɗe hannuwansa waje guda Sokoko nake kallonsa "Sadeeq ƙafata ƙafarka a barin gidannan babu wanda ya isa yai sadaukarwa da kai muddin ina numfashi, banzo don na bar ɗaya daga cikinku ba,don haka tashi ɗauki Abba muje" na faɗa ina miƙewa, shima Sadeek ba tare da musu ba ya ɗauki Abba a kafaɗa, riƙe hannunsa nayi nace ya rufe idonsa ko me zaiji karya buɗe a hankali na buɗe bakina ina mai ƙara karanta ɗalasiman tsafika, sauke ajiyar zuciya nayi ina mai buɗe idona na saukesu a gidan dana kassara Abba, Saddek na umarta daya buɗe nashi idon shima, cikin tsoro ya buɗe yana kallon tsarin ginin tshohon gidan mai cike da al'ajabi "shiga ɗakin can ka sauke Abba" na faɗa ina nuna mishi tsohon ɗakin, koda ya fito na umarceshi daya koma ɗayan ɗakin komi za yaji karya tsorata shiga ɗakin nayi, idona ne ya sauka kan tsohuwar macen data duƙe kanta a ƙasa tana shesheƙar kuka, ƙarasaowa nayi wajenta ina ƙare mata kallo, ganin JUWALA ce yasa na sauke ajiyar zuciya Ƙarasowa wajen nayi ba tare dana tanka mata ba, "RAIHANA yaƙin ba naki bane ke kaɗai, tabbas nima ina da Alhakin temaka miki keda yarona" Juwala ta faɗa tana mai dafa kafaɗata Murmushi na sakar mata ina mai sheƙewa da wata kalar dariya wacce tasa ɗakin juyawa yana girgiza, a hankali kuma na kafe tshohuwar da ido ina faɗin "wasan kwaikwayon ya isa haka, Aunty Amarya, ƙara ki fito man a suffarki, ke har kina tunanin zaki iya ƙarasa kingin rayuwar Abba domin ki cika muradanki da burukanki? dukda cin mutuncin da kuka mishi bai miki ba har sai kin biyoshi nan, tun ba yanzun ba nasan da cewar kina ɗaya daga cikin mutanen Jogu, kuma nasan tabbas kina bibiyar rayuwata, nasan da cewar kin auri Abba ne bisa ga umarnin Jogu, saidai ina mai sanar dake Albishir ɗin cewa wasan daga yanzu yazo ƙarshe zaku girbi abinda kuka shuka" sororo ta tsaya tana kallona, kafin daga bisani ta sheƙe da dariya tana girgijewa ta dawo Aunty Amarya, "Raihana kenan ban zaci hatsabibancin naki yakai ya haka ba, kisan da cewa ban fito ba saida na shirya, bazan fuskanceki ba saina karanci lagonki" tana gama faɗa ta ɓace ɓat a gurin Kaina ne ya dinga juyawa ina tunanin abubuwa goma da Ashirin sun haɗe man, daga bisani na saki murmushi wanda bai kai zuci ba, a hankali na ɗauko wata ƙwarya wacce ke cike da ruwan magani, cikin dakiya da dauriya na fara karanta *"Inna fatahana lakha fatahannubin, liyaghafura lakha ma taqaddama min zanbikha, wama ta akkhara, waya tummah ni'imatahu Alaikha waya hadika siraɗal mustaƙin, wa yansurakallahu nasaran azizah, huwwallahul lazina anzala fi ƙulubin mumunin li yazdadun imanin ma'a imanihim, walillahil junudi samawati, walardi wa kanallahu Aliman hakima"* (addu'a ce sosai wacce take maganin dukkan wata musifah data tunkaro ka, ana yinta ne yayin da kaga masifa na tunkaroka) na ƙarashe Addu'a a galabaice ina sheƙawa Abba ruwan, wata irin girgiza ɗakin ya fara yi yayinda Abba shi kanshi ya dinga wani masifaffen tari jikinsa na mimmiƙewa, wani irin kumfa ne da jini_jini ke fitowa a bakinsa, cikin dakiya na dinga mai_maita addu'a, daga bisani kuma naji komai ya ɗauke ɗuf, wata ajiyar zuciya na saki da hamdallah ganin na samu na ceto rayuwan Abba, ji nayi nauyin daya danne zuciyata ya ragu dubana nakai kanshi, ganin yadda yake motsi da baki ya kafeni da idanu hawaye na zubowa, da sauri na kama hannunshi ina sakar masa Murmushi, "Abba kayi haƙuri ga dukkan abinda ya faru ni kaina nasan banyi maka adalci ba, wanda koda yaushe abinda na aikata maka shine ke kai kawo a zuciyata, ka yafeni insha zan zamo makangi gareka, ba zan taɓa bari dukkan wani abu na cutarwa ya sameka ba" na faɗa ina mai share mashi hawayen fuskanshi **************** wani uban ihuuu Jogu ya saki yana tarwatsa madubin dake gabanshi, "me ke faruwa dani ne, me yasa na kasa sarrafa gangar jikinta? tabbas nayi sake dake Raihana, me yasa ban raunata Ruhin Saddiƙa ba? na tabbatar da shine ƙarfinki shine ya tazgarar da ikona a wajenki, komai nawa ya lalace, wallahi ba zan ƙyakeki ba, ba zan duba matakin nasarata ba zan kawar dake a duniyar da masu taimakonki" haka Jogu yaita surutai kamar wani zararre idanuwansa sun kaɗa sunyi jajir Kamar zai tashi sama ya shiga wani ɗaki yana mai rufe idonsa yana waɗansu surutai waɗanda baza ka gane abinda yake faɗa ba, buɗe jajjayen idanuwansa yayi ya saukesu akan Sajeeda wacce take duƙe da kanta bai wata_wata ba ya gaura mata kai da banga, sannan ya ƙara gaura mata kai wanda yai sanadiyar fashewa yana malalar da jini, halshe yasa yana lashe jinin dake zuba a kanta, yana gurnani "Sajeeda banyi niyyar kasheki ba amma tabbas ƴarki taja miki Mutuwa a hannuna, kuma ta sanadin baƙar fatan da kike man ya fara hawa kaina, wanda koda zai ida hawa kaina bana fatan ace kina raye" Modibbo ya faɗa yana mai sake lashe jinin dake malalowa "tirrrr da rayuwarka Modibbo, wallahi zaka ɗanɗani kuɗar azaba, don ka kasheni ni ba zanji komai ba, illa farinciki da zanyi da gode maka, Modibbo ko yanzu na faɗi zanyi farinciki sakamakon ganinka a bala'i na tunkaroka, nasan koka kasheni bazan daɗe a inda naje ba zaka biyoni" Ammi ta faɗa tana sakin murmushin takaici falla mata mari yayi, yana mai yaye zanin data lulluɓe jikinta dashi, haɗe ƙafafunta tayi, tana mai ja da baya, da ƙarfin gaske yasa hannu ya jawota, rufe ido yayi yana surutai harya koma wata mummunar halitta ta daban, ɗakin a aka banko da ƙarar da aka ƙwalla ita tasa hankalin Modibbo dawowa, halittar jikinsa na dawowa, a hanzarce ya juyo hankali tashe yana kallon Matarsa Uwani wacce ta ƙame waje guda tana makyarkyata don tsoro Wani yawun takaici ya haɗiye yana kallonta, ganin ta ƙara jaza mishi wani bala'in don ba ƙaramar musifah bace yana cikin tsafi wani ya ganshi, tabbas ya zama wajibi ya kashe matarsa dukda mugun son daya ke mata hakan bazai hanashi ɗaukar mataki ba *Ɓangare guda kuwa* cikin bacci Hajiya Bilkisu taji an buga mata wani ƙaton abu aka wanda yai sanadiyyar farkawar ta a mugun firgice, tsawa aka daka mata ana faɗin "miƙe don ubanki, kamar yadda kika lalata rayuwan ƙanwata wallahi kema saina miki yaga_yaga yau" Innnalilahi....." bata idasa ba aka buga mata gindin bindigar a kai, "zaki sauki ko saina ƙaraso nan?" Mutumen ya faɗa yana nufota, jiki na kyarma ta sauko ta fita Falo, ya rufa mata baya, kneel down tayi jikinta na kyarma, kukan Sabreen da taji ne yasata tashi zata nufi ɗakinta, dakatar da ita wanna Mutumen yayi, hakan yasa ta tsaya cikin tashin hankali, Sabreen ce ta fito wani ƙaton mutum na binta a baya "don Allah ku ƙyale man ƴa kar kuyi mata komai, ku ƙyalemu wallahi ko mi kuke buƙata zan baku" Hajiya Bilkisu ta faɗa kuka na kubce mata "tabbas dukkan wata dukiya da kika mallaka nake son ki mallaka min harda wacce mijinki ya bar miki, da dukkan wasu ƙaddarori" ƙaton mutumin nan ya faɗa fuska haɗe kamar baƙin kumurcin nan Hajiya Bilkisu ta Amince dukkan wasu kadarori dake gidan saida tasa hannu ta bashi, hatta sarƙoƙinta na gold saida ta bashi, hakka dukkan kuɗin dake account ɗin ta saida ta zazzage musu su tukun, wata kalar dariya ta mugaye mutumin ya sheƙe da ita yana faɗin " ko duniyar zaki mallaka min bazai taɓa dawo da ran ƙanwata da kika siyar ba ta hanyar karuwanci, don nima haka a gabanki zanyiwa ƴarki fyaɗen cin mutunci ke kuma nasa yarana suyi miki yaga_yaga yadda ba zaki sake amfanuwa" kuka Hajiya Bilkisu ta fashe dashi, buga mata tsawa Bobbos yayi wanda yasa ta yin shiru, a gabanta, ya cirewa Sabreen kaya tana ihu tana komai, ya far mata, haka zalika yasa yaransa sukai ma Hajiya Bilkisu fyaɗe wanda yasa tana suma zasu farfaɗota da azaba, (ni ai saidai ince Allah ya biyaku😻)...✍️ *To fans ku fito ku kawowa Hajiya Bilkisu da Sabreen ɗauki* Ina mai bama mutane haƙuri sakamakon jina shiru, na dawo kenan insha Allah, har sai mun kammala, kudai ku dinga man Comment kawai Wannan kenan *Comment, Share fisabilillah* Waɗannan su ne ƙwarin guiwata By Riamcool Hasken Royal star ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ [2/8, 8:34 AM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *Book 2* *By Mariam sani Riamcool* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* Bismillahirrahmanirrahim Page 92&93 __________Haka zalika yasa yaransa sukai ma Hajiya Bilkisu fyaɗe,wanda yasa tana suma zasu farfaɗota da azaba, tun tana ihu harya kai ga ko motsin bata iyayi saida sukai mata raga_raga suka haɗa mata da ɗan banzan duka wanda ƙafanta harya kare Sabreen ma saida Bobbos yayi mata raga_raga har jini na malala, sannan ya ƙara saka yaransa suma suka ƙara kwasar gara da salon mugunta, sannan itama ya haɗa mata da ɗan banza duka, ya kwasheta ya tafi da ita, suka bar Hajiya Bilkisu nan yashe tana neman agaji, suna fita me gadi dake laɓe yai wuf ya fito ya shiga, yana kwance shima zariyar wandonsa yaga banza ya far mata, don dama ba ƙaramin haushinta yake ji ba, shima saida yayi shagalinshi sosai, sannan ya ƙyaleta, yana gamawa ya kwashe ƴan komatsenshi ya bar gidan, don safiya nayi zai bar Lagos ya koma ƙauyen su washe gari da safe ƴan aikinta suka zo, ganinta cikin wannan halin yasa, suka ɗauke ta suka kaita Hospital, haka Asibitin suka murje ido suka ki amsarta suka je dole saida Police sannan su amsheta, *RAHEENATU* Raheenatu kuwa al'amurra sunyi mata sauƙi sanadin su Mai kayan harka, har school sun sakata tana karantar Nursing, kasancewarta mai son karatun tuni ta maida hankali a School ɗin, duk wani iskanci data koya wajen su Hajjo ajeshi take idan ta shiga School sai ta dawo ta zubashi san ranta, haka zalika bata jin saka kaya ko wane kala ne ta fita Zaune take bisa 2 seater tana karatun exam data gabato, jin ana shafa mata wuya yasa ta ɗago kanta tana kallon Elejon dake sakar mata murmushi, gashi ɗan kyakkyawa fari tas dashi haɗe rai Raheenatu tayi tace " Elejon How many times will I tell you? to stop touching me because our religion and yours are not the same" ta faɗa da tsantsar ɓacin rai, shima cikin damuwa ya ɓata fuska da yamutsata yace "I'm sorry, it's a mistake to love, I won't do it again, but don't you stop wearing clothes like those who suck your body, I'm going to go into a situation when I see you like that" ya faɗa kamar ya fashe mata da kuka, harara ta banka mashi sai kuma ta washe baki tace "idan Adewole ubanka shi ya siya min kayan sai ka hana shi ya ya daina daga yau, kuma kaya dai bazan daina sakawa ba aha" ta faɗa tana kashe mashi ido kamar wata maganar kirki take mashi Shima washe haƙora yayi yana mai jin daɗin sauka da Raheenatu tayi, kallonshi tayi tace "i will go up, when you go home and call me" tana gama faɗa ta wuce saida tazo hawa step ɗin benen ta juyo tana girgiza mishi boobs tana faɗin "ka gani ka gani ƙwalelanka,ka gani ka gani ƙwalelanka, haka taita girgijewa tana hautsina ma Elejon tunani, dariya ta kece da ita tana faɗin "kaji ɗan banza daga ganin lafiyayyin ƴaƴa na motsi har ka haukace" gwalo tayi mashi ta haura sama da gudu tana dariya shafa kanshi Elejon yayi yana yana dariyar halayyar Raheenatu shidai ba ƙaramin birgeshi take ba, ga wata zazzafar ƙaunar da sonta daya riga ya kamashi, lumshe idanunsa yayi yana shafa ɗan gemunsa, ya fice Raheenatu na shiga ta faɗa kan gado tana mai sake lumshe idonta, ita kanta tasan Elejon na sonta amma saidai koda ya musulunta bazata iya aurensa ba saboda wani dalili nata na daban, dukda bawai itama bata sosnshi ba, saboda babu macen da zata ga Elejon tace bata sonshi, a hankali ta furzar da iskar bakinta, tana tunanin yadda rayuwa ta sauya mata, tana fatan kamar yadda tata rayuwar ta sauya ta Raihana itama ta sauya, duk lokacin data tuna Ahalinta takan tsinci kanta cikin damuwa sosai, *RAIHANA* A hankali na miƙe jiki ba ƙwari na nufi inda Sadeeq yake, bacci na iske ya kwashesa, hannu nasa ina bubbuga ƙafaɗarsa, "tashi ka ɗauki Abba mu tafi" na faɗa ina ficewa, bayana ya biyo yana ɗaukar Abba, rufe idona nayi na riƙe hannun Sadeeq, bamu buɗe idonmu a ko ina ba sai gidan Mommy, kai tsaye wani ɗaki nakai su Part ɗin Mommy, Ni kuma na haura sama ina shiga, na faɗa bisa bed ɗin ina maida numfashi, ji nake duk jikina yayi man tsami, kiraye_kirayen Sallah asuba yasa na miƙe na shiga Toilet nayi wanka sannan na ɗoro Alwalla, Sallah nayi saidai yau naji da sauƙi babu azabar nan da nake ji, ina gamawa na tada Hameeda tayi Sallah, har Azkar na ɗan taɓa har gari ya waye, sannan na kwanta ina kwanciya bacci mai nauyin gaske ya ɗauke ni, wanda sai 12:00pm na tashi, shima saida Hameeda ta tadani wai Hamma yace ta tadani inyi Break, wanka na shiga nayo, nai shirina tsaf sannan, sanye nake da Arabian gown wacce taji adon Stone na fito sai walwali nake, a hankali na sauko inata zuba ƙamashi, kafeta da ido Nuraim yayi yana jin kamar ya hadiyeta ciki don ƙaunarta, Murmushi na sakar mashi ina ƙarasowa na zauna kusa da Mommy, gaida ita nayi, ta amsa da murmushi Kallon Hamma nayi ina gaida shi, da fara'a a fuskarsa ya amsa yana nuna min abinci "kije kiyi Break kar yunwa ta kamaki naga bakya son cin abinci" ya faɗa yana kauda kanshi gefe Da to na amsa ina miƙewa na nufi dinning Abinci kaɗan na ɗan ci, na miƙe, "ina zakije baki karasa kingin ba? maza zauna sai kin cinye shi" ya faɗa yana nufo inda nake, ganin haka yasa Mommy tashi ta haura sama, da kallo nabi Mommy kamar zanyi kuka, "maza kici wannan abincin da kika ɗan ci shine kinci abinci" , turo bakina nayi kamar na fashe mashi da kuka nace na ƙoshi fa Hamma" shima kamar yadda nayi haka ya turo bakin yana faɗin "sai kinci da yawa fa" ya faɗa da salon da nayi maganar, dariya na kece da ita ganin yadda yayi "Spoon ɗin ya ɗauka yana ebo Abincin yace "buɗe bakin" buɗewa nayi ya bani ina ci ina yamitsa fuska a haka ya dinga danna min abinci, saida ya tabbatar na ƙoshi sannan ya ƙyaleni da kanshi ya bani ruwa nasha, "ko kefa amma ki zauna kina wasa da cikinki, bakya son cin Abinci" shiru nayi ina wasa da zoben dake hannuna daga bisani kuma na yamitsa fuska ina ƙara turo baki nace " kaga Hamma ka mini ɗure abinci da yawa cikina duk ya cunkushe da ƙyar fa nake fitar da numfashi" na faɗa a shagwaɓe Lumshe idanunsa yayi yana jin wani yanayi a tare dashi don shi duk lokacin da Raihana ta turo mashi bakin nan gaba ɗaya hautsina masa lissafi take, yarasa me yasa ko dai da gayya take masa hakan, kiran sunanshi da tayi ne yasa shi saita nutsuwarsa yana kafeni da idanunsa masu ƙara narkar dani a duk lokacin dana haɗa ido dashi hannuna ya kalla yana taɓa zoben dake walwali a hannun yace "a ina kika samu zobe mai kyau haka ne?" murmushi nayi ina ƙara shafa zoben nace "Yayana ne ya bani shi" haɗe fuska yayi yace "wane yayan ?" "YAYA FAUZAN" na bashi amsa a taƙaice, "ɗan gidanku ne?" "eh mana" "kuma shine zoben har yanzun bai miki kaɗan ba?" Ya faɗa da son jin ƙarin zance, shiru nayi shima share zancen yayi, miƙewa nayi nace zanje wajen Mommy ina son faɗa mata wani abu, kai kawai ya ɗaga min yana bina da kallo Koda naje gun Mommy na zauna na faɗa mata dukkan abinda ya wakana, hamdala tayi tana min faɗa akan me ban faɗa mata ba, Nuraim ta kira ta faɗa masa komai, babu ɓata lokaci suka nufi inda Abba yake, dukkansu saida suka tausaya mashi, donma wai nan da sauƙi, tunda har magana yana yi tunda na shiga ya kafeni da ido yana hawaye a hankali ya miƙo man hannunshi da nufin nazo yana kiran sunana, jiki babu ƙwari na nufi wajenshi a hankali ya buɗe baki yace "Raihana tabbas na fidda tsammani da rayuwa, sai gashi a lokacin da banyi tsammanin ba kin kawo man ɗauki, nasan ni kaina banyiwa rayuwarku inganci ba, dukda ƙarfina a kafi abin na mini ciwo Raihana ta yadda na kasa baku kulawa,ni har gobe bani ganin laifinki Raihana tunda ba yin kanki bace, hasalima duk wata matsala data sameki a ta sanadina ne, na gaza Bama mahaifiyarki kulawar data dace, harta koma ga mahaliccimmu, haka zalika kuma ban ma rayuwarku inganci ba, wadanda naso su na ririta sune suka guje suka yunƙurin guntule kingin rayuwar data rage man, waɗanda naƙi na tozarta sune suka tarairayeni a lokacin da jarabta ta saman" kuka sosai Abba yake nima kukan nake, da ƙyar mukayi shiru da bada bakin su Mommy, daga bisani kuma aka ɗauki Abba zuwa asibiti don a ƙara duba lafiyar shi, muna zuwa aka amsheshi aka bashi gado, Saida Abba yayi watanni a Hospital suna bashi kulawa ya murmure yanzun ya fara maida jikinshi, sosai yake janmmu a jikibsa wanda koda yaushe muna tare, haka zalika har nayi kwanaki da gama Iddah, sosai Baba ke ƙara shiryani nida Nuraim wanda ranar Juma'a za'a ɗaura auren.........✍️ Wannan kenan *Comments, Share fisabilillah* Wadannan su ne ƙwarin guiwata *By Riamcool Hasken Royal* ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ [2/9, 2:09 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* Book 2 By Mariam sani Riamcool *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Bismillahirrahmanirrahim Page 94&95 ______________✍️Dukda bikin ba wani dogon lokaci aka saka ba, amma babu laifi ana shirye_shirye, haka Mommy ta zage tana gyara Raihana, ciki da waje, fatar nan tata sai sheƙi take tayi kyau sosai abinta, Nuraim kuwa sai rawar ƙafa yake da rawar kai akan Raihana, Abba kuwa jiki ya ƙara murmurewa an sallame shi a Hospital, harya fara maida jikinsa, sosai yake jammu a jikinsa,ga Lagos Nuraim ya bada cigiyar Raheenatu, don yadda Abba ya damu akan son ganin Raheenatu, haka zalika ya riga daya saka damuwar Ammi a ranshi ganin tana hannun Baba Modibbo, zaune nake Mommy ta tasa ni gaba akan sai nasha wani magani wanda Baba ya bada aban, kurɓa ɗaya nai mashi naji Brain ɗina na neman juyawa, ga kuma wani Azababben ciwon kai lokaci guda daya rufeni, kallon Mommy nayi ina ƙwal_ƙwal da idanu alamun zanyi kuka nace "Mommy don Allah na barshi hakanan tunda na kurɓa, wallahi bakiji yadda Brain ɗina ke juyawa ba, ga kaina dake wani irin sara man,kuma fa ga lalle da zamuje ayi mana" na faɗa kamar na fashe mata da kuka Nuraim dake tsaye bakin ƙofar tun ɗazun ya harɗe hannuwansa a ƙirji yana kallonta don tunda Mommy ta saka aka fara gyara Raihana gaba ɗaya ta hanashi ganinta, ta ɓoyeta, gaba ɗaya cikin kwana biyun daya yayi bai ganta ba, ya shiga cikin wani yanayi, yanzuma da Mommy ta shigo ɗakin ta mance bata kulle ba shiysa harya samu damar shigowa, kallonta yake sosai don daga ita sai wata ƴar ɓingilalliyar riga wacce ta bayyana halittun ƙirjinta waɗanda suka cika fam dasu sunyi tsaye, ga fatar jikinta dake sheƙi sosai ta ƙara ja da haske tayi ɓulɓul, a hankali ya tako harya iso daf da ita, Cup ɗinda ke hannuna ya amsa yana ɓata fuska yace "Mommy tunda har kanta na ciwo daga shanshi kamata yayi ki ƙyaleta tunda ta sha" sake da baki Mommy ke kallonshi don ita batama san da shigowarsa ba, sai yanzun "bazan ƙyaleta hakanan ba saifa ta shanye tas sannan, kai da kanka kasan fa muhimmancin maganin nan" Mommy ta faɗa tana amsar Cup ɗin dake hannunsa, da ƙyar na shanye shi, ina matsar ƙwalla lallashina Hamma ya dinga yi, "idan kin gama ƙwallar ƴar Mommy sai ki tashi kiyi wanka kuje ayi maki lallen" Mommy ta faɗa Cikin ɓata fuska Nuraim ya kalli Mommy yace "Mommy ina kuma zata tafi, a hakan yadda tayi kyau ɗinna? gaskiya Mommy ta zauna mai lallen tazo da kanta tayi mata, bani son wani koda ɗan yatsanta ya kalla, Mommy, bare tayi ɓulɓul da ita sai sheƙi take kuma ta fita, tunda na tabbata ta fita sai wani ya kalleta, nifa ko Abdurrahim ban son ya kalleta bare kuma wani na daban, Uhmm Uhmm ta zauna nida kaina zan aika a ɗauko mai lallen" Nuraim ya ƙarashe zance da ƙara haɗe fuska Mommy kuwa zama tayi sake da baki tana ƙare mashi kallo tace "Nuraim yaushe ka koyi rashin kunya ne,? to tashi ka fice man anan, tunda daman ai saida na hanaka shigowa ka shigo, wannan rawar ƙafa haka" Mommy ta ƙarashe zancen da miƙewa, shi kuwa Nuraim ma ko a jikinsa saima ƙoƙarin jana da fira da yayi, ni kuwa duk a takure nake, saida Mommy tayi mashi jan ido sannan ya fita kamar ya fashe da kuka haka zalika lallen da banje ba kenan saidai ya saka aka ɗauko tai man a gida, sosai mai lallen ta zauna ta tsara mani shi wanda ba ƙaramin ɗaukar hankalin Mutane lallen yayi ba, ya ƙara haska fatana na fito washar ,su Hameeda da Aunty Ni'imatu sai yabawa suke, *Raheenatu* Sanye take cikin wata haɗaɗɗiyar gown wacce tasha mata jiki komai na jikinta na motsi sai ɗan siririn veil ɗin dake kanta, Hand back ɗinta ta ɗauka suka fice ita dasu mai kayan harka, wajajen shaƙatawa suka nufa, duk wanda ya kalli Raheenatu sai yaso ya ƙara kallonta saboda kyan da tayi, saidai tunda ta shigo taga, wani mutum daya kafeta da ido yana kallonta, ga photo a wajenshi duk idan ya kalli Photon sai ya kalleta, Mutumin ne yazo yai mata sallama ta amsa sannan yace idan bazata damu ba yana son magana da ita babu musu suka keɓe da ita, Photon dake wayarshi ne ya gwada mata yana faɗin "ko kin san wanna?" amsar Phone ɗin tayi tana duba Photon gabanta ne ya bada sautin dummm ganin Photon Raihana Cikin rawar murya ta ce "eh ai nice nan ɗin" ta faɗa tana jin tsoron kar ace ko kisan kai Raihana tayi aka ganota,shiysa tace ita ce don ƙara ayi mata hukuncin da za'a yanke wa Raihana, Murmushi Mutumin yayi yace "amma...." "abinda yasa kaga ƙwayan idona normal yanzun wannan abin da ake sakawa a ido ne bansa ba shiysa, tunda ka gano ni buga mini ankwa kawai mu tafi" dariya ce taso kufcewa mutumin yace "Calm down bafa laifi kikayi ba Hajiya, nasan da cewa wannan ɗin bake bace ƴar uwarki ce to mai gidanmmu ne wanda zai aureta ya bada cigiyar a ganoki anan gari" harara ta maka masa tace "har wani auren zatayi baya ga wanda ke gareta? da ce man kayi Mijinta ne ya bada cigiyata zan yarda tunda nasan tana da aure" "Wallahi shine idan kuma baki yarda ba zan kira sai kiji daga bakinta" ya faɗa yana karɓan Phone ɗin dake hannunta yana lalabo Number Nuraim, lokacin Nuraim na Falon Mommy, jin wayarshi na ruri yasa shi dubawa ganin ɗaya daga cikin waɗanda ya saka aikin gano Raheenatu ne yasa ya ɗaga da sauri bai bari anyi magana ba yace "ya ake ciki ne kun ganota" "eh Oga amma fa taƙi yarda shine nace bari na kiraka sai ka bama ita ƴar uwar tata" "ok" Nuraim ya faɗa yana kashe Wayan, kallonshi Mommy tayi tace "meke faruwa ne?" "MOMMY Raheenatu ce aka gani to shine ita bata yarda ba sai taji muryan Raihana sannan, yanzun bari na kaiwa Raihana sai suyi magana" hamdala Mommy tayi tace "bani Phone ɗin nakai mata ko ka bani Number mutumin na kira" babu musu yaba Mommy Number mutumin, miƙewa tayi ta nufi inda akewa Raihana lallen "masha Allah ƴar Mommy wannan lalle da aka zuba miki haka, ai dole na bama mai lallen babban tukucin fito man da ƴata da tayi" Mommy ta faɗa da Murmushi ɗauke a fuskanta nima Murmushin nayi ina miƙewa don wanko lallen saida na wanke tas sannan Mommy tace muje zamuyi wata magana binta nayi har bedroom ɗin ta sannan ta kalleni ta ce "dama Raheenatu ce aka gani shine nake so ki amshi waya kuyi magana, sosai farinciki da annurin fuskana ya ƙaru ina amsa wayar da Mommy ta dannawa wata Number kira ana ɗauka cikin murna nace "Raheenatu" Mutumin daya ɗaga ya miƙawa Raheenatu waya yace ga shinan kuyi magana da ƴar uwar taki, jiki na kyarma ta amsa "Raheenatu kina jina kuwa " taji muryan Raihana ta dakar mata kunne, "eh Raihana ina jinki ashe da gasken kece dai?" "To idan bani bace wacece? Ni ɗin daice Raihananki ba wata ba" na faɗa ina sakin Murmushi, itama sautin Murmushi naji tayi tace "Allah hakimun ashe da gaske dai zan sake jin muryarki zan kuma ƙara ganinki, Raihana, ke koma dai mafarki nake, kai don Allah ɗan kafta man mari inji idan ba mafarki nake ba" "Kefa Raheenatu bakida kai har yanzu" na faɗa ina dariya itama dariyar tayi, nan nace ta biyo wannan mutumin su taho gobe ta Flight, Suna gama wayar Raheenatu ta dubi mutumin tace muje kaga gidan da zaka zo gaben sai mu tafi, ko su mai kayan harka bata jira ba suka tafi da mutumin yaga gidan, tana shiga ta hau harhaɗa kayayyakinta, duk abinda take buƙata saida ta haɗashi, Koda su Hajjo suka dawo suka ga tana haɗa kaya suka tambayeta ina zata je ne , nan ta faɗa masu inda zata je sunyi murna sosai suma da jin ta samo ƴar uwarta, haka Raheenatu ta kwanta da ɗokin gobe tayi taganta Abuja gurin Raihanatu ɓangaremmu muda su Abba ma haka dukkamu mun kwanta da ɗokin ganin Raheenatu, Washe gari Raheenatu dukkan wani shiri tayi shi haka ta nemi kayan mutunci ta saka, Atamfa ce jikinta ɗinkin fitted gown ga babban mayafi data ɗauka ta yafa ba laifi tayi kyau sosai itama, 6:30 am nayi mutumin yazo, har Airport su Hajjo suka rako su sunce duk yadda ake ciki tai musu waya, sunyi sallama cikin kewar juna, daga Mommy sai Raihana da Abdurrahim suka nufi Airport don Raihana tace Abba ya zauna don suyiwa Raheenatu Suprise domin tarban Raheenatu, sun ɗan daɗe sannan jirginsu ya sauka, tunda mutane suka fara fitowa na zuba ido ina kallo so nake kawai nayi tozali da ƴar uwata, a hankali Raheenatu ta safko daga jirgin cikin nutsuwa itama tana ƙarewa mutanen wajen kallo don ganin ta inda zata ga Raihana, tunda ta safko su Mommy suka kafeta da ido suna mamakin tsantsar kamanninsu da Raihana don komai nasu ɗaya ne ƙwayar idonsu ne kawai ya banbanta, da juna ta nan ne kaɗai zaka banbance su, idonta ya sauka kaina wanda nima ita nake sakarwa Murmushi, bata damu da mutanen dake wajen ba haka haka ta kwaso da gudu ta nufoni..........✍️ Wannan kenan *Comments, Share fisabilillah* Waɗannan su ne ƙwarin guiwata *By Riamcool Hasken Royal* ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ [2/14, 8:39 AM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *BOOK 2* *By Mariam Sani RIAMCOOL* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *Bismillahirrahmanirrahim* Page 96&97 ___________✍️Nima haka na kwasa da gudu muka rungume juna cikin shauƙi da matsanancin farinciki, sakina tayi tana sake dubana tace "wai Raihana kece nake gani? ko dai gizo kike mani ko kuma mafarki" dariya nayi nace "ke dai baki gajiya da shirme har yanzun zo muje gasu Mommy can" "wacece kuma Mommy, ina kika sameta.?" ta tambaya, hannunta na kama muka je wajen dasu Mommy ke tsaye, kallon su Mommy tayi ta gaida su a ladabce sannan nai mata bayanin wacece Mommy, rungume Mommy tayi da tsantsar farinciki, tana murnar itama yau gata ga dangin Ammi ga kuma Raihana "Anya yau zan iya bacci don murna.?" "tsaf kuwa zaki baccinki harda saleɓa ƴata" Mommy ta faɗa tana dariya, itama dariyar tayi tana shiga Mota, muma shiga mukayi, kai tsaye gidan Mommy muka wuce Koda muka je saida Raheenatu tayi wanka sannan taci Abinci nace tazo zata gaisa muje biyoni tayi muka je har Part ɗinda aka bama Abba, a hankali muka tura ƙofar Falon, muna shiga Raheenatu tayi turus ganin Abba zaune kan 2 seater wanda fuskarshi ɗauke take da yalwataccen farinciki da maɗaukakin murmushin da yake sakar mana, miƙo mana hannu yayi da nufin muje mamaki ne fal a ran Raheenatu wanda take cike da farinciki da gudu ta nufi Abba ta faɗa jikinsa ta saki kukan farinciki nima hannu ya miƙo man da nufin na taho haka mu Ukku muka rungume Abba, ƙwallar data cikawa Abba ido ne ya samu damar zubowa a hankali yasa hannu ya ɗauke, yana rarrashin Raheenatu tai shuru "haba ƴar Raheenatun Abba kiyi haƙuri ki daina kukan nan, yanzu ba lokacin da zamu dinga tuna abubuwan da suka faru bane, lokacine da zamu godewa Allah da ya haɗa mu, dukkan abubuwan da nai maku wallahi bana cikin hayyacina" Abba ya faɗa yana sake rarrashin Raheenatu sannan tayi shiru, sosai Abba ya dinga mana fira muma muna taya shi haka muka dinga fira cikin nishaɗi da maɗaukakin farinciki, mun jima sannan muka fice daga Part ɗin Abba muka koma, Side ɗin Mommy nanma wata firar ce muka dasa mu dasu Ni'imatu da Hameeda, nan Mommy take bamu tarihinsu ita da Ammi, sosai muka tausaya musu na kuma ƙara ɗaura aniyar ƙwato Mahaifiyata daga hannun Modibbo, dan zanso sai komai ya dai_daita sannan su haɗu da Mommy suje gun Mahaifansu, sosai na ƙara kwantarwa Mommy hankali koda dare yayi nanma muka zauna muka dasa wata firar nan take sanar dani abinda ya faru da ita tsakanin ta da gidan Alhaji Bashir, na tausaya mata sosai, nima na faɗa mata duk abinda ya faru tsakanina da Alhaji Muttak'a, dariya tayi tace "Yo ke Raihana gaba ta kaiki gaban gaba ma wallahi, idan nice ke wallahi saina haɗa dashi na zuƙe jininsa, yanzun dai kina nufin kice wannan ɗan baturen zaki aura, ba ɗan baƙin ba.?" dariya nayi nace "eh" Hameeda ce tace "Wallahi Raheenatu ki rufawa kanki asiri ki daina cewa Yaya Abdurrahim ɗan baƙi don yaƙi jinin ace masa ɗan baƙi" ta faɗa tana dariya taɓe baki tayi tace "yo ba ɗan baƙin bane, kuma ga faɗin rai da gadara, ko baturen gidan nan bai da gadararsa shi kuwa matarsa nasan ta bani da baƙin rai" dariya mukai Hameeda tace "ai bashi da Mata fa" "to Allah ya bashi irinsa mai faɗin ran" Raheenatu ta faɗa tana jawo wata firar saida muka daɗe sannan mukai bacci washe gari da muka tashi haka muka je Saloon akai mana gyaran kai, mun ɗan jima sannan muka dawo, muna dawowa Mommy ta nuna man lefen da Hamma Nuraim yai man tsayawa nayi da mamaki ina kallon akwatina 16 dake lode da kayayyaki, wai danma lokacin bikin ne ya ƙure shi yasa, nayi farinci sosai da godiya dana dinga zubawa Mommy kamar ba gobe, ɓangaren Dada kuwa dukda ba wani son auren Raihana da Nuraim take ba haka tayo gayyar ƴan uwa da abokan arziƙi, don Dada tunda Raihana ta shigo gidan ta zubar da makaman yaƙinta, taja mutuncinta ta riƙe, haka yanzu ta bar cin mutuncin Mommy, dukda tana tsoron Raihana bai hanata janta a jikinta ba, don a bikinnan itama sosai take nuna tata bajintar Nafisa kuwa ita da baƙin ciki ya isheta tuni ta haɗa kayayyakinta tabar ƙasar ta tafi London nan take Nuraim ya buga mata kingin sakin igiya biyun data rage ya ida katseta wanda ba ƙaramin baƙin ciki ta shiga haka yasa ta ƙara ɗaukar aniyar ganin Raihana, Yau Friday ranar da za'a ɗaura aure, zaune nake nayi zugum duk tunanin duniya ya isheni babu abinda nake tunani sama da naga na amso Ammi daga hannun Modibbo, sosai na tuna da ita gabana ke faɗuwa ba nida wani burin daya wuce naga, naga bayan Modibbo, ga duk yau yadda na tsinci kaina cikin faɗuwar gaba don koya na tuna za'a ɗaura mani aure sai naji gaba ɗaya bani so, naji gaba ɗaya auren ya fice man a rai, shigowar Raheenatu ne yasa ni ɗago da kaina ina kallonta, sosai tayi kyau cikin bugaggiyar shaddar ta wacce taji aiki Kallona tayi tace "Raihana wai meke damunki na ganki sukuku.?" ƙwalla naji sun cika man ido nace "Raheenatu auren ne bani so wallahi." "kamar ya baki son auren? yanzun dai ki tashi kiyi wanka ki shirya" ta faɗa tana miƙar dani, sannan ta shiga Toilet ta haɗa man ruwan wanka, nayi ina fitowa ta fito man da wani haɗaɗɗen bride material fitted gown ɗauka nayi na shirya cikinsa raina duk babu daɗi, Hameeda ce ta shigo da mai Make up ta zauna ta tsantsara man, ba dan raina yaso ba, sannan tayiwa su Raheenatu, ga yunwa data addabi cikina don koda na tashi ko ruwa ban sha ba haka su Mommy sukai ta fama da naci abinci amma naƙi , saida Mommy tai man Jan ido sannan naɗan tsakura Photuna ma ba don ina so ba na fito mukayi ansha photuna wanda har saida na gaji haka dai aka ci gaba da hidima, wanda Mommy ko mp ta hana a kunna, da Hameeda sunso ayi wani abin amma fir Mommy ta hana, saidai kawai ƙarfe huɗu da za'ayi Walima Ɓangaren Nuraim kuwa shar sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda sky blue wacce ta ƙara fiddo da tsantsar kyawunsa da cikar haibarsa, fuskarshi sai fitar da annuri take, yau dai Allah zai cika masa mafarkinsa da kuma burinsa na mallakar Raihana wacce ya daɗe yana mafarkin mallakarta, "Nuraim wannan fa ɗoki naka yayi yawa" Jabir ya faɗa yana dariya shima dariyar yayi ya wani juya ido kamar mace yace "Jabir ya san ranka idan banyi ɗokin wannan ranar ba me kake so nayi, dole ne yau na ƙara godewa Allah da zai mallaka min wacce na daɗe da mafarkin samunta a rayuwata, na kuma ci buri akanta, wacce na daɗe da mafarkin zata haifa man gudan jinina" nan dai Jabir yaci gaba da tsokarnarshi kingin abokansu waɗanda sukai karatu tare suna tare masa, 1:30 nayi Nuraim ya sake shiga wanka ya shirya cikin wata dakakkiyar Shadda fara Sol wacce taji aikin hannu, haka ƴan gidansu da Abokansa su kayi ankon Shadda Ash color suma ba ƙaramin kyau da tsari sukai ba, ƙarfe 2:30 dai_dai dubbanin mutane suka shaida ɗaurin auren Raihana Nuraddeen Usman da Kuma Muhammad Nuraim Haris Ali, wanda Abba tsabar murna kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha, daga wajen ɗaurin auren anci an sha anyi bajinta sosai, sannan suka shigo cikin gida danyi Photuna lokacin ina ɗaki na janza wani haɗaɗden leshi wanda ya amsa sunansa fari mai ratsin golden, haka zalika aikin dake jikinsa golden ne, kwalliyar aka sake gyara mun wacce nai shar gwanin kyau, Raheenatu ce tace na taso zamuje mu gaisa da abokan ango sannan ayi mana photuna, babu musu na tashi ina yamitsa fuska, tunda ta fito ya wani kafeta da ido kamar zai cinyeta sosai tayi masa kyau ba ƙarami ba, gani yake kamar ba Raihanarshi ba saboda kyan data ƙara kamar Aljana dan tsabar kyau ji yake kamar ya mayar da ita ciki dan tsananin ƙauna, murmushi mai ma'anoni ya saki yana kawar da fuskarshi tunda na iso ta ƙasan ido nake kallonshi ganin kyan da Hamma yayi saida zuciyata ta tsinke, cikin kasalalliyar murya na gaishe dashi sannan na gaida kingin, suka amsa suna tsokanata, ina yaƙen dole don bazan kirashi da murmushi ba saboda azabar da nake ji ta daban a jikina Raheenatu kuwa Abdurrahim ta ƙurawa ido ganin shima mugun kyau ɗin daya zuba "ashe dai baƙaƙe ma akwai masu kyau shidai gashi ɗan baƙi amma akwai kyau ɗin, saidai mugun faɗin ranka ya ƙwareka" ta faɗa a ranta Abdurrahim ganin yadda Raheenatu ta zuba masa ido yasa shi maka wata jar harara kamar idonsa zasu faɗo, itama hararar ta maka masa tana masa kallon sama da ƙasa sannan ta murguɗa masa baki, ƙwafa yayi yana kauda kanshi "lallai yarinyar nan zan koya miki hankali, yaushe ma kika ga mkwancina da har zata rainani haka hada harara, lallai kuwa zanyi maganinki" ya faɗa yana cije lips ɗinsa na ƙasa Hameeda ce data lura da duk abinda ke faruwa ta kece da dariya tace "Raheenatu alƙur'an kin tsokano Yaya Abdurrahim ku fara wasan ɓuya dashi, don nasan ba zai ƙyaleki ba" taɓe baki tayi tace "can shi ta matse mawa da gama ya samu an kalleshi fuska sai kace baƙin ɗuwawu, shi ba wani kyau ba,kawai dai abinda yasa na ɗan kalleshi ne ina son na ƙara gano muninshi ne, gashi kuma na gano" karaf sai a kunne Abdurrahim Zuciyarshi ce tai mashi zafi ji yake da babu mutane babu abinda zai hanashi falla mata maruka lafiyyayyu Photuna muka sha hadasu Dady da Abba dasu Sadeeq daya shige cikin su Hameed kamar wasu sa'annisa, ansha photuna ba laifi, jin kaina ya ɗan fara sara mun yasa na sulale na haura ina shiga na faɗa kan bed na fashe da kuka ko zan samu salamar ƙuncin da nake jin ya addabi zuciyata a halin yanzu, jin shigowar Mutum ya sani miƙewa zaune ina goge hawayen fuskana ganin Hamma ne yasa ni haɗiye abinda nake ji na sakar masa murmushi, a hankali cikin nutsuwa ya tako har ya iso ya zauna dab dani kafaɗunshi na gugar nawa, tallafo fuskana yayi ya kafeni da ido cikin damuwa da kwantar da murya yace "me ya faru dake kike kuka?" "ba komai" na furta wasu hawayen na sake wanke mun fuska, "ba komai kuma kike kuka?" "eh kawai dai naji kukan yazo man ne tunawa da Ammi da nayi" "Ok ya isa hakanan, kiyi shiru ki daina zubar da hawayenki insha Allah komai yazo ƙarshe Ammi zata dawo garemu da izinin Allah"ya faɗa da sigar rarrashi yana goge man hawayen, "muje na wanke miki fuskanki nasan duk wannan kwalliyar ya isheki amma kafin nan bari na fara rage miki wani nasan ai kina so na rage miki ko?" shiru nayi ina wasa da yatsun hannuna, wanda Nuraim ya saki murmushi yana ƙara juyo da fuskana ga tashi a hankali ya kai tashi fuskan ga tawa yana goga karan hancinsa ga nawa, wanda muka saki wata nannauyar ajiyar zuciya, a hankali ya kai bakinsa a nawa yana sakar man wani hot kiss wanda saida ya sani shiɗewa cikin salon ƙwarewa ya dinga sarrafani da hot kiss ɗinshi mai wuyar fassarawa wanda yasa ni manta wata damuwata, na ƙarɓi sakon da yake aiko man saida ya daɗe yana kiss ɗinna sannan ya ƙyaleni yana Murmushi, hatta jan bakina saida ya shanyeshi tass sanna, murmushi ya sakar mani yana kashe mani ido wanda nai saurin janye nawa idanun ina murmushi, da kanshi ya ɗaukeni ya kaini Toilet ya wanke mun kwalliyar, saida ya tabbatar babu damuwa a tattare dani sannan ya fita Yana fita su Jabir suka ci gaba da tsokarnarshi, ganin jan baki a farar shaddarshi, murmushi kawai yayi yana shafa kanshi ƙarfe 4:30 pm nayi aka fara walima wadda Mommy ta ɗauko wata shahararriyar Malama, tayi faɗakarwa sosai akan zamantakewar aure,6:00 nayi aka tashi, haka dai aka ci gaba da hidima har 7:00 pm sannan na shirya cikin wata haɗaɗɗiyar lifaya mai kyau na saka sanna aka kaini wani Part wanda Nuraim ya ƙara gyarashi sosai, sosai tsaruwar Falon da mugayen Furniture ɗin da aka zuba a Falon zai birge mutum waɗanda suka kasance Set biyu Milk da brown, har wajen takwas su Aunty Ni'imatu na ƙara kimtsa ko ina ya buge da ƙamshi sannan suka tafi suka barni ni kaɗai, basu daɗe da fita ba su Hamma suka shigo, tsokanata suka fara yi sannan sukai mana nasiha daga ƙarshe suka rufe da addu'a sannan suka tafi suna fita Nuraim ya ƙara matsowa dab dani yana yaye mayafin lifayar sannan ya ƙurawa fuskana kallo, sadda kaina ƙasa nayi "sarkin kunya da anyi abu sai duƙar da kai ƙasa, tashi muje muyo wanka da Arwalla" zaro ido nayi nace "Hamma kana nufin a tare zamuyi wanka?" dariya yayi yana shafa kumatuna yace "Yes i mean a taren zamuyi wanka, tashi mu shiga" ganin zai takura man yasashi tashi ya shiga yayo nashi da wanka da kuma na maganin da aka umarcemu muyi shi, yana fitowa nima na shiga nayo, saidai ina kama ruwa da wani ruwan magani naji faɗowar abu a ƙasana, da sauri na duba naga ko minene hankalina tashe, saidai ganin wata ƙankara_ƙankara yasa gabana faɗuwa tunawa nayi da lokacin dasu Jogu suka saka man ita, hakan yasa na saki nannauyar ajiyar zuciya naci gaba da wankana nayi Alwalla, sannan na zira doguwar rigar dana shiga da ita, na fito a gurguje na ɗan shafa Lotion da turaruka sannan muka tada sallah mun daɗe mun add'oi sannan muka tashi, da ƙyar na ɗansha sasanyar madara da kuma naman dana ɗan yaga kaɗan shima don Hamma ya tsareni akan sai naci muna gamawa da kanshi yayo man brush sannan ya ɗauko rigar bacci ya saka man da kanshi dukda matsananciyar kunyar da nake ji, shima daga shi sai boxer wanda nake jina duk a takure, light ɗin ya kashe muka kwanta gabana na dukan Ukku_ukku, jin jikina da nashi a haɗe, ƙara juwo dani yayi muna fuskantar juna kafin a hankali ya saka hannu yana yawo dashi a sassan jikina, sannan ya saka fuskanshi a tsakanin ƙirjina yana yawo da ita ko ina a hankali ya dinga yo sama da fuskar har ya iso ga laɓɓana haka ya cafkesu ya ci gaba da tsotsa cikin fitar hayyaci, haka hannuwansa naga boobs ɗina waɗanda yake shafasu da yamitsasu san ransa yana shiɗewa cire bakinsa yayi sannan ya cire man ƴar ɓigilar rigar yan tilli da ita cikin wani irin salo mai wuyar fassarawa ya dinga sarrafani wanda ni kaina ban san lokacin dana ajiye dukkan wata kunya dake nuƙurƙusata ba naci gaba da tayashi, har ya kai ga neman hanya, wanda sai a lokacin naji dukkan wani abu na jikina ya daina aiki, wata muguwar ƙara na saki mai fidda amo da sauti wacce ni kaina bansan abinda nakeyi ba wanda naci gaba da wani irin masifaffen gurnani........ *harda na jiya da banyi muku ba na haɗe, kuma ku haɗe kuyi man Comment*. Wannan kenan Comments Share fisabilillah Waɗannan su ne ƙwarin guiwata By Mariam sani Riamcool Hasken Royal star ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ [2/14, 8:39 AM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *Book 2* *By Mariam sani Riamcool* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Bismillahirrahmanirrahim P 98&99 ______________✍️Tun ina gurananin nan a hankali har yakai ga inayi da ƙarfi, a hankali wani baƙin abu ya dinga fita daga bisani kuma hankalina ya fara dawowa jikina, saidai jin uwar azabar da nake ji tattare da Hamma ya sani fashewa da kuka ina roƙonsa ya ƙyaleni hakanan tunda ikon Modibbo ya fita, amma ko alamar jina ma ba yayi, tun ina iya yin kukan sosai har yakai ga ko fita ma ba yayi saboda tsabar dishewa da muryata yayi, saida nasha baƙar azaba sannan ya sarara man yana mayar da numfashi, jawoni yayi na tureshi ina ƙara ma kukana kaimi, murmushi mai ƙayatarwa ya saki yana shafa gemunsa don jinsa yake yau babu wanda ya kaisa A hankali ya ƙara jawoni jikinsa yana rarrashina, wanda da ƙyar ya lallaɓani nayi shiru, beed sheet ya janza, da kanshi ya ɗaukeni ina zillewa ina kuka ya gasa ni sosai sannan mukai wankan tsarki, ya ɗaukoni ya shafe man jikina tas sannan ya saka man rigar bacci, ya kwantar dani ina sauke ajiyar zuciya hawaye na biyo kuncina, shima kusa dani ɗin ya dawo ya ƙara jawoni a jikinsa ni kuwa na lafe luf baccin wahala na ɗaukata shima nan take baccin ya ɗaukesa kiran sallar Asubah shi ya farka dashi, ya buɗe lumsassun idanunsa ya zuba su a kyakkyawar fuskarta dukda gashin daya rufe mata fuska hannu yasa yana janye gashin, yana sake zuba mata idanunsa, yadda take bacci a nutse time to time takan saki ajiyar zuciya, ƙaunarta da tausayinta ne yaji ya ƙara nunkuwa a ransa, a hankali ya kai bakinsa yana kai mata kiss sannan ya miƙe ya shiga Toilet ganin zai makara a jam'i Alwalla ya dauro sannan ya fito ganin ta tashi yasashi ƙarasowa wajenta yana sakar mani murmushi ni kuwa kawar da fuskana nayi ina turo bakina, murmushinsa mai ƙayatarwa ya saki yana ƙara kai fuskanshi saitin tawa "fushin ne har yanzu baki daina dani ba.?" kauda kaina nayi gefe, ina ƙoƙarin miƙewa,cicije leɓe nayi na miƙe hawaye na biyo kuncina, taimaka min yayi da kanshi na miƙe ina tafiya a hankali, ina shiga Toilet ɗin na datse ƙofar, sumarsa ya shafa yana murmushi ya fice ina shiga na ƙara haɗa ruwan zafi na gasa kaina sannan naji salama, wanka nayi da Arwalla na fito na kabbara Sallah sai dai yau babu wannan azabar da nake ji idan zanyi sallar lami lafiya lau na yita a nutse sannan harna samu nayi karatun ƙur'ani nayi addu'oina sosai na ƙara godewa Ubangiji, ina lazimi Hamma ya shigo, sosai yake kallonta yana ƙara godewa Allah daya bashi ita, abinda Nafisa bai taɓa ganin tayi ba shine lazimi ko Karatun ƙur'ani, sallar ma da yaya take yinta saida na kammala sannan na ɗago da fuskata ina kallonshi "Hamma ina kwana" na faɗa ina mai jin kunyarsa da nauyin abinda mukayi jiya, a hankali yasa lallausan hannunsa yana kama hannuna ya kafeni da ido yace "sai yaushe za'a daina kirana da wannan sunan?" murmushi nayi ina mai ƙoƙarin zame hannuna daga nashi amma yaƙi bani damar yin hakan saima ƙara riƙesa da yayi kam, yana sake jawoni jikinsa lafewa nayi ina sauke ajiyar zuciya, hijab ɗin ya cire man sannan yasa hannunsa bisa tulin gashin kaina wanda yake fitar da ƙamshi, a hankali cikin salo da ƙwarewa yake shafashi, yana lumshe ido, ni kuwa muƙui nayi ina jin tsoro, ɗago da fuskana yayi sannan ya haɗe bakimmu waje guda yana tsosa kamar ya samu wani sweet jin hannunsa a boobs ɗina yasa na ƙara tsorata ina zare idanu, tsorona guda karya sake min abinda yai man jiya, hawayen da nake riƙewa ne suka zubo jikina na kyarma, jin ɗumin hawayen yasa Nuraim dawowa daga duniyar gajimaren daya tafi, cire hannun nashi yayi daga boobs ɗina, amma bai daina tsosar bakin ba, saida ya tabbatar ya ɗan rage zafi sannan yana cirewa ya saki ajiyar zuciya yana mai rungumoni a jikinsa ina ƙoƙarin zamewa murmushi yayi yace "Calm down Hayatee ba ƙari zanyi ba duk kinbi kin tada hankalinki" hawayen na share nace "to amma dan Allah kada ka sake" murmushi yayi yace "muje mu kwanta to" ya faɗa yana ɗaukana cak sai bisa bed, jikinsa na shige wani bacci mai cike da daɗi da kwanciyar hankali na ɗaukana, *JOGU* tun lokacin da yaga Uwani matarsa a tsaye wajen ya kalleta hawaye na zuba a idonsa yace "haƙiƙa Uwani kin shigo sha'anin da dole sai na kawar dake a doron duniya, dukda ba haka naso ba, ƙaunarki da sonki bazai saka na ƙyaleki ba" yana gama faɗar hakan ya yunƙuro da niyar cimma Uwani wacce ta ƙame waje guda don tsoro da matsanancin mamaki, hannu yasa ya jawota, ɗakin yasa makulli ya datse, Uwani idan banda hawaye babu abinda take, haka ya ɗaɗɗaureta ya ɗakko sharɓeɓiyar wuƙa ya ɗora a wuyanta zai mata yankan Rago, rufe ido tayi tana jiran tsammani harna tsawon minti biyar, jin shirun yayi yawa ya sata buɗe idanun, kallonshi tayi malemale cikin jini ga Ammi da wuƙa a bayansa tana huci zuwa Ammi tayi tana kunce Uwani ta miƙar da ita, jiki na rawa da kyarma, kallon Modibbo Ammi tayi tace "Modibbo ka sani wallahi ƙarshenka yazo ko baka mutu a yanzu ba zaka wulaƙanta dukkan abinda kake taƙama dashi na tsafi yana hannuna, ba dai wannan ne taƙamarka ba" ta faɗa tana ɗaga mashi zoben dake hannunsa, dukda raɗaɗi da zafin azabar da yake ji hakan bai hanasa ƙwalla uwar ƙara da ihu ba ganin Abinda ya dogara dashi na hannun Ammi, wanda ya kashe rayuwa ba adadi don ya mallakesa, wanda ya kashe ƴar uwarsa don ganin ya mallakesa, ace yanzu shine a hannun Ammi muddin kuwa babu zoben nan a hannunsa ya tabbatar tashi ta ƙare don yanzu dashi da sauran mutane duk ɗaya suke, ya tabbatar tashi ta ƙare Ya zaiyi da Ruhikan dake son cimma fansa, da ƙaraji da ihu yake faɗin "Sajeeda ki bani wannan zoben kada kija na aikata abinda banyi niyya ba kada ki kassara man da muradina ki taimaka min ki mayar min da kayana, nayi miki Alqawarin rabuwa dake da kuma yaronki Fauzan" ya faɗa da azaba murmushin takaici Ammi tayi tace "Modibbo kenan ka sani wannan zoben ya haramceka zaka wahala kafin kayi mutuwar wulaƙanci, sannan zoben nan nida kaina zan kaishi inda za'a warware mugayen tsafikanka na salwantar dashi" tana gama faɗa Uwani taja hannunta suna rufe Modibbo a ɗakin da kwaɗo, sannan cikin tashin hankalin da Uwani take ciki taja Ammi ta ƙofar baya suka gudu daga gidan saboda security wanda kowa zai fita saida izinin Modibbo hakan yasa ta fita ta ƙofar sirrin da ba kowa ya santa ba, sai ita, wanda bata taɓa binta ba saboda gargaɗin da Modibbo ya gindaya mata da addu'a ɗauke a bakunansu suka buɗe ƙofar sai dai abinda suka gani ne yasa su ja da baya, ganin kawunan mutane da kuɗaɗe zube birjik a wajen cikin tashin hankali suka bar wajen suna ketar uban dajin wurin da gudu, sun daɗe suna gudu kafin su iso bakin get ɗin ƙarshe, makullen da Uwani da ɗauko suka saka suka buɗe wajen, ganin su bakin titi yasasu sakin ajiyar zuciya a suna dosar hanya, don titin kanshi tsit yake babu mutane, don tunda suka fito basu ga mutum ko guda ba, dukda gajiyar da suke ciki bai saka su sun tsaya da tafiya ba, tun suna bin titi har suka kawo ƙarshen titin, ganin wata hanyoyi biyu daya raba ƙarshen titin ya sakasu bin ɗaya, haka suka dinga hanyar har Allah ya kaisu wani ɗan ƙauye na Fulani wanda babu laifi sunada yawa suna isa suka yada zango wani waje suna maida numfarfashi, saida suka huta suka tambayi gidan mai gari aka rakasu, ganin yanayin yadda suke birkice kuma gasu da gani ba ƴan garinsa bane cikin mutuntawa ya tarbesu yana musu iso cikin gida, cikin mutuntawa da tashin hankalin da bai saki Uwani ba ta kalli mai gari tace "don Allah taimakonka muke so mu ba ƴan gari bane garkuwa akai damu muka gudo da ƙyar, wanda mun kwana biyu muna tafiya sanan muka samu muka iso nan, kaga ƴar uwata babu lafiya" ta faɗa tana nuna Ammi tana zubar da hawaye kallonsu mai gari yayi da tausayawa yace musu ba damuwa nan yasa aka basu masauki sannan yasa aka kai masu ruwan wanka,saida sukai wanka sosai sukai salloli , ko abinci da aka aiko musu dashi basu ci ba saboda kowa da abinda ke damunsa, Uwani kwana tayi kuka saida Ammi tai ƙarfin halin rarrashinta haka suka zauna a garin cikinsu kowa da abinda ya damesa, ga mai gari ya sa aka dinga ma Ammi magani,(kunsan maganin Fulani ) cikin ikon Allah ta dawo Nml wannan baƙin da rama da tayi duk ya fara ɓacewa ta ɗan ciko gashi suna samun kulawa wajen mai gari ba laifi, hakan yasa hankalinta fara dawowa jikinta, *Ɓangare guda kuwa* tunda aka kai Hajiya Bilkisu Asibiti suka ƙi amsarta yasa ƴan aikin zuwa Police Station ɗin suka zo, sannan aka amsheta lokacin ta galabaitu ga bata a hayyacinta ma, sun duddubata sukai mata ɗinki, sannan ƴan aikin suka kira mai ɗori ya ɗora ƙafar data kare, saida ta share kusan wata guda sannan ta fara dawowa hayyacinta wanda tana tashi da sunan Sabreen ta tashi, sallamarta Doctor yayi ganin ta samu sauƙi, hakan yasa ta tattara ta koma gida, gashi tunda abin ya sameta ba taga ko mutum ɗaya a cikin ƙawayenta ba, hakan ya sata zuwa gidajensu, sai dai a cikinsu dak wurin wanda taje da kalar tarbar da zai mata a wulaƙance, kamar ma basu santa ba, don Turai gwadawa ma tai ita bata santa ba jiki ba ƙwari ta dawo gida tasha kuka kamar ranta zai fita, wanda sai a lokacin tayi da nasani halayenta da biyewa ƙawayen banza, harta lalata rayiwarta da kanta, gashi lokacin da duniya ta juya mata baya, suma sun juya mata nasu bayan, wanda hada ƙarin cin mutunci da suka haɗa mata, wanda sune suka zuga ta ta kashe mijinta, Kuka sosai take Sabreen kuwa tunda Bobbos ya tafi da ita yake gana mata azaba kala da kala, wanda kullum sai yayi amfani da ita ya kai sau ukku, sannan ya bama yaranshi su shana suma, sosai ta koɗe ta lalace, wanda saboda tsananin lalacewa kai baka ce Sabreen bace.........✍️ Wannan kenan *Comments, Share fisabilillah* Waɗannan su ne ƙwarin guiwata By Riamcool Hasken Royal star ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ [2/14, 12:29 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *Book 2* *By Mariam sani Riamcool* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Bismillahirrahmanirrahim *P.100&101* __________✍️Sosai Sabreen ta wahaltu kullum cikin kuka da ciwo, da dana sanin halayen Mahaifiyarta, wacce koma minene ita ce silar, komai kuma muddin ta kuɓuta tayi Alƙawarin zata shiryu ta gyara halayenta, kullum cikin kuka da takaici take *Raihana* Sai ƙarfe 11 na buɗe idona naga Hamma baya nan miƙa nayi na miƙe Toilet na shiga nayi wanka na fito daure da towel lotion na shafa sannan na ɗan shafa powder da kwalli sai lip gloss dana shafa, wata riga Italiono gown mai shape sosai da buɗaɗen wuya Red color wanda rabin ƙirjina duk a waje yake, sosai rigar ta amshi jikina feshe jikina nayi da haɗaɗdun turaruka jin yunwa yasa na nufi dinning don nasan Mommy ce zata aiko dashi, zama nayi naci nai nak sannan naɗan gyara gidan dukda ba ɓaci yai ba sosai amma haka na zage na gyara shi tas, ko ina ya fito tsaf ƙamshi tako ina, kwanciya nayi kan ɗaya daga cikin kujerun Falon, jin ana danna door bell ya sani miƙewa na buɗe su Raheenatu ne da Hameeda, da farinciki na tarbesu sannan muka zauna muka sha fira sun ɗan jima sannan suka ce zasu tafi, harara na aikawa Hameeda nace "nan da nan ɗin shine kike cewa wai zaku tafi ga baki ga hanci" dariya tayi tace "ke Wallahi Mommy tace karmu daɗe muzo mu gano mata lafiyarki, to kuma mun ganki garas kike" dariya nayi suna miƙewa suka fice wayar Raheenatu na amsa ko ta ɗan rage man kewa, zama nayi naita game har Hamma ya dawo koda ya dawo yace na saka Hijab zamu je gurin Baba ni dashi da Mommy muka je, koda muka je yauma ya ƙara miƙo man ruwa a ƙwarya yace na kalleta sannan na rufe idona, yadda yace nayi hakan nayi, Kallo ɗaya zaka masa kasan cewar duk a razane yake hankalinsa ba'a jikinsa yake ba, duba da yadda ya zurawa waje guda ido babu abinda yake kira idan banda Sajeeda ta dawo masa da kayansa haka daga bisani kuma zaki ga ya toshe kunnensa yana ihuu da kururuwa yana su ƙyalesa bai son su ɗau fansa, wanda wannan ihun ne ya janyo masu gadin asibitin Mahaukatan zuwa suka rirriƙesa sukai masa allura, laƙwas yayi ya kwanta, sai dai ko yanayin baccin daya kwashesa zai tabbatar maka da cewar ba'a tsanake yake yinsa ba duba da yanayin yadda yake zabura ya shura ƙafafu, dariya na kece da ita ina buɗe idanuna, kallon Baba nayi na faɗa masa dukkan abinda ke faruwa wasu ruwan ya sake bani na wanke fuskana sannan yace na rufe idona, yadda ya umarceni haka nayi na rufe idon nawa, Kamar koda yaushe zaune take ta rabka uban tagumi tana sana'ar tata wato Tunani wacce ta zame mata al'ada kullum tunani shine abokin firarta, "haba Sajeeda wai sau nawa zance miki ki daina tunanin nan tunda har Allah ya kuɓutar dake miye na kuma tunani, kita Addu'a insha Allah, Allah zai haɗaki da ƴaƴanki duka, kuma Fauzan nasan ko wace ƙasa yake ki bari nida kaina zan samo miki shi, nasan dana kirasa zai ɗauka" sauke ajiyar zuciya Ammi tayi tana share hawaye tace "tunanina ɗaya ne Uwani ya zanyi da Amal?" idan ta Amal karki damu ai ƙaddara ce babu kan wanda bata hawa, koni zan iya riƙe miki Amal a hannuna zan bata kulawa fiye da kowa bazan taɓa bari tasan cewar bani na haifeta ba" girgiza kai kawai Ammi tayi tana miƙewa don ita kaɗai tasan kalar baƙin ciki da takaicin da take ciki, a fakaice Uwani ta share hawayenta itama tana miƙewa buɗe idona nayi ina sauke ajiyar zuciya, na faɗawa Baba duk yanda akai "To Alhmdllh da Allah ya kuɓutar da ita a hannunsa sannan ya fara girbar abinda ya shuka ana tun kafin yaje can, yanzu abinda nake so daku gobe ku dawo zamu rangaɗa mu duka muje can, nasan ke tsaf zaki kaimu wajen da take" ɗaga masa kai nayi sannan mukai sallama muka koma muna komawa na gwada ya barni wajen Mommy ko nafi samun sauƙin abinda nake ji don ganin Mahaifiyata saida ya tada man da tsohon mikin Jogu, koda Raheenatu ta tambaye mu inda naje, na faɗa mata dukkan abinda ke faruwa, sosai ta kaɗu da jin zancen cewar wai Ammi na raye, tayi kuka sosai wanda har zazzaɓi ya rufeta, saida nai Ishsha'i sannan na koma gida ban daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗauke ni wanda na kwanta da son kaiwa Jogu ziyara, kwance yake wanda yayi nisa cikin tunanika tun lokacin dasu Uwani suka gudu yake kwance yana buga ƙofar ɗakin yana surutai, wanda ya jawo hankalin Security ɗin gidan suka ɓalle ƙofar ganinsa a haka ya tada masa hankali suka kaishi Asibiti wanda yayi kusan wata sannan ya warke sai dai tunda ya warke da ihun kiran Sajeeda ta bashi zobe ya tashi, wanda kuma duk rufe idon da zaiyi haka zaiga wasu kalar Halittu da jinane a jikinsu sunzo suna zasu ɗau fansa haka zai tashi ya zura da gudu yana karku ɗau fansa, wanda bilhaƙƙi da gaske yake ganinsu, Mutane kuma na ganin ya haukace hakan yasa aka kaishi gidan Mahaukata ana bashi magunguna da da Allurai, wanda suka ƙara birkita masa ƙwalwa, ga abin nashi babu sauƙi, wanda shi dai ya san da hankalinsa, Naseer ma wajensa kusan haka abin yake dan tun lokacin da Zoben nan ya bar hannun Jogu shima komai nasa ya lalace, duka ƴan ƙungiyar su ta tagayyara komai nasu ya lalace, wanda da dama a cikinsu duk sunyi Mutuwar wulaƙanci wanda aka rasa wanda ke ma ƴan ƙungiyar su kisan gilla Alhaji Naseer ganin abinda ya faru da Abokinsa ya tabbatar da shima bazai tsira ba, kullum da zillimi yake kwanciya, a hankali shima ya fara ganin Halittun da Jogu ke gani wanda suke binsa kullum da Jinane a jikunnasu suna dariya suna kuka don harda Saddiƙa yake gani wacce tafi tsorata sa da siffofin halittu da dama, gashi kullum da azabar da take gana masa, wanda nan akai tsammanin shima ya zare don saida takai shima ana mashi Allurar Mahaukata da bashi magunguna Jogu yayi nisa cikin wannan tunanin yaji dirar abu a gabansa, rufe idonsa yayi don baya son yai tozali da mummunan abinda ke gabansa don ya tabbatar koma miye a gabansa bana Alkhairi bane, sai dai da sauri ya buɗe idon nasa saka makon ganin abubuwan da suka kusan bugar masa da zuciya Idanunsa ya sauke akan Raihana wacce tai tsaye waje guda tana kallonsa, tana sakar masa wani Miskilin Murmushi wanda ya hautsina masa lissafi, daga bisani kuma ta haɗe rai tan tunkarosa ja da baya ya ke "Raihana ki taimaka kiyi mani rai don Allah nasan nida kaina banyiwa rayuwarki adalci ba, nine sanadin ɓata rayuwarki amma ko don darajar ɗan uwan Mahaifinki ki ƙyaleni kada ki kasheni, ki barni da bala'in dake tattare dani" ya faɗa yana fashewa da wani kalar matsanancin kuka dariya na fashe da ita ina tunkarosa da wata kalar murya mai fita biyu nace "Jogu wallahi sai kayi Mutuwar wulaƙanci wanda ko arziƙin Sallah ba zaka samu ba ina tabbatar maka da sai dai Namun daji sun cinye gangar jikinka sannan kan Abokinka Naseer zaka fara ganin kisan gillar da zan mashi a gabanka" na faɗa wanda nidai bani ce ke Maganar ba sai dai inga bakina na motsi kawai wanda na tabbata da Ruhin dake jikina ne ke wannan maganar Modibbo da jikinsa ke kyarma don ganin Alhaji Naseer a gabansa Jini na shatata, ta cikinsa inda aka tsaga, a hankali wani baƙin hayaƙi ya fito a jikina yana rikiɗewa ya zuwa wata yabiɗaɗɗiyar tsohuwa wadda tasa hantar Modibbo ƙara ƙaɗawa yace "Saddiƙa kiyiwa Allah da Manzonsa ki ƙyaleni don Allah bani son mutuwa yanzun ki taimaka man,ki dubi ƴan uwantakar dake tsakanina dake" wani kalar kuka ta fashe dashi mai gunji da fidda amo, hawayen jini na shatata a kuncinta, tace "Modibbo tuni na yakice wannan ƴan uwantakar da kake ikirari, tuni na fidda kai a layin waɗanda na sani, dukda nasan abinda nayi ne nima na girba harka kasheni, amma ka sani kaima ba zan ƙyaleka ba a tare zamu je can inda ba'a dawowa mu karɓi hukunci" tana gama faɗa ta kece da wata kalar dariya sannan tasa hannu tana shaƙe Naseer wanda idanunsa sukai luhu_luhu kakari yake yana roƙonta amma taƙi sakinsa hakan yasa jinin dake malalowa tasa halshe tana lashewa tana Kallon Modibbo tana gurnani tana wata kalar dariya, saida ta lashe jinin jikinsa tas sannan ta sake shi,zaƙo_zaƙo farcenta ta cakawa Naseer sannan tasa hannunta tana ɓara cikinsa yadda kasan ana fafe cikin dabba haka ta fafe cikin Alhaji Naseer tana dariya haka da hannuwanta tasa tana ƙwalƙwale masa idanu, tana cin ƴan cikin da zuciyarsa, kallon Jogu tayi wanda tsabar firgici tuni ya sume iskar bakinta mai ƙarfi ta hura masa wanda ya sashi farfaɗowa da ihun ceto amma babu wanda yake jinsa, buɗe idanunsa yayi ya kalli Saddiƙa wacce ke cin zuciyar Naseer jini na shatata bakinta jage_jage da jini dariya ta kece da ita tace "Saura kai, kaima bada jimawa zakai irin tasa mutuwar yadda nai masa kai saina linka maka taka biyu" tana gama faɗa ta juyo wajena da siffarta ta Saddiƙa lafiya lau, kallona tayi yadda nima na ƙame waje guda don tsoron daya kamani, hawaye naga na bin kuncinta tace "tace jeki Raihana kiyi rayuwa kamar kowa, ƙarshenshi yazo nida kaina zan ɗau fansata wanda ko ba komai kema zaki ga irin mutuwar da zaiyi" tana gama faɗa bata dawo jikina ba ta ɓace da gawar nima firgigit na tashi zufa na wanke man jiki ina kyarma wanda hakan ya tada Hamma faɗa jikinsa nayi na fashe da kuka tambayata yake me ya faru amma ba bakin magana ganin haka yasa shi tofa man addu'a wacce ya sani yin shiru ina sauke ajiyar zuciya na koma bacci, da Assuba ko Sallah da zai fita rirriƙesa nayi ina jin tsoro ya fita ya barni hakan yasa shi ja mana Jam'i mukai tare, bayan ya kwantar man da hankali ya ce na faɗa masa abinda ya tsorata ni, kwashe dukkan abinda ya faru nayi na faɗa masa, ƙara kwantar man da hankali yayi,na koma bacci, raina fess na tashi yau sakamakon ganin an kawo ƙarshen ɗaya saura Modibbo Yauma ƙarfe ɗaya na rana muka shirya harda Baba da Daddy yau muka nufi hanya wanda sai dai kawai naji na faɗa musu sunan garin da zamu je, haka muka dinga tafiya ina nuna musu hanya wanda nima umarni ne naji ana bani, wanda dai_dai wani gida na nuna musu muka tsaya, Daddy ne yaje yaiwa mai gari Sallama suka gaisa sannan yace masa dama suna neman wata baƙuwa ne wacce aka tabbatar masu da tana nan, da farinciki mai gari yace "tabbas haka ne suna nan dama Sajeeda kullum cikin tunani da rashin walwala gashi Allah ya kawo ku cikin sauƙi, ku shiga daga ciki" saida muka shiga aka bamu ruwa muka shiga sannan Mai gari ya shiga gidan yana ƙwalla kiran Sajeeda da sauri Ammi ta fito daga ɗakin da Hijab sanye a jikinta, "to Alhmdllh Sajeeda ga ƴan uwanki nan da sunzo nemanki don harda wata ƴarki wacce kuke kama mai bilalen ƙwayar ido, ku shiga ku gansu" gaban Ammi idan banda dukan ukku_ukku babu abinda jin cewar ƴan uwanta kuma ma wai harda ƴarta mai bilalen idanu, to ita ina taga wasu ƴan uwa ma, kodai Modibbo ne ya biyo sahunsu? sai dai kuma abinda ya tsaya mata a rai jin cewar ƴarta mai kama da ita da blue ɗin ido, hakan yasa ta nufi ɗakin zuciyarta na halbawa da sauri........✍️ Wannan kenan *Comments, Share fisabilillah* Waɗannan su ne ƙwarin guiwata *By Riamcool Hasken Royal* ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ [2/17, 2:24 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *Book 2* *By Mariam sani Riamcool* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Bismillahirrahmanirrahim *P. 102&103* _________✍️Hakan yasa ta nufi ɗakin zuciyarta na halbawa, ɗaga labulen tayi da sallama ɗauke a bakinta, sai dai sallamar tata maƙalewa tayi saka makon ganin Mommy da sauri zuciyarta ta sake halbawa wanda tai luuu baya ta faɗi, saboda ba ƙaramar razana tayi ba, da gudu su Mommy suka nufota suna kiran sunanta wanda ko motsi, ruwa Mommy ta ɗauko tana yayyafa mata, ta buɗe idanunta tana kallon Mommy wanda nan take ta rufe idanunta zata ƙara sumewa girgizata Mommy tayi tana kuka tace "Sajeeda na roƙeki da girman Allah karki ƙara somewa ki buɗe idanunki nice dai Yaya Fatima, ga kuma ƴarki Raihana" ta faɗa tana kuka itama Ammi kukan ta fashe dashi ta rungume Mommy tace "Yaya Fatima ashe ina da rabon na sake ganinki? na fidda rayuwa da tsammani sake ganin wani nawa Yaya Fatima" ƙara ƙanƙameta Mommy tayi tana kuka tace "Sajeeda banyi maki adalci ba, dukkan wata ƙaddara data sameki na dan gantata a kaina, saboda nice silar shigarki cikin ƙuncin rayuwa, nasan da ace ban raboki gaban iyayemmu ba, da baza ki taɓa shiga cikin ƙuncin rayuwar nan ba" girgiza mata kai Ammi tayi tace "kada kice haka Yaya Fatima can wannan ɗin itace tawa ƙaddara, koda baki taho dani ba nasan saita sameni, komai da kika gani a rubuce yake ki daina danganta hakan daga gareki" Nima a faƙaice na share hawaye ina ƙara godewa Allah, yau wata nutsuwa ta daban naji tana ratsani da kwanciyar hankali wanda tunda nake a rayuwa ban taɓa jinsu ba, lura da Ammi bata ganni ba yasa nace "Ammi" wanda ya sata saurin kallon inda nake da gudu nazo na rungumeta na fashe mata da kuka itama hawayen take tana bubbuga bayana tare da sake ƙanƙameni kamar wani zai ƙwaceni, ni kam nai luf a jikinta, sosai mukai kuka wanda da ƙyar Nuraim ya rarrashemu daga ni harsu Mommy Ammi ce ta kira Uwani wacce tunda na ganta na ɗauke kaina wanda kallonta kanshi sake tada man da mikin Modibbo yake, wanda da ƙyar na gaishe da ita, ita kanta kasa sakewa tayi itama don yau zata tattara tabar garin ta koma garinsu Gombe, don Ammi ce dama yasa ta tsaya, Address ta basu ta kuma taya Ammi murna sosai Wanda ƴan kwanakin da suka yi yasa su shaƙuwa, sallama sukai wanda Nuraim yaiwa mai gari Alkhairai da Sha tara ta arziƙi wanda tsabar murna mai gari kasa godiya yayi, haka cikin kewa suka rabu ana musu fatan Alkahiri haka muka nufi hanyar gida wanda ina kusa da Ammy ko wane motsi zatai ina kusa a haka har muka isa koda muka je su Raheenatu na Falon Mommy zaune da Sadeeq duk sunyi zugum, wanda idanuwansu ya sauka kan Ammi, murza idanunta Raheenatu ta ƙara yi kar ace gizo suke mata ganin Ammi tsaye ƙara murzasu tayi don tabbatarwa wanda hakan da tayi ya bawa Kowa dariya, ganin da gasken dai sune yasa ta nufi wajenta da gudu tana rungumeta wanda Sadeeq ya rigata isa wajenta sake ƙankamesu Ammi tayi tana murmushi da hawaye, itama Raheenatu hawayen farinciki take da ƙyar ta rabu da Ammi da kanta Mommy ta haɗa mata ruwan wanka tayi, wata Abaya mai kyau Mommy ta fiddo mata dashi tasa, sannan taci Abinci aka zauna ana firar yaushe rabo,wanda nan Mommy take sanar da ita dukkan abinda ya faru sosai tai murna da farinciki, jin cewar harda aure nayi ga kuma yanzu na dawo nrml kamar kowa wanda tayi farinciki iya farinciki ta ƙara godewa Allah, haka Nuraim duk inda ya matsa tace ya dawo kusa da ita, sai take ganin abin kamar almara ganin dukkammu yanda muka girma,haka zalika ta tausaya mana da dukkan jarabtar da muka gani wanda ta ƙara ƙarfafa man guiwa akan yadda da ƙaddara, ga shinan yanzu sai dai muce komai ya zama labari, haka Abba shima yazo ya dinga neman yafiyar Ammi akan abinda yai mata, don wallahi duka bada saninsa ya aikata mata ba, nuna mashi tayi ba komai ya wuce nan ya roƙi alfarmar ta koma ɗakin aurenta, don yanzun yanda yake jin masifaffiyar ƙaunarta, wanda Ammi itama nata ɓangaren haka yake, babu musu ta Amince ko dan ta ƙara gina rayuwarta wacce za tayi mai cike da farinci, sannan ta bama Mijinta farinciki wanda ya rasa tsawon shekaru mun daɗe nan sannan muka tafi wanda harda ƙwallata na zira Hijab ɗina naso ace nima ya barni na kwana kusa da Ammi, dariya Raheenatu tayi tana man gwalo tace "bake babu ƙara shiga jikin Ammi, mudai yau muna jikinta maza a tafi gida" harara na banka mata da kunƙuni naima kowa sallama ina wucewa, koda muka je gida ban kulashi ba, Hijab ɗin ya cire man yana jawoni jikinsa yace "wai Habeebty fushin me ake dani?" turo baki nayi da ƴar shagwaɓa ina doka ƙafafu nace "to ba kaine ba yau ka hanani kwana wajen Ammi ba" Murmushi yayi wanda ya ƙara masa kyawu har dimple ɗinsa na lotsawa wanda ya sani tsaye ina kallonsu hannu nasa dai wajen ina taɓawa, "ko ya burge ki ne?" murmushi nayi ina daga masa kai "kema ai ga naki nan" "ai bai kai naka ba" na faɗa da ƴar shagwaɓa dariya yayi yace "kin gaji muje muyi wanka mu kwanta" da to na amsa ina cire rigar jikina wanda tunda na cire ya kafeni da ido, zuwa nayi na cire masa nasa kayan sannan nace "muje yau ni zan maka wanka" dariya yayi yace "to kunyar tawa da kike ji ki kaita ina?" dariya nayi nace "ta gudu ai indai kunya ce yanzu ɗaukarni marar ita" dariya yayi yace "haka kika ce?" nace masa "eh mana" wanka mukayi wanda shi yai mani nima nai masa, wanda sai da ya fara laguda ni tun a can, a tsorace na shirya don ina gudun karya sake, koda muka kwanta nasa ba zai man komai ba amma haka ya zage yai abinsa,wanda na yau ma naji jiki, saida muka tsarkake jikimmu sannan muka kwanta, *Canada* Kaykkyawan matashi ne ajin farko ke harhaɗa kayansa tunda hankalinsa ya dawo yake tunanin gida da ƴan uwansa, yake kuma tunanin abinda ya kawo sa ƙasar nan shi dai ba zaice ga taƙa maiman abinda ya kawo shi nan ba saboda ba zai iya tunawa ba, dukkan wani abu nashi da yasan mai muhimmanci ne haka ya tattara ya baro ƙasar sai Nigeria, ganin duk inda ya nufa ana girmamasa saboda zamansa Young millionaire, da ƙyar ya tuna inda suke da zama, hakan yasa shi nufar Goriba road, sai dai tunda ya nufi gidan yaga sauyi da dama, zuciyarsa na masa dukan ukku_ukku yasa shi tunkarar gidan, mai gadin ya miƙawa hannu yace yana son ganin mai gidan tsammaninsa ko su Abba na nan, babu musu mai gadi ya isar da saƙo,wanda ba'a daɗe ba sai ga wani mutum ya fito, da mamaki Fauzan ke kallonsa, mai gadin ya kalla yace "kai cewa fa nayi kayi mani sallama da mai gidan" "bawan Allah to ai nine mai gidan" gaban Fauzan ne ya faɗi yace "ina fa nufin Alhaji Nuraddeen" mutumen ne ya dafasa yace "kaga ni ban wani san wani Nuraddeen Ali ba, siyen gidan nan, waɗanda kake nufi tuni suka tashi" dafe kansa yayi dake masa ciwo ya ɗaga kan yana shigewa Motarsa, wani iska mai zafin gaske ya furzar yana wa motarsa key, kai tsaye gidan su Baba Sa'adu ya wuce, sosai su kayi mamakin ganinsa, wanda da ƙyar suka ganesa, dukda hantar cikinsu ba ƙaramar kaɗuwa tayi ba ganin yadda Fauzan ɗin ya zama wani attajiri Jikunnasu a sanyaye suka tarbesa suka tabbatar da lallau Nuraddeen yai musu fintinkau da zarra, babu kamar Sharu shine jikinsa yai sanyi sosai,kamar wani abu bai taɓa faruwa ba haka Fauzan ya nunawa su Sharu, nan suke sanar masa ga dukkan abinda ya faru, hantar cikinsa ba ƙaramar kaɗuwa tayi ba jin abubuwan da suka faru bayan bashi nan, sai dai tabbatar masa da cewar suna Abuja hankalinsa ya kwanta haka washe gari yabi Flight ya tafi Abuja gidan Modibbo, sai dai tunda yazo get ɗin gidan ya tuna dukkan abinda ya faru dashi da kuma gidan daya gani, da kuma mutumen dake ciki wanda yake masa kallon Mahaifinsa, shine ya kaishi England yayi karatu akan business har Allah ya kawo shi a wannan matakin inda yake da babban Company a can ƙasar Canada, sai dai ganin gidan a ƙargame babu alamar mutane a ciki yasa shi tambaya sai dai abinda aka faɗa masa yai matuƙar kaɗashi, haka yasa aka kaishi inda Modibbo yake, wanda yanzun ya sake birkice musu da ihun da yake yana ganin Fauzan yayo kanshi da gudu jikinsa duk farfashe da ciwon daya jiwa kansa, cikin ƙaraji yace "Fauzan kada kace gurina kazo ni ba Mahaifinka bane, nine na tsafa kanwarka Raihana sanna kuma na sace Mahaifiyarka na azabtar da ita nai mata ciki muka haifi ɗiya, sannan kaima daga baya na saceka na ɓatar maka da hankali, ƙanwarka Raihana tazo ta gudu da Babanka ka bada cigiyar su a garinnan nasan tana nan ni ɗinnan mugu ne ɗan shan jini ne, idan baku yarda ba kuje gidana kuyi bincike zaku ga kawunan mutane da kayan tsafi, Ihuuu ku ceceni ku kasheni kawai kada ku barni, wallahi kisan gilla zatai manj idan ta dawo, Ihuuu jama'a ni ɗan shan jini ne, idan baku kasheni ba zan kashe kaina na cinye zuciyata" ihuu yake tuɓuru da kururuwa yana ɓarke kayan jikinsa yana cizon kansa sanna yaje ga bango ya dinga buga kansa Ƙasa tsayuwa Fauzan yayi ya sulale ƙasa yana mayar da numfashi kamar wanda yayi gudun tsere zuciyarsa da ƙarfi take halbawa, miƙewa yayi a zuciye zai nufi inda Modibbo yake ya cakumesa ji yake yau idan bai kawo ƙarshen numfashin Modibbo ba ba zaiji salama ba, da sauri Security ɗin wajen suka riƙesa, suma dukda shock daya kama su, na maganganun Modibbo kuma tabbas akwai ƙamshin gaskiya a maganarsa............. [2/17, 2:24 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *Book 2* *By Mariam sani Riamcool* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Bismillahirrahmanirrahim *P. 104&105* ____________✍️Da huci da raɗaɗin zuciya Fauzan ya fice ya shiga motarsa yana mayar da numfashi, kai tsaye yaje gidajen Radio da television ya bada cigiyar su da sunayensu, haka kuwa aka watsa a labarai da gidajen rediyo zaune muke nida Hamma na aza kaina a ciyarsa yana wasa da gashina, nikam na maida hankali da Tv ina kallo dukda,hakanan naji son kamo tashar labarai, ina kamowa Abinda na gani ne ya sani miƙewa zaune, ina ƙara kafe Photon saurayin da ido wanda dukda girma da sauyi da kuma yanayin kuɗi ya zauna a jikinsa hakan bai hanani ganesa ba, cikin ruwan murya na furta "Hamma Fauzan" na faɗa da tsantsar farinciki, shima Hamma fuskanshi ɗauke da farinciki yake hamdala da ƙara godewa Allah, daya haɗa dukkan zuri'arsu waje guda, dama abinda yake so kenan, daman Fauzan da Ammi kawai yake jira, ya kai su Mommy wajen iyayensu waɗanda ya daɗe da gano inda suke a zaune da maɗaukakin farinciki na yana mayafin Abayar bisa kaina zan nufi Part ɗin Mommy, da gudu, riƙeni Hamma yayi yana zaro ido yace "bi sannu fa karki Mani asara Maybe ko nayi ajiya a ciki" ya faɗa da ƴar dariya nima dariyar nayi ina maka masa hararan wasa nace "duka yaushe akai auren da zakai ajiyar?" dariya yayi yana kama hannuna muka nufi sashen Mommy koda muka je suma Falon ya rikice da murna, haka muka ɗunguma mu dukkammu muka nufi inda aka bada Address, koda muka je baya nan saida aka kirashi, a gaggauce yazo wanda faɗin iya kukan da farincikin da mukayi ma ɓata baki ne, shi kanshi Abba sai da ya ƙara kukan farinciki da murna ya kuma Alƙawarta ma kanshi cewar yanzu zai bama su Ammi farincikin da suka rasa a baya, Dada ita kanta sai da tazo tunda aka gano Ammi tazo ta nemi yafiya tace kuma mafarin barin Ammi gidan Aminiyarta ce tai mata kurciya, Ammi bata nuna mata komai ba ta yafe mata, haka Dada ke nan da nan da Mommy dasu Ammi komai tace Faɗima da Sajeeda,haka da kanta zata zo wajen Mommy ayi fira da jikoki ai raha, koda Fauzan da Nuraim suka haɗu ashe sun san juna sosai dan Abokan kasuwanci ne sai dai rashin sani, dukda ga kamanni nan dasu Raihana, sai da Ammi ta gyagije sosai ƙibarta da haskenta ya dawo sannan Nuraim yace su shirya zai kaisu wani waje, haka dukkammu muka shirya muka shiga motoci na Alfarma, Raheenatu ce zaune kusa da Abdurrahim, shi kam ya kafeta da yana sakar mata wani lallausan murmushi ita kam juya masa ido tayi tana ƙara masa fari da ido, "My beloved kinyi fa kyau sosai" ƙara juya masa ido tayi tace "really" "yeah" ya furta yana kashe mata ido guda ita kuma ta ɗaga masa gira tana dariya gyaran murya nayi nace "Yaushe abin nan ya faru bamu sani ba, sai dai kullum mu a gabanmu a dinga ƴan harare harare irin Alamun baku jituwa to ashe kun ɗinke" na faɗa ina dariya, shima Nuraim dariyar yake Sosa kansa yayi yana driving yace "ga tanan ki tambayeta, tun ranar ɗaurin auren ki tace man wai fuskana na kama da baƙin ɗuwawu, wai ba kyau gareni ba hakanan take kallona, to nayi niyya na kafta mata rashin mutunci, to ina zuwa zan karta mata rashin mutunci shine ta kashe man ido wanda gabana ya bada dam tai man kwarjini ke Raihana wallahi sai naji tsoronta nake ji, kawai sai nai mata yaƙen dole na fice, washe gari duk inda na ganta sai ta kashe man ido kuma ta girgiza mani ƴaƴan laushi, wallahi nifa na rasa ganewa, sai kawai na dawo nace mu ƙulla ƙawance tace mani Allah ya sawaƙe ta ƙulla ƙawance da ɗan baƙi kamata, ke dan bani da kuma zuciya da yake zuciyata ba'a ƙirji take ba nazo na dinga binta sai da ƙyar muka ƙulla ƙawance, mu ba soyayya muke ba, yanzu haka komi tace nayi zan iya idan cewa tai na faɗa rami da wannan motar da muke ciki tsab zanyi shahada na faɗa" dariya dukkammu nace "a ƙawancen ne ta zama your beloved ɗinka?" da sauri Raheenatu tace "suɓutar baki fa yayi,amma ga wadanda suka fiddo soyayyar su fili Yaya Fauzan da Hameeda" dariya nayi nace "ai dukkansu ƙwararri ne" ganin munzo wata katafariyar unguwa ta manyan masu kuɗin da ƴan siyasa, kan wani ƙerarren gida muka tsaya da motocimmu, horn akayi aka wangale mana ƙaton get ɗin muka shige, tsayawa misalta muku kyan gidan da tsaruwarsa ɓata baki ne don saina cika Page guda ban faɗa muku ba, Dada farkon fitowa tana ƙarewa gidan kallo ta kalli Nuraim tace "kai Nura ko dai ɓatan kai kayi? me ya kaika kawo mu nan gidan wanda kana kallon mala'ikun Jahannamar duniya sunyi mana ƙur da idanu, ga gida tako ina gilashi" dariya dukkammu mu kayi Nuraim yace "Calm down Dada biyoni kuga" harara Dada ta zabza mashi kamar idonta zasu faɗo tace "Nura idan ma zagina kayi nasan matsayin da zan ajiye ka yo idan banda lalata ka wani cemin kom dawon, a'a dawo ba dowon ba" ta faɗa tana gyara ɗaurin zaninta, banza Nuraim yayi da ita yai gaba muma muka bishi a baya da sallama ɗauke a bakunanmu muka shiga haɗaɗɗen Falon wanda ƙamshi da sanyi Ac ne ke tashi tako ina, zama mukai sannan Nuraim ya hau sama yace bari yazo, ba'a daɗe ba kuwa sai gashi da wani dattijo wanda fara'a da annurin fuskarsa yaƙi ɗaukewa kallo ɗaya zaka mashi kasan cewa kwarjini da haiba da kamala na tattare dashi, dukda farin gilashin dake manne a idonsa, hakan bai hana mu ganin ƙwalla dake cike tab a idonsa ba Mommy da Ammi kuwa tunda yake sakkowa daga Step ɗin benen suka kafe Mahaifin nasu da ido wanda ƙwalla suma ta cika musu,ido miƙewa dukkansu sukayi suna nufar Mahaifin nasu wanda shima tunda suka nufo shi, su yake kallo, da hanzarinsa ya ida sakkowa suka faɗa jikinsa suna fashe masa da matsanancin kuka, wanda Dattijuwar dake bayansu itama batai ƙasa a guiwa ba ta haɗesu su dukkansu, ta rungume tana kuka, rasa mai rarrashin su akai saida suka fidda tsohon mikin dake zukatansu sannan Abbi ya rarrashesu da ƙyar aka zauna ana sake gaisawa, nan Nuraim ya gabatarwa Abbi kowa da kowa wanda sai da yayi hawayen farinciki ganin zuri'a guda duk tashi ce "Alhmdllh ban san da wane baki zan godewa Mahalliccina ba akan ni'imar da yai man wanda a da ban ganota sai a yanzu, wanda ada nayiwa Ubangiji shishigi ya gwada mani iyakata, wanda dukkan abinda ya faru inada hannu dumu dumu a ciki, sai dai shi kuskure babu wanda baya aikata sa, to muna roƙon Allah ya yafe mana, Fatima na yafe muku ku dukkanku Allah yayi Albarka" ya faɗa da yalwataccen murmushi akan fuskarshi duk girman su Mommy bai hana su kwanciya jikin Mahaifiyarsu ba, ita kuwa Alexandera wacce ta koma A'ishatu a yanzu sai shafa kansu take tana sa musu Albarka [2/17, 2:24 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA* *Book 2* *By Mariam sani Riamcool* *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* Bismillahirrahmanirrahim Last page *P.106&107* ____________✍️ Sosai akayi fira da raha akai wasa da dariya,kowa ka ganin fuskarsa cike take da annashuwa da Annuri,haka ranar Abbi yace dukkammu dasu Mommy zamu kwana Dada kuwa mamaki ne ya kasheta ganin gidan su Mommy da kuma ganin yadda suke da maƙuddan kuɗaɗe,amma ta baro gaban iyayenta ta biyo ɗanta, kuma ta shuka mata rashin mutunci ta bata wahala, sosai jikinta ya ƙara yin sanyi ta kuma ƙara neman yafiyar su Mommy haka shima Dady ɓangarensa jikinsa yai sanyi sosai, yayi nadamar abinda ya aikata mata, yanzu kuwa zai ririta matarsa tamkar tsoka ɗaya a miya, ranar haka muka kwana,sosai na tashi da kewar mijina, washe gari sai wajen Ishsha'i sannan muka bar gidansu Mommy, wanda Abbi yace a ƙara barin su Raheenatu dasu Sadeeq, haka muka barsu muka dawo gida dukda a gajiye muka dawo hakan bai hana mu murzar juna ba, sai da muka tsarkake jikunnammu sannan muka kwanta, Kamar yadda ya saba hauka tuɓuru da kukan jinjirai marassa daɗi haka yake ji duk yayi baƙi ya lalace shi kaɗai yasan kalar azabar da yake sha, wacce da ita da mutuwa basu da maraba, jin wani Mugun iska ya ɗaga shi sama ana kecewa da wata kalar sheɗaniyar dariya wacce ta ƙara rikirtar dashi,ihu da kururuwa yake na neman ceto amma ina babu wanda ke jinsa, haka wannan iska ya dinga gudu dashi yana ihu, har ya kaishi dokar dajin da baka jin sautin komai sai wasu kalar dariyoyi dake tashi da kuma wasu kalar kuka marassa dadin sauraro, wata muguwar tsawa aka buga da walƙiya wacce, tasa wasu yara suka bayyana, suna dariya suna nufosa, nan take ya gane yaran da yakewa fyaɗe ne kuma ya kashe su ta hanyar tsafi, da wata kalar murya ƴar yarinyar tace "jamu ɗau fancarmu jamu kaceka kamar yadda ka kacemu jamu lalata maka da caccan jiki kamar yadda ka lalata mana kafin ka kacemu" ta faɗa tana fashewa da wani kalar kuka mai firgita mai sauraro wata kalar dariya Uwargijiya ta sheƙe da ita tana faɗin "Modibbo na fasa kasheka da hannuna waɗannan sun isheka,iyakata na tsaya nai kallo idan sun gama dakai mu tafi tare" kuka ya fashe dashi yana roƙonsu akan su ƙyalesa amma ina haka yaran nan suka fara azabtar dashi ta hanyar cire masa Jarumarsa, wacce yai lalata dasu, wani ihu da kururuwa ya ƙara saki, sannan zaƙoƙon farcen hannunsu suka cakawa idonsa nan take jini ya malalo saida suka ƙwalƙwale masa ido sannan suka ɓara cikinsa suna ciccire kayan cikinsa haka suka masa yaga_yaga kai daban ƙafa daban duk sunyiwa kayan cikinsa daban_daban, sai da sukai masa kisan wulaƙanci, naman jikinsa duk sun mashi gutsin_gutsin, haka suka ɗaukesa suka nufi inda suka ɗaukosa suka ajiye,suna sowa da murna suka ɓace harda Saddiƙa Uwargijiya A firgice na miƙe ina sharce zufar data wanke man fuska, hamdala da godiyar Allah nayi daya gwadawa Modibbo ƙarshensa ya kuma kawo ƙarshen zaluncisa, a hankali na sauko daga kan gadon Arwalla na ɗauro na dinga salla ina ƙara godewa Allah, saida nayi sallar Asubah sannan na koma wani kalar bacci mai daɗin gaske na ɗaukata, sai wajen 12 na tashi na gyara gidana tsaf ko ina na ƙamshi lungu da saƙo, sannan nai girki, wanka na shiga nayo nazo na shirya cikin wata haɗaɗɗiyar shadda pink color wacce tasha aiki, sosai naci kwalliya sai kace wacce zata gidan biki, sai uban ƙamshi nake zubawa, kallo na kunna, naje tashar labarai, ganin ana hasko gawar Modibbo wacce akaiwa gutsin_gutsin, wacce ana bada labarin abinda aka gani a gidansa, waɗanda mutane da dama sunyi ala wadai da halinsa, da ƙyar aka samu wasu suka haƙa rami a gidan nasa aka birnesa, jikina ne yai sanyi laƙwas, tsoron duniya dana mahaliccina na ƙara shigata, Hamma ne ya shigo,wanda tunda ya shigo yake tazbihi ga Allah daya mallaka masa wannan haɗaɗɗiyar kyauta, wani sassanyan murmushi yake aiko man dashi wanda nima ban kasa a gwiwa ba na aika masa da nawa ina tashi na rungumesa ina dariya, shima haka ɗaukana yayi cak yana juyi dani, sannan ya ajiye ni, bedroom muka shige na temaka masa ya cire kayan sannan nace masa muje na temaka masa yai wanka, "No kada ki ɓata kwalliyarki ban moreta ba barshi da kaina zanyi, sannan nazo na bada tukuici" ya faɗa yana kashe man ido guda dariya na saki ina kai masa dukan wasa a chest ɗinsa shigewa yayi toilet ni kuma na miƙe na zaɓo masa wasu haɗaɗdin ƙananan kaya waɗanda nasan zasu matuƙar amsar jikinsa,ina nan zaune ya fito, ni da kaina na shafa masa lotion da kaya na saka masa, turare ya ɗauka yana fesa jikinsa dashi, wanda naji tukar amai Toilet na faɗa da gudu ina sheƙashi kamar zan juye hanjin cikina, a rikice ya shugo yana man sannu, da kanshi ya wanke man baki ina daɗe hanci sannan ya gyara, wajen bedroom ɗin na fita saboda jin ƙamshin turaren, Falo na fita na faɗa bisa 3 seater ina kwanciya, jin fitowarsa yasa na marerece fuska nace "Baby dan Allah kaje ka cire kayan ka wanke jikinka turaren nan ya fita, wallahi shi ya sani Amai" na faɗa kamar nayi kuka da matsanancin farinciki yace man "da gaske" "eh mana" na faɗa kamar zanyi kuka, juyawa yayi saida ya sake wani wanka kamar zai canja fatar jikinsa sannan wasu kayan ya janza ya fito fuskarshi ɗauke da Annuri, da sauri ya nufo wajena yana shafa cikina yace "ashe dai da gaske nayi ajiyar" kallonshi nayi da mamaki nace "ban fahimta ba" "ba zaki fahimta ba tashi muje Hospital" ya faɗa yana miƙar dani "wallahi Baby nifa lafiyana ƙalau" na faɗa ina raurau da idanu, bai bi ta kaina ba haka ya ɗauko man mayafi na yafa muka tafi, koda muka je Doctor yai mana ƴan gwaje_gwaje ya tabbatar da ina ɗauke da juna biyu na tsawon sati ukku wanda nan take Nuraim saboda tsabar daɗi ya ɗaukeni yana juyi dani har hawayen farinciki saida yayi sannan yaiwa Doctor ɗin gwaggwaɓar kyauta, nima kaina nayi farinciki sosai haka muka taho, wajajen shaƙatawa ya kaini wanda mun daɗe muna yawo sannan muka dawo, Part ɗin Mommy muka sauka wanda Nuraim ya sanar dasu ba ƙaramin farinciki sukai ba wanda kamar su zuba ruwa ƙasa susha dan murna, nikam kunya duk ta isheni saida muka jima sannan muka nufi namu Part ɗin wanda muna komawa shi da kanshi yai mani wanka ya shiryani tsaf, ko Abincin kirki bai iya ci ba saboda tsabar murna hannuna ya ɗauka yana damƙa mani yace in buɗe,ina buɗewa naga wata haɗaɗɗiyar Iphone 15, tsalle na doka ina faɗawa jikinsa da murna, zaro ido yayi yace "bi sannu fa kada ki mani asara" dariya nayi na shiga kwarara masa godiya har saida ya haɗe bakimmu waje guda sannan nai tsit, cikin wani irin salo yau nake tsosar lips ɗinsa na ƙasa, shima cikin salo da ƙwarewa ya dinga aika man da hot kiss, da ƙyar na zille ina saka wayar a chage sannan na dawo muka dasa daga inda aka tsaya,sosai na zage na faranta wa Mijina wanda nasha saka Albarka, haka muka dinga gudanar da rayuwarmu cikin farinciki da wanda su Raheenatu tuni sunyi nisa a soyayya ita da Abdurrahim Hameeda kuma da Yaya Fauzan, ganin ko wane a shirye yasa aka saka rana bada jimawa ba, Ammi ma tuni an mayar da aurensu da Abba wanda Yaya Fauzan ya gina musu katafaren gida anan Abuja ya zuba musu ma'aikata da dalla_dallan Motoci sannan ya bawa Abba wani baban Company sa, Nuraim ma wani Company nashi ya damƙawa Abba a matsayin kyauta wanda Abba arziƙinsa yanzu ya linku, babain sabuwar soyayya suka gina da Ammi haka Abba ya zage yake bata kulawa, ga duk Sati ake zuwa gidan iyayen su Mommy wanda ba abinda zamu ce a yanzu sai dai godiyar Allah dan family ɗimmu yanzu cike yake Farinciki, wanda kamar ba'a taɓa fuskantar wani ƙalubalen rayuwa ba, dukkan rayuwarmu data rushe yanzu ta ginu ciki ƙarko da aminci Su Baba Sharu da Baba Sa'adu sun tabbatar da cewa tabbas Kainuwa dashen Allah ce, dukkan abinda Allah ya nufi bawa dashi to tabbas saiya sameshi baƙin ciki ko Hassada bai isa ya hana mutum ci gaba ba, sun nemi yafiyar Abba kuma nan take ya yafe musu, wanda Mama ƴan London suma sunzo sun nemi yafiya kuma nan take ya danƙara mata saki ɗaya,kuma yace mata yasan da cewar su Suhailat ba ƴaƴansa bane ƴaƴan Sharu ne, wanda tuni yasan da hakan sai dai asirin da Mama tai masa ne ya hanasa fitowa fili ya faɗa, su Suhailat sunyi baƙinciki da takaici, wanda sunyi kuka marar adadi gashi waɗanda suke wulaƙantawa a gidan ashe sune masu gata da ƴanci, gashi yau ƴaƴan Sajeeda sun zamo waɗansu abu, jiki a sanyaye suka juya suka koma Katsina, da ƙyar Suhailat ta samu wani ɗan lebura ya aureta, ita kuma Zulfa'u wani mai mata ukku babban mutum sa'an Abba ya aureta wanda suke ganin wulaƙanci iri_iri, baƙin ciki da ciwon hawan jini shine ya kama Mama daga ƙarshe dai shine ajalinta wanda su Suhailat suka shiga ƙuncin rayuwa, sadda rayuwar su Raihana ta ginu su kuma a lokacin ne tasu rayuwar ta rushe Aunty Amarya dama ita ƴar ƙungiyar Jogu ce tuni tabi sahun ƴan ƙungiyar don itama kisan gilla aka mata, Abba ya amso Islam ɗiyar Aunty Amarya, wadda Ammi bata wani ji ƙyashi ba ta amsa ta tausaya mata ta riƙeta tamkar ƴar cikinta, Amal kuma kamar yadda Uwani tai Alƙawarin zata amsheta haka kuwa a kai ita ta gano Amal inda Modibbo ya kaita ta amsota, ranar da Ammi ta ganta saida ta ƙara zubar da hawaye don ba don tana so za'a tafi da Amal sai don kawai zata fi samun sauki acan ni kaina Amal ta shiga raina don dana ganta saida na zubar da hawaye kowa ya tausaya mata, haka Uwani ta ɗauketa ta tafi da ita tare da Alƙawarin zata dinga kawota tana ɗan ganin Mahaifiyarta *Ɓangare guda kuwa* Sabreen saida taji jiki sannan su Bobbos suka ƙyaleta saida tayi jinya Hospital sannan ta samu sauƙi haka ta dawo gaban Hajiya Bilkisu wacce itama yanzu ta tuba da halayenta, Bobbos ya ɗanji tausayinsu ya maido musu da wasu ƙadarorin da ƴan kuɗadensu waɗanda zasu ishesu rayuwa, taimakar kanta Hajiya Bilkisu tayi ta samu sana'a tayi sannan kullum cikin istigfari da neman yafiyar Ubangiji suke dukkansu, Sabreen ma ciki waɗansu maza masu neman aurenta tuni ta samu ta aura wani mai mata guda ita ce ta biyu, haka ta raɓa ta auresa wanda ba wani daɗin auren dai take ji ba,don waccan matar ita ke juyasa, Sabreen kuwa ta zama ƴar kallo haka take lallaɓawa don ko dukanta yake yana kwallon da ita tayi alƙawarin zata zauna Nafisa kuwa duniyar tai mata dukkan wani abu nata ta rasashi tsafinma ta rasashi, don ta sanadiyyarsa tsafin ta rasa ido guda ga ta dawo mai shanyayyen hannu haka yasa ta dawo Nigeria gida da zama, wanda ba don tana so ba, don bata so taga Nuraim ko kaɗan saboda ciwon sonsa dake nuƙurƙusarta, Aunty mahaifiyar Nafisa koda taga yadda Nafisa ta koma wata halitta daban ta ƙara tsorata da lamarin tsafi, tuni ta jinginar da nata ta tuba ga Allah, Nafisa kuwa kowa ya ganta sai yayi mamakin yadda ta koma Bikin su Raheenatu nata matsowa ana shirye_shirye nikuwa cikina ya fara girma a lokacin dan ya wani fito tartsetse dashi,7 Month ne dashi amma idan ka ganshi sai kace ya wuce haihuwa don yadda yai ƙato dashi gashi cikin farko ne hakan yasa kowa ke mamaki kwanci tashi aka ce asaran mai rai, yau bikin su Raheenatu saura 3 days wanda yaune akai kamu wanda amaren sunyi Azababben kyau anci ansha aka tashi wanda ni duk wannan kamun da aki banje ba saboda Nuraim daya hanani zuwa naci kuka kamar mi tun Ammi na rarrashina harta kai ga man faɗa washe gari da ƙyar ya barni zanje Diner da za'ayi tunda safe mai lalle tazo ta tsara mana shi da amare, haka da aka zo aka mana haɗaɗden make up wanda aka tsara mana, ankon wani dakakkanen leshi wanda aka fiddo muka sa wanda akai Mani ɗinkin doguwar riga wacce taji aiki, babu karya anyi, kyau haka Nuraim shima Shadda brown yasa wacce ta amshi fatar jikinsa sosai, haka ya kamo hannuna yana yaba irin kyawun da muka sha, nima ina yaba nasa dukkammu fuskarmu ɗauke da farinciki da murmushi, hannunsa ya ɗora kan cikina yace " ba don Mommy tayi magana ba fa da ba zaki je ba, hakanan a wahalar man da baby, nace ki zauna nai maki tausa amma kin kafe sai kinje" turo baki nayi ina doka ƙafafu da shagwaɓa nace "wai kai Baby wannan ɗan shi zai hanani rawar gaban hantsi aiko shi ba zai so ayi zaune waje guda ba ballantana bikin uwaywnshi sunkutukum" dariya yayi yana jan kumatuna sannan ya duƙa ya sumbaci cikina hannuna ya jawo da kanshi ya buɗe man mota na shiga shima Security ya buɗe masa muka shiga Driver naja wani ihuu Nafisa ta saki da gunjin kuka dan dukkan abinda su Raihana da Nuraim keyi a gabanta ne kuka taci ta godewa Allah sannan ta tashi da ƙudirin koma miye zai faru gobe sai taje gun wani shahararren Boka ya raba Nuraim da Raihana da wannan ƙudirin ta koma Mukau koda muka je anci ansha anyi ɓarin nera haka su Mai kayan Harka da Hajjo sunzo suma sunyi bajinta a gurin Bikin dan suma tuni sun tuba sunyi aurensu, ko wane manyan masu kuɗi suke aure suna watayawa son ransu, wannan iskancin nasu tuni sun barshi sun nutsu haka washe gari akayi Mother's day wanda su Mommy suka shirya shima anci an sha anyi bajinta da ɓarin nera wanda bikin ba ƙaramin ƙayatar da mutane yayi ba Washe gari haka aka ɗaura auren Raheenatu da angonta Abdurrahim Hameeda kuma da angonta Fauzan ko wane katafaren gidajensu aka miƙa su wanda tsayawa faɗa muku tsaruwarsa ɓata baki ne, cikin hukuncin Allah da ikonsa aka kammala biki lafiya, wanda sati guda da gamawa Amaren da angwayen suka tafi Honeymoon America Bayan an kare Biki Nafisa ta shirya zuwa wajen Boka, wanda a hanyar zuwa wajen Bokan motarsu tai haɗari wanda ƙafarta ta fita daban ƙarfe ya ida cakar mata idon guda wanda kafin aje Asibiti rai yayi halinsa, kowa na nan ba ƙaramin tashin hankali aka shiga ba wanda ni kaina naji mutuwar, Nuraim kuwa ko a jikinsa iyaka ya yafe mata sannan yai mata addu'a haka aka ƙarashe zaman makoki muka dawo Rayuwar mu cikin farinciki cikin so da kauna da tattalin juna muka dinga kula da junammu muna bawa cikin jikina kulawa harya isa haihuwa wajen Mommy na koma da zama wanda Nuraim bai jin kunya haka zai ƙetare kowa yazo gurina ya kashe arna nima kuwa na bashi goyon baya, Ranar wata Laraba da sassafe naƙuda ta kamani wanda hankali tashe muka nufi Private Hospital ban wani daɗe ba na haifo ƴaƴa biyu kyawawa masu kama da Mahaifinsu sak mace dana Miji gyaramu akai tsaf nida yarana wanda tunda na kallesu naji sonsu da ƙaunarsu irin na Mahaifiya na ratsani, nan take asibitin ta cika da ihun murna da ƴan uwa, haka Nuraim kanshi ruɗewa yayi haka duk mutanen dake ciki bai hanashi tsallake su ba ya manna man sunba a goshi yana saka mani albarka haka yaran ya amshesu yana zuba musu addu'a haka muka baro asibitin su Raheenatu ma an sanar dasu wanda cikin Satin suka ce zasu taho,kulawa nake samu sosai tako ina haka nake samu, Su Raheenatu kuwa a cikin satin suka diro Nigeria suma ko waccensu da ɗan matashin cikinsu,murna sosai suke wanda yaran kullum suna wajensu iyakata basu Nono kawai haka akayi suna na bajinta inda yara sukaci suna Ahmad da A'isha wacce muka ɓoye sunan saboda sunan Grandma dake gareta muna ce mata Samha haka ranar sunan da kanshi Nuraim ya damƙa man makullin dalleliyar Mota wacce a ƙalla takai 10M sannan ya damƙa man makullan danƙareran gida, gidan Mommy na zauna naci gaba da wanka wanda ina gamawa muka koma danƙareran gidammu da Nuraim ya ƙera mana kai kace a ƙasar waje aka ƙerasa saboda haɗuwa da tsaruwarsa, har kukan farinciki saida nayi ganin yadda rayuwa ta sauya man, ranar da muka dawo mun murji juna na gwada masa irin kewarsa da nayi haka muka reni yarammu cikin so da ƙauna da tattali ga arziƙin su Nuraim dake ta bunƙasa yanzu, bayan watanni suma su Raheenatu sun haifi ɗiyansu inda Raheenatu ta haifi ƴa mace Hameeda kuma namiji, wanda anyi shagali ba kaɗan ba saida su Samha sukai 5 year sannan na sake samun wani cikin wanda yazo man da laulayi sosai haka Nuraim ke nan da nan dani wanda su Samha da Ahmad sai dai ya kaisu wajen Ammi wacce duk lokacin data gansu take ƙara godewa Allah da ni'imar da yayi mata kamar bata wani taɓa shan wahalar rayuwa ba saida cikina ya sake wata goma cif sannan na sake haihuwar ɗa Namiji wanda shima kamanni ubansa ne sak wannan karimma anyi shagali iya shagali inda yaron yaci sunan Abba wato Nuraddeen muna kiransa da Abilkhairi haka rayuwa taci gaba da tafiya wanda kallo guda zakai man kasan kuɗin da jin daɗi da kwanciyar hankali sun zauna man a jiki driving nake cikin jin daɗi wanda nida Hamma ne na amshi Driving ɗin don bana son Driver ya tuƙamu yau, Abilkhairi ne riƙe a hannunsa ya kafe Raihana da idanu wacce take jin waƙar Zinoleesky a hankali tana ɗan rausayawa dariya yayi yace "Habibte bi a hankali damu kada ki ɓarar damu nan" dariya kawai nayi ina ci gaba da Driving ɗin har muka isa wani ƙaton shopping mall wanda na ɗan tsitstsinci abinda nake buƙata sannan muka nufi wani waje na shaƙatawa wanda wajen baro wajen ne naji an kira sunana wanda cak na tsaya ina juyowa ganin Alhaji Muttak'a wanda na ƙarasa wajensa muka gaisa a mutunce sannan ya tambayeni nayi aure na faɗa masa harma da yara nan na gabatar masa da Nuraim wanda yake ta haɗe fuska, murna sosai Alhaji Muttak'a ya tayani wanda yayi mamakin mashahurin mai kuɗin data aura wato Nuraim, sannan daga gani daɗi da kwanciyar hankali ya zauna mata Koda muka koma gida da ƙyar na lallaaho Nuraim ya saki fuskanshi daga nan kuma muka faɗa farantawa junammu rai, a hankali rayuwa taci gaba da tafiya cikin jin daɗi da kwanciyar hankali wanda ba abinda zance da Allah sai godiya tabbas na yarda da cewa mahaƙurci mawadaci na yadda da zalunci baya nasara akan gaskiya haka kuma mai haƙuri yana tare da Allah,danni sai dai nace Alhamdulillahi komai nawa ya warware Rayuwata data Rushe ta ginu, babu abinda zance da Mijina sai godiya dan shine matakin dukkan wata Nasara tawa, ni kam sai dai nace Alhamdulillahi Alhamdulillahi nima dai nace to duka_duka anan na kawo ƙarshen littatafin Rushewar Rayuwa Abinda ke ciki Allah ya bamu ikon Amfani dashi, insha Allah sai mun haɗe ahy sabon zazzafan littafina *BAYAN WUYA* hmm akwai cakwakwiya iya cakwakiya a ciki fatan zaku biyoni kamar yadda kuka biyon a RUSHEWAR RAYUWA, ina godiya mai tarin yawa ga wadanda suka biyoni a wannan littafin much love oll ku sani ba zan taɓa mancewa daku ba ina godiya