[05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: _🌹RUMAISA SALMAN_🌹 👨🏻‍🚒 ```MATAR``` ~```SOJA```~ 👨🏻‍🚒 (_Labarine da ya kunshi soyayya,tausayi, fadakarwa,Ilmantarwa da kuma Nishadantarwa_) Story and written By Maman khausar✍🏻 ( *INTELLIGENT WRITErs ASSOCIATION* *[onward together]* *{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}* ```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑``` *```JUST GIVE US FOLLOW..** [ ```~BISMILLAHIRRAHMANI RAHEEM!~``` ➡page 1 🌹 _TSOKACI_ 🌹 ********Kasancewar jiya ban yi bacci ba gabadaya.ina idar da sallar Asuba ban San sanda bacci barawo ya saceni ba daga zaune nake bacci sosai. Buga kaina da nayi a jiki drawer shi ya tashen na dafe kaina da yake mun ciwo dama ga damuwa ga rashin bacci . Kama kan nayi da karfi ina karanto addua..... Bansaki kan ba naji kamar horn din motarshi. Ban San sanda na saki kan na mike da sauri na tafi window kasancewar window din bedroom dina tana facing harabar gidan. Ina daga labule Rass! Zuciyata ta tsinke. Naji wani irin bacin rai da bakin ciki kamar na hadiye zuciyata. Da sauri na fita daga dakin na nufi harabar gida ko ganin gabana banayi tsabar bacin rai. Can na hangoshi ya fito gabadaya sojojin gidan sun zo suna kwasan gaisuwa. Da sauri na nufi can wurinshi a lokacin da ya juyo shi kuma ya bude gaban motan . Bansan sanda na tsaya na saki baki ina musu kallon mamaki. Itama ni take kallo daga fitowarta fuskarta daukeda tsoro da fargaba . Ganin yadda muke kallon kallo yasa shi riko hannunta a hankali suka nufo inda nake ka min su karaso tuni na daga musu hannu. Na kalleshi cikin tsantsar mamaki nace" me zan gani?Nafisa a gidana?me ya faru? Fuskarsa ba yabo ba fallasa yace "lfy ta dawone. Na zaro ido hade da fadin what! Wlh bazai yiwu ba wnn karon bazan dauki iskanci da rainin hankali da aka mini a baya ba bari kaji ni bazan zauna da Nafisa a gidan nan ba. Na nunata da yatsa nace " wata daya da suka wuce aka kawota gidan nan a matsayin amaryarka ta yanki jiki ta fadi ta suma 'yan uwanka suka sakoni a gaba da zagi ciki harda mahaifiyata sukace mu mukayi tsafi don mu wargaza aurenka da Nafisa. Hawayene masu zafi suka gangaro bisa kumatuna na ce"jiya jiyan nan aka kai maka ita a gidan ka na Abuja mukayi sallama da kai sannan ka daukota kuyi sammako kuzo min gida kace ta dawo? Ko kallo ban ishe shi ba ya kalleta yace ke shiga ciki ina zuwa. Ta wuce jikinta a sanyaye na bita da kallo har ta shige. Sannan na dawo da kallona gareshi.nace" shikenan tunda haka ka zaba ni zan bar maka gidan ka yanzu ba sai anjima ba kaje ka zauna da matarda mahaifiyarka da 'yanuwanka suka zaba maka. Wucewa yayi ba tare da yace min komi ba. Kamar zan fashe don bakin ciki nayi ciki a zuciye Na dauki jakata da wayata da key din motata . Juyawan da zan yi sai ganin mutum nayi tsaye ya zuban ido fuska daure. Ban kulashi ba Na saka takalmina Na karaso bakin kofan ba tare da na kalleshi ba nace ban gu in wuce. "Ina zakije? Ya fada can kasan makoshinsa. Shiru na masa . Juyawa yayi zai fita yace min Salim yazo da Farida suna palona . Daga nan ya fice Zuciyata ce ta buga nace Farida da sassafen nan me ta ballo kuma? 🤦🏻‍♀wayyo Allah da wanne zanji ni RUMAISA? Na ajiye jakata na tafi side dinshi a Palo na samesu suna zaune shiru Farida na zaune a kasa kanta a kasa. Na karaso na zauna jikina a mace na kalli Salim nace "ya Salim ina kwana? Cike da kulawa ya amsa min lfy RUMAISA. Shiru ya biyo baya daga bisani ya Salim ya gyara zamansa yace" to kun ganta nan duk yadda naso ta zama mutum abin ya faskara RUMAISA ke kam kinsan komi gameda halin ta dama Salman Kaine muke boyewa saboda gudun zuciyarka amma yau an wayi gari fareeda da kanta tace min in dawo da ita gaban iyayenta ina muzguna mata dan bani na haifeta ba. Zaro ido nayi na kalli Farida nace "fareeda dama rashin hankalin naki har ya kai haka wai shin yaya suwa suke hure mata kunne ne haka? Salim yaci gaba da fadin hmm har yanzu bata rabu da Farouq ba rumaisa maganar da nake miki jiya har karfe dayan dare na ganota a wurin club suna tare bayan duk tsaro da na sa akanta sai da tasan yadda tayi tayiwa momynsu wayo ta fice jiya gaba daya bamu yi bacci ba Dan bakin ciki na tambayi fareeda me takeso a rayuwa in mata don ta rabu da Farouq shine tace in dawo.......... Sai lokacin yayi magana ta hanyar katse ya Salim" waye Farouq din? Ya tambaya yayinda ya dauki Kofin ruwa dake gabansa yana sha. Salim ya danyi shiru sannan yace hmm Farouq dane ga Alhaji Ahmad umar ministern Ab..... Tuni ya kware ya kama tari. Nikam na kara zaro ido a tsorace don ban taba sanin Farouq Dan Ahmad Umar ba ne sai yau . Kamar da wasa tarin sai tsananta yakeyi ya Salim ya mike da sauri ya isa wurinshi "Sannu don Allah karka daga hankalinka kan wnn maganar. Hannu ya daga masa sannan yace ba komi. A hankali fareeda tace sannu daddy. Ya dago jajayen idanunsa ya kalleta sannan yace " zo nan. Ta mike ba tare da fargaba ko dar ba don tasan yana matukar ji da ita baya muzguna mata duk zafin sa. Ta karaso ta zauna kusa da kafarsa. Ya fara magana"fareeda haka kika zama? Me yake damunki don Allah ki fada min koma me kk so zan miki amma bana son wnn banzar dabiar taki. A shagwabe ta fara magana tace daddy ni bana son inje makaranta ni zan yi aure ne.... Nikam na bushe a zaune Dan tsabar mamaki. Yace" waye ne kk so? Tace Daddy Farouq........ Ya mike tsaye idon nan ya kara yin jazir yace fareeda ni bazan yarda Dan wajen Ahmad ya aureki ba koda kuwa babu maganar aure tsakaninki da munir bare kuma kin gama amuncewa munir kk so har munyi akan in ya dawo daga kasar waje zayi bikinku.don haka bazanyi magana biyu ba don ni ba mutumin banza bane.Farida ko kiso ko ki ki munir shine mijinki...Sannan kinga wnn? Ya nuna ya Samir yace"Dan uwana banda kamarsa idan kin kyautata masa kamar ni kikayiwa idan kin masa biyaiya kamar ni kikayiwa haka nan idan kika masa rashin biyaiya kamar ni kk yiwa naji kince don ba shi ya haifeki ba to bari kiji duk duniya bakida Ubanda ya wuce Salim.ina so ki Sani akan Salim zan iya rabuwa dake.don haka se kije ki nemi wani uban bani ba tunda kince Salim ba mahaifinki bane. Tunda ya fara maganar kuka takeyi . Ta durkusa gabanshi tana daddy don Allah kayi hakuri ka yafe min na tuba..... A fusace ya bugeta da kafa ya fice ciki. Ta na kuka ta mike ta iso gabana ta durkusa tace mama don Allah kuyi hakuri wlh ...... Tsaki nayi nace don Allah tashi gabana Mara hankali me zakice min? Tana kuka ta juya gun ya Salim tace daddy don Allah kayi hakuri ka yafe min. Dagota yayi yace na yafe miki fareeda Allah ya shiryeki. Sannan ya mike yace ni na tafi. Nima na Mike nabi bayansa A bakin kofa mukayi kicibis da Nafisa bats ce mn komai ta wuce ciki na bita da kallo sai naga ta wuce direct dakinsa. Wani irin kishi naji to waye nuna mata turaka bayan dazu tazo? Tabe baki nayi. Bayan ya Salim ya tafi na dawo dakina na rasa me yake min dadi a rayuwata dole ne kawai inje in sameshi domin mu tattauna maganar fareeda. Na tashi na fita a babban Palo na tarar da khalilullah yana kallo. Yana ganina yayi murmushi yace mama ina kwana? Nace lfy Babana ina ka shiga tun da safe ban ganka ba? Yace na tafi gidansu Innah ne a can nayi breakfast ma. Na gyada kai nace yayi kyau babana.jeka duba min daddyn ka yana Palonsa ne? Yace to Sannan ya mike ya tafi ba,a jima ba ya shigo yace mama yana nan. Nace "Nafisa fa? Yace aunty Nafisa dazu ta wuce kitchen. Nace to ina fareeda? Yace na ganta ta fita dana tambayeta tace zata kai karar daddy gun innah.mama me ya sami sister ne? Na danyi shiru sannan nace maganace mai tsawo kar ka damu ina zuwa. Na wuce palonsa a zaune na sameshi yana waya da abokan kasuwancinsa na sami guri na zauna har ya gama. Ya zuban ido sannan yace lfy? Na girgiza kai nace ba lfy ba nazo ne mu tattauna yadda zamu bullo ma lamarin fareeda kamin yafi karfinmu. Yace hakane ina jinki. Na gyara zama nace " ni a ganina gara a bar ta tayi auran ta auri Farouq din tunda akansa ne take wannn...... Ya katseni da fadin lallai bakida hankali kina tunanin cewa ni SALMAN zan dauki 'yata ta cikina in bawa Dan Ahmad aurenta! Ni na yanke hukunci koda zatayi aure yanzu to munir ne zata aura bare ma kuma makaranta zata tafi.har sai munir ya dawo. Nace "yaran nan fa na zamanin yanzu daban suke da na da tunda kaji ta bude baki bayaji kunya ba tace ma aure takeso to ka barta kawai karkace zaka tursasa mata domin watarana zata bijire. Kallona yake rai bace sannan yace" zata bijire min in dai mugun halinki ta dauka da banzar dabiarki........ Raina bace na Mike nace OK haka kace to bari kaji ni yata aure zatayi kuma Wanda takeso zata aura Farouq din tunda aure bai haramta tsakaninsu ba ni a matsayina na uwa na gama yanke nawa hukuncuin. Har zan tafi yace tsaya! Ya mike ya karaso gabana ya zuba min manyan idanunsa da sukayi jazir Dan bala'i yace " sai yanzu na fahimce ki rumaisa wato saboda Ahmad tsohon saurayinki ne shine kk son dansa ya auri 'yarki ko? Kai tsaye nace eh hakane sai me?kasancewar Mahaifiyar Farouq din Salima tsohuwar budurwarkane don haka me a ciki? Na juya zan tafi ya fincikoni da iya kacin karfinsa wani irin kykkyawan riko ya min. Sai faman kwatar kaina nakeyi na kasa. Murmushin mugunta yayi yace "yanzun kin fahimci banbanci dake tsakanina dake? Ya sassauta min rikon yace ni ne nakeda ikon aurad da fareeda ga duk Wanda naso bake ba don na fiki karfi a wajanta.ke kanki a karkashin ikona kk don haka bakida ikon zartar da komi a gidan nan. Hawayene ya ya ciko idona fal har ya fara saukowa don takaici. Yana kallona yace kina da wani abu da zakice kuma? Na girgiza mishi kai. Ya sakeni hade da fadin good girl haka nake so. Fita nayi na tafi daki kuka na kama yi kamar raina zai fita Karar wayata ce na jiyo a kan bedside drawer ban kula ba har ya tsinke. A Jere aka kira sau uku ana hudun na lalubo wayar ban lura da kowaye ba nayi answering. Muryana a sarke nace Salamu alaikum. Muryar Inna na jiyo tana " to uwar makirai annamimiya ba sallamarki na ke bukata ba ki fada min me yasa kk ce Salman ya dawo da Nafisa kano alhalin jiya jiya aka kai ta Abuja ? Cikin muryar kuka nace inna banine nace ya dawo da ita ba nima jiya mukayi sallama akan sai bayan sati daya zaizo kano kawai sai gasu sun yo sammako..... Ta katse ni.da fadin don Allah rufe min baki da zancen wofi .Wai kawai ganinsu kk yi makarciyar banza to bari kiji na gaya miki idan kk kuskura ko ciwon kai Nafisa tayi sai kin gane kurenki wlh .don haka ki kiyaye don hakane na kira ki.Sannan abu na biyu ga 'yarku nan taxo ta fada min komi.wato bazaku mata aure ba sai ta yi karatu.to me karatun zai tsinana mata? Ke kanki lokacin da uwarki ta nace sai kinyi jamia ina karshenta a karuwanci da shaye shaye kk kare ko an gaya miki na manta ne.to wlh bari kiji ahir dinki daga ke har Salman Ku kiyayi fushina. Ka min nayi magana tuni ta kashe wayar. Tirkashi! Wai ni yau da wanne zanji ne? [05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: _🌹RUMAISA SALMAN_🌹 👨🏻‍🚒 ```MATAR``` ~```SOJA```~ 👨🏻‍🚒 (_Labarine da ya kunshi soyayya,tausayi, fadakarwa,Ilmantarwa da kuma Nishadantarwa_) Story and written By Maman khausar✍🏻 ( *INTELLIGENT WRITErs ASSOCIATION* *[onward together]* *{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}* ```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑``` *```JUST GIVE US FOLLOW..** [ ```~BISMILLAHIRRAHMANI RAHEEM!~``` ➡page 2 🌹 _LABARINA_ 🌹 Rumaisa Ibarahim sunana knn. Na taso a kauyen.Gano Jahar kano mahaifiyata sunanta Amina. Na tasone cikin kulawa da samun kyakkyawar tarbiyya daga mahaifiyata.idan ka ganni bazaka ce a kauye nake ba saboda yadda Mamana take kula da suturata tun ina karama .kasancewar ta mace mai zafin nema na tashi naga tana sana,a sosai kusan duk abinda ake so a kauyenmu tana kawowa har irin kayan sawa na gwanjo ,takalmi,su 'yan kunne ba irin kayanda bata sayarwa na amfanin yau da kullum. Ta na shiga birnin kano sati sati don haka ko wani zuwa sai ta saya min kaya masu kyau irin na 'yan birni. Ta sakani a makaranta da islamiyya. Allo kuwa tun ina primary na sauke. Ya zamanto a kauyen duk inda na shiga bina ake da kallo wasu na shan,awata wasu ko bakin ciki sukeyi dani. Tun ina karama wasu lokuta na kanga mama na tana kebe kanta a daki tayita kuka in na tambayeta tace min kanta ke ciwo. Har yanzu da na girma shekarata goma sha shidda ina SS2. Watarana mun taso daga makaranta ina ta sauri in dawo gida don mkrntan akwai nisa da gida Jinayi ana kiran sunana a na juya da sauri don inga waye sai naga ashe Bello ne makwaftanmu ya nace min kullum sai ya aika a kirani gashi mama tace kada in kuskura koda wasa in saurari wani a kauyen nan bataso Ina cikin wnn tunani ya karaso yana murmushi yace har kun taso ne? Fuskata ba fara,a nace eh mun taso. Yace Rumaisa baki ga sakona bane? Nace na gani mn. Yace amma baki ce komi ba. Shiru nayi sannan nace nifa mama ta hanani kula kowa tace karatu zan yi kuma sai na gama Jami,a Dariya yayi sannan yace jamia a kauyen nan ne har zaki yi jamia?kinga rumaisa bari in gaya miki gaskia aure shine ya kamaceki yanzu ba wani book tunda Allah yasa kin sauke Qur'ani.ki amince in rufa miki asiri in aureki ba sai an tsaya tone tone.watakila shine mamanki take tsoro yasa tace makaranta zakiyi.ni ba ruwana da Asalinki haka nake son ki. Jikina ya mutu tunda ya fara maganan domin gaskia ni bansan waye BABANA ba .wani bai taba zuwa wai dangin Babana ba.kai harma mama ban San kowa NATA ba. Hawayene ya zubo min da Na tuna kusan kullum Na kan ga mama a damuwa in ta kebe ita daya. Gaba daya Na manta da wani bello da sauri Na barshi a gurin yana ta kwalan kira nayi banza dashi. Tfy sauri sauri nake har na isa gida ina haki mama tana ganina tace ke lfy Na ganki haka ? Waya koroki? Na girgiza kai nace babu Na shige ciki Na kwanta . Shiru shiru tags ban fito Na nemi abinci ba ta shigo ta zauna kusa dani tace Rumaisa me Nene yake damunki ne kin shigo cikin yanayin damuwa ko abinci baki nema ba. Na girgiza kai nace" bab....... Ta katseni da sauri ta ce akwai abinda kk boye min.rumaisa bakida kowa a garin nan sai ni don haka dole ne ki fada min damuwarki. Na mike na zauna snn na kalleta nace mama tambaya zan miki zaki ban amsa ? Ta ce in har na Sani me zai hana na baki amsa. Nayi ajiyar zuciya nace "mama WAYE MAHAIFINA? Nan da nan naga fuskarta ta sauya ta mike rai bace tace " uban Wa ya saki kizo ki min wnn tambayar fada min . Tsoro ya rufeni ganin yadda ta fusata. Tsawa ta daka min"nace uban Wa yasa ki zo ki min wnn tambayar. Na kara rikicewa da kyar bakina ya iya fadan bello ne dama yace........ Na fada mata komi Ta gyada kai tace OK wato har yanzu baki rabu da bello ba ko?ba na fada miki cewa bazakiyi aure ba sai kin gama Jami,a?to bari kiji ko kin gama ma ba a kauyen nan zakiyi aure ba don haka ko da wasa kar na kara jin ko ganinki da bello kai kowa ma indai anan kauyen ne. Tunda ta fara magana nake ba ta hkr. Tace tashi ki fita kije ki debi abinci kici. Ina cin abinci naga ta dauki hijabinta ta yi waje rai bace. Daga wnn rana na shiga damuwa ba abinda nake son illa in San wacece ni. Uwa uba kuma gidansu bello yan,uwansa sun Sani a gaba tunda mama taje ta fadawa mahaifiyarsa maganganu akaina.ya kasance duk inda suka ganni sai sun zageni hade da yi min gorin asali. Na shiga damuwa sosai har ya kasa boyuwa kana ganina ko baka sanni ba kasan ina cikin damuwa. Bayan na taso daga islamiya don yanzu banda kawaye ma duk sun juyan baya. Kannen bello suka tareni a hanya zainab da Kulu . Na kallesu nace yau kuma me ya faru? Kulu ta harareni tace kudaden da yayanmu ya kashe miki zaki tattara ki bamu. Cike da mamaki nace wane kudade kuma?ni bello bai taba bani ko sisi ba.... Zainab ta katseni da fadin karya kikeyi shegiya munafuka dole ne kawai ki fito da kudin nan ki bamu ehe! Kulu ta karba tace "duk karuwancin da akace mamanki takeyi a birni ta dawo da lodi lodin kaya da kudi bai isheku ba sai kin kara dana ya bell...... Raina ya balain baci na kallesu nace gaskia Kulu abinda kuke min ya isheni don kun fara wuce gona da iri .zaku min komi in shanye amma banda naganar zagin mahaifiyata . Zainab tace an zageta sai me ? Waye ita a garin nan banda karuwa?idan karya muke mata gaya mana waye ubanki? Kulu ta karba tace tunda muka taso a garin nan bamu taba jin Wanda yace ya sanku ba....... A fusace na tsinka mata mari. Nan da nan muka kaure da kokuwa. Dama hakan suke so don haushina da sukeji . Nan aka taru a wurin ana rabamu sai zagina suke suna cewa mama na karuwa ce. Da kuka na bar wurin Allah Allah nake na isa gida don wlh hada kayana zan yi in bar garin nan in shiga duniya Neman asalina. Horn din mota nakeji tun dazu a kunne na Wanda ya ki karewa nan da nan na birkice na rasa ina zan yi. Kawai na tsaya cak! Idona rufe ina sauraren ta inda motar zai kwasheni. Sabanin hakan sai na ji takun mutum ya na zuwa inda nake kamshin turarene mai dadi ya daki hancina da sauri na bude idona Rass! Naji zuciyata ya tsinke da ganin Wanda ke gabana. Wayyo wani saurayi ne sai kun ganshi in tsaya kwatancen kyaunshi bata lokaci ne. Kawai dai ya hadu ga kwarjini. Sai dai na lura kamar ransa a bace yake don wani irin kallo yake min kaman zai dauke fuskata da mari. Sai lokacin na gane a tsakiyar hanya wucewar mota nake ta tafiya gashi sun ta min hon amma ko a jikina don ma mota basu cika shiga layin sosai ba ko adaidata sai da su sauke ka can babban hanya basa shiga saboda gargada da yashi. Shine ya sauko ransa a bace. "Wnn wane irin rashin hankaline haka? Ya fada a fusace.yaci gaba da fadin "Yar kauyen kawai don Allah tashi a hanya zamu wuce. Ba tare da na dami da abinda ya fada ba don ba shine a gabana ba.na tsallaka gefe naci gaba da tfyna Fizge motar yayi da karfe ya bade ni da kura ya wuce sai lokacin na lura Ashe su biyu ne. Nayi gaba kadan sai naga motar sun paka shi sun fito suna zaune a kai tabe baki nayi nace duk uban saurin nan naka dama nan zaku tsaya. Har zan wucesu dayan yace minmalama don Allah muna da tanbaya. Tsayawa nayi nace "to Allah sa na sani Fuskarsa dauke da fara,a yace "ke kuwa 'yar kauyen nan ne? Nace " eh.ka tambayi abinda zaka tambaya don sauri nake in isa gida. Murmushi yayi ya kalli Dan,uwansa da ya kame ko kallonmu bayayi yana latsa wayarsa. Yace kaji ai 'yar kauyen ne. Ba tare da ya dago ba yace to ka tambayeta kawai mn. Mai fara,an ya juya gareni yace"ya sunanki? Cike da mamaki nace "tambayar taku knn? Yace " aa ba shikenan ba akwai wata mata da mukaxo nema a kauyen nan. Nace "wace mata knn me sunanta? Yace " sunanta Amina kuma tana da 'ya Rumaisa ko Rumasa,u na Dan manta. Bansan lokacinda nayi murmushi ba don tuni jikina ya bani 'yan,uwana ne. Shi ma murmushi ya min nace " gidan na can gaba muje nima can zani. Yace OK in ba damuwa zo muje a mota. Na girgiza kai nace aa ni bana shiga motan da bansan masushi ba. Dariya yayi yace gaskiarki kar a sace ki .to muje a kafa. Ya juya ya kalli danuwansa yace"to oga munyi gaba ka biyo mu a mota. Ko dagowa baiyi ba bare a sa ran amsa. Muka jera dashi sai tadi yake min gashi da abun dariya. Nace wai wancan me motar Dan,uwanka ne kuwa? Yayi dariya yace Dan uwana ne ba kya ganin kamanni? Nace hakane naga shi baya fara,a ko an bata mishi rai ne? Yace "ke rabu dashi miskilancine zalla ba wani abu ba. Na juya baya har lokacin yana zaune kan motar Mun isa kofar gida Nace bari na shiga me zance da ita? Yace kice mata baki daga birni. Nace to. Na shiga ciki da sallama can daki mama ta amsa min na sameta a dakin Nace mama kinyi baki sunce daga birni suke. Tace baki daga birni kuma ?to ina suke? Nace maza ne su biyu inaga ma kamar 'yan biyu ne sunzo da mota. Ta danyi shiru daga bisani tace to sa musu tabarma kije kice su iso. Nace to . Bayan na shimfida tabarma na je na samesu Ashe har miskilin ya karaso na kalli dayan Nace ta ce bismillah Ku iso ciki. Na wuce gaba suna biye dani a baya har ciki na nuna musu tabarma suka zauna . Mama ta fito duk ta bisu da kallon rashin Sani suma kallonta suke. Ta yi musu sannu da zuwa ta zauna a kujera suka gaisa. Shiru ya biyo baya mama ne ta yanke shirun da fadin " sai dai ban ganeku ba kuyi hakuri don Allah. Mai fara,an yayi murmushi yace "eh bazaki gane mu gaskia amma mu mun ganeki mu yaran.... Mama ta katse su da fadin tsaya in canka. Murmushi ta yi ta mike ta karaso inda suke ta kallesu cike da fara,a tace" SALMAN da SALIM ne Ta nuna miskilin tace Kaine salman. Sannan day an kuma tace kai kuma salim. Murmushi salim din yayi yace "hakane goggo Amina mune. Mama cike da farin ciki ta zauna tana fadin Allahu Akbar kune kk zama samari haka? Ta kalli salman tace" Salman ina innarku?ina yaya na ? Yace duk suna lfy goggo amina da saninsu muka zo nan mun Dade muna nemanki. Ta danyi dim sannan tace ayyah Sannan ta kalli salim tace salim ya aunty Zuwaira da yaya kasim kannenka nawa? Ya na murmushi yace su biyu ne fa,iza ne sai hakim. Tace Allah sarki salman kaifa? Yace su hudu ne mata sadiya da raihana.sai sakina da zainab yaran mama. Mama cike da fara,a tace masha Allah gida ya cika. Sun danyi shiru snn Salman yace Goggo ina yarinyarki ta girma sosai ko? Mama tayi dariya tace " ta girma sai a fara shirin bikinku dama kai nace zan bawa. Ta karasa maganar da dariya.shi ma ya Dan murmusa ya sunkuyar da kai. Salim yayi dariya yace goggo kin ganshi wai bayaso to ki bani kawai goggo in ta girma muyi aure. Mama tasa dariya tace wane girma kuma ta kusa gama secondary Cike da mamaki suka dago suna kallonta tace ai itace ta muku jagora Rumaisa ba. Salim yayi saurin fadin wow masha Allah goggo kin haifo mn indiya masha Allah salman kawai kayi serious ka ji in kuma bakayi ni dai ayi dani goggo. Harararsa salman yayi bai ce komi ba. Mama ta yi dariya Sannan ta kwala min kira tana "rumaisa ki fito ki ba yayyunki ruwa mn. Bata San duk abinda suke ina tsaye a window gabadaya murna kamar ya kasheni ba da sauri na saka hijabina na fita duk ido suka sa min kunya kamar na nitse. Na wuce na dauko jug din roba na sa musu ruwa a randa na kawo musu da cup sannan na saka musu. Mama ta kalleni tace rumaisa wnn yayyunki ne salman da salim yaran yayyuna biyu Wanda muke cike daya. Murmushi nayi na kalli salim sannan na kalli salman abin mamaki sai naga yana kallona muna hada ido ya Dan saki fuska yace " kanwata kiyi hkr da abinda ya faru dazu. Nace "babu komi laifina ne. Mama tace ta yi muku rashin kunya ko? Yace aa goggo nine na mata laifi. Anan suka dinga min tambayoyi akan mkranta ina amsawa mama kam bata sa mn baki ba ta tafi ta hura wuta ta dora tuwo don tuni nayi miya. Magriba yayi na kawo musu ruwa a buta sukayi alwala na fita na nuna masallaci suka tafi. Bayan sun idar da sallar magriba suka dawo na kawo musu abinci sunci kuwa sosai.bayan sun gama mama tace in tattara kwanuka bayan na kai tace in tafi daki in dau torch light in yi karatu. Anan na barsu suna hira har karfe takwas sukayi sallama.mama ta kira ni tace inje muyi sallama. Tuni har sun fita salim ya shiga mota salman ne ke tsaye . Na Dan russuna nace yaya Ku gaida gida mun gode da ziyara. Na juya zan tafi naji yace"zo Rumaisa. Na juya cike da mamaki na tafi gunsa. Ya numfasa yace "zamu dawo nan da one week me kk bukata inzo miki dashi? Na girgiza kai ina jin kunya nace" babu komi yaya na gode da kulawarka. Bai ce komi ba yasa hannu a aljihunsa ya ciro kudi bansan ko nawa ba ya mika min Na girgiza kai nace "aaa yaya na gode Yace ki karba in baki son bacin raina . Dole na karba nayi Godiya ya salim ma ya fito mukayi sallama sannan suka tafi. Bayan nayi sallar isha ne na fadawa mama abinda su Kulu da zainab suka min. Sosai ran mama ya baci tace babu komi zan kai karasu gun mai anguwa don a sawatar nasan uwarsu ce ke zuginsu. Duk yadda naso mama ta ban labarin 'yan,uwanta sai kauce min take har na hakura . Amma abin na damun raina duk da ma yau naga 'yanuwana . [05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: _🌹RUMAISA SALMAN_🌹 👨🏻‍🚒 ```MATAR``` ~```SOJA```~ 👨🏻‍🚒 (_Labarine da ya kunshi soyayya,tausayi, fadakarwa,Ilmantarwa da kuma Nishadantarwa_) Story and written By Maman khausar✍🏻 ( *INTELLIGENT WRITErs ASSOCIATION* *[onward together]* *{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}* ```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑``` *```JUST GIVE US FOLLOW..** [ ```~BISMILLAHIRRAHMANI RAHEEM!~``` ➡page 3 Bayan sati daya sai gasu sun dawo har da yayun mama. Sun Dade suna tattauna Wa don ni mama tace in tafi islamiya tun bayan ba gaishesu. Har na fita ya salman ya biyo ni "Rumaisah! Na juyo hadi da fadin na,am Ya karaso gabana sanye yake da kananan kaya sun matukar amsarsa yana sanye da bakaken glass Wanda ya kara masa kwarjini. Yace " muje na kaiki islamiyar a mota tunda akwai nisa. Nace na gode yaya amma islamiyar mu in sunga an saukeni a mota......... Ya katseni da fadin " ce musu zakiyi yayanki ne ai zo muje. Ya bude min gaban motar banda zabi haka na shiga muka tafi har muka isa bamucewa juna sannu ba. Ya sauko ya zagayo ya bude min ina fita sai ga Kulu da zainab sake baki sukayi suna kallommu har da tsayuwa. Yace "nasan kamin ki dawo mun tafi.saboda haka ki kula da kanki kinji. Kai na daga masa . Aljihunsa ya lalubo ya ciro five hundred yace " gashi kiyi kudin break... Na girgiza kai nace "aa na gode. Yace" zamu bata fa waya gaya miki ana maida hannun kyauta baya? Na karba hadi da Godiya baice komi ba ya shiga motar yaja ya tafi. Su Kulu suka karaso wurina kallonsu nayi na dauke kaina na wuce. Da sauri suka sha gabana zaunab tace " ke waye wancan mai motar? Na harareta nace "ina ruwanku? Kulu tace" kar ki yadda ki fada mana bakar magana yanzu anan muyi miki shegen duka. Nace "hmmm bismillah mana. Zainab ta harareni tace zaki fada in muka tare ki a lungu yasin Taja hannun Kulu tace Kulu mu tafi Kulu ta harareni tace karuwa kawai uwarki karuwa kema karuwa Allah wadaran zuriarku wlh. Binsu nayi da kallo har hawaye ya taru a idona. Bayan an taso islamiyya canza hanya nayi don in kuma haduwa da su zainab. Bayan na idar da sallar isha nayi shirin kwanciya mama ta kirani naje tace " zauna. Na zauna tace "rumaisa yayuna sun yanke shawarar daukeki a kauyen nan ki koma birni gidansu salman. Na dago da sauri nace " alhamdulillh mama dama garin nan ya isheni kwanan nan su Kulu sun sakoni gaba. Jikinta a mace tace "hmmm rumaisa ba don kar suce na kara bijire musu ba da nace su barki kawai.domin gidansu salman zamanki a wurin akwai matsala Innar su salman bata da kirki ko kadan. Nace mama ina tare Zamu tafi ? Ta girgiza kai tace ni aure zanyi kwanan nan rumaisa. Cike da mamaki nace" a ina mama? Tace a birni gara nayi aure kawai da in koma zaman gidan yaya da matarsa.ke kanki naso ace gidan ya kasim wato mahaifin salim aka kaiki don matarsa mutumiyar kirkice amma salman ya fi so ki zauna a gidansu. Nayi shiru na rasa me zance can nace "mama to ki tafi dani gidanki mn. Tace baxai yiwu in Dora mishi dawainiyarki ba alhali ba shi ya haifeki ba. A raina nace to ki kaini gidan Babana mana. Ta lura da yanayinda na shiga tace" karfa ki dani kanki ke dai ki taka tsan tsan ki zauna da kowa lfy kinji. Haka ta dinga kwantar min da hankali har bacci ya daukeni. Sati biyu akai ya salman ya dawo daukana shi kadai na tambayeshi ya salim yace ya koma Abuja. Dama na shirya kuma na sallami kowa wasu na min fatan alheri wasu ko kallon arziki basuyi min ba. Haka muka sallami ta rakomu har waje tace "to Salman ga Rumaisa ka kula da ita sosai kar ka sassauta mata idan ta kauce don bana son ka shagwabata ba gata bane. To,kawai yace yayinda yake sa kayana a mota. Ta kalleni tace ke kuma kiyi taka tsan tsan da kowa domin birni ba kauye bane ki maida hankali ki nitsu banda rawar kai ki girmama kowa ki mutunta kowa kuma sai kiga kin zauna qalau sannan ki maida hankali wurin karatunki sosai banda wasa. Nace to mama Hawaye ya cicciko min ido . Ya bude min gaban motan na shiga ya rufe . Ya sallami mama sannan ya zagayo ya shiga ya tashi motar mama ta daga mana ta yi ciki. Na goge hawaye da ya gangaro min ya kalleni yace" daura belt. Bansan me yake nufi ba na shiga dube dube. Bai ce komi ba naga ya Dan kwanto yasa hannu ya jawo igiya ya zagayeni hannunsa na taba jikina naji wani iri. Ya kalleni yace "sorry belt din zai taimaka miki sosai. Naga shi ma yaja ya daura daga nan muka fara tfy. Sanda muka isa gidansu a Gadon kaya rana ta yi sosai. Ya sami unuwa yayi parking Sannan ya bude min yace sauko ga gidan nan. Na kalli gidan da ya nuna mun babban gidane gsky wata ce ta fito daga cikin gida zamuyi sa,a da ita cike da fara,a ta karaso tana min sannu da zuwa. Ya Salman yace " yawwa sakina zo ki tayata Ku dauki kayan nan ki kaita dakin Inna ta huta. Rass! Naji zucuyata ta tsinke bansan sanda na tsaya ina kallonshi ba har sakinan ta dauki kayana tana mu tafi banjita. Ya karaso gabana yace"me ne ne? Girgiza kai nayi nace ba komi. Yace OK shiga ciki. Na dauki ragowar kayana na bi sakina ciki. Abinka da Dan kauye sai kalle kalle nake ta yi. Har muka isa gidan a tsakar gida naga wata mata tana wanke shinkafa wata yarinya kuma ba daka tattasai. Na hangi wata kuma can tana wanki sai wake wake take. Matar ne data ganmu cike da fara,a tace "sannunku da zuwa lallai kun shawo hanya sakina ki wuce da ita dakin innarku. Na Dan russuna na gaisheta da fara,a take amsawa har tana tambayana mama. Wancan da take wankin ta dago a yatsune tace " sannunki da zuwa. Na amsa sannan na gaisheta ta amsa min a wulakance. Sannan matar ta kalli wacce take daka tace"zainab baki ga yayarki ba? Wacce aka kira da zainab ta kalleni cike da fara,a tace sannu da zuwa.ina wuni. Na amsa mata ina murmushi sannan muka shiga dakin innan da yake ciki da Palo ne mun sami wata kuma kwance akan kujera da kyar ta amsa mana sallama sakina tace mata "raihana kicewa inna ga bakuwa. Ta dago ta kalleni tace ki zauna mn innan zata fito yanzu ai. Na zauna sannan na gaisheta. Sakina kuwa tana ajiye kayana tace ina zuwa rumaisa mama ta aikeni shago. Na ce " ko in rakakine ? Tace aa ya salman yace ki huta tukunna. Ta fita da sauri. Muna zaune shiru da raihana. Sai ga wata mata ta fito daga dakin.kyakkyawar mace fara jikinta dai dai batada tsawo sosai ga gashi bakinta baki irin na 'yan kamaru daga gani ma 'yar kamarunce.kamanninta da salman yasa na fahinci itace innar Sam bata tsufa ba har matar wajen nan ta fita girman jiki. Da sauri na sauko daga kujeran nace"ina wuni. A wulakance take kallona sannan daga bisan tace lfy sannunki da zuwa. Na amsa kaina a sunkuye gaba daya na tsorata da irin karbanda yan dakin suka min ni wlh da dakin su sakina ma aka kaini mamarsu tafi fara,a. Munfi minty talatin zaune ba Wanda yakara cewa komi har mai wankin ta gama ta shigo ta na cewa inna sabulu na ya kare naga wani a leda na dauka na karasa wankin. Inna tace "ke dai sadiya wlh baki da tattali duk girman sabulun har kin karar? To ba ruwana wancan da kk dauka na salman ne ba ruwana ki tanadi amsa in ya tambayeki don yace in yaron nan mai masa wanki yazo a bashi sabulun. Raihana ta mike tana cewa tab! Yarinya kin taro aradu sabulun ya salman? Hmmm yau zamu sha kalli a gidan nan. Sadiya ta harareta tace " ba abinda zaiyi ai wanki nayi kuma sabuluna ne ya kare.Inna ina akwai wani sabulu a karkashin gado Wanda su nenne suka kawo miki da kamaru? Inna ta harareta tace ba duk kun karar ba ko Maman sakina ma ban basu ba kwaya daya ya rage na bawa salman shine kk dauka.dama ai abu a dakin nan baya dadewa ko man shafawa abbanku ya siyo ya raba sai Ku karar nasu sakina na nan sabulun wanka haka man goge baki ma haka kafin ace me wnn kun karar sannan kuce na fiye korafi kuna dai ganin su sakina a dakinsu yadda suke tattalin kominsu.alhalin ba Yawa muka fisu ba Sadiya tace wlh inna ba wani tattali suka fimu ba makon tsiya ne dasu. Inna ta tabe baki tace ai shikenan Ku kuka Sani gashi yanzu mun karu kuma . Raihana ta ce kai wnn yar kauyen a dakin nan zata sauka? Inna tace a to ga dai kayanta nan kun gani. Sadiya tace tab sai dai ta kwanta a kasan kafet wlh Inna tace oho kunfi ni kusa da ita. Nikam duk naji ba dadi na kara takurewa wuri daya. Sakina ta shigo da kulan abinci ta ajiyae tace Inna ga abincin yaya salman. Inna tace"baya nan ne? Sakina tace eh abokansa sunzo sun tafi tare . Sannan ta kalli su sadiya tace kuzo muje waje muci abunci rumaisa zo muje waje. Da sauri na mike nabi sakina waje ta shimfida taburma an saka abinci a babban tire da miya a roba sai ruwan Leda me sanyi a cikin wani tire. Sakina ta kalleni da fara,a tace bimillah muci su sadiya kam sai sun gama yanga zasu zo. Munacin abinci suka fito bayan sun wanko hannu suka karaso sadiya tace sakina da 'yar kauyen nan zamu ci tuwo?Allah ya sawwaka. Ta wuce kitchen ta dauko plet ta diba gefe har zata sa miya sai ta yatsuna fuska tace hmm miyan duk ta jagwalgwala bari inje in dibi na tukunya. Ta wuce kitchen. Raihana ta kalleni tace "ke kar ki kuskura ki taba min gabana don naga baki iya cin tuwo ba kuma ki rage loma da kk yankowa kato sai kace an sakoki daga igiya ko da yake baki saba da jar miya ba. Nidai bance komi ba sakina ne tace wlh duk abinda kk fada a kunnen ya salman ko Abba Sadiya dake zaune can tace to munafuka ai sai ki fada din tunda karya aka mata. Ni dai na har naji gara min kauyen mu. Don zama da wayan nan sai anyi da gaske! *Muje*zuwa* !!!! Hauly ce😍 [05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: _🌹RUMAISA SALMAN_🌹 👨🏻‍🚒 ```MATAR``` ~```SOJA```~ 👨🏻‍🚒 (_Labarine da yA kunshi fadakarwa,Ilmantarwa da kuma Nishadantarwa_) Story and written By Maman khausar✍🏻 ( *INTELLIGENT WRITErs ASSOCIATION* *[onward together]* *{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}* ```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑``` *```JUST GIVE US FOLLOW..** [ ```~BISMILLAHIRRAHMANI RAHEEM!~``` ➡page 4 Satina biyu a gidan na fara zuwa makaranta da Islamiyya ajinmu daya da sakina da raihana sadiya na gabanmu don yanzu zata zana ssce Gaskiya rayuwa bata min dadi a yanzu .a inda nake samun sassauci shine idan na tafi mkrnt ko islamiyya. Amma in muka dawo gida ko motsi kwakkwara ban isa inyi ba Inna da sadiya sun sakoni gaba sosai.har gara in Abba na gida .gashi ya salman tun randa ya kawoni washe garin yayi tafiya.ni a bakin sakina ma naji tace min ya koma makaranta a Lagos. Bazan mata wata rana muka wayi gari ana ruwan sama kamar da bakin kwarya.duk muna zazzaune a palon innah su sakina suna dakinsu suma. Inna ta kalleni tace niko rumaisa ina son in miki wata tambaya tun tuni. Nace to innah. Tace ko mamanki ta taba baki labarin mahaifinki? Na girgiza kai zuciyata ta shiga bugawa.nace bata taba bani ba. Tace " Hmm Amina knn ai bazata gaya miki ba domin labarine Mara dadin ji rumaisa bakida kykkyawan asali mahaifiyarki ta cuceki ta sameki ta hanyarda bata dace ba. Na dago da sauri na kalleta .Sadiya ma ta yi farat tace "inna knn rumaisa shegiyace. Raihana tace hmm kuma shine a rasa inda za,a kawota sai nan don aja mana abun kunya ayita nuna mu. Sadiya ta kalleni sannan tace ni dai kar ki kuskura ki nunani matsayin 'yar uwarki ehe. Sunkuyar da kai nayi bansan sands na saka kuka ba .me yasa mama tayi min haka ta sameni ta kaxamar hanya dama wnn shine dalilinda yasa batason in tambayeta waye mahaifina kuma ta na yawan kebe kanta tayita kuka adaki... Inna ce ta katseni da fadin " ke don Allah bama son kukan munafurci tashi kije ki hura huta maza ki Dora tuwo . Sadiya tace wlh kuwa don mukam 'yunwa mukeji Raihana ta karba tace bare ma anyi ruwa kam dama sai yunwa. Na mike idona tuni har yayija na fita sai ruwa ake tayi kamin na isa kitchen har na jike charkaf Ashe itacen ma sun bari a waje ruwa ya gama jikawa. Haka na kai kitchen na hada murhu na hura huta na nemi wuri na zauna naci gaba da kuka sosai ina bakin cikin kasancewata a raye dama mutuwa nayi. Na kai awa daya ina kokarin hura wuta amma ina yaki kamawa ga hayaki ya turnuke kitchen ko gani banayi da sauri nayi waje a gigice idona duk yayi ja sai kwallah. Sadiya ta fito zata ban daki har zata wuce ta leka kitchen taga hayaki. Ta shiga tafa hannu tn salati tace yanzu tun fitowarki baki dora ba muguwa so kike ki kashe mu da yunwane? Shiru na mata tace ina miki magana kina tsaye ko?to wlh kamin na fito ban daki ki fifita wutan nan ya kama.bayan yunwa har horo zaki mn da hayaki ki cika mn ciki muguwa kawai anyi gadon mugunta. Ta wuce bandaki zuciyata kamar zata fashe hawaye kuwa yaki yankema idona. Ta fito daga bandaki ta sameni zaune a wurin Tace kan ubancan lallai ma yarinyan nan taurin kai zaki min ko? Zan nuna miki na fiki danyan kai. Ta rufe leman hannunta ta wuce randa fuuu!ta debo ruwa cikin botiki ta nufi kitchen da isarta tajuye ruwan cikin murhu. Zaro ido nayi ina kallonta na tuna irin wahalar da nasha akan hura wutan nan. Murmushin mugunta ta yi tace "duk sanda kika gama hutawa kyaje ki hura wani don bazaki kashemu da hayaki ba. Ta shige daki.na bita da kallo sannan na fashe da kuka. Durkusawa nayi a bakin kitchen ina ta rusar kuka. Sai kawai ga ya salman Ashe tuni ya dawo ruwa ya hanashi shigowa shine yanzu da ruwan ya Dan dauke ya shigo. Yana ganina cikin wnn yanayin yace" subhanallah! Ke me kikeyi a ruwan nan? Ban kulashi ba kukana kawai nakeyi. Ya karaso bakin kitchen ya riko hannuna yana "taso taso. Ya kalleni yace me ya faru dubi yanda kk jike don Allah tafi ciki ki cire wayan nan kaya. Inna ce ta fito daga daki tace " ba wani canza kaya da zatayi don Allah sabar munafurci ba wuta nace ki hura ba? Shine kk barmu da yunwa kk zauna cikin ruwa kika jike don munafurci ko? Na girgiza kai nace Inna har na hura wutan sadiya taxo ta Debi ruwa ta zuba a murhun kuma dama itacen sun jike. Tace madalla ina tun lokacinda hadari ya hadu nace Ki shigar kitchen kikayi banza da maganata don ba uwarki bace ni ko? Nace aa inna raihanace kk ce ta shigar...... Ta katseni da fadin zaki wuce kije ki hura wutan ko zaki tsaya kina min musun raini shegiyar yarinya. Sai lokacin yayi magana yace "aa inna gaskia bazata iya hura hutan nan ba saboda murhun ya jike.kawai suje da raihana su sayi gawayi don gaskia ina jin yunwa. Inna batayi magana ba ta wuce ciki . Ya kalleni yace jeki cire kayan kice sadiya da raihana su zo yanzu ina jiransu an an. Na wuce ciki ya bini da kallo duk kunya ya kamani saboda yanda rigan ya kama jikina da ya jike. Bayan na kirasu sai hararata suke na wuce ciki. Ko da suka fita yacewa sadiya maza ta wuce kitchen ya bata minti. Talatin ta hura wuta in ba haka ba zata ci duka. Ya bawa raihana kudi yace ta wuce taje ta sayi gawayi. Sannan ya. Shigo palon innah. Nikam bayan na canza kayana Sai naji bugun zuciya ta ya canza kirjina ya to she numfashina ya fara fita sama sama har wani barazanar daukewa yakeyi. Bansan sanda na fara kiran inna ina zan mutu wayyo Allah na ina dafe da kirji. Ta gudu suka shigo suka sameni cikin wnn yanayi inna kam Sai salati ya salman bai tsaya wata wata ba ya fita waje da sauri kamin ya dawo tuni numfashin ya dauke .cak! Yayi dani ya tafi ya Sani a mota Sai asibity emergency aka karben nidai bansan inda kaina yake ba. Lokacin da na dawo hayyacina Sai kalle nake doctor ne ya shigo da ya salman Ya sake duddubani sannan yace "yanzu kam ba wata matsala ko? Shiru na masa. Yayi murmushi yace me kk ji a Jikinki yanzu? Nace " babu komai jikinane ba kwari. Yace ba wata matsala a hankali zaki warware . Sannan ya juya wurin salman yace "don Allah a kulada ita sosai ciwon asma nada hadari. Da kai ya amsa masa docton yaci gaba da fadin kuma akwai ulcer ma don haka a sayi magunguna da aka rubuta mata duka Allah ya bada lfy kuna ita tfy. Anan suka fita da ya salman.ba jimawa ya shigo ya kalleni yace zaki iya tashi? Na daga mishi kai alhalin naji jikina ba kwari . Ganin yadda nake ta kokarin tashi na gagara yasa shi isa bakin gadon ya dagoni Dan kwalina ne ya zame ya fadi gabadaya gashi na ya baje har fuska dama ya tsawo ga cika ga kuma yauki gashi ban iya parking ba na saba da kitso. Kallon gashin yakeyi har ya shagala da sauri na fara lalubo Dan kwalina. Sai naga ya kai hannu ya tattara gabadaya ya ce ina rivom? A kunyace nace bandashi . Ba zato ba sammani naji yace dama an taba yin budurwa ba rivon ne? Ke dai 'yar kauyece. Na girgiza kai nace mama tana saya min amma sun bata ne wasu kuma sun sake. Baice komi ya tattara min gashin sannan ya kawo hijabi ya sakamin ya riko hannuna yace mu tafi . Yana rike da hannuna har muka isa bakin mota. Muna isa gida muka tarar inna har ta shirya da mmn sakina zasuje asibityn. Suna ganinmu cike da mamaki Maman sakina tace har an sallamota ?ikon Allah. Inna ta karba tace "har mun tsorata yarinya kamar baza ta tashi ba ? Salman ya kalli sakina yace " sakina zo ki rike hannunta kuje ciki. Sakina ta riko hannuna duk sai sannu suke min mun shiga palon inna na kwanta sakina ta kawo min pillow. Nan naji ya salman yana cewa "inna rumaisa asma take dashi likitan yace a kula da ita sosai don ciwonta bai son sanyi baison hayaki ko kura da makamantansu don Allah a kiyaye. Sannan ya kalli sadiya tace " ke kuma wlh wlh ki kiyayeni don idan kk kuskura kk shiga hannuna sai ki yabawa aya zakinta muguwa kawai. Ya kalli raihana yace ke kuma idan kk ce zaki dinga biyewa sadiya zaki ji jiki wlh nonsense kawai. Ya juya ya fita innah ta bishi da kallo sannan tace " jeka masifaffe mutum ne baza a taba maganar arziki da kai ba kullum cin magani.naga matar da zata aureka da wnn bakar zuciya taka. Maman sakina tayi dariya tace " wlh kuwa matarsa na nan gau a leda. Raihana ta karba tace don ma bakiga yanda 'yan mata ke binsa yana gwalesu bane. Inna tace " a hakan?mtswww Maman sakina tace ai ina mamakin yanda ya nace akan Salima alhalin ba bashi aurenta zasuyi ba. Inna tace "saboda sun ganshi Dan talaka ne ai bai da komi sai uban zuciya da miskilanci. Sadiya tace aa so suke suyi mata auren dangi ne.yaya kuma sai dagewa yake yi akanta....... Shigowarsa ne ya katseta gabadaya shiru sukayi suna binsa da kallo. Ya ji su sarai sai dai baiyi magana ba ya wuce dakin innah ya sameni ina kwance yace "kinci abinci? Nace"aa. Dan tsaki yayi sannan ya fito ba jimawa ya shigo da plet guda biyu da cokula . Ya dauko kular abincinshi yayi mn serving jalof ne da wake da manja. Ya taura min gabana yace tashi kici bari in gama inje in sayi maganinki. Na mike a hankali na jingina da kujera na fara ci kadan kadan ina ware wake gefe guda. Yace " ba kya son wakene? Nace,"eh Yace" ke dai 'yar kauyece. Bance komi ba har ya karasa cin abincinshi zai tashi inna ta shigo tace "yawwa salman zauna inada magana. Ya koma ya zauna ba tare da yace komi ba. Inna tace ,su sadiya sun kawo min korafi akan in suna tsaye da samarinsu kn zuwa ka musu wulakanci ka koresu hakane? Kai tsaye yace" eh Inna ta matukar kulewa tace"to meyasa jika su zamuyi musha ne? Yace " karatu zasuyi. Inna ta harzuko ta kama bala,i makarantar banza mkrantar wofi baza suyi ba wlh.mkrnt indai irin wacce goggonku Amina tayi ne Allah wadarai wlh.domin ni tun kan goggonku amina naga illar nitsa a karatu don haka ni yarana suna gama wnn secondary aure zasuyi shine rufin asirinmu baki daya.don haka kar in kuma jin ka sake Koran musu samari ba ruwanka kai da kk zuwa naka zancen Wa ya tanka?to ka kiyayeni wlh. Baiyi magana ba mikewa yayi ya fita. Nikam na kasa cin abinci saboda maganganun inna na Dade ina juya maganar a raina. Tunda na gama shan magunguna na na warware tass . Naje gaida kawu a daki na tarar kawuna na Abuja ma yazo .na gaishesu cike da fara,a suka amsa Abbansu salman ne yace " Rumaisa mamarki ta yi aure daurin auren mukayi dazu a kofar gidan nan. Kaina a sunkuye nace "Allah ya bada zaman lfy. Suce amin suna dariya sannan daddynsu salim yace " sai in ta tare za,a kaiki kinji? Nace to. Daga nan na mike na musu sai anjima. Ina fita muka tafi shago da sakina. Muna dawowa a kofar gida na hango ya salman zaune kan kujerar roba da wata tsugunne gefensa kanta sunkuye abin mamaki fuskarsa daukeda murmushi. Naja hannun sakina da sauri mukayi baya tace lfy? Nace"aa ya salman na gani da wata ko itace saliman naga har murmushi yake tayi dama yana dariya? Sakina ta yi dariya tace nima tun tashina ban taba ganin yana fara,a ba sai da Salima.yaya yana son Salima sosai amma iyayenta basaso sunfi so su hadata auren dangi da danuwanta kuma ma gidansu sai sunyi jamia tuku...... Na katseta da fadin dama bata gama secondary ba? Sakina tace kin ganta tafi girma ko ? Yarinya ce jin dadine kawai amma fa ta fimu don sa,ar su sadiyane yanzu zasu gama secondary. Tabe baki nayi nace nace hmm sun dace mu tafi. Mun iso kofar gida har zamu shige ya kirani Sakina kam ta yi ciki. Na dawo nace"gani. Yace in ba abinda kikeyi je ki share min dakina. Nace "to. Salima ce ta dago ta kalleni tace " wacece wnn ban Santa ba? Yace 'kanwatace. Haka kawai na tsinci kaina da jin haushinta. Harara na watsa mata nayi ciki. Kallonshi ta yi cikin mamaki tace"amma dai ba 'yar gidanku ba? Yace ke dai kin cika tambaya Tace kaga wata uban harara da ta buga min duk kannenka suna respecting dina amma ita ko gaisheni ba ta yi ba. Murmushi yayi yana kallon fuskarta snn yace " ki tashi kije gida kamin au Abba su fito su sameki kiji kunya. Tace ai na gaya maka yau nazo ne don ka kaini in gaida innahrmu. Ya mike yana to muje . Sun shiga cikin gida.har dakin inna ya kaita suka gaisa. Ta rikowa inna sayayya cike da Leda sabulan wanka ne da rurarrruka masu tsada sai Wanda ya gani.dayan ledan kuma juices ne kala kala. Inna sai waahe baki take tn zuba Godiya. Ya kai ta dakin mama ma suka gaisa sannan ya rakata har gida sannan ya dawo ya sameni har na gama sharar daki ina tsaye ina kallon hoton salima kato manne a dakin tn murmushi kyakkywace gaskia gata 'yar gayu. Ko da ya shigo baimin magana ya wuce abinsa ya fara cire shirt din jikinsa. Motsin da naji ne yasa na juyo da sauri sai ganin mutum nayi da vest ba Riga yana kokarin cire belt din wando ma. Zaro ido nayi a tsorace don ban taba ganinshi haka ba. Gashi kirar karfi ne da shi hannun nan a murde. Naja baya zan gudu kawai sai naci karo da stool Da zafin nama ya taroni don saura kiris in kife. A tsorace na rikeshi baice komi ba sai da na dawo hayyacina na ga yadda na masa kyakkyawan riko kunyane ya kamani. A hankali na cire hannuna da kyar na iya fadan "yi hakuri. Yace" zauna. Na zauna a kasa yace "gobe zan koma Lagos ki fada min abubuwanda baki dashi sai na siya miki don in na tafi zanyi watanni biyu a can. Ji nayi kamar ince kar ya tafi don ko ba komai su sadiya suna suna raga min in yana nan. Hawayene ya taru a idona har ya fara zubowa nace " babu komai. Shiru yayi yace "aa tuna dai? Na girgiza kai nace babu. Yace kina da man shafawa da sabulu? Nace aa Yace me sunan manki? Nace cocoa butter Yace " turare fa ? Nace "babu. Yace " wanne zan sya miki? Nace "smart collection ne mama ta ke saya min ko Vanilla. Ya gyada kai yace " pad fa.... Da sauri na sunkuyar da kai cikin jin kunya na kasa dago kaina. Yace " ko baki sanshi ba? Nace 'mama tana tsiyamin. Yace OK Ya sake cewa me size na bra dinki da pant. Shiru nayi kaina a ksa ganin banda niyyar magana yace au ba tambayarki nake ba kk min shiru? Har yanzu kaina a sunkuye nace ina da pant...kuma bana sa bra.... Yace" ke dai yar kauyece to me kk sawa a kasan kayanki? Nace "mama ta na saya min have vest. Yace" lallai Maman nan tn kokari wurin kula dake duk da a kauye kk. Ni dai duk na kosa yace in tafi . Can kuma ya dauko maganar makaranta yace " naji ana yabon kokarinki a makaranta ki Kara kinji kanwata ina son gaba daya dis year Ku rubuta ssce Wani irin dadi naji har nayi murmushi don babu abinda nake buri irin naganni a Jami,ar bayero da nake jin labarinta. Yace shikenan kince ba wani abu ko? Nace"aa yaya dama inaso in anyi Hutu inje gun Mamana. Ya girgiza kai yace mamanki amaryace bazakije ki takurata ba.za dai kije ki dawo in ta tare.amma in kina so in anyi Hutu zan yiwa salim magana yazo ya daukeki ya kaiki Abuja . Wani dadi naji zanje Abuja naji ance garin'yan Hutu ne da jin dadin rayuwa😀 Nayi murmushi nace "na gode yaya . Hannu ya daga min snn yace " kina iya tfy. Na tashi na fita ya bini da ido ya rasa dalili tausayina yake sosai don haka yake kokarin jawoni jiki yaji matsalolina amma shi bai iya sakin fuska irin na salim ba.duk yadda yaso ya sakar min fuska abin ya gagareshi. Ina shiga gida na tarar duk suna sakar kowa da goran juice a hannunsa ana sha ana zuba zance sadiya sai washe baki ake. Da shigata innah ta kalleni tace "tuntuni sai yanzu kk gama sharar dakin salman din?ni kinga har na gama rabiya na manta dake ungo ragowar nawa ki karasa sai kizo ki min kitso. Na kallesu nace 'bako akayi a gidan ne ya kawo abinsha. Sadiya tace " bakuwa ce aunty Salima matar da yaya zai aura itace ta kawo mn. A take fuskata ta sauya a raina nace shine suke ta rawar jiki..... Inna ta katseni da fadin ungo amshi mana. Na girgiza kai nace aa inna na koshi bari in dauko comb in zo muyi kitson. Na wuce ciki fuskata ba fara,a. Muna kitson ya salman ya shigo Inna tace yaje ya dauki juice ta ajiye mai a fridge din Abba yace ni bazan sha ba aba rumaisa. Inna tace "to ai taki sha ban Sani ba ko ta rainane don na bata kadan to in mun gama kije fridge din palon kawunki ki dauki na salman din. Nace " ni na koshi ne inna. Zata yi fada ya katseta da fadin rabu da ita inna 'yar kauyece bata San juice bane. Snn yace Inna gobe fa da sassafe zan koma in akwai wani abu a gaya min zan shiga kasuwa yanzu. Ta danyi shiru snn tace "ni ban bukatar komi kudi zaka bani. Yace " to zan turo muku Abba zai Baku. Shiru ta yi kamar bata so. Shi kam tashi yayi ya tafi. [05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 (👨🏻‍🚒Matar soja👨🏻‍🚒) _(Labarine da ya kunshi fadakarwa,Ilmantarwa da kuma Nishadantarwa_) Story and written By Maman khausar✍🏻 *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION* *[onward together]* *{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}* ```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑``` *```JUST GIVE US FOLLOW..** ```~BISMILLAHIRRAHMANI RAHEEM!~``` ➡page 5 Yaya salman kamin ya koma Lagos sai da ya saya min duk abinda nake bukata. Sannan ya ban dubu biyar yace in ajiye in wata bukata ta taso in dauka In kashe kuma ya gargade ni yace banda yawo. Naji kewa sosai duk da ba magana mai tsawo ke shiga tsakaninmu ba. Munyi exams an bamu Hutu na tsawon wata daya. A cikin week din ya salim yazo ya sauka a dakin ya salman ranar raba dare mukayi a dakinshi muna hira saida mmn sakina taxo ta kira mu tace mu bar shi ya huta. Washe gari kuwa muka shirya ya kaimu gidan mama dake borno avenue. Babban gida ne tsarin ginin zamani ga kayan alatu. Alhaji Aminu shine mijin mama shahararren Dan kasuwa ne matansa uku mamace cikon ta hudu yaransa goma sha shidda yawanci sunyi aure wasu kuma na makaranta . Ko wacce mace da sashinta da kuma masu aikinta. Wlh ko da naga irin jin dadi da Mamana ke ciki ji nayi kamar nayi zamana. Ta kawo mana kayan ciye ciye kala kala ga 'ya'yan itatuwa da lemon kwalba ga abinci iri iri. Muka bude ciki mukayita ci. Bayan munyi azahar ne ta kaimu dakunan kishiyoyinta muka gaggaisa har palon alhaji ta kaimu ya karbemu kamar yaran cikinsa. Ban samu na kebe da mama ba Sam saboda su sadiya har dare karfe 7 ya salim yazo yace mu tafi . Gaskia kishiyoyin mama suna da kirki ko wacce sai da ta cikamu da kaya. Shima Alhaji ba,a barsa a baya ba.kudi ya raba mana dubu goma goma. Anan mukayi sallama da kowa kamar ince zan kwana. Ganin yadda na bata fuska hawaye na kokarin zubowa yasa ya salim yaji tausayina yace " Goggo Amina rumaisa ta kwana jibi zanzo in dauketa...... Kafin ta yi magana har sadiya ta yi farat tace " to muma zamu kwa...... Tsawa ya salim yadaka mata"don Allah wuce mota malama .in kun kwana suwa zasu yi aikin gida. Suka shige mota nik am tuni na tafi gun mama. Yace "Goggo kamata yayi ma rumaisa ta miki sati saboda kun jima baku hadu ba amma zatayi kwana biyu kawai don ina so ranar Sunday mu wuce Abuja da ita tayi hutunta. Cike da fara,a mama tace babu komai salim na gode sosai Allah ya kaimu rai da lfy. Ya mata sallama nima na daga masa hannu ina murmushi. Motarsu na fita mukayi ciki da mama. Har bedroom na wuce na fada gado ina birgima ga AC. Mama ta yi murmushi tace to meye hakan kuma? Nace wlh mama rabona da in kwanta kan gado tun kauye a dakin inna a Palo nake kwanciya ni kadai akan kujera in ta jin tsoro kuma da asussuba take tashina in ran girkintane ta yi ta Sani aiki ga zagi da gori. Nan na tsinke da bada labarin su Inna . Tun mama na tsaye har ta gaji ta zauna ta na kallona . Har na gaya mata asma na ma ya tashi. Ta numfasa tace "hmm Allah shi kyauta shatu dai bata canza hali wlh ni dama dakin rabi kk zauna. Nace" ai yaya salman ne ya kaini dakinsu nima bana so. Tace kar ki damu ke dai kici gaba da musu biyaiya kiris ya rake idan kk tafi jamia hostel kawai zaki zauna.tunda salman yace zakuyi ssce dinku a ss2 Nace eh haka yace. Hira mukeyi har sha dayan dare bamu sani ba. Mama ne ta kalli agogo tace tashi kije bandaki kiyi wanka. Nace"mama sai kin nuna min yadda ake yin komi fa a bandakin naki. Dan dariya ta yi tace "wayyo rumaisa muje to. Muka shiga ta nuna min komi sannan ta fita. Bayan nayi wanka ta ban zaninta da t shirt na saka ina ma kaina dariya a madubi. Itama ta shiga ta yi ta shirya sannan muka kwanta. Bacci na rika yi da kyar na tashi nayi asuba na koma mama kyaleni tayi nayita sharar baccina har sha daya yunwa ya tashen. Nayi wanka nayi brush na shirya sannan mama tace in tafi dining inje in karya. Habawa nayita zuba kauyancina. Da wuri ya salim yazo ya daukeni don gobe zamu wuce Abuja. Mama ta bani waya. Karama Nokia tace in rike zamuna gaisawa.kuma ta bayarmin kaya kala bakwai amin dinki. Dadi kamar zai kasheni. Mun dawo da daddare ina parking inna ta sameni a daki. Tace" ke shirin me kk yi hakane? Nace " inna gobe ne tfyr tamu Abuja ai. Tabe baki tayi tace " shiyasa kk ta rawar jiki haka .kinje kun gama munafurci da uwarki sai shigewa salim kk.to me zaiyi dake waye yasan asalinki? Kaina a sunkuye tuni hawaye ya fara zubowa . Saida ta kare min zagi tass snn tace" ki tashi kije kiyi wanke wanke tunda sammako zakuyi ga kuma zanin gadona guda biyar na jika ki wanke tass sannan ruwan kumfan ki je ki wanke ban daki. In kin gama Na daura pepe soup na ganda a wuta kiyi hadi ki Kira ya nuna ki sauke.gobe da ssassafe ki tashi ki hura wuta ki dora ruwan shayi saura ki kuskura ki in tashi in sami ba kiyi min yadda nace ba kiga abinda zan miki. Ta na gamawa ta fita nasan dakin Abba zata tafi don yau gurkinta ne. Na kalli agogo karfe goma har yayi da sauri na tashi na fita wanke wanke nayi na gama na kama wanke bedsheets inayi ina duba girkina har na gama wankin naje na karasa parking ina zaune a Palo har saida na sauke pepe soup din sannan na kwwnta a gajiye . Asuban farko na Riga kowa tashi naje na hura huta na Dora ruwan tea snn na wanke ban daki don jiya naga dare yayi ina tsoro.wanka nayi nayi brush hade da alwala. Kamin inna ta fito har na shirya tsaf don har da ki da tsakar gida na share. Shida saura ta shigo ta sameni a shirye tsaf. Na gaisheta harara ta watsa min tace " kina ta rawar jiki zaki Abuja wai har kin gama aikin ne? Nace"I na gama Tabe baki ta yi ta shige ciki naji tana tashin su sadiya.daga bacci sai fada take musu. Bayan mun karya karfe bakwai muka dauki hanya. [05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` ➡ page 6 Mun isa Abuja lfy. Nikam sai kallon kauyanci nakeyi.lallai Abuja babban birnine . Gidan kawu kasim kam ba magana don ya tsaru iya tsaruwa kai gabadaya anguwan haka gidajen suke sai ka rikice ka rasa wanne yafi. Muna sauka sai ga fa'iza wacce take bin ya salim da kuma Dan karaminsu hakim. Da fara,a suka mana sannu da zuwa. Fa,iza ta dauki kayana mukayi ciki.anan naga mummynsu ita ma da fara,a tace" mutanen kano oyoyo marabanku da zuwa. Na Dan russuna nace" ina kwana aunty..... Cike da fara a tace" aa kinga' yata kuje ciki kiyi wanka ga breakfast na shirya muku a dining in kun gama kije ki kwanta ki huta. Ta dafa kafadana ta na murmushi tace" in yaso sai mu gaisa a nitse. Naji dadin yadda suka karbeni sosai. Faiza ta kaini dakinta ta nuna min ban daki nayi wanka na canza kaya na fito dining tuni ya salim da hakim kam suke jira. Anan fai,za ta musu serving ta kalleni tace" rumaisa me zan sa miki. Nayi murmushi nace komi ma na inaci. Tace"wow ya salim na sami ' yar uwa. Dariya yayi yace" sai kuyi ta ci. Itama dariyar ta yi sannan ta sakamin dankali soyayye da kwai sai pepper soup na kayan ciki.sannan ta tura min kayan tea itama ta hada nata Mun fara ci tace"wayyo ya salim na manta ban gaya maka abinda ya faru a BEYHAD ba. Ya salim yace" an wuceni sosai ko. Sai lokacin hakim yace" ya salim series ya fara dadi kasan me ya faru?...... Fa,iza tayi saurin fadin " MAYA ta kashe maman ARJUN. Da sauri yace "don Allah fa an kamata? Hakim yace ina za,a kamata ka mantata ne ai tuni ta yi makirci wai ta mutu arjun ya kasheta .aka kama arjun aka jefashi prison. Ya salim ya Dan dafe kai yace" ai dama nasan za,ayi haka.don she is very dangerous. Haka suka dinga hiran series har muka gama break fast.muka dawo Palo . Ya salim kam yana da saukin kai don hira yake da kannensa sosai ba kamar salman ba. Nan da nan na sake .faiza ta dinga koya min ado .yayinda mummy kuma take koya mn girki zamani kala kala. Yauma bayan mun fito daga kitchen wanka mukayi ina bayan mun gama shiryawa na kalli.fa,iza ina murmushi nace " faiza shigarki tn burgeni wlh naga ke baki damu da saka Riga da siket ko da zani ko wando sai dogayen riguna. Tace " ni banson abinda zai takurani ne rumaisa don nafi feeling free a cikin dogayen riguna. Ta karaso kusa dani ta zauna tace'kema in kina so ki fara sawa. Na tabe baki nace " ina na ga kayan ma tukun dududu dogayen rigunana basu wuce uku bane. Ta yi dariya tace " kar ki damu ina da sabbi na zaman gida guda biyar zan baki kuma nasan zamuje shopping in daddy ya dawo zai bamu kudi.sai ki zabi iya son...... Karar wayar ta ne ya katseta ta dauko sai naga ta saki murmushi ta daga hade da limshe ido tace" hello yaya. Ta danyi shiru snn tace"yaya munyi missing dinka sosai yaushe zaka zo Abuja? Ta sakeyin shiru snn tace " gata nan muna tare a bata ne? Da sauri ta mika min waya hade da fadin ya salman ne. Na karba da nasa a kunne nace" yaya ina wuni? Lfy.ya fada snn yace" me ye full Name dinki da kk using a school? Nace RUMAISA IBRAHIM AHMAD. Yace " OK Sannan ya kashe.na mikawa faiza nace ya kashe ta karba tana murmushi tace gaskia wnn guy din zai kasheni da sonsa. Zaro ido nayi ina kallonta nace waye faiza? Ta mika min wayar ta ina dubawa photon ya salman na gani cikin kakin sojoji. Rass naji gabana na faduwa na mika mata da sauri nace" faiza ai yaya salman ne me ya hadashi da kayan mugayen nan kuma? Dariya ta yi ta zauna tace" kina nufin baki San yaya soja bane? Na girgiza mata kai snn nace ban Sani ba wlh. Tace to soja ne ki Sani daga yau . A tsorace nace " ya rasa abinyi ne....... Dariya ta yi tace" aa ra,ayinsa ne kawai. Shiru nayi ban kuma cewa komi ba. Tace "wlh rumaisa son ya salman nake kamar zan mutu wlh ko rumaisa ni inaga zan fada masa kawai duk abinda zaiyi ma yayi na gaji da noke noke. Nan da nan annurin da ke fuskata ta gushe.na rasa dalilin da yasa maganar ta ya ban haushi. Har ta gane tace" lfy rumaisa . Nayi ajiyar zuciya nace" hmm faiza zanso ace ke ce matar ya salman amma kinsan ya salman ba wacce yake so kamar Salima to ya zakiyi ki cusa kanki ? Kuma inna ma dasu sadiya sonta suke kamar zasu hadiyeta tsabar alherinda take musu. Jikin fa,iza a mace tace " hmm ai rumaisa ni kaina nasan labarin wnn salimar tashi bansan ya zan yi ba sakina tace min yana sonta sosai. Nace abin takaici wlh kuma ma naji ance iyayenta sunce baza su bashi ita ba amma sai dagewa yake ko me ya gani a jikinta ne oho. Faiza ta danyi shiru snn tace" ni fa inaga daddy Na zan fadawa . Nace eh kin kawo shawara kuma wlh zasu amshi maganar hannu bibbiyu sabida zumunci ya kara dorewa.Allah dai ya sanya alheri. Tana murmushi tace amin sis Na gode da kulawarki gareni. Gaskia faiza ba karamin so takewa salman. Nayi wata Na daya Abuja .ana saura one week a bude school ya salim yace in shirya salman zaizo daga Lagos mu wuce kano tare. Kawu kasim ya bama aunty Zuwaira kudi masu yawan gaske yace akaini shopping Na sayi duk abinda nake so. Murna Na dinga yi nan muka shirya da faiza muka tafi da Momy gaskia nasha siyayya kam masha Allah. Har waya Na canza katuwa nima Na shigo gari. Ko da muka dawo faiza ne ta koya min yadda zan dinga amfani da wayar nan da nan Na gane komi. Wai sai ga rumaisa a Facebook,WhatsApp.har da Instagram Tunda na sami waya bana komai sai aikin danne danne. Fa,iza ta shigo da sallama ban ma jita ba ta wuce toilet wanka ta yi ta fito ta zauna gaban mirror ta fara kwalliya. Ajiye wayar nayi nace " to sai ina da wnn yammaci ko zamuje shan ice cream? Ta harareni ta cikin madubi tace " wani ice cream kinaga har ya salman ya kusa shigowq Abuja ban mushi kwalliya ba. Dariya nayi nace " to yanzu wnn adon duk na yayan ne? Ta yi fari da ido tace kwarai da gaske. Nace " yayi👍🏻 Ta tashi ta dauko dogon riganta na atamfa tasaka ta zauna ta murza daurin Dan kwali har gaban goshi ta zubo da gashi kan kafada. Dariya nayi nace abin naki fa da gaskene.to sis ya sunan daurin nan? Tace" sunansa" ture kaga tsiya" Na saka dariya nace aikuwa na gani matar soja Ta daga min gira hade da fadin " yessss Sannan ta dauko turare ta fara fesawa da sauri na tashi gudun kar ya shige min hanci. Aikuwa cikin rashin sa,a ina mikewa ta fesa setin hancina. Wayyo nan da nan na rikice numfashina ya sauya kirjina ya fara toshewa. Jifa ta yi da turaren ta kamani tana " na shiga uku rumaisa asma dinki ne ko sorry ina inhaler dinki. Da kyar na nuna mata jakana ta je ta dauko ta kawo min ta sa min a hanci ina shaka.amma Sam numfashina bai daidaita ba. Kawai ta kira Momy ganin halinda na shiga yasa Momy tace kar a bata lokaci mu tafi asibity. Muna zuwa aka min allura cikin jijiya cikin ikon Allah numfashina ya dawo dai dai.sannan muka dawo gida. A harabar gida muka ga ya salim da wani sanye da kayan soja. Nan naji zuciyata ta tsinke don tsabar tsoro don mu a kauye ko police ma gudunsa muke bare kuma soja. Muna fita suka karaso wurinmu. Da kyar na iya dagowa jin kamar muryar ya salman yana gausheda Momy. Aikuwa ina dagowa muka hada ido da sauri na sauke idona nayi ciki da sauri. Momy da ya salim har hada baki suke lfy rumaisa? Faiza ne ta yi dariya tace "tsoron ne taga ya salman da kaki.kunsan a kauye police ma na basu tsoro. Dariya sukayi gabadaya banda ya salman don shi haushi ma yaji. Momy tace " aikuwa gara ta cire wnn tsoron. Salman yace" Momy ina kk je ne haka? Momy tace" wlh tsautsayi ne faiza ta fesawa rumaisa turare a hanci shine ciwonta ya tashi .ba bata lokaci muka tafi asibity don dazun da kyar take numfashi ma. Ya salim yace" subhanallah! Allah ya bata lfy. Sukace Amin . Daga nan suka nufi Palo.faiza ta kalli salman murmushi tayi tace" yayana na shirya maka abinci da abinsha kala kala. Ba tare da ya kalleta ba yace" nagode. Bayan sallar isha muka hadu a dining. Da kyar na iya kallon ya salman ashe ya cire kakin nasa. Muka hada ido da sauri na sauke idona nace" ina wuni yaya? "Lfy " ya amsa. Daga nan naja bakina nayi shiru sai faiza da hakim suke ta zolayata yau dai na kasa sakewa bare in basu amsa. Muna gamawa na tashi zan wuce daki faiza tace" ke za.a fara BEYHADH yanzu ko kin manta ne? Nace" aa ni bacci zan yi. Ya salim yace " ko dai har yanzu ba kya jin dai dai ne? Na Dan yi murmushi nace " aa Alhamdulillahi naji sauki so nake inje in karasa parking inyi bacci da wuri saboda in tashi da wuri. Yace" OK to Allah ya tashe mu lfy. Nace " Amin. Hakim yace " aunty rumaisa ki tsaya ki gani mn. Harararsa nayi Na shige ciki. Fa,iza kam Na gefen ya salman akan kujera ko da muka hada ido ma gwalo ta min. Da safe kuwa muna gama breakfast muka je muka sallami daddy anan Na kara yi masa Godiya. Yace" babu komai rumaisa wani hutun ma kizo don munji dadin zuwanki. Momy tace kwarai kuwa. Murmushi nayi. Mun fito harabar gida . Na gaisheda ya salim sannan Na kalli ya salman shima ni ya zubawa ido Na rasa dalilin yawan kallona da yake tun jiya. Nace" yaya ina kwana. Yace lfy. Momy tace" salman ban yarda da kallon nan da kk mata ba . Murmushi yayi yace " Momy na ga 'yar kauyen ta canza ne gabadaya. Sukayi dariya Momy tace tukunna ma.kai dai in kana yi ka shigo daga ciki muyi ' yar gida gida kawai. Yace " Allah ya sawwaka ni me zan yi da 'yar kauye? Faiza ta yi Farat tace " yaya ni fa? Murtuke fuska yayi yace " ke ni sa,anki ne? Da sauri ta koma bayan Momy . Salim yayi dariya yace " kai dai kaje kayi tunani duk wacce kaga tafi dacewa da kai acikinsu. Momy tace " dukkansu ma zamu iya baka my son . Yace " Momy kuna magana a ga ban yaran nan sai su dauka da gaske su rainani.don Allah Ku bari. Ya kalleni yace" ke Dan Allah shiga mota. Dariya suke ta masa. Daga nan Momy ta mn addua faiza kam har da kuka nima sai da hawaye ya cicciko min ido . Har mun fara tfy yayi parking ya kalleni yace " yar kauye daura belt. Na fara lalubowa ganin zan bata masa lokaci yasa ya Dan kwanto jikina yaja belt ya daura min .cikin rashin sa,a hannunsa ya taba bakina sai ga Jan baki a hannun shirt dinsa ya fitar da shape din bakina mai kyau a jikin rigana. Ya kalli hannun rigar tsaki yayi yace " dubi yadda kk batan Riga da Jan bakinki anya ba da gangan kikayi. Saura kadan dariya ya subuce na matse nace" yi hakuri ban Sani ba ne. Baice komi ba ya tashi motar aikuwa gudu yake kamar zai tashi sama nikam kamar Na saki fitsari don tsoro kai ya salman bai da dadin sha,ani. Ranar da muka zo da ya salim a hankali yake tfy munata hirarmu har muka isa. Tsabar gudu sai gashi mun iso da wuri ni dai sai hamdala nake ganin mun isa lfy. Salima ne Na hango ta fito daga cikin gida. Nikam ina fito da kayana ko kallo bata ishen ba. Shine ma yana hangota ya saki murmushi kamar ba shi ba. Ta karaso cike da fara,a tace " oyoyo dear. Yace " ranki ya Dade gimbiyar mata.yaushe kk dawo? Tace hmm nima dazu Na dawo ai bansan kana Abuja da mun taho tare . Yace "waya gaya miki ina son ki yi taravelling by road ? Murmushi ta yi tace " to kaima ka daina. Murmushi yayi ya harde hannayensa kan kirji yana kallonta Anan ta ga Jan baki a hannun rigarsa nan da nan yanayin fuskarta ya sauya . Ta kalleni harara Na watsa mata naja akwatina. A fusace ta juya zata tafi yace" zo kiji Salima. Bata ma saurareshi ba tai tfyrta. Har zan shiga gida ya tsaida ni ya karaso yace" me kk mata ta yi fushi? Nace" ni ban mata komi ba. Hade fuskarsa yayi yace " Na lura da irin kallon banzan da kk mata wlh zan mugun bata miki.daga yau in kinganta ki girmama ta ki gaisheta kina jina ko. Cikin jin haushi Na amsa masa " eh . Ya wuce ciki Na bishi a baya. [05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` ➡ page 7 Ina dawowa washegari na tafi gidan mama. Nine ban dawo ba har ana gobe Monday driver ne ya dawo dani. Na sami ya salman a waje yana zaune shi kadai . Nan da nan na murtuke fuska don tun randa muka dawo Abuja da yamun magana akan Salima nake jin haushinshi. Da kyar na iya fadin " yaya ina wuni? Kai kawai ya daga min .nashiga ciki .daga inna harsu sadiya ba Wanda ya min ko sannu nima ban ce musu ba dakin mama na wuce muna hirar school da sakina. Tun ranar na daina kulasu in dai na gama aikina ciki zan koma inyi kwanciyata wayana nane abokin hira na a yanzu.in dai kaga fara,ata to na tafi mkrnta ne ko islamiyya. Har ya salman ya koma Lagos bana kulashi.dama ba wani kula juna muke ba. Lokaci na tfy gashi har mun kusa mu fara WAEC don haka Abba ya biya mana jamb dukanmu mukayi kuma duk mun ci sa,a sadiya ce kawai ta fadi faiza munyi waya tace ta haye. Haka nan WAEC and NECO nida sakina da faiza munci amma sadiya da raihana duk sun fadi. Bakin ciki gun Abba da ya salman ba,a magana inna dai ko ajikinta zugasu ma take suyi aure wai su huta.don har ta sami Abba da maganar. Yace shikenan tunda haka suka zaba ko wacce ta turo Wanda zata aura ko cikin satin zai musu aure. Inna kam farinciki sosai take. Da farko ya salman yaso ya roki Abba akan kar ya auradda su amma da ya tuna irin kwashe kwashen samarin da suke sadiya kam nata daban ma don har aka barta gaba kadan zata janyo musu a in kunya.don haka ya shafawa kansa lfy. Nidai ina shan Hutu gidan mama .har ma na sami admission na BUK sakina kuma ABU a tare da faiza. A haka aka saida maganar auren su sadiya .yanzu sati biyu ya rage. Dole na tattara na dawo don mu fara shirye shirye don mune kawayen raihana.faiza ma tazo.don haka a tare muke ta tsula tsiyarmu. Mama tazo sai dai a sashin kawu kasim ta sauka tare suke da momyn su salim na lura Sam Sam bata shiga harkar inna sai dai mmn sakina. 'Yan kamaroo sun cika gida inna sai fulatanci ake ta yi .kyawwawan mutane wlh gasu farare sannan na lura ko wacce mace bakinta baki irin na inna ko me suke shafawane oho. Ranar walima a wani filin ya salman da salim muka shirya zamuyi kuma kusa da gida ne sosai aka zo aka mana decorating din wurin yy kyau. Kawaye munsha ankon material mai kyau. Salima ma tazo anci adon nan kam kamar hauka sai ji da kanta take tana zuba yanga ta fito da iPad dinta sai hotuna take ma amare. Ni da faiza kam duk mun cika da haushinta faiza ta Ciro nata iPad din tace" rumaisa zo muje muma muyi photo. Na tashi muna rikeda hannun juna har muka isa inda saliman take faiza kam sai da tasan yadda ta yi ta bangajeta. Da sauri Salima ta juyo tace" malama ba kya ganine kk tureni. Faiza ta juyo ta kalleta a wulakance tace" o Ashe mutum na ture sorry fa. Wani irin kallo tayiwa faiza sannan tace" da gangan kk tureni kenan ...... Harara na sakar mata nace" ke Dan Allah yiwa mutane shiru an tureki din sai me? Ta yi saurin fadin ke banyi magana dake ba kija bakinki ki mn shiru na lura Sam bakida kunya. Na tako na isa gabanta na kalleta nace " Ashe kin gane .gaskiane banda kunya ko kadan kuma kk kuskura kk yi magana anan zaki ga yadda zan yi dake. Faiza ta harareta tace" kinji ai. Shiru ta yi tana kallonmu. Nace ' kuma wannan da kk gani itace matar da ya salman zai aura don haka ki daina mafarkin kece matar ya salman. Naja hannun faiza muka tafi. Dariya muka ringa yi nace faiza wlh ta tsorata. Faiza ta yi dariya tace ba dole ba? Ke koni ma na tsorata kinga yadda kk dunga bude mata wuta Ashe haka kk da tsiwa. Mukayi dariya. Nace " hmm kunsan me wlh idan ta fadawa ya salman zamu fuskanci hukunci sosai . Tace "kinsan Allah ban ko tunashi ba. Nayi dariya na ce " koni wlh hmm Allah dai ya somu in ba haka ba akwai matsala wlh. Washe garin daurin aure an kawo 'yan kidan kwarya . 'Yan matan kamaroo sai rawa suke. Koda muka shiga har mun ma fisu iyawa don haka kowa mu yake kallo. Momy da Mamana har spray suka mana. Muna cikin rawa sakina tazo tayiwa faiza rada. Faiza tazo nima cikin kunnena tace" ke ga ya salman ya shigo kuma ya ganmu sai kinga yadda yake jifanmu da wani irin...... Na juya ban ganshi ba nace" ke ni ban ganshi ba rabu dani. Tace " innace ta kira shi suna dakinta. Nace " ke shareshi don Allah. Dariya mukayi mukaci gaba da rawarmu. Da yamma tuni 'yan daukar amarya raihana sunzo don ita a zoo road za a kaita sadiya kuma a cikin unguwar tamu amma can gaba kadan. Don haka muka fita don ganawa da abokan ango.sai janmu suke da hira mu ta yi har da dariya in ka ganmu zaka dauka mun shekara tare. Kwatsam zai ga ya salman ya danno kai da motarsa .ni ban ganshi ba sai tadina nake sakina tuni ta yi cikin gida tana ce mn ga ya salman. Shareta mukayi ni da faiza. Koda ya sauko tsayawa yayi ya kare mn kallo ya gyada kai yayi cikin gida. Bayan an kai Amarya mu a can aka barmu sai washe gari aka sallamemu . A motar abokin ango muka dawo su biyu ne dayan yace yana sona daya kuma wai sakina.faiza kam da an tabota sai tace ai an mata miji. 🤭 Mun dawo dakin inna Na shiga na sameta da yan uwanta suna ta filatanci na gaishesu.tace " rumaisa har kun dawo? Nace eh Tace" ina kayan da nace ki amso min? Nace" inna wai ki bar mata duka bedsheets din tana so. Tace" ai raihana bata dama duk zata hada ta bata gashi ba wanki take so ba. Nace " inna ai gidan raihana ba irin gidan nan bane mai wanki mijinta zai samo mata. Tace" Allah yasa Nace " amin Tace" kije ciki ki dauko flaks din salman da kofinsa ki kai masa nasan baya son shiga gida cike da mutane ne. Ai sai da naji kirjina ya buga a sanyaye na tashi na shiga na dauka na tafi dakinsa. Nayi sallama jin ba,a amsa ba yasa nace ko yana waje don haka kai tsaye na shiga ina murna har da 'yan wake wake. Ina dagowa kawai karaf muka hada ido. Bansan sanda nace " wayyo .yaya kayi hakuri na dauka ko baka nan ne. Na russuna nace 'ina kwana? Kallona kawai yake baice min ko kala ba. A tsorace nace " dama inna ce tace in kawo maka tea dinka. Na ajiye na tashi zan fita yace " zo nan . Zaro ido nayi a tsorace nace" na,am? Yace " zaki zo ko sai na tashi ? Da sauri na isa gabanshi na durkusa . Bai kuma cewa komi ba naga dai yana daddana waya can yasa a kunne naji yace " Momy kice faiza tazo yanzun nan ina jiranta. Nikam na kara zaro ido jikina ya shiga rawa. Ba jimawa faiza ta shigo da alamu har ta soma bacci. Zama ta yi a kasa tace" yaya ina kwana? Kallonmu kawai yake mun dauki kusan minti biyar a haka . Sannan ya fara magana " duk kunsan me kk yi don da gangan kuka dinga rashin kunya son ranku . Ya kalli faiza wacce ta nitsu kunnenta ya cafko ya murda da karfi ta saki ihu Tsawa ya mata " shut up ! Sannan yace " Salima ta gaya abubuwa da kk yi mata na rashin mutunci .bansan faiza baki da hankali ba sai yanzu .don haka nake ja miki kunne akan Salima wlh wlh wlh Salima ta kuma ce min ko kallon banza kk mata kinsan saura. Ya kara murde mata kunne yace " irin abubuwanda kk dinga yi a bikin nan duk na gani kuma zan gayawa daddy ya miki aure karki fi haka lalacewa. Kuka faiza takeyi ya saki kunnen ta yace " tashi ki bar nan nonesense. Ta mike da sauri ta fita . Ya kalleni yace " ke kuma ..... Jin yayi shiru yasa na dago a tsorace.mukayi ido hudu na sunkuyar da kai nace" yaya don Allah kayi hakuri wlh na tuba wlh...... Hannu ya daga min sannan yace " me na gaya miki a baya akan Salima? Nace ' yaya faiza ce ta zage.. Ya katseni " keep quite before I bounce on you .an gaya miki bata fada min irin zaginda kk mata bane wlh ki kiyayeni kece baki sanni ba kar ki kuskura ki kaini bango don wlh bazai miki dadi ba. Hawayene ya fara zubo min nace " kayi hakuri bazan sake ba. Yace,kima sake in kinga dama . Ya danyi shiru sannan yace " daga yau idan na kuskura na kara ganinki da wani kuna tsaye ko a bayan idona naji labari zan mugun saba miki. Kamar yadda mamanki tace karatu za kiyi to karatun zakiyi kuma dolene ki cire tunanin aure a ranki don ba yanzu zakiyi ba.don haka ki maida hankali. Kamin ki kureni nayi miki mummunan hukunci. Kaina a sunkuye nace" kayi hakuri. Yace tashi ki ban guri..... Ai tun kan ya karasa na tashi abuna. Hauly ce👍🏻😍 [05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` ➡ page 8 Biki ya kare an watse gida sai mu. Ni da sakina tuni mun fara shirye shiryen mkrnt don har ya salman ya mn registration. Ina cikin dakin inna ya shigo a Palo ina jin yana cewa inna. " ina rumaisa ne? Tace " ina zaka ganta a waje Dan tsabar bakin hali a daki take zama kamar mayya. Yace" ai ki daina damun kanki inna ' yar kauyece. Tabe baki ta yi tace " lfy kk nemanta? Yace" eh so nake su shirya itada sakina suzo mu tafi suyi siyayya kayan bukatarsu na makaranta kinga a satin nan zasu tafi. Tace" yawwa zauna dama ina son magana da kai. Ya zauna yana ksllonta. Tace" na lura sai faman kashe kudi kk akan karatun wnn yarinyar lfyn ka kuwa yaushe ka fara aikin harda zaka dinga kashe kudinka a banza. Yace " inna naga ya dace ne in tsaya mata ta yi karatu ta cikawa mamanta burinta na son taga yarta ta yi karatu me zurfi kuma in kin lura rumaisa tana da ilimi uwa uba kwazo da kokari kinga ai bai kamata ace an barta a banza ba..... Ta katseshi da fadin " hmmm ina jiye maka tsoron shishigi da kk Wa yarinyan nan wlh .salman bari kaji in fada maka rumaisa bazata taba yin abin kirki ba in kun kaita jamia lalacewa zatayi domin halin uwarta tayo .dama zaku gane Ku lallaba Ku mata aure zai fiye muku sau dubu.ka daina bata kudinka a banza. Ya danyi shiru sannan yace" inna in Allah ya yarda ba abinda zai faru da ita ki mata fatan alheri. Tace " shikenan ,amma ka fita harkanta ka daina kashe kudinka akan ta.in kudi ne da kai ka fara gininka ka min nan in mahaifin Salima ya amince kayi aure yafi maka .in ba haka ba kuma ka bawa sadiyq da raihana jari su fara sana,a a gidajensu yafi maka alheri akan wnn asaran da kk yi .makarantar rumaisa bazai amfanar mn komi ba naga abbanku da alhaji kasim ma sai dagewa suke akanta suna ganin zatayi abun arziki hmm Allah ya kyauta. Yace" amin inna ina son ki daina damun kanki .gini dai mun fara tara kudi tare da salim a hankali zamuyi.snn sadiya da raihana daddy yace zai basu kudi suyi jari.kuma duk kudin nan da kk ganin nake kashewa rumaisa ba duka kudina bane goggo Amina tana turo kudi yanzu ma ita ta turo min dubu Dari biyu tace ayima sakina da rumaisa siyayya.... Inna ta Dan zaro ido tace " dubu Dari biyu ! Aminan? Me takeyi haka? Kai tsaye yace" kasuwanci mn kinsan ta na da kokarin nema tun a kauyema bare yanzu ta na cikin gari kuma mijinta babban mutum ne kin Sani. Ta Dan tabe baki tace da kyau kaje ta na ciki inaga bacci take. Yace" to Ya same ni a daki rufe idona nayi kamar me bacci. Tsayawa yayi yana kare min kallo sanye nake da dogon Riga marar hannu irin roba dinnan yabi jikina sosai. Kamar kullum gashina ko parking babu haka na sake shi har ya Dan rufen fuska don kiwiyan parking nakeyi don yawan gashin bana iya gyarawa ni daya mama ne mai gyara min nan kuma sakina ce ko zainab suke tayani.yanzu ma rabon in gyara har na manta haka nake sakeshi ko in kama in daure don ko kitso ba mai son yi min. Dan ajiyar zuciya yayi a ransa fadi yake" kamar aljana Allah na tuba. Pillow da nake kwance ya bubbuga da kyar na iya bude ido .kamar mai bacci gaske. Na kalleshi fuskarsa ba fara,a yace" ki tashi ki shirya ina jiranku keda sakina a waje. Na tashi a hankali na zauna mika nayi sosai hade da salati na turo kirjina gaba. Kauda kai yayi da sauri don yaji wani iri a jikinsa. Yace" kiyi sauri inada wurin zuwa da yawa. Yana fada ya fita.nima bayansa nabi inna na Palo bance mata komi ba na fita na Debi ruwa a bucket na shiga wanka.a gurguje na shirya muka fita da sakina muka samu yana jiranmu a mota baya na shiga sakina a gaba. Mun Dade a kasuwa don ba abinda bamu tsiya ba. Mun kai kwana uku muna parking. Sakina ta rigani tfy don saida ya salman ya kaita ya dawo kamin nan nima na je na sallami mama nasiha ta min sosai akai rayuwar jamia Haka nan Abba ma da mmn sakina inna kam cewa tayi"ayi dai mu gani. Ko kadan bata farin ciki da tfyrta mkrnt. Ya salman kam yaja min kunne sosai a gameda kawayen banza da kuma samari. A ranar da ya kaini shima ya koma Lagos. Randa muka fara lectures na hadu da Salima itama Ashe bangarenmu daya accounting muke. Ko kallo bamu ishi juna ba. A hostel dakinmu mu hudu ne da wata Maryam sai blessing da Juliet .dukansu shaidanu ne 'yan duniya.don haka ni na zama wawiya a tsakaninsu.kuma na lura blessing kam tana shaye shaye ma.don har wani abu take dashi naji suna ce masa shisha har ce min tayi baya bugarwa kawai yana sanya nishadi ne a zuciya koni in ina so zan iya sha. Nace mata aa nagode. Binsu nake da kallo kamar wata wawiya gashi basa son suturta jikinsu sai su tsaya su tube kayansu gabadaya haihuwar uwarsu amma ko a jikinsu haka suke fita har corridor🤦🏻‍♀ Ni dai gaskia inaga canza daki zan yi ina tsoron zama da gurbatattun mutane gaskia. Hauly ce👍🏻😍 [05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` ➡ page 9⃣➡1⃣0⃣ Zuwa yanzu kam na saba da makaranta nima na kara wayewa da kuma gogewa domin gaskia Jami,a kam duk Wanda ya samu ya shiga dole kawai ya waye. Muna waya da fa,iza da sakina sosai suna fama da ABU dinsu su kam sai anyi hutu zasu dawo amma ni ko wani asabar in mun gama lectures gidan mama nake tfy sai Monday nake sammako na dawo makaranta. Akwai wani satin da mama bata gari sun tafi umrah da maigidanta. Don haka gidan kawu na koma asabar da yamma mai adaidaita ya saukeni a kofar gidan na sauka na biya kudin sannan na shiga ciki a tsakar gidan na samesu gabadaya har kawu inna ke girki mmn sakina na wanki zainab na shara kawu na zaune a kan kujera. Nayi sallama kawu ya amsa cike da fara,a yace" maraba da ' yar jamia. Murmushi nayi nace" yawwa . Maman sakina da zainab suka min sannu da zuwa inna kam sai cewa ta yi sai yau kk ga daman zuwa ki ganmu da ke uwarki bata gari? Murmushi nayi nace"aa inna wnn karon dama ko mama na gari ma nan nayi niyyar tahowa. Tace" ba wani ke dai..... Kawu ya katseta da fadin" kya bata ruwa tasha tukunna dai ko? Mmn sakina tace" gaskia kam.zainab jeki palon abbanki ki kawowa rumaisa ruwa a fridge. Nace" na gode mama amma banjin kishin ruwa. An an na gaida kawu yana tambayata labarin makaranta mun jima muna tattaunawa dashi .sannan daga bisani muka gaisa dasu inna na wuce dakinta na canzo kaya na fito na karbawa inna girkin. Bayan sallar isha na tafi gidan sadiya wacce rabona da gidanta tun aure. Gaskia banji dadin yanayin da na sami gidan sadiya ba gabadaya kamar ta yi shekara biyar alhalin ko haihuwa batayi ba gida duk kazanta ga tarin kayan wanki ga wanke wanke abinka da damina kuma ko ta ina a jijjike sai karni ke tashi ba karamin daurewa nayi ba na shiga palon da sallama. Da kyar ta amsa min tana kwance duk ta yi baki ta rame. Muna hada ido tace " dama kece kk doka sallama kamar wata bakuwa? Tsabar haushinta ko zama na kasa yi nace" yo ba dole in ta doka sallama ai na ma dauka kun kaura don gidan naku baiyi kama da gidan amare ba.sadiya me haka me zan gani? Dan tsaki ta yi tace " ba kya ganin halin da nake ciki ne? Ta fadi hakan yayinda ta jawo wani gwangawani ta bude ta zuba yawu.😜 Kauda kai nayi da sauri ina toshe hancina. Cikin jin haushi tace " banson iskancifa rumaisa .in rashin kunya kk zo kiyi min na rokeki ki fita ki bar min gida. Girgiza kai nayi nace" Sam Sam bashi ya kawoni ba nazo na gaisheki ne dama. Tace " to ki zauna mn kin tsaya min akai kamar kina bina bashi. A kyamace nake ganin ko ina nace" ni bazan iya zama a gidan nan ba sadiya.amma me zai hana tunda baki da lfy ja,afar ya samo miki yarinya wacce zata miki su shara kamin nan ki sami lfy amma zama cikin kazanta haka babban matsalace wlh zaki iya samin damuwa da mijinki wlh.ni bazan iya dogon bayani ba don gaskia karni ta ishen zan daure na dawo gobe tare da zainab inga abinda zamu iya yi miki a gidan. Ban saurari me zatace ba na juya ko sallama ban mata ba na fita . A get din fita na hadu da ja,afar muka gaisa da fara,a yace " ya makaranta ? Nace Alhamdulillah muna fama. Yace to Allah ya taimaka . Nace" amin nagode. Har zan wuce yace" am rumaisah baki ji bah. Juyowa nayi nace" Na,am. Ya danyi shiru sannan yace" matsalar yayarki sadiya ne wlh ya fara isata a gidan nan wlh kwanan nan duk inata tunanin ko gida zan turata kawai ta huta. Nace" subhanallah me ya faru yaya ja,afar. Yace rumaisah sadiya tunda ta sami ciki ta koyi lalaci da kazanta bata kula da komi Na gidan nan ko girki ma batayi wlh ni gabadaya na gaji da da abinda sadiya keyi a gidan nan. Nace " kayi hakuri ya jafar amma kasan da ba haka take ba laulayi ne ya maidata haka.kuma insha Allah in Allah ya safketa lfy zata koma kamar yanda kk so dinnan. Ya danyi shiru sannan yace hmm lamarin sadiya sai addua nafa dauko mata yarinya domin ya dinga kula da gida amma sai ta dinga zargen wai son yarinyar nake. Murmushi nayi nace ya jafar kasan sadiya tana sonka sosai shiyasa take kishinka don Allah ka kara hkr inshaa Allah komi zai wuce. Yace to shikenan rumaisah tunda kin dai ki laifin ' yar uwar taki. Dariya nayi nace " ni na isa ne ? Yace amma dai ki gayawa inna tayiwa sadiya fada ta dinga hkr a rayuwq. Nace insha Allah . Daga nan mukayi sallama na dawo gida .daki na wuce na dauko handout dina na fara karatu knn naji karar wayata ina dubawa naga ya salman ne. Dan murmushi nayi sannan na dauka sallama nayi masa kamar kullum can kasan makoshinsa ya amsa. Murmushi nayi nace " yaya ina wuni? Yace lfy Nace " ya aiki? Yace " kin cika dogon gaisuwa .zanzo kano gobe insha Allah inna tace min kinzo so nake kije gidanmu ki share man dakinmu salim ma zaizo. Nace " babu damuwa yaya. Yace " yawwa nagode. Daga nan kashewa yayi har lokacin fuskata daukeda murmushi .gaskia na gama yarda tuni zuciyata ta fara dawainiya da son ya salman da dai nakan karyata zuciyata amma yanzu na yarda sonshi nake shiyasa a koda yaushe burina bai wuce inga na raba shi da Salima ba. Inna ce ta shigo ta sameni ta zauna a gefan gadon tace" ya kk sami sadiyan? Mikewa nayi na zauna sannan na kalli inna duk da ina tsoron yadda zata karbi maganar amma hakan nan na dake na fada mata komai. Aikuwa ranta ya balain baci tace amma sadiya anyi lalatacciyar yarinya mai taurin kan tsiya.a zamanin yanzun nan wani namiji ne zai yarda da wnn halin kazantar? So take taja mana balai ko ya kara aure ko ya shiga neme nemen mata daga karshe ya sakota ta dawo gida wayyo ni shatu ka haifi da baka haifi halinsa ba wlh. Nace hmm kiyi hakuri inna dama so nake gobe muje da zainab muyi mata shara da goge goge mu gyre koina mu tattara kayan wanki mu ba ko almijiri ya wanke .in yaso daga nan sai a sami wacce zata zauna da ita. Tace" gashi salman yace suma zaki share musu dakinsu kuma zai turo shefane ayi musu girki .don haka kawai ke ki zauna ki masu aikin don ni bazan iya girke girken Ku na zamani ba. Nace" sadiyan fa..... Ta katseni da fadin barni da ' yar banza zanje da kaina in ci ubanta Mara kunya.so take ta tona mana asiri ina zaune Qalau. Ta mike ta fita nikam tabe baki nayi naci gaba da karatuna har bacci ya kwasheni. Naso na makara da kyar na tashi nayi sallar asuba daga nan ban koma na karbi makullin gidan su na tafi . Ban tsaya bata lokaci ba na share tsaf nayi moping na wanke toilet na canza bedsheets da yake kowanne da dakinsa Palo a tsakiya da toilet a coridoor .na fesa roomfresh ta ko ina na rufe na dawo gida karfe . Ina kwance ya salman ya kira na dauka na gaisheshi Kamar kullum ya amsa da lfy sannan yace " kin mana sharan? Nace" eh har na gama. Yace" good.na tura sadiq kasuwa zai kawo miki cefane ki mn girki ni tuwon semo nake so da miyar kubewa sai kunu. Salim yace fried rice da pepper chicken sai fruit salad . Murmushi nayi nace babu damuwa yaya Allah ya kawo Ku lfy. Yace" ameen. Daga nan ya kashe. Azahar na gama komai har na kai musu .na dawo sai lokacin su inna suka dawo daga gidan sadiya ta cire hijabinta ta kalleni tace " Allah sa dai kin gama don yunwa nakeji ko ruwa bansha ba tunda mukaje dama azumi na dauka. Nace " to Inna me yasa? Ta harareni tace a gidan sadiya kk so naje na bude ciki nayi ta ci ai dadewar da nayi ma kamawa ta yi dole don so nake inga koina yayi fes sannan hankalina ya kwanta. Dariya ne yaso ya kubuce min na kanne na je palon Abba na dauko mata ruwa mai sanyi sannan na dauko mana kulan abunci da plets. Tace" wai ina Rabi ne? Nace " ta shiga wanka. Tace" to gaskia bazan jirata ba in tazo taci tare daku. Nace sai dai Zainab don gaskia ni sai nayi wanka ji nake ko ina jikina karni da warin hayaki. Bata ce komi ba taci gaba da diban abinci. Bayan nayi wanka zama nayi na bata lokaci wurin tsara ado.dogon rigana saka na atamfa green Wanda yasha stone work na dage na daura dankwali gashina yasha parking har gadon baya na dauko akwatin sarkana don in zaba sai naji sallamar ya salim anan naji su inna na musu sannu da hanya nayi maza na gama sakawa har zan fita kiran fa,iza ya shigo wayata kamar bazan dauka ba na daure na daga nace " hello sis ya kk? Tace" qalau 'yar uwa don Allah rumaisa ki kulan min da Sojana naji suna kano dazu ya salim ke shaida min wai zasuyi bikin abokinsu don Allah kar ki bari waccar banzar taje kusa dashi. Jikina ne ya mutu nace" hmm faiza kema kinsan ban isa in hana Salima zuwa kusa da yaya salman ba. Tace O my God wlh rumaisa wannan karon muna samun Hutu kano zanzo shawararki zanbi kawai in cire kunya in fadawa kawu ko ya kk gani? Tunda shi har yanzu ko kallo ban ishe shi ba. Gabadaya naji maganar ta gundureni na dai daure nace"eh hakan zaifi ai sis akan ki ta zama kina wahalar da kanki kullum ai gwara ayita ta kare. Tace" shikenan sis hakan za,ayi kawai.na gode da shawarwarinki gareni. Nace" babu komai sis.bari inzo I will call you back. Ban saurareta ba na katse wayar . Dafe kai nayi nace wayyoni rumaisa gaskia gara in koya Wa zuciyata hkr da son ya salman data fara domin fa,iza ta fini sonsa gefe guda kuma ga Salima . Dan tsaki nayi a dai dai lokacin da naji inna na kwalan kira na tashi da sauri ina amsawa na fito tace" ana ta kira ni na dauka bacci kk.to yi maza ki kai musu makulli ke suke jira. Da sauri na koma daki na dauko key da gyalena na fita tuni har sun shiga suna jirana a coridoor su ukune tare da wani da ban sanshi ba. Tundaga nesa suke kallona nikam duk na tsargu na dai karaso kaina a sunkuye nace" barkanku da zuwa. Ya salim ne da mutumin suka amsa.na rasa Wa zan baiwa key din kawai na wuce na bude musu kofa. Nace" bismillah. Ya salim yace "yawwa mun gode 'yar uwa. Murmushi nayi .ina tsaye suka wuce ciki ya salman kamin ya shiga ya kalleni yayi kasa kasa da murya yace" tafi kije ki sanyo hijabi sai yawo kk tsirara a cikin mutane kefa ' yar kauyece. Haushi naji shikam tuni ya wuce.wai har yanzu bazai bar ce min ' yar kauye bane? Da sauri na bar gidan na dawo ai ko minti biyar banyi ba ya Kira ni wai nazo nayi serving nasu. Haka na tashi na saka hijabi na sake komawa . Na tarar tuni ya salim da abokin shi sun fara cin abinci shi kam ya salman yana wanka. Anan na zauna na gaishesu ya salim yana zolayata yace" rumaisa kinga Ra'is sai santi yake ni na masa waigi. Sunkuyar da kai nayi ina murmushi . Murmushi yayi yace" hakane girkin yayi dadi kwarai da gaske kanwata. Nima murmushi nayi nace" nagode sosai. Ya salim yace " rumaisa wannan shine abokinmu Ra'is ko kina jin sunansa gun faiza shekararsa biyu a Malaysia sai cikin satin nan ya dawo. Nace " Ayya da fatan ka dawo lfy. Yace lfy lau kanwata ya karatu? Nace Alhamdulillah muna fama Yace " Allah ya taimaka. Nace " amin. Anan ya salman ya fito sanye da 3 quarter da rigan shan iska. Ya zauna kan kujera yace " sai yanzu naji normal. Ya salim yace" kai dai ka saba da sanyin Lagos in ba haka ba aini dai dai nakeji ba wani zafi. Ya salman yace" kai dama can ai bajin zafi kk ba. Ya kalleni tace " a min serving yanzu na shirya. Nace "to Nan na mishi serving tuwon semo miyar kubewa na cika masa kunu a cup na kawo masa ruwan wanke hannu. Nan suka shiga zolayarsa wai shi dan gargajiya ne. Baima kulasu ba.ni dai ya hanani tfy sai da ya gama Na tattara na gyre wurin tsaf sannan ya barni na tafi duk na gaji. Da sassafe kuwa na tashi na shirya tfy makaranta don muna da lectures karfe 7:00. Lokacin da na fita na sameshi a waje shikadai sanyeda kayan motsa jiki. Na Dan rage tsawo" yaya ina kwana? Ya dago da alamun yanzu ya ganni yace" lfy . Daga nan na wuce don ko na kara bazai amsa ba. Kamin na isa kan titi sai gashi nan da mota ya sauke glass yace min " zagayo Ba musu na zagaya na bude na shiga snn na rufe baice min komai ba yaja muka tafi har muka isa sannan yace min" yaushe zaku taso. Na danyi shiru sannan nace " karfe biyar. Yace " zanzo in daukeki mu koma gida. "To" kawai naçe masa. Daga nan na sauka na tafi har na danyi nitsa na juya sai naga har lokacin bai tafi ba ko me yasa oho. Da yamma kuwa mun tashi banje hostel ba ina jiran shi nida Maryam ne muna cikin hira sai ka wata bakar mota ta yi parking a gabanmu kyan motar ya dauki hankalinmu sosai ni da Maryam. Mun shagala da kallo har mai motar ya fito wani saurayi ne Dan gayu dogo kyakkyawa ya fito sanyeda 3 quarter da t shirt kansa kuwa ya tara gashi Wanda yasha gyara idonsa sanye da bakar glass. Lokaci daya muka kalli juna da Maryam sannan muka kalleshi murmushi naga ya sakar min hade da daga gira yayinda ya cire glass ya karaso gabanmu . Ban taba tunanin sallama a bakinsa sai kuwa naji ya mana cikakken sallama . Maryam ce ta amsa nikam kauda kai nayi.ina jinsu suna gaisawa sannan yace" kawar taki bata magana ne? Maryam tace " tanayi mn. Yace" ni ai gabadaya wurinta nazo amma kuma sai ta juya min baya. Maryam tace" to ko na baku waje ne. Ta fada yayinda ta mike nace" don Allah kiyi zamanki ba inda zaki Tace" ke dai bari na dan baku waje. Da sauri na mike nima nace" muje kawai. Shima yazo gabana da sauri yace" haba baby bai kamata ki min haka ba wlh saboda ke na shigo BUK a irin wnn lokacin pls ko bazakice komi ba ki dan bani lokaci da zamu hadu da kuma contact dinki. Maryam dai tuni ta yi gaba. Kallonshi nayi cikin jin haushi nace" malam ban sanka baka sanni ba bamu taba haduwa in dau number ta in baka? To kaga nifa ba irin ' yan matan da kk tunani bane don haka ka kama gabanka. Murmushi ya yi yace" na Sani ke nitsassiya ce mai tarbiya da kamun kai shiyasa ma nazo gareki domin in Isar da sakon zuciyata.ni sunana AHMAD mahaifina Alhaji Umar Affan ma,ana GOV kano state.pls ki daure..... Na katseshi da fadin " naji kuma na gode amma ni bazan fada maka wacece ni ba. Ya sake fadada murmushi yace" nop ba sai kin fada ba na Sani.sunanki RUMAISA IBRAHIM. Kallonshi nayi da mamaki ya daga min gira yana murmushi na kauda kai kamin nace wani abu wayata ya soma ringing da sauri na ciro ta a jaka ina dubawa naga ya salman ne sai da zuciyata ta tsinke .a tsorace na dauka kamin nayi magana yace " gani nan ina jiranki. Ya kashe ina juyawa gefe naga motarsa can yana tsaye ya harde hannayensa a kan kirji yana hangomu. Ai da sauri na wuce na bar wnn sarkin nacin a gurin . Ya salman hade fuska ya yi sosai idonsa har ya sauya yana kallona rai bace yace"waye wancan dan iskan da kk tsaye dashi? Aikuwa hanjin cikina har rawa suke don tsoro nace" nima yau na ganshi ...... Ya katseni da tsawa " zaki fada min gaskia ko sai naje na sameshi naci ubanshi tukun? Jikina har rawa yake nace " wlh wlh wlh yaya yau na fara ganinshi nima. Ya daka min tsawa" shiga mota mu tafi. Da sauri na zagaya na shiga tuni hawaye ya fara bin kumatuna don bana son fada a rayuwata. Yana tsaye har Ahmad yazo ya wuce da motarsa sannan ya shigo mota ya kalleni yace " bari na miki first and last warning idan na kara ganinki da wannan dan iskan kai ko labari aka bani wlh na lahira sai yafi ki jin dadi kinaji na ai? Na daga nasa kai a tsorace .ya tashi motar rai a bace ya fizgeta da gudu nikam da sauri naja belt na daura. Kamin mu isa gida ya zagi mutane sunfi goma a hanya alhali kuwa shi yake tukin ganganci kana ganin fuskarsa kasan yanaji da bala,i don ma anci sa,a ba Wanda ya tanka masa da sunsha Mari waya Sani ma ko alluransa ne suka motsa. Allah dai ya dawo mu gida lfy da sauri na fita ina hamdala a raina na wuce cikin gida ana na sami inna da mmn sakina suna ma sadiya fada ita kam said kuka take har zan tambaya me ya faru sai ga ya salman ya shigo fuskar na a murtuke don haka shiru nayi Ya na ganin sadiya yace" ke kuma me aka miki kk kuka? Inna ta karba me za a mata kuwa ? Dadine ya isheta wai jafar yace bazai dauko mata mai aiki ba sai ma ya turo kanwarsa tazo ta zauna da ita.don haka ba zata iya zama da yarinyar ba ta dawo . "Ta dawo? Ya fada cike da mamaki. Ya kalli Sadiya yace" ke tashi ki tafi Ta kara fashewa da kuka tace"yaya wlh son yarinyar yake cin amanata suke ni bazan zauna da jafar ba... Ya katseta da fadin rufe min baki dan Allah dama bakisan Dan iska bane kk aura ko hauka zaki manna mana? Run muna shiri da juna ki tashi ki bar gidan nan. Ta kara turbunewa tace" ni wlh ba Inda zan je sai dai in ta bar gidan . Yace " OK taurin kai zaki min ? Ya fara kunce belt a kugunsa ido na zaro nayi ciki da gudu kar ya hada dani . Sadiya ko kan ta ankare tuni ya fara sauke mata belt ko ta ina baya ko sararawa . Ihu take yi tana wayyo inna yaya zai kasheni wayyo mama don Allah yaya kayi hkr zan koma Inna kam shiru ta yi tana kallonsu sai da mmn Sakina ta tashi ta rike hannun ya salman tace " salman lfyrka kk dukan matar mutum da ciki? Ka Wa Allah ka barta zata koma ai . Ya kalli sadiya rai bace yace zaki tashi ki tafi ko sai na kashe ki da duka? Aikuwa da sauri ta mike takalminta a hannu ta yi waje. Ya bita a baya. Nikam sai godewa Allah bake da bai rufeni da duka dazu ba. Na idar da sallar isha inna tace nazo na dauki abincinsu kamar nace mata bazani ba don tsoro haka na daure don zainab bata nan . Na isa gidan har zanshiga Palo na jiyo muryarsa yana fada kasancewar kofa a bude na danyi baya na ajiye abincin a bakin kofa har na juya sai naji yace" look Salima in har sai Ahmad zai auri rumaisane kamin a bani aurenki to sai dai a bari don wlh bazan taba yarda Ahmad ya hurewa rumaisa kunne ba. Na zaro ido yayinda na dafe kirji . Sai naji muryarta cikin tsigar lallashi ta na" my dear don Allah ka bar Ya Ahmad yaci gaba da soyayya da rumaisa hakan shine zaisa daddy na ya yarda muyi aure kaga fa tuntuni kk so a fara maganar aurenmu amma su dad sunki saboda ya Ahmad to yanzu Allah ya karbi rokonmu ya Ahmad ya daina kulani yanzu ya dawo rumaisa yake so baka ganin wannan wata damace muka samu..... Ya katseta da fadin " sai yanzu na fahimceki Salima ke muguwace .nifa bari kiji ba don komai na jajrce da son aurenki sai don ina tausayin hadaki da Ahmad da za,ayi don kinfi kowa San in halinsa na shaye shaye da koyawa yaran mutane tantiranci.amma ke kina cewa wai na amince Ahmad ya batawa kanwata rayuwarta ? Don kawai in aureki to bari na sake jaddada miki Salima idan akan rumaisa ta yi soyaiya da Ahmad gwara na rabu dake. Muryanta naji ta na kuka tace " shikenan dama ba sona kk ba yaudarace kawai na gode. Nima tuni na fara sheshshekar kuka ban ma San ta fita ba .sai jin muryar ya salman nayi kusa dani yana " Rumaisa me ya sameki? Na dago fuskata da ya jike da hawaye na kalleshi amma sai na kasa magana kawai durkusawa nayi gabansa naci gaba da kuka. Jikinsa a mace yake kallona...... Hauly ce👍🏻😍...... [05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 _Wannan_ _page_ _naki_ _ne_ *UMMI* *ABDALLAH* _na_ _gode_ _kwarai_ _da_ _irin_ _kulawarki_ _gareni_ _Allah_ _ya_ _saka_ _da_ _alheri_ 🥰🥰😀👏🏻 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page1⃣1⃣ Ya daure yace" shikenan taso muje ciki. Ba musu na tashi na dauki abincinsu ya wuce gaba na bishi baya. Bayan mun zauna ya dan numfasa yace" bansan me yasa kk kuka ba amma dai nasan kinji maganata Salima. Rumaisa ko dai kina son Ahmad? Girgiza kai nayi nace" yaya ni bansanshi yau ne haduwarmu ta farko kuma ni dama banjin zan soshi. Yayi ajiyar zuciya sannan yace " to meyasa kk kuka? Na share hawayen da ya ke zubowa nace" bana son ace nice silar rabuwarka da Salima bayan kun dade kuna soyayya. Shiru yy tsawon lokaci na dauka ma ko maganar tawa ta bata masa rai ne har ya kasa magana. Don haka nayi kasa da murya nace" kayi hkr idan maganar da nayi ta.... Ya girgiza kai yace" baki bata min rai ba.kawai abinda nake son ince miki shine ki dinga sanin irin mutanen da zaki na mu,amala dasu.domin duniya ta zama abin tsoro. Na gyada kai nace" hakane yaya Yace " bansani ba kila kina da ra,ayin yin aure idan kk sami Wanda kk so.bazan hanaki ba kar ki ga abinda ya faru dazu kiji tsoro.sai dai faa ki Sani bazan taba yarda ki auri mutumin da bai cancanta domin nayiwa goggo Amina alkawarin zan kula da dukkan lamuranki don haka bazan taba yarda kiyi mu,amala da gubatattun mutane ba.ki kula da kyau. Na daga mishi kai hade da fadin insha Allah yaya bazan watsa ma kasa a ido ba. Yace " shikenan kina iya tfy. Na dan Sosa kai nace" uhmm yaya dama.... Nayi shiru na rasa ta inda zan fara maganar. Shiru yayi yana saurarena jin nayi shiru yasa shi fadin" shikenan ki tafi sai kin tuno jeki. Na daure nace" yaya dama shawarace nake son in baka in ranka bazai baci ba. Yace" ina jinki. Na Sosa kai nace" uhm dama dama....nace ....me ..zai zai hana idan iyayen Salima sunki ka aureta.....ka ...auri ...uhm uhmm....faiza kawai. Ina gama fada naji zuciyata na bugawa ina jiran saukan tuni na dafe kumatuna da hannuna duka biyu. Duk abinda nake yana kallona sannan yace" sai dai ki nemo min wata amma fa,iza kam tuni wani ya rigani. Na girgiza kai nace" bata da kowa yaya take so. Kai tsaye yace " bana son ta ki nemo min wata kawai yanzu ina nan ina jira sai naji daga gareki.tashi kije dare nayi. Na mike jikina ba kwari bakina ya Jan yo min masifa ni ina nasan zan samowa ya salman budurwa.gaskia fa,iza da ya salman sun Sani a matsala babba. Da wnn tunanin na bar dakin shikam bina yayi da ido har na fita na hadu da ya salim da rais a waje sun dawo a mota muka gaisa ya salim yacewa ra,is " baka gani ba saboda ita salman yaki yarda muje meeting din friends wai ya gaji wato so yake mu tafi ya samu yy hira da rumaisa. Murmushi nayi nace" kai yaya ba fa haka bane abinci na kawo muku yanzu. Ra,is yayi murmushi yace" ba wani nan mun ganoku tuni. Dariya nayi nace" wlh ba komi abincinku na kawo. Ya salim yace" shikenan idan tayi tsami ma ji. Ni dai na musu sai da safe na wuce gida.ina Allah Allah kar In sami inna a daki. Aikuwa banci sa,a ba ina zuwa tace" ke kuma daga kai abinci kk je kika zauna ? Wai ina kk je ne? Don nasan tun dazu ba gidan kk ba tunda su salim yanzu dawowarsu salman kuwa nasan ba dariya ma yake miki ba bare ince gunsa kk zauna.ina kk je? Na danyi shiru sannan nace inna yaya ne ya Sani aikin shirya masa kaya a drawer. Ina fada na wuce ciki bina tayi da kallon tuhuma amma tayi saurin watsarwa taci gaba da harkokinta. A kwanakin kowa sai da ya fahimci salman ya sami sabani da salima don kuka ta dinga yi tazo ta gayawa inna ta fadawa ya salim harma da sadiya don shirme😜 Inna kam bata ji dadi ba ta tambayi ya salman yace " shi dama ba wani son ta yake ba tausayi take bashi ganin tana da hankali amma ake son hadata aure da wani shashasha mara tarbiyya. Inna tace" hmm salman knn Salima ta gayan komi saboda Dan,uwanta yace zai auri rumaisa......... Yace" inna Ahmad fa ba mutumin arziki bane zai batawa rumaisa rayuwarta ba kuma auren ta zaiyi ba. Tace" to sai me? Waya fada maka rumaisa zatayi abin kirki? Bari kaji indai amina ce ta haifi rumaisa to rumaisa bazata taba zama ' yata gari ba.don ma kaji da kyau don haka ka fita harkanta taje tayi duk abinda take so ba ruwanka.Salima kuwa ita tafi dacewa da kai don haka ga dama ta samu karkayi wasa da shi. Shiru yy yace " inna Ahmad fa ba auren..... Ta katseshi da fadin" na shiga uku ina maka maganar Salima kana min maganar rumaisa .ai sa,a ma taci da Ahmad yace yana sonta Dan babban gida irin nan sannan uwa uba mahaifinsa gwamna?ai ba Wanda ya kaita sa,a in dai zai aure ta da bakun fentin da take...... Ya katseta da fadin " kawai inna ki bar maganar nan babu dadin ji.ni zan tafi in kina bukatar wani abu ki turo zainab. Ya fita da sauri ransa a nace". Faiza kuwa koda mukayi waya na fada mata duk yadda nayi da ya salman. Shiru ta danyi sannan tace" hmmm rumaisa kinsan meya faru? Ina cikin damuwa sis. Nace " me ya faru ne sis? Tace hmmm wai kinsan me ashe tuntuni wai yaya Ra'is wai sona yake tuntuni babu Wanda ya fadan a cukinsu wai suna jiran sai na fara University kiji wani al,amar kuma don Allah? Cikeda mamaki nace" waya gaya miki? Tace" shekaranjiya suka shigo Zaria dukansu ai shine fa suke fadamin.kinga yanda yaya ra,is din ya rikice daga ganina ko kunyan su yaya baiji ya dinga min sambatu? Dariya nayi nace" wayyo sisi na aikuwa guy din ya hadu wlh ki amince daga ganinsa mayen love ne.ke kuma dama haka kk so ai na sanki da mugun jarabar tsiya aure kk so ido rufe. Tace"ai aure abin so ne sai dai fa nafi son jarumi Wanda za,aita harka ba gajiya kinga shiyasa nake son yaya salman saboda ance sojojin sunfi iya harka in mace ta shiga hannunsu sai ta yabawa aya zakinta😜 Zaro ido nayi nace" to shine kuma kk dagewa so kk ki wahalane? Tace" ke ni fa tuni na gane type dina. Nace " ban gane ba. Tace wlh na gane ni HARIJA ce Da sauri nace" what!🤭wlh faiza baki da kunya . Tace gara na fada miki gaskia don ni inaga ma bazan iya karasa makarantan nan ba aure ba kar inje in lalace gaskia Dariya nayi nace kai faiza. Tace " wlh serous nake miki wnn maganar har cikin raina. Nace to shikenan yanzu dai shawaranda zan baki ki amince da auren ra,is din tunda kinga ya nuna da gaske yana sonki.batun jarumta kuma kuma ki bari in anyi auren kya bamu labarin don daga ganin idanunsa shima fa Dan hannune kamarki. Tace" Allah dai yasa ai ban isa na bijire ba yanda su yaya suka dage shi kuma uban gayyan cewa yy auren a karshen wnn shekaran za,ayi yanzu muna watan hudu . Nace" masha Allah Allah muma ya samu a danshinki nida sakina. Tace" sai da ke mu tayaki da addua sis amma sakina kam ta sami wani Hafiz babban lecturer ne kinga yadda yake rawan jiki akanta hmm amma fa kiyi shiru kinsanta da zurfin ciki wai bata son kowa ya Sani sai maganar tayi karfi. Nace" masha Allah ni dai har yanzu shiru. Tace " kar ki damu sisi na Allah zai kawo na gari Insha Allah. Nace" Allah yasa. Tace ameen anan mukayi sallama. Na zauna shiru ina tunanin rayuwata yadda zata kasance ni kuma..... ~Comments~..... Hauly ce👍🏻 [05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page1⃣2⃣ Yau mun gama lectures da wuri don haka na shirya zan tafi gidan mama sai ga Salima tazo dakinmu abin ya ban mamaki nasan dai tana shigowa hostel gun kawayenta don nikam bamu ishi juna kallo ba. Maryam tayi mata magana inaji suna gaisawa nikam naci gaba da harkokina kamar ban ganta ba. Maryam tuni ta fita don tace zatayi wanki ne. Tana zaune shiru har na gama shiryawa na dauki jakata zan fita a sanyaye tace" rumaisa gunki nazo faa. Na kalleta cike da mamaki sannan nace " ni kuma ? To Allah sa lfy ne? Tace" lfy qalau in ba damuwa ki zauna mn Nace " aa wlh da damuwa don kuwa sauri nake zan tafi cikin gari.ke dai ki fadi maganarki ina jinki daga nan. Ta numfasa tace" nasan kinsan komai gameda abinda ke faruwa tsakanina da ya salman. Kallonta nayi sama da kasa na yatsuna fuska nace" uhummm. Tuni hawaye ya ciki idon ta tace " rumaisa nazo in rokeki ne don Allah ki amince da yaya Ahmad wlh duk abinda ake fada a kansa zai daina domin da bakinsa yace min in dai har kk amince masa zai iya barin komi saboda bai taba jin son ' ya mace kamar yadda yake sonki ba wlh rumaisa ya Ahmad na sonki kamar yadda ya salman ke sona don Allah kiyi hkr da abinda ya faru a baya ki karbi soyayyar ya Ahmad ko nima zan samu su dad su Amince da aurena da salman. Murmushin nayi sannan nace " hmmm wnn magana taki kamar tatsuniya wlh .Salima ni bana son Ahmad ko da kuwa baida wata mugun hali.tsakaninki da ya salman kuma shawara daya zan baki shine ki tashe tsaye wurin addua kwanciya baccin dare ba naki bane ki tashi kiyi nafila ki dinga istikhara ki kaiwa Allah kukanki ya miki zabi mafi alheri ba wai ki dinga kuka kije nan kije can kina a taimakeki ya salman ya juya miki baya ba.abin kunyama yake bani nikam. Share hawaye tayi sannan tace " hmm bazaki gane ba don har yanzu baki San meye so.amma babu komai nagode. Ta mike ta fita na bita da kallo hade da tabe baki nace" ke da kk San shi me ya amfanar miki banda bakin ciki da takaici.ai namiji sai a slow duk yanda ya ke riritata dinnan lokaci daya ya juya wai shi ba wani sonta yake ba tausayi take bashi.🤔 Ban sake biyowa ta kanta ba gidan mama naje da isana ban sameta ba na wuce bedroom na ajiye jakata kitchen na nufa na shiga dube duben me zanci. Daga karshe indomie kawai na tafasa da kwai da sardine na dauko lemo mai sanyi na zauna a dining hankali kwance kaman gidan Ubana . Na soma ci kenan saiga kiran ya salman Murmushi nayi nace " su yaya sai yau aka tuno dani. Na daga hade da yin sallama. Ya amsa nace" yaya ina wuni. Yace " lfy qalau komai lfy. Murmushi nayi nace" naga sakon kudin yaya na gode Allah ya kara budi.na ta kiranka baka dauka ba. Kai tsaye yace " aiki nakeyi. Muka danyi shiru yace " kina ina ne? Nace" yanzu nazo gidan mama ne Yace OK ya maganarmu na jiki shiru? Rass naji zuciyata ya tsinke nace" yaya dama tuntuni na ke so in kiraka in gaya maka nifa ban samu ba wlh. Da sauri yace " what shine kk sa na saki jiki ina jiranki bayan kinga mun fara gini nan da watanni kadan zamu kammala salim fa tuni ya sami mata a Abuja. Shiru nayi hnklina tashe. Yace" kinga ni fa ke nake jira.ki samo min fara doguwa kyakkyawa mai gashi mai ilimin Arabic da boko wayaiyiya mai tarbiyya nitsassiya kin gane ai? Na baki satar amsa yanzu sai naji daga gareki. Wayyo Allah na na fada a raina na daure nace " yaya kawai ka auri saliman ...... Ya katseni da fadin " kar ki kuma kawo min zancen Salima daga yau nai miki last warning. Nace " bazan kara ba kayi hkr. Yace " shikenan ki gaida goggo Amina. Ya kashe wayar rai a bace. O Allah mutum kamar mai aljanni. Nayi shiru ina tunanin irin matar da yake so wai dama yaya yana lura da Mata ne ya irgo ....... Hmmm kawai na tsinci kaina da yin murmushi na mike na tafi dakin mama gaban madubi na tsaya ina karewa kaina kallo a madubi. Ni dai farace kuma doguwace haka nan ina da gashi .to ko ince mishi gani 🙈 Kunya ce ta kamani da sauri na juya na bar gaban madubin na fita zuwa dining anan naga mama zaune a palon taci kwalliya da wata less mai shegen tsada sai kamshi take tashi . Tana ganina tace " ke kuma yaushe kk zo? Nace bai jima na shigo ba kya nan. Batayi magana ba na wuce na dauko abinci na a dining duk ya huce ma na dawo Palo na zauna nace"mama ina wadancan dogayen riguna da kk ce kin ajiye mun zan tafi dasu in zan koma? Tace" hmmm da na baki ba cewa kkyi kaya sun miki yawa ba ? Ai tuni na bawa masu bukata . Na bata fuska nace " mama fa cewa nayi ki ajiye mun sai nazo. Tace" to sai in tsaya jirankine ? Sai ki hkr in na sake zuwa Dubai a kawo miki wasu. Shiru nayi ina cin abinci. Ta kalleni tace" ba kije gidan naku bane? Nace " ni na Kai wata banje ba sai dai in kira kawu a waya mu gaisa. Tace" baki kyauta ba ni shekaranjiya naje na sami Raihana a gida tana wanki shine yayan yake ce min wai sakinta akayi. Na zaro ido nace " raihana kuma ba sadiya ba? Tab aiki ya sami Inna don sadiya ma tana hanya ba fata nake musu ba.hmmm bari ya salman yazo kano ya sameta sai ya sassaba Mata. Mama tace" hmm Allah ya kyauta ni banga laifinsu illah kaifin uwarsu duk ta bi ta bata yara da rashin tarbiya ga rashin kunya a zamanin yanzu namiji ka bishi sau da kafa ma ya kk kare bare ma kuma kana mishi fitsara. Allah ya shiryesu. Nace " ameen. Kwana daya kawai nayi a gidan mama na yi shirin komawa school saboda shirin exams. Ina isa shiga mkrnt sai ga Ahmad cikin wata mota kuma na daban yazo yy parking a gefena ya sauko da glass ya leko da kai yana murmushi yace " my Queen Allah yy haduwarmu yau na jima a nan ina nemanki ashe kina cikin gari. Kamar bada ni yake ba tuni nayi wucewata. Sai kawai naga mutum ya tari gabana yana haba Queen of beauty wulakanta mutum ba dabiarki bane ba na Sani kowa nakine banzo gunki ba sai da mutane suka tabbatar min da haka me yasa kk zabe ni a cikin mutane kk wulakantani? Don Allah ki gaya min laifina pls my Queen. Kauda kai nayi nace " hmm ni ba wulakantaka nake ba sauri nake I have more important things to do so pls let me...... Yayi saurin fadin " no no my Queen bazan iya barinki ki tafi yau dai kawai so nake ayita ta kare. Kallonshi nayi cikin mamakin yadda ya wani marairace.na tabe baki na raba gefe zan wuce kawai ya sake shan gabana sai gashi ya durkushe a gabana . Na zaro ido ina mamaki na shiga waige waige ai tuni gayun BUK sun fara cika wurin kasancewar daddaya ne wayanda basusan Ahmad ba yasha zuwa yana musu karyan kudi a hada casu kowa ya rabarbashe son rai don naji labarin har clubs ne dashi. Da sauri na kalleshi nace" mene ne haka don Allah ka rufa min asiri ka tashi.kaga tuni ka fara sa attention din mutane ya dawo kanmu. Ya girgiza kai yace " ban damu ba kowa ma ya ganni a haka me ne ne a ciki don na durkusa a gabanki wlh kin cancanci in miki kuka ma babban burina shine ki amince min ko da kuwa bada soyayya ba burina inga muna tare muna gaisawa muna mutunta juna shikenan faa kawai. Shiru nayi na rasa mafita na kalleshi nace shikenan naji na amince zamu dinga gaisawa hade da mutunta juna amma babu maganar soyayya ka amince? Murmushi yayi yace" yes my Queen. Ya mike yana kakkabe kayansa sannan ya juya ya kalli mutanen da ke kewaye damu yana murmushi yace" guys nayi winning heart dinta Ku tayani murna yau zan shirya mn party na musamman kowa ya cashe. Tuni gayu suka shiga ihu suna tafi ni dai anan na barsu sai ruwan kudi yake musu. Ina zuwa hostel na cire kayana na nemi wando da vest na saka na jawo takarduna na hau karatu don ko da wasa banson in fadi jarabawata . Anan wayata ta shiga ringing na duba naga sadiq ne mijin raihana dan tsaki nayi nace" anyita kira baka dauka ba tuntuni sai yau ka gani . Kamar bazan daga amma dana tuno da raihana kawai na dauka. Bayan mun gaisa nace"malam na nemeka tun shekaranjiya sai yanga ake mn ko dai an sami wata ce aka share mu? Yace" uhumm ke dai rumaisa bari Ku din ne sai a slow. Nace " ba wnn ba malam yanzu dai gaya mn laifinmu mu baka hkr. Ya danyi shiru yace yace " rumaisa wlh ba,a son raina hakan ta faru ba kindai San ina son raiha amma abubuwa da yawa yasha faruwa daga aurenmu zuwa yanzu ina ta hkr amma yanzu abin ya wuce kaina ya koma iyayena da ' yan uwana ni kuma gaskia wnn kam I can't tolerate shi yasa na sawwaka mata amma ba don ban son ta ba kin gane? Na ce " eh na gane kuma a gaskia raihana bata kyauta ba kayi hkr dama shiyasa na kira don in baka hkr malam ka daure ka dawo da ita ba don halinta ni kuma inshaa Allah zan yi kokari inga yawa ya salman domin a mata magana tasan cewa aure ba abin wasa bane sannan iyaye ko basu suka haifeka ba basu cancanci ka wulakanta su ba.inshaa Allah zata daina kayi hkr. Yace " babu komai Rumaisa idan har raiha ta gyaru me zai hana in dawo da ita ai mugun halinta yaja na sallameta. Nace " to shikenan malam mun gode sosai Allah ya bar kauna. Yace " na gode rumaisa Allah ya saka da alkhairi . Nace" amin sai anjima. Daga nan ya kashe .shiru nayi ina mamakin hali irin na sadiya da raihana kullum case. _Hauly_ _ce_ 👍🏻😍 [05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 __Godiya ta mussamman a gareku masoyan MATAR SOJA na gode matuka Allah ya bar kauna_ _Wannan page naku _ne_ _INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION _FANS_ _ALFAHARI_ _NOVELS_& _RASHIN NAZARI FANS_ _Ina ganin comments kuma ina jin dadi na gode matuka_ _Allah ya bar kauna🥰🥰🥰🥰👏🏻_ ```BISMILLAHI RAHMANIR RAHEEM``` *PAGE* ➡1⃣3⃣ ****** Alhamdulillah cikin ikon Allah mun gama exams. Don haka yau gidan mama zan wuce tukunna. Ina cikin shiri blessing ta shigo ta kalleni tace" Queen ba dai har kin gama sjiri ba? Nace" tsaf ma kuwa. Tace " mutumin ki yana can yana nemanki yace layinki bai shiga in ya kira duk ya damu. Murmushi nayi nace " Ai Ahmad ? Hmm matarsa na da aiki. Yau dai zan bude wayar kowa zai sameni tunda exams ya kare Tace" kinga ni bara inje in shirya Ahmad zai shirya gagarumin casu yau .akwai harkar shisha Queen zanzo ace kinje night club dinnan kiga yadda za,a cashe. Tabe baki nayi nace " hmm Me ya kaini zuwa wani club ni kuma ? Kuma Allah ya shiryeku . Na karasa rufe zip din jakata na tashi nace " ni na tafi sai munyi waya ki salami Juliet da Maryam ' yan iska ana exams suna tfy hotels da samari. Allah ya shiryeku. Blessing ta yatsuna fuska tace " ke dai jeki tunda ba kya ra,ayi. Ina barin hostel saiga kiran Ahmad na dauka na shaida mishi gani nan tahowa. Ya na ganina ya saki murmushi ya tashi ya karaso ya karbi jakar hannuna yace" ranki ya dade Queen of beauty. Murmushi na sakar masa nace " tare da nake ya kwana da yawa? Yace " ke dai bari my Queen exams ya boye min ke. Nace wlh kuwa.amma yau ina free me ka tanadar min? Yana murmushi yace" yau zan hada casu so nake ki sami halarta domin so nake na Nada ki Queen of beauty na BUK. Dariya nayi nace" ai tuni na zama Queen domin yanzu sunan ya game bakin mutane da dama.kuma kaga ni bana son zuwa casu am sorry. Ya danyi shiru snn yace" OK no problem yanzu dai ina zan kaiki ? Nace" gidan Mamana Yace OK ba matsala Mun iso gidan alh aminu har zan sauka yace" my Queen sai yaushe ? Nace " hmm sai na jika. Shiru yayi yayinda ya zuban ido nace " lfy? Ya danyi tsaki snn yace " wlh zan yi missing dinki sosai don Allah ki dai na kula samari naga wasu guys suna dan damunki da shirme ki dai na kulasu please hakama wnn sojan yayan naki na lura .... Na katseshi da fadin " kaga don Allah idan muna tare ka daina kawo maganar ya salman ! Yace" hmm shikenan. Nace" ni zan shaga cikin gida sai munyi waya ayi casu lfy. Har na bude kofa ya riko hannuna . Na juyo muna fuskantar juna wani shu,umin kallo yake jifana dashi har ya saukar min da kasala. Kusan minti biyar muna haka. A hankali yace" RUMAISA bansan wani irin so nake miki ba lokaci daya kin mamaye ko,ina a rayuwata wlh banson mu rabu my Queen. Dan murmushi nayi nace" ai bazamu rabu ba ga waya. Yace hakane. Ya dauko wata Leda fari mai kyan gaske ya Dora min a hannu yace " wnn iPad dinki ne da nace miki tuni na bada oda sai yau yazo. Na Dan zaro ido nace " kai dama da gaskene? Yace"eh mn Girgiza kai nayi nace na gode da kulawarka aamma ka bar...... Hade fuska yayi yace" ba,a maida hannun kyauta baya sai dai ko in kin raina. Na girgiza kai nace " ko kadan na gode Allah ya saka da alheri. Baiyi magana ba sai naga ya dauko check ya rubuta ya mika min.hade da fadin " ba yawa one million ne kiyi bukatunki dashi zan kara miki? Cike da mamaki nace "don Allah ka bari ni bana bukatar kudi komi kankantarsa bare wnn yayi min yawa ka bar shi kawai. Ya girgiza kai yace " na riga da nayi niyya don haka dole ne ki karba. Nace" aa wlh ka bari .... Yace " kinsan Allah idan baki karba ba binki zan yi har cikin gida in fadawa mama abinda kk mun. Ganin fuskarsa ba alamun wasa yasa na karba ina jujjuyawa cike da tsoro da fargaba. Na dago na kalleshi snn nace" na gode Allah..... Yayi saurin fadin " shiiiiii ba sai kin min Godiya ba .yanzu dai ina jiranki idan kin bude ipad din . Nace OK ba matsala.thank you Yana murmushi yace " ur wlcm ki gaida mama. Da haka muka rabu ba Dan ransa naso ba. Na shiga ciki side din mama na wuce a Palo na sameta da wasu mata suna ta harkar business ga kayaiyaki birjik. Na gaishesu cikeda girmamawa mama ta kalleni cikin kulawa tace" ki shiga ciki RUMAISA ina zuwa. Nace,to mama Na wuce ciki gado na fada na shiga waya da mutanena . Ashe sakina tuni ta dawo faiza kam ta wuce abuja amma tace min next week zata zo kano Hutu nake sha a gidan mama hankali kwance muna waya da Ahmad sosai bayan shi har da wasu samarina😉 Yau kam har na makara ban tashi da wuri kasancewar ina period kuma mun kwana waya da doctor hakim gashi an tafka ruwan sama har gari ya waye ma ana ruwa. Lokacinda na tashi na dubi agogo karfe sha daya saura. Da sauri na sauko daga kan gado na zira takalmina na mike tsaye rigar bacci ne a jikina Wanda da kadan ya wuce gwiwa na hannun sa siriri sannan rabin kirjina a waje haka na fita da nufin na tafi dakin mama. Jin maganarta a Palo yasa na nufi palon ina hamma hadda Dan mika na. Dubawanda zan yi kawai karaf mukayi ido hudu da ya salman harara ya sakar min ya kauda idonshi. Mama ta kalleni tace" ke bakida hankaline zaki fito har Palo da kayan bacci? Juyawa nayi ba shiri na wuce ciki ina gunguni. Ban daki na wuce na yi wanka hade da brush na kintsa na danyi simple make up na gyara gashina nayi parking nadauko dogon riga na 'yar kanti irin mai bin jikin nan na saka kaina ba dankwali na fita zuwa Palo har lokacin hira suke. Kusa da mama ba zauna hade da fadin mama ina kwana ? Tace lfy kije kiyi break fast kizo kisha maganinki kwanan nan duk na lura kirjinki na son toshewa kuma ke ba kyaji ba kya kula da kanki yanzu haka da ruwan sanyi kikayi wanka gashi ana sanyi Allah ya shiryeki. Banyi magana ba na dan saci kallon yaya salman nace" yaya sannu da zuwa. Da kai ya amsa min Nace " yaya yaushe kazo? Yace jiya. Anan muka gaisa yace" kiyi sauri ki gama breakfast din mu tafi sauri nake. Na mike a sanyaye na wuce dining gaskia ni banson zuwa gidansu inna dama an barni an an Ina gama breakfast na koma daki na sake shiri na fito fuskata ba faraa, Yana ganina ya mike yayiwa mama sallama ya fita . Kamar zanyi kuka na bishi a baya bayan na sallami mana . Tunda muka kama hanya bamucewa juna ko sannu ba har muka isa na sauka na wuce ciki cikeda bacin rai Abin mamaki na tarar da sadiya ma a gida to fa kallon mamaki nake binsu dashi bayan mun gaisa da inna sai faman daddaure fuska take.ni dai ban kulasu ba na tafi gun sakina muka shiga hirar mkrnta. Nazo da kwana 2 faiza ma tazo don haka muka tattara ni da sakina muka koma sashin daddy a can muke tsula tsiyarmu don kwana muke muna hira a waya fa,iza kam harda vedio call ake da Ra,is Nace" sisi yanzu kam alamu sun nuna rais dai ya winning heart dinki ? Tace" fada ma bata lokaci ne rumaisa guy dinne ya hadu na karshe sai yanzu na gane shieme da wauta dana so na tafka waini yaya nake so hmm yanzu wlh yaya ko zai durkusa a gabana yana kuka yana fa,iza ki auren zance banayi. Muka kwashe da dariya nida sakina har da tafi sakina tace" me ma zaiyi dake ,tunda Salima ma sun rabu.ai bari kiji yayana zai je ya zabo mana mata kyakkyawa ajin farko wacca ta fiki kome da kome yar rainin hankali. Fa,iza tace" gaki nan babban yar rainin hankali bari kiji wani labarinda baku Sani ba dukanku ya salman tuni aka bashi mata a Cameroon ' yar yayan Inna don Abba har ya gayawa daddyna ni ma a gun.Momy naji. Zuciyata ta shiga bugawa na rasa dalili sai naji raina ya mugun baci tashi nayi a fusace ganin sun bini da kallon mamaki yasa nayi saurin wayancewa nace kuna zaune dare ya tsala so kuke mu makara alhalin nace muku ina son zuwa kasuwa gobe kuma ma zan yi bako daga Kaduna. Ganin har lokacin bina suke da ido yasa na rasa me zan yi kawai na dauki maganin sauro na spray na wuce daki da sauri tuni faiza ta mike ta biyoni tana rumaisa ki tsaya zan fesa..... Fuuu na wuce ko kulata banyi na shiga daki na kama fesawa ba kakkautawa raina a bace sosai Da gudu faiza ta shigo ta kwace ranta a bace" rumaisa me yake daminki kin manta kina da asma ? Taja hannuna da sauri tace " mu je Palo. Ko kamin mu iso Palo tuni numfashina ya carke anan na zube da kyar nake fizgar numfashina Gabadaya suka rude sakina ta dubi agogo karfe sha biyu saura tace " innalillahi bari in kira ya salman. Ta dauki waya faiza kam kuka takeyi don ganin yadda nake numfashi gani take kamar bazan kai labari ba. Anci sa,a ya dauka cikin bacci sosai yace" sakina lfy ? Jikinta na rawa tace ' yaya rumaisa ne.... Gata nan ...... Nan da nan ya fahimceta yace " shikenan gani nan yanzun nan. Aiko minti biyar baiyi ba sai gashi yana buga kofa nikam ji nake kamar bazan tashi ba. Sakina ta bude da sauri don tafi fa,iza karfin hali. Ba tare da Neman Karin bayani ba daukana yayi cak kamar wata yar baby kayan baccine a jikina Riga da wando baiko kula ba yayi waje dani yanacewa sakina zo muje faiza ki biyomu ki rufe gidan. Abu kamar da wasa har ya kaimu ga saida aka sa min oxygen Ya salman ma ya tsorata sosai ko zama ya kasa yi yana hango doctor zai tareshi ya kama tambaya. Sai kusan asuba aka barsu suka shigo banma Sani ba nikam. Ya kalli sakina yace " sakina ya akayi hakan ta faru ? Tace " kawai yaya muna hira a Palo ta dauko maganin sauro zata je ta fesa a daki shine faiza ta bita ta kwace amma har ta rigada ta feffesa ma shine faa ta fadi numfashinta ya kama daukewa.kuma mun nemo inhaler dinta bamu gani ba. Yace" tasha maganinta ? Tace" aa bata sha ba tace taji sauki Shiru yy ya zuban ido sannan daga bisani ya kalli agogo ya tashi yace " bari in je masallaci. Ana idar da sallar asuba saiga mutanen gida sunzo tare da faiza Wanda ko bacci ya gagareta yanzun ma da tazo taga halinda nake ciki kuka ta shiga yi tana " sakina har da oxygen aka sawa rumaisa? Ya salman ne yace" suje waje su zauna dasu sadiya. Karfe shidda mama tazo don Abba ya fada mata banji dadi ba.itama ta tsorata ganin halinda nake ciki. Kiran salman ta yi suka koma gefe ta na tambayarsa ya fada mata. Tace" baka gani ba abinda nake gaya maka rumaisa batada hankali ita take jawo wnn ciwon da karfin tsiya tazo tn wahalar da mutane . Sunjima suna tsaye Sadiya kam mamaki ne ya kamata yadda taga ya salman sunyi gefe da mama suna magana zata so ace taji meyene don taje ta gayawa innah. Sai da nayi sati a asibity sun tabbatar na warware sannan suka sallamoni mama ta dinga ja min kunne fada ta yi min kaman zata dakeni daga nan sukayi sallama da yaya salman ta tafi da driver dinsu ni kuma mu ka dawo a motar ya salman Mun iso gida ina shirin fita yace " tsaya ke. Ya fito ya zagayo inda nake ya riko hannuna yace " kibi a hankali jikinki baiyi karfi ba har yanzu. Gaskia na rame kam sosai Ya rufe motar yana rike da hannuna har cikin gida mmn sakina ta tashi ta kamoni suna min sannu a palon inna na kwanta . Ya salman kafin ya fita saida na jishi yana jawa su sadiya kunne akan kar wacce ta yarda yaji wata magana a bakinta don yasansu kamar shaidanu suke kuma karsu hanani bacci. Inna kam bimmu kawai take da kallo duk ta bi tayi kicin kicin da fuska ko me aka mata ne oho. _Comment_ _and_ _share_ _Hauly_ _ce_ 👍🏻😍 [05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` ➡ page 1⃣4⃣ *********zuwa yanzu na warware tass mun koma iya shegen mu da fa,iza. A wnn lokacin gabadaya samarina saida suka zo har gida suka dubani Ahmad kadai na hanashi zuwa gudun kar ya salman ya ganshi don ya min gargadi akansa. Yauma da yamma doctor hakim yazo doctor din asibityn mu na school akwai lokacin da nayi ciwon Mara naje ya dubani shine fa ya daddage wai yana sona zai auren Kuma gaskia hakim baida matsala kamilin mutum ne mai ilimin. Arabic da boko sannan yana da fara,a gashi kyakkyawan mutum daga gani bafulatani ne.gaskia hakim ya hadu ba kushewa. Muna cikin hira a cikin motarsa ya kalleni cikin nitsuwa yace " Rumaisa ya kamata zuwa yanzu kam ki gabatar dani gun iyayenki domin ayi komai a wuce wurin. Na Dan zaro ido nace"kai doctor me kk sauri? Yace " ina tsoron kar in tsaya garin kallon ruwa kwado ya min kafa . Mukayi dariya lokaci daya nace" hmm " ba komai zan tuntunbeka idan na shirya. Ya juyo muna fuskantar juna sosai yace" rumaisa ko dai akwai Wanda kk so ne daban? Na girgiza kai nace " ba kowa kai kadaine mutumin da maganar aure ya shiga tsakaninmu don haka insha Allah karka damu da kai za,ayi Murmushi yayi min nima na maida masa yace" thank you so much my love Na lumshe ido ina murmushi nace " doctor ina matukar........ Karar wayatace ta katseni ina dubawa naga kiran ya salman ne kin dauka nayi. Muka ci gaba da hiranmu cikin nishadi haka yaci gaba da kira har sau uku hakim yace " me yasa bazakiyi picking ba? Nace yanzu lokacin ka ne doctor bazan amsa kiran kowa ba. Yayi murmushi yace" nagode sosai my love. Mukaci gaba da hira tex ya shigo wayata na ya salman ina dubawa naga: *_Zaki_* *__zo_* *_ko_* *_sai_* *_na_* *_sameki_* *a* *_wurin_*? Da sauri na dago kaina sai lokacin na ganshi yana tsaye a bakin gate din gidansu Yanayin fuskar ya tsinkar min da zuciya sosai tsoro ya gama rufeni. Hakim ma na lura shi yake kallo . Ya juyo yace" rumaisa wancan kamar.... Nayi saurin fadin " yayana ne shi yake kirana dama.don bayaso mu dinga dogon hira dama Na fada a kidime. Ya gyada kai cikin gamsuwa yace" OK ba damuwa yanzu dai kije gida sai kara zuwa insha Allah. Sama sama mukayi sallama Nikam na rasa yanda zan yi duk tsoro ya gama rufeni ganin yadda ya salman ya hade fuska ya ke min wani irin kallo mai cike da tuhuma. Yana ganin na nufi inda yake ya shige cikin gida haka nayi shahada na bishi a baya. A Palo na same shi ya juyan baya Hakan ya dan bani kwarin gwiwa fadin" yaya don Allah kayi hkr wayata tana silent shiy...... Juyowa yayi a fusace idonsa tuni ya rine ya zama jazir yace " waye wancan Dan iskan da kk shiga motarsa kina wage masa baki? Sunkuyar da kaina nayi a tsorace Tsawa ya daka min har na gigice tuni hawaye ya ciko idona fall " zaki fada min ko sai nayi ball dake! Da kyar na iya bude bakina jikina na karkarwa nace doctor Hakeem ne. Yace" OK Wanda yazo jiya fa wayeshi? Ganin yana matsowa yasa na danyi baya nace" Mubarak ne....... Ya katseni da fadin "Wanda na ganki da shi shekaran jiya fa wayeshi ? Ya fadi hakan yayinda yake kara kusanto ni a tsorace nayi baya sai jina nayi na jingina da bango . Runtse ido nayi ina jiran saukan mari sai jin hannayensa bisa kafaduna Nikam tuni nasha jinin jikina yace" bazaki gaya min ba? Na girgiza kai ina kuka nace" yaya Abdul majid ne. Zuba min ido yayi yana huci kamar bakin kumurci. Ba shiri naji ya kama jijjjiga kafaduna da karfi yana" dama ashe ba karatu kk ba iskanci ya kaiki makaranta kin tara yan iska kina mu,amala dasu ko? Na girgiza masa kai cikin jin zafin abinda yake min Yaci gaba da fadin " to bari kiji baki isa ki bamu kunya ba aurar dake zamuyi ba bata lokaci.don haka ki fada min a cikin ' yan iskan samarin naki waye kukayi zancen aure da shi? A tsorace na girgiza masa kai nace " babu? Aikuwa ko kan na rufe baki sai ji kk tass! Ya sauke min mari yana shirin sauke min wata. Na zube durkushe a gabansa ina kuka mai tsanani na rike kafarsa ina" yaya don Allah kayi hakuri bazan sake ba wlh yaya sune suke matsa min amma daga yau na maka alkawarin bazan sake kula kowa ba Naci gaba da kuka sosai . Janye kafarsa yayi jikinsa ya mutu sosai ya zuban ido sannan yace,taso Na tashi har lokacin kuka nake mara sauti. Hannayena ya rike yace" ki fada min waye kk yi zancen aure da shi a tsakaninsu? Cikin dauriya nace" doctor Hakeem ne? What!!!? Abinda naji ya fada a rikice.nima na kara tsorata . Ji nayi ya kara rike min hannu yace " rumaisa ina jiye miki tsoron shiga matsala amma bazaki gane ba.kinsan waye hakim? Na girgiza kai nace,"aa A sanyaye yace" hakim mijin surayya yayar Ahmad ne.akwai matsala idan kk kuskura kk shiga gidansa familyn su Salima bazasu taba barinki ki zauna lfy ba.kima kanki gata ki rabu da hakim rumaisa ki nemi wani a cikin samarinki. Mamaki ne da tsoro ya cika ni don ban taba sanin matar hakinm yar uwar Ahmad bace tab lallai na hadawa kaina case babba. Ganin nayi shiru yasa shi fadin " ko dai kin fi son hakim din? Na girgiza kai sannan nace,ko kadan dana San matarsa yar uwarsu Salima ce da ban amince da shi ba amma yanzu bai baci ba don ban amsa masa akan maganar aure don haka daga yau na rabu da shi kayi hkr yaya ni ba wanda zan kuma amincewa da shi .na bar maka zabi ka zaba min mijin da kaga yafi dacewa da rayuwata. Hawayene ya zubo min Jikinsa ya mutu sosai yace" ki daina kuka maganar ya wuce. Hannunsa ya saka yana gogemin hawaye abinka da farin fata tuni fuskata tayi ja musamman gefen da ya mareni. Nadama yayi sosai gabadaya tausayina ya gama mamayeshi ba shiri ya jawoni jikinsa cikin sanyi n murya yace " kiyi hakuri ba,a son raina na miki haka ba rainane ya baci dazun Nikam tuni na dada kwanciya jikinsa dama son jikine dani😜 Rumgumeni yayi yace " kanwata insha Allah zan zaba miki miji Wanda zai rikeki da amana ya kyautata miki ya sanyaki farin ciki kinji? Kai na daga masa idona lumshe ina jin yadda kirjinsa ke bugawa. Ya rasa dalilin da yasa yaji baison dagani daga jinkinsa . Mun dauki tsawon lokaci a haka.kowa da abinda yake ransa. Gyaran murya muka jiyo da sauri na dago daga jikinsa shima ya sakeni jikinsa a mace sosai. Ya salim ne ya shigo ganin mu a haka ba karamin mamaki ya bashi ba. Don binmu yayi da kallon tuhuma gabadaya. Kunyane ta kamani kamar na nitse a kasa. Yayinda ya salman ya daure yace " yaushe ka karaso? Tsaki yayi ya wuce dakinsa ba tare da ya ce komi ba. Ya salman ya bishi da kallo sannan daga baya ya juyo da kallonsa gareni a cikin wata kasalalliyar murya yace" ki tafi gida kuma kisha maganinki kar ki manta. Nace " to A sanyaye na juya na fita. Ya kalli agogo hade da fadin subhanallah what har magriba ya wuce ko kiran sallah banjiba. Ya salim da ya fito daga daki ya amsa masa da fadin" ta ya zaka ji kiran sallah da ba don nazo ba asuba ma zaiyi kuma baza kaji kiran sallah ba. Ya kalli ya salim fuska daure baice komi ba ya wuce toilet alwala ya dauro ya fito . Zai wuce daki sai ya lura ya salim yana ta binsa da kallon tuhuma. Yace" salim bana son irin kallon nan da kk min faa Salim ya ce" hmm guiltiness! Gani nayi alwala kawai kuma kamata yy kayi wankane kamin alwala..... Ya katseshi da fadin " kai! Dama dan iska ka daukeni OK bari in idar sallah inzo. Ya salim yace" ina nan jiranka domin akwai tarin tambayoyi da zan maka . Tsaki yy ya wuce ciki. Nikam isa na gida direct na wuce sashin daddy a Palo na sami fa,iza ,Sakina,sadiya,r Raihana da Zainab suna kallon wani series da akeyi a joyprime(Ashoka samrat) Wucewa daki nayi bance wa kowa komi ba naje toilet nayi alwala nazo nayi magrib anan na zauna har nayi isha daga nan na jawo pillow na kwanta abubuwanda ya faru tsakanina da ya salman ya dinga dawo min. ******"sai tambayarka nake meye tsakaninka da yarinyar nan kayi shiru kana kallona. Ya salman yace" so kake kaji? Salim yace kwarai ma kuwa. Salman yace"SONTA nakeyi. Cike da mamaki ya salim ke kallonsa. Nan yaci gaba da baiwa ya salim labarin duk abinda ya faru har zuwa lokacin da ya samemu tare. Ya salim ya sauke ajiyar zuciya yace " me na gaya maka abaya ? Ka tsaya kana jan aji wai kai baka son ta rainaka waye waye..... " da ace tuntuni ka bi shawarata ka fito mata da sonda kk mata da tuni an wuce wurin kuma wlh da bazatayi wasu samari ba.salman tun randa muka fara ganin rumaisa a kauye na lura da kai na fahimci sonta kk.bare kuma da ta dawo nan naga irin special kulawa da kk bata sai na gaskata sonta kk kuma na fahimci cewa Salima tausayi take baka ganin za,a hadata aur...... Salman ya katsrshi da fadin ya isa mallam don Allah ni dai yanzu kaina yy zafi.salim rumaisa ta fara rikitani ina tsoron kar taje ta fara soyayya da wani pls salim ka ban shawara ya zan yi? Ya salim yace " waya San maka .ba kace zaka zaba mata miji ba? To waye mijin? Salman yace" nima bansani ba fada kawai nayi. Ya salim ya ce " OK ba matsala ga shawara me zai hana ka gabatar dani a matsayin Wanda ka zaba mata? Salman ya zuba masa ido hade da fadin " serious faa Ya salim yace" wlh kuwa am very very serious. Shiru salman yayi har na tsawon minti biyar sannan yace" OK shikenan. Ya salim ya mike hade da fadin " yawwa na gode Dan,uwa ina jiran ranar da zaka yi introducing dina a gun GIMBIYAR MATA RUMAISAH.sai da safe. Kai kawai ya daga masa Salim na shiga daki shima ya tashi a sanyaye ya wuce daki ranar baiyi bacci har gari ya waye yana idar da sallar asuba ya tafi airport don yin booking jirgin Lagos yaci sa,a kuwa sha daya ya wuce Lagos ba tare da ya sallami kowa ba kuma wayarsa ya kashe don kar a nemeshi🤦🏻‍♂ Comment and share Hauly ce👍🏻😍 Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` ➡ page 15 **********Shiru shiru ba Wanda ya ganshi har shadaya kuma gashi layinshi bai shiga. Abba da Inna duk sun damu.ya salim kam jikinshi yana bashi Lagos ya koma don haka ya kira Mohd abokinsa ya tambayeshi. Yace" eh yanzu ma suka rabu. Ya salim ya kalli Abba yace" wai wani kiran gaggawa aka masa ya tafi ba shiri wayarsa kuma ta sami matsala ne shiyasa. Abba yace to ai shikenan Allah ya taimaka. Sai lokacin inna ta saki ranta. Muna shirin tfy gidan mama ya Salim ya shigo muna hada ido naji kunya ya kamani na sunkuyar da kai . Faiza ne tace " yaya kun sami yaya salman din? Yace " eh yana Lagos Wani irin ajiyar zuciya na sauke hade da hamdala a raina. Ya salim ya ce" rumaisa ya jikin? Nace" da sauki yaya Yace kinsha maganinki? Nace" eh nasha. Yace" OK Allah ya kara lfy sai ki dinga kiyayewa kuma.yanzu ina zakuje? Fa,iza tace" gidan goggo Amina Yace" Ku bari sai da yamma na kaiku in yaso ki kwana . Tace" kai yaya don Allah mu dai ka.... Sai lokacin sakina ta yi magana" shikenan yaya kawai da yamman sai muje. Yace" yawwa kanwata rumaisa faa? Murmushi nayi nace " Allah ya kaimu. Yace "amin. Yana fita faiza ta rufe mu da balai nida sakina sai dariya muke mata muna cikin haka raihana suka shigo da Sadiya . Sadiya ta kalleni tace "Rumaisa don Allah ki min girki mana Inna tace kafarta na ciwo yau ni kuma kinga da kyar nake komi. Faiza tace " mu fita zamuyi fa ba ga raihana ba tayi miki mana Raihana tace" ke ni na gajine komi ni nakeyi a dakin Inna gaskia ni na gaji wlh tunda bani kadai nake cin abincin ba. Sakina tace " amma dai kunsan rumaisa bata da isashen lfy ko kuma hayaki ma tada mata ciwo zaiyi kuma ya salman ya fada yace duk wani aikin kura ko hayaki ko ruwa ta nisanceshi kuma kar a sata. Sadiya haushi kamar ta mari sakina tace" don na yau kadai shine me ? Don Allah rumaisa ki taimaka min. Fai,za ta karba" ba fa inda zataje don bata warke ba ko sai na gayawa ya salim ne. Anan fa suka kama sa,insa harda sakina da raihana. Shiru kawai nayi ina kallonsu har suka gaji dan Kansu suka bari. Na numfasa sannan nace"duk Allah ya huci zuciyoyinku abin bai kai ga haka ba . Na kalli sadiya nace " yanzu da kinyi hkr kin zauna gidanki yaushe hakan zai faru dake ? Na fada miki ki daure ki koma komai mai wucewa ne a rayuwa .... Ta tari numfashina da fadin " ke nifa bazan koma gidan dan iskan nan ba.in ma shi yake aikoki. Sakina tace " ba kinji matsalarki ba wlh sadiya kima kanki fada duk nan kece fa babba .ki dinga hkr mana. Tsaki taja ta tashi tana cewa" don na sake muku ne kk raina ni. Fita tayi ranta a bace. Na kalli raihana nace" wlh raihana ki dai na biyewa sadiya har yanzu mallam na min zancanki Anan muka rufam mata nida sakina faiza kam fushi tayi dama tun dazu na lura ' yan halin sun murdo. Raihana jikinta a mace tace,wlh nima na gaji da zama gidan nan banda wahala ba abinda nake sha duk aiki inna da sadiya sun sakarmin ni daya a gidana kuwa girki kawai da gyaran dakin sadiq nakeyi duk sauran aiyukan ina da mai aikina. Nace "to kinga lallaba ki koma ki huta. Ashe duk abinda muke fada a kunnen sadiya da ta labe bata tafi ba don haka tana gama ji taje ta mayarwa inna harda Karin gushiri. Aikuwa inna ta tura zainab ta kirani ni da raihana duk mun dauka a kan maganar girkinne. Amma muna zuwa palonta ta rufe raihana da fada har kamar zata daketa tana" Ashe bakida hankali bansani ba da rumaisa kk hada kai ki zagi 'yar uwarki? Raihana tace" laa inna wai tace mun zageta ? Wlh ba Wanda ya zageta.... Sadiya ta Karba" naji Ku sarai rumaisa harda cewa take inawa raihana bakin ciki ne. Inna ta buga salati nikam tsabar mamaki na kasa cewa komai Inna tace" ooo wato so kk ki bata ta da muguwar dabia irin taki dana uwarki .ina kk taba jin an saki mace sannan ta koma da kanta ba tare da anyi bikonta ba ? To bari kiji mu nan miji ke bin mace ba mace ke bin miji ba wnn abin kunyane .kuma abinda kike zuga raihana ta yi mu bamu sanshi ba wnn halin gogaggun mata karuwai ne .dama na fada in har kk tafi jamia ba abinda zaki tsinana to gashinan kinje kin koyi karuwanci zaki zuga min ' ya to wlh a hir dinki ki fita idona in rufe hawainiyarki ya kiyaye ramata .Uwarki ma duk karuwancinta ta buga dani ta barni bare ke karan Kad'a miya. Tuni hawaye ya cicciko idona nace, " inna kiyi hkr in Allah ya yarda bazan kuma yi muku shishshigi ba. Sadiya tace" hmm da yafi miki . Raihana tace " wlh tunda abin ya zama haka gara in fito muku fili ni komawa zan yi kuma ba wanda ya isa ya hanani.kuma Ku daina zagin rumaisa don ba ruwanta Ku zageni ni. Ta mike ta fita tana gunguni . Suka bita da kallon mamaki sadiya tace" Inna bakin gani muna zaman zamanmu yaya yaje ya dauko wnn shegiyar yarinyar ya kawota dama ya barta can gidan uwartata.kinga daga zuwanta har ta zuga raihana ta na son ta bijire miki ba. Cike da takaici inna tace" tama bijire ai bakiji maganganun da ta gaggaya mana ba . Sadiya ta harareni hade da fadin " sai ki zuba ruwa a kasa kisha munafuka kawai. Inna tace" sai anyi magana ki tashi kinawa mutane kukan munafurci.kamata yayi kije ki tambayi uwarki waye UBANKI kuma aina yake ba wai ki zauna kina shirya munafurci ba .don haka ki tashi ki bace min da gani. Mikewa nayi ko ganin gabana mai kyau banayi na fita tsabar bakin ciki naji wani abu ya taso ya tokare min kirji ban tashi Sanin ina nake ba sai bude ido nayi na ganni a gadon asibity. Anan na fara tuna komai daya faru . Na kalli mama dake zaune kan kujera da kyar na iya bude bakina nace,mama. Riko hannuna ta yi tace" rumaisa ya jikin me kk ji? Bari in kira doctor. Ta fita da sauri sai ga doctor ya shigo da ya salim ya salim duk ya shiga damuwa.bayan ya sake duddubani yace" ba matsala yanzu kam amma ta kiyaye sosai domin ciwonta har bacin rai ma yana iya tayarwa don haka a kula don Allah. Kuma ayi kokari tasha magungunan da zamu rubuta mata yadda ya kamata Daga nan ya fita ya salim ya bishi baya. Karfe 9 na dare muka isa gidan mama ina ji tun a mota ta kira abba tace mishi an sallameni kuma zata koma dani gidanta saboda ina sakaci gun shan maganina. Nasan dai ta fadane amma daga jin yanda take magana nasan ranta a bace yake. Anan mukayi wa ya salim sai da safe muka shigo gida bayan mun idar da sallah mukaci abinci nasha magani na.har na kwanta mama ta shigo tana tambayata abinda ya faru. Nan na kwashe duk na fada mata. Ranta ya mugun baci tace " lallama shatu har yanzu tana neman magana dani amma very soon zan maida mata da martani. Nikam zuwa yanzu nafi jin haushin mama da kowa ta boye min labarina koma ta hana in tambayeta wnn wace irin rayuwace ? Ni yaushe zansan mahaifina ko zan huta da gori😭 Hauly ce👍🏻😍 [05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` ➡ page16 ***********Gabadaya na rage walwala tunda abin nan ya faru mama ta kasa gane kaina. Kwana na biyar a gidanta rannan ina bacci da rana sai ga kiran ya salman da kyar na iya lalubo wayar nayi receiving ba tare da nasan ko waye bane. Muryar ya salman naji ya kira sunana" rumaisa. Ai da sauri na bude idona na mike na zauna hade da fadin" na,am yaya ina wuni? Yace " lfy ya jikinki? salim yace bayan tfyna kin kuma rashin lfy. Nace" eh amma na warke. Ya danyi shiru snn yace" ya akayi hakan ta faru? Nace" haka kawai....... Ya tari numfashina snn yace " nasan bazaki fadamin gaskia ba dama.kuma na hanaki karya. Nace" kayi hkr. Yace" shikenan amma dama na gargadeki akan karki saka kanki a cikin matsalar su sadiya ko? Nace" eh ka gargadeni. Yace" kinki jin maganata shiyasa hakan ya sameki.don haka ki kula nan gaba kome zai faru da su ki zuba ido kawai. Nace" insha Allah yaya zan kula. Yace" ya maganarmu? Kin samo min? Shiru nayi na rasa me zance. Yace" kinyi shiru. Na kama Sosa kai nace " am yaya dama ni duk na dudduba ban samo irin wacca kk so ba.kayi hkr .....in yaso...sai ince su...faiza su duba maka...a ABU.... Ya katseni da fadin" wnn maganar sirri ne tsakanina da ke.karki yarda na jita a koina. Nace" to yaya zan kiyaye. Ya danyi shiru snn yace tunda kin kasa samomin shikenan duk wacca na samo karki kushe. Ban San lokacin da nayi murmushi nace " na isa in kushe abinda kk so yaya? Yace" shikenan.kuma ki shirya duk sanda nazo kano zan zo miki da mijinda na zaba miki. Nan da nan gabana ya fadi na daure nace"to yaya Allah ya kaimu. Yace" ameen .yaushe zakuyi resuming school? Nace" next week inshaa Allah. Yace" OK Allah ya bada sa,a ki gaida goggo Amina. Nace" to yaya zataji na gode. Daganan ya kashe sauke wayar nayi ina murmushi nace hmm lallai ni nafi kowa sa,a yaya yana hira dani har sirri muke yi dashi😜 Ina shirin Shiga wanka sai ga faiza da sakina sun dawo dama tunda na dawo gidan mama muke tare dasu yanzu ma kasuwa sukaje don yi mana shopping din komawa makatanta. Sakina tace " a rumaisa sauki ya samu naga yau kam kina fara,a. Faiza ta harareni hade da fadin to sarauniya sai kije ki duba abubuwanda kk ce a siyo miki din ai. Hannu na daga mata " hey don't talk to me like this.ki bari sai sanda nayi ra,ayi naje na gani. Zaro ido tayi hade da fadin " what! Sakina tasa dariya hade da fadin ni kunga wanka zan shiga . Faiza ta ce,wlh rumaisa kinci sa,a don bakida lfy amma kin dau bashi. Ta fita nima binta nayi a dakin mama muka zauna nan na baje kayan ina dubawa. Faiza tace,goggo kinga uban wahalar da mukasha amma muka dawo rumaisa ko sannu batayi mn ba saima rufeni tayi da balai.don nace tazo ta duba kayanta. Mama tace" ai Ku rabu da ita bakin halinta ne ya motsa. Nace" mama fa karya take..... Faiza tace" ke ban fada miki ba raihana fa ta koma. Da dan zaro ido nace "don Allah kunje gidane? Tace" munje shine mama tace mn ta koma wai ba yanda su inna basuyi ba amma taki fir. Dariya muka sa lokaci guda hade da tafawa.nace" sadiya zata mutu da bakin ciki.mama kinsan sadiya bakinciki takewa raihana don taga ta sami miji kamili ba kamar jafar ba.har admission yace min ya samowa raihana zata fara zuwa BUK amma part tym . Mama tace" hmm in kuma ta biye wa sadiya zata yi asara don sadiya kam sai dai shiriyan Allah. Faiza tace " goggo wlh idan zan gaya miki yadda na tsani sadiya sai kinji mamaki. Mama tace" aa faiza ki bari ba kyau 'yar uwarki ne adduan shiriya kawai zamuyi musu.yanzu tashi ki shaga wanka kar wani ya sameki da towel haka. Tace" goggo sakina ta Shiga wanka tun dazu ita nake jira. Mama tace" aa tashi ki shiga toilet dina kiyi wankanki sai muje muci abinci tun tuni ku nake jira Faiza ta tashi ta shige toilet . Mama tace " to ke kuma hjy rumaisa tashi zakiyi ki tattara kayaiyakin nan ki kai dakinku. Nace" yawwa wnn karon bana son komawa makaranta da soyayyen kaza.mama nafi son a soya min nama da yawa kuma ayi min stew ne.ni zan dinga siyan abinci ne bana son wani tarkacen kayan abinci da yawa Mama tace" kudine dake haka bansani ba? Nayi dariya nace" mama duk kudaden da kk turamin fa ban wani kashe sosai ba kuma gashi ya salman da ya salim suna turo min ga daddy ma yana turowa .kawu ma yana turowa wasu lokutan. Tace" lallai Ku ' yan gata ne .yanzu kudin naki zai kai million daya ko fin haka? Na danyi shiru snn nace " zasu danfi. Tace " to me zai hana ki fara juyasu ne akan kashe kashen banzan nan. Nace"mama business knn? Tace" eh mn Na dan turo baki nace" mama ni da nake ' yar mkrnta me ya hadani da wani business? Tace " ke tafi can banson rashin wayo .waye gaya miki makaranta na hana kasuwanci?. Kina dai gani da kasuwancin nan na rufa mana asiri da bamu kai wnn matsayin ba a yanzu. Nace " to mama sai dai na baki kudin sai ke ki juya mun. Tace " to yaushe zaki koyi kasuwanci knn? Shiru nayi tace" hmm ki yi tunani duk abinda kk yanke ki fada min. Nace "to Sannan na tattara kayaiyakin na kai daki nan na sami sakina har ta fito wanka nima na shiga. ****a kwana a tashi ba wuya gun Allah gashi har mun koma mkrnta karatu ya fara nitsa. Ahmad kuwa sosai muka kara shakuwa gaskia ina samun kyaututtuka na ban mamaki a gurinsa ga kayayyakin sawa masu tsada na kece raini da yake siyo min ya kasance duk inda nabi sai bina ake da kallo Kadan ne wayanda basu sanni da Ahmad ba a yanzu kuma yawanci yanzu kowa ta koma kirana da suna QUEEN OF BEUTY.ina jin dadin wnn sunan sosai. Matasan yan makaranta da yawa in suna Neman taimako gurina suke zuwa don indai nayiwa Ahmed magana shikenan kawai . Gaskia na sauya sosai fatana har wani sheki take sosai na zama yar hutu gabadaya ' yan hostel ma girmamani suke saboda 'yan canji Doctor Hakeem kam tuni na ture batunsa a gefe.bama shi kadai ba harda sauran samarin. Ya salman ma rabonda da in kirashi har na manta dama shi ba kullum yake kira ba sai da dalili. Watarana bayan mun fito lectures Salima ta karaso wurinmu suka gaisa da su Juliet. Ni ko kallonta ma banyi ba ina kokarin neman Ahmad. Ta kalleni tace Rumaisa inada magana dake mu biyu. A yatsune na kalleta sannan na cire idona na wuce gaba ta biyoni muka sami guri muka zauna .nace" ina jinki. Ta dan numfasa tace" Ya salman ya wulakantani duk soyayyar da mukayi a baya.maganar da nake miki yanzu saura sati biyu aurena da yaya Ahmed.amma sai na lura abubuwa da yawa na faruwa .kar dai kice min soyayya kukeyi ? Nace " ni faa har yanzu ban fahimci dalilinki na ajiyeni anan ba kawai kin tsinke da bani labarin da be shafeni ba.kinga in bakida abin fada ni inada abinyi a gabana da yawa. Na mike har zan tafi tace" just a minute rumaisa. Ba tare da na juyo ba ta zo gabana tace" So nake ki rabu da Ahmad domin yanzu kiris ya rage ya zama mijina ki yanke duk wata alaka dake tsakaninki da shi domin ya fi karfinki kin rigada kinyi sake tun farko .amma duk da hakan ma kin ci rabonki tunda gashi har kin sauya tashi guda hmm. Sai ki godewa Allah.snn kije ki nemi wani don Ahmad kam ya miki nitsa. Murmushi nayi nace" shikenan abinda zaki fada min din? Tace" shikenan sai a kiyaye kuma don a zauna lfy. Na gyada kai nace" to ba damuwa. Daga nan wucewa nayi na barta a gun tana bina da kallon mamaki. Da yamma muna gurin shakatawa da Ahmad ya kalleni yana murmushi yace" Queen yau baza kisha ice cream bane ? Nace" no yau banjin sha,awar komi kuma ma ina tsoron asmana kar ya tashi. Yace" eh to hakane amma yau dinma fa ban fahimci yanayinki ba.ko zuwa wurin koyon driving dinma kinki muje yau. Nace" hmm ai ni yanzu na zama expert kai da kanka shaida ne . Dariya yayi snn yace " hakane yanzu kam saura ki jira zuwan motarki. Nace " wa! Rufa min asiri me zance a gida? Yace,ke wai yaushe zaki waye ayi harka dake? A raina nace" hmm ai kawai biye maka nake inci rabona kuma in kece raini inyi suna kuma a BUK.in kafa tarihi in zama abin kwatance . Na kalleshi nace" ba wnn ba my king.Ashe kai kuma tsakanina da kai har akwai wani boye boye? Yace " me ya faru Queen? Nace " hmm naji ance aurenka da Salima har saura 3 weeks shine baka sanar dani ba? Dariya yayi yace O my Queen come on dama akan wnn ne kk ta daure fuska tun dazu? Ni wlh ban dauki aurena da Salima da mahimmanci ba don wlh ni bana sonta amma su dad sun dage sai nayi aure wai don in shiryu kuma in nitsu.bayana na fadawa daddy duk abubuwanda nakeyi dinnan ina son in more kuruciyata ce kawai amma nayi mishi alkawarin in nayi 40yrs duk abinda nake zan tuba in bari kuma nayi aure.amma dad yaki saurarena sai lika min ita sukeyi kawai na rabu dasu suyi kawai ni ba ruwana da shirye shiryensu don haka kar ki damu. Murmushi nayi a raina nace" Salima ina tausayinki. ba,a banza ya salman ma yake tausayinki ba ashe. Na kalleshi nace" to ni dai ina rokon alfarma daya a gunka idan ka min wnn ka gaman komai. Yace" wane irin alfarmace? Nace" so nake ka nisanceni har tsawon wata biyu.kaje kayi hidimomin bikinka kuci amarcinku in kun gama sai ka dawo kaga ai ban shiga hakkin Salima ba ko? What! Ya fada sannan ya girgiza kai yace" bazan iya ba Queen.kuma waya gaya miki ina sha,awar sex yanzu? Ni faa ban gama more rayuwata ba tukun don haka bazanje in kula Salima ta yi ciki ba.haka kawai azo ana kirana da daddy kwana biyu na tsufa ? No ba haka na tsara rayuwata ba Sam don haka karki damu kanki da zancan wani amarci not now. Hmm Ahmad knn na fada a raina snn nace" to naji wnn ra,ayinka ne .amma ni ina son ka nisanceni mu kasance a waya kawai in ba haka ba wlh ' yan uwanka suka gane muna tare ko ya salman akwai matsala tunda gashi zasuce kayi aure kamata yayi ka nitsu.don haka dole mu canza taku. Yace,waya gaya miki ina tsoron wasu su gane muna tare wlh ni duk duniya in zasu San ina tare dake ba damuwata bane. Nace to don Allah ka taimaka min ni dai bana son a Sani. Ya danyi shiru snn yace hmm matsoraciya ce ke wasu lokutan to naji indai wnn ne tunda kince zamu kasance a waya. Na saki murmushi nace" yawwa my king Na gode sosai Daga nan yace mu tafi ya ban key din mota da kaina na tuka har cikin mkrta nan mukayi sallama. Tun ranar bai kuma zuwa ba sai dai mu yita vedio call da daddare . A kwana a tashi sai gashi an soma biki ni dai banje ba duk da magiyar da ya dinga min amma na ki yarda. Ranar Saturday sai ga wayan ya salman abin har ya ban mamaki don mun dade bamuyi waya ba. Bayan mun gaisa yace " nazo ina gari tun Monday amma baki Sani ba . Nace,wlh kuwa yaya ba Wanda ya gaya min Yace " to ki shirya anjima in ba kida lectures zamuzo da Wanda na fada miki din domin Ku fahimci juna. Nan take yanayin fuskata ta sauya kamar nayi kuka ni me yasa na amince masa ne ?gashi kuma ina tsoron ince mishi na fasa. Haka na daure jikina a sanyaye nace" to yaya sai kun zo . Ya amsa hade da katse wayarsa. Nafi awa daya ina zaune ina tunanin mafita.kai nifaa inaga zan fito baro baro ince mutumin baimin ba kar in cuci kaina a banza. Can karfe uku da rabi ya sake kira wai har sunzo ya fada min inda suke. Kirjina sai dukan uku uku yakeyi na daure dai na tafi gaban mirror na sake gyare fuskata da powder na shafa lipstick kadan dama less ne a jikina swiss mai kyau army green da adon pink don haka takalmi na da gyalena pink ne masu kyan gaske gaskia ba laifi nayi kyau sai dai ban damu da in birge Wanda yazo da yayaba . Dan humra kadan na shafa dan ciwona baison turare mai karfi ko Wanda ake spraying shi yasa nafi amfani da humra da kuma kulacca marasa tashi sosai ma,ana masu sanyin kam shi Lokacinda na karasa mamakine ya bayyana karara a fuska ganin shi da ya salim ne kawai duk sunsha jumper da hula sunyi matukar kyau sosai. Ya salim ya fito daga cikin mota cike da fara,a yace" you are welcome gimbiyar mata. Murmushinda bai kai zuci ba nayi na shiga waige waige ko zan ga wani na duba motar ma ba kowa sai ya salman din kadai ya kame fuskarnan a murtuke ko kallo ban isheshi ba .a raina nace" to Allah na me ke faruwa. Na daure na gaishesu ya salim ya kalleni cike da fara,a yace kina ta dube dube kina neman wanda yayanki ya kawo miki koh.? Shiru nayi Yace" rumaisa karki wahalar da kanki NI NE!!!!! Ido na zaro cike da mamaki na kalli ya salman wanda har lokacin bai ma juyo ya kallemu ba .na sake kallon ya salim Wanda sai murmushi yake tayi min. Na shiga uku !!!! Na fada a raina...... Hauly ce👍🏻😍 [05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 Page➡18 **********Kwanana biyu a gida Sadiya ta haihu.ta sami da namiji. Wai murna gun inna abun ba magana.hakama Abba don wnn shine jika na farko a gidan. Amma abin mamaki Sam uban yaki zuwa hakama danginsa abinda ya dami kowa knn don sadiya har kuka ta yi Saida inna tayita lallabata. Ya salman cewa yayi ita ta jawo. Ranar suna ma shiru ba uba ba danginsa anan fa inna tace sai taje ta samesu taji dalili.Abba yace kar ta kuskura taje bama ita ba kowama yaje ko ya tanka bai yafe ba abarsu kawai.don haka ya sawa yaro suna Abdulwahab. Bayan mun gama hidimar suna ne Auren Ahmad ya tashi da salima. Abinka da bikin manyan mutane duk inda kaje zakaji anata sanarwa tuni hotunansu ya yadu koina na pre wedding a social media's. Ina zaune a palon inna ina shirya Abdul bayan an mishi wanka Ahmad ya turon hotunansu. Gaskia sunyi kyau sosai ina kallo ina murmushi a raina nace ba girin girin ba dai ta yi mai. Sadiya ta shigo na kalleta nace" yawwa ki shirya ki zo ki karbi Abdul zan wuce makaranta ina da lectures shadaya. Tabe baki ta yi tace" ke dai baki son rike yaro na lura ko ya zakiyi da naki oho. Ban kulata ba ta wuce ciki ta shirya ta dawo Palo ta zauna ta karbeshi ta fara bashi mama. Har zan tashi ta kalleni ta yi kasa da murya tace" yawwa rumaisa don Allah in kin fita kina ganin ja,afar? Nace" eh ina ganinsa sai me? Tace" kiyi magana a hankali kar inna ta jiyo ki. Ta shiga dube dube snn tace " so nake ki rakani gunsa da daddare. Tabe baki nayi nace" ki masa me. Harara ta sakar min snn tace " in masa me kk tambaya.to bari kiji zanje ne na mashi wankin babban bargo daga shi har iyayensu bazan ragawa kowa ba sai nai musu rashin mutuncinda basu taba tunani zan iya ba.... Na tari numfashinta da fadin" to shine me inkinyi hakan? Tace" kinga in zaki rakani ki rakani in kuma baza ki rakani ba ki fada min kawai . Tsaki naja nace " bazanje ba ko da kuwa neman tsulhu zaki bare kuma neman fitina.bari kiji Sadiya in kin manta ni ban manta ba anan nayiwa raihana magana kikazo kk hada ni da inna kuka zageni don haka ba ruwana da abinda ya shafi rayuwarku........ Inna ce ta shigo hade da fadin " da akayi me? Tana kallona na sunkuyar da kai na rasa me zance . Ta kalli Sadiya tace " me kuma ya hada ki da ita bayan kinsan ba kunya ne da ita ba. Ba kunya ba tsoron Allah sadiya ta kalleni snn ta kalli inna tace" wai fa inna tun akan maganar raihana da mukayi shine wai mun mata gorin asali ni da ke kuma munce batada uba Shine ta kama zaginmu. Cike da mamaki nake kallon sadiya kafin na bude baki tuni inna ta hau kaina da fada" eh munce bakida dangi kuma bamu San waye ubanki ba.in ya dameki kije ki zo mana da ubanki da danginnaki mugani mara kunya kinzo kin sako mu a gaba kina zaginmu waye sa,anki a cikinmu? Ko uwarkice ta aikoki ki zo ki zagemu? Hawayene ya cicciko idona har ya fara zuba wlh da ba don darajar ya salman ba da inna bata isa ta dinga fada min maganganu ba bare Sadiya. Sadiya ta karba " sai anyi magana ki fara kukan munafurci anjima ki fadi kice kirji na ciwo.ai sai kiyi ya salman na nan shi ya saba kinkimarki yana kaiki asibity sai yazo ya kaiki..... Inna ta katseta da fadin ko mutuwa zata yi salman bazai zo ba muddin ni na tsugunna na haifeshi don wlh ya isheni abubuwanda yake ma wnn shegiyar yarinya...... Aikuwa bata karasa ba muka jiyo sallamarsa . Da gangan na dafe kirji na na fara numfashi sama sama ina kokarin faduwa kasa daidai lokacin da ya shigo aikuwa da hanzarinsa ya tareni a rude yana " rumaisa me ne ne me yake damunki ? Kara damkoshi nayi nace" yaya.... Yana kallon fuskata yace,"na,am ko muje asibity...... Inna ta katseshi da fadin" iye! A lallai na kara tabbatarwa kaina yarinyar nan bayan rashin kunya da munafurci harda kirsa da kissisina ma ta iya.to bari kaji saketa babu inda zaka kaita ta mutu intaga dama. Shikam bai ce komai ba ya sake dubana idona na lumshe ko a jikina yace" me kk ji? A hankali nake magana ni a dole mara lfy nace" jiri nakeji yaya. Yace" ba kiyi breakfast ba koh? Na daga mishi kai Inna da sadiya kam sun gama cika fam har wuya. Yace" me yasa kk wasa da lfyrki ? Yanzu tsaya ki breakfast idan jirin bai bari ba sai muje hospital. Ya saukeni kan kujera sannan ya kalli inna yace" inna ina tea yake? Wani uban harara ta watsa mishi tace" ban Sani ba ubana. Bai damu ba ya kalli sadiya yace" ke ina tea? Tana zumbure da baki tace" yana flaks a daki. Baice komai ba ya je ya dauki Kofi da cokali ya wanke ya shiga ya hado min tea da madarar mai jego ya lafta madara da milo ke kyace kunu ne ya dauko ledan bread ya kawo gabana inna tsabar takaici fita ta yi sadiya kuwa daki ta shige don haushi. Ya ce" taso kisha tea sai muje asibity. Na tashi a hankali sannan nace " naji sauki yaya ba sai munje ba zan tafi school. Ya zuba min ido hade da fadin " are you sure? Na gyada masa kai . Cikeda gamsuwa yace" to gashi oya sha mu tafi na kaiki school din. Na karbi cup din na fara sha bread slize daya kawai naci da kyar sannan na shanye tea din. Na shiga ciki na karasa shirina sadiya sai bina take da kallo ni dai ko oho ko ba komai nasa su jin haushi. Ashe ni bansan cewa na jawo mana BABBAN MATSALA wacce ba zamu taba mantawa ba . Bayan tfyr mu inna ta shigo ta sami sadiya a daki ta zauna jikinta a mace tace " sadiya maganar da kk gaya min tuntuni inaga shi yake shirin faruwa..... Sadiya ta tabe baki tace" yake faruwa dai ba shirin faruwa ba inna.wlh wlh wlh ko kaffara bazanyi ba ya salman son rumaisa yake. Inna ta dafe kirji da fulatanci tace" hande mi woni min shatu(yau na shiga uku ni shatu)!!!!! Sadiya tace " inna zama bai samemu ba kwata kwata. Inna ta gyada kai tace" gaskia ne don kuwa wlh bazan taba yarda hakan ta faru ba. Ta kalli sadiya tace" me abinyi kaina ya daure gabadaya. Sadiya tace "hmm kiran goggo Amina zakiyi ki gargadeta domin itace ta shirya komai dama na fada miki tuntuni sai wani Jan ya salman take a jiki.har girki take shiryamasa ta kirashi yaje yaci anan ta dinga Barbada mishi magani har suka shawo kanshi.ki lura da kyau yaya in yaga goggo Amina tazo har rawan jiki yake yana mata fara,a alhalin ke tsakaninki dashi kullum gaisuwa ya bi ya daure fuska.inna duk da nasan haka halinsa yake amma wlh da kuna zama kuyi shawara amma yanzu faa? Rabon da ki zauna da yaya kuyi tadin arziki tin yaushe? Inna ta yi zumbur ta mike ta shiga sintiri a dakin sannan daga bisani tace" lallai na so nayi babban sake.amma Na gode da kk maidani kan hanya sadiya Allah ya miki albarka. Ta dauki wayarta ta mikawa sadiya tace " yanzu lokaci yayi da zan nunawa amina karyarta tasha karya wlh.kira min ita da sauri. Sadiya ta lalubo number din mama ta kira bugu biyu yayi ta daga hade da sallama Da yake a handsfree suka sa Inna tace" amina Mama tace" na,am lfy? Inna tace" aike zan tambaya.shin ke kika haifa min salman ne? Mama tayi dariya tace" aa bani na haifa miki shi ba amma dana ne nima kuma ina da iko akansa a matsayina na kanwar mahaifinsa wacce basu da tamkar ni duk dangi.wnn tunatarwa ce kawai nake miki don nasan kin Sani . Inna tace" ooo wnn shine dalilinda yasa kk juya min.da kamar ke kk tsugunna kk haifeshi? Mama tace " kinga shatu na lura na lura akwai maganar taki tana da yawa ni kuma dama yanzu ma nike shirin zuwa gidan naku don naji ya kasim na gari ki jira har nazo sai ki fadi abinda kk so iya San ranki kar ki bata katinki. Kafin inna ta yi magana ta kashe sadiya tace kinji munafurci ko inna so take ta hadaki da su Abba ne. Inna tace "ai kuwa koma meye ne yau za,ayita ta kare. Ba tare da an dau tsawon lokaci mama ta iso kamar kullum kanta tsaye ta wuce palon Abba nan ta sameshi da daddy. Cikin fara,a suka tarbeta ta zauna suka gaisa ta kalli daddy tace" ya kasim tunda kk zuwa garin nan baka taba zuwa ka gaisa da alhaji ba sai complain yakeyi. Abba yace" a kasim baka kyauta ba gaskia. Daddy yace" kiyi hakuri Amina zanje watarana. Mama tace" ni dai naki. Daddy ya kalli Abba yace" ka jita ko yaya ai inaga shi Alhajin ne ya kamata yaxo ya gaisheni tunda kanwata yake aure ko? Gaba daya dariya sukayi yace" amma ba komai in ya miki gobe zanje. Mama tace " yawwa yanzu naji magana. Suka danyi shiru sannan Abba yace yanzu Amina abinda za,ayi kira min shatu kuxo tare. Mama ta danyi dim sannan ta mike ta tafi dakin inna daga bakin kofar palon ta tsaya ta daga labule sadiya ta gani suna hada ido sadiya ta hade fuska kamar bata taba dariya ba. Mama tace" sadiya ina innar taku? Tace"tana daki. Mama tace" kice mata Abbanku na kiranta. Har ta juya zata fita ta dawo tace" au bamu ma gaisa ba ya jego ya dan naki? Kunya ne ya dan kama sadiya ta amsa da lfy. Mama tace" to haka akeso. Ta juya ta tafi dakin mmn sakina suka gaisa a tsassaye sannan ta koma gun yayunta. Tuni kuwa ta sami inna taje. Ta sami wuri ta zauna gabadaya palon ya danyi tsit Daddy ne ya fara magana" mun taraku anan ne saboda wata magana mai mahimmanci da ta taso.shi ya kawo ni takanas ta kano. Ya fada yana murmushi. Sannan yaci gaba da fadin" a gaskia ni da yaya mun jima muna son hada auren zumunci tsakanin yaran mu don ganin yadda rayuwa ta koma an daina mutunta zumunci.gaba dayanmu ana mun Sani daga kano har Kaduna muna da yan uwa da dangi amma zumuncin yaki dorewa tsakaninmu munyi munyi har mun gaji mun bari yanzu ta kai ta kawo yaranmu basu san wasu daga cikin dangi ba.to ba yanda muka iya tunda sun ware mu basu son zumunci damu shine mu ke son mu mu hada 'ya'yanmu auren don dorewar zumunci. Ya dan numfasa sannan yace" mun so mu hada salman aure da faiza amma Allah baiyi ba saboda yaron nan RABI'U ISA(Ra'is) ya dade da nuna yana son faiza kuma akwai kyakkyawan alaka tsakanimu da mahaifinsa.dole muka hakura .daga baya shi kuma salim munso mu hada shi da sakina amma baiyiwu ba kowanne daga cikinsu ya riga yayiwa kansa zabin abokin rayuwarsa ba yanda muka iya don bamu son takura masu. Amma sai gashi kwatsam Allah ya dubi zuciyoyinmu da zumuncin da muke son karfafawa sai ya hada SALMAN da RUMAISA soyayya. Wayyo inna ji ta yi kirjinta kamar zai fado ta sa hannu ta dafe gaba daya taji ta wata iri tsabar bakin ciki har bata gani mai kyau. Mama kam bata yi mamaki ba don babu abinda salman ke boye mata duk da dai bata San yaushe maganar mu tayi karfi haka ba. Abba da daddy kam fuskarsu dauke da fara'a. Daddy yace,salman da kansa suka je Abuja jiya da danuwansa ya sanar dani da bakinsa cewa sun fahimci juna da rumaisa don haka na bar komai a jiyan na taho kano tare da su na kira rumaisa ni da ita na tambayeta tace hakane kuma ta amince.shine nace alhamdulillah mun gode Allah shine muka taraku mu gaya muku wnn abin farin ciki me kuka ce. Mama ta saki murmushi tace " masha Allah yaya babu abinda zance ni dai sai Allah ya tabvatar da alhairi kuma na gode da kulawarda kuka bamu ni da 'yata. Alhamdulillah sukace Abba ya kalli Uwar gidansa yace" shatu bakice komai ba. Ai kaman jira take a mata magana kawai ba sai ta fashe da kuka ba lol! Daddy ya kalli Abba yace " to me kuma na kuka. Mama kam dariya abin yaso ya bata. Abba ya kallerta yace,shatu kukan fa na meye? Cikin muryan kuka tace" ba dole inyi kuka ba in ba kuka nayi ba me zan yi ? Kun hada kai kun dauki shegiya wacce ba,a San asalinta ba,a San waye ubanta kun likawa dana dan kun tsaneshi.me ye salman ya muku a rayuwa kk mishi irin wannan abubuwan da farko kun daukeshi kun turashi makarantan mugaye yanzu kuma kun rasa wacce zaku bashi duk dangi a matsayin matarsa sai RUMAISA? Ta kara tsananta kuka . Abba yace,kinga shatu duk abinda kk fada ba haka bane salman da kansa yace zaije makaranta soja sannan shi ya zabi rumaisa a matsayin wacce zai aura sanin kanki ne bama takura ma yaran mu abinda suke so shi muke musu in dai basu kaucewa fadin Allah da manzansa ba. Innatace "wlh salman ba son rumaisa yake ba kawai dai makircine. Abba ya fusata " kaji zancen banza to su waye suka hada makircin....... Daddy ne ya katseshi da fadin " yaya karka bata rai bari in kira salman yazo Nan da nan daddy ya kira salman aiko minti biyar mai kyau ba,aiba sai gashi ya shigo hankalinsa ya tashi ganin inna na kuka . Aikuwa tana ganinsa ta mike tun kan ya zauna ta fuskance shi cikin tashin hankali tace" Salman fada min wai Kaine da kanka kace kana son rumaisa ? Shiru yayi ya rasa me zai ce mata ya riko hannunta yace " inna zauna bana son inga kuka. A fusace ta wanke shi da mari cikin tsawa tace " zaka amsa min tambayata ko kuwa. Ya dafe kuncinsa yayinda ya sauke kansa a kasa yace " eh inna ni nace ina sonta kuma nake son aurent..... Bata bari ya karasa ba ta sake dauke fuskar sa da mari tana shirin karawa Abba ya ce" kar ki kuskura ki sake marinsa ya isa haka. Riko wuyar rigar salman tayi tana kuka tana cewa" duk duniya ka rasa wacce kk so sai RUMAISA? Kasan wace ce ita ? Kasan ta wace hanya aka sameta? Salman ina so ka Sani ban amince ka auri rumaisa ba kuma wlh idan ka aureta sai ka biyani NONO na da kasha!!!!! Ta fice tana kuka mai tsanani. To fa!!!!!!!! Hauly ce👍🏻🤝🏻😍 [05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *Wannan* *page* *_naku* *ne* : *CHUBADO *MOH'D* ( *Uwar* *dakinmu* ) *&* *UMMI* *ABDULLAH* *na* *gode* *da* *kulawarku* *sosai* . ```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` Page➡17 *********Ganin yanayinda na shiga yasa ya salim riko hannuna ya na kallona yace" rumaisa ko dai ban miki ba? Naga kamar bakiyi farin ciki da zumuncinda muka kulla ba. Kai na sunkuyar jikina a mace sosai na kakaro murmushi na dole Wanda yafi kuka ciwo duk da ni kaina bansan dalilinda yasa naji banson ya salim ba. Murmushi yayi yace " kinga shiga mota bari inje in siyo drinks ina zuwa. Ya bude min gaban motar ya salman na kame ko a jikinsa don tsabar duniyanci waya ma yakeyi hankali kwance. Ya salim ya kalleshi yace" Oga sir gata nan ka mata karin bayani ina zuwa naga ka dage sai soyewa kk a waya .in ka gama kayita daurewa mutane fuska tsabar mu ka raina. Ni dai na shiga na kuma zauna ya salim ya rufe kofar ya tafi. Mamakin yanda ya salman ke waya cikin nitsuwa da nishadi har da 'yar fara,a nake.na dai San sun rabu da Salima ko dai ya samo wata ne? Maganarshi ta karshe naji wani rass! "Ki kula da kanki sweet heart komai zai daidaita insha Allah tnx u bye. Ya sauke wayar a hankali ba tare da ya kalleni ba ya kunna na,urar sanyaya mota hade da daga glass sannan yace" gaskia kano ana zafi. Sai lokacin ya kalleni kamar bai son yin maganar yace " Salim din ya gama yi maki bayani ai? A sanyaye nace"eh yaya. Yace" Good, to me kk ce? Na danyi shiru snn na daure gudun kar na cuci kaina a banza nace" amma yaya kamar ka ce min ya salim ya sami wata a Abuja har maganar su tayi karfi? Shiru yayi har na tsawon minti biyar har na cire ran zaiyi magana sai naga ya juyo sosai ya fuskanceni cikin sanyi murya yace" ba salim ne na zaba miki ba. Da sauri na dago na kalleshi cike da mamaki sannan na juya na duba bayan mu ba kowa na sake kallonshi a karo na biyu shima ni yake kallo da sauri na sunkuyar da kai nace" to wayene? Ba zato ba sammani naji yace"SALMAN ne ma,ana nine. Tsabar mamaki bansan sanda na zaro ido na saki baki ina kallonsa ba shima ni yake kallo . Bansan tsawon lokacinda muka dauka a haka ba kowa da abinda ke ransa. Hannuna da ya riko shi ya dawo dani duniyar tunani dana tafi da sauri na sadda kai kasa. A hankali naji yace" RUMAISA kaina na zabawa ke a matsayin abokiyar rayuwata.amma fa sai kin Amince don ko da wasa bazan so kaina in kuntata miki ba. Ya dan numfasa sannan yace"Rumaisa INA SONKI zuciyata ta dade da fara sonki. Nikam zuwa yanzu tsoro ma na koma yi bayan mamaki. Ban ankara ba naji ya matso da fuskarshi dab da tawa har muna exchanging numfashi a hankali ya furta" kin amince? Wani masifaffen kunya ne ya ziyarceni har na kwaci hannuna ba shiri na rufe fuskata.a can cikin zuciyata kuwa farin ciki nake sosai don ina matukar son yayana. Sautin murmushinsa na jiyo sannan yace" kunya ko? Bari kiji yanda na zo da kaina na Isar da sako ba tare da na aiki kowa ba kema haka nake son ki ban amsata kawai. Kai kawai na iya daga masa don har lokacin fuskata rufe. Ji nayi ya riko hannayena duka ya sauko da su sann yace" to oya gaya min kin Amince? Ya fada yana kallon fuskata . Duk na rasa yanda zanyi saboda kunya. Da kyar nace" eh! Wayyo ji nayi kamar na nitse gashi ya tsura min ido kallon ma na daban ne yau. Murmushi yayi sosai yayinda ya jawoni jikinsa rumgumeni yayi sosai a cikin kunnena yace min" masha Allah kanwata na gode sosai gaskia bazan iya manta wnn rana a tarihin rayuwata ba .Kanwata ina sonki sosai ke din dabance a cikin mata.Allah ya miki albarka. Nikam dada kwantar da kai nayi a kirjinsa ina jiyo bugun zuciyarshi ido na lumshe ina shakar kamshin turarensa mai dadin gaske yayinda sanyin Ac ke ratsani.wani dadi da farin ciki nakeji mara misaltuwa. Ya dago kaina a hankali sannan ya riko hannuna ya zuba ma yatsuna ido sai naga ya Ciro wata container mai kyau a aljihunsa sai daukan ido yake ya bude wata zobe ya cire tsiriri mai kyan gaske na gold yana ta daukan ido ya kamo yatsata na hannun dama ya saka min . Murmushi yayi yace" wnn tukuicin kyautar da kk min ne kanwata na gode sosai Allah ya miki albarka Allah ya nuna mana aurenmu rai da lfy. Kaina a sunkuye nima ina murmushi nace " na gode yaya Allah ya saka da alkahairi. Yace" yanzu kije ki shirya kizo mu tafi gida . Nace " to Daga nan na bude motar na fita hade rufo masa kofar . Har na isa hostel bakina ya kasa rufuwa don farin ciki wayyo Allah ba dadi zai kasheni anya akwai macenda ta kaini sa,a kuwa? Lol Da sauri na dauko jakata da wayoyina Wanda na saka a silent. Ina zuwa ashe ya salim ma ya dawo don haka na shiga baya mun fara tfy ya salim ya dinga zolayata nikam duk kunyansu nakeji ya salman kam baice komi ba Sai da ya gama zolayarmu snn yace" to yanzu kuma saura na maku nasiha a kan zamantakewar rayuwa. Ya danyi gyaran murya sannan yace" rumaisa ga dan uwana amana ki rike shi da kyau ki nuna masa so da kulawa ki masa biyaiya sannan kiyi hakuri da halinsa kinji . To. Na fada a hankali Sannan yace " kai kuma ga ' yaruwata maganar daure fuska tsawa fada da makamantansu duk ka aje su a barikinku sosai zaka zage ka nuna mata so da kulawa ka jawota jikinka kaji matsalolinta Ku zauna Ku fahimci juna a tattauna kowa yasan me Dan uwansa yafi so me kuma ya tsana don a kiyaye sannan duk wuya duk rintsi a rike gaskia wnn shi zaisa soyyayya ta dore har ta kai ga aure fatan ka fahimceni? Shiru ya masa kamar ba da shi yake maganar ba. Can muna cikin tfy ya salim yace" wai ni baka fada min yadda kuka kare da mutumiyar ba. Sai lokacin yace" ta yi serious kan maganar nan fa kawai ka hkr ka nemi fili a abujan.in dai don ni kk son zaman kano na yafe don nima ba mazaunin nan bane..... Tsaki ya salim yayi yace" wayace maka saboda kai ne? Ni ra,ayina nafison in zauna cikin dangina don haka ba wacce ta isa ta juyani.wlh salman zan iya rabuwa da rumasa'u akan wnn.. Ya salman yace" kar ka fara don rumasau tana sonka ka Sani kawai dai tafi son zama Abuja kusa da iyayenta ne ga kuma makarantarta don haka a wnn tfyr dai kaine baka da gaskia.in zaka bi shawarata Ku zauna Abuja tunda kaima acan kk aikinka in yaso in kun samu hutu sai kuzo kano a hankali a hankali watarana sai kaga kun dawo kanon gabadaya ko ya ka gani? Ya salim yace" hmm na tuna wnn amma kasan me ya bata min rai? Irin yadda naga take ta fishi akan nace a kano zamu zauna.anya kana ganin wannan yarunyar zata so min ' yan uwa da dangina? Ni faa nafi son matar da zata so min yanuwana ta zauna cikinsu a hada kai a zama daya. Salman yace " na fahimce ka kuma insha Allah sweet heart ma tana daga cikin jerin matan da kakeso karka damu. Ya gyada kai yace" to Allah yasa. Har muka isa gida suna hirar wnn yarinyar da naji sunace mata Rumasa'u Tare muka shiga gida palon abba muka shiga na gaisheshi ya amsa da fara,a kamar kullum ya sanya min albarka ban mmn sakina ta kawo ma su yaya abinci ni kam fita nayi bayan mun gaisa da ita na wuce dakin inna a Palo na sameta da sadiya suna Dan hirarsu sadiya ciki.ya kara girma ko yau ko gobe Inna na ganina ta kauda kai sadiya kuwa cewa tayi " yau kuma ya salman yaje ya daukoki muna cikin zaman lfy mtsww. To! Inda sabo na saba bance komi ba ba zauna na gaida inna da kyar take amsawa. Ni dai yanzu tunani daya ya inna zatayi in taji maganar aure tsakanina da ya salman ? Shin zata amince? Masoyan rumaisa salman kuyi hakuri da rashin post dina na jiya yanayin rayuwa ne sai a slow. Na gode da irin kulawarku gareni. Hauly ce👍🏻😍 [05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 Page➡19 *******A makaranta dana je banda labarin auran Ahmad da Salima ba abinda ake ni dai ko a jikina. Da yamma ya salim ne yazo ya daukeni nace" ya salim ina yayana? Yayi murmushi yace"yana gida cewa yayi kansa na mishi ciwo. Cikin yanayin damuwa nace" Allah ya sawwaka. Yace,ameen Muna isa gida.gidansu ya salman na shiga a Palo na sameshi yana kwance ido ya zubama TV amma ko kadan da gani ba TV dinne a gabansa ba. Sai da nayi sallama baki biyu sannan yajini ya amsa yayinda ya zubo min ido hade da fadin " har kun dawo? Zama nayi a kujera one seater ina fuskantarsa nace" eh.ya salim yace kanka na ciwo shiyasa nazo na gaisheka. Ya danyi murmushi yace" na gode kanwata.yanzu kije gida kici abinci sai ki shirya na kaiki gidan goggo Amina . Nace" to yaya. Na tashi ntsoro a gida na wuce amma ina sallama kofar dakin innah kamin in shiga Naji wata uban tsawa da ta daka min har na gigice " Uban me zaki shigo ki mana a dakin yanzu kuma tunda burinku ya cika ke da uwarki kun raba ni da dana. Sadiya ta harareni tace " ko da wasa kar ki kuma yarda kafarki ta sake takowa dakin nan munafukai masu hada da da uwarsa. Jin maganganun nasu nake kamar a mafarki jikina a mace na juya na nufi dakin maman sakina. A daki na sameta na zauna a sanyaye nace" mama me ya faru ne ? Tace" hmm rumaisa komai ma ya faru yau a gidan nan tsakanin inna da mamanki sunyi ba dadi wlh. Nan da nan na zaro ido a tsorace. Mama ta gayamin komai Ashe har sun danyi sainsa ma da Mamana kuma tace in salman ya kyskura ta aureni saita tsine mai Anan ta fusata Abba yace wlh in ta tsine masa sai yasa an daureta lol! Nikam gaskia jikina ya mutu sosai tuni hawaye ya fara gangarowa wani na bin wani. Tashi nayi na dauki jakata na fita ban zame ko ina ba sai gun ya salman . A inda na barshi nan na kuma samunshi. Yana ganina a birkice ya mike da sauri yace" lfy me ya sameki? Zama nayi a kasa ina mai ci gaba da kuka da kyar na iya cewa yaya don Allah ka janye maganar auren nan wlh yaya akwai babban matsala bana son inna ta maka baki yaya. Naci gaba da kuka sosai . A hankali ya fara min magana cikin tsigar rarrashi yace" bana son kina daga hankalinki saboda kar ciwonki ya tashi. Rumaisa ko ba soyayya zan aureki domin in kawo karshen gaba dake tsakanin goggo Amina da Inna Wanda tun ba a haifemu ba sukeyi don haka a ganina aure tsakanina dake zai iya sa Kansu ya hadu su daina wnn gaba mai tsanani duk da cewa ba karamin aiki ne a gabanmu ba don haka dole ne mu tashi tsaye duk wuya duk runtsi kar muja baya da soyaiyar mu mu hada da addua har Allah ya kawo karshen abin. Rumaisa bayan wnn ina sonki banjin zan iya rabuwa dake ba. Har lokacin kuka nike nace" yaya bana son inna ta maka baki. Murmushin karfin hali yayi yace" wnn ce matsalarki ? Na daga mishi kai yace" to ki kwantarda hankalinki da kaina zan shawo kan inna kuma zata amince in har bata saurareni akwai yayanta a Cameroon in na fada mishi zai mata magana kuma zata hkr insha Allah don bata tsallake maganarsa.don haka kwantar hankalinki. Ya yanko tissue ya mika min yace" ungo goge fuskarki ki maida kwalliyarki. Ya fada yana murmushi. Sai lokacin naji sanyi a raina na karbi tissue na goge fuskar nace" Allah yasa ta yarda. Yace" ameen kanwata ina hodar taku? Shashshafa sai mu tafi in kaiki gidan manan naki Nace" babu yana hostel Yace " to shiga toilet ki wanke fuskarki kizo Na tashi na shiga toilet na wanko fuskata daga nan na fito muka tafi. Mama kam ko a jikinta har hira suka kamayi da ya salman ni dai har lokacin ban saki jiki ba. Sai bayan sallar magrib ya koma . Nikam bayan nayi isha na sami mama a daki anan ta fara kwantar min da hankali akan kar in damu ba abinda ze faru insha Allah. Da kyar na danci abinci nasha magani na kwanta.bansan sanda bacci ya dibeni. Sai kawai na fara wani mugun mafarki wai inna tazo da wuka a hannunta ta caka min a ciki ihu nayi Wanda ya tashi mama a bacci tana subhanallah don yau a dakinta na kwanta. Wutar dakin ta kunna tana " rumaisa me ne ne. Tuni na jike sharkaf da gumi duk da Ac bakina na rawa nace " mama inna na gani a mafarki da wuka kuma ta caka min. Dafe kai mama tayi don itama ba ihuna ya tasheta mafarki tayi inna ta hankadata a rami baki wulik sai dai bata fada min ba gudun kar in tsorata Tace,yanzu abinda za,ayi ki yi addua ki koma ki kwanta . Nace" to " sai zazzaro ido nake tsabar tsoro Nayi addua na canza kwanciya na koma na kwanta mama kam bacci ya gagareta Alwala taje tayi tazo tasa hijabi ta hau sallaya ta kama nafila har asuba. Inna kuwa kamar a kunnenta aka kira sallah. Abba na tfy masallaci ta lallaba ta fita sai tashar mota don yau ba abinda zai hanata tfy garinsu. Don Allah amin afuwa bacci yaci karfina.kuyi manage da wnnpage har gobe in Allah yaso sai in karasa Tnx so much masoyana ina muku fatan alheri👍🏻 Hauly ce👍🏻😍 [05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 Page➡20 *********Da asuba mama ta tasheni nayi sallah bayan na idar muka gaisa.tace" dama yau naso inje gun wani malami a yakasai in fada masa halinda muke ciki gabadaya yasa almajirai su mana saukan Qurani ayi sadaka don bazamu zauna mu saki jiki haka ba saboda wahalar da nasha a baya. Nace" mama ai sai na rakaki tunda bani da lectures yau. Tace" bazaiyiwu ba .kina toilet Hajia babba ta kirani a waya tace jiya jikin Alhaji ya tashi basu koyi bacci ba dama next week muke shirin fita kasar waje dashi saboda Ji kin nasa amma yanzu dole kawai zamuyi kokarin tfy. Nace" mama meye ne yake damun Abban? Tace" ciwon kodane wlh. Nace" subhanallah Allah ya bashi lfy Allah sarki Abba. Jikin mama a mace tace amin Nace" kema zaki ne? Tace" eh nine ma zan tafi da shi sai babban dansa doctor Shamsu. Don hajiya babba bata cika lfy ba itama.sannan Hajia ikhlima suna fama da jiyyar mahaifiyarsu suma. Hajiya Fauzi kuma dama ita ake bari a gida kullum in irin haka ta taso. Kamar ince mama ta zauna ita aunty Fauzi taje amma nasan ko na fada ma bazaiyiwu ba. Mama ta tashi ta Dan gyara jikinta tace" bari naje na dubo Alhajin kema zan kiraki in ya fito palo se kije ki gaisheshi. Nace" to mama a masa sannu Allah ya bashi lfy. Tace"ameen. Ta fita Karfe takwas har ya wuce Abba ya ga shiru baiga inna ba don itace da girki amma ko ruwan zafi babu a flaks. Ya fito tsakar gida zai tafi dakinta knn salman ya shigo nan suka gaisa.Abba yace " yawwa kira min innarku Salman yace"to Ya wuce daki amma abin mamaki sadiya kadai ya samu yace" ke ina inna? A tunaninsa ko ta zagane. Sadiya tace"bata nan Yace ban gane ba ina taje da sassafen nan? Kai tsaye sadiya tace" kamaru. "What! Ya fada hankali tashe Yace" a yaushe knn ? Sadiya tace " tun Karfe biyar ta tafi tasha. Salman ya fita hankalinsa tashe yaje ya fadawa abbab shima Abba abin ya bashi mamaki sosai lallai shatu ta dauki maganar nan da zafi . Salman yace" Abba zan bita kawai. Abba yace" aa salman rabu da ita kamaru fa ba,a nan yake ba Allah dai ya kaita lfy. Salman yace Abba da dai ka barni nabi bayanta din Abba yace "aikinka faa? Salman yace " ai sai nan da sati daya zan koma Lagos. Abba ya danyi shiru yace" to bazaka je kai daya ba ka tafi da salim tunda shi hutu ya dauka. Salman yace" Abba salim ya dauki hutune saboda aikin gini in muka tafi tare wazai kula da aikin gini? Ya fada yayinda ya saka waya a kunne ba jimawa ya soma magana da harshen fulatanci abin mamaki kamar ba salman ba.don shi kadai ya iya fulatanci a yaran inna su sadiya sai dai su ji amma mayarwa ba sosai ba.Abba ma yana ji amma bai mayarwa. Ya dan jima yana magana daga bisani ya sauke wayar alamun ya gama. Abba yace" me kawun naka yace ? Salman yace" cewa yayi inje Adamawa tukun kasan suna boda da kamaru suma shiga kamaru ta wajajen yafi sauki don hanyar baida matsala kuma yace in har naje Adamawa to zuwa kamaru ba nitsa. Abba yace " eh ta wajajen mubi na gane.to indai hakane ka bari gobe sai ka tafi Adamawa da flight in yaso sai ka wuce kamarun don garin da 'yanuwan nata suke yafi kusa da Adamawa kana isa boda tfy awanni kadan ne zai kaika kauyen nasu. Ba don ran salman yaso ba ya hkr amma a ransa yana fatan Allah sa inna ta isa lfy. Haka ta kasance ranar ko breakfast baiyi ba. Da yamma ina zaune a palon mama hira muke da Ahmad idona a lumshe. Yace" My Queen wlh nayi missing din ki sosai. Dan tabe baki nayi nace" kaida gobe za,a daura auren akai maka amaryarka kuci amarcinku son rai. Tsaki yaja yace" Queen bana son ki min wnn maganar nifa ban girma ba tukun wnn aure da za,a min kunyarsa nakeji wlh ko friends dina na na nan ban gaya musu ba bare na kasar waje amma abin mamaki duk sunji. Dariya nayi sosai nace" haba king maganar aurenka ina ne baije ba birni da kauye? Waje da gida? Yace " gaskia Queen su dadi sun bata min rayuwq ina Dan yarona inje ina gaisawa da mutane suna tambayata kwanan iyali.. Na saka dariya sosai. Yace" Queen mugunta koh? Nace" no ba haka bane am sorry..... Jin kamar motsin mutum da kamshin turare lokaci daya yasa na bude ido da sauri. Ganin ya salman tsaye a kaina ya zuban ido yasa na mike da sauri gabana na faduwa.danna wayar nayi na kashe ina kame kame "Yaya sannu da zuwa. Kamar ba da shi nake ba .nikam duk na tsorata. Tsunkuyar da kai nayi na kama tattara gashina na zuba baya. Na Dan dago still ni yake kallo nace" am yaya zauna mana. Baice komai ba ya zauna na mike Na wuce dining side na kawo masa drinks ina dire tire din a gabansa na bude kwalin lemo na zuba a cup na dauka na mika masa a tunani bazai karba ba sai naga ya karba harda cemin ya gode. Nace"yaya ya mutanen gida? Yace" je ki rufo kanki tukunna sai ki zo mu gaisa. Murmushi nayi na tashi na wuce daki bina yayi da kallo ji yake kamar ya kamoni ya rumgume jikinsa.da kyar ya iya controlling zuciyarsa ya kauda idonsa daga kallona Nikam hijabi na sako na fito ya kalleni yace " yawwa ko kefa. Nayi murmushi na zauna yace" wannan iPhone me tsada waya baki? Rass naji zuciyata ya tsinke nace" uhmm yaya ma....mama ne ta saya min. Ya gyada kai sannan yace" to dawa kike waya kuma? Na dan Sosa kai sannan nace" Maryam ce. Yace" OK Mukayi shiru sannan yace " goggo Amina bata nan ne? Nace" tana side din Abba Nan na fada masa rashin lfyr Abban. Anan yace muje ya gaisheshi. Muka tafi side din Abba duk yawanci yan gidan suna nan kuma ya ma sami sauki . Muka gaisheshi cike da fara,a ya amsa. Mun dan zauna kadan sannan mu ka dawo side din mama harda ita. Anan ya salman yake gaya mata gobe zai tafi kamaru . Ya gaya mata komai bai boye ba. Ta danyi shiru sannan tace" Salman idan faa aurenka da Rumaisa alkhairi ne za,ayi insha Allah don haka Inai muku fatan alkhairi ita kuma Allah ya huci zuciyarta ta amince. Yace" amin. Tace koda yake gobe nima zamu fita India da Alhaji. Yace " Allah ya kaiku lfy sannan ya bashi lfy. Tace "amin salman kaima Allah ya kaika lfy kuma a gaishesu duka. Yace" insha Allah goggo. Nan ta mike ta shiga ciki ba,a jima ba ta fito sanye da hijabinta tace" zan fita sai na dawo. Nan muka mata a dawo lfy. Shiru muka zauna shi baice komi ba ni kuma har yanzu dan nayin shi nakeji.na rasa tadin da zan masa. Ganin zaman shirun yayi yawa yasa na dan dake nace " yaya gobe zakayi tfy knn baza ka sami zuwa daurin auren Salima ba? Kamar ba zaiyi magana ba har na fara tunani ko laifi nayi sai naji yace" salim zaije ai. Nace" hakane kuma. Sannan yace " rumaisa yaushe zaki koma hostel to? Nace" gobe insha Allah don muna test ma. Yace"OK Muka sake yin shiru .hmm lallai soyaiyar kurame mukeyi lol! Na lura yaya Sam bai son hiran soyayya ba kamar Ahmad ba . A hakan dai muke hiran jefi jefi har azahar ya tafi. Washe gari kuwa mukayi sallama dashi ta waya na mishi Allah ya kiyaye hanya Abba ma da mama na masu sallama mama ta ban kudi masu yawa dan tace bata San yaushe zan dawo ba.duk naji ba dadi na ce " mama weekend fa? Tace" ki tafi gidanku. Nace" wayyo mama su sadiya sun sakoni gaba faa. Tace" to ya za,ayi ki koma dakin rabi. Nace " kawai mama zanci gaba da zama a hostel abina. Tace,aa ban yarda ba wlh ki dai dawo gidan. Nace to mama Haka mukayi sallama kamar zanyi kuka.na koma makatanta. Ranar Monday na hadu da Amarya Salima an kawota har da guards(ke ko ba dole ba surukuwar gwamna) Sai rigima takeyi tana ta shan kam shi. Dariya ta bani ace kiyi aure miji ya ajeki fanko? Meye amfanin auren to? Ya salman bayan isarsa kamaru sunyi case sosai a can da inna don sai da yayyunta sukayi da gaske sannan ta amince anan ta yafe mishi kuma tace zata dawo amma ba yanzu ba sai ta Kara one week bata gama shirye shiryenta ba tukun. Dole ya hkr ya dawo ranar talata saboda zai koma Lagos . Haka nan yazo mukayi sallama a tsassaye Washe gari laraba ya tafi Lagos. Muna waya da mama ma sai dai jikin abban ya tsananta sosai.duk sun shiga damuwa abin tausayi sai fatan Allah ya bashi lfy. Hauly ce👍🏻😍 [05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 Page➡21 ***********Ranar asabar da yamma na gama shirin tfy gida. A get din fita mkrnta sai ga Ahmad ya danno kai da mota. Yana ganina ya saki murmushi ya gyara parking ya fito. Murmushi na danyi nace"Ango Nan da nan ya hade fuska yace" bana son ki kirani da wnn suna Queen. Yanayin yadda yayi maganar ya tabbatar min yasha ya bugu ne don idonsa yayi ja sannan da kyar yake iya bude ido gashi ko tsayuwa mai kyau bai iya yi ba. Takaici ne yabi ya isheni gaskia ko bazan auri Ahmad ya kamata inyi wani abu.don ya kamata inyi amfani da son da yake min in hana shi shaye shayen nan tunda neman mata dai bai dashi.kamin hankalinsa ya koma can I have to do something. Bude min gaban motan yayi yace" my Queen zo ki shiga muje na kaiki nasan gida zakije. Na girgiza kai nace"aa na gode.amma kasan me na ke so da kai? Ya girgiza min kai kaman wani karamin yaro. Nace" to yanzu dai zo mu samu wuri mu zauna . Muka je muka zauna . Na kalleshi nace" king ba girmanka bane ka dunga shiga mutane cikin maye yanzu haka nasan Salima na makarantan nan don na wuceta da kawayenta zakaje kasa taji kuny....... Cikin daga murya yace" O my God ba kinga dalilinda yasa nace miki bana son aure yanzu ba queen wlh...... Na tari numfashinsa da fadin kaga ni bana son jin komai daga gareka domin baka cikin hayyacinka don haka bani wayarka Na kira driver yazo ya kaika gida kaje ka kwanta kayi bacci. Zaiyi magana nace uhm uhm bana son jin komai . Ya lalubo wayar sa yace"amma fa queen yawa kk yi.don fa kece. Shiru nayi fuskata a hade . Ya kira driver da kansa naji yana gaya masa inda yake.. Kusan minti goma sha biyar sai ga shi yazo a daidaita. Ya gaishemu cikin girmamawa. Na mika masa key nace" rikeshi kuje mota kaishi gida yaje ya huta Da yake duk sun San halinshi na shaye shaye sun saba na kalleshi nace " idan ka warsake zamuyi magana . Idonshi a limshe yace " kizo muyi dropping dinki mana. Nace" aa kuje kawai na gode. Saida naga tfrysu sannan nace" Allah ya shiryeka Ahmad. Nan na nemi abin hawa na tafi gida. Duk tunani na ko inna bata dawo ba ashe ta dawo ina ganinta saida zuciyata ta buga. Don tunda ake rikicin nan bamu hadu ba. Ga mamakina sai naga cikin fara,a tace min rumaisa yanzu kk tafe? Cike da mamaki nace" eh inna. Na Dan russuna na gaisheta har da tambayata ya makaranta nace lfy. Tace"jeki ciki sadiya na nan. Nace" to. Na wuce daki a raina ina hamdala an shawo kan inna yanzu kam bamuda matsala. Na sami sadiya tana ba Abdul nono itama dai ba yabo ba fallasa ta min magana har mun gaisa don a karshe ma tare muka ci abinci. Ban taba jin dadin weekend a gida irin na wnn karon ba sadiya har kitso ta min dake ta iya irin kitson 'yan kamaru kanana masu kyau.ina rike da Abdul. Bayan mun gama tace"wnn kitson gaskia yaya yazo biyani? Nace" kar ki damu zan gaya masa ya biyaki. Na kwantar da Abdul nace" bari tunda yayi bacci inje in karbi inna. Tace" to.nima bari inyi shara inzo inyi wanki. A kitchen na sami inna tace"har kun gama? Nace " eh wlh munyi sauri ai.nazo in karbeki ne kije huta. Tace"ai na gama ma yanzu saidai ki debo kwanuka muzo mu kwashe tuwo. Nace" to. Tare muka kwashe na kai na Abba na dawo na tattara sauran na share kitchen . Da safen Monday tuni na shirya tsaf nayi break fast ina shirin fita inna ta fito daga daki ta mika min wani dan roba kamar na Robb tace" ga wnn rumaisa maganin sanyi ne kina shafawa in kinzo kwanciya in Allah ya yarda zaki ji saukin toshewar da kirjinki keyi. Na karba ta sake mikawa sadiya irinshi tace" ke ma gashi kina shafawa yaron nan sakacinki yasa duk yaro ya kamu da sanyi tun bai kai ko ina ba.Allah dai ya bamu lfy naji suna yabon maganin a garinmu sunce hadine na man kadanya nima zan gwada ko kafafuna zai warke. Sadiya ta bude ta sa a hanci tace " eh inna man kadanya ne amma anmasa wasu hade hade kamar da tafarnuwa ma.mun gode wlh zamu shafa kwanan nan duk dama mura yakeyi.munsha magani har mun gaji sai dai yayi sauki. Inna ta ce" ya dai rage naku in kunga dama Ku jefa a jaka kar kuyi amfani da shi ni dai na baku. Nayi dariya nace" aa inna wlh zamu shafa .mun gode. Daga nan mukayi sallama naje na sallami Maman sakina ma na fita. A lokacinda muke exams mama suka dawo jikin Alhaji aminu yayi sauki naje na dubashi amma gaskia ya rame sosai . Sati daya da komawata makaranta mama ta kirani a waya yanayinda naji muryarta na tabbatar ba lfy bace nace" mama ya jikin Abba ? Tace" rumaisa abbanku ciwo ya warke baya bukatan komei sai addua. Dam! Naji zuciyata ya buga na bude baki zan yi magana sai kawai ga hawaye. Na sauke wayar na dafe kai hawaye na zuba .bansan me yasa ba tun da naje naga jikinsa satin can hankalina yaki kwanciya ban gamsu da saukin da sukace ya samu ba.don yanzu ma shirin tfy gida nake inje in sake dubo shi. Allah sarki Alhaji Aminu Allah ya jikansa da Rahma yasa aljannace makomarsa don kuwa mutum ne na mutane tsakaninsa da kowa fatan alkhairi duk arzikinda Allah ya bashi baya kyamar mutane talaka da mai kudi duk nasane kuma yayi fice wurin taimakon Alummar annabi. Karar wayatace ta katseni na duba sai naga ya salman ne na daga masa sallama. Ya amsa hade da fadin "daga jin muryarki nasan ba lfy waya tabo min ke? Nace" babu komai yaya saidai yanzu mama ta kirani take sanar dani Abba ya rasu........ Ya tari numfashina da fadin" what!!!! Alhaji aminu ya rasu ? Yaushe? Na goge hawaye da ya zubo min nace" yanzune tunda kaima bakaji ba. Yace"naga missed calls na goggo Amina nima sai dai na kira kuma bata dauka ba.Allahu Akbar Allah ya jikansa da Rahma. Nace "amin. Daga nan ya min sallama shima jikinsa a mace. Nima da sauri na saka hijabina na tafi. Tuni an cika kofar gida da cikin gida makil da jama,a. Mama kam kam kamin akaishi ma zazzabi ya rufeta ruf ko motsi bata iya yi tsabar tashin hankali. Yaransa na kusa duk sunzo na nesan ma wasu sunzo. Aka shiryashi akayi masa sallah aka kaishi gidansa na gaskia Iyalanshi sun shiga cikin damuwa na rashinshi sai dai ayi masa addua Allah ya jikansa da Rahma. Sati biyu da rasuwarsa sai a lokacin mutane suka watse .amma har lokacin mama ta na kwance sai dai ta danji sauki . Mun gama exams don haka na tattara na dawo gidan mama don ba kowa a gunta sai mai aikinta ga takaba. Dawowata ya dan rage mata damuwa da kewa . Ranar muna zaune muna hira nace" mama yanzu in kun gama takaban gida zaki koma? Tace" dole na ai ya zan yi? Nace" mama yanzu inna ta daina halayenta Mara kyau ai ta tuba. Dan murmushi mama ta yi sannan tace" hmmm ki dai bi a hankali kar ki saki jiki da ita ni ban yarda da ita ba har yanzu. Nace" mama kawai ki zauna a sashin daddy tunda ba kullum suke zuwa ba. Tace" eh shima yayan haka yace sai dai gaskia ni na yanke shawaran dan filina da suka bar min a cikin gidan zan gina nawa zan fi sakewa da kayaiyskina.don ban cika son takura ba.yanzu tuni ma nayiwa ya Mohd maganar kuma na tura kudi a fara aiki. Nace" to Allah ya taimaka. Tace "amin Daganan shiru mukayi. Ina shirin shiga kitchen sai ga wayar faiza wai gasu nan a kano itada sakina sun fasa tfy Hutu Abuja nan zasuzo mu zauna da mama. Nan da nan na hau murna na wuce kitchen ina fadin " kai faiza uwar surutu zata zo. Gaskia hutun ba laifi har muka gama ba wani tashin hankali.mama kam zuwa yanzu tuni sun saba. Mun dawo makaranta sai dai Sam ban gamsu da yanayina ba.ina yawan jin ciwon mara sannan ciwon kai. Haka naje asibity aka hada dubani wai ko infection ne aka rubuta min magani na saya na sha amma kamar a banza saima abinda ya karu ciwon mara har da kyar nake iya tfy. Don haka na yanke hukuncin zuwa gun doctor Hakim tun bayan rabuwarmu yau sai gani a office dinshi cikin fara,a ya karbeni sama sama muka gaisa anan na fara mishi bayani yanayinda nake jin maran da kuma...... Ganin nayi shiru yasa shin fadin" kar ki boye min komai saboda insan irin treatment dinda zakiyi ki daure ki fada min. Kaina a sunkuye cikin jin nauyinsa da kuma kunya nace" ina yawan jin sha,awa sosai har na kanji wani lokacin kamar na je na nemi........ Na kasa karasawa saboda kunya. Ya numfasa yana kallona sannan yace" na fahimceki rumaisa kuma in sha Allah zamu shawo kan matsalarki kar ki damu. Naji dadin maganarsa nace" na gode Doctor Anan shima ya rubuta min magunguna yace in dawo after 2 weeks Hakan kuwa akayi bayan sati biyu nakoma yace min yaya meye labari. Nace"alhamdulillah ciwon Mara yayi sauki sai dai faa wancan har yanzu sai abinda ya karu. Ya danyi shiru ya zuba min ido can yace"to yanzu kinsan ya za,ayi ki yawaita azumi kawai kuma ki dinga yawaita istigfari a kowani lokaci sannan daga karshe ina mai baki shawaran ki sami miji kiyi aure kar ki jefa rayuwarki a halaka.kina iya tfy. Na mike a sanyaye gabadaya naji ba dadi don na lura doctor hakim ya fara min kallon 'yer iska don haka na yanke shawaran bazan kuma zuwa asibity ba. Sai sai kuma na kasa yin azumin hasalima sallar ma yanzu ba son yinta nake ba wasa gaske rayuwata ta sauya gabadaya cikin kankanin lokaci. Na kasa hkr da yanayinda nake ciki.don haka dolene in samawa kaina mafita. Wayata na lalubo na kira Ahmad ringing biyu yayi ya daga yace" Queen lfy cikin wnn Daren. Nace" hmm aina kk naji hayaniya . Yace" wlh yanzu nazo club. Nace " to don Allah kazo ka daukeni ina gidan saurayin Maryam da ka taba zuwa ka daukeni dinnan ka gane? Yace" eh na gane amma me ya kaiki gidan keda ya kamata ace yanzu kina hostel. Nace " eh wlh tunda muka gama lectures tace na rakata shine faa kaga suka shanyani ...... Ya katseni da fadin ganin nan zuwa Nace"to A raina kuwa dadi naji sosai maryam ta kalleni tace" 'yar rainin hankali gara da kika samawa kanki mafita wlh don kinga ni yanzu in baby ya dawo daki zamu wuce sai dai ince miki sai da safe. Shiru nayi ina dafe da kai Ahmad koda yazo waya yayi min yace gashi nan da sauri na suri jakata Maryam nace min sai mun hadu a school Queen. Tuni na fita na sami Ahmad tuni na fada mota nace " king wlh ina cikin wani yanayi na damuwa . Yace " ai na gani tun jiya ki gaya min menene kina da kamata bai kamata ki shiga damuwa ba Queen . Nace,wlh nima ban San meye bane kawai in dai kana da maganin damuwa ka bani. Ya danyi shiru sannan yace" yanzu ki yarda mu tafi night club dinnan kawai zaki ji duk damuwarki ta yaye ki samu kiyi rawa..... Na katseshi da fadin muje kawai . Yayi murmushi cikin jin dadi yace,thaz my Queen. Ya tashi mota.wai yau sai ga RUMAISA a NIGHT CLUB. Ganin Sam ban saki raina ba yasa shi fadin ina zuwa .ba jimawa ya dawo daukeda kwalba ya zauna hade bude kwalban ya zuba a Kofi ya mika min yace" karbi wnn kisha zaki ji zan zan har ki gode min . Na yatsuna fuska nace" meye wnn ? Yace" maganin damuwa ne da hayaniyar duniya kinasha zakijiki cikin nishadi da annashuwa. Na sa hannu na karba ina kallonsa. Ya daga min kai hade da fadin " sha zaki ban labari. Na kai baki na Dan kurba wani dandano ne na tashin hankali naji kan harshena ba shiri na xubar a kasa nace" Ahmad me ye wnn babu dadi. Dariya yayi yace kin taba jin magani mai dadi? Ya sake tsiyaya min wani a cup yace,yanzu dai gashi ki rufe ido kisha . Na girgiza kai nace" wlh aa. Ya mike yana dariya ya zo kusa dani ya rikoni aikuwa ji nayi kamar an jona min shocking na wuta lokaci guda naji tsigar jikina ya tashi yarrrrr! Dada rikeshi nayi mai kyau na kwantar da kaina a jikinsa nace"wayyo my king don Allah ka taimakeni. Cikin mamaki yake kallona sannan yasa hannu yana shafa kaina yace,my Queen na fahimci irin matsalarki. Lumshe ido nayi bance komai ba. Shima shirun yayi na Dan wani lokaci sannan ya sake dauko cup din yace" yanzu dai daure kisha wnn sai mu tafi. Haka ya dinga bani inasha ina yatsuna fuska har na gama yace" good yanzu ba abinda zaki kuma ji sai nishadi. Shima ya daga kwalban ya kwankwada. Tun ina ganinsa mai kyau a take naji kaina na juyawa kallon kowa nake bibbiyu a hankali naji idona ya kasa budewa ban sake sanin inda kaina yake ba sai............ Hauly ce👍🏻😍 [05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 Page ➡22 **********"Queen! Queen!! Queen!!! Muryar Ahmad naji yana tashina a bacci. Da kyar na iya bude idona na kalleshi. Murmushi ya sakar min yace" are you ok? Ban kulashi ba kawai na shiga bin dakin da kallo to nan din inane? Nan na fara tuno komai da ya faru a daren jiya. Dan ajiyar zuciya nayi na kalleshi shi ma ni yake kallo fuskarsa daukeda murmushi yace" tashi gari ya dade da wayewa. Da sauri na tashi na zauna nace" karfe nawa? Yace" karfe sha daya ya wuce da minti goma sha uku. Na zaro ido nace wayyo Allah lectures biyu ya wuceni Ahmad me yasa baka tasheni da wuri ba? Yace" my Queen nima tashina knn ko toilet banje ba.amma bana son ki damu kanki da yawa.lectures dinnan kamar kinje kin gama. Kawai zamu shiga school din tare in mun gama shiryawa. Yana gama fadin haka ya janye bargon da muka rufu ya mike ya shiga toilet ina jinsa ya saki shower ba jimawa ya fito daga shi gajeren wando da towel yana goge jikinsa ido na zuba masa nan da nan naji wani iri a jikina ba shiri na mike na isa gabansa na karbi towel din muka zubama juna ido murmushi nayi nace meye amfanina anan to? Na shiga goge masa jikin naja hannunshi muka zauna bakin gado na dauko mai ina shafa mishi lumshe ido yayi yace"my Queen karfa ki rikitani da irin wnn shafar man. Murmushi kawai nayi na ci gaba da abinda nake masa . Can ya riko hannuna yace kinga jeki yi wanka kizo. Na tashi na dauki towel na shiga toilet wanka nayi anan naga sabon brush na dauka na goge bakina nayi alwala na fito daga ni sai towel gashina har gadon baya na zubo shi. Gaba daya ya kasa dauke idonsa a kaina na karaso cikin takun jan hankali na isa wajensa na zauna nace" nima ka shafa min mai. Yace" an gama gimbiyar mata . Ya dauko karamin towel ya goge min jikina sannan ya fara shafa min mai Lumshe ido nayi ni kadai nasan me nakeji a jikina ji nake kamar na cire towel din. Bayan ya gama na bude ido nace" tnx my king Yace " yanzu idan baccin bai isheki ba sai mu koma.ko sai munyi breakfast? Na Dan zaro ido nace" ina fa tsoron kar Salima ta shigo ta samemu. Tsaki yayi yace" waya gaya miki nan gidan Salima take? Nace" ni ina na Sani to? Yanzu nan din inane? Yace" nan ma gidana ne amma ba nan Salima take ba. Nace " yanzu ka barta ita kadai kazo ka kwana anan? Wlh bai dace ba. Daure fuska yayi yace " ita ta jawo.tana ganin na debo gajia nadawo nayi wanka har na kwanta amma da ke bata da kunya wai tazo ta dubi tsabar idona wai na bata hakkinta.kinji fa har da wani dagewa tana min kuka wai ina cutarta waya fadi waya tashi......shine kawai na tashi na bar mata gidan nayi ficewata club Tunda ya fara maganar nake kallonsa har ya gama nace" amma king ya kamata kaje ka binciki kanka watakila bakada lfy ne.ya za,ayi a shekarunka kace baka bukatar mace? Kuma Salima matar ka ta sunna ? Har ta cire kunya irin na 'ya mace tazo tana nemanka amma kaki? Yace" hmmm baza ku gane yadda na tsara rayuwata bane .amma dai ina mai baki tabbscin lfyta qalau ina jin abinda kowa keji sai dai ban shirya sa kaina a trouble bane. Nace"trouble? Kamar ya knn? Yace,ban shirya haihuwa yanzu ba sai na girma. Nace,to sai kuyi family planning. Yace"no bana so kar naje Na lalata mata mahaifa a banza. Nace,to Ku dinga using condom. Ya girgiza kai yace " wnn duk ba dabara bane ni ban shirya sex bane kawai ..... Na dan tabe baki ban kuma cewa komai ba Na maida kayana . Muka fito tea kadai muka sha sannan muka tafi yana ajiyeni a mkrnta mukayi sallama. Da daddare muna hira a hostel nake gayawa maryam yadda mukayi da Ahmad. Dariya tayi ta ce"abu mai sauki ai tunda yace lfyrsa lau komai yazo da sauki kawo kunnenki kiji. Na matso ta rada min wasu maganganu masu zafin gaske har na zaro ido ina toshe baki. Na kalleta nace kice wlh kawata Tace " hmm ke dai zaki bani labari. Ta fito da wani kwalba a jakarta tace " kinga wnn turaren hmm bala,insa Nada yawa dan kadan zaki sa a yatsa ki shafa a mararki wlh in ya shaka to fa ranar sai Allah ya kwaceki a hannunsa don sai ya miki raga raga tunda ke virgin ce shawara daya zan baki ki tanadi magungunanki na pain relief a jakarki. Na danyi shiru sannan nace" Maryam ni kuwa kinsan Allah nafi son ya salman ne ya fara sanina kamin wasu. Tace" to sai kije ki sameshi. Na zaro ido nace" ke! Ba zai yarda ba wlh zai tsaneni ya fasa aurena. Ta harareni tace" waya gaya miki? To sai dai in bai shaki kamshin nan ba gabdaya zai fita haytacinsa sai yadda kikayi dashi wlh har ya kusanceki to kin gama mallakarshi ko uwarsa ba zai ji maganarta ba sai ke .wlh da wnn sirrin muke rike mazan mutane amma fa ki iya style..... Na katseta da fadin " Allah kawata yanzu kina ganin zan shawo kan ya salman da wnn maganin? Don bazan ce turareba. Tayi dariya tace" sosai ma amma fa ina tausayinki idan kika shiga hannun soja wlh su fa daban ne.don bazan manta ba Na taba haduwa da wani soja nima saida Na yabawa aya zakinta a hannun...... Na tari numfashinta nace,bar wnn batun don Allah nifa jina nake wata iri. Tace " ki kira Ahmad mana sai Ku dan rage zafi. Tsaki naja . ******daga haka rayuwata ta zama shiririta kusan kullum Ahmad muna tare ko wani dare sai munje casu . Shaye shaye kam ya zamo min jiki in ban sha ba bana jin dadi kwata kwata . Yanzu ya salman kawai nake jiran zuwansa. Randa ya kirani yace min yana Abuja zasu dawo kano da mama wacce tun bayan fitarta takaba ta tafi Abuja. Gashi yanzu an kare gininta na cikin gidsnsu inna.daki biyu da Palo a tsakiya sai kitchen da store sai toilet a kowane daki Tsarin ginin yayi wlh tuni aka shirya komai har kayanta Na ciki. Ranar asabar Na tafi gida da wuri don ya salman yace " gobene zasu kamo hanya. Na isa gida da yamma Na tarar da kowa a tsakar gida inna da Sadiya kamar basu ba sai fara,a suke min. Na karbi Abdul yaron ya girma yayi wayo sosai naje gun Maman sakina karbo mukullin side din mama. Ta kalleni cikin bacin rai tace"gaskia rumaisa irin wnn shiga da kkyi bai dace da yar musulma ba dubi don Allah tundaga jamiar bayero kika taho a haka da kayan da ke nuna siraicin ki hakama sati biyu da ya wuce kikazo ba Khan gani me yasa kk zama haka? Kaina a sunkuye nace" in Allah ya yarda ba zan kuma sa irin wadan nan kayan ba kiyi hkr mama. Tace " babu komai rumaisa Allah dai ya shirya. Ta dauko makullin ta bani anan Na wuce side din mama. Washe gari kuwa Na kintsa koina nayi musu girki mai rai da lfy sannan Na tafi naje Na gyarawa yaya salman dakinsa . Bayan Na gama wanka nayi Na zauna Na tasara kwalliya kamar wacce zata gasar sarauniyar kyau ta duniya. Har bayan azahar suka iso gaskia naji dadin ganin mama ta yi jiki ta kara haske gwanin sha,awa gaskia hutun abuja ya karbeta. Ya salman kam duk inda nayi bina yake da kallo ni kuwa dagewa nayi wurin jan hankalinsa da yin wasu abubuwa da yawa. Bayan sunci abincine ya koma gidansu. Anan muka fara hira da mama cikin nishadi da kwanciyar hankali amma bangare guda Na zuciyata tunanin ya salman nake nasan yana can jikinsa ya gama mutuwa Na hada shi da damammiyar nono mai fura harda flavor din pineapple. Tunda ya fara sha yaketa santi .a raina nace zaka fadane. Bayan sallar isha Na tafi daki wanka nayi ko sallar banyi ba don ba kullum nskeyi ba.Na saka rigar bacci iyacinta cinya da hannun vest Na fito da turaren da Maryam ta ban Na toshe hancina sannan Na shafa a marata Na dauki zani na da daura na dauko katon hijsbi har kasa ga nauyin tsiya na saka daga nan na fita don mama na dakinta. Na shiga palon kai tsaye baya nan ga badaya a matse nake don haka ba tare da tunanin komai ba na wuce dakinsa kai tsaye nan ma baya nan a raina nace to yana toilet ne don baiyi nitsa ba tunda dakinsa a bude. Na zauna gefen gadon ina jiranshi Can ya shigo Ashe wanka yayi don naga yana goge kansa da towel jikinsa sanyeda jallabiya. Yana ganina fuskarsa dauke da mamaki yace"baby ya akayine? Murmushi nayi nace" yaya a wnn sanyin kayi wanka? Yace eh mana ba dole ba kin sa nasha fura duk jikina ya mutu shine na sake watsa ruwa ko naji daidai. Dariya nayi nace " yaya akwai ma ragowarsa a fridge dinku na Palo ko na kawo ? Yace" aa sai dai ke kisha abinki kinga fa daga yanzu bacci nikeji kanwata . A shagwabe nace " yaya hira fa nazo muyi kasan nayi kewarka sosai tunfa rasuwar Alhaji aminu da kazo taaziyya baka kuma zuwa gaskia yaya ni dai ka bar aiki a Lagos dinnan ka dawo gida kano...... Tunda na fara maganar bina yake da kallo har na gama sannan yace" to yanzu dai albishirinki ? Murmushi nayi nace " goro fari Sol. Yace " na sami canjin gurin aiki daga Lagos na dawo kano Cikin tsantsan farin ciki nace" wayyo yaya ban taba jin albishir mai dadin wnn ba . Ya danyi shiru sannan yace " to a ban goro na . Na Mike ina murmushi da nufin inje gurinsa . Da gangan na ture stool wai a dole ni nayi tuntube aikuwa ko kan ya ankara tuni na fadi Faduwata yayi daidai da fashewar cup din ruwansa dake kan stool. Subhanallah ya dagoni da sauri yana sorry baby ince dai baki ji ciwo ba. Dada rikeshi nayi ina kukan shagwaba nace yaya abun cup din ya sokeni a ciki ka cire min Na fada ina nuna masa marana. Ya kai hannu a rude ya shafa maran yace" ba komai baby ko dai kin buga wurin da karfi ne. Ya dan danna wurin na saki ihu kamar da gaske nace " yaya ka duba min wlh naji ciwo. A rude yace" shikenan ki daina kuka.sorry Ya daga hijabin da sauri har yasa hannu zai daga rigar baccin nikam tuni na lumshe ido ina sauraro. Sai dai shiru naji yayinda ya dauke hannunsa daga jukina yace" baby inga gara muje as..... Bai karasa ba na sake sakin ihu . Wanda ya rikitashi ba shiri ya daga rigar yana kokarin kauda kai kamshin da ya fara ji dazu ne ya sake dukan hancinsa sosai anan fa labari yasha ban ban. Don tuni hankalinsa ya bar jikinsa ya shiga shafa marata yace " baby nan ne? Yanayin da yayi maganar yasa na fahimci ya shigo hannu . Nace" eh yaya. Yace gaba da shafawa sannan yace " sorry my baby. Jawoshi nayi muka fada gado kamar jira yake nan da nan ya rumgumeni ya shashshafani yayinda yake sakin numfashi . Kamshin shu,umin turaren ya kara gauraye dakin musamnan da yaya ya shafa marata gabadaya hannunshi kanshin turaren. Abinka da mai ciwon asma sai naji kamshin turaren yayi min karfi da yawa har banson shakar numfashi. Cikin rashin sa,a kuwa ya kai hannunsa zai shafa kaina .nayi wani irin wawan shaka.nan da nan numfashina ya shiga barazanar daukewa. Ai kuwa nan muka shiga kokuwa da shi ni ina kokarin tashi.shikuma yana kokarin danneni kan gadon . Kukan gaske na shiga yi ina wayyo Allah yaya ka bari don Allah numfashina zai dauke zan mutu. Cak! Ya tsaya da abinda yakeyi tuni idonsa sukayi jazir yace" baby pls karki min haka ....... Ai ban tsaya jiransa na tashi da hanzari na fita kasancewar kofar a bude da kyar na isa gida ina wani irin numfashi mama na ganina ta rude tana" rumaisa mene ne? Da kyar nace" ma...ma....inhaler na .....yana... Cikn...Jakata. Da sauri ta tafi ta dauko ta kawo min. Tana rike dani duk hankalinta ya tashi sosai. Da taimakon inhaler din numfashina ya daidaita anan mama ta ce" ko na kira salman yazo mu tafi asibity ne? Jin sunan salman yasa gabana ya fadi ko a wani hali yake oho. Nace " mama basai munje asibity ba akwai maganina bari nasha zai daina. Na Mike ta bini da ido. A karshe bina dakin ta yi tace inzo muje mu kwana a dakinta don bazata barni ni kadai ba. Muna zuwa dakin ta har na kwanta tace" rumaisa wannan wane irin turarene tun dazu yaki barin jikinki? Nace " mama wlh shi ya tada min ciwo na Maryam ne ta bani sai na jefa a wardrobe dina Ashe ya zube a hijabina da Na saka dazu tunda na fita nake danji ina zaune a palonsu ya salman ina jiran ya dawo sai naji kirjina na toshewa shine nayi maza na dawo. Tace" to wnn wane irin turarene haka? Nace" nima ban Sani ba tace dai yana da dadi ta diba ne gun yayarta shine nima ta dibo min . Tace" ke dai bansan yaushe zakiyi hankali ba haka kawai baki San mutum ba ya dauki abu ya baki kisa hannu ki karba.wlh idan baki kula ba nan gaba zai dameki.kuma gari na wayewa ki dauko turaren nan ki bani . Nace "to" gabadaya na tsorata da abinda ya faru. Ga kamshin turaren sai damun hancina yake duk na sake wanka da ruwa mai dumi dazu kuma na canza kaya amma Sam ban daina jin kamshin ba. Gabadaya bacci ya gagareni mama kam tuni ta yi bacci sai dai karfe daya nayi alarm ya tasheta ina ganinta taje ta dauro alwala ta zo ta kama nafila kamar yadda na Santa har karfe uku sannan ta fara addua ta jima sosai sannan ta shafa ta dauko Quran ta fara karatu shima saida akayi assalatu sannan ta rufe ta gabatar da sallah ta idar ta yi azkar .sannan ta tashi tazo kusa dani ta fara tashina Bata San likimo nayi ba. Bayan Na idar da sallah dole na dauki hisnul Muslim na bude ina karatu kamar dole da kyar na gama azkar. Ashe duk tana lura dani Anan ta ajiyeni tace " rumaisa kin canza me yake faruwa? Kaina a sunkuye nace " ba komai mama. Tace karyane rumaisa ba haka kk da ba .bari na fada miki abinda yasa nace kin sauya na farko kina sakaci da ibada na biyu kin koyi karya . Zaro ido nayi a tsorace ta ce " kwarai kuwa don haka kima kanki fada kima kanki gata ki daina wadan nan dabiun in ba haka zai dameki nan gaba. Ta tashi hade da fadin " Allah ya shiryeki . Ta fita gabadaya jikina ya mutu haka nan na tashi sama sama na shirya tea kadai nasha ina shirin fita mama ta kirani tace " ina turaren? Na he na dauko na bata ta kalleni cikeda zargi tace " ki tattara kominki daga hostel ki dawo gida. Kai tsaye ta yi maganar sannan ta wuce kitchen . Ni dai kamar an zare min laka haka na fita . Aikuwa sai ga ya salman ya na tsaye kamar ni yake jira duk cikina ya duri ruwa .gashi fuskarsa a murtuke kamar bai taba fara,a ba Ina kokarin gaisheshi yace " ki zo inada magana. Ya wuce gidansu na bishi a baya duk a tsorace nake wayyo ni rumaisa nayi abinda ya dameni. Muna shiga gidan ko Palo bamu kai ba ya juyo ya tsareni da manyan idanunsa masu shegen kwarjini yace" me kika shafa a jikinki jiya da daddare ? Na shiga girgiza masa kai cikin tsoro nace" babu komai... Ya katseni da fadin " kinsan Allah daya ko? Wlh idan baki gaya min sai na kakkaryaki Nan na dake nace" na fada maka babu komai..... Dauke fuskata yayi da mari ransa a bace ya shiga huci yace"rashin kunya zaki min ? Rumaisa gabadaya daga jiya na fahimci kin canza halaiyarki kin zama wata daban.yanzu abinda kikeyi kina ganin ya dace kenan! Hawayene ya ciccika idona har yana zuba nace "me na maka zaka mareni ? Abinda ya faru jiya laifina ka gani ? Ko ka manta cewa duk sanda namiji ya kebe da mace shaidan ne na ukunsu amma ka dauki laifin duk ka dora min.... Kallona yake cike da mamakin maganganuna Ya sassauta murya yace " rumaisa wlh karya kikeyi akwai abinda kike boyewa.jiya ne na fara kebewa dake mu biyu? Goge hawaye nayi nace" OK naji kana zargin na fara iskanci ko? Shine nazo zan ja ra,ayinka hakane? To naji duk abinda kake zarge hakane!!! Cike da mamaki yace"whatttt!!!! Rumaisa me ya sameki. Harara na sakar masa na juya nayi tfyta.!!!!! To faaa !!!!!!! Kuyi hkr da rashin post dina kwana biyu banda lfy ne👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 Hauly ce👍🏻😍 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡23 *************Bina yayi da kallo fuskarsa dauke da mamaki mara misaltuwq.har na bace. Ya koma Palo ya zauna jikin nsa a mace ya lalubo wayarsa ya kira layin salim ba bata lokaci salim ya dauka " Dan uwa ya akayi ne ? Yace" hmmm salim akwai abinda yake shirin faruwa dani Wanda bazan iya barinsa a zuciyata ni daya ba. Salim yace " subhanallah me ya faru salman? Anan ya kwashe komai ya fada masa bai rage komai ba. Hankalin salim ya matukar tashi sosai yace" Rumaisa ne ta zamo haka? Ya salam! Wnn matsalar ta shafe mu gabadaya salman dole ne mu dauki mataki tun wuri kafin abin yafi haka lalacewa. Salman yace" salim wlh zuciyata ta fara bani shawaran rabuwa da rumaisa don sanin kanka ne bazan iya auren mata mai irin wnn halin ba wlh salim na gwammace me yasa nace ina son Rumaisa. Salim yace" haba danuwa kawai daga an sami matsala sau daya tak! Har ka karaya? Bari kaji dole ka daura damarar fuskantar kowace jarabawar da Allah zai daura maka akan soyayya ka kokari kaci jarabawar don haka dole ka yaki zuciyarka kaci gaba da sonta ka mata uzuri har Allah ya kawo karshen abin. Shiru Salman yayi ya rasa me zaice Salim ne yace"amma kar ka damu zan shigo kano ranar Saturday zamu San me zamuyi akai. Kayi hkr don Allah ka danne zuciyarka. Yace shikenan danuwa sai kazo. Sukayi sallama jikinsa ba kwari ya mike har zai shiga daki Sadiya ce ta shigo da sallama tana rike da Abdul Wanda tunda yaga salman ya fara dariya yana mika hannu a daukesa. Ya amsa sallamar sannan ya mika hannu ya karbi Abdul yana cewa" kana min dariya ba fa inda zani da kai. Ya kalli Sadiya yace " yaya? Tace" yaya dama nazo in rokeka ne ka dan bani kudi in yiwa Abdul siyayya in ba damuwa. Shiru ya danyi sannan yace" Allah ya kawo in baki. Tace " ameen yaya na gode. Ta mika hannu zata karbi Abdul nan da nan ya noke Murmushi yayi yace"jeki kawai in yayi kuka zan kawo shi. Ta fice ta na mai jin dadin yadda yaya ke son Abdul. *****Ni dai tunda na shiga makaranta raina a bace sama sama nake sauraren lectures . Har aka kare da yamma na wuce hostel na tattara duk wani kayana bama yawa da yake ban son tara tarkace. Maryam ta shigo ganin na tattara kayana yasa tace " Queen lfy ina kuma zakije? Harara na sakar mata nace" dama ke nake jira don ko bakizo ba zan nemeki. Nan na kama sauke mata kwadon bala,i akan turarenda ta bani .ta inda na shiga ba ta nan nake fita ba . Mamaki ne ya rufe har sai da na dasa aya . Tace " Queen kiyi hakuri wlh an sami matsala ne wnn yayan naki inaga ba a zaune yake ba.me zai hana kizo muje wajen wani malamina aikinsa kaman yankan wuka nan da nan a shawo miki kansa. Tsaki naja raina a bace nace" sai nayi tunani tukun.ni yanzu barin hostel zan yi Mamana tace in koma gida. Cikin rashin jin dadi Maryam tace" Allah sarki Queen zamuyi kewarki. Na harareta nace"zan ga mai muku gadin dakin yanzu tunda duk ficewa kuke yawon iskanci. Dariya tayi anan ta tayani rike kaya muka fita. Muna fita saiga doctor hakim a motarsa tsayawa yayi ya sauke glass ya kalleni yace"Hajia rumaisa sai ina haka da yamman nan ga kaya kuma? Ba tareda na saki fuska ba nace" gida zan koma. Nan da nan ya sauko ya bude bud ya sassaka kayan ni dai binsa nake da kallon mamaki . Sannan ya kalleni yace"zo muje na kaiki dana ina da muhimmiyar magana da nake so muyi. Na gyada masa kai sannan mukayi sallama da Maryam na zagaya na shiga motar. Mun fara tfy ya kalleni sannan ya maida hankalinsa kan tukinsa yace" rumaisa tun bayanda kikaje guna akan matsalarki ban kuma ganinki ba me ya faru ba dai fushi kk ba? Na tabe baki nayi nace" eh fushi nake saboda na lura kana min kallon 'yar iska ka dauka na kai maka jikina ne da wayo. Murmushi yayi yace" No ba haka bane kiyi hakuri. Shiru mukayi har muka fara nitsa sai naga yayi parking gefen hanya ya juyo muna fuskantar juna sosai ya zuban ido yace" to yanzu kuma yaya kikeji ? Nace " yadda na fada maka kwanaki. Ya danyi shiru snn yace " rumaisa bayan tfyrki banyi niyyan nemanki amma abubuwa da yawa na lura ya sauya.domin wlh bazan miki karya ba complains yayi yawa akanki gaba daya ki canza halayenki masu kyau kin biyewa rudin zuciya da zugin shaidan kina aikata abinda bai kamata ba gaskia hankalina ya tashi sosai me yasa kika zabi wnn mummunar hanya? Shiru nayi kaina a sunkuye kusan minti biyu sannan na dago na kalleshi nace " ni kaina bansan meye dalilin da yasa na zamo haka ba. Ya numfasa yace " idan bazaki damu ba ina son ki sake bani dama a karo na biyu na gabatar da kaina gun iyayenki ma,ana ina son ki amince ki aureni .ina son in tsamoki daga wnn rayuwa da kk ciki. Na girgiza kai nace" bazaiyiwu ba doctor kasan ina tare da Ahmad kuma surayya matarka yayarsa ne ga kuma Salima a gefe akwai matsala gaskia. Yace" hmmm banji kin kawo hujja daya kwakkwaraba na kin aurena.kasancewar surayya matata yayar Ahmad saurayinki shine me ? Haramun ne aure tsakaninmu? Na girgiza kai nace " hmm doctor bazaka gane ba ne amma dai na fada maka akwai matsala........ Ya tari numfashina da fadin " kinga yanke hukunci cikin gaggawa ba naki bane don haka kina bukatar isasshen lokaci don ki nitsu kiyi tunani da kyau. Nace" shikenan naji kuma zan yi hakan inshaa Allah. Yace " shikenan sai najiki. Daga nan ya tashi motar muka tafi. Har kofar gida ya ajiyeni ya fito ya sauke min kayana mikayi sallama don magriba tayi. Duk abin nan ya salman na tsaye a get din gidansu ya zuba hannunsa a aljihu yana kallonmu. Har saida yaga tfyr doctor hakim sannan ya wuce masallaci . Ko kallo bamu ishi juna ba na tattara kayana na wuce cikin gida.Na sami mama na sallah.nikam banyi tunanin yin sallar ba kawai na hau shirya kayana a wardrobe. Duk raina a bace yake . Don haka ina gamawa nayi wanka nazo na bude jakata na dauko abin sha na a kwalba na bude na kwankwade.na boye kwalbar don kar mama ta gani. Kafin kace meye na bugu tilis jina nake sama sama idona a lumshe . Mama ta shigo ta sameni tace " rumaisa ya najiki shiru ? A hankali nace" na gajine kawai bacci nakeji. Tace" kinyi sallar isha ne? Na daga mata kai. Tace" to zokici abinci in yaso sai ki kwanta. Girgiza mata kai nayi nsce" ni na koshi. Ita duk tunaninta baccin ne ya maidani haka. Don haka tace " to kiyi addua kamin kiyi baccin? Ban kulata ba ta fita yayinda taja min kofa. Tabe baki nayi nace" kanki akeji. Da haka bacci ya daukeni. Gari na wayewa na tashi sumul na jini normal . Tuni na shirya Na fito Palo na sami mama tana kallon news a TVC Na zauna a one seater na kalleta nace" mama ina kwana? Tace " lfy ya ciwon kan naki? Nace" da sauki. Tace" to yi maza ga breakfast dinki kiyi ki tafi kar kiyi letting. Nace" yau sai ten muke da lectures . Tace" shine kk shirya da wuri haka. Murmushi nayi nace" eh kawai na...... Sallamar ya salman ya katseni ya shigo cikin shiri shima don sanye yake cikin kakinsa Wanda yayi balain yi masa kyau da kara masa kwarjini. Mama tace" salman har ka fito ? Yace"eh goggo ina kwana? Tace" lfy ka shigo mana. Yace" banson cire takalmi ne .kuma ina sauri na kusa late. Tace " to ba komai Allah ya tsare hanya sai ka dawo. Yace " na gode. Har ya juya zai tafi nace" yaya ina kwana. Juyowa yayi ya kalleni nima kallonsa nake gyda kai yayi yace " lfy. Nayi murmushi nace" da kyau.a dawo lfy Allah bada sa,a. Ba tare da ya juyo ba yace "ameen. Ya fice. Bayan na gama breakfast na shiga gida na gaida kawu sannan na shiga dakin inna muka gaisa tace " rumaisa yaushe ne kike da lokaci ? Nace" wani abin kike so inna ? Tace" zan aikeki gidan raihanane. Nace" ai ba komai ki aikeni kawai.yanzu sai naje in yaso daga can sai na wuce makaranta. Sadiya tace " bakida lectures da wuri kenan? Nace" eh. Inna tace" to kice mata ya najita shiru kuma ko wayarta ma na kira bata dauka .kice ina son ganinta gobe goben nan. Nace " to inna. Daga nan naje na gaida mmn sakina na fita . Daga gidan raihana nayiwa Ahmad waya ya zo ya daukeni don banson shiga school. Yace" bari dai na turo driver yazo ya daukeki ni bana son fita yanzu. Nace"to. Na gaya mishi anguwan da nike. Bayan mun gama waya raihana ta kalleni tana murmushi tace yanzu rumaisa kunci shekara biyu a makarantar nan? Na harareta nace" kar ki maida mu baya man yanzu muna shekararmu na uku. Tace " kai amma yayi sauri. Nace" a wajanki ba? Ta yi dariya tace " ke albishirinki nima zan fara zuwa Malam ya gama min komai. Nace " don Allah fa? Tace" wlh kua Na ce " to fa wnn tumbin naki ko yau ko gobe fa? Ko dashi zaki je makarantar? Tace sosai ma aini ba full t..... Shigar call a wayata ya katse mana hira na dauka driver dinne ma.sai naga yaya salman ne cike da mamaki na daga shiru na masa. Shine yayi magana yace" ina kike? Na dan yatsuna fuska nace ina gidan raihanane Baice komai ba ya katse kiran. Kusan awa daya sannan driver din Ahmad yazo ya daukeni. A gidansa da muka saba haduwa driver ya kaini. Ina shiga Palo na sameshi yana zaune sai shan shisha yake . Raina a bace nace"wnn wane irin wulakancine kasan ina zuwa shine ka zage kk ta busa hayakin banza? Na to she hancina na wuce daki na fada gado yayinda na cire hijabina na jefar. Kusan minti biyar sannan ya shigo hannunsa dauke da kwalbar..... Da cup biyu ya karaso ya ajiye sannan ya kalleni yace " bismillah. Na tashi na zauna a tsakiyar gadon nace" ni ban shirya buguwa yanzu ba. Baice komai ba ya zuba ya fara sha a hankali. Dafa kafadarsa nayi nace"king me ya faru ne naga ranka a bace tunda na shigo. Ya danyi tsaki yace ke dai bari kawai. Na ce"don Allah ka gaya min mene ne ? Kasan banson bacin ranka.pls tell me Cikin bacin rai yace" ni da shegiyar matar nan ne ' yar iska ta zo har gida ta raina min wayo ta maidani sai kace karamin yaro. Na gintse fuska nace"wace kenan? Yace " doctor surayya mana Na ce " kana nufin sister dinka? Yace" eh. Dan ajiyar zuciya nayi na rumgume shi ina shafar kansa a hankali nace " me tayi maka da zafi haka? Don ban taba ganin bacin ranka irin haka ba. Ya danyi shiru yace " ba na fada miki Salima tana mata korafi akan zamanmu ba? Na daga masa kai yace" kawai shine yau ta yi mana sammako wai na fada mata ko banida lfy ne nace mata lfyta lau amma bata yarda ba wai zata gayawa su mum. Shine da na shiga daki suka tasa Salima ta bini ta kama kofa ta rufenmu ta ciki wai dole sai na kula Salima in ba haka ba zata gayawa su dad akaini asibity a dubani ko bani da lfy.kiji fa matar nan zata disgracing dina a....... Dariyar da nake dannewa ne ya gagara bansan lokacinda na dinga dariya ba . Shikam haushi yaji ya tureni daga jikinsa ya daga kwalbar sa ya shiga sha. Da sauri na kwace nace " me ye haka idan ka bugu ka fita hayyacinka wa zai karasa min labarin? Idanunsa sunyi jazur yace" Queen ki daina wasa don Allah wlh seriously abin nan ya dameni ba kadan ba kinsan ni sarai ba haka na tsara rayuwata ba. Na danne dariyata nace" amma ina bakayi mata komai ba. Yace" ai dole ne kawai in ba haka ba zasu tara min jama,a ayita min kallon raggo mara lfy.shine na nuna musu lfy ta garau. Ya fadi hakan ne yayinda yake lumshe ido yaci gaba da fadin " da gangan na ki binta a hankali tunda ita ta jawo na mata raga raga yanzu suna can asibity .kuma ta kuskura tayi ciki sai na bar musu kasar nan.lol! Kauda kai nayi ina dariya ciki ciki sannan na kamoshi na kwantar dashi nace " rabu dasu kai dai ka sauke nauyin da Allah ya dora maka sauran kuma ya rage nasu.yanzu bari na maka tausa. Ya jawoni ya rumgume a jikinsa yace " my Queen amma fa da dadi. Murmushi nayi nace" wow kace ka more lol! Yau dai ka zama ango! Toshe bakina yayi sannan ya dada rumgumeni anan muka fara romancing din junanmu sai dai ba,a kai koina ba ya saki jiki sai bacci. Zuba mishi ido nayi cikin takaici na lura shaye shayen nan shi ke hana Ahmad komai a rayuwa . Nan na kwanta a jikinsa naci gaba da kidana da rawana ni kadai har na dan sami relief daga nan bacci mai nauyi ya daukeni . Bamu muka tashi ba sai wajan karfe hudu na yamma da kyar na tasheshi Bayan munyi wanka nace " ni zan tafi. Rumgumeni yayi ta baya yace " no ba yanzu ba kizo muje muci abinci tukunna. Na ce " kamar kuwa kasani yunwa nakeji tun breakfast. Yayi murmushi yayinda ya sumbaci bakina yana shafa cikina yace " eh gaskia kina jin yunwa my Queen mu tafi. Nan muka fita sai wata hadaddiyar restaurant muka ci muka koshi daga nan muka fita wajen shakatawa kusan magriba nace " king gara in tafi gida shugaban 'yan sa ido na gari. Yace " Salman ko? Na ce"eh Yayi tsaki yace " forget about him yau akwai casu na musamman muje kiyi koda one hour ne inyaso... Na ce " kai mama zata kashe ni!!!! Yace " kawai kice musu kin kwana a hostel ne. Na ce hmm Mamana 'yar duniyace zata gane .amma fa duk da haka casun nan ba zai wuceni ba . Murmushi yayi yace " daz my Queen! Na ce " to albishirinka yau lectures uku na rasa sai kasan yadda zakayi. Yace " karki damu da wnn my Queen kamar kinje kin gama ne. Har bayan sallar isha muka tafi gidansa bayan mun biya kanti na zabi kayan zuwa casu mini siket ne da riga ko vest ' yar karama cibiya a waje yau nayi niyyar duk Wanda ya kulani zan kulashi tunda Ahmad bai iya komai ba sai Shaye shaye. Wayoyina kuwa na kashe tuni yau dai duk abinda zai tafasa ya kone.! Karfe goma muna wurin casu an saka music masu zafi rawa kawai muke wuri duk ya rude.da nishadi da annashuwa.( _wa_ , _iyazubillah_ ) Caraf naji an rumgumeni ta baya . na duba gabana banga Ahmad na juya da sauri a tunani na shine kawai sai mukayi ido hudu da wani hadadden gaye Wanda ya tafi da imanina . Murmushi ya sakar min nima na maida masa . Kawai ya dada rumgumeni tura hannunsa yayi ta gaban rigana yana wasa da......... Lumshe ido nayi ina jin wani irin dadi gaskia wnn ya hadu a cikin rawa kawai har ya kusa sumar dani inaga in mun shiga ciki? Tuni kuwa na manta da wani Ahmad yana can yana shan shisha hankalinsa kwance. Tuni mukayi gefe da wnn gayen ya kalleni kamar zai hadiyeni yace" baby kin hadu wlh kamata yayi muyi cinikin kwana. Na kashe masa ido daya nace " ka fini haduwa ai.ba matsala sai yanda kace. Ya sakar min murmushi yayinda ya riko hannuna da nufin tfy. Kawai sai ganin Ahmad mukayi a gabanmu yana huci kamar wani bakin kumurci . Da sauri na janye hannuna cikin na gayen a tsorace na koma gefe . Ya kalleni yace baby waye kuma wnn. Da kyar na daure nace" dashi nazo dama...... Tsawa Ahmad ya min hade da fadin ki wuce mota ki jirani. Tab! Nan ko ake yinta ina zan iya barin wnn hadadden gaye? Na fada a raina don haka na dake nace" gaskia king ni ba yanzu zan tafi gida ba kawai kaje daga baya na taho. Ya dubeni fuska a daure yace "ko? Na ce " sosai ma. Ya gyada kai sannan ya kalli mutumin yace" ina maka last warning akan wnn babyn idan ka kuskura ka sake kulata sai nasa an batar da kai! Ran gayen ya mugun baci yace" kai waye da zaka sa a batar dani? Ahmad yace" sai ka kulata din zaka gane. Ya finciko hannuna yana jana ina tirjewa har bakin mota ya bude bayan motar ya jefani ya kulle Ya zagayo ya shiga ya zauna ya tada motar. Nikam ban iya nace komai ba a halinda ake ciki ma jina nake sama sama kamar a gajimare. Bansan ma me ake ciki ba kawai sai ji nayi ya fincikoni waje yace" ki bude idonki da kyau ki gani nan kofar gidanku ne na kawoki ga can Dan iskan yayanki sojan nan yana tsaye yana ganinmu sai kije Ku karata tunda 'yar iska ce ke. Yana kokarin sakeni na damkeshi cikin maye nace mishi" ba komai kai ni.....wurinshi...kasan ...nasha da yawa bazan iya tfy ba....... Yace " yayi kyau tunda haka kika zaba . Ya riko hannuna har wajen ya salman. Da take tsaye mamaki da tsoro ne ya rufe shi ganina a cikin yanayin maye kuma karfe sha biyun dare. Ahmad ne ya katseshi da fadin" ga nan kanwarka na dawo maka da ita sai ka kaita gida. Bai ce komai ba ya kamoni yayinda Ahmad ya juya ya shiga motarsa ya fice ya salman ya bi motar da kallo har ya bace daga layin. Sannan ya kalli fuskata kasancewar akwai hasken farin wata sosai . A take yaji wani abu ya taso ta tokare masa kirji tsabar bakin ciki ya rasa mai zai ce. Don tunda magriba suke nemana da mama a waya basu sameni ba. Ganin hankalin mama ya tashi yasa shi cewa ya kira kawata kuma tace ina hostel wayana ba chagy shiyasa in an nemeni baya shiga.da haka ya lallaba mama . Shi ma yanzu abinda ya tsaida shi a waje yana tunanin ta inda zai fara nemana ne.gashi yayiwa mama karya hankalinta ya kwanta shi kuma ya kasa bacci. Ya sauke ajiyar zuciya ya daukeni cak! Yayi cikin gidansu a Palo ya saukeni kan 3 seater sannan ya koma ya kulle koina ya dawo ya zauna ya zuba tagumi yana kallona Banma San yanayi ba .don tuni bacci yayi awon gaba dani!!!!!!!!! Hauly ce👍🏻😍 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page ➡24 *************Nice ban tashi ba sai goma. Ganina kwance a palon su ya salman yasa hankalina yayi mummunan tashi Da sauri na tashi zaune ina Salati na bi kayan jikina da kallo anan na tuno abinda ya faru duka Na zaro ido hade da fadin wayyo Allah na shiga uku ni yau ya zan......... Shigowar ya salman ne ya katseni.nan naji wata irin faduwar gaba da ban taba ji ba tsoro ya lullubeni jira kawai nake naji saukan duka. Kaina a sunkuye na kasa yarda muyi ido hudu. Zama yayi akan kujera ya kalleni cike da bakin ciki mara misaltuwa ya hadiye bacin ransa yace" sai yanzu kika tashi? Jikina a sanyaye kunya ne ya rufeni sosai na zamo daga kan kujeran na durkusa gabansa nace" yaya kayi hkr don Allah wlh sharrin shaidan ne. Kauda kansa yayi yace ki shiga dakina akwai kayanki a gado ki saka sai kizo. Kunyane ya dada lullubeni na mike a hankali na shiga daki na sami dogon rigata na atamfa da hijabina na saka na bar masa mini skirt din da vest akan gadon na fito sai lokacin ya kalleni sannan ya mike yace " muje gida. Cikina ne ya duri ruwa na zazzaro ido waje ina tunanin me zancewa mama in naje. A karo na biyu yace muje mana. Anan na kalleshi nace " yaya dama ina son inje toilet ne fitsari nakeji lol! Baiyi magana ba ya koma ya zauna ni kuma na wuce toilet na fi minti goma a ciki ina tunanin karyar da zanyiwa Mamana. Haka na daure na fito. Muka fita INA biye dashi har side din mama. Muna isa sai naga ya kamo hannuna ya riko yayi sallama . Mama dake Palo ta amsa hade da yi masa iznin shiga. Ganinmu tare yasa ta mike tana cewa" zuwa kayi ka dawoda ita? ai da ka barta muga iya gudun ruwanta. Ya girgiza kai yace " goggo ba haka nan taki dawowa ba.zazzabine ya rufeta shine sukaje asibityn makaranta suka mata allurai hade sa mata ruwa banason hankalinki ya tashi gashi dare yayi shiyasa ban fada miki ba .shine dazun da zan tafi asibityn na tura Zainab ta karbo kayanta don sunce wancan ya baci da amai.shine da naje suka sallamota. Ya kalleni ni kam kaina a sunkuye ina mamakin yadda yaya ya zage ya na shirga karya hankalinsa kwance. Yace" kije ki kwanta bari in je in siyo magani. Ya saki hannuna sai lokacin mama tace" sannu rumaisa Allah ya sawwaka .amma INA wayarki in mun kira muji a kashe? Nan na tuno gabadaya jakata ma na motar Ahmad .na dago na kalleta bansan me zance ba. Ya salman yayi farat yace" sunce ba cajine kuma sun bari a hostel Mama ta ce" OK.jeki kwanta bari a kawo miki abinci. Na wuce daki na cike da mamaki ya salman me yasa yake rufa min asiri? Wunin ranar nayishi a kwance a dole banda lfy. Duk kuwa na jini a takure da ban fita ba .ga sabonda nayi kaina na shaye shaye duk sai naji ina sha,awar shan wani abu gashi banda komai a gida. Haka dai ta kasance Washe gari wartsakewa nayi na shirya tfy school . Mama ta ce" na bari sai gobe in na kara jin sauki. Nace mata na watke tass banajin komai yanzu Maimakon inje mkrnta sai na tafi gun Ahmad duk da banda tabbacin yana gida tunda ba waya a hannuna. Aikuwa naci sa,a yana shirin fita na iso juyowq yayi yana kallona fuskarsa a hade nima babu alamun wasa a fuskata . Nace" kai kuma na gode da abinda ka min ka daukeni ka kaini gida a yanayin maye sannan babu sutura mai kyau a jikina.Ashe karya kk ba sona kk ba tunda kana son ka tona min asiri na gode..... Wani irin kallo ya bini dashi sannan yace" bari kiji na sanar dake indai kina son asirinki ya rufu to ki daina kula wani saurayi ni na isheki me kika nema kika rasa? Kudi? Sutura ? Ko me? Harararshi nayi nace " kudi da sutura ba sune a gabana ba.abinda nake bukata baza ka iya yi min ba don haka dole ne inje in sami mai biya min shi. Ya girgiza kai yace " ai na Sani maganarki knn kullum .kin kuwa San masifa da balai da ke tattare da zina ?Allah ya fada mana a littafinsa mai tsarki yace kar mu kusanci ZINA.don haka mu gujeta don ta kasance....... Daga mishi hannu nayi nace" sai ka fada min a wani littafi akace shaye shaye kuma halak ne sannan ka gaya min a wani littafi aka hatamtawa namiji ya kusanci matar sa har sai ya kai shekara arba,in. Ya danyi shiru sannan yace " wannan kuma wani abu ne na daban. Nace " to kaga kada ka kuskura idan muna magana ka kawo zancen addini a ciki domin daga ni har kai bai kamata aji batun Allah yace annabi yace a bakinmu ba don ba shi mukeyi ba. Yace " eh kema kince wani abu.don ni dama ba wani Sani nake dashi ta bangaren addini ba nasan ke din ma hakane. Ya fada yana murmushi . Harara na sakar mishi nace " kai dai baka Sani ba ni kam Alhamdulillah har haddar Al-qur'ani nayi kuma nasan hadisai..... Zaro ido yayi yace" what !! Shine kika zama haka? Rumaisa Allah ya shiryeki. Tsaki naja nace " ya shiryemu baki daya.bani jakata ni zan tafi mkrnta. Yace" yau bazaki min massage ba? Bance komai ba na wuce gun drawer na dauki jakata sannan na kalleshi nace " daga yau in ka sake gsnina da wani karka kuma yarfani tunda baza ka iya biya min bukatata ba. Har zan wuce ya rikoni yana kallona sannan yace "zauna na fada miki wata magana mai mahimmanci. Ya zaunar dani sannan ya zauna yace " Queen duk lalacewarki kar ki dinga bin maza a wnn a zamanin namu cututtuka sunyi yawa idan kikaje kika bata rayuwarki wlh ba wani namiji da zai aureki da kima kingan ni nan wlh bana son mace 'yar'iska.jiya ba na fada miki yadda mukayi da salima ba? To wlh har mukaje club dake hankalina ya kasa kwanciya saboda halinda na barta a ciki tausayinta na rikaji ba kiga na kasa yin kome ba? Shisha kawai nasha.don haka duk iskancinki ki tsare budurcinki ba don komai ba sai don ki tsira da mutuncinki kinji? Tabe baki nayi nace " hmm bazaka gane ba .ni kaga tfy zanyi in ka gama wa,azin naka. Shiru yayi yana kallona sannan yace " hmm kije rayuwarki ne ai ba tawa ba . Na mike har zan fita ya sake rikoni yace " Queen don Allah karki kula maza wlh in har kika min haka wlh na miki alkawarin in na cika 40yrs zan aureki !don wlh ina kishinki bana son wani ya rigani saninki don daga gani ke din special ce ! Tsaki naja nace " har yaushe knn shekarunka zasu kai 40 din ? Ka bi ka isheni da shekara 40 40 40 ! Nagaji da ji ni dai! Yayi murmushi yace " Albishirinki! Shiru na masa yace " saura min shekara biyu na cika 40yrs din kinga by then kin gama service sai muyi aurenmu kawai ki haifa min yara kyawawa masu kama dake. Dariyar mugunta nayi nace " what a dream! To naji amma kasan akwai maganar aure tsakanina da yaya salman ko? Kuma iyayenmu sun Sani kuma ko yau in salman yaga dama zai iya cewa a daura mana aure yana bukatar matarsa...... Daga min hannu yayi cike da jin haushi yace " don Allah daina kawo min maganar salman.shi waye ne ? Ke bari na fada miki in kin auri salman wahala zaki sha kawai karkiga don Dan,uwanki ne.don haka ki rabu dashi kuzo gurina na miki babban tanadi na jin dadi har karshen rayuwarki. Murmushi nayi nace " to ai shikenan. Na fadi hakan ne don mu rabu lfy don ni ko kadan ba aure nake so ba a yanzu. Yace " yawwa my Queen .yanzu mu tafi na kaiki. Mun fita harabar gida wurin jerin motocinsa har guda hudu. Wata bakar mota na tsurawa ido ta matukar burgeni sai daukan ido yake. Ya kalleni yana murmushi yace " yaya? Motar ta miki kyau ko? Nace " eh yaushe ka siyeta? Yace " kwanaki ai shine motarki da nace miki yana hanya amma kikace ke kina tsoro .kawai in baki so sai na baiwa Salima tukuicin budurcinta da ta kawo min( ' *yan* *mata* *Ku* *tsare* *budurcinku* *da* *kyau* *itace* *mutuncinku* *da* *kimarku*) Nace" don me baza ka siya mata wani ba sai nawa ? Ina son abina kawai lokaci na ke jira ka bar min ka siya mata nata. Yace " an gama sarauniyar mata daga ke an rufe kofa. Haka ya dinga lallabani har ya kai ni mkrnta. Ko da muka tashi gida na koma duk da ba dadin gidan nakeji ba na rasa me yake damuna guda daya wlh. Karfe takwas nayi nace mama zan kwanta don bacci nakeji ina son in tashi da wuri . Don haka na shiga na kulle kaina a daki . Wanka nayi na saka kayan bacci na mai kyau da Jan hankali na kwanta lalubo wayata nayi na kira wnn gayen don na karbi num din sa yace min sunanshi fahad bautar kasa ne ya kawo shi kano amma shi dan Maiduguri ne. Bayan mun gaisa nace " wlh bazan boye maka ba tunda muka hadu da kai jiya hankalina ya kasa kwanciya sai dai bansan ya zanyi mu hadu ba gidanmu akwai takura. Cikin muryarsa me Jan hankali yace" baby kar ki damu zan shirya mana yadda zamu hadu very soon kuma ba Wanda zai Sani kinji? Dadi naji sosai nace "da gaske? Yace " sosai ma . Nace "wow Allah ya nuna min ranar amma don Allah kamin nan me zaka min ne inji dan relief wlh ina cikin wani yanayi ne yanzu gashi ban tanadi komai nasha ba. Murmushi ya yi hade da fadin " indai kin shirya shi yafi komai sauki don nima yau a hannu nake kuma banje koina ba daga aiki na dawo masaukina. Nace " wlh na shirya tsaf ma kuwa. Yace OK bari muyi vedio ne. Nan ya kirani vedio call ina dauka saida gabana ya fadi don ganinsa da nayi haihuwar........ A hankali ya dinga bi dani yana gaya min abinda zanyi da yanda zanyei....... Gaskia ranar naji dadi da nishadi mara misaltuwa wnn guy dole ne kawai mu hadu ko ta wani hali ma . Da safe kam har na makara a gurguje na gama shiri na fita naci sa,a mama na kitchen don haka na fita da gudu don nasan zata min fadan rashin bude kofa da banyi ba don tun asuba take damuna da knocking in tashi inyi sallah naki tashi. Ina fita sai ga ya salman ma ya na kokarin shiga motarsa don tfy wurin aiki. Da sauri nace " yaya ina kwana ? Ko kallo ban iheshi ba Na dan Sosa kai nace am yaya don Allah kayi dropping dina mana nayi letting ne sosai. Kamar ba da shi nake magana ba A raina nace oho ni dai ka saukeni kawai. Ina shirin zagaya in shiga kawai ya figi motarsa da gudu ya barni tsaye baki bude. Abin ya matukar kona min rai sosai kuma in Allah ya yarda yau da motata zan dawo gida sai dai ayi wacca za,ayi! Aikuwa muna fita lectures na kira Ahmad nace ina bukatar motata . Dariya yayi yace " kin canza shawara ne ? Nace " eh Yace " da kyau bari insa a duba miki ita tukun sai insa driver ya kawo miki. Nace " na gode my king. Aikuwa Karfe hudu driver ya kawo min don haka muna gama lectures na hau Na dawo gida . Nayi sa,a kuwa ya salman na waje da abokansa a gabansu nayi parking na sauka na kulle abina nayi cikin gida cikin takun kasaita.lol! Ya Bini da kallo sannan ya kalli motar kawai ya girgiza kai ya hadiye abin a ransa yaci gaba da hira da aboksnsa.!!! Tirkashi al,amarin rumaisa sai addua!!!! Hauly ce👍🏻😍🤗 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡25 ************Ana idar da sallar isha ya shigo side din mama yana " goggo Amina ina RUMAISA? Tace " tana dakinta lfy naga kamar ranka a bace. Yace" aa ba komai zata bani ajiyata ne. Ya fada yayinda ya wuce kai tsaye zuwa dakina. Binshi tayi da ido har ya shiga. Ni kam ina zaune gaban madubi daure da tawul hannuna kuwa rike da hand dryer ina gyara gashina don na wanke ne.kawai naji an bankado kofa .ban juyo ba don na ganshi a mirror. Share shi nayi na ci gaba da abinda nakeyi. Haushi ya gama cikashi fam. Don haka yace min ' ki tashi ki saka hujabinki zanyi magana dake. Juyowa nayi a hankali na kalleshi sannan nayi murmushi Nace"dama idan mutum zaiyi magana da matarsa sai tasa hijabine? Kauda kai yayi fuskarsa a daure yace" motar waye a wajen nan? Mikewa nayi na isa gabanshi muna fuskantar juna Nace" motatace any problem... ... Ya tari numfashina da fadin " waya baki? Juyar da idona nayi nace " Allah ne ya bani ta hannun Ahmad. Duk maganar da muke kallonsa nake har cikin ido yanda shima ya kafe ni da ido. Ya gyada kai yace" kin tanadi amsar da zaki ba mamanki da Abba da sauran mutan gida in sun tambaya? Murmushi nayi nace"yes of course amsar nan dai dana baka shi zan basu ko dai ? Ya girgiza kai cikin bacin rai yace " RUMAISA me yake damunki? Rike kafaduna yayi yana jijjigani da karfi runtse idona nayi ina jin zafin jijjigar har cikin raina. Ban Ankara ba naji saukan mari guda biyu masu rai da lfy har saida na yanki numfashi na. Ban gama dawowa hayyacina ba ya sake sauke min wata yayinda ya hankada ni da karfi . Allah yaso ina saitin gado don haka kan gado na fadi naji kaina sai juyawa yakeyi .da kyar na dawo dai dai. Cikin karfin hali na tashi ina kallonsa nace" don me zaka mareni ? Me na maka? Idanunsa sun kada sunyi jazir yace" saboda ki dawo cikin hayyacinki kisan dawa kike magana. Murmushi nayi na karaso gabanshi nace" ko kadan ban fita hayyacina ba nasan kuma da Wanda nake magana SALMAN ne ko? YAYANA kuma mijina in Allah ya yarda.wai me yasa kk abu kamar baka waye ba yanzu don nazo da mota shine laifi? Ko kishi ke damunkane? OK na gane kishi ke damunka. Amma bari na tuna maka kuskuren da ka tafka.Yaya Kaine mutum na farko dana fara kai maka kaina amma kaki amincewa.da ace ka amince wlh ba abinda zanyi da wasu mazan kai kadai ka isheni domin nasan SOJA na jarumine! Na karashe maganar ina murmushi. Shi kam gabadaya yanzu tsoro ma nake bashi don haka ido kawai ya sanya min. Juyar da idona nayi cikin salon Jan hankali nayi juyi a gabansa sannan na kara matsawa dab dashi.nace" ka ganni na hadu sosai in ka amince zan mantar da kai dukkan hayaniyar duniya. Na riko hannunshi nace" zo mu zauna na fada maka irin tanadin da na maka yayana. Fizge hannunshi yayi da karfi. Murmushi nayi nace " karka damu ko a tsayenma zamuyi. Ina shirin rumgumeshi ya ja baya hade da fadin " Auzubillahi mina shaidanir rajim!!! Rumaisa kinyi nitsa ba kyajin kira .Na lura ba ma a cikin hayyacinki kike ba Allah ya shiryeki . Dariya nayi nace " amin amma ni ina cikin hayyacina.duk da ma dai nasha amma ban bugu ba dan kadan nasha kawai. Girgiza kai yayi cike da takaici ya juya zai fita kawai sai ganin mama yayi ta daga labule ta karasa shigowa ta kalleshi tace,duk abinda kukayi ina jinku salman. Tabe baki nayi a raina nace" wnn kuma matsalarkice tunda kin cika bin kwakkwafi. Juyawa nayi na wuce wardrobe don dauko rigata . Ta kalleshi tace"Salman har yaushe zaka ci gaba da boye min halinda rumaisa take ciki? Salman kana ganin kai kadai zaka iya gyara wnn al,amari mai girma? Ta girgiza mishi kai yayinda hawaye ya cicciko idanunta tace" Salman dole ne in San halinda rumaisa ke ciki koda kuwa zan hadiyi zuciya na mutu.nasan kana tausaya min ne gudun kar na shiga wani hali..... Ta karasa hade da fashewa da kuka. Ya girgiza kai idansa ya kara yin jazir yace " don Allah goggo amina ki bar kukan nan. Ina jinsu na musu banza sai da nasa rigana sannan na zo gabansu nace" mama don Allah kiyi hakuri ki daina kuka ya salman yana son saka miki hawan jinine kawai shiyasa ya saka min ido idan kika biyeshi zuciyarki zai buga ki mutu ba shine da asara ba nine...... Ji kake Tass! Ya kuma wankeni da mari. Mama ma ta shararamin wata marin hade da fadin " da ba don gudun karki fi haka lalacewa ba da na TSINE miki rumaisa amma bazan miki baki ba Allah ya shiryeki. Ta fada cikin kuka. Ni kam raina ya masifan baci duk da ma kaina ya fara daukan caji. Nace" mama kika bude baki kika ambaci tsinuwa? To wlh bazan kuma zama dake ba ki fada min inda ubana yake in koma gurinsa tunda kin daina sona. Na kalli ya salman nace" kai kuma munafuki azzalumi se ka zuba ruwa a kasa kasha kayi nasarar raba uwa da 'yarta. Mama kam dada sananta kukan tayi ta na " na shiga uku ni Amina me zan gani ? Tsaki nayi nace" wlh bazan barka ba bari naje na gayawa inna ta shiga tsakanina da kai. Na kalli mama nace" kema zanje na hadaki da yayanki ki maidani gun ubana duk Ku huta tunda na zame muku matsala. Na fita yayinda jiri ke dan dibana. Ta kalli salman tace"kaga ta tafi. Da sauri suka bi bayana. Aikuwa a tsakar gida suka sameni ina zazzagewa inna dukkan abinda ya faru. A haka Abba ma ya shigo ya samemu yana tambayan me ya faru. Anana na fara kai mishi karar mama da ta maidani gidan ubana. Kwata kwata bansan me nake fada ba maganganu kawai masu nauyi ke fita a bakina. Abba ya girgiza kai cikin tashin hankali yace" innalillahi wa inna ilahirrajiun! Mama kam kuka take ta yi kamar ranta zai fita Maman sakina ke ta bata hkr Inna da Sadiya kam murna fal zukatansu don wnn shine babban burinsu dama.kuma gashi nan sunci nasara.sun jefa tsanata a zuciyar kowa bama salman kadai ba. Abba ya kalli mmn sakina yace" Rabi zo ki rike yarinyar nan ki kaita dakinki ta kwanta ta sami isasshen bacci har sai ta warware. Maman sakina tace to. Anan tazo ta kamoni muka tafi dakinta. Abba ya kalli mama yace " amina tun yaushe hakan ke faruwa. Ta dan tsagaita kukan ta fara gaya mishi abinda ke faruwa duka salman kam har yana mamaki don har randa na kwana a dakinsu ta sani. Abba kam sai salati . Yayinda ya salman ya dafe kansa dake matukar yi masa ciwo. Inna ta tabe baki tace" hmm ai dama nasan za,ayi haka kun dauki yara kun turasu jamia alhalin kun Sani sarai yanda rayuwar tamu a yau ta zamo.musamman wnn yarinyar na Dade da karantarta tsaf alhaji daga kai har salman na fada muku Ku mata aure tun wuri kukace sai tayi jamia tunda mamanta naso kun hadu gabadaya kin fifita duniya akan lahira to gashi nan kun ga sakamakon. Ta kalli mama tace " Amina ba kuka zakiyi ba kamata yayi ki tuba ki gyara halinki domin abinda kika shuka ne kike girbewa.kin dauka abubuwanda kikayi a baya Allah zai barki ne? Hmm ai bazaiyiwu ba don haka gashi nan 'yarki ma..... Abba ya katse ta da fadin "don Allah ki mana shiru tunda ba alkahairi zaki fada ba .wai baki ganin halinda take cikine? Mama ta girgiza kai tace" yaya ka barta ta fadi duk abinda take so rumsisane taja min. Inna ta tabe baki tace " bari ma kuji na fada muku wlh salman bazai auri 'yar iska karuwa mai shaye shaye ba .uwa uba kuma shegiya.don haka Amina ki raba 'yarki da dana don salman dana kamili ne ba watsasse ba. Tana fadin haka ta juya ta koma dakinta. Abba ya bita da kallo cike da takaici sannan ya kalli mama yace"amina kiyi hakuri nasan da zafi amma babu abinda ya gagari Allah kima rumaisa addua Allah ya shiryeta muma zamu yi mata don bazamu kyamaceta ba. Mama ta share hawaye tace"Na gode yaya.amma maganar shatu gaskia ne bai kamata salman kamili ya auri rumaisa ba don haka kawai batun aure tsakaninsu ma abarshi don bata dace dashi ba. Abba ya girgiza kai yace"wnn ba maganarmu bane in dai salman yana sonta to wlh ba Wanda ya isa ya hana ayi auren nan! Jin maganar Abba yasa salman mikewa rai bace ya fice. Sosai yake jin tsanata! Ni kam tuni nayi bacci abina. Mama kuwa ta koma sashinta taci gaba da kukanta. Yayinda inna da Sadiya suka kwana zuciyarsu fal farinciki. Hauly ce👍🏻🥰 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡26 ***********Maman sakina ne ta je ta sami mama a side dinta ta shiga bata hkr. " Amina matsalar da rumaisa ke ciki fa kamar asiri ne. Mama tagoge hawaye tace"nima abinda nake tunani knn rabi domin lokaci guda rumaisa ta sauya. Mmn sakina tace"Amina ance zato zunubi amma inaga abinnan kamar a gidan nan aka mata. Mama ta tabe baki tace" kin rigani a baki na riga ki a zuci ne rabi.amma Allah mun tuba . Mmn sakina ta Dan waiga bayanta taga ba kowa sannan tace " da dadewa na jiyo hirarta da sadiya naji tana cewa" indai ta yi amfani dashi shikenan bukatarmu ta biya.wlh Amina a lokacin ban kawo tunanin komai ba nama dauka ko raihanace don a kwanakin da ta dawo kamaru raihana ta yi ta zuwa kiji sunyi kus a daki na dauka ko itace .amma fa da naga halinda rumaisa ta shiga sai na fara tunanin ko dai ita suka bawa wani abun. Mama tace" zai yiwu ai rabi don kina ganin rumaisa kamar wayayyiya wlh muguwar wawiyace yarda da mutane take da wuri Maman sakina tace" kinsan Allah amina matar nan abar tsoroce wlh ni kaina da kika ganni da kyar na sami lfy ni da yarana a gidan nan. Sai da na tafi kauyenmu gun wani kakanmu na nemo mana taimako sannan muka sami lfy. Abinda za,ayi in rumaisa ta warware gobe muje kawai koma me yake damunta insha Allah zamu dace.kuma ba malamin tsubbu bane irin mutanen nan ne da aljanu suka budewa ido wlh baya duba adduoi kawai yake badawa sai rubutun sha kuma.sannan yasan magungunan gargajuya sosai. Mama ta danyi shiru sannan tace to ba matsala Rabi sai muje ai. Mmn sakina tace" to yanzu ki kwanta ni zan koma sai da safe. Sukayi sallama .ni dai ina ta sharar baccina ko a jikina. Da safe mama tuni ta shirya tsaf ta dauki makullan mota ta fita sai gidansu ya salman. Abin mamaki ta sameshi kwance a Palo har da Karin ruwa aka masa. Cikin tsoro ta karaso tace" salman me ya sameka? Cikin karfin hali yace" goggo zazzabine wlh shine Na kira abokina doctor James kawai naga dare yayi kuma banson in daga muku hankali. Mama ta girgiza kai tace"sannu Allah ya baka lfy .nasan duk sanadin rumaisa ne ka shiga cikin wnn hali. Ya giigiza kai yace"aa goggo karkice haka kuma ma ai naji sauki sosai kinga ruwan kawai nake jiran ya kare na cire na tafi nayi breakfast ko inna ma basu Sani ba. Mama tace " Allah ya baka lfy salman. Yace"amin ina zakije goggo? Tace " zamuje mu nemawa rumaisa maganin matsalartane. Yace" me yake damunta? Tace" ban Sani ba salman amma wadan nan abubuwa ba a banza takeyinsu ba.dole in tashi tsaye wurin ne ma mana mafita. Shiru ya danyi sannan yace " goggo da dai kinci gaba da mata addua sai kiga koma meyene Allah zai yaye. Ta yi murmushi ta ce" hakane salman addua kam kullum a cikin ta muke sai dai kasan Allah ma yace tashi in taimakeka. Shiru yayi sannan ganin kamar hankalinsa bai kama bayasa tace" karka damu salman ba gun malaman tsubbu zanje ba ko kadan bazan yarda na kauce ba ka kwantar da hankalinka. Yace " shikenan goggo na fahimceki Allah yasa a dace kuma. Mama ta ce"amin Anan doctor James ya shigo da sallama suka gaisa da mama. Ta kalli salman tace " yawwa salman tunda naji kace salim ma zaizo ga nan makullin motarda rumaisa ta kawo a maida wa maishi kawai bama bukata. Ta ajiye makullin a gabansa sannan ta fita. Ina tashi na koma sashinta nayi wanka na shirya don maman sakina tace akwai inda zamuje. A raina nace Allah ma yasa gidan Babana zata kaini in huta. A palon Abba na sami mama nima na zauna na gaisheshi. Nasiha ya dinga min sosai har da ayoyi ya dinga ja min.nikuwa ina karasa masa a raina. Mama kam shiru kawai ta yi har Abba ya gama sannan muka tafi. Nikam a baya na zauna mama da ke tukin mmn sakina a gefenta. Suna hirarsu.har muka isa don kauyen ba nitsa sosai. Gaskia har na manta rayuwar kauye.don haka komai sai ya dinga ban dariya. Gidan da mukaje babban gidane na wani malami don harda almajirai muka tarar a waje suna karatu don haka muka wuce gidan. Aka kawo mana tuwon dawa miyar kuka gaskia nikam zagewa nayi naci. Mama kam sun gagara ci.sai masara aka gasa musu sukaci. Har sai bayan azahar Malam ya turo muje. Sosai suka dinga hira da maman sakina ya na tambayarta labarin birni. Sannan daga bisani ta yi masa bayanin komai. Nan ya danyi shiru sannan yace"zaiyiwu asirin ne don gaskia bata da aljannu.amma akwai maganar sakaci da addini ma. Ya kalleni yace" kafin hakan ta faru kin taba yin wani mugun mafarki? Shiru na danyi sannan nace"eh nasha yi. Yace " kamar me kike gani a mafarkin? Na ce"eh na taba yin mafarkin wata mata ta sokamin wuka a ciki.sannan ina mafarki maciji ya sareni ko kare ya cijeni. Ya gyada kai yace " Allah ya sawwaka yanzu zamu baku adduoi da zakuyi sannan za,ayi amfani da ganyen magarma insha Allah indai asiri ne to kome karfinsa bi.iznillah zai karye. Amma fa adduoin da yawa kuma sai kun jajirce kuma akwai na tofawa a ruwa tasha ta kuma shafa kullum har tsawon sati biyu.daga nan fa zakuga sauyi in Allah ya yarda. Mama ta gyada kai cike da gamsuwa tace" in Allah ya yarda baba zamuyi kuma mun gode matuka. Yace" ba komai sai dai kuma ina mai bata shawara ta yi riko da addini hannu bibbiyu azkar safe da yamma kar ya wuceta sannan duk abinda zatayi ta fara da addua. Mama ta kalleni tace" kina dai ji koh. Kai na daga mata don ni tuni na gaji da zaman maganar tasu ma haushi yake bani. Sun jima suna tattaunawa.sannan daga bisani ya bamu komai a rubuce da bayani. Sai kusan magrib muka dawo. Mama kam ba alamun wasa a fuskarta duk wayoyina ta kwace ta kashe sannan tace a dakinta zan kwana. Da kanta ta dinga min tofi a ruwa ta ban na shanye. Da asuba kuwa ta tasheni bayan mun idar da sallah ta sakani gaba sai da nayi azkar din safe na karanta Qur,ani izu biyu don rabawa mana tayi tace ko wani Safiya zamu dinga karanta izu biyu. Kitchen ma ranar tare mukaje.karfe shidda na gama shirin tfy mkrnta nayi breakfast duk abin nan idanunta na kaina har na gama ta karbi jakata ta duba sosai sannan ta kalleni tace jirani inzo in kaiki. Ta shiga ciki ta dauko hijabinta da key din motarta muka fita. A waje muka hadu da ya salim da ya salman suna shirin shigowa cikin gida. Anan suka gaisheda mama nikam idona na kan ya salman yayi matukar kyau cikin kakinsa kamar na rumgumeshi wlh. Shiko baima San ma inayiba na danyi gyaran murya nace " yaya ina kwana? Ba tare da ya kalleni ba yace " lfy. Nayi murmushi nace " ya jiki kuma? Bai kuma ce min komai ba . Na kalli ya salim nace " yaya jiya bamu ko gaisa ba kazo lfy ya kabarsu mummy? Yace" kowa lfy . Sannan ya kalli mama yace" goggo ina zakuje? Mama tace makaranta zan kai ta. Salim yace haba goggo gamu bari muje na kaita ki koma gida. Ta girgiza kai tace" aa salim gabadaya yanzu na ajiye komai zan kula da tarbiyar rumaisa har ta gama makaranta! Salman yace"aa goggo bazaki iyaba ki bar komai a hannuna.na miki alkawarin baza a kuma samun matsala ba . Nan suka yi gefe sunata maganganunsu ni dai tabe baki nayi a zuciyata nace " kwaji da shi yan sa,ido. Sai naga mama ta koma ciki ya salim ya kalleni yace" dan jiramu bari muje mu gaida su Abba sai mu tafi. Bata rai nayi nace ni gaskia nayi letting. Ya salman kam tuni yayi shigewarsa fuskar nan a daure. Ya salim yace" ki jiramu nace ba dadewa zamui ba. Ya shiga ciki shima na bisu da harara. Basu jima ba suka fito muka tafi a motar ya salman. Ya salim a hanya shima fada ya dinga yi min . Ni dai gani nake kamar kowa ya tsaneni. Har muka isa ya salman kam baice komai ba!!! Hauly ce🤝🏻😍 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *_Dedicated_* *_to_* *_Ummi_* *_Abdallah_* ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page ➡27 ***************Haka sukaci gaba da sanya ido a dukkan lamurana na fuskanci takura sosai a kwanakin. Ahmad ya nemeni a waya har ya gaji kawai ya sameni a school anan ya nuna bacin ransa akan wai ya salman da ya salim sunje sun maida mishi motarsa kuma sun masa kashedi akaina. Nima na gaya mishi yadda suka takura min a gida kwanan nan amma nace ya kwantar da hankalinsa so nake a gama exams ne nasan yanda zan bullo musu.haka na lallabashi ya tafi. Salima da kawayenta ya kasance duk inda muka hadu sai sun zageni suce min karuwa saboda Ahmad ya kasa rabuwa dani alhalin ba aurensa zanyi ba.Ni dai bance komai ba. Tunda muka fara exams nakejin kaina na ciwo kadan kadan addua kawai nake kar ya hanani jarrabawata don wani lokaci haka kawai sai inji kan ya Sara har naji hankalina ya bar jikina sai a hankali nake dawowa dai dai . Anan naje nayiwa doctor hakim complain kasancewarsa general doctor ya rubuta min magunguna.kuma na sha amma shiru kakeji. Allah ya karbi adduata randa muka gama exams ina fita kawai na yanki jiki na fadi ji nake duniyar na juyawa dani. Jin dalibai nake sama sama sun kewayeni suna me ya sameta ko ta suma ne? a zo a kaita clinic. Daga nan ban kuma sanin inda nake ba har tsawon kwana 2 Sannan na fara gane wayanda suke kaina. Mama na gani sai fa,iza da sakina . A hankali na bude baki nace"sis yaushe kuka dawo? Sai naga fuskokinsu cike da mamaki suna kallona mama ta rike hannuna tace"rumaisa kina nufin kin ganemu? Nace" mama na ganeku mana ai nasan lokacin da na fadi dazu ne aka kawoni nan kuma a ka sanar daku. Ta girgiza kai tana share hawaye tace " rumaisa yau kwananki biyu anan baki San inda hankalinki yake ba.ba kya gane kowa. Na mike da sauri sai naji kaina na juyawa. Da sauri mama ta rike ni tace" kwanta kwanta bari na kira doctor. Sakina Ku lura da ita. Mama ta fita anan su fa,iza suka shiga yi mun sannu. Doctor hakim ne ya shigo. Nan ya kalleni yayi murmushi yace"Rumaisa ya jiki? Nace,da sauki doctor. Yace" yanzu me kk ji ? Nace ciwon kai kadan kadan sai jiri kuma ina jin tsigar jikina na tashi. Anan ya gwada min bp sannan ya kalli mama yace" mama kinga jininta ya fara sauka ma.yanzu dai alhamdulillah.abinda za,ayi a sama mata abinci taci tasha magungunanta mugani zuwa anjima zan dawo in dubata. Mama tace" to doctor mun gode. Yayi murmushi yace " babu komai mama Allah ya bata lfy. Mama ta ce amin. Anan ya fita. Mama tasa min abinci na danci nasha magunguna na kwanta anan bacci yayi awon gaba dani. Har yamma na tashi anan ya salman da ya salim da Abba suka shigo suka min sannu. Naji sauki sosai Ahmad ma yazo don su ya salman na fita ya shigo cikin shigan many an kaya kamar bashi ba. Ya gaisheda mama sannan ya kalleni yace"Queen ya kika karaji? Nace" da sauki waya fada maka banda lfy? Yace" Juliet ce. Daga nan shiru na masa. Har ya kari zamansa sannan ya tashi bandir din dubu dubu ya fitar ya ajiye a gefena sannan ya kalli mama yace " mama Allah ya bata lfy na tafi. Mama tace " kuma har da dawainiya haka ? Mun gode a gaida gida. Ni dai ban kuma ko kallonsa ba har ya fice. Mama ta kalleni tace" wai waaye wannan din kuma? Nace"Ahmad ne...... Ai ko kan na karasa naga mama ta kura min ido ido cike da mamaki tace" au shine Ahmad din. Shiru nayi ita kuma ficewa tayi. Sati na daya aka sallamoni. Amma gabadaya na kasa sakewa duk da su faiza na nan amma wnn karon basu gane min ba. Banda aiki sai Kuka Sunyi rarrashin duniya sun gaji haka ma mama. Ranar da daddare bacci ya gagareni don tsabar bakin cikin rayuwa.na tashi na tafi dakin mama banyi mamakin ganinta akan sallaya ta idar da sallolinta tana karatun Qur'an Kusa da ita na zauna Dan haka ta sami aya ta tsaya sannan ta rufe Qur'ani ta kalleni tace"wai har yanzu bazaki bar wnn kuka ba? Da kyar fa jininki ya sauka bayan asma kina son sawa kanki hawan jini ne? Kina 'yar karama amma kina son ki dorawa kanki damuwa.in dai da tsawon rai to baki fara komai ba a rayuwarki tunda ba kiyi aure ba baki haihu ba.abinda yake gabanki yafi na baya yawa don haka gara ki rage damuwa. Hawaye na zubowa nace"mama wlh abubuwanda ya faru dani yasa naji komai na rayuwa ya fitan min a rai mama ni kunyan kowa nakeji a gidan nan musamman ya salman da Abba. Na karasa maganar cikin matsanancin kuka. Jawoni tayi jikinta tace"ya isa haka nan kuka.haka taki kaddarar take baki isa ki tsallakeba.kuma ki daina dawoda hannun agogo baya ki bar wnn maganar don ya wuce sai dai a kiyaye na gaba.kuma kinga sakaci da addini shi ya ja miki.da ace kin rike addininki hannun bibbiyu wani abun ko zai sameki sai kiga yazo da sauki. Na gyada kai ina goge hawayena nace"mama ina zargin wani abu gameda maganin da inna ta ban...... Anan na bata labarin yadda duk mukayi da inna da Sadiya. Shiru tayi ta zuban ido sannan daga bisani tace"su suka Sani da mahaliccinsu.yanzu dai da fatan kin hankalta.kuma in Allah ya kaimu rai da lfy gobe kije ki gaida Abba ki bashi hkr da salman. Na daga mata kai. Daga nan na koma daki na shiga toilet na dauro alwala nazo na hau sallayata. Da safe har 10:00am na tashi don haka na fada wanka bayan na fito na shirya tsaf cikin Riga da siket na atamfa.na saka hijabina na fito A Palo na sami mama da faiza da sakina suna breakfast sai hira suke. Suna ganina faiza tace "Queen an fito? Harara na sakar mata nace" nace bana son sunan nan ko? Tace"ai ko baki so dashi zan kiraki tunda haka naji yan makarantarku ke kiranki duk Wanda suka je dubaki a asibity. Sakina tayi dariya tace"Ranki ya dade Queen of beauty ! Faiza tace"amma na BUK. Shiru na musu na ficewata cikin gida na side din Abba na shiga kasancewar yau Sunday yana nan.muka gaisa anan na bashi hkr. Murmushi yayi yace" ni kuma me kika min rumaisa? Ai babu komai Allah dai ya tsare gaba Nace amin Daga nan dakin mmn sakina na shiga na gaisheta. Sannan na tafi dakin inna na sameta da Sadiya suna hirarsu harda dariya. Suna ganina naga yanayin fuskarsu ya sauya Sadiya tace" lfy kika shigo mana ba sallama? Fuskata a daure nace"don me zaki ji sallamata kina dariya shewa kamar ba musulma ba. Tace"au dariya da shewa laifine? Tsaki nayi nace " ni ba wurinki nazo ba. Na kalli inna wacce naga gabadaya ta zuban ido. Na mika mata goran mai data bani nace" inna maganin da kika bani naji dadinsa kwarai nayi amfani dashi yadda ya dace ga nan robar na dawo miki na gode sosai Allah ya biyaki abun kika min. Gabadaya sai naga mamaki ya bayyana a fuskarsu . Yayinda tuni hawaye ya ciko idona na ajiye robar na fita. Gidansu ya salman na tafi na sameshi ya shirya zai fita. Sallamata tasa shi juyowa muka hada ido da sauri na sauke idona kasa duk sai naji kunya kamar na nitse. Tunda ya amsa sallamar bai kuma ce min komai ba. Na daure nace" yaya ina kwana? Bai amsa ba kuma badhida niyar amsawa. Durkusawa nayi har kasa nace" don Allah yaya kayi hakuri ka yafe min laifin da na maka wlh ba laifina bane na wayi gari kawai na tsinci kaina a cikin mummunan yanayi. Na karasa maganar cikin kuka. Ido ya zuba min shi kadai yasan me yakeji a ransa. Ya daure yace " shikenan na yafe miki amma don Allah ki daina zuwa inda nake don ban son ganinki Sam Sam! Na girgiza kai nace" yaya idan ka juya min baya bazan ji dadi ba a rayuwa don Allah ka daure ka manta da abinda....... Cikin tsawa yace" ki tashi ki tafi nace bana son ganinki... Cikin kuka nace " yaya wlh bazan iya wnn horon ba gara ka min wan...... Yace" OK tunda bazaki tafi ba ni bari in bar miki gidan. Ya tashi da sauri nima na tashi na fita ina kuka. Tun daga nan fa komai ya fara birkicewa tsakanina da ya salman don gabadaya baya ko son jin muryata a sanadin hakan har ya daina zuwa kofan mama. Kafin mu gama hutu tuni an anzo anyi maganar auren faiza da sakina hakama ya salim anje an masa tambaya don so ake a hada gabadaya ayi shi a karshen wnn shekara wato December. Sai dai ya salman yace shi bai gama shiryawa ba tukun . Abinda ya baiwa kowa mamaki don tuni sun gama tsara gininsu kuma sun aje kudi dai dai gwargwadon shagalin bikinsu sannan yanzu dawowarsa kano harda business sukeyi da ya salim kuma Allah ya sanya albarka komai na tfy dai dai da yadda suka tsara. Amma yace shi bai shirya aure yanzu ba. Don haka su Abba suka sakoshi a gaba akan ya fada musu meye matsalarshi ? Yace ba komai kawai shi ba yanzu zaiyi aure ba. Su dady suka kirani suka tambayeni ko dai akwai wani abu da ya hada mu ne? Nace babu. Anyi juyin duniya dashi ya fadi mecece matsalarshi amma ya kafe kan ra,ayinshi Wanda a karshe daddy yace Wa Abba su barshi a hankali zasu shawo kanshi!!!!! Inna kam babu Wanda ya kaisu farin ciki domin komai na tfy yadda malaminsu ya tsara musu a nasu tunanin knn. Nikam nayi kuka har na gode Allah mama ta ce in yi hakuri kawai mu barwa Allah komai. Gaskia wnn karon hutun baiyi dadi ba har aka bude makaranta su fa,iza suka koma ni kuma naci gaba da zuwa ina dawowa.ganin na nitsu hankalina ya dawo jikina yasa mama ta barmin motarta da kaina nake zuwa in dawo kuma Alhamdulillah na daina kula kowa dama ni ba wani kawayene dani ba.don haka in naje abinda ya kaini kawai nakeyi in mun gama lectures na dawo gida.anan ma ba na fita daga kofar mama na daina kula harkar kowa. Ya salman tuni na watsar da lamuransa don na gane ba son aurena yake ba.shiyasa yake wani cewa be shirya ba. Ahmad kam ba yanda baiyi dani ba mu koma kamar da amma naki na saurareshi don haka ma nace mishi in har da gaske yana sona to ya tuba ya bar shaye shaye yazo muyi maganar aure don ni aure nake son yi. Tunda mukayi haka bai kuma nema na ba.haka ma fahad muka rabu daga randa nace ni aure zan yi. Yanzu doctor hakim ne kawai ya rage yana ta bina akan Na amince ya turo magabatansa nace mishi sai nayi tunani. Watarana Na dawo makaranta Na shiga cikin gida don in duba jikin Zainab don tana zazzabi . A tsakar gida naga wata wacce kusan zamuyi sa,a fara doguwa ga gashi kam da ga gani ba tambaya 'yar kamaruce don tana shigen yanayi da inna. Muna hada ido sai naga ta harareni ta shiga palon inna hannunta daukeda kulan abinci da plate. Murmushi nayi Na wuce dakin mmn sakina Na gaishta Na tamvayeta jikin zainab don tana bacci. Tace" jiki kam da sauki sosai rumaisa yau kun tashi da wuri. Nace " eh munyi test ne. Muka danyi shiru nace" mama wacece Na wuce a tsakar gida? Tace " hmm latifa ce 'yar yayan inna.ta miki magana ne? Nace "aa kawai naga ta na min wani irin kallo kamar mun taba haduwa hakan nan kuma ni ko aurensu Sadiya ma ban ganta ba. Mama ta tabe baki tace"wnn gogaggiyar 'yar duniya ce daga gani don in kinga rashin kunya da takeyi a gidan nan sai kin rike baki.gara ma da baki shiga don tuni Sadiya ta gama gaya mata komai akan kowa .wai naji inna na cewa itace salman zai aura .amma Sam batada respect Allah dai ya kyauta. Dan murmushi nayi cikin karfin hali nace "amin mama bari in isa side dunmu .ayi ma zainab sannu in ta tashi Allah ya sawwaka. Tace" to rumaisa amin Na gode. Na tashi Na fita a tsakar gida Na sami inna a kitchen. Na gaisheta ta amsa hade da fadin kira min Sadiya a Palo. Nace"to. Tun kan Na shiga palon naji kamshin turaren ya salman wnn ya bani tabbacin ya na palon. Na daure Na shiga da sallama wata tsiririyar murya naji ta amsa min Na shiga nan da nan naji kirjina ya soma bugawa. Ya salman na gani yana zaune ita kuma tana zaune kusa dashi ko dan kwali babu akanta ta zuba gashi har tsakar baya. Abinci yakeci ita kuma tana mishi hira da fulatanci kamar mai rada ta kwantar da murya tsabar kissa da kisisina kamar zata shige jikinshi. Nayi matukar kokari nayi controlling din kaina na kauda ido na akansu na wuce dakin ciki labule na daga Na kalli Sadiya dake shirya Abdul nace " Sadiya inna na kira. Duk da ma nagane ba aiken gaske ta min ba kawai tana so inje inga ya salman da wata ne. Don koda na fita sai naga fuskarta cike da fara,a tace min kin kirata? Nima murmushi nayi nace eh inna tana zuwa ma. Tace" to. Daga nan na wuce kofar mama . Duk yadda na daure abun ya gagara don haka kawai kuka na shiga yi ni kadai nasan me nakeji a zuciyata A haka mama ta sameni tace"yau kuma meye faru? Nace" mama ya salman ya daina sona ya sami wata. Shiru tayi ta rasa me zata ce min can ta numfasa tace " kinsa mi labarin zuwan lathifa ne? Na dago ina kallon mama nace " mama dama kema kinsan tazo ne? Ta ce min eh shatu ne ta kirani ta sanarda ni zuwanta kuma ta kara ja min kunne akan alakarki da salman don bata so ga mata can ta zaba mishi. Don haka abinda nake so dake ki kara hkr komai zai wuce kinji. Na share hawaye nace" mama insha Allah daga yau na daina zubda hawaye akan ya salman kuma na hkr dashi ni zan bawa doctor hakim dama ya turo magabatansa aure zan yi mama mu huta da wnn bakin cikin. Tace" Rumaisa karfa ki biyewa zuciyanki kije ki auri Wanda bashi kike so ba.ki sake tunani kin shirya auren hakim kin yarda zaki zauna dashi a kowace irin yanayi? Sannan aure fa idan kinyishi ki tabbatar kinyi knn mutu ka raba ba wai zuwa zakiyi ki dawo ba. Saboda haka kar ranki ya baci kije kima kanki zaben tumun dare. Nace " ko kadan mama hakim ya dade yana bina tun farkon zuwata jamia kuma duk abinda ya faru dani ya Sani amma bai taba nuna min tsana ba dai dai da second daya kuma tunda muke dashi maganarsa dayace bai wuce in yarda in aureshi ba don haka inaga yanzu lokaci yayi da zan faranta masa rai nima. Mama ta ce " to shikenan idan har hakan ta kasance bazanyi bakin ciki ba sai dai in sanya albarka.sai dai Allah sa su yaya su fahimcemu. Nace" karki damu mama zasu fahimcemu. Daga nan fa na daddage na fara cusawa kaina tsanar ya salman . Tuni nayi wa doctor hakim albishir daya turo magabatansa kuma banson auren ya wuce nan da wata daya tunda yace ya shirya nima na shirya.!!!!!!!!!! To faaaaa!!!!!!!! Don Allah ayi hkr da rashin post dina banjin dadi ne kuma ga matsalar rashin wuta👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 Hauly ce👍🏻😄😍 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *_Dedicated_* *_to_* *_Ummi_* *_Abdallah_* ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡28 **************Nan da nan maganata doctor hakim ya kam kama don a cikin satin nan yace zai turo magabatansa. Koda mama ta fadawa Abba cike da mamaki yace" Amina ko dai akwai abinda ya faru tsakanin salman da rumaisa ne ? Kinsan fa ruwa bata tsami banza yaran nan su suka shirya Kansu suka fada mana amma gashi yanzu matsala ta faru a tsakaninmu duk mun tambayesu sunki su bamu cikakken bayani bare mu shiga al,amarin mu gyara gashi yanzu rumaisa zata turo wani daban akan maganar aure.gaskia ya kamata dai mu San abunyi don baza mu zuba ido ba.bari na kira kassim yazo dai tukun. Mama tace" to yaya duk yadda kukayi dayane.Allah ya kai mu. Daga nan ta mashi sallama ta dawo side dinta ta sameni na gama shiryawa cikin atamfa Riga da siket nasha daurin dankwali na zuba sarka da 'yan kunne har da warwaro da zobuna na dauko jakata da tayi matching da takalmina.nasha gyale kuwa don ko Aisha buhari a yau diinan zan iya jerawa da ita. Mama kallo na take tace" Rumaisa yau kuma makarantan kikewa kwalliya haka ? Aa to sai dai kisa hijabi indai zakiyi driving. Dariya nayi nace "kai mama wai har kin manta nace miki zanje ne bikin wata 'yar makarantanmu ? Tace" na manta yaushe zan zauna rike shiririta ga abubuwa da yawa a gabana. Murmushi nayi sannan na suri makullin motarta nace"bazan ma shiga makaranta ba daga gidan bikin dai zan dawo. Tace" ki dai kula da kanki Allah ya tsare . Na ce"amin mama. Na fita cikin sa,a kuwa saiga ya salman cikin kakinsa ya sunkuya yana gyara takalminsa. Yana dagowa mukayi ido hudu.na Riga shi kauda kaina sakamakon zuba min ido da yayi kamar mai shirin fadin wani abu. Ba tare da na sake kallonshi ba nace" yaya ina kwana? Kamar ba zai amsa ba daga bisani yace" lfy. Ni dai tuni na shiga mota na tayar da gangan na fizgi motar da gudu kamar zan tashi sama. Ya kuwa Bini da kallo Saida na hau titi na rage gudu. Nan naji wayata na kira na lalubota na duba sai naga raihana ce. Na dauka nace" hallo Tace" rumaisa don Allah kizo sai nemanki nake. Na ce to fa lfy dai kk ta nemana? Tace"lfy lau karkiji komai don Allah kizo kayane daga sokkoto nayi muku odarsu keda sakina da fa,iza amma kuma sai naji labari mara dadi akanmaganarki da yaya...... Na katseta da fadin kinga bari nazo ina tuki ne. Na kashe sannan naci gaba da tuki. Gidanta na fara zuwa ina isa na sami Sadiya da lathifa a Palo ana zuba hira da fulatanci cikin nishadi sai dariya suke. Nan da nan fara,ar da ke fuskata na nemeshi na rasa. Sukam kallona suke tamkar basu sanni ba. Raihana tace"lallai rumaisa irin wnn ado haka ina zuwa? Na ce"wlh biki zani. Tace"to ki zauna mana. Na ce"aa wlh naga kinada manyan baki ni zan tafi sai watarana. Sadiya tace" ko dai mu baku guri ne? Na ce"aa kuyi zamanku. Tace"au ga fa lathifa rumaisa Baku gaisa ba. Na kalli lathifa ina murmushi nace ai na ganta sai dai da yake ita batajin hausa ni kuma banajin fulatanci shiyasa ban mata maganaba.... Raihana ta katseni da fadin kinga zo muje ciki Malam ne yake son magana dake. Taja hannuna muka tafi side din Malam a Palo muka zauna tace" rumaisa me faru tsakaninki da ya salman? Nace" ba komai raihana. Tace"aa wlh ban yarda ba haba rumaisa me yasa zakuyi haka kuna fa son juna da yaya sosai don Allah ku maida soyaiyar Ku kinga wlh kayan mata na muku oda daga sokkoto naki ma yafi yawa don so nake ki rikita yaya sosai amma kawai sai naji Sadiya na cewa wai ai kun bata waye waye yanzu lathifa zai aura. Nayi murmushi nace " haka Allah yaso don ni a halin yanzu har na ba wani dama ya turo magabatansa.to kinga yaya kuma ga lathifarsa don haka yanzu abinda ya rage kawai ki mana adduan fatan alheri. Tsaki taja tace"wlh daga ke har yaya kuna shirin TAFKA KUSKURE babba a rayuwarku don wlh aurenku shine alheri karku yarda Ku rabu. Nace"ai ya wuce tunda ni na sami wani miji shi kuma ga matarsa nan kuma yar uwarku ce. Tayi tsaki tace" yaruwarmu ce amma basu dace ba don wlh lathifa kam 'yar duniyace cikakkiya wlh gaba daya ta gagari iyayenta amma shine kika ga inna da kwashe kwashe ta kwasota wai yaya ya aureta sai kace asiri akama inna ? In ba haka me yaya zaiyi da wnna 'yar iskar? Na tabe baki nace" ke dai kika ga hakan sukam basu gani ba. Kinga ni tfy ta zan yi sauri nake. Jikinta a mace tace" rumaisa shikenan tunda kinki ki ban hadin kai.amma fa ki Sani bazan bar wnn maganar haka ba domin wlh sai Na wargaza dukkan shirin inna da Sadiya in Allah ya yarda . Nace" ni dai ba ruwana ki bar zancan nan anan. Daga nan na mata sallama. Gidan biki Na wuce inata tunanin maganganun raihana. A cikin satin daddy yazo kano Abba ya gaya masa komai gaskia abin ya damesu sai dai sun kasa ganewa salman kwata kwata don yaki yarda ya fada musu matsalarsa. Mama kam cewa ta yi kawai suyi hkr su barshi haka Allah yaso . Duk yadda suka so su gyara alamarin ya gagara haka suka hkr ba don ransu ya so ba.daddy yace zai jira zuwan yan uwan doctor hakim domin azo ayi maganar aurenmu.shi kuma salman sai ya nemo matar da zai aura don basa son bukukuwan ya wuce ending of this year Inna kam ba Wanda ya kai ta jin dadi ita da Sadiya domin sunci nasarar rabani da salman gaskia wnn karon aikin malaminsu yayi kyau akaina ni da salman . Sai dai a yanzu damuwarta bai wuce taga Sadiya ta koma gidan ja,afar ba amma abin ya gagara duk shige shigen duniya sun gama amma ko labarin ja,afar babu.tunda ta saki Sadiya bai kuma waiwayarta ba har yau gashi yaronsa ya girma har ana shirin yayeshi amma baisan ubansa ba . Wnn abun yana damun inna sosai. Yayinda Sadiya kam tuni ta fita harkar ja,afar zuwan lathifa yasa idonta ya kara budewa ta dinga zuga Sadiya akan kar ta koma gidan ja,afar kawai ta yaye Abdul ta sami wani bazawari mai kudi zai fiye mata. Don haka yanzu kominsu daya da lathifa sun mannawa inna hauka.su suna harkokinsu don tsabar RASHIN NAZARI irin na Sadiya. A satinda doctor hakim yace zai turo sai muka ji shiru Na kira wayarsa ma a kashe. Gaba daya hankalina ya tashi ga daddy yana jira suzo don ya wuce Abuja a yau. Amma shiru shiru har bayan isha sannan sukazo.har naji sanyi a raina don dazun har kuka nayi. Anan Na fara trying Na layin doctor hakim amma har yanzu a rufe. Mama ta shigo ta sameni tace" hmm yanzu kam hankali ya kwanta koh? Dariya kawai nayi tace " to sai kiyi bacci don mu tashi da wuri. Nace to mama. Na kwanta knn sai ga kiran hakim da sauri Na dauka ina murmushi nace doctor ina ka shiga tunda safe wayarka switch off? Yace" wlh ayyuka ne suka min yawa a asibity. Nace " ayya shiyasa mana naji muryarka a sanyaye nasan ka dibo gajiya. Shiru yayi jin shirun yayi yawa yasa nace"lfy doctor? Yace " ba lfy rumaisa akwai matsala akan maganar aurenmu? Da sauri na tashi zaune kirjina Na bugawa nace" me ya faru doctor wayanda ka turo sunzo fa. Yace" eh sun je sai dai basu daidaitq da su kawunki ba.domin sun nemi su gana ne da dangin mahaifinki sai dai kuma ba wata cikakkiyar bayani da aka musu akan waye ne mahaifinki kuma aina yake? Nikam tuni na fara kuka hkr ya shiga bani yace" rumaisa ban San me yasa suka min haka ba ni a ganina ba ruwansu da waye mahaifinki ko danginsa tunda yanzu a cikin danginki suka sameki kuma su kawu ma sun isa su daura miki aure ba sai an tsaya bincike ba. Na girgiza kai cikin matsanancin kuka nace" banga laifinsu ba ko kadan don wlh nima ina son sanin waye mahaifina.... Na karashe maganar da kuka shiru yayi yace " rumaisa kiyi hkr ki bar kuka insha Allah zamu daidaita komai kuma ki kokari ki tambayi mama labarin mahaifinki idan har bata saurareki ba wnn karon ni zan tayaki mu binciko..... Nace" aa ka bari kawai hakim kar ka shiga maganar nan. Na kashe wayar naci gaba da kukana. Ranar banyi bacci ba cikin dare koda mama ta zo don ta tasheni sai ta sameni akan sallayata ina sallah don haka takoma. Washe gari su Abba suka kiramu a palonsu.ananfa daddy ya bayyana mata yadda sukayi da yanuwan doctor hakim. Shiru ta yi sannan daga bisani tace" to yaya ni ban ma San me ma zance ba.kawai abar wnn maganar domin batada wani amfani..... Abba ya katseta da fadin " Amina ki daure ki fada mana waye mahaifin Rumaisa domin nasan ko itama tana son sanin waye mahaifinta musamman yanzu da maganar aurenta ya fara samun matsala akan..... Bacin rai sosai ya bayyana a fuskar mama ta ce" yaya har yanzu baku yarda dani ba shiyasa bana son tuna abinda ya faru.Rumaisa dai tana da uba amma nima bansan inda yake ba.in sunga zasu iya barin ayi auren haka to in kuma sunce sai sunsan waye mahaifinta to ni dai ban shirya amsa wnn tambayar ba.kawai su hkr da juna Allah ya kawo mata wani mijin.ni yaya a ganina kuma kun isa Ku zamewa rumaisa dangin uwa dana uba don haka ni bana bukatar a sake kawo min zancen waye mahaifin Rumaisa! Nikam tsananta kukana nayi na ce "mama don Allah ki taimakeni nima ina son sanin waye mahaifin nawa. Ta girgiza kai tace " bazaiyiwu ba! Sosai mama ta kafe ba yanda su abba basu yi ba da mama ta basu labarin inda mahaifina yake taki ta fada .daddy kam tuni ransa ya baci ya kama yima mama fada. Nikam sai kuka na Sani. Inna ce ta shigo ta kallemu gabadaya sannan tace" kassim ka daina bata ranka a banza amina bazata gaya muku komai ba domin labarin ta baida dadinji.domin tasan ba ta hanya mai kyau ta sami yarinyar nan ba. Ba tare da ta tsaya jin Karin bayani ba ta kalleni tace " Rumaisa bari na fada maki ko hankalinki ze kwanta. Ta ci gaba da fadin " sunan mahaifin ki IBRAHIM.Wanda a shekarun baya da suka gabata shine ya hure Wa mahaifiyarki kunne ta dinga bijire ma yayyunta har ta kai ta kawo ya dauketa sun gudu.bamu sake sanin inda take ba baya wasu shekaru kawai ta dawo tare da ke kina yar shekara biyu kuma yayunta sunce matukar zata zauna dasu to sai dai ta maidaki wajen ubanki domin su bazasu zauna da ita da tarin abun kunya ayita zaginsu. Shine ta daddage ba kunya ba tsoron Allah ta shuka masu rashin mutunci daga karshe ta fice Wanda bamu sake sanin inda kuke ba sai daga baya muka gane tana wani kauye domin tana shiga cikin gari acewarta tana kasuwanci amma ba kasuwancin take ba....... Abba ya katseta da fadin " ya isa shatu don Allah! Mama tace" ai kawai ku batta ta karasa. Ta kalli inna tace" ki karasa maganarki shatu. Inna ta yi murmushi ta kalleni tace rumaisa...... Mikewa nayi da sauri na bar palon ina kuka masananci. Na tafi na barsu.kan kace meye wnn na hada kayana na fita da sauri sai ga ya salman ya kare min kallo yace " ina zakije? Kai tsaye nace"Neman mahaifina! Cike da mamaki yace " ke ! Kina cikin hayyacinki kuwa aina zaki je ki nemeshi? Kinsanshine? Na girgiza kai nace " ko ban sanshi ba zan bi duniya har sai na gano inda yake. To fa! Abu kamar wasa magana ta zama babba domin har su Abba sai da suka shiga vani hkr da ni dai na dage yau bazan zauna ba zan tafi nemansa domin ya isheni gorin da ake mani. Inna ta yi dariya hade da shewa tace " jeki abinki rumaisa Allah ya bada sa,a. Abba ya harzuko yace" shatu wai ke wace irice? Ana kokarin daidaita magana tun dazu amma sai kara hura wuta kike kamar wata shaidaniya wai ina ruwanki ne a cikin wnn maganar to wlh karki kuma sa bakinki bana so don na lura baki son zaman lfy. Ya kalli mama yace " amina rike rumaisa Ku je ciki kuyi hkr don Allah maganar ya isa hakan nan Mama ta girgiza kai fuskarta jike da hawaye saboda irin bakaken maganganu da inna ta dinga gaya mata tace" yaya ai babu amfani in tsaida Rumaisa taje kawai.shatu ta rigada ta hargutsa komai ta tayarwa rumaisa hankali ta yanda bazata taba saurarona ba don haka zamanta anan baida amfani taje ta. Ta kalleni tace "Rumaisa ki je ba komai .mahaifinki cikakken sunanshi IBRAHIM AHMAD GALADIMA.Cikakken Dan Adamawa ne a yola.ina miki fatan alkhairi Allah ya tsareki kuma a duk inda kike a fadin duniya! Ta karasa tana kuka sosai ta wuce side dinta. Inna ta tabe baki tace " hmm ayi dai mugani.. Na kalli ya salman da su Abba kawai sai na juya da niyyar tfy daddy da Abba sukace in dawo kar in tafi. Hawayen idona tuni ya kafe nace" kuyi hakuri kawu zan tafi tunda mama ta vani izni sai dai zan dawo in har bukatata ta biya. Da sauri na fita Salman ma da sauri ya juya zai bini Wata uban tsawa inna ta daka mishi. Ni dai tuni na fice na barsu bansan ta suka kare ba. Bank na wuce Na Ciro kudi daza su ishen karfe shadaya ina tasha na kuwa ci sa,a na sami motar Adamawa saura mutum daya na biya kudi na bada address dina da number din Mamana saboda halin tafiya. Nayi addua yayinda nake shirin shiga mota........... Haulyce🥰👍🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *Dedicated* *_to_* **Ummi** *Abdallah* 🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡29 *********Jinayi an riko hannuna ta baya. Ina juyawa naga ya salman ne. Ya zuban ido nikam tuni na kwace hannuna. Girgiza min kai yayi yace" Rumaisa babu inda zakije kawai kizo mu koma gida. Nace" wlh bazan koma ba don banga dalilin da zai maidani gidanku ba mahaifiyarka da 'yar uwarka sun sakoni a gaba da zagi da gori don banda asali to zanje in samo asalin nawa kuma bazan dawo gidanku ba. Shiru yayi kamar bazai yimagana ba yace" ni dai nace kizo mu tafi ba wai ki daga min murya attention din mutane ya dawo kanmu ba. Aikuwa na daddage naki wasa gaske kuwa saida naso tara masa mutane a tasha .don ma driver din babban mutum ne saida ya shiga maganar duk tunanin kowa ya salman mijinane. Shidai yana rike da hannuna yace bazan shiga mota ba yayinda ni kuma nace sai na shiga yace" Rumaisa kinsan zan iya daukarki ko? Driver dinne ya dinga bani hkr yace in bi mijina har da nasiha ya fito min da kayana . Kuka na kama yi nace " ashe da kai aka hada baki ake kuntata mana ni da mahaifiyata a gidanku...... Ya katseni da fadin " ni dai mu tafi kawai. Ya dauki kayana ya mayar motarsa ya dawo ya kalleni yace " kiyi hakuri ki bar wnn tfyr ko don mkrantarki . Sai a lokacin na tuna wani abu wai makaranta Wanda a yanzu mun shiga shekararmu ta karshe kuma jibi ma zamu fara test. Don haka dole na hkr muka tafi Muna isa gida ko kayana ban sauke ba na fita na nufi bangaren mama Ina shiga na sameta a kwance tana bacci. Na karaso gabanta na fara tashintq ina" mama kinga har na tafi amma ya salman yaje ya dawo dani don Allah mama kice ya barni in tafi wlh in naje zan dawo ko don makarantana. Ganin bata ko motsa ba yasa naji zuciyata ta buga da karfi na mike a tsorace . Na juya ya salman ne na gani ya shigo nace" kazo kaga me ya sami mama? Yace " bacci takeyi bayan tfyr ki ta tsinci kanta a wani yanayi har jininta yayi mugun hawa shine aka ce a barta ta sami isashen bacci bayan tasha magani. Hawayene ya zubo min nace" ka gani ko? Duk abin nan da yake faruwa dani saboda kai ne ! Don Allah don Annabi ka daina shiga harkana ko na sami salama gun Inna. Bai ce komi ba kawai ya juya ya fita nabi bayanshi a Palo naga mmn sakina ta shigo tana zaune bayan ya salman ya tafine ta ajiyeni ta dinga min magana hade da rarrashi. Gaskia a kwanakun mun fama da kuncin rayuwa.Inna dai ba abinda ya canza a halinta duk da ba shiga gida muke sosai ba amma duk sadda muka shiga sai ta dinga mana habaici. Sadiya da lathifa kuwa tuni suka manna ma inna hauka sai harkokinsu suke.Sadiya ta kara wayewa musamman da lathifa tazo ta kara wayar da ita tuni ta yaye Abdul haka suke barinshi gun Inna suyi ficewarsu . Lathifa kam ta tata samari sosai ma su kudi kunsan kanawa da son farar mace gata kuma kalar Jan hankali don ta iya salon karuwanci sosai. Don haka tuni ta tara samari .Sadiya ma ba laifi ta sami zawarawa.don haka suke buga rons dinsu son ransu. Duk abunnan basu San ya salman na timing dinsu ba. Ranar da abun ya isheshi sunje biki wai amma sukaki dawowa har shadayan dare sun bar Inna da Abdul sai faman kuka yake saida ya salman ya karbeshi suka je waje har yayi bacci snn ya dawo dashi ya kwantar ya koma wajen ya ci gaba da jiran dawowarsu Sadiya. Can kuwa karfe sha daya ta Dan wuce kadan wata dalleliyar mota ta zo dab da kofar gida ta yi parking abun mamaki sai yaga Sadiya ta fito anci ado a matse cikin riga da siket. Ba ta ma ganshi ba ta wuce gida aikuwa da sauri yabi bayan ta lathifa kam ba ta ma fita daga motar ba kasancewar motar saurayinta ne ta tsaya suyi sallama. Yaya salman kuwa a tsakar gida ya tadda Sadiya fuskar a murtuke yace" ke daga ina kuke ? Ta danja da baya kadan don ganin yana shirin kwance belt daga kugunsa. Ta fara magana cikin tsoro " yaya na raka lathifa ne gidan biki. Yace " gidan bikin uban Wa? Kuma da iznin waye kuka fita? Da sauri ta ce"yaya inna ce tace muje... Inna dake zaune shiru take kallon Sadiya cikin takaici da bakin ciki tace" yanzu don bakida kunya karya zaki shirya min ina jin ki.ina nace karku fita shine da kukaga na shiga wanka kuka yi ficewarku kuka barni da yaro ya bi ya fitineni da kuka don tsabar rashin hankali da rashin tausayi irin naki. Sadiya ta tura baki tace " to inna haka zamuyi ta za.... Ba ta karasa ba salman ya daka mata tsawa yayinda ya karasa cire belt ya shiga dukanta ko ina ai tuni ta shiga ihu tana wayyo Allah inna yaya zai karyani.yaya na tuba wlh na tuba. Inna tace" ai gwara ya karyaki din inyi jinya da irin yawon tsiya da kikeyi. Ya salman kam bayaji baya gani sauke mata belt kawai yake. Ihunta ya tashi Abba Wanda tun shigowarsa ya tambayi inna su Sadiya tace suna can dakin ciki. Da sauri Abba ya rike salman yana cewa kai salman me ta maka da zafi haka kake dukanta? Sadiya jikinta duk ya faffashe tuni ta yi daki tana kuka. Cikin tsananin bacin rai salman ya shiga gayawa Abba abubuwanda su sadiya keyi. Abba ma ransa ya baci sosai ya kalli inna yace" kinga abinda nake fada miki tuntuni ko?to wlh ni bazan bari Sadiya ta janyo min abun kunya ba don haka na baku wata daya taje ta daidaita da daya daga cikin maneman nata a daura musu aure kowa ya huta sai kuje kuyi shawara. Ya kalli ya salman yace " ina ita kuma lathifar? Ya salman yace " ta na waje tsabar rashin tarbiyya yanzu karfe sha biyu ta na zaune da wani a mota. Yana fadin haka ya fita ransa a bace. A kofar gida suka hadu zata shigo bai tsaya wata wata ba kawai itama ya rufeta da duka a rikice tayi ciki don bata San duka ba a gidansu. Da gudu ta isa tsakar gida ta rirrike inna tana kuka.ta na ta magana da fulatanci Ya salman kam sai huciyake Abba yace" ka min dai dai salman kuma na gode maka Allah ya maka albarka tafi kaje ka kwanta abinka. Tare suka fita da Abba shi ya tafi gidansu Abba kuma ya rufe get. Inna da ' yan dakinta kwana sukayi basuyi bacci ba.lathifa tuni ta hada kayanta wai ita bazata iya zama ana dukanta kamar jaka ba don tsabar mugunta a hakan ne za,a ce suyi aure watarana yaje ya kasheta? ita kam bazata iya ba. Sadiya dai ta kwana zazzabi yayinda lathifa kuwa asubanci ta yi ta tafi juyin duniya inna ta yi da ita ta hkr amma taki. Ni dai bansan me suke ciki a bakin mmn sakina muke jin labarin tabe baki nayi nace" hmm kadan ma inna ta gani. A lokacin muka fara shirye shiryen exams kai ya fara daukan zafi da karatu. Banda lokacin kowa yanzu sai na karatuna da ibada.ko ina gida bana fita a daki nake wuni abina. Mama yanzu ta fi maida hankali a harkar kasuwancinta. Kwatsam ranar saiga Ahmad gar gida yazo rabona dashi tun lokacin da na mashi nasiha akan shaye shaye . Kawai yaro ya shigo wai ana sallama dani. Cikin mamaki na fita ina ganin shine na koma gida na gayawa mama tace in shigo dashi Palo mu zauna . Don haka naje nai mishi iznin isowa bayan na kawo mishi drinks. Ya kalleni yace " my Queen tunda muka rabu zuciyata ta kasa hkr shine na dawo. Babu alamun fara,a a fuskata nace" ina fatan dai baka manta yanda mukayi da kai ba? Yayi murmushi yace " my Queen ki kalleni bakiga na canza ba. Na Dan kalleshi nace na gani amma.... Ya tari numfashina da fadin kinga yanzu na daina shan kome kuma bana zuwa casu wlh yanzu na zama mutumin kirki kuma wnn karon banzo da wasa ko da yaudara ba nazo ne da niyyar aurenki in har kika ban dama ko gobe za,a daura mana aure Na shirya. Shiru kawai na masa yace" Queen na baki dama kiyi tunani wlh ina son ki zan iya yin komai akan ki. Murmushi nayi nace " shikenan Ahmad zan yi shawara kuma zan tuntubeka . Ya saki murmushi yace" thank you my Queen. Anan muka taba hira lallai na yarda Ahmad ya canza. Da yazo tfy kudi ya zube min na rakashi har waje a bakin motarsa muka tsaya hira Wanda har ya salman ya dawo daga aiki.ya fito motarsa cikin kakinsa .ido muka hada dashi nayi saurin kauda kaina. Shikam ji yake kamar ya zo ya shako Ahmad . Sai kawai naga ya nufo inda muke cikin tfr jarumta da isa duk yabi yayi kicin kicin da fuska . Ni dai kauda kaina nayi amma zuciyata na tsinkewa. Gabana ya karaso yana fuskantata kai tsaye yace" muje gida. Cike da mamaki na bude baki zan yi magana Ahmad ya tari numfashina da fadin " no Queen kije kawai sai na kara zuwa. Na kalli ya salman shima ni ya tsare da manyan idanunsa masi kwarjini. Na juya na tafi gida kuma ya bini a baya har side din mama..... Hauly ce 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰 *Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤* ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡30 *******Daki na wuce direct. Ya bini a baya juyowa nayi na kalleshi duk ya bi hade fuska. Zama nayi a bakin gado ban kulashiba. Ya dauki kusan minti biyar a tsaye kamin nan yace" me ya kawo wancan Dan iskan gidan nan? Nace" ba Dan iska bane Ahmad ne kuma yazo ne akan maganar aurenmu. Ya dada tamke fuska yace " waya ce miki auranki zaiyi .rumaisa idan baki daina kula Ahmad ba zakiyi da na Sani don yaudararki zaiyi. Shiru na masa . Yace " kuma ki gargadeshi kar ya kuma takowa kofar gidan nan. Raina ne ya balain baci har ya juya zai fita nace "yaya! Tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba. Nima ban damu ba nace" me yasa ka hanani barin gidan nan? Ya juyo yana kallona kai tsaye yace" saboda makarantarki. Na gyada kai nace " naji wnn ko zaka gaya min dalilin da yasa duk Wanda yace yana sona kk cewa Dan iska ne? Nan yace" saboda 'yan iskane . Murmushi na danyi snn nace " yaya ina girmamaka sosai ka gane don kana da kima a idona.saboda haka don Allah ka rabu dani .ni yanzu na shirya ko ban gama school ba aure zan yi na bar muku gidanku ..... Shigowar mama ne ya katse ni ta kalli ya salman cikin alamun tsoro tace salman lfy ? Murmushi ya kirkiro Wanda bai ma gama mamayar fuskarsa ba yace"lfy lau goggo Amina. Daga nan yayi saurin fita . Mama ta kalleni tace mai ya hadaki dashi yau kuma. Nan na fada mata komai ta danyi murmushi tace " hmm salman knn. Anan ta kawo zancan Ahmad ko da na fada mata maganar aure tace" da wnn yaron mara tarbiyya ? Nace " mama Ahmad ya shiryu kamar yadda na baki labarinshi a baya shaye shaye ne kawai illarsa domin na fada miki Ahmad yana daya daga cikin mutanen da suka taka muhimmiyar rawa a rayuwata a lokacin da na tsinci kaina a cikin wancan mugun yanayi har na tsira da BUDURCINA. Hawayene ya zubo min dana tuna wancan lokacin . Jikin mama a mace tace " gaskia ne wnn kuma amma baki ganin alamun salman kamar har yanzu bai janye maganar aurenku..... Nace " hmm mama ki rabu da yaya har yanzu shi kanshi bai San me yake so ba. Tace " rumaisa salman yana bukatar addua ki sashi a addua ki don Allah domin salman yana sonmu wnn abu da yake faruwa mahaifiyarshi ne sila. Nima jikina yayi sanyi nace hakane mama.insha Allah zan tayasa addua. Tace " yawwa Allah ya miki albarka.kuma ba komai na amince da maganar aurenki da Ahmad din.kinga ko ba komai kyayi aurenki ki huta. Allah dai ya sanya alheri. Murmushi nayi nace " amin mama na gode. Sosai muka sake bude sabon littafi na soyayya nida Ahmad .tsaftatacciyar soyayya ba kamar da ba don Ahmad ya sauya sosai. Magana tayi karfi sosai munyi maganar zai turo magabatansa ma. Salima kam duk ta rikice kamar zatayi hauka in ta ganni a makaranta kamar ta shakoni . Bayan tfyr lathifa da sati sai ga wata ma ta zo daga Cameroon ita ma yar yayan innane sunanta Nabila . To ba laifi tafi lathifa kyau gaskia da kuma hankali sai dai yarinyace na girmeta. Anan da inna ta fara lallaba salman da ya aureta. Shi dai Sam bata kwanta mishi a rai ba. Zuwa yanzu mun gama exams na fara shirye shirye n zuwa Hutu Abuja don munyi dasu faiza acan zamu hadu duk na kosa in tafi saboda gidan ya gundureni. Na fito tsakar gida ina shanya undies dina dana wanke a toilet naji sallama. Na juya da sauri wata mata na Sani mai Dan jiki doguwa taci bleaching kana ganinta kaga kirar manyan mata don tuni turaren ta ya gauraye tsakar gidan idonta sanye da bakin glass daga ganinta zatayi rashin mutunci Gabana ya dinga faduwa na daure nace " sannu da zuwa mu isa Palo. Girgiza min kai tayi tace " Amina na nan? Nace " eh tana nan Tace" kice mata tayi bakuwa Nace" to Har zan shiga Palo sai ga mama nikam a rikice nake nace " yawwa mama ga bakuwa tazo gunki. Mama ta karasa fita cike da fara,a tace" sannu da zuwa mu isa mana. Tabe baki tayi tace " ba sai na shiga ba don ba zama nazo yi ba.Amina ina son ki bani hankalinki anan . Cike da mamaki mama tace"to ina jinki. Tace "yawwa ni sunana DOCTOR SURAYYA AHMAD.matar DOCTOR HAKIM sannan yayar AHMAD UMAR da SALIMA Lokaci guda muka kalli juna da mama. Taci gaba da fadin " nazo nan ne domin in gargadeki da ki jawa 'yarki rumaisa kunne da ta fita daga harkar Ahmad domin ba ajinta bane shi. Sannan ta cire glass din idonta ta kalleni up and down ta ce " ke kuma duk abubuwanda kikeyi muna sane daga lokacin da kike tare da doctor har zuwa yanzu da kk likewa Ahmad.don haka yauce zuwana na farko kuma na karshe ina mai kara gargadinki akan Dan uwana da mijina domin idan kk kuskura na sake jin wani abu to ki kuka da kanki. Ta kalli mama tace " ke kuma kamata yayi ki nemawa ' yarki dangin ubanta ko da kuwa bata hanyar halak kika sameta ba wnn shawarace domin in ba haka ba 'yarki bazata taba samun mutunci da kima a idon mutane ba. Babu wani Dan arziki da zai iya auren ta a garin nan don haka ki maida hankali wurin nemawa ' yarki UBANTA ba wai Ku tsaya kwadayi da buri ba. Ina fatan kun fahimci inda maganata ta dosa? Nikam kallon mama nake . Sai naga ta danyi murmushi tace " shikenan abinda ya kawo ki? A yatsine tace" eh shikenan amma fa idan yarki bata fita harkar Dan uwana ba zaku fuskanci wulakanci da rashin mutunci da tozarci ....... Mama ta girgiza kai tace " ba sai an kai ga haka ba.in Allah ya yarda ma ta rabu da shi .ki kwantar da hanakalinki. Ta sauke ajiyar zuciya tace" kun kyautawa kanku. Ta juya ta fita muka bita da ido har ta bace nikam hawayene ya taru a idona da sauri na wuce daki mamace ta karasa shanya min kaya. Ahmad na kira bai dauka ba har tsinke sannan ya kira ni na dauka da sauri.cikin nishadi yace" my Queen! Sarauniyar mata!ina fatan kina lfy? Nace" Ahmad ba lfy. Da sauri yace" what!!! Nace " yanzu doctor surayya ta bar gidan nan bayan ta gama shimfida mana rashin mutunci.... Nan na gaya mishi komai hankalinsa a tashe ya kashe wayar. Tuni ya tafi asibityn da take aiki ya sauke mata kwandon bala,i hade da yi mata gargadi sosai akan kar ta kuma shiga rayuwarsa don bai shafeta ba. Yazo har gida ya yita baiwa mama hkr mama tace ita dama ranta bai baciba kawai tunda abin ya zama haka dole ne kawai ya rabu dani domin bazata yarda in shiga familinsu ba tunda abin yazo da haka. Juyin duniya yayi da mama amma Sam taki yarda hasalima taki yarda mu hadu jikinsa a mace ya bar gida nikam ina daki ba abinda na Sani sai kuka. Yana komawa gida yaje ya sami his Excellency ya kai karar surayya .bai taba tunanin mahaifinsa zai juya masa baya ba amma sai gashi kiri kiri ya nuna masa yana sane da maganar kuma shima yana goyon bayansu su surayya. Anan Ahmad ya fahimci hada baki surayya tayi da Salima da mahaifiyarsa suka rusa maganar aurenmu ta hanyan bata min suna a cikin familynsu. A ranar Ahmad ya bar kasar gabadaya da don tsabar bacin rai. A bangarena ba rabuwa da Ahmad ne kawai ya dameni ba 99% abinda yafi damuna maganar waye MAHAIFINA?Ina son sanin asalina ko na huta da gori. Ranar ko abinci nakici mama tayi ta shiga tana min magana amma naki in kulata . Haka muka kasance har dare. Hankalinta ya kasa kwanciya. Ta kuma shigowa ta sameni kamar yadda ta barni. Zama tayi a bakin gado tace" haba Rumaisa har yanzu bazaki bar kukan nan ba ? Tunda safe kike aiki daya. Ta danyi shiru sannan ta sa hannu ta dagoni tace " kinga kiyi shiru ba amfanin kukan nan addua zamuyi Allah ya kawo miki wani mijin...... Cikin kuka nace " ni ba shi ya dameni ba. Tace " to me nene rumaisa? Nace" ni so nake nasan waye MAHAIFINA da danginsa. Ta zuba min ido tace " shikenan? Na daga mata kai. Ta danyi shiru sannan tace " to ki ta shi kici abinci kiyi wanka ki kintsa ki sameni a daki na. Ta jawo tray din abinci da ta shigo dashi tace " to sauko kici. Na goge fuskata na sauko na danci amma ba mai yawa ba. Sannan na shiga wanka na fito banga mama ba na shirya cikin kayan baccina na tafi dakinta amma bata nan zama nayi akan gado ina jiranta can ta shigo yayinda take cire hijabinta tace " naje gun yaya ne. Ta bude wardrobe dinta ta dauko wani jaka Wanda yake a kulle sai da tasa keys ta bude sannan tazo dashi ta zauna gefena.tace " rumaisa komai dinki yana cikin jakar nan zan fada miki inda mahaifinki yake kuma zaki tafi goben nan insha Allahu amma sai Na baki labarin rayuwata da yanda aka sameki har zuwa yanzu ban Sani ba ta iya yiwuwa kiji dadin labarin ta iya yiwuwa kuma bakin cikinda kike ciki ya karu amma koma meyene kiyi hkr. Ta share hawaye da ya taru a idonta. Ta mika min wani hoto Na karba tace " wnn shine mahaifinki IBRAHIM. Na zuba ma photon ido kyakkyawan saurayi daga gani bafilatani ne usul don fari Sol ba shakka a gurinsa Na dauki haken nan domin su mama basu da haske sosai.kuma daga gani wayayyene nitsasse. Kawai Na tsinci kaina da sakin murmushi . Mama ma murmushi tayi tace " rumaisa mahaifinki dan babban gida ne dan manyan mutane kuma suna da tarin arziki kuma mutane ne masu kirki da karamci da mutunta Dan Adam. Fara,a sosai ya bayyana a fuskata hakama mama taci gaba da fadin " wani albishir ma da zan miki shine ni da mahaifinki aure mukayi muka haifeki ba zina ba.kuma mahaifinki yafi sonki a cikin dukkan yaransa.amma daga baya da kansa ya koreni a gidan........ Ta karasa maganar cikin kuka . Ido na zuba mata !!! Hauly ce🥰👍🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰 *Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤* ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡31 🌹 *_LABARIN_* *_AMINA_* 🌹 *************Amina Suleyman yakasai Wanda aka fi Sani da ( meenah) Amina ta tasone cikin kulawar yayyunta kasim da Mohd domin iyayensu sun rasu tun tana primary. Asalinsu kanawa ne domin dukkan danginsu anan suke. Amma tun bayan rasuwar mahaifinsu babu Wanda ya kula dasu a dangi kowa yayi watsi da lamuransu. Mohd shi ya dauki dawainiyarsu domin a lokacin yana malamin primary kuma yana taba kasuwanci. Kasim kuwa yana bautar kasa a Kaduna. Yayinda Amina take ss2 kuma boarding school Mohd ya hadu da shatune a lokacin da suka tafi kamaru daurin auren wani abokinsu anan Allah ya hadashi da shatu wacce ta matukar fizgar hankalinsa domin dama kunsan kanawa da son farar mace lol! Bare kuwa shatu kam bayan haske ga kyau ga gashi ga kuma diri. Nan fa ya like mata bai wani sha wahala ya sami amincewarta har maganarsu ta yi karfi gun iyaye.basu cika shekara ba akayi bikin aurensu shatu ta tare a gidan Mohd Na Kaduna domin acan aka masa transfer A lokacin amina tana ss 3 kasim kuma ya kare bautar kasarsa. Koda su Amina sukayi hutu kasim ne ya tafi kano domin ya daukota. Aikuwa tana ganinshi ta kama tsalle da murna tana " kai yaya nayi kewarku wnn term ko visiting Baku zo min ba. Yana murmushi yace " ke dai bari kanwata ni din na zama busy ne. Tana dariya tace'kai yaya ina auntyna ne? Yace " tana gaisheki au albishirinki ? Tace"goro fari Sol yaya na. Yace " yaya yayi aure last 2 weeks yanzu haka in mun koma zakici girkin Amarya.... Cikin tsantsan farin ciki tace wayyo yaya amma naji dadi domin ina son yaya yayi aure dama masha Allah ni har ma na kosa inga mun isa gida.bari inje in sallami friends dina. Ta juya da sauri ya bita da kallo yana dariya . Sun iso Kaduna da yamma Amina tun daga kofar gida take ta rafka sallama hade da fadin " ina aunty amaryar yayan nawa? A lokacin da ta isa tsakar gida sukayi arba da shatu wacce take shara ko a jikinta kamar ba sallama ake ba. Turus amina tayi tana binta da kalli kasim ne yace " madam baki ganmu ba? Ta dago tana murmushi tace " na ganku mana . Sannan ta kalli Amina cikin hausarta da bai gama nuna ba tace " shannunku da juwa ga taburma. Ta wuce ta dauki taburma ta shimfida kasim kam cewa yayi ni dai na zauna a kujera ki bani abinci na inci in wuce shago nasan yaya na jirana ya samu ya dawo gida yaga amaryatsa Murmushi tayi tace " to kasim Ta wuce kitchen amina har lokacin tana tsaye kasim yace " to wai bazaki shigar da kayanki kije ki zauna ba kin wani tsaya kina binta da kallo? Amina tace " yanzu fisabilillah ya Mohd ga ' yanmata a cike a gari wayayyu shine ya tsallaka kamaru har kauye yaje ya dauko wnn bigidajiyar yarinya da ko Hausa bata iyaba? Gaskia ni wlh matar nan bata min ba wlh wnn ai abun kunya ne ma in nunata a matsayin matar yaya na. Taja tsaki ta suri jakarta a lokacin shatu kuma ta fito daga kitchen Anan sukaci karo shatu ta zubawa Amina ido. Yayinda Amina ta watsa mata harara tace " wai kallon me kk min ne ? Mtswww Ta wuce daki. Ran shatu ya baci sosai sai dai kasim ya bata hkr yace haka halin amina yake. Kwata kwata amina bata sakarwa shatu fuska kuma ko girkinta bata ci bare ta tayata aikin gida hasalima in su biyu ne a gidan zakice kurame ne ba mai uhm bare uhm uhm. Shatu kuwa idan akwai abinda yake damunta bai wuce ganin Mohd yana ji da amina kamar tsoka daya a miya kuma baya ko ganin laifinta. Don sau da yawa Amina zatayi laifi amma sai yaki yi mata fada ko kuma ya maida laifin kan shatu Wanda hakan yana matukar kona mata rai.domin zama da Amina yana son ya ja mata matsala da mijinta. A lokacin da amina ta gama secondary ta sami sakamako mai kyau ba ba ta lokaci aka samo mata jamiar Kaduna ta fara zuwa A lokacin kasim kuma Allah ya hadashi da ubangida na gari Wanda ya jawo shi a jiki ya bashi aiki a companynsa.ganin amana da gaskia irin na kasim yasa ya bashi 'yarshi Zuwaira ya aura anan suka hada kudi da Mohd suka sayi gida Dan madaidaici suka koma anan akayi bikin cikin aminci. Zuwaira ma ' yar jamia ce don ta wuce amina ma da shekara daya don haka tare suke zuwa . Sosai Amina take shiri da Zuwaira kominsu daya domin acewarta bata har ka da kauyawa. Shatu kuwa ba karamin damuwa ta shiga ba daga zuwan Zuwaira gidan don sosai take kishinta musamman gashi daga zuwanta har ta sami ciki ita kuwa shiru har kuka ta rikayi gashi bata da kowa a garin Mohd yana kokari wurin rarrashinta don har islamiyya ya sata ya kuma bata jari ta fara sana,oin cikin gida ko zata rage damuwa. Cikin ikon Allah kawai ranar itama ta tsinci kanta a yanayin rashin lfy ranar sai amai take tayi. Amina ce ta shigo gidan da kawayanta ganin shatu na amai yasa ta ja dogon tsaki tace" wai ke yaushe zaki wayene ? Kinzo tsakar gida kina ma mutane amai don tsabar kazanta? Kawar amina mai suna fati ta kalli Amina tace" wacece wnn meenah? Amina ta yatsuna fuska tace " hmm 'yar aikin mune. Shatu ta dago da sauri kuma cike da mamaki . Amina ta watsa mata harara ta kalli kawayenta tace " kuzo mu isa ciki gun auntyna Nan suka wuce gefan Zuwaira wacce take fama da laulayi Sun gaisa anan suka shiga hirar makaranta. Amina ta fita taje gun shatu dake kawance tace" wai kin gama girki ne kikazo kika kwanta?kin bar mutane da yunwa? Shatu kam tana fama da kanta da kyar ta iya fadin " na gama miya tuwo ne kan wuta. Amina ta dan yamutsa fuska tace" to da kike kwance anan kin fadawa yayan bakida lfy ne? Girgiza kai tayi Amina taja tsaki tace " ke dai bansan yaushe zaki waye ba. Ta fita zuwa kitchen ta debo kwanuka ta raba abinci duk ta kai wa kowa nashi. Bayan sun gama cin abinci kawayenta sun tafi ta kalli Zuwaira tace " aunty shatu fa ba lfy dazu mun shigo sai amai take kuma ko girki bata karasa ba ni nayi. Zuwaira tace" subhanallah shiyasa mana yau bata shigo ta biya karatunta ba. Amina ta yi dariya tace " kina kokari da kike koyarda ita wlh wnnn mata bazata taba wayewa ba yaya dai hasken nan da dan kyan nan ya rudeshi yaje ya auro wacce in sun haihu bazata iya tarbiyantar masa da yara ba. Zuwaira tace " don Allah Amina ki rabu da matar nan haka. Amina ta tashi tana dariya tace " bari naje na sameta muje clinic tunda su yaya baza su dawo da wuri ba. Zuwaira tace " gaskia ne kam gara akaita din. Anan amina taje tacewa shatu ta shirya su tafi asibiti. Sun fita a hanya suna jiran mai keke napep. Anan wata sabuwar mota dalleliya tazo gabansu ta tsaya anan mai motar ya fara sauke glass a hankali . Wani matashin mutum ne kyakkyawa fari Sol ga hanci har baki yana sanyeda jumper da wando sky blue ga hularsa mai tsadar gaske da ya kafata ya tafi da yanayin kyaun fuskarsa mai cike da saje. Ya kalli Amina wacce kwata kwata hankalinta baya kansa. Ya saki murmushi yace" meenah Sai lokacin ta kalleshi cikin mamaki mara misaltuwa tace" laa Ib yaushe a garin namu? Fuskarsa cike da fara,a yace " tun last week.ai tunda Ku kun share mu dole muzo. Tayi dariya tace " kaji Ib wai mun shareku. Yace " eh mana meenah ko waya ba,a samunku . Tace" o sorry Ib wancan layin ya dade bana amfani da shi. Murmushi yayi ya kalli shatu yace " aunty ina wuni? Can ciki ta amsa da lfy ta kauda kanta. Amina tace " bata jin dadine 'yar uwar matar yayana ne ta zo daga kauye . Yace" eyya sorry Allah ya bata lfy.yanzu asibity zakuje ne? Amina tace " eh wlh . Yace " to muje mana na ajiyeku ai ba damuwa. Amina tace " no Ib ka tafi harkokinka kawai. Yace" ai meenah ke mai tsadace bai dace a barki anan kan hanya ba. Dariya tayi sannan tace " shikenan mun gode. Ta kalli shatu ta danyi kasa da murya tace " wlh kika kuskura kika masa amai a mota hmmm kinsan saura .kuma ba wai in kin shiga ki dinga kalle kalle kina zare ido kina kauyanci ba nitsuwa zakiyi don ma dai na Riga na fada mishi ke din daga kauye kikazo amma dai ki kula.wnn mutum da kike gani wayayye ne dan boko bai son kauyanci. Shatu ta hade rai tace " to aini bance miki ina bukatar shiga motar saurayinki ba.da kike cewa daga kauye nazo waye waye a haka yayanki ya gani kuma yakeso. Tsaki amina taja tace " asircesshi kukayi. Ta bude kofar motar na baya tace " zo ki shiga. Shatu ta shiga ba dan ranta naso ba amina ta rufe sannan ta bude gaba ta shiga tana murmushi ta kalli Ib bayan ta rufe tace " Ib kuna shagalinku. Yayinda suka fara tfy yace Amina ke dai banda zolaya kinga nki yadda kike shining kamar wata Zara a cikin taurari wai meye sirrin ne? Murmushi amina tayi tace kaima ka zolayeni ni.da nake koduwa a school? Haka suka manta da wata shatu suka dinga hira wani hadadden private hospital ya kaisu ya hadasu da doctor nan akayiwa shatu gwaje gwaje aikuwa cikine har na wata biyu da satittika. Anan amina ta hau murna itama kanta shatun farin ciki ya gama cikata bayan sun gama komai Ib ya ne ya dawo da su yayinda ya cika su da kudi.yacewa amina zaizo. Suna shiga gida amina ta kalli shatu tace " to saura inji kin kuskura kin gayawa yaya abinda ya faru. Zuwaira ta kalli shatu tana murmushi tace " shatu me yene kk boye mana ke da kanwar taki? Shatu tace " hmmm saurayi ta samu ya rinka dawainiya damu. Zuwaira tace " ayya Amina tace " ke shareta Ib ne fa. Zuwaira tace " kai ? Yaushe yazo? Tace " hmm wai tun last week akwai aikinda aka turoshine anan KD Tace " aunty Zuwaira albishirinki? Zuwaira tace goro fari Sol! Tace " shatu ma ciki ne kuma har wata biyu da satibiyu tare ma zaku haihu don watannin cikinku daya. Zuwaira ta kalli shatu cike da tsantsan farinciki tace " wayyo yar uwa na tayaki murna wlh naji dadi sosai. Shatu kam ba ta yi magana ba ta wuce daki ta kwanta. Da daddare su kasim suka dawo bayan sunci abinci sun huta an fara taba hira amina ta kalli Mohd tana murmushi tace " yawwa yaya akwai albishir da zan maka. Mohd yace " to kanwata ina jin ki. Ta kalli shatu tana murmushi wacce ita kam tuni ta mike ta yi daki saboda kunya irin namu na Fulani. Tace " yaya shatu na dauke da ciki har na wata biyu da sati biyu dazu na kaita asibity. Ta mika shi takardar scarning. Sosai Mohd ya nuna murnarsa a fili ya dinga Godiya ga Allah nan da nan ya mike ya bita daki amina da kasim suna dariya. Tundaga ranar Amina ta dauke nauyin hidima dasu domin babu abinda take so a rayuwa da ya wuce taga sun tara zuria suma tunda dangi sun guje su. Shatu kam duk tattalinta da amina takeyi gani take kamar ta hada bakine da Zuwaira don a ganinta Sam basa sonta. Amina da Ib sun kulla soyayya mai karfi a tsakaninsu har ta gabatar da shi gun yayyunta amma abin mamaki sai ta lura Sam basu yi na,am dashi ba .domin a ganinsu.bai kamata amina ta yi nitsa dasu ba kamata yayi ta yi aure kusa dasu domin Susan duk abinda take ciki. IBRAHIM AHMAD GALADIMA wato Ib cikakken dan Adamawa ne a garin yola dan babban family ne domin in kaje yola kace galadimas family to ba Wanda bai saniba. Ib ya hadu da Amina ne a sakamakon wani aiki da ya kawo shi KD bai bata lokaci gurin nuna mata yana sonta ba amma ta dinga ja mishi aji har yaxo ya koma . Dawowarsa na wnn karon ne yasamu ya shawo kanta amma ya lura kamar yayyunta basu karbeshi ba hankalinsa ya tashi kwarai don a ganinsa zai iya yin komai akan yaga sai ya aureta. Akwai dan yayan Zuwaira Farouq da yake matukar son Amina amma ita bata so yayyunta kuma sunfi sonshi ba don komi ba sai don danuwan Zuwaira ne sannan dan Kaduna kuma mahaifinsu mutumin kirki ne ya rike kasim kamar dan cikinsa don haka suna ganin auren amina da Farouq shi zai kara musu dankon zumunci. Amma Sam amina taki yarda ita dai IB take so. Zuwaira kam har ga Allah bata yi fushi da Amina ba don tasan halin soyayya.har kokari take ta baiwa yaysnta hkr da ya hkr ya nemi wata kawai amma kasim ya hanata yace ta bari zasu shawo kan Amina. Shatu kam taso ace amina ta fuskanci tsanani gun yayyunta don bata son su lallabata don haka ta dinga ingiza Mohd tana kara cusa musu tsanar Ibrahim tana nunan musu ai shi yake zuga Amina yana hure mata kunne ta bijire musu. Koda amina ta fahimci shatu na shiga harkokinta anan ta zage ta rufe ido ta zuba mata rashin mutunci ta zage ta tass tun shatu na amsawa har wasa gaske har amina ta fi karfinta ta koma sai kuka takeyi ranar dai sunyi ba dadi . Saida Zuwaira tayi da gaske sannan amina ta bar maganar. Aikuwa Mohd suna dawowa ya tarar shatu taci kuka har ta kode anan ya shiga tambayarta ko lfy . Cikin kuka tace " wlh ni abubuwanda Amina ke min a gidan nan ya isheni me nayi wa amina a rayuwa ta tsaneni?wai yau amina har da bude baki ta zagi iyayena.amina har cewa tayi duk matan garinmu karuwai ne nima asiri na maka ka aureni ba wai sona kake ba. Murmushi ya danyi yace " haba shatu yaushe zaki biyewa maganar amina har ta dameki aini nasan ko ke wacece nasan kuma iyayenki mutanen kirki ne sannan kuma ni har ga Allah saboda soyayyar da nike miki na aureki ba wai asiri kika min ba.don haka kiyi shiru abinki kuma zanjawa amina kunne sosai. Hankslinta ya dan kwanta amma sai ta ga ba wani kwakkwaran hukunci da Mohd ya dauka akan amina.don amina indai ta na gidan shatu bata da zaman lfy ko ruwa bata isa ta sha ba nan ma Zuwaira na hanata. Cikinsu na wata bakwai 'yan uwan shatu suka zo sukace zasu tafi da ita taje ta haihu a garinsu kuma har sai ta gama wanka ta dawo Mohd baiso ba amma dole ya hkr suka tafi da ita gida . Cikin ikon Allah a kwana a tashi ba wuya gun Allah cikinsu na cika wata tara suka haihu yara maza.shatu ta fara haihuwa da kwana biyu itama Zuwaira ta sauke. Murna gun amina da yayyunta baa magana. Ranar suna aka sanyawa yara suna suleyman. Mohd kam yana can kamaru sai da aka kare suna ya dawo. Shatu na gama wanka mohd ya kira yayyunta yace zai zo ya dauketa.da yake itsma iyayensu sun rasu. Anan shatu ta shiga shirye shiryen komawa ta kama shanunta har uku ta siyar suka tafi gurin wani malami ita da matar yayanta . Anan shatu ta fadawa malamin bukatarta shine a shiga tsakanin Amina da yayyunta su tsaneta har zaman gidan ya gagareta na har abada domin idan ba hakan tayi ba Amina bazata barta tasha ruwa ba.gashi ita bata kowa a can in ta koma bare ta samu tayi shige shigen don haka kudi sosai ta zubewa malami a mata aikin gaske kuma ta na so ya kasance duk abinda ta fada Mohd da kasim su bita kamar rakumi da akala. Shatu bata dawo Nigeria ba saida ta gama shirinta tsaf! Hauly ce 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰 *Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤* ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡32 🌹 *AMINA* 🌹 ************Ranar da shatu ta dawo Amina na makwabta Zuwaira ta kirata a waya tace" ina kk shiga meenah ga mutumiyarki sun iso. Amina tace " gani nan yanzun nan ai dole in dawo ko dan dana. Amina na shiga gida dakin shatu ta wuce ta sami aunty Zuwaira a gurin Cike da fara,a tace " Ashe kun iso shatu. Shatu tace" eh mun iso .ya kuke ya kwana da yawa? Amina tace lfy tunda kika tafi naji gidan ba dadi don bani da abokiyar fada . Shatu tace " ai gashi na dawo sai mu Dora. Amina ta karasa shiga tana dariya ta dauki suleyman dake bacci tace " kai kai shatu yaron nan fari Sol wanke hannu ka taba tubakallah masha Allah ya girma wlh nauyinsu daya da SALIM.ya kuke kiransa don nasan bazaki kira shi da sunanshi ba? Shatu tace " BAR'KINDO.... Amina ta zaro ido tace "me? Wnn wane irin sunane haka ? Kinga karki batawa Babana suna da irin wannan sunayen kauye meye haka ? Aunty Zuwaira kinaji? Zuwaira tace " eh .amma gaskia shatu karki batawa yaron nan suna. Shatu tace " don dai baku jin fulatanci ne amma barkindo ai sunane mai daraja dan albarka knn. Amina ta hade rai tace " aa mu anan baza mu kirashi wani barkindo ko me ba.sunanshi SALMAN kuma tuni su yaya ma haka suke ce masa.wnn kuma SALIM. Shatu tace " to ai shikenan. Ni dai nayi mai wuyan. Tsaki Amina tayi ta kalli yarinyar da shatu ta zo da ita daga kauye tace " shatu wnn kanwarkice ko? Shatu tace " aa 'yar yayana ne takwarata ce sunanta Aisha amma muna ce mata A'i Amina ta tabe baki tana kallon yarinyar kamar wata aljana tsabar kyau da haske. Tace " amma batajin Hausa ko? Zuwaira tayi dariya tace " sai dai muyi kurma kurma da ita . Amina tace to meyasa shatu kika rabota da gidansu makaranta fa? Shatu tace " bani ita akayi zata tayani aikace aikace kuma zamu sata makaranta anan. Amina tace tab zaki Dora mana wani nauyi dai waya gaya miki a zamanin yanzun nan ana rike yaran mutane? Zuwaira tace " kai Amina ai ba wani dawainiya Shatu dai shiru tayi yayinda amina ta fita rike da salman. Ya kasance indai Amina na gida ba Wanda zai taba salman da salim shan nono kadai take kaisu. Yau ma bayan sunyi wanka ta shirya su tsaf tace " wai ni shatu ina son tambayarki wani abu tuntuni me yasa yaron salman kike sa masa irin wadandan riguna (gobe suna)? Sai kace wani dan kauye gashi kinbi duk jikin yaro kin dafdaure da igiya ga uban laya a wuya na meye ne? Shatu tace " wnn layan maganin bakine da mayu.igyar nan kuma maganin ciwon yarane? Amina taja tsaki tace dan kauye dai bazai taba wayewa ba .to Ku bani kayanshi in sa mishi anjima IB zai karaso yana son yagansu. Shatu tace A'i taje ta dauko . Ai ta kawo kaya ta mikawa Amina wani irin kallo amina ta mata hade da fadin " dan Allah can wnn gobe sunan za,a sa masa? Ta mike a fusace ta wuce dakin shatu ta fara bubbude akwatina tana fadin " ni dai nassn yaya ya siyawa salman kaya masu kyau kin boyene saboda tsabar mugunta irin naki kin maida yaro sai kace dan kauye. Ta Ciro kaya mai kyau tasa mishi yayinda ta yanke igiyoyinda aka daura masa da layan duka ta ajiyewa shatu a kan gado tana fadin " kina zuwa islamyya amma ba kya fahimtar komi yaron nan addua zaki dinga tofa masa ba wai ki bi jikinshi da laya ba haka na lura in yana bacci sai ki dauki wuka ki ajiye gefensa maimakon ki kunna Qira,a a wayarki ki ajiye gefensa ba kya ganin yanda aunty Zuwaira keyi da salim ne me ya sameshi to? Shatu dai bin Amina take da kallo cike da bacin rai akan layan nan da ta tsinka a wuyan salman. Ib yazo har palon kasim ta kaishi ranar ta kai mishi yaran ya karbesu cike da fara,a yace " kai masha Allah kamar twins lallai meena kinaji da yaran nan Ta yi murmushi tace sosai ma Ib .idan munyi aure zan yi kewarsu sosai . Yace " ai kar ki damu zamuna zuwa snn in baki manta ba nima ina da yara na har biyu maza. Tace " hakane in munyi aure zan dauki samir in barwa aunty Jamila awwal. Dariya yayi yace " inde Jamila ce dukkansu ma sai ta bar miki. Haka suka ci gaba da hira suna dariya.har kasim ya dawo kallo daya yayi musu ya hade rai . Cike da fara,a Ibrahim ya gausheshi.amma shi da kyar ya amsa. Don haka Ibrahim yayima amina sallama yayinda ya cika su salim da tsarabar kaya masu tsadan gaske. Amma amina ta lura Sam Ibrahim bai samu karbuwa ba har yanzu domin yayyunta sai kara cusa mata Farouq suke ita kuma ta dage bata son Farouq . Wasa gaske Amina ta fara fuskantar matsaloli tsakaninta da yayyunta abu kadan su dinga mata fada ya kasance tsakaninta da su babu wata maganar arziki bare sakin fuska kamar da ta kai ta kawo kasim kam ma ko magana baya mata kuma in ta mishi baya amsawa.duk wani abu in ta rokesu basa bata. Amina ta shiga damuwa sosai gurin Zuwaira kawai take samun sassauci. Shatu kam yanzu komai na gidan itace kan gaba don ita take directing na Mohd da kasim son ranta duk abunda tace shi sukeyi. Watarana Amina ta dawo daga makaranta tana shiga gidan shatu ta watsa mata ruwan wanki Ranta yayi masifan baci tace " shatu kika watsa min ruwan datti a jiki? Shatu ta harareta tace " sai me? Amina tace " OK hakama zakice? Amina ta wuce a fusace ta dauko ruwa cikin boket tayi ma shatu wanka daga sama har kasa. Tace " sai inga uban da ya daure miki gindi. Shatu kam abun nema ya samu.su Mohd Na dawowa ta taryesu da kuka tana fada masu abinda Amina ta mata. Kasim ya kalli Mohd yace " kagani koh yaya ? Amina bata son taga ana zaune lfy.nace maka yaya muyiwa amina aure da Farouq ko bata so mu huta da masifarta. Mohd ya gyada kai yace " hakan shine ya kamata tunda dama auren fari iyaye ke zabawa yarinya miji. Amma tsorona daya amina bata da kunya kar taje ta bamu kunya gun mutanen nan ksga mahaifin Zuwaira mutumin kirkine hakama Zuwaira da Farouq. Kasim yace "ai yaya ka barni da ita kawai dole ne mu dau mataki akanta don nan gaba kadan sai tafi karfinmu. Amina dai bata San me ake ciki ba kawai ranar taga anata shiga da akwatina.daki ta koma tayi zamanta sai da aka gama komai ta fito anan shatu tace " yswwa kije yayyunk na son ganinki. Amina ta wuce Palo batace komai ba . Anan suke sanarda ita maganar aurenta da Farouq nan da sati daya. Tashin hankali amina ta saka kuka yana fadin kawai don sunga bata da gata shine zasu mata auren dole ai da iyayensu na nan bazasu mata haka ba. Ransu ya matukar baci da magsnunta sosai. Ita kuwa tuni ta fita daki ta nufa ranar ko bacci batayi ba ta kulla wnn ta keance har dare ya raba biyu. Gari bai gama wayewa ba ta fita kamar mai tfy mkranta kawai ta wuce tasha motar Adamawa ta biya kudi ta shiga. Mota na cika su ka daga sai yola. Tana ganin wlcm to yola tace a sauketa dama ta gaya wa Ibrahim zata zo amma Sam ta lura bai yarda ba. Ta na sauka ta kirashi tace gata nan a wlcm to yola. Sam bai yarda ba saida tayita ransewa snn ya amince aikuwa yana zuwa da ya ganta da katuwar jaka ya zuba mata ido hankalinsa tashe!!!!! Haulyce🥰👍🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰 *Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤* ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡33 ********"Amina lfy na ganki haka? Hawayene ya fara zubo mata tace"Ib ba lfy gudowa nayi daga gidanmu saboda yayyuna suna shirin yi mun auren dole ni kuma bana so. Ib ya dafe kai hade da fadin " ya Salam! Amina kam kuka ta fara yi sosai tace" don Allah Ib ka taimaki rayuwata banda kowa a yanzu sai Allah sai kuma kai masoyina. Ib kam hankalinsa ya tashi matuka yace " kinga meenah zo mu shiga mota muyi magana kar a ganmu kinga nan kan hanyane. Suka shiga mota Ib ya cire hularsa ya goge gumi sannan ya juyo yana fuskantar Amina sosai yace" meenah akwai matsala ni dinnan Dan babban family ne domin danginmu suna da yawa sosai so kankanin abu zai iya jawo min matsala ni yanzu idan nace zan taimakeki ina zan kaiki? Amina ta zuba mishi ido cike da mamaki tace " Ib anya kana sona? Yace " haba meenah ina sonki mana amma ina jiye mana tsoron abinda zai biyo baya ne.don haka ni dai shawarata kizo muje na kai ki gidan abokina in Allah ya kaimu gobe sai in kaiki tasha ki koma gida zanzo KD din muyi setling na komai a hankali kingane. Amina tace " haba Ib ina maka maganar saura sati daya a daura min aure da Farouq kana in koma KD in jiraka? Shiru Ib yayi duk kansa ya dau zafi ya rasa me zaiyi. Amina ta ci gaba da kuka tace " shikenan Ib na gane ba sona kake ba dama yaudarace .domin da,ace son gaskia kake min da zaka iya komai akaina kamar yadda na bar gida na zabi in zauna da kai akan 'yan,uwana.Ib kasa a ranka mun rabu rabuwa ta har abada.don in nakoma Kaduna ba abinda zai hana ayi aurena da Farouq. Ta na gama fadin haka ta fita daga motar tana kuka tace " bude ka ban jakata zan juya daga nan. Tausayinta ne ya rufe shi a gefe guda kuma yana tunanin mafita ganin yadda taketa kuka yasa ba shiri ya fita yace" kinga ki daina kuka zo mu shiga mota nasan me zanyi. Bayan sun shiga mota yace " Amina ina sonki so na Allah da annabi don haka bazan cutar dake ba don haka zan kaiki gidanmu kuma zan yi magana da mahaifiyata sai dai ina bukatar ki nitsu kiji me zan fada miki domin fa dagani har ke zamu iya shiga damuwa dan haka dole ne mu fara neman mafita kamin mu tinkari Ummahta. Anan ya dinga mata bayani sosai ta gamsu.da haka suka tafi yola family house na galadima Wanda yake kusa da gidan maimartaba lamidon Adamawa . Babban gidane sashi sashi.sai dai Alhaji Ahmad galadima wato mahaifin Ib ya jima da rasuwa.so gidan yanuwansa maza da mata cike da iyalansu.sai kuma matansa biyu Hajia Zubaida da Hajia rumaisa 'ya'yansa kuwa ashirin da uku hajiya Zubaida nada goma sha uku don itace uwargida.Hajia rumaisa kuma goma ciki harda IB domin shine danta na tara sai 'yar auta Ummi wacce bata wuce sa ar Amina ba Sai dai wani ikon Allah familyn galadima basu cika samun haihuwa yara mata ba domin gaba daya family in zaka duba babu Wanda ya sami yara mata sai kalilan cikinsu domin ko su Ib yara mata biyu ne kawai karima 'yar hajiya Zubaida sai kuma Ummi kanwar Ib . Don haka familyn suna matukar balain son 'ya'ya mata.don haka duk sanda aka yi haihuwa a familyn in akaci sa,a an sami 'ya mace to akwai kyaututtuka na mussaman daga kan kaya gwalagwalai ,motar ,kujeran hajj,fili da dai sauransu. Amina tunda take bata taba shiga babban gida irin wnn ba domin In kai bakone zaka bata a gidan Sashinsu hajiya rumaisa suka shiga. Suna palon da hajiya Zubaida kamar kullum suna hirarsu kamar ba kushiyoyi. Cike da girmamawa Ib ya gaishesu cikin harshen fulatanci. Anan amina ma ta gaishesu da Hausa ga mamakinta da hausan suka amsa mata don batayi tunanin sunaji ba. Suka danyi shiru Ib ya daure ya kalli mahaifiyarsa yace " Ummah wnn itace Amina da nake baki labarinta . Haj rumaisa tace " o ayya yanzu daga Kaduna tazo gunka ko dai tanada wasu dangi a garin nan? Jikin ib a sanyaye yace" aa ummah wani babban al,amari ne ke tafe damu. Anan ya gyara zama cikin ladabi ya shiga yi musu bayani bai boye musu komai ba. Ran umma ya matukar baci sosai bata San ta juya harshe da Hausa ta kalli amina tace" yanzu wnn har ya kai dalili da za ki bar gida saboda shi? 'Yan uwanki sun zaba miki miji Wanda suke ganin zai rikeki amma kikasa kafa kika bar gidanku don tsabar rashin tarbiyya ko? Shi lbrahim din da kika zo gunsa kina da tabbacin idan ya aureki zai soki....... Haj Zubaida ta tari numfashinta da fadin " Haj rumaisa hkr zakiyi mu bi abin a sannu kinsan fa halin dan yau. Ib kam sai hkr yake ta baiwa ummah yayinda Amina kuma take kuka don sai yanzu ta gane tayi babbar wauta. Umma tace " kunga Ku tashi Ku bar gidan nan tun kafin kowa yasan wnn maganar. Ta kalli Ibrahim tace " kaga lamido ka rabu da wnn yarinyar ka nemo wata .ke kuma ki koma garinku kije kiyi hkr ki auri Wanda yayyunki suka zaban miki. Ib yace" don Allah ummah kiyi hkr ina son Amina wlh ummah amina tana hankali .yayyunta so suke su zalunceta sunga iyayensu basa raye. A fusace Umma ta Mike ta tafi ciki Amina kam jikinta yayi sanyi yanzu tunsninta ina zata je ? Dole ta koma gida ta hkr da zabinda aka mata. Haj Zubaida kam ta lura da gaske Ib da Amina son juna suke don haka ta yi niyyar shawo kan Haj rumaisa sai dai bata San ya zatayi da bappanan su ib da yayyunsa ba. Ta kalli Ibrahim tace " kaga lamido kwantar da hankalinka in Allah ya yarda Amina matarka ce kaji yanzu abinda za,ayi kai ta dakinsu karima ina zuwa. Ib cike da farin ciki yace " nagode mama Allah ya kara miki tsawon rai. Daga nan yayiwa Amina jagora zuwa dakin su karima da Ummi.duk suna nan sun dawo daga mkrnt. Ya kallesu yace " ga ban bakuwa Na kawo muku sunsnta Amina don Allah karima ta samu tayi wanka taci abinci. Cike da fara,a suka karbi amina.har ta danji sanyi don dama tana son irin wnn gida mutane cike gwanin sha,awa. Ib dai daga nan ya wuce masallaci don ankira sallar magrub. Haj Zubaida kuwa da kyar ta shawo kan Haj rumaisa ta amince da zamsn amina a gidan amma dole ne a kira family meeting domin aji ta bskin kowa . Amina da Ib ranar kamar hadin baki basuyi bacci ba kwana sukayi suna nafila hadi da rokon Allah ya dorasu kan iyayen nasu. Wnn shine karo na farko a rayuwar Amina da ta hana kanta bacci ta mikawa Allah kukanta.don ta sa a ranta daga yau zata zama mai kula da ibadarta domin duk matsalolin da ta shiga sakacin ta da ibada ya jawo. Da safe kuwa duk family sun hadu a babbar palonsu na meeting. Ciki harda ibarahim. Da yawa daga cikinsu sunki amincewa yayinda wasu kuma basu damu ba .tunda shi zai zauna da ita. Haj Zubaida ganin yanda lamarin yaki daidaituwa yasa ta tafi gidan maimartaba lamidon Adamawa domin aminin marigayi Alhaji Ahmad galadimane amuntar tasu har ta koma kamar 'yanuwan juna don haka ne ma Ibrahim yaci sunan maimartaba shiyasa ake kiransa lamido maimartaba yana son Ibrahim sosai domin shi yake debe masa kewar marigayi Amininsa. Aikuwa koda Haj Zubaida taje da wnn batu kuma ta hada da fadin ranka ya dade yaran nan suna son juna idan an rabasu bamusan me zasuje suyi ba kasan halin Dan yau don haka ni anawa tunanin ranka ya dade a barsu suyi auren idan yaso in an natsu sai aje a baiwa yayyunta hkr a masu bayani kuma akan illar auren dole.don yana jefa rayuwar 'ya'ya mata cikin mummunar yanayi .Allah ya ja zamaninka. Maimartaba ya gamsu matuka da maganar Haj Zubaida. Don haka Allah ya amshi adduar Amina da Ib sunci nasara a karshe don haka saura daurin aure. Haj rumaisa duk da hakan bata saki ranta ba don haka ta hana ib ganawa da amina tace ya bari sai sunyi auren tukunnna. Don haka ib ko yazo gidan bata bari ya hadu da Amina. Amina ma bata damu ba ibadarta kawai tasa a gaba. Amina ta shaku da Ummi da karima sosai don sunji dadin zama da ita haka itama taji dadin zama da su. Abinka da family house tuni akaje aka gayawa Jamila matar ib labarin Amina. Ta kasa hkr sai da tazo taga Amina aikuwa hankalinta ya matukar tashi domin amina ta fita da komai . To anan fa aka bazama gidan bokaye 'yan tsubbu amma abu ya gagara. Zuwa yanzu Amina ta samu karbuwa a zuciyar kowa domin kowa ya fahimci halayenta nagari ne.kasancewar ta bahaushiya ta iya zama da mutane sosai cikin hikima da dabara take bin kowa a yanda halinsa yake. Haj rumaisa sai godewa Allah take da ib ya sami mace kamar Amina domin gabadaya hkr yake da Jamila saboda bakin hali ga rashin kunya ga kuma girman kan tsiya. Amina tuni ta watsar da batun yayyunta da mkrntarta . Bayan dawowar mai martaba daga umrah aka daura auren Amina da Ibrahim. Jamila dai ta zama kamar mahaukaciya ganin bata samu nasara ba yasa ta koma tunanin wata hanyar don haka ba tare da tunanin komai ba ta tafi gidan galadima kai tsaye ta nufi sashin su Ummi ta sami Amina na karatun novel. Ko kan ta ankare tuni Jamila ta yi kan ta da duka tana shegiya karuwa nice ajalinki.. Anan Amina ta fara kokarin kwatar kanta don bazata iya fada da Jamila. Zuwan karima ne ya ceci amina nan da nan karima ta sanar da su hajiya. Amina kam taga ta kanta ranar . Jamila ta rufe ido ta zubawa su ummah rashin mutunci son ranta. Aikuwa ib bai barta ba sai da taci na jaki sannan ya hankadata gidansu da saki daya. Ita kuma ta zube masa yaransa biyun samir kam ma ko yayeshi ba,aiba haka ya tattara su ya kawo wa ummah.anan Amina kuma ta zage ta dauki dukkan dawainiyarsu ba tare da gajiyawa ba. Anan Ib ya fara rokon ummah da don Allah ta bari Amina ta tare. Ummah tace " karka damu Amina matarkace ai.so muke in mun dawo hajj lokacin bikin Ummi da karima sai a hada da naku kaga itama budurwace ya kamata muyi mata gata itama ko kuwa de? Cikin gamsuwa ib yace " hakane ummah na gode da kika fahimci Amina. Umma tana murmushi tace " amina tana da hankali sosai lamido na yaba da halayanta kaga kaima yanzu hankalinka zai kwanta. Haka sukaci gaba da tattaunawa daga karshe daya ta shi dakin Amina ya tafi don tunda ta zama surukuwar gidan aka ware mata daki ita kadai. Su Ummi ma suna tare da ita ga kuma yaran ib.in ka shigo dakin zakace amina ta dade a gidan don hira suke sosai suna dariya har da tafawa . Ib ya danyi gyaran murya yace " me ake tattaunawa ne haka 'yan mata. Amina ta juyo da sauri ta kalleshi shi ma ita yake kallo har ya shagala murmushi ta sakar mishi .shima ya maida mata. Ummi ta kalli karima suka sa dariya hade da fadin soyayya. Ib ya dauki awwal daya masa oyoyo ya karaso yana cewa " magulmata. Ummi tace " yaya muna hiran yadda bikinmu zata kasance ne. Karima tace bama wnn ba ya Ib duk dinmu anan zamuyi service . Ib yace " hmm ba matsala sai a canza muku ai.ke Ummi a Abuja ke kuma karima a Maiduguri amma sai kunyi auren tukun. Ummi tace " ya ib meenah ma ya kamata a zauna a tattauna maganar makarantarta. Ib ya ce " to ai taki maganar ne tuntuni amma tunda kune kawayanta sai Ku bata shawara Karima ta mike tace " kamin nan bari mu baku guri. Ummi ma tabi bayan karima ta na"asha soyayya lfy. Suka fita duk da yaran. Anan ib ya zauna kusa da Amina ya kalleta yana murmushi yace " meenah kinga yadda Allah yake al,amarinsa ko? Tana murmushi tace " Alhamdulillah. Yace " yanzu kinga sauran miki ki tare.meenah nayi muku dukkan tanadi na jin dadi in kinzo gidana. Amina ta lumshe ido cikin jin dadin maganarsa lokaci guda kuma yayyunta suka fado mata a rai. Ganin sauyi a fuskarta yasa ib fadin lfy meenah? Hawayene ya zubo mata tace" ib ina tunanin su yaya ne suna can suna ta nemana. Ta fashe da kuka tana wayyo Allah Ibrahim wlh ban kyauta musu ba. Rumgumeta yayi ya shiga bata hkr yana cewa idan ta tare in Allah ya yarda zai kaita. Da haka ya shawo kanta nan fa labari yasha banban ib tuni ya canza salo ya fara kissing dinta ko ina. Amina duk ta rikice ta lumshe ido tana karban sakonsa Har sun kwanta kan gado sun dau tsawon lokaci a haka jin da Amina ta yi ib yana kokarin wuce gona da iri yasa ta yi maza ta ta shi tana kallonshi tace " don Allah ka bari . Idonsa a lumshe yana maida numfashi yace " kefa matatace kuma kinga nama yi kokarin..... Ta katseshi da fadin " don Allah ka ta shi kar su ummah suji ka dade kunya nakeji. Yayi murmushi har lokacin jikinsa a mace yace " me kuma ya hada bahaushe da kunya? Amina ta mike tace " au hakama zakace? Ya ta shi ya ya kamota yana kokarin cire mata zip din rigarta suka shiga kokuwa tana Dan Allah ka bari kofan nan a bude kowa na iya shiga fa ya ganmu. Shikam cewa yake " meenah bazan iya barinki ba sai na danji relief haba dear ba kya tausayina ne? Wlh ina cikin wani yanayi kuma kunga su ummah sun dage sai sun mana biki ni bazan iya jira ba kawai ki dinga zama cikin shiri zan zo in karbi hakkina. Suna cikin haka Ummi ta shigo da sauri ib ya saki amina ya kalli Ummi fuska daure yace " ke ba kya sallama ? Da sauri Ummi ta juya tana dariya tace " wlh sai naje na gayawa ummah abinda kukeyi ba ta hanaku ba? Tace ka bari sai ta tare. Da gudu ta fita shima ya bita da sauri. Aikuwa ummah korinsa ta yi tace " karya kuskura ya kara yiwa amina komai sai ta tare. Ib kam ya tafi yana ta jin haushi shida matarsa a hanasu soyewa.bari su tafi hajj yasan me zaiyi. Hauly ce🥰👍🏻 [ 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰 *Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤* ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡34 ********A satin da su ummah suka tafi hajj Ib ya fara tunanin yanda zai sami ya shawo kan Amina ta amince dashi. Kasancewar a sashin su aminan kawai suka rage sai 'yan aiki.don haka Ib ya tafi kai tsaye sai dai yayi rashin sa,a su Ummi suna gida ya samesu a Palo suna kallon film. Bayan sun gaisa ya kalli Amina yace " meenah a kawo min abinci yunwa nikeji ko baku dafa ba? Ta yi murmushi tace " mun dafa sai dai ya kare don bamuyi lissafi da kai ba. Ummi ta ce yaya ai munga a gidan yaya nasir kake cin abinci shiyasa. Yace " to yau dai an an zanci kuma girkin meenahta. Amina ta saki murmushi tace" an gama lamidon Adamawa(Allah rene). Sukayi dariya hade lokaci guda karima tace"yaya yanzu Amina tana jin fulatanci kuma har tana mayarwa kadan kadan Yana murmushi yace" gaskia ta yi kokari. Amina ta tashi hade da fadin " to lamido me za a dafa maka. Ya kalli agogon hannunta sannan ya tashi ya matso kusa da ita ya na kallonta yace " akwai gasashiyar kaza? Tace "aa Ummi ta cinye sai dai a gasa ma wata a oven. Yace " no bana son ki wahala kawai ki hada min fruit salad .ni yanzu masallaci zan tafi magrib ta yi.kinje kiyi sallah tukun ko kina off ne? Ta sunkuyar da kai hade da fadin aa . Murmushi yayi na jin dadi a ransa yace " zaki fada ne yarinya. A zahiri kuwa ce mata yayi sai na dawo zan mana adduar samun baby kina so ko? Sunkuyar da kai tayi cikin jin kunya darya yayi ya fice. Shiru shiru bai shigo ba har amina ta yi tunanin ko ya wuce gidansa ne. Tana shirin kiransa sai gashi ya shigo da sallama hannunsa rike da ledoji Suka amsa Ummi ce ta tashi ta karbeshi yace" nagode ina su awwal? Ummi ta ce " sunyi bacci har na kaisu daki bayan meenah ta musu wanka. Yace OK ya nuna mata ledojin yace " wnn nakune keda karima wnn kuma Ku ajiye ma yaran.wnn kuma ki bani namune Karima tace " kai kai kai yaya ya naku yafi girma ne? Ummi ta yi dariya tace " eh wlh yaya wnn ai selfishness ne. Karima ta yi dariya tace " kuma yaya bai kamata babba da kai ka dinga sayarda kifi ba(selfish) Yace" to Baku ga ni babba bane lamido faaa. Ummi tace " eh to kana da gaskia kaima. Amina kam tana zaune sai murmushi takeyi. Ib ganin su karima zasu tsaidashi da surutu ya kalli Amina yace " meenah kawo min fruit salad dina da plet da cup da cokali Yana fadin haka ya wuce ciki zuwa dakinta ba jimawa itama ta sameshi yace " yawwa Allah sa bakici komai ba don yau da kaina zan baki abinci wnn damammen ciki sai ya taso. Ya fadi hakan yayinda ya cafa cikinta. A shagwabe tace " wlh ib na koshi bai jimaba da mukaci indomie da kwai mun kuma sha fruit salad dinnan. "Indomie abincine? Ya fada yayinda ya bude leda daya gasassun kajine har guda biyu manya gaskia sun gasu sunji hadi nan da nan kamshi ya gauraye wurin . Dayar ledar kuma drinks ne kala kala masu sanyin gaske Ya kalleta yana murmushi yace" wani juice kike so ? Ko soft drink zaki sha? Tace" uhmm to inaga ni hollandia zansha. Yayi dariya yace " ai na sanki yar madarace . Ya zuba musu a cup yace,to oya ki dauki kaza daya ki fara ci har ki cinye Zaro ido amina ta yi tace " ni zan cinye kaza daya sukutum? Yace " kwarai ni kuma naci daya oya mu yi rige rige. Ya yago cinya ya fara ci hade da fadin bismillah. Amina kam ta gagara ci don kunyarsa takeji. Ganin taki sa komai a bakinta yasa shi ya dinga bata a baki ba dan taso ba haka ya dinga dura mata A karshe saida suka cinye kaza daya sannan ya tashi ya shiga toilet. Ita kuma ta tattara wurin ta fitar zuwa kitchen ta wanko hannunta sannan ta fito har lokacin su karima sai hira suke suna cin kajinsu cike da nishadi. Ta wuce daki suna zolayarta . Tana shiga a bakin kofa ta tarar dashi tace " au har zaka tafi ne? Murmushi yayi yace " dare baiyi ba ai. Kawai ya tura kofa yasa key Amina ta juyo da sauri ta kalleshi da mamaki tace"ya zaka sa..... Hannu yasa a baki "shiiiiiiiiiiii! Ya kamota yayinda yake fadin " ke baki tausayinane ? Amina wlh ina cikin tsananin bukatarki kinsan fa Jamila bata nan kuma kinga ni ba manemin mata bane...... Da sauri tasa hannu a bakinsa sannan tace " nasani lamido shiyasa nake dada sonka amma kasan ummah ta.... Ya tari numfashinta da fadin" don Allah ki bar wnn maganar zo kiji. Ya jawota bakin gado yayinda ya kashe wutar dakin gabadaya. Su karima sai dai kawai suka jiyo ihun Amina rikicewa sukayi Ummi tace " wlh ya Ib bai kyauta ba ummafa tace ya barta sai ta tare . Karima tace " rabu dashi ya ma kansa dama ai ana so a tsumata ne sosai yanda zaiji dadi ... Ummi ta yi dariya tace " karima bakida kunya wlh yanzu me zamuyi. Karima tace " ai zuwa zamuyi mu gayawa aunty sa,a tunda itace ummah tace ta kula da meenah kar yaya lamido ya matsa Mata. Suka tashi lokaci daya suka tafi sashin yayansu nasir Wanda ib ke bi .a gidan yake zaune da matarsa aunty sa,a nurse ce da yaransu maza biyar. Ib kam bai saurarawa Amina ba saida ya tabbatar ya rabata da budurcinta ya maidata mace sosai .sannan ya barta.gaskia tasha albarka gabadaya ya rikice ya fita hayyacinsa gaskia aminarsa special ce rumgumeta yayi sosai a jikinsa yana rarrashinta hade da sa mata albarka . Amina kam ta ji jiki gaskia tayi kuka har ta godewa ubangijinta. Da kanshi ya hada mata ruwan dumi ya dauketa sai da ya gasa mata jiki sosai sannan ya taimaka mata tayi wankan tsarki sannan ya riketa da kyar take iya taka kafarta don tsabar azabar da take ji a kasanta. Don ko zama ta kasa yi sai dai kwanciya. Ya zuba mata ido cikeda kulawa " sorry my dear zakiji sauki kinji ? Allah ya miki albarka. Ya shiga toilet din a gurguje yayi wanka shima ya dawo ya maida kayansa.sannan ya kalli agogo karfe sha daya saura da sauri ya kalli Amina yace " ina zuwa dear. Ya fita da niyyar ya je ya Kira aunty sa,a.kawai sai ya ganta a Palo suna zaune da su karima. Ya dan Sosa kai ganin yadda ta sa mishi ido yace" aunty dama nace don Allah kizo ki duba Amina. Aunty sa,a tace " haba lamido meyasa kayi haka yanzu me zance da ummah? Ya dan tausasa murya yace " aunty ni a ganina tunda.... Ganin yadda su Ummi sukayi shiru suna jinsa ya sashi tamke fuska yace " kai Ku tashi Ku wuce ciki ana magana kuna binmu da kallo kun baza kunnuwa tsabar gulma. A tare suka tashi suka shiga ciki aunty sa,a kam bata saurareshi ba ta wuce dakin Amina. Ta tarar da ita kwance idonta rufe hawaye na bin kumatunta. Ta kalli bedsheet din duk ya baci da jini. Da sauri ta karaso ta riko amina tana "sannu amina kinga ni ko? Shiyasa nace ki yi taka tsan tsan da lamido dama nasan bazai barki ba. Ibrahim be bar gidan ba saida ya tabbatar amina tasha magani tayi bacci snn ya tafi. Ranar dai ya gagara bacci sai juyi yake domin ji yake kamar ya koma gaskia Amina dabance. Tun ranar ya kasance ib sai ya je ya biya bukatarsa tun Amina na ki yau da gobe har ta saba har Allah Allah take yazo. Sun mori amarcinsu a haka har su ummah suka dawo sunji dadin samun kowa lfy. Sai dai dawowarsu ko sati basuyi ba Amina ta soma laulayi Wanda ya kasa boyuwa duk Wanda ya ganta sai ya fahimci cikine. Abinda ya bawa Haj rumaisa da Haj Zubaida mamaki lallai yaran yanzu sai a barsu. Umma ta kira aunty sa,a ta yiwa amina test don kara tabbatarwa haka akayi kuwa cikin ne. Anan amina taji wani irin kunya da nauyin su ummah kamar ta nitse da kasa. Sa,a kam ta fara kame kame daga karshe dai ta gaya ma ummah gaskia. Umma ta kalli Amina ta ce kingani ko amina shiyasa nace miki kar ki kula lamido ba kunya ne da shi ba.yanzu kinga wnn laulayin shi zai hana a miki biki tare da su Ummi kawai sai dai ki tare . Hawayene ya ciko idon amina domin tana so ayi bikin nan da ita. Amma Allah ya rigada yayi ikonsa. Uban gayya kam ko a jikinsa da maganar biki cikin jikin amina kawai yakewa tanadi .yana ta addua Allah ya basu 'ya mace . Bikinsu Ummi sai matsowa yake ana ta shirye shurye. Kwatsam amina ta wayi gari da ciwon mara mai tsanani har sai da sukaje asibity anan kuwa jini ya balle cikin jikinta ya fita. Sosai ib yayi bakin ciki ita kam Amina bayan ta warke ko a jikinta aka shiga hudimar biki da ita. Duk abinda aka sayawa karima da Ummi itama Amina sai da aka saya mata gaskia Amina taga gata da mutuntawa a familyn galadima. Amare duk sun tare Ummi a Abuja karima a Maiduguri Amina kuwa a gidan ib dinta dake MAFIYAS QUATERS. sunyita kukan rabuwa har an shiga tayasu. Amina da Ibrahim suka shimfida rayuwar soyyaya cikin jin dadi da annashuwa. Ta tare da watanni biyu Jamila ta dawo don taga ba sarki sai Allah. To haka dai zaman ya kasance da dadi ba dadi har Amina ta koma school. Shekara biyar da aurensu gashi har ta gama makaranta shiru ba labarin ciki tun barin da tayi da farko shikenan. Jamila kuwa har ta haifi da bai zo da rai ba. Su Ummi da karima duk suna da yara bibbiyu maza. Tun Amina bata damuwa har ta shiga damuwa yanzu sunje asibitoci da dama amma bincike ya nuna ba wani matsala rabone bai sauko ba. Da wnn ib ke rarrashunta har ta saba. Saida Amina tayi shekara tara cif a gidan ib sannan Allah ya amshi adduarsu ta sami cikin RUMAISA.Jamila ma kuma a lokacin ta haifi Hafiz . Amma duk da haka Jamila tana matukar jin haushin cikn nan na jikin Amina domin ita anata son kar Amina ta haihu kwata kwata. Anan fa zaman lfy yayi kaura a gidan don kullum Jamila sai ta kirkiro matsala ta hana Amina sukuni nan ma ib na taka mata birki sosai. Haulyce👍🏻🥰 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰 *Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤* ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡35 *********Don haka Haj rumaisa tace amina ta dawo gida ta haihu . Haka Amina ta kasance cikin kulawar su Haj rumaisa har cikin ta ya kai wata tara. A lokacin ta fara labour a hankali har haihuwar yazo gadan gadan ba bata lokaci aka kira Ib suka tafi asibityn BOSHANG dake jimeta amina na shiga labour room sai ga kan baby. Ba bata lokaci ta haifo babynta katuwar gaske da ta kara kadan ma sai C.S Nurse ta fito lokaci guda Haj rumaisa da ib da aunty sa,a suka mike har suna hada baki " nurse ya..... Ta katsesu cike da fara,a ta ce ' Ku keantar da hankalinku Amina ta sauka lfy Alhamdulillah suka furta . Haj rumaisa tace " fatan yaron lfy? Nurse tace " baby girl ce....... Ib ya kalli nurse da sauri yace " kikace mene amina ta haifi baby girl? Nurse tace kwarai ma kuwa baby girl ce katuwa lafiyayyiya . Gabadaya hamdala suka dinga yi cike da farin ciki domin wnn itace jika ta farko 'ya mace a bangaren galadima. Ib yace " nurse zamu iya shiga? Tace "aa ana shiryasu sai sun fito. Ib yace " OK .am nurse gaskia kin cancanci kyauta daga gareni don haka ki ban phone number dinki sannan account number dinki. Nurse ta washe baki tuni ta fara godiya tun ba,a bata ba . Amina kam bacci takeyi yayinda ib yake rike da ',yarsa kamar zai maidata ciki. Bayan Amina ta huta sosai aka sallamesu don kuwa tuni familyn galadima sun soma cika musu asibity. Tun randa aka haifi rumaisa Jamila ta shiga damuwa sosai har kuka ta yi Dan bakin ciki . Yayinda amina kuma tun ranar ta fara karbar kyaututtuka abun sai Wanda ya gani masha Allah. Ranar suna baby taci sunan hajiya rumaisa inda mahaifinta yace a kirata da IHISAN. A hankali rayuwa ke tfy amina da 'yarta sun sami dukkan gata da kulawa har ta manta da matsalar rayuwa . Watanta biyu cif a gidan galadima snn ta koma gidanta ba don su Haj rumaisa sun gaji da ita ba sai don matsin Ib.don kullum yana gidan yana makale da ' yarsa. Aikuwa suna dawowa kulawar ib ya ninka na da sau dubu don ko kiris yaji kukan rumaisa ransa baci yake ya kama yiwa Amina balai. Har tadi yake yi da ita yana Ihsan Mamana ina son ki kamar raina Allah ya raya min ke ya muku albarka keda sauran yayyunki. Amina tayi murmushi tace " amin. Rumaisa Nada wata hudu ta fara rashin lfy nimonia abinda ya dagawa ib hankali matuka don yana wahalar da ita sosai musamman in anyi sanyi.don haka dole ya tashi tsaye wurin kula da ita. Ummi ma ta haifo baby girl karima ne dai har yanzu yaranta hudu duk maza. Jamila kuwa tana nan tana shige shigenta bata fasa ba sai dai Sam bata nunawa Amina a fuska yanzu zamansu lfy suke harda hira suke sosai hankalin ib ya kwanta sosai. A lokacinda rumaisa ta kai shekara daya da wata bakwai amina ta yayeta. A wnn lokaci ne kuma ta fahimci Ib ya fara sauya mata don ya daina kulata daga ita har rumaisa. Abin yana matukar baiwa Amina mamaki tayi ta tambayatsa amma sai yace mata aiki ne ya masa yawa. Wasa gaske abun sai gaba gaba yake har ya kasance baya cin girkinta kuma in taje dakinsa baya damuwa da ita rumaisa ma ya daina daukarta in tana kuka ma baya damuwa sai dai yace ta dameshi. Amina tayi kuka har ta gode Allah Ta dinga rokon ib akan ya fada mata laifinta Rannan kam ranshi a bace yace " amina bansan da wani yare zan miki magana ba wai me yasa kk damuna ne? Kinga in bazaki iya zama dani haka ki kama gabanki ke kinga na ma sawwake miki kawai ki dauki 'yarki Ku bar min gida. Cike da mamaki da tsoro amina tace " what Ibrahim me kk nufi? Kai tsaye yace " amina na sakeki saki daya. Yana fadin haka yayi ficewarsa amina kam jiri ne taji ya fara dibanta a hakali ta fara fadin innalillahi wa inna ilairrajiun !!! Da kyar ta dawo hayyacinta ta fashe da kuka mai tsanani ta rumgume rumaisa. Sai da tayi mai isatta snn ta shirya kayanta ta tafi gidan galadima anan ta sanar ummah komai. Hankalin Haj rumaisa ya tashi matuka don haka ba bata lokaci ta nemi Ib tayi masa tatass kuma tace dole ya maida Amina. Haka ya hkr amina ta koma yayinda Haj rumaisa ta cewa Amina ta dage da addua domin sakacinta ne ya jawo mata hakan Ita kanta Amina tsan da hakan domin yanzu ta saki jiki ta shagala ba kamar da ba don haka dole ta mike tsaye. Wnn karon wulakancin Ib ya ninka na da sau dubu don ko girki amina batayi bare kuma zuwa turaka. Jamila da yaranta kawai ke cin karansu babu babbaka a gidan. Wasa gaske amina ya kasance sai tayi sati bata ga ib ba. Abinci ma sai Jamila taso amina keci a gidan don a yanzu ko 'yan aiki sun fita daraja. Ranar aka wayi gari rumaisa ba lfy nimonia dinta ya tashi kirjinta na toshewa. Amina tayi sa,a ta sami ib a dakinsa yana karatun jarida Durkusawa tayi tace " lamido don Allah don annabi ka tausaya rayuwata data ihisan gata nan ba lfy ko bacci ba muyi ba jiya don Allah ka taimaka ba don halina ba ka kaita asibity. Ba tare da ya ko kalleta ba yace " ki kaita mana kawai meye sai kinzo kin matsa min Amina cikin matsanancin kuka tace" don Allah Ibrahim ka gaya min abinda na maka kake min irin wnn horon ? Ko ka manta banda kowa sai kai din ka tuna fa na bar garinmu yayyuna na bijire musu saboda kai yanzu ina kk so nasa rayuwata? Murmushi yayi yace " na godewa Allah da kika gane kuskurenki na rashin biyayya ga yayyunki. Ya numfasa yace karki damu lokaci bai kure miki ba kina iya zuwa ki nemi gafarar su indai nine matsalarki amina kije daga yau na yanke igiyoyin aurena dake kanki ma,ana na sakeki saki biyu in kin hada da waccan ya zama uku! Amina ta mike da sauri ta kalli Ib cikin bacin rai tace " Ibrahim kana cikin hayyacinka kuwa ko kasan me kk fadi? Yace na sani sarai amina zama dake ya isheni bana son ganinki daga ke har 'yarki Ku fita Ku bani wuri kuma na baki yau da gobe ki tattara Ku bar min gida na har abada ke da ' yarki kar Wanda ya kuma dawowa gareni bana bukatarku. Ya karasa fada cikin tsananin fushi . Tashin hankali ranar amina taga matsifar rayuwa haka ta sanyawa zuciyarta hkr ta dauki ' yarta ta kaita hospital bata fadawa kowa ba don yanzu kam tsakaninta da ib ya kare tunda babu sauran igiyar aure don haka babu amfanin taje ta fadawa Hajia rumaisa . Bayan sun dawo ta tattara kaysnta da gwalagwalanta duka kudadenta kam ta adanasu a bank. Kafin ta bar Adamawa sai da ta tabbatarwa ib bazata kuma dawowa ba daga ita har 'yarta sai ya nemesu da kansa. A wulakance yace "alhamdulillah haka nake son ji .don ki Sani nima bazan nemeku ba kuma har abada matsiyata kawai!!! Da wnn bakin ciki amina ta bar Adamawa ba tare da sanin su Haj rumaisa ba . Gaskia amina ta yanke wa kanta hukunci cikin fushi don saida ta isa Kd ta fara tunanin da wani ido zata ga yayyunta kuma me zatace musu.???? Hauly ce🥰👍🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰 *Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤* ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡36 ***********Amina ta isa gidansu zuciyarta sai tsinkewa yake haka ta daure ta shiga sai dai sam ba su tasamu ba wasu ne daban anan ta shiga yi musu bayani amma basu gane ba. Abin mamaki makwaftansu ma data ke shiga sun kaura dake gidan hayane. Amina a karshe dai gidansu Zuwaira taje gaskia taga kallon banza babu Wanda ya kulata sai maigadine yake fada mata su Zuwaira sun koma kano da zama shekaru kusan shidda yanzu. Don haka amina bata tsaya ba ta sake samun motar kano ta tafi har cikin dare ta isa .dake tasan gidansu na gado don nan ne yayyunta sukayi gini. Duk da haka sai da tasha wahala snn ta gane .ta shiga gidan da sallama yayinda take bin gidan da kallo sungyareshi yayi kyau ginin zamani lallai arziki yaci uban Nada. Wata matace ta fito rikeda yarinya. Anan fa amina ta fara tunanin ko ba gidanneba. Suka gaisa da matar cike da fara,a Amina tace " don Allah nan ne gidansu Mohd da kassim? Matar tace " eh nan ne. Amina tayi ajiyar zuciya tace " Zuwaira na nan ? Matar tace ' eh yanzu kuwa ta tafi sashinta bari na fada mata tayi bakuwa. Anan matar ta tafi amina ta bita da kallo a ranta tana fadin wnn din kuma wacece? Tana cikn wnn tunanin suka fito amina tuni ta gane Zuwaira amma ita sai da ta matso ta karewa amina kallo ta dafe kirji tace"Amina!!! Hawayene ya ciko idon Amina suka rumgume juna da Zuwaira suna kuka Wanda yaja hankalin yaran gidan kanana . Sai kuma shatu data fito wanka ganin amina yasa ta saki salati tace amina! Kece? Dama kina raye? Tab bari nayiwa yayyunki albishir . Da sauri ta wuce Palo inda su kasim da Mohd suke hira sai su salman da salim Wanda a lokacin suna da shekara 13 a duniya . Anan shatu ta sanar dasu dawowar Amina. Gabadaya suka fito tsakar gidan ganin da gaske amina ce.yasa Mohd yin murmushin takaici yace " Amina dama nasan dole ne ki dawo watarana don bakuda wayanda ya fimu. Ya kalli shatu yace " shatu kuje da ita Ku kwanta dare yayi koma meye a bari sai gobe.duk kuje Ku kwanta..... Kasim da yaketa cika da maganar Mohd yace " haba yaya ina zata je wlh ta bar mana gidanmu mu muka San daga ina ta fito? Shatu ta karba" kuma gata da goyo ko ina ta sami yarinya kuma oho. Sai lokacin duk suka lura da goyon Kasim ya kalli Mohd yace " kagani ko ? Amina sai da tagama yawonta taje ta debo mana abin kunya snn ta dawo wlh Sam zaman Amina a gidan nan bazaiyiwu ba. Shatu tace " wnn gaskiane kasim . Ta kalli amina dake kuka tace " sai yanzu da kika gama yawon karuwancinki zaki dawo mana da goyo? Amma amina kinji kunya wlh ..... Ta karasa fada hade da fashewa da kukan munafurci tana fadin yanzu fisabilillah abinda zaki mana knn dama tunda kk tafi yanuwanku sai nuna mu suke wai mun kasa baki tarbiyya mun barki kin tafi karuwanci alhalin sauran sati daya da bikinki.yanzu shine kk dawo da yarinya don ki tabbatar musu karuwancin kk je? Maganar shatu tayi tasiri a zuciyan Mohd da kassim . A fusace kassim ya kalli amina yace " ki fita daga gidan nan tun kamin na miki illah in yaso kije kici gaba da karuwancinki . Matar can ne da ta fara ganin amina tace " haba kassim Ku saurareta mana..... Mohd ya tari numfashinta da fadin " kar ki shiga maganar nan rabi domin baki San komi ba. Zuwaira ta goge hawayenta tace " amma yaya ya kamata ace Ku saurari amina watakila abinda kuke tunani ba haka bane.don Allah Ku barta haka sai da safe...... Kassim yace " ke Zuwaira bari kiji amina bazata kwana a gidan nan ba don haka ta fice daga gidan nan kawai ta koma gun wayanda ta zabesu fiye damu...... Zuwaira tace " yanzu a cikin Daren nan a naka tunanin ina zata je? Kai tsaye yace " ta koma inda ta fito. Zuwaira tace " wlh bazaiyiwu ba babu inda amina zataje don itama nan din gidan mahaifinta ne kuma tana da gadonta ko karyane? Don haka ba inda zata je don naga ka dage da yawa.baka San kuskure bane ko bakasan kaddara ba? Kasim ya harzuko yana shirin yiwa Zuwaira magana Mohd yace " ka rabu da ita kawai barsu aminan ta kwana in yaso gobe sai tasan inda dare ya mata. Kasim ya kalli Zuwaira cike da jin haushi yace " wlh da ba don yaya ba kema da sai kin bar gidan nan cikin daren nan. Zuwaira tayi mishi wani irin kallo sannan ta watsar ta kalli su salman tace " kai salim kuzo Ku dauki kayan goggonku Ku kai dakina . Lokaci guda sukace " to Momy Zuwaira ta kama hannun amina tace "zo muje ciki amina yi hkr. Shatu tace " lallaima Zuwaira har wani hkr kk bata ? Anan kiri kiri babu tsoron Allah tace bata son danuwanki. Zuwaira tace " sai me don tace bata son danuwana ana son dole ne? Mohd da kassim shiru kawai sukayi . Yayinda rabi ta wuce dakinta shatu kam har lokacin magana takeyi tana kara ingiza su Mohd . Zuwaira kuwa ranar taki zuwa turaka anan suka zauna da amina sukaci kukansu har suka gaji . Tace " amina ina kk shiga kk barmu cikin tashin hankali ni da yayyunki? Amina tace " aunty Zuwaira labarin mai tsawone sai gobe in Allah ya kaimu zan fada miki . Zuwaira tace "to Allah ya kaimu.kin dawo kinga gida ya cika da yara ko? Bayan tfyrki shatu ta maida yayyunki kamar remote control sai yanda tayi ni nan bata barni ba duk da ba kulata nake ba amma saida tasa yayanki ya tsaneni Amina ba abinda bangani ba na makircin shatu sai da na tashi tsaye da rokon Allah ba dare ba rana snn Allah ya ya kawo min sauyi ba kiga tun kan salim ban kuma haihuwa ba? Sai yanzu dana samu faiza wlh yayanki munfi shekara biyar da yayanki a gidan can ko hannuna baya rikewa. Amina ta zaro ido cike da mamaki tace " kuma kika jure? Zuwaira tace " gidanmu na koma wlh amma abin mamaki bai taba nemana ba sai da nayi good 3 years ance ya sakeni yaki karshe dai haka Abbana ne yace in dawo inci gaba da addua don sunsan abin ba haka kawai bane.don haka sai na dawo shatu kam sai abinda taso takeyi a gidan bayan tfyrki ta haihu har sau biyu amma yaran Allah baiyi zasu rayuba. A lokaci guda Allah ya amshi adduata .komai ya dawo normal. Inda reshe ya juya da mujiya shatu ta somagirbar abinda ta shuka ita da yayanki har dukanta yayi da cikin Sadiya sannan yaje ya kawo mata kishiya wato rabi matar kirki wlh batada tashin hankali da kowa kinga lokaci guda da zuwanta guda ya canza .shatu bayan ta haifi Sadiya ta sake samun raihana ta haifi raihana da wata daya na haifi faiza sati daya akai itama rabi ta haifi sakina sune kika gansu gabadaya suka taso Kansu daya yanzu shekarunsu bibbiyu da dorin watanni. Amina ta jinjina kai tace " aunty kinyi matukar kokari wlh gaskia na jinjina miki don shatu babu alkhairi a tare da ita zama da ita sai an jajirce. Zuwaira ta sauke ajiyar zuciya tace "yanzu dai Alhamdulillah mun gama gininmu a Abuja ma zamu koma har da salman don ni na ke kula da dukkan lamarinshi shida salim yadda suka taso kamar twins haka muke so har su girma yanzu mu da kano sai dai muzo Hutu. Amina tace " gaskia aunty Zuwaira na tayaki murna kuma nauyin tarbiyyan salman da kk dauka Allah ya biyaki. Zuwaira tace " amin yanzu ki kwanta nasan kin gaji da yawa. Da haka suka kwanta Amina dai bata yi bacci ba sai juyi take ta rasa me yake mata dadi a rayuwa. Gari na wayewa Zuwaira ta tashi ta shirya wa amina breakfast mai rai da lfy yayinda ta duma ruwa tayiwa rumaisa wanka ta shirya ta tsaf cikin pink din Riga da wando masu nauyi don ana sanyi daganan ta bata maganinta. Ta kalli amina tana murmushi tace " meenah wnn yarinya tana kama da Ibrahim ko dai 'yarsa ce bani labarinki. Amina ta gyara zama da niyyar baiwa Zuwaira labarinta kawai sai ga shatu ta fado dakin ko sallama babu ta kalli amina fuska daure tace " kin wani mimmke kafa kin dauka zamu barki kici gaba da zama ne ki tashi yayyun naki na kiranki. Amina ta zubawa shatu ido daga bisani tace " shatu ki dinga sa tsoron Allah a lamuranki ni yanzu banda lokacin ki. Ta be baki shatu tayi tace " kima ce wani abu mana ki gani. Zuwaira tace kinga shatu kawai kije tana zuwa. Shatu tace " wlh Zuwaira ki taka tsan tsan da Amina in ba haka ba igiyar aurenki na daf da tsinkewa . Zuwaira tace" tunda ke kika kulla ko? Shatu ta fita tana fadin " ki dai bi a sannu. Amina ta tashi ta fita zuwa palon Mohd a tsakar gida ta gaisa da rabi cike da fara,a. Tana shiga palon ta samesu zaune dukansu biyu fuskarsu kamar an aiko da mutuwa ta zauna tana shirin gaishesu Mohd ya daga mata hannu hade da fadin " bamu bukatar gaisuwarki Amina kawai ki fada mana me kk zo yi nan gidan? Amina ta sunkuyar da kai hade da fadin " na dawo ne yaya.... Kasim ya karba "saida kk gama yawon iskancinki da Ibrahim din zaki dawo? To bari kiji idan har kina so zama da mu to sai dai ki dauki shegiyar yarinyarki ki maidata gun ubanta!! Amina ta dago a tsorace tace " aa yaya don Allah Ku rufan asiri wlh bazan iya rabuwa da 'yata ba. Mohd yace " to kuwa zaki bar gidan nan don bazamu rike shegiya ba zabi ya rage naki. Amina ta sa kuka tace wlh yaya rumaisa ba shegiya bace . Kasim yace " kinga kar ki manna mana hauka kawai mun baki nan da 24 hrs ki zaba ko ki maida wnn shegiyar yatinyar inda kk sameta ko kuma ki tattara ta Ku bar mana gida. Amina ta fusata sosai don haka ta mike ta share hawayenta ta kallesu tace " wlh babu Wanda ya isa ya rabani da 'yata kwaya daya da nakeji da ita kamar rai don kawai na dawo shine zaku wulakantani saboda kunga iyayenmu basa raye wnn shine wasiyyar da mahaifinmu ya bar muku a kaina? A tunanina ko me zan yi a rayuwa baza Ku gujeni ba.amma na gode kuma in dai na amsa sunana Amina ni kuma daga yau na yanke duk wata alaka dake tsakanimu bazan sake nemanku a rayuwa ba HAR ABADA!!!!! Tana fadin haka ta fita cikin fushi taje ta dauko kayanta tana kuka Zuwaira ma kuka takeyi tana don Allah amina ki tsaya Ku fahimci juna. Amina ta ce " wlh bazan tsaya ba kawai ki barni zanje inyi rayuwata ni kadai da ',yata har abada. Ta fita da sauri ta bar gidan tana kuka ba tare da ta San inda zata ba. ******************** Mama ta kalleni yayinda ta share hawayenda ya zubo mata tace " kinji dalilin zamana a kauyen gano knn don bazan iya zama cikin gari dangina suna nunani ba . Bayan tafiyata momynku hajiya Zuwaira bata hkr har bayan sun bar kano sun koma Abuja anan ta dinga bama salman da salim labarina da yadda na ke sonsu tun suna kanana.da taimakonta dana salman da salim yayyuna suka sauko daga fushin da suke har sukaje kauye suka nemeni muka yafewa juna snn suka ce suna son na dawo gidan nan da zama.ni kuma bana son dawowa nan saboda shatu shiyasa na amince wa Marigayi Alhaji aminu kawai don ya Dade yana son muyi aure ina kauce masa saboda ke don bana son abinda zai taba mutuncinki RUMAISA. Sannan ina son ki Sani na baki labarin ki ne domin hankalinki ya kwanta ki daina zargina amma ko kadan bana son tunawa da rayuwa da nayi a YOLA. RUMAISA yanzu me kike ga yafi dacewa dake zaki hkr da neman mahaifinki ne ko kuma zaki nrmeshi? Nima kuka nake sosai na daure na goge fuskata nace " mama gaskia kin fuskanci tsananin rayuwa amma inshaa Allah komai zai zo karshe ni na yanke shawaran neman mahsifina koda kuwa bazai karbeni na tabbata dangina suna sona.mama zan tafi yola goben nan kuma ki kwantar da hankalinki zan dawo cike da farin ciki in Allah ya yarda Kuma INNA zataji KUNYA !!!!!! Mama tace " da kyau ni kuma ina miki adduan fatan alkhairi kuma da kaina zan kaiki ki hau mota amma kamin ki tafi ina son ki daure kije ki fadawa salman da kanki kuma ina son ki daina jin haushinshi ki masa uzuri dik abinnan da yake miki ba laidinshi bane rumaisa salman na sonki sosai matsalar daga mahaifiyarshi ce sai dai muci gaba da addua. Na goge hawaye daya sauko min na ci gaba da kallon photon mahaifina IBRAHIM AHMAD GALADIMA ( LAMIDO) haka kawai na tsinci kaina da sakin murmushi na kalli mama nace " mama amma kinsan daddyna ba,ason sa ba ya miki haka ba asiri aka muku don a rabaku kuma nasan zuwa yanzu asirin ya karye. Mama tace " to amma a tunani ya kamata ace ya nememu ba wai nitsan guri ba. Jikina a mace nace " eto amma Ki kwantar da hankalinki komai zai daidaita insha Allah! Tace "to Allah yasa. Da haka muka kwanta gaskia ranar nayi baccin dadi don har mafarki nayi wai ina hanyar tfy YOLA! Hauly ce🥰👍🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰 *Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤* ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡37 ******** Gari na wayewa kuwa tun shidda na gama shirina tsaf cikin bakar Riga doguwa mai kyan gaske yasha stones nayi mflng din gyalen na fito tamkar jinsin larabawa. Tea kawai nasha nacewa mama bari inje in sallami ya salman. A harabar gidansu na sameshi yana goge motarsa . Jin takuna yasa shi juyowa karaf mukayi ido hudu saida naji gabana ya fadi kai ya salman akwai kwarjini. Da sauri na cire idona shikam ya shagala da kallona har ya manta mota yake gogewa. Ina shirin karasawa gunsa kawai naji an bugeni da karfi saura kadan in fadi Allah ya rufa asiri. Dubawanda zan yi sai naga ashe nabila ce ta shigo da saurinta ta kawo ma ya salman break fast shine kamar an korota tsabar rawar kai. Bata ma San ta bugeni ba tuni ta isa wurinsa tana kaudi shikam fada ya shiga yi mata da fulatanci kamar zai daketa duk da bajin su nake ba amma na fahimci yana fada ne akan tureni da tayi kuma bata ce min ko sannu ba. Ta juyo jikinta a mace ta kalleni hade da fadin "Isa wadu munyal( sannu kiyi hkr) Na gane hkr take bani murmushi nayi na girgiza mata kai nace " babu komai . A raina kuwa cewa nayi wnn abun ne ya salman ze aura lallai akwai kallo . Ta wuce palonsa don ta ajiye mishi abincinsa . Gabadaya binta mukayi da kallo tfy take bazar bazar har tana tuntube.abun ya ban mamaki lokacin da ta zo wata wawiya da ita shiru shiru bansan a yaushe ta koyi rawar kai haka ba. Na Dan numfasa snn na karaso gabansa nace " yaya ina kwana? "Lfy lau kin gama shiryawa ne? Nace " eh Yace " to ki dan je ki jirani barin inyi breakfast nayi wanka. Murmushi nayi nace " ni ba Abuja zanje ba Adamawa zan tafi yanzu ma tasha zani shine nazo na sallameka . Zuba min ido yayi na dauka ma bazaiyi magana ba naji ya danyi kasa da murya yace " wato bazaki hkr da zancan tfyr yolan nan bako? Shiru na masa yaci gaba da fadin " shikenan a sauka lfy Allah ya kiyaye hanya Nace" amin,kuma dan Allah ka yafe min duk abinda na maka saboda halin tfy. Na fadi hakan yayinda hawaye ya zubo kaina a sunkuye . Shima jikinsa a mace yace babu komai Allah ya kiyaye hanya ya kuma bada sa,ar abinda kk je nema. Nace " ameen na gode. Na juya jikina a mace kwata kwata na lura kamar ya salman har yanzu fushi yake don ya kasa sakin jiki dani mukoma kamar da. Har na fara tfy a hankali naji yace "RUMAISA! Na juyo da sauri nace " na,am Ina sauraren me zaice amma shiru yayi . Har saida ya ga dama yace min " in kin fita ki rufe min get pls. Haushi ne ya kamani har nayi dana sanin zuwa da nai don sallamarsa gaskia na tsani mutum da baya yafiya a rayuwa. Da kai Na amsa snn na fita na koma gida tare da mama muka shiga cikin gida don yiwa Abba sallama gaskia Abba baiso na tafi sai dai ba yanda ya iya tunda yaga dagani har mama muna so. Na sallami Maman sakina ma inna kam bance masu komi ba na fita tuni mama ta saka min kayana a mota ina zuwa na shiga ta ja motar sai tasha. Mun sami mortar Adamawa yola mai kyau sienna saura mutum biyu mama ta biya sannan ta bada number dinta. Sai da ta tabbatar zamu tafi ta kalleni hawaye tuni ya cika a idonta tace"Rumaisa ki kula da kanki ki kuma tsare mutuncinki.Allah ya baki sa,ar haduwa da danginki .idan sun karbeki Alhamdulillah in kuma sunki don Allah kar ki damu ki dawo gareni rumaisa zanci gaba da baki dukkan kulawa. Nima hawayen ke xubowa nace " inshaa Allah mama karki damu kici gaba da addua kawai. Ta daga min kai snn tace" Allah ya kaiku lfy ya kuma dawo min dake lfy ya tsareki da dukkan sharri. Nace amin mama nagode. Da kyar muka rabu don har motarmu ya tashi tana tsaye hannu ta daga min har muka bace. Munyi tfy kusan Na awa daya kafin na daina kuka. Wasa gaske tfy muke tayi muna wuce garuruwa kauyuka da jeji ni dai sai kallo nake domin iyakacin nitsan tfy na shine kano to Abuja. Tuni na fara gajiya ga yunwa kuma amma na kasa cin komai. Koda naga munyi azahar a hanya tunani mun kusa ashe tfy kam da saura. Tabdi sai da naga karfe hudu ta cika na kalli abokiyar tfy ta wacce muke dan taba hira sama sama kasancewar ta mai son bacci a mota. Nace " yar uwa har yanzu bamu kusa ba ? Ta kalli agogo tace " hmm zamu kai karfe bakwai na dare fa domin hanyar Adamawa bata da kyau tana cin lokaci sosai. Na zaro ido nace subhanallah to nan din inane? Tace" yanzu dai nan kumo ne bamu fita Gombe ba tukun . Kwantar da kai nayi akan seat nace ya salam . Sosai driver yake sharara gudu sai gashi mun shiga hanya mai cike da gargada tun ina daurewa amma ina har na fara korafi domin cikina sai ciwo yake tsabar jijjigar da muke sha gashi ban sababa. Ta kalleni tana murmushi tace " daga gani baki saba dogon tfy ba ko? Nace" wlh kuwa. Tace "karki damu Mun kusa nan din dajin savannah ne. A haka dai munaji muna gani har magriba tayi mana a numan mukayi sallar magrib muka sake daukan hanya . Mama ta kirani har sau biyu da layin mmn sakina don tace min wayarta ta nema bata gani ba harda kudin Jakarta saidai tana ganin kamar a tasha aka sache mata. Faiza da sakina ma sun min waya haka Abba ma da ya salim. Ina gyara zama Sai kawai na hango WELCOME TO YOLA👍🏻 Murna kamar ya kasheni dan har ajiyar zuciya nayi na furta Alhamdulillah . Matar nan Sai dariya take min tana hankalinki ya kwanta yanzu ko? Nace " eh Sai lokacin driver yace " hmm ai da Hajia kin dauka zamu sayar dake koh? Dariya nayi kawai Munyi tfy kadan Sai gamu a bakin kasuwa don na gane hakan ne saboda cinkoson jamaa kuma naga katon sign board an rubuta. JIMETA MODERN MARKET YOLA👍🏻 Anan drivern ya tsaya hade da fadin Alhamdulillah !! Kowa ya sassauka mukayi sallama da juna na sami gefen hanya na kira mama nace "na isa bakin kasuwa . Tace " to yanzu abinda za,ayi ki hau bus zama ki gansu suna cewa yola yola saboda inda kk yanzu jimeta ne yola north knn can inda zaki kuma shine asalin yola wato yola south kar a kidima ki ki nitsu sosai . Ina dube dube nace " mama ai ba bus ba kuma acaba Sai adaidaita sahu kuma naji suna cewa yola zanine? Tace "to ki hau kice musu zaki sauka a jippu jam domin nan zaifi saurin kwatance .in kin sauka ki kirani. Nace to mama. Na kashe wayar na tare adaidai da kyar na iya fadin jippu jam zanje. Yanayinda nayi maganar yasa mai keken dariya yace " JABBAMA dai hajiya tunda zuwa kikayi . Nace " aa jeka ni dai jippu jam akace min. Ya sake yin dariya yace to muje. Ya tayani sa kaya sannan na hau muka tafi. Munyi tfyr da bata wuce minti ashirin ba sai gamu a wata roundabout mai dauke da katon kwarya da ludayi a raina nace zansha fura knn! Muna zagayawa na katon kofofi guda biyu daya an rubuta JIPPA JAM( sauka lfy ) Daya kuma JABBAMA(barka da zuwa) Sannan ga wani katon allo Wanda akayi shi da siminti anyi rubutu da arabici da kuma boko *NDEMEN* (muyi noma) *DUREN* (muyi kiwo) *JANGEN* (muyi karatu) Mai adaidaitan ne ya min bayani nikam murmushi nayi nace masha Allah don abin ya matukar birgeni. O wai yau ni rumaisa Sai gani a yola mahaifata.Allah abun Godiya!!! Na sauka na biyashi kudinshi mukayi sallama ina masa Godiya. Ya tafi ba jimawa Sai ga wani adaidata yazo ya paka a gabana su biyu ne duka kuma a gaba suka zauna alhali bayan empty Sai na lura da kafansu silifas din roba suka sa irin taka biredi dinnan na mata kuma duka takalmin iri dayane Abin dariya ya bani don naga matasa ne da alamu shi ake yayi a garin . Mai tukin yace min " hajiya bye pass ko cikin gari ko 'yolde pate? Nayi murmushi nace " eto minti daya ina zuwa Nan na kira mama na gaya mata tace inba mai adadaita ta mishi bayani. Anan na bashi wayar sainaga sun kalli juna da dayan mutumin suka kalleni lokaci guda amma basuce komai ba Ya amsa sun jima suna magana snn ya kalleni yace " gashinan shiga muje dama mafiyas Quarters din zamuje har get zamu kai ki. Nayi mutmushin jin dadin yayinda nayi sallama da mama tana cewa" to rumaisa Allah bada sa,a sai na jiki don zan maidawa rabi wayarta. Nace to mama zan kiraki in na isa . Na katse kiran tuni sunsa kayana don haka na shiga muka fara tfy . Hanyar bye pass ne muka bi shiru kk ji gidajen manyan mutane gashi gidajen suna dan nesa da juna kasancewar lokacin damina an kuma yi ruwa don naga koina a jike sai kukan kwadi nakeji gabadaya arean tsit kakeji.tsoro ne ya fara kamani na kalli time a wayata karfe 8:30 ne . Anan suka saya sukace Mun isa Hajia na sauka na duba banga wani gida kusa ba na kallesu yayinda suke sauken kaya nace " to banga gida snan din ba sai acan nake hango gidaje. Mai adaudaitan yace " eh can din zaki karasa gida na farko shine gidan Alhaji Ibrahim lamido din Yayinda nake cire kudi a jakata don na biyasu kawai sai naji sun fizge jakar na dago da sauri kuma a tsorace . Dayan matashin yasa hannunsa a baki " shiiiiii karki mana ihu. Jikina ne yake rawa ji nayi kafata ta gagara daukana tsabar tsoro. Mai tukin yayi murmushi yace " ke 'yar alhaji lamido galadima ne koh? Duk da a tsorace nake amma sai dabara ta fado min nace "aaa ni ba yarsa bane 'yar uwar matarsa ce. Yace " eh kina da gaskia domin family basa haifan yara mata.yanzu kinsan me muke so dake ? Na girgiza kai jikina na rawa nace "aa Dayan ya karba yace " ki bamu wnn wayar taki domin ta shiga ranmu sosai Anan na matairace fuska hawaye na zuba na tuna abubuwana muhimmai dake ciki...... Ban gama yanke shawara ba naga sun fito da kananan wuka a hannunsu masu tsinin gaske suka kalleni suka ce " ke don fa Mun ganki bakuwa ce wlh kashe mutum a wurinmu ba komai bane. Da sauri na mika musu wayar na juya da niyyar gudu. Kawai sai wani gib! An buga min abu akai kamar dutse Na saki wata irin razananniyar kara cike da azaba na rike kaina da jini ya balle. Sukam tuni suka sawa machine dinsu wuta suka gudu da jakata da kuma wayata. Hauly ce👍🏻🥰 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰 *Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤* ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡38 *************Ihun da na ke ta yi ina neman agaji ya sa masu gadi suka kawo min agaji. Nace" wayyo jakata wayata suka kwace sun gudu dashi. Wani mutum ne yace" baiwar Allah keko ina zaki je cikin Daren nan me ya kawo ki bye pass? Wani a cikinsu yace" dubi yadda kanta ma ya fashe . Da sauri ya karbi Dan kwalin abayata ya daure min kai anan suke tambayata ina zanje. Cikin muryan kuka da azabar ciwon kai da nakeji na fada musu komai a takaice. Wani daga cikinsu yace " amma ai alh lamido basu da wani dangi a kano..... Wani ya katseshi da fadin haba isa wnn shirme kkyi kawai ka dauki Jakarta kuje kaga fa taji ciwo akai. Sannan yace " kinga Hajia wnn shine maigadin gidan Alhaji lamido gashi can ki lallaba mu karasa. Nan suka dauki jakar kayana nikam binsu kawai nake don gani nake kawai karya suke min da akwai inda na Sani bazan ma bisu ba to ya na iya gani bakuwa gashi bansan koina ba ga shi banda waya banda kudi a jikina ga dare yayi. Kaina ne yake tsarawa sosai da kyar na lallaba muka karasa bakin wani tafkeken get mai kyaun gaske ga hasken wuta ko ina ga shukin furanni da suka saka get din a tsakiya ya kara kawata ginin. Anan muka shiga harabar gidan da mai gadi wayyo an shuka kudi ba kadan ba a gidan nan domin babban gidane mai kyan tsarin gaske ga shuke shuken fulawowi.parking space motoci a jejjere masu rai da lfy.can kuma dawakaine guda hudu an dauresu.kai abindai se wnda ya gani don komai ya tsaru iyakar tsaruwa. Mai gadi ya kalleni muje. Na dai bishi a baya har bakin kofar da zai kaika ko ina na gidan . Muka shiga wani makeken Palo in tsaya kwatancen kyaunsa bata lokaci ne. Yace min " ki zauna bari in..... Bai karasa ba saiga wani matashi ya fito daga wani bangare. Nan maigadin ya shiga gaisheshi cike da girmamawa yace " yallabai Hafiz dama bakuwa ce tazo gun alhaji daga kano sai kuma akayi rashin sa,a ta hadu da....... Daga wa maigadin hannu yayi snn ya kalleni yace " baiwar Allah gun waye kk zo? Da kyar na iya fadin gun alhaji Ibrahim Ahamad galadima nazo. Zuba min ido yayi daga baya ya koma ciki baice komai ba nikam ina tsaye duk zafin ciwon kai yabi ya dameni ga uban daurin da suka min ya kara mun radadin azaba. Anan fa baga wasu mata su biyu da saurayin nan na dazu da wani kamar ya salman sai kuma alhajin Wanda shine a gaba yana sanyeda jallabiya milk colour idansa sanye cikin farin glass. Ni dai zuwa yanzu ko gani mai kyau banayi jiri ne nake ji. Da sauri Alhajin ya karaso ya kalleni yace " baiwar Allah daga ina kuma waya turoki........ Maganar tasa ta makale ne sanda ya karaso daf dani gabansa ne yayi mummunan faduwa da ya jima baiji irinsa ba. Da sauri ya rikeni hade da fadin " subhanallah! Me ya jimiki rauni kuma naga jini? Ya fadi hakan ne yayinda yake kallon fuskata . Da kyar na iya bude idona tsabar jiri da nakeji na bude baki da kyar nace " sunana RUMAISA IBRAHIM daga kano mahaifiyata AMINA SULEYMAN ce ta turoni tace.......... Ban karasa ba na fita hayyacina. A rude ya kalle su yace " wnn ko shakka banayi IHISAN ce itace!!!!! "Samir zoka dubata me ya sameta? Gaba daya ya rikice su Kansu abun ya basu mamaki . Wanda ya kira da samir din yazo da sauri ya dagani daga jikin alhajin ya kalli wancan matashin na dazu yace " Hafiz yi sauri dauki key din mota mu karasa da ita asibity. Suka fita da sauri su biyun. Alhajin ma da sauri zai bisu daya daga cikin matan nan tace " alhaji dare fa yayi kazo ka kwanta ina kuma zakaje? Ka bari kawai mn sukaita. Bai biyo ta Kansu ba ya fita da sauri. FMC YOLA suka kaini kasancewar shine asibity asibity mafi kusa dasu don ko da kafa mutum zaije. Ni dai kwata kwata bansan ma ina kaina yake ba bayan ciwon kai ga yunwa ma duka. Ban tashi sanin inda nake ba sai da nayi awanni biyu masu kyau . Ganinsu nayi su uku duk sun zauna sun zuban ido sunyi shiru. Gabana ne ya fadi na dada kallon su sosai nan da nan fa jikina ya bani wayan nan yanuwana ne wnn kuma shine mahaifina ! Da sauri na tashi na zauna ina kara kallonsu. Suma hankalinsu na kaina alhajin ne ya riko hannuna ya zuba min ido yace " ihisan Mamana kece? Ko dai .... Nima zuba mishi ido nayi a hankali na iya fadin tabbass shine a hoton da mama ta nuna min don dai kawai yanzu ya zama babban mutum sosai ne sabanin can kuma saurayine da bai wuce su yaya salman ba . A hankali nace" kaine mahaifina tabbas kaine a photo da mama na tanuna min. Ya gyada min kai da sauri ya kara rike hannayena yace " kwarai ihisan nine kuma duk da na rabu dake tun kina karama amma na gane ki ga kamannin amina sosai a tare da ke Mamana.... Ya karasa fada cikin hawaye da murmushi duk lokaci guda. Anan samir da Hafiz suka matso inda nake har hada baki suke " daddy ihisan ce. Daga musu kai yayi cikin tsan tsan farin ciki yace " itace kanwarkuce . Ya kalleni yace " ihisan wnn yayyunki ne samir da Hafiz. Samir kam rumgumeni yayi a jikinshi yayinda yake fadin " Allah mun gode maka da ka dawo mana da 'yar uwarmu. Ya dago kaina daga jikinsa yana murmushi anan ya Hafiz ma ya rumgumeni yace " kanwata munyi matukar farin ciki da ganinki. Ya kalleni cike da fara,a yace " kanwata daddy yana gaya mana labarinki kuma har da hotunanki dana mama muka gani. Murmushi nayi nima ina yiwa Allah Godiya sosai da ya takaita min wahala ya hadani da mahaifina ga yanuwana kuma. Daddy har lokacin hawaye ke zuba a idanunsa ya kasa tsaidasu . Ya kalleni yace" ihisan Mamana ina Amina? Nace "Tana kano tace in gaidaku . Da sauri ya daga hannu sama yace Alhamdulillah Allah mun gode maka. Anan fa ya samir ke tambayata yadda akayi naji ciwo akai. Nan na basu labari duk yadda nayi a hanya . Kuka ne ya kufce min nace " yanzu bansan wane hali Mamana zata shiga ba gashi wayarta ta bata nima nawa ya bata. Gaba daya sun tausaya min daddy yace"to wai suwayene wa,yan nan din? Hafiz ya karba yace " daddy ai ko shakka banayi matasan nan ne kungiyar 'YAN SHILA da suka addabemu da kwatan wayoyi da jakukkuna kuma har kashe mutum sunayi. Daddy yace " subhanallah !har yanzu matasan nan ba,a dauki mataki akansu ba? Yara kanana saboda Allah sun zama criminals nan gaba kadan in sun kara me muka San zasu zama? Ya samir yace " ai abin daddy sai dai muce Allah ya ktauta . Gaba daya mukace ameen . Daddy ya kalleni yace " ihisan Mamana karki damu ga wayata kisa numbern da kk rike sai ayi sauri a gayawa Amina abinda ake ciki kar ta shiga damuwa. Ya mika mun karamar wayarsa nan na tuna bayan num din mama sai na ya salman na rike. Don haka nasa num din ya salman na kira amma har ya yanke no answer .na kira har na gaji bai dauka ba. Anan ya samir yace " ki musu sending massage kawai. Ina cikin yiwa yaya salman massage aka kira assalatu don haka daddy yace " ihisan Mamana bari muje muyi sallah. A hankali nace "to sai kun dawo. Suka fita dukansu daddy kam sai da ya kuma waigowa gani yake kamar a in ya dawo bazai sameni ba. Bayan na turawa ya salman massage ba jimawa sai ga reply abin mamaki ina dubawa naga an rubuta. *OK* abin ya ban matukar mamaki don a tunani na in yagani zai kirani don duk masoyina yaka mata ya tayani murna yau gani cikin dangina mahaifina ya karbeni. Anya kuwa salman yana sona? Gaskia yau zuciyata ta tabbatar min salman ya daina sona don haka ya zama wajibi in cire ya salman a raina tunda ba shi kadai ne da namiji ba!!!!! Hauly ce👍🏻🥰 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰 *Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤* ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡39 ************Tuni daddy ya sanar da danginsa na nesa da kusa dawowar 'yarsa. Karfe shidda da rabi bayan an kawo breakfast na danci na samu nayi wanka na canza kayana don naji dauki yanzu sai dai kawai matsalar rashin bacci da gajia da kuma rashin sa mun mama a waya in sanar da ita yanda ake ciki.duk na bi na damu. Yayinda daddy kuma sai amsa waya yakeyi ana ta tayashi murna. Bayan ya je ya sa mu yy kinsa tsaf ya dawo da matan nan dukkansu biyu da wani kuma. Suma suna cike da farincikin ganina duk sai da suka rumgumeni ni dai binsu nake da kallo. Daddy yayi murmushi yace " Ihsan wnn da ke kusa dake babban yayanku ne awwal nasan mmnki ta baki labarinsa Na daga mishi kai yayinda na ke kallon ya awwal ina murmushi shima murmushin yake min . Daddy ya nuna dayan matar yace " wnn Haj rukayya itace uwargidata shekararmu goma da yin aure amma Allah bai bamu haihuwa ba. Ya kalli dayar kuma yana murmushi yace "wnn kuma gimbiya Sameera ce kanwata 'yar gidan me martaba itama yanzu shekararmu biyar da yin aure kuma itama bata haihu ba. Na bisu da kallo ina murmushi snn nace " ina mummyn mu ? Daddy ya danyi shiru yace " Jamila ko? Na daga mishi kai . Sai naga ya girgiza kaicikin wani yanayi yace " Jamila Allah ya mata rasuwa kusan shekara goma sha biyar knn yanzu sakamakon ciwon cancer na mahaifa. Gaskia abin ya matukar bani tausayi kai duniya! Jikina a mace nace" Allah ya mata Rahma Gaba daya sukace amin . Shiru nayi ina son tambayar labarin Haj rumaisa da Haj Zubaida da su goggo Ummi bakina yanai min nauyi saboda gajia da kuma bacci. Daddy yace yanzu ihisan ki daure ki tashi tunda an sallameki mu tafi babban gida tun dazu sai waya suke min suna tambayarki nace zamuzo domin na hana kowa zuwa asibity saboda yawansu. Nace" to ba komai. Na tashi aunty rukaiyace ta rike hannuna muka tafi har inda motar daddy yake ya awwal ne ya tuka daddy na gefensa nida su aunty a baya sai kuma ya Hafiz da ya samir sun tafi a motarsu daban. Lamido palace muka fara zuwa muka shiga fada muka gaida lamido a fada sosai ya nuna murnarsa a fili ya taya daddy murna. Munje gidansa mun gaida matansa duk sun tsufa harshi mai martaba. Kamin mu bar gidan mai martaba ma mun kai awa biyu daga nan muka fita sai family house gidan galadima. Tabdi ranar naga jama,a dama haka nake da gata amma nake shan gori gunsu inna. Dangina na nesa dana kusa sunzo 'yan kalilan ne da suke kasashen waje basu zo ba . Da kunga yanda aka cika gidan nan zaku dauka biki akeyi gagarumi. Sashi sashi muka shiga na gidan kamin muka isa gunsu Haj rumaisa. Allah sarki duk sun tsufa sai dai dake akwai kudi basu lalace ba da kwarinsu. Haj rumaisa da Haj Zubaida kam rumgumeni sukayi sai kuka suna ta sambatu Haj rumaisa sai fadi take "Allahu Akbar Allah mai iko Allah mun gode maka da ka dawo mana da ihisan cikinmu. Ta kalleni tace" rumaisa tuni muka cire ran gsninku amma kinga ikon Rabbi yau sai gaki rabon mu dake tin kina 'yar shekara biyu. Ta dada fashewa da kuka . Goggo Ummi da goggo karima Suma sun shigo haka suka rumgumeni suna kuka nima na shiga tayasu. Daddy ma hawayen ke zuba yana gogewa da hankacif. Haka akayita shigowa ana min sannu da zuwa yayinda umma da Haj Zubaida suka dinga gabatar min da kowa. Kai masha Allah dangina kaf ban sami matsala da kowa ba sun karbeni hannu bibbiyu. A ranar wasu suka koma ciki har da goggo Ummi da karima. Har Karfe tara na dare snn aka gama watsewa sai ' yan gida. Anan ya awwal ma da matarsa hadiza har dansu daya me sunan daddy .suka mn sallama suka tafi. Daddy ya kallisu aunty samira yace" to muma sai mu tafi ko? Anan ummah tace"lamido a bar mana ihisan ta kwana...... Ya Hafiz ya tari numfashinta da fadin " bazata kwana ba bamu gaji da kallonta ba kinjiki da wata magana 'yaruwarkice? Harararsa tayi ta ce " ja,iri to sai ta kwana ko ba 'yaruwataba. Haj Zubaida tayi dariya tace" mai gidan nawa kk masa haka? Ya samir yace wa umma kinga tsohuwa ihisan fa ba lfy ne da itaba ga gajia ga bacci don haka tana bukatar hutu sosai. Daddy dai baisa baki ba haka ya samir ya dinga lallabasu har suka yadda muka tafi Bayan mun isa gidanmu daddy ya kalli aunty rukayya yace "rukayya ihisan kuje ta kwana a dakinki kamin a gyara mata daki. Aunty samira tace" Alhaji ai tuni nasa an gyara mata daki. Daddy yace" ai so nike asa mata komai sabo fil a dakinta. Aunty rukayya tayi murmushi tace" gaskia ne alhaji .to ihisan muje mu kwanta. Ya samir yace " akwai maganinta da alluranta guda daya bari muje na mata inyaso sai tayi baccin. Daddy yace " to ba matsala. Ya kalleni yace " Mamana ina fatan baki da wata matsala ? Na sunkuyar da kai nace " eh sai dai ina son inyi magana da Mamana. Yace " eh gaskia kam ya kamata kuyi magana amma kiyi hkr zuwa gobe insha Allah zamu San yadda zamuyi mu nemota kiyi hkr kinji? Nace " babu komai daddy na gode. Anan ya mun saida safe. A dakin aunty rukayya bayan ya samir ya bani magunguna nasha ya zuba min ido yace " ihisan me ya faru nake jin numfashinki sama sama ? Nace " sanyin nan da akeyi ne. Yace " kina da asma ko? Na daga mishi kai yace" da kinyi magana da wuri na kawo miki magani ai ina inhaler dinki? Nace " yana cikin jakata da aka sace. Da sauri yace" to fa gaskia bazan barki ki kwana haka ba ina zuwa. Ya tashi da sauri ya fita kan ya dawo ma nayi bacci. Da kyar aunty rukayya ta tasheni nayi sallar asuba na idar nayi azkar ina shirin komawa bacci daddy ya shigo dakin na gaisheshi cike da fara,a ya amsa hade da fadin ihisan Allah ya maki albarka. Nace "amin Yace " dama nazo in dubaki ne ina fatan dai ba wani abu koh? Nace" eh daddy ba komai. Yace " to shikenan yanzu kiyi bacci lfy. Daga nan ya fita aunty samira ma ta shigo muka gaisa snn aunty rukayya ta kawo min tea tace " Ihsan kisamu kisha tea samir zai zo ya baki maganinki kamin ki koma bacci. Haka dai suka dinga dawainiya dani ba,a bari ko tsinke in daga ni dai aikina daga bacci sai cin abinci sai wanka. Daddy ya kawo min wayarsa yace" ihisan har na fita sai naga an turo maki sako ta wayata. Ya mika min na karba ina dubawa naga ya salman ne ya turo min tex kamar haka *Ga* *num* *din* *Goggo* *Amina* Murmushi nayi na duba naga num din ta nada ne inaga tayi wlcm back ne. Na kalli daddy nace " ya salman ne ya turo min num din Mamana tayi wlcm back. Murmushi yayi yace OK kema ya kamata ki samu kiyi ai. Yanzu kirata sai kuyi magana . Nace to Nan nayi dialing num din mama ba jimawa ta daga hade da sallama. Na amsa hade da fadin mama nice Tace" rumaisa fatan dai komai lfy hankali na duk a tashe salman ne yace min kin isa lfy ba komai hakane? Murmushi nayi nace hakane mama kuma na sami kowa lfy kuma kowa ya karbeni cikin farin ciki. Tace " Alhamdulillah Allah mun gode maka yanzu sai na sami lokaci in kiraki insha labaru. Sai dai layinki duk basa tfy meyasa? Nace" mama wayar ya batane amma zan yi wlcm back sai muyi magana . Tace " to ba matsala ina mahaifinku ? Murmushi nayi na kalli daddy nace " gashina nan ko na bashi....... Kamin na karasa ta katse. Daddy kuwa tuni mika hannu yana murmushi yaji ina cewa in bashi. Jikina a mace nace " ta katse. Ya karbi wayar sa yace " ihisan karki damu komi ze wuce insha Allah kinji? Kai kawai na daga masa. Sati Na daya a gidanmu sai lokacin mutane suka rage zuwa ganina. Yanzu na saba kullum ina tare da yayyuna da daddy muna hira gaskia naga gata. A yanzu in kunga wayar hannuna ma se kun rike baki ga kyau ga tsada kuma furniture din dakina ma kawo photuna akayi in zaba na zabi komai pink . Bayan Na samu an zaga dani koina dangi 'yanuwa da abokan arziki. Watarana daddy ya tafi dani gidansu gunsu ummah bayan mun gaisa dake ranar Haj Zubaida bats nan. Anan na kwashe labarina kaf Na gayawa daddy da ummah da irin wahalar da mama tasha dani kaina. Ummah kam kuka sosai a yayinda daddy ma idanunsa sunyi jazir tsabar tashin hankali. Yace" ihisan duk abun nan ya faru a rashin sani .Jamila itace tayi sanadiyar rabuwarmu duk da bana son tuna abunda ta yi tunda tana kwance a kabarinta yanzu. Bayan tfyrku da mahaifiyarki ban sake gane inda hankalina yake ba komai sai abinda Jamila tace ko nan gidan na daina zuwa gaida umma saida suka shiga yi mun addua sosai .an dauki tsawon lokaci kamin nan Allah ya kawo karshen abun a in da Jamila ta fara rashin lfy wasa wasa har ta kwanta mun je asibitoci ansha yi mata aiki amma ina abun ya gagara haka muna ji muna gani cancern jikinta yayi chronic . Jamila ta tabbatar ciwonta bana tashi ba shine fa ta fadi dukkan abinda ta aikata kuma ta nemi gafara a in da tace don Allah ko bayan ranta in nemo amina don ta yafe mata da zaluncinda ta mata. Bayan rasuwar Jamila Ihsan hankalina yayi matukar tashi musamman in na tuna yanda na rabu da mamanki. Na tafi Kaduna da kyar na gane gidansu amina saboda anguwan ta kara cika da gine gine amma abin mamaki gidan nan na yayyun mamanki na samu ya kone sakamakon wutan NEPA da aka kawo da karfi. Nan mutanen anguwan suka tabbatar min da kowa na gidan babu Wanda ya fita da rai. Hankalina yayi mummunar tashi Wanda tun a lokacin na kamu da hawan jini nasha jinya sosai Wanda ya dauki tsawon lokaci kamin na warke amma zuciyata ta kasa hakuri sai da na kuma dawowa Kaduna da photon mamanki ina nemanta anan ne na fahimci ba Ku ne a gidan lokacin da akayi gobara ba don da nayi bincike sosai na tabbatar 'yan hayane ma a gidan . Amma abun mamaki kowa na nuna Wa photon mamanki sai suce basu Santa ba.da yake Allah baiyi zamu hadu ba har kanon ma naja don ta taba bani labarin cewa su kanawa ne. Dole na sawa raina dangana na shiga adduan Allah ya bayyana mun Ku. Bayan rasuwar Jamila da shekara biyar ne na auri rukayya mutumiyar kirki tana da hankali da biyayya sai dai Allah bai bani haihuwa da ita ba Bayan shekaru kadan shine maimartaba yabani auran 'yarsa Sameera . Ya numfasa ya kalleni yace ' ihisan kinji irin abubuwa da suka faru bayan barinku garin nan da mamanki. Ni da ummah duk kuka muke. Anan na share hawayena na shiga baiwa ummah hkr ina nunan mata komai ya wuce yanzu kam. Anan daddy ya barni ya tafi. Kwanan biyu a gidan snn driver ya maidani gidanmu. Nan na tarar tuni an gyara min dakina tsaf komai sabo dal kuma komai pink ne da white har toilet . Gaskia naji dadi ba kadan ba naje nayiwa daddy Godiya . Murmushi yayi yace" Mamana banda wani buri a rayuwa da ya wuce in faranta miki rai karki damu wnn kadan ne daga cikin abinda na miki tanadi.ihisan duk abinda kk so kizo ki sanar dani inshaa Allah zan miki Nace " nagode daddy Allah ya saka maka da gidan aljannah. Yace "ameen Mamana yanzu abinda nake so dake shine ki tayani addua sosai domin ina son in dawoda mahaifiyarki sai dai kinsan ba karamin aiki bane ta yarda dole sai mun dage da addua. Cikin jin dadi nace " insha Allah zata amince daddy . Yace "Allah yasa. Nace " ameen daddy . Yace "akwai hotunan motoci a wurin hafiz ya nuna miki ki zabi wacca kk so. Zaro ido nayi nace " duk ni kadai daddy? Murmushi yayi yace"kwarai da gaske Mamana ai komai na miki ban fadi ba yanzu lokaci ne da zaki ji dadi sosai a rayuwa kema. Godiya na dinga zuba masa. Anan aunty samira ta shigo ta samemu tace " ihisan dinkunanki sun dawo muje ki gwada duk Wanda bai miki ba sai a mayar. Ni dai yanzu kam na ma rasa mai zance sai dai Alhamdulillah Allah. Hotuna na dunga yi ina turawa mama dasu faiza don ina waya dasu sosai . Hutunmu ya kusa karewa yanzu kam gaskia ba don mkranta da mama ba banga abinda zai maidani kano ba. Naci kwalliyata mai rai da lfy ina kwance kan makeken gado na ina ta hira da faiza da sakina a watsapp don group muka bude mu uku kawai muna zuba iya shege son ranmu. Ya samir ne ya shigo da sallama . Na dago ina murmushi nace "yaya har ka dawo? Yace" ban tafi ba sai anjima yanzu dai ki aje wayarki ki tashi kizo muje kiga wani surprise . Murmushi nayi na tashi hade da fadin " ni dai dadi zai kashe ni yaya bayan jiya ma kabani surprise din motata data karaso. Hannuna ya kama hade da fadin " zo muje ke dai. Muka fita da sauri a harabar gida ya min nuni yace " kinsan waye wancan? Na kalli inda ya min nuni rass naji gabana ya fadi anan na fara murza idona don in tabbatar da abinda nake gani. Har yanzu shi nake gani da sauri na juya da nufin inyiwa ya samir magana amma sai naga wayam babushi. Wayyo to ko mafarki nakeyi? Ina tsaye kamar gumki har ya karaso gabana. Da kyar na iya budan baki nace " yaya Kaine? Ba zato ba sammani naga ya sakar min murmushi hade da gyada kai yace " kwarai kuwa nine rumaisa. Mamaki ne ya cika ni sosai wai ya salman ne a gidanmu to waya nuna masa kuma mai ya kawo shi? Ban Sani ba a fili na fadi maganar. A hankali ya amsa min da fadin " rumaisa meye tunaninki ? Kina ganin zan iya rayuwa ba tare da ke bane? Ya danyi shiru snn yace " rumaisa bazan taba iya rabuwa da ke ba so duk India kk shiga a fadin duniya sai na nemoki . Ni dai tsabar mamaki ban iya cewa komai ba ....... Hauly ce👍🏻🥰 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰 *Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤* ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡40 *********Ganin shirun yayi yawa yasa shi isa dab dani yace" Rumaisa kinyi farin ciki da ganina? Murmushi nayi nace " kwarai da gaske kuma na yarda da abinda kace yaya . Ya danyi murmushi yace " to baki min sannu da zuwa ba. Russunawa nayi na karbi jakar da ya rataya ina murmushi nace" yaya barka da zuwa. Na fada yayinda na rataya jakar nace " mu isa ciki...... Ban gama rufe bakina ba naga mai gadi ya bude kofa motar daddy ne ya shigo. Da sauri na kalli ya salman nace" kaga ma ga daddy ya dawo. Ya juya ya kalli motar ba tare da yace komai ba. Bayan driver ya gama parking ya sauko da sauri ya budewa daddy kofa. A yayinda muka karasa nida ya salman . Murmushi nayi nace " daddy sannu da dawowa. Shima murmushi ya sakar min yace yawwa mama na . Ya salman ya Dan russuna ya fara gaida daddy. Ya amsa fuska sake nace " daddy yaya salman ne ......... Cikin fara,a daddy yace" Masha Allah dana sannu da zuwa. Ya fadi hakan ne yayinda ya rumgume ya salman yace" naji dadin zuwanka kwarai dana. Snn ya kalleni yace" mamana yanzu ne zuwansa. Nace" eh. Yace OK to muje ciki ai ya kwaso gajia. Suka wuce yana rike da hannun ya salman kamar wani yaro karami. Ina biye dasu a baya dariya nake musu kasa kasa don na lura ya salman nauyin daddy yake ji sosai baisan daddy kan ba ruwansa ba . Har palonsa muka shiga yace " ihisan kira min Sameera .....au gata nan ma. Aunty samira ne ta shigo taci kwalliya cikin less mai tsadan gaske tana zuba kamshi . Ta karaso wajanmu tana murmushi tace." Sannu da dawowa ranka ya Dade. Daddy yace " yawwa gimbiyar mata. Ta sake fadada murmushi snn ta kalli ya salman tace" sannu da zuwa bako mukayi? Daddy yace " babba ma kuwa .wnn da kk gani surukinkine . Aunty samira ta kalleni da alamun neman Karin bayani gyada mata kai nayi nace " ya salman ne aunty. Murmushi ta yi tace" da kyau 'yata. Anan suka gaisa daddy yace "kindai shirya dining koh ? Aunty samira ta ce " sosai ma alhaji Yace " to kira rukayya tazo ta gaisa da surukinta kafin muci abinci. Tace " to" Ta fita da sauri ni dai Sai murmushi nske tayi tun dazu domin naji dadin zuwan ya salman kwarai .Allah sarki so duk abin nan da ya faru a baya amma gashi lokaci guda na manta. Bayan an gaggaisa daddy yace " inje da ya salman dining yaci abinci kamin nan shi zaije ciki. Duk sun watse suka barmu mu . Ya salman yace " Rumaisa gaskia na tayaki murna haduwa da mahaifinki da 'yan uwanki.mahaifinki mutumin kirki ne hakama 'yan uwanki Masha Allah! Murmushi nayi nace " yaya na gode ya kabar mutan gida ina su kawu ya Mamana? Yace " duk suna lfy Sai dai ban fadawa kowa nan zanzo ba so ba Wanda yasan nazo gunki. Nace " to waya baka address din gidan nan? Yace" tuntuni goggo Amina ta sanar dani . Nace " ikon Allah yaya naji dadin ganinka kwarai da gaske .domin ko kadan bana jin dadin fushi da kakeyi dani duk naji kano ya fitan min a rai. Na karasa fada kaina a sunkuye shiru yayi baice komai ba . Jikina a mace nace" yaya don Allah ka yi hkr nasan abinda nayi bai dace ba kuma ya kauce amma wlh yaya nima bansan me ya faru dani a wancan lokacin ba har........ Hannu ya daga min tuni yanayin fuskarsa ta sauya yace,don Allah ki bar wancan maganar ya wuce a wurina kuma ni ba na fushi dake kawai ina bakin cikin abinda ya samekine.amma komai ya wuce insha Allah gani na dawo gareki da soyayyata zan Dora daga inda na tsaya. Sunkuyar da kai nayi cikin jin kunya sosai nasa hannuna na rufe fuskata. Dan murmushi yayi ya taso ya isa gabana ya dan rankwafo a hankali yace " baby tsantsar so nake miki zallah bazan taba iya rabuwa da ke ba .abinda ya faru baya kaddarace baki isa ki tsallaka ba amma ina son ki Sani ni salman ke nake so ba Gangar jikinki ba !!! Maganarsa ta karshe ta matukar girgizani har na dago ba shiri na kalleshi dama zarginda ya salman ke min knn? Ganin fuskata ta sauya yasa shi fadin " no kar ki damu abinda Na gaya miki gaskia ne har cikin raina. Murmushi na sakar masa nace " yaya Na gode tabbas ka cika masoyi na gaske .ni kuma duk randa ka aureni zan baka babban *SURPRISE* Na karasa fada ina murmushi shima fuska sake yace " Allah ya nuna mana rai da lfy *IHISAN* 'yar gatan daddy Dariya nayi nace " kai yaya .to muje kaci abinci ka samu ka huta. Yace " ai ba gajia tunda jirgine Abuja to yola ba nitsa. Muka isa dining na gyara mishi wurin zama ya zauna hade da fadin " thank you. Ruwa mai sanyi na dauko a fridge na zuba masa a cup snn na mika masa ya karba . Nace " to yanzu me za,a zubo maka tuwon semo miyar kuka ko jallof da peppe chicken ko dai pepe soup na rago zan zubo maka akwai kuma snacks. Tunda na fara magana ya zuban ido har na gama baice komai ba sai kallona kawai yakeyi. Da sauri nace "au afwan yayana nasan kafi son tuwo musamman semo da miyar kuka ko kubewa. Ya saki fuska yace " ai na dauka ko kin manta abubuwanda nafi so ne? Na ce " tab na isa ? Na fada ina murmushi na dauko plet na masa serving tuwon semo miyar kuka da yasha naman rago ga daddawa da man shanu .gaskia mutanen yola sun cira tuta wajan dafa miyar kuka . Ya salman yaci sosai don ya yaba miyar sosai har yace min " gaskia girkin nan yayi ki koya sosai ina so. Nayi murmushi nace to. A yayinda yake wanke hannunsa na mika masa tissue nace " amma yaya bakaci da yawa ba fa in kara maka mana. Yace" what! A gidan surukai fa nake kuma ma am OK nagode sosai. Nace " to muje ka huta ya samir Na jiranka in yaso da yamma Sai muje gidan galadima. Muka fita Na kaishi gun ya samir don ya samu ya huta. Ni. Kuma na dawo dakina Na fada gado zuciyata cike da farinciki nan na fara tunanin me zanyiwa ya salman in Dada burgeshi domin ina matukar ji da *SOJAN* nan nawa. Aunty samira ce ta shigo ta sameni. Bayan ta zauna kusa dani ta kalleni tana murmushi tace" ihisan yau dai naga ya salman dinnan da kk damunmu da sunanshi motsi kadan yayana yayana yayana!!! Dariya mukayi lokaci guda nace " aunty to ya kk ga yayan nawa. Tace " eh na ganshi kyakkyawa ga cikar kamala ga kuma kwarjini ga natsuwa amma fa yayan baki yanada matsala daya. Fuskata tuni ta sauya nace" meye matsalar aunty gimbiya? Tace" yayan naki baya dariya Sam kuma baya magana sosai me yasa? Dariya nayi nace " aunty yayana haka halittarsa yake amma fa a hankali in ya saba da mutum to zakuyi hira kuma zaiyi miki fara,a kuma kinga sojane a bariki ba,a San wani dariya ba... Dariya mukayi lokaci guda kamar kawaye . Aunty rukayya ma ta shigo tana cewa" daryar mi akeyi? Aunty samira tace " tadin surukina muke. Aunty rukayya tace " gaskia surukin mu ya hadu sai dai rashin magana ko dai kunya ne. Nace " eh aunty. Ta yi murmushi tace " to ba wnn ya kawo ni ba nazo ne in tambayeki me surukin nawa yafi so a dafa masa. Nace uhmm to surukin naku Dan gargajiyane tunda yaci tuwo da rana to da daddare kunu zaisha sai kuma in yazo kwanciya yakan sha fruits shikenan. Aunty rukayya tace " OK to da safe fa ina son komai ya zama ready ne kar a sami matsala kinsan daddy zai yi fushi . Nayi murmushi nace " breakfast dinnan na lura bai cika zabe ba amma na lura yana son tea da bread da pepe soup ko wane iri. Aunty rukayya tace " O Ihsan kinaji da yayan nan naki. Sunkuyar da kai nayi nace "aunty ..... Tace " banson sunan nan na aunty kuce mun Momy kamar yadda yayyunki ke ce mun ga nan auntynku. Ta nuna aunty samira . Mukayi dariya .aunty samira tace " kai Momy kema fa kamar auntynce don baki tsufa ba. Aunty rukayya dai fita ta yi ta barmu. Na kalli aunty samira nace " yawwa aunty dama ina son nono mai kyau ko fresh milk yayana yana so.naga rannan an kawo wa daddy. Tace " eh ai sati sati ake kawo masa madarar mu muke maidashi ( kindirmo) gashi na wnn satin ya kare wlh.dama daga garken sa ake tatsowa... Nace " kash amma banji dadi ba yanzu aina zan sa mu? Tace " kwantar da hankalinki yanzu ma ba don yamma yayi ba da sai muce a kawo amma gobe in Allah ya yarda zan sa a kawo miki fresh milk sabon tatsa ma kuwa. Nace " to aunty Allah ya kai mu. Tace " amma na lura kin damu sosai me zai hana in aiki driver akwai SARE KOSAM can kusa da Jippu jam sai a siyo mishi. Nace " yawwa aunty bari ma naje da kaina ina son in dana motata dama ko zaki fadawa daddy? Tace ba komai kije amma kar ki Dade Allah ya tsare ba dai kin tabbatar kin iya driving ba? Nace " eh. Tace " to sai kin dawo. Tashi nayi da sauri na dauki gyalena na yafa snn na dau jakata da key din motata. Na fita harabar gida nan nace mai gadi ya buden get. Ba jimawa naja motata na fita bansha wahalar gane kwatancen ba ina isa naga an rubuta *SARE* *KOSAM* Bayan na gama parking na sauka na rufe motata na shiga gaskia wurin ya burgeni na tarar da mutane da yawa wasu suna shan fura da nono wasu madara wasu kuma youghut . Gaskia naja hsnkalin mutane sosai domin ba maza kadai ba harda mata bina suke da ido . Wasu har daga min gaisuwa suke da fillanci bansan me suke fadi ba amma dai komai akace min nakance musu ' *JAM* '(lfy) Bayan na sayi fresh milk da kindirmo na fita da sauri wani har bina yayi yana ce min da fulatanci " hajjajo noi chomri( hajiya ya gajia.?) Nace " bana jin fulatanci yi hkr kuma sauri nake ..... Karar wayata ta katseni na Ciro ta a jakata ina dubawa naga sunan daddy da sauri nayi receiving kamin nayi magana yace " ihisan kina ina ne? Nace " yanzu ina wajen jippu jam .. Ya katseni da fadin to ki dawo karki tsaya koina garin nan namu cike yake da kidnappers ga kuma wayan nan matasan masu kwacen wayoyi ki kula sosai Allah ya dawo dake lfy. Aikuwa a tsorace nace amin daddy . Tab ai ban biyo ta kan wnn mutumin ba na fada mota ina waigawa inga su waye a bayana ganin ba kowa yasa na fizgi motar da gudu sai gida . Ina fita daga motar ya salman da ya samir suka karaso guna ya samir yace " ke ihisan yaushe kk gama gane kan garin ne da zaki fita ki rufa mana asiri don Allah. Na kalli ya salman snn na kalli ya samir a shagwabe nace " naga duk hankalinku ya tashi aunty samira ma sai kirana take ina tuki .ban fa yi nitsa ba naje na siya ma yayana ne fura da nono sai fresh milk don nasan yana so ko yaya? Na fada ina kallon ya salman yace " hakane amma da baki fita ba sai ki aika kinga ke bakuwa ce a garin kuma macece don Allah kar ki kuma fita ke kadai kanwata. Na bata fuska kamar zan yi kuka nace " to . Daga nan na wuce ciki. Gun daddy naje tukun kamin na koma dakina na sake wanka na sake shiryawa cikin material dogon Riga na zauna gaban madubi na sake zuba make up . Bayan na gama na je na sami su yaya samir muka tafi gidan galadima. Su ummah da mama sai Jan salman suke da wasa suna ya rabu dani ga su nan sun fini kyau . Gaskia ya salman yaji dadin zuwansa yola domin an karramashi sosai . Kwanansa biyu duka daddy ya hana shi kwana hotel a gida yake kwana da ya samir sun saba sosai . Gaba daya naji ba dadi da yazo tfy duk da nasan nima na kusa tfy tunda mkranta za,a bude. Daddy yayiwa ya salman Godiya sosai da irin kulawar da ya bani don na bashi labarin. Ni da ya samir muka rakashi airport duk naji ba dadi wlh banki muyita soyaiyar mu a yola don ba sa,idon su inna . Hauly ce🥰👍🏻 [9/25, 6:21 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰 *Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤* ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡40 *********Ganin shirun yayi yawa yasa shi isa dab dani yace" Rumaisa kinyi farin ciki da ganina? Murmushi nayi nace " kwarai da gaske kuma na yarda da abinda kace yaya . Ya danyi murmushi yace " to baki min sannu da zuwa ba. Russunawa nayi na karbi jakar da ya rataya ina murmushi nace" yaya barka da zuwa. Na fada yayinda na rataya jakar nace " mu isa ciki...... Ban gama rufe bakina ba naga mai gadi ya bude kofa motar daddy ne ya shigo. Da sauri na kalli ya salman nace" kaga ma ga daddy ya dawo. Ya juya ya kalli motar ba tare da yace komai ba. Bayan driver ya gama parking ya sauko da sauri ya budewa daddy kofa. A yayinda muka karasa nida ya salman . Murmushi nayi nace " daddy sannu da dawowa. Shima murmushi ya sakar min yace yawwa mama na . Ya salman ya Dan russuna ya fara gaida daddy. Ya amsa fuska sake nace " daddy yaya salman ne ......... Cikin fara,a daddy yace" Masha Allah dana sannu da zuwa. Ya fadi hakan ne yayinda ya rumgume ya salman yace" naji dadin zuwanka kwarai dana. Snn ya kalleni yace" mamana yanzu ne zuwansa. Nace" eh. Yace OK to muje ciki ai ya kwaso gajia. Suka wuce yana rike da hannun ya salman kamar wani yaro karami. Ina biye dasu a baya dariya nake musu kasa kasa don na lura ya salman nauyin daddy yake ji sosai baisan daddy kan ba ruwansa ba . Har palonsa muka shiga yace " ihisan kira min Sameera .....au gata nan ma. Aunty samira ne ta shigo taci kwalliya cikin less mai tsadan gaske tana zuba kamshi . Ta karaso wajanmu tana murmushi tace." Sannu da dawowa ranka ya Dade. Daddy yace " yawwa gimbiyar mata. Ta sake fadada murmushi snn ta kalli ya salman tace" sannu da zuwa bako mukayi? Daddy yace " babba ma kuwa .wnn da kk gani surukinkine . Aunty samira ta kalleni da alamun neman Karin bayani gyada mata kai nayi nace " ya salman ne aunty. Murmushi ta yi tace" da kyau 'yata. Anan suka gaisa daddy yace "kindai shirya dining koh ? Aunty samira ta ce " sosai ma alhaji Yace " to kira rukayya tazo ta gaisa da surukinta kafin muci abinci. Tace " to" Ta fita da sauri ni dai Sai murmushi nske tayi tun dazu domin naji dadin zuwan ya salman kwarai .Allah sarki so duk abin nan da ya faru a baya amma gashi lokaci guda na manta. Bayan an gaggaisa daddy yace " inje da ya salman dining yaci abinci kamin nan shi zaije ciki. Duk sun watse suka barmu mu . Ya salman yace " Rumaisa gaskia na tayaki murna haduwa da mahaifinki da 'yan uwanki.mahaifinki mutumin kirki ne hakama 'yan uwanki Masha Allah! Murmushi nayi nace " yaya na gode ya kabar mutan gida ina su kawu ya Mamana? Yace " duk suna lfy Sai dai ban fadawa kowa nan zanzo ba so ba Wanda yasan nazo gunki. Nace " to waya baka address din gidan nan? Yace" tuntuni goggo Amina ta sanar dani . Nace " ikon Allah yaya naji dadin ganinka kwarai da gaske .domin ko kadan bana jin dadin fushi da kakeyi dani duk naji kano ya fitan min a rai. Na karasa fada kaina a sunkuye shiru yayi baice komai ba . Jikina a mace nace" yaya don Allah ka yi hkr nasan abinda nayi bai dace ba kuma ya kauce amma wlh yaya nima bansan me ya faru dani a wancan lokacin ba har........ Hannu ya daga min tuni yanayin fuskarsa ta sauya yace,don Allah ki bar wancan maganar ya wuce a wurina kuma ni ba na fushi dake kawai ina bakin cikin abinda ya samekine.amma komai ya wuce insha Allah gani na dawo gareki da soyayyata zan Dora daga inda na tsaya. Sunkuyar da kai nayi cikin jin kunya sosai nasa hannuna na rufe fuskata. Dan murmushi yayi ya taso ya isa gabana ya dan rankwafo a hankali yace " baby tsantsar so nake miki zallah bazan taba iya rabuwa da ke ba .abinda ya faru baya kaddarace baki isa ki tsallaka ba amma ina son ki Sani ni salman ke nake so ba Gangar jikinki ba !!! Maganarsa ta karshe ta matukar girgizani har na dago ba shiri na kalleshi dama zarginda ya salman ke min knn? Ganin fuskata ta sauya yasa shi fadin " no kar ki damu abinda Na gaya miki gaskia ne har cikin raina. Murmushi na sakar masa nace " yaya Na gode tabbas ka cika masoyi na gaske .ni kuma duk randa ka aureni zan baka babban *SURPRISE* Na karasa fada ina murmushi shima fuska sake yace " Allah ya nuna mana rai da lfy *IHISAN* 'yar gatan daddy Dariya nayi nace " kai yaya .to muje kaci abinci ka samu ka huta. Yace " ai ba gajia tunda jirgine Abuja to yola ba nitsa. Muka isa dining na gyara mishi wurin zama ya zauna hade da fadin " thank you. Ruwa mai sanyi na dauko a fridge na zuba masa a cup snn na mika masa ya karba . Nace " to yanzu me za,a zubo maka tuwon semo miyar kuka ko jallof da peppe chicken ko dai pepe soup na rago zan zubo maka akwai kuma snacks. Tunda na fara magana ya zuban ido har na gama baice komai ba sai kallona kawai yakeyi. Da sauri nace "au afwan yayana nasan kafi son tuwo musamman semo da miyar kuka ko kubewa. Ya saki fuska yace " ai na dauka ko kin manta abubuwanda nafi so ne? Na ce " tab na isa ? Na fada ina murmushi na dauko plet na masa serving tuwon semo miyar kuka da yasha naman rago ga daddawa da man shanu .gaskia mutanen yola sun cira tuta wajan dafa miyar kuka . Ya salman yaci sosai don ya yaba miyar sosai har yace min " gaskia girkin nan yayi ki koya sosai ina so. Nayi murmushi nace to. A yayinda yake wanke hannunsa na mika masa tissue nace " amma yaya bakaci da yawa ba fa in kara maka mana. Yace" what! A gidan surukai fa nake kuma ma am OK nagode sosai. Nace " to muje ka huta ya samir Na jiranka in yaso da yamma Sai muje gidan galadima. Muka fita Na kaishi gun ya samir don ya samu ya huta. Ni. Kuma na dawo dakina Na fada gado zuciyata cike da farinciki nan na fara tunanin me zanyiwa ya salman in Dada burgeshi domin ina matukar ji da *SOJAN* nan nawa. Aunty samira ce ta shigo ta sameni. Bayan ta zauna kusa dani ta kalleni tana murmushi tace" ihisan yau dai naga ya salman dinnan da kk damunmu da sunanshi motsi kadan yayana yayana yayana!!! Dariya mukayi lokaci guda nace " aunty to ya kk ga yayan nawa. Tace " eh na ganshi kyakkyawa ga cikar kamala ga kuma kwarjini ga natsuwa amma fa yayan baki yanada matsala daya. Fuskata tuni ta sauya nace" meye matsalar aunty gimbiya? Tace" yayan naki baya dariya Sam kuma baya magana sosai me yasa? Dariya nayi nace " aunty yayana haka halittarsa yake amma fa a hankali in ya saba da mutum to zakuyi hira kuma zaiyi miki fara,a kuma kinga sojane a bariki ba,a San wani dariya ba... Dariya mukayi lokaci guda kamar kawaye . Aunty rukayya ma ta shigo tana cewa" daryar mi akeyi? Aunty samira tace " tadin surukina muke. Aunty rukayya tace " gaskia surukin mu ya hadu sai dai rashin magana ko dai kunya ne. Nace " eh aunty. Ta yi murmushi tace " to ba wnn ya kawo ni ba nazo ne in tambayeki me surukin nawa yafi so a dafa masa. Nace uhmm to surukin naku Dan gargajiyane tunda yaci tuwo da rana to da daddare kunu zaisha sai kuma in yazo kwanciya yakan sha fruits shikenan. Aunty rukayya tace " OK to da safe fa ina son komai ya zama ready ne kar a sami matsala kinsan daddy zai yi fushi . Nayi murmushi nace " breakfast dinnan na lura bai cika zabe ba amma na lura yana son tea da bread da pepe soup ko wane iri. Aunty rukayya tace " O Ihsan kinaji da yayan nan naki. Sunkuyar da kai nayi nace "aunty ..... Tace " banson sunan nan na aunty kuce mun Momy kamar yadda yayyunki ke ce mun ga nan auntynku. Ta nuna aunty samira . Mukayi dariya .aunty samira tace " kai Momy kema fa kamar auntynce don baki tsufa ba. Aunty rukayya dai fita ta yi ta barmu. Na kalli aunty samira nace " yawwa aunty dama ina son nono mai kyau ko fresh milk yayana yana so.naga rannan an kawo wa daddy. Tace " eh ai sati sati ake kawo masa madarar mu muke maidashi ( kindirmo) gashi na wnn satin ya kare wlh.dama daga garken sa ake tatsowa... Nace " kash amma banji dadi ba yanzu aina zan sa mu? Tace " kwantar da hankalinki yanzu ma ba don yamma yayi ba da sai muce a kawo amma gobe in Allah ya yarda zan sa a kawo miki fresh milk sabon tatsa ma kuwa. Nace " to aunty Allah ya kai mu. Tace " amma na lura kin damu sosai me zai hana in aiki driver akwai SARE KOSAM can kusa da Jippu jam sai a siyo mishi. Nace " yawwa aunty bari ma naje da kaina ina son in dana motata dama ko zaki fadawa daddy? Tace ba komai kije amma kar ki Dade Allah ya tsare ba dai kin tabbatar kin iya driving ba? Nace " eh. Tace " to sai kin dawo. Tashi nayi da sauri na dauki gyalena na yafa snn na dau jakata da key din motata. Na fita harabar gida nan nace mai gadi ya buden get. Ba jimawa naja motata na fita bansha wahalar gane kwatancen ba ina isa naga an rubuta *SARE* *KOSAM* Bayan na gama parking na sauka na rufe motata na shiga gaskia wurin ya burgeni na tarar da mutane da yawa wasu suna shan fura da nono wasu madara wasu kuma youghut . Gaskia naja hsnkalin mutane sosai domin ba maza kadai ba harda mata bina suke da ido . Wasu har daga min gaisuwa suke da fillanci bansan me suke fadi ba amma dai komai akace min nakance musu ' *JAM* '(lfy) Bayan na sayi fresh milk da kindirmo na fita da sauri wani har bina yayi yana ce min da fulatanci " hajjajo noi chomri( hajiya ya gajia.?) Nace " bana jin fulatanci yi hkr kuma sauri nake ..... Karar wayata ta katseni na Ciro ta a jakata ina dubawa naga sunan daddy da sauri nayi receiving kamin nayi magana yace " ihisan kina ina ne? Nace " yanzu ina wajen jippu jam .. Ya katseni da fadin to ki dawo karki tsaya koina garin nan namu cike yake da kidnappers ga kuma wayan nan matasan masu kwacen wayoyi ki kula sosai Allah ya dawo dake lfy. Aikuwa a tsorace nace amin daddy . Tab ai ban biyo ta kan wnn mutumin ba na fada mota ina waigawa inga su waye a bayana ganin ba kowa yasa na fizgi motar da gudu sai gida . Ina fita daga motar ya salman da ya samir suka karaso guna ya samir yace " ke ihisan yaushe kk gama gane kan garin ne da zaki fita ki rufa mana asiri don Allah. Na kalli ya salman snn na kalli ya samir a shagwabe nace " naga duk hankalinku ya tashi aunty samira ma sai kirana take ina tuki .ban fa yi nitsa ba naje na siya ma yayana ne fura da nono sai fresh milk don nasan yana so ko yaya? Na fada ina kallon ya salman yace " hakane amma da baki fita ba sai ki aika kinga ke bakuwa ce a garin kuma macece don Allah kar ki kuma fita ke kadai kanwata. Na bata fuska kamar zan yi kuka nace " to . Daga nan na wuce ciki. Gun daddy naje tukun kamin na koma dakina na sake wanka na sake shiryawa cikin material dogon Riga na zauna gaban madubi na sake zuba make up . Bayan na gama na je na sami su yaya samir muka tafi gidan galadima. Su ummah da mama sai Jan salman suke da wasa suna ya rabu dani ga su nan sun fini kyau . Gaskia ya salman yaji dadin zuwansa yola domin an karramashi sosai . Kwanansa biyu duka daddy ya hana shi kwana hotel a gida yake kwana da ya samir sun saba sosai . Gaba daya naji ba dadi da yazo tfy duk da nasan nima na kusa tfy tunda mkranta za,a bude. Daddy yayiwa ya salman Godiya sosai da irin kulawar da ya bani don na bashi labarin. Ni da ya samir muka rakashi airport duk naji ba dadi wlh banki muyita soyaiyar mu a yola don ba sa,idon su inna . Hauly ce🥰👍🏻 [9/25, 6:21 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰 *Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤* ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡45 ************Bansan sanda ya tafi ba ni dai bayan na gama kukana toilet na wuce na wanke fuskata . Da yake tuni mukayi sallama da daddy kawai na salami su aunty rukayya fatan alkhairi suka min yayinda sukace in gaida Mamana. Ya samir ne ya kaini gidan galadima na ma su Haj rumaisa sallama daga nan muka kama hanyan airport. Sam ban gayawa kowa ina hanya ba.don gudun kar ya salman ya nemeni ma rufe wayoyin nayi. Ya samir ya lura ina cikin damuwa sosai jikinsa a mace yace" ihisan duk naji ba dadi da wnn hadin da za,a yi na aurenki da yarima tun kan kizo daddy ya kiramu ya sanar damu amma wlh dagani har awwal da Hafiz bamu ji dadi ba kuma mun cewa daddy ya fadawa mama( Haj Zubaida) halinda ake ciki ta fadawa mai martaba cewa kina da Wanda zaki aura kuna son juna amma daddy yace maimartaba umarni ya bashi kawai kai tsaye..., A hankali na katse ya samir da fadin " babu komai yaya zan yi biyayya sosai ga iyayena kuma zan auri yarima da zuciya daya in masa ladabi da biyayya. Sai dai matsalata dayace a rayuwa ta yaya zan fuskanci ya salman da wnn maganar? Na karasa fada cikin kuka ya samir ya girgiza kai cikin damuwa yace " babu komai Ihsan hakan nan zaki masa bayani duk da munsan abune mai nauyin gaske .amma ba komai addua shine zai warware mana wnn matsalar. Na gyada kai nace " hakane yaya. Daddy ya kirani ta wayar ya samir don bai sameni a tawa ba haka muka sake sallama. Ya samir yayta rarrashina sai da yaga tashin jirginmu snn ya tafi. Na isa Abuja lfy kasancewar daddy yayi goggo Ummi magana tuni driver ke jirana kawai muka wuce gidan goggo Ummi. Ruma da gudu ta tarbeni cike da farin ciki domin sai yau Allah yayi haduwar mu don bana samunta. Ta kalleni tana murmushi tace" yaruwa rabin jiki. Nima murmushi na mayar mata amma na karfin hali nace" na,am 'yar uwa yau Allah yayi haduwarmu sau biyu zuwana baki nan. Tace " eh wlh duk naji haushi. Anan ta karbi jakata mu ka tafi ciki goggo Ummi cike da fara,a ta rumgumeni tana min sannu da hanya. Sai bayan munyi isha muka hadu muka ci abinci mun dan taba hira kadan. Muna shirin kwanciya knn goggo Ummi ta shigo dakin ta zauna kan gadon kusa dani ta kalleni tace " Mamana naji labarin mara dadi jiya lamido ke sanar dani. Sunkuyar da kai nayi kawai bance komai ba. Tace " kiyi hkr Ihsan duk bama son wnn hadin mun fi so ki auri zabin ranki.amma mai martaba yafi karfin mu bijire ma umarninsa.kiyi hkr Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a gareku. Nan da nan hawaye ya ciko ido nace " amin goggo. Ruma tace " mummy me ye faru? Goggo Ummi tace " mai martaba ne yace a hada Ihsan aure da yarima Abdallah...... Mikewa ta yi da sauri tace"what!!! Mummy Ihsan kuma a hadata aure da Yarima ? Akan me to? Goggo Ummi tace " to gashi nan dai mai martaba ya Riga ya yanke hukunci..... Dan tsaki ruma taja tace " ni bansan me yake damun tsohon nan ba.Wnn Yarima Abdallahn mummy in dai ba Allah ya shiryeshi bama Ihsan bazata iya zama dashi ba matansa ma hkr suke yi dashi don tsabar jiji da kai ga balain tsiya ga kuma shan taba da ya mayar kamar wani cin........ Goggo Ummi ta katseta da fadin ke dan Allah kyaleshi hakan nan wayace miki yana shan taba? Na goge hawaye na nace " yana sha goggo dazu kamin na taho ma yazo kuma hayakin taban ya buson a hanci kuma inada athsma. Goggo Ummi tace " subhanallah wai yaushe Abdallah zai shiryu ne ni Ummi ? Ruma tace " mama yanzu shikenan raba Ihsan za,ayi da salman wlh mama salman yana da kirki don Allah mummy kar Ku bari ayi wnn auren don wlh basu dace ba babbane fa sa,anku mummy snn matansa uku ina Ihsan zata kaishi. Ta karasa maganar cike da takaici ta ce" mama da kinsan bana son a kaini kano amma koda naji an ce Ihsan yaruwatace kuma zata auri salman mu zauna gida daya Sai naji dadi sosai a raina har hankalina ya kwanta amma mama kawai azo ace Yarima zata aura? Goggo Ummi shiru ta yi don itama Sam bata so. Ni dai kuka naci gaba da yi. Yayinda ruma taci gaba da maganganunta. Goggo Ummi rarrashina ta ringa yi har saida taga hankslina ya kwanta snn ta tafi. Washegari kuwa da sassafe na gama kintsawa mukayi sallama driver ya dawo dani kano lfy ko ruwa bai tsaya sha ba ya juya Abuja ni kuma na shiga gida sashin mama.kawai ta ganni cike da mamaki tace " ke kuma daga ina da sassafe haka ? Nace "daga Abuja gidan goggo Ummi can na kwana. Tace " ai ban Sani ba da na kirata don ke dai layinki duk a rufe salman duk ya bi ya damu Allah sarki yayana na fada a zuciyata snn na wuce daki na ina cewa mama" sauri ma nake zan wuce nakaranta yanzu motata batayi datti ba koh? Tace " ba abinda ya sameta jiya da yamma ma da ita na fita unguwa. Nace " to Bayan na ajiye kayana na dau jakar makarantata da key din mota na fice ina mama Sai na dawo. Lokacin da na fito da motata Sai ga ya salman cikin shirinshi tsaf da kakinsa ido na zuba mishi don tsabar yanda naga ya kara min kyau yau kuma ko dan kakin yana matukar amsarsa sosai. Ina shirin fita in gaisheshi kawai saiga sukhaina ta fito daga cikin gida zata kai mishi breakfast tasha uban kwalliya ga daurin dankwali da ta kashe ta zuba gashi baya har canza tfy da ta ganshi. Hmm binsu nake da kallo cike da yanga take masa magana amma Sam hankalinsa na kaina ganin banyi niyyan sauka ba yasa shi karasawa sauke glass nayi fuskata ba yabo ba fallasa nace" yaya ina kwana? Shiru yayi tukun kamar mai nazarin wani abu.ni dai inda sabo na saba. A hankali yace " baby yaushe kk dawo ? Nace bai jima ba Yace" OK yanzun school zaki tafi? Nace" eh Ya gyada kai snn yace "a dawo lfy. Nace " na gode. Naja motata na kara gaba ina lura da kallon da sukhaina ke bina dashi yau ma nace " hmm kyaji dashi. Yau makarantan ma banji dadinsa ba duk lectu lectures da akeyi ba Wanda ya shiga kwakwalwata. Bayan nayi sallar azahar ina shirin dawowa gida Maryam ta sameni tace " Queen yau ya na ganki very doll haka? Nace hmm ke dai bari kawai Maryam gaba daya Na rasa me ya ke man dadi a rayuwa. Tace " to me ya faru? Kamar bazan yi magana ba sai naga kuma gara na fada mata ko zata bani shawara nan na gaya mata. Gyara zama ta yi tace " tab babban magana Queen haka zaki zuba ido a rabaki da salman matashi jarumi kyakkyawa? Aje a hadaki da tsoho mai mata uku da yara shidda? Nace "ba fa tsoho bane ke. Tace" kk ce sa,an mamanki ke bari kiji wlh kika aureshi ba abunda zaki samu a jikinsa duk romon an kwashe salam zakijishi........ Tsaki naja cike da takaici nace " ke dan Allah dakata da maganganunki na banza ke ba daman a miki tadin arziki dake sai kin kawo iskanci a ciki? Dariya ta yi tace " ai gaskia ne Salman shi ya dace dake kinga gashi jarumi kakkarfa soja yanaji da lfy zai gamsar dake hundred % wancan kuma wlh duk basir ya cika mishi ciki. Takaicin Maryam yabi ya isheni shiru kawai nayi ina kallonta . Bayan ta gama maganganunta na banza ta ce" kinga Queen abinda za,ayi akwai wani malamina aikinsa kamar yankan wuka idan mukaje gunsa a cikin sati guda zai wargaza wnn auran ke dai ki tanadin kudi kawai masu tsoka? Harara na watsa mata nace "wai ni rumaisa kk tunanin zan dauki kudi na inje in kaiwa wani katon banza ya shirga min karya? Inzo daga baya ina dana Sani? To ba dani ba kema Allah ya shuryeki ki gane hanya madaidaiciyq. Ta shi nayi na dauki jakata nace " kinga ni tfyta zanyi se gobe. Jikinta a mace tace " to Queen amma ki daiyi tunani. Nace" naji se anjima. Ina isa gida wanka na yi na goge jikina na shafa mai na saka doguwar rigana na material sallar La,asar nayi snn na zauna gaban dressing mirror na fara gyara gashina . Tsaki nayi nace " kai gaskia ya kamata inje saloon kaina ya cushe da yawa sai zafi yake min ina ta.... Ta cikin mirror na ga ya salman tsaye a bayana ya zuban ido ko kyaftawa bayayi. Mikewa nayi na juyo muna fuskantar juna fuskana ba yabo ba fallasa nace " yaya. Shikan murmushi ya min hade da fadin " yaushe kk fara magana ke kadai? Sunkuyar da kaina na yi bance komai ba . Yace " nazo karbar tsabar furana nasan kin kawo min. Jikina ya mutu sosai domin ban kawo mishi ba. Ganin nayi shiru sosai yasa shi fadin " ya dai? Na daure nace " kayi hkr yaya wlh ban kawo maka komai ba amma zan sa a kawo....... Hannu ya dagamin yace " aa ki bari kawai. Na dago a hankali na kalleshi nace " kayi fushi ne? Ya girgiza min kai yana kallona yace" rumaisa jikina yana bani akwai wani mummunan abu da yake shirin faruwa dani. Musamman dana lura da yanayunki daya sauya rumaisa me yake faruwa? Ba shiri na saka mishi kuka. A rude yace " subhanallah me ya faru rumaisa ki gaya min don Allah. Ya kamo hannuna ya zaunar dani gefen gado yace" Rumaisa don Allah ki bar kukan nan yana tayar mun da hankali . Ya tsugunna gabana yace" kinga fada min me ne ne? Kauda kaina na yi naci gaba da kukana. Mikewa yayi jikinsa a mace ya fita ba jimawa ya shigo tare da mama yace" kingan ta nan goggo Amina taki ta gaya min me yake damunta sai kuka. Mama ta zauna gefena ta jawoni Jikinta tace "rumaisa nima na lura tun dawo warki akwai damuwa a tattare dake ki fada mana me kk tattauna da mahaifinki ? Na rasa ta inda zan fara fada masu kawai naci gaba da kuka. Mama ta ce " to ko kina da Wanda tafini ne? Girgiza kai nayi da sauri. Tace"to kinga ki fada mana me ne yake faruwa. Cikin dauriya na goge hawayena nace " mama daddy ne yace mai martaba yace za,a hadani aure da yarima Abdallah. ... Ido ya salman ya zaro hade da fadin " what!!!!! Kirjina sai da ya buga na sunkuyar da kai da sauri. Mama ta ce"Hmm lallai ma wlh bazaiyiwu ba kawai daga ganin kin koma wajansu? Baki fadawa daddyn naki akwai maganar aure tsakaninki da salman ba? Cikin muryar kuka nace " mama ya Sani. Tace " OK yana sane ya take yabi son zuciyansa amma dai ai sunsan ba kyau nema cikin neman aure . Nace "wai mai martaba umarni ya bashi ba neman izninshi yayi ba. Ya salman dafe kai yayi da sauri sakamakon jinda yayi kansa ya Sara ya runtse ido. Mama ta mike da sauri tana cewa" kar ka damu salman in kaga baka auri rumaisa ba to sai dai wani ikon Allah. Zanje na yi magana dasu yaya a tada zancan auranku kwanan nan inga ubanda ya isa ya hana. Ta kalleni tace " ke kuma daga yau bazaki kuma zuwa yola ba har sai kunyi aure da salman in yaso in yaga dama kije kuma wlh Ibrahim ya kuskura ya min wata magana akan ki sai na fada masa abinda har ya mutu bazai manta dani ba. Sai yanzu yasan dake har zai fara nuna ikonsa a kanki to wlh bai isa ba dagashi har mai Martaban. Na dago cike da mama ki ina kallon mama gaskia ranta ya mugun baci idonta har yayi jazir. Ya salman kam ya ma rasa me yake masa dadi a rayuwa . Mama har ta juya zata fita ta kuma dawowa tace"to ke me kk ce masa da ya kawo miki zancan? Na dan saci kallon ya salman kirjina sai bugawa yakeyi nace " mama naga daddy ya shiga cikin damuwa sosai shiyasa kawai na...na..na aminc....... Maganata ba karamin girgiza ta salmanyayi ba .a zuciye ya fice ya bar dakiin. Mama ma takaici na kamar ta rufeni da duka tace"Ashe vakida hankali rumaisa ? To wlh ko kin amince ni ba ruwana. Tana fadin haka ta fita nikam kifa kaina na yi akan gado naci gaba da kukana hankalina tashe!!!!!!! *Fans* *bar* *ka* *da* *sallah* *fatan* *munyi* *sallah* *lfy* ? *Ubangijin* *Allah* *ya* *maimaita* *mana* 👏🏻🙏🏻 _Haulyce_ 🥰👍🏻 [9/25, 6:21 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰 *Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤* ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡46 ********* Mama bata bar maganar ta kwana ba ta kira goggo Ummi tukun . Anan goggo Ummi ta nuna itama bata goyi bayan aurena da yarima . Bayan sun gama waya da goggo Ummi ta kira daddy da kanta. Mamaki ya rika yi sosai ya duba agogo karfe sha dayan dare ya wuce da mintuna ya juya ya kalli aunty Sameera dake ta sharar baccinta hankali kwance. Daukar wayar yayi hade da SLM Da kyar ta amsa yace" Ameena lfy kk kirani yanzu? Tace" ba lfy lamido.rumaisa tazo ta gaya min auren dole da kk shirin yi mata bayan tana da Wanda takeso.kuma kasani.... Ya katseta da fadin " haba Amina yanzu dama akan 'yar maganar nan shine zaki kirani cikin dare ? Ai mun rigada mun gama magana da Ihsan kuma ta amince to menene....... Cikin tsananin bacin rai ta tari numfashinsa da fadin " wlh bazaiyiwu ba babu Wanda ya isa yasa ayi auren nan muddin ina raye !!! Rumaisa Salman ne mijinta kuma kwanan nan za,ayi auransu dan ma kaji da kyau lamido. Kwantar da murya yayi yace " meena kiyi hkr mana kinfa San komai kinsan matsayin maimartaba a wurina domin shine ya bada goyon baya akayi aurenmu ni da ke har muka haifi Ihsan yanzu kina ganin ya kyautu in bijire ma umarninsa? Yatsuna fuska ta yi tace " wnn ya rage naku ni abunda na Sani shine farin cikin 'yata! Don haka ba ruwana da matsalarku. Ta na gama fadin haka ta katse kiran. Shafa kansa yayi hankali tashe yace"ya salam. Aunty samira da ta tashi tun dazu tana sauraron maganganunsa ta tashi ta zauna wutan dakin ta kunna ta kalleshi tace" yaya wai meyasa kake bin matar nan a hankali ne? Ihsan fa 'yarkace kana da ikon aura mata duk Wanda dama dama.don haka ka daina wani sauraranta tana bata ma lokaci. Ta karasa fada cikin jin haushin mama domin tana matukar kishinta. Ya dan numfasa yace" hmm ba zaki gane bane Sameera yanzu dai mu kwanta koma meye sai da safe. Yana shirin kamota ta juya masa baya cikin fushi tana " ai shikenan Allah ya kai mu. Baice komai ba ya kwanta. Ni dai banyi bacci ba don bacci ya ki zuwa idona bacin ran da na gani a idon ya salman ya tayar min da hankali sosai. Tashi nayi na shiga toilet na dauro alwala na fito na saka doguwar rigata da hijabi na shimfida pray mat dina na shiga jero nafila ina kaiwa Allah Ku kana. Bayan na idar da sallar asuba da carbi a hannuna bacci ya saceni daga zaune. Kawai nayi mafarkin wai naje gun ya salman da nufin na bashi hkr . Ransa a bace kawai ya dauko bindigarsa ya saitata a goshina yana cewa koda sunan wasa in na kuma zuwa inda yake sai ya harbeni don baya sona kuma ya TSANENI! A firgice na tashi ina fadin " subhanallah me ya kawo wnn mummunar mafarkin kuma..... Da sauri na tashi ina karanta addua a cikin zuciyata na wuce toilet a raina ina fadin dama ance baccin safe bayi da kyau ai. Brush nayi na fita na dan kintsa jikina snn na fito Palo bansami mama ba amma naji motsinta a kitchen. Na shiga na gaisheta fuskarta a daure ta amsa. Nace " mama zanje in gaisheda ya salman ne dama . ..... Ba tare da nuna damuwa ba tace " don me zaki je gunsa tunda ba sonshi kk ba. Shiru nayi kaina a sunkuye tace " ki dauki flaks blue dinnan ki kai masa kununsa ne a ciki. Da sauri na dauka na fita .koda na isa gidan nasu nan zuciyata ya shiga bugawa tunowa da nayi da mafarkina na dazu. Kamar na juya sai kuma na daure na shiga Palo da sallama . Ina sa kai rass naji zuciyata ta tsinke sakamakon ganinsa da nayi rikeda bindiga kuma ya yi saitin inda nake. Ido na zaro na saki flaks din ya fadi anan ya tarwatse tsabar tsoro na kasa gudu jikina sai rawa yake. Shi Sam bai lura da shigo wata ba faduwar flaks ne ya fahimtar dashi komai da sauri ya maida bindigarsa aljihu ya karaso inda nake . Yana shirin riko hannuna bansan me ya tuno ba sai naga ya fasa kuma fuskarsa ta sauya yace" ya ya? Kaina na sunkuyar nace" ina kwana. Ya juya ya koma ya zauna kan kujera ba tare da yace min komai ba. Nima na karasa cikin dauriya na zauna nace " yaya me yasa kk wasa da bindiga a cikin gida?ka tsoratani sosai shigowata. Kai tsaye yace " wayace miki wasa nakeyi da bindiga ? Ina shirin yin magana yace " kinga ki fada min abunda ya kawo ki kawai ina da abun yi a gabana. Jikina a sanyaye na ce " yaya na fuskanci ranka ya baci sosai da maganata .hankalina ya kasa kwanciya ban iya nayi bacci ba yaya wlh na shiga damuwa sosai ban San me ye mafita ba. Tunda na fara magana ya zuba min ido har na karasa hawayene ya biyo bayan maganata. Kauda idonsa yayi ya tashi hade da fadin " don me zaki sa zuciyarki cikin damuwa har ki kasa bacci ? Bayan kin rigada kin gama amuncewa wani zaki aureshi? Nace " yaya ba amince masa nayi ba..... Ya katse ni da fadin kinga rumaisa ni banda lokacin jin maganganunki na yaudara na dade da fahimtar dama ba sona kk ba zuciyata ce kawai take karyatani don haka yanzu da zuciyata da gangar jikina duk sun gama amuncewa ba kya sona ya zama wajibi a gareni in cire ki a zuciyata nima don haka daga yau babu ni babu ke ki tashi ki fita! Kuka na shiga yi sosai nace " don Allah yaya kayi hkr ka fahimceni inka juyan baya zan shiga damuwa wlh yaya ina sonka . Tsaki yayi ya shige ciki ya barni ina mai ci gaba da kuka na rasa me yake min dadi a duniya ni rumaisa. Kamshin turarenda naji yasa na dago da sauri sukhaina ce ta shigo ta kawo mishi break fast kamar kullum taci kwalliya har ta gaji. Muna hada ido ta watsa min harara ta wuce ta ajiye masa breakfast din snn ta fita ba jimawa ta dawo da tsintsinya ta tsaftace inda flks ya fashe ta goge koina tsaf ta fitar da dattin tana shigowq ya fito daga daki yana ganinta ya saki murmushi yace " wldn kanwata. Murmushi ta mayar masa cike yanga ta fara gaisheshi da fulatanci . Don tsabar wulakanci gabadaya suka mance dani sai hira take mashi da yaransu yayinda yake amsa mata jefi jefi. Anan suka zauna ta mashi serving. Tashi nayi na fice zuciyata ta yi baki kirin don tsabar bacin rai har bana kallon gabana. Na koma gida ranar ko makaranta banje ba ina kwance ji nake kamar zazzabi ma na son rufeni. Karfe sha daya sai ga daddy a kano dama tuni mama ta fadawa Abba har ya kira daddyn ya salim don su tattauna yanda zasu bullowa maganar kawai sai ga daddy . Anan daddy yayiwa su Abba bayani dalla dalla snn ya kara da rokonsu akan su yu hkr shima ba,ason ransa ba. To fa ! Anan mama tace wlh bazaiyiwu ba sai yanzu suka San dani ?bayan ba irin rashin mutunci da bai shuka mata ba kafin su rabu....... Nan fa mama ta dage tayita zuba ma daddy rashin mutunci da gori sai da Abba ya dakatar da ita. Ran daddyna ya matukar baci har fuskarsa ta nuna yace " koma meye ne nine na haifeta koh? Kuma inada cikakken iko akanta da kk lissafin kin dauki dawainyarta waye waye ki mun lissafi in biyaki ! Mama tace " au hakama zakace wlh lamido baka isa ka biyani ba kuma maganar aure Na fada ni AMINA bazaiyiwu ba kuma a shirye nake da nayi komai domin har kotu zamuje Indai baka janye ba. Daddy zaiyi magana Abba yace " yanzu meye amfanin wnn maganar da kk yi ne? Don Allah Ku bari. Ya kalli mama yace "Amina duk kin tada hankalinki akan maganar da bai taka kara ya karya ba rumaisa ta amince hundred % zatayiwa mahaifinta biyayya don haka bana son jin wata magana kawai ki musu fatan alkhairi kuma indai akan salman ne ki kwantar da hankalinki zan shawo kansa shikenan? Mama ta fara magana cikin muryar kuka tace " shikenan yaya za,ayi ma yarinya auren dole kuna ji kuna gani yarinyanda mu muka mata komai a rayuwa har ta zama mutum kawai suzo su rabamu da ita .yaya Ku taimaka min wlh lamido so yake ya rabani da ' yata alhalin ita kadai Allah ya bani. Alh kasim ne yace" kiyi hkr Amina ba Wanda zai rabaki da rumaisa kece dai mahaifiyarta .abunda kawai mukeso ki mata fatan alkhairi domin ba,a cika so mu iyaye mu dinga hayaniya akan 'ya'yanmu ba. Kuka mama ta shiga yi sosai tace " shikenan yaya tunda kunki Ku fahimceni ya zan yi? Tausayine ya kama daddy na sosai ya kalli su Abba yace " kuma dama Alhaji na dade ina yiwa Amina maganar mu maida aurenmu amma taki amuncewa kunga da Allah zaisa ta amince inaga ai shikenan matsalarta yazo karshe zataci gaba da rayuwa da yarta kamar yanda take so tunda tana ganin kamar zan rabasune. Abba ya gyada kai cike da gansuwa yace " ai hakan zaifi muku alkhairi . Ya kalli mama yace " amina don Allah ki amince Ku maida aurenku komai ya wuce. Alh kasim yace " nima ina goyon bayan Ku maida auranku Amina kinga daga......... Mikewa tayi ta fita ranta a bace . Daddy bai sami matsalar su Abba ba Sam sun nuna masa ba komai Allah yasa shine alkhairi. Har sun taba hira kadan bayan sunyi sallar azahar sunci abinci suka fara shirin komawa Abuja shida alhaji kasim . Anan ya nemi ganina amma lokacin ina jin zazzabi sosai .a tare da alhaji kasim suka shiga side din mama ko kallo basu isheta ba daddy kam hankalinsa ya tashi don haka yace kawai muje asibity. Kasancewar zazzabi baiyi serious ba kafin su wuce Abuja naji sauki sosai mukayi sallama na musu fatan alkhairi. Mama ta shiga damuwa sosai har ta dan rame nima daurewa kawai nakeyi. Ya salman kam ya dauki abin da zafi wnn karon ma ko gaisuwata baya ansawa. Anan ya fara tilastawa kansa soyayya da sukhaina . Ba karamin dadi inna taji ba domin aikin malamunta yayi duk da cewa ba hakan taso ba. Sadiya ta shigo ta sami inna ta buga uban tagumi ta zauna hade da fadin " Inna lfy? Dan tsaki tayi tace " ke dai bari Sadiya aikin malamin nan bai min yadda naso sosai ba. Sadiya tace haba inna ki godewa Allah mana meye ne zaki ce baiyi ba ya salman ya rabu da rumaisa rabuwa ta har abada snn ya fara son sukhaina ni kuma ja,afar ya dawo gareni sai juya shi muke son ranmu.to menene kuma? Inna ta sauke ajiyar zuciya tace " abunda kadai ke Sani farin ciki in na tuna amma bayan wnn akwai matsala. Ta mike tana kai komo cikin dakin Sadiya tana binta da kallo Anan ta fara magana" yarinyan da nakeso a ruguza min rayuwarta a hana ta duk wani farinciki na rayuwa snn yau wai itace zata auri na babban sarki snn mai jiran mulki? Sadiya ta zaro ido a tsorace tace " inna kina nufin rumaisa ce zata auri dan sarki? Inna tace " kwarai kuwa abun takaici ma kuma shine dan sarkin da zai gaji sarauta nan ba da dadewa bama domin a duk cikin sarakunan arewa lamidon Adamawa shine bsbba ya tsufa sosai sai jiran lokaci.kuma ance yariman bai taba haihuwar da namiji ba shiyasa suke sa ran idan ya auri rumaisa zai sami da namiji tunda zuriarsu...... Sadiya tace " don Allah ki bar wnn maganar inna tana tayar min da hankali. Inna tace " na fiki shiga damuwa Sadiya zuciyata kamar zata fashe. Wai rumaisa zata auri dan sarki ko ince sarki. Sadiya tasa hannu ta to she kunnenta cikin bacin rai tace wlh inna dama kin barta sunyi aure da yayan mu ta gana mata azaba mu hanata zaman lfy da yafi akan tayi wancan auren. Inna tace " hmm ai wlh nima bansan hakan zata kasance ba!! _Hauly_ _ce_ 👍🏻🥰 [9/25, 6:21 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰 *Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤* ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡47 **************Inna ta ce amma ba komai nasan me zan yi ina dai bukatarsu haihuwan da namiji ne? To bazata haihu ba sai dai ta gama rayuwarta a gidan ba tare da ta haihu ba. Sadiya ta yi murmushin mugunta tace " gaskia inna kin kawo shawara mai kyau amma yanzu kina ganin Abba zai barki ki koma kamaru? Inna tace " kar ki damu indai wnn ne munyi waya da addanku A'i zatazo kwanan nan kuma zata wuce kamaru ita zan tura ta min komai kuma kinga dama kudi ba matsalarta bane ko ban bata ba zatamin komai . Sadiya tace " Inna nima ina son zuwa wlh Inna tace " aa ke dai kici gaba da shirye shiryen komawa gidan mijinki kinga duk yabi ya ishemu da zuwa yana ta rokon Abbanku don Allah ki dawo don ma salman bai sake masa fuska bane don haka kawai ki koma din. Murmushi Sadiya ta yi tace " inna da dai kin bari naci gaba da gwara shi. Inna tace hmm ai Abbanku bazai yarda ba. ke dai ki shirya kawai ki koma kije kiyi ta gwarashi acan kuma iyayensa kar ki raga musu tunda shegu ne 'yan banza. Sadiya tace " ai bari ke dai inna nasan irin rashin mutuncin da na tanadar musu. A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah yanzu mun gama makaranta saura saura service. Maganar aurena da yarima kuwa ya kara bazama koina tuni. Aka fara shirye shiryen bikin. Mama har lokacin bata sauko ba duk da dai ba fushi takeyi dani ba. A haka na tattara Na koma yola raina ba dadi tunanin ya salman dana Mamana ya na hanani sukuni amma ba yanda na iya da raina. A lokacin aka tsaida date din auran ya salim da ruma faiza da Ra'is,sakina da hafiz dinta sai ya salman da sukhaina. Saidai bikina zai riga nasu don sai anyi nawa da 3 weeks kan nasu. Aunty samira sai dura min kayan mata taketayi a cewarta tana son na rikita yayanta sosai jinta kawai nake wani abun ma indai ta ban ajiyewa nakeyi. Ranar wata Saturday ina kwance a dakina hira mukeyi da faiza a watsapp aunty samira ta shigo ta sameni tace " ihisan yarima yazo . Nan da nan annurin da ke fuskata ta gushe ajiye wayar nayi nace " to aunty ina zuwa. Tace " ai kafatq kafarki yanzu tashi zakiyi ki gyara fuskan nan taki ki sauya shiga. Nace" aunty ai nayi wanka dazune na saka wnn kaya kuma me aibunsu? Ta girgiza kai tace " so nake ki mallaki zuciyar yarima Ihsan zakiji dadi sosai don yarima yana son kyakkyawar mace mai son kwalliya da kamshi. Tashi nayi nace " to bari na gyara fuskar kan nan ki zaba min kayan da kk ganin ya dace na saka masa. Ta yi murmushi tace " to ko ke fa gimbiyar mata. Nima murmushi nayi . Da taimakon aunty samira na kwalliya na fito fess dani tace "wow haka kwalliya ke karbanki amma baki son yi haba Ihsan. Nace " mu tafi koh? Tace " eh amma tsaya muyi selfie. Haka dai na biye mata mukayi hotuna.sannan muka wuce palon daddy tare muka sameshi da daddy suna hira . Tunda na shiga kaina a sunkuye a kasa na zauna kaina a sunkuye na mishi sannu da zuwa. Ya amsa a kasaitance. Daddy ya tashi hade da fadin " Abdallah ni bari na je gida sai ka fito. Yace" to yaya. Anan daddy ya fita aunty samira ta kalleshi cike da girmamawa tace " yaya ga gimbiyar nan na kawo mata. Sautin murmushinsa na jiyo snn yace " na gode gimbiya samira yanzu saura alkawarinmu. Tace" hakane ka bani minti goma ina zuwa . Ta fita da sauri.bayan kamar minti biyu da fitanta masu aiki suka kawo Wa yarima drinks da snacks. Ni dai har lokacin kaina a sunkuye kuma banyi niyyar yi masa magana ba. Shi ma shiru yayi da farko da yaga banda niyya yasa shi mikewa yayi ya iso gabana da sauri na dan ja baya . Zuba min ido yayi snn yace" hmm gimbiya Ihsan knn .kema fa kina ji da kanki kamar wata sarauniya. Ya mike ya zauna kujeran da ke kusa dani snn yace" fatan na sami gimbiyar tawa lfy. Can ciki na amsa da lfy. Yace " good ! Nazo ne akwai inda nake so ki rakani . Sai lokacin na dago ba tare da na kalleshi ba nace" ina ne? Yace " zamuje muyi pre wedding pics namu. Sai lokacin na dago na kalleshi cikin jin haushi da takaici nace " ni bana daukar hoto. Yace" ko baki yi yau zaki fara kar ki damu.kuma ki koyi biyayya tun kan ki shigo gidana domin ni nafi son idan nace abu ace min to kawai . Raina ne yayi masifar baci don haka nace " ni na fada maka bana daukar hoto kuma bazan dauka ba.snn maganar biyayya ka bari se na shigo gidan naka in yaso kayi yadda kaso dani. Tashi nayi na kalleshi nace " kaga yarima ina respecting dinka don haka ka rike girmanka ka daina kokarin tilastani. Shima tashi yayi yana kallona yayinda muke fuskantar juna yace"duk abinda nace shi za,ayi umarnina dole ne abi .ke kinma ci sa,a nazo nan saboda ke wlh da badon mai martaba ba abinda zan yi dake. Tabe baki nayi nace " nima saboda daddy nake sauraranka kuma nake respecting dinka. Murmushi yayi yace "hmm yaro yaro ne. Ya fito da kwalin tabarsa a aljihu ya zaro ya kunna nan da nan ya fara busawa da sauri na juya zan fita. Caraf! Ya kamo hannuna yace" ina kuma zakije ? Kai tsaye nace" ni bana son hayakin taba yana takurani . Yace" OK yanzu kije ki shirya mu tafi akwai kayaiyakin da na tanadar miki. Ya karasa fada yayinda ya buso hayakin tabar . Na kauda kai ina shirin yin magana naji shigowar aunty samira nan wata dabara ta fado min na shiga tari da gangan ina rike da kirji da hannu daya. Aikuwa ta karaso da sauri tana" subhanallah Ihsan menene? Ta kamoni yayinda ta kalli yarima tace " ranka ya dade ai Ihsan bata son hayaki.ciwontq ne ya tashi. Nan na takarkare na kama Jan numfashi da kyar . Shima hankalinsa ya tashi nan ya kira ya samir. Aunty samira ta gudu ta dauko min inhaler na. Koda ya samir ya iso ya kalleni yace " me ya faru ihsan? Da kyar nace mishi kirjina ke toshewa. Yace " sorry kwanta. Kwantar dani yayi Aunty samira tace " to ko a kira daddynku ne ai gara kuje asibity kawai . Duk ta rikice. Ya samir yace " aa ba komai baiyi tsanani ba. Anan yarima yace " ni bari na tafi Allah ya bata lfy. Ya samir yace " amin. Ya kalli aunty samira yace" gimbiya muje inada magana dake. Ta bishi suka fita ya samir ya bisu da kallo snn ya kalleni yace " Ihsan me yasa zakiyi karya da ciwo. A hankali nace" yaya wlh bana son yarima idan yazo kullum sai ya nemi ya taba jikina kuma yanzu wai cewa yayi muje muyi pics din aure ni kuma bana son binsa shiyasa nayi karya da rashin lfy. Yace" kin min dai dai wlh.banda yarima da budurwar zuciya ma hmm Allah dai ya kyauta. Haka naci gaba da pretending na rashin lfy har maganar daukar photo ya wuce. An shiga hidimar biki yanuwa da abokan arziki na nesa dana kusa duk sunzo gidanmu tuni ya cika .an kawo kayan lefe na gani na fada akwatina set uku kowanne sha biyu .gashi sun koshi da kaya na gani na fada ga gwalagwalai har da mukullin mota. Daddy yasa aka kai kano saboda su mama su gani.tunda tace ita bazata zo ba. Sakina da faiza sunzo duk da ma mama bata son suzo don tace muje muyi bikinmu da dangin mahaifina ita ba ruwanta.su Abba ne sukace bazaiyiwu ba dole ne dangin mahaifiyata suje ko ita bataje ba don haka Abba yace Maman sakina da mummy Zuwaira ma zasuje . Ni dai da yake auren bai dameni ba ban damu da wasu kawaye bama bayan sakina da faiza sai kuma ruma dayake dama ni ban damu da kawaye bama. Sune suke Sani shirin dole .don ni nace bayan walima banason komai aunty samira tace " su zasuyi dinner nasu na dangin ango. An shirya kayataccen walima sai Wanda ya gani don walimar ya amsa sunan walima duk da banso sai da aka min kwalliya na mussaman kowa ya ganni sai ya yaba.munyi hotuna kuwa abun sai Wanda ya gani. Kasancewar ranar alhamis akayi walima gobe jumma,a daurin aure da walimar saukar karatu. Bayan mun dawo walima ne muka tarar da su Maman sakina da mummyn su ya salim Ashe har sun iso an saukesu a wani side na musamman. Bayan munyi sallar isha na tafi palon daddy don gaisawa da Abban salman da daddyn salim da ya salim din . Muka gaisa suka min fatan alkhairi sukace mama tana gaisheni . Kaina a sunkuye murmushin yake kawai na tuna ni kadai nasan me nakeji a zuciyata. Anan suka ce zasu wuce masauki Nida ya salim muka rage a Palo na kalleshi nace " ya salim ina yaya salman? Yace " hmm yana nan da kk je yiwa mamanki sallama baku hadu bane? Nace " eh yaki yarda mu hadu har na dawo. Yace" to ya za,ayi haka Allah ya kaddara haka zakuyi hkr . Goge hawayen da zubo min nayi nace " shikenan yanzu mun rabu da yaya? Jikinsa a mace yace " haka Allah yaso rumaisa dama can ba kece matarsa bace kuma dama ance matar mutum kabarinsa Allah dai ya sanya alkhairi . Amin" na fada ina kuka haka ya tashi ya min sai da safe ya fita. Da kuka na koma cikin gida goggo Ummi ne ta sameni a daki tace " haba Ihsan har yaushe zaki bar kukan nan. Suka shiga rarrashina da aunty rukaiya. Washe gari asuban farko kowa ya tashi masu hidimar girki nayi masu gyaran gida nayi . A babban palo kuwa su goggo Ummi sai shirya sevonias suke Wanda ba karamin kudi suka kashe ba ba abinda babu daga kan sallaya Alqurani su memo ga kayan kitchen har da su turaran wuta komai a wadace. Sai hira suke cikin nishadi suna dariya. Na idar da sallar asuba na fito palon binsu kawai nake da kallo su da tarkacensu na tabe baki har zan wuce da nufin zuwa sashinda aka sauke su Maman sakina. Fitowar daddy daga sashinsa ne ya dakatar dani ina shirin gausheshi amma sai na lura hankalinsa a tashe yake sosai don ko takalmi babu a kafarsa. Aunty samirq ta biyoshi da sauri tana " yaya lfy ? Yace " ina zuwa. Ya fita da sauri. Nan hankalin kowa ya tashi a palon goggo karima tace " samira lfy kuwa? Tace " nima bansani ba wlh naga kawai ya amsa waya lokaci guda ya fita. Ta karasa fada hankalinta tashe anan goggo Ummi ta tashi tace to bari nazo. Tana shirin fita daddy ya sake dawowa gabadaya hankalina kowa a tashe suka shiga tambayarsa me ya faru. Yace " ba komai Ku kwantar da hankalinku. Ya kalli aunty samira da take zaune shiru duk jikinta ya mutu yace " Sameera dauko takalmina da key din mota. A hankali ta tashe hade da fadin to. Ya na ganin shigarta ya kalli su goggo Ummi yace " gabadaya hkr zamuyi Allah yayiwa mai martaba rasuwa dazu......... Duk palon aka dauki salati baki daya ana muka jiyo ihun aunty samira lokaci guda da faduwarta dama abinda daddy ke tsoro knn saboda karamin ciki datake dauke dashi Wanda ba kowa ya Sani ba sai su. Da sauri kuwa duk mukayi kanta haka daddy ya dauketa kamar jinjira sai asibity. Tuni jini ya balle dama cikin wata biyu ne sai dai fatan samun wani. Ni kadai aka bari a asibityn duk sun tafi gidan mai martaba .gari duk ya rude domin mutuwar lamido ya girgiza kowa sosai. Aunty samira lamarinta sai addua don kwata kwata bata cikin hayyacinta. Da haka maganar daurin aure Na a ranar ya watse!!!!!! Sai dai muce MAIMARTABA Allah ya jikansa da Rahma!!!!!!!! Hauly ce [9/25, 6:21 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🎨‍`MATAR``` ```SOJA`👨🏻‍🎨 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰 *Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤* ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡48 ***********Kwana uku da rasuwar maimartaba su Abban salman suka koma. Mukam muna gidan mai martaba don ni ke kula da aunty samira .duk da an sallamemu jikin nata bai gama warwarewa ba. A ranata hudu ne da rasuwarsa na sami ganin yarima Abdallah har na gaisheshi sai dai zakusha mamakin yadda yake ta walwala abinsa kamar ba tsohonsa ne ya rasu ba don ko ni rasuwan bawan Allah n nan ya tsaya min a rai amma yarima kamar dama jira yake. Har ce mun yayi " Ihsan kinga ikon Allah ko ? Da yanzu kina gidana amma kar ki damu za,a daura aurenmu a ranar da za,a nada ni.kinga bikin sai yafi wancan ma armashi. Tsabar takaici banko sake tanka mishi na tashi nayi tfyta. Sai da akayi Sandakan bakwai na koma gidanmu na bar aunty samira. A ranar Mama tazo da ya salman daga kano jirgi suka bi.saida sukaje gidan galadima tukun sukayi gaisuwa aka kaisu gidan mai martaba duk suka gaggaishesu acan suka samu daddy ma don shi ya kawo su gidanmu Ina can ina ramuwar baccin gajia aunty rukayya ta tasheni tana " Ihsan mamanki tazo da salman tashi muje ku gaisa. Aikuwa da sauri na tashi nace " to Momy ina zuwa. Toilet na wuce na watsa ruwa da sauri na fita na dan gyara fuskata snn na saka kayana na fita a Palon daddy na samesu cike da murna na isa wurin mama nace" mama yau kece a yola? Murmushi tayi ta ce " eh nima ban taba tunanin zanzo ba amma dole inzo inyi gaisuwar rasuwar mai martaba. Aunty rukayya ta ce " haba aunty Amina ke da muke so ki dawo yolan gabadayama. Mama tace " hmmm yolan naku sai ku rukayya. Daddy kam shiru kawai yayi baice komai ba don har yanzu bai sake ba rasuwar mai martaba ya shiga jikinsa sosai. Sai lokacin na dago na kalli ya salman ya kame ya danna wayarsa ko a jikinsa kamar baisan na shigo ba. Jikina a mace nace" yaya sannunku da zuwa. Sai lokacin ya dago ba tare da ya kalleni ba yace" yawwa. Nace " ya gajia ya kuka bar mutan gida? Yace " lfy ya hkr ? Nace " mun gode Allah. A takaice yace " Allah ya jikansa da Rahma. Gabadaya muka amsa da amin . Aunty rukayya tace "kun sami ganin samiran kuwa? Mama tace eh mun ganta. Daddy ya kalli agogon hannunsa snn yace " salman mu tafi masallaci La,asar yayi . Suka tashi suka fita anan muka tafi dakina da mama bayan ta idar da sallah nace " mama zamu kwana ko? Tace " aina ? Hmm zamu tafi mu kam yanzu ma in salman ya dawo daga masallaci. Nace " haba mama ko abinci bazaku tsaya kuci ba? Tace " ai munci a gidan galadima. Ta fada yayinda ta mike ta na kallona tace " to ya maganar auran naku kuma? Bata fuska nayi nace " ya na nan amma wai sai nan da wata biyu in zaayi bikin nadin sarauta sai a hada. Tabe baki tayi tace " hmm yayi kyau. Ta dauki jakarta tare muka fita a lokacin su daddy sun dawo nan sukayima aunty rukayya sallama daddy yace in dauko hijabina mu rakasu airport. Haka kuwa akayi sai da suka tafi muka dawo Sam banji dadin yanayinsu ba daga mama har salman din duk sunki sakar min fuska . Bayan rasuwar mai martaba da sati biyu na tafi Abuja gidan goggo Ummi saboda aurensu ya salim saura one week. Bayan na huta da kwana biyu na tafi gidan kawu kasim su faiza da sakina ana nan ana ta faman gyare gyaren jiki gaskia sunyi matukar kyau jikinsu yasha gyara sai sheki suke Na taba jikin faiza nace " wai hmm rais zai more Harara ta sakar min tace " wlh rumaisa munyi fushi dake. Nace " to fa me ya faru Sakina tace " maimakon kizo nan muyi shirye shiryen mu tare dake sai kika tafi kika sauka gidan goggonki. Faiza ta harareni tace " wlh zamuyi maganinki. Nace " Allah sarki yanzu dan wnn ne ya sa ku fushi don Allah ? Me yasa baku tambayeni dalili ba? Faiza tace " ba wani dalili wulakanci ne kawai irin naki. Dariya nayi nace " ke dan Allah can kin cika daukar zafi .anan kika dage sai na miki kawance sakina ma tace sai na mata nayi nayi daku daya ta hkr nayiwa daya amma kunki ya kuke so nayi to? Shi yasa kawai na raba fada na tafi gun ruma kuma kunga ita kadai ce ba ta da mai tayata zirga zirga tunda ita kadaice mace a gidansu.ku kuma ku biyu ne shiyasa .amma ba wai na sauka gidan goggo Ummi saboda wani manufa bane. Anan muka sake muka shiga hiran makaranta da maganar tfyr mu service .daga nan muka shiga hiran bikin yadda zamu shirya programs dinmu . Na kalli sakina nace " ya salman ma a nan za,a daura aurensu ko a kamaru ? Tace " anan dai tuni 'yan kamarun sun cika mana gida ai. Nace " to ina labarin Sadiya kuma ? Faiza tace " hmm da kyar suka lallaba jafar aka maida auransu. Nace " masha Allah. Daganan shiru nayi na fada kogin tunanin ya salman . Har dare driver goggo Ummi yazo muka koma. A kano kuwa 'yanuwan inna sun cika gida tun saura sati biyu biki wasu ma a side din mama suka sauka don gidan ya cika ga kuma 'yan uwan Maman sakina ma. Amarya sukhaina sai jiji da kanta take a ganinta tafi kowa sa,a a rayuwa da tayi winning heart din salman har ya yarda zai aureta. Ana saura kwana biyu daurin aure bayan anyi walima da Fulani day dinsu don mu kam muna can Abuja acan muke ta shagalinmu mun bar ma su inna gida.har mama Abuja ta tafi ta kulle dakinta ta barmusu Palo kawai da tsakar gida Ya salman ya shiga cikin gida sashin Abba abokan wasansa sai zolayarsa suke amma bai ko kulasu ba dama can ba wasa yake yi musu ba shikam. Ya sami Abba da daddy suna cin tuwo ya zauna hade da gaishesu . Daddy yace ya akayi ne ango? Ya danyi shiru yana tunanin ta inda zai fara magana . Abba yace " ko akwai matsala ne? Yace " eh Abba . Abba yace " toh ta mefa? Salman yace " jiya ne da daddare ina kwance wani ya kirani da num kamaru yake sanar dani cewar sukhaina na daukeda cutar kanjamau! Daga Abba har daddy hada baki sukayi wurin fadin subhanallah ! Daddy yace " ko dai karya ake mata ai gara Ku gwada.dama ana son ayi gwaji kamin aure yana da kyau. Salman yace " shine jiya yau na dauketa da safe naje gun doctor James da ita an gwada kuma an tabbatar min har ma ya sake kaiwa asibitoci biyu..kunga ma sakamonta. Ya fitar da nata result da nashi ya mikawa daddy. Daddy ya duba ya baiwa Abba ma ya duba. Suka rasa me zasuce Salman yace" shine naga ya dace na sanar daku tunda gobe da safe za,a daura auren anan kamin a wuce abuja a daura auren salim.don haka ni dai a cireni a lissafin daurin auren nan kawai a daura na sakina da faiza. Daddy yace " ai ko baka fada ba domin ba yanda ma za,ayi a hada mai lfy da mara lfy.kai subhanallah zamanin namu sai addua ka duba yara kanana suna daukeda manyan cuta irin wnn. Kuma don mugunta sai taki sanar da kai? Abba yace " hmmm ai dama ba sonshi take sakani da Allah ba . bari shatu ta zo ta sameni wlh daga wnn ya isa haka so suke su cutar min da yaro to ta Allah ba tasu ba sai tasan yadda zatayi da 'yanuwanta su fice man daga gida tunda azzalumai ne. Abba ya fada cikin tsananin bacin rai. Daddy yace " yaya a dai bi abun a hankali Abba yace "kai dai barni dasu. Salman yace " Abba ni yanzu Lagos zan wuce dama akwai aikin da zai kaini ranar Monday to kawai nayi deciding in tafi yau na sami jirgi karfe takwas zamu wuce. Abba yace " to baza ka tsaya daurin auren su salim dinba? Ya salman yace " ba damuwa Abba nayiwa salim bayani kuma ya fahimceni. Abba kam tausayin dan nasa ya kamashi sosai don kullum yana cikin jarrabawa. Ya gyada kai yace " to Allah ya kiyaye hanya kuma don Allah kayi hkr da irin jarrabawar rayuwa da kk fuskanta insha Allah watarana sai labari.Allah ya maka albarka. Yace " amin Abba nagode. Daddy ma ya mishi fatan alkhairi daga nan fita yayi ko gefen su inna bai duba ba saboda gaba daya yaji ya tsani dangin mahaifiyarsa su wane irin mutanene da basu maida hankali gun baiwa yaransu tarbiyya kawai sun bar yara sun maida iskanci ba,a a bakin komai ba Shi dai yana kara godewa Allah daya soshi baiyi auran nan ba . Da haka ya tafi airport jirgi ya daga dasu sai Lagos Gidan goggo Ummi kam ya cika da 'yan yola sai hidima ake tayi cikin farin ciki. Muna zaune da ruma ya salim ya kirata sun jima suna waya kamin nan sukayiwa juna sallama ta kalleni tace " yar uwa tashi ki rakani akwai inda zani. Nace " inane ? Tace "ke dai muje zan gaya miki. Haka muka sa hijabi muka fita driver tayiwa magana . Muna cikin tfy tace" tuni har an daura auren su faiza a kano don sun kamo hanyan Abuja salim yace su har sun iso don sai bayan an daura namu zasuyi reception anan. Nan da nan naji jikina yayi sanyi nace " yar uwa yanzu shikenan salman yayi aure? Ta girgiza kai tace " an fasa daura auren salman maganar da nake miki ma yana Lagos. Zaro ido nayi nace" me ne? Don Allah me ya faru? Ruma batace komai ba saboda a daidai lokacin muka shiga harabar wata private hospital anan naga ya salim yana jingine da motarsa alamun mu yake jira. Bayan driver ya gama parking muka fito mukaje wurinsa Ya kalli Ruma yana murmushi yace " Amarya kinsha kanshi irin wnn kyau haka ina na gane ki. Muka gaisheshi anan ya fara yi mana bayanin abinda ya faru gaba daya a kano . Ni kam tsananin mamaki da tsoro sake baki nayi ina kallon ya salim. Ya karasa maganar da fadin " shine daddy yace gaba daya muje muyi test domin kowa yasan me status dinshi ina fatan dai hakan bazai bata ran gimbiya ba Ruma tayi murmushi tace" hakan shine daidai ko kadan raina bai baci ba.sai dai fa ina tsoron allura. Ya salim yayi dariya yace " ai na sanki uwar tsoro ce su faiza ma yanzu suka bar nan da ra'is Tace " to sis sakina fa? Yace " su sunfi mu wayewa Ashe tuni sunyi abinsu har sau biyu ma. Murmushi tayi tace" to Allah ya kayautq. Yace " muje ko? Ni dai ina tsaye kyam kamar an dasa ni ina ta juyayin wnn al'amari . Anan suka barni suka tafi suka gama gwaje gwajensu suka fito ya salim ya kalleni yace " to gimbiya ki kula min da amaryata sosai . Murmushi na kirkiro nace " kar ka damu yau a gidanka ma zata kwana. Murmushi yayi yana kallontayace" masha Allah yau Ruma zata zama ta Sulayman insha Allah. Sunkuyar da kai tayi da haka mukayi sallama sai da yaga tfyrmu da driver snn shima ya tafi. A hanya na kalli ruma na ce" ruma wlh tausayin ya salman nakeji sosai. Hawaye tuni ya ciko idona tace " ai kamata yayi ki tayasa murna ne yar uwa irin wnn masifa da ya tsallaka be fada ciki ba kawai addua zamu ci gaba da yi masa Allah ya bashi mace ta gari. Na goge hawaye hade da fadin " amin yar uwa . Haka akaci gabada hudimar biki bayan an daura aure tuni an tafi da kaya mutane sun fara tfy. Sakina da faiza tun safe suka tafi kano don suyi sallama da dangi ita faiza Lagos zasu wuce daga can ma sai London don ba ,a nan zasu zauna ba .sakina ne a Zaria . Ruma kuma kano mun isa kano da yamma ko ina cike da mutane na nesa da kusa har yanuwansu Abba da basu damu da zumunci sun dan zo. Mutanen inna kam ko daya ba wacce ta rage sun tattara da yarsu sun tafi jiki babu kwari .sun bar inna da bakin ciki da jin kunya uwa uba gashi salman sai fushi yake ko wayarsa bata samu dama wurin Abba take samun sassauci shima wnn karon haushinta yakeji. Haka inna take wuni da bakin ciki ta kwana dashi har bikin nan ya kare aka watse sai fatan Allah ya bada zaman lfy. Ni dai ban tafi da wuri ba ina nan kano nace daddy ya barni inyi ko sati biyu ne kamin na koma muje mu sake namu shirin wnn kaddararren auran . Sadiya ana gidan jafar sai gwarashi take son ranta yanuwansa ba Wanda ya isa yaje gidansu haka nan bai jin maganar kowa sai nata. Inna sunci nasara ta nan kam . Satina daya a kano ya salman ya dawo ba Wanda ya gayawa sai ganinshi kawai mukayi ranar muna zaune da ruma a gidanta sai hiran gidan faiza muke yi na London don ta turo mana hotuna bayan mun gama waya da ita. Kawai muka jiyo ana knocking kofa ruma ta jawo hijabinta da sauri dariya nayi nace " ke dai wlh ya wuce zainab ce? Na tashi ina mata dariya na nufi kofa ina budewa naji wani rass. Runtse idona nayi na sake budewa na kalleshi shima ni yake kallo . Ba Wanda ya iya cewa komai a tsakanimu sai kallo rumasau ne ta karaso da hijabinta tana " lfy yar uwa. Ganin ya salman ya sata sakin murmushi tace " laa darling yaushe a garin namu? Sai lokacin muka farka daga duniyar da muka tafi dukanmu biyu. Da sauri na kauda idona daga kallonsa yayinda shi kuma ya kirkiro murmushi ya dora kan fuskarsa yace " yanzun nan kuwa sweety ina danuwana? Tace " a darling ko gausawa bamuyi ba ka fara tambayar dan uwanka? Zo muje ciki tukun yana nan bai jima da dawowa daga aiki ba. Suka shigo nima na biyosu a baya bayan ya zauna ta ce " minti biyu don Allah darling. Ta fada yayinda ta shiga ciki ta barmu. Duk na jini a takure a hankali na dago kaina na kalleshi nace " yaya ina wuni. Yace " lfy. Daga nan shiru mukayi ni dai na rasa dalilinda yasa ya salman yaketa fushi dani alhalin yasan ba laifina bane. Jikina a mace na tashi na bar gidan na koma na sami mama tana girki nace " yawwa mama dama yunwa nakeji. Tace " ni kuma jiranki nake dama ki dawo in tambayeki meyasa kk matsawa su salim da zuwa gidansu ne? Nace " mama ya salim tuni ya koma wurin aikinsa baima zama a gida yanzu kuma ba anan muna zaune ruman ta kirani ba? Tace " hmm ki dai barsu su sake yafi Nace " to shikenan mama ai dama...... Karar wayata ta katseni na dauka aunty samira ce " hello aunty Tace " na,am Ihsan kinyi shiru a kano abinki muna ta kewarki. Murmushi nayi nace " zan dawo ai Aunty Tace " hmm yaushe? Nace " next week insha Allah. Tace " tabdi har next week? Ihisan gara fa ki dawo kawai maganar gyaran Jikinki da sauran kayan sokkoto da na miki oda duk suna ready ke suke jira kuma kinga gara ki dawo da wuri ki fara amfani da komai don wnn karon bazan yarda da asaran da kk min last time ba. Nace " kai aunty wancan danayi ta yi ma fa yana nan karfa ya ja min matsala kinsan abu in yayi yawa. Tace " ba wani yawa da zaiyi so nake ki zama tauraruwa a idon yayana.don haka yanzu munyi magana da daddynku ki dawo jibi kawai . Na bata fuska nace " haba aunty jibi. Tace " to bari ince daddyn ya fada miki da kansa. Nace" aa kawai sai na dawo. Tace " to za,a turo miki kudin jirgi ki gaida ruma da sauran yan gida. Tura baki nayi nace" to zasuji. Ta katse na kalli mama nace" kinji mama wai jibi na koma fa. Tabe baki tayi tace " hmm ummah ta gaida assha ni don kin zauna anan ma me yake kara min ? Tunda shatu ta sakoki a gaba gara dai ki koma gidanku yafi tunda Allah ya baki sa,a matan babanki naji dake. Nace" wlh kuwa mama kowa sona yake aunty samira duk jiji da kanta muna shiri kamar kawaye wlh. Mama ta yi dariya tace" to ai kusan kawayen ne koda yake dai ta girme ki tunda sa,ar yayanki samir ne.ni wlh mamakin lamido nakeyi da ya rasa wacca zai aura sai 'yar cikinsa saboda budurwar zuciya irin tasa. Nace " laa mama daddy bai tsufa ba kinganshi da aunty samira sunfi matching sosai saidai fa tana sawa yana biye mata sosai ko a gabanmu ne tayita zuba mishi shagwaba yana biye mata haushi ya samir sukeji ni dai ko a jikina. Dariya mama ta yi sosai snn tace" hmm maza knn.da kyau .ita rukayya ba,a nuna mata soyayya? Nace" aa Momy ba ruwanta wlh bata cika damuwa da harkar kowa bama. Tace" ai naga alama tunda har ce min take na koma gidanku . Nace "ai mama gara ki koma din ai kinga tunda daddy ya matsa sosai su ya awwal ma suna so ki dawo. Tace" kinga ni kin isheni da surutun banza zo ki dauki kular abinci ki kai Palo in yaso ki dawo ki dauki plet kije kici ni wanka zan shiga don kasuwa ma zanje. Nace " to."yayinda na dauki abinci na fita palo Ya salman haka muka dinga wasan buya a cikin kwana biyu kan in tafi don bai son mu hadu. Ni ko naso mu hadu nayi mashi sallama don har kiransa nayi bai amsa ba.na fita harkarsa. Ruma bata so tfyna ba Sam dole ta hkr Nima kaina in na tuno da wnn auran nakanji kamar kar na tafi wlh. Hakan dai na daure na tafin!!!!!! Hauly ce [9/25, 6:21 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🎨```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🎨 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰 *Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤* ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page➡49 ***********Na dawo yola da kwana biyu aka fara min gyaran jiki yanzu ko fita ba,a so nayi.aunty samira ko ta dage sai duddura min kayan mata take wasu ma ban ko taba jin sunayensu ba ga na tsugunno daga Maiduguri wasu na shafawa ne . To ni dai ba yanda na iya haka nake ta faman amfani dasu . Jikina kam yayi kyau abun ba,a magana koina kuwa kamshi ke tashi a jikina. Yanzu duk gari ansan nice amaryar Sarki Abdallah duk da ba fita nake ba amma tuni yarima ya turo dogarai gidanmu suna nan suna a bakin get koda yaushe.ga hadimai kuwa sun kai shidda masu yi min hidima tun banje gidansa ba.ko motsi nayi sai an min sannu duk inda na zauna fifita ake min abinci ma da na bari a baki za,a bani in na fita kuwa koina sai praising dina ake.wayyoni Rumaisa Ashe haka sarauta keda dadi? Tuni sunana ya tashi daga Ihsan na koma gimbiya. Abdallah kam shirin nadin sarauta ya boye shi yanzu ba mai ganinsa nima tunda na dawo kano ban ganshi ba sai dai yakan kirani wasu lokutan amma ba sosai ba. Wnn karon daurin aure kawai za,ayi ba wasu shagali saboda nadin sarauta. Gari duk ya cika da jama,a na nesa dana kusa ga manyan sarakuna sunzo na arewa har da sarkin musulmai yola ta cika ba ko inda za,a sa tsinke. Gidanmu ma haka gidan galadima ma ba,a magana wnn karon ma daddy da Abba sunzo tare da Maman sakina da mummynsu salim. Ana gobe daurin aure da daddare karfe sha daya yarima yazo aunty rukayya ne ta zo ta gaya min wai yana palon daddy nace" tab Ashe maimartaba zai sami lokaci har yazo? Aunty rukaiya ta yi dariya tace " a to gashi nan dai yau yana son ganin amaryarsa ne. Nayi murmushi snn na tashi na gyara jikina nasa turare muka fita koina cike da yanuwa da abokan arziki.muka wuce palon daddy . A tsaye muka sameshi da manyan kaya Wanda suka kara masa kwarjini palon kuwa duk ya cika da kamshin turarensa mai dadin gaske . Cike da girgimawa aunty rukayya ta ce masa" ranka ya dade gata. A kasaitance yayi mata magana"ina yaya ? Tace" bai dawo ba ranka ya dade dake kasan yanada manyan baki yau. Kai kawai ya gyada mata. Ta mike hade da fadin " a huta lfy. Tana fita ya kalleni kaina a sunkuye nace " ranka ya dade ka zauna mana. Kai tsaye yace min ba zama ya kawoni ba Ihsan sauri nake banida isasshen lokaci yanzu. Nace" hakane amma lfy kazo a wnn lokacin? Ya danyi shiru snn daga bisani yace " eto lfy za,ace .amma a gaskia na zo ne in sanar dake da kaina daurin aurena dake bazaiyu ba ..... Mikewa nayi ba shiri ina kallonsa a razane nace" mene? Don Allah me kake shirin fada min ? Anya kuwa kana cikin hayyacinka ? Maganar aurefa ba wasa bane don Allah kar ka kuma yi min irin wnn wasan ranka ya dade. Murmushi yayi yace" wasa kuma? Ni Abdallah na taba wasa dake a iya sanina da kikayi? Jikina ne ya mutu hawaye suka fara zubo min nace " yanzu abinda zaka min knn ? Ka rabani da dukkan farin cikin rayuwata snn yazo kace ka fasa aurena bayan an gama sanarwa koina duk fadin Nigeria sunsan da maganar auren nan amma shine zaka zo ka mana irin wnn wulakanci ? Don Allah karkasa daddy na yaji kunya kayi hkr ka fada min laifina zan gyara.amma kar ka jefa daddy na cikin bakin ciki ya gayyaci abokansa na nesa dana kusa har da wayanda basa kasar nan duk sunzo idan akace an fasa auran nan bansan........ Daga min hannu yayi yace kinga ni sauri nake banida isasshen lokaci kamar yadda na fada miki a baya kiyi hkr ki samo wani kawai. Cikin muryar kuka nace " to me yasa? Me na maka? Juyowa yayi muna fuskantar juna sosai yace " mummunan labari naji akanki akan irin abubuwanda kika dinga aikatawa a jamiar bayero a kano kinsan ni yanzu babban mutum ne mai daraja da kima a idon jama,a bazan iya auren matar da ta gama zubar da ajinta da mutuncinta da kimarta na 'ya mace a waje ba.don bazan gurbata rayuwar gidana ba a matsayina na babban mutum mai jagorantar alumna...... Tsananin mamaki da ya bayyana a fuskata karara ko motsi ban iya nayi ba kallonsa kawai nakeyi har ya gama fada ya kama hanyarsa zai fita sai ko ga daddy anan ya lura da yanayinsa ya tsaidashi yana" Lfy Abdallah? Shiru yayi baice komai ba ganin baiyi niyyar magana ba yasa daddy ya kalleni yace " ke Ihsan lfy? Na goge hawaye nace " daddy wai cewa yayi ya fasa aurena.. Daddy yace" subhanallahi me ya faru Abdallah? Kai tsaye yace " ka tambayeta na fada mata dalilin da yasa. Daddy ya kalleni cikin tashin hankali yace" Ihsan ki fada min me ke faruwq don Allah? Kuka nake mai tsanani nace " nima daddy bansani ba. Daddy ya riko hannunsa yace " kaga kanina don Allah ka fada min me ke faruwa kar Ku Sani a damuwa don Allah! Kai tsaye yace " saboda bana son ka bata min lokaci zan fada maka .Ihsan ta zubar da mutuncinta da kimarta na 'ya mace a jamia ...... Anan ya tsunke da fada masa nikam hannu na dora akai ina rusar kuka kamar raina zai fita wnn wane irin balaine ? Yana gama fada ya ficewarsa daddy kam jikinsa ya gama mutuwa da kyar ya iya karasawa ya zauna kan kujera ya dafe kansa da yake mugun sarawa. Nikam durkushewa nayi a gabansa ina kuka na rasa me zance. A cikin wnn yanayin aunty rukayya da aunty samira wacce bata Dade da dawowa ba suka shigo palon. Ganin halinda muke ciki yasa hankalinsu ya tashi matuka suka shiga tambayar me ya faru. Daddy ya daure yace " ba komai 'yar matsala aka samu Abdallah yace ya fasa auranta . Aunty samira tace" innalillahi wai me ya samu yayane me yasa zai mana haka. Aunty rukayya ma ta shiga damuwa. Ni dai har lokacin kuka nake daddy ya riko hannuna yace " taso taso ko kadan ba zan yi fushi dake ba Mamana. Ya dagani daga durkusawa da nayi a gabansa ya zaunar dani a kusa dashi snn yace " amma ina son ki min aljawarin zaki fada min gaskia dukkan abinda ya faru. A tsorace na dagawa daddy kai duk da bansan ta yanda zan fara fada masa wnn mummunan labari mara dadi ba. Yace " da kyau Mamana . Snn ya mike ya kalli su aunty rukayya yace gata nan kune mata yan uwanta zata muku bayanin komai . Daga nan ya shigewarsa ciki . Anan su aunty suka dinga rarrashina hade da tambayata me ya faru? Ban boye musu komai ba na kwashe duk abinda ya faru dani a baya na fada musu sai dai ban fada musu Inna ce tasa aka min wnn asirin ba na dai sanar dasu asirine. Gabadaya saida suka zubar da hawaye. Mun jima sosai a haka kamin daga bisani aunty rukayya ta ce " Amma duk Wanda ya miki wnn abun bai kyauta miki ba Ihsan Allah sai ya saka miki kuma mun gode Allah ma da kk tsira da budurcinki. Aunty samira ta gyada kai tace " kwarai kuwa .amma ya Abdallah bai kyauta ba saboda wnn dalilin zaice zai fasa auran Ihsan ? Fisabilillah karuwai ma ana auransu su zauna kuma. Ta kalleni tace " tashi muje mu kwanta karki daga hankalinki zanyi magana da manyan mu in Allah ya yarda gobe za,a daura auran nan. Haka ta lallabani muka tafi dakinta muka bar aunty rukayya . Haka kuwa akayi aunty samira cikin Daren ta dinga kiran bappanansu wayanda yarima ke jin maganarsu tana fada musu. Amma har gari ya waye ba wani cikakken bayani . Daddy dai bai kuma cewa komai ba su Abban Salman kawai yayiwa bayani sai kuma mamana. Haka akaci gaba da hidimomi ba Wanda yasan me ake ciki kwata kwata.ni dai ina daki zuwa yanzu zazzabine ya rufeni.saboda kuka dana kwana inayi don bakin ciki da takaici nayiwa Inna Allah ya isa yafi a irga .duk da ba son auren yarima nake ba amma banso rabuwar mu ta kasance haka ba yanzu shikenan haka kowa zaici gaba da yi min kallon 'yar iska. Aunty rukayya ce ta wuni dawainiya dani tana ta rarrashina don aunty samira kam sammako tayi ta tafi gidansu. Bayan an sauko daga Sallar jumma,a kuwa goggo Ummi da goggo karima suka sakoni gaba sai inyi wanka in shirya.su basu San me ake ciki ba Sam sai walwalarsu sukeyi. Haka suka taimaka min nashirya cikin wata swiss less mai shegen tsada kana gani kasan an kashe kudi sosai gashi dinkinma ya hadu riga da siket ne ya zauna das a jikina na zuba set din gwala gwalai na Wanda daddy ya saya min a Dubai gashi nasha bridal make up abun ba,a magana . Ni dai daurewa kawai nakeyi kowa ya shigo sai yaba adona yayinda aka rinka daukan hotuna dani. Goggo Ummi ta kalleni tana murmushi tace " masha Allah 'yata yanzu daddynki ya kirani yace a miki albishir an daura aurenki. Ajiyar zuciya nayi sai dai kuma a take naji zuciyata ta shiga bugawa wayyo Allah shikenan wai yau ni rumaisa na rasa Salman. Hawayene ya zubo min lokaci guda goggo Ummi tace " assha Ihsan kar ki bata kwalliyarki kinji ba kuka ya dace kiyi farin ciki zakiyi da hamdala kinsan meye dalili? Shiru nayi ina kallon goggo Ummi ta yi murmushi tace"Mamana auranki da *SALMAN* aka daura ba yarima ba!!!! Da sauri na kalli goggo Ummi ........... Hauly ce [9/25, 6:21 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page ➡50 ***********Sake baki nayi ina kallon goggo Ummi dan jin maganar nake kamar a mafarki wai an daura aurena da *SALMAN*? Goggo karima tayi murmushi tace" muma yanzu hankalinmu ya kwanata ihisan mun aurar dake ga Wanda kk so fatan mu dai Allah ya baku zaman lfy da zuria ta gari. Sunkuyar da kai nayi sai kawai naji wani irin farinciki mara misaltuwa ya lullubeni hamdala na dinga yi a zuciyata tabbas da zasu barni ni kadai alwala zan yi yanzu nazo nayi nafila na godewa ubangijina kasancewata matar salman ayau. Shigowar ruma ne yasani dagowa daga gani yanzu ne isowarta kan na ankara tayi jifa da Jakarta ta rumgumeni cike da farinciki tace" 'yar uwa nazo ne in tayaki murna yau na kasa hkr dole ne kawai nazo don nima ayi murnar dani. Murmushi nayi bance komai ba goggo Ummi tace" kin daici sa,an samun jirgi . Ruma tace" wlh kuwa Momy Anan suka shiga gaisawa bayan sun gama goggo karima tace " to tunda kinzo se ki zauna da yaruwarki mu dai tunda an daura aure zamu wuce gidan mai martaba gabadayanmu Ruma tace " to sai kun dawo. Nidai Allah Allah nake su fita suna fita na riko hannun ruma nace" yar uwa ina yaya salman? Tayi murmushi tace " nasan dole ki tambayeshi ai.baya nan tun last week yana porthacout. Nace " can ya koma kuma ? Tace " aa aikinsane ya kaishi amma zasu dawo nan da 2 weeks munyi waya dazu ya gaya min da kyar ma ake samunshi saboda aiki ya masa yawa wlh. Na zubawa ruma ido snn nace" ruma ni ina mamakin yadda aka daura auren nan da ya salman ko gaya min ba,ayi ba. Tayi dariya tace " ko shi ma Darling ba,a gaya masa ba ai Kawai da yarima ya ce ya fasa daddy ya kira goggo Amina ya fada mata snn ya gayawa su Abba shine Abba yace ba amfani a sake watsewa kamar wancan karon kawai a bari in jama,a sun taru a daura auren da ya salman .nan da nan daddyn Abuja yaje ya ciro kudin sadaki ya kawo saida aka hadu za,a daura auren snn daddy ya kira shi take sanar dashi dukkan abinda yake faruwa cewa yayi to Allah ya sanya alkhairi kinji yanda kk zama *MATAR* *SOJA* murmushi nayi nace " ruma wlh bazan iya misalta miki irin farin cikin da nake ciki ba.to ina innah? Tace " suna can suna fama da bakin ciki yau dinnan da kyar ne in innah batayi zazzabi ba amma naji salim na cewa bata nuna damuwa sosai ba kuma nace to Wa yasani ko na ciki na ciki ne? Nace" aikuwa dai kam.ko don mai zugata bata nan? Tace " Wa ? Sadiya kk fada? Aikullum Sadiya na gida sai dare take komawa gidanta kinsan sister dinsun nan tana nan ? da wata yarinya ma an kawo ta sa,ar su zainab Cike da mamaki nace" kuma dai? Lallai inna bata daddara ba. Na fadi hakan yayinda na wuce bandaki nayi alwala nazo na gabatar da nafila na godewa Allah na kara da adduar neman zaman lfy. Bayan na gama ruma tazo tana gyara min kwalliyata anan naji wayata na ringing ta dauko tana dubawa tace " hmm faiza ce. Murmushi nayi nayi receiving kan nace wani abu tace" amaryar yayanmu wayyo Allah dadi kamar zai kasheni yau danaji labarin nan mai dadi ji nake kamar nayi fika fiki nazo NIGERIA. murmushi nayi nace " to kiyi mana. Tace " Allah sarki rabo ashe duk abubuwan nan dake faruwa Allah ya riga da ya tsara abunsa congratulations sis Lumshe ido nayi nace " thank you sisi na ya ra'is ya London? Tace "Alhamdulillah wlh ina nan ina shan soyayya a wajansa sai shagwabani yake yana riritani ke bari kiji har nayi batan wata ki min barka.... Toshe baki nayi ina dariya nace " har kin kwaso kai faiza ba ko kunya to service dinfa? Tace " ke dan Allah ni ina ruwana da wani service ? Ko kadan bazan iya rabuwa da mijina ko na seconds ba. Nayi dariya nace " lallai faiza Ra,is ya baki giyar so kinsha . Tace " tatil ma nayi bari kiji ehe. Nace " to Allah ya shiryeki. Tace " me abun Allah ya shiryeni ibada fa nake.kema kin shiga layi munafuka ai kin ma fini jarabar son miji tun ba,ayi auren kika ishemu da YAYANA YAYANA YAYANA to ai shikenan yanzu takurun kus! Abinda ya rage saura shine ...... Nayi saurin katseta da fadin " ni fa ya isheni in ba dai so kk in fadawa yayana ba. Tace " ki fada mana kice injini nace saura yaye zani! Toshe baki nayi nace " laaa ni dai bazan fada mishi ba sai dai ko ke din tunda bakida kunya.. Ta yi dariya tace to ai shikenan zan fada masa da kaina.don haka ke kuma in kina neman karin bayani akan first night karkiji kunya ki tambayeni ni faiza zan miki bayani dalla dalla! Shiru kawai nayi na rasa me zance da ita. Ta yi dariya tace " hmmm zaki fada yarinya sai na jiki ke dai bari in tafi gun mijina bye! Kan nayi magana har ta katse nace " hmm faiza Allah ya shiryeki .kina jinmu ko ruma? Ta yi dariya tace " ina junku. Bayan ta gama dauran dankwali muka fito babban Palo. Ranar gaba daya na wuni amsa kiran waya domin duk masoyanmu saida suka kira suka tayamu murna amma shi uban gayya shiru tun bana damuwa har na gaji na gayawa ruma tace kar in damu zai kira ni. Su daddy kam ana can bikin nadin sarauta har dare suka shigo da aunty samira duk ya gaji gaba daya. Aunty samira ma sai da ta tayani murna tace " ihisan ashe duk tsumaki da na dinga yi rabon salman ne ba yayana ba. Sunkuyar da kai nayi ina murmushi tace " ai shikenan yayi ma kansa Ku kuma Allah ya baku zaman lfy da zuria ta gari. Nace " Na gode aunty .ai na dauka zaki kwana a gidanku yau kam Tace " tab bazan iya ba Wa zai kulan min da daddyn naku? Dariya nayi nace " kai aunty ga nan Momy . Tace "ke manta Momy ko ran girkinta ma ba wani cikakken kulawa take bashi ba bare. Ta fada hakan yayinda ta ce " kije daddyn ki na parlour . Nace " kai aunty ki barshi kawai sai gobe ya huta. Tace " to ai shikenan. Da yake a dakinta ta kirani muke tadin nan da nan ta shiga wanka saida ta sheka wankanta mai rai da lfy ta fito ko kunya babu tazauna ta gyre jikinta tsaf tasa kayan baccinta mai kyan gaske turarrurka kuwa ba,a magana don har na ji hancina ya fara toshewa tashi nayi nayi mata sai da safe . Can dare inata juye juye na kasa bacci tunanin ya salman kawai nake ji nake kamar na kira shi ni din. Aikuwa kamar ya Sani kawai sai ga kiransa naso naja aji amma na gagara da sauri nayi receiving sallama na yi masa. Ya amsa can kasar muryarsa kamar bai son magana yace " kina nan qalau koh? Murmushi nayi nace " lfy yaya yau dai fushin ya kare koh? Kamar ba zaiyi magana ba yace " fushin me zan yi ? Ai nasan wnn mutumin bazai aureki ba rumaisa. Nace " meyasa kace haka yaya? Yace " saboda ni kadai ne mutumin da zan iya auranki a kowani irin hali don sanin kanki ne rumaisa ni ke nake so ba gangar jikinki ba.yanayinda kika tsinci kanki a baya bazaisa naki auranki ba .don haka nake da banbanci da sauran manemanki hope kin fahimceni? Shiru nayi jikina ya mutu sosai har hawaye ya taru a idona gaskia Innah ta cuceni sai yanzu nake jin zafin abun a raina sosai .wato ya salman har yanzu yana ganina da wnn tunaninsa duk wata mutuncina ya zube koh? Murmushi nayi lokaci guda nace " Na gode yaya da ka taimakeni ka aureni amma fa ka Sani akwai babban suprise da zan baka Wanda bazaka taba mantawa dashi a rayuwarka ba. Ba tare da kulawa ba yace " naji kuma ina jira saboda kin matsa min da maganar anyway,dama na kira ki ne in tambayeki ko zaki hkr ki zauna a gidanku in yaso in na gama da ayyukana Na dauki hutu sai nazo na daukeki in yaso 'yan bikin suje suyi jerensu suga gida su watse ko dai kin fiso a kaiki kanon a gama bikin kawai zaki jirani har sai na dawo ? Don gaskia ni bazan dawo ba sai ayyukana sun kare. Shiru nayi Na lura Sam ya salman bai damu da auran nan ba don baya murna kamar yadda ni nakeyi sai kace ba ango ba wai bazai bar aiki ya dawo ayi bikin ba alhalin nasan zai iya bada excuse a barshi ya taho. Hawayene shar shar a idona na ce" duk yadda kk so hakan za,ayi . Ina fadan haka na katse kiran na kifa kaina akan pillow na shiga rusar kuka kamar raina zai fita. Kukana ya tashi rumasau don mu biyu ne kawai a dakin banda wasu kawaye. Ta kunna wuta tana subhanallah Ihsan lfy? Duk ta damu haka na daure nace " ruma kina jin wani irin wulakanci da ya salman yake shirin yayi min sai kace auren bazawara . Nan na fada mata komai ta sauke ajiyar zuciya ta dafe kai tace " case dinki da salman baya karewa don Allah ki daina damuwa akan wnn Ihsan yana fa sonki kawai fushi yake don yana ganin kamar kin daina sonsa ne amma ba wani abu bane . Ganin Sam ban saki raina ba yasa tace " amma zan kira salim in fada msa kwanta ke dai sai da safe!!!!!! Ayi hkr da rashin post kwana da yawa naje bikine amma yanzu na dawo🥰😘😍 Hauly ce👍🏻🥰 [9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` Page ➡51 ************ Washegari kuwa ba bata lokaci motocin kaya sun tafi kano da sauran jama,a masu tfyr mota sauran masu bin jirgi kawai. Anan daddy ya kirani palonsa shida su ya awwal na tarar na gaushesu dukansu suka amsa cike da fara,a. Anan daddy yace " Ihsan kinga ikon Ubangiji koh dama ance ba mai auren matar wani.don haka ko kadan bana fushi dake bana fushi da Abdallah na dauki abinda ya faru a matsayin kaddara Wanda Allah ya rigada ya rubutashi.snn rukayya ta min bayanin komai akan rayuwarki ta jamia na godewq Allah da ya tsare min ke Ihsan kuma duk Wanda ya miki wnn abun shi yasani da Allah . ko ba haka ba? Ya juya gun su yaya ya awwal ne yace" hakane daddy tunda komai ya rigada ya wuce. Daddy yace " to don haka Ihsan ki tsarkake zuciyarki ki zauna da mijinki lfy Salman zabinki ne kina sonshi yana sonki don haka sai Ku zauna lfy.a dinga hkr kuma snn ladabi da biyayya kuma ko kadan karkiyi watsi da ibadarki ki rike addininki hannun bibbiyu shi zai taimakeki duk abinda ya sameki mai kyau ko mara kyau( ba fata ba) sha,anin rayuwane ki tattara lamarinki ki mikawa ubangijinki shi zai miki maganin komai .kar ki yadda ki dauki kudinki kije gaban wani kato da sunan kin kai masa matsalarki ya magance miki bazan taba yafe miki ba har in kinyi hakan.snn kima iyayensa biyayya da 'yanuwansa ki yi koyi da halin mahaifiyarki domin biyayyarta yasa ta shiga ran kowa a familyn galadima har gobe in an tashi ana bada misali da ita don haka nake son kema ki zamo hakan Mamana .banda bin zugin kawaye duk da ma naga ke baki damu da kawayen ba. A karshe ina muku fatan Allah ya baku zaman lfy da zuria ta gari. Tunda daddy ya fara magana jikina ya fara sanyi hawaye ya fara zubo min na goge da mayafina ba tare da na dago ba nace " insha Allah daddy zan yi duk abinda kace nayi Wanda ka hana kuma zan kiyaye .na gode da irin kulawar da kake bani Allah ya saka maka da gidan aljannatul firdaus. Cikin jin dadi yace " amin Mamana Allah ya muku albarka. Snn ya kalli su yaya yace " idan akwai abinda na manta ban fada ba sai Ku fada mata . Anan ya awwal ma yayi nasa nasihan ya samir ya karba yayi snn ya Hafiz daga karshe har da ce mun yay " in kuma anki asha bulala. Hararsa nayi daddy yayi dariya yace " to meye na bulala kuma ana zaune qalau. Yace" daddy ai Ihsan ta rainani ne da yawa bansan me yasa kuka gaya mata tsakaninmu ba nisa ba. Dariya sukayi gabadaya nikam muna hada ido na masa gwalo. Yace " au dama kukan na munafurci ne don kar ace bakiyi ba koh? Da sauri na sunkuyar da kaina daddy yace kaga je ka kira min su rukayya da goggonka suzo suyi su tafi gidan galadima kar lokaci ya kure musu. Anan ya kira su suka zo suma suka min nasu nasihar daganan fa mukayi sallama da daddy don daga gidan galadima sai airport su Maman sakina suna can gidan galadima don sune 'yan daukan amaryq daga dangin ango itada aunty zuwaira .Ruma ma tace ita ma dangin ango take. Gaskia naji ba dadi rabuwa da daddyna da yanuwana a dan zaman da nayi a yola mun shaku sosai.lallai aure wani babban al,amari ne a rayuwar 'ya mace! *******A kano kuwa su inna tuni an fara shirin tarbar Amarya harda girki na musamman don ma wnn karon 'yanuwanta na kamaru basu zo sun cika gida ba. Kasancewar daurin auren yazo a kurarren lokaci bata samu ta yi gayya ba daga ita sai adda A'i raihana Sadiya da sa,adatu itama 'yar yayan innace wacce take gaban adda A'i da zama don tun auren ya salman da sukhaina da sukazo aka fasa basu koma ba suna nan .dama ita adda A'i a Lagos ma take aure .in baku manta ba ita a gaban inna ta girma tun haihuwar ya salman aka baiwa inna ita .kuma su Abba sun sata makaranta ta yi har secondary inda samari suka mata caa! Kunsan kanawa da farar mace lol! Nan ta zabi wani hamshakin dan kasuwa Alhaji Shamsu aka musu aure yanzu suna Lagos da zama da yaransu shidda duk sun girma. Sadiya kam ta kasa zaune ta kasa tsaye .tunda motar kaya ta iso kano da 'yan Jere sai shiga da fita takeyi a yayinda matan baffanayena suka sanya mata ido don sunga shiga da ficen nata yayi yawa. Hankalinta ya kasa kwanciya sai da taje ta sami su inna tace" Inna kinga kaya ?Subhanallahi wani abun ma ban taba gani ba .da kyar wasu abubuwan in ba su koma da kayansu ba don gidan zai musu kadan. Inna ta tabe baki tace" hmm ai gara hakan kinga yanzu da gidan sarki aka kaita zasuyi ta rigima son ransu .ai dama su 'yan yola 'yan son girmane zasuji haushi sosai kasancewar yarsu a nan don ba haka suka so ba. Sadiya tace " wlh kuwa hmm ai zasu ga wulakanci na musu tanadinsa buhu buhu . Adda A'i ta yi dariya tace " kai Sadiya ba mutunci . Snn ta kalli inna ta ce " goggo ki kwantar da hankalinki kamar tsumma a randa ni da Sadiya mun ishesu. Raihana da tun dazu take zaune shiru tana kallonsu da abun ya isheta fita ta yi don in ta kuskura tasa baki zaginta zasuyi .don inna kwanaki har cewa ta yi zata tsine mata akaina ni da mama kawai dan tana goyan bayan gaskia. An gama jere kam masha Allah sai Wanda ya gani domin daddy yayi rawar gani gun hado min duk wani kaya na more rayuwa domin duk kayana ma ba anan aka saya ba. Kayan kichten kuwa har anso ayi rigima akansa domin mama ta ce gabadaya kitchen dina kayanda ta saya min za,a jera su aunty sa,a sukace bazaiyiwu ba ga na daddy ga na dangi ya za,ayi da su sai dai a zauna a rarraba.mama tace ai ta rigada ta fadawa daddy kar kowa ya kawo kayan kitchen har sai da aka kira daddy yace wa aunty sa,a shikenan asa kayan maman kawai nasu kuma a nemi wajan adanawa a ajiyemun. Aunty sa,a tace " lamido ni wai me ya faru da Amina ne? Yace " hmm ke dai Hajia bari fushin ne har yanzu taki sakkowa wlh. Aunty sa,a tace " to gaskia zan mata magana fushin ya isa haka . Daddy yace " toh inkinyi hakanma kin kyauta kuma kinga dama can 'yar dakinkine ke kk San yadda zaki lallasheta ta sauko. Tace " to shikenan duk yanda akayi zakaji sai an jima. Bayan sunyi sallama .anan sukayi yadda mmn keso . Mu dai sai wajen 03:00 pm muka isa kano jina nake wata iri. Cikin gida aka kaini gun su inna ko ince dakinta su goggo Ummi suka gaisheta a mutunce snn suka damka mata amanata suna" karki riketa a matsayin suruka ki dauketa tamkar yar cikin ki idan tayi ba dai dai ba kamin mu mu Sani ki dauki mataki ki nuna mata abinda ya dace . Inna tayi murmushi tace " haba ai babu komai rumaisa ko da can ma ai a dakin nan take kafin mamanta ta dawo gidan nan ni dai banda matsala da ita kawai dai in kun karantar da ita yanda rayuwar aure yake ai shikenan sai muce Allah ya basu zaman lfy. Gabadaya suka amsa da amin su goggo Ummi suka kara da Godiya . Anan akayi addua aka shafa snn suka kaini kofar mama itama tayi nata nasihar dagan nan muka wuce gidana . Wayyo Allah na koda naga na shiga jina nake kamar babu sauran matsala kuma a rayuwa .bayan nayi addua na shiga da kafar dama kamar yadda su goggo Ummi suka ce nayi. Gaskia gidan kam ya tsaru sosai duk da dai flat din baida wani girma amma masha Allah an tsarashi yadda ya dace da zamani babban Palo ne mai daukeda coridoor uku daya dakina ne da dakin baki sai toilet a kowanne . Snn daya kuma dining side ne sai kitchen da store .gefe daya kuma side dinsa ne Palo madaidaici da daki da ban daki sai kofar baya. Haka tsarin na ya salim yake. Komai dai ya zauna yayi kyau masha Allah ga kamshi kota ina. Muna dakina ni da su ruma da sakina Amarya sai aunty hadiza matar ya awwal muna hira su Sadiya suka shigo anan muka gaisa raihana tace " rumaisa anya bazan zo na tare a gidan nan ba Mukayi dariya Sadiya kam sai yatsine yatsinen fuska takeyi.daga nan ma fita tayi ta taradda adda A'i a Palo suka shiga gulma da fulatanci wai duk zatonsu ba maiji ko da gangan sukayi don tada fitinane oho. Sun dai sa goggo karima har ta fusata ta shiga basu amsa daga nan suka shiga sa,ainsa da adda A'i har tana cewa " in ba kaddara bama me salman zaiyi da yarku duk ta zubar da mutunci a titi... Goggo karima tace " karyane wlh babu abinda ya taba mutuncinta dashi tazo gidan nan. Adda Ai tayi dariya tace "aikuwa dai kam.tunda kince haka ya akayi sarki yaki auranta ? Bari kiji Hajia babu abinda bamu Sani ba akan yarku kawai ta zauna ta shirya muku karya da gaskia kun hau kun zauna .kaf garin nan waye baisan irin abubuwanda tayi ba na yawon karuwanci da shaye shaye..... Goggo karima ta katseta da fadin " ya isheki haka ki kama hanyarki ki fita anan ... Suna cikin haka goggo Ummi da aunty samira suka fito daga kitchen goggo Ummi ta ce " haba karima banso kk tanka musu ba wlh mene ne amfanin biye musun ne kawai ki barsu duk abinda zasu fada ma su fada . Goggo karima tace " Ummi kina fa jin irin maganganu marasa dadi da suke fada akan Ihsan to me ta musu? Goggo Ummi ta dafata tace " babu komai ki rabu dasu je kiyi alwala kizo muyi sallah mu wuce gun Amina. Daga nan ta ja ta suka tafi ciki aunty samira kuwa harara ta bisu dashi ta wuce ciki. Sadiya tayi dariya tace " kin min dai dai adda A'i. Adda Ai tace " tukunna ma basunce yarsu budurwa bace to ni kuma wlh sai na basu kunya da ni suke zancan. Daga nan suka fita. Su goggo Ummi kam abun ya damesu sosai ba yanda suka iya haka suka kara min magana da insan irin zamanda zanyi dasu. Washe gari bayan sun gama shiryawa gabadaya suka tafi Abuja.bayan munyi sallama naci kuka sosai aunty samira ma kukan ta tayani. Sun tafi sun barni ni kadai sai daga bayane ruma da sakina suka shigo suka tattara koina suka share sukayi goge goge .mama da aunty Zuwaira da Maman sakina suka shigo don suga gida haka suka dinga yabawa daga nan fa mama suka ja min kunne kan su Sadiya don babu abinda suke so sai tashin hankali da rigima don haka kar na biye musu.da haka suka barni sakina ma mijinta yazo ya dauketa sun tafi ruma kuma ta wuce side din ta don ya salim sai damunta yake da kira tun dazu. Zainab aka turo min don ta tayani kwana. Duk bidirin nan ya salman shiru kakeji ko layinsa ma kashewa yayi. Duk na shiga damuwa sosai wlh . Aunty samira kuwa sai damuna take da wadan can tarkacen wai sai dai nacigaba da amfani dasu kamin ya dawo bayan ni yanzu gabadaya abun ya min yawa har ciwon mara yake sa min. Ya salman sai da yayi satinsa biyun nan cif snn ya dawo ba bu Wanda ya Sani sai dai ganinsa kawai akayi gidansu ya fara sauka bayan ya gaggaishesu snn ya shigo gida anan ya salim ya tsare shi da tambaya wai ina zaije ? Kallonsa yayi cike da mamaki yace " zanje gidana gun amaryata. Ya salim yayi dariya yace " Malam ko kunya babu. Ya salman ya harareshi yace " kai sanda kaje gun amaryarka waya sanya maka ido. Ya salim yace " amma ni ai rakani kukayi don haka kaima ka jira saida daddare mu rakaka kaje a siyi baki. Tsaki ya salman yayi dole kawai ya juya side din su nada yayi wanka. Ni dai tunda zainab ta fada min dawowarsa na kasa zaune na kasa tsaye in shiga in fita duk sai naji gabana sai faduwa yake. Shigowar ruma ne ya taimaka min muka karasa girki bayan munyi isha ta zabo min kaya ta ajiyeni ta tsara min ado na gani na fada . Adon da ya daukemu tsawon lokaci har suka shigo da ya salim da abokansa shima ango yasha ado cikn sye blue din gezn Wanda yasha guga ya kwanta yana sheki ga hula kuwa an sakashi yadda ya dace kamshin turarensu ya gauraye koina. Su bakwai suka shigo . Bayan ruma ta gama shiryani muka fara tunanin fita haka dai muka daure muka fita kaina a sunkuye na kasa dagowa shikam tunda muka fito yake kallona ya kasa dauke idonsa. Ruma ta kaini har kusa dashi ta zaunar dani murmushi ya sakar mata yace " weldone sweet heart aikinki na kyau. Murmushi tayi tace " thank you darling. Snn ta koma kusa da mijinta ta zauna anan abokan ya salman suka shiga zolayarmu aka shiga tadi da dariya ni dai kaina a sunkuye fuskata rufe da gyale . Ya salman dai tunda suke ta faman zolayarsa baiyi magana ba ganin zasu bata masa lokaci yasa shi fadin " dare fa nayi guys . Anan suma suka mana nasu nasihar suka rufe da addua snn suka tashi zasu tafi ya salim ya ajiye ledoji a gabana yace " to ga kayan siyan baki Amarya. Wani daga cikin abokan yaya yace" asha amarci lfy sai mun dawo barka. Duk kunya ya lullubeni ji nake kamar in nitse kasa. Ya salman ya tashi ya rakasu ba jimawa ya dawo shi kadai ya rufe kofan palon yasa key snn ya karaso inda nake ya zauna kamshin turarensa ya bugi hancina . Hannun yasa ya cire gyalen da na rufe fuskata wani irin ajiyar zuciya yayi yace " masha Allah ! Amaryata . Hade fuska nayi na turo baki alamun fushi . Da sauri yace " o na manta fushi akeyi dani ban bada hkr ba. Snn ya danyi murmushi yace" am sorry babyna yau dai abar batun tuna baya tashi muyi alwala muyi sallah tukun mu godewa Allah da ya nuna mana wnn ranar da muka dade muna tsumayensa. Ya riko hannuna muka tashi a tare.... Karar buga kofa ne ya dakatar dashi ya juya hade da fadin wayene kuma ? Nikam na tsorata duk da dai karfe sha dayane . Yana budewa adda A'i ce ta shigo tare da sa,adatu da Sadiya. Murmushi tayi tace sory mun zo mun matsa maka zaka shiga dakin Amarya ko? Ta fadi hakan yayinda ta karaso gabana ta kama hannuna tana murmushi tasa min ledan da ta rike tace " to Amarya wnn farin bedsheet ne dazu na bada kudi aka siyo ki shimfida Ku kwanta akai in Allah ya kaimu gobe zan dawo inga result dinda aka samu . Tana fadan haka ta juya suka fice . Bai ce musu komai ba ya maida kofa ya rufe. Ni dai tuni hawaye ya taru a idona koda ya karaso guna kamin yayi magana na juya na tafi daki da kuka.......... Hauly ce👍🏻🥰 [9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` *PAGE* ➡52 *********** Tuni ya bini dakin ya karaso bakin gadon ya dago fuskata hade da fadin " baby yau ba ranar bakin ciki bane don Allah ki daina kuka kinji. Shiru na masa hawaye kuma ban daina zubarwa ba. Yace " rumaisa kukan na menene ? Ni fa na fada miki ba gangar jikinki nake so ba zuciyarki nake so don haka kar ki bari maganar adda A'i ta bata miki rai kinji? A hankali nace " yaya. Yace" na,am Na sunkuyar da kai snn nace " kaima kana zargina koh? Girgiza kai yayi yace" ko kadan a baya ma da nayi fushi rainane ya baci amma nasan duk abinda ya faru ba a cikin hankalinki bane wani ya miki don yaga ya tozarta rayuwarki. Har zan yi magana yace" no karkice komai yanzu ba lokacin wnn maganar bane don haka ki tashi kiyi alwala kizo muyi sallah. Na tashi na tafi ban daki nayo alwala na fito na samu ya shimfida mana pray mat nan na dauki hijabina na saka. Ya shige gaba ya tada sallah raka a biyu mukayi daganan ya fara zuba mana adduoi mun jima haka har na fara lumshe idonsa snn daga karshe muka shafa . Daganan ya juyo muna fuskantar juna yace " yanzu ki cire hijabin nan muje Palo kici kazarki kar yayi sanyi. A kunyace nace" na koshi ..... Ya tari numfashina da fadin " ban yarda ba tashi muje ki kara kadan nasan ki dama ba kya son ci dubi duk kin rame. Ya fadi hakan yayinda ya mike ya cire hularsa da agogonsa da zoben azurfansa.yace " mu tafi. Na tashi na cire hijabi muka fito Palo yace in dauko plate da cups . Kitchen na tafi na dauko snn na dawo na zauna anan ya baje kaji kam da zafinsu sun gasu kuwa kamshi kawai ke tashi. Haka ya dinga gutsura yana bani a baki ina karba amma Sam naki yarda mu hada ido don yau kam kunyarsa nakeji sosai . Kaina a sunkuye nace " yaya na koshi naci abinci dazu fa. Yace " to naji saura kisha milk amma bazan baki mai sanyi ba . Ya fada yayinda yake sa min a cup ya mika min yace ki shanye fa Na karba na fara sha a hankali . Bai barni ba sai ya tabbatar na koshi nima kaina har naji dadi don rabona da inci abinci haka har na manta don haka na mike nace ni bacci nakeji yace mun to saida safe. Na wuce daki ya bini da kallo yana murmushi Godiya yayi Allah a ransa snn ya danci naman ya wuce part dinsa ya sake sheka wanka hade da brush ya shirya cikin kayan baccinsa kamshi na tashi koina snn ya dauko wayarsa ya fito ya nufi part dina. Ni Sam ban kawo a raina zai dawo ba ina zuwa daki na cire kayana naje na sake wanka da ruwa mai dumi don inji dadin jikin nayi brush na na fito na zauna na goge jikina na shafa mai har zansa rigar bacci sai natuna da turarenda aunty samira ta ban tace indai yaya na nan in shafa sai dai ko in baya gari. Na dauko kamar bazan shafa ba amma naji baida matsala kamshin mai sanyi ne bazai takurani ba. Na shashshafa snn na saka rigar bacci na iya gwiwa na hau gado na kwanta na jawo bargo na rufa na fara karanto adduoin kwanciya. Ban gama ba ya salman ya shigo kasancewar bed side lamp a kunne yana hango fuskata . Ya karaso bakin gadon ya kalleni yace " bakiyi bacci ba har yanzu? Shiru nayi zuciyata sai tsinkewa yakeyi na fara lumshe ido . Murmushi ya sakar mun snn ya zauna gefen kaina hannunsa ya dora kan gashina yace" baby nazo na tayaki kwana ne kar kiji tsoro ke Kadai. A tsorace na ce masa " to. Shiru yayi yana ci gaba da shafa kaina a hankali lumshe ido yayi yayinda kamshin turaren nan ke ratsa duk ilahirin jikinsa. A hankali ya fara gangaro da hannunsa yana shafan koina na jikina ni kam gaba daya na tsinke ban gama tsinkewa gaba daya saida naji yana kokarin rabani da rigar anan fa na fara mishi kuka ina yaya don Allah ka bari. Ji yayi kamar na xugashi yayi ne tuni ya rabani da rigar hannunsa ya dora kan bobs dina a inda ya gama rikicewa gabadaya knn sai sarrafasu yake son ransa . Ai tuni na sa mishi kukan gaske ganin zan takura shi kawai yayi mai gaba daya ya cire kayansa ya jawo bargon ya rufemu janyoni yayi jikinsa ya rumgumeni sosai yana sakin numfashi da kyar cikin rada yace min baby kiyi hkr ki daina kukan nan kinji? Nidai ban fasa kuka ba don basan yau kam ba mai kwaceni a hannunsa sai Allah don gaba daya ya gama birkucewa idonsa tuni ya canza launi. Bakinsa ya hada da nawa daga nan topic ya fara canzawa ya shiga yin komai zafi zafi duk ya rikice min sai aakin nishi yakeyi sosai . Gyara min kwanciya yayi inda ya karanta adduar saduwa da iyali yana shirin shigata na yunkuro da sauri na fara kuka sosai hade da yaya don Allah ka bari akwai zafi. Ina baima San inayi ba kokarin shigewa kawai yakeyi amma babu hanya Sam Sam nan da nan jikinsa ya fara sanyi hankalinsa ya komo jikinsa ya dakata da abinda yakeyi . Nikam har nayi ajiyar zuciya hannunsa ya kai ya shafa kaina snn ya rada min dai dai kunnena yace' baby duk abin nan da ya faru ashe bai taba min budurcinki ba ? Lumshe ido nayi naji wani sanyi dadi a raina shima sauke ajiyar zuciya yayi snn yaci gaba da fadin " rumaisa wnn shine SURPRISE dinda kk ce zaki bani koh? Ni dai har lokacin ban iya cewa komai ba. Da kansa ya baiwa kansa amsa yace " tabbas shine gaskia I can't explain my happiness baby naji dadi sosai kuma na godewa Allah da ya tsare mun ke .Allah ya miki albarka na gode sosai ! Ya fada yayinda yake shafa kaina snn ya ya tashi nima ya dagani da sauri na jawo bargo na rufe kirjina. Murmushi yayi snn yace " ina bedsheet din da aka kawo maki? Da hannu na masa nuni kan drawer yace " yanzu tashi bari na shimfida koh? Ba musu na tashi duk da bargon ina ta faman boye jikina kunna shikam bedsheet ya dauko ya shimfida snn yazo inda nake ban ankara ya janye bargon ya dagani kamar baby ya kwantar kan gado hannuna nasa na kare kirjina gaba daya yau dai na gama jin kunya murmushi yayi yace " nan ne kadai ba kyaso na gani koh sai faman boyewa kk yi. Gaskia ya salman baida kunya ni duk tunani na barina zaiyi inyi bacci amma ina sake bude wani sabon babi yayi tuni na fara kuka ina masa magiya. A hankali yace min " karki damu bazan miki da karfi ba a hankali zan biki kinji. Ya fada snn ya hade bakinmu gu daya don kar in masa magiya saida ya gama rikita tunani da salonsa na ban mamaki don tuni ya fara mantar dani a wace duniya nake ashe romancing dina yayi sosai duk mun gama fita haytacinmu daga nan fa labari ya fara canzawa na fara kokarin kwatar kaina amma ina bakin alkalami ya bushe tuni ya shiga hanyar da ya dade yana mafarkinsa. Wata irin azababbiyar ihu na saki Wanda nasan duk gidan sai sunji saboda wani irin azaba da ban taba ji ba naji yau don har yanke numfashi nayi . Shikam ubsn gayya ya gama fita haytacinsa sai sambatu yake zuba min duk ya rikice duk sanyin Ac dinnan sai gumi yake . Ni dai azabar duniya yau na sha shi tun ina bashi hkr ina hada shi da Allah har nakoma neman agaji duk dangina ba Wanda ban kira ba amma ya salman baima San inayi ba .nayita tureshi har da yakushi amma kamar zugashi nake kara yi karfina ya kare jikina ya fara sakewa. Shidai bai tashi sanin halinda nake ciki ba sai da ya sami nitsuwa snn ya fahimci halinda na shiga snn ya sarara min Ya kwanta gefena yana maida numfashi jawoni yayi jikinsa ya rumgumeni sosai yana bubbuga bayana alamun rarrashi. Sai daga baya ya samu da kyar yace " min baby am sorry kinji zafi sosai koh? Kukan zuci na koma yi don gabadaya wuyana ya bushe hawaye sun kafe a idona. Ina jinsa yana ta faman zuba min Godiya da sanya min albarka har barcin wahala ya dibeni bansan ya ya karasa ba. Aikuwa har ya makara bai sami jam,I ba . Yana idar da sallar asuba ya zo kusa dani yace " baby ki tashi kiyi wanka kinga har mun makara. Hawayene masu dumi suka zubo min idona a rufe na soma kokarin tashi ai da sauri na koma Na kwanta saboda yanda naji duk jikin na ciwo kasana kamar ana hura wuta dan azaba. Ya fahimci yanda nakeji tausayi na bashi sosai yace min " sannu baby insha Allah zakiji sauki bari in hada miki ruwan dumi sai in taimakamiki . Ya tashi zai shiga toilet knn wayarsa ta fara ringing ya dawo ya dauka naga yayi shiru daga karshe yace " ina zuwa. Daga nan ya fita ba jimawa ya shigo tare da adda A'i ya kalleni snn ya kalleta yace......... Hauly ce👍🏻🥰 [9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` *PAGE* ➡53 ********"Adda gata nan kince gurinta kk zo ni bari in baku wuri. Ji nayi kamar na fasa ihu don haushi gaskia matar nan batada kunya. Shikam tuni ya fice ita kuma ta karaso tana ta yatsinar fuska ta zauna kan bedside drawer. Da kyar na iya budan bakina nace" ina kwana adda. Harara ta watso min tace " bashi ya kawoni ina maganarmu na jiya? Kauda kai nayi bance komai ba. Tace " kin ga tashi zakiyi ki ban bedsheet din ba zama ya kawoni ba . Aiko kusa bazan iya tashi ba yanda jikina yayi tsami ko yatsata banson motsawa gashi ba kaya a jikina ni tsorona ma karta fizge bargon naji kunya.yayinda nake yima kaina tambaya a zuciya ta na idan na tashi bata ga komai bafa tunda ance ana iya disvirgining wata ma babu ko digon jini.ba lallai ne sai anga jini bane cikar budurci ba .ni dai ina dan jin danshi a kasana. Ganin na mata shiru tace " sauri fa nake..... Shigowar rumasau ne ya katseta.bayan tayi sallama ta karaso bakin gadon ta kalleni snn a hankali tace " sannu 'yaruwa darling yace inzo in taimaka miki ki tashi sannu. A hankali nace " ruma banda kaya fa. Tace " ki tashi da bargon kawai . Na girgiza kai nace " aa bazan iya ba gaskia Mikewa adda ai tayi ta juya mana baya tace "na baku minti biyar Ku gama shiriritarku . Da sauri ruma ta kalleni a hankali tayi magana yadda adda ai bazata jiba tace" kinsan me ki daure ki dan dago kadan bari in xaro bedsheet din sai ki koma ki kwanta tunda naga kamar dorashi kukayi akan naki. Da taimakon ruma na samu ta cire bedsheet din na koma Na kwanta ina cije leba sai lokacin naga bedsheet dagani har ruma zaro idon mukayi don tsoron yadda bedsheet din yayi stain abinka da farin abu ga kuma ja ya fito radau!! Kauda kaina idona nayi ina jinsanda ruma ta yi ajiyar zuciya tace " to ga nan bedsheet din . Juyowa tayi da sauri aikuwa tana gani itama saida ta gwalo ido mamakinta ya kasa boyuwa a nan take jikinta yayi sanyi . Ba tare da tace komai ba ta fice jiki babu kwari ta wuceshi a Palo ko sannu bata ce masa ba shima kuma baice mata ba yasan abinda ya faru kawai wayarsa ya daddana ya kira inna wai Sadiya tazo yanzun nan. Tare suka shigo da Sadiya kai ni dai yau ina ganin ikon Allah Daren farkona ya banbanta Dana kowa lol! Ban yarda mun hada ido ba Sam don yau idan akwai Wanda nake jin kunyarsa da nauyinsa a duniya to yaya ne . Duk ya cika dakin da kwarjininsa ya kalli ruma yace " sweety har yanzu ba ta yi wanka ba . Tace " darling gaskia bazata iya tashi ba bansan ya za,ayi ba. Yace " da kyau shiga toilet ki hado min ruwan dumi. Snn ya kalli Sadiya yace " ke kuma ga bedsheet din nan ki dauka ki kaiwa adda ai sauran in sami labari baki kai ba kiga yanda zan yi dake. Sadiya ma jikinta a mace zuciyarta fal bacin rai ta dauki bedsheet din ta fita. Ruma koda ta hada ruwan ta fito ta gaya masa ya kara so bakin gadon ya dagani cak! Kai ya salman akwai wulakanci cire bargon ya barni haka ya tafi dani toilet runtse idona nayi kam! Yayinda na sa hannu na kare kirjina . Murmushi yayi yace " nan ne kadai ba,a so na gani koh? Duk kunya ya rufeni na kasa bude ido. Saida ya direni cikin ruwan ba shiri na saki ihu don azaban da naji ya karu da ya Sani a ruwan rike hannunshi nayi ina kokarin tashi don har naji karfina ya dawo tsabar azaba ina ta yunkurowa yana danneni ina " yaya don Allah ka barni wlh zafi yake min zan mutu! Yayi saurin fadin "shhhhhh! Alamun nayi shru haka yaci gaba da dawainiyar canza min ruwa har saida yaga na bar kukan snn yace " kiyi wankan tsarki ina jiranki. Ya juyan baya haka na daure nayi ina gamawa na janyo towel na daura da sauri. Ya juyo snn " ko na daga kine? Kan nayi magana tuni ya daukeni muka fito kan gado ya direni ruma tuni ta tafi. Haka ya dinga dawainiya dani yana ta lallabani kamar kwai har na kintsa cikin doguwar riga na atamfa na samu nayi sallah ya hado min tea mai kauri nasha da kuma magani pain relief anan bacci yayi awon gaba da no. Shafa kaina yayi ya sumbaci goshina snn yace " Allah ya miki albarka baby. Snn ya fita. Adda A'i suna can innah ta sako su gaba da zagi tana " wlh baku kyauta ba meye na bin diddigi haka ? Mtsww ni bansan ya zan bullo ma wnn lamarin ba. Adda A'i tace " hmm Goggo wlh salman baida kunya dubi yadda ya turo mana da zani gadon Cikin jin haushi inna tace " ba wnn na tambayeki ba A'i. Adda A'i tayi shiru yayinda Sadiya tace " inna ni inaga a cusa ma ya salman kiyayyarta a zuciyarsa yafi kawai ya dinga wulakantata har daga baya ya koreta gabadaya. Inna ta gyada kai tace " eh kin kawo shawara amma fa ni a ganina Amina ma ba,a zaune take ba .ta yaya za,ayi ace wai rumaisa budurwace ? Kai! Gaskia wnn abun ya bani tsoro fiye da tunaninku. Adda A'i ta gyada kai tace " kwarai kuwa ni ban yarda da goggo Amina ba Sam dole sai mun dage munyi damara sosai fa don kinga har zuwa yanzu salman ko kallon sa,adatu mai kyau baiyi ba. Inna tayi tsaki cikin takaici tace" ki bar batun sa,adatun nan kawai don na lura babu haske .gata nan har yanzu bazar bazar bata karasa wayewa ba duk zaman da tayi a gurinki snn dan kwalliyan nan na zamani da 'yanmatan keyi ma bata iyaba sai aukin son karatun boko kamar me.shi yasa a duk 'yan uwan naku nafison lathifa saboda taso ta ja hankalin sa sosai matsalarta dayace yawo da son tara samarin banza nabila kuma 'yar banza rawar kan tsiya ne da ita banda sakani asara ba abinda ta iya.ita kuma sukhaina kinga taje ta debo ma kanta mutuwa garin yawon banza na iskanci.gaskia ni shiyasa yanzu nake tsoronsu domin kwatata su yaya sun daina maida hankali kan tarbiyyar yaran nan sun barsu kara zube ni wlh ba haka suka min ba sanda nake gabansu amma ...... Adda A'i tace " goggo kawai ki bar wnn maganar haka.shiyasa na dauko sa,adatu na taho da ita Lagos don ta waye kuma kinga dama ita dabance ta sami tarbiyya gun babanta sosai tunda ita kadai Allah ya basu kuma kinga yarinyar akwai ilimi da basira.da kyar ma kawun ya yarda ya bani ita don naci sa,a ta nuna itama tana son bina ne. Sadiya ta tabe baki tace " to sai ki koma da ita don nan dai ba abinda ta iya sai kazantar tsiya. Adda A'i tace " tun yaushe zatayi clean ta goge ta waye bare ma in bokon nan ya shigeta wlh baza musha wahalar cusawa salman ita ba. Inna tace " ai ki barta nan kawai zata min 'yan aikace aikace sai a sata a makarantar su zainab in yaso in tayi hutu taje wajanki kinga ni yanzu banda yaro a gabana kuma ayyuka suna min yawa. Sadiya tace " don Allah inna ki bar maganar nan anjima kwa yita ni yanzu matsalata kawai musan yadda zamuyi da wnn shegiyar rumaisan da uwarta. Anan suka dawo da hirarsu akaina da mama.suna shirya tuggun da zasu mana. Ni ina can ina ta baccin gajia labarin first night dina ya baza dangi don ruma sai da ta fadawa aunty samira kaf yanda akayi snn ta fadawa goggo Ummi abinka da babban family nan da nan magana ta isa har kunnen daddy . Mama kuma a gun Maman sakina taji labari don tana jin abinda su adda A'i suke fadi. Ban tashi ba har azahar ina farkawa naji jikin yayi sauki sai dan abinda ba,a rasawa Godiya nayiwa Allah na tashi na nufi toilet don yin alwala sai dai har lokacin ina jin dan zafi haka na daure naje nayo alwala na dawo nayi sallah snn na koma na kwanta. Ba jimawa ya salman ya shigo da sallama . Rufe idona nayi da sauri wai ni a dole bacci.ya karaso yana murmushi ya zauna dab dani ya dagoni ya kwantar a jikinsa yace" baby nasan bakiyi bacci ba don Allah ki bude idonki in fada miki wata muhimmiyar magana. Kin budewa nayi saboda kunya yace " OK na fahimce ki so kk mu kara ko ?to ai ba matsala bari ki gani. Yana shirin kwantar dani na bude ido na da sauri nace " wayyo yaya in ka sake mutuwa zanyi akwai wahala sosai. Yayi murmushi yace " haba dai me abun wahala kefa MATAR SOJA ce ragwanci ba naki bane. Ya fada yayinda yake kokarin zuge zip din rigana ta baya. Ni kam a tsorace na fara yaya dan Allah ka barni na tuba......... Hauly ce🤗👍🏻 [9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` *PAGE* ➡54 **********murmushi ya danyi snn yace "so nike nan da wata tara ki bani babyna ne. Da sauri nace" yaya don Allah karka kuma yi wlh da zafi. Lokacinda ya karasa cire min rigar yace " ai zai daina baby dama don baki taba yi bane amma in kk daure kk bani hadin kai sosai nan da sati zakiji kin warware harma ki nema da kanki. Duk kunyar maganarsa nakeji gashi duk ya bi ya manneni da jikinsa sai shashafani yake nan da nan har yanayinsa ya fara canzawa ya shiga aiko min da sakon kiss masu zafi cikin salonsa mai rikitarwa Lumshe ido nayi sosai nake amsar sakonsa har lokacin da naji yana kokarin shigata da sauri na yunkoro cike da tsoro na fara kuka da magiya . Shikam kwantar dani ya sakeyi baice komai ba sai ma lalubo bakina da yayi cikin nasa daga nan ya shiga juyani son ransa. Duk zafi da radadi ya isheni nayita masa kuka yau ma. Shi dai bai ma San a wace duniya yake ba sai sauke numfashi yake ta yi har sai da ya sami nitsuwa snn ya kyaleni .kallon agogo yayi da sauri ya sauka ya shiga toilet ba jimawa yayi wanka ya zo ya saka kayansa snn ya kalleni idona a rufe hawaye na zuba . Cikin tsigar rarrashi yace,baby kiyi hkr kinji in. Allah ya yarda daga wnn bazaki kuma jin zafi ba bari inje masallaci inyi azahar inzo in miki wanka kinji ? Kai kawai na daga masa ya fita da sauri don kar ya rasa jam'i Amma yana isa bakin get ya ci karo da salim na shigowa yace " Salim wai har an idar ? Salim ya kalleshi yayi dariya yace " jiranka zasuyi knn sai ka gama....... Ya katse shi da fadin " kaga Malam banson dogon surutu. Salim yace " dole ne in maka dogon surutu mana asuba ma ai baka sami jam'i ba kawai ka gane yar mutane kana ta wahalar da ita wlh ka rage kar kasa taji tsoronka ta gudu. Ya salman yayi dan murmushi yace " hmm ai zata dawo ko ta gudu bari na je nayi sallah anjima ina da magana da kai. Ya salim yace" to naji Oga sir! Ni dai koda naga fitarsa lallabawa nayi da kaina na shiga ban daki na yi wanka da ruwa mai dumi snn naji Dan dama dama na fito Na gabatar da sallar azahar. Akan sallayar na kishingida . Har ruma ta shigo ta sameni tace " yaruwa sannu ya jikin dai ? Nace " hmm ruma ke dai bari da sauki dai. Tace " to muje Palo kici abinci tunda safe ma bakici abinci ba Darling yace . Nace" ai nasha tea kan nayi bacci. Na lallaba na tashi muka tafi Palo da kyar nake iya tfy haka nan zama ma saida da dabara don ban isa in zauna da bom bom dina mai kyau ba sai dai in dan jingina kadan . Tare muka ci abinci anan Ruma ta kalleni tace " yar uwa gara da first night dinki ya kasance haka kinga kin huta zargin kowa yanzu kam uwa uba su inna dole ne kawai yanzu kam su sarara maki. Nace " Hmm ruma amma nasha wahala wlh yaya bai sassauta min ba ko kadan dazu ma fa saida ya kuma gaskia 'yar uwa ina jin biki . Dariya ta yi tace " hmmm shiyasa nace maki a baya ki rage shan abubuwan nan ai don ina guje miki faruwar hakan ne ni nasan mai naji tunda har yanzu salim bai daina like min ba har barin aiki yake ya dawo gida. Nace " gaskia yaruwa naki da sauki tunda banga alamun kin wahala irin nawa ba. Dariya tace " ke kuwa ba dole ba Soja ne fa aiki ki zage kawai zaifi don bazai taba barinki ki huta ba amma kar ki damu zaki saba a hankali ba gashi na sababa? Nace " hmm aini ba aninda zan kuma sha ya isheni gaskia kawai aunty samira tasa nayita durawa gashi ina shan wahala bata ma Sani ba. Ruma ta yi dariya tace " nan gaba da kanki zaki nemi aunty samira ta baki daga zaran kin fara enjoying kema . Bayan mun gama cin abinci tatattara wurin ta yi snn muka ci gaba da hiransu inna anan na samu na kira aunty samira ma. Muna zaune su ya salman suka shigo tunda suka shigo idonsa a kaina. Nikam ya salim na gaida yace" ya jikin ? Kaina a sunkuye nace " da sauki . Yace " to masha Allah . Ya kalli matarsa yace " my dear mu tafi mu basu guri kinsan gidan amare ne ba,ason ana takurasu da zuwa. Ruma ta yi dariya tace " gaskia ne muje honey. Aikuwa ruma na tashi bansan sanda nima na tashi ba nabi bayansu. Ya salman yace " ina zakije? Tsayawa nayi snn nace " dama zan raka ruma ne. Murmushi yayi yace " kinyi sallar la,asar ne? Nace "aa. Yace " to mu tafi ciki kiyi sallah. Nan da nan naji zuciyqta ta tsinke kamar ince masa ni bazanje dakin ba. Haka na daure na wuce shi na shiga dakina biyoni yayi da sauri na shige toilet alwala na dauro na fito na sameshi yana zaune kan gado yana jirana. Bayan na idar da sallah na shafa addua na tashi da nufin fita duk da ma kwanciya naso amma tsoro nikeji kar a kuma irin na dazun. Har na kai bakin kofa yace " ina zaki je. Nace " zanje kitchen ne. Tashi yayi ya karaso kusa dani ya zuban idanunsa snn yace " dama Amarya tana zuwa kitchen ne? Shiru na masa ya riko hannuna yace " kinga zo muje ki kwanta ki huta sweet heart zata miki komai kinji. Muka isa gado kwantar dani yayi a jikinsa ya ture Dan kwalin kaina ya shiga shafan kaina yace " baby wlh I can't explain my happiness to you kin sanyani cikin farin ciki da nisgadi da ban taba shiga a rayuwata ba.babyna ke alkhairice a rayuwata Allah ya miki albarka Ni kuma Allah ya bani ikon rike ki da gaskia da amana Allah ya bamu zuria ta gari. Idona lumshe bance komai ba ya dago fuskata yana murmushi yace " bakice amin ba ? Rufe fuskata nayi da tafin hannuna don kunya Dan dariya yayi yace " kunya tsakanina dake ya kare tun jiya yanzu lokaci ne da zamu nunawq juna irin soyayya ko ba haka ba? Shiru na masa yace " shikenan na fahimceki so kk na kuma yi ko? Ya fara kokarin kwantar dani da sauri nace" yaya don Allah kayi hkr wlh yaya jikina duk ciwo yake. Baiyi magana ba saida ya gama cire min rigar jikina kuka na fara yi ina rokonsa ina hadashi da Allah. Shafa cikina yayi yace " kinga kiyi shiru ba da karfi zan miki ba a hankaline .so nike in samo mana baby nan da wata tara insha Allah. Ni dai na shiga uku da ya salman yau ko tausayina bayaji. In takaice muku labari ya salman kwata kwata ya kasa hkr in dai ya barni to lokacin sallah ne haka ya dinga asaran jam'i kuwa. A cikin kwana biyun na gurzu sosai tun ina jin azaba har nazo na fara sabawa don baya fita koina daga masallaci sai kuma gidansu in yaje gaisheda su Inna. Inna duk ta lura da yanayin Dan nata sai yawan nishadi yake gashi in ya shigo baya jimawa kamar da. Don haka gabadaya abun duniya ya dami inna gani take shikenan na gama mallake mata danta kwalli daya. Haka ta dinga tura min sa,a wai da sunan ta tayani aikace aikace ya salman na shiga yake korarta. Adda A'i kam munci sa,a tunda ta kwashi kunyanta ta koma muka sami salama. Kusan kullum sai nayi waya da mutanen yola. Sai da nayi sati daya mai kyau snn na warware tass sai lokacin na samu naje gida don gaida su Abba . Abba ajiyemu yayi ya dinga mana nasiha sosai daganan ya mana fatan alkhairi tare da shi muka je dakin mmn sakina muka gaisheta snn dakin inna. Da kyar na samu ta amsa gaisuwata snn tace " me yasa rumaisa idan na tura sa,a taje ta tayaki aikin gida kk korarta? Sunkuyar da kai nayi na rasa mai zance ya salman yace " inna nine fa nake kora..... Fuska daure tace " kaga banyi magana da kai ba don ka rigada ka zama shanyayye mijin tace. Snn ta kalleni tace " to bari kiji wlh kar ki kuma korar yarinyan in taje domin mahaifinta ya baiwa salman ita don haka ko kina so ko baki so a gidan naku zata zauna kuma yau zata tattara kayanta ta koma se ki shirya .kuma wlh kk kuskura ko kallon banza kk mata wlh ranki in yayi dubu sai na batashi . Ta juya gun salman tace " kai kuma sai ka shirya ka samawa sa,a makaranta na kudi mai kyau da islamiyya yanzu kulawarta ya dawo hannunka tunda mahaifinta ne yace don haka koda wasa ka bari ran ta ya baci zaka gamu da fishina.Ku tashi Ku bani waje. Na tashi da sauri na fita anan na bar ya salman yana mata magana. Nidai gurin mama naje a daki na sameta anan nima na zube kan gadonta muna hira jefi jefi nan na fada mata yanda mukayi da inna. Dariya tayi tace " ni wlh matar nan ina guje mata kar ta sami tabin hankali domin tana sanyawa kanta damuwa yana yawa sosai Allah ya kyauta ke kuma abinda zance miki kar ki sa damuwansu a ranki kuma duk abinda sukeyi kar ki tanka musu.yarinyar nan kuma tunda sun ce sai gurinku zata zauna ba damuwa ki riketa da zuciya daya duk abinda zakiyi kiyi tsakaninki da Allah karki muxguna mata inshaa Allah ba wani abu da ze sameki duk muguntarsu zai koma musu. Jikina a mace nace " to mama Amma banji dadi ba wlh ko wata daya banyi za,a dayki 'ya budurwa a bani dan tsabar mugunta. Muna cikin hira ya salman ya shigo suka gaisa da mama sun Dan taba hira ni dai ban sa musu baki ba har ya tashi ya sallametq ganin har zai fita ban tashi ba yasa shi fadin "mu tafi ko? Bata rai nayi nace " ina zuwa daga ba..... Mama tace " aa tashi kuje umma ta gaida assha . Ta fada tana mana dariya shikam tuni ya fita na bishi a baya juyowa yayi ya kalleni snn yace " ai da baki fito dagaki zan yi hmm kar ki kuma wlh don zan saki jin kunya . Yana gaba ina biye dashi a baya har muka isa gida. A Palo muka tarar da sa,adatiu da bakkon kayantq tana jiran mu dawo a bata daki. Nan naji wani irin bacin rai sosai har na kasa boyewa da sauri na shige ciki.bance mata ko kala ba!!!!!.. Ayi hkr da rashin post kwana biyu bani da isashen lokacin typing ne ga kuma matsalar NEPA. Ina fatan fans zaku min uzuri🤗🤗🤗🤗🤗🤗🥰🥰🥰🥰🥰🥰 Hauly ce👍🏻🥰 [9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` *PAGE* ➡55 *******Dakin ya biyoni da sauri ya sameni ina kokarin cire hijabina in ninke. Ya karaso gabana murya a sanyaye yace " baby kiyi hkr don Allah da maganganun inna snn don Allah ki dauki sa,a kamar kanwarki komai ze wuce insha Allah. Karasa cire hijabin nayi snn Na boye bacin nayi murmushi nace " haba yaya don Allah ka daina bani hkr ni fa ba bakuwar inna bace kuma maganar sa,a kar ka damu zan dauketa matsayin kanwata.hp nayi solving problems dinka? Ya gyada min kai snn yace " eh kinyi. Sannan ya juya har zai fita yace min " baby ina fa jiranki. A raina nace " hmm yaya kullum abu daya kamar cin tuwo . Nace " to yaya amma ai bamuci abinci ba tukun . Dawowa yayi yace "ai ba dadewa zamuyi ba ..... Ya fadi hakan yayinda ya riko hannuna yana kallona yace" yaushe zaki fara zuwa turaka ? Sunkuyar da kai nayi shikuma ya saki murmushi yace " wai ke yaushe zaki daina wnn kunyan ne? Juyar da kai nayi da sauri ina shirin shiga toilet ya rikoni yace " baki bani amsata ba sarkin kunya . Nace " yaya wanka zan yi? Yace " muje nima zan yi se muyi tare . Zaro ido nayi har na bashi dariya nace " yaya kaje kayi to in ka fito se in shiga. Yace " no naki wayon kawai cire min kayana yau bazan bar dakin nan ba sai na cire miki kunyan nan duka. Juyawa yayi yaje ya sawa kofa key snn ya dawo ni dai ina tsaye gabana sai faduwa yake kai ya salman baida kunya gaskia . Yana karasowa gabana ya janyoni ya cire min zip din rigata dake doguwar rigace haka nan ya cire shi ya barni da pant da bra duk kunya ya rufeni suma din kan kace meye ya cire min snn ya bani towel na daura yace " to oya cire min nima. Haka ba yanda na iya da raina na cire masa wando kadai na bar mishi snn namika mishi towel shima. Ya zuba min ido snn yace " sauran wando fa Wa zai cire min? Sunkuyar da kai nayi nace " yaya don Allah ka cire . Murmushi yayi yace " naji zan cire. Yana kokarin cirewa da sauri na juya zan shige toilet don bazan iya tsaywa ba . Sai kawai naji ya jawoni jikinsa rumgumeni yayi yayinda ya daukeni cak yayi kan gadon dani cire towel din Jikina yayi ya jefar daganan muka lula duniyar masoya duniyar da ke mantar damu dukkan hayaniya duniyar da ba komai cikinta sai tsan tsan farin ciki da nishadi da annashuwa . Saida muka gamsar da juna hundred % snn ya rumgumeni ya rada min a kunne yace " baby kin fara enjoying yanzu kam? Da sauri Na daga masa kai murmushi yayi ya daukeni muka tafi toilet ranar tare mukayi wanka muka fito bai barni nayi komai ba shi ya shiryani tsaf har da ajiyeni gaban mirror ya shafa min hoda da jambaki snn ya saka min 'yan kunne da sarka ya kalleni ta cikin madubi ido daya ya kashe min yace "you look so so so beautiful dear Murmushi nayi nace " thank you yaya Yace " to tashi muje nima ki shirya ni. Nace " to yayinda na daura Dan kwali na na tashi yana rikeda hannuna muka fita . A Palo muka sami sa,adatu Na zaune da kayanta Sadiya ma ta shigo ashe. Duk ido suka zuba mana nayi saurin cire hannuna cikin nashi. Sadiya ta gaisheda ya salman ya amsa snn ya wuce side din sa ni kuma na karasa gunsu Na kalli Sadiya nace " ina Abdul kk shigo ke daya. Harara ta sakar min tace " ke kuma Dan tsabar wulakanci mutane suna zaune suna jiranki kuka shige ciki kuka zauna. Nace " to ai banma San kinzo ba kuma ai bamu dade da shiga ciki ba . Tace " ba wani nan kunfi awa biyu a dakin wai me yasa kk hakane ? Duk kinbi kin maida ya salman kamar wani soko shi kuma ya biye miki kullum yana manne da ke a gida. Murmushi nayi nace " hmm to Allah ya baki hkr. Ta sake watsa min harara snn tace "da hkrn ya mutu sadakar nawa kk bayar.kuma ga nan sa,a tun dazu tace take zaune anan da kayanta baki nuna mata dakinta ba ko a palon zata zauna? Na girgiza kai nace" aa ba,a nan zata zauna ba. Snn na dauki jakar kayan sa,a na kalleta itama ni take kallo tun fitowata nayi murmushi nace " muje in nuna miki dakinki kanwata. Ta tashi har da Sadiya muka shiga dakinda ke fuskantar nawa shi ma an sa masa komai da komai . Na kalli sa,an na nuna mata wardrobe nace ga nan zo ki shirya kayanki kuma ga toilet. Kai ta gyada min tace hade da fadin " to aunty na gode. Sadiya kam sai kalle kalle take nace " Sadiya bari na kawo muku abinci anan ko zakuci a palo? Ta yatsuna fuska tace " aa tukunna yanzu zamuzo Palo. Ta kalli sa,adatu snn tace " to ga daki kam banda kazanta nasanki sarai bazar bazar kamar ba 'yanmata ba tafi kije kiyi wanka kizo in miki kwalliya kamin na tafi. Ni dai tabe baki nayi na fita na barsu sashin oga na wuce Na tarar tuni ya gama kintsawa. Cikin kananan kaya da sukayi matukar amsarsa murmushi nayi nace " yayana kayi kyau sosai . Matsowa yayi dab dani kamshin turarensa ya bugi hancina lumshe ido nayi ina jin wani yanayi mai dadin gaske a hankali yace" Allah ya soki dama yanzu nake shirin inje in daukoki ai. Nace" wayyo da zakasa naji kunyan Sadiya da sa,a. Fito da iPhone dinsa yayi ya saita camera yace " gyara muyi selfie. Murmushi nayi na dan kwanto kirjinsa ya saita mai kyau ya daukemu kuma yayi kyau sosai don duk muna murmushi. Yace " masha Allah se muje muci abincin ko ? Nace" yes. Ya rike hannuna muka fita zuwa dining nayi mana serving yana bani a baki nima ina bashi cikin tsantsan so da kulawa. Haka su Sadiya suka fito suka samemu na kalli yadda Sadiya ta dage tayiwa sa,a kwalliya tasha daurin dankwali kamar wata Amarya murmushi nayi nace" har kun gama knn masha Allah. Sadiya ta yi murmushi tace" eh bakiga tayi kyau sosai ba? Nace kwarai tayi kyau. Ya salman tunda suka fito yatamke fuskarsa kamar bai taba sanin meye dariya ba haka nan bai dago ya kallesu ba hasalima tashi yayi hannunsa rike da cup din milk ya tafi side din sa. Duk suka bishi da kallo nikam murmushi nayi nace " bismillah kuzo muci abinci. Sadiya tace" wai yaya har ya koshine ? Nace" eh nima ai na koshi Snn na tashi yayinda sukazo sukuma suka zauna nace " aci lfy. Na bi bayan oga . Sadiya kusan yini tayi a gidan don har goshin magriba ta koma a raina nace lallai sun sami ja,afar yadda sukeso in ba haka ba wani namiji ne zai bar matarsa ta dinga fita kullum snn ta wuni ba tare da ya damu ba? Sa,a dai bayan tfyr Sadiya daki ta koma .mukuma bayan munyi isha muka tafi sashin ya salim a can mukasha hira har ten snn muka dawo dakina ya rakani na dau kayan baccina muka kulle koina muka wuce bangarensa tare mukayi wanka yanzu ma mukayi brush muka zo kowanne yasa kayan baccinsa na tigashi hayewa gado naja bargo na rufe na lumshe ido a dole nayi bacci. Yana gama abinda yakeyi ya kashe wutan dakin ya sameni shima ya shiga bargon ya jawoni ya rumgumeni jikinsa kamar zai maidani cikinsa kai ya salman sai a barshi dama haka ya salman ya iya soyayya kamar a film gaskia nikam na more nayi dace da miji Wanda ya iya tattalin mace da bata kulawa har ya mantar da ita wacece ita lol! Tundaga ranar batun kunya ya kare nima yanzu na waye a harkan har wasu lokutan ni nake kai kaina domin musamman yake ajiyeni yana koyar dani salon....kala kala kai ya salman abun dai ba,a magana. A lokacin. Muka tafi Abuja nida shi gidan kawu kassim da Goggo Ummi kwananmu daya muka wuce yola . Gaskia daddy yayi farin cikin ganinmu .haka su aunty rukayya sai ce mun suke na kara jiki nayi kyau na kara haske . Daddy kam side na musamman ya baiwa surukinsa ya kwana acewarsa baison a takurashi . Da daddare kasancewar aunty rukayyace da girki nan muka sake da aunty samira muna hira kamar wasu kawaye muna kwasan dariya bamu Sani ba har sha biyu. Tana ganin time tace" la la la Ihsan dare ya raba kin bar salman shi daya tashi ki Shirya ki tafi. Nace " haba aunty ni me zan masa ne yanzu ? Zaro ido tayi tace " au haka ma zaki ce ? Bari kiji zamanin yanzu mata rike mazajensu sukeyi sosai gudun karsuyi sake wasu su kwace musu oya tashi kisa kayan baccinki tunda kinyi wanka dama. Haka tasakoni gaba har na shirya ta mika min wani abu a cup tace" sha wnn don ba,a zuwa turaka haka nan ba shiri. Nace"aunty meye wnn din ? Tace " hmm sai kinsha tukun in kinje kinga yadda surukina zai riki...... Zaro ido nayi nace" wayyo aunty ya salman fa dama ba bari na yake.... Ta tari numfashina da fadin " ke dan Allah can banson ragwanci oya karba kisha emergency ne ma sha yanzu magani yanzu . Haka na karba na kwankwade tayi murmushi tace da kyau yanzu kuma saura.... Ta dauko wata kwalbar turare ta bude kauda kaina na danyi sanin halin da nake ciki. Tace " gogggoki karimace ta kawo min daga Maiduguri kisa yatsanki kadan a ciki sai ki shafa kan mararki. Hakan kuwa na yi Allah ya soni ba irin mai katfin nan bane kamshinsa mai sanyi ne da sanya nishadi a zuciya . Tace " to madallah sai ki kirashi kice mai gakinan kina zuwa ya bude miki kofa. Aikuwa ina zuwa ya salman yanajin kamshin turaren nan ya rikice min jikinsa har rawa yake komai da zafi zafi yake min . Gaskia ranar kam ido na har ya raina fata aiki daya muka kwana yi na gaji likis har ban iya tashi da asuba ba saida ya dawo sallar asuba ya taimaka min nayi wanka nayi sallah daga kan praymat ya dagsni sai gado da kyar na kwaci kaina na gudu cikin gida breakfast dinsa ma kin kaiwa nayi nasa masu aiki suka kaimishi. Nikam baccin gajiya na shiga yi har saida aunty samira ta tasheni tana min dariya ni dai bata rai nayi tace tashi to tuni salman ya shirya ke yake jira Ku tafi babban gida. Nace" to. Hauly ce🥰👍🏻 [9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``` *PAGE* ➡56 *********bayan na gama shiryawa na fito na samesu shida ya samir suna jirana. Tunda na fito ya ke ta kallona har na dan tsargu ya samir kam tuni ya shige mota yana jiranmu. Na karaso kamin nayi magana yace " O wato guduna kkyi da safe koh. A shagwabe nace" yaya wlh na gaji ne sosai fa wuni nayi ina bacci. Yace " ai ba laifina bane ke din ne jiyan kin kara sugar sosai har na manta gidan surukai nake sorry baby. Banyi magana ba na bude gidan baya na shiga yayinda shima ya shiga gaba. Muka tafi gidan galadima. A takaice dai a ranar muka bi jirgin yamma muka dawo kano cike da kewar yan yola . Munje mun gaida su inna don Abbah kam baya nan daga nan muka tafi sashin mama har mun fara hira ya salman ya ce" yawwa Goggo Amina don Allah ina neman wata alfarma a wajanki. Tace " wace irin alfarma kuma salman? Ya kalleni nikam kaina na sunkuyar ya danyi shiru snn daga bisani yace " am don Allah Goggo Amina kiyi hkr ki koma gidan daddy......... A take yanayin fuskarta ya sauya ta tari numfashin ya salman da fadin " ok wato zugoka yayi kazo ka mun wnn maganar? To bazan koma ba!! Shiru yayi ya rasa me zaice mata nikam kwantar da kai nayi nace" ayya mama don Allah kiyi hkr daddy yana matukar so yaga kin koma... A fusace ta mike hade da yi mana nuni da kofar fita tace" Ku tashi Ku fita Ku bani guri! Gaba daya tashi mukayi ya salman yace" haba Goggo Amina katfa ki dauki maganar da zafi kiyi hkr.Allah ya huci zuciyarki . Tace " salman don Allah kar Ku kuma kawo min wnn maganar domin yana bata min rai matuka. Ya gyada kai snn yace" insha Allah zamu kiyaye. Snn ya kalleni yace " shall we go? Kai na daga masa jikina a mace daga nan mujayiwa mama sallama muka fita. Haka muka dawo gida jikina a mace ni wlh taisayin daddyna nakeyi yadda ya damu da mama ta dawo amma ita Sam baya gabanta. Bayan nayi sallar isha ina kan praymat sa,a ta shigo da sallama. Na amsa ba tare da na kalleta ba. Tace" aunty sannunku da dawowa Nace " yawwq ina kk je ne banganki a gida ba? Tace" dama ina gidan adda Sadiya ne tunda kk tafi shine dazu Goggo tace mun kun dawo. Gyada kai nayi snn nace " ya mkrnta ? Tace " lfy lau dama na shigo in tamvayeki ne ko da abinda za,a girka muku? Nace" aa kar ki damu yanzun a koshe muke don mama ta bamu abinci se dai ke in zakici wani abu ki shiga kitchen ki girka . Tace " nima saida naci a gidan adda Sadiya tukunn nazo. Muna cikin haka ya salman ya dawo daga masallaci. Ta mashi sannu da zuwa hadi da gaisheshi ya amsa hade da fadin " ina kk je dazun ba kya gida? Kanta a sinkuye tace" ina gidan adda Sadiya ne . Bai kuma yin magana ba ita ma tashi ta yi ta fita Tana fita yace " sweety na ba lfy fa tace shi ya hanata shigowa ko muje ki tayata hira ne? Ta shi nayi ina ninke praymat nace"me ya ke damunta? Murmushi yayi yace " mun kusa samun baby ne first born dinmu na hanya saura second kuma .... Murmushi nima nayi nace" kai yaya kana son yara sosai. Na karaso kusa dashi janyoni yayi jikinsa ya zuban ido snn ya tura hannunsa ya shafa marata yace" hmm baby haihuwa na da dadi sosai fatanmu Allah ya bamu yara na gari. Nace " ameen yaya nima ina son yara sai dai kuma akwai abinda yake damuna ba sosai ba amma. Ya ce " mene ne baby na. Nace" yaya gani nayi familyn mu ba,a cika haifan yara Mata....... Ya tari numfashina da sauri yace" ba haka bane kar ki canfa in Allah ya yarda zaki haifomin kyakyawan yara Mata kamarki. Murmushi nayi nace " yaya nafi son yarana suyi kama da kai sosai amma su dauki fara,ata..... Hancina yaja sosai har na danyi kara yace"ai na fiki fara,a Dariya na danyi nace " hakane yayana amma fa baka dauki fara,an inna da Abba ba. Yace "duk na fisu koh? Nace " kwarai kuwa. Na tashi ina dariya yace " ina kuma zaki? Nace " wanka zan yi se mu tafi gunsu ruman Yace " baki bari sai mun dawo muyi tare . Nace " to yaya duk yadda kaso haka za,ayi. Ya saki murmushi yace" thank you my dear shiyasa son ki yake kara ratsa zuciyata a kowani seconds. Ya tashi muka fita sai part din su ya salim anan muka hadu sai hiran duniya muke amma munfi maida hankali kan hirar business dinsu ya salman domin zuwa yanzu komai yana tfy yadda ya kamata don sun gama shiryawa tsaf zasu bude katon shopping mall da sunan *S* & *S*wato salim da salman ko sulayman da sulayman. Ruma tace" haba kusa R&R mana darling. Ya salman yace" karkiji komai zamusa kinsan ke yanzu lallabaki zamuna yi . Nace"ai gaskia kam. Murmushi tayi ta ce" kema ai kin kusa ...... Ya salman yace" Allah dai yasa hakan ne ina son Ku cika mana gida da 'yan jarirai. Ya salim sai lokacin yace" kai dai sai kace mutumin da wlh ni fa a tsarina in ta haifi wnn cikin zamu fara planning na haihuwarmu sai after ten years kuma. Ya salman ya zaro ido hade da fadin " what kana haukane ? Ban taba tunanin wnn maganar a bakinka don Allah kar in kuma ji. Ni da ruma ma binshi mukayi da kallo murmushi yayi yace" wai to kallon mi kuke min haka na tsara rayuwata. Ya salman kam ya gama kulewa dan haka mikewa yayi yace " ke mu tafi. Yana fadin haka ya fita da haka hiran ya watse nima na musu saida safe. Muna isa part dinmu muka iske sa,a kwance har ta yi bacci na tasheta nace " ta tafi ta kwanta a daki. Ya salman kam tuni ya wuce side din sa ni kuma na kulle koina na wuce daki na wanka nayi na shirya cikin kayan baccina na bata lokaci gun shafe shafe da gyare gyare saida na tabbatar koina jikina yana kamshi snn na fita na kulle dakina na wuce dakinsa . Sai dai ina sa kai naji wani irin faduwar gaba lokaci guda kuma gidan ya kama girgiza dani ba shiri na runtse idona ina fadin innalillahi Wa inna ilaihir rajiun duk tunani na ko girgizan kasa ne . Haka na dinga jin hayaniya a kunnena wasa gaske na fara lumshe ido yayinda jiri ke dibana. Ya salman kuwa ganin yanda na sauya lokaci daya yasa shi mikewa ya riko ni yana " baby me ne ne? Ba sosai ma nake jinsa abinda bakina ke iya fadi shine " yaya ka kaini gida gun mama bazan iya zama a gidan nan ba. Wasa gaske ya salman ya kasa gane kaina don haka kawai ya yanke hukuncin maidani gidan. Ya kira mama ya sanar da ita komai tace " to zata bude get. Da sauri ya daukeni a hannu har zuwa gida a dakin mama ya saukeni kan gado. Hankalin mama ya tashi sosai basu tsaya dogon turanci ba suka shiga tofeni da addua har tsawon wani lokaci dana fara dawowa dai dai na daina jin jiri da hayaniya a kunnena kamar dazu har na bude idona nan na fara binsu da kallo. Mama tace " rumaisa me kk ji ? Nace " babu komai yanzu kam mama. Ya salman yace dazun yaya kk ji? Nan na fara yi masu bayani . Duk shiru sukayi suka rasa me zasuce daga karshe mama ta numfasa tace " to Allah ya kyauta sai Ku tashi Ku tafi dare yayi kuma kiyi addua. Hankali tashe nace"mama ni bazan koma gidan can ba wlh. Cikin tsoro nake maganar jikina ya na rawa. Ya salman ne yace "shikenan shikenan ya isa Goggo a barta anan din sai gobe.ni bari naje na bar get a bude saida safe. Jikin mama a mace tace" to muje nima sai na rufo get din gidan nan. Suka fita ni dai na gyara kwanciyata ko kan mama ta dawo har nayi bacci ita kam baccin ya gagara. Ya salman ma ranar baiyi bacci ba sai juye juye yaketayi da ya gaji kawai tashi yayi ya je ya dauro alwala ya kama nafila . Abu kamar wasa saida na share one week a gida don naki yarda na koma ya salman yace min ba komai amma Sam naki yarda gani nake idan naje gidan zai rushe dani. Sa,a kam tuni salman yace ta dawo kofar inna anan ne inna ta sami labarin komai a ranta tace " hmm kadan ma suka gani dani suke zancen!!!!!!! Fans din matar soja don Allah kuyita hkr dani matsalar NEPA ya wuce yanda kuke tunani sai dai Allah ya kyauta .insha Allah in komai ya daidaita zaku dinga ganin post akai akai. Hauly ina son Ku sosai masoya na da bazarku nake taka rawa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻🥰🤗🤗🤗🤗🤗👍🏻 Hauly ce🥰👍🏻 [9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡57 *********Tuni innah ta kira Sadiya tayi mata albishir . Sadiya tace" amma inna kinfa San Goggo Amina ba a zaune take ba in kin lura duk abinda muke mata baya ko girgizata ita. Inna tace" hmm aini tunda naci nasara akan rumaisa to banda wata matsala .kuma wnn karon abun yafi na kullum wlh suka kuskura suka ce ta koma gidanta ina mai tabbatar miki haukacewa zatayi gabadaya yanzu abinda nake jira knn kuma nasan za,ayi haka kwanan nan. Sadiya tace" hauka inna? Inna tace" sosai kuwa kuma bazata taba warkwwa ba har sai an tone wadannan layu da aka binne a gidan. Sadiya tayi dariya tace" tab Ashe zamusha kallo knn kwanan nan. Haka inna da Sadiya suka dinga hirarsu cike da nishadi. Da daddare ina kwance a dakin mama duk najini wata iri a cikin satin nan kasala sosai nakeji. Sa,a ce ta shigo da sallama na amsa bayan ta gaisheni tace " aunty rumaisa yaya na kira . Nace "yana ina? Tace" yana motarsa a waje. Nace " to ina zuwa . Bayan ta fita na tashi na kintsa sosai snn na sallami mama na fita. Yana cikin motar na shiga na sameshi yana sanye da kananan kaya wando 3 Quarter na sojoji da farin Riga sun matukar karbarsa. Kallonshi nake ina murmushi nace " monin sir! Fuska daure yace" me yasa tuni nake kiran wayarki baki dauka ba? Nace " wayar na silent ne yi hkr yaya. Shiru yayi tsawon wasu lokuta snn ya juyo muna fuskantar juna yace" yakamata zuwa yanzu kam ki dawo gida domin gaskia na gaji da zamanki a gun Goggo amina kina shiga hakkina dauriya na ya kare. Kaina na sunkuyar hankalina tashe don bana kaunar ace in koma gidana .nan da nan na fara zubar da hawaye. Cike da mamaki yace" don Allah meye abun kuka kuma anan yanzu. Aikuwa sai na fashe da kukan nace" yaya wlh bana son komawa gidan can tsoro nakeji. Yace" amma ai na fada miki ba komai koh? Shiru na masa naci gaba da kukana. Jikinsa ne yayi sanyi ya jawoni sosai ya rumgumeni hade da goge min hawaye yace" shikenan kiyi hkr ki bar kukan bazan tirsasa miki ki dawo ba amma don Allah nima a tausaya min hkr na ya kare. Ya fadi hakan yayinda ya shiga shashshafani yana sauke numfashi da kyar ya lumshe idonsa da suka fara canza launi Ni kuma uwar sonjiki dada lafewa nayi a kirjinsa idona lumshe nace " yaya mota ne fa. Dago fuskata yayi cikin wata kasalalliyar murya yace " hmm baby nayi missing dinki sosaine bazan iya hkr ba gaskia. Yana fadin haka ya hade bakinmu gu daya ya shiga sarrafani son ransa. Ganin yana kokarin zarcewa yasani fadin" yaya ka bari motane fa za,a ganmu. Da kyar ya sakeni idonsa tuni ya kada yayi jaxir ba tare da yace mun komai ba ya tashi mortar muka bar kofan gida. Nima jikina a mace ban kuma ce mishi komiba. Mun danyi tfy kawai sai gamu a wata hadaddiyar hotel mai ktau da tsarin gaske. Bayan mun gama parking muka sauka yana rike da hannuna muka tafi yaje ya biya kudin kwana . Muna zuwa dakin bai tsaya sauraran komai ba yayi kan gado dani ni dai ranar ina ganin ikon ubangiji. Yau ma naji jiki da kyar ya saurara min sai lokacin hankalinsa ya komo jikinsa dai dai . Bayan munyi wanka ne muka kwanta amma duk wani motsi sai ya kawai ya sake jawoni kwana mukayi muna abu daya.saida mukayi sallar asuba muka fara rama bacci. Sai sha daya muka tashi mukayi wanka nikam komawa nayi na kwanta kasala nakeji sosai .na lumshe ido sanyin AC na ratsani. Kallona yayi fuska sake yace " baby me zakici ? Na danyi juyi nace " yaya black tea kawai zansha. Zama yayi kusa dani yace" haba baby tun jiya da daddare bakici komai ba fa me yasa baki son cin abinci to? Kwanciya nayi a jikinsa nace" yayana wlh bana son cin komai ne. Yace" pls ki daure ko kadan ne kici kinji? Na daga mishi kai. Bayan mun gama karyawa muna shirun dawowa kawai na fara jun tashin zuciya sai amai ya biyo baya nayita kwarawa anan ya salman ya dinga min sannu Wanda daga bisani asibity ya kai ni a in da aka tabbatar mishi da ina da shigar ciki na wata daya . Wai karkuso kuga murna kamar yayi yaya da ransa ko motsi kwakkwara ya hana inyi haka ya dinga dawainiya dani har muka dawo gida ba kunya ya fadawa mama komai. Don haka minti minti yana kofar mama har ta gaji tace " maza in tattara in bishi ita ta gaji da ganin rashin kunyarmu. Ba don raina yaso ba na bishi gabana sai faduwa yake . Aikuwa na gudu ban tsira ba don muna isa gidan bakina yaki budewa inyi addua gabadaya naji tsigar jikina ya tashi na fara jin gidan gabadaya yana girgiza dani anan na yanki jiki na fadi sumammiya . Ya salman kam ya gama rukicewa rumgune yayi yana kiran sunana . Ni dai vankuma sanin ina kaina yakeba sai ......... Hauly ce🥰👍🏻 [9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡58 ************Saida na shafe sati guda ba tare da nasan ina nake ba . Babu ci babu sha babu magana ba bacci kuma da ido kawai nake bin kowa ko an kira sunana ban amsawa ban ma San dani ake magana. Tun ranarda abun ya faru asibity aka kaini amma basu gane komai ba suma in banda drip ba abinda suke sa min. Hankalin ya salman da mama ya tashi matuka mama ta kasa daurewa sai kuka take yi ba dare ba rana addua kuwa bata fasa ba. Daddyna da aka sanar mishi yace kawai a fita dani kasashen waje mama tace masa wnn ba case din asibity ba addu a kawai shine mafita . Anan daddy ya ware kudi masu yawan gaske akayita saukan Qur,ani dare da rana ba fashi ana kuma sadaka . Duk wani masoyina in yayi Sallah sai ya min addua.ya Salman har ya rame ya rasa me ke masa dadi a duniya ko abinci bai iya ci gashi ya koma bakin aikinsa don hutunda ya dauka ya kare. Tuni aka sallameni na dawo gida anan ake ta dawainiyar saka min drip. Mama kullum tana gefena tana zubar da hawaye .ta yaya ma zata iya wani aure a yanzu ta tafi ta barni wa zai kula dani ? Da ta fara shawaran amincewa ta koma gidanmu amma ganin har yanzu rayuwata tana cikin matsala yasa ta fara tunanin ta hkr da komai zata zauna kusa dani domin ta bani kulawa. Tana cikin wnn tunani sa,adatu ta shigo ta gaisheta hade da fadin Goggo ya jikin aunty Rumaisa. Mama ta dan goge hawaye tace" da sauki sa,adatu. Zama tayi shiru na tsawon wasu lokuta snn tace " Goggo in Allah ya yarda aunty rumaisa zata sami lfy domin yau na tone wnn asirin da aka mata Wanda ni aka baiwa naje na binne da hannuna a cikin gidan can... Sakin baki mama ta yi tana kallon sa,a cike da mamaki duk da tasan komai ma zasu iyayi. Mama tace" yanzu sa,a kina nufin kinsan abinda ke faruwa da rumaisa ko ince da hadin kanki aka mata ? Meye tai muku ne don Allah me yasa kuka cutar min da ita ki fada min ? Sa,adatu ta girgiza kai tace " Goggo ni ma bansani ba su innah ne suka bani wani fai fai zagaye da layu adda Ai ne ta kawo daga kamaru lokacin da su aunty rumaisa suka tafi yola shine innah ta bani tace inje in binne maganin tsarin gidane na karba na binne amma wlh ba don nasan na miye bane duk abubuwanda ke faruwa da aunty rumaisa hankalina bai zo kan layun nan ba amma tun shekaranjiya nake mafarki akan wnn abu dana binne shine yake da alaka da rashin lfyn aunty rumaisa to shine ban yi shawara da kowa ba na je na tone sai na boye a bayan flowers anjima zan kawo maki ki gani. Mama ta share hawaye tace" nagode sa,a tabbas kin cika 'yar halal bansan da wasu kalmomi zan yi amfani dasu wurin gode miki ba. Sa,a tace " ba komai Goggo sai dai Dan Allah ki rufan asiri karki bari su inna su Sani ko yaya ma ban son yaji don Allah Goggo wlh idan suka Sani zan shiga damuwa. Mama tayi murmushi tace " bazan fada musu ba sa,a suje su da Allah kuma salman ma bazan bari ya Sani ba sai lokaci yayi da kansa zai gane komai ni dai fatana samun lfy rumaisa. Sa,a tace " inshaa Allah Goggo bari in tafi kar inna ta nemeni. Mama ta gyada mata kai tace " shikenan sa,a na gode. Da daddare sa,a ta tafi ta dauko wnn faifan me zagaye da layu ta kawowa mama cikeda tsoro mama take bin faifan da kallo a ranta kuwa tana fadin" anya shatu na tsoron ubangijinta? Kai amma jahilci baiyi ba a rayuwa .Tabbas addua bata faduwa kasa banza Allah ne ya karbi adduoinda aka dinga yin min. Tare da sa,a suka zagaya dashi bayan dakunanta suka zuba masa kero suka kyasta ashana amma abin mamaki har keron ya kare layun nan ko gezau gara ma faifan ya kurmushe don haka mama ta yanke shawaran gobe zata je ta jefa a ruwa. Ikon Allah knn a Daren hankalina ya soma dawowa Jikina lokacin na fara tuna abinda ya faru dani sanda muka koma gida da ya salman amma banda wnn ba abinda na iya tunawa kuma sai kuma ganin mama da nayi yanzu tana sallah na duba agogo karfe biyun dare ne. A hankali na tashi zaune sai lokacin na lura da drip da aka samin nabi ruwan da kallo cike da mamaki. Mama kuwa tana sallama ta mike da sauri ta karaso inda nake rumgumeni ta yi ta fara hawaye tana Alhamdulillah. Jikina a mace nace" mama mene ne ya sameni? Ta dago a hankali ta kalleni snn tace " yau satinki daya knn kina kwance........ Bata boyemin komai ba hankalina ya tashi matuka kuka na dinga yi ina" mama me nayiwa inna ta min haka? Ni yaushe zan daina fuskantar matsala a rayuwa ta.yaushe su inna zasu barni na huta? Kuka sosai na dinga yi mama bata ce min komai ba sai da nayi mai isana snn tace" shikenan ya isa haka ki godewa Allah ma tunda duk abubuwa da suke miki Allah yana bamu ikon gane makircinsu Alhamdulillah ni dai na barwa Allah komai kema kuma sakacinki ne ya jawo miki da ace kina riko da addininki yadda ya kamata da Allah bazai basu ikon cin nasara akan ki ba.amma ba komai Allah ya saka miki. Ni dai dafe kai kawai nayi hawaye na bin kumatuna. Mama kuwa a cikin daran ta kira ya salman inajinta tana ce masa " salman rumaisa ta tashi don Allah yau kam ka samu kayi bacci. Yace " Alhamdulillah Goggo gani nan zuwa ki buden get . Tace "aa salman kaidai sai da safe na fada maka ne don ka samu yau dai kayi bacci. Ba don ransa naso ba ya amince a in da yaci gaba da sallolinsa. Daddy ma a lokacin yana kan sallaya mama ta kirashi ta sanar da shi daganan fa duk sukaci gaba da nafila suna godewa Allah . Ana idar da sallar asuba yaya ya shigo a lokacin na idar da sallah ina kan praymat mama kuma tana kitchen . Ina shafa addua na juya mukayi ido biyu tattausan murmushi na sakar mishi . Ta shi nayi na nufi inda yake da sauri ya kamoni ya rumgumeni kamar zai maidani cikinsa yace " masha Allah babyna kin sami lfy Allah na gode maka. Muka zauna bakin gado na dago na kalli fuskarshi nace " yaya me yasa ka rame haka. Ya dan shafa wuyansa yace " baby dole kawai na rame halunda kk shiga ya tayar min da hankali sosai . Nace " to yanzu kaga na warke yaya zaka dinga cin abinci akai akai banson ganinka cikin damuwa. Murmushi yayi yace " nagode babyna . A hankali na kamo hannunsa na dora kan marata nace " yaya yau baka taba kaji lfyn babynmu ba. Na karasa fada ina murmushi hade da kallon fuskarsa amma sai naga yanayinsa ya sauya bai dai ce komi ba sai marata da yake shafawa. Nace " yaya lfy? Sauke numfashi yayi yace " baby kiyi hkr amma babu babynmu a jikinki tun randa kk shiga wancan yanayin doctor James ya tabbatar min da hakan ...... Nan da nan hankalina ya tashi na fara hawaye tausayin ya salman ya kamani irin yanda ya kwallafa ransa a kan cikin nan. Ya shiga share min hawaye yace " lfyrki ta fi min komai rumaisa don Allah ki daina sakawa kanki damuwa Allah zai sake bamu wani kinji? Haka ya dinga lallabani har mama ta shigo hannunta rike da tire .bamusan ma ta shigo ba. Dan gyaran murya tayi da sauri na tashi daga jikin ya salman shima ya cire hannunsa da na dora kan marana. Cikin jin kunya na gyara zaman rigana. Mama ta kalleshi tace" Salman har ka shigo. Ya amsa snn ya gaisheta ta amsa snn tace " to Ku sauka kuci abinci duk kun rame wlh . Ya salman yace " mun gode Goggo. Daga nan fita tayi ta barmu . A baki ya dinga bani har saida na koshi dam nayi gyasa yace " Alhamdulillah. Nace " saura kai . Nan na fara bashi shima saida ya koshi snn ya kalli time yace " bari inje in shirya tfyn aiki baby Allah ya kara lfy kuma kici abinci sosai . Kai na daga mishi hade da fadin " to yaya sai ka dawo Allah ya kiyaye hanya. Yana fita gidansu ya shiga ya gaida Abba da Maman sakina snn ya tafi dakin inna. Bayan sun gaisa tace" ya jikin rumaisan ? Murmushi yayi yace " inna rumaisa ta warke.sai mu godewa Allah. Ba karamin girgizata maganar yayi ba tace " kana nufin ta warke har tana magana? Yace" kwarai kuwa inna ai yanzu ma daga gunta nake zaki iya zuwa ki dubata. Kan inna yayi wani irin sarawa ba shiri ta dafa kan hade da fadin " wash. Ya salman yace " subhanallah lfy inna ? Cikin dauriya tace " ba komai kaina ne yake mun ciwo duk kwanan nan. Yace " sannu inna Allah ya baki lfy bari in dawo aiki zan gwada miki bp dinki amma kan nan kisha maganinki kuma Dan Allah ki rage yawan damuwa. Cikin kosawa tace " naji jeka Allah ya kiaye. Daga nan fita yayi yaje ya shirya ya tafi aiki. A ranar daddy na yazo da su ya awwal munyi hira sosai daddy ya dinga godewa Allah ya hadani da su Haj rumaisa muka gaisa. Zuwa yanzu na lura mama da daddy an fara dasawa hira suke ta yi cikin fahimtar juna dadi naji a raina sosai. A ranar suka tafi acikin kwanakin anyi ta zuwa duba jikina . Inna kuwa tun ranar ciwon kai yaki sarara mata jininta ya mugun hawa har aka cire mata sammani ya salman ya sake birkicewa Allah sarki yayana gaskia ba don jarumtarsa ba matsalolin rayuwa ya isa ya kwantar dashi shima. Sadiya hankali ya tashi sosai adda ai ma tazo gani suke kamar mamace ta yiwa inna asiri kunsan abinda mutum keyi sai yaga kamar kowa ma shi yakeyi. Inna taji jiki sosai jini kuwa yaki ya zama normal ta ramene na fitan hankali ciwon kan nata in ya tashi kamar zatai hauka sai an rirriketa. Wlh koni sai da na tausaya mata amma nafi tausayin yayana da kyar nake samu ya danci abinci. Hauly ce🥰👍🏻 [9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~` *PAGE* ➡59 *********** Inna ciwo kamar wasa har ya kaita sati biyu a asibity saida aka kaita Abuja duk Wanda yasan inna a da yanzu in ya ganta sai ya zubar mata da hawaye tasha wahala sosai kamin ta fara samun sauki. Ni dai zuwa yanzu har na maida Jikina na koma gidana babu abinda yake damuna sai rashin kwanciyar hankalin ya salman . Satin inna biyu a Abuja aka sallamota ta sami sauki sosai don ban Wanda bai cire mata tsammani ba . Don haka inna tayi likis yanzu ko magana bata so banda yawan istighfari ba abinda take dama ance jiki magayi. Yayinda Adda A'i da Sadiya kuwa wutar fansa ke dada ruruwa a zuciyatsu gani suke kamar mamace tayiwa inna wnn aikin . Inna dai ce musu tayi " bata yarda su maida martani ba . Sadiya tace " wlh inna ko zan tafi tsirara bazan bar rumaisa taji dadi a gidan ya salman ba .Inna kina ganin yadda suka bi suka maida yaya wani iri sai yanda suka so sukeyi dashi yaya da kk Sani baya dariya yanzu wlh in kin ganshi da rumaisa sai kin rike baki . Hawaye ne ya zubowa inna tace" ni dai banida abinda zancewa Amina sai dai Allah ya isa tunda suka maida min da kamar wani bawansu .komai ya taso indai akan amina da rumaisa ne jikinsa na rawa. Adda A'i takaici ne yabi ya rufeta ta kalli inna tace " ai Goggo da kk cewa a rabu da su so kk su kasheki ? Goggo wlh malamina ya gaya min magana data girgizani don ce mun yayi salman ne da kansa ya tono wancan asirin kuma kuma Goggo Amina ce tasa shi ya tono suka kona. Inna da Sadiya suka zaro ido cike da tsoro inna tace " to waya fada mata an binne abu a gidan ? Sadiya tace " haba biri yayi kama da mutum nayi mamakin samun lfy rumaisa lokaci guda. Adda A'i tace " to yanzu Goggo dabara ya rage naki sai ki tashi tsaye akansu ko kuma watarana idan sun gaji dake su kasheki gabadaya. Inna ta dafe kirji ido waje tace " na shiga uku na ni shatu . Nan da nan taji kanta ya fara ciwo . Raihana da ke kwance tun dazu tana jinsu sai yanzu ta tashi hade da fadin " adda don Allah Ku bar sakawa inna damuwa ko bakuji abinda likitoci suka fada bane ? Meye amfanin wnn maganar da kk yi.ai kune kk shirin kasheta da wayan nan maganganun naku .ba komai ke damun inna ba sai ciwon zuciya da hawan jin ba wani asiri don haka addua zamu mata Allah ya bata lfy ba wai Ku zauna kuna wasu maganganu marasa tushe ba. Sadiya ta cika fam har wuya harara ta watsawa raihana hade da fadin " ke Dan Allah wa ya sakoki cikin wnn maganar? Adda A'i tace " hmm ni tsoro nikeji kar a hada baki da raihana a cutar damu watarana don itama an gama da ita tuni. Inna tace" da kuwa sai na tsine mata wlh. Raihana ta mike da sauri tace " don Allah inna ki daina ambatan zaki tsine mun kiyi hkr bazan kuma sa bakina cikin maganarku ba Allah ya huci zuciyarki. Ta dauki Jakarta ta kallesu tace " ni na tafi. Sadiya tace " umma ta gaida assha. Inna kam da harara ta bita har ta fita. Bayan fitarta sa,a ta shigo da warmers din abinci daga gidana ta ajiye snn tace wa inna " Goggo aunty rumaisa tana gaidaki . Inna ta zubawa sa,adatu ido snn tace " banso gaisuwarta kuma ki dauki abincin nan maza ki maida mata karta kuma turo min tunda kasheni suke shirin yi da uwarta. Kallon ta sa,a ta tsaya yi yayinda adda ai ta buga mata tsawa tace " ko bakiji me aka ce maki bane inci ubanki! Sadiya tace " anya wnn yarinyan itama basu gama da ita ba ? Nifa na daina yarda da sa,an nan hmm. Adda A'i tace "lallai kuwa dana maida ta kauye taci gaba da talle inga ta yanda zarayi bokon har ta zama likitan. Adda A'i ta kalli sa,a tace " kije ki maida abincin nan ki dawo yanzu ina da magana dake domin na lura kamar bazakiyi abin arziki ba . Sa,a batace komai ba ta dauki warmers din abinci ta fita. Ina zaune a Palo kawai naga ta shigo da warmes cike da mamaki nace " kar dai juye musu kikayi ? Ta girgiza kai tace " aa ba juyewa bane inna ce tace in dawo miki da abincin bazata ci ba . Ta fadi hakan daidai sanda ya salman ya fito daga part dinsa don haka shiru kawai nayi . Ya karaso ya kalli sa,an yace " to me yasa ? Kuma me aka mata ? Sa,a tace " nima ban Sani ba...... Tsawa ya daka mata saida ta gigice yace " kune munafukai ai da kuke zugata !! Jikinta na rawa tace" kayi hkr yaya.... Ya tari numfashinta da fadin " bace min anan munafukan banza kawai. Ta fita da sauri a zuciye yabi bayanta ni dai bance komai ba don ko nayi masa magana bazai saurareni ba yanda yake ta faman cin rai dama tun safe da adda A'i tazo ta gaggaya min maganganu ransa ya baci. Yanzu gidan ya tafi da isarsa kuwa ya shiga sauke musu kwandon balai Sadiya kam har da mari ta samu snn ya koreta kuma yace " kar ya sake ganinta a gidan tunda munafurci ke kawota . Adda A'i ma bai raga mata ba yayi mata tass har ta yi zuciya ta dauki Jakarta ta fice gidan Sadiya. Inna kam kuka ta saka tace " shikenan nima sauran ni in ka sake dawowa ka koreni .amma kafin nan bari in bar maku gidan ..... Yayi kasa da murya yace " haba inna ta ya zan koreki wlh inna su adda so suke su tayar miki da ciwonki bayan ni a duniya ba abinda nafi so irin inga kin warke.... Ta katse shi da fadin " ba wani nan salman Amina da 'yarta sun riga sun gama da kai yanzu bakada wasu abokan gaba saini da 'yanuwanka. Ta dada fashewa da kuka ya salman ya girgiza kai cikin damuwa ya riko inna yace" ba haka bane inna ba Wanda ya isa ya shiga tsakanina dake.kefa kika haifeni duk duniya banida kamarki bayan Allah da manzonsa fa to fa saike din Goggo Amina da rumaisa basu isa su rabani dake ba wlh don haka indai akan wnn ne ki kwantar da hankalinki . Sai a snn inna ta danyi sanyi ya zaunar da ita kan gado hade da fadin " inna dubi yadda kk rame baki son cin abinci in kin biyewa su Sadiya fa wlh zasu dinga saki a matsala kullum su dinga sawa zuciyarki shakku .ni nan da kk gani har gobe zuciyata na tare da ke inna ba Wanda ya juyan hankali don haka ki rabu da zancen su Adda A'i kinji. Tsakanin da da mahaifi sai Allah nan da nan inna ta sauko tace " ni dama tsorona kar su mallake min kai ka daina kula dani ne salman kai kadai Allah ya bani da namiji kuma nakeji da kai kamar tsoka daya a miya lol Dan murmushi yayi yace " hakane inna nima kuma haka nake ji dake banson abinda ya tabaki ko kankani.Allah dai ya kara miki lfy da tsawon rai. Daga naan ya kwalawa sa,a kira yace taje ta kawo masa abincinsa . Ni ina zaman jiransa muci abinci kawai ya turo wai abashi abincinsa tsabar takaici haka nace sa,an ta tattara harda Wanda ta kai musu dazun tunda ba ita kadai bace a gidan in bataci sauran 'yan gidan zasuci ai. Haka sa,a ta shiga dawainiyar kai abinci nikam daki na wuce Na kwanta . Shikuma lallaba inna yayi har saida sukaci tare ya tabbatar ta koshi tasha maganinta snn ya tafi masallaci Dan yin sallar azahar .yana dawowa kuwa ya tarar har ta soma bacci don haka yace sa,a ta kula da ita. Sai a snn ya dawo ya sameni har kwalliyata ta fara gogewa Ya zauna gefen gadon kusa dani a hankali nace " ka dawo? Yace " eh na dawo? Kinci abinci kuwa. Shiru na masa don bansan wace amsa zan bashiba. Hannu yasa ya dagoni hade da fadin taso ki gaya min waya tabo min ke? Ko dai maganar adda Ai ne na safe..... Girgiza mishi kai nayi yace " to kinga koma shi ne kiyi hkr kinji babyna karma ki daga hankalinki akan duk abinda zasu maki . Kuma kinga inna yanzu tana bukatar kulawata so dole ne in maida hankali sosai domin ta samu lfy bayan nan ba wani abu kuma. Gyada kai nayi nace" hakane yaya nima ina son kula da ita amma taki ta bani fuska abinda ke damuna knn ina son inna ta soni nima..... Murmushi yayi yace " karki damu zata soki sosai fiye da tunaninki babyna lokacine .kuma kici gaba da kyautata mata kinji? Kai na daga masa yace " yawwa my dear yanzu fada min me kk son ci inje in dafa miki? Na girgiza kai hade da fadin " kawai zanje inci abinci a gun ruma ne. Yace " banyarda ba in kinje baki son dawowa ni kuma yanzu hutawa zanyi so ina bukatarki a kusa dani. Yana gama fadin haka ya tashi hade da fadin " bari in dafa miki indomie da kwai nasan shine abinci ki ai. A shagwabe nace " uhumm ni yaya bazanci indomie ba. Yace " to me zakici? Nace " ni cornflex kawai zansha. Yace " cornflex kuma abincine haba baby to ai gara kisha kunu . Kamar zanyi kuka nace " ni dai cornflex nake San sha. Yace " shikenan ai nasan maganinki Vitamin C zan dinga dura miki tunda baki son ci. Ya fita ba jimawa sosai ya hado cornflex mai yawan gaske da kanshi ya dinga dura min har na koshi. Muna cikin hira cikin nishadi inna ta mishi flashing yana kiran ta wai sai cewa tayi yaje . Nan da nan ya tashi yace min yana zuwa nayita jira shiru shiru kawai danayi sallar la,asar na tafi gun ruma. Tundaga ranar inna ta gane yayin indai ta tabbatar ya salman na gida tofa batada kwanciyar hankali ta dinga daminsa da kira knn.abinci ma ta daina ci sai dashi indai yana gida yanzu gabadaya dare kadai nake samun hankalin ya salman shima don ba yanda ta iya da ranta ne da ta hana. Rabon da naci abinci da yaya har na manta daga breakfast har dinner can gurin inna ake kai masa suci tare.ni kuma sai dai inci da sa,a gabadaya naji ba dadi saboda sabo. Da nagaya wa mama tace haka zanci gaba da hkr har ya wuce.gaskia ina fuskantar matsi wlh ba daman yaya ya dawo gurina nan da nan zata turo ayi kiransa da daddare ma bai shigowa sai 10: 00 gajiya ma bai barinsa yayi abin kirki yana wanka zai kwanta bacci. Aikuwa ranar wata Sunday sammako nayi na gama komai dina na fada toilet wanka nayi mai rai da lfy na zauna na fesa ado na dauko wasu arnan English wears mini siket ne Wanda in na sunkuya bombom dina a waje da wata 'yar riga mara hannu tsayinta bai rufe ciki ba don cibiyata a waje haka ma bobs dina rabinsu a fili gashina yasha gyara kuwa sai sheki yake ga kamshi da daura rivoms masu kyau.anan na tuno da turaran da aunty samira ta bani tun a yola dana shafa ban kuma ba yau kam na dauka na shashshafa snn na dauko wani tsumi Wanda sai kin tabbatar zakije gun oga kan kisha saboda emergency ne sha yanzu magani yanzu. Murmushi nayi a raina nace " yau bake ba ganin danki ! Tunda mugunta ne nima ake mani! Saida na tabbatar komi zan zan snn na fita zuwa part dinsa na tarar ya shiga wanka don haka na hau gyara dakin ba jimawa na gama na saka room fresh mai sanyin kamshi snn na kunna Ac. Na koma bakin gado na harde ina jiransa . Ya fito daure da towel karamin kuma yana goge jikinsa . Aikuwa idonsa na sauka akaina sainaga ya bushe a gurin yana kallona tashi nayi cikin takun jan hankali na karaso gabansa ina murmushi saida na dafa kafadansa snn ya dawo hayyacinsa da sauri yace " baby irin wnn kyau haka ai zaki sa in birkice in rasa ina nake. Tuni idonsa ya fara canza launi dagani yayi sai kan gado tuni ya fara sunsunata kotaina ina yana sakin numfashi da kyar ranar nasha wahala har na gwammace ga yunwa kuwa sai jinsa nake don cikina empty nake jinsa. Bansan lokacin da na fara masa kuka ba da kyar ya iya bude bakinsa yace " baby menene? Da sauri nace " yayana yunwa nakeji sosai. Shiru yayi yana kokarin sake lalubata yace " to bari mu kara daya kawai nima ina jin...... Nace " wayyo yaya wlh bazan iya ba don Allah ka bari haka . Aikuwa bai saurareni ba saida ya kara din snn ya varni ya tafi toilet inaji ya saki shower akansa. Ni dai na gagara tashi tsabar naji jiki yau gabadaya HQ dina se radadi yake tsabar yaji jiki. Saida ya fito ya taimaka min nayi wanka muka fito ya kalleni yace " ki daure muyi azahar don har biyu tayi. Zaro ido nayi na tuna sanda na shigo na sameshi karfe takwas ne ba dole ma naji yunwa. Nace mishi " gaskia yaya bazan iya yin komi ba yunwa nikeji. Fita yayi yaje ya hadon tea mai kauri ya kawo min daganan ya saka jallabiyarsa ya fara sallah nikam saida na shanye tea din snn na tashi na tafi dakina nayi sallah a Palo na sameshi muka wuce dining na fara serving mana abinci duk yadda nayi sai bina yake da kallo har na dan tsargu nace " yaya menene? Yace " hmmm ba komai kawai ban gaji dake bane so nake mu gama lunch se mu koma ...... Zaro ido nayi a tsorace nace " wayyo yaya don Allah ka bari sai dare ! Murmushi yayi yayinda ya fara cin abinci yace " No matar soja gara ma ki saba da yanayina . Ba shiri nace masa yau fa yaya bakaje gun Inna ba . Yace " eh wlh sai nayi la,asar zanje yau gabadaya ranarki ce babyna so nake yau dinnan in samomana baby insha Allah kinji? Bata fuska nayi bance komai ba . Bayan mun gama anan muka sake lalacewa a Palo don ba kowa tun safe da sa,a ta tafi hadda na rufe koina nasa key. Har la,asar snn ya salman ya sake wanka ya fita masallaci bayan ya idar da sallah ma gida ya dawo ya sameni a Palo yace " kizo mu je mu gaida su innah Nace" to Hijabina na dauko na saka muka tafi. A dakin inna muka sameta tana kwance ko sallamar mu bata amsa. Ya salman ya zauna kusa da ita yayinda ni kam a kasa na zauna. Yace " sannu inna ya jikin? Harararsa tayi tace " sai yanzu taga daman barinka ka shigo ka dubani ..... Ya katseta da fadin " ba haka bane inna akwai wasu ayyukane da suka dan sha kaina . Tabe baki tayi tace " hmm sau nawa ina tura sa,a taje ta dawo tace min kun kulle kofar ku snn na kiraka yafi sau goma baka amsa ba ka mannan hauka yau dan abincin da kuke sammani babu kun barni da yunwa ai sai ku fada min tunda yau rashin mutuncin matarka ta motsa ta hanaka zuwa inda nake kuma ta barni da yunwa don ba uwarta bace ba kaikuma ka biye mata. Ya salman ya rasa mai zaice haka taci gaba da fadin duk abinda taga dama a karshe harda fashewa da kuka tana tamvayana me ta mini nake son rabata da danta Cikin dauriya nace " inna don Allah kiyi hkr . Harara ta tayi tace " dan Allah can munafukar banza ki tashi ki bamu waje.wato har binsa kikayi don kar ya dade koh? To ma wai shin ke kk haifamin shine? Ya salman ne yace" don Allah inna kiyi hkr wlh ba laifin rumaisa bane ni bata hanani zuwa gunki ba inna na fada miki ayyukane..... Hannu ta daga mishi nikam tuni na tashi na fita abuna. Na tafi gun mama na samu tana waya da daddy bayan sunyi sallama ta kalleni tace" kin shigo? Nace" A mama ina wuni? Tace " lfy lau yanzu kuwa daddynku ke tambayarki wai gobe zaizo. Murmushi nayi nace " to Allah ya kawo shi lfy .yanzu kam mama kin yarda zaki koma koh? Tace" idan na yarda na koma gidan naku wa zai kula dake ? Tunda ke har yanzu baki iya kula da kanki ba dan tsabar sakacinki . Nace " mama in dai dan nine wlh ki koma zan kula da kaina sosai . Tace " hmm ba inda zanje ina nan ma ya kk kare da su shatu bare idan na biye ta mahaifinki na koma yola ai wlh ba zasu taba raga miki ba. Nace " Allah mama karki damu zan kula da kaina. Tace " nifa banson komawa gidan nan naku uwardakinki kishina take sosai bata so na koma Dariya nayi nace " Allah sarki aunty samira gani take kamar zaki kwace mata daddynne. Tabe baki mama tayi tace " taje da abinta ni bance zan koma bama. Nace " ni dai mama don Allah ki yarda a maida auranku ko anan sai kiyi zamanki. Tace" aa ni bana son takura kowa nima banson a takurani. Duk yadda naso mama ta amince amma sam hankalinta bai kama ba. A haka na barta gida na koma side din ya salim na sami ruma ta gama girki taci kwalliya tana zaune a Palo tana kallo . Murmushi nayi nace " mai ciki kina hutawa. Tace " ai yanzu nake tunanin sake shiga gunki kafana biyu kofar ku a rufe bayan kuma motar darling na nan. Nayi murmushi nace " hmm ke dai bari . Dariya tayi tace " har yanzu kuna shan amarci da Darling koh? Na zauna hade da fadin yau ko girki ba wlh . Tace " ai ya tura min text yace inyi girki daku kin gaji ina yake ? Nace " yana can inna ta hanashi ko motsi kwakkwara . Tsaki tayi hade da fadin " kai 'yar uwa kina kokari da wnn matar mai abin haushi . Nace " ya zanyi ruma. Anan na bata labarin yadda mukayi yau. Dariya tayi tace " hmm yau dai ku kuka tsokanota gaskia ace tun safe danta baije ya duba ta ba snn baku kai mata abinci ba. Nace " kinsan Allah bamusan time ya gudu ba wlh har na gwammace me yasa na hanashi fita. Dariya ta kuma yi tace " ke ma kinsan halin kayanki dama can to na meye zakisha wadan nan abubuwan ? Nima fa ranar da kk bani nasha da kyar na tsira. Nace " ai koda baiwa faiza labarin sa cewa tayi in ajiye mata sun kusa zuwa kinsanta muguwar jarababbiyace . Ruma tace " hmm har Na tausaya mata don duk jarabarta sai ta yabawa aya zakinta nima kiris ya rage na ja miki Allah ya isa. Dariya muka sa lokaci daya . Shigowarsu ya salman ya katse mana hira ya salim yace " to gulmar mi akeyi? Ruma tace " gulmarku mukeyi honey. Yace " ai dama tatsuniyar baya wuce na gizo da koki. Nace " yaya hira muke akan sevice dinmu. Ya salim yace " tab ni har na manta da maganar service din naku ma. Ruma tace " a lallai kuwa ka fara tsufa. Yace " ba dole ba! Don Allah kizo ki mana serving yunwa mukeji kinga salman ko magana baiyi ba. Na kalli yaya duk yabi yayi kicin kicin da fuska nace " yaya lfy? Kai tsaye yace " lfy baby. Anan muka tafi dining don cin abinci. Bayan sun dawo daga sallar isha ne muka dan taba hira ya salman kam har lokacin bai sake ba. Saida muka koma part dinmu mukayi wanka muna shirin kwanciya na fara lallabashi ina tamvayarsa me yasameshi. Yace " baby so nake na koma Lagos da zama. Da sauri nace " saboda me to? Yace " baby bana son yanda inna take mana gaskia. Jikina a mace nace" to ya zamuyi sai mu dinga hkr hakan nan komawar mu Lagos ba shine solution ba. Shiru yayi bai kuma ce mun komai ba duk maganar da nake ta mashi. Hmm ai dole ma ransa ya baci tunda duk abinda muka ma inna ba gani take ba ! Ga zagi da rashin mutunci da take mana sai dai muce Allah ya kyauta!! Hauly ce👍🏻🥰 [9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡60 *************Kamar yadda ya fada kuwa bayan kwana biyu da faruwar hakan ya tafi Lagos saida yayi sati daya kamin ya dawo duk naji ba dadi wlh saboda sabonda yayi min kullum muna manne da juna. Da yake tuni ya fada min zai dawo don haka na shirya tsaf nayi lalle sa,a ta watsa min kitso kanana irin nasu na 'yan kamru 3 step ne mai seven seven. Randa zai dawo na shirya mishi girki na musamman da kaina naje airport na dauko shi don ya salim baya nan. Tun a airport dana ganshi na tafi da sauri na fada jikinsa shima cike da fara,a ya rumgumeni. Nace " you are welcome yayana. Yadago fuskata yayinda yake murmushi ya kissing bakina yace " thank you baby.ya kk ? Na ce" hmm yaya inata missing dinka wlh da kyar nake bacci. A hankali yace " really ! Aiko nima wlh baby da kyar nayi satin nan duk na kosa in dawo gareki babyna. Ya fada ysyinda ya kai hannu ya Shafa cikina ya yi kasa da murya yace " ya babyna? Rufe fuskata nayi da tafin hannuna nace " yaya ba komai fa period ma nake yi.... Da sauri yace "what !! Juyawa nayi ina dariya. Bayan mun dawo gida na gyara parking ina shirin sauka hannuna ya rike jikinsa a mace yace" baby har yaushe zaki gama period dinne? Murmushi nayi nace " I'm joking fa yaya jiya na gama Sauke ajiyar zuciya yayi yace " har naji sauki insha Allah next month bazakiyi ba. Ya fada yana murmushi zare hannuna nayi cikin nashi nace " kai yaya to muje ciki ka fara wanka na shirya maka delicious Yace " yawwa baby dama nayi missing girkinki mai shegen dadin nan. Dariya nayi daga nan muka fita na kulle motar muka tafi cikin gida. Zuwa part dinsa muna shiga yace " wow kamshi baby haka dakin nawa yasha gyara? Thank you Allah yamiki albarka. Amin yaya Na fada ina murmushi na wuce toilet na hada masa ruwan wanka na fito na taimaka mishi ya cire kayansa ya wuce toilet daure da towel ni kuma na bude wardrobe ina kokarin Ciro masa kayansa knn wayata tayi ringing akan madubi naje na dauka ina dubawa naga *INNAH* saida gabana ya fadi don nasan ba kiran lfy bane. Haka na daure na daga hadi da yi mata sallama . Ba tare da ta amsa sallamar tawa ba tace " ina salman yake? Nace " yana wanka innah Tace " oo wato hanashi zuwa wajena kikayi koh? Nace " aa innah da...... "Rufe min baki makira kawai .tunda nake da salman duk inda yaje in ya tashi dawowa sai ya fara shiga nan ya gaishemu ni da mahaifinsa amma gashi yanzu daga auroki kinzo kin rabani da dana...... Ta karasa hade da fashewa da kuka tana cewa " wlh ba abinda zance miki sai dai Allah ya isa kin mallake min da sai yadda kkyi da shi keda uwarki to wlh ki sani Allah sai ya saka min azzalumai kawai!!! Tana gama fadin haka ta katse . Sauke wayar nayi a hankali na sami gefen gado na zauna hawayene ya shiga zubowa daga idanuna ni bansan me nayiwa inna ba a rayuwa. Har ya fito daga wanka bansani ba sai da ya karaso gabana ya zuban ido jikinsa a mace yace " baby lfy? Da sauri na kauda kai na goge hawayena hade da fadin " ba komai yaya . Daga nan na tashi nace " idan ka saka kayanka kaje ka gaisheda su innah in yaso in ka dawo sai muci abincin. Na karasa fada hawaye fal idona snn na juya da sauri na fita. Jikinsa a mace ya karasa goge jikinsa jallabiyatsa ya zura da sauri ya fita zuwa gidansu. Abba kam baya nan don haka gun Maman sakina yaje ya gaisheta kamar yadda aka saba snn ya wuce dakin inna samunta yayi ta buga uban tagumi tana zubar da hawaye. Hankali tashe ya tsugunna gabanta yace " inna me ya sameki ? Harararsa ta yi tace" ka fita anan na yafewa amina da rumaisa kai. Da sauri yace " haba inna wace irin magance wnn ? Don Allah ki daure ki fada min me ya faru? Wani irin kallo ta masa snn tace" salman da duk inda kaje da in ka dawo sai kaxo ka gaishemu amma sai gashi yau wata can ta hana ka zo ka duba mu alhalin ni ka barni ma banda lfy baka damu dani ba yanzu salman sun mallake zuciyarka ka daina bani kulawa kamar da. Girgiza kai yayi yace" inna ki daina wnn maganar don Allah wlh dama niyyana in nayi wanka nazo na dubaki ne don tunda na tafi Lagos kece a raina inna so nake inzo mu zauna muyi hira shiyasa na fara isa gida amma ba dan wani manufa kiyi hkr ki yafe min don Allah innah kuma insha Allah hakan..... Da sauri ya dafe kansa da yaji ya fara ciwo saboda gajia da yayi gashi daga dawowarsa ya kama dogon bayani alhalin shi ba son dogon surutu yake ba. Haka ya daure yaci gaba da rarrashin innah har saida yaga ta sauko . Har tana ce masa " rabon da naci abinci sosai tunda ka tafi saboda dan sabon da ka min muke ci tare anan. Yace" ai ba komai innah ina sa,a tazo ta kawo mana abinci sai muci. Tace " hmm wai sun tafi lesson ne ko meyene oho musu ita da zainab ba mamaki ma sun tafi gun yawonsu na tsiya. Baiyi magana ba ya tashi ya fita gida ya dawo ya sameni a palo ina jiransa muci abinci . Kai tsaye ya wuce dining na bishi a baya ya kalleni yace " baby don Allah ki hkr bari naje naci abinci da inna Kinsan tunda ta yi rashin lfyn nan sai a slow Murmushin karfin hali nayi nace " hakane yaya babu komai Allah ya bata lfy. Na juya da sauri saboda hawaye da ya ciko idona na goge da sauri ba tare da na juyo ba nace " in ka dawo ka sameni gun ruma. Yace " OK baby. Da sauri na fita na barshi.amma duk da haka inna saida ta tambayeshi wai me yasa ya dade? Haka inna taci gaba da takura mana tana hanamu sakewa ya salman duk yaji ba dadi yace min in fara parking kayana zamu tafi Lagos zamu dade kuma. Na dai bishi da to haka kuwa akayi duk nayi mana parking . Aikoda muka sallami kowa inna kam kuka ta kama yiwa ya salman wai in ya tafi wazai kula da ita. Saida ya bata lokaci gun rarrashinta tukunna kan muka tafi muka sallami mama. Misalin karfe biyun rana muka isa lagos wani abokinsa ne yazo ya daukemu zuwa army barrack! _Fans_ _ayi_ _manage_ _da_ _wnn_ _page_ _banda_ _chgy_ _ne_ . Hauly ce🥰👍🏻 [9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡61 **********Gidan abokin nasa mai suna Hassan mukaje matarsa tayi mn kyakkyawar tarba duk da ma ba hausa ta iya sosai ba don yarbawa ne sunanta silfa Ta kawo mana abinci sakwara ne da miyan edika'ikon Wanda yaji manja . Gabadaya muka hadu a dining muka ci abinci gaskia naji dadin girkin don koda su ya salman suka fita suka barmu sai da na tambayeta ta koya mun don na lura ya salman ma yaji dadin girkin. Dariya tayi tace " ai saboda shi ma mukayi salman yana so sosai. Gyara zama nayi dan ba abinda nake so a duniya irin inga ina farantawa yayana rai a koda yaushe shine burina Nace " don Allah gaya min har in akwai wasu girke girken ma da kk lura yana so fada min. Duk hiranda muke yi munayi ne yayinda nake tayata aikin gida tana in bari ni kuma naki. Quarters din nasu ya burgeni duk kusan gidajen iri dayane 2 bedrooms ko wanne da toilets ga palonsu babba sosai da dining side sai kitchen da store. Daga wajen gidan kuma garaje ne sai BQ a gefe . Bayan mun gama aiyukan gida mukayi sallar magriba a dakin matar anan muka ci gaba da hira har mukayi isha ya salman basu dawo ba duk na gaji ya dawo duk da bansan ina ne masaukin mu ba don bai gaya min. Matar ta fahimci na gaji murmushi tayi tace " kiyi hkr sun shiga gari ne kuma kinsan Lagos da chinkoso sunje suyi cefane ne. Nace " ai ba komai. Muna cikin haka wata ta shigo ko sallama babu har naji tsoron yadda ta fado dakin gata wata jibgegiya ga tsawo taci bleaching har ta gode Allah wasu matsassun kaya ta saka riga da guntun siket kai ba dankwali inaga ma ba musulma bace. Da brokin ta gaishemu sai naji tana tambayar silfan wacece ni ? Silfa tace mata amaryar Suleyman ne. Wani irin kallo tayi min har naji gabana ya fadi snn ta juya harshe tana yiwa silfa yarbanci amma na lura silfan kaman bata son maganar. Tana gama yaranta ta fita Silfa ta kalleni tace" Amarya muje wai sun dawo suna Palo Nace " OK. Daga nan muka fita muka samesu a Palo da waccar matar tsabar rashin kunya zama tayi a tsakiyarsu ya salman tana zuba musu surutu duk haushinta ya cikani ni dai. Yana ganinmu ya tashi hade da fadin" baby kinji mu shiru koh. Murmushin karfin hali nayi nace " ai ba komai. Yace " yanzu kam zamu isa masaukinmu sai mu huta nasan kin gaji. Ya kallesu yace " to zamu wuce sai da safenku. Nima nayi musu sai da safe suka amsa cike da faraa matarcan da tun dazu sai bin ya salman take da kallo tace" Suleyman bakace komai game da laces din ba. Ba tare da ya kslleta ba yace " No khabirat sai nayi shawara da Salim tukunna yadda mukayi duk zan fada miki ki turon pics dinsu. Ta danyi far da ido snn tace " OK to sai ka jini. Muna fita maimakon inga mun shiga mota sai naga mun fara tfyn kafa bansan lokacin da nace" wayyo yaya na gaji fa bazan iya tfy mai nitsa ba. Hannuna ya rike yace " haba matar soja kamata yayi ki zama jaruma fa.mu nan matan mu harda kungiya suke dashi da uniform kuma suna training kema zaki fara ai. Na bata fuska nace " ni yaya bazan iya ba. Yace " koya miki zan yi baby na. Shiru na masa muka ci gaba da tfy ba wani jimawa sai gamu gaban wani flat kamar dai sauran sai dai kowa ya kawata gaban gidansa da shuke shuken fulawa .shiru kk jin wurin sai kukan karnuka duk na tsorata. Muna isa bakin asalin main door na gidan ya salman ya fito da keys ya bude snn yace " to bismillah. Muka shiga ya maida key ta ciki ya kulle snn ya kalleni yace " nan ne gidanmu anan zamu zauna mu da kano sai dai hutu. Da sauri na kalleshi nace " yaya har sai....... Hannu yasa a baki " shiiiiiiii! Banson jin komai muje kiga koina ko akwai abinda bai miki ba. Nan ya shiga dani koina har kitchen anan naga loading cefane a store ba abinda bai saya ba yanzu na kara tabbatarwa mun dawo Lagos da zama . Gaskia ni dai nan din yafi min kwanciyar hankali don ba fitinan su innah sai dai kuma nan sanyi ne yayi yawa ga zaman kadaici in ya salman ya tafi aiki. Gaskia mun sake sosai sai zuba soyayya muke son ranmu ko da rana in aiki ba yawa zai dawo muyi ta shan soyayya don ya salman baya taba gajia dani ko yaushe aiki daya ko cin abinci ya salman bai bashi muhimmanci kamar wnn ba. Don haka watanmu daya na fara sabon laulayin ciki Wanda da alamu wuya zansha don bana iya cin komai in kuma na ci wani abu to fa se amai don haka tuni na rame idona ya fada sai dai kirjina da ya cika dam kowani riga na saka sai ya matseni wurin kirjin nan don haka kullum hannun ya salman na wajan indai yana gida. Gashi na koyi dan banzan son jiki da ragwanci ga kasala ko wanka sai ya salman ya min in dare yayi kuwa mun dinga batawa knn saboda bana jure harka kaman da. Daga zuwana Lagos zuwa yanzu na fahimci wnn kabirat son ya salman take sosai domin a fili take nuna min kishi kuma sau da yawa tana kiranshi da daddare in bai amsa ta tura mushi text ranar kam har hotunanta na gani a wayarsa da ya bani wai in duba laces din da ta turo idan yana da kyau zai Sara da yawa ya tura kano. Ina cikin gani kawai sai ga hotonta cikin kananun kaya kai ba dankwali rabin kirjinta a waje wani irin kwanciya tayi akan gado na jan hankalin duk wani namiji lafiyayye . Nan da nan naji wata irin faduwar gaba da ban taba ji ba har na dafe kirji tsoro da kishi duk ya lullube min ido har bana iya ganin komai!!!! Hauly ce🥰👍🏻 [9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡62 ************Hankali na ya matukar tashi sosai fiye da tunanin Ku domin ko matsalar inna bata jefani cikin mummunan yanayi kamar wnn ba shin anya ni Rumaisa zan iya zama da kishiya? Wayyo Allahna ina matukar kishin ya salman amma dole in sawa raina hkr kar ciwon zuciya ta kashe ni. Cikina na wata uku na fara samun saukin laulayi yanzu.har na fara cin abinci na dan murmure. Ganin haka yasa ya salman yace in shirya yau muje gidan adda A'i. Don haka na gama komai da wuri na shirya cikin lace dina mai kyau Riga da siket colon pitch and maroon na saka gyale maroon da takalmi maroon sai jaka pitch mai dan adon maroon na zuba fashion kuwa sosai don haka na fito chas! Nayi looking unique sosai . Ya salman ya rigani fita yana jirana a mota don haka a gaggauce nayi maza na fito ina kokarin kulle kofa. Juyawa da zanyi in tafi wurinsa kawai naga khabirat ta nufi gunsa fuskarta cike da fara'a da yake yana tsaye ne kawai daga isarta naga ta bude hannu zata rumgumeshi da sauri na kauda kaina hadi da rumse idona ina fadin Innalillahi Wa inna ilaihir rajiun.karkuso kuji yadda kirjina ke beating da karfi kamar zai fado nasa hannu na dafe kirjin sosai ina ci gaba da karanto addua a zuciyata. Jin an dafani yasa na bude ido ya salman yace " mu tafi koh? Da sauri nabi bayan khabirat da sauri tfy take tana juya mazaunai. A hankali na dawo da kallona gareshi sai naga shima ita yake bi da kallo. Nan da nan sai naji hawaye ya taru a idona yana kokarin zubowa da sauri na goge nace " yaya don Allah meye hadinka da wnn matar? Sai lokacin ya juyo da kallonsa gareni hannuna ya riko yace " don Allah mu tafi saboda mu samu dawowa da wuri. Bance komai ba har muka shiga mota tfy muke a hankali har abin ya ban mamaki wai yau ya salman ne ke tuki a hankali . Nace " yaya me ya faru yau kk tuki a hankali? Juyowa yayi ya kalleni snn ya saki murmushi ya maida hankalinsa kan hanya yace " saboda babyna kar ya wahala. Shiru nayi yace " hope baki takura ba koh? Nace " aa ban takura ba . Yace " to ko na sa miki music ne sarauniyata? Tabe baki nayi nace" wakokinka duk babu dadi nasan wakan sojojine ...... Ya tari numfashina da fadin" haba matar soja yanzu wakan sojoji ne ba dadi? Kan nayi magana yace"is ok bari in sa miki irin music da kk so ba cellin Dion bane? Nace "yawwa ai kamar ka shiga raina. Gyada kai yayi yana murmushi ni kuwa ina sauraron inji waka kawai naji yasa kira,ar Sudais a surar Baqara. Na kalleshi nace " kai yaya ka jani . Ya danyi dariya yace " bana son kina shan kida baby ba kyau musamman ma yanzu da yake ba ke daya ba.ina son sabawa babyna da karatun Alqurani ne.saboda in ki haifo min Hafiz ko Hafiza. Murmushi nayi nace " hakane yaya. Daga nan shiru mukayi muna sauraren kira,ar a hankali yakeshiga jikinmu har muka isa gidan adda A'i. Wai karkuso kuga kyan gida lallai mujin adda A'i ba karamin mai kudi bane .babban gida ne sosai cike da ma,aikata maza da mata. Yaranta suka tarbemu cike da fara,a yayinda daya daga cikinsu taje ta gaya wa adda A'i munzo. Mun kusa hour daya kamin ta fito cikin takun isa da kasaita ta karaso fuskarta ba yabo ba fallasa tana " Sannunku da zuwa salman sai yau ku ka ga daman zuwa tun yaushe naji labarin kuna nan? Kai tsaye yace "to ba gashi munzo ba ? Ta zauna hade da kwalawa yan aikinta kira nan da nan aka cika mana gabanmu da kayan ciye ciye kala kala ga drinks harda fruits . Sai lokacin na gaisheta ta amsa kamar bata so snn ta kalli ya salman tace " nayita kiranka amma baka dauka nayima text ba reply me yasa? Yace " aikine ya min yawa. Tace " hmm salman knn aikinne zai hanaka daukan kirana ko karanta text dina ka min reply? Yace " kina son yawan magana wlh na fada miki aiki ne ya min yawa to mene ne kuma kk damuna bayan gani nazo kefa haka kk da son takurawa mutum! Ganin zai bata rai yasata fadin " sorry sir! Yi hkr.amma ai yau dinma da kk zo nasan Goggo ce ta matsa maka..... Mikewa yayi yace " na lura bakida abun fadane Rumaisa tashi mu tafi kawai anzo gidanki kina ta yiwa mutane wulakanci . Da sauri ta riko hannunshi snn tace " yi hkr kanina ta yaya zaka zo gidana kuma na maka wulakanci? Zauna don Allah na tuba. Zama yayi rai bace duk yabi yayi kici kicin da fuska. Ta numfasa tace " to dama madeeha ce tunda tazo take son zuwa gidanka tayi muku koda one month ne shine nace bari in tuntubeku tukun watakila matarka bata son baki. Shiru ya mata baice komai ba don haka ta kalleni tace " shiyasa Rumaisa nace madihan ta hkr kawai da zuwa gidan naku. Kaina na sunkuyar nace " adda ai ba komai ta shirya kayanta mu tafi. Ya salman yayi min wani irin kallo snn yace " wayace miki gida zamuje? Adda A'i ta yi murmushi tace " karka damu driver zai kai ta dama amincewar matarka nake so nasan kai bakada matsala abinda matarka tace shi kk bi. Tashi yyi ya kalleni fuska daure yace " ke mu tafi Tun kan na mike tuni yayi gaba adda A'i ta tashi da sauri tana cewa" bari to na kira madihan ku gaisa. Ko kulata baiyi ba ya fita nabi bayanshi ita kuma tayi cikin gida. Ina isa bakin motan nace " yaya bamu sallameta...... Ya katseni da fadin " zaki shiga mota mu tafi ko sai na barki anan? Da sauri na bude mota na shiga a raina ina Allah ya bada hkr. Nasan ba don cikin jikina ba ba karamin gudu zai yi da mota ba . Mun iso gida har lokacin fuskarsa a daure ya wuce bedroom ina biye dashi ina sauke jakata Na karaso gabanshi na fara balle masa bottins din shirt dinsa snn nace " yaya dan Allah ka dinga sanyawa ranka hkr bana son ganinka cikin bacin rai yaya sai inji ba dadi . Shafa kaina yayi yace " shikenan baby na daina bata rai don banson abinda ze taba min ke da baby na. Ya sauke hannun sa kan marana yace " babyna na motsi ne? Murmushi nayi nace " nima bansani ba kasan sabon shiga ne ni . Na karasa fada yayinda na cire trouser na barshi da boxers da vest. Na tattare koina snn na fita Palo na sameshi yace " baby zo naji ko cikinki na motsi. Dariya nayi nace " naki wayon abinci zamuci . Tashi yayi da sauri na nufi kitchen ina dariya shima ya bini a baya . Knocking din kofa da akeyi shi ya dakatar damu juyawa yayi ya nufi kofar yana budewa khabirat ya gani a tsaye nan da nan ya sauya fuska yace " lfy ? Murmushi tayi masa hade da kashe masa ido daya tace " good afternoon ololufemi. Kauda kai yayi ba tare da ya amsa ba ya juya ta bi bayanshi hannunta rikeda warmers nikam bushewa nayi a tsaye ina kallonsu. Muna hada ido da ita ta watsa min harara snn ta tafi kusa dashi ta zauna hade da fadin " na kawo maka abincine ? Tashi yayi ya koma dayan kujera yace " na gode . Jikinta a sanyaye ta zuba masa ido hade da marairacewa kamar zata mishi kuka nikam tuni na wuce daki don bazan iya juran abin haushin nan ba. Amma ina shiga daki kuma zuciya ta ta fara tuna min in koma inje inji me zata ce masa. Samunsu nayi shi yana tsaye ita kuma tana durkushe a gavansa tana " pls suleyman forgive me wlh komi kaga nakeyi akan sonka ne zuciya ta taki ta hkr da sonka idan na ganka wlh gabadaya jinake hankalina ya bar jikina ...... Ya tari numfashita da fadin " look khabirat ni bana son jin komai daga gareki ki tashi ki fita kawai kuma karki sake zuwa gidana bana bukatarki . Mikewa tayi suna fuskantar juna ta girgiza kai tace " aa suleyman ban yarda baka sona ba kawai fada kk yi amma in da gaskene ka fada min naji. Nuna mata kofar fita yayi yace " get out! Tace " bazanje koina ba sai dai ko...... Tsawa ya daka mata " I said get out! Tsoro ne ya kamani daga inda nake labe ina lekosu. Amma ita ko gezau batayi ba sai ma murmushi tayi tace " nasan kana sona kuma har gobe bazaka daina sona ba suleyman tunda gashi ka ki ka gaya min baka sona ba nasan matsalar ka bai wuce akan wnn bahaushiyar daka je ka auro bane amma kar ka manta addininmu ya halatta maka auren mata hudu don haka ni banda problem da matarka kawai abinda nake so ka aureni !!!! Girgiza kai yayi yace " khabirat ki fita nace ! Murmushi ta kuma sakar masa ta dora hannunta duka biyu kan kafadarsa tace " Suleyman ban taba son da namiji kamarka ba kuma wlh bazan taba rabuwa da kai ba sai munyi aure..... Tureta yayi yayinda ya daga hannu ya shararata mata mari kyawawa har guda biyu yace " 'yar iska mara kunya ki fita nace ! Nikam zuwa yanzu na gama rikicewa jikina har rawa yake tsabar yadda naji kalaman khabirat ya girgizani matuka nan naji marana na ciwo sannun a hankali naji sai gaba gaba ciwo na karuwa durkushewa nayi na fara murkususu ina kiran sunan ya salman tuni na hada gumi. Da sauri ya karaso inda nake yayinda khabirat ta fice rana kuka. Ganin ina rikeda ciki ina kuka ba karamin daga masa hankali ya yi ba ya durkushe a wurin yana " Rumaisa me nene cikinki na ciwone ? Da kyar na iya fadan yaya cikina zan mutu! Da sauri ya dagani a rikice gabansa ne yayi mummunan faduwa ganin yadda siket dina yayi stain din jini!!!!!!! _Masoyan_ _Rumaisa_ _salman_ _ku_ _kara_ _hakuri_ _don_ _Allah_ _akan_ _irin_ _matsalolinda_ _Rumaisa_ ke _fuskanta_ _amma_ _inshaa_ _Allah_ _komai_ _zai_ _daidaita_ 🤗🤗🤗🤗 Hauly ce👍🏻🥰 [9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡63 **************Ba bata lokaci ya kaini asibity dake cikin barrack din. Wnn karon ma cikin ba rabon mu bane snn a wnn karon nasan zafin miscarriage don nasha azaba sosai yayin wanke ciki ya salman tausaya min sosai da ana karbawa mutum ciwo da ya karba min . Gashi nayi ta bleading har saida aka debi jininsa aka kara min. Saida yaga na fara samun lfy snn ya buga ya gayawa Mamana. A ranar adda A'i ta zo ta dubani wai taje gidanmu bama nan shine ta tambayi neighbors sukace muna asibity. Har tambayar ya Salman takeyi wai mai yake janyo min bari? Shiru yayi ya rasa wani amsa zai bata Tace " amma in an sallameku ya kamata ta koma gida domin ta sami jinya mai kyau in yaso sai ta dawo . Yace " eh zata koma. Tace " to Allah ya bata lfy ni zan tafi . Yace "amin Nima nace " na gode adda a gaida mutan gida. Ya salman ya rakata ya danjima kan ya dawo . Ya kalleni cikin kulawa yace " baby ya kamata ki tashi kici wani abu lokacin shan maganinki yayi kan doctor yazo ya sallameki. Nace " to yaya Ya riko hannuna snn ya dagani na zauna mai kyau yace " sannu Allah ya baki lfy. Hawayene ya zubo min nace " amin . Jikinsa a mace yace " kiyi hkr baby ina iya kokarina wurin kiyaye bacin ranki tunda wnn shaidaniyar matar ta fara matsa min wlh ko kadan banida wata alaka da ita hasalima a dalilinta na bar Lagos na koma kano tun kan muyi aure ba na son ta na tsaneta amma taki ta fahimceni bansan wani irin zuciyane da ita ba. Na goge hawaye dake zubo min nace " yaya rayuwa tayi min kunci bansan ina zan sa raina inji dadi ba yaya a tunani na idan munyi aure dukkan matsalolina ya kare amma sai gashi matsalolin sai kara yawa yake bansan ya zan yi da raina ba . Rumgumeni yayi a jikinsa yace " baby karkisa damuwa a ranki komai zai wuce insha Allah ke kadaice matar da nake so kuma zanci gaba da so har karshen rayuwata ba Wanda zai rabamu kuma insha Allah zansan yadda zan yi in sanyaki farinciki da nutsuwa babyna.batun khabirat ki cireta a ranki zan dauki mataki na karshe a kanta don bazan kuma barinta. Haka yaci gaba da lallabani har sai da yaga na daina kuka snn ya saka min abinci a plet ya zauna gefena yace " yanzu kici abinci kisha magani zan miki wani albishir da zai faranta miki rai. Haka ya dinga bani a baki har saida na koshi ya bani magani nasha yayi murmushi yace " Alhamdulillah kar ki so kiga yadda naji dadi da kk ci abinci baby. Nace " yaya kaima kaci. Yace " zanci amma kamin nan albishirinki? Nace " goro fari Sol. Yace " yawwa hankalinki ya kwanta yanzu kam Goggo Amina sun maida aurensu da daddy..... Da sauri na mike daga kishigidar da nayi fuskata daukeda fara'a nace " really! Wayyo Allah na gode maka kai yaya wnn albishir din yayi min dadi sosai. Rumgumeshi nayi ina dariya shima murmushi yakeyi yace " sai muyi musu fatan Allah ya basu zaman lfy da zuria ta gari. Dagowa nayi na kalleshi nace " yaya kana nufin Mamana zata iya haihuwa yanzu? Ya gyada kai yace " sosai ma ai bata wuce haihuwa ba ki shirya samun kanne. Dariya nayi nace " kai yaya. To Allah yasa.wlh naji dadi sosai Yace " masha Allah Allah ya kara miki lfy ina son ranar Friday mu tafi kano insha Allah. Nace "to Allah ya kaimu A ranar aka sallamoni muka dawo gida ya barni a daki ina dan gyare gyare Ashe gidan hassan ya tafi . Tunda hassan ya ganshi haka yasan ba lfy ba don yayi yayi dashi ya zauna ma yaki Yace " suleyman nasan maganar khabirat ne ko........ Ya tari numfashinsa da fadin " tunda Allah yasa ka gane meke tafe dani fine ! Hassan ina so ka gargadi khabirat ta fita daga rayuwata ta daina zuwa gida na idan kuma ka sake baka dauki mataki ba ni zan dauki mataki da kaina kuma bazai muku dadi ba dukanku!!! Yana gama fadan haka ya fita hassan ya bishi a baya yana kara bashi hkr amma ko sauraronsa baiyi ba. Don haka hassan yana komawa gida ya kira khabirat da matarsa silfa nan ya shiga fada yana jawa khabirat kunne akan ta fita harkar ya salman . Amma sai cewa tayi " yaya ni wlh ba wani abu bane sonshi nake kuma har in zai amince aurensa zan yi don Allah yaya ka taimaka min ka rokeshi ya aureni wlh bazan taba iya rabuwa da suleyman ba. Hassan yace " khabirat rabuwa da suleyman ya zama dole domin.suleyman bazai taba auranki ba don haka ki sawa zuciyarki hkr ki auri Wanda yake sonki Girgiza kai tayi tace " yaya bazaka gane bane rabuwa da suleyman mawuyacin abu ne a......... Ransa a bace yace" ni dai na fada miki ki rabu dashi idan kinki kuma duk abinda ya miki karkice ban gaya miki ba. Daga nan ya tafi dakinsa khabirat kuka ta fara yi tana " aunty Silfa wlh ina son Suleyman bazan iya barinshi ba. Silfa tace " to khabirat ni bansan ma me zance miki ba . Ta kara fashewa da kuka tana " O my God suleyman why why why me yasa bazaka soni ba ? Khabirat ta zama tamkar mahaukaciya sai sambatu take silfa na bata hkr a karshe cewa tayi wlh sai tayi komai ma domin taga ta mallake zuciyar salman ya zama nata ita daya. Koda ya dawo gida ya sameni ina kwance yanayinda na ganshi na fahimci ransa a bace yake nan na fara tambayarsa me ya faru. Bai kulani ba ya wuce toilet. Kamar yadda ya fada kuwa ranar Friday muka shirya abokinsa David ya kaimu airport wai sai gamu a kano dama na yiwa mama waya nace sa,a da zainab ta basu mukullin gidana suje su share su goge koina. Gida muka fara zuwa palon kawu muka gaisheshi cike da fara,a ya amsa hadi da yi mana jajen rashin lfyta. Maman sakina ta kawo mana ruwa mai sanyi muka sha itama muka gaisheta snn muka tafi dakin inna suna Palo da Sadiya sai Abdul dake ta kiriniya. Nayi mamakin ganin yadda inna ta tarbemu da fara,a muka gaisa har tasa Sadiya ta kawo mana tuwo . Ta kawo ta ajiye inna ta ce " to saka musu man bakiga sun kwaso gajia ba. Tasa mana tuwon masara mai laushi da miyar busashen kubewa yaji kifi da wake ga man shanu .gefe kuma furace aka damata da kyau a kwano tasha sugar Sadiya tasa mana a Kofi. Ya salman tuni ya wanke hannu ya fara ci cikin jin dadin girkin har yace " innah nayi kewar girkinki wlh . Murmushi tayi tace " ai shiyasa na shiga kitchen da kaina na dafa maku da yake nasan itama Rumaisa 'yar gargajiyace. Ya salman yace " tashin kauye kuma lol! Ya fada yayinda ya kalleni yana dariya hade rai nayi don yasan banson ace min tashin kauye. Inna tace " Rumaisa ya kk zaune bakici ? Sunkuyar da kai nayi nace " zancine innah. Tashi tayi tace " keda baki sabawa da mutane wnn kunyar taki har yaushe? Ta shige daki anan ne na fara ci ya salman kam har ya kusa cinyewa ya dora Abdul a kafarsa yana ci yana bashi. Gaskia ya salman na son yara sosai. Sai lokacin ya kalli Sadiya yace " ke zoki kara ma Rumaisa abinci wnn mun cinye da Abdul. Kamin ta tashi nace " aa ki bari wnn ma zaiyi nafi son insha furan nan da yawa. Sadiya tana zaune tana kallonmu sai zumbure zumburen baki takeyi kallonta yayi yace " wai lfy nazo na sameki anan?ko kin sake halin ne? Tace " aa fa yaya nazo ne in gaida inna Ya kalli agogo yace " to gashi magriba ya kusa uban me kk jira da bazaki koma gidanki ba? Tace " yaya dama jiran isowarku nake dama ina so....... Katseta yayi " ki tashi ki dauki yaron nan ku tafi koma me kk so ki hkr sai gobe kizo ki sameni tunda ke ba,a rabaki da matsala kullum. Tashi tayi tace " Abdul zo kasa takalmi mu tafi. Abdul mannewa ya salman yayi yace " uhm uhm. Ya salman yace " kinga rabu dashi ki tafi zainab ko sa,a zasu kawoshi. Sadiya ta fita tana ta faman fushi ko na meye ne oho. Bayan mun gama ci na tattare gurin ina sharewa ya salman ya fita don zuwa masallaci. Inna ta fito tana cewa " ai da kin bari zan share. Nace " na gama ma innah. Daga nan na sallameta na wuce side din Mamana. Nayi mamakin ganinta a wnn lokacin tasha ado cikin atamfa Holland purple mai kyau dinkin ya karbeta ta zuba gold dinta tasha kitso da lalle ni dai bayan na idar da Sallah ina kan praymat sai bin mama da kallo nake har da sakin baki . Bayan ta gama abinda take yi ta zauna bakin gado ta kalleni tace " wnn kallon Rumaisa na mi nene? Nayi dariya nace " mama wlh naga kinyi kyau ne sosai kamar wata budurwa .. Na tashi yayinda na cire hijabi na dawo gefenta na zauna ina murmushi nace "mama yaya Salman ya gaya min labari mai dadi bakiga yadda nayi murna ba mama Allah ya sanya alhairi . Tace" Amin. Nace " mama yaushe zaki tare? Tace " anan zan zauna sai dai daddynki yace zai sayi fili yayi min gini anan kano don nace bazan iya zaman yola ba. Nace " gaskia kam mama ko don nima zamanki a kusa yanada mahimmanci snn banson ki koma yola kar aunty samira ta shiga matsala kinsan tana matukar kishin daddy. Dariya mama tayi tace " hmmm tanada gaskia .to ya Lagos din ya jikinki? Nace" Alhamdulillah na warke. Muna cikin hira ya salman ya leko da Sallama yace " Goggo Amina daddy yace zai wuce masauki . Mama ta kalleni snn ta ce " au na manta Rumaisa daddynki na gari muje ku gaisa. Murmushi nayi a raina nace " shiyasa mama ta cancara kwalliya haka knn. Ya salman tuni ya fita mama ta nufi wurin dressing mirror tana gyra dankwalinta ta kalleni nima ita nake kallo tace " ki tafi man ina zuwa. Murmushi nayi har zan fita tace " au na manta ki kara yi masa Godiya ya biyawa inna da Maman sakina kujeran hajj. Murmushin jin dadi nayi nace " kai gaskia na tayasu murna. Ashe shiyasa yau inna ke mun fara,a haba nasan ruwa bata tsami banza. Fita nayi na bar mama tana fesa turare. Ina zuwa Palo na sami daddy da ya salman suna hira kamar wasu abokai na gaida daddy ya amsa da fara,a yace " mamana ya jikin ? Nace " Alhamdulillah daddy naji labari mai dadi Allah ya sanya alheri. Cike da fara,a yace " amin Mamana na gode Anan na kara yi masa godiya hajj da ya biyawa su inna hadi da yi masa kyswawan addua. Ya salman ma yaji dadi sosai kuma yayi wa daddy Godiya. Mama ta fito ta samemu ya salman ya gaisheta snn yace inzo mu tafi gida. Mukayi musu sallama . Daga nan muka koma gida side din ya salim ikon Allah cikin ruma har ya girma . Duk inda tayi binta nake da kallo ya salman kam zolayarta yake yana" ki dinga tfy a hankali fa kar ki wahalar min da baby naga yanda kk ta fizgar jikinki kamar ba mai juna biyu ba . Dariya tayi tace " to sweety zan kula. Ya Salim yace " ainima fadan da nake mata knn kullum . Ya salman yace " daukanta zaka dinga yi ba wai ka barta tana wahala ba kai kuma. Ya salim yace " tab mai daukan ruma yanzu ai sai yaci damara. Dariya mukayi gabadayanmu ruma tace " kai honey. Sai bayan isha muka koma side din mu 'yanmatan nan mun samesu a Palo suna kallon series sun gyare koina tsaf don haka sashin ya salman muka wuce mukayi wanka a tare snn muka shirya bacci don mun gaji. Hauly ce🥰👍🏻 [9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡64 ************Washe gari kuwa da daddy zai tafi muka tafi tare don ya Salman zai koma Lagos ran Sunday. Na sami 'yan yola cikin koshin lfy sai hamdala . Anan na fara samun special kulawa gunsu aunty samira kunsan bata wasa ta nan . Ko abinci sakoni a gaba suke sai na cinye kamar wata karamar yarinya . Koda yake na rame kam sosai gashi na dada haske sosai daddy har cewa yake kodai jinin ne bai isheni a kara ya samir yace mishi aa kawai abinci masu karin jini zanci ba sai an sake kara min wani jini ba tunda ga kuma magunguna na. Abinka da 'yar gata satina daya na warke tass nayi jiki na dada kyau abina. Yaya kuwa kusan kullum muna manne a waya sai dai in aiki ya masa yawa. Yanzu ma shi nake kokarin kira don jiya yace mun ya kwana da ciwon kai ko hira mai kyau bamuyi ba . Karfe 6:00 ne na safe na kira har sau biyu bai daga ba ana ukun ne ya daga ina shirin yin magana kawai naji muryar mace tace " hello ya shiga wanka fa. Damm naji kirjina ya buga cikin dauriya nace " wacece ke? Dariya tayi tace " khabirat ce da wa kk tunani? Hawayene ya cika idona fal na sake duban agogo snn nace " ina salman din? A tsiwace tace min " bakiji nace miki ya shiga wanka bane? Da sauri nace" OK OK shikenan. Na katse kiran jifa nayi da wayar bansan ko a ina ta fada ba na kifa kaina a fillow na kama rusar kuka kamar an aiko min da sakon mutuwa. Haka aunty Samira tazo ta riskeni anan ta shiga tambayata me ya faru. Ko kadan ban boye mata ba duk na kwashe na fada mata don bazan iya kumsan wnn bakinciki a raina ni kadai ba. Itama hankalinta a tashe tace" kaji matsalar ai zaman bariki baiyi ba snn cikin kabilu se a hankali Ihsan ni dai shawara daya zan baki kisan duk hanyan da zakibi ku dawo kano zakifi samun kwanciyar hankali . Ni dai ba abinda na Sani sai kuka aunty samira tace " ta iya yuwuwa kuma makircine irin nata don ta hadaki da mijinki . Haka ta dinga rarrashina hade da bani shawarwari har saida taga na dan sami nitsuwa. Har kusan azahar ya salman ya kirani kamar bazan daga ba na dai daure na daga . Shi ya fara fadin baby yau banji muryarki ba sorry wlh bacci nake tunda safe bsnjima da tashi ba. Nace" yaya ko dai zazzabin ne ? Yace " shine fa kamar da wasa wlh . Nace " wayyo to Allah ya baka lfy ai na kira amma baka dauka ba. Yace " ikon Allah aiko missed calls kuma ban gani ba how comes? Na tabe baki hade da fadin " Allahu alamu .yaushe zaka zone kafa ce min zaka zo ka daukeni. Ya danyi shiru snn yace "zanzo baby ayyuka ne suka min yawa da ba don rashin lfyn ba da ina Maiduguri ma cikin week in nan. Nace " to yanzu ba rana knn? Yace "eh gaskia sai na sami natsuwa tukun na. Hawayene ya zubo min na rasa me zan kuma ce masa kawai na kashe wayar gabadaya . Kwana biyu wayata a rufe aunty samirace tasaka na bude abin mamaki ko text din ya salman ban samu ba. Da daddare ne wata number ta kirani na dauka macece muka gaisa tace " kin ganeni kuwa ? Nace " kai aa Tace " madame Fatima ce daga army barrack neighbor dinku . Nace " o Allah sarki matar oga bello ko ? Tace " eh ya kk ? Ya jikin kuma? Nace " da sauki wlh. Tace " to Allah ya kara sauki .wai yaushe zaki dawone amarya? Nace " babu rana gaskia akwai wata matsalane madam? Tace" eh to gaskia akwai matsala domin ina yawan ganin khabirat tare da maigidanki kuma har tana zuwa gidanku da daddare abinda kuma bai taba faruwa ba sai dis time shine nayi deciding na kiraki na fada miki domin ki bar komai ki dawo inaga zaifi domin kinga ke bakuwace a barrack dinnan bakisan komai ba mazajenmu na yanzun nan fa ba irin yadda kk tunani bane don haka karki sake ki sake nitsa da mijinki domin akwai matsala so ki dawo kawai. Tunda ta fara magana nake kuka sheshshekar kukana dataji ne yasa tace" no don't worry ba wani abu bane normal ne daddayane a zamanin da muke yanzu ki sami miji kamili .kinma ci sa,a don suleyman baida neman mata shikam bai kuma shan komai na maye and ba ruwansa da shiga harkar mutane kowa ya shaidesa amma wnn karon an sami akasi domin wnn khabirat taja ra,ayinsa sosai shiyasa na yi maza na kiraki gara ki dawo kar abin yayi muni gara kizo ki dauki mataki. Cikin muryar kuka nace" to ni madam wace mataki nasan zan dauka anan ni me na sani ? Kawai ni inaga rabuwa zamuyi...... Da sauri ta katseni da fadin " kash ! Da wuri haka ? Hmm Amarya ke yarinyace har yanzu bakisan komai ba .mu munsha gwagwarmaya da karuwai har ya zame mana jiki don haka kema dole ne ki cire duk wata tsoro ki tashi tsaye ki daura damarar yakar ko wace ' yar iska idan tazo kusa da mijinki.amarya zaman bariki ya wuce tunaninki fa .don ma yanzu Alhamdulillah mun dan sami 'yanci ba kamar da ba namiji yasa hannu yayi ta jibgar matarsa akan karuwa ko in yaje yasha giyarsa ya dawo.amma yanzu da zaran mijinki ya tabaki kina da right ki kaishi ga manyansa su hukuntashi to kinga mun sami sauki .snn mu matan barrack mun hada kai munada kumgiya tamu ta matan sojoji da muke meeting sau 2 a month in kinaso ki tamvayi mijinki ki shigo cikinmu na tabbata zaki zama jaruma kuma duk tsoron nan zaki bari.wnn kuka da kk yi duk zaki daina tunda nima na bari.don haka ki dawo kawai. Tsabar kukan da na ci har kaina ya fara ciwo don haka nace " to madam zanyi yadda kk ce din Allah ya saka da alheri na gode sosai. Anan mukayi sallama tashi nayi na shiga kai komo a dakin ina tunanin mafita . Gaskia naga tashin hankali yadda nake ganin rana haka nake ganin dare hankalina gabadaya a Lagos yake gani nake kamar kullum ya salman na manne da waccan 'yar iskar. Don haka ya samir nayiwa magana nace " ni gaskia ina son komawa ya salman kuma yace ba yanzu ba. Don haka ya samir ya kirashi sukayi maganar yace masa ga ni nan na matsa zan koma Lagos ba yanda ya iya da ransa yace to kawai in dawo din amma shi bazai samu zuwa ba don ayyuka sun mishi yawa. Ya samir yace ba komai. Don haka ya gayawa daddy daddy yace ba damuwa sai in tafi tunda jirgine . Nan na fara shirye shiryen tfy wnn karon da kaina nace aunrty samira ta hadomin dukkan magungunan nan in tafi dasu Ranar Saturday daddy ya kira ya salman ya sanar dani ina tafe. Haka nayi sallama da kowa ya samir ya kaini airport . Sai gashi nan na sauka lfy na sami ya salman don haka ba bata lokaci muka kamo hanya har mun danyi nitsa yaga ko kulasa banyi ba don haka ya gaji yace " ya kk bar mutanen yola? Nace " lfy Ya dan numfasa snn yace " why are you so quite ne yau ? Tabe baki nayi nace " Kaine naga kamar baka yi murnar dawowata ba. Yace " hmm Rumaisa case. Daga nan bai kuma yin magana ba nima haka har muka isa gida muna fitowa daga mota sai ga khabirat tana tahowa hannunta rikeda warmers na abinci a raina nace watakila anan ta samu ta ciyar dashi magani. Ganina baisa taji komai ba don koda mukayi ido hudu harara ta watsa min nikam kauda kai nayi na dauki jakata na wuce ciki na barsu . Ya jima a wajen kamin ya shigo nidai da na duba koina fes fes wanka nayi nazo na saka kayana snn na fara canza bedsheet . Ya shigo ya sameni snn yace "ai wnn bedsheet din a wanke yake ko baki gani ba? Nace " na gani mana. Yace " to me yasa zaki canza? Ba tare da na kulashi ba nace " to nasan ko su waye da waye suka kwanta akai? Ya gintse fuska yace " bangane ba akwai wanda kk bari a gidan nan ne bayan ni? Nan ma ce masa nayi " oho. Hannu na ya rike ya fizgoni jikinsa da karfi na fadi kirjinsa na runtse ido cikin jin zafin fizgoni da yayi Kallona yake snn yace" zargena kk yi ko? Shiru nayi masa don haka ya hankada ni na fada gado yace " karki kuma yi mun irin wnn maganan! Daga nan fita yayi nikam kuka na shiga yi.bansan sawan lokacin da na dauka ina kuka ba kamin daga baya na rarrashi kaina. Shi kuma bansake ganinsa ba har karfe sha daya da ido kawai nake binsa har ya gama shirin kwanciya ya dauki bargo da pillow ya fita palo to fa!!! Aikuwa ranar banyi bacci ba har gari ya waye tsabar tashin hankali. Da safe kuwa ina hada mana break fast a kitchen ya shigo ya dauki flaks din ruwan zafi ya tafi dining ya hado tea ya kama sha da bread ganin haka yasa nayi masa na saka masa chepps da plantain dana soya da wsinar kwai a plet na kai mishi dining hade da fadin " yaya yau fa Sunday ina kk sauri zakaje? Yace " zanje wani wuri ne. Na danyi shiru snn nace " to kaci dankalin mana bari in kawo ma pepper soup.... Yace " na koshi sai dai in na dawo anjima. Ya fada yayinda ya mike tsaye ya kalleni nima shi nake kallo yace " any problem? Kai na daga masa yace " ina jinki. Nace " so nake inje gun madam Fatima ina son shiga kungiyarmu...... Yace " ba damuwa kina iya zuwa koina a cikin barrack din nan na baki dama ko da bana nan sai dai fa ki kula da kyau da irin mutanen da zaki dinga muamala dasu. Gyada kai kawai nayi nace " zan kiyaye dama gidanta kawai nake son zuwa don tana da kokari wurin zumunci. Baiyi magana ba ya juya hade da fadin sai na dawo. Bin bayansa nayi da kallo nace a dawo lfy. Yana fita na zauna kan kujeran dining na zuba tagumi ina kallon plet din abinci dake gabana gabadaya kaina ya daure na rasa ta inda zan fara nema mana mafita. Da kyar na lallaba na gama abinda nakeyi na tafi gidan captain bello Na sami matarsa ta karbeni da fara,a sosai inda ta kaini har daki ranar kam ba abinda bata sanar dani ba akan rayuwar Lagos ko ince barrack tarihin mata daban daban da suka sha fama akan mazajensu da karuwai.gaskia na karu da abubuwa da yawa.kuma ta koya min dabaru da yawa Har la,asar na dawo a gaggauce na dora girkin dare bayan na gama na shirya a dining .naje nayi wanka naci adona cikin English wears wando da riga mai kyau ya matse ni sosai ya fitar da duk wani shape na jikina. Karfe biyar ya shigo da sallama hannunsa rike da ledoji na tashi da sauri ina mishi sannu da zuwa na karbi ledojin hannunsa amma na lura ko kallo ban isheshi ba.ya wuce daki abinsa. Snn da daddare kuma muna zaune a Palo bayan mun gama cin abinci khabirat ta kirashi wai gata nan tazo nan da nan ya tashi ya zira jallabiyarsa ya fita tashi nayi nabi bayansa ina yaya ina kuma zakaje? Yace " ina zuwa ba nitsa nayi ba. Tsayawa nayi a jikin window ina lekonsu mota suka shiga ina jiran ya tashi motar amma shiru shiru suna ciki ko me sukeyi oho O ni Rumaisa naga ta kaina tunda na dawo bangane kan ya salman ba sai yawan fushi da fada snn ya daina kulani ba wata alaka ta aure dake shiga tsakanimu to a Palo ma yake kwana abinsa. Ranar da ya isheni na dawo palon na sameshi na cire dukkan kunya da fargaba nace " yaya don Allah me nayi maka ne ka sauyamin gabadaya? Shiru yayi kamar vazaiyi magana ba snn yace " na sauya miki kamar ya? Nace " yaya tunda na dawo yola babu wani abu da ya shiga tsakaninmu alhalin da ba haka muke ba gashi gabadaya baka kwana a daki tare da ni don Allah ka sanar dani dalili zan gyara. Tashi yayi ya zauna yace " Rumaisa tunda kin tambayeni to bazan boye miki ba .duk sanda nazo kusa dake na kanji wani warin magani da bansan meye sa kk shafawa ba kuma ni banson warinsa. Zaro ido nayi nace " magani kuma yaya to ai ni bana amfani da kowane irin magani nidai in nayi wanka maine nake shafawa sai turare shima ba kowanne ba tunda kaga ina da........ Katseni yayi da fadin " nidai na fada miki ki daina kawai don banson warinshi. Jikina a mace na tashi na koma daki ina zubar da hawaye. Tun ranar duk wani turarena na ajiye amma bai fasa ce mun ina warin magani ba. Snn kullum sai ya fita gun khabirat su shige motarsa Allah kadai yasan me sukeyi . Abubuwa sai kara tsanani suke don daga baya har turaran wuta na gida in nasa ce wa yake nasaka magani kuma yace min bayaso ranar gabadaya ya balbaleni da masifa da nace tak! ma nasan duka zan sha saboda nasa turaran wuta Ranar bai kwana a gida ba hankalina ya tashi sosai na kasa hkr kiran mama nayi a cikin Daren na sanar da ita komai ban rage ba. Abu na farko data fara ce mun shine " yaushe rabonki da ki tashi dare kiyi sallah ki gaya wa Allah matsalarki ? Shiru nayi na rasa mai zance. Ta sake fadin " yaushe rabonki da ki bude Quran ki karanta koda aya dayace ? Nan ma shiru nayi ta sake fadin " azkar fa ? Nace " mama inayi Tace "azumin litinin da alhamis fa? Shiru nayi Tace" hmm nasan bakida amsar da zaki bani Rumaisa ya kk dauki rayuwane ? Waya fada miki a zamanin yanzu ana zama hakan nan ne ? Nace " mama wlh tunda na dawo banma sami natsuwa bane....... Ta katseni da fadin " bana son dogon surutu idan har kina son ganin haske a lamuranki to fa dolene sai kin koma kan turbar da na doraki . Nace " to mama zanyi . Tace " don haka sai da safe!!!!! Kamin nace wani abu har ta kashe don haka da sauri na tashi Na wuce toilet na dauro alwala na fito......... Hauly ce👍🏻🥰 [9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡65 ************Kwana nayi ina sallah hade da gayawa Allah bukatuna har gari ya waye ba tare da gajiyawa ba. Karfe shidda na shiga kitchen na shirya breakfast dina dan kadan don nasan ba lallai ne yaci ba tunda har yanzu bai dawo ba. Na gama komai na aikin gida har na snn nayi wanka na kintsa jikina tsaf cikin English wear Riga da siket don sune kayana anan garin turare kadai ban fesa ba. Daga nan na dauki Qur'an na bude na fara karatu sai dai kuma ko aya biyar ban karanta ba bacci ya fara dibana. A fili nace" Auzubillahi minash shaidanir rajim ai yau banga abinda zai hanani karatun nan ba. Don haka na tashi na dawo Palo na zauna kan kujera . Karfe takwas ya Salman ya shigo da Sallama . Na dago na kalleshi snn na amsa hade da fadin "yaya ina kwana ? Fuskarsa ba yabo ba fallasa yace" lfy lau . Rufe Qur'ani na nayi na tashi snn nace bari a hado ma ruwan wanka. Na fada yayinda na wuce bedroom bayan na hada ruwa na fito daga toilet kawai na sameshi ya shirya cikin kakinsa yana daura igiyar takalmi . Jikina a mace nace " yaya har na hada ma ruwan wanka. Kai tsaye yace" nayi wanka a inda na kwana. Nace " to ga breakfast a kan dining muje kaci. Nan ma yace min " na koshi. Daga nan ya tattara wayoyinsa zai fita nace " Allah ya bada sa,a . Har yace amin zai fita bansan me ya tuna a ransa ba ya juyo ya kalleni yace " kina bukatar wani abu ne? Nace " eh ina son dama inje saloon ne . Ba tare da yace komai ba yasa hannu a aljihunsa ya Ciro wallet ya bude ya dauki 5k ya ajiye kan dress mirror ya fita. Na bishi da kallo hade da fadin Allah ya kyauta . Ba jimawa na shirya na tafi saloon da ke cikin barrack din . Ana cikin gyara min gashi khabirat ta shigo ta madubi ba ganta da sauri na cire idona . Ta kalli matar tace " mansura nazo wash and set kuma sauri nake suleyman na jirana a office Matar tace" to ki zauna bari na gama yiwa wnn parking. Yamutsa fuska tayi tace " ni gaskia indai sai na jira wnn ne gwara kawai na tafi. Matan tace " to kira blessing ta miki naga kamar ba kya son yaran su wanke miki Kaine. Dan tsaki tayi tace " to bari kawai na fada mishi yazo nan ya biyani mu tafi. Ta kama latsa wayarta tasa a kunne ba jimawa naji ta kwantar da murya hade da fadin" hello my love don Allah kazo ka biyani a saloon sai mu wuce. Ta danyi shiru snn tace " OK bari na shirya to. Ta kalli matar tace" hmm bari kawai sai na dawo . Ta dauki jakarta ta shiga wani dan daki. Anan mansura ta kalleni tace " madame ya kk yi sake haka kk bar khabirat da mijinki?wlh batada mutunci ko kadan . Murmushi nayi Wanda yafi kuka ciwo nace" to ya zan yi fadan da yafi karfinta ai sai ka maida shi wasa. Tsaki tayi tace " hmm khabirat dince tafi karfinki to wlh tun wuri ki tashi tsaye a kan wnn lamarin. Dan dariya nayi nace " ai kawai ki bar wnn maganar ni bazan iya rigima da karuwa b........ Ban rufe bakina ba kawai naji ta amsa daga bayanmu " to muna fukai duk abinda kk fada naji sarai a kunnena. Tayi min wani irin kallo tace " ke kuma wlh sai na fadawa suleyman ce min da kkyi karuwa..... Tashi nayi na juyo muna fuskantar juna nace " kina da sunan da yafi wnn ne? Ai duk matar da take bin maza karuwace ko kuma karya...... Ta zaro ido tace " what nice karyq? Nace" kece karya domin halin karnuka kk yi. Murmushi tayi tace " da kyau kuma abinda kk fada a kunnen suleyman. Nace" ki fada masa mana sai me? Tace " wlh kinci sa,a ni na rokeshi ya barki da tuni ya koraki amma tunda kk fara hada kai da matan barrack kina zagina dole ne in fada masa domin ya gaggauta daukar mataki akan ki. Kallonta nayi sama da kasa snn naja tsaki na kalli matar can nace " nawa ne kudinki? Tace" 3k Na bude jakata na cire na bata snn na fita na barsu a wurin tanata zage zagenta matar na bata hkr. Ina fita sai ga ya salman ya karaso bakin saloon din yana parking mun hada ido bance masa komai ba na wuce gida. Koda na koma sai naji na kasa kuka izuwa yanzu na fara sabawa knn. Shine bai dawo ba har shadaya da rabi ina tsaye a window na hangosu ta sauka sukayi sallama ta wuce gidansu shi kuma ya nufo kofar Palo. Da sauri na sauke labule na koma daki yana shigowa tun kan nayi magana yace min " ke kuma dazu me ya hadaki da khabirat kk zageta kk ce mata karya? Shiru nayi na rasa me zance masa . Karasowa yayi gabana nikam tsoro yasa naja baya da sauri na fara " don Allah yaya kayi hkr...... Fizgoni yayi ya murde min hannu na saki ihu cike da azaba don har ji nayi kamar ya karyani . Snn ya saki hannun ya kalleni yace " saboda na baki freedom shine duk inda kkikaje sai ki zauna da matan barrack kina zagin khabirat koh ? To daga yau bazaki sake zuwa koina ba tunda munafurci kk koya . Yana fadin haka ya wuce toilet nikam ina rike da hannun ina kuka gabadaya na rasa me yake min dadi a duniya ji nayi bazan iya ci gaba da zama a gidan nan ba. Tashi nayi a zuciye na dauki jakata da wayoyina da ATM card dina na jefa jaka. Ina sa takalmi ya fito kallona yayi cike da mamaki yace " ina kuma zakije ? Ko kallonsa banyi ba na gyara hijabina na fita da sauri ya bini har kofan palon yasha gabana cikin daga muryq yace " nace gidan ubanwa zakije cikin Daren nan. Dakewa nayi nace " Agege zanje! What !! Ya fada da sauri snn yace " kinsan inane agege kuwa? Nace " na Sani gidan karuwai zanje........ Ban gama rufe baki ya dauke fuskata da mari yace " ki koma daki maza ! Busar da idona nayi nace " wlh bazan koma ba koda zaka kasheni ne .yau banga Wanda ya isa ya hanani fita ba . Sassauta murya yayi yace " to me zakije kiyi a agegen? Harararsa nayi nace " zanje nayi karuwancine . Subhanallah! Ya fada da sauri snn yace " don me...... Katseshi nayi da fadin" naga karuwancin yafi komai riba kuma karuwai sunfi matan aure daraja don haka nima zan tafi naje nayi karuwan...... Da sauri ya fizgoni na fada kirjinsa yace " ki bar wnn maganar don Allah na rokeki agege fa ba anan yake ba. A yayinda nake kokarin kwatan kaina a jikinsa nace " kar ka damu ko ban samu isa can ba in na fita hanya na sami 'yan good evening zan yi joining dinsu .... Sa hannunsa yayi a bakina yace " Rumaisa ki daina wnn maganar nace ko?. Ture shi nayi na fizge hannuna cikin nashi hawaye tuni ya fara zuba a idona na kalleshi nace" yaya don Allah ka barni in fita ina yanzu a dalilin karuwa ka murde min hannu zaka karyani ka sake marina idan naci gaba da zama da kai bansan me zaka min nan gababa. Yace " kuma shine zaki yankewa kanki mummunan hukunci ? Nace " hukuncin da na yanke shine dai dai anan kake bari na ka fita da karuwa kuje kuyitq holewarku tunda na dawo daga yola babu wani abu daya shiga tsakaninmu jiya har kin kwana kayi a gidan nan...... Da sauri ya sake fizgoni jikinsa yace " ya isa haka zo muje ciki indai wnn ne dalilinda zai sa ki fita zan miki solving problem dinki yanzu okey? Tirjewa nayi nace " bana so ...... Cak! Yayi dani ya wuce daki saukeni yayi kan gado yana kokarin cire min hihabina yayinda nake ta faman tureshi nace " bana so ba ce mun kayi ina warin magani ba? Yace " ba kyayi yau baki Shafa ba..... Ya fada yayinda ya karasa cire min siket din jikina. Kuka na shiga yi ina tureshi hade da ce mishi bana so. Ko kulani baiyi ba har ya gama cire mun kayana dama shikam towel ne kawai ya daura tuni yayi jifa da towel din ya jawo bargo ya kashe wutan dakin . Aikuwa naji jiki ba kadan ba don nasha gyara na musamman a yola gashi an kwana biyu ba,aiba don haka naji zafi sosai. Yaya kam rikicewa yayi ya dinga min sambatu .da kyar na samu na kwace kaina . Ina shirin tashi ya jawoni jikinsa ya rumgumeni nace " ni ka sakeni kar na makara . Yace " a mene yanzu Karfe hudune fa. Nace " sahur zanyi so nike in tashi da azumi. Dada rumgumeni ni yayi yace " No ban yarda ba ki bari sai monday sai muyi tare. Nace " to ka sakeni inje inyi sallah. Nan ma yace " nima ai zan yi.ki dai bari mu kara daya........ Kuka na fara yi mishi don haka ya rabu dani da sauri na wuce toilet nayi wanka na gasa jikina sosai nayi wankan tsarki na fito da sauri ko goge jikina ban tsaya yiba na zira doguwar tigata da hijabi na dauki Qur'an dina na fita Palo na hau sallayata na shiga kaiwa Allah kukana don gashi nan ga dukkan alamu na fara ganin haske tunda gashi har ya kulani......... _Fans_ _ayi_ _hkr_ _banda_ _chagy_ _ne_ 🙏🏻 Hauly ce🥰👍🏻 [9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* 66 *************07:00am dai dai na gama komai har wanka na sake daukan Qur,ani na naci gaba da karatuna . Har ya shirya ya fito cikin kakinsa. Ya kalleni yace " Rumaisa inada magana dake. Aya na samu na tsaya snn na ajiye Quranin na kalleshi ba tare da nace komai ba. Ya karaso inda nake ya zauna kan hannun kujera ya kamo hannu na ya rike hade da fadin" daga yau bana son ki kuma maida hankali akan khabirat kar ki kuma zaginta bana so matukar ba so kk ki ga bacin raina ba. Haushi duk ya bi ya kamani bansan sanda nace masa" ni kaga idan zama dani ya isheka fa babu dole kawai ka sawwaka....... Da sauri ya sa hannunsa ya toshen baki hade da fadin" karki sake fadan wnn kalman babu kyau waya gaya miki zan iya rabuwa dake ? Hawayene ya cicciko idona don tsabar takaici bance komai ba. Ya sake fadin " kawai dai nace bana son ki kuma zagin khabirat ko a bayanta snn abu na biyu shine akan maganar da kk fada min jiya na cewa zaki tafi ......ba son maimaitawa nake ba pls na rokeki kar ki kuma fadan haka kina jina ? Kaina a sunkuye hawaye na zuba nace mishi" to. Rikoni yayi yace " muje muyi breakfast. Girgiza mishi kai nayi yace " tome kk ci ?kodai kin dauki azumin ne ba tare da amuncewata ba don yanzu gabadaya kin koyi taurin kai. Nace" ai da kace kar nayi banyi ba . Yace " to muje kici abinci . Muka tafi dining. A haka dai muke tafiyar da zamantakewar da dadi ba dadi saukin dai kawai yanzu muna kwana tare kuma yana cin abinci na.nidai inaci mai ci gaba da mana addua hade da azumi. Ranar silfa tazo na tarbeta ba yabo ba fallasa muna zaune a Palo tace " Rumaisa tuni nake son shigowa amma ina tunani ta ya zaki karbeni. Nace " meya faru silfa? Tace " hmm akan maganar khabirat ne wlh daga ni har hassan bamu son abinda take miki amma tafi karfinmu don Allah kiyi hkr. Murmushi nayi nace " haba silfa dama akan dan wnn kankanin abun kk daga hankalinku ke da maigidanki?ai babu komai karki damu duk Wanda yayi mai kyau don kansa ne. Ta dan waiga snn ta kalleni ta sassauta murya tace " in ba damuwa kema ki tashi mana ki shiga malamai ki fara neman taimsko..... Da sauri nace " subhanallah ! Ni bazan iya biye biyen malamai ba kuma Mamana da dad dina sunce idan nabi malamai basu yafe min ba duniya da lahira. Tace " to Rumaisa ya zakiyi da wnn babban alamari ai gara ki tashi ki nemawa kanki mafita. Nayi murmushi nace " karki damu na mikawa Allah dukkan lamurana kuma na zuba ido kema ki zuba very soon zakuga ta inda Allah zai saka min! Jikinta a mace tace " hakane. Da haka ta sallameni ta tafi ko rakata banyi ba nace a raina " dangin munafukai kawai. Ta zo da kwana biyu kawai ranar sai ga khabirat ina kitchen nema ina shiryawa ya salman lunch don ya dawo ya shiga wanka naji ana knocking na kofa don haka naje na bude kawai na ganta tsaye cikin kananan kaya ruguna da wando taci kwalliya har ta gaji ido a tsassaye gashi ta kara eye lashes snn tana ta faman taunan chewing gum . Ganin na bude kofa yasa ta kalleni sama da kasa snn tace " gunki nazo . Banyi magana ba na juya ta biyoni a baya . Ba tare mun zauna ba na kalleta nace" lfy me ke ...... Da sauri ta katseni da fadin ke don Allah ya isa ba surutun babzanki nazo ji ba nazo inja miki kunne a karo na biyu ki daina zama da wasu kina zagina idan kin isa mace ki yi yadda duk zakiyi ki rabani da mijinki ba wai ki dinga zama kina zagina ba. Tunda take maganan kallonta nake cike da mamaki .taci gaba da balbali tana zagina . A hankali nace kinga malama... Hannu ta daga min tace " ki daina wani ce mun malama khabirat sunana... Nace " hmm ai bana tuna sunanki ba shiyasa nake ce miki malama ... Harara ta watso min hade da isa dab dani tace " idan bazaki iya kirana da khabirat ba sai kice mun farkar mijinki! Muna cikin haka ya salman ya fito ya samemu ya kallemu yace " lfy ? Kamin na bude baki nayi magana kawai ta fashe da kuka ta isa gabanshi tana cewa " my love matarka ta tsaneni duk inda taje zagina take waini karuwa har take gayawa aunty silfa wai zatayi komai akaina domin taga ta rabamu don Allah suleyman ka roketa kar ta rabamu wlh ina sonka kaima ka Sani I love you so much! Ta fada yayinda take kokarin shigewa jikinsa bansan lokacin da nayi sauri nasha gabanta wani irin zafi nake ji a zuciyata a fusace na nuna mata kofar fita nace " kinga ki fitan min a gida kije waje ki jira har yaje ya sameki !! Cikin kissa da kisisina tace " my love kana ganinta ....... A hasale na dauke fuskarta da mari nace " I said get out ! Kinsan Allah idan baki fita ba sai na miki mugun illah domin I zuwa yanzu kin kaini bango kin kureni. Dafe kunci tayi ta na kalleni cikin mamaki tace " what you slap..... Na katseta da fadin " yes and am ready to do it again idan har baki fice min a gida ba.idan ke baki San koni wace ce ba ki tambayeshi zai fada miki don na lura kinai mun kallon wawiya bagidajia ko ? "To wlh idan har kin cika mara kunya ki tsaya ki jirani har na fito kinga yanda zan yi dake jarababbiya dangin munafukai kawai. Da sauri na wuce kitchen ya salman kam yana tsaye kyam kamar an dasa bishiya ya rasa me zai ce mana. Tabaryata na dauka na kirban sakwara na fito a guje na nufo inda take sai dai nayi rashin sa,a ina fitowa ta ganni a tsorace ta zaro ido hade da sakin ihu ta kamkameshi . Yayinda sai a lokacin yayi maza ya rikeni a fysace hade da kwace tabaryar ya kalleni fuska daure yace " yanzu rashin hankalinki har ya kai haka bansani ba ? Kasheta zakiyi koh? Nima ba tare da Tsoro ba nace" ka fada mata ta fuce min daga gida kawai . Ajiye tabaryar yayi ya kalleta kamin yayi magana ta sake tfy zata fada jikinta. Yayinda ni kuma na shirya tsaf don yi mata dukan tsiya in ta tabashi. Aikuwa da sauri naga yaya ya hankadeta sauran kadan ta fadi bai saurara mata ya dinga daukar fuskarta da mari har sai da ta fadi kasa a gigice tana wayyo Allah idona suleyman idona bana gani Bakinta ma ya fashe sai jini Sunkuyowa yayi ya dagota yace " ko ba kya ganina nasan kina jina don haka bari na maki last warning khabirat daga yau bani ba ke na TSANEKI bana son sake ganin ki a RAYUWA ta ki fita anan. Ya fada cikin tsawa da daga murya. Kuka ta shiga yi sosai tana sambatu da yaransu ko me take fadi oho. A fusace ya fizgo hannunta ya jata yayi waje da ita snn ya dawo ya maida kofa ya rufe. Nikam mamaki ne sosai bayyane a fuska ta. Ina ganin shigowar sa na juya jikina a mace zan tafi daki A hankali ya kira sunana RUMAISA! Tsayawa nayi cak ba tare da na juyo ba. Har ya karaso gabana yanayinda na ganshi ya tabbatar min ya yi nadaman abinda ya faru. Da sauri na fada kirjinsa na fashe da kuka mai tsima zuciya. Rumgumeni yayi sosai yana Shafa bayana alamun rarrashi .don ya kasa cewa komai baisan ta inda zai fara bani hkr ba.............. 🤦🏻‍♀ *fans* *kuci* *gaba* *da* *mun* *uzuri* *bamuda* *wuta* *ne* *am* *sorry* 🤗🤗🤗🥰🥰🥰🥰🥰 Hauly ce🙏🏻🤗🥰 [9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *KYAUTAR_* *SHAFI* *NA* *MUSAMMAN* *A* *GARKEKU* *INTELLIGENT* *ASSO* *GROUP* 1 Maman sadeeq🥰 Ummin Khadija Nafeen nura Hebbert Aysha A Umar Asma'u Haleemath Ummu suhaima Ummansukhaina Reemat Ummu khalifha Aisha Husnah Umma salma@ Mum nawwal Hussaina Farhat 'yar baba *INTELLIGENT* *ASSO* *GROUP* 2 Zubaida minna Rukayyat Rukayyah Musa Bintu Amysher Mmn mahamud Aishatu Maman zahra Aisha Aliyu🥰 Maman saleem Murjanatu yahuza Maman sayyeed Hussainah Ismajee Zeemah Ilelah Habiba Ahmad Ameenah uthman Ummu Ansar Duk Wanda bata ji sunanta ba tayi hkr ba haka naso ba don Allah .amma dai zuciya ta tana tare da ku masoyana hauly ina yinku over 🥰🤗 _Na gode sosai da irin kaunar da kuke nuna ma wnn littafi RUMAISA SALMAN ina ganin comments kuma ina matukar jin dadi Allah ya saka da alkhairi Allah ya bar kauna da zumunci mai dorewa🙏🏻🥰🥰🥰🥰🥰🥰_ *Wnn shafin nakune kuyi duk yanda kuka dama dashi👌🏻*🤗 *PAGE*➡ 67 **********Rabuwar ya Salman da khabirat yasa hanakalina ya kwanta sosai domin yaya ya dawo da soyayya da kulawa da yake min. Khabirat kuwa ansha case da ita sosai akan marinda yaya ya mata wai wlh bazata yarda ba sai taje gaban manya an bi mata hakkinta.da kyar case din ya mutu don yayanta hassan yaki ya bata goyan baya a karshe ma korarta yayi harda matarsa silfa ma da ya fahimci itace take zuga ta ranar taci dan banzan duka a wajansa ya ce sai dai kome ma a masa daga karshe duk ya korasu dama ba suda yara don haka shi kadai ya rage a gidan. Na kira mama da aunty samira na sanar dasu mama kam a lokacin suke shirin fita Dubai da daddy wai daga can ma zasu wuce umrah a can zasuyi azumi. Murmushi nayi a zuciyata nace " hmm mama da daddy masoyan asali. Shigowar ya Salman yasani juyowa da sauri na tafi na fada jikinshi ina murmushi . Rumgumeni ni yy sosai yace " baby sai sallama nike tayi tun a kofar Palo. Na dago kaina hade da fadin wlh yaya banjika ba sannu da dawowa yayana. Murmushi yayi snn ya sumbaci bakina yace " thank you babyna. A hankali na fara balle masa ma ballin rigarsa . Saida na gama cire masa komai snn na kawo towel na bashi nace "asha wanka lfy bari in shirya mana dining. Har zan wuce ya jawoni hade da fadin baby na gaji fa sosai bazan iya yin komai ba kuma kin Riga kin saba min . Nace " hmm naki wayon sai dai in ka min alkawarin baza ka jikani ba. Yace " bazan jikaki ba baby gudun kar ciwon ki ya tashi gashi kwanan nan sanyi ake sosai . Nace " to muje. Bayan yayi wanka ya fito na sake taimaka mishi ya shirya snn muka tafi Palo muka ci abinci . Anan muka shiga hira ina kwance kan cinyarsa. Nace" yaya mun kusa fara service fa. Yace "aina zakiyi a kano ko nan? Nace " gaskia ni yaya bazan iya yi anan ba bansan kan Lagos ba. Yace " ai ke dama 'yar kauye...... Da sauri na zumbura baki hade da tashi daga jikinsa nace " yaya ni fa banaso Dan dariya yayi yace "sorry sorry bazan kuma ba.yanzu zo muje ciki na baki labari mai dadin gaske . Nace " fara bani anan. Yace to shikenan. Daga rigata ya Shafa cikina snn yace " yau so nake mu samo baby insha Allah. Murmushi nayi nace "Allah yasa yayanah yanda kk son haihuwan nan Allah ya bamu yara na gari masu albarka. Ya Shafa kaina hade da sakin murmushi yace " ameen my dear. Mama da daddy kam ana Dubai ana shan love.don tunda suka maida aurensu bai samu yanda yake so a gurinta sosai ba don taki tarewa a yola shikuma yana dan jin nauyinsu Abba gashi bazai iya jira a gama gininsu na kano ba don haka kawai yayi shawarar dauketa daga kasar ma gabadaya. Aikuwa tun mama na dan jin kunya dole ta saba basu fi sati biyu a Dubai ba suka shiga gwadawa juna tsantsar soyayya. Aunty samira kuwa tana nan sai kewar daddy take dan bata son yayi nitsa da ita. Watansu daya a Dubai suka tafi umarah.hmm rayuwa knn. Nikam da sojana mun shimfida rayuwar soyayya kamar zamu hadiye junanmu.in yana gida har kitchen tare muke zuwa wanka tare in ya tafi aiki kuwa ina indai ya samu sarari sai ya buga min waya ko yace in turo masa hotan kwalliyata da English wears musamman kirjina O! Ni Rumaisa ya Salman dan duniyane. Karkuso kuga yadda na dada kyau da haske gwanin sha,awa duk Wanda ya kalleni sau daya sai ya kara don haka nema ya salman ya hanani sa gyale in zamu fita sai dai hijabi. Ana Azumi saura kwana biyu ne ranar naji anata mana knocking na kofa dama ina waya da sakina ne don haka na tafi da sauri na bude kofar. Watace na gani saida zuciya ta ta buga don daga gani ' yaruwarsu ya salman ne na cameroo don gata kamanninsu duk daya dasu adda A'i kyau kam kamar su sukayi Kansu. Ganin ina tsaye banyi magana ba yasa tace " lfy . Murmushi nayi na karfin hali nace " ai ke za,a tambaya. Tsaki taja hade da fadin " kaji rainin hankali nan ba gidan ya salman bane? Nace " eh nan...... Tun ban karasa ba ta dauki jakarta ta tureni da karfi saura kadan in fadi tana cewa" dan Allah malama ni ki bani hanya kin tsaya kina batama mutane lokaci. Binta nayi da kallo hade da fadin " hmm another trouble. Na rufe. Kofa bance mata komai ba na tafi daki na tarar ya salman sai baccinsa yake hankali kwance don haka bana son in tasheshi. Dole na koma Palo na kalleta nace " yayan na bacci. Hararata tayi hade da fadin " nuna min dakinda zan sauka don ba yau zan tafi ba dadewa zan yi . Nace " to ai ba matsala. Sai cewa tayi " hmm in ma dashi ina ruwaana. Nidai shiru kawai na mata yayinda na dauki jakar kayanta na kai mata dayan dakin da yake kallon namu.ba komai a dakin daga katuwar katifa sai wardrobe na jikin gini.ga kuma toilet. Saida ta tsaya ta karewa dakin kallo tsaf snn tace" hmm ki bani tsintsinya wnn daki naku kamar akurki sa,a daya akwai Ac da bazan zauna ba. Ni dai yau ina ganin ikon Allah.bayan na kawo mata tsintsiya na dawo Palo ina zaune ya salman fito dagashi sai vest da boxer. Murmushi na masa nace" yaya har ka tashi Zama yayi kusa dani hade da fadin " wayo kk min kk sani bacci shine kk gudo Palo ko? Dariya nayi hade da fadin " wlh yaya na gaji ne. Yace" anya baby ba Amarya zan kawo miki ba? Don kefa bazaki iyani ke kadai ba saida mataimakiya ko? Nan da nan yanayin fuskata ya sauya na fara fushi. Yayinda ya shiga ratrashina. Muna cikin hakan mara kunyan ta fito don ni bansan sunanta ba. Wando tasa 3quarter da vest ta sake gashunta dayasha kara yayinda kamshin turarenta ya rigata fitowa. Tana fita ta sakarwa ya salman murmushi .shi kam lokaci daya daya ganta annurin fuskarsa tuni ta gushe ya tamke fuska tamkar bai taba sanin maiye dariya a rayuwarsa ba. Ni kuwa haushin suturarta naji kamar nayi yaya da raina. Cike da fara tace mishi " yaya yau kam na cika alkawari nazo...... Rai bace yace" wnn wane irin iskanci da rashin kunyane haka ? Don Allah koma ciki ki nemi kayan mutinci kisa wawiya kawai. Dan zumbura baki tayi snn ta juya tayi cikin daki tana guna guni.!!!!!!! Fans ayi hkr rasuwa aka Mani!!!!!🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻 Hauly ce🤗🙏🏻 [9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡68 ***********Hankalina ya tashi matuka da zuwan madiha ya salman har ya gane don haka yace in hankalina bai kwanta ba to gara fa ta koma . Nace" aa wlh babu komai Yace " Rumaisa nasan kina tsoron abinda ya faru ne kwanaki amma karki damu insha Allah bazan kuma sakaci da kaina irin na baya ba kuma a koda yaushe ina alfaharin kasancewar ki abokiyar rayuwata Allah ya maki albarka. Murmushi nayi zuciyata fess nace amin yaya na. Yace " ina fatan kin yi niyyar azumi? Nace " sosai ma ka ma tuna min bari naje na fadawa madiha don kila bataji ba. Yace " OK kuma idan ta maki rashin kunya ki fada min inje in sameta. Murmushi nayi bance komai ba na fita zuwa dakin da madiha ta sauka. Na samets tayi bacci don ga laptop din ta ta kunna tana kallon film koda na matso sai naga ashe bf ne abun ba kyaun gani .har naji zuciyata ta tsinke. Da sauri na kauda idona na fara tashinta. Wani dogon tsaki taja hade da fadin wai mene ne ? Nace " ya salman yace a fada miki ki kwana da niyyar azumi gobe snn kuma madiha a matsayinki na musulma ina baki shawara ki daina ganin irin wadan nan films babu kyau masifa ne........ Hannu ta daga min hade da fadin " ina ruwanki ne wai rayuwar ki ko tawa? Nace " hmm taki ce amma dai na fada miki ki gyara. Mtswww taja tsaki hade da fadin " naji amma in kina son ganin na bari ki bawa mijinki shawara ya aureni domin ina son shi . Murmushi nayi nace " Allah sarki mijina ya maki nitsa kwata kwata va kya jerin matanda yakeso. Na dafa kafadanta nace " madiha tunda kk zo gidan nan nasan dalilin da ya kawo ki .am sorry to say yayana bazai iya auren mace irinki ba zaki gama yayinki ki koma ne yadda suhaila ,nabila da sukhaina sukayi suka barshi ...... Tura hannuna tayi a kafadarta da sauri ta mike hade da fadin " hmm ni MADIHA na wuce tunaninki Rumaisa ban taba neman abu a rayuwata na rasa ba don haka ya salman ma na sameshi na gama kuma wlh wlh wlh kinji na maki rantsuwar musulunci idan na auri ya salman sai ya sakeki ! Ki rubuta ki ajiye. Dariya nayi sosai snn nace " ni kuma madiha ina mai tabbatar miki da cewa karo na farko a rayuwar ki zaki rasa abinda kk so don ba zaki taba samun salman ba salman nawa ne ni kadai! Ki rubuta ki aje. Ina gama fadin haka na fita ba tare da na kula da bakaken maganganu da take jifana dasu ba . Koda na koma daki na tarar da ya salman yana waya da inna nasa key a kofa hade da kashe wuta nazo na kwanta kusa dashi. Da asuba koda muka tashi dama na rigada nayi mana miya tun dare so tuwon semo na tuka nasa a kula ya salman ya kaiwa hassan don har zuwa lokacin bai dawoda silfa ba shi kadai a gidan. Madiha kuwa kin fita tayi har muka gama duk abinda muke yaya yaje massllaci ya dawo muka koma daki muka kwanta. Sai nine ya salman ya tashi yayi wanka ya shirya don koda nazo taimaka masa cewa yayi karna tabashi azuminsa ya karye. Don haka koda ya gama na rakashi a Palo muka sami madiha yau ma tasha English wears musamman kirjin nan kusan kadan ne a cikin rigan komai nata a waje tana zaune a dining tana shan tea. Gabadaya kallonta mukayi ya salman ya tamke fuska sosai hade da fadin " ke !bakiyi azumi bane? Ta juyo ta kalleshi hade da shagwabe fuska tace " ni yaya inada olsa ne banayin....... Da sauri ya tari numfashinta da fadin " don Allah rufe min baki mara kunya dama ai ke ba damuwa kkyi da ibada ba inaga aljanun kanki arna ne kekam .kuma ki tashi maza kije ki cire wadan nan shaidanun kayan idan kk kuskura na sake ganinki da wadan nan banzan shugan wlh zaki yabawa aya zakinta nonesense ! Tashi tayi tana gyara gaban rigarta snn ta wuce ciki tana kada mazaunai hmm! Ikon Allah sai kallo. Tsaki yaja snn ya kalleni yace" ke kuma ba barinta zakiyi tana rashin kunya son ranta ba taka mata birki zakiyi domin wlh rashin kunya irin na madiha ya wuce yadda duk kk tunani. Yana gama fada ya fita ransa a bace dama yaya........ Tunda ya mata fada akan kananan kaya ta daina sawa azumi kuwa dole yace sai tayi in kuma taki to sai dai ta koma inda ta fito. Tayi guda biyu rak rannan da daddare kawai muka jiyo ihunta muka fita da sauri a Palo muka samets rike da kirji wai kirjinta na ciwo Koda ta samo ya riketa gabadaya ta narke a jikinsa acikin daren muka kaita clinic ba komai sukace ba illah suka rubuta maganin olsa. Tun ranar da taga ya salman ya fara sassauta mata shikenan sai tadinga matsa mana muna shiga daki da daddare take zuwa tayi mana knocking na kofa wai kirjina nta na ciwo bata son kwanciya ita kadai kar wani abu ya sameta cikin dare kuji min iskanci. Haka ya salman yake cewa inje mu kwana da ita . Duk ta takura ma na ya salman duk ya rasa yanda zaiyi gashi azumi ne in gari ya waye shikenan ba harka. Mun kai 2 weeks madiha tana ta mana wnn iskancin. Da rana kuwa garau dinta wuni take rawa ta kunna music maimakon wa,azi ba daman zama a Palo dole nake wucewa daki in kunna wa,azi inajin abuna . Ranar kawai sai gashi ya dawo yayi mantuwa don haka ya sameta a Palo ta kunna music tana rawa. Aikuwa ya zuba masifa ranar saura kadan ya mata duka nice na bashi hkr da kyar amma har ya fita masifa yake tayi. Da daddare kuwa yace tunda abun nata iskanci ne ita kadai zata kwana ni in dawo daki. Ya kuma ce mata wlh idan kk kuskura kk kwankwasa mana kofa idan na fito sai na harbi kwakwalwarki da bindiga! Zaro ido tayi a tsorace hade da fadin " kayi hkr yaya. Yace " tashi ki tafi ki bani wuri mara kunya kawai. Tunda daga ranar muka sami salama da daddare mu samu muyi bacci zuwa karfe biyun dare tfy tahajjud mukeyi da yaya mu barta a gida.da kyar take bude mana kofa in mu dawo. Sosai na lura takejin haushina bare ma ta taga irin kayayyakin da ya salman ya siya mun masu tsadan gaske na adon sallah duk hsnkslinta ya tashi ranar wuni tayi a daki tana ta waya da 'yan uwanta tana fada musu. Gaba ta karu don yanzu indai gani gata sai dai in kauce in bata hanya in ba haka ba sai dai tasa kafada ta tureni da karfi taja tsaki ta wuce tana zagina abin yana min ciwo don haka daya isheni rannan da naxo shiga kitchen ita kuma tazo fita tana jiran na kauce mata kawai taga na tsaya a bakin kofa. Cikin tsiwa tace " dan Allah ki ban hanya in wuce kona tureki. Takaraso da sauri ta ture kafadata zata wuce . Da sauri na jawota na dawoda ita muna fuskantar juna na kalli fuskarta cikin tsanani fushi na sharara mata mari mai rai da lfy har ta sunkuya idonta nan da nan ya cicciko da hawaye ! Cikin zafin nama ta daga hannunta zata rama na rike hannunta snn nace " ko kinsan duk abinda kk yi ina tara miki ne to yau kam dubunki ya cika wlh idan kk kuskura ki kace tak anan sai nai miki shegen duka in yaso in kun isa kusa Salman din ya sakeni. Sake baki tayi tana kallona cike da mamaki ta kasa fadan komai tuni na wuce na barta a wurin !!! Fans na gode da kulawar da kk nuna min sosai Allah ya bar zumunci🙏🏻 Hauly ce👍🏻🥰 [10/9, 10:36 AM] +234 703 558 2498: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 *WANNAN* *SHAFI* *KYAUTACE* *A* *GAREKU* *MASOYAN* *KWARAI* 👍🏻🤗 *AL*- *FAHARI* *NOVELS* *ONLY* Hauwa Ado 😄 D yuguda Sadiya sulayman Mum Abulkhair Maman ummee HAUWA.U M Shauwa Mamar Ramadan Maman Amir Aji Abubakar Safiyya Atiku Maman zee Maryam Dango Ummah bala B Aisha Abdullahi Maman Nabil. Ummu hybat🥰 *RASHIN* *NAZARI* *FANS* Mmn amcy Maman baraka Ummu aslam Phertyma Useexer Basmah Aisha Ardo Aisha lafene Mom ruky Khadija Maman al'amin Maman Abba Maam khyry Ummu shahid Laweezat imam Halima Harira Isa 38 Zynab Duk wayanda basu ji sunansu ba su min uzuri ba hakan naso ba ayi hkr ngd🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗👏🏻 _🥰🥰🥰🥰Ina yinku sosai fans kamar yadda kk kaunar *RUMAISA* *SALMAN* nima ina matukar kaunarku Allah ya bar _zumunci_ _da_ _kauna_ _mai_ _dorewa_ _tnx_ _so_ _much_ 🥰🥰🥰🥰🥰🥰 _Hauly_ _ina_ _tare_ _da_ _ku_ a _kowani_ _lokaci_ 👍🏻👍🏻👍🏻😄😄😄😄 *PAGE* ➡69 *************A ranar ta tattara kayanta don tsabar munafurci zata tafi ni kuwa ko a jikina cewa nayi umma ta gaida assha in yaso taje ta fadawa adda A' i tazo ta sameni. Tana fita ta hadu da hassan ya fito daga motarsa zai shiga gidansa don haka da sauri ya fara tambayarta me ya faru yaga tana kuka? Dake ya santa wasu lokuta ita take kai mishi abinci. Kawai sai ce masa tayi wai na kamata na mata shegen duka alhalin batada lfy don haka zata koma gidansu. Anan ya shiga rarrashinta akan kar ta tafi da kyar ya shawo kanta ta amince shine harda dauko mata jakar kaya suka dawo kawai naji ana buga kofa ina budewa na ganshi tsaye tare da ita sai harara data watso min. Nan na fara gaisheda hassan ya amsa hade da fadin " haba madam me ya hadaki da kanwarmu har kk mata duka? Cikeda mamaki na kalli madiha murguda min baki tayi na kalli hassan hade da fadin " ni ban daketa ba kawai....... Ya katseni da fadin" its ok shikenan kawai ta koma don Allah ku zauna lfy pls madam i beg you Nace " ba komai ni dama ban koreta ba. Yace ok thank you. Ya kalli madiha kauda kai tayi tace " nifa bazan shiga taje ta kasheni ba kawai zan zauna anan ka kira ya salman. Murmushi yayi yace " come on kiyi hkr mana babu komai. Nidai shigewa ciki nayi na barsu. Shiru shiru banji shigowarta ba har na kuma lekowa don na bar kofata a bude amma abin mamaki sai ban ganta ba . Don haka na maida kofata na rufe. Na wuce daki naci gaba da harkokina har ya salman ya dawo bayan ya dan watsa ruwa a jikinsa ina kitchen ya sameni yace" sannu da aiki baby. Murmushi nayi nace"yawwa ya aiki? Yace" Alhamdulillah yau ina madiha ne banji motsinta ba tunda na shigo. Na danyi shiru snn daga baya na kwashe duk yadda akayi na fada masa duk na tsorata kar ya min fada amma sai naji yace" kinyi abinda ya dace kuskurenki daya ne da baki kirani a waya kin fada min hassan ya dauketa ba . Nace" ni ma bansan sun fita ba . Dan tsaki yayi ya fita da sauri wayarsa ya dauka ya kira hassan ya tambayeshi ina madiha wai gata nan suna tare sun fita ya kaita ta sha iska ne. Hankalin ya salman na lura ya tashi sosai don ko zama ya gagareshi sai kai komo yake a palo mamakine ya kamani nace " yaya lfy naga ka daga hankalinka ? Tunda yace suna tare ai shikenan zasu dawo ka kwanta ka huta. Ya girgiza kai yace" rumaisa bazaki gane bane hassan fa ba mutumin arziki bane so yake ya bata mata rayuwarta........ Da sauri nace" haba yaya kasan me kk fada kuwa ? Ko ka manta a watan ramadan muke? Murmushin gefen baki yayi yace" shiyasa nace miki bazaki gane ba din kawai kije kici gaba da ayyukanki. Jikina a mace na koma kitchen. Shiru shiru sune basu dawo ba har nine .ya salman duk ya gama cika Tana shigowa naga ya tashi a fusace ya fita nasan gun abokin nasa zaije. Ni dai ina ganin iko Allah ranar yana dawowa ya wuce dakinda madiha take banyi mamakin jin ihunta ba don a yadda naga rainshi a bace nasan komai ma zai aikata. Da sauri na shiga na sameshi hannunsa rikeda belt dinsu na sojoji duk ya faffasa mata jiki da kyar na rikeshi ina ya salman kaiwa Allah ka rabu da ita karka mata lahani kaga fa duk ka faffasa mata jiki ? Pls ka barta yaya dan Allah mu tafi....... Juyawa yayi ya fita ba tare da yace komai ba. Na kalli madiha wacce take dunkule wuri daya tana kuka nace" hmm kinga abinda rashin kunyanki ya jawo miki ko don haka in kina da hankali yanzu sai ki san me kk yi. Na fita kayana. Washe gari da sassafe yace ta fita maza ya maidata gida. Ba yanda banyi dashi akan ya kaita asibity ba amma muguntan su na sojoji ya hana shi ganin halinda ya jefata ciki haka suka tafi ko ya zasu kare da adda A'i ne oho. Daga nan dai na samu zaman lfy a gidana ana saura kwana biyu sallah muka dawo kano. Anan muka fara hidimar sallah cikin kwanciyar hankali ba takurar inna fa,iza ma sunzo kuma a kanon suka sauka .itama ciki yayi nauyi da kyar tashi ga ruma ma haka sakina ma ko yau ko gobe.bansan yanda zasuyi service dinnan ba.gaskia nima na fara sha,awar cikin nan Allah Allah nake inga na tsallaka wata amma sai wata yayi nitsa in mun fara expecting ni da ya salman sai period na yazo duk sai na shiga damuwa ya koma yana rarrashina . Bayan sallah da sati uku mama ta dawo don dama ta yola ta sauka wai karkuso kuga yadda mama tayi wani irin kyau da haske gashi tayi jiki a bakin maman sakina naji wai mama tana da ciki ni duk kunya ne ya rufeni gani nake kamar ta tsufa da haihuwa in na fadi hakan ya salman ya kama yi mun dariya yace " ba wani ke dai kk ganin haka don kinga ta haifi kamarki . A lokacin aka gama ginin gidan mama na kano.wai karkuso kuga kudinda aka kashewa gidan nan abin sai wanda ya gani ga sabuwar mota dalleliya da ya sake sai mata ya komai na more rayuwar duniya daddy yazubewa mama a gidan nan nima kaina inada dakina a gidan masha Allah sai dai fatan alkhairi. Gagarumar walima muka shirya a wnn gidan na tarewar mama .faiza cewa tayi ba don cikin nan da ya mana cikas ba Allah na tuba da casu zamusha. Dariya mukayi hade da tafawa nace" karki damu sisi sai ta haihu kamin nan kuma kun sauke sai mu hada casun? Zaro ido tayi tacs" sis karkice mun goggo Amina nada ciki ? Hannu nasa na toshe mata baki nace " ke karki daga murya ta jiyo mu tazo ta sauke min . .... Shigowar ruma ya katseni tace " ihsan oganki yazo ku tafi . Bata fuska nayi nace " haba ya salman shi kuma bayan munyi dashi kwana zamuyi dukanmu anan shine zaizo . Sakina tace" kema kinsan zaiyi wuya ya salman ya iya barinki tunda sanin kanki ne tun kan kuyi aure ma in yazo daga lagos bai sameki a gida ba sai yaje ya daukoki ko a makaranta ko a gidan Alh Aminu... Harararta nayi nace " wai waya sako bakinki ne ke kuma kiji da nauyin jikinki don Allah ba wanda ya tambayeki tarihi. Sukayi dariya ruma tace " ki dai tashi ku tafi in kuma kin tsaya bata lokaci yanzu ya shigo ya samemu anan ya sauke mana kwandon balai. Faiza tace" hmm to wai shi yaya don ya hkr na yau kadai mene ne? Sakina tace " bazai hkr ba mutum da matarsa ke yanzu ra'is in ya ce kizo ku tafi wlh nasan da gudu zaki debi jiki ki bishi duk da nauyin cikin nan naki . Faiza tace" tsab ma kuwa ksmar kin sani. Muna cikin haka mama ta leko tace" wai rumaisa ba,a gaya miki salman yazo kun ajiyeshi sai faman jira yake gashi dare nayi. Shagwabe fuska nayi nace" mama don Allah ki rokeshi na kwana..... Ta ce" ba ruwana wlh tashi zakiyi ku tafi yanzu ina nan sai naga tashinki Mikewa nayi ina bata fuska na dauki veil dina da jakata mama kuwa tafita. Su sakina sai dariya suke min nace " ruma kema zo mu tafi kema bai dace ki kwana ba ya salim yana jiranki. Dariya tayi hade da fadin " ke dai jeki ni kam mun tsufa don na kwana yau daya ba komai kune har yanzu baku gama cin amarci ba. Faiza tayi dariya tace " a soye lfy sisi ina ma in zama tsuntsuwa inje inga yadda kuke soyewa . Harararta nayi nace " Allah ya maidaki tsuntsuwan Gabadaya mukayi dariya tace " hmm yanzu sisi ya salman dinnan har yana iya bude baki yace miki i love you rumaisa? Tsaki naja na fita suna min dariya ruma tace " ki gaida gida mu kam muna nan sai mun gama more sabon gida. Ya Salman har ya gaji da jira a mota ya kwantar da kai akan seat kamar mai bacci. Ina shiga nace " am sorry yaya. Kallona yayi hade da fadin " kingama yangan naki knn? Nace" yaya ba dama munyi da kai zan kwana bane ? Kallona yayi snn yace " na fasa ne . Nace " to Daga nan ya tashi motar muka fara tfy nace " yawwa yaya in munje kan hanya wurin suya a siya min kaza da youghut wlh yunwa nikeji . Baiyi magana ba har muka isa wurin suya yayi parking ya fita yaje ya siyo ya dawo . Nace" yaya meya faru ne naga kamar ranka a bace ? Yayinda ya tashi mota muka fara tfy yace " kece kk bata min rai tun dazu nike jiranki kinsan irin gajiar da nayi kuwa yau dinnan? A raina nace dama kana gajiane? A fili kuwa murmushi nayi nace"yaya kayi hkr don Allah su fa,iza ne suka matsa min da surutu. Mun iso gida karfe goma da rabi bayan munci kajinmu muka sha youghut daga nan mukayi wanka muka kwanta. Da safe kuwa bayan na gama aikin gida nayi wanka naci ado cikin atamfata holland nayi kyau sosai sai kamshi ke tashi ko ta yaya na motsa. Naje dakinshi har lokacin yana kwance. Nace" yaya yau bazaka tashi bane tun dazu breakfast ke jiranka fa. Ya danyi mika hade da fadin" ba yanxu zan tashi ba. Nace" to yaya wa zai kaini gidan maman ko in tafi da motata? Yace" ke kin cika son yawo je ki ci abinci kizo mu kwanta. Bata fuska a shagwabe nace"yaya su faiza suna jirana fa kuma nace ma zanyi sallama da 'yan yola da sukazo. Yace" shikenan se kin dawo . Ya fada yayinda ya jawoni na fada jikinsa ya fara kokarin cire min kayan jikina. Nace"wayyo yaya ka fa ce min sai na dawo....... Bai bari na karasa magana ba ya hade bakina da nashi ya shiga aikamin sakonninsa masu zafi . Don tuni na lumshe ido na fara karba ji nayi bazan iya tabuka komai ba dole na bada kaina kai ya salman ba dama. Saida muka soye son ranmu muka gaji dan kanmu snn mukayi wanka na maida kwalliyata ina daura dankwali ya shigo dakin ta cikin madubi muke kallon juna . Ya sakar min lallausan murmushi yace " weldone baby na . Yazo ya rumgumeni ta baya yace"sannu da kokari kinyi kyau sosai in kin gama mu tafi mu gaida su inna sai na kaiki Nace" har kayi breakfast dinne? Yace"eh Na dauko gyalena ina shirin yafawa yace"amma dai na hana ki sa gyale. Na kalleshi a shagwabe nace" yaya tare fa zamu fita. Yace"duk da haka dai ki sa hijabi yafi rufin asiri. Ba yanda na iya na dauko hijabina na saka na dauki jaka muka fita. A gida muka sami inna tana kitchen da sa,adatu don haka daki muka wuce muka jirata har ta shigo muka gaisheta ta amsa fuska sake tace wa ya salman " jiya nayi mafarki mai dadi . Yace" mafarkin me knn ? Tace" mafarki nayi rumaisa ta haifi 'ya mace ka saka mata sunana. Murmushi yayi yace" innah Allah ya kawo masu albarka in kinje hajj ki mana addua . Tace" insha Allah gabadaya na kosa naga jininka salman kar na mutu....... Ya katseta da fadin haba inna Allah ma ya baki tsawon rai zaki ga jikokinki insha Allah. Tace " to Allah yasa kaga sadiya ma cikine da ita yanzun har ta fara damuwa ganin raihana yara uku amma ita tun Abdul shiru se yanzu. Yace" to Allah ya raba lfy Ta sake cewa " kaga bana jikoki zasu cika gida ga salim ga sakina ga faiza ga sadiya inaga ma shiyasa na damu da son kaima inga ka samu salman. Yayi murmushi yace " karki daga hankalinki inna muma zamu samu kinga ai auren namu ai bai jima ba tunda ko su salim ma shekara bai zago ba. Tace " hakane Allah kawo masu albarka. Nidai kaina a sunkuye ban sa musu baki ba jikina dai yayi sanyi sosai .duk da ma dai yaushe ne auren namu. Muna nan sadiya ta shigo duk ta rame dama ita laulayin tsiyane da ita . Bayan mun gaisa ta kalleni tace" rumaisa ya naga kin wani zauna shiru ko dai kema.... Ta fada tana dariya snn tace " kinsan mun kosa muga babyn ya salman mutanen kamaru ma sai tambaya suke. Inna tace" eh wlh su yapendo duk sunce baza su zo ba sai matar salman ta haihu sun shirya zuwa tsaf don basu samu sunzo aure ba. Haka sukaci gaba da hiran haihuwa ya salman ma shiru yayi daga baya yace mu tafi Muka tashi jikina a mace . Har muka isa gidan mama ya shiga ya gaisheta snn ya kalleni yace " in salim yazo ki bishi ku dawo. Nace"to. Na shiga daki na samu masu cikin duk suna cin abinci nan na zauna sunata zolayata basusan meke damuna ba...... Hauly ce🥰🤗 [10/9, 10:37 AM] +234 703 558 2498: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 *BAN* *MANTA* *DA* *KU* *BA* *MASOYANA* *NA* *GROUPS* *DIN* _Mis _umar_ _Haske_ _writter_ _Home_ _of_ _novels_ _Asmail_ _hausa_ _novle_ _Roome_ _of_ _cool_ _novels_ _Umma_ _yasmin_ _hausa_ ... _Leema_ _fans_ _Novels_ _🥰🥰🥰🥰Ina yinku sosai fans kamar yadda kk kaunar *RUMAISA* *SALMAN* nima ina matukar kaunarku Allah ya bar _zumunci_ _da_ _kauna_ _mai_ _dorewa_ _tnx_ _so_ _much_ 🥰🥰🥰🥰🥰🥰 _Hauly_ _ina_ _tare_ _da_ _ku_ a _kowani_ _lokaci_ 👍🏻👍🏻👍🏻😄😄😄😄 *PAGE*➡70 **************Haka muka sha hutunmu na wata daya a kano snn muka koma lagos a lokacin su inna ana shirye shiryen tfyrsu hajj. Mun koma lagos wnn karon bamuda matsalar komai rayuwar mu na tfy cikin jin dadi da nishadi .a lokacin na kara gogewa da zaman barrack idona ya kara budewa nima na koyi jarumta da dauriya irin na matan soja lol! Munje gidan adda A'i har sau biyu a tunani na ko zata min maganar madiha amma shiru ba tace komai ba bayan mun dawo nake tambayar ya salman labarin madiha wai ashe sun maidata kamaru don tunda muka zo hutu kano ashe ta dinga zuwa wurin hassan anan barrack ko shi yaje ya dauketa su tafi hotel haka ya dinga yaudararta har yayi mata ciki suka zubar wai zai aureta dama yana son yagane ita mai haihuwa ne ko dai bata haihuwa sunsha case sosai akan madiha ashe amma ban sani ba shine ya salman yace wa adda A'i ta maidata kamaru kawai kar tafi haka lalacewa shine suka tattarata suka mayar da ita . Wnn dalilin yasa ya salman da hassan suka sami sabani har sunso suyi fada don shi hassan cewa yayi lokacinda ya salman yake tareda kanwarsa khabirat ai bai hanasu sheke ayarsu ba.don haka bai kamata ya salman ya damu ba don shi yana tare da madiha tunda yace aurenta ma zaiyi. Case din har gaban manyansu a inda suka baiwa ya salman laifi aka zauna aka sasanta su amma duk da hakan ya salman yaki sakar masa fuska.koda matarsa silfa ta dawo ma cewa yayi kar naje na rabu da su.dama ni ba zuwa zanyi ba. Haka nake ci gaba da rayuwata a barrack ni daya in ya salman baya nan in kuma ya dawo shikenan muna manne da juna komai tare mukeyi. Hakan ma yafi min dadi da kwanciyar hankali . Bamu sake zuwa kano ba sai da su innah suka dawo. Tare da adda A'i muka taho kano hmm sai kunga inna yanda tayi kyau ta sanya hakorin makkah kowa yazo yi mata sannu da zuwa sai an bashi labarin makkah . Ni dai a kwanakin nasha hidiman girke girke don ni keyin girkin gidaje biyun gabadaya ga ruma bata nan ta koma Abuja acan zatayi service dinta ga kuma haihuwa ko yau ko gobe faiza ma tana Abuja rais ya barta nima yanxu ya salman zai barni anan ya koma lagos shi daya. Su sadiya da Adda A'i sune kan gaba wurin raba tsarabar makkah. Nayi mamakin ganin sa,a ta kawo min akwati guda na tsarabata kuma wai ni kadai na ya salman nashi daban ne. Ban bude ba har saida ya salman ya shigo da nashi dariya na mishi nace "nawa yafi naka yawa akwati sukutum inna ta cika min da kaya . Yace"zamu raba ai don ban yarda ba. Dariya nayi najawo akwatin nayi na bude don muga kayan ciki abin mamaki kayan jirajirai zallah ne a ciki har da set din mayuka da sabulan yara har da diapers da su takalmi da socks zuwa hula hmm abin se wanda ya gani. A tare muka kalli juna da ya salman a inda yace" to ai nan duk kayan babys ne inaga ba wnn ne taki tsarabar waya kawo miki? Jikina a mace nace "saadatu ce. Yace " may be sadiya akace ta kaiwa ko an canza akwatin tun a gidane bari gobe zamu mayar mata yanzun dare yayi muje mu kwanta . Haka kuwa akayi washe gari tare muka shiga dashi wurin innah bayan mun gaggaisa yace" inna wnn akwatin ko na sadiya kk canza baki sani ba aka kaiwa rumaisa don kaysn babys ne kawai a ciki. Inna tayi murmushi tace"ina sane sarai rumaisan na kawowa ko dai bata da cikine? Sunkuyar da kai nayi ya salman ma shiru yayi. Tace " ikon Allah kamar na sani Allah to ya raba lfy na kosa inga yaranka salman Da sauri ya salman yace" inna rumaisa fa bata da ciki sai dai muna fatan...... Zaro ido tayi tace"har yanzu? To ko batada lfy ne ? Kai gaskia akwai abin dubawa a wnn lamarin kamata kuje asibity a dubaaku don asan daga ina matsalar take . Yace"innah ai haihuwa daga Allah ne kuma ni a ganina ba wata matsala tunda ta taba bari har sau biyu kuma kinga aurenmu ko shekara baiyi ba....... Ta katseshi da fadin" salman ai auren yanzu ba kai shekara ake haihuwa ko baka ganin 'yanuwankane faiza da sakina duka suna da ciki ga matar salim ma ko yau ko gobe amma kai shiru gaskia akwai abin dubawa. Sai lokacin adda A'i tayi farat tace " kamata yayi dai kuje ku bincika don watakila rumaisa tana da problem tunda kaga tayi bari har sau biyu gashi daga lokacin shiru har yanzu.ba zama zakuyi hakan nan ba ku dai je a duba se a bata magani. Inna ta karba " wnn shine abinda yafi dacewa kuyi don ni na kosa inga yaranku koda naje hajj ma nayita muku addua. Shiru kawai mukai ni da ya salman don ranshi ya matukar baci daga bisani mikewa yayi ya kalleni yace" ke tashi mu tafi. Haka na tashi jiki ba kwari har zan fita sadiya tace" kin manta kayan naki fa. Inna tace"aikuwa dai kizo ki dauka kije ki adana mai kyau har ki haihu . Na dawo na dauki akwatin hade da yi mata godiya na fita. Ya salman tuni ya fita banma ganshi ba. Ina zuwa gida daki na wuce na dora akwatin kan wardrobe snn na koma kan gado na kwanta kukanda nake kokarin hana kaina ya gagara haka na shiga kuka sosai na rasa me yake min dadi a duniya. Har ya salman ya shigo jikinsa a mace ya karaso ya zauna yayinda ya dagoni ya kwantar da ni a jikinsa yana shafa kaina. A hankali ya fara magana " baby kiyi hkr don Allah nasan dolene maganganunsu inna ya dameki nima kaina banji dadi ba amma zan sami inna in mata magana kinsan wani abun duk su Adda A'i ke ingizata. Nidai bance masa komai ba kukana kawai naci gaba dayi yayinda shi kuma yaci gaba da rarrashina . A kwanakin sosai na shiga damuwa akan maganar haihuwa.don kullum na shiga gun inna kusan maganarta knn . Ya salman tuni ya koma lagos ya barni a lokacin mun fara sevice dinmu inda nake dan samun sauki knn in na fita don bana zama gida sam sam. Bayan dawowarsu inna haj da sati biyu ne fa,iza da sakina suka haihu tsakaninsu 2 weeks ne faiza ta sami fatima zahra sakina kuma ta sami da namiji Abduljabbar. A lokacin ni kadai a gida sai 'yan matan nan sa,a da zainab. Bayan sunan babyn sakina da kwana biyu ne ruma ma ta saukea masha Allah an sami baby boy murna a gun ya salman har yafi na ya salim abun har mamaki ya ban. Suprise kawai ranar na dawo gida na sameshi bai gaya min zaizo ba. Nace"yaya shine ko ka fada nmin na shirya tarbanka? Zuba min ido yayi yana kallon kayan jikina.har na dan fara tsarguwa. Nace"yaya lfy? Ce min yayi" ke yanzu haka kk fita kamar wata arniya? Na dubi kayan jikina riga ne da wando kayan copers sai dan karamin hijabi snn na kalleshi nace" yaya hijabi fa nasa kuma kaga da motata nake zuwa na ...... Ya tari numfashina da fadin" matukar kina son kici gaba da service dinnan to dole ne ki dinga suturta jikinki duka .wnn hijabin da kk takama dashi ki bari sai kinje can ki saka amma ki tabbatar da kin dauki babban hijabi kin saka kamin ki fita daga gidan nan haka ma in kin tashi dawowa karkiga wai don a motarki kk dawowa. Jikina a sanyaye nace" to yaya zanyi yanda kace . Ya gyada min kai snn ya fita. Ni kuma na wuce ciki don cire kayan jikina . Ko wanka ban tsaya yi ba na wuce kitchen da sauri na shiga shirya mishi girki. Ana kiran sallar magriba na gama na shirya dining snn na wuce daki na fada toilet nayi wanka hade da alwala . Sai da na idar har sallar isha snn na tashi na fara shiryawa.ado nayi na musamman na saka doguwar riga na material mai combination nayi kyau sosai. A lokacinda na fita palo suma suka shigo da ya salim nayi musu sannu hade da fadin " mu isa dining . Ya salim yace "aiko bakice ba . Dariya nayi nace" yaya angon karni ashe ka dawo ya kabar maman baby da babyn? Yana murmushi yace lfynsu lau suna gaidaki wai yaushe zakizo. Na kalli ya salman shima ni yake kallo amma baice komai ba don haka nace" ai zanjene kar ta damu. Muka wuce dining na musu serving nima nayi na zauna muka soma cin abinci muna dan taba hira ni da ya salim shi dai bai sa mana baki ba har saida ya salim yace masa " yaushe zakaje kayiwa dan naka huduba? Kai tsaye yace gobe insha Allah. Da sauri nace "yaya nima zanje don Allah. Yace"aikin naki fa. Nace"ba damuwa. Hade fuska yayi yace in kk je gobe bazaki je suna ba zabi ya rage naki. Ya salim yace" kaifa salman bakada kirki wani lokacin to meye a ciki don taje sau biyu? Shiru yayi ya salim ya kalleni yace " rumaisa ki shirya dake zamu tafi goben in Allah ya yarda. Murmushi nayi nace " to yaya nagode. Shidai bai kuma cewa komai ba na luro yau 'yan halin nasa sun murdo gaban goshine.ni dai inda sabo na saba don haka ban damu ba. Ya salim kam muna gamawa ya fita ya barmu. Na kalleshi cikin kwantar da murya nace" yayana don Allah waya bata maka rai ne ? Shiru ya min na sake cewa "inde akan maganar sutura ne kayi hkr daga yau na daina kwata kwata banson bacin ranka yayana. Ba tare da yace min komai ba ya wuce side dinshi binshi nayi da sauri na iskeshi yana kokarin cire kayanshi da sauri na karasa gabansa na soma tayashi. Snn nace" yaya don...... Ya katseni da fadin" banson yawan surutu pls na gaji ina son in hutane. Jikina a mace nace " to yaya . Ya wuce toilet ya barni nima fita nayi na tafi dakina rai ba dadi. Da safe kuwa tunda na gama komai daki na koma nayi kwanciyata. Jin shiru shiru ban fito ba yasa shi shigowa cikin shirin tfy Abuja? Ya kalleni cike da mamaki yace"baki tafi aikin ba? Nace"eh. Yace " to meya faru? Tabe baki nayi nace" ni na hkr da aikin bautar kasarne zaman aurena yafi min komai muhimmanci don haka bazan so na dinga bata maka rai ba yaya. Ya karaso bakin gadon hade da fadin " wayace miki fushi nakeyi? Hawayene ya cicciko idona nace" ba gashi nan ba tun jiya sai baka hkr nikeyi . Ya zauna hade da jawoni jikinsa yace" shikenan na hkr karkiyi kuka pls. Ya dago fuskata yana share min hawaye snn yace in tashi na shirya mu tafi Abujan suna jirana. Muhammad kassim shine sunanda ya salman ya zabawa babyn . Bayan mun gama shagalin suna a tunanina yaya zai wuce lagos amma shiru koda na tambayeshi ce min ya dawo kano ne. Don haka wasu lokutan shi yake kaini wurin aiki. Ranar kawai yana saukeni ya tafi sai ga wata mota baka da tintet tayi parking a gefena ban kula ba nayi wucewata " *Queen* " Kamar a mafarki naji muryar *Ahmad* Da sauri na juyo shi din ne kuwa na gani ya sauko daga motar yana murmushi Ahmad ya kara kyau da jiki ga haske gaskia. Ya karaso gabana fuskata na yabo ba fallasa nace" Ahmad dama kana duniyar nan. Dariya yayi yace" gani kina ganina queen ya dai ya kwana da yawa ya share wa? Nace"hmm Ahmad knn bakaji labarin nayi aure ba? Yace " naji kunyi aure da salman mana. Nace "ok ina salima ta haihu ne? Yayi murmushi yace" eh mun samu baby boy umar farouq. Sai lokacin nayi murmushi nace " Allah ya raya bari in shiga ciki sauri nike. Yayi murmushi snn yace" ai na gani amma dan bani minti daya pls. Ya tafi motarsa da sauri ba jimawa ya dawo ya mika min wani card na kalleshi nace"wnn din na meye ? Yace" karba ki duba? Na karba murmushi yayi yace" thank you sai na jiki. Binshi nayi da kallo har ya shiga mota ya tafi ban biyo ta kan card dinba na jefa a jaka. Bayan kwana biyu da faruwar haka kawai ranar aka kirani da boyayyiyar number ina dagawa naji muryar ahmad ce mun yayi " queen shiru shiru har yanxu baki amsa gayyata na ba. Jin motsin shigowar ya salman yasa na kashe da sauri kuma cikeda tsoro da fargaba. Ya karaso kusa dani yace " keda waye a waya kuma a wnn daren? Nace"nima ban sani an boye numberne an kirani . Yace"to karki kuma dagawa. Da ssuri nace masa to A jiye wayar nayi nace"bari yaya na kawo ma fruit salad dinka Da sauri ya kamoni yace" ki barshi kawai yau dinnan ke kadai nake bukata baby. Murmushi nayi nace" yaya dare fa yayi sosai is time for sleeping. Ya rumgumeni hade da lumshe ido yace" no bazan iya bacci ba baby weather din yau bana bacci bane . Ya karasa fada yayinda ya soma shashshafani nima lumshe ido nayi na fara karbar sakonninsa a shagwabe nace" yayana. A hankali ya sauke ajiyar zuciya snn yace" babyna! Na dada kwantar da kaina a kirjinsa ina wasa da gashin kirjansa nace"yaya idan ina tare da kai mantawa nake da dukkan hayaniyan duniya .kai din na musamman ne. Ya dago fuskata yana murmushi snn yayi kissing din bakina yace " thank you dear nd kema kinsan your so so so special sonki kullum dada mamaye koina na jikina yake bana iya zama na second daya ni kadai ba tare da na tuna ki ba babyna i love you! Na dada kwantar da kaina ina murmushi nace " i love you too ...... Da sauri ya soma rikita tunanina da salon soyyayyarsa mai sanyawa zuciya nitsuwa gaskia ya salman daban ne a cikin maza zaiyi wuya mace ta sanshi ta iya rabuwa dashi .don haka nake kara zagewa wurin ganin na toshe duk wata kofa a zuciyarsa kar wata ta shigo don a yadda nakeji a jikina kamar bazan iya sharing dinsa da kowacce mace ba. Da safe kasancewar ranar sunday ce bacci mukayi sosai har sha biyu muka yi breakfast bayan munyi wanka shikam tuni ya fita yace sai bayan sallar la,asar zai dawo. Nace" to a dawo lfy. Bayan fitarsa ne na koma daki na duba wayata wanda naji lokacinda massage ya shiga. Ina dubawa na fara karantawa kamar haka. Queen! Pls ina rokonki ki amsa gayyatana ko sau daya ne a guest house dina address dina shine na baki ranar sai na ganki!!!!!!! Shiru nayi ina maimaita sakonsa a zuciyata mamaki da tsorone ya rufeni a lokaci guda to meye ahmad yake nufi da in amsa gayyatarsa. Daukar num dinsa nayi da sauri na kirashi ba jimawa ya dauka hade da fadin"queen...... Na katseshi da fadin" Ahmad don Allah don Annabi ka rabu dani na fada ma nayi aure me kk so dani ne? Cikin wata irin murya yace" queen wlh nima ba,ason raina nake damunki ba na kasa hkr dakene wlh ganinki ranar ya matukar tayar min da hankali sai yanzu na gane saken da nayi a baya pls queen ki daure mu hadu a guest house dina ko sau daya ne nayi miki alkawarin ba wanda zai sani.kuma shikenan zan rabu dake. Hawayene ya zubo min nace" ahmad ashe har yanzu baka shiryu ba kasan abinda kk shirin cewa mu aikata kuwa ?to nikam ba dani ba kaje can ka nemi shashasha yar iska irinka nikam bazan iya cin amanan aurena ba kuma pls daga yau ina maka gargadi da babbar murya kar ka sake nemana a rayuwa in ba haka ba zan dauki mummunan mataki...... Ya katseni da fadin" queen koma me zaki fada ki fada rabuwa dake bazan iya ba kawai.na baki one week kiyi tunani zan tuntubeki .ba wani abu bane kawai haduwa zamuyi sau daya tak na miki alkawari daga nan bazan kuma nemanki ba ...... Tsabar rakaici katse wayar nayi zuciyata cike da nadaman meyasa na kirashi .kuma nayi alkawarin bazan kuma sauraran shirmensa ba sai dai ya kari maitarsa ya rabu dani !!!!!! Hauly ce🥰👍🏻 [10/9, 10:36 AM] +234 703 558 2498: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 *HAR* *ILA* *YAU* *KUMA* *BAN* *MANTA* *DA* *KU* *BA* ❤ _Masoyana_ _na_ _group_ _din_ *BASMAH* ' *YAR* *LELE* _wnn_ _shafin_ _nakune_ _Allah_ _ya_ _bar_ _zumunci_ _nagode_ _sosai_ 🥰🥰🥰🥰🥰🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡71 ***********Tun daga ranar ban kuma biyo wa ta kan Ahmad ba naci gaba da harkokina. Ranar wata monday na fito daga wurin aiki sai gashi nan saida gabana ya fadi. Daure fuskata nayi tamkar ban taba sanin meye dariya ba na wuce da sauri zan shige motata shima din cikin hanzari yasha gabana. Cike da mamaki nace" Ahmad anya kanka daya kuwa ? Kasan me kk yi kuwa? Cikin sanyin murya yace"my queen pls ki saurareni dan Allah wlh ko kadan bana son in cutar dake amma...... Na katseshi da fadin " bakada hankali Ahmad Allah wadarai da yawan shekarunda baida amfani wlh gara min rayuwarka ta baya da baka cika shekara 40 dinba.inde haka zaka zama. Murmushi yayi yace Queen karkiga laifina a shekarun baya ashe shirme nakeyi da nike cewa in na kai shekara 40 zan bar wasu abubuwan dan a ganina zan manyata ne sosai amma kalli dubeni fa sai ma kara jin kaina nake anan na fahimci cewa yanzu ne nake dai dai da cin zamanina. Tsaki naja hade da fadin " Allah wadaranka wlh ni ka ban hanya na wuce .in yaso kaje can kaci gaba da shashancinka rayuwarkace ai ba tawa ba . Ina kokarin ratse shi na wuce naji caraf ya rike min hannu . Na zaro ido cike da tsoro na fara kokarin kwatar hannuna ina waige waige nace"wlh idan baka sakeni ba ihu zan maka in tara ma mutane. Murmushi yayi ya ce" bani minti daya kamin kiyi ihun. Nidai sai kokarin kwatar hannuna nake ina don Allah ka sakeni Wayarsa ya ciro ya bude hade nuna min yace" duba nan kiga. Na kai kallona ga wayar ai saida gabana yayi mugun faduwa har jakar hannuna ya fadi ganin irin hotunan da mukayi ta dauka dashi a wurin clubs da gidanshi wani muna rumgume da juna wani ma ina kissing dinshi ga watsu arnan kaya da na saka wanda dashi da babu du daya. Haka yayita nuna minsu yana murmushi snn daga baya yace" kingani ko to akwai vedios ma idan kk bani hadin kai da hannuna zan baki ki goge idan kuma kk ki yanzun nan zan turawa salman snn yanxu haka in zaki duba can bangaren zaki ga ana daukar mu hoto zan sa a wanke in turawa salman har gida. Ya saki hannuna hade da sakin murmushin yaudara yace" gobe ina jiranki a gidana da yamma in kina so asirinki ya rufu. Jin ya saki hannuna yasa da sauri na juya yace " ungo jakarki. Fizgewa nayi na shige motata da sauri na tashi motar Allah ne dai ya kaini gida lfy. Gabadaya ranar na rasa mai yake man dadi a rayuwar duniya Ya salman ma har ya fahimci ina cikin damuwa yayita tambayana nace masa babu stress ne ya min yawa .Allah sarki yayana kusan kwana mukayi yana min tausa.da kyar na samu na lallabashi yayi bacci dan haka na samu damar tashi na dhiga kai komo a dakin ina tunani mafita! A karshe dai yanke shawara nayi bazanje ba sai dai komai ma yafaru. Washe gari kasancewar ranar sunday ce muna gida ni da yaya bamu je koina ba muna manne a daki muna ta soyewarmu tuni na manta da batun wani Ahamad. Na dauka ko zai sake turon sako ko ya kiran sai naji shiru ina ta zaman jiran mai zai faru amma har gari ya waye banji komai ba don haka sai naji hankalina ya dan fara kwanciya. Ya salman ya rigani fita yau don sammako yayi yace min zasuje maiduguri amma may be bazasu kwana ba.nai mishi Allah ya kiyaye hanya.duk naji banson tfyr tasa don gabadaya maiduguri babu zaman lfy sai dai mu tayasu da addua.snn ceto rayukan mutane wajibi ne akansu sojoji koda zasu rasa nasu ran don haka adduace tawa domin tun ina daga hankalina da tfy tfyn ya salman har na saba. Nima na tafi aiki a motata.ina ta tunani ta inda Ahmad zai bullo min sai addua nike a zuciyata. Da yamma na fito da niyyar dawowa gida har nasa key zan bude motata kawai sai ji nayi kamar daga sama an fizge jakata da sauri na juya hade da fadin wayyo Allah jakata an kwace! Kasancewar ba kowa a wurin haka inaji ina ganin wanda ya fizgen jaka ya gudu dashi. Sa,a na daya wayata da mukullin motata na hannuna abinda ke cikin jakan Atm dinane sai dan canjina da sauran tarkace....... Hankalina ya tashi kwarai ba yanda na iya haka na wuce gida cikin bakin ciki.ya salim naje na fadawa don ya salman kam tunda ya isa maiduguri daya kirani shikenan yace min ba lallsine in sameshi a waya a kai akai ba don haka sai dai sun dawo kawai. Kamar da wasa ya salman saida suka shafe 2weeks snn suka dawo gaskia sunsha wuya suma yana bani labarin maiduguri ina kuka tsabar tausayi. Ganin hankalina ya tashi sosai yasa ya shiga rarrashina yana cewa amma yanxu komai ya lafa Alhamdulillah ki daina damuwa baby su kuma haka tasu kaddarar yazo. Nace " hakane Allah ya kawo musu agaji . Yace amin ina son ranar sunday muje abuja nayi missing din muneer wlh. Murmushi nace "to Allah ya kaimu dazu ma munyi waya da ruman ta tambayeni yaushe zaka dawo ashe kuna hanya. Yace" baby 2 weeks dinnan kamar shekara biyu naji ina ta missing dinki. Nayi murmushi nace"nima wlh yaya haka da kyar nike bacci wani lokacin barin yan matsn nan nake a dakina in tafi dakinka in kwana wlh da kyar nake samin bacci yayana amma yau hankalina ya kwanta da naga ka dawo lfy. Rumgumeni yayi sosai hade sumbatar goshina yace"nima naji dadi da na sameki cikin koshin lfy baby hope ba wanda ya bata miki rai. Dan dariya nayi nace"wlh ba kowa. Kusan raba dare mukayi muna hira snn daaga bisani muka yi bacci. Washe gari kuwa har na tafi yaya na ramuwar baccin gajia.don haka kyaleshi kawai nayi. Da yamma ina dawowa na fada wanka ina fitowa ya salman ya shigo dakin yanayin fuskarsa dana gani sai da gabana ya fadi. Ban gama tsorata ba sai da naga jakata da aka kwace a hannunsa. Ai a take jikina ya kama rawa jinayi kafafuna ya kasa daukana. Takowa yayi da niyyar ya iso gabana da sauri na ja da baya bansani ba har na jingina da jikin wardrobe . Ya karaso gabana ya zuban manyan idanunsa da sauya kala zuwa ja yace " aina kk zuwa bayan bana gari? Girgiza kai na soma yi cikin muryar kuka nace " babu yaya . Yace " to daga ina wnn jakar ya fito. Nan ma nace" bansani ba fizgeta akayi a hannuna kuma har na sanar da ya salim....... Ban rufe baki yaya ya daukeni da wata mari har saida na yanke numfashina tsabar azaba idona tuni ya kawo duhu na dafe gun . Cikin tsananin bacin rai yace"karya zaki min .saboda kinga bana gari ! Meye wnn? Ya fada yayinda ya bude jakar ya fitar da wasu kanan pills na family planning ya zube su akan gado snn ya fitar da hotunanmu nida ahmad kuwa birjik tun na da can abin mamaki harda na ranar da ya tareni ya rike hannuna ina kokarin fizgewa .ga kuma pant da breziya duk a cikin jakar . Dora hannuna nayi akai nace"na shiga uku wlh Ahmad sharri yake min don naki sauraransa yaya ka yardada......... Girgiza kai yayi yace" Rumaisa ashe ni kadai nake haukana dama abinda kike aikatawa knn wato baki rabu da wnn dan iskan bako ? Cikin tsananin kuka na durkusa gabansa nace" yaya wlh wlh wlh ...... Ya katseni ta hanyar daga min hannu cikin tsawa yace" karki kuskura kice wani abu kawai ki saurari hukuncinda zan miki! Da sauri na mike a tsorace kar dai yaya sakina zaiyi da kuwa na shiga uku! Jinayi kirjina ya fara toshewa numfashina ya fara daukewa yayinda marata ta fara wani irin azababben ciwo . Nan da nan na sake durkushewa ba shiri na shiga janyo numfashina da kyar ! Duk da tsananin bacin rai da yake ciki bai hanashi bai hanashi kulani ba don da sauri ya dagani ya zaunar dani bakin gado ya dauko inhaler na ya mika min hannuna na rawa na karba. Daga nan bai kuma ce mun komai ba har sai da yaga numfashina ya daidaita snn ya jawo stool ya zauna muna fuskantar juna yace" are you ok? Kai kawai na iya daga masa. Yace " ina son ki gaya min gaskia idan kika kuskura kk min karya wlh sai nasa bindiga na harbeki ki mutu nd no one will ask me why . Zaro ido nayi yayinda ya ce min " yes! Ina son ki fadamin yaushe kk fara haduwa da Ahmad ? Snn me ya hadaki da family planning pills ? Ajiyar zuciya nayi snn na fara mishi bayanin komai daga ranarda muka fara haduwa da Ahmad har kawo sanda a fizge jakata. Ido ya zuba min tunda na fara magana har na gama ya jima yana nazarin maganata snn daga bisani ya mike a fusace ya fita koina ya tafi oho. Nidai a inda nake zaune jina nayi na jike da sauri na tashi don ganin me yeke faruwa dani . Jini ne na gani gabadaya ya bata bedsheet din .ga wani irin ciwo da marana keyi jini kuwa ina daga tsaye yake bin kafana . Durkusawa nayi a wurin na kama kuka ina rikeda mara .bansan tsawon lokacinda na dauka ba har jinai jiri yana dibana sannu a hankali na sulale na fadi kasa a sume!!!!! Hauly ce🤗🥰👍🏻 [10/9, 10:37 AM] +234 703 558 2498: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡72 ****************Ba yanda ya salim baiyi ba don ya hana ya salman zuwa gun Ahmad amma abun ya gagara ce mishi yayi "salim don Allah don Annabi ka rabu dani ko ba a gabanka bane dan iskan nan ya turo da jaka a bani ka manta ne? Salim ya girgiza kai yace"ban manta ba salman amma kasan ba kyau yanke hukunci ciki fushi yana haifar da dana sani kayi hkr kazo kaji abinda........ A zuciye ya salman yace" kaga salim ni banson ranka ya baci kwata kwata don haka ka rabu dani babu ruwanka cikin wnn maganar kaje ciki ka kula da rumaisa. Yana gama fadin haka ya wuce motarsa da gudu ya fizgi motar kowa sai gudu yake yana matsawa kar a bugesu. Ya salim kam girgiza kai yayi cike da damuwa yace" Allah ya tsareka salman. Ya shigo cikin gida side dinmu tun a palo yayita sallama shiru ya zauna zaman jiran ko zan fito yaji shiru don haka kai tsaye ya shigo dakina ganin halinda nske ciki yasa da sauri ya fita ya je gida ya kira mmn sakina yace tazo a tafi asibity. Nidai bansan a wace duniya nike ba. Ya salman kuwa yayi sa,an samun Ahmad a guess house dinsa yana zaune da abokansa a harabar gidan sunata hiran duniya . Ai baiyi wata wata ba ya iske shi a wurin ba tare da tunanin komai ba ya hau kansa da duka da naushi yana fadin " me ye hadinka da matata! Abokan Ahmad da kyar suka kwace shi a hannun ya salman duk ya mishi jina jina abun babu kyan gani! Anan ya mishi warning sosai snn ya kama hanyarsa ya tafi ya barsu. Dole aka tattara Ahmad aka kaishi asibity don yaji masa ciwo sosai. Ni dai koda na dawo hayyacina na ganni kwance a gadon asibity banyi mamaki ba .don gashi har ma da karin jini aka min. Hawayene ya cicciko idona nan da nan dana tuno cikin jikina nasan babu shi a yanzu cikinda ko shi ya salman baisan da zamanshi ina ta son in mishi albishir din yau sai gashi ya janyo sanadin mun rasa cikin . Ya salim ne da mama sai sannu suke min ina amsa musu da kai. Muna nan innah suka shigo da sadiya sai da naji gabana ya fadi wlh. Bayan an gaggaisa suka jajantawa mama kamar abin arziki inna ta kalleni tace" Rumaisa ya jikin? Nace da sauki innah. Tace" kinga abinda nake fada muku ko keda salman kunki yarda matsalar haihuwar nan daga wajanki ne sau uku knn kina bari ba tare da wani kwakkwaran dalili ba don haka gaskia ni a shawarce ina ganin gara ku kyale salman ya kara aure domin yaga kwansa a duniya.duk sa,o,insa sai haihuwa suke don haka a duba dai a masa adalci duk da cewa nasan maganata zata muku zafi amma dai gaskia dayace kuma dole a fadeta a duk lokacinda bukatan hakan ta taso. Shiru mukayi dagani har mama ba wanda ya tanka ya salim ma haka . Sadiya kuwa cewa tayi " a duba dai ayima ya salman adalci....... Ya salim ya katseta da fadin " ke yi mana shiru dan Allah waya sako bakinki? Turo baki tayi inna tace" ai gaskia ne sadiya take fadi salim . Ya salim yace" amma inna ai naga haihuwar nan nufin Allah ne kuma rumaisa ba ita ta dorawa kanta lalurar ba...... Mama ta katseshi da fadin" salim don Allah ka bar wnn maganar kira min rabi ni tfy gida zanyi. Ya salim ya fita nikam da tunda inna ta fara magana nake zubar da hawaye sai yanzu nace" mama dan Allah karki tafi ki barni. Tace" ga rabi zata kula dake rumaisa nima bana jin dadine kiyi hkr sai gobe zanzo Allah ya baki lfy. Daga nan fita tayi inna ta tabe baki tace" hmm ummah ta gaida assha . Snn ta kalleni tace kekuma bari kiji na gaya miki ko zaki mutu salman aure zai kara don bazaici gaba da zama dake da wnn lalura taki ba sadiya tashi mu tafi. Sadiya ta kalleni hade da fadin "sai anyi magana ki zauna kina ma mutane kukan munafurci yaya aure zaiyi ba fashi ehe! Ni dai ban musu magana ba suka kama hanyarsu suka tafi dama ba zuwan Allah da annabi sukayi ba. Bayan sallar isha ya salman ya shigo tunda na ganshi na juyar da kaina saboda wani irin haushinshi danake ji yau na daban ne. Bayan sun gaisa da maman sakina fita tayi ta bamu waje.don haka ya samu damar zama kan gadon kusa da kaina yace"Rumaisa ya sannu ya jikin? Kamar badani yake ba shiru na masa kuma ban juyo ba. Shima shirun yayi tsawon wasu mintuna snn yace " kiyi hkr rumaisa don Allah raina ne ya baci dazun ba wai zarginki nake ba . Yana ffadin haka ya juyo da kaina a hankali yana kallon fuskata nikam rufe idona nayi don ko ganinsa banson yi. A hankali yace" pls say something baby Shiru na masa still.ya sauke numfashi yace " baby bana son kiyi fushi dani kiyi hkr kinji don Allah ki bude idonki ki min magana pls ba don halina ba. Sai lokacin na bude idona ba tare da na kalleshi ba nace" ni ka rabu dani kawai inji da abinda yake damuna yaya tunda nayi aure zuciyata bai huta ba kullum a cikin matsala nike yaushe ni zan sami farin ciki a rayuwata ? A tunani na koda duk duniya zasu zargeni kai bazaka zargeni ba yaya amma sai gashi lokaci guda ka juya kamar baka sanni ba yanzu dubi halinda ka jefani a ciki ? Snn ga gorin su innah da wanne kuke so naji? Ina kuke son na saka raina? Na fada cikin matsanancin kuka. sassauta murya yayi yayi yace " kiyi hkr rumaisa tabbas nasan kina cikin wani hali amma ki min afuwa ...... Girgiza kai nayi nace" ya isheni haka ni gabadaya yanzu bazan iya wani hkr ba kawai ka rabu dani kaje kayi wani auren ko mahaifiyarka zata sami farin ciki...... What! Ya fada cike da mamaki yace " rumaisa kece kk irin wnn maganganun..... Zuciyata kamar zata fashe nace " nima fa zuciyane a kirjina kamar kowa yaya don haka kawai ni ka rabu dani zama da kai ya isheni gabadaya daga nan asibity gidan mu zan wuce ko zuciyata zata huta. Na karashe maganar da kuka sosai.shiru yayi hankalinsa a tashe ko kadan bazai iya juran kukana ba Rumgumeni yayi a jikinsa yace "haba baby ki daina kukan nan don Allah wlh yana matukar daga min hankali bazaki gane bane . Haka yaci gaba da bani hkr yana rarrashina nidai ban kuma ce masa komai ba ganin nayi shiru ya sashi tunanin na huce don haka ya min sallama ya tafi. Washe gari da aka sallameni nace ni bazan koma gidan ya salman ba gidanmu zan tafi tunda ga gidan ubana na nan a garin nan! Duk juyin duniyan nan ya salman da ya salim da mmn sakina sunyi amna na ki yarda nan da nan ya salman ya kira mama a waya ya gaya mata komai sunjima suna magana snn daga bisani ya shigo ya samemu ya kalkeni yace"shikenan rumaisa mu tafi zan maida ke gidan naku kamar yadda kk zaba. Sanyi naji a raina don haka muka tafi gidan mama a motarsa ya salim kuwa sun tafi da mmn sakina. Muna isa gidan mama na bude motar na fita ko waiwayensa banyi ba na wuce ciki na tadda mama a babban palo tana kwance mai aikinta lami na danne mata kafa. Sallamata kawai ta amsa yayinda ta dauki key ta mika min hade da fadin " ga makullin dakinki . Na karba na wuce ina fadin haka kawai ga gidan ubana a zauna ana wulakantani ai da ba yanzu bane. Na shiga dakin na tarar an share fess an goge koina sai kamshin room fresh dakin keyi gashi ya dauki sanyin ac . Ban tsaya wata wata ba na wuce toilet wanka nayi da ruwa mai dumin gaske har naji dadin jikina na fito daure da towel ya salman na gani zaune bakin gadon da alamun ya gaji da jirana. Yana ganin fitowata ya tashi da sauri ya karaso gabana ya zuban idanunsa masu kwarjini snn yace" baby hukuncinda zaki yanke mana knn ? Ban taba tunanin haka daga gareki ba.amma babu komai idan kin huce zan dawo in dauke ki kinji ki kula da kanki da kyau Allah ya baki lfy. Daga nan ya juya ya fita nabi bayansa da kallo jikina ya mutu sosai hawaye kuwa kamar jira yake nan da nan ya fara zubowa. Na zauna bakin gado naci gaba da kukan. _Fans_ _kuyi_ _manage_ _da_ _wnn_ _page_ _ba_ _yawa_ _saboda_ _rashin_ _chagy_ 🤗🤗🤗🤗🤗🤗 hauly ce🥰👍🏻 [10/9, 10:37 AM] +234 703 558 2498: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡73 **************Su innah ba karamin dadi sukaji ba da na koma gidanmu don haka ta kira salman tace masa" Salman kaifa mijin mace hudune kuma Allah ya baka yadda zakayi dai dai gwargwado.don meye zaka tsaya mace na wainaka ? Wlh bari kaji rumaisa bazata taba abin kirki ba nasha fada maka a baya amma baka yarda ba to yanzu gashinan ka gani.don haka abinda nake so da kai ka nemi wata kawai . Cike da mamaki yace" haba inna ni me zanyi da wani karin aurene yanzu kwata kwata aurenmu baifa yi shekara ba don Allah kima bar wnn maganar ba dadinta nikeji ba. Tace " hmm aure kuwa dolene ka kara domin bazaka zauna ba haihuwa ba duk sa,oinka sun fara tara zuria kai kana zaune ko alama babu.don haka bari kaji salman ko kana so ko baka so aure zaka kara domin ni shatu bazan zuba ido ina gani Amina da 'yarta suyita cutar da kai ba! Ran ya salman yayi mugun baci sosai don haka mikewa yayi ya fita ba tareda yace da ita komai ba. Nidai zuwa yanzu na warware tass har na fara fita.ya salman kuwa kusan kullum sai yazo ya dubani amma bai min batun komawa ba.haka ma mama ko zancen bata taba bani fuska munyi ba.gashi dama wnn cikin nata gabadaya ya maidata wata silent bata son yin magana gabadaya shiru shiru kawai. Ni kuwa tuni na gaji da zaman gidan namu duk da ban rasa komai ba amma kewar ya salman nake sosai sau da yawa ko bacci gagarata yakeyi. Ahmad kuwa tunda mahaifinsa yaga abinda salman ya masa hankalinsa ya tashi matuka yace wlh bazai taba barin salman ba sai dai aka mashi sai da mahaifin salimane ya hanashi hade da yi masa alkawarin zai jawa salman kunne.haka kuwa akayi ya kira ya salman ya tambayeshi meya hadashi da Ahmad ya salman ya fada masa komai .koda mahaifin salima yaji cewa Ahmad ne ya nemi rigima don haka ya baiwa ya salman hkr sosai hade da ce masa zaiyiwa ahmad magana .da haka aka gama wnn case. Salima kam koda taji wnn zancen kuka tayi sosai hade da yiwa Ahmad adduan neman shiriya. Yau bayan ya tashi daga wurin aiki gidan mama yazo ya sameni zaune akan dining ina cin abinci . Kallo daya na mishi na dauke idona don yanda naji a jikina. A hankali nace" yaya sannu da zuwa . Bai zauna ba ya karaso guna yana kallona yace" ya akayi? Nace"babu komai ka zauna in zubo ma abinci. Ya girgiza kai yace " na koshi. Na kalleshi cike da damuwa nace" daga wurin aiki fa kk tunda naga kaki ne a jikinka. Yace " hakane amma tuni da baki nan Aisha ce ta dauki dawainyar kawo min abinci a wurin aiki. Nan da nan naji wani dam! Duk yadda naso in boye kishina abin ya gagara nan da nan na mike fuska daure nace" tunda Aisha ta baka abinci me kuma ya kawo ka guna? Yace"nazo in duba lfyr ki ne my dear. Haushi naji sosai nace" naji sai anjima ka gaida gida. Cike da mamaki yace what korata zakiyi? Kai tsaye nace " to tunda bazaka tafi ba ni bari na tafi. Na wuce fuuu da sauri ya riko hannuna hade da fincikoni na fada kirjinsa ya maida hannunsa duka biyu yarumgumeni sosai kamar zai maidani cikinsa inajin yadda numfashinsa ke fita.nima jikina yayi sanyi sosai na kasa rabuwa da jikinsa lumshe idona nayi. A hankali ya fara magana yace"baby na don Allah kizo mu tafi gida rashinki a kusa dani babban matsalace wlh nayi kewarki don Allah kiji tausayina baby ko kin manta wani irin mutum ne ni?bazan iya jure rashinki a tare dani ba pls ki daure ki manta da komai kizo mu koma gidanmu. Tunda ya fara maganar sai shashshafani yake tayi ganin ya rikice gabadaya ya manta inda muke har tura hannunsa yayi cikin rigana ....... Da sauri nayi karfin halin tureshi nace" don Allah yaya ka bari in kuma mama tazo ta ganmu fa? Ya sake janyoni jikinsa yace"aiko ta gani ba matsala tunda ke matatace halaliyata ko dai ? Ya fada hade da kashe min ido daya Kauda kaina nayi nace" ni dai bana so ka tafi kawai. Na janye jikina daga nashi na wuce dakina biyoni yayi da sauri harda maida kofa yayi ya rufe da key Nan ya fara kokarin cire kakinsa. Zaro ido nayi cike da mamaki nace"yaya don Allah me kk shirin yine wai ka manta ban gidan surukanka ne? Saida ya gama abinda ya keyi snn ya iso kusa dani yace" and so what don gidan surukaina ne hakkina nazo amsa ko shima laifine? Sake baki nayi ina kallon yaya salman . Shikam kamoni yayi ya zuba min manyan idanunsa da suka sauya kala nan da nan saboda jaraba lol! Yace"baby kina son ki jefani wani haline ? Nifa gabadaya 2 weeks da ba kya nan dinnan saura kiris ki jefani cikin mummunan yanayi don haka naga bazan iya hkr ba kawai nazo... Sosai naji tausayinsa amma na danne nace"shikenan kuma sai kazo ka matsamin a gidanmu bana so wlh kar kace zaka taba...... Rumgumeni yayi da sauri yayi kan gado dani muka fada fadon da sauri na fara kokarin kwace kaina ina yaya ni wlh bana so ka barni wai dolene wlh zan maka ihu mama tazo...... Hade baki na yayi da nashi sosai ya shiga sarrsfani yadda yaga dama nan da nan ya rabani da kayan jikina yaja bargo ya rufemu daga nan labarin ya sauya tun ina nonnokewa har naji bazan iya ba ba shiri na shiga tayashi duk mun rikice sai sambatu gabadaya mun tafi wata duniyar ta daban duk mun fita daga hayyacinmu tsawon lokaci muka dauka cikin wnn yanayin ba abinda ke tashi a dakin sai fitar numfashina da nashi. A hankali nikam ido ya raina fata na gaji tilis sai neman kwatan kaina nake yaya kam kamar zugashi nake kara yi a karshe sai da na fara mishi kuka tukun ya rabu dani da sauri ya wuce toilet sai kace gidansa kai namiji ba kunya . Ba jimawa ya fito ya maida kayansa ya matso kusa dani nikam har lokacin ina cikin bargo duk jikina yayi tsami ya sunkuyo yayi kissing bakina hade da shafa kaina yace God bless you dear na gode sosai bari in tafi magriba ta wuce bamu sani ba. Binsa kawai nayi da kallo a raina nace"a sauka lfy. Ya fita da sauri ya kuwa ci sa,a mama bata fito ba don haka palon ba kowa da sauri ya fita. Tunda ya koma gida ya kasa nitsuwa don haka gidansu ya wuce wurin mmn sakina tunda ta ganshi tasan akwai matsala don haka ta tattara hankalinsa gurinshi tace"ya akayi salman? Ya dan sosa kai yace"wlh mama ina cikin damuwa har ysnzu rumaisa taki yarda ta dawo kuma goggo Amina taki cewa komai akai hasalima ko daddyn yola bai san da maganar goggo amina bata sanar dashi ba ni mama bansan me nayiwa goggo amina ba ta sauya min. Mmn sakina tace"ai kaima Salman da naka tun farko nace ma kazo ka gaya wa abbanka wnn maganar kaki sai ma ce mishi kayi rumaisa ta koma gida do tayi jinya ne.ni nasan bazaka iya daurewa ba da tun lokacin ka bi shawarata ka gayawa abba da tuni rumaisa na nan .kuma goggonka Amina ranta ne ya matukar baci da maganganunsu innah ta ya za,ayi rumaisa na cikin halin rashin lfy suje suyita fadan maganganun marasa dadi akanta kaga ai suma basu kyauta ba . Shiru yayi ya rasa me zaice don tsabar bakin ciki da bacin rai wai ko yaushe inna zata daina irin wadan nan abubuwane oho. Ganin yana zaune shiru yasa mmn sakina cewa " yanzu dai ka yi hkr nasanme zanyi zanje in sami abbanku da maganar inshaa Allah rumaisa zata dawo kwantar da hankalinka . Yayi ajiyar zuciya snn yace" yawwa mama na gode sosai. Da haka ya fita ya tafi dakin innah. Koda maman sakina tayi wa abba maganar nan da nan ya kira mama danjin karin bayani anan ta gaya masa komai ya bata hkr nima abba sai da ya kira yayita bani hkr har naji kunya ya kamani don haka da daddare ya salman yaje ya daukoni gabadaya ranar jinsa yaje cikin yanayin nishadi karkuzo kuga yadda ya dinga tarairayata hadi da lallabani Inna kam ba haka suka so ba sai dai ba yanda suka iya da ransu domin abba ya ja mata kunne sosai akan maganata ita da sadiya don haka dole suka sarara min da maganar gorin haihuwa. Ya salman kuwa asibity ya kaini gun kwararrun likitan mata don a duba masa ko akwai wata matsalane da take hana mahaifata rike ciki amma bincike ya nuna lfy lau nike sai dai na lura hankalunsa bai kama ba don cewa yayi in na gama service zamu fita waje a sake dubawa dai. A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah mama ta sauka lfy Allah ya azurta ta da samun twins wani karin farinciki mace da namiji ne sai wanda ya gansu gwanin sha,awa Murna a gun daddy da familyn galadima abin ba,acewa komai don tunda ta haihu aka fara cika gida ga kyaututtuka daga ranar data haihu har kawo ranar suna .mama ta roki daddy da ya sanyawa baby girl din sunan aunty rukayya kuma ta sake cewa a bata babyn tunda ita Allah bai nufa tana cikin jerin masu haihuwa ba.haka kuwa akayi baby girl taci sunan RUKAYYA shikuma boy yaci sunan SULAIMAN wato sunan babansu mama. Kai gaskia aunty rukayya taji dadi sosai sai godiya take tayiwa daddy da mama.bama ita kadai ba duk familyn galadima sunji dadin wnn abin kowa sai kara yabon mama yake. Tasha kyaututtuka kuwa abin ba,acewa komai sai sam barka . Bayan mama ta haihu da wata daya aunty samira ma ta haifo santalelen danta namiji mai kama da daddy kwabo da kwabo aka maida masa sunan marigayi lamido wato IBRAHIM khalil.gaskia gida ya cika da farinciki sosai masha Allah. Nikam ba labarin ciki har yanzu tuni mun gama service dinmu faiza har ta koma ruma ta dawo sai kunga yadda munir yayi wayo yaro mai shiga ran mutane saboda yawan dariyarsa da rashin kiwa.gabadaya ya salman daukeshi yayi ya dawo dashi gurinmu nono kadai ke kaishi gun uwarshi shima ba sosai yake sha ba dama don ya fara cin komai ya salman ya saba mishi don haka yafi sabawa damu akan iyayensa . Inna kuwa tayi tayi da ya salman ya kara aure abin ya gagara don yaki yarda sunyi shige shigensu malamai har sun gaji sam abin ya gagara.gabadaya innah ta kara shiga damuwa gashi kullum ya salman sai ci gaba yake samu a wurin aiki saboda kwazimonsa da jarumtarsa ga jajircewa.haka nan idan mun juya bangaren business sai hamdala abun sai kara bunkusa yake a lokacin muka fita india don a sake duba lfyta amma duk bincike ya nuna kalau nike rabone bai sauko ba don haka muka shafawa kanmu lfy. Saida muka tafi umrah snn muka dawo Nigeria sai kunga wani irin kyau da muka kara da haske hankalinmu ya kwanta sosai yaya ya sake min mota sabuwa dalleliya sai wanda ya gani wayyoni rumaisa dadi kamar zai kasheni irin yadda ya salman yaketa kara ji dani.su innah duk shige shigensu wnn karon babu nasara sam don maimakon haka saima ci gaba da muke samu . Don ya salman tuni ya sayi fili kato a GRA har an fara gini ya salim kuwa a Abuja don yanzu harkokinsa yafi yawa acan.Ruma na yaye munir suka tafi honey moon abinsu don ya salim cewa yayi shi baici amarcinsa yadda ya tsara ba daga aurensu ruma tayi ciki don haka yanzu lokacin cin amarcine don haka suka bar mana munir yana shekara daya da wata biyar sukayi tfyrsu.Allah sarki rayuwa gashi mu Allah bai bamu ba muna so wasu kuma sun samu bai damesu ba. Kasancewar munir a wajanmu ba karamin debe mana kewa yake bama damuwa da rashi haihuwar tunda dai munsan daga Allah ne dan haka muke ci gaba da addua!!!! Hauly ce👍🏻🥰 [10/9, 10:37 AM] +234 703 558 2498: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡74 *********Su Ya salim sai da suka shafe watanni shidda kan suka dawo.gaskia sunsha amarci kam a cewarsu lol.sai mamakin girman munir suke duk da ma muna tura musu hotonsnsa.ya girma sosai gwanin sha,awa gashi da surutu komai ya iya fada ya salim yace sai a shigardashi makaranta. Ya salman yace " hauka knn yaronda bai cika 3 yrs dinba zan kaishi makaranta? Ya salim yace"kaifa mutumin da ne wlh salman. Ya salman yace"naji kuma na yarda yaro dai bazan kaishi school yanzu ba kar kazo min da yahudanci . Dariya mukayi gabadaya.duk yadda suka so su dauki munir yaki yana makale damu . Dole suka hkr ranar munsha hira sosai kamin daga bisani mukayi musu sallama muka koma part dinmu na mika munir gun sa,adatu wacce tuni har tayi bacci sai da na tasheta.snn na tafi na shirya cikin kayan baccina na wuce dakin ya salman shima ya gama shirinsa tsaf har ya kwanta don haka nasa key a kofa snn na kashe wuta mai haske na isa wurinshi ina fadin"yaya mu yaushe zamu tafi namu honey moon din ? Na karasa fada yayinda na kwanto jikinshi. Murmushi yayi ya shafa kaina hade da fadin " sai kin kara zama jaruma kin daina jin tsoron sex ..... Cikin jin kunyar maganarsa nace "yaya ai na daina tuni. Ya dago fuskata hade da fadin "zaki iya yi sau 10 a rana? Zaro ido nayi yayinda kirjina ya shiga bugawa nace"yaya sau ten ? Ya daga min gira hade da kashe min ido daya yace"yess indai zaki jure to zamuje honey moon don karki manta indai muka tafi bamuda aikin komai sai na soyayyah. Sunkuyar da kaina nayi ban kuma cewa komai ba . Dan dariya yayi yace"ya kk yi shiru? Nace" yaya ai mun gama maganar. Yace "kingani ai bazaki iya ba kawai ki bari sai kin zama jaruma sosai. Hade fuska nayi nace"yaya don Allah yanzu ni wai baka ganin kokarina ne? Da sauri yace"ni na isa ince ba kya kokari? Wlh kinayi babyna kina gamsar dani hundred%. Murmushi nayi nace" to mu yaushe zamuje namu honey moon din? Yace "karki damu zamuje ayyukane ya mani yawa kinga yanayin aikinmu sai a slow amma zan duba bayan mun gama gininmu mun kaura sai in fara tsara mana tfyrmu karki damu babyna. Murmushin jin dadi nayi hade da fadin Allah ya nuna mana lokacin Allah kuma ya kara wadata. Yace"ameen my dear. Su Inna kam har yanzu basu hkr ba burinta bai wuce a kullum ta ganni cikin kunci da bakin ciki ba don haka suke neman hanyoyi daban daban da zasu sa ya salman ya kara aure amma abin ya gagara. Hankalinsu bai gama tashi ba saida ya kare gini muka kaura sukaje sukaga gidanmu na GRA . Subhanallah gidan ya hadune to the bastard level!! Lol ni kaina ban taba tunanin haka ya salman ya zuba kudi a gidan nan ba don bai taba yarda ya kaini ba.funitures kawai ya kawo min hotuna na zaba da kayan kitchen. Kowa sai da ya yaba kyan gidan gaskia naji dadi ba kadan ba gabadaya yanzu yayanah arziki yaci uban nada hanyoyin arziki kullum budewa yake daga shi har ya salim Allah ya daukakasu don su sun rigamu gama gininsu a Abuja sun koma kasuwancinsu kuwa da taimakon daddyn su ya salim suka bunkasa suka zama shaharrarru sai sam barka . Gagarumar walima muka shirya ranar kauranmu har faiza dake london sai da suka zo mutanen yola ba,a barsu bayaba duk masoyana sai da suka tayani murna su inna na gefe duk abin nan da akeyi basu ko leko ba har saida aka gama ribibin sabon gida. Munata ramuwar baccin gajian zirga zirga da muka sha. A ranar suka zo da inna da sadiya adda A'i a motar adda A'i ya salman suka kira wai sunzo. Tashina yayi a bacci hade da fadin "baby ki tashi kinyi baki. A raina nace"yau ma ? Mika nayi cikin bargo hade da salati snn na zira kafafuna kasa ya salman tuni ya tashi yayi toilet . Nima binsa nayi tare mukayi wankan muka fito na taimaka masa ya shirya snn shima ya rakani side dina na shirya cikin riga da siket na lace mai shegen tsada daga gani ba sai antabaya ba gashi dinkin yayi matukar kyau yasha kayan ado kuma ya zauna a jikina sosai na zauna na kashe dauri gashi dama nasha kitso da lalle domin gyara na musamman nayiwa jikina na dawowa sabon gida. Ya salman ya kalleni yana murmushi yace" Gaskia baby kinyi kyau what kin ganki kuwa kamar zahra a ciki......... Bai karasa maganarsa ba wayarsa ta kuma ringing yana dubawa yace " muje muje sun gaji da jira. Ya riko hannuna na dan turo baki nace" yaya ai baka karasa yabona ba kuma bamuyi selfie ba. Yace" karki damu zamuyi in mun sallami bakin namu. Nace"su waye sukaxo ne yaya? Yace"su Inna ne. Nan da nan naji wani rass a zuciyata nace" ko da wacce suka zo oho. Can palon kasa muka iskesu suna zaune sadiya na aikin kalle kalle adda A'i kuma na daukar hotuna inna kam shiru ta zauna tana kallonsu ita kadai tasan mai takeji a ranta gameda wnn gida . Muka karasa saukowa fuska sake nace "sannunku da zuwa innah. Ya salman kam fuskarsa ba yabo ba fallasa ya nemi wuri ya zauna yayinda tuni na wuce kitchen na shiga hidimar kawo musu abubuwan motsa baki snacks sai kuma drinks kan kace meye na cika musu gabansu da kayan ciye ciye. Sadiya tuni ta sauko ta fara ci hade da ce mun "ke rumaisa duk wnn dadin kk ci ba dole ki kara kiba ba dubi daga dawowarku gidan nan zuwa ysnzu duk kin cika palo gaskia ki rage ciye ciye da yawa baida amfani kuma ga almubazaranci ...... Wani irin mugun kallo ya salman ya bita dashi ba shiri tayi shiru. Nidai ban kulata ba na fara gaisheda su innah da kyar suka amsa min Adda A'i tace "salman ya gidan naku shiru haka? Ba dadi babban gida irin wnn ba hayaniyan yara sai ku biyu kawai Shiru yayi kamar bada shi take ba inna kuwa ta karba "ina munir din to? Sai lokacin ya amsa mata "sun tafi makaranta da sa,a duka. Inna tace "hmm to meye kake ta wani fuskar shanu tunda ka ganmu ko dai baka son zuwan namune? Kai tsaye yace " ba haka bane innah kawai bansan da wacce kk zo bane . Adda A'i tace "au haka ma zaka fada salman ? Ko kunya bakaji ba? Inna tace" hmm ai karma ki bata bakinki A'i barni dashi kawai. Snn tace" Salman bari kaji har yanzu ina kan bakana auren nan ko baka so zaka kara domin ba yanda za,ayi ka gina wnn makeken gida snn ace ka zauna da mace daya kuma ma ba yaro . Adda A'i tace "wnn hakkun ne . Ya salman takaici kamar zai kasheshi yace "don Allah inna ki bar wnn maganar ni banida ra,ayin mace biyu na fada miki tun da dadewa don Allah ki bar matsa min . Adda A'i tace " salman ai ko bakada ra,ayin mata biyu yanzu ya zama dole ka kara ko dan ka samu haihuwa domin bazaiyiwu ka zauna babu da ba salman maganan da muke maka tuntuni amma kaki ka gane.munsan matsalarka baka son ka kuntatawa rumaisa ne amma gaskia fisabilillahi yanzu kam ko ita ma ya dace ta baka shawara ka kara aure tunda ita ba mai haihuwa bace...... Daga mata hannu yayi yace " ya isa adda don Allah wai ke meyasa kk son shiga cikin tsabgar da ba naki ba? ni don Allah don Annabi ku daina matsa ma rayuwata ku bar zuciyata ta huta auren nan da kk cewa nayi ince dai sai inaso....... Inna kam fashewa tayi da kuka tana cewa " shikenan salman haka ma zaka ce wato ka nuna min ban isa da kai ba ko? Adda A'i ta watso min harara hade da cewa inna "goggo ba fa laifin salman zaki gani ba ga nan munafukar da take juya mikishi sai abinda taso yakeyi . Inna cikin muryar kuka tace"hakane A'i maganar ki gaskiane. Inna ta kalleni ni kam gabadaya a tsorace nake tunda suka zo nasan zuwan nasu babu alkhairi ciki dama. Tace "Rumaisa don Allah don Annabi na rokeki dan iyayanki ki rabu da salman yayi aure domin kinfi karfina a yanzu dole na biki a hankali ki duba fa yanzhu aurenku shekara hudu knn amma shiru tun barinda kk yi sau uku a shekariun baya baki kuma ba don Allah ki yiwa salman adalci ki barshi ya kara aure. Hmm tabdi yau akeyinta hankalina duk ya tashi tuni hawaye ya fara saukowa.inajin inna haka taci gaba da rokona tana hada ni Allah da Annabinsa. Na share hawayena nace" innah ni fa ban taba hana yaya ya kara aure ba ku daina ganin laifina .in ma hakan kuke tunani to shikenan na amince masa ya auri koda mata ukune ni banida matsala da wnn tunda ko wacce da halinta zata zauna .idan kuma zamana dashine baku so sai in tafi kawai.... Na karasa fada cikin fashewa da kuka mai tsanani na mike da sauri na haura stairs . Ya salman ya mike shima gabadaya hankali tashe ya kalli su inna yace" inna bakin gani ba rumaisa tun tana hkr daku har ta fara maida muku martani irin wnn ranar nake gudu dama yanzu meye amfanin hakan to? Aurene nace miki bazan kara ba bana so ki rabu dani mana! Gabadaya sake baki sukayi suna masa kallon mamaki inna kam ba sai ta kara rushewa da kuka ba ta mike hade da fadin haka kace tou shikenan sai ka zaba koni ko rumaisa! Tace A'i ku tashi mu tafi. Tayi gaba sadiya na biye da ita adda A'i kuwa tsayawa tayi tace " wlh salman kaji tsoron fushin uwa don ba karamin abu bane. Da haka suka fita jikinsu babu kwari. Ni dai ina daki ina ta rusar kuka kamar an aiko min da sakon mutuwa ji nake zuciyata kamar zata fashe. Musamman ma da yaya ya shigo yana bani hkr. Nace"don Allah yaya ka daina bani hkr duk abubuwan nan kai kake ja min wlh. Da sauri yace "haba baby ni kuma ne na miki ? Nace "yaya tun yaushe inna take matsa maka da maganar karin auren nan nace ma kayi! kayi !! Kayi kawai ni ba ruwana idan madihan suke so ka aureta in ma sa,an suke so duk dai na amince nikam ko dukansu biyu ma ni kawai kayi auren ko na huta da zagi da gorin haihuwa da suke min alhalin ni bani na dorawa kaina ba. Na karasa fada da tsananin kuka Ya salman ya lura raina ba karamin baci yayi ba don haka ya sassauta murya sosai ya jawoni jikinsa yana aikin bani hkr. Yace"baby bana son ganin bacin ranki ko kadan kiyi hkr don Allah zanje nayi magana da abbana yayi wa inna magana kinji ?sorry my dear kwanan nan ma naso mu fita honey moon dinmu sai dai wani aiki ya taso mana na gaggawa don haka na biya miki kujerar hajj insha Allah kuma zakije sai ki mana addua sosai. Duk da kuka nake bai hanani jin dadi ba kuma nace" nagode yaya da kokarinka na ganin ka faranta min duk da har yanzu ni na kasa baka farin ciki a gidanka...... Shiiiiiiiii.yasa hannunsa a bakina yace " kar ki kuma fadin haka rumaisa haihuwa nufin Allah ne in Allah ya yarda muma zamu samu kawai mui ta addua wata rana sai labari kinji ko my dear. Nace"naji yaya amma ina neman alfarma daya a wajanka. Ya danyi shiru snn yace "ina jinki my dear. Na goge hawayena nace " yaya so nike ka kara aure........ Mikewa yayi da sauri yace " wai bazaki bar wnn maganar ba ko so kk ki batan rai yanda su inna suka mani? Tashinnayi cikin karfin hali nace " yaya matukar nima baka son ganin bacin raina to kayi auran nan ko don farin cikin inna snn nima na samu salama wlh har ga Allah na amince maka hundred %Allah ya bada sa,a. Na fada da murmushi a fuskata . Shiru yayi yana kallona snn ya girgiza kai yace "hmm rumaisa bazaki gane bane....... Na katse shi da fadin"no na gane komai yaya kuma ni ce nan na baka full support na kaje kayi auran nan insha Allah baza a samu matsala ba. Jikinsa a mace ya riko hannayena yace "rumaisa ban taba ganin matarda ta baiwa minjinta goyan baya ya mata kishiya ba don haka ko kadan bazan so abinda zai bata miki ba ..... Nan da nan na bata rai nace" ni kuma wlh zagi da gorin nan tafi min kishiya zafi a halinda ake ciki yanzu karin auren nan yafi min komai muhimmanci da kwanciyar hankali a rayuwata. Girgiza kai yayi yace"ba gaskia bane rumaisah. Sa hannu nayi a bakinsa nace " ko kafi son in zaba maka mata da kaina ne? Shiru yayi yana kallona nayi murmushin karfin hali nace "nima na zaba maka sa,adatun domin nafi gamsuwa da tarbiyanta akan madiha..... What!!! Ya fada cike da mamaki snn yace "rumaisa kinfa yi serious da wnn maganar !! Nace " kwarai kuwa so nake in tsiratar damu daga bakin innah ko kafi son kullum ta dinga bata rai a kanmu ne? Shiru yayi bai kuma cewa komai ba. Na dada rike hannayensa duka biyu ina kallon fuskarsa nace yaya ka amince da zabin da na maka? Da sauri ya zare hannunsa cikin nawa yace " ban amince ba rumaisa ko zanyi aure bazan auri 'yanuwana na kamaru ba sai dai in samo wata can daban tunda kun matsa min amma kuma ku sani musamman ma ke duk abinda ya faru karkiga laifina. Ji nayi kamar na fasa ihu tsabar yadda nake jin kirjina na min wani irin zafi amma hakan na daure na saki murmushi wacce tafi kuka ciwo nace "insha Allah ma babu abinda zai faru yayana lfy lau zamu zauna da duk wacca ka auro. Gyada kai yayi yace " shikenan amma dai na baki lokaci ki kara tunani in har kin canza ra,ayinki ina maraba dake!!!! Yana gama fadin haka yasa kai ya fita rai bace! Hauly ce🥰👍🏻 [10/9, 10:37 AM] +234 703 558 2498: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡75 *************Inna fushi takeyi da ya salman tun ranar da abin nan ya faru ko yaje bata kulashi haka ma bata amsa gaisuwarshi.gabadaya ya damu uwa uba ga matsina nima.don haka dole kawai ya yanke shawarar kara auren. Ya sami inna yau ma kamar kullum sai faman daddaure masa fuska take taki ta amsa gaisuwarsa cikin damuwa yace" innah don Allah fushin nan ya isa haka kiyi hkr indai maganar can ne na amince zan kara auren shikenan? Nan da nan fara,a ya bayyana a fuskar inna tace"haba ko kaifa yanzu naji sanyi a raina salman Allah ya maka albarka. Fuskarsa babu fara,a yace" amin inna sai dai nima ina da nawa maganar. Cikeda fara,a innah tace " fadi ko menene salman. Ya numfasa yace"inna ni zan nemo matata da kaina banso a zabo min snn ni bana son don Allah ki kuma min maganar madiha da sa,a . Inna ta yamutsa fuska tace"haba salman karfa ka manta madiha ko sa,a su sukafi dacewa da kai yakamata ka zabi daya daga cikinsu.in banda abinka ma meye illarsu? Yace"innah ni sa,a na dauketa kamar 'yata ce burina bai wuce taci gaba da karatunta ba har ta samo miji na mata aure kuma hakan mukayi da mahaifinta ta yaya zan danka sa,a amana a hannun rumaisa kuma ta riketa fisabilillah snn in juya in aureta? Inna ta tabe baki hade da fadin" har yanzu banji ka kawo aya da hadisi ba to naji wnn madihan fa? Ya salman yace"Madiha kuma kinsanta bata da mutunci ke kanki ba raga miki take ba snn tana nan da yawonta na iskanci don har yanzu suna tare da hassan abokina taki rabuwa dashi a halinda ake ciki ma zaman kanta take a lagos ko addan bata baki labari ba? Inna ta danyi shiru snn daga bisani tace" to tunda dai ka daddage ba komai Allah ya baka mace ta gari amma fa ka sani bana son auren ya wuce nanda watanni biyu idan har ya wuce hakan dole ne ka dawo ka auri daya daga cikin yaran nan ko kuma ka gamu da fushina ka daiji na fada maka . Yace "eh naji inna ki dai sani a addua . Tace"babu komai Allah sa a dace .amma haka kurum kayita zama da mata daya ba haihuwa sai dai aci abinci a cika masai da kashi ina dalili? Har cikin ransa yake jin zafin maganarta amma hkr ya zame masa dole don su rabu lfy tunda uwace. Ni dai gani nan maganar auren ya salman ya fara shiga jikina har na dan fara ramewa.gashi haka kawai sai inji jiri na dibana. Sa,a nace tazo ta gwadan bp don dama fannin aikin asibity take karantawa kuma ta mayi nitsa yanzu. Bayan ta gwada ta dago ta kalleni tace"aunty gaskia ki rage yawan damuwa jininki ya dan hau dubi duk fuskarki ya dan soma dan kumburi ma fa . Murmushin karfin hali nayi taci gaba da fadin "aunty kinga tunda yaya yace miki ki sake tunani to ki koma kice masa kawai kar ya kara aure. Dariya nayi nace" hmm sa,a knn har yaushe ?ai gara yayi auren kona huta matsalata dayace bansan wacce zai kawo min gashi kinki ki bani goyon baya sa,a kuma kece na gamsu da hankakinki dari bisa dari. Nan da nan yanayin fuskarta ya sauya tace"aunty ya salman nakine ke daya bana son ya miki wata kishiya bare ni wlh bazan iya ba.saboda duk garin nan banda kowa dama su inna ne kuma kingani tunda na fara goyon bayan gaskia suka tsaneni don kinga da suke cewa yaya ya aureni ma bafa don suna sona bane kawai suna so ne su kuntata miki.ni kuma abinda nake dubawa idan na auri yaya wani abu ya hadamu watarana wa zan kaiwa kukana? Ta girgiza kai hade da fadin "kinga babu kowa.amma idan na auri wani can daban duk abinda ya faru zan zo gurinki keda yaya in fada muku saboda kune madadin iyayena a garin nan.don haka ni gaskia in ma kin dage yaya ya kara aure ki cireni a lissafi ni bana son jin maganar ma . Nace"shikenan ai sa,a. Muna cikin haka ya salman ya shigo tare da munir . Cikin karfin hali na saki fara,a yayinda nake kallon munir nace oyoyo good boy zo ka gaya min ina kukaje da daddy. Da sauri yazo ya rumgumeni yace"momy munje gurin aunty ne. Dam!naji kirjina ya buga na dago da sauri na kalli ya salman murmushi ya min nima haka na daure na maida masa hade da fadin"yaya sannuku da dawowa. Sa,a kam fita tayi ta barmu ya karaso kusa dani ya zauna hade da fadin "ya na ganki kamar mara lfy ne ? Girgiza kai nayi nace"ni lfyta qalau dama hirarmu muke da sa,a .muje kuci abinci. Ya kalli munir snn yace "good boy jeka gun aunty sa,a zanyi magana da momynka Munir ya tashi da sauri hade da fadin to daddy. Ya fita da sauri ya salman ya matso kusa dani ya riko hannayena yace"baby pls ki rage damuwan nan dama nasan abin nan is not easy amma kin dage sai anyi ni yanzu gashi kun takurani kuma kin takura kanki dole ne yanzu sai na nemo matar da zan aura wacce bazata takura maki ba. Murmushi nayi nace "babu komai yaya Allah ya shige mana gaba kar kaji komai muje kaci abinci. Haka na dinga daurewa ina nunan masa ba wata matsala. Kasancewar yana yawan zama a S&S shopping mall dinsu yanzu don tunda ya salim ya koma Abuja komai a hannunsa yake shida hakim kaninsu ya salim wanda daga faiza sai shi don haka kowani dare yana can sai kusan 09:30 yake dawowa . Don haka anan nefa Allah ya hadashi da wata wacce ya lura tana yawan zuwa sayayya a wurin har ta saba da kowa hakim kam har wasa sukeyi snn ta saba da munir ma tana son maganarshi shima haka in ya ganta da sauri zaije ya rumgumeta . Sai dai sam shi ya salman bai taba bata fuska har ta gaishe shi ba duk da a yanzu yana lura da duk wani movement dinta . Yau ma kamar ko wani sati ta shigo cikin kwalliyarta mai jan hankali kamar kullum fuska sake tafara gaisawa da kowa snn ta kalli hakim tace "bros yau ina my boy? Hakim yace"au bai fada miki zaije Abuja hutu ba ai tun jiya ya tafi. Tace"kuma bai fada min ba Allah sarki my boy zanyi missing dinshi wlh. Hakim yace"to ki bishi man kawai. Harararsa tayi da wasa tace" banida lokacinka yanzu bari in fito tukun na. Dariya yayi yace" ina nan jiranki . Ta shige ciki. Shikam sai lokacin ya dan bita da kallo snn yace da hakim"wai wnn wacece mai shegen surutun tsiya? Hakim yayi dariya hade da fadin"hmm *SALMAH* ce yaya yar gidan ambassador isah basuda nitsa sosai da nan. Ya salman yace"ok . Daga nan ya danyi shiru ya fara tunani a kanta ko dai ya gwada sa,arsa ne? Tashi yayi ya kalli hakim snn yace"daga yau in tazo ko siyyayyan nawa tayi kar a karbi kudinta . Cike da mamaki hakim ya bi ya salman da kallo snn yace"ok ba damuwa. Daga nan ya fita . Zama yayi a cikin motarsa yana jiran fitowarta tsawon awa biyu har ya gaji yana shirin tfy sai gata ta fito an rakota da kaya niki niki an sassaka mata a bud Ta shirin shiga motar ta ya karaso gunta hade da yi mata sallama juyowa tayi cike da mamakin ganin mai mata magana. Ta amsa sallamarsa hade da fadin lfy? Kauda kai yayi daga kallonta snn yace"lfy lau idan bazaki damu ba ina son yin magana dake. Ba tare da ta damu ba tace"banda lokacin yin wata magana saboda sauri nake dare nayi ko dai agogonka baya aiki ne.? Shiru yayi bai kuma ce mata komai ba . Don haka ta juya da nufin shiga motarta har ta bude kofa yace"ysushene kk da lokaci sai inzo mu tattauna ....... Ta katseshi da fadin ya salam! Ni malam bana bukatar wani saina tattauna da kai please excuse me! Ta shige motarta da sauri. Ya dan ja baya kadan ba tare da ya damu ba don yasan jan ajine kawai na kankanin lokaci .yana ganinta taja motarta ta fice daga harabar wurin murmushi yayi a zuciyarsa yana cewa "in ba kaddara ba me zanyi da ke ni da nake da tauraruwa a gida . Da sauri ya shige notarsa ya dawo gida ya sameni duk na gaji da jiransa bacci nakeji sosai tun dazu. Ban tambayeshi dsga ina yake ba don zuciyana yana bani daga wurin wata kawai ya fito don haka na shareshi. A haka ya salman yaci gaba da nacewa Salmah har ya shawo kanta ta amince masa ya turo iyayensa saidai salmah bazawarace ta taba aure sun rabu da mijin har tanada yarinya . Saida suka gama shiryawa ya gaya min a fili na tayashi murna amma a zuciyata na kasa hkr haka na dinga kuka damuwanda nake ciki ya karu musamman daya tura magabatansa an tsaida lokacin biki nan da sati biyu.su mama ne suka kai kayan lefe .tabdi ashe haka mata keji in za,a musu kishiya? Wlh duk dauriyana mutum yana ganina sau daya zai fahimceni.sa,ana daya za,ai bikin bana nan ina saudiya don lokacin tfyrmu ta kusa. Ya salman sosai yake lallabani ko kadan baya son yaga bacin raina don haka na sawa zuciyata dangana ina danne zuciyata da addua. Ayi hkr fans page din yau bayawa saboda rashin wuta ayi manage🤗🤗🤗🤗🤗🥰 Hauly ce🥰👍🏻 [10/9, 10:37 AM] +234 703 558 2498: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡76 ************Tuni 'yanuwan inna sun cika gida an fara hidimar biki. Adda A'i kam a gidana ma ta sauka a cewarta bata iya kwanciya daki cike da mutane kuma ba A.C. Don haka sadiya ma kullum tana nan duk idanunsu na kaina ni kuma na danne zuciyata ban bari sun fahimceni ba. Suna ta hidimar bikinsu ni kuma ina ta zirga zirgan tfyta kasa mai tsarki don har naje yola ma na sallami su daddy saboda na kwan biyu banje tun auren ya samir gashi aunty samira har ta kuma haihuwan da namiji.daga yola ne na dawo Abuja kwanana biyu a gidan ya salim naje gidan kawu kasim da goggo Ummi ina shirin dawowa kano munir wai sai dai ya bini. Na ce"good boy kayi hkr ka karasa hutunka kaji babana yanzu in mun koma kano bazaka ji dadi ba kaga aunty sa,a na fama da school . Yace"momy zan zauna da daddyna ne. Nayi murmushi nace"daddynka kwanan nan duka he is busy ka dai yi hkr ka kara one week sai hakim yaxo ya daukeka ko dai mamee na dukanka ne ? Daga min kai yayi hade da sa min kuka daukarshi nayi na kalli ruma nace"wato abinda kk masa knn koh? Bayan kamin a kawoshi kina ji daddynshi na kara jadda da muku don Allah ko kallon banza kar ku masa tunda ku ba kwason yara a gidanku! Tayi dariya snn tace " wayace miki muna hutawa ne tukun.kuma kinga wnn dan naku ba sosai yake jin magana ba shiyasa nake zaneshi kadan kadan. Haushi naji sosai a raina nace"to Allah ya yaye muku .yanzu ki tashi ki hado min kayanshi zan kaishi gidan mama duk da ana hidimar biki nasan zata kula dashi tunda ga uncle dinsa hakim ma.ke kuma da mijinki saikuyita zama ku biyu din kamar mayu Allah ya shiryeku. "da akayi me? Ya salim ne ya shigo ashe yana jina. Na dan turo baki nace"haba yaya dan hutun nan da good boy yazo shine dubi har ya rame. Murmushi yayi yace" saboda bai cin tuwo ne kinsan mu bama cin tuwo saboda nauyi munfison abinci marasa nauyi ku kuma gidanku tuwo kukeci so ya saba da tuwo nan kuma babu shiyasa ya rame. Tabe baki nayi nace "turawa ba.to nidai gaskia zan tafi dashi bazan barshi ya karasa satin ba tunda na lura ya takuraku ku ba kwason yara . Yace"inji wa ? Don Allah karkije ki hadani da salman yazo ya kama min bala,i dama yana cike dani kwanan nan. Na kwantar da murya nace"to don Allah yaya salim ku daina family planning din ya isa ka duba fa good boy yana neman 5 yrs yanzu. Yace" ke fa tuntuni bamayi dama inplan ne aka saka mata kuma mun cire tun last year rabon ne baizo ba don haka in kinje hajj muma kisa mu a addua. Daga nan yace "in kun gama shiryawa kizo mu wuce oganki duk sai damuna yake a waya wai bayaso ki kara kwana Abuja. Yana gama fadin hakan yafita na kalli ruma nace" kingani ko Allah ya baku haihuwa kun kama kuna wani family planing yanzu gashi tunda kk bari shiru . Jikinta a mace tace" ke dai bari ihsan duk na shiga damuwa wlh gani nake shima kamar za,a zuga shi ya kara auren. Nace"ba wanda zai zugashi ku dai dage da addua kawai. Daga nan ta karasa parking kayan munir ta rakamu mota daga nan tace " to ihasan Allah ya kaddara saduwar alkhairi ki mana addua baki daya. Nace"insha Allah! Daga nan muka kamo hanya ya salman sai damuna yake da kira na rasa me zanje in masa a gidan. Koda muka shiga kano ma gidan mama muka wuce don bana son munir ya koma gidanmu har sai an gama ribibin biki don gudun kar su sadiya suyita hantararsa nasan halinta ba son yaran mutane take ba kamar ba uwa ba. Bayan mun huta mama ta ce muci abinci ta gama shirya dining don haka mukaci abinci ya salim yace"mu tafi ba oganki ya matsa min. Na dan yamutsa fuska nace"don Allah ya salim ka rabubdashi in ya matsu yazo ya sameni anan ni bana komawa gida yanzu sai da daddare bana son fitinarsu adda A'i. Ya salim yace"yaushe sukazo? Nace"tabdi ai tuni sun jima anan don tsabar zumudi kuma don wulakanci su rasa inda zasu zauna sai gidana. Ya salim yace"ai laifin salman ne da ya barsu a tsohon gidanmu ai part dinku na da ai zai ishesu duka. Dariya nayi nace"hmm wlh don baka je gida kaga uban gayyan da inna tayi bane ni wlh na dauka duk yan uwanta na camaroo sunzo don gabdaya sun cika part din mama na da snn sun cika gidanmu da kk magana.section din kawu ma ba don momy zasu zo bikin ba da an bude musu . Shima dariya yayi yace"da kyau ashe bikin zaiyi arnashi . Nace'a sosai ma Allah dai ya tabbatar da alkhairi. Yace"amin ke kuma saiki kara hkr tunda kin fahimcesu wani abi duk sunayi ne don su kuntata maki. Nace"wlh babu komai yaya inda sabo ai na saba yanzu. Da haka yayi mana sallama ya tafi mama kuwa tana can da su Amira da khalil ga munir ma don haka ta biye musu suna ta mata shirme. Na samesu a dakin nace"mama ya salim yace a sallameki ya wuce sai ko gobe zaizo. Tace"to ke me ya hana ki bish? Nace"ya salman nake jira kamin nan zan dan kwanta na huta don Allah kar amira suzo su dameni. Tace "to munji uwar son hutu. Dariya nayi snn nace"aunty rukaiya wai tayi missing din yaranta su koma don Allah. Mama tace"hmm ai nima fitinarsu ta isheni daddynku yace in yazo daurin auren nan zai koma dasu ai karta damu. Tabe baki nayi nace"wai harda su daddy a zuwa daurin auren fisabilillahi? Mama ta watso min harara tace"to ya son ranki? Ko shima din so kk ya tayaki kishi? Shiru nayi na sshafawa kaina lfy na wuce dakina wanka nayi na dan shirya jikina nasha maganina snn na kara powern Ac na haye gado na kwanta nan da nan bacci yayi awon gaba dani A cikin baccin na dinga jin kamar ana shashsha fani da kyar na iya bude idona na kalleshi murmushi ya sakar min . Limshe idona nayi na dada shigewa jikinshi nace"yaya yaushe kazo? Yace"bai jima ba. Ya cigaba da shashshafani snn yace "sai jiranki nake tun dazu ashe ke kina nan kinata baccinki. Nace "wlh yaya na gaji sosai ne shiyasa na sauka gidan mama don in huta kadan. Yace"to yanzu tashi zakiyi ki dauki hijabinki mu tafi gida akwai important issue da nike so muyi discussing...... Na katse shi da fadin" anan ne zamufi samun freedom mu tattauna ai yaya ko ka manta su adda A'i suna gida baza su taba bari ni da kai mu kebe ba? Yace"sun isa su hanamu kebewa? Nace"to ai gani nayi motsi kadan sai suyita kiranka a waya in muna tare duk da ma na amince za,ayi auren. Na karasa fada ina tura baki yace"ki rabu dasu tashi mu tafi don Allah baby na matsu fa... Nace"kai yaya ni dai ban yarda wani tattaunawa zamuyi kawai dai ka ce.... Sa hannunsa yayi a baki yace"keep quite ! Tashi kawai mu tafi . Na tashi na dauki jakata da hijabina muka je muka sallami mama daga nan muka tafi gida. A main palour muka same adda A'i da sadiya da wasu sun baje da yaransu suna abinda sukaga dama. Tunda muka shigo suke ta kallonmu gashi sunga ya salman na rikeda jakata. Ganin basuda niyyar yin magana yasani fadin"sannunku da hutawa. Na zauna muka fara gaisawa ya salman tuni ya haura sama bai ko kulasu ba. Adda A'i tace "rumaisa yanzu saura kwana hudune daurin auren nan amma ke na lura ba wasu shirye shirye da kk yi ko 'yanuwanki da kawayenki ma baki gayyacesu ba me yasa? Murmushi nayi nace Adda ai ni bana nan yana iya kasancewa kafin a daura aure ma na wuce saudi yau nefa kadai nakeda lokaci fa to in nayi gayyan da wa zasu zauna ? Sadiya tace "hmmm ke dai fadi gaskia ko dai kishine? Ai ba haka akeyi ba dannewa zakiyi . Nace"hmm ba damuwa ke dai in ma shi din ne.dama ni bukatata inga hankalinku ya kwanta tunda na lura yanzu hankalin naku ya kwanta ai shikenan Allah ya tabbatarda alkhairi. Amin suka fada yayinda na tashi na wuce can side din ya salman na tafi ina shiga dakinsa naji an rumgumoni ta baya nace"wayyo yaya ka tsorata ni. Yace" kefa na lura bakisan halinda na shiga bane a dan kwanakin nan da ba kya nan shiyasa kk ta ja min aji. Nace"kai fa yaya ango ne amarya za,a kawo maka dal a leda. Dada matseni yayi a jikinsa yace"inji waye ?ba dal a leda bace kece dal a leda shiyasa ban gsjia dake. Lumshe ido nayi inajin yadda yake ta faman yamutsani nace"kai yaya amarya fa amaryace dadinta daban ne. Bai kuma yin magana ba kawai ya shiga kissing dina ko ta ina yana sauke numfashi da kyar ya fara magana cikin kasalallliyar murya"I'm going to miss you baby don Allah na yau daya ki barni na more. Yayi cak dani zuwa kan gado ya shiga juyani son ransa nima na biye masa muka shiga faranta ma juna rai har mun so mu makara da sallar magrib da kyar ya daure ya sakeni ya wuce toilet nikam ina kwance jikina duk ya gama mutuwa. Wayarsa na gani yana haske kasancewar yasashi a silent ina duvawa naga sunan *SALMAH*! har naji kirjina ya buga don haka na mayar na ajiye yana fita ma ban gaya masa ba har yasa jallabiyarsa a gurguje ya tafi masallaci ya bar wayan. Bayan na idar da sallar magriba na fita palo har lokacin su sadiya na nan ko sun yi sallahne oho nidai kitchen na wuce ina tunanin me zan dafa simple da zamuci kawai na yanke shawarar dafa macaroni da dankali haka kuwa nayi nasa hanta na hada kayan kamshi nan da nan kamshi ya gauraye koina sai ga sadiya ta shigo tana cewa"uwar gida me kk dafa mana ?kamar kuwa kinsan yunwa mukeji don yau ba,a kawo mana abinci daga gida sun san kin dawo dama da ba kyanan innah take turo mana wasu lokutan adda A'i ta tura driver dinta ysje ya siyo mana gasassun kaji muci da drinks. Kamar bazanyi magana ba na daga baya nace"hmm kema a gidan nan kk kwana knn? Tace"eh kinsan mune kirjin biki. Nace"gaskia kam Allah ya taimaka . Tace "amin ta fita" na bita da kallon mamaki lallai mijin sadiya ya shiga hannu sosai a yanda nasan jafar da wlh bazai taba barin sadiya tayi duk abinda taga dama ba Allah dai ya kyauta . Na gama gikina knn na dauko fruit na fara yankawa sa,adatu ta shigo murmushi nayi nace"sai yanzu? Tace"hmm bari kawai aunty tailor dinnan yana wainamu nida zainab yau kusan yini mukayi muna zaune a shago da kyar ya hada mana kayan da zamusa jibi . Murmushi nayi nace"au haka fa jibine sisters daya ko? Tace"A wlh aunty naso kina nan kiga rawar su adda A'i kici dariya har cikinki yy ciwo wlh adda A'i bata iya rawa ba saboda tsabar kiba amma ta dage sai anyi har da dinner ma. Dariya nayi nace"wlh bakida mutunci sa,a to kidaiyi a hankali kar ta jiyo mu tazo ta balbalemu . Tace "wlh kuwa dama yanzu ma da zan shigo sai faman hararata take.yaya ne ma yace in kirawo ki kawo fruit din na karasa ysnka miki . Anan na bar mata komai na wanke hannuna na dauki kulan abinci na fita a palo nace "sadiya na gama sa,a zata kawo muku . Sadiya tace"to uwar gida ran gida. Na wuce banyi magana ba. Ina zuwa na sami ya salman yana waya da alama da amaryar yake waya don haka nai sallar isha kafin na idar ya gama waya . Don haka koda na idar dining muka wuce don cin abinci sa,a ta kawo mana fruits ko da ya lura na kasa cin abinci don haka ya daddage ya dinga bani a baki har saida na koshi yace"yawwa baby ko ke fa. Nace hmm yaya ka daina kirana da babyn nan kar amaryarka ta rainani ta dauka babynce. Dan dariya yayi yace"babyn ce mana tunda bata wuce a bata abinci a baki ba . Bayan munyi wanka muka sake komawa duty aikin knn ranar ko baccin kirki ya salman ya hana muyi sai na dan fara bacci ya sake lalubata har asuba duk nayi tsami wlh.a cewarsa na bankwana ne. Haka kuwa akayi washe gari na gama komai a ranar jirginmu ya daga ina cike da kewar ya salman. Tunda na sauka kasa mai tsarki gabadaya na manta da dukkan damuwa na shiga ibada sosai yayinda nake kaiwa Allah kukana musamman akan maganar haihuwan nan . A kano kuwa ana nan sai shan biki akeyi duk da ma su inna sunso ace ina nan don su cusan bakin ciki amma Allah bai nufa ba.amma mama kam tasha bakar magana gun innah sai dai sam bata kulata ba har amarya salmah ta tare . Ya salman bai wani marmarinta ba da farko ko dan bazawarace oho amma a daren amarcinsu yaji dadinta sosai domin tayi mishi tanadi na musamman gashi dama bazawarace ba wsni kunya dagewa tayi sosai don ta birgeshi aikuwa ta rikitqshi da nata salon .A ranar kasa fita yayi suna manne. Gaskia sun sake sunci amarcinsu yadda ya kamata . Sa,adatu kam komawa makaranta tayi yayinda munir har lokacin yana gidan mama .sai da suka yi 2weeks suna cin amarcinsu kafin suka fara fita sunje gidan mama daga nan sai gidansu innah Inna sai washe baki take duk ta rasa inda zata saka su don murna abin ya matukar bawa ya salman mamaki. Su innah har da nasiha tana cewa salmah kar ta dauketa suruka ta dauketa kamar uwa don ita uwace a gareta yayinda ta jawa ya salman kunne akan wlh in ya sake ya batawa salmah rai sai ta saba mishi . Salmah taji dadin yanda aka karbeta a familyn mijinta sosai.sadiya kam bata sati bata je gidan ya salman ba tuni ta kwashe labarina ta gayawa salmah har tana cewa tayi taka tsan tsan dani don ni ba mutumiyar arziki bace hmm duk karyar duniya da sharri ba wacce sadiya bata fada a kaina ba sai da ta tabbatar ta bakantani a gun salmah har ta fara shiri akaina.don a tunaninta in bata mike tsaye ba in na dawo zan iya rabata da mijinta. Ina can kasa mai tsarki ban ma san wace wainar ake toyawa ba nikam ban kuma taba kawo komai a raina ba tunda ya salman na kirana kullum har sau biyu a rana. A haka muka gama ibadarmu lfy lau ba wani matsala yanzu har muna shirin dawowa!!!!!!! Haulyce🥰👍🏻 [10/9, 10:37 AM] +234 703 558 2498: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡77 ***************Tun daga airport haka kawai na tsinci kaina cikin faduwar gaba ko don bansan me zanje in tarar ba a gida. Haka dai na dinga yiwa kowa fara,a Ruma tace"ihsan kinganki kuwa masha Allah kinyi looking fresh wlh.kamar kece ma amaryar Murmushi nayi yayinda nace" hmm na isa? Raihana tace min a hankali "ke kin ma fi amaryar kyau 'yar uwa wlh . Sukayi dariya da sakina nace"Allah ya shiryeku to ni duk banga yayana ba kuma shine ya kamata na fara gani anan? Ruma tace"baya gari yayi tfy bakuyi magana ba koh? Nace"eh na nemi layinsa shiru ma. Raihana tace"kwantar da hankalinki zai dawo kuxo mu tafi. A motar ruma muka dawo gida tunda muka shigo nakejin wani iri . Munir ne ya taho da gudu yana momy oyoyo shida sa,a da zainab suka rumgumeni. Daga munir nayi sama duk da girmansa ina dariya nace"oyoyo good boy nayi missing dinka sosai dear. Na sumbaci goshinshi ina murmushi daga nan muka wuce ciki zuwa part dina da su zainab suka gyara min shi fess dama kuma kan na tafi ya salman yace zai sake min funitures har ina ce masa ai komai sabone ya bari kawai.sai gashi na tarar da komai sabbi dal ga kayayyakin sawa an dinka su tirim daga kan atamfa laces material da shadda gaskia naji dadi sosai har naji sanyi a raina. Su ruma kuma sun shishshirya min girki na musamman komai da komai masha Allah. sai zuwa ake yi min barka da dawowa 'yan uwa da abokan arziki amma abin mamaki har lokacin banga matar gidan ba.kuma ban tambaya ba. Ya salman ma ya kirani cike da murna yace"hajia barka da dawowa . Murmushi nayi nace"yawwa yaya duk na kosa na dawo na ganka nayi missing inka sosai yayana. Sautin murmushinsa na jiyo yace"nima babya inata missing dinki aiyukan ne suka mini yawa amma zan dawo karki damu ya gajia to? Na kwantar da murya nace "Alhamdulillah. Yace"Masha Allah saidai fa naji muryartaki bata fita sosai....... Bai rufe bakinsa na fara tari yace"subhanallah baby mura koh? Na dan gyara murya nace"bari kawai yaya ina fama da mura kirjina sai toshewa yake. Na fada yayinda na lalubo inhaler na. Yace"sorry baby Allah ya baki lfy zance salim ya kaiki asibity ko na kira doctor james azo a dubaki. Nace"ba komai yaya sai ka dawo Allah ya kawoka lfy. Yace "ameen ki kula da kanki sosai ina raihana? Nace"gata nan Yace"bata wayar. Na mikawa raihana wayar ta karba fita tayi waje . Ruma tace min "to ki dan kwanta mana ihsan . Sakina tace"ai naga kamar bacci ma kk ji. Murmushi nayi nace" ai bazan iya bacci ba sai zuwa anjima saboda baki da suke zuwa. Raihana ta shigo tana mika mun waya tanacewa don Allah kuji min munafurcin mata? Sakienah tace"wacce? Ta zauna hade da jan tsaki tace"Salmah mana. Ruma tace"wai me? Raihana tace"wai tace ma yaya bamu fada mata dawowar rumaisa ba alhalin tana gidan nan duk wani zirga zirga da muke tana sane tun dazu baki sai zuwa suke ta sani sarai amma kinji wai munki mu sanar da ita ai bama sonta ne bama kula da ita sadiya kadai da innah suke sonta harda wani guntun kukanta. Dariya mukayi sakina tace"yayan ke fada miki hakan? Raihana tace"eh man sai kinji ma uban tsawa da yake min kamar ya fasa wayar ya shigo ya sameni. Sakina tace"lallai yaya ma dai daga an kwashi karya da gaskia an sanar dashi sai ya hau kai ya zauna? Raihana tace"bari kedai naji haushin matan nan sosai yanzu yaya wai muje dake mu sanar da ita kuma mu kawota ta gaida rumaisa. Sakinah tace"tab ni wlh bazanje ba irin kallon banza data ke ma mutane duk sadiya tabi ta bakanta mu a wurinta. Ruma tace"to ya zakuyi hkr kawai zakuyi tunda amaryarkuce.amma dai nima nazo gidan nan tun jiya mun gaisa har na fada mata ihisan zata dawo yau ko ta manta ne? Sakinah tace"iskanci dai kawai. Murmushi nayi nace "don Allah kuje ku sanar da ita kar ku kara laifi ni dai ace daga dawowata har an fara samun matsala. Raihana ta tashi hade da fadin gaskia kam don ba mamaki sadiya taje ta hadamu da inna ma. Sakina ta tashi suka fita.na kalli ruma nace"'yar uwa bani labarin amarya don Allah. Ruma tace"hmmm amarya kam se kinyi taka tsan tsan yar uwa domin sadiya ta rigada ta sanar da ita komai karya da gaskia kuma kinga innah naji da ita don haka dolene kisan irin zaman da zakuyi . Jikina a mace nace"to Allah shi kyauta . Tace"amin hmm. Kusan minti goma da tfyrsu sakinah sai gasu nan duk da amaryar tasu da sadiya . Ba laifi Salmah kyakkyawace doguwa tana da dan haske kuma ta dan fini jiki kadan.taci kwalliyarta cikin shadda riga da skirt tasha daurinn dankwali ta zuba sarkoki se kamshi ke ta faman tashi tunda ta shigo.gashi tasha lalle kuna ganinta kunga amarya. Fuskarta ba yabo ba fallasa ta karaso nikam murmushi nayi mata hade da yi mata sannu da shigowa. Ta zauna kan stool nikam ji nake gabana na faduwa wani irin kishinta nakeji sosai tabdi ashe haka mata keji in an musu kishiya? To sai dai ince Allah ya bamu hkr ya sanyaya zuciyoyinmu. Nan muka fara gaisawa tace"ashe kin dawo ai na dauka sai koh gobe . Murmushi nayi nace "aa yau din ne dama..... Sadiya ta karba "to rumaisa ga amarya aunty salmah nasan yau ne haduwarku ta farko koh? Nace"hakane yau ne . Tace"fatan zaki bata hadin kai domin bata da matsala ko kadan tana da saukin kai kuma tana mutunta kowa don haka pls ki bata hadin kai ku zauna lfy. Murmushi nayi nace"to sadiya naji karkiji komai Allah ya hada kanmu. Raihana tace da sadiya"to da kika gabatar da ita a gun rumaisan ai ita ma kamata yayi ki gabatar da ita gun amaryar ko? in dai duniya da adalci . Bata saurari abinda sadiya zata ce ba ta kalli salmah tace"to ni bari in gabatar miki da rumaisa ko ince uwar gida kan gida kin ganta nan ko kadan bata da matsala hkr ne da ita sosai snn tana da kirki da sanin ya kamata don haka ki zauna da ita lfy . Murmushi tayi tace" babu matsala ai raihana dama suleyman ya fada min komai kuma insha Allah lfy lau zamu zauna Ta kalleni tana murmushi tace"to me za,a dafa miki yanzu zan shiga kitchen dama. Nima murmushi nayi nace"in dai dan nine ki huta wlh ga abinci kam nan mama ta turo min raihana ma ta kawo snn mmn sakina ma ta turo no need se kinyi girki se dei ko naki . Tace" ok dama ke dince zan girkawa.don suleyman ya turo cefane yace a maki girki tun tuni bansan kin dawo ba . Nace "babu komai wlh na gode da kulawarku gareni. Ta mike hade da fadin ba komai bari na danje na kwanta na huta. Nace"to ba laifi a tashi lfy. Ta fita sadiya ta kalli raihana tace"ke kuma munafuka anan zaki kwana ne? Raihana ta daure fuska tace"munafurcin me na maki ? Anan zan kwana sai me kinada matsala ne? Sadiya tace "don me zaki kwana anan yaranki kinje kin zubewa innah tanata faman dawainiya dasu alhalin tana fama da ciwon kafa ke kinzo zaki kwana anan..... Raihana tace"au yarana ne zasu zamewa innah dawainiya ke naki yaran da kk zube mata ba dawainiya bane koh? Tace"to aini yanzu zan tafi kuma can zan biya in daukesu mu koma gida. Raihana tace"se ki hada da su gabadaya ku tafi gidan naki tunda duk yarankine kokuwa? Tsaki sadiya tayi snn ta fita tana cewa "zakuji da munafurcinku ai.ni kunga tfyta. Sakinah tace"ummah ta gaida assha . Tana fita raihana tace " yanzu zataje ta shirya min karya da gaskia gun innah . Rumah tace " ko muma baza mu tsira ba ai. Nace" hmm kema dai raihana tunda kinsan halinta dama baki tanka ba wlh. Haka mukaci gaba da tattauna irin halin sadiya kamin daga bisani na bacci ya yi awon gaba dani na barsu ruma na ta hira . Kwanan su ruma biyu suka koma da sakina raihana ma haka a ranar da suka tafi aunty samira kuma tazo naji dadin zuwan aunty samira sosai musammn ma da ta sauka a gidana ranar kwana mukayi muna hira duk gajian da nayi na daure. Anan ta kawo min tarkacen mu na mata hade da yi min bayani sosai tana ihsan yanzu kam zagewa fa zakiyi sosai fiye da da don yanzu kinga ku biyu ne musamman ma da naga kishiyar taki idanu a tsassayen nan snn kuma kinga dama kince mun bazawara ce don haka ki kula sosai kinji? Nace"Insha Allah aunty. Tace"yanzu yaushe salman din ze dawo? Nace"inaga sai nan da sati mai zuwa. Tace"yawwa to don Allah ki dage ki fara ki fara kintsa kanki indai kinbi yadda na fada miki to fa kema zaki zama amarya zakiga yadda zai dinga nan nan dake. Murmushi nayi nace"to aunty. Snn ta nuna min wasu kayayyakin bacci sunfi kala ashirin tace"zuwanmu dubai da daddynku ne na siyo miki su nasan zaki matukar jan hankalin surukina dasu don wlh se kinga nawa da nasaka nima........ Kunya ne ya dan kamani nace"na gane aunty Dariya tace"to shikenan tunda baki son jin karashen labarin . Haka muka kwana hira washe gari karfe sha daya ta wuce gidan mama bata wani zauna ba ta wuce airport ni kuma ina nan ina ta faman gyare gyaren jikina wanda a cikin kwana uku rak har na fara jin sauyi nima . Amarya kuwa tsakaninmu gaisuwa kawai kowa na harkar gabanshi .sai in sadiya tazo su kule a daki suyi ta gulmarsu Kwanana goma da dawowa ya salman ya dawo unexpected ko waya bai mana ba ina kwance a palon kasa naci kwalliyata mai kayatarwa su sa,a da munir basa nan amarya kuma na kitchen .kawai sai gashi ya shigo muna hada ido bansan lokacinda na yi wani tsalle na tafi na fada jikinshi . Dagani yayi kamar wata baby ya shiga juyawa dani a palon muna dariya sannan ya saukeni kankujera ya zauna shima hade da rumgume sam a jikinsa kamar zai maidani cikinsa yace"baby gaskia nayi matukar farinciki da kk dawo lfy. Ya fada yayinda ya sumbaci goshina nayi murmushi nace"yaya wlh nayi missing dinka sosai. Sha fa gefen fuskata yayi yace"adduan me kk mana baby? Nace" komai ma da muke bukata saida na roka mana yaya musamman adduan samun baby.... Da sauri yace"wow! Naji dadi Allah ya ansa my dear mu sami baby. Ya fada yayinda ya tura hannunsa cikin rigata yana shafa cikna a hankali yana murmushi yace"Allah ya bamu masu albarka. Duk abinnan da mukeyi salmah na ganinmu can dining side a yayinda take shirya dining din gabadaya ganin yadda ya salman ya rikice a kaina take mamaki sam bata taba ganin ya salman na fara,a ba duk tunaninta ta dauka baya dariya amma sai gashi ta gani dariya yake sosai .don haka ji tayi kirjinta na bugawa kamar tazo ta shakoni. Ta dai danne hade da karasowa cikin tfyr daukar hankali tana murmushi tace "amin ya Allah karkuce na sa muku baki a maganar ku. A tare muka juya da ya salman muka kalleta da sauri na bar jikin ya salman shi kuma kallonta yakeyi har lokacin fuska ba yabo ba fallasa yace"salmah Murmushi tayi hade da kwantar da murya tace"na,am honey barka da dawowa .tunda kace min kana hanya na shiga kitchen na hada maka girki na musamman honey na yanxu muje tukun kayi wanka ko dai? Gyada kai yayi snn yace hakaneh thank you so much. Snn ya kalleni yace"hajia bari inzo koh?ki jirani pls Murmushi karfin hali nayi nace "sai kun fito. Tuni salmah ta shige gaba rike da jakarsa shi kuma yana biye da ita a baya.suna haura stairs sai tfy take tana jujjuya mazaunai.haka kawai na fara tunani in sun shiga daki rumgumeta zaiyi yayita nuna mata soyayya su manta dani a palo wayyo zuciya! Nan da nan naji hawaye ya cicciko idona ban iya na daure ba dakina na koma na kulle na fada gado na shiga rera kukan da bansan a wani matsayi zan fassarashi ba!!!!!! Hauly ce🥰👍🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡78 **************Kusan 30minutes snn yaya ya kirani a waya wai in sauko muci abinci nace"to. Na tashi na shiga toilet na wanke fuskata naxo gaban madubi na maida kwalliyata snn na fita na iske su a dining table nima naja kujera na zauna. Salmah ta kalleni da murmushi a fuskarta tace"hajia me za,ayi serving naki? Na danyi shiru ina tunanin me zanci don bana kwadayin komai wlh. Ya salman yace" ki bata pepper soup kawai nasan ba wani cin abinci take so da daddare ba Salmah tace an gama ranka ya dade. Bayan ta gama itama ta gyara zama muka fara ci nikam sai faman jujjuya spoon nake a cikin bowl abincin sam baya shiga. Ya salman ya kalleni cikeda kulawa yace" my dear ya bakicin komai ko ba kya jin dadine? Nace"wlh yaya nayi loosing apatite dina ne bana jin dadin komai . Yace"ko dai muran ne har yanzu? Kina ma shan magungunanki? Nace"eh inasha. Yace"to ki daure ki danci abincin nan ko kadan ne Allah ya baki lfy Nace"ameen. Sai lokacin salmah tace " sannu Allah ya sawwaka. Na danyi murmushi nace"ameen na gode da kulawarku gareni. Bayan mun gama cin abinci ana ya ajiye mu a palo ya fara yi mana magana akan zamantakewa yayi ta mana nasiha masu sanyaya jiki daga karshe yace " don Allah ku zauna lfy karku bari aji kanku ni kuma zan yi kokari yin adalci a tsakaninku . ya kalleni yace"Rumaisa na sanki da hkr dama to ki kara akan wanda kk dashi babu komai ku zauna lfy shine farin cikina da kwanciyar hankalina . Na gyada kai nace"Insha Allah yaya zamuyi duk abinda kk so. Ya kalli salmah yace"kema ina fatan hakan daga gareki salmah ku zauna lfy. Ta kwantar da murya hade da cewa"insha Allah honey lfy lau zamu zauna Allah ya baka ikon yin adalci a tsakaninmu. Yace "ameeni na gode muku da hadin kai da kk bani Allah ya muku albarka.yanzu se maganar raba kwana.inaga kwana bibbiyu ai yayi ko dai? Nan naji gabana na faduwa hmm anxo wajen gaskia idan akwai abinda ke daga min hankali bai wuce inga salmah ta shigan min turakar miji ba sai dai ya zanyi itama mijintane. Maganarsa ce ta dawo dani daga duniyar tunani yace"rumaisa bakice komai ba. Nace"ba komai yaya hakan yayi amma ina bukatar wani alfarma a gunka. Yace" ina jinki my dear. Na danyi shiru snn nace"ina bukatar na huta na wata daya kan mu fara raba kwana. Nan da nan ya sauya fuskarsa yayinda ita kuma salmah ta dan washe baki da alama maganar ya faranta mata rai. Bai amsa min ba kawai dai ce mun yayi muje na rakaki kije ki kwanta. Na tashi muka tafi side dina muna shiga bedroom ya kalleni fuska daure yace"don me zakice a barki se kin huta har na one month kina haukane akan me zan barki har one month bakida lfy ne? Fuska sake nace"haba yaya one month ne fa ba one year ba nide kayi hkr don Allah so nake na huta sosai ne. Ya kamo hannuna duka biyu ya zaunar dani kan bed snn shima ya zauna yana kallona yace"baby kiyi hkr idan akwai wani abu daya bata miki raine.wlh baby bazan iya one month dake a gidan nan ban kusanceki ba.yanzu ma hkr kawai nakeyi don Allah karki min haka . Zare hannuna nayi cikin nashi nace"yaya sai kace ba amaryace da kai ba don Allah ka barni na huta pls pls pls don Allah. Na fada cikin kwantar da murya.aikuwa mikewa yayi cikin bacin rai ya gyada kai ya fita. Nikam binsa nayi naje na rufo kofan side dina gabadaya na dawo na kwanta na kama kuka alhalin ni nayiwa kaina hukunci. Da safe kuwa kamin mu fita muyi break fast ko wacce sai da ta kure gindin akwatinta batun kamshi ba,a magana koda muka hadu a dining wani irin kallo salmah ke min duk jikinta ya mutu don tasan na fita kyau nesa ba kusa ba . Shikam oga ko a jikinsa tunda ya amsa gaisuwata bai kuma ce mun komai ba sai ma daddaure mun fuska da yakeyi.don haka can tsakaninshi da amaryarshi suke dan hira jefi jefi. Ni kuma saida na tabbatar munir ya koshi snn nace "to oya ka tafi kaje ka yi ta tusa karatunka kamin time din islamiyya yayi. Yace"to momy . Yana tfy nima nayi maza na gama cin abincina na tashi hade da fadin "to a huta lfy ! Har nayi nitsa yace"ki shirya zamuje gida yanzu. Na kalleshi kamar bashi yayi maganar ba saboda kwata kwata ba side dina yake kallo ba . Murmushi nayi nace"to dama a shirye nake bari na dauko veil dina da jakata kamin nan kun gama. Ban jira amsa ba don nasan bazan samu ba na wuce kayana. Ina kokarin fita hakim ya shigo muka gaisa yace min"ina munir ya shiryane? Nace"eh ya shirya suna dakin sa,a . Yace"ok bari inje in sameshi mu tafi kar yayi letting . Har ya fita ya sake dawowa yace"yawwa aunty rumaisa yaya yace in kin gama suna jiranki don har suna shirin fita ma. Nace"ok yayinda na tashi da sauri na dauki gyale har zan lulluba sai na tuna zai iya maidani don baison insa gyale da sauri na jawo hijabina da jakata na fita dakin sa,a na leka nace"sa,a bari muje gida don Allah ki kula da gida na bar side dina a bude. Tace"to aunty sai kun dawo. Na fita da sauri na iskesu a harabar gida suna kokarin shiga mota . Tuni salmah ta bude gaba ta Harde. Tabe baki nayi na bude gidan baya na shiga na rufe kofar ina gyara zamana karaf muka hada ido dashi ta cikin madubi murmushi nayi yayinda shikuwa ya dada tamke fuskarsa ya tashi motar muka tafi. Sai gashi mun isa gidan dama ni tunda na dawo ma ban fita koina ba. Wurin abba muka shiga muka gaisheshi anan ya mana nasiha sosai daganan muka fita a tsakar gida muka sami mmn sakina muka gaisheta itama snn muka shiga dakin innah. Gabana sai faduwa yake . Tana bedroom ko da ta jiyo sallamarmu ta fito fuskarta daukeda fara tace" ashe kuna tafe sannunku da zuwa. Muka amsa darduma ta dauko tazo ta shimfida ta kalli salmah tace"zoki zauna anan salmah wnn shimfida nakine ke daya. Snn ta kallemu tace ku zauna ga kujera. Ya salman ya zauna ni kuwa a kasa na zauna gefen kafansa muka gaisheta. Taje ta kawo mana ruwa snn ta zauna salmah tace"inna sadiya bata zo bane yau? Duk na kosa nazo na ganta kwana biyu shiru ko wayarta bai shiga lfy? Inna tace"Allah sarki 'yartace ba lfy wayar kuma wai ta lalace ne itama kwanan nan duk tana ta zancanki har tana cewa gobe zataje. Salmah tace"ayya inna me yake damun amiran? Inna tace"zazzabi ne na maleria kinsan mutumiyar taki da sakaci bata taba maida hankali kan yaran. Salmah tace"subhanallah Allah ya bata lfy . Nima sai lokacin na sa masu baki nace"Allah ya bata lfy Inna tace"amin Shi dai yaya baice uffan ba. Anan innah ta fara "to rumaisah ga salmah nan Allah yayi ita ma matar salman ce don haka ku zauna lfy.kiyi hkr salman ba yayi auran nan don ya muzguna maki bane ko kadan ba haka bane.kinga kuma salmah yarinyar kirkice tasan ya kamata kuma da bawa kowa darajarsa bata rainah kowa don haka bazaki taba samun matsala da ita ba sai fa in kece kika ki ku zauna lfy don na sanki da murdadden hali da rashin hkr don haka nike rokonki don Allah kar ki muzgunawa salmah ku zauna lfy. Hmm innah knn na fada a raina snn a zahiri nace" babu komai innah zanyi duk abinda kk ce snn zan kiyaye mu zauna lfy da salmah. Tace"to dai hakan zaifi . Daga nan ta dawo kan ya salman shima tayita ja mishi kunne har da cewa in ya bari ran salmah ya baci to wlh bazata barmu ba duk sai mun gamu da fishinta. Har ta gama magananta baice komai ba sai daga bisani yace"to za,a kiyaye Ya mike yana shirin fita salmah tace"yawwa don Allah ina son zuwa gidan sadiya. Yace"ba yau ba yanzu gidan goggo Amina zamuje. Inna tace" ka rabu da ita taje inda take so don me zakace sai taje gidan Amina ko ke kk ce zaki je? Salmah tace"aa ni na dauka nan zamu yini ne ma. Inna ta kalli ya salman tace"to ku tafi ku barta ita anan zata zauna in yaso in kungama yawonku kuzo ku dauketa. Bai ce mata komai ba kawai yace" rumaisah ki tashi mu tafi. Nace"to yaya. Na bude jakata na dauko container din sarkan gold da 'yan kunne har da zobensa na ajiye a gaban innah nace"innah ga taki tsarabar .dama yana cikin kayana ne ban duba ba sai jiya. Yatsuna fuska tayi tace"hmm sai yanzu kk ga daman kawo min ? Ai na dauka ma ban kai matsayin ki bani tsaraba ba . Jikina a mace nace"kiyi hkr na fadawa sadiya ta fada miki cewar sarkanki na cikin kayana ban gani bane.watakila ta manta ne. Tace" ba wani nan dama baki yi niyya ba don haka dauki abinki in kinga dama ki baiwa wadda kk so ni tun kan a haifeki nake sanya sarka.kuma gashi kingani ma yanzu a wuyana . Ta fada yayinda ta daga sarkan wuyanta tace" kingani ko gold ne salmah ce diyar albarka ta bani tunda ke ba kya mutuntani.dauki abinki bana so. Nace" innah wnn ma gold ce kuma babbane bayan kaina ke kadai na siyawa gold don Allah ki karba ko baaki sa ba ki..... Ta tabe baki tace" ki barshi kawai na gode !ki tashi ki tafi salman na jiranki. Salmah tace"innah da dai kinyi hkr kin karba kamar yadda tace miki gold ne kuma mai tsada kuma dama kinsan ance ba a maida hannun kyauta baya kiyi hkr ki karba. Harara innah ta watso min hade da fadin"to barshi tunda salmah tasa baki zan karba ba don halinki ba. Hawayenda nake kokarin hana shi zubowa saida ya zubo na goge hade da fadin "na gode. Snn na tashi nayi musu sallama na fita.ashe ya salman bai tafi ba yana tsaye bakin kofa yana jinmu ganin fitowata yasashi wucewa gaba ni kuma na tsaya sallamar mmn sakina. A waje na sami yaya na shiga mota muka fara tfy ba tare da mun ma juna magana ba. Duk yadda naso na daure ya gagara kamin mu isa gidan mama kuka mara sauti nakeyi sosai. Ya salman ya samu gefan hanya inda ba hayaniyar jama,a sosai yayi parking. Ya kalleni hade da fadin" kiyi hkr rumaisah ki daina kukan ya isa haka. Ya mika min tissue na karba yayinda na goge fuskata.tuni har idona ya kumbura yayi canza kala. Jawoni yayi jikinsa ya rumgumeni sosai yace"baby ni kaina bana jin dadin abinda innah take miki kuma ina iya kokarina wurin ganin ta daina amma abun ya faskara kiyi hkr nasan dole ne kiji zafi amma bana son ki dinga kuka yana daga min hankali.ki kara hkr muci gaba da addua insha Allah watarana sai labari kinji? Kai kawai na daga mishi.a hankali ya dago fuskata ya shiga share min hawaye yanacewa "sorry my dear kukan ya isah haka. Yaci gaba da rarrashina haka nan na hkr ba yanda na iya amma gaskia abinda innah ta min yau a gaban salmah ya min ciwo sosai . Ganin na hkr yasa ya tashi motar a hankali ya juya yace"mu bar zuwa gidan goggo aminah sai gobe kawai don bana son ta ganki cikin wnn yanayin itama zata shiga damuwa. Ni dai bance mishi komai ba. Har muka isa gida side dina na wuce na kulle kaina a bedroom . Ya salman ya shiga damuwa sosai gabadaya ya rasa mafita sai dai addua. A haka zaman namu ya kasance ba dadi wata dayan nan kamin ya cika duk na rame kullum ina cikin damuwa. Don haka ya salman ya dauki hutu ya shirya mana tfy london don acewarsa ina bukatar hutu sosai. Maganar tfyrmu ba karamin dagawa salmah hankali yayi ba don har kuka saida tayi ma ya salman hkr ya bata yace in zaije dubai zaije da ita. Da haka muka tafi sai gamu a london fa,iza ta rasa inda zata samu don farin ciki don ya salman yaki yarda in fada mata zamuzo daga ita har ra,is kawai suka ganmu ba zato gaskia sun nuna murnarsu a fili ranar kwana mukayi hira .duk da ba haka ya salman yaso ba. Saida mukayi sallar asuba snn mukayi shirin rama baccin.da yake a gidan muka sauka side na musamman suka bamu cewar ra,is ku huta sosai kamin mu fita kuga gari. Ya salman yace"kamar kuwa ka sani mun gaji sosai muna bukatar ku barmu mu huta. Ra,is yayi dariya hade da fadin"na sani ni oga baka wasa . Fa,iza kuwa ta matso da bakinta saitin kunnena tace"Asha Soyyayya lfy Allah sa mu samu baby yau. Tana fada taja hannun Ra,is suka fita suna dariya girgiza kai nayi a zuciyata nace,kai fa,iza bata da kunya. Na kalli ya salman da ya zuba min ido tun daxu kallon ma na daban da sauri na karasa gunsa tuni muka fada gado kashe wutar dakin yayi mai haske ya bar bedside anan ya wani rumgumeni kamar zai maidani cikin shi ya shiga rada min kalaman soyayya masu zafi a kunne yayinda hsnnunsa ke yawo ko wani sashi da lungu na jikina lumshe ido nayi gabadaya na rasa a wace duniya nake gaskia nayi kewar yayanah sosai tabbas na axabtar da kaina bana wasa ba. Duk mun rikice mun fita hayyacinmu ya salman sai sambatu ya dinga min tun ba,aje koina ba . Gaskia ranar na ma naji jiki har na tuno first night dinmu da kyar na samu ya salman ya barni don sai da ya tabbatar mun gamsar da juna sosai ya kyaleni . Daga nan mukayi wanka tea kadai muka sha muka kwanta ya rumgumeni jikinsa yaja bsrgo ya rufemu sai bacci. Gabadaya zuciyarmu fess musamman ma ni ji nayi duk wani bakin ciki da nake ciki yau babu shi.sai tsantsar farin ciki da nishadi ga yanayin weather din garin mai dadi don haka kullum ni da yaya muna manne da juna muna gwadawa juna soyayya!!!! Hauly ce🥰👌🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡79 **************Mun huta sosai a Birnin London dan saida mukayi watanmu daya kamin nan muka dawo Abuja muka sauka gidan ya salim nan ma saida mukayi one week kamin muka karasa kano . Salmah ranar farinciki kamar tayi yaya da ranta tun a airport take ta mannewa ya salman tana ta zuba mishi shagwaba har muka isa gidansu innah .bayan mun gaishesu muka koma gidanmu .innah sai faman shan kunu take yau ma sai dai naci sa,a yau bata jefeni da bakaken maganganu ba. Muna isa gida munir kamar zaiyi ya da ransa da murna ya salman ya daukeshi yana dariya yace"big boy dan wata daya da bama nan ne ka wani kara tsayi haka ? Masha Allah naji dadin ganin big boy dina cikin farin ciki ina aunty sa,a? Yace"tana ciki daddy.daddy ka kawo min tsarabar allura? dariya mukayi ya salman yace"big boy allura kuma doctor kk so ka zama knn? ya dagawa ya salman kai Ya salman ya gyada kai yace"wow daz good !Allah ya nuna mana rai da lfy . Yace"amin. Salmah tuni ta wuce sashinta ta barmu da a palo mun biye wa munir sai hira muke anan sa,a ta fito cike da fara,a tayi mana barka da dawowa hade da gaishemu Ya salman yace"ina zainab kuma? Sa,a tace"adda sadiya ta aiketa gidan addah raihana dazu. Yace"sadiyan tana nan ne? Tace"eh tana side din aunty salmah. Yace " ok Muna nan zaune kuwa sadiyan ta fito tayi mana barka da dawowa ya salman bai amsa ba kawai ce mata yayi "ana kk zo kika tare yaran naki kuma kin barsu da waye? Shiru tayi ta da da sunkuyar da kai. Girgiza kai yayi yace"Sadiya knn wai ke har yaushe zakiyi hankaline? Anya sadiya zakiyi abin arziki a rayuwarki? Yayi shiru yana kallonta snn daga bisani yace"koda yake bazan ma bata bakina ba. ya mike ya wuce sama abinsa Dagowa tayi ta kalleni hade da fadin"to wai kallon me kk min ke kuma? Nace"hmm kin tsargu knn ? taja tsaki hade da fadin "daga dawowarku har yaya ya fara min fada sai kace wata karamar yarinya kuma don wulakanci a gaban sa,a. Ta wuce fuu tana ciccika. sa,a tayi dariya tace"aunty mu isa side dinki na gyara miki komai ki samu ki huta. Tashi nayi muka tafi a bedroom muka zauna nace"sa,a me ya sami sadiya ta lalace haka? sa,a tayi dariya tace"aunty labari mai dadi ne albishirinki? Nace"to fa goro fari sol! Ta sakeyin dariya tace"bayan tfyanku bai dade ba sadiya ta samu sabani da jafar ya mata dan banzan duka sai kinga yadda ya faffasa mata jiki satinta daya a asibity da kyar ta fara gane mutane....... Hannu na dagawa sa,a hade da fadin"haba sa,adatu wnn shine labari mai dadin har da yi mun albishir ?to meye abin dadi a cikin labarin ?kemafa macece Dariya ta shiga yi sosai nikam binta nake da kallon takaici tace"wlh aunty sadiya ta fara girbar abinda ta shukane alhakinki ya fara kamata don haka bana bakin ciki ko kadan da abinda ya sameta.don ma bakiji farkon labarin bane. Shiru nayi ina kallon sa,a tace"hmm kinsan su innah duk tunaninsu sun kama jafar a hannune suna juya shi son ransu ai ? To ashe ba haka bane jafar yana can yana sheke ayarsa da matan waje sadiya bata da labari.ita a ganinta tuni ta mallakeshi shine kawai ranar ta koma gidanta ta tarar dashi da wata 'yar makwabciyarsu wacce take kula da yaran sadiya in ta fita yawon banzanta ashe sun dade tare kuma a gidan suke harkarsu sai ranar ne kawai dubunsu ya cika tazo ta iskesu haka.karkiso ki ga irin haukar da sadiya tayi ranar gabadaya sai da ta tara musu mutanen anguwa ta debi tafasashen ruwa ta watsa musu a jiki shine jafar din ya fusata ya mata danbanzan duka se kinga yadda suka tara jama,ar anguwa sadiya ta dauki wuka wai wlh sai ta kasheshi.maganar kamar da wasa har ya isa gida nan da nan innah ta sabi hijabinta taje gidan don tayiwa sadiya magana anan jafar ya kama zagin innah sai da ya mata tass tukun snn yace ya saki sadiya saki biyu ta tattara 'yarta su bar mishi gida kuma a bar masa yaransa . Tunda suka dawo innah ta yanki jiki ta fadi jininta ya mugun hawa haka aka tattarasu da sadiya aka kaisu asibity abba yayi ta fama da dawainiya har Allah yasa sukayi sauki suka dawo.sadiya duk ta lalace bata ko iya cin abinci gashi mutanen anguwan se maganarta suke duk inda tayi ba damar ta fita..... Dafe kai nayi hade da fadin" Innalillahi wa innah ilaihirrajiun yanxu sadiya shikenan ta rabu da ja,afar ? Wlh na tausaya mata dolene kawai ta rame . Sa,a tace"shine fa kika ga wnn uwar iyayi da kissa da kisisina tace wai sadiya ta dawo gidan nan su zauna ko zata rage yawan damuwa.wlh aunty tunda sadiya ta dawo gidan nan ko motsi kwakkwara bamu isa muyi ba nida munir sai ta kama zaginmu aunty salmah kuwa shiru takeyi shiru nayi yayinda na shiga tunanin zamanmu da sadiya a gidan nan don ba karamin matsala zata haifar ba.dama yaya hmm Allah dai ya kyauta . Mun jima muna tattauna matsalar sadiya da sa,a. Ni dai inda nake godewa Allah ya salman yana kula dani sosai ko kadan bai son abinda zai bata min rai don haka ma ya gargadi sadiya akaina domin in ta kuskura ta min wani abu zata bar masa gida . Don haka duk iya shegensu kasa kasa sukeyi.anan suka dinga kulla makirci duk ranar girkina su faki idona su debi gishiri su cika min a miya ko su cika barkono kai watarana har da sugar kuma a kwanon ya salman suke sawa don kawai su hada mu amma abin mamaki sam bai yi fada ba kuma ya gane makircinsu ne don haka ya kwace makullan side dinshi gabadaya ya bar guda daya yace duk wacce takeda girki ta rike a hannunta sai ta gama ta bawa 'yar uwarta ni kuma ya gargadeni akan duk ranar girkina na kula na sa ido sosai akan duk wani motsinsu. Ganin basu sami nasara ba yadda suke so ba sai suka koma suka canza plan duk ranar girkina indai sinjini a kitchen sai su kunna burner su zuba turaren wuta mai karfin gaske su cika gida da hayaki ko wani corner . Sau biyu suna yin hakan sai na koma sama da sauri ince sa,a ta karasa min girkin in kuma bata nan in sauke in jira har sai ta dawo.don bazan iya juran hayakin ba zai tada min da asmma dama da gangan sukeyi .ni dai har lokacin ban tanka ba. Shine wata rana sadiya taje ta samo musu garin magani da katon kasko suka zo suka cika gida da hayaki ina kitchen na fara jin warin magani ga hayaki nan dan ya turnuke koina gidan da sauri na yi maza na kashe gas cooker . Na fita da sauri na nufi side dina ko ganin gabana banayi da kyar na samu na shiga dakin na kulle kofa inata jera atishawa ba kakkautawa da sauri na jawo inhaler na duk kamar a banza don tuni na fara jin kirjina na toshewa don haka ne ma nayi maza na kira ya salman yana jin yanayin maganata ya gane ba lfy don haka ya kashe wayar da sauri bar abinda yakeyi ya fizgi motarsa da gudu ya dawo.yana shiga ya tarar hayaki har lokacin ya cika gida baiyi magana ba ya wuce sama zuwa side dina ya sameni ina ta kokarin lalubar numfashi da kyar don haka yayi maza ya dagani ya fita dani zuwa motarsa yaja sai asibity emergency suka karbeni nan da nan aka min alluran cikin jijiya wanda tunda ya fara shiga jikina numfashina ya fara komawa normal a hankali a hankali kamin su cire alluran har numfashina ya dawo dai dai cikin ikon ubangiji. Ya salman ya sauke ajiyar zuciya hade da fadin Alhamdulillah sannu baby ya kk ji yanzu? A hankali nace"normal ba komai. Yace"to sai mu gode Allah .Amma hayakin me kuka sa a gidan ya turnuke koina ? Idona a limshe nace"nima ban sani ba ina kitchen kawai naga haya ki....... Karar wayarsa ne ta katseni nayi shiru ya daga hade da fadin " hakim ina jinka. Sai naga ya mike da sauri hade da fadin"what!!!gani nan zuwa yanzu. Kirjinane ya shiga bugawa da sauri na yunkuro zan tashi ya salman ya kamani ya kwantar dani hade da girgiza min kai yace"kwanta ke kam . A rikice nace"yaya menene ka fada min kar zuciyata ta buga. Yace"babu komai ba wani abu bane salmah ce ba lfy.ina zuwa ke dai kiyi hkr zance doctor james a kula dake da kyau ina zuwa. Ya fita da sauri. Hmm hausawa sukace in zaka gina ramin mugunta ginashi gajere don watakila kai zaka fada. Ashe hayakin nan da suka turnuke gida dashi ya jawo salmah ta shiga wani yanayi nan dan ta fadi ta kama shure shure idanu suka kakkafe sadiya ta rikice ta kama shiga da fita ta rasa yanda zatayi duk da ma ta fitar da kaskon hayakin ta kashe amma ko da ta dawo a sume ta tarar da salmah anan sadiya ta kama kuka hade da salati tana yau ta shiga uku ya zatayi. A cikin hakan hakim ya samesu a lokacinda ya dawo da munir daga school shine ya fadawa ya salman a waya . Anan hakim ya debo ruwa suka shiga shafawa salmah don ta farfado.aikuwa tana farfadowa ta fara maganganu da wani irin murya na daban . Daga hakim har sadiya sunja baya da sauri a tsorace da ganin yadda salmah ta koma alamun aljannune ita . A haka ya salman ya samesu hankalinsa ya tashi sosai ya kimkimeta itama suka zo asibity . Anan doctor yace masa salmah ciwonta bana asibity bane na gidane su koma gida a ne mi maganin aljannu don haka ya salman ya kira ya sanar a gidansu nan da nan suka zo suka tattarata sukayi gida da ita ashe su dama sun san tana dasu sa,arsu daya ne basa tashi akai akai kuma iyayenta sun tsaya mata tsayin daka wurin nemo maganin shiyasa abun nata baiyi tsanani ba. Ni dai ban kwana a asibityn ba muka dawo kuma na warware tass sadiya kuwa tuni ta debi kayanta ta koma gida tun ya salman bai dawo ba don tasan in har ya dawo ya sameta zata yabawa aya zakinta. Tana xuwa gida ta fadawa innah komai innah ma ta tsorata sosai ta shiga yiwa sadiya fada tana cewa wlh duk randa kk bari kk hadu da salman a gidan nan karki nuna kin sanni wai ke baki da hankaline ? Sadiya dai ta rasa ina zata sa ranta taji dadi a ranar. Salmah kam tana can gidansu sai magani ake tayi hade da rukiyya wasa gaske sai da ta share two weeks a gida snn ta warke ta dawo . Sai lokacin hankalin ya salman ya kwanta don haka ya je gida ya sami sadiya yana tambayarta labarin hayaki . Kame kame ta soma yi da farko sai da ya wanketa da kyawawan mari guda biyu masu kyau snn yace"zaki gaya min ko sai na kakkaryaki? Anan tace"yaya wlh turaren wutane aka kawowa salmah daga maiduguri...... Ganin ya fara kwance belt yasa sadiya ta tashi da sauri tayi bayan innah tana "wayyo innah yaya zai kasheni da duka. Inna ta kalli ya salman hade da fadin"yanzu kai ko kunya bakaji ba a gabana kazo kana tuhumar 'yar uwarka akan laifinda bata aikata ba....... Sosai maganar inna ta kara fusatar dashi yace"haba inna har yaushe zaki daina goyan bayan wnn shaidaniyar.. Inna tace"au 'yar uwar taka ce shaidaniya ? To bari kaji shaidanu suna can gidanka ka tara su.don haka ka fita ka bani guri tun kamin raina ya baci don zan mugun bata maka. Kai tsaye yace"zan fita innah amma daga yau ki gargadi sadiya bani ba ita kar ta kara zuwan min gida idan kuma ta kuskura na kara ganin kafarta a gidana duk abinda na mata karkiga laifina na fada muku kuma zan gayawa abba ma.... Inna tace"kai dai kaji kunya salman akan wasu banzaye kake ikirarin ba bu kai ba 'ya uwarka . Yana fita ta kalli sadiya tace "ba kinga abinda kk je kika janyo ma kanki dan tsabar rashin hankali to ai shikenan se ki zauna anan din gaki ga abbanku tunda shima har yau yana cike dake bama ke kadai ba ni kaina bai barni ba. Haka kuwa akayi abba na dawowa ya rufan musu daga innah har sadiya bai raga musu ba don har cewa sadiya yayi wlh ba don ina tsoron karki fi haka lalacewa dana koreki daga gidana don matsalarki ta isheni wlh duk cikin ku ba mara ji irinki addua nake miki dare da rana sadiya Allah ya shiryeki. Ya kalli inna yace "ke kuma shatu ke kk daure mata gindi tana tana abinda ranta yakeso to wlh ki kiyayeni.daga yau ina dada ja muku kunne ku fita daga tsabgar gidan salman don suna cikin zaman lfynsu sadiya ta kashe aurenta taje ta tare a gidan don ta rusa musu zamansu don haka daga yau kar ta kara zuwa gidan salman banaso ! To tunda akayi wnn case din aka gama sadiya bata kara zuwan mana gida ba don haka muna zaune lfy na ciki na ciki.competition kawai mukeyi wurin kwalliya da girki da kuma kyatatawa oga . Sadiya kuwa duk yadda taso ta kara jan salmah a jiki abin ya gagara salmah taki bata hadin kai kamar da don haka sai ta koma kullawa salmah munafurci a gun innah tana cewa "innah yau da gobe sai Allah auren ya salman da salmah kinga har ya cika shekara daya cif yanzu. Inna ta ce"hmm haka fa nayi lissafi jiya jiyan nan kamar kin shiga raina.amma shiru itama salman ba labarin ciki. An sosawa sadiya inda yake mata kaikayi ta gyara zama tace"innah salmah fa ba matar da zata haihu bane wnn matsalar aljanun nata bazasu taba barinta ta haihu ba domin tunda tazo gidan ya salman ko 'yawu bata taba tsartsarwa ba har gara rumaisah tayi bari sau uku . Inna tace"ai kuwa kina da gaskia snn ma ni ba wnn ba tunda kuka samu matsalar can ta daina min waya da kuwa tana kirana akai akai mu gaisa to me yasa? Sadiya ta tabe baki tace hmm inna dama munafurcine kawai fa da neman gindin zama yanxu kuwa kinga tunda ta sami kan mijinta kinga ta daina kulaki . Inna tace"lallai kam munafurcine na yarda.amma babu komai da ni suke zancen. Sadiya tace"hmm ai tunda kikaga nima ta hadani da yaya har yana cewa babu ni babu shi kinsan ba karamar munafuka bace innah kinaga har yau yaya ko gaisuwata baya amsawa ni narasa ma da wanne zanji innaah ga matsalar jafar ya hanani inje inga yarana ya hana suzo in gansu abba kuma ya ki ya dauki mataki akai. Inna tace "karki damu sadiya ki kwantar da hankalinki duk zanyi maganinsu.amma kamin nan salman zaizo ya sameni a gidan nan ta kansa zan fara domin ya isheni takaici da bakin ciki da yake cusa min . Sadiya tace"ai sun gama dashi kinga ma ko zuwa ba ya son yi kamar da. Inna tace dauko wayata ki masa flashing. A lokacinda innah ta kira ya salman muna tare ranar nice da girki da safene ina kwance kan gado a dakinsa duk na rasa me yake min dadi . Tunda suka fara wayar hankalina na kanshi a zuciyata nace hmm yau kuma innah waya da sassafe Allah sa ba laifi mukayi ba. Yana gama wayar ya turata aljihu ya karaso inda nake ya zauna bakin gadon ya taba wuyana yace " baby kwana nan duk na lura kamar baki jin dadi sosai me yake damunki? Nace"wlh yaya ba komai ke mun ciwo ba kawai dai kasala nike ji bana son yin komai wlh. Dagoni yayi daga kifuwar da nayi ya juyo dani ya kwantar kan kafarsa ya daga rigana ya shafa cikina yace"ko dai akwai ajiyata ne a wnn shafaffen cikin? Shiru nayi yace" yace nasan dai kinyi mensis last month dis month kuma in har baki yi ba nan da five days zamuje asibity a duba ko Allah ya amshi adduar mu da muka dade munayi . Jikina ne ya kara mutuwa tausayin ya salman ya kamani sosai domin indai ba tsananin rabo ba yanzu a inda nake kwance ma ina jin sign din period dina zaizo don bayana da marata sai ciwo yake min bana son fada masa ne kar ya daga hankalinsa. Bayan ya taso daga aiki gidansu yaje don amsa kiran innah ba zato ba sammani inna ta bijiro masa da batun wai ya sake aure ya auri madiha. Maganar ya matukar girgiza shi cike da mamaki yace "innah me ya faru kuma? Tace"kai har yanzu baka san mai ya faru ba tsabar sun gama da kai ba kama damu da rashin haihuwar nan ba duk sa,oinka sai haihuwa suketayi gwanin ban sha,awa amma banda kai. Yace"Inna haihuwar nan fa daga Allah ne ba wai daga rumaisah ko salmah bane don haka kawai addua zakici gaba da yi mana sai kiga inda rabo za,a dace....... Ta katseshi da fadin ya isa dan Allah ko yaushe aka taboka sai ka nuna kafi kowa sanin Allah to bari kaji aurene sai ka kara kuma madiha zaka aura . Yace" haba inna ni fa nace miki madiha ba matar aurena bace kinsan halinta banda yawon iskanci a lagos ba abinda ta iya..... Inna tace"eh ai dole kace haka idan yawon iskanci ne wani iri ne rumaisa batsyi ba bayan karuwanci ina har da shaye shaye ma amma ba gashi da ka aureta ta shiryu ba kamar ba ita ba to itama madihar idan ka aureta zata nitsu. Tashi yayi ransa a bace yace"ni gaskia innah abar ma batun madiha bana bukatar mata uku biyun ya isheni haka kawai ki hkr kici gaba da yi mana addua. Yana gama fadin haka ya fice da sauri ransa a cunkushe. Ya dawo a lokacin na gama komai ina zaune a palon kasa muna hira a waya da ruma tana bani labarin tana daukeda ciki tsawon wata uku gaskia na tayata murna ba kadan ba don suma har sun fara damuwa tundaga kan munir shiru yau ga munir shekara shidda. Shigowar ya salman ya katse mana hira mukayi sallama na tashi da sauri na karasa gabanshi fuska sake nace"yaya ka dawo...... Da kai kawai ya amsa min ya wuce side dinshi jikina a mace na bishi a baya. Ranar ko abinci ya kasa ci na tambayeshi amma bai gaya min ba don haka ban matsa mishi ba.sai dai duk bamuyi baccin kirki ba ranar . Da asuba kuwa bayan idar da sallah na shiga kitchen na shirya mana breakfast kamin na gama duk naji bacci ya cika min ido don haka a daddafe na shirya dining na bar sa,a da gyaran kitchen na koma part din ya salman na kwanta na barshi yana ta faman waya da abokan aikinsu. Bacci ne ya daukeni har ya gama abinda yake ya shirya cikin kakinsa yazo ya dan tattabani yace"baby tashi ni zan tafi muje muyi break fast Mika nayi sosai hade da salati idona a lumshe nace" yaya ni bacci nakeji sosai kuma na koshi ma. Kallona ya keyi snn ya danyi murmushi yace"to shikenan gimbiya asha bacci lfy.sai na dawo. A hankali nace a dawo lfy . Naja bargo na kara rufe kaina naci gaba da baccina. Ban tashi ba har shadaya nayi wanka snn na fita na kulle sashin ya salman na wuce nawa sashin na na zauna na bata lokaci wurin tsarawa kaina kwalliya. Ina daura dankwalina sa,a ta turo kofa hade da sallama na amsa ina murmushi nace" yau ba lectures ne? Tace"yanzu ma nakeso nazo na tafi .aunty su innah sunzo fa yanxu suna zaune a palon kasa da sadiya.innah tace kije. Nan da nan fara,ar da ke fuskata ta gushe. Kamar bazanje ba na dai daure na fita ina ta addua a zuciyata ina ganin yanayin fuskokinsu nasan akwai matsala. Nayi musu sannu da zuwa basu amsa ba sadiya sai hararata takeyi . Na zauna a kasa na fara gaisheda innah da sauri tace"dakata da gaisuwarki don bashi ya kawoni ba ina dayar mara kunyar kuma take tun dazu nace a kirata shine ta ba banza ajiyarmu.don haka kije ki kirata. Har ina shirin tashi sai ga salmah na saukowa itama cikin kwalliyarta sai dai fuskarta ba fara,a ta karaso ta yiwa su inna sannu da zuwa . Inna tace"nemi wuri ki zauna kema. Salmah ta zauna ba tare da tace komai ba . Inna ta numfasa tace "to zuwa nayi wurinku don ku bar min gidan dana yau dinnan saboda shi kun gama dashi baya ganin laifinku amma ni baku gama dani ba don haka ko wacce shegiya ta tattara kayanta ta bar gidan nan yanzu don zamanku a gidan nan bai da amfani komai bakuda wani aiki sai dai kuci abinci ku cika masai da kashi....... Salmah tace subhanallah innah me yai zafi kk fada mana irin wnn kalaman? Sadiya ta watsa mata harara tace "har ma kinada bakin tambaya keda kk hadani da danuwana ko magana baya min. Salmah tace"lallai ma sadiya nice ma na hadaki da danuwanki ..... Anan fa sadiya suka shiga sa,insa da salmah suka shiga gaggayawa juna bakaken maganganu innah kam sake baki tayi tana kallon salmah cike da mamaki . Tace"ashe salmah bakida kunya haka bansani ba ? Salmah tace"inna ai banice mara kunyarba ga mara kunyar nan data zo har gida na zata ci mun mutunci shikenan kuma sai in kyaleta ? Inna tace"to yayi kyau sai ku wuce kuje ku tattara kayanku ku bar gidan nan kamin salman ya dawo ya bi kowacce da takardan sakinta. Salmah tace"tabdi wlh babu wanda ya isa ya fitar dani daga gidan nan gidan mijinane bai koreni ba don haka ba inda zanje ehe! Gabadaya mamaki ya rufemu ni kam da ido nake binsu gabadaya Sadiya tace " salmah kinsan da wa kk magana kuwa? Salmah ta yatsuna fuska tace"da inna nake magana sai me ....... Ji kake tass sadiya ta dauke fuskar salmah da mari itama batai wata wata ba ta rama anan suka shiga kokuwa tashi nayi da sauri ina kokarin janye sadiya ina don Allah ku bari ba amfani kuyi hkr . Na kwalawa sa,adatu kira nace tazo itama muka shiga raba fada inna kam ta rasa me ma zatayi kawai sai ta fashe da kuka tana cewa sa,adatu kira min salman yanxu yanzun nan yazo yaga irin cin mutuncinda matansa suka mini. Ta rike hannun sadiya tace "sadiya rabu da ita yau dinnan salman sai ya sallamesu dukansu biyun tunda ba gidan uban su bane gidan dana ne kuma dolene ku barshi a yau. Ni da naga ba sarki sai Allah tuni na tafi side dina na dauki wayata na kira salman nace yazo yau ma gida ba lfy kuma ni tfy ma zanyi. Daga nan na katse kiran na jefa wayar cikin jakata na dauki hijabina da key din motana na fita ta kofar baya na figi motata sai gidan mama bansan ya suka kare ba!!!!!!!!! Hauly ce🥰👍🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡80 ***********Salmah zagewa tayi ta rufe ido ta dinga zubawa innah rashin mutunci kuma tace wlh babu inda zata je don nan gidan mijintane. Inna tace"amma dai banji kince gidan ubanki bane ba koh?to wlh zaki tafi bari salman din yazo yau sai dai ya zaba koni ko ke mara kunya fitsararraiyar banza fitsararriyar wofi ......... Salmah tace"hmmm wlh babu inda zanje aurena da suleyman mutu ka raba bari kiji da kyau.don ni nafi karfin tunaninku ko kin dauka nima shashasha sakarai ce kamar rumaisa ? Duk fa abinda kukeyi ina sane manna muku hauka nayi kawai inga iya gudun ruwanku.idan ba munafurci waye ...... A hasale sadiya tace "wlh ki sawa bakinki limzami ya isheki ciwa mahaifiyarmu mutunci.don na lura bakida tarbiya hala haka uwarki ta koya miki kizo kiyi mana koh? Salmah tace "sadiya bana gargadeki akan karki kuma sa bakinki ba ?to wlh ku tashi ku fice min daga gida tun kamin na aikata muku abinda ba kwa tunani. sadiya tace"idan gidan ki ne ba sai ki fitar damu da karfi ba mara mutunci..... salmah ta gyada kai tace ok jirani ina zuwa. ta wuce kitchen da sauri tabarya ta dauko cikin store ta fito babu ko tsoro ta nufo sadiya ta daga zata buga mata. Daga inna har sadiya zaro ido sukayi cike tsoro sadiya tayi bayan inna da sauri. salmah kuwa a rashin sani tuni ta sauke tabaryar akan innah ji kake tim!!!!!! Inna ji tayi dif kamar an dauke wutan nepa a hankali jiri ya soma dibanta a take ta yanki jiki ta fadi sadiya tasa ihu a razane hade da fashewa da kuka tana "wayyo Allah na shiga uku ta kashe mana uwa. Sa,adatu ma a rude ta shiga girgiza innah tana kuka . Salmah kuwa tuni tayi jifa da tabaryar tayi part dinta a rude jikinta na rawa domin sam ba innah taso bugawa tabarya ba kaddarace dai kawai ..... Nan ta mike cikin gaggawa ta fara neman hijabinta da makullin gidan domin tasan duk inda ya salman yake yanzu ya kusa isa gida in kuma yazo yaga halinda mahaifiyarshi ta shiga to fa kashinta ne zai bushe. A tare ya salman suka isa gidan da hakim wanda ya dawoda munir daga makaranta . ko parking mai kyau ya salman bai tsaya yi ba ya fito da sauri ya nufi cikin gida bai ko kula munir da ke masa oyoyo ba hakim ya fahimci ba lfy da sauri ya bishi cikin gidan. a sume har lokacin ya samu innah su sadiya sai kuka suke tayi . Salman ba karamin tsorata yayi ba yazo ya daga innah yana"me ya sameta ? Sadiya tace"Salmah ce ta daketa da tabarya ! what !!! Ya fada cikin yanayin mamaki da sauri ya daga innah ya fita da ita a guje sai cikin motarsa yace da mai gadinsa kar ya kuskura ya bar salmah ta fita daga gida yaja motar da gudu sai asibity gabadaya gani yake kamar inna mutuwa zatayi hankalinshi ya tashi sosai idan nan ya kada yayi jazir yayinda zuciyarsa ke tafarfasa ya na tunani wani irin hukunci zaiwa salmah . Bai bar asibityn ba saida ya tabbatar innah ta farfado kuma a lokacin abba yazo don haka bai ko sallamesu ba ya bar asibityn ya dawo gida ya iske salmah cikin yanayin tsoro bai tsaya tambayarta komai ba ya zare belt ya shiga dukanta ta koina ihu take tana neman agaji Allah ya sota kofa a bude ta sami ta fita a guje Hakim ne ya bita da sauri ya isketa hanyan get jikinta duk jini abun babu kyaun gani don haka shi ya dauketa a motarsa ya kaita asibity. Ni kuwa tunda na isa gida mama ta ganni hankali tashe tace"lfy yau kuma me ya faru? nace"hmm komai ma ya faru mama. Ba bata lokaci na shiga bata labarin abinda ya faru na karashe maganar da fadin "na barsu bansan ya zasu kare ba ni dai bazan iya zama ya salman ya dawo su doran sharri ba. Cike da mamaki mama tace"hmm baga irinta ba shatu dai bansan meyake damunta ba.gashi taje taja ma kanta cin mutunci a gurin surukarta Allah dai ya kyauta ni dai banga laifin salmah ba wlh Nace" mama ban taba tunanin salmah zata maidawa su innah martani ba. Mama tace"Ai ni ta burgeni irin halin shatu sai hakan.. Muna cikin tattaunawa daddy ya shigo da sallama cike da fara,a mama ta amsa. Nace"au dama daddy kana gari? Yace"daxu nazo mamana baki sani ba koh? Nace"eh.mama bata fada min ba. Mama ta harareni hade da fadin"saboda banida aikin yi koh? Na danyi dariya snn na gaisheda da daddy hade da tambayarsa labarin mutanen yola duka yace lfy. Daga nan ya wuce sashinsa mama tabi bayansa. Ba awani jima sosai ba daddy ya kirani akan maganar da nazo da ita ce min yayi"ihsan a kara hkr duk da dai alhamdulillah ban taba jin kinyi tashin hankali da kowa ba to hakan nakeso kici gaba da hkr har Allah ya kawo karshen abin.snn duk sanda salman yazo ki bishi ku koma kinji tunda kinga yana sonki kuma baison bata miki don haka kema kici gaba da kyautata masa . Nace insha Allah daddy . Yace"Allah ya miki albarka. Ameen nace daga nan na tashi na tafi dakina sai da dan gyaggyara snn na yi wanka na kwanta.duk naji na gaji ko don raba fada da nayi ne oho. Salman kuwa bayan ya gama da salmah kan sadiya da sa,adatu ya dawo yana tambayarsu yadda akayi yayinda yacewa sadiya" ke ban ma hanaki zuwa gidana ba? Wato bakijin magana koh? Nan itama ya sauke mata nata rabon ranar tasha belt har ta gigice kuma yace ta fitan masa daga gida kamin ya kakkaryata daga nan fita yayi cikin fushi sai asibity .ya samu innah ta dawo daga hayyacinta daidai . Fuskarsa a murtuke ya mata sannu bata amsa ba kawai binsa take da kallo . Salmah kuwa daga asibity da hakim ya kaita gidansu ta koma hankalin iyayenta ya tashi sosai har mahaifiyarta na cewa baga irinta nan ba saida muka hanaki auran wnn sojan kince ke kinji kin gani su fa sojojin nan ba imani ne dasu ba zasu iya kashe mutum ma yanxu dubi yadda ya ji miki ciwo koina wlh bazaki kuma komawa gidansu ba kuma wlh zai fuskanci bacin ran mahaifinku . Salmah kam na kwance kanta sai ciwo yake. Hankalina ya tashi ganin har dare ya salman bai zo gurina ba ko abinci na kasa ci na rasa me yake min dadi bacci ma ba sosai na samu nayi ba. Da safe muna cin abinci a dining kawai na soma ji tashin zuciya na mike da sauri daddy yace"ihisan lfy ? Nace"amai nake ji..... Ko kan na rufe baki tuni na shiga kwara amai ba shiri mama ta mike ta rikeni daddy yace"subhanallah Amina dama bata da lfy ne? Mama tace"hmm gatanan dai ni tunda tazo jiya ban gamsu da yanayinta ba amma tace babu abinda ke damunta. Nan daddy ya rikice yace"to maza kuje ta shirya mu tafi asibity. Mama ta kalleni tace"sannu kin gama ne? Kai na daga mata tace"to jeki ki wanke jikinki kisa kaya kizo muje asibity. Nan na tashi daddy yace" Amina ki riketa mana karta fadi. Ganin yadda daddy ya damu yasani fadin "zan iya tfy daddy . Daga nan na fita mama kuwa ta shiga gyara gurin bayan ta gama ta dawo palo gun daddy tace"lamido ka kwantar da hankalinka inaga ihsan kamar fa cikine. Nan da nan daddy ya saki fuska yace"Allah yasa hakan ne Amina . Tace"amin bari naje na dubota. Mama ta sameni ina kwance ruf da ciki idona lumshe tace" ki daure ki tashi muje asibity rumaisah. Haka na daure muka tafi asibity.bayan sunyi gwaje gwajensu nan suka tabbatar da ina daukeda *CIKI* tsawon wata guda........ Haulyce👍🏻🥰 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡81 **********Farin ciki a gun mama da daddy ba,a magana don sun kasa boyewa nima sosai na godewa Allah hade da rokonsa wnn karon yasa rabonmu ne . Anan doctor da ya dubani yace ya bani bedrest kuma a kula dani sosai. Da farin ciki muka dawo gida daddy ko motsi kwakkwara baiso nayi haka mama ta rike min hannu har zuwa dakina kamar wata karamar yarinya tace" to kindaiji abinda doctor yace saboda haka ki kiyaye duk abinda kk bukata ki fada min ko lami . Nace"to mama zan kiyaye. tace"yanzun me kk sha,awan ci a dafa miki? Na dan yatsuna fuska nace "a bani black tea kadai nasha yanzun bana sha,awar komai. tace"aa bazaiyiwu ba black tea kadai me zai maki ?ke da tun breakfast da kk yi ba ki kara cin komi ba .to shi dinma ai duk kin amayar. nace"to mama a bani kunun tsamiya in yaso anjima sai naci wani abu tunda zansha maganin amai yanzun ko naci amai zanyi. Tace to Allah dai ya raba lfy. Daga nan ta fita nan na lalubo wayata na fara neman uban gayyan sau biyu ina kiransa bai daga ba don haka na rabu dashi.ina ta tunanin a wane hali yake.can sai ga message dinshi ya shigo ce min yayi nayi hkr yana busy ne zai zo daga baya .kuma ya tambayeni lfyta .na masa rply da cewa lfyta qalau kuma ba matsala sai yazo din da haka muka rabu. Allah sarki yayanah yana can yana fama da case din innah da Salmah.don saida abba ya shiga maganar sosai aka samu aka daidaita domin har gidansu salmah sukaje shida daddyn su ya salim akan maganar don mahaifinta ranshi ya baci matuka da irin dukan da ya salman ya ma 'yarsa .amma koda yaji nata laifin sai ya sassauto aka daidaita ya salman ya amince ta dawo kuma itama ta yarda zata dawo don a cewarta bazata iya rabuwa da ya salman ba.takaici kamar zai kashe uwarta.don haka sukace sai ta warware zata dawo. Inna kuwa tana asibity tana fama da kaddarar da ya fado mata gashi abba yazo ya dada sauke mata kwandon bala,i yayi mata wankin babban bargo a asibityn yace kuma idan ta sake shiga lamarin gidan salman zai saketa! saida daddynsu ya salim ya dinga ba abba hkr.sadiya kuwa bayan tasha dukan ya salman abba ma kara mata yayi taji jiki sosai abin gwanin tausayi . Inna kuwa tun ba,aje koina ba nadama ne ya shigeta sosai da kuma da na sani tabbas a yanzu ta gane kuskurenta kuma tasan alhakina ne ya kamata don haka daga wnn lokacin ta sama zuciyarta salama!(dama hausawa sukace jiki magayi Allah ya kyauta) Ni sa,adatu ce ma tazo ta bamu karashen labarin ni da mama lol!ranar mama yini tayi tana juyayin wnn lamarin hade da fadin Allah ya kyauta . Ni dai ina ta kaina domin a dan kwana biyun nan gabadaya laulayin sai karuwa yakeyi abinci ko wani iri naci sai nayi amai .ina sha magani amma a banza ba abinda ya ragu don haka ya kasance sai drip ake sa min lokaci zuwa lokaci. Sai da nayi kwana hudu a gidanmu snn ya salman ya samu ya zo. Ina kwance a dakina kasancewar kofata a bude ina dan jiyo hirarsu da mama . Don har mama tace mishi "rumaisan ma bata jin dadi salman. Yace"Subhanallah goggo Amina me yake damun rumaisah? Mama tace kai dai ka isa tana dakinta waka a bakin me ita ai yafi dadi. Ta karashe maganar da murmushi. Shi dai bai fahimceta ba don haka kawai ya shigo dakin ya sameni kwance ga drip. Har yaji kirjinsa na bugawa ya karaso gadon da sauri yace"Innalillahi baby abin har ya kai fa haka dubi yadda kk rame baby me yake damunki? Murmushi na sakar masa hade da fadin"yayana kar ka daga hankalinka rashin lfyata na karuwa ne..... Ya katseni da fadin"what....baby are you serious? Gyada masa kai nayi ina murmushi nace"sosai ma yayana munje asibity an tabbatar min ina daukeda cikin babynka wata daya kaga sai mu gode wa Allah mu kuma rokonsa yasa wnn karon rabonm...... Bai bari ya karasa jin karshen labarin kawai ya rumgumeni ya shiga kissing dina ko ta ina tsabar murna ya manta da drip dinda aka samin sai da na tuna masa ya dago da sauri yana murmushi yace" my dear da inada ikon bude zuciyata tabbas da na bude miki domin kiga irin farin cikin da take ciki bakina bazata iya bayyana tsanrsan farin ciki da zuciya ta ke ciki ba masha Allah Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki daya bamu wnn kyautar da kudi baya siya.sai dai fatan Allah ya raba lfy. Tunda ya fara magana nake murmushi nace"amin yayanah. Ya rike hannuna daya yace"babyna kwanan nan duk na shiga cikin wani yanayi na damuwa amma gashi lokaci guda daga zuwana wajanki damuwata ta yaye duka tabbas rumaisah ke alkhairice a rayuwata na godewa Allah da yabani ke a matsayin abokiyar rayuwata Allah ya maki albarka . Nace"ameen yayanah nima burina a kullum bai wuce inganka cikin farin ciki da annashuwa ba domin hakan ba karamin faranta min yake ba Allah ya barmu tare yayanah nima na gode da irin kulawa da tattali da kk nuna min.Allah ya biyaka da gidan aljannah. Murmushi yayi yace"baby me kk so na miki neh ? Dariya nayi nace"yaya babu komai. Yace"no please tell me me kk so don Allah?kina so na goyaki ko na miki rawa? A tare mukayi dariya sosai har na koma ina mamakin yadda yaya yake kwasan dariya kamar bashi ba . Haka muka kasance cikin farin ciki kamin ya tafi ya shafa marata yafi a irga. Daddy ya kirashi akan maganar cikina da abinda doctor yace anan daddy yace"yanzun ya kk ganin za,a dauki matakin kulawa da ita? Ya salman yace"daddy ni inaga kawai gara na barta anan gidan domin zata fi samun kulawa tunda ni ba mazauni bane kullum kuma ga yanayin cikin yazo da laulayi don haka na ke ga gara ta zauna kusa da goggo Amina domin zatafi samun kulawa sosai har Allah ya yaye mata laulayin. Daddy yace"madallah dana dama nima tunanin da mukayi knn da goggon naka amma mukace baza mu takuraka ba sai munji ra,ayinka . Ya salman yace babu komai daddy Allah ya rabalfy Mama da daddy suka amsa da amin. Daga nan ya salman ya tafi gidansu ya sanar da abba komai abba yayi farin ciki sosai snn yace"kunyi dabara gara a barta gaban Aminan zata fi samun kulawa don haka kayi kokari kaje ka dawoda matarka domin bazaiyiwu kabar gidanka ba kowa ba. Shiru ya salman yayi don gaskia baya son ya dawoda salmah tun yanxu yafi son sai ya gama azabtar da ita don yasan tana balain son ta dawo don kullum sai ta mushi text na ban hkr. Anan abbah yaci gaba da bashi hkr yace zai dawoda ita amma sai ta karasa samun saukinta jikinta. Sam ya salman yaki fadawa innah batun cikina hasalima yanxu ya daina sakin fuska suyi hira don haka itama innah fita harkarsa tayi acewarta sai ya sauko ta bashi hkr. Ni dai a bangarena naso in koma gidana domin nafi bukatar yayana a yanxu musamman da naji salmah zata dawo gani nake kamar zata hanashi zuwa wajena. Kullum ya salman sai yazo gidan mama indai aiki bai masa yawa ba sosai nake samun kulawa bana komai daga kwanciya sai cin abinci se wanka da sallah . Salmah kuwa sai da tayi wata daya a gidansu snn ya salman ya dawo da ita kuma yace matukar tana son su shirya to sai taje ta baiwa innah hkr kuma tayi alkawarin hakan bazai kuma faruwa ba. Tace ta amince don dai wnn ai mai saukice tunda tana sonshi komai ma zata iya yi. Hakan kuwa akayi ya kaita gidansu don ta baiwa innah hkr. Suna shiga palon innah da sallamah sai da kirjin inna ya buga dam don haka ko sallamarsu bata amsa ba ta mike da sauri ta shige dakin ciki. Jikin salmah a mace ta kalli ya salman kamin tayi magana ya katseta da fadin "zauna ina zuwa. Daga nan ya bi bayan innah ya sameta a zaune bakin gado sadiya kuwa tana kan gadon sai sheka bacci take . Yace"innah ga salmah tazo kuma gunki tazo domin ta baki hkr? Inna tace"tazo ta bani hkr ko ta karasa ni ? Kaga salman don Allah don Annabi ka tattara matarka ku bar gidan nan bana bukatar ganin ko mai kama da ita a rayuwata. Ya salman ya sassauta murya yace"kiyi hkr innah salmah tayi nadaman dukkan abinda ta aikata ki sake bata dama a karo na biyu don Allah inna kije ku gaisa. Inna ta girgiza kai tace"ba dani ba wlh tattarata ku tafi na yafe mata duniya da lahira kuje kawai ba sai na fita mun gaisa ba kuma dan Allah kar kuma kawota gidan nan bana bukatar ganita . Ba yanda salman baiyi da inna ba amma sam taki yarda ta fito su gaisa da salmah don haka ya hkr ya fita.kawai yace salmah su tafi gida. Tundaga ranar innah ta daina sa mana ido ta shafawa kanta lfy .ni kuwa koda taji labarin cikina ba karamin farinciki tayi ba don haka ba,a kwana biyu bata kira taji lfyta ba.tun ina danjin tsoron me zai biyo baya har na saba yanxu . Salmah kam shiru ba labarin ciki don haka ta shiga nuna damuwarta da kishinta a fili ganin yadda ya salman ke kula dani duk da ba gidan nake ba . Bangaren sadiya kuwa sam batayi murnar samin cikina ba daga ita har adda A'i domin su da so samune ya salman ya rabu dani ya auri daya daga cikin 'yanuwansu na kamaru. Yanxu adda A'i da sadiya su biyu suka rage bakinsu daya innah kam tuni ta rabu da harkarmu . Amma sadiya bata nuna min a fuska ba don tana zuwa ta dubani har ta wuni ma a gidanmu .yau da gobe har na saki jiki da ita in tazo musha hira da dariya . Cikina na wata hudu na fara samun saukin laulayi yanxu sai dai kwadayi komai mama ta dafa baya burgeni . Don haka sai incewa sa,a ta dafo min dambu ta kawo min wani lokacin kuma ince rogo da kuli har da su awara duk abinda bai dameni ci ba da yanzu sune abincina. Ranar sadiya da kanta ta dafo dambu ta kawo min don sa,a bata da isashen lokaci sosai suna exams . Naji dadi sosai nace lami ta dauko min plet . Tana kawo min nayi serving har na diba a spoon zan kai baki sai naji wani irin tashin zuciya .............. Hauly ce👍🏻🥰 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡83 ***********Salmah ta fara tunanin bin shawaran kawayanta don haka ta yanke hukuncin bin malamai .amma wani abun takaici duk abinda tayi baya cinmu gabadaya abin ya daure mata kai gashi ta kashe kudadenta duka har ta koma sayarda gwala gwalanta amma shiru babu abinda ya sauya. Zuwa yanzu na warware tass ba abinda ke damuna na laulayi sai nauyi da cikin ya kara yi kasancewar yanzu ina wata na bakwai Ban kuma yin sakaci da kaina ba domin kullum cikin yi mana addua nake akan Allah ya tsare mu da sharrin dukkan makiya kuma dama nasan ya salman ma ba baya ba wurin riko da ibada.haka nan na biya kudina akayita mana saukan Al-qurani mai Girma akai akai .to Alhamdulillah komai na tfy normal. Su sadiya ma sunyi sunyi abin ya faskara domin daga baya lagos din ma ta koma gabadaya saboda suji dadin kullah makirci .tun suna bin malamansu na nan arewa da kamaru har suka koma bin bokayen kudu mushrikai masu tsafi sunta kashe kudi amma a banza don haka kawai suka zubawa sarautar Allah ido. A wnn lokacin Ruma ta haifo babynta katuwa mace karkuso kuga murna a familyn galadima kasancewar haihuwar yara mata ba yawa don haka ruma ta dinga samin kyauta tin randa ta haihu har zuwa ranar suna . Nima aje suna inda baby taci suna ummul khairi anyiwa Goggo ummi takwara .fa,iza ma tazo mutanen london yanzu yaranta uku sakina kuwa hudu .sun sakoni a gaba da zolaya nidai ban kulasu ba ina ta kaina don sai kunga yadda cikina ya girma a lokacin wata takwas kai dama haka masu ciki ke fama bacci ma da kyar nake samu nayi.ga babyn cikina sai motsi yake sosai musamman da daddare. ya salman kuwa tausaya min yake sosai ganin yadda nake fama tashi da kyar zama da kyar in dai yazo gidan mama ya dinga dawainiya dani knn duk nauyina dinnan haka yake kimkimata ya kaini toilet don yanxu shine mai min wanka lol! Jiransa nakeyi se yazo . kwanana uku a Abuja na dawo kano ya salman duk ya bi ya damu da bana nan din sai waya yake ta min akan na kula da kaina.gaskia ina samun kulawa kota ina sai sambarka. Nima cikina na cika wata tara da sati daya na soma nakuda bazan manta ba ranar ya salman yazo muna tare a daki muna dan hira kawai sai na fara jin marata da bayana ya fara ciwo kadan kadan ya lafa .haka na dinga cijewa don kar ya salman ya daga hankalinsa . har karfe tara dare ya sallameni ya tafi .aikuwa tfyrsa keda wuya na fara jin zafin na karuwa nan da nan na gayawa mama aikuwa ba bata lokaci ta tattaro min kayana muka tafi asibity muna zuwa suka karbeni suka duba kawai wai na kusa ga kan baby.zaro ido nayi a tsorace duk da wani wahala nasha sosai ba. don haka ko minti ashirin bamuyi da isa asibity na haifo babyna katuwa son kowa kin wanda ya rasa gashi ban.wani sha wahala ba sam. nan aka kintsa mu aka nade baby cikin kayan sanyi overall pink da hula sai kun ganta katuwa jazir tubarkallah masha Allah duk da ba a cika gane kamannin jaririya ba amma kuna ganita sak!ya salman har da gashin kanta ikon Allah knn. mama kam murna kamar tayi yaya da ranta sai shiga da fita takeyi ta rasa wa zata fara kira tsakanin ya salman da daddyna.tsabar farinciki . murmushi nayi nace"mama ki gayawa yayana don Allah tace"gaskia kam ya kamata bari na kirawoshi in mishi albishir in yaso se in kira daddyn ku. ta fadi hakan tana murmushi yayinda ta lalubo layin ya salman ta kirashi ringing biyu yayi ya daga hade da fadin"goggo lfy dai kam ? Tayi dariya tace"lfy lau salman yau Allah ya amshi adduarmu rumaisa ta sauka lfy ta samu diya mace yau kaima ka zama uba salman sai mu gode Allah. Allahu Akbar" abinda bakinsa ya fara fada cike da farin ciki mara misaltuwa ta ce"goggo Amina ina fatan dai ba wata matsala daga rumaisa har babyn? mama tace"lfy lau wlh babu komai rumaisa gats zaune tana shan tea baby kuwa tana gadonta ...... Yayi wani irin ajiyar zuciya hade da fadin Alhamdulillah Allah abin godiya goggo Amina ina zuwa yanzu don bazan iya bari gari sai ya waye ba..... Mama tace" haba salman sha biyu fa ta kusa ka hkr mana sai da sa...... tuni ya katse kiran dariya nayi nace"mama yaya wai sai yazo ko? Mama tace"ai bazai iya hkr ba .yanxu bari na kira daddyn ku kuma. Nan mama ta kira daddy ta sanar dashi shima nan da nan ya warsake daga bacci ya fara tambayar lfy ta tukun mama tace Qalau nake yace "to amaryartawa fa? mama ta dan tabe baki tace"gata can kan gadonta tana baccin ragwanci. daddy yayi dariya yace"kodai baccin gajia wato kin fara kishi tun yanxu ko ? Mama tace"me abun kishi a wurin wnn 'yar mitsisiya. dariya sukayi daddy yace"masha Allah Allah mun gode maka Allah ya raya mana ita bisa sunnah ya Albarkaci rayuwarta tare da dukkan yaran musulmai. Mama tace"amin . yace"insha Allah gobe zanbi flight din safe nazo naga amaryata. mama tace"Allah ya kaimu rai da lfy a gaida mutan gida.daga nan sukayi sallama. Ta sake kiran Abbansu ya Salman ta fada masa shima sosai ya dinga farin ciki hade da kyawawan adduoi.daga nan mama tace shikenan sauran mutane sai da safe ta fada musu. Ya salman kuwa yana katse kiran mama tashi yayi ya wuce toilet alwala yayi ya fito ya zira jallabiyarsa ya shimfida pray mat ya fara jera nafila na godiya ga Allah da ya bashi wnn babbar kyauta da kudi baya saya . Bayan ya idar yayi adduoinsa ya tashi ya dauki wayoyinsa ya dura aljihu da makullin motarsa . Snn ya kalli salmah dake ta sharar bacci har da minshari lol Ya karaso a hankali yafara tashinta da kyar ta iya bude idonta ta kalleshi ganinshi cikin yasa ta fadin "honey in kuma zakaje cikin daren nan? Murmushi ya sakar mata yace"asibty zanje rumaisah ta haihu.... Ba shiri ta mike zaune kirjinta sai bugawa yake tace"cikin daren nan? Yace"dama haihuwa yana da takamaiman lokacinsa ne...... Tace"a....ina nufin....ince cikin daren nan zaka tafi bazaka bari da safe ba? Binta yayi da wani irin kallo yayinda ta kuma cewa "honey kasan fa anguwan nan ba lfy kwanaki da baka nan 'yan fashi sunyi ta shigowa anguwan suna barna sai da ka dawo abin ya lafa snn yanzu kace zaka fita kai kadai cikin wnn daren ? Murmushi yayi hade da fadin karki damu babu abinda zai sameni .sai na dawo ki tashi ki rufe kofa. Ya wuce zai fita da sauri tasha gabansa a shagwabe ta fara magana"honey don Allah kar ka tafi ka barni ni daya tsoron gidan nikeji se dai mu tafi tare. Yace"to kiyi maza mu tafi karki batan lokaci banda abinki gidan nan fa cike da securities yanzu snn hakim da munir suna nan ga mai aikinki. Ita dai tuni ta daura zani kan kayan baccinta ta saka hijabi .daga nan fita sukayi zuwa harabar gidan har zasu shiga mota suka jiyo karar harbin bindiga ba shiri salmah tasa ihu ta kamkame ya salman . Dan tsaki yayi yace"ke ba komai fa don Allah mu tafi . Jikinta na rawa ta fada motarsa tuni ya shiga yaja motar suka fita. Lokacinda suka iso ni kuma muna kokarin ba baby nono mama da wata nurse suke nuna min yadda zanyi tab ashe bada nonon ma wani aikine daban. Su ya salman na shigowa na saki murmushi shima da sauri ya karaso tini na mika masa babynsa karbanta yayi ya rumgume a jikknsa cikeda farin ciki sai dariya yake. Mama tace"salman sai da kuka zo cikin daren nan .Salmah sannunku da zuwa zauna kan kujeran can. Salmah da tunda suka iso sai yatsunar fiska take taje ta zauna akan kujeran ta fara gaisheni hade da yi min barka snn ta gaida mama . Ya salman kam ya manta damu gabadaya babynsa kawai yake karewa kallo hade da daukarta hoto a waya.yana murmushi sai Masha Allah yake ta maimaitawa. Gabadaya zuba masa ido mukayi ni da mama muna dariya salmah kuwa sai in mun hada ido ta danyi yake. Can ya dago ya kalleni snn ya kalli mama yace"goggo Amina babyn nan fa dani tayi kama sosai ko kin lura? Dariya sosai mama tayi tace"eh da kai take kama salman .amma fa tun dazu kake rike da ita baka baiwa salmah ita ba. Salmah tayi murmushi tace"Goggo kawai ki barshi sai ya gaji da kallon babynsa. Mama ta mike hade da fadin "to bari na baku waje . Har zata fita ta juyo ta kalleni tace"rumaisah ki bata nono fa kinji abinda nurse dinda ta fita tace koh? Nace"eh mama. Tana fita yaya salman ya mikawa salmah baby ta karba tana murmushin da bai kai zuci ba . Tana karban babyn ya rumgumeni cike da fara,a ko kunyar salmah baiji ba ya shiga kissing dina hade da fadin"baby nagode sosai Allah ya miki albarka gaskia bazan iya fada miki irin murnar da nake ciki a yau ba . Murmushi nakeyi yayinda nake dan janye jikina daga nashi saboda banson salmah ta ji wani iri. Ya dago yana kallona yayinda yake rike da hannayena yace"babyna ina fatan dai bakijin komai yanzu? Nace"babu komai yaya lfy lau nake jina . Yace"masha Allah gaskia naji dadi sosai. Gabadaya mun shagala muna hira mun manta da wata salmah. Can mukajiyo kukan baby da sauri ya salman ya mike ya karbeta yana cewa "salmah me ya sameta? Tace"inaga yunwa takeji ka bata mamanta tasha nono. Da sauri yaya ya kawota ya mika min yana "gaskia kam yunwa takeji ki bata tasha. Na karbeta hade da fadin "nifa ban wani iya bada nono ba ka kira min mama tazo ... Ya katseni da fadin "ba sai an kirata ba gyara ni zan koya miki yadda ake shayarwa. Ya dada kusanto yana shirin kai hannunsa gaban rigana . Salmah haushi duk ya cika ta don haka bazata iya gani ba kawai ta mike ta fita. Mu dai bamusan ma ta fita ba sai kokarin sawa baby nono muke a baki ni dashi da kyar muka samu ta kama. Yaya ya sauke ajiyar zuciya hade da fadin"Alhamdulillah har naji sanyi a raina wlh banson jin kukanta. Bayan ta dan sha ya salman ya karbeta anan ya mata addua ya mata huduba da suna *AISHA* innah ta samu takwara Allah dai yasa kar ta dauki halin innah *amin* Inna kuwa kasancewar ba ita ce da girki ba bata sami labarin haihuwar ba abbah yace sai gari ya waye zai sanar da ita. Aikuwa yana dawowa daga masallaci ya tafi dakinta ya sanar da ita cike da farin ciki innah ta washe baki tace"Alhamdulillah Allah mun gode maka me aka samu alhaji? Abba yace "mun samu Aisha salman ya fada min ke yayiwa takwara..... Abba be gama magana ba innah ta rangada guda wanda ya tashi sadiya wacce yau kwananta biyu da dawowa daga lagos. Abba kam dariya yayi yace"shatu ba kyau fa hamdala zakiyi kedai. Inna cike da fara,a tace"Alhamdulillah Alhaji amma ka barni inyi guda ma Allah ya amshi adduata. Abba yace"to se ki shirya muje asibity. Inna tace"yanzu kuwa. Abba ya fita yana dariya . Sadiya kuwa tunda gudan innah ta tasheta ta fito palo tana kallon innah sai da abba ya fita tace"innah gudan meye kikeyi? Inna ta juya tana murmushi tace"na karuwa mana yau Allah ya amshi adduata rumaisa ta haihu kuma harma salman ya min takwara. Dam! Xuciyar sadiya ta buga duk yadda taso ta boye bakin cikinta ya gagara sai da ya fito fili Tace wa innah shine har da wani guda kamar yau kk fara samun jika innah? Nan da nan inna ta daure fuska tace "to uwata gaya min.wai ma ina ruwanki da ni ne? Gsnin haka yasa sadiya fadin Allah ya baki hkr innah. Ta juya ta tafi daki cike da bakin cikin wnn labarin mara dadi. Kamin gari ya karasa wayewa asibity ya cika da mutane.in tsaya fayyace muku irin farinciki da muke ciki bata lokacine . Tunda na haihu nake ta samun alkhairai ta koina Alhamdulillah. Ranar sunan *AISHA* *FAREEDA* gidan mama ya cika taf ba masaka tsinke .kaya kuwa mun samu har mun rasa inda zamusa . Inna ma tayi rawar gani gun hado ma takwararta kayayyaki sai wanda ya gani.bangaren ya salman da daddy ba,a magana . Anyi suna qalau an watse qalau ba wata matsala sai sambarka . Masu bakin ciki suna fama su sadiya da adda A'i.Salmah kuwa har fushi tayi tace zata tafi gidansu sabida ya salman ya daina kulata tunda na haihu baida lokacinta yana danne mata hakki. Aikuwa ko kallo bata isheshi ba har ta gama fushinta ta fasa komawa gidan nasu lol! Don ta lura in dai ta salman ne bai ki ta tafin ba..... Hauly ce🥰👍🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡84 **********Alhamdulillah yanzu kam Rayuwa tayi mana dadi babu wata matsala. Saida mukayi satinmu shidda snn muka fara fita gidansu innah muka fara zuwa wai karkuso kuga farin ciki gun innah kamar ta goyamu .ta karbi farida tayi ta mata rawa. Gashi tayi wayo sosai ga ta dama tubarkallah katuwa hasken fatarta kullum karuwa yake ga dariya kuwa ko wani motsi in dai idanta biyu dariya takeyi ko fanka ta gani yana kadawa ta dinga dariya knn. Gaskia na lura ba karamin shiga ran innah farida tayi ba motsi kadan zata dauketa har da goyo wani abin dariya ma har Tadi take mata. Sadiya kuwa ba karamin haushi takeji ba don har ta gaji tacewa innah"kai innah irin wnn so haka naga ba,a kanta kika fara samun jika ba ko dan takwararki ne? Ga Abdul dina shine jikanki na farko wanda a gidan nan na haifeshi a dakinki yayi wayo amma sam baki damu dashi kamar wnn ba...... Inna ta katseta da fadin"don me zan damu da Abdul din irin rashin mutunci da ubansa ya dinga shimfida mana a anguwan nan ba irin zagin duniya da bai mana ba nida abbanki musamman ma ni marainiyar wayonsa ranar da naje don a sasanta ina rufe ido yayi ya zageni tass .kina nan kwanaki na tura sa,a nace a kawo min su Abdul na gansu ba turowa yayi yace"baza a kawo su ba saboda shi mara kunya baisan darajar babba ba.don haka ni ba ruwana da wasu Abdul suje can suyita zama da dangin ubansu din marasa mutunci. Nida nake zaune shiru tun dazu bansa musu baki ba sai yanzu nace"sai hkr innah basu kyauta ba gaskia amma duk daren dadewa yaran nan in suka girma zasu zo gun uwarsu abu gari daya anguwa daya ma wlh karki daga hankalinki. inna ta tabe baki tace"oho ya rage nasu yanzun ma da ya hanasu zuwa Abdul ai indai ya tashi makaranta baya kwana biyu bai biyo ta nan ya gaida uwarsa ba. Nace "Allah sarki kinga ya yi wayo knn.Allah ya rayasu ya masu albarka. inna ta amsa da" amin kawo kayan shatu a samata mun gama shafe shafenmu yanxu kam saura musa napkin da kaya. murmushi nayi nace"to bari na dauko. Sadiya kuwa tunda innah ta fara magana taja bakinta tayi shiru na lura ranta ba karamin baci yayi da maganar innah ba duk da dai tasan gaskiane . bayan na dauko kayan farida da pampers na kawowa inna da turaranta innah ta karba hade da fadin"au matar har da turare ma takeda shi? nan ta shirya farida tsaf ta kama yi mata wasa sunata dariya yayinda sadiya duk ta gama cika.A ha ka ya salman ya shigo ya samemu tunda ya shigo ya saki fuska yace"Innah hira kk yi da mai sunan naki knn? Inna tace"eh mana baka gani sai dariya take tayi kazo zaka katse mana hiranmu na kawaye. dariya mukayi ysyinda innah ta mikawa ya salman farida tace"riketa kuje ta gaida maigidanta nima wanka zanyi yanzu inzo inyi kwalliya sai muyi hoton solfie da me sunana.ko ba solfie kk cewa ba turawa. Bani kadai ba harda ya salman saida yayi dariya snn yace " hakane innah selfie ba. Inna tace"koma dai bahaka ba tunda kun fahimceni ina zuwa. daga nan ta tashi ta fita.ya salman ya kalli sadiya hade da fadin ke kuma lfy kk ta wani zumbure zumburen baki ? fuska daure tace"babu komai ina kwana. ya amsa mata da lfy.snn ta tashi ta wuce daki. ya salman ya zauna kusa dani hade da fadin "wai don Allah yaushe zaki dawone babyna wlh inata kewarki. murmushi nayi nace"yaya ai bangama yawon arba,in ba sai naje Abuja da yola tukun. yace "haba baby na gane yanzu ba kya missing dina sam . a hankali nace"inayi mana yaya sai dai kasan dole ne inyi wadan nan tfy tfyn sai dai ka kara hkr idan mun dawo dai shikenan ai. yace"to ya na iya Allah ya bada sa,a ya kuma kiyayeku. Nace"ameen. ya kalli fareeda yana murmushi yace"innata zaki tafi ki bar daddy ko? ya mika min ita hade da fadin gaskia a bata nono tashi tana jin yunwa na taba cikinta ba komai. karbanta nayi tasha baysn ta koshi ya dauketa suka fita .basu shigo ba har bacci ya daukeni .bansan ya suka kare ba su innah ko anyi selfien oho. Satinmu daya da kyar innah ta barmu muka wuce Abuja gidan kawu kasim na fara zuwa kwanana biyu snn naje gidan goggo ummi itama na yi kwana biyu daga nan sai gidan ya salim gaskia ruma taji dadin zuwanmu ga babynta mimi ta girma ita ma sai wayo.munsha hira sosai kwanan mu biyu muka wuce yola Gidan galadima na fara sauka gunsu hajia rumaisa gaskia sunyi ta murna har da 'yan koke koken murna abinka da tsufa lol! Sai da na gama zaga dangi kaf snn na dawo gidanmu kai masha Allah gidanmu ya cika da yara kamar yadda daddy yakeso ga na aunty samira maza biyu ga kuma na mama su biyu don haka gidan ya min dadi sosai kamar kar in tafi doma aunty samira tace gyaran jiki za,amin na musamman wnn karon sai na koma kamar sabuwar amarya kai aunty samira ba dama don haka na dakata aka fara yi min gyare gyare kamar wata amarya. sati biyu muka dauka muna abu daya ya salman ya damu da batun dawowata har aunty samira ma sai da ta gane tace "gaskia ihsan ki gode Allah mijinki naji dake sosai ki duba duk da yana tare da wata amma kullum sai ya kiraki ya tambayeki yaushe zaki dawo. murmushi nayi bance komai ba ta sake cewa don haka ki rikeshi hannu bibbiyu ki kyautata masa ki masa biyaya sosai kinji? Nace"in Allah ya yarda zan masa biyayya aunty . Tun kamin na bar yola yaya ya turo min hotunan funitures in zabi wanda raina ke so za,a canza min gaskia sun hadu ba karya nan na zabi wanda raina keso na nuna masa. Kamar gobe zan tafi na tafi aka rangadamin kitso kanana irin na amare da lalle se kunga yadda nayi kyau kamar wata amarya don sam banyi kama da me shayarwa ba .ni kaina inaji a jikina zam zam ne. Washe gari kuwa muka tafi airport bayan mun sallami kowa gaskia Farida ta sami kudi sosai kyaituttuka kullum akan samu muke sai godiyar Allah. Da yamma muka iso yaya ne ya zo ya daukemu a airport tunda muka sauka ya karbi farida yana kallonta yana murmushi yace"mama na barkanki da dawowa inata missing din dariyarki. Nace"itama tayi missing din daddy dinta sosai. Ya kalleni yana murmushi yace"baby irin wnn kyau haka kamar amarya to ko dai transfer zanyi mu koma yola da zama ne naga garin ya karbeki sosai kin koma fresh . Dariya nayi bance komai ba na wuce mota ya bini da kallo snn ya danyi ajiyar zuciya ya mika min fareeda . Mun fara tfy salmah ta kirashi bansan me tace mishi na daiji ya amsa mata da "Aa ban yarda kije ba ki aika aje a dubota tunda ba asibity take ba in yaso ranar sunday ni se na kaiki da kaina . Yayi shiru yana sauraranta nan naga ya daure fuska yace"kinga nifa ban yarda ba idan kuma kk fita to saidai ki koma gidanku! Da sauri na kalleshi yayinda shi kuma ya katse kiran nace"yaya mene ya faru? Dan tsaki yayi yace"baby ban gane meke damun salmah bane na lura kullum tafi son ta dinga batan rai . Nace"amma kamar naji kuna magana ne akan mara lfy zataje ta duba.... Ya katseni da fadin eh hanan dintace baban ya bugo mata wai bata da lfy serious bataje ta dubata ba shine ta daga hankali zataje. Nace"haba yaya ai be kamata ka hanata taje ta duba 'yarta ba koda kuwa ba rashin lfy ba.ka dinga hkr kana sassauta zuciyarka don Allah. Fuska daure yace"Rumaisa ni fa bana son rainin hankaline idan har da gaske rashin lfyr serious ne me sa ba akaita asibity take kwance a gida yanzu ke kin yarda rashin lfyr ne da gaske? Ni fa kinga duk abinda zamuyi da mutum nafi son muyi gaskia da gaskia kawai ta fito ta gaya min tana son zuwa taga yarta amma ba wai ta tsaya tana kwana kwana ba. Murmushi nayi nace"yaya kenan amma ni kuma a tunani na ba yanda za,ayi uwa tayiwa yarta fatan rashin lfy.ka dai bincika kaji.amma ni nafi tunanin kawai baka son salmah taje gidan tsohon mijinta ne. Ya juyo da sauri ya kalleni yace"ke sharri zaki min ido da ido ? Dariya nayi nace"ni dai don Allah ka cire wnn a ranka ka barta taje ba bu komai pls nima na rokan mata ga fareeda ma tana son ka bar auntynta taje ta dubo 'yarta. Ya girgiza kai yace"yanzun na rigada na zartar da hukunci ko zan barta taje sai gobe. Nace"to shikenan Allah ya kaimu yau da goben duk daya ne a wurin Allah ai. Daga nan shiru yayi har muka isa gidan mama tun kan mu shigo mama ta fito ta tarbemu cike da fara,a ta karbi farida tana cewa "o sarkin dariya duk nayi kewarki wlh .jiya har mafarkinki nayi gashi zaki koma gidanku ki barni da kewa. Kallon juna mukayi da ya salman muna murmushi.mama tace"ku isa ciki ni dama kawata nazo yiwa oyoyo. Muka wuce ciki ta kawo mana drinks da snacks tace"an kusa gama girki ku kara hkr. Ya salman yace ba komai goggo ni a koshe ma nake .yanzu ma kuma zan koma wajan aiki. Mama tace"shiyasa na ganka cikin kaki. Anan suka gaisa tace "kamin ku iso dazun salmah ta kirani tace min 'yarta ba lfy tana son taje ta dubota kai kuma ka ce bazata je ba in kuma taje ta koma gidansu hakane? Ya danyi shiru snn yace"hakane goggo ni fa na gajine da rainin hankalinda salmah suke min da tsohon mijinta motsi kiris sai ya nemeta.alhalin yasan ba zaman kanta take ba kawai don suna da'ya kwalli daya sai su dinga ..... Mama ta katseshi da fadin"haba salman karka bari zuciyarka ta tuna maka wani abu daban ni dai kawai ka barta taje domin hankalinta ya tashi sosai tunda kaga har ta kirani ta gaya min . Yace"to shikenan goggo ki fada mata taje da sa,adatu kuma kar su wuce awa biyu su dawo . Mama tace to shikenan na gode. Tashi yayi yana shirin fita nace"to yaya a huta gajia. Ko kulani baiyi ba ya fita dan dariya nayi nace"mama kin batawa danki rai . Tace"ai salman halinsa se shi in ba murdadden haliba meye abin daga hankali anan. Nace"hmm.ai yau kinja mata bala,i in ya koma gida ya sameta ta shiga uku shi fa baison akai kararsa. Mama tace"to ba dole ayi kararsa ba tunda yayi ba dai dai ba . Nace"ni ina mamakin ma yadda salmah ta kira ta fada miki ko don har yanzu innah ta ki sakan mata fiska. Mama tace "hmm ai shatu ma halinta se Allah bata da yafiya ko kadan abu tuni ya wuce amma tana ta riko. Nace"Allah de ya kyauta.bari ma inxo in kirata in ce mata mun iso qalau. Na lalubo wayata na kira innah ba jimawa kuwa ta daga hade da yi mun sallama. Na amsa fuska sake nace"innah mun iso faa. Tace"to Alhamdulillahi barka ya mai sunana ? Nace "gata nan innah gobe in Allah ya yarda zan kawo miki ita. Tace"da kuwa kin kyauta nayi kewan arhan dariyan nan.to yanxu ke yaushe zaki koma dakinki ne don a gaskia kin dade a gidanku tun cikinki na karami .yanzun ai yakamata ki koma koh? Murmushi nayi nace eh dama innah jibi zamu koma don ma ina son kintsa yan kayanmu ne. Tace"har jibi ? Ni da nake son in ce ki koma yau.amma gaskia jibi kam yayi tsawo gobe dai ki koma in yaso Amina ta biku da kayanku daga baya .kinga salman yana bukatar shatu kusa dashi yanzu. Nace"to ba komai innah zamu koma goben in Allah ya kaimu rai da lfy. Tace"yawwa to nagode ku huta gajia. Nace"toh nagode. Na katse wayar na kalli mama nace"mama kinji innah tace mu koma gobe jibi yayi nitsa. Mama tayi dariya tace"shatu knn hmm aini ko yanxu in kunga dama kwa iya tfy na sallameku in yaso daga baya idan na hada muku kayayyakin ku zan hada lami da driver a mayar muku. Tashi nayi na wuce dakina ina cewa mama goben dai. Haka kuwa akayi washe gari muka shirya tsaf yaya yazo ya daukemu da yamma gidan innah muka fara zuwa snn muka wuce gidan mu. Mun tarar da salmah a babban palo ta hakikance kan babban kujera anci kwalliya ana jiran dawowan oga inaga bata san da dawowana ba don tana ganinmu tare dashi na ga ta mike da sauri tana binmu da kallo. Nidai mamakin yadda salmah ta zauna ta gina jiki nakeyi wato taji dadi sosai bayan bana nan tana cin karanta ba babbaka gashi ya cika mata gida da 'yan aiki kota ina ko tsinke sai taso take dagawa don haka tayi wani irin jiki har ta so tayi muni. Fuskarta ba yabo ba fallasa ta tashi tanai mana sannu ta karbi farida dake hannun ya salman tana cewa" farida ta girma honey tubarkallah masha Allah. Baiyi magana ba har zamu wuce ya juyo ya kalleta yace"ya jikin hanan din ko har an sallamesu? Tace "da sauki ba,a sallamesu ba yanzu dama jira nake ka dawo inje in sake dubota. Har ya fara hawa stairs snn yace"ki gaisheta.Allah ya bata lfy. Tace"ameen. Ni ma na mata adduan samun lfy snn nabi bayan ya salman muka tafi side dina tunda na shiga nake bin funitures dina da kallo dama duk na kosa inzo in gani .gashi sa,adatu ta gyara koina tsaf se kamshi ke tashi na ajiye jakata nazo gaban yaya fuskata cike da murmushi nace" gaskia yaya ka birgeni sosai nagode Allah ya kara budi Allah ya barmu tare . Na karasa fada yayinda na kwantar da kaina jikinsa kamar jira yake ya rumgumeni sosai yace"amin babyna ina matukar ji dake my dear kasancewarki abokiyar rayuwata ba karamin farin ciki kika sanya ni ba gabadaya rayuwata ta sauya Allah ya miki albarka. Nace"ameen yayanah. Wayarsa ce ta kira nan yayi reciving ni kuma naci gaba da bin koina da kallo cike da fari ciki . Har ya gama waya ya kalleni yace"ki shirya kece da kitchen yau zaki mana dinner. Na dan zaro ido nace"yaya why not gobe.... Yakatseni da fadin"bazan iya hkr har gobe ba yanzu ma da salmah nayi magana tunda zata tafi asibity yanzu kuma dama tace batayi dinner din ba se kiyi ke. Nace"yaya kana ganin bazata damu ba.ni a ganina da ka bari sai gobe..... Rumgumeni ya kara yi yace"ni bazan iya hkr ba yau .kinganki kuwa my dear yadda kk koma kamar wata budurwa 'yar shekara 20 se kace ba kece maman baby ba sai wani shining kk kinyi fresh gwanin sha,awa.ina yau fa ki hkr kawai ki shirya tahowa turaka don gaskia na miki shiri na musamman nima. Ya shafa marata hade da fadin "zamu samowa innata kani. Zaro ido nayi da sauri yayinda yayi dariya ya sakeni yace"bari inje in dauko farida . Ya fita nima tuni nayi gama abinda nakeyi nayi shirin shiga kitchen duk da cewa ya sanar dani akwai masu aiki amma nace ni bana son a min girki zanyi da kaina na kara da fadin me za,a dafa maka? Yace"tuwo da miya don na jima banci girkin ki mai dadi ba.ki min miyar kuka irin naku na 'yan yola mai dadin nan da tuwon semo . Nayi dariya nace"kai yaya lallai kaji dadin wancan miyar har ka tuna min bari inje in sa maka furanka a fridge. Na wuce yayinda ya bini a baya yana cewa bari nazo mu tayaki ni da farida kuma kisa min furan a cup na fara sha . Nace"to.amma fa bazan baka da yawa ba kar kazo baka ci tuwo ba. Tare muke girki a kitchen muna hira har munir ma ya dawo tare da hakim da sa,a munir ya rumgumeni yana momy oyoyo . Nace "oyoyo good boy nayi kewarka dear. Na fada ina shafa kansa nace"kuje palo bari inzo in shirya mana dining in mun ci abinci se muyi hira yau zaka bani labarai ka shirya kaji? Yace"ok mum. Sa,a kuwa tuni ta karbi fareeda. Ina shirya dining magriba tayi don haka su yaya suka tafi masallaci nima da na ga ma na tafi nayi sallah . Sai bayan anyi sallar isha ne muka hadu a dining gabadaya harda salmah don ta dawo. Bayan sun zazzauna na fara yi mana serving.hakim yace"wow wnn miyar zaiyi dadi sosai na sani don nayi missing din miyar gargajia. Ya fada yayinda ya kashewa salmah ido harara ta sakar masa tace "kaji da munafurcinka dai. Sa,a tayi dariya tace"gaskia ni ma yau sosai zanji hakim. Munir yace "ni momy bana son irin miyar gidansu innah. Nace"to me zakaci good boy? Yace"a dafa min indomie da kwai kawai . Har zan tashi ya salman yace"ki zauna. Snn ya kalli munir yace"big boy miyar fa yayi dadi sosai kaci zakaji dadinsa indomie bazai maka amfanin komai ba bakaga yanzu ka dan rame ba kaci tuwo sosai zaka girma ka zama doctor. Yace"to daddy mummy a min serving kadan. Hakim yace"ai yaya karkaga laifin munir aunty salmah ce tace mana miyar kuka na toshe brain. Dariya nayi nace"a lallai shiyasa good boy yace bazaici ba ashe. Munir ya kalli farida dake hannun babanta yace"daddy farida yaushe zata fara cin tuwo ta zama big girl. Ya salman yace"very soon dear. Snn ya kalli sa,adatu yace"sa,adatu yaushe innata ya kamata a fara bata abinci kune likitoci. Sa,a tace"da tayi wata shida za,a fara bata ruwa da kunu snn a fara bata fruit kadan kadan da dan abinci masu gina jiki kadan kadan har ta saba. Nace "hmm naji kina da an fara bata ruwa mu fa bama exclusive breastfeeding ruwa muke bata sosai kuma tana sha. Tace"ai kuwa aunty da kunyi yana da kyau yaranda suke shan nono zallah daga haihuwa zuwa wata shida sunfi masu shan ruwa lfy . Hakim yace "ai se ki bari in kin haihu se kiyi tunda daga ke har saurayin naki likitocine. Harara ta watsa mishi tace"hakim wlh ka kiyayeni. Dariya nayi nace"hmm to ya isa haka aci abinci dare yayi . Ya salman da salmah tuni suka tashi inaga dakinta ya bita.don tun dazu sai wani ciccika take . Sai da na tabbatar masu aiki sun tattare koina snn hakim da munir suka min se da safe saura ni da sa,a nace "to matar doctor hafiz ina kuka kwana da zancenku yanzu ai makaranta ya kare kuma kinga zainab tuni an kawo komai na aurenta har date kuma ya kamata ace an hada gabadaya mu kauda ku mu huta . Tace"aunty ai hafiz din ne..... Na katseta da fadin ba wani ya hafiz don shikam tuni ya dhirya komai ce min yayi kina ta mishi kwana kwana ko dai baki sonshi ne? Tace"aa wlh aunty dama zance masa ya turo ayi maganar ne kwanan nan amma yace min yana tunanin aina zamu zauna shine nace to se ya gama tunanin. Nace"hmm lallai a gaisheku dukanku bari kiji daga ke har ya hafiz idan baku cire jiji da kai ba bazaku daidaita kanku ba.maganar aure fa ya wuce wasa ba wai ku zauna kunaja ma juna aji ba. Dariya tayi tace"aunty wlh shine yake ja min aji kinsan samarin yola fa aunty girman kai ne das.... Nace"au abin harda cin fuskane. Tayi dariya tace to shikensn aunty kiyi hkr kwanan nan zakiji labari mai dadi. Nace"to Allah yasa. Daga nan tayi min sai da safe nima na wuce dakina wanka nayi mai rai da lfy na zauna na bata awa guda gun kintsawa sai da na tabbatar koina tsaf tukun snn na saka kayan baccina mai shara shara komai na a waje hannunsa tsiriri kuma tsayinsa iya gwiwa sai da nayi juyi a gaban mirror naga yadda rigar ya zauna min a jiki snn na daura zani na saka hijabina na dauko chewing gum dina orbit na bare na jefa baki snn na fita na kulle sashina na wuce part din oga na sameshi har ya dawo daga dakin salmah yayi wanka shima ya shirya cikin kayan baccinsa farida ma ya mata wanka na tarar yana ta kokarin sa mata pampers dariya na musu. Ya juyo ya kalleni hade da fadin "ba kin shanya mu ba tun dazu muke jiranki. Nace"ni na dauka kuna hira a dakin salmah ne fa, Yace"tuni mun dawo zo ki sallami mamana kamin nan bari inje in tabbatar kun rufe koina da kuma kayan wuta don kuna barin komai a kunne. Ya fita ni kuma na karasawa farida shiri na bata nono tayi bscci da ya shigo kawai ya shimfide ta ya mata addua snn ya kalleni hade da kashe min ido daya yace "yau fa jina nake kamar ango. Ni dai mamakin yadda ya salman keta zumudi nake. Ya karaso gabana yace"taso in ga kwalliyarki. Cikin jin kunya nace "yaya rigar baccine fa wanda ka saya min...... Tuni ya dagani duk kunya yabi ya rufeni shikam bina yake da kallo koina nan da nan ya yanayinsa ya fara canzawa. A raina nace"yau kuma nasan sai nayi da gaske zan kwace kaina a hannun yaya. Tuni yaya ya shiga sarrafani cikin salonsa me tfyr da hankali nan da nan jikina ya shiga karbar sakonninsa ba shiri na cire kunya na shiga taimaka masa haba aikuwa kamar na kara zuga shi sai zuba min kalaman soyayya masu zafi yake duk ya rikice tun ba,aje koina ba don haka tuni ya cire rigan baccin jikina yayi jifa da shi ya kashe wuta mai haske ni kam ido ya raina fata a yayinda yake karanto adduan saduwa da iyali don ni kaina nasan na koma na matse sosai don haka da kyar ya wuce har na saki ihu ba shiri da sauri ya hada bakinsa da nawa gudun kar mu tashi fareeda .amma da tfy tayi nitsa tuni muka manta da wani fareeda ni kam kuka na soma yi sosai don na fara jin jiki shikuwa sai sambatu yake zuba min .da kyar na samu ya rabu dani gabadaya jikina yayi tsami gashi an kwana biyu ba,a hadu ba gabadaya nayi laushi shi kam da ya dawo hayya cinsa rumgumeni ya dada yi yace"baby kinjiki kuwa yau kinfi zuma zaki wow gaskia yau kin gama tfyr da hankalina gabadaya na manta a wacca duniya na shiga.sorry nasan kinji jiki sosai bari zan taimaka miki kiyi wanka da ruwa mai dumi ko zakiji dadin bacci .Allah ya miki albarka babyna gaskia kin sanyani nishadi mara misaltuwa. Nidai kin magana nayi don na gama jigata don haka tashi yayi ya wuce toilet ya hado ruwa mai dumi snn ya fito ya sameni yaye bargon yayi maimakon ya taimakamin mu tashi kawai ba sai naga yana kokarin ware min legs ba ba shiri na sa mishi kuka nace ya ya ka bari don Allah wlh yaya jikina ciwo yake. Rumgumeni yayi yana shafa kaina a hankali yace"pls dear ki taimaka min bazan dade ba wlh ban gaji dake ba. Kamar da wasa ya salman kwana yayi aiki daya kamin gari ya waye ko yatsana ban iya dagawa gashi yaci sa,a farida batayi rigima ba. Saida ya taimakamin na gasa jikina da ruwan dumi sosai snn ya barni ya tafi masallaci koda ya dawo ya sameni ina gyangyadi a kan sallaya murmushi yayi yazo ya dagani ya kaini gado ya kwantar dani. Duk yadda naso in tashi in shirya mana breakfast abin ya gagara saida sa,ane ta shiga kitchen da masu aiki suka shirya komai . Mu ne bamu fito ba har sai sha daya da rabi.koda muka fito salmah sai faman daure fuska take kamar zatayi kuka........ Hauly ce🥰👍🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡85 **********Ya salman yace mata "salmah ya akayi. Tabe baki tayi snn tace "ina kwana? Yace"lfy . tace "tun tuni nake jiran ka ka fito zan je asibity in sake dubo hanan. yace"ki jira bari muyi breakfast sai muje dukanmu har da rumaisa.ina sa,adatu. Tace "nima ban ganta ba . Ni dai tuni na wuce dining na barsu karshe ma ce mishi tayi ita bazatayi breakfast ba . Bayan mun gama muka tafi asibity gabadaya muka bar sa,adatu a gida da farida don babanta yace bai son muje asibity da ita saboda cututtuka gashi jikinta danye. Allah sarki ashe asma ne hanan din ke fama dashi kirjin nan ya toshe gabadaya sai da akasa oxygen gaskia na tausaya mata gata kankanuwar yarinya bata wuce shekara shidda ba sa,ar munir ce. kuma batayi sa,ar matar uba don bata kula da ita shiyasa gabadaya hankslin salmah ya tashi. bamu wani jima da zuwa ba baban yarinyar yazo wato tsohon mijin salmah.hmm nan da nan ya salman ya murtuke fuska ko gaisuwar arziki bai yarda sunyi ba yace"ke mu tafi. A hankali tace"don Allah suleyman ka barni anjima zan dawo hanan tana bukatana a kusa da ita. Har zaiyi magana nace"aa yaya ka barta dan Allah in yaso anjima sai ta dawo . Baiyi magana ba ya fita na kalli salmah snn nace"Allah ya bata lfy bari mu tafi. shiru tayi bata ce min komai ba. na fita na iske yaya a mota muka dawo gida mun tarar farida sai wasa take da saurri ya salman ya karaso ya dauketa yana dariya yace"innata gaskia kina da hkr . Ya kalleni hade da fadin kizo ki bata nono tasha gaskia tana jin yunwa . haka na zauna na baiwa farida nono har tayi bacci sa,adatu ta dauketa taje ta kwantar nima nabi bayanta ina kokari canza kayana in tafi kitchen ya salman ya kirani a waya ina dauka wai inzo dakinshi in sameshi. Kai yaya baya gajia ni har yanzu jin jiki nake ina dai dauriya ne kawai. Na kalli sa,a nace"sa,adatu kar ki jirani kuje ku fara girki kawai zanzo daga baya. Tace"to aunty me za,a dafa? Nace"ki duba time table na manna jiya. Tayi dariya tace"gaskia aunty kina da kokari wurin tsara aikin gida ya tafi normal yadda ya kamata. murmushi nayi nace"ai komai da tsari yafi sauki saadatu. Tace"hakane . tana fita saida na shiga toilet na sake wanka tukun na shirya snn na tafi dakinsa na sameshi kwance ya kure Ac dakin ya dauki sanyi sosai idonsa a rufe alamun bacci yake . Hamdala nayi a zuciya ta na yi sanda a hankali na je na kwanta gefensa ina shirin jawo bargo na rufe kawai naji an rumgumeni ba shiri nace "wayyo Allah yaya dama ba bacci kk ba. Kissing lips dina yayi hade da fadin" ina zan iya bacci dear ba tare da naji dumin jikinki ba snn kamshin turaranki mai sanyin kamshi. Ya fada yayinda ya fara shafa kaina a hankali cikn wani irin murya mai cike da shauki yace "babyna. Nima a hankali na amsa da "na,am yayanah. Yaci gaba da shafa koina jikina yace "kinsan me nakeso dake? Girgiza kai nayi don bazan iya magana ba saboda yadda yake ta shashshafani duk naji jikina wani iri na lumshe ido ina sakin ajiyar zuciya . yace"ina son duk abinda na miki nima ki mun kinji? kai na daga mishi.don haka nan da nan muka lula duniyar masoya mai cike da nishadi da annashuwa.nima na dage wurin ganin na rikitashi sosai saida muka gaji dan kanmu muka saki juna.sai faman ajiyar zuciya muke tsawon lokaci muka dauka ba tare munyima juna magana ba. Karar wayarsa ce tasashi mika hannu ya daukota hade da yin receiving yace"ina jinka Solomon. yayi shiru yana sauraran bayanansa snn yace"okey ba komai kuci gaba da aikinku . Daga nan ya kashe wayar tashi yayi ya wuce toilet wanka yayi snn nima yazo ya dagani cak mukaje toilet ya min wanka.bayan mun fito ya taimaka min nasa kayana daganan yace na kwanta nayi bacci yana zuwa. Ya shirya a gurguje ya fita Nima yana fita na tashi ina fadin wani bacci zanyi na bar sa,a ita kadai ga farida ga kitchen duk da ma akwai masu aiki amma sam aikinsu bai cika burgeni ba . Don haka na tashi na fita palo nima. Ya Salman bai dawo ba har sai bayan sallar isha suka shigo tare da salmah nayi musu sannu da zuwa yaya ya karbi farida ita kam salmah ko kallo ban isheta ba ta wuce zata hau stairs nace"salmah dinner fa is ready ku muke jira dama ko se kin fito? Kai tsaye tace "ni na koshi. Daga nan ta haura sama ya salman ya bita da kallo snn ya kalleni yace"karki damu inaga taci a asibityn ne. Nayi murmushi snn nace"babu komai ya jikin hanan dinne ? Yace"da sauki an sallameta ma . Nace"masha Allah Allah ya kara lfy. Daga nan muka tafi dining mun fara cin abinci knn munir da hakim suka shigo don haka bayan mun gama hira muka shiga yi a palo bamu sani ba har ten ya salman ya tashi da farida suka tafi. Anan muka watse nima naje na yi wankan tfy turaka lol! Duk da inajin jiki amma bana iya sassautawa kaina duk abubuwanda aunty samira ta bani wnn karon bana wasa amfani nake dasu sabanin da sai dai inta ajiyarsu. Da safe kuwa misalin 10:30 muka gama shirinmu. Yana tsaye a window yana hangen harabar gida nikuma ina shirya farida bayan na gama na kalleshi nace"yaya mun gama. Jin da nayi shiru yasa ni tashi na tafi window din nima ina lekawa naga salmah ce da tsohon mijinta wanda ya kawo 'yarsu don an bude masa get be shigo ba saida ta fita taje ta dauko 'yar. Da sauri ya saki labulen bai biyo ta kanmu ba ya fita da sauri nikam haka kawai naji gabana na faduwa na bishi da sauri da nufin na mishi magana amma tuni ya fita. A babban palo muka hadu da salmah ta shigo da yarinyar da kuma kayanta. Bai mata magana ba ya fita. Salmah kam tuni jikinta ya bata ya gansune don haka ta tsorata sosai .ina tambayarta jikin yarinyan ma bata jini ba. Na kalli yarinyan nace"hanan ya jiki? Tace"da sauki. Har zan wuce dining se gashi ya shigo fuskar nan a murtuke kamar be taba sanin meye dariya ba ya kalli salmah yace"ke me ya kawo wancan dan iskan kofar gidana kuma waya baki iznin fita ki magana dashi? Shiru tayi ta rasa me zatace.cikin daga murya yace"ko ba dake nake maganah. Ya matsa kusa da ita da sauri taja baya hade da sauke yarinyar da ke hannunta tace"suleyman kayi hkr ba wani abu bane dama ya kawo hanan ne saboda ta matsa zata zo gurina shine ya min waya akan naxo na karbeta...... Bata gama rufe baki ba ya dauke fuskarta da mari sai da ta gigice yace"maganar banza ba nayi warning dinki akan wnn mutumin ba ko kin dauka dan iskane ni? Meyasa bazai turo a kawota ba sai yazo da kansa harda kiranki a waya kije ko? Shine kk je kin bude baki kina masa dariya kun maidani dan iska to bari kiji wlh idan makamancin hakan ta kuma faruwa zaki koma gidanku! Don bazan lamunci rainin hankali ba....... Cikin muryar kuka tace"haba suleyman me yasa duk sanda ranka ya baci hankalinka ke barin jikinka? Na gane tuni zargina kake kuma wlh be kamata ba ni babu abinda ke tsakanina da wnn mutumin da ya wuce case din hanan.kuma nice uwarta dolene in tsaya akan komi nata laifine don nayi hakan .in kana tunanin har yanzu sonsa nake meyasa ban koma gidansa ba nazo na aureka....... Ya katseta da fadin wnn kuma ke zaki baiwa kanki amsa ni dai na fada miki idan kika kuma sauraransa zaki bar min gidana! A zuciye tace"yanzu kuwa zan bar maka gidanka don wlh bazan bari rayuwarta 'yata kwalli daya tak! Ya shiga cikin garari saboda son kanka ba. Ta ja hannun hanan da sauri ta suka wuce sama . Karasawa nayi gurinsa nace"a gaskia yaya baka kyauta ba kuma wlh salmah ta fika gaskia ba ka mata adalci ba. Yace"Rumaisa bansan me yake damuna ba nima haka kawai zuciyata ta kasa yarda dasu! Riko hannunsa nayi na zaunar dashi yayinda na tausasa muryana nace"ka daina zargi ba kyau yaya.kamar yadda salmah ta gaya maka inda tana sonshi me zaisa ta barshi tazo ta aureka? Kuma yaya salmah uwace kasan uwa kuwa tana iya sadaukar da dukkan farin cikinta ...... Fitowar salmah ne ya katse mu tana rike da jakar kayanta alamun tfy zatayi. Da sauri na tashi nace"haba salmah ina zakije?yanzu saboda wnn maganar zaki bar gidanki?kiyi hkr mana insha Allah komi ze wuce ..... Na karasa gabanta na rike hannun hanan na karbi jakar hannunta kuka ta shiga yi tace"dama kin barni na tafi dan zamana a gidan nan baida amfani kowa ya tsaneni. Na girgiza kai nace"ba haka bane ki hkr . Na kira sa,adatu nace tazo ta maidawa salmah kayanta ciki.ni kuma na daga ilham muka tafi dining. Ta juya ta koma ciki tana kuka shikam yana zaune baiyi magna ba alamun jikinsa ya yi sanyi ya gane bai kyauta mata ba. Tun ranar fa suka dinga samun matsala har ya janyo aljanunta suka motsa nikam gabadaya na tsorata ganin yadda salmah ta koma lokaci daya don wancan lokacin bana nan aljanun nata suka motsa. Sai da tayi sati biyu anata yin magani kamin ta dawo dai dai don har iyayenta na shirin tfy da ita gida sai ta warke.amma sun tafi da ilham. Ya salman dolensa ya sauko suka sasanta.yanzu kam an fara dasawa har yana cewa da ita zasu je umrah tunda ni ina shayarwa a raina nace ku sauka lfy. Don haka salmah take wani jiji da kanta yanzu harda daddauke min fuska take ko na mata magana bata kulani se tayi kamar bataji ba.don haka na shafa ma kaina lfy na kama gabana.dagani har ita yanxu ba mai shiga harkar juna. Har lokacin tfyrsu umrah yayi suka tafi.ya salman ya barmu da kewa ni da fareeda don yanxu tayi wayo sosai har kuka take in yaya zai tafi . Tuni muka fara shirye shiryen auren sa,adatu domin ya salman na dawowa da sati daya za,ayi bikin an riga an kawo komai. Nida innah sai shirinmu muke mu biyu don su adda A'i basa son maganar auren sa,adatu da hafiz sam donma ba yadda suka iya ne da tuni sun wargaza lamarin...... *Kuyi* *hkr* *fans* *jiya* *kunji* *shiru* *Nepa* *ne* *sukayi* *halinsu* 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻 Hauly ce🥰🙏🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡87 ************"Don Allah karki kashe wayar nan ki tsaya kiji wata magana mai muhimmanci queen! Shiru nayi bance komai ba. Yaci gaba da fadin " ko kinsan aurena da salima ya mutu tuntuni tana gida? Tsaki nayi nace"to ni me ye nawa a ciki ..... Yace"So nike in sanar da ke cewa salman ya fara zuwa wurinta neman aure kuma za,a bashi wnn karon nasani don nayi maza na kiraki don na fada miki saboda ba kowa yasan da maganar ba. Shiru nayi gabana na faduwa . Yayi murmushi yace"Nasan ko kadan bazaki so salman ya auri salimah ba domin itace first love din shi yafi sonta dake tunda kinga daga mutuwar aurenta har ya koma yana neman aurenta.yanxu kinsan me nake so dake? Cikin sanyin murya nace"se ka fada. Yace"good.yanzu abinda nake so dake my Queen ki daure mu hadu ko da sau daya ne ni kuma na miki alkawari zan bi kowacce hanya inga na maido da salimah gidana . What! Na fada cikin bacin rai nace"Ahmad har yanxu baka canza ba ? Auzubillahi minasshaidanir rajim! Bari kaji na fada maka ni rumaisa har abada bazan taba yi maka abinda kk so dinnan ba.kuma batun salman da salimah babu komai yaje ya aureta ai dama shi mijin mace hudune don babu komai a ciki yanxun ma bani kadai bace kuma in yaga dama bayan saliman ya karo wata ma mu cika mu hudu! Kuma don Allah na rokeka don girman iyayenka ka rabu dani bana son ka sake kirana ! na katse kiran da sauri ba tare da na saurari me zaice ba. Tashi nayi na zauna tsakiyar gado baccin idona tuni ya watse.tabdijam ana wata ga wata knn indai maganar Ahmad gaskiane lallai akwai jan aiki a gabana. Haka na dinga juyayin maganar Ahmad a raina yinin ranar ko abinci da kyar na daure naci. Ban fito ba sai can yamma lokacinda ya salman ya kusa dawowa don dama kullun in zai dawo gabadsya haduwa muke a palo kowacce ta kure gindin akwatinta. Yau ni English wears na saka riga da skirt mai kyau da jan hankali saboda yanda yake kyalli gashina kuma yasha parking sosai.nayi make up na shashshafa turaruka kala kala farida ma na mata ado tasa gown dinta mai kyau gashi tasha kitson roba tayi kyau. Daga nan muka sauko babban palo. Mun tarar da salmah tana zaune itama ta sake cin gayu kasancewar itace da girki yau. Mun zauna ba tare da nace matq komai ba don ko na mata magana bata amsawa.sai dai in taga dama ta na daukan farida har ta mata wasa. Yauma hakan ne muna isowa ta dauki farida tana cewa"ina kika shiga ne yau ko ki fito ki tayani hira farida. Tashi nayi naje na dauko lemo a fridge da cup nazo na zauna na zuba ina sha ina kallon series din india da akeyi *YOUNG* *DREAMS* .kusan kullum sai na gani sai dai in banzo palon ba. Ban jima da fitowa ba madiha ma ta fito hmm cikin wasu damanmun riga da wando ksmar zata fashe a ciki gashinan gabadaya ta zubo shi kan kafada yasha gyara kuma ko dan gyale bata yafa ba.haka tazo ta zauna a kujeranda ke facing din salmah ta buga cross leg tana taunan cingam.ta kalli salmah tace"wai sai yaushe za,a gama girkine ni yunwa nikeji gidan nan na lura baku iya tarban baki ba.tunda nazo se wani kallon banza ake bina da shi.saboda ba,ason zamana a gidan nan kuma sai na zauna. Salmah ta buga mata harara hade da jan tsaki. Ni dai ko sannun bance ba haka ta dinga jifanmu da bakaken maganganu . Har saida ta tinzura salmah cikin fushi tace"wai ke mara kunya zagin me kk mana ne?ko turoki akayi kizo ki zagemu? To bari kiji in ma turo ki akayi wlh ba matsalata bace in miki rashin mutunci don ni bazan taba daukan rainin hankalinku ba yawwa. Madiha tace"hmm gaki babbar 'yar rainin hankali ai wlh idan bakiyi hankali ba sai na gyara miki zama a gidan nan. Salmah tayi murmushi tace" ai nasan turoki akayi wurina.kuma wlh ni salmah na wuce tunaninku babu wanda zai daga min yatsa a cikinku ban sauke ba.... Madiha ta mike ta nufi dining tana cewa "zamanki a gidan nan ya kusa karewa ashe. Salmah tace"idan igiyar auren a hannunku yake ba? Madiha ta wuce kitchen tana ci gaba dafadan maganganu son ranta. Nidai kallon series dina nake ko kallon basu isheni ba. Karfe biyar da rabi ya salman ya shigo palon da sallama yana sanye cikin kakinsa. Da sauri salmah ta mike cike da fara,a ta karasa gaban sa tana" honey barka da dawowa. Dan murmushi yayi yace"thank you sweety. Snn ya kalli farida dake ta faman daga masa hannu tana dariya ya karbeta a hannun salmah yana dariya shima yace"oyoyo innata kinyi kyau . Ya sumbaci goshinta snn ya kalleni a nima shi nake kallo na danyi murmushi nace"yayanah barka da dawowa. Yace"yawwa ya na ganki yau ba kamar kullum ba?are you feeling ok? Na daga mushi kai hade da fadin" wlh lfy lau. A lokacin madiha ta fito daga kitchen hannunta rike da plet mai daukeda indomie da da faffen kwai harda pepper chicken. Ta kalli ya salman cikin harshen fulatanci ta masa sannu da dawowa hade da gaisheta sama sama ya amsa mata snn yace"da wa kk zo ? Tace"da mummyn farida.(don tasan in ta kuskure tace rumaisa zai mata rashin mutunci) Yace"wannan dan iskan kaya da kk sa kina yawo dashi cikin mutane fa na meye ne ? A shagwabe tace"yaya ni banda wasu kaya fa se wnn...... Daure fuska yayi sosai ba alamun wasa yace"ki tafi kije ki cire kayan nan tun kamin ranki ya baci.ni fa bazan yarda da rashin tarbiyya a gidana ba in shi ya kawoki maza ki kama hanyarki tun muna shaida juna. Bata kuma cewa komai ba ta wuce dakinta da plate din abincinta. Snn ya kallemu yace"kar ku dinga barin madiha a gidan nan tana abinda ta ga dama ku dinga taka mata birki don bata da kunya ko kadan. Salmah kam tabe baki tayi. Yayinda nace"hmm Allah ya shiryeta. Salmah tace"honey muje kayi wanka. Ta fada yayinda ta wuce gaba yana biye da ita yayinda yake tambayarta ina munir tace ya tafi hadda. Nima tashi nayi na tafi sashina na don magriba tayi na wuce toilet nayo alwala. Ban tashi daga praymat ba saida nuka idar da sallar ishah nayi azkar ina cikin adduoina ya salman ya shigo. Tare muka shafa adduan snn na tashi na ninke sallayar na dawo kusa dashi kan gado na zauna hade da fadin "har ka dawo masallaci? Kamar bazai yi magana ba yana kallona sannan daga bisani yace"baby why are you so silent ne yau me yeke damunki ? Cikin kwantar da murya nace"babu komai baka yarda bane? Riko hannayena yayi ya fuskantoni sosai hade da fadin "Rumaisa na sanki tun kina 'yar yarinya ...... Ba shiri na saki dariya hade da fadin "yaya ni fa da girmana ka sanni. Hancina yaja yana murmushi yace"kina son girma kaman meye.lokacinda kika dawo gida shekarunki nawa? Shiru nayi ina kallonshi yace"hmm shekara goma sha bakwai. Nace"amma kuma kake ce min yarinya? Shekara goma sha bakwai aiko a birni na kai aure . Yace"O baby kina son girma.to shikenan am sorry tashi muje muyi dinner . Tare muka tashi yana rike da hannuna muka fita palo mun sami hakim ma ya shigo munir ma ya dawo tuni don haka muka hadu a dining harda madiha sai dai koda wasa har muka gama cin abinci batayi mana rashin kunya ba don tasan halin yaya Salman. Haka dai zaman madiha ya kasance a gidan in dai ya salman baya nan to fa ta dinga neman magana da mu knn musamman ma salmah kam ko don ita ta cika saurin fushine oho .kullum sai ta nemi salmah da magana tun tana biyeta har ta gaji ta shiga kai kararta gun ya salman akan wlh idan madiha bata bar shiga harkarta ba zata mata duka don haka ya salman ya shiga maganar snn aka dan sami zauna lfy. Ahmad kuwa bai daina matsa min da kira ba da tura texes ba duk da naki sauraransa kwata kwata text dinsa ko ya shiga gogewa nakeyi.a karshe ma canza layina nayi ya salman ya tambayeni dalili nace na gaji da layin ne kawai. Rannan muka fito daga shopping da yamma nida fati(nanin farida) tana rike da kaya nikuma ina rikeda hannun farida. Muna shirin shiga mota sai ga Ahmad ya taho gunmu da sauri ban ganshi ba ma kawai naji ance" *Queen* Da sauri na juya na kalleshi ba shiri na dafe kirjina hade da fadin innalillahi wa inna ilaihir rajiun Ahmad don Allah ka rufan asiri ka rufawa kanka ka rabu dani don wlh ya salman ya wuce duk yadda kk tunani yanzu.koina ya baza masu tsaro suna ..... Murmushin yaudara ya sakar min hade da fadin"Zan rabu da ke queen amma se kin min alkawarin zaki saurareni in na kira ki a waya..... Bai rufe bakinsa ba sai kawai ganin sojoji mukayi sun kewayemu anan suka rufe Ahmad da duka ba ji ba gani. Ni kam tausayinshi naji sosai ba shiri na fara kuka ina don Allah ku barshi hakan nan ..... Daya daga cikin sojojin ne ya daka min tsawa saida hanjin cikina ya kada yace mu shiga mota ya karbi key din motar Ahmad kam daga baya jefashi cikin motarsu ma sukayi suka fizgi motar da gudu koina zasu kaishi ne oho . Nima wnn wnn sojan shi ya maida mu gida gabadaya a tsorace nake bansan me zance da ya salman ba gashi nice da girki yau. Da daddare kuwa ban yarda mun hadu ba har saida ya nemeni da kansa. Haka na daure na tafi side dinshi na bar farida da fati. Ina shiga bedroom dinsa na tarar dashi sai kai komo yake. Da kyar na iya karasawa bakin gado na zauna zuciyata sai tsinkewa yake gabadaya cikina ya duri ruwa. Ya isa gabana fuskar nan kamar an aiko masa da sakon mutuwa cikin murya mai cike da bacin rai yace"me ya hadaki da Ahmad yau kuma? Cikin dauriya nace " kawai ni ganinsa nayi yazo zai mana magana ban kula...... Tass! Naji saukar mari ba shiri nayi zumbur na mike ina dafe da gun. Cikin daga murya yace"zaki fada min gaskia ko sai na babballaki? Nima a fusace nace"ka kasheni in kaga dama amma abinda na gaya maka shine gaskia in kaga dama ka yarda ya rage naka . Yace"what ni kike gayawa haka ? Na katseshi da fadin"kai dinfa? Don me zaka mareni ? Wlh ka kuma marina bazan yarda ba. Fizgoni yayi na fada jikinsa yace" ramawa zakiyi ne? Tureshi nayi hade da fadin oho Da sauri na kama hanyar fita raina a bace bansan me ya tuna ba da sauri yasha gabana yace"ina kuma zakije ? Hawayene ya cicciko idona nace"dakina zan koma tunda yau wulakancinka ya motsa kaina.. ... Fizgoni ya sakeyi da karfi ya jefani kan gado ya biyoni hade da fadin " Babu inda zakije sai kin amsa min dukkan tambayoyin da zan miki .... Ban kulashi ba har ya gama maganganunsa snn yace" wlh rumaisa idan baki rabu da Ahmad ba zan kasheshi! Cike da mama ki na zaro ido ina binsa da kallo to ko dai alluransa ne suka motsa? Tattara hankalina nayi sosai na nitsu ina kallonsa snn nace"ni fa iyakar gaskiata na fada maka amma in kana ganin kasheshin shi ne mafita shikenan.kaje ka kasheshi kai da mahallincinka don wlh bazaka kasheshi a banzaba . Ina fadin haka na juya masa baya na gyara kwanciyata . Jikinsa ya danyi sanyi don haka bai kuma yin magana ba ya zauna kan kujera . Haka muka kwana ba bacci ranar .yanda yaketa fama da fushinsa nima a kwanan haka nake ta fushi dashi.har ya sauko dan karan kanshi ya dawo yana bina ko kulasa banyi ba. Saboda na tabbatar da gaskiar maganar Ahmad ya Salman yana zuwa gun salimah kuma suna waya akai akai .duk a tunaninsa ban sani ba. Watarana da yamma na shiga dakinsa na sameshi yaci gayu cikin sky blue din shadda dakakkiya mai kyan gaske ya kafa hulan nan ya dauki turare zai fesa na shigo don haka ya ajiye turaren ya dauki agogonsa yana daurawa. Bayan ya gama ya juyo muna fuskantar juna na ce"ina zakaje da yamman nan? Kai tsaye yace"gidan abokina. Murmushi nayi nace"hmm duk wnn haduwa da kayi gidan abokinka zakaje ni wlh ca nake ko wata bazawarar ka samo . Bina yayi da kallo yayinda ni kuma ko a jikina na shiga gyaran daki don yau na karbi girki. Ya jima a tsaye yana kallona snn ya dauki key din motarsa zai fita nace"sai ka dawo ka gaisheta. Dawowa yayi da sauri yana kallona yace"wacce? Nace"ita man . Yace"ita waye bata da suna? Kai tsaye nace" *SALIMA* Na fada yayinda na juya hawaye fal idona ya bini da kallon mamaki kuma jikinsa ba karamin mutuwa yayi ba don haka ya matsa kusa dani ya kamoni ya juyo dani yace"baby waya gaya miki wnn maganar ? Hawayene ya zubo min ban kulashi ba naci gaba da zubda hawaye rumgumeni yayi yace" kiyi hkr ki daina kuka na miki alkawarin in na dawo zan warware miki gaskiar lamarin. Ya dagoni hade da sharemin hawaye ya zaunar dani kan gado daganan ya suri key din motarsa ya fita. Nikam fashewa nayi da kuka tabbas maganar nan haka yake ya salman ya koma soyyayya da salimah tunda gashi bai musa min ba. Haka na dinga rusar kuka idona ya kumbura yayi jazir kirjina ya dinga min zafi. Abu kamar wasa kawai daya dawo da daddare basai ya kira ni da salmah yana fada mana ko kunya babu wai zai auri Salimah. Nikam bin ya salman nayi da kallo cike da mamaki lallai namiji baida kunya ko kadan mamakin yadda ya salman ya juya lokaci guda nakeyi kamar wanda aka asirce. Salmah kam bata gama jin karshen zancan ba ta mike a fusace ta bar palon ........ *Hauly* *ce*🥰👍🏻 [10/22, 9:33 PM] +234 813 454 8600: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡87 ************"Don Allah karki kashe wayar nan ki tsaya kiji wata magana mai muhimmanci queen! Shiru nayi bance komai ba. Yaci gaba da fadin " ko kinsan aurena da salima ya mutu tuntuni tana gida? Tsaki nayi nace"to ni me ye nawa a ciki ..... Yace"So nike in sanar da ke cewa salman ya fara zuwa wurinta neman aure kuma za,a bashi wnn karon nasani don nayi maza na kiraki don na fada miki saboda ba kowa yasan da maganar ba. Shiru nayi gabana na faduwa . Yayi murmushi yace"Nasan ko kadan bazaki so salman ya auri salimah ba domin itace first love din shi yafi sonta dake tunda kinga daga mutuwar aurenta har ya koma yana neman aurenta.yanxu kinsan me nake so dake? Cikin sanyin murya nace"se ka fada. Yace"good.yanzu abinda nake so dake my Queen ki daure mu hadu ko da sau daya ne ni kuma na miki alkawari zan bi kowacce hanya inga na maido da salimah gidana . What! Na fada cikin bacin rai nace"Ahmad har yanxu baka canza ba ? Auzubillahi minasshaidanir rajim! Bari kaji na fada maka ni rumaisa har abada bazan taba yi maka abinda kk so dinnan ba.kuma batun salman da salimah babu komai yaje ya aureta ai dama shi mijin mace hudune don babu komai a ciki yanxun ma bani kadai bace kuma in yaga dama bayan saliman ya karo wata ma mu cika mu hudu! Kuma don Allah na rokeka don girman iyayenka ka rabu dani bana son ka sake kirana ! na katse kiran da sauri ba tare da na saurari me zaice ba. Tashi nayi na zauna tsakiyar gado baccin idona tuni ya watse.tabdijam ana wata ga wata knn indai maganar Ahmad gaskiane lallai akwai jan aiki a gabana. Haka na dinga juyayin maganar Ahmad a raina yinin ranar ko abinci da kyar na daure naci. Ban fito ba sai can yamma lokacinda ya salman ya kusa dawowa don dama kullun in zai dawo gabadsya haduwa muke a palo kowacce ta kure gindin akwatinta. Yau ni English wears na saka riga da skirt mai kyau da jan hankali saboda yanda yake kyalli gashina kuma yasha parking sosai.nayi make up na shashshafa turaruka kala kala farida ma na mata ado tasa gown dinta mai kyau gashi tasha kitson roba tayi kyau. Daga nan muka sauko babban palo. Mun tarar da salmah tana zaune itama ta sake cin gayu kasancewar itace da girki yau. Mun zauna ba tare da nace matq komai ba don ko na mata magana bata amsawa.sai dai in taga dama ta na daukan farida har ta mata wasa. Yauma hakan ne muna isowa ta dauki farida tana cewa"ina kika shiga ne yau ko ki fito ki tayani hira farida. Tashi nayi naje na dauko lemo a fridge da cup nazo na zauna na zuba ina sha ina kallon series din india da akeyi *YOUNG* *DREAMS* .kusan kullum sai na gani sai dai in banzo palon ba. Ban jima da fitowa ba madiha ma ta fito hmm cikin wasu damanmun riga da wando ksmar zata fashe a ciki gashinan gabadaya ta zubo shi kan kafada yasha gyara kuma ko dan gyale bata yafa ba.haka tazo ta zauna a kujeranda ke facing din salmah ta buga cross leg tana taunan cingam.ta kalli salmah tace"wai sai yaushe za,a gama girkine ni yunwa nikeji gidan nan na lura baku iya tarban baki ba.tunda nazo se wani kallon banza ake bina da shi.saboda ba,ason zamana a gidan nan kuma sai na zauna. Salmah ta buga mata harara hade da jan tsaki. Ni dai ko sannun bance ba haka ta dinga jifanmu da bakaken maganganu . Har saida ta tinzura salmah cikin fushi tace"wai ke mara kunya zagin me kk mana ne?ko turoki akayi kizo ki zagemu? To bari kiji in ma turo ki akayi wlh ba matsalata bace in miki rashin mutunci don ni bazan taba daukan rainin hankalinku ba yawwa. Madiha tace"hmm gaki babbar 'yar rainin hankali ai wlh idan bakiyi hankali ba sai na gyara miki zama a gidan nan. Salmah tayi murmushi tace" ai nasan turoki akayi wurina.kuma wlh ni salmah na wuce tunaninku babu wanda zai daga min yatsa a cikinku ban sauke ba.... Madiha ta mike ta nufi dining tana cewa "zamanki a gidan nan ya kusa karewa ashe. Salmah tace"idan igiyar auren a hannunku yake ba? Madiha ta wuce kitchen tana ci gaba dafadan maganganu son ranta. Nidai kallon series dina nake ko kallon basu isheni ba. Karfe biyar da rabi ya salman ya shigo palon da sallama yana sanye cikin kakinsa. Da sauri salmah ta mike cike da fara,a ta karasa gaban sa tana" honey barka da dawowa. Dan murmushi yayi yace"thank you sweety. Snn ya kalli farida dake ta faman daga masa hannu tana dariya ya karbeta a hannun salmah yana dariya shima yace"oyoyo innata kinyi kyau . Ya sumbaci goshinta snn ya kalleni a nima shi nake kallo na danyi murmushi nace"yayanah barka da dawowa. Yace"yawwa ya na ganki yau ba kamar kullum ba?are you feeling ok? Na daga mushi kai hade da fadin" wlh lfy lau. A lokacin madiha ta fito daga kitchen hannunta rike da plet mai daukeda indomie da da faffen kwai harda pepper chicken. Ta kalli ya salman cikin harshen fulatanci ta masa sannu da dawowa hade da gaisheta sama sama ya amsa mata snn yace"da wa kk zo ? Tace"da mummyn farida.(don tasan in ta kuskure tace rumaisa zai mata rashin mutunci) Yace"wannan dan iskan kaya da kk sa kina yawo dashi cikin mutane fa na meye ne ? A shagwabe tace"yaya ni banda wasu kaya fa se wnn...... Daure fuska yayi sosai ba alamun wasa yace"ki tafi kije ki cire kayan nan tun kamin ranki ya baci.ni fa bazan yarda da rashin tarbiyya a gidana ba in shi ya kawoki maza ki kama hanyarki tun muna shaida juna. Bata kuma cewa komai ba ta wuce dakinta da plate din abincinta. Snn ya kallemu yace"kar ku dinga barin madiha a gidan nan tana abinda ta ga dama ku dinga taka mata birki don bata da kunya ko kadan. Salmah kam tabe baki tayi. Yayinda nace"hmm Allah ya shiryeta. Salmah tace"honey muje kayi wanka. Ta fada yayinda ta wuce gaba yana biye da ita yayinda yake tambayarta ina munir tace ya tafi hadda. Nima tashi nayi na tafi sashina na don magriba tayi na wuce toilet nayo alwala. Ban tashi daga praymat ba saida nuka idar da sallar ishah nayi azkar ina cikin adduoina ya salman ya shigo. Tare muka shafa adduan snn na tashi na ninke sallayar na dawo kusa dashi kan gado na zauna hade da fadin "har ka dawo masallaci? Kamar bazai yi magana ba yana kallona sannan daga bisani yace"baby why are you so silent ne yau me yeke damunki ? Cikin kwantar da murya nace"babu komai baka yarda bane? Riko hannayena yayi ya fuskantoni sosai hade da fadin "Rumaisa na sanki tun kina 'yar yarinya ...... Ba shiri na saki dariya hade da fadin "yaya ni fa da girmana ka sanni. Hancina yaja yana murmushi yace"kina son girma kaman meye.lokacinda kika dawo gida shekarunki nawa? Shiru nayi ina kallonshi yace"hmm shekara goma sha bakwai. Nace"amma kuma kake ce min yarinya? Shekara goma sha bakwai aiko a birni na kai aure . Yace"O baby kina son girma.to shikenan am sorry tashi muje muyi dinner . Tare muka tashi yana rike da hannuna muka fita palo mun sami hakim ma ya shigo munir ma ya dawo tuni don haka muka hadu a dining harda madiha sai dai koda wasa har muka gama cin abinci batayi mana rashin kunya ba don tasan halin yaya Salman. Haka dai zaman madiha ya kasance a gidan in dai ya salman baya nan to fa ta dinga neman magana da mu knn musamman ma salmah kam ko don ita ta cika saurin fushine oho .kullum sai ta nemi salmah da magana tun tana biyeta har ta gaji ta shiga kai kararta gun ya salman akan wlh idan madiha bata bar shiga harkarta ba zata mata duka don haka ya salman ya shiga maganar snn aka dan sami zauna lfy. Ahmad kuwa bai daina matsa min da kira ba da tura texes ba duk da naki sauraransa kwata kwata text dinsa ko ya shiga gogewa nakeyi.a karshe ma canza layina nayi ya salman ya tambayeni dalili nace na gaji da layin ne kawai. Rannan muka fito daga shopping da yamma nida fati(nanin farida) tana rike da kaya nikuma ina rikeda hannun farida. Muna shirin shiga mota sai ga Ahmad ya taho gunmu da sauri ban ganshi ba ma kawai naji ance" *Queen* Da sauri na juya na kalleshi ba shiri na dafe kirjina hade da fadin innalillahi wa inna ilaihir rajiun Ahmad don Allah ka rufan asiri ka rufawa kanka ka rabu dani don wlh ya salman ya wuce duk yadda kk tunani yanzu.koina ya baza masu tsaro suna ..... Murmushin yaudara ya sakar min hade da fadin"Zan rabu da ke queen amma se kin min alkawarin zaki saurareni in na kira ki a waya..... Bai rufe bakinsa ba sai kawai ganin sojoji mukayi sun kewayemu anan suka rufe Ahmad da duka ba ji ba gani. Ni kam tausayinshi naji sosai ba shiri na fara kuka ina don Allah ku barshi hakan nan ..... Daya daga cikin sojojin ne ya daka min tsawa saida hanjin cikina ya kada yace mu shiga mota ya karbi key din motar Ahmad kam daga baya jefashi cikin motarsu ma sukayi suka fizgi motar da gudu koina zasu kaishi ne oho . Nima wnn wnn sojan shi ya maida mu gida gabadaya a tsorace nake bansan me zance da ya salman ba gashi nice da girki yau. Da daddare kuwa ban yarda mun hadu ba har saida ya nemeni da kansa. Haka na daure na tafi side dinshi na bar farida da fati. Ina shiga bedroom dinsa na tarar dashi sai kai komo yake. Da kyar na iya karasawa bakin gado na zauna zuciyata sai tsinkewa yake gabadaya cikina ya duri ruwa. Ya isa gabana fuskar nan kamar an aiko masa da sakon mutuwa cikin murya mai cike da bacin rai yace"me ya hadaki da Ahmad yau kuma? Cikin dauriya nace " kawai ni ganinsa nayi yazo zai mana magana ban kula...... Tass! Naji saukar mari ba shiri nayi zumbur na mike ina dafe da gun. Cikin daga murya yace"zaki fada min gaskia ko sai na babballaki? Nima a fusace nace"ka kasheni in kaga dama amma abinda na gaya maka shine gaskia in kaga dama ka yarda ya rage naka . Yace"what ni kike gayawa haka ? Na katseshi da fadin"kai dinfa? Don me zaka mareni ? Wlh ka kuma marina bazan yarda ba. Fizgoni yayi na fada jikinsa yace" ramawa zakiyi ne? Tureshi nayi hade da fadin oho Da sauri na kama hanyar fita raina a bace bansan me ya tuna ba da sauri yasha gabana yace"ina kuma zakije ? Hawayene ya cicciko idona nace"dakina zan koma tunda yau wulakancinka ya motsa kaina.. ... Fizgoni ya sakeyi da karfi ya jefani kan gado ya biyoni hade da fadin " Babu inda zakije sai kin amsa min dukkan tambayoyin da zan miki .... Ban kulashi ba har ya gama maganganunsa snn yace" wlh rumaisa idan baki rabu da Ahmad ba zan kasheshi! Cike da mama ki na zaro ido ina binsa da kallo to ko dai alluransa ne suka motsa? Tattara hankalina nayi sosai na nitsu ina kallonsa snn nace"ni fa iyakar gaskiata na fada maka amma in kana ganin kasheshin shi ne mafita shikenan.kaje ka kasheshi kai da mahallincinka don wlh bazaka kasheshi a banzaba . Ina fadin haka na juya masa baya na gyara kwanciyata . Jikinsa ya danyi sanyi don haka bai kuma yin magana ba ya zauna kan kujera . Haka muka kwana ba bacci ranar .yanda yaketa fama da fushinsa nima a kwanan haka nake ta fushi dashi.har ya sauko dan karan kanshi ya dawo yana bina ko kulasa banyi ba. Saboda na tabbatar da gaskiar maganar Ahmad ya Salman yana zuwa gun salimah kuma suna waya akai akai .duk a tunaninsa ban sani ba. Watarana da yamma na shiga dakinsa na sameshi yaci gayu cikin sky blue din shadda dakakkiya mai kyan gaske ya kafa hulan nan ya dauki turare zai fesa na shigo don haka ya ajiye turaren ya dauki agogonsa yana daurawa. Bayan ya gama ya juyo muna fuskantar juna na ce"ina zakaje da yamman nan? Kai tsaye yace"gidan abokina. Murmushi nayi nace"hmm duk wnn haduwa da kayi gidan abokinka zakaje ni wlh ca nake ko wata bazawarar ka samo . Bina yayi da kallo yayinda ni kuma ko a jikina na shiga gyaran daki don yau na karbi girki. Ya jima a tsaye yana kallona snn ya dauki key din motarsa zai fita nace"sai ka dawo ka gaisheta. Dawowa yayi da sauri yana kallona yace"wacce? Nace"ita man . Yace"ita waye bata da suna? Kai tsaye nace" *SALIMA* Na fada yayinda na juya hawaye fal idona ya bini da kallon mamaki kuma jikinsa ba karamin mutuwa yayi ba don haka ya matsa kusa dani ya kamoni ya juyo dani yace"baby waya gaya miki wnn maganar ? Hawayene ya zubo min ban kulashi ba naci gaba da zubda hawaye rumgumeni yayi yace" kiyi hkr ki daina kuka na miki alkawarin in na dawo zan warware miki gaskiar lamarin. Ya dagoni hade da sharemin hawaye ya zaunar dani kan gado daganan ya suri key din motarsa ya fita. Nikam fashewa nayi da kuka tabbas maganar nan haka yake ya salman ya koma soyyayya da salimah tunda gashi bai musa min ba. Haka na dinga rusar kuka idona ya kumbura yayi jazir kirjina ya dinga min zafi. Abu kamar wasa kawai daya dawo da daddare basai ya kira ni da salmah yana fada mana ko kunya babu wai zai auri Salimah. Nikam bin ya salman nayi da kallo cike da mamaki lallai namiji baida kunya ko kadan mamakin yadda ya salman ya juya lokaci guda nakeyi kamar wanda aka asirce. Salmah kam bata gama jin karshen zancan ba ta mike a fusace ta bar palon ........ *Hauly* *ce*🥰👍🏻 [10/22, 9:34 PM] +234 813 454 8600: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡88 *********Tashi yayi yabi bayanta da sauri. Nikam a inda nake zaune ko motsi na kasa yi tsabar mamakin da ya Salman ya bani.wato yaya har yanzu son salima yake ?gaskia na yaudari kaina dana yarda cewa ni kadai ya Salman yafiso. Hawayene ya zubo min ba shiri.gaskia dolene in dauki wani mataki akan wnn maganar domin banjin zan iya zama da Salima a matsayin kishiya! Salmah kuwa tana shiga dakinta ta sauke katon jakan kayanta ta bude ta shiga dibar kayantw a wardrobe tana zubawa baji ba gani. Yana shigowa yace"Salmah meye hakan kuma?ina zakije ? Ko kallo bai isheta ba taci gaba da abinda takeyi da sauri ya karaso gaban ta ya rike hannayenta hade da "I'm asking you Ina zakije? Ta fizge hannunta da sauri ta watso mai harara tace"gidan mu zan tafi kuma bazan dawo ba saboda zama da kai ya isheni. What! Ya fada da tsananin mamaki a fuskarsa snn yace"to me aka miki ko akan dan maganar danayi muku yanzune? Wani irin kallo ta bishi da shi batare da tace komai ba. Yace"salmah meyasa ke bakida hakurine eh.ba kya ganin rumaisa ne ki koyi da halayanta mana rumaisa tanada hakuri sosai....... Hannu ta daga masa tace"kaga malam kar ma ka bata bakinka ba sauraranka zanyi ba salmah daban rumaisa daban.kuma indai hakuri irin na rumaisane bana fatan Allah ya sanya min a zuciyata! Haba suleyman abubuwanda nake fuskanta a gidan nan yayi yawa.mahaifiyarka ta tsaneni 'yan uwanka duk basa sona ka duba yanzu tun zuwan madiha gidan nan ta sakani a gaba kullum sai ta nemeni da fada .snn tunda nazo gidan ka ba wani ci gaba dana samu tunda ko batan wata ban taba yiba duk da nasan haihuwa na Allahne.duka wnn na jure snn yanxu kaje ka kirkiro wani abun kuma na daban.gaskia ni suleyman indai zakayi wnn auren to ni dai bazan zauna ba gidanmu zan tafi ka biyoni da takardata!!! Tunda ta fara magana yake kallonta har ta gama ta ja zip din jakanta ta rufe tana shirin sanya hijabinta yace"Salmah karki yarda ki fita daga gidan nan ban baki izini ba. Ta girgiza kai cike da takaici tace"bana neman izininki a halin yanzu domin ni tuni na cire ka a zuciyata don haka dole ne in tafi. Gyada kai yayi yace"ok fine.amma ki sani in har kika tafi bazan taba bikonki ba! Yana fadin haka ya juya ya fita a tunaninsa in ya fadi hakan zata hkr daga baya a daidaita don yasan tana sonshi.sai dai wnn karon bata saurara ba ta ficewarta. Nima din dana gama zamana a palon kawai na yanke hukuncin tfy gidanmu don na lura ya salman baya duba irin hkr da nakeyi a gidansa har nema yake ya kuntata min bayan na samu da kyar na rabu da matsalar innah.duk da hakan ma ga adda A'i da sadiya snn ga wnn fitsararriya madiha.ga salmah a gefe snn ya sake dauko min salimah? Ina bazaiyiwu ba. Ina shirin tattara kayana ya shigo dakin ganina tsaye a gaban wardrobe yasashi karasawa gabana yace"rumaisa ke ma tfyn zakiyi? Murmushi na sakar masa wanda yafi kuka ciwo snn nace"ina zanje cikin daren nan yayah ? Kai ko gari ya waye ma ai ba inda zanje ni dole in zauna ..... Ido ya zuba min yana son ya karanci wani abu a tattare dani da sauri na juya na kama shirya kaya a wardrobe. A hankali yace"baby. Na juyo muka kalli juna hannayena ya kama ya rike snn yace"Rumaisa nasan dama ko kowa zai juyan baya ke bazaki juya min ba snn nasan duk abinda nasa a gaba ke mai iya supporting dinane a kowani hali shiyasa nake dada sonki a cikin zuciyata.Rumaisa ko kadan ba ina son in auri salimah don na kuntata maki bane kawai dai ina tausayin halinda salima take ciki ne tunda tayi aure wahala take sha kuma kinga........ Gabadaya na gama cika fam tsabar haushi da takaici amma na danne zuciya ta nayi murmushi nace"na gane yayah Allah ya bada sa,a. Na zame hannuna cikin nashi a hankali snn na juya da sauri na shige toilet na kulle. sai da na tabbatar ya bar dakin snn na fito da sauri na sawa kofata key. Koda gari ya waye yana tfy daki na tattara da fareeda sai gidan mama. Na sanar da mama dukkan abinda yake faruwa amma sam mama na lura bata damu ba har kokari take in koma gidana. don haka wata dabara ta fado min airport na tafi nayi booking tfy abuja na kuwa ci sa,a jirgi zai tashi 3:00pm. ba tareda sanin mama ba muka daga Abuja da farida.mama duk tunaninta gida drivernta ya kaini . shi kuma yana can wurin aiki be san gidansa ya watse sauran madiha da yan aiki.don munir ma na ce hakim ya kaishi gidan mama kawai. ba jimawa muka iso Abuja gidan kawu kasim na sauka don alredy na fadawa momy zuwaira ina zuwa . Bayan munci abinci mun huta anan na fada mata komai. Cikeda mamaki tace"lallaima salman abinda yake shirin yi knn?saboda rashin hankali kuna zaune lfy shine bai masa ba yake son tada wani fitina?don ni banga dalilinda zai sa ya sake kara aure ba .duk da ma dai nasan ba haramun bane. nidai kuka na shiga yi tsakani da Allsh nace"momy wlh bazan iya zama da salima ba.ni wlh matsalolin gidan ya salman ya isheni daga wnn sai wnn. momy tace" wlh banga laifinki ba rumaisa kinmayi kokari kuma kin daure don haka ki kwantar da hankalinki bazan taba barinsa yayi auren nan ba in Allah ya yarda tashi ki hau gado ki kwanciyarki ki bacci abinki shi kuma zaizo ya sameni se munsa kafan wando daya dashi. Tana gama fadin haka ta dauki farida suka fita. Da farko kawu kassim ya ce lallai sai in koma inci gaba da hkr amma ina momy ta dage sosai akan bazan koma sai ya salman yazo tukunna.bansan ya tayi ta lallaba kawu har ya yarda na zsuna ba. Tunda ya fahimci ina Abuja gidan su momy gabadaya hankalinsa ya tashi don yasan tabbas in yazo momy zata masa ba dadi. Gabadaya ya shiga damuwa ga salmah ta tafi kuma taki dawowa kuma sai zugata akeyi akan ko ya nemeta kar ta dawo ya saketa kawai don haka ta matsa dole sai ya saketa ita ya isheta zama dashi har da ce mishi matsalar rashin haihuwa da batayi ma daga wajansa ne shine yake da problem lol! Da yake rabon zama tsakaninsu ya kare sai ya biye mata ya saketa din. Dama innah ma tace kar ya dawo da ita kawai dai ya je yayi kokari ya dawo dani ya lallabani in yi hkr ya kara auren.domin ita har goyon baya take bashi na ya auri saliman.dama can kunsan tana son salimah. Gabadaya al,amarin ya dagule masa dole ne kawai yayi niyyan zuwa abj don ya dawo dani. Don haka koda ya sami time tuni ya taho da jirgi gidan ya salim ya fara zuwa.tun a hanyarsu na dawowa gida daga airport ya salim yace masa" salman mu fara zuwa mu gaida su momyn mana. Yace"kai barni tukun se munje gidanka na gama tunanin yanda zan fuskanci momy in yaso daga baya se muje. Don wlh jikina yana bani akwai matsala tunda kaga mummy da daddy suka yarda rumaisa ta zauna gunsu ba tareda sunce min ko sannu ba to fa kasan akwai matsala. Salim yayi dariya yace" to banda abin salman ka hkr mana kawai da maganar auren salima ni fa banga meye dalilinda zaisa kayi wnn auren ba. Sauke numfashi ya salman yayi yace"hmm kasan meye salim wlh tausayi saliman ta ban ko kasan cewa ita da kanta ta rokeni dana aureta ? Salim yace"what da kanta ? Ya salman yace"wlh kuwa tunda Ahmad ya saketa ta buga ta sanar dani snn ta kara da gaya min irin mugayen halin Ahmad don tace yanzu bayan shaye shaye ga neman mata na bala,i har matan aure yake bi.snn ita tsakaninta dashi sai wulakanci har da duka shine kaga a karshe yazo ya saketa snn don rashin adalci irin na familynsu sai suka dinga dora mata laifi.mahaifinta ne kadai take samun sassauci daga wurinsa har yana ce mata in ta gama idda tayi maza ta sami miji ya mata aure ta huta .don baya son azo daga baya ace za,a daidaita su da Ahmad saboda kaga akwai yara uku a tsakaninsu.to fa shine da ta gama iddan take rokona dana aureta don Allah kuma ta min alkawarin zata zauna lfy da rumaisa .kuma kasan dama ita batada problem da inna. Ya salim ya danyi shiru snn yace"hmm to ni bansan me zance akan wnn maganar ba salman. Ya salman yace"karka damu kawai ni so nake muje da kai gun momy mu mata bayani yadda zata fahimceni .in yaso ita rumaisan zan san yadda zanyi in lallaba abata kasan batada matsala. Ya salim yace"ai kuwa wnn karon kam da matsala don daga ganin yanayin rumaisa bazata hkr ba.amma kasan ance tsakanin mata da miji se Allah kai kasan matarka kasan yadda zakayi ka shawo kanta kuma nidai sai dai ince Allah ya bada sa,a. Har suka iso gidan ya salim suna tattaunawa. Ruma ta fito ta tarbesu da fara,a cikin jikinta wata hudu har ya dan fita a jikinta. Ya salman yace"sweety ki bi a hankali fa. Hade fuska tayi tace"ni mantawa ma nayi darling fushi nakeyi da kai? Ta fada yayinda ta koma cikin gida ta barsu tsaye ya salman yace" hmm mata knn akan kishiya sun dinga daga hankalinsu alhalin Allah bai haramta ba. Ya salim yayi dariya yace" hmm kai dai muje ai ka barowa kanka matsala. Sai da sukayi sallar la,asar suka tafi gidan kawu kassim. Suna shiga suka ganni a harabar gida ina taya farida wasa muna dariya. Ni duk tunani ya salim ne kadai yazo har na dauki farida ina cewa muje ga daddy yazo. Ganin ya salman yasa na hade fuska na juya da sauri na nufi cikin gida. Aikuwa da saurinsa ya sha gabana tsayawa nayi ba tare da na kalleshi ba . Ya karbi farida dake masa dariya tunda ta ganshi yace"haba baby me yasa kika min haka. A daidai lokacinda ya salim ya karaso don haka da sauri na shige palo. Momy na ganina tace"ya ya me ya faru? Nace"ya salman ne yazo. Itama daure fuska tayi a take tace"je ki daki karki yarda ki sakan masa fuska kome zaice miki . Ina wucewa daki suka shigo da sallama ta amsa ba tare da ta kallesu ba. Jikin ya salman a mace suka zauna kan kujera ya kalli momy ya dan sosai kai yace"momy ina wuni? Harara ta watsa masa ta tashi ta barsu a palon Ya salim yace"hmm kagani koh? Jikin ya salman yakara yin la,asar don sam momy bata fushi dasu tun suna kanana idan sukayi laifi saidai ta musu fada in ya wuce kuma shikenan.amma da girmansa bai taba gaisheta ta ki amsawa ba se yau don haka ya kalli salim yace"anya danuwa rumaisa ba sharri tazo ta min ba kaga fa momy bata taba yi min haka ba. Haka suka dauki tsawon lokaci suna zaune shiru momy bata fito ba har sun yanke hukuncin tfy sai gata ta fito don a tunsninta sun jima da tfy. Suna ganinta ya salman ya tashi da sauri zai karasa gunta ta daga masa hannu hade da fadin"karka yadda kazo inda nake. Bai saurareta ba ya karasa gabanta da sauri ya durkusa ya rike kafanta yace"please mom kiyi hkr karkiyi fushi dani wlh bazan iya walwala ba momy .momy fushinki babban tashin hankaline a gareni don Allah momy ki min wani hukuncin amma ba irin wnn ba. Ya juya gun ya salim yace"danuwa baza ka sa baki bane? Ya salim ya boye dariyarsa yace"gaskia ya kamata insa baki .momy don Allah ki yi hkr kinga fa soja guda durkushe a gabanki.manyan gari mala'ikun duniya masu bada horo ....... Bai karasa fada ba momy ta jefeshi da wata harara don haka mikewa yayi ya fita yana dariya. Shi dai ya salim har lokacin yana durkushe gabanta yana aikin bada hkr. Har kawu kasim ya dawo tare suka shigo da ya salim nima ina labe ina kallonsu. Kawu kasim na shiga yaga ya salman a dukkushe yace"yau me zan gani manyan gari ne durkushe haka.tab lallai zuwaira kina abinda kika ga dama soja da kansa zaki baiwa punishment. Fuska daure tace"ni ina ruwana in ya kama duka ma basai a masa ba ai bai wuce duka ba. Ya salim yace"wlh kuwa momy dama bulala kika samo da zaifi akan fishin nan. Ya wuce ya bi bayan daddy yana dariya. Ta kalleshi hade da fadin "kaje ka gaida daddynku bayan kunyi sallar isha se ka sameni a daki. Da sauri yace"to momy. Ya tashi ya tafi palon daddy. Sai a snn na koma daki.bansan ya sukayi da momy ba washegari dai ya nemi ganina momy taki yarda haka ya hkr ya tafi. Bayan tfyarsa ne na tambayi momy yadda sukayi take gaya min wai ai taimakon salima zaiyi ya fitarda ita daga wahala ba wai zai aureta ne don son ransa ba.shine momy tace tace ta bashi lokaci yaje yayi tunani da kyau akan abinda yake shirin yi. Al,amarin gabadaya ya kwabe masa domin su inna kadai ke goyon bayan wnn maganar .don ko mama bata ce komai ba amma ya fahimci ranta ya baci duk da bata son ya gane. Abba kam cewa yayi ma baza aje neman masa auren salima ba.tunda tun farko da ya nuna yana sonta sunki yarda ya aureta saboda sun ganshi talaka sai yanzu da sukaga Allah ya azurtashi snn zasu amince ya auri yarsu don haka shima bai yarda ba. Snn bangaren salimah ma tunda mahaifinta yayi zancen aurenta da ya salman da 'yanuwansa suka ki amincewa saboda irin rashin mutuncinda yayi wa Ahmad kwanaki.a maimakon hakan ma kawai sukace a daidaita auren salima da Ahmad taci gaba da hkr da halinsa tunda gashi yaransu uku. Wayyo salima taci kuka ne na fitan hankali domin bata kaunar komawa gidan Ahmad sai dai ba yanda ta iya sai hkr. Ya salman kuwa tunda abba yaki bashi goyan baya snn ga momy da dad ma sunki bashi hadin kai don haka ya yanke shawarar ya hkr da auren salima kawai. Don haka ya gayawa salimah tayi hkr kawai maganar auren nan bazsiyiwu ba akwai matsala.ita ma ta fada mishi halinda take ciki.don haka dolensu suka hkr da juna. Inna kam bata so hakan ba tayi bakinciki sosai.amma bata ce komai ba . Kasancewar ya dauki hutu tattarawa yayi ya dawo Abuja momy kuwa tace min kar in yadda in sakan masa fuska in rabu dashi shima ya dandana yaji zafin abin. Ai dama nima ina cike dashi wnn karon nayi niyyan gwarashi sosai na lura hkrn danakeyi yasa yake min wasu abubuwan.don haka daga yau nima na daina hkrn. Duk yadda yaso mu hadu kauce masa nakeyi.daddy kuwa har rokon momy ya fara yi akan ta barni in kulashi don ya lura dan nashi na cikin damuwa. Momy tace"hmm ai Alhaji ka rabu da shi sai na ganar dashi kuskurensa tukunnaa Daddy yace" hmm ba ruwana kiji tsoron gamuwarki da shatu. Dariya tayi tace har ka tuna min shekarun baya can lokacinda muka tura salman training na soja a kaduna kirana tayi a waya na musamman tana tambayata wai shin ni na haifa mata salman ne?nace aa ke kika haifeshi. Sukayi dariya lokaci daya yace"amma don Allah ki barshi ya sake da matarsa karki zake da yawa kizo kiji kunya tsakanin mata da miji se Allah.tunda kika ga ya tattara yazo ya zauna anan kinsan yana cikin damuwane yana bukatar matarsa. Momy tace"mara kunya ba har da wani tare mana yayi a gida.shikenan zan duba din. Shikuwa ya salman gabadaya hankalinsa na kaina yana son yayi timing lokacinda momy bata gida don yazo ya tsara ni.har wani daukan farida yake su kwana kawai don na biyoshi dakinda ya sauka ni kuma naki haka ya dinga tura min text na rarrashi hade da kalaman soyayya duk naki.shine harda charting a watsapp wai in turo masa hotona da kayan bacci lol! Tuni nayi blocking dinsa domin fa nima ya fara tayarmin da hankali .don gabadaya ya salman ya batani nima na zama wata jarababbiya.gabadaya nayi kewarshi hkr kawai nskeyi ina kokarin cire abin a zuciyata da dole. Ya salman kuwa harda yiwa salim complain yace"wlh danuwa ina cikin matsala rumaisa da momy sun sani a cikin matsala.salim kasan halina wlh bazsn iya rayuwa ba mace a kusa dani ba musamman da nazo na saba da mata biyu kuma .gashi lokaci guda sun watse ba ko daya wlh ina jin jiki.don Allah menene mafita. Ya salim yayi dariya snn yace" ka yiwa doctor james mutuminka complain tunda shi ya saba yi maka solving din wnn matsalar taka a duk sanda ka shiga.kuma ka ci gaba da azuminka na litinin da alhamis ka dinga addua insha Allah momy da rumaisa zasu hkr. Shiru kawai yayi ya rasa ya zaiyi ya salim yace ko kuma ni zanyi iya kokarina zanje in taho maka da rumaisa har gidan nan kaga shikenan. Ya salman ya saki ajiyar zuciya yace"yawwa good idea wlh da kuwa na dinga sa maka albarka. Suka gama gama hada plan dinsu tsaf ranar ya salim yazo yana ce min yaushe zanje in kwana gun ruma tana ta tambaysna . Ya salman ya karba "babu inda zata wlh ban yarda ba. Momy tace"ina ruwanka ?karka kuma sa bakinka a cikin maganar rumaisa. Ta kalli salim tace"zataje gobe in Allah ya yarda amma bazata kwana ba. Ya salman ya tashi ya fita adole wai shi yayi fushi ashe hauka suka manna min nida momy. Washe gari da wuri ya salim yazo ya daukeni lokacin ya salman na breakfast a dining shida farida bai ce mana ko sannu ba. Muna cikin hira da ruma gabadaya mun shagala sai dariya muke harda kyakytmatawa sai gashi ya shigo da sallama ruma ce ta amsa nidai tuni na hade fuska kamar bani ba. Ya kalleni hade da fadin "kixo ina son magana dake . Na tura baki nace "ni ka rabu dani ba inda zani. Ganin zan bata masa lokaci yasa kawai ya dagani cak ko kunyan ruma baiji ba ya fita dani zuwa sashin baki nayi nayi in kwace na gagara. Muna isa ya direni kan gado ya kulle koina ya dawo ya soma cire kayansa cikeda mamaki nace"nifa kar kazo kusa dani babu abinda zan kuma yi maka . Baiyi magana ba ya karaso kan gadon ya rumgunmeni jikinsa yayinda ya zuge zip in rigana ta baya yace"baby kinsan ko kadan bazan iya hkr da rashinki a kusa dani ba meyasa zaki min haka. Ya fada cikin muryarsa data fara sauyawa yayinda ya shiga romancing dina cikin zafin nama yana sakin numfashi. Nima dayake a hannu nake bansan yaushe na fara biye masa ba.tsakanin mata da miji sai Allah wlh har tausayi ya ban yanda naga ya rikice min gabadaya.don haka na kyalesa har yayi second round da third round snn ya rabu dani yana ta sanya min albarka ba don ya gaji ba sai dai duba da time din sallar azahar har ya wuce don haka yayi maza ya tsarkake jikinsa ya fice masallaci. Sai da ya tafi na shiga jin haushin kaina da yanda nake sakar ma ya salman jikina da wuri haka........... *WANNAN* *PAGE* *NAKINE* *UWAR* *DAKI* 😉 *CHUBADO* *MOH'D* *MARUBUCIYAR* ( *_AMINTACCIYA_* *_CE_* ) *ALLAH* *YA* *BAR* *KAUNA* *DA* *ZUMUNCI* *ME* *DOREWA* 🥰🥰🙏🏻🙏🏻🙏🏻 Hauly ce🥰👍🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡89 ***********Haka na tashi na tafi cikin gida na sami ruma bata nan tana side din ya salim don haka na samu nayi wanka hade da alwala nayi sallah. Har bayan la,asar ruma ta shigo ta sameni dariya ta yi snn tace"mummyn farida ya gajia dai? Harararta nayi nace "wato da ke aka hada baki koh?wlh sai na fadawa momy . Ta sake yin dariya tace"ni fa bansan komai ba honey ne yake fadamin dazun.yau munsha weekend bakiga nima na jima a side dinsa ba? Nace"ke yanxu da cikin nan kike ba kanki wahala? tace"hmm mazan mu na yanzu basa son mace raguwa sunfi son da sunzo kawai ki basu hadin kai.don haka kema ina kara baki shawara duk da ma nasan kin san komai.amma fa ki dage sosai domin darling ba wasa a wnn harkar bare ma ya dandana zama da mata biyu tofa dole se kin zage dantse kin cire ragwanci ki zama always ready yana zuwa da bukatarsa ki biya masa. Nace"hmm ai nima yanzu na zama gwana zama da ya salman ya bata ni ruma .bakisan irin yadda nakeji ba idan bana tare da yaya. Dariya tayi tace"da kyau yanzu kuzo muje zamu maidaki gida.momy ta kira salim tace maza ki dawo. Tashi nayi nace"to muje. Na saka hijabina muka fita.mun samesu a harabar gida ya salman zuba min ido yayi kallon ma na daban har ya shagala bai sani ba. Nidai turo baki nayi na kauda idona akansa. Ya salim ya kalleshi yace"to oga sai ka dawo mu zamu wuce. Ba tareda ya janye idanunsa akaina ba yace"ok se kun dawo nima in naje na gaida goggo ummi zan dawo gidan may be zan sameku. Kamar ince zan bishi gidan goggo ummin . Ya salim yace "to ka gaisheta da kyau mu kam jiya munje mun kai mata mimi. Daga nan muka shiga motar ya salim har lokacin yana jingine da mota yana kallona ko kallon meye oho. Koda ya dawo da daddare kirana yayi a waya wai in zo. nace"nifa kayi hkr ba wani zuwa da zanyi inxo in maka meye? Yace"haba baby hakkina zaki bani mana.kinsan fa babu kyau miji ya nemi matarsa a shimfida ta juya mai...... Katse kiran nayi nace"Hmm se kayi kuma. Na gyara kwanciyata da shirin bacci. Haka ya kasance tsakanina da shi har hutunsa ya kare rannan muna breakfast ya kalli momy yace"momy don Allah ki hkr rumaisa ta rakani lagos zanyi one week ne kawai akwai aikinda ze kainine. Momy tace"one week in ne se kaje da rumaisa to me zata maka tunda naji kace aiki ne ze kaika ? shiru yayi ya rasa me zaice don haka tace kayi tfyrka Allah ya kaika lfy ya dawoda kai lfy.in yaso zan duba zuwa nan one week din se ka dauki matarka amma yanxu ba inda zata. Ba don ransa yaso ba yace "to momy Allah ya kaimu. Yayinda ya kalleni muka hada ido gwalo na masa na sunkuyar da kai ina dariya kasa kasa. Gyada kai yayi snn yace"momy don Allah to ko rakiya ne ta min a get zanyi magana da ita. momy tace "naji kuma minti biyar na baka ka gama magana da ita ka kama hanyarka ka tafi.in ya wuce minti biyar zan fito in sameku kuma kasan sauran zancen. Yace"to momy. Yana fita momy ta kalleni tace"ya fara shiga hankalinshi yanzu kam. Murmushi nayi bance komai ba . momy tace"tashi kije kuyi sallama. Na tashi na fita na sameshi yana tsaye rataye da jakansa muna hada ido nayi saurin janye idona na juya masa baya nace"gani. Shiru yayi kamar bazaiyi magana ba snn yace"hmm baby ina jiye miki tsoron randa zaki shiga hannuna don wlh bazan saurara miki ba saboda kin azabtar dani dayawa. Murmushi nayi don nasan baya kallon fuskata nace "haka kace to wlh se na gayawa momy abinda kace. Na fada yayinda nayi gaba da sauri ya bini ya rikeni yace"wasa fa nake miki karki gaya mata don Allah. kokarin kwace kaina a jikinsa nake saboda yanda ya rikeni sosai ko kunyar driver da mai gadi bayaji. Muna cikin haka sai ga momy ta fito aikuwa tana ganinmu tace"ok wnn shine maganar da zaka mata din? Da sauri ya salman ya sakeni ya bude mota ya shiga ya kulle dama driver na jiranshi don haka mai gadi na bude get suka fita . momy tace"mara kunya ai da ka saya har inzo in sameka. Muka koma ciki a ranar ya salim yazo ya dauki farida duk da kayanta yace zai kaita gun mimi su dinga wasa bibbiyu. Nikam ya salman na tfy da kwana biyu na kama rashin lfy ciwon kai daga baya marata da bayana a rana ta hudu kuwa sai amai duk abinda naci sai amai kawai.hankalin momy ya tashi sosai don haka ta kira doctornsu har gida yazo ya dubani bayan ya tambayeni yadda nakeji na fada masa kawai ya jefomin tambaya"yaushene last kikayi menstruation dinki? Na dan saci kallon momy naga ta kafeni da ido kawai nace"na manta. dariya doctorn yayi yace "bakiyi ba last month? Shiru nayi don haka yace zai min gwajin ciki aikuwa yanayi ya kalli momy yace "Hajia cikine! Dam!naji kirjina ya buga ban iya na dago na kalli momy ba .snn can zuciyata kuma farinciki na shiga yi abin nema ya samu. Bayan momy ta sallami doctor ta dawo ta kalleni tace"Rumaisa ya akayi hakan ya faru don nasan cikin nan anan abuja kika samu saboda lokacinda kika zo nan kinyi period dinki.gaya min yaushe kuka hadu da salman. Sosai kunya ya kamani kamar zan nitse momy tace"wato hauka kuka manna min ke da salman kuna ta shagalinku koh ?to meye amfanin zamanki anan ai dana san kun daidaita kanku da tuni na barki kika bishi Kaina a tsunkuye nace"wlh momy ba abinda kike tunani bane wayo ya min suka hada baki da ya salim yazo ya daukeni ya kaini gidansa shi kuma yaje ya sameni.kuma wlh momy sau dayan ne kawai...... Ta katseni da fadin ya isa .ai zaizo ya sameni daga shi har salim din. Ta tashi har zata fita ta kuma dawowa tace" to yanxu dai kinji abinda duk doctor ya fada don haka ki kula da kanki sosai don ba ke kadai bane yanzu.Allah ya raba lfy. Shiru nayi har lokacin kaina a sunkuye murmushi momy tayi tace"meye kuma najin kunya ai ba haramci kika aikata ba rumaisa.yanxu dai gaya min me kike son ci a dafa miki ? Na danyi shiru snn nace"momy kawai zansha kunu in wanda akayiwa daddy ya rage. Tace"aikuwa ya kare amma zanje nayi mishi sabo yanxu jirani mintuna kadan .gara na dage wurin kula da ke watakila maigida zaki haifo min. Ta fita tana dariya nima murmushi nakeyi zuciyats wasai jina nake kamar wacca akayiwa albishir da gidan aljanna.ya salman in yaji wnn labarin ba karamin dadi zaiji ba nasani. Satinsa daya da tfy ya sake dawowa bamu san zaizo ba kawai muka ganshi bazata ya samemu a palo da momy ina shan kunu don shine kawai abinda raina keso. Momy tace"salman irin wnn zuwan bazata ko ka buga ka sanar damu. Yace"wlh momy wani mafarki nayi mai dadi dama ba yau nayi niyyan zuwa ba se gobe. Momy tace to wani mafarki knn? Yace"momy mafarki nayi rumaisa na da ciki . Momy ta harareshi tace "da yake kasan abinda ka aikata kamin ka tafi ba . Sunkuyar da kai yayi yana sosa keya momy tace"hmm to ai shikenan .mafarkinda kayi gaskiane cikin ne da ita Da sauri ya dago ya kalleni nikam daure fuskata nayi na danne dariyata naci gaba da shan kunu na. Dariya yayi yace"Alhamdulillah Allah mun gode maka. Ya kalli momy yace"momy dolene in baki tukuicin wnn albishir da kika min domin naji dadi sosai wlh. Momy tace"to maza hanzarta ka bani. Tashi nayi na wuce daki abuna na barsu a palo hira suka dinga yi da momy kamar ba itace ke ta faman fushi dashi ba. Har daddy ya dawo ya samesu yace"zuwaira gaskia yanzu kam a bar soja ya tafi da matarsa. Momy tayi dariya tace"ai dolena in barsu yanxu kam .amma fa kaja mishi kunne kar ya sake aikata wani kuskuren Daddy yaja kunnen ya salman hade da fadin"kaji ai naja kunnenka da baya jin maganan nan wlh ka kukura ka kuma batawa rumaisa rai sai mun saka tsallen kwado. Dariya momy tayi yayinda shikuma yace"inshaa Allah dady bazan kuma ba. Da daddare ya shigo ya sameni har nayi shirin bacci don yanxu da wuri nake jin bacci. Hawa gadon yayi ya yaye bargon da na rufa ya tura hannunsa cikin jikina yana shafa marana yana murmushi snn ya kalli fuskata nima murmushin nakeyi a hankali ya dagoni ya rumgumeni a jikinsa yace"Alhamdulillah my dear Allah mun gode maka karkiso kiji irin farin cikin da nayi wlh.nan bada jimawa zan sake samun baby. Ya shiga shafa kaina snn ya dago fuskata yayi kissing din bakina yace"babyna Allah ya miki albarka Allah ya barmu tare. Nidai bance masa komai ba yace"mene ne kodai har yanzu fushin ne ?pls ki manta da komai rumaisa mu maida rayuwar soyayyarmu kamar nada . Turo baki nayi nace"yaya ni na daina yarda da maganarka .zaka sa in saki jiki da kai nan gaba kace zaka kara aure...... Da sauri yace"waya ce miki zan kuma yin aure?ni bazan sake yin wani aure ba in Allah ya yarda ke kadai kin isheni dear. Tabe baki nayi nace"hmmm . Yace "means baki yarda ba shikenan zaki gani.yanxu abinda nakeso dake kiyi parking din kayanki gobe jirgin safe zamubi na rigada na gyara mana gida yanda zamu sake sabon rayuwa don har nasa an mana saukan Qur,an a gidan Allah ya kade mana dukkan masifu dake ciki don haka yanxu ba ruwana da wani karin aure ke kadai kin isheni babyna. *KI* *YARDA* *DANI*. Murmushi nayi nace"na yarda da kai yaya hundred % amma don Allah .... Ya katseni da fadin "magana ya kare dear. Ya sake kissing din bakina snn ya shafa marata yace"Allah ya raba lfy. Nace"ameen yayahna. Daga nan ya sallameni ya fita. Washe gari kuwa karfe shadaya muka bar Abuja bayan momy da daddy sun zaunar damu sun mana magana sosai.farida mun barta gidan ya salim don sun saba da mimi sosai basa son rabuwa(wnn shine sanadin zaman farida a gaidan ya salim) Gidan mama muka fara sauka mun sami daddyna ma yazo bayan mun gaisa bamu zauna ba muka tafi gidansu innah to ba laifi ta tarbemu da mutunci amma sam na lura bata wani fara,a duk ta sake sauyawa kuma.sadiya kam bata nan tana cameroo don rashin auren ta ya fara damun innah don haka ta turata kamaru a sama mata maganin matsalarta na rashin samun tsayayyan bazawari. Madiha kam tana nan don haka tana ganinmu ta hada kayanta wai zata biyo mu yaya salman yace mata ba yanzu ba ta bari tukun sai daga baya haka ta koma daki tana ta tura baki. Inna kuwa bata ce mana komai ba har muka tafi. Hmm rayuwa knn gidanmu mu kadai yanzu se munir da hakim da masu aiki.mun shimfida rayuwar soyayya kamar zamu cinye junanmu sosai yaya ya shiga nuna min so da kulawa gashi munci sa,a cikina ba laulayi sosai. Daga baya madiha ta dawo inda ya salman ya mata jan kunne sosai akan idan ta sake ta min rashin kunya zata bar masa gida kuma ta fitar da miji tayi aure zamanta hakan nan ya isheshi.don haka yanxu rashin kunya ta rage sai dai munafurci kusan kullum tana gidan innah ta kwashi karya da gaskia a kaina ta fadawa innah.sadiya ma ta dora da nata da yake tuni ta dawo daga camaroon. Kuma taci sa,a tana dawowa ta sami wani Alhaji nasir babban dan kasuwa yana da mata uku da yara goma sha biyar.hmm wayaga sadiya da kishiyoyi Allah dai ya sa ta iya zama da wnn banzan halin nata.tuni maganar tayi karfi don har an daura aure sauran tarewa tace sai ta shirya don haka ta shiga neme neme kullum ana gidan malamai don ance mata gida da kishiyoyi sai ta shirya sosai kamin ta shiga.kuma ita a son ranta Alh nasir ya sota sosai ya kashe mata kudi. Cikina na wata shidda sadiya ta tare bayan mun gama shan biki tarewan ne sa,adatu ta haihu an sami da namiji mai sunan daddy .ruma ma ta haifo babynta namiji ya salim ya sanya masa sunan ya SALMAN wayyo karkuso kuga farin ciki gun yaya salman na samun takwara. A halin yanzu rayuwa na tfy normal sai dai dan matsala da muke samu da innah a dalilin madiha don ko yaushe sai ta min sharri a gun innah .innah ta kira ni a waya tayi ta gaya min maganganu marasa dadi don haka na zaunar da madiha nayi mata magana akan abinda takeyi nayi warning dinta sosai domin na gaya mata daga ita har sadiya ya isheni bazan kuma saurara musu ba . Don haka taje ta gayawa su innah har da adda Ai wai na zagesu nace yanzu bana tsoron kowa a cikinsu kowa yayi min magana da banga dama ba zan maida masa da martani. Don haka innah ta gaya wa ya salman wai na zageta yazo yana tambayata na fada masa komai ban boye ba.don haka ya samu abbansa yace shi gaskia madiha zata bar masa gida domin tana jawo matsala tsakanina da innah.don haka abba ya ce zai kira mahaifinta ya gaya masa madiha zata koma don tafi karfinsu dama shi yasa baki ya salman ya yarda ta zauna da tuni ta koma kamaru. Haka akayita case din madiha a karshe dai dataga za,a maidata kamaru a mata auren dole sai kawai ta sami wani daga cikin samarin nata costom ne ta ce yazo gida ayi maganar aurensu .aikuwa ba bata lokaci akayi bikin ta tare a maiduguri ko ya zaman zata kasance oho. Nidai duk shagalin bikin madiha da akeyi banyi gigin zuwa ba don nasan bazan taba samun kallon arziki a gurinsu innah ba domin yanxu gani suke na mallake ya salman ina zaune ni kadai a gidan ina juyasa son raina na rabashi da kowa don haka suke jin haushina sadiya da adda A'i ko gaisuwata basa amasawa. Hmm ni dai ina fama da kaina domin cikina ya shiga wata tara ba,a gama watsewa bikin madiha ba na haifo yarona kato tubarkallah masha Allah sai kun ganshi ranar suna ya salman ya sanya masa sunan daddyna *IBRAHIM* muna ce masa *KHALILULLAH* daddy yayi farin ciki sosai kuma ya yi wa mai sunansa kyaututtuka na ban mamaki. Alhamdulillah rayuwa na tfy normal yanxu ni da sojana kullum muna manne da juna cikin so da kulawa.domin yanzu nafi karfin su innah da karfin addua suka shafa min lfy nake rayuwata da mijina cikin farin ciki. Sadiya kam aure yaki dadi sam kishiyoyi sun sakota a gaba sun hanata sukuni saboda yanda suka lura Alhajin yake ji da ita kuma har yana kokarin fifitata akansu gashi yana kashe mata kudi fiye da su da yayansu don haka kowacce ta tashi tsaye akan sadiya.don haka abin se ya mata yawa akwai kwanakinda har tayi wani rashin lfy kamar hauka sai da aka dawoda ita gida wai wasu irin halittu take gani in ta rufe idanta don haka ko bacci batayi dalilin rashin baccin ya jawo mata matsalar kwakwalwa innah ta shiga damuwa sosai musamman da likitoci kuma suka riketa a saikatiri don haka inna har jininta ya hau itama tayi rashin lfy sosai kasancewar sadiya a saikatiri ba karamin tada mata hankali yayi ba sai da salman yayi da gaske wurin nunan mata cewa sadiya ba haukacewa tayi na har abada ba domin likitoci sunce zata samu sauki su sallameta. An dauki tsawon watanni kamin sadiya ta gane kanta domin shima Alhajin nata ya dage sosai wurin nemawa sadiya magani ya kashe kudi sosai har akayi dace ta dawo daidai .sai kunga yadda rayuwa ta maida sadiya ta rame tayi baki sosai domin tasha wahalar jinyan nan nata. Saida ta warware tass snn ta koma gidan mijinta .amma ko shekara ba,ayiba ta sami ciki kuma da yake wahalar da ita watanta hudu a gida tana fama da laulayi cikin har ya kai wata bakwai amma daga baya shiru ciki ya kwanta ita bata haiihu ba bata yi bari ba kuma babu alamun ciki sunje sunyi scarning amma sunce basuga komai ba bayan kwanaki kuma sunyi scarning sunce tana da ciki lokacin wata biyar.don haka gabadaya hankalin innah ya tashi sosai sai neman maganin gida aketayi yanxu akan wnn kwantaccen cikin saidai muce Allah ya yaye. Gashi dangin mijin kaf sun tsaneta saboda yanda danuwansu keta kashe kudi akanta .shima kanshi Alhajin yanxu hankalinsa baya kan sadiya ya daina kulata sam sam don koda aka masa magana ma cewa yayi kawai shi bazai maidata gidansa ba ta cika laulayi don haka a ci gaba da nemamata magani in anyi dace ta warke in ta sami miji tayi aure kawai ya sawwaka mata. Tab aikuwa innah kadan ya rage tayi hauka don tsabar bakin ciki.gashi yanxu adda Ai gabadaya ta juyawa su inna baya tun akan maganar madiha a cewarta inna taki yarda a hada ya salman auren dangi da 'yanuwanta.don haka taketa fushi. Yanxu innah ita kadai take ji da matsalolin ta ga na sadiya.Raihana da sa,adatu sune masu kokarin kwantarwa innah hankali yanxu .se kuma yaya salman din . Toh sai dai muce Allah ya kyauta.......... Hauly ce👍🏻🥰 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡90 ***********Sanadin doguwar jinya da sadiya tayi ya sanya gabadaya tayi sanyi kamar ba ita ba har na kanji mamaki wasu lokutan in muka je gaida inna sam bata shiga tsabgar kowa. Da kyar ta samu Allah ya rabata da wnn kwantaccen cikin wanda akayita faman neman magani kusan shekara hudu sai daga baya akayi dace ta samu magani ta warke tass har ta fara maida kamanninta nada.sai dai kuma babu abinda yake damun zuciyanta da ya wuce taga itama ta samu gidan aure inda zata nitsu ta sami miji mai sonta na gari amma ya gagara.Jafar ma taso komawa gidansa amma sam bai bata fuska ba.hankalin sadiya ya tashi sosai musamman ma da yanzu taga jafar din yayi kudi gashi yanzu ya shiryu sanadin kamilalliyar mata daya samo ya daina neme nemen mata ya zama kamili ga kudi yaran sa kuwa yana basu kulawa sosai ba kamar da ba haka nan yanxu yana barinsu suje su gaida su innah amma sam baya yarda su dade a cewarsa baya son su dauki mugun halin uwarsu.don haka gabadaya sadiya hankalinta a tashe yake babu abinda tafi maida hankalinta akai yanxu kamar taga ta koma gidan jafar tunda wani aure ya gagara amma ina abun ya gagara (sai dai fans ku taya sadiya da addua lol!) Mu kam zuwa yanxu mun ci gaba sosai a rayuwa arziki yaci uban nada.ta kowanni fanni yaya salman samun ci gaba yake don yanxu yana daya daga cikin manyan sojoji da ake ji da su a *NIGERIA* wayanda sunansu sukayi fice wurin jarumta da jajircewa akan duk wani abinda ya shafi kasar nan.don haka nima ba,a barni a baya ba duk inda na fita ansan matar oga ce! girmamani ake sosai snn bana fita hakan nan ba security kamar da.kar kuso kuga yanda na sake yin kyau na dada haske fatata ta kara kyau da laushi gashi nayi sa,a sam banda kiba jikina daidai structure na kamar yanda kuka sanni da can lol! Don in ba wanda ya sanni bazaice nice na haifi yara biyu ba.sosai nake jin dadin rayuwata a yanxu ya salman riritani yake kamar zai karbe min numfashi ko kuda baiso ya taba jikina nima haka nake kokari sosai wurin tarairayarsa bana yarda in zama sanadin bata masa rai don ko wani ya bata mishi sai nasan yanda nayi nasahi ya huce nan da nan.Sai dai zakusha mamaki tun kan khalilullah haihuwa ta tsaya .yanzu khalil nada shekara goma farida sha uku . *HMMM* *RAYUWA* *KNN* Zakusha mamaki in kunga yadda farida ta girma a shekara sha ukun nan duk wani alamomin budurci ya bayyana. Gashi ya Salman ya dauki son duniya ya dora mata ko laifi farida tayi baya gani ya sakar mata kudi kuwa tayi yadda ta ga dama don ma ba a gabanmu take ba.don ma wani abin duk ya salim na taka masa birki hade da nunan masa ba haka ya dace a tarbiyantar da yaro ba.ni kam ko na fada masa baya yadda . A wannan lokacin munir ya kuma ya gama secondary shima sai kunganshi ya zama saurayi ga nitsuwa ga kyau ga tsafta uwa uba ga gayu barema training din hakim ne ko ysushe tare suke tun bai kai koina ba ya iya driving da duk wani abu da samari suka iya shima fa ba,a barshi baya ba.don haka ma yacewa ya salman a London yake so yayi jamiarsa .ba bata lokaci kuwa ya salman yayiwa ra,is da faiza magana aka gama masa komai ya tafi. Su innah kuwa aka rushe musu gidan nan aka sake yin gini irin na zamani sai wanda ya gani kyaunsa baya misaltuwa section uku kamar da gefensu inna da na mama duk da bata gidan da kuma na kawu kassim duk su ya salman sun sake musu sabon fasali mai kyau. Gefensu innah itada maman sakina kowa sashinsa daban dakuna buyu kowanne da toile ga kuma kitchen ga dining side. Snn a waje ma akwai kitchen da store na kowa da kowa don yanzu babu abinda su inna sukeyi na aikin gida an kawo musu mai girki shara da wanke wanke.Hmm yanzu in munje gidan sai dai mu sami inna harde kan 3seater hannunta rikeda remote don innah irin mutanen nan masu son kallon tv sosai musamman ga channel din *arewa24* mai tfy dai dai da zamani don haka wuni take yi tana kallo ga AC ta koina yana ratsata. Sadiya kuwa duk ni,imar nan da take ciki sam bata jin dadi burinta ta samu dakinta itama don a halin yanzu bata da abokin shawara duk 'yan uwanta suna gidan mazajensu hatta mara kunyar nan madiha ta nitsu a gidan mijinta tun farkon auren da ta fara rashin kunya mijin ya saitata ta nitsu tsaf ta dawo hankalinta.su nabila kam tuni dama suna gidajensu.adda A'i kuma har yanzu bata wani shiga harkarsu.ga raihana da sa,adatu ma ba ruwansu da ita.dama innace mai share mata hawaye da bata kalamai to inna ma yanzu sai a slow ta daina damuwa da halinda sadiyan ke ciki.sha,ani yau da gobe se Allah.don haka komai ya dagulewa sadiya sai addua. Watarana da mukaje gaida inna har rokon ya salman takeyi wai don Allah ya roki jafar ya maidata gidansa ta zauna da yaranta. Wani irin kallo ya mata wanda yasa ta nitsu lokaci daya bata kara magana ba ta mike ta shige daki ko shakka banayi nasan kuka zatsyi tuni naji tausayin sadiya na ratsa ni . Inna tace"hmm ai wnn jafar din da sadiya zata gane da ta rabu dashi don baida mutunci ko kadan amma ta kasa cire shi a ranta kullum kamar zuga ta ake. Ya salman yace"wai inna ba abba yace min ta sami wani Alhaji hamid ba har yana so ya turo maganar aure? Inna tace"hmm wai ita bata son mai mata da yawa tsoro takeji don haka ta hanashi turowa . Ya salman yace" aikuwa tayi babban rashi wlh domin mutumin nan yana da hankali sosai gidansa akwai tarbiyya fiyeda yadda kk zato.bansan meyasa abba ya barta ta koreshi ba. Inna tace to ya zaiyi da ita tunda tace batayi sadiya ai ba yarinya bace yanzu bare mu mata dole . Shiru ya salman yayi bai kuma cewa komai ba. Can inna tace"yawwa ya maganar dawowar shatu nan ne ? Naji sake yin shiru ? Ya salman yace"inna kinga farida ta riga ta saba da Abuja bazata yarda ta dawo nan ba.snn salim bazaiji dadi ba shida matarsa idan nace farida ta dawo kano tunda kinga tun tana shekara uku take wurinsu ..... Inna ta katseshi da fadin "ai dama nasan zaka fadi hakan yanzu shikenan ni banida jika ko daya a gabana bsnida wanda zasu tayani hira ga rabi nan ko wani hutu sai an kawo yaran sakina da zainab sunsha hutunsu anan.amma ni kiri kiri kana gani raihana bata taba yarda ta kawo min yaranta suyi hutu sai dai wuni shi kuma jafar sai kusa kusan nan ya fara barin Abdul da Amira suna zuwa su gaishemu shima a tsassaye ko ruwa basa tsayawa sha.snn shima khalil baya son zuwa wajena bansan me uwarsa ta fada masa akaina ba gabadaya yabi ya tsaneni .... Ya salman ya katseta da fadin "ba haka bane inna khalilullah haka nan Allah yayi shi baya sakewa da kowa komu nan ba sosai yake sakewa damu ba .don Allah ki daina daga hankalinki akan wnn.jikoki dai kici gaba da addua Allah zai kawosu suxo su tayaki hira . A tunaninsa zata saki ranta haba ai kamar ya zugata don cewa tayi"yaushe knn zan tara jikokin tunda naga ai ku kun daina haihuwa gabadaya tunda khalil yanzu har zama saurayi shekara goma..... Sam na lura bai son maganar don haka yace don Allah inna ki bar wnn maganar kawai kidai ci gaba da addua ke dai. Daga nan ya tashi ya kalleni yace" rumaisa mu tafi Tashi nayi jikina a mace muka mata sallama muka tafi a hanyarmu na komawa gida nace"yaya don Allah ka duba lamarin sadiyan nan wlh ta na bani tausayi. Yace"hmm barta dai tukunna nafi so sai tayi laushi sosai ta gane Allah dayane snn zan shiga lamuranta . Nace "haba yaya wani laushi kuma shekara nawa tana fama?ai yanzu in ka lura sadiya ta shiryu ta daina shiga tsabgar kowa matsalarta kawai ta samu tayi aure ta huta kamar kowacce mace.don Allah yaya ba dan halinta ba ka taimaka ka duba lamarinta kasa baki..... Yace"naji zan yi tunani akai baby shikenan. Murmushi nayi nace"yawwa yayanah ko kaifa? Bai kuma yin magana ba har muka isa gida mun sami khalil ya dawo islamiyya na kalleshi cike da kulawa nace"daddyna innah tana gaisheka kuma wai tana missing dinka sosai kamata yayi gobe sunday sai kaje ku wuni har lokacin tfyn islamiyya sai ka dawo. Hade fuska yayi yace"ni momy bana son zuwa gidansu innah ta cika son fada. Yana fadin haka ya juya ya tafi ciki ya barmu.dagani har ya Salman binsa mukayi da kallo nace"hmm dama ai khalil kam baya son mutane bansan ya zanyi dashi ba. Shidai baiyi magana amma na lura baiji dadin maganar khalil ba duk da ma yasan matsalar daga wurin innan ce tana son jikoki amma bata iya bi dasu a hankalli ba.kullum adduarsa akan innah yafi yawa saboda halayanta.burinsa bai wuce yaga inna ta daina halayanta marasa kyau dinnan. ABUJA Farida kuwa tunda suka fara zuwa secondary itada mimi sun kara wayewa sun zama big girls gashi Allah yayi su da girman jiki musamman ita farida don haka tuni ta fara jan hankalin samari duk inda ta shiga sai ta sami saurayi .tun bata kulasu yau da gobe har ta fara gane meye soyayya don haka tun tana jss 3 ta fara tara samari sabanin ita mimi bata yarda da wasu samari karatunta kawai tasa a gaba kuma tafi farida hankali da nitsuwa nesa ba kusa ba duk da farida ta fita ilmi sosai. Ruma kam hankalinta ya tashi sosai da irin halayen farida domin a yanayinda ta karanci halin farida da dabiunta duk irin bangarensu innane.(Allah mai iko)da farko taso ta boye min amma daga baya taga babu amfani gara ta sanar dani. Hankalina ya tashi sosai don nima din naga alamu da tazo wani hutu gabadaya hankalinta na kan charting da samari maganar makaranta kuwa bata kaunar mimi ta kawo mata.kamin su gama hutu su koma sai da na kwace wayarta na kuma cewa ya salim kar ya kuma barinta ta rike waya sam sam. Na sami mama da maganar na fada mata komai tace"hmm ai dole ne farida ta dauki halayansu sadiya rumaisa jini fa ba wasa bane.ni banga abin damuwa sosai anan ba addua ce kawai zaku rika yi mata hade da maida hankali akan duk wani lamarinta insha Allah babu abinda zai faru da ita su sadiyan ma da kk gansu hakan harda rashin samun tarbiyya ne tun farko shatu ta riga ta batata da mugayen dabiunsu gabadaya kuma danginsu haka suke basa lura da tarbiyan yaransu shiyasa suka tashi a haka.amma ita farida idan har kuka tashi tsaye a kanta da addua in Allah ya yarda zata shiryu tsaf har kiyi mamaki . Nace"to Allah yasa wlh gabadaya na shiga damuwa mama har bacci bana iyayi sosai. Tundaga lokacin na zage wajen yiwa farida addua sosai a hankali kuwa sai abin yayi sauki da ikkon Allah domin ruma tace min yanxu ta daina kula samarinkuma ta maida hankali gun karatunta.dadi naji sosai na godewa Allah! Hauly ce🥰👍🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡91 *******Duk abin nan dake faruwa na matsalar farida ban taba gayawa ya salman ba sanin halinsa har Allah yasa ta daina.Alhamdulillah naji dadin yanda ruma ta gaya min farida ta nitsu sosai har tana zuwa farko a ajinsu dama ililmi kam akwai shi masha Allah. Dama ya salim ya musu alkawarin suna gama junior waec zasu tafi umrah gsbadayansu.don yanzu ya salim yaransa biyar ne bayan munir da mimi da Salman junior akwai mohd me sunan abban salman snn Ahmad me sunan mahaifin Ruma.gsbadaya zasu tafi har da khalilullah daga can ma london yace zasu wuce don suje su kaiwa su faiza da ya munir ziyara don gabadaya munyi kewarsa nima ba don aiyuka sun ma ya salman yawa ba da mun tafi duka. bayan sun gama aikin umrah suka tafi london ranar karkuso kuga murna gun faiza da rais da yaransu shidda suma.don haka gabadaya aka hadu aka shiga tadi cikin nishadi da annashuwa har lokacinda munir ya dawo makaranta yana ta dokin son ganin 'yan nigeria don yayi missing dinsu sosai. yana shiga palon yaran gabadaya suka tashi suka masa oyoyo hade da rumgumeshi . Dariya yakeyi yace"karfa ku kada ni. Farida ce ta kalleshi cike da fara,a tace"ya munir munyi missing dinka sosai kaga yanda ka zama babban mutum kuwa gabadaya ka zama kamar uncle hakim . Shikam murmushi yace"ai gabadaya ni kuma farida girmanki yafi bani mamaki dubi yadda kika zama 'yanmata keda na barki yar kankanuwa. Nan da nan farida ta zumburo baki ta kama fishi akan munir yace mata yar kankanuwa harda kararsa ta kai gun daddynsu salim. shikam munir binta yakeyi da kallo duk yanda tayi gabadaya baima san ya shagala da kallon kanwar tashi ba. Faiza kuwa tuni ta fahimci irin kallon da munir din yakewa farida murmushi tayi hade dan gyaran murya tace"son to baka zo ka gaida su mum dinka ba . Da sauri munir ya isa gunsu ya salim yana dan sosa keya hade da satan kallon farida wacce bata ma san yanayi ba.sai tsokanar su mimi takeyi dama ita farida gwanar tsokanace ga son fada in dai tana guri babu zaman lfy ta dinga neman magana knn. Munir ya gaida iyayensa cike da biyaiya don bai cika sakin jikinsa dasu ba.sai ni da ya salman .anan yake tambayarsu labarinmu ya salim yace"suna ta gaisheka sunyi kewarka sosai sai dai kawai daddynku aiki ya masa yawane. munir yace"ayya daddyna ai to daya bar mummy tazo daku. Faiza bata san lokacinda tace "tab hmmm ya salman bazai taba bari rumaisah tayi nitsa dashi ba ai.su har yanzu basa tsufa da so........ Harara da ya salim ya sakar mata yasa takama bakinta tana dariya don tama manta yara na nan. Farida kuwa tayi caraf tace"ai goggo bakisani ba mamana bata son inje hutu saboda indai naje daddy baida lokacinta....... Ruma tace"kinci gidanku farida waya sako bakinki a cikin wnn zancen? munir ya danyi murmushi yace"kannena ku tashi mu tafi sashina mu barsu suyi hirarsu anjima se mu dawo . Ya tashi farida tuni ta shige gaba ta jera dashi tana cewa "ya munir nima in na gama secondary nan london zanzo karatu garin naku ya birgeni. munir yana kallonta yace"really . daga masa gira tayi hade da fadin"yeah. Ya gyada kai yana murmushi yace"Allah ya kaimu lokacin. Munir ya yi hira da kannensa sosai hade da tambayarsu labarin makaranta suna amsa masa.ranar kwana sukayi hira har gari ya waye. Gaskia munir ya rikice akan farida sosai sai yanxu ya gane da can ma sonta yake ashe don ya dauka shakuwace kawai irin na yanuwantaka amma yanxu ya fahimci soyayya ce me karfi. Haka nan faiza ta karance shi tsaf don haka ta gayawa rais suka kirashi suka tambayeshi don baya boye musu komai anan ya tabbatar musu yana son farida.ba karamin dadi faiza taji ba don haka ta sami ya salim ta gaya masa amma abin mamaki sam bai damu ba don cewa yayi ta bar maganar nan kawai jikin faiza ya mutu sosai ta gayawa ra'is shima ya tambayi salim din meyasa yace sudai bar zancan don haka sukayi shiru ba tareda sanin dalilinsa ba. Munir kam ya gama rikicewa akan farida abin har ya wuce misali don gani yake in sun koma Nigeria kamar za,a kwace masa ita don haka ya fara tunanin furta mata.amma ya salim ya hanashi yace farida na makaranta kar ya raba mata hankalinta biyu. Haka suka karasa hutunsu suka dawo Nigeria kano suka fara isa ranar na wuni ina musu girke girke na musamman. Ya salman kuwa ya tura aka kwashesu a airport.a lokacin Abdulwahab dan sadiya ma yazo muna tattauna batun mahaifinsa da mamansu dashi don ya damu sosai yana son mahaifiyarsa ta koma gidansu.a inda ya salman yake ce mishi tunda yanxu ya girma shi ya kamata yasan yanda zai daidaita tsakanin mahaifinsa da mahaifiyarsa. Muna cikin tattaunawa dashine yan London suka iso don haka gida ya kaure da murna tuni farida ta tafi ta rumgume mahaifinta tana"daddy nayi missing dinka sosai wlh.daddy ya munir ya gaisheka sosai.muje ciki na baka labarin hutunmu . ta rike hannunshi wai su tafi sashinsa murmushi yayi yace"ai karki damu mamana anjima zan kiraki muyi hira sosai kinji? Ya fada hade da shafa kanta tace daddy maganace mai tsawon gaske in muka bari se anjima kwana zamuyi muna hira. yace"to fakice babbar maganace kike tafe da shi mamana? ta daga masa kai hade da rike masa hannu tana jansa su tafi har tana ce mishi daddy na maka tsaraba mai yawan gaske sai ka gani muje daddy ciki in baka labarin london da saudi. Harararta nayi nace wai ke farida yaushe zakiyi hankali ne?kina gani ko gaisawa dasu daddynki baiyi ba zakice ku tafi ? Kuma wnn ba yayanki Abdul bane tun shigowarku yana nan duk yaran nan sun gaisheshe amma banda ke. Sai lokacin ta kai kallonta ga Abdul wanda shima tun shigowarsu yake ta binta da kallo duk inda tayi. fuska a daure tace"ya Abdul yi hkr ban ganka bane ya kk ya aiki? Cikeda fara,a Abdul ya amsa mata gaisuwan. Ganin magriba yayi yasa gabadaya muka watse su yaya suka tafi masallaci mu kuma muka wuce dakina da ruma sai farida da mimi suma suka wuce dakinsu.bayan sallar ishane mukayi dinner anan muka shiga hira har sai sha biyu kowa ya tafi makwancinsa farida kam taso tayi hira sosai da babanta amma sam naki bata fuska.saida sukayi bacci gabadaya muka shiga hira da ruma ya salman kuwa jin shiru yasa turo min text wai inzo ya gaji da jira.don haka nay maza na kintsa ruma na cewa "kina tfy nima zan lallaba in tafi gun... dariya nayi nace"kije kawai amma asuban fari ki dawo . Tare muka fita ita ta tafi sashin baki ni kuma na wuce oda room inda na sameshi ya gaji da jira ina karasawa na fara bashi hkr cikin kwantar da murya nace "am sorry yaya wlh na dauka ko zaka hkr na yau dinnan.... Wani irin kallo ya min wanda ya sani yin shiru da wuri ina murmushi hade da toshe bakina. A hankali na tafi na kwanto jikinsa nace"wlh yaya na gaji sosai yau massage nake bukata . gyara min kwanciya yayi snn yace"kwanan nan kina wahalar dani sosai baby me yasa ne ? Ko kin manta irin mijin da Allah ya bakine ? shiru nayi ina murmushi yace"ko kina bukatar in kawo miki kanwa ne mai tayaki hidima .... Nan da nan na canza fuska na yunkuro zan tashi da sauri ya maidani ya kwantar yana dariya yace" kwanta da wasa nake miki dear. ya fada yana dariya duk da hakan na kasa sakin raina. nayi.don haka ya rumgumeni a jikinsa yayinda ya kai bakinsa saitin kunnena yace" ke kadai ce a zuciyata babynah ba wata.kin ishe ni komai a rayuwa bana bukatar wata don haka ki dada kwantar da hankalinki ni salman nakine ke kadai rumaisa. Murmushi nayi na kara shigewa jikinsa na kwantar da kaina kan kirjinsa nace"yaya ina jin dadi sosai a duk lokacinda kake gaya min irin wnn maganar Allah ya barmu tare. Yace "ameen babynah. Murmushi nayi nace"yaya gaskia ni yanzu na girma a daina kirana da baby kaga fa akwai lokacin da ka manta ka kirani baby a gaban farida dariya ta dinga mana. Murmushi yayi ya manna min kiss a baki yace"shareta kawai ni babyn nan bazan iya barin kiranki da shi ba. Anan ya kashe wutan dakin ya jawo mana bargo daga nan topic ya canza.gaskia ya salman daban ne a cikin maza ya iya gwadawa mace soyayya gaba daya rikitani yake har in manta a wace duniya nike gabadaya. Washe gari kasancewaar ranar asabar ne gabadaya muka tafi gidan mama mun sami ruky da imran (twins din mama)sunzo jiya . Ya salman ya kalli ruky hade da fadin"ke kuma ya isheki ja mana rai haka kawai ki amsa a wuce wurin. Ya salim yace"Wai a dole ita jan aji take mana mummuna ma irinki Dariya tayi ta kalli mama tace"mama kinajinsu ko ya hakim yaje ya hadani dasu. Mama tace"to ai gaskiane rukayya tun yaushe hakim ke binki da kin amsa tuni anyi auren nan amma kinki kice komai . Tace"mama ni wlh ya hakim ya min tsufa da yawa . Da sauri nace"amma bakida mutunci ruky yanxu hakim dinne zaki wani cewa ya miki tsufa? Imran yace "ai gaskiane aunty ihsan gara dai ya nemi daidainsa. Harararsa nayi nace"to waya sako bakinka wai kai mai yaruwa koh? Na kalli ruky nace"ke kuma wlh zan fadawa daddy don gaskia ba za mu zuba miki ido kina abinda ranki yakeso ba. Ya salman yace"da kin kyauta wlh .tama ci sa,a hakim yace yana sonta mummuna ma irinta. Ya salim ya karba yace"ai nima na rasa me hakim ya gani anan.duk familynmu itace mummuna. Turo baki tayi tace"mama kina dai jin su yaya abinda suke fadi koh? Mama ta tabe baki tace"kun fi kusa ai rukayya. Ruma tace"gaskia ya isa haka ku daina zagin kanwata. Ta rike hannun ruky tace,zo muje ciki kanwata ki fada min mece ce matsalarki. Daga gidan mama sai muka tafi gidansu innah.farida wani tsalle ta daka ta fada jikin innah ba shiri inna ta sakar mata dundu a baya tace"jaira so kk ki kasheni? Farida tayi dariya tace"tsohuwa me ran karfe kina nan abinki.wlh ni duk tunanina kafin mu dawo hutu zamu dawo mu samu kin tafi. Inna tace"uwarki ce zata tafi ni kam ina nan sai na goya yaranki. Farida ta daure fuska tace"kinga matsalata dake ko.na gaya miki wasa wasa banda maganar zagi bana so ki daina sako uwata a cikin zancenki. Inna tace"to yi hkr naga nan da nan har kinyi fushi . Farida tace"nayi fushi sosaima yanxu kawai ki tashi ki mana dan wake muci snn in huce. Innah tace"an gama shatu ai dole kawai in tashi da kaina in muku danwaken nan. Innah tana kokarin mikewa nace"innah don Allah ki rabu da ita in zasu ci danwake suje su fadawa hajara tayi musu. Ruma tace"gaskia kam inna kar ki biyewa farida . Inna tace"karku damu sam da kaina zan mata.inaji da mai sunana dinnan sosai. Murmushi mukayi nida ruma inna kam fita tayi farida da mimi suka bita a baya saura ni da ruma da sadiya don su ya salman da yara mazan nan suna sashin abba muka barsu. Na kalli farida nace"sadiya meye labari ne? Jiya Abdul ya kai mana ziyara. Ta danyi murmushi tace"wlh rumaisa ba wani labari yanxu Abdul din nake jira . Nace"to Allah ya doraki a kan mahaifin nasu . Tace"amin. Mun dade a gidan sosai muna ta hira da sadiya kamar ba ita ba ikon Allah knn. Da yamma muka raka mutanen Abuja airport suka tafi. Munir kuwa a can london tunda su farida suka dawo hankalinsa yaki kwanciya gani yake za,a kwace masa ita don haka ya fadawa goggonsa faiza tace shifa kawai zai gayawa farida sonta yake don kar ya tsaya garin kallon ruwa kwado ya masa kafa. Itama faiza ta bashi goyan baya amma tace ya bari sai ta tuntunbi ya salman . Aikuwa ba bata lokaci ta fadawa ya salman komai amma tace masa ya salim yaki amincewa bata boye masa ba. Gaskia ya salman yayi murna sosai saidai ya rasa dalilin da yasa ya salim yaki amincewa don haka yayi niyyan zuwa Abuja domin suyi maganar....... Hauly ce🥰🙏🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡92 *************Ya salman a cikin satin ya shiga Abuja suka zauna tattauna maganar farida da ya Salim. Ya salim yace"dama nasan fa,iza bazata bar wnn maganar ba sai ta fada ma.amma ina son ka kwantar da hankalin ka kar ka fassara maganar da wata manufa. Ya salman yace masa nifa ba wnn ya kawoni ba har yanxu baka gaya min dalilinda yasa baka so mu hada yaran nan auren zumunci ba. Salim ya danyi shiru kamin daga bisani yace"Salman abinda yasa kaga naki bada goyon baya shine kaga dan wajan Raihana Jamil da kuma fadil dan gidan sakina sun jima da yi mun magana akan suna son farida kuma dukansu the are very serious domin shi fadil har da turo min babansa ma kawai dai na dakatar dasu nace su bari sai farida ta gama makaranta tukun .snn da zuwan mu london shikuma munir ya fara shiyasa nace bana so ya bar maganar domin zata iya haifar da matsala.suma su jamil bansan ya zanyi daya ya hkr ya barwa daya ba....... Ya salman ya daga masa hannu hade da fadin"wnn shine kadai dalilinda yasa zaka hana munir fareeda? shiru sukayi na dan wani lokaci snn ya salman yayi murmushi yace"to abinda baka sani ba shine dan wajan sadiya Abdulwahab ma sonta yake kuma ya sameni da maganar da dadewa snn kuma mamanta ta gaya mun cewa dan yayanta samir ma hamis yana son faridan. Ya salim gabadaya ya rasa me zaice akan maganar domin gabadaya yasan nan gaba abin zai zama matsala babba na family . Cire hulan kansa yayi ya ajiye gefe ya kalli ya salman yace"to fa yanxu kai me abinyi ina mafita ?don kasan fa akwai matsala gaskia. ya salman ya danyi dariya yace"duk ka bi ka rikice akan wnn maganar don Allah ka kwantar da hankalinka.abinda nakeso da kai kowa a cikinsu ka barshi yaje ya gwada sa,ansa duk wanda ta zaba shikenan sai saura suyi hkr kaga ai ba hannunmu a ciki tunda yanxu duk sun san cewa zabin yarinya ake bi an daina auren dole .don ka bari tukunna tunda munir ya kusa dawowa idan ya dawo shikenan mu barsu kowa ya gwada sa,anshi.amma ni ina son ka sani har cikin raina nafi son munir ya auri farida saboda nafi yarda hankalinsa da tarbiyansa .amma babu komai zanci gaba da addua Allah ya tabbatar musu da abinda yafi alkhairi dukansu tunda gabadaya 'ya'yanmune. Ya Salim ya gyada kai cikeda gamsuwa yace"hakane. Ni dai tunda ya salman ya gaya min maganar nabi na rikice domin ina tsoron kar wnn abin ya haifar dagaba a cikin family. Abdulwahab din sadiya gashi sai kara dagewa yake har ya fadawa innah da kuma mahaifiyarsa anan innah ta dage akan maganar sadiya ma sai da tazo wurina akan maganar na rasa me zanyi gabadaya don ma naci sa,a yanzu sadiya da innah duk sunyi sanyi bama sadiya da wanda duniya ta gogata yanzu nitsu sosai kuma taci sa,a albarkacin yaranta jafar ya maidata gidansa amma ba wani dadi da takeji domin da ta danyi kuskure kadan ya kama zaginta da yi mata gori hakama danginsa kaf sun sakota a gaba da kiyayya hakan nan take lallabasu domin ta samu ta zauna domin tasan in ta kuskure tayi wani abun sallamarta zaiyi.(Allah sarki duniya mai maida akawu kuku.a shekarun baya sadiya ke juya jafar son ranta duk ta rabashi da danginsa amma gashi yanzu ina ba abinda ta isa tayi dole ta bi komai a sannu). Munir kuwa bai iya barin farida haka nan ba ya shiga nuna mata kulawa ta musamman kullum sai ya kira sunyi hira sosai don haka suka kara shakuwa sosai kamin ya dawo. Suna ss 3 munir ya dawo don haka kowani weekend yana Abuja. Gabadayansu samarin kowanne ya gabatarwa farida da bukatarsa .don haka gabadaya ta rikice ta rasa wa zata zaba wa zata bari. Wani zuwanta hutu babanta ya tambayeta wa takeso a cikinsu tace munir take so ita don haka ba bata lokaci ya salman ya sanar da abbansa dama yasan komai jira kawai sukeyi suji wa zata zaba cikinsu.anan abba ya kira jamil,fadil da abdul ya basu hkr akan su hkr su barwa munir farida ... Hmm anan fa innah ta kama balai musamman tayi kiranmu da ya salman ta shiga zazzaga mana rashin mutunci ya salman yayita bata hkr akan ba laifinsa bane farida ce ta zabi munir. Amma sam innah bata hkr ta sakomu a gaba nida ruma tace mune muka hada wnn munafurci muka tilasta farida akan ta zabi munir . Raihana da sakina kam sun hkr da maganar kuma duk sun ba yaransu hkr hade da fahimtardasu komai.hakama hamis dan samir shima ya hkr.shima Abdul da farko ya hkr amma daga baya haka inna ta dinga zugashi akan kar yaja baya da neman auren farida.Ya salman kuma ya ce bazai yiwa farida dole ba.Sadiya kam duk da batace komai ba amma ta shiga gaba dani ko na mata magana sama sama take amsa min .Innah kam gabadaya yanxu ta dawoda halinta nada kullum shan zagi nake akanta. A lokacinda su farida suka gama secondary akayi bikin ruky da hakim bayan bikin ne munir ya sake tfy US don yin wani course na shekara daya wanda ya salman yace insha Allah yana dawowa zaayi bikinsa da farida hmm karkuso kuga farin ciki a gurinsu dukansu da kyar suka iya rabuwa tunda ya tafi farida ta shiga kewarsa sosai. A lokacin shi kuma fadil din sakina ya koma son mimi don haka gabadaya in munir ya dawo za ai bikin Amma tfyn munir da watanni hudu kacal farida ta hadu da faruq (dan wajen Ahmad da Salima) a wani dinner party din bikin wata kawarsu da suka xo akayi shi a kano su farida suna cikin kawayen amarya shi kuma farouq yana daya daga cikin manyan abokan ango anan yaga farida gabadaya ya gama rikicewa akannta duk da taki sauraransa da farko amma sai da yasan hanyarda yabi ya dinga mata kalaman yaudara har ta fara sauraransa har tanaji a ranta farouq yafi munir iya nunawa mace soyayya anan ta fara jan baya da munir ko ya kira bata dauka in kuma akaci sa,a ta dauka bata wani hira dashi duk hankalinsa ya tashi don haka ya ke sanar da ruma hade da tambayarta kodai akwai wanda yake hurewa farida kunnene? Tace ya kwantar da hankalinsa zata bincika. Wasa gaske gabadaya halin farida ya fara sauyawa kuma gashi ta koyi karya sai ta fice ta bar gida ba tareda ansan inda taje ba.anan fa ga salim ya gane wanda yake hure mata kunne hsnkalinsa ya tashi matuka domin yasan in ya salman yaji wnn labarin hmmm..... Anan ya shiga kokarin raba farida da farouq...... ****** Mu dai bamu san me ake ciki ba akan maganar farida domin ya salim bai fada mana ba.matsalar innah ma kadai ta ishemu.duk da Abdul din ma daga baya ya hkr amma innah taki barinmu hakama sadiya bata daina gaba dani ba. A wnn lokacin innah taje camaroo ta dade sosai don tayi wata biyu a can kamin ta dawo . Kawai bayan dawowarta aka fara maganar hada ya salman aure da Nafisa yar autarsu adda A'i wacce kwata kwata bata wuce sa,ar munir ba .kawai ya salman yazo yana gaya min magana kamar a mafarki wai mahaifin adda Ai ya bashi nafisa ya aura kuma bazai iya bijire masa ba yanajin nauyinsa don bai taba neman alfarma a wajansa ba se wnn karon . Haka kawai jikina ya bani akwai wata a kasa domin yadda na lura da ya salman kamar ba,a cikin hankalinsa yake ba.don haka nace masa babu komai na amince Allah ya tabbatar da alkhairi dadi yaji sosai har ya mun kyautar mota sabuwa dal wacce ake yayinta yanzu. Su innah abin nema ya samu wnn karon kam Adda Ai ma tuni ta dawo sun fara dasawa dasu innah an fara shirye shiryen biki nan da nan .yayinda ni kuma suka sakoni a gaba da habaici adda A'i har cewa take nafisa zata zo ta cika ma ya salman gida da yara tunda dama ni wani haihuwa nake ba. Duk abinda sukeyi ban tanka masu ba sai dai hankalina ya tashi matuka ganin yadda ya salman yake rawan jiki da auran nan har baya iya boyewa a gabana.na shiga damuwa sosai har bacci bana iya yi cikin dare kwana nake yi ina juyi tunanin auran ya salman da nafisa ya hanama zuciyata sukuni. Ya salman ko a jikinsa kwana yake baccinsa baima san halinda nake ciki ba........ Fans kuyi hkr kwanan nan ban cika samun lokacin typing ba ina zuwa makaranta.don haka ku dinga manage da wanda kk samu😄🥰🥰🥰🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻 Hauly ce👍🏻🥰 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡93 *********Ana sauran sati biyu biki tuni aka fara hidimomi an bubbbuga kati ana ta rabawa gashi sunyi niyyar kece raini a wnn bikin saboda parties ya kai kala hudu zasuyi.Adda A'i ta fitarda da ashobi masu kyau da tsada duk da ma yanxu arzikinsu yayi baya ba kamar da ba.nima sun turon da samples din wai ko zanyi.ya salman yace zai bani ko nawa ne in saya nima inyi.hmm ya salman yanaji da wnn auran domin duk abinda su adda a'i suka ce ya kawo bayarwa ya keyi sosai ya zage ya shiga kashe kudinsa a wnn bikin. Wata ranar lahadi na gama girkin break fast ina shirya dining sai na dinga jin jiri na dibana kadan kadan yayinda duhu ya fara mamaye koina kamin na samu isa in zauna kujera tuni hankalina ya bar jikina na yanki jiki na fadi kasa a sume. A haka ya salman ya fito ya sameni kasancewar a part dinsa ne dama na barshi zai shirya ya tafi gidansu innah. Hankalinsa tashe ya iso ya dagani yana jijjigani yana"rumaisa menene? Da sauri ya kwantar dani kan kujera yaje ya dibo ruwa ya shiga shafa min a fuska nan nayi ajiyar zuciya na fara bude idona a hankali . Shafa kaina yayi yace"baby meyeke damunki dama ba kya jin dadine baki gaya min ba? a hankali na iya motsa bakina nace"yayah Hannuna ya rike hade da fadin"na,am menene? Shiru nayi yace"bari inzo mu tafi asibity kawai. A hankali nace"Yayah ka bani ruwa nasha don Allah Da sauri ya tashi ya kawo min ruwa ya dagoni nasha snn ya kwantar dani. ai kuwa nan da nan naji tashin zuciya sai amai na kamayi na ruwan da nasha. Ya salam ya fada hankali tashe nan ya dauki waya ya kira doctor. Haka ya dinga hidima dani har sanda doctor yazo ya duddubani hade da bani shawaran in rage tunani kuma in dinga cin abinci nan ya rubuta magunguna kuma ya dauki jinina domin yaje yayi min teses.snn ya dora min drip. Ya Salman tuni ya kira drivernsa ya bashi takardan maganin akan ya je ya siyo in fara sha tun da wuri. Da haka ya fasa tfy gidansu innah yana zaune ya sakoni a gaba duk ya shiga damuwa da rashin lfy na har yana cewa" Rumaisa ko akan maganar auren nan ne kk daga hankalinki ?kinga fa shiyasa tunda farko sai da na nemi amincewarki kuma kin nuna min ba matsala amma gashi yanzu kinzo kin shiga damuwa. Girgiza mishi kai nayi nace"yayah ba maganar aurenka bane ya sani rashin lfy don haka bana so ka shiga damuwa akaina sosai.... Ya katseni da fadin"rumsisa dolene in shiga damuwa in dai kema na ganki a cikinta. Ya rike hannuna daya yana kallon fuskata yace"kinga tashi guda duk kin rame yanxu....... Knocking din kofa da akayine ya katse masa maganarsa dan haka ya tashi yaje ya bude farida ce ta shigo tana dariya hade da fadin Salamu Alaikum . Ya salman ya saki murmushi ws,alaikumussalam mamana kece da safe. haka?ina sauran yan uwan naki? Tace"aini kadai driver ya kawo ni dinma da kyar mummy ta yadda inzo ...... Ta karaso bakin gado da sauri hade da fadin"Subhanallah daddy me ya sami mamana? dama mamana bata da lfy shine ba a gaya min ba?ina can Abuja hankalina kwance? Ta rike hannuna ta fara hawaye tace "mama me yake damunki mama kin ga yadda kk rame? Na zare hannuna cikin nata a hankali snn na shafi gefen fuskarta ina murmushi nace"karki damu farida ba wani rashin lfy ne na sosai ba tambayi daddynki dazun nan ne abin ya faru kamin nan ma nice na hada brekfast nayi komai. Ta kalli daddynta shima gyada mata kai yayi yace"hakane mamana.olsa ce take damun mamanki bata son cin abinci shiyasa. Da sauri ta tashi hade da fadin mama don Allah me yasa ba kya son cin abinci? Kinga fa mama ciwon nan na olsa bafa karamar ciwo bane kinga ya fara kwantar dake ko?pls mama ki dinga kiyayewa don Allah. Nace"Insha Allah zan kiyaye farida bazan kuma barin ya kwantar dani ba. Tace"to indai hakane bari inje in kawo abinci kici sosai kisha magani tunda nazo bazan barki da yunwa ba.kuma ko na koma Abuja zan nayin waya kullum in tabbatar kinci abinci? Ta tashi ta fita da sauri muka bita da kallo muna murmushi. Ya salman yace"pls baby ki dinga kula da kanki kinga kin fara samu cikin damuwa koh yanxu khalil ma in ya shigo ...... Bai rufe baki ba saiga khalil ya shigo shima hankalinsa a tashe ya shiga tambayar daddynsa meye sameni ? Haka ya dinga rarrashinsu hade da nunan musu ba wata rashin lfy sosai bane yake damuna farida kuwa ta dage sai naci abinci.aikuwa ina ci sai amai duk hankalinsu ya kara tashi.bayan nasha magani ne naji dan sauki nayi bacci. Anan ya salman ya tafi gidan su ya bar su farida suna kula dani .yana zuwa inna tace "salman ina ka shiga tun dazu muke ta nemanka a waya ? Yace"ina gida innah rumaisace ba lfy wlh. Tabe baki innah tayi snn tace "to me yake damunta kuma ? Yace"zazzabine da olsa Innah tace"hmm Allah ya sawwaka.yanxu dai ba wnn ba ya maganar masu zuwa kamaroo daukar amaryar ne ? Ya salman yace"ai innah ku zaku shirya masu zuwa anan din sai dai kawai kar mutane suyi yawa tunda kinga suma can suna da yawa zasu zo. Inna tace" to dama ai shiyasa nace kazo ayi maganar kar azo se an shirya kazo kana cewa anyi yawa. Yace"kawai inna ki bari mutane hudu suje tunda in an daura aure nan za,a dawo ayi dukkan parties . Tace"to su waye don A'i tace zata je hakama sadiya bansan raihana ba don madiha ma tace zata je. Yace"hmm ai kuma basu ya kamata suje daukar amarya ba don gashi ma hidimomin da ke gabansu nada yawa.ni anawa tunanin.momymu da maman sakina da goggo Amina in yaso da sa,adatu ko raihana suje .su adda Ai su hkr suci gaba da hidimarsu. Innah tace"Aminah kuma me zai kai Amina daukar maka amarya ? Yace"ai itace ma ya kamata taje daukar amarya domin banida wata goggo bayan ita kinsani so dolene itace a gaba kuma nasan ko bance ba zata je. Inna tace"hmm bana tunanin aminah zataje har kamaru don daukar maka amarya... Kirar wayarsace ya katseta ya dauka hade da fadin"ya akayi mamana ya jikin maman taku? Kome tace masa ne yace"to bari naxo yanxun nan. Ya katse wayar hade da tashi yace"innah bari inje gida in duba rumaisah Kauda kai tayi hade da fadin" to Allah ya sawwaka. Yana fita ta kira adda A'i ta fada mata duk yadda sukayi da salman Adda A'i tace"ai kar ki damu goggo hakan ma yayi Allah ya kaimu rai da lfy.ita kuma rumaisa ko ta tsiri rashin lfy ma se anyi bikin nan dan wlh ko gadon asibity aka kwantar da ita dole ne ayi bikin nan baza a daga ba. Inna tace"ai shine nima na fada a zuciyata ai dama rashin lfyn na munafurcine saboda a daga bikin.ta bakinki ko gadon asibity aka kwantar da ita biki dai ba fashi. Adda A'i tace"atoh. Tare suka shigo da doctor saboda yanda jikina ya dauki wani zafi zazzabine sosai ya rufeni kamar da wasa har na fita hankalina farida kam sai kuka takeyi . Saida doctorn yazo ya min wasu allurai lokaci guda kuwa zazzabin ya fara sauka.hankalin ya salman ya tashi sosai ya kalli doctor din yace"doctor me yake damunta ba kuyi teses din bane. Doctor yayi murmushi yace "karka daga hankalinka rashin lfyr madam na karuwa ne.domin tana dauke da juna biyu.... Da sauri ya salman yace"what kana nufin kace min rumaisa nada ciki? Doctor ya gyda masa kai yace "kwarai kuwa bayan wnn se kuma damuwa da rashin cin abinci . Ya salman ya dawo kusa dani ya riko hannuna daya yana kallon fuskata cike da jin dadi yace"baby kinji abinda doctor yace koh ?pls ki cire damuwa a ranki ki dinga cin abinci domin samun lfyrki dana babynmu kinji? Murmushi nayi cikin jin dadi domin dagani har yaya mun cire batun sake haihuwa a lissafunmu domin tun bayan haihuwar khalil ko bari ban kuma yi ba tun muna sa rai har muka cire.sai gashi Allah ya kawo a lokacinda ba mu zata ba. Bayan doctor ya gama abinda ya kawo shi haka ya salman yaci gaba da kwantar min da hankali . Zuwa yamma kuwa na warware tass amai danakeyi ma ya tsaya tunda nasha magani.don haka nayi wanka na fito palo . Farida tazo tana tambayana"mama me za,a dafa miki? Na rike hannunta hade da fadan zauna farida ki huta kin gaji sosai.yanxun bana jin yunwa se anjima zanci abinci kinji? Tace"haba mama don Allah kici wani abu mana to yanxu bari in je ko fruit salad ne in kawo miki . Ta wuce fridge da sauri ta saka mana fruit salad ta dawo ta mika min na karba ina murmushi nace"na gode Allah ya miki albarka. Ta zauna hade da fadin "amin mama na gode. Can tace"mama naso ace ina gidan nan domin wlh bazan bari su innah su dinga ci miki mutunci ba.meyasa kuka kaini Abuja? Da kun barni anan a gabanku wlh da abubuwa da yawa basu faru ba.ki duba fa don Allah mama a rasa wacce za,a aurawa daddy se Nafisa yar cikinsa gaskia wlh ni banji dadin wnn alamari ba kuma wlh ko ta shigo gidan nan sai nasa ta fita don bazan taba barin Nafisa ta mike kafa a gidan nan ba bare har su sami daman yi miki rashin mutunci. Nace"uhm uhm farida ban yarda ba bana so ki ce komai karki shigar da kanki cikin matsalar da bai shafeki ba.domin tun ba,a haifeki ba nake tare da su a cikin irin wnn yanayin kuma na saba baya damuna don haka ki kyalesu dukkansu domin ba sa,o,inki bane. Ta dan turo baki hade da fadin "naji mama amma wlh in dai.... Hannu na daga mata hade da fadin "ya isa haka bana son ji komai. Shiru tayi ranta a bace.don haka tashi tayi ta wuce daki tana waya. Tana shiga ba jimawa Sa,adatu ta zo da ya hafiz da yaransu Cike da fara,a nake tarbarsu yayinda sa,adatu take bina da kallo tace"aunty me ya sameki kika rame haka? Murmushi nayi nace"haba Sa'adatu ko hutawa bazakiyi ba tukunna mu gaisa. Hafiz yace"ai gaskiane nima naga ramar . Murmushi na kuma yi nace"hmm yaya rashin lfyn na yau ne fa kadai kuma gashi har na warware. Anan muka gaisa ya salman ma ya shigo ya samemu. Bayan sun gaisa ya salman yace"doctor hafiz ina da meeting daku. Ya hafiz yace"yaushe knn? Ya salman yace"sai an gama hidimar bikin nan tukunna zamu zauna meeting da kai da doctor samir da james da doctor sa,adatu. Murmushi sa,a tayi tace"har dani yaya ? Yace 'sosai ma ai meeting din na likitocine ina son in ginawa yarona asibity duk da ma dai ya nuna min yafi son yayi aiki a karkashin asibityn gwammanati amma hakan bazai hana ya mallaki asibitynsa na kansa ba ko dai. Ya hafiz ya gyada kai hade da fadin sosai ma wnn shawaran yayi Allah ya nuna mana. Sa,a tace"gaskiane yaya Allah ya taimaka. Yace "ameen Nima na amsa da ameen" Bayan sallar isha ya hafiz ya tafi ya bar su sa,a don biki tazo ta sauka a gurina. Saura kwana biyu daurin aure ya salman da abokansa suka tafi cameroo.washe garin su mama,momy,mmn sakina da raihana suma suka tafi don in an daura aure sune masu daukan amarya su dawo ayi biki anan. Su Adda A'i kuwa kusan kullum suna nan gidana sunata aikin jere da sadiya da madiha.babu yanda banyi da sa,adatu da farida akan suje su tayasu ba amma sam sunki. Nace"sa,adatu be kamata ba abinda kukeyi keda farida kuna so ku ja min zagine a gunsu suce ni ke zugaku . Sa'adatu tace"hmm ba sai su fada ba kina gani jiya ina gaisheda da adda A'i ta kama zagina haka kawai wai don na sauka a gidan nan ban sauka a gidansu innah ba. Nace"ai gaskiane kamata yayi kije can kuyi hidimar bikin tare har a gama ba shikenan ba.ni dai gaskia in ba so kuke ku ja min magana ba kuje ku taya su aikin jeren nan yana da yawa kinga tin jiya suke aiki daya . Sa,datu ta tashi hade da fadin to bari naje aunty tunda kin matsa. Ta kalli farida dake aikin chatting tace"muje farida. Farida ta bata rai tace"gaskia ni goggo sa,a bazan je ba kina fa gani jiya na kai musu abinci goggo sadiya ta dinga min tsawa wai banida nitsuwa. Nace"hkr zakuyi gabadayanku tashi kuje dan Allah. Haka ta tashi ba don ransu na soba suka tafi. Gaskia a cikin kwana biyun nasha habaici gun su sadiya tunda suka fara jeren nan zagina suke har Allah Allah suke su sameni a babban palo domin suyita min habaici don haka da na gane daki nake shigewa abina har suka gama jerensu suka kulle side din amaryan suka koma gidansu innah Bayan an daura aure a camaroo gabadaya suka kamo hanyar Nigeria su angwayen sun riga dawowa.kamin daga baya gayyan amarya kuma suka iso gidan innah suka sauka harda amaryarsu domin aci gaba da hidimar biki sei an kare tukun kamin amarya ta tare. Murna a gun su innah ba,a magana domin biki akayi sosai na kece raini .duk da banda lfy haka nake daurewa.naje parties din duka har aka gama saura kawo amarya. Randa aka kawo amarya gabadaya muna babban palo nida ruma sa,a farida sakina aunty samira da rukyn Hakim munci adon na kece raini domin karbar amarya haka nan suma tawagar amaren sunsha ado abin ba,a cewa komai domin suna isa gida ya gauraye da kamshi. Sun kawo min amarya wurina hade da yi mana nasiha . Kallo daya nayiwa amaryar naji gabana ya fadi don gaskia nafisa kyakkywace first class ma kuwa ga haske ga gashi gata yarinya karama hmm ai dole ne kawai ya salman yayi rawan jiki akanta Allah dai ya bani ikon hkr akan duk abinda zan gani. Bayan su yan uwan innah sun gama nasiharsu Adda A'i ta karba "don haka rumaisa kece babba ki rike girmanki domin se kin rike ne nafisa zata girgimamaki.saboda nafisa yarinyace akanki .kuma kiji tsoron Allah karki zalunceta domin nafisa bata da tashin hankali ko kadan kuma tana da hkr da juriya . Murmushi nayi nace"karki damu adda A'i kowacce da halinta zata zauna Allah ya bamu zaman lfy . Gabadaya sukace amin. Yayinda suka tashi suka nufi side din amarya madiha ke cewa kuma wani wani shekaran zamu dawo bikin suna. Sadiya ta karba "in Allah yarda yaruwa ta. Mudai bamu ce musu komai ba farida ce take ta faman cika tana batsewa domin tuni na gargadeta akan kar ta kuskura tace komai domin babu sa,anninta a cikinsu bana son raini. Sukuma suna isah kofan dakin amarya zasu shiga kawai sai ga amarya ta yanki jiki ta fadi kasa sumammiya Subhanallah gabadaya suka rikice sai faman salati suke anan raihana tayi maza ta kawo ruwa aka zuba mata ta farfado amma gabadaya bata cikin hayyacinta sai nuni take musu da kofan dakin tana cewa ga wata mata da wuka tana zuwa zata soka mata . Su dai basu ga komai ba lokaci daya ta kuma kurma ihu ta sake sumewa. Ihunta yasa muma muka ji da sauri muka tashi muka zamu tafi sashin sai ga raihana ta fito da sauri har hada baki muke "raihana lfy. Ta girgiza kai tace"babu lfy rumaisa ina ya salman . Kamin nayi magana tace "ki kirashi a waya yazo akai nafisa asibity suma tayi har sau biyu. Subhanallah muka fada gabadaya yayinda sa,adatu tayi sauri suka tafi da raihana side din amarya. Nikuma muka koma palo da da su ruma anan na shiga neman wayar ya salman amma busy don haka na kira ya salim na fada masa komai yace shikenan bari yazo shi yanxu. Yana zuwa muka tafi dashi sashin nafisa inda muka samu sun shimfideta kan kujera suna ta mata fifita hade da yi mata sannu. Na karasa wurinsu da sauri nace"ku riketa muje akaita asibity....... Ko kan na rufe baki nafisa ta shiga nuna ni tana cewa "gata nan wayyo Allah zata soka min wuka gashi a hannunta . Ta kuma sumewa. Ni kam cak nayi a tsaye na rasa me zance . Tab aikuwa su Adda A'i abin nema ya samu me zasu jira gaba daya suka taso min kamar zasu cinyeni danye ya salim yayi kokarin dakatar dasu amma ina zagina suke yi inaga ba don ya salim ba da dukana ma zasuyi . Ya salim ya ja hannuna da sauri muka fita daga side din gabadaya amma don jaraba har binmu sukayi madiha da adda A'i da sadiya . Anan fa su sakina da ruma ma suka shiga maida musu martani harda farida. Side din ya salman muka wuce da ya salim ya zaunar dani kan gado hade da fadin" ki zauna anan karki yadda ki fita.ina zuwa. Ya fita da sauri yayinda yaja kofan. Inna kuwa labari na samunta ba sai ta fashe da kuka ba ta kama fadin ai dama tasani tunda Amina na cikin yan daukan amarya tofa dolene hakan zata faru .haukatarda nafisa muke so yi kuma wlh bamu isa ba. Da kyar ya salim ya kashe wutar a na gidanmu yace su dauko nafisa su tafi asibity suka ce wnn ba rashin lfyn asibity bane asiri nayi ma nafisa tunda gashi tana nunani tace nazo kanta rikeda wuka ta suma. Don haka suka tattarata suka dawo gidan innah kowa da abinda yake fadi . Ya salman kuwa sun nemeshi har sun gaji shiru.dama suna dawowa daurin aure daga cameroo ya tafi lagos . Nikam ya salim na fita na fashe da kuka cikin tashin hankali na kira mama na shiga sanarda ita abinda ya faru duka. Itama hankalinta ya tashi sosai tace" abin nema ya samu.ta nan suka bullo kuma?dama abinda suke so knn wayasani ma ko plan suka shirya don su hada ki da salman ?hmm wa'yan nan mutanen sun fara bani tsoro nidai .yanxu kina inah ? Nace"ina side din ya salman gabadaya mama sun taso kamar zasu cinyeni danya wai asiri nayi wa nafisa zan haukatata yayinda wasu daga cikinsu har cewa tsafi mukeyi muna so mu hallaka nafisa ni da ke. Mama tace innalillahi wa inna ilaihir rajiun o ni Amina wnn bala,i da me yayi kama? Ina salman ? Nace"baya nan. Tace "yanxu kiyi hkr don Allah karki fito inda suke ina tsoron kar suje su miki wani abu ki bari se komai ya lafa se ki fita in kuma basu hkr ba kawai ki taho nan gida ki bar musu gidan kar su miki illah gashi dama ba lfy ne ya isheki ba. Nace"to mama. Da haka mukayi sallama. Kusan awa uku ina side din ya salman yadda ya salim ya zaunar dani haka nake zauna na kasa motsi kwakkwara. Har ya salim din ya kuma dawowa ya kalleni cike da kulawa yace"rumaisa don Allah karkice zaki tashi hankalinki akan wnn maganar kinga bakida lfy. Kuka na saka hade da fadin ya salim bansan me nayiwa mutanen nan ba suka sakoni a gaba kanajin irin sharrin da suka min ? Snn ga zagi da cin mutunci ciki harda mahaifiyata da dukkan dangina ni ya zanyi ne? Zama yayi kan bed side drawer yace"hkrn dai zakici gaba da yi komai zai wuce insha Allahu . Nace"har yaushe ya salim har yaushe? Abu shekara da shekaru.... Karar bude kofa ne ya katseni ya salman ne ya shigo hankalinsa tashe ya karaso gabana yana kallona yayinda ya zauna gefena ya jawoni jikinsa hade da fadin "rumaisa don Allah bana son ki daga hankalinki kan abinda ya faru naji komai kuma nasan ba gaskia bane sharrine kawai amma ba komai nasan matakin da zan dauka akai .ki daina kuka kinji bana son ki daga hankalinki kinga ba ke kadai bane yanxu. Haka ya dinga rarrashina har sai da ya shawo kaina na dan kwantar da hankalina snn ya kalli ya salim yace"dan uwa sannu da kokari ba don kai ba bansan wani hali rumaisa zata shiga ba. Ya salim yace "ba komai amma ya kamata duk inda zakaje ka dinga sallama kuma me yasamu wayoyinka a kashe? Yace"wlh ba kashewa nayi muna wani wuri ne da babu network sam sam jirginmu kuma ya samu matsala .wani aikin gaggawa ne ma ya taso mana wlh shiyasa na tafi ba sallama. Ya salim ya tashi hade da fadin to Allah ya kyauta ni bari in je in kwanta dare yayi karfe sha biyu ... Ya salman yace"ok dan uwa ka huta gajia na gode. Bayan ya salim ya tafi ya salman ya da da kwantar da murya yana kara rarrashina hade ce min in kwantar da hankalina. Haka ya sakani naci abinci nasha maganina mukayi wanka muka kwanta.na samu da kyar bacci ya saceni Washe gari kuwa da sassafe ya tashi ya tafi gidansu innah. Sati daya ana abu daya kusan kullum su adda A'i sai sunxo sun zageni sai da ya salman ya taka musu birki ya zazzagesu kuma yace kar wanda ya kara zuwan masa gida in ba haka ransu zaiyi masifar baci.inna kuwa a waya ta kira ta zageni tass ta gama haka nan ta kira mama ma ta zageta hade da ja mana Allah ya isa. Nafisa kuwa anata jinya don anyi na asibity shiru na gargajia ma haka sai da suka koma islamic medicine sannan ta fara samun sauki.anan suka fahimci aljannu ne. Raihana tazo gida tana bani hkr akan abinda su adda Ai suka dinga yi mun nace babu komai raihana inda sabo ai na saba. Haka nan taje ta baiwa mama hkr .sai lokacin na sami salama.tuni yan kamaru sun koma haka nan sa,adatu tun ranar da abin ya faru washegari ta tafi farida ma nasa driver ya maidata Abuja gudun kar taje ta ce zata tanka musu don itama rashin hkr ne da ita .gida ya rage sai ni daya . Bayan nafisa ta warware tass anan suka fara shawarar dawo da ita amma tace sam ita bazata zauna gida daya dani ba sai dai a canza mata gidanta anan innah tace wa ya salman ya nemawa nafisa gida yace shi baida kudi lol! Sai dai ta zauna a tsohon gidanmu wanda ke kusa da su innah anan adda A'i tace Allah ya sawwaka nafisa tafi karfin wancan tsohon gida sai dai a kaita gidansa na Abuja. Haka suka dauki kayayyakinta suka mayar Abuja ba tare sun tsaya jin ra,ayinsa ba don haka shiru ya masu ya xuba musu na mujiya ranar da zasu maida nafisa Abuja inna ta kirani tana ja min kunne akan in ta kuma jin kiris wlh sai ta saka ya salman ya sakeni don ya isheta zamana a gidan danta. Da yamma ya salman ya dawo ko abinci ban barshi yaci ba nace ya shirya ya tafi Abuja an kai masa amaryarsa can kar ya zauna ana kuma ya ja min matsala suce ni na hanashi zuwa gun matarsa. Wani irin kallo ya min snn yace "ke yanzu tunaninki ya baki zan bar abinda nakeyi in tafi Abuja saboda wata? Ya girgiza kai snn yace bazai yiwu ba wlh tunda sukayi abinsu ba shawara su suka sani ni ba inda zan je kuma kema karki matsa min. Ba shiri na soma hada shi da Allah ina don Allah yaya salman kayi hkr ka tafi Abujan nan ka rufa min asiri kar su innah su zargeni akan nice na hanaka tfy gun amaryarka . Yace"ke ni fa ba inda zanje karma ki bata bakinki. Tashi nayi na fita da sauri raina a bace na koma part dina waya nayi wa mama na gaya mata abunda ya faru.don haka ba bata lokaci ta kirashi itama tayi mishi magana.ba dan ransa naso ba ya shirya ko sallamata baiyi ba ya fita yana ta fushinsa ko ya sami jirgi ya tafi ko da mota ya tafi nidai ban sani ba........ Hauly ce👍🏻🥰 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡94 *********Farida tun ranar da aka kawo nafisa sukayi sa,ainsa da su goggonanta dama washe garin suka koma Abuja.tunda ta koma hankalinta na nan kano ita a son ranta tafi so ta dawo nan mu zauna. Kuma dama ruma ta fada min duk halinda faridan ke ciki sanda tazo biki.amma tashin hankalin da na shiga na bikin nan ya hana inyiwa farida maganar har suka koma Abuja. Bayan komawarsu suka ci gaba da soyayyarsu da farouq har ya kaita gun iyayensa ta gaishesu anan Ahmad ke tambayan farouq din farida yar gidan wayene? Salima dake zaune tayi murmushi tace"ka dubeta da kyau dawa tayi maka kama? Ahmad ya kalli farida wacce kanta ke sunkuye a dole ga mai surukai Yace"gaskia dai fuskar tayi mun kama da tsohuwar fuska dana sani a baya. Salima tayi dariya tace"hakane faridace wnn 'yar gidan Salman da Rumaisah . Cike da mamaki Ahmad yake kallon farida yace"ikon Allah yanxu wnn yar queen ne ta girma haka?masha Allah taso taso yata ai nan gidanku ne ki saki jikinki sosai karki kuma yin bakunta a gidan nan kinji? farida ta daga mishi kai tana murmushi yace"tashi ki zauna kan kujera. Kusa da salima farida ta zauna salima tace "kaga ni kuma tafi min kama da ya salman akan rumaisa. Ahmad yace"ai ke dama bakisan kama ba.ai wnn kina ganinta kinga rumaisah bata wani kama da salman. Farouq yayi dariya yace"ai mum karkuja maganar da nitsa ma.da mum dinta da dad dinta suna kama sosai da juna shiyasa kuka rasa da wa take kama a cikinsu.duk kamanninsu daya ni da na gansu a hoto har ina mamakin kamanninsu sai da ta gaya min cewa ai yanuwane auren dangi sukayi. Ahmad yace"hakane yan uwane. Salima tace"son ya kamata idan kaje kano kaje ka gaishesu tunda yanxu maganarku tayi karfi . Farouq yace "in Allah ya yarda mum zanje. Haka suka dinga hira da dariya farida kam ba karamin dadi taji ba yanda iyayen farouq suka karbeta da mutunci har tayi kawance da kanwar faruk mai suna Rumaisa amma suna ce mata Islam Ahmad ya gayawa farida cewa Islam takwaran mamanta ne.anan farida ta fara tunanin shin meye alakar mamanta da Ahmad ? Lokacinda faruk ya dawoda ita gida ta tambayeshi ko ya sani. Murmushi yayi yace"Aisha sarkin tambaya.zan fada miki amma sai lokaci yayi yanxu dai ki shiga gida kinga magriba ta kawo kai.amma gobe zanzo da yamma in daukeki tunda kika dawo daga kano bamu samu mun fita ba kuma goben ma akwai dinner din wani abokina da nake so muje. tace"hmm ai baka sani ba dadyne baya son yawan fitan nan yau ma basu sani ba na fita nasan zasuyita nemana ban ma san wani karya zan musu ba wlh. dan tsaki farouq yayi yace"gaskia uncle dinki nan ya cika sa miki ido da yawa yanxu fa zamaninmu ne be kamata a matsa miki ba haba don Allah su lokacinda sukaci zamaninsu waya sa musu ido? Farida tace kai dai bari kawai dear gabadaya ni yanxu na gaji da zama gidan nafi son in koma gidanmu domin daddyna baya sa min ido duk abinda naga dama nakeyi. farouq yace"ai daga gani dad dinki wayayyen mutum ne kinsan zaman bariki ai dama. suka danyi dariya daga nan farida tace"kaga bari in shiga gida nasan dad zai fito domin tfy masallaci. Rike hannunta farouq yayi sannan ya matso da fuskarshi dab da nata yana mata wani irin kallo yayinda yayi kasa da muryarsa yace"Aisha bana son rabuwa dake ko na second daya saboda irin son da nake miki. Murmushi farida tayi hade lumshe . farouq ya sauke ajiyar zuciya snn yace"ki yi yadda zakiyi duka mu fita goben nan kar ki ce kin fasa. Cikin kwantar da murya tace"Insha Allah. Suna cikin haka kuwa Salim ya fito tare da su Salman junior zasu shiga masallaci gabadaya sun ganta amma ba wanda yayi magana suka wuce masallaci. Farida ta tsorata sosai don haka sukayi sallama da farouq ta shige cikin gida.ba kowa palo tasan mum dinsu ta shiga daki yin sallane dan haka ta wuce dakinsu da sauri inda ta sami mimi ma na sallah bandaki ta shiga dan yin alwala. Bayan sallar isha Salim ya kirata yana tambayarta ina taje kuma ita da wayene ya gansu a mota? Bata da zabi dole ta fada mishi gaskia tunda ya gansu. Kanta a sunkuye tace"dama daddy munje gidansu farouq ne na gaisheda iyayenshi shine ya dawo dani gida bayan nan ba inda naje. Salim yace"amma ba hanaki kula wnn shashashan yaron ba? shiru farida tayi kanta a kasa yace"farida wnn yaron ba dan arziki bane in kika biye mishi zai bata miki rayuwa ne kawai.don Allah ki rabu da shi ki daina biye masa yana zuwa ya na daukanki kuna fita kinji? ta daga mishi kai hade da fadin"to daddy. Yace"kinga ma har naje na samo muku admission keda mimi zaku fara zuwa makaranta kwanan nan don haka ki daina biyewa wnn yaron don Allah . Shiru farida tayi don bataji a jikinta kamar zata iya rabuwa da farouq . Salim yace"shikenan tashi kije ki kira yan uwanki kuzo gabadaya muyi dinner. Tashi tayi hade da fadin to. Tana fita ya kalli rumasau yace"Ruma gaskia lamarin farida ya fara bani tsoro kinga fa yarinyan nan ta canxa gabadaya kuma duk abinda muke gaya mata bata ji.don haka dolene se mun tashi tsaye akan tarbiyan farida don kar muzo muji kunya. Ruma tace"gaskiane kaga wlh ni dazun bansan yaushe farida tasa kafa ta fice ba ina bacci. Salim ya ce"don haka dolene ki bar baccin rana ki kula da shiga da ficenta.domin hanata fitan shine mafita a garemu don muddin in tana fita suna haduwa da wnn yaron to watarana zata bijire mana. Ruma tace insha Allah zan maida hankali sosai a kanta . Suna cikin hakan yaran suka shigo gabadaya amma banda farida don haka dadynsu ke tambayansu ina take? Mimi tace"tana daki wai ita ta koshi bazataci komai. Shiru salim yayi ya rasa me zaice.rumace ta tashi ta tafi gun farida. Gaba daya farida rashin jinta se gaba gaba yakeyi .farouq se kara zugata yakeyi don hska ta daina jin maganar kowa sai nashi.munir kam ta ma daina zancansa gabadaya don yanxu ko ya kira ta layin mumynsu in yace a bata kin karba takeyi .gashi ta tsiri bakin hali bata kula kowa a gidan kuma bata sakewa tunda dad dinsu ya saka mata doka akan kar ta kuma fita shine ta shiga gaba da kowa.yayinda farouq ke kara zuginta akan ta bijire musu yana nunan mata sam basa sonta a gidan. Watarana yace mata zasuje club da daddare tayi duk yanda zatayi ta fita su hadu don haka ta shiga lallaba mom dinsu akan ta barsu suje gidan kankansu Alh Kasim su wuni da kyar ruma ta yarda suka shirya gabadaya driver ya kwashesu ya kaisu. Momy zuwaira ta cika da murnar ganin jikokinta dama ga yaran hakim ma sunzo harda mamansu wato ruky. Nan aka shiga hiran duniya cikin nishadi a inda farida tayiwa farouq text din inda take yazo ya dauketa. Ba jimawa kuwa yazo lokacin yamma yayi sosai don haka ta fita suka tafi ba tare da sanin kowa ba. Sai da akazo tfy gida suka nemeta suka rasa duk gidan bata nan.mai gadine ya tabbatar musu da wani mai mota yazo ya dauketa sun tafi Anan ruky ta kira ruma tana tambayanta ko farida ta dawo tace bata dawo ba. Shiru shiru ba labarin farida har bayan isha.Salim ya dawo ya sami labarin don haka bai zauna ba ya fita domin nemota . Har kusan shabiyun dare Salim ya binciko ya gano inda suke.yana zuwa ya sami farida acikin yanayinda ya matukar tsoratashi koda wasa bai taba tunanin farida zata zo club ba bare tasaka irin wadan nan damanmun kaya dake nuna siraicinta a waje.gata rumgume jikin farouq anata casu. Kansa ne yayi wani irin mugun sarawa ba shiri ya dafe kan hade da fadin"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Ya tafi inda suke da sauri ko ganin gabansa bayayi yana zuwa wurin ya janyo farida da karfi ya sharara mata mari saida duk wurin suka nitsu. Da sauri ya fizgota sai mota Allah yaso da driver yazo da bazai iya tuki ba tsabar bacin rai . Farida kam kuka takeyi sosai.har suka isa gida bai saurara mata ya shiga dukanta baji ba gani ruma ta tsorata sosai ta rikeshi tana"kayi wa Allah da manzonsa ka barta haka kar ka ji mata ciwo don Allah kayi hkr. Ya salim yana huci yace"rumasau kinsan inda naje na samo yarinyan nan? Ruma ta girgiza kai tana dada rikeshi. Cikeda takaici yace"bakiga kayan jikinta ba ? A wurin casu naje na samesu da wnn dan iskan yaron.... Nan da nan ruma ta dafe kai ta zauna kujera hade da fadin innalillahi wa inna ilaihir rajiun. suka kalli farida wacce take kuka kamar ranta zai fita .Salim yace"tashi ki bani wuri . Tana fita ruma tace"kaga ko shiyasa nace maka gara mu gayawa mahaifinta dukkan halinda ake ciki domin gabadaya musan matakin da zamu dauka akanta.don ni kwanaki na gayawa ihsan abinda ake ciki nasan matsalolinda take ciki na tun bikin nan ne ya hana cewa komai.amma ni gaskia a shawarce inaga gwara kawai su sani domin su tsananta yi mata addua. Ya salim ya zauna ya dafe kai snn yace"rumasau gaskia ni ina ganin kamar abun kunya ne a wurina in fuskanci salman da wnn maganar kamata yayi mu tashi tsaye kawai akan case din farida don haka ni zanyi shawaran yadda zamu bullo ma lamarinta ba tare da mun sanar da iyayenta ba kuma kema abinda ya faru yanxun nan don Allah karki fadawa rumaisa domin tana cikin wani hali tun na bikin nan kuma kinga bata da lfy ma . Ruma tace "hakane Allah ya kyauta.don dazun ma ta kirani take ce min jikin amaryar ya warware har ma za,a kawota nan gidan Ya salman na Abuja snn tace min don Allah kar in bari farida tace zata je gidan.gabadaya yanayinda take min maganar kasan tana cikin tashin hankali . shiru sukayi cike da tunanin yadda zasu bullo ma lamarin farida.ranar ba suyi bacci ba a zaune a palo suke har gari ya waye. Farida kuwa kwana tayi tana kuka mimi ta dinga bata hkr hade danunan mata abinda takeyi bai dace ba shiyasa ake mata haka ba wai dan an tsaneta ba. Aikuwa kamar mimi na kara ingizata ne tace"an tsaneni mana in ba haka ba ina kema every weekend in ya fadil yazo daga zaria daukanki yake ku tafi wajajen shakawa har dare kuke dawowa amma ban taba jin dad ko mum sunce komai ba amma ni duk sun bi sun takurani saboda basu suka haifeni ba.... da sauri mimi tasa hannu a bakin farida hade da fadin " haba farida meyasa kike irin wnn maganar wlh ba haka bane... Ture hannun mimi tayi da karfi tace"ni ki rabu dani goben nan in Allah ya yarda zan bar muku gidanku tunda an fara cin zalina. Haka ta kwana tana kuka gari na wayewa ta gama kintsa kayanta tsaf mimi tayi maza taje ta sanar da su daddynsu ga farida can tana shirin tfy kano. Da sauri suka fita suka isketa a harabar gida da kayanta zata fita.Ruma tayi saurin riketa tana cewa "ina zakije farida? Kai tsaye tace gidanmu zan koma tunda kun tsaneni ba kwa sona. Ruma ta girgiza kai yayinda hawaye ya ciko idonta tace"aa farida ba tsanar ki mukayi ba kawai muna fada miki gaskiane kiyi hkr kizo mu koma kinji ?ki fada min duk abinda kk so 'yata. Ta rike hannun farida wacce ta fizge da sauri ta tafi wurin Ya Salim tana kuka yace"daddy don Allah ka maidani gidanmu ina son yin magana da daddyna. Ya salim idanunsa suka kada sukayi jazir tsabar bakin ciki amma ya daure ya hadiye ya rike hannun farida yace"shikenan farida zan mayar da ke kamar yadda kikace amma kizo muje ciki kisha koda tea ne kan nan in shirya se mu tafi. Don haka ta amince suka tafi ciki.Ruma kam ta kasa hkr daki ta koma tana kuka ko kadan bata son farida ta bar wajansu don tun batayi shekara uku ba take gabansu. Haka suka kasance cikin tashin hankali a ranar gabadaya. *******Ya salman kuwa bayan ya isah Abuja misalin karfe goman dare .ba kowa a gidan don haka ya wuce toilet ya yi wanka ya shirya cikin kayan baccinsa anan ya fara tunanin shin yaje gun nafisa ko ya barta? Ya jima yana tunani kamin daga bisani ya gama yanke hukunci ya tashi ya dauki wayoyinsa ya fita ya rufe dakin ya tafi dakinda yake tunani can aka kaita. Can ya sameta kuwa tana kudundune cikin bargo cike da mamaki ya karasa bakin gadon ya yaye bargon da sauri . Ita kuwa a tsorace ta kurma wani ihu jikinta na rawa don bata taba tunani shi bane a zatonta wasune daban don tunda aka watse aka barta a gidan ita daya da taga dare yayi gabadaya ta tsorata duk da ma ga sojoji masu tsaron gidan. Da sauri ya rumgumeta jikinsa hade da cewa"ke nine. Snn ya saketa ya fahimci gaba daya a tsorace take. Anan ta nitsu a hankali ta sunkuyar da kanta kasa cikin jin kunyarsa.domin tunda aka fara maganar aurensu da duk wani jinya datayi bata taba kebewa dashi ba sai yau don haka gabadaya sai taji kwarjininsa ya mamaye koina dakin. Shi kuma zuba mata ido yayi Allah kadai yasan me yake tunani a ransa. Can ya numfasa ya fara magana "Nafisa bazaki iya zama a gidan nan ke kadai ba ni kuma kinga ba mazauni bane don haka maganar gaskia shine ki shirya mu koma kano goben nan .kuma bana son jin wasu kananan maganganu don haka ki tsarkake zuciyarki mu zauna lfy.rumaisa bata da matsala ko kadan kuma tana da hkr zakiji dadin zama da ita fiye da tunaninki don haka ki daina bin maganar su Adda A'i matukar kina son mu shirya kinajina? Kai kawai ta daga mishi .yayinda yaci gaba da yi mata magana har da nasiha kuma ta gamsu yayinda jikinta yayi sanyi sosai. Anan ya umurceta da ta tashi tayi alwala suyi nafila ta ma,aurata. Kanta a sunkuye tace mishi tana period. Baiyi magana ba ya tashi yayi nafilarsa snn yaje ya dauko musu ledar da ya shigo da ita na drinks da gasassun kaji yazo ya baje su yace ta sauko taci. A kunyace ta sauko ta zauna kanta a kasa har lokacin yace mata"wai ke ba kya gajia da wnn sunkuyar da kan ne? Snn yayi murmushi cikin zolaya yace"ko don banzo da abokai na mun siyi bakin amarya bane? Da sauri nafisa tasa tafin hannunta duka biyu ta rufe fuskarta tana murmushi. Shima murmushi yayi yace"to shikenan kiyi hkr yanzu ki dago kanki kici naman nan nasan kina jin yunwa ko dai na baki a bakine? Da sauri nafisa ta girgiza kai snn ta sa hannunta ta dan fara ci. Shikam bayan ya danci toilet ya tafi ya wanke hannunsa hade da kuskure bakinsa ya dawo ya kwanta ba tare da yace mata komai ba. Da farko tunanin halinda ya barni yaso ya hanashi bacci don yasan ina cikin damuwa snn gashi ina daukeda juna biyu amma daga baya daya tuna yanda na sakoshi a gaba akan lallai sai yazo Abuja sai yaji haushi ya kamashi ya dan ja tsaki ya gyara kwancciyarsa da bai biyo takan nafisa ba bacci yayi awon gaba dashi . Washe gari kuwa bayan ya dawo daga masallaci ya isketa har ta gama shirya kayan sawanta a jaka . Cike da biyayya tace mishi "yaya ina kwana? Ya karaso gabanta hade da fadin lfy ya tsoro? Da sauri ta sukuyar da kai tana murmushi snn yace"duk kin gama shirinki koh? Tace"eh na gama. Yace"to ina zuwa. Daga nan suka kulle koina ya taimaka mata tasa kayanta a mota suka kama hanyar Abuja basuyi nitsa sosai ba ya salim ya buga mishi waya yana tambayarsa yana Abuja ne ko kano. Yace yanxu nake hanyar barin Abuja zan tafi kano a mota amma. Ya salim yace"to nima gani nan zuwa kanon da farida. Ya salman yace"da sassafen nan snn lfy zaka zo da faridan? Ya salim yace"lfy lau sai mun karaso kawai. Ya katse kiran .nan ya salman jikinsa ya bashi zuwan bana lfy bane. *****Kasancewar jiya ban yi bacci ba gabadaya saboda tunanin ya salman da amaryarsa.ina idar da sallar Asuba ban San sanda bacci barawo ya saceni ba daga zaune nake bacci sosai. Buga kaina da nayi a jiki drawer shi ya tashen na dafe kaina da yake mun ciwo dama ga damuwa ga rashin bacci . Kama kan nayi da karfi ina karanto addua..... Bansaki kan ba naji kamar horn din motarshi. Ban San sanda na saki kan na mike da sauri na tafi window kasancewar window din bedroom dina tana facing harabar gidan. Ina daga labule Rass! Zuciyata ta tsinke.ganin motar ya salman ne. Naji wani irin bacin rai da bakin ciki kamar na hadiye zuciyata na mutu. Da sauri na fita daga dakin na nufi harabar gida ko ganin gabana banayi tsabar bacin rai. Can na hangoshi ya fito gabadaya sojojin gidan sun zo suna kwasan gaisuwa. Da sauri na nufi can wurinshi a lokacin da ya juyo shi kuma ya bude gaban motan .kawai sai ganin nafisa nayi ta fito Bansan sanda na tsaya na saki baki ina musu kallon mamaki ba. Itama ni take kallo daga fitowarta fuskarta daukeda tsoro da fargaba . Ganin yadda muke kallon kallo yasa shi riko hannunta a hankali suka nufo inda nake ka min su karaso tuni na daga musu hannu. Na kalleshi cikin tsantsar mamaki nace" me zan gani?Nafisa a gidana?me ya faru? Fuskarsa ba yabo ba fallasa yace "lfy ta dawone. Na zaro ido hade da fadin what! Wlh bazai yiwu ba wnn karon bazan dauki iskanci da rainin hankali da aka mini a baya ba bari kaji ni bazan zauna da Nafisa a gidan nan ba. Na nunata da yatsa nace " wata daya da suka wuce aka kawota gidan nan a matsayin amaryarka ta yanki jiki ta fadi ta suma 'yan uwanka suka sakoni a gaba da zagi ciki harda mahaifiyata sukace mu mukayi tsafi don mu wargaza aurenka da Nafisa. Hawayene masu zafi suka gangaro bisa kumatuna na ce"jiya jiyan nan aka kai maka ita a gidan ka na Abuja ka tafi.snn yau ka daukota kuyi sammako kuzo min gida kace ta dawo? Ko kallo ban isheba dama jiya da haushina ya tafi Abuja.don haka ya kalleta yace "ke shiga ciki ina zuwa. Ta wuce jikinta a sanyaye na bita da kallo har ta shige. Sannan na dawo da kallona gareshi.nace" shikenan tunda haka ka zaba ni zan bar maka gidan ka yanzu ba sai anjima ba kaje ka zauna da matarda mahaifiyarka da 'yanuwanka suka zaba maka. Wucewa yayi ba tare da yace min komi ba. Kamar zan fashe don bakin ciki nayi ciki a zuciye Na dauki jakata da wayata da key din motata . Juyawan da zan yi sai ganin mutum nayi tsaye ya zuban ido fuska daure. Ban kulashi ba Na saka takalmina Na karaso bakin kofan ba tare da na kalleshi ba nace ban gu in wuce. "Ina zakije? Ya fada can kasan makoshinsa. Shiru na masa . Juyawa yayi zai fita yace min Salim yazo da Farida suna palona . Daga nan ya fice Zuciyata ce ta buga nace Farida da sassafen nan me ta ballo kuma? wayyo Allah da wanne zanji ni RUMAISA? Na ajiye jakata na tafi side dinshi a Palo na samesu suna zaune shiru Farida na zaune a kasa kanta a kasa. Na karaso na zauna jikina a mace na kalli Salim nace "ya Salim ina kwana? Cike da kulawa ya amsa min lfy RUMAISA.ya jikinki ? Nace"jiki da sauki Alhamdulillah Shiru ya biyo baya daga bisani ya Salim ya gyara zamansa yace" to kun ganta nan duk yadda naso ta zama mutum abin ya faskara RUMAISA ke kam kinsan komi gameda halin ta dama Salman Kaine muke boyewa saboda gudun zuciyarka amma yau an wayi gari fareeda da kanta tace min in dawo da ita gaban iyayenta ina muzguna mata dan bani na haifeta ba. Zaro ido nayi na kalli Farida nace "fareeda dama rashin hankalin naki har ya kai haka? wai shin ya salim suwa suke hure mata kunne ne haka? Salim yaci gaba da fadin hmm har yanzu bata rabu da Farouq ba rumaisa maganar da nake miki jiya har karfe dayan dare na ganota a wurin club suna tare bayan duk tsaro da na sa akanta sai da tasan yadda tayi tayiwa momynsu wayo ta fice jiya gaba daya bamu yi bacci ba Dan bakin cikin fareeda na rasa me zan mata a rayuwa don ta rabu da Farouq .......... Sai lokacin ya salman yayi magana ta hanyar katse ya Salim da fadin " waye Farouq din? Ya tambaya yayinda ya dauki Kofin ruwa dake gabansa yana sha. Salim ya danyi shiru sannan yace hmm Farouq dan gidan Alhaji Ahmad umar ministern Ab..... Tuni ya salman ya kware ya kama tari. Nikam na kara zaro ido a tsorace don ban taba sanin Farouq Dan Ahmad Umar ba ne sai yau . Kamar da wasa ya salman tarin sai tsananta yakeyi ya Salim ya mike da sauri ya isa wurinshi "Sannu don Allah karka daga hankalinka kan wnn maganar. Hannu ya daga masa sannan yace ba komi. A hankali fareeda tace sannu daddy. Ya dago jajayen idanunsa ya kalleta sannan yace " zo nan. Ta mike ba tare da fargaba ko dar ba don tasan yana matukar ji da ita baya muzguna mata duk zafin sa. Ta karaso ta zauna kusa da kafarsa. Ya fara magana"fareeda haka kika zama? Me yake damunki don Allah ki fada min koma me kk so zan miki amma bana son wnn banzar dabiar taki. A shagwabe ta fara magana tace daddy ni bana son inje makaranta ni zan yi aure ne.... Nikam na bushe a zaune Dan tsabar mamaki. Yace" waye ne kk so? Tace Daddy Farouq........ Ya mike tsaye idon nan ya kara yin jazir yace fareeda ni bazan yarda Dan wajen Ahmad ya aureki ba koda kuwa babu maganar aure tsakaninki da munir bare kuma kin gama amincewa munir kk so har munyi akan in ya dawo daga kasar waje zayi bikinku.don haka bazanyi magana biyu ba don ni ba mutumin banza bane.Farida ko kinaso ko ba ki so munir shine mijinki...Sannan kinga wnn? Ya nuna ya Salim yace"Dan uwanane banda kamarsa idan kin kyautata masa kamar ni kikayiwa idan kin masa biyaiya kamar ni kikayiwa haka nan idan kika masa rashin biyaiya kamar ni kk yiwa naji kince don ba shi ya haifeki ba to bari kiji duk duniya bakida Ubanda ya wuce Salim.ina so ki Sani akan Salim zan iya rabuwa dake.don haka se kije ki nemi wani uban bani ba tunda kince Salim ba mahaifinki bane. Tunda ya fara maganar kuka takeyi . Ta durkusa gabanshi tana daddy don Allah kayi hakuri ka yafe min na tuba..... A fusace ya bugeta da kafa ya fice ciki. Ta na kuka ta mike ta iso gabana ta durkusa tace mama don Allah kuyi hakuri wlh ...... Tsaki nayi nace don Allah tashi gabana Mara hankali me zakice min? Tana kuka ta juya gun ya Salim tace daddy don Allah kayi hakuri ka yafe min wlh na gane kuskurena Dagota yayi yace na yafe miki fareeda Allah ya shiryeki. Sannan ya mike yace ni na tafi. Nima na Mike nabi bayansa A bakin kofa mukayi kicibis da Nafisa batace mn komai ta wuce ciki na bita da kallo sai naga ta wuce direct dakinsa. Wani irin kishi naji to waye nuna mata turaka bayan dazu tazo? Tabe baki nayi. Bayan ya Salim ya tafi na dawo dakina na rasa me yake min dadi a rayuwata dole ne kawai inje in sami ya salman domin mu tattauna maganar fareeda.duk da ma na lura fushi yakeyi 'yan halin nasa sun murdo gaban goshi. Na tashi na fita a babban Palo na tarar da khalilullah yana kallo. Yana ganina yayi murmushi yace mama ina kwana? Nace lfy Babana ina ka shiga tun da safe ban ganka ba? Yace na tafi gidansu Innah ne a can nayi breakfast ma. Na gyada kai nace yayi kyau babana.jeka duba min daddyn ka yana Palonsa ne? Yace to Sannan ya mike ya tafi ba,a jima ba ya shigo yace mama yana nan. Nace "Nafisa fa? Yace aunty Nafisa dazu ta wuce kitchen.a raina nace har ta karbi girki knn? Hmm amaren zamani. Nace to ina fareeda? Yace na ganta ta fita dana tambayeta tace zata kai karar daddy gun innah.mama me ya sami sister ne? Na danyi shiru sannan nace maganace mai tsawo kar ka damu ina zuwa. Na wuce palon ya salman a zaune na sameshi yana waya da abokan kasuwancinsa na sami guri na zauna har ya gama. Ya zuban ido sannan yace lfy? Na girgiza kai nace ba lfy ba nazo ne mu tattauna yadda zamu bullo ma lamarin fareeda kamin yafi karfinmu. Yace hakane ina jinki. Na gyara zama nace " ni yaya a ganina gara a bar ta tayi auran ta auri Farouq din tunda akansa ne take wannn...... Ya katseni da fadin lallai bakida hankali kina tunanin cewa ni SALMAN zan dauki 'yata ta cikina in bawa Dan Ahmad aurenta! Ni na yanke hukunci koda zatayi aure yanzu to munir ne zata aura bare ma kuma makaranta zata tafi.har sai munir ya dawo. Nace "yaran nan fa na zamanin yanzu daban suke da na da tunda kaji ta bude baki bataji kunya ba tace ma aure takeso kuma ga wanda ta zaba to ka barta kawai karkace zaka tursasa mata domin watarana zata bijire. Kallona yake rai bace sannan yace" zata bijire min in dai halinki ta dauka da banzar dabiarki........ Raina bace na Mike nace OK haka kace to bari kaji ni 'yata aure zatayi kuma Wanda takeso zata aura Farouq din tunda aure bai haramta tsakaninsu ba ni a matsayina na uwa na gama yanke nawa hukuncuin. Har zan tafi yace tsaya! Ya mike ya karaso gabana ya zuba min manyan idanunsa da sukayi jazir Dan bala'i yace " sai yanzu na fahimce ki rumaisa wato saboda Ahmad tsohon saurayinki ne shine kk son dansa ya auri 'yarki ko? Kai tsaye nace eh hakane sai me?kasancewar Mahaifiyar Farouq din Salima tsohuwar budurwarkane don haka me a ciki? Na juya zan tafi ya fincikoni da iya kacin karfinsa wani irin kykkyawan riko ya min. Sai faman kwatar kaina nake kokarin yi na kasa. Murmushin mugunta yayi yace "yanzun kin fahimci banbanci dake tsakanina dake? Ya sassauta min rikon yace ni ne nakeda ikon aurad da fareeda ga duk Wanda naso bake ba don na fiki karfi a wajanta.ke kanki a karkashin ikona kk don haka bakida ikon zartar da komi a gidan nan. Hawayene ya ya ciko idona fal har ya fara saukowa don takaicin ya salman. Yana kallona yace kina da wani abu da zakice kuma? Na girgiza mishi kai kawai. Ya sakeni hade da fadin good girl haka nake so. Fita nayi na tafi daki kuka na kama yi kamar raina zai fita Karar wayata ce na jiyo a kan bedside drawer ban kula ba har ya tsinke. A Jere aka kira sau uku ana hudun na lalubo wayar ban lura da kowaye ba nayi answering. Muryana a sarke nace Salamu alaikum. Muryar Inna na jiyo tana " to uwar makirai annamimiya ba sallamarki na ke bukata ba. ki fada min me yasa kk ce Salman ya dawo da Nafisa kano alhalin jiya jiya aka kai ta Abuja ? Cikin muryar kuka nace inna banice nace ya dawo da ita ba nima kawai sai ganinsu nayi sun yo sammako..... Ta katse ni.da fadin don Allah rufe min baki da zancen wofi .Wai kawai ganinsu kk yi makarciyar banza to bari kiji na gaya miki idan kk kuskura ko ciwon kai Nafisa tayi sai kin gane kurenki wlh .don haka ki kiyaye don hakane na kira ki.Sannan abu na biyu ga 'yarku nan taxo ta fada min komi.wato bazaku mata aure ba sai ta yi karatu.to me karatun zai tsinana mata? Ke kanki lokacin da uwarki ta nace sai kinyi jamia ina karshenta a karuwanci da shaye shaye kk kare ko an gaya miki na manta ne.to wlh bari kiji ahir dinki daga ke har Salman Ku kiyayi fushina. Ka min nayi magana tuni ta kashe wayar!!!!! Jefar da wayar nayi na fashe da kuka mai tsanani na rasa me yake min dadi a rayuwata ni rumaisa! *Hmm* *masu* *karatu* *ina* *fatan* *kuna* *biye* *dani* ? Wnn shine Asalin labarin rayuwar rumaisa.ku biyoni a pages na gaba don jin ci gaban labarin. Shin ya zata kasance tsakanin farida da iyayenta ? Ya Amarya nafisa zata kasance a gidan salman? Ya kamata Innah adda A'i da sadiya asirin su ya tonu .ta ya ya? A karshe rumaisah ce....... 🤪🤪🤪🤪Don jin karashin wnn labarin sai ku biyoni a ragowar pages masu zuwa nan gaba.nagode fans din rumaisan salman Allah ya bar kauna.❤❤❤ *WNN* *SHAFIN* *KYAUTACE* 👌🏻 *TA* *MUSAMMAN* *A* *GAREKI* *AUNTY* *MARYAM* (Shugabar kungiyar mu ta intelligent writer's asso. *Boss*😎👍🏻) *ALLAH* *YA* *KARA* *MIKI* *LFY* *YA* *TSARE* *KI* *DA* *DUKKAN* *SHARRIN* *MAKIYA.YA* *KARA* *JEFA* *SOYAYYARKI* *A* *ZUCIYAN* *OGA* *YA* *RAYA* *AFRAH* *DA* *MUHAMMAD* 🥰🙏🏻🙏🏻 Hauly ce🥰👍🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡95 ******Ji nayi zuciyata kamar zata huda kirjina ta fito tsabar azaba . Dafe kirjin nayi sosai ba shiri na fara fadin Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Na fara kokarin lalubo wayar da nayi jifa da ita amma ina ya gagara sai ma wani tari dana kama yi wanda yake kara min radadi da ciwon kirjin...... Sosai na fita hankalina ina dafe da kirji ga tari kuma matsananci. Cikin sa,a Allah ya kawo ya salman dakin domin haka kawai xuciyarshi ta bashi ba lfy nake ba. Haka kuwa yana shigowa ya ganni cikin halinda ya matukar tsoratashi.da sauri ya isa wurina ya kamoni yana"Rumaisah menene? Ina dafe da kirji nace"yaya mutuwa zanyi ka yafe min duk abinda na maka ka rokan min mama da daddy su yafe min ........farida da khalilullah duk na yafe m.....musu .....ka kula min da fareeda ......don ...Allah nasan mutuwa...... jikake dif numfashi ya dauke.idonsa ya kada yayi jazir saboda tashin hankali don bai taba ganina a cikin wnn yanayi na yau ba. Rumgumeni yayi sosai a jikinsa zuciyarsa ta karaya sosai da kyar ya iya fadin"Rumaisa bazaki tafi ki barni ba in Allah ya yarda . Da sauri yayi na maza yayi cak dani da matukar hanzari ya fita dani sai mota nan da nan drivernsa ya shiga yaja sai asibity . Muna isa suka amsheni emergency ya salman na biye da su hankalinsa tashe . Nan da nan likitoci uku suka hadu akaina sai shiga da fita sukeyi suma hankalinsu ya tashi sosai oxygen aka samin kamin su samo numfashina ya dauki lokaci sosai har sun fara cire ran zan sake numfashi a duniya . ya salman yau kam fa babu batun jarumta duk yadda yaso ya daure abin ya gagara shi kadai ya dinga magana kamar zautacce har ya ba likitocin tausayi ce musu yakeyi "idan rumaisa ta mutu doctor bazan yafewa kaina ba domin a dalilina take ta shiga matsaloli kala kala.pls doctor kuyi iya kokarinku ku dawo min da lfyr matata. Doctor ya girgiza masa kai hade da fadin"Salman Insha Allah zamuyi iya kokarinmu dan ganin rumaisa ta tashi amma fa sauki na wurin Allah shi zaka roka ya tashi kafadunta in kuma rabon shan ruwanta ya kare a duniya....... Tab! Ai bai karasa ba saboda wani irin mugun kallo da ya Salman ya jefeshi da shi har ya tsorata ya danja baya snn yace"am sorry Allah ya bata lfy. Daga nan ya tafi. Hankalinsa bai kwanta ba saida numfashina ya dawo ya daidaita nan ya fara hamdala hade da godewa Allah. Doctor ya kirashi office nan yace masa gaskia na kamu da ciwon zuciya sakamakon damuwa da ya min yawa ga kuma jinina da ya hau sosai don haka ina bukatar kulawa sosai da kuma addua domin lamarin ya tsananta matukar ba,a maida hankali wurin kula dani da kiyaye bacin raina ba to fa akwai matsala babba..... Ya salman ya fahimci inda maganar doctorn ya dosa hankalinsa ya kara tashi sosai har ya rasa me zaice . Doctorn yace"karfa ka damu shi cuta ba mutuwa bace insha Allah zata warware tass kuma zamu dorata akan magunguna a dinga barinta tana samun bacci sosai ta dinga hutawa kuma ku guji duk wani abu da kk san zai bata mata rai.in dai kun kiyaye wnn insha Allah zata warke. Ya salman da kai ya iya amsawa doctor. Doctor yace"kuma kaga munci sa,a sosai duk halin nan data shiga ba abinda ya sami cikin jikinta.sai ka godewa Allah. Ya salman sai lokacin yace "Alhamdulillah sai dai ni a yanxu samun lfyr rumaisa ta fiye min komai a duniya. Doctor yace"insha Allah zata samu lfy. Haka Doctorn yaci gaba da kwantar masa da hankali. ******Nafisa kuwa bayan fitan ya salman ta kira adda A'i .... Tun basu gaisa ba adda A'i ta shiga balbaleta da masifa"ke kuma shashasha mara hankali ashe kin yarda salman ya miki dadin baki kika biyoshi kano? Muna raba ki da wahala da zama da kishiya ke kuma .... Nafisa tatari numfashin adda A'i da fadin"adda don Allah ki tsaya kiji mana nifa wnn ya salman din tsoro yake bani wlh ni inaga kamar bazan iya zama da shi ba shiyasa ma na kiraki dama fa kinsan niba shine zabina ba ke kika dinga zuga baba akan sai an hadani aure dashi .... Adda A'i tace"kan uban can.Nafisa wnn wane irin magana kikeyi ? A ina ma kk tukunna? Nafisa ta turo baki tace"a dakina nake kuma ni kadaice ya salman baya nan ya kai mummyn farida asibity. Tsaki adda A'i taja snn tace"wnn matsalarsu ce in yaso ta mutu ma ni ina ruwana?yanxu dai kina jina? Nafisa tace"inajinki mana. Adda A'i tace "to don ubanki ki saurareni da kyau.dama nice rufin asirin familynmu gabadaya kuma yanxu kinsan cewa abubuwan duk ba kamar da bane komai na ya kare nayi iya kokarina wurin ganin na farfado da arzikina kamar da amma abin yaci tura kamar abin asiri gashi yanxu Alhaji baya taimaka min kamar da don shima kansa arxikin nasa yayi kasa.snn duk burin da naci akan yarana mata ya tashi a banza domin duk babu wacce ta auri wani mai maiko sosai bare nayi tunanin zasu min wani abun .ba yanda banyi da mahaifinsu ba akan ya bari su samu ma hannu da shuni amma yaki ya bi zabin ransu gashi nan yanzu babu wacce take tsinana mana komai.snn shi kuma mujahid shine kadai namiji kuma karami a cikinsu har yanzu bai wani karfi da zai iya rikemu ba.abubuwa duk suna neman kwabewa....... Nafisa tace"ni adda wlh zaki cinye min kati kawai ki yi min maganar da ta shafeni . Adda A'i tace"ke har yanxu bakida hankali ashe ? To bari in fito miki fili kinaji koh zagewa zakiyi da kissa da kisisina kija rabonki a jikin salman don kinsan kudi kam yana dashi domin kullum kwanan duniya arzikinsa karuwa yake.snn gashi baisan taimako ba kanshi kawai ya sani se kuma iyayenshi da yanuwansa na jiki snn ita kuma goggo (inna) ba ruwanta bata nunan masa ya taimaka mana ki duba halinda iyayenmu ke ciki har yanzu ba wani ci gaba da aka samu tunda dama ni dince mai yin komai ni nake kokarin sanya ku makaranta in kawo ku birni ku waye domin ku sami mazaje masu kudi mu hada kai mu kula da iyayenmu mu fitar dasu daga kauye.amma kinga abubuwa sunki nikam gabadaya jikina yana bani karayar arzikice tazo mana ga nabila can suna fama dama ita haka nan Allah yayita bata da kashin arziki daga aurensu mijinta komai ya koma baya.snn na dora buri akan madiha itama gashi babu abin kirki data ke tsinanawa.sa,adatu kuma kinsan ta muguwa ce ga tarin arzikin amma bata taimakawa kowa kuma bata da niyyar taimako duk da arzikin da mijinta ke dashi bama iya shi ba har ita kanta haihuwar ta na uku kasancewar ya mace ta haifa ba abinda dangin mijinta basu mata ba daga kan kyautan gida mota da gwalagwalai ga filaye batun kudi ba,a magana. amma kinganta ko a jikinta bata yi wani yunkurin taimakonmu ba. Don haka nafisa yanxu duk wani burinmu akanki ne .kuma zan tashi tsaye wurin ganin kin mallaki zuciyar salman ta kowani hali domin ki sami naki kason babba a cikin tarin arzikin da Allah ya bashi wanda baya amfanar mana da komai a ciki tsabar mugunta.Don haka ki ajiye duk wata kiyayya da kk masa ki fara cusa ma zuciyarki sonsa ki dage da ladabi da biyayya haka nan kissa da kisisina na jan hankali gaki kyakkyawa duk cikinmu ba mai kyanki snn gaki yarinya mai kananan shekaru mazan yanxu sunfi son irinki.don haka kiyi amfani da wnn baiwar da Allah ya maki .ki ja mana kaso mai tsoka ta kowani hali kanwata kinji koh? Nafisa ta danyi murmushi snn tace"na fahimceki adda amma ni gaskia yayan ne yake min kwarjini da yawa. Adda A'i tace "kar ki damu kiris ya rage ya dawo a tafin hannunki sai yanda kika juya shi tunda aka daura aure kika tare anyi mai wuyan abinda ya rage shi yafi komai sauki kwantar da hankalinki.hmm baki ma fada min ba wani kyauta ya baki tunda nasan jiya ba karamin rikitashi kikayi ba nasan irin gyaran nan da kk sha dole yayi miki kyauta ta musamman. Tabe baki nafisa tayi tace"hmm ni adda ce masa nayi ina period..... Ran adda A'i a bace tace"saboda shashanci irin naki? Anya nafisa za,ayi abin arziki da ke kuwa.ke kinga tunda wuri gara ki fada min in baza ki iya ba in nemi wata dabarar. Nafisa tayi murmushi tace"haba addanmu ki kwantar da hankalinki kamar tsumma a randa na miki alkawarin nan da sati daya zakiji alert mai tsoka a account dinki domin ki sake tada jari.ai yanda kika tallafawa rayuwarmu bazan taba barinki hakan nan ba dole ne in taimaka miki ta ko wani hali ma ke dai kawai ki zuba ido. Adda A'i tayi dariya cikin jin dadi tace"Allahu Akbar gaskia ba karamin sanyani farin ciki kikayi ba kanwata Allah ya miki albarka kuma Allah ya biya mana dukkan bukatunmu Nafisa tace"ameen adda Har zasuyi Sallama adda A,i tace"au na manta ban gargadeki ba akan sadiya koda wasa karki sakan mata fuska bare ta gane me muke ciki don nasanta muguwar yar sa ido ce kiyi taka tsan tsan da ita. Nafisa tace,in Allah ya yarda adda zan kiyaye . Daga nan adda Ai taci gaba da zanawa nafisa yanda zasu bullo ma salman su yagi rabonsu a cikin arzikin da Allah ya bashi har tana cewa Allah yasa kamin shekara ya zagayo kin haifa masa yan biyu maza. Nafisa tayi dariya tace amin adda. Sukayi sallama. ******Farida kuwa tana can gidan su innah taci kuka har zazzabi ya soma rufeta Inna kuwa wuni tayi tana ta masifa akan maganar da farida ta gaya mata wai don meye zamu hana yarinya wanda takeso muce zamui mata auren dole ?ai dama tasan munafurci ne muka kulla ni da ruma muka hada farida da munir alhalin ba sonshi take ba.gashi nan tun bayan tfyrsa farida tace ita ba shi takeso ba don haka wlh bamu isa mu mata auran dole ba ko muce sai taje makaranta dole ba. Tayita ta kiran wayar ya salman amma shiru baya dauka don haka ta kira nafisa anan nafisa ke shaida mata halinda ake ciki don haka ta barwa nafisa sako akan lallai lallai idan ya dawo tace tana son ganinsa. Fareeda dake kwance shiru tun dazu tace "innah me ya sami mamana? Inna ta tabe baki hade da fadin "hmm waya sani ai ita rumaisa kullum ba,a rabata da kanan laulayi kila zazzabine. Cikin dauriya farida ta tashi hade da lalubo hijabinta ta saka tana shirin tashi inna tace"to ina kuma zakije? Farida tace"asibity zanje don inga halinda mamana ke ciki. Tana fadin haka bata saurari me inna zatace ba ta fita tabe baki inna tayi tace"kije duk abinda suka sake yi maki ke kika jawo. Farida kuwa tana fita tayiwa drivern su inna magana akan ya kaita asibity don tasan asibity dayane muke zuwa asibityn doctor james. Suna isa ta fara neman inda muke har ta gano tuni ta hango babanta a zaune yayi zurfi cikin tunsni fuskarsa cike da damuwa. Tuni ta isa gabansa tana "daddy ya jikin mamana? Shiru ya mata hade da yi mata nunni da dakin na ta shiga .hawayene suka fara zubowa daga idan farida ta shiga dakin da sauri yanayinda ta sameni ba karamin daga mata hankali yayi ba sosai ta sa kuka ta zauna gefena ta rike hannuna tana"mama don Allah ki tashi karki tafi ki barmu.mama in dai akan wnn maganar kika shiga cikin wnn mugun yanayin wlh na hkr zan bi dukkan abinda kk so don Allah mama ki tashi. Kuka take da karfi tanata maganganu hade jijjigani Nan da nan na'urorin da aka jona min ya shiga yin wani kara wanda yaja hankalin masu kula dani da sauri sukayo kaina haka ma ya salman ya karaso cikin ganin yadda farida keta jijjigani da karfi yasa yayi maza ya jawota jikinsa hade da fadin "mene ne hakan kuma farida wai baki ganin halinda take ciki ne addua take bukata ba kuka ba kuma ma wayace miki rashin lfyn nata yayi tsanani. Kwantar da kai tayi ajikinsa tana kuka tace"daddy naga har ansawa mamana oxygen amma kuma kace min rashin lfyr bai yi tsanani ba? Yace"dama kinsan mamanki nada asma shine ya tashi da kyar take numfashi so dole sai an taimaka mata.amma kar ki daga hankalin ki zata warware kinji? Tace"to daddy. Anan tace mishi daddy don Allah kuyi hkr ku yafe min wlh na gane kuskurena kuma nayi nadama insha Allah zanyi dukkan abinda kukace. Ya salman yace"shikenan shikena ya isa ki bar kukan haka kar yaja miki ciwon kai. Suna cikin haka mama tazo da imran suma din hankalinsu ya tashi musamman ma mama . Haka suka kwana a asibityn jugum jugum farida kam zazzabi yayi tsanani har saida aka bata gado.shi kanshi ya salman dauriya kawai yakeyi amma ba don haka ba shima yana bukatar gadon. Haka ta kasance gari na wayewa asibityn ya fara cika da yan dubiya.daddyma tuni yazo kuma har ya nemi doctor da yayi masa bayani abinda ke faruwa. Aikuwa daddy da suka je gida da mama cewa yayi gaskia shi matsalolinda nake fuskanta a gida ya salman ya isheshi kawai gara ya salman ya sawwaka min ko na samu zuciyata ta huta da masifa kullum daga wnn sai wancan . Sosai daddy ya dage akan lallai sai ya salman ya sawwaka min. Mama tasan ransa ne ya baci don haka shuru ta masa sai daga baya da taga ya dan nutsu snn ta fara bashi baki tana rokonshi da su kara hkr dai in Allah ya yarda wataran sai labari. Da kyar ta shawo kansa ya hkr. Zuwa yanzu na fara samun sauki har ina gane kowa ina dan cin abinci. Ya salman da farida hankalinsu ya fara kwanciya yanxu don haka sosai suka shiga bani kulawa wani lokacin har tausayi suke bani gashi duk sun rame saboda tashin hankali ga rashin cin abinci. Amarya nafisa kam tuni ya salman ya ajiye batunta a gefe duk da a gidan yake kwana amma sam hankalinsa baya kanta.bata damu ba don ita ba wnn ya kawota ba .suna nan suna ta shige shigen malamai da adda Ai na yanda zasu janyo hankalin ya salman domin ya sakar musu hannu su dibi arziki iya son ransu don ita nafisa anata tunanin tana samun babban kaso zata bar masa gidan domin bashi takeso ba tanada wanda zuciyarta keso yayinda adda ai kuma ba hakan takeso ba.so take nafisa ta zauna daram ta cika gida da yara suci arziki kuma su juyawa su inna baya.domin babu abinda ke cin ran adda A'i irin yadda salman ya tara dukiya haka amma sam yaki sakar masu da hannu yadda yakamata snn inna kuma bata nuna masa hakan sai ta barshi kawai yana abinda ransa keso.a maimakon ta dinga sashi yana sakar musu dukiya su fantama ciki su kece raini suyi abinda ransu keso. Satina biyu a asibity na warware tass kamar bani ba ikon Allah knn hankalin kowa ya kwanta mussamman ya salman da farida wanda suke ganin sune sanadin shigata damuwa. Ana sallamata ya salman ya shiga bani wata irin kulawa ta musamman tuni ya ajiye komai gefe .hakama farida duk tayi sanyi kuma tuni tasa a ranta zata rabu da farouq ta koma makaranta domin ta faranta mana rai.duk da tana matukar sonshi . Ya salman kuwa duk wasu hanyoyi da yasan zasu iya sani cikin damuwa ya na kokarin yaga ya toshe.har na samu lfy na fara rayuwata normal kamar da kuma nima ina kula da kaina yayinda nake kauda kai akan duk wata damuwa. Da farko na dauka zamanmu a tare da nafisa zai dinga kawo mana matsala amma sam.na lura babu ruwanta ko ran girkinta bata cika fitaba sai dai kawai ta gaya wa masu aiki duk abinda zasuyi.ranar girkina kuwa ko ganinta ba mayi sai lokacin cin abinci a dining Shikanshi ya salman ya yaba da halinta kuma yaji dadin yadda ya sameta da budurcinta gaskia ya rikice sosai a kanta duk da yana basarwa gudun kar na gane.nima kuma kauda kaina nake a lamarinsu gudun kar na fahimci halinda suke ciki in sake jefa kaina a damuwa.yanxu farida da khalil sune abokan hirana domin suna kokari wurin debe min kewa a ranar da ba girkina ba. Nafisa kuwa abin nema ya samu yanxu ta saki jiki sosai dashi batun ladabi da biyayya kuwa ba,a magana sosai ta kwantar da kan ta domin cikar burinsu...... Hmm fans muje zuwa 🤗🤗🤗🤗 Rumaisa salman kirkirarren labarine ba true life story bane.domin akwai masu tambaya da yawa.nagode sosai da irin zafafan comments dinku dana ke samu maman khausar ina sonku sosai fans Allah ya bar kauna🥰🥰🥰🥰👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻 Hauly ce🥰👍🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡96 *********Na fito wanka daure da towel ina tsane kaina da karamin ya salman ya shigo da sallama na amsa hade da juyowa. Ido ya zubo min nace"yaya lfy? Ya karaso gabana hade da fadin"hmm lfy lau. Ya kamo hannuna muka zauna bakin gado a tare har lokacin kallona yakeyi snn yace"ya jikin? Murmushi nayi nace"na warke yayanah ba abinda yake damuna. Ya shafa marata hade da fadin"babyna fa? Nace"baby lfy yaya na. Yace "masha Allah my dear burina a koda yaushe in ganki cikin farin ciki.pls rumaisah idan akwai abinda ke damunki ki fada min ko mene ne shi ni kuma na miki alkawarin zan magance miki... Ya fada yayinda ya kwantar dani jikinsa yana gyara min gashina da ya baje har yana kokarin rufe min fuska Murmushi nayi nace"babu komai yayana komai ya wuce. Na fada yayinda nake shirin tashi daga jikinsa nace"kar farida tazo ta samemu haka. Bai ce komai ba kawai naga ya fito da check ya rubuta ya mika min na karba na duba snn na kalleshi da sauri nace" five million? Ya daga min gira Nace"na miye? Yace"nakine. Da sauri nace"haba yaya me zanyi da kudi mai yawa haka bayan ka wadatani da komai na more rayuwa ba abinda na nema na rasa a gunka..... ya katseni da fadin"Nafisace ta rokeni kudi zata fara business shine na bata .kema na kawo miki.... Murmushi nayi nace"gaskia yaya ni na yafe bana bukatar komai irin kulawarka Na kwantar da kaina a kirjinsa kamar jira yake ya rumgumeni yace"insha Allah babyna zan baki kulawa yadda ya kamata.amma ki karbi kudin nan pls kinsan fa ba,a maida hannun kyauta baya. Murmushi nayi nace"ba haka bane yaya kayi hkr kaga ni bana business bare in kara jari.kuma banida wata bukata ta kudi saboda komai kana yi mun ko na karba ajiyewa zanyi..... Yace"ki karba ki ajiye dear ni dai na baki. Nace"to yaya na gode Allah ya kara arziki da wadatar zuci. Yace "amin dear bari na tayaki shiryawa. Tashi yayi ya dauko mai yazo zai shafa min na karba nace"nagode yaya zan shafa da kaina. Bai bari na shirya ni kadai ba sai a tare yana tayani bayan na kintsa tsaf yace masha Allah yanxu..... Knocking din kofa da akayine ya katse shi snn yace"yes come in. Fareeda ce ta shigo hannunta dauke da tray ta karaso ta ajiye a gabanmu a kasa snn ta dago ta kallemu tana murmushi tace"daddy lokacin cin abincin mamana yayi snn tasha magani. Kauda kai nayi don banson cin abinci sam yayinda ya salman ya kalli agogo yace"hakanefa. Snn ya kalli farida yace" Allah ya miki albarka mamana.yanda kike hidimar kula da mamanki kema Allah ya baki yara da zasu nuna miki kulawa. A tare muka ce amin snn tace"nagode daddy bari na barku to. Ta tashi ta fita. Shikuma saida ya tabbatar naci sosai nasha magani snn ya ce"bari in barki ki huta .amma please anjima kizo da wuri karki zauna hira da yaran nan ki shanyani . Har zai fita ya sake dawowa yace"kuma don Allah karki ce zaki shiga kitchen da kanki . Murmushi nayi nace"to yaya . Daga nan ya fita. Nafeesa da Adda A'i sun gama shirinsu akan ya salman tsaf domin ko wata uku batayi ba suka fara cin kudinsa don indai tace ga bukatanta to baya ko tambaya yake cire kudi ya bata.yayinda ita kuma a take take turawa adda A'i. Farida kuwa tuni babanta ya samo mata admission BUK har an gama mata komai ta fara zuwa. Hkr ya salman ya baiwa ya salim da ruma akan farida bazata koma Abuja ba domin ya fi son ya nesantata da farouq gabadaya kafin munir ya dawo ayi bikinsu. Inna kuwa duk yadda taso ta tada bala,i akan maganar farida bata sami fuska gun ya salman ba dole ta shafawa kanta lfy. Farouq kuwa duk abinda ya faru ya sani don haka ya sanar da mahaifiyarsa abinda duk ya faru. Salima ta danyi shiru snn tace"ai nasan za,ayi haka farouq zai yi wuya ya salman ya amince ka auri yarsa . Yace"mum pls ki taimaka min don Allah wlh ina son Aisha. Salima ta danyi shiru snn tace"to zanyi tunani akan me ya dace ayi.amma fa kaima ya kamata ka nitsu kasan cewa ka girma yanxu ba yaro bane kai tunda aure kk son yi ma. Farouq yace"mum mi nayi kuma? Salima tace"ai kasani sarai akan abinda nake maka magana kullum .maganar zuwa party shaye..... Da sauri yace"O my God mum nace miki na bari wlh na bari ni yanxu in na auri Aisha shikenan burina ya cika . Tace"hmm tou shikenan.Allah dai ya kara shiryawa. Farouq ya tashi ya fita baice komai ba. Ranar wata sunday kawai se ga saliman tazo nayi mamakin ganinta sosai don rabona da in sata ido har na manta snn ban taba tunanin zata zo gidana ba. Amma cike da fara,a muka gaisa kamar ba abinda ya taba shiga tsakaninmu farida ma tazo ta gaisheta mun dan taba hira snn ta tambayeni ko ya salman na nan wurinsa tazo akan maganar farouq da farida. Kasancewar ranar girkin Nafisa ce don haka bana son shiga part dinsa farida na aika taje ta gaya masa yayi bakuwa. Aikuwa ba dadewa ta dawo tace "yace ki iso mum . Cike da fara,a salima ta amsa muka tashi da ita zuwa palon ya salman. Bayan sun gaisa yace"hajiya salima lfy yau na ganki a gidana? Murmushi tayi tace"lfy lau wlh ya salman munzo bikin nadia yar doctor surayya ce shine nace bari nazo mu gaisa. Yace"masha Allah gaskia na mun gode sisai da ziyara. Ta danyi shiru snn daga bisani tace"yaya Salman dan Allah ina rokon wata alfarma. Shima shirun yayi kamin yace"wane irin alfarma salima. Nan ma shiru ta kumayi kusan mintu biyu snn ta gyara zama tace"yaya salman dama akan maganar yaranmu ne farouq da farida kaga fa suna matukar kaunar junansu saboda haka nazo gareka in rokeka ka amince mu kulla zumunci ta hanyar hada yaranmu aure.kaga ma shi Ahmad har ya amince kuma yara ma suna son junan su don haka yanxu amincewarka kawai muke jira. Shiru ya salman yayi nima na zuba mishi ido ina jiran me zaice........ 😴😴😴kuyi hkr fans zuwa gobe zan muku typing sosai .kuyi manage da wnn. Allah ya bamu alkhairi🤗🤗🤗🤗🤗🤗 Hauly ce🥰👍🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡97 ********Can ya numfasa snn ya fara magana "Salima sai dai ki ba farouq hkr kuma kuyi hkr domin maganar aure tsakaninsa da farida bazai yiwu ba saboda na rigada nayi wa munir alkawarin bashi auran farida bayan ya dawo.bana son in saba alkawari kuyi hkr don Allah. Salima ta danyi shiru snn tace"amma ya salman farida farouq takeso baka tunanin akwai matsala idan aka hadata aure da wanda ba zabinta ba ? Yace"babu wata matsala insha Allah domin shine zabinta tundaga farko . Shiru mukayi gabadaya tsawon wasu lokuta Salima ta dan numfasa tace"to ba komai Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi a garesu baki daya. muka amsa da amin ya salman yace "don Allah kiyi hkr salima .. Murmushi tayi tace "ba komai ya salman haka Allah ya kaddara. Muna cikin haka nafisa ta shigo cikin kwalliyarta na jan hankali tayiwa salima sannu da zuwa cike da fara,a snn taje ta zauna kusa da mijinta . Cire idona nayi akansu Salima tace"Rumaisa ko wnn ce amaryar ya salman? murmushi nayi nace"itacr. salima tayi murmushi tana kallon nafisa tace"Ayya Allah ya bada zaman lfy. Nace amin yayinda Nafisa ta sunkuyar da kai wai ita ga me kunya. Daga nan salima tashi tayi ta yima ya salman sallama ni kuma na rakata har motarta ta kalleni tace"gaskiya rumaisa kinyi sanyi da yawa ba haka na sanki ba. Nayi dariya snn nace"me kika gani kika ce haka? Tace"yanxu kinaji kina gani ya salman yaje ya auro wnn mitsisiyar yarinya da bata wuce sa,ar yarki ba. Daria na kuma yi nace"to ya zanyi salima Allah ne ya bashi dama ya auri mata har hudu. Tace"hmm shiyasa nace kinyi sanyi da yawa rumaisa don da ba haka kk ba kishin ya salman kk sosai. Nace"hakane.amma in kin lura kullum kwanan duniya shekaru karuwa yake kinga ya kamata dama idan mutum yana girma ya kara hankaline.tsiwar da nayi a da ko kusa bazan iya yinshi yanxu ba. ta gyada kai tace hakane hmm Allah ya kyauta.kinga ni kuma sai daga baya na fara jin dadin aure saboda a yanxu banda matsalar komai wlh. Nace"masha Allah na tayaki murna Allah ya kara muku son juna. Mukayi dariya a tare snn tace"don Allah rumaisa kiyi hkr da abinda ya faru a baya . Nace"haba wnn ai ya wuce salima. Tace"hakane Daga nan muka kara sallama taja motarta ina daga mata hannu cike da fara,a snn na koma ciki a kofar shiga palonmu nayi karo da ya salman yazo fita banma ganshi ba na daijini kawai a jikin mutum na dago da sauri na kalleshi shima ni yake kallo snn yace"baby ki dinga kula da kanki sosai fa. Murmushi nayi nace"to yaya. Ya dan sassauta murya yace"tanadin me ake min ne gobe ? Nace"kai yaya kai da kk da amarya gau a leda me..... Hannu yasa a baki na yace"da tsohuwar zuma ake magani baby.kuma ke dabance ki godewa Allah domin ya baki ni'ima sosai a kullum na kasance dake wani irin nishadi nakeji da annashuwa.a cikin mata dari yana wuya a sami irinki biyar babyna.ke din special ce.kinfi zuma zaki..... Murmushi nayi har hakorana suka bayyana nace"hmm yaya na kana zugani da yawa fa.ai kaima yayana ba baya bane.ka hadu ta koina ka iya mantar dani a wace duniya nake idan ina tare dake kai yaya nakan mance komai wlh .salon soyayyar ka daban ne yayana ..... Bai barni na karasa ba ya hade bakinmu guri daya ya shiga bani hot kiss mai rikitarwa ji nayi kamar zan suma na dada kamkameshi gabadaya har mun mance a bakin kofan falo muke. Nafisa ce ta fito da sauri cikin shirinta dama zasu fita ne. Ganinmu yasa tayi turus cike da mamaki take kallonmu bamu ma san tanayi ba.haushi sosai taji ko ince kishi amma wane bangare na zuciyarta yace mata don me zakiyi kishin wanda ba sonsa kike ba . Tabe baki tayi ta karaso daf damu hade da yin gyaran murya. da sauri muka saki juna sai lokacin muka tuno inda muke gaba daya kunyar nafisa naji sosai naji duk ba dadi a raina. Shhikam ko a jikinsa don basarwa yayi ya kalli nafisa yace"mu tafi koh? Murmushi tayi tace eh.snn ta kalleni tace"mummyn farida bari muje mu gaida su innah ko kina da sako? Girgiza kai nayi har lokacin jikina a mace nace"sakon gaisuwace kawai ku gaishesu se kun dawo . Tace"to" snn ta shige gaba shi kam tsayawa yayi yana kallona snn yace"ya akayine? Naga kinyi slow nan da nan. Dan tabe baki nayi nace"ba kai bane duk ka bi ka sa jikina yayi..... Ban karasa ba na juya na tafi ciki. Dan dariya yayi ya gyara zaman shirt din jikinsa ya tafi ya iske nafisa na jiransa daga nan suka tafi gidansu. Inna kamar zata goya nafisa tuni ta cika mata gabanta da kayan ciye ciye da na sha. Yatsine fuska nafisa tayi tace"ni goggo dama biki wahalar da kanki ba banajin son cin komai. Inna tace to me ye faru baki jin dadine? Nafisa tace"nima ban gane ba wlh jin baki na nake ba dadi komai baya min dadi wlh tun shekaran jiya. Ta fada hade dan kwantar da kanta kan hannu kujera dab da ya salman a shagwabe tace "ko bacci banyi sosai fa. Inna ta washe baki cikeda farin ciki tace"masha Allahu.aikuwa gashi na gani duk wata alama na mai juna biyu ya bayyana a jikinki. Da sauri nafisa ta dago kai tana kallon innah ta rasa me ma zatace kawai ta maida kai ta kwantar ta kama sharbar hawaye. daga innah har ya salman mamaki ne ya kamasu sai dai shi baice komai ba kawai tashi yayi ya fita domin ya je ya gana da yan anguwa. Inna kuwa ta shiga rarrashin nafisa tana cewa ke ana samun ciki ana murna kin kama kuka? To kukan na miye? Nafisa tace"haba goggo ni ko rabin shekara banyi da aure ba zan fara shan wahalar ciki? Inna tace"wayace miki da wahala ? Haba yar autanmu ai haihuwa ba wahala tsantsar dadine kawai kwantar da hankalinki Allah ya raba lfy.ince dai waccan jarababbiyar bata musguna miki? Girgiza kai tayi tace"ni bata min komai. Yace"ta samawa kanta lfy.don wlh in ta tabaki wnn karon sai nasa salman ya saketa. Tabe baki nafisa tayi batace komai ba.Innah tace"hmm yawwa nafisa ina son ki rokar min salman don Allah ya baiwa sadiya jari itama ta fara siye da siyarwa ta daina zaman nan na banza ga raihana tuni mijinta ya dorata akan harkar kasuwanci har mota ta siyawa kanta bayan wacca mijin ya sai mata a baya.amma sadiya don tsabar mugunta irin na mijinta ba ruwansa da ita bare ya bata jari .kullum na roki salman sai yace min sai ta shirya da kanta ta rokeshi snn zai bata kinsan shi da murdadden hali to ya ma ki ya bata fuska bare ta roke shin kullum suka hadu sai ya kama daddaure fuska.shine nace don Allah ki lallabashi mana ki masa magana ita ma ya taimaka mata ta sami abinyi. Nafisa tace"hmm ai goggo ita adda sadiyan ne batada wayo ace duk kudin mijinta bata san yanda zata lallabashi ya bata wani abu ba se ta roki yaya wani abu haba dan Allah shima fa yaya yana da hidimomi da yawa a gabansa kuma kwanan nan duk se cewa yake baida kudi ma . Inna tace"haba nafisa baki ganin halinda take ciki ne kwanan nan duk ya sake juya mata baya dama albarkacin yaranta takeci a gidan. Nafisa tace"to shikenan goggo zan roki yaya ya taimaka mata karki damu. Inna tace"yawwa yar autanmu Allah ya miki albarka ai tunda salman ya samu mace irinki yanxun zamuji da dadi sosai fiye da da.don wancan jarababbiyar..... Nafisa ta katse innah da fadin don Allah goggo ki bar matar nan ta huta .bata da laifin komai ku daina aibatata . Inna ta gyara zama zata fara magana se ga ya salman ya shigo don haka tayi shiru amma magana na cinta a rai. Ya salman ya kalli nafisa yace"ke mu tafi . Anan suka yi ma innah sallama suka tafi. A hanya ya dan kalli nafisa data kwantar da kanta kan seat tana limshe da ido.ya dan rage gudu snn yace"ya kamata muje asibity a duba ki ko ? Shagwabe fuska tayi snn tace"za,a min allura? Yace"baza suyi miki ba ki kwantar da hankalinki ai nasan tsoron alluran ya hanaki ki fada min baki jin dadi. Asibity suka tafi nan doctornda ya saba dubani ya duba nafisa sunyi gwajin ciki aikuwa nan da nan sai ga result ya tabbatar musu nafisa na daukeda ciki. Murmushi ya salman yayi cike da jin dadi don gaskia yana son haihuwa sosai burinsa yaga gidansa ya cika da yara kota ina.nan da nan ya shiga hamdala yana godewa Allah. Nafisa kam gabadaya hankalinta ya tashi kuka ta shiga yi mishi wai ita tsoran haihuwa takeji. Murmushi ya salman yayi ya jawota jikinsa ya shiga rarrashinta yace"babu wani wahala nafisa. Nan suka dinga mata magana da doctor suna fahimtar da ita. Har suka dawo gida bata saki ranta ba.don ita kwata kwata bata kawo lissafin haihuwa a tsarinta ba so kawai take ta tara dukiya tayi gaba. Farida kuwa bayan na fada mata yanda mukayi da salima sai na lura jikinta ya mutu sosai haka ta wuni sukuku yau ba walwala. Da daddare duk waya da mukeyi da munir nida khalil kallonmu kawai take sabanin da takan ce in gaisheshi.domin bata yarda suyi waya har yanxu shima kuma ya daina tambayarta don ya rigada yasan komai akan abinda ke faruwa don haka yake fushi da ita sosai.ni dai bansan ya lamarim farida da munir zai kasance ba. Nafisa kuwa ana can turaka ya salman sai riritata yake har da tsokanarta da cewa "maman twins Allah sa ki haifa min twins don ina sha,awar su sosai. Bata fuska tayi tace"mummyn faridace zata haifa maka twins insha Allah . Yace"ita triplets zata haifa min ba twins ba. Dan zaro ido tayi tace"tab hmm bari ta ji ka ni ba ruwana. Yace"ai ita tana son haihuwa sosai don haka murna zatayi ba kamar ke matsoraciya ba. Murmushi tayi daga nan shiru ya biyo baya can ta dago ta kalleshi tace"yayah pls ina rokon wata alfarma a gunka. Yace"fadi ko menene momyn twins zan miki in dai bai fi karfina ba. Murmushi tayi tace"hmm dama yaya ina son ka dan kara min wasu kudi saboda business dinda nake son karawa . Ya danyi shiru snn yace" naji zan baki amma da sharadi. Tace"sharadi wane iri? Yace"so nake ki kawo min business plan dinki na gani.domin tunda nake baki kudi har yanxu banga wani business da kk fara ba. Murmushi tayi tace"aikuwa inada business plan a rubuce ma.domin so muke mu bude company buga turame kuma ni da kaina zan dinga zana designs masu kyau . Yayi danyi murmushi snn yace"da kyau hakan yayi keda su waye zaku hada hannu? Tace"nida Adda A'i da adda madiha . Yace"nabila da sa,a fa? Tace"hmm adda nabila komai na arziki idan an shigo da ita lalacewa yake.Adda sa,adatu kuma bata da lokacin wani business nasani. Yace"amma ya kamata duk abinda zakuyi kusa ka nabila a ciki koda da shawarace zata taimaka muku kamata yayi ku hada kanku gabadaya ku tallafawa junanku. Tabe baki tayi tace"hmm adda nabila fa bama sata a lissafin mutane ma domin komai ta taba lalacewa yake.Allah sarki dama dai adda Sukhaina nada rai ne ma ita kam bata da matsala gata wayayya. Shiru yayi bai kuma yin magana ba sai ma tunanin maganganun nata da yakeyi. Can tace"yaya se kuma maganar adda sadiya goggo tabi ta damu tana son ganin adda sadiya ta samu abinyi ta daina zaman banza.amma kuma sam na lura ita adda sadiyan bata wani damu da zaman banzan ba tunda ko damunta bayayi.ita babu abinda tasa a gaba sai dai ta dinga daukar maganganun mutane taje tana kaiwa goggo . Nan da nan fuskarsa ta sauya cike da jin haushin sadiya yace"sai taci gaba da zama hakan ai. Nafisa ta kwantar da murya cike da kirsa tace"haba yaya a taimaka mata dan Allah kaga fa har ta na gaya wa goggo wai baka sonta kana nuna mata banbanci tsakanita da adda Raihana da adda sa,a. Tsaki yayi ya gyara kwanciyarsa bai kuma yin maganaba.murmushi tayi ta kashe wutan dakin ta kwanta itama taja bargo hade da fadin "don Allah yaya kayi hkr in dai akan maganar adda sadiya ce insha Allah bazan kuma kawo maka maganarta ba ka juyo dan Allah. Bai sake kulata ba da haka har sukayi bacci. Da safe farida tuni ta gama duk wani shirye shiryenta na tfy makaranta na lura sai fushi take tayi har yanxu.koda ta kawo min tea da maganina na kalleta nace"Farida wai menene yake damunki tun jiya kk ta fushi ? Tace"babu komai mama kawai kaina ke mun ciwo . Duk da nasan ba haka bane amma ban matsa mata ba nace"sannu Allah ya sawwaka yanxu kamin ki tafi kije kiyi breakfast se kizo ki sha pcm Ta dan ja tsaki hade da fadin wnn nafisan don mugunta yau kosai tasaka akayi da kunu ... Na katseta da fadin"kefa macece farida idan an dafa abinda ba kya so ba sai ki shiga kitchen ki dafa abinda ranki yake so ba. Tace"kawai mama ki bar maganan nan wlh bata mun rai yakeyi.daddy zan gayawa domin ya fada mata duk ranar girkinta kamata yayi ta tambayi kowa abinda ransa keso a dafa masa kamar yadda kikeyi.ba wai kawai ta dinga kwaba abinda ranta yakeso ba. Nace"ke dai kin fiye raki wlh ni har ga Allah banga laifin nafisa ba domin ta dafa abinda daddynku yafi sone don haka ki bar maganar nan ki dauko handbag dina ki kawo na baki kudi in kinje makaranta kici abinda ranki ke so shikenan. Ta ce"inada kudi da daddy ya bani shekaran jiya. Snn ta juya zata fita tace" don Allah mama ki kula da kanki se na dawo. Nace"a dawo lfy. Bayan ta fita khalil ma ya shigo ya gaisheni snn ya sallameni duk na bisu da kyakkyawar addua. Inna kuwa tunda sukayi maganar sadiya da nafisa take ta zuba ido amma shiru ba abinda nafisa tace mata har ta gaji ta fara neman nafisa a waya amma sam layin nafisa yaki shiga hakama sadiya ta kirata shiru baya wucewa ta kalli innah tace"inna nifa na lura nafisan nan tana da wani mugun haline itama. Inna tace "aa bana so karki fara aibatata don ke haka kk da son zagi da kushe mutane kina aibata su.karki ga laifinta salman ne baiga dama ba don haka se kiyi hkr na lallabashi a hankali randa ya ga dama ya baki . Sadiya tace"haba innah ki duba fa duk yanuuwana sunci gaba sun barni.ace ina da dan uwa kamar ya salman a garin nan amma ko motar hawa ni banida ita har yanxu? Inna tace"hmm hkrn dai zakici gaba dayi. Haka sadiya ta koma gida da fushi ta kira adda A'i tana gaya mata adda A'i ta bata hkr snn tace insha Allahu zata san me zatayi akai. Amma shiru da yin maganansu ya fi wata biyu yanxu. Sai kawai ga wayar sadiya ranar ta kirani kamar kar na dauka amma haka nan na daure na dauka muka gaisa anan ta fara gaya min bukatanta hade da rokona akan insa baki ya salman ya bata jari itama tana son ta fara business.nace mata insha Allah zan rokan mata. Amma koda na tuntubi ya salman da maganar kin saurarata yayi a karshema ce min yayi in daina kula sadiya bayason sadiya ta kuma shiga rayuwata. Nidai banji dadin hakan ba don haka a cikin kudin da ya bani kwanaki na dauki milliyon biyu na bata wai karkuso kuga murna ranar taje ta gaya wa innah.innah tace"hmm ai ta rigada ta gama mallakeshi duk abinda tace mishi baya ko bata lokaci yakeyi . Sadiya tace"hmm Inna ni dai tunda na samu ai shikenan. Inna kam haushi ne taji sosai saidai bata kuma cewa komai ba. Su nafisa kuwa tuni kasuwanci ta kamkama Allah ya basu sa,a sun fara da kafar dama don haka komai na tfyn musu yadda suka tsara.adda A'i burinta ya fara cika yanxu kam . Yayinda sadiya ta shiga sanya ido a lamarinsu a hankali domin tana son gane me sukeci saboda ziciyarta ya shiga zarginsu........ Hmm Allah ya kyauta Hauly ce🥰🙏🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡98 *******Alokacinda yaran nan suka sami hutun december muka tafi yola muka bar yaya a gida da nafisarsa. Gidan galadima muka fara sauka Allah sarki rayuwa gabadaya tsoffina nan babu su a yanxu dai dai suka dinga tfy har suka kare.sai adduar Allah ya rahamcesu a koda yaushe nazo yola gidan galadima sai na zubda hawayen tunawa da haj rumaisa da hajiya zubaida mutanen kiriki Allah ya jikansu. Mun jima agidan don saida muka shiga kowane sashi a karshe gidan mai martaba muka tafi kasancewar ba lokacin fada bane mun samu ganinsa mun gaisheshi cike da girmamswa.sarki Abdallah girma ya fara zuwa gaskia. Muna nan gidan lamido har isha snn muka wuce mafiyas quaters gidanmu.sosai kannena suka shiga murnar ganinmu haka ma su aunty samira bayan munci abinci muka baje a palon daddy muka shiga hirar duniya yayinda su farida suke ta tsokanar daddy nan ma ina taka musu birki sosai. Karfe goma kowa ya kwanta nikam ina tareda aunty samira a dakinta hiranmu yaki karewa hmm dama kunsanmu indai mun hadu to kwana muke muna hira ko itace da girki bata zuwa dakin daddy a ranar. Nan ta fara tambayata tace"ihsan ya kike jin zama da wnn yar mitsisiyar yarinya da surukina ya aura?nasan kina ta ganin iyayi iri iri. Dariya nayi nace"hmm babu sam aunty nima da farko na dauka hakanne amma sam nafisa babu ruwanta bata ma shiga tsabgar komai na gidan bata maida hankalinta akan komai. Aunty samira ta tabe baki tace"to Allah yasa ta dore gaskia na miki murna.kinsan kwanaki da bakida lfy sosai daddynku ya dage akan gaskia sai salman ya sawwaka miki saboda wahalar da kk sha tinda kukayi aure da kyar aunty amina ta lallabashi. murmushi nayi nace"hmm aunty bazan iya rabuwa da yayanah ba wlh.kinsan ko ni a lokacin da yake na dan fusata sai na yanke shawaran barin masa gidan kamin akai ga hakan nazo na kama rashin lfy wlh aunty irin kulawarda yaya ya dinga bani sai naji kawai bazan iya barinsa ba dan gabadays ya manta da wata amaryarsa hankalinsa gabadaya akaina yake har saida na warke.kuma kinga aunty duk abubuwan nan dake faruwa dani a rayuwa yayana bai taba juyan baya ba yana sona sosai kuma ya yarda dani hundred percent snn baya wulakantani.aunty wnn shine dalilinda yasa ko su inna sun min wani abun nake hkr bana nuna fushina ko damuwata tunda wanda nake zamansa bai taba juyan baya ba. murmushi aunty samira tayi tace"hakane ihsan Allah ya kara muku hkr da son juna wlh ihsan rayuwarki da salman tana birge kowa. dariya nayi nace"amin aunty. Snn na sake cewa aunty kamin na koma gyara nake so a min na musamman ina son in koma amaryace nima. dariya tayi tace "babbar magana kice kuma kara,i ya tashi.to banda abinki ihsan cikin nan fa. na dan bata fuska nace"ai bazai hana ba aunty. Tace"tab to wlh badani ba.kinga ki bari sai Allah ya raba lfy yawwa sai mu aika har nijar sokkoto maiduguri kayan kamshi duka .amma yanxun zaki danyi sama sama kawai . murmushi nayi nace"yawwa aunty dama ina son farida in fara dan kinsata kamin nan kinga munir dawowarsa saura wata daya yanzu kuma ya salman yace yana dawowa da wata biyu za,ayi bikinsu.kinga har sun gama komai har gininsa na kano. Aunty samira tace da kyau Allah ya nuna mana.kuma gaskia gara mun fara tsumata .to ya batun asibitynda za,a bude kuma? nace"ai kinsan aikin asibity yanada bukatan nitsuwa don haka ana nan ana shirye shirye a kanshi Tace "masha Allahu.Allah ya nuna mana . Nace amin ya rabb Har karfe biyu snn muka kwanta bacci. Washe gari muka shirya sai gidan ya awwal yini mukayi snn muka dawo. Snn washe garin kuma gidan ya samir.haka dai muka dinga zaga dangi.su farida ba karamin alkhairi aka musu ba yayinda samarin yola sukayiwa farida caa wai sonta suke. Satinmu biyu muka shirya dawowa ba don mun gaji ba sai don matsin ya salman . ranar jumma kuwa muka taso jirginmu na safe sai gamu kanon dabo. tinda muka sauko na hango ya salman na saki murmushi shima ya maida min.ganinsa nayi ya koma saurayi dan shekara talatin domin kanan nan kaya ne a jikinsa snn ya toshe ido da bakin glss hannunsa daure da agogon azurfa sai daukan ido yake yayinda fuskar nan tasha gyara hmm yaya gayu. Muna karasawa yaran nan suka rumgumeshi cikeda murna yana mana sannu da hanya. farida ta kalleshi tace"daddy wlh da kyar na ganeka. khalil yace "koni daddy.gabadaya ka zama wani dan saurayi. Murmushi yayi yace"dama ni tsoho ne? Suka sa dariya yayinda farida ta rike hannunsa ta kamo nawa ta hada da nashi tana murmushi tace"wlh mama da daddy kunyi kyau sosai yau dinnan kamar wasu sabbin couples Ta kalli khalil tace "ibrahim daukesu hoto. khalil yace yanxu kuwa. nan ya fitar da iphone dinsa ya shiga daukarmu hoto ya salman don tsabar daurewa karya gindi har wani canza style yake mana . Bayan sun gama gabadaya haduwa mukayi farida tayi mana selfie. daga nan muka kama hanyar gidansu innah don mu gaishesu.khalil turo baki yayi yace"ni wlh dama gida muka fara zuwa ba gidansu innah ba. Nace" kai dai daddyna baka son mutane haka nan hutunda mukayi a yola duk kabi ka ishemu da mu dawo. farida tace"shi ai yafi son zama waje daya kana da aiki ai. Ya salman dai baice mana komai ba. Mun iso gidansu inna tuni su farida suka shiga suka barmu nan ya kamo hannuna ya rike yayinda ya cire sun glss na idonsa ya min wani irin kallo da naji gabadaya tsigar jikina ya mike matso da fuskarsa yay dab da tawa har muna exchanging numfashi ya sassauta murya yace"baby nasha wahala sosai two weeks dinnan da ba kya kusa dani ji nayi tamkar two years ne. ya fada yayinda ya kashe min ido daya hade da daga min gira daya yayinda ya ke murza hannuna a hakali cikin nashi snn yace "gaskia you are very special ke din ta musammance my dear. ganin yana kokarin shagalantar dani yasa nayi saurin fadin"yaya mu shiga ciki don Allah kar wani ya fito ya samemu muji kunya. Yace"naji amma ki fada min irin tanadi da tsaraba da kk yo min daga yola. murmushi nayi nace"kai yaya kaida kk da amarya kamar nafisa. nan da nan yanayin fuskarsa ta sauya tabe baki yayi ya saki hannu na ya shige gaba ni kuma na bishi a baya cikin rashin jin dadin yadda fuskarsa ta canza. A palon inna muka iske su farida tana ta zolayar inna tana dariya . nan muka xube hade da gaisheta ta amsa fuskar nan a tamke tunda muka shigo su farida tashi sukayi suka tafi dakin mmn sakina. Nafisa ce ta fito daga bedroom din innah tana mana sannu da xuwa ni kadai na amsa shi kam ko kallo bata isheshi ba nace"ashe kinzo kina nan? sunkuyar da kai tayi tace,"eh. daga nan shiru mukayi gabadaya nafisa ce taje ta kawo mana ruwa da lemo inna sai harararta takeyi. bamu jima ba mukayk musu sallama muka tafi na dauka nafisa zata bimu amma shiru. mun iske gida kowa lfy sojojin sai kamewa suke suna gaida oga shikam ko a jikinsa. mun tarar gida fes koina kamshi anan yaran nan kowanne ya wuce room dinsa nima ina kokarin wucewa side dina kawai naji anyi cak dani da sauri nace"wayyo yaya so nike na danje nayi wanka da ruwa mai dimi tukun ko naji dadin jikina. baice komai ba ya nufi side dinshi dani a hanni kamar wata karamar yarinya muna ziwa ya saukeni kan gadonsa ya koma yasawa kofa key snn ya wuce toilet ya hadomin ruwan wanka ya fito da kansa ya shiga hidimar cire min kaya hade da fadin"banji lfy babyna ba ma. Ya soma shada cikina wanda ya dan fara tasowa don yanzu ina wata na biyar. Saida yayi mai isarshi snn ya sake daukata sai toilet wanka yayi min shima yayi daga nan muka dawo daki ina goge jikina na juya na kalleshi nace"yanxu idan matar gidannan ta shigo ta kamamu fa munji kunya gaskia daure fuska yayi yace"saboda haramci muke aikatawa? Da sauri nace"Allah ya huci ranka yayanah ba haka nake nufi ba. na karasa gabanshi ina rike kunnena kamoni yayi mukayi kan gado.hmm dsga nan fa labari yasha banbam nan muka shiga gwadawa juna so ya salman ya kamkameni tamkar zai maidani cikinsa sai sakin numfashi yake nima din hakane duk mun kasa cewa komai. da kyar mukayi sallar azahar ya sake janyoni muka koma gado kai ya salman baya gajia ni tuni nayi laushi jikina ya fara ciwo. sai la,asar ya rabu dani. Kwanan mu biyu da dawowa shiru banga nafisa ta dawo ba ina son tambayarsa ina jin tsoron fushinsa. sai ranan kawai raihana ta zo mi. yini a gurinta nake jin labari wai nafisa tayi bari koda suka je asibity aka binciko shine doctor ya tabbatar ma ya salman cewar abotion tayi wnn abin ya kona masa rai kwarai dan haka ransa ya baci yace ta bar masa gidansa .shine taje ta fadawa inna.innah kuwa ta kama masifa wai ai makirci ne na tafi naje na kulla a yola gashi daga tfyna nafisa tayi bari kuma na sanya wa ya salman kiyayyarta har ya koreta .don haka ba inda nafisa zata je .tana warkewa kuma zata dawo gidan nan don ban isa in zauna ni daya a gidan nan ba Hmm Inna knn Allah ya kyauta. Nafisa kuwa bata damu da abinda ya faru ba don ita yanxu a ganinta burinsu ya gama cika ko yanxu ya salman ya bata takardanta hankalinta ya kwanta zata je ta auri masoyinta. Amma adda A'i na zuwa ta saka nafisa a gaba tai mata tatass don kebewa sukayi tace"ni bansan bakida wayo ba se yanxu waya gaya miki yanxu ana sure don soyayya ?to bari kiji yanxu don kudi ake soyayya shi wanda kk son kashe aurenki akansa me zai tsinana miki? Matsiyacin banza ma irinsa . Nafisa ta bata fuska tace"adda suraj ne fa kinsan mun dade muna tare munyi alkawarin zamuyi aure dashi kune kuka rusa mana soyayyarmu. Adda A'i cike da jin haushi tace"kinci gidan ku .shashasha mara hankali idan kk auri suraj din uwar mi zai tsinana miki?ai naji labarin shi yake zugaki ki kashe aurenki ki koma shine kk biye masa harda zubar da cikinda mukaci buri akansa.wlh nafisa ki kiyayeni bar kiji dolene ki koma gidan salman domin mu dora daga inda muka tsaya idan kk kuma sauraran wani suraj wlh sai nasa an batad dashi shashasha kawai. Kuka nafisa ta shiga yi sosai ana sadiya ta shigo ta samesu wacce ta gama jin komai amma sai tayi tamkar bataji ba ta kalli adda ai tace"haba adda ki daina mata fadan mana abun nan kaddara ne fa. Adda A'i tace barni sadiya wnn rashin hankali da nafisa tayi dole ne kawai nayi fada. Nafisa kam rashi tayi ta koma dayan dakin na baki ta kwanta tana kuka inna ma fada ta dinga yiwa adda A'i. Adda A'i bata bar kano ba sai da ta tabbatar inna ta daidaita salman da nafisa snn ta koma hade da yiwa nafisa gargadi da jan kunne na sosai. Da kyar ya salman ya sauko ya fara kulata amma sam yaki sakar mata fuska kamar da kuma ya daina bata kudi kwata kwata.to fa anan al,amari ya fara dagulewa adda A'i ta farawa kutsawa malamai. Nidai bansan wacca waina ake toyawa ba asalima muna nan muna shirin dawowar munir. Yayinda farida kuwa gabanta ya shiga faduwa. Kasancewar ta Abuja ya dawo gabadaya muna can tunda yace mana yana hanya. Ranar airport cika tayi da yanuwa da abokan arziki farida kuwa ta rasa inda zata sa ranta don gabadaya tunaninta ta yaya zata fara ido hudu da munir me zata ce masa? Don haka kamin mu taho airport tace cikin ta na ciwo bazata iya zuwa ba. Haka muka kyaleta muka tafi. Ba jimawa munir ya iso wayyo karkyso kuga murna nida ya salman muka rumgumeshi cike da farin ciki gashi ya kara kyau da haske ga wani jiki da yadanyi ya dada girma da kwarjini kasancewar kana nan kaya ne a jikinsa se ka rantse baturene. Kannensa suka dinga tsalle da murna shikam murmushi yayi ya fara baza ido amma baiga farida ba abin ya bashi mamaki amma baice komai ba ya tafi gun abokansa suka gaisa snn muka kama hanyar gida sai lokacin yace "mama ina Aisha? Dan murmushi nayi nace"mun bar ta gida tace cikinta na ciwo. Bai kuma cewa komai ba har muka isa gidan kawu kassim tukunna momy zuwaira cike da jin dadi ta rumgume jikanta tana mishi sannu da hanya. Nanma mun jima don saida momy tasa mukaci abinci tukin kamin muka koma gidan ya salim kowa ya samu yayi wanka dan dare yayi shikam munir yana can da kannensa su khalil da junior da mimi.. Na iske farida a daki har ta soma bacci na tasheta hade da fadin "ya cikin naki? Tace"da sauki . Nace"hmm ya kamata kije kiyiwa yayanki barka da dawowa su mimi duk suna gunshi Dan guntun murmushi tayi jikinta a mace tace"kawai a barshi ya huta se gobe naje gunsa. Har zanyi magana ruma tace"aa kinga ki kyaleta se goben kinga har yanxu jikinta ba karfi. Shiru nayi kawai yayinda ruma ta ce da farida koma ki kwanta my dear se goben in Allah ya kaimu. A hankali ta kwantar da kai tace"tnx mummy. Washe gari kuwa a dining muka hadu yin breakfast gabadayanmu sai lokacin munir da farida sukaga juna gabanta ne ya fadi ganin yadda munir ya cika dining din da kwarjininsa gashi ya wani tsare idonsa na cikin farin glass medicated data kara masa kwarjini sosai. Shikam kallo daya ya mata ya cire idonsa cike da mamakin yadda ta kara cika a dan shekara daya sosai yaga ta kara masa kyau gashi gabadaya ya rikice da ganin irin kiran structure dinda Allah ya bata gashi dama uwar son yanga ne shiyasa dole kawai duk inda ta shiga take jan hankalin samari kanta.shiyasa gabadaya in zata fita bake sata ta dinga sanya manyan hijabai musamman ma in zata je makaranta. Munir ya sake satan kallonta a karo na biyu aikuwa caraf suka hada ido gabadaya suka kasa dauke idonsu daga kallon juna. Ruma kuwa sai kokarin yi mana serving take yayinda ya salman suke dan hirarsu .haka ma sauran yaran sai fadawa ruma abinda zasuci sukeyi. Ni kuwa hankalina na kan su farida sanyi naji a raina ganin yadda suke kallon juna nasan tabbas soyayyar nan tasu tana nan sai dai yanxu kowannensu yanaji da jan ajine. Murmushi nayi nace"uhm farida tashi kima yayanki seving ke kuma kinga momynku tun dazu take ta fama dasu khalil. Tashi tayi a hakali ta kalli munir snn tace"ya munir me za,a maka serving? Hankalinsa ya mayar kan wayarsa ya dan tabe baki yace"ke baki iya gaisuwa ba hala. Hmm lallai wnn guy din yanaji da kansa cewar farida a ranta.kawai ta tsinci kanta da sakin murmushi tace"o sorry ina kwana. Bai amsa ba sai can yace hada min tea sai kidan sa min chips kadan da source. Ta dauki cup hade da fadin"tea dinka kamar yadda na sani da ba sugar. Kai kawai ya daga mata kamar an masa dole.haka kuwa tayi masa. Anan muka fara cin abinci shikam sai satar kallonta yake har lokacin .ita kuwa tuni ta fara halinta na tsokana da dariya don ba yadda za,ayi farida na wuri bata sa mutane surutu ba. Salman junior da khalil ta sako a gaba yayinda mimi take shigan musu. Saida ya salim yace"haj innah banace miki in ana cin abinci ba,a magana ba? Murmushi tayi tace "to daddy na bari. Gwalo salman junior ya mata da sauri tace daddy bakaga junior yana min gwalo ba? Ya salim ya sakar wa junior harara yace "bakajin magana koh?da wani katon kanka a wajan Nace"oga da kansa zakace baijin magana?har da ce masa yana da katon kai Dariya mukayi lokaci guda banda ya salman don sai cewa yayi "junior rabu dasu kaji koh zamuyi maganinsu. Sai lokacin munir yace"hmm karfa muji tashin bindigogi Nace"ai kuwa dai kam. Haka muka gama breakfast cike da jin dadi da annashuwa kana ganin fuskokinmu kasan muna cikin farin ciki. Kwana biyu mukayi a Abuja muka tattaro harda munir muka dawo kano muka bar su ya salim da kewa. Sati biyu mukayi gidanmu se baki ke ta zuwa yiwa munir barka da dawowa. Tsakanin shi da farida kuwa sei gaisuwa amma gabadaya jan aji ya hana su zauna suyi hira tsakaninsu.ko da na gayawa ya salman yace in rabu dasu zasu shirya kansu. Dawowar munir ba dadewa ya fara xuwa aiki a FMC a matsayinsa na babban doctor aikuwa yan mata suka mishi caa wai ni yau har zuwa akeyi gaisheni.gashi sam yaki sake musu fuska sosai yake ji da kansa. Farida kuwa kishi ya kamata har ce mun takeyi munir yanata tara yan mata marasa tarbiyya in masa magana.murmushi kawai nayi nace mata to. A lokacin cikina ya kai watanninsa haihuwa ko yau ko gobe har nazo na fara labour amma ina haihuwa ya kasa zuwa da kansa saida ya salman yasa hannu aka min C.S aka cire min twins kyawawa masu kama da ubansu mace dana miji sai kun gansu manya kamar gwanin sha,awa. Haihuwar twins ba karamin yiwa ya salman dadi yayi ba bama shi kadai ba duk family dina sai da sukayi murna kai hatta inna da sadiya hakama nafisa ta dinga daukansu a waya tana cewa duk sunfi kama da yaya. Shikam uban gayyan tuni ya shiga hidimar suna sosai ya zage ya kashe kudi abun har yaso ya wuce kima. Ranar suna baby boy yaci sunan abbah MUHAMMAD (Hanif)baby girl kuma taci suna mama AMINA(hanifa) Gaskia mun sami kyaututtuka kamar bamu taba haihuwa ba se yanxu kasancewar mun kwana biyu.abin dai ba,a cewa komai se sam barka A lokacinda ya salman ke ta faman hidimar suna nafisa kuma ta shiga tunanin yanda zatayi ta samu kudin masu yawa a gunsa.don gabadaya adda A'i ta sakota a gaba wai me take jira har yanxu bata samo musu komai ba ga salman se kashe min kudi yake tayi yakamata itama ya bata kasonta mai tsoka. Haka nafisa ta shiga kwantar masa da kai cikin kissa da kisina har ta shawo kanshi dama yana cikin farin cikin haihuwar twins don haka ya bata kudi masu tsoka har tana mamakin yawansu anan tunaninta ya fara canzawa shin ta turawa adda A'i ko kuwa ta rike kayanta don gaskia tana son kamin ta bar gidan salman ta samu ta taimakawa suraj shima don yanxu shine babban burinta a.amma wata zuciyar kuma na gargadinta akan karta ta kai kololuwa gurin kyautatawa namiji a karshe yazo ya juya mata baya .gashi kudin sunada yawa dolene ta nemi shawara don haka ta kira nabila don tafi yarda da ita akan madiha da sa,adatu don a ganinta zata fi rike mata sirri......... Hauly ce🥰🙏🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡99 **********Kafin ta kai ga kiran nabila sai ga kiran suraj ya shigo wayanta nan da nan ta dauka fuskarta cike da fara,a yayinda take wani kwantarda murya. Hira suka shiga yi sosai anan ya shiga tambayarta yaushene zata kashe auren nata gashi ta kusa shekara daya yanxu?kuma har yanzu babu abinda ta samo musu ..... Shigowar salman ne ya sa tayi maza ta katse kiran cikin tsananin tsarguwa ta tashi tana karasawa gabansa tace"yayah yaushe ka dawo? Ya danja hancinta snn yace"tun dazu na dawo har na kuma shirin fita ban ganki ba shiyasa na shigo naga ko lfy. Hannunshi ta rike hade da fadin"lfy lau yayah wlh na danyi baccine kawai. Ya zuba mata ido har ya bude baki zaiyi magana sai kuma ya fasa. Tace"zauna mana yaya.me kk so na kawo maka ruwa ko lemo? Ya daga mata hannu yace"no am ok.yanxun gidanmu zanje in zaki je ki shirya mu tafi. Harga Allah bata son zuwa gidansu innah amma bazata iya cewa salman bazata ba don haka dole ta shirya. shi kuma da ya fita part dina ya shigo ya sameni da larai wacce mama ta samomin don tayani hidimar yara. Ina baiwa Hanif nono yayinfa hanifa ke kuka a hannun larai tana jijjigata take .A haka ya shigo ya samemu da sauri ya karbi hanifa a hannun larai ita kuma ta fita. ya karaso bakin gadon yana jijjigata yace"me ya sami goggona take kuka? Nace"tashi sukayi a bacci suna jin yunwa........ Ya katseni da fadin"to ki bata mana itama tasha haba baby .kawo abbana ki karbeta. Ko har yaushe yaya salman zai daina kirana babyn nan ne oho. Na mika masa hanif snn na karbi hanifa ina fadin "shikenan mamana yi hkr am sorry. na fara bata nono. Snn na kalleshi nace"yaushe ka dawo ban sani ba? Yace"tun dazu kuma yanxu ma fita zanyi ina son in bar miki sako idan munir ya dawo kice ya jirani kar yaje koina.don na kira wayarsa bai daga ba. Nace"to ba matsala.wayartashi kuma inaga ya sata a silent ne kuma ya manta kasan shi da mantuwa ai.amma lfy dai koh? Yace"lfy lau so nake in bashi wani aikine don gobe zan tafi lagos. ya fada yayimda ya kwantar da hanif ya sumbaci goshinsa yana murmushi yace"good boy. Ya matso kusa dani yana shafa kan hanifa dake shan nono "Allah ya muku albarka my kids. ya rankwafo itama ya mata kiss a goshi snn ya dago muka hada ido bazan iya juran kallonsa ba don haka na sauke idona kasa ina murmishi nima din kissing dina yayi yana cewa"ki kula da kanki da twins bari muje gida mu gaida su innah. Murmushi nayi nace"se kun dawo ku gaishesu da kyau. ya tashi hade da fadin to zasuji. Yana fita ya tarar nafisa tana jiransa a babban palo taci kwalliya kamar wacca zataje party. Daga nan suka tafi.a hanya sai tunani take akan wadan nan kudin nata har suka isa. Inna na harde a palo tana aikin kallon shirin dadin kowa na arewa24 kasancewar ba itace da girki ba yau.Ac na ratsata ta koina hmmm. Kusa da ita nafisa ta zauna tana cewa"goggo yau ke kadai kk hutawa kayanki . Ya salman ya zauna can nesa kadan. Inna ta kalli nafisa tace"daga ina kuke irin wnn kwalliyar. Nafisa tayi dariya tace"daga gida mana. Salman ya gaisheda innah cike da girmamawa snn ya tashi ya fita.anan inna ta kalli nafisa tace"Ya maganar tfyr naki kamaru? Nafisa ta dan bata fuska tace"ba na gaya miki yaki yarda ba kuma kema kinki kisa baki ai idan kk masa magana ze amince .... Inna tace"ke dai ki hkr mana nafisa sai in zanje muje tare kinsan salman da ra,ayin tsiya in ya kafe ba mai tankwarashi. Nafisa ta dan turo baki tace"ai shikenan? Inna tace"yawwa ko kefa .ni nama fi so se kin haihu sai kije da danki ko yarki a hannu su hamma zasu yi farin ciki sosai. Nafisa ta tabe baki tace"ai ni goggo banda komai. Inna tace"Allah zai kawo kullum sai na miki adduq nafisa.naso ace ke kk haifi yan biyun nan amma ba kome kema zaki samu naki. amma don Allah karki kuma yin irin abinda kikayi a baya. Tace"insha Allah goggo bazan kuma ba wlh tun lokacin nadama nake.domin koda naga momyn farida ta haifi twins se naji abin ya matukar bani sha,awa. Inna tayi murmushi tace"kar ki damu 'yar auta kema zaki samu mu dage da addua. Haka inna da nafisa suka dinga hirarsu har salman ya shigo suka tafi a hanya saida suka biya shopping mall nafisa tayita diban kaya son ranta.snn suka dawo gida . Mun fito palo muna zaune dawowar munir bai jima ba yayi wanka ya sauya shiga snn ya zo palon ya zauna kusa dani hade da kallon twins yana murmushi yace"twins fatan kun wuni lfy. Ya dago ya kalleni yace"mama daddy bai dawo bane? Nace"ya dawo har ma yace ka jirashi karka kuma fita.don ya kira ma baka daga ba. Da sauri ya ciro waya a aljihu yace"o my God na mance wayar na silent tun zanje masallaci. Nace"ai kai dama ka cika mantuwa da yawa. Ya kwantar da kansa kan kujera yace"mama wlh yunwa nikeji.kuma ni matsalata bana son girkin yan aikin nan. Nace"to za,ayi nafisa dai kasan yanxu itace da girki kullum kuma ita bata girki dama masu aiki ke komai . Tabe baki yayi ya lumshe ido snn yace"inaga kamin ki soma girki gidan hajiya Amina zan na zuwa inci abinci ko ince ta dinga turo min tunda ita da kanta take girki. Nace "tab aiki ya sameka..... Farida ce ta fito daga dakinta wacce tunda ta dawo school take ta bacci wai kanta na ciwo se yanxu ta fito ko kallonmu batayi ba ta wuce dining side. Na kalli munir nace"ga farida nan ka fada mata me zakaci se ta dafa maka. Sai lokacin ya dago ya kalli farida wacce tayi kici kicin da fuska jin zancan zata shiga kitchen dan bata son girki a rayuwarta. Tashi yayi ya isa wurinta yaja kujeran dining ya zauna . Sanin halinsa yasa ta fadin "ina wuni? Ya amsa da lfy Tace"me za,ayi serving naka? Ya girgiza kai yana kallon kulolin abincin snn yace"bazan ci ba. Sai lokacin ta dago ta kalleshi snn tace"o sorry na mance ashe baka son girkin masu aiki.to me zakaci knn? Ya dan daga kafada yace"nima ban sani ba.ke zaki nemo min abinda zan ci din in kingama cin abincin naki . Farida ta bata fuska tace"ya ka daure kaci wnn mana pls. Girgiza kai yayi yana tashi snn yace"in kin dafa min ki kawo min part dina ina jiranki. Ya wuce abinsa a ranta tace"za kaci girki kuwa wlh in dai nice. Tayi kwafa.a dai dai lokacinda ya salman suka dawo knn Nafisa na rike da ledoji tayi sallama. Na amsa snn ina musu sannu da dawowa. Nafisa ta zauna kusa dani tana murmushi ta dauki hanifa tana cewa momyn farida wani riguna na sayawa my baby (hanifa) masu kyau bari in gwada mata in gani . Murmushi nayi nace"to abin son kai ne knn babynki kawai kk ma sayayya ina na hanif dina? Dariya tayi tace"na saya mishi takalmi shima harda agogo. Nima dariyan nayi anan ta shiga gwada musu tanayi tana daukansu a hoto. Khalil yace"aunty nafisa ni ina nawa tsarabar to? Tace"karka damu dear naka special ne dan albarka . Nace"to ni kuma fa? Sai lokacin ta dago ta kalli ya salman da tunda suka shigo muka mishi sannu da dawowa ya zauna a kujera yana kallonmu bai ce komai ba. Murmushi tayi tace"naki special ne yana gun yaya. Nace"gaskia naki wayon ai shi bai shigo da komai ba gaki kece da kaya niki niki snn ki hanani duk kin dauka kin rabawa yaranki. Dariya tayi tace"karki damu momyn farida bari na baki turare body spray mai dadi.tsabar dadinsa yasa na siyeshi guda biyu ko yaya ma saida ya yaba kamshin. Ta bude jakarta ta dauko body spray tana murmushi ta bude ko kan na ankara tuni ta fesa min da sauri na kauda kai cikin rashin sa,a kuwa iska ya kwashi turaren zuwa hancina direct wani wawan shaka na masa wanda yasa a take numfashina ya dauke na wucin gadi.anan fa al,amari ya canza na dafe kirji numfashi na fita wani iri ......... Ya salman ne ya karaso gunmu da sauri shida khalil Farida ma ta taso dama tun dazu taketa hararar nafisa na lura haushin nafisa takeji sosai se kace itace nafisan kishiyarta nan ma ina taka mata birki. Sannu suka hau yi mun ya salman ba shiri ya jawo ni zuwa jikinshi ya kalli khalil yace"khalil je ka dauko inhaler dinta a drawer da sauri. Nafisa duk ta tsorata tana jeramin sannu yayinda tuni tayi jifa da turaren gefe. Farida ta sakar mata harara tace"kinsan mama ciwonta bai son a fesa mata turare direct amma kk zo kk dinga fesawa a hancinta wnn ai gangancine. Nafisa ta dago ta kalli farida hade harararta tace"wai ke me yake damunki ne farida kinga ni fa ba sa,arki....... Ya salman ya daga mata hannu da sauri yace"ki tashi kije ciki and kuma kar ki sake maimaita wnn kuskuren da kkyi yanxu. Tashi nafisa tayi jikinta a sanyaye ta wuce part dinta ko kayan da ta siya bata dauka ba. Nidai ina ta kaina don saida na dauki tsawon lokaci kamin numfashina ya dai daita har munir ma ya fito ya samemu haka suna zagaye dani sai da sukaga na koma normal snn hankalinsu ya kwanta. Snn ya salman ya tashi yace munir yazo suyi magana. A tare suka tafi .kallona na mayar kan farida nace"me yasa kika fadawa nafisa irin wnn maganar ? Tace"mama fa tasani sarai ciwonki zai iya tashi in ta fesa miki turaren nan Na harareta hade da fadin "ina ruwanki.farida nasha warning dinki akan nafisa amma ba kyaji to wlh ki kiyayi fushina kuma kije ki bata hkr yanxu. Tace"kiyi hkr mama zanje yanxu. Ta wuce ranta a bace.lokaccinda ta shiga dakin nafisa ta gama waya da nabila don haka ta kalli farida tace"me nene kuma. Cikin jin haushi farida tace"kiyi hkr da abinda na fada miki dazun. Murmushi nafisa tayi tace"babu komai farida ya wuce ya jikin momyn ku? Farida bata amsa ba ta fita kitchen ta wuce don ta girkawa munir abinda zai ce gashi magriba ya kawo kai duk ta gaji gashi ranta a bace . Nabila kuwa duk maganar da sukayi da nafisa suna gamawa ta kira adda A'i ta gaya mata komai tana"don haka kiyi saurin karbar wnn kudin a hannun nafisa in ba haka ba wlh zata kashe a banza da wofi.don har na roketa ta ban wani abu aciki taki. Adda A'i tace"waya gaya miki ita zatai amfani dashi?hmm ai dan iskan nan nasan zata bawa wadan nan kudaden ko shakka banayi.kedai ki yi shiru nasan me zanyi akai. Anan sukayi sallama adda A'i ta kira nafisa ta dauka ko gaisawa basuyi ba adda A'i ta fara kora mata bayani. Sakin baki nafisa tayi don bata taba tunanin nabila zata mata haka ba don haka ranta ya matukar baci tace"adda kudin nan nawa ne kuma ina bukatar abina don haka ni bazan bayarba. Adda A'i a fusace tace"kinsan Allah nafisa idan kk kuskura kika ba suraj kudin nan sai na matukar batamiki don haka ki turo kudaden nan maza na baki nan da kwana biyu.shashasha mara hankali kawai bazaki gane me nake fada miki ba se kinyi kuskuren raba aurenki da salman! Ta katse wayar rai bace a bangaren nafisa itama ranta a bacen tace"hmm wlh bazan tura miki ba se dai ki kari jarabarki mutum sai shegen son kudi duk abinda kika samu baki gode Allah ba. Mtswww taja tsaki yayinda ta kira nabila amma bata dauka ba cije lebe tayi tace"wlh adda nabila sai nayi maganinki tunda kin iya hada munafurci. Daga nan fitowa tayi ta sameni a dakina tana min sannu hade da bani hkr. Nace mata babu komai karta damu ya wuce . Adda A'i kuwa jin har sati daya shiru nafisa bata turo kudin ba kuma in ta kira ma bata daga wayar yasa ta ajiye komai ta taho kano inna sai mamakin zuwan nata takeyi tace"A'i lfy? Adda A'i tace wlh lfy lau goggo nazo na duba ku ne . Tsaraba sosai tayiwa innah don haka inna baki har kunne ta dinga sanya albarka. Sadiya kuwa jin zuwan adda A'i yasa gabadaya hankinta yana bata ba zuwan haka kawai bane.sai dai tayi tayi da ja,afar ya barta amma yaki yace idan ta kuskura ta fita to karta dawo mishi gida.don haka sadiya ta hkr amma hankalinta na gida. Adda A'i salman ta kira ta sanar dashi zuwanta wai yabar nafisa tazo tunda ita ya hanata zuwan masa gida. Yace"hmm ni ai bana gari adda ina lagos daga nan ma dubai zan tafi.amma lfy kk je kano a wnn lokacin ? Tace"lfy lau nazo ne bikin gidan hajia fati. Yace"ok to kawai zan ce taje ku hadu a gidan innan amma bayan nan banason kije koina da ita ba. Dan tabe baki adda A'i tayi tace"ni dama ina zanje da ita kawai tazo mu gaisa ne . Yace shikenan. Daga nan sukayi sallama. Don haka ya kira nafisa yace ta shirya driver ya kaita gidan innah. Daga nan bai kuma yi mata karin bayani ba don harkokinsa nada yawa. Nafisa tsaki tayi tace ni wlh goggon nan ta cika matsala ko uwar me zanje na matane oho. Sai da tay baccinta iya son ranta har azahar snn ta shirya hankalinta kwance ta fito dakina ta shigo ta sameni ina kokarin shiga wanka muka gaisa tace"bari naje gidansu inna. Nace"to lfy dai koh? Tabe baki tayi tace"wayasan ma goggo da fitina kawai yaya ya kirani wai in shirya driver ya kaini gida. Nace"to Allah sa lfy ki gaishesu . Ta dauki hanifa tace "zamuje da babyna ki bata nono don kar muje tayi kuka. Nayi murmushi nace"ai kuwa sunsha yanxu sun koshi kuje kawai ni wanka zan shiga. Don haka da fara,arta ta suka fita. Bayan driver ya saukesu suka shiga gida a palo ta tarad da inna ita kadai ta zauna suka gaisa innah ta karbi hanifa tana cewa " o nafisa ko arbain basuyi ba kk fita da ita.wato rumaisa dai bazata taba yin hankali ba.inke baki san komai ba ita ai ta sani yaushe zata bari ki fita da wnn jaririyar tun basuyi arba,in ba. Nafisa tace"kai goggo sauran fa sati daya ne suyi arbain din kuma meye a ciki dan na dauketa munzo nan tunda naga ai gidane. Inna tace" to kije ciki A'in na daki. Nafisa ta dan zaro ido tace"adda A'i kuma yaushe tazo? Inna tace au baki sani ba ai tun jiya ta zo . Nafisa ta tashi zuciyarta cike da fargaba ta shiga dakin ta sami adda A'i tana waya da mutanenta na kasuwa tana ganin shigowar nafisa ta watso mata harara da ya kara tsoratata.don haka ta nemi wuri ta zauna . Bayan adda A'i ta gama waya ta kalli nafisa tace"se yanxu kikaga daman zuwa? Nafisa ta dake tace"aini adda bansan kinzo ba sai dazun yaya ya min waya..... Adda A'i ta daga mata hannu tace ya isa haka ina kashe min waya kk in na kira a karshe ma kk sani a blacklist to gashi nazo yanxun kuma me zakiyi? Shiru nafisa tayi ta rasa me zatayi adda ai ta gyara zamanta mai kyau ta kalli nafisa tace"kinsan Allah idan baki bani kudin nan ba zanyi mugun saba maki.domin wlh bazanyi dawainiyar karatunki a banza ba.dubi yadda kk koma kk yi clean duk cikinmu ba wacce tayi jamia ma sai ke irin kudin da na kashe a kanki ko yarana ban kashe musu ba amma yanxu ni zaki juya baya don kinga yanxu komai dina yana kokarin watsewa... Nafisa tace"haba adda kuma shine da gori.amma ai kudinda nayita tura miki kike business dashi kina juyawa sun isheki don haka bance ki dawo min da ko sisi ba ki rikesu a madadin wanda kk kashe a baya kika yi dawainiyar tawa dashi nasan zasu isheki ai? Adda ai ta hasala sosai wata uwar harara ta dokawa nafisa tace"har wani kudin kirki kike tunanin ki banine to bari kiji harda kudadena na cika snn kika business dinnan yayi karfi haka.don haka ni yanxu kikawo wnn kudin kawai in yaso idan kika ban wnn din se ki kashe auran naki kije ki zauna da matsiyacin suraj din inga uwarda zai tsinana maki tunda bakida hankali wawiyace ke. Nafisa tace"hmm adda kudin can fa ki barma maganarsu don babu su a halinda ake ciki yanxu nayi bukatuna dasu. A fusace adda A,i ta dauke fuskar nafisa da mari zuciyarta kamar zai fashe tace"kin dai baiwa dan iskan can zakice to wlh bari kiji na baki nan da wata daya ki nemo kudin nan duk inda suka shiga ki bani don bazan sha wahalarki a banza ba.in ba haka ba wlh sai na fadawa baba duk abinda kike shirin yi kuma kinsan matakin da zasu dauka akanki in sunji baze miki dadi ba.shashasha kawai mara wayo.ana miki gata baki gani an gaya miki samun miji kamar salman a wnn zamanin yana da sauki ne? Nafisa tana dafe da kunci ta tashi da hawaye tace"shine xaki mareni akan dan kudinda kk kashe min ?to shikenan ince dai in na biyaki zaki kama gabanki ki rabu dani? Adda a'i tace sosai ma in dai kk biyani to shikenan ba ruwana dake in yaso ki kashe auren kije ki auri dan iskan naki kamar yadda nace miki a baya. Nafisa ta gyada kai ta fice zuciyarta na suya a palo ta sami inna karbar hanifa tayi inna na tambayarta lfy amma bata ce komai ba ta fice . Nima da ta dawo ban gane mata ba duk da na tambayeta tace min babu komi. Bayan sati da faruwan haka ya salman ya dawo daga dubai bazata sai ganinsa kawai nayi gashi nafisa bata nan tunda safe don haka na karbi dawainiyarsa. A dakinsa na sameshi ya na kokarin rufe jakarsa me cike da kudi kuma dollars ne zalla. Na kalleshi nace"yaya irin wnn kudi haka a gida? Yace"no ba ajiyesu zanyi anan ba dama gobe zan kai bank kudin wani kwangilane.... Ya karasa rufewa ya mika min jakar yace ungo adana min bari inyi wanka inzo inji lfyrki momyn twins. Na karba ina murmushi shikuma ya shige toilet yayinda nasa kudin a drawer na kulle na fita don shirya masa abinda zaici don yace min ya kwaso yunwa. Bayan ya fito palo nan yace na kawo twins nace duk sunyi bacci yaci abinci tukun ya huta kan nan sun tashi . Muna cikin hakan nafisa ta shigo gabadayq zuciyarta ta shiga fargaba wani karya zata mishi na fitarta. Ina ganinta na tashi hade da fadin alhamdulillah mai fili yaxo mai taburma se ya nade. Nayi mata sannu da dawowa daga nan na fita barsu na lura ransa ya baci da fitanta sosai .ko ya zasu kare oho. Aikuwa sunsha drama don har kyawawan mari ta samu guda hudu masu kyau yayinda ya Koreta daga part dinsa gabadaya. Ni ban me suke ciki ba kawai da daddare ya kirani wai inkawo masa twins dinsa.bace aina? "Dakina mana. Na kalli agogo snn nace"haba yaya me zai kawo ni wurinka yanxu ina nafisa taxo ta daukan maka su..... Ya katseni da fadin"nafisa bazata kwana anan yau ba don haka ki kawo min twins dina su tayani kwana ina jiranki yanzu. Ko kan nayi magana ya kashe wayarsa.don haka dole na tashi zuciyata cike da tunani kala kala na dauki yaran duk bacci suke na tafi na kai masa su tuni yayi shirin bacci yana rumgume da fillow Ya nuna min gefensa alamun na kwantar dasu. Ina kwantar dasu na juya zan tafi da sauri naji caraf ya riko hannuna a hankali yace "ina zakije? Nace"dakina mana? "saboda me ?ya jefo min tambayar yayinda yake kallona sosai. Nace"haba yaya kasan fa bana girki har yanxu.idan na kwana anan ya nafisa zataji?kuma kaga duk abinda ta fada tana da gaskiarta don haka ni bana son rashin hankali. Fincikoni yayi na fada kirjinsa yace "ni ina son tashin hankali. Ya fada yana kallona ido cikin ido da sauri na janye idona daga kallonsa ba shiri naji ya hade bakina da nashi wuri daya ya shiga sarrafani son ransa gabadaya ya rikice se sakin numfashi yake .ganin yana kokarin wuce gona da iri yasani fadin"wayyo yaya ka bari ko ka manta banda lfy. Dakatawa yayi da abinda yakeyi a hankali ya sakeni yana sauke numfashi idonsa a lumshe. Nikam da kyar na lallaba na fita na barshi da yaran na koma daki da yake suna shan madara na tanadi komai na ajiye musu na dawo nayi kwanciyata. Washe gari da asuba ya shigo dakina ya tasheni hade da fadin zan tafi masallaci kije ki kula da yaran karsu tashi suyi kuka. Daga nan ya fita.nima ba bata lokaci na tashi na tafi sashin nasa har lokacin bacci suke. Nima ba jimawa baccin ya kuma dibana koda ya shigo bai tasheni ba shima baccin ya koma. Sai karfe goma muka tashi saboda yunwa da kuma kukan su hanif don tuni suka rigamu tashi . Part dina na koma a sace kar nafisa ta ganni .larai tayiwa yara wanka nima nayi snn na basu nono duk bacci sukayi ni kuma nan na samu daman fara tawa kwalliyar. Ya salman ta kira wayata wai nazo na daukan masa ajiyarsa zai fita.yana fada ya katse kiran don kar na kawo excuse A gurgujuje na karasa abinda nakeyi na tafi sashin nasa ina duba wurin ajiyan kudin sukace daukemu inda kk aje. Da sauri na kalleshi nace"au ka canzawa jakar wurin zamane? Kai kawai ya girgiza min yana daura agogonsa. Nan da nan naji kaina ya sara . Wasa gaske muka nemi jakar kudi kaf dakin muka rasa tirkashi!!! Zamewa nayi na zauna kasa na dafe kai hawaye ya wanke min fuska nan da nan............ Fans kuyi hkr da rashin jina kwana biyu ban cika jin dadi bane🥰.need your prayers my sisters🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻 Hauly ce🥰🙏🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡100 *********Karasowa yayi gabana ya tsugunna ya zuba min ido fuskarsa cike da damuwa. Hannu ya mika ya dangwali hawayena dake sauka bisa kumatuna. Ajiyar zuciya yayi a sanyaye yace"Rumaisa me kike tunani?kina ganin zan zargeki ne akan batan wnn kudaden? sai lokacin na dago kaina na kalleshi nace"ba haka bane amma na shiga damuwa ta yaya za ayi jiya jiyan nan na ajiye kudin nan kuma ba wanda ya shiga dakin nan daga ni sai kai snn a rasa wnn jakar.bayan gidan nan........ Hannu ya daga min snn ya tashi tsaye nima mikewa nayi ina kallonshi hannunsa ya zuba cikin aljihu ya na tsaye shiru tsawon wasu lokuta snn ya gyada kai ya fice abinsa. Nikam hankali na ya tashi kwarai na dada birkita dakin ina neman jakar kudi amma ina bangani ba. Yinin ranar gabadaya mun yishi ba dadi a gidan dagani har yaran nan. Farida kasa hkr tayi tace"mama kinsan me kudin nan ko shakka banayi aunty nafisa ce ta dauka.... Harara na watso mata nace"rufe min baki kin ganine? Ba fa nason abinda kikeyi.ai jiya kwata kwata nafisa bata ma kwana a dakinsa ba . Munir yace"Mama amma maganar Aisha da kwai ksmshin gaskia domin fa kinsan gidan nan kaf kewaye take da securities kai bama gidan nan kadai ba anguwan gabadaya saboda barayi shakkan anguwan nan sukeji saboda sunsan gidan daddy na nan.don haka ba yanda za,ayi har a shigo a dauki kudin nan a fita dashi ba wanda ya sani kai impossilble wnn satan a cikin gidan nan ne kuma kudin nan yana nan cikin gidan. Farida ta gyada kai tace"oo hmm Ta matso kusa dani tace"mama wlh na gaya miki ko nafisace don nasan wlh ba don Allah ta auri dad ba dama tana son kudinsa ne kawai. Jikina ya mutu sosai kaina ya kulle gaskia banason in zargi nafisa don sanda aka kawo kudin nan bata nan kuma bata kwana a dakinsa ba bare tasan dasu. Farida tace"mama ki barni inje in sameta wlh wlh wlh sai ta fitar da kudin nan ko bata so don ita ta dauka ko shakka banayi. Kafin nayi magana munir yace"no bazakiyi haka ba Aisha ki barta a hankali ake bin komai. Farida ta dan bata fuska . Nikam tashi nayi don naji kaina na min ciwo na koma daki nayi kwanciyata don su hanif ma se baccinsu suke. ina tashi munir ya taso yazo kusa da farida ya zauna ya dan zuba mata ido snn yace"me nene na bacin rai kuma? Tace"inajin haushin yadda kuke min ne kai da mama.wlh da zaku ban dama abubuwa da yawa da basu faruba a gidan nan. Ba shiri munir ya dan saki kasaitaccen murmushi yana kallon yanda farida ke cika tana batsewa. yace "to shikenan na baki dama kije ki same ta ...... Ai bai rufe baki ba farida ta tashi da sauri zata wuce part din nafisa. munir yayi masa ya kamo hannunta ya jawo ta baya yayinda ya juyo da ita suna fuskantar juna yace"baki fada min me zaki gaya mata ba in kinje ? kai tsaye farida tace"cewa zanyi kudin daddy da ta dauka ta dawo dashi ko kuma jikinta yayi laushi. Dariya munir yayi sosai yayinda farida ke binsa da kallon haushi . Janta yayi suka zauna snn ya dan nitsu ya kalleta har lokacin hannunsa na cikin nata yace"my dear farida meyasa kika cika saurin fushi da yanke hukunci ba shawara ne? shiru farida tayi munir yaci gaba da fadin "ki bar wnn maganar kudin nan insha Allah ko sisi bazai yi ciwon kai ba kudin daddyne fa hmm. ya fada yana kashe mata ido daya snn ya danja hancinta wanda har zufa yakeyi tsabar masifa. Sun danyi shiru tsawon mintuna biyar snn ta zame hannunta daga cikin nashi ta kalleshi shima ita yake kallo tun dazun gabadaya ya kasa dauke idonsa ga barin kallonta. A hankali tace"lfy? kai ya gyada mata snn yace"ya maganar mu ..... Da sauri ta sunkuyar da kai ta rasa me zata ce masa ita gabadaya abubuwanda ta masa yasanya takejin kunyarsa da nauyinsa a yanxu.amma tabbas zuciyarta tana sonshi ta rasa dallilinda yasa tayi soyyayya da farouq domin gaskia munir yafishi komai ...... katse mata tunanin yayi lokacinda ya matso da fuskarsa dab da nata saukar numfashinsa taji akan fiskarta A hankali yace"Aisha ki daina boye boye ki fada min gaskia abinda ke ranki na baki nan da one week kije kiyi tunani . daga nan tashi yayi ya fita tabi bayansa da kallo har ya bace snn tayi murmushi tace"ya munir ina sonka kuma insha Allah kaine...... duk da ita kadai ne saita tsinci kanta da jin kunya don haka tashi tayi ta tafi dakinta. Haka Oga ya dawo gidan bai samu kowa ba part din nafisa ya wuce kai tsaye ya sameta a bedroom tana kwance hankalinta na kan latse latsen waya ganin ya salman ya sata tashi bakinta har rawa yake tace"yaya sannu da dawowa. Bai amsa kawai kai tsaye ya fara magana"Jiya na shigo da kudina gidan nan amma se na nemesu yau na rasa..... Zaro ido nafisa tayi tace"Subhanallah anya kuwa yaya ka duba da kyau? Ni kaga ma bansani ba don koda na dawo ma rufeni kayi da fada harda mari na kayi ka ce na tafi na bar maka part dinka..... Daga mata hannu yayi yace"enough bana son dogon surutu abinda nakeso dake kawai ki tattara kayanki ki bar gidan nan har sai na nemeki. Ta zaro ido hade da fadin what! Yaya me nayi? Kai tsaye yace"sau nawa nasha warning dinki akan in bana gari ki daina fita ?don haka ya isheni rainin hankalinki.karki yadda na dawo dakin nan na sameki. Yana fadin haka ya juya ya fita. Tabe baki nafisa tayi snn ta saki murmushi tace"gaba ta kaini gobarar titi a jos Allah sa ma ka bini da takardata. Ni kuma tunda naga dawowarsa ta window din dakina don haka na tafi dakinsa amma ban sameshi ba kuma alamu ya nuna baya toilet ma.don haka na zauna jiransa . Har na gaji zan tashi sai gashinan ya shigo dakin kallona yayi yace"ya akayi my dear sauke ajiyar zuciya nayi nace "sannu da dawowa yaya Da kai ya amsa na karasa gabansa nace"ya maganar kudin nan ne? Yace"no karki sa kanki a matsala kudina suna nan bazasu bata kuma zasu dawo insha Allah. Binsa nayi da kallo na rasa me zance to. Nafisa kuwa tuni driver ya sauketa gidansu inna kawai sai ganinta inna tayi da lodin kaya gaban inna yayi mummuna faduwa tace"lfy nafisa na ganki da jakar kaya...... Nafisa ta fashe da kuka tace "goggo yayana ne yace in bar masa gidansa. Tashin hankali innah ta dafe kirji tace"na shiga uku ni shatu to me kk masa ? Nafisa tace"bai gaya min ba nima. Inna ta dan runtse ido tace lallai salman baida mutunci zai zo ya sameni ne kuma wlh bai isa ba. nafisa kuwa kuka ta shiga yi sosai . inna kuwa nemanshi tayi a waya tace yazo . washe gari da yazo ta kama tambayarsa me ya hadashi da nafisa ya korota? yacewa inna ta tambayi nafisan ta fada da bakinta. A yayinda nafisa tace ita bata san me ta mashi ba Abu kamar wasa duk sun saka inna a damuwa salman yaki cewa komai har lokacin abu kusan sati uku knn. Farida da munir kuwa tuni suka dinke suka shiga gwadawa juna soyayya da kulawa ta musamman gabadaya mun gane hakan nida ya salman don haka ba karamin dadi mukaji ba addua da muka dade munayi ya karbu Allah mun gode maka .yanxu abinda ya rage sai shirye shiryen biki.masha Allah. Inna kuwa gabadaya abin duniya ya dameta zaman nafisa a gidan ba tare da wani dalili ba ya dameta do gashi tuni nafisa ta sake abinta sai harkokinta take normal salman kuma yaki cewa komai maganar da akeyi har yanxu bata san me ye takamaiman abinda ya hada salman da nafisa ba don kullum ta tambayeshi sai yace nafisa tayi bayani da kanta.nafisa kuma tace bata san me tayi masa ba.don haka sun matukar daurewa inna kai.har taje ta sanar da abba akan yayiwa salman magana .amma shiru ba wani yunkuri da abba yayi. Inna ta gaji gabadaya ta kira Adda A'i,sadiya,raihana,nabila,madiha,sa,adatu. Tace lallai suxo ga Nafisa a gida kuma bata san me ya hadasu da salman don taki fada shi kuma yace ita zata fada da bakinta. Ba shiri adda 'Ai ta taho kano a ranar washe gari sai ga madiha ma daga maiduguri haka ma nabila kuma daga yola sai sa,datu daga kaduna.sadiya da raihana kam tuni sun iso. Kasancewar adda A'i tun jiya tazo tare suka kwana da nafisa tana tambayarta me ya faru? Nafisa tace kawai don ta fita sun hadu da suraj da yazo ne ranar a hotel take tunanin kila wani munafukin ya gayawa salman din don bayama kasar a ranar ya dawo . Haushi ya cika adda A'i ba shiri tace"haba yaushe kk zama haka ? Da aurenki zaki fita kina kula wani katon ?ai kema kinsan dolene salman zai sani ko baya kasar domin Allah kadai yasan yawan securities da yake zagaye daku gaskia nafisa kinyi wauta babba. Nafisa tace"adda fa kawai tattaunawa mukayk sama sama dashi don ya biyo ne kawai zai wuce lagos a ranar muka gaisa. Adda A'i ta ce"hmm to gashi nan dai kin gani yanxu ni bansan ta wani hanya zan warware wnn matsalar ba ni shatu. Kwana adda A'i tayi tana sake saken yadda zata bulloma lamarin . Shine washegari da su ka hadu gabadaya Adda A'i ta kalli inna tace"duk ku kwantar da hankalinku musamman ma goggo don kinga fa kinada hawan jini.nafisa ta gaya min komai akan dalilinda yasa salman ya juya mata baya. Nan ta gaya musu komai sai dai ta boyemusu suraj saurayin nafisa ne duk da ma madiha da nabila kam sun sani har ma da sa,a . Inna ta kalli nafisa cike da takaici tace"ke kuwa me ya kaiki aikata wnn kuskure bayan kinsan halin salman sarai yanxu duk duniya ba mai fahimtar dashi ya gane gaskiar maganar ba abinda yake zargi bane . Gabadaya palon tsit sukayi kowa da abinda yake tunani a ransa sadiya kam sam hankalinta bai kama maganar adda A'i ba Don haka ta kalli nafisa tace"ke ki dai fadi gaskia ko saurayinki ne domin ke ma fa ba tayar baya bace..... Madiha ta katse sadiya da fadin"haba sadiya da auren nata zata kula saurayi ?ai ita nafisa ko da can da bata yi aure bama bata kula samari a dalilin hakan ne yasa ska hadata da yaya salman aure don haka me zaisa yanxu ta kula wani saurayi da auranta . Nabila ta karba "gaskia sadiya bai kamata maganar nan ta fito a bakinki ba. hmm kunsan sadiya ba hkr nan da nan ta harzuko tace"yo mata nawa suke bin maza da aurensu? Duniyar nan da muke ciki yanxu me ba,ayi a cikinta ku daina daure mata gindi wlh tunda kukaga ya salman ya juya mata baya kunsan dalilinsa babbane. Raihana ta gyada kai tace"gaskiane nan kuma.mu dai bi maganar a sannu zaifi ni a ganina . Sai lokacin sa,adatu tayi magana tace"nidai koma meye ne kuyi hkr kawai mu nemi ya salman mu bashi hkr itama kuma nafisan ta bashi hkr ta mishi alkawarin bazata sake ba. Adda A'i tace"madalla wnn shine mafita ko ya kika gani goggo ?don fa se kinsa baki kan salman ya sauraremu . Inna tace hakane karku damu na kirashi kuma yace yana nan karasowa. Nafisa ta bata rai tace"ni wlh ba wani hkr da zan bashi kawai tunda bai yarda dani ba ya sawwake mun..... Ko kan ta karasa tuni sa,adatu ta make bakin nata. Kuka nafisa ta saka yayinda ta kifa kanta jikin adda A'i Nabila da madiha suka watsowa sa,adatu harara yayinda adda A'i tace " duka ba shi zai gyara wnn lamarin ba sa,adatu . Sadiya tace "ai hakan shine maganinta tunda ita bata da kunya fitsararriyace... Fadin haka da sadiya tayi yasa gabadaya ta kara kular da su madiha anan suka shiga sa,insa . Inna kam dafe kai tayi ta rasa me zata ce . A haka salman ya iske su cikin takunsa na isa da nuna tsantsar jarumtaka fuskar nan a tamke kamar be taba sanin meye dariya ba.gabadaya basu isheshi da kallo ba inna kadai ya gaisar cikin ladabi.yayinda su madiha suka gaisheshi can kasan makoshinsa ya amsa adda A'i kam tabe baki tayi tana kallonsa . A dry dinsa yacewa inna lfy kika kirani a wnn lokacin. Inna ta gyara zama tace"akan dai maganarka da nafisa ne shiyasa kaga duk na tara yanuwanta ma domin suyi mata fada nasan tunda ka yanke irin wnn hukuncin to tayi maka laifi babba ne. Adda A'i ta gyada kai tace"hakane don Allah Salman kayi hkr kasan nafisa yarinya ce har yanxu .gaskia abinda tayi bata kyauta ba ta fada mana komai don haka kayi hkr...... Cije lebensa yayi yana kallon adda A'i snn yace"laifin me ta fada muku tayi min? Adda Ai tace"akan maganar fitarta ba ka gari ne bayan nan sai haduwarta da ..... Nan adda A'i ta shiga kame kame Wani irin murmushi yayi mai cikeda takaici ya kallesu daya bayan daya snn ya dagawa adda A'i hannu yace" kiyi shiru kawai na fuskance ki.sai dai ni ba wnn ne kadai laifinda ta aikata min ba.nagode Allah kasancewarku gabadaya anan domin bayan wnn ina tabbatar muku da itace ta daukan min kudadena da na ajiye a dakina masu yawan gaske don........ Gabadaya zuciyoyinsu ya tsinke musamman Nafisa wanda bata taba kawowa a ranta salman zaiyi wnn maganar. Fashewa tayi da kuka ta sake kifa kanta jikin adda A'i tace"ni ban daukan maka kudi ba .dama ashe ni kk zargi ban sani ba alhalin ni ban ma kwana a dakinka ba a ranar kuma duk gidan ka rasa wacca zaka zarga sai ni? Shi dai bai kuma cewa komai ba Inna kam salati ta kamayi ta kalli ya salman tana mai neman karin bayani. Anan ya fada mata komai har ya kara da fadin"a nata wautar ta dauka bazan ganeta ba ta yaya ma za,ayi nafisa ki dauki kudi irin wannan masu yawan gaske snn kiyi tunani kinsha..... Adda A'i tace"dakata salman wnn wace irin magana kkyi ne haka? Nafisance zata daukan maka kudi ?wlh karya ne kawai ka fito fili kace ka gaji da zama da ita amma ba ka kirkiro wata zancen wai ta daukan maka kudi ba.duk yawan mutane dake gidanka a rasa wanda zai satan ma kudi se nafisa? Shidai ido ya zuba ma adda A'i har lokacin bai kuma cewa komai ba. Sadiya kuwa dama irin wnn rana take jira don haka tacewa adda A'i "ki daina goya wa nafisa bayafa don kinsan in har bata aikata ba ba yanda za,ayi yaya ya mata karya... A fusace adda A'i ta dakawa sadiya tsawa"dan Allah can munafuka na lura da take takenki fa tun dazu wlh kisan me kk fada in ba haka ba..... Sadiya ta harzuko tace"in ba haka ba sai me? Sai me nace? Ke fa bari kiji nifa ba tsoranki nakeji ba.kuma yanxu lokacin tonon asirinku ne yayi dama kece kike kulla duk wani munafurci har auren nafisa da yaya ke kika dage sai anyi dan ki cimma wani burinki... Anan sadiya ta rufe ido ta karewa adda A'i tanadi tsaf! Ta kara da fadin "kudin nan kuma nasan ita dince ta dauka kuma dole ku dawo dashi .wlh adda A'i kinji kunya. Adda A'i kam tuni ido ya fara raina fata amma dake gogaggiyar yar duniyace kawai sai tasa kuka ta kalli innah tace "goggo kinajin abinda sadiya take gaya min koh? Inna kam jikinta ya mutu sosai a yanxu haka ma su nabila kamar ruwa ya cisu.nafisa kam sosai gabanta yake ta faduwa tun dazu musamman yadda taga salman ya yi shiru bai kuma cewa komai ba. Inna ta kalli nafisa tace "don Allah nafisa me cece gaskiar wnn maganar? Nafisa cikin muryar kuka tace"wlh goggo bani na dauka ba ina zan kai kudi masu yawa haka me zanyi dasu? Madiha tace "nima dai shi na gani . Nabila ta kalli ya salman tace"yaya a dai bincika dai tukunna ..... Adda A'i tace"wlh tun wuri yaje ya nemi wacca ta satar masa kudi.kuma daga yau salman kasa a ranka aurenka da nafisa ya kare .kuma sharrin da ka mata sai Allah ya saka mata. Ta karasa fada tana goge kwalla. Inna kam hankalinta a tashe ta kalli salman tace"Salman don Allah mecece shaidarka na tabbatarda nafisa ce ta daukan ma kudi? Tashi yayi ya fita ba tareda yace komai ba can ya dawo rike da laptop dinsa ya zauna yana bude laptop din hade da fadin "yanxun zan cire zuciyoyinku daga shakku abinda na fada zaku ganshi zahiri. Sadiya ta gyda kai tace"da kyau! Bai jima sosai yana latse latsen computern ba can ya turata gabansu kusada inna. Duk hankalinsu na kan computer can sai gashi ta fara nuna komai daga sanda ya fita zai tafi masallaci sallar asuba.ita kuma ta shiga dakin ta zauna bakin gado kusa da twins ta buga tagumi alamun tana jiransa can kuma kamar an minsineta sai ta tashi ta kama yan dube dube harda bude masa drawer.bincike ta shiga yi sosai har Allah ya bata ikon gano side din drwar da na ajiye kudin ganin jaka yasata ta dauki gashi da nauyi tana budewa ta zaro ido cikeda tsoro da alajabi nan ta shiga waige waige ganin ba wanda ya ganta yasa ta rufe jakar ta dauka tasa cikin hijabinta ta fita da sauri......... Ganin haka yasa nafisa ta fara mimmikewa nan ta zube musu a wurin ta shiga yin wasu abubuwa irin nasu na masu aljanu. Addai madiha nabila gabadaya jikinsu ta mutu ji sukayi kamar kasa ta tsage su shige Yayinda sadiya taketa harararsu tace"ba gashinan ba gaskia ta bayyana yanxu kuma me zakuce? Raihana da sa,adatu kam tuni suka kama nafisa suna tambayarta lfy ? Inna kuwa gabadaya duk A.C palon gumi takeyi sosai inna ta shiga salati tana dafe da kanta wanda yake matukar sarawa. Ya salman ya tashi kallonsu yayi gabadaya snn yace"idan kun gama shawarwarinku a dawo min kudina domin sisi idan yayi ciwon kai a ciki...... Girgiza kai yayi hade da kwafa ya fice abinsa. Tab koni ban taba sanin ya salman yasa cameras a part dinsa ba . _Muje_ _zuwa_ _fans_ Hauly ce🥰🙏🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡101 ***********Gabadaya jikinsu ya mutu sosai kunya ya kama adda A'i don bata taba tunanin asirinsu zai tonu nan kusa ba. Sadiya ta kalli nafisa tace"ki gama duk wani haukanki kuzo ki fitar ma ya salman kudinshi.macuta kawai. Ta kalli Inna tace"Inna yanxun ba kin gani ba? Tuni na rigada na gane komai ina ta kokarin fahimtar da ke amma kika ki to yanxu gashi nan kingani kuma kinji don haka yanxu sai kisan matakin da zaki dauka....... Raihana ta katseta da fadin "haba sadiya don Allah ki bari za,a fahimci juna a hankali.yanxun bakiga halunda nafisan ke ciki bane?kuma yanda kk daga murya kowa zai iyaji kuma abin kunyane a wurinmu don dukkanmu anan yan'uwane ba bare ko daya ..... Habawa ai raihana kamar sake tunxuro da sadiya tayi don sake daga murya tayi tace"wayan nan macutan sune yanuwan nawa?Allah ya kiyaye bari kuji na fada muku gabadaya yanxu ba wani sauran mutunci da ya rage tsakaninmu da ku domin mun gane ku din ba masoyanmu na gaskia bane don haka daga yanxu kowa ya kama gabansa.ku tattara yar uwarku ku fice mana daga gida kuma ku tabbatar kun maido ma yayana kudinshi ehe. Haka sadiya ta zage ta dinga zuba rashin mutunci.duk tsit sukayi suna jinta . Yayinda raihana da sa,adatu suke ta yiwa nafisa addua suna tofeta har ta nitsu bacci ya dauketa . Inna kam ba magana tunda salman ya fita take jin kanta kamar zai tsage don haka daga karshe tashi tayi ta koma daki. Da kyar raihana ta lallaba sadiya ta bar maganar.yau adda A'i taga ta kanta.madiha duk rashin kunyarta haka ta hkr suka zubawa sadiya ido. ****Lokacinda ya dawo gida ransa a bace matuka da abinda su nafisa sukayi masa.don haka direct dakinsa ya wuce bai nemeni ba zama yayi bakin gado yana juya wnn alamari a ransa. Ni kuma ina can na gama shirin tarbansa tsaf don nasan lokacin dawowarsa yayi haka ma su hanifa na shiryasu cikin kayansu mai kyaun gaske se kamshi muke tashi.ganin sun koma bacci yasa na kira aunty samira muka shiga hira anan tace min"abubuwanku sun gama haduwa fa ihsan zan turo miki kuma komai a rubuce.naki daban na farida daban.don ita akwai wasu takardu ma dana hada mata ki bata kuma ta karanta zai mata amfani sosai a zamantakewar aure don nasan ba komai zaki mata bayani ba. Nayi murmushi nace gaskia kam aunty .wani abun da nauyi fada wlh duk da ma farida ba kunya ne da ita ba har wasu tambayoyi take min masu nauyin gaske . Aunty samira tayi dariya tace hmm ke kuma kina kunyar 'yar fariko? Nace"aa wlh kawai dai wani abun se inga be kamata ta sani ba. Aunty samira tace"ke dai ihsan kinji dadinki wlh.to banda abinki me ya rage yarinya ta kusa aure ba gara tasan komai ba.kuma ai ko baki fada mata ba wasu zasu gaya mata don haka gara ki zage ki cire kunya ke da farida yanxu kawayene. dan dariya nayi nace"tou shikenan aunty zan daure. Itama dariyan tayi snn tace"Allah dai ya kaimu lokacin bikin rai da lfy.bari na barki naga magrib tayi. Daga nan mukayi sallama tashi nayi na fita palo zuciyata cike da dsmuwan rashin dawowar ya salman har yanzu Fitowata knn se gashi nan ya fito daga part dinshi sanye da jallabiya ash colour. Da sauri na karasa gunsa cike da mamaki nace"yaya dama ka dawone ban sani ba? Kamar bazai amsa ba har ya wuce snn yace"na dawo .bari naje masallaci kar na rasa jam,i. Nace"to a dawo lfy. Amin ya fada tuni ya wuce na bishi da kalllo.gaskia na lura yau ransa a bace yake sosai kawai dai baison nuna min ne. Bai sake shigowa gidan ba har sai bayan isha yanxun ma sashinshi ya wuce. Khalil ne ya shigo ya sameni yace min"mama daddy yace kije ya dawo. Nace"ok to.ina munir ne ? Yace "yana palo da sister farida. Nace"to kar ku jiramu kuje kuyi dinner dinku.muma muna zuwa kuma in ka fita kace larai tazo yanxu. Yace min to Ya fita ba dadewa larai ta shigo nace"larai kunci abinci? Tace,eh hajia munci. Nace"to ga nan su hanifa ki kula dasu da kyau ina zuwa yanxu. Tace"to hajia . Na tafi gaban mirror na dan gyara fuskata snn na fita. A bedroom dinsa na sameshi zaune gaban computer dinsa sallamata ta saka shi dagowa yana amsawa. Snn ya maida hankalinsa kan computer din. Bakin gado na zauna ina kallonsa. Kusan twenty minutes dakin shiru snn ya kashe system din ya tashi ya karaso bakin gadon yayinda ya cire eyeglass din idonsa ya ajiye kan drawer muryarsa a sanyaye yace"Rumaisa. Nima jikina a mace nace"na,am. Ya danja numfashi snn yace"duniya ta zama abin tsoro.domin cike take fal da makiya .wai ace ni su adda A'i zasu hada kai su cuceni ..... Bai karasa maganar ba saboda wani irin bacin rai da ya rufeshi. Zuba mishi ido kawai nayi don har yanzu ban fahimci inda ya dosa da maganarsa ba. A hankali ya riko hannayena duka biyu snn ya shiga gaya min komai tundaga farko har karshe abin mamaki duk wani plan din adda A'i tun kamin ya auri nafisa ya sani bayan ya aureta duk abinda suke kullawa ya sani .haka nan yasan duk wani alakar nafisa da suraj. Nidai tsoro da mamaki suka cika min zuciya na kasa cewa komai . A hankali yace"rumaisa yanda inna take sonsu kamar me musamman adda A'i inna ta sota fiye dani domin tasha musguna min akanta .inna ta ba adda ai dukkan wata kulawa da gata ta jata a jiki fiye dani amma kinga wai yau aka wayi gari ta hada kai da yanuwanta zasu cuceni..... Sai lokacin nace"kayi hkr yaya duk da nasan basu kyauta maka ba amma bana son ka dauki wnn maganar kasa a ranka bare ya dameka.kawai ka barsu da Allah shiyasan yadda zaiyi dasu.kuma ni bana son ka juya musu baya saboda wnn matsalar da kk samu yanxu.nafisa ma ka yafe mata kuma kaja mata kunne ta dawo kuci gaba da zamanku.na tabbata yanxu tunda suka gane kasan komai zasu nitsu. Girgiza kai yayi yana murmushi snn yace"shikenan. Nima murmushin nayi nace"yawwa yaya na gode.yanxu ka tashi muje muci abinci. Yace"ba abinci nake bukata ba baby. Nace"to me kk bukata? Ya zuba min ido cikin wani irin salon kallo da ya sanya ni jin tsigar jikina na tashi da sauri na tafi na fada kirjinsa maida hannu yayi ya rumgumeni sosai yayi wani irin ajiyar zuciya yace"baby wlh ina missing dinki sosai .nasan bazan dawo dai dai ba har sai na kasance dake my dear pls a taimaka min. Lumshe ido nayi nace"doctor yace sai na huta tsawon watanni shidda kamin nsn.... Cije lebensa yayi da karfi ya dada kamkameni yace"wlh bazan iya ba baby dole ne mu koma gun doctorn nan ya sake yin wani bayani. Ba shiri na saki murmushi snn na dago na kalleshi nace"to shikenan yanxun tashi muje kasan yaran nan idan basu ganmu a dining ba suma basa taba cin abinci. Ya dan dafe kai snn yace "to muje.don bazan iya barinsu da yunwa ba duk da ma banajin son cin komai. Tare muka tashi ina fadin hakan dai zaka daure komai zai wuce insha Allah. Yace "hakane my dear. ****Nafisa kuwa har dare ta tashi da matsanancin ciwon kai saida adda Ai ta bata paracetamol tasha da kyar ta dansha kunu.ta kwanta a lokacin sadiya da raihana sun koma gidajensu tuni. Adda A'i kuwa kasa bacci suka yi suna ta shawaran yadda zasu bullo ma wnn lamarin don su gyara kuskurensu. Sa,adatu tace"hmm yanxu baga irinta nan ba kunxo kunyi abinda ya dameku. Madiha ta harareta hade da fadin "ke dan Allah yi mana shiru da zancan banza. Snn ta kalli adda ai tace"wlh adda da nasan wnn abin kunya da nafisa tayi ne aka kiramu da banzo ba. Nabila ta ce "koni ma wlh Adda A'i ta karba tace"hmm ai ku bari kawai ni nan wlh da na sani da tuni na zare kaina na barta yar banza ta karata dasu. Hawayene ya zubowa nafisa a hankali tace"Adda duk kece sanadiyar sanya ni cikin wnn .... Adda A'i ta katseta ta hanyar zaro ido tac"nice nace kiyi sata!!! Nafisa ta tashi ta zauna tace "kwarai kuwa saboda kin hanani jin dadi da sakewa da walwala da farko kunyi sanadin aurena da ya salman alhalin kinsan ni suraj nakeso maganarmu har tayi karfi amma saboda son zuciya irin naki saida kikayi duk yadda zakiyi kika raba mu ta hanyar sanya tsanarsa a zuciyan iyayenmu .kikazo kika sa na auri ya salman saboda dukiyarsa kullum cikin sakani a matsala kike duk ..... Haushi ya cika adda A'i a fusace tace"bana son zancan banza.ai ba shi na tambayeki ba.kuma da kk wani cewa ni na saka kika auri salman gata na miki ko cutar ki nayi? Wawiyar banza kawai wlh idan salman ya sakeki ba karamin nadama zakiyi ba don bazaki taba samun kamarsa ba. Sa,adatu tace "hmm ba wnn ba adda yanxu ta fada mana wnn uban kudin meyesa ta dauka kuma ina ta kaisu? Duk tsit sukayi anan nafisa ta fashe da kuka sa,adatu ta jawota jikinta tana lallabata . Nan ta fada musu yadda sukayi da adda A'i akan maganar kudi duka.snn suraj ma da yazo kano suka hadu bukatar kudince ta kawoshi wai so yake ta kara mishi wasu kudaden domin ya fadada kasuwancinsa zuwa lokacinda zata kashe aurenta suzo suyi aure su shimfida rayuwarsu mai dadi. Koda ta dawo gida tunanin yadda zatayi ta samo kudade masu yawa takeyi domin dolene tasan yadda zatayi ta toshe bakin adda A'i wacce tace in ta kashe aurenta zata gayawa iyayensu komai kuma tasan in dai bata bata kudin ba zata iya aikata komai da ta fada.Snn kuma tana son suraj ma ya fadada kasuwancinsa domin suji dadin more rayuwarsu in sunyi aure don haka dolene sai ta nemo kudin nan ko ta wani hanya domin taga komai ya wuce ko zata huta itama.wnn dalilin ya sanya ta daukar kudi a dakin salman. Tana karasa gaya musu ta ci gaba da kuka tana fadin"duk kun sani a matsala gashi nazo nayi abinda ya dameni ..... Su adda A'i tuni suka hau kan ta da fada da zage zage wai ai tayi rashin hankali . Sa,adatu ne ta dinga lallabata tana bata hkr akan ta bar kuka kar zazzabi ya rufeta. Su adda A'i kuwa har lokacin zaginta suke wanda hakan daga baya ya tunxura nafisa sosai ta tashi ta bar musu dakin. Washe gari kasancewar lahadine Salman ya kira inna a waya yace gashinsn zuwa yanxu su fito mishi da kudinshi. Dama sadiya da raihana ma sunzo duk suna palo. Inna kuwa dama ko fita batayi ba tinda gari ya waye sai da salman ya kirata ne ta fito ta samesu dukansu a palo nafisa na kwance jikin sa,adatu saboda zazzabi da ta tashi dashi da kyar tasha tea sa,a ta bata magani . Sadiya kam jiran kiris take yau ma tayi rashin mutunci sai dai lura da hakan yasa su adda A'i ba wacca ta tanka mata. Breakfast ma da maman sakina ta turo musu ba wacce ta iya ci a cikinsu. Saida sadiya ce ta zo dama bata tsaya yin breakfast ba a gidanta tunda ta samu jafar ya barta dai ta kamo hanya tazo don haka tana shigowa taja warmers ta cika cikinta ta hada tea tana sha tana jifansu da harara. A haka inna ta fito ta samesu duk ta bisu da kallo. Nan suka gaisheta bata amsa ba kawai tace "Salman yace yana nan tafe ina fatan kun fito masa da kudin nasa? Gabadaya nafisa suke kallo lumshe idonta kawai tayi batace komai ba. Sadiya ta ajiye kofin tea tace"hmm ai dole ma kawai kudin nan ya fito. Inna bata kuma yin magana ba ta juya ta ciki abinta. Har saida ya salman ya shigo gabadaya saida kirjinsu ya shiga dukan uku uku nafisa kam kasa bude ido tayi don tana matukar jin kunyarsa da nauyinsa yayinda zuciyarta fal da nadama.domin a iya zaman da tayi dashi ya gwada mata soyyaya na ban mamaki kuma yasha ajiyeta yana mata nasiha akan duk abinda zatayi a rayuwa ta dinga sanya tsoran Allah a ranta ashe yana sane da abinda take masa sarai hmm. Ya zauna gabadaya suka gaisheshi yau har da su adda A'i don tasan bazai gaisheta ba lol. Ya kalli raihana yace" ke ina innah ? Ko kan raihana tayi magana sai ga inna ta fito tanacewa gani. Snn ta zauna. Kai tsaye yace ina fatan kun fito minda kudina? Tsit sukayi.da farko.nafisa ce tayi karfin halin mikewa ta shige dakinda ta sauka ba jimawa kuwa sai gata da jakar kudi su adda A'i har suka ji sanyi a ransu ysyinda ita kam nafisa kunya sosai takeji haka dai ta daure ta karaso gaban salman ta durkusa kanta a sunkuye tace"Yaya don Allah kayi hkr ka yafe min nima ba yin kaina bane sharrin shaidan ne da kuma son zuciya ta kaini ga aikata wnn babban kuskure a shirye nake dana karbi dukkan hukuncinda zaka min amma kamin nan ya zama dole na fada komai gameda aurenmu...... Nan ta bashi labarin komai daga farko har karshe duk da yasan wasu amma wasu kam baisani ba . Inna kam bata taba tunanin hakan daga garesu ba sosai mamaki da tsoro ya bayyana a fuskar innah. Adda A'i sosai ta shiga hada gumi gashi babu daman karyatawa. Yayinda nafisa ta fashe da kuka tace " yaya don Allah don son Annabi ka yafe min wlh nayi nadama.kuma zan koma gidanka inci gaba da zama a yanda kake sona bazan sake bin zugin kowa ba pls yaya ... Ajiyar zuciya yayi baice komai ba ya bude jakar kudi data ajiye a gabansa ya duba da kyau yaga ko sisi ba a taba.Allah ya toni asirinta tun kan tayi kasafinsu. Jinjina kai yayi ya maida jakar ya rufe snn ya kalleta har lokacin tana durkushe a gabanshi tana kuka . Kamar ansa shi dole yace"Nafisa na yafe miki dukkan laifin ki.tunda kudina suka dawo gareni ba tareda ko sisi yayi ciwon kai ba. Su adda A'i harda ajiyar zuciya tayi najin dadin yadda salman yace ya yafewa nafisa. Sadiya kam ta gama cika fam sai dai salman bai bata fuskar tankawa ba. Anan su Adda A'i madiha da nabila suma suka shiga rokonsa da alkawarin hakan bazai kuma faruwa ba. Mamakin rashin kunyarsu yake sosai amma baice komai ba. Sa,adatu da raihana sunji dadin yadda al,amarin ya warware ba tareda samun matsala.nan sukayiwa salman godiya. Inna dai tana zaune binsu take da kallo har lokacin bata tanka ba. Ya salman mikewa yayi ya zuba hannunsa cikin aljihu ya kalli nafisa snn ya zaro wata farar takarda ya mika mata. Hannunta na rawa ta karba fuskarta na bayyana alamun neman karin bayani. Murmushi yayi yace"Hmm wnn tukuicin dawo min da kudina da kikayi ne na baki.sauran bayani na ciki. Snn ya kalli Inna yace"Inna gasu nan duk hukuncinda kikaga ya dace da su ki yanke musu ni na gama nawa. Yana fadin haka yasa kai ya ficewarsa. Nafisa da ta gama karanta takarda ta fashe da kuka ta karasa gaban inna ta durkusa tana "Goggo yaya sakina yayi har saki uku . "Uku!!! Duk suka maimaita yayinda sadiya tace"Alhamdulillah.lol! Nafisa ta dada fashewa da kuka tace"wayyo na shiga uku na lalace ni nafisa me zance da su baba?Adda kun cuceni kun bata mun rayuwata..... Ta dada fashewa da kuka mai ban tausayi.sa,adatu da raihana ne suka kamata suna bata baki amma ina ta kasa sauraransu. Maganar inna ce ta sasu nitsuwa dukansu suka maida hankali kanta. Cewa tayi "Ban taba tunanin haka daga gareku ba musamman ma ke A'i.ba irin gatan da ban miki ba a rayuwa kai bama ke kadai ba gabadaya danginmu don sanin kanki ne nice na tsaya tsayin daka wurin ganin samun ci gaban danginmu gabadaya.a cikinkun nan wacece ban jata a jiki ba na nuna mata kauna kamar ni na haifeta? amma da yake dan Adam butulu ni sai gashi da abunda kuka saka min.to ku sani kanku kukayiwa bani ba.don haka ba tare da son jin dogon bayani ba ke A'i madiha da nabila ku tattara nafisa yanxun nan ku bar gidan nan kuma kar in sake ganinku na yanke duk wata alaka dake tsakanina da ku kuma yanxu zan kira in sanar da iyayenku dukkan halinda ake ciki don su sani . Tashin hankali tuni su adda A'i suka zube sunata rokon inna yayinda sa,adatu da raihana ma suke tayasu. Sadiya kam ko a jikinta sai ma dadi dataji sosai. Ba irin magiyar duniya da basuyi ba fir inna taki sauraronsu tace lallai lallai su tashi su fice mata daga gida. Don dole kowacce ta hada kayanta jiki babu kwari zasu tafi adda A'i ta kalli nafisa tace"se ki tashi mu tafi ai. Nafisa dake aikin kuka tun dazu ta harari adda A'i tace Allah ya sawwaka har abada bani baku wlh ni anan zan zauna bazan bikuba. Inna tace"aikuwa ko cibiyarki aka binne anan dole ki barshi ki tashi ki bisu nagodewa Allah da baki haihu da salman ba kuje can ku karata duk wanda tsautsayi ya dibeshi ya kwasheki. Anan nafisa ta tubure tace ko kasheta inna zatayi bazata bi su adda A'i ba. Anan sa,adatu tace shikenan in ta tashi tfy gidanta su tafi tare. Wata uban harara inna ta zubawa sa,adatu amma batace komai ba. Su adda A'i haka suka fice jiki babu kwari. Haka sa,adatu da raihana ma kamin azahar duk sun fice .nafisa ta hada kayanta tabi sa,adatu kaduna. Saura sadiya da inna suna zaune jugum jugum sallah kadai ke tashinsu. Can sadiya ta dago ta kalli inna tace"Inna ni a ganina duk wnn abubuwa da ya faru alhakin RUMAISA ne ya kamamu . Hawaye ya zubowa sadiya taci gaba da fadin"Inna nikam nayi nadamar abinda na aikata irin nadamar da ban taba yi ba a rayuwata .inna mun zalunci rumaisa bana wasa wlh innah idan har bamu nemi gafarar rumaisa da goggo Amina ba bazamu taba ganin dai dai a rayuwarmu ba. Sadiya ta fashe da kuka tace"Inna kullum na tuna abubuwanda mukayi tayiwa rumaisa sai bacci ya kaurace ma idona .tabbas duk wahalanda da nayita sha a rsyuwa alhakin rumaisa ne ya kamani don haka nikam nayi nadama kuma zan nemi gafararta daga ita har goggo Amina da yaya salman..... Ta karasa fada cikin matsanancin kuka sosai ta kifa kanta kan kujera. Inna kam ta kasa fadin komai saboda tsabar ciwon kai da yake damunta har idonta baya gani mai kyau lallabawa tayi ta koma daki ta kwanta tana dafe da kai . Sadiya kuwa data kari kukanta ta tashi ta fice. ****Ganinsa da nayi da jaka ba karamin dadi naji ba sai dai banga nafisa ba.bayan na bashi hkr akan ya yafe mata ta dawo har ya amsa min. Binsa nayi zuwa dakinsa na amshi jakar na bude na duba snn na mayar na rufe nace"Alhamdulillah bisa dukkan alamu ba,a taba ko sisi ba. Ya gyada kai hade da fadin hakane. Nace masha Allah amma ya baka dawo da nafisan ba. Murmushin takaici yayi yace"kiyi hkr rumaisa bazan iya ci gaba da zama da ita ba har karshen rayuwata don haka na sallameta ...... Zaro ido nayi ina shirin yin magana ya daga min hannu yace"bana bukatar jin komai daga gareki indai akan su nafisane. Jikina a mace na fita tamkar wacca kwai ya fashewa a ciki. Nan na kira sa,adatu don tace min tazo tana gidan inna akan case din nafisa. Tana daukar kirana tace muyi magana ta watsapp ne.anan na shiga watsapp dina tayi min bayanin komai har ta gaya min nafisa tace bazata bi su adda Ai ba inna kuma tace bazata zauna gunta ba.don haka nace sa adatu ta dauketa su koma kaduna don ni wlh harga Allah tausayin nafisa nakeji sosai a raina domin duk abinda tayi ba yin kanta bane zugine ga kuma yarinta. Sa'adatu kin amincewa tayi da farko da kyar na shawo kanta se take nuna min in ita ta amince hafiz fa ?ta yaya zata dauki nafisa ta kai masa gida ba tare da yasan komai ba.nan ma nace zan mishi bayani. Saida na kira ya hafiz na mishi bayani kuma na rokeshi da ya bar nafisa ta zauna gunsu.yace min ba komai.daga nan na fadawa sa'adatu.wnn shine dalilinda yasa sa,adatu ta tafi da nafisa kaduna. *****Inna fa kwana tayi juye juye ciwon kai kamar zai halakata bata taba tunanin za.a wayi gari tana raye ba. Aikuwa ko sallar asuba batayi ba haka ta lallaba ta fito da nufin zuwa sashin abba domin ta sanar dashi halinda take ciki. tana ta dafe dafen gini don ko idanunta ba sosai take iya budesu ba tsabar azaban ciwon kai. Bata karasa sashin abba ba jiri ya dinga kwasheta sai gata zube a kasa ta suma!!!!!! Fans ayi hkr da rashin post dina na kwana biyu rashin wutane.🙏🏻🙏🏻🥰🤗 Hauly ce🥰👍🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡102 *******Bayan ya dawo sallahr asuba ne ya samemu a kitchen da farida. Ta dan russuna tace"Ina kwana daddy? Yace"lfy mamana. Snn ya kalleni yace"yanzu Abba ya kirani yace min sun kai innah asibity jininta ya hau sosai. Subhanallah muka fada a tare da farida nace"wayyo Nasan yanxu akan matsalarsu nafisa ne .Allah dai ya bata lfy. yace"amin yanxu bari inje asibityn in kin gama breakfast sai kuzo daga baya da munir . Nace"to Allah ya sawwaka a gaisheta . ya amsa yayinda ya fita farida ma tace "a gaisheta dad nima zanzo. yace to. Yana fita munir da khalil suka shigo kitchen don haka muka shiga aikin tare sunata hirarsu ni dai ban samusu baki ba ina ta tunanin su Innah. karfe takwas muka fita har farida don tace bata da lectures se 10:00 khalil ne kadai ya tafi makaranta tuni. Mun tarar Inna tana bacci kuma an hana yawan zirga zirga kanta don bata son hayaniya. Yadda Sadiya tayita faramfaram dani abin ya ban mamaki sosai nidai ban wani sake ba gaskia don sam bana yarda da tuban inna da sadiya. tunda mukaje inna bacci take har sai bayan azahar ta farka . Ta danji saukin jikinta don babu ciwon kan sosai sai dai kawai jikinta ba karfi. Ya salman ne ya matso kusa da ita yayinda ya dagota yana"Sannu inna kin tashi? Kai ta daga masa a hankali yace"jikinki ba karfi ki kwanta kawai bari na kira doctor. Ya gyara mata kwanciya ya fita da sauri. Sai lokacin sadiya da raihana suka mata sannu. Nima na matso ciki dar dar nace"sannu innah ya jikin? Lumshe ido tayi sai kawai ga hawaye ya zubo a hankali tace"da sauki rumaisah. jikina ya mutu sosai don na kula da bakon yanayi a tattare da innah. Inna tayi sati a asibity kan aka sallameta a lokacin 'yan uwanta na kamaru sunxo harda mahaifinsu adda A'i duk da ma ya tsufa sai dai da ke jikinsa nada kyau yayi sa,a ya tsufa da lfynsa. Hakuri suka baiwa innah da ya salman akan abinda su adda A'i sukayi don su basu san ma abinda su madiha suka dinga shiryawa ba. Dole su Adda A'i suka zo aka sake sabon meeting sosai mahaifinsu ya nuna musu fushinsa don ransa ya baci sosai. Da kyar dai aka sasanta.suka ba innah da ya salman hkr nafisa kam ta rame sosai duk da kulawar da take samu a gidan su sa,a.mahaifinta yace ta shirya su koma kamaru can zai mata aure da duk wanda yaga dama.da kyar abbansu salman ya roki yayan innah ya bar nafisa anan ta zauna. Kwanansu uku suka koma aka bar nafisa ta koma da sa,a su madiiha ma suka koma ko wacce jikinta a mace duk sunyi nadaman faruwar wnn al,amari. Inna dai har lokacin bata tunanin zata sake sakin jiki da su don gabadaya sun fice mata a rai. Tunda aka sallami innah a asibity hankalinta ya kasa kwanciya duk irin makircinda ta shuka da shi yake damunta a yanxu domin ba karamin nadama tayi sai dai tana fargabar ta yanda zata fara yin wnn maganar. Ni dai yanxu hankalina ya dada kwanciya sosai su hanifa sun yi wayo watansu hudu don har sun fara zama . A lokacin aka bude asibityn da ya salman ya ginawa munir don tuni an gama shirya komai.an samu kayayyakin aiki masu kyau da nagarta don anjima ana tanadi da zurfafa bincike akan komai.hakama ma,aikata an samu kwararru sosai gaskia abin dai sai godiyar Allah rayuwa taci gaba sosai. Cikin Sa,a munir ya shiga gabatar da aikinsa a asibitynsa wanda yayi farin jini a kankanin lokaci tuni jama,a suka gane asibityn don haka ake ta zuwa kuma munir yanada taimako hadi da tausayi. Inna fa ganin tunanin abinda ta shuka bazai bar zuciyarta ya huta ba ta yanke shawaran fadan duk abinda tayi duk da batasan mi zai biyo baya ba.Hmmm Allah ya kyauta. Ranar wata friday ranar da bazan taba mantawa ba a cikin tarihin rayuwata. Abban Salman yakiramu da safe ta wayar ya salman wai muzo inna tana son ganinmu. Na kalli ya salman fuskata daukeda son karin bayani .yadan tabe baki yace"sai dai munje muji. jikina a mace nace"To Allah sa lfy yace "amin. A gurguje muka shirya muka tafi ni dashi kawai. Nayi mamakin ganin motar mama ma a harabar gidan da safen nan . ban gama tsinkewa ba saida muka isa palon daddy muka tarar da shi zaune da inna da mama kallon ya salman nayi kirjina ya shiga dukan uku uku yanayinsu kadai ya tabbatar mana ba lfy ba don innah kam daga gani kuka ma tasha sosai fuskar nan duk ya kumbura. Ya salman ya kasa yin shiru yace"Abba lfy kuwa na ganku a cikin wnn yanayin? Abba ya numfasa yace ku zauna innarku ce ta taramu anan bansan me take son gaya mana ba. Da kyar na isa gefen mama na zauna . shima ya zauna anan muka gaishesu gabadaya. Shiru palon yayi tsawon wasu lokuta Abba ya danyi gyaran murya ya kalli inna yace"to shatu gasunan na tara miki su. Jikin inna a mace ta goge hawayenda ya sauko mata ta shiga bayanin abubuwanda tayi ta shukawa a baya tun lokacin da mama take budurwa har zuwa kaina tiryan tiryan bata rage komai ba. Tashin hankali.Abba da ya salman mamaki da tsoron inna ne ya cika su don basu taba tunanin kiyayyarda take mana ta kai haka ba.har da asiri da sharri ta dinga binmu. Hmm nida mama ko kadan bamuyi mamaki ba munsan komai .sai dai kawai mamakin yadda inna ta zauna ta tonawa kanta asiri da kanta muke. Hamdala nayi a zuciyata ko ba komai Allah ya wankeni a gun ya salman duk bai taba muzguna min ko gaya min magana mara dadi a kan abinda ya faru dani a shekarun baya da suka shude ba. Sosai inna ta dinga kuka tana rokon mu ni da mama da mu yafe mata dukkan abinda tayita mana a baya. mama ta danyi ajiyar zuciya tace"babu komai shatu maganar nan ta wuce don dama munsan komai don haka dagani har rumaisa bakida matsala mun yafe miki duniya da lahira. A halin yanxu nima kuka nake na dago na kalli mama da kai ta min magana tashi nayi na isa gaban inna na durkusa gabanta na riko hannayenta duka biyu na kalleta yayinda nake girgiza mata kai nace"Inna don Allah ki daina kukan nan indai akan wnn maganar ne ki kwantar da hankalinki.na yafe miki duniya da lahira . Ubangijin Allah ya gafarta mana baki daya. Rumgumeni tayi gabadaya muka fashe da kuka mama ma saida ta share hawaye. Inna tace"nagode sosai Amina. Rumaisa Allah ya saka miki da alkhairi .ban taba tunanin abubuwanda na muku a rayuwa zaku yafe min cikin kankanin lokaci ba tabbas na cutar da rayuwarku na zalunceku musamman ma ke rumaisa ....... Na katseta da fadin innah don Allah ki bar wnn maganar ya wuce a gurinmu kuma mun yafe miki duniya da lahira don haka ki daina daga hankalinki . Sosai Inna ta dada rumgumeni tace"Allah sarki rumaisa Allah ya miki albarka na gode sosai kuma in Allah ya yarda daga yanxu bazan kuma muzguna miki ki yarda dani. Kai na daga mata ina murmushi hade da hawaye. Abba ya dan gyara zamansa gabadaya hankalinsa a tashe yace"a gaskia shatu ban taba tunanin kiyayyarda kikewa Amina da yarta ya kai haka ba.shatu kin cutar da rayuwar bayin Allahn nan kin zaluncesu duk akan.... Mama ne ta katse shi da fadin"don Allah yaya ka daina maido da hannun agogo baya komai ya wuce tunda ta riga tayi nadama kuma ta roki yafiyarmu dagani har rumaisa munce mun yafe mata don haka a bar wnn zancen gabadaya Allah Ya gafarta mana duka.kuma kaima yaya kayi hkr don Allah ka yafe mata. Abba ya girgiza kai snn yace"Hmm Allah ya kyauta.shatu Allah ya yafe miki. Inna tace "amin na gode muku gabadaya. A hankali ta dago ta kalli ya salman.wanda gabadaya ji yake kamar ya hadiye zuciya ya mutu don tsabar bakin ciki da takaicin abinda inna ta aikata.tuni idonsa ya kada yayi jazir. Inna tace"salman don....... Mikewa yayi fuu! Ya fice ya barmu a palon baki bude. Inna kam tuni tasaka sabon kuka yayinda abba yace"Wlh banga laifin salman ba ni kaina shatu kin ban tsoro kuma kin bani mamaki da ba don ke kk fada da kanki ba wani abun kam zan karyata amma ina rokon Allah ya yafe miki. Ni kam da sauri nabi bayan ya salman hankalina a tashe yanayinda ya fita komai ma na iya faruwa dashi gashi ba da driver muka zo ba. Ina zuwa harabar gidan tuni yaja motar ya fice dafe kaina nayi hade da fadin"wayyo Allah na na shiga uku ni rumaisah. Da sauri na koma ciki hankali tashe ban biyo ta kansu inna ba nace"Abba ya salman ya fita cikin fushi kuma da kanshi yake tuki abba ku taimaka min kar wani abu ya faru da yayana....... Na karasa fada cikin kuka gabadaya tashi sukayi anan inna kam ta sake sumewa! Gabadaya muka rikice abba ya kira driver akai inna asibity yayinda shi kuma da kanshi ya bi bayan ya salman duk da baisan ina zai tafi ba. Nikam hankalina a tashe sosai kuka nakeyi maman sakina tanata bani hkr.mama kam tuni tabi bayan abba a motarta. Ko alamun motar ya salman basu gani ba tsabar yanda ya ke sharara gudu hankalinsa baya kan tukin baima san ina zaije ba idonsa rufewa yayi tsabar bakin ciki baya ganin gabansa haka kawai yaketa kutsawa cikin motoci kowa sai bashi hanya yake yi hankalin jama,a ya tashi sosai a lokacinda wata babbar mota ta sako kai. Kowa dafe kai yayi ya runtse ido . Cikin ikon Ubangiji kamin babbar motar ya karasa tuni salman ya kauce duk da ba sanin me yakeyi ba haka motar sa ta dinga gangarawa gefen hanya har yaje ya samu ya dogara da wata katuwar bishiya inda ya buga kansa sosai daga nan numfashinsa ya dauke. Batun barnar da yayi kuwa akan hanya ba,a magana. Hankalin dukkan mutane dake wurin ya tashi matuka tuni aka kira asibity. Mutane sun taro a wajen sosai .a haka abba da mama suka isa gurin tunda suka hango motar salman sunsan me yafaru hankalin abba a tashe ya sauka daga motarsa mama kam bata iya saukowa ba. Har Ambulance yazo wurin ............. Hauly ce🥰👍🏻 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹 👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒 *Story* *and* *written* *By* *Maman* *khausar* ✍🏻 *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚 *DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰 *BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰 *INTELLIGENT* *WRITERS* *ASSO* *KUMA* *GA* *NAKU* *SHAFIN* 👇🏻👇🏻😉😄 Nagode da gudumawar da kuka dinga bani.Allah ya kara hada kanmu ya kara daukaka mana kungiyar mu ameen🙏🏻 ~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`` *PAGE* ➡103 *THE* 🔚 *********Gabadaya naji baxan iya hkr ba kawai nima na kalli maman sakina nace"mama don Allah ki barni in tafi. Mmn sakina tace"bazaiyiwu in barki ki tafi a cikin wnn halin ba rumaisa kiyi hkr kici gaba da addua in Allah ya yarda babu komai. Wayata na lalubo na shiga kiran abba amma no answer haka ma mama don haka hankalina ya tashi sosai. Tashi nayi nace"mama dan Allah ki barni bari naje ... Ta katseni da fadin rumaisa kinga ba mota ko daya a gidan nan sai dai kiyi hkr bari in tura mai gadi ya samo miki adaidaita. Ta dauki hijabinta ta fita ba jimawa ta dawo haka ta dinga kokarin kwantar min da hankali.amma ina ko jinta ma banayi. Can sai ga munir yazo mmn sakina na ganinshi tayi hamdala tace tunda ga munir mu tafi tare kawai. Ko gaisawa basuyi da mmn sakina ba yace mu tafi asibity dukanmu. kallonshi nake cikin yanayin tsoro don na lura jikinsa a mace amma sai ya kauda kai ya fice bai bari na tambayeshi. haka nan tunda muka shiga motar waya yakeyi yaki yarda mu tambayeshi komai har muka isa asibityn. Abba kadai muka samu da mama wacce take zaune cikin tagumi yayinda abba yake kai komo da likitoci da suke ta shiga da fita daga wani daki.a haka muka iskesu. Da sauri na isa gaban mama jikina ya rigada ya bani babu lfy don haka durkusawa nayi gabanta kuka na shiga yi . Da sauri ta rike hannuna tana fadin"rumaisa kiyi hkr ki bar kukan nan anan baida amfani salman addua yake bukata ba kukanki ba. Kallon mama nayi cikin yanayin tsoro da firgita nace"mama me ya samu yayanah?ina yake a wani hali yake? shiru tayi sosai na kara rikicewa nace "wayyo Allah na shiga uku ni rumaisa yayana zai tafi ya barni da yara......... Munir ne yayi karfin halin karasowa gabana ya dagani yana girgiza min kai yace"mama karki daga hankalinki domin ciwonki zai iya tashi.daddy yana raye kuma ba wani abu bane sakamakon accident da yayi ne ya bugu akai sosai wanda har ya shiga halin coma amma insha Allah nan da wasu kwanaki zai tashi bayan wnn babu wani rauni a jikinsa . Maganar munir gabadaya ya kara tayar min da hankali na ce don Allah a barni inje in ganshi amma ina ba dama har yanxu likitoci na kansa. Hankalin abba ya tashi sosai domin abun ya hadun masa ga inna can itama tunda ta suma aka kawota asibity likitoci na kanta don jikinta yayi wani irin zafi ne na tashin hankali sai nishin azaba take tayi ita kanta bata san a wani hali take ba tsabar tsanani zazzabi da take ciki ga jininta da yayi mugun hawa.likitocin kansu sun fara cire sammanin tashin innah kawai suna dai iya kokarinsu. Nima a karshe saida aka bani gado dole tashin hankali da kuka ya haifar min da ciwon kai mai tsanani sai da aka min alluran bacci. Farida da khalil kuka suka dinga yi saida suka ba kowa tausayi a asibityn.su hanifa kuwa mama ne ta karbesu aka dinga basu madara sunyi kukan sun gaji sun bari da suka sha madara aka musu wanka se bacci.doctors sun hana a kawosu kusa dani. Abu kamar wasa sai da nayi kwana uku a gadon asibity snn na dan samu sauki. Inna kam har lokacin tana jin jiki.ya salman kuwa ba,a maganarsa don baya ko motsi kwance tamkar gawa bai ma san a wace duniya yake ba.abin mamaki kuwa babu ko kwarzane a jikinsa ta ciki yaji ciwo domin ya buga kansa sosai. Ba kowa ke shiga inda yake ba don baya bukatar kowa sai dai ma,aikata dake kula da na,urorin da ke jikinsa wanda yake taimaka masa. nayi kuka har na gaji na na baiwa kaina hkr na rumgumi kaddara naci gaba da yiwa salman adduan samun lfy. Gaskia a kwanakin asibityn ya cika da sojoji ga manya manyan yan siyasa da yan kasuwa anyi ta zuwa dubashi . Inna kam gabadaya lamarinta itama sai addua kullum maganarta bai wuce akaita taga halinda salman ke ciki ba duk da an gaya mata bai mutu amma bata yarda ba. Kullum kuka takeyi da nadamar abubuwanda ta aikata gashi sanadin haka ta jefa rayuwar danta cikin wani mugun yanayi da babu wanda yasan zai rayu ko zai mutu se Allah. Su adda A,i ma sunzo kuma duk hankalinsu ya tashi haka ma nafisa tayita kuka ranar da ta fara zuwa. Wasa gaske fa saida muka cinye wata daya amma shiru ya salman ba labarin tashinsa. Inna kam don dole ta hkr ta rumgumi kaddara itama dan ta dan sami sauki amma ta rame sosai. Haka asibity ya zame mana gida ni da yarana . Addua kuwa ana tayi ba kakkautawa harda masallatai don ya salman yana da alkhairi sosai. Cikin hikimar ubangiji bamu kai wata biyu ba ya fara motsawa.fadan murna da mukayi ba,a magana. A lokacinda muka yi wata biyu tuni sauki se ya samu sai dan abinda ba,a rasawa . Nikam ina kusa dashi kullum sallah kadai ke tashina don ko gida bana zuwa tunda abin nan ya faru duk na rame. Rannan zuba min ido yayi sosai a hankali ya kai hannunsa yana shafan kaina ya furta "rumaisah. Na dago da sauri dama kaina na kifa kan gadon nayi zurfi cikin tunanin cike da mamaki na kalleshi. Nace"yaya kai ka kira sunana? Kai ya daga min ai hade da fadin"nine. Ba shiri na rumgumeshi cike da farin cikin ci gaba da aka samu yau ma kuka na shiga yi yayinda ya shiga bubbuga bayana alamun rarrashin. Aikuwa da sauri na fita na kira doctor a lokacin su abba sun tafi bai jima ba su sadiya kuma suna gun innah. Kowa yayi farin cikin samun saukin ya salman.don yanxu Alhamdulillah har ya fara cin abinci kadan kadan sai dai sam baison hayaniya . Inna kam tazo tayita rokon gafarasa tana ta kuka amma ko kallo bai isheta ba domin yaki ce mata komai haka ma sadiya dama ba wani shiri suke sosai ba. Watammu uku aka sallamemu muka dawo gida sosai ya samu sauki har yana fita masallaci da kansa. Amma har lokacin inna da sadiya basu isheshi kallo ba .Abinda ya daga min hankali knn don kullum sai sunxo inna tayita kuka tana rokonsa. Da zaran na masa maganar sai inga bacin rai karara a fuskarsa don bayace dani komai. Don haka na yanke shawarar kiran momy zuwaira da kawu kassim suxo su masa magana harda daddyna ma. Don sam yaki sauraran mama da ya salim dani wnn karon kam.abba kuma yaki cewa komai domin shima abinda inna tayi ba karamin bata ransa yayi ba. Saida su daddy suka zo har gida sukayita masa nasiha hade da tunatar dashi darajar mahaifiya snn Allah da kansa ana masa laifi a rokeshi ya yafe bare mu 'yan Adam. Kalamansu ya sassauto dashi har yayi wa inna magana kuma ya yafe mata hade da bata hkr.hakama sadiya yace ya yafe mata. Inna ta jima bataji farin ciki irin ranar ba haka ta dinga saka mishi albarka. Sadiya ma ji tayi tamkar ta sauke wani kaya mai nauyi a kanta don nima tuni ta rokeni da na yafe mata na ce mata komai ya wuce. Allah sarki inna da sadiya sun rame sosai don ni tausayi suka dinga bani . ( _Hmm_ _Allah_ _ya_ _bamu_ _ikon_ _fin_ _karfin_ _zukatanmu_ )🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻 ***Na gama duk wani shirina na bacci na fito daga dakina na kulle dakin farida na leka na sameta ciikin bargo sai sheka bacci take hankali kwance ko wutan dakin bata kashe ba ga A.C data kure dakin yayi sanyi tamkar kankara. Girgiza kai nayi na karasa shiga dakin na rage A.c snn na karasa bakin gadon na tasheta.da kyar ta bude ido hade da fadin"na,am mama Nace"ki tashi kiyi addua nasan bakiyi ba haka kk zube kika kama bacci. Tashi tayi ta kalleni tace"mama lfy baki yi bacci ba har yanxu. Murmushi nayi nace"yanxu ne dare ya fara yi ai hajia inna ke dai dan kinyi bacci da wurine kinga agogo yanxu ne goma saura minti shidda. Ajiyar zuciya tayi snn tayi addua ta kwanta hade da fadin "mama ina missing din su hanifa meyasa bazakice hajiya Amina ta dawo dasu ba? Murmushi nayi don nima kaina ina kewar twins dina sosai tunda muke asibity mama ta daukesu suna gurinta yanxu watanninsu takwas har sun fara takawa ko ina cikin ikon Allah gashi basuda laulayi kuma komai suna ci don haka mama tace in barsu kawai inci gaba da kula da ya salman. Farida tace"mama gobe zanje in daukosu. Nace"ai mama bazata yarda ba sai dai kije ki gansu ki dawo. Tace"to inaga zanyi oneweek acan. Na girgiza kai nace "bazaiyiwu ba domin yanxu dama nake shirin gayawa daddynku tunda kun samu hutu yola zaki tafi aunty samira zata miki wasu shirye shiryen don kinga daddynku yace baison bikinku ya wuce karshen wnn wata kinga knn yanzu sati uku ya rage da kwana biyu bamuda isasshen lokaci sosai.gara kije yolan ki karasa sauran shirye shiryenki acan. Sunkuyarda kai tayi tana murmushi tace "mama why not kice daddy a bari sai next month don gaskia nanda 3weeks ya min kadan. Nace"nima kaina zanso ya bari sai next month din saboda shirye shiryena nima amma kinsan daddynku sai a hankali.sai dai zan gwada rokon ya salim. Tace"yawwa mama in kin gayawa dad kam zai yarda kuma zai shawo kan daddynmu. Na ce"to shikenan yanxu ki tashi ki rufe kofanki ki kashe wuta kiyi addua ki kwanta se da safe. Tace "Allah ya tashemu lfy. Nace amin snn na fita. Dakin khalil na tafi je shima na samu yayi baccinsa hankali kwance .daga nan na wuce sashin oga. Ina tura kofa sai duhu ya min maraba cike da mamakin abinda yasa ya kashe wutar dakin nake na karasa shiga ina kunna wuta snn na rufe kofan. Can na hangeshi kan gado yana kwance a rigingine hannunsa duka biyu ya rumgume kirjinsa yayinda idonsa ke kallon saman daki alamun yayi zurfi cikin tunani don baima san na shigo ba. Da sauri na karasa gadon na zauna ina fadin"yaya lfy bakayi bacci ba har yanzu kasha magani kuwa? Tashi yayi a hankali ya zauna snn ya kalleni yace"nasha tun dazu. Ajiyar zuciya nayi na matsa kusa dashi sosai na dora kaina kan kirjinsa ina lumshe ido nace "yaya har yanxu kamar baka saki ranka ba akan abinda ya faru.domin kana takurawa zuciyarka da tunani kuma doctors sun hana ka. Shafa kaina ya shiga yi a hankali yace"baby ya zanyi ne ? Tunanin abubuwanda su inna suka muku yaki barin zuciyata nakan rasa dalilinda yasa innata miki wnn abun.Rumaisah tausayinki ya hana ma zuciyata sukuni abinda ya faru dake a shekarun baya su ke dawo min ko wani lokaci..... Gabana ne ya fadi jin dumin hawaye ya sauka a fuskata ba shiri na daga kai na kalleshi da sauri. Dan zaro ido nayi hade da dafe kirji nace"what! Hawaye ? Yaya hawaye a idonka? Kawai nasa mishi kuka na kifa kaina a kirjinsa rumgumeni yayi yace"baza ki gane yadda nakeji a zuciyata bane rumaisah Inna bata kyauta ba kuma gaskia ta zalun....... Hannu nasa a bakinsa ina girgiza masa kai nace "ka daina maida hannun agogo baya yaya komai ya wuce a gurina tuntuni.dama haka Allah ya kaddara hakan zata faru gareni ban isa in tsallake kaddarata ba.don haka nidai ka bar tuna abinda ya faru a baya ka share komai muci gaba da rayuwarmu cikin farin ciki. Nasa hannu na ina goge masa hawaye hade da fadin"kasan me? Zuba min jajayen idanunsa yayi hade da girgiza min kai . Na danyi shiru snn nace"da ba don abinda ya faru dani a baya ba da yanxu ba kaine mijina ba.ko ka manta yarima Abdallah ya fasa aurenane saboda abubuwanda yaji akaina lokacinda nike jami,a ? Da ba don faruwar hakan ba da aurenmu baiyiwu ba yaya.amma kaga ikon Allah yana cewa ya fasa aurena a daren washe garin aka daura aurena da kai .... Na lumshe ido ina murmushi hade da hawaye ajiyar zuciya yayi yayinda ya shiga share min hawaye yace"shikenan maganar ya wuce kinsan a rayuwa bana son duk abinda zaisa inganki cikin tashin hankali. Nace"nima haka yayanah bana son ganinka cikin damuwa ko kadan. Dada rumgumeni yayi yace "Allah ya miki albarka my dear ina alfaharin kasancewarki mata a gareni.duk duniya babu wanda ya kai salman dace da mata ta gari mai hkr da sanin ya kamata. Dan dariya nayi nace "Yaya karkasa kaina ya fashe don Allah.yanxu dai mu kwanta bari in maka addua kayi bacci kasan doctor yace ka na samun isashen bacci domin kwakwalwarka ta huta sosai. Murmushi yayi yace"yau ba bacci nake bukata ba.matata nake bukata don gaskia yau kam hkr na ya gaza . Ya karasa fada yana kashe min ido daya kunya ne ya dan kamani nace"kai yaya ka bari dan Allah sai ka kara samun lfy.... Yace"what? Ainin na gama samun lfy insha Allah.kwanan nan zan samowa su hanif kani ko kanwa tunda sun girma yanxu. Ina shirin yin magana kawai ya hade bakinmu wuri daya . To fa daga nan labari ya sauya lumshe ido nayi ina karbar sakonninsa ba shiri na shiga maida martani. Aikuwa ya tabbatar min da ya samu lfy don da kyar na kwaci kaina kunsan yaya dama ba sauki a wnn harkar . Da kyar nayi sallar asuba don saida na gasa jikina sosai. Yana dawowa masallaci muka sake komawa ..... Mune bamu samu fitowa ba a ranar har sha daya shima yunwane ya tashemu kuma gashi lokacin sha maganinsa har ya wuce.don haka dole muka tashi mu ka sake wanka na taimaka masa ya kintsa cikin kananan kaya shirt and trouser da suka matukar karbarsa ya koma kamar saurayi dan shekara 30 Ina fesa masa turare nace"yaya gaskia kamin wayo da yawa dubi yadda kk kullum kamar wani saurayi in ka jera da munir kamar friends fa. Dariya ya danyi yayinda yaja hancina snn ya sunkuyo ya manna min kiss a baki yace"kema fa hakan ne baby har yanxu baki tsufa ba keda farida kamar kawaye.babu wanda zai yarda ke da darling(ruma) da fa,iza da sakina da raihana sa,o,ine don duk kinga sun koma iyaye amma ke har yanxu kina a babynki. Ya lumshe ido hade da fadin hmm gabadaya jinki nake kamar wata budurwa duk kin rikitani jiya baby domin kin sake zama fresh kuma gabadaya kin tuna min da first night dinmu jiya.don Allah meye sirrin ne? Rufe fuskata nayi da tafin hannuna ina dariya na wuce gaba bina yayi a baya har muka fita palo yace"muje na tayaki shiryawa kema Riko hannunsa nayi na zaunar dashi nace "na hutar da kai bari na kira munir yazo ya kara duba min kai kaga ma bakasha maganinka ba bamuyi breakfast ba.... Shigowar munir da sallanarsa ne ya katseni. Na dan saki hannun ya salman snn na kalli munir ina amsa sallamarsa nace"kaga dan halak dama yanxu nake shirin in kiraka baka fita ba knn? Yace"yanxu dawowata mama nazo in duba daddyne . Nace"to bari yayi break fast. Bayan mun gama breakfast na barshi da munir na tafi dakina nima don in shirya. Sosai na dage naci kwalliya nasaka riga da siket na lace blue mai adon orange nayi kyau sosai domin kuwa na fito tamkar wata budurwa .gaskia ya salman ya fada domin har yanxu jikina babu alamun tsufa don da can ni ba mai kiba bane sabanin su sakina duk sun cika palo sun zama manyan hajiyoyi har gara fa,iza yanayinmu daya.sadiya kam ta zama kamar wata goggonmu lol! Farida ta shigo dakin da sallama na juyo hade da amsawa ta gaisheni snn tace"mama daddy wai kije in kin gama shiri. Nace"to gani nan zuwa. Murmushi tayi tace"mama gaskia kinyi kyau sosai don Allah muyi selfie. Nace"keni don Allah ki rabu dani da wani selfie dinki. Murmushi tayi ta maso kusa dani ta rumgumeni ta saita camera ta daukemu ta sake karawa zata kara na tureta nace "ke ya isa haka don Allah. Na fita ta bini a baya tana dariya tace "hmm ai bari naje yola zamusha selfie da sweetyna . Nace"waye kenan? Tace"Alhaji ibrahim lamido .... Da sauri na juyo nace"kinci gidanku.ga tsohonki a palo kije kuyita selfie amma ba nawa tsohon ba. Dariya taskeyi har muka isa palon ya salman A tare suka kallemu da munir da alamu suna tattauna wata muhimmiyar magana muka shigo. Ya salman ya kallemu yace"ya dai na ganku haka? Farida ta zauna kusa dashi tana dariya tace"daddy munsha selfie ne da mamana.saura kai don kaima daddy ka koma saurayi yau kuma. Murmushi yayi yace"Hmm ke dai farida ba,a raba ki da shiririta. Na zauna ina fadin "kinga ma yanxu lokacin tashin su khalil a islamiyya yayi kije ki duba driver ko ya tafi. Ta tashi da sauri ta fita. Munir da hankalinsa ke kan latsar waya tunda muka shigo sai yanxu ya dago ya kalleni yace"mama jikin daddy Alhamdulillah sosai ko yau daddy ya ga dama zai koma aiki.pls hankalinki ya kwanta don gaskia kin rame ga rashin cin abinci kuma. Nace"Hmm munir kai dai bari.Allah dai ya karawa daddyn lfy insha Allah yanzun hankalina ya kwanta sosai ma.Allah ya maka albarka. Yace ameen mama nagode. Ya salman ya shafa kansa yace"ina alfahari da kai good boy. Dariya mukayi gabadaya daga nan tashi yayi ya sallamemu cike da girmamawa ya fita don yace zai koma asibity ne anata jiransa. Yana fita ya salman ya dawo kusa dani ya zuba min ido hade da fadin"baby kinganki kuwa ? Irin wnn kyau haka. Ya kashe min ido daya hade da fadin "gaskia ban gaji ba mu koma ciki . Dan zaro ido nayi nace"Wayyo yaya dama so nake mu je mu gaida innah fa. Fuskarshi ce ta dan sauya kadan amma baiyi magana ba. Don haka na kauda zancen da fadin"yawwa yaya idan ba matsala ina son in rokeka alfarma guda biyu. Yace"uhm ina jinki. Nace"ina son dama farida taje yola ne tayi 2weeks akwai shirye shiryen da zasuyi da aunty samira.snn abu na biyu kuma don Allah yaya idan ba matsala a daga bikin nan zuwa next month don kaga gabadaya dis month muna da bukukuwa Abdul din sadiya da amira snn ga nabilan raihana.ana gama nasu da 2weeks sai na gidan sakina kuma wanda gabadaya inaga bazaiyiwu a hada da nasu farida anan ba zirga zirgan zai mana yawa.so pls yaya a duba dai a daga zuwa next month din don Allah. Shiru yayi kamar bazaiyi magana ba snn yace"sai na tuntubi salim tukun na. Murmushi nayi don nasan ya salim baida matsala . Daga nan na sake masa maganar zuwa gaida su innah haka dai na lallabashi driver ya kaimu.Inna taji dadin ganinmu sosai sai nan nan take dani ta kawo mana lemo kala kala ta sake kawo mana fruits . Ta kalleni cike da fara,a tace "rumaisa ko akwai abinda kike sha,awa ne insa a dafa muku. Fuska sake nace"babu komai inna wnn ma yayi. Na fada yayinda na dauki apple na fara ci. Muka gaisa ta tambayi ya salman ya jiki ya amsa mata da Alhamdulillah. Hmm zakusha mamakin yadda mukayita shan hira da inna kamar ba ita ba har tana bani labarin rashin lfyr mijin adda A'i yayi tsanani sosai yanxu har sun fita kasar waje jinya. Cewa nayi Allah ya bashi lfy. Tace"ameen ita wancan shashashar ince dai ta nitsu a gidan yayan naki ?ko dai tanayi musu rashin kunya da fitsara? Nan na fahimci nafisa take nufi nace"aa wlh lfy lau suke zaune inna kinsan fa ita nafisa bata da matsala gaskia yanxu haka ya hafiz yace mun ta samu bazawari wani abokinshi doctor ne babba yana Abuja ya dage yana sonta zai aureta. Inna ta tabe baki tace hmm ni tsorona kar taje taja mana abun kunya don wlh tsoron wayan nan yara nike ji. Murmushi nayi nace"babu komai innah ki musu fatan alkhairi. Tace "to hakane Allah sanya alkhairi. Nace amin daga nan muka dauki hirar bikin farida.ya salman dai bai sa mana baki ba dama shi bai cika sa baki ba a maganar da ba tashi ba.sai dai ya fara jin sassauci a zuciyarsa ganin yadda inna ta fara sona gashi a cikin kankanin lokaci har na saki jiki da ita muna hira sosai.fatansa Allah sa hakan ya dore.amin. Tuni na tura farida yola nan fa muka shiga hidimar bikin gidan sadiya ga na raihana.wnn karon fa,iza ma tazo ga ruma a gidana suka sauka.kusan komai a gidana akeyi sadiya komai sai ta bani shawara takeyi .don haka nasha hidima sosai har muka kammala lfy.mun huta na sati daya kawai muka sake tfy zaria bikin yaran sakina anan ma mune kirjin biki anyi komai cikin kwanciyar hankali aka watse daga nan muka dawo kano harda ruma saboda shirye shiryen auren munir da farida wacce har yanxu tana yola tana shan gyara hmm wnn bikin special ne. Fa,iza tace "ai dolene muyi mothers night domin zan cashe ba karya. Dariya mukayi nida ruma snn nace"zamu cashe 'yar uwa a matsayina na uwar ango ace bikin dana guda ban cashe ba ai ban kyauta ba. Dariya mukayi harda tafawa ruma tace ku dai Allah ya shirya ku wlh gani kuke kamar baku girma bako ? Fa,iza ta harareta da fadin"ke fa se mun cashe ehe garama karki bata bakinki . Muna cikin haka ya salman ya leko dakin da sallama muka amsa duk suka gaisheshi ya amsa fuska sake snn ya kalleni yace rumaisa kizo ina da magana. Daga nan fita yayi fa,iza tana dariya tace"wayyo yaya ya yi missing diin matarshi shiyasa ya zo da kanshi bai tura yan aike ba.don Allah tashi kije asha soyayya lfy. Harararta nayi bance komai ba na tashi na gyaggyara jikina har zan fita faiza tace"hmm in munji shiru mu rufe kofa ko? nace"bansani ba? Dariya sukayi nikam tuni na fita Ina zuwa dakinsa na sameshi zaune bakin gado hannu ya miko min na karaso na kama hannunsa na zauna ina kwantar da kai a jikinsa a hankali yace"kina min horo kwanan nan my dear .ganinki ma fa da kyar sai na yanki ticket. Dariya na danyi nace "yaya na zama busyne ai kwanan nan.yanxu ma kaga muna maganar walima ne da dinner..... Yace"kuma ita amaryar yaushe zata dawo kunje kun boyeta a yola ko bikin yanuwanta bata zo ba. Murmushi nayi nace"kasan ita amarya boyeta ake dama anfi so ta kasance cikin hutu.kaga inda ace anan take ta dinga zirga zirga knn tayita tarawa kanta stress.amma yanxu acan ba ruwanta da wani zirga zirga mun fiso sai ana sauran kwana hudu daurin aure ta dawo. Gyada kai yayi cikeda gamsuwa yace"gaskiane.to shi ango ba,a boyeshi ya huta ne? Good boy tausayi yake bani kwanan nan baya ko hutawa sai zirga zirga ga abokansa duk sunzo . Dariya nayi nace"ka taba ganin ango ya huta lokacin bikinsa?ai shi dolene kawai ya zama busy.itama faridan da ba don mimi na nan zata kula da duk wani abunsu na kawaye ba da dolene kawai ta dawo. Yace"gaskiane.itama mimi naso a hada bikinsu da farida in yaso in anyi bikin fadyl din ya koma karatun nasa amma yanxu sai an jira ya gama har zuwa next year sai nakega yayi nitsa. Nace"babu komai akwana a tashi sai kaga nan da nan lokacin yazo ai ko ita sakinan taso fadyl din ya hkr ayi bikin duk da na kannesa da mukayi kwanaki.amma ta lura yafi son sai ya kammala karatunsa ya dawo kuma kaga itama mimin bata damu ba.don haka muyi musu fatan alkhairi dukansu. Ya gyada kai hade da fadin "hakane Allah ya sanya alkhairi. Murmushi nayi nace"ameen maigida ran gida. Dariya yayi yace kodai uwargida ran gida? Nace"duka. Snn na dan taso daga jikinsa nace"kaga bari naje su fa,iza suna jirana .... Da sauri ya rikoni da fadin ina zakije kuma ai kawai su hkr sai gobe yanxun lokacinane. Nace"yaya wlh zolayata zasuyi tayi suce har yanxu bamu tsufa da soyayya ba. Murmushi yayi yayinda ya kwantar dani kan gado shima ya kwanta muna fuskantar juna sosai yace"hakane bamu tsufa da soyayya ba kuma insha Allah in da rai da lfy baza mu tsufa da soyayya ba my dear.domin kullum jinki nake kamar wata budurwa Allah ya baki ni,ima da wata baiwa wanda ni kadai nasan kayana.a cikin mata 100 samun irinki yana matukar wahala.karkiga laifina idan ina miki sambatu hmm ni kadai nasan irin dadin da nishadi dana keji yayinda na kasance dake my dear.don haka pls a daina min horo da yawa. Ya fada yayinda ya hannayensa ke yawo a dukkan sassan jikina cikin wani salo mai rikitarwa dole na limshe ido ina sakin ajiyar zuciya. Fuskarsa ya matso dashi daf da tawa sosai muke exchanging numfashi yayinda kamshin turarenmu ya gauraye wuri daya yana fitar da wani kamshi mai dadi da sanya zuciya cikin shauki. A hankali yace"my dear ke din special ce bazan gaji da gaya miki ba. Ya manna bakinsa da nawa.daga nan fa.......... Su fa,iza sai da safe suka ganni aikuwa tayita zolayata harda ruma.ni dai bance komai ba a ranar sakina ma tazo. Haka muka ci gaba da gudanar da shirye shiryen bikin cikin farin ciki.tuni gida ya cika da yanuwa da abokan arziki amarya ma ta dawo hmm sai kunga yadda ta koma fresh fatar nan tayi kyau ga laushi wani haske ta kara na musamman yayinda kamshi ke tashi a jikinta ta ko ya ya ta motsa gashi tasha kunshi mai kyau da jan hankali haka gashinta ya sha gyara.batun can kam ba,a magana wnn sai ango ne zai bada bayani lol! Su madiha sunzo nafisa kam tayi sati ma a gidan don duk wasu hidimomi da ita mukayi tareda sa,adatu yadda ta saki jikinta damu kamar ba abinda ya taba faruwa a baya.adda A'i ce kawai bata zo ba itama saboda jinyar mijinta da suketayi.ciwo dai yaki ci yaki cinyewa don sunce ciwon koda ne.sai faman kashe kudi ake tayi. Haka hidimar bikin ta kasance cikin farin ciki yayinda yaya salman ya baza sojoji ta koina ana bamu tsaro ta musamman don mun sami halartar manya mutane na kasa.salima ma tazo hakama Ahmad yazo daurin auren kuma ya nemi ya salman da ya yafe masa abubuwanda suka faru a baya ya salman yace babu komai ya wuce shima kuma ya yafe masa.Allah sarki rayuwa. Haka bikin ya kare babu wata tashin hankali ko hayaniya Amarya ta tare a gidanta na nan GRA don bamu da nitsa sosai ya salman yace baison suyi nitsa damu. A hankali aka dinga watsewa har ya rage gida sai mu kadai .khalil ma Abuja ya koma don sun gama secondary suma can za,a turasu malaysia karatu shida salman junior. Hanif da Hanifa kuwa har lokacin suna gidan mama don sun saba da ita ko ya salman ya kawosu yini basu yarda sun dinga kuka se an maida su gun mama. Nafisa ma an yi bikinta da abokin ya hafiz doctor jalal.a Abuja suke zaune hankali kwance. Adda A,i kam jinyar mijinta gabadaya ya karar da duk wata arzikinsu a yanxu basuda komai sai dai da taimakon yan uwa da abokan arziki yayi jinya mai tsawo kafin Allah ya dauki ransa.gaskia fadan tashin hankali gun adda A,i ba,a magana duk ta rame tayi baki kamar ba adda A'i ba duk wanda ya ganta a yanxu sai ya tausaya mata. Bayan ta gama takaba ta dawo gidan Inna ba don innah taso ba sai don abba ne yasa baki akan ta dawo ta zauna ba yanda inna ta iya.hakama ya salman baiso hakan ba. Amma cikin ikon Allah kuma babu wata hayaniya tunda ta dawo ta nitsu tsaf kamar ba ita ba .yaranta kuma suna bata kulawa dai dai gwargwado.yayinda take ci gaba da kasuwancinta a hankali don yanxu fa babu harka kamar da sai dai ana manage kawai. Nima tsakanina da ita yanxu mutunci ta daina saka kanta a lamuranmu kamar da. _Rayuwa_ _knn_ ***A karshe wnn shekaran mukaje Abuja bikin mimi da fadyl din sakina gaskia munsha hidima sosai kasancewar suma auren dangi ne. A lokacin farida kuma take ta fama da laulayin ciki da ya hanata sukuni duk yadda taso ayi hidimar bikin mimi da ita abin ya gagara .tana kwance kawai ko ruwa tasha amai.munir duk ya shiga damuwa minti minti sai ya shigo ya duba ta . Anan ruma ta kama yi masa fada wai baida kunya ya bari mana sai sun koma gidansu. Bayan ta gama yi masa fada ya fita yana bata hkr na kalleta nace"gaskia ruma bsnji dadi abinda kk ma munir ba meye laifinsa anan don yazo ya duba lfyr matarsa kinsanfa shi likita ne.snn tun farko ya ma fada mana farida bazata iya zuwa bikin nan ba don bata da cikakkiyar lfy kika matsa sai tazo gashi kinxo kina ta masa fada da wanne...... Ta katseni da fadin "rabu dashi baida kunyane tun dazu yaketa shigowa ko kunyan mutane baiji sai kace akansa za,a fara haihuwa.laulayin cikin kowa yasan yanda yake ya rabu da ita mana sai sun koma gidansu suje yaci gaba da rashin kunyarsa can inda suka saba. Dariya nayi nace"nidai banga abin tsanani anan ba kema fa in baki manta haka kuka tayi da ya salim sanda kk da cikin munir din ke kam ma bakida wani laulayi amma sai tarairayarki ya salim yake .don haka yadda kikaci naki zamani suma ki barsu suci zamaninsu..... Fitowar farida daga toilet ne ya katseni na kalleta duk ta rame ko magana bata iyayi. Ruma ta kamota ta kwantar da ita jikinta tana shafa kanta tace"sannu kinji ? Kiyita hkr insha Allah daga zaran cikin yayi kwari zaki daina duk wani laulayi nasan yanda kikeji sorry my dear.in an gama bikin nan kiyi zamanki anan har ki sami lfy kinji? Kai kawai farida ta daga mata ni dai kallonsu kawai nake. Muna shirin fita wurin walima ya salim ya shigo dakin ruma ya samemu fada ya shiga yi mana wai don me muka ce sai farida tazo bikin mimi alhalin bata da lfy.don haka ta tashi maza munir na jiranta a mota su koma kano .ai sai da lfy ake kome. Ba don ruma taso ba haka ta kyale munir ya tattara matarsa suka bar Abuja . Ruma ta gama cika fam tace zai dawo ya sameta ne. Nidai sai dariya nake mata ina mamakin irin wnn karfin halin nata. Da haka mukaci gaba da hidimar biki har aka kare lfy amarya ta tare a zariya su sakina an zama suruka. Mun dawo kano gida ni kadai sai sojoji da masu aiki don ya salman daga Abuja ya wuce lagos amma yace min kwana biyu kawai zaiyi ya dawo. Ban wani huta ba na daiyi wanka na shirya da kaina nayi driving gidan munir naje tukun . Na samesu a palo farida sai zuba mishi shagwaba take son ranta ganina baisa sun fasa abinda suke ba don ni dama sun saba yi a gabana kuma ban taba nuna damuwa kamar ruma ba. Bayan mun gaisa farida ta kalleni tace"mama yaushe kk dawo Abuja? Nace"daxun bai jima ba. Tace'daddy fa? Nace"ya wuce lagos. Snn na tambayeta ya jikin tace da sauki. Munir kuwa ya shiga hidimar kawo min drinks da abinci Murmushi nayi nace"sannu da hidima wnn duk aikinka ne na sani tunda ku ba kwa yarda da yan aiki. Murmushi yayi yace"mama yan aikin ne kazamai. Nace"hmm kai dai ka cika kyama.amma yanxu tunda na dawo karka kuma shiga kitchen kana wahalar da kanka zan na turo muku abinci har Allah ya bata lfy. Da haka na tashi munir yace"mama baki ci komai ba fa. Dariya nayi nace "ni a koshe nake kuma sauri nake gidan mama zanje in dubasu snn in wuce gidansu Innah suma na gaishesu. Farida tace ai kuwa jiya inna tazo muka sata yini dole. Dariya nayi nace"zaku aikata. Daga nan muka fita suka rakani har bakin mota munir yace"mama me yasa baki dauki driver ba bayan kinsan dad baya so kina driving? Na danyi shiru snn nace"yau kwadayin driving da kaina nake kuma kaga ai ba wani nitsa zanyi ba. Mukayi sallama na motata sai gidan mama daddy ma yana gari don haka hira muka shiga yi sosai har yamma na tafi gidansu inna ina isa ana kiran sallar magrib don haka sai da muka idar da sallah muka samu damar gaisawa inna tace"rumaisa ashe kun dawo? Nace"eh inna na dawo tun dazu amma ya salman ya wuce lagos. Tace"ayya A'i ma dazu ta tafi lagos din nusaibarta ta haihu. Murmushi nayi nace"o nusaiba dai ta cika gida da yara Allah ya raya . Tace "ameen jiya naje na duba shatu ma anata fama da laulayi amma ja'ira haka suka sakoni a gaba wai sai na kwana a gidansu nace wlh bazan iya kwana a gidan ba ina ganin irin rashin kunya da sukeyi a gabana. Dariya nayi nace"hmm Allah ya kyauta dai. Tace"ameen bari a kawo miki abinci kici kamin ki tafi. Haka kuwa akayi sai da naci abinci na yi sallar isha har ina shirin dawowa amma hiranmu da inna taki karewa a karshe ma ce mintayi kawai mu kwana tunda ya salman baya gari kuma ba kowa a gidan namu sai masu aiki da sojoji. Don haka nan na kwana mukayita hira kamar uwa da yarta.don gado daya muka kwanta har gari ya waye. Muna breakfast sai ga ya salman ya shigo da sallama inna ta amsa yayinda nikam gabana ne ya fadi don ko gaya masa akan na zo gidansu inna banyi ba don bamuyi dashi zai dawo yau ba. Aikuwq hararata yayi yace"ke kuma da iznin waye kika zo kika kwana anan? Inna ta karba "nice nan nace ta kwana ko laifine don ta kwana anan? Yace"inna nifa bamuyi da ita zata zo nan ba. Inna tace to zuwa nan din laifine knn? Shiru yayi yayinda ya zauna ya fara gaisheta.ko da na gaisheshi kin amsawa yayi.inna tasa aka kawo masa breakfast ni dai tashi nayi na barsu na koma dakin inna nan na fara gyara dakin. Ina cikin gyarawa ya shigo ya sameni banji shigowarsa ba kawai saiji nayi an rumgumeni ta baya kamshin turarensa ne ya bugi hancina. Kokarin kwace kaina nakeyi ina fadin yaya don Allah ka bari kar inna tazo ta samemu muji kunya. Cewa yayi wlh se dai ta shigo din wayace kixo nan ki kwana? Tureni yayi nafada gado ya bini shima ya min rumfa zaro ido nayi da kyar na iya fadin"yaya akan gadon innah don Allah ka bari wlh zata iya shigowa...... Shhhhiiiii yasa hannunsa a baki snn ya fara kissing dina ta koina ni dai naki biye masa duk a tsorace nake don kar inna ta shigo ta samemu akan gadonta kai namiji baida kunya lol! Da kyar ya rabu dani yana sauke ajiyar zuciya ya kalleni da idanunsa ta suka canza nan danan yace"kiyi sauri kizo mu tafi ina jiranki a mota karki bata min lokaci. Ya fita yana gyara rigarsa. Nikam dole na sake gyara gadon snn na dauki hijabina da jakata na fita bansami inna a palo ba sai mai aiki dake ta moping tace min inna na side din abba. Don haka na fita na sallami mmn sakina snn na leka palon abba na sallami su inna daga nan na fita na sameshi yana jirana tunda yaga fitowata ya zuba min ido kamar yau ya fara ganina har na karasa na shiga motar bai ce komai ba yaja motar muka tafi. Muna isa gida ko kunya baiji ba ya dagani cak daga cikin motar sojojinsa sai kame masa sukeyi shi dai ko kallonsu baiyi ba yayi cikin gida dani nidai yau na gama shan kunya don shikam ko ajikinsa yau 'yan barikin ne suka tashi. Bai direni koina ba sai kan gado a dakinsa kokarin cire min ......yakeyi nace"wayyo yaya don Allah ka bari wlh na koshi sosai amai zanyi. Shafa cikina yayi yace"so nake in samowa twins kannene ba wani abu ba. Nace"yaya ni fa na gama haihuwa tunda farida ta fara.... Ya katseni da fadin inji wa? Bai barni na amsa ba ya hade bakinmu wuri daya yana juya ni san ransa. ****Bayan waasu watanni farida Allah yayi ta sauka lfy ta haifo katuwar baby girl mai kama da ubanta ba abinda ta bar masa Hmm farinciki a gun munir ba,a magana .muma hakane. Ranar suna baby taci suna RUMAISA(intisar) Allahu Akbar nida ruma mun zama kaka lol! Abuja ta koma wankan gida don ruma ta dage sosai ni dai ban damu ba don ko ta dawo wajena bazata wani samun kulawa har can ba.tunda ya salman kullum kwanan duniya kara manne min yake baya taba yarda nayi nitsa dashi abin har yana bani mamaki ni a tunani na tunda yanxu mun tsufa abubuwan zasu ragu amma ina sai ma abinda ya karu .gashi gida dagani sai shi su hanifa sai dai akawosu weekend. Haka rayuwa taci gaba da tfy cikin jin dadi sai dan abinda ba,a rasawa....! Nida ya salman zamanmu lfy lau sai dai muce *_ALHAMDULILLAH_* 🔚🥰🥰😭 *_Anan na kawo karshen_* *_wnn_* *_labarin_* *_na_* *_RUMAISA_* *_SALMAN_* .Godiya ta tabbata ga *ALLAH* Subhanahu wata ala da ya kawo ni wnn lokaci *ALHAMDULILLAH*🙏🏻 snn ina salati ga fiyayyen halitta Annabi *MUHAMMAD* ( *SAW* )🙏🏻🙏🏻🙏🏻 Da fatan zamuyi koyi da duk wani abu mai kyau daga cikin labarin.Sannan muyi watsi da marasa kyan.Allah sa mu dace(ameen)🙏🏻🙏🏻 Sannan ina rokon Allah kuskuren da nayi a cikin wannan labarin ya gafarta min(ameen)🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻 *_GODIYA MAI TARIN YAWA A GAREKU FANS DIN RUMAISA SALMAN A DUK INDA KUKE.NAGODE SOSAI DA IRIN COMMENTS DINKU DA NA KE GANI AKAN WNN _LITTAFIN_ _ALLAH_ _YA_ _BAR_ _ZUMUNCI_ _DA_ *_KAUNA_* 🥰🥰🥰🙏🏻 _Maman khausar bazan taba mantawa da ku ba soyayyarku🥰 daban ne a cikin zuciyata❤😁😁😁😁👍🏻_❤❤❤❤❤ _Ina yinku sosai da sosai.😉🥰❤_ *Tammat* *bihamdillah* ✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻🔚🔚🔚🔚