11/05/2023, 10:59 - Les messages et les appels sont chiffrés de bout en bout. Aucun tiers, pas même WhatsApp, ne peut les lire ou les écouter. Appuyez pour en savoir plus. 14/06/2023, 07:11 - Le délai avant disparition a été mis à jour. Les nouveaux messages disparaîtront de cette discussion ‎90 jours après avoir été envoyés, sauf s'ils sont gardés. Appuyez pour modifier. 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HARUN* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *1* *WANI LOKACI* Da gudu yayi niyyar fitowa daga falon dan neman agaji, ba dan biyayya da kuma sanin *Mu'az Mika'il* mahaifin sa bane, da a wannan shekarun nashi da ya fara kama ƙasa tsabar ƙarfi, da zai dambatu ne da shi komai girman sa, amma har yau har yanzu bai wuce yayi zaune mahaifin shi na shi na masa dukan mutuwar da ya saba yi masa ba a duk lokacin da matar tasa wato *matar babanshi* ta kawo masa tsegumin yayi wani laifin ko da kuwa bai yi ba. Duk da ya so zillewa ya bar musu gidan, amma kasancewar mahaifin nashi wato Mu'az ƙaƙƙarfan matashi ne da bai kai a kira shi da tsoho ba duk da shi ne ɗan sa na farko sannan ya haura shekara arba'in da kaɗan, bugu da ƙari soja ne da ko a cikin sojawan yake amsa sunan Sergent sannan shugaban tawagarsa. Ƙafar matashin yaron da a ƙalla zai kai shekara 14 ya cabko, hakan ya tilastawa yaron wata irin faɗuwa ya dabsu da ƙasa tare da gwara kan shi da murfin ƙofa, cikin raɗaɗin azaba yayi waa razananniyar ƙara ya dafe kan nashi yana kiran "Wayyo Allah na, Wayyo Baba kaina, kaina ya fashe." Bai saurari magiyar da yake masa ba, tamkar yana jan wata dabba haka ya dinga jan ƙafarshi har saida ya ja shi zuwa ɗakin baccinshi ya rufo ƙofa, wannan ɗamarar (belt) tasu ta sojawa mai ƙarfin ikon ladabtar da duk wanda tsagerancinshi bai kai matakin gawurta ba ya cire daga ƙugunshi, kafin ka ce kwabo ya shiga zabgawa *Jabir* da tunda ya ji ya rufo ɗaki ya tashi zaune yana faman haɗewa jikin gado yana bashi haƙuri kan laifin da bai san ya aikata ba, dan shi dai yna shigowa gidan ya ji mahaifin nasa da bai san ma ya dawo daga daji ba ya ce ya wuce uwar ɗaki, shi kuma da ya ji haka yasan ba sirri ko hirar arziƙi zasu yi ba, Shiyasa ma ya nemi tserewa ya bar gidan. Dukansa yake da wannan ɗamara, ba wai mutum mai rai ba, ko gawar wannan dabbar wato jaki ce ake ma dukan nan, wanda ke nesa ma kaɗai zai iya tsayawa yana zubar mata da hawaye, bare kuma idan kana jin gunji da sautin kukan da kai ka tabbatar yaro ne matashin da ya wuce wannan dukan. Tsabar ɗorawa kai wahala shi kan shi mahaifin nashi a wahalce yake matuƙa, dukan namiji da ya kai shekaru sha huɗu zuwa sha biyar hatsari ne, Shiyasa ma yake ta gumi kuma zaka rantse dambatuwa ne suke idan kana jin su daga waje saboda irin kwaramniyar dake fitowa daga ɗakin, dan Jabir dai ba zaune yake wuri ɗaya yana duka shi ba, ƙoƙarin kare jikin shi yake da riƙe ɗamarar, hakan ya jawo idan ya riƙe ɗamarar da kyau har ya kan kasa ƙwatarta sai ya dinga harbinshi da ƙafa yana kuma marinshi ta ko ina yana faɗin "Saki, saki nace, ba zaka saki ba? Ka rainani ko?" Cikin azaba za ka ji Jabir yana cewa "A'a Baba, a'a wallahi, zan saki to, amma kayi haƙuri karka dakeni dan Allah, ka yi haƙuri ba zan sake ba koma menene." Suna tsaka da wannan tirƙa-tirƙa aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin, cikin haki da masifa ya kalli ƙofar yace "Wa ye?" Daga waje muryar matar tashi ita ma da yanayin masifa tace "Ni ce, ka buɗe ɗakin nan ku fita waje Baban *Uzeifatu*, wallahi tallahi idan kuka min ɓarna a ɗaki sai ka biyani, kaga fa haka kwanakin baya kuke karya min gado, da ƙyar ma ka samo min mai gyara, dan haka ku fito min daga ɗaki, sannan hayaniyarku tana hana min yarinya bacci." Tabbas hargagin da take masa ya kai yasa ya haɗa da ita ya jibgeta, to amma ba zai iya hakan ba dan ita ce Hajiar gidan, ɓacin ranta daidai yake da rugujewar tattalin arziƙin gidanshi, hakan yasa tamkar wni ɗan zakin da bashi da haƙora ya amsa mata da" Shikenan, kiyi haƙuri to, ina fata dai Uzei bata tashi ba?" Duk yayi maganar ne yana buɗe ƙofar ɗakin daya rufe da makulli, hakan yasa Jabir ma tasowa yana shahseƙa da sosar jikin shi suka fito, zaune suka same ta tana jijjigar Uzei da take so tayi bacci, kusanta ya zauna yana ɓalle botiran rigar shi tare da share gumin da yayi. Jabir take Harare da ya kama hanyar fita daga falon, ganin hareren da take ma yaron duk da ɗan cikin sa ne shi ya haifi abun shi yasa shi daka masa tsawa da cewa "Kai!" A razane ya dakata yana kallon shi da jiran jin me zai ce, cike da gargaɗi da nuna shi da yatsa yake cewa "Maza ka ɗauki jarkokin nan ka tafi yanzun nan ka debo mana ruwa, tunda ai kasan aikin ka ne amma ka tafi yawon ka baka ɗebo ruwan ba." Da mamaki jin haka Jabir ya kalli *Bara'atu*, ruwa kuma? A kansu aka masa wannan dukan? Bayan bai tafi makaranta ba saida ya cika mata kaf abubuwan da take cewa sai ya cika mata da ruwa tsabar son ta sa ya makara har da kansu jarkokin guda biyu saida ya cika su ya aje sannan ya tafi, duk me aka yi da ruwan? Wannan kallon da yake mata yasa ta daka masa tsawar "Lafiya wai? Ni na saka aikin ne da zaka tsaya kana harara ta? Ka ɓace min da gani malam." Zabura yayi sannan ya juya ya fita yana jin uban na faɗin "Za ka gane baka da wayo idan baka ɗauko ruwan nan ba." Kallonshi tayi cike da kissa da kwarkwasa tace "Baban Uzei, gaskiya ni yaron nan wallahi ya fara bani tsoro, ina gudun wata rana ya rufeni a ɗakin nan ya zaneni, tunda Kaga kai ba zama kake ba, shi kuma yanzu ya idasa lalacewa duk ya zama wani iri, ni fa ina tunani kamar Jabir ya fara shan sigari." A razane ya kalle ta ya maimaita kalmar" Sigari?" Da son tabbartar masa ta ɗaga kai sannan tace" Ƙwarai." " Jabir ɗin?" Ya sake nanatawa don abun a bazata ya z mishi, ko shi da yake ubansa kuma soja sigari bata taɓa birge shi ba, ba ma shi ba har da wasu daga cikin milyoyin sojoji, amma a ce ɗansa? Lura da kamar kokonton maganar ta yake yasa ta sake cewa" Kai baka ga idanun shi kullum jajir dasu ba kamar na mai shan wiwi, ga wata rama da yake kamar ana miya dashi, ni dai gaskiya ka raba ni zama da yaron nan." Dafa kafaɗarta yayi a tausashe yace" Ki ƙara haƙuri kinji Bebe, idan fa kika duba shekara nawa ta rage ma na kaishi makarantar horon soja shi ma ya zama kamar ni, ai shekarun da kikayi dashi a baya yanzu ko rabin rabinsu ba zaku yi a tare ba." Turo baki tayi gaba tana cewa" To ya koma can wajen su Mama da zama mana, dan nidai n'a gaya maka tsoro yake bani yanzu, ga rashin kunya da ya ƙara koya bana saka shi aiki kai tsaye yayi sai na sha wahala." Cikin rarrashi yana shafa wuyan ta yace" Bébé ke fa kinsan komai, Mama ba zata taɓa haƙuri ta karɓi Jabir ba, kin fi kowa sanin muhawarar da aka tafka kan Mama ta karɓeshi bayan *rasuwar mahaifiyarshi* tun yana da shekara *huɗu* a duniya, bare yanzu da ya girma ya isa ya ma ka shi komai. Kiyi haƙuri duka Bebe, ina tabbatar miki zan ja masa kunne, ba zaki sake yi masa magana sau biyu ba idan zai miki abu, kin ji?" Taɓe baki tayi tace" Shi kenan." A ranta kuma ayyanawa take _" Ina dalili ina ɗan mafari, an haɗani da jaraba tun ina amarya ko amarcina ban ci da kyau ba, to Kakar sa ma ta ƙi shi bare ni da ban haɗa komai dashi ba? Sa'ar sa ɗaya bamu zauna da uwar ta sa ba wallahi, da Ace ta min ba-daɗi da a kanshi zan rama wallahi."_ *Jabir* kuma na fita jarkokin ruwan guda biyu ya ɗauka hannun shi dafe da kanshi dake masa mugun ciwo mai raɗaɗi, a daddafe yake tunkurarar wurin ɗiban ruwan dake ɗan nesa da gidan amma ba sosai ba, tsoron hanyar yake ji sosai saboda sabuwar unguwa ce mai kama da dajin Allah, wurin nada haɗari sosai musamman yanzu da zafi yayi yawa, haka yasa ganin kunama da maciji a wurin ba wani abu bane, shi kanshi ya kashe wa matar babansa kunama tafi a ƙirga. Tashin hankalinshi yanzu shi ne jiya tun da rana ba wanda yaje fanfon nan ɗebo ruw saboda macijin da aka gani a wuri kuma an tabbatar mai dafi ne, shi ne yanzu ba tare da tunanin komai ba mahaifinshi ya ce ya zo ya ɗiba, bayan ya san ya cika mata komai da ruwa. Da wannan tunanin yake tafe yana lumshe idanunshi saboda kanshi har yanzu zugi yake masa, sannan kuma idanunshi da kularshi duk suna kan hanyar ne, babu hasken fitila ko ɗaya a dai nan layin nasu idan ba ka shiga kwanar gidan Alhaji *Kabiru* ba, ba dan babu wuta a gidan su ba sai dan unguwar ce babu mutane sosai, hakan ke haifar da duhun dake samar da rashin amince ga ma'abocin fitar dare a wannan unguwa. Ga dai ƙofar gidan a zai ɗibi ruwan a rufe alamar sun kwanta, ba zai yarda ya koma babu ruwan nan ba, dan haka gwara ya tashesu dan ya ceci kanshi daga dukan mutuwar da za'a mishi a gidan nan, dan haka a nutse kamar yadda halayenshi da ɗabi'arshi suka zama masu sanyi ya dinga bubbuga ƙofar tare da yin sallama, dan ko da firgici ya sa sun saka tasowa sallamar tashi zai iya saka wani daga cikin mutanen gidan ya ɗauki muryarsa musamman ma dai mai gidan malam *Sule* da yaron gidan *Mujittafa*. *LOKACIN* da yake buga ƙofar nan daga cikin manyan gidan masu hankali da sanin ta kamata duk idanunsu biyu, sun sa ƴarsu gaba ne suna tattauna wata matsalar tasu da ta kunno musu kai a daren nan, wanda su dai iyayen suke ganin ba dan ƴar ta tsaya kai da fata kan cewa za ta iya ba, to fa da ba zasu lamunce b dub da wasu dalilai. Maganar son auren *Ummu Kulsum* da Alhaji Kabir wato mai gidan da suke ciki zaune ya zo musu ya zo musu da ita ta girgiza su, mutum kamar shi? Mai tarin dukiya da alfarma da kuma suna, sannan mai shekarun da suka ninka ninkin ba ninkin na Ummu Kulsum, sannan mai mata uku cif sannan wayayyun mata, yana da yara da jikoki bila adadi, a hakane zai ce zai auri ƴar su mai shekara sha bakwai a duniya. Ina! Wannan abu ne da gaskiya da kamar yiwuwar shi. *Mariƙin* (Ba su ne asalin iyayen ta ba) na Ummu da ya ji ana ci gaba da buga ƙofar ne ya miƙe yana dafa kafaɗar Ummu Kulsum ɗin cikin rarrashi yace "Kinga daina kukan, da safe zamuyi magana kin ji, n ji ana buga ƙofar gida ne zan je na duba." Cikin sanyayyar muryar ladabi Ummu Kulsum dake daf da *uwar marayu* kamar za ta fashe da kuka tace "Baba, wallahi na gaya muku da zen aure shi, na yarda ina sonshi Baba, idan ma shi ne ya zo ku ce masa na amince zan aureshi." Tsura mata idanu yayi takaci na baibayeshi kamar zai wanke mata fuskar ta da tafi, sai dai kafin ya ce mata wani abu uwar marayu data gane me kallon shi ke nufi gareta ta ja hijabin Ummu har saida tayi kamar za ta kwanta a jikin ta, cike da son ta dawo da ita hayyacinta cikin ɗaga murya tace "Wai ke kanki ɗaya kuwa? Ya daga ji magana kawai za ki wani damemu da kina sonshi za ki aureshi, wannan ɗin tsaranki ne a aure ko shekaru? Kin ma hango abinda muke hango miki ne? To bana ciki da iskanci." Sai kuma ta kalli malam Sule dake kallonsu tace "Malam, ka je ka duba Kaga waye a daren nan? Na ji har yanzu bugawa ake, Allah dai yasa lafiya." Ajiyar zuciya ya sauke ya nuno Ummu da yatsa yace "Ki ce ta shiga taitayinta." Yana fita Ummu da ta bishi da idanu tayi saurin duban Maman nata, duk da ba ita ta haife ta ba, amma ita ta raineta tun tana jaririya, yadda aka bata tarihinta shi ne, an ce a *bola* aka tsince ta an jefar da ita, shi ne *Amina* ta ɗaukota ta kawo ta gidan ta ta raineta har yanzu da take shekaru *sha bakwai*, sun bata tarbiyya iya iyawarsu, basu bambamta ta da yaran da suka haifa ƙwaya biyu ba rak a duniya, hasalima *Lukman* ne kawai gaba da, bayan ta fara tafiya suka haifi *Nabila*. Hannun uwar marayun ta kamo ta riƙe tana jijjigawa cikin taushin muryar da ya zam halittarta ce take faɗin "Mama, ai kinsan ban taɓa neman abu a wurin ku na rasa ba ko? Mama ina son Alhaji Kabir, ina so na aure shi Mama, dan Allah ki wa Baba magana ya amince." Hannu uwar marayu ta ɗaga na damanta, kafin Ummu Kulsum ta ankara ta zabga mata shi a fuskar ta ranta a matuƙar ɓace, da sauri ta dafe kuncin ta tare da kallon maman nata tana zazzare idanu, cikin ɓacin ran da ba kasafai suka fiya gani na uwar marayun ba ta miƙe tana gyara ɗaurin kallabinta, ɓangare ɗaya kuma cikin faɗa take kallon Ummun tana cewa "Ummu dama a tarbiyar da na miki akwai ranar da zaki iya tsare ni da mahaifin ki kina mana magiyar mu miki aure? Dama ban sani ba har kin yi buɗewar idanun da zaki nemi yi mana kuka kina faɗa mana gaba da gaba kina son Alhaji Kabir sannan a aura miki shi? Ba ki ji kunya ba don Allah? Ummu idan ni kin ɗaukeni ƙawarki, shi Babanki abokin wasan ki ne?" Girgiza kai ta yi cikin shasheƙar kuka duk da bata fara hawayen ba tace "A'a wallahi Mama, ba raina ku nayi ba, kiyi haƙuri." Cike da bayar da umarni uwar marayu tace "Da kyau to, idan Babanki ya shigo ki gaggauta bashi haƙuri, sannan maganar auren ki da Alhaji Kabir babu ita, dan baku dace da juna ba ko kaɗan, kin gane." Ƙurawa uwar marayu ido tayi tana kallon ta zuciyar ta fal da tunanin _"Me yasa ba zata fahimce ta ba? Me yasa ma dukansu ba zasu fahimta ba?"_ Ita ma *ba son shi take ba*, yadda taji suna tattauna matsalar a tsakanin su da butulcin da suke shirin yi masa matsayinshi na wanda ya dubesu ya basu masauki, gidan nan da suke ciki hada wutar lantarki ga kuma ruwa, ko ɗaya ba sa biyan ko sisi na wannan abubuwan, dan ruwa ma gabaɗaya unguwar anan ake ɗiba, sannan ga jarin da ya ba wa Baban nasu yake juyawa har suna samun abinda suke ci. Ita kanta ko da suka tsince ta suka kawo ta anan gidan ta gansu, a ƙalla shekarar su goma sha tara a gidan nan, bai taɓa cewa ku tashi ina buƙatar wurin ba, shi dai kawai ana kawo masa wasu kayayyakin da suka shafi kasuwancinsa ana aje masa a mangazar (store) dake cikin gidan. Hakan yasa take ganin bai kamata a ce yau ya zo musu da butun son aurenta ba à ce sun ƙi amince masa, ita dai a yadda ta san ba su suka haife ta ba, ba za ta yarda Hakan ya zamar musu matsala ba, dan tana ji a ranta idan har basu amince ba, to zai iya tashinsu daga nan ɗin, kuma ko da m halayen da suka sanshi da su na karamci basu barshi ya tashe su ba, to ai da kunya suma su ci gaba da zama, to idan sun tashi in zasu koma? Baban su bai d halin da zai iya biyan kuɗin hanya da wuta da ruwa, Hakan kuma zai sa rayuwa ta sake tsananta a gare su ta musu zafi fiye da yanzu. Uwar marayu na shinfiɗa a fargajiyar gidan malam ya dawo, da kulawa take tambayar shi "Malam waye yanzu a daren nan?" Saida ya sauke numfashi ya bata amsa da "Wallahi yaron nan ne Jabir, ruwa ne ya zo ɗauka." Da mamaki a fuskar ta sosai tace "Ruwa kuma? Yanzu a daren nan?" A kasalance yace "Wallahi kuwa, ya ɗauka ya tafi, na bar mishi fanfon a kunne, dan ya ce Babanshi ya ce sai ya cika musu komai da ake zubawa ruwa gidan." Ita ma ajiyar zuciya ya sauke tana girgiza kai sanda take ƙoƙarin ɗaura gidan sauro tace "Bawan Allah, to ko da safe fa anan ya ɗibi ruwa." Girgiza kai yayi cike da jimami yace "Ke dai Allah ya kyauta, amma wannan mahaifi nashi kam sai du'a'i, dan yanzu haka in da kin ganshi wallahi da alama dukanshi ma yayi, dan har fuskar shi ta kumbura, ya ce min kanshi ke ciwo idan ina da magani na bashi, ni kuma na san ba lallai a samu ba a cikin gida, sai dala ashirin na bashi na ce ya si ya sha." Cike da tausayawa uwar marayu tace" Bawan Allah, Allah ya jiƙan mahaifiyarshi, shi kuma Allah ya wa rayuwarsa albarka." "Ameen." Ya faɗa yana cire takalmin shi ya bi ta kan shinfiɗar ya shiga cikin ɗakin, kusa da Ummu ya sake yin zaune yana kallon ta cike da kulawa yace "Kuka kike yi Ummu Kulsum?" Da sauri ta girgiza kai tace "A'a Baba, dan Allah ka yi haƙuri ka yafe min, na san na ɓata maka rai ɗazu." Girgiza mata kai yayi yace "A'a Ummu, ni baki min komai ba wallahi, sai dai ina so ki sani cewa, ke da Alhaji Kabir baku dace ba, Ummu Kulsum ni kaina Alhaji Kabir ya haife ni, saboda babban ƴar sa ma ta girmeni nesa ba kusa ba, kenan kinga akwai tawaya sosai idan aka ce a haɗaki aure da shi, ba zaki mori ƙuruciyarki ba Ummu Kulsum, ni kuma abinda bana fata kenan, ina so yadda na reneki cikin kulawa da kyautatawa, na haɗaki da wanda zai san mutumcinki sannan ya dace dake, ta yadda ko bayan raina ruhina zai samu salamar cewa na barki a hannun da ya dace." Ta gamsu ƙwarai da abinda ya faɗa mata, dan haka ta jinjina kai tace" Nagode Baba, nima dama ban hango abubuwan da kuka hango min bane, kawai dai Naji ina so na aure shi ne saboda kirkinshi da nagartattun halayenshi, amma tunda baku amince b na haƙura." Zuba mata idanu yayi yace" Ummu, da gaske abinda yasa kike so ki aure shi kenan?" Jinjina kai tayi tare da kallon shi tace" E Baba, daga gare ku nake jin kuna yabon halayensa da kirkinshi, ni kuma sai naga dama ana son mutum ne don kyawawan halayenshi, sannan ko mutum ya girmeka zaka iya zaman aure da shi indai kana da tabbacin zai girmamaka sannan ya mutumtata iyayen ka." Shiru yayi na wasu daƙiƙu, sai kuma ya jinjina mata kai yace" Ummu, kin tabbata tsakani da Allah kike son Alhaji Kabir?" Sadda kanta tayi ƙasa tace" E Baba." Sai kuma ya sake jinjina kai ya miƙe yace" Shikenan, idan sun sake waiwayarmu da maganar zan faɗa musu ra'ayinki, amma idan sun yi duba da abinda na faɗa musu tun farko na nuna ƙin amincewa ta, to nasan ba zasu sake dawowa ba sai dai ya aiko mana ɗan aike cewa mu bar masa gida." Da kallo ta bi shi har ya fice sannan ta sauke ajiyar zuciya, tana jin muryar mahaifin nata na tambayar uwar marayu wai har yanzu Mujittafa bai shigo ba? Da e kawai ta bashi amsa ta ji sun ɗauki wata hira. Mujittafa ɗa ne ga ƴar uwar uwar marayu, bayan rasuwarta ta ce a bata tunda mahaifi shi ba zama yake ba. Daddaɓa Nabila tayi dake bacci duk tayi gumi saboda zafin dake akwai, tashin da za ta yi cikin magagi tana kama zanenta, Hakan yasa abu faɗowa daga cikin zanen nata, Ummu da ta kula da hakane ta sunkuya ta ɗauka tana dubawa. Ganin kuɗi ne har jaka biyu yasa ta kalli Nabila da tuni ta fice a ɗakin ta faɗa kan shinfiɗar da uwar marayun ta gama, kuɗin ta sake kalla ta kalli Nabila, sai kawai ta nufi wurin kayan islamiyarta ta buɗa littafin ta na hisnul muslim ta saka kuɗin ciki da tunanin Allah ya kaisu safe lafiya ta tambaye ta ta ji ina ta same su? Duk da ta san Nabilar na wasu halaye da kullum kake jin hayaniyarta da uwar marayu, amma bata so a ce gaske ne abinda ta ji zuciyar ta na raya mata, bata fatan à ce ƙin jin Nabila har ya kai wannan matakin. *ME CE CE DAMUWAKI*? Rashin ni'ima? Rashin gamsar da mai gida? Warin gaba? Bushewar gaba? Ƙaiƙayin gaba? Kurajen gaba? Zubewar nono? Cikowar nono ? *Kina buƙatar...* Fatarki tayi laushi? Tayi santsi? Ta kwanta luf? Kina walkiya da annuri tamkar amarya? Sabulu kike so ko haɗin shafawa ki wanke ko mai na shafawa? Ki wadatu da sahihin ƙamshin haukata mai gida? Humra da zaki saka mijinki bacci bai shirya ba? Humra da zata tayar da sha'awarsa? Kulaccha da zata saka mijinki ya kasa yi miki tsara a fannin ƙamshi? Kulaccha da zata gagari manyan mata suffanta kalar sunan turarenki? Turaren wuta irin na asali barebari? Turaren da zaki fesa à zanin gadonki har ya rike mai gida ya kasa tashi? Turaren da zaki zuba ga ruwan wankan mai gidan ki? Turare don yaranki? _Idan duka kina buƙatar ɗaya daga cikin kayan nan, to ki tuntuɓi wannan lambar ta WhatsApp *82-21-91-74* wanda suk gwada sun san ingncin kayanmu, ba buƙatar ɓata lokacin cika muku baki. Wani abun farin ciki kuma, duba da yanzu ba kowace mace ke son shan garin magani ko matsi ba, akwai haɗi irin su *tsumi*, *ruwan tsumi*, *tukunya*: dayawa sun san tukunya, don da itace muke tutiya, kuma tukunyar nan akwai na ruwa dana dafawa a nama, sannan akwai kankat wato haɗin *kayan marmari*. *Garabasa* Ga waɗanda sukayi nisa kuma haɗin kayan marmari ba zai kamacesu ba, duba da kafin sakon yaje garesu zai fara lalacewa, don haka ga sauki ya samu, madadin kuɗin mota da zaki yi, zaki biya 1000k kacal don a sanar dake yadda zaki had, ba iya guda kawai ba, dama sauran haɗi irin na kayan daya shafi na marmari da ɗanye, musamman ma *sirrin kankana* da kuma *cucumber*. *JANNAT HOUSE.*🧕 *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HARUN* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *2* Yana kai wannan ruwan ya juye ya fito, kai tsaye bakin titi ya nufa da niyyar siyan magani ya sha sannan ya ci gaba da zuwa ɗaukan ruwan, amma yana zuwa sai ya ji yunwar cikinsa ma ta isheshi, dan haka ya ga ya fi buƙatar abincin fiye da maganin, bredi ya siya na goma da kunu na goma, haka ya dinga cin bredin yana kora shi da kunun da ko sugar babu, Alhamdulillah dake ya ci da sunan Allah ya kuma yi hamdala bayan ya kammala sai ya ji ya dawo hayyacinshi, dan haka ya ɗauki jarkokin ya sake nausawa gidan su Ummu dan ci gaba da ɗauko ruwan. *Sa'ilin* da ya gama ɗauko ruwan gabaɗaya ya kwanta a farfajiyar gidan inda ke ɗauke da kayan shinfiɗarshi da duka kayan da suka shafe shi, dan wannan haka ya taso ya gani, ba wani dalili da ke sa ya shiga ɗakin matar Baban nashi, wannan rumfa dake farfajiyar gidan ita ce ɗakinshi kuma wurin hutun shi. Saida ya cire rigar shi saboda zafi ga gumin da ya haɗa sannan ya fara shinfiɗa dan ya kwanta, masifar raɗaɗin da kanshi ke masa duk sanda ya duƙa yasa ya zauna ƙasa ya dafe kan nashi da shi bai ma san ya kumbura ba saida malam Sule ya gaya mishi... *Wani* irin nishi ne ya dinga fitowa daga ɗakin da iyayen nashi suke, rintse idanu yayi da ƙarfi ba tare da ya kalli ɗakin ba ya furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un !" Wannan tashin hankali da me yayi kama? Me yasa mahaifin nashi ke yin haka? Me ya sa suke haka? Me yasa ba zasu yi abun su a sirrince ba? Da sauri ya buɗe idanu shi ya miƙe da sauri ya nufi hanyar fita, ƙofar gida ya je yayi zaune kan dakalin da ruwa ke taruwa na banɗaki, ya gagara sabawa da wannan ɗabi'ar tasu da suke son saba mishi da ita, ya saba da horon yunwa da dukan mahaifinshi, kyara hantara, zagi duk ya saba dasu daga gareta itama, amma wannan abun nasu, tun bai san me ye ba, tun bai san me wannan kururuwar tasu ke nufi ba, tun bai gane menene ke faruwa ba har ya zo a makaranta aka sanar dasu akwai wata alaƙa dake shiga tsakanin ma'aurata, hakan yasa ya fahimci abinda mahaifinshi da matarsa suke aikatawa a irin wannan lokacin, wanda a makaranta malam ya faɗa musu cewa manzo Allah (S. A. W) ya ce kuyi nesa da ko da jariri ne dake bacci daga gare ku, ƙarin bayanin da malamin su ya musu shi ne idan yaro ya kasance hakan na faruwa a kunnuwa shi ko idanu shi, ya kan yi wuya ya manta abun, idan kuma Allah bai shirya maka ba yaro zai yi sha'awar aikata irin wannan abu dan shi ma ya ga ana yi. Wannan ƙuncin ne yasa zuciyar sa karyewa ya fashe da kuka tare da haɗa kanshi da guiwa, bai san me matar Babansa ke so da shi ba? Bai san me take nufi da rayuwarsa ba? Amma gaskiya ya gaji da ganin tsiraicinta, ya gaji da yawan nuna masa tsiraicinta da take musamman idan mahaifi sa baya nan. Bacci ne ya ɗaukeshi daga nan har yayi kwance kan dakalin, mahaifinshi kuma bayan sun gama abinda suke ne ya fito dan yin wanka, ganin baya kwance a shinfiɗarshi yasa ya zuro jallabiya ya fita yana mitar wannan yaro ya rainashi. Samun shi kwance a kan dakalin yasa ya dafe ƙugu yana tunanin ta yadda zai fara tashin shi, daga ƙarshe takalmin ƙafarshi silifas ya cire mai nauyin gaske ya ɗaga iya iyawarsa sannan ya kwantara masa shi a ɗuwawu... Wata mahaukaciyar zabura Jabir yayi idanunshi a rufe gam gam yana ƙwalla ihun "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Hasbunallahu wani'imal wakil !" Duk yana maganar ne yana sosa ɗuwawunshi da ya ji kamar zasu fita, a haukace mahaifin nashi ya sake kashe fuskar shi da gigitaccen mari yana daka masa tsawar "Shiru! Yi min shiru, ɗan iska kawai, maza wuce ciki." Wallahi sai lokacin ma kaɗai ya gane wanene ya dakeshi, dan haka ya dakata daga juyin da yake yana faɗin "Dan Allah Baba kayi haƙuri, kayi haƙuri wallahi ba zan ƙara ba." Bayar da haƙuri da alƙawarin ba zai ƙara ba ya zama jikin shi ta yadda ko bai san abinda yayi ba zai bayar, tsawa ya sake daka masa yace "Wuce ciki nace, in ba iskanci ba da son ka ja min zagi, ga cikin gida miye na fitowa waje ka kwanta Jabir? Dan kawai kana so ka ga a unguwar nan ana zagina da cewa bana kula da kai." Da sauri sumui-sumui ya shiga ciki ya bi bayan shi yana ci gaba da masa faɗan ya kwanta waje. Suna shiga da sauri ya ma manta da ciwon da kansa ke mishi ya shiga yin shifiɗar, yana gamawa ya kwanta lamo duk da a lokacin baccin ya fita idanunshi, hakan yasa ya jima bai yi bacci ba yana tunanin rayuwarshi da burin dake ran shi. *DA SAFE* Shigowarta ɗakin kenan daga wanka tana shirin tafiya islamiyya ta samu Naila ita har ta shirya sai haukan neman kuɗi ta take na jiya duk ta birkice kayan ɗakin, sanin me take nema yasa a tsanake ta ƙarasa shiga tana cire hijabin ta ta aje kan jakar kayan ta tana faɗin "Me kike nema haka?" Ba tare da juyo ba tace mata "Wani abu." Taɓe baki tayi tana kallon bayan data bata tace "Wani abu ko kuma jaka biyu?" Da ƙarfi ta juyo ta sauke dubanta kan Ummu data fara shafa mai, sai kuma ta matso kusanta ta tsuguna da sigar rarrashi tace "Aunty Ummu, idan kin ganta dan Allah ki bani, wallahi ba kuɗina bane Safara'u ta bani ajiyarsu." Da idanu ta tsare ta sai da ta gama maganar tace "Safara'u? Ita ina ta samu kuɗin? Nabila na san ki fa." Marairaicewa tayi tace "Wallahi aunty na Safara'u ne, ki bani na kai mata kuɗnta kar su Mama su ji ma." Jinjina mata kai tayi cike da gargaɗi tace "Na ji zan baki, amma wallahi Nabila idan na sake ganin ki gidan samarin nan dake karatu sai na gaya wa Baba, kin ji ko?" Da sauri ta jinjina kai tana ma Ummun kallon _"Sam aunty ba zaki gane ba, ban da abin ki zan zauna na rayu cikin talauci ne da rashin kayan more rayuwa?"_ Ummu da taji ba tace komai ba ne tace" Ki ban amsa da baki, kuma ma wai in tambaye ki? Me yake kaiki gidan su tunda kinsan duk maza ne?" Da fara ƙaguwa da zancen Nabila ta kyaɓe fuska tace" Aunty ba fa wani abu ke kai ni ba, jiya ma da kika Ganni ɗaya daga cikin su ne ya aikeni na siyo masa abu." Hararenta tayi tace" Ki siyo masa me?" Da alamar rashin gaskiya tace" Sigari, kuma wallahi da naje ban samo ba na maido masa kuɗinsa, amma ba zan ƙara ba, ni dai dan Allah ki bani kuɗin." Girgiza kai Ummu tayi tana ayyana" Allah ya shirya ki." A zahiri kuma kuɗin ta nuna mata inda suke ta ɗauko da sauri ta fice ba tare da ta nemi abin karin kumallo ba, hakan yasa uwar marayu ƙwalla mata kira amma ba ta dawo ba dan kar su tsayar da ita. Mujittafa dake cin nashi ɗumamen ne yace" Lallai yau wace rana? Nabila da ba abinci abinci." Uwar marayu dake tunanin tabbas akwai wani abu, ba dan haka ba Nabila ko me zaka mata bata zuciya da abinci bare kuma ba abinda aka mata, dole sai dai in ta san akwai inda za ta samu abinci, dan so da dama ita ko Ummu ne ke haƙura da nasu abincin su bata ita ta ci, dan in fa bata ƙoshi ba ta kma raki kenan tana kiran cikin ta ba komai. Wannan ne ma yanzu ke haɗata da uwar marayu, dan wata ɗabi'a ta tsira ta shiga gidan maƙwabta ta ɗauki awanni a can tana cin abinci, hakan ya sa take cika dare musamman idan ta san Babansu na wurin sana'arshi. **************** Tunda asuba Baban nashi ya kama hanyar komawa wurin aikinshi, dama kuma haka yake yi, ko yana bakin aiki kasancewar yana da ɗan matsayi sai ya zo wani lokacin ya kwana gida sai yayi sammakon komawa. Tun da yayi sallah bai koma ba ya tafi ɗebo ruwa dan ya ƙarasa cika abinda babu ruwan, yana kammalawa da ɗauki butar da ta ce dole da ita zai dinga ɗiban ruwan wanka dan kar a ɓata mata ruwa. Tana hangenshi ta taga kawai ta fito da ƙaramin towel ɗin ko cinyoyinta bai gama rufewa ba ɗauke da Uzeifatu, tunda ya ga abin dake jikin ta ya sunkuyar da kai yace "Ina kwana Aunty." Harara ta maka mishi sannan ta miƙa mishi Uzei tace "Maza ka shirya min ita wurin aiki zan tafi yanzu kar na maka." Ba musu ya amshi yarinyar da har so take ya ɗauke ta saboda wasa da yake mata, juyawa tayi ta koma ɗaki tana faɗin "Ka kai min ruwan wanka." Nan ma ba musu ya gyara ɗaukar da ya yarinyar sannan ya ɗauko bokiti ya cika da ruwa ya kai mata ya ɗauki kwandon sabulu ya kai mata sannan ya zo ƙofar ɗakin ya tsaya a tausashe yace "Aunty na kai ruwan." Jin shiru ya shi juyawa zuwa ga yarinyar dan ita ma ya shirya ta, yana gama shirya ta yayi daidai da ita ma ta fito kenan ya miƙa mata ita, ruwan da ya ɗiba dan yin wanka ya ɗauka, da sauri ta kalle shi zai shiga banɗaki tace "Me zaka yi?" A ladabce ya juyo ya bata amsa da "Wanka." Cike da takaici tace "Kutumar uban can! Kuma a ganinka zan iya zaunawa jiranka har ka gama ko? To banda wannan lokacin, malam fice min a gida zan rufe ƙofata." Jiki a sanyaye ba gardama ya aje butar ya nufi wurin kayanshi na islamiyya ya ɗauka ya fita hawaye na silalo masa a kumatu, ƙwara yake so yayi wanka ko dan dattin dake jikin shi, a yanzu ba wanda zai ganshi ya yarda cewa wannan Jabir ɗin ne wanda *Fatime* (Fatima) buzuwa ta haifa, dan dalilin da yasa ma kenan kakar shi wacce ta haifi Babanshi take ƙinshi kenan, saboda kawai Bata son Maman shi dan tana buzuwa, ita kuma ta yarda cewa idan ɗanka ya auri buzuwar mace ko babarbara ko zallar bahaushiya to an raba ka dashi kenan, Shiyasa har shi Jabir duk da maraicinshi da shekarunshi lokacin da Maman shi ta rasu bata tausaya masa ba, a cewarta ai saida ta hana Mu'az ya auri Fatime amma bai ji ba, dan haka ba ruwan ta da zuri'ar Fatime. Wata irin kakkarwa jikin shi ya fara tsabar shekararriyar yunwar dake daskare cikin shi, a ƙalla shi dai ya kai sati bai ci abincin gidan uban shi ba, shi ne kawai ke fafutuka yana samun abinda zai ci ɗin. Jin yunwa na neman kayar dashi da sauri ya nemi inuwa ya zauna yana sauke numfashi, tunanin abun yi yake yi amma ya rasa, daga ƙarshe zabura yayi ya miƙe da sauri ya kama hanyar zuwa inda malam Sule ke siyar da wake da bredi da safe har da Shayi. A jigace ya isa wurin nashi, dake safiya ce ko ya samu ana ta msa ciniki, hakan yasa shi rakuɓewa yana hangenshi daga nesa yaa jira ya ga mutanen sun tsagaita, amma da malam Sule ya juyo ya ganshi zaune daga yadda ya ganshi ya bashi tausayi sai ya nufo wurin shi, yana zuwa da kulawa yace "Jabir, lafiya dai na ganka anan zaune? Wani abun za'a baka?" Da Yan kame-kame na kunyar abinda bai saba ba yace "Baban Lukman dama, dama islamiyya zan tafi, kuma gashi Babana har ya koma daji...kuma ina jin yunwa, shi ne na zo ka zuba min abincin idan Babana ya zo zan karɓo k..." Tun bai ƙarasa ba malam Sule yayi dariya ya dafa kafaɗarshi yace "A Haba Jabir, ba komai kaji ko, bari na zubo maka, da kayi magana ma tun ɗazu ai da na baka." Juyawa yai ya koma wurin sana'ar tashi ya fara ƙoƙarin zuba mishi, Jabir dake kallon shi kuma sai yake jin ba daɗi na alfarmar da ya nema, dan haka ma ya ci alwashin ba zai sake neman irin ta ba a dai duniyar nan, gwara yayi aikin ƙarfin zai fi masa alkairi ya ciyar da kanshi tunda dai namiji ne shi. Yadda mai wadatattun kuɗi zai siya à zuba masa haka malam Sule ya zuba mishi, nak yayi bawan Allah ya ƙoshi sosai take nutsuwa da hankalin shi suka dawo jikin shi, godiya ya masa ya tafi makaranta duk da ya makara. *Kamar* yadda yake duk sanda ya taso daga makaranta ya kan dinga watangaririya ne a cikin unguwa har sanda matar Babanshi zata dawo saboda gidan a rufe kuma bata bashi makulli, yau ma hakane, sai dai da yaji ya fara jin yunwa tun kafin ta hauka tashi sai ya tafi wajen malam Sule, ya same shi yana kasuwarsa ta rana wacce yake siyar da salade da bredi da dankalin turawa. Da fara'a malam Sule na ganin shi yace "Jabir har an sauko? Zauna to na gyara maka salade ko?" Kamar ya yi abinda ya ce, sai kuma ya tuna alwashin da ya ci, sai kawai yace "A'a Baban Lukman, zuwa nayi idan akwai wani aikin da zan dinga yi maka sai ka ding bani abinci, Kaga kenan ba kyauta za'a dinga bani ba." Dariya malam Sule yayi ya kalli fuskar Jabir ɗin, yaron nan lokacin da ya sanshi jajir dashi kamar ka taɓa jini ya fito, amma tsabar wahala da shatin duka duk yayi duhu kamar ɗan wiwi, ya girmama tunaninshi da yunƙurin son dogaro da kanshi, duk da shi dai ba wani aiki bane gareshi dayawa, amma dan ya ƙarfafa masa guiwa kan neman na kanshi sai yace "Ai ko Kaga da ka kyauta min, dan kullum da rana gyaran salade ɗin nan ma aiki yake bani, ga kuma wanke wanken kwanuka da shara idan na tashi." Sai kuma ya gimtse fuska yace "kana gana duk zaka iya?" Dariya Jabir yayi yace "Baban Lukman zan iya mana, har girki fa nake yi wa aunty wani lokacin, duka ba abinda ban iya ba ai." Cike da tausayawa yace "To shi kenan, amma kana ganin ba wata matsala daga gidanku?" Girgiza kai yayi yace "Babu, tunda dama idan na taso daga makaranta ma sai dai nayi ta yawo." Jinjina kai yayi yace "Hakane kuma, shi kenan to, Allah ya bamu sa'a da rabo." "Ameen." Jabir ya faɗa da farin cikin ya samu aiki har da tambayar "To yanzu me zan yi?" Wani bugun salade ya nuna mishi yace "Kaga salade nan ɗauki ka fara gyarawa, wanda za'a siyar da daddare ne." Da azama kam ya ɗauka ya fara aikin inda bai gane ba yana tambayawa, yana cikin aikin mlam Sule ya gyara mishi salade ya bashi ya ci, irin farin ciki da murnar daya gani a fuskar shi bayan ya gama ci ne yasa shi tambayar" Ya dai? Naga sai dariya kake kai kaɗai." Ba tare daya daina wannan murmushin ba yace" Na manta ranar da na ci abinci sau biyu ne, yau gashi na ci da safe kuma na ci da rana, a hakan ma duk abinci mai rai da lafiya." Da tausayawa malam Sule ya kalleshi, sai ya ji tsanar uba irin na Jabir, shi ba dan an tabbatar masa da shi ya haife shi ba wallahi b zai yarda ba, dan ko ɗan riƙo iya muguntar da zaka masa kenan. *Rayuwa* na tafiya da daɗi ba daɗi, a gurin Jabir kuma da daɗi take zuwa masa tunda yana ci yana ƙoshi sannan yayi aikin da ake biyan shi, sai dai *mutuwa* riga ce da kowane ɗan adam sai ya sakata, rasuwar malam Sule ta bazata ita ta sake sauya abubuwa da dama, ga Jabir ma yayi kuka tamkar ɗaya daga cikin yaran shi, haka suma iyalinshi sun yi kukan rashin matallafi a garesu. Kamar yadda rasuwarshi ta zanca wasu abubuwa, haka kuma ta sake dawowa da wasu abubuwan, musamman ma tsananta rayuwar uwar marayu da yaran su da kuma son auren Ummu daga wajen Alhaji Kabir. Wannan tsoron na abinda ka iya biyowa baya yasa Ummu ce wa ita fa ta yarda tana so, hakan ya ƙona ran uwar marayu dan lokacin data ce ta yarda wanda Alhaji ya turo yana zaune ne, hakan yasa ya ce tunda dai yarinya na so kawai kar su tauyeta. ****************** Wajen Jabir kuma rayuwarsa ta baya ce ta dawo masa sabuwa, iya aikin matar Babansa kawai yake, idan ya taso kuma ya dinga yawon bin inuwa har sanda za ta dawo, idan tana da abinda zai mata ya yi mata yamma nayi ya sake tafiya islamiyya dan an shiga hutun makarantar boko, idan ta taso kuma yana gida daga magariba har safe, abun takaici abinci ma sai dai ta gyara iya bakin ta kawai, wasu lokuta ma siyowa take ta ce ita kanta bai isheta ba bare ta ba wani. Wannan sabo da ya fara na ci ya ƙoshi Shiyasa yanzu daya fara jin yunwa sai ya ji kamar zai mutu, ana cikin haka wani abun yayi sanadin faruwar wani abun. Yunwar da yake ji yasa ya ga idan ma yayi zaune za ta addabe shi ne, dan haka ya shiga zagayen unguwar cikin nutsuwa, yana kawowa daidai wani gida wata mata da alama ma'aikaciya ce saukowarta kenan daga aiki tana kan babur ɗinta tace "Ɗan saurayi zo mana." Da sauri ya zo yana faɗin "Ina wuni?" Da fara'a ta amsa da "Lafiya lau, nace ba dan Allah a unguwar nan kake?" A nutse ya amsa mata da "E, gidan mu na can baya." Da rarashi tace "Dan Allah ko zaka iya ɗauko min ruwa? Almajirina ne baya nan ya tafi garinsu, gashi na sa mai ɗauko min ruwan." Bai yi tunanin abinda zata biya shi ba, hasalima hakan bai zo masa ba a lokacin, abu ɗaya da ya tuna shi ne ai idan ya fara aikin ma zai bar jin Yunwar, dan haka yace mata" To aunty, kawo inda za'a ɗebo." Da jin daɗi yadda ya amsa mata ba gardama dan jiya wuni tayi ba ruwa sai ita ke ɗaukowa a wahalce ta ƙarasa shiga ciki da babur ɗin ya bi bayan ta, bokiti ta bashi tace" Yawwa gashi, amma dai za ka iya ko? Dan sau uku ake min da shi." Dariya yayi yace" Zan iya aunty, ni da nake ɗauko jarka biyu a tare." "Da gaske?" Ta faɗa har da zaro idanu, jinjina kai yayi ya sunkuya ya aje kayan makaranta shi sannan ya fita daga gidan, dake abu ne daya saba kuma ya taso babu kasala da son jiki, sai gashi dan danan ya gama zub mata ruwan ya ce ya ida zai tafi, fitowa tayi da plate a hannu tace "Karɓi wannan to ka ci, ga kuma wannan..." Ta ske miƙa mishi kuɗin da ya saka shi ɗaga ido ya kalle ta da rashin fahimtar me take nufi, saida ta sake cewa "Karɓi mana." A raunane yace "Aunty kuɗin fa?" Murmushi tayi tace "Na aikin ka ne mana, Karɓi nagode ka ji." Saje kallon hannun ta yayi dake riƙe da dala hamsin ba ko canji, ga kuma plate da miyar nama da guntun bredi, karɓa yayi da hannu biyu yana ta godiya ya koma gefe ya zauna ya fara ci, yana ci hawaye na zubo masa har cikin kwanon abincin, ganin bashi da maraba da almajiri, duk da kalmar almajiri na nufin mai neman ilimi ne, amma na zamanin yanzu yana nufin *marasa gata* ne, shi kuma ya rasa wannan gatan, kenan shi da almajiri ko maraya duk uwa ɗaya ce ta haife su. Yana idawa yayi sallama ya bata plate ɗin, har zai fita sai kuma ya dakata yace "Aunty, nace gobe ma zan iya zuwa na kawo miki ruwan?" Da farin cikin jin haka tace "Me zai hana, ai nima ban maka magana bace dan na ga har da kayan makaranta jikinka da alama kaima ɗan gata ne, amma in zaka iya ai ba damuwa." Dariyar yaƙe kawai yayi yace "To shi kenan, na zo goben." "Allah ya kai mu." Ta faɗa tana bin shi da kallo har ya fice, wannan ne sanadin da ya sa Jabir ya zama *ɗan ga-ruwa*, dan kuwa wata amarya m'a da aka kawo unguwar ba jimawa mijin da kanshi da ya ga Jabir na kawo ruwa nan ya msa magana ya ce ya dinga kawo mishi, sannu sannu sai gashi yana ɗauko hayar kura da jarkoki yana kawo musu ruwa har ma da wasu gidajen kuma ba tare da Sanin kowa na shi ba. Sai dai ita kanta matar Babanshi ta lura da rashin zamanshi yanzu daga magariba har zuwa safe, sannan ta daina ganin shi da alamar yunwa, hasalima har ƙarar canjin kuɗi take ji wasu lokuta a aljihun shi kafin daga bisani ya dinga bawa malamar makarantar nan tana saka masa a asusu. *ME CE CE DAMUWAKI*? Rashin ni'ima? Rashin gamsar da mai gida? Warin gaba? Bushewar gaba? Ƙaiƙayin gaba? Kurajen gaba? Zubewar nono? Cikowar nono ? *Kina buƙatar...* Fatarki tayi laushi? Tayi santsi? Ta kwanta luf? Kina walkiya da annuri tamkar amarya? Sabulu kike so ko haɗin shafawa ki wanke ko mai na shafawa? Ki wadatu da sahihin ƙamshin haukata mai gida? Humra da zaki saka mijinki bacci bai shirya ba? Humra da zata tayar da sha'awarsa? Kulaccha da zata saka mijinki ya kasa yi miki tsara a fannin ƙamshi? Kulaccha da zata gagari manyan mata suffanta kalar sunan turarenki? Turaren wuta irin na asali barebari? Turaren da zaki fesa à zanin gadonki har ya rike mai gida ya kasa tashi? Turaren da zaki zuba ga ruwan wankan mai gidan ki? Turare don yaranki? _Idan duka kina buƙatar ɗaya daga cikin kayan nan, to ki tuntuɓi wannan lambar ta WhatsApp *82-21-91-74* wanda suk gwada sun san ingncin kayanmu, ba buƙatar ɓata lokacin cika muku baki._ Wani abun farin ciki kuma, duba da yanzu ba kowace mace ke son shan garin magani ko matsi ba, akwai haɗi irin su *tsumi*, *ruwan tsumi*, *tukunya*: dayawa sun san tukunya, don da itace muke tutiya, kuma tukunyar nan akwai na ruwa dana dafawa a nama, sannan akwai kankat wato haɗin *kayan marmari*. *Garabasa* Ga waɗanda sukayi nisa kuma haɗin kayan marmari ba zai kamacesu ba, duba da kafin sakon yaje garesu zai fara lalacewa, don haka ga sauki ya samu, madadin kuɗin mota da zaki yi, zaki biya 1000k kacal don a sanar dake yadda zaki had, ba iya guda kawai ba, dama sauran haɗi irin na kayan daya shafi na marmari da ɗanye, musamman ma *sirrin kankana* da kuma *cucumber*. *JANNAT HOUSE.*🧕 *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HARUN* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *3* *Wata huɗu* Jabir yana ga-ruwa a cikin unguwarsu yana tara kuɗin shi, dan burinshi shi ne idan aka yi ƙaramar sallah zai fasa asusun ya siyo wasu abubuwa da ya ga za'a iya siya à unguwar nan ta su, duba da duk inda ake siyar da abubuwan buƙata sai anyi tafiya mai ɗan nisa sannan an tsallaka titi, hakane yasa yake da burin kafa nashi teburin shi ma ya tsaya da ƙafafuwansa. *Wata biyu* da ya wuce ya fara kai ruwa gidan wasu samari su uku da suke hayar wani gida suna karatu, rashin tarbiyarsu da abinda suke aikatawa marar kyau a gidan ya dameshi sosai, sai dai tunda bai da ikon hanawa sai kawai yake ƙyamatar abun da gabaɗaya zuciyar sa. Yau ma da rana ya kawo musu ruwa kamar kullum, yana zuwa ya ƙwanƙwasa kamar yadda yake yi, daga ciki aka tambaya da "Wa ye?" A nutse ya amsa da "Ni ne, ruwa na kawo." Ya kusa minti ɗaya kafin ya ji an zare sakatar daga ciki, wangale ƙofar aka yi amma bai ga wanda yaai buɗe ba, hakan yasa shi dai ɗaukar jarkokin biyu ya shigo yana yin sallama da kallon takalmin mutanen dake bakin ƙofar shiga falon dake nuni da mata ne da maza a ciki, ga hayaƙin dake ta fitowa daga ciki da warin shisha ko yace ƙamshin flavour kamar yadda suke faɗa. Har ya fara buɗe bakin jarkar ya ɗaga zai bulbula a cikin babban bokitin da yake zuba musu ya ji an dafashi daga baya, hakan ba ƙaramin tsoratashi yayi ba dan ya ɗauka wanda ya buɗe masa ƙofar ma ai har ya koma ɗakin saboda zafin da ake kwararawa. Gaban shi ne ya fara faɗuwa sosai kafin ya shiga firgicin ganin abinda bai taɓa gani ba, yana ganin tsiraicin matar Baban shi, amma bai taɓa ganin irin wannan ba haka, wata kakkaurar budurwa daga ita sai bras da pant, ba abinda ke jikin ta bayan waɗannan sai takalmi, to dafashi da tayi da wata manufa tayi ko? Abinda ya tambayi kanshi kenan. Sai dai kafin ya samu amsa cikin tatausa murya ba tare da ta ɗauke hannunta ba tace da shi "Jabir, idan ka gama zuba ruwa ka shigo ciki, zamuyi magana da kai." Jabir da tunda ya ga shigar dake jikin ta bai sake kallon inda take ba jinjina kai yayi alamar to sannan ya ci gaba da zuba ruwan, bai yarda ya kalli bayan da ta juya ba don komawa falon, sai dai har lokacin yana jin gabanshi na faɗuwa dan sosai yake ji a jikinshi wata manufa ce yarinyar take da a kanshi. Jarka uku ya zuba musu sannan ya ƙwanƙwasa musu ƙofar falon tare da faɗin "An zuba ruwan." Daga ciki muryar namiji ya bashi umarni da "Shigo." A sanyaye ya ɗaga labulen ya shiga, irin yadda maza biyun ke jikin wasu ƴan matan biyu duk da shigar da bata rufe tsiraicinsu ba yasa Jabir sunkuyar da kanshi ya tsaya daga ƙofar, ɗaya daga cikin samarin ne ya ciro kuɗi kamar kullum ya miƙa mishi yana faɗin "Gobe kar ka kawo ruwa, dan a makaranta zamu wuni saboda jarabawar da zamuyi." Da sauri Jabir da ya matso ya bar ɗakin ko dan hayaƙin da ya gauraye ɗakin wanda ya ga budurwar da ta ce zasu yi magana tana ta busawa ya zura hannu ya karɓa yana faɗin "To." Da azama a juya ko godiyar da ya saba yi wa duk wanda ya biya shi haƙƙinshi a take bai yi ba saboda son ya bar wurin, har ya yaye labulen zai fita budurwar nan ta miƙe tsaye tace "Jabir." Dakatawa yayi ya juya ya kalli gefen da take yana sissine kai, takowa ta fara yi tana matsowa inda yake, hakan yasa duk ya sha jinin jikinshi, kusan shi ta tsaya tana ƙarewa ƙasan shi kallo da kuma kyakyawar fuskarshi da take ganin idan har ya bata haɗin kai za ta mayar da shi babban yaro, hakan kuma ba ƙaramin fito da asalinshi na buzu zai yi ba, dan ko tambaya babu da Kaga Jabir ka ga mahaifinshi ka san mahaifiyarsa ce duk ya ɗauko, hatta da gashin shi mai saurin tsayi da mummurɗewa. Cikin wani irin salo da fara buguwa da abubuwan da take sha tace "Jab..ir, zo muje ciki..muyi magana." A ɗarare Jabir da duk tsoron lamarin matar ya kamashi ƙara ja baya yayi sannan yace "Idan wani abu zan siyo miki ki kawo kuɗin." A nutse ta sake matsawa daf da shi shima kuma ya ja baya tana cewa "A'a Jabir, ba abinda za ka siyo min, ni da kai ne nake so..." Yadda take ƙoƙarin ɗora hannun ta a sashen da ko ubansa baya so ya kai nashi hannun a waje bare kuma wani daban yasa shi saurin ƙoƙarin zagayawa ta bayanta dan inda take tsaye kamar ta tare ƙofar ne yana faɗin" Kiyi haƙuri, ina sauri ne zan kai ruwa wani wuri." Kafin ta ankare ya fice a ɗakin da sauri ya tattara jarkokinshi ya yi gaba, ƴan matan biyu dake kwance ƙafafun samarin ne suka saka mata dariya inda ɗaya ke faɗin" Maganin ki kenan jarababiya, ke in ba ɗaukar hankali ba ina abun so yake ga yaron can almajiri? Gashi yanzu a banza ya wulaƙantaki." Tsaki tayi tare da komawa inda take ta zauna, hakan yasa ɗaya daga cikin samarin ya kalle ta yace" Tunda mu mun kasa yi miki yadda kike so ai sai ki bishi ko, na rantse da Allah yau sai kin bar gidan nan." Harara ta dalla mishi tace" Ka ga ba ruwan ka, ba kai ka kawo ni ba dai." Cike da gadara yace" Bani na ne ba, amma shi wanda ya kawoki ai ni na kawoshi." Ɗaya daga cikin ƴan matan ne tace" Kinga kedai yanzu kiyi shiru, kai ma kuma ka bar cewa za ta bar gidan nan, ka san ku kuka gayyatomu tun daga garinmu, ina ta sani nan da za ta je?" Cike d takaici saurayin yace" Ta san da haka ita shine zata maƙalewa wani yaro, dama zuba mata idanu nayi naga tsiyarta, ina abun burgewa yake a jikin yaron can? Ina ma abinda zai iya ɗura mata bare tasan har an shigeta? Kawai gantalewa ce irin taku ta ƴaƴan tasha?" Cikin faɗa da takaici ita ma budurwar tace" Na gaya muku ba ruwan ku dani, rayuwa ta ce kuma zanyi abinda nake so ne, dan kun gayyatomu ai ba auren mu kuka yi ba da zaku hanamu kula wasu, kuma Jabir ni naga abinda na gani a jikin yaron, Shiyasa nake so na reneshi dan ya zama tamkar bawana ni kaɗai, idan Kaga ba zaku iya ba ku sallamemu mana muyi gaba." Caaaa! Ƴan matan suka yo mata suna faɗin me yasa za ta ce a sallama su? Nan ɗin fa ga wuta, ga ruwa, ga abinci wanda ransu yake so shi suke siyo musu, kuma ba dafawa suke ba a gyare ake kawo musu shi, gidan kuma idan suka koma me zasu yi? Ɗaya daga cikin su kawai gidansu ke da wuta, amma dukansu babu mai tabbaci zai samu abinda zai ci da rana idan ya gama cin na safe. ******************** Ummu ta kalla tana saka hijab ɗin ta tace "Bari in leƙa in ga idan Arɗo ya dawo daga kiwon, ina so ya siyar min da akuya ɗaya sai muyi walimar bikin da ita." A kunya Ummu Kulsum tace "Mama, ba zaki bari gobe da safe sai kije ba? Ko kuma ni ki turani tunda kinga fa sai jibi ne zaki fita daga takaba, kuma fitar nan ba dole bace." Murmushi tayi tace "A'a Ummu, ina zamuyi wannan abun kunyar, ke da zuwa cinikin akuyar bikin ki? Bari dai ni na je ai ya zama dole." Jinjina kai Ummu tayi tace "To Mama sai kin dawo." Jinjina kai ita ma tayi tare da kallon Nabila dake kwance tace "Shanshani uwar yawo, idan na fita kuma ki fice kema." Dariya Ummu tayi tana kallon Nabila data turo baki gaba tana gunguni tace "Karki damu Mama, ba za bari ta fita ba ma." "Shikenan to." Ta faɗa tana ficewa daga tabkeken gidan, Nabila na jin haka ta tabbatar Ummu ba zata bari ta fita ba, kuma gaskiya tana so ta fita dan wannan kullen da aka mata yau dake ba makaranta ba ƙaramin taɓata yayi ba, bata leƙa gidan samarin nan ba yau, kuma dama tana musu ƴan aikace aikace irin su shara, gugar ɗaki da siyo wani abu, wani lokacin ma idan suka siyo nama ko ƙwai ita suke ba ta sarrafa musu ita ma ta ci ta ƙoshi, ga kuma kyakyawan biya da saurayin ke yi mata wanda take ganin yanzu yana sakar mata fuska sosai da kulawa da ita, to kulawa mana, tunda komai suka ci sai ya aje mata ko bata nan. A hankali ta tashi daga kan tabarmar tana faɗin "Aunty Ummu gyara daga nan na ɗauko kayan shinfiɗa." Kallonta Ummu tayi dake duba littafinta na siratul-nabawiy tace "Tun yanzu zaki kwanta yau?" "Umm." Ta faɗa tana shigewa ɗakin, a tsanake ta dinga fito da kayan tayi shinfiɗa Ummu na karatunta, tana idawa ne ta ɗauki buta sai ɗan kwali a kanta ta shiga banɗaki, sai dai tana shiga tsaf ta fito cikin sanɗa ta zagaya ta bayan bukkar su Lukman dake suna kusa da ƙofar shigowa ne ga kuma duhu ta wajen su dan fitila ɗaya ce mai bada haske duka girman gidan, hakan ya sa Nabila ficewa daga gidan ba tare da Sanin Ummu Kulsum ba. Yana hanyarshi ta komowa gida cike da taraddadin masifar da zai sh gurin matar Baban shi saboda daren da yayi, kuma hakan ya samo asali ne sakamakon fita da amaryar nan tayi dan haka ita bai kai mata ruwa da rana ba sai yanzu mijin ya nemoshi ya ce ya kai musu, sai kuma ya samu su Lukman na shayar da dabbobin ƙanin mahaifinsu Arɗo ga kuma wasu suma zasu ɗibi ruwan. *Nabila* ya gani tana fitowa daga gidan nan, da mamaki ya shiga binta da kallo tana gabanshi yana binta a baya kamar a tare suke, duk da ba wani abu da ke haɗashi da mutanen gidan, Mujittafa ne kawai suke gaisawa har sukan iya tsayawa suyi hira, amma ko lokacin da yake aiki tare da margayi idan ya shiga gidan dan kai masa kayan sana'arshi, ko kuma ya aiko shi ya kawo musu kuɗin cefanai ko idan an raga abincin ya turo ya kawo musu, sannu kaɗai ke haɗashi da yaran. Dan haka yanzu ma bai ce mata uffan ba har tayi gaba shi kuma ya shiga gidan su da sanɗa saboda rashin sanin abinda zai tarar. Gabaɗaya ƙofar farfajiyar ya tarar a rufe, dan haka ya ɗan ɗaga hannu ya bubbuga ƙofar a nutse, shiru ba motsi ba kuma alamar za'a kula shi, dan haka ya ci gaba da bubbugawa a nutse da tunanin tayi bacci, ko kuma tana uwar ɗaki suna waya da mahaifinshi, dan in suna wayar nan bata jin komai da kowa. Ya ɗan jima yana bubbugawa kafin ta taso ranta a ɓace cike da masifa tace "Wanene?" A ladabce sosai cikin ruwan sanyi yace "Aunty ni ne." Cike da gatsali tace "To sai aka yi me? Ka dawo daga gantalin ne yanzu ka zo in buɗe maka ƙofa? To bari kaji yaro, wallahi daga yau na zo gidan nan baka nan rufe ƙofata zan dinga yi, dan ni ba ƴar iska bace da zan dinga jiran sanda ka dawo sannan na rufe ƙofata, unguwar nan da mutum ma tsaf za'a yankashi har yayi mushe ba wanda ya sani, shine zan kai ƙarfe goma ban rufe ƙofa ba?" Duk ratatun masifar nan da take idanunshi a lumshe suke, ga gajiya a tare dashi, ga matsanancin bacci, ga kuma rashin son hayaniya a rayuwarsa, cikin nutsuwa ba tare daya buɗa idanunshi ba yace" To aunty, kiyi haƙuri dan Allah, ba zan ƙara ba daga yau." Wani dogon tsaki taja tare da faɗin" Ka ma ƙara mana, dan yau ba za'a kwana min gida ba, ko ka koma inda ka fito, ko kuma ka kwana a nan." Jin takon tafiyar ta alamar tana komawa ciki yasa shi saurin cewa" Aunty Dan Allah? Dan girman Allah ki buɗe min, wallahi ba zan sake kai magriba a waje ba." Bata kula da tsiyarshi ba, hasalima sai ji yayi tana rufe ƙofar ɗakinta sannan ta kashe wutar waje, wanda hakan yasa ɗan hasken ma da yake gani ya ɗauke, ajiyar zuciya ya sauke yana tunanin mafita, ina zai je? Wa ya sani? Wa zai bashi wurin kwana? Idan ya kwana nan a tsaye kenan? Cikin gidan ma ya aka ƙarata da miyagun ƙwari bare kuma nan farfajiyar da duk shukoki suka fito tamkar wata gona saboda damina da ta soma wucewa ma. *Dalilin* zaman da yayi a farfajiyar gidan a wannan dare saida ya kashe wani ƙwaro da ake kira namijin kunama har guda biyu, sanin cewa duk inda aka ganshi to tabbas kunama na kusa yasa bai yi zaune ba sai kai da kawo, sai ya gaji ne yake jingina a bango har sai bacci yayi kamar zai ɗaukeshi sai ya farka. Abun ka ga bacci ɓarawo sai da ya zaunar dashi nan ƙasa ya ɗora takalmin shi ya zauna ya haɗa kai da guiwa, a cikin baccin nan daya kwashe shi mai daɗin gaske saboda gabatowar asuba kawai yaa zabura yana salati tare da miƙewa tsaye yana duƙawa da sosa damtsen ƙafarshi da ya ji an tsikareshi. Duk dubawarshi bai ga wani abu ba da zai ce shine ya cijeshi, kuma gashi ba cizon cinnaka ba, jin an fara kiran sallah sai kawai ya juya ya bar gidan, fanfon gidan su Ummu ya je yayi alwala ya nufi masallaci, sai dai har lokaci yana sosa ƙafarshi saboda tsira masa da take. *Bayan Kwana Huɗu* Duk da tafiya yake, amma haka ya ɗan dakata ya zura ƙafar ɗaya ya sosa ƙafarshi wanda ya tattare Ƙafar wandon har wuce ijiyar-sau, da azama ya ci gaba da tura kurar ruwan da yake ɗaukowa haya dan so yake yayi sauri ko ya gama ya zauna ya huta saboda Ƙafar nan tasa sai ruwa take yi. Yana karyo kwana kenan ba tare da sanin zai ganta a nan ba sukayi kiciɓis, matar Babanshi ce yau bai san me ya dawo da ita da wuri daga wurin aiki ba, tana kan babur ɗin ta tare da wata mace da alama gaisawa suke yi, cikin rashin jin daɗin ganin ya turo ruwan nan sannan matar da suke gaisawa ma yana kai mata ruwa ya lumshe idanu tare da ci gaba da turawa dan dukansu sun ganshi tunda suna kallon kwanar ne. Yana kawowa daf da su da ladabi ya kalle ta yace "Sannu da dawowa aunty." Sai kuma ya kalli matar dan yasan ba amsa masa zata yi ba yace "Ina kwana?" Da fara'a matar ta amsa mishi da "Lafiya lau Jabir, har an ɗauko ruwan?" Kasa amsa mata yayi sai murmushi kawai, ita sam bata san akwai sanayya tsakanin Jabir ɗin da Bara'atu ba bare wata dangantaka ko alaƙa, dan haka da taga yayi haramar wucewa sakamakon kallo mai ma'anoni da mamakin ganin shi da kurar ruwa da matar Baban nashi ke masa yasa ta cewa "Jabir, idan ka kai ruwa dan Allah ka sake tunawa Firdausi ta kai min niƙa kafin na dawo, dan na barosu suna kallo tana iya mantawa." Sororo Jabir ya juyo ya kalle ta, sai kawai ya jinjina kai ba dai tare da ya amsa ba, kuma hakan bai dame ta ba ita ma dan a zaman da sukayi ta fahimci yaro ne miskili da bai cika magana ba, dan ko yaran ta suna son janshi da wasa da hira, amma shi sai dai yayi shiru ko murmushi bai cika magana ba. Har ya wuce Bara'atu na sake juyawa ta kalle shi, sai kuma ta kalli matar nan tace "Maman Firdausi, waccen yaron shi yake kai miki ruwa?" Da fara'a tace "E wallahi, kin san ruwan nan idan ba tsayayye gareka ba sai ka sha wahalar rashin ruwa, amma Kinga tunda na samu Jabir wallahi hankalina kwance, gashi baya da matsala yaron wallahi komai kika bashi karɓa yake yayi godiya." Tsura mata idanu kawai tayi tana jinjina kai, a zuciyar ta kuma hangowa take har ta faɗawa ubansa ce wa ya zama ɗan ga-ruwa da yadda zai dakeshi, da haka sukayi sallama matar na ƙorafin Bara'atu bata taɓa leƙawa gidan ta ba, ita kuma tana murmushi tana cewa za ta je, amma a ranta ayyanawa take _"Me zan je na tsinta, ni sam rayuwarku bata min ba."_ Ƙwarai Jabir ya san ya kaɗe, dan haka yana gama kan ruwan ya mayar da kurar, cikin kuɗin da ya samu yau bai kai wajen madame ta aje masa ba kawai ya tafi da su ya siyo su alawa da biscuit da saurensu da niyyar kai wa Uzei, hakan ko zai sa ya zama toshiyar baki ga matar Babanshi. *Har* zai wuce ta ƙofar gidan samarin nan ya hangi Nabila tana ɗiban ruwa dake ƙofar a buɗe take, yanayin da ya ganta kuma ruwan a bokitin wanka ne ta ɗiba za kuma ta shiga banɗaki sannan da ɗaurin ƙirji yasa shi dakatawa. Abinda bai taɓa tunanin yi bane ya aikata, dan kuwa tsaf ya tura ƙofar da sauri ya shiga tare da kallon ta sa'ilin da ta ji tsoro ta tsaya turus dan bata ɗauka ƙofar a buɗe take ba, cikin taushin murya amma kuma a kausashe yace "Ke Nabila, wai ba na ji Ummanku tana hanaki zuwa gidan nan ba? Me kike yi hka da zkiyi wanka bayan ga gidan ku?" Turo baki tayi tna kawar da kai ba tace komai ba, a tsawace ba alamar wasa yace "Maza canza kayan ki ki bar nan ko naje na sanar da Ummanku." Jiki a sanyaye dan Jabir tsaran Yayanta Mujittafa ne ta aje bokitin ta juya da niyyar komawa ta sako kayan ta ta fita, sai dai saurayin da yayi nasarar ribantar yarinyar yau bayan jimawa yana kwaɗayinta, yau gashi har ta saki jiki dashi sukayi wasa har ta zama silar tsiyayar da ruwan jarabarshi, hakan ba ƙaramin daɗi ya masa ba dan yana hango yadda haɗuwarsu ta gaba zata kasance har ya kai ga zuwa matancinta. Dake ya fi Jabir shekaru sosai sai kawai ya haɗe fuska yace "To kai ina ruwan ka? An gaya maka b'a san ta zo bane? Kaga fita a nan, ruwa ne kake kawo mana ka bar shi daga yau bana so, kuma idan na sake ganin ka saka mata ido wallahi zaneka zanyi." Da sauri Jabir ya kalli tsakiyar idanun saurayin, sai kawai wani murmushi ya so suɓuce masa amma sai ya dake kawai, tabbas ya girmeshi kuma zai iya wahalar dashi idan dakuwa zasuyi, amma ya zaneshi? Sam abune da ba zai yiwu ba, to ai ko mahaifinshi biyayya da girman haihuwa ne yasa yake yin shiru yake Dukanshi, amma ba duk da haka da yaya yake tanƙwarashi yanzun? A gadarance tamkar wanda ya taso a gidan sarauta ya kalli Nabila fuskar shi a haɗe yace "Na ce ki ɗauko kayanki ko?" Da sauri sauri Nabila ta kama hanyar ɗakin, hakan ya ɓata ran saurayin har ya matso daf da shi yace "Kai! Wai raina mutane ne kayi? Ina ruwan ka da ita? Ka fice min anan nace ko?" Ba alamar tsoro Jabir yace "Ita nake jira dama, da ta fito ai fita zanyi." Cike da takaici saurayin yace "OK, haka ka ce? To ina zuwa, dan Allah idan ka isa ka tsaya na same ka a nan." A fusace ya juya zuwa cikin ɗakin, da kallo Jabir ya bishi sannan ya taɓe baki ko a jikinshi, bai gusa daga nan ba, bai matsa daga inda yake ba har saurayin ya fito tare da Nabila a bayanshi shi kuma yana riƙe da belt ɗinshi. Saida yayi mamakin sake ganin Jabir ɗin tsaye bai tafi ba, hakan yasa har yaji anya kuwa? Karfa a zo ya sha ruwan kunya! Ai kuwa yana zuwa a fusace cike da son birge Nabila ya ɗaga belt ɗin nan zai zabgawa Jabir yana faɗin "Kai marar kun..." Tun bai ƙarasa faɗa ba Jabir ya riƙe belt ɗin a fusace shi ma yana faɗin "Wallahi ka dakeni ba zan kasa ramawa ba tunda baka haife ni ba." Da gudu Nabila ta ƙaraso ta shiga tsakiyarsu tana faɗin "Dan Allah Ashir ka ƙyaleshi, ka rufa min asiri kaji? Kai baka san idan kuka yi hayaniya aka shigo ba nan za'a san me ya faru bane?" Hakan yasa Ashir ɗin dakatawa tare da nuna musu ƙofa dukansu yace "To ku fice min a nan kafin na ji wa wannan yaron ciwo." Nabila ce ta fara yin gaba tana cewa Jabir "Muje dan Allah." Bin ta yayi a baya suka fita daga gidan, tunda suka fita kuma bai ce mata ƙala ba, tana dai gaba yana biye da ita a baya kamar mai tsaronta, ganin sun tunkari gidansu wanda kafin ta fito ma ta baro mutanen arziƙi da maƙota ana ta shirye shiryen ɗaurin auren aunty Ummu gobe, ita kuma dama sam auren Alhaji Kabir ɗin bai mata ba Shiyasa ba ruwanta da sabgar, tunanin kar ya je ya tona mata asiri ya sa ta juyowa ta tsaya a marairaice tace " *Yaya* Jabir, dan Allah dan Annabi kar ka faɗawa Mama ka ganni zani wanka a can, dan Allah kaji?" Yana so ya mata magana, irin maganar nan ta Yaya da ƙanwa, faɗa yake so ya mata mai cike da hargagin da zai iya ɗauke fuskar ta da mari, sai dai kashh! Bakin shi ya masa nauyi, sannan yana ganin ai bai da wata alaƙa da ita da idan ya faɗa zata ɗauka har tayi anfani da shi, dan haka sai kawai ya bita da wani kallo kamar na ki shiga hankalinki sannan ya raɓata ya ci gaba da tafiya. Gadan gadan gidansu ya tunkara, dan haka ta dinga binshi cikin sanyin jiki har suka isa ƙofar gidan. *ME CE CE DAMUWAKI*? Rashin ni'ima? Rashin gamsar da mai gida? Warin gaba? Bushewar gaba? Ƙaiƙayin gaba? Kurajen gaba? Zubewar nono? Cikowar nono ? *Kina buƙatar...* Fatarki tayi laushi? Tayi santsi? Ta kwanta luf? Kina walkiya da annuri tamkar amarya? Sabulu kike so ko haɗin shafawa ki wanke ko mai na shafawa? Ki wadatu da sahihin ƙamshin haukata mai gida? Humra da zaki saka mijinki bacci bai shirya ba? Humra da zata tayar da sha'awarsa? Kulaccha da zata saka mijinki ya kasa yi miki tsara a fannin ƙamshi? Kulaccha da zata gagari manyan mata suffanta kalar sunan turarenki? Turaren wuta irin na asali barebari? Turaren da zaki fesa à zanin gadonki har ya rike mai gida ya kasa tashi? Turaren da zaki zuba ga ruwan wankan mai gidan ki? Turare don yaranki? _Idan duka kina buƙatar ɗaya daga cikin kayan nan, to ki tuntuɓi wannan lambar ta WhatsApp *82-21-91-74* wanda suk gwada sun san ingncin kayanmu, ba buƙatar ɓata lokacin cika muku baki. Wani abun farin ciki kuma, duba da yanzu ba kowace mace ke son shan garin magani ko matsi ba, akwai haɗi irin su *tsumi*, *ruwan tsumi*, *tukunya*: dayawa sun san tukunya, don da itace muke tutiya, kuma tukunyar nan akwai na ruwa dana dafawa a nama, sannan akwai kankat wato haɗin *kayan marmari*. *Garabasa* Ga waɗanda sukayi nisa kuma haɗin kayan marmari ba zai kamacesu ba, duba da kafin sakon yaje garesu zai fara lalacewa, don haka ga sauki ya samu, madadin kuɗin mota da zaki yi, zaki biya 1000k kacal don a sanar dake yadda zaki hada, ba iya guda kawai ba, dama sauran haɗi irin na kayan daya shafi na marmari da ɗanye, musamman ma *sirrin kankana* da kuma *cucumber*. *JANNAT HOUSE.*🧕 *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HARUN* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *4* Cikin sa'a yana shiga gidan ya ci karo da Ummansu tana ɗaukan itace daf da shiga ƙofar, da fara'a da sakin fuska suka gaisa kafin a saiɓance ya shiga nuna mata ciwon dake ƙafarshi yana faɗin "Umman Lukman, dama ciwo ne Naji, to ƙafata sai kumbura take kuma tana yin ruwa, shine nace dan Allah idan kin san maganin da zan yi anfani da shi ki faɗa min?" Cike da kulawa da tausayawa ta duƙa tana duba ƙafar tana faɗin "Subhanallah! Jabir me ya sameka a ƙafar?" Kafin ya bata amsa kuma sai tayi saurin ɗagowa tana kallon shi tace "Kai! Jabir ai wannan shegen ciwon ne, wani abu ya cijeka ne?" Gaban shi ne ya fara faɗuwa jin ta ce shegen ciwo, sai kuma tayi saurin fara takawa tana faɗin "Biyoni Jabir, akwai magani a wurina ma." A hankali ya shiga takawa yana binta yana kuma gaishe da matan dake gidan suna ta hayaniya, har cikin falonsu ta umarce shi da ya shigo, bin umarni ta yayi ya shiga ya zauna bakin ƙofa akan tabarma dake ba kowa a ɗakin, uwar ɗaki ta shiga jim kaɗan ta fito ta fita waje jim kaɗan ta sake shigowa riƙe da ludayi a hannun ta, tana zuwa ta zauna kusanshi tace "Mu ga ƙafar?" Zuro ƙafar yayi yana kallo ta laƙato maganin a yatsarta sannan ta rufe ido tana motsa bakin ta alamar wani abun take faɗa, sai kuma ta riƙe ƙafar tashi kusa da ciwon ba tare da ta buɗa idon ba, ta jima haka kafin ta buɗa idanun ta sannan shiga shafa mishi maganin tun daga kan ciwon har zuwa zagayenshi, saida ta gama shafa mishi sannan ta miƙo mishi wani ƙullin tace "To ga wannan, idan zaka kwanta sai ka sake shafawa, gobe ma haka zaka yi, in sha Allah zuwa jibi za ka ga ya ƙame tare da maganin..." Sai kuma tayi murmushi tace "Wannan maganin na ɗaya daga cikin laƙaninmu, wannan ciwon naka zai warke ne ba tare da yayi ruwa ko jini ba kamar yadda aka saba gani, zai ƙame ne kawai kuma zai kashe wanda ke cikin jiki ba idan ya sakar maka wasu dafin a jiki, sannan kariya wannan ciwon ba zai sake harbin ka ba sai dai wani ciwo daban kuma." Da jin daɗi sosai Jabir kamar zaiyi kuka yace" Nagode sosai Umman Lukman, Allah ya saka da alkairi." Murmushi ta masa tana kallon fuskarshi cike da tausayawa tace" Ba komai Jabir, sai dai har sanda ciwon zai warke kar kayi ta'ammali da abincin da ya shafi wake da hatsi." Jinjina kai yayi sai kuma ya shiga miƙewa yana faɗin" To Umman Lukman, kuma shi ma wannan ciwon zan iya shafa mishi wannan maganin...?" Yayi maganar yana ƙoƙarin ɗaga rigar shi sannan ya ci gaba da faɗin" Shima kwana biyu kenan yau nake jin ciwo a wuri kuma kamar ya kumbura shi ma." Miƙewa tayi tana kallon bayan nashi can sama kusa da kafaɗa, dai dai lokacin kuma *Ummu Kulsum* ta fito daga uwar ɗaki ta sauke duban ta kan bayanshi da kaso biyu cikin uku duk raɗo raɗon shtin bulala ne da ya masa baƙi abun ka ga fatar dake da haske. Daga Ummu har Mama dukansu sun san zaman da yake a gidan uban shi, dan haka ba wacce tyi magana face tausaya masa da sukayi, Mama n dubawa kuma tace "Jabir ai shine har ya sakar maka wani bakin, amma bari na shafa maka na yanzu a bayan." Tana daf da laƙato maganin ta shafa mishi wata matashiya duk da kuwa mata ce ga ƙanen margayi mijinta, amma dake su ɗin Fulani akwai ƙaramin jiki ya sa zaka ɗauka budurwa ce, ba tare da sallama ba ta faɗo ɗakin saboda albishir ɗin da ta zo yi wa *Hafsat* ɗin da zumuɗi tana ganinta bata ma kula da me take yi ba cikin harshen fulatanci tace "Adda Bulo, ki zo kiga abun arziƙi?" Dakatawa tayi daga shafa masa maganin da take shirin yi ta kalle ta tace "Lafiya dai ko?" Cikin dariya ta saki labulen tana cewa "Ke dai ki zo, kar su tafi baki basu tukuici ba?" Jin abinda ta faɗa yasa maman dakatawa ta fuskanci Jabir, amma kafin ta faɗa masa ya mata uzuri ta je ta dawo sai ta ga Ummu da tunda ta fito take tsaye tana kallon bayan Jabir ɗin duk ta yi takwaf takwaf da fuska alamar tausaya mishi. Murmushi ta mata sannan tace "Yawwa Ummu, zo mana ki ƙarasa shafa masa maganin nan a baya, hannun shi ba zai kai ba ai da ya saka da kanshi." A ladabce sosai Ummu ta saki labulen uwar ɗakin tana tahowa ta amsa da "To Mama." Tana zuwa ta karɓi ludayin Mama kuma ta fita, tunda ya juyo sau ɗaya ya kalli fuskar Ummu bai sake kallon ta ba bai kuma ce mata uffan ba, haka ita ma ba ta ce masa komai ba sai laƙatar maganin da tayi cikin saiɓi sosai ta kai yatsarta tana ɗan shafa mishi maganin wanda ke nuni da tana yin hakane saboda ba ɗan uwanta bane na jini. Sosai take ci gaba da duba jikin shi da duk ke farfashe tsabar suka, wani wurin m har yanzu a birdinshi yake bai baje a jikinshi ba, gani take me yasa mahaifinshi ke masa haka? Me yasa shi kuma Jabir ba zai dain abinda yake yi ba har ake dukansa? Sannan me yasa mahaifinshi bai lura cewa ɗansa yayi girman da ya wuce duka ba? *A* wajen Jabir kuma nasa tunanin sam bai bi hanyar tunanin Ummu Kulsum ba, tunaninshi bai wuce yadda sam a unguwar nan babu yarinya mai nutsuwa, hankali, kunya kamar Ummu, shi dai duk iya ganinshi da ita a waje to za ta tafi islamiyya ko kuma ta taso, idan ba haka ba sai dai gidan su, sau goma idan za ka shigo zaka sameta tana aiki ne. Abun burgewa a tare da ita shine, yadda ko islamiyya da makarantar boko da take zuwa bayan tayi shigar mutumci har da niƙab take sakawa, hakan yas wasu ma basa ɗauka budurwa ce sai dai a mata kallon matar aure. Tunda yake bai taɓa ganinta a haya tare da ƙawa suna tafe suna dariya da buɗar baki a titi ba, kusan kullum ita kaɗai za ka gani musamman ma a dai nan erea unguwarsu, a sanyaye kum a nutse za ka ganta tana tafe, idan ta ga wanda ta sani sai dai ka ji ta gaisheshi da ina kwanan ku? Amma shi, shi dai gaskiya a rayuwarsa ma maganar da sukayi da ita ƙidayayya ce, shi a titi ma basu taɓa ko da gaisawa ba, ita bata mishi magana bai san me yasa ba? Shi kuma miskilanci ke hana shi gaishe ta duk da kuwa yana sane sosai ta girmeshi a ƙalla da shekaru *uku* ko ma fiye da haka. Gefenshi data koma tana kallon shi tace "An gama." Ya sa ya gyara rigar shi tare da kallon fuskar ta shi ma, fara ce sosai, ga ta kyakkyawa da manya idanu farare tas, ga ta kuma doguwa, don yanzu haka da suke tsaye ta fishi tsayi dan bai wuce kafaɗarta ba. *Kallon* cikin tsakiyar idanun shi da tayi da niyyar yi masa magana ya shi saurin ɗaga idanunshi sama ya kalli daga goshinta zuwa sama kaɗan, luwai luwai ɗin baƙi ƙirin ɗin gashin da ya kwanta a goshinta luf-luf yake kallo, dan tana kallon idanunshi gaban shi ya faɗi sannan ya ji ta masa kwarjini sosai, haka kuma sai yake hango *yarintar ta* a cikin idanun nata da har yake ji a ransa anya kuwa wannan *auren* da za ta yi tayi ma kanta adalci? Shin ta ina suka dace ita da Alhaji Kabir? Amma da ya tuna ita ɗin fara ce sol kuma kyakkyawa, su kuma masu kuɗi burinsu kenan su kwashe kyawawan mata su ɓoye a gidansu, sai ya ga ai hakan ba wani abu bane. Ummu kuma dake wasa da maganin cikin ludayin da nutsuwa sosai tana kallon fuskarshi kamar wacce za ta rarrasheshi tace "Dan Allah, ka daina ɓatawa Abbanka rai har yana dukanka, idan ka ga zai dakeka kayi gaggawar bashi haƙuri, ko dai baka san ka wuce duka da bulala bane? *Jabir*?" Duk da ya so sadda kanshi sanda take magana, dan ita yanzu ai babbar Hajia ce tunda gobe za'a ɗaura aurenta da mutumin da shi kansa bai san adadin dukiyar daya tara ba. To amma yadda take magana tana dakatawa hutu, da yadda take yin maganar a nutse matuƙa sannan kamar wacce ke jin bacci, sai hakan ya ɗauki hankalinshi har ya saci kallon leɓunanta da na ƙasan ke kalar jajir na saman kuma yana da haske sosai. Sosai maganar ta ta so bashi dariya har ya ji kamar ya tambayeta _"Shin baki san mahaifina yana dukana bane ko babu laifi? Ko baki san ya kan dakeni bane idan matarsa ta faɗa masa ƙarya a kaina? Sannan baki taɓa tunanin ina bashi haƙuri ba, amma baya ji saboda bushewar zuciya?"_ Madadin ya mata wannan tambayoyin, sai kawai yayi murmushi, ko ba komai ya ji daɗin shawarar ta gareshi, kuma zai iya cewa wannan rana ta musamman ce gareshi, yau har Ummu ta yi masa doguwar maganar da ta ci sakanni kusan ashirin. Da fara'a ya rusuna ya ɗauki ledar alawar da ya siyowa Uzei tare da maganin da Mama ta bashi sannan ya sake kallon fuskar ta sannan ya buɗi baki shi shi ma a nutsen yace "Tom, nagode... *aunty*." Sai kuma ya gyara tsayuwarshi a ladabce yace "Kuɗin maganin fa? Nawa ne ake biya? Sai..." Da sauri amma a hankalce kamar mai raɗa ta ɗaga masa hannu tarie da cewa "A'a, ba'a karɓan ko sisi..." Sai kawai ta raɓashi kaɗan ta duƙa ta ɗauki jug mai ruwa wanda dama ita ta fito ɗauka, tana ɗauka koma ta juya zata koma ɗaki dan bata iya fita saboda mutanen dake nan kuma saboda sabgarta ne. *Tunda* ta duƙa tarin jigidar dake ƙugunta tayi ƙara kacacauuuu sakamakon doguwar riga ce a jikinta ga kuma cikin ta da yunwa, hakan yasa tana duƙawa jigidar ta zubo mata tana tashi tsaye kuma ta sake komawa kan ƙugu ta zauna... Wannan saurin sosai ya so ɗaukar hankalinshi, amma sai ya gaggauta fita daga ɗakin shi ma, dan da fari ya fara tunani me ye a jikinta ke ƙara haka? Sai kuma ya tuna cewa akwai jigida da mata ke sakawa, dan haka kawai ya share abun ya fita. A ƙofar gida ya samu Nabila tsaye tana son shiga amma tunani Jabir na ciki kuma bata san me yake yi yasa bata shiga ba, kallon ta yayi ya ɗan taɓe bakin shi yace "Ki shiga, ban faɗawa kowa ba, amma ki sani mutumcin ki ya fi komai daraja a gareki, idan kika yarda suka lalata miki ƙuruciyarki, wata rana za kiyi nadama." Yana gama faɗa mata haka ya wuce zuwa na su gidan, da sallama ya shiga, amma kamar yadda ya sani ba amsawa take ba, don haka a ɗar ɗar ya ɗan ƙarasa cikin filin farfajiyar yana satar kallon ta tana zaune gaban tukunya tana girkin da sai ranar da ta ga dama take bashi musamman idan Baban shi na nan, Uzei da ya gani zaune cikin bahon wanka na yara cike da ruwa tana wasa ya tsuguna gabanta yana mata wasa tare da aje ledar nan gabanta yace "Gashi, na siyo miki kayan daɗi ke kaɗai." Ɗan satar kallon Bara'atu yayi amma ko kallon inda suke bata yi ba, hakan yasa ya ɗan juya sosai ya kalle ta cikin taushin murya yace "Aunty, dan Allah kada ki faɗawa Abba abinda ya faru, wallahi na daina daga yau." Juyowa tayi ta kalle shi a hasale ranta a ɓace tace "Kar na gaya masa? Jabir ka zubar mana da mutumci kuma shine zaka ce kar a faɗa masa? Me ka nema ka rasa a gidan nan? Kawai salon ka sa a zageni a ce ni muguwar matar uba ce, sannan a zagi mahaifinka a ce na fi ƙarfin shi?" Jinjina kai tayi irin Haba ɗin nan sannan tace" Ba damuwa, ni tuni na kira na gaya masa abinda kake a unguwar nan, idan ya zo shi ka masa bayani dalla-dalla, amma ba zan ɗauki wannan iskancin ba." Ƙarasa durƙushewa yayi gabanta yana haɗe hannaye alamar roƙo yana faɗin" Dan girman Allah aunty kiyi haƙuri ki kira shi ki ce wasa kike masa, aunty wallahi kusan kasheni zaiyi, ke ma kin sani ko? Dan Allah ki bashi haƙuri wallahi na daina, kuma har kuɗin ma dana tara nayi alƙawari zan kawo miki su duka ki ɗauka na baki, amma ki ce masa wasa kike yi dan Allah aunty." Sama da ƙasa ta galla masa harara tace" Kuɗinka ɗin banza, ni za ka ba cin hanci Jabir? T ka jira idan ya zo shi uban naka sai ka bashi kuɗin dan ya ƙyaleka." Rufe tukunyar ta tayi tare da miƙewa tana jan dogon tsaki, kusa da Uzei ta ƙarasa ta ɗauketa daga cikin ruwan sannan ta wuce ɗakin ta fuuuu kamar an tura ta. Dafe goshi yayi yana huro iska daga bakinshi, tunanin mafita ya shiga yi da son sanin yadda zai yi ya kaucewa dukan haukan da yake hangowa maahaifin shi zai masa idan ya zo. *BAYAN KWANA UKU* *Ƙarfe 05:47 na safe* Cikin nauyayyen baccin daya ɗaukeshi ya ji saukar rikitacciyar ɗamarar ƙugun mahaifinshi a jikinshi, a rikice shi ma ya miƙe yana sosa jikinshi da waiwaigawa da son ganin wanda ya dakeshi, bai bashi damar shiga hayyacinsa ba ya kuma zuba masa wata bulalar da ta saka Jabir yin gurnanin zaki ya shiga jikin mahaifin nashi, dan kuwa tsaf ya gane mai dukanshi saboda kirarin da yake na shi zai tozarta a gari? Ruƙumƙumesa yayi tamau a jikinshi, wasa wasa sai ga Mika'il na neman kasa kubcewa a jikin Jabir da shi fa tsabar kiɗima da raraɗi ne ya shiga jikinshi har ya ma mhaifinshi wannan cakumar. Sosai hakan ya haifar da kaurewar sarƙaƙiyar kokawa tsakanin ɗa da uban, dan Jabir iya ƙarfin da ubangijinshi ya halicceshi da shi ne yasa ya riƙe uban sosai, yayin da shi ma yake ta kiciniyar ƙwatar kansa da ma bulalar da duk Jabir ya haɗesu ya tumurmushe, a zafafe yake faɗin "Saki, Jabir saki bulalar nan? Na ce ka saki ko?" Cikin kiɗima da rarrashi Jabir shi ma ya ke ihun faɗin "To Abba, zan saki, zan saki wallahi, amma ka ce ba zaka dakeni ba, kayi haƙuri Abba na tuba don Allah da ma'aikinsa." Alƙawarin daina dukanshi ya ƙi ɗauka masa, dan haka ya ga kenan dai yanzu ma aka fara, dan haka shi ma ya ƙi saki sai ihun kiran sunana aunty yake wacce tana ɗaki zaune tana kallon tv, daga ƙarshe ma a zafafe ta fito saboda jin hayaniyar tayi yawa tace" Wai ni Abban Uzei me yasa kuke takurawa rayuwata?" Dake yau ran shi ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, wani arnen kallo ya mata a kausashe yace" Za ki ɓace min da gani ko sai na takaki a wurin nan?" Sama da ƙasa ta watso masa harara ta murguɗa baki sannan ta juya ta koma ciki tana faɗin" Kai ma ka san ai tatsuniya ce kake faɗa wallahi." Har ta zauna sai kuwa ta ji ƙarar faduwar babur ɗin, kuma tabbas tasan kan robar wankan Uzei ya faɗa dan gaf da babur ɗin robar take, a wani irin tsiyace ta fito da gudu tana ihu yadda kasan ita ma dukan nata ne ake tana faɗin" Na shiga uku na lalace ni Bara, wai fisabilillah me kuke son maidani ne? Shi..." Bata idasa faɗin abinda tayi niyya ba, Mika'il ganin Jabir zai ɓata msa lokaci yasa ya shiga gwada ƙarfi da yaron, sai dai yau ɗin Jabir ƙwarai da gaske ceton kansa yake son yi, hakan tasa shi ma ci gaba da cimimiye mahaifin nashi har saida suka faɗa kan babur ɗin nan kuma Abban nashi ne a ƙasa shi a sama. Samun mijinta kwance kan babur ga ɗan a samanshi yana ƙoƙarin jan wuyan rigar shi da uban ya riƙe tamau ne yasa ta kasa faɗin ƙarshen zancenta. Dama ce yau da Allah ya ara ma Jabir, yana samu ya kubce rigarsi da tsiya da wani irin gudun ceton rai ya fita daga farfajiyar gidan tare da nufa hanyar fita, bai damu da gajeran wandon baccin dake jikinshi ba, bai kula da rigar sa t-shirt data yage da tsiya ba, bare ya tuna cewa babu takalmi a ƙafarsa, haka ya tunkari ƙofa da fatan kar ta tsayar da shi wajen buɗeta a kama shi. Ai kuwa ƙafa yasa ya hanɓari ƙofar nan, dama kuma Abbanshi bai rufe ba saboda bala'i da ya dawo dashi gidan, dan aikinsa ma baroshi yayi da lamuncewar babban dake kula dasu, hakan yasa bai rufe ƙofar ba da kuma ganin ai har an fara sallah asuba wasu wuraren. Ko da ya samu ƙofar ta buɗu bai yi wata wata ba wajen kama hanyar da zata sadashi da titi ba tare da ya tsagaita da gudun nan ba, Abbanshi kuma saida ya fito har ƙofar gida shi ma da gudun yana ƙwala masa kiran ya dawo fa, wallahi zai yi ajalinshi idan ya kamashi. *Wannan furuci* yasa Jabir yin nesa da unguwar nan, bai san kowa ba a garin nan, bai kuma san ko ina ba tunda ba su da kowa, mutanen arziƙin da iyayenshi suma kansu ba su haɗa shi da su ba bare yau yaje ya nemi taimakon su, wasa wasa, saboda gudun kar mahaifinshi ya kamashi ya kuma aiwatar da ƙudurinshi a kansa na cewa zai yi *ajalinshi* yasa har ya kai commune 2 ba tare da ya dakata ba. *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HARUN* *MURA'ATU ULTIMATE COLLECTIONS* shin kin zuba tagumi ne uwar gida da amarya da tunanin ta inda zaki haɗa kayan kitchen ɗinki? Ko kuma fabrics kike da buƙatar canzawa na kece raini a cikin sa'o'inki? Shin kina so ki san a inda gawurtattun mata ke haɗa nasu perfumes ɗin? Ko lausasan zanen gado da kyawawan electronics gama hawa kike da bukata? To Matso kusa, zan faɗa miki inda ba ke kawai ba, hatta mai gidanki zaki iya rakawa dan siyo nashi electronics ɗin da sauransu, wato *MUC* mun shahara a saida Kayan *kitchen*, *fabrics* na kere sa'a masu quality, *bedsheets*, *electronics*, *beauty products*, *perfumes* da *kayan kwalliya* . Bugu da ƙri Hajia ta akwai data tare da *katin waya* ta kowane network and *catering services*, da wannan nake cewa daku, sai an gwada akan san na kwarai. *MUC* 🤝🤝🤝🧕BAMU DA SA'A. Ga mai buƙatar tuntuɓarsu, ga lambar WhatsApp: 07038274166 Call: 07038274166 & 07031057802 Location: Kano with nationwide delivery. _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *6* Hambali na ɗaga wayar Emanuel yace "Sir, wata shawara ce nayi, shine nace bari na sanar maka, idan ka amince sai a fara aikin." A daƙile ya amsa mishi da "Uhum!" Cikin nutsuwa Emanuel ya shiga faɗin "Sir, kaga harkarmu ta fitar da ƙwaya tana neman ta ja baya saboda tsauraran matakan da gwamnati ta shinfiɗa, hakan yasa bamu fiya samun masu kasadar tsallakar mana da ƙwayoyinmu ba, shine nake ganin me zai hana muyi anfani da yarinyar nan wajen turawa *Sa'ad* kaya, dan kasan fa babban mai ciniki ne kuma satin da ya wuce yayi ikrarin daina harka damu tunda mun Gaza, Kaga ko da an samu saɓani an kamata a bakin boda, to indai abinda nake tunani a kanta ya tabbata gaskiya, tana da juriyar ƙwayar da zata iya jure fiye da adadin da kowa zai iya jura sannan ko an mata gwajin shan miyagun kayen maye ba zasu taɓa samun ta a buge ba, amma ya ka gani?" Dariyar da Hambali yayi mai nuni da jin daɗin lamarin yasa Emanuel ma darawa jin tsaran shi na kan daidai, cike da jin daɗi Hambali yace" Ema Ema, Shiyasa nake masifar son aiki da kai, Emanuel, idan wannan sabon tsarin namu ya tafi daidai ko? Na maka alƙawarin zan baka duk abinda ka tambaye ni." Da fara'a Emanuel ya amsa da" Nagode yallaɓai, kenan na fara mata gwajin kayan mayen?" Cike da tabbaci Hambali yace" E mana Ema, ka fara aikin kawai, idan komai ya tafi daidai sai ka kira ni. " " Shikenan yallaɓai." Ya faɗa yana aje wayar tare da maka mata harara, dan wannan ne karo na farko a rayuwar aikinsa da Hambali da ya ji ya tsane shi har ma kamar ya kasheshi. *GDN ALH KABIR* Ummu na ɗaki suka shigo, dan haka ya ma Jabir umarnin zama kan kujera ya ce da shi "Ina zuwa, bari na kira uwar gidan." Jabir dai da ido kawai ya bishi, saida ya shiga wani ɗaki bayan ya ƙwanƙwasa sannan ya maida duban shi kan tsaruwar ɗakin da ƙayatuwar shi. Alhaji Kabir kuma na shiga ya samu Ummu na saka siket ɗin ta na kayan kanti, da sauri ta juyo da ladabi saboda ita idan ta kalli fuskar nan tashi sai ta ga ai wannan ya ma wuce uba a gareta sai dai Kaka, cikin nutsuwa tace masa "Sannu da zuwa." Shi kuma baki har kunne cike da fara'a ya matsa daf da ita ya jawo ta jikin shi yace "Yawwa Ummuna, har kin tashi kenan?" Jinjina masa kai tayi dan ita ko komawar ma bata yi yadda yake tunani, ɗan ƙoƙarin ƙwace kanta take daga jikin shi shi kuma ya fara lalubar zif ɗin dake bayan siket ɗin yana faɗin "Bari na taimaka miki mana amaryata." Murmushin yaƙe kawai tayi ta sakar masa ragamar komai ɗin dan ba zata iya jayayya da shi ba, yana saka mata ya sake rumgumeta a jikin shi yana shaƙar ƙamshin turaren nan irin na Saudia a wuyan ta idanunshi a rufe yake faɗin" Ina ƙaunarki Ummuna, Allah ya miki albarka." Ummu dake son fita daga jikin shi a ɗarare ta amsa da" Ameen, nagode." Raba jikin shi yayi da nata amma hannayen shi na riƙe da nata hannayen ya kalli fuskar ta da bata shafa komai ba sai zallar mai, amma yadda gashin ta mai sulɓi ya kwanto kan goshinta da kuma yadda girar ta tayi zar zar zar baƙi ƙirin yasa tayi kyau sosai, cikin nutsuwa yace mata "Ina da baƙo fa a waje, an kawo miki abinci ne?" Saida ta fara jinjina msa kai alamar e sannan tace "E, an kawo ɗazu." Sai kuma ta sake tausa muryarta tace "Baƙo? Yanzu da safe?" Murmushi yayi cike da zolaya yace "Uhum! Ko ba kya so wani baƙo ya zo ya ga tafiyar ki ta sauya dalilin daren j..." Kunyar da ta kamata ne yasa ta saurin kai tafin hannun ta a bakin shi ta rufe masa tana sunkuyar da kanta duk ta shagwaɓe fuska alamar za ta yi kuka, dariya yayi tare da janye hannun nata yace" Shikenan to na daina." Sai kuma ya gyara tsayuwarshi yace" Wallahi wani yaro ne na gani zaune ƙofar gida, to ina tambayar shi me yake yi anan sai kawai ya fara amai, na ɗauka bashi da lafiya ne, amma sai na kula aman na yunwa ne dan babu komai a cikin shi sai ruwa, kuma ya ce min tafiya zaiyi wai wani gari ko me ne ban dai fahimce shi da kyau ba, shine na ce ya zo cikin gida ya ci abinci sai na ji ina ya nufa, idan ma bashi da kuɗin mota ne sai a bashi ai." Fuskarshi ta kafe da kallo, ƙwarai zai kai shekara 65 ko ma sama da haka, gemun da ya tara sai ka ce wani malami, ko da yake za ta iya kiran shi da malami, dan kwana uku da tayi gidan shi ta kula tsufan shi ya zo mishi da son addini matuƙa, dan daga bayan magrib zuwa isha'i ma ɗaukar karatu yake zuwa masallacin dake jikin gidan nashi wanda shi ya gina, kafatanin gashin kanshi da gemun duk yayi fari tass, duk da hakan ba dan tsufa bane wasu halitta ce haka. Tsantsar ƙaunar shi da jama'a da son taimakon su take hangowa a fuskar shi, ta tabbata hakan ma dalili ne da ya isa ya baka nagartaccen tsufa, bata taɓa jin wanda ya faɗeshi ba da alkairi ba a unguwar su da ma wajen ta, dan haka da ya zo da buƙatar auren ta ma bata bari mariƙanta sun hana masa ba saboda nagartar tasa. Jinjina masa kai tayi tace "Shikenan, bari na saka hijab sai naje a zuba mishi." Murmushi yayi na jin daɗin abinda ta faɗa, saboda matsalar rashin saka hijab din nan Atika ma da suka shekara ashirin har da ɗaya kullum fama yake da ita, amma saboda fifita sabgoginta sai ta ga ai wayewar kenan, tana siyar da kayayyaki na mata ta ya zata dinga fama da manyan hijab? Ko da yake ai ranar da ya ga Ummu har da niƙab ya gani tare da ita, Shiyasa ma ya tambaya wacece da ya ga ta shiga ɗaya daga cikin gidajen da yake ba wa marasa shi su zauna, da ya tabbatar budurwa ce kuma ya ce dole sai ita. Tana saka hijab din tace masa "Muje?" Kama hannun ta yayi suka nufi hanyar fita, jira take ta ga ya saki hannun ta idan suka kusa isa inda ya san ya aje baƙon nashi, amma sarautar Allah tsaf Alhaji Kabir ko na ce Baba😌 ya tamke hannunta har suka kai inda Jabir ke zaune ya na kallon taga da hasken rana ya fara ɓullowa. Ba Ta tabbatar ba zai saki hannunta ba saida yace da Jabir "Malam..." Da sauri Jabir ya juyo yana amsawa da "Na'am." Take idanunshi suka sauka cikin na Ummu da ita ta ƙara waro idanu da mamakin dama yaron Jabir ne? Mamakin hakan har ya sa ta faɗin "Jabir? Dama kai ne ?" Da fari ƙurawa fuskar ta idanu yayi dake ta ƙyalli amarci, sai kuma ladabi da nutsuwa ya saka shi sauke dubanshi zuwa ƙasa sannan yace "Ina kwana aunty Ummu?" Da mamaki Alhaji Kabir ya kalle su musamman ma Ummu yace "Kun san juna ne dama?" Kallon Alhajin tayi da ladabi tace "E, ɗan unguwar mu, ai gidan mu da nasu babu nisa." Da matsanancin mamaki ya sake cewa "Haba? Kenan dai da gaske ne da ya ce ba almajiri bane? To kuma nan garin kake naji kana maganar kuɗin mota da tafiya?" Da mamaki a fuskar ta ita ma ta kalli Jabir ɗin tace "Tafiya? Ina zaka j kuma Jabir?" A hankali ya sunkuyar da kan shi cikin ladabi yace "E, tafiya zanyi, Abbana ne..." Sai kuma yayi shiru, hakan yasa Ummu fahimtar ba zai iya faɗa ba, kallon da Alhaji Kabir ke mata ya sa ita ma ta kalle shi sannan ta masa alama da idanu ya biyo ta a baya, ba jayayya ya bi bayan nata bayan ta kalli Jabir tace masa" Ina zuwa Jabir, bari a kawo maka abinci." Suna shiga ɗaki kafin tayi magana yace" Me yake faruwa wai? Me ya sa kika ce na zo?" A tausashe ta kalle shi tace" Jabir yana cikin matsala ne." Da kulawa yace" Wace irin matsala?" Gyara tsayuwarta tayi tace" Yana zaune ne tare da matar Baban shi d..." Duka labarin Jabir ta bashi da irin matsalolin da yake fuskanta da yawan dukan shi da mahaifin na shi ke yi, girgiza kai yayi cike da rashin jin daɗi yace" Kuma kin tabbata shi ya haife shi?" Da tabbaci tace" Shi ya haife shi mana, kawai dai matar sa tafi ƙarfin shi ga kuma zafin kai,dan na tabbata ba duka sojoji ne haka ba." Girgiza kai yayi cike da rashin jin daɗi yace" Allah ya kyauta, amma wannan sam bai kyauta ba, ta ya zaka biya ta abinda mace take faɗa maka, sannan yau idan yaron nan ya lalace wa ya lalacewa? Ita tana da wata asara ne? Ita fa ko a jikin ta." Sai kuma ya sake girgiza kai ya juya zai fita yana faɗin" Ki kawo masa abincin ya ci dan Allah." "To." Ta faɗa suka fito tare ita ta nufi wajen teburin cin abinci shi kuma ya koma in da Jabir yake, sai dai yana isa wurin Jabir baya nan, babu shi babu alamar sa? Da sauri ya kama hanyar fita dan ya san yaron ya tafiyar sa ne, tun bai isa ga ƙofar ba yake ƙwala kiran sunan Ilya dake bakin ƙofar, amsawa yayi tare da ƙoƙarin shigowa, amma sai ya dakatar da shi da cewa "Yaron da muka shigo tare ina kaga ya nufa?" Da ladabi yace "Yallaɓai ai yanzun nan ya fito ina ga bai yi nisa b..." Kafin ya kammala yace "Maza kirawo min shi, kar ka bari ya tafi Ilya." "To." Ya faɗa da gudu yana ficewa daga gidan, Jabir har ya fara nisa Ilya ya dawo da shi, ya so yi mas tirjiya dan sosai baya so ya sanar da kowa lbarinshi da kuma abinda yake shirin aikatawa, amma Ilya ya dage sai fa sun zo dan shi umarni Alhaji ya bashi, ba dan yana so ba ya biyo bayan Ilyan suka dawo gidan. Suna samun Alhaji tsaye farfajiyar gidan ya taresu da faɗin "Jabir ya haka? Me ya sa ka tafi? Wani abu aka maka da baka ji daɗi ba?" Girgiza kai yayi cike da kunya yace "A'a." "To me yasa ka tafi?" Yadda ya tsareshi da kallo yasa ya sadda kai, da idanu Alhaji Kabir ya ma Ilya ya tafi shi kuma ya sake kama hannun Jabir sukayi hanyar komawa ciki, Atika suka haɗe da ita za ta fita aikin ta cikin kyakyawan ado da mayafi a kafaɗar ta. Sai lokacin ya tuna bai ma leƙa dan gaishe da matan nasa ba kamar yadda yake yi, yasan kuwa biyu daga ciki za su ce amaryar da yayi ce ta hana shi zuwa gaishe sun. Ɗan gefe ya mayar da hannun Jabir sannan ya tare ta yana mata murmushi duk dan su zauna lafiya, shine ya fara da "Mamie Hayat barka da safiya? Har kin shirya za ki fita kenan?" Yatsina fuska tayi tana ƙare masa kallo tace "Umm! Ina kwana ?" Sai kuma ta kalli Jabir tana taɓe baki tace "Wannan kuma wanene? Mai aiki ka ɗaukowa amaryar ta ka?" Ba tare da ya daina murmushi ba yace "A'a, ba mai aiki bane, wataƙila ma ya zama ɗaya daga cikin yaran gidan nan." Sake taɓe baki tayi har da girgiza kai tana ayyana _"Sarkin kwashe-kwashe."_ A fili kuma hanya ta kama dan zuwa inda motar ta take mai gadi ya wanke ta sai walwali take, da kallo ya bita kafin y sake riƙe hannun Jabir ya shiga da shi inda suka fito. Ummu na tsaye da mamakin ina Jabir ɗin da kuma Alhaji sai gasu sun shigo da sallama, amsawa tayi tace "Dama fita kuka yi?" Sakin hannun Jabir yayi yace "Shine ya tafiyar sa, Shiyasa na fita na dawo da shi." Sai kuma ya kalli Jabir yace "Me yasa ka tafi wai? Ba ka yarda dani bane?" Gumtse bakin shi yayi saboda ƙwallan dake cika masa idanu, da ƙyar ya buɗa baki cikin muryar kuka yace "Bna so na ske zama a garin nan, shiyasa na tafi." Da azama da kuma son ƙurewa yace mishi "To ina za ka je?" Saida ya ja majina ya haɗe wani kukan sannan yace "Ban sani ba, ni dai ko ina ne ma zan je, tunda Abbana baya ƙaunata, ya ce sai ya yi ajalina idan ya kamani saboda kawai nayi ga-ruwa dan na samu abincin da zan ci..." Sai kuma zuciyar sa ta karye ya fashe da kuka tare da durƙushewa ya kifa kanshi a kujera yana faɗin" Ni na gaji da dukana da yake yi, ba wanda yake so na da shi da ahalinshi, ban san me na yi wa duka danginsu ba da basa ƙaunata, tafiya kawai zanyi na shiga duniya idan na zama babba na dawo." A hankali Alhaji Kabir ya zauna kan kujera ya dafa shi, cikin sigar rarrashi da tausayawa yace "Jabir, so kake ka shiga duniya? Idan ka kangare sai ka dawo masa gida a matsayin gagararre? Ko kaɗan ban goyi da bayan ka akan haka ba, dan haka ka sake wata shawara ka ji." Cikin shasheƙar kuka Jabir ya ɗago yace "Idan ma na koma yanzu ba zai haƙura ba, cewa yayi fa ajalina zai zama, dan kawai na nemi abinci? Baya hira dani, baya min dariya, baya min komai da uba yake ma ƴaƴansa, ɗinki kawai ke shiga tsakanina daa shi shima kuma daga ƙaramar sallah ne zuwa wata ƙaramar sallah, sallahn da ta wuce ma cewa yayi ni na haƙura aunty ta ce wai dole ya ma Uzeifatu kaya masu tsada, haka ina kallo su sukayi ni kuma na saka tsofaffin kaya, dan Allah wane uba ne yake wa ɗan sa haka ABBA?" Kallon shi Alhaji Kabir yayi yace" To idan baka koma wajen shi ba Jabir ina zaka je yanzu? Ba ka da Kakani ne ko wasu ƴan uwan?" Cikin sasheƙa da sigar tausayawa kanshi yana jan majina yace" Ina da su, amma duka ba sa ƙaunata, har kakanina ma da suka haifi Mamata ba sa sona." Da yanayin tashin hankali Alhaji Kabir yce" To wai me yasa? Me ka musu da ba sa sonka?" Saida ya share hawayen dake zubo mishi sannan yace" Kakata da ta haifi Babana wai bata so ya auri Mamana ba, shiysa bata son ta nima kuma haka, Kakanina kuma da suka haifi Mamana sun yi hushi ne da Abbana saboda bayan rasuwar Mamna ya karɓeni pouta ce shi zai kula dani saboda baya so tarbiyata ta lalace, suma shine abinda ya ɓata musu rai suka ce har abada ba su ba ni, idan mun haɗu a titi na gaishe su zasu amsa, idan ban gaishe su ba kuma ba ruwansu dani suma." Jiki a sanyaye Ummu ta zauna kan kujera tana faɗin" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! To su duk basu damu da yadda rayuwarka za ta kasance ba? Kowane manufar sa ce kawai ta dame shi?" Kallon fuskar Ummun yayi, a sanyaye ya jinjina mata kai alamar ohon musu! Alhaji Kabir ma da ranshi ya gama ɓacewa ƙwarai da gaske ne ya dafa kan Jabir yace" Jabir, ba kana karatu ba?" Ɗaga kai yayi yace" E." Jinjina kai yayi yace" Kuma ai nasan kana da buri ko?" Nan ma gyaɗa kai yayi har da ɗan murmushi yace" E." Shima da fara'a yace" Uhum! Faɗa min naji me ye burin ka ?" Saida ya faɗaɗa murmushin shi ya kalli fuskar kamalar Alhaji Kabir sannan yace" A rayuwata, ina so naga na zama *malami* mai faɗakarwa, sannan ma ina so na *dogara* da kaina." Daddaɓa kafaɗar shi yayi da jin daɗi yace" Da kyau Jabir, yanzu ka san me zamuyi?" Girgiza kai Jabir yayi alamar a'a, dan haka ya ɗora da" Ka fara cin abinci, zuwa dare idan na dawo zamu sake tattaunawa da kai, lokacin na gama yanke hukuncin abinda ta kamace ka, amma ka sani ba zamu bari rayuwarka ta lalace ba, mun godewa Ubangiji da ya tseratar da kai a baya da yunwa ko takura basu saka fara wasu mugayen halayen ba har ka zaɓi kayi sana'a dan ka ciyar da kanka, amma daga yanzu b zamu bari ka sake zubar da hawaye ba, kaji ko?" Jinjina kai yayi a ɗarare yana kallonshi yace" Amma ABBA bana son zama a nan, Abbana zai iya ganina wata rana." "In sha Allah ba zai ganka ba, Jabir idan har ka amince da abinda nake tunani a kanka, mahaifinka ba zai sake ganin ka ba a ƙasar nan sai bayan wasu shekaru." Jinjina kai kawai yayi inda Alhaji Kabir ya tashi, UMMU ma kawo masa abincin tayi sannan ta bi bayan Alhajin, sai dai duk son ta da Sanin me yake shirin aikatawa bai gaya mata ba, ya dai ce ta jira har ya dawo za ta ji kuma za ta gani. *ME CE CE DAMUWAKI*? Rashin ni'ima? Rashin gamsar da mai gida? Bushewar gaba? Zubewar nono? Cikowar nono ? *Kina buƙatar...* Fatarki tayi laushi? Tayi santsi? Ta kwanta luf? Kina walkiya da annuri tamkar amarya? Sabulu kike so ko haɗin shafawa ki wanke ko mai na shafawa? Ki wadatu da sahihin ƙamshin haukata mai gida? Humra da zaki saka mijinki bacci bai shirya ba? Humra da zata tayar da sha'awarsa? Kulaccha da zata saka mijinki ya kasa yi miki tsara a fannin ƙamshi? Kulaccha da zata gagari manyan mata suffanta kalar sunan turarenki? Turaren wuta irin na asali barebari? Turaren da zaki fesa à zanin gadonki har ya rike mai gida ya kasa tashi? Turaren da zaki zuba ga ruwan wankan mai gidan ki? Turare don yaranki? _Idan duka kina buƙatar ɗaya daga cikin kayan nan, to ki tuntuɓi wannan lambar ta WhatsApp *+227-82-21-91-74* wanda suk gwada sun san ingncin kayanmu, ba buƙatar ɓata lokacin cika muku baki._ Wani abun farin ciki kuma, duba da yanzu ba kowace mace ke son shan garin magani ko matsi ba, akwai haɗi irin su *tsumi*, *ruwan tsumi*, *tukunya*: dayawa sun san tukunya, don da itace muke tutiya, kuma tukunyar nan akwai na ruwa dana dafawa a nama, sannan akwai kankat wato haɗin *kayan marmari*. *Garaɓasa* Ga waɗanda sukayi nisa kuma haɗin kayan marmari ba zai kamacesu ba, duba da kafin sakon yaje garesu zai fara lalacewa, don haka ga sauki ya samu, madadin kuɗin mota da zaki yi, zaki biya 1000k kacal don a sanar dake yadda zaki had, ba iya guda kawai ba, dama sauran haɗi irin na kayan daya shafi na marmari da ɗanye, musamman ma *sirrin kankana* da kuma *cucumber*. *JANNAT HOUSE.*🧕 *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HARUN* *MURA'ATU ULTIMATE COLLECTIONS* shin kin zuba tagumi ne uwar gida da amarya da tunanin ta inda zaki haɗa kayan kitchen ɗinki? Ko kuma fabrics kike da buƙatar canzawa na kece raini a cikin sa'o'inki? Shin kina so ki san a inda gawurtattun mata ke haɗa nasu perfumes ɗin? Ko lausasan zanen gado da kyawawan electronics gama hawa kike da bukata? To Matso kusa, zan faɗa miki inda ba ke kawai ba, hatta mai gidanki zaki iya rakawa dan siyo nashi electronics ɗin da sauransu, wato *MUC* mun shahara a saida Kayan *kitchen*, *fabrics* na kere sa'a masu quality, *bedsheets*, *electronics*, *beauty products*, *perfumes* da *kayan kwalliya* . Bugu da ƙri Hajia ta akwai data tare da *katin waya* ta kowane network and *catering services*, da wannan nake cewa daku, sai an gwada akan san na kwarai. *MUC* 🤝🤝🤝🧕BAMU DA SA'A. Ga mai buƙatar tuntuɓarsu, ga lambar WhatsApp: 07038274166 Call: 07038274166 & 07031057802 Location: Kano with nationwide delivery. _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *5* Hasken da ya fara mamaye gari da kuma wata irin yunwa da ƙishin ruwa da suka sako shi gaba yasa shi ƙarasawa jikin wani tabkeken gida da kai daga gani a waje da ido kasan gidan wanda suka tara abun duniya ne kamar su kaɗai ke nema, cikin sa'a yana kawowa daf da gidan sai ya samu fanfo, da sauri ya ƙarasa ya kunna fanfo ya fara wanke hannayen shi sannan ya tarasu ya sha ruwan sosai da burin su cika masa ciki ko yunwar nan za ta bar shi yayi tunanin abun yi. Saida ya cika cikin shi fam da ruwa har yana jin suna taso mishi sannan ya zauna kan wani dakali dake zagaye da shukoki masu kyau ya rabka tagumi, ƙwarai daga yau dai ka ya bar gidan mahaifinshi kenan, zai shiga duniya ne kawai shi ma ya zama ɗan iska kamar yadda yake faɗa masa, zai je duniya idanunshi su buɗe sannan ya dawo ya gagareshi, tabbas idan har ya yi girman da ba zai daku a hannun Abbanshi ba, to shakka babu sai ya nuna kan mahaifinshi da bakin bindiga, idan kuwa ba haka to zai saka masa hawan jinin da zai zama ajalinshi. Kuɗi yake so wanda zai hau mota, gashi kuma kuɗinshi suna hannun madame bai karɓo ba, ba kuma zai iya zuwa unguwar nan ba yanzu, zai jiras ne zuwa rana sai ya tafi, lokacin dai tabbas Abbanshi baya unguwar ma, yana karɓo kuɗinshi to zai faɗa garuruwan dake maƙwabtaka da garin nan ne, ba kuma za'a sake ganinshi ba sai bayan wasu shekaru. Ɗan jinginar da yayi a bango yasa bacci ɗaukarsa saboda yanayin mai daɗin gaske, ga iska dake huro iskan shukokin nan dake fito da wata sanyayyar iska mai ƙamshi kala daban daban. Alhaji *Kabir* da dawowarsa kenan daga masallaci, dama kuma idan ya tafi baya dawowa gida sai gari yayi haske, wasu lokuta ya kan yi tattaki ne a cikin unguwar, wani lokaci kuma asibiti babba yake zuwa dan gaishe da marasa lafiya, yau ziyarar shi a maƙabarta yayi ta tun asuba, Shiyasa ya dawo har rana ta fito sosai. Dake ta bayan gidan ne ya biyo inda Jabir ke bacci, tunda ya ganshi ya tabbatar mai gadi bai ganshi ba, dan baya barin baƙuwar fuska suna zama a wurin nan, har ya ɗan wuce zai yi tafiyar shi...sai kuma tunanin ko almajiri ne? Kuma ta yiwu yanzu ana can ana karatun safe a makaranta su, shi kuma bacci ya ɗaukeshi yasa ya dawo kaɗan ya tsaya gaban Jabir dake kwasar bacci. A hankali ya mayar da carbinshi a ɗaya hannunshi sannan ya zura hannun ya daddaɓa guiwar Jabir, a tsorace ya farka tare da tashi tsaye zunbur yana zazzare idanu, yanayin da ya tashin ya sake tabbatarwa da Alhaji Kabir Jabir almajiri ne, wataƙila haka malamansu suka saba tashinsu, cikin tattausan murya Alhaji Kabir cike da dattijantaka yace masa "Me kake anan baka je makaranta ba? Ko ba kwa karatun safe ne?" Kame-kame Jabir ya fara yi yana ƙyaƙyabta idanu da mi-mi-mi da baki, cike da kulawa Alhaji Kabir ya sake cewa "Ko ba kwa karatun nan? Na ga yau ai Lahadi ce." Madadin ya bashi amsa, sai kawai ya rusuna cike da ladabi da darajanta shekarun shi yace "Ina kwananku." Ajiyar zuciya Alhaji Kabir ya sauke tare da faɗin "Na ɗauka ba ka magana ai." Ɗan sosa ƙeya Jabir yayi yana sadda duban shi daga kan fuskar dattijon mai cike da kamala da haiba yace "Ina yi, ban san me zan ce bane *Abba*." Da mamaki Alhaji Kabir yace "Ba ka san me zaka ce ba? Ba ka zuwa makaranta kenan?" Cikin saiɓi Jabir yace "Ni ba almajiri bane, islamiyyarmu ba'a nan take ba." A nutse Alhaji ya shiga ƙare masa kallo daga sama har ƙasa, ɗan taɓe baki yayi ya zubawa fuskarshi idanu yace "To me kake anan?" Saida ya sauke numfashi kafin yace "Hutawa ne nake, ina jiran rana tayi ne zan tafi amso kuɗina dan na biya kuɗin mota sai na tafi." Jinjina kai Alhaji Kabir yayi yace "Ohh! Dama kai ba ɗan garin bane?" Buɗa baki yayi zai bashi amsa, sai kawai yaji ruwan nan da ya tatila suna neman taho mishi ta baki, hakan yasa ya ɗanyi shiru yana kallon Alhaji, da ya ga ya tsare shi da idanu kamar mai tuhumarsa, sai ya ga ai bai kyautu ba yana magana kuma yana ƙyaleshi, dan haka ya Buɗa bakinshi yace "A'a, nan ga..rin...Bab..ana yak..." Da sauri ya matsa gefen hanya ya duƙa ya shiga amayo ruwan nan da ya ɗirkawa cikinsa, hakan ya tayar da hankalin Alhaji Kabir ya bi bayan shi yana masa sannu da tambayarsa daa bashi da lfy? Ba tare daya ɗago daga durƙushen ba ya dafe kanshi kaɗan ya furta "Jiri ne kawai nake gani, lafiyata ƙalau." Da son jama'a da taimaka musu yasa Alhaji Kabir tallabo hannun Jabir ya miƙar dashi tsaye, ba tare daya sake shi ba suke takawa zuwa inda ƙofar shiga gidan take yana cewa "A'a, kana ganin jiri ina lafiya take, muje ciki sai ka faɗa min inda zaka je, ta yiwu yunwa ce ke addabarka, dan duk abinda ka amayo babu abinci, zallar ruwa ne kawai." Suna zagayo ta ƙofar gidan mai gadi dake zaune yana sauraren radio ya taso da sauri yana masa sannu da zuwa da kuma faɗin "Alhaji baƙo kayi? Ko dai almajiran nan ne masu zuwa ta bayan gida suna cirar mana mangwaro da Lemun tsami?" Ba tare da ya saki hannun Jabir ba yace da shi "A'a Ilya, nima anan na gan shi zaune, da alama bashi da lafiya, kuma dai ya ce shi ba almajiri bane." Sai kuma ya nufi ƙaramar ƙofar zai shiga yana cewa "Bari na shiga da shi ciki, har da yunwa ke damunshi ma." Take musu baya mai gadin yayi ya buɗe musu ƙofar sannan ya rufe yana addu'ar Allah ya sawaƙe, suna shiga katafaren filin tsakar gidan Jabir ya kalla dake ɗauke da ɓangarori guda huɗu kuma maka-makan da suka bayyana akwai girma da ɗakuna a kowane ɓangaren. Ɗan satar kallon Alhaji Kabir yayi da ya ga ya ja birki shi ma yana kallon ɓangarorin kamar yau ya fara ganinsu. Alhaji Kabir kuma ba komai ya saka shi tsayawa yana kallon su ba sai son gane ɓangaren da zai nufa da Jabir ɗin ya samu kulawa ta abinci da hutawa kafin ya san wanene shi kuma daga ina yake sannan ina zai nufa? Hajia *Lubabatu* ita ce babba a gidan, mata ce mai dattako da kawaici, a ƙalla akwai yara maza da mata da suka tashi a hannun ta wanda shi yake bata riƙonsu saboda bata taɓa haihuwa ba, *Khamis* shine yaro na ƙarshe ɗan abokinshi da ya kawo shi yake karatu anan, yayi alƙawarin daga shi ba zai sake haɗata da ɗan kowa ba, duba da za ta ga kamar dna bata haihuwa e ake bata riƙon har wanda ma basu haɗa jini da su ba. Hajia *Asiya* kuma, mace ce mai saɓanin halayen Hajia Lubabatu, bata da kara, bata da kawaici, bata da sani baroe sabo, tun farkon farawa da ya so bata riƙon *Saudat* sam ta ce bata yarda ba, to da wane za ta ji? Nata yaran ko na wasu? Hajia *Atika* kuma, bata da lokacin nata yaran ma bare na wasu, ma'aikaciya ce kuma ƴar kasuwa da ita dai harkokin ta kawai ta sani a gaba, dan haka ma ba ya jaraba tafiya da Jabir can ba ya ce ta bashi abinci ya ci sannan ta samo mishi kaya a cikin ko da na *Hayat* da yasan zasu kai tsara da wannan yaron. Dan haka kawai ya karkata akalarshi zuwa ɓangaren margayiya *Aminatu*, wanda yasan da tana raye bai da matsala dan wannan, amma duk da haka zai kai shi wurin wanda a yanzu ke ɓangaren wato *Ummu Kulsum*, dan sak halayen da take nuna masa a ƴan kwanakin nan irin na margayiya Aminatu ne, duk da dai yasan tana fama da kanta sakamakon jiya dai ya lallaɓata ya samu buɗe budurwarsa, amma yasan ba za ta gagara ciyar da baƙonshi ba tunda ya ba Hajia Lubabatu saƙon a kawo mata abinci, zuwa yanzu kuma yasan zai tarar da an kawo mata ɗin. *WANI GARI* A tsawace manajan (manager) ya sake nunosu da yatsa yana jadadda musu "Wallahi ba zai yiwu ba, ku gaggauta fito da ƴan matan nan biyu da suka ɓata tun kafin yallaɓai ya samu wannan labarin, dan in har ba'a samu ba to ina mai tabbatar muku kafin a koreni a nan ni zan fara korarku, dan shakka babu kuna da masaniyar inda yaran nan suke." Cike da bayar da tabbaci wani dattijo yace" Yallaɓai, ka yarda dani, wallahi ban san komai a kan ɓatan yaran nan ba sai dai ko idan abokin aikina da yayi aikin kwana." Wanda ya faɗa tare da nuna shi ne ya zabura ya kalli tsohon yace" A'a, ya zaka ce haka? Ko aikin kwana nayi ai naga har dare dai muna tare da kai, kuma nima ba san komai ba da ya faru gaskiya, sai dai ko su masu kula da ɗakunan ƴan matan." Manyan mata ne a shekaru ɗayar kuma har da ƙiba, ganin duk an kallesu yasa matsakaiciyar faɗin" Wallahi yallaɓai nima ban san komai ba gam..." Kafin ta ƙarasa ɗayar ma mai ƙibr tace" Nima kuma haka, yallaɓ.." A tsawace manajan ganin suna neman haukatashi bayan kuma shi yasan zai fuskanci hukunci mai tsanani wajen mai gidansa yace" Ku dakata." Ɗaya bayan ɗaya ya dinga nunosu da yatsa yana cewa" Wannan ba shine na farko ba da ƴan mata ke ɓacewa a wannan gidan *marayun*, ku sani wannan ba abu bane da hankali zai ɗauka, idan muka sake maganar nan ta fita wallahi kaf ɗinmu gwamnati zata sa a rufemu, dan haka tun muna shaidar juna wanda duk yasan da hannunshi a ciki ya fito ya faɗa, ni kuma nayi alƙawarin sassauci da kuma rufa masa asiri, dan wannan ba abu bane da zamu bari ya fita gari har ƴan jarida su sakomu gaba." Kallon kallo suka dinga yi wa junansu, sai kuma kowa ya taɓe baki ya kawar da kai alamar shi dai fa ba shi bane, jinjina kai yayi da ya fahimci me shirun su ke nufi sannan yace" Shikenan, kuje..." Sai kuma ya gyara tsayuwarshi yace" Zan wa aminina magana ya min bincike akan lamarin kasancewa rasa jami'in tsaro, ku sani idan har binciken sa ya zaƙulo min ɗaya daga cikin ku, to haƙiƙa zan tsaya ne tsayin daka wajen ganin an rataye mutum, dan har da ɓatan ƴan mata *goma sha shidan* da suka ɓace a cikin shekara uku kacal zan sa a yi." Ma fi aksarin su duk ɗaga kafaɗu sukayi alamar ba komai a yi ɗin, inda suka juya suna fita daga ofishin nashi, matar nan mai ƙiba ce kaɗai jikin ta yayi sanyi take tafiya kamar wacce ƙwai ya fashe ma a ciki, da kallo ya bisu har suka fita sannan ya koma ya zauna yana lalubar wayarshi dan kiran aminin nasa kamar yadda ya faɗa. *Matar* nan kuwa mai ƙiba na fitowa cikin sauri ta fita waje kamar za ta yi wani uzurin ta shiga banɗaki, wayar ta ta jawo ƙarama ta danna wa wata lamba kira, ana ɗagawa cikin ladabi da yin ƙasa da murya tace "Yallaɓai, ni ce ke magana, *Lami*." Daga can ɓangaren cikin wata ƙosasshiyar murya da dattako haɗe da jan aji a taƙaice aka amsa da "Me ya faru?" Sosai ta sake sauta muryarta sannan tace "Yallaɓai, duk da dai ban san manufar da tasa kake sa ana ɗaukar ƴan matan da suke gidan tallafin da ka gina, amma dai ya kamata a ɗauki mataki akan manajan *Buhari*, dan yanzun nan daga ofishin shi nake, kuma yayi kirarin damƙa maganar nan ga jami'an tsaro, Shiyasa na kira dan na sanar da kai kayi wani abu, yallaɓai ka da asirina ya tonu." A daƙile cike da rashin son can zancen yace "Shikenan, zan yi wani abu a kai." Yana faɗan haka ya yanke kiran, ita ma tusa wayar tayi cikin rigar Mamanta sannan ta fito cikin sanɗa tana waiwaye waiwaye da fatan kada kowa ya ganta bare a zargeta. *HY* Hospital, a keɓantaccen ɗakin gwaji na musamman aka killace ƴan matan tare da kwantar da su kan gadon aka ɗauresu gudun matsala, kan ta farkon wani likita mai fararen kaya ya ƙarasa tare da soka mata allurar kashe zafin jikin da ta saka ta yin siririyar ƙara sai kuma ta rufe idanu, a hankali a hankali bacci ya fara ɗaukarta har dai tayi nisa sosai. Ɗaya matashiyar na kallo ta ga yayi tsaga a tsakiyar rigar ɗayar gefen cibiyar ta daga ƙasa kaɗan, tana kallo ta ga yana ta gabato da kayayyakin aiki a gabanshi har saida ya kawo komai sannan ta ga ta ɗauki wata ƙaramar wuƙa irin ta likitoci ya daidaici inda ya shafa wani alcohol a ƙasan cibiyar yarinyar gefen hagunta ya ɗora ya fara yankawa... Ita duk wannan abu da ta ga yana yi bata ɗauka cutar da su zaiyi ba, duk da tana da yaƙinin inda suke akwai haɗari, dan basu ma san a ina suke ba, amma dai bata ɗauka cutarwar ta kai haka ba har saida ta ga jini na fitowa a jikin yarinyar da ita ko a jikin ta sai wani lullumshe idanu take dan ba wani nauyayyen bacci ne ya ɗauketa ba duba da allurar ba ta bacci bace. Ƙodar yarinyar ya cire duka biyun, saida ya fara killace su dan sune abu mafi soyuwa da daraja a gare su kafin ya dawo dan yi mata ɗinki, yana gamawa ya nufi *Nana Aisha*, take ta fara ihu da fizge fizge tana jijjiga gadon tamkar za ta kwance ta gudu, kuka take kwarai da gaske tana kiran "Kayi haƙuri, kayi haƙuri dan Allah Babana, ka yafe mana laifin da muka maka ba zamu sake ba, Wayyo, Wayyo Allah na, taimako, jama'a taimako, zai kashe mu jama'a a taimaka mana." Duk da ya ga hagagi take, kuma yasan ba zai wuce na bashi haƙuri kar ya taɓa ta ba, amma shi Sam ba ya ma jin me take faɗa da harshen hausanta, dan haka ya daidaici hannun ta ita ma ya soka mata allurar nan... Wata ƙara ta sake ƙwallawa har lokacin da ya cire tsinin allurar, amma bayan haka sai ta ci gaba da fizge fizge tana bashi haƙuri. Shi kuma ɗan gefe kaɗan ya koma ya bata mintunan da sinadarin zai fara aiki kanta, minti ɗaya ya shuɗe, biyar haka har ya ga an kwarari minti goma, da yanayin tashin hankalin da ya fara ziyartar sa ya kalli agogon hannun shi sannan ya yi sauri ya ɗauki ƙaramar kwalbar dake ɗauke da sinadarin da ya zuƙa ya zuba mata ruwa yana ƙara karantawa. Da gaske ruwan ne, kuma tabbas sun shiga jikinta, hakazalika sune aka zubawa waccen ɗayar da ba yanzu allurar za ta sake ta ba, sanin da ya yi idan ya ce ya sake mata wata a nan take babban haɗari ne ga lafiyar ta yasa shi komawa da baya ya nufi inda wayar shi take, ɗauka yayi ya kira ogan nasa. Bugu uku aka ɗaga cike da zumuɗin son jin labari mai daɗi aka ce "Dr. Emanuel, ya ake ciki? Anyi nasarar aikin?" Da sigar tashin hankali Emanuel yace "Sir, da matsala fa." Amsawa aka yi da "Wace irin matsala kuma Ema?" Saida ya zuba idanu shi kan Aisha da ke kallon shi ita ma tana tunanin to ko dai ya ji roƙon da ta masa ne sannan yace "Ɗaya yarinyar yallaɓai." "Me ya same ta? Ƙodar ta na da matsala ne?" Ya tambaya da son sanin me ye matsalar, cikin rashin sani da tabbas Emanuel ya shiga faɗin "Sir, na mata allurar kashe jiki, amma sai naga sam allurar ba ta yi tasiri a kan ta ba, har yanzu fa jijjiga take a gadon bayan kuma an samu shuɗewar minti goma yanzu da yi mata allurar." Da son gasgatawa mamallakin asibitin kuma mamallakin gidan marayun da aka ɗauko yaran yace" Ka tabbatar?" " E yallaɓai." Ya faɗa da alamar cike yake da mamaki sannan ya ɗora da" Da haɗari babba idan na sake mata wata yanzu ba tare da an ɗauki wani tsawon lokaci ba, shiyasa na kira na gaya maka." Ajiyar zuciya *Hambali Ya'u* ya sauke sannan ya bashi umarni da" Ka sake mata wata allurar Ema, ta hakane zamu tabbatar wane rukuni ne jininta, na san kasan akwai wanda jininsu ke da ƙarfin da ba magani ke musu kai tsaye ba." A tsanake Emanuel yace" Sir... Are u sûre about that?" " Yes Ema, do it." Ya faɗa cike da tabbaci, jinjina kai yayi sannan yace" OK sir." Ya kashe wayar tare da sake tunkarar Aisha da ta ɗan yi lamo tana sauraren shi duk da yaren da yayi da farko bata san komai da yace ba bayan tambayar tabbaci da yake daga wajen abokin hirar sa sannan kuma ya ce shikenan. Ganin da gaske ita zai sake wa allura ta shiga ci gaba da jijjiga gadon tana kiran a taimake ta zai kashe ta, yanzu ma allurar ya mata, amma ya sake bata wasu mintuna shiru ba alamar ma ita aka wa bare ta ji. Hakan ya tsorata shi ya kafe Aisha da idanu, gaba ɗaya shekarun yarinyar ba zasu wuce *16* ba, to amma ya aka yi bata jin wannan allurar? Ba tare da ya sassauta kallon tsoro da mamakin da yake mata ba yace da ita a harshen turanci "Wacece ke?" Duk da cikin firgici take da ɗimuwa, amma ɗabi'arta na nan ba abinda ya sauya, sanyin magana kamar mai raɗa tare da lullumshe manyan idanunta dake farare tass tace " *Nana Aisha Mukhtar Saheeb Ahlan*." Sake tsatsarta da idanu yayi kamar zai haɗeta yace" Alhan? Ahlan? Ɗaya tak na sani a rayuwata, attajirin mai ikon faɗa aji, babban ahalin da zai yi wuya a rasa wanda ya san su, kina nufin shi dai dana sani?" Manyan idanunta ta fara yin luuuu da su tamkar dai wata wacce ke cikin maye, sai kuma ta sako da wasu hawaye ta girgiza masa kai a sanyaye sosai tace" Ban sani ba, ban san su ba nima, na dai san kawai sunana Aisha Mukhtar Saheeb Ahlan in ji *Mother*." Ɗan jinjina mata kai yayi alamar gamsuwa sannan yace" Ke ƴar *Agadez* ce?" Girgiza kai tayi a marairaic tace" Ban sani ba, ban san ma ina ne haka ba, ni a gidan marayu na tashi." Sak kafeta yayi da ido kamar zai faɗa cikin fuskar ta, dan shi sosai yake hango wani abu a fuskar ta, sai dai kuma abun ya shige masa duhu ƙwarai, a rashin sani, a rashin me bakinshi ya furta ba tare daya daina kallon ta ba yace" *Da buƙatar ki waiwayi tarihin ki*... A'isha." Ita ma manyan idanunta masu kama da na ƴan maye ta zuba masa tare da furta" Tarihina?" Sai lokacin ya tuna suɓul da bakan da yayi, da sauri ya juya mata baya yana sake lalubo wayar sa ya kira oganshi, yanzu ma ba ɓta lokaci aka ɗaga ana tambayar sa ya ake ciki? Da kiɗima da kuma saranda yace" Yallaɓai, gaskiya yarinyar nan ba mutum bace, yallaɓai na sake mata allurar nan, amma fa ba wani abu da ya nuna sinadarin zai yi anfani a jikinta, ina ga mu barta haka." Cikin gigita Hambali ya miƙe daga inda yake cikin hargagi yace" Ba zai yiwu ba Ema, ka sanni ka kuma san yadda nak kasuwancina, rashin jin allurar kashe jiki ita ya shafa, ni abinda na sani kawai shine ka cire min duka Ƙodar ta biyu ka adana min, idan ta rayu zamu kula da ita ne har lokacin da za ta kasa rayuwa sakamakon rashin wasu muhimman sassa a jikin ta, idan kuma ta mutu daga nan wurin, ta hutar da kanta da wannan rayuwar marar tabbas, dan haka kayi aikin ka kawai." Dafe kai Emanuel yayi da hannu ɗaya yana ɗan sosa ƙeyarshi har sanda Hambali ya kashe wayar, yadda Aisha ta ƙura masa ido haka shi ma ya ƙura mata suk kallon juna, ba zai iya aikin nan akan yarinyar nan ba, shi wata sanayya yake ji game da yarinyar, ga kuma abun al'ajabin dake tare da ita. Dan haka kwatsam wata dabara ta faɗo ran shi, da sauri ya sake bugawa Hambali dan dol sai ya sanar da shi, idan ba haka ba ya taimaki Aisha ta gudu to fa kai tsaye shi zai tunkaro, ya kuma san waye Hambali tsaf zai raba shi da rayuwar sa. *ME CE CE DAMUWARKI*? Rashin ni'ima? Rashin gamsar da mai gida? Warin gaba? Bushewar gaba? Ƙaiƙayin gaba? Kurajen gaba? Zubewar nono? Cikowar nono ? Shin kin san da akwai garin da ba'a baki sai an tabbatar baki da kishiya saboda kar ki ɗauki alhakinta? *Kina buƙatar...* Fatarki tayi laushi? Tayi santsi? Ta kwanta luf? Kina walkiya da annuri tamkar amarya? Sabulu kike so ko haɗin shafawa ki wanke ko mai na shafawa? Ki wadatu da sahihin ƙamshin haukata mai gida? Humra da zaki saka mijinki bacci bai shirya ba? Humra da zata tayar da sha'awarsa? Kulaccha da zata saka mijinki ya kasa yi miki tsara a fannin ƙamshi? Kulaccha da zata gagari manyan mata suffanta kalar sunan turarenki? Turaren wuta irin na asali barebari? Turaren da zaki fesa à zanin gadonki har ya rike mai gida ya kasa tashi? Turaren da zaki zuba ga ruwan wankan mai gidan ki? Turare don yaranki? _Idan duka kina buƙatar ɗaya daga cikin kayan nan, to ki tuntuɓi wannan lambar ta WhatsApp *+227-82-21-91-74* wanda suk gwada sun san ingncin kayanmu, ba buƙatar ɓata lokacin cika muku baki._ Wani abun farin ciki kuma, duba da yanzu ba kowace mace ke son shan garin magani ko matsi ba, akwai haɗi irin su *tsumi*, *ruwan tsumi*, *tukunya*: dayawa sun san tukunya, don da itace muke tutiya, kuma tukunyar nan akwai na ruwa dana dafawa a nama, sannan akwai kankat wato haɗin *kayan marmari*. *Garaɓasa* Ga waɗanda sukayi nisa kuma haɗin kayan marmari ba zai kamacesu ba, duba da kafin sakon yaje garesu zai fara lalacewa, don haka ga sauki ya samu, madadin kuɗin mota da zaki yi, zaki biya 1000k kacal don a sanar dake yadda zaki had, ba iya guda kawai ba, dama sauran haɗi irin na kayan daya shafi na marmari da ɗanye, musamman ma *sirrin kankana* da kuma *cucumber*. *JANNAT HOUSE.*🧕 *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HARUN* *MURA'ATU ULTIMATE COLLECTIONS* shin kin zuba tagumi ne uwar gida da amarya da tunanin ta inda zaki haɗa kayan kitchen ɗinki? Ko kuma fabrics kike da buƙatar canzawa na kece raini a cikin sa'o'inki? Shin kina so ki san a inda gawurtattun mata ke haɗa nasu perfumes ɗin? Ko lausasan zanen gado da kyawawan electronics gama hawa kike da bukata? To Matso kusa, zan faɗa miki inda ba ke kawai ba, hatta mai gidanki zaki iya rakawa dan siyo nashi electronics ɗin da sauransu, wato *MUC* mun shahara a saida Kayan *kitchen*, *fabrics* na kere sa'a masu quality, *bedsheets*, *electronics*, *beauty products*, *perfumes* da *kayan kwalliya* . Bugu da ƙri Hajia ta akwai data tare da *katin waya* ta kowane network and *catering services*, da wannan nake cewa daku, sai an gwada akan san na kwarai. *MUC* 🤝🤝🤝🧕BAMU DA SA'A. Ga mai buƙatar tuntuɓarsu, ga lambar WhatsApp: 07038274166 Call: 07038274166 & 07031057802 Location: Kano with nationwide delivery. _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *7* Abinci ya ci duk da ba wani sosai ba amma ya gamsu. Alhaji Kabir da ya bar shi nan ya shiga ɓangaren matan nashi dan gaisawa da su kamar yadda ya saba, lafiya lau suka gaisa da girmamawa da mutumtawa shi da uwar gidan nashi Lubabatu, amma wajen Asiya sai da ta fara tsegumin yau bai shigo suka gaisa tun da safe ba? Sannan ta ɗora ita fa bata son wulaƙanci da raini, ya ma amaryar sa magana kar ta ce zata rainata, dan jiya ta shigo gaishe ta a tsatsaye tace wai sauri take zata yi aiki. Kasancewarsa marar son matsala kawai ce mata yayi "Za'a kiyaye Hajia." Ya juyo ya baro mata ɗakin, ɓangaren Atika ya shiga ya samu *Zeinab* na shirin fita makaranta, da tausayawa ya kalli yarinyar wacce kullum sai ta makara saboda sai ta yi ayyukan gida take tafiya, duk da kuwa tana asubancin tashi, amma samun ta yarinya mai ladabi yasa sai Hajia Atikar ta ƙirƙiro aikin da za ta sakata ƙarshe ta makara. Da ladabi ta sunkuya tace "Abba ina kwana?" Da kulawa ya amsa da "Lafiya lau Zeinab, antashi lafiya?" "Lafiya lau Abba, dama zan je na gaisheka ne sai na tafi." Ta faɗa tana sake gyarawa jakar ta zama, da fara'a yace "Hakane, nima wani abun ne ya tsayar dani ban shigo ba, ammm... Ina Hayat?" Ya tambaya har da waige-waige kamar zai hango Hayat ɗin, da kulawa tace "Abba Hayat ai ya riga da ya tafi." Cike da gamsuwa yace "Shikenan, dama wani yaro ne na shigo da shi gidan, to ina so ne ya bashi riga da wando a cikin kayan shi, dan na jikin yaron sun yage, ko zaki shiga ɗakin nashi sai ki samo min?" Dake Hayat ɗin ƙane ne a gareta ba ta ji shakkar komai ba ta ce "To Abba." Da sauri ta juya tayi hanyar ɗakin nashi, ta kusa minti biyar kafin ta fito, dan sau da dama sai ta ɗauko wasu kayan sai ta tuna yadda Hayat ɗin ke ƙaunar su sai t mayar, da ƙyar ta ɗauko wanda suka dace da fatan kar ya mata masifa kan ta bayar da kayan shi waɗanda ya fi so. Tana kawo mishi saida ya ɗan ɗaga kayan sannan ya mata murmushi yace "Yawwa sun yi, maza to ki kama hanya ki tafi." Da haka ya sake komawa wajen Jabir ya same shi ya zaune, banɗakin dake daga waje ya masa umarni ya shiga yayi wanka ya fito ga kaya nan sannan ya bashi damar kimtsawa a tsanake ta hanyar komawa ɗakin Ummu dan shi ma ya shirya. ******************* Ta wahala sosai ta yadda har shi kan shi saida ya ji tausayin ta, ba dan jinin ta mai ƙarfin gaske bane da yanzu maganar kawar da gawar ta ake ba wannan ba, amma kuma ta wata fuskar ya ji daɗi dan ya samu hanyar da zai tseratar da ita, da farin ciki ya sanar da Hambali ƙwarai yarinyar nan za ta musu anfani, dan haka a fara mata shirin barin ƙasar, shi kuma zai tabbatar da ya ɗura miyagun ƙwayoyin à cikin jikin ta. Da ƙyar ya samu bacci ya ɗauke ta kafin ya mata wannan tiyata mai haɗarin gaske da yanzu ƴan duniya wanda idanun su ya rufe da son neman kuɗi suke bi don fasa-ƙauri, abinda ya mata yanzu ba wani sabon abu bane, dan hukumar kula da safara sun sha kama mutane bila-adadi da makamai ko ƙwaya ta hanyar da babu wanda zai yi tsammanin za'a iya fitar da su. An kama mace da bindigogi ta yi ciki da su, wanda za ka ɗauka mai tsohon ciki ce amma makamai ne a cikin. An yi basaja matsayin mata da miji zasu yi tafiya, matar ta shaƙe jakar ta da miyagun ƙwayoyi, kankat ma an kama maza biyu da suka saka hodar iblis a kororon roba (comdom) sannan suka haɗiyeta a cikin cikinsu suka haura wata ƙasar, ire-iren haka dai da dama. Sai da tayi sati biyu a asibitin suna kula da ita, inda Emanuel kuma ya gama tsara mata hanyar kubcewar ta daga gare su, yarda da Emanuel ya sa Hambali bai haɗata da kowa ba kamar yadda ya so yayi amma Ema ya hana, dan haka suka tura ta zuwa Niger ita ɗaya, sai dai sun samu tabbacin yaran Sa'ad ne za su tarbeta a filin jirgi sannan su kai ta gare shi. *Niamey=11: 29 na dare*: lafiya lau wani ƙosassen namiji gajere ya sako ta gaba har in da mota take, da kan shi ya buɗe mata ƙofar jibgegiyar motar ta shiga sannan shi ma ya shiga gaba sannan ɗaya namijin ya ja motar, abu ɗaya da ta ji ya furta shine "Wurin oga zamu kaita." Mai tuƙin motar ne ya kalle shi da ɗan yanayi na mamaki yace "Maraɗi fa kake nufi?" "Yeah." Kawai ya faɗa bai sake cewa komai ba, shi ma bai ce komai ba face jan motar da ya ci gaba da yi yana mamakin girma da darajar yarinyar har ma da mahimmancin ta da ya sa zasu ɗauki hanya yanzu cikin daren nan dan kai ta wajen oga. Sau uku suna tsayawa dan bata abinci kamar yadda aka faɗa musu su kula da ita, sai dai duka abincin ba mai nauyi ake bata ba saboda su sun san me ke cikinta, haka ruwa ma wanda basu da sanyi ake bata kamar yadda aka hana bata abu mai zafi har sanda za'a sake mata tiyata a cire abinda ke cikin ta. Tunda taga sun shigo garin Maraɗi wato (Bienvenue, welcome) ta fara kalle kalle da kuma son fara aiwatar da abinda Ema ya faɗa mata da zaran an shigo garin. Yanayin mai kyau ne saboda babu rana ko ɗis sakamakon safiya ce sosai, hasalima ɗaiɗaikun mutane ne ke kai da kawowa, saida ta bari sun yi nisa sosai a cikin garin inda aka shiga da ita unguwar da gidajen da suke ta karo da su kawai ya shaida mata unguwar masu kuɗi ce, dan kusan duk ginin dake wurin ba na wasa bane, hakan yasa sanda dreban ya rage gudun motar alamun ya kusa isa inda yake harin zuwa ita ma ta gyara zaman ta sannan ta dafe marar ta ta kalli wanda shi ke ba wa dreban umarni cikin muryarta mai sanyin gaske da yanayin magana tamkar irin na sangartattun yara tace "Malam, zanyi fitsari, dan Allah ku tsayar da motar?" Saida ya juyo ya kalli idanunta da suka ƙara fitowa tsabar baccin dake idanunta sannan ya maida kallon shi a hanya yace "Ki jira kaɗan, mun kawo inda zamu sauka." Cikin sangarta da son lallaɓashi ta sake cewa "Ba zan iya ba malam, na jure fa, tun a can can nesa nake matsewa, dan Allahhhhh?" Bai ko yi alamar zai kula ta ba, dan haka ta sake matse ƙafafun ta kamar da gaske fitsarin za ta yi tace "Assshhhh! Zan...zai...kar na ɓata muk... Wayyo! Ya taho..." Saida ya fara ma dreban alama da hannu a dake yace "Dakata." A hankali dreban ya ja ya tsaya, kafin su bata umarnin fita ma ta buɗe motar ta fita da ɗan gudu gudu ta nemi shiga wata kusurwa dake tsakanin wasu gidaje, da sauri ƙaton nan ya fito daga daga motar ya nufi kusurwar shima, amma yana ganin Aisha tana shirin saɓule siket ɗin ta sai yayi saurin juya mata baya bayan ya bita da kallon oho! Ashe kina nan ? Ganin ya juya baya yasa Aisha fara takawa a hankali tana ɗan ja baya tana yi kuma kamar za ta duƙa har saida ta shige kwanar dake jikin gidan, kafin kace kwabo ta faɗa wani matsakaicin gida wanda mai gidan ya buɗe ƙofar yana shirin fita wajen aiki... Yadda ta faɗo gidan yasa shi dakatawa daga shirin jefa jakar shi cikin mota yana kallon ta, sai kuma ya kalli amaryar tashi da ko wata uku basu cika ba da aure yace "Kin san ta ne?" Wani kallo ta fara jifan shi da shi matashiyar, sai kuma tace "Kamar ya na santa? Idan ma na san ta za ta shigo mana hakane da gudu?" Aisha da bata yi tsammanin ganin mutane a farfajiyar ba tsare su take da shanyayyun idanunta kamar wacce aka aiko ta ta karancesu, jin mai gidan na faɗin "Shiyasa nake gaya miki ki kiyaye jawo min maƙwabtan nan, b dama suka gana sake musu fuska sai su..." Kafin ya gama faɗa Aisha tayi saurin gyara siket ɗinta da ta tattare tana ɗan takawa kusa da su tana cewa "Assalama alaikum, kuyi haƙuri dan Allah? Na shigo muku kai tsaye haka ba, wallahi wasu mutane ne suka satoni tun daga garinmu, kuma ni ban san su ba kuma ban san nan a ina muke ba, yanzu ma wayo na musu shine na gudo, dan Allah ku taimaka min? Idan suka duba basu Ganni ba nasan zasu tafiyar su sai na tafi." Kallon juna matar da mijin sukayi, sai kuma dukansu suka bita da kallon rainin hankali da rashin gamsuwa da abinda ta faɗa, sai kawai mijin yace" Baiwar Allah, dan Allah ki fitar min a gida kin ji, nan ba wajen taimako bane, sannan ni na sha haɗuwa da ire-irenku, dan haka ki fita ko na fitar dake ta ƙarfi." *Dake* ƙofar gidan nasu ce kawai a buɗe a wannan lokacin, hakan yasa dreban nan da ƙaton da suka biyo ta da gudu gudu suna duddubawa dn ta ɓace musu yasa su leƙo kawunansu cikin gidan, da sauri kuma suka janye kawunan nasu ba tare da sun ga Aisha dake gefen hagunsu ba ta raɓe tunda ta ji kamar sautin gudu an nufo gidan, dreban ne ya ɗan ɗagowa mai gidan hannu dake bin su da wani irin kallo har ya rufe mota ya tunkaro su da niyyar sai ya mari ɗaya à cikinsu, dan yadda suka faɗo masa gida haka tare da kalle masa mata dake sanye da kayan bacci a jikin ta abun ya ƙona masa rai, kafin ya isa gare su kuma dreban da ya ɗgo masa hannu alamar gaisuwa ne yace "Barka yallaɓai, dan Allah wata yarinya muke nema, bata shigo nan ba?" Matar da ta ji mijin bai amsa ba, sannan yana tunkarar su da yanayin nan nashi na rigima da ta sani dan yaje garesu ayi duk wacce za'a yi yasa ba tare da tayi tunanin komawa ɗaki ta saya shigar ta ba tace" Yarinya? Ɓacewa tayi?" Da azama dreban yace" A'a madam, nemanta ne muke, har gidan oganmu ta shiga ta ɗaukewa matarsa sarƙarta mai tsada da kuma kuɗi, daga yin talla fa, dan Allah kun ganta ne? Na tabbata bata yi nisa b..." Tunda ya fara magana matar ke kallon Aisha da ta rarako manyan idanunta tana girgiza mata kai da mata alama dan Allah tayi shiru da bakin ta, shi ma mijin daga ƙarshe kallon ta yayi sai kuma ya kalle su yayi saurin katse shi da cewa" To dan kuna neman yarinya shine zaku faɗo min gida haka dan Allah? Yanzu idan kune aka wa haka zaku ji daɗi?" Tunanin kar mijin ya fallasa yarinyar yasa matar saurin cewa" Allah sarki, bamu ganta ba gaskiya, bata shigo nan ba." Da sauri mijin ya juyo ya kalle ta jin ta zabga ƙarya daga nan tsaye, shi fa so yayi ya faɗa dan a kamata, wato da ta shigo musu nan dan su ma ta yaye su ne ko? Amma bai ce mata komai ba sai kallon _" Ya haka kuma?"_ Da ya bita dashi sannan ya kalle su yace" Bamu ganta ba." Ɗaya ƙaton nan tsaf ya karanci yanayinsu, amma tunda safiya ce sai ya jinjina kai kawai ya ma dreban alama da su tafi, amma tabbas zai dakonci fitar mijin ya dawo gidan dan yarinyar n'a cikin gidan nan. Suna tafiya ya faɗawa dreban yadda zasu yi, Aisha ma na ganin tafiyar su ta fito daga ɗan lungun daya shamakesu da ganinta ta haɗe hannaye ta ce ma matar "Nagode sosai Aunty, nagode miki ƙ..." Ɗaga mata hannu tayi tace "Kinga, ni bana taimake ki bane dan ina goyon bayan halinki, tausayi kawai naji kina bani dana kalli idanunki, amma ki sake hali ƙanwata, wannan ɗabi'ar bata dace da namiji ba ma bare mace." Kallon mijinta tayi tace masa "Sai anjima Bebe, sai ka dawo, idan ta fita ka kulle min ƙofata ta baya." Murmushi ya mata ya jinjina kai sannan ya kalli Aisha yace "Bismillah ko?" Marairaicewa tayi tace "Dan All..." Sai kuma taga tuni matar ta shige ɗaki, hakan yasa ta juya jiki a saɓule da kuma ɗar ɗar ta fita a gidan tana leƙe, ganin bata hangesu ba sai tayi hannun ta na hagu duba daga hannun hagu ta fito ta shigo gidan nan, tana leƙa kwanar ta tabbatar babu su anan ma da gudu ta sake yankar na kare, inda mijin nan yayi yadda matar ta faɗa masa ta hanyar rufo ƙofar da makulli daga baya sannan ya fita yana ta nanata abinda ya faru yanzun. ******************** Murmushi ne ya suɓuce mata na murnar abinda Alhajin ya faɗa mata ya yanke shawara a kan Jabir, ba ƙaramin farin ciki tyi da hakan ba, dan haka ma ita ce gaba cike da ƙarfin guiwa dan su sanar da Jabir ɗin abinda suka yanke. Zaune suka same shi yana kallon ciwon shi na ƙafa da ya kame sosai saboda maganin da Maman su Ummu ta bashi, ba dan yadda y fito daga gidan ba shiri ba ma ai da ya taho da maganin shi ya ci gaba da shafawa, fitowar su ta sa shi gyara zamanshi a ƙasan carfet yana sadda kanshi ganin Alhaji Kabir ya riƙe hannun Ummu Kulsum dake ta hanzarin ta kawo ga Jabir su zauna su faɗa masa abinda suka yanke, fatan ta shine ya amince, burin ta ya amince da shawarar tasu, dan gaskiya ita fa ta tsani mahaifin nan nashi bare kuma matar sa. Alhaji Kabir kuma da ya ga Jabir ya sadda kanshi ƙasa baya kallon su, sai ya samu damar riƙo ƙugunta ya dawo da ita baya kaɗan saboda tashin hankalin dake ziyartar shi sakamakon tafiyar da take da sauri jigidarta kuma sai sauti take bayarwa dake nuna ana tafiya ita kuma tana kaɗawa. Cikin salo da dubara ya ɗan rufe mazaunanta da babbar rigar shi sannan ya shafi inda ke ɗauke da jigidar yana tsare fuskar ta da kallo cikin sigar raɗa yace "Ita wannan abar haka take ne da tonon silili?" Ummu Kulsum dake ta zaro idanu tunda ya riƙo hannun ta take juyawa dan ta ga ko Jabir na kallon su, sai taga dai kanshi na ƙasa kuma har wannan lokacin, cikin dubara da son ƙwatar kanta dan kunya ta mishi raɗa ita ma da cewa" Ba haka bane, sake ni mana kar ya gan mu fa." Ɗan kallon Jabir yayi sai kuma ya kalle ta yace" Yaro ne mai nutsuwa da hankali, dubi, kanshi a ƙasa? Yanzu amsa min tambayata." Cikin sigar shagwaɓa da turo baki tace" Ba haka bane, nima ban san me yasa take haka ba, haka dai take kawai." Ɗauke hannun shi yayi daga ƙugun nata tare da sakin ta yace" Tana ɗaukar hankalin na kusa da ke, ina fata ba duka namiji zai ji kaɗawar sautin ta ba, dan ƙarar ta na ɗaukar hankalina sosai." Murmushi tayi tana ƙara nutsa kanta cikin babbar rigar shi da kunya tace" Da gaske? To ai Maman mu ce ta saka min, kuma tun ina yarinya ma nake da ita, kawai tana sassauya mana ne." Wani basaraken murmushi ya sakar mata yana jin kamar ana dawo masa da ƙuruciyar sa ne ya laƙaci hancinta yace" E mana, a ƴan kwanakin nan da muka yi tare da ke, da sautinta nake iya gane nisan tazarata da ke." Faɗaɗa murmushi ta tayi tare da rufe fuskar ta, shi ma dariya ya yi ya shiga gaban ta ya samu kujera ya zauna yana kallon Jabir da kanshi ke ƙasa har yanzu yace" Malam Jabir kana zaune?" Ummu ma takowa tayi ta samu kujera ta zauna sa'ilin da Jabir ke faɗin" E Abba, sannu da fitowa?" Yana gyara zamanshi yace" Yawwa Jabir, sannu, ka ci abincin kuwa?" Da nutsuwa yace" Na ci Abba, Alhamdulillah." " Ma sha Allah." Ya faɗa yana sake maida dukkan hankalinshi ga Jabir ɗin sannan ya kira sunan shi da" Jabir." A tausashe shi ma ya amsa da "Na'am." Cike da dattako ya fara faɗin "Jabir, ina da yaro mai sunan Aliyu, burinshi ɗaya da naka wato zama mai ilimi, sai dai kai kana son faɗakarwa idan ka koya saɓanin shi da kawai yana so ya koya ne dan ya san yadda zai bautawa ubangijinsa, yanzu haka yana Saudia a babbar jami'ar dake ƙasar yana karatun shi, shekarar sa ɗaya da tafiya, kuma yana so idan ya kammala da nan akwai malamai da alarammomi da ya faɗa min yana son zuwa Sudan dan koyon karatu a wurin su har ma da kalar ƙira'o'i, da wannan ne na yi shawara da Ummu Kulsum kuma ta bani goyon baya." Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ɗora da" Jabir, idan muka ƙyale ka a wannan halin sheɗan zai iya ribantar ka ya jefaka halin da kayi tunanin gaɗawa tun farko, bamu san ina za ka je ba? Da su wa za ka haɗu? Wace irin rayuwa ke jiranka a inda za ka je? Wannan dalilin ya sa naga madadin mu ƙara samun *ɗan ƙasa marar tausayinmu*, me zai hana mu taimake shi da ƙarfin iyawarmu, sai ubangiji ya dafa mana ka zama na gari, idan ka amince Jabir, madadin shiga duniya da kayi ikrari, na tura ka Saudia in da Aliyu ke karatu, ka ga sai kuyi karatunku tare duk da yana gaba da kai a shekarau, a sanin da na ma Aliyu zai riƙeka ne tamkar aboki kuma ɗan uwa, ya ka gani? Hakan ya maka?" Kallon Alhaji Kabir yayi, wani irin ganin girman mutumcin da karamci da kyawawan halayen mutumin yake, bai san shi ba? Bai san wanene shi ba? Bai san komai a kan shi ba? Amma yake so ya taimaka mishi saboda tausaya masa da tunanin halin da zai jefa rayuwar sa a ciki, yaro ne shi da bai da saurin hawaye a rayuwar sa idan ba abinda ya tsaya masa a wuya ba, amma wannan dattakon da dattijon ya nuna masa sai ya saka shi fashewa da kuka ya kifa kanshi a guiwar ƙafar shi. Cikin kulawa Alhaji Kabir ya dafa kanshi yana shafawa tare da daddaɓa shi yana faɗin "Yi shiru mana haka ya isa, yanzu faɗa min mecece amsar ka? Ka amince?" Ɗaga kai yayi cikin kuka sosai da ya ci ƙarfin shi ya riƙo hannun Alhajin dake saman kanshi yace "E... Abba, nagode Abba, Allah ya saka da alkairi, in...ina...*ina ƙaunar ka*, Allah ya biyaka." Da farin cikin ganin ya saka wani kukan farin ciki yayi dariya yace "To daina kukan mana, baka san namiji ne kai ba, ko baka san kuka na mata bane? Za ka zama ragon maza idan kana saurin yin kuka fa, kuma ma a gaban *ƙanwar ka*." Da sauri Jabir ya Ɗaga kanshi ya kalli Alhaji Kabir, sai kuma yasa hannu yana share hawayen fuskar tashi yana kallon bakin Ummu data turo tana faɗin" *Ni ba ƙanwar sa bace wallahi*, na girmeshi fa nesa ba kusa ba." Da mamaki Alhaji Kabir ya kalli Jabir yace" Wai haka?" Da kunyar yadda suka sako shi a zancen su ya Ɗaga kai cikin ladabi yace" E, *wataƙila*." Ƙara haɗe fuska tayi tana ma Jabir wani kallo, wataƙila? Bai gamsu bane har da zai ce wataƙila? Harara ta maka mishi tare da kawar da kan ta, hakan yasa Alhaji Kabir yin murmushi ya kanne wa Jabir ido ɗaya alamar su tsokaneta yace" Ban da abun Ummuna, ai ko shekara biyar kika bashi ina ga yana gaba dake tunda namiji ne, baki san cewa wata rana zai iya zama *garkuwar ki* ba?" Ƙara turo bakin ta tayi gaba ta maƙale kafaɗa tace" Ni wallahi na girme shi, ni fa yanzu shekara ɗaya da na shiga jami'a, shi kuma yanzu ajin kusa dana ƙarshe yake kafin jarabawar shiga jami'ar." Alhaji Kabir ƙyalƙyalewa yayi da dariya ganin ita fa tsakanin ta da Allah take so ta nuna musu ta girme shi, dan haka ya kalli Jabir yace" Jabir, ka bata girman kaji, tunda gashi ƙarara ta nuna Baby ce ita har yanzu, ka sallama mata ka ji ko?" Jabir dai banda murmushi yna sunkuyar da kai ba abinda yake yi sai yanzu da Alhajin ya sake sako shi ya gyaɗa kai sannan yace" Abba ni dama aunty nake kiranta, ita ce babba ai ni kuma ƙanenta, gashi ta tabbatar da haka." Kallonta Alhaji yayi yace" To kin ji ba? Ya baki girman, hakan yayi ko nima na ƙara miki nawa shekarun?" Tintsirewa tayi da dariya tare da rufe fuskar ta, sai kuma ta tashi da gudu ta nufa hanyar ɗakin ta saboda kunya. Girgiza kai Alhaji yayi ya bita da kallo yana faɗin" Hmmm! Mata da son girma, sai Allah." Sai kuma ya kalli Jabir suka ci gaba da magana da shirin abinda zai fishe su kan tsarin tafiyar shi da abinda ya kamata su yi. *ME CE CE DAMUWAKI*? Rashin ni'ima? Rashin gamsar da mai gida? Warin gaba? Bushewar gaba? Zubewar nono? Cikowar nono ? *Kina buƙatar...* Fatarki tayi laushi? Tayi santsi? Ta kwanta luf? Kina walkiya da annuri tamkar amarya? Sabulu kike so ko haɗin shafawa ki wanke ko mai na shafawa? Ki wadatu da sahihin ƙamshin haukata mai gida? Humra da zaki saka mijinki bacci bai shirya ba? Humra da zata tayar da sha'awarsa? Kulaccha da zata saka mijinki ya kasa yi miki tsara a fannin ƙamshi? Kulaccha da zata gagari manyan mata suffanta kalar sunan turarenki? Turaren wuta irin na asali barebari? Turaren da zaki fesa à zanin gadonki har ya rike mai gida ya kasa tashi? Turaren da zaki zuba ga ruwan wankan mai gidan ki? Turare don yaranki? _Idan duka kina buƙatar ɗaya daga cikin kayan nan, to ki tuntuɓi wannan lambar ta WhatsApp *+227-82-21-91-74* wanda suk gwada sun san ingncin kayanmu, ba buƙatar ɓata lokacin cika muku baki._ Wani abun farin kuma, duba da yanzu ba kowace mace ke son shan garin magani ko matsi ba, akwai haɗi irin su *tsumi*, *ruwan tsumi*, *tukunya*: dayawa sun san tukunya, don da itace muke tutiya, kuma tukunyar nan akwai na ruwa dana dafawa a nama, sannan akwai kankat wato haɗin *kayan marmari*. *Garaɓasa* Ga waɗanda sukayi nisa kuma haɗin kayan marmari ba zai kamacesu ba, duba da kafin sakon yaje garesu zai fara lalacewa, don haka ga sauki ya samu, madadin kuɗin mota da zaki yi, zaki biya 1000k kacal don a sanar dake yadda zaki had, ba iya guda kawai ba, dama sauran haɗi irin na kayan daya shafi na marmari da ɗanye, musamman ma *sirrin kankana* da kuma *cucumber*. *JANNAT HOUSE.*🧕 *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HARUN* *MURA'ATU ULTIMATE COLLECTIONS* shin kin zuba tagumi ne uwar gida da amarya da tunanin ta inda zaki haɗa kayan kitchen ɗinki? Ko kuma fabrics kike da buƙatar canzawa na kece raini a cikin sa'o'inki? Shin kina so ki san a inda gawurtattun mata ke haɗa nasu perfumes ɗin? Ko lausasan zanen gado da kyawawan electronics gama hawa kike da bukata? To Matso kusa, zan faɗa miki inda ba ke kawai ba, hatta mai gidanki zaki iya rakawa dan siyo nashi electronics ɗin da sauransu, wato *MUC* mun shahara a saida Kayan *kitchen*, *fabrics* na kere sa'a masu quality, *bedsheets*, *electronics*, *beauty products*, *perfumes* da *kayan kwalliya* . Bugu da ƙri Hajia ta akwai data tare da *katin waya* ta kowane network and *catering services*, da wannan nake cewa daku, sai an gwada akan san na kwarai. *MUC* 🤝🤝🤝🧕BAMU DA SA'A. Ga mai buƙatar tuntuɓarsu, ga lambar WhatsApp: 07038274166 Call: 07038274166 & 07031057802 Location: Kano with nationwide delivery. _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *8* Mother, ta faɗa mata wata mata ce ta kawo ta gidan marayun na sannan ta faɗa musu sunan ta, duk yadda take jin ba daɗi akan rashin sanin kowa nata, da kuma tashin hankalin d ta gani a asibitin Hy da ita kan ta halin da take ciki, bata taɓa jin ɗaci irin na yau da take ta yawo a garin da bata sani ba kuma bata san kowa ba, tayi yawo ta gaji ta tsaya ta huta, sa'ar ta ɗaya ruwan sha da take samu a sauƙaƙe, amma yunwa ƙwaƙular mata ciki take kuma ta rasa mai taimaka mata, dan ta shiga gidaje sama da guda shida amma ko ina tsoron taimaka mata ake ji, hakan yasa ta shiga tunani da tambayar kanta wane irin fanti mutane marasa imani suka ma sauran masu neman taimako haka? Ƙarshe ma tana zaune a wata inuwa kusa da wata ma'aikatar siminti maza masu aikin wurin na ta shiga da fita, wani marar tsoron Allah tsayawa yayi wurin ta ganin magariba tayi yace "Ƴan mata sannu ko?" Kanta na haɗe da guiwa ta kalle shi da idanunta da tsabar yunwa suka sa suka ƙara fitowa waje kamar za su faɗo tace "Ina wuni?" Murmushi ya sakar mata tare da amsa mata yace "Lafiya lau, ya na ganki zaune a nan tun tuni? Wani kike jira? Ko ɓata kika yi?" Kukan dake son kubce mata ta dinga ƙoƙarin haɗiyewa tana ƙara sadda kanta tace "Ban san kowa a nan ba, shiyasa nake zaune ni kaɗai." Da mamakin abinda ta faɗa ya yi irin tsugunnon nan yana cewa "Ba ki san kowa ba? Daga wane gari kike?" Saida ta ɗan sake kallon shi, yanayin shigar shi da kayan jikin shi y nuna daga aiki yake kuma irin aikin ƙarfi, dan duk datti ne kayan nashi haka ma jikin shi, ƙara sunkuyar da kanta tayi sannan tace "Daga nesa nake, wasu ne suka sato ni." Wani ƙayataccen murmushi ya sake saki saboda ganin tarkon sa zai kama kurciya, a ƙalla idan ta yarda da shi dai ba zai gagara ɗaukar nauyin abinda za ta ci ta sha ba, hakan zai sa su jima haro sanda zai gaji ya kubce mata, hakan kuma na nufin zai more ta ƙwarai, a hankali ya ɗaga hannun shi dake riƙe da baƙar leda ya mayar da ita ɗaya hannun sannan ya zura shi ya dafa hannun ta data yi ma guiwoyinta zobe da shi, cikin sigar yaudara yace "Karki damu kin ji ? Muje inda nake kwana sai ki zauna a can, kinga nan magariba ta gabato, idan duhu yayi kuma akwai hatsari a wurin sosai, tashi muje, sai na siya miki abinci ma, na san kina jin yunwa ko?" Fiƙi-fiƙi ta mishi da idanu tana ƙyabta su, cike da tsoro da fuskantar inda duniya ta fara sa gaba saboda Mother tana koyar da su abubuwa dayawa kasancewar su ƴan mata tace" Kai da wa ye a gidan? Kuma zan iya kwana babu matsala?" Ba tare da ya daina mata murmushin nan b yace" Ko kaɗan ba wata matsala, kuma ba gidan iyayena zan kai ki ba, inda nake kwana tare da abokaina zan kai ki." Saƙe tayi tare da ƙura masa idanu har da sakin baki alamar dai mamaki ƙarara, ƙwarai ta gane me yake nufi ta wani ɓangaren, amma ta wata kusurwar sam bata fahimta ba, shi da abokan shi? To su nawa? Ita sai ta kwana a ina? Tana mace su suna maza? Kuma yana ganin hakan ya dace? A hankali ta fara jin tsoron shi yana kamata, dan haka ta yunƙura da sauri ta miƙe tana kakkaɓe siket ɗin ta a baya tace "A'a ka bar shi, nagode sosai." Hanya ta kama za ta raɓashi ta wuce, da sauri ya miƙe tare da riƙe babban kallabinta data rufe jikin ta da shi yana faɗin "To shikenan na gane, yanzu faɗa min nawa ne farashin?" Juyowa tayi da mamaki ta sake kallon shi tace "Farashin me?" Ba tare da fargaba ba ko kunya yace "Ina nufin farashinki?" Sosai ya sake durmiyata tunani, ba ta san me yake nufi da farashinta ba gaskiya, dan haka ta zuba masa idanu kawai tana kallon shi, shi ma kallon fuskar ta yake yi musamman ma idanunta da shi suka fi mishi kama da na wacce ta sha babban abu mai bugarwa irin su giya haka, idan ko ba wani abu ta sha ba to tabbas gogaggiyar ƴan bariki ce dake fara jan hankalin abokin harƙalla da idanunta, sai kuma gashin dake kwance gaban goshinta, shi dai idan zai bata suna sai ya ce da ita *baƙar buzuwa*, dan duk da fatar ta mai duhu ce tana da kyau da kuma alamar yalwar gashi. Da son nuna mata ƙwarewar shi a harkar nan ya sake cewa "To kinga? Ki faɗa min nawa zan biyaki a kowane kwana ɗaya? Sannan abokaina ma zaki iya samun wanda zai yaba, kinga kenan kin ƙara samun kasuwa ta dalilina." "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un !" Aisha ta faɗa tana fizge kallabinta tare da ja baya, hawaye ne suka fara gangaro mata a kumatu tasa hannu ta share da mugun sauri ta raɓashi ta wuce ba tare da ta ce masa ci kanka ba, da kallo ya bita shi ma dan ba zai iya bin bayanta ba dan ta nufi hanyar titi ne dake da mutane, ƙugunta mai dirin kwalbar koka cola ya dinga bi da kallo da jin takaicin rasa ta da ya yi. ******************* Bai taɓa sanin ya iya murmushin nan da ake cewa malalacin murmushi ba sai yau kuma yanzu ya tabbatar bayan jin wani zance daga wajen mahaifin nashi, ba tare da ya daina murmushin nan ba ya kalli mahaifin nashi da matsakaitan idanun nashi tare da kai yatsar shi yana shafa girar shi cr ɓaren daman shi wanda hakan ɗabi'ar sa ce, bai ce da shi ƙala ba har saida ran mahaifin nashi ya sake ɓacewa ya gyara tsayuwar shi yace "Da Kai fa nake magana *Sa'ad* ka min shiru? Ka san dai ba ƙarya za'a maka ba ko, idan har ka san kana sana'ar da bata dace ba ka daina tun wuri, dan ikona bai isa ya hana ka fuskanci hukunci ba idan har aka kamaka da laifi." Tsaf! Take ya haɗiye wannan murmushi da yake yi tare da gyara tashi tsayuwar shi ma yana fuskantar shi, duk da ran shi ya ɓace ne kuma martani ne yake son mayarwa, amma ɗabi'arsa ce sanyin murya ta yadda wanda bai san shi sosai ba zai yi gardama idan aka ce maka Sa'ad na faɗa ko hargagi, cikin tattausan muryar shi mai sanyin da bata da maraba da ta wata macen yace faɗin "Iko? Iko gareka dama? To ai dama ban ce ina son taimakon ka ba? Idan an kamani dan Allah kar ka nuna ka sanni, *Ibu* (Ibrahim, sunan mahaifin nashi) na ɗauka duk sana'ar da na fara kai ne sila, to me ye kuma yanzu na tsare ni kana min wannan maganganun? Ko ka manta lokacin da duk na roƙeka hatta da abun goge baki sai ka min gorin rashin sana'a? Zan zauna ne talauci ya kasheni?" Gemunshi da ba yawa gare shi ba illa kewaye bakin shi da ya yi zuwa kumatu ya shafa sannan ya ci gaba da faɗin" Idan an kamani kar ka nuna musu ka sanni, ni zan yi ƙoƙari na fito da kaina, idan kuma matan ka ne suka zugoka a kaina to ka faɗa musu wallahi su fita a harkata, idan ba haka ba zan musu ba daɗi." Wayoyin shi dake saman gajerar katangar dake ɗauke da kullaye masu shukoki ya ɗauka babba da ƙarama tare da raɓawa zai wuce dan ɓangaren ƙofa ɗaya ce ta shigowa kuma dole sai ya bi ta gaban mahaifin nashi zai iya fita, hakan yasa Alhaji *Ibrahim* ɗin ya riƙe damtsen shi dake ɗaure tamau cikin matsatsiyar rigar shi mai dogon hannu ta kayan motsa jiki, dakatawa yayi sukayi ido huɗu da sauri kuma ya kawar da kanshi yace "Zan fita." A hassale Alhajin yace "Me kake nufi kenan Sa'ad? Ka fi ƙarfin a faɗa maka gaskiya? Duk abinda zai same ka dole ne ya shafe ni tunda ni na haifeka, sannan matana da kake magana ka daina saka su a ciki dan basu san komai ba, na faɗa maka aminina ya gaya min abinda ake zarginka da shi, sun kuma tabbatar min idan har gaskiya ne za su hukunta ka daidai da kowa." Juyowa ya sake yi yana kallon fuskar shi, kamar ma karanta wani abu a fuskar shi sai kuma ya kalli hannun Baban nashi dake riƙe da damtsen shi ya furta" Hannuna?" A hankali Alhaji Ibrahim ya janye hannun shi daga na Sa'ad ɗin yana ƙara gyara tsayuwar shi, Sa'ad na takawa ɗaya biyu ya sake cewa" Ban gama magana da kai ba." A ƙufule ya dakata tare da juyowa ya zuba masa idanu kamar zai fashe da kuka yace" Wai me yasa kake son takura min? Za ka je harkokin ka har kayi wata biyar ko shida ba kya ƙasar nan, amma ranar da duk ka zo ta kaina kake farawa." Cikin ɗaga murya Alhaji Ibrahim yace" Yes, dole ne na fara ta kanka." "Saboda...?" Sa'ad ya tambaya cike da izgilanci, a take Alhaji Ibrahim yace "Saboda kai ne ɗa namiji babba a gidan nan, dan haka dole zan saka maka ido." A nutse ya saki wani murmushi tare da takowa ya tsaya gabanshi yace "Ibu, kana da abun dariya wallahi, to ina jinka? Me kuma na sake yi?" A tausashe kamar mai tsoron faɗin abinda ke bakin shi Alhajin ya ce "A cikin gida ne, sun faɗa min har yanzu ba ka daina kawo musu mata ba, bana so Sa'ad, bana son ka na kawo min mata cikin gida." A hankali ya girgiza kai tare da ɗaga girar sa ɗaya yace "Rayuwata ce fa..." A ƙfule Alhaji ya katse shi da cewa "Ni kuma gidana ne nan, dan haka nace bana so ka sake kawo min mata a ciki, na gaya maka..." Ya ƙarashe da nuna shi da yatsa, murmushi Sa'ad ya yi tare da ɗaga kafaɗu yace "Me kake ci na baka na zuba Ibu? Bai fi kwana ƙalilan ba na kammala ginin gidana ba nima, ina kammalawa sakan ba zan sake yi a cikin gidan ka ba, kuma idan na tafi na tafi kenan sai ranar da ka neme ni." Yana gama faɗa ya juya a hassale ya nufi inda ƙofar fita take yana ta ƙoƙarin saƙala abun sauraro a kunnen shi saboda ya saba in dai zai fita gudun nan na yamma sai ya saka abun sauraro yadda hayaniyar ababen hawa bata damun shi. Da kallo Ahaji Ibrahim ya bishi har ya fita daga gidan, ajiyar zuciya ya sauke tare da fara takawa zuwa nashi ɓangaren, bai san yaushe za su shirya da ɗan nashi ba? Bai san yaushe zai fara masa kallon uba ba? Shi da mahaifiyar sa ma bata gidan nan saim ya ce ko dai matanshi ne suka shiga tsakaninsu, abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, ya san yana da laifi tun farko shi ma, amma me yasa Sa'ad ba zai gane ya fahimci kuskurenshi ba kuma yana so su sulhunta? Me yasa ba zai sake bashi wata damar ba su fahimci junansu? Amma matsayin shi na babba ɗa kuma namiji a ce haka na faruwa tsakanin su? Ai Sam bai dace ba, idan ya faɗi ya rasu wa ye zai kula da gidan nan? Gashi ƙannai gare shi masu tasowa da masu wayo, komai da yake ai suna kallo kuma wasu za s iya koya daga gare shi, dan an ce daga n'a gaba ake gane zurfin ruwa, hatta sunan da yake kiran shi da shi Ibu sai da Mujahid ya fara kiran shi haka mamanshi dai tayi gaggawar dakatar da abun. Amma haka Sa'ad yake kallon shi gatsau yana kiransa da Ibu, sunan da tun da ƙuruciya ne ake faɗa masa shi. Yana shiga tunkarar ɓangaren shi ya fara jiyo hayaniyar da ta saka shi girgiza kai yana ambaton "Uhum ! Na dawo ba, na zo garin ba." Ba tare da wani sassarfa ba ya ci gaba da takawa har ya hango matan na shi su uku tare da tsohuwar mahaifiyar shi da alamu ya nuna rabon rigimar take amma abun ya ci ƙarfin ta, saida ya ƙara matsawa kusa da su ya fara fahimtar akan me ake faɗan kuma wacece silar tayar da rigimar. Isowar shi daidai da Hajia Uwani dake ta cira tana kumfar baki kamar za ta daki Hajia Zarah duk da kuwa shekarun ta da ma kasancewar ta matar shi ta farko, amma faɗi take "Da kunnuwana na ji ki ai kina masa gulmar Sa'ad, shikenan yaro kamar ba gidan ubansa ba, ku da yaran ku sai kuyi abinda kuke so, amma shi da yayi sai ya zama laifi, burinku kullum shine ku ga shi da ubansa ba sa ga maciji, to na gaji da munafurcinku, wallahi aka kuma sa min yaro gaba sai na ci uban kowa a gidan nan, idan ya so a koreni tunda ni da ɗana ai ba ƙaunarmu ake ba dama." Zarah kam girgiza kai tayi cikin rashin jin daɗin abinda ke faruwa tace" Subhanallah, Haba Hajia, ya zaki yi jam'i bayan kin san a gidan nan akwai manya, kuma ni na faɗa miki wallahi ba ni na tado maganar Sa'ad ba, Alhaji ne ya tambaye ni ko ya daina abinda yake ni kuma na faɗa masa gaskiya." Cikin zaƙalƙakewa Hajia Uwani tace" E mana kya ce haka, in da ɗanki ne ai ba zaki faɗa masa gaskiyar ba, sai dake na wa ɗan ne daya tsone muku idanu ko? To ni dai na faɗa muku wallahi, a sakar ma yaro mara ya yi fitsari mana, haka kawai za'a nemi tisa min yaro a gaba, ba ma tun ranar da labari ya yaɗu a gari cewa yana ginin da a shekara goma da ta wuce ba matashi kamar da ya yi irin wannan ginin, kuma anan kusa ma ba za'a samu ba, shikenan sai a dinga bi shi da jafa'i kala kala." Hajia da tun tuni take ta ba Uwani baki ta ƙi sauraren ta ne ta kalli Zarah a tausashe tace" Ke Zarah, wuce ciki kinji? Kar na sake jin bakin ki a nan, wuce maza ga abin da zai fisheki." Jin haka Hajia Sabira da ita ma haƙurin take ta bayarwa ita ta fara saurin shigewa falon sannan Hajia Zarah ta biyo bayan ta, Hajia ma juyawa tayi za ta bar wurin Uwani ta taɓe baki tace" Su dake ƴaƴan so ne ai an faɗa musu haka, wallahi i da ɗana ne dai kabewar kan kabari ne baƙin cikin mai taushe, ehe..." Juyowa Hajia tayi ta mata wani irin kallo, tsohuwa ce tabbas tunda an kwarari shekara sittin da ƴan kai, amma kuma kulawa da rayuwar jin daɗi ya sa kai tsaye ba zaka ce ta kai wannan shekarun ba, bugu da ƙari tana kama jikinta sannan bata san wasa, fuskar nan a haɗe take kallon Uwanin data fara shan jinin jikinta, dan za ta iya cewa Hajia ta zame mata ƙarfen ƙafa, ba tun yau suke gwagwarmaya da matar nan ba, ta kuma buga da ita dole ta bar ta a inda take, dan haka suke zaman lafiya kawai idan ba haukanta ya motsa ba ta sako tsohuwar a ciki, to tasss take mata dan bata ɗauka ko kaɗan. Cike da dattako da kuma gargaɗi har tana runtse idanu tace "Uwani, kin san dai ni ba tsaran ki bace ko? Sannan duk wanda ya yi zagi a kasuwa ya san da wanda yake, to ki iya bakin ki, sannan ki sani duk abinda ya samu shamuwa, to watan bakwai ne ya ja mata, da ba'a yi daren ba kuma gari ba zai waye ba, ba ke ko ɗan ki ba, *Iro tela* (Alhaji Ibrahim) ma bai isheni bare kuma ku, dan shi da kike taƙamar da shi ni na tsuguna na haifi abuna, ki kiyaye ni." Juyawa tayi za ta wuce, sai kuma ta tuna da wani abun ta tsaya tare da juyowa, da yatsa cike a gargaɗi tace mata" Ki turo min idan ya dawo daga guje-gujen nashi, idan kuma ya bar gidan nan bai zo inda nake ba, laifin a kan ki." Sake juyawa tayi a nutse tana takawa, ganin haka ne ya sa Iro tela in ji Hajia tahowa suka haɗe, duk da sun gaisa dan kusan wurin ta ma ya wuni, amma daɗin yadda ta kashe masa wutar nan wanda yake da tabbacin da shi ne sai Uwani ta ɗaga masa hankali kaɗai hankalinta zai kwanta ya sa shi sake rusunawa ya gaishe ta, amsawa tayi da fara'a tare da wucewa nata ɓangaren. Suna haɗa ido da Uwani ta turo masa baki tare da juyawa a hassale ta shiga ciki ita ma tana raya _"Ba zan turo shi ɗin ba, ki yi abinda za ki yi."_ Amma take wata zuciyar ta gaya mata _" Um um ! Kar ki bari ta ja miki abun kunya a cikin kishiyoyi, ko kin manta da Hajia *Yakura*? Matar da ta ga kina neman ɗagawa ɗanta hankali lokacin da zai auro Sabira, take, sau ɗaya tak ta ce ma Alhaji ce ta tafi gidansu sai ka nemeta, haka kuma aka yi ba ki kwana a gidan ba, dan haka yi haƙuri ki tura shi kawai, ai ba faɗuwa kika yi ba."_ Alhaji Ibrahim kuma ko a jikin shi, rigima, masifa, bala'i inda na Uwani ne ba wanda bata biya masa shafin shi ba kuma ya hardace shi tsaf a kai, dan haka idan ta so su suhulta a zauna lafiya, idan ta ƙi kuma ya ba banza ajiyar ta kamar yadda ya saba har sai ranar da ta ga dama ta nemi sulhu da kanta. Yana cikin gudu wayar shi ta dinga ƙara, ta abun sauraron ya danna OK tare da faɗin "Ina ji?" Da fargaban abinda zai iya yi masa ƙaton nan daga ɓangaren shi yace "Oga barka?" Ba tare da ya dakata da gudun shi ba cikin haki na gudun da yake yi yace "Ido na zuba maka ai na ga za ka kirani ko kuma a'a, DG tun jiya fa kuka taso da yarinyar nan, kuma duk iskancin ku na tabbata 08:00 na safe sai kun iso garin nan, amma shine dake ni ga ɗan isa kuka wani yi banza dani ko? To ina jin ka?" Cikin duburburcewa da rashin gaskiya yana inda-inda yace" Ka yi haƙuri Oga, wallahi an ɗan samu matsala ne." Daga inda yake akan titi ya tsaya cak yana ci gaba da huci ya dafe ƙugu yace" Wace rin matsala?" A saiɓance ya furta" Yarinyar ce ta ɓata Oga, ta ɓace mana." Shiru yayi yana kallon titi da ababen hawa, sai kawai ya ƙara tausasa muryar shi yace" Kun kyauta, amma ka sani ba zan yi asarar kwabo ba, milyoyin kuɗina ne a cikin yarinyar nan, ba'a turo min ita ba sai da na tura kuɗina, dan haka ka da ka sake kirana har sai ka nemo yarinyar, idan ba haka ba wallahi za ka biyani kuɗina ne." Jin yana shirin katse wayar yasa DG saurin faɗin" Oga dan ka saurare ni?" Tafiya ya fara yi akan titin yace" Ina jin ka?" Cikin magiya yace" Ka yi haƙuri Oga, wallahi cikin neman ta muke har yanzu, yarinyar ta ribace mu ne har ta gudu, kuma gidan da muke zargin ta shiga a erea muka wuni muna dakon ta amma ba ta fito ba, yanzu bayan dawowar mai gidan mun karya doka mun shiga gidan muka bincike amma ba mu same ta, Shiyasa na kira dan ka san halin da ake ciki, amma na tabbata zamu samo maka ita yallaɓai." Cike da halin ko in kula Sa'ad ya taɓe baki yace" Matsalar ka ce, na gaya maka ka da ka sake kirana muddin baka same ta ba." Da sigar rarrashi DG ya sake faɗin" Oga, dan Allah to ka mana wani taimako? Da za ka yi magana da Yallaɓai ya turo mana ko hoton ta hakan zai taimaka mana, sannan fa ka san tana cikin hatsari saboda ba komai za ta ci ba saboda kayan nan dake cikin ta, har a samu matsala ledar ta fashe mu zo muyi haihuwar guzuma." Tabbas gaskiya DG ya faɗa, dan haka bai watsar da maganar sa ba illa kawai cewa da yayi" Na ji." Sannan ya kashe wayar tare da ci gaba da gudun shi. Duk yadda ya so ya isa gida kafin sallah magariba abun bai yiwu ba, hakan yasa dole ya tsaya a matsalacin hanya yayi sallah, duk da yayi gumi sosai amma kuma zufar na fitar da ƙamshin Turaren Gucci da ya yi anfani da shi, ana idar da sallah ya fito dan ƙarasawa gida. Tafe yake yana turawa Hambali saƙon ɓatan yarinyar da kuma son ya turo mishi hoton ta, yana gama tura masa saƙon ganin ya shigo layin gidan nasu ya sake mayar da wayar aljihu ya fara gudu sai dai a hankali ƙwarai, fitowar *Aisha* da gudun bala'i sakamakon wasu samari su uku da tun tana sallah a bakin wani gida sukayi tsaye suna mata magana, da ta idar ta tashi dan bar musu wurin kuma sai suka dinga kiranta suna mata magana, hakan yasa ta dinga sauri ba ta kula su ba, dan ta lura suma sheɗanu ne kamar dai wannan na ɗazu, hakane yasa suka shiga bint suma da sassarfa suna daka mata tsawa da cewa "Ke! Ke! Ba ki ji ne? Da ke ake magana." Dalilin da yasa kenan ta tsorata matuƙa ta zabga da gudu tare da karyo kwanar da take tunanin ko ta samu maceci, cikin ikon Allah Sa'ad dake ɗan gudun shi a nutse ta kawo masa karon da ya saka shi yin baya da ƙarfi saboda abun bazata ya zo masa, hasalima bai taɓa tsammanin zuwan mutum ba a wannan lokacin, sai gashi an fito masa da ƙarfi an kuma yi awon gaba da shi, rashin sanin waye da kuma wace manufar aka bangazoshi haka yasa Sa'ad yin azamar riƙo damtsen jinsin da bai gama tantance namiji ne ko mace ba, shi dai kawai ya jawo wanda ya kawo masa karo ne dan su yi mutuwar kasko. Mummunar faɗuwa yayi da ta sa duka sassan jikin shi amsawa har saida ya runtse idanunshi sannan ya furta "Aouuuu!" Aisha ma duk da akan jikin shi ta faɗa amma sai da ta ƙwala ƙara dan ba tayi zaton abun ba ita ma, wannan ƙarar ta ankarar da shi da mace ya yi karo kenan, a hankali ya sa hannayen shi ya ture ta gefe ɗaya sannan ya yunƙura ya tashi yana kaɓe jikin shi tare da yi mata wani kallo sanda take tashi tsaye ita ma tana waiwayawa bayanta tana faɗin "... *ME CE CE DAMUWAKI*? Rashin ni'ima? Rashin gamsar da mai gida? Warin gaba? Bushewar gaba? Zubewar nono? Cikowar nono ? *Kina buƙatar...* Fatarki tayi laushi? Tayi santsi? Ta kwanta luf? Kina walkiya da annuri tamkar amarya? Sabulu kike so ko haɗin shafawa ki wanke ko mai na shafawa? Ki wadatu da sahihin ƙamshin haukata mai gida? Humra da zaki saka mijinki bacci bai shirya ba? Humra da zata tayar da sha'awarsa? Kulaccha da zata saka mijinki ya kasa yi miki tsara a fannin ƙamshi? Kulaccha da zata gagari manyan mata suffanta kalar sunan turarenki? Turaren wuta irin na asali barebari? Turaren da zaki fesa à zanin gadonki har ya rike mai gida ya kasa tashi? Turaren da zaki zuba ga ruwan wankan mai gidan ki? Turare don yaranki? _Idan duka kina buƙatar ɗaya daga cikin kayan nan, to ki tuntuɓi wannan lambar ta WhatsApp *+227-82-21-91-74* wanda suk gwada sun san ingncin kayanmu, ba buƙatar ɓata lokacin cika muku baki._ Wani abun farin ciki kuma, duba da yanzu ba kowace mace ke son shan garin magani ko matsi ba, akwai haɗi irin su *tsumi*, *ruwan tsumi*, *tukunya*: dayawa sun san tukunya, don da itace muke tutiya, kuma tukunyar nan akwai na ruwa dana dafawa a nama, sannan akwai kankat wato haɗin *kayan marmari*. *Garaɓasa* Ga waɗanda sukayi nisa kuma haɗin kayan marmari ba zai kamacesu ba, duba da kafin sakon yaje garesu zai fara lalacewa, don haka ga sauki ya samu, madadin kuɗin mota da zaki yi, zaki biya 1000k kacal don a sanar dake yadda zaki had, ba iya guda kawai ba, dama sauran haɗi irin na kayan daya shafi na marmari da ɗanye, musamman ma *sirrin kankana* da kuma *cucumber*. *JANNAT HOUSE.*🧕 *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HARUN* *MURA'ATU ULTIMATE COLLECTIONS* shin kin zuba tagumi ne uwar gida da amarya da tunanin ta inda zaki haɗa kayan kitchen ɗinki? Ko kuma fabrics kike da buƙatar canzawa na kece raini a cikin sa'o'inki? Shin kina so ki san a inda gawurtattun mata ke haɗa nasu perfumes ɗin? Ko lausasan zanen gado da kyawawan electronics gama hawa kike da bukata? To Matso kusa, zan faɗa miki inda ba ke kawai ba, hatta mai gidanki zaki iya rakawa dan siyo nashi electronics ɗin da sauransu, wato *MUC* mun shahara a saida Kayan *kitchen*, *fabrics* na kere sa'a masu quality, *bedsheets*, *electronics*, *beauty products*, *perfumes* da *kayan kwalliya* . Bugu da ƙri Hajia ta akwai data tare da *katin waya* ta kowane network and *catering services*, da wannan nake cewa daku, sai an gwada akan san na kwarai. *MUC* 🤝🤝🤝🧕BAMU DA SA'A. Ga mai buƙatar tuntuɓarsu, ga lambar WhatsApp: 07038274166 Call: 07038274166 & 07031057802 Location: Kano with nationwide delivery. _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *9* Tsaye tayi ita ma tana waiwayawa bayan ta tana faɗin "Ka yi haƙuri dan Allah, wallahi wasu ƴan iska ne suka biyo ni, ka yi haƙuri na bige ka ko?" Ko ƙyabtawa bai yi ba yana kallon ta mamaki na sake baibaye shi, faɗuwa fa ya yi ƙasa da ƙarfi, yanzu haka ji yake ƙasusuwanshi na ta motsawa, dole ma sai kakar shi ta masa ruwan zafi, dan in ba haka ba jikin shi zai yi ta ciwo ne, shi ne za ta wani tambaye shi wai ta bige shi? Kuma ta ƙara da ko? Han! Ƙafarshi yayi niyyar ɗagawa dan ya tafiyar shi, sai kawai ya ji tana faɗin "Ni Aisha na shiga uku, Allah ka taimake ni." Dakatawa yayi ya kalleta, dake ba haske a wurin sosai bai ga sararin tsaya yi mata kallon ƙwaƙwaf ba, sai dai abu ɗaya da baya ɓuyuwa à fuskar ta shin idanunta, har da ɗan leƙa fuskar ta yayi saboda tana ta ƙakkaɓar jiki ne har da daf guiwar ta da take jin kamar ta bugu sosai, da halin ko in kula da kuma basarwa yana mata wani kallo mai kama da harara yace "Kina da ido manya, amma da alama madubin su baya aiki ko?" Da sauri ta kalle shi, sai kuma ta sa rage girman idanun nata tana masa wani kallo ƙasa ƙasa tace "Tubarkallah, ma sha Allah." Ɗaga gira yayi ya bita da kallon "Oho! Na gane fa." Sai kawai ya ja siririn tsaki ya gifta ta gaban ta zai wuce yana ji kamar ma ya mata Allah ya isa kada shin da ta yi, da kallo ta bi bayanshi, yadda bai ma mata magana akan yadda ta kawo masa karo ba, duk da kuwa ta kayar da shi matsayin shi na babban mutum, sai ta ji kamar zai yi kirki ai, dan haka wata zuciyar ta raya mata ta nemi mafi ƙanƙantar abinda ta fi so yanzu a taimake ta da shi. Da sauri ta bi bayan shi tana faɗin " *Abbu*, Abbu." Juyowa yayi a saiɓance ya zuba mata matsakaitan idanun shi da mamakin furucin ta, rashin tabbaci yasa har saida ya jujjuya dama da hagu don san ya ga ina Abbu ɗin? Amma bai ga kowa ba a wurin, Aisha da ta ƙaraso kusa da shi da murmushi a fuskar ta tana ta ƴan kame-kame tace "Abbu, dan Allah wa..." Da yatsa ya nunota cike da gargaɗi yace "Ke! Ni ba Abbun ki bane, Kinga nayi miki kama da wanda ya fara tara iyali ma bare wanda ya isa haihuwar ki?" Kamar da gayya sai kuwa Aisha ta kalle shi daga ƙasa har ta sake dire duban ta a kan fuskar shi, manyan idanun ta da ta zuba mishi yasa ya ji kamar ya tsargu har saida ya ɗan kawar da kan shi sannan ya sake yunƙurin tafiyar sa, da azama ta sake bin bayan shi tace "Dan Allah fa nace, wallahi yunwa nake ji sosai, gashi ban san ina zai je ba." Dakatawa yayi tare da sake juyowa ya kalleta, da sigar tuhuma yace "Daga ina kike?" Daidaita nutsuwar ta tayi sannan tace "Daga wani gari, kuma ban san kowa ba anan." Gyara tsayuwar shi yayi yace "To me kika zo yi nan?" Marairaicewa tayi tace "Ba ni na zo da kaina ba, wasu ne suka kawo ni nan, masu satar mutane ne." Zaro idanu ya ɗan yi a tsanake sai kuma ya nuna alamar basarwa yace "Me kuma ya haɗaki da su?" Cike da ƙuruciya tace "Nima ban sani ba, nan suka kawoni, ina ga siyar da ni zasu yi sai su kai ni in da za'a yanke min kaina." Ɗan karkata kan shi yayi garin kallon ta da nazarin abinda ta faɗa, e kam ba abinda ba za'a iya aikatawa ba, sai dai mamakin shi shine, ashe dai gaba da gabanta, duk iskancin shi kuma akwai na gaba da shi, yana ganin baya kyautawa kan shi a kan sana'ar nan ta miyagun ƙwayoyi, ashe akwai wanda suka dame shi suka shanye? Shi kam ai duk neman kuɗin shi gaskiya ba zai iya salwantar da rayuwar mutum kamar shi ba. A ƙalla dai ya ji a ran shi tana buƙatar taimako, dan haka ya juya a wani gadarance cike da halin ko in kula sannan yace "Muje..." Da saurin ta ta bi bayan shi fuskar ta ɗauke da murmushi, amma kuma tuna mutumin nan na farko, sai ta dakata cak ta kalli ƙeyar shi tace "Ina za ka kaini?" Juyowa yayi ya kalle ta da yanayin fara hassala yace "Ba taimako kike nema ba?" Murya a sanyaye tace "E, amma ba ta kowace hanya ba." Tsurawa bakin nata idanu yayi da ta yi maganar da shi, sai kawai ya sake juyawa yace "Gidan mu." Ba tare da ta ƙara tako ɗaya ba tace "Kuma kai kaɗai ne a ciki?" A zafafe ya dakata tare da juyo ya kalleta yace "Ke, idan ba kya son taimakon shikenan, ya za ki tsareni da tambayoyi bayan kuma ni ya dace a ce na miki wannan tambayoyin? Muje gidan, idan bai miki ba sai ki tafiyar ki, wani ne zai riƙe ki?" Da gaske kai ya sa yana tafiya, dan haka ta bi shi da sauri dan tafiyar tasu ba ɗaya ba, ba wata tazara mai tsayi ta ga ya tunkari wani makeken gidan ya tura ƙaramar ƙofa ya shiga, rage saurin ta tayi sosai ta shiga da sallama, farfajiyar na da girma, sai ai dake akwai ɓangarori da shukoki da kuma motoci sai ta zama ƙarama, bin shi kawai take har suka tunkari babban ƙofar wani falo, a hankali ya tura ƙofar da gaba ɗaya madubi ne ya lulluɓeta, suna shiga ta fara jin hayaniyar mutane alamar sun zo in da ke da mutane. Abun mamaki yana shiga falon da sallama ƙasa-ƙasa ta ga duk yaran dake falon har ma da matan biyu duk sun yi shiru sai magana ƙasa-ƙasa. Sabira da Zarah da kansu ke haɗe ƙusƙus ɗin wannan kuma wacece suke? Wato sun faɗa ma Alhaji har yanzu yana shigo da mata, shine yanzu ma ya shigo da wata? Dan ya nuna musu ba su isa ba kenan? Ɗaya daga cikin matasan dake falon ya kalla yace " *Leila*, ina Mama?" Da ladabi Leila wacce take ƴa ga Sabira tace "Tana ciki Yaya." Jinjina kai yayi, Leila na da ladabi a duk cikin ƙannenshi ya fi son ta, dan haka ya mata murmushi yace "Nagode." Hanyar da zai sada shi da ɗakin Maman ta shi ya nufa bayan ya kalli Aisha da ke sunkuyar da kai cike da kunyar yadda matan ke ta kallon ta da ainahin tuhuma alamar ta taho, a nutse ta ɗaga ƙafa ta bi shi sai ga Mama ta fito daga ɗakin ta tana faɗin" Ruƙayya, bai gaya miki kar ki kusa zuba min kayan ki a kan ku..." Ganin suna shirin karo da Sa'ad yasa ta ja birki tana kallon shi tace" Babana, har ka dawo?" Sai kuma ta kalli Aisha dake bayan shi tana ta sunkuyar da kai ta sake kallon shi sannan tace" Wannan kuma fa Babana? Wacece ?" Fuskar shi a haɗe sosai cikin dakakkiyar murya yace" Baƙuwata ce, ta zauna a wajen ki, zamuyi magana." Ba ita da aka ba amanar Aisha ba, har su Zarah saida mamaki ya nemi halaka su, sai Sabira data rufe bakinta da tafin hannu tana son yin dariya har ma tayi rawa ta girgiza ta faɗi da babbar murya cewa _" Yau dai Allah ya yi, bayan ma shigowa da ake da su yau har da ba wa gyatuma ajiyar ɗaya daga ciki."_ _Hajia Uwani, kai tsaye ba zamu ce ga yadda halina yake ba, amma dai muga aikin ta kai tsaye sai mu san wace irin mata ce_, Cikin yanayin faɗa ta shiga kallon shi da ma Aishar da ke ta sinne kai tace" Na tambaye ka wacece, ba ka amsa min ba, shine kake ce min na ajiye maka ita wai baƙuwar ka ce, wacece ita ɗin?" Cike da nuna gajiyawa yace" Mama, cewa fa kawai nayi baƙuwata ce ta zauna wurin ki, kuma na ce zamu yi magana daga baya, a dole sai kowa ya ji har ma a saka mana ido?" Cikin hargagi da faɗa tace" To ba zan riƙeta ɗin ba, ka ga ka gaggauta fita da ita a gidan nan, ba dan kana son ka nuna mana lalacewar ka ba? Macen za ka kawo mana gida ka ce baƙuwar ka ce, kai ba matar ka ba, ba ƴar uwar k ba? Ba komai na ka ba haka kawai." Sai kuma ta maida kllonta ga Aisha ta shiga nuna da hannu tana cewa" Ke, dube ki fa dan Allah? Ƙaramar yarinya da ke, amma ki sa kanki rayuwar bin maza..." Da ƙufula da son katse numfashi ta Sa'ad yayi gaggawar faɗin" Mama..., ba fa haka take ba." "To ya take? Da ta biyo ka nan karatu za ka koya mata?" Sai kuma ta sake kallon Aisha tace "Ke, fita a Gidan nan kafin na saɓa miki kamanni." Aisha data fara hawaye tunda ta ce tana bin maza d sauri ta juya za ta bar falon, tana jin muryar ta tana ci gaba da faɗin "Aikin banza, banda lalacewar zamani, yarinya ƙarama da ke har ki biyo namiji cikin gidan su, wannan ai rashin kunya ce da fitsarewa, idan ma iskancin ne kuyi à can waje mana wa ya hana ku? Amma a cikin gida ziƙam-ziƙam ki biyo shi, mtssssss!" Juyawa Sa'ad yayi ya ga ta fice a falon, sai kuma ya kalli su Zarah dake ta haɗe kawunansu suna son tattaunawa, haka ƙannenshi dake ta kallon rikicin mahaifiyar tashi, hakan ya s ake hasala shi ya kalle ta a zafafe yace" Har abada ni ba zan iya yin abun arziƙi ba a gidan nan, ina ganin ke kaɗai ce wacce ke gareni da zan tunkara da wannan lamarin, amma kema kin watsa min ƙasa a ido, yarinya ce fa da bata fitsarar ƴar ki ba, bata san a ina take ba, ɓata gari ne suka kawota nan da alama siyar da ita zasu yi ko dai wani mugun nufin ne da su a kan ta, shine kawai fa na taho da ita nan, amma dake ni bunsuru ne kowa ma kulawa nake, shine da kanki za ki zargeni da fasiƙanci..." A hassale ya juyawa shi ma ya fita a falon, sai dai yana fitowa ya ci karo da Kakar shi tare da Aisha tsaye tana goge hawaye, a saiɓance ya ƙaraso ya samu Hajia na tambayar ta wacece ita sannan me aka mata? Yana zuwa da ladabi yace mata" Ina wuni Hajia?" Kallon shi tayi da kulawa da kuma fara'a ta amsa da" Lafiya lau Sa'ad." Kafin ta sake cewa komai yace da ita" Hajia, nasan ke kaɗai ke ƙaunata a gidan nan, dan Allah ki min taimako ɗaya?" Da murmushi da kuma dattako tace" Sa'ad, bana son kana cewa haka, kowa a gidan nan yana ƙaunar ka, rashin fahimta ne kawai kai da su, yanzu faɗa min? Wane irin taimako zan maka?" Aisha ya fara kalla sannan yace" Wannan yarinyar yanzu muka haɗu da ita a hanya, bata san kowa da ko ina ba anan, ta ce wasu ne suka kawota garin nan kuma bata da kowa, shine na kawota nan ta zauna na kwana biyu sai a mayar da ita gidan su, haka yayi Hajia?" Faɗaɗa murmushi tayi ta kalli Aisha tare da dafa kafaɗarta ta rumgumata a jikinta tace" Ba komai Sa'ad, sai ta zauna a wurina ai, zan kula da ita fiye da zaton ka, Kaga nima na samu ƴar raino." Murmushi yayi yana jin hankalin shi na kwantawa, har zai tafi sai kuma ya dakata saboda jin Kakar ta ce" Ya sunan ki ƴan mata?" Cikin shasheƙar kuka Aisha ta furta" Nana A'isha." Murmushi Kaka tayi tace" Suna mai daɗi, sunan uwar muminai kenan, Allah ya azurtaki da halayen mai sunan." Sa'ad kam taɓe baki yayi ya kalli Hajia yace" Hajia, zan shiga ciki na shirya, zan dawo in sha Allah." Jinjina kai tayi alamar to sannan ta ja hannun Aisha tana faɗin" Bari in shiga da ita ciki." Kowanensu ɓangaren shi ya nufa musamman Sa'ad da yana shiga ya faɗa banɗaki dan yin wanka, sai da ya kimtsa kan shi ya fito falo ya zauna ya sake ɗaukar wayar shi dan duba ko an turo masa saƙon hoton yarinyar da ya buƙata. Ganin saƙon dake tabbatar masa hoto ne ya danna alamar buɗewa cike da zumuɗin son ganin wannan yarinya mai wayon da ta kubce daga hannun DG. Kan baƙin kallabin dake ɗaure a kan ta a fara sauke idanu, sai lumsassu kuma shanyayyun idanun mayen ta da ta musu wani iri kamar za ta yi bacci daga tsaye da take, a zabure ya miƙe yana ci gaba da rarako ido yana kallon hoton da son gasgata wai ita ce? Ko dai kama ce? Ko ya mata kallon tsoro ne da har yake ganin kamar ita ce aka turo masa hoton ta a wayar shi? Baƙa ce, sai dai kyakkyawa da ta dace da ita kanta ɗin, a ruɗe ya danna alamar kiran lambar da ta turo masa hoton yana tattaki a cikin falon da ƙaguwar a ɗaga kiran a kuma tabbatar masa ita ce a ka turo masa hoton ta, ko kuma dai waccen yarinyar dake wajen kakar shi ture ne aka masa? ******************** Saida ta ƙara yin ƙasa da muryar ta sosai cikin harshen buzanci kamar marar gaskiya tace "Kana nufin har yanzu ba'a ganshi ba? To ina ya tafi? Dama ya san mutane ne a garin?" Shiru tayi na wasu daƙiƙu kafin ta sauke ajiyar zuciya tace "Ko me ye ya faru sakacin Mu'az ne, kar ya ga nayi banza da lamarin Jabir, idan fa ba'a ga jikina ba na rantse muku da Allah sai nayi shari'a da shi, ni dama takaicina yadda yana jariri muka nemi ya bar mana shi dan zamu i kulawa da shi, amma tsaf Mu'az ya kalle mu ya ce tunda mahaifiyar shi na raye ita za ta kula da yaron, amma wallahi idan ya salwantar min da yaro sai na ɗaure shi." Shiru ta sake yi na wasu daƙiƙu, cikin ɓacin rai har ta mance da bata so abokan zamanta su san abinda ke faruwa ta ɗaga murya tace" Ni dai na gaya maka, kuma tunda kai kana waya da shi kace wall..." Ƙwanƙwasa ɗakin da aka yi ana faɗin" *Hajir*, Hajir kina ciki ?" Gane muryar yasa ta yi saurin aje wayar akan gado tare da fitowa tana murmushi, kallon juna sukayi ita da matar da kana ganin ta ka ga wayayya sannan mai ji da kan ta, kamar ba kishiyoyi ba saboda yadda suke girmama juna musamman ma dai yadda Hajir ɗin ke rusuna ma *Mardiyya* kamar ba ita ce gaba da ita a shekaru da ma zuwa gidan nan ba. Mardiyya da hankalin ta ke tashe sakamakon kiran da aka mata ƙanwar ta jikin ta ya sake tashi, sai dai duk da fuskar ta ta nuna damuwa da rashin nutsuwa, amma Wani basaraken leshe ne jikin ta mai manyan duwatsun da ke nuna tsabagen tsadar shi sannan ga idon mai kallo sassauƙa ne, ga mahaukacin mayafin da ya dace da shi da kuma jaka data saɓa à kafaɗar ta. Ba kwalliya a fuskar ta ko alama, amma Wani irin sheƙi da walwali da fatar ta ke yi a zahiri za ka gane fatar a nutse take sannan tana samun kulawa, dan kuwa mai ma da Mardiyya ke shafawa sai wanda suke a babban shagon da ya fi kowane a kuma matakin da ya fi kowane, ma'ana a VIP, mayuka ne da ko basu gyara maka jiki don Allahn da ya yi maƙerinsu ba za su gyara maka dan tsadar su ma mai iya saka talaka jin faɗuwar gaba. Da yanayin tashin hankali Mardiyya tace "Yaya, zan tafi gidan *Nuriyya* ne, an kira ni wai jikin ta ne ya sake tashi." Da yanayin tashin hankali Hajir ta fito daga ɗakin gaba ɗaya tana faɗin "Subhanallah! Jikin Nuriyya ne? Me kuma ya same ta?" Cike da damuwa tace "Wallahi nima ban sani ba, sun dai wai ko tana madafa ne ta yanki jiki ta faɗi, ni nasan ba zai wuce ta ga wani abu da ya tuna mata da *yaran ta* bane, amma dai zan je na gani." Cike da tausayawa halin da ƙanwar abokiyar zaman nata take ciki tace "To ba damuwa, Allah ya bata lafiya, Allah ya kuma bayyana mata su, sai kin dawo ɗin, ko a can za ki kwana?" Da sauri tana ƙara gyara zaman gyalenta tace "A'a, zan dawo ba jimawa, tar..." Odar da aka yi daga ƙofar gida yasa ta canza akalar maganar zuwa "To kin ji ma , har ya fara min oda, bari naje sai mun dawo." Da mamaki Hajir tace "Au ! Wai tare da Alhaji za ku je ne?" "E wallahi, yana shigowa ya same ni muna waya ya ce bari ya kaini." Duk tayi maganar tana tafiya inda ita ma Hajir ke bin ta har zuwa ƙaramin falon nasu dake ɗauke da ɗakunan su da kuma na yara, jiki a sanyaye dan maganar gaskiya jin wai tare da mijin nasu za ta tafi wanda yau girkin ta ne kuma bata ma san ya dawo ba ya sosa mata rai ƙwarai, ko dai ya shigo ta ganshi ma? Sannan ya faɗa mata ga in da za su tafi, shikenan sai ya yi gaban kan shi kawai? Dan dai kawai Mardiyya na da kuɗi saboda ƴar babban gida ce, sannan tana taimaka masa ƙwarai da gaske, dan tunda ya yi ritaya ma ita ta bashi jari yake kasuwanci, sannan yanzu haka gidan ita ke aje kayan abinci, kuma bata taɓa nunawa gazawarta ko ta musu gori ba, amma dai ai ba kuma a ce a mata yadda aka ga dama ba, ko dan ta tsufa ne? Ko kuma ta kai shekarun da yake ganin ba ta da wata mamora a jiki? Mardiyya na fita ta same shi yana jiran ta, dan haka ta shiga motar suka kama hanyar zuwa gidan ƙanwar ta ta dake aure a babban ahalin da kowace uwa burin ta a ce ƴar ta na gidan nan, saboda shaharar su wajen riƙe muƙamai da asalin mai gidan yayi da dama, ga alaƙa mai ƙarfi da suka haɗa da masarautar Agadez, kai tsaye basu zame ko ina ba sai ƙofar katafariyar fadar gidan *Saheeb Ahlan*. *ME CE CE DAMUWAKI*? Rashin ni'ima? Rashin gamsar da mai gida? Warin gaba? Bushewar gaba? Zubewar nono? Cikowar nono ? *Kina buƙatar...* Fatarki tayi laushi? Tayi santsi? Ta kwanta luf? Kina walkiya da annuri tamkar amarya? Sabulu kike so ko haɗin shafawa ki wanke ko mai na shafawa? Ki wadatu da sahihin ƙamshin haukata mai gida? Humra da zaki saka mijinki bacci bai shirya ba? Humra da zata tayar da sha'awarsa? Kulaccha da zata saka mijinki ya kasa yi miki tsara a fannin ƙamshi? Kulaccha da zata gagari manyan mata suffanta kalar sunan turarenki? Turaren wuta irin na asali barebari? Turaren da zaki fesa à zanin gadonki har ya rike mai gida ya kasa tashi? Turaren da zaki zuba ga ruwan wankan mai gidan ki? Turare don yaranki? _Idan duka kina buƙatar ɗaya daga cikin kayan nan, to ki tuntuɓi wannan lambar ta WhatsApp *+227-82-21-91-74* wanda suk gwada sun san ingncin kayanmu, ba buƙatar ɓata lokacin cika muku baki._ Wani abun farin ciki kuma, duba da yanzu ba kowace mace ke son shan garin magani ko matsi ba, akwai haɗi irin su *tsumi*, *ruwan tsumi*, *tukunya*: dayawa sun san tukunya, don da itace muke tutiya, kuma tukunyar nan akwai na ruwa dana dafawa a nama, sannan akwai kankat wato haɗin *kayan marmari*. *Garaɓasa* Ga waɗanda sukayi nisa kuma haɗin kayan marmari ba zai kamacesu ba, duba da kafin sakon yaje garesu zai fara lalacewa, don haka ga sauki ya samu, madadin kuɗin mota da zaki yi, zaki biya 1000k kacal don a sanar dake yadda zaki had, ba iya guda kawai ba, dama sauran haɗi irin na kayan daya shafi na marmari da ɗanye, musamman ma *sirrin kankana* da kuma *cucumber*. *JANNAT HOUSE.*🧕 *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HARUN* *MURA'ATU ULTIMATE COLLECTIONS* shin kin zuba tagumi ne uwar gida da amarya da tunanin ta inda zaki haɗa kayan kitchen ɗinki? Ko kuma fabrics kike da buƙatar canzawa na kece raini a cikin sa'o'inki? Shin kina so ki san a inda gawurtattun mata ke haɗa nasu perfumes ɗin? Ko lausasan zanen gado da kyawawan electronics gama hawa kike da bukata? To Matso kusa, zan faɗa miki inda ba ke kawai ba, hatta mai gidanki zaki iya rakawa dan siyo nashi electronics ɗin da sauransu, wato *MUC* mun shahara a saida Kayan *kitchen*, *fabrics* na kere sa'a masu quality, *bedsheets*, *electronics*, *beauty products*, *perfumes* da *kayan kwalliya* . Bugu da ƙri Hajia ta akwai data tare da *katin waya* ta kowane network and *catering services*, da wannan nake cewa daku, sai an gwada akan san na kwarai. *MUC* 🤝🤝🤝🧕BAMU DA SA'A. Ga mai buƙatar tuntuɓarsu, ga lambar WhatsApp: 07038274166 Call: 07038274166 & 07031057802 Location: Kano with nationwide delivery. _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *10* *Abida* suka ci karo da ita farkon shigar su, da gudu gudu Abida ta taso ta faɗa jikin Mardiyya tana fashewa da kukan da ya sake ɗaga hankalin Mardiyyar har tayi saurin ɗagota tana kallon fuskar ta tace "Abida, lafiya kike kuka? Me ya samu Nuriyya? Ta mutu ne?" Cikin kuka ta rufe fuska tana share hawaye ta girgiza mata kai tace "A'a, ba ta mutu ba." Da sauri Mardiyya tace "To me ya faru kike kuka?" Saida ta ja majina tana ta sauke ajiyar zuciya tace "Na damu sosai da halin da *ƴar uwa* take ciki, a madafa fa ta faɗi sumammiya, da babu kowa a kusa ba mu san me ye zai faru da ita ba, shiyasa na yanke shawarar zama da ita a duk inda take, dan gaskiya barin ta ita kaɗai haɗari ne." Ajiyar zuciya sosai Mardiyya ta sauke tare da dafa kafaɗar ta tace" Kwantar da hankalin ki kinji Abida, in sha Allah ba abinda zai faru sai alkairi, yanzu muje na ganta." Jinjina kai tayi tare da shiga gaba Mardiyya na bin ta a baya cike da tausayawa Abidar da kuma jinjina zuciyar girma irin ta ta, za ka rantse ciki ɗaya suka fito da Nuriyya, ko ita da suke uwa ɗaya ba ta jin ta kai Abida damuwa da ita da nuna mata ƙauna, sosai take jin daɗin yadda Abida ke fara taimakawa ƙanwar ta ta idan ta tsinci kanta a wani hali kafin ita ta kawo mata ɗauki, dan haka suke girmamata da mutumta ta tamkar ƴar uwar su ta jini. Hawa na biyu suka isa ɗakin Nuriyya, ƙofar ma a buɗe suka same ta saboda likita dake dubata sannan akwai mutane a ciki, kan tabkeken gadon ta suka same ta kwance ba ta san wanda ke kan ta ba, sai likita tsaye yana cire mata abun awon tension daga damtsen hannun ta. Gefen gadon kuma *Fa'iza* ce zaune fuskar ta ba yabo ba fallasa, hasalima kamar abun bai wani dame ta ba saboda yadda ita hankalin ta ma ba kansu yake ba, gefe kuma kuma da kan Nuriyya dake bacci Hajia *Radiya* ce riƙ da hannun Nuriyya tana ta murza tafin hannun ta. Shigowar Mardiyya ta sa Hajia Radiya faɗin "Mardiyya kin ƙaraso? Shigo ciki, zo zauna." A hankali ta zagaya inda take ta zauna suna fuskantar juna suka zubawa Nuriyya idanu, Abida kuma na tsaye kusan su tace ma Hajia Radiya "Ammi na sa a kawo mata, sannan na miƙa *Kabil* wajen Papi." A tausashe ta kalle ta tace "To shikenan, sannun ki da ƙoƙari." Cike da gadara da yatsina fuska Fa'iza da tunda ta ga Abida ta shigo ta shiga haɗe fuska tana wani ciccije baki tace ma Mardiyya "Ina wuni aunty Mardiyya?" Sarai Mardiyya ta ganta, yi ne kawai ta yi kamar ba ta gani ba saboda ita fa ta tsani Fa'iza kuma bata birge ta, yarinya ba kowa ba ba ƴar kowa ba, amma sai ɗaukar kan bala'i da raina mutane wai ita tana auren babban ɗa ga Saheeb Ahlan wanda kuma yanzun yake minista na man fetur, dan haka tana shigowa da ta ga ta juyo ta ganta kuma ta ɗauke kai ta ƙyaleta sai ita tayi kamar ba ta ganta ba dan ta nuna mata ita ɗin ƴa ce ga *Abdus-salam Asgar*. Da yanayin dake nuna kamar yanzun ta ganta tace "Kai, Fa'iza ce? Lafiya lau, muna lafiya?" Ba Ta jira me za ta sake ce wa ba ta maida dubanta ga dattijuwar arzikin nan tace "Ammi, ya jikin nata?" Kafin ta bata amsa likitan da ya gama haɗa kayan shi ya kalle su yace "Ran ki shi daɗe, jinin ta ya haura kamar dai yadda aka saba, shan magani ba zai rage mata komai ba muddin ba ta cire damuwa da yawan tunani a ranta ba, dan Allah a ƙara kiyayewa, idan kuma akwai abinda ke sakata farin ciki, to a yi ƙoƙarin ganin an sadata da shi kowane lokaci." Jinjina kai Hajia Radiya tayi tace" In sha Allah likita, mun gode sosai." "Sai anjima." Ya faɗa yana ficewa daga ɗakin, ganin haka Fa'iza da ita fa ba za ta iya zama anan ga kishyar ta ba wato Abida, miƙewa tayi ta kalli Hajia tace "Hajia ni zan koma, na baro ɓangaren ba kowa, Allah bata lafiya." Ƙwarai Mardiyya ta ji zafin abinda Fa'iza ta aikata, wannan ne yasa a kowace rana take sake ji a ranta Fa'iza na da hannu a cikin *ɓatan yara biyu* na Nuriyya d suka ɓata ɓat har yau babu labarin su, kasa riƙe ɓacin ranta tayi har saida ta juya ta kalle ta tace mata "Ameen, in da gaske kike." Da mamakin kalaman Mardiyya Fa'iza ta dube ta da kyau, a hankali ta muskuta ta hanyar gyara tsayuwar ta tace "Ban gane in da gaske nake ba? Me kike nufi?" Miƙewa Mardiyya tayi tsaye sannan ta juyo ta fuskance ta, hakan ya sa Hajia Radiya tashi tsaye ita ma tana riƙo hannun Mardiyya da faɗin "A'a Mardiyya, ka da kiyi haka, kin ji?" Cikin ladabi ta kalli Hajian tace "Ba komai fa Hajia, wannan ce kawai nake so na mayar wa da aniyar ta, ina so ta gane abinda take fata ko so ya samu Nuriyya, da izinin Allah ba zai same ta ba." Da matsanancin mamaki Fa'iza ta ƙanƙance idanun ta tana mamakin lamarin Mardiyyar, kamar dai wacce dama take jiran ta? Kamar wacce dama ta zo mata a shirye? Daga addu'a? Shikenan sai a fassara ta, ajiyar zuciya ta sauke cike da wannan halin nata na ko in kula tace "Ban faɗa dan ranki ya ɓace ba, iya gaskiya ta kawai na faɗa ko da hakan zai ɓata wa wani rai, amma aunty Mardiyya na miki wani abu ne ban sani ba?" A zafafe Mardiyya ke kallon ta tana addu'ar ko kaɗan ne Fa'iza ta mata wani gangancin da zai saka ta ɗauke fuskar ta da mari, cikin ƙufula tace mata" Me kika gani? Kin ji kin tsargu ne?" Waina idanu Fa'iza tayi sannan tace" Ba haka bane, na dai ji kalaman da kika faɗa min kamar na wacce ta ƙullace ni." Wata hararar ke kik jiyo Mardiyya ta zabga mata tare da faɗin" Wannan kuma matsalar ki ce, ni dai nasan komai daren daɗewa gari zai waye, kuma in sha Allah za'a yi walƙiya halin kowa ya fito." Cikin nutsuwa da dattako Hajia Radiya tace" Mardiyya, dan Allah, ki ji da halin da ƴar uwar ki take ciki mana, ina ke ina rigima a wannan yanayin?" Wani malalacin murmushi Fa'iza tayi ta kalle su dukansu tace" Saida safen ku." Ba ta sake jiran jin ta bakin kowa ba ta fice daga ɗakin, hakan yasa Mardiyya komawa ta zauna tana bin ƙofar da harara, da sauri Abida ta zauna kusa da Mardiyya ta dafa kafaɗarta kamar wata tsarar ta tana faɗin" Kiyi haƙuri aunty Mardiyya, sam Fa'iza bata kyautawa lokuta da dama, ni kaina wallahi ina zarg..." Da gaggawa Hajia Radiya ta tare numfashin ta da cewa" Kul Abida, ki faɗi alkairi ko kiyi shiru, idan har kin san baki da hujja ko tabbas akan abinda za ki faɗa, to kar ki bari mala'iku su rubuta a littafin ki." Da sauri Mardiyya ta kalli Hajiar tace" Hajia, ki barta ta faɗa mana, ni kaina wallahi ba zan taɓa yarda cewa wai babu hannun Fa'iza a ɓatan yaran ƴar uwata." "Me ce ce hujjar ki?" Cewar Hajia Radiya tana tsare ta da idanu, ba tare da shakku ko ɗar ba Mardiyya tace "A bayyane yake mana Hajia, Fa'iza shekarar ta shida da aure a gidan nan amma ko ɓatan wata bata taɓa yi ba, a shekarar ta ta bakwai aka yi auren *Mukhtar* da Nuriyya, wata goa da auren su ta haifi ƴar ta ta fari, irin kyaututtuka da farin ciki da kuma soyayyar da duka ahalin ku suka nunawa yarinyar dalili ne da ya isa yasa Fa'iza ta sace yarinyar tun bata yi sati biyu da haihuwa ba. Duk da tashin hankalin da ake ciki da rikicewar da Nuriyya ta yi, a haka ubangiji ya sake azurtasu da cikin *Eesha*, amma ita ma fa aka sake biyo baya aka ɗauke duka wata shida da haihuwar ta, Hajia me yasa ba zamu zargi Fa'iza ba, tunda har yau da take da shekara ashirin da huɗu ba ta yi ko da ɓari ba." Ba wai dan ita kanta bata wannan tunanin ba, so da dama idan ta ga Fa'iza ta kan ji ranta ya ɓace har taji kamar ma ta shaƙi wuyan ta tace _"Ki fito min da jikokina Fa'iza."_ Amma kuma ba ta da hujja, bata san da wane dalili za ta tuhuma surukar ta ta ba wanda yin haka ta san har shi kan shi ɗan nata Bilal ba lallai ya yarda ba, amma ita kanta tana zargin Fa'iza kuma wasu lokuta ayyukanta sukan sake jefa zargi a zuciyar mai saka mata ido, dan sau *biyu* tana kamata tana waya, amma da ta ganta sai ta aje wayar ta ce za ta sake kira, hakan na sake sakata jin anya kuwa! Anya Fa'iza ba akwai abinda take aikatawa marar kyau ba? Amma yanzu dan bata so gabaɗayansu su gina zarginsu akan rashin tabbas ta kuma zama babbar da ta goyi da bayan ganin laifi marar tushe, sai kawai ta wani basar tare da ƙara gyara gilashin wayar ta da wani murmushi a fuskar ta tace "Shikenan? Saboda wannan ne zamu zargeta da wannan babban laifin?" Rusunawa Abida tayi cikin sanyin murya da ladabi tana kallon Hajia tace "Ammi, lamarin *aunty* Fa'iza akwai abun ɗaure kai da saka mutum shakku, ko ni dake abokiyar zamanta bana gane mata, ku duba fa ku gani rana ɗaya aka yi bikin mu da su Nuriyya, amma har yau ni da ita bayan gaisuwa ba abinda ke haɗamu, kullum fuskar ta a haɗe sannan tana ɗakin ta tana faman ƙuminiya da wayar ta." Cike da son kwantar da tarzomar ta sake cewa" Na ji, yanzu dai bana so na sake jin wannan maganar, Mardiyya..." Ta faɗa tana kallon Mardiyyar tare da ɗorawa da" Ki zauna da ita na wani lokaci, zan je na duba Kabil na ga ya yake? Na tabbata za ta farka anjima kaɗan, idan ya so sai ki tafi ko?" Jinjina kai tayi tace" To shikenan Hajia, bari na kira Alhaji na faɗa masa ya bar ni nan." Sanda Hajia Radiya ta miƙe ne ta kalle ta tace" Wai dama tare kuke da shi? Kuma kika barshi a waje?" Murmushi tayi tare da sadda kanta tace" Tare muke Hajia yana nan falo, cewa yayi dare ya fara yi ba zai bar ni nayi tuƙi ba, amma zan faɗa masa sai ya koma kawai, ni idan na ida sai na tafi." Murmushi Hajia tayi tace" To shikenan, tunda yana falo ma ai mun gaisa." Inda Hajia ta tashi Abida ta zauna tana kallon Nuriyya dake kwance ba ta san me suke ba tace "Allah ya baki lafiya ƴar uwa, kina ganin jarabawa, in sha Allah komai zai tafi daidai." Jinjina kai Mardiyya tayi tace "In sha Allah, mai son ganin bayan ta ma Allah ba zai bar shi ya gani ba, tunda har bayan an rabata da *ƴan matan ta* sai Allah ya bata *namiji* (Kabil)." Kallon Mardiyya Abida tayi jiki a sanyaye tace "Gaskiya ne, ban ma faɗa miki ba..." Ta faɗa cike da zumuɗi da fara'ar ta sannan ta ɗora da "Ina nan ina shiryawa Kabil murnar ƙarin shekara, amma fa sirri ne ka da kowa ya ji, dan ko ita ƴar uwa ban faɗa ma ba haka ma su Ammi." Da mamaki mai ɗauke da murna Mardiyya tace "Dan Allah? Amma fa Abida za ki yi kashin kuɗi, duba da yadda ahalin Ahlan kuke shirya taro komai ƙanƙantar sa ba kwa masa da sauƙi." Dariya suka fara sakawa, sai kuma Abida ta ɗaga kafaɗu alamar ko a jikin ta tare da cewa "To me ye a ciki aunty Mardiyya? Kuɗin ba komai bane idan aka haɗa da ƙaunar da nake wa Kabil, dan haka ni dai dan Allah ka da ki bari kowa ya ji sai ranar kawai." Jinjina kai Mardiyya tayi tace "To shikenan, amma nima zan bayar da gudummuwata." Da fara'a ta ɗaga kai alamar gamsuwa tace "Shikenan." Haka suka ci gaba da taɓa hira da jiran farkawar Nuriyya su ga yanayin jikin nata. *Bayan* ta gaisa da Kakan na Jabir *Alka* ta wuce zuwa na ta ɓangaren, a tsakiyar tabkeken falon nata ta samu Alhaji Saheeb ɗin da Kabil suna buga tamola cikin farin ciki da ƙyaƙyata dariya, dakatawar su ya samo asali ne daga shigowar ta da sallama da kuma fara'a tana tunkarar su, farar rigar sa daya riƙe da hannu saboda tsayin ta zai hana shi gudanar da wasan tamolan da jikan nashi ya saki tare da sassauke numfarfashi yana kuma yi mata murmushi. Ƙarasowa tayi ta rumguma Kabil ɗin a jikinta tana shafa kan shi da faɗin "Wato ana ta guje-guje ko? Har sai ka gajiyar min da bangona?" Murmushi Kabil ɗin yayi, duka yanzu ne zai yi shekaru huɗu, dan haka bai ce mata komai ba sai ci gaba da buga Ball ɗin sa, maida dubanta tayi ga dattijon tace "Shine ka biye masa kuke buga min tamola a tsakiyar falo?" Dariya dattijon yayi yace "Shigowa ta kenan daga masallaci na same shi yana bugawa, shine na ke taya shi." Jinjina kai tayi a hankali tace "Da kyau to, sannun ku da ƙoƙari." "Ameen." Ya faɗa, na wasu daƙiƙu kuma sai ya zura hannun shi ya riƙo nata hannun, hakan yasa suka kalli juna a tausashe yace "Ya jikin maman shi?" Saida ta kalli Kabil dake bal ɗin shi cikin taushin murya tace "Jikinta da sauƙi, sai dai har yanzu bata farka ba, amma na bar su Mardiyya wajen ta su kula da ita." A tsanake yace "Allah ya bata lafiya." A sanyaye ta amsa da "Ameen." Shiru sukayi na wasu shuɗaɗɗun mintuna suna kallon Kabil na wasar shi shi kaɗai cike da bege da sa ran ina ma yana da wasu ƴan uwan da za su riƙa taya shi wasa? Wayar Alhajin ce ta shiga siriyar kururwar da take nuna tana buƙatar agajin shi, cikin dattako ya lalubo wayar daga aljihu, duk da bai san lambar ba, amma kasancewar shi mutum mai jama'a kala-kala sai ya ɗaga saboda jin cewa koma wanene to na kusa da shi ne ko wanda ke kusa da wanda ke kusa da shi, dan ƙaramar wayar sa ce aka kira kuma babu mai wannan lambar tashi sai ahalin shi kawai. Yana ɗaga daga can ɓangaren aka fara da "Assalama alaikum?" Cike da dattako muryar shi na fita ɗai-ɗai yace "Wa'alaika salam warahmatullah wa barkatuhu." Cikin muryar ladabi aka ce "Alhaji barka da dare? Kana magana ne da sifetan jami'an tsaron Zinder4, na kira ne dama dan na sanar da kai mun kama *ɗan ka*." Cike da dagiya da ƙarfin hali dattijon ya lumshe idanun shi, ba tare da ya buɗe ba a ƙasan zuciyar sa yake faɗin "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" A zahiri kuma cikin murɗaɗiyiyyar murya yace " Subhanallah! Wane yaron nawa?" Daga can ɓangaren aka bashi amsa da "Alhaji *Fahad* ne." Idanunshi ya buɗe tare da zuba su ya kalli Hajia Radiya dake gefen shi ta zuba masa idanu tunda ta i ya ambaci tsarki ya tabbata ga Allah, ɗan ɗauke wayar yayi daga kunnen shi tare mhsa kai tafin hannun shi ya rufe daidai inda sauti ke shiga da fita cike da son samun tabbaci yace "Radiya, ina Fahad?" Da rashin tabbaci da kuma mamaki take bashi amsa da "Rabona da shi tun safe, ya ce min zai je gidan abokin shi *Ja'afar*, wani abu ne ya faru?" Girgiza mta kai yayi alamar a'a tare da maida wayar a kunne cikin nutsuwa yace "Ina jin ka sifeta, a ina ne kuka kamany shi?" Daga can ɓangaren aka ce "Yallaɓai anan ne Zinder, mun kama su ne a mota suna tuƙin ganganci, kuma Yallaɓai babu takarda ko ɗaya tare da su, hasalima shi Fahad da ke tuƙin shekarun shi basu cika sha takwas ba, da aka dakatar da su kuma sai suka nemi yin rashin kunya ga jami'anmu, Shiyasa suka kawo su nan." Shiru yayi, tunanin abubuwa da dama yake a lokacin, Fahad dai, Fahad dai, kullum Fahad, ba shi ya fara haihuwa ba, amma dake shine auta a gidan sai yake neman ya zamar musu dodo, Allah ma shaida ne basu mishi rainon da za' a ce laifin su bane, tunda ba akan shi suka ɗanɗani daɗin haihuwa ba, kasancewar shi auta bai sa suka masa sako-sakon da za'a ce matsalar daga su bane, yara shida suka haifa kafin shi na bakwai, Bilal ma dake babba bai wahalar da su ba, suka zo kan *Murjanatu* mai sunan mahaifiyar shi, lokacin da Mukhtar ya zo duniya kuma Bilal ya ƙara sanin ciwon kan shi, dan haka da taimakon shi ma suka raine shi, har zuwa kan su *Marfu'a* da *Sabeer* kafin shi Fahad ɗin. Saida ya ɗan sosa gaban goshin shi kafin ya feso zazzafar iska daga bakin shi yace "Shikenan, zan wakilta wanda zai je kuyi sulhu da shi, kasancewar ba gari ɗaya muke ba, hasalima ba mu san ya tafi can ɗin ba." Hankali Hajia Radiya ne ya sake tashi har ta matso daga zaman da tayi cikin kujerar tana ta kallon shi, tana ganin ya aje wayar tace" Alhaji lafiya? Wai abu ne ya samu Fahad ɗin ? Yana ina ne?" Kallon ta yayi irin kallon shirun nan kamar mai nazarin abinda zai faɗa mata, miƙewa a hankali ya na lalubo ɗaya babbar wayar tashi daga aljihu, da sauri ita ma ta miƙe tsaye tana matsowa kusan shi da sake tambayar" Alhaji, wai me yake faruwa ne? Me ya samu Fahad ne?" Ba tare da ya kalle ta ba yana neman lambar manajan shi dake kula da gidajen man shi dake garin yace" Me kuwa zai same shi, yana lafiya." Da zumuɗi tana gyara gilashin ta tace" Amma ai naji akan shi ake magana, har da maganar sulhu da Zinder... Dan Allah sanar dani me yake faruwa?" Ɗan ɗaga idanun shi yayi ya kalle ta tare da kai wayar a kunnen shi saboda ƙara da ta fara yi alamar kiran na shiga yana cewa" Yana Zinder, wai an kama su suna tuƙi, yaushe ma Fahad ya koyi tuƙin mota ne ban sani ba? Ko ke kin sani?" Da tsananin mamaki ta zaro idanun ta da a zahiri basu da wata matsala face fara dakushewar ganinta har sai ta saka tabarau tace" Tuƙi? Mota? Fahad ɗin?" Wayar da aka ɗaga tashi yasa shi ɗan takawa zai bar falon yana faɗin" Ki kwantar da hankalin ki, idan ya dawo gidan zamu yi magana da shi." Da kallo ta bishi har ya fice, sai kuma ta dafe goshin ta tana sauke ajiyar zuciya tace" Yaushe ya koyi tuƙi ban sani ba?" Rashin mai bata amsa ya sa ta kallon Kabil da ya ɗauko tamolan shi daga waje ya rumgumota ya shigo falon, kama hannun shi tayi tace" Muje ayi wanka ka canza kaya ka kwanta, yau dai zaka kwana anan ko?" Ɗaga kai yayi ya kalle ta yace" Abbu fa?" Da fara'ar da ta ƙaƙarota ne kawai ta amsa mishi da" Abbun ka ai baya gari, amma ya yi alƙawarin zai dawo gobe, sai ka kwana tare da shi." Jinjina kai yayi alamar gamsuwa har suka shiga ɗakin nata. *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *11* Rintse idanunta ta ƙara yi saboda raɗaɗin ciwon kan da ta ji ya fara ziyartar ta tun bata buɗa idanunta, sai kuma jikin ta da shi ma ta ji ya kwashi na shi ciwon sakamakon faɗuwar da ta yi a ƙasa sosai sa'ilin da komai na jikin ta ya daina aiki, sannu sannu ta dinga yatsina fuskar ta tana ƙoƙarin buɗa idanunta, buɗewar farko dishi-dishi ta gani, sai da ta ƙara rufe su ta buɗe kafin ta ga Mardiyya zaune kusa da ita tayi taguma tana kallon wayar ta. Saida ta fara motsa bakin ta sannan ta ɗaga laɓɓanta da ƙyar ta furta "Aunty..." Da sauri Mardiyya ta juyo ta kalle ta, sai kuma ta aje wayar ta akan cinyoyinta ta riƙo hannun ta tana faɗin "Nuriyya, kin farka? Sannu, ya jikin naki?" Cikin lullumshe idanu da buɗa baki da ƙyar haɗe da yamutsa fuska tace "Aunty..., me ya faru ne?" Girgiza kai Mardiyya ta fara yi sannan tace "Nuriyya, ke zamu tambaya ai, me ya sumar dake a madafa?" Ƙara yatsina fuska tayi tana kallon Mardiyyar cike da son tuna abinda ya faru da ita ɗin, a nutse ƙwaƙwalwar ta ta fara taro mata abinda ya wuce wasu awanni baya. *Tabbas* tana madafa tana gyara kayan cincincin wanda yanzu shi ta fi son ci dan bata sha'awar komai, a faffaɗar tvn dake madafar can saman bango kawai ta ji waƙar da ko a mafarki ta ji ta tasan ta me ce ce, tana ɗaga kanta zuwa ga tvn ta ga hotunan da aka ɗauka taron sunan Eesha, hakan ne ya saka ta jin wannan yanayin da aka tabbatar mata wai hawan jini ne da ita tunda take jin wannan alamun, gashi ta kafe idanunta akan tvn tana kallon hotuna bila adadi da aka ɗauki Eeshar har zuwa sanda ta fara wayo. Bata san idanunta na fito da ruwa ba saida ta ji lema a hannun ta, sam ba ta yi tunanin ya aka yi tvn ta kunnu ita ɗaya ba, ganin hoton yarinyar na ƙarshe tana ɗauke da ita da kuma kayan da aka karɓe yarinyar daga hannun ta da ita yasa aikin komai dake jikin ta sake ninkuwa har saida ta ji idanunta sun rufe sannan jiri ya ɗebe ta zuwa baya... Daga shi bata sake sanin komai da ya faru ba sai yanzu. Yunƙurawa tayi za ta tashi zaune da sauri Mardiyya ta miƙe ta kamata har ta zauna tana faman jera mata sannu, cikin kulawa tace da ita "Na kawo miki ruwa ne?" A hankali ta jinjina kai alamar e, da sauri ta miƙe gefen gadon ta ɗauki jug ɗin ta kwalba ta tsiyaya mata ruwan a kofin tangaran, kusanta ta zauna ta miƙo mata sannan ta zuba mata idanu tana shan ruwan, saida ta sha ta miƙo mata kofin, karɓa tayi ta aje sannan ta sake duban ta tace "Abinci fa?" Yatsina fuska tayi tana lumshe idanu, sai kuma ta kalle ta da kyau cikin sanyayyar muryar dake ɗan disashe kamar mai mura tace "Aunty, ƴaƴana, ƴaƴana aunty, suna ina? Ya suke yanzu? Wa ya... Wa ya *ɗauke min* yarana ? Aunty wa ye yake son ganin bayana? Me nai masa?" Cike da tausayawa Mardiyya ta matso kusan ta tare da jawo kanta ta kwantar a kafaɗar ta tana shafa bayan ta cike da rarrashi tana cewa" Ya isa haka Nuriyya, kiyi haƙuri kin ji, in sha Allah ina tabbatar miki wata rana zaki ga yaran ki, kuma da izinin Allah a duk inda suke yanzu suna cikin kyakyawan yanayi, wataƙila ma..." Ta faɗa tare da ɗago kanta ta tallabo haɓarta tana murmushi duk dan ta kwantar mata da hankali tace" Wataƙila ma *Kuwailat* ɗin ki tayi aure." Murmushi ta saki duk da cikin kuka take, cikin rikicewa da tashin hankali da rashin madafa ta shiga nuna ƙirjinta tana faɗin" Da gaske aunty? Idan hakane da nayi farin ciki marar misaltuwa, amma ni wannan shirun ko? Ɗaga min hankali yake aunty, ni a ƙalla ma wanda ya ɗauke su ya faɗa min halin da suke ciki, a inda suke ba sa fuskantar kowace irin tsangwama? Sai hankalina ya kwanta, amma..." Sai kum t sake ɓarkewa da kuka mai cin rai tana faɗin" Aunty idan ƴaƴana fa suna fama da yunwa, da matsin rayuwa, da takura, da rashin gata? Bayan kuma su ɗin jikokin Saheeb ahlan ne, mutumin da ba iya gwanatinmu ba, sauran gwamnatoci ma suna karɓan bashi a hannun sa, shi da kansa bai san iya adadin abinda ya mallaka ba, sannan kuma jikoki ne ga Abdus-salam Asgar, tsohon malamin makarantan da ya taka muƙamai da dama har yanzu da yake ambasader na Paris, aunty ba zamu yafe ma kanmu ba idan yaran nan suka kwana da yunwa ko sau ɗaya, ba zamu yafe ma kanmu ba, kin san ko?" Cike da tausayin halin da ƴar uwar ta ta take ciki ta sake kwantar da ita a jikin ta tana goge ta ta ƙwallar cike da dauriya tace" Yi haƙuri ƙanwata, kiyi haƙuri kin ji? Wannan ita ce *RUBUTACCIYAR KI*, ka da ki gaza cinye ta kin ji? Kiyi haƙuri kin ji, in Allah ya yarda yaran ki na hannu na gari." Yadda take rera kukan yasa dole Mardiyya ma fashewa da kuka, wanda hakan ma dalili ne da ya sa bata son zuwa in da Nuriyya take kullum, ya za ta yi? Su biyu kaɗai iyayen su suka mallaka a duniya, ba su nemi komai a duniya sun rasa ba, duk abinda suke so shi ake musu, ko ita dake auren wanda ake ganin bai dace da ita ba wato Alka, ita ce ta zaɓi abun ta a haka duk da Tsoho ne kuma mai mata, amma iyayen ta basu hana ta ba suka barta ta aure shi, ita kanta Nuriyya auren soyayya ta yi da Mukhtar, yarinya kyakyawa fara tas da ita, amma rayuwa da yanayin da take ciki ya sa duk ta rame wcce a da kuma jikin ƙiba gare ta. Ba tare da ta daina shafa bayan ta tace "Ki daina kuka kinji, ki ci gaba da yi musu addu'a, in sha Allah za ki ga yaran ki..." Duk da ta kai ƙarshe amma da sauri ta ɗago tace "Yaushe? Yaushe aunty?" Da rarraba idnu Mardiyya tace "Wata rana, in sha Allah nan kusa kaɗan, ina ji a jikina kin kusa haɗuwa da su dukansu." Kawar da kai tayi kaɗan tana zubo da wasu hawayen tace "Aunty, ko dai na fara haukacewa?" Da mamaki Mardiyya tace "Me yasa kika faɗi haka?" Saida ta kalle ta tace "TV kawai na ga ta kama da kanta ina madafa, kuma hotunan Eesha aka dinga nuna min...aunty ina jin tsoro ko na fara haukacewa." Ƙura mata idanu Mardiyya tayi tana nazarin abinda ta faɗa, tv aka kunna? Anya kuwa abu ne mai yiwuwa? Ko Dai... To! Ko dai ana bibiyar rayuwar Nuriyya ne? Duba da yadda yaran ta ke ɓata a gidan nan duk da tarin masu tsaro da masu aikin gidan nan, shekara biyu kenan da Saheeb ahlan ya sauka daga muƙamin fra minista (Premier ministre), har lokacin tarin jami'an dake gidan basu rage ba sai dai canja su da aka yi, ƙofa ɗaya ce ta shigowa da kuma fita, ba ka shigowa ba tare da an san ina ka nufa ba sannan an ji daga bakin masu gidan bayan wasu mutane da suka ware cewa su shigo kai tsaye ba sai sun jira izini ba, Mardiyya na ɗaya daga ciki kuma, hatta sabga idan ana yi gidan iya katin da aka raba wanda ya samu katin kawai ke iya shigowa, shi ma sai jami'ai sun tabbatar kana ɗaya daga cikin waɗanda aka gayyatar, musamman da aka sace Kuwailat a farko, jami'an sun tabbatar ba wanda ya shigo bare ma a ce ya fita da jariri, hakan ya sa an sake tsaurara matakai da ƙara masu kula da gidan. Amma sai gashi a haka aka ɗauke Eesha, a nan za'a iya cewa an samu makama, dan kuwa mai aikin gidan da ta zo bayan fitar ta ne aka nemi yarinyar aka rasa, a gidan babu wanda ya dasa zarginshi a kan ta, dan kuwa lokacin ma tsohon ciki gare ta sannan an tabbatar bata fita da wani abu ba da zai nuna ta ɗauki ɗan mutum. Abu ɗaya da Mardiyya ta raya a zuciyar ta yanzun shine *na gida* ne ke aikata wannan laifin, kuma ba za ta taɓa daina zargin Fa'iza, dan ko mai aikin da t zo ranar wacce ita bata yarda bat da hannu a ciki ba ai sun fi ganewa juna ita da Fa'iza, à sanyaye ta ci gaba da shafa bayan ta tace "Ki yi haƙuri, Allah zai saka miki, alamu sun nuna wani ke bibiyar ki." ******************** Yadda ya bankaɗa labulen ya shigo ya sa Kakar saurin juyowa ta kalli mai shigowa, da mamaki ta zuba mishi idanu daga inda take riƙe da wata tasa a hannun ta dake cike da fura mai sanyi tace "Sa'ad, lafiya ka faɗo mana haka ba ko sallama?" Da wayar shi riƙe da hannun shi ciki yanayin rashin nutsuwa yace ma Kakar "Hajia ta, ina yarinyar nan take?" Da yatsa ta fara nuna mishi ɗakin ta sannan tace "Tana ciki, ta kasa cin abinci ne saboda cikin ta ya ƙulle, shine zan kai mata furar nan, na barta tana wanka, lafiya kake neman ta haka?" Da azama ya nufi hanyar ɗakin ba tare da ya bata amsar tambayar ta ba, da ɗan sauri ita ma ta shiga bin bayan shi tana cewa" Sa'ad, ka dakata mana, wanka fa take, baka san a ya..." Ganin ya tura ƙofar ɗakin ya buɗe kuma ya shiga yasa tayi shiru kawai ta ci gaba da bin shi, zaune suka samu Aisha da ɗaurin ƙrji sai dai ta rufe daga wuyan ta har zuwa kafaɗun ta da kallabin ta. Kallon masu shigowar tayi, ganin sune da suka taimake ta sai ta tashi tsaye tana kallon fuskar Sa'ad da ta ya kalli bangon wayar shi sannan ya sake zuba mata idanu, tun daga kan gashin kanta dake baƙi ƙirin mai ɗankaran tsayi ga kuma waya, a ido zaka gane bai sa sulɓi dan bai yi yar yar ɗin nan ba, sai dai daga yadda kowane sili na gashin yake da mummurɗewa zaka gane yana da taushi sosai, fuskar ta ta ya sake ƙurawa idanu har saida bakin shi ya furta "Ke ce?" Da mamakin tambayar da ya mata ta ƙanƙance idanun ta tare da kama kallabin ta ta ƙara rufe jiki tace "Ni ce wa?" Da sauri ya saita nutsuwar shi tare da ɗan kawar da duban shi daga kanta yace "Amm...ina nufin, idan kin gama ki fito zamuyi magana." Bai kuma cewa komai ba ya juya a sukwane ya fita, da kallo ta bi bayanshi har ya ɓace ma ganinta duk da ya bar mata ƙamshin Turaren shi a ɗakin, Kaka dake tsaye tana kallon su a hankali ta tako ta aje mata furar gaban madubi ta dube ta tace" Ki shafa mai gashi nan, bari na samo miki ko da kayan Leila ne kafin zuwa safe mu san abun yi." Da murmushi tace" Tom, nagode sosai." Juyawa Hajia tayi tana da ce mata" Kuma ki tabbatar kin shanye furar nan kafin na dawo." Yadda tayi maganar cike da gargaɗi yasa Aisha yin murmushi, sai kuma ta kalli tasar ta zaro idanu kaɗan tana ayyana ta ina za ta iya shanye furar nan, ai ita cikin ta baya ɗauka dayawa. *Bayan 30mnt* ba tayi tsammanin samun shi a falon ba, kallon ta Kaka tayi ta mata alama da hannu ta zo da cewa "Zo nan ƴar rikona." Da sauri ta ƙara tana zuwa ta zauna ƙasa kusan ƙafafun ta, dafa kanta kaka tayi cikin fara'a tace "Sa'ad ne yake so ya ji, wai ina iyayen ki suke da har aka satoki aka kawo ki nan?" Ƙara sadda kanta tayi ƙasa tayi shiru na daƙiƙu, sai kuma ta ɗaga kanta ta kalli Kakar hawaye na tararo mata a kumatu tace "Mamie, ban san su ba nima, a gidan marayu na girma, Mother kuma ita ce Maman mu, ita take kula damu take mana komai, amma ni ban san su waye iyayena ba." Cike da tausayawa Hajia Kaka ta tallabota ta zaunar da ita kan ƙafafun ta ta rumgume, Aisha dake kuka ya ci ƙarfin ta bata ma san a ƙafafun Kakar take zaune ba, cikin rarrashi Hajia Kaka ke faɗin" Yi shiru haka ya isa kin ji Nana Aisha, kiyi haƙuri, ai bai san da haka ba da bamu tambaye ki ba ma." Kuka take yi Hajia Kaka tana rarrashin ta, cikin daƙilewa Sa'ad ya miƙe tsaye tare da cewa" Zamu san abun yi zuwa gobe." Da sauri Kaka ta kalle shi tace" A'a Sa'ad, mu barta kwana biyu ta samu nutsuwa, ka ji fa ta ce a gidan marayu take, idan babu tsaro a can wanda suka sato ta ai zasu sake komawa dan ita." Kallon Kakar yayi da tunanin ko wa ya ce ma Hajia za'a mayar da ita nan kusa? Sai dai kuma tayi gaskiya a maganar ta, tunda *makashin su yana tare su*, mai basu agaji da sunan gidan marayu shi ke musu ɗauki ɗai-ɗai, bai ce ma Kaka ƙala ba ya nufi hanyar fita, sai da ya yi ɗan nesa da su ya tsaya tare da juyowa, zamn Aisha a ƙafafun Kakar tashi ya kalla, cikin taushin murya yace "Ki zauna kan kujera, ba'a ƙafafun Kakata ba." Da sauri Aisha ta miƙe tsaye tare da zaunawa ƙasa, Hajia kuma murmushi tayi ta bi shi da kallo, Sa'ad kenan, yanzu nan kafin Aisha ta fito da ta zaunar da shi tana mishi magana a kan sana'ar da yake yi, kallon ta kawai yayi yace _" Karki damu Hajia, ai laifin Ibu ne."_ Da ta sake kallon shi ta masa magana akan sunan mahaifin shi da yake faɗa gatsau, sai ya yatsina fuska tare da taɓe baki yace _" Na saba ne ai."_ Shine yanzu zai wani nuna mata kulawa, bayan yana gwasale mata ɗan ta, girgiza kai tayi tana dariya tace" Allah ya shirya min kai." Sai kuma ta kalli Aisha tace" Kin ga taso na sake rumgume ki, rabu da shi kin ji, kishi yake saboda ya ga za ki ƙwace masa ni." Dariya Aisha tayi tana satar hanyar da ya bi da kallo, sosai take girmama taimakon da suka mata, a ƙalla dai ko mutamin banza ne ya taimake ta kuma ta ji daɗi, iya kwana ɗaya ma idan suka bata ta gode, bare kuma bata ga alamar tafiyar ta gobe ko jibi ba. ******************** Cikin kwanaki kaɗan aka gama ma Jabir shirin tafiyar shi, kafin lokacin tafiyar tashi kuma ya zauna ne a ɓangaren Ummu, daga wajen ta da Alhaji Kabir ba wata matsala da yake fuskanta ko ta ƙwayar zarra, amma a wajen mutanen gidan, Hajia Atika da Hajia Asiya da wasu daga cikin yaran su, yana ganin tsangwama da ta sa Ummu ta gargaɗe shi da nufa ma inda suke, dan ita kanta sosai take ganin raini a wajen wasu yaran gidan saboda kawai ta auri uban su, dan haka yake kiyayewa ba ya nufa inda suke, har daren da ya shiga ya musu ba kwana dan zai tafi. Sosai Hajia Lubabatu ta bishi da addu'a da yi masa nasiha ya maida hankali ga abinda ya kai shi, ya ji daɗi ƙwarai kuma ya ɗauketa a matsayin uwa ko ma Kaka, wajen Hajia Asiya kuma kallon wulaƙanci ta bishi da shi cike da zaƙuwar ya bar mata falo tace _"Allah ya kiyaye, sai anjima."_ Suna fitowa shi da Ummu dake rakiyar sa suka nufi ɗakin Hajia Atika, daga ƙofa tana hangosu ta miƙe da waya a hannu tana faɗin" Zeinab idan sun fita ki rufe min ƙofata zan kwanta ne, bana son hayaniya." Hayat da Zeinab ne suka nuna rashin jin daɗin su har Hayat ɗin ya rakosu har ɓangaren Ummu yana basu haƙuri, shirye shirye ya ci gaba da yi har zuwa ƙarfe 03:00 na dare Alhaji Kabir da Khamis ɗan riƙon Hajia Luba suka kai shi gidan mota bayan yayi sallama da Ummu. Bai taɓa sanin ya yi sabo da su haka ba sai da ya ga zasu juya su bar shi gidan mota, cike da so da ƙauna ya faɗa jikin Alhaji Kabir din yana riƙe shi gam, cike da dattako Alhaji Kabir ya shafa kanshi yace "Jabir, ba dai kuka kake ba ko? Ka ga maza shiga layi an fara kiran suna." A hankali ya ɗaga daga jikin shi, kallon fuskar shi yayi ya furta "Nagode ABBA, *ina ƙaunar ka*, ba zan taɓa mantawa da kai ba." Murmushi Alhajin yayi yace "Nima Haka Jabir, kuma madadin godiyar ka ina so ne ka dawo min nan da cikar burin ka, ka fahimta?" Jinjina kai yayi cike da ƙwarin guiwa yace "In sha Allah Abba." Ƙara dafa kanshi yayi sannan ya kalli Khamis dake musu murmushi yace "Nagode Yaya Khamis." Hannu Khamis ya bashi suka gaisa yace "Ka kula Jabir, duk da nasan ma Aliyu zai kula da kai, ku maida hankali ga karatun ku." Nan ma kai ya jinjina yace "In sha Allah yaya Khamis." Da haka suka bar shi a gidan mota zuciyar shi ba komai a cikin ta sai ƙaunar mutanen da suka taimake shi a rayuwa har suka zame mishi wani ɓangare na rayuwa wanda zai iya kiran su da *Ka fi ɗan uwa*, dan ba wanda ya tallafe shi a rayuwar shi sai su, kuma jigon hakan ita ce *auntynsa* Ummu Kulsum. *Bayan wata ɗaya* Kiran d ya shigo wayar ta gashi kuma tana cikin falon tare da mutane, kuma wayar sirri ce da ba zata iya amsa ta a gaban su, da sauri ta miƙe bayan ta kalli mijin nata Bilal da bai fita ba sakamakon shagalin da za'a gudanar nan da awwani biyar na taya murnar ƙarin shekara da Kabil yayi fuskar ta ba fara'a tace mishi "Ogana, ina zuwa, zan ɗan amsa waya." Babban mutum ne da fuskar shi ke wadace da annuri na riƙo da turbar addini da kuma sheƙin wadata, saida ya fara kanne mata ido ɗaya sannan yace "OK, amma ki dawo yanzu." Ita ma kanne masa idon ɗaya tayi sannan ta juya tana fadin "Yanzu." Saida ta bi Nuriyya da ido wacce ke rungume da Kabil ƙam ƙam a jikin ta saboda Abida da zata fita da shi siyayya kafin lokacin yayi, tana ji kamar wani abu zai faru da shi ne, bata son rabuwa da shi ko na sakan dan shi kaɗai ya rage mata a duniya, idan tayi sake shi ma za'a iya raba ta da shi. Wani shaƙiyin murmushi ta yi mai tarin ma'anar da ita kaɗai ta san shi, tana kaiwa bakin ƙofa suka ci karo da Abida ta gama shiryawa ta shigo da fara'a tana faɗin "Yarimana, na barka kan.." Haɗewar da sukayi da Fa'iza yasa ta yin shiru suna kallon juna, wayar ta Fa'iza dake ci gaba da vibration yasa Abida kallon wayar, da sauri Fa'iza ta ɗan juya wayar yadda Abida ba zata ga allon wayar ba bare har ta ga sunan da aka kira ta da shi, wani murmushin ko a jikina Abida ta sakar mata tace "Aunty ina zuwa kuma? Ko masu gyaran wurin sun iso ne?" Fuska a haɗe kamar dai yadda ta saba zama a gidan kullum cikin haɗe fuska tace "Ba su bane, zan iya wucewa?" Taɓe baki tayi tare da kauce mata a hanyar ta fita sannan ita ma ta shigo tana kallon Kabil dake san saukowa daga ƙafafun Maman shi, da sauri ta ƙaraso ta ɗauke shi tana kallon Nuriyya da idanunta duk suka cika da hawaye tace" Haba ƴar uwa, ba fa jimawa zamuyi ba, kuma ga kawun shi ma a tare damu ko?" Ta faɗa tana nuna Sabeer dake zaune ya ɗora ƙafa ɗya kan ɗaya yana danna wayar shi, jin ta ambace shi ya ɗago manyan idanun shi ya zuba mata, sai kuma ya kalli Nuriyya da duk tayi kalar tausayi yace" Aunty *Nur*, idan hankalinki bai kwanta ba, me zai hana mu tafi tare to?" Da sauri ta miƙe tsaye tana murmushi tace" E, hakan ma zai fi, gaskiya na fi so mu je tare." Murmushi Abida tayi tace" To shikenan, Muje ko?" Sai kuma ta kalli su Hajia tace" Hajia zamu tafi, baku da saƙo?" Alama Hajia ta mata da hannu kan ta zo tare da cewa" Zo muyi sirri." Dariya Abida tayi ta nufi Hajiar, tana zuwa ta durƙusa ta miƙa kunnen ta kamar yadda Hajiar ta buƙata. Suna cikin magana da Hajia da babu wanda ke ji Fahad ya shigo falon da yanayin sauri, ba sallama, ba sannunku, ba kallon kowa kawai ya nufi hanyar da yasan ɗakin yana nan, Alhaji da Mukhtar da ke zaune shia daf da inda Nuriyya ta miƙe tsaye tana gyara kallabi n doguwar rigar ta dan tafiya da kuma Bilal duk suka kalle shi, Sabeer da ya ɗan fi su zafi ne ya kalle shi shima ya daka masa tsawar "Kai! Baka ga mutane bane zaka shigo mana ɗaki babu sallama?" Dakatawa yayi baya ya turo baki, sai kuma ya shafa wata tarin suma da ta ci uwar ta breaker🚶‍♀️ya kalle su ɗaya bayan ɗaya yace "Salam, ina sauri ne Yaya, wani abu nake nema." Kama hanya yayi zai sake wucewa Bilal ya miƙe yana kallon wani zanzaro da Fahad ɗin yayi, a hankali Bilal ɗin yake zagaywa inda Fahad yake wanda hakan yasa Fahad ja baya saboda a banza ma Bilal mutum ne mai jiki, gashi kuma duk cikin su shi ne ba shi da tsayi ga kuma ƙiba tubarkallah da ɗan tumbinshi luwai luwai, ganin Fahad na ja baya yasa Bilal cewa "Dakata nan, wallahi kana matsawa zan sa Sabeer ya ɗaure min kai na jefa ka a bayan gida, sai kayi sati baga hasken rana ba." Cikin tashin balagar samartakar dake ɗibanshi da jin kamar za'a takura masa ya wani shiga jijjiga yana nuni da hannaye yana cewa "To wai ni dan Allah me na muku yanzu daga shigowa ta? Shikenan ni dan kun tsane ni ba damar na shigo sai kun ce nayi laifi, shiyasa ma na zaɓi nayi zamana a waje babu mai takura min, wallahi ni idan haka za'a ci gaba da yi min to kawai zan bar muku gidan, kunga shikenan kun huta da gani na." Sabeer dake ji da fiye da tashi ƙuruciyar ne ya miƙe yana ƙoƙarin haurawa ta kujerar da yake zaune a zafafe yana faɗin" Kai Fahad, mu sa'anninka da ka tsaya a kanmu kana faɗa mana maganar banza?" Miƙewa Hajia tayi duk hankalinta ya tashi amma kuma ta kasa magana dan ita kanta tasan Fahad baya kyautawa, sai dai kuma hukuncin da Sabeer ɗin ne zai masa bata so, dama dai Bilal ne tasan duk hargagin da zai masa ba zai masa marin da ya zarce biyu ba, amma Sabeer kuma zai ce ma sai ya saka masa ɗamara ko waya. Ganin Sabeer ya kai ga Fahad ya ɗaga hannu zai ɗauke fuskar shi da mari ya sa ta runtse idanu ta kai tafin hannun ta ta rufe baki kamar za ta yi kuka kuma ita dai bata hana ba, bare kuma Alhaji da ko kallon ɓangaren nasu ma baya yi dan shi idan ta shi ne su casa shi tunda shi ya ga ƙarfin shi ya ƙare baya iya wa da shi. Tausassan murya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da kuma dattijantaka Abbu Mukhtar yace "Sabeer...kar ka taɓa shi." Cak! Sabeer ya tsaya tare da juyowa yace "Amma Yaya Mukhtar..." A dake sosai cike da mazantaka da bayar da umarni yace "Ya isa..." Sai kuma ya mishi nuni da idanu ta hanyar nuna masa Hajia da kamar za ta yi kuka, a nutse Sabeer ya kalle ta sai kawai ya juya ya kalli Fahad da ya cije leɓen ƙasa ya na jiran Sabeer din ya taɓa shi shima ya rama, jinjina kai Sabeer yayi tare da yin ƙwafa yace "Zamu haɗu da kai yaro." Dawowa yayi kujera shi ya zauna, Bilal kuma ƙarasawa yayi kusan Fahad ɗin ya riƙo ƴan tsirarun gashin da suka masa tsatsaye a tsakiyar kai ya murɗe sosai yadda saida Fahad ɗin yayi ƙara yace "Zafi Yaya Bilal, kayi haƙuri dan Allah." Cikin ɗaga murya Bilal ɗin yace "Me ye wannan? Na ce me ye wannan? Fahad za ka min aski ko sai na sa an maka ƙwal kwabo?" Da sauri Fahad ya amsa da "Na yi, nayi wallahi Yaya." "Kayi alƙawari?" Bilal ya tambaya ba tare da ya saki gashin ba, da sauri ya amsa da "Na yi yaya Bilal." Sakinshi yayi shi maya dawo ya zauna wurin shi, lokacin kaɗai Hajia ta zauna ita ma suka ci gaba da maganar su da Abida haro ta ciro kati a ƙaramar post ɗin ta ta miƙa ma Abidar. Ga mai son shiga grp ɗin *RUBUTACCIYA* kuma wanda ta shirya comment to ta yi min magana akan wannan lambar *+227-82-91-21-74*. *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *12* Jikin motar Sabeer ta maƙale tana amsa kiran idanun ta kuma akan ƙofa dan tana so taga mai shiga da fita kar a ritsa ta, ba wani alamu dake nunawa na nesa wayar da take ta rashin gaskiya ko wacce ke buƙatar sirri ce take amsawa da "Na ji, naji DG, na gaya maka akwai abinda nake shiryawa yau ɗin nan, in sha Allah kuɗin ka cass a asusun ka, amma kar ka manta da wani abu..." Sai kuma ta shiga yanayin gargaɗi har tana nunawa da yatsa dan san samun tabbaci tace "Ina kammala biyan ka kuɗin ka aikina kawai za ka shiga, dan kasan yarjejeniyar mu haka ta ce." Daga can ɓangaren DG ya amsa da "Ba ki da matsala Hajia, ai rashin biyana kuɗin gaba ɗaya ya jinkirta aikin, da izuwa yanzu fa kun gama sabawa." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Shikenan, da zaran wannan harƙallar da na haɗa ta faɗa, zaka ga saƙona a asusun ka, sannan..." Gyara tsayawa tayi ta ci gaba da cewa "Daga yanzu zuwa sati ɗaya ka da ka kirani a wayata, idan buƙatar yin magana da kai ta taso zan kirana da kai." Daga wurin DG cewa yayi "To idan kuma ni nake so nayi maganar dake fa?" A ɗan kausashe tace "DG, ka daina min abu mana kamar wani wanda ya aureni ko yake shirin mallakata, ni fa na zaɓeka ka min aiki kuma biyan ka zanyi ba kyauta ba, sannan na faɗa maka yau idan ban biyaka cikon kuɗin ka ba gobe zan biyaka, dan abinda nake shirin aikatawa ya fi ƙarfin ahalin Ahlan su tsaya ɓata lokaci dan sun fi ƙarfin abinda zan nema, dan haka ka daina ƙoƙarin gwada ikon ka a kaina, ka gane?" Cike da lalaci da shashantar da abinda ta faɗa ɗin DG yace" To naji, amma ki sani idan har buƙatar maganar dake ta taso zan kira ki." Cike da gadara da iko Fa'iza tace" Ni kuma sai na saka ka a baƙin jadawali... Ba iya a wayata kawai ba, har akan aikin nan, kasan kuma maza basu yi ƙaraci a duniyar da muke rayuwa ba, kuma abinda na tura maka ko a jikina bare ka yi tunanin ko zai bibiye ka su ne, dan na wuce wannan ajin." Da sauri da kuma ladabi yace" Kiyi haƙuri ranki shi daɗe, ki yi haƙuri, sai kin kirani ɗin." Tsaki tayi mai sauti tare da yanke kiran tana daddana wayar sannan ta koma zuwa ɗakin, tana zuwa ta samu an canza tsarin, yanzu Nuriyya za ta tafi tare da su, murmushi tayi wanda iya laɓɓa ya tsaya tana cewa" Haba dai ƴar uwa, ya zaki tafi tare da su kuma bayan duk gamu a gidan? Kinga ki zauna kawai sai mu tafi mu tare da Kabil ɗin, dan ni daga nan zan wuce karɓo cake ɗin da Kabil zai yanka anjima, Kinga ke sai ki kula mana da abinda yayi saura nan, duk da dai masu aikin da Abida ta ɗauko suna ƙoƙari, dan daga ƙasa na hangi yadda suka ƙawata wajen da kwalliya mai ban sha'awa." Miƙewa Mukhtar yayi tare da jawo Nuriyya dake ƙiƙƙifta idanu jikin shi ya rumgumata yana mai kallon tsakiyar fuskar Fa'iza fuskar shi ba yabo ba fallasa yace" Babu abinda za ta yi a nan, kawai ta tafi tare da shi, idan ke ma zaki je ba damuwa, dukanku kuje, nima Kinga sai na rakaku ai." Kai tsaye maganar Mukhtar ta nuna shi kanshi bai da nutsuwa da Fa'iza kuma bai yarda da ita ba, kamar yadda tun farko bai cika son shiga sabgar ta ba dan bata da sakin fuskar ma da mutum zai shiga lamuran nata, ba zai yarda yayi wasarere da rayuwar Kabil ba wanda shi kaɗai ne jika a gidan nan wanda ya fito daga tsatson namiji. Fa'iza da taji ba daɗi har zuciyar ta wani shaƙiyin murmushi tayi marar makama tana kallon shi ita ma tace "Haba mana Abbun Kabil, ni da Abida ai mun isheta komai, ba hidimar shagalin ƙarin shekara ba, ai ina ga ko aure Kabil zaiyi mun isa mu tsaya mata, ko ba haka ba Mamie?" Ta faɗi hakan tare da maida duban ta inda Hajia take, maganar ta gaskiya ce, musamman ma su suna da kara akan lamura irin waɗannan, hakan yasa Hajia jinjina kai tace" Hakane, Mukhtar, ka bar su su tafi, mu sai muyi wani abun a gidan." Kallon Hajiar yayi da ladabi sosai da kuma tausasa murya yace" Kuyi haƙuri Ammie, hankalina zai fi kwanciya idan muka tafi tare da shi, Ammie yara biyu na rasa a dalilin yarda da mutane, ba zan yarda na sake rasa Kabil ba da irin wannan yardar." Kaf maganar yayi ne yana kallon cikin madubin idanun Fa'iza, da fari ta shiga wani yanayi na me yake nufi? Amma da ya dire kalaman sai ta gane ina ya dosa, sai kawai ta bishi da wani makirin murmushi har da ɗan ɗaga masa gira tayi sake yin murmushin gefen laɓɓa tana kallon nashi idanun ita ma tace "Shikenan, tunda haka kace, za mu gani." Da kallon tsana da jin haushi ya bita, wallahi ba dan matar Yayan sa bace da sai ya kauɗeta da tafi, shi kam da ɗan uwa na sakin matar ɗan uwan sa a kowane irin hali, Allah da sai ya sake ta saki dubu uku ma kuwa rasss zai yanka mata. Haka dai Abida da Nuriyya na rumgume da Kabil suka tafi suka dawo aka ci gaba da shirye shirye. Ƙwarai Abida ta sake shiga ransu da irin wannan bajinta da tayi, masu shirya wurin taro ta ɗauko musamman suka kula da komai ta biya su, hatta cake ɗin da ta bayar oda daga wani garin aka kawo shi sak mai suffa da girman Kabil ɗin wanda hakan ya birge mutane ƙwarai tare da ban ƙawa har aka dinga magana akan haka. Lokacin da maƙiya suka ruɗe shine sa'ilin ba wa Kabil kyaututtuka, duk mai mugu da ƙudirin nufi ya so bayyana sai dai kawai ka ƙara ɓoye shi dan kar ka fallasa kan ka, hasalima irin kyautar da Saheeb Ahlan ya ma Kabil ko ƴaƴan da ya haifa zai iya gayyato hassadar su da kuma baƙin cikin su akan yaron, bare kuma waɗanda suke ganin su basu da wanda za'a ma wannan kyautar su ji daɗi. Kyautar hannun jarin shi ya ma Kabil da ya saka a wani kamfani dake Austriya, kamfanin da a yanzu suke ta jin raɗeraɗin nema yake ya zama nashi dan dama yanzu hannun jarin nashi ya fi yawa dan kaso sittin da biyar gare shi a cikin ɗari, haka kuma daga wata majiya mai ƙarfi suna kyautata zaton ya kusa siye kamfanin saboda matsalar da ta faɗawa mai ɗaya hannun jarin, ba maganar milyoyi bane, bilyoyin kuɗi ke shigo masa ta wannan kamfanin, shine kacokam ya mallaka shiyar ga Kabil ɗan shekara huɗu a duniya. *Gagara* jura Fa'iza tayi sa'ilin da Ammie ta ba wa Kabil kyautar wani sit na kayan wasan da daga ƙasar waje ma sit ɗin ya haura miliyan biyu, dan ko jirgin wasar kamar na gaske yake dan har da matuƙin jirgi ke akwai a ciki sai dai ƙarami ne. Tana shiga ɗakin ta ta rufe cilli tayi da wayar ta kan kujera ta shiga sauke wasu numfarfashi saboda yadda zuciyar ta ke tafasa, irin zafi da ƙunar da take mata yasa ta zuwa ta ɗauko ruwa masu sanyi ta buɗe robar ta kifa kai, ba ruwa take buƙata ba, hakan yasa har ta ƙware ruwan suka zubar mata a jiki, cikin ɓacin rai da tafasar zuci shi ma goran ruwan ta yi jifa d shi kawai ta durƙushe a wurin nan ta fashe da wani irin kuka mai tsanani wanda daga zuciyar ta ne... Abubuwa ne suka taru suka mata yawa, ga rugujewar tsarinta wanda da ta samu kuɗin nan tabbas ita ma da ta fara hango kanta matsyin wacce wata rana za'a ma ɗanta irin kyautar nan, ga kuma wannan kyaututtuka da ta kalla ana ma Kabil, ko mijinta fa tana kallo y bashi babban kwalin da bata san me ye à ciki ba, amma tafi tunanin na'ura ce dan Kabil ɗin na yawan ce masa yaushe zai siyo mishi? Tun d y sme shi wata rana yana aiki da ita shi ma har ya daddana. Ta jima tana kuka ita kaɗai kafin ta wanke fuskar ta ta duba madubi ta gyara fuskar ta da kyau sannan ta ɗauko wayar ta ta sake fitowa, tun daga nesa take hango mutane na tafiya, a haka kuma ta hango Fahad na shirin fita hannun shi riƙe da waya yana amsawa da kuma wata farar takarda mai kau an yanka masa cake ɗin sa a ciki yana ci, daga nesa take iya gane Hajia dake masa magna akan fitar da zai yi ne da kuma kashedin cika dare dan abinda kullum sai an yi ne kamar dai karatu. Take sheɗan ya raya mata tunda à yanzu dai Kabil ya mata nisa bata samu damar cika ƙudirin ta ba, to ai ga Fahad, tasa duk lalacewar sa ba zasu kasa biyan diyyar da zasu yanka musu ba. Wani murmushi ne ya suɓuce mata da ya saka haƙoran makkar ta sun bayyana a fili, babbar wayar ta mai tsadar gaske ta ɗaga ta shiga daddanawa, jim kaɗan aka ɗaga cike da girmamawa aka gaishe ta, ba tare da ta kawar da idanun ta daga Fahad ba tace "Tsarin...da kuma abun farautar duk sun canza, ka tabbatar kana kan manhajar Maps, zan turo maka da lambar abun farautar mu yanzun nan." Amsa ɗaya kawai aka bata ita ce "Angama Hajia." Daga haka ba tace komai ba sai yanke wayar da nufa wajen taron, ganin Fahad na shirin ɓacewa ganinta ya fit a gidan a ƙafa yasa ta yin saurin ƙwalla masa kira, dakatawa yayi yana kallon ta har ta ƙaraso, da fara'a a fuskar ta tace "Fahad, dan Allah ka taimaka in baka wani saƙo mana?" A wani ciccije yace "Na me?" da fara'a tace "Ka ga akwai wani mai ne da nake anfani da shi na hannaye, to gashi ya ƙare, shine nake so na baka a siyo min dan Allah." Fuskar shi ba fara'a yace da ita "Kawo to, dan sauri nake gaskiya." Murmushi tayi tare da ciro kuɗi a rigar wayar ta ta miƙa mishi, kallon ta yayi bayan ya karɓa yace "Duka wannan?" Jinjina kai tayi, juyawa yayi ya fita yana mamakin yanzu almubazzarancin matan gidan nan ya kai su dinga siyan man shafawa a hannu na wannan kuɗin? Murmushi tayi har ya fita a gidan sannan ta juyo tare da tura lambar Fahad ɗin ga wanda za su mata aikin nan, daga haka kuma ta shiga harkokin ta cike da tsammanin jiran sakamakon aikin nata. *02:14* ta leƙa ɗakin nashi kamar yadda ta saba a kowane dare ta kan tabbatar ya shigo gidan kafin ta kwanta, duk da ta sha yi masa faɗa a kan cika daren nan, amma Sam Fahad baya jin magana gashi kullum lamarin shi ƙaruwa yake, Alhaji dai kuma ya zuba masa idanu ne kawai bai cika yi mishi magana ba. Saɓanin kullum wayam ta samu ɗakin ba Fahad ba labarin shi, tun a lokacin hankalin ta ya tashi ta kuma yi kwanan zaune dan duk rashin jin shi in dai ka ga bai kwana gidan nan ba to tabbas baya garin, abinda ya saka ta damuwa kuma shine jiya har fiye da 11 na dare yana gidan nan dan har aka gama shagalin nan. Ta kira wayar shi amma a kashe, shi ma dai wani yanayin tashin hankali ne na daban. Tun da aka idar da sallah asuba ta sa Sabeer ya je ya dubo gidan su Ja'afar, bai mata musu ba ya tafi saboda kallon da Mukhtar ya mishi, yana zuwa can ya samu abokin yawon ba inda yaje hasalima a gida ya kwana, dan haka ya dawo ya sanar da su abinda ke faruwa, ba dan ta samu gamsuwa ba dai har suka zauna kan babban teburin cin abinci. Lokaci ne da ya kamata Ace suna cikin farin ciki saboda duka Ahalin sun haɗu babu wanda ba ya nan, sai dai rashin Fahad da kuma damuwar da Hajiar ta nuna ƙiri-ƙiri yasa ba mai wannan farin cikin, an yi zugum ne ana kai abincin baki ba dan ana jin daɗin shi ba. Cikin dubara Fa'iza ta kai yatsunta biyu kan bakinta ta rufe bakin d su tana kallon mijin nata Bilal dake cikin wata dakakkiyar shaddar da aka ma ƙaramin dinki, ma'ana hannayen ma iya guiwar shi suka tsaya tsayin rigar ma daga guiwanshi na ƙafa ne, ma fi aksari haka shigar sa take ta manyan kaya kuma ba mutumin saka hula bane, abinci yake ci hankalin shi na kan Hajia yana riƙe da hannun ta ɗaya yana ta mammatsa mata shi. Inda ta dubi Mukhtar kuma da hankalinshi ya fi karkata kan Kabil yana mishi wasa, sai kuma lokaci lokaci ya kan kalli Nuriyya da ita ma take duƙowa tana ma Kabil ɗin wasa suna ƴar hira duk da basu fito da farin cikin su a fili ba, Abida kuma na kusa da Sabeer ne har tana ɗn tambayar shi iya inda za'a iya samun Fahad kenan? Taɓe baki Fa'iza tayi cikin zuciyar ta take ayyana _"Me yasa wai basu kira ba har yanzu?"_ Cikin dattako Alhaji dake sanye da wani sassauƙan yadi kalar bleue ganin yadda Hajiar ke neman rikice musu tana son fara kukan da zai iya jawo mata ƙarin matsala a idanun ta dake ciwo yasa shi aje cokalin hannun shi yace" Shikenan, ki daure ki ci abincin, kuma kar ki yi kuka, ni kuma zan fita yanzu na nemo miki shi, hakan ya miki?" Kallon shi tayi tana ɗaukar tissue a tsakiyar teburin tana goge hannayen ta tace" Ba haka bane, ni ba kuka zanyi ba, kawai dai ina tunanin me yasa wayar shi bata shiga? Sannan ina yaje a wannan lokacin da ya fita daga gida, balaguro yayi cikin dare?" Bilal da shi ma ya aje cokalin shi kallon ta yayi yace" Ammie, na tabbatar Fahad yana lafiya, kin san shiriritar sa idan ta motsa, amma ga Sabeer zai je ya nemo miki shi a duk inda yake." Sai kuma ya kalli Sabeer ɗin dake cin abinci yace" Sabeer, ka yi sauri ka idar ka je ka sake dubawa gidan sauran abokan shi." Jinjina kai Sabeer yayi yace" To Yaya." Ya ci gaba da cin abincin, Abbu Mukhtar ma kallon Hajiar yayi cikin nutsuwa yace" Ammie, dan Allah ki kwantar da hankalin ki, zamu fita tare da Sabeer mu duba miki shi, za mu samo shi in sha Allah." Jinjina kai tayi sai Nuriyya da tace" Nima n kira aunty Mardiyya dan naji ko yana tare da *Aslam*, amma ta ce sam basu haɗu ba ma saboda Aslam yana gida yana karatu dan jarabawar su ta kusa." Gudun ƙarawa kanta zargi da kawar da tunanin kowa a kanta Fa'iza ma ta ɗan taɓe baki cike da halin ko in kula tace" Gaskiya na damu sosai, dan ni fa haro saƙo na bashi da zai fita na ce idan zai dawo sai ya kawo min, gashi yanzu bamu san a halin da yake ciki ba." Abida kam da zumuɗi da fara'a tace" In sha Allah ma ba abinda ya same shi, zai dawo cikin ƙoshin lafiya." Kafin wani ya sake cewa wani abu wayar Bilal tayi ƙarar da ta saka Fa'iza saurin kallon shi fiye da kowa, Bilal da saida ya gama duba lambar da ke ɓoye kafin ya ɗaga da yin sallama, daga ɗaya ɓangaren ba tare da an amsa sallamar ba aka ce"I zuwa yanzu nasan kun gama tabbatar da autanku baya tare da ku, sannan ni ne wanda zai iya sanar da ku yana cikin ƙoshin lafiya ko akasin haka." Da mamaki da kuma canza yanayin fuskar shi cikin tausa murya yace" Wa ye kai malam? Ya aka yi kasan Fahad baya tare da mu." A tsanake aka sake cewa" Sanin wa ye ni ba shine abu mai mahimmanci ba a yanzu, halin da ƙaninku yake ciki shine ma fi a'ala, id..." Da sauri Bilal ya katse shi da cewa" Malam ina ƙanena yake? Idan kasan inda yake k..." Shima da gadara ya katse shi da cewa" Ya zama na ƙarshe da za ka sake katseni ina magana, Fahad na tare da ni yanzu haka kuma a ƙarƙashin kulawa ta, kuɗin fansar da zaku biya na baku shi kuma sune miliyan hamsin kacal, dan haka idan kun shirya kan kuɗin nan da minti ashirin zan kira ka dan sanar da kai inda za ku kawo kuɗi ku karɓi ɗan ƙiriniyar gidan ku, sannan kuma..." Numfashi ya sauke sannan ya ci gaba da cewa" Sanar da jami'an tsaro halin da kuke ciki zai tunzurani na kashe yaron nan, haka ma ɓata min lokaci wajen haɗa kuɗin ko tunanin ku min wasu dubaru, to shakka babu zan kashe *ƙwayar cutar gidan ku*..." Ya ƙarashe tare da kifawa Fahad marin da ya saka shi ƙwala ƙara ya kira sunan _" Yah Bilaaaaaal."_ Da mugun sauri Bilal ya zabure ya miƙe a rikice yana dafe teburin gaban shi cikin ɗaga murya yace" Ka ga malam ka da ka sake dukar min ƙanena, zan kawo muku kuɗin yanzu, amma dan Allah ku daina dukanshi, yaro ne ƙarami bai saba da wahala ba, dan Allah n'a roƙe ku..." Yadda ya dire maganar kamar zai fashe da kuka yasa Sabeer miƙewa a zafafe dan tuni Hajia ta miƙe tana riƙo hannun Bial da tsare shi da idanu, Sabeer na zagayawa ya so karɓan wayar dan yayi masifa, amma sai Bilal ya kauce tare da zabga mishi harara yana ci gaba da faɗin "Zan kawo kuɗin yanzu, ku gaya min inda zan je na kai, amma kada ku sake cutar da shi." Cike da shaƙiyanci aka furta "Yaron kirki, nan da minti sha biyar zan kiraka, nasan miliyan hamsin ba komai bace dama ga ahalin Ahlan, a ƙyabtawar ido ma zaku iya yin atshawar ta, da kyau." Yana faɗin haka ya yanke kiran ya bar Bilal baki sake yana nanata kalmar yaron kirki da ya kira shi, ba dan iskanci na mutane ba da ubangiji ya albarkace shi da haihuwa da yanzu an fara tara masa jikoki fa shima, wataƙila rashin haihuwar ne yasa har yanzu yake ɗanye sharaf abin shi kamar bai wani zarta arba'in da tsiraru a kai ba. Muskutawa yayi da nufin jaye kujerar d yke zaune baya dan ya wuce zuwa sashen shi, hannun shi da Ammie ta riƙe a rikice tana faɗin "Bilal, Bilal ɗina, ya aka yi? Me ya faru da Fahad ɗin? Su waye suka kira ka? Me suka mishi? Yana ina yanzu?" Fuskar ta ya kalla cike da tausayawa musamman da take neman fashewa da kuka, dafa kafaɗar ta yayi cikin nutsuwa yace "Ammie, ki kwantar da hankalin ki, zan fita ne yanzu zan dawo miki da shi, nayi alƙawari." Girgiza kai ta fara yi tana faɗin "A'a Bilal, mu tafi tare, na ji kana magana kamar wani abu ya samu Fahad ko? Ka faɗa min gaskiya mana." Abbu dake zaune ya zuba musu idanu kawai yana kallo ne ya tsare Bilal ɗin da idanu yace "Masu garkuwa da mutane ko? Sun kama shi ne?" A hankali Bilal ya kalle shi, bai gyaɗa mishi kai ba kuma bai bashi amsa ko da idanu ba bare baki, shirun kuma ya tabbatar ma da kowa halin da ake ciki, hakan yas Abbu sunkuyar da kanshi yace "Nawa suk ce suke da buƙata?" Saida ya ja numfashi ya sauke sannan furta "Miliyan hamsin." Ammie da ta gama rikicewa a gigice ta sake riƙo duk hannayen shi ta shiga jijjigawa tana magana "A basu mana Bilal, a basu kuɗin mana su sakar min yarona, ni...ni zan basu kuɗi, ina da kadarorin da na gada wajen mahaifina, Bilal a siyar a biya mana." Tallabo kumatunta yayi cikin nutsuwa yace "To Ammie, abinda nake ƙoƙarin yi kenan, ba sai kin siyar da kadararki, ni zan biya Ammie, ina da kuɗin zan biya na karɓo miki shi in sha Allah." Nuriyya dake kusan ta riƙota tayi cikin muryar kuka dan har ta fi Ammie shig tashin hankali ta rumgume Ammie a jikin ta tana faɗin" Ammie kiyi haƙuri, Yaya Bilal zai dawo miki da shi ki ganshi, na fahimci abinda kike ji, kum da rashin sanin inda abinda ka haifa yake, Gwara a ce gawar sa ce a gaban ka ka samu tabbacin yana cikin ƙasa ya fi kwanciyar hankali." Duk zubawa Nuriyya idanu sukayi, hakan yasa tana maƙale da jikin Ammie ta kalle su ita ma hawaye na bin kumatunta tace" Ƙwarai, akwai raɗaɗi sosai, raɗaɗi ne mai zafin gaske da baya warkewa a zuciya, samun namiji tamkar dubu ya kasa sakawa mu manta da ƴan matanmu, ina ma an nemi n biya kuɗin fnsarsu ne, ni kam da na yi komai dan na biya fansar su daga ciki har da *sata* ma." Kalaman ta suka saka Ammie ƙara rumgume t ƙwarai suna fashewa da kuka, hakan yasa Ammie cikin kuka take faɗin" Kamar muna da laifi ko? Ya kamata mu fara cigiyar su ta kowane irin hali." Ganin kamar za'a daina maganar Fahad yasa Fa'iza miƙewa tana kyaɓe fuska kamar za ta yi kuka tace" Abun tausayi, gaskiya ya kamata ayi maganar Fahad, dan bamu san halin da yake ciki ba, na damu akan shi sosai saboda ina tsoron kar wajen karɓo saƙona ne abun ya faru da shi." Kallonta duk sukayi, hakan yasa ta ɗan wayance da sake cewa" Ina fata ba abinda suka mishi." Jinjina kai Bilal yayi ya kalli Mukhtar da ba abinda yace face yanzu da yake bin Fa'iza da kallon tsana da kuma aza équation a kan ta, daga alamar tarawa da ɗebewa har da ruɓanyawa da ninkawa yake duk a take, cikin taushin murya Bilal yace" Ɗan uwa, k kula da Ammie, ni zan je na kai musu kuɗin, sun ce za su kira da minti sha biyar kacal." A tausashe Mukhtar ɗin ya kalle shi sai kawai yace" A'a, zamu tafi tare da kai ne." Girgiza kai Bilal yayi zai yi magana kawai Mukhtar da bai cika magana ba ya kama hanyar fita daga falon, hakan yasa Bilal bin bayan shi da tunanin zai rarrashe shi a can har ya samu y zauna kar ya bi shi. Kafin ya fit daga ƙofar Ammie ta ɗago ta kalle shi tace "Bilal..." Juyowa yayi ya amsa da "Na'am Ammie." Cike da bada umarni tace "Idan ka samo Fahad, ina so mu san labarin yaran ɗan uwanka guda biyu da suka ɓace, a jikina da na mahaifiyarsu muke ji suna raye, kuma da kashe su ake son yi da an kashe su lokacin da aka samu damar keɓanta da su, amma sai ba'a yi haka ba aka ɗauke su daga nan, dan haka duk wani gidan radiyo da telebijin da yake na kuɗi ina so mu siyi babbar shiya a ciki dan a mana talla, ko Allah zai sa mu dace." Kaf kowa kallo ta yake a wurin, Bilal kuma da mamakin ta yadda zasu fara yace" Amma Ammie, ta ina zamu fara? Sannan bamu da wata makama d zamu iya bayar da wata shaida akan yaran..." Da sauri Nuriyya ta kalle shi tace" Akwai Yaya Bilal, a duk inda na ga yarana zan iya gane su, Kuwailat tun tana jinjira na saka mata wasu duwatsu a ƙugunta, ba lallai ta girma da su a jikin ta ba, amma kuma robar da aka ɗaura duwatsun tana ja ne sosai ta yadda in har ba ta cire ba to suna nan har yanzu a ƙugun nata, sannan tana snye da ƙananun ƴan kunnen zinariya masu ƙaramin jan dutsi, ba kowa zai gane anfanin su ba bare a rabata da su, sannan a wuyan ta, akwai wani tabo mai ɗan duhu wanda lokacin da aka haife ta mutane suna cewa wai mahaifa ce ta taɓa wuyan nata, Shiyasa ya fita daban da hasken fatar ta..." Sai kuma ta raunana murya tace" Iya wannan ma hujja ce da zan iya gane ƴata Yaya Bilal, dan Allah ka taimaka min." Jinjina kai yayi ba dan ya wani gamsu ba yace" Shikenan, zan ƙoƙarta." Sabeer dake tsaye kuma cewa yayi" To Eesha fa?" Kallon shi Nuriyya tayi sai kuma ta kalli Bilal tace" Eesha kuma tana da a..." Tsaf! Da sauri Fa'iza dake tsaye har lokacin ta katse ta da cewa" Zamu iya neman Eesha da cikakken sunan ta ai, ma'ana *Nana Aisha Mukhtar Ahlan*." Da sauri kowa ya zuba mata idanu har da Abbu dake zaune ya tangale haɓa yana sauraren su da kallon su, da mamakin abinda ta faɗa Abida ta miƙe tsye tace"... *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *13* Da mamakin abinda ta faɗa Abida ta miƙe tsaye tace "Amma ta ya zamu saka sunan t cikakken bayan na tabbata wanda ya sace ta zai canza mata komai nata?" Da i-ina da kuma rashin tabbas Fa'iza tace "Eeew...hakane,ina nufin muyi anfani da sunan, wataƙila muyi sa'ar samun ɗaya daga cikin su." Sabeer dake kallon ta ne yace "Ba abu mai yiwu bane, idan muka ce muyi abinda kike tunani, to ina tabbatar miki a kwana ɗaya zamu tara Eesha cike da gidan nan, dan kowa zai yi ƙoƙarin alaƙanta kan shi da mu ne." Sai kuma ya kalli Bilal yace "Yaya Bilal, ka je, idan ka dawo zamu tattauna a tsanake." Da sauri Yaya Bilal ɗin ya juya ya fice daga falon, hakan ya sa Mukhtar bai ma san akan me suka tattauna ba, cikin alhini da tanzanko suka kasance musamman da ya zama babu mai labarin abinda ke faruwa, gashi kuma su biyu suka tafi amma babu wanda ke ɗaga waya idan aka kira dan a ji me ke faruwa, sun fi awa biyu kafin su dawo gidan tare da Fahad da yunwa da ƙishin-ruwa duk suka jigata shi, ga tafin da ya sha wanda har lokacin kumcinshi bai yi nasarar lashe shatin hannun ƙaton mutumin ba. Ta wata fuska sun samu daidaituwar Fahad, dan kuwa gaba ɗaya ya daina fita a gidan, ba inda yake zuwa daga cikin gida sai masallaci. Haka kuma gidajen labarai na kuɗi sun ɗauki harama ana ta bayar da sanarwa akan yaran da suka ɓata tare da zayyana lambar da za'a kira idan an same su, sannan ga duk wanda ya san inda suke ko ya bada wani bayani a kan su, to yana da kyautar miliyan biyar cif. *Cikin* tashin hankali da ɓari har kamar za ta yi kuka take cewa "Yanzu Hajia ya zanyi idan garin neman yaran nan aka gane da hannu na a ciki? Hajia tsoro nake ji wallahi, dan Allah kiyi wani abu a kai." Cike da rashin damuwa Fa'iza tace "Kinga *Rabi* kar ki ɗaga min hankali, na ɗauka burinmu kenan akan ɓatan yaran nan, dan haka kar ki wani ɗaga hankalin ki." Cikin ɗar-ɗar Rabi ta sake cewa "Na sani Hajia Fa'iza, ni tsorona shine kar a gane ni na ɗauke yarinyar daga gidan." Cike da tabbaci Fa'iza tace "Hakan ma ba zata faru ba, ki kwantar da hankalin ki." Daga inda take amsawa ta jinjina kai tace "Shikenan Hajia, Allah ya sa mu dace." Ba tare da ta amsa mata ba ta yanke kiran tare da kiran lambar DG kai tsaye, ba ɓata lokaci DG ya ɗaga dan kiran nata yake ta jira kena tsawon lokaci, yana ɗagawa yace "Kiran ki nake ta jira dama Hajajju." A daƙile tace "Ina fata an samu ci gaba game da abinda na saka ka?" Da ƙwarin guiwa ya shiga labarta mata "Hajia, kamar yadda kika sani ina yin bincike kuma akwai masu tayani binciken, yau mun yi nasarar gano wani gidan marayu ta dalilin wani Dr. E manuel, shine ya bani masaniya akan gidan marayun ya kuma tabbatar min zamu iya dacewa idan muka duba can, dan haka nake ta jiran kiran ki dan na sanar da ke yau zan bar ƙasar nan, kuma da yardar Allah ba zan dawo ba sai da wannan yarinyar." Ajiyar zuciya ta sauke mai sanyin gaske tare da yin murmushi tace" Shikenan DG, naji daɗin wannan labarin, daga yanzu har ka dawo zaka iya kirana a duk sanda ka so dan ka sanar dani ci gaban da ake samu." "Shikenan Hajia, sai kin ji ni ɗin." Ya faɗa tare da yanke wayoyin na su, zaune tayi tana sakin murmushi na farin ciki da jin daɗi, ta kashe milyoyin kuɗaɗe duk dan a gano mata yarinyar da har da kuskuren ta a ɓatan ta, wanda da bata bayar da goyon baya ba da yanzu tana tare da iyayen ta, amma in sha Allah za ta gyara wannan kuskuren da ta aikata ta hanyar dawo da yarinyar wa iyayen ta. ******************** Sallamar sa tasa Hajia Kaka gyara zamanta tare da dakatawa daga cin abincin ta amsa tana kallon shi, shi ma kallon ta yake yana kuma ƙarewa ɗakin kallo saboda hayaƙin turaren da yake tashi mai ƙamshin daɗi, ƙarasawa yyi ya zauna kujerar dake gefen ta yana faɗin "Hajia, wa ya cika miki ɗaki da gobarar nan?" Kallon ɗakin Hajia ta fara yi sannan ta kalle shi tace "Gobara kuma? A ina?" Cike da wofantarwa yace "Na ga ɗakin sai hayaƙi yake." Murmushi tayi cike da jinjina hali irin na Sa'ad tana sake kai lomar biskin ta dake matuƙar yi mata daɗi a baki musamman ma kifin da take taunawa a kai a kai, tana taunar abincin tace "Yanzu Sa'ad ba ka ji ɗakin nan na ƙamshi ba, yaushe rabon da ka samu ɗakina a kimtse haka? Sai da ka kawo min ƴar rainon nan tawa da bata da ƙiwar aiki." Taɓe baki Sa'ad yayi tare da ƙara lafewa jikin kujera ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana danna wayar shi, jin bai ce mata komai ba yasa ta sake dubanshi tace" A zubo maka abincin?" Fuskar ta ya fara kallo, sai kuma ya kalli farantin abincin dake gaban ta, rasa fahimtar me ye ma take ci ɗin yasa shi yatsina fuska yace" Me wai?" Murmushi ta sake saki tace" Biski ne, wallahi yarinyar nan ba dai iya girki ba, wai ka ji daɗin biskin nan kuwa? Ni ban ma san a ina ta koyi haɗa shi ba, bari ka ji..." Ta faɗa tana miƙewa da ƙyar ta nufi inda yake da loma a hannun ta da kuma farantin tana cewa" Ɗanɗana ka ji." Ƙara yatsina fuska yayi kamar ta nufo shi da wani mugun abu, tana zuwa ta tunkari bakin shi yana girgiza kai tare da cewa" Um um! Bar shi kawai Haj..." Kafin ya rufe baki ta ɗura masa lomar da ta saka shi ƙura mata ido, shi ba kallon takaici ba bana jin haushi ba, ba yadda ya iya da ya wuce ya shiga tauna lomar à tsanake haro yana wani waina idanu da son tantance ɗanɗanon, Hajia da ta zuba mishi idanu tana murmushi da fara'a tace "A zubo maka ko?" Jujjuya idanu ya dinga yi alamar yana tunani, dan yunwa kam yana jin ta fa Shiyasa ma ya shigo ɓangaren nata dan ya ci abinci, uwa uba kuma abun ya birge shi a baki, saida ya kawar da kai yace "Kaɗan." Dariya tayi ta koma ta zauna tana ƙwala kiran sunan Aisha, amsawa tayi daga madafa ta fito da sauri... Kallo ɗaya tak yayi niyyar yi ma yarinyar nan, to amma ai sanin kowa ne shaiɗan na farmakar bayi na ƙwarai ta kowace irin kusurwa, in ba haka ba, ta ya yarinyar nan sheɗan zai ribace shi har ya dinga kallon shigar ta wacce ta yi ne kawai dan daga ita sai Kaka gidan, kuma atamfa ce jikin ta ɗinkin riga da siket, kawai kyau da kum dacewa da surar t a sukayi, sai ya zamana babu kallabi ko hijabi à kan ta, hakanne ya sa kitsonta da yau kwana uku da suka yi shi tare da Leila manya manya ya zubo a bayan ta har wasu wutsiyar gashin suka diro kan ƙirjin ta. Tunda ta gan shi ta kyaɓe fuska kasancewar ta gwanar shagwaɓa har ta ƙaraso, tana zuwa ta tsaya tsakiyar kujerar da yake da inda Hajia take tana kallon shi kamar za ta yi kuka tace "Abbu, ina ka je? Kwana huɗu fa kenan Hajia tana ta neman ka." Kallon ta Hajia tayi tana ɓoye dariyar ta, ko ita fa bata tambaye shi ba kuma bata tambayar shi idan yayi irin wannan shirun, hakan yasa take dariya da kuma kallon shi tana so ta ga zai amsa ma Aishar ko shariyar za ta samu ita ma. Sa'ad kuma lamarin ne ya so girman tunanin shi, to shi yanzu wannan ƴar za ta tsare tana tambaya inda yaje? Har tana masa wani kuka-kuka da kuma shagwaɓa kamar wata iyalin shi? Hajia kuma ta wani kasa dakatar da ita har ta na mishi dariya? A kausashe ya kalle ta cikin daƙilalliyar murya yace "Ke! Ni ba Abbun ki bane ba kuma na kowa ba, kika ake kirana Abbu sai na zubar miki da haƙora." Jin haka yasa Aisha bi ta gabanshi ta zauna ƙasa kusa da ƙafafun Kaka tana mishi wani irin kallo ta riƙe hannun Hajiar tace "Hajia ai ba zaki bari ya fasa min baki ba ko?" "Ba zan bari ba kam." Ta faɗa tana dariya, sai kum tace "Je ki kawo mishi abinci, yunwa yake ji." Yunƙurawa tayi za ta miƙe tana kallo shi tace "To amma Hajia ya faɗa mana ina yaje kwana huɗu, kuma bai faɗawa kowa zai yi tafiya ba, fisabilillah haka ya dace?" Duk ƙoƙarin Hajia saida ta tintsire da dariya tana kallon Sa'ad da ya bita da wani kallo yace "Ba zan faɗa ba ke, ɗanki ne ni ɗin?" Sai kuma ya kalli Hajia dake dariya ya nuna mata Aisha data nufi madafa yace "Ki gaya mata ta daina min irin haka, a kaf gidan nan babu mai min irin gangancin nan, ciki kuwa har da Ibu." Juyowa Aisha tayi ta kalle shi cikin marairaicewa tace "Gaskiya bai dace ba, *Abbu* ake cewa fa ba *Ibu* ba, ka ji *Abbuna*." Idan ranshi ya ɓace kallon shi na gudana da sauri sauri ne, ma'ana ya kan dinga yawan ƙyafta idanu, to ganin haka yasa Kaka tabbatar da ya yi ful fa a wannan ɓangaren, dan haka ta juya ta kalli da lallai take son maida Sa'ad ɗin abokin wasan ta tace "Ƴar rainona, maza je ki kawo mishi abinci, baki san ko Iro tela ba ya mishi irin haka ba? Maza je zubo mishi abincin." Turo baki Aisha tayi ta juya da sauri tana faɗin "To Mamie, ni dai ai gaskiya na faɗa mishi, kuma Kinga ko ni ina girmama shi ina kiran shi da Abbu, kenan shi ma ya dinga kiran Papina da Abbu." Zunbur ya miƙe tsaye ya nufi madafar da mugun sauri, hakan yasa Hajia Kaka juyawa ta bishi da kallo tana kiran" Sa'ad, Sa'ad, Kaga Sa'adu..." Cak! Kuma sai ya dakata ya juyo ya kalli kakar kamar yana shirin kai mata duka, cikin taushin muryar nan tashi kamar ta mace yace" Hajia, ban ce bana son sunan nan ba? Ni ba sunana Sa'adu ba." Murmushi tayi tace" Shikenan naji, yanzu ina ka nufa?" Nuna mata madafa yayi yace" Waccen ƴar taki zan takawa birki daga neman hawa min kai da take shirin yi, naga fa alama ke kika ɗaure mata gindi a gidan nan, to wallahi za ta bar gidan nan idan ta sake hassalani." Zaro idanu Kaka tayi ta riƙe haɓa tace" Ni kuma? Ban da laifi kai ma ai shaida ne ko, amma zan manta magana ta daina, kai kuma ka bar maganar za ta bar gidan nan, dan wallahi na saba da ita yanzu bana so mu rabu." Kamar wani mai bata umarni ya nuna mata wajen zamanta yace" To je ki zauna ina zuwa." Yana faɗa yayi hanyar madafar, tsaye tayi ba ta gusa ba dan ita tasan waye Sa'ad, yadda bata da tabbacin ya daina kula wasu mata, haka ba yadda za'a yi ta bar shi yana samun kusanci da ƴar mutane, dan haka take tsaye bakin ƙofar tana jira ta ga ya jima ta kutsa kai. *Yana* shiga Aisha na zuba miyar a farantin tare da cokali a hannun ta da zata kai mishi, kalmar "Ke!" Da ya faɗa a kausashe yasa ta zabura har ta liƙe idanu, amma da ta ɗauki muryar sai ta juyo a hankali tana kallon shi tace "Na'am Abb..." A hassale à kuma zafafe ya sake faɗin "Ke ba Abbu ba, ni ba Abbunki bane, ban da aure, ko baki fahimta bane? Sau nawa zan gaya miki ne?" Ganin dai yanzu daga ita sai shi ne yasa ta jinjina kan ta turo bakin ta tace "Kayi haƙuri, ai ba sai ka haifeni ba zan kira ka da Abbu, girmamawa ce saboda taimakon da ka min." Saida ya ɗan kawar da kan shi yace "To bana son girmamawan, idan zaki iya kirana da Yaya ki kira, idan ba zaki iya ba kuma kirani da Sa'ad." Ɗan buɗa ƙaramin bakin ta tayi da mamaki tace "Lahhh! Kiran sunan ka a wajena ai zunubi ne babba." A ƙufule yana kallon ta yace "To kirani da kai, idan ba haka ba kuma ranki zai ɓace." Zuba mishi idanu kawai tayi bata tanka mishi ba, dan haka ya ƙarasa kusa da ita ganin ta zuba miya a abincin kuma yunwa yake ji da ba zai iya hushi da abincin ba yasa shi ɗaukar farantin tare da maka mata harara sannan ya nufi hanyar barin madarar... Ƙarar wayar shi ta sa ya shiga lalubanta a aljihu, yana cirowa ganin sunan Hambali ne ya sa ya ɗan yi tsaye, shi ya ma manta da shi saboda wasu sabgogi da ya ƙara durmiya kanshi à ciki duk da dai wannan halatattu ne, wannan kiran kuma ya sa shi iya tunawa da akwai fa ajiya a acikin yarinyar nan, dan zaman da sukayi da ita tausayi take bashi sai kuma Allah ya ɗauke tunanin shi daga kanta. A hankali ta danna ok sannan ya ɗora a kunne ba tare da ya ƙara tako ɗaya ba yace "Ina ji?" Ba tare da Hambali ya damu da yadda ya amsa mishi ɗin ba dan hakan ɗabi'ar sa ce yace "Sa'ad, wai me na maka ne daka daina ɗaukar kirana? Ko dan yarinyar ta ɓata ne kafin ta shiga hannun ka?" A wani gadarance Sa'ad ya waina idanun shi yace "Ba wannan maganar, ya aka yi yanzu?" Cikin yanayin tashin hankali Hambali yace "Sa'ad akwai gagarumar matsala, dan gane da rashin ganin yarinyar nan, Sa'ad kai ne Maraɗi, dan girman Allah ka taimaka min a ga yarinyar nan." Kyaɓe fuska yayi tare da taɓe baki yace "Wace irin matsala kuma?" Da rashin gaskiya Hambali yace "Ba sai ka ji ba Sa'ad, kai dai ka taimaka min mu ganta, na maka alƙawarin biyan ka kuɗin da kayi asara har da ninkin su ma, ni dai kawai na ga yarinyar." Ajiyar zuciya Sa'ad ya sauke ya buɗa baki yace "Ka ga, ni yanzun w..." Muryar Dr. Ema ya ji yace "Oga, ba ni shi a wayar zan masa bayanin haɗarin da take ciki." Da sauri Hambali yace "Yawwa, Sa'ad ga Ema zakuyi magana." Ba tare da ya musa ba ya saurara har saida ya ji Muryar Ema yace "Oga Sa'ad, yarinyar tana cikin haɗari." Da wani irin yanayin sauri Sa'ad ya juyo ya kalli Aisha da tun farko shi take kallo, amma da ta ga wayar shi yake sai ta ci gaba da goge madafar, à tausashe ya furta "Wane irin haɗari?" Cikin tashin hankali Ema yace "Oga, a ƙa'ida bai kamata abinda ke cikin ta ya wuce sati biyu ba, yanzu kuma Kaga wata ɗaya fa kenan, yallaɓai idan baka damu da yarinyar ba, dan Allah kayi ƙoƙarin samota kafin a ɗora wani sati a kai, dan daga yanzu zuwa kowane irin lokaci ledar robar da aka zuba cocaïne ɗin da ƙwayar da ake sarrafa benelin da kuma tramol za su iya fashewa, hakan kuma zai iya ja wa yarinyar mummunar matsala, lalacewar kayan cikin ta, taɓa ƙwaƙwalwarta har ma da shafar jijiyoyin dake lura da gudanar tafiyar jinin ta, Oga, a taƙaice dai ba mutuwar farat ɗaya za ta yi ba, daga hanci, bakin ta da kunne kowane zai iya aman jini, bayan haka ba za'a iya gane kan matsalar ba kai tsaye, kafin a gano kuma... An makara." Kallon da yake ma Aisha tana ta gugar tiles fuskar ta ɗauke da murmushi, tunani yake idan abinda ya zayyana ya faru fa? Zai rasa *ƙwaya ɗaya tak* dake duban shi tana faɗa mishi gaskiya, zai rasa mai kallon shi tana mishi shagwaɓa son ranta kamar wata matar shi. A rashin sanin yana kallon ta ta ɗago kan ta, sai kuwa tayi sa'ar sauke idanun ta cikin nashi idon yana mata wani marayan kallo mai ma'anoni, a take ta saki murmushi ta furta "Abbu..." Wata razana yayi da bai san dalili ba har saida ya saki farantin ya fashe abincin ya zube, ƙarar farntin kuma ta haddasa mishi wata faɗuwar gaba da sarawa da kan shi yayi, a hankali ya buɗe idanun shi daga rufewar da ya musu, sai kuma ya juya mata baya da ƙyar ya iya furta "Tana cikin wannan haɗarin, shine ba ku gaya min ba?" Cikin Ema dake son sanar da Sa'ad ɗin wani abu ya matsa nesa da Hambali sannan yace "Oga, ai tun za'a kawo ta na faɗi wasu ƙa'idoji da ya kamata a kiyaye, misali shan abu mai zafi, zai taimaka wajen narkewar robar da wuri lokacin narkewar ta baiyi ba, shan abu mai sanyi ƙwarai kuma zai sa robar tayi gautsi ma'ana kamar bokitin robar da rana ta daka, shi ma dai Kaga fashewa ne a ƙanƙanin lokaci, magana ta gaskiya oga Hambali ba yana son ganin yarinyar bane dan wani abu, yana son ganinta ne dan ya killace ta a wannan asibitin tamu a ɓangaren mahaukata." Da ƙarfi Sa'ad ya furta "Me? Mahaukata ? Saboda me to?" Duk yayi tambayar yana barin madafar tare da nufa falo kai tsaye ya bar Aisha da tunanin wane irin sakaci ne ya sa shi zubar da abincin, a asiirinci Ema yace "Yallaɓai, yau na ji yana waya game da wata cigiya da ake yi a gidajen telebijin na wata yarinya da ake nema jika ga Saheeb Ahlan, koma wacece yake waya da ita ina kyautata zaton bata da kyakyawan nufi akan yarinyar nan da nake da tabbacin ita ce wannan ƴar da ake nema da tsabar kuɗi miliyan biyar ga wanda ya san wata masaniya a kan ta, Oga, ka yi wani abu dan ka ceci yarinyar nan, rabata da iyayen ta ya isa haka, ka da a sake salwantar da rayuwar ta ta hanyar mayar da ita mahaukaciya tuburan, dan Allah ka yi wani abu a kai." Da maɗaukakin mamaki Sa'ad da yayi mutuwar tsaye yace" *Saheeb Ahlan*? Ita jikar shi ce?" Cike da tabbaci Ema yace" Ƙwarai yallaɓai, na tabbatar da haka, dan shi kanshi bai sani ba saida ya ga Labaran nan yasa aka sake binciko masa cikakken sunan ta, akwai ayar tambaya ga duk wanda ya kawo ta gidan marayun nan, dan kuwa yayi anfani da sunan ta na asali wanda ya san ko ba jima idan ta girma za'a gane wacece ita da wannan sunan ahalin." Da ɗaure kai Sa'ad ya dinga shawagin a falon musamman da Kaka hankalin ta ke kan telebijin yace" Ahlan fa a Niger suke, ta ya aka yi dogon zango da ita ƙasa mai nisa haka? " Da rashin tabbas Ema yace" Hakane yallaɓai, nasan kuma zasu yi iya yin su ne dan ganin sun nesanta ta da gidan ahalinta." Ƙwarai bakin shi so yayi ya ce ma Ema _" Kar ka damu, yarinyar na tare da ni duk wannan lokacin."_ Amma kuma jin wani irin haɗari dake tattare da rayuwar yarinyar mai sarƙaƙiyar gaske, sai kawai ya basar cike da izza da isa yace" Shikenan, zan duba na gani." Bai tsaya sauraren abinda zai sake faɗa ba kawai ya yanke kiran tare da dawowa madafar nan hankali tare da mugun sauri, shi kan shi bai san me ye ba, amma dai daga ƙasan zuciyar shi yake jin rudun na sake hauhawar masa. Yana shigowa Aisha ta ɗauki bokitin ruwan za ta juyesu a banɗakin dake ciki, wata damƙa ta ji an ma hannun ta ba zato da ta sa ta saurin sakin bokitin ta kalli wanda ya riƙe ta. A razane ta sa ɗaya hannun ta ta riƙe wanda ya riƙeta da shi cikin Muryar ruɗu tace "Abbu... Yaya, ka yi haƙuri wallahi zan dinga cewa Yaya, kar ka dakeni ka ji Ab...Yaya." Ɗora yatsan shi yayi à bakin shi yace "Shiiiii! Je ki ɗauko gyalen ki zaki rankani wani guri." Wani kallon yan shaye-shaye ta mishi tace "Na raka ka? Ni ɗin?" Sakin hannun nata yayi yace "E, ko ba zaki je ba?" Ɗan ja baya tayi tace "Abbu ai b..." Kallon da ya mata ya sa ta kame bakin ta, tako ɗaya ya ƙara yi ya zo inda take, da sauri ta ja baya shi ma kuma ya bi ta har saida ta haɗe da ƙofar banɗakin dake rufe, hannayen shi ya buɗe tare da dafe bangon yana kallon tsakiyar fuskar ta. Sosai ya haifar da kusanci a wannan zaman nasu wanda ya gagareta samun numfashi mai kyau, dan gaba ɗaya numfashin shi ma a cikin fuskar ta yake sauka. Wani narkakken kallo yake bin fuskar ta ta da shi yace "... *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *14* Wani narkakken kallo yake bin fuskar ta ta da shi yace "Ke wai baki da wani tunani ne sai na za'a miki lalata?" Lumshe idanun ta tayi da ɗan firgici tace "Lahhhh! Ni wallahi ba haka bane Abbu." Bakin nata ya ƙalla da ta furta Abbu da shi, leɓen ta na sama baƙi sai na ƙasa kuma kalar Pink da sirkin ja shi ma kuma ba ƙwarai ba, ba tare daya ɗauke idanun nashi daga bakin ta ba da ya ke jin wani abu mai kama da haɗiyar yawu a maƙoshin shi cikin wani siririya kuma tattausan murya yace "To me yasa baki yarda ki tafi da ni ba?" Idanunta na kallon ƙasa bakin ta har rawa rawa yake tace "To ai ba daidai bane ko?" A hankali, ya fara manta me ye alaƙar shi da ita, dan haka ya sake matsawa har saida ya ji tsinin dogon hancin ta ya taɓa na shi hancin, sai kuma ya ɗan wara idanun shi sosai a hankali ya matsa kaɗan yana cewa "To ai ni *Abbu ake kirana ko*?" Kallon fuskar shi tayi a wannan lokacin, sai kawai ta saki murmushi har da rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta tana faɗin "E mana, Abbu." Jin numfashin ta na yin sama kuma ya ƙi yin nesa da ita yasa ta ɗan kallon haɓar shi dake kewaye da wani matsakaicin saje da gemun da ya zagaye bakin shi gaba ɗaya, da gaske numfashin ta neman ƙwacewa yake, tubarkallah Abbun nata akwai tsayi ga kuma wani sirri da kayan jikin shi suka bayyana wato ƙwanji da murɗaɗɗiyar sura, duk zaman ta da shi bata ganshi sanye da shadda ba, zallar kayan shi yadi ne irin masu kyau ɗin nan da tsada, sai yake musu mabambamta ɗinkuna, wasu dogon hannu wasu gajere, ɗinkuna dai kala-kala kamar wani mai tallar kayan sakawa, cikini ɓarin murya tace "Abbu ɗan matsa mana, ba kyau fa haka ko kaɗan, ai ni ƳAR riƙon ka ce." Karo na farko a zaman shi da yarinyar da yaji ta saka shi dariyar da har saida haƙoranshi biyu na gaba masu ɗan tsayi suka fito waje, ja baya yayi dan sai zuciyar sa ta raya masa ai hakane ɗin, dafe ƙugun shi biyu yayi yana ci gaba da murmushi yace" Kin yi karatu?" Ɗagowa tayi daga bangon banɗakin da mamakin tambayar shi tace" E Abbu, na yi." Ba tare daya daina kallon ta ba yace" Nawa kike ci a jarabawa?" Cike da fari da idanu wai ita za ta faɗi ƙoƙarin ta tace" jimilla 88 cikin ɗari." Jinjina kai yayi cike da gamsuwa yace" Uhum! Amma kuma shine ƙwaƙalwar ki ta kasa gaya miki ni ban isa zama Abbun ki ba?" Turo baki tayi gaba tare da kawar da kanta b tace komai ba, numfashi ya sauke sannan yace" Muje to, asibiti za ki rakani." Da mamaki tace" Asibiti, baka da lafiya ne?" Iska ya feso dake nuna gajiyawar shi da kuma ƙaguwa, ita ma da ta ji bai bata amsa ba sai tace" Oho! Na gane, kenan baka da lafiya ne Abbu, Shiyasa kwana huɗu baka zo ba Hajiata duk ta damu." Sai kuma ta kama hanyar barin madafa tace" To muje na gayawa Hajia zan kai ka asibiti." Kallon ta ya so yayi na mamakin ƙarfin halin ta, shi har shine za ta kai asibiti dan bai da lafiya? Wai me yarinyar nan take ji da shi ne? Alamu nuna mi shi suke tana da son barkwanci dama ce kawai bata samu ba, to amma a kan shi ne za ta yi barkwancin nata? Lamari na sheɗan da ba tsoron Allah a ciki, sai ya wani ja idanun shi ƙasa kaɗan da bayan ta ya dire su akan ƙugun ta.... Ya salam! Ya salam! Ya salam! Abinda ya samu kanshi da ambatawa kenan a ƙasan zuciyar shi, bugo ƙofar da ta yi ne ya dawo dashi hayyacin shi har ya zabura ya juya ma ƙofar baya yana zaro ido kamar barewar da ta kubto daga hannun zakin da ya damƙi wuyan ta. To wai! Shi abun mamakin ma anan shine, yarinyar can dake da ɗan matsakaicin jikin can, ita ce ke da wata irin2 dirarriya ƙira haka wacce ta dame ta Fanta da kwalbar sprit? Sai fa da ta juya ne ya ga wani shafaffen cikin ta daya fitar da surar shi tamkar ta sabon wata, hakan ya fito da wani irin ƙugun ta da bashi da tudu sosai, amma dai ƙirar... Kai hasbunallah wani'imal wakil, anya kuwa a ƴan matan da ya gani ya taɓa haɗuwa da mai irin waccen zubin? Anya kuwa *ƴar shi*...? ******************** Azabar wahalar da ta kai mata karo ne yasa cikin zafin nama ta ɗaga hannu ta tabki Uzei ɗin dake goye a bayan ta tana ta kuka wanda ita kan ta zafin ranar da suka dame ta ne take ga kuma yunwa, wannan tiƙar da ta mata yasa ta ƙara fashewa da mugun kuka wanda duk mai sauraro zai gane an ma yarinyar wani abu ne, cikin faɗa da masifa Bara'atu da ta rasa ina za ta sa kanta ta ji daɗi ga bokitin da ta ciko da ruwa tana tafe suna zubar mata a jiki ga zufa saboda ranar da ake ƙwalawa yasa duk tayi wata kala kamar wacce ta fito daga daji. Kamar wata zararriya tana tafe take faɗa wa yarinyar goyen cewa "Wallahi Uzei zan ci ubanki idan baki min shiru, ina dalili ina mafari, abun duniya ya damu mutum ke ma kuma ki addabeni da kuka? Da wane zan ji to? Kukan ki na masifa ko bala'in dake kaina." Da haka ta shigo cikin gidan ta aje bokitin da ƙyar ta buɗe ƙofar sannan ta shiga da ruwan, tana shiga ɗaki tana sauke Uzei a goye wayar ta ta sake ɗaukar kururuwa, ta ɗauka kafin ta ɗaga kiran ta lura an kira ta ma dayawa bata ɗaga ba, ganin baban Uzei ɗin ne yasa ta yin tsaye kamar tana gaban shi cike da masifa tun bata ɗaga ba tana faɗin "Dama ko baka kirani ba zan kira ka, wallahi na gaji da masifar gidan ka." Tana faɗa ta ɗaga kiran a kausashe kamar wata namiji tace "Hello!" A ɗane yake à inda yake, bare tunda Jabir ya bar gidan ya kan rasa wanda zai doka idan hannun shi na Ƙaiƙayi, cikin masifa da hargagi yace "Ke wani irin iskancin ne wai ki aje waya ana ta kiran ki b zaki ɗaga ba? Kin san kira nawa na miki? Gidan uban wa kika shiga?" Cikin kwaratsi da hargagi ita ma wanda kwanan nan ya kunno musu kai ita ma tace "Ban sani ba, haka kawai daga ɗaga kiran ka zaka rufe ni da bala'i, ba sai in ina gidan bane zan ɗauki kiran ka ba?" A wani mugun zafafe yace "Ni kike faɗawa haka? To ina kika tafi? Ai baki gaya min zaki fita ba." Cikin jin haushi da tafasar zuci tace "Ɗaukar ruwa na tafi, kuma wallahi in gaya maka ni na gaji, na gaji da wannan wahalar, Haba dan Allah, da wanne zan ji to? Aikina ko kula da gidan? Ko kuma rainon wannan yarinyar mai shegen kuka?" Cikin takaici Mu'az yace "To yanzu ya kike so na miki? Ni zan dinga zuwa ina ɗauko miki ruwan?" A zafafe tace "Cikin biyu kayi ɗaya wallahi, ko a sama min almajirin da zai dinga zuwa yana ɗauko min kafin na fita aiki, ko kuma ka canza min gida mu koma inda ake samun ruwa, amma ni na gaji wallahi." Cike da rainin wayo yace "Ƙaddara ban ɗauki ko ɗaya ba, ya zaki yi kenan?" A take tace" Sai na bar maka gidan ka." Cikin wofantarwa yace" Ba wannan ya sa na kira ki ba, Jabir bai dawo ba?" Cikin wani sabon takaici tace" Bai dawo ba, da ya zo da zan maka ƙorafin ɗauko ruwa ne?" *Dammmm*! Ya ji gaban shi ya amsa, kamar ya? Me take nufi? Ɗan nashi kenan y zama mai kawo mata ruwa kawai? Kenan bai da wani anfani bayan wannan? Hakan na nufin ba ɓatan shi ne ya dame ta ba, ita kawai ko yanzu ya dawo za ta ci gaba da saka shi ɗaukar ruwa ne kamar wani jaki? Karo na farko da ya ji yana nadamar kasancewar ta *matar shi*, karo na farko da ya ji yayi nadama akan abinda ya aikata wa ɗan shi, cikin jin zafin abinda ta faɗa yace "Kenan yanzu kin fara sanin anfanin shi? Da yana gidan baki taɓa rashin ruwa ba, har wasa kike da su dan su ƙare ki ce ya ɗebo miki, kenan yanzu kin fara gane anfanin zaman Jabir a tare da ke?" Cikin turo baki da shashantarwa tace "Ban sani ba." Gaskiya ya gode Allah da baya kusa, dan ba abinda zai hana shi taɓa lafiyar jikin ta, cikin gargadi yace "Za ki sani ne malama, ba dai ya bar miki gidan ba? Za ki sani wallahi." Cikin ɗaga murya tace "Dakata malam, wai lafiya kake neman ɗora min laifin da ba nawa ba? Duk abinda na ma Jabir ai a gurin ka na gani, dan haka ni kada ka sake min maganar wannan yaron, kuma zan rayu da Jabir ko babu shi." Tana gama faɗin haka ta kashe kiran, wanda hakan ba ƙaramin ƙon masa rai yayi ba haro saida idanun shi sukayi ja kuma suka kawo ruw na takaici da baƙin ciki, amma ba komai za su haɗu, sati nawa ya rage ya dawo garin? Za Ta gane kuren ta. ******************* Tsaye ta same shi Hajia Kaka na tambayar "To ko dai abincin ne ya zube? Na ji faɗuwar faranti ai a ciki." A daƙile kawai ya amsa da "E, idan na dawo na ci." Da kulawa ta dube shi tace "Za ka dawo ɗin ne?" Jinjina kai yayi yace "Zan dawo Hajia." Jinjina kai tayi tace "To à dawo lafiya." Hanyar ƙofa ya nufa Aisha ta bishi tana kallon Kaka da cewa "Mamie sai mun dawo." Da al'ajabin da ya kusa sheƙe Hajia daga zaune ta dakata daga lashe yatsunta da ta ci abinci tace "Ke kuma fa ina zaki je ? Ban gane sai kun dawo ba?" Dakatawa Aisha ma tayi ta juyo da mamaki tace "Abbu bai faɗa miki ba?" Yana kusan fita ne ya ji wannan deba sai ya tsaya yana kallon su, lokacin Hajia ta girgiza mata kai tace "Bai gaya min komai ba, ya dai ce zai fita." A tsanake Aisha ta juya ta kalli Sa'ad da a lokacin ya kalle ta shi ma, da kamar tuhuma ko son ƙurewa tace "Ya haka kuma Abbu?" Dantse leɓenshi na ƙasa ya yi yana ci gaba da kallon ta kawai da tunanin hanyar da zai bi yasa ta daina kiran shi Abbu, dan za ta iya kashe mishi kasuwa a wajen ƴan mata fa, juyowa ta sake yi ta kalli Hajia tace "Hajia, Abbu ne bai da lafiya ya ce na raka shi asibiti." Da wani irin yanayi Hajia ta miƙe tsaye tana jin hankalin ta na shirin tashi, ba wai na rashin lafiyar da ta ambata ba, hasalima ba ta yarda bai da lafiya ba dan ba alamun da ya nuna yana ko ciwon kai, zuciyar ta tsintsinkewa ta fara yi, dan kuwa ita abinda ya zo mata a rai shine kar dai Sa'ad nema yake ya kai yarinyar nan inda zai mata lalata? Dalilin da yasa take ta kaffa-kaffa da ita kenan, dan bata ga alamar buɗewar idon yarinyar ba ta wannan sigar, Shiyasa bata so a ce jikan ta sila, musamman da ta yarda yarinyar ta kai macen da za ta iya ɗaukar hankalin shi, dan tafi dayawa daga cikin matan da yake shigo musu da su gidan nan. Saida ta kai inda Aisha take ta riƙe hannun ta jim a nata sai ta kalle shi tace "Asibiti za ka je? To ka tafi kai kaɗai mana, Allah ya tsare ya baka lafiya." Ba tare da tunanin me Hajia ke nufi da abinda ta yi ba ya ɗan sassauta murya yace "A'a Hajia, ai tare za mu tafi, ki barta Muje yanzu zamu dawo." Girgiza mishi kai tayi tace "A'a Sa'ad, ka je kawai, gaskiya bana son ta fita a daren nan." Ɗan matsowa ya sake yi yana kallon Hajian yace "Hajia, wallahi ba jimawa zamuyi ba, kuma zuwan nata na da mahimmanci ne." "Me ya kawo mahimmancin zuwan nata asibiti da kai?" Hajia ta faɗa tana kallon shi, ɗan kallon Aisha yayi sai kuma ya kalle ta yace "Hajia, idan na dawo zan miki bayanin komai, wallahi abu ne mai mahimmanci, kuma ya shafi sanin asalin ta." Da irin kallon hangen nesa ta bishi da kuma rashin samun sukuni, ba ta ce mi shi komai ba kuma bata saki hannun Aisha ba alamar bata gamsu ba, zubawa Hajia idanu yayi yana hango wasu abubuwa, sam ba wai bata son rabuwa da ita bane ko kuma bata so ta fita dan dare yayi, ai gaba ɗaya ma yanzu ƙarfe 08:00 tayi, sai ya ji zuciyar shi na neman raya mishi wani abu na daban a kan Hajia wanda baya so ya ji haka game da ita, dan abinda ke haɗa shi da mahaifiyar shi kenan, ya san yana neman mata kuma ba wai sun zama rayuwar shi bane da zai ce sai da su zai iya rayuwa, a'a kawai yana neman macen da yake ganin ta dace da tsari da zubin ajin shi ne kawai idan buƙatar shi ta motsa, Allah bai mi shi jarabar da komai ke iya tayar da sha'awar sa ba, illa kawai idan ya ga abu ne zahiri ko kuma yana kallo ya ga mace da namiji sun samu kusanci sosai, hakan kaɗai ke tayar da sa buƙatar. *Ƙwarai* da gaske tafiyar da Aisha tayi bayan ta juya bayan ta ya ji tsigar jikin shi ta tashi gaba ɗaya har ya ji kamar zai fara harbin iska, amma kuma wallahi har ƙasan zuciyar shi bai ji a ran shi zai iya ko da bari ta san halin shi na neman mata ba bare har ya nuna mata hakan da kan shi, bai san me ya sa ba? Amma mutanen nan sun kasa gane yadda yake *jin kunya* da kuma kawaici ga yarinyar, dan haka ba zai iya yarda ya mata lalata ba ko da wasa ma. Raunana kallon shi yayi ga Hajia idanun shi har kamar za su kawo ruwa yace "Hajia, ke ma?" Da sauri ta sunkuyar da kan ta ƙasa saboda sai ta ji ya bata tausayi, a hankali ta saki hannun Aisha sai kuma ta kama na shi hannun suka fita daga falon, saida suka kai farfajiyar ta saki hannun shi tana kallon fuskar shi a sanyaye tace "Sa'ad ka gane wani abu, yarinyar nan marainiya ce bata da kowa sai Allah sai kuma mu, kai ka kawo ta gidan nan da sunan taimako, mahaifiyarka ba ta karɓe ta saboda sanin halin ka, dan mahaifin ka bamu samu matsala da shi ba game da ita, ya kake gani idan nayi sake har sheɗan ya shiga tsakanin ku? Ba zan ji daɗi ba kuma ya rayuwar yarinyar za ta kasance?" Bai taɓa jin nadaman neman mata da yake yi ba sai yau, dan kuwa ganin hakan yake ba matsayin maganin matsalar shi dan kar ya halaka, ruwa ne suka cika idanun shi taf yana duban Hajian da ita ma ke kallon shi yace" Hajia... Ta ya? Ta ya zan iya aikata wannan aikin da yarinyar da ba ta fi tsarar Leila ba? Hajia ko auren ta nayi a wannan shekarun nata ni mai kawar da kaine daga gareta har sai ta zama cikakkiyar mace, amma a haka...yarinyar da ke kirana da *Abbu*? Hajia kallon fa uba take min, ta ya to zan yarda sheɗan yayi galaba a kaina game da lamarin ta? Bayan kuma ita ɗin *ƴata ce*." Hajia ma saida ta ji ƙwlla a idanun ta, dan haka ta sa hannu ta ta share tana jan majina tace" Shikenan Sa'ad, na yarda da kai ɗari bisa ɗari, kuje Allah ya tsare." Har ta juya za ta koma ya riƙo hannun ta ta juyo, cikin kallon idanun ta yace" Na miki alƙawarin sanar dake komai Kaka idan muka dawo daga asibitin, in sha Allah, kuma Hajia zan sanar da ke ne saboda ban da abokiyar hira a gidan nan bayan ke, kuma bana so ki yi hushi da ni ko kema ki aje ni gefe, dan Allah kakata?" Zuba mishi idanu tayi tana kallo tace" Sa'ad, ba dai wani mummunan abu bane ko?" Girgiza kai yayi yace" Zan sanar dake Kakata, kar kiyi hushi dani." Jinjina kai tayi tace" Shikenan Sa'ad, ba zanyi hushi ba." Murmushi yayi ya saki hannun ta, juyawa tayi tana cewa" Bari na turo maka ita." Yana kallo ta shiga falon, sai dai labulen daya rufe ɗakin ya sa bai iya ganin komai sai fitowar Aisha tana ƙara gyara gyalenta a saman kai, juyawa yayi ya nufi inda motar shi take dan ya san za ta ƙaraso. Yana buɗe ƙofar mota zai shiga muryar Alhajin Ibrahim ta daki kunnuwan shi wanda ya jima da shogowa gidan wata muhimmiyar waya ta tsayar da shi nan yana faɗin "Ina wuni Baba *Usmanu*?" Dakatawa Sa'ad yayi ba dan yasan da shi ake ba, amma da yaga mahaifin sa ne ke tahowa kuma tabbas shi yake nufi sai ya fahimci wai Gatse ne yake mi shi? Gani yake ya gan shi ƙyale shi ne yayi? Duba da Aisha dake tahowa kuma baya so ta san komai dake faruwa a gidan nan har sanda zai sa a mata aiki a rabata da cutar da ke cikin ta sai ya tausasa murya har ma da kanshi a ladabce yace "Ina wuni Ibu?" Alhajin dake tahowa da yanayin ɓacin rai saida ya zo kusa da shi sannan yace "Sa'ad, yanzu dan rainin wayo ni ina gidan nan amma ka ganni ba za ka iya gaishe da ni ba? Saboda kawai ka nuna ni banza ne a wurin ka?" Ɗan waigawa yayi kaɗan ya ga Aisha na tahowa ƙiris ya rage ta ƙaraso, da sauri ya kalle shi yace "Ku yi haƙuri, ban kula da mutum a wurin bane." Kamar mai neman shi da faɗa sai kuwa ya ɗaga murya yace "Ƙarya kake, ban san ka bane da zaka gaya min haka? Zan iya yin tafiya na kwashe watanni bana garin nan, faɗa min rana ɗaya da idan na zo kake shiga sahun masu zuwa gaishe ni." Ƙyaƙyabta idanu yayi alamar ba komai ɗin nan sannan ya sake cewa "Ka yi haƙuri, zan kiyaye." Aisha da ta ƙaraso da ladabi da kuma fara'a duba da duk gidan bayan Hajia da Leila shine mutum na uku dake sakar mata fuska, cikin taushin murya tace "Ina wuni Papi, sannu da dawowa?" Kallon ta yayi yana murmushi sosai cikin kulawa yace "Yawwa Aisha, kina lafiya?" Da rusunawa ta amsa da "Lafiya lau." Da kulawa ya sake cewa "Ina na za ki je na ganki da lulluɓi haka?" Cike da kunya ta ɗan kalli Sa'ad da ya shiga mota yana ƙoƙarin rufe ƙofar tace "Abbu ne ya ce na raka shi asibiti." Take ya haɗe walwalar dake fuskar shi saboda jin wani bahagon zance, ganin Aisha ta zagaya ta buɗe mota yasa shi saurin buɗe ƙofar da Sa'ad yake, a zafafe ya damƙo hannun shi ya fito da shi daga cikin motar yana kallon shi yace" Wace asibiti za ku je? Wa ye ba lafiya? Me kake shirin aikatawa?" Hawa masa kai yake! Hassala shi fa yake! Ƙoƙarin kai shi bango fa yake? Duk a kan me? A kan me ne? Da fari fizge hannun shi yayi yana mishi wani kallo tare da faɗin" Dukan mu ne ba lafiya, shikenan?" Cikin ɓacin rai ya sake kama murfin zai shiga Alhaji ya jawo wuyan rigar sa ya dawo da shi baya yana cewa" Kai dakata bana son ƙananan iskanci, me za ka je ka yi wa ƴar mutane? Ka san da tana zaune gidan nan ne dan kace bata da kowa." Cikin wani irin tafasar zuci da ɓacin rai Sa'ad ya sake fizge wuyan rigar sa yana faɗin" Sai me to? Zan fita da ita Ibu kuma zan yi abinda na ga dama da ita, kana da matsala da hakan ne? Haba! Haba! Ya kake so da ni ne?" Girgiza kai Alhajin yayi yana taɓe baki a sanyaye yace" Idan ka yi haka kuwa ka cika cikakken marar martaba mata, dubeta fa yarinyar?" Irin kallon nan na raini da murmushi a fuskar Sa'ad ya dinga yi yana kallon Alhajin da saida ya ji ya tsargu ya kuma yi dana sanin faɗin wannan maganar, hakan yasa shi kawar da kai irin yana so a basar ɗin nan, Sa'ad kuma ba tare da tsoro ko shakka ba yace "Ibu, kai ne za ka wa wani magana akan sanin martabar mace?" Sai kuma ya sake yin murmushi har da sauti yana girgiza kai, maida ƙofar motar yayi ya rufe ya sake matsawa daf da shi yace "Idan ma haka nake, to ina ga ai sawun baya nake takawa, kasan kuma an ce Barewa ba zata yi gudu ba ɗan ta yayi rarrafe, kar ka manta Ibu a gaban idanu na kake ɗauke fuskar mahaifiyata da tafin da har jini ke ɓalle mata a hanci, Ibu, da wayona casss ka sakar min uwata saki ɗaya saboda kawai budurwar ka ta kira ka ita kuma ta ɗauka har sukayi cacar baki, Ibu, ka daina taƙala dan bana so ina tuna abubuwan da suka gabata wanda ni da kai duk hakan baya mana daɗi." Da ƙarfi ya jawo murfin motar ya buɗe ya shiga ya bar shi nan tsaye yana kallon shi, har suka fita daga gidan bai gusa ba sai da ya gaji da tsayawa da Takaicin baya da irin abubuwan da ya aikata. *Suna* ɗaukar hanya ta ɗan saci kallon shi ganin sai huci yake yana dantse leɓe alamar ɓacin rai ƙarara, gabanta ta kalla cikin son mantar da shi abinda ya ɓata masa rai tace "Abbu, ni kuwa yaushe za ka yi aure ne? Na ga burin Hajia kenan." Ɓacin ran da yake ciki ba zai bar shi ya ƙyaleta ba, dan haka a tafashe ya amsa mata da "Ki min, tunda kin gaji da yawon da nake a gaban ki." Cike da shashantar da abun tace "Lahhh! Abbu, ni fa ba haka nake nufi ba." Da yanayi irin na mata ya koyi muryar ta cikin masifa yace "Lahhhh! Abbu..." Sai kuma ya koma muryar shi ta maza yace "Kika sake kirana Abbu sai na taka wuyan ki, tunda ke ba kya fahimtar yaren bakina." Ya sauke maganar yana ta ci gaba da huci kamar wanda ya haɗiyi kububuwa, a raunane Aisha ta jinjina kai cikin shagwaɓa tace "Allah ya baka haƙuri, amma Abb..." Birkin da ya taka saboda Abbun da ta sake faɗa ya sa ta dakatawa, kafin ta ankara kuma ya ɗago hannun shi ya nufi fuskar ta da niyyar gaura mata marin da zata gane me yake nufi, to amma rashin sabo da kuma yadda Aisha ta tsorata tayi wuffff! Da hannun da ya ɗaga ta rintse idanu har da ƙwala ƙara sai ya tsaya kamar wata Mage mai bacci yana kallon ta, ganin ta ƙi sakin jikin ta haka ma bata buɗe idanu ba yasa shi furta "Sake min hannu?" A hankali ta saki hannun ta manne a jikin ƙofar motar tana satar kallon shi, saida ta ji ya tayar da motar sun ci gaba da tafiya sannan ta saki jikin ta, ba ta ƙara cewa komai ba dan gaskiya ba ta son duka, sam ba ta son haɗa hanya da duka, ta ga kuma a yadda yake din nan yau so yake ƙarfi da ya ji sai ya taɓa mata lafiyar jikin ta. *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *15* Kai tsaye ya ga likitan da dama da shi suka shirya ana kawo Aisha shi zai mata aiki, yanzu haka suna zaune yana kallon Aisha har ya zauna kan kujerar shi yana cire safar hannun shi tare da cewa "Ya sunan ki?" Tana sunkuyarda kanta da tunanin me yasa yake ta kallon ta sannan baya duba Abbu Sa'ad ta bashi amsa a tausashe da "Nana Aisha." Ba tare da ya ɗauke idanun shi daga kanta ba yace "A'isha, shin kina jin wani abu a jikin ki haka?" Kallon shi tayi da mamaki a fuskar ta na me ya haɗata da wannan tambayar kuma? Sa'ad ta ƙalla da kujerar shi ke fuskantar ta ta kujerar, ya jingina a kujerar nan ya rufe bakin shi da yatsun shi uku kawai ya zubawa fuskar ta idanu yana kallo, turo baki tayi ta bishi da kallo _"Ya haka kuma Abbu?"_ A sanyaye sosai ba tare da ya ɗauke hannayen shi ba yace" Ki bashi amsa, kar ki ɓata min lokaci." A shagwaɓe ta kalle shi cikin sassauta murya tace" Abbu, me yasa sai kayi ta yi min faɗa? Ni ai ba ni ka ce za ka kawo asibiti ba ko?" Ƙura mata idanu yayi kawai yana kallo dan yanzu bai shirya yin magana ba, dan haka kallon gargaɗi kawai yake bin ta da shi, da irin jin haushin nan ta kalli likitan tace" Ba na jin komai." Murmushi likitan yayi ya kalli Sa'ad da yanayin zolaya yace" Boss, da alama ka samu wacce za ta iya tafiya da kai." Lumshe ido yayi ba tare da ya motsa daga yada yake ba yace" Bar shashanci, kayi aikin ka." Maida hankalin shi yayi ga Aisha yace" Aisha, ki nutsu ki amsa tambaya ta, shin ba kya jin wani abu da ya shafi haka ciwon ciki? Ciwon mara? Kasala? Ko ciwon kai haka?" Shiru tayi tana tunanin abubuwan da ya faɗa, to ita za ta iya cewa wataƙila aikin da azzaluman nan suka mata ne, dan haka ta ɗaga kai ta kalle shi tace" Gaskiya dai...watana da ya zo ne nayi ciwon ciki sosai." Daga likitan har Sa'ad sun fahimci me take nufi, wanda Sa'ad ya ji gabanshi ya faɗi ba gaira ba dalili, ɗaya ɓangaren kuma ya ji daɗin amsar da t bayar har ya ji ya martaba shekarun ta da suka bata damar hangen nesa, kallon ta likitan yayi da kulawa yace "Kuma ba kya jin haka a ɗabi'a?" Kanta a ƙasa cike da kunya ta girgiza kai tace "Gaskiya bana yi ko kaɗan." Ta ƙasan idanu Sa'ad ya kalle ta, da wasa wasa sai zuciyar sa ke raya masa anya kuwa? Anya kuwa anyi *jarababbiya* a wurin nan? Yayin da likitan kuma yace "Bayan haka kuma bai sake miki ciwo ba?" Girgiza kai tayi alamar a'a, dan haka ya kalli Sa'ad yana wasa da hannayen shi yace "Boss, ina ga nan da k..." Aisha da ta taɓe baki jin yana kiran shi da sunan ƴan daba ne tayi saurin cewa "Na tuna, ranar ma ya min ciwo har Mamie ta bani magani, sannan kuma..." Ta faɗa tana dafe cikin ta tace "Anan inda aka min ɗinki, yana ɗan yi min Ƙaiƙayi wurin wasu lokuta." Da son ɗauke hankalin ta daga wannan aiki da kuma son tabbatar mata ba shi da masaniya akan komai Sa'ad yace "Ɗinki?" Jinjina kai tayi har da ɗan ɗaga mishi gira tace "E, wani likita ne da ban san shi ba ya farke min cikina, kuma ban mishi komai ba." Miƙewa likitan yayi yana ɗaukar wata sabuwar safar hannu tare da cewa "Zo kwanta nan in duba ki in gani?" Jiki a sanyaye t miƙe tana kallon Sa'ad ɗin, yanayin shi ya ji yana so ya canza, kamar tashin hankali yake ji na son ziyartar shi, kamar wani abu yake ji mai kama da tsoro ne ko haushi? Shi bai ma sani ba, amma dai a gajerar kalma zai iya cewa *bai ji daɗi ba da likitan nan zai duba cikin ta*, hakan yasa har ya ji kamar yana ɗan jin haushin komai na likitan haka da ma likitan kan shi. Ba su fi minti uku ba ya dawo ya zauna kujerar shi haka ma Aisha, kallon shi yayi yace "Boss, ina ga a gaggauta yi mata aikin nan dan lafiyar ta kar ta fara salwanta." Kallon shi yayi a wani daƙile yace "Yaushe kake gani to?" Cikin nutsuwa yace "Ka fara kawo ta gobe da sassafe zan sa a mata hoto da kuma eco dan na ga mazaunin abinda yake cikin ta, idan ya so sai mu saka lokacin aikin, sai dai ba zai wuce gobe ko jibi ba." Cike da gamsuwa ya jinjina kai tare da Miƙewa yace "Shikenan, Allah ya kai mu goben." Miƙewa tayi suka tafi, kai tsaye kuma bai zame ko ina da ita ba sai gida, sai dai gaggawa ta sa bai zauna ya ce ma Hajia komai ba, sai dai ya sake mata alƙawarin gobe zai gaya mata idan sakamakon Aisha ya fito na aune-aunen da likitan ya ce zai mata. *Washe Gari* Bayan fitowar sakamakon likitan ya tabbatar masa da za'a mata aiki, tsoron abinda zai iya faruwa yasa shi faɗa ma Hajia Kaka cewa "Hajiata, jiya da muka je asibiti yarinyar nan nasa aka duba, ashe tana da ɗinki a cikin ta wanda aka mata bayan an mata wata tiyata, abinda binciken likitan ya ce shine, akwai wani ciwo ne a cikin ta da yake ɗan sakata ciwon ciki, da na tambaye ta kuma ta ce wata asibiti ce da aka satosu ita da wata aka kawo su nan, tana kallo aka kashe ɗayar ita kuma aka barta a raye, ɗazu ma da safe da muka tafi asibiti radio aka mata, kuma likitan yace dole anjima a mata aiki dan kar abu yayi girman da ba zai taɓu ba." Daidai dire maganar shi Aisha ta fito daga ɗakin Hajia kakan riƙe da carbinta da ta ce ta ɗauko mata, da kallo ta bi Aishan har ta zo tana miƙo mata carbin, karɓa ta yi tare da kamo hannun Aisha ta zaunar da ita kan ƙafafun ta cike da tausayawa tace" Aishatu na, ashe baki da lafiya baki taɓa gaya min ba?" Sunkuyar da kai Aisha tayi ba tace komai ba, hakan yasa Hajia Kaka ɗaga rigar atamfar Aisha daga ƙasa tana cewa" In gani?" Ɗan ƙara ɗagawa tayi dan Hajia kakar ta gani da kyau, sai dai ba ita Kaka kawai ta gani ba har da Sa'ad da ya zuba musu idanu yana kallo, amma ganin cibiyar ta irin mai tsinin nan kuma bata da girma sosai sai ya ji kamar bai dace ya kalli al'aurar ta ba, hakan yasa ya shiga sissine kai shi kaɗai kamar mai jin kunya haɗa ido da siriki, da ƙyar ya iya ganin shatin ɗinkin irin na tsayen nan ne tun daga ƙasan cibiyar ta da kaɗan har bai iya hango inda ya tsaya ba, hakan kuma bai rasa nasaba da siket din dake jikin ta. Kallon shi Hajia tayi tace "Sa'ad, wane lokaci to za'a koma asibitin?" A sanyaye ba tare da ya kalle su ba yace "Ya ce da ƙarfe 05 mu isa, zuwa 06:00 zai mata aikin." Jinjina kai Hajia tayi tace "Shikenan to, zan tafi tare da ku sai na ci gaba da kulawa da ita, amma kuma Sa'ad tunda wannan ɗinkin bai jima ba, kana ganin ba matsala a sake fasata da gaggawa haka?" Girgiza mata kai yayi yace "Ya ce ba matsala, kamar ayi aiki ne a samu matsala, ana gaggauta gyara matsalar ko da kuwa sai an sake fasa mutum." Jinjina kai tayi tace "Allah ya sa ayi à sa'a." Ta faɗa tana jawo kan Aisha ta rumgume a ƙirjin ta, miƙewa Sa'ad yayi ya bar musu ɗakin, inda Hajia kuma ta ɗaga Aisha tace "Miƙo min wayata a can kan teburi na kira tela na gaya mishi zan tafi tare da ke asibiti nayi jinyarki har a sallame mu." Da sauri Aisha ta miƙe ta je ta kawo mata wayar, bayan ta kira Alhajin ta gay mishi sai da ya ji ba daɗi na zargin da ya ma Sa'ad kan tunanin zai fita da Aisha ne kawai dan ya mata wani abun, amma yanzu da ya ji haka sai ya gano Dalilin fitar shi da ita asibiti jiya kenan, da tabbaci ya ce ma Hajiar zai je asibitin bayan an mata aikin ya duba ta, daga haka sukayi sallama. *An mata* aiki cikin nasara kuma an ciro wannan bala'i da aka zuba mata a ciki kalar ledar har ta canja kala, duk da ɗaya robar ta bashi wahala wajen cirewa, tayi nesa da inda aka ajiye ta sannan ta yi taushi sosai saboda mugun zafin ciki, hakan ya sa da ya taɓa sai ta huje da ƙyar da dubara ya ciro ta ya sake mata wani sabon ɗinki cike da ƙwarewa irin ɗinkin nan na ciki wanda idan ya warke ba lallai ka gane mutum na da aiki a cikin shi ba. Gado a ka bata a sashe na musamman na kuɗi, inda Hajia Kaka kuma ta zauna da ita na kwana uku a asibitin har aka sallama ta suka koma gida. *Bayan Kwana Biyu* Ya so yin sallama, amma tsinkayar Aisha da yayi tana ƙoƙarin duƙowa daga tsaye ta ɗauki jug ɗin ruwa bai san Dalilin jin jikin shi na tsuma ba kawai ya taho a sukwane yana faɗin "Dakata malama..." Yana ƙarasowa ya duƙa ya ɗauka sannan ya miƙa mata yana kallon yadda take ta tattare zane dan yanzu dole take anfani da su, cikin yanayin masifa yace "Ba ki da hankali ne, ruwan ne ba zaki jira a zo a baki ba? Baki san an hana ki motsa jikin ba bane da har kike shirin duƙawa ?" A marairaice Aisha dake sanye da t-shirt fara ta tattare ta har ƙrjin ta, sai zanen da gaba ɗayan shi yae hannun ta tana ta riƙo saboda baya ɗauruwa sosai a ƙasan mara. Kafin ta ce wani abu Sa'ad da duk yake jin ya damu da lafiyar ta ya kama hannun ta na dama, hakan yasa ta kalli hannun nashi sannan ta ɗaga idanun ta da suka ƙara shanyewa sakamakon har yanzu ɗan kumburin da tayi bai gama sacewa duka ba ta kalle shi, shi ma kallon ta yayi sai kawai ya basar ta hanyar juya mata kai ya shiga jan ta a hankali tana takawa yana cewa "Ki dinga kula da lafiyar ki mana." Saida suka zo kan kujerar ya kamata ta zauna da kyau sannan ta kalle shi cike da jin daɗin irin kulawar da yake bata tun da aka mata aikin nan tace "Nagode Abbu." Ba tare da ya kula ta ba ya kalli ƙofar ɗakin Hajia Kaka yace "Ina Hajia?" Saida ta fara buɗe jug ɗin ruwan tace "Tana ɗakina, kayan wanki da suka taru take cirowa." Jinjina kai yayi har idanun shi suka sauka kan ƙafafun ta da suka fi komai kumburi, a hankali ya durƙusa gaban ƙafafun nata har ya sa yatsa ya latsasu, sai kuma ya kalli fuskar ta yace "Me yasa ba su daina kumburin nan ba?" Girgiza kai tayi tana ƙara gyara zanen ta gudun kar ta sakar masa wani abu tace "Ban sani ba nima." Ɗan gyara tsugunnon shi yayi yana lalubo waya daga aljihu yace "Bari in kira likitan nan in faɗa masa, *bana son ganin haka* gaskiya." A tausashe sosai Aisha tayi saurin cewa "Abbu, ba sai ka kira shi ba, zan warke fa, haka nayi waccen ma." Zubawa idanun ta nashi idanun yayi, dolen shi ne fa ya kula da ita har ya ga ta koma garas yadda take, shine silar wannan halin da take ciki, shine musababbi, ba dan shi ba wataƙila tana ƙasar su tana karatun ta, dan haka yake ɗaukar komai nata da matuƙar mahimmanci, yake kuma *jin ta sosai a zuciyar shi*, shirin shi a kan ta shine ta samu lafiya sosai ya tabbatar ba wata matsala, sai ya ɗauketa da kan shi ya kai ta garin su wajen iyayen da aka ce mishi sune nata. Kafin ya ce wani abu Hajia Kaka ta fito da irin kwandon nan na zuba kayan datti a ciki tana ƙwala kiran "Kai Inusa, kana ina?" Da ƙarfi almajirin ya amsa da "Na'am Hajia." Tana tahowa tace mi shi "Zo ga kayan." Wanda aka kira da Inusa ne ya shigo da sallama, lokacin da Sa'ad ya miƙe tsaye yana kallon Hajiar yace "Hajia, wanki za'a miki ne da safiyar nan?" Tana kallon shi ita ma tace "Wanki za'a min Sa'ad, tun jiya na sa aka kira shi na gaya mishi, shiyasa na ce ya zo da sassafe dan kayan da ɗan yawa tunda har da na Aisha." Da wani irin mamaki a fuskar shi yake kallon Hajiar ya maimaita kalmar "Aisha?" Kallon shi tayi sa'ilin da take miƙawa Inusa kayan ya amsa ya nufi hanyar fita tace "E, tunda Kaga ba lafiya gare ta ba da zata yi wankin, ni kuma dama ba iyawa nake yi ba yi min ake." Juyawa ya fara yi ya kalli Inusan dake daf da fita, à tsanake ya juyo ya sake duban Hajia Kaka cikin wata irin murya kamar wanda zai faɗi abun arziƙi yace "Hajia, kuma saboda Allah waccen ganɗamemen ne zai wanke kayan wannan yarinyar?" Haɓa Hajia ta riƙe tana faɗin "Laha'ilaha illallahu ! Sa'ad, yo Inusa bargo ma ɗan Libiya ba yana wankewa ba bare kayan ita ƴar taka? Me ye a kayan nata da ba zai iya wankewa ba?" Ƙura mata idanu yayi sai kuwa ya fara wani marmarmar ɗin da ido dake nuna mata ran shi ya fara ɓaci cikin saurin magana yace" Ba wannan nake magana ba Hajia, ta ya waccen balagaggen zai wanke kayan budurwa, zai ga surarta, zai ga komai nata har ma ya ji ƙamshin tufafin ta, to ni gaskiya bana so, wanki ne tunda ke ba zaki iya ba ni zan muku wankin..." Ya faɗa yana juyawa tare da faɗin" Kai, bani kayan nan?" Da mamaki Hajia ta kalli Aisha da ita ko a jikin ta tana dai kallon su ne, sai kuma ta bi bayan shi da sauri tana faɗin" Sa'ad, da gaske kake? Har da kayan nawa? Ko iya nata kawai?" Duk da ya fita saida ya dakata ya juyo ya kalle ta, to me take nufi da na Aisha kaɗai? Ko har da nata? Idan ya ce ban da nata yayi abun kunya gaskiya, to wai ma ku dakata? Me ya faɗawa Hajia a ɗaki ne...? Sala-sala ya shiga tariyo abinda ya faɗa, sai kuwa ya tuna tsaf, amma sai yake mamaki da tambayar kanshi anya shi yayi maganar nan? Kai aiki ne dai irin na iblis la'ananne kawai, dn haka ya basar dan yasan Hajia ma ai ta gane komai, fuskar ta ya kalla yace "Harda nakin." Murmurshin farin ciki Hajia ta saki ta kalli Inusa da ya aje kayan gabanshi tace "Tafiyar ka kaji Inusa, dama rashin mai min wankin yasa nake kiran ka, yau kuma kaga zan ci albarkacin ƴar rainona Sa'ad ya min wanki." Bakin Hajiar ya bi da kallo da tayi maganar, sai ya ji ya tsargu da abinda ta faɗa har ma kamar ya ce ya fasa, amma kuma ai hakan ba girman shi bane, musamman ma da yake a gaban yaron nan da yarinyar can... To a ida gizo yake saƙar shine, shin zai iya wankin kaya masu yawa haka? Gaskiya ya jima rabon da yayi wanki, hatta fa ɗan kamfanshi cikin kayan wanki yake tattarawa ya haɗa, dan haka shi bayan bakin shi da jikin shi ba abinda yake wankewa. *An ɗebo ruwa kenan*? Ai ko dai maza an ɗebo ruwa, anyi wanki amma a wahalce, ba dan rashin iyawa ba sai dan jimawa ba'a haɗu ba, sai dai daga wannan wankin ya koyi wasu darusa a rayuwar shi, na farko shine _yana da kyau bawa ya dinga hangen gaba da kuma baya yana yin abun da ko da kuwa ya fi ƙarfin yin shi_, na biyu kuma shine _zai dinga ƙoƙartawa ko da a wata uku ne yana ma Hajia Kaka wanki_, dan farin cikin da ya gani a fuskar ta ba kaɗan bane dan kawai yana mata wankin nan, na uku kuma shine _wahala bata da daɗi ko ya take kuwa_, sai darasi na ƙarshe da ya kasa tantance me zai auna a kan shi shine _me yasa ya ma yarinyar nan wanki_? Rashin sanin wannan amsar yasa har ya gama wankin ya shirya jiki a sanyaye ya fita yana son gano wannan amsar, me yasa ya yi? Me yasa ya damu har ya dinga faɗa dan wani zai mata? Me ye na ɓacin ran wai? Amsar da ya samu har ta saka shi sauke ajiyar zuciyar dake nuna ya samu nutsuwa ya kuma gamsu da amsar ita ce *saboda kai ne silar zuwan ta nan*. Kula mai suna kulawa Sa'ad yake ba wa Aisha a wajen jinya, duk da ƙaracin shekarun ta da rashin saka abu a kai saida ta fara jin wani sabon yanayin da yake sakata tunani barkatai, musamman ma canjin da ta fara gani a tare da ita, wato yanzu idan suna tare sai ta fiya jin kunya da nauyin zance saɓanin can da take kiran shi Abbu kan ta tsaye take aikata abu, amma yanzu ko ido bata son ɗagawa ta kalle shi saida dalili, magana kuma ta ke mata wuya sai dai ta furta um! Ko um um ko a'a ko ma ta girgiza kai a wasu lokuta. D sannu sai shaƙuwa ta shiga tsakanin su wanda shi kan shi gogan bai ankare da haka ba sai daga baya, yadda da yake kwanaki bai leƙo gidan ba, yanzu ko wani abu ya ɗaui hankalin shi haa zai dawo gidan ya kwana saboda wani abu da yake ji mai kama da kana da wani muhimmin abu a wurin kuma dole ka na son kasancewa tare da shi, sannu sannu shi ma sai ya zama mai tausasawa à gare ta ba tare da Sanin shi ba, sai ya zama mai kunyar aikata wasu abubuwa a gaban ta, sannan mai jin fargaban aikata wani lamari idan tana usan shi. Babban wani abun duba shine, yadda ya j sam baya so ma yana tuna cewa shi ɗin ya san *ahalinta*, gani yake idan ya sadata da su zata mishi nisa kenan, duba da yasan wannan ahalin wanda ko ƙafar su mahaifin shi bai kama wajen dukiya, dan haka har yanzu ya ƙi saka ranar da zai kai ta ga Ahalin ta, bai ma faɗa ma kowa ya sani ba, sai dai kuma ya manta da wani abu, wannan abun kuma shine Hambali da DG da *suke neman ta*, gashi kuma yanzu sukan yawan fita ita da Leila wata rana ma da sauran yaran, Hajia kuma dama ita ce abokiyar yawonta. *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *16* Duk da babban falon su guda ne, amma dake kowace tana da nata falon kuma b yara gare u ba yasa ba mai zama yayi wani abu a falon, dan haka kai tsaye ta shigo da shi ta wannan ƙofar da tunanin ba wanda zasu haɗe da shi. Sai dai Kashhh! Sai da suka gama shigowa cikin nishaɗi Abida na faɗin "Amma dai wayar ka ta mutu ko?" Girgiza kai wani matashin yaro yayi da bai wuce shekara ashirin da biyu zuwa da uku ba yace "A'a aunty, me kika gani?" Taɓe baki tayi tace "To ai naga ina ta kiran ka ne bata shiga, da fa ban sa a tarbeka ba?" Murmushi yayi yace "Ba zan gagara gane kwatancen da su Hajia suka min ba ai." Murmushi ita ma tayi tana nufa hanyar ɗakin ta tace "Da wannan kuma, tunda gidan ba ɓoy..." Cak ta tsaya tare da yin shiru sakamakon ido huɗun da sukayi da Fa'iza zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya tana ta aikin latsar waya, da fari Abida tsoro ta ji dan bta saba ganin wani zaune a falon ba, ko baƙi sukayi kana kai shi falon ka ne amma ba wannan falon ba, kai idan fa sun zauna nan to tare da mijin su ne idan ya buƙaci su yi karin kumallo tare, bayan haka kowace na sashen ta dan babu wacce ke sauke girman kai ta je ma ƴar uwar ta. Da ta gaa fahimtar wacece wurin sai ta sauke ajiyar zuciya ta ɗanyi murmushi yaƙe tace "Sannu aunty, anan kuma ake zaune yau?" Cike da jin haushin Abida da tsanar ya Fa'iza ta wanka mata wani kallo wanda ƙarara na harara ce da kuma zallar tsana a ciki a daƙile ta bata amsa da "Ummmm!" Ganin wannan kallo da Abida tayi yasa ta haɗe ta ta fuskar ita ma ta mata wani kallo na ɗaga gira tamkaro muguwa tana kallon fuskar ta tace "Uhmmm! Allah yasa dai *barewa* ba tana shirin shiga sabgar da babu ruwan ta bane, dan *damisa* bata da sani bare sabo..." Sai kuma ta shiga mata kallon sama da ƙasa a wulaƙance tace "Bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane, tsalle ɗaya zaki yi ki faɗa rijiya, dubu sau dubu kuma ba zai fito dake ba, dan *ni ce zan gina rijiyar*, ni kuma komai nawa da lissafi nake yin shi, saɓanin..." Wani masifaffen murmushi ta sakar mata kamar wacce ta mata albishir da aljanna sannan ta ɗora da" Saɓanin ke auntyna da kike gayyato idanun kowa a kan ki." Cike da takaici Fa'iza dake zaune ta Taɓe bki tace" Ai ko da goma ta lalace ta fi biyar albarka, wanda ya rigaka kwana kuma dole ya rigaka tashi, ki sani *wata kokawar* ba sai kai abokin karawar ka ƙasa bane ya zama kayi nasara, ni kuma na fi ƙarfin taka sawuna bayan naki sawun, hakan yasa nake buga *lissafina a cikin taki ƙwaƙwalwar*, ki kiyaye, dan da alama baki taɓa gani ko a documantary ba cewa barewa na iya daka tsallen ya son ranta a gaban *zaki* ma kuma ta kuɓuta, bare kuwa wata halitta wai *damisa* da ba'a halicceta da jinin *halacci* ba." Cike da wani irin makirci Abida tayi murmushi tace" Shikenan, zan ga ta inda lissafin ki zai ci na wa lissafi, duba da shekaru nayi ina buga nawa équations ɗin, dan kawai naga na gagari tunanin mai tunani." Ba tare da ta motsa daga inda take ba ta saki murmushi ita ma tace" Kin manta da ko jami'in sirrin sirrintaka yana kwaɓar da alamar da za'a iya gane shine, bare kuma ke da bana jin kin fita daga ajin da ni na jima da wucewa? Ba komai, muje a haka dan ina so naga mamaki a fuskar ki, amma ki sani sirrin da kika binne shekaru sha bakwai da suka wuce, *ni nan* zan sake busa masa rai sannan na tono shi kowa ya gani." Gaban ta ya faɗi sosai, kuma ta ji jinin jikin ta ya tsinke, amma saboda kar ta nuna mata wata alama da zata bata ƙofar zargin ta sai kawai tayi dariya ta ɗan taka gaba kaɗan tana faɗin" Zan gani, zan kasance cikin jiran ganin haka ta faru, ko ba komai nasan zan yi dariyar ganin rashin nasarar ki." Idanu Fa'iza ta zuba mata ta bi ƙeyar ta da kallo tana murmushi tace" Za ki gani kuwa... *ABIDA HAMBALI YA'U*." Juyowa Abida tayi da murmushin izgilanci tare da" Alhamdulillah, nawa mahaifin shahararre ne har a ƙasar waje ma." Gyara zama kaɗan Fa'iza tayi da murmushi tace" Hakane kam, tunda shine mammallakin asibitin HY...haka ma gidan marayun HY, gidajen da ba kowa ya san sirrin dake danƙare a ƙarƙashin fondation ɗin ginin ba, sai waɗanda suka kasance maƙura a kusanci da shi gyatumin." Fa'iza bata fahimci Abida ta shiga halin rudu da ɗimuwa bane? Ko ta fahimta tana so ta sake samun wasu makamai ne a hannun ta na ci gaba da yaƙar Abidar? Ba dan haka ba irin ƙwalalo idanun da Abida tayi, sannan fuskar ta ta rikiɗe har jikin ta ya ɗauki wani ɓari ɓari ko wanda bai san komai ba zai gane akwai matsala... Ta ya tasan asibitin da gidan marayun duk na mahaifin ta? Ta ya kuma tasan akwai wasu sirrika a wannan gidajen? Ita kanta bata san su ba sai ƴan tsirarun shekarun da suka gabata da basu fi biyu zuwa uku ba, shi ma ta sani ne lokacin da Maman ta ta dage sai mahaifin su ya sake ta, da suka sakata gaba da tambaya ne take faɗawa ita Abidar dake mace cewa ga abinda ta gano yana aikatawa a can inda ya fi zama, shiyasa take so ta rabu da shi dan ba zata iya zama da azzalumi ba. Cike da shaƙiyanci Fa'iza ta miƙe ta kalli matashin nan da sam babu haɗi ta fuska ko fata tsakanin shi da Abida, dan da alama yaron ɗan buzaye ne na gaske, fatar shi jajir take kamar karas, cike da son ƙular da ita tace "Wannan shi kuma ƙanin ki ne? Amma dai uba ne uwa ce ɗaya ko? Ko da yake..." Sai kawai ta nufi hanyar nata falon tana faɗin "Akwai ƴan uwa na nesa, ba lallai shi wannan na kusa bane." Suna kallo ta ɓacewa ganin su ba wanda ya iya dakatar da ita, dan ko matashin nan da bai san komai ba akan abinda suka tattauna, sai da ya ji a ran shi lallai akwai ƴar tsama tsakanin matan nan ba kaɗan ba, kuma a yadda ya fahimta kamar waccen matar ta fi Abida salo da iya tako, dan kuwa Abida ko ba komai ai ita ta fara mata magana, gashi yanzu ta sossoka mata magana son ranta ta bar su tsaye. Fuuuuuu! Abida ta wuce nata falon tana kai da kawo da zazzaro idanu na mamakin ya aka yi Fa'iza ta san batu akan asibitin da kuma gidan marayun? Ya aka yi haka? Hakan na nufin kenan ta san komai ɗin da take shiryawa? Hakan na nufin Fa'iza za ta iya nasara a kan ta kenan? Kai... Kai! Ba zai yiwu ba gaskiya, da ƙarfin gaske ta daki teburin gaban ta har da faɗin "Wallahi ba zai yiwu ba, ba zan bari ta tona min asiri baaaaaa!" Yadda ta ƙarashe maganar da ɗaga murya yasa matashin tsorata, sai yake ganin kamar wannan ɓacin ran nata ba zai bar shi yayi abinda ya kawo shi gidan ba, shi kuma a kowace safiya mafarkin future rayuwar shi yake, addu'a yake burisu shi da ita ya cika, ita ta samu abinda take so shi ma ya samu nashi abinda yake da buƙatar. Gudun kar ya koma ba tare da komai ya wakana ba ya sa matashin nan cike da shaƙiyanci da fitsara ba tare da duba shekarun Abida sun ruɓanya nashi ba, ko da yake ita ta ja ma kanta, hasalima ita ta zaɓeshi a haka dan cikaro burin ta, kuma a haka ita ke biyan shi kafin gwagwaɓan biyan da tayi alƙawarin yi masa idan har ta samu abinda take da buƙatar. Cire da ƙwarewa da shashanci ya jawo ta jikin shi tare da ƙoƙarin dawo da kallon ta ga fuskar shi... Cikin ɓacin rai take son fizgewa har tana faɗin "Mtssss! Sake ni dan Allah, kai bak..." Sanin lagon ta ya sa matashin nan zura harshen shi cikin bakin ta idanun shi na kallon nata idanun a tsatsaye, a hankali ya riƙo hannun ta ya sauko da shi kan abinda ta sha gaya mishi tana so ya fi haka girma, cimma wannan faɗan nata kuma yasa sukayi wata basu haɗu ba sai yanzu da ya tabbatar ya samu yadda take so, dan kuwa shaye shayen duk abinda ya san zai ƙara mishi girman daraja ya dinga yi har yanzu da shi kanshi girman nata da riƙewar ta ke bashi tsoro, dan ga duk mai hankali yana ganin shi yasan ba asalin shi bane kawai dubaru ne. Jin abinda hannun ta ya taɓa sai kuwa Abida ta zaro idanu tayi saurin jaye bakin ta daga nashi ta kalli ƙasan tace "Kai ne! Da gaske kai ne *Hashim*? Wow ! Ka yi min yadda nake so wallahi, wannan ai..." Sai kuma ta durƙusa ƙasa jikin ta har rawa yake ta cire mishi zif ɗin wandon cike da jaraba ta jawo shi tana kallo har wani gwale ido take uwa ɗiyar mayya, dariya tayi tace" Wow! Kai kayan nan a haka harka ne wallahi, ka ganka kuwa? Ƙarami sai kayan ladabtar da mace." Kamar yadda suka saba haka ta ja shi zuwa ɗakin baccin ta inda mijin ta ke shiga yayi tashi wadaƙar suka dinga masha'arsu da ƙaramin ƙanin ta dan kawai ta ga ita ma ta kafa tarihi a Ahalin Ahlan, sannan ta ga tayi fintinkau wa kishiyar ta, sam ba tayi tunanin abinda zai iya biyo wa baya ba, tunanin yanzun kawai take yi. *A Gurguje* Yaya Luƙman ta fara haɗewa da shi a ƙofar gidan, da fara'a da shaƙuwa ya tarbe su yana musu sannu da zuwa, Alhaji Kabir ba tare da girman kai ko wani abu ba ya bashi hannu suka gaisa, har yana tambayar shi karatu? Da zolaya ya kai hannu zai karɓi kwanon dake hannun Ummu Kulsum ɗin yana cewa "Kawo na ɗaukar miki ƙanwata, kar Mama ta ga na bar ki da kaya ta dakeni." Murmushi Ummu tayi, yarinya ce da ke da miskilanci ba ta da hayaniya da yawon surutu, hakane ma ya sa a taƙaice kawai tace mi shi "Yaya kenan." Alhaji Kabir kuma cike da zolaya da dattako yace "Ai ko Luƙman kayi kyan kai, kaga ni ban yi wannan tunanin ba, ashe da ni za ta sa a ma dukan." Faɗaɗa murmushin ta tayi cikin shagwaɓa tace "Ni dai ka daina bana so." Shiga ciki sukayi Alhaji da Luƙman na hirar su suka shiga da sallama, Mama da Mujittafa dake cin abinci suka amsa suna musu maraba, Mujittafa kujera ya ɗauko ma Alhaji ya aje ya zauna suna gaisawa da Mama, inda Ummu ta zauna kan tabarmar da Mama ke zaune da wata yarinya gaban ta ita ma tana cin abinci da bata fi shekara uku ba, har suka gama gaisawa Ummu dake ta duban yarinyar da bata sani ba tace "Mama, wannan kuma ƴar wacece? Ban san ta ba." Da fara'a cikin sassauta murya Mama ta ƙara tura kwanon abincin gaban yarinyar tace "Jiya aka kawo min ita ta ɓata, ita kaɗai aka samu tana ta kuka, gata nan dai ina jira na ji masu cigiyar ta sai na miƙa musu ita." Murmushi Ummu tayi tana kallon Maman tace "Allah sarki Mamana, kina ɗaukar kowane yaro dake duniyar nan a naki, ba kya ƙamar ɗan kowa bare ki kasa riƙe shi fiye da yadda zaki riƙe naki." Murmushi Maman tayi ba tace komai ba, sai Mujittafa dake ta yanka lomar tuwo bakin shi yace "Ki bari kawai aunty, Mama fa ina ga har addu'a take yaro ya ɓace." Dariya suka kwashe da ita har Alhaji Kabir, sai Ummu da tayi murmushin da ya bayyanar da haƙoranta, hakan yasa Mujittafa yace "Allah kuwa, to yaro na ɓacewa za ta yi ram da shi ta fara raino." Juyawa Mama tayi ta kalle shi ta mishi daƙuwa, hakan yasa ya kalli kwanukan da Luƙman ya aje gaban Mama yace "Yaya Luƙman, ɗan miƙo min abincin gidan aunty Ummu in ji?" Cikin jin haushi Mama ta kalleshi, haka ma Luƙman da Ummu da saida ta Harare shi, cikin halin ko in kula yace "Kuyi haƙuri to, naga ai ban taɓa zwa gidan ta ba bare na ci abincin ta, kuma duk zuwan da take bana nan kuma ba'a aje min." Dariya Alhaji Kabir yayi ya ɗauki kwandon ya miƙawa Mujittafan yana cewa "Da gaskiyar ka Mujittafa, ban san da haka ba ai da na sa ta maka girkin ka na musamman." Dariya sukayi shi kuma ya amshi kwandon ya aje gaban shi sai dai bai sake taɓawa ba, dan fitsararshi ba ta kai ya buɗa kwanukan a gaban Alhaji Kabir ba, sun ci gaba da ɗan taɓa hira kafin Alhaji Kabir ɗin ya miƙe zai tafi, da sauri Ummu ta kalle shi sannan ta kalli Mama tace "Mama, ki mishi godiya fa, jiya ya kai ni naga sabon gidan da ya baku zaku koma, yanzu ma albishir ɗin n zo yi muku." Da sauri Mama ta kalle ta, Luƙman da Mujittafa kuma farin ciki ne ya baibaye su suka shiga yi mishi godiya, ganin godiyar tayi yawa kuma ya gaya ma Ummu kar ta faɗa har sai ya tafi dan barin ta kafin ya dawo ya ɗauke ta yasa ya kamo hannun Luƙman ya ce ya raka shi, da ƙyar Mama ta buɗa baki ta mishi godiya saboda kukan da ya ci ƙarfin ta. Saida suka fita Ummu ta matsa kusan Maman sosai tace "Mama, ki daina kuka mana, dama ya jima da gaya min yana nema muku gida matsakaici mai kyau, wallahi baki ga gidan ba ƙaramin mai kyau kuma duka a shafe yake da tiles, kuma Mama har da banɗaki a ɗakunan sannan ga wata a waje, gwanin sha'awa wallahi." Kallon fuskar Ummu tayi, yarinyar dai da ta tsinta a tsumma tana ta kuka, ita iya girman ta ma ya isheta alfahari, amma gashi ta fara zuwa mata da abun alkairi irin wannan, shafa fuskar Ummu tayi cikin kuka tace" Allah ya miki albarka." Da fara'a ta amsa da" Ameen Mama, nagode." Mujittafa ma zumuɗin gidan ya dinga yi har Mama ta ƙara mishi abincin da Ummu ta kawo musamman da yake kiran a dai ƙaro mishi naman nan na zabuwa, dariya kawai suke yi har ya gama ya fita ya samu Alhaji da Luƙman ya shiga mamakin me suke tattaunawa haka a kai. Mama kua da ta watsa ma yarinyar ruwa ɗaki ta shiga ta ɗauko mata wando tare da jigidar da ta gyara ɗazu da yamma dan ta saka mata, tana saka ma yarinyar ganin bacci ne sosai a idanun ta yasa ta rumgume ta a ƙafafun ta, murmushi Ummu tayi ganin yarinyar fa ta kai shekara uku ko kusan huɗu ma, riƙo hannun yarinyar Ummu tayi tace "Ke ma ba zaki manta da Mama ba ko kuwa gobe za ki ga ahalin ki, nagartattun halayen Mama yasa ba ma iya mata butulci." Sai kuma ta sake yin murmushi tace "Ya sunan ki?" Cikin baccin da ya fara fizgar ta tace "Khaiyat (Khairat)." Jigidar mai roba ta fara ƙoƙarin sakawa yarinyar, Ummu na ganin jigidar ta yi saurin riƙota tana cewa "Lahhhh! Mama, wannan jigidar fa mai kyau?" Ita ma mama murmushi tayi tace "Wannan...?" Sai kuma tayi shiru na wasu sakanni, wannan ? Wannan jigidar? A ƙugun Ummu ta same ta tun tana jaririya, ta cire mata ita ne sanda ta girma duwatsun kuma suna warewa saboda ta musu girma, har ta mance da ita fa, la'ilaha illalah! Kallon Ummu tyi tace" Kina so?" Da murmushi Ummu ta kalle ta tace" Tana da kyau Mama, dubi duwatsun fa, ni ban taɓa ganin irin su ba tun da nake, gasu da ɗaukar hankali kamar dai wasu na musamman da ba'a samu a ko ina." Kallon tausayi Mama ta mata tace" To kinga, ki ɗauketa kawai." Kallon Maman tayi tace" A'a Mama, ba ta Khairat bace? Kuma ma ai b zata min ba." Girgiza kai tayi tace" Ba Ta ta bace, ta jima sosai ina ɓoyeta, da a ƙugunki take girma yasa na cire miki ita, amma ki ɗauka tunda kina so." Dariya tayi tace" Mama ai b zata min ba." Ƙin karɓar jigidar tayi tace" Ki samu wasu duwatsun masu kyau da zasu dace da waɗannan, Kinga sai ki samu wata robar da zata yi daidai da ƙugun ki kawai, shikenan fa." Da farin ciki Ummu tace" E, kuma fa Mama kin kawo shawara." Murmushi Maman tayi tana girgiza kai tace" Ummu kenan, ke dai ba'a rabaki da son jigida, idan ban yi ɓatan lissafi ba ina ga ɗaurin jigida goma sha uku ke a ƙugun ki, wai ke ko isar ki ma bata yi?" Dariya Ummu tayi tana sunkuyar da kai dan Alhaji kullum shafa ƙugun ta yake yace tana birge shi abar nan, da sauri mama tace" Ba wannan ba, ya gidan naku? Komai dai lafiya ko?" Ajiyar zuciya Ummu ta sauke ta kalle ta tace" Mama, gidan mu babu daɗi ta wata kusurwar, Alhaji mutumin kirki ne sosai, ba ruwan shi da damuwar duniya, yana min duk abinda nake so, kuma ya na maida kanshi ƙaramin yaro a gabana, hasalima Mama ya zama kamar abokin wasa a gare ni, sai dai mutanen gidan shi..." Iska ta feso daga bakin ta sannan ta ɗora da" Hajia babba ita ce ke da hali irin na Alhaji, ba ta da matsala sannan tana da kirki, amma sauran matan da ƴaƴansu mata masu aure, duk tayasu kishi suke saboda wai na auri uban su, amma f Mama hatta babban ɗanshi wanda yake da aure har da ɗiya budurwa, wallahi kar ki so kiga yadda yake girmama ni ko da gaishe ni zaiyi, ƴan mazan ba ruwan su su amma matan, Zeinab kaɗai ke gaishe ni da girmamawa kuma har muke hira da ita, ko ma dai yaya ne Mama ni dai ina farin ciki da zamana da shi, bai tauye ni ta ko ina ba, dan haka ma bana shiga harkar su bayan gaisuwar mutumci." Jinjina kai Mama tayi cike da tausayawa rayuwar Ummu, ita gaba ta fi hango mata wallahi, ta sani a shekarun ta yanzu da kuma na Alhaji dole wata rana za ta tawaya, to amma ta ga ita sam bata hango haka, hasalima yarinta ta sa bata wannan tunanin, dan haka ita ma bata so ta dinga mata irin wannan hirar, cike da rarrashi tace "Ki ci gaba da haƙuri kinji, kowace rayuwa dama da kika gani akwai ƙalubale a tare da ita, amma idan kika yi haƙuri komai zai zo ya zama tarihi." Yadda Mama ta faɗa mata kuwa haka aka yi, dan tun a hanyar su ta komawa ta cika shi da shagwaɓa sai ya tsaya ta siyi duwatsu, tun yana dariya da cewa ta bari ta zo gobe ta siya har dai ya ga da gaske take, dole ya tsaya ta siya sannan suka wuce gida. ******************* Kasancewar an shiga watan ruwa da babu ƙaƙƙautawa yasa tun jiya da safe ke ta ruwa kuma har yanzu da yamma tayi ana ta yayyafi, sanyin da gari ya ɗauka sosai yasa ciwon ƙafafun Hajia kakar ya tashi, ganin dai ba sauƙi kuma maganin ta y ƙare, dole Sa'ad ya fita tare da Aisha dan siyo mata maganin, a hanyar su ta dawowa bakin hanya inda babu nisa da gida ya tsaya wajen wankin mota yayi magana da ɗaya daga cikin yaran wurin kan zai kawo motar yanzu a wanke mishi, amma a jira ya kai Aisha gida, kallon shi tayi tace "Abbu, ka bayar mana yanzu, sai mu taka a ƙafa ai." Kallonta yayi ta ƙasan idanu yace "Idan fa kika jiƙe d ruwa?" Sadda kanta tayi tace "Babu komai ai, kuma ma yayyafi ne kaɗan." Da wani irin narkakken kallo ya kalle ta yace "Kin tabbata?" Ba tare data kalle shi ba ta jinjina kai alamar e, dan haka suka fita ya bar motar dan yana son fita anjima, a hankali suke tafe yayyafin nan na sauka jikin su, yanayin yayi kyau sosai inda sama tayi kalar shuɗi gwanin sha'awa, ledar maganin na hannun ta tana wasa da ita inda kanta ke ƙasa bata kallon ko ina sai ƙafafun ta, Sa'ad kuma dake satar Kallonta jefi-jefi ne yace "Kin taɓa riƙe waya taki?" Ba tare data kalle shi ta girgiza kai cike da kunya tace "A'a." Jinjina kai yayi ya kalli gabanshi yace "To saurayi fa?" Da sauri ta kalle shi, yana juyowa ya kalle ta sai kunya ta sake rufeta ta rufe fuska da hijabi tana murmushi, wani basaraken murmushi ya saki yana girgiza kai yace "Ba zaki gaya ma Abbunki ba? Ko baki so muyi surukun taka ne?" Cikin kukan shagwaɓa ta dinga bubbuga ƙafafu kamar zata tashi sama tana cewa "Abbu ka daina, ni bana da wani saurayi, ba ruwana da su." Ajiyar zuciya ya sauke yana Kallonta yace "Saboda me? Naga ai kin isa aure ko?" Kallon shi tayi tare da turo baki tace "To ai Mother bata barin mu kula maza kuma ba'a barin mu fita sakaka, ko waɗanda sukayi aure ma a gidan marayun duk mafi aksarin su auren haɗi ne ko kuma idan anyi katari ka fita wani muhimmin abu sai saurayin ya ganka ya kuma biyo ka." Kallonta yayi yace" Da kyau, kenan ke baki taɓa irin fitar katarin ba da zata haɗaki da saurayi?" Girgiza kai tayi a tausashe tace" Um um." Shiru sukayi na wasu daƙiƙu suka ci gaba da tafiya, suna daf da gida ya sake kallon ta yace" Me yafi miki daɗi?" Kallon shi tayi da mamakin wannan tambayar, sai kawai ta kalli sama tana sauke numfashi tace" Kallon sama bayan ɗauke ruwa, yanayi mai daɗin gaske." Shiru suka sake yi, hakan yasa ta kalle shi ita ma tace" Kai kuma fa? Me ya fi birgeka?" Saida ya ɗan cije leɓe yana jin kamar ya faɗi abinda ke ran shi, sai kawai yace" A da dai akwai abubuwa dayawa, a yanzu kuma *zama tare dake* ya fi min komai daɗi." Cak! Ta tsaya tare da zuba mishi idanu tana kallo, kallon da take mishi ya ankarar da shi abinda ya faɗa, da sauri ya shiga gaba yana tafiya da cewa" Ba abinda kike tunani bane." Ba Ta iya ɗaga ƙafafun ta ba har saida ya kusa shigewa gida sannan ta bi bayan shi jikin ta na sake yin sanyi da kuma tunanin abinda ya faɗa ɗin. A zabure ta tsaya tana waigawa inda saurin ya fito, ganin shi tare da baƙo yasa ta tausasa murya tace "Ina kwana?" A sukwane ya nufe ta cike da faɗa da bala'i yna faɗin "Ke dallah riƙe gaisuwar ki, idan ban kwana ba zaki ganni ne?" Yana isa gare ta sai kuma ya rasa ainahin me zai ce mata, faɗa akan ta fito babu hijabi? Kar fa ta fara zargin shi akan wani abu, sai ta ga zaƙewar shi tayi yawa ai. Kasa kallon fuskar ta yayi yana ta sissine kai da yace" Maza shiga ciki..." Da rashin fahimtar shi gaba ɗaya ta raɓa jiki a sanyaye tana taɓe baki, har ta ɗan yi nisa yana tsaye bayanta ƙerere sai kuma yace" Ji nan...?" A hankali ta juyo ta sauke dubanta gare shi ta amsa da" Na'am." Saida ya haɗe fuska irin kar ta ga damar san nan yana kakkawar da kai yace" Ki daina fitowa haka ba sutura, maza na shigowa kowane lokaci." Da maɗaukakin mamaki ta kalle shi za ta tambaye shi ya sutura? Bayan wannan ta jikin ta? Amma sai ta ga ya juya ya bar ta nan tsaye, sai kawai ta juya tana sake duban shigar ta, to ita yanzu me ye aibun rigar tan nan? Girgiza kai kawai tayi ta furta" Allah ya shirya ka Abbu, ashe shiyasa kullum addu'ar Hajia kenan akan ka." Tunda yake tunkaro DG ya fahimci kallon ƙurilla da yake mata da kuma mamaki a fuskar shi hakazalika tambayoyi fal bakin shi, yasan ba zasu ƙarke a daɗi ba, dan haka ya ci magani sosai ya ƙaraso a tsume dan in cin uwa ma ta kama sai a yi ya tsaya gaban shi, cikin dakakkiyar murya ya dafe ƙugu ya kalle shi yace "Mun gam magana, za ka iya tafiya?" Kallon idanun Sa'ad ɗin yayi da matsanancin mamaki yace "Oga, wa...ccen yarin...yar...kamar...wacce muk..." Gaba da gaba dan ya nuna musu ya tafasa fa baya tsoron ƙuna yasa kai tsaye ya katse shi da cewa "Ita ce DG." Da mamaki DG ya sake kallon hanyar da Aisha ta bi yace "Amma me take nan? Dama kuma tana hannun ka shine ka ƙyalemu muke ta haukan karaɗe gari a kan ta? Me yasa *Sa'ad*?" Saida ya sauke numfashi yana kallon fuskar DG ɗin sannan yace "Tana da mahimmanci a rayuwata, bana so na rasata kuma ba zan iya rabuwa da ita ba, dan haka kawai ku bar maganar neman ta." Da yanayin fara hasalla ganin milyoyin kuɗaɗe ya karɓa akan yarinyar nan DG yace "Ba zamu iya haƙura ba, kai ne zaka haƙura ka bamu ita, ni ba cutar da ita zanyi ba, kawai ka bani ita Sa'ad, saboda na karɓi kuɗi masu yawa akan ta, kuma nayi alƙawarin zan samo ta." Wani malalacin murmushi Sa'ad yayi ya ɗan ja baya yana ƙare mishi kallo yace" Wato in baka ita ko? Tunda kaine Ibu? In ɗaukota in baka ka tafi da ita ni ga sakarai wawa marar anfani ko? To bari ka ji..." Matsowa ya sake yi daf da shi ya ɗora yatsarshi a ƙirjin DG yana daddagashi da ƙarfi yana faɗin" Zai fi kyau ku rabu da ita, idan ba haka ba kuma zamu samu babbar matsala da ku, kun san ni haka nima na san ku." Cikin haɗe fuska DG yace" Ai kuwa zaka yi nadama, dan a shirye muke mu karɓi yarinyar nan ta kowace irin siga." Murmushin gefen laɓɓa Sa'ad yayi yace" Ka san wani abu? Siyar da ƙwaya kawai nake kafin yanzu, ko sigari bata taɓa ban sha'awa ba wallahi, dan nasan kaɗan a aikin ƙwaya ne yasa ka aikata fiye da abinda kake faɗa za'a aikata yanzun." Cike da jin haushin wannan abu da Sa'ad ya faɗa dan ƙarara nufi yake ƙwaya ce ta sa yayi wannan ambatun tsabar bai ɗauki abinda ya faɗa da mahimmanci ba, jinjina kai yayi yana ja baya yace" Shikenan, zan tabbatar maka da aikin ƴan ƙwaya, kuma zaka yi nadama akan haka, mu zuba ni da kai." Murmushi ya mishi cike da wofantar zancen yace" Sauka lafiya." Da irin jinjina kan nan na zaka gane kuren ka ya juya ya fita cike da alwashi kala-kala akan Sa'ad ɗin, kuma yay alƙawari yau ko gobe yarinyar nan za ta shigo hannun shi, dan haka akwai buƙatar yayi aiki cikin gaggawa da zai raba yarinyar da gidan su Sa'ad ɗin dan ya damƙa ta hannun Hajia Fa'iza, ruwan ta ne ta dafa ta ta cinye ko ta gasa, shi bai dame shi ba tunda ya samu kuɗin shi. *Ga mai son shiga grp ɗin RUBUTACCIYA ya tuntuɓi wannan lambar 82-21-91-74* *Idan aka zuba comment zaku iya samun wata page in sha Allah.* *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *17* Kiran DG ne ya tashe shi da safiyar nan, cikin jin haushi ya ɗaga kiran bai ce komai ba yana saurare, a tausashe DG yace "Oga, ina nan cikin gida, na zo muyi magana ne." Akwai magana sosai a bakin shi, amma takaici yasa kawai ya yanke kiran ya taso ya fito a harzuƙe dan ya ji me ye na zuwa musu gida a wannan lokacin? Shi dai ya ɗauka ba komai tsakanin shi da su daya rage, kasuwanci ne kuma ya daina shi yanzu wasu sabgogin yake yi da suke bashi halaliyar shi, kuma yanzu hankalin shi ya fi kwantawa da haka, zai ma iya rantsuwa ya fi wata uku bai ga ƙwaya da idanun shi ba idan ba wacce aka ciro a cikin Aisha ba, tana nan ana ajiye a cikin motar shi a ƙasan kujera yana so ya samu inda zai binne ta, daga nan ba shi ba sake taɓa ƙwaya har abada. Yana zuwa ya same shi tsaye yana wasa da bishiyar mangwaron da tayi shar shar tana daf da fara fidda ƴaƴa, DG na hango shi ya yi wani shu'umin murmushi, dan yadda ya haɗe fuska ya san ran shi ɓace ya fito nan, hakan yasa ma ya fito daga shi sai singlet baƙa da wando tree quater, yana ƙarasowa ya tsaya yana dafe ƙugu yace "Ina ji?" Gyara tsayawa DG yayi yace "Barka da safiya Oga, dama akan maganar ɓatan yarinyar nan ne, yall..." A tsanake cikin tausasawa da kasala Sa'ad yace "Kaga, ba abinda ya dame ni da yarinyar nan, ku je ku nemeta idan kun ganta ku riƙe na bar muku, ni yanzu wannan sabgar bata gabana, amma ka san wani abu guda..." Ya faɗa cike da gargaɗi da nuno shi da yatsa yace "Ku cire idonku a kan yarinyar nan, ta fi ƙarfin ku kuma tana da masu tsaya mata idan wani abu ya same ta, dan haka ina baku shawara ku rabu da ita...." Kafin ya dasa aya inda yake fuskanta ya hangi Aish ta fito daga ɓangaren su Maman shi riƙe da bokiti, yadda alamu suka nuna mishi ba komai a bokitin bai ɗaga hankalin shi ba kamar ganinta da hula a kanta wacce duk rabin gashin ta a fili yake, sanye kuma da doguwar rigar kanti dake fito da surar jiki duk da bata matse ta ba, La'ilaha illallah ! Me yake damun Aisha ne? Dubi fa rigar nan rawa take a jikin ta, ga shi ta fito mata da ɗan ƙirjin nan nata da wannan shafaffen cikin... Ganin idan ta ci gaba da tafiya za ta kai ga kusurwar da idanun DG na iya sauke dubansu ga ƙugun ta, dan haka yayi azamar daka mata tsawa da ƙarfi yace "Ke!" A zabure Aisha ta tsaya tare da waigawa inda sautin ya fito, ganin shi tsaye tare da wani kuma a yanayin da bata taɓa ganin shi ba sai ta ji kunya ta rufe ta, sadda kanta tayi a tausashe tace "Ina kwana?" A sukwane ya tunkare cike da bala'i yana faɗin "Ke dallah riƙe ina kwanan ki, da ban kwana ba zaki ganni ne yanzu?" Da mamakin faɗan kuma na miye? Me tayi yanzu kuma daga haduwar su har ya ƙaraso kusan ta ya ɗan kakkareta yana kallon fuskar ta dan baya son kallon komai bayan nan ɗin yace "Ya zaki dinga fitowa babu sutura a jikin ki? Bayan kin san ba ke kaɗai bace a gidan." Ƙarin mamaki akan wanda ya bata, ƙanƙance shanyayyun idanun ta tayi ta shiga kallon kan ta, sutura? To bayan wannan? Tsirara ta fito ne? Da mamaki ta kalle shi tace "Amma...." Saida yayi maganar ne ya kuma gane kamar fa yayi tsauri dayawa, me yasa ya aikata haka? Idan fa tayi tunanin wani abu a kan shi? Cike da basarwa irin ba shi ɗin nan bane ya kawar da kai a tausashe yace "Ki kula, ki daina fitowa haka, Kinga maza na shigowa da ba muharramanki ba." Ita dai bata daina kallon shi da mamakin nan ba har ta jinjina masa kai tace "To, zan kiyaye." Da ido ya mata alamar ta wuce to, ɗan taɓe baki tayi ta juya a sanyaye ta wuce ciki tana addu'ar "Allah ya shirya ka Abbu." Dan sai yanzu ta fahimci Dalilin da ya sa kullum addu'ar Hajia kenan a kan shi. Tunda ya juyo y ga fuskar DG cike da mamaki yana bin Aisha da kallon ƙwaƙwafi ya san sauran zancen, kuma ya san ba zasu kwashe lafiya ba, dan haka ma ya cika fuskar shi tam da haɗewa ta yadda idan ma cin uwa ta kama ai zai iya akan ƴar shi ko? Yana zuwa gabanshi ya dafe ƙugu yana kallon shi yace "Ina ji?" Ba tare da ya daina kallon hanyar da ta bi ba yace "Oga, yarinyar can..." Katseshi yayi da cewa "Ita ce, sai me?" Da mamaki DG ya kalli Sa'ad ɗin yace "Sai me? Oga sai me kake tambaya?" Sai kuma ya ɗaga murya yana faɗin "Oga yarinyar nan fa ita ce muke ta haukan nema a garin nan kamar za mu tashi duniya, tana hannun ka dama ka mana shiru? Me yasa? Me yasa zaka mana haka? Tu yaushe take tare da kai? Me kuma kake mata?" A kausashe Sa'ad da ranshi ya fara ɓaci na hawar masa kai da DG ke neman yi yace "DG waye kai da zaka titsiyeni kana min wannan tambayoyin? E ɗin tana tare da ni, da yadda zaka yi ne? Tun ranar da ta kubce daga hannun ku muka haɗu da ita, sai me...?" Sai kuma ya matso daf da shi sosai ido cikin ido yace "Tana hannuna, kuma a halin da ake ciki yanzu ji nake ta zama wani *ɓangare na rayuwata*, dan haka ku manta da ita kawai kamar ma baku taɓa sanin ta ba, alaƙa ce ta kasuwanci dama kuma babu bashi tsakanina da Hambali, dan haka kai ma kaje kayi harkar ka kawai." Wani sakaran murmushi DG yayi yana girgiza kai yace" Ƙarya ne wallahi, ni ba ina neman ta bane dan Hambali, saboda kaina nake neman ta, milyoyin kuɗi na karɓa akan alƙawarin zan isar da ita inda ake da buƙata, dan haka kawai *Sa'ad* ka bani yarinyar nan." Shi ma malalacin murmushin yayi ba tare da damuwa da sunan shi da ya kira ba bayan baya faɗa ɗin a tausashe yace" Ban damu da nawa ka karɓa a kan ta ba, amma ka sani alhali gareta a nan ɗin, DG *ina son yarinyata*, kuma zan iya yin komai a kanta, ba zan bari ta shiga hannu ku ba inda ina numfashi, dan haka kamar yadda na faɗa maka kawai ka manta." Girgiza kai DG yayi yace" Nima n ba gaya maka ba zai yiwu ba, wallahi sai ta dawo hannuna ta kowace irin siga, kuma zan iya yin komai dan ganin haka ta faru." Wata sakaryar dariya Sa'ad yayi yana faɗin" Ka ganni nan DG, siyar da ƙwaya kawai nake amma bana shan ko sigari, dan nayi imani idan ina bushe-bushen nan wata rana zan iya aikata aiki irin wanda yanzun kake aikatawa." Cike da jin haushin abinda Sa'ad ɗin ya faɗa nufin shi kenan yana shan ƙwaya, jinjina kai yayi yace" Shikenan, zan kuwa nuna maka aikin ƙwaya ziryan, abinda nake so na sani shine, shin tasan wanene kai?" A haussale, a mugun harzuƙe Sa'ad ya sa tafin hannu shi na dama ya tura DG saida yayi baya ƙwarai kamar zai faɗi à zafafe yace" Wa ye kai da zaka min wannan tambayoyin? Ko Ibu zai tsare ni da wannan tambayar ne bare kuma kai banza wawa." Da yatsa manuniya ya nuno shi cike da gargaɗi yace" Ka cire idanun ka akan *ƴata*, ko na maka abinda baka tsammani." Yana faɗa ya juya a harzuƙe yayi ɓangaren shi, da kallo DG ya bishi cike da tsana da takaici, saida ya ɓace ma ganin shi sannan ya jinjina kai cike da cin alwashin yau ko gobe zai yi iya yin shi yarinyar can ta dawo hannun shi, dan ba zai barta hannun Sa'ad ba, kuma ta kowace hanya zai bi don ganin ya dawo da ita gare shi sannan ya sadata da wacce ta dace kuma ta masa baban biyan da yanzun yake shaƙatawar shi da wannan kuɗaɗen. *A ranar* aka riƙe *Sauban* asibiti saboda ciwon sanyin ƙashi dake damun shi, ruwan da ake yi a kai a kai kuma shi ke janyo mishi dandanan bai da lafiya, Alhaji har mamaki yake yadda Sa'ad ke ta kai da kawo da larurar ƙanin nashi duk da ba uwa ɗaya suke ba, wanda a baya ba haka yake yi ba, yanzu ma haka bayan ya karɓo sakamakon da aka tabbatar sai an ƙarawa Sauban ɗin jini ya miƙawa maman Sauban ɗin wato Sabira takardun tare da cewa "Bari naje na siyo jinin, sun ce yanzu suke buƙata." Karɓa tayi jiki a sanyaye tana kallon shi da mamakin sababbin halayen shi tace "To, angode Sa'ad." Juyawa yayi ya fita ba tare da ya ce mata komai ba, Hajia Uwani dake zaune tana kula da duk shige da ficen Sa'ad ɗin tana mamakin wai me ye haka? Shin bai san duka matan baban shi ba ƙaunar sa suke ba? Bai san suna mishi hassada da rufin asirin da Allah ya masa ba? Shine zai yi ta wani rawar ƙafa akan ɗn Sabira dan bai da lafiya? Da sauri ta tashi ta bi bayan shi tana ƙwala mishi kiran Baban ta Baban ta! Saida ya sauka daga matakalar ɗakin ya tsaya yana juyawa ya kalle ta, tana ƙarasowa cikin gyara gyalenta tace "Babana, wai lafiya na ga sai wani hidima kake yi da yaron nan? Kuɗin banza ka samu ne?" Da mamakin tambayar ta, da wani dogon kallo mai kama da hangen nesa yace "Mama, dama ana samun kuɗin banza ne?" Cikin raɗa tace "Kai bana son iskanci, to in ba kuɗin banza ba, uwar yaron nan kasan ba ƙaunarka take ba da ni kaina, ba su da abun magana idan ba gulmar ka ba da tsegumin kana aikata abinda bai da kyau, su fa burin su kullum bai wuce suga ci bayan ka ba hankalin su sai ya kwanta, shine zaka zo kana ta wahalar da kan ka, bayan ga uban ka nan shi da ya auro jaraba can ya ƙarata da ita." Ya kasa gane wannan hali na Maman shi? Ita wai me yake damunta? Shine fa babba a gidan su? Fisabilillah hanyar da take ɗora shi a kai ta dace kenan? Kenan bata fata ko bayan ran mahaifin su shi ya zama uba a gare su? Girgiza kai yayi a hankali yace" Mama, kenan na cire hannuna tunda dai ba ke kika haifi Sauban ba kamari yadda kika haife ni?" Da yanayin rashin gaskiya tace" E to, ni nufina ka daina hakanan mana, ina laifin ka? Ai kayi ƙoƙari ko?" Gyara tsayuwa yayi yace" Zan je na siyo jinin na kawo, zan koma gida na ɗauko Aisha, Hajia ta ce ta bar ta tayi girki t taho da shi." Wawan tsaki taja tare da kawar da kai tace" Hmmm! Aisha, Aisha, Aisha dai, wai kai me ye tsakanin ka da wannan yarinyar? Yaushe za ka maida ta inda ka ɗauko ta?" A hankali ya raɓa zai wuce, a zafafe ta riƙe rigar shi tana faɗin" Ƙashin babakere.... 🤣" Wata ashariya ta malmala mi shi ta ɗora da" Ina magana da kai za ka wuce ka barni kamar wata ƴar iska? Bari jin ina kiran ka Babana, wallahi tallahi zan mugun saɓa maka a kan yarinyar nan da ta nace maka, ni baƙin ciki na ma da ban san zaman da take a gidan nan ba, shikenan dan ka raina mutane kai ba za'a gaya maka ka ji ba?" Ƙurawa fuskar ta idanu yayi yana kallo dake ɗauke da yanayin faɗa sosai, a hankali zuciyar shi ta fara raya mishi ko dai Dalilin da yasa kenan Ibu ke saurin kai hannu a jikin ta? To kana miji mata na nemanka da masifa, ka miƙe dan ka bar mata wurin kuma ta riƙeta ta na ci gaba da yi, shin ko baka da saurin hannu ba ka koye shi ba? Da sauri ya kawar da wannan tunanin ta hanyar sanyaya murya yace "Ga Ibu nan tafe, kar ya miki faɗa cikin jama'a." Da sauri ta juya inda taga yana kallo, ai kuwa Ibun ne tafe daga masallacin dake cikin asibitin, a hankali ta sake shi tare da kausasa kallon ta gare shi tace "Kar ka ɗauka mun gama maganar nan kenan, wallahi yarinyar nan sai ta bar gidan, dan canzawar ka ma nada nasaba da ita, har wanki fa Mujahid ya ce min ya ga kana mata." Sai kuma tayi ƙwafa ta shige ciki tun kafin Alhajin ya ƙaraso, shi ma kuma a sukwane ya nufi hanyar shi tare da kallon Alhajin a taƙaice yace" Sannu da zuwa." Madadin amsa mishi sai ya bishi da kallo yace" Sai yaushe za ka dawo?" Juyowa yayi a hankali ya furta" Yanzun nan." Kawai ya sake juyawa ya wuce zuwa inda za shi. Bai ɗauka zai dawo yanzun ba kamar yadda ya faɗa, amma sai gashi ya shigo da jini da kuma likitar da zata saka mishi ƙarin jinin, hakan ya sake bashi mamaki har ya dinga saka mishi albarka a zuciyar shi, amma a zahiri da sun haɗa ido sai kowa ya ɗauke idanun shi ana ƙara shan kunu kamar wasu abokan gaba. Bayan sallah magrib ya kawo Aisha asibitin, kamar yadda ta san babu mai ƙaunar ta a gidan, hakan yasa da ta zo ma tana zaune kan tabarma rakuɓe tana kallon su kawai, duk zaman da tayi a gidan nan haka take bata shiga rayuwar su, tana iya take kwana uku ma bata leƙa ɓangaren su ba, Leila ce ka kaita kuma tana zuwa da kan ta ɓangaren na Hajia, har ƙsan ranta take jin ta kamar wata tsiya ta yadda bata son rainin wayo, dan haka take baya-baya da su ita ma. Duk son ta da son ta samu kusanci wajen maman wanda take zaune gidan dominshi haka ta haƙura dan ta gama lura tana da wuyar sha'ani, so da dama t kan ga ko ta ji saɓani tsakanin ta da ɗan nata ma , hakan yasa bata taɓa ganin suna hira ta arziƙi tsakanin su ba. Har ƙarfe 09:00 tana zaune ba um ba um-um dan Hajia ta tafi gida tun yamma, Sa'ad kuma ba zaune yake tunda suka zo ba yana ɗan kai da kawo ne, har sai yanzu da ya kalli agogon hannun shi sannan ya kalle ta, karo na farko a zaman su da ita da ya kira sunan ta da "Mu tafi ko *Eesha*, lokacin hutawar ki ya yi." Kallon shi tayi tana murmushi saboda jin daɗin sunan da ya kirata da shi da ba wanda ya taɓa kwatanta hakan, a hankali ta yunƙura ta miƙe tsaye, dan har yanzu a hankali take bin jikin ta saboda aikin da aka mata, shi ma miƙewa yayi hakan yasa Uwani kallon shi tace "Gida kuka nufa kai tsaye? Ko wani wurin na daban?" Saida ya runtse idanu saboda jin zafin maganar, sai ya dake kawai saboda mutanen dake ɗakin yace "Gida zamu je Mama." Yunƙurawa tayi tana gyara gyalenta tana cewa "Bari in biku to, na ɗauka ai wani gurin za'a je daga nan, na ji kace lokacin hutawar ta ya yi..." Sai kuma ta taɓe baki ta harari inda Aisha take tace "Hmmm! Ƴar gwal kenan, Allah wadaran naka ya lalace." Aisha sam bata gane me tambayar ta ke nufi ba, dan haka ba ta ji zafi ba hatta da karin maganar nan da ta yi, ita ta fara fita bayan ta musu sallama sannan Sa'ad ya bi bayan kafin Maman shi. *Shirin Farko Na DG* Suna hanyar su akan titi da dama kullum da jami'ai saboda kusa da gidan gwamna ne, anan jami'an suka tsayar da shi wai zasu bincike shi, ya so faɗa musu ba uban da ya isa, amma dake yana tare da mata biyu masu mahimmanci a rayuwar shi, sai kawai ya ƙyale su suka shiga lalubar aljihunshi da lalabe komai na jikin shi, ɗaya jami'in kuma na duba cikin mota, kallon juna jami'an sukayi suka girgiza kawunansu, dan haka ɗaya yace "Zaka iya tafiya." Kallonshi kawai Sa'd yayi yana hardace kamanninshi a cikin ƙwaƙwalwar shi, zagayawa yayi ya shiga ya rufe ƙofar, haro zai wa motar key suka sake dakatar da shi, ɗaya daga ciki ne yace "Yallaɓai, zamu binciki matan ne, musamman ma wannan yarinyar." Da mamaki ya kalle su yana fitowa yace "Matan?" Da tabbaci jami'in yace "E, ai Yallaɓai mata yanzu sun zama dillalan miyagun kasuwanci, ma fi aksari kuma cikin lulluɓin su." A tsanake Aisha ta buɗe motar ta fito tana kallon su, hakan yasa ɗaya jami'in nufa inda take yana faɗin "Yawwa ƙanwata, ɗan cire hijabin naki?" Duk da ba hijabin bane jikin babban mayafi ne da ta rufe har kan ta, cikin tsawa da hargagi Sa'ad ya nufesu yana faɗin "Ba zata cire ba, ke, me ya fito da ke?..." Sai kuma ya kalle su yace "Kunga, ban ce zan shiga aikin ku ba, ban kuma kayan da kuke sanye da su ba, nasan ni mai laifi ne da cancanci kowane irin ƙasƙanci, amma sam ban da wannan, ban da ta hanyar Eesha." Taruwa sukayi à kan shi suna tabbatar mishi su fa aikin su suke, dn haka ka da ya taka dokar da zata ɗaure shi, Mama kuma da takaici ya gama kamata duba da duk wannan zaƙewar yana yi ne akan yarinyar nan, kasashe ta zuro kanta tan faɗin me yasa ba zai bari su yi aikin su ba? Hannu jami'in ya kai a jikin Aisha kawai ya finciko gyalen nata, hakan yasa gyalen biyo hannun shi ɗan kwalin ta kuma ya faɗi ƙasa saboda irin ɗaurin nan ne na Zarah buhari, kuma gashi duka ta ɗora gyalen har saman kan... *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *18* Shi kishi ya kan ziyarce ka ne kawai akan wanda kake tsananin so da ƙauna, haka kuma kana iya yin komai dan kare mutumcin wanda kake so. Irin hakane ya faru ga Sa'ad, shi kan shi bai san lokacin da ya ɗauke jami'in nan da mari ba duk da kuwa a cikin kayan aikin shi yake, a lokacin da idanun shi suka rufe bai hango girman hatsarin dukan jami'in dake bakin aiki ba, shi dai kawai ya ga ƙato ya yaye hijabin dake ɓoye masa *sirrin shi* yake kuma tayashi kare *mutumcin shi* a gaban shi, hakan yaa ya ji kenan ma jami'in ya raina mishi wayo? Kenan ma bai ɗauke kasancewar shi tare da ita a bakin komai ba? Bai hango cewa shi ɗin yana nan ne dan kawai ya *bata kariya* ba? Bayan ya kashe fuskar jami'in da mari a sukwane shi ma cikin zafin nama bayan ya dafe kumci ya yi kan Sa'ad hannun shi sama da niyyar ramawa duk da yana da tabbacin idan ba'a yi gaggawar raba su ba tsaf zai sha wahala dan Sa'ad ya fi shi komai, bayan tsayi da kaurin jiki da ƙwanji, har da kazar-kazar ma na cikakken ingarman doki. Cike da neman jaraba ido rufe Sa'ad yayi ram da duka hannayen jami'in bai yarda ya taɓa jikin shi ba ma bare ya mare shi, hakanne yasa suka kaure da kiciniya a wurin kamar wasu ƙananan yara, tuni hankalin jama'a ya fara dawowa kan su, inda masu tafiya suke tsayawa dan ganin ƙwam, da ƙyar aka raba su inda Sa'ad ke ta maimaita kalmar "Ba dan ka ɗaukeni ɗan iska ba, ta ya za ka cire mata tufafi? A gidan ku ba mace ne? Ko bishiya aka girgiza ka faɗo ne da baka san kimar mace ba? Kai ba namiji bane? Ba ka san ya mutum ke ji idan an taɓa masa mutumcin sa ba, idan binciken zaka yi ka sa ƴar uwar ta mace mana kada idan zan damu, amma haka kawai zaka saka ƙazamin hannun ka ka cire mata tufafi." Cikin tafasar zuciya da baƙin ciki jami'in nan yace" Ni dai ka mara ko? Wallahi za ka gani, za ka gani nake faɗa maka, kuma na gane fuskar ka." Cike da shaƙiyanci Sa'ad yace" Ka gane fuskata? Wai da baka shaidani ba ma? Bari ka gani..." Ya faɗa yana saka hannu aljihu ya ciro katin shi tare da cilla mishi yace" Katina ne wannan, cikakken sunana da sunan ubana da inda nake zaune duka yana nan, idan kuma baka iya karantawa ba to ka ji da kyau, *Sa'ad Ibrahim tela* nake." A fusace ya zagaya ya samu Aisha tsaye duk tayi sanyin da ta kasa motsawa ko kaɗan, to ita bata ma san me za ta ce ba, Sa'ad yayi abun da ya saka ta tunanin to ko dai da gaske *son ta* yake kamar yadda kwanan baya Leila ke faɗa mata saboda kwanakin da ya dinga bata kulawa, sannan da bakin shi ya ce zama tare da ita shine abinda ya fi mishi komai a yanzu, ga kuma irin wannan dambatuwa da ya yi duk saboda ita, Gaskiya ko da tana da ƙaracin shekaru ai za ta fahimci akwai soyayya a nan. Dake ran shi a ɓace yake yana zuwa kusa da ita dama ƙofar motar a buɗe take, dan haka ya ɗan ɗora hannun shi a damtsen ta ta hanyar tura ta cikin motar sannan ya mayar ya rufe kawai ya shiga ya tayar suka bar wannan taron ana ta maganganu a kai, sai dai dayawa mutane da suka fahimci jami'in ne bai da gaskiya sai kawai Sa'ad ya birge su matuƙa, inda jarumta da ƙarfin halin shi suka sake ɗaɗasu a ƙasa duba da saida ya bar ma jami'in masaniyar da zai gano shi a sauƙaƙe tunda ya san yana da gaskiyar shi. *Muje* da sauri, kun san dole Mama za ta yi magana, tayi faɗa, tayi bala'i, tayi kumfar baki kamar za ta ci Sa'ad, amma lokacin idanun shi a rufe suke, bai tanka mata ba yana dire su gida ya sake tuƙa mota ya yi wani wurin, bai kuma dawo gidan nan ba saida ya tabbatar da ya salwantar da wannan kayan mayen da aka ciro daga cikin Aisha, rame yayi mai zurfi sannan ya banka musu wuta sannan ya tafi. Da sassafe sammaci ya ziyarce shi na marin jami'in nan, sai dai da jami'in yasan abinda zai faru da bai shigar da ƙarar ba, dan daga abinda Sa'ad ya faɗa ya haɗasu kuma da bakin shi ya tabbatar aka bashi rashin gaskiya, amma dan sulhunta babban jami'in ya ma Sa'ad kashedi da kiyaye saurin dukan, sannan ba za'a ci shi tara ba dan an so tozarta *iyalinsa* ce kamar yada ya faɗa musu yanzun da aka zo ana bibbika zancen, sai dai dole ya bashi haƙuri, tsaf ya murje ido ya kalle shi yace "Zan bayar da haƙuri, amma sai shi ma ya fara bata haƙuri." Lallaɓa shi jami'in yayi dake sulhu yae so suyi ya fara bashi haƙuri sannan shi ma aka kira Aisha ya ce tayi haƙuri, daga haka aka kashe wannan matsala ta zo ƙarshe. Sai dai DG bai haƙura ba dan baiyi nasara a karan farko ba, wani shirin ya shiga tsarawa wanda ya san da wuya Sa'ad ya tsallake shi. *Bayan Kwana Biyu* Yamma lis ya dawo gidan a matuƙar gajiye da kuma yunwa, dake nan yake cin abinci da gaggawa Aisha ta gabato mishi da abinci tare da abun sha mai sanyi ta aje mishi, har ta juya da niyyar ta bashi wuri dan tun da yayi faɗan nan da take dangantawa da a kn ta yayi shi ta ƙara jin kunyar shi na rufe ta, ɗaga idanun shi yayi yace "Karɓi?" Juyowa ta fara yi sannan ta dawo baya kaɗan ta rusuna, wata dalleliyar waya dake kan tebur ɗin ya ɗauko ya miƙo mata yana faɗin "Duba ki ga ta miki kyau?" Hannu biyu tasa ta karɓa tana duba wayar da son gane me yake nufi? Jin bai ce komai ba yasa ta cewa "Tana da kyau." Sai kuma ta miƙa mishi dan bata tunanin ita ya ba, hakan yasa ya kalle ta yace "Ta ki ce, idan kuma bata miki ba ki faɗa a canza." Da mamaki tace "Ta wa?" Jinjina mata kai yayi alamar e, ƙara kallon wayar tayi sai tayi murmushi ta sunkuya tace "Nagode, nagode sosai, Allah ya saka da alkairi." Bai ce mata uffan ba har ta juya za ta koma ciki, da sauri kuma ta dakata saboda jin jiniyar mota kamar irin motar gwamna haka na shigo cikin gidan, shi kan shi Sa'ad mamaki ya sa ya kalle ta yace "Su waye?" Ɗaga kafaɗa tayi da taɓe baki kaɗan tace "Ban sani ba nima." Hakan yasa shi miƙewa yana duba ƙofar dan ya ga me ke faruwa, Aisha ma cikin sanɗa ta dinga bin bayan shi har ta fito tsakiyar berandar Hajia. *Bayan* motar dake jiniya wasu jibga jibgan motoci guda uku suka take mata baya, dake akwai wajen ajiye motoci kuma ko Sa'ad da ya shigo waje ya baro ta shi motar, hakan yasa motocin suka layu wata na bin wata, masu tuƙin motar ne suka fara fitowa suna buɗe ƙofofin baya, cikin nutsuwa da dattako mutanen ciki ke fitowa... *Sa'ad* yana sauke idanun shi akan dattijon da fuskar shi ba ɓoyayya ba ce ko a telebijin saboda muƙaman da ya taka wato *Saheeb Ahlan* ya sa shi rarako idanu ya ji gaban shi ya faɗi, a take kuma ya juyo inda ya san ya baro Aisha, amma sai ya ganta à farfajiya ita ma tana kallon mutanen da mamakin su kuma su waye? Wane irin zuwa ne wannan kusan magariba haka? Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tarie da lumshe idanu ya ayyana _"Shikenan, yau zan rabu da ita."_ Alhaji Ibrahim ma a tunanin shi ko baƙi yayi haka da babu sanarwa, bai jima da dawowa gidan ba yana shirin shiga wanka sai kawai ya fasa ya fito, ai kuwa ganin dattijon da shi kan shi ya san shi amma fa a telebijin sai ya sukwano da sauri ya nufo su da kuma mamakin jin ta yiwu ɓatan kai sukayi, amma a fara gaisawa kafin su san me yake tafe da su. Kafatanin ahalin gidan ne a tafe dan kawai su gasgata abinda aka faɗa musu cewa an samu Eesha a wannan gidan, shin da gaske? Eesha dai ta su? Kamar zai yi ruku'i a gaban Alhaji Saheeb haka Alhaji Ibrahim ya rusuna yana gaishe shi da mishi sannu da zuwa, saida ya gama mishi sannu da zuwa sannan sukayi musabiha da su Yaya Bilal da Abbu Mukhtar har ma da Sabeer, nuni ya musu da hanyar shiga ciki yana faɗin "Bismillah, ku shigo ciki." Cike da dattako Alhaji Saheeb yayi murmushi yace "A'a ka bar shi, na san ai kana mamakin ganin mu warhaka gidan ka, hakane?" Da ladabi Alhaji yace "Gaskiya ne Alhaji, ina fata dai lafiya? Dan nafi tunanin ko ɓatan kai kuka yi." Dariya yayi cikin nutsuwa yace "Ko kaɗan, ba ɓatan kai muka yi ba, shasalima tare muke da waɗanda suka kawo mu nan." Jinjina kai yayi da gamsuwa yace "Ma sha Allah, to mu shiga ciki sai mu tattauna ko?" Ƙara dakatar da shi yayi da cewa "A'a fa, ba sai mun shiga ba, dama mun zo ne akan wata muhimmiyar magana, nema muka zo, dan haka idan bamu samu abinda muka zo nema ba zamu yi wani wajen ne dan ci gaba da nema." Da mamakin furucin dattijon ya ɗan kalle shi na sakanni sannan ya rusuna yace" To Alhaji, zanyi fata a ce kun samu abinda kuka zo nema a nan ɗin, farin cikina ne hakan." Gyara tsayuwa Alhajin yayi ya kalli Hajia Radiya dake kusan shi sannan ya kalli Alhaji yace "Wani bayani aka bamu kan cewa *Eesha tana gidan nan*." Da wani sabon mamaki Alhaji Ibrahim ya kalle su dukansu sannan ya maimaita kalmar "Eesha?" A tsanake Alhajin ya jinjina mishi kai alamar e, girgiza kai yayi da yanayin rashin sani yace "Kuma a gidan nan Alhaji?" Kafin wani cikin su ya bashi amsa Hajia ta fito daga ɓangaren su Mama da ta shiga duba jikin Sauban dan yau suka dawo daga asibiti, hangen su tsatsaye kamar ba lafiya ba ga tarin mutanen da alamun su ya nuna mata manyan mutane ne yasa ta nufowa wurin dan ta ga ɗanta tare da su, tana zuwa cike da dattijantaka tayi sallama suka amsa sannan suka gaisa, kallon Alhaji Ibrahim kawi tayi ya fahimci kallon nata, cikin nutsuwa da ladabi yace "Hajia, wata suke nema wai Eesha, shine ban gane ba." Murmushi Alhaji yayi yace "Ina ga zaku fi fahimta idan kuka ji daga bakin wannan..." Y faɗa yana ɗan juyawa bayan shi, hakan yasa wani jami'i da suke tare da su dan kare lafiyar su y jinjina kai alamar fahimta tare da juyawa da sauri ya fita waje... Jim kaɗan sai ga shi tare da DG wanfa yayi shiga cikin manyan kaya har da hula. Sa'ad na ganin shi kuma saida ya kalli Sa'ad ɗin dake nesa da su ya mishi wani bahagon murmushi sannan ya ci gaba da tafiya, da sauri Sa'ad ya tunkare su gadan gadan tare da kallon Aisha da har lokacin take tsaye yace "Maza shiga ciki." Ba tare da saɓa umarnin shi ba ta juya za ta shiga, sai kuma ta ɗan yi jim tare da tsayawa tana ƙara gyara tsayuwar ta da leƙa bishiyar mangoron da take ɓoye mata fuskar wani matashin dattijo da ta so ganin wani abu a tare da shi... Take bakin ta ya buɗe, idanun ta suka firfito waje, gabata ya yanke ya faɗi haka ma jikin ta ya ɗauki rawa, ba tare da Sanin tana saɓa umarnin Sa'ad ba ta shiga takowa a hankali kamar wacce ƙafafun ta ke mata ciwo. DG na ganin Aisha na tahowa da sauri ya nuna musu it da yatsa a gigice yace "Yawwa gata can, ita ce waccen, wallahi ita ce." Cak! Ta tsaya inda tsoro ya mamaye ta ganin ana nunota kuma kafatanin kowa ya kalle ta... Raɓa tsakanin Mukhtar da Abida Nuriyya tayi tana baza idanu sosai tana ƙara kallon ainahin kamar *mijin ta Mukhtar* akan ƴar tasu, abu ɗaya da ya bambamta Aisha da mahaifin ta shine idanu ta fi shi kasancewar ta mace kuma irin idanun nan ne masu charme, haka kawai halittar take. Sannu sannu take tunkaro Aisha har ta zo kusan ta, haka shi ma Abbu Mukhtar bayan ta ya biyo yana kallon kamaninshi a fuskar yarinyar, tana zuwa ta tsaya gaban ta da fuskar alhini da kuma hawaye dake kwaranya a idanun ta, hannu ta kai ta shafi kumcin Aisha tana murmushi tace "Eesha, ke ce kika girma haka?" Aisha dai mamaki ne a fuskar ta da son sanin me ke faruwa da ita ne da take jin kamar tana ƙaunar mutanen nan har ma da musu *haukan so*? Musamman wannan matar da taji wani abu da zata iya cewa da *jinin jikin ta ne* ke fizgar ta zuwa ga matar da son ta rumgume ta, Mukhtar ma na zuwa tallabo haɓarta yayi ya ƙurawa fuskar ta idanu, sai kawai wasu hawaye suka kwaranyo mishi, da mugun ƙarfi ya jawo Aisha jikin shi ya rumgume kamar za'a ƙwace mishi ita. Liƙe idanu Aisha tayi gam gam saboda matsar da yake mata ba kaɗan bace, suna haka Aisha cikin sanyayyar murya tace " *Abbu* na kasa numfashi." Dariya ce ta kubce mishi tare da ɗan sassauta mata sannan ya raba jikin shi da nata, kallon fuskar ta yayi yace "Kenan kema kinsan ni ne Abbun ki?" Rarraba idanu ta fara yi, dan ita fa ta faɗi hakane saboda ai babba ne ba zata kira shi da kawu ba, kafin ta ce wani abu Mama Nuriyya ta sa hannaye biyu ta juyo da Aisha zuwa duban ta tana faɗin "Ƴar mu ce mana, wannan Eeshar mu ce, gashi ma kana gani..." Sai kuma ta raunana kallon ta wasu sababbin hawaye na zubo mata tace "Eesha, Eesha..." Sai kawai ta ruƙumƙume Aisha tana rera kuka kamar ranta zai fita tana ma Aisha wata matsa kamar za ta mayar da ita cikin ciki, shi ma Abbu Mukhtar ɗin haka ya saka su jikin shi dukansu ya ƙwaƙume suna ta kukan farin ciki... Matsowa su Alhaji duk sukayi suna kallon su cike da tausayawa, inda Fa'iza ta kalli Abida da ita ma take kallon ta cike da tsana da takaici, dan suna zaune kawai ta ce wani ya kira ya ce an samu labarin Eesha, kuma ta hana su shaƙat ta ce a taho da gaggawa, Sam bata bata wata dama ta aiwatar da wani abun ba, yanzu haka hankalin ta a tashe yake, bata san me ye shirin Fa'iza a kan ta ba, idan fa niyyar ta tona mata asiri ne? Ai da ta sakata a damuwa babba kuwa, musamman ma yanzu da ta fara jin canji a jikin ta har take jin za ta je asibiti a duba ta, idan aka yi sa'a ciki ne da ita shikenan fa ita. Wani shu'umin murmushi Fa'iza ta mata, burin ta ita dama aga yaran, bata so ta tonawa Abida asiri yanzu da wuri haka har sai ta ga inda gudun ruwanta zai tsaya, dan take-taken Abida da wasu abubuwa da take gani, da kuma ganin matashin yaron nan har sau biyu a gidan su, jikin ta ya bata akwai abinda take shiryawa, dan haka zata zuba mata ido ta ga me take son isarwa, ta fi so ta mata *kamun kazar kuku*. Mamaki ne yasa Hajia Kaka dake kallon wannan al'ajabi tace "Wai kun san Aisha ne?" Hajia Radiya dake ta murmushi tana kallon Aisha ne ta kalle ta tace "Hajia, wannan yarinyar ina kyautata zaton Eeshar mu ce." Da sauri Mama Nuriyya ta kalli Hajia Radiya tace "Mamie, ita ce, wallahi Eesha ce, da ita zamu tafi yanzu, ba zan bari ta sake suɓuce min ba." Kamar suɓutar baki Sa'ad dak daf da Alhaji Ibrahim ya kalli Aisha jin an ce za'a tafi da ita yace "A'a, ba zaku tafi da it...." Sai kuma yayi gaggawar yin shiru saboda kallon shi da jama'an gurin sukayi, a hankali ya sunkuyar da kanshi ƙasa ya runtse idanu, Yaya Bilal ne ya nuna Sa'ad ɗin da yatsa yace "Wanene wannan?" Alhaji Ibrahim da ya ji kunyar abinda Sa'ad ɗin ya yi a sanyaye yace "Ɗana ne, shine ya taimaka mata ya kawo ta nan gidan." Jinjina kai Bilal ɗin yayi ya matso kusan shi ya miƙo mishi hannu yace "Kayi ƙoƙari ƙanena, ka kyauta mana sosai." Da ƙyar Sa'ad ya miƙa mishi hannu suka gaisa, Alhaji Ibrahim ne ya kalli Aisha dake kwanc kan ƙirjin Mama Nuriyya ta hana ta motsawa yace "Aisha, ashe ke ƴar babban gida ce?" Alhaji Ahlan ne ya kalle shi da fara'a yace "Alhaji, abubuwa da dama sun faru da ba zamu tsaya tattauna su da ku ba, amma yarinyar nan da ka gani tun tana wata shida a duniya aka saceta daga gare mu, bau sake sakata a idanu ba sai yanzu." Da mamaki Alhaji Ibrahim da Hajia Kaka suka kalle shi tare da jinjina lamarin, Hajia Radiya ce ta jawo hannun Aisha ta tallabo fuskar ta suka kalli juna, dariya sukayi a tare Hajiar tace" Kin gane ni?" A hankali Aisha ta girgiza kan ta sannan tace" Mamie, da gaske kun ahalina? Na kasa yarda da hakan?" Da sauri Mama Nuriyya ta fuskance ta tana faɗin" Da gaske ne Eesha, mu iyayen ki ne, kinga ni c mahaifiyar ki, ni na haifeki Eesha, ga kuma Abbun ki..." Ta faɗa da nuna mata Abbu Mukhtar, sannan ta nuna Alhaji babba tace" Ga kuma Papin ki, sannan ga Mamin ki..." Ta Nuna Hajia Radiya sannan ta ci gaba da nuna mata sauran tana faɗin" Ga Goggon ki, wannan ma haka, ga Baffan ki, ga kuma kawun ki, ga kuma ƙaramin ƙanin ki, Eesha dukanmu nan ahalinki, baki da sama da mu Eesha, ki yarda dan Allah, kin ji." Duk cikin wanda aka nuna mata ta fi kafe duban ta ga Kabil, ƙaramin yaro wanda yayi kama da mama Nuriyya kyakkyawa da shi, a hankali Aisha ta matsa kusan shi ta rusuna gaban shi, hannu ta bashi suka riƙe hannun juna gam, murmushi ta mishi tace" Me ye sunan ka?" Kamar yadda ya saba faɗa a makaranta ya faɗa mata cewa" Kabil Mukhtar Saheeb Ahlan." Tsare shi tayi da idanu na sakanni, sai kuma tayi murmushi ta shafa kan shi tare da miƙewa tsaye, a hankali ta juya ta kalli inda Sa'ad yake kamar gunki, ba wai bai ji daɗin ganin ahalinta bane, sai dai dama ya san suna haɗuwa dole su raba su, Aisha kuma a yanzu za ta girmi matsayin shi ne ta yadda ba lallai ma ya iya jerawa da ita ba, shine fa Dalilin da ya sa *ya ƙi haɗata da su*. A hankali ta tako ta zo gaban shi tace "Ka ji me suke faɗa, ya ka ce *Abbu*? Ka yarda da su? Idan baka amince ba babu inda zan tafi." Da ƙarfi Mama Nuriyya ta sauke wani numfashi ta tsurawa bakin Sa'ad idanu, inda Mukhtar ya ƙara matsowa shi ma amsar shi yake so ya ji, ganin duk shi ake kallo yasa Sa'ad maida hankalin shi gaba ɗaya kan Aisha, a raunane, cikin raunatacciyar murya ya buɗa baki yace "Na yarda mana Eesha." Daga haka bai sake cewa komai ba sai kallon Hajia Kaka da yake kamar ya ce mata tace Dan Allah su barta nan za su kula da ita, muryar DG suka ji daga baya cikin kwaratsi yana faɗin "Aisha ai ba zai iya musawa ba cewa su iyayen ki ne, saboda ya fi ki sanin su dama." Da mamaki aka sake maida kallo ga DG dake maganar har Aisha ma dake hararen shi tace "Kamar ya?" Taɓe baki yayi yace "Kamar yadda kika ji na faɗa, Sa'ad ya jima da sanin ke ƴar wacece kuma yasan inda zai samu Ahalin ki, amma son zuciya da mummunan ƙudirin da yake da shi a kan ki yasa yake ɓoye ki baya so kowa ya san ke wacece." Sama da ƙasa ta sake watsa mishi harara tace" Ƙaryar banza, Abbuna ba zai taɓa min haka ba, da ya san ahalina kafin yau, na tabbata zai haɗa ni da su ba sai sun neme ni ba." Wani murmushi yayi yace" A ganin ki kenan, amma ai gaya nan gaban ki, ya musa abinda na faɗa ya ce ƙa..." Cikin ɓacin rai Sa'ad ya nufe shi yana faɗin "DG ka daina wannan wasar bana so, idan ba haka ba zan raunataka a wurin nan." Alhaji Ibrahim da Sabeer ne suka riƙe Sa'ad ɗin ida Sabeer ke bashi baki "Yi haƙuri abokina, abun bai kai na haka ba ai." Alhaji babba ne ya gyara tsayuwa yace "Ko ma dai me ye, mu alkairi ya mana tunda ya taimake ta, dan haka zamu tafi da ita yanzu." Da sauri Hajia Kaka ta riƙo hannun Aisha ta fashe da kuka tana faɗin "Hasbunallah wani'imal wakil, ƴar rainota, ban taɓa tunanin rabuwar mu da wuri haka, lallai na yarda da ake cewa sabo tirken wawa, Aisha bana so ki tafi ki barni, haka ma Sa'ad." Sa'ad ɗin da Kaka ta faɗa yasa Aisha kallon shi tana ƙanƙance idanu ba ko ƙyabtawa tace" Abbu, da gaske wai ka san komai kafin yanzu?" A rayuwar nan dai bai taɓa tunanin akwai abinda zai tsorata shi ba bare ya kayar masa da gaba, amma sai gashi tambayar Aisha ta jefa shi a wannan halin na tsananin firgici, sai kuma ya shiga rarraba idanu da fargaban amsa mata tambayar nan, baya so ya mata ƙarya, kuma yana tsoron abinda faɗan gaskiyar zai iya jawo masa a wannan halin, shirun shi ne yayi yawa har saida ta sake matsowa kusan shi tana kallon shi jiki a sanyaye tace "Abbu, ka amsa min mana, ko dai gaskiya ya faɗa?" Iska y feso daga bakin shi, sannan ya ɗaga kanshi sosai ya kalle ta ido cikin ido ya furta "E Eesha, da gaske, amma ba gaskiya bane da ya c..." Aisha da ɓacin rai da rashin son ɗaukan raini, a tafashe ta ƙura masa idanu tana mishi wani kallo tace "Da gaske ne? To wace manufa ce gareka a kaina?" Da sauri ya kalle ta yace "Babu Aisha, bana da wata mummunar manufa a kanki sai alkairi, karki yarda da abinda wannan..." Cike da son ƙara hura wuta DG yace "Shin zaka ce baka sa aka mata tiyata ka loda ƙwayoyi a cikin ta bane? Ai ita Aisha da wayon ta, kuma tana cikin hayyacin ta aka mata aikin." A razane Abbu Mukhtar ya kalli DG da mamaki yace "Me? Ƙwaya fa ka ce?" Da sauri Mama Nuriyya ta yo kan Aisha tare da jawo ta kusan ta a rikice ta shiga ɗaga rigar Aisha har tayi nasarar ɗagata ƙasan cibiyar ta ya fito, Mama Nuriyya, Abbu Mukhtar, Yaya Bilal, da Hajia Radiya duk zazzaro idanu sukayi suna kallon cikin na Aisha wanda suka ga shatin dake nuna tabbas ɗinki aka yi duk da ɓaro-ɓaro ba'a gane ɗinki ne saboda kwarewar likitan, sai kuma suka kalli Sa'ad ya ji ya gama sarewa da komai tare da ƙudirin kawai ma ya miƙa kan shi tunda dai dama dole za su raba shi da ita. *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *19* Cike da makirci DG yace "Uhummm! Kun gani, ba na faɗa muku ba." Da sauri Hajia Kaka ta isa gaban DG, shi ai bai ɗauka tsohuwar nan zata iya taɓuka wani abu ba, Shiyasa ko a jikin shi har ta tsaya gaban shi, ɗaga hannu tayi ta dallawa fuskar shi wani kyakyawan tafi tana faɗin "Shashancin banza..." Sai kuma ta dinga nuna shi da yatsa tana cewa "Wa ye kai? Me ye tsakanin ka da shi? Me ya maka a rayuwa da son ganin bayan shi ya zama maudi'inka?" Da irin kallon tsana da takaici yake kallon ta har Sa'ad ya yi gaggawar riƙeta dan shi dai baya son tone-tonen nan a yanzu da ya shiryu, da a baya ne ai ba zai ji kunya ba, dan iyayen shi ma kai tsaye yake faɗa musu gaskiyar magana bare kuma waɗanda basu haife shi ba. Cike da murmushin makirci DG ya shafa kumcin shi yace "Shi ya san waye ni Hajia, ba zan damu ba dan kin mare ni, amma hakan ba zai hanani faɗan gaskiya ba, ƙwarai Sa'ad da ɗaya ogan sune suka sa aka farka cikin Aisha sannan aka loda ƙwayar da nauyin ta ya kai garam (g) ɗa..." Take Aisha ta ɗaga mishi hannu alamar yayi shiru, ai kuwa shirun yayi yana kallon ta har ta matso kusan su tana kallon Sa'ad a kausashe tace" Da gaske ka san da wannan abun dake cikina?" Cike da tashin hankali Sa'ad ya raunana kallon shi gare ta ya furta" Eeshaaaa...." Da sauri ta katse shi da" Ba Eesha ba, gaskiya nake so ka faɗa min?" Kamar zai fashe da kuka kuma kamar zai daketa a hassale da Takaicin DG yace" E hakane, amma ni kasuw..." Cikin tafasar zuci da ƙunar rai Aisha ta jefa mishi wayar da ya bata ɗazun a ƙirjin shi, hakan yasa shi saurin dafe ƙirji sai kuma wayar ta faɗi ƙasa, a kausashe sosai cike da tsana ta furta" *Na tsane ka Sa'ad*." Juyawa tayi a fusace da niyyar zuwa kusa da mahaifiyar ta tace ta gaggauta ɗauketa daga nan, sai Hajia Kaka ta riƙe hannun ta tace" Aisha, kar kiyi haka, alkairi ya miki a rayuwa, kar ki saka mishi da sharri mana." Girgiza kai Aisha tayi ta riƙo hannun Hajia Kaka tace "A'a Hajia, ba sharri zan saka mishi da shi ba, amma Hajia me yasa ya min haka? A duniyar nan taimako na da wahala sosai, kafin na haɗu da shi nayi barar abinci a wurin jama'a amma ba wanda ya bani ko loma ɗaya, daga ƙarshe wasu kallon banza suka dinga min har da min tayin kwana tare da su, a wani gidan kuma korar kare aka min har da sharrin sata, amma *shi*..." Numfashi ta sauke tace" Bai yi wani tunanin komai a kaina ba ya taimake ni, hasalima a lokacin ko sunana bai tambaya ba, Hajia Kaka wannan dalilin ya sa ya cancanci girmamawa a wajena har nake kiran shi da sunan *Abbuna*, dan uba ne kawai zai iya wannan kasadar akan bin da ya haifa." Sai ta karkace a raunane ta ɗora da" To amm Hjia kaka ko ni ban san me ke damuna ba, kema haka baki taɓa sanin ina da fashi a cikina ba, sai shi kawai ya ce sai mun je asibiti, sai gashi dalilin zuwan nan har saida aka sake farkani, shin Hajia Kaka idan ban zarge shi ba me zan yi? Ko ya faɗa miki abinda aka ciro a cikin nawa ne? Ko kuma ni da ke ya nuna mana abinda aka ciro ɗin? A sanina ko ɓari mace tayi ana nuna mata abinda ya fito daga cikin nata dan tasan menene ko kuma a nuna ma wani nata, haka ma idan ciwo ne ana nunawa dan a ga menene, amma ni dai ban iya tuna an gwada mana ba." Kallon Sa'ad Hajia Kaka tayi da tambayoyi fal a ranta, amma kafin ta ce wani abu Alhaji Ibrahim da kunya da nadama suka bakbaye shi ya kalli Sa'ad yace" Na sha gaya maka ka daina wannan banzar ɗabi'ar taka, amma baka saurarata saboda ka raina ni, ga irin ta nan." Aisha ya kalla ya ɗan dafa kanta yace" Kiyi hakuri kinji ƴar rainon Hajia, zan iya kiran haɗuwar ki da Sa'ad a matsayin mummunar *RUBUTACCIYA*." Matsawa yayi inda Aisha ta bishi da kallo tana ayyana _" Ya kuwa san yadda take ji akan Abbun ta?"_ Kusan Alhaji babba ya karasa sukayi magana da babu wanda ya ji, daga haka sukayi musabiha ya nufi hanyar shigewa ɓangaren shi, da kallo Sa'ad ya bishi kamar ya ƙwala ƙara koma duk ya fita ran shi, fata kawai yake a barshi da DG a wurin nan yayi ƙuli-ƙulin rakiya da shi a gidan nan. Da wani sabon makircin na son ganin ya kai Sa'ad ƙasa DG ya kalli Alhaji babba yace "Alhaji, ina ga da mun sa jam'i..." Hannu Alhajin ya ɗaga mishi fuska a gimtse, saida ya fara zura hannu ya jawo Aisha ya runguma ta jikin shi tare da sumbatar kan ta, sannan ya kalli mutanen wurin yace "Koma me ya faru mu alkairi ya mana, abinda kake faɗa kula zan sa a bincika min, idan da gaske ne zan bar hukuma tayi aikin ta, yanzu kuma zamu tafi da Eesha, dan dama ita ta kawo mu gidan." Daga haka ya kalli Hajia Kaka yace "Mun barku lafiya." Juyawa yayi da Eesha jikin shi da ta juyo tana kallon Sa'ad da ke bin ta da kallo kamar zai fashe da kuka, sai kuma ya sauke huce tare da kawar da kan shi, duk sallama suka ma Hajia Kaka da ita ma ta juya tana kasa amsawa tana jin dacin wannan rabuwa da suke yi da Aisha da bata taɓa zaton za su yi irin ta ba. Sannu sannu sai idanun shi suka fara ƙyabtawa da sauri sauri kamar yadda idan ran shi ya ɓace yake yi, yana kallo duk suka juya suka dinga shiga mota har suka gama shiga tsaf amma DG na tsaye gaban shi, saida suka fara fita daga harabar gidan DG ya matso kusa da shi yana murmushi yace "Oga kenan, ya Kaga wasan? Shin ban faɗa maka ba dama sai na ƙwaceta daga gare ka?" Sai kuma ya haɗe fuska yace "Karka ɗauka a nan aka zo ƙarshe, ka ci gaba da taka tsantsan, dan ba zan barka ba har sai na ga shari'a ta yi hukunci a kan ka, sannan kuma..." Ya faɗa yana ɗan juyawa kaɗan sannan ya kalle shi yace "I zuwa yanzu na san kaa fahimci girman matsayin ta, kuma ko ban faɗa maka ba nasan kasan yanzu ta fi ƙarfin ka, Eesha Mukhtar Saheeb Ahlan, a yanzu dai ko tsilin gashin ta ba z aka iya taɓawa ba." Da dai kam fuskar shi a haɗe take sosai yana kuma tafasa da jin ya kai mishi naushi, to amma a yanzu ban da wannan kuzarin saboda tafiya da kaso ma fi tsoka da Aisha tayi na daga cikin kuzarin na shi, dan haka ya ƙirƙiro murmushi mai ciwon gaske cike da ƙwarin guiwa Sa'ad yace "A ganin ka kenan, amma idan nayi niyya zan ga Eesha sanda nake so, kuma har na taɓa jikin ta a lokacin da nake so." Wata dariya DG ya ɗauke da ita irin ta haukan nan kafin ya tsagaita yace "Eesha dai? Ka kuwa san a inda take rayuwa? Ka taɓa zuwa fadar Ahlan ka ga a inda suke tasu rayuwar...?" Girgiza mishi kai yayi da dariya a fuskar shi yace "Kar ka ɗauka gidan su kamar irin naku ne, Sa'd idan ka shiga gidan su Eesha, za ka rantse da Allah baka taɓa shiga gida mai blocx na simitin ba, gida mai ƙofa biyu cike da jami'an tsaro, falo huɗu, jimillar ɗakuna ashirin da huɗu, fafaɗan tabkin ninƙaya, gidan gona ɗauke da mabambamta dabbobin da ake kiwo, ga kuma matsakaiciyar guardin mai fitar da kayan marmarin da kai sun isheka ka kafa kasuwanci, ma'aikata goma sha huɗu dake aikin kula da gidan, a haka, kake jin zaka iya ganin ta duk sanda ka so? Bayan tsaurara mataki da sukayi tunda suka rasa yaran su guda biyu." Girgiza mishi kai yayi tare da kai hannu zai dafa kafaɗar shi, wani arnan kallo kawai ya mishi da ya saka DG fahimtar me yake nufi, sai kawai ya maƙale kafaɗa alamar oho tare da juyawa yace" Sai sun sake haɗuwa." Kallon ƙeyar DG ɗin Sa'ad yayi ya ɗan fara takawa yana faɗin" Na san idan na faɗa maka zan zama *siriki* a wannan gidan ba zaka yarda ba, amma zan sa hakan ta yiwu har ka yarda ni Sa'ad zan zama *miji* ga wannan *ƴar*... In sha Allah, sannan daga ƙarshe, kai zan ce ka kula, daga yanzu zan fara buga lissafina a ciki naka ne, DG ba zan bari ka sha iska a doron duniyar nan ba har sai naga ka fara gudanar da sabuwar rayuwar ka a maƙargama." Yana faɗa mishi haka kawai ya raɓashi a sukwane ya bar gidan gaba ɗaya ba tare da tunanin yaushe zai sake dawowa ba dan wacce ke daw da shi gidan kullum bata nan. Da kallo DG ya bishi yana mamakin kalaman shi, sai kuma ya taɓe baki ya kalli wayar da Aisha ta jefawa Sa'ad din, sai kawai ya juya shi ma ya bar gidan yana tunanin Sa'ad bai da lafiya da yake tunanin zai auri Aisha bayan duk abinda ya faru. *Tun* daga lokacin Aisha ta fara cin karo da abubuwan mamaki daga gurin Ahalin nata, yadda kowanen su ke ta kira yana sanar da ƴan uwa da abokan arziƙi an ga Eesha, da kuma jin yadda suke amsa addu'a da ameen Ya matuƙar bata mamaki, sai Hajia Kaka da ta ji na waya tana amsawa da _"In sha Allah, ita ma bamu cire rai da ganin ta ba a ko yaushe, yadda muka ga Eesha a kusa da mu, muna fata zamu ga Kuwailat haka."_ Ta shiga tunani da tambayar kanta to me ya sa aka raba su da iyayen su? Shin wanda yake ɗauke su ba ya da imani ne? Bai taɓa haihuwa bane? Me iyayen ta suka masa da zafi haka? Da hukuncin su dole ya zama raba su da ƴaƴan su ne har guda biyu? Shiyasa yanzu da suka ganta suke ta naniƙeta a jikin su musamman ma mahaifiyar ta da ƙyar ta yarda ta koma jikin Hajia. *Duk* da za ta iya cewa da ɗan wannan haɗuwar ta mintuna, da kallo ɗaya kuma ta ɗan fahimci kamar akwai wanda basa son lamarin ta, wato kowa ya rumgume ta a jikin shi har da sumbatar ta hatta da kawun ta Sabeer, amma sam ban da matan nan guda biyu da suke binta da ido kawai, sai wacce aka ce ita ce matar farko ga Yayan mahaifin ta (Fa'iza) kawai dake mata murmushi ta ɗan shafi kan ta kaɗan. Ta taɓa shiga jirgi, dan a cikin shi ta zo wannan ƙasar, amma bata taɓa ganin jirgi mai zaman keɓantattun mutane ba sai yanzu da suke sararin samaniya zuwa na su garin wanda ma fi aksari mota ake hawa, daidai wannan lokacin ne iskan da take shaƙa da jin ta a duniyar gajimare ya bata damar tuno da Abbun ta da ta baro a can, me ya sa yayi haka? Me yasa ya ɓoye mata abubuwa dayawa? Kenan bai da niyyar sadata da danginta? Kenan so yayi ya siyar da ita? Ko ma ya kashe banza ba mai tayar da maganar? Me yasa? Me yasa? " *Me yasa Abbu?*" Har saida maganar zuci da take ta fito fili duk na kusa da ita suka jime ta ce, da sauri Mama Nur ta dafata cike da kulawa tace "Eesha? Lafiya? Me yake damunki?" Sororo ta kalle ta, sai kawai ta girgiza kai tayi murmushin yaƙe tace "Ba komai... *Mamie*." Murmushi Mama Nur tayi ta ƙara riƙe hannun Aisha gam har saida Aisha ta kalle ta sai kawai tayi murmushi ita ma ta sake maida duban ta ga taga. Cikin ƙanƙanin lokacin da bai zarta awa da rabi ba suka isa gidan su bayan tarbar su da aka yi, anan Aisha ta sake kallon ikon Allah tana kuma gode mishi, ashe anan aka haifeta, anan tayi watanni shida da haihuwa, amma rashin imani da tsoron Allah ya sa aka ɗauketa ta rayu a inda take kwana a gadon ƙarfe mai yaloluwar katifa, ta rayu a wurin da kullum suna cin abinci ne dan maganin yunwa ba dan daɗi ba. Maganar da Abbu Mukhtar yake so yayi da Fa'iza ta sa ya kalli mai aikin su da duk suke nan dan taya su murnar ganin Aisha yace mata "Mama *Laura*, dan Allah ki tafi da Eesha ki nuna mata ɗakin ta, tayi wanka ta yi sallah kafin anjima." Da girmamawa dattijuwar ta amsa da "To yallaɓai..." Take kuma ta kalli Eesha tace "Muje *Hajia ƙarama*." Wani kallo Abida ta ma mai aiki, sai ta ji zuciyar ta ta sake yin zafi kamar za ta ƙone, amma sai ta dake kawai ta yi murmushi, Aisha dake riƙe da hannun ƙanin nata Kabil tare suka tafi yana mata hira tana amsawa, burin shi dai ta je ɗkin shi ya nuna mata kayan wasan shi. Ganin haka yasa Sabeer da Bilal duk motsawa da niyyar su ma su samu su yi sallah isha'i, dan magariba tun a Maraɗi sukayi gidan aminin Alhaji da ya tarbe su tun zuwan su kuma ya haɗasu da drebobi da motock aka tuƙo su. Cikin dakakkiyar murya Abbu Mukhtar ya kalli Fa'iza da ita ma ta juya za ta nufi nata ɓangaren yace "Fa'iza..." Ƙwarai da gaske gaba. ta ya faɗi sosai har saida duk tsigar jikin ta ta tashi, a hankali ta dakata sannan ta juyo à sanyaye tace "Na'am." Sai kuma ya kalli Yaya Bilal a tausashe yace "Ka yi haƙuri Yaya, ba zan ci gaba da ɓoyewa ba, musamman a yanzu da na samu ƴata ɗaya, dan na gaji da zama da muke da *makashinmu*, ɗan uwa Bilal, ina so ka sani matarka Fa'iza nake zargi da ɓatan yarana guda biyu, saboda wasu dalilai masu ƙarfin gaske." Babu wanda ya razana ba jin furucin shi, dan ko da akwai masu zargin ta babu mai niyyar yi mata wannan fallasar, kawai dai kowa yayi shiru ne a zuba mata ido an san dubun ta zata cika wata rana, a kiɗime Yaya Bilal yake kallon shi da tsantsar mamakin da babu algus a ciki yace "Mukhtar, kasan me kake faɗa kuwa? Matar tawa?" Ya kai maƙura ne, dan haka ya kalle shi tare da jinjina kai yace "E ɗan uwa, ita dai." Cike da dattako Alhaji ya kalli Mukhtar ɗin yace "Uban Kabil, kayi shiru ka ji, ka bar maganar, zamu tattauna anjima." Sai kuma ya kalli Fa'iza da zaka rantse sassaƙata à kayi a wurin yace "Fa'iza, je ki sashen ki kin ji, je kuyi sallah." Da sauri Abbu Mukhtar yace "A'a Abbu, dan Allah ka bari muyi maganar nan." A ɗan kausashe Yaya Bilal yace "Wace irin magana zamuyi Mukhtar, matata ? Kake zargi da sace yaran ka? Me cece hujjar ka?" Ajiyar zuciya Abbu Mukhtar ya sauke yana kallon fuskar Yaya Bilal ɗin sannan yace "Kowa a gidan nan ya san Rabi Fa'iza kaɗai take ma aiki, nesa da sukayi yasa ta bar aiki anan daf da haihuwar Eesha, amma a daren da ta zo mana barka sai muka nemi Eesha muka rasa, sannan su Hajia sun ce ta zo da cikin da suke ta mamakin dama da ciki ta bar gidan nan, tun daga haka kuma su dai basu ji labarin haihuwar ta ba, sai zuwan da tayi kwanakin baya ne take faɗa ma su Hajia wai abinda ta haifa bai zo da rai ba. Bayan duk wannan Yaya Bilal duk damuwar da muke shiga ta ɓatan yaran nan ko a kwalar rigar matar ka, sannan ranar da aka ce a bayar da sanarwa, wataƙila ta manta ne ko kuma wata manufar da ban tasa tayi haka, ita ce ta faɗa mana a saka cikakken sunan Aisha Mukhtar Ahlan, wanda muna hanya yanzu na tambayi Aisha ta ce a gidan marayu haka ake kiran ta, sannan..." Sai kuma ya kalli Fa'izan dake kallon shi ga da ga sannan yace" Ita fa ta zo mana da labarin wani ya kira ya ce an samu inda Aisha take, ita ta jagorancemu har inda yake sannan ya kai mu gidan da Eesha take, shin dukanku bakuyi mamakin yadda mutumin yana ganin Fa'iza ya gane ita ce ba sannan yake girmama ta? Ta ya mutumin da ya kira lambar ta ne kawai ya san *wacece* ita a cikin mata huɗu da muka tafi da su? Sannan me yasa *sai lambar ta aka kira*? Bayan kuma a lambobin da muka bayar wanda za'a iya kiran idan an samu masaniya ko lambar *uwar da ta haifi Eesha* babu." Ƙwarai maganar shi ta kama hankalin su har suka shiga kallon Fa'iza irin suna jira su ji ta bakin ta, shi kan shi Yaya Bilal da yayi niyyar kare mutumcin ta da iya ƙarfin shi sai ya samu kan shi da zuba mata idanu yana jira ya ji me za ta ce? Ganin kow ita yake kallo da tuhuma har da Abida da ta saje a cikin su sai hankalin Fa'iza ya sake tashi ta shiga rarraba idanu cikin ɓarin murya ta shiga faɗin "Eee..haba...Abbun Kabil, ni me zai sa na sace yaran...nan? Wal..." Da hannu Abbu Mukhtar ya dakatar da ita tare da faɗin "Dakata Fa'iza, nan babban gida, kuma muna girmama ki matsayin ki na matar babban Yayanmu da muke kallon shi uba gare mu, ba wai nayi haka bane dan ina so na ɗauki fansa ko a hukunta ki ba, kawai nayi magana ne dan kisan mun san ke ce sannan ki kiyaye, dan wallahi yanzu duk abinda ya samu ɗaya daga cikin yarana, na rantse da Allah zan ɗauki mummunan matakin da ba zai yiwa bawa daɗi ba." Yana gama faɗin haka ya juya a fusace ya bar falon, da kallo duk suka bishi har ita Fa'iza, sai Yaya Bilal da ya matso kusa da ita yan binta da wani kallo yace" Fa'iza, abinda zaki min kenan ni da ahalina?" A hankali ta girgiza mishi kai kamar za ta yi kuka tana faɗin" A'a Bab, wallahi ban aikata komai ba, ba gaskiya bane abinda kuke zargina, ta ya kuke tunanin zan iya aikata haka gare ku? Wallahi ban aikata ba." Sabeer dake maka mata harara ne ya ja tsaki yace" To idan zargin ki ne ake ki wanke kanki mana." Kallon shi tayi sai kuma ta jinjina kai ta kalli su Hajia tace" Mamie, dan Allah Mamie ki sa baki, wallahi ban aikata komai ba Mamie, Abbu..." Tsawa Yaya Bilal ya daka mata yace" Shiru dallah malama! Idan ƙarya aka miki ki musa mana..." Sai kuma ya girgiza kai cike da takaici yace" Kin ban mamaki Fa'iza, ban taɓa tunanin zaki iya aikata haka ba." Raɓata yayi zai wuce d sauri ta riƙo hannun shi tana fashewa da kuka da cewa" Bab...bani na aikata ba, na yarda nayi wasu kurakurai, amma wallahi don taimakon ahalin nan ne, daidai da rana ɗaya ban taɓa tunanin cutar da mutanen gidan nan ba, matsala ta kawai *da na san mai hannu a ɓatan yaran kuma nayi shiru* da bakina saboda wata manufa, amma zan faɗa muku gaskiya Bab, dan Allah kar kayi hushi da ni." Gyara tsayuwa yayi alamar yana so ya ji me zata faɗa, hakan yasa Abida fahimtar Fa'iza fa na shirin ɓallo mata ruwa, ai daidai Fa'iza na buɗa baki tace" Ranar da aka..." Sai kuwa Abida tayi luuuuuu! Ta faɗi ƙasa tamkar wacce ta suma da gaske duk da kuwa ta ji bala'in ciwon faɗuwar, amma haka tayi gaggawar dakatar da tafiyar numfashin ta sa'ilin da aka yi caaa! A kan ta ana salallami da jimami da kuma son bata agaji. Da sauri Yaya Bilal ya ɗauketa ya kwantar a kan kujera yana murza tafin hannun ta da kiran sunan ta a nutse, da kulawa Hajia ta dube shi tace "Bilal, ka kira likita mana ya zo ya duba ta." Da sauri ya jinjina kai sai kuma Sabeer yayi azamar ciro wayar shi yace "Bari na kira Zeinab." Da gaggawa ya aika kiran, jim kaɗan kuma ta ɗaga yake sanar da ita abinda yake faruwa, da tabbaci ta ce mishi tana zuwa ba da jimawa ba, jugum-jugum sukayi babu mai magana sama da minti sha biyar kafin Dr. Zeinab ta iso gidan, kai tsaye ta shigo babban falon a taƙaice kawai suka gaisa da mutanen ta nufi inda Abida take, gwajin da duk ya kamata tayi mata ta mata har da ɗaukar jinin ta akan yatsa sannan ta sadashi da inda za'a fayyace halin da jinin nata yake ciki, hatta ciki idan tana da za'a iya ganewa ta wannan awon dan abun gwajin babba ne na gaske. Kafin sakamakon jinin ya bayyana ne ta kalli Yaya Bilal ɗin da duk hankalin shi ke tashe tace "Gashi kuma ba jinin ta bane ya hau." Sai kuma ta kalli Abida da ta farka take ta lumshe idanu tace "Kan ki yana ciwo ne?" Girgiza mata kai tayi a hankali alamar a'a, ɗorawa tayi da "Jiri fa?" Cikin kwantar da murya kamar mai ciwon gaske Abida tace "Kaɗan kaɗan nake ji yanzu." Murmushi Dr. Zeinab ɗin tayi tare da ɗauko gwajin tana faɗin "OK, bari mu ga me gwaji..." Kasa ƙarasa maganar ta tayi ta dubi Yaya Bilal dake kallon ta shi ma, sai kuma ta kalli Abida tana murmushi tace "Barkanmu Ahalin Ahlan, amma kafin na faɗa..." Sai kuma ta kalli dukkansu sannan tace "Zaku bani goron albishir." Da azama Yaya Bilal yace "Zeinab, me yake faruwa da Abida?" Miƙewa tayi tsaye tana faɗin "Oga, Abida fa ta fara nauyi." Hajia da Alhaji ne suka zaro ido da ɗumbin mamaki, lokaci ɗaya kuma farin ciki ya baibaye su jin wannan abu da suka ɗauki shekaru suna nema ido buɗe, musamman ma Yaya Bilal da ya rasa inda zai saka kan shi dan farin ciki da rashin tunanin ganin wannan rana rayuwar shi. Farin ciki mai sunan farin ciki an gan shi a wannan iyali, Abida na ganin kulawa tamkar babu gobe, riritawa take samu daga wajen kowa a gidan nan, musamman da ta zama macijin ƙaiƙayi ce sari ka noƙe, a wajen ire-iren su Mama Nuriyya ganin su sakawa Abida da alkairin da ta musu na nuna kulawa tamkar wajibi ne a gare su, dan haka kowa ke bayar da tashi gudummuwar. Yayin da Abbu Mukhtar kuma duk ya watsar da lamarin matan Yayan nashi ya shiga nemawa Eesha magani, da fari aikin da aka mata ne yasa shi zuwa dan a tabbatar mishi tana lafiya, sai kuma gwaji ya nuna ƴaƴan hanjinta sun yi kusa da samun matsala sakamakon abubuwan da aka saka mata a ciki, wanda dama masu irin hakanan kasada ce suke yi da rayuwar su, wasu ma kafin wannan aikin diyya ake basu su bar wa iyalinsu. Bai faɗawa ko ita kan ta Aisha ba haka suka fita ƙasar waje suka sake ganin ƙwararren likita, daga nan aka ɗorata magani har tsawon wata uku, bayan nan su sake komawa dan ganin ci gaban da aka samu. Wannan abu da ya faru sai Fa'iza ta zama kamar mujiya a gidan, ga dai mai laifin na samun kulawa da riritawa, amma ita sai kowa yayi gefe da ita hatta mijin nasu kan shi ya ƙaurace mata a komai ma, su Hajia kaɗai ke mata kara da kawaicin amsa gaisuwar ta da yi mata magana idan ya zama dole, sai kuma Aisha da Kabil da basu san me ke faruwa ba, dan Fahad ma ba'a batun shi da ba zama yake a gidan ba, dan kuwa lamarin shi yana ƙaa girma ne lalacewa na ƙara zuwa mi shi kamar mai shafar aljanu. *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes. *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata. Sayen na gari mai da kuɗi gida, sai an gwada akan san na ƙwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a ƙasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI- SIRRIN MANYAN MATA)._ _Bismillahir-rahamanir-rahim._ *20* *WATA UKU* da tafiyar Aisha komai ya lalace mishi, gida ba dadi waje ba daɗi, mahaifin shi ya daina kula shi gaba ɗaya ma, yanzu ko ɗan faɗa da rigimar nan sun daina, haka ma Hajia Kaka da yake jin daɗin zama da ita ta canza mishi, sai kuma mahaifiyar shi da ta tsiro da wasu sababbin halaye na zuzuta Ahalin Aisha har ma take faɗin _"Ai da na san yarinyar nan tana da alaƙa ta jini da Ahalin Ahlan, wallahi tallahi da ban bari an tafi da ita ba sai na sa ka aure ta."_ Sosai ya fahimci maman shi kenan auren jari take so ta mishi, auren ƙwarya ta bi ƙwarya, a wata ukun nan ya gane yana mugu-mugun son yarinyar nan da gaske, ƙwarai take hana shi sukuni har ya gagara nutsuwa a baccin shi, sunan *Abbu* shi ya fi komai tsaya mishi a rai, narkakkun idanun ta wanda ya ga irin su a fuskar mahaifin ta, da kuma tatausan muryar ta sanda take mishi ƙiriniya. Amma abun da ke ɗaga mishi hankali shine idan ya tuna ranar da ta kalli fuskar shi ta furta mishi cewa ta tsane shi, hakan dagula mishi lissafi yake, kiɗima tunanin shi hakan je yi, wani lokaci har ya fara sakin layi bai sani ba, dan abun da bai kai na rigima ba sai ya dinga masifa yana neman bala'i ido rufe. A ƙarshe kawai sai ya ji ba zai iya zaman garin nan ba, take ya haɗa kayan shi kawai ya sanar da ƙanin mahaifin shi Alhaji *Hisham* cewa yana zuwa zai zauna tare da su. *Bayan* zuwan shi can ya samu canjin yanayi da ruwa da ma abinci, sai dai damuwar shi na nan tare da shi, hasalima wata sabuwar damuwar da ta kunno mi shi kai wato *Fadila*. Ƴa ce ga ƙanin mahaifin shi, shi da zai ganta a hanya ma kafin zuwan shi nan ba zai gane ta ba, amma daga zuwan shi yarinyar nan da bata wuce 17 ba take ta ta ƙoƙarin shiga jikin shi tana son samun kusanci da shi, komai dai *Yaya Sa'ad*, abinda ya fahimta game da haka kuma a zahiri shine *son shi take*, yayin da shi kuma neman sassaucin soyayyar wata ne ya kawo shi garin su har ma take mishi wannan rawar kan. Ba ma ita ba, kawun shi ne a gaban shi yanzu da ya fuskanci kamar yana ɗan yawan damuwa, wanda damuwar ta haifar masa da hawan jinin da yake ganin likita duk sati biyu zuwa wata ɗaya, ya tambaye shi sau ɗaya bai faɗa mishi komai ba, hakan kuma ya kasa haƙura duba da yana damuwar fiye da kima. Dan haka yanzu ma ya sake tunkarar shi da maganar, amsa ɗaya da ya bashi ita ce _"Kar ka damu da damuwata Sa'ad, domin kuwa bata da magani, kawai kai da ka tayani da addu'a Allah ya gafarta min zunubin dana aikata a baya."_ *Zunubi*? Zunubi? Wane zunubi Kaxun shi ya aikata a rayuwar shi haka da ya dame shi? Ko da yake kowane bawa mai aikata saɓo ne, na wani kawai ke fin na wani girma, dan haka zai tayashi da addu'a Allah ya gafarta mishi, kamar yadda shi ma addu'ar shi bata wuce _Allah ya mantar da shi Eesha idan ba alkairi bace a gare shi, idan kuma alkairi ce Allah ya kawo ƙarshen matsalar shi da ita da Ahalin ta_, addu'a ta gaba kuma d yake yi ita _Allah kawo ranar da zai ga ƙarshen DG_, dan duk da yana wani garin yanzu haka bai daina samun labarin shiga da ficen shi ba, kuma wannan burin yana da shi na ganin ya gurfanar da shi ƙasa wanwar. ******************* Tana zaune kan kujera da ƙaramar carbin ta tana ja ɗaya daga cikin masu kula da ɓangaren su ta shigo da sallama falon nata, a sanyaye ta amsa tana waigawa, ganin ita ce kawai ta dawo da dubanta tana ci gaba da abinda take, tana zuwa mai aikin ta durƙusa gaban ta tace "Sannu da hutawa Hajia?" A tsanake ta amsa da "Sannun ki, lafiya ?" Da ladabi mai aikin ta miƙomata enveloppe ɗin hannun ta tace "Yallaɓai ne ya ce na baki wannan, sannan na gaya miki sun tafi Amerika, kuma ba zasu dawo ba sai Hajia Abida ta haihu." Kamar wacce bata gane yaren na mai aikin ba take kallon bakin ta, ganin dai ita ma mai aikin na ɗan kallon ta yasa da mamaki tace "Wane yallaɓan ne ya baki?" A ladabce tace "Hajia Yallaɓai dai naki." Wani mamakin ne ya sake baibaye ta, to ita fa tasan Bilal baya garin nan, yau kwana huɗu kenan da tafiyar shi Singapour wai zai je duba kamfanin Alhaji a yadda ya faɗa mata, to yaushe ya dawo? Ko da yake zai iya yiwuwa turowa yayi, dan haka tace" To wa ye ya kawo saƙon?" Mai aikin dai da rashin gane mahimmancin tambayoyin tace" Shine da hannun shi ya bani." A ɗan razane tace" Ya baki? Yaushe?" " Yanzu, yana bani suka fita ni kuma na taho kawo miki." Cewar mai aikin, girgiza kai Fa'iza ta dinga yi alamar gigicewa ta kalli enveloppe ɗin tace" Shi da kan shi? To yaushe ya dawo? Kuma shine bai neme ni ba?" Da mamaki mai aikin tace" Hajia...ai Yallaɓai a gidan nan ya kwana." Kasa magana Fa'iza tayi sai kallon bakin ta kawai a ranta tana nanata a gidan nan ya kwana? Tafasar da zyciyar ta ke yi yasa kawai ta mata alama da hannu cewa ta tashi, miƙewa mai aikin tayi za ta fita sai kuma Fa'iza ta ɗan juya tace" Ina ya ce miki zasu tafi?" A ladabce ta bata amsa da" Amerika, wai sai ta haihu zasu dawo." Shiru Fa'iza tayi har saida ta ji fitar mai aikin da sauri ta miƙe tana ɗaukar wayar ta dan kiran lambar shi, abun mamaki tsaf ta dinga kiran shi sai kiran ya dawo alamar dai ya jefa lambar ta a baƙin jadawali. A haukace ta jefa wayar a kujera ta ɗauki enveloppe ɗin ta shiga buɗewa da sauri. Kuɗi ne a ciki ba ko naira ko cfa ba, dollar ce ya aiko mata ba tare da ko gajeran saƙo ba, rashin sanin me kuɗin ke nufi? Me shirun shi ke nufi da ita yasa ta faɗawa kan kujera ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, saida ta ci kuka abun ta ta ƙoshi ta shiga ɗakin ta, *niyya* ɗaya ta sata shiga a wannan lokacin, shine zata tattara kayan ta ta tafiyar ta, to amma Abida fa, wacce ita ce mai laifin? Sannan kullum Habaici take mata ita ta iya takonta, sannan ba zata yarda ta ƙare a asararriya ba kamar ita, dan haka ma ta nemawa kanta mafita. Abubuwa uku suka sa ta canza wannan ƙudirin, *na farko* shine: Abida da zata bari gidan ta ci karen ta babu babbaka, na *biyu* kuma ba ita ce mai laifin ba Abida ce, na *uku* ma bata so asirin Abida ya tonu yanzu, dan Abida makira ce ta ƙarshe, dan haka dole sai tayi taka tsantsan wajen kawo ƙarshen tuggunta, idan da haka ba zata sake ruftawa da ita a banza, dan haka sai ta sa kowa ya san wacece ita sannan idan ma barin gidan ne su bar shi tare. ******************** Hankali tashe Hajia *Soueiba* ta dinga bubbuga ɗakin Sa'ad kasancewar basu da wani ɗa namiji babba da zai iya taimaka musu, Fadila ita ce babbar ƴar desu bayan wacce suka fara haifa ta rasu, shi ma d ai hankalin nashi ne ya tashi dan daga jin bugun ƙofar yasan ba lafiya ba, ai ko y ana buɗewde cikin kuka take cewa "Sa'ad muje dan Allah ka taimaka min mukai Alhaji asibiti." Da sauri ya juya bayan shi ya kalli agogo data nuna mishi ƙarfe 04 saura kaɗan, sai kuma ya sake kallon ta da girmamawa yace "Me ya samu kawun? Bashi da lafiya ne?" Cikin rashin nutsuwa tayi gaba zata wuce tana faɗin "Daga ya shiga ban ɗaki zaiyi alwala ya yanki jiki ya faɗi, muje da sauri dan Allah?" Bai ƙara ɓata lokaci ba ya fito daga ɗakin tare da jawo ƙofar ya rufe ya bi bayan ta, dake mutum ne shi mai tsayi amma babu jiki, dan damuwa ma duk ta ƙara zabge shi ya fita hayyacin shi kamar wanda baya ci yana ƙoshi, haka Sa'ad yayi jarumtar tallabar shi da ƙyar ya saɓa a kafaɗa suka kai shi mota, Fadila ce ta buɗe muu mota dan basu da mai gadi sannan ta rufe duk gidan ta koma ciki dan kula da gida da ƙannenta biyu kamar yadda Hajia Soueiba ta bar mata sallahu kafin su ga abinda hali ya yi. A taƙaice said yayi *kwana huɗu* asibiti, anyi sa'a da ya farfaɗo babu shanyewar ɓarin jiki, dan haka likitocin suka sake jan kunne kan a tsananta kula da shi, duk da ba gari ɗaya bane saida mahaifin Sa'ad da Hajia suka zo duba shi, a ranar Alhaji ya koma Hajia kuma ta kwana biyu sannan ta tafi, har lokacin gaisuwa kawai ta haɗata da Sa'ad, sai Fadila data kula tana shiga lamarin shi sosai shi kuma yana share ta, ta ji a ranta cewa zata iya yin wani abu a kai, ko ba komai tana son Sa'ad kuma tana ƙaunar sa da shiriya sosai, amma har ta tafi babu wanda ta faɗa ma ƙudirin nata bare a sani. Sosai yake kula da shi tamkar shi ya haife shi, yana wuni gidan tare da shi yana taimakawa Hajia Soueiba wajen jinyar shi, yana kuma ganin mutane kala kala dake zuwa waje shi dubiya, a hakane kwana tara da faruwar wannan abu da dare ya fita masallaci tare da autan gidan *Marwan*, yana dawowa ya tarar da baƙon da bai taɓa tsammanin wani a jihar Maraɗi ba ma ya san shi bare a nan ɗan garin da kawun shi ke aiki, ganin *Hambali* a gidan nan ya matuƙar kiɗima shi da jefa shi a lisafin me ya haɗa kawun shi mutumin arziki da Hambali? A ina suka san juna? Me ye tsakanin su? Damuwar kawun na da alaƙa da Hambali ko sana'ar shi? Ya shiga ruɗani sosai fiye da tunanin mai tunani, har saida ya samu dakali ya zauna ya dafe kai, dan baya so ma su haɗu da Hambali bare kawun ya san shi ma ya san shi. *Ƙara* duban shi sosai Hambali yayi cikin nutsuwa yace "Alhaji Hisham, me yasa ba zaka manta da abun nan daya faru ba ka fuskanci gaba kawai? Ni banga abun ɗaga hankali a ciki ba, laifi aka maka ka kuma ɗauki fansa, to sai me? Me ye na damun kanka har kana neman ka kashe kanka a banza, bayan kuma iyalinka suna buƙatar ka a raye, ko manta da haka ne?" Kanshi na kallon ƙasa ya girgiza kai a sanyaye yace" Ba zan iya mantawa ba Alhaji Hambali, abinda na aikata a baya sharrin sheɗan ne da ruɗin zuciya, hukunci na yanke cikin hushi wanda yanzu shi ke barazanar kawo ƙarshen rayuwata, me yasa na yi haka? Me yasa na cutar da wacce bata ji ba kuma bata gani ba? Me yasa na zalince ta? Bayan kuma bata san komai ba ma daya faru? Me yasa zan ɗauki fansata a kan ta?" Ɗan tsaki Hambali yayi irin na jin haushin nan sannan yace" Ai fansar da ka ɗauka ta dace da muhallinta, tunda wanda kayi dan shi yana fama da wannan raɗaɗin har yanzu, ko kasan ahalin Ahlan suna fuskantar ƙuncin rayuwa da rashin walwala saboda abinda ka aikata?" Cikin ƙunar zuci da dana sanin kuskuren nashi ya ɗago ya kalle shi a kausashe yace" Ba dan taimakawar ka ba, ni nasan da ban iya aikata komai ba ga wannan iyali, Hambali, zan iya cewa tarayya ta da kai asara ce, bata ƙare ni da komai ba sai dana sani, ka sani ina ta neman afuwar Allah akan abinda na aikata, ina nan kuma ina bibiya har sai naga na sake dawo da wannan farin cikin da na zama sanadiyar dakushewar shi ga ahalin arziki kamar wannan, kai kuma... Ka sani lokaci ne zai maka nashi hisabin, kai da ƴar ka duk zaku girbi abinda kuka shuka da yardar Allah." A hankali ya miƙe tsaye jiki ba ƙwari yayi tsaye yana kallon shi yace" Na roƙeka daga yau kar ka sake zuwa gidana, dan bana son sake wata mu'amala da kai." Da mamaki Hambali ya tashi tsaye yana kallon shi yace" Hisham, ni kake kora a gidan ka? Har kake cewa baka son sake ganina?" Kallon shi kawai yayi bai ce uffan ba dan bai da lokacin ɓatawa, jinjina kai yayi cike da gargaɗin nan tare da miƙewa tsaye yace" Shikenan, zaka san ni ka wulaƙanta, ka sani na taimake ka a lokacin da ka nemi taimakona, ba biyana kayi ba bare ka raina min wayo, kamar yadda babu wata riba da naci dangane da hakan." Ya juya zai tafi Alhaji Hisham yace" Kai ko ka ci riba, ko ka manta kai ka kawo shawarar yadda za'a yi? Sannan kaima kayi hakane dan farin cikin ƴar ka da son zuciyar ka, Alhaji Hambali, kamar yadda na faɗa maka tarayyata da kai asara ne, dan ai daga baya na fahimci kawai anfani kayi da ni wajen cimma burinka a wajen mutanen wannan gida." Yana gama faɗin haka shi ma ya juya ya shige ciki ya bar shi nan, da kallo Hambali ya bi shi sai da ya ɓacewa ganin shi sannan ya nufi inda motocinshi suke da masu tsaron dake take mishi baya. Har suka fita daga gidan basu haɗu da Sa'ad ba, saida ya ga fitar su ya tashi ya shiga ciki, a saman kujeran cin abinci ya hangi kawu na cin abinci, Hajia ya ma sannu da hutawa ya yi hanyar nufa wajen kawun, Fadila ma da fara'ar ta na son ɗaukar hankalin Yayan nata t mishi sannu da zuwa, da murmushin yaƙe ya amsa mata ya wuce inda zai tafi kawai. Yana zuwa daga tsaye yace "Kawu, ina so zamuyi magana?" Kujera ya nuna mishi yace "Bismillah Sa'ad." Saida ya ja kujerar ya zauna sannan ya kalle shi yace "Lafiya Sa'ad ? Me ya faru?" Ba alamar wasa ko kaɗan ya kalle shi shi ma yace "Kawu, dama kasan Hambali ne?" Da mamaki ya kalli Sa'ad ɗin tare da cewa "Hambali kuma?" Jinjina masa kai yayi yace "E kawu, wanda na gan ku tare, kuma yanzu ya fita daga gidan nan." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya aje cokalin abincin shi tare da ture farantin gaban shi ya fuskanci Sa'ad sosai sannan yace "Na gane wanda kake magana a kai, na san shi Sa'ad, hasalima zan iya ce maka na san abubuwa dayawa a kan shi, kuma ban san abubuwa dayawa a kan shi ba." Da yanayin shiga damuwa da ƙanƙance idanu har da saurin maganar da yake yi idan ya shiga tashin hankali ko ɓacin rai yace" Amma kawu me ye haɗin ka da shi? Hambali fa ba mutumin arziƙi bane." Da mamaki sosai kawun ya kalle shi yace" Sa'ad, ka san shi ne? Ya aka yi ka san ba mutumin kirki bane?" Ɗan maƙale kafaɗa yayi da rashin gaskiya yace" Kawu na san shi ne kawai a bakunan mutanen gari, amma dan Allah kai me ye ya haɗaku ? Kawu ina tsoron abinda zai iya zama shine silar haɗuwar taku?" Numfashi kaxu Hisham ya sauke ya sake duban Sa'ad da yadda yaga ya rikice sosai sai yake ji a ran shi kamar tsantsar kulawa yake bashi, dan haka a tausashe yace" Sa'ad, shekaru sha bakwai da suka wuce na aikata wani kuskure da a yanzu ya zamar min tashin hankali da barazana a rayuwata, da na sani da ban aikata abinda Hambali ya izani na aikata ba, da na yi dogon tunani da ban bi abinda zuciyata ke raya min na aikata ba a wannan lokacin, amma bayan na *raba hanta da jini* sai na kasa samun sukuni, har yau da nake maka maganar nan bana da kwanciyar hankali, bana isashen bacci, bana cin abinci cikin salama duk saboda tunanin *ina yarinyar take*? Me take yi? Hannun wa take? Na gari ko mugu? Shin ta mutu ne? Wani abun ya cinyeta tun a inda muka jefar da ita...?" Ƙasa yayi da kan shi cikin yanayin matsanancin tashin hankali ya sunkuyar da kan shi yana shasheƙar kuka har da hawaye, sosai Sa'ad ya fahimci abun mai girma ne kuma mai tayar da hankalin kawun na shi, dan haka ya miƙe tsaye ya rusuna gaban shi ya ɗora hannun shi a cinyar kawun cikin rarrashi yace "Kayi haƙuri kawu, barin matsalar nan a zuciyar ka ba shine maslaha ba face ya ci gaba da girmamar da damuwa a gareka, ka tattauna hakan da ni idan ka yarda zan iya taimaka maka da wani abu, dan Allah kawu, ka faɗa min abinda ya faru, wataƙila na taimaka sosai wajen fitar da kai daga matsalar nan, duba da nasan waye Hambali, kuma kawu sani na sosai ba sanin shanu ba. Kallon shi yayi, sai ya ji zuciyar shi na samun nutsuwa da gamsuwa akan ya faɗa wa Sa'ad din abinda ya faru, nauyayyan numfashi ya sake saukewa sannan ya mishi nuni da ya koma ya zauna, kallon shi yayi yana share ƙwallar idanun shi sannan yace "... *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes. *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata. Sayen na gari mai da kuɗi gida, sai an gwada akan san na ƙwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a ƙasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI- SIRRIN MANYAN MATA)._ _Bismillahir-rahamanir-rahim._ *21* Kallon shi yayi yana share ƙwallar idanun shi sannan yace "Shekara sha bakwai da ta wuce ai kun samu labarin haɗarin da maman Fadila tayi ko?" Jinjina kai Sa'ad yayi cike da kulawa yace "E kawu, haɗarin da yayi sanadiyar rasa abinda yake cikin ta." Shima jinjina kai yayi da gamsuwa yace "To wannan abu da ya faru shi ya ja komai, lokacin da Maman Fadila ta matsa min tana so taje Agadez bikin Yayar ta data haihu ban yarda ba, saboda lokacin tsohon ciki ne jikin ta wanda muke saka mata ran haihuwa a kowane lokaci, amma sai ta shiga damuwa da ɓacin rai wanda ni kuma bana son hakan, dole na haƙura na amince ta tafi tare da sauran ƴan uwan ta, sun isa lafiya kuma anyi suna lafiya har ma suka fara shirye shiryen dawowa, suna gobe zasu taho da sassafe da mukayi waya ta ce min zata je wajen kitso da lalle dan tana so ta dawo min kamar amarya, na bata izini ta tafi cikin farin ciki, tayi lalle da kitso har tayi wasu siyayya a hanya duk dan zata taho washe gari, amma Allah bai nufi hakan ya kasance ba, duk lokacin da na ga kiran Soueiba sai gabana ya faɗi da tunanin ta haihu ne, dan mahaifiyar ta ma da suka je saida ta kirani tayi ta faɗa me yasa na barta ta je a wannan halin? Hakan yasa nake saka rai dayawa da a kira a ce min ta haihu, amma wannan kira da aka min daf da magrib sai aka ce min idan na samu lokaci naje an mata aiki ne sannan abun bai zo da rai ba. Na shiga tashin hankali sosai Sa'ad na rasa inda zan saka raina, a lokacin ƙaramin ma'aikaci ne ni da albashina ba wani bane, gashi ina so na isa wajen matata akan lokaci, dole na ranto kuɗi na biya jirgi dan shi kaɗai zai kai ni gareta da gaggawa, na je...sai dai na samu Soueiba da raunika a jikin ta bayan aikin da aka mata aka ciro yaron, kasan me ya faru?" Ya tambayi Sa'ad da gaba ɗaya ya zuba mishi idanu yana kallo, girgiza kai yayi a hankali alamar a'a sannan ya ci gaba da cewa" Sai lokacin aka sanar da ni haɗari tayi a hanyar ta ta dawowa gida, wani mai mota ya kaɗeta, sannan...abin..." Sai kuma kuka ya so cin ƙarfin shi said ya dakata ya sauke numfarfashi kafin ya kalle shi yace" Abinda yake cikin ta ma buguwar da yayi ce ta zama silar fitowar shi babu rai, dan hoton da likitan ya nuna min na yaron ya nuna min yadda kan jaririn daga gefe ya faɗa sosai kamar zaiyi rame, ya tabbatar min ko da ya rayu zai wahala ne mu ma mu wahala, dan ba tabbacin ƙwaƙwalwar shi zata kasance cikin ƙoshin lafiya, abun takaici da baƙin ciki, abunda ya ɓata min rai har ya saka ni aikata abinda na aikata yanzu shine, babu wanda ya kaɗeta a wurin, yana ina? Wai sai aka ce min _"Kasancewar shi ɗan babban gida kuma babban mutum, zaman shi anan ba tsaro kuma labari zai iya yaɗuwa kan abinda ya faru, amma ya bar maƙodan kuɗin da za'a kula da lafiyar ta har ta warke."_ Wannan magana ce Sa'ad? Ka buge mata mai tsohon ciki, amma saboda rashin sanin darajar ɗan adam ka ce wai ba zaka ko tsaya ka duba ta ba? Wannan abu ya ɓata min rai ƙwarai da gaske, hatta kuɗin da aka yi ragowa na aikin ta Maman ta ta bani wai mu koma gida ban karɓa ba, kuma wallahi kuɗin sun isheni na ja jari, to amma fa ɗana na rasa da lafiyar matata. To a inda muka haɗu da Hambali shine zamu fita daga asibitin ya tsayar dani muka gaisa sai ya bani katin shi ya ce na kira shi zamuyi muhimmiyar magana, ban yi ƙasa a guiwa ba wajen kiran shi bayan na kaɗaita, daga yadda na fahimta baya ƙaunar wannan ahalin, sannan ƴar shi ma dake aure a gidan ba dan Allah take zaune a can ba, sannan alamu sun nuna ko ta ina Hambali yana bibiyar rayuwar mutanen nan ne, Shiyasa ma ya san da labarin wannan haɗarin, ya sake rura min wutar tsanar su da ƙiyayya, ya nuna min an ci zarafina ne dan ban da ƙarfi, dan haka zai tsaya min na ɗauki fansa, dama raina a ɓace yake, a hassale nake da abun har lokacin, sai ban yi tunanin komai ba kawai na amince, kasan me muka shirya?" Sa'ad dai dake kallon shi girgiza kai ya sake yi alamar a'a dai, dan haka ya sake numfasawa yace" Alhaji Mukhtar Saheeb Ahlan, shine ya banke matata kuma yayi tafiyar shi, ashe a lokacin shima ta shi iyalin tsohon ciki ne da ita, dan a ranar da muka haɗu da Hambali yake ce min ta haihu dan a ranar da muka bar asibiti ranar aka yi suna, ya tunzurani kan mu sace ƴar shi shima sai ya ɗanɗani zafin rabuwa da ɗan da kake so, na amince da shawarar ɗari bisa ɗari, ya nuna min shi kawai taimaka min ne zai yi ya jagoranci abun, amma ni ne mai bayar da umarni kuma shugaban aikin, da jami'in da basu yi tsammani ba muka ɗauke yarinyar daga gidan dan lokacin ba wani ƙwaƙwaren tsaro kamar yanzu, lokacin... Lokacin da na kalli yarinyar dake ta kuka tana son mamanta, na ji tausayinta har na ce ma Hambali a mayar da ita kawai zamu ɗauki fansa ta wata hanyar, yadda ya hana a lokacin da yadda ya dinga nuna min, sai kawai na ji a raina shima dai akwai wata manufar a zuciyar shi game da haka, da amincewar mu aka yi nesa da yarinyar daga mahaifarta zuwa wata jaha da basu tsammani, madadin na samu salama na aikata abinda nake ganin na kyauta, sai na rasa nutsuwa daga lokacin, na nemi zaucewa saboda mafarkai da kullum sai nayi, ko dai naga yarinya na kuka, ko mace na ta kuka ko mutane dayawa ma, a lokacin da taimakon Allah dana Soueiba ne na fara dawowa hayyacina, dan saida malamai suka shiga lamarina, cewa suke jifa ce, ture ne, shiga gaba ne, amma ni nasan menene kuma na ƙi faɗa musu komai... Kwatsam watanni kaɗan da suka wuce na ga labarai ana neman wannan yarinyar, kayan da aka zayyana dake jikin ta lokacin ni nasan ita ce, to amma kuma *wa ya sace ta biyun*? Ya ake so iyalin nan suyi da rayuwar su? Shin ba'a san rasa ɗa ɗaya bama na iya sa mutum ya kauce hanya ko ya haukace? Bare kuma guda biyu? Ni ubangijin da ya bani shi ne ya karɓi abun sa, na kasa haƙuri da Ƙaddarar har na kauce hanya, ina ga su da yara biyu kuma mata, sannan basu ga gawar su ba bare ma su kwantar da hankalin su, shin ya ake so suyi ne da ransu? Ya mahaifiyar su take ji? Wane irin hawan jini ne zai kamata?" Iska ya feso daga bakin shi tare da dafa kafaɗar Sa'ad yace" Ɗana, ka ji abinda na aikata, da le zaka iya taimaka min?" Ya shiga ruɗani sosai, amma Wani irin dace da aka yi kasa kawai ya yi gefe da ruɗanin yana wasu tunanin na daban, kenan Hambali ƴar shi na aure a gidan su Eesha? Zai iya yiwuwa ita ma ba ta ƙwarai bace kamar uban? Ko da yake kawu ya faɗa, to ya zaman Aisha a yanzu? Idan kawun shi su suka ɗauke Yayar Eesha, to wa ya ɗauke ita kuma Eesha? Tabbas dai a gidan nan akwai bara-gurbi. D hanzari Sa'ad ya kalle shi yace "Kawu, ka kwantar da hankalin ka, ka ci gaba da neman gafarar Allah, a yanzu ba abinda kake buƙatar kamar samun yafiyar mutanen nan, idan suka yafe maka zaka samu nutsuwa, bugu da ƙari idan aka ga yarinyar." Da mamaki mai cike da tsoro kawun yace "Yafiyar su? Ta ina zan gansu? Da wane ido zan kalle su Sa'ad? Ba zan iya ba." "Zaka iya kawu." Ya faɗa yana tsare shi da idanu sannan ya ɗora da "Zaka iya Kawu, yadda ka faɗa min komai yanzu haka zaka faɗa musu, babu abinda zai faru kawu." Zuba mishi ido kawai yayi yana kallo kafin yace "Kai kuma a ina kasan Hambali?" Kallon kawun yayi, sai kawai ya mishi murmushi yace "Karka damu Kawu, zan sanar da kai idan lokacin ya yi, bari na barka ka huta, amma dan Allah ka cire tunanin nan a ranka, na maka alƙawarin komai ya kusa tafiya daidai da izinin Allah." Jinjina kai kawun yayi yana murmushi yace "Na yarda da kai Sa'ad." Murmushi ya sake mishi ya juya ya fita da sassarfa da kuma abubuwa dayawa a kan shi yana saƙawa da kuma niyyar sai ya cimma su da yardar Allah. *A gurguje*: an ƙara shafe watanni kusan biyar da wannan magana tsakanin Sa'ad da kawu Hisham, a wannan lokacin da aka ɗauka Sa'ad ya sake bibiyar abubuwa dayawa da kuma ƙara sanin wasu abubuwan masu mahimmanci, zai iya cewa yayi nasara ta kowane ɓangare, sai dai abu ɗaya da ya kasa samun koda makama ɗaya wato neman Kuwailat da ya saka kan shi, dan haka ya shirya dan zuwa garin da masoyiyar shi take, wanda a bayanan da ya samu Aish ta koma makaranta abun ta sannan tana farin ciki a cikin ahalinta. Yayi sallama da kawu tare da faɗa masa ya zama cikin shiri, idan har abinda ya sa a gaba ya tafi daidai, to zai kira shi ya je dan neman yafiyar Ahalin nan, ya bishi da fatan sa'a da son dacewa dan shi kan shi ya samu salama. *AHALIN AHLAN* Cikin rufewar ido da ɓacin rai na kai wa maƙura akan wulaƙancin da Yay Bilal ɗin ke mata ta kalle shi wanda shigowar shi kenan gidan bayan watannin da suka kwashe a ƙasar waje dan haihuwar Abida tace "Na rantse da Allah sai ka sanar dani zaman da nake a gidan nan, haka kawai zaka maidani wata ƴar iska da ban san me nake ba, me na maka Bilal? Dan bana haihuwa ne ni zaka min wannan wulaƙancin? To ka sani wallahi ba'a canzawa tuwo sunan shi." Kasancewar ya fita sabgar Fa'iza saboda abubuwan da ta aikata, sai ya wurga mata harara yace "Aikin banza, ke baki san ƴan duniya sun ma tuwo suna iri-iri ba? Wasu da *gagare* suke kiran shi, wasu kuma da girmamawa zaki ji sun ce *Mr. President*, yayin da wasu ke ce mishi *mai gida*, wasu kuma da izgilanci zaki ji sun ce *Mudi*, shine har zaki wani ce wai tuwo sunan shi tuwo." Malalacin murmushi tayi tace" Na sani, amma ba a kaina nake magana ba, akan ka nake magana Bilal." Da mamaki ya dube ta yana gyara tsayuwar shi yace" Me kike nufi?" Nan ma murmushi ta mishi ta gyara tsayuwar ta ita ma har da ɗan gyara ɗan kwalin ta sannan tace" Ka auro Abida ne dan ta zo ta haifa maka yara saboda kana ganin ni na kasa, amma shekara nawa muka ɗauka tare da Abida babu wacce tayi ko ɓatan wata? Sai yanzu ne Abida zata zo maka da rainin hankalin wai tana da ciki har ma ta haihu? Hmmmm! Bilal, Abida anfani take da son ganin kai ma ka zama Baba, shiyasa take rainawa kowa hankali dake gidan nan." A ɗan fusace kuma a kausashe ya nufe ta yana faɗin" Me kike nufi Fa'iza ? So kike ki ƙalubalanci ubangiji da ya fara bata kafin ke? Ko kuma wani ƙudirin ne a kan ki game da haka?" Baya ta ja kaɗa dan yayi kamar zai kai mata duka ne tace" Ko ɗaya, ni a wa da zan ƙalubalanci mahaliccina? Ina so ne dai na maka hannun ka mai sanda, kuma ƙiris ya rage ayi walƙiya halin kowa ya fito fili." Taɓe baki yayi ya bita da wani ƙasƙantaccen kallo yana faɗin" Tabarmar kunya kike so ki naɗe da hauka, Fa'iza kin gama fice min a raina gaba ɗaya." Sunkuyar da kanta ta fara yi a tausashe tace" Kamar yadda zaman gidan ka ya jima da fice min a raina Bilal, ina zaune ne kawai dan bana so a kirani da butulu, bana so a zargeni da guje maka lokacin da kake buƙatata." Baya ya ja yana ƙare mata kallo sama da ƙasa yana dariya yace" Ke dai? Ke har kina da bakin da zaki ce zaman gidana ya fita ranki? Me kika nema kika rasa anan? Me ye baki fi ƙarfin shi ba Fa'iza?" Murmushi ta mishi tace "Hakane, amma ka sani dukiya ba ita ce jin daɗin duniya ba, idan so samuna ne nima a ce ina da yarana, amma indai da kai zan ƙare rayuwa, to bana tunanin zan ga wannan ranar." Ƙanƙance idanu yayi yana kallon ta da mamaki sosai yace "Me kike nufi?" Saida ta kalle shi ba alamar tsoro tace "Ina nufin *kaine baka haihuwa*..." Duk da ta kai ƙarshe saida ya ɗaga hannu ya wanke fuskar ta da zazzafan marin da ya saka ta tangaɗawa baya kamar za ta faɗi, kafin ta samu ta dire kan ƙafafun ta cak tana kallon shi dafe da kumcin ta, cikin hargagi da kaushin murya ya fara faɗin"... *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes. *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata. Sayen na gari mai da kuɗi gida, sai an gwada akan san na ƙwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a ƙasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI- SIRRIN MANYAN MATA)._ _Bismillahir-rahamanir-rahim._ *22* Cikin hargagi da kaushin murya ya fara faɗin "Fa'iza, iskanci da fitsarar ki ta kai haka dama? Ni zaki kalla ki ce wai bana haihuwa? Me kike nufi da maganar ki? Kina so kai tsaye ki ci zarafina ne? Sannan ki aibata ɗan da ko suna ban raɗa mishi ba daga haihuwar sa, me yasa Fa'iza? Wacece ke? Akan me? Kin aikata babban laifi, amma duka gidan nan muka saka miki ido muna kallon ki, shin kenan ba kara bace muka miki? Shine har zaki gaya min wai bana haihuwa, ko kin san da zan iya shari'a dake akan wannan furucin naki?" Da maɗaukakin mamakin dake neman halaka ta ta dube shi tace" Ni ka mara? Bilal saboda na faɗa maka gaskiya?" A tsaurare yana zaro idanu yace" Kuma zan sake wanka miki wani marin kika sake furta maganar banza a kaina ko iyalina." Hawayen da suka gangaro mata tasa tafin hannu ta shafe tare da yin murmushin laɓɓa tace" Shikenan, ka sani ban yi auren duka da kai ba, kuma ba zan sake kwana a gidan ka ba dan na lura a makance kake da abubuwan dake faruwa, amma duk ranar da ka gane gaskiya, na san zaka neme ni da kanka, amma ba zan kasa maimaita maka cewa *baka haihuwa ba*, Bilal matsalar daga gareka take, kai ma kuma fargaban hakan yasa ka ƙi yarda shekara da shekaru muje asibiti, amma ni nayi gwajin lafiyata ba da sanin ka ba, kuma ina zaune gidan nan ne dan kawai *ina son rayuwa da kai*." A hassale ya yarfa mata hannu yana faɗin" Ki tafi mana, ki tafi nace Fa'iza, sai me? Zan gagara rayuwa ne idan kika tafi? Kuma in dai nine ki sa ran ki a inuwa, na rana ɗaya ba zan sake tunawa dake ba bare har na sake maimaita kuskuren da nayi a baya na sanin ki da nayi a rayuwata, ki tafi, ki fi ruwa gudu." Ƙwarai kalamanshi suka soke ta, duk son ta da zaman gidan nan ko dan ta kawo ƙarshen Abida abun ya faskara, ba zata sake kwana ba bayan wannan kalamai da suka fito daga bakin Yaya Bilal, dan haka ta tafi a guje zuwa ɗakin ta, shi ma a fusace ya fita daga ɗakin nashi zuwa falon Abida da suka dawo tare ɗauke da santalelen yaron su. Shigar shi ke da wuya Aisha ma ta shigo falon, bayan kyau da ta ƙara da sheƙi da fatar ta keyi wacce Mamanta ta ɗorata a salon shafa mayuka masu gyara jiki kamar dai ita, har da ƙiba ta ƙara ga kuma wayewa da ta samu a ƙanƙanin lokacin nan. Sanye take da abaya kalar ja mai duhu mai duwatsu sosai da kallabinta ta yane kanta da shi, sai takalmi masu tudu da sukayi kala da rigar tana goye da jakar makarantar ta a baya sai babbar wayar ta a hannu, cikin nutsuwa tayi sallama kusan mutanen falon suka amsa. Idanun Mama Nuriyya na kanta har ta ƙarasa kusa da ita tana kallon inda Abida ke zaune kan kujera Hajia Kaka ta gama mitar ta ƙi zama kan katifa wai ita ai a ƙasar waje ta haihu duk ba buƙatar wannan al'adun, da fara'a Aisha tace "Aunty ina wuni, ya baby?" Saida ta ma Aisha wani kallo mai kama da harara, kafin ta kawar da kanta a yatsine ta amsa da "Lafiya lau, gaya nan yana ta bacci." Ba tare da damuwar komai ba Aisha ta maida duban ta kusa da mamanta tace "Mamie, na gama shiryawa zan tafi, sai na dawo." Hannunta Mamie ɗin ta riƙo a hankali ta jawo ta kusa da ita sannan ta rumgumata jikin ta, cike da kulawa da ƙauna ta shafa bayan ta tana faɗin "Ki kula da kan ki Eesha, dan Allah ki dawo da wuri." Ɗagowa Aisha tayi a tsanake ta zuba idanun ta a fuskar maman nata cike da ƙauna ita ma tana murmushi tace "Zan dawo Mamie, in sha Allah." Sake tallabo kumatunta tayi da hannaye biyu ta manna mata sumba a goshi sannan ta sake ta, murmushi Aisha tayi tace "Nagode Mamie, saina dawo." "A dawo lafiya." Mamie ta faɗa tana kallon Aisha data nufi inda Hajia ke zaune, tana zuwa ta ɗan rumgume Hajiar tana faɗin "Mammie sai na dawo." Da fara'a Hajia ta shafa bayan ta tace "A dawo lafiya, ki bige mana jarabawar." Dariya Aisha tayi tana ficewa a falon bayan tabbacin da ta bata na zata ci in sha Allah, a ƙofar falon ta samu dreba na jiran ta ya faka motar yana zaune ciki, fitowar ta tasa da sauri ɗaya jami'in da Abbu Mukhtar ya ɗauke shi kawai dan fita tare da Aisha a duk inda zata je saboda a kullum gani yake za'a ƙara raba shi da ita ya buɗe mata mazaunin baya ta shiga ya mayar ya rufe sannan shi ma ya buɗa gaba ya zauna, a hankali yake tura hancin motar har suka fita daga makeken gidan. ******************* Ƙara riƙe rigar shi tayi gam tana girgiza kai cike da shagwaɓa tace "Ni dai wallahi a'a, haka kawai kana so a ce ina saka aiki, kawai ni ka bari zan yi da kaina, idan wani ya gani fa to?" Murmushi kawai Alhaji keyi yana kallon ƙafafun da take ta dirawa ba ta ko jin nauyin cikinta da ya tsufa yake wata na takwas yace "To ni nace wani ya ganni ne? Kuma me ye a ciki dan na taimakawa amaryata? Ke baki ga halin da kike ciki bane." Turo baki tayi gaba tana faɗin "To ai dai zan iya da kaina ko." Girgiza kai yayi shi ma yace "Ban yarda ba, ina zaki iya ɗaukar wannan katifar ki kai falo?" Cikin jin haushin da tunda ta ɗauki ciki ya zama sabon ta ta saki rigar shi ta ja baya tana ɓata rai tace "To shikenan, na fasa kwana a falo ma." Dubanta yayi da kyau sai ya matsa da niyyar jawo ta jikin shi, ƙara ja baya tayi tana faɗin "Karka taɓani ni, kawai ka bar shi." Sake matsawa yayi kusanta dan yasan le hakan ke nufi yace "Wai har kin yi hushi?" Da sauri ta kalle shi ta galla mishi harara sannan ta juya a hankali ta shiga takawa zata bar ɗakin, murmushi yayi ya bi bayan ta yace "Kinga to zo ɗaukida kan ki, shikenan?" Ba fa alamar wasa tace "Ka bar shi fa nace na fasa." Dariya yayi ya bi bayan ta har suka isa falo ta zauna kan kujera tare da miƙe ƙafafun ta, tsugunnawa yayi gaban ta yana kallon fuskar ta ya riƙe hannun ta yace "Haba mana Ummu, kiyi haƙuri kin ji, indai nine na daina gardama dake daga yau, shikenan?" Ƙala bata ce mishi ba kuma bata saki fuskar ta ba alamar ta huce, jinjina kai yayi yace "Shikenan tunda ba zaki haƙura ba, bari na kira Mama na sanar da ita kina hushi dani..." Duk da ya kai ƙarshe da sauri ta kamo hannayen shi ta hana shi tashi tana turo baki tace "Shikenan to na daina hushin, kasan da Mama na iya ɗauke fuskata da mari ba ruwanta fa." Komawa yayi ya durƙusa yana shafa cikin ta da bai da wani girma sosai, ko dan tanada tsayi ne? Ko kuwa dai girma ne abinda ke cikin ta baya da? Amma ba dai rashin ci ba, dan alhamdulillah tana ci sosai sai dai idan bata ga abin cin ba. Cikin rarrashi yace "To yanzu na ɗauko miki katifar?" A hankali ta ɗaga kai alamar e, miƙewa yayi yana murmushi ya nufi ɗakin, ƙarar da wayar shi tayi yasa shi da ita suka kalli wayar, agogo ta kalla dan ita dai tasan dare yayi sosai, shaf ta manta da mai kiran shi a kullum a wannan lokacin, saida ya dawo yana ɗaukar wayar tare da cewa "Ke ma dai, har sai kin kalli agogo? Bayan kinsan Jabir ne." Sai kuma tayi murmushi tace "Hakane fa?" Ɗaga wayar yayi suka shiga gaisawa a tsanake shi da Jabir wanda tun tafiyar shi kafin Alhaji Kabir ya kwanta bacci sai ya kira shi ya mishi saida safe, haka kuma gari na wayewa a nan zai kira ya mishi ya tashi lafiya ko da can wajen su dare ne, hakan yasa Alhaji Kabir na ƙara ƙaunar Jabir ɗin, shaƙuwa kuma ta sake shiga tsakanin su kamar dai ɗa da uba. Ganin hirar tasu na yin tsayi dan a yadda ta kula labarin abubuwan dake faruwa game da karatun shi yake bashi, kuma cikin nutsuwa da bashi kula yake sauraren shi, inda ya kamata ya bashi shawara sai ya bashi, inda kuma taimako zai mishi sai ya ce zai yi kaza, saida suka gama hirar su tsaf kafin ma Jabir ya ba wa Aliyu wayar ya gaisa da mahaifin nashi shi ma, lokacin kuma har Ummu ta ɗauko katifar ta fara shinfiɗa, dan kwana biyun nan ne bacci a gado baya mata ɗaki, shine wata mata a wajen awo ta bata shawara ta jaraba kwana a katifar ƙasa. ****************** Wani sabon mamakin ne ya sake lunluɓe tsohuwar har ta riƙe haɓa tana kallon shi tace "Mu'azu, da gaske wai takanas ta Kano ka ɗauko hanya ka zo nan dan kawai ka ga ko Jabir yana nan? Bayan ni na faɗa maka ban gan shi ba nima." Sunkuyar da kai yayi a ladbce yana shafa kanshi yace "Ba haka bane Ayya, wallahi na damu ne sosai da ɓacewar Jabir ɗin, abu kamar wasa fa kun ga har ana neman shafe shekara da barin shi gida, shine da muka yi magana da aminina Alhaji Hisham yake faɗa min ko dai yana wajen ku, ta yiwu kuna son horani ne, shine kawai sai naga bari na zo bazata, wataƙila haka ɗin ne." Taɓe baki tayi tace" To ai ko in gaya maka ka tabka asarar kudin mota Mu'azu, dan Jabir kasan ko karan hauka ya cije shi ba zai zo inda nake ba, dan haka ka je can ka nemi inda ɗan ka yake." Tana gama faɗa masa haka ta miƙe tayi ɗakin ta tana mitar ba dai Jabir ba Alka, kar ma ya ɓata mata rai tana zaman zamanta mana, da kallo ya bita, sai zuciyar shi ke raya mishi wai ita da gaske bata damu da ɓatan yaron shi ba? Yaro kamar Jabir mai nutsuwa da hankali, a ce an neme shi ɓat an rasa, kuma shi ba ƙaramin yaron da za'a ce ya ɓata hanyar zuwa gida, kenan yanzu idan ya fahimta dai *shi ya rasa Jabir*? Tunda gashi hatta da kakanin shi babu wanda yake ko da kiran shi ya ji y nan ina ? Ko da yake laifin shi ne. ******************** Tsaf ta kammala jarabawar t ta fito tana goya jakar ta a baya, har ta tunkaro mota jami'in tsaron nan ya buɗe mata ƙofa kanta a ƙasa tana duba wayar ta, saida ta zo daf da motar ta ji muryar da ta jima bata ji ba, muryar da take yawan hana ta sukuni, muryar da zata iya cewa tayi kewar mai ita sosai, kuma muryar wanda take jin haushi idan ta tuna abubuwan da ya mata, idan ta auna su a sikeli sai ta ji ranta ya ɓace ƙwarai, sai ta dinga ganin komai kawai ya tafi ne yadda ya tsara shi. Cikin wannan tattausan muryar tashi yace "Barka da fitowa." Tsayawa tayi saboda jinin jikin ta da taji duk ya tsinke gaban ta kuma ya faɗi, saida ta ɗauki sakanni a haka kafin ta iya ɗaga kanta sannan t kalli inda ta fi jin sautin. Saida ta wara idanunta saboda ganin Sa'ad tsaye ya jingina a mota ya harɗe hannayen shi yana mat wani irin kallo mai ma'anoni da dama, murmushin da bata san da zuwan shi bane ya kubce mata, ba wani abu da y canja a tare da shi, sai ma kamar ramewa da ta ga yayi kaɗan, amma dai magana ta gaskiya yana nan a dogon shi kuma kyakkyawa, baya ga haka ya ci ado cikin ɗanyen boyle kalar bleu mai haske ya mishi kyau sosai musamman ma ɗinki daya kasance irin na ƴan zamani. Tuna cewa tana hushi dashi yasa ta kawar da duban ta izuwa gefen shi kaɗan tana haɗe fuska irin ohon nan, Sa'ad kuma daya fahimci ma'anar sai y saki murmushi ya fara takowa inda take, lura da hakan yasa jami'in nan saurin shiga tsakanin su yana ƙoƙarin tare shi, a daƙile tace da shi "Ka bar shi, na san shi." Jinjina kai yayi tare da kaucewa daga gabanta, sai kuma ta ɗan juy kamar za ta tafi tana mai jin kunyar abinda ta aikata, saida ya zo daf da ita ya tsaya cikin sigar zolaya da tsantsar farin cikin ganin ta yace "Abbun ake juya ma baya? Anya ana neman tabarruki a wurin nan." Da ɗan sauri ta juyo tare da kallon shi fuskar ta a haɗe sosai tace "Na kira ka Abbu ne lokacin da nake ganin alfarma ka min, daga lokacin da na gane tarkon ka ne ya kama kurciya na janye wannan suna mai daraja da na baka." Ba alamar y damu da maganganun ta ya ɗaga kafaɗa yace "OK, to yanzu wane sunan aka bani? Ina so na fara sani kafin doguwar magana." Saida ta sake ƙura mishi idanun ta da har yanzu suna nan yadda suke kafin tace " *Sa'adu* mana, ko ba shine sunan da baka so ba?" Kallon ta yayi yana gyara tsayuwa da murmushi a fuskar shi, wato wata irin katafariyar rigima ce yake hangowa à idanun Aisha, wai ƴar nan da yake ma tsawa yana cewa ta daina kiran shi Abbu, ita ce yanzu ke kiran shi da mafi munin sunan da baya so, da fara'a ya zuba hannaye aljihu yace mata "Na ji, na kuma ɗauka tunda daga bakin ki ya fito, yanzu kin san me ya kawoni?" Fuskar ta a gimtse ta bashi amsa da "Idan ma baka faɗa min ba ai zan tambaye ka, dan bana son magana da kai." Saida yayi kalar serious sosai yana kallon tsakiyar idanun ta kamar yadda ita ma take kallon shi sannan yace " *Ina sonki*, na zo ne dan na faɗa miki haka, sannan na *nemi auren ki* idan kin amince." Wani galala ta kalle shi, bata san Dalilin da ya sa a ƙasan zuciyar ta take jin wani abu mai kama da murna da farin ciki ba? Bata san me yasa ta ji dariya da murmushi na son kutsowa su bayyana a fuskar ta ba? Amma ɓacin ranta a kanshi sai ta sake basarwa ta haɗe fuska tamau tana kallon shi ta rumgume hannayenta a ƙirji tace "Allah sarki, to idan fa ban yarda ba? Ta ya ka bari har sheɗan ya maka wannan bahaguwar saƙar da mugun zare? Sa'adu ko a mafarki ka ga haka bai kamata ka jefi sheɗan ba sannan ka gyara kwanciyar ka?" Murmushi ya sakar mata tare da zaro hannun shi ɗaya yace"... *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes. *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata. Sayen na gari mai da kuɗi gida, sai an gwada akan san na ƙwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a ƙasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI- SIRRIN MANYAN MATA)._ _Bismillahir-rahamanir-rahim._ *23* Murmushi ya sakar mata tare da zaro hannun shi ɗaya yace "Zaki yarda ne Eesha, ban zo dan na koma ba har sai na samu amincewar ki." Girgiza mishi kai tayi a tausashe tace "Kayi haƙuri, gaskiya ni yarinya ce ma ban isa fara soyayya ba, ni yanzu karatu ne a gabana dan shine burin iyayena a kaina, kuma ko zan fara soyayya, to ba da kai ba." Tana gama faɗin haka ta juya zata tafi, da kallo ya bita fuskar shi a haɗe yace "Zan zo gidan ku anjima." Da sauri ta juyo ta kalle shi da mamakin jin wani sabon ƙarfin hali daga gare shi, sai tayi murmushin da ya saka Sa'ad karkata kai yana kallon laɓɓan nata cike da begen su har yana lumshe ido, cikin raha tace "Gidanmu dai? Za ka zo? To ka zo, ni dai nasan kowa na hushi da kai a gidan nan, cikin biyu ko za'a yi ɗaya..." Tana cikin maganar ya tako ɗaya biyu zuwa na uku ya iso daf da ita, za ta yi saurin ja baya lokacin da ta yi shiru kuma ya riƙo hannun jakar dake goye a bayan ta, hakan yasa dole ta tsaya a inda take ta kuma sadda kanta ƙasa, tsare fuskar ta yayi da idanu cikin wata irin siga mai kayar da gaban mumini tamkar mai son sakata bacci yake faɗin "Ni da nasan idan muna daf da mutum baya iya ɗaga kai ya kalle ni, to a haka zan nemi auren mutum kuma a bani da amincewar sa, idan an musa maganata kuma a ɗago sannan a sake faɗa min *wai an tsane ni*." Lumshe idanu Aisha tayi tana son dakatar da rawar da jikin ta yake son yi, da ƙyar ta ɗaga idanun ta ta kalli fuskar shi amma ba cikin ido ba tace" Sake min hannuna dan Allah?" Cike da shaƙiyanci ya ƙara jawo hannun jakar yace" Hannun ki fa? Wannan hannun ki ne? Ni jaka na riƙe." Sai kuma ya sake gyara tsayuwa ya sake matse mata wuri har numfashin shi na sauka a fuskar ta cikin taushin murya yace" Dan ba kya jin kunya wai har ki kalle ni ki faɗa min wai kin tsane ni, ni ko? Ni *ƴata* zaki ce kin tsane ni?" Da sauri ta ɗaga kai ta kalli fuskar shi sosa cike da masifa da bala'in dake ciciyar ta tace" Ba wai bane, da gaske ne na tsaneka yanzu Abb... Sa'ad, na tsaneka Allah." Kamar mai son fusata ta sai kuwa ya saki murmushi yana tsare ta da matsakaitan idanun shi yace" Oya, kalli idona sai ki faɗa min, zan fi yarda da ke a haka." Ɗaga dara daran idanun ta kam tayi ta zuba su cikin nata, amma wallahi kwarjinin shi da wata kunya sai suka baibayeta ta rasa ƙwarin guiwar maimaita mishi haka, a ƙarshe idanun ta suka cika taf da hawayen da har ta fara sako su cikin rawar murya kamar mai jin sanyi tace "Ni...dai...Abbu gi...da nake..so na tafi." Dariya ta bashi har saida ya ɗan dara sannan ya saki hannun jakar ya ja baya kaɗan yace "Ƴa mai ƙaryar ta tsani Abbun ta." Satar kallon shi tayi sai kawai ta murguɗa mishi baki tare da juyawa a sukwane zata bar wurin, da kallo ya bi ƙeyar ta yana faɗin "Ni ko?" Bata juyo ba bare ta kula shi har ta shige motar aka ja suka bar harabar makarantar, shi ma tashi motar ya shiga ya bar makarantar dan zuwa masaukin shi kafin magariba ya isa gidan su Aisha. Tunda suka bar nan Aisha ta saki murmushi tare da hango Sa'ad a tsaye yana kallon tasu motar, saida ta daina ganin shi sai kuma ta taɓe baki tace "Hmmm! Wai yana sona? Kaji ƙarfin hali ga Abbu, ko kunya baya ji?" Sai kuma ta riƙe haɓa tana tuna tabbacin da ya bata akan zai zo gidan su, to idan fa da gaske ne? Babu wanda zai saurare shi, musamman ma Abbun ta, yana hushi sosai akan larurar da taso samunta Dalilin kayan da aka loda mata a ciki, idan ya zo gidan su zai ji ba daɗi ai, saï kuma wata zuciyar ta raya mata _"Da wuya ma ya zo, wasa kawai yake."_ Dan haka sai ta share zancen zai zo kawai, amma fuskar ta ta kasa daina murmushi na haɗuwar su, maganar gaskiya ta ji daɗin ganin shi kuma ta yarda tayi kewar shi, sai dai bata san a wane sikeli zata auna hakan ba, shaƙuwa ce ko ƙauna? *Sosai* Mama Nuriyya ta ga canji game da ita tunda ta dawo, dawowar Abbun ta yasa ta fito da hijabin da tayi sallah tana mishi sannu da zuwa, dafa kanta yayi yana murmushi cikin kulawa yace "Eeshar Abbu, ya dai naga kamar kina ta annashuwa." Ƙara sunkuyar da kai tayi tana karɓan jakar hannun shi tace "Ba komai Abbu, muje Mamie tana ciki." Hannunta ya kama ɗaya gefen kuma hannun Kabil ne ya riƙe yana faɗin "Kin tabbata?" Ɗaga kai tayi tace "E Abbu." Ɗorawa yayi da "Kin yi sallah?" Da ladabi tace "E Abbu nayi." Murmushi yayi yace "Kin yi mana addu'a?" Da tabbaci tace "Sosai ma Abbu, kuma nayi addu'a Allah ya bayyana mana aunty Kuwailat." Da fara'a sosai da jin daɗi yace "Allah ya aminta yar Abbu, kai fa Kabil ?" Ya tambaya yana kallon Kabil, shi ma da fara'a yace "Nayi Abbu, kuma ma tare da aunty Eesha muka yi." Shafa kanshi yayi har suka ƙarasa ɗakin Mama Nuriyya, tana ta sauri ta gama ɗaura ɗan kwalin ta suka shigo, da sauri ta juyo tana turo baki kamar ƙaramar yarinya cikin shagwaɓa tace "Haba dai, ya zaku shigo ban gama kwalliyata ba? Ni gaskiya ku koma." Dukansu dariya sukayi sai shi da ya dakata yana kallon ta yace "Ni ko har da yaran?" Cikin shagwaɓa ta ɗan juya tana maƙale kafaɗa tace "Har da kai mana." Ba tare da ya motsa ba yace "To ai naga an gama kwalliyar?" Girgiza kai tayi tace "A'a, ban ɗaura ɗan kwali ba ai." Da sigar zolaya yace "Dan ɗan kwali ? Bari na ƙarasa ɗaura miki." Ya faɗa yana matsawa inda take, Aisha kuma ƙarasawa tayi ta aje jakar Hannunta inda taga maman ta na ajiyewa, tuni ko ya zaunar da ita gaban madubi ya fara durfafa mata ɗaurin, dariya Aisha tayi ta zagaya kusan su tace" Gaskiya Mamie ki bar min Abbuna ya huta, ni zan ɗaura miki." Dariya yayi yana matsawa gefe saboda ƙoƙarin kama kallabin da Aisha ke yi yace" Nagode sarauniyata, Kinga ƴa ta fanshi Abbun ta." Kallonshi tayi duk da Aisha ta fara mata ɗaurin tace" Ɗaurin ma da nasan dama ba iyawa za'a yi ba." Da sauri Aisha ta ƙarasa mata ɗaurin ganin Abbun ta na cire machete ɗin hannun shi alamar zai cire kayan jikin shi ya shiga wanka, tana gama ɗaura mata tace" Mamie duba madubi kiga, nasan baki taɓa irin wannan ɗaurin ba." Miƙewa tayi daga kujera ta juya kan madubi tana dubawa, yayi kyau kam ɗaurin, juyowa tayi dan yi ma Aisha magana sai taga har ta janye Kabil sun bar ɗakin, dan haka ta ƙarasa kusa da mahaifin nasu dan taya shi wanka da duk abinda ta san ta saba yi mishi a wannan lokacin. Suna cin abinci a falo cike da raha da jin ina ma ɗaya ƴar su tana nan? Ai da farin cikin ya fi wanzuwa, ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ne ya danna alarme na ƙofa, juyawa sukayi suka kalli ƙofar, sai kuma mai aiki da ta fito kai tsaye ta nufi ƙofar ta buɗe, ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ne sukayi magana sannan ta maida ƙofar ta rufe ta dawo inda suke da ladabi ta tsaya tana kallon Abbu tace "Yallaɓai, wai kayi baƙo a waje, ya ce yana son ganin ka." Kallonta yayi da mamakin wanda ya zo masa ba tare da ya san da zuwan nashi ba yace "Wa ye?" Da ladabi tace "Bai faɗa ba, amma dai ya ce a ce wai baƙo ne, kuma sunan shi Sa'ad ne." Da mamaki ya sake ƙanƙance idanu dan shi har ga Allah ya ma manta da sunan wanda ya taimaki Aisha, hakan yasa ya shiga waina idanu yana son tuna inda ya taɓa jin sunan. Mama Nuriyya da ta kalli Aisha tunda aka ambaci Sa'ad ta ga tayi wani iri ta zaro idanu tace "Eesha, ko dai mariƙin ki ne?" Kallon Maman nata tay da yanayin rashin gaskiya tace "Ban sani ba Mamie." A kausashe Abbu ya kalli Mamie yace "Ba dai mariƙin ta ba, sai dai mazalincin ta, wanda ya nemi halaka mana yarinya?" Tsaki yaja tare da kallon mai aikin yace "Kinga, ki je kiga idan har shine wanda yake ikrarin ya taimaki Eesha, to a gaggauta fitar min da shi daga nan, bana son sake ganin shi a rayuwata." Yana faɗa ya maida hankalin shi kan cin abincin shi, tunda yayi maganar Aisha ta zuba mishi idanu kamar za ta fashe da kuka tana kallon shi, Mama kuma tsaf take lura da ita har mai aikin ta fita daga falon, tsakurar abincin kawai ta shiga yi tana jin duk ba daɗi, zuciyar ta kawai raya mata take ta tashi ta je ta same shi, amma kuma bata so tayi hakan gaskiya. Suna haka mai aikin ta dawo falon, kai tsaye wajen su ta sake nufowa saboda saƙon da Sa'ad ɗin ya bata, ita kanta sai da ya bata tausayi da ta ga ya juya jiki a sanyaye ya fita bayan takardar da ya bata ta ba Aisha, tana zuwa kam ta tsaya ta miƙowa Aisha takardar tace "Hajia ƙarama , in ji shi wai a baki." Da sauri abin ka da wanda zuciya ke marari ta sa hannu zata karɓa, sai kuma suka haɗa ido da mahaifin ta dake mata wani irin kallo mai tarin tambayoyi da mamaki, ƙin karɓa tayi tare da sadda kanta ƙasa ta furta "Ku gafarce ni." Da sauri ya sa hannu ya karɓi takardar ya shiga warwarewa, inda mai aikin ta bar wurin shi kuma ya karanta gajeran saƙon kamar haka _"Na tafi, amma zan dawo gobe ma, saboda ina sonki, kuma na zo ne dan na koma dake a matsayin matata."_ Cikin jin haushi Abbu Mukhtar ya kalli Mama Nuriyya ya nuna mata takardar ya ce" Ki ji fa, me yaron nan yake taƙamada shi? Ba Ya ce gobe zai dawo ba? To ya zo, wallahi da jami'ai zan haɗa shi." Ƙwarai tayi jarumtar riƙe hawayen da suka cika mata idanu, amma da ya ambaci jami'ai sai ta ture farantin gabanta ta miƙe da gudu ta nufi kusurwar ɗakin ta, dan fashe musu zata yi da kuka duk da ita ma bata san dalili ba. Da kallon mamaki suka bita, sai kuma Mamie da ta haɗa da kallon tausaya mata, to ya zasu yi tunda ya gama yi musu illa? Duk da ba haka ta so ba, amma ba zata bari hakan ya zama silar shiga damuwar ƴar ta ba, za ta mata duk abinda take so saboda ita kaɗai gare ta. *WASHE GARI* Tayi ɗaukin shi a makaranta yau ma kamar jiya, sai dai sam bata gan shi ba har suka gama ta dawo gida, haka ta wuni ba fara'a ba walwala, hatta sashen aunty Abida bata leƙa ba ko sau ɗaya. *Da* yamma tana saman bene wurin da aka ware dan shan iska tana karatu, dake tsaye take tana ɗan kai da kawowa saboda abinda take so ta hardace a kan ta, kamar an ce ta juya saitin ƙofar shigowa ta hangi Sa'ad da jami'in dake tsaron ƙofar suna gaisawa da fara'a kamar dai sun san juna, amma sai ta fahimci kamar ba zai bari ya shigo ba dan yadda taga yana ma Sa'ad ɗin magana a nutse kamar kwatanta masa wani abu yake, yayin da shi kuma yake sake bashi hannu da jinjina kai sannan ya yi niyyar juyawa zai fita, da sauri ta dawo ta ɗauki wayar ta dake kan farin teburin tare da jakar ta, wata gajeruwar lamba ta rattaɓa sannan ta ɗora a kunne, tana kallo jami'in ya zagaya ya ɗauki wayar tangarahon dake nan yana faɗin "Na'am." Da sauri Aisha tace "Ka shigo da shi, na san shi." A ladabce duk da ya san wacece yace "Hajia ƙarama nima na san shi, abokina ne ai, amma jiya Alhajin Kabil ya bamu umarnin kar mu sake barin shi ya shiga." A ɗan kausashe tace "Ni nace ka bar shi ya shigo." Da ladabi ya sake cewa "Kiyi haƙuri Hajia ƙarama, wallahi Alhajin Kabil ya mana alƙawarin ɓacin rai idan muka barshi ya shiga, abinda na kwatanta masa kenan kuma ya fahimta, duk da dai ya ce zai dawo ko da za'a kashe shi." Cikin jin haushi da takaici ta aje wayar tare da tattare kayan ta da sauri ta shiga sauka daga benen riƙe da jakar ta, tana dirowa falon su Mamie na zaune da wayar ta a hannu da kuma wasu tilin wasu shaddodi gaban ta na ankon bikin Abida da ita aka ba kwangilar fiddowa, tsaye tayi gaban ta a rikice tace "Mamie, me yasa Abbu zai ce kada a bari Sa'ad ya ƙara shigowa?" Da mamaki ta kalle tada rashin gane gaban zancen tace "Sa'ad kuma? Shine ya gaya miki? Yaushe aka yi haka ma ban sani ba?" A tsaurare tace "Mamie, gashi can ya zo amma an hana shi shigowa, wai ya ce Abbu ne ya basu umarni kar su bari ya sake shigowa." Ajiyar zuciya Mamie din ta sauke tare da tara mata hannu alamar ta taho, ƙara gimtse fuska Aisha tayi ta turo baki tare da yin takwaf takwaf da fuska alamar za ta yi kuka, hakan yasa Mamie yin murmushi tace" Haba sarauniyata, zo mana in ji." Hannun ta miƙo mata a sanyaye ta matso ta zaunar da ita kan cinyar ta, ƙurawa fuskar Aisha idanu tayi tace" Uhum! Ina jinki! Me ye tsakanin ki da Sa'ad ɗin nan ne?" Girgiza kai tayi à sanyaye suna kallon juna tace" Ba komai Mamie, amma ai ya taimake ni, bai kamata a mishi haka ba, tunda dai bai muzguna min ba a zamana da shi." Murmushi tayi ta jinjina kai tace" Hakane, to me ya sa naga kina damuwa da shi sosai? Kin tabbata ba son shi kike ba?" Da sauri ta waro idanu ta kalle ta tace" Mamie, so fa ? A'a wallahi, ni kawai Abbuna na ɗauke shi." Ba tare data daina murmushi ba tace" Ki faɗa min gaskiya Eesha, zan taimaka miki ne ai." Cikin shagwaɓa sosai ta turo baki tace" Mamie ba komai ba." Jinjina kai ta sake yi da sigar zolaya tace" Amma ai shi ya ce yana sonki, shin ke ba kya jin son shi ne?" Da sauri Aisha ta sa wutsiyar kallabin ta ta rufe fuskar ta saboda kunya, rumgumata tayi a jikin ta tana dariya tace" Na ganoki sarauniya, karki damu kin ji, zanyi magana da Abbun ki idan ya dawo." Jinjina kai tayi ta miƙe daga ƙafafun ta ta nufi ɗakin ta cike da kunyar abinda tayi har Mamie ɗin ta gane ta. Sa'ad kuma kamar yadda ya faɗa zai dawo, yana idar d sallah magariba ya sake dawowa da burin ganin mahaifin Aisha ido da ido, ba zai yi hushi ba, ba kuma zai ɓata ran shi ba dan ƴarsu yake so, kuma yana ganin tashi soyayar a idanun ta ita ma, dan haka ba zaiyi abinda zai kawo naƙasu a yi musu biyayya ba. *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes. *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata. Sayen na gari mai da kuɗi gida, sai an gwada akan san na ƙwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a ƙasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI- SIRRIN MANYAN MATA)._ _Bismillahir-rahamanir-rahim._ *24* Suna cikin sake gaisawa da jami'in nan motar Alhaji babba ta tsaya tana oda, ganin Sa'ad yasa Alhaji babba sauke gilashin baya inda yake zaune yana leƙowa, da girmamawa Sa'ad ya matsa kusan motar yana rusunawa, sai lokacin ne Alhaji ya gane shi sosai, da girmamawa shi ma ba tare da tuna wasu abubuwa ba bayan alkairin da ya musu ya buɗe motar gaba ɗaya ya fito yana bashi hannu suna gaisawa sosai har da tambayar shi yaushe ya zo? Ya kuma ya ganshi a nan? Daga amsar da ya bashi yasa Alhaji faɗin "A'a ai bai kamata kana tsaye ƙofar gida ba, muje ciki ko?" Da girmamawa ya fara takawa à bayan Alhajin kamar yadda Alhajin ke takawa a ƙafa bayan ya ma dreba umarni ya shiga da motar ciki, suna tafe suna ɗan hira yana ƙara tambayar shi, dake gidan akwai girma kuma Sa'ad na tafe ne da yanayin tafiyar Alhaji, hakan yasa ko rabin isa kusa da falo basu yi ba aka danna oda motar Sabeer ta shigo gidan, amma dake tare da Abbu Mukhtar suke yana ganin Sa'ad tare da Alhaji suna nufa ciki ya sa Sabeer dakatawa bai ƙarasa can ba. Yana fitowa ranshi ɓace yana kallon Sa'ad yace "Kai, ya aka yi ka shigo nan? Ba na ce kar a barka ka sake sh..." Kallonshi Alhaji yayi da mamakin yadda Mukhtar ɗin ke neman zama mafaɗaci bayan ko magana ba cika yi yayi ba yace "Mukhtar, lafiya ? Me yake faruwa? Ban gane ka hana ya shigo ba? Baka gane shi bane?" Sai lokacin ya kalli Alhaji a tausashe da ladabi yace "Abbu, wannan yaron ne bana son ganin shi a nan, ban ɗauki abinda ya ma Eesha a matsayin taimako ba, saboda Dalilin abinda ya mata saida aka ɗorata à magani, sani ne kawai ba kuyi ba Abbu, yanzu haka jarabawar da take yi nake jira ta gama zamu sake komawa a duba ta dan a ga ci gaban da aka samu." Girgiza kai Alhaji babba yayi a tausashe yace" Koma me ye Mukhtar ka nutsu mana ka ji me ya kawo shi, ya ce min tun jiya yake zuwa ana hana shi shiga." Da tausasawa ya dubi Alhaji babba yace" Abbu, dan Allah ka bari mutumin nan ya fita daga gidan nan." Tsare shi yayi da idanu yace" Shin bai taimaki Eesha ba?" Kai tsaye ya bashi amsa da" Abbu tarkon shi ta faɗa." Da sauri amma cikin ladabi da tausasa murya Sa'ad ya tari numfashin su yace" Ba haka bane, haɗuwata da Aisha ba shiri bane, *Abba* tun jiya nake zuwa ina son yin magana da kai mai mahimmanci, haƙiƙa ni mutumin banza ne amma a baya, na kasance mai siye da siyar da miyagun ƙwayoyi, amma shigowar Eesha rayuwata wallahi na canza, na tuba daga aikata duk wani abu marar kyau sannan na nemi gafarar ubangijina..." Numfasawa yayi yana kallon fuskar Abbu ɗin da ya ci magani sosai ya kawar da kai ya ci gaba da faɗin" Tabbas nayi cinikin wasu ƙwayoyi da aka ce min za'a min safarar su a cikin wata yarinya marainiya, sannan sun bani ita ne da zaran na cire kayana a cikin ta na mayar musu da ita dan zasu dinga safara da ita, ban san komai a kan ta ba, suna ko hoton fuskar ta bare wani abu da ya dangance ta, ban san komai ba wallahi, a ranar da nake jiran ganinta sai yaran suka kirani kan cewa ta ɓace musu, ni kuma a lokacin na haɗu da Aisha tana neman taimako saboda ɓata garin da take ta haɗuwa da su, na taimaka dan Allah ba tare da na san ko da sunan ta ba a lokacin, saboda abu biyu dana yi duba shi, na ɗaya *tsaran ƙanwata ce*, na biyu kuma *da wa za ta haɗu a gaba idan na bar ta*? Wannan ya sa na tafi da ita gidan mu, gaskiya ne a ranar na san ita ce yarinyar da aka turo ɗauke da kayana, sanadiyar hoton da aka turo min dan muyi neman ta, amma..." Murmushi yayi shi kaɗai saboda tuna rayuwar da yayi da ita a wannan lokacin, hakan yasa har Sabeer dake tsaye lokacin ko mota bai kashe ba ya zuba mishi idanu ya ci gaba da cewa" Tana da daɗin sha'ani, tana girmama ni, tana da barkwanci, sannan bata da shakkar gaya min komai ya zo bakin ta, kaf gidan mu ba mai iya tsare ni ya tambaye ni *ina naje*? Amma ita haka take tambaya ta kai tsaye, wani lokaci ma har ta ce zata hanani abinci idan ban faɗa mata ba, ban sani ba ashe shaƙuwa nake yi da yarinyar da ban an asalin ta ba, kwatsam sai na fahimci na kamu da soyayyar ta, a lokacin da na fara shirin canza rayuwata saboda ita, sai likitan da ya mata aiki ya kira yake sanar da ni tana cikin haɗari, bayan haka ana bibiyar ta saboda an gano ahalinta kuma ba'a so ta haɗu da su ko ta wane hali ana so a sake yin nesa da ita, a lokacin naji kamar zan rasa raina saboda tabbas idan wani abu ya same ta *ba zan rayu* ba nia, a take na a kaita asibiti kuma aka saka mana lokacin komawa a mata aiki, ban yarda na sake ɓata ko da sakan ɗaya ba har saida na ga an mata aiki cikin nasara." A zabure Abbu ya kalle shi kamar zai haɗe shi, inda Sa'ad ya marairaice yace" Wallahi ABBA tunani na shine idan na dawo da ita gidan nan mai farautar ta zai iya kamata kuma ya cutar da ita, amma idan tana tare da ni ba mai dawo da hankalinshi kanta bare ma a saka mata ido, sai kuma zuciyata da na ji ba zata iya rabuwa da ita ba, ina ganin zata min nisa kenan na har abada, saboda matsayina da nata ba ɗaya bane, wannan shine dalilin da ya sa na ƙi saurin sada Eesha da ku, amma ina so kuma burina kullum shine na ga kun haɗu, har ayyana irin farin cikin da zata yi nake, musamman idan ya zamana ni na kawo ta da kaina, nasan da na ci gaba da samun darajar da zata ci gaba da kirana da *Abbu*." Murmushi Sabeer yayi ya matso kusan shi ya dafa kafaɗar shi dan ya burge shi sosai, inda Sa'ad ya ci gaba da kallon Abbu da ya ɗan fara sakin haɗewar fuskar nan yace" Dalili biyu ya kawo ni nan, na farko shine na nemi auren Eesha a wurinku, saboda bayan tafiyar ta na gane ba zan iya anfanuwa ba idan babu ita, na biyu kuma shine na *kawo kawuna ya nemi afuwarku* akan ɓatan ɗaya ƴar taku *Kuwailat*." Sake ɗaure su yayi da mamaki suka sake zuba mishi idanu, gyara tsayuwa yayi ya jinjina kai yace" Dole zaku yi mamaki, amma Alhaji..." Ya faɗa yana kallon Alhaji babba da yasan ya isa fara gajiyawa da tsayuwar nan yace" Mu shiga ciki ka zauna, zan muku bayanin ta inda labarin kawuna ya haɗu da naku." Ƙwarai sun gamsu da haka, dan haka duk suka rankaya zuwa falon su Hajia, a falo suka samu Hajia tana kashe abun turaren wuta na wutar lantarki ɗakin sai daddaɗn ƙamshi, wuri sua samu suka zauna inda suka gaisa ita da Sa'ad sosai har da tambayar shi Hajia Kaka ? Abbu Mukhtar da ke ƙaguwa da son jin bayani game da babbar yarinyar sa ne yace "Muna sauraron ka, ta ina kuma kuka haɗu da Kuwailat?" Gyara zaman shi yayi sosai a ƙasan carfet ɗin sannan ya ɗora da "Ƙanin mahaifina ne uwa ɗaya uba ɗaya, ya faɗa min abinda ya faru shekara goba sha bakwai da ta wuce, matar shi ta samu haɗari..." Tsaf ya basu labarin kamar yadda kawu Hisham ya sanar da shi, Hajia Kaka ita kaɗai ce mace a wurin, dan haka tuni ta shiga fadin" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Dama abinda ya faru damu fansa aka ɗauka a kan mu?" Kallonta Sa'ad yayi da ladabi yace" Kusan haka Kaka, amma wallahi tun lokacin da abun nan ya faru baya da kwanciyar hankali, kullum cikin shan magani yake, sannan kullum cikin ganin likita yana duba shi, babu abinda yake buƙata yanzu da ya wuce yafiyar ku, amma mutumin da na faɗa muku yana da hannu a cikin ɗauke ƴar ba kowa bane face sirikin gidan nan." Wani ruɗanin suka sake shiga da ya saka Abbu Mukhtar gyara zama akan kujerar yana kallon Sa'ad yace" Wai dakata! Kana nufin matar da na kaɗe shekaru sha bakwai, ita ce mijin ta ya ɗauke min ƴa ? Abun nan da ya faru ni na ma manta da shi a rayuwata, sai yanzu da kake maganar na iya tuna haka ya faru, akan shi ne aka raba ni da ƴata, wacce yanzu ban san a halin da take ba?" Tsaki yaja tare da yunƙurawa zai miƙe Alhaji yayi saurin dakatar da shi, komawa yayi ya zauna yana girgiza kai cike da damuwa da takaici da kuma rashin sanin makama yace" Na kas gane wannan abun? To wa ye mutumin da ya taimaka mishi?" Sabeer ma gyara zama yayi yace" Hakane, muna so mu sani, wa ye?" Kallon su Sa'ad yayi sosai sannan yace" Hambali ne, mahaifin Abida matar Bilal." Alhaji da Hajia ne suka fara kallon juna, sai kuma Hajia da Abbu Mukhtar suka kalli juna da mamaki, suna cikin zazzare idanun nan Sa'ad yace" Nasan dole abun ya rikita ku, abinda nake so daku shine, ku kwantar da hankulan ku sannan kuyi haƙuri, akwai shirin da nake da shi a ƙasa kuma nake so ku bani goyon baya a kai, Hambali shine wanda ya taimakawa Kawuna aka sace Kuwailat, sannan shine Aisha ta taso a gidan marayun shi, kuma shine wanda nake siyan kaya a gurin shi lokacin da nake gurɓatacciyar harƙalla, ma'ana shi ya jagoranci farka cikin Aisha sannan aka sako ƙwayoyin nan, sannan ma shine na samu labarin ya tashi hankalin shi yana neman ta ido rufe saboda ya ji labarin ana neman ta, Abba..." Ya faɗa yana kallon Abbu Mukhtar ya ɗora da" A bayyane yake akwai wata manufa da ake so a cimma, sannan a bayyane yake ba ƙaunarku yake ba, bamu da hujjar da zamu tuhumi ƴar shi ma, sai dai akwai abubuwa dana gano masu ɗaure kai game da ita, haɗin kanku kawai nake nema wajen yin shiru da bakunanku da kuma nuna ma kowa kamar komai bai faru ba, ta hakane zan samu abinda nake son samu, sannan mu gano sauran masu hannu a cikin ɓatan yaran har ma da masu zama da ku da mummunar manufa." A nutse Alhaji ya cire hular kan shi tare da share zufa yana duban Sa'ad yace" Yaro, to ya kake so muyi? Hambali? Ƙasan waye Hambali kuwa? *Yarona ne fa*, a ƙarƙashina yake aiki, ladabinsa da shekarun da muka ɗauka ya sa har na amince da ƙudirin da ya zo min da shi na haɗa auren ƴar shi da ɗana, shine zai min haka?" Sai kuma ya riƙe haɓa yace" Hasbunallah wani'imal wakil !" Jinjina kai Sa'ad yayi yace" Kamar yadda nace Alhaji kuyi shiru, ba wai wa iyalin shi ba kawai, hatta da Abba Bilal kar yasan abinda ke faruwa, dan sanin zai sa ya kasa ɗauke kan shi daga gare su ƙarshe mu rasa abinda muke nema." Sabeer ne yace" Kamar ya? Kana ganin zamu san da wannan abun ne kuma mu kasa sanar dashi? Ai ba zai yiwu ba." A take Sa'ad yace" Zai yiwu, idan dukanmu nan muka ja bakin mu muka yi shiru bamu sanar da shi ba." Abbu Mukhtar da abun ya gama ɗaure shi sosai ne ya dube shi yace" Hambali? Ƙasƙantaccen bawan da muka rena da hannun mu?" Kallon shi Sa'ad yayi yana jin kamar Abbu ɗin yana da ɗan ra'ayin nan na ba kowane mutum yake so ko yake ja a jiki ba, da ladabi yace" Dama ai wanda ka yarda da shi shi yake ci maka amana, idan baka bashi yardar ba ta ina ma zai ga damar ka?" Jinjina kai yayi da gamsuwa yace" Gaskiya ne wannan, yanzu me ye abun yi?" Ya tambaya yana kallon Sa'ad, a nutse ya sake nanata musu su yi shiru kawai kar kowa ya ji, duk jinjina kwunan su sukayi sai Hajia da tace" Ni wallahi gaba ɗaya ma naji matan gidan nan tsoro suke bani." Murmushi Sa'ad yayi yace" Kar su baki tsoro Hajiarmu, in sha Allah ba abinda zai faru, kawai ina so ne san wasu sirrika daga hannun ko da ita ƴar tashi ce, sannan mu bibiye su wataƙila sun san wani abu akan Kuwailat, tunda har Aisha ta girma a hannun shi." Dafe kai Abbu yayi na tsawon lokaci kafin ya ɗago idanun shi jajir yace" Zanyi hakane kawai dan ina so nasan inda babbar ƴata take, ina sonta, ina so na ganta fuska da fuska, da kewarta kullum nake kwana, kullum hango jaririyar yarinya ta nake da aka ɗauke a gadon bacci ta, kullum tunanin yadda ta rayu nake, ina hango irin kukan da ta dinga tsalawa à wannan lokacin bayan neman Mamanta bata same ta ba, amma ba dan haka ba... Wallahi da na nemi inda Hambali yake sannan na masa yankan rago, dan ya cutar da ni dayawa, ban damu dan nayi kasonshi ba." Sai kuma ya kalli Sa'ad yace" Zanyi shiru kamar yadda ka buƙata, Allah ya bamu sa'ar gano asirin su." "Ameen Ya Allah." Suka faɗa a tare, da yanayin raha Abbu ya numfasa ya kalli Sa'ad yace "Tom, yanzu sai ka dawo nan da zama ko? Kaga daga nan ka ci gaba da neman yaƙin zaɓenka a zuciyar sarauniya Eesha, ko ba haka ba?" Ya faɗa yana tambayar Sabeer, dariya duk sukayi sai Sa'ad da ya kalle shi da mamakin wai ya yarda kenan? Kai amma yayi farin ciki, bai yi tsammanin zuwan abun da sauƙi ba, cike da kunya yayi murmushi tare da shafa ƙeyar shi yace" Abba a yanzu dai naji kun yafe wa Kawuna shi na fi son ji, dan n'a baro shi cikin damuwa kuma na mishi alƙawarin zan kira shi da komai ya daidaita." Ɗan dafe gaban goshin shi yayi kaɗan sai kuma ya ɗago kanshi yace" Ba damuwa, a waccen ranar..." Sai kuma ya kalli Sa'ad yace" Kasan me yasa à waccen ranar ban zauna asibitin ba na tafi da gaggawa?" Girgiza kai Sa'ad yayi yana tsare shi da idanu da son jin dalili, a tausashe yace" A kiɗime nake, lokacin an kirani daga gida cewa *Ummu Kuwailat* na naƙuda, haihuwar fari ce ban san ya abun yake ba, abinda ya ja min kiɗimar kenan har na bugeta ba da gangan ba, Shiyasa na kasa zama na ƙagu na je na ga ya nawa iyalin take? Ban san cewa kaɗewar da na mata ta kai har ta rasa abinda ke cikin ta ba, dan sai bayan sabgar Kuwailat na tuna da wata na kwance a dalilina, da na je asibitin sai suka bani tabbacin ta ji sauƙi tuni ma sun sallame ta, ban dai yi dubarar bibiyar su ba bare na sake waiwayan lamarinsu, wallahi indai abinda ka faɗa min à kanshi gaskiya ne, to ina ga ko nine a halin da yake ciki wataƙila nayi hakan, dan haka ba komai ni na yafe mishi, kuma zan ma Ummu Kuwailat bayanin komai ita za ta yafe mishi duk kukan da ya sakata." Durƙusawa yayi duk da zaune yace ya shiga yi mishi godiya, da farin ciki da zumuɗi ya miƙe yace zai tafi sannan za kira kawu gobe ma zai zo garin nan dan neman su afuwa da kan shi, ko da Sabeer ya sake mishi maganar kwana nan murmushi yayi yace" Idan ma aka janye umarnin da aka ba wa jami'an na hanani shigowa ma ya wadatar." Dariya sukayi haka ya bar gidan da fara'a da farin ciki marar misaltuwa, bai nemi Aisha ba duk da ya so ganinta ko da daga nesa ne dan ya ji daɗi, amma sai bai matsa ma kanshi ba ya fita da tunanin gobe zai dawo ai tunda an janye mishi takunkumin. *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes. *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata. Sayen na gari mai da kuɗi gida, sai an gwada akan san na ƙwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a ƙasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI- SIRRIN MANYAN MATA)._ _Bismillahir-rahamanir-rahim._ *25* *Bayan kwana biyu* da faruwar hakan Kawu Hisham ya zo, sun karɓi juna da mutumtawa da girmamawa kamar wa da dama suka jima da sanin juna, an nemi yafiyar juna tare da jadadda yafiyar da kuma alƙawarin manta baya, bayan kammala tataunawar su kuma Abbu ya zo da wata magana da saida ya kalli Sa'ad yace "Ɗan bamu wuri ko? Zamu yi wata magana ne." Miƙewa Sa'ad yayi yana mamaki da ji a ranshi yaushe ma aka sulhuntar da har zai zama saniyar ware kuma yanzu? Shi dai ya fita ko ba komai yana farin ciki. Saida yayi jim kaɗan na wasu sakanni bayan fitar Sa'ad sannan ya kalli kawu Hisham yace "Ina so ne muyi magana a kan shi Sa'ad da Eesha." Da irin kallon tunanin wani abu ne ya faru ya kalle shi yace "To, wani abu ne ya faru tsakanin su?" Murmushi ya kalli Alhaji dake gefen su shi ma yana murmushi sannan ya kalle shi yace "Ba abinda ya faru, dama shi Sa'ad ɗin da ya zo yake faɗa mana aurenta yake so yayi, gaba da gaba fa yake faɗa min haka..." Yayi maganar da sigar raha har saida kawu Hisham yayi dariya yana girgiza kai, sannan ne ya ɗora da "To shine nace kafin ka tafi gwara muyi magana, a yadda naga yaron nan nasan zai iya sace Eesha su gudu, to zai fi min na miƙa mishi hankalina ya kwanta." Dariya Alhaji da kawu Hisham suka sake yi har Alhaji na faɗin "Gaskiya kam, dan ni hirar da muka yi da shi jiya ma roƙona yake nasa baki ka bashi ita." Da fara'a Abbu Mukhtar ɗin yace "To ka ji, dan haka nake so mu shiga maganar, matsayin ka na uba gare shi ina mai sanar maka da na ba wa Sa'ad auren Eesha ko bayan raina, na gamsu da tubanshi kuma na girmama zuciyar shi, sai dai ina so ko za'a ɗaura auren sai Eesha ta kammala wannan zagon na karatun ta, burina shine tayi dogon karatu, amma banga alamar haka ba, idan ya so zai iya barin ta tayi a gidan shi, idan bai da ra'ayi kuma ban da matsala da hakan, sai dai bikin auren su na tsayar da rana nan da *wata shida* ne in sha Allah." Da farin ciki maɗaukaki, murna marar misaltuwa kawu Hisham ya dinga faɗin" Alhamdulillah, gaskiya abu yayi daɗi, ban taɓa tsammanin bayan yafiyar da zan samu ba har da tagomashin babbar kyautar da girman ta ya fi a haɗata da komai, gaskiya ba zan taɓa mantawa da wannan rana ba, mun gode sosai Allah ya saka da alkairi, kuma in sha Allah ina komawa ma kai tsaye gidan su zan fara sauka na sanar da iyayen shi wannan abun alkairi." Da haka suka ci gaba da tattaunawa tsawon lokaci kafin su yi sallama da juna, tunda ya sanar da Sa'ad wannan lamari farin cikin shi da zumuɗin shi ya kasa ɓoyuwa. *Abun* mamaki shine yadda Uwani wato maman Sa'ad ta dinga wata irin murna da farin cikin wannan haɗi , ta manta da yarinyar ta zauna gidan nan babu irin tsanar da bata nuna mata, hasalima Sam basa shiga harkar juna daga kyara sai hantara da Harare, amma yau har habaici da yada maganganu take wa kishiyoyinta cewa ɗanta Sa'ad dama ai ƙashin arziki ne dashi, shi mai kuɗi kuma gashi ya ɗauko ƴar babban gida da kowace uwa zata yi alfahari da haka. Hajia Kaka ta so ɗauko maganar Fadila, amma da haka ta faru sai kawai ta share zancen musamman da ta ga take-taken Uwani ta san ba zata so haka ba sai idan dole aka mata, shi ma kuma Sa'ad tunda yana son Aisha sai kawai ta bar abun a ranta tana ma Fadila samu wanda ya fi shi alkairi. Sa'ad kanshi mamakin Mamanshi yake da halayenta, wani ɓangare kuma kunya yake ji na abinda take yi, gaban kowa fa ta nuna bata ƙaunar Aisha, amma yanzu dan tasan asalin ta take wannan zumuɗin haka? Shin haka zata yi a gaban Aisha ma? Shi da take cewa mai kuɗi, zai iya cewa yanzu rufin ashirin Allah ne kawai, dan ginin da ya ɗauko ma na gani na faɗa ɗin tuni ya siyar da gidan ga wani hamshaƙin mai kuɗi, iya jarin da ya fara wannan harkar da shi kawai ya cire ya samu wani gida mai kyau ƙarami ya siya, yanzu haka shine yake so ya ma gyara sosai kafin lokacin, sauran kuɗin kuma a asusun marayu ya tura su tare da sake ƙasƙantar da kanshi ga Allah, yanzu haka dai dake yana da sha'awar Fashion, maɗinka ya samu sannan ya kama hayar shago ya zuba teloli da sauran kuɗin nan aka fara ɗinki. Iko na ubangiji, wani kamar arziki a jinin shi yake, sai kawai Allah yake jefo mishi manyan mutane, kuma ma irin masu shegen son ado da kwalliyar nan, dan Sa'ad bai san da ana iskanci a duniyar nan ba sai da ya shiga harkar nan, yanzu haka saida ya ƙara ɗauko hayar maɗinki sakamakon wani Alhaji da ya basu ɗinkin shi na shekara shekara da yake yi har set ɗari, wai fa kawai kayan sakawa (wallahi na ga haka sosai, mutum ɗaya ya bayar da ɗinkin kaya lokaci ɗaya guda ɗari ko ɗari biyu, kuma babu yadi ko shadda ta ƙasa da dubu ashirin, Allah ka datar damu duniya da ƙiyama), to irin wannan manyan harkokin ne yanzu haka sun sake maida Sa'ad ƙaramin mai kuɗi shi ma, dan duka abinda ya caza musu basa tayawa suke cirewa su bayar. *Wata Shida da sati biyu* Alhamdulillah, Allah abun godiya, farin ciki marar misaltuwa ke wanzuwa a zuciyar Sa'ad, saboda jiya an ɗaura auren shi da Aisha wanda yau yake zaune a falon mahaifin ta sunzo yi musu godiya shi da manyan abokanan shi, bayan gaisawa da kuma yin abinda ya kawo su Abbu ya kalle shi da kulawa cikin nutsuwa yace "Sa'ad, ina farin ciki da wannan rana, na gode Allah da ya sa Eesha ta dawo gare mu kuma har yau na aurar da ita, wataƙila da Kuwailat na nan, ta yiwu tare aka yi auren su ko kuma ita har ma ta haihu, Sa'ad, na so Eesha tyi karatu, sannan na so ta samu miji a garin nan tayi aure dan ta zauna kusa da mu, amma tunda mahaifiyar ta ta sanar dani ta ga soyayyar ka a zuciyar ta, sai na ruguza nawa burikan, a yanzu alƙawari ɗaya nake so ka min Sa'ad? Shine zaka kula da ita, dan har yanzu a jariri nake kallon ta, ranar da ta dawo gare mu ranar ne muka sake haihuwar Eesha, ban san ko mun saɓawa shari'a ba, amma a ranar da Eesha ta zo gidan nan tare da ni da mahaifiyar su da ƙanin ta muka kwana a gado ɗaya, dan a lokacin in ji kamar za'a sake rabani da ita ne, ban taɓa tsammanin zan yi nesa da ita da wuri haka ba, amma Kaga duka bai fi shekara da watanni da zuwa ta ba gashi zata sake komawa gare ka, dan Allah ka ce min zaka kula da ita kamar yadda nima zanyi?" Cikin tausayawa halin da suke ciki Sa'd ya kalle shi ba alamar wasa yace" Abba, na maka alƙawarin kula da Eesha kamar yadda kai ma zaka yi, na yi alƙawari ba zan taɓa bari hawaye ya zuba a idanun ta ba, sannan na maka alƙawarin cika maka burinka a kan Eesha na son tayi dogon karatu, in sha Allah." Miƙewa Abbu yayi da farin ciki ya zo kusa da Sa'ad da ya miƙe tare da abokan shi saboda girmamawa, rumgume Sa'ad yayi yana mishi godiya, kafin ya sallame su suka tafi dan ci gaba da sabgogin su. A farfajiyar ya haɗu da Fahad zai fita, gaisawa sukayi irin gaisuwa nan ta ƴan duniya, kallon Fahad ɗin da yayi kawai yasa shi yin murmushi, wato a kowane gida akwai tsutsar da zaka ga ta fita daban, a gidan Ahlan kuma Fahad ne wannan zakkar tsutsar, dan kwanaki ma Alhaji na masa maganar an tura shi makarantar kwana amma ya dawowar shi gashi sun rasa ya zasu yi da shi, ya faɗa mishi a duk gidan Sabeer ne mai zafafa mishi, amma kuma ya fi tsoron Abbu Mukhtar wanda yake zuba mishi idanu kawai, dan shi Abbu da idanu kawai yake sanar da shi abi da yake so ya fahimta. Ya gode Allah ƙwarai da kuma godewa Abbu da ya basu gidan nan su zauna nan da sati ɗaya kafin su wuce maraɗi, ba dan haka ba da ina zai kai wannan ɗumbbin ƙauna da kewa ta Eesha da ya wuni da ita tunda suka haɗu da safe aka musu hotuna kuma Alhaji babba ya tarasu ya musu nasiha da jan kunne, hakan yasa duk burin shi na son sai sun koma gidansu komai zai wakana yana da tamtama a kan tsayuwar shi yanzu, dan baya jin zai iya cika wannan alƙawarin, musamman yanzu da ya same ta da shigar kayan amarci ta idasa rikita shi. *A* buƙace ya kai harshensa kan dokin wuyanta a hankali ya shiga lasa yana ƙara buɗe idanunshi a kusan kitsonta dake fitar da wani irin sansanyan ƙamshi, hannunshi dake saman mamanta ya kuma murzawa da kyau a hankali ta yadda gaba ɗayanta ta mimiƙe kamar zata sume kafin ta koma ta zube saman gadon tana kara ƙanƙame jikin ta da idanunta gam gam, a hankali ya janye rigar ya cire mata ita ta yadda ta dawo daga ita sai pant, zaune ne yana cire jallabiyar da ya saka, a hankali kuma sai ya kamo ƙafar ta ya yi sama da ita wajen bakinsa, bata tsamata ba sai jin ɗumin laɓɓansa ta yi saman kafarta a hankali yana tsotsa, gaba ɗaya ta ji tana ɗan jijiga kafin ta kuma komawa ta kuma riƙe shi da kyau tana ta sauke ajiyar zuciya a jere. Harshensa ya ɗora saman pant ɗin ta yana lasa tamkar...hakan ya saka Aisha zazzaro idanu tana marairaicewa cikin dakusashiyar murya tace "Abbbbbbuuuuuu...." Da ƙyar ya ɗaga idanun shi ya sauke a fuskar ta, sai kuma ya sake mayar da su ya rufe cikin wani gurnani gurnani ya amsa da "Uhummmmm...,ƴar Abbu." Neman zillewa tayi saboda jin yana jaye pant ɗin nata da bakin shi yana son rabata da shi tare da faɗin "Abbu...ni ce fa." Riƙe cinyoyinta ya sake yi gam gam ba tare daya ɗauke bakin shi daga gurin ba yace "Nima ni ne fa ƴar Abbu." *Bayan Awa Ɗaya* Ta jigata iya jigata ta yadda a lokacin da ya zare jikinsa a nata ita kanta bata sani ba domin ta tafi wata duniyar ita bata suma ba, ita bata tare da shi a farke. A yau shi da kan shi sai da ya gasa jikinsa kafin ya ji ƙarfin shi na dawowa, sai wani irin bacci dake fizgarshi mai ma'ana, amma ya san ba zai fara yanzu ba alhalin ƴar dake kiran sa Abbu na kwance kamar ba rai. Ruwan ɗumi ya tara mata masu zafin da yasan su kaɗai zasu iya taimaka mata yau ɗin nan, da lallaɓawa ya ɗaukota ya nufi ban ɗaki da ita tana fitar da numfashi a hankali a hankali. Da dubara ya sakata cikin bahon wanka, tana zabura a gigice dan ta miƙe tsaye ya rirriƙeta yana faɗin "Shiiiii! Dan Allah Eesha, zauna kin ji ?" Girgiza mishi kai tayi tana ayyana _"Ashe wata azabar ba gaba take da wata."_ A zahiri kuma cewa tayi" A'a Abbu, wallahi ƙonewa nayi." Shima girgiza mata kai yayi yace" B ki ƙone ba, amma ruwan nan ne kaɗai zasu taimaka miki kiji daɗin jikin ki." A marairaice ta koma à hankali ta zauna ba duka gaba ɗaya ba, saida ta ji komai ya daidaita kafin ta idasa damɓasuwa a cikin ruwan, da tausayawa yake shafa ƙafar ta a cikin ruwan, hakan yasa Aisha ta tsurawa fuskar shi idanu tana kallo da tunanin wai dama Abbu Sa'ad zai iya yi mata haka? Ita fa ƴar sa ce? Me yasa zai mata haka? Tana tsaka da tunanin nan ya ɗago idanun shi, suna haɗa ido ya ji ya tsargu dan kamar kallon zargi da tuhuma take mishi, dan haka ya sadda kanshi a tausashe sosai yace " Kiyi haƙuri ƴar Abbu, ban san na kasa riƙe kaina ba, ba haka na tsara mana ba, amma haka Allah ya so." Idanunta ta lumshe tana kallon yadda yake ta shafa ƙafar ta bata ce ƙala ba har ya sake canza mata ruwan kafin ya tabbatar ma kanshi ta samu kulawar da take buƙata ya fito da ita. ******************* Zaune take kan kujera da wayar ta a hannu tana bin saƙonnin wani sabon grp da ta samu kanta a ciki yanzun mai sunan *RAYUWARMU A YAU* (zan dawo da shi in sha Allah 😕, ina son grp ɗin nan), daga yadda ta ga farawa da abubuwan ƙaruwa ta san za'a ƙarun, sai dai bata sai ba ko kamar sauran grps ne da akan fara da zafi daga baya ayi sanyi saboda yau da gobe kayan Allah ne, sai yanzu da ta duba komai na grp din sai taga ita kanta *admin* ce a ciki sannan ƙawarta *Sumayya* ita ce ta buɗe gidan, a zuciyar ta kawai tayi addu'a Allah yasa alkairi a wannan gidan, sannan ta nemi lambar Sumayya ta mata magana kan grp din dan ta ji me ye tsare tsaren shi? Suna cikin magana kiran Mama ya shigo wayar ta, da nutsuwa ta ɗauka tana murmushi saboda farin cikin ganin kiran. Da nutsuwa ta yi sallama mama ta amsa, saida suka gama gaisawa har tana tambayar ta ina kishiyar ta? Murmushi tayi ta kalli yarinyar da ta haifa wacce har ta fara zama sai ƙoƙarin ɗauko kayan wasan da ta cika mata gaban ta da su tace "Gata nan mama tana wasa, yanzu rarafe ne kawai a gaban ta." Da raha Mama tace "Ja'ira, wato ƙiriniyar ki take so ta koya? A wata na shiga kin fara son miƙewa tsaye." Dariya Ummu tayi ba tace komai ba, sai Mama da tace "Ya mai gidan? Yana lafiya?" Da fara'a ta amsa da "Lafiya lau Mama, suna can basu dawo ba, amma dai munyi waya ɗazu ya ce in sha Allah yana sa ran gobe su kwana a Dubai kafin su ƙaraso." Da kulawa ta amsa mata da "To Allah ya yarda, Allah kawo su lafiya." Da farin ciki ita ma ta amsa da "Ameen Ya Allah Mama." Jim sukayi shiru ya biyo baya sannan Mama tace "Ummu, Nabila bata zo gidan ki ba?" Gaban Ummu saida ya faɗi tare da jin tashin hankali ya ziyarce ta lokaci ɗaya tace "Mama Nabila kuma? Bata gida ne? Ina taje to?" Cikin muryar dake nuna kuka mama ke yi tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un? Ummu Nabila bata gidan nan tun jiya, ban san ina take ba, Ummu yanzu a ce kamar Nabila bata kwana gida ba kuma ni mahaifiyar ta ban sani ba? Ina take to? Gidan uban wa taje ta kwana? Tana me?" Ummu ma cikin tashin hankali ta miƙe tsaye tana kallon *Kuwailat* dake wasar ta tana faɗin" Mama dan Allah kiyi haƙuri, ki tura su Mujittafa da Yaya Luƙman su nemo miki ita, nasan ba zata wuce gidan ƙawa ba, amma Mama ki daina mata kuka dan Allah, ki mata addu'ar shiriya kawai." Cikin shasheƙar kuka mama tace" Ina yi Ummu, ina mata kowane lokaci, duba kiga har Luƙman da baya son ko ɓacin ranku, amma haka ranar da ta kai shi bango yarinyar nan saida ya zaneta har ta kasa fita, amma kin ga shine yau daga fitar ta har taje ta kwana." Da rashin jin daɗin wannan lamari da hango rayuwar da Nabila ke neman tsumduma kanta a ciki Ummu ta dinga ba Mama haƙuri da kwantar mata da hankali, har suka gama waya Ummu bata zauna ba tana kai da kawo da tunanin matsalar Nabila, Allah ya gani tun ba yanzu ba mama ke iya yin ta akan Nabila, amma kullum lamarin ta ƙara lalacewa yake yi kamar ba'a kwaɓa, gashi ta kai yanzu har ta fara kwana ba a gida ba? Ita kam za ta je gidan ta ba Mama shawara kawai a samu kawu *Idi* su sama mata miji a aurar da Nabila tun wuri, dan in ba haka ba wallahi za'a kai lokacin da za ta fi ƙarfin su. *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes. *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata. Sayen na gari mai da kuɗi gida, sai an gwada akan san na ƙwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a ƙasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI- SIRRIN MANYAN MATA)._ _Bismillahir-rahamanir-rahim._ *26* *BAYAN WANI LOKACI* Shekara goma sha shida ne da ita yanzu, amma yanda ta fito ƙofar gidan dan ɗiban ruwan da zata yi wanka, yanayin ta, dirinta da buɗewar idanun ta za ka ɗauka ta kai sha takwas ko ma fiye da haka, kitso ne a kanta manya wanda aka y da gashin doki duka bai fi guda goma ba, da alama kuma kitson sabo ne saboda yadda yake ɗaure à kan nata, wuyan ta kuma wata ƙaramar sarƙa ce srriya ta cika wuyan nata dam da shi, inda kunnuwan ta ke ɗauke da huje har guda huɗu kowane kunne, uku jere sai ɗaa dake saman kunnen kuma da wayon ta tasa aka mata shi tas. Riga mai sirraren hannaye ne jikin ta wacce ta fito da halluttar ta sosai sai zane da ta ma wani irin ɗauri ya kusa kaiwa ga guiwoyin ta, fatar ta na da haske sai dai fuskar ta tafi haske, dan kuwa kwanakin nan mai ta sa kanta saboda ra'ayi kawai. Aje bokitin tayi tana kara ƙaramar wayar ta a kunne wacce take jin kunyar riƙewa ko a cikin ƙawayen ta, dan haka yanzu take fatan haɗuwa da gwaskan da zai iya cire ta raini, cike da tsiwa da wulaƙanci da rashin kunya da duk ta koya a sabuwar duniyar ta take faɗin "Dallah malam ni ka dame ni, na gaya maka bana sonka mana, ko ana so dole ne? Ka rabu dani mana ka samu wacce ta dace da kai." Daga ɗaya ɓangaren saurayin ya amsa da "Ba zan iya rabuwa da ke ba Nabila..." Tana kunna fanfon tace "Saboda?" A take shi ma yace "Saboda ina sonki, ki bani dama mana na zo gidan ku, idan ba haka ba zan zo da kaina na nemi aurenki." Wani wawan tsaki taja tana riƙe da kan fanfon tana faɗin "Kana ji ko? Wata takwas da ya wuce ƙannan Babana suka ce wai sun min miji kuma zasu ɗaura min aure saboda sun ga na fara fitsarewa, ka san me nayi?" Saida ta gyara tsayuwa ba wani alamar wai ɗar ta ci gaba da cewa "Saida suka turo yaron wajena wai dan mu fahimci juna na zo mishi da wuƙa na kuma tabbatar masa da zan zama ajalin shi idan har ya yarda ya aureni, to dake ba ɗan mahaukaciya bane sai ya gane yare na ya ce ba zai iya ba, iyayena kuma na faɗa musu idan har suka sake min irin haka wallahi zan gudu na bar musu gidan, tun daga shi suke lallaɓa ni suna so suga na fito da mijin da kaina nayi aure, kai kuma baka da tsari irin na mazan da nake so, shikenan sai na kaika gidan mu? Ka min me to?" Jikin shi sanyi yayi sosai hakan ma yasa shi cewa "Shikenan, Allah ya kyauta." Cike da tsiwa da harare harare kamar yana gabanta tace "Ya ma kyauta fiye da haka." Da sauri ta yanke kiran tare da matsawa daf da fanfon ta kashe ruwan dan ya mata yadda take buƙata duk da bai cika ba, ta yunƙura zata ɗauki ruwan wani kira ya sake shigowa wayar ta, tun kafin ta duba wayar ta fara faɗin "Tofa! Allah yayi dare gari ya waye, yadda kasan Nabila ce kaɗai budurwa da ta rage, kowane su-su-su da al..." Ganin ƙawar ta ce ke kura yasa ta yin murmushi ta ɗaga tare da gyara tsayuwar ta tana faɗin "Ina jinki ƙawata?" Wacce ta kira da ƙawar ta ta ita ma da fara'a ta shiga tambayar ta za ta zo ne? Da zumuɗi Nabila tace "Me zai hana ƙawata? Shagalin bikin ki a ce ban zo ba, wa zai zo garin nan to? Ki kwantar da hankalin ki, yanzu haka fa wanka ne zanyi ina so naje wajen wannan marar mutumcin Zizo ɗin naga idan ya ɗinke min nawa ankon, kin san shi ɗan iska ne ai." Da irin hargagin nan na kangararrun yara dan kuwa wacce Nabila ke kira da ƙawar ta ma ta girmeta nesa ba kusa ba, kawai ƙawance ne irin na ɗan duniya ya samu ɗan uwansa ɗan duniya, zigata take kan ta je dan kar ya mata halin da ya saba, dan idan bata saka nata ankon ba ita ma ba zata saka ba. *Fahad* da yau ƙiriniyar ta kawo shi Maraɗi saboda shagalin bikin da za'a gabatar gobe na budurwar abokin cin mushen nashi wato Ja'afar, mota sukutum ba'a sani ba Ja'afar ɗin ya ɗauko kuma suka tuƙota har nan, Allah ne da kariyar sa suka kawo garin nan lafiya lau da kuma katin shaidar ɗan ƙasa da dukansu suke da, tun jiya suka zo kuma suke neman gidan da zasu zauna na sati ɗaya, an kaisu gidaje dayawa daga jiya zuwa yau amma bai musu ba, shine fa aka musu kwatancen nan da tabbacin zasu samu. To yanzu ma tambaya ne suke so su yi shine suka dakata saboda ganin Nabila da sukayi yasa Ja'afar taka birki yana fitowa daga motar da cewa "Bari mu tambayi wannan yarinyar." Fahad da ya hangi fanfo fitowa yayi da niyyar wanke hannayen shi daya gama cin sandwich kafin ya sha faro dake motar, ganin tana waya sai Ja'afar ya ɗan dakace ta har ta idar, Fahad kuma na fitowa kai tsaye wajen bokitin ya nufa, ganin ba sai ya sha wahalar kunna fanfon ba sai kawai ya saka hannun shi na hagu da ya fi iya anfani da shi yana ɗebo ruwan yana wanke duka hannayen nashi biyu. Lokacin ne Nabila ta kula da abinda ke faruwa, tana shirin ba wa ƙawar ta ta amsa ta kashe kiran tana juyowa gaba ɗayanta tana faɗin "Kutumar babakeren kan buru'uban nan... Malam ruwan wankan nawa? Kai! Kai dakata." Duk tayi maganar ne a yanayi na hauka da ɗaga murya da kuma jaye bokitin a haukace tana mishi wani arnen kallo kamar zata kifeshi da mari. Tunda ta fara wannan hargagin duk suke kallon ta har shi kan shi Fahad da ya ɗago da niyyar ko ƴar gidan uban waye sai ya zabga mata mari sannan ya bar wurin, to amma yana ɗora idanun shi a fuskar Nabila, sai siririn kyawunta da kuma fuskar duniyancin da ya gani ƙarara a suffar ta sai suka birge shi, ba zato ba tsammani gabanshi ya faɗi, zuciyarshi ta buga da ƙarfin gaske tare da jin wani yanayi na daban da zai iya kira da matuƙar birgewa. Zahirin gaskiya duk wannan rayuwar da yake yi baya neman mata, babu macen da zata nuna kanta tace shi ya taɓa nemen ta, abu ɗaya kawai da ya saka a gaban shi shine shaye-shaye, to a Dalilin shaye-shayen har ya kan iya ɗaukar kuɗin iyayen shi duk dan ya yi, kai a yanzu ba ma abinda ba ya iya ɗauka dan ya samu kayan maye, har agogon Sabeer ya ɗauka ya bayar aka bashi kayan shaye-shaye, kuma abu mafi masa daɗi ita ce shisha ya mata haɗin kakkauran flavour da ɗan sinadari mai bugawar a ciki, shikenan to rayuwa na yi masa daidai. A yanzu da yake kallon Nabila, sai ya ji yarinyar ta birge shi kuma har ya ji kamar ya ce mata *yana son ta*, sai dai wace irin soyayya? Shi kan shi bai sani ba a yanzun, yanayin ɓacin ran ya fara haɗiyewa kafin ya tsurawa fuskar ta idanu yace "Ke ce kike wannan ashariyar?" A kuwa kausashe kamar za ta haɗeshi tace "Ni ce da kaina, idan ba ni ba wa? Ya zaka saka min hannun ka da ban san me ka taɓa da shi ba a ruwan da zanyi wanka, nasan najasar dake hannun ka ne?" Da ɓacin rai Ja'afar ya matso shi ma a kausashe yana duban ta yace "Ke dallah ƙaramar ƴar ƙwaya, kinsan wanene shi da kike faɗa masa haka? Wace najasa zai taɓa da zata lalata ruwan wankan ƙazama irin ki?" A rikice ta kalli Ja'afar da mamakin kalaman shi, ranta ya sake ɓaci sosai, a yanzu dai ba abun da ta fara sha, amma tana ganin su *Arkiya* nayi musamman ma shisha, kuma tana sha'awar farawa ita ma ko dan baƙin cikin rayuwa, baya ga haka ma tana son taga ita ma ta iya jan hayaƙin nan sannan ta feso shi ta hanci cikin ƙwarewa. To amma yadda Ja'afar ɗin ya mata sai ta ga da buƙatar ta nuna mishi hali irin na su Arkiya idan suka bugu, dan haka a gigice ta sunkuya ta juye ruwan na bokiti suka zube ƙasa a banza, ba ta ɓata lokaci ba ta ɗauki bokitin sai kuma a fuskar Ja'afar da haro ga Allah da ya ga abinda take yi bai taɓa kawowa a ran shi wai shi za ta nufa da sunan ta buga ma ba. Ai kuwa ji kake rumutsuuu a fuskar Ja'afar da wahalar bazata ta saka shi yin wata ƙaƙƙarfar ihu tare da sunkuyawa dafe da fuskar shi, lokaci ɗaya kuma azaba da zafin kalaman da take faɗi bayan ta ragargaza mishi fuska cewa "Aikin banza, har ni zaka kalla ka kira ƙazama? Ka ga ƙazami ma irin ka jahili da baka san me kake yi ba." A zafafe ya yi niyyar nufa kanta bayan duba tafin hannun shi ya ga jinin da ya fito daga bakin shi yana faɗin "Na rantse da girman All..." Da mugun sauri Fahad ya rirriƙe hannayen shi tare da fuskantar shi ya tare shi yana murmushi ganin yadda idanun Ja'afar sukayi jajir yana faɗin "Come on abokina, share kawai, yarinya ce fa." Da maɗaukakin mamaki ya kalle shi yace "Yarinya? Wannan karuwar? Na rantse da Allah ko shugaban ƙasa ne ubanta yau sai ta gane bata da gata a duniyar nan, dallah kauce min!" Yadda yayi maganar à tsawace tare da ƙoƙarin ture Fahad shi kuma ya ƙi bashi damar hakan yana sake bashi haƙuri da cewa "Ka manta nace Ja'afar, yarinya ce, kar ka biye mata dan Allah." Ƙara kallon shi yayi yace "Wai akan me zaka ce na ƙyaleta? Oho! Dan ba kai ta ma ba ko? To wallahi sai na rama." Da ɗan ɗaga murya Fahad yace "Ba zaka rama ba Ja'afar, ba zan bari ka rama ba." A kausashe Ja'afar yace "Wallahi sai na rama, sake ni Fahad?" Shima a kausashe yace "Ba zan sake ba, ba zaka rama ba Ja'afar, saboda..." A tsawace yace "Saboda me?" Saida ya saci kallon Nabila da ta dafe ƙugu tana hararensu tana ayyana _"Sake shi ya zo mana, maza dama na iya faɗa da mata ne? Mun fa san lagon naku, banza kawai, wallahi kana zuwa tsiyata ka zanyi ba kai ba sake moruwa a gaban mace."_ Murmushi ya sake yi saboda kallon Nabila da yayi, sai kuma ya kalli Ja'afar ya sassauta murya cikin raɗa yace" Saboda *ina son ta*, ta yi min, dan Allah ka min kara ka ji." Kallon Fahad ɗin yayi sosai yana tuna ai bai ta;à mishi irin wasan nan ba, ma'ana ya ga mace ya ce yana so, wataƙila da gaske yake tunda ya faɗi hakan à kan wannan da zai bawa sunan *bugagga*, ɗan siracewa yayi ya jinjina kai a sanyaye yace" Shikenan, amma fa idan har ba gaskiya bane ka sani wallahi yarinyar nan ko hayar ƴan daba sai na ɗauka dan su zane min ita." Dariya Fahad yayi yana juyawa ga Nabila yace" Ba ma zaka saka ba, dan da gaske ta birge ni, kai baka ga ƴar duniya bace ta ƙarshe? Kunnuwan ta sun fi komai ɗaukar hankalina." Yana jayawa ga Nabila ya zuba mata idanu yace "Ya sunan ki?" Sama da ƙasa ta ƙwala mai wata arniyar harara sannan ta sake jan tsaki kawai ta nufi da bokitin ta bakin fanfon ta sake kunna ruwa, kusanta ya matsa ya sake cewa "Ya sunan ki dan Allah? Nan ne gidan ku?" Ya faɗa yana nuna gidan nasu, bata kula shi ba har ta ɗibi ruwan ta ta ɗauka juya ta shige cikin gida tana binsu da harara, ganin inda ta shiga yasa shi girgiza kai yana jinjina tantirancin yarinyar, a girme ya girme ta sosai, amma ya ga ta fi shi iya dabanci yarinyar, tunda gashi da ɗaurin ƙrji ma take fitowa daga gidan su, juyawa yayi ga Ja'afar ya kama hannun shi yace "Muje abokina, tunda mun ga gidan zamu sake dawowa." Taɓe baki kawai Ja'afar yayi bai ce mishi ƙala ba yana ta murza bakin shi da ya ji kamar ya fara kumbura har suka shiga mota suka bar ƙofar gidan da niyyar su tambayi wani a gaba. *Haɗuwar su* ta biyu sun yi ta a wajen shagalin Arkiya, inda suka cika da mamakin yadda suka san juna, a bayan Arkiya ta faɗa mata wanene Fahad da irin gatan shi ne ma ta ji zata iya sauraren shi ba dan kuɗin su ba sai dan tunanin zai iya yi mata wata bajinta duba da yadda Arkiya ke faɗa mata irin ɗawainiya da kashe kuɗin da Ja'afar ke mata. Jingine take a jikin motar su tana wasa da ƙaramar wayar ta cikin wata irin fitsararriyar shigar ankon da sukayi na shadda, riga da siket ne ɗamammu da suka lafe a jikin ta kanta babu ɗan kwali ko kaɗan, yatsina fuska ta sake yi ba tare da ta damu da yadda ya matse ta sosai ba kamar zai kwanta jikin ta tace "Wane irin so kake min?" Murmushin shaƙiyanci yayi yana kallon ta yace "Irin wanda kike da buƙata a miki? Kowane iri zuciyar ki ta raya miki, to shi nake miki." Tsakiyar idanun shi ta kalla ba kunya bare fargaba tace "Kenan da iskanci kake sona? Bayan ka samu abinda kake so Shikenan?" Da wani irin masifaffen kallo ya bita da shu'umin murmushi yace "Ko ma haka ɗin ne ai kin san kin kai a so ki dan hakan, bare kuma ni ina ji har ƙarshen rayuwa nake so mu rayu." Sake yatsina fuska tayi tana ɗauke kai tace "Idan ma aure ne ya kawo ka gaskiya ban da lokacin shi yanzu, dan sai da aka so yi mi auren nan amma na ƙi, dan haka zaka iya ƙarawa gaba ka nemi wacce ta shirya aure." Tsareta yayi da idanu yace "Me yasa? Me ya sa ba kya son auren yanzu?" Waina idanunta tayi tana taɓe baki tare da gyara tsayuwar ta tace "Ba wai ban isa auren bane, dan kai da gani kasan zan iya zama da kowane irin namiji, kawai dai ina da wasu burika ne da nake son cikawa kafin auren, idan kuma auren ya gaggauta zuwa min ban shirya ba, a gaskiya kashe shi zanyi na fito na yi rayuwar da nake sha'awa, daga baya na sake yin wani auren." Murmushi Fahad yayi jin wani dace, dan kuwa Ali ne ya ga Ali ai, shi ma gyara tsayuwar yayi yace" Tunda hakane, me zai haka mu fara gudanar da rayuwar da muke so, daga baya sai muyi auren." Wata shaƙiyiyar dariya Nabila tayi tana kallon shi tace" Mahaukaci, ta ya kake tsammanin zan yi rayuwar da nake hasaso ma kaina da kai, sai kuma na ƙare da auren ka?" Gyara tsayuwar shi ya sake yi sosai tare da rumgume hannayen shi a ƙirji yana kallon ta ba alamar wasa yace" Idan kin yarda zaki yi soyayya dani, ni zan iya yi miki komai da kike so a rayuwa, amma sharaɗina shine ba zaki kula kowa ba, ina da kishi da kuma ƙyanƙyami, hakan zai sa ko *bayan abada ma dake kawai zan rayu*, ke ma kuma baki da wani zaɓi da ya wuce ki rayu da ni." Cike da shaƙiyanci Nabila ba tare da tayi tunani akan abinda ya faɗa ba ta kalle shi sama da ƙasa sannan ta ɗauke idanun ta tace" Ka tabbata za ka iya riƙe ni?" Kusa sosai ta yadda kaf jikin su ke gugar na juna ya matso ta da salon nashi shaƙiyancin yana ɗora hannayen shi a mota ya mata rumfa yace" Shafa da kyau kiji, dan ki tabbatar zan yi." Wannan shine mafarin sake fanɗarewar Nabila gaba da baya, tun da ƙuruciyar ta dama dalilin gidajen haya rayuwar ta ta fara gurɓacewa, sai dai duk da haka tana riƙe da budurcinta saboda dogon burin ta da son ganin wanda ya dace da ita, sakamakon shigowar Fahad rayuwar ta kuma sai ta damƙa mishi ragamar komai nata har da mutumcin kan shi, tamkar wasu miji da mata haka suka fara rayuwa a gidan da suka kama haya kafin tafiyar su. Shaƙuwa tayi shaƙuwa, soyayya ta kai soyayya sai dai gurɓatacciya, ido sun ƙara buɗewa Nabila inda ta sake kankaro wulaƙanci da rashin mutumci, tana juya kuɗi yanzu yadda take so, dan da babbar waya tana cazar duk gaulan da ta so kuɗi, amma kuma bata son ta haɗu da kai bare ka nuna ka na da buƙata gare ta, dan kuwa alƙawari ne da ta riƙe la Fahad ba wanda zata ba kanta bayan shi. Da wannan suka zama tamkar tamtabaru, sun daina zama a gidajen su sai lokaci lokaci, kullum suna cikin yawo da fita garuruwa shagulgula, wani sa'ilin ma zai kawo mata ziyara har garin ta, sai ta tare à wajen shi har sai ya tafi. Garin hakane har Nabila ta fara koyon busa sigari a hannun Fahad, kawai yana sha ta same shi, ranta ɓace na faɗan da Mama ta mata da nasiha sa kawai ta kar;e karan ta zuƙa, tari ta fara yi kamar za ta mutu, sai ya karɓa ya shiga nuna mata yadda ake yi, da hakane sai komai ya sake lalacewa. Hakan jarabta ce, wataƙila ta wani kuskure da suka aikata ko kuma dai dan jaraba imanin su, ba dan haka ba duniya za ta yi mamaki a ce ƴar Mama Amina uwr marayu ce a wannan rayuwar, magana dai kam ba ta wanda take ji, bata sauraren kowa bare ta nutsu, fata da addu'ar shiriya kawai Mama da duk wani makusanci da abun yake damu suke kan yi. *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes. *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata. Sayen na gari mai da kuɗi gida, sai an gwada akan san na ƙwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a ƙasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI- SIRRIN MANYAN MATA)._ _Bismillahir-rahamanir-rahim._ *27* Cikin tashin hankali Mama ta haɗa kanta da hannun kujerar zaman mutum ɗaya ta rufe fuska da hijabi tana kuka za ka rantse da Allah ita ce ake duka, Nabila kuma da Yaya Luƙman le mata dukan sababi a falo kuma ya rufe ƙofa ihu kawai take da neman ceto da agaji amma babu mai kawo mata ɗauki, ta kai shi maƙura yau ta yadda a karo na biyu ya sake taɓa lafiyar jikin ta, ba son ran shi bane a ce kamar shi da iyalin shi ace yana dukan balagaggiyar ƙanwar shi da ke ɗauke da shekara *ashirin da shida*, a ce wai gawurtar Nabila ta kai yanzu har tana iya share wata uku babu ko wanda ya ce ya ganta ma bare ta leƙo gidan, wata uku fa! Akan wane dalili, dan kawai sun ce za su aurar da ita ga abokin shi? Tunda ita ta ƙi fito da mijin, yaron kuma da aka mata tsakani da shi ta ƙi fita harkar shi. Ba wai rashin dawowar bane babban tashin hankali, yadda Nabila ta dawo musu gidan ne ya sake ɗaga hankalin su, kamar yadda da ta ji matsa a hannun Yaya Luƙman ɗin take faɗa mishi tana Niamey, daga can wa ita da ƙawar ta suka je aka musu allura wacce take saka hasken fata, madadin shafe-shafen mayuka an samu ci gaba sai dai allura kawai, shine Nabila tayi wani irin haske kamar zabiya ga wata ƙiba da tayi mai kyau fa dan kyau, to bayan dukan da tasha ne yake tambayar ta wannan sarƙar ta ƙafar ta fa, dan shi yana ji a cikin gari ai ya kuma san me haka ke nufi a wasu lokutta, shine ta rantse masa da Allah ba ta harkar matan banza, hasalima ko maza bata kulawa bayan Fahad, kawai shi Fahad ne ya ce hakan na birge shi sai ya siyo mata ta zinare ta saka. Cikin tashin hankali Mama ta rufe kunnuwan ta dan ta gaji da jin sunan wannan Fahad da Nabila ke ta ambata, Yaya Luƙman kuma dake ɗaki da ita wata shaƙa ya ma wuyan ta a matuƙar hassale yana faɗin "Shi kuma wannan askin fa? Na rashin mutumcin gidan uban waye? Aski fa Nabila ? Kina mace? Baki san haramun bane? Shi ma Fahad ɗin ne ya ce kiyi ko? Tunda shine uban ki ?" Idanunta dake warwaje duk sun fito tana ta neman ɗauke numfashi, jin ba ta ce komai ba saboda ya shaƙeta sosai ya sake ta tare da gwara kanta da bango yana faɗin" Ina jinki?" Shasheƙa kawai take à zuciyar ta Allah Allah take ƙofr ɗakin nan ta buɗe, ta fita ko? Ta dai samu ta fita ko? Wallahi su da ganinta sai sun neme ta, Shiyasa kaf bata shiga harkar su, Ummu kaɗai take yin ta da ita saboda ita ka fi ƙaruwa ma da ita, a haka ma dan tana ɗaga ƙafa ne kan wani abun saboda Ummu, ba dan haka ba su sun isa yanzu ma su ganta ne? Ai dan Ummu ce ta ce ta zo ta ga Mama mana, shine za'a mata wannan dukan a wannan jar fatar ta ta da tayi kyau. Aski kuma ko? Ta je tayi, kitso aka mata a salon zane mai kyau Fahad ya ce ya birge shi, dalilin haka ya tara gashin shi abunka ga buzu dandan yayi tsayi ya je aka mishi irin kitson, shine ya gora mata wai yayi kitso saboda ita, ita fa me zata iya yi? Shine ita ma ta aske nata kan aka mata irin askin da ya fi yi, yo à haka ma ai gashin ya fara fitowa ne ba kamar askin na sabo ba. Hmmmm! Yaya Luƙman kenan, kenan mutuwa zaiyi da hargagi idan ya ga tatoo ɗin dake ƙrijin ta da kuma tsakiyar ƙugun ta da na bayan wuyan ta da aka rubuta sunan Fahad? Haka kawai abi a takura mutum. Ganin ta ƙi magana sai kawai ya jefar da zabgegiyar wayar da yake dukan ta da ita ya fito daga ɗakin tare da kulle ta daga ciki, yana zuwa ya ba mama makullin yana faɗin "Ki aje wannan mama, dan girman Allah kar ki bar yarinyar nan ta fita, wallahi Mama yau zan nemawa yarinyar can miji gobe sai an ɗaura auren ta, idan an kai ta ɗakin miji ta kashe kanta in za ta iya." Nabila dake ji da saurare tasowa tayi jiki na mata rawa na raɗaɗin duka, amma a haka ta haɗa kanta da ƙofa tana cewa" Wallahi ba zan kashe kaina ba, amma shi wanda ka aura min sai na kashe shi, na rantse da Allah sai na kashe ko ɗan uban waye, idan ya so Kaga ni da kai duk sai a kama mu, tunda kaine silar mutuwar koma waye." "Ke! Ni kik..." Ya faɗa tare da juyawa a zafafe zai sake komawa ɗakin, da sauri Mama ta riƙe hannun shi tana girgiza mishi kai, cikin sigar tausayi da kukan da tasha tace "Kar ka zma ajalinta Luƙman, bar ta da halin ta." Jinjina kai yayi sannan ya sake miƙawa mama makullin ta karɓa, yana faɗin "Zan nemi yaron nan Fahad a duk inda yake, na gaji da iskancin da yake mana, ko ɗan waye shi wallahi zan masa kashedi akan ƙanwata, dan b..." Bai ƙarasa faɗa ba Nabila daga ɗaki ta fashe da kuka irin mai ihun nan tana faɗin "A'a fa Yaya Luƙman, wallahi kar ka je ka zubar min da mutumci a idanun saurayi, kar ka same shi dan girman Allah, wallahi ajina zaka zubar." Kamar zai mutu dan takaici haka yayi, sai kawai ya jinjina kai yana ci gaba da duban Mama yace "Ni zan wuce Mama, saina dawo." Jinjina mishi kai tayi tace "Allah ya tsare." Da "Ameen." Ya amsa sannan ya fita, shiru Nabila tayi ba ta sake magana ba, hasalima ɗakin ta ta shige tare da tunanin hanyar da zata sake barin gidan, dan ya ɗauke wayar ta ita wannan damuwa bace, kar dai ta haɗu da Fahad tasan zai siya mata wata, dan haka fitar ta ce kawai gaban ta. Kiraye-kirayen sallah ya sa mama tashi ta ɗauro alwala, tana buɗe falon ta shiga ba ta gan ta ba, ɗakin ta ta kalla ta gane tana ciki, a sanyaye ta taka zuwa ɗakin, dake ba ƙofar rufewa labulen kawai ta yaye, kwance take ruf da ciki tana ta tunanin hanya duk da kuwa bacci take ji sosai, kamar yanzu ne ta fara ganin ta da wannan shigar haka ta sake bin ƙafafun ta dake sanye da takalmi ƙafa ciki farare, zuwa sarƙar dake ƙafar ta wacce ta fito sosai, dan wando dake jikin ta irin wanda ake tattarewa ne ya fito da ƙwabri sosai kamar dai irin wandon fulani, har zuwa kan ƙugun ta da aka yi sa'a rigar ta ɗage mata sai ta ga wannan zane mai kamar kore mai duhu alamar na gasken ne, ba wai rashin jigidar da ta san ta da ita bane matsalar, yadda ta ga kamar an zana hoton fuskar wata dabba, a hankali ta dinga cira kanta har zuwa kan damatsenta da suka fito fili sakamakon rigar siraren hannaye ne da ita, a hankali ta sake sauke duban ta kan wani zanen dake tsakiyar wuyan ya, duk da bata san me aka rubuta ba, amma dai nan rubutu ne aka yi da irin waccen abun da aka yi na farko. Girgiza kai Mama tayi idanun ta na sake cika da ƙwalla saboda ganin askakken kan ta, yarinya mai gashi kuma gashin ma mai kyau Nabila take da, amma ta aske kan ta haka ya zama kamar na maza, wannan wane irin zamani ne aka shiga da maza ke barin ɗabi'ar su suna komawa ta mata, mata kuma na barin ta su su koma ta maza? Allah kawai zai mana maganin wannan matsala. A tausashe tace mata "Tashi kiyi alwala kiyi sallah." Juyowa tayi ta fara kallon Maman kafin ta tashi zaune tana faɗin "To." A matuƙar sanyaye kamar dai ta nutsun. Juyawa Mama tayi ta fita da ƙudirin idan sun idar da sallah ta zaunar da Nabila kamar yadda ta saba sannan ta mat nasiha ko Allah zai sa a dace, dan haka Mama ta shinfiɗa sallaya a falo ta kabbara sallah, Nabila kuma jiki a sanyaye ta fito falon ta kalli Mama dke sallah, ƙofa ta ƙalla t ga a buɗe, sai tayi murmushin ganin Mama har tayi halin na ta na mantuwa, ta bar ƙofar buɗe bayan an ce ta kulle ta kar ta fita, ko kuma dai yarda da ita ne yasa tayi haka tana gani ba zata fita ba? Ai kuwa Mama tayi kuskure, dan gaskiya fita zata yi ba kuma ta sa ranar dawowar ta ba. Dama dai da takalmin ta a ƙafar ta, dan haka tana fita cikin sanɗa ta tura ƙofar gidan sannan ta fice ba tare da tasha wahala ba, tana fita da sauri da kuma waiwayen bayanta har ta isa bakin titi, kayan dake jikin ta sam bata ɗauke su a matsayin wani abu ba bare ta damu, dan haka ta samu adaidaita ta shige tare da faɗa mishi inda t nufa, hannu ta sa aljihu tana lalubo kwalin sigari dake aljihun wandon ta, abun kunnawa ta fara nema amma bata samu ba, tsaki taja tare da zago kara ɗaya na sigari tana faɗin "Shashanci, nasan ma na jefar da shi a can..." Sai kuma tayi ƙwafa tace "Yaya Luƙman, wallahi ina ɗaga maka ƙafa, ka kiyayi ranar da zaka kaini bango." Mai adaidaitar ta kalla tace "Abokina zan samu maƙyasta?" Ɗan juyowa yayi ya kalle ta, ikon Allah? Sai ya rasa amsar da zai bata wallahi. Shi bai taɓa kwatanta rayuwar hayaƙi ba, akan me za ta tambaye shi? Tana mace, ba kunya ba tsoron Allah? La'ilaha illalah ! Girgiza mata kai yayi ba tare da ya ce mata komai ba, hakan ya hassalata tace "Ka ji ɗan rainin hankali, idan babu ka ce babu mana, me ye na tsayawa kana ƙare min kallo." Tsaki taja tare da maida karan sigarin a aljihun ta tana ci gaba da kallon gari ta matsu su kai wurin sahibin nata ta sanar da shi abinda aka mata. ******************** Bacci take mai cike da mafarkai da shu'umin yanayin dake neman sakata yin ihu a cikin baccin ta har tana haɗe ƙafafun ta alamar abinda ke faruwa a mafarkin yana ratsata. Da sauri Kuwailat ta shigo riƙe da wayar Maman nata, tana zuwa da sauri ta daddaɓata tana faɗin "Ammie, Ammie gashi, Abba ne yake kira." A nauyaye, a kasalance matuƙa ta buɗa idanun ta, kafin ta dubi Kuwailat ɗin dake tsaye a kan ta tana miƙo mata wayar, da ƙyar ta yunƙura tana tashi zaune tana furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Bata karɓi wayar ba sai kanta data dafe da ta ji ya sara mata da mugun ƙarfi, a tausashe ta ci gaba da nanata sunan Allah a bakinta dan ta ji daidai, da sigar ƙaguwa Kuwailat a ladabce ta sake faɗin "Ammie, ki karɓa kar ta tsinke, Abba ne." Kallon fuskar yarinyar ta sake yi wacce take kama da ita kamar tayi kaki ta tofar, a hankali ta sa hannu ta karɓi wayar, sai dai kafin ta ma duba ta tabbatar Alhajin ne kiran ya yanke, hakan yasa tayi wani tsaki ta aje wayar kan gado tare da kallon Kuwailat a mugun raunane tace "Kuwailat, ban faɗa miki bana son kina tashina kai tsaye idan ina bacci kuma da hargagi ba?" Sunkuyar da kai Kuwailat tayi kafin ta tausasa murya tace "Kiyi haƙuri Ammie, wallahi gani nayi Abba ne ke kira, wataƙila zai gaya miki ranar da zai dawo ne, kin san fa munyi kewar shi..." Ta ƙarashe maganar da sigar tausayi, ƙura mata idanu Ummu tayi, taɓe baki tayi a hankali tare da gyara zamanta a kan gado tana gyara rigar baccin da kasala da damuwa yasa ta kasa cirewa gashi har azahar ta gabato, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da sake duban wayar da aka ƙara kira. Magana ta gaskiya *haushin Alhaji Kabir* take ji sosai, bata sani ba tana aikata zunubi ne haka? Amma fa abun daga zuciyar ta ne yake, ta kasa dakatar da hakan, fisabilillah a ce tana da miji, amma kuma sha'awa na neman halaka ta a cikin gidan nan, baya da lokacin ta saina harkokin shi, idan ma yana gidan tare da ita to ba tsiyar da yake tsinana mata, ai da ba haka yake ba, me yasa yanzu ya zama haka? Me yasa ya ke ƙin kula ta sai ya ga dama? Idan ma ya zo matan a sakanni kaɗan ya kawo nashi ruwan ya tashi ya bar ta? Ita abun ma ya fara fin ƙarfin ta, shekara sama da uku haka na faruwa, har yanzu ta zama sai yawan ɓacin rai da damuwa da kasala dake mugun damunta, dan haka ma yanzu bata wani damu da dawowar shi ba, indan ma ya zo ba abinda zai mata ai, wataƙila ma ranar da zai dawo ba ranar girkin ta bane, dan haka ba buƙatar ta san zai dawo ɗin. A yangance ta ɗaga kiran ta ɗora wayar a kunne sai kuma tayi shiru, Alhaji Kabir da shi kam har yanzu Ummu na nan a yadda take a zuciyar shi da fara'a da farin cikin abinda zai sanar da ita yace "Ummun gidana, hala girki kike ina ta kira baki ɗaga ba?" A taƙaice kamar wacce bata son maganar tace "Umm, ina wuni?" Da sautin fara'ar shi ya sake amsawa da "Lafiya lau Ummuna, ya kike ?" "Alhamdulillah." Ta faɗa bata sake cewa komai ba, fahimtar kamar tana cikin damuwa yasa shi rage karsashin dake tare da shi yace "Ummuna, kina lafiya?" Saida ta zuro da ƙafafun ta daga kan gadon tana kallon ƙofar da Kuwailat ta bar mata a buɗe wacce ta fita tun da taji suna magana tace "Me ka gani? Lafiyata lau." Da rashin kuzari ya sake faɗin "To ai naji kamar kina cikin damuwa ne." Ƙarasawa tayi gaban madubi tana kallon kan ta, Alhamdulillah ba ta rasa ci, sha, sutura kai har ma da kuɗin biyan buƙatu ba, a shekarun nan da suka ƙaru har da jikin ta ma ya sauya, dan yanzu ita ɗin fa uwar dake mallake da shekara *talatin* ce cif a duniya, ta ƙara tsayi, ta ƙara ƙiba sannan fatar ta ta ƙara haske na cima mai kyau da kyakyawan muhalli. Hannu tasa ta shafi kanta dake ɗauke da ƙananan kitso ta shafa tare da faɗin "Ba komai, kawai dai kaina ne yake ɗan ciwo, amma na sha magani." Cike da kulawa yace "Ayya! Sannu amaryata, to kin ga kwanta ki huta, amma dai ina fata kin ci abinci?" Yatsina baki tayi dan ita wallahi bata jin daɗin yanayin ta, ina ma Kuwailat ta bar ta ta kai ƙarshen mafarkin ta, ita bata ma san da wa take tare ba, kawai dai ta ga kanta a wata duniya da take fatan ziyarar ta a zahiri, a ƙasan maƙoshi ta amsa da" Um um, gashi can Kuwailat na dafawa." Murmushi yayi dan yasan Kuwailat ɗin ai za ta iya, tunda ta fara zama budurwa, dan haka yace" Shikenan to, idan kin ce sai ki kwanta ki huta, amma kafin nan albishirin ki?" Da sigar ƙaguwa ta amsa da" Goro." Da fara'a ya ce mata" Anjima zamu taso, dan haka kiyi shirin tarbata." Ba ta so yin doguwar magana da shi ba, amma shirin tarban shi da ya faɗa yasa mamaki bayyana a fuskar ta har ta maimaita" Shirin tarban ka?" Dariya yayi wacce har saida ta ji sautin ta yace" E mana, na miki bazata ko? Dama ai haka nake so, ki shirya ke dai, sai na zo in sha Allah." Yanke kiran yayi Ummu na kallon kan ta a madubi, tsabar takaici yasa har idanun ta suka cika da hawaye, da ƙarfi ta aje wayar gaban madubin tare da shugewa ban ɗaki dan tayi wanka tayi alwala tayi sallah azahar da ake daf da fara kiran ta. A tsanake tayi wanka ta fito ta shirya cikin kayan da ta fi sha'awa a rayuwarta wato duguwar riga musamman ma abaya, rigar wani tattausan yadi ne jikin ta mai maɗauri a baya, saida tayi sallah ta shafa sahihun turarukan da bata iya rabuwa da su a rayuwar ta wato na *gidan ƙamshi* da Hajia *Fussam* ke siyarwa, abun daɗi ga kayan ta shine hatta turaren da mace zata yi anfani da shi yayin zuwa wajen oga da shafawa dan fita gama-gari tana da, yadda Ummu tayi mugun sabo da turarukan tana ji a jikin ta idan aka ce yau ta kasa samun turaren nan to zata shiga babbar matsala, dan kuwa turaren Hajia Fussam *maƙura* ne, turaren Hajia Fussam *ƙarshe* ne, turaren Hajia Fussam *duniya* ne da duk macen da ta san kanta ya dace ta ƙulla abota da su dan kankaro na ta mutumcin, wani abun sha'awar kuma shine, in dai da turaren ta kike anfani, to da wuya ki haɗu da wata mai irin ƙamshin turaren ki, sai dai idan ita ma a wajen ta take siyayya. Sallah ta gabatar kafin ta cire hijabin ta ta fita falon, Kuwailat ita kaɗai ta samu zaune tana kallon tashar Manara da kuma littafi a hannun ta tana karatu sannan tana kallo, saida ta ƙarasa ta ɗauki remonte ta kalle ta tace "Kin yi sallah?" Da raha yarinyat tace "E Ammie, kin fito?" Saida tayi nufin zama a kujera sannan ta amsa da "Um, kin yi girkin?" Da fara'a a fuskar ta da sakewa alamar dake nuna ƙawaye ne su ɗin tace "E Ammie, tunda kika ce nayi ai dole nayi, na kawo miki ne?" Amsar da Kuwailat ɗin ta bata yasa ta yin murmushin da ya fito da haƙoran makkarta duga biyu ta girgiza kai tace "Sai anjima zan ci." Cikin shagwaɓa Kuwailat ta turo baki tace "Ammieeee..., Abba fa ya ce na kula dake kafin ya dawo, kuma ya ce so yake kiyi ƙiba, amma ba kya cin abinci tunda ya tafi." Ƴar harara ta aika mata tace "Ke, bana son iskanci." Dariya Kuwailat tayi tace "Shikenan, amma zan sanar da Abba idan ya dawo." Girgiza mata kai tayi tare da faɗin "Ɗauko min wayata ɗaki." "To Ammie." Ta faɗa tana miƙewa da sauri, shigar ta ke da wuya Hajia Atika ta shigo ɗakin da wata sallama ciki-ciki cike da raini da wulaƙanci. *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes. *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata. Sayen na gari mai da kuɗi gida, sai an gwada akan san na ƙwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a ƙasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI- SIRRIN MANYAN MATA)._ _Bismillahir-rahamanir-rahim._ *28* Ko dan yau bata yanayin farin ciki? Sai kawai take ji a ranta yau ba zata saurarawa Hajia Atika ba, basu taɓa haɗuwa da matar nan ba tare da ta ce ga abinda Ummu ta mata ba, ta nuna mata ƙiyayya tun tana amarya, ta sha masifa da bala'in matar nan har yanzu ma da take shigowa ita tasan ba alkairi bane ya kawo ta, musamman da ta ganta cikin shiri irin na fita sannan sai wani saɓa mayafi take, fuskar nan kuwa tsaf da kwalli har da su hoda, duk da fa shekaru sun ja sosai yanzu, amma ƙarfin guiwa da kwalliyar ta na birge ta sosai, dan bata yarda shekaru, ɗiya da jikoki sun hana ta yin ado da kwalliya ba. Kamar yadda tayi sallamar ƙasan maƙoshi hkaa ita ma Ummu ta amsa, sai dai da sakin fuska har da faɗin "Aunty, ke ce tafe? Ƙaraso ?" Ba ta amsa mata ba sai yatsina fuska da take har ta zo gaban ta ta tsaya nesa da ita, ba komai da komai hannu kawai ta tara mata tace "Bani makullin motar Alhaji zan fita." Da mamakin buƙatar da Hajia Atika ta zo da ita ta kalle ta sosai tace "Motar Alhaji kuma aunty? Ta ki fa?" Saida ta kawar da kai sannan tace "Ta wa ta samu matsala, na kira za'a zo a duba min, bani sauri nake." Ba tare da ta tashi daga inda take ba ta kalle ta ita ma tace "To aunty na baki, shine ya ce na baki? Ni gaskiya bana son matsala, haka waccen lokacin kika ce a ba Hayat aki aike shi, ya je ya samu matsala da motar nan, da Alhaji ya zo wallahi ni ya ma faɗa, dan haka ma yanzu da zai bani shi tunda ai ranar girkina ne ya tafi saida ya min gargadin kar a taɓa mishi mota." Wata irin tsayuwa tayi da yanayin jin bala'i tace" Me kike nufi ? Ba zaki bayar ba ko me?" Girgiza mata kai tayi sanda Kuwailat ke fitowa ɗauke da wayar ta tace" A'a aunty, ki kira shi dai, idan ya ce a baki wallahi take zan baki, amma idan bai ce ba sai kiyi haƙuri." A zafafe tace" Ba zan kira shi ɗin ba, kema ai kin san Alhaji ba bari yake ana taɓa mishi mota ba, ki bani kawai zan je in dawo ne sai ya zama matsala, dan kin ga à hannun ki take ? Da ke ce kika buƙata ai sai dai mu ga zaki fita da motar tunda ke ce matar so." Girgiza kai Ummu tayi ta kalli Kuwailat, suna haɗa idanu da ido ta mata alamar ta shiga madafa, da sauri ta nufi madafar tana kallon Hajia Atika, saida ta ga shigar Kuwailat sannan tace" Aunty, ni dai ba rigima nake so muyi ba, ga wayata ma zan iya kira miki Alhajin, idan ya ce na baki ni banda matsala da hakan." Cikin ɓacin rai Hajia Atika tace "Bana so, karki ki kira shi, ko kin fini sanin lambar shi ne? Ai ni dama nasan za'a rina, ke dai wallahi ki ji tsoron haɗuwar ki da Allah, tunda Alhaji ya aureki duk kin mallake shi, komai nashi ke ce kamar je kaɗai ya mallaka, daga ke sai ƴar ki yanzu kuke yadda kuke so a gidan nan, gaba ɗaya kin susuta ma Tsoho nutsuwar shi, hatta yaran shi idan suna son abu gare shi sai dai su bi ta hannun ki idan suna so su samu, mtssss! Ke da Allahn ki." Tana gama faɗa ta juya a fusace ta bar falon, saida ta ɓacewa ganinta ta sauke ajiyar zuciya, Shiyasa ta fi ƙaunar Hajia Asiya, dan ita bata da hayaniya, ita idan Kaga ta shiga harkar Ummu to kawai an taɓa ta ne, bare kuma yanzu da tsufa ya zo mata mutumci kawai suke, amma shine har Hajia Atika take faɗa mata wai ta ji tsoron Allah, to ita me take yi da ya saɓa? Alhaji bai taɓa yi mata abu bai musu ba, bata taɓa yarda an tauye wata a dalilin ta ba, idan ya tashi tafiya yana ɗakin ta ne duk abu nashi muhimmi ya kan aja a ɗakin ta, idan ma ɗakin wata tafiyar ta kama shi ya kan ba wacce yake wurin ta ne, to ina kuskure a nan? Maganar yaran su kuma da take idan suna son abu, a iya sanin ta Zeinab ce kawai da ta sa kanta kasuwa tana son kuɗi masu yawa, kuma ita da Zeinab kamar ƙawaye ne, zata iya cewa ma sun zama ƙawaye kuma aminai shine ta sanar da ita ta ce ta faɗawa abban, dan tana tsoron ya hana ta, kuma da Ummun ta faɗa sai ya amince har ya bata jarin wanda yanzu take fantamawa abun ta, to ina matsala anan Shima? Wayar da Kuwailat ta kawo mata ta ɗauka tare da gyara zaman ta dan shiga WhatsApp ta ga yau wace wainar a ke toyawa a daɗaɗɗen grp ɗin su mai tarihi da ya kwashe shekaru har yau ana damawa a cikin shi wanda dalilin shi abubuwa dayawa sun faru kuma an ƙaru da mutane dayawa sannan an buɗe wasu grp ɗin. ****************** Da sallama a baki Fa'iza ta shigo falon tare da mahaifiyar ta a bayan ta, da sauri Yaya Bilal ya kalli ƙofar saboda sanin muryar wacece, ai kuwa fuskar ta ya kafe da kallo kamar yau ya fara ganin ta, ko da yake kusan hakane, shekaru kenan da dama da suka wuce tunda ta tafi ta ƙi dawowa, su Hajia sun je bikon kan ta dawo amma ta ƙi ta ce sai ya zo da kan shi, shi kuma yana ganin ai shi ta ɓatawa rai sannan kuma iyayen shi sun je, a ƙalla ta fi shekara uku wajen Yayanta dake aiki a Moscow, ba ma wannan ba fa, labari da ya samu wai makaranta ta koma da auren na shi. Ita fa Fa'iza bata ciki da rainin hankali ne, kuma bata ciki da ƙalubalen wahalar zaman aure, idan zai yiwu kawai a yi, amma tayi yaji ya ƙi biyo ta kuma a haka yake so ta dawo? Sam ba zata iya wannan ba. Har suka zauna bai daina kallon ta ba tana gaisawa da su Hajia da kuma Alhaji dake kwance wanda kwna biyu kenan baya da lafiya, saida t gama gaisawa da kowa kafin ta kalli inda yake, yana nan yadda yake, ko rashin yara dayawa ne yasa baya tsufa? Oho! A taƙaice tace "Y mai jikin?" Shi ma da ya kasa daina kallon ta ganin kamar yadda ta fita daga gidan zaka rantse shekaru basu ƙaru a kan ta ba yace "Da sauƙi, yaushe kika dawo?" Saida yayi tambayar sai kuma ya gane ba anan ya kamata ya mata tambayar ba, ba tare da ta daina kallon shi ba tace "Sati kenan da na dawo." Jinjina kai yayi da irin yanayin nan na yayi kyau hamshaƙiya sannan yace "Da kyau, an sha karatu?" Da fara'a a fuskar ta kamar mai son ƙular da shi tace "Umm wallahi, yanzu haka ma ina neman aiki ne a babban banki, kuma na samu hanya in sha Allah ina sa ran zan samu." Wani shegen kallo ya mata irin _"Ke dai kika sani ɗin nan."_ Kafin ya ɗauke kan shi, jim kaɗan suka kalli juna ita da Maman ta tace" Mu tafi ko?" Kallon ta Hajia tayi tace" Fa'iza, kin dai ƙi dawowa gidan ki ko? Hajia..." Ta faɗa tana kallon Maman Fa'izan tace" Kun ƙi ku sa baki ta dawo gidan ta?" Kallon ta duk sukayi sai maman Fa'iza da tayi murmushi dake irin matan nana ne ƴan boko sosai tace" Ba haka bane Hajia, ita ta ce ba zata dawo ba sai ya je da kanshi yana son ta dawo ɗin, to kuma Kinga bai je ba, kenan ba ya da buƙatar ta ne a gidan shi?" Wallahi kunya ce sosai ta kama Yaya Bilal ya sadda kanshi, kallon shi Hajia tayi tace" To ka ji, ban an har yaushe kake so mu ci gaba da zuwa yi maka bikon mata ba, alhali kai kuma ba yaro ba." Sabeer dake tsaye ɗauke da ƴar shi a kafaɗa tana bacci wacce it ce ƴar shi ta uku, dariya yayi yace" In sha Allah zamu je tare da shi Hajiyoyi, yau sai ya je munyi bikon auntynmu." Murmushi kawai Fa'iza tayi tana kallon Sabeer tace" Sabeer, zan dawo ko bai zo ba, dan akwai aikin da nake so na kammala a gidan nan, amma fa sai na cika burina na zama ma'aikaciyar da zan iya tsayawa da ƙafafuna, ta hakane ko Allah ya sake ƙaddara ana rabuwa ba za'a min gorin ban rasa komai ba anan sannan ayi tunanin na rasa wani abu a can ɗin." Idanun shi ya ɗago ya kalle ta lokacin da ta juya dan fita daga falon, sai kuwa Abida ta shigo da sauri tana riƙe da hannun yaron ta wanda Yaya Bilal ya raɗa ma *Aslam* amma ita ta ce sunan nan bai mata ba ita *Aswan* take so, hakan yasa wannan lamari yin tsamarin da Abida ta sake fita a ran su, dan har yau ita Aswan tae kiran shi, dan kuwa tsaf tasa aka yanka mishi ƙatuwar saniya ta raɗa mishi wannan sunan, abubuwa fa sun faru a shekarun da suka gabata. Irin murmushin muguntar nan Abida ta saki saboda ganin Fa'iza, a kullum kallon asararriya take ma Fa'iza wacce ba ta da rabo, da azama ta riƙo hannun Aslam dake gaba tana faɗin "Dakata mana, zo ka gaishe da auntynka." Hajia da ganin Abidar ya sa ta kawar da kai haka ma Sabeer da ya bita da harara, Yaya Bilal kuma tuni ya maida hankalin shi ga Aslam yana mai matsuwa da ya ƙaraso wajen shi ya rumgume shi ko ya ji sanyi a ran shi, Abida kuma cike da izgilanci ta turo Aslam gaban Fa'iza kaɗan tana faɗin "Ga ɗan naki." Murmushi Fa'iza ta mata irin na babba da yaro sannan ta shafa kan yaron tana kallon shi har da ɗago haɓar shi tana faɗin "Ma sha Allah, Aslam ne zan ce ko dai Aswan?" Sai kuma tayi murmushi tace "Ko da yake dama ai kai ɗin ɗan Maman shi ne, da Abbun ka ya fahimci haka da tuni ya jefar da ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda." Da ƙarfi Abida ta jawo hannun Aslam tana mai hararan Fa'iza tace "Matsalar ki kenan, ba damar a haɗu da ke sai kin yi zaurencen d za'a kasa gane ki." Raɓata tayi za ta wuce Fa'iza ta bita da kallo tana faɗin "Hmmmm! A juri zuwa rafi dai, da sannu tulu zai fashe." Sabeer dake ƙufule da Abida kallon ta yayi yace "Me ye abun da ba'a ganen ba a maganar ba? Hausa ga ta yi." Kallon shi tayi fuskar ta a haɗe, magana ta gaskiya ta jima da fahimtar akwai canji da zaman ta da mutanen gidan nan, yadda suke da yanzu ba haka suke ba, ba ta san me yasa ba, kuma bata so ta sani tunda mijin ta dai suna zaune lafiya, sannan yana bala'in son ɗan ta, dan haka bata da matsala da wannan, ba tare da ta saki fuska ba tace "Hausa ta yi, amma ai da lauje cikin naɗi a hausar ta ta." Wani malalacin murmushi Sabeer yayi yace "Hmmmm ! Dama ai idan da laujen cikin naɗi sai mutum ya ji ya tsargi kan shi." Da mamaki yanzu ta dube shi jin kamar akwai abinda yake nufi da ita tace "Tsarguwa? Tsarguwa fa ka ce Sabeer, wace irin tsarguwa kuma kamar wata wacce ta aikata laifi?" Saida ya bita da shashashan kallo sannan yace "Kusan haka." Yana faɗa ya ɗauke kan shi, da wani mamaki ta sake kallon shi tace "Ban gane me kake nufi ba Sabeer? Ya kake magana kamar kana son faɗin wani abu." Kallon ta ya sake yi yace "Ina nu..." Da sauri Hajia ta katse shi da "Sabeer kana lafiya wai?" A ldabce ya kalli Hajia yace "Kiyi haƙuri Hajia." *ME CE CE DAMUWAKI*? Rashin ni'ima? Rashin gamsar da mai gida? Warin gaba? Bushewar gaba? Zubewar nono? Cikowar nono ? *Kina buƙatar...* Fatarki tayi laushi? Tayi santsi? Ta kwanta luf? Kina walkiya da annuri tamkar amarya? Sabulu kike so ko haɗin shafawa ki wanke ko mai na shafawa? Ki wadatu da sahihin ƙamshin haukata mai gida? Humra da zaki saka mijinki bacci bai shirya ba? Humra da zata tayar da sha'awarsa? Kulaccha da zata saka mijinki ya kasa yi miki tsara a fannin ƙamshi? Kulaccha da zata gagari manyan mata suffanta kalar sunan turarenki? Turaren wuta irin na asali barebari? Turaren da zaki fesa à zanin gadonki har ya rike mai gida ya kasa tashi? Turaren da zaki zuba ga ruwan wankan mai gidan ki? Turare don yaranki? _Idan duka kina buƙatar ɗaya daga cikin kayan nan, to ki tuntuɓi wannan lambar ta WhatsApp *+227-82-21-91-74* wanda suk gwada sun san ingncin kayanmu, ba buƙatar ɓata lokacin cika muku baki._ Wani abun farin ciki kuma, duba da yanzu ba kowace mace ke son shan garin magani ko matsi ba, akwai haɗi irin su *tsumi*, *ruwan tsumi*, *tukunya*: dayawa sun san tukunya, don da itace muke tutiya, kuma tukunyar nan akwai na ruwa dana dafawa a nama, sannan akwai kankat wato haɗin *kayan marmari*. *Garaɓasa* Ga waɗanda sukayi nisa kuma haɗin kayan marmari ba zai kamacesu ba, duba da kafin sakon yaje garesu zai fara lalacewa, don haka ga sauki ya samu, madadin kuɗin mota da zaki yi, zaki biya 1000k kacal don a sanar dake yadda zaki had, ba iya guda kawai ba, dama sauran haɗi irin na kayan daya shafi na marmari da ɗanye, musamman ma *sirrin kankana* da kuma *cucumber*. *JANNAT HOUSE.*🧕 Kallon Hajia Abida tayi tace "Mamie, ki bar shi ya faɗi abinda ke ran shi, dama na jima da fahimtar kamar akwai wani gani-gani da ake min a gidan nan, ban san me yasa ba ko me nayi, a sanar dani mana ai zai fi ko? Madadin ayi shiru ana kallona da abun ni kuma ina jin ba daɗi..." Saida ta kawar da kanta cike da raini da gawurta tace" Dan raina zai iya ɓacewa har na zo nayi abinda zan bayar da mamaki." Gyara tsayuwa Sabeer yayi, kafin ya ce wani abu Abbu Mukhtar da ya shigo tare da Sa'ad wanda yau ya zo dan duba jikin Alhajin wanda gaisawa m'a da su Fa'iza ya tsayar da shi kuma ƙofar a buɗe take, dan haka ya ji komai da suke tattaunawa yace" Ki ji ba daɗin mana, ƙwarai akwai abinda muke ɓoye miki, wanda da mun bi ta zuciyoyin mu da Allah ne kaɗai ya san me zai faru, mu da kika ma laifi muka haƙura muna zama dake abisa tilas, sai ke ce ba zaki iya ba saboda ki nuna mana ke gawurtatta ce a rashin imani da aikata miyagun laifuka." Da matsanancin mamaki Abida ta kalle shi, Aslam da tubarkallah ya girma ya riƙo hannun ta yana faɗin" Mamma muje, ke fa kika ce zaki kai ni yau, Muje mana." Fizge hannun ta tayi daga riƙon da yaron ya mata tana faɗin" Kai dakata na gama da wannan gayyar." Sai kuma ta dubi Abbu Mukhtar wanda girma ya ƙara zuwa mishi gemun shi duk furfura ne kamar shi ke gaba da Yaya Bilal tace " Me kuke nufi? Ni kai tsaye nake so ku faɗa min ku daina nuƙu-nuƙu." Gyara tsayuwa Sa'ad yayi da yanayi na ɓacin rai da takaicin ta, dan ko kwana biyu da ya wuce sun yi magana da Hambali, dan haka a ɗan kausashe yace "To wai me yasa kike ta nanata a faɗa miki ne? Kina jin har kin cimma burikan naki ne da har kike jin ko yanzu asirin ki ya tonu baki da matsala? Ki ci albarkacin Alhaji dake kwance ba lafiya, ba dan haka ba wallahi da na feɗe miki biri har wutsiya." A kausashe ita ma ta kalle shi tace" Kai a wa da har zaka sa mana baki a maganar nan? Asirina ya tonu? Ya tonu ɗin, ka tona mana idan ka san shi, kada ka ga an yi shiru har auren ka ya ɗauru da Eesha, rashin sanin waye kai a baya yasa iyayen ta yarda da kai, ko ka ɗauka bamu san a baya dillallin ƙwaya da hodar iblis bane kai?" Girgiza kai Sa'ad yayi ya gyara tsayuwar shi, da sauri Hajia ta miƙe tsaye tana matsowa kusansu tace" Kunga, dan Allah bana son tashin hankalin nan, ku rabu da ita kawai, kowa yayi na gari ai dan kan shi." Wani kallo ta ma Hajia ta murguɗa baki tare da kaɗa kan ta, hakan an sa Sa'ad jinjina kai sannan ya kalle ta ƙasa ƙasa yace" Hakane, baki yi kuskure ba, ni dilallin ƙwaya ne a baya, amma Alhamdulillah tunda na jima da karɓan tuba, a duniya kuma mutum ya san kuskuren shi sannan ya gyara kuskuren shine alkairi ma fi girma, shi waccen... *tsohon najadun* ai har yanzu sana'ar shi kenan, kuma na gama shirya yadda zai zo ƙasar nan, wallahi daga inda ya sauka ko numfasawa ba zai yi ba zan sa a kma shi." Sai kuma harare ta sama da ƙasa yace" Idan kin isa ki hana shi zuwa, idan kuma kin isa ke ki hana faruwar abinda zai yi Dalilin barin ki gidan nan bayan kama ki da mugayen laifuka." Da yanayin hassala Sa'ad ya gifta zai wuce sai kuwa Yaya Bilal ya riƙe hannun shi, kallon juna sukayi inda Bilal yace" Me ka sani? Matata ce fa? Duk me kuke nufi da maganganun ku?" Saida Sa'ad ya kalli Abida data zuba musu ido, sai kawai ya girgiza mishi kai yace" Ba komai kawu." Da rashin fahimta Yaya Bilal yace" Kam..." Kafin ya faɗa Abida ta dafa kafaɗar shi tace" Tunda ya ce maka ba komai to ba komai ɗin, da suna da wata hujja ai da tuni sun yi aiki da ita a kaina, ni fa na jima da fahimtar ana nuna min tsana a gidan shiru kawai nayi, ni Kaga ba wannan ba, zamu fita ne da Aswan, kuɗi muke buƙata?" Kallon ta Yaya Bilal ɗin ya yi, sai ya ga mahaifin shi na kwance za ta zo da maganar kuɗi za su fita, sai kawai ya figo hannun ta zuwa falo, da kallo duk suka bisu kafin Hajia ta kalli Sabeer da Sa'ad tace" Bana son fitina, dan Allah ku barta da halin ta." Sa'ad ne ya zauna kan kujerar da Yaya Bilal ya tashi yana faɗin" Ba zamu barta ba Hajia, mun yi iya shirun da zamu iya, ya kamata ta san cewa duk shekarun nan alfarmar rufa mata asiri muka yi." Abbu Mukhtar ne yace" Har ma zuwa yaushe za mu ci gaba da ƙyaleta Hajia? Wanda ina ji a jikina da sa hannun ta a ɓatan Eesha." Jinjina kai Sa'ad yayi ya kalli Abbu yace" Dole ma ta girbi abinda ta shuka, duk shekarun nan da tunanin yadda zan wargaza shiri ta nake kwana nake tashi, komai tafiyar wahainiya yake saboda suna da kuɗi, amma yanzu abu ɗaya kawai ya rage da zan fallasa ta." Da sauri Sabeer ya kalle shi yace" Me kenan?" Saida ya kalli Aslam da98 sai yanzu ne yake bin bayan iyayen nashi yana faɗin" Na haɗu da ɗaya daga cikin mutanen da sukayi garkuwa da Fahad shekarun da suka wuce, duk da yanzu sun bar harkar dan dama can ba aikin su bane, ya min alƙawarin haɗani da wanda ya jagoranci aiki, shi kuma zai sanar da ni wanda ya saka su kama Fahad, daga nan komai zai zo ƙarshe." Zaro idanu duk sukayi musamman ma Abbu da yace" Sa'ad, wai dama har haka kake bibiyar wannan lamari? Ka tabbata baka sa kan ka a haɗari ba?" Murmushin yaƙe yayi dan ko wayar da sukayi da Hambali gargaɗi yake mishi ya zuba ido akan abinda ke faruwa a gidan nan kawai yace" Ba komai Abba." *Falo* kuma a kausashe Yaya Bilal yake duban ta yace"... *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes. *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata. Sayen na gari mai da kuɗi gida, sai an gwada akan san na ƙwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a ƙasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI- SIRRIN MANYAN MATA)._ _Bismillahir-rahamanir-rahim._ *29* A kausashe Yaya Bilal yake duban ta yace "Kuɗin me ? Abida baki da hankali ne? Uban nawa na kwance kike cewa na baki kuɗi zaki fita da yaro? Ina zaku je ? Me zaku y?" Wani irin juyi tayi da irin an takura mata ɗin nan ta juya mishi baya tana cewa "Kai! Ni fa gaskiya abun nan ya isheni, wai me na muku ne haka? A gaban ka fa ƙannan ka har da mijin ƴar ku suke gaya min magana, gaban idanun ka Sa'ad ya kira Babana da tsohon najadu, me ka yi? Na ƙyaleka sai kuma kai ma ka ɗora naka, to na gaji gaskiya, Haba." Juyawa yayi inda zai fuskance ta yace" Duk abinda suka faɗa bana jin zasu faɗa babu dalili, Abida na fara gajiya da abubuwan ki, tunda kika haifi yaron nan kuɗ kawai kike karɓa a hannuna, me kike yi da su?" Da mamaki ta ƙanƙance idanun ta tace" Me nake yi da su? Zargina ma kake?" Saida ya gyara tsayuwar shi da kyau tare da harɗe hannayen shi yana kallon fuskar ta yace" E, zargin ki nake." Sassauta murya tayi dan ta fara ganin alamun kamar baƙar rana ce yau a gare ta tace" Me yasa to?" A take ya bat amsa da" Saboda karɓan kuɗin ki ya yi yawa." Taɓa baki tayi à sanyaye ta kama hannun Aswan da ya same su nan tace" Shikenan, ka riƙe naka kuɗin, ni zan kai shi shan iska kamar yadda na mishi alƙawari." Jan hannun Aswan ta fara yi inda shi kuma cike da wayo da kuma abinda ke ran shi kenan yace" Ni fa Mamma shiyasa na fi son kawu Hashim." Da sauri ta kalli Aslam ɗin tare da mishi alamar _" Kai! Yo shiru."_ Sai kuma ta juyo a hankali ta saci kallon Bilal da suka bari nan tsaye, duk da ya ji abinda ya faɗa yaron bai kawo komai a ran shi ba, amma kuma yanayin da Abida ta nuna da juyowa da tayi ta kalle shi, sai kawai ya ji kamar bai yarda da ita ba tare da dasa mata alamar tambaya, in ba haka ba miye na ma yaron nuni da ya yi shiru? Miye na wani juyowa ta kalle shi? Waye kuma kawu Hashim ɗin da yaron ya faɗa? Ummmmm! Ya tuna, wanda ta taɓa nuna mishi a matsayin cousin ɗin ta ko? Hakane, to amma me yasa Aslam ya faɗi haka? Wace shaƙuwa ce ta shiga tsakanin su? Bayan ta faɗa mishi shi Hashim ɗin ba ma a nan garin yake ba, sannan a ranar da ya fara ganin shi ta ce ranar ne farkon zuwan shi gidan nan ya kawo mata ziyara, har ya gama tunanin shi bai kawo komai a ran shi ba, dan ko ranar da ya samu yaron har madafa shi da ita suna hira bai ji zargin su a ran shi ba, ya bar hkan a matsayin zumunci ne kawai. Murmushin yaƙe ya yi ya koma ɗakin da ƙudirin idan suka dawo zai zauna da yaron dan jin me kawu Hashim ke mishi da har ya fi ƙaunar shi da shi uban da ya haife shi yake kula da shi da ɗaukar duk wata ɗawainiyar shi. *Ɓangaren* Mama Nuriyya kuma farin cikin zuwan su Aisha ya sa har yanzu bata koma wajen su Hajia ba, yanzu haka rumgume take da ƴar da Aisha ke goyo wacce ita ce ƴa ta uku da ta haifa kuma duk mata, inda ta maida gaba ɗaya hankalin ta kan Aisha dake zaune kusan ta kamar ƙawayen juna tana tambayar ta "Kenan dai har yanzu sarakuwar ki na son ki?" Murmushi Eesha tayi na mamakin irin tambayiyin da Mama ke mata tace "E mana Mamie, ita fa irin matan nan ne masu son kuɗi, ina mata kyauta sannan ina mata ladabi da biyayya, shiyasa take sona kuma har gargaɗi take ma Abbu kar ya ɓata min rai, ranar ma fa cewa tayi idan ya muzguna min bata yafe masa ba." Dariya Mamie tayi tace" Iyeh! Lallai kin samu soyayyar ta, to shi fa, ba ya miki komai dai ko?" Da sigar ƙaguwa Aisha tace" Mamie, kin tambaye ni fa ɗazu." Turo baki tayi tace" To ki sake bani amsa mana, hankalina ba zan kwanta ba idan ba kya farin ciki a gidan ki." Riƙo hannun Mamie ɗin tayi da fara'a a fuskar ta tace" Mamie, yana sona, yana kyautata min, har yanzu fa kamar ango da amarya muke, kuma kinga yana zama dani a gida muyi hira, yana tayani aikin gida, Mamie, idan kika cire saɓanin da akan iya samu a kowane zama, bana da wata matsala da Abbu, ki yarda dani." Ɗaga mata gira Mamie tayi da yanayin raha ta kalle ta sama da ƙasa tace" Umm! Na gani ai, tunda ga jikin ki nan ya nuna, Amma dai Eesha kin daina motsa jiki ko? Dubi fa nema kike ki zama ke ce mahaifiyar ta wa." Turo baki. Aisha tayi cikin shagwaɓa ta dora kanta a kafaɗar Mamie tace "Mamie, wallahi fa shi ƙibar nan yake so, a haka fa wai cewa yake baya so idan kuka ganni ku ce yana barina da yunwa." Dariya ita ma Mamin tayi tace "Ban san wane irin raino Sa'ad yake miki a gidan nan ba, duk ya lalata min ke wallahi." Murmushi Aisha tayi tana shafa hannun Mamien da ita kuma take jijjiga Yusrah dake bacci, jin ba ta ce komai ba yasa ta ƙoƙarin aje Yusrah tana faɗin "Bari kiga in tashi, akwai wani abu da nake son haɗa miki ki tafi da shi, nima a wajen *aunty Ummu* na koya." Kallon ta Aisha tayi tace "Mamie, wai har yanzu grp ɗin nan yana nan?" Kallon ta tayi bayan aje Yusrah da yanayi irin wanda kake magana da ƙawar ka tace "Sosai ma, ai kullu gidan mu gaba yake ci, a ƙalla grp biyar aka buɗe duk ta dalilin shi, ke har da fondation muka buɗe na taimakawa mabuƙata (in sha Allah mu ma muna nan muna shirin yin haka, ga duk wacce take neman lahira da burin ta barin duniya aikin alkairin ta na bin ta, to ta shirya sannan ta mana magana, in sha Allah zamu buɗe ƙungiya dan taimakon marayu da mabuƙata, kuma ba sai mai kuɗi ba, da naira ɗaya zaki iya taimakawa wanda ba ya da ita, Allah ka tallafa mana akan wannan ƙudiri namu)..." Sai kuma ta tsaya da kyau tana kallon Aisha tace" Wai dakata, kenan baki taɓa bayar da taimako ga gidauniyar mu ba?" Girgiza kai Aisha tayi tace" Mamie baki taɓa faɗa min ba ai, kenan dai kun tsayu kan ƙafafun ku?" Da irin kurin nan Mamie har da juya idanu tace" Ƙwarai ma, kuma wallahi sai kin fara bayar da gudummuwar ki ma." Dariya dai Aisha tayi tana kwantawa kan doguwar kujerar tace" Na ji to Mamie, yanzu dai a kawo min abinda aka aje min." Nufa ɗakin ta tayi tana faɗin" Bari na dawo, amma sai na sake tambayar auntyna yadda ake haɗawa." Jima kaɗan ta dawo riƙe da wata leda a hannu, tana zuwa ta miƙo ma Aisha tana faɗin "Bari na kira ka tsaye na tambaye ta naji, shi wannan cristaux de mente ya ne za'a yi gyaran gashi da shi?" Da mamaki Aisha ta kalle ta tace "Gyaran gashi kuma Mamie?" Kallon ta ita ma tayi tace "E, ko ba za ki yi ba?" A sanyaye ta girgiza kai tace "Mamie ni na isa? Amma ai ba abinda ya samu gashina kuma yana da tsayi." Tsaki Mamie tayi tace "Shirme, nea nake yadda zan gyara miki shi." Kiran da ta aikawa lambar Ummu ya sa sukayi shiru, kuma ba jimawa ta ɗaga dan lokacin tana madafa tsaye kan ƙafafun ta tana girkawa Alhaji abinda zai ci dan suna hanya, tana ɗauka da fara'a da kuma sabon da sukayi da matar da take kira aunty tace" *Auntyna* ina kwana?" Ita ma da fara'a da shaƙuwar da Allah ne kawai ya saka ta a tsakanin su tana murmushi mai cike da jin ƙaunar aunty Ummun tace" Ina kwana aunty, ya gida ya aiki?" Daga wajen Ummu ta amsa da" Lafiya lau wallahi, ya naku hidiman?" " Alhamdulillah." Ta faɗa tana hararen Aisha dake dariyar jin kowa aunty ke kiran kowa, to ina aunty a cikin su kenan? Cikin taushin murya Mamie tace" Aunty Ummu, wai gyaran gashin nan da kika faɗa min, ai na nuna miki mayukan duka na same su, to shi Cristaux ɗin ne nake so na ji ya za'a yi da shi? Dan na ganshi garai-garai kamar ƙanƙara." Da kulawa sosai Ummu tace" A'a aunty, ba cristaux ɗin ba, sai idan ba'a samu man shi bane ake anfani da shi kaɗan, zaki iya yin garin shi sai ki cakuɗa a cikin haɗin." Ɗan dafe gaban goshi Mamie tayi tace" Ayya, ni kuma ban nemi man ba iya shi kawai na nema, amma bari yanzu zan je na samo shi." Dariya Ummu tayi daga inda take tace" E, zai fi anfani gaskiya, amma idan babu karki damu aunty, kawai ki sa wannan ɗin, amma fa kaɗan." Da fara'a ta sake amsa mata da" Shikenan auntyna nagode." Ita ma da farin ciki ta amsa da" Ba damuwa, ana tare." Har za ta kashe wayar sai kuma Mamie tace" Tun safe ban gan ki en ligne ba, ko dai ana ta shirin tarban Yayan mu ne?" Jim! Ummu ta yi saboda Yayan nasu da ta faɗa, ko da yake da ta san shekarun mijin ta da bata faɗi haka ba, wanda ya cika saba'in a duniya har ya fara haurawa, hmmmm! Dariya kawai ta yi, dan duk shaƙuwar su da hirar su akan iyalin su ko mazan su wani lokaci basu taɓa tattauna matsalolin su ba, hirar maza ma ba dayawa suke yin ta ba gaskiya dan har yanzu ko hoton juna basu taɓa gani ba, hakan yasa suna kula da sirrikan su da abinda zasu tattauna tsakanin su, duk da tana da matsala a baɗini, amma a zahiri sai ta ce "Gaskiya kam, dan suna daf da higowa gari ma, Shiyasa bana kula wayar idan ba kira aka yi ba." Da fara'a da kuma zolaya Mamie tace mata "To shikenan, Allah ya taimaka, nasan dai mu da sake ganin ki a grp kuma sai ko nan da kwana biyu, dan nasan Yayana zan rufe ki a ɗaki ne kuyi ta raya sunna." Wata ajiyar zuciya Ummu ta sauke da murmushi a fuskar ta na fatan hakan ya kasance musamman ma da ta haɗawa kan ta haɗin da aka bata tabbaci namiji na jimawa idan haro ya ci abinci da yajin tace" In sha Allah aunty, amma dai za ku ganni." Daga haka sukayi sallama inda Aisha ke ta duban Maman nata, miƙewa Mamie tayi tana faɗin" Bari na ɗauko gyalena muje mu siyo man cristaux ɗin." Da shagwaɓa Aisha tace" Mamie da wuri haka? Mu jira har gobe mana." Da yanayin tsawa tace" Ke dallah ni taso, a hanya ma zan kira gyatumin ki na nemi izinin." Miƙexa Aisha tayi a sanyaye tace" Allah sarki Abbuna, yana cikin gidan fa." Jiyowa tayi ta kalle ta tace" Sai muje can mu nemi izinin, kinga kema kya tambaya daga nan." Murmushi kawai Aisha tayi, ita tasan wannan kulawar duk hada dan ƴar uwar ta bata nan ne, to amma ya zasu yi? Ko mijin ta Sa'ad da ya dinga nema da bin salsala ya haƙura a lamarin Kuwailat dai dan babu cigaba ko nasara, wataƙila fa ta rasu ne, amma har yau Abbun ta shi dai bai yarda a ce ta rasu ba, shi kawai ƴar sa za ta dawo ko yaushe ne, hakan yasa ya fi Mamie damuwa? Ko kuma dai damuwar shi fili tafi ta Mamie fitowa? Dan har farin gashi yayi wanda ko Kawu Bilal baya da shi, gashi baya daɗa yin jiki sai ma tension da ya sako shi gaba yanzu wanda ake ta ƙoƙarin kiyayewa. Fitowar Mama ta sa ta ɗaukar Yusrah dake bacci suka fita, kai tsaye falon su Hajia suka nufa, anan suka same su zaune har Alhaji da ya farka yana cin ayaba, saida suka sake gaisawa kamar yanzu suka haɗu kafin su tambayi jikin Alhaji, da tabbaci Hajia tace "A'a jiki yayi kyau sosai, sai fatan Allah ƙara lafiya kawai." A tare suka yi addu'a da "Allah ya ƙara lafiya, Allah ya sa kaffara ne." Daga zaune Alhaji ya kalli Aisha yace "Amarsu, duk da ciwon son ki ne ke wahalar dani amma kin ƙi kulani ko? Saboda wannan ɗan ƙiriniyar mijin naki." Turo baki Aisha tayi tana kallon shi tace "Ai laifin ka ne Alhaji, kai ne fa kace ka fi son ganin Kuwailat dan ita c farin cikin ka, shiyasa nima na kama nawa mijin na bar ka da margayi.." Tun bata ƙarasa ba Sa'ad ya zaro ido ya kalli Abbu da yake da tabbacin sai ya tsawatar mata, ai kuwa tuni ya ɗaga murya yace" Eeeeeeshhha..." Da sauri ta dantse leɓenta ta kalle shi, a ladabce tace" Kayi haƙuri Abbu, ba zan sake ba." Suna haɗa idanu da Sa'ad ya mata kallon wuce daga nan, haka kawai ki ja a mare ki anan kuma ba zan iya rama miki ba, ƙarshe ni ne da jin ciwo da wahala, to wuce gaskiya, turo baki tayi da yanayin da ta saba yi mishi magana na shagwaɓa tace" To ai fita ne zanyi in dawo." Gyara zama yayi yace" I..." Sai kuma suka haɗa idanu da kawu Bilal dake ta murmushi, hakan yasa ya sassauta murya cikin raɗa yace" Ina kuma? Ke da bamu jima da zuwa ba." Ƙara matsawa tayi daf da shi ta sunkuya cikin kunne tace mi shi" Ni da Mamie ne zamu je can siyan wani abu, dan Allah ka barni na je, na faɗawa Mamie kana yin duk abinda nake so fa." Wani irin kallo ya mata yace" Ke dakata! A me kika ɗauke ni? Ba dai gulmata kawai kike yi tunda kika shiga can ba?" Girgiza kai tayi a marairaice tace" Wallahi ban yi ba Abbu." Sama da ƙasa ya kalle ta yace" To ba zaki je ba, dan ni ba mijin hotiho bane." Kyaɓe fuska tayi irin za ta yi kukan nan tace" Kayan gyara fa Mamie zata siyo mana." Irin hararan gefen nan ya mata yace" Da gaske?" Jinjina kai kawai tayi, hakan yasa yace" To shikenan maza a tafi, amma kawo Yusrah na riƙe miki." Da farin cikin jin haka ta miƙa mishi ita, hakan yasa ta ɗagowa ta juya inda Mamie take, sai ta ga da ido kawai Maman ta take nuna wa Abbun ta zasu fita yanzu za su dawo, kallon Abbun tayi ta ga ya lumshe idanu da murmushi alamar to, ita kanta murmushin tayi saboda birge ta da sukayi, kama hannun Maman ta tayi tana mata raɗa "Wallahi Mamie har yanzu ke da Abbu kamar amare." "To da menene?" Ta tambaya da sigar faɗa, da raha dai suka fita suna tattaunawar su, inda Sa'ad ya bisu da kallon so da ƙauna, yana son ganin su a irin wannan farin cikin, Shiyasa yake yawan ziyartar su tare da ƴar su dan su ji daɗi, to amma ya ga Maman m'a duk in suka zo sai ya ga wani sabon salo dag gurin Eesha, hakan na nufin dai Mamie so take ya zama raƙumi kawai da akala? To shi a haka ma aka bar shi ai ƴar shi ta gama da shi ko? Tunda ya iya tuɓewa gaban ta ya dinga haife ƴaƴan ta, to kuma me ya yi saura da ake nema sai hargitsa sauran nutsuwar ta shi? ******************** Sun sauka lafiya kuma iyalin shi sun tarbe shi, musamman ma Ummu da ke da shi a wannan ranar, tayi farin ciki sosai da ta ga ya ci abincin nan ƙwarai wanda ta zuba yajin mza a ciki, burin ta ya neme ta yadda za ta gamsu ta kuma yarda tana da miji ita ma, kwalliya ta biya kuɗin sabulu, dan kuwa ana kiran sallah la'asar ya fara rumgumar ta da shinshinar dadaɗan ƙamshin ta da baya jin shi a ko ina a duniyar nan sai a wajen ta, tayi shaye-shaye ita ma saboda zuwan shi, hakan yasa Ummu fin shi rikicewa ta dinga cire kayan ta tana taimaka mishi shima, ya kai maƙura na son kawai ya sauke abinda yake ji wanda bai taɓa jin irin haka ba har ya rasa hankalin shi. Komai ya kankama inda Ummu ta kai maƙura kuma ta buɗe mishi hanya dan yayi yadda yake so, amma abun takaici da ya saka Ummu ɗagowa tana kallon shi shine yadda ko minti biyu bai yi ba ta ji yana tiltila mata ruwan dake nuna shi fa har ya zo, da kallo ta bishi har ya shiga ban ɗaki yna faɗin "Ashe har an tayar da sallah?" Tana kwance bata motsa ba har ya gama shirin masallaci cikin doguwar riga ya fita, saida ya fice kawai ta ji ta fashe da kukan da ba ta san na me ye ba ita kan ta, jawo zanin rufa tayi ta rufe ciki ruf tana ta rizgar kukan ta, kafin ta ankara har ya dawo ya same ta tana kukan nan, hankali tashe ya tunkare ta yana tambayar "Subhanallah ! Maman Kuwailat, lafiya ? Me ya same ki?" Shiru tayi ba ta kula shi ba sai rage sautin kukan da tayi ta yunƙura ta tashi zaune tana rufe fuskar ta bata so su haɗa ido, juyo da fuskar ta yayi yana kallon ta yace "Ummu, lafiya ? Me ya same ki? Wani abu aka miki?" Kallon shi tayi da idanun ta da sukayi jajir cikin ɓacin rai da fitar hayyaci tace "... *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes. *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata. Sayen na gari mai da kuɗi gida, sai an gwada akan san na ƙwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a ƙasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI- SIRRIN MANYAN MATA)._ _Bismillahir-rahamanir-rahim._ *30* Cikin ɓacin rai da fitar hayyaci tace "Me aka min ? Ban sani ba, ni kawai ka rabu da ni nayi kukana." Hankalin shi ne ya ƙara tashi, sam Ummu Kulsum ta kasa gane irin girma da matsayin da take da à wurin shi, ba dan haka ba da bata yarda tana zubar da hawaye a gaban shi ba, son ta yake sosai, ƙaunar ta yake matuƙa, baya son ɓacin ranta, saboda yarinyar ta bashi farin cikin da yake nema a gidan duniya, ta sa ya ji ƙuruciya a tare da shi lokacin da ciwo ya so kama shi, ta zama rigakafin duk wata cuta gare shi, shi ya sa Shima sai inda ƙarfin shi ya ƙare a kan ta, dan haka ya riƙo hannayen ta cike da kulawa yace "Ummu, dan Allah daina kukan haka ki faɗa min me ya faru? Kin ɗaga min hankali fa, wani ne ya miki wani abu a gidan? Ko ni ne na ɓata miki rai." Kallonshi tayi tana shasheƙar kuka, zuciyar ta na raya mata ta faɗa mishi, sai kuma kunya da kawaici su mata katanga da faɗin haka, sadda kanta tayi ta girgiza kai tace" Ba komai." Girgiza kai yayi yace" Ban yarda ba komai ba, dan Allah ki faɗa min Ummu, idan ba haka ba zan ɗauka an miki wani abu ne a gidan nan kuma kin kasa faɗa min." Cikin shasheƙar kuka ta tausasa kallon ta gare shi cikin rawar muryar da ta fara dakushewa tace" Papan Kuwailat, kayi haƙuri idan abinda zan faɗa zai ɓata maka rai, dan Allah kayi haƙuri ka ji?" Girgiza mata ka yayi ya tallabo haɓarta yace" Saurara Ummu, koma menene ki faɗa min, ni mijin ki kuma zan iya karɓan gyara daga gare ki inhar daidai ne, dan haka faɗi ina jin ki." Saida ta ja majina ta sauke numfashi sannan ta sake duban shi a sanyaye sosai tace" Dama...Papan Kuwailat, ka faɗa...min me...yasa yanzu ka...daina sona? Bana jin daɗin haka da kake min yanzu." Da maɗaukakin makaki ya kalle ta yace" Na daina son ki kuma? Ummu, kin kuwa san yadda nake jin ki? Ummu har yanzu ban yi zama da macen da nake matuƙar a rayuwata ba sama da ke, UMMU ina son ki, ina ƙaunar ki fiye da tunanin ki, amma me yasa kikayi wannan tunanin?" Saida ta sa hannu tana share hawayen ta tace" Saboda yanzu baka jimawa idan kana mu'amala dani, me yasa? Bana gamsar da kai ne? Wallahi ina kula da kaina kuma ina anfani da abinda zai sa ka gamsu, ban san... " Fashewa ta sake yi da kukan da ya saka shi jawo ta jikin shi ya rumgume cike da tausayi, ƙwarai ta birge shi da ta iya faɗa mishi haka dan duk cikin samun maslaha ne, to amma ya zaiyi? Bai taɓa tunanin za ta zo da buƙatar da zai kasa magance mata ba, daddaɓa bayan ta ya dinga yi tare da faɗin "Yi shiru to, kukan ya isa haka, saurare ni muyi magana." A hankali ta tsagaita kukan tana kallon shi, cikin nutsuwa yana murza tafin hannun ta yace "Ummu Kulsum, ba sonki na daina yi ba, hasalima soyayyar ki kullum ƙaruwa take a zuciyata, sai dai abinda nake so ko gane shine, ni yanzu ba kamar da bane sanda muka yi aure, Ummu ai idan kika yi nazari lokacin da muka yi aure ina da sauran ƙuruciyar da nake iya gamsar dake, kuma duk da ƙarancin shekarun ki haka nake iya tafiya dake saboda ke kanki a lokacin baki gama zama cikakkiyar mace ba, shekaru kusan goma sha uku fa suka ƙaru akan waɗanda ke kaina, to ta ya zan iya yi miki abinda nake miki baya? Wallahi tallahi Ummu bana jin wani abu mai sunan sha'awa a yanzu da nake faɗa miki, amma ƙaunar ki da kuma salon da kike zuwa min da su, su suke jan ra'ayina har nake jin ina so na kusance ki, amma maganar gaskiya ke kaɗai kike samun haka a duk cikin matana." Numfashi ya sauke mai nauyi kafin ya kalle ta sosai inda Ummu ma dake kallon shi duk ta zaro idanu gabanta na faduwa saboda abinda ya faɗa, to kenan ya zata yi? Haka za ta ƙarar da rayuwar ta? Ya Allah! Ɗorawa yayi da" Kiyi haƙuri kinji, in sha Allah wata rana sai labari, ni ba ma wannan ne ya fi damuna ba, yadda tunda kika haifi Kuwailat baki sake samun wani cikin ba? Bayan kuma lafiyar ki ƙalau." Kalmar ta yi haƙuri ita tafi nanatawa, ta yi haƙuri kawai? Haka kenan za ta ci gaba da zama? Tsaf ta haɗe hawayen ta tare da janye hannayen ta ta sauka daga kan gadon, rufewar da idanun ta sukayi yasa ko zanin da ta rufe jikin ta bata ɗauka ba, haka ta shiga takawa zuwa ban ɗaki ba komai a jikin ta face tarin jigida da bata iya rayuwa babu it a jikin ta har ta shige ban ɗakin, saida ta ɓace ma ganin shi ya sauke numfashi, ya zai yi yanzu? Yana son Ummu, ba zai iya rabuwa da ita ba gaskiya, in sha Allah zasu samu mafita akan wannan matsalar, ina ma yana da ƙwarin da miƙewar nan da tayi babu kaya zai iya ranƙwafar da ita a gaban shi sannan ya auna mata kaya ya shiga bata wuta? Tashi yayi ya fita daga ɗakin dan ya samu Kuwailat su tattauna dan sun jima basu yi hira ba. Wuni tayi cikin yanayi marar daɗi, tun tana jin kasala har mararta ta fara mata ciwo kaɗan kaɗan, ta kasance komai sai ta ji yana bata haushi, ranta na ɓacewa, hatta abinci ba ta ci tare da shi da Kuwailat ba, tana kwance ɗakin ta cikin wannan mawuyacin halin ta ji muryar Nabila daga falo suna gaisawa da ita, lumshe idanu tayi tana tunanin ko me ya kawo ta kuma? Ita dai tasan wannan zuwan na dare akwai abinda Nabila take so... Wayewar Nabila da kuma buɗewar idanun ta yasa Ummu tunanin ko dai za ta iya neman taimakon Nabila? Tana cikin tunanin nan ta ji kawai ta buɗo ɗakin ta shigo ba tare da neman izini ba, buɗa idanu tayi à hankali ta ɗan ɗaga kan ta ta kalli Nabila dake faɗin "Aunty Ummu, ba dai bacci kike tun yanzu ba? Dan Allah tashi aunty ki saurare ni." A tsanake Ummu ta tashi zaune cike da kasala tana yatsina fuska saboda jikin ta da taji duk yana ciwo ga ɓacin rai da take ji, kallo ɗaya ta ma Nabila ta gane shigar dake jikin ta, doguwar rigar kanti ce sai wani yalolon kallabi dake kafaɗar ta kanta ɗauke da hular gashin dokin da take sakawa idan tana son rufe askin dake kan ta. Zaune Nabila tayi tana kallon idanun Ummu da mamaki saboda ganin sun yi jajir alamar ta ci kuka, duk da akwai uzurin da ya kawo ta, amma ƙaunar da take ma Ummu yasa ta dafa kafaɗar ta tace "Aunty, lafiya ? Me aka miki kike kuka ? Baki da lafiya ne?" Kallon ta Ummu tayi da yanayin ɓacin rai tace "Me ya kawoki gidana a wannan daren Nabila?" Ba tare da damuwa ba Nabila tace "Aunty wajen ki fa na zo, na zo ki ban aro ne?" Wata harara da bata taɓa kwatanta yi mata ba ta zabga mata tare da faɗin "Amma ai na sha gaya miki ki daina zuwa min gida da shigar nan ta banza, ko so kike a raina min wayo ne?" Da sigar rarrashi Nabila tace "Yi haƙuri aunty Ummu ba zan sake ba, amma wallahi kafin na zo saida na suturta sosai." Wata hararen ta sake yi mata kawai ta ɗauke kai tace "Me kike so?" Da kulawa Nabila tace "Kafin wannan aunty Ummu, me yake damun ki? Na ga Abban Kuwailat a falo shi da ita, ke kuma kina nan ke kaɗai kina kuka? Me ya faru aunty?" Girgiza mata kai tayi tare da gyara zaman ta tace "Ba komai." Miƙewa Nabila tayi cike da masifa da hali irin na ƴan tasha tace "Billahillazi idan baki gaya min ba to zan ɗauka Alhaji Kabeer ne kuma zan same shi na mishi akuyanci, idan ba shi ba kuma to sai idan wannan matar tashi ce Atika take ko wa da take ɓata miki rai ita ma, dan haka wallahi sai na tashi hankalin kowa yanzu." Da sauri Ummu ta riƙo hannun ta ta zaunar da ita kan gadon tana faɗin" Ke bana son iskanci, Nabila zan ci uwar ki wallahi, dama raina a ɓace yake za ki ƙara min wani." Dariya Nabila tayi tace" Allah huci zuciyar ki aunty, faɗa min me aka miki kike kuka?" Kallon ta tayi sosai cikin nutsuwa da taraddadin abinda take son faɗa mata sannan tace" Nabila, nasan ke kin san magunguna, dan Allah wane magani kika sani da idan namiji ya sha zai..." Kunya da nauyi yasa ta kasa ƙarasawa, amma dake Nabila shaƙiyiya ce tuni ta harbo jirgin nata tace" Na gane aunty, kar ki damu wallahi zan kawo miki wani magani da Fahad ɗina yake sha, ina gaya miki aunty idan ya sha shi kwana muke ni da shi ba gajiya ba tsayawa hutun zango." Da irin kunyar nan Ummu ta dinga sosa girar ta da ɗan yatsa ba tace komai, Nabila kuma tausasa murya tayi da sigar rarrashi tace" Auntyna, dan Allah zuwa nayi ki ara min sarƙar nan ta ki ta ƙafa ta zinariya, bikin ƙawata za'a yi jibi na kece raini, ina so nayi anfani da ita na cire wannan." Wani kallo Ummu ta mata tace" Wa? Ni zan ɗauki sarƙata mai tsada na baki? Wacce mijina ya siyo min dan so da ƙauna?" Ƙara marairaicewa tayi tace" Dan Allah fa nace aunty, wallahi babu abinda zai sameta lafiya lau zan dawo miki da ita." Ba da son ran Ummu ba haka ta ɗauki sarƙar taa bata saboda tana ta mata magiya, haka ta tafi da alƙawarin gobe zata kawo mata maganin nan ita mata jaraba ta gani, taji daɗin haka dan tana ganin kamar za'a samu ci gaba wannan karan. ******************* A nutse ya zuro jar ƙafar tashi daga cikin lafiyayyen jirgin ƙasan yana mai sake riƙe jakar goyon shi fuskar shi fal fara'a na nasarar da yayi a gasar musabiƙa da aka gabatar a Iran na Alƙur'ani mai girma musamman akan tajwidi, abun farin ciki ne a ce ka bige Larabawa da mutane suka fi ganin ai kamar su ne masu abun, dan haka shi ma yake wannan farin cikin na nasarori da yake ta yi akan cikar burin shi. Aliyu na bayan shi wanda tare suka tafi dan har saida suka sake koyon wani abu a tafiyar tasu, cikin farin ciki da ƙaunar juna Aliyu ya daf kafaɗar ta Jabeer tare da bubbugawa suna murmushi, lumshe idanu Jabir yayi sannan ya sauke su fes akan Aliyu cikin wata nutsatsiyar murya wacce dama tun fil'azal yana da ita, amma yanzu da ya ke kan kwankwaɗar madarar ilimin addinin islama sai nutsuwar sa ta ƙaru, kamalar sa ta ninku, haiba da dattakon shi suka ruɓanya, cikin sautin da kai tsaye ba zaka kira shi na zallar bahaushe ba yace "Alhamdulillah, mun iso Madina lafiya, saura gida." Da fara'a Aliyu da ya fi shi tsayi saboda baya da ƙiba siriri ne sai tarin ƙasunba yace "In sha Allah, zamu fara sanar da Abba muna shirin komawa gare su." Murmushi Jabir ya sake yi lokacin da suka tari taxi da zata kaisu masaukin su yace "Hakane, amma fa ni zumuɗi yasa tuni na sa *Imran* ya kama min hanyar gidan da gauro kamata zai iya sauka kafin mu ga yadda Allah zai yi damu." Da mamaki Aliyu ya kalle shi, amma sai Jabir ya shiga taxin kafin shi ma Aliyu ya shiga yana rufewa tare da faɗin" Gidan haya kuma Jabir? Za ka kama a garin maraɗi in da Abba yake?" Rashin son magana da hayaniya yasa Jabir kallon Aliyu, amma ƙala bai ce mishi ba kamar b da shi yake ba, a zaman da sukayi yanzu babu wanda ya san Jabir sama da Aliyu, dan sun zama aminan juna da basa ɓoyewa juna komai, dan haka Aliyu bai ji komai ba sai ma kawar da kai da yayi yace "Ba zai yiwu ba wallahi, kuma zan sanar da Abba yasan abinda kake shiryawa." Jabir ma ba tare da yana kallon Aliyu ba yace "Um um, kar ka faɗa." Daga haka bai sake cewa komai ba har suka isa masaukin su, wanka suka fara yi suka shirya, Jabir na cikin kayan da ya fi so wato baƙar doguwar riga da tattausan wandon yadi fari daya saka daga ciki, suna zaune kan kujera suna fuskantar juna Aliyu ya kira wayar Abban. *A lokacin* shi da Kuwailat ne Ummu na ɗaki cikin rashin jin daɗin yanayin da take ciki har bacci ya fara ɗaukar ta mai cike da mafarkai barkatai. Bayn sun gaisa Aliyu kam yake faɗa mishi abinda Jabir ɗin yake shirin yi, a take Alhaji yace "Bani Jabir ɗin ?" Jabir da ke kallon Aliyu tunda ya fara magana bai ce komai ba, yana miƙo mishi wayar ya karɓa da girmamawa suka gaisawa, cikin tuhuma Alhaji yace "Jabir, gidan haya ka sa a kama maka bayan kana d gida? Wani abu aka maka da baka san zama da mu?" Saida ya lumshe idanu ya jingina sosai a kujerar sannan ya furta "A'a Abba, ba komai." A take Alhaji yace "To in dai hakane kada na sake jin maganar kama gida a bakin ka, ku dawo tare da Aliyu ku zo gidan mahaifin ku, ina da wurin da zan sauke ku." "Shikenan Abba." Ya faɗa a tausashe kafin ya gyara zama yace "Abba, kana kula da shan maganin ka?" Murmushi Alhaji yayi na jin daɗin yadda Jabir ke kulawa da shi yace "Sosai Jabir, ina kulawa, Allah ya maka albarka." Duk da idanun shi a rufe suke kamar bai bacci bai hana shi faɗin "A gaida *Maama*...da kuma Kuwailat." Da kulawa Alhaji yace "Za su ji." Dan kuwa Ummu ita ce Maama, da yana kiran ta da aunty, amma bayan wasu shekaru sai yake kiran ta da Maama, a cewar shi ai ita ta zama uwa gare shi, dan haka ta cancanci haka. Suna gama wayar Jabir ya cillawa Aliyu wayar da jin haushin sanar da Alhaji da yayi abinda yake shirin yi tare da sake rufe idanun shi, tsawon lokaci Aliyu ya san Jabir na yawan rufe idanu yana kallon sama, baya takura masa a irin wannan lokacin, saboda ya faɗa masa yana tunanin mahaifin shi ne da yana so ya neme shi, amma kuma ya fi so sai ya zama mutum kafin mahaifin shi yasan da yana raye. Jabir kuma tunanin shi bai wuce lambar wani abokin mahaifin shi da ya samu a fecebook wato Hisham, ya mishi magana tare da sanar da shi shine Jabir ɗan Mu'az, yanzu haka ya bashi lambar mahaifin nashi, to tunanin shi shine ya mishi magana yanzu? Ko ya bari sai sun koma gida? Daga haka har ya shiga tunanin yarintar shi, abubuwan da suka faru, matar Baban shi, ƙanwar shi, Kakanin shi, komai da komai sai yake zuwa mishi a ƙwaƙwalwa tamkar yana kallo a allon bango. *Washe Gari* Da yanayin gaggawa ya shigo falon, wanda hakan da yayi yasa Aisha da Mamie har da Abbu kallon shi da mamaki dan ko sallama bai yi ba, kai tsaye wurin Aisha dake shirya Yusrah ya nufa dan ya ce mata sammako zasu yi, ta ɗauka ko à kan fitar ne, amma sai ta ji yace "Bani lambar aunty Fa'iza." Da matsanancin mamaki ta dube shi tace "Aunty Fa'iz..." Tun bata kai ƙarshe ba tace "E ita, maza bani dan Allah?" Miƙewa tayi tana faɗin "Wayar na ɗaki, kuma ban da lambar a kaina, bari in ɗauko." Bai amsa mata ba sai bin ta da kallo, hakan yasa Abbu matsowa kusan shi da doguwar riga dan ko shirin fita bai yi ba yace "Me ya faru ne Sa'ad?" Kallon shi yayi da girmamawa yace "Za ka sani Abba, zan kira ta ne." Suna nan tsaye har ta fito tana gaya mishi lambar yana ɗauka, yana gama ɗauka ya tura kira, ba jimawa kuma Fa'iza ta ɗauka, suna gaisawa da hanzari yace "Aunty Fa'iza Sa'ad ne, dan Allah ko zaki iya zuwa gida yanzu?" Da mamaki tace "Gida kuma? Nan wajen su Hajia?" "E." Ya bata amsa kai tsaye, da mamaki ta sake cewa "Lafiya? Wani abu ne ya faru?" A hankali yace "Ba komai aunty, dan Allah ki zo idan kina iyawa." Gabanta sai ya faɗi, zuciyar ta ta raya mata ko dai Alhaji ne ya rasu? Dan haka ta bashi amsa da gata nan zuwa, gaba ɗaya hankalin ta ya fi bata kan Alhaji ne ya rasu, dan haka da damuwa da zulumi ta tuƙo motar ta zuwa gidan nan. A falon Alhaji ta same su, kowa na zaune saboda Sa'ad ya buƙaci da su zauna sai shi Sa'ad ɗin dake tsaye yana kai da kawowa, da Hajia kawai ta iya gaisawa dan har Alhaji kallon ashe ba shi bane ya mutu take masa, kafin ta numfasa Sa'ad ya tsare ta da idanu yace "Aunty Fa'iza, kin san Rabi'u?" Har ga Allah ta manta da shi, sai kawai ta kalle shi da mamaki tace "Wanene hakanan kuma? Rabi'u?" Da alamar ƙaguwa Sa'ad yace "Aunty Fa'iza, ba wasa na tara mu muyi ba, Rabi'u wanda kika sa *sukayi garkuwa da Fahad* nake magana a kai." La'ilaha illalah! Gaba ɗaya yasa kayan cikin ta sun murɗa, hankalin ta ya tashi ƙwarai da gaske, dan wallahi ita ta manta ma da wannan abu da ta aikata, gaba ɗaya yanayin rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita, gashi kuma kowa ya kalle ta ana mamaki, Abbu kuma dama bai yi mamaki ba yasan za ta aikata ai, dan haka Sa'ad ya sak faɗin "Aunty Fa'iza, da bakin shi ya gaya min, idan kina so zan iya kiran shi ya zo, bayan shi ma har da Rabi zan iya kira dan ta faɗa gaban ki cewa ke kika sa ta kai Eesha gidan marayu na HY." Cikin tashin hankali Fa'iza ta furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un !" Harara Abbu ya zabga mata yace "E mana, kya faɗa, tunda asirin ki ya tonu ba." Kallon shi tayi idanun ta taf da hawaye tace "Na yarda ka kira Rabi, dan za ta faɗa muku bani na sa ta ɗauke Eesha ba, ni kawai na faɗa mata inda za ta kaita ne." Cikin jin haushi Abbu yace "Ka ji wani rainin hankali kuma." Kallon shi Sa'ad yayi yace "Ba rainin hankali bane, gaskiya ta faɗa." Cikin duhun kai da ya saka kowa Mamie tace "Kamar ya? Wai me kake so ka faɗa ne?" A nutse ya kalle ta yace "Mama, aunty Fa'iza ba ita tasa a ɗauke Eesha ba, sannan ita tasa aka yi garkuwa da Fahad, amma kuɗin ta bayar da su ne dan kawai *nemo Eesha*, dan a lokacin ta ɓace daga gidan marayun ana nemanta ido rufe." Alhaji dake zaune ne ya dube shi yace "To kenan wa ya sa a sace Eesha?" A hankali Sa'ad ya juya kaɗan ya kalli Abida da tuni idanun ta suka fito ta fara ruɗewa, haka ma Fa'iza kallon ta tayi tace "Abida ce." Salallami ɗakin ya ɗauka, hakan yasa Abida fashewa da kuka ta ɗora hannu a kai tana faɗin "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! Sharrin da zaku min kenan? Sace mutum kuma?" Wata muguwar tsawa Yaya Bilal ya daka musu dukan su, da jin haushi da takaici daga Fa'iza har Abida yace "Ku min shiru, ku fice ku bar min gida, sheɗanun mata kawai da baku san ciwon kawunan ku ba, dukan ku ƴan ta'adda ne wallahi." A fusace ya raɓa zai wuce Sa'ad yace "Kawu ka dakata dan Allah." A ƙufule yace "Me zaka faɗa min? Waɗannan matan basu da imani, me na musu? Daga aure shikenan sai su zame min annoba cikin alhali, babu wacce bata cutar da mu ba a cikin su?" Cikin kwantar da murya Sa'ad yace "Hakane kawu, amma aunty Fa'iza ba ta yi komai ba, lokacin da ake shirin sace Eesha daga gidan nan, Rabi da zata yi aikin ta same ta ta faɗa mata, wanda Abida ta zaɓeta ne sabo a ta ga suna da kusanci da Fa'iza, da ta sanar da ita sai ta ce ba damuwa ta yi abinda ta saka ta, ban san me ye nufin ta na yarda da hakan ba, amma dai ta umarci Rabi da ta kai ta gidan marayu na HY inda anan Abban Abida yake kula da marayu, sai kuma kuɗi da ta buƙata bata da su wanda ya sa dole ta sa aka kama Fahad dan ta biya DG ya nemo mata Eesha tare da kawo mata ita gidan nan cikin tsaro, na san hakane daga bakunan duka mutanen nan." Kallon Fa'iza yayi dake kuka har ta zau'a kan kujera yace" Me yasa kikayi haka aunty Fa'iza?" Cikin matsanancin kuka tace" Ban aikata haka dan ina so Eesha tayi nesa da iyayen ta ba, na yi tunanin Abida za ta sa wasu su mata aikin saboda ta riga da tayi niyyar aikatawa, idan kuma aka ɗauke ta bmu san me za ta ma yarinyar ba, zaku fahimci niyya ta ba mummuna bace daga yadda na sa Rabi ta bayar da yarinyar da cikakken sunan ta, bayan samun labarin ɓatan ta kuma hankalina ya tashi, gashi DG ya gaya min mahaifin Abida na neman ta zasu cutar da ita, na sa ya min alƙawarin nemota ya kawo min lafiya, amma dole zan bashi kuɗin da suka ninka wanda Hambali zai biya si, hakan yasa na yi garkuwa da Fahad aka ban miliyan hamsin, ƙwandla ban anfana da ita ba a kuɗin nan, wallahi na rantse muku." Hajia da ita ma ke zaune ce tace"... *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *31* Hajia dake zaune ce tace "Hakan na nufin Fa'iza bata da laifi kenan? Duk da muna kallon ta a mai laifi." Da tabbaci Sa'ad ya kalle ta yace "Ƙwarai Hajia, mai laifin dai wannan ce..." Ya faɗa yana nuna Abida da tunda Yaya Bilal ya mata tsawa tayi shiru, yanzun ma shi ya kalle ta yana girgiza kai yace" Kin yi asara wallahi, da zuciya ɗaya na karɓi auren ki lokacin da mahaifin ki ya bani *sadakar ki*, amma wai ke ce zaki saka mana da haka? Lallai mutum mugun ice." Zaune yayi kan kujera tare da ciro wayar shi yana faɗin" Na rantse da Allah idan uban ki shugaban ƙasa sai ki ɗauru a garin nan, dan ba ƙaramin tashin hankali kika jefa mu ba." Da sauri Hajia ta rufe baki saboda zagin da yayi ta san ya hau sama ne, ba wanda yayi yunƙurin dakatar da shi dan gaskiya Abida ba irin wanda za'a tausaya ma bace, duk sun yi shiru suna sauraren Yaya Bilal na waya da abokin shi dake jami'in tsaro, ba zato ba tsammani suka ji ƙarar mari a fuskar mutum mai rai da lafiya. A gigice Abida ta dafe kuncin ta, kafin ta ankara Mamie ta sake kashe fuskar ta da mari, ba ta bata damar dawowa hayyacin ta ba ta shaƙi wuyan ta a zafafe tana faɗin "Makira azzaluma, ashe dama ke maciya amana ce? Na yarda dake ban taɓa zargin ki akan abinda ke faruwa dani ba, kina shiga sha'anina fiye da Fa'iza, hakan yasa nake ganin kamar ita ce macuciyata, ashe duk makircin ki ne, me na miki? Me yasa kika ɗauke min yarana?" Da sauri Aisha ta shiga ƙoƙarin ɓanɓare Maman ta, Abida na jin ta saki wuyan ta da gudu ta ƙarasa kusan Alhaji ta durƙusa tana faɗin" Alhaji, Abbu, Abbu dan Allah ka min rai, wallahi sharrin sheɗan ne, ban da tunanin komai a kaina saida Abbana ya sa na shigo gidan nan matsayin mata, dan Allah ku yafe min Abba na tuba, wallahi zan gyara kuskure na." Wani kallo Alhaji ya mata, duk da yana jin jikin shi ba daɗi, haka ya daure yace mata" Me yasa kikayi haka Abida? Mun yarda dake fa." Cikin kuka sosai tana share hawaye tace" Abbu Babana ne, duk laifin shi ne wallahi, shi ya nuna min kar na yarda wata ta rigani haihuwa, hakan zai sa kima da darajata su zube sannan zan kasa samun soyayya, sai kuma na ga hakan bayan haihuwar Nuriyya, shine da fari ya ɗauke Kuwailat, amma kuma hakan bai sa na samu ciki ba, kafin mu ankara ta sake samun cikin Eesha, ban yi wani tunani ba a lokacin kawai na ga mu sake ɗauke yarinyar, kuma..." Saida ta kalli Fa'iza dake tsaye tana kallon ta a wulaƙance sannan tace" Na fahimci Fa'iza bata da faran-faran da shiga al'amura kai tsaye, sai nayi anfani da hakan ta hanyar saka Rabi ta ɗauke Eesha ta goya a cikin da duk kuka ɗauka tana da ciki sannan ta bar gidan, bayan shi ban yi komai ba wallahi, dan Allah ku yafe min." Cikin zafin nama Mame ta tintsire Abida saida ta kusa kai wa Alhaji karo t'a faɗin" Ƙarya kike munafuka, sau nawa ana tsorata ni gidan nan? Daga na ji kukan jarirai sai na ga tv da hotunan yarana, har ban ɗaki idan na shiga ina fitowa zan samu hotunan su Eesha zube a kan gado, kina so ki ce ba ke bace?" Cikin shasheƙar kuka Abida tace "Na ji na yarda ni ce, i ce wallahi, Abba dan Allah ka ce kar ya kira jami'ai, Abba ɗaure ni zasu yi wallahi, bana son zaman maƙargama." A kausashe matuƙa Abbu Mukhtar dke kallon ta yana son saka mata hannu amma yana tsoron abinda zai iya faruwa yace "Kenan da nufin ki ki haukata ta ko me?" Shiru tayi ba tace komai ba dan gaskiya abinda ta so kenan, shiru aka yi ba wanda ya sake magana na wasu wasu mintuna har suka ji ƙwanƙwasa ƙofa, da sauri Yaya Bilal ya kalli Sabeer da duk abin nan da. Ak e bai ce komai ba kuma matar shi ma bata wurin yace "Ce su shigo." Da sauri Sabeer ya ƙarasa ya buɗe musu ƙofa, jami'i biyu ne sai mace ta ukun su, suna shigowa ya nuna mishi Abida fuskar shi a haɗe yace "Gata nan Mansur." Jinjina kai Mansur ɗin yayi tare da ɗan waigawa ya kalli jami'a macen nan, gane yaren shi yasa ta tunkarar Abida da tuni ta sake ruɗewa ta rarrafo ƙafafun Yaya Bilal tana faɗin "Dan girman Allah Bilal kar ka bari su tafi da ni, na tuba, na tuba Bilal, Haba Bilal ya zaka min haka? Ka min dan girman Allah, wallahi ba zan ƙara ba, ka tausaya min Bilal ko dan Aswan dake tsakanin mu." Ba wanda ya saurare ta har jami'ar nan ta ji haushin yadda Abida take riƙe carfet har tana neman gaggaɓoshi daga inda yake ta finciketa da ƙarfin bala'i, jan ta take yi a ƙasa dan ta ƙi tashi ko zaune bare tsaye, ba sunan wanda bata kira ba a wurin har da Sa'ad kan shi, amma kowa da idanu yake bin ta yana tsaki da taɓe baki, wahala ta kai mata karo, yanayi ya ɗimautar da ita, gashi har yanzu janta ake kamar wata dabba ana gaf da fita da ita, cikin tsananin ƙunar zuci da ɓacin rai da rufewar ido haɗe da lokaci idan ya zo na abu to ba makawa sai ya faru, ta mance da me ke fitowa daga bakin ta, ita dai kawai tasan ranta ya ɓace na ganin dukansu suna kallo ana mata wannan wulaƙancin, ai ko me ta yi za su iya taimaka mata a tona mata asirin asirrance, hakan ya tunzura ta take faɗin "Tirrr daku wallahi, dukanku sai naga bayan ku, kun ji haushin duniya wallahi, kuna kallo ana min wannan wulaƙancin, har kai Alhaji dake Tsoho, Tirrr da halin ku marasa imani kawai, dukiyar ku ta banza? Nima zan yi kuɗin kuma sai na wulaƙantaku a duniyar nan, banzaye azalumai, kai kuma Bilal..." Ta Kira sunan shi har da juyowa tana kallon inda yake zaune tare da ƙoƙarin tashi da tayi tsaye tana ci gaba da faɗin" Ka ji haushi wallahi, banza lusarin namiji, ka je ka tuntuɓi likita su gaya maka gaskiyar magana ita ce baka haihuwa, kar ka saki ka ɗauka *ɗana* ɗanka ne, wallahi baka haihuwa kuma ba a banza Allah ya hana ka haihuwa ba, dan baka tausayin mace ne a rayuwa..." Tunda ta ambaci ba ya haihuwa ya tashi a zafafe yayi kan ta, rufewar da idanun ta sukayi yasa ba ta ma ga yana tunkarar ta ba saida ta ji shaƙar da ta ruɓanya wacce Mama Nuriyya ta mata, dan kuwa wannan tsaf ta ji numfashin ta ya ɗauke ta inda ta tabbatar idanun ta sun fito waje, ba ta ji tambayar da shi yake mata ba sai ƙoƙarin ɓanɓareta da jami'an ke yi daga hannun shi suna bashi haƙuri, sai lokacin ta ji yana faɗin "Ku sake ni na kashe ta na kashe banza, ɗan waye Aslam? Na ce ɗan uban waye?" Kallon shi tayi duk da tana ganin shi hazo-hazo haka ta dage da ƙarfin guiwa dan ta ga Shima hankalin shi ya tashi, to Gwara a yi mutuwar kasko kawai kowa ya ji ba daɗi, cike da dariyar mugunta tace" Ba banza za ka kashe ka ba Bilal, Abida za ka kashe wacce ta kafa maka tarihi, Aslam ba ɗan ka bane, kuma ka sani na raina ka ne tun ranar da Hashim ya min cikin da kai ka kasa yi min." *Hashim*! *Hashim*? Hashim ! Tangal tangal yayi baya zai faɗi da sauri Mansur ya riƙe shi, da sauri Sa'ad da Sabeer suka nufe su tare da riƙo Yaya Bilal da idanun shi biyu amma dai baya da maraba da wanda ya shiga duniyar suma. Zaunar da shi sukayi inda aka ƙarasa fita da Abida kowa na wurin jikin shi ya mutu tare da sake tsanar Abida, an ɗauki lokaci kafin Yaya Bilal ya ji abinda ya tokare mishi zuciya da maƙoshi ya ɗan sake shi, duk da girman shi haka ya fashe da wani irin kuka na takaici da dana sani haɗe da nadama, cikin kuka yake faɗin "Rashin haihuwata na Allah, Ubangiji ne ya nufe ni a zama haka, kula ko da gaske ne wannan matsalar daga ni ne, ban jin zan damu kaina dan ba ni na ma kaina ba, amma a ce kamar ni mata ta ta haɗani neman ta da wani sakaran ƙaramin yaro." Duk mazan dake wurin babu wanda bai auna wannan lamari da kan shi ba, sun tausaya mshi matuƙa hakan yasa ba wanda ya ce da shi yayi haƙuri, sun jima haka shiru ban da shi dake fito da abinda ke ran shi, abun ka ga wanda kake so, sai tausayin shi ya lulluɓe Fa'iza ta sunkuya gaban shi ta dafa kafaɗar shi tana faɗin "Bab, kayi haƙuri dan Allah, Allah zai saka maka cutar da suka maka, wallahi ba zai barta haka ba, kuma gashi ta fara gani tun yanzu, dan Allah karka rikita min kan ka, ka ji?" Kallon ta yayi, sai kawai ya sunkuyar da kan shi yana neman fashewa da kuka da faɗin" Kaicona, Fa'iza ashe ke ce mai sona, soyayar ɗa ta rufe min ido na wulaƙanta ki." Rufe mishi baki tayi tace" Ya isa haka, ni fa dan Allah nake son ka, ko kana haihuwa ko baka yi zan zauna da kai har abada, in dai zamu kasance cikin farin ciki da kwanciyar hankali, to haihuwar ma nasan Allah zai bamu yaran aljanna idan mun je can." Hajia dake share hawaye kallon su tayi ta dubi Fa'iza sosai tace" Allah ya miki albarka Fa'iza, Allah ya saka miki da alkairi." Da murmushi ta amsa da" Ameen Mamie, ni ma kuma ina ƙara baku haƙuri akan ruɗu da tashin hankalin dana jefa ku a ciki na ɓatan Fahad." Abbu Mukhtar ma gaskiya ya faɗa mata cewa shi kan shi fa da haushin ta yake ji saboda yana ganin bata da kirki, daga nan aka yafi juna cike da kyakyawan darasin da aka koya na rayuwa, Alhaji da ya jima da kula Yaya Bilal baya cikin ƙoshin lafiya ne ya kalli Sa'ad da Sabeer yace "Ku kama shi zuwa ɗakin shi ya samu ya kwanta, naga jikin shi rawa yake." Da azama sukayi kan shi dan cika umarnin na Alhaji, amma sai Fa'iza tace "Ku bar shi ma kawai, ni zan raka shi." Sabeer ne yace "Amma aunty ba wurin aiki zaki tafi ba? Kin makara fa." Murmushi tayi ba tare da ta kalle shi ba tace "Wane aiki kuma Sabeer? Idan ya amince na ci gaba da zuwa zan je, idan bai amince ba ai bani da aikin da ya fi hidimar gidan shi." Da jin daɗin abinda ta faɗa Yaya Bilal ya kalle ta lokacin da take tallabo shi jikin ta, saida suka fara takawa ya sake duban ta yace" Nagode Izza." Kallon shi tayi tace" Godiya kuma? Saboda na dawo ɗakina? Ko dan na taimakawa mijina?" Da mamaki ya kalle ta yace" Kina nufin kin dawo kenan?" Ita ma kallon shi tayi tace" Kana nufin har yanzu baka so na dawo kenan?" Murmushi yayi yace" Wane ni? A yanzu ai babu abinda Bilal ya fi buƙata a rayuwar sa kamar Fa'iza." Murmushi ita ma tayi da sigar zolaya tace" Amma fa ba yana nufin ba zaka siye bakina bane a daren yau, dan har kaza zaka kawo min ta amarci." Dariya yayi yana jin wani sanyi na ratsashi yace" To ya zaki yi da Mama da ta ɗaure miki gindi kina taya ta kwana?" Ɗan dukan shi tayi a hannu tace" Mamana ce fa, kuma ba ita ta hanani dawowa ba." Cikin nishaɗi da farin ciki suka isa ɓangaren nasu suna jin kan su tamkar ranar ne suka fara zama matsayin ma'aurata. ******************** Ranta ne ya fara ɓaci har ta fara bubbuga ƙofar ɗakin kamar za ta ɓalata biyu tana sababin "Ka ji kunya Fahad, ka kwanta bacci kamar wani jaki ko jin abinda ke duniya ba kya yi, za ka buɗe min ko sai na rurruga maka ashar ne?" Shiru ba alamar za'a buɗe, a haukace ta sake faɗin "Idan ma da wata ƴar iska ne kake kwance yau dubun ka ta cika wallahi, ɓalla ɗakin zan yi na shigo daga kai har ita na sos ..." Buɗe ƙofar da yayi da irin zafin naman nan yasa ba ta ƙarasa faɗa ba, yadda ya zuba mata idanu a kausashe da sigar ɓacin ran da tasan idan yayi shaye-shqye jiya to fa zai ci uwar ta ne a banza yasa ta sadda kanta tace" Ina kwana ubana Fahad?" Wata arniyar harara ya watso mata yace" Ina kwana uwata Nabila, kin gama min faɗan?" Sai kuma ta ɗaga kai ta kalle shi, raɓa shi tayi ta wuce falon tana faɗin" Kai dallah ni kauce min ɗan rainin hankali kawai, ina shegiyar da kuka kwana tare t..." Damtsen ta ya figo da ƙarfin da ya saka ta dawowa haro saida ta gwara kanta da nashi kan, cikin kakkawar da kan shi dan tashin shi kenan daga kwana yace" Me kike faɗa kafin na buɗe ƙofa?" Kallon shi tayi da yanayin rashin mutumci tace" Cewa nayi da wace ƴar iska kake tare?" Turata yayi tayi baya kamar za ta faɗi yace" Ke da wane ɗan iskan kika kwana waje?" Da mamakin abinda ya faɗa ta dube shi tace" Ɗan iska kuma? Amma ai dama na gaya maka zan kwana wajen kamun ƙawata." Wawan tsaki ya ja yace" Dak kuma mahaukaci ne ni kin ɗauka na yarda ko?" Tsaki tayi ita ma ta jefa jakar ta kan kujera tare da kallabi ta zare zif ɗin rigar ta za ta cire tana faɗin" Allah sa da abinci gidan, nasan ka da shegen cin jaraba ba lallai ka rage komai ba." Tunda ya sauke idanun shi kan gaba ɗaya jikin ta data saɓule doguwar rigar ta daga ita sai bras da fant, da sauri ya rumgumota ta baya yana faɗin" Akwai abinci sauran na jiya, amma kafin nan ki buɗe min ƙafafu mu ɗan fara ko zagaye huɗu ko?" Ture shi tayi daga jikin ta tana faɗin" Nabila jaka ko? Dan bani da aikin yi sai in zauna yanzu da safiyar nan ka min ci huɗu?" Sake riƙo ta yayi yana haɗawa da jikin shi a tausashe yace" N ji to, to muyi biyu, kin san da kewar ki na kwana jiya, na so na same ki wurin kamun, amma sanin halin ki yasa na fasa." Cike da masifa tace" Da ka je wallahi ka sa aka kira ka da bita zai zai da gaba ni da kai har duniya ta tashi." Murmushi yayi yana shafa mazaunanta yace" Na sani, shiyasa ai ban je ba, dan ban shirya yin gaba da ke ba na kwana uku ma, shikenan mu kullum muna ibada ba'a karɓa saboda baƙin halin mu." Banɗaki ta nufa tana faɗin" Wanka zanyi na ci abinci wajen lalle zan tafi." Bayanta ya bi yana faɗin" Muje tare muyi wankan to." Juyowa tayi ta kalle shi, sai kawai ta matso daf da shi ta tallabo fuskar shi tana son haɗa bakin su, kaucewa yayi yace" Ban yi brush ba fa." Sake juyo da fuskar shi tayi suna kallon juna tace" Na sani, Nabilan ka ce fa, ai kasan babu abin da ba zan iya yi maka ba ko? Kuma bana tsantsenin ka." Murmushi yayi tare da tallabo mazaunan ta ya ɗauke ta suka nufi ban ɗakin tarie da sakar mata ragamar fuskar shi gaba ɗaya, tun a ban ɗaki suka sha hidimar su kafin su fito su ɗora, iya iyawar su kuma son ran su kafin su tsagaitawa juna kowa ya fara shirin fita dan yin wani muhimmin uzurin. Saida ta gama shiryawa tsaf ta dawo falo ta buɗa jakar ta ta ɗauko wayar ta dan yin kira, sarƙar da ta gani yasa ta tuna maganar su da auntyn ta, da sauri ta koma ɗakin ta samu Fahad dake ɗaura ɗamara tace "Yawwa jariri, dan Allah ina maganin nan naka mai ƙarfin doki? Aunty Ummu nake so na kai wa." Wani sheƙeƙe ya kalle ta yace "Ban gane Ummu ba? Na maza ne fa." Zaune tayi kan gado tace "E na sani, ka gane ko? Jiya ne da naje na same ta tana kuka...." Duk abinda ya faru ta gaya mishi, hakan yasa Fahad faɗin "Nima dama ai nasan an yi haka tunda na ga mijin ta, wai ku me yasa kuka aura mata shine kamar dai maza sun ƙare? Ni wallahi ba dan bana ra'ayin kul wata mace ba bayan ke a rayuwata da na ce ki ara min ita na wuni ɗaya wallahi zan zazzage mata abinda ya cunkushe mata a mara." Kallon shi Nabila tayi, sai ta ji zuciyar ta tafasa kuma ranta ya ɓace, cike da masifa ta miƙe tsaye kamar sauran aradu kawai ta ɗauke fuskar Fahad da marin da saida ya dafe kunci ya kalle ta idanun shi waje tsabar mamaki dan haka bai taɓa faruwa ba, tana dai jawo masa rigima kuma yasan tana da faɗa da masifa, amma shi ba su taɓa na duka ba irin haka sai na fatar baki, cikin zafin rai har idanun ta sun yi jajir tace "... *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *32* Cikin zafin rai har idanun ta sun yi jajir tace "Yayar tawa? Aunty Ummun kake faɗawa haka?..." Sai kuma ta shaƙo wuyan rigar shi a haukace tana faɗin "Kamar uwa fa na ɗauketa, kenan akuyancin ka har ya kai ka ji kana sha'awar uwata? Allah ya tsine maka albarka Fahad, wallahi b zan taɓa yafe maka ba, sai naga bayan ka Fahad dan ban ga anfanin rayuwar ka ba." Ko gezau Fahad bai yi ba, e ya san bai kyauta ba da ya faɗi haka, amma ya za ta mare shi? Suna samun saɓani sosai, amma basu taɓa kwatanta dukan juna ba, dan haka ma ran shi ya ɓace kawai ya ɗauketa da marin da ya saka ta faɗawa kan gado, a gigice ta kalle shi dafe da kuncin ta tana tashi zaune tace "Ni ka mara? Fahad ni ka mara?" Da shaƙiyanci yace "Fuskata ba fuska bace kenan? Sai ta ki uwata Nabila?" A haukace ta yunƙura zata tashi tsaye tana faɗin "Allah ya tsine ma..." Da ƙarfi ya tura ta ta sake faɗawa kan gadon, cikin zafin nama ya tausheta tare da rirriƙe hannayen ta yace "Ni ba ɗanki bane ko sakarai da zaki dinga tsine min, ki san me kike faɗa min, banza wawuya." Kallon shi tayi tana sauke numfashi, yanzu nan da ta sake ɗaga mishi murya ya ɗauko ƙwayoyin nan ya haɗa, sai idanun shi su rufe ya duƙar da ita ya fara caccaka ba tausayi, dan haka sanin halin shi sai kawai ta sassauta murya tace" Na ji, ɗaga ni." Saida ya harare ta sama da ƙasa sannan ya ɗagata ya ci gaba da shirin shi, tashi tayi ita ma a tsanake ta buɗa wani cof da ta ga yana aje magungunan shi, ta kuwa yi sa'ar ganin wanda take nema, dan haka ta zari sashe ɗaya tare da juyawa ta fita ko kallon inda yake ba ta yi ba, dan tayi niyya sai ya gane kuren shi ya kuma bata haƙuri sannan za su shirya, idan ba haka ba kuma to sun fara gaba kenan da ita da shi. Tana fita falo jakar ta da ɗan kwalin ta ta ɗauka tayi gaba ko sallama, Shima yana fitowa ya ga bata nan taɓe baki yayi dan yasan me hakan ke nufi, an fara gabar kenan sai kuma bayan wasu kwanaki, ama ba zai yarda su jima ba dan rashin ta na saka shi tashin hankali da jin ba daɗi. Fita yayi ya rufe gidan dan wasu uzurrrinkan shi kafin gobe tayi yana so zai je gida dan kuɗaɗen shi sun yi ƙasa, da ya je kuma ya samo ko ta halin ya ya zai sake dawowa ne ya ci gaba da rayuwa da Nabilan shi. ******************** A karo na ba adadi kenan ta sake dafe marar ta dake mata ciwo sosai kuma ciwo ne ba irin na al'adar ta zata zo ba, hasalima ko sati biyu bata yi ba da gamawa, runtse idanu tayi sosai saboda ciwon ba daɗi, kama yake da na wanda wani abu ya maka nauyi a mara, hakane yasa har tayi tsaki ba tare da sanin ya fito fili ba. Kuwailat dake kusa da ita suna aiki tare ne tace "Mamie lafiya? Ko baki da lafiya ne?" A hankali ta buɗe idanun ta ta kalle ta, sai tayi murmushi ta girgiza kai tace "A'a, lafiyata ƙalau." Cikin kulawa yarinyar tace "Amma Mamie naga kamar za ki yi kuka, har idanun ki fa sun yi ja." A wahalce Ummu ta girgiza mata kai tare da ɗaukar cokalin miyar za ta juya tace "Ba komai, marata ce kawai ke ɗan min ciwo." Da kulawa Kuwailat tace "Sannu Mamie, Allah baki lafiya." "Ameen." Ta faɗa a taƙaice. Ba ta sake cewa komai ba har Alhaji Kabir ya shigo madafar da sallama, amsa mishi sukayi inda ya ƙaraso da fara'a yana cewa "Ashe duka anan kuka tare kuka barni can ni ɗaya." Ji take kamar laulayi take, hakan yasa daga can ƙasan zuciyar ta tana jin farin ciki na zata sake samun haihuwa bayan duk wannan shekarun, to amma yaushe ne cikin ya shiga, sati biyu da ya gabata ta ga jini, ranar da tayi tsarki Alhaji ya bar ƙasar, kafin nan ya ɗan sadu da ita, bai dawo ba sai jiya, to kenan cikin bai yi sati biyu ba? Rashin kuzari da kasala ba daga ita bane, dan haka yanzu ma ba alwawala tare da ita kawai ta amsa mi shi da "Muna nan muna maka girki." Murmushi yayi yace "Kuna min girki ko kuna mana?" Ba fara'a a fuskar ta tace "Duka." Kallonta yayi, kawai shi yasan akwai abinda yake damun ta tun jiya, maganar da sukayi ce ko kuma dai wani abun na daban? Shine kuma bai sani ba dai, yajin da ta ja tare da riƙe robar hannun ta gam ta furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Cikin kulawa ya matsa daf da ita tare da dafa kafaɗar ta yace "Ummu, lafiya? Ƙonewa kikayi?" A raunane ta girgiza mishi kai tace "A'a." Da kulawa ya sake cewa "Ko baki da lafiya ne?" Nan ma girgiza mishi kai tayi tace "Ba komai." Kuwailat da ta ji amsar da ta bashi sai ta dube shi a ladabce tace "Abba, marar ta ce wai take ciwo." Kallon Kuwailat yayi da tayi maganar, sai kuma ya kalli Ummu ya sake riƙe hannun ta yace "To ko muje asibiti na raka ki?" Kamar wanda ya mata wani abu sai kawai tace "A'a, bana so, naji sauƙi." Yadda tayi maganar kamar a kausashe yasa shi ɗan yin jim yana kallon ta, lura da kamar ba ta kyauta ba sai kuma ta wayance tace "Shikenan, idan bai daina min ba har aka jima zamu je." Jinjina mata kai yayi yace "Shikenan, dan Allah fa idan kin ji abun ya tsananta ki faɗa min.?" Jinjina masa kai tayi kafin ya juya ya fita ya bar su dan su ci gaba da aikin su, haka ta ƙarasa aikin à daddafe da taimakon Kuwailat har suka idar. Suna cin abinci bayan sallah azahar Nabila ta kawo mata maganin da yanayi na sauri saboda adaidaita da ta tsayar a waje, tana bata maganin tace "Gashi aunty, Fahad biyu yake sha, amma kinga tunda ke ai tso..." Da sauri Ummu ta buge mata baki, maganar da bata ƙarasa ba kenan sai dariya tayi ta juya da gudu ta fice tana faɗin "Sai kin kira ni aunty kin bani labari." Da kallo ta bita har ta fice, sai kuma ta kalli maganin kamar tana tuhumar kan ta ko maganin, ƙarasa cin abincin sukayi inda Kuwailat ta gyara wurin da wanke kwanukan da aka ɓata dan lokacin tafiya islamiyyar ta ya kusa kasancewar uku na rana suke shiga. Har ta kammala girkin dare ba ta da wani kuzari a jikin ta, haka ta gama ta yi duk yadda ta saba yi tare da haɗin lemu na ɗanyar citta da lemun tsami, saida ta ware wanda zasu sha ita da Kuwailat sannan ta jefa maganin a na Alhaji ƙwaya biyu da tunanin idan zai iya to su kwana dare yana haƙar ta har ta rabu da abinda ke damun ta, duk da kuwa tunanin ta ya fi raja'a da ƙaramin ciki gareta, amma sai ta ayyana _"Ba abinda zai samu ɗan cikina, sai ma lafiya da zai ƙara."_ *Bayan* sallah isha'i ya shigo kamar yadda ya saba, sai dai da wani yanayi na kasala da kamar damuwa, a gajiye ya zauna kan kujera kusa da ita yana cire hular shi tare da dafe kan shi, cike da kulawa ta kalle shi tace" Abban Ummu, lafiya?" Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kalle ta a sanyaye yace" Wallahi kaina ne kawai yake min ciwo." Da yanayin tashin hankali ta ɗago daga kujerar ta dafa shi tace" To bari na kawo maka magani." Girgiza kai yayi a tausashe yace" A'a, ki bar shi ma, na sha magani yanzu kafin na taho, ina so dai na kwanta ne kafin anjima." Da gamsuwa ta jinjina masa kai tace" To, Muje na raka ka." Tashi yayi da ƙyar saboda nauyin da jikin shi ya mishi wanda shi kanshi fa ya tabbatar shekaru fa sun ja sosai, saida ya shafa kan Kuwailat da ta kalle shi da tausayawa tace" Sannu Abbana, Allah baku lafiya kai da Mamie." Murmushi ya mata yace" Ameen ƴar Abba, mun gode." Ɗakin suka shiga inda ta taya shi cire babban rigar shi har da ta cikin sannan ya kwanta, zane ta jawo masa ta rufe mishi rashin jiki saboda acn da ta kunna dan baya zama sai da ac shi ɗin, har za ta miƙe ya riƙe hannun ta suka kalli juna, cikin nutsuwa yace "Dan Allah Ummu Kulsum, ki je asibiti gobe a duba ki, idan baki je ba kuma jibi idan su Aliyu suka dawo zan sa Aliyu ya tirsasa ki ki je." Murmushi tayi saboda tuna yadda Aliyu ke girmama ta shima, sai dai bayan girman da yake bata ma yana iya faɗa mata gaskiya kai tsaye sannan kuma ya ce wallahi Mamanmu sai kin yi kaza fa, jinjina mishi kai tayi tace" Shikenan, zan je." Murmushi shima yayi tare da lumshe idanu, hakan ya sa ta miƙewa ta fita daga ɗakin ta rufe mishi ƙofa, sai lokacin ne da ta ga teburin abinci da kayan da ke sama ta tuna da maganin da ta saka a lemu, wani mlalacin murmushi tayi kawai ta maida hankalin ta gaba ɗaya kan Kuwailat dake biya mata karatun ta. ******************* Wani tagumin ya sake yi yana ƙurawa lambar da ya aika kira idanu, yana ji tana ƙara har ak yi nasarar ɗauka, cikin wata kakkausan muryar dattijon da daga ji kasan mazan fama ne aka ce "Hello." Wani mummunan faɗuwa gaban shi yayi saboda jin muryar, inda tafin hannun shi ya jimƙe wayar gam ya rintse idanu, take tsigar jikin shi suka tashi duk kwantancen gashin dake hannun shi ya nemi miƙewa, samun kan shi yayi à yanayin da kai tsaye ya kasa iya fassarawa, dan bai san tashin hankali bane ya shiga na jin muryar mahaifin na shi? Ko kuma dai kewa ce cike da bege na mahaifin da ka jima baka haɗu da duk wani abu da ya shafe shi? Wannan ƙaƙƙarfan muryar da ya ji an sake ambaton "Hello, ina ji !" Hakan ya saka shi buɗa idanu da sauri ya yanke kiran saboda jin kamar mahaifin nashi a hassale yake magana, sannan bai san me zai ce mishi ba bayan kwashe wannan shekarun da aka yi, bai san ta ina zai fara magana da shi ba, shin har yanzu mahaifin shi na nan da ƙudirin kalmar nan da ya faɗa ta sai yayi Ajalin shi? Ko kuma dai shekaru da kuma lokaci ya sa ya manta da abinda ya faru? Dafe gaban goshin shi yayi tare da feso iska daga bakin shi ya lumshe idanun shi ruf, a tausashe ƙwarai ya furta "Ba zan iya ba." A ƙufule, kuma a hassale Aliyu dake zaune gaban shi shi ya tirsasa shi kiran mahaifin nashi yace "Za ka iya Jabir, za ka iya magana da mahaifin ka, mantawa kake da shi kaɗai ne ya rage maka ko? Jabir a ganin ka da mahaifiyar ka tana raye za ta bar wannan daɗɗiyar gabar ta ci gaba da wanzuwa a tsakanin ku ne?" Da sauri Jabir ya ɗago ya kalli Aliyu da ya tsare shi da idanu, idanun shi tuni sukayi jajir abun ka ga jar fata, sai kuma ya tausasa kallon shi ga Aliyu ya girgiza kai yace" Ba gaba muke ba." Wani sakaran murmushi Aliyu yayi yace" Ba gaba kuke ba? Me kuke to? Shekara goa sha uku ko gaisuwa ba t haɗa ka da mahaifin da ya haife ka ba, kuma ka ce ba gaba kuke ba? To e kake yi da shi?" Shiru yayi sai wayar da yake ci gaba da kallo kawai yana sauke numfashi, cike da bada umarni Aliyu ya sake cewa" Ka kira Jabir, idan ba haka ba zan kira Abba na sanar da shi ka samu lambar mahaifin ka fiye da shekara ɗaya, amma ajiyar ta kawai kake a waya ka ƙi kiran shi." Zubawa Aliyu idanun shi yayi, kallon da yake ma Aliyu shi kan shi sai ya kasa fahimta, hakan yasa Aliyu miƙewa yayi hanyar ɗakin su na bacci yana faɗin" Zan ƙarasa shirin kayan mu." Saida ya ji Aliyu ya shige ɗakin ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya, wayar ya sake kallo, Abba? Ba Ya so Aliyu ya faɗawa Abba komai, dan take zai bashi umarni kuma dole ya bi dan alƙawari ya ɗauka tsakanin shi da ubangiji kan cewa zai yi duk abinda bawan nan ya saka shi matuƙar bai saɓawa shari'a ba, ya yi niyya zai yi duk abinda ya umarce shi sau ɗaya ba sai ya maimaita sau biyu ba, dan haka ya sake sauke numfashi sannan ya sake tura kiran. Nan ma ƙara ta dinga yi wayar har ta kusa tsinkewa kafin ya ji an ɗaga a zafafe yace "Oui ina ji, wa ke magana?" Ɗaga bakin shi yayi zai yi sallama, amma sai ya ji kamar wani abu ya tokare mishi maƙoshi, hakan yasa ya kasa cewa komai yanzu ma, da yanayin nan na zafi da yasan Abban shi da shi yace "Ko ma waye ke kira idan baya ji ne ko nine bana jin shi dan Allah ya haƙura da kiran dan ba zan iya haɗa tashin hankalin da nake ciki da wannan shirmen ba." Niyyar yanke kiran yayi, amma da Jabir ya ji mahaifin shi ya ambaci tashin hankali sai shima nashi hankali ya ɗan miƙe tsaye saboda rashin sanin ma me ke faruwa to? Hakan yasa shi saurin faɗin" *Aba*." Tsit! Dukansu sukayi sai numfashi suke saukewa, shi dai duk canzawar da mai muryar nan ya yi, duk da rashin tabbacin da yake da akan sanin mai muryar, ba zai kasa faɗin cewa kamar tattausan muryar ladabin yaron shi ba da ko wane lokaci muryar shi a nutse take fita, amma rashin tabbaci da kuma son ya gane shi ɗin ne ya tuna da shi yau ya kira shi? Ko kuma dai wani ne mai irin muryar ɗan sa Jabir, dan haka a tausashe cike da zaƙuwa da zumuɗi yace " *Jabir*? Kai ne?" Shiru Jabir ya yi sai dafe goshin shi da yayi na wasu sakanni, da zumuɗi Aban nashi ya sake faɗin "Jabir? Kai ne? Ka yi magana mana in ji?" Shi fa bai ɗauka akwai wani tausayi ko ƙauna tsakanin su ba, amma iko na Allah kawai sai ya ji yana lumshe idanu hawaye sun gangaro kan kumatun shi irin masu zafin nan dake nuna halin da zuciya take ciki, da sauri da kuma rashin yarda cewa hawaye ne yake ya goge tare da jan majina ya sake furta "Aba, ni ne." Wani irin salati ya ji mahaifin nashi yayi da sam bai tsammaci zai yi shi, cike da kewa da nadama ya fashe da kuka a wayar yna faɗin "Jabir, dama za ka yafe min ka kirani? Ban taɓa tunanin za ka sake waiwayata, Jabir na jima da cire tsammani a kan ka, na ɗauka nayi asarar ɗana ɗaya tilo da na mallaka a rayuwata." Sai kuma yayi shiru yna ci gaba da kuka, cikin rashin jin daɗi Jabir ya miƙe tsaye a tausashe sosai yace" Aba, ka daina kuka dan Allah, ka yafe min Aba, nayi kuskure nima da na tafi na bar ka kuma ban sake waiwaya ba, amma Aba ba dan *Abbana* ba da wataƙila fanɗarewata ta isa tasa na ƙi waiwayar ka har abada." Cikin raunin murya kamar zaiyi kuka ya sake cewa" Aba ka yafe min, jibi zamu dawo ƙasar nan in sha Allah, zan sake neman afuwar ka akan ɓata maka da nayi." Da farin cikin jin zai dawo ya ce" Jabir za ka dawo? Jibi jibin nan? Allah ya dawo da kai lafiya Jabir, Jabir baka min komai ba a rayuwa, ni ne na zalince ka na kasa riƙe amanar da Allah ya bani, ni ne mai laifi a nan dan ni ne silar komai." Ajiyarp zuciya ya sauke yace" Aba baka da laifi, kai ka haife ni, kuma ka isa ka min komai idan nayi ba daidai, laifina ne." Da farin ciki Aban yace" Ba komai Jabir, ni na jima da yafe maka, amma dai da gaske za ka zo ko? Za ka zo in ganka Jabir? Na san ka girma sosai yanzu, wataƙila ni ka biyo ko kuma Maman ka, zan so ganin haka." Yadda yayi maganar da tsantsaar gaskiyar shi kenan yasa Jabir yin wani bahagon murmushi, ɗan ɗaga idanun shi yayi ya kalli madubin dake jikin ƙofa, a ranshi ya ayyana _" Ni ɗan Mamata ne Aba, kama da ita nake sak."_ A zahiri kuma cew yayi" Zan zo Aba, in sha Allah." Shiru ne ya ɗan biyo Da sakanni inda kowa da abinda yake saƙawa a ranshi, kafin daga bisa Jabir ya nisa yace" Aba, ina aunty? Da Uzeifatu?" Duk da a waya ne ba sa ganin fuskar juna, amma daga yadda ya bashi amsa da" Suna nan, lafiya lau." Ya fahimci ba ya da karsashi kuma akwai wani abu a ƙasa, dan haka ya sake tambaya da" Lafiya ko Aba? Na ji kana maganar matsala ɗazu?" A sanyaye ya bashi amsa da" Ba komai Jabir, Allah ya maka albarka, sai jibin idan kun taho, amma dan Allah ka ci gaba da kirana har sanda za ka zo." Ƙwarai ya gasgata ɗari bisa ɗari akwai matsala, wataƙila babba ce da bai kamata su tattauna ba a waya, dan haka zai jira har ya koma gidan, dan haka ya amsa mishi da in sha Allah zai ci gaba da kira, sannan ya ce a gaida kowa da kowa sannan suka aje wayar, wata ajiyar zuciya ya sauke mai nauyin gaske tare da jin wani irin sanyi a ƙasan ranshi da ma zuciyar shi mai kama da na ka sauke kayan da suka fi ƙarfin ka a kai. Aliyu duk yana jin abinda ke faruwa, dan haka saida suka gama sannan ya fito tare da nuna bai san da sun yi waya ba yace "Jabir, Abba nake ta kira wallahi wai wayar à kashe, Abba kuma ai baya kashe waya ko?" Kallon Aliyu yayi gaba ɗaya da kulawarsa tunda ya ji ya ambaci Abba d baya wasa da lamarin shi a sanyaye yace "Abba ba ya kashe waya ai." Sai kuma ya ji gaban shi yayi wata sanyayyar faɗuwa, da sauri ya shiga neman lambar Abba a wayar shi, kira yake shima amma kashe, hankalin shi ne ya fara tashi, yasan ba ya kashe waya komai rintsi, sannan kuma yana fama da matsanancin tension, dan haka hankalin shi da tunanin shi ya fi bashi ba lafiya ba. Aliyu dake kallon shi yana aika kiran wani bayan wani ne yace "Ko za mu kira Hajia babba mu ji lafiya?" Zuba masa idanu Jabir ya yi bai ce komai ba, amma sai Aliyu y aga kamar Jabir na aika mishi saƙo ne da idanun shi cewa _"Ka manta Hajia girma ya gama cimma ta, ta yadda take fama da matsalar idanu ga kuma ta ƙafafu, sannan ga ciwon sugar da ya sako ta gaba shima, yau lafiya gobe ba lafiya?"_, sai kawai Aliyu ya hankalta yace" Hakane fa, to ko Umma (Hajia Asiya Maman Aliyu) za mu kira?" Sai kuma yayi saurin girgiza kan shi yace" Um um, abar maganar Umma, ina kira sai ta yarfo maganar da za ta sa ka ksa ganewa, ga maganar aure da take min kullum." Ɗauke duban shi yayi daga kan Aliy cike da miskilanci bakin shi ya furta " Maaama." Take kuma ya ɗora wayar a kunne alamar har ya aika kira wa lambar ta Ummu, ƙara wayar ta dinga yi ba'a ɗaga da wuri ba, hakane yasa Jabir kai da kawowa a tsakiyar falon cike da ƙaguwar ta ɗaga ya ji ina Abban shi? Sannan me ke faruwa? *Na kusa fara daarasin kayan marmari ƴan uwa, ki garzayo ki yi register akan farashi mai sauƙi zaki koyi abubuwa dayawa har na tsawon kwana biyar* in sha Allah. SAI KUN ZO *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *33* *11:20* Ummu nufi ɗaki dan kwantawa bayan Kuwailat ta kwanta, tayi mamakin samun shi idanun shi biyu, da mamaki ta ƙarasa tana faɗin "Abban Kuwailat, dama ba bacci kake ba?" Murmushin yaƙe ya mata yace "Na dai farka." Kusanshi ta zauna tana faɗin "Na haɗa maka ruwan wanka ko?" Jinjina mata kai yayi yace "Um." Dan haka ta miƙe da azama dan haɗa mishi ruwan, tana gama haɗawa ta dawo tace "An haɗa." A gajiye ya tashi zaune da ƙyar, sai dai ƙafafun shi da sukayi bala'in nauyi ya kasa ɗagawa, dan haka yace "Taimaka min na tashi?" Ta yi iya ƙoƙarin ta na taimaka mishi amma gaba ɗaya ne ƙafafun shi suka ƙi takuwa, ga kan shi da ya ce har yanzu bai daina ciwo ba, dan haka tayi saurin zuwa ta samu Hajia babba ta sanar da ita da kuma Khamis wanda duk da ba Alhaji bane ya haife shi amma ya zama babba ɗa na gidan, da taimakon su ne aka ɗauki Alhaji zuwa asibiti, kwantar da shi aka yi tare da bashi kulawar da ta dace sannan aka mishi allurar bacci. Khamis ne ya ɗauki wayar Alhajin ya kashe ya ce saboda ka da a takura mishi, shine Dalilin da ya sa ake kira ba'a samu. *Yana* kiran lambar Ummu sai kuwa ta shiga, ta jima tana kallon lambar tana tunanin waye ke kiran ta da wannan code ɗin? Dan ita sam ba ta da lambar Jabir, ba ta nema ba kuma shima bai neme ta ba, ita a ganinta ai muharramin ta ne, dan haka bai kamata suna waya ba, abinda ya faru ya faru kawai ya wuce, sannan kuma ba lambar Aliyu bace wanda tana da ita, cikin wannan hali na tamtama da rashin sanin waye ta ɗaga kiran sannan ta kara a kunne. Jin ta ɗaga saida ya sauke ajiyar zuciya ta farin cikin a ƙalla zai san ina Abban shi yake? Dan haka shi sam ya ma manta da ya mata sallama bare ya gaisheta, abu na farko da ya furta a nutse sosai kamar mai mata raɗa shine " *Maaama*." Ya salam! Hasbunallah wani'imal wakil ! Shine abun da ta faɗa ita ma a zuciyar ta, dan kuwa wannan yanayi da ya mata magana da shi sosai ya saka gabanta faɗuwa tare da jin wani yam yam ! A jikin ta, sarai ta gane wa ke magana, dan a duniyar nan shi kaɗai ke bata girman da ko Kuwailat da ta haifa ba ta bata irin shi, iska ta fara fesowa daga bakinta kafin tace "Barka." Ɗan ɗaga girar shi yayi irin mamakin kan nan nashi ya kama shi, cikin matuƙar tausasawa yace "Maaama ina Abba? Yana lafiya?" Saida ta kalli Alhaji dake bacci sannan ta tausasa murya ita ma kamar bata son kowa dake kusa da ita yaji tace "Yana bacci, yana lafiya." Sai ya ji kamar bai yarda da ita a ba, dan gaskiya muryar ta babu walwala à ciki, hakan yasa shi kasa gasgata ta saida yace "Kun tabbata? Ku bani Abba, ina so nayi magana da shi?" Ƙurawa Alhaji idanu ta sake yi tana mamakin yadda yake wani kiran ta da *ku* tsabar girmamawa, numfashi ta sauke sannan tace "Muna asibiti ne, bai ji daɗi ba, an mishi allurar bacci yana hutawa, amma jikin shi da sauƙi sosai, kar ku damu." Ya ɗauki kusan minti ɗaya bai ce komai ba kafin ya numfasa yace "Shikenan, Allah bashi lafiya, zan sake kira, amma dan Allah Maama..." Sai kuma ya sake yin ƙasa da murya sosai yace "Na roƙe ku idan ya farka ku sada ni dashi." Saida ta sauke nauyayyan numfashi sannan tace "In sha Allah." Tana sauraro har ya yanke kiran sannan ta ɗauke wayar da ga kunnen ta, aje wayar tayi sannan ta sake maida hannun ta ga marar ta ta dafe da har yanzu take murɗa mata. *Washe Gari* Khamis da Hayat ne riƙe da Alhaji da suka dawo daga asibiti, Ummu na bayan su riƙe da wasu kayayyaki a hannayen ta suka nufi shiga falon ta, suna kusan isa ɓangaren Hajia Asiya tayi saurin fitowa daga falon ta wacce ta ga shigowar su tace "A'a, ku dakata malamai, ina ce yau kwanana ne ko?" Dakatawa sukayi duk suka kalle ta, sai lokacin kaɗai Ummu ta iya tunawa da yau ya kamata ya koma ɗakin ta, dan Hajia babba ta cire kanta a lamarin kwanan nan, a ladabce Ummu tace "Ina kwana Maman Aliyu, kiyi haƙuri wallahi na manta ne." Ba ta jira me za ta ce ba kawai ta kalli su Khamis tace "Ku raka shi, zan je na aje kayan sai na zo na sake duba shi." A gatsalce Hajia Asiya ta harare ta tace "Ba buƙata, naga ai ke kika kwana dashi asibiti, sannan kun dawo gida tare, ni ba zan iya kula da shi ɗin bane?" Murmushi kawai Ummu tayi dan ita yanzu ba ta ga abun rigima a rayuwar gidan nan ba, a tausashe ta sake cewa "Kiyi haƙuri." ba ta sake jiran abinda za ta ce ba kawai ta yi hanyar shigewa, tsaki tayi ta bita da harara tace "Aikin banza, ka ji munafurci wai ta mance." Su Khamis dai na kallon ikon Allah, haka suka raka shi har falon ta suka zaunar da shi wanda shima ya zuba musu ido kawai bai ce komai ba akan hatsaniyar tasu, shi da zasu ji ta tashi ai da sun bar shi wajen Ummu har ya samu lafiya, dan Hajia Lubabatu dai ta kanta take ita ma bare ta yi jinyar shi, Asiya kuma masifa da tsirfa kala kala zai sha da hayaniya, Atika kuma jaraba da rashin kulawa, dan haka Ummu ce za ta iya kuma sun hana. ******************* Mamaki ne ya cika Hajia Radiya ganin yau kira ɗaya tak ta ma Fahad amma ya ɗaga, gaisawa sukayi sosai cike da farin cikin to ko dai Allah ya fara karɓan addu'arta ne? Dan ko umra da ta tafi iya Fahad kawai ta ambata gaban ɗakin mai kowa da komai da iko akan komai, cikin kulawa tace mishi "Fahad, yaushe za ka zo gida? Abubuwa da dama suna ta faruwa babu kai, yanzu Faha haka kake so ka ci gaba da rayuwa?" Da alamar ƙaguwa yace "Mamie, gani nan fa zuwa gidan, ina kan hanya ne, zan zo ai." Saida ta kalli Alhaji dake kallon farin cikin da take sannan tace "Da gaske? Amma dai idan ka zo ba zaka koma ba ko?" Da yanayin zafi Alhaji ya figi wayar ya ɗora a kunnen shi yace "Babu inda zai koma, ka ji da kyau idan har ka zo to babu komawa, ka zo kenan, dan aure zan maka." Wata irin dariya kawai Fahad yayi dan shi ai ya ga zuwan shi da komawar shi, yo Nabilan shi ma ta gudu daga gida bare kuma shi? Shi fa? Ko a haure ba ya haura katanga ba, ba tare da son doguwar magana ba tunda ai gidan zai zo kuma sai ya zo ɗin tunda yana buƙatar kayan abinci da kuɗi yace "Abbu kai dai jira na zo, aure kuma kamar wata mace? Idan ma auren za ka min ka min da Nabila mana, amma ba da wacce bana so ba." Yana gama faɗin haka ya kashe wayar ba tare da ya ji me Alhaji zai ce ba, hakan yasa Alhaji miƙa mata wayar ta yace "Kina ji? Ki duba min cikin dangi wacce kike ganin za ta dace da shi, yana shigowa gidan nan aure zan ɗaura masa, wataƙila ya yi hankali." Da tsananin mamaki Hajia tace "Aure? Auren dole fa kenan za ka mishi?" A kausashe ya kalle ta yace "E ɗin, idan bamu mishi auren dolen ba ai shi ya je yana zubar mana da mutumci a dole, to ni dai abinda na faɗa kenan, idan za ki duba ki duba ko ni na sa a duba min." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Allah baka haƙuri, amma na ga mu kanmu ya muka iya da Fahad da har za mu yarda a aura masa ƴar mutane ba ya so, zai iya yin komai ba." Cike da dagiya Alhaji yace "Ya yi ɗin, zan ga ni da shi wa ya haifi wani? Na jima ina zuba masa idanu, yaran ki kuma suna ƙyale shi ne saboda Fahad ya zamar miki kamar ido ɗaya, ana taɓa shi zaki fara hawaye, su kuma basa son tashin hankalin ki, amma daga yanzu an zo ƙarshe." Shiru ta yi ba ta ce ƙala ba, ita dai tasan ba hanya mai ɓillewa ba ce yake son bi, saboda Allah su kan su ya suka iya da lamarin Fahad? Sai kuma a ɗauko wata yarinya da ba ya so a aura mishi? Salon ya dinga muzguna mata, ita kuma tana da yara mata dan haka ba za ta so a ci zarafin mace ba ko dan gujewa ƴaƴan ta. Kiran Sa'ad da ya shigo wayar Alhaji yasa shi ɗago kan shi ya dubi wayar, da sauri ya ɗauka dan Sa'ad ya wuce mijin da ke auren jikar shi sai dai jika, yana ɗauka suka gaisa kamar kullum sannan Sa'ad yace "Alhajin mu, ba ka san an kama sirikin ka ba?" Da mamakin jin sirikin da ya ambata yace "Sirikina kuma? Wane daga ciki? Wa kuma suka kama shi?" Daga wajen Sa'ad cewa ya yi "Sirikin ka Hambali mana, ya shigo jiya da dare saboda matsalar ƴar sa, sai dai hujojjin da na tura sama sun fi ƙarfin ayi fatali da su, hakan yasa dole aka kama shi, dan akwai wani ɗan jarida da ya taimake mu sosai, kuma kusan shi ya mana aikin ma, daga ƙarshe dai maƙiyan ku sun shiga hannu." Wani sahihin murmushi Alhaji ya saki tare da lumshe idanu yace" Sa'ad, ina alfahari da kai, yau ka sa na daina kishi da kai akan matata da ka rabani da ita, Sa'ad, haƙiƙa shigowar ka rayuwar mu alkairi ne, ka taimake mu ka taimake mu sau da dama, ama har yanzu mun kasa saka maka da alkairi ɗaya, Allah ya saka maka da alkairi, Allah ya baka abinda kake nema duniya da lahira, mun gode sosai." Da farin ciki Sa'ad yace" Ba komai Alhaji, tunda kuka bani Eesha nima na zama ɗaya daga cikin ahalin nan, dan haka ba ku nayi wa ba, kanmu na wa." Murmushi Alhaji yayi yace" Hakane, zamu yi waya anjima, tsohuwar nan ce sai kallon bakina take saboda son jin gulma duk ta rikitani da idanun ta." Dariya Sa'ad yayi yace" Da gaskiyar matata, a faɗa mata ko hankalinta ya kwanta." Aje wayar sukayi inda Alhaji ya sanar da ita abinda ya faru, ƙwarai ta ji daɗi kuma ta yi murna, sannan ta yabawa Sa'ad da namijin ƙoƙarin da ya yi a kan su. *Har* magrib Fahad bai iso ba, lokacin Mamie suna waya da aunty *Marfu'a* wacce ita ke bin bayan Yaya Bilal tana faɗa mata abinda Alhaji ya zo musu da shi, cike da goyon baya aunty Marfu'a tace "Gaskiya Mamie na goyi da bayan Abbu, a ma Fahad aure wataƙila sai Allah ya shirya shi sanadiyar haka, amma idan ba haka ba Fahad zai jawo mana magana." A tausashe Mamie tace "Ba wannan ba Marfu'a, wacece zamu haɗa da Fahad? Sannan bamu tauye ta ba? Idan ya zo ya zalince ta mu ma fa muna da kamasho." Cike da son kwantar mata da hankali tace "A'a Mamie, ni ina ganin mu duba cikin ƴaƴan kawu *Abbas*, kinga duk abinda ke faruwa shi ya sani, idan har ya amince koai zai zo da sauƙi in sha Allah." Ajiyar zuciya Mamie ta sauke ta jinjina kai tace "To, in dai hakane ina ga zamu iya nema mishi auren *Fati*, dan yarinyar tana da nutsuwa ga kuma ƙoƙarin koyi da addini." Cike da farin ciki aunty Marfu'a tace "Da kyau Mamie, wallahi kamar kun shiga zuciyata, nima wacce nayi tunani kenan, idan har abun nan ya tabbata, to za ta iya zama silar shiryuwar shi ma." Murmushi Mamie tayi tace "To shikenan, Allah ya tabbatar mana da alkairi, zan faɗa ma Alhaji shaw..." Da mamaki Mamie ta sake duban Fahad ɗin da ya shigo take kuma tace "Fahad, sai yanzu ka iso?" Aunty Marfu'a dake saurarenta ne tace "Fahad fa? Zuwan magriba?" Da tabbaci Mamie dake kallon Fahad da ya shigo ɗakin nata ya zauna bakin gado tace "Ga dai shi." Taɓe baki tayi kamar suna kallon juna tace "An waiwayo gida, hakan na nufin kuɗin yake so, ku gaishe shi Mamie." Murmushi kawai Mamie ɗin tayi ba tace komai ba ta aje wayar, kallon da ta mishi yasa ya shafa kai yace "Mamiena." Girgiza kai tayi kawai tace mishi tace "Ya hanya?" Saida ya marairaice yace "Da dama, da abinci a gidan Mamie?" Da alamar tuhuma tace "Wane a ciki? Dafaffe ko ɗanye?" Da mamaki ya kalle ta yace "Mamie ban gane ba? Ya ɗanye kuma?" Gyara zamanta tayi sosai tana dubanshi tace "To ai naga ɗanyen ma ɗiba kake ka tafi da shi, dole na tambaye ka wane kake so." Murmushi yayi yace "Mamie ko zan ɗiba ai sai na tashi tafiya ko? Kuma fa kinga Beela ce nake ɗiban ma abincin saboda ba sai ta dinga siya ba." Da wani bahagon kallo ta dube shi da ya saka shi jin ya tsargu tace "Fahad, kai ko kunya baka ji ka dinga maganar wata mace da ba matar ka ba kuma ba muharramarka ba a gaban mu?" Shafa ƙeyar shi yayi da irin kunyar nan yace "Mamie, ba wai bana jin kunyar ku bane, kawai dai ina faɗa ne dan ku gane son da nake ma Beela." Girgiza kai tayi cike da takaici tana kallon shi tace "Fahad, so fa kace? Wace irin soyayya ce a rayuwar da aka ginata akan turban sheɗan? Fahad baku dace da juna ba, ita ma kuma na tabbata ba kai take so ba, wani abu naka take so, dan haka ka rabu da ita mana, ka zauna gida Fahad ni nan zan haɗaka da wacce za ta dace da kai." Zunbur ya miƙe tsaye yana wani girgiza kai irin fa an takura shi ɗin nan yana faɗin" Ni fa Mamie shiyasa bana son zuwa gidan nan, Mamie Nabila tana sona sosai, bata kula kowa bayan ni kaɗai, kuma bata fara kula kowa ba sai da muka hadu ta fara a kaina, Mamie na faɗa muku idan zanyi aure to ita zan aura, yanzu haka mun fara shirin auren mu, kawai bikukuwan ƙawayenta ne muke so a gama sai mu ma ku sa mana rana." Alhaji da ya ɗan jima bakin ƙofar yana jin su ne ya ƙarasa shigowa yana faɗin" Ba ranar da ni dai a matsayina na ubanka zan saka maka da wannan tantiriya kuma sheɗaniyar yarinyar da kuka gama fitsarewa a waje, ka ji da kyau Fahad, in dai nine uban ka wallahi ba kai ba wannan yarinyar." Kallon Alhajin yayi idanun shi cir a cikin nashi yace" Abbu, wai da gaske kake dama? Na ɗauka abinda ka faɗa à waya wasa kake min, to gaskiya Abbu ba zaka min auren dole fa, namiji ne ni, tunda ina son ta a aura min mana." Da sauri Hajia ta tashi tsaye ta shiga tsakiyar su saboda ganin fuskar Alhaji da maɗaukakin ɓacin rai yana shirin mayar ma da Fahad ɗin martani, cikin sigar rarrashi tace mishi "Dan Allah Alhaji, karka biye mishi, ka bari ni zanyi magana da shi." Sai kuma ta juya ga Fahad fuskar ta haɗe sosai tace "Maza wuce ɗakin ka, kar na sake jin ka ce wani abu a nan." A fusace Fahad ɗin ya wuce yana jin ba fa zai yarda ba, wallahi sai dai ayi duk wacce za'a yi amma ba za'a aura masa wata mata ba Nabila ba, to ya zama sakarai ma kenan? Sannan duk alƙawarin da ya ma Nabila ya tashi a banza, bayan ita ta riƙe mishi alƙawari? Lallai ma. *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *34* Kiran ta yayi har ya gaji ta ƙi ɗagawa saboda tana hushi da shi, Ja'afar ya kira yana ɗagawa yace mishi "Kana gida ne?" Daga wajen Ja'afar ya amsa da "E, ina gida, ya aka yi?" Da sauri yace "Nabila fa?" Da rashin tabbaci yace "Ban sani ba, kasan ba shiga wajen ku nake kowane lokaci ba, musamman baka nan." Da gaggawa yace "Dan Allah duba min, idan tana nan bani ita a waya." A kasalance Ja'afar yace "Ok." Tare da tashi ya nufi ɓangaren, yana zuwa falon ya shiga kai tsaye, kwance ya same ta da doguwar riga iya guiwanta, take ya faɗawa Fahad "Gata fa kwance." "Bani ita nace?" Cewar Fahad a ɗan kausashe, miƙa mata wayar yayi yace "Ke yana son magana da ke." Wata uwar harara ta watso mishi wanda tun shigowar shi ko kallon arziki ba ta mishi ba sannan ta ja tsaki tace "Ban da lokacin ku, ai ina da waya, kuma ina ganin kiran shi, ban yi niyyar ɗauka bane, idan kuma akwai ubana a cikin ku kusa in yi magana da shi." Taɓe baki Ja'afar yayi yace "Jaraba." Maida wayar yayi a kunnen shi yace "Ta ce tunda ba ubanta bane kai ka shafa mata lafiya." Daga wajen Fahad bai kama yarda ba ita ta faɗi hka ba dan yasan za ta aikata, amma dake yasan lagon ta sai yace ma Ja'afar "Ce mata abubuwa sun tsananta a nan, a taƙaice ma Abbu ya hanani fita ko ina, ya ce *auren haɗi* zai min." Yana faɗin hka ya kashe wayar, kallon ta Ja'afar yayi yace "Kin ji ya ce a faɗa miki wai dagus ɗin shi ya saka shi a mari, kuma suna daf da ɗaura masa aure da ƴar dangin su." Wani irin mummunan faɗuwa ne gaban ta yayi, cikinta ya hautsina da ƙarfin bala'i, tsigar jikin ta ta tashi da wani irin bala'en'en yanayi, take zufa ta fara tsatsafo mata, amma fa duk wannan tashin hankali da ruɗun da ta shiga tsaf ta ƙi nunawa, sai ma basarwa da tayi ta kalle shi tace "Sai me ? Ina ruwana to?" Da mamaki ya sake wara idanu ya kalle ta, sai kawai ya juya ya fita a ɗakin yana faɗin "Hayaƙi ya fara yawa a kan ki." Saida ta tabbatar ya tafi, ta tabbatar yayi nisa, tasan ba zai ji ta ba, sai kuwa ta yi tsal ta tashi zaune ta fashe da wani irin kuka mai cin rai tana laluban wayar ta dake kan kujerar tana faɗin "Na shiga uku na lalace, Fahad kar ka ci amanata, kar ka ci amanata Fahad dan Allah, wallahi kai kaɗai nake so, Fahad kai kaɗai nake kulawa, duk ƙawayena sun san ni da kai kaɗai, idan bamuyi aure ba Fahad bakin duniya kashe mu zai yi....maza mana ka ɗaga." Ta ƙarashe faɗa saboda kira da ta aikawa Fahad ɗin, saida ya ɗan basar sannan ya ɗaga, kafin ta ce wani abu yace" Mun shirya kenan?" Sake fashewa tayi da kuka, hakan yasa Fahad zabura ya miƙe tsaye hankali tashe yana faɗin" Nabila, me aka miki? Wa ya saka ki kuka?" Cikin fitar hayyaci tace" Ban sani ba, da gaske ne za'a maka auren haɗi?" Wani shaƙiyin murmushi yayi dan ya gane dalilin da ya sakata kuka, dan haka saboda ya wahalar da ita yace" E, Abbu ma fa ya kulle ni a ɗaki." Tana jin haka ta ja majina tace" Shikenan, zaka gani." Take ta yanke kiran ta miƙe tsaye ta nufi uwar ɗaki tana faɗin" Zaka gani, Fahad Saheeb baka san wacece Nabila ba har yanzu, shima kuma tsohon bai san wacece ni ba, wallahi gidan zan je na fito da kai, yadda na ƙi jin maganar iyayena na ƙi auren kowa, kai ma baka isa ka zauna da kowace mace ba idan ba ni ba." Ƙwarai da gaske take, dan kuwa kaya ta haɗa a jakar ta matsakaciya sannan ta canza kayan ta ta fito da niyyar zuwa ta ciro ticket ɗin tafiya inda Fahad yake da daren ranar, dan so take kafin ya farka baccin safe ya gan ta gaban shi. *WASHE GARI* Da safe sosai Mama ta zo duba jikin Alhaji da Ummu t faɗa mata bashi da lafiya, har ɓangaren Hajia Asiya ta raka ta suka dubo shi, basu jima ba saboda rashin kyakyawan tarbe da Maman ta samu a wajen Hajia Asiyan suka miƙe dan tafiya, har za su tafi Alhaji dake zaune cike da rashin jin daɗin yadda ya ga Asiya ba ta saki fuska suka gaisa da Mama ba yace "Maman Kuwailat." Da sauri ta juyo cike da ladabi ta amsa da "Na'am." Da fara'a à fuskar shi yace "Munyi waya da yaran nan, in sha Allah zuwa bayan azahar suna isowa, na ce ko zaki iya saka tukunyar ki dasu?" Wani ƙayatacen murmushi ta saki da ladabi tace "Me zai hana? Ma sha Allah, har sun taso kenan? To Allah ya kawo su lafiya, sai sun zo ɗin." Jinjina kai yayi da farin ciki da kuma son ya ce shima yana buƙatar fura, amma kuma sai ya ƙyale kawai saboda gudun rigima, Mama ma barka ta mishi da fatan su iso lafiya sannan suka fice. Tana raka Mama ta koma ɓangaren ta ta shiga aiki ba ɓata lokaci, abinda ya shafi gashi da soyawa kawai tayi sai lemu da ta haɗa na zoɓo da cucumber, kafin azahar ta kammala komai dan Kuwailat ma da ta taso ta taya ta aikin, hakan yasa sukayi saurin ƙarasawa sannan suka shirya sukayi sallah. Tana kan sallaya aka yi sallama ƙofar ɗakin, Kuwailat da ta riga ta ida wa ta amsa tare da nufa dan ta gane muryar mai gadi ce, jim kaɗan ta dawo da ledaa hannun ta ta aje gaban Maman ta tace "Mamie, Idi ne ya ce wai Abba ya ce ki dama mishi furar nan yanzu." Da kulawa ta amsa da "To, ɗauko min tasar da nake damu da ita." Ba ta zauna ba ta wuce madafar dan ɗauko abinda ta aike ta, jim kaɗan ta kawo ma ta tasar da ludayi ta aje, juyawa tayi ta sake ɗauko ruwa da zuma ta aje, a tsanake ta shiga damun furrar nan har ta kammala sannan ta kai fridge tare da kama hanyar ɗakin ta dan ta canza kayan ta kafin nan furar tayi sanyi ko kaɗan ne sai ta kai mishi. Kuwailat ce ta fara jin odar mota, da sauri ta miƙe tsaye da zumuɗi da kuma fara'a a fuskar ta tace "Lahh! Ga su Yaya nan." Da gudu ta tunkari ƙofa za ta fita, hakan yasa jigidar dake ƙugun ta kaɗawa sosai tana bayar da sautin cacas cacas, da mugun sauri Ummu da ta ji haka saboda yadda ta yi wayo ta ga jigida a ƙugun ta da na Nabila to ta a ganin ta kamar jigida kwalliya ce da take cika adon cikakkiyar mace, dan haka Kuwailat na fara zama ta fara saka mata, ba dan ma Nabila da duniyanci ya sa ta cire ama ta ce tana saka wa ba kullum ba dai. Da sauri ta katse ta da "Ke dakata." Dakatawa tayi tana kallon ta da tunanin to me ta yi kuma? Cike da gargaɗi tace mata "Kina mace kina gudu kamar tsuntsuwa, malama tafi a hankali." A ladabce ta amsa da "To Mamie." Sai kuma ta ƙarasa fita da sauri fuskar ta fal da murmushi na za ta ga Yayun ta biyu wanda Jabir har yau ba ta san shi ma ba ɗan gidan nan bane dan ba wanda ya faɗa mata. Ummu kuma shigewa tayi ɗaki dan ta canza kayan ta sannan ta fito. *Tana* fita motar su na tsayawa, tsaye tayi ita ma tana ƙurawa motar idanu, Yaya Khamis ne ya fara fitowa bakin shi har kunne yana faɗin "Yau ai saraki kuke, motar ma ni zan buɗe muku." Yana buɗe motar ƙafa Aliyu ya fara zurowa kafin ya fito gaba ɗayan sa fuskar shi fal murmushi yana kallon Khamis cikin wani tattausan harshen da sai ka yi da gaske gane hausar yace "Kai dai ka sani Khamis, ka maida mu wasu Kakanin ka ko?" Idanun Kuwailat tsaf a fuskar shi, mamaki take? Al'ajab take? Farin ciki take? Sai ta rasa me za ta ji game da hakan, ita fa balarabe take gani ya fito daga mota, ana haka kuma sai Jabir da ya fito ta ɗaya ɓangaren ya zagayo inda suke cikin wata sassauƙar shiga ta doguwar riga kalar fara tas, ba hula a kan shi bayan dogon wandon da kake iya gani ta ƙasan ƙafafun shi da kuma wasu lafiyayyun takalmi ƙirar Turkey da suka fito da kan yatsan shi ɗaya, sai agogo kawai irin ta fata baƙa da ta kama tsintsiyar hannun nashi. Ƙara sake bakin ta tayi tana ayyana _"Dukansu larabawa ne."_ Da gaskiyar Kuwailat, dan kuwa dukansu jajir da su basu da maraba da larabawan, babu wanda bai gane ta ba a cikin su, dan hoton Kuwailat ne ma a profil ɗin Alhaji kasancewar ta auta kuma yarinyar da yake so ƙwarai a cikin yaran shi, dan haka suka gane ta musamman ma Jabir dake jinjina girman yarinyar da kuma hango irin tarbiyar da ta samu duba da hoton da Alhaji ya ɗora tana sanye da hijab, yanzu ma gata da hijab à jikin ta duk da bai ga wani abu ba a jikin ta da yake kyautata zaton shi take ɓoyewa. Aliyu ne ya fara matsawa kusan ta tare da dafa kanta yace "Autan Abbanmu, ashe kin fi girma a zahiri?" Cike da kunya Kuwailat ta rufe fuskar ta da hijabi, wanda hakan da tayi ya sa Jabir tsurawa *bakin ta* idanu yana ganin kamannin mahaifiyar ta a fuskar ta sak, ba wanda ya tanka masa, ba wanda ya saka shi dariya, sai kawai tsintar kan shi da yayi da yin murmushi saboda kawai murmushin da Kuwailat tayi mai cike da kunya da nutsuwa, Aliy ma dariya yayi tare da dafa kafaɗar ta ya juya da ita zuwa ɓangaren mahaifiyar shi yna faɗin "Kina lafiya autanmu?" Sauke hannayen ta tayi tace "Lafiya lau Yaya, an zo lafiya?" Amsawa yayi da "Lafiya lau, ya jikin Abba? Yana wurin Mama ko?" Ɗaga kai tayi ta dube shi sannan tace "Lafiya lau, jikin shi ma yayi dama." Khamis dake janye da jakunkunansu cike da tsokana yace "Kuwailat baki gaishe da *Alaramma Jabir* ba kinga fa sai kumbura yake." Da sauri Kuwailat ta ja birki tare da juyowa ta kalle Khamis da yayi maganar, a hankali ta cira duban ta zuwa ga Jabir ɗin da ya bita da wani narkakken kallon da bai san ma ya mata shi ba, dan maganar da Khamis yayi tasa ya ji kamar wata kunya kunya da kuma farin ciki, abun nan dai da yake birge shi sosai a tare da ita ko ya ce abinda ke saka shi jin yana ƙaunar duk mai hali irin wannan wato kunya ta kalle shi tare da yin murmushi cikin wata tattausan murya tace "Yaya Jabir, an zo lafiya? Ba ka yi fushi ba ko?" Wani nagartaccen murmushi ya sakar mata, matsawa daf da shi Kuwailat tayi da burin shima ya shafa kanta kamar yadda Yayan ta Aliyu ya yi, amma kuma Jabir sai bai yi haka ba, hasalima gaba yayi ya bar ta a bayan cike da shan ƙamshi ya amsa da" Ban yi ba." Ba zai iya taɓa jikin ta ba, ba wai dan ba uwa ɗaya suke ba kuma ba su haɗa uba ba, kawai dai ba zai iya bane saboda... Bai gama tantancewa ba, amma dai yana jin kamar zai iya sakawa Alhaji da duk abinda ya mishi ta hanyar ɗaukar ragamar kula da ɗaya daga cikin yaran shi har ya mayar da ita gimbiyar da za'a dinga kwatance da ita a fannin kulawar da take samu daga gurin *shi*, a sanin shi kuma babu wata budurwa mace yanzu da ta rage a gidan nan sai Kuwailat kawai, dan haka yana hango yiwuwar ƙulluwar wata kyakyawar dawamammiyar alaƙa tsakanin su, dan haka zai fara kiyayewa tare da aika mata saƙo a sirrance har lokacin da za ta zama *mace*. Turo baki Kuwailat tayi, sai kawai ta ga bari ita ta riƙe hannun Yayan ta, ita fa auta ce, ko ya manta? Da irin gudu gudun nan mai kama da tafiya Kuwailat ta cimma Yayun nata dake jere sun durfafi sashen Hajia Asiya, kafin ta isa Jabir kunnuwan shi suka jiyo mishi sautin da ya saka gaban shi ya yanke ya faɗi gaba ɗaya, tsigar jikin shi ta tashi, hankali ya yi sama shima tare da hauhawar nashi jinin, ba komai ya kawo haka ba sai tuna wata rana, tuna waccen lokacin da ya ji irin wannan sautin daga ƙugun mahaifiyar yarinyar da yake da tabbacin ita ce ta taho a guje haka. Ya Allah! Hasbunallah wani'imal wakil ! Daga zuwan shi? Wa ya turo ta? Me take nufi? Me take nufi da ta riƙe tafin hannun shi sannan ta tausasa murya tace "Yaya Jabir, hushi kake dani dan ban gaishe ka da wuri ba? Kayi haƙuri to, ka yafe min dan Allah." Sai ka ce wanda ya haɗiyi mugun abu, da tsananin ƙarfi ya feso wani irin numfashi da ya tokare mishi ƙirji, lumshe idanu yayi ya kasa bata amsa, dan gaba ɗaya lamarin ya fi mishi kma da irin a farmake kan nan daga zuwan ka wuri. Aliyu da ya san mutumin nashi tsaf ya dawo baya dan yana jin abinda Kuwailat ɗin ke faɗa, kama hannun ta yayi da rarrashi yace "Kin san me ? Yunwa ce yake ji, kinsan Yayan naki da rashin juriyar yunwa, da kin bashi abinci ya ci yanzu zai fara ƙiriniya." Kallon Aliyu tayi da kyau tace "Kenan yanzu na kawo mishi abinci?" Ɗaga mata kai yayi yace "Sosai ma, maza ki kawo mishi." Sakin hannun Jabir tayi da sauri ta juya ta nufi nasu sashen dan a can ta san abincin da zasu ci yake. Satar kallon Aliyu yayi da ya taimake shi matuƙa, ƙwarai baya juriyar yunwa dan idan ta fara gasa shi fita hayyacin shi yake, sai kuma ya galabaita ta hanyar tuna zamanin da yake fafutuka dan abinci kawai, shiyasa indai yana da yadda zai yi ba ya yarda yunwa ta fara galabaitar da shi har ya kai ga tuna tarihinshi da ya wuce. Rankayawa sukayi zuwa cikin ɗakin da sallama, nan fa suka samu dayawa da suka amsa musu dan kuwa kaf ƴaƴan Hajia Asiya suna zaune falon har ma da wasu daga cikin yaran Hajia Atika, farin ciki ne ya kaure na haɗuwa da ƴan uwan su da aka kwashe shekaru, wasu ba dan yanar gizo ba da ba zasu iya shaida Aliyu ba, dan tun yana yaro ya tafi kuma sau ɗaya ya zo hutu bai sake dawowa ba sai yau ɗin nan. *Gobe week-end in sha Allah, ba zaku samu posting ba saboda ina so na yi dogon pages na turo ranar Litinin in sha Allah. Luv u guys😍* *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *35* Daf da la'asar taxi ta aje ta ƙofar gidan, ko jakar ta bata ɗauko ba ta kalli mai taxin tace "Jira na fito sai na biya ka." Da irin tsiwar nan ta wasu mutane mai taxin yace "Ke ma dai haka ake? Ai da tun a can zaki faɗa min ko." Cike da bala'i da masifa da tsohuwar yunwa da take ji tace "Ka ga malam kar ka gaya min ba daɗi, ba cewa nayi ba zan biya ka, kai da ganin gidan da ka kawoni kasan ni ba matsiyaci bace, sarakuwar Saheeb kenan." Cike da shaƙiyanci mai taxin ya kalli ƙasan ƙafafun Nabila, takalmin ta ƙafa ciki baƙake da sarƙar ƙafa ya fara cin karo, sai ɗamamen wando fari da kuma doguwar riga irin ta yadi shara-shara wacce aka yanke tsakiyar ta ɗaga gefe, hakan yasa dole ake saka mata dogon wando daga ciki, kallabi ne a kan ta ta mishi irin ɗaurin Zahra Buhari, sai kitson gashin dokin ta da ta zuba shi har kan gadon bayan ta, fuskar ta kuma babu kwalliya sai gashin ido da ta maka da kuma wata kyakyawar ƙaramar sarƙar hanci, dan kyau da tsari tana da shi, sai dai shi marar tarbiyya yake kallo a gaban shi, dan haka ya taɓe baki yace "A haka ɗin? Amma dai ke baƙuwar sanin Ahalin Ahlan ce ko?" Cikin hargagi ta nuna shi da yatsa yace "Kai, in bamu ci buru'uban juna ba Allah tsinen, waye kai? Me kake ji da shi da zaka min wannan tambayar? Har da wani ƙare min kallo, to bari ka ji wallahi na gayawa Fahad ka kalle ni sa da ƙasa idan bai ƙwaƙule idanun ka ba shegiya nake..." Wannan hayaniyar ta fito da mai gadin dake da ya hau aiki safiya yau a ƙofar ta farko, yana ganin abinda ke faruwa ya ƙaraso yana faɗin" Assalama alaikum, dan Allah lafiya? Me yake faruwa ne?" Kallon mutumin Nabila tayi, duk da kakin soja ne jikin shi amma ko à jikin ta, dan sojawa ma ai mutanen ta ne wanda ba dan ta ƙi basu haɗin kai ba da tuni sai yadda ta yi a ƙasar nan tace" Ba komai malam, kai kuma wa ye?" Ɗan taxin ne ya fito daga ciki yana faɗin" Ba komai bane malam, ka barni da wannan yarinyar ka ga yadda zan yi da ita..." Sai kuma ya kalli Nabila yace" Bani kuɗina malama?" Cike da gadara ta kalle shi ita ma tana dafe ƙugu tace" Nayi niyyar biyan ka, amma da kake son faɗawa wannan cewa kai akwai yadda zaka iya yi da ni, to so nake naga yadda zaka yi dani ɗin, ba zan biya ka." Gyara tsayuwa yayi cike da masifa yace" Ke baki isa ba, ƙaramar ƴar iska ce ke walahi, idan kika ji inda nayi nawa iskancin suma za ki yi, dan haka in kinga na matsa daga nan to kuɗina kika bani." Cikin hargagi Nabila tace" Suma? Kai nan har ɗan iska ne? Ni kake buɗewa ido kuma kake so na ji tsoron ka? Wace kalar ƙwaya kake sha? Wani kalar hayaƙi ne a cikin kan ka da kake tunanin babu shi a nawa? To mu zuba mu gani ni da kai, na rantse da Allah ruwan randa ma kawai zan sha wallahi na farka cikin ka na yago duk wani abu dake ajiye a cikin naka." Cikin tashin hankali jami'in nan nan dake ganin abinda bai taɓa gani ba yace" Ku dakata dan Allah, ai matsalar dai ta kuɗi ce ko? To ina zuwa..." Aljihun shi ya fara laluba dan ya raba masifar su gaggauta barin ƙofar gidan nan, dan abu biyu ne ya zo mishi à tunanin shi, na farko in ma faɗan ne da gaske? Ko kuma dai wani laifin za su aikata a gidan suke son ɗauke hankalin su jama'an, ciro kuɗin yayi ya kalli mai taxin yace "Nawa ne kuɗin?" Kafin ɗan taxin ya bashi amsa Nabila tayi caraf da walet ɗin jami'in tana faɗin "Billahillazi ba zaka biya shi ba, kai dakata ka gani..." Rigar wayar ta ta cire daga wayar, sau ga kuɗi a ciki wanda tayi guzuri da su, nuna ma jami'in tayi tace "Ka gani, ba wai kuɗin ne bani da ba, da na zo ce mishi nayi ya jira ya fito, niyya ta in amso kuɗin a wurin wanda ya sa ni zuwa garin nan sannan in bashi, amma ɗan rainin hankali ya gaya min magana, shiyasa na ce ba zan biya ba, yayi yadda zai yi da ni dan Allah, kai ma kuma ka cire hannun ka, in ba haka ba wallahi zan kirta maka naka daidai gwargado." Sabuwar rigima ce ta sake kaurewa a gurin, shi jami'in burin shi ya karɓi lalitar shi da ya ga ta riƙe gam, dama ƙarfin hali ne zai yi ya biya kuɗin shi dai dan su bar ƙofar gidan nan, amma a yadda wata yayi nisa ɗin nan dole yake tattala komai, ba dan ma ubannin gidan nashi masu kyauta da tausayi bane? Ai da sua ganin rayuwa, shiyasa ba ya nadamar aiki a ƙarƙashin su. Suna tsaka da wannan hayaniya har jami'i na biyu dake ƙofa ta biyu ya ga abinda ke faruwa ta ƙaramar kamara dake gurin, yayi tunanin ba lafiya ba dan haka ya fito shima, sai dai ɗaya jami'in na cikin faɗa mishi abinda ke faruwa motar Yaya Bilal ta sulalo tamkar kifi dan ko sautin ta baka cika ji ba ta dakata ƙofar gidan. Tun daga cikin mota ya kula rigima ce a ke, amma shi saɓanin jami'an tunanin da ya yi na farko shine _Ko dai ta bugu dayawa ta rasa ina ma za'a kai ta_, _ko kuma dai bata da kuɗin taxin kua shi matuƙin ya fahimci haka shiyasa ya direta ƙofar gidan su_, dan kuwa shi dai ya ga yarinyar babu tarbiya, duk da shigar ta a wannan zamani akwai matasan da suka ɗauka ita ce wayewa, amma dai yasan duk wacce ta samu ginshiƙi mai kyau to ba zata yi haka ba, da ladabi jami'an suka gaishe shi inda ɗaya ya ɗora da "Yallaɓai, kar wannan ya dame ka, ka shiga ciki dan Allah zamu yi maganin matsalar." Cikin taushin muryar da dattako ya dube su yace "Me yake faruwa ne?" Kallon Nabila ta sake yi sosai da niyyar tambayar to shi ma wanene wai? Da kowa ya zo zai yi ta tambayar me ke faruwa? Su basu ga abinda ke faruwa bane? Amma kuma sai wani irin kwarjinin mutumin ya lulluɓeta, sahihiyar fuskar kamalar shi, da shigar shi sun fi ƙarfin ta masa rashin kunya, dan alamun shi basu yi kama da na wanda zai ɗauki raini daga gare ta ba, basa kama da Fahad, dan wannan duhun fata gare shi sannan yana da ƙiba, amma kuma ko da babu kama ta fuska akwai kama ta yanayi sosai tsakanin su, ƙwarai da gaske zubin shi irin na Fahad ne, yatsun ƙafa da na hannu da muryar shi, gashi yadda yayi tsaye dandanan ya dafe ƙugu da hannun dama yadda Fahad ke yi ya ƙara fito da suffar su. To ko shine Saheeb Ahlan ɗin ? Amma kuma wannan? Yadda Fahad ke faɗa mata ai ba shi kaɗai bane ya haifa, yana da yayu maza da mata fa, bai kamata a ce wannan shi kaɗai ba shine Saheeb. Girgiza kai Yaya Bilal yayi cike da takaici sanda wani jami'in ya sanar da shi abinda ke faruwa ɗin, aljihunan shi ya laluba, sai kuma ya duba gaban rigar shi dan baya son taɓa kuɗin da ke wasu aljihunan sakamakon dawowar da yayi Fa'iza zai kai siyayya na kayan baby da matar Yayan ta ta haihu, daga can kuma zai wuce wani muhimmin uzuri shi ma, jakar biyar ba ko canji ya ciro ya miƙa ma mai taxin yace "Karɓi nan, je ka dan Allah." Da sauri ya karɓa yace "Canjin fa?" Cikin yatsina fuska Yaya Bilal yace "Barshi kawai, tafi kai dai." Da sauri zagaya ya ciro akwatin ta ƙarama ya aje mata gaban ta sannan ya shiga taxin shi ya tayar ya bar ƙofar gidan, cikin bala'i Nabila ke kallon taxin tana faɗin "Ka yi asara wallahi, dama irin ku kuna yin hakane dan kun san akwai masu zuciyar imani da zasu iya biyan ku har da ƙari, banza ɗan daudu mai faɗa da mata, ka yi sa'a bana dambe da ƴan daudu irin ka, da tuni wani zancen ake ba wannan ba, dan jinsina ya fi naka ƙarko." Saida ta gama wannan zazzaga suna haɗa idanu da Yaya Bilal ta ga ashe ita yake kallo, cikin dattako yace mata" Shikenan ya isa, ɗauki jakar ki tafi gida ki huta." Yana faɗin haka ya juya ya koma ga motar shi, masu gadin ma da sauri kowa yayi bakin ƙofa dan buɗe mishi, madadin su ga tayi wani wurin janye da jakar ta, sai suka ga ta ja jakar tana neman shiga ta ƙaramar ƙofa, Yaya Bilal ma da ya ga haka tunanin kenan dai bala'in bai ƙare ba yayi, dan haka ya sake fitowa daga motar tare da yi ma jami'in alama kar ya buɗe babbar ƙofar kawai zai wuce ma ta ƙarama, Nabila dake ta ƙoƙarin kutsa kai ya haɗe ma fuska yace "Wai ke lafiya? Dan Allah ki bar nan wurin, ko so kike na rasa aikina ne?" Hararan shi tayi tace "Kaga dai ina jin kunyar ka, kar kasa mu raba hali da kai yanzu." Yaya Bila da ya ƙaraso ne yace "Ina zaki je nan ? Kinsan wani ne a gidan?" Wani murmushi tayi tace "Allah sarki, ko dai kaine Abbun Fahad? Ina wuni Abba?" Jin ta ambaci Fahad y sa ya haɗe fuska, dan zai iya ceda ya fara gano inda matsalar take, fuska a haɗe yace "Kin san shi ne? Me ye tsakanin ki da shi? Wacece ke?" Tambayoyin nashi kama suka mata da na rainin hankali, amma kuma kwarjini ba ya bata damar cizga shi ko kaɗan, dan haka ta tausasa murya fuskar ta a gimtse tace "Sunana Nabila, ni budurwar Fahad ce, kuma wacce zai aura." Da mamakin dama wannan ita ce Nabila ya kafeta da idanu, dan samun tabbaci ya nuna ta da yatsa yace "Ke f de Beela?" Murmushi tayi wai da jin kunya tace "Ni ce Abba." Wani irin murmushi yayi da shi kanshi bai san na menene ba, muskutawa yayi yana kallon ta yace "Ba ni ne Abbu ba, Yayan sa ne ni, yanzu me ya kawo ki? Na ɗauka Maraɗi kike?" Murmushi tayi tace "E hakane Yayan mu, wurin shi na zo ai, yana nan ne?" Girgiza kai yayi yace "Ban sani ba, amma dai na bar shi gida yana kwana." Ƙara jan jakar ta tayi tace "To shikenan, bari in shiga ciki." Da azama jami'in ya sake niyyar tare ta, amma sai Yaya Bilal ya mishi alamar ya bar ta, dan idan suka ce zasu hana ta wata masifar ce kuma, gyara ta shiga idan ya so shi ya kwatanta mata a tsanake cewa Fahad ɗin nan shirin su a kan shi shine yau za su je nema mishi auren Fati, idan har kawu Abbas ya amince to fa yadda Alhaji ya ce shine a sati ɗaya za'a ɗaura musu aure, dan haka zai fi kyau ta haƙura da Fahad. Ko motar bai waiwaya ba ya bita ciki har zuwa falon Hajia ind anan ɗakin Fahad ɗin yake, Mama Nuriyya na zaune tare da Hajia tana shafa mata maganin ciwon ƙafafu suna ƴar hirar su Yaya Bilal ya shigo Nabila na bayan shi tana ta rarako idanu tana kallon irin daular da Fahad ke ciki, amma shine ya zaɓe ta ita da ta rayu a filin *share zauna*, a ganin ta kamar basu dace ba, amma soyayya ba ta da haka ai, saï dai kuma ta tabbatar da Fahad bai da hankali tunda har ya girma a nan amma yake rayuwa da ita a wannan ƙaramin gida, duk da shima gidan ɗaya ne daga cikin mallakar mahaifin shi, amma ai ko ganin shi ba za'a yi ba idan aka ga wannan. Mama Nuriyya da Hajia baƙuwar fuskar suka ƙurawa idanu, har suka matsa kusa da su kafin Yaya Bilal ya gaishe da Hajia Mama Nuriyya ma ta mishi sannu da zuwa, ɗorawa yayi da "Mamie ina Fahad?" Da mamaki ta sake kallon shi, kuma sai gaban ta ya faɗi saboda tunanin ko yarinyar na da alaƙa da neman da yake ma Fahad ɗin? A tausashe tace "Fahad yana ciki, ina jin bacci yake, amma lafiya kake neman shi?" Numfashi ya sauke tare da juyawa ya kalli Nabila sannan yace "Wannan ita ce Nabila, ita ke neman shi." Da sauri Hajia ta tashi tsaye saboda wani irin fargaba na zulumin idan fa Alhaji ya same ta gidan nan za'a yi ɓatacciya, kallon Nabila tayi da ta sunkuyar da kai dan ta fahimci ita ce surukar ta ta, cikin taushin murya Hajia tace" Me yasa kika zo nan? Jiya jiya ne shima ya zo, shine kika biyo shi?" Kallon ta Nabila tayi da girmamawa tace" Ba haka bane Mama, na zo ina so na gan shi, akwai wata matsala ne." "Wace irin matsala ce da za ta sa ki biyo saurayi har gidan su?" Cewar Hajia tana kafe ta da kallon tuhuma, shiru Nabila tayi dan ba zata iya faɗa musu abinda ya kawo ta ba, dan haka Hajia ta sake haɗe fuska sosai tace "Ki gaggauta barin nan, bana so mahaifin shi ya same ki gidan nan, dan ranki zai ɓace." Cikin ladabi da tausa murya Nabila ta dube ta tace "Kiyi haƙuri Hajia dan Allah ku bani damar ganin shi, da zaran na sanar da shi abinda ya kawo ni zan tafi, dan ban taɓa zuwa nan ba kuma ban san kowa ba." Gaban Hajia ne ya ƙara faɗuwa, abu ɗaya ya zo mata duba da yadda ta tirje tana son ganin shi, dan hka ta kalli Nabila a gigice tace" *Ciki* ne dake yarinya?" Zaro idanu Nabila tayi ta kalle ta, sai kuma tayi murmushi tana gyara tsayuwa cike da kunya tace" Ah haba dai Mama, ai ba zamu yarda muyi ciki, ina shan magani kuma shima yana kulawa ta hanyar anfani da kor..." Mama Nuriyya dake ma Nabila kallon kamar ƴar da ta haifa tunda tana da ƴan mata ne tayi saurin daka mata tsawa da" Ke? Wa ya tambaye ki?" Hajia da ta kyaɓe fuska alamar za ta yi kuka Yaya Bilal ta kalla tace" Dan Allah kira shi a waya ya fitar min da ita daga gida." Da ladabi ya jinjina kai ya ciro waya ya kira lambar Fahad ɗin, ta jima tana ƙara saida ta kusa tsinkewa ya ɗaga, a taƙaice ya ce da shi" Ka sauko ƙasa kana da baƙuwa." Da tsananin mamaki Fahad dake sharar bacci yace" Baƙuwa kuma? Daga ina? Wacece? Ko dai baƙo?" Saida ya saci kallon Nabila sannan yace" Nabila ce." "Nabila?" Ya faɗa da ƙarfin gaske tare da zabura ya tashi zaune yana sake maimaita "Beelata dai?" Kafin ma a bashi amsa ya yanke kiran ya taso daga shi sai wando tree quater ya sauko daga saman, tunda ya fara tako matakala Nabila ke kallon tana murmushi har ya zo tsakiyar su yana kallon ta shi mamaki ne yake kashe shi na yadda ta zo bata sanar da shi ba. Duk zuba musu idanu sukayi, Nabila kuma da fara'a tana kallon shi tace "Barka jariri." Satar kallon Yaya Bilal yayi da shi mamaki ne suke bashi, Fahad kuma farin cikin shi ɗaya ba Abbu Mukhtar bane da zai dinga mishi kallon da shi da kan shi zai ji kamar yayi fatan mutuwa, Sabeer kuma, da shine ai da tuni ya kashe shi da mari, Beela kuma da tuni ya karya mata ƙafa ya watsar à ƙofar gida, cikin raɗa yace mata "Me ya kwo ki nan Beela? Ya zaki zo gidan mu kai tsaye? Baki san akwai kuraye bane?" Saida ta kalli Hajia da Yaya Bilal sannan tace "To nima ba kurayen na baro can ba, kuma kasan da su ai, magana na zo muyi sannan na fito da kai daga kurkukun da aka saka ka." Juyawa yayi ya kalli Hajia, sai kawai ya kalli Nabila ya ɗan yi gaba yace "Muje waje za mu yi magana." Ɗaukar jakar ta tayi tare da kallon su dukan su tace "Sai anjiman ku." Sai kuma ta kalli Hajia ita kaɗai da duk tayi kamar bata hayyacin ta tana kallon su tace "Mama dan Allah kiyi haƙuri idan na ɓata miki rai." Tana faɗa ta bi bayan Fahad suka fita farfajiyar, Yaya Bilal na ganin fitar su ya zaunar da Hajia yace "Mamie, dan Allah kar hakan ya ɗaga miki hankali, zan ɗauki mataki akan abun nan, ki masa addu'a kawai." Bai jira Cewar ta ba ya fita shi ma dan uzurin gaban shi, Mama Nuriyya ce ta zauna kusa da ita tana rarrashi. Fahad kuma suna fita ya dafe ƙugu cike da masifa ya fara faɗin" Nabila da uban wa muka yi da ke zaki zo nan? Tunda muke na taɓa zuwa gidan ku kai tsaye haka? Ya zaki ja min wata jarabar?" Tsaki tayi da irin abun bai dame ta ba ta zauna kan akwatin ta tace" Ka ga dan Allah samo min abinci na ci, wallahi yunwa nake ji kamar masifa, ban ci komai ba tun jiya." Harara ya maka mata sannan ya juya a fusace ya koma falon, yana shiga duk da ya gan su zaune bai kula kowa ba ya wuce madafa, jim kaɗan ya dawo ɗauke da flate shaƙe da lafiyayyan abun ci, yana zuwa ya miƙa mata, kallon hannun ta tayi da tasan yana buƙatar ta fara wankewa, amma dake ba ruwa kusa sai kawai ta kawo wandon Fahad dake jikin shi ta goge hannun sannan ta saka ta fara ci tana faɗin "Jariri, ashe à wannan fadar kake rayuwa? Gaskiya ku masu kuɗi sosai, shine dan munafunci ka kasa mayar da ni sarauniya kake yafata min canji kawai." Cike da takaici da fargaban zuwan Abbu Mukhtar ko Sabeer dan shi su kaɗai yake shakka yace "Nabila, me ya kawo ki?" Kallon shi tayi tace "Na gaya maka ai." Jinjina kai yai yace "Shikenan, yanzu ki je ki samu taxi ki ce ya kai ki duk hôtel ɗin da ya sani, idan kin sauka zan kira ki faɗa min zan je na same ki can." Saida ta juya mishi baki sannan tace "Ban da kuɗi, kuma ina so na je salon ma, wannan kitson ya ishe ni." Wani huci ya sauke yace "Nima ban da kuɗin." Sama da ƙasa ta kalle shi tace "Ƙarya kake, ai na daina yarda da kai yanzu wallahi idan ka ce baka da kuɗi tunda na ga gidan ku." Saida ya sake maka mata harara yace "Shikenan, bari na samo miki wajen Hajia, amma fa ni bana da kuɗi, ai kinsan ba neman su nake, dayawa da nake kashe miki satar su nake yi, haram ce kike ci." Juyawa yayi a sukwane, cike da shaƙiyanci tace "Nake ci? Kake ci dai, kuɗin da kake bani ina ci nima ba ci na kake ba, ka ji ƙaramar ɗan iska kai." Juyowa yayi ya harare ya ja tsaki yace "Ƴar wahala." Sama da ƙasa ta harare ita ma tace "Wahalallu dai." Ta faɗa tana ci gaba da cin abincin ta dake ɗauke da nama kuma gashi ya mata daɗi sosai. *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *36* Yana shig falo kusa da Hajia ya zauna cikin rarrashi saboda kallon tuhuma da take mishi yace "Mamie, dan Allah ki bani wasu ƴan kuɗi zan ba yarinyar can ne ta tafi, ni ban da ko sisi a jikina." Kamar za ta fashe da kuka tace "Fahad, yanzu wannan rayuwar ka ga tana gyara ka ko? Yanzu idan mahaifin ka ya same ta gidan nan fa? Ba kai ba har ni ba zan ji daɗi ba." A tausashe yace "Mamie ai shiyasa nake so na sallame ta ta tafi kafin ya shigo." Gaskiya ya faɗa, dan haka tace mishi "Je ka ɗakina ka ɗauko min jaka ta akan gado?" Da farin cikin samun yadda yake so ya tashi ya nufi ɗakin, Mama Nuriyya dai na kallon su bata tanka musu ba, saida ya dawo da jakar sannan ya bata, kuɗin ta ciro isashi ta bashi, da fara'a ya karɓa yace "Nagode Mamie." Da sauri ya sake fita daga falon, yana zuwa ya same ta tana cin abincin, karɓe farantin yayi ya bata kuɗin yace "Karɓi, maza dan Allah tashi ki tafi Nabila, bana so Abbu ya shigo ya same ki, idan kin isa ki kira ni zan zo." Miƙewa tayi tana hararren shi tace "Ka ji haushi Fahad, ni kake ma rowan abincin gidan ku, kai arrr wallahi." Bai kula ta ba saboda kuɗin da ta karɓa tana dubawa, murmushi tayi ta saka su cikin bras ɗin ta sannan ta ja jakar ta tna faɗin "Jariri sai ka zo, nayi kewar ka fa." Har ta ɗan wuce sai kuma ta juyo ta dawo, da mamaki yake duban ta har ta zo kusa da shi, bai ankara ba kawai ya ji hannun ta a dokin shi bakin ta kuma cikin nashi baki, kamar wata mayunwaciya cike da shaƙiyanci ta kamo harshen shi ta tsotsa kamar za ta cire mishi baki tana murza dokin shi sannan ta sake shi ta mishi murmushi, ɗaga mishi gira tayi sannan ta koma ta ja jakar ta ta tafi. Kallon ta yake yana lashe leɓe, ta tsokano shi, ji yake kamar... Cike da shegantaka ya sake lashe baki yace "Wow! Shegiya Nabila." Saida ya ga ta fita daga ƙofa ta biyu ya sauke ajiyar zuciya, yana juyawa dan komawa ya sauke duban shi kan Mama Nuriyya da ta ga komai, suna haɗa idanu kawai ta kawar da kan ta tare da saurin nufa nata ɓangaren tana mishi addu'ar shiriya, Fahad kuma ko a jikin shi sai ma shigewa falon da ya yi, duk da ya ga Hajia zaune tayi tagumi bai tsaya wajen ta ba ya haura sama dan ya shirya kafin Nabila ta kira ta faɗa mishi masaukin da ta samu. ******************* Tun daga nesa Ummu da ta taho take jiyo hayaniyar dake tashi daga falo, tun kafin ta shiga ta gayyato murmushi a fuskar ta sannan ta cire takalmin ta, cikin sanyayyar murya ta rangaɗa sallama, daga ciki suka amsa mata sannan ta shiga ɗauke da kyakyawar tasar furar nan, kallon duk mutanen ɗakin tayi da fara'a à fuskar ta tace "Sannun ku da hira, kuna ta shan hira abun ku?" Wasu da murmushi a fuskar su suka amsa mata, yayin da wasu ba yabo ba fallasa suke kallon ta basu tanka ba, saida ta ƙarasa tsakiyar falon ta tsaya kusa da kujerar da Alhaji yake zaune, saida ta rusuna ta zauna sannan ta aje tasar ta ɗaga kai dan duban Alhajin, ido biyu suka haɗa da Jabir dake kusa da Alhaji yana riƙe da hannun shi sai murzawa yake kamar mai mishi tausa, murmushi ta sake faɗaɗawa har haƙorin makkar ta suka bayyana guda biyu tace "Sannun ku da zuwa.?" Cikin taushin murya da kuma girmamawa ya sauke idanun shi ƙasa yace "Ina wuni Maama?" Da fara'a ta amsa da "Lafiya ƙalau, ya hanya?" Kafin ya bata amsa Aliyu ma dke murmushi yace "Auntynmu mun same ku lafiya?" Kallon shi tayi shima yana gefe ɗaya na Alhajin ta amsa da "Lafiya lau Yaya Aliyu, an zo lafiya?" Masu yin Ummu ne a ɗakin suka fashe da dariya har da Alhaji dake faɗin "Ka ji wani shirme a gurin uwar autata, ɗan naki kike kira da Yaya kuma?" Dariya Aliyu ma yayi yace "Abba ai haka take faɗa, dama nace sai na zo zaka mana tsakani." Ummu da kunya ta kamata ne ta rufe fuska da hijabin ta mai hannaye, Jabir dake kallon me ke faruwa a ran shi ya ayyana _"Daga uwa ta gari ta koyi kunya."_ Buɗe fuskar ta tayi ta kalli Alhaji tace" Ga furar nan." Tana faɗa kuma sai ta miƙe tana faɗin" A kawo musu abincin ne?" Kallon ta Alhaji yayi yace "Ki tambaye su." Kafin ta tambaye su Aliyu yace "Ai autar Abba ma ta je ta kawowa wannan acicin da ba ya juriyar yunwa, ban san ya aka yi ta jima ba?" Da mamaki ta kalli Aliyu bayan kallon Jabir da tayi tace "Kar dai motsin ta na ji a madafa?" Jinjina mata kai yyi yce "Ƙwarai." Yunƙurawa tayi ta miƙe tana cewa "Bari na duba ta kar ta min ba daidai ba." Ta y tako huɗu zuwa biyar a falon Hajia Asiya da ke zaune tuntini tana ta hararen Ummu ta gyara zama cike da jin an mata ba daidai ba tace "Kenan da furar da abinci duk ke kika gyara?" Tsayawa Ummu tayi ta kalle ta tace "E Hajia." A daƙile ta amsa da "Ya yi kyau." Sai kuma ta kalli Alhaji tace "Na ɗauka aikina ne, sannan yarona ne zai zo, na sa ƴan uwan sa sun mishi girki, ya zamuyi kenan? Na ƴar gold ka zaɓa masa ya ci saboda mu ba mu iya ba?" Dafe gaban goshi Alhaji ya yi, me ye na wannan maganar a gaban yara? Ita sam abun faɗa da tsegumi ba ya mata kaɗan? Kuma ka san à inda zaka yi maganar mana, shikenan ko ina ma sai ka saki baki? Kallon ta yayi dan kar maganar tayi tsayi yace" Shikenan, ki basu wanda kika dafa ɗin." Sai kuma ya kalli Ummu yace" Maman Kuwailat k...." Da sauri Ummu da abin ya ƙuna mata rai sosai har idanun ta sun cika da hawaye tace" Shikenan Alhaji, a rayuwar nan dai ai ba'a rasa maciya abinci." Tana faɗin haka ta juya ta bar falon, da kallo duk suka bita musamman da Hajia Asiya ta harare ta tace" Munafurcin banza, haka kullum kike nuna ke ta Allah ce ai." Tunda aka fara maganar nan kan Aliyu ke ƙasa haka ma Jabir, da yana daga cikin ladabin da suka koya a karatun su, Aliyu na cike da wannan takaici ya ji ta ci gaba da faɗin" In gama kashe kudi dan kawai ɗana dana jima ina jiran dawowar shi, sai a wani ce wata wai ta dafa, akan me to? Mu bamu iya bane? Ko guba za mu saka mishi? Ba dan ma an zo mana da baƙo ba, abincin ma ai sai mu bashi a baki." Lumshe idanu Jabir yayi wanda ya ji an koma kan shi kuma, a hankali ya buɗa idanun shi tare da yin tsam ya tashi tsaye yana sakin hannun Alhaji, bai yarda ya saurari kowa ba ya kama hanyar fita dan basu wuri su gana matsayin su na alhali guda, saida ya fice daga falon Khamis ma ya bi bayan shi, hakan yasa ma shi da Khamis din suka nufi wajen Hajia Lubabatu dan gaishe ta. Khamis na fita a bayan Jabir Alhaji ya kalli Hajia Asiya cike da takaici yace "Ke har abada ba ki iya tausa bakin ki ba, me ye haka dan Allah? Kamar wata ƙaramar yarinya ki tsaya kina abu irin haka, me ye wani kwana da girki a wannan shekarun namu? Suna da mahimmanci ne yanzu a rayuwar mu?" Tsaki ya sake ja ya kawar da kan shi yna kallon yaran da ta ci albarkacin su da ya datsa mata maganar da ta fi haka sannan yace" Yadda kike jin Aliyu ya zo gidan ubaan shi, haka Jabir ma nan gidan uban shi ne, Allah ya azurtani da komai na rayuwa, daga ciki har da yara maza da mata, sai dai n ba fi saka tsammanin samun rahamar ubangiji ta dalilin taimakawa yara irin su Jabir, ban rantse miki ba, amma kuma ban ce miki zan yi kaffara ba idan har na ce na fi ganin zallar soyayyar da uba ya kamata ya samu daga gurin yaran da ya haifa a idanun Jabir, wataƙila kema kin ga haka, ko kuma kin gani kin take sani saboda ƙin gaskiya." A hankali ya shiga kiciniyar tashi tsaye, hakan yasa Aliyu miƙewa ya taimaka mishi ya tashi yana jin shi ma rigimar maman shi tasa yake son ci gaba da zama a can, amma ya zai yi? Mahaifiya ce, dole yayi haƙuri da ita. Saida suka fara takawa Alhaji ya sake faɗin "Kar ki sake min irin haka, duk ƙiyayyar ki da Jabir ki nuna mishi ita a bayan idanun shi, amma ban da gaban idanun shi." Ficewa sukayi tare da Aliyu da shima abun bai mishi daɗi ba, saida suka fice ɗaya daga cikin yaran na Hajia Atika tace "Lallai ma, yanzu Abba akan wani bare yake faɗa miki haka? Wannan idan gaban shi ne ai sai ya raina ki." Da rashin sanin abun yi Hajia Asiya tace "Hmmmm!" *Suna* ƴar hirar ƙasar da suka baro da Hajia Luba Kuwailat ta shigo da kwando ɗauke da kwanukan abinci Ummu ta zubo ta ce ta kawo ma Hajia ba sai an mata girkin dare ba kawai, wannan abincin da ta kawo Khamis ya ce a zuba mishi yana jin yunwa, sai kuma ya kalli Jabir yace "Alaramma, a zuba da kai ne? Na ji Yaya na cewa ba ka juriyar yunwa." Kallon Khamis ɗin yayi d wani irin kallo yace "Kusa a buga a jarida mana, naga sai maimaitawa kuke, tabbacin ni mutum ne fa kenan." Dariya Khamis yayi yana kallon Kuwailat dake zuba abincin, inda shima Jabir ke kallon hannayen ta dake da ragowar lallen ta dake daf da zubewa, cikin wata nutsatsiyar murya Jabir dke kallon Kuwailat yace" Zuba da ni." Kallon shi tayi ta saki murmushi tace" To Yaya, ai nasn idan ka ci abincin nan da muka girka ni dq Mamie za ka daina hushi dani." Kallon ta Hajia Luba tayi tace" Subhanallah! Hushi kuma ? Ke da Yyan naki? Daga zuwan shi?" Kallon ta tyi tace" E mana Mama, wai dan ban gaishe shi da wuri bane yake hushi dani." Dariya Hajia tayi tace" Any dai, to amma dai zuba mishi abincin mu gani zai daina hushin ko kuwa." Tana gama zuba musu ta aje gaban su tare da ɗauko cokali, tana dawowa ta samu Jabir zaune dangal dangal ƙasa ya wanke hannun shi ƙofar ɗaki har ya saka ya fara cin abincin da ya saka shi haɗiyar yawu, da mamaki ta kalle shi tace" Lahh ! Yaya, kai baka cin abinci da cokali?" Kallon ta yayi tare da sakin wani tattausan murmushi ya nuna mata tafin hannun ta yace" Me yasa Allah ya mana wannan? Saboda abubuwa dayawa da basu misaltuwa, daga cikin ladubban cin abinci kuma akwai ci da hannu dan ya fi albarka, sannan da tanɗe hannun bayan gama cin abincin, dan haka kar a min dariya idan an ga ina lashe yatsuna." Dariya duk sukayi har da Khamis da yace" Yaya mai wayo, wato ka kare kan ka daga tuhuma tun kafin ka aikata laifin." Ɗaga mishi gira Jabir yayi alamar" E mana." Sauka ci gaba da cin abincin su, suna tsaka da ci Aliyu ma ya shigo suka gaisa da Hajiar, lokacin kuma aka fara kiran sallah la'asar suka nufi masallaci, suna dawowa Jabir ya shirya a ɗakin da aka ware musu shi da Aliyu dan kuwa Aliyu ne ya ce maa Abba a haɗasu ɗaki ɗaya dan sun saba kwana tare, yana gama shiryawa tare da Aliyu da Khamis suka kaa hanyar zuwa gidan mahaifin Jabir dan duba shi. Tiryan-tiryan suka bi kwatancen gidan, suna isowa inda Jabir ke kyautata zato ya fita yana faɗin "Bari na fara dubawa na tabbatar ko nan ɗin ne." Aliyu ma fita yayi daga motar ya zagaya yana cewa "OK, shiga ka duba, zamu jira ka a nan." Cikin nutsuwa yake takawa har ya isa daf da ƙofar, a buɗe ƙofar take sai matsakaicin soron dake shafe da siminti, tsayawa yayi da niyyar yin sallama, sai dai kafin yayi sallamar ya ji muryar mahaifin shi a zahiri wacce ya jima bai ji ta ba, ya so jin shauƙin na jin wannan muryar cike da begen haɗa idanu da mahaifin nashi, ya ɗauka zai same shi cikin farin ciki marar misaltuwa, ya ɗauka zai same shi cikin nutsuwa ne da amince, amma sai yake jin muryar shi na tashi da irin yanayin nan da ya san shi da shi, cikin ƙaraji da ɓacin rai yake faɗin _"Shikenan Bara'atu, ba kin ce haka ba? To na daina yi ma Uzeifatu faɗa dan ta dinga tayaki aikin gida, amm ki sani akwai ranar da zaki yi dana sani, dan ni nasan ba yadda za'a yi a raini mace ba tare da koya mata aiyuka irin na gida ba, ki ci gaba Bara'atu." Sai kuma ya kalli Uzeifatu dake zaune tana ta turo baki yace" Ke kuma ki ji da kyau, tunda ita ba zata saka ki aiki ba ni daga yau na ɗora miki sharar gidan nan da wanke wanke, kika bari na sake tarar da ke zaune da waya a hannun ki alhalin mahaifiyar ki na aiki, to sai na rarraba ki gida biyu." A fusace ya fito daga farfajiyar ya iso soro, Jabir ya samu tsaye ya juya bayan shi kan shi na kallon ƙasa kamar wanda ya faɗa duniyar tunani, duk da bai gane wanene ba, dan haka ya rage saurin da yake yana kallon ƙeyar mutumin da mamakin wa ye har cikin tsakiyar soron gidan shi? Jabir da ya ji abinda ke faruwa, ya kuma fahimci inda matsalar take da kuma yadda za'ayi ma ayi maganin matsalar, jin tako a bayan shi ya kuma tabbatar na mahaifin sa ne yasa shi juyowa da sauri, suka kallon kallo ya tabbatar da mahaifin shi, inda shi ma Baban nashi ya shaida shi ne tun bai faɗa masa shi bane ta fuskar kama da ya gani da margayiya mahaifiyar Jabir ɗin, sai dai bai sani ba zama ne a cikin jajayen mutane yasa ya ma fi ta kyau nesa ba kusa ba? Wangale baki yayi har kunne irin ka ga abinda kake mararin ganin nan, da wani irin sauri ya tunkaro Jabir da shima yake sakin murmushi mai cike da bege da kewar mahaifi ya fara takawa, cikin zaƙuwa mahaifin nasa ke faɗin "Jabir, kai ne? Shine ka zo baka kirani ba?" Rumgume juna sukayi ƙam ƙam, duk rashin tsayi irin na Jabir irin tsarin nan zololo sai gashi kai da kai da shi da mahaifin shi, dan shi ma ba mutumin tsayi bane sosai ɗin nan. Hawaye masu zafi ne suka sauka a kafaɗar mahaifin Jabir, hakan ya tabbatar masa da kuka yake yi, dan haka ya ɗago shi yana murmushi tamkar gonar audiga yace "Jabir, kuka kuma? Kai share hawaye mana, me yasa kake kuka yanzu? Ni ba ka ga dariya nake yi ba? Yi murmushi ka ji Jabir ɗina." Tafin hannun shi ya sa ya share hawayen sannan ya kalli fuskar mahaifin shi, yana nan har yanzu da ƙarkon shi kamar ba shi ya haife shi, jikin shi a murɗe haka kuma kan shi ɗan tsili tsilin farin gashin kaɗan ido ke iya hangowa, irin wanda za'a ƙidaya din nan a kan mutum, riƙe hannayen juna suka yi gam inda a tausashe cikin muryar kuka da rauni Jabir yace "Aba, ka yafe min? Na wahalar da kai wajen nema na ko?" Murmushi yayi yana jijjiga hannayen Jabir ɗin yace "Karka damu fa, tun ranar ai na gaya maka ni ban riƙe ka ba Jabir, idan da mai laifi ai ni ne, ni na takura na dinga azabtar da kai har saida ka bar gida, ka ga kenan ni zan baka..." Da sauri ya girgiza mishi kan shi dake kallon ƙasa saboda ya fahimci haƙuri zai bashi yace "Shikenan Aba, nagode da ka yafe min..." Sai kuma ya ɗaga kai ya sake kallon fuskar shi sosai cikin nutsuwa yace "Aba kana lafiya?" Murmushi ya sake mishi yace "Lafiya lau nake Jabir, kai ma haka?" Jinjina kai yayi alamar e tare da sadda kan shi, shiru ne ya gifta na sakan biyu, a hankali Aba ya zare hannun shi na hagu daga cikin na Jabir, cikin nutsuwa ya tallabo haɓar shi yana kallon shi da so da ƙauna, a hankali kamar da wasa yake zagaya sajen da ya zagaye kumatu har zuwa kunnuwan Jabir, da wani kwantaccen gashi dake ƙasan bakin shi kaɗan, zuwa wanda ke zagaye da bakin shi na sama, da fara'a yake yin haka yna jin daɗi yana kuma kallon fuskar ta shi yace "Jabir ka girma, kamar ba kai ne ka gudu daga gare ni kana shekara sha huɗu ba." Faffaɗan murmushi Jabir yayi ya sunkuyar da kai cike da kunya yace "Hakane Aba, yanzu ɗan ka shekarar shi ashirin da bakwai, sannan ya zama alaramma da zai iya ja wa kowane babban malami baƙi, sannan ya ƙara gogewa a fannin neman na halak ɗin shi, Aba..." Ya kira sunan shi suna kallon juna, ɗorawa yayi da "Zan iya neman kuɗi a duk inda suke, Aba ina bin kowace hanya dan neman na kaina, amma ban da haramtacciyar hanya, sannan kuma Aba bana raina samu ko ya yake, ba dan komai ba saboda bana so na ji yunwa, sannan na ga na taimaki mai neman taimako kamar yadda Abba ya taimake ni lokacin da nake kusa da faɗawa garari." Cikin farin cikin jin haka Aba ya sake jawo Jabir jikin shi ya rumgume yana daddaɓa bayan shi tare da cewa" Ka kyauta Jabir, Allah ya maka albarka, Allah ƙara maka buɗi na alkairi, Allah baka ikon neman halak ɗin ka a duk inda take, Allah kuma ya sauƙaƙa maka neman ta." Ƙwarai! Yanzu ne ya fahimci ya jima yana rayuwa cikin kuskure, duk abinda mahaifin shi yayi bai kamata yayi watsi da shi ba, tunda dai shi ya haife shi, wasu ma Allah azurtar su yake da iyayen da basa bautawa Allah, ko kuma masu yin shirka gare shi, amma su yi haƙuri su zauna da su, gashi yanzu daga yi masa addu'a ɗaya ya ji wani irin yaƙinin na cewa wannan addu'a karɓaɓɓiya ce kuma tafi tasiri fiye da ta Abba Kabir, dan kuwa da bambamci ai tsakanin su, wannan shi ya kawo shi duniyar, sannan ya wahala da shi tun yana jariri har ya kai ɗan sha huɗu. Yayin da daga nan Abba kuma ya ɗora har zuwa yanzu da ya zama cikakken mutum mai aƙida da riƙo da shari'a ta gari, kowanen su ya bada gudummawa a cikin rayuwar shi, dan haka iyayen sa ne dukansu. Da sauri Jabir ya janye jikin shi saboda tunawa da su Aliyu yace "Aba, tare da su Aliyu muke?" Da mamaki ya kalle shi yace "Kua ka baro su waje? Ba shine ka bani muka gaisa daren shekaran jiya ba da ka sake kirana?" Murmushi yayi a tausashe yace "Shine Aba, na shigo ne dan na tabbatar ko nan ɗin ne." Da sauri Aban ya fita yana cewa "Bari na shigo da su sai ku wuce." Yana fita ya same su suna ta hira, rusunawa sosai sukayi suka gaishe shi sannan ya musu iso, suna shigowa Jabir ya yi murmushi saboda harara da Aliyu ya mako mishi yana faɗin "Shikenan sai ka manta da mu, kamar Aban naka ne kai kaɗai?" Rusunawa Jabir yayi yace "Kayi haƙuri *babban Yaya*." Murmushi kawai Aliyu yayi dan ya fahimci me yasa ya bashi haƙuri, ba ya so su yi rigima ne har ya ɓata mishi rai a yanzu, haka suka rankaya da sallama a bakunansu. *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *37* Bara'atu na yankar albarka na abincin dare da za ta ɗora wanda na daga cikin abinda ya kwo rigimar nan, dan saida ta yi abincin da ya ce ta yi na tarban Jabir, ganin la'asar tayi ba su zo ba ta ce ko ba sai tayi girki ba kawai dan dama ta gaji? Daga cewa ta sa Uzei tayi girkin daren mana take faɗin Uzei ce z ta iya aikin nan? Ina ba za ta saka ta ba, amsa sallamar tayi tana tsare masu shigowa da idanu, ya dai ce mata Jabir kawai zai zo, ta yi duk iya tunanin da za ta yi wajen gano daga ina zai zo? Da wane kalar rashin mutumci? Da wace kalar shigar? A ganin ta Uzeifatu ma da ake kulawa take gaban iyayen ta ta zama yadda ta zame musu, ina ga Jabir da ba mai kwaɓa? Ba uwa ba uba sai Allah (tunda kin yarda yana da Allah ai ya gama komai), so take ta ga wani da ƙananan kaya yayi irin asdown ɗin nan, da irin askin nan na gogaggun marasa tarbiyya, idan ma abun yayi daɗi har ta ga ɗan kunnai a kunnen shi da huje a hanci, a taƙaice dai ta ga Jabir a mummunan yanayi da shiga wacce ko a ƙasar waje sai fetsararru na ƙarshe ne ke irin ta. Amma sai taga duka cikin su kowa shiga ce ta kamala, ba wai Jabir da Aliyu da suke cikin dogayen riguna ba, Khamis ma manyan kaya ne jikin shi, ɗinkin shadda ce da kuma hular shi a kai, tun daga nan ta ji zuciyar ta ta sake baƙan ta, ranta ya sosu ta ji ba daɗin da har saida ta taɓe baki ta ci gaba da aikin ta. Uzeifatu na zaune da waya a hannun ta tana ta danne danne, cike da takaici Aba ya raɓa ya ɗauka musu kujeru cikin ɗaki ya kawo musu suka zauna, duk gaisuwar da suke mata ba wani yabo ba fallasa take amsawa ciki-ciki, Uzei kuma Aliyu da ya matuƙar birge ta ta tsare da idanu tunda ta fahimci Jabir ne Yayan ta, da irin yanayin rashin kamun kai ta washe baki tace "Ina yini?" Wani arnan kallo Jabir ya mata, mai tattare da saƙonnin dayawa, na farko shine ki kama kan ki, na biyu kuma zan yi maganin ki, na uku kuma bana son iskanci, na ƙarshe kuma shine tashi daga nan saboda suturar jikin ki. Take Uzei ta ji murɗawar ciki, kwarjinin shi ya kamata, ko ba Yayan ta bane ya mata kallon nan dole ta kimtsu, bare kuma Yaya ne da tasan zai iya falle ta da mari, dan haka ta miƙe tana kallon Aliyu da shi wallahi bai ma kula da ita ba bare ya ga tsiyar da take, Aba kawai dake ta zube musu kayan ci da sha yake kallo, irin farin cikin da yake ciki, da zumuɗi da murnar ganin ɗan sa, za ka rantse yanzu ne aka haifo Jabir a duniyar. Jabir mamaki yake sosai da yadda matar Baban nashi ta tarbe shi, me ya mata? Me ya sa bata ƙaunar shi? Shin ya taɓa mata wani abu ne a zaman su? Ko laifin Maman shi ne ya shafe shi? To amma ai basu zauna tare ba bare har wani abu ya haɗa su, ko dai halin ɗan adam ne da shi kanshi yake ƙin abu ba'a bisa tsari na koyarwar addini ba? Share zancen kawai yayi suka ƙara gyara zama suna cin abinda mahaifin nasa ya tanadar musu duk da basu jin yunwa, wasa wasa basu bar nan ba sai da sukayi sallah magrib, da ya ce zai tafi Abansa kamar zai yi kuka saboda rashin so, dan kuwa har ɗakin da ya ware mishi ya kuma sa aka gyara saida ya nuna ma Jabir ɗin, amma sai ya rarrashe shi da zai dawo, matsalar ya ce ma Abba zai zauna tare da su ne, yanzu kuma baya da lafiya, bai kamata ya bijiro masa da maganar komowa nan ba, amma zai so idan ya samu lafiya sosai, shi kan shi Aban sai yaje ya ganshi har ya masa godiya kan taimkon da ya ma Jabir ɗin, daga nan kenan sai ya dawo wajen Aban shi shi ma, to da hakane sukayi sallama suka tafi suna mai cike da begen juna. ****************** Cikin nutsuwa ta fito daga wankan ɗaure da towel ɗin da ana ɗaurashi a akai ne idan an wanke a ƙugun ta, hakan yasa ya tsaya mata iya cinya wanda da za ta duƙa tsaf za'a ga jikin ta, sai kuma sama da ba ta rufe ba ko alama, wayar ta dake kan gado ce ta ɗauki kuka tare da sake bubbuga ƙofar da aka yi, cikin jin haushin kalar bugun da ake mata wanda bata da tabbacin ko waye duk da tasan Fahad ya ce mata yana zuwa tace "Wai waye yake neman karya wa mutane ƙofa?" A tsawace Fahad da takaici ya gama kama shi yace "Ke dallah buɗe wa mutane ƙofa, ƴar wulaƙanci." Ƙarasawa tayi ta buɗe ƙofar tare da hangameta, gyara tsayuwa yayi da niyyar zazzaga mata, amma da ya gan ta hakan sai ta sake ɗaga masa hankali, dan dama tun abinda ta mishi a ƙage ya zo har yana ɗiga a hanya, sai kawai ya auka ɗakin kamar an hankaɗa shi tare da cakumota ya rarumi ƴan biyun ta inda ya sa ƙafa ya turo ƙofar. *Bayan wasu awanni*; tana kwance kan ƙirjin shi yana shafa kan ta har zuwa fuskar ta cikin sanyin murya dake nuna gajiya yace "Beela." A tsananin gajiye ta amsa da "Ummm!" Yana ci gaba da shafa ta yace "Cewa nayi..me zai hana muyi aure? Tunda Kinga da gaske gida maganar aurar da ni suke, kuma bana so Nabila, bana son wata mace idan ba ke ba, dan Allah ki bari muyi aure yanzu, ba laifi munyi rayuwa irin wacce muke so, mu bari yanzu shari'a ta halatta mana junanmu, zamu fi jin daɗi." Tashi tayi zaune ta na lalubar towel ɗin ta tana faɗin" Mun yi alƙawari ba zamuyi aure ba sai nan da shekara biyu, me yasa zaka yi maganar yanzu? Na zo ne dan na dakatar da auren, amma ba dan mu muyi ba." Tashi tayi tsaye tana tana ɗaura towel ɗin, da sauri ya miƙe ya riƙo hannun ta har ya sauko daga kan gadon yana cewa" Nabila har yaushe zamu yi ta jan rayuwar nan? Ya isa haka mana, son ki nake Beela, kuma da aure, ya kamata muyi aure mana." Yatsia fuska tayi tace" Gaskiya ban shirya ba." Dafe ƙugu yayi yace" Sai yaushe? Lokacin da kika ga dama kenan? Nabila ba'a ma aure haka, komai da kike gani lokaci gare shi, idan ya zo miki to kiyi anfani da damar ki, idan ba haka ba za'a kai lokacin da kike son shi ido rufe ki kasa samu, sannan Nabila ki yi tunani mana kiga mu misali ne ga mutane dayawa, ƙawayen ki nawa ne samarin da suka zama abokan lalatar su suka ci amanar su ta hanyar auren wasu? Da idanun ki kinga ƙawar ki an dake ta kuma aka jefar akan titi saboda saurayin zaiyi aure ta ce ita ya kamata ya aura ba wata ba, sannan Kinga wanda à ƙarshe har saida alƙali ya raba su saboda ta ce ba zai auri kowa ba bayan shi ya lalata ta, shin me kuma kike nema bayan haka Nabila? Tun farko na faɗa miki ina son ki, kuma har yanzu ina son ki kuma da aure, abinda muka yi bai sa na ji kin fita a raina ba, na yarda dake da gaba ɗaya zuciyata, Nabila nasan da ni kaɗai kike mu'amala, haka kem kuma kin sani dake kaɗai nake rayuwa, to me muke so bayan haka?" Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi dan ta gamsu da abinda ya faɗa, amma ai tasan shi ba zai mata haka ba, dan haka ta nemi raɓawa ta wuce tana faɗin "Ni ba bana son auren bane, amma dai..." Da sauri ya fizgota har ta faɗa jikin shi yana cewa "Amma dai me? To ni ne baka so ki aura? Akwa wani abun da kike ɓoye min ne?" Grgza mishi kai tayi alamar a'a sannan tace "A'a, ba komai." Ƙara tausasa murya yayi yace "To me ya sa ba zaki amince ba Beela? Muna son junan mu, kuma mun yarda da junan mu." Wani bahagon kallo ta masa tace "Yarda? Fahad yarda kake magana? Shin ko kasan na ɗaya daga cikin abinda yasa auren ƴan duniya baya ƙarko? Wannan yardar da ka ambata, Fahad ba wai bana so muyi aure bane, amma maganar gaskiya mu faɗawa kanmu ita, wane irin zama zamuyi? Me duniya za ta ce a kan mu? Idan mun haifi yara zasu iya tausaya mana? Ba ma wannan ba, muna da tabbacin ubangiji zai bamu haihuwar? Bayan ni da kai ɗin nan har ciki mun zubar, a bar ma maganar magani da nake sha dan hana ɗaukar ciki, kana ganin bayan duk wannan zamu iya yin zama na gaskiya da amana da kai?" Girgiza mishi kai tayi tace" Fahad, duk son junan mu sai mun fara tsanar kan mu, idan muka yi aure a haka ni ba zan samu salama ba haka kai ma, duk da dai na sani da iya junan mu kawai muke mu'amala, amma bana jin idan ka fita cikin garin zuciyata za ta nutsu sannan shaiɗan ba zai raya min kana wuraren da muka saba zuwa tare da kai ba, idan kuwa har za ka je wurin da ka saba zuwa sannan kasa duk wani abu da zai sa ka fita a hankalin ka, to fa da yiwuwar ka iya kula kowace mace ma. Sannan kai, zai iya yiwuwa duk sanda zan fita ka ji baka yarda da na tafi ni kaɗai ba, za ka iya tunanin zan tafi wani wurin ne daban, imma wajen ƙawayena, ko biki, ko wani shashancin dai daban, to da haka ta ya zamuyi aure Fahad?" Ƙanƙance idanu yayi yana kallon ta yace" Abubuwan da kika faɗa, kamar kai tsaye kina so ki ce ba zaki iya aurena ba kenan?" Da sauri ta girgiza kai tace" Me zai sa nace haka? Zan iya auren ka mana jariri, kai ma fa kasan kai kaɗai nake so, zan iya auren ka, amma idan ka min alƙawarin duk wannan matsalolin da na zayyano zamu kiyaye faruwar su, sannan zamu canza rayuwar mu canzawa kuma ta har abada." Ajiyar zuciya Fahad ya sauke, a hankali ya ja baya kaɗan daga gare ta sannan ya zube guiwar shi ɗaya yana kallon ta yace" Nabila, ni Fahad na miki alƙawarin kiyaye duk wani abu da zai zama matsala a zaman aurenmu, sannan na yi alƙawari tsakanina da ubangijina kan na daina duk wani abun da nake yi daga yau, ba zan sake aikata wani abu da yayi kama da wanda na aikata a baya ba, in sha Allah." Sai kuma ya tara mata hannu alamar ta taho tare da faɗin" Za ki iya aurena Nabila?" Rufe bakin ta tayi da tafin hannu cike da farin ciki har da hawayen jin daɗi sannan ta miƙa msa hannun, jawo ta yayi ya zaunar da ita kan cinyar ta, haɗa goshin shi yayi da nata ya sake faɗin" Uhum?" Cikin kukan farin ciki Nabila ta jinjina masa kai tare da faɗin" Na amince mana Fahad, na amince na sake sabuwar rayuwa da kai, sannan na ci gaba da rayuwa da kai har mutuwa ta riske ni." Sai kuma ta kai bakin ta za ta haɗa bakin su, da sauri ya janye yace" O'o, yanzu fa kika sa na ɗauki alƙawari, ai ba zamu sake kusantar juna ba kuma har sai ranar da aka ɗaura mana aure." Ɗan dukan shi tayi à ƙirji tare da yin murmushi ta sake haɗa goshin su tace" Ina son ka." "Ni la ina son ki." Ya faɗa yana tada ta tsaye Shima ya miƙe yana cewa "Yanzu ki haɗa kayan ki, zan je gida nayi magana da su Mamie, gobe zan kaiki ki gaishe su, dan Kinga haɗuwar ku ta yau ba ta yi daɗi ba, daga nan kuma zaki koma gida sai ki shiga istibra'i." Da sauri ta kalle shi da mamaki tace "Menene hakanan kuma?" Kallon ta yayi da kyau yace "Oh ! Istibra'i na nufin zaki yi wata ɗaya ba tare da sake wata mu'amala ba har kiga jini ɗaya, hakan na nufin kin tsarkaka, sai a ɗaura mana aure." Riƙe haɓa tayi tace "To, kai kuma à ina kasan haka?" Wani kallo ya mata tare da nufa hanyar fta yace "Ke, akwai fa sanin, takewa ne kawai aka yi, amma in sha Allah mun tuba kenan, zamu ci gaba da yin istigfari, dan ita ke cinye zunubi tamkar yadda wuta ke cin busashen icce." Ficewa yayi hakan yasa ta bishi da kallo, faɗawa tayi kan gado tana sauke numfashi, sai kuma ta saki murmushi kawai tare da tashi dan ta ƙara yin wanka ta shirya. Tana gama shiryawa ta fita ta samu taxi ta ce a kai ta salon, ba su yi nisa ba ma ta ga salon ɗin dan haka ta tsaya nan, tana shiga faɗi abinda take da buƙata a mata musamman ma da take saka ran zuwa gaishe da surukanta gobe kamar yadda Fahad ya ce, dan haka ta sa aka since mata kai tare da wanke shi sannan aka mata wanki ƙafa da hannu. *Alhamdulillah.* 29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *38* *Tun da* sanyin safiya tana ɗain baccin ta ko madafa ba ta shiga ba, hasalima yau niyyar ta shine kawai Kuwailat ta sha ko da cascroot ne ko cornflakes ta tafi makaranta, sam ba ta da karsashin yin girkin yau ma, dan haka ta tashi ba walwala, bugun ƙofar da ake yi ne yasa ta ƙwala kiran sunan Kuwailat, daga ɗakin ta ta amsa da "Na'am Mamie." A kasalance tace "Ki duba ki ga wa ye a ƙofa." "To Mamie." Ta amsa tana ɗaukar kallabin ta ta ɗaura a kai sannan ta fito, tana buɗewa tayi tozali da Aliyu da Jabir, shigowar su kenan daga masallaci tun asuba suke ta zagayen gaishe da iyayen gidan, murmushi ta sakar musu tare da kauce musu a hanya tace "Yaya, ina kwanan ku ? Ku shigo ciki, Mamie tana ɗaki." Aliyu ne ya fara shigo yana sake yin sallama, sai kuma Jabir da ya biyo bayan shi, ƙamshin Turare ne ya musu maraba, kuma abun burgewa da mamaki shine yau ba ta samu tayi Turare ko ɗaya a ɗakin ba, ba ma haka ba, tun jiya da safe da ta yi ba ta sake saka wani turaren ba, amma ya kama ɗakin saboda tana yawan anfani da shi kuma turaren mai kyau da inganci, sannan kujeru ma da labulayen ta duk tana da turare na musamman da take fesa musu, hakan yasa ƙamshin su ma ya ishi kwantar da hankalin bawa, ta ƙofar ɗakin Ummu kawai za ka wuce amma sai ka ji ƙamshi a gurin, na daga cikin dalilin da yasa indai za ta ce ma Alhaji ya bata kuɗi za ta sa a kawo mata turare yke bata jikin shi na rawa tare da ƙarfafa mata guiwar a ci gaba da saka ƙamshi. Aliyu dake ma Kuwailat ne murmushi dafa kanta yayi yace "Auta, ki faɗawa aunty mun zo gaishe ta ne." Da sauri ta juya tana faɗin "To Yaya." Tana shiga ɗakin Aliyu ya ɗaga kai yana kallon ɓangaren yana faɗin "Ka ga wurin nan kamar ba iri ɗaya da na su Mama da Hajia ba, sai naji kamar nayi bacci wallahi saboda ƙamshi." Wani kallo Jabir ya watsa mishi kawai ya ɗauke kai bai ce uffan ba, hakan ya sa Aliyu yin murmushi yace "Alaramma ka dinga yin magana mana, wannan shirun naka yayi yawa." Nan ma shirun ya mishi bai ce komai ba sai maida hannayen shi biyu da yayi baya ya ɗan juya yana kallon ƙofar shigowa, ba jimawa Kuwailat ta fito tare da nufa ɗakin ta saboda Maman nata na bayan ta, a nutse Ummu ta fito da hijabin ta fari tas mai hannaye da ƴar fara'a a fuskar ta. Ƙarasowa tayi tana faɗin "Assalama alaikunna." Murmushi Aliyu yayi ya amsa da "Wa'alaiki salam, auntynmu barka da safiya?" Yadda yayi maganar har da rusunawa ɗin nan ya saka ta jin kunya ta amsa da "Barka babban Yayan su, antashi lafiya?" Kafin ya bata amsa Jabir ma ya juyo, saida yayi irin ranƙwafawar nan kamar zai yi ruku'u kamar kuma zai yi tsugunnon maza cikin taushin murya ba tare da ya kalli fuskar ta ba yace "Barka da safiya Maama?" Da murmushi shima ta amsa mishi da "Barka Jabir, antashi lafiya? Ya gajiya kuma?" A tare suka amsa da "Alhamdulillah, gajiya ta bi lafiya." Da farin cikin girmamawa dar ta samu daga gare su tace "Ma sha Allah, nagode sosai da kulawa, Allah ya saka da alkairi." Murmushi duk sukayi sai Aliyu da ya nufi wajen teburin cin abinci da ya ga an masa kwalliya da kwanukan abinci masu irin ƙyallin nan da babbar flask da sauran kayan da dama kawai ana kwalliya da su ne, kasancewar shi mutum mai saurin sabo da barkwanci da son zama da kowa lafiya yasa yake faɗin "Auntynmu Allah sa zamu samu abinci? Kinsan bana son *zakina* ya fara jin yunwa ban tanadar masa komai ba, matsala ake samu da haka." Dariya Ummu tayi ta saci kallon Jabir da ya sunkuyar da kai ƙasa yana girgiza kai shima, cikin taushin murya Ummu ta kalli Aliyu tace" Babu abinci gaskiya, sai dai za'a iya haɗa muku idan kuna buƙatar hakan?" Dakatawa yayi daga shirin isa teburin ya juyo yace" Gaskiya zamu so haka, dan Mama ta ce wai masu aiki ke haɗa mata abun kari, shi kuma oga ko a can baya cin abinci ko ina." Juyawa Jabir yayi ya kalle shi, da idanun shi ya mishi alamar zamu haɗu, daga haka ya kalli Ummu cikin nutsuwa da ladabi da burin son samun albarka daga bakin duk wanda yake gaba da shi, musamman ma su da yake musu kallon iyaye ya ƙara rusunawa yace" Maama, zan wuce ni, muna buƙatar addu'arku?" Ɗan jim tayi ta kalle shi da mamakin ita kuma? Sai kuma tayi murmushi ganin har lokacin bai ɗago daga rusunawar da yayi ba tace" Addu'ar mu ta alkairi kullum tana tare da ku Jabir, Allah ya albarkaci rayuwar ku, Allah kuma ya sa kuyi anfani da abinda kuka karanta, Allah kuma ya baku zuri'a ta gari." Da jin daɗi matuƙa ya amsa da" Ameen ya Hayyu ya Qayyum Maama, Allah ƙara lafiya." Aliyu kuma da tsokana ya saci kallon Jabir yace" Me yasa ban ji kayi ƙorafin ba'a maka Addu'ar yin aure a kwanan nan ba? Naga abinda kake so kenan." Jallon shi Jabir ya yi, sai kawai ya juya ya fice bai sake juyowa ba, Aliyu kuma da murmushi dan yasan sai ya fito zasu yi rigimar, dan gaskiya yana al'ajabin yadda Jabir ke girmama Ummu, wani irin maɗaukakin girma ne yake bata kamar na ɗa da uwar da suka rayu tare amma bisa koyarwa irin ta addini, kunyar ta yake, girmama ta yake, nauyin ta yake ji, ganin ƙimar ta yake yadda ko fuskar ta shi yasan ba zai iya kalla ba. Shima shirin ficewa yayi Ummu na tambayar "To me za'a haɗa?" Da fara'a yace "Ko me ma muka samu auntyn mu Alhamdulillah." Jinjina kai tayi alamar shikenan, saida suka fita ta cire hijabin ta aje kan kujera ta shiga madafa tana faɗawa Kuwailat dake ɗaki ta same ta can kafin ta wuce. Tsakiyar shukoki suka samu Alhaji zaune kan kujera yana jin daɗin yanayin sosai, suna isowa duk suke zaune suna sake gaisawa duk da sun haɗu masallaci, saida suka gaisa ya nunawa Aliyu kujerun dake wajen mai gadi yace "Ɗauko ku zo ku zauna na ji." Bin umarnin shi Aliyu yayi, jim kaɗan ya dawo da kujerun ya aje suka zauna shi da Jabir, sake kallon su yayi yace "To ina sauraren ku, kun ce akwai maganar da zamuyi idan kuka dawo?" Jabir ne ya fara kallon shi yace "Abba ba yanzu ba, ka bari har jikin ka ya ƙara yin kyau." Murmushi Abban yayi ya dafa kafaɗar shi yace "Karka damu Jabir, burina yanzu shine naga ku manyan ƴaƴan nawa kun hau kan turbar da ta dace, Alhamdulillah kun samu ilimin addinin da nasan ko iya shi kawai ya isheku rayuwa mai nagarta, amma bayan haka ina so na ji abinda kuke son faɗa min da wuri wuri, dan naga ko da taimakon da zan iya muku?" Kallon juna sukayi shi da Aliyu, da idanu suka gama yanke shawarar kawai su sanar da shi ɗin tunda ya matsa, Aliyu ne ya kalli Abban a ladabce yace" Abba, ba wani abu bane dama, kamar yadda kuka sani ina son yin koyarwa, to shine nake so ku tsaya min dan ina son buɗa islamiyya, zan tafiyar da ita ne akan wani tsari da na gani a Madina, sai shi kuma Jabir, kun san dama shi dai ɗan kasuwa ne, kuma har tafiyar can ma bai daina aikin wahala ba dan ya samu kuɗi, to Alhamdulillah ya tara kuɗin kam..." Aliyu yayi maganar yana dariya saboda hararan da Jabir ya watso mishi, dariya Alhaji ma yayi yana ci gaba da sauraren Aliyu da ya ci gaba da faɗin" Ya nemi kuɗi sosai Abba, yayi aikin wahala ya wa larabawa bauta duk dan ya tsaya da ƙafafun shi, da taimakon Allah kuma ya fara siyan kaya a can yana turowa wani abokin mu anan, to Alhamdulillah zan iya cewa ya zama babban gwaska ta nan wajen, dan yanzu haka a Saudia da Madina da Lebanon akwai wasu da yayi sabo da su kuma yake siyan kayan nan namu na gida yana raba musu suna bashi kuɗin, Abba, a taƙaice dai Jabir ya tsayu sosai." Gyara zama Aliyu yayi yace" Abinda yasa na faɗa muku haka Abba, yana son buɗa babban shagon da zai zama a cikin yake ɗaukan kayan da yake rabawa, to shine yake son ka saka masa hannu, dan yana son shagon ya kasance a idanun jama'a ne, sai taimako na gaba kuma da yake buƙata Abba... Conteneur ɗin ka dake yawan tasowa daga Dubai da Chine, yana so idan ana muku lodi ya dinga bada nashi saƙon, idan abubuwa suka yi kyau wata rana shima sai mu rasa wurin zama tsabar yawan conteneur ɗin da ya kawo a garin nan." Dariya Alhaji yayi yana kallon Jabir dake girgiza kai ya rasa me ke damun Aliyu, cike da ƙarfafa guiwa Alhaji yace" Ma sha Allah Jabir, ni dama nasan babban ɗan kasuwa ne za'a yi tun da ka faɗa min har ga-ruwa kayi da wanke wanke a gurin mai siyar da abinci, Allah ya sa albarka Jabir, Allah ya tallafe ka har kai ma ka tallafi dubbunnai." A tare shi d Aliyu suka amsa da" Ameen Abba." Sai kuma ya ɗora da" Duka ba damuwa, na ji buƙatun ku kuma ba zasu gagara ba, da izinin Allah za'a muku yadda kuke so, Allah ya dafa mana." Amsawa suka ƙara yi inda suke ta murmushi da mishi Addu'ar ƙarin lafiya mai anfani, shi kuma shiru yayi na wani lokacin kafin ya kalli Jabir yace" Jabir, akwai wani babban wurin aje kayan gonana dake nan bayan ofishin ƴan sanda kan titin dake zuwa babban likita, me zai hana ka je ka duba? Idan ya maka Kagaai shikenan ko, sai a fara abinda ya kamata, dan gaskiya wurin titi ne sosai kuma fuskar jama'a." Kallon shi Jabir yayi, a nutse ya kamo hannun shi yana tattausawa idanun shi taf da hawaye yace" Abba, ba damar mu zo da abu muna so sai ka mana shi? Abba yaushe ne zaka ce ba zaka mana ba saboda bai dace ba? Abba da wuri haka?" Murmushi ya mishi yace" To ai ku ɗin ne ba kwa zuwa da abinda bai dace ba, shawara kuke yi da kuma hangen nesa kafin ku zo da buƙatar, shiyasa kullum nake jinjinawa tunanin ku." Jinjina kai Jabir yayi yace" Mun gode Abban mu, ba mu san ya zamu yi ba idan ba kai? Abba Allah ƙara maka lafiya da nisan kwana mai albarka." "Ameen Ya Allah." Ya faɗa da fara'a sosai a fuskar shi, Aliyu ya ƙalla dake kallon tsantsar ƙaunar da suke ma juna yace "Aliyu, tunda na siyi wannan gidan na su Hajia Mairo, da gida na so yi muku kai da Jabir da Khamis ku zauna nan dan aure zan muku, to tunda ka zo da maganar nan ina ga zaka iya shiga kai ma Kaga idan girman sa zai maka yadda kake so, Kaga daga nan sai a fara ginin makarantar ko?" Da jin daɗi Aliyu ma ya sumbaci hannun Alhaji yana mishi godiya da addu'a sosai, ba su tashi daga nan ba haka suka ci gaba da tattaunawa har rana ta fito. A shirye auta ta fito sanye da zunbulelen hijab ɗin ta na islamiyyar da ya saka Jabir sake mutuwa akan yarinyar har saida ya furta "Ya Arrahaman." Ba kwalli ko ɗigo ɗaya à fuskar ta, yarinya ce ƙarama, amma shigar nan da tayi ba ƙaramar kamala da fuskar manya ta yafa mata ba, a zahiri kake gane ƴar dattijo da dattijuwa ce, ma'ana ƴar manyan mutane da ta samu tarbiyya, zai so hakan, zai so a bashi ita tun yanzu, ya ji ya gani zai iya rainon ta har sanda za ta gama cikar kamalar ta, amma ba zai juri nesa nesa da ita ba, maza yanzu mace ta gari suke so, dan haka ƙaracin shekarun ta ba zai hana namiji na ƙwarai wawar ta ba. Yadda yake kallon fuskar ta dake ɗauke da murmushi irin na maman ta yasa har ya ɗan shagala da kallon nata, ba tare da sanin shi ba kuma yake taya ta murmushin sakamakon tsokanar da Aliyu ke mata cewa ta kusa daina zuwa islamiyyar kowa sai tashi, amma hakan ba yana nufin za ta makara ya ƙyaleta ba, zane ta zai yi. Da fara'a Abba ya ɗan rumgumata jikin shi yana shafa kan ta yace "Aliyu autata ce fa, ko ni ban taɓa dukan ta ba." Dariya duk suka yi sai Kuwailat dake rufe fuska dan kunya, jin Jabir bai sa baki a maganar ba duk da dama zai yi wuya ya furta wani abun, amma sai Abba ya juya ɓangaren da yake yana faɗin "Kai Jabir ka yarda ya dak..." Ba wai kallon da ya kama Jabir ɗin na ma Kuwailat bane ya bashi mamaki, sai yadda yayi saurin sadda kan shi cike da basarwa da kuma kunyar yadda Alhaji ya kama shi yana kallon ƴar tashi, wani murmushi Alhaji yayi irin shikenan ɗin nan na gano ka tare da dafa Kuwailat yace "Autar Mamien ta, maza kama hanya tafiyar ki, Aliyu bai da tausayi zai iya zane min ke anan." Da fara'a ta kma hanya tana musu bye bye da cewa "Sai na dawo." Ɗaga mata hannu Aliyu yayi yace "A dawo lafiya." Saida ta tafi Alhaji ya sake duban su yace "To yanzu ya maganar aure? Na ji gaba ɗaya tunanin ku kan yadda zaku kyautata rayuwar ku ne kawai, ban ji wani cikin ku yace na je gidan dattijo wani na karɓo masa ragamar kulawa da wata kyakyawar matashiya ba?" Dariya Aliyu yayi inda Jabir ya kalli Alhaji cike da tsarguwa sai kuma yayi murmushi yasx girgiza kai, Aliyu ne ya shafa kan shi cike da kunya yace" In sha Allah Abba, muna nan muna nema shima, da zaran mun samu waɗanda suka dace, zamu izaku gaba ku nemo mana ɗin." Girgiza kai Alhaji yayi da rashin jin daɗi yace" Gaskiya ban ji daɗi ba, ace kamar ku babu ma mai niyya a cikin ku, yadda na so fa shine kuna zuwa da kamar sati ɗaya bikin ku za'a yi." A tausashe sosai cikin ladabi Jabir yace" In sha Allah Abba zamu gabatar muku da su nan da ɗan lokaci." Jinjina kai yayi ba fara'a tare da shi yace" Shikenan, Allah ya yarda, amma ku sani idan naga kun share sati ɗayan nan kuna neman cinye na biyu, to fa zaku gane Abban ku bai da tausayi, dan kuwa tsaf zan nema muku mata ku aura." Murmushi duk sukayi inda Aliyu ya ƙara shafa kanshi yace" A'a Abba, in sha Allah ma ba zata kaimu ga haka ba." Sai Jabir da ya kalli Alhajin da kyau cikin nutsuwa yace" Abba, ko auren je ka ga ɗakin ka kuka mana zamu karɓa da kulawa muyi godiya, kun isa damu ne kuma zamu karɓa muyi biyayya da yardar Allah." Kallon shi Alhaji yayi cike da jin daɗin yadda ya nuna zai masa biyayya, inda Aliyu ya kalli Jabir da mamaki yace" Ka tabbata Alaramma, sami'ina ne wa aɗa'ana?" Da idanu ya amsa mishi da tabbas ta hanyar lumshe su sosai, jinjina kai Aliyu yayi da tsokana yace" Ko da yake ai kana da wurdin da zaka yi ne ku zauna da soyayya, ni kuma ka ga ba ruwana ko?" Murmushi dai Alhaji yayi yana jin farin ciki yadda suke fahimtar junan su a kamar ƴan uwa abun na birge shi. Daga nan ya miƙe ya bar su ya tunkari ɓangaren Ummu da suka fi kusa da shi dan gaishe da matan kamar yadda ya saba kamar ya shirya ɗakin Hajia Atika dan yau ita ce da shi. *In sha Allah mun kusa fara darasi na kayan marmari.* *Alhamdulillah.* 15/08/2023, 20:13 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *38* *Tun da* sanyin safiya tana ɗain baccin ta ko madafa ba ta shiga ba, hasalima yau niyyar ta shine kawai Kuwailat ta sha ko da cascroot ne ko cornflakes ta tafi makaranta, sam ba ta da karsashin yin girkin yau ma, dan haka ta tashi ba walwala, bugun ƙofar da ake yi ne yasa ta ƙwala kiran sunan Kuwailat, daga ɗakin ta ta amsa da "Na'am Mamie." A kasalance tace "Ki duba ki ga wa ye a ƙofa." "To Mamie." Ta amsa tana ɗaukar kallabin ta ta ɗaura a kai sannan ta fito, tana buɗewa tayi tozali da Aliyu da Jabir, shigowar su kenan daga masallaci tun asuba suke ta zagayen gaishe da iyayen gidan, murmushi ta sakar musu tare da kauce musu a hanya tace "Yaya, ina kwanan ku ? Ku shigo ciki, Mamie tana ɗaki." Aliyu ne ya fara shigo yana sake yin sallama, sai kuma Jabir da ya biyo bayan shi, ƙamshin Turare ne ya musu maraba, kuma abun burgewa da mamaki shine yau ba ta samu tayi Turare ko ɗaya a ɗakin ba, ba ma haka ba, tun jiya da safe da ta yi ba ta sake saka wani turaren ba, amma ya kama ɗakin saboda tana yawan anfani da shi kuma turaren mai kyau da inganci, sannan kujeru ma da labulayen ta duk tana da turare na musamman da take fesa musu, hakan yasa ƙamshin su ma ya ishi kwantar da hankalin bawa, ta ƙofar ɗakin Ummu kawai za ka wuce amma sai ka ji ƙamshi a gurin, na daga cikin dalilin da yasa indai za ta ce ma Alhaji ya bata kuɗi za ta sa a kawo mata turare yke bata jikin shi na rawa tare da ƙarfafa mata guiwar a ci gaba da saka ƙamshi. Aliyu dake ma Kuwailat ne murmushi dafa kanta yayi yace "Auta, ki faɗawa aunty mun zo gaishe ta ne." Da sauri ta juya tana faɗin "To Yaya." Tana shiga ɗakin Aliyu ya ɗaga kai yana kallon ɓangaren yana faɗin "Ka ga wurin nan kamar ba iri ɗaya da na su Mama da Hajia ba, sai naji kamar nayi bacci wallahi saboda ƙamshi." Wani kallo Jabir ya watsa mishi kawai ya ɗauke kai bai ce uffan ba, hakan ya sa Aliyu yin murmushi yace "Alaramma ka dinga yin magana mana, wannan shirun naka yayi yawa." Nan ma shirun ya mishi bai ce komai ba sai maida hannayen shi biyu da yayi baya ya ɗan juya yana kallon ƙofar shigowa, ba jimawa Kuwailat ta fito tare da nufa ɗakin ta saboda Maman nata na bayan ta, a nutse Ummu ta fito da hijabin ta fari tas mai hannaye da ƴar fara'a a fuskar ta. Ƙarasowa tayi tana faɗin "Assalama alaikunna." Murmushi Aliyu yayi ya amsa da "Wa'alaiki salam, auntynmu barka da safiya?" Yadda yayi maganar har da rusunawa ɗin nan ya saka ta jin kunya ta amsa da "Barka babban Yayan su, antashi lafiya?" Kafin ya bata amsa Jabir ma ya juyo, saida yayi irin ranƙwafawar nan kamar zai yi ruku'u kamar kuma zai yi tsugunnon maza cikin taushin murya ba tare da ya kalli fuskar ta ba yace "Barka da safiya Maama?" Da murmushi shima ta amsa mishi da "Barka Jabir, antashi lafiya? Ya gajiya kuma?" A tare suka amsa da "Alhamdulillah, gajiya ta bi lafiya." Da farin cikin girmamawa dar ta samu daga gare su tace "Ma sha Allah, nagode sosai da kulawa, Allah ya saka da alkairi." Murmushi duk sukayi sai Aliyu da ya nufi wajen teburin cin abinci da ya ga an masa kwalliya da kwanukan abinci masu irin ƙyallin nan da babbar flask da sauran kayan da dama kawai ana kwalliya da su ne, kasancewar shi mutum mai saurin sabo da barkwanci da son zama da kowa lafiya yasa yake faɗin "Auntynmu Allah sa zamu samu abinci? Kinsan bana son *zakina* ya fara jin yunwa ban tanadar masa komai ba, matsala ake samu da haka." Dariya Ummu tayi ta saci kallon Jabir da ya sunkuyar da kai ƙasa yana girgiza kai shima, cikin taushin murya Ummu ta kalli Aliyu tace" Babu abinci gaskiya, sai dai za'a iya haɗa muku idan kuna buƙatar hakan?" Dakatawa yayi daga shirin isa teburin ya juyo yace" Gaskiya zamu so haka, dan Mama ta ce wai masu aiki ke haɗa mata abun kari, shi kuma oga ko a can baya cin abinci ko ina." Juyawa Jabir yayi ya kalle shi, da idanun shi ya mishi alamar zamu haɗu, daga haka ya kalli Ummu cikin nutsuwa da ladabi da burin son samun albarka daga bakin duk wanda yake gaba da shi, musamman ma su da yake musu kallon iyaye ya ƙara rusunawa yace" Maama, zan wuce ni, muna buƙatar addu'arku?" Ɗan jim tayi ta kalle shi da mamakin ita kuma? Sai kuma tayi murmushi ganin har lokacin bai ɗago daga rusunawar da yayi ba tace" Addu'ar mu ta alkairi kullum tana tare da ku Jabir, Allah ya albarkaci rayuwar ku, Allah kuma ya sa kuyi anfani da abinda kuka karanta, Allah kuma ya baku zuri'a ta gari." Da jin daɗi matuƙa ya amsa da" Ameen ya Hayyu ya Qayyum Maama, Allah ƙara lafiya." Aliyu kuma da tsokana ya saci kallon Jabir yace" Me yasa ban ji kayi ƙorafin ba'a maka Addu'ar yin aure a kwanan nan ba? Naga abinda kake so kenan." Jallon shi Jabir ya yi, sai kawai ya juya ya fice bai sake juyowa ba, Aliyu kuma da murmushi dan yasan sai ya fito zasu yi rigimar, dan gaskiya yana al'ajabin yadda Jabir ke girmama Ummu, wani irin maɗaukakin girma ne yake bata kamar na ɗa da uwar da suka rayu tare amma bisa koyarwa irin ta addini, kunyar ta yake, girmama ta yake, nauyin ta yake ji, ganin ƙimar ta yake yadda ko fuskar ta shi yasan ba zai iya kalla ba. Shima shirin ficewa yayi Ummu na tambayar "To me za'a haɗa?" Da fara'a yace "Ko me ma muka samu auntyn mu Alhamdulillah." Jinjina kai tayi alamar shikenan, saida suka fita ta cire hijabin ta aje kan kujera ta shiga madafa tana faɗawa Kuwailat dake ɗaki ta same ta can kafin ta wuce. Tsakiyar shukoki suka samu Alhaji zaune kan kujera yana jin daɗin yanayin sosai, suna isowa duk suke zaune suna sake gaisawa duk da sun haɗu masallaci, saida suka gaisa ya nunawa Aliyu kujerun dake wajen mai gadi yace "Ɗauko ku zo ku zauna na ji." Bin umarnin shi Aliyu yayi, jim kaɗan ya dawo da kujerun ya aje suka zauna shi da Jabir, sake kallon su yayi yace "To ina sauraren ku, kun ce akwai maganar da zamuyi idan kuka dawo?" Jabir ne ya fara kallon shi yace "Abba ba yanzu ba, ka bari har jikin ka ya ƙara yin kyau." Murmushi Abban yayi ya dafa kafaɗar shi yace "Karka damu Jabir, burina yanzu shine naga ku manyan ƴaƴan nawa kun hau kan turbar da ta dace, Alhamdulillah kun samu ilimin addinin da nasan ko iya shi kawai ya isheku rayuwa mai nagarta, amma bayan haka ina so na ji abinda kuke son faɗa min da wuri wuri, dan naga ko da taimakon da zan iya muku?" Kallon juna sukayi shi da Aliyu, da idanu suka gama yanke shawarar kawai su sanar da shi ɗin tunda ya matsa, Aliyu ne ya kalli Abban a ladabce yace" Abba, ba wani abu bane dama, kamar yadda kuka sani ina son yin koyarwa, to shine nake so ku tsaya min dan ina son buɗa islamiyya, zan tafiyar da ita ne akan wani tsari da na gani a Madina, sai shi kuma Jabir, kun san dama shi dai ɗan kasuwa ne, kuma har tafiyar can ma bai daina aikin wahala ba dan ya samu kuɗi, to Alhamdulillah ya tara kuɗin kam..." Aliyu yayi maganar yana dariya saboda hararan da Jabir ya watso mishi, dariya Alhaji ma yayi yana ci gaba da sauraren Aliyu da ya ci gaba da faɗin" Ya nemi kuɗi sosai Abba, yayi aikin wahala ya wa larabawa bauta duk dan ya tsaya da ƙafafun shi, da taimakon Allah kuma ya fara siyan kaya a can yana turowa wani abokin mu anan, to Alhamdulillah zan iya cewa ya zama babban gwaska ta nan wajen, dan yanzu haka a Saudia da Madina da Lebanon akwai wasu da yayi sabo da su kuma yake siyan kayan nan namu na gida yana raba musu suna bashi kuɗin, Abba, a taƙaice dai Jabir ya tsayu sosai." Gyara zama Aliyu yayi yace" Abinda yasa na faɗa muku haka Abba, yana son buɗa babban shagon da zai zama a cikin yake ɗaukan kayan da yake rabawa, to shine yake son ka saka masa hannu, dan yana son shagon ya kasance a idanun jama'a ne, sai taimako na gaba kuma da yake buƙata Abba... Conteneur ɗin ka dake yawan tasowa daga Dubai da Chine, yana so idan ana muku lodi ya dinga bada nashi saƙon, idan abubuwa suka yi kyau wata rana shima sai mu rasa wurin zama tsabar yawan conteneur ɗin da ya kawo a garin nan." Dariya Alhaji yayi yana kallon Jabir dake girgiza kai ya rasa me ke damun Aliyu, cike da ƙarfafa guiwa Alhaji yace" Ma sha Allah Jabir, ni dama nasan babban ɗan kasuwa ne za'a yi tun da ka faɗa min har ga-ruwa kayi da wanke wanke a gurin mai siyar da abinci, Allah ya sa albarka Jabir, Allah ya tallafe ka har kai ma ka tallafi dubbunnai." A tare shi d Aliyu suka amsa da" Ameen Abba." Sai kuma ya ɗora da" Duka ba damuwa, na ji buƙatun ku kuma ba zasu gagara ba, da izinin Allah za'a muku yadda kuke so, Allah ya dafa mana." Amsawa suka ƙara yi inda suke ta murmushi da mishi Addu'ar ƙarin lafiya mai anfani, shi kuma shiru yayi na wani lokacin kafin ya kalli Jabir yace" Jabir, akwai wani babban wurin aje kayan gonana dake nan bayan ofishin ƴan sanda kan titin dake zuwa babban likita, me zai hana ka je ka duba? Idan ya maka Kagaai shikenan ko, sai a fara abinda ya kamata, dan gaskiya wurin titi ne sosai kuma fuskar jama'a." Kallon shi Jabir yayi, a nutse ya kamo hannun shi yana tattausawa idanun shi taf da hawaye yace" Abba, ba damar mu zo da abu muna so sai ka mana shi? Abba yaushe ne zaka ce ba zaka mana ba saboda bai dace ba? Abba da wuri haka?" Murmushi ya mishi yace" To ai ku ɗin ne ba kwa zuwa da abinda bai dace ba, shawara kuke yi da kuma hangen nesa kafin ku zo da buƙatar, shiyasa kullum nake jinjinawa tunanin ku." Jinjina kai Jabir yayi yace" Mun gode Abban mu, ba mu san ya zamu yi ba idan ba kai? Abba Allah ƙara maka lafiya da nisan kwana mai albarka." "Ameen Ya Allah." Ya faɗa da fara'a sosai a fuskar shi, Aliyu ya ƙalla dake kallon tsantsar ƙaunar da suke ma juna yace "Aliyu, tunda na siyi wannan gidan na su Hajia Mairo, da gida na so yi muku kai da Jabir da Khamis ku zauna nan dan aure zan muku, to tunda ka zo da maganar nan ina ga zaka iya shiga kai ma Kaga idan girman sa zai maka yadda kake so, Kaga daga nan sai a fara ginin makarantar ko?" Da jin daɗi Aliyu ma ya sumbaci hannun Alhaji yana mishi godiya da addu'a sosai, ba su tashi daga nan ba haka suka ci gaba da tattaunawa har rana ta fito. A shirye auta ta fito sanye da zunbulelen hijab ɗin ta na islamiyyar da ya saka Jabir sake mutuwa akan yarinyar har saida ya furta "Ya Arrahaman." Ba kwalli ko ɗigo ɗaya à fuskar ta, yarinya ce ƙarama, amma shigar nan da tayi ba ƙaramar kamala da fuskar manya ta yafa mata ba, a zahiri kake gane ƴar dattijo da dattijuwa ce, ma'ana ƴar manyan mutane da ta samu tarbiyya, zai so hakan, zai so a bashi ita tun yanzu, ya ji ya gani zai iya rainon ta har sanda za ta gama cikar kamalar ta, amma ba zai juri nesa nesa da ita ba, maza yanzu mace ta gari suke so, dan haka ƙaracin shekarun ta ba zai hana namiji na ƙwarai wawar ta ba. Yadda yake kallon fuskar ta dake ɗauke da murmushi irin na maman ta yasa har ya ɗan shagala da kallon nata, ba tare da sanin shi ba kuma yake taya ta murmushin sakamakon tsokanar da Aliyu ke mata cewa ta kusa daina zuwa islamiyyar kowa sai tashi, amma hakan ba yana nufin za ta makara ya ƙyaleta ba, zane ta zai yi. Da fara'a Abba ya ɗan rumgumata jikin shi yana shafa kan ta yace "Aliyu autata ce fa, ko ni ban taɓa dukan ta ba." Dariya duk suka yi sai Kuwailat dake rufe fuska dan kunya, jin Jabir bai sa baki a maganar ba duk da dama zai yi wuya ya furta wani abun, amma sai Abba ya juya ɓangaren da yake yana faɗin "Kai Jabir ka yarda ya dak..." Ba wai kallon da ya kama Jabir ɗin na ma Kuwailat bane ya bashi mamaki, sai yadda yayi saurin sadda kan shi cike da basarwa da kuma kunyar yadda Alhaji ya kama shi yana kallon ƴar tashi, wani murmushi Alhaji yayi irin shikenan ɗin nan na gano ka tare da dafa Kuwailat yace "Autar Mamien ta, maza kama hanya tafiyar ki, Aliyu bai da tausayi zai iya zane min ke anan." Da fara'a ta kma hanya tana musu bye bye da cewa "Sai na dawo." Ɗaga mata hannu Aliyu yayi yace "A dawo lafiya." Saida ta tafi Alhaji ya sake duban su yace "To yanzu ya maganar aure? Na ji gaba ɗaya tunanin ku kan yadda zaku kyautata rayuwar ku ne kawai, ban ji wani cikin ku yace na je gidan dattijo wani na karɓo masa ragamar kulawa da wata kyakyawar matashiya ba?" Dariya Aliyu yayi inda Jabir ya kalli Alhaji cike da tsarguwa sai kuma yayi murmushi yasx girgiza kai, Aliyu ne ya shafa kan shi cike da kunya yace" In sha Allah Abba, muna nan muna nema shima, da zaran mun samu waɗanda suka dace, zamu izaku gaba ku nemo mana ɗin." Girgiza kai Alhaji yayi da rashin jin daɗi yace" Gaskiya ban ji daɗi ba, ace kamar ku babu ma mai niyya a cikin ku, yadda na so fa shine kuna zuwa da kamar sati ɗaya bikin ku za'a yi." A tausashe sosai cikin ladabi Jabir yace" In sha Allah Abba zamu gabatar muku da su nan da ɗan lokaci." Jinjina kai yayi ba fara'a tare da shi yace" Shikenan, Allah ya yarda, amma ku sani idan naga kun share sati ɗayan nan kuna neman cinye na biyu, to fa zaku gane Abban ku bai da tausayi, dan kuwa tsaf zan nema muku mata ku aura." Murmushi duk sukayi inda Aliyu ya ƙara shafa kanshi yace" A'a Abba, in sha Allah ma ba zata kaimu ga haka ba." Sai Jabir da ya kalli Alhajin da kyau cikin nutsuwa yace" Abba, ko auren je ka ga ɗakin ka kuka mana zamu karɓa da kulawa muyi godiya, kun isa damu ne kuma zamu karɓa muyi biyayya da yardar Allah." Kallon shi Alhaji yayi cike da jin daɗin yadda ya nuna zai masa biyayya, inda Aliyu ya kalli Jabir da mamaki yace" Ka tabbata Alaramma, sami'ina ne wa aɗa'ana?" Da idanu ya amsa mishi da tabbas ta hanyar lumshe su sosai, jinjina kai Aliyu yayi da tsokana yace" Ko da yake ai kana da wurdin da zaka yi ne ku zauna da soyayya, ni kuma ka ga ba ruwana ko?" Murmushi dai Alhaji yayi yana jin farin ciki yadda suke fahimtar junan su a kamar ƴan uwa abun na birge shi. Daga nan ya miƙe ya bar su ya tunkari ɓangaren Ummu da suka fi kusa da shi dan gaishe da matan kamar yadda ya saba kamar ya shirya ɗakin Hajia Atika dan yau ita ce da shi. *In sha Allah mun kusa fara darasi na kayan marmari.* *Alhamdulillah.* 15/08/2023, 20:13 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *39* Ciwon da marar ta ke yi mata mai tsananin gaske yasa ta yin durƙushe dafe da marar tana ta yarfa hannu da faɗin "La'ilaha illallah! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un !" Da sauri Alhaji ya ƙarasa shiga falon tare da druƙusawa yana tabbalo yace "Ummu, ciwon marar ne? Na ce ki je asibiti Ummu, ban san me yasa kika ƙi ba, ce min kawai kike yi to." Cike da ƙarfin hali ta ɗaga kan ta tana basarwa ta dube shi, miƙewa tayi tsaye haka shima tana faɗin "Ina kwana Aban Kuwailat ?" Gatsine fuska yayi da jin haushi yace "Ni ba shi nake miki magana, Kinga maza je ki shirya, zan je na canza kaya mu tafi asibiti, na gaji da wannan wahalar da kan naki da kike ni kuma kina raunata min zuciya." A daddafe ta matsa kusan kujera ta zauna tana faɗin "Ba fa komai, kawai yana murɗa min, ni nafi tunanin al'ada ta ce za ta zo, sai kawai na kwasa na je asibiti dan zanyi baƙon da dama na san da zuwan shi?" Wani kallo ya mata yana dafe ƙugu yace "Ƙarya kike Ummu, ba al'adar ki bace." Wani galala ita ma ta kalle shi tace" Ƙarya kuma? Ni ɗin?" A ɗan kausashe yace" Ke ɗin mana, Ƙarya kike." Haɗe fuska tayi ta kawar da kan ta, maganar ta soke ta sosai, fisabilillah ya kalle ta da girman ta ya ce ƙarya take? Idan ma ƙaryar ce ai ba zai faɗa mata kai tsaye haka ba ko? Sai ya bar abun à ranshi, amma da ɗiyar ta budurwa da shekarun ta *talatin* cif a duniya ya ce ƙarya take kai tsaye, gaskiya ba ta ji daɗi ba kuma ranta ya ɓace. Cikin faɗa Alhaji ya ci gaba da faɗin "Za ki tashi ki shirya ko sai na ɓata miki rai? Ummu ke yarinya ce ƙarama da za'a zauna ana yawan nanata magana da ke?" Wani kallon sama da ƙasa ta mishi tace "Kasan ba yarinya bace ni ka ce ina ƙarya?" Shi fa ya ɗan sha'afa da wacece matar sa, dan haka kuwa ya sake faɗin "E ɗin na faɗa, duka sati biyu da kika gama al'adar ki, to mahaukaciya ce al'adar da zata sake dawo miki yanzu." Tashi tayi tsaye da irin masifa ita ma tace "To kai baka san al'ada bane? Wane irin canji ne ba ta yi wa mata? Idan baka sani ba ka je ka tambaya ka ji, bayan jinin lafiya ai har na ciwo ke akwai, a wata ɗaya ne ba zan iya jini biyu ba? Bayan kuma wasu matan suna iya yin jinin sati biyu har zuwa kwana na goma sha biyar ma, daga nan idan ya wuce ya zama na ciwo, sai ka tsaya kana faɗa min ƙarya kike ƙarya kike kuma ba ko tausasawa ma, da girmana ne zan zauna ina maka ƙaryar?" A hassale ta kama hanyar madafa dan dama girkin da su Aliyu suka saka ta take yi, da kallo ya bita, yadda take maganar alamar ta hassala ne, sai kuma ya tuna da maganar daa ta yi wai da girman ta zai ce tana ƙarya? OK, shine ya sa tayi hushi kenan? To sh yanzu Ummu ta kalle shi ta gaya masa girma? Jinjina kai yayi shima cike da jin ai shine mijin ya bita madafar, daga bakin ƙofa yace "Za ki je asibitin ko na tafiya ta hsabgogina?" Ba tare da ta juyo ba ranta ɓace tace "Ka je kawai, ni dama ban hna ka zuwa sabgogin naka ba ai, kuma nima ina da harkokina da nake yi ai ka sani, ba zaman banza nake yi gidan ba." To! To wai me ya mata? Daga magana? Taɓe baki yayi ya juya zai fice yace "Sannu mai aikin yi, kar ki je ɗin." Duk da ya fita, amma takaicin wai ita zai ce wa kar ta je ɗin? Alhaji raina ta ne yayi ko me? Ita fa ba yarinya bace yanzu, me yasa yake datsa mata magna ne haka ? Da gasken gaske ƙwalla ce ta cika mata idanu, ya sani sarai ta tsani duk abinda zai kawo mata raini a rayuwa, ya sani bata son rashin girmamawa, ko ya fi ta shekaru ai ya mutumta ta saboda ita ma tana da shekarun, cikin wannan ƙwalla dake neman gangaro mata da ɓacin rai ta ɗaga murya tace "B zan je ɗin ba, idan ma asibiti zan je ai ba kai zaka kai ni ba, ni ba yarinya bace zan iya kai kaina, kuma wallahi kar ka sake kulani dan ba zan kula ka ba ni." Yana jin me take faɗa, ta ɗan bashi mamaki da fari na yadda ta hassala lokaci ɗaya, amma kuma sai yaji ta bashi dariya da kuma tausayi, dariyar da ga bashi ita ce yadda da gaske take maganar, tausayin ta kuma da ya kama shi bai wuce yadda ya san Ummu da wani irin hali na son girma ba, ita dai a rayuwar ta a girmama ta kawai, kaɗan ne fa a aikin Ummu ta yi kuka dan kawai ta yi sallama a grp na WhatsApp kuma ga wasu online amma a ƙi amsa ta, da fari da wasa y ɗauki wannan matsalar, amma daga baya ya fahimci kawai hakane take, shiyasa tunda ya gane ta yake girmmata da furta mata kalmar da babu raini a ciki, yau ma ran shi ne ya ɓace ganin ita ba yarinya ba amma ta zauna da ciwo a gida. ******************** Kallon shi Hajia ke yi har ya ƙaraso kan teburin da suke cin abincin, ba mutum ne dake tashi da sassafe ba, yau me ya faru da ya taso warhaka? Wannan mamakin ya sa take kallon shi har ya zauna bayan ya gaishe da mutanen dake wurin, Hajia dake masa wani irin kallo ya kalla yana murmushi yace "Mamie ina kwana?" Ba yabo ba fallasa ta amsa da "Barka da safiya." Maida duban shi yayi ga abincin da duk suke ci, sai ya ture farantin gaban shi kaɗan alamar ba abinci zai ci ba, kofi ya ɗauka ya fara haɗa ma kan sa shayi, babu dai mai cewa komai kowa na abinda ke gaban shi, saida aka kwashe mintuna haka kafin Yaya Bilal ya kalle shi yace "Jiya da muka dawo daga gidan su Fati baka nan, har na kwanta ni dai ban ji shigowar ka ba." Kallon shi yayi da girmamawa yace "Hakane, na ɗan je wani wuri ne." Ajiyar zuciya Yaya Bilal ɗin ya sauke tare da ci gaba da cin abincin shi yace "Dama dan mu sanar da kai ne kawu Abbas ya amince da auren ka da Fatima, Abbu kuma ya saka rana nan da juma'a mai zuwa in sha Allah, dan haka ka fara shiri." Wani kallo ya ma Yaya Bilal ɗin a rashin sani irin mai kama da hararan nan, sai kawai yayi wani irin murmushi dake nuna kuma dai da wasa kuke, saida ya ƙara kurɓa shayin shi sannan yace" Yaya Bilal, akwai wacce nake so na aura, Nabila, kun san ta ai dan jiya ta zo nan, ban so mu samu matsala da ku akan maganar aurena, ko mace yanzu ba'a mata auren da bata so bare kuma namiji, na yarda muna rayuwa ni da Nabila wacce bata da kyau, amma ko ma menene ni na koya mata komai, dan a gaban iyayen ta na same ta, dalilina ta fara yin nesa har take bijirewa umarnin su, ita akwai abinda take hango mana wanda take ganin bai dace muyi aure tun yanzu ba, ni kuma na kawo mata hujojjin d suka fi nata ƙarfi tare da nuna mata auren shi ya fi alkairi gare mu ko dan mutumcin ku, na sha wahala sosai kafin na sa ta yarda za ta yi aure dani yanzu, kuna ganin ya dace na juya mata baya a wannan gaɓar? Dan Allah ku barni na aure ta, tun farko na fara son ta ne saboda soyayya ta aure, sheɗan ne kawai ya rinjaye mu har muka dinga abinda bai dace ba." Sosai da sosai Abbu Mukhtar ya fahimci Fahad, bai san me yasa ya ji ya bashi tausayi ba har da ita yarinyar kan ta? Haka kuma bai san me yasa ya ji ya dace a bar su suyi aure ba? Ko dan ƴaƴan shi duka mata ne? Shi dai a ganin shi suyi aure, tunda har ya gamsu zai iya zama da ita ai ba matsala bane, kuma ya faɗa da bakin shi shi ya fara kangarar da ita, to ya iyayen ta za su ji idan aka ce ya juya mata baya? Gaskiya ba adalci a ciki. Abbu kuma da jin haushi ya kalle shi yace "Me zai faru idan ba'a bar ka ka auren ta ba?" Kallon fuskar Abbu ɗin ya yi, sai bai ce komai ba ya ƙurawa kofin dake gaban shi idanu, hakan yasa Alhaji faɗin "To ba zaka aure ta ba, na faɗa maka haka ba tun yanzu ba, wataƙila ka ɗauka wasa nake maka shiyasa, ka yarda ka auri Fatima ita ce ta dace da kai saboda tarbiyyar ta, amma yarinyar da kake so ka kawo mana cikin ahalin mu, sam bata dace ba dan ƴar ƙananan mutane ce..." Da sauri Fahad ya katse shi a kausashe da cewa" A'a Abbu, kar ka zargi iyayen ta akan gurɓacewar tarbiyyar ta, wai me yasa kake hakane? Shikenan duk wanda bai da tarbiyya to laifin iyayen sa ne? To me zaka ce a game da ni kenan? Kenan da gaske sakacin ku ne ko naka?" A tsawace Sabeer ya miƙe yana neman cakumo Fahad tare da faɗin "Fahad! Mahaifin namu kake faɗawa haka?" Da sauri Yaya Bilal da ya san yana dukan shi Hajia za ta fara hawaye yayi gaggawar riƙe shi yace "Kar ka taɓa shi Sabeer, yi masa magana kawai." Cike da takaici Sabeer ya kalli Yaya Bilal ɗin kamar zai cije shi yace "Wai me yasa kuke hakane? Yaron nan tun ba yau ba ya kamata a ɗauki mataki akan iskanxin shi, amma da nayi yunƙurin haka sai ku hana, me yasa? Ta hakane zai gyaru? Har kamar Fahad ne zai zauna Abbu na faɗa yana faɗa? Bai kamata ɗaya a cikin mu ya ladabtar da shi ba?" Ba tare da ya miƙe tsaye ba ya kalli Yaya Sabeer ɗin yana taɓe baki yace" Gaskiya fa na faɗa, iyayen Nabila mutanen kirki, mahaifin ta ma fa baya raye, mahaifiyar ta kuma matar arziki ce, wacce kullum take ɗaukar ƴaƴan kowa a matsayin nata..." Hajia da ta cije leɓe dan hana kanta kuka ya kalla yace" Mamie, kin san wani abu? Uwar marayu fa ake kiran ta a unguwar su, ba wai ga wanda ya rasa uwa ko uba ba, hatta yaran da suka ɓata gidan ta ake kai su, ni ban taɓa ganin mutuniyar kirki a wannan zamanin ba kamar ita, ta aurar da yarinyar da ba ita ce ta haife ta ba, ta raini ɗan ƙanwar ta har ya yi aure shima, idan ba Nabila da ta faɗa min ba, ban taɓa sanin ba ita ta haife su ba." Sai kuma ya kalli Alhaji da ke ta kallon shi jikin shi na tsuma yace" Duk girman gidan nan da kuɗin ka da alfarmar ka da ikon ka wa ka taɓa ɗaukowa a gidan marayu ko cikin ƴaƴan ƴan uwa ka raina har ya cimma wata matsaya a rayuwar sa ? Babu Abbu, kai dai kullum daga mu wanda ka haifa sai iyalen mu da jikokin ka, akan su kaɗai kake tayar da hankalin ka, amma wa yake neman taimako? Wa yake cikin matsala, wa ya kwana bai ci ba? Wa ke buƙatar kuɗin magani? Duk bai shafe ka ba, ban ce baka taimako ba, ina so ne dai na nuna maka dattakon iyayen Nabila, sai sun fita suke nemowa su kawo a ci, suna iya kwana basu ci ba kafin yanzu, amma a haka suke sake ɗaukar ragamar kula da wasu ba tare da tunanin yadda za su yi ba..." Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ci gaba da kallon kofin shayin shi yace" Ko ma dai menene Nabila yarinyar kirki ce kafin ta haɗu da ni, ni na fara keta rigar mutumcin ta, ni na fara miƙa mata zaren shisha a hannu, ni na fara bata kwalbar sirup ta sha, sannan ni na fara koya mata shan sigari, bayan wannan har...har c..." Ƙara sunkuyar da kanshi yayi sosai yace" Kuyi haƙuri idan na ɓata muku rai, amma har ciki nayi wa Nabila kuma na umarce ta aka zubar da shi, rayuwarta ta shiga garari a wannan lokacin, amma haka ta samu lafiya kamar ba abinda ya faru, ni na sa Nabila take shan maganin hana ɗaukar ciki, yanzu saboda Allah ya dace na juya mata baya." Wani irin kuka mai sauti Hajia ta fashe da shi, wanda hakan yasa Sabeer jan wani wawan tsaki tare da ture kujerar shi a zuciye ya bar falon, dan idan ya ci gaba da zama tsaf zai taka wuyan Fahad ya yanka shi, da kallo matar shi ta bi shi tana ayyana _" Ran maza ya sosu fa, yau sai yadda ta yiwu."_ Mama Nuriyya kuma Fahad take kallo, wani mugun tunani ne ya ɗarsu a zuciyar ta, wannan tunanin kuwa shine _" Yanzu idan fa Kuwailat ɗin ta ta haɗu da namiji irin Fahad, shikenan haka take rayuwa a gurɓace?"_, Ƙwarai ta ji tausayin yarinyar da iyayen ta ya kamata, musamman ma dai mahaifiyar ta da take ganin za ta fi shiga tashin hankali, hakan yasa har tayi kuskuren tsoma bakin ta ta hanyar kallon Abbu da yayi kamar baya da rai tace" Abbu, dan Allah ka barsu su auri junan su, tunda ya ji ya gani ita yake so, auren ya fi alkairi akan rashin yin auren." Saida ta dire Abbu ya juya a hankali kalle ta, da mamakin kalaman ta yace" Nuriyya, na bari ya aure ta fa kika ce? Ina alkairi a auren da aka ɗaura bayan rashin sanin darajar juna? A ganin ku auren su zai zama alkairi ne? Ko yayi ƙarkon da ake da buƙata a kowane aure? Ba zai yiwu ba, saboda auren ƴan tasha ne, ni kuma in dai ina raye ba za'a yi wannan auren ba, dan duk inda aka je a ka dawo za'a nuna wannan ƴar duniyar ne a matsayin surukar Ahlan, ba zai yiwu ba na faɗa muku." A kausashe Fahad ya miƙe tsaye shima yana kallon Alhajin yace" Shikenan, tunda ka ce haka ni zan bar maka gidan ka sai na je a ɗaura mana aure da ita, zan goge sunan Ahlan daga gaban sunana, ka ga kenan sai a kirani da sunan mahaifin Nabila, tunda shi dattijo ne." Duk da rashin zuciyar shi kamar ta Sabeer, saida ya jefe shi da cokalin hannun shi ya kira sunan shi a kausashe, suna haɗa idanun nan nashi masu maiƙo da charme Fahad ya nemi fitsarar nan ya rasa, Shiyasa ma fa tun farko yake ta rusunawa yana tausasa murya, dan idan Abbu Mukhtar na wuri ya fi ƙarfin yayi rashin kunya. Kafin ya ci gaba da yi masa wannan kallon ya dubi Hajia da ta rufe idanun ta da tissue tana share hawaye ya dafa kafaɗar ta a raunane yace "Mamie, na wa Nabila alƙawarin za ta zo ta gaishe ki yau saboda yadda haɗuwar ku ta jiya ta kasance, dan Allah Mamie ki nema min mutumci a gurin ta ta hanyar tarban ta da mutumtawa, daga yau ba lallai ki sake ganin mu a kusa dake ba, bare har mu saka ki kuka." Da sauri ta ɗago ta kalle shi da mamakin kalaman shi, amma da ya juya ya fice daga falon da sauri sai ta sake fashewa da wani sabon kukan, Fa'iza da abun ya fi ƙarfin tunanin ta, da ƙyar ta taso ita da matar Sabeer suna rarrashin Hajia kan tayi haƙuri. Abbu Mukhtar kuma da idanu ya ma Yaya Bilal nuni da Abbu, hakan yasa suka tashi tare suka kama hannayen shi suka nufi ɗakin baccin shi da shi, dan gaba ɗaya jikin shi ya saki baya cikin nutsuwa. Saida suka kwantar da shi sannan suka fito, Yaya Bilal da ya ƙufula ya hassala ne ya kalli Hajia yace "Mamie ki daina kuka, ba ya ce za ta zo ba yau? Ba laifi ta zo, zai ga yadda ake tarba, na rantse da girman Allah ɗaure yariyar nan zan yi." Da sauri Hajia ta kalle shi, haka ma Mama Nuriyya da ta ji kamar ya ɗaure ta kuma? A dake ta sannan a hana ta kuka? Ga mari ga tsinka jaka? Haba dai, rashin adalcin yayi yawa, Abbu Mukhtar ma duban shi yayi a sanyaye yace" Ba zaka ɗaure ta ba, idan kayi haka abinda muke gudu ne zai faru, wato zubewar mutumci, dan Abbu yayi hushi ne sosai, amma ni da za'a ji shawarata a aura musu juna kawai, ba adalci ya lalata ƴar mutane kuma a ce ba zai aure ta ba, haka na faruwa da mata dayawa, idan ya ƙaurace mata zai iya haɗuwa da hukunci tun anan duniya, me zai hana mu musu fatan hakan ya zama silar shiriya gare su?" A kausashe Yaya Bilal ya kalle shi yace" A amince wai? Ya za ka faɗi haka kai ma dai kamar wanda y..." Da sauri Hajia ta miƙe tsaye fuskar ta a ɗaure tace" Ba Ya ce za ta zo ba, to ta zo ɗin, ni zan tarbe ta, bana buƙatar taimakon kowa akan yadda zan karɓi baƙuawata, dan haka kowa ya min shiru da bakin shi a wurin nan." Raɓasu tayi za ta bar falon sai kuma ta dakata ta juyo ta kalli Yaya Bilal tace" Ka kira Alhaji Abbas, ka faɗa masa ni nake neman Fati, dan Allah ya turo dreba a kawo min ita anjima." Da mamaki suka kalle ta, amma sai Yaya Bilal ya amsa da" Shikenan Mamie." Duk sun yi mamakin me ya sa Mamie za ta ce a kawo Fati anjima? Amma dai ba wanda ya zurfafa tunani suka kama gaban su daga wurin suma kowa zuciyar shi a jagule. ******************* Ya jima tsaye yana so ya samu wanda zai ba wa farantin dake hannun shi ya miƙawa Maama, fita yake so yayi ga shi kuma Aliyu ya riga shi fita ma, ba ya so kuma ya tura mi gadi saboda tunanin ai gwara ma a ce shi ya ki dan shi *ɗan ta* ne, amma mai gadi sam bai dace ba gaskiya. Gyara tsayuwa yayi ya ɗan taka da tunanin bari kawai ya sallama ya kai da kan shi, sai kuma ya ji an turo ƙaramar ƙofa alamar ana shigowa, yana juyawa ya saki wani murmushi, dalili biyu ya sa shi wannan murmushin, na farko shine yadda ya ga wacce zai iya cewa yana mararin son gani, na biyu kuma ita tafi kowa dacewa da ta kai kwanukan. Sai dai murmushin nashi bai kai ko ina ba ya tsaya cak saboda ganin ta ɗauke da wata ƙatuwar leda da kuma jug har guda biyu a hannun ta, ƙiri-ƙiri kake gane kayan sun mata nauyi dan da ƙyar take ɗaukar su. Kamar wani bita-zai zai sai kawai ya nufe ta da niyyar taimaka mata, ina dalili a ce ƴar Kuwailat ce ke lailayar kayan nan. Ita ma tana ganin shi ta saki murmushi tare da sunkuyawa ta aje kayan hannun ta tana yarfa hannun ta tana cewa "Washhhh! Wallahi nauyi kayan." Da fari ƙura mata idanu yayi har ta gama maganar ta, sai ya ga kamar kallon yayi yawa, hakan yasa ya dubi ledar da ta aje ƙasa ya tara hannu alamar ta bashi yace "Kin gaji ne?" Saida ta kyaɓe fuska cike da shagwaɓa tace "Na gaji wallahi, a daidai kwana na haɗu da Yaya Khalis, shine ya bani wai na kawo wa Mamie kayan ta ne da aka kai abinci shago." Ledar ta ɗauka ta miƙa masa, hakan ya sa shi yin gaba yana faɗin "Muje." Bayan shi ta bi da sauran kayan har suka kai ɓangaren nasu, dakatawa yayi sai ita ta shi gaba tare da yin sallama a gajiye, hakan yasa Ummu dake kwance tana kallon sama tayi nisa a tunani sam ba ta ji ba, yaye labulen tayi, dake Ummu na kwance ne kan kujerar dake kallon ƙofar ɗakin baccin ta, hakan yasa ta ba ƙofar shigowa baya sosai, Kuwailat kuma da ta ji ƙamshin girki na fitowa daga madafa sai ta ɗauka tana ciki, musamman da ba ta ji an amsa sallamar ta ba, kai tsaye madafar ta nufa tana faɗin "Yaya Jabir shigo ka aje kayan falo, zan dawo na ɗauka yanzu." Jin haka sai ya tabbatar wa kan sa ba kowa kenan, dan haka ya yi dubara ya ɗaga labulen tare da yin wata irin sanyayyar sallama can ƙasan maƙoshi... *In sha Allah Litinin za mu fara darasin.* *Alhamdulillah.* 15/08/2023, 20:13 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *40* Ɗaga labulen yayi da dubara cikin wata sanyayyar sallama can ƙasan maƙoshi.... Ummu da tun da Kuwailat ta ambaci Yaya Jabir Ummu ta zabura ta tashi zaune tana juya da kallon ƙofar, tashin da ta yi ne kuma ya sa ta ji saukar hawaye a kumatun ta masu zafi da ya nuna mata tunanin matsalar ta da take yi yasa ba ta ma ji hawayen na fita ba sai saukar su kawai. Haɗa idanu suka yi da Jabir, hakan yasa shi ganin wannan hawayen da suka ma kumatun ta ƙawanya, mummunan faɗuwan gaba ne ya ziyarce shi, abu ɗaya tunanin shi ya haska mishi shine *me ya sa Maama ke kuka?* Dama tana da matsalar da ke damun ta ne a gidan nan ko a rayuwa? E, kowane ɗan adam yana da abun da ke damun shi, amma bai so hakan ba ko kaɗan, bai so a ce matsalar Maama ta kai girman da take saka ta zubar da hawaye ba. Sai kuma ya ji rashin jin daɗi na yadda ya shigo har ya ga haka, na ɗaya daga cikin Dalilin da suka sa aka ce a nemi izini kafin shiga wurin da ba naka ba. A kunya ya ɗan ƙarasa tare da sunkuyawa ya aje kwanukan, tsaye yayi kan kujera yana kallon ƙasa ba ya son duban fuskar ta musamman da ya ga ba hijabi jikin ta, cike da kulawa ya furta "Maama, lafiya?" Saida ta gayyato murmushi kafin ta ƙara gyara zaman ta ta girgiza kai tana share hawayen tace "Ba komai, ai da baka zo da kan ka ba ma, ko Kuwailat za ta je ta ɗauko." *A* hankali ya cira matsakaitan idanun shi ya dire a fuskar ta, wani irin kallo na tausasawa da girmamawa ya mata, sannan ya sake ɗorawa da "Maama, kuka fa kike?" Faɗaɗa murmushi tayi a dole sai take ta nuna ba komai tare da haɗe hannayen ta tace "Ba komai fa Jabir, kawai dai... Kar ka damu Jabir." Cirawa tayi da irin azamar nan tayi tsaye, doguwar riga ce jikin ta kuma ba ta wani kama jikin ta ba, hakan ya haifar da ƙararrawar jigidar ta wacce ke yawan motsawa duk sanda ta jijjiga jikin ta, wani irin tsammmm! Ya ji jikin shi ya amsa, da sauri ya juya ba tare da ya amsa mata kawai ya kama hanyar barin ɗakin har idanun shi na neman lumshewa. Ya salam! Ya salam ! Maama dama ba ta girma da saka abaun nan na yara ba? Maama dama har yanzu tana ɗauke da abun nan a ƙugun ta? Maama dama duk shekarun nan ba ta canza ba? Ya salam! Ita ta saka kuma Kuwailat ma ta saka? Wani shu'umin murmushi yayi na gefen laɓɓa, sai kawai ya girgiza kai yana ayyana _"Wataƙila idan Kuwailat ta fara haifa mata jikoki ta daina."_ Tana shirin shiga madafa Kuwailat na fitowa, murmushi tayi tace "Mamie, ashe kina nan?" Kallon ta kawai tayi, gaban Jabir ma daurewa ne ta yi, raɓata kawai tayi ta wuce tana cewa "Ɗauko kayan can." "To." Ta faɗa tana wucewa, ita ma tana shiga ta duba tukunyar ta ta koma ta dawo ta zauna, wayar ta ta ɗauka dan yanzu Kuwailat na gidan ba ta so ta nuna fuskar damuwa ko ya ya, a hankali take bin duk abubuwan da aka yi a grp ɗin nasu na gado, har sai da ta ci karo da wani posting da aka yi wai abinda mace za ta haɗa tasha, ba iya ni'ima zai ƙara mata ba har da shi kan shi mijin zai sa ya jima yana jima'i. Duk abinda aka ce zai ƙarawa namiji kuzari tana son shi, dan haka ba jayayya ba tunanin ba lallai gaskiya bane ta hardace abubuwan, kuma mafi yawa tana da su ajiye kaɗan ne za ta nemo ma, dan haka kuwa ta rubuta kayan da take da buƙatar ta tura Kuwailat ta kira mata mai aikin Hajia babba sannan ta aike ta nemo su. Ba gardama mai aikin ta karɓa dan tasan aiken Hajia Ummu alkairi ne gare ta ba kaɗan ba ******************* Tun da Fati ta zo gidan take mamakin dalilin da ya sa aka kira ta, ita dai ta ga ko a baya ba wani abu ke kawo ta gidan ba, gashi tun da ta zo ita ba a saka ta wani aiki ba, kuma ba komai ake mata ba, da fari tayi tunanin to ko nufin su ta tare kenn har a ɗaura auren? Ita gaskiya ba ma ta son Fahad, tana da saurayin ta wanda ya kasance malami gare ta, dan haka ita Abban ta take so idan ya mata maganar sai ta faɗa masa a'a ba ta so, bayan haka ma ai lokacin da aka saka ya yi kusa sosai, lokaci ne aka sa da ya yi kama da na wanda ke akwai wata matsala ana so a ɗaura auren da gaggawa, to ta ji ma a tafi a haka, ita gaskiya ko wanda take so ɗin ba za ta yarda a ɗaura mata aure da shi ba a ƙasa da sati uku ma, bare kuma wannan aure da take tunanin idan har ya yiwu to za ta iya kiran shi da *RUBUTACCIYAR TA*. Yanzu haka zaman ne ya ishe ta har ta shiga madafa ita da masu aiki suna aiki, ba ta taɓa ƙarewa madafar kallo ba sai yau, ba wai maganar haɗuwar ta take yi ba, yadda dai aka kashe dukiya tamkar ba wani talaka dake da buƙata ne yake bata mamaki, ta kusa hauka kuwa sa'ilin da ta ga wajen ajiyar kayan abinci da aka buɗa za'a ɗauko ƙwai da maggi, ko wane mahaluki ya samu wannan a matsayin katafaren shagon sa to sai fatan kasuwa mai albarka, dan a yadda dama ta taɓa ji daga wurin ƴan uwa shine kayan abincin su ma trela ce ke sauke su, dan komai tanne ake zubewa, ta tabbatar yau da ta ga makeken gurin da aka ware dan zuba kayan abincin da ita ta tabbatar a shekara biyar ba zasu cinye su ba, shiyasa duk ƙarshen shekara suke fito da kayan abincin ana rabawa talakawa sai a zuba sabin fitowa kula sabuwar ƙira. Sun kammala aikin su tsaf suna gyara madafar ba tare da tunanin komai ba Fati ke aikin nan da ma'aikata, sai kawai wata mai aikin da ke kai kayan abincin kan teburi ta shigo tana faɗin "Hajia Fatima, Hajia na miki magana." Juyowa tayi ta kalle ta, duk da mahaifin ta ya kai ta ƙasa mai tsarki kuma ta sauke farali, amma dai girman da suke bata kamar ya fi ƙarfin shekarun ta, dan haka tayi murmushi a sauƙaƙe tace "Ke ma dai, ki kira ni da Fati kawai, ba sai kin ce Hajia ba." Murmushi mai aikin tayi tana ganin sauƙin kan nan tace "Ai Hajia ce, kuma Hajia ta faɗa mana ke ce wacce Alhaji Fahad zai aura." Murmushi kawai tayi ba ta ce komai ba tare da juyawa tana wanke hannayen ta tace "Shikenan, gani nan zuwa." *Falo* kuwa minti ashirin da ya gabata suka karɓi baƙuncin Nabila bisa jagorancin Fahad da ya ɗauko ta tun daga masaukin da ta sauka har zuwa nan ɗin, jar abaya ta saka mai duwatsu da kyau da tsada, ba ta yi kwalliya ba ko kaɗan face hoda da ta shafa, cikin nutsuwa ta zo gida har ranta tana jin za ta auri Fahad, dan haka za ta girmama ahalin shi da mutum ta shi kan shi Fahad ɗin. Tun da ta shigo falon da sallama ta ga mace har uku zaune amma babu wacce ta amsa mata sallamar da kulawa a cikin su, da taimakon jagorancin da Fahad ke mata ta zauna kan ta a ƙasa ba ta haɗa ido da ko ɗaya daga cikin matan ba, cike da kunya da rusunawa ta sunkuya tana gaishe su, Mama Nuriyya da ita dai take jin kamar ba'a kyautawa ce ta dinga amsa mata har da ƴar fara'ar ta, amma Fa'iza wannan miskilancin nata ne ke aiki da kuma mamakin rashin kunyar Nabila da Yaya Bilal ya bata labarin haɗuwar su ta jiya, inda Hajia ma mamakin ne take na Nabila da kuma ƙarfin halin ta. Ma'aikaciyar nan da ta fito ɗauke da kwanuka Mama Nuriyya ta kalla tace "Jummai, ki kawo wa baƙ..." A daƙile cike da gadara Hajia ta dube ta tare da ɗaga hannu tace "Bar shi kawai Nuriyya." Sai kuma ta kalli inda Nabila take zaune kanta ƙasa har lokacin, Fahad dake ta zabga murmushi yana tsaye ne ya kalli Hajia da tunanin ko akwai wani tanadi da ta ma Nabilar da ya sa ta dakatar da Mama Nuriyya, zaune yayi kusan Nabila yana duban su Hajia da Mama Nuriyya yace "Mamiena, aunty Nur, aunty Fa'iza, ga Nabila." Murmushi kawai Nabila tayi tana ƙara sadda kan ta ƙasa, Mama Nuriyya ce ta sake yin murmushi tace "Ma sha Allah, Nabila, sannun ku? Tubarkallah da ita kuwa." Cike da jin daɗi Fahad yace "Nagode aunty Nur." Murmushi ita ma tayi tace "Ba komai, Allah ya tabbatar mana da alkairi." Da wani sabon farin ciki ya sake amsawa da "Ameen aunty Nur." Shiru ɗakin ya ɗan ɗauka na sakanni, hakan ya ba Fahad damar kallon Hajia da ba ta ce komai ba sai kallon Nabila yace "Mamie... Ga Nabila." Ƙafa Hajia ta ɗora kan ɗaya tana ci gaba da kallon Nabila tace "Na gani, Nabila ko?" Sai kuma tayi murmushi ta kalli Nabila tace "Ki ɗago kan ki mana, mu ne fa, ko baki gane mu bane? Jiya ai kin zo nan muka gaisa ko? Kuma naga jiya ba haka kika zo mana ba." Wulwula idanu Nabila tayi da kanta ke ƙasa gabanta ya fara faɗuwa, Fahad ma dai jikin nashi ne ya fara wani yanayi saboda sam bai tsammaci haka zai iya faruwa ba. Kallon shi Hajia tayi tace" Fahad, ka samu Bilal a ɓangaren shi, ka ce ya zo ina son magana da shi." Kallon Hajia ya yi, sai yake jin baya da nutsuwa ko kaɗan, amma sai ya kasa musa mata musamman ma da ya yi alƙawarin zancawa, dan haka ya miƙe ya tafi zuciyar shi ba daɗi yana kuma jin kamar akwai wani abu, saida ta ga ficewar shi ta saki wani murmushi. Zama Hajia ta gyara sosai cikin wata dakakkiyyar murya tana kallon Nabila tace" Ke! Nabila." Yadda Hajia ta kira sunan ta ya fi ƙarfin ta share, dole ta ɗago kan ta ta dubi Hajia har ta amsa da" Na'am." A kausashe Hajia ta furta" Kalle ni da kyau, bana buƙatar sadda kan ki a yau, ki kalle ni kamar dai jiya sannan kiyi magana da ni kan ki tsaye, ni ce mahaifiyar Fahad, amma ban da mahimmanci gare ki, tunda har kika iya zuwa min gida jiya kika yi abinda kike so." Da yatsa ta nuno ta tana mai sake kausasa murya tace" Kina ji, bana son auren ki da Fahad, gaskiyata ce nake faɗa miki, ba kuma iya ni kaɗai ba, har da mahaifin shi da ma duk wani dake gidan nan, idan kika auri Fahad a haka to sai dai idan za'a yi ɗaya cikin biyu, imma ki fuskanci ƙiyayya da muzgunawar mu, ko kuma dai kuyi nesa ku auri juna ba tare da albarkar mu ba, dan haka nake so in shaida miki ki fita a harkar Fahad, dan ba zamu yarda ki aure shi ba, mu ba mahaukata bane da zamu yarda haka ta faru bayan kun gama lalacewa a waje, dan haka ki cire shi a rayuwar ki, ki manta da shi gaba ɗaya." Tana gama faɗa kuma mai aikin nan ta dawo, shine ta kalle ta tace "Kice Fatima ta zo." *Fati* na fitowa ta same zaune tare kuma da baƙuwar fuskar d ba ta sani ba, dan haka a nutse ta ƙaraso tsakiyar falon, duk dai ba wani girma ne ta gani a fuskar Nabila ba, amma da ladabi ta kalle ta tace "Sannu, ina wuni ?" Wani kallo Nabila ta mata irin ba ka hayyacin ka, gashi dai tana ji, kuma tana gani ma, kum har abinda Hajia ɗin ta faɗa ta fahimci abinda take so ta fahimta, amma dai jikin ta ya ƙi yarda da saƙon, sai take ji da kuma gani kamar Fahad ya kawo ta ne dama dan a faɗa mata haka. Hajia ce ta katse mata tunani sanda ta nuna Fati da yatsa sannan tace "Kinga wannan? Ƴar ƙanin mahaifin Fahad ce, ita ce zai aura nan da kwana shida masu zuwa, ki dube ta da kyau ki gani, shigar ta, kamalar ta, nutsuwar ta, tarbiyyar ta ba, ke har ma da nasabar ta duk mun gamsu da su, dan haka nake sake jadadda miki Nabila ki fita harkar Fahad, ba ta yadda zamu yarda ya aure ki, ku haihu yaran ki watarana su tambaye mu _da gaske maman su ƴar shaye-shaye ce_? Ban shirya ba wa ɗan uban kowa wannan amsar ba, dan haka can ki ƙara ta da tsiyar ki, yanzu tashi ki fice min a gida kafin Fahad ya dawo." Saida Nabila ta runtse idanun ta, kuka wanda za ta iya kira da kuka, irin kukan nan da ake cewa daga zuciya yake, shi ta ji tana yi a lokacin, ƙwarai hawaye da take jin ana faɗa masu zafi, ba ta sani ba ko rasuwar mahaifin ta tayi kuka irin haka, dan gaskiya bata da cikakken wayon da za ta fahimta, amma dai bayan shi bata taɓa kuka irin wannan ba, tun daga irin dukan da Yaya Luƙman da ma Yaya Mujjittafa suke mata, zuwa faɗan da Mama da Ummu ke mata, har kan faɗa da cin mutumcin juna da suke da Fahad, zuwa ga ranar farko ma da ya fara keta mata mutumci, duk babu ranar da ta ma irin kukan nan da take jin yanzu yana taho mata kuma ba alamar tsayawa. A hankali ta buɗa idanun ta sauke kan ƙafafun Fati dake tsaye tana kallon ta da tunanin dama ita ce budurwar Fahad ɗin? To me yasa Hajia ke faɗa mata haka? Ai kamar bai dace ba ko? Hakan yasa Fati ta ji ta tsargu sosai, sai take fatan Allah ya sa dai ba iya wannan dalilin bane kawai ya sa aka gayyato ta gidan nan, dan tunda ta zo bayan gaisuwa da wasu tambayoyi bakin su bai ƙara haɗuwa da na Hajia ba, dan magana ta gaskiya ahalin Ahlan akwai wani abu da ake kira wai shi *isa* da *gadara* gare su, ba dan komai ba sai dan kuɗi da Allah ya basu, shiyasa duk alaƙar su wallahi ba ta shiga shirginsu sai in da dalili mai ƙarfin gaske. Ƙwarai Nabila kan dogaten ƙafafun Fati ta fara sauke duban ta, zuwa surar ta dake cikin wani shanɓareren hijab mai hannaye, fara ce tass da ita fiye ma da Fahad, kuma ba za ka ce mata mummuna ba gaskiya, dan tana da idanu da matsakaicin baki, gashi fuskar ta ma ba kwalliya sai kamala da kuma tabon sallah dake manne a goshin ta ya yi baƙi. Ƙwarai wannan ta fi dacewa da Fahad, ƙara lumshe idanu tayi wasu hawayen suka sake zubowa har wasu na korar wasu, jiki a sanyaye ta miƙe da wani irin ƙwarin guiwar jin ta haƙura da Fahad kenan har abada, ko da kuwa shi ne autan maza, ko kuma soyayyar shi za ta kashe ta. Ba ta waiwaya gare su ba, ba ta kalli kowa a cikin su ba ta kama hanya tana share hawaye, tana kai wa ƙofa Fahad na shigowa suka haɗe, ba tare da ta goge hawayen ta ba take kallon shi kamar yadda yake ta tsare ta da idanu yana aika mata da tambayar kukan nan fa? Ina kuma za ta je? Cikin sanyayyar mrya yace "Beela, me aka miki kike kuka? Ina za ki je ?" Cikin kakkausan murya amma a tausashe tace "Ba komai kawai, ka je wajen Maman ka tana neman ka." Raɓa shi tayi za ta wuce da azama da yanayin tashin hankalin da ya fara ziyartar shi na hango wasu abubuwa dake bayyane, tura shi kiran Yaya Bilal da shia yaje can ya tsare shi da wasu maganganu marasa kan gadon da basu shafe shi ba, zuwa yanzu da yake ganin Nabila na kuka haka, tattausan riƙo ya ma hannun ta yace "Me ye? Me aka miki? Faɗ..." Fizge hannun ta tayi, sannan ta sa hannu da ƙarfi kuma cikin ɓacin rai ta tura shi gefe har ya kai wa bango karo, sannan ta nuna shi da yatsa tace "Kar ka sake taɓa jikina Fahad, ka fita a rayuwata dan Allah, daga yau ka manta da wannan tantiriya kuma fitsararriyar Nabilan da ka sani a rayuwar ka, nima daga yau ba zan sake ta'ammali da mai irin sunan ka ba ma bare na tuna da kai a rayuwata, dan haka ka rabu da ni ka je ga zaɓin iyayen ka." A haukace ta taka ta fice daga falon, sai kuma ta tuna wata magana da bata faɗa mishi ba, hakan yasa ta juyowa ta dawo da ƙarfin tsiya, yayin da shi ma Fahad ya sake aniyar bin bayan ta, hakan yasa suka kusa yin karo da junan su, nuna shi ta yi da yatsa tana wani bahagon murmushi tace "Kasan me? Ni shashasha ce, da nayi tatoo saboda kai har na rubuta sunan ka, sannan na aske gashin kaina duk saboda kai, sannan na canza suffata ta asali duk dan ka ji daɗin mu'amala dani, amma daga yau komai ya ƙare, na manta da cewa ɗan duniya ba ya auren ƴar duniya kamar sa, sai dai mace irin waccen..." Ta faɗa da nuno inda Fati ke tsaye, sannan ta ɗora da" Amma ka sani, mu ma iyaye ne suka haife mu, kuma da tarbiyyar mu kuke ganin mu, ku kuke ruguza mana komai, daga baya kuma ku watsar da mu, amma ba komai, mu zamu muku alkairi, sannan akwai ranar da zaku ji kunyar abin nan da kuka aikata, *Fahad Saheeb Ahlan*." Taɓe baki tayi ta sake wucewa kamar iska za ta kwashe ta zuwa sama ta fice a gidan, inda Fahad kuma ya tsaya jin ba'asin me ya faru? Mama Nuriyya à ranta ta ji cewa yarinyar nan duk abinda ta faɗa da Hajia ne take ba Fahad ba, kuma gaskiya ta bata tausayi yarinyar sosai. Fahad ko dake tambayar me ya faru Hajia ta masa shiru, à haukace ya nuna Fati da yatsa yace "Akan wannan ce ko? To bana so, bana son ta Hajia ku kai kasuwa idan ta rasa miji ne, amma ku sani ba ku kyauta min ba, ko me zaku mata ku mata ba sa'ilin da ni na gayyace ta gidan nan ba, amma hakan da kuka yi, ya sake nuna min nan ɗin ƙaramin gida ne." A fusace ya juya zuwa ga Fati dake tsaye ta rasa abun yi, kamar zai cije ta yace" Ki fita a sabgata, ni bana son ki." Ƙasa da sama ya kalle ta a hassale ya fita a gidan shima, Fati m'a da taji zafin maganar nan da gudu ta juya zuwa ɗakin Hajia da ta bar jakar ta a can dan ta bar musu gidan su, dan sai yanzu ne ta gano dalilin zuwan ta gidan nan. *Alhamdulillah.* 15/08/2023, 20:13 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *40* Ɗaga labulen yayi da dubara cikin wata sanyayyar sallama can ƙasan maƙoshi.... Ummu da tun da Kuwailat ta ambaci Yaya Jabir Ummu ta zabura ta tashi zaune tana juya da kallon ƙofar, tashin da ta yi ne kuma ya sa ta ji saukar hawaye a kumatun ta masu zafi da ya nuna mata tunanin matsalar ta da take yi yasa ba ta ma ji hawayen na fita ba sai saukar su kawai. Haɗa idanu suka yi da Jabir, hakan yasa shi ganin wannan hawayen da suka ma kumatun ta ƙawanya, mummunan faɗuwan gaba ne ya ziyarce shi, abu ɗaya tunanin shi ya haska mishi shine *me ya sa Maama ke kuka?* Dama tana da matsalar da ke damun ta ne a gidan nan ko a rayuwa? E, kowane ɗan adam yana da abun da ke damun shi, amma bai so hakan ba ko kaɗan, bai so a ce matsalar Maama ta kai girman da take saka ta zubar da hawaye ba. Sai kuma ya ji rashin jin daɗi na yadda ya shigo har ya ga haka, na ɗaya daga cikin Dalilin da suka sa aka ce a nemi izini kafin shiga wurin da ba naka ba. A kunya ya ɗan ƙarasa tare da sunkuyawa ya aje kwanukan, tsaye yayi kan kujera yana kallon ƙasa ba ya son duban fuskar ta musamman da ya ga ba hijabi jikin ta, cike da kulawa ya furta "Maama, lafiya?" Saida ta gayyato murmushi kafin ta ƙara gyara zaman ta ta girgiza kai tana share hawayen tace "Ba komai, ai da baka zo da kan ka ba ma, ko Kuwailat za ta je ta ɗauko." *A* hankali ya cira matsakaitan idanun shi ya dire a fuskar ta, wani irin kallo na tausasawa da girmamawa ya mata, sannan ya sake ɗorawa da "Maama, kuka fa kike?" Faɗaɗa murmushi tayi a dole sai take ta nuna ba komai tare da haɗe hannayen ta tace "Ba komai fa Jabir, kawai dai... Kar ka damu Jabir." Cirawa tayi da irin azamar nan tayi tsaye, doguwar riga ce jikin ta kuma ba ta wani kama jikin ta ba, hakan ya haifar da ƙararrawar jigidar ta wacce ke yawan motsawa duk sanda ta jijjiga jikin ta, wani irin tsammmm! Ya ji jikin shi ya amsa, da sauri ya juya ba tare da ya amsa mata kawai ya kama hanyar barin ɗakin har idanun shi na neman lumshewa. Ya salam! Ya salam ! Maama dama ba ta girma da saka abaun nan na yara ba? Maama dama har yanzu tana ɗauke da abun nan a ƙugun ta? Maama dama duk shekarun nan ba ta canza ba? Ya salam! Ita ta saka kuma Kuwailat ma ta saka? Wani shu'umin murmushi yayi na gefen laɓɓa, sai kawai ya girgiza kai yana ayyana _"Wataƙila idan Kuwailat ta fara haifa mata jikoki ta daina."_ Tana shirin shiga madafa Kuwailat na fitowa, murmushi tayi tace "Mamie, ashe kina nan?" Kallon ta kawai tayi, gaban Jabir ma daurewa ne ta yi, raɓata kawai tayi ta wuce tana cewa "Ɗauko kayan can." "To." Ta faɗa tana wucewa, ita ma tana shiga ta duba tukunyar ta ta koma ta dawo ta zauna, wayar ta ta ɗauka dan yanzu Kuwailat na gidan ba ta so ta nuna fuskar damuwa ko ya ya, a hankali take bin duk abubuwan da aka yi a grp ɗin nasu na gado, har sai da ta ci karo da wani posting da aka yi wai abinda mace za ta haɗa tasha, ba iya ni'ima zai ƙara mata ba har da shi kan shi mijin zai sa ya jima yana jima'i. Duk abinda aka ce zai ƙarawa namiji kuzari tana son shi, dan haka ba jayayya ba tunanin ba lallai gaskiya bane ta hardace abubuwan, kuma mafi yawa tana da su ajiye kaɗan ne za ta nemo ma, dan haka kuwa ta rubuta kayan da take da buƙatar ta tura Kuwailat ta kira mata mai aikin Hajia babba sannan ta aike ta nemo su. Ba gardama mai aikin ta karɓa dan tasan aiken Hajia Ummu alkairi ne gare ta ba kaɗan ba ******************* Tun da Fati ta zo gidan take mamakin dalilin da ya sa aka kira ta, ita dai ta ga ko a baya ba wani abu ke kawo ta gidan ba, gashi tun da ta zo ita ba a saka ta wani aiki ba, kuma ba komai ake mata ba, da fari tayi tunanin to ko nufin su ta tare kenn har a ɗaura auren? Ita gaskiya ba ma ta son Fahad, tana da saurayin ta wanda ya kasance malami gare ta, dan haka ita Abban ta take so idan ya mata maganar sai ta faɗa masa a'a ba ta so, bayan haka ma ai lokacin da aka saka ya yi kusa sosai, lokaci ne aka sa da ya yi kama da na wanda ke akwai wata matsala ana so a ɗaura auren da gaggawa, to ta ji ma a tafi a haka, ita gaskiya ko wanda take so ɗin ba za ta yarda a ɗaura mata aure da shi ba a ƙasa da sati uku ma, bare kuma wannan aure da take tunanin idan har ya yiwu to za ta iya kiran shi da *RUBUTACCIYAR TA*. Yanzu haka zaman ne ya ishe ta har ta shiga madafa ita da masu aiki suna aiki, ba ta taɓa ƙarewa madafar kallo ba sai yau, ba wai maganar haɗuwar ta take yi ba, yadda dai aka kashe dukiya tamkar ba wani talaka dake da buƙata ne yake bata mamaki, ta kusa hauka kuwa sa'ilin da ta ga wajen ajiyar kayan abinci da aka buɗa za'a ɗauko ƙwai da maggi, ko wane mahaluki ya samu wannan a matsayin katafaren shagon sa to sai fatan kasuwa mai albarka, dan a yadda dama ta taɓa ji daga wurin ƴan uwa shine kayan abincin su ma trela ce ke sauke su, dan komai tanne ake zubewa, ta tabbatar yau da ta ga makeken gurin da aka ware dan zuba kayan abincin da ita ta tabbatar a shekara biyar ba zasu cinye su ba, shiyasa duk ƙarshen shekara suke fito da kayan abincin ana rabawa talakawa sai a zuba sabin fitowa kula sabuwar ƙira. Sun kammala aikin su tsaf suna gyara madafar ba tare da tunanin komai ba Fati ke aikin nan da ma'aikata, sai kawai wata mai aikin da ke kai kayan abincin kan teburi ta shigo tana faɗin "Hajia Fatima, Hajia na miki magana." Juyowa tayi ta kalle ta, duk da mahaifin ta ya kai ta ƙasa mai tsarki kuma ta sauke farali, amma dai girman da suke bata kamar ya fi ƙarfin shekarun ta, dan haka tayi murmushi a sauƙaƙe tace "Ke ma dai, ki kira ni da Fati kawai, ba sai kin ce Hajia ba." Murmushi mai aikin tayi tana ganin sauƙin kan nan tace "Ai Hajia ce, kuma Hajia ta faɗa mana ke ce wacce Alhaji Fahad zai aura." Murmushi kawai tayi ba ta ce komai ba tare da juyawa tana wanke hannayen ta tace "Shikenan, gani nan zuwa." *Falo* kuwa minti ashirin da ya gabata suka karɓi baƙuncin Nabila bisa jagorancin Fahad da ya ɗauko ta tun daga masaukin da ta sauka har zuwa nan ɗin, jar abaya ta saka mai duwatsu da kyau da tsada, ba ta yi kwalliya ba ko kaɗan face hoda da ta shafa, cikin nutsuwa ta zo gida har ranta tana jin za ta auri Fahad, dan haka za ta girmama ahalin shi da mutum ta shi kan shi Fahad ɗin. Tun da ta shigo falon da sallama ta ga mace har uku zaune amma babu wacce ta amsa mata sallamar da kulawa a cikin su, da taimakon jagorancin da Fahad ke mata ta zauna kan ta a ƙasa ba ta haɗa ido da ko ɗaya daga cikin matan ba, cike da kunya da rusunawa ta sunkuya tana gaishe su, Mama Nuriyya da ita dai take jin kamar ba'a kyautawa ce ta dinga amsa mata har da ƴar fara'ar ta, amma Fa'iza wannan miskilancin nata ne ke aiki da kuma mamakin rashin kunyar Nabila da Yaya Bilal ya bata labarin haɗuwar su ta jiya, inda Hajia ma mamakin ne take na Nabila da kuma ƙarfin halin ta. Ma'aikaciyar nan da ta fito ɗauke da kwanuka Mama Nuriyya ta kalla tace "Jummai, ki kawo wa baƙ..." A daƙile cike da gadara Hajia ta dube ta tare da ɗaga hannu tace "Bar shi kawai Nuriyya." Sai kuma ta kalli inda Nabila take zaune kanta ƙasa har lokacin, Fahad dake ta zabga murmushi yana tsaye ne ya kalli Hajia da tunanin ko akwai wani tanadi da ta ma Nabilar da ya sa ta dakatar da Mama Nuriyya, zaune yayi kusan Nabila yana duban su Hajia da Mama Nuriyya yace "Mamiena, aunty Nur, aunty Fa'iza, ga Nabila." Murmushi kawai Nabila tayi tana ƙara sadda kan ta ƙasa, Mama Nuriyya ce ta sake yin murmushi tace "Ma sha Allah, Nabila, sannun ku? Tubarkallah da ita kuwa." Cike da jin daɗi Fahad yace "Nagode aunty Nur." Murmushi ita ma tayi tace "Ba komai, Allah ya tabbatar mana da alkairi." Da wani sabon farin ciki ya sake amsawa da "Ameen aunty Nur." Shiru ɗakin ya ɗan ɗauka na sakanni, hakan ya ba Fahad damar kallon Hajia da ba ta ce komai ba sai kallon Nabila yace "Mamie... Ga Nabila." Ƙafa Hajia ta ɗora kan ɗaya tana ci gaba da kallon Nabila tace "Na gani, Nabila ko?" Sai kuma tayi murmushi ta kalli Nabila tace "Ki ɗago kan ki mana, mu ne fa, ko baki gane mu bane? Jiya ai kin zo nan muka gaisa ko? Kuma naga jiya ba haka kika zo mana ba." Wulwula idanu Nabila tayi da kanta ke ƙasa gabanta ya fara faɗuwa, Fahad ma dai jikin nashi ne ya fara wani yanayi saboda sam bai tsammaci haka zai iya faruwa ba. Kallon shi Hajia tayi tace" Fahad, ka samu Bilal a ɓangaren shi, ka ce ya zo ina son magana da shi." Kallon Hajia ya yi, sai yake jin baya da nutsuwa ko kaɗan, amma sai ya kasa musa mata musamman ma da ya yi alƙawarin zancawa, dan haka ya miƙe ya tafi zuciyar shi ba daɗi yana kuma jin kamar akwai wani abu, saida ta ga ficewar shi ta saki wani murmushi. Zama Hajia ta gyara sosai cikin wata dakakkiyyar murya tana kallon Nabila tace" Ke! Nabila." Yadda Hajia ta kira sunan ta ya fi ƙarfin ta share, dole ta ɗago kan ta ta dubi Hajia har ta amsa da" Na'am." A kausashe Hajia ta furta" Kalle ni da kyau, bana buƙatar sadda kan ki a yau, ki kalle ni kamar dai jiya sannan kiyi magana da ni kan ki tsaye, ni ce mahaifiyar Fahad, amma ban da mahimmanci gare ki, tunda har kika iya zuwa min gida jiya kika yi abinda kike so." Da yatsa ta nuno ta tana mai sake kausasa murya tace" Kina ji, bana son auren ki da Fahad, gaskiyata ce nake faɗa miki, ba kuma iya ni kaɗai ba, har da mahaifin shi da ma duk wani dake gidan nan, idan kika auri Fahad a haka to sai dai idan za'a yi ɗaya cikin biyu, imma ki fuskanci ƙiyayya da muzgunawar mu, ko kuma dai kuyi nesa ku auri juna ba tare da albarkar mu ba, dan haka nake so in shaida miki ki fita a harkar Fahad, dan ba zamu yarda ki aure shi ba, mu ba mahaukata bane da zamu yarda haka ta faru bayan kun gama lalacewa a waje, dan haka ki cire shi a rayuwar ki, ki manta da shi gaba ɗaya." Tana gama faɗa kuma mai aikin nan ta dawo, shine ta kalle ta tace "Kice Fatima ta zo." *Fati* na fitowa ta same zaune tare kuma da baƙuwar fuskar d ba ta sani ba, dan haka a nutse ta ƙaraso tsakiyar falon, duk dai ba wani girma ne ta gani a fuskar Nabila ba, amma da ladabi ta kalle ta tace "Sannu, ina wuni ?" Wani kallo Nabila ta mata irin ba ka hayyacin ka, gashi dai tana ji, kuma tana gani ma, kum har abinda Hajia ɗin ta faɗa ta fahimci abinda take so ta fahimta, amma dai jikin ta ya ƙi yarda da saƙon, sai take ji da kuma gani kamar Fahad ya kawo ta ne dama dan a faɗa mata haka. Hajia ce ta katse mata tunani sanda ta nuna Fati da yatsa sannan tace "Kinga wannan? Ƴar ƙanin mahaifin Fahad ce, ita ce zai aura nan da kwana shida masu zuwa, ki dube ta da kyau ki gani, shigar ta, kamalar ta, nutsuwar ta, tarbiyyar ta ba, ke har ma da nasabar ta duk mun gamsu da su, dan haka nake sake jadadda miki Nabila ki fita harkar Fahad, ba ta yadda zamu yarda ya aure ki, ku haihu yaran ki watarana su tambaye mu _da gaske maman su ƴar shaye-shaye ce_? Ban shirya ba wa ɗan uban kowa wannan amsar ba, dan haka can ki ƙara ta da tsiyar ki, yanzu tashi ki fice min a gida kafin Fahad ya dawo." Saida Nabila ta runtse idanun ta, kuka wanda za ta iya kira da kuka, irin kukan nan da ake cewa daga zuciya yake, shi ta ji tana yi a lokacin, ƙwarai hawaye da take jin ana faɗa masu zafi, ba ta sani ba ko rasuwar mahaifin ta tayi kuka irin haka, dan gaskiya bata da cikakken wayon da za ta fahimta, amma dai bayan shi bata taɓa kuka irin wannan ba, tun daga irin dukan da Yaya Luƙman da ma Yaya Mujjittafa suke mata, zuwa faɗan da Mama da Ummu ke mata, har kan faɗa da cin mutumcin juna da suke da Fahad, zuwa ga ranar farko ma da ya fara keta mata mutumci, duk babu ranar da ta ma irin kukan nan da take jin yanzu yana taho mata kuma ba alamar tsayawa. A hankali ta buɗa idanun ta sauke kan ƙafafun Fati dake tsaye tana kallon ta da tunanin dama ita ce budurwar Fahad ɗin? To me yasa Hajia ke faɗa mata haka? Ai kamar bai dace ba ko? Hakan yasa Fati ta ji ta tsargu sosai, sai take fatan Allah ya sa dai ba iya wannan dalilin bane kawai ya sa aka gayyato ta gidan nan, dan tunda ta zo bayan gaisuwa da wasu tambayoyi bakin su bai ƙara haɗuwa da na Hajia ba, dan magana ta gaskiya ahalin Ahlan akwai wani abu da ake kira wai shi *isa* da *gadara* gare su, ba dan komai ba sai dan kuɗi da Allah ya basu, shiyasa duk alaƙar su wallahi ba ta shiga shirginsu sai in da dalili mai ƙarfin gaske. Ƙwarai Nabila kan dogaten ƙafafun Fati ta fara sauke duban ta, zuwa surar ta dake cikin wani shanɓareren hijab mai hannaye, fara ce tass da ita fiye ma da Fahad, kuma ba za ka ce mata mummuna ba gaskiya, dan tana da idanu da matsakaicin baki, gashi fuskar ta ma ba kwalliya sai kamala da kuma tabon sallah dake manne a goshin ta ya yi baƙi. Ƙwarai wannan ta fi dacewa da Fahad, ƙara lumshe idanu tayi wasu hawayen suka sake zubowa har wasu na korar wasu, jiki a sanyaye ta miƙe da wani irin ƙwarin guiwar jin ta haƙura da Fahad kenan har abada, ko da kuwa shi ne autan maza, ko kuma soyayyar shi za ta kashe ta. Ba ta waiwaya gare su ba, ba ta kalli kowa a cikin su ba ta kama hanya tana share hawaye, tana kai wa ƙofa Fahad na shigowa suka haɗe, ba tare da ta goge hawayen ta ba take kallon shi kamar yadda yake ta tsare ta da idanu yana aika mata da tambayar kukan nan fa? Ina kuma za ta je? Cikin sanyayyar mrya yace "Beela, me aka miki kike kuka? Ina za ki je ?" Cikin kakkausan murya amma a tausashe tace "Ba komai kawai, ka je wajen Maman ka tana neman ka." Raɓa shi tayi za ta wuce da azama da yanayin tashin hankalin da ya fara ziyartar shi na hango wasu abubuwa dake bayyane, tura shi kiran Yaya Bilal da shia yaje can ya tsare shi da wasu maganganu marasa kan gadon da basu shafe shi ba, zuwa yanzu da yake ganin Nabila na kuka haka, tattausan riƙo ya ma hannun ta yace "Me ye? Me aka miki? Faɗ..." Fizge hannun ta tayi, sannan ta sa hannu da ƙarfi kuma cikin ɓacin rai ta tura shi gefe har ya kai wa bango karo, sannan ta nuna shi da yatsa tace "Kar ka sake taɓa jikina Fahad, ka fita a rayuwata dan Allah, daga yau ka manta da wannan tantiriya kuma fitsararriyar Nabilan da ka sani a rayuwar ka, nima daga yau ba zan sake ta'ammali da mai irin sunan ka ba ma bare na tuna da kai a rayuwata, dan haka ka rabu da ni ka je ga zaɓin iyayen ka." A haukace ta taka ta fice daga falon, sai kuma ta tuna wata magana da bata faɗa mishi ba, hakan yasa ta juyowa ta dawo da ƙarfin tsiya, yayin da shi ma Fahad ya sake aniyar bin bayan ta, hakan yasa suka kusa yin karo da junan su, nuna shi ta yi da yatsa tana wani bahagon murmushi tace "Kasan me? Ni shashasha ce, da nayi tatoo saboda kai har na rubuta sunan ka, sannan na aske gashin kaina duk saboda kai, sannan na canza suffata ta asali duk dan ka ji daɗin mu'amala dani, amma daga yau komai ya ƙare, na manta da cewa ɗan duniya ba ya auren ƴar duniya kamar sa, sai dai mace irin waccen..." Ta faɗa da nuno inda Fati ke tsaye, sannan ta ɗora da" Amma ka sani, mu ma iyaye ne suka haife mu, kuma da tarbiyyar mu kuke ganin mu, ku kuke ruguza mana komai, daga baya kuma ku watsar da mu, amma ba komai, mu zamu muku alkairi, sannan akwai ranar da zaku ji kunyar abin nan da kuka aikata, *Fahad Saheeb Ahlan*." Taɓe baki tayi ta sake wucewa kamar iska za ta kwashe ta zuwa sama ta fice a gidan, inda Fahad kuma ya tsaya jin ba'asin me ya faru? Mama Nuriyya à ranta ta ji cewa yarinyar nan duk abinda ta faɗa da Hajia ne take ba Fahad ba, kuma gaskiya ta bata tausayi yarinyar sosai. Fahad ko dake tambayar me ya faru Hajia ta masa shiru, à haukace ya nuna Fati da yatsa yace "Akan wannan ce ko? To bana so, bana son ta Hajia ku kai kasuwa idan ta rasa miji ne, amma ku sani ba ku kyauta min ba, ko me zaku mata ku mata ba sa'ilin da ni na gayyace ta gidan nan ba, amma hakan da kuka yi, ya sake nuna min nan ɗin ƙaramin gida ne." A fusace ya juya zuwa ga Fati dake tsaye ta rasa abun yi, kamar zai cije ta yace" Ki fita a sabgata, ni bana son ki." Ƙasa da sama ya kalle ta a hassale ya fita a gidan shima, Fati m'a da taji zafin maganar nan da gudu ta juya zuwa ɗakin Hajia da ta bar jakar ta a can dan ta bar musu gidan su, dan sai yanzu ne ta gano dalilin zuwan ta gidan nan. *Alhamdulillah.* 15/08/2023, 20:13 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *41* Tana fita kamar wani tsari ta ci karo da taxi, dan haka ko da Fahad ya bi bayan ta bai gan ta ba, kuka take kamar ranta zai fita, kuka ne da ita dai a sanin da ta ma rayuwar ta bata taɓa yin irin shi ba, amma sai gashi yau tana yi dalilin wulaƙantata da aka yi, tsaf taxi ya kai hôtel ɗin ta ta sauka ta biya shi, har za ta shiga ciki sai ta tuna tabbas Fahad zai zo nan, ita kuma bata son sake haɗuwa da shi, dan haka da azamar ta kama wata hanyar daban duk da bata san ina za ta kai ta ba ga kuma magrib da aka fara kira. A cikin tafiyar ta ta haɗu da wurin siyar da magani, cikin kukan nan har muryar ta ta shaƙe ta siyi magani na ruwa na tari har da na ciwon kai, garin neman canji da mutumin ke yi Nabila ta ɗauke kwalin sigari guda dan tana buƙata, kuma ta san tana cewa ya bata za'a dinga mata wani kallo, dan haka ta ce ya bata ashana guda ɗaya kafin ya bata canjin. Tana tafiya daga nan duhu ya sake yi, a wani fili ta zauna bakin bishiya ba tare da tunanin komai ba ta buɗe kwalbar maganin nan ta kifa kan ta, saida ta shanye tas ta dafe kan ta saboda juya mata da yake yi, ba ta sha maganin ciwon kan ba sai sigari da ta sake bankawa wuta. Komai dake faruwa a rayuwar mu da ma mafari gare shi, dalilin abun nan da ya faru Nabila bata iya tashi daga nan ba saboda ta bugu sosai har bacci ya ɗauke ta tamkar wacce aka zarewa rai. Inda Fahad ke can y a neman ta tare da kiran wayar ta da ke ƙara sannu sannu ba yadda za ta damu mutum ba. Matasan gari ne suka ga Nabila a wurin, daga post ɗin ta, zuwa ƴan kunnen ta na zibare da Fahad ya siya mata, har kan sarƙar ƙafar Ummu dake ƙafar ta da agogo, har takalmin ta da ranar sakawa na biyu ta musu masu kyau da tsada ne, haka suka yaye ta suka bar ta nan yashe ba ta san me ke faruwa ba. *Dama* tunda Sabeer yayi aure Alhaji ya sa aka buɗa mishi ƙofar da za ta shigo da Sabeer ɗin ɓangaren su kai tsaye, da wannan ne kowace asuba Alhaji ya kan je ya tashi Sabeer, duk da mafi yawan lokutta yana samun su a farke, amma dake ya sba sai ya je ya tashe shi sai su je masallaci tare. Tun da safe jiya da abinda ya faru ya farun nan bai sake fita ko masallaci ba, hakan ya sa ma saida limamin masallacin ya leƙo da magrib dan duba ko lafiya, wanda ka saba gani yau kuma shiru ba labari, ya fita suka jima suna hira har isha'i kafin ya dawo, kuma lafiya lau suka kwanta da shi da fatan ganin safiya lafiya. Sai dai komai mafari gare shi, Hajia ta gigice yadda ta kasa aiwatar da komai bayan ta fahimci da gawar Alhaji take kwance, jikin shi sanyi ƙalau yadda ta kasa bambamce tun da suka kwanta ne rai yayi halinsa? Ko kuma dai bayan dre ya raba ne ko kuma ma yanzu kusan asubar? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Kawai take maimaitawa a bakin ta, ta ƙi yin kuka kuma ta ƙi tashi daga nan kan gadon da take bare ta nemi ɗauki. Sabeer na ta duba lokaci ya ga lokacin da Alhaji ke zuwa ya wuce bai zo ba, gashi ana daf da tayar da sallah, sai kawai shi ya fito ya kuma zo dan duba ko lafiya? Ya ƙwanƙwasa amma shiru Hajia ta kasa mishi magana, dan haka ya ji hankalin shi bai kwanta ba, to iyayen su biyu a ce ba wanda ya amsa idan lafiya? Turo ƙofar yayi a hankali yana ɗan zuro kai, Hajia da ya gani a yanayin da bai taɓa ganin ta ba ya sa ya kutso kai cikin ɗakin. *Sun* tsinci kan su a tashin hankalin da ba su saka mishi rana ba, sun yi jimami da ƙoƙarin kwantarwa da mahaifiyarsu hankali wacce suka ga ta fi su shiga ɗimuwa. Suna wannan yanayin Fahad da bi kwana gidan ba ya shigo a hargitse, niyyar sa ita ce ya buɗe wuta kan abinda aka ma Nabila dan bai gan ta ba tun jiya, yarinyar mutane ta zo saboda shi, amma ya neme ta ya rasa? Sai dai ba wannan ba, mahaifin da ya haife shi ma ya shi duniyar ya bar musu baki ɗaya, ga dai shi kwance cikin farin yadin da ake lulluɓe tsoho da yaro, mace da namiji, mai kuɗi da kuma talaka, tunano abubuwan da suka faru tsakanin shi da mahaifin na shi, da yadda yake masa magana, da yadda ya bijire masa, irin ɓacin ran da ya dinga saka shi, sai ganin Fahad sukayi ƙasa ya suma saboda bala'in zafi da nauyi da kan shi ya ɗauka. *Rigar kowa* (mutuwa), ta su Alhaji ta ƙare daga nan, mai kyau aka aikata ko akasin haka, wannan dukiyar da gida na alfarma, da Soyayyar nan ta iyali duk ya bar su a nan gidan duniya, inda aka ɗauke shi da aikin shi izuwa gida na haƙiƙa, iko, dukiya, taƙama da isa duk an bar wa *magada*. Allah ka sa mu cika da imani. ******************* Halin da ta samu kan ta bayan farkawar ta daga baccin da bai da maraba da suma ya matuƙar sake ɗaga hankalin ta da dawo mata da damuwar ta sabuwa fil a leda, ba komai na jikin ta face doguwar rigar, dan kallabin ta ma iska ne ya fara kaɗashi har mai buƙata ya yi gaa da shi, ba komai, ba komai a tare da ita, ba kuɗin komawa gida, ba mana taxi bare ta kai ga komawa gida, kuma ba abun siyarwa. Ba wannan ne ya fi ɗaga mata hankali ba, yanzu da ace wanda suka yasheta ba kayan jikin ta kaɗai suka ɗauka ba, in da fa har da fyaɗe suka mata? A halin da take ba za ta iya hana su ba, da shikenan an ci banza kenan? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! Wannan shi ya fi ɗaga mata hankali har ta durƙushe tana faɗin "Tirrr! Tirrr ! Nabila ba ki wa kanki adalci ba, wannan wace irin rayuwa ce? Shaye-shaye bai yi ba, Nabila kin cuci kan ki." Sai kuma ta zabura ta tashi kamar mahaukaciya ta kama hanyar zuwa hôtel ɗin ta ɗauki ko da kayan ta ta kama hanyar komawa mahaifar ta. Da ƙyar suka bar ta ta shiga dake sun san ta, amma yadda suka ga bata da ko takalmi sun ɗauka sabuwar kamu ce, haka ta tattaro kayan ta sannan ta canza kaya ta bar hôtel ɗin, dake safiya ce sosai ɗaya daga cikin ma'aikatan ya bata aron waya ta kira uwa maba da mama, uwar ta mai share kukan ta wato Ummu... Ummu dake ta kai da kawo a tsakar ɗaki ta kasa zaune ta kasa tsaye tun jiya da ta sha abun da ya fi ƙarfin ta da ƙudirin ta samu kan Alhaji, amma ƙiri-ƙiri ya nuna mata ba fa kwanan ta bane, shi kuma ba zai yarda mata su kai shi wuta ba, har saida ta kai tana roƙon ya mata ko da wasa ne amma ya ce baya so su wuce gona da iri, haka ya fita ya bar ta ba tausayi bare tunanin halin da za ta shiga. Kiran da Nabila ta mata ya katse mata tunanin da take yi ta ɗaga, cikin matsanancin kuka Nabila ta furta "Aunty Ummu, aunty Ummu." Take hankalin ta ya watse, tunanin damuwar ta ya gushe, da kulawa ta furta "Nabila, ke ce? Lafiya? Me ya faru? Me aka miki?" Cikin kuka Nabila ta sake cewa "Ni ce aunty Ummu... Dan Allah ki taimaka min?" Hankali tashe Ummu ta sake faɗin "Nabila, kuka fa kike? Faɗa min me ya faru? Me aka miki?" Cikin tsananin kuka Nabila tana share idanu tace "Aunty Ummu sun kore ni, sun wulaƙanta ni, sun ce bana da tarbiyya da mutumci, ni kawai gida zan dawo, aunty bana da kuɗin mota, dan Allah ki taimaka, ina so na zo gida wajen ki yau." Lumshe idanu Ummu tayi tace "Hasbunallah wani'imal wakil!" Shiru tayi na sakanni kafin tace "Kina ina Nabila?" A taƙaice ta furta "Agadez." Cikin rarrashi Ummu tace "Shikenan, karki damu, bari na bayar a ciro miki ticket, komai dare za ki zo gida yau in sha Allah." Cikin kuka tace "To aunty, nagode." Da sauri Ummu tace "Sannan, ki riƙe katin ki da kyau, zan tura miki kuɗin da zaki sha ruwa a hanya, kin ji?" Wani Sabon kuka Nabila ta fashe da shi tace "Aunty an sace komai nawa, shiyasa na kira ki da wata wayar, sun kwashe komai aunty, har..har sarƙar ki ma." Cikin kulawa Ummu tace "Subhanallah, amma dai babu abinda ya same ki ko?" Girgiza kai Nabila tayi tace "Babu, idan na zo zamuyi magana aunty, kaina ciwo yake sosai." Da haka suka yi sallama Ummu ta manta da matsalar ta saboda neman Khamis da tayi ta tura shi ya ciro ticket ɗin, da kuma taimakon shi aka samu abokin shi dake aiki a wurin tura kuɗi Nabila ta samu kuɗi a hannun ta kashh! Ba jimawa ta hau mota dan dawowa garin ta, kuma har lokacin ba ta daina kuka ba sboda abubuwa dayawa dake ta zuwa mata ƙwaƙwalwa. ******************** Tun la'asar ciwon marar nan ya sake tsananta gare ta, a daddafe tayi sallah ta canza kaya, wuya tayi wuya sai gashi da kan ta ta ba Kuwailat wayar ta tace ta kira Baban ta ce za ta tafi asibiti, kafin ta kira shi ɗaki ta koma ta saka pad kamar wata mai jinin haila saboda tun jiyan nan take yoyo wanda ba ta jin daɗi haka ko kaɗan, fatan ta ita dai ba wata gagarumar matsala bace, yana bata OK ta sa kai ta fita a motar ta zuwa asibitin kuɗin. Bayan cika ƙa'ida da sharuɗai dai ta samu ganin likita daf da magariba. Tsura mata idanu ya yi, tun yana kallon ta da gilashi har ya cire ya aje shi gefe, jim kaɗan ya fara ɗan lashe baki yana tausasa kallon shi gare ta kamar mai son jawo hankalin ta, ba yarinya bace ita, kuma sarai ta gane me kallon shi ke nufi gare ta, amma ba ta san matsalar ta ce ta jawo yake mata wannan kallon ba. Haɗe fuska tayi sosai, ba dan rashin kunya ba ya kalli kamar ta yasan dai ta girme shi, amma yana mata wannan iskancin? Mtsssss! A ɗan kausashe tace "Ina ji likita, sauri nake, ina da abun yi." Muƙut! Ya haɗiye yawu tare da gyara zama, alƙalamin hannun shi ya fara wasa da shi cike da shaƙiyanci yace "Madam, matsalar ki ba babba bace idan kika ɗauki mataki, ba wani abu yake damun ki ba, kuma ba ciki bane kamar yadda kika ce kina tunani, kawai dai hanyar fitar ruwa ce ba'a buɗe ba." Yatsina fuska tayi tace "Ban gane ba? Fahimtar da ni?" Saida ya wulwula idanu sannan ya sake gyara zama cikin raɗa yana tsare fuskar ta da kallo yace "Kin gane, kamar dai kwalbatin da ya cika da ruwa, sai kuma aka toshe ƙofofin da zai iya ambaliya, Kinga ai an cutar da shi, dan cikin biyu za'a yi ɗaya, imma ya yi bindiga ya fashe ya shafi gidan kowa, imma a bashi hanya ya wuce." Da irin hassala ta nuna kan ta tace" Zauren ce ka min, nufin ni ce kwalbatin?" Cike da shaƙiyanci likitan ya sake tausasa murya yace" Madam, kin fi kwalbati, dan ke alamu ya nuna ƙorama ce, ƴar talatin fa ce, shekarun haɗari ga mata kenan, Madam, mafitar ki ɗaya ce, ko ki samu mai fito da ruwan nan, k..." Da azama ta miƙe tsaye tana huci, kallon shi take a kausashe sosai tace" Wallahi ba dan a aikin ka na same ka ba, da na tsintsinkawa fuskar ka mari, banza da bai san darajar mace ba, ka dinga bu irin na mutane mana, amma wannan ai halayyar alade ka ke yi." Ƙasa da sama ta harare shi tare da ɗaukar katin ta da jakar ta da makullin mota zata fice tace" Kare kawai, kuma! Allah ba zai barka haka ba wallahi, komai daren daɗewa sai an wa wacce ka fi so a rayuwar ka haka." A ƙufule ta fita daga ofishin nashi, tana kaiwa daidai ciriddor da babu mutane ta durƙushe ta fashe da wani irin kuka marar sauti... *Jabir* da shima fitowar shi kenan daga gurin wani likita da suka san juna ya kuma yi alƙawarin kawo masa ziyara ne ya tsaya cak, bai gane wacece ba dan fuskar rufe take tsakanin guiwowyin ta, amma dai ya ji ba daɗi duba da mace ce a wurin tana kukan wata matsala, gashi kuma alamun ta ya nuna mai aure ce, dan haka kuma ba ya so ya mata magana tunda bai san ta ba. A hankali yake takawa kamar mai sanɗa zai wyce, sautin takalmin mutum da Ummu ta ji ya sa ta saurin ɗago kai ta kalli inda take jin sautin, suna haɗa idanu da Jabir da mamakin ya aka yi ya zo nan? Ta san kuma sai ya tambaye ta, dan haka ta zabura ta miƙe tsaye ba tare da ta juya ba kawai ta kama hanya da sauri dan bata so ya mata wata magana. Tun miƙewar ta tsaye makullin motar ya faɗi da niƙab ɗin ta dake rataye jikin hannun jakar ta, mamakin ganin ita ce da kuma yadda ta fita ya sake tabbatar masa da matsalar dai kenan? A hankali ya tako ya ɗauki makullin da niƙab ɗin sannan ya fita shi ma. Jikin motar ya same ta tana ta duba jakar ta, har ya tsaya gefen ta yana kallon yada take neman makullin a rikice hannayen ta sai ɓari suke bata san yana tsaye ba, ya gane ba zata iya tuƙi ba, sai kawai ya furta "Gashi nan, mu je." Daga haka bai sake cewa komai ba, motar kawai ya buɗe ya shiga tare da tayar wa, kallon shi tayi, karo na farko da ta ji halin shi bai mata ba, ita ce zai wani cewa wai gashi nan, Muje? Kamar wani mai iko da ita? Tsaye tayi tana kallon shi ranta duk ya sake ɓacewa, inda Jabir kuma ke ta kallon hanya ynajiran ta shigo kuma yayi niyyar ba zai sake mata magana ba sai dai su kwana wurin nan. Tsamukar da marar ta ta sake yi, da kuma jin kamar jini ya bulbulo ta gaban ta yasa ta dafe marar ta cije leɓe, a hankali ta shiga takawa har ta buɗe baya ta zauna idanun ta a rufe, waina idanu Jabir ya yi sannan ya tayar da motar suka bar harabar asibitin. Yadda idanun ta ke rufe haka ta ke hango likitan nan yana mata kallon iskanci da maganganun da basu dace ba, shaf sai ta manta tare da wa take ta fashe da kuka na ƙunar rai da takaici, a hankali Jabir ya ji jikin shi na tsuma, tsigar jikin shi na tashi saboda yadda take rera kuka, nutsuwar kuma da gaske neman ƙwace masa take yi, dan haka yayi gaggawar taka birki a inda ya dace ya yi shiru, ita ma jin ya tsaya sai ta dakata da kukan sai shasheƙa take, sun jima haka kafin cikin nutsuwa ba tare d ya juyo ya kalle ta ba yace "Maama me ke faruwa?" Irin a hassalen nan tace "Ba komai." Tana kallo ya gyara madubin mota dake tsakiya har saida ya hango fuskar ta a ciki, ba alamar wasa ya sake cewa "Da komai, me yake faruwa?" Har runtse idanu take tsabar bala'i tace "Ba komai na ce maka, dan Allah ka kai ni gida wajen Mama, ko ka bani na je." Numfashi ya sauke yace "Abba ya san za ki je can?" Saida ta fashe da wani marayan kuka tace "Bai sani ba, Jabir can nake so zuwa wajen Mamana." To shi kam ba za'a yi haka da shi ba ba, dan haka tsaf ya tuƙa motar zuwa gidan auren ta ba gidan Mama ba, tana kula da haka ta sake gyara zama ta ce "Jabir gidan Mama, sabon gidan su." A daƙile ya amsa da "Na sani, tunda Abba bai sai ba bai kamata ki je ba." Kam bala'i! Kam bala'i ! Me Jabir nufi? Ko Dai bai gane ta bane? To amma ba ta yanayin daɗi gaskiya, dan haka ba ta tanka mishi ba kawai ta ƙyale shi suka isa gidan. A wannan dare dai ta ci kuka kamar za ta mutu, sai dai ta yi niyyar za ta je gida ta faɗawa mama abinda ke faruwa, dole ne wannan. Jabir kuma na aje ta gida wajen mahaifin shi ya je suka sake tattaunawa kan abinda Jabir ɗin ya saka a gaba, Alhamdulillah filin da Alhaji ya bashi a rubuce aka yi kan ya mallaka masa shi halak malak, sai kuma nashi mahaifin da ya masa abinda ya ji daɗi duk da bai so haka ba, wato wani fili da ya mallaka gadon shi ya siyar ya damƙa masa kuɗin ya ce ya fara ginin wurin tunda ya ce ba zai ci kuɗi masu yawa ba, hakan yasa Jabir shi ma dake wani tunanin ya samu wani matsakaicin tsohon gida da ake shirin siyar da shi nan kusa da gidan mahaifin shi kawai ya siye ya sa aka fara ruguje shi sannan a fara ginin, kuma so yake sai an fara aikin ya sanar da Alhaji, dan ba ya so ya ce zai sake mi shi wani abu, iya haka ma ya isa Alhamdulillah. *Alhamdulillah.* 15/08/2023, 20:13 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *42* Tana dai zaune ne tare da su, bayan duba wayar ta ne ta ji labarin rasuwar sirikin auntyn nata à grp, sosai ta ji ba daɗin da a kurkusa za ta iya rantsewa bayan mutuwar Baban ta mutuwar tsohon nan ta ji ta taɓa ta sosai duk da ba ta san shi ba, yanzun haka kiran Mama Nuriyya tayi kai tsaye take mata gaisuwa da cewa ba ta sani ba sai yanzu, har Alhaji ma ya ce ta miƙa masa ta shi gaisuwar dan shi ya san dattijon sosai a harkokin shi, sai dai harka bata taɓa haɗasu ba sani ne dai irin na gari kawai. Sosai ta ji daɗi da yi musu godiya sannan sukayi sallama, Ummu na kallon Alhaji da Kuwailat dai suna hirar su bayan sun yi karatu tare, amma ƙala ba ta ce musu ba dan shima share ta ne ya yi da ya tambaye ta me ya faru a asibiti? Tana so ne idan suka keɓanta sai ta faɗa mishi, amma da ta ce ba komai sai ya jinjina kai da cewa wai shikenan. Ƙarfe *01:00* saura kaɗan Nabila ta diro gidan, da farin ciki Ummu ta fito dan tarban ta, amma ganin idanun Nabila jajir ga damuwa sosai a fuskar ta sai duk ta nemi farin cikin ta rasa, Kuwailat dama tana bacci, dan haka suna gaisawa da Alhaji da Shima ya ga damuwa tare da ita Ummu ta ja ta zuwa ɗakin ta, suna shiga ta saki hannun taa tace "Aje kayan naki ki shiga kiyi wanka, idan kin fito ki canza kayan ki kwanta." Juyawa tayi za ta fita, sai kuma ta dakata ta juyo tace "A kawo miki abinci ne?" Girgiza kai Nabila tayi alamar a'a, dan haka Ummu ta ci gaba da takawa za ta fita, da sauri Nabila ta kamo hannun ta ta juyo, kallon ta Ummu tayi tace "Lafiya?" Sadda kai Nabila tayi tana zubo da hawaye tace "Ki min faɗa aunty Ummu, ki min faɗan tun yanzu ko na ji daɗi." Hannu ɗaya Ummu ta sa ta tallabo haɓar ta tana kallon hawayen dake sauko mata, a tausashe Ummu kamar za ta yi kuka tace "Ya juya miki baya ne?" Dama mai jiran taɓi sai kuwa Nabila ta sake fashewa da kuka ta faɗa jikin Ummu tana faɗin "Aunty Ummu iyayen sa basa sona, sun wulaƙanta ni saboda na watsar da kaina, na shiga uku aunty Ummu, nayi nadamar rayuwata, na ji ina ma ban biyewa son zuciyata ba, yanzu gashi wanda nake so ya min nisan da ba zan iya cimma shi... Aunty Ummu na rasa Fahad kenan har abada." A hankali Ummu ta dinga shafa bayan ta ba ta ce uffan ba tana dai nazari kan lamarin da ganin ko zasu samu mafita, sun jima haka tana shafa bayan ta kafin Nabila ta sake ɗagowa a raunane tana kallon ta tace" Aunty Ummu ki ce wani abu, ki min faɗa sosai kamar yadda kike min, wallahi na shirya sauraren ki kuma zan ji abinda kika ce, sannan ba zan sake yin wani abu da ba daidai ba daga yau, na tuba aunty ku yafe min..." Kamo hannayen ta tayi cikin nutsuwa tace" Aunty gobe zamu je dake na roƙi Mama ta yafe min, wallahi na tuba daga duk abinda nake yi marar kyau." Jinjina kai Ummu tayi a tsanake tace" Shikenan, Allah kaimu goben, ki kwanta kiyi bacci, ki daina kukan hakanan." Girgiza kai Nabila tayi tace" Aunty ba zan daia kuka ba, ta ya zan iya tintsawa bayan ubangiji ya taimake ni na tuna abinda na jima da mantawa? Na saka Mama kuka na hawaye kamar za ta mutu, Yaya Luƙman na saka shi ɓacin rai da damuwa, kema na saka ki cikin damuwa da halayena, aunty na saɓawa ubangijina ba dare ba rana, to ya zan yi na sake kwana ba tare da ina kai goshina ƙasa ina neman gafarar ubangiji ba?" Kallon tuhuma Ummu ta mata tace "Shi ya gayyace ki zuwa gidan su? Ko ke kika je?" A raunane Nabila tace "Aunty abubuwa dayawa sun faru, da kaina dai naje garin saboda ya ce min yana cikin matsala, zuwana na farko gidan su na je ne a mummunan yanayi, kuma..." Da sauri Ummu ta katse ta da "Dakata, mummunan yanayi kamar ya? A buge kike nufi?" Da sauri ita ma tace "A'a, na...kayana dai da kuma yadda ban gane Yayan shi Bilal ba na dinga masa magana a tsatsaye, to a ranar ne muka shirya yin aure, sai ya ce na je mu gaisa da su na kuma basu haƙuri akan haɗuwar mu ta farko, shine suka wulaƙantani, na san dama karambani nake yi da nake soyayya da Fahad, ɗan babban gida ne aunty wanda duka Nijar ma aka san da zaman su, Kinga zai yi wuya Ahalin Saheeb Ahlan su yarda ɗan su ya auro wacce a da suka yi rayuwa ma a share ka zauna." Girgiza kai Ummu tayi tace" Yanzu kinga abinda muke faɗa miki? Na gaya miki ba lallai abokin rayuwa irin naki daga ƙarshe ya maka hallaci ba, ko da shi ya so yin haka ahalin shi ba zasu amince ba, a haka ma fa Nabila wanda kuka yi rayuwar tare ne, ina ga wani ne daban yake ƙoƙarin shigar da ke cikin zuri'ar sa? Sannan babban tashin hankalin ma idan ka haihu, ba ma miki fata, amma a tarihi yaran ki ma su ji wacece ke à baya, ina daɗi a nan? Wannan shine illar rayuwar duniyaci ga ƴa mace, haɗari ne ga mace da namiji, amma ya fi illa ga mace dan ita ake aura sannan ita ce mai tarbiyar yara, in dai da gaske ne kin tuba daga aikata komai marar kyau, to ki yi tuba na gaskiya tare da duƙufa wajen yin istigfari, sannan kiyi da cikakken yaƙinin ubangiji zai gafarta miki, kuma ki raja'ar da yaƙinin tare da tsoron azabar ubangiji, ina miki fatan tuban ya zama na har abada." Shafa gefen kumatun ta tayi tace" Allah ƙara shirya mana ke, Mama zata yi farin ciki da jin haka." Kuka sosai Nabila ke yi har saida Ummu ta kama ta suka matsa baya ta zaunar da ita bakin gado, ganin kukan nata ba mai ƙarewa bane ya sa ta juyawa za ta fita, sai kuma ta tuna wani abu, da sauri ta dakata tace" A'a, dakata ? Ɗazu na ji kin ambaci wani alhali ko?" Cikin kuka Nabila ta jinjina kai tace" E aunty, Saheeb Ahlan." Jim Ummu ta ƙara yi tana nanata sunan, ƙwarai sunan ne a lambar aunty Nuriyya, inda ta rubuta _mdm Mukhtar Saheeb Ahlan_, haka ma kuma Aisha ma d suka fara gaisawa yanzu bayan Maman ta t bata lambar Ummu ita ma dai hakane a sunan nata, amma dan tabattar sai ta kalle ta tace "Ahlan, shi kaɗai ne a Nijar ko akwai wani?" Kallon ta Nabila tayi cikin dakusashiyar murya tace "Aunty, kina nufin baki san ahalin ba? Shi kaɗai ne dai a sanina, me ya faru?" Da rashin tabbas Ummu tace "Ahlan? In dai shine to fa ina kyautata zaton Baban Fahad ya rasu." A ɗan firgice Nabila ta dafe ƙirji tace "Me? Ya rasu? Yaushe? Ya aka yi kika sani aunty?" Girgiza kai Ummu tayi tace "Ban da tabbaci, amma akwai aunty Nuriyya da muka san juna ta WhatsApp, to yau sirikin su ya rasu, kuma naga tana anfani da sunan matar Mukhtar Saheeb Ahlan, sannan su ma Agadez suke." Dafe kai Nabila tayi tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! Baban Fahad ? Wayyo Allah jarir..." Sai kuma ta tuna da ba zata sake kula shi ba, dan haka sai ta taɓe baki tace "Allah jiƙan shi da rahama." Daga haka ba ta ce komai ba, amsawa Ummu tayi da "Ameen Ya Allah." Sannan ta sake kama hanyar fita tana faɗin "Ki kwanta ki huta, sai da safe." Kallon ta Nabila tayi tace "Saida safe kuma? Aunty ni kaɗai zaki bari anan?" Ba tare da ta juyo ba tace "Abinda yake ci na ya cinye ki." Wani murmushi Nabila tayi ta bita da kallo, saida ta fice ta sauke ajiyar zuciya, ta ji daɗi da ba ta mata faɗa sosai ba irin wanda take nuna ta da yatsa kamar za ta mare ta, amma da ta mata gajeruwar nasiha ta sake ƙarfafa mata guiwar ta kama kan ta sosai. ******************** Saida Fahad ya share awa biyu kafin ya farfaɗo, Ja'afar ne tare da shi sai kuma Sabeer da bai jima da shigowa ba dan duba shi kamar yadda Hajia ta umarce shi, dafe kan shi yayi da yaji yana masa ciwo, a hankali ya buɗa idanun shi ya kalli Sabeer yace "Yaya, wai da gaske Abbu ya rasu? Yaya Sabeer Abbu ya rasu?" Jiki a sanyaye Sabeer ma dake fatan ina ma ya suma ya dawo ɗin nan ya ɗaga masa kai tare da cewa "Abbu ya rasu Fahad, ka mishi addu'a kawai." Kuka mai ƙarfin gaske Fahad ya fashe da shi daga kwance yana girgiza kai, cike da rashin jin daɗi Ja'afar yake ta daddaɓa kafaɗar shi yana faɗin "Kayi haƙuri Fahad, ba kuka zaka yi ba, addu'a za ka ma Abbu, Allah ya mishi rahama." Sabeer ma dafa kafaɗar shi yayi yace "Hakane, kayi haƙuri Fahad, Abbu ba kukan mu yake buƙata ba, ka masa addu'a kawai shi ya fi so yanzu." Girgiza kai Fahad yayi cike da takaici da nadama yace "Ba zaku gane bane Yaya Sabeer, ina tsoron kar Abbu ya tafi da hushina, idan har ya rasu yana hushi dani ya zan yi kenan? Ya zan gudanar da rayuwata alhalin mahaifina ya rasu da baƙin cikina? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Yaya Sabeer ya zanyi." Cikin rarrashi Sabeer ya riƙe hannun shi yace" Haƙuri zaka yi Fahad, bana tunanin Abbu zan tafi da hushin ka a zuciyar shi, duk da dai ka masa ba daidai ba, amma ka nemi gafarar ubangiji akan haka, shi mai gafara ne kuma mai jin ƙai." Cikin kuka ya sake girgiza musu kai yace" Ba zaku gane abinda nake ji ba, na ɓatawa Abbu rai fiye da kima, na faɗa masa magana son raina, na bijirewa umarnin sa akan mace, jiya jiya na yi musayar yawu da shi, yau sai a ce min babu shi? Bayan tun jiya ba saka shi a idanu na ba." A tausashe Sabeer yace" Haka Allah ya so Fahad, wataƙila kuma akwai abinda yake nufi wanda mu bamu san shi ba, kamar yadda na faɗa maka kawai ka yi ta istigfari." Kuka Fahad ya ci gaba da yi yana faɗin" Wallahi Allah ni nasan Abbu da ɓacin raina ya rasu, to ina zan gan shi bare na nemi yafiyar sa? Ubangiji kuma ba ya yafe laifin wanda aka cuta har sai idan shi ne ya yafe laifin, a jerin manyan laifuka na duniya kuma a gurin Allah daga shirka sai saɓawa iyaye, kuma duk wanda bai bisu ba ba zai taɓa ganin daidai a rayuwar sa ba." Girgiza kai Fahad yayi yace" Kar ka ce haka Fahad, in sha Allah ma Abbu bai rasu da hushin ka ba, kai dai kamar yadda na faɗa maka kawai kayi ta istigfari kana neman gafarar Allah, in sha Allah zai yafe maka, sannan za ka iya zama yaron kirki idan kana so Abbu yayi farin ciki da kai, kar ka manta daga yanzu duk abun kirki ko na tsiyar da muka aikata za'a bijarar wa Abbu da shi har da kamashon shi, idan na gari na tsiya ne shima haka za'a tashe shi a nuna masa aikin sharrin da yaran da ya bari duniya suke yi sannan a rubuta masa nashi kason." Kallon Sabeer ɗin ya yi, e abinda ya faɗa ya kama hankalin shi, dan haka sai ya gyara kwanciyar shi tare da tashi zaune yana faɗin" Da gaske Yaya Sabeer? Idan na aikata aikin alkairi Abbu a za'a iya bashi ladar?" Cike da tabbaci yace masa" Sosai ma, kamar yadda kuma duk zunubin da zaka sake aikatawa musamman ma da dukiyar shi sai a raba muku shi tare." Da sauri ya girgiza kai yana share hawaye yace" A'a, ba zan sake aikata wani zunubi ba, in sha Allah Abbu lada zai dinga samu, ina fatan Allah ya sa bai rasu da ɓacin raina ba." Jinjina kai Sabeer yayi d gamsuwa yace "Allah ya sa ƙanina, idan kayi haka da ka faranta mana rai dukanmu, musamman ma Mamie." Jinjina kai Fahad yayi yana ɗaura niyyar ba fa zai sake ɓata musu rai ba, ba kuma zai sake aikatawa wani abun da za'a nuna shi a ce ɗn margayi Saheeb ne, sannan burin da ya rasu da shi ma zai cika masa shi na auren Fati, zai yarda ya aure ta kuma zai yi biyayya ga umarnin sa ta hanyar ba wa Nabila haƙuri ta manta da shi, amma ba zai sake gigin ɓata musu ba, kar a zo mahaifiyar da ta rage musu ita ma baƙin cikin shi ya kashe ta, ba zai iya jura ba idan haka ta faru! Kuma wallahi da ya san Ajalin Abbu na kusa, da ba wai zai fara masa ladabi bane na iya kwanaki biyu da y zo garin nan, da zai fara ne shekaru da suka wuce dan kawai shi ma yayi farin ciki da shi. ******************* Tana shiga ɗakin ta same shi kwance idanun shi na kallon sama alamar akwai abinda yake tunani, har ta rufe ɗakin ta zauna kan gadon tana cire abayar ta bai kalle ta ba, tana gama cire ta ta aje gefe sai rigar baccin ta da ta bayyana, juyawa tayi ta kalle shi tace "Barka." A hankali ya kalle ta, sai ya ƙaƙaro murmushi dan baya so ta tambaye shi me yake tunani? Ba lallai abinda yake tunani ya mata daɗi ba tun yanzu, ga kuma matsalar ƙanwar ta da yake so ya zaunar da ita ya nuna mata rayuwa, idan ba haka ba daga ina ƴar nan take a wannan lokacin? Alamu sun nuna balaguro tayi, sam ba ya jin daɗin ko da haɗewa da ita cikin gari ne y nuna ta a matsayin wacce ya sani, ko da yake abun ba iya nan ya tsaya ba, tunda ya taɓa ganin wani abokin shi tare da ita, aka ce masa wai soyayya suke yarinyar kuma na bashi wahala, amma ba ta ma son su haɗu, to idan dattawa masu shekaru irin na shi zasu dinga kula yara kamar Nabila, ta ya kenan za'a yi ƙoƙarin canza su suma su zama na gari? Idan masu hangen nesa da hankali kuma waɗanda ake girmamawa ne abokan taɓarar su, kenan yaushe za su shiryu? Wa ye zai musu nasihar gyara kayan ka? Wa zai musu faɗa ya ce haka bai dace ba? Bai ce maa komai ba saida ya tashi zaune ya matso kusa da ita, ɗan jawo ta yayi jikin shi yana shafa lallausan fatar ta da duk sati take murje ta da kayan gyaran jiki na gidan Hajia Fussam musamman ma irin su dukkhan, wanda shi ya fi komai birge ta ko dan sahihancin itacen da take haɗawa, cikin nutsatsiyar murya yace "Me ya faru a asibiti? Me suka ce yake damunki?" A nutse ta sake kwantawa jikin shi tana sauke numfashi, kafin daga bisani ta numfasa cike da tausayawa kan ta da baƙin ciki da Takaicin abinda likitan nan ya mata tace "Ba komai, sun ce matsala ta ba babba bace tunda ina da miji, kawai ruwa ne ke son fita daga jikina." Jim! Dakatawa yayi daga shafar dantsen ta da yake yi, ɗan girgiza kai yayi yana jin wai me yasa wannan matsalar ke neman sako shi gaba? Shin idan aka kai irin wannan ƙadamin ba haƙuri ake yi da komai bane? To me yasa sai ita za ta damu kan ta? Bayan hakan na iya jefa ta halaka idan ba ta cire haka a ran ta ba? Ɗan jaye ta yayi daga jikin shi ya kalli fuskar ta yace "Abinda ya saka ki ciwon mara kenan?" Sunkuyar da kai tayi à kunyace ta ɗaga alamar e, jinjina kai yayi yace "To, yanzu ban san ya kike so nayi ba Ummu, raunin ba daga ni bane, daga shekaruna ne, shin ke da a haka kike? Ba yarinya ce ɗanya sharaf ba? A lokacin auren mu har gani kike ina takura miki da yawan buƙata ta, saboda a lokacin ke baki damu da abun ba kuma buƙatar ki madaidaiciya ce, nima kuma à lokacin ina da buƙatar sosai kuma an iya ji dake, amma sannu sannu shekaru duk suka mayar da mu haka, ki dubi ƴan uwan ki ki gani, kaf cikin su babu wacce yanzu ke kawo kanta ɗakina da sunan tayi bacci kusa dani, saboda su sun san jiya ba yau bace, kuma munyi girman da ya kamata mu aje duk wannan abubuwan gefe, amma ke..." Kafin ya ƙarasa faɗa Ummu ta miƙe tsaye a zuciye, rigar ta kawai ta ɗauka ta mayar jikin ta tare da juyawa ta fita a ɗaki ba ta ce da shi komai ba, saida ta ɓace ma ganin shi ya girgiza kai cike da jin ba daɗi da kuma haushi na yadda yana magana ta katse shi ta tafi ta bar shi zaune kamar sakarai? Jinjina kai yayi ya muskuta da niyyar gyara kwanciyar shi, sai kawai ya hango kan shi a madubi, duk da zaune yake amma saida ya hango tumbin shi, ai da baya da shi girma ne ya sa shima ya zo, ba kuma iya muryar shi ta canza ba har da kan shi da yayi fari ƙal da ma gemun shi, ta duba mana ta ga Hajia Luba wacce ta ma haƙura da kwana da shi, idan ka gan shi wurin ta kawai shine ya je dan ya duba ta sannan su yi hira, me ya kawo haka? Girma ne fa, amma irin rayuwar da sukayi da Hajia Lubabatu ma idan Ummu ta gani ba sai ta suma ba dan yadda abun zai dake ta, shine za'a wani dame shi da baya iya komai? Haba mana dai. Wannan tunanin da maganganun da duk ya faɗa mata ne ya faɗe su ne saboda dama akwai abinda yake tunani har ya fara caza mishi kai, Shiyasa bai yi tunanin komai ba ya kwanta tare da ci gaba da tunani akan Kuwailat da Jabir, da kuma Nabila da Maman ta da ya san dole tana damuwa akan rayuwar da take yi sosai, a haka bacci ya ɗauke shi bai sake waiwayar matsalar Ummu ba face ma ɓacin rai kawai game da matsalar ta ta da ta haifar masa. *Alhamdulillah.* 15/08/2023, 20:14 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *43* Ba dan Nabila na gidan ba so tayi ta share shi kawai, yo me yake nufi da ita? Kenan zai kasara ta kamar yadda matan shi suka kassara? Ya zai haɗata da tsofaffin matan shi ne saboda Allah? Wacece ba ta haife ta a cikin su ba? Shi a cikin jikokin shi ba akwai wacce t girme ta ba da wacce suke tsara? Shine zai zauna yana gaya mata hakanan? To bata ƙaunar shi kuma bata ƙaunar taimakon shi, ya je ya riƙe kayan shi dama ai ba anfani suke mata ba, ita fa ba zai raina mata wayo ba kan wannan, ba fa za'a raina ta ana gaya mata magana kan abinda ita ke cutuwa, aikin banza kawai. Sallama kaɗai ta yi ƙasan maƙoshi t shiga ɗakin, ba ta kalli inda yake ba ta aje faranti kwanukan abincin kawai tare da juyawa ta fita, shima bai ce mata komai ba ya bita da kallo har ta fita yana ayyana _"Ummu kenan! Ita ko gajiya ba ta yi da rigima."_ Sai kuma ya ƙaraso kusan farantin yana buɗawa, murmushi ya saki yana ayyanawa a ran shi _" Bayan ta saka siket shine ta tfi bata bari na yaba kyan ta ba?_" Girgiza kai yayi yana murmushi, shi iya haka ma ai ya ishe shi rayuwa da ita, su rayu abun su mana cikin farin ciki, ga ƴar su guda ɗaya tamkar dubu mai ladabi da biyayya wacce yke jin baya son rabuwa da ita tun yanzu, amma kuma haka zai haƙura y miƙa ta hannun wanda yake da tabbacin zai so masa ƴar sa fiye da yadda shi yake yi, su gode Allah man da ni'imar sa gare su, ta dubi Hajia Luba ma ko haihuwar ba ta taɓa yi ba, haka t haƙura take zaune dashi har yanzu dake yake fatan ita ta binne shi sannan ta msa takaba, duk yaran da suke kiran ta da Mama ƴaƴan ƴan uwan shi ne da nata ƴan uwan ta raina har ta aurar da wasu daga ciki. To kenan idan Ummu ce ba zata iya wannan haƙurin ba? Wanda rashin haihuwa na iya saka komai, na iya saka mutum ya kauce hanya ma. Kuwailat ce ta shigo ta gaishe shi sannan ta ɗora da faɗin saƙon da ak aiko ta cewa "Abba, wai in ji Mamie za su tafi gidan Mama tare da aunty Nabila." Kallon fuskar Kuwailat yayi, ba wai fa tana neman izini ba, a'a zasu tfi ka ce masa? Zai iya cewa a'a saboda ya isa kuma ba'a tambaye shi da girmamawa ba, ko da dai ran ta ɓace yke ai zata iy bashi wannan martabar, to amma mecece macen ma gaba ɗaya? Wata karkatacciyar halitta ce da ke tunani da zuciyar ta, sai kawai yayi murmushi matsayin sa na dattijo yce ma Kuwailat "Har sun shirya kenan? To ki ce ta zo na sallame ta." Da sauri ta amsa tare da juyawa ta fita, sanda ta isar mata da saƙon saida ta yi jim kamar ba za ta tafi ba, sai kawai ta miƙe tana faɗawa Nabila ta yi sauri ta gama cin abincin za su wuce. Tana shigowa ta tsaya gaban shi tace" Ka ce na zo?" Kallon ta yayi sosai ya dakatar da cin abincin yace" A ganin ki ya dace ki turo min Kuwailat wai zaku fita? Yaushe muka yi dake zaki fitar?" Ƙofa ta ƙurawa idanu ranta ɓace tace" Ina so naje ne saboda muhimmin abu, kuma zan raka Nabila ba wa mama haƙuri." Jinjina kai yayi da yaji abinda zai kai ta ɗin, hannu yasa aljihu ya ciro kuɗi ya miƙo mata yace" Ki sha mai da wannan?" Girgiza kai tayi tace" Ka bar shi nagode, akwai mai kuma ina da kuɗi ko da yake ƙarewa." Ƙwarai ran shi ya sosu kuma so take ta hassala shi ta ga ɓacin ran da bata san shi da shi ba, amma sai ya sake dakewa yace" To karɓi, tukuicin kwalliyar nan ne?" Da wata irin zuciya dake hawr mata sama tana sauka ta sake yatsina fuska tace" A'a, ka bar shi wallahi, nagode Allah saka." Juyawa kawai tayi za ta fita tana faɗin" Sai mun dawo?" Yadda ran shi ya sosu sosai ya sa ko abincin bia ci ba shima ya miƙe ya fita. Lokacin su Ummu har sun fice ita da Nabila tare da Kuwailat suka aje ta makaranta duk da kusa ne sosai. A gidan suka samu Yaya Luƙman ya zo gaishe da Mama kafin ya wuce aiki, bayan gaisawa Yaya Luƙman ya kalli Nabila yace "Gimbiya, an ga damar zuwa yau duba mutane?" Sai kawai ya girgiza kai dan haushi zai iya saka shi make ta, da kunya Nabila ta sadda kan ta tare da share ƙwalla na tausayin yadda ta ga Mma ta rame sosai kamar ba ta jin daɗi, ta san sauyin ba zai rasa nasaba da tunanin matsalar ta ba, har zai fita yana faɗin "Nasan dai ba jimawa zaki yi ba zaki tafi, to ki gaida mutanen can, ba zamu sake riƙe ki ba Nabila, kije duk inda kike so." Ummu ce ta kalle shi tace "Yaya." Kallonta yayi yace "Na'am." A nutse tace "Dan Allah ka zauna, magana ce ta kawo mu mai mahimmanci." Bai mata gardama ba ya zauna yana kallon su, cikin nutsuwa Ummu ta dube su tace "Mama, Yaya Luƙman, ga dai Nabila ta dawo gida, jiya ta zo daga Agadez, ta zo min cikin wani irin yanayi tana kuka, Mama..." Ta faɗa a tausashe sannan ta ɗora da "Mama ki yafe wa Nabila duk abinda ta miki wanda ya ɓ...." Da sauri Mama da tuni ta fara hawaye ta rufe bakin Ummu tare da fashewa da kuka tace "Kar ku fara Ummu, ban taɓa riƙe Nabila a zuciyata ba, nasan illar yin haka, shi ya sa ban taɓa kwatantawa ba, kullum tsakanina da ita addu'a shiriya ce da kuma fatan alkairi a duk inda take, ban taɓa riƙe ta, ban taɓa kwana da ɓacin ranta a zuciyata ba, saboda ban san ko zan iya farkawa daga baccin ba ko kuma tazarce zan yi, dan haka ta je na yafe mata, kuma Allah ya shirya ta." Nabila dake kuka kamar ranta zai fita ne ta faɗa jikin Mama cikin matsanancin kuka take cewa" Mama ki yafe min, nayi kuskure a rayuwata mama, wanda na bijire muku saboda shi ya ci amanata, iyayen sa sun zaɓa masa mata a gidan, sun ce ni ba zai aure ni ba saboda ban dace da shi ba, Mama ki yafe min dan Allah, ki taya ni roƙon Allah ya yafe min." Daddaɓata kawai Mama ke yi tana kuka ita ma, Yaya Luƙman da ya fara ƙwalla miƙewa yayi ya fice ba tare da ya ce musu komai ba, haka suka ci gaba da yafe wa junan su da kuma kuka na farin ciki. An gama da wannan matsalar, Ummu na so tayi wa Mama magana kan matsalar ta, amma bakin ta sai yayi nauyi kunya kuma ta rufe ta, sai ta yi shiru ta share zancen, a ƙarshe har saida ta kira sunan Mama bayan gama sallah la'asar ɗin su tace "Mama." Kallonta tayi da kulawa tace "Na'am Ummu." Bakin ta buɗe yake irin kana so ka faɗa ɗin nan, sai kuma tayi cak ta kasa furta komai, sai kawai ta wayance da "Nabila na ce me zai hana a maida ita makaranta, dan Kinga fa duk abinda tayi a baya har da rashin maida hankali ga karatun ta." Jinjina kai Mama tayi ta kalli Ummu da farin ciki, irin kallo da Mama ke mata yasa tayi murmushi tace "Ya dai Mama?" Girgiza mata kai tayi tace "Ba komai, ina dai tunanin ko a ina iyayen ki suke? Me shin suna neman ki? Sun damu dake? Me suke ji game da rashin ki a kusa da su? Ko ma dai yaya ne ni kin zame mana alkairi Ummu, Allah ya bayyana miki iyayen ki komai daren daɗewa." Wani malalacin murmushi Ummu tayi tace" Mama kenan, ni ban damu da na san su ba, kuma ma da suna so na me zai sa su jefar dani a bakin titi har ki tsince ni, ko ma dai menene ni alkairi suka min da suka jefr dani kuma ya zama ke kika tsince ni." Girgiza kai Mama tayi tace" Kar ki ce haka Ummu, ba ki san irin neman da iyayen ki suke miki ba, ba zamu sani ba saboda bamu haɗu da su ba." Dariya Ummu tayi tace" Mama, kinga yanzu da jimawa akwai wata sanarwa da gidan su Fahad tsohon saurayin Nabila suka dinga yi suna neman yaran su da suka ɓata tun suna ƙanana ƙwarai, Mama ai kinga wannan sun damu da yaran su kenan, basu da wat makama da zasu iya shaida yaran, amma fa hka suke bayar da kwatancen su ga jama' ko Allah zai sa su dace, har da suffanta kayan dake jikin yaran a lokacin da jigida mai tsada dake ƙugun ɗaya daga ciki, sannan kuma suka saka kuɗi miliyan biyar ga wanda kawai ya zo da labarin inda suke ba wai ya kawo su ba, dan haka Mama ni ban damu da na san su ba." Kallon Ummu kawai mama ke yi tana tunanin kenan ta san da abin nan da ya faru, murmushi Mama tayi tace" To ba kya tunanin ki iya kasancewa ɗaya daga cikin wanda suke nema?" Wata irin dariya Ummu tayi tace" Ba zai yiwu ba Mama, hakan ba zai iya kasancewa ba." Daga haka Mama shiru tayi ba ta sake cewa komai ba, haka ana yin magariba Ummu ta kama hanyar gida cike da baƙin cikin kasa faɗawa Mama abinda take son faɗa. Tana zuwa gida a farfajiya ta samu Alhaji da Jabir da kuma Baban shi suna ta hira, saida ta fara yin tsaye tana tunanin abun yi, Baban Jabir haushi yake bata tun shekarun baya, ba dan komai ba sai dan riƙon sakainar kashi da ya ma ɗan shi, gaskiya ta tsane shi kuma har yanzu ba ta jin za ta kalle shi da darajar da take kallon wasu da ita. Alhaji kuma ai yau gaba suke, sai ya bata haƙuri ta za ta huce su shirya, dan kawai kwanan nan wani abu yake mata mai kama da rainin hammata. Jabir kuma... Hmmmm ! Wai *ɗan nan* shine jiya da ce mata wai _"Gashi nan, muje."_ Wallahi babu ladabi a maganar yaron nan ta jiya, sannan ya sake hassala ta ta hanyar hana ta zuwa gida kamar wani shi ne uban ta, wai tunda Abba bai sani ba bai kamata ki je ba. Da ƙyar dai ta ɗaga bakin ta dukan su tace da su" Ina wunin ku?" Abban Jabir kaɗai ya amsa da" Lafiya lau, anwuni lafiya?" Ba dan ya san ta ko ya gane ta ba ya faɗa mata haka, sai da Alhaji yace da shi" Amaryata kenan, Ummu Kulsum." Ba ta tsaya ta ji me suke faɗi ba ta wuce abun ta tana taɓe baki da ayyana _" Ohon muku."_ Sun jima suna ta hirar su kafin Alhaji ya dubi Abban Jabir yace" Kuma in sha Allah zan je gidan da kaina muyi wata magana mai mahimmanci game da ɗan naka." Murmushi Abban Jabir yayi yace" A'a Alhaji ɗanka dai, in dai maganar ta shafe shi to ka bani lokaci ni sai na zo na same ka." Shi ma da fara'a yace "Ayi haka? To shikenan, ina ga ko zuwa ranar asabar ya yi?" Jim Abban Jabir yayi yana kallon shi yace "Umm ! Nan da kwana huɗu kenan?" Jinjina masa kai yayi yace "E." Shima da gamsuwa yace "To ai shikenan, ina ga ba wata damuwa, Allah ya kai mu." Da haka sukayi sallama shi suka tafi tare da Jabir Alhaji kuma saida ya fara zagaye matan suna gaisawa da ɗan taɓa hira kafin ya nufo ɓangaren Ummu. Ummu tunda ta shiga tayi wanka tayi shirin bacci, wani film na India ta ɗauko a YouTube tayi kwancin ta tana kallo, dan duk tashoshin dake gidan wanda suka shafi wa'azi ne da addini, Alhaji ba ya yarda da kallon wani abu na daban. Dan ya san da kawai ita yanzu ba ruwan ta da shi kafin ta kwanta ma saida ta kulle ɗaki ta kashe wuta sannan ta kwanta, kamar dai yadda aka sani film ɗin India da waƙa da kuma iya tsarin soyayya, iya waƙa kawai idan aka saka Ummu sai jikin ta yana amsawa, tun tana jurewa tana kallo har ta kai tana fara jin shauƙi sosai tare da ayyanawa ita ce a wannan halin, tana hakane Alhaji ya turo ƙofa sai ya ji ta rufe gam, murɗawa yayi ya dai tabbatar rufe take, sai kawai ya juya dan ya san da gangan ta yi ai, to ba matsala, zai nunawa Ummu shine mijin ta ba ita ke auren sa ba, ya sha ɗaukar ƙuruciya da hauka daga gareta, amma ban da yanzu da yasan ta mallaki hankalin kan ta. Raba dare tayi tana wannan kalle kallen, abun ka ga YouTube har suka fara bata film irin na kauce ƙa'idar nan, daga haka sai gata warwas a jerin jadawalin kallon batsa (sex) abinda take ji a jikin ta ita kaɗai ta sani, haka yasan ko tunani ba ta yi ba kawai ta faɗa kallon abinda bai dace ba, tun Ummu na jin kamar ita ce tana jin shauƙi a jikin ta bata ankara ba ta ji ruwa na fita a jikin ta, ko da ta duba ta samu tabbacin daga jikin ta suke. Abinda zai iya jefa rayuwar wani a haɗari ƙarami ne, wani kuma babban abu ne, wasu kuma ba sa ankara suka abkawa haɗarin, kamar dai Ummu da kafin ta ankara sai gashi ta ɗauki kwana *uku* kowane dare abinda take kallo kenan kafin ta kwanta. Suna zaune tare da Kuwailat ta ɗauki wayar ta ta ta buɗe tsaron kasancewar ta san shi, dama idan ta ɗauki wayar ba abinda take dubawa daya wuce wa'azizzika da wani lokacin ma ita ke sa wa a turo so a wayar, yanzun ma kai tsaye wajen videon ta nufa, Ummu na ganin haka kuma duk videon da ta kalla ya birge ta ɗauko shi take ta sauke a wayar. A razane Ummu da bata taɓa tunanin abinda take yi munin shi ya kai ta ji bata son ƴar ta ta kalla ba ta fige wayar da ƙarfi, da sauri Kuwailat ta kalle ta tace "Mamie, wa'a..." A ɗan hassale cikin tsawa Ummu "Kar ki sake ɗaukar min waya, kin ji na faɗa miki." Kafin Kuwailat ta ankara da tunanin me ta aikata to kawai ta tashi ta bar ta nan ta shige ɗaki. Gyara zama Kuwailat tayi tasa tv gaba tana kallo, Alhaji ne ya shigo da sallama ta amsa, dafa kan ta yayi yace" Autata, ke kaɗai zaune ? Ina maman taki take?" Nuna masa ɗaki tayi tace" Tana ciki. " Jinjina kai yayi yayi nufi ɗakin, duk da ba shiri suke ba har yanzu amma dai baya so yar su ta gane haka, dan haka ya shiga ɗakin da sallama a bakin shi, zaune ya same ta tana goge abubuwan da tunanin kawai za ta dinga kallo ne ta wuce, ƙasan maƙoshi ta amsa mishi sallamar, tsaye yayi gaban ta ganin ko kallon shi ba ta yi ba shima ya ɗauke kai yace "Ku shirya ke da Kuwailat, anjima zamu je sauraron wa'azi Sheikh Rayaddun Ja'afar, Jabir kuma zai yi masa ja baƙi, shine karon shi na farko a garin nan, dan haka nake so mu kasance tare da shi." Ko da ya faɗa mata haka ya juya ya fice a ɗakin shima ba tare da ya sake kula ta ba, da kallo mai kama da harara ta bi shi, sai kuma ta taɓe baki tana ayyana _Ina abinda ya dame ni to? Aikin banza da wofi, ka tsaya ka fuskanci matsalar mutum ka gagara yin haka. "_ Ƙwafa tayi ta gaske, (ku fahimta, halin da Ummu ke ciki na jawo raini tsakanin mata da miji da rashin girmamawa da jin haushin juna), kwance ma tayi kan gado dan ba wani abu da za ta yi ko take yi yanzu bayan ta sa Kuwailat ta share mata ɗaki ta saka mata Turare, har girki ma yanzu iya cikin su kawai take dafawa dan ma dai yana can zagayen kwanan ɗakin matan shi da ba wata tsiya suke tsinanawa juna ba a ganin Ummu. *Alhamdulillah.* 15/08/2023, 20:14 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *44* Tare suka fito cikin shirin tafiya masallacin, yana gaba yana ta faman saɓa babbar rigar shi inda Ummu da Kuwailat ke baya tare da zagayawa zasu shiga motar, mai gadi da ya hangi fitowar su ne ya taho da gudu, gaisawa sukayi da Ummu kai tsaye kuma suka gaisa da Alhaji, sannan ne yake sanar da shi "Alhaji dama akwai wasu ma'aikatan wutan lantarki da suka zo ɗazu nan zasu yi aiki, sun ce an samu matsala ne da waccen dogon tsanin gashi kuma damuna ke tafe in sha Allah, to da suka zo ɗazu sun ɗauka ma aikin ba zai jima ba, amma sun ce gobe zasu dawo su ci gaba, da yiwuwar a share awa ashirin da huɗu, duba kuma da gudumuwar da kuke bayarwa, yasa suka ci to a sanar da kai, dan har a gidan redio ma an faɗa za'a samu ɗaukewar wutar wasu unguwanni dan jama'a su sani." Da kulawa Alhaji yace" Asha kuwa! Ka ga kuma ban ji ba wallahi, Gwara da ka sanar da ni, hakan zai sa mu ankare kam." Jinjina kai mai gadin yayi yace" Hakane Alhaji, kuma naga ai da generator." Shima jinjina kai yayi yace" Hakane, in sha Allah ma zuwa goben zan tayar da shi." Juyawa yayi a ladabce yana faɗin" To nagode, zamu ɗan fita ne nan masallaci, sai mun dawo." Da addu'ar a dawo lafiya ya bi su sannan suka fice, Ummu na jin duk abinda suka tattauna, ita a WhatsApp ta gani da sunayen unguwannin da aikin zai iya shafa, kawai bata sanar da shi bane dan bata son magana da shi. Haka suka ɗauki hanya ba wata hira sosai tsakanin su, shine ma dai da ya fi damuwa da kar Kuwailat ta fahimci abinda ke faruwa har yake ɗan cewa Ummu ɗin "Kina ganin na tura Kuwailat tare da Hajia Atika da zata tafi umra azumin nan? Ko na bari ta tafi Hadj sai na zuba muku tare?" Duk da ta ji daɗin hakan sosai, dan ba abinda zai kai a mata albishir ɗin tafiya ƙasa mai tsarki daɗi a rayuwarta, amma dai bata nuna farin cikin a fili ba tace" Gaskiya zan so na tafi tare da abata." Farin ciki ne ya bayyana fuskar Kuwailat, dan gaskiya bata ga sakewar da zata yi ba tare da Maman su Zeinab, bata san me ta musu ba? Amma dai ba wanda take zuwa ɓangaren shi ta zauna bayan Hajia babba, dan haka ita ma take nesa da su, jinjina kai yayi yace "Shikenan, Allah ya kai mu." Fuska a ɗaure Ummu tace "Ameen, Allah ƙara arziƙi." Daga haka basu sake cewa komai ba sai shi da Kuwailat dake hira yana bata labarin ƙasa mai tsarki da abubuwan da za ta gani idan Allah ya ƙaddarar tafiyar ta, anan ne har yake faɗa musu mutanen da ya zuba ma zasu tafi, biyar a cikin dangi ne biyar kuma wasu daga cikin maƙwabta wanda suka rage bai biya ma ba. Sun isa wurin wa'azin, kai tsaye wajen mata suka nufa dake sama suka zauna, tunda aka gabatar da malam da kuma mai ja baƙi wato *Alaramma Jabir Mu'az Mika'il*, lasifika aka miƙa ma Jabir da zai fara buɗewa da surar da malam zai yi tafsirin ta, amma a ƙalla saida ya ɗauki kusan sakan talatin saboda rashin sabo ganin ana haskawa ga kuma mutane da dama, a Saudia da Madina duk ba irin haka yayi ba, a cikin aji ne kawai dan a gwada shi wani lokaci kuma cikin masallaci ne a wani ɓangare na masallacin, yana fara a'uziyya bai kai ga bismillah ba masallacin ya sake yin shiru sosai tamkar babu mutane a cikin shi, dan ko sautin numfashi wani ba ya jin na kusa da shi. Haka kuma ya sa Ummu da suma sukayi shiru ta ji tsigar jikin ta ta tashi sosai, gabanta ya wani yanke ya faɗi irin a sanyayyen nan, wani irin yanayi ta ji tana samun kan ta da duk ta tsargi kan ta, hakan yasa ta sunkuyar da kai sosai tana ci gaba da sauraren suratu Aal'Imran, saida ya kai inda zai tsaya ya dakata malam ya fara wa'azi, wa'azi malam ke yi cikin nutsuwa da kamanta faɗin abinda yake daidai, inda Jabir ma ke nashi aikin, dan duk surar da ya buƙaci ya kawo haka zai jawo ta, abun burgewa ga Alarammomi bai wuce yadda idan aka ce su bayar da misali ba tare da an sanar da su surar ko shafi ko aya ba suke kawowa, haka Jabir shima ya kasance yana yi. Daga ƙarshe tafsiri yayi nisan da har saida malam ya dinga nusar da al'umma akan kallon abubuwan batsa da kuma sauraren abinda bai dace ba, tare da faɗa musu gaskiya ranar gobe kowace gaɓa dake jikin mu mai bayar da shaida akan muce kuma zata yi magana ita ma. Take Ummu ta ji kamar da ita ake, ta tsargu sosai sannan ta sake yarda ashe da gaske ne da ake cewa malamai na iya wa'azi su taɓo abu ka ji kamar da kai kawai suke. Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! Ashe ta jima tana aikata saɓo? Ya aka yi ta manta da abinda ta karanta? Ya aka yi ta manta da abinda malam ke faɗa yanzu? Ya aka yi ma ta manta da abinda Alhaji ya faɗa mata cewa ta san me za ta yi da waya, dan waya da take gani za ta iya kai ta wuta kuma ta kai ta aljanna, dalilin da ya sa ma kenan yake ƙarfafa mata guiw akan grps ɗin su da suke abubuwan ƙaruwa da wayar da kan mata, wanda dalilin haka har suka buɗa grp na taimakon junan su da marayu da marasa ƙarfi. *Kuka* ta ci sosai, har saida ta kusan ta ta yi tunanin ko karatun da sabon Alaramma ke ja ne, dan gaskiya matashin nan akwai murya, ga taushi ga zaƙi ga sanyi, Ummu kuma ita kaɗai ta san me take ma kuka, har dariyar da ta ji an ɗauka à masallacin yasa ta ɗaga kan ta, ba ta san me aka ce ba wallahi, amma sai ta ji na bayan ta na faɗawa wata da ita ma bata ji da kyau ba tana cewa _"Malam ne ya ce wai yana gabatar mana da sabon Alaramma da in sha Allah zasu yi tafsirin azumi tare, kuma wai gauro ne baya da mata, dan haka a cikin mu mu bashi ƴar mu mai nutsuwa da za ta iya ƙara zaburar mana da shi mu sha ruwan ayoyi, amma fa ba ƴar zamani ba wacce idan ta gaso shi daga gida zai zo ya yi ta ja mana ayoyin mata a wuta."_ Hakan bai sa Ummu murmusawa ba saida ta ji yanzu malm ɗin na sake faɗin" Hakane mana, wallahi duk muraja'ar shi idan ya haɗu da mace sai a hankali, haka zamu ga matashin zakin nan namu a gigice ya zo yana haɗa mana hadda wuri ɗaya, mu muna tafsirin kafiran ƙuraishawa shi yana kawo mana hadisin dake nuna butulcin mata ga mizajensu." Murmushi kawai tayi, ita ba ta ma taɓa hasaso matar da Jabir zai iya aura ba, amma dai tana masa fatan samun ta gari kamar yada yanzu ɗin ma malam ke ta mishi addu'a da fatan alkairi dan sosai ya san Jabir, dan shi da za'a bashi dama zai iya bayar da tarihin Jabir ko zai zama izina ga matasan yanzu. ********************* Yana daf da shiga falon yaji Hajia na magana a tausashe tana faɗin "Ka yi haƙuri Alhaji, ban so haka ta faru ba, amma zai fi kyau ka tafi da Fati gida, idan tana da wanda take so ko ya dace da ita ka aurar masa ita, Fahad ya ƙi yi mana biyayya, kuma gaskiya ni dama tun farko ban goyi bayan Alhaji da yake cewa zai aura masa ita dole ba, ko da Fahad bai gudu ba kamar yadda ya ce, zai iya takurawa Fatima da gallazawa kala kala, wanda kuma kaga hakan ba zai ma kowa daɗi ba, dan Allah kuyi haƙuri da ɓata muku lokaci da muka yi." Jinjina kai Alhaji Abbas yayi cike da gamsuwa yace" Ba damuwa Hajia, nima saida nayi ƙoƙarin fahimtar da Alhaji haka, amma ya nuna Fahad ba shi ya haife shi ba, shi kuma irin wannan abun ba'a masa hawan ƙawara, yau idan muka aurar da shi ba ya so, ba wai dan Fati na ƴata ba, amma ina daɗi kuma kullum muna hanyar tara su yi musu sulhu? Ko kuma muna kokawa da matsalar su? Ai ba'a samu ci gaba ba a haka kuma, amma tunda ke kin fahimta ba komai, Allah ya zaɓa musu ma fi alkairi." Sai kuma ya sake gyara zama ya tausasa murya yace" Sai dai Hajia, ina ganin me zai hana ku zauna da Fahad, ku masa magana akan yarinyar da yake so, idan sun yarda zasu canza halin su sai a aura musu junan su, ko ya kika gani?" Da sauri Fahad ya shigo yana furta" Assalama alaikum." Hajia na ɗaga kai ta kalle shi ta sake sunkuyar da kan ta, sai Alhaji Abbas ne ya amsa, zaunawa yayi kusa da shi suna sake jajanta ma junan su da ƙarin haƙuri, saida Fahad ya kalli Hajia da ya fahimci kamar hushi take da shi tunda abun nan ya faru yace" Kawu, na ji duk abinda kuke faɗa, kawu wallahi zan auri Fatima, ina son ta yanzu, kar ka tafi da ita dan Allah kawu." Da mamaki suka kalle shi har da Hajia ma, sai Alhaji da ya gyara zama yace" Fahad, ka san me kake faɗa kuwa? Fati dai da ka ce ba zaka aure ta ba, idan aka maka dole za ka gudu ka yi nesa da mu." Girgiza kai Fahad yayi a ladabce yace" Kawu na faɗi haka a baya, amma yanzu bana so na sake ɓatawa kowa rai, wallahi zan zauna da Fatima, burin Abbu ne na ƙarshe, ku taimaka min na cika masa shi dan Allah." Da irin kallon tuhuma Alhaji Abbas ya bishi yace" Ka tabbata?" Da tabbaci ya jinjina kai yace" Na tabbata kawu." Sai kuma ya sake tsare shi da idanu yace" To... Nabila fa?" Da sauri yace" Na haƙura da ita Kawu, tun da ba kwa son ta wataƙila ba alkairi bace gare ni, ni tun ranar ma da muka zo gidan nan tare ban sake sanin ina take? Me take? Ta koma ? Ban san komai akan ta ba yanzu, kuma wallahi bana so na sani, tunda ba kwa son ta nima na haƙura da ita." Cike da dattijantaka Alhaji Abbas yace" Fahad, kana nufin ba ka son Nabila yanzu?" Fahad da har ga Allah ba zai iya cewa ba ya son ta ba, dan in ya faɗi haka ƙarya ya yi, da ita ya fara so, kuma ita ya fara sani ƴa mace, a hankali ya jinjina msa kai yace" Na haƙura da ita kawu." Wani murmushi yayi mai cike da kamala da dattako sannan yace" Shikenan, tashi ka je, zan yi magana da mahaifiyarka yanzu." A marairaice ya kalli kawun yace" Kawu Fatin fa? Za ka bar ta nan har a ɗaura mana aure, kawu na tuba wallahi, na daina duk abinda nake yi yanzu, na yi alƙawari tsakanina da mahaliccina ba zan sake aikata saɓo ba." Kallon shi dai Alhajin yayi yana murmushi, hakan yasa Fahad ya ji a ran shi kenan bai yarda ba, dan haka ya sake riƙe ƙafar shi da rarrashi yace" Kawu Hajia ma fa hushi take dani, dan girman Allah ka ce ta yafe min, wallahi ko kula ni ba ta yi, ta tausaya min mana, ba ta ga yadda muka rabu da Abbu ba? Fita fa kawai nayi sai dawo..." Sai kuwa hawaye a fuskar Fahad sharrrr! Har suna sauka a jikin shi, cikin kuka ya ci gaba da cewa" Dawo kawai nayi na tarar da gawar Abbuna, kullum cikin musayar yawu nake da shi, amma wallahi a raina ji nake akwai ranar da zan durƙusa na nemi afuwar sa ya yafe min sai na daina ɓata masa rai, ashe ni ina nawa tsarin ne Ubangiji ma yana na shi, sai gashi ban samu damar sake ganin shi yana numfashi ba, ko kallon ƙarshe ban ma fuskar sa ba, har yau na kasa manta safiyar da muka haɗu cin abinci na gaya masa magana da bakin nan nawa, ashe a lokacin duk..." Haɗa kan shi yayi da guiwar Alhaji Abbas yana kuka sosai har da shasheƙa, shafa kan shi Alhaji Abbas ya dinga yi wanda ya aske ma tarin sumar nan da yake caje ta ya shafe ta da mai, cikin rarrashi Alhaji Abbas yake faɗin" Ka yi haƙuri ka daina kukan haka Fahad, mu ba wai ba ma son Nabila bane, ka gane wani abu Fahad, a lokacin da ka ce ita kake so ka aura, idan muka amince ku a haka zakuyi auren, wanda nasan niyyar da kuka gina auren a kai ba mai kyau bace, wataƙila abokanan ku ne sun yi aure? Kuma kuke so kuyi, ko kuma an fara takura muku ko saka muku ido? Dan haka kuyi tunanin ku halatta haram ɗin, ko kuma dai wata manufar can ta daban da babu Allah a cikin ta, amma Fahad ka ga da ace kun gane gaskiya ne sadidan, sannan kai da ita kuka tuba ga Allah kukayi alƙawarin ba zaku sake aikata alfasha ba, sannan ka umarci yarinyar nan da ta yi istibra'i, to da ni nan da kaina na ɗaura muku aure, ko ba komai Bilal ya gaya min cewa ka faɗa musu kai ne ka fara sanin ta ƴa mace, kuma kai kaɗai kakae mu'amala da ita, wataƙila kana da yaƙinin ko bayan auren ku zata ci gaba da kare martaba auren ka, ga kuma ciki da ya faɗa min ka mata har aka zubar, to mu kuwa me zai sa mu goya maka baya ka mata butulci? Na san duk inda take yanzu tana jin haushi da tsanar duka ahalin mu, kuma abinda aka yi ma yarinyar nan ba'a kyauta ba, dan ni ina duban matsalar ta wata fuska ce daban, shin idan a ahalin mu ne haka ta faru da wata, zamu goyi bayan a wulaƙanta ta? Ko zamu tsaya ne mu ƙwatar mata ƴancin ta?" Sai kuma ya kalli Hajia da kan ta ke ƙasa sai dai sosai hankalin ke kan abinda yake faɗa, ɗorawa yayi da" Hajia Radiya, magana ta gaskiya ba kya kyautawa yarinyar nan ba, Fati ta gaya min abinda ya faru, kuma Alhaji Mukhtar ma ya sanar da ni komai, me ya sa? Kun manta kuna da yara mata ne? Kuma suma hayayyafa suke yi? Sannan yara irin wannan yarinyar suma haihuwar su ake ta mahaifa da kuma sa ran su zama na gari, da a ruwan sanyi kuka rabu da ita tare da yi mata nasihar da za ta ratsa ta, amma ta irin sigar da kuka tarbe ta ba, wataƙila dalilin haka ta sake shiga uwa duniya? Ko ta gane gaskiya Allah ne masani." Kuka Fahad ke yi sosai da sosai, ɗakin shiru y ɗauka na tsayin mintuna uku, kafin daga bisani Fahad ya tsagaita da kukan yace "Kawu, wallahi ban kawo Nabila gidan nan ba saida muka yi alƙawarin mun tuba ba zamu sake ba, daga wannan ranar na ce ta fara istibra'i dan aure zamuyi, amma basu fahimce mu ba, ba ma wanda ya zauna ya tambaye mu ko ya ji menene damuwar mu, ni kuma har ga Allah ina son ta ne da aure tun farkon haɗuwar mu, sheɗaan ne kawai da son zuciya ya rinjaye mu da son rayuwar holewa, amma da na ga abun yayi yawa na ce mata aure nake so kuma ta amince, duk da ta so nuna min kamar bamu dace ba saboda rayuwar da muka yi, amma na ce mata mu bar wa Allah komai, zai dubi kyakyawar niyyar mu ya tallafa mana." Sai kuma yasa hannu yana share hawaye tare da faɗin" Ni tsorona kar ta je gidan nan tayi ta shan duk abinda ya tarbi gaban ta, ga Nabila da idan tayi zuciya ba ta cin abinci, ina tsoron yunwa ta kamata..." Yadda ya ƙarashe maganar yana rushewa da kuka ya sa Alhaji Abbas dafa bayan shi yace" Fahad, daina kukan hakanan kar kan ka ya fara ciwo, yanzu tashi ka je ɗakin ka ka kwanta ka huta, in sha Allah komai zai yi daidai." Jinjina kai yayi da ƙyar ya tashi tsaye zai tafi sai kuma ya dakata ya kalli Alhaji yace" Kawu, ka bata haƙuri ya yafe min, bana so na sake rasa wani daga cikin su alhalin suna hushi da ni, Dan Allah ka sa baki." Jinjina masa kai yayi yace" Kar ka damu Fahad, in sha Allah Hajia za ta yafe maka har abada, je ka kwanta." Wucexa yayi a sanye haro ya shige ɗakin shi, sai lokacin sautin kukan Hajia Radiya ya fito fili, cikin nutsuwa Alhaji Abbas yace" Hajia, haƙuri zakuyi ku nemi iyayen yarinyar nan sannan ku nemawa Fahad auren ta, tunda har sun ɗauri niyyar gyarawa, mune muka lalata komai." Da sauri ta dakata daga share hawaye ta kalle shi tace" Auren ta? Nabilar?" Da tabbaci ya bata amsa da" E, baki ga yadda yake magana akan ta bane? Ya yarda zai auri Fati ne dan kawai ya muku biyayyar da ya kasa yi muku a baya? Amma har yanzu yarinyar nan ce a ran shi, kina gani fa ya kasa cewa baya son ta, sai dai ya ce ya haƙura kawai, gashi ya damu da son sanin halin da take ciki, amma da fari ce mana yayi ba ya so ma ya san me ke faruwa da ita, Hajia Radiya, ina tsoron wata ƙaƙƙarfar alaƙar da kan iya zuwa da tsananin rabo ce ta zo da guguwar da ta ɗauke Alhaji Saheeb, wanda idan muka ce kokawa zamu ci gaba da yi bamu san rayuka nawa za ta ɗauka ba, dan Allah ki bar shi ya aure ta, ki mishi addu'a Allah ya sa haka shi ya fi zama alkairi, ina ji a jikina zaman su zai kafa tarihin da ba'a cika rubutawa ba a duniya, dan Allah?" Shiru tayi na sakanni, nazarin ta bai wuce yanzu nan sai ya auri yarinyar nan? Alhaji ai ya ce ba ya son ta, kuma idan aka ga Fahad ya auri Nabila sai dai idan *bayan ran shi*, to ko dai da gaske ne? Hakan na nufin wataƙila akwai aure a tsakanin nasu har ma da rabo? Shi ya sa ma furucin Alhaji ya tafi da shi makwancin shi? Y Allah! A nutse ta kalli Alhaji ta jinjina kai tace "Na amince, ka yi abinda ya dace kawai." Take murmushi ya bayyana a fuskar shi yace "Ma sha Allah, naji daɗin jin haka gaskiya, Allah ya tabbatar mana da alkairi, Alhaji kuma Allah ya jiƙanshi da rahama." "Ameen Ya Allah." Ta faɗa a tausashe, sannan kuma ya sake cewa "Sai kuma maganar hushin nan da kike da shi Ha.." Da sauri Hajia ta katse shi da "Ni bana hushi da shi, kawai ina so ya gane gaskiya ne, amma abinda ya faru ya zame min izini, ba zan yarda na kwanta da ɓacin ran ɗaya daga cikin su ba, dan ban san ko zan farka ba." Nan ma dai da farin ciki ya amsa mata sannan yace "Sannan zan ga Bilal na masa magana akan abinda ya kamata a sama wa Fahad ɗin ya fara yi shima, dan bai iya nema ba ko kaɗan, a bashi ya kashe kawai ya sani, to yanzu tunda za'a masa aure ai ya kamata ya fara sana'a shima." Jinjina kai tayi tace "Hakane, Allah ya ƙara shirya mana su, amma dai ina da shawara." Cike da kulawa yace "To, ina jin ki?" A nutse tace "Yadda Alhaji ke ma yara idan zai ɗora a kasuwa, kai tsaye ba ya saka su a harkokin shi, yana fara basu kuɗi ne su ja jarin su na kan su, a shekara ya kan buƙaci da su dawo da abinda suka samu, idan kuɗin sun ƙaru ko da kaɗan ne shine yake alamta mishi yaro na iya tattalawa, to daga nan yana iya saka yaro a kowace irin harkar sa, idan kuma ya salwartar, to yana ƙara masa ne har sau uku, to daga nan ban san matakin da yake niyyar ɗauka ba, dan gaskiya daga Bilal zuwa Mukhtar da Sabeer babu wanda aka sake ba wa jari sau biyu, na farko suka ɗora riba a kai su kawo sai su fara fita tare da shi, to shima Fahad a masa haka mu gani ko Allah zai sa a dace." Cikin jin daɗin shawarar Alhaji Abbas yace" Wannan ai shawara ce mai kyau, hakan ya yi sosai, ina ga ma ni zan bashi jarin ya fara juyawa, tunda yanzu komai dake nan na magada ne, bai kamata a taɓa ciki ba, zan bashi ko miliyan biyu ya fara mu ga kamun ludayin shi." A hankali ta girgiza kai tace "Sun yi yawa, ka bashi ɗaya ya fara jarabawa mu gani." Dariya yayi yace "To ai kinga bayan wata ɗaya akwai hidimar auren shi da za ta taso, dole zai buƙaci kuɗi." A sanyaye tace "Duk da haka, ni zan ɗauki nauyin auren nashi." Murmushi yayi yace "To shikenan, Allah ya saka miki alkairi, Allah kuma ya ƙara shirya mana shi." Amsawa tayi da "Ameen." Kafin suka ɗn taɓa wata hirar da ba ta shafi Fahad ba, ya dai jima suna tattaunawa kafin ya koma, inda Fati da suke waje ta so ta bi shi ya ce ta jira maman ta na zuwa sai su koma tare. *Alhamdulillah.* 15/08/2023, 20:14 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *45* Kamar wacce ta dawo daga wata uwa duniya a ƙafar ta tsabar yadda ta shigo a kasalance, watsa ruwa kaɗai ta yi ta kwanta bayan sun yi saida safe ita da Kuwailat, Alhaji kuma tun daga farfajiya ma sukayi sai da safen, bacci ta so ya ɗauke ta mai nauyin gaske, sai dai tana kwantawa matsalar ta tayi mata sallama, haka ta shiga saƙa da warwara na abinda ke damun ta. Gyara kwanciyar ta tayi a karo na tsohon dare, kamar kuma motsin ta ake jira sai kuwa wutar gidan gaba ɗaya ta ɗauke ɗiff! A hankali ta lumshe idanu dan ta san yanzun nan zafi zai gigita mata lissafi, shiru tayi tana sauraren da gaske marar ta ce ke motsi? Ko da yake ba sabon abu bane ai, dan haka tayi tunanin bari ta jaraba shan Lemun tsami mana a lipton yadda take jin maza na yi, shin zai yi mata ita ma? A hankali ta miƙe tare da lalubar wayar ta ta fito daga ɗakin. Karo sukayi da Alhaji zai shiga ɗakin dake daf da madafa wanda b ɗaki bane, kawai an masa ƙofa ne sai ka ɗauka ɗaki ne, amma inda aka aje generator ne tun ma kafin ya auro Ummu yake nan, kasancewar babban generator ne dake ɗaukar gaba ɗaya unguwar, kallon ta yayi yana murmushi yace "Hajia, zafi ya tashe ki ko?" A kasalance ta amsa mishi da "A'a, madafa zan shiga." Da mamaki ya dube ta yace "Ba dai yunwa ta tashe ki ba?" A hankali ta furta "Kusan haka." Da kallo ya bita ta shiga madafar, buɗe ɗakin yayi da makulli ya haska da fitilar wayar shi ya hangi generator ɗin dake cikin wani irin babban keji, barin ɗakin yayi buɗe tare da leƙa madafar ya hangi Ummu dake tsaye tana ɗauko maysakaiciyar tukunyar da zta ɗora ruwan zafi yace "Bari in duba in ga Jabir ɗin ko ya samo man, idan babu ko na motar ki sai mu tsiyaye mu tayar da gen ɗin ko?" Juyowa ta yi, da gaske dai shi so yake ya dinga jan ta da magana, dan kar ya ga ko tana wulaƙanta shi ne tayi murmushin yaƙe kawai tace "To shikenan, ai dai kun san mai yana tsada ko?" Dariya yayi, ko ba komai ya ji daɗin yadda ta amsa mishi sannan yace "Nufin ki siya zan yi kenan? Ko dan ƴar ki ai kin bamu kyauta ko?" Murmushi tayi mai sauti kawai tace "Shikenan to, na bayar." Fita yayi ita ma ta ci gaba da abinda take yi, Alhaji kuma ƙofar gida yayi tsaye yana jiran Jabir wanda tun kafin a ɗauke wutar dama yayi tunanin sai an ƙara mai a gen ɗin, hakan yasa ya zo ɗakin su, sai ya samu Aliyu kwance Jabir ya faɗa masa magani ne ya sha na zazzaɓi ya kwanta, dan haka ya ce shi bari ya je ya samo man bakin hanya, haka ya fita Alhaji na ma Aliyu sharrin ragon maza ya zama ba zaki ba tunda canjin yanayi ya kwantar da shi, dariya Aliyu yayi yace mishi _"Jabir ma fa yayi kalar nasa zazzaɓi Abba, kawai dai dan baya so komai sai ka sani ne, kuma shi nashi zazzaɓin har da rashin mace ya jaw..."_ Da sauri Alhaji ya kwaɓe shi da _" Aliyu, bana son maganar banza."_ Ya ɗan jima nan kafin Jabir ya dawo ɗauke da jarkar mai a ciki, da mamaki Alhaji ya tare shi yana faɗin" Jabir, har man nawa ka siyo mana?" Murmushi kawai yayi bai ce komai ba, raɓawa yayi zai wuce Alhaji yace" Kawo na shiga da shi ciki ko?" Da sauri Jabir ya kalle shi yace" Subhanallah ! Abba ni fa?" Murmushi Alhaji yayi na ganin yadda Jabir ke ɗauke da jarkar man ka rantse da Allah man kaɗan ne a ciki bayan kuma cike yake, ko da yake ai Jabir ya yi ga-ruwa, dan haka tun yana matashi ya saba ɗaukar wannan jarkar cike da ruwa (biyu ma yake haɗawa☹️). Bayan Jabir ya bi yana faɗin "Muje to sai ka juye." Suna kusan shiga ɓangaren Alhaji dake gaba ya dakata saboda kiran da aka masa a waya, wanda ya kira dole ne ya amsa duk da 12 na dare ne lokacin, amma dake ya wakilta ya zauna inda ake can yanzu haka ana sauke masa kayan shi, to kiran zai iya yiwuwa da matsala ko akasin haka. Dan haka ya dakata ya ma Jabir alama da ya wuce tare da faɗin "Ina zuwa, je ka kawai ɗakin buɗe yake ka juye man." Cire takalmin shi yayi ya shiga falon da sallama a tausashe da kuma ciro wayar shi ya kunna fitila. Ummu dake tsaye ta yanka lemun tsami guda biyu, na uku ta ɗauka za ta yanka sai ta ji sautin sallamar Jabir cikin wannan ƙasaitacciyar nutsuwar, bata san dalilin da ya sa gaban ta ya yanke ya faɗi ba, cikin ta ya hautsina gaba ɗaya, hakan yasa ta juyawa da sauri da razanin me ya shigo da shi yanzu? Kar dai kuma ya shigo nan gashi ita rigar bacci ce jikin ta iya guiwan ta kuma. Garin wannan ƙoƙari da firgici juyawar da ta yi wuƙar nan ta sauka a tsakiyar tafin hannun ta, yadda yankan ya ratsa ta ya ta rintse idanu da ƙarfi tare da sakin wuƙar ta ɗaga murya a sirance ta furta "Ahhhhhhh! Subhanallah!" Ƙn buɗa idanun tayi sai hannun da ta ji yana ci gaba da yi mata zugi take ta yarfa shi tana addu'a kala kala. Jabir na daf da shiga ɗakin gen ɗin ya ji wannan sautin da ya saka gaban shi faɗuwa kuma tsigar jikin shi ta tashi, tabbas daga madafa ne ƙarar, kuma ba ihun Kuwailat bane wannan, ihun Maama ne, *Maaman shi* ce wannan, to amma me ya sa tayi ihun? Sanin da ya ma mata ko kyankyaso zai iya saka su wannan ihun bare fiye da haka, dan ya sha jin haka daga matar Baban shi, sai ya zaburo ta ce ƙadangare ne ko ɓera, ya so share abun kawai. Amma sai yake jin sautin addu'o'i ƙasa ƙasa haka, sai ya aje jarkar da ɗan sauri kawai ya leƙa kan shi da niyyar ya nemi izinin shiga, hannun da take yarfawa tana safa da marwa idanun ta rufe ta siririn hasken wayar ta da bai gama zagaye madafar ba ya gani, sai ya ji abu mai kama da tashin zuciya... Um um! Tashin hankali, gushewar lissafi haka, da dai rasa nutsuwa gba ɗaya sun ziyarce shi, Maama, me ya same ta? Shiga kawai yayi ƙarewa madafar kallo da son ganin me ye ya tsorata ta? Sai kuma hannun nata da shima yake kallo, bai taɓa sanin zai iya yin magana cikin irin muryar dake nuni da tashin hankali ba sai yau, yadda ya ji bakin shi ya furta "Maama, me ya same ki?" A firgice ta buɗa idanun ta ta kalli fuskar Jabir, kafin tayi wani tunani ita tsiraicin ta ne a gaban ta, da mugun sauri ta durƙushe ƙasa duka guiwoyin ta a ƙasa tare da saka hannu ɗaya taa rufe kafaɗar ta dan kar ya kalar mata ƙirji tace" Me ya haka Jabir? Ya za ka..." Kalmar _" Subhanallah!"_ Kawai ta ji ya ambata, kafin ta ankara da me ya sa yayi sai ganin shi tayi durƙushe gaban shi shima, ba wannan ba... Ba wannan ne ya ɗaga mata hankali ba, ba shine ya tsayar mata da tunani ba sai ganin Jabir ya damƙi hannun ta da ita kan ta bata san danshin jinin da yake yi har yaa kai yana ɗasa ƙasa ba ya riƙo shi da kyau tare da tattara hankalin shi yna kallon hannun. Har ga Allahn da ya halicce shi shi kallon mahaifiya yake mata, har zuciyar shi bai riƙo hannun ta da wata manufa ba, sai dai ya yarda kawai sharrin sheɗaan ne da ya saka shi jin gaban shi ya yanke ya faɗi har yake masa raɗa a kunne da cewa _"Hannun Maaman ka taushi, ga kuma ɗumi."_ A zuciyar shi yayi a'uziyya tare da zura hannu aljihu ya ciro hancki ya warware shi, da sauri ya ɗora shi a hannun nata ya fara kiciniyar ɗaure mata ko jinin ya daina zuba. Har cikin ranta take jin wannan haɗa hannun d sukayi, wataƙila yanayin da take ciki ne ya yi tasiri har kan ƙanin bayan ta wanda ke kiran ta da sunan Maama? In ba haka ba me zai sa ta dinga jin wannan abubuwan game da shi dan ya taɓa hannun ta, daga tafin ƙafar ta fa ta fara jin an tsikare ta har zuwa wurin d ya jima yana mata Ƙaiƙayi an kasa sosa mata, ga fuskar shi da take kallo a razane sai sheɗaan ya fara faɗa mata _"Dubi fuskar shi kyakyawa kamar ta jaruman da kike kall..."_ A rikice Ummu ta miƙe tsaye bayan ta fincike hannun ta daga na Jabir, rintse idanu tayi, ranta ya gama ɓacewa, hankalin ta ya ƙarasa tashi, idanun ta sun gama rufewa da wannan abu da ke faruwa da ita. Cikin ɗimuwa da zautuwa Ummu da ta miƙe tsaye cikin ɗaga murya tace "Bana so, bana son taimakon kowa, me yasa baku da tausayi? Duk halin ku ɗaya, ba kwa taɓa zama da mace kusan me ce ce matsalar ta, burin ku kawai mace ta halaka a sanadiyar ku, to ƙarya ne wallahi, duk da ina jin shauƙi akan haka, Jabir ko waye ma ba zan taɓa yarda na aikata abinda bai dace ba, kayi nesa dani tun kafin mu faɗa halaka, ka gane mana, matsalata babba ce, kuma..." Sai kuma ta dafe kan ta kawai da mugun sauri ta juya ta kama hanyar barin madafar, ɗimuwa ya sa ta manta rigar dake jikin ta, bayan ƙarama ce ta fito mata da surar jikin ta. Jabir da duk abinda take faɗa tsaf yake riƙe shi akan shi, albarkar haddar Alƙur'ani tasa komai ma yana riƙe shi da gaggawa sannan ya jima bai manta shi ba, ya la kowace kalma muhallinta na musamman, wuri kawai yake jira ya samu ya aje équations sannan ya tantance su da kyau, to amma da ta juya a fusace, shi kuma ya juya a mamakance ya bita da kallo, sai kawai la'anannen Allahn nan ya tilasta masa duban ƙasa kaɗan daga bayan ta, hakan yasa idanun shi sauka tsaf kan wani irin nagartaccen ƙugu da ya iya hango wasu irin duwatsu duwatsu dake nuni da jigidar ce nan tari guda kenan. Kai jama'a, anya kuwa Maama lamarin ta ba shafar iskokai? To abu take irin na ƴan iska fa gaban shi, wannan saboda Allah tafiyar da ta dce tayi ce ko da dai ranta na ɓace? Da ƙyar ya muskuta ya kashe mata wutar da bai san me za ta yi da ita ba, juyawa yayi jikin shi duk a kasalance ce ya bar madafar, har ya fara zuba man sannan Alhaji ya same shi, suna zubawa aka tayar da shi gaba ɗaya unguwa ta ɗauki haske. *Tana* kwance ta kifa kanta tana rizgar kuka na bara bara ta ga haske ya mamaye ɗakin inda sanyi ya daki fatar jikin ta, tashi tayi zaune ta kalli ɗakin sannan ta kalli inda madubi yake, sai kawai ta share hawayen ta tare da gyara zaman ta kan gadon tana mai ɗaura niyyar _"In sha Allah gobe zan je gidan Alhaji Sagir, zan faɗa masa duk dan ya sama min mafita, nasan shi zai fahimce ni sannan ya taimaka min, amma ba zan halakar da kai na ba."_ Da wannan ƙudurin ta kwanta duk da kuma ba tayi bacci ba a daren, amma dai ta wayi gari da shi. A shekaru goma sha uku zuwa sha huɗu da suka ɗauka tare na rayuwar su, ko maƙwabta bata taɓa shiga ba da izinin sa ba, shi kan shi ya yi mamaki sosai da Kuwailat ta ce wai Maman ta ta riga ta fita, ta fita ta je ina? Ba ta gyay masa ba kuma? To me take nufi? Matsalar tasu har ta fara kai wa haka? Bai da matsala dan ta fita bai sani ba, ya san duk inda Ummu za ta je ba z atpa je inda ba zai ji daɗi ba, to amma kuma me yasa sai yanzu kwatsam kuma da safe haka? Sannan Kuwailat ma bata san ina taje ba. *Ummu* dake gaban amaryar Alhaji Sagir suna hira bayan tabbatar mata yana zuwa yanzu dan ta faɗa masa yana da baƙuwa, cikin raha Hajia Zeinabu ke sake mitar "Wallahi Ummu ba kya da kirki, yanzu yaushe rabon ki da gidan nan?" Ummu da ƙyar take murmushi, kuma ita Hajia Zeinabu ta fahimci haka, dan tunda ta ganta a wannan lokacin kuma ta ce Alhaji take son gani, amma dai tana son jan ta da hira dan fa kullum suna tare a waya, suna gane ma juna kasancewar sune amaren gidajen mazajen nasu dake aminai. Cikin taushin muryar Ummu dake yaƙe tace "Wallahi Maman Na'ima ba kya rabo da tsokana? Na ga ko ban zo ba kullum fa muna manne da juna ta waya." Cike da neman rigima ko Hajia Zeinabu tace "E na sani, amma ai waya daban zumuncin gida kuma daban." Murmushi Ummu ta sake yi ta muskuta za ta yi magana kenan Alhaji Sagir ya sallamo falon, da kulawa suka amsa mishi inda suka gaisa sosai da Ummu, miƙewa Hajia Zeinabu tayi tana faɗin "Bari in baku wuri, idan kun gama zamu zauna." Wuri ya samu ya zauna yana faɗin "Maman auta , ya gida? Ina autar tamu?" Da ƴar fara'a tace "Lafiya lau." Hankalin shi ya mayar kan ta kacokam tare da faɗin "Hajia Ummu, lafiya dai ko? Na ji hankalina ya nemi tashi duba da irin haka bai taɓa faruwa ba." Kan ta na ƙasa sosai tana ta wasa da makullayen ɗakin ta da na mota, cikin shasheƙa da fargaba ta fara faɗin "Dama...dama Alhaj... Shine yak..." Nauyi, kunya, kara suka saka Ummu yin shiru hawaye na neman ɓalle mata, cike da kulawa Alhaji Sagir dake kallon ta ya kuma gane komai yace "Ummu, faɗa min naji menene matsalar? Me Alhaji Kabir ɗin ya miki? Ki faɗa min mana, na ɗauka kin zo ne dan kin san na isa da shi kuma zan iya yi miki maganin matsalar ki, sannan ina ɗaya daga cikin waɗanda suka je nema masa auren ki, kuma aka duba girma da kimar mu aka bashi." Sai kuma ya tausasa murya sosai yace" Faɗa min Hajia Ummu, ina sauraren ki." Ɗan ɗaga kan ta tayi da niyyar tayi ƙarfin halin faɗa, amma sai ta sake kasawa, zuciyar ta nuna mata take a'a, da kunya ai, ba tare da ta shirya ba ta miƙe tsaye, dama komai nata yana hannun ta, bare rikicewa ta saka ta manta wani abu a wurin, dan haka ko juyowa ba ta yi ba tace "Ba komai, nagode, sai anjima." Da kallo ya bita bayan ya yinƙura da niyyar ya mata magana, amma nauyin jiki ya sa dole ya dakata ya bita da kallo har ta fice, yana nan zaune har ya ji fitar motar ta a gidan, koma menene ya san akwai matsala kawai, tunda ba ta taɓa masa irin haka ba, dalilin ma da ya sa kenan ya ji tausayin ta ya kama shi, dan ya san ta rasa mafita ne kawai ta tunkaro shi. *Alhamdulillah.* 15/08/2023, 20:14 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *46* Da wuri ne sosai, hakan ya sa ta same shi gida ko fita bai yi ba, yada ta shigo tana sharar hawaye riƙe da rigar ta doguwa da take jin ta mata nauyi da yawa yasa kawai Alhaji Kabir ya fahimci Ummu ba ta cikin nutsuwa irin wacce ya san ta ciki, ko sallama ba ta yi ba fa, shi à yadda ya gani ma kamar ba ta gan shi ba, dan neman shigewa tayi ciki saida ya miƙe tsaye yace "Daga ina kike?" Cak! Ta tsaya tare da juyawa ta kalle shi, saida ta sunkuyar da kan ta cikin wata irin raunanniyar murya tace "Na fita ne, amma ban jima ba, ka yi haƙuri sanar da kai ba." Yadda ta yi maganar da haƙurin da ta bashi yasa shi jin nutsuwa a zuciyar sa, sai kawai tausayin ta ya mamaye masa zuciya, abin ka da wanda kake so, a hankali ya matsa kusa da ita, kafin ta ankara ya rumgumata jikin shi cikin rarrashi yana faɗin" Ummu, me ye matsalar ki ne wai? Kinga yadda duk kika shigo a gigice? Sai ka ce fa wacce na ke zanewa cikin dare." Dama a raunane take, ita kan ta tausayin kanta da kan ta take yi, kuka kuma ta jima tana yin shi har ta gode Allah, sai kawai ta fashe da kuka tare da sakin jakar ta tana cimimiye shi, a nutse yake daddana bayan ta yana shafawa, Ummu da ta fara jin abun kamar wasa yake mata sai ta fara rage sautin kukan ta, a hankali ta fara kame ƙafafu, shi kuma take ya fahimci hakan daga gare ta, sai kawai ya ɗago kanta daga jikin shi ya kalle ta yace "Amaryata, muje ɗaki ne?" Duk da abu ne da take so, amma sai ta sunkuyar da kan ta, kama hannun ta yayi zuwa ɗakin ta, duk da yasan ba kwanan ta bane yau, amma dai ya fahimci har da nesa da sukayi da juna ya ƙara ta'azzara halin da take ciki. Lallai ta kai maƙura, dan kuwa duk wata taɓawa da ya mata sai ta ji ambaliya daga ƙasan ta, tun tana kukan jin daɗin ƴar wasar da ta samu yana yi da ita, har ta fara kuka na tsananin buƙatuwa da son ta ji yana jijjiga jikin ta, sai dai yana shiga jikin nata ba jimawa ya kawo, sa'ar ta ɗaya wasa da ta samu yau har ta yi nasarar tsiyayyar da wasu ruwan. Alhamdulillah. *A* yammacin wannan ranar Alhaji Sagir ya zo da kan shi dan jin me ke faruwa? Saboda saida ya haɗu da Alhaji Kabir amma ya nuna masa komai fa lafiya lau, dan haka yake ganin kar a zo Ummu ce ke cutuwa su tauye ta. Tunda aka ce mata yana sallama ta san me ya kawo shi, sai dai tayi niyyar ba fa za ta faɗa ba, kawai za ta bar hakan a matsayin Ƙaddarar ta, wataƙila kawai tanadin da ubangiji ya mata. Sai dai Kashhh! Alhaji Sagir da ya zauna yana faɗa mata "Ummu ba ki min adalci ba idan har baki faɗa min matsalar ki ba, ni na ɗauka sanin na isa ne ya sa har kika tako kia zo inda nake, to amma me yasa za ki ɓoye min? Kar jin nauyina ko kunya tasa ki cuci kan ki, idan kuma kin gagara faɗa min, to zan je wajen mahaifiyar ki na sanar da ita kina cikin matsala amma kin kasa sanar da kowa, wataƙila ita idan ta zo kya sanar da ita." A dole ta dakatar da shi da sauri da cewa" A'a, zan faɗa, b sai Mama ta sani ba, bana so ta san me ke faruwa." Gyara zama yayi yace" To ina jin ki." Hijabin ta ta ƙara jawowa ta rufe fuskar ta, kan ta na ƙasa sosai tana kallon carfet, cikin kunya da ladabi cikin siririyar murya tace" Dama.. Ni ce ban da lafiya...to naje asibiti...kuma....na faɗa masa komai, amma sai ya...faɗa min girma ne ya zo masa yanzu, ba zai...iya komai ba, amma wai...nayi haƙuri tunda suma su Hajia Atika duk haƙuri suke yi,... To ba...ba." Rintse idanu tayi sai hawayen da take riƙewa suka sauko kan kumatu, shiru tayi na sakanni tana sauke ajiyar zuciya. Komai ya fahimta a ƙanƙanin lokacin, ba kuma komai ya birge shi da yarinyar ba sai yadda ta sakaya zancen tayi alkunyya ta ƙi faɗan komai gatsau, sai dai duk babba mai tunani idan yayi nazari zai gane me take nufi, ƙwarai ya ji ya ƙara tausaya mata, kuma ya ji Alhaji bai kyauta ba da maganar ta yi haƙuri, ta yi haƙuri ma kamar ya? Da sha'awar? Wacce ubangiji ya halicci mutum da ita, ta ya ma ake haƙurin ta? Idan ma ana yi ai na ɗan lokaci ne, idan ba haka ba kuma za'a samu saɓani. Shiru ya yi bai ce komai ba, dan ya fahimci ba iya zancen kenan ba, saida ta gama shasheƙar kuka ta sai ta nutsuwar ta sannan ta sake sunkuyar d kan ta tana share hawaye tace "Na gwada yin haƙurin ba tun yau ba, kasawa ne nayi har na sanar da shi abinda ke faruwa, ina so na manta da matsalar sannan na ci gaba da rayuwata, amma ciwo ya sakoni gaba, da naje asibiti kuma sai likitan ya nemi yi min lalata, ya ɗauka ko ni ɗin ƴar iska ce?" Shiru ta sake yi na sakanni kafin ta ɗora da" Ba ma kallon duk wani abu da bai shafi addini ba a gidan nan, amma abun nan dake damuna ya sa na fara karance karancen abinda bai dace ba da kuma kallon finfinai, na jima da faɗawa halaka duk saboda ƙin ɗaukar matsalar da mahimmanci... Abban Na'ima..." Ta Kira sunan da take kiran shi da shi tana kallon fuskar shi ta ɗora da" Ta kai ta kawo ko ya na kalli kusancin macen da namiji sai na ji a jikina, bayan na tuba daga aikata kallace kallacen nan, sai ga sheɗan la'anannen Allah har ya fara haska min Jabir wanda yake kallona a matsayin uwa kuma nake kallon sa ƙanena har ya ƙawata min shi a fuska, daga tsautsayi ya sa Jabir ya riƙe hannuna dan taimaka min akn ciwon da naji, sai kawai naji jikina na amsawa, to wannan wace irin halaka saboda Allah? A haka zan ƙare?" Ta dire maganar da wani sabon kuka, kan Alhaji Sagir na ƙasa yana ta nazarin abun yana masa wani kallo a wata mahanga da ta dace da hankali da shari'a, a bakin shi kuma salati kawai da tasbihi yake yi, dan shi ya hango ƙiris ya rage yarinyar ta fara aikata ba daidai ba, ba wai zina tsakanin mace da namiji ba, mata ma ƴan uwan ta suna nan irin ta suke nema, ba kuma za ta musu wahalar shawo kan t ba, tunda a bakin gaɓa suka same ta ƙarasa jan ta kawai za su yi. Cikin nutsuwa da yi ma matsalar ta kallon basira yace "Na fahimta Hajia Ummu, wannan ma ai maganar banza ce, kiyi haƙuri ? Ta ya zai ce haka? Kamar dai ƙaramin yaron da bai san inda rayuwa ta dosa ba?" Sai kuma ya jinjina kai yace "Shikenan, karki damu Hajia Ummu, zan same shi in sha Allah, daga nan gurin shi zan nufa, zan yi magana da shi, kuma in sha Allah za ki ga biyan buƙata." Jinjina kai kawai tayi amma kuka ya hana ta magana, miƙewa yayi yana sake jadadda mata "Ki daina kuka fa, wallahi zan masa magana, ni ban ma san ya aka yi ya bari har haka ta faru ba da har wani ɗa iskan likita zai miki rashin ɗa'a, zan same shi muyi magana, ki daina kuka kin ji." Cikin kuka ta amsa mishi da "Nagode, Allah ya tsare." "Ameen." Ya faɗa yana fita tare da faɗin "A gaishe min da auta, ba zan tsaya jin rigimar ta ba yau." Ba Ta ce da shi komai ba har ya fita daga falon, saida ta goge hawaye ta sai ta nutsuwar ta sannan ta miƙe ta ci gaba da abinda take yi kafin zuwan Alhajin. ******************* Lokacin da Maama ta buga sammako ta fita ɗan nata na kwance, ba wai baya tafiyar shi Saudia ba, shi tun yana rayuwa gaban mahaifin shi ba zai iya tuna ranar da har rana ta fara fitowa yana kwance ba, yayi sallah tun asuba dan jam'i ma ya samu, amma wai yana dawowa ya koma ya kwanta saboda matsananciyar kasalar da ya tashi da ita bayan mummuna kuma wani ɗaɗɗatan mafarkin wai yana tare da mace.... Anya kuwa ma a rayuwar sa ya taɓa irin mafarkin nan? Bai taɓa yi ba, to me yasa sai jiya? Kawai dan ya riƙe hannun Maaman shi? Saboda dai tsabaro fitina irin ta ɗan lis? Fitowar Aliyu daga wanka ta sa shi gyara kwanciyar sa ya lumshe idanu, dan ya san yanzu ya tisa shi gaba da sharri kala-kala, ai ko Aliyu sarkin tsokana idan ya so kuma ya zama zaki a sha miskilanci da fara'a a yaren larabcin da suka saba da shi yace "Allah gafarta malam, yau ba za'a fita bane? Ko irin fitar masu mata zaka yi yau? Dan naga ka farka tashin dare alamar an fara kaɗa maka ƙararrawa." Yawu Jabir ya haɗiyi sannan ya buɗa idanu a hankali ya tashi zaune, saida ya jingina a gadon ya rumgume hannaye sannan ya dube shi yace" Zan fita." Aliyu dke neman kayan da zai saka da kulawa yace" Ya kamata dai, dan ka ce sammako zaka yi kaje wajen Abba akan maganar tafiya Agadez." Shiru Jabir ya sake yi bai ce komai ba saboda tuna masa da wani abu da Aliyu ya yi, Agadez? Wajen su Anna? Hmmmm ! Zai je, ba zai ce a'a ba, tunda Abban shi ya ce ya je saboda Anna da Abbu sun damu zai je, sai dai ba zai taɓa manta wofantar da shi da sukayi ba, bai da laifi, bai taka ma ko ɗaya daga cikin su ba, amma haka suka banzatar da shi ba wanda ya tallafe shi a rayuwa? Yana cikin wannan tunanin ya ji muryar Aliyu yace "To, ni zan wuce, wataƙila ma yau mu wuni bamu sake haɗuwa ba, dan dukanmu sabgogi ne a gaban mu." Hannu Jabir ya miƙo masa sukayi musabiha sannan ya furta msa "Fatan nasara." Murmushi Aliyu yayi yace "Kaima haka." Daga haka ya fice daga ɗakin, ganin haka sai Jabir da baya jin zai iya tashi lokacin ya sake komawa ya kwanta, shi ruwan ɗumi ma yake sha'awar yin wanka da su, ka ga kuwa da mata gare shi sai ta dafa masa ai. A hankali ya sauke numfashi tare da ayyana _" Rashin mata bai yi ba."_ Gagarumin bacci mai cike da salamar da ya rasa daren jiya ne ya kwashe shi, sai da kiran Abban nashi ya tashe shi kaɗai ya farka, rana tayi fauuu sosai yadda ba ka iya ɗaga ka kalle ta, a gurguje ya shirya ya fita daga gidan ba tare da ya bi ta kan kowa ba. Ƙofar gida ya samu Abban shi tare da maƙocin shi suna hira, ko d suka gaisa sosai Abban ya ƙarewa Jabir kallo, sai kawai ya girgiza kai tare da mayar da hankalin hi kan maƙocin nashi, saida suka gama tattauna abinda ya haɗa su bayan ya tafi sannan ya sake kallon Jabir, cikin nutsuwa ba kuma alamar wasa yace masa "Jabir, za ko ka iya jiran *Kuwailat*?" Wani irin *rassss* gaban shi ya bada, a rikice ya kalle shi har yana neman sarƙewa yace "Na'am Abba? Ban....ban gane ba?" Murmushi Abban nashi yayi ya gyara tsayuwar shi yace "Ba munyi da Alhaji zamu haɗu ba dama ranar asabar? To ai akan maganar ka da Kuwailat ne, amma sai nake ganin kai kuma kamar..." Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! Kuwailat ? Me kenan Abba ya aikata? Kuwailat ya bashi tun yanzu? Ya gane me yake ji akan ta ne dama? Ya fahimce shi kenan? Kenan dai Abba ya fahimci yana son Kuwailat? Yayin da shi kuma wannan Abban ke neman fahimtar mafarkin da ya kwana yana yi daren jiya? To wai su manya nan.... Maama, it ta sake zuwa masa a rai, kalaman nan nata, sun jirkita masa lissafi sosai ta yadda har yanzu ya kasa gane me yasa ta faɗa, sai dai abu ɗaya da zai ce yake tunani a kai bai wuce kamar tana da damuwar da Abba ya kasa fahimta ba, shiyasa ma ta zunduma musu kuɗin goro duk ta watsar. Shirun nan ne ya tabbatar ma mahaifin shi da gaskiya ne, inda shi kuma tunanin da yake yi ne yasa yayi shirun, dafa kafaɗar shi yayi yace "Kar ka damu, Abban naka ai mai ƙaunar ka ne da tausayin ka, da ya fahimci hakan zai yi ƙoƙarin kawo maka mafita, yanzu ya maganar tafiya gaishe da su Anna? Da kuma su Mama?" Sunkuyar da kai Jabir yayi, cikin ladabi da kunyar abinda mahaifin nashi ke ta gani a tare da shi ya amsa da" Abba, duk yadda ka ce, haka za'a yi in sha Allah." Jinjina kai yayi da jin daɗi yce" Shikenan to, ina ga ko zan je islamiyyar su Uzei na nemo mata izini a wajen malamin su, kaga sai mu tafi tare dukanmu ai, dan gaskiya mun jima rabon mu da can." Jinjina kai yayi yace" Shikenan Abba, Allah ya yarda." Juyawa yayi da niyyar shiga ciki yna faɗin" Mu shiga ciki ku gaisa." Duk da ba ya ƙaunar yadda matar Baban ke share shi tana hararen shi, amma haka ya bi bayan shi bai masa musu ba, idan da sabo dai ai ya saba ko? Kuma da hakan cutuwa ne gare shi da ya mutu tun yana ƙaramin shi ma. Rabon ayi ya sake shigowa gidan saboda tunanin ko ta manta ko kuma ganin Jabir zai sa ta yi shiru, sai dai ya manta wacece Bara, tana ganin shi ta taso daga kan kujera cike da hargagin bala'i tana faɗin "Ahaf! Dama ba na gaya maka ka dawo ba? Ai baka da inda ya fi nan, to gashi ka dawo ni kuma ina nan kan bakana, babur ɗina wallahi tallahi sai ka biyani, kai har ka isa ka raina min wayo? Daga fita da babur ka dawo ka ce wai wata tsiya an ɗauke, to baka isa ba Billahillazi, ka biyani ko kuma kotu ce zata rabani da kai." Duk wannan abu da take Jabir na kallon ta, takaici na mamaye masa zuciya, tausayin mahaifin shi na sake baibaye shi. A rikice Abban ya wawuri takalmin shi da niyyar ya cakume ta ya gaggaura mata dukan tsiya, da azama Jabir ya riƙe shi... Wani irin tattausan riƙo ne ya mishi, amma da ya sake ƙoƙarin ƙwacewa dan ya kai ga jikin Bara sai ya ji shi ram a hannun ɗan shi, ya sani dama ba daga nan in dai Jabir ne, to tun yana da shekarun shi bisa kai dama idan yayi niyyar kafewa ba ya iya juya shi, bare yanzu da ya zama bqlagaggen baligi haka, baya ga wannan ai ba zai manta ranar da ya wuntsila shi akan babur ɗin wannan jarababbiyar matar ba. Cikin nutsuwa Jabir ya juya ya kalle ta sai kuwa faɗi take "Sake shi mana, aikin banza, bashi ya zo dan Allah naga me zai yi, kai dai ka manta ni ko?" Cikin yanayin ƙufula da hassala Jabir yace da ita "Dan Allah shiga ciki, ba na son tashin hankali." Yanayin hassalar da yayi mata magana da shi yasa ta ƙura masa idanu, sai kawai ta ji ta kasa masa gardama, ɗan ta ne fa, tunda ɗan mijin ta ne ai, amma tsaf ta haɗiye abin da ke ranta ta juya ta shiga ɗakin kuma wanda ta san ko shi uban shi ya bata wannan umarnin ba zta yi abinda ya ce ɗin ba. Ganin haka sai Jabir ya saki mahaifin nashi à sanyaye yana faɗin "Bana so gaskiya, bana son haka Abba." Bai jira ya ce komai ba kuma sai ya raɓa shi ya fice yana faɗin "Zan dawo anjima." Da wannan haushin ya fita a gidan, kai ina dalili ina anfani mata irin matar Baban shi? Ba fa dan ba kyau ba, da sai ya dakonci mahaifin sa baya nan zai shigo mata cikin dare ya rufe ta a ɗaki wallahi ya zane ta, to amma babu kyau haka ai, amma dai mata irin ta baban shi, irin su ne suka saka ka aiki da ayar da ta ce a dake su dan su gyara, Haba. Gashi yanzu ta hassala mahaifin shi, shi ma kuma ta harzuƙa shi, almubazzarancin da ya ba so yayi da kuɗin shi saboda aikin dake gaban shi, shine ta sa ya yi, dan kuwa wasu irin dalla-dallan babur guda biyu ya yanko mata ita da mahaifin nashi, mark ɗaya sai dai kala kowa da ta shi, to akan babu ɗin take cewa za ta kai uban shi kotu? Ita ga mahaukaciya ba. A cewar mahaifin Jabir ba'a taɓa masa sallama mafi ƙolokuwar arziƙi irin ta yau ba, bayan an bashi makullayen su da takardu aka shiga da su ciki, saida yayi ƙwallan farin ciki, dama rashin abun hawan ya sa yake karɓan nata ai, to ɗan sa ya huce masa takaici, tun yana ƙofar gida Jabir ya kira shi, bayan ya amsa sa albarkar da ya masa à nutse ya furta "Abba." Shima a nutsen ya amsa da "Na'am, Jabir." Cikin sigar rigima Jabir yace "Abba, ni fa ka gaya wa matar ka, gaskiya ta daina ɗaga maka hankali, kai kaɗai gare ni fa." Wani daɗi ne ya kama mahaifin shi, sai yayi saurin juyawa cikin gida yana saka wayar a amsa-kuwa dan kawai ya bata haushi dan halin Bara'atu sai Allah yana faɗin "Ban ji ba Jabir, me ka ce? Kamar sadarwa ba kyau." Ya ƙarashe maganar da hararen Bara da ta rikice ganin moto guda biyu sai zagaye su take tana kallo tana taɓawa da neman ƙarin bayanin na waye? Cikin siririyar murya kuwa Jabir da bai san ya saka shi amsa kuwa ba yace" Abba, na ce ka faɗawa aunty ta daina ɗaga maka hankali, bana so ko kaɗan, zuciyata gaza ɗaukar hakan take yi." Bai jira ya ce komai ba kuma sai yace" Sai anjima Abba." Wani shaƙiyin murmushi ya saki yana maida wayar aljihu ba tare da ya kalle ta ba yace" Ɗana Jabiru kenan, Allah ya maka albarka." Taɓe baki tayi tana ayyana _" E lallai Jabir ya ƙaro wulaƙanci, yanzu ita yake gayawa haka? Gashi kuma yanzu ba zai daku ba, to w ma zai dake shi? Dama can ai uban dake da kashi ɗaya take saka wa yana dukan nashi, to yanzu kuma sun ɗinke."_ Makulli ya cilla mata yace" Ki ɗauki ɗaya, ɗayan nawa ne, Ɗana ya siya min sannan ya min shamaki daga tonan asirin ki." Bai ko kalle ta ba ya wuce ɗaki yana faɗin" Bari nayi wanka na fita zaga gari, yau hankalina kwance." Da kallo ta bishi, sai ta sake Taɓe baki, ita ta rasa me suke nufi da ita? Kamar wata mai hassadar su, sai wani abu suke yi haka dai... Ko ba komai dai ta ji daɗi, sabon babur fa aka siya mata madadin tsohon da take fama da shi, ita kam me ya fi ran ta? Da alama ma ladabi za ta fara yi ma Jabir ɗin, in dai zai dinga mata irin kyautar nan, to me ye a ciki? Duniya ce fa da bata da tabbas. *Alhamdulillah.* 15/08/2023, 20:14 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *47* Ƙara ƙyalƙyalewa Nabila tayi da dariya tana ci gaba da kitsewa Mama kan ta tana faɗin "Allah Mam ba zan iya sana'ar kitso ba, duba fa mama ke kaɗai amma na huta ya kai sau uku, to ina ga idan mutum biyu ne ko sama da haka? Ai kwana zamuyi ana abu ɗaya." Mama ma dariyar tayi tana taɓe baki tace "Shirmen banza, son jiki ne ba komai ba, ama sana'ar kitso ai sana'a ce mai kyau da idan kina yin ta ba ke ba talauci." Murmushi Nabila tayi tace "Hakane Mama, gaskiya ni dai ban iya zaman nan, amma idan kika ce na dinga yi sai na fara yi wa ƴan unguwa." Jim Mama tayi, a ranta take ƙara godewa Allah da ya shirya mata Nabila, yanzu fa ko ƙofar gida ta daina leƙawa, ta ce istibra'i take jira ta gama duk wanda Mama ta zaɓa mata za ta aura, daga nan kuma ta koma islamiyya ta ci gaba da karatu. Kafin Mama ta ce wani abu Mujittafa ya shigo da sallama suka amsa, gaisawa suka fara yi kafin ya miƙowa Nabila ledar hannun shi ƙarama yace "In ji Yaya Luƙman , ko layin ki ne ya canza miki ko ya ya ne ma ni ban gane ba." Karɓa tayi tana faɗin "Ayya, Allah sarki Yaya Luƙman, shi da nace ya siya min sabo, ni bana son tsohon nan gaskiya." Kallon ta Mama tayi tace "To me ya sa wai? Tsohon da shi aka san ki ai." A ladabce tace "To ai shine matsalar Mama, da na saka yanzu duk mai lambata ai zai neme ni, ni kuma bana son sake mu'amala da mutanen da nayi a baya." A tausashe Mama tace "Ki saka layin ke dai, ai ba'a taru a lalace ba, dole akwai na ƙwarai a ciki wanda nasan kina jin daɗin tarayya da su, ko ba haka ba?" Mujittafa ma murmushi yayi yace "Gaskiya kam, kuma a cikin su ma zaki iya samun wanda shi da gaske auren ki yake so yayi, ke ce kawai kika kawo shashanci." Shiru ta ɗan yi, gaskiyar Mujittafa akwai masu son auren ta sosai, musamman ma wani Alhaji Babangida, jinjina kai tayi tace "Shikenan, duk yadda kuka ce haka za'a yi." Buɗe wayar tayi ƙarama ce kamar yadda ta buƙata, saka layin tayi sannan ta kunna wayar, Mujittafa ta kalla da Mama ke tambayar sa iyali tace "Yaya idan ka je ka ce wa Yaya Luƙman nagode sosai, zan kira shi ma na masa godiya da kaina." Bai ce ƙala ba shi dai ya juya yana cewa Mama "Zan tafi, dama hanya ce za ta ɗauko ni ya tsare ni da saƙon ƴar nan." Tafiya ya yi inda Nabila ta ci gaba da yi wa Mama kitso. *Amma* ba'a kai ko ina ba kiran *Fahad* ya shigo wayar... Tunda aka amince da maganar auren su yake kira hankali tashe amma waya kashe, ya ɗauka shine bata son Magana da shi, ya karɓi wata wayar ya kira amma dai ba'a samu, haka ya tisa Ja'afar gaba ya bashi lambar ƙawar ta ya tambaye ta Nabila, ita dai amsar ita ce ta jima rabon ta da ita, kuma tana kiran ta ba ta samu, dan haka yake ci gaba da kira dan Hajia ta ce su Alhaji da Yaya Bilal da u aunty Fa'iza za su je dan yin magana da Maman ta akan auren su. Ta san lambar shi dama, dan haka tana ganin kiran ta ja tsaki ta yanke tare da cewa Mama "Wai Mama kin san wa yake kirana? Fahad ne fa." Saida gaban Mama ya faɗi da jin sunan, amma ai ta dake tace "Fahad kuma? Dole ya kiraki mana tunda kin jefar da waccen wayar." Taɓe baki tayi tace "Ba zan ɗaga kiran shi ba Mama." Cikin nutsuwa ba tare da ta kalli fuskar ta ba Mama tace "Saboda me Nabila ? Ina ce duk kin bani labarin abubuwan da suka faru tsakanin ku, har da abinda aka miki a gidan su ma, ni sai nake ganin da gaske yana son ki, ki ɗaga ki ji me zai ce miki?" Katsewar da kiran yayi yasa Nabila kallon wayar sannan ta kalli Mama a tausashe ita ma tace" Mama, bana musun son da Fahad yake min, kuma na yarda da aurena da yake son yi, sai dai na ksa yarda ba hannun shi a cikin abinda aka min gidan su, Mama..." Ta Kira sunan Mama da wani irin yanayin da saida Mama ta ɗan janye kanta ta juya ta kalle ta da kulawa, ɗorawa tayi da" Ban sani ba Fahad alkairi ne haɗuwata da shi ko kuma sharri, sai dai ya min alkairin da ba zan manta da shi ba a rayuwata, domin kuwa shine ya nuna min abinda muke yi ba kyau, sannan ya ce mu tuba ga Allah sannan muyi aure, hatta jiran ganin tsarki ɗayan nan da nake shine ya koya min, sannan..." Sai kuma tayi murmushi kafin ta ɗora da" Shine ya sa na sake dawowa gare ki, Mama a dalilin shi ne yanzu nake jin zan iya saka ƙafar wando ɗaya da duk wani abu da zai ɓata miki rai ko da kuwa bana da iko akan hakan." Narai-narai tayi da idanu tare da sako da wasu hawaye masu zafi tace" Na fahimci mutanen gidan su ba sa ƙaunata, kuma ni na jawo wa kaina hakan, sai dai sun zurfafa ƙiyayar su gare ni, yayin da ni kuma da na kalli tsohuwar nan matar nan... Mama, mahaifiyar Fahad." Sai kuma ta sake yin shiru, dan ita sai yanzu ne abun ya zo mata a rai, tunda jimawa tana tunanin da wanene? Ko wacece? Saboda bata tunanin a kusa da ita duba da ba wata alaƙa, amma yanzu da ta tuna aunty nata sai tayi saurin kallon Mama tace" Mama, wallahi mahaifiyar Fahad duk da tsohuwa ce, amma idan kika ganta yanayin ta sak irin na aunty Ummu, sai dai gaskiya ita bata da kirki ko kaɗan, hasalima ko murmushi ni ban ga tana yi ba." Shiru Mama tayi na sakanni, kamar ba za t yi magana ba kafin ta numfasa tace" Allah sarki, kinsan akwai kamanni a duniya." Kiran da ya sake shigowa ya sa Nabila kallon wayar sannan ta ja tsaki, hakan yasa Mama cewa "Nabila, ina ce yanzu kika gama faɗa min Fahad ya miki alkairi a rayuwa?" Cikin kumburo baki tace "E Mama." A nutse tace "To me yasa zaki saka masa da haka? A ƙalla ki ɗaga mana ya san halin da kike ciki, idan ya so sai ki faɗa masa ya fita a harkar ki." Jinjina kai tayi tana ɗaukar wayar tace "Shikenan Mama." Sakin kan na Mama tayi tare da miƙewa ta nufi ɗaki, dan dole ta san za su buƙaci suyi sirri, da kallo mama ta bita duba da shigar dake jikin ta, riga da zane ne da kuma ƙaramin hijabin ta, wanda waje ma Nabila ta fita kusan tsirara bare cikin gida? Amma yanzu dake ubangiji yayi ikon sa gashi tana gyarawa. Tun bata shige ɗaki ba ta ɗaga wayar tare da faɗin "Hello salama alaikum?" *Fahad* dake ɗakin shi yayi baka-baja da shi saboda damuwa da ɓacin ran rashin sanin me yasa Nabila ke masa haka? A gigice jin an ɗauka ya miƙe tsaye yana ƙarasawa gaban madubi yace "Hello! Beela, wai ya kike min hakane? Ya zan ta kiran ki ki kashe min waya? Me yasa Nabila? Me na miki dan Allah?" kin kashe wayar ki kowa ya kiraki ya ce ba ya samu, na kira ki sau ba adadi da layina da na mutane ke har Mamie ma ta bani wayar ta na kira ki, amma amsa ɗaya ce wayar ki kashe." Duj wannan dogon bayanin da jawabin, daga ƙarshe cike da basarwa da taɓe baki Nabila ta furta" Dan Allah wa ke magana? Ban gane murya ba." Saida gaban Fahad ya faɗi, dan abu ɗaya ya zo mishi ta sha tayi mankas ko? To kar dai a ɗakin wani ƙato ma take, ai kuwa da ya ci buru'uban Nabila a duniyar nan, cike da takaici dan shi fa bai ma kawo a ran shi wai za ta yi hushi da shi ba yace" Nabila, ki maida hankali mana, hankalina tashe na kwanaki, amma abinda za ki gaya min kenan? Nabila har m..." Katseshi tayi da faɗin" Dakata malam, ni ban gane mai magana ba, idan kana da abinda za ka faɗa mai mahimmanci ka faɗa min, idan kuma babu malam zan koma gaban uwata nake ina mata hidima ka taso ni." Shi fa ko da ta ce uwa Ummu ya ɗauka, dan yasan tana kiran ta da sunan Maman ta a gaban shi, wani lokaci ma ta ce uwa mai share kukan ta, cikin jin daɗin tana cikin salama yace" Nabila, me yasa ranar kika tafi baki jira ni ba? Ko da na fita waje na samu har kin ɓace, na..." Nan ma sake katse shi tayi da faɗin" Dan Allah malam ka rabu dani da tatsuniyar nan ko? Haba!" A ɗan ƙufule shima dan ya fahimci iskanci ne ba a buge take ba yace" Nabila bana son isakanci, ya zan share kwanaki ko abincin arziƙi bana iya ci saboda rashin ki, na kasa walwala da sukuni saboda tunanin kina ina? Na zo na rasa mahaifina ma, amma duk da wannan jimamin bai hana ni tambayar, ina kike? Ya kike? Me kike yi? Sannan daga ƙarshe na tambayi kaina ko Nabila ta ci abinci? Dan nsan idan kina cikin ɓacin rai ba kya ko kallon abinci, sannan Nabila dalilin ki na ƙauracewa gidan mu saboda sun nuna ba sa sona da ke, hakan fa yasa muke ta samun matsala da iyayena, har yanzu na kasa yarda Abbu bai rasu da hushina ba Nabila, saboda safiyar washe garin ranar da zai rasu mun samu matsala da shi sosai kuma akan ki ne, hakan yasa nake jin mahaifina ya rasu da hushina, sannan jima ma an sake tattauawa akan matsala ta, duk da na yarda zan musu biyayya, amma dai sun fahimci ke ce kawai a raina, hakan yasa suka amince da auren mu yanzu, amma da sharaɗin zamu daina duk abubuwan da muke aikatawa maras kyau, sannan zaki kammala istibra'in da kika fara..." Shiru yayi na wasu daƙiƙu, hakan yasa ita ma take sauraren shi har tana share hawaye saboda bata so kuka ya ci ƙarfin ta, a hankali ya ɗora da" Nabila, duk wannan soyayyar tamu, shine zan kira ki kina ma nuna baki gane ni ba? Ƙarshen satin na iyayena sun ce zasu zo gidan ku dan ganawa da naki iyayen, shiyasa suka ce na kira ki dan na samu amincewar ki akan zaki yarda ki aure ni, amma shine za ki dinga min hali irin na ƴan maye? Me yake damunki?" Saida Nabila ta lumshe idanu saboda a tsawace ya yi maganar ta ƙarshe, da irin yanayin nan nashi da tasan da suna tare ne sai ya falle ta da tafi ko ya mata mahaukacin zuwa a gadon da zai gajiyar da gaɓɓan jikin ta, duk da ya bata tausayi ƙwarai, abun ka ga abin da zuciya take so, ta ji kamar ta ce ta amince za ta aure shi kawai su zo, amma ina! Dole ta nuna musu ba matse take da auren Fahad ba. Cikin nutsuwa bayan ta ja majina ta furta "Ka ce kar su wahalar da kan su, Fahad na fasa auren ka, yanzu haka istibra'i nake yi, kuma Yaya Luƙman ya samo min mijin da zan aura da zaran na idar, dan haka Allah ya sada mu da alkairin sa, Allah kuma ya baka zaman lafiya kai da wacece ma yarinyar? Mai nutsuwar nan, da saka hijabin nan, da ladabin nan, ba irina watsatsiya ba tantiriya, kaga sai ku ta haifawa Hajiar ka waliyai da manyan shehunnai, hakan ba matsalar Nabila bace." Niyyar yanke kiran tayi, Fahad kuma ya san me za ta aikata, dan haka yayi gaggawar faɗin" Kina kashe min waya Nabila na rantse da Allah yau zan zo Maraɗi kuma har gidan ku sannan na ɗaga miki hankali." Giyara tsayuwa Nabila tayi, e ƙwarai kuwa zai aika in dai Fahad ne, amma dan kar ta nuna ta tsorata sai ta basar tace "Mun ce mun tuba daga aikata komai, amma har yanzu aikin ka irin na masu kurɓe-kurɓen nan ne." Cikin ɓacin ran da tunda ya aje shan komai har sigari ma yake sake ta'azarra masa rayuwa yace "E ɗin Nabila, kuma ko yanzu sai in daddarza miki ba daɗi wallahi, ke bari kiji, ni tunda na gan ki a rayuwata na sa ma raina ke tawa ce, wallahi Nabila baki isa ki auri wani a duniyar nan ba bayan ni, ke dai kin san irin tatabɓurzan da na sha da iyayena akan ki, da wani wai Yaya Luƙman ɗin da ko dakuwa zan iya yi da shi ne ba zan iya ba? Ya aurar da ke ɗin ya gani, na rantse da Allah da shi da wanda ya aure ki duk sai na saka su barin garin nan." Nabila da tsabar mamaki tace" Yayan nawa? Kamar fa uba na ɗauke shi." Cike da shaƙiyanci Fahad yace" E ɗin... " Sai kuma ya numfasa ya furta" Dallah kauce can malama, kuma iyayena zasu zo, idan sun zo ku dafa su ku cinye, ni kuma na san me zan yi." A tausashe Nabila ta furta" Me za ka yi? Ai na gaya maka ka ce kar su zo, wallahi na fasa auren ka." Cike da alfahari yace" Ba can kina hana ruwana yin tasiri a jikin ki ba? To zan zuba wasu kuma baki isa ki hana su zama ɗan mutum ba, kuma ko ba kya so sai kin aure ni." Yana gama faɗa ya kashe kiran tare da cilla wayar a gado yana murza sumar shi, haka kawai duk ta wani ɓata masa rai, shi za ta gaya wa an mata miji? Mijin ƙaniya kawai, ba damuwa zai nuna mata nashi kalar halin tasan da munanan ayyuka ne aka watsar, amma kuma akwai ɗabi'a da barin ta wahala ne da shi. Nabila kam jiki a sanyaye ta janye wayar daga kunnen ta, lallai Fahad dai ɗan ƙunar baƙin wake ne na ƙarshe, a haka fa so yake ta aure shi ko? To ita ko lokacin da take maye ya mata wannan abun ya yarda ta aure shi? Bare kuma yanzu da hankali ya fara samuwa, kuma ita dake mayen dama tana yin shi ne kawai dan ado ba wani sosai take yin shi ba, dan haka abu biyu ne ke bata wahala, na farko rashin bacci sai tayi ta juye juye wani lokaci har gari ya kusa wayewa tana farke, amma ta samu yanzu tayi maganin wannan matsalar, dan tana jin haka take tashi tayi alwala ta fara sallah, na biyu kuma kasala dake lulluɓe ta wani lokacin, amma dan sigari da shisha ko ganin su ma bata son yi yanzu. Fitowa tayi ta ci gaba da yi wa Mama kitso, kuma a canjin da ta samu na rayuwa tayi niyyar sanar da Mama komai dake kai kawo a rayuwar ta dan su dinga shawara, dan haka yanzu ma bata ɓoye ba ta faɗawa Mama abinda ya faɗa, amma fa ta ce ma Mama bata so kuma ba za ta yi ba, ita ma Mama bata tilasta mata sai ta amince ba kawai aka bar maganar. ******************** Tsabar tana farin ciki yau har juyen ɗaki ta yi, ta yi shiri na musamman tare da girki na musamman dan tarban shi yau dan ita ce da kwana, dalili biyu ya sa take wannan farin cikin, na farko: yadda yau Alhaji ya yi wasa da ita har ta ji marar ta ta fara yin sakayau, burin ta shine yau ma ta ja shi a gado suyi wasa ko da iya abinda zasu yi kenan, dan ta gane ita ɗin daga wasa ma tana iya feso ruwan ta. Na biyu kuma shine: ta faɗa ma wani matsalar ta, wannan wanin kuma dattijo ne da take da yaƙinin zai kawo mata canjin da take da buƙata, dan haka yau take jin ta tamkar za ta samu ƴanci daga wata uƙuba da aka jima ana tabka mata a gidan nan. Hatta Aliyu da ya zo karɓan abinci saida ya tsokane ta da _"Aunty hala yau sai mun rako Abba?"_ Rashin fahimta ya sa ta ce ba ta gane ba, sai ya sake yin dariya yace _" Ina nufin mu rako ango wajen amarya."_ Bayan duk wannan abu ta zauna tana jiran Alhaji, *amma*... Ko motar shi bata ji shigowar ta ba, tana tsaye tana ƙara gyara ɗan kwalin shaddar ta kawai ta ji banko ƙofar da tunda take bata taɓa ji ko ganin wanda ya shigo mata haka ba, da saurin bala'i ta juya tana zaro idanu har gaban ta na faɗuwa saboda tunanin ba lafiya ba. Wai sai ta ga Alhaji ne ya shigo, Alhaji dai Alhaji Kabir ɗin nan, mai nutsuwa da dattako da sanyi akan komai, ba ta san me ya faru ba? Wa ya taɓo shi daga waje... Ka da wuya ma ace wani ne ya ɓata masa rai, dan bai taɓa shigowa da ɓacin ran wani gidan nan ba, yadda ta ga maɗaukaki kuma shahararren ɓacin rai a fuskar shi har ma ya wuce a mugun fusace zuwa ɗakin shi, abun ya matuƙar tsorata ta, tun da take da shi, tun da take da Alhaji Kabir har ma Hajia babba da suke hira har tana bata labari akan irin zaman su, bata taɓa gaya mata yana da hushi irin wannan ba, to me aka masa kenan? Da sauri ta kama hanyar ɗakin nashi dan ta ji wa ya taɓo shi da har ya hana shi ganin kwaliyar ta da gyaran da tayi wanda ba dan ɓacin ran nan ba da yanzu yana nan yana jujjuya kan shi yana ƙarewa ɗakin kallo da ita kan ta, daga ƙarshe sai ya kalle ta yace _"Ummuna, so kike dai ki hana tsufa zama kusa da ni."_ Abun mamaki ya rufe ƙofar da makulli, hakan yasa Ummu jingina a ƙofar cikin taushin muryar da take ganin za ta fara sauko da ɓacin ran nashi ta ɗan kwanƙwasa sannan tace" Dattijon arziƙi, ka buɗe min ƙofa na shigo na ji wa ya taɓa ka, dan Allah kar ka ɗaga min hankali da ganin wannan fuskar taka, na roƙe ka ka buɗe in gan ka, ka ji?" *Wani* arnan kallo Alhaji Kabir ya ma ƙofar, Ummu ko? Ummu ta kai shi maƙura, kuma za ta gane bata da wayo, za ta gane ba lalaci da kasawa suke saka shi yin fatali da duk abinda ta mi shi ba, zai nuna mata yana da ɓacin rai, kuma kaf matan shi ba wacce ta taɓa yin abinda ta gayyato ɓacin ran shi ƙololuwa, amma ita ta yi, ta kai shi bango ta yadda zai nuna mata kuskuren ta. Shi ba ƙarar sa da ta kai wajen Alhaji Sagir bace ta fi ɓata masa rai, ba kuma sirrin sa da ta fallasa bane ya fi tsaya masa a rai, dan Alhaji Sagir aminin sa ne da bai da kamar shi a duniya, ko shi mai iya zama ne ya faɗa mishi wannan matsalar, sannan suna sanin abubuwan da suka shafi iyalin su musamman na saɓani, sannan suna ba wa juna shawara game da hakan, musamman da shi Alhaji Sagir da shi aka nemo masa auren Ummu. Amma fa yana da kishi, kuma matuƙar son da yake ma Ummu yasa ya ji kamar ta yi tsirara a gaban aminin shi ne, akan me? Akan wane dalili Ummu da ya fi so a matan shi ya kuma fi ganin kima da darajar ta har za ta tsaya gaban aminin shi tana cewa ita mai buƙata ce? Hakan fa na nufin ta faɗa masa ita wace iri ce, ta gama faɗa masa ita kowace irin mace ce, me ya sa zata masa haka? Shin hakan ta kamata ne? Bai kamata ba ai, tunda da bakin ta ta faɗa ma Alhaji Sagir da ta je asibiti likitan ya so yi mata lalata, me ya kawo haka? Saboda ta nuna masa ita kowace irin mace ce, wato ita ga fitinanniya jarababbiya mai sha'awar da ba'a iya biya mata buƙata ko? Shiru yayi bai tanka mata ba sai hushi yake yana cire kayan shi, yayi dana sani da Takaicin wannan rana, ya yi fatan ina ma ana siyar da ƙuruciya? Shi kam na wannan daren kam da ya sadaukar da duk abinda ya mallaka an bashi ƙuruciyar awa biyar kawai, wallahi da sai ya ma Ummu zungurar da idan ta yi ihu sai ta suma, da awanni biyar ɗin nan sai sun ƙare yana kan ta ba tare da ko tsayawa hutun minti ba. Ummu ko da bata san ɓacin ran daga ita bane a tausashe ta sake marairaicewa tace "Dan Allah mana aljannata, ka buɗe ƙofar nan ko na kira Kuwailat mu yi ta yi maka kuka, Kaga dai ni marainiya ce ko?" Taɓe baki yayi, sai anyi magana ta kama kumbura wai ita mai shekaru talatin, ko ina talatin ɗin take? Kuma fa can sai ta kira Kuwailat ɗin, ƙwafa ya yi yana ayyana _" Kuwailat ma ta fiki hangen nesa, amma sai jarabar son girma kamar rimi."_ Jin shiru ya san tana iya kiran Kuwailat ɗin, dan haka ya taka da sauri da hassala ya buɗe ƙofar, kallon juna sukayi, take Ummu ta sako hawaye akan kwalliyar ta kawai na kissa ba wai na abin ya kai ta yi kuka ba, a sanyaye ta matso tare da buɗe hannayen ta tana shirin faɗawa jikin shi, baya ya ja tare da tokare ta da hannu ya ƙi bata damar rumgumar shi... Da mamaki ta kalle shi ta turo baki duk da kuwa ta ga fuskar shi baƙiƙrin, cikin wani kakkausan lafazi murya a tsume ya furta "... *Alhamdulillah.* 15/08/2023, 20:14 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *48* Cikin wani kakkausan lafazi murya a tsume ya furta "Bana son damuwa, ki ɓace min daga nan." Take jikin ta ya ɗauki wani irin sanyi gaban ta kuma ya faɗi, da mamaki tace "Abb...." Da sauri ya katse ta da "Dan Allah bana son jin komai, ki tafi kawai Ummu, ki je kiyi duk abinda kike so, amma Ummu kin bani mamaki wallahi, har ni zaki zauna da Alhaji Sagir kina faɗa masa matsalar da mu kawai ta shafa, na ɗauka ko mahaifiyar ki ba zaki iya faɗawa maganar nan ba saboda ƙololan sirrin mu ne na kan gado, amma sai gashi kina barbaɗawa ga aminina, Ummu kin bani mamaki." Sake shigewa yayi ya rufe ƙofar, tsae take sororo kamar bata numfashi, kalaman shi take ta aunawa, kuma wallahi sai zuciyar ta ke raya mata hakane fa, amma kuma... Matakin da ta ɗauka shine daidai, ba zata iya faɗawa Maman ta ba gaskiya saboda bata so dangin ta su dinga kallon Alhaji da abun, amma Alhaji Sagir ai shine ya dace saboda aminin shi ne, suna kashewa tare su kuma rufe tare, idan ta ƙi faɗa ta zauna haka, ita ke cutuwa kuma za ta ci gaba da cutuwa tunda ba ta wuce shekarun da za ta buƙaci namiji ba, amma shi abinda yake so ya nuna shine kawai ta yi haƙuri ko? Bayan haƙuri irin wannan ya jefa mata bila adadin halakar da basu san iyakar ta ba, baya ga haka iyayen mu da duk matsalar da zaka je musu da ita in dai ta gidan auren ka ce sai su ce kayi haƙuri, ka yi haƙuri kawai. To a gaskiya it akwai rayuwar da ba zata iya jura ba kawai dan an ce tayi haƙuri, ubangiji da ya halicce mu ya saka mana sauƙi a cikin kowane abu, hatta bauta masa da sai munyi zamu shiga aljanna ai akwai sauƙi, ma fi ƙolokuwar aiki shine sallah, amma akwai sauƙi sosai a ciki, aka ce idan ka idar da alwala ka tuna baka wanke wani wurin ba, to kawai ka wanke iya shi ɗin ko da bayan ka idar da sallah ne, sauƙi ne soai8da ba'a ce sai ka sake alwala ba sannan ka yi sabuwar sallah, idan a cikin sallah ka mance wajibi, sai aka ce ka yi ƙabli ko ba'adi, idan babu ruwa ba'a tsananta maka sai ka nemo ba, aka ce kayi taimama idan kana jin tsoron wucewar lokaci.... Da irin haka fa ubangiji da ya halatta *aure* sai kuma ya halatta *saki*, ba dan komai ba saboda idan ɗaya daga cikin ma'auratan yana cutuwa sai a rabu dan a zauna lafiya, dan ma fa a rabu a mutumce yadda za'a dinga ganin juna da mutumci har ihsani Allah ya ce maza su ba mata bayan rabuwar, sukutum fa aka saukar da sura mai sunan *saki* (Thalaƙ), saboda me to? Da haƙuri shine mafita a wasu lokutan ai da surar haƙuri aka saukar, da haƙurin shine maslaha a wata matsalar ai da ubangiji bai gindaya mana rabuwa a tsakanin zamantakewar mu ba. Girgiza kai tayi jiki a sanyaye ta koma falon ta zauna, sai dai duk ƙoƙarin ta na son ta ƙeƙashar da zuciyar ta saida tayi kuka saboda ganin kamar ana dukan ta ne kuma ƙarfi da yaji a ce kar ka buɗa bakin ka bare ma kayi kukan. *BAYAN KWANA HUƊU* Tunda suka shigo tare da Aliyu dan gaisawa kamar yadda suka saba yake hangen fuskar ta daga nesa, abu ga farar fata fuskar ta duk ta koɗe tsabar kuka, hancin ta ya fita daban yayi jajir uwa uba idanun ta, daga haka ya gane akwai fa damuwa sosai, dama kuma kwana biyu ya ɗan fahimci Abba ba kamar yadda yake ba, a baya da wuya su zauna doguwar hira da shi bai sako hirar Ummu ba, dan ko Kuwailat za ta wuce ya kalle ta sai ya yi murmushi ya ce kamar uwar ta Ummu sak, amma kwana biyu bai ji bakin shi ya ambaci sunan Ummu ba, gaskiya hankalin shi ya tashi da ganin wannan damuwar dake kan fuskar ta, shi f alƙawari ne yayi in da yana raye ahalin Alhaji ba zasu shiga damuwa ba, sai dai idan ta fi ƙarfin shi kawai. Dake kwanan Hajia Luba da ba ya kwana ɓangaren saboda yara, kwana biyun a wurin Ummu ya yi, amma ko gaishe shi ta yi ba ya amsawa ba sai idan Kuwailat na wurin, yanzu ma shigowa ya yi bayan shigowar su Aliyu da suka gama gaisawa, ita bata gan shi ba sai yanzu, dan haka dag tsaye da take da ladabi ta kalle shi har tana rusunawa tace "Ina kwana Abban Kuwailat." Amma tsaf Alhaji ya haɗiye harshen shi ya ƙi ko da kallon inda take bare ya amsa mata, sadda kan ta tayi tsbar kunya dan bata yi tunanin zai iya share ta gaban su su, ta ɗauka kamar yadda ba ya son Kuwailat ta san komai haka suma zai kiyaye, kukan da ya taho mata tayi saurin tarewa da tafin hannu. Aliyu da ya ga komai kallon Jabir ya yi dake satar kallon idanun Ummu da ya ga sun cika taf da hawaye, yana kallo har ƙwallan nan suka faɗo kan hijabin ta, saida ya ɗan rintse idanu saboda yadda ya ji wani irin duka a zuciya shi, da sauri ya kawar da kan shi yana dantse leɓe, ƙarfi da ya ji nutsuwar sa so take ta bar shi bayan san me yasa ba. Aliyu kuma da abun ya dame shi ta wata siga daban kallon Ummu yayi dake tsaye yace "Auntyn mu, lafiya dai ko?" Ɗaga kan ta tayi ta kalle shi, a hankali hawayen nan suka fara sulalowa kan kumcin ta, da sauri ta sa tafin hannu ta share tana ƙaƙaro murmushi tace "Ba komai, lafiya lau wallahi." *"Ba gaskiya bane Maama, kuka fa kike."* Cewar Jabir da ya tsare fuskar ta da idanu, ɗaga nata idanun tayi ta kalli inda yake, da sauri ta kawar da duban ta dan ita wallahi Jabir da ta kalle shi ranar nan take tunawa sai taji jikin na wani irin yam yam haka ba daɗi dai, shiru ɗakin ya ɗauka ba wanda ya sake cewa komai, sai daga bisani Aliyu ya sake duban ta yace "Aunty, dama Jabir yau zai tafi Agadez gaishe da kakanin shi, yana so ya miki salama." Ba tare da ta kalli inda Jabir ɗin yake ba tace "Ahan! Allah ya tsare, Allah kiyaye hanya." Sai kuma ta ɗan yatsina fuska tace "Zan shiga ciki nayi wanka, dake ina so zan tafi gida, masu neman auren Nabila ne za su zo yau in sha Allah." Da farin ciki Aliyu ya mata Allah ya sa alkairi, amma Jabir hankalin shi na kan mecece matsalar ta? Shi fa damuwar nan baya son ta gaskiya, har ta juya ta shige Aliyu ma ya miƙe zai fita Jabir na tsaye yana kallon ƙasa. ******************** Wani shaƙiyin murmushi Sa'ad ya kuma saki saboda ganin da gaske Mama ta ɓallo magani za ta ba wa Aisha dan amai ya tsaya, marairaicewa da tayi ta kalle shi tace "Babana, ka mata magana tasha magani kaji? Aman ne ni bana so wallahi, galabaitar da mutum yake lokaci ɗaya." Murmushi ya sake yi yace "Mama, da kin gaya min zaki siyo mata magani da ban bari kin siyo ba, kamar dai kin manta wacece Aisha, allura ma sai anyi sa'a take karɓan jikin ta, ai yadda kika san jikin ta yayi expire haka take." Aisha dake durƙushe ta gama kelaya amai ta ɗaga kai ta kalle shi, turo baki tayi sannan ta sake sadda kan ta ita dai ba ta ce komai ba, ɗauke kai yayi daga gare ta yana faɗin" Bani na kar zomon ba, ciki ne naje nayi kuma." Da azama Mama ta kai masa duka a baki ya goce yana dariya, harara ta wanka masa tana cewa" Marar kunya fitsararre, ɓace min da gani malam." Matsowa yayi kusan su yana faɗin" Mama, bari kiga haɗin da nake mata take samun lafiya." Yayi maganar yana shiga falon su, jim kaɗan ya fito da kofi a hannun shi, garin hulba ne da ya tafasa a ruwa ya ta ce ya miƙo mata yace" Gashi ki sha?" Karɓa tayi ba gardama ta yi bismillah ta kifa kan ta, jim kaɗan ko ta shanye ta aje kofin, kama hannun ta yayi a hankali suna takawa har suka shige ɗaki ya zaunar da ita, shima kusan ta ya zauna ya ɗauki kwalban man hulba ya cika cokali ƙarami ya bata shima ta shanye, duban ta yayi yace "Kwanta sai na shafa miki zabada (jibda)." Kwance tayi kan kujerar ya ɗauki jibda ya shafe mata jiki da ita sannan ya rufa mata zane, cike da tausayawa yake kallon fuskar ta yana shafa kwantaccen gashin ta baƙi siɗik, inda Maa ke kallon su tana faɗin "Ikon Allah, a ce mutum ba shi ba maganin bature, ai ko kin raba kan ki." Murmushi Sa'ad yayi yace "Mama paracetamol idan kwali za ta sha ba zai mata maganin zazzabi ba kona minti ɗaya, amma yanzu Kinga nan? In sha Allah zuwa azahar ta fara dawowa hayyacin ta tana addabata da ƙiriniya." Duk da ita kaɗai tasan me take ji, hakan bai hana ta ɗan ture shi daga kusan ta ba tace" Abbu ka daina." Murmushi yayi ya ci gaba da shafa kan ta yace" To na daina ƴar Abbu." A hankali ta fara lumshe idanun ta, maganar da yayi take tunani akan ta, ba wai hulba da su man zeitun da alayyadi na mata aiki kai tsaye bane, ƙwarai sun fi karɓan jikin ta, amma kuma shine warakar ciwon ta, kulawar da yake bata idan aka ce kan ta kawai na ciwo, yadda yake ɓarin jiki da kai da kawo duk dan ta samu lafiya, hakan ke matuƙar ɗaɗata ga ƙasa, shiyasa ko bata jin daɗin wasu lokuta take daurewa saboda shima shiga tashin hankali yake. Har bacci ya fara ɗaukar ta taji yana faɗawa Mama "Mama, ki zauna da ita nan zan je na dubo Abban ta da suka shigo ɗazu, da tare zamu tafi kuma gashi ita bata jin daɗi." Da farin ciki Mama tace "Dan Allah? Ziyara suka zo mana kenan? Shine ba ka faɗa ba?" Murmushi yayi yace "A'a Mama, neman aure ne suka zo, zan je mu gaisa da su saina dawo." Da sauri Aisha ta buɗa idanu ta kalle shi tace "Abbu, nima zan je, mu tafi tare dan Allah na ga Mamie, wallahi jikina yayi sauƙi sosai." Girgiza mata kai yayi yana miƙewa taye yace "A'a ƴar Abbu, gaskiya ba zaki à wannan halin da kike ciki ba." Da sauri ta tashi zaune da zumuɗi tace "Wallahi Abbuna na warke, ka gani? Zan iya tafiya ma f.." Katse ta yayi da "A'a Eesha, ba zaki je ba gaskiya, salon ki sa Maman mu tayi ta min kallon tuhumar me na miki ko? Gaskiya a'a." Marairacewa tayi tace" Allah ba zan yi koma da zata gane ba." Kallon Mama yayi yace" Mama, dan Allah ki zauna ba zan jima ba nima." Kallon Aisha yayi da ta fara haɗe fuska yace" Ina abincin tarban su da kika girka?" Haɗe hannaye tayi a ƙirji ta turo baki ba ta ce mishi komai ba, hakan yasa ya sake gyara tsayuwa yana kallon ta, abinda yake so kenan dama suyi dan su rabu ana hushi, dan haka da irin gadarar nan yace" Ba dake nake ba kika min shiru? Ka ji min lukutar yarinyar nan, nace ina abincin yake." A ɗan hassale ta kalle shi tace" Ban sani ba mana Sa'adu, ka duba ai gidan ba baƙon ka bane." Jinjina kai yayi tare da nuna ta da yatsa yace" OK, shikenan to, idan kuma na duba ban gani ba ina zuwa zan rufe ki da duka, da kika raina mutane." Da kallo Mama ta bishi tace" Ba zaka kuskura ka taɓa min ƴa ba Sa'ad, an je an faɗa din kuma." Suna nan ya fito da manyan kwado har biyu ya nufi hanyar fita ko kallon Aisha bai yi ba wacce ya hanga ta gefen idanu sai kumbura take ita ya ƙi tafiya da ita. ******************** Dake ta ji bai sa makulli a ƙofar ba, su Aliyu na fita ta buɗa ƙofar ta faɗa ɗakin shi, zaune ta same shi bakin gado ya dafe kan shi, saida ta ji ba daɗi sosai saboda kar dai a zo bai da lafiya, ga kuma wannan damuwa da ya saka wa ran shi da tasa ko kallon ta ya daina. A hankali ta ƙarasa ta zauna kusa da shi, cikin sanyayyar murya tana kallon shi tace "Abban Kuwailat, dan Allah ka daina damuwa da abinda na aikata, na yarda na aikata maka kuskure, kayi haƙuri ba zan sake maimaita kamar sa, na rasa sukuni tunda ka juya min baya a gidan nan, gaba ɗaya ni da Kuwailat mun zama kamar wasu marayu, dan Allah kayi haƙuri ka ji." Ba tare da ya ɗauke hannun shi daya dafe kan shi ba cikin wata sarƙaƙƙiyar murya yace" Na kasa yarda ke kika aikata haka Ummu, kamar dai dama jirana kike yi? Ummu me kike nema daga gare ni? Me kika ce min kina so ban yi miki shi ba? Wace soyayya ce bana yi miki ke da ƴar ki, hatta matata ta farko Ummu bana jin ta a zuciya kamar yadda ke da kika shigo gidan nan jiya nake jin ki, amma ki rasa dame zaki saka min sai wannan?" Fashewa tayi da kuka saboda zuciyar ta sai harbawa take da sauri, maganganun shi sun mata kama da na wanda yake ƙullace da ita, wataƙila hannun da suka haɗa da Jabir ya sa yake jin haushin ta haka? Dan ta san Alhaji Sagir ai zai gaya masa duk dan a sama mata mafita. Hakan yasa Ummu tunanin wannan ɓacin ran ne ke damun shi, sai kuwa ta sauka daga kan gadon ta durƙusa gaban shi cikin kuka tana faɗin "Ka yi haƙuri dan Allah, wallahi tallahi Abban Kuwailat ban yarda shaiɗan yayi galaba a kai na ba tsakanina da Jabir, yana riƙe hann..." Da wani irin mugun yanayi ya ɗaga kan shi ya kalle ta, mamaki ne fal a fuskar shi da kuma kamar firgici haka, dole Ummu tayi shiru saboda kallon da yake mata da babu rahama a cikin shi, cikin ɗaga murya a tsawace yace" Ban gane tsakanin ki da Jabir ba? Me ya faru tsakanin ki da Jabir ɗin? Ummu me kuka aikata ke da ɗana Jabir?" Ƙyaƙyabta idanu ta fara yi tana girgiza mi shi kai, hakan ya sake hassala shi a mugun tsawace har yana miƙewa tsaye yace" Dake nake magana Ummu, me ya shiga tsakanin ku?" Yadda muryar shi ta daki kunnuwan ta yasa ta faɗuwa dandaɓar ƙasa tana ja baya, haɗe kukan ta tayi tana girgiza masa kai tace" Wallahi ba abinda ya faru tsakanin mu? Ta ya ma zaka min wannan zaton? Ba ab..." Cikin daka mata tsawa idanun shi har ja suke yi yace" Ya zaki ce ba abinda ya faru? Bayan ke kika faɗi wai tsakanin ki da Jabir, ina so nasan me ya faru?" Da hannu ta masa alamar yayi haƙuri tare da faɗin" To naji, zan faɗa maka, amma dan Allah kar ka dake ni, zan faɗa wallahi." Tsaye yai ƙiƙam gaban ta ya dafe ƙugu alamar yana sauraren ta, cikin shasheƙar kuka ta fara faɗin" Ranar ne fa da aka ɗauke wuta na yanke hannuna a madafa, shine Jabir ya shigo sai yayi ƙoƙarin taimaka min, hannuna kawai ya riƙe yana ɗaure min ciwon da jini ke zuba, wallahi bayan haka ba abinda ya faru, shi ko kallona ma bai yi ba." Ƙura mata idanu yayi yana kallo, sai kuma ya girgiza kai ya raɓa ta zai wuce, hakan ya sa ta juya ta bishi da kallo tana cewa" Zan je gida, za'a zo neman auren Nabi..." Tun bata gama faɗa ba ya furta" Ki je kawai, ki je duk inda kike so ban hana ki ba." Ficewa yayi Ummu kuma ta yi saƙe tana kallon ƙofar, miƙewa tayi tana share fuskar ta ta fice a ɗakin ita ma zuwa nata ɗakin. Tana shiga ta samu kira ya tsinke, lambar aunty Nuriyya ce, dan haka saida tayi zaune sannan ta sake maida kira, jim kaɗan ko aka ɗaga suka gaisa inda kowa ke kiran kowa da aunty. Mama Nuriyya ce ta ɗora da "Muna fa garin ku?" Da mamaki Ummu da ita matsalolin ta ma ya sa ta manta da akwai alaƙa tsakanin Fahad da su tace "Haba dai aunty, yaushe kuka zo? Shine ba sanarwa?" Da fara'a Mama Nuriyya tace "Ba haka bane, ƙanin mijina muka zo nemawa aure, to kin san tafiya irin wannan, shiyasa ban gaya miki ba sai da muka sauka lafiya." Sai lokacin Ummu ta tuna da wani abu, dan haka ta gyara zama tace "Aunty, ni kam na ce na ga a lambar ki kina anfani da sunan Ahlan, ko dai kun san Fahad ne?" Tayi tambayar ne dan ta samu tabbaci, sai kuma Mama Nuriyya tace "Fahad ai shine muka zo nemawa auren, ƙanin mijina ne uwa ɗaya uba ɗaya, kin san shi ne dama?" Murmushi Ummu tayi tace "Hakan na nufin ni da ke aunty zamu zama sarakan juna, saboda Nabila nima ƙanwata ce." Da farin ciki Mama Nuriyya tace "Haba dan Allah? Ƙanwar ki dai? Ka ga wani ikon Allah ko? Kenan duk bidirin nan da aka sha tsakanin Nabila da Fahad Ƙanwar ki ce dama?" A tausashe Ummu tace "Um, ƙanwata ce, sai dai...e ƙanwata ce." Da ta so faɗa mata ita fa bata ma san iyayen ta ba, sai kuma ta ga kawai bai dace ta faɗa mata ba, haka suka dinga tattaunawa har Ummu ta faɗa mata tana shirin tafiya ma gida dan tarban su, anan Mama Nuriyya ke cewa" Fahad ma ai ya faɗa mana ta ƙi amincewa da shi, shiyasa Hajia ta ce mu zo mu same ta da iyayen ta mu bata haƙuri kan abinda ya faru, idan ta amince kum a saka musu rana kawai." Murmushi Ummu tayi, ba zata bata tabbacin Nabila za ta amince ba, dan ta ji zafin abinda suka mata gaskiya, hakan zai sa ba zata takura Nabila ba, idan tana son Fahad ta amince, idan kuma ta daina son shi faƙat. Da fara'a tace" In sha Allah ma alkairi ne zai faru, amma dai aunty ba yau zaku koma ba ko?" Amsawa Mama Nuriyya tayi da" Gaskiya a'a, dan ni na jima rabona da nan, tun haihuwar Ikram ta Eesha, yanzu kuma ƙanin Ikram ma shekarar sa uku, to ina so zan yi sati ɗaya, idan mun samu amincewar Nabila fa kenan, dan in bata amince ba wallahi uban Eesha ba zai barni ba." Dariya Ummu tayi da farin ciki tace" To Allah ya yarda, ni kaina zan zo ku mana sati, kunga ai sai na zagaya da ku kuka gari." Haka dai suka dinga hirar su kafin daga bisani su yi sallama da sai sun haɗu gida. *Alhamdulillah.* 15/08/2023, 20:15 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *49* Tunda ta je gidan Mam ta san akwai matsala, Ummu bata taɓa zuwa gidan nan idanun ta fari ƙal ba, amma yau bbu kwali, babu jan baki ko ya ya, ga idanun nata sun yi fari fat alamar anjima ba'a shafa kwallin ba, amma dake ta sake tana walwala haka ma Kuwailat da suka zo tare, sai ta share da niyyar za ta tambaye ta daga baya, dan damuwar Ummu tashin hankalin ta ce. *Bayan* sallah la'asar baƙin nasu suka iso, ba wanda aka gayyata saboda har lokacin Nabila faɗi take ita fa ta haƙura da auren Fahad, amma tunda ya dage sai ya turo ba damuwa su zo, amma za ta rama abinda aka mata ita ma cikin ruwan sanyi, maƙwabcin su malam Adam ne kawai sai Yaya Luƙman suka tarbe su tun daga ƙofar gida, cikin nutsuwa suka dinga yi musu iso har suka shigo ciki. Alhamdulillah dake lokacin ba waccen gidan nasu bane, kuma duka su huɗu ne suka zo, sai kawai suka wuce har falo suka zauna kn kujeru suna ta gaisawa. Ummu na ɗakin Nabila ta idar da sallah, da sauri ta miƙe za ta fita Nabila tace "Auntyna, dan girman Allah kar ki bari Yaya Luƙman ya bayar dani haka kawai, ku ce musu ban tashi aure ba karatu nake." Dariya Kuwailat tayi tana kallon Nabila, hakan yasa Nabila kallon ta tace "Ƴata ko kin gaji dani? Wulaƙantani fa sukayi ?" Girgiza kai kawai Kuwailat tayi alamar a'a, hakan yasa Ummu saurin kallon ta tace" Ke kuma zaman me kike yi nan? Ki tashi ko ruwa mana ki kai wa baƙi." Da sauri Kuwailat ta miƙe tana ɗaukar hijabin ta zata saka Nabila tace" Kuwailat da hijabj akwai amana, aunty to ki barta ta taya ni zaman ɗaki mana?" Girgiza kai Ummu tayi tace" A'a muje ta ba baƙi ruwa." Kuwailat ce ta fara fitowa falon, kuma daga inda ta fito mutanen dake zaune duk suna fuskantar ta ne, hakan yasa kowa idanun shi ya sauka kan ta... *Daga* wajen Mama Nuriyya da Abbu Mukhtar harbawan jijiyar dake isar da gudanar jini ne ya wakana lokaci ɗaya, inda zuciya ma ta harba da gudun ƙarfin da ya sa tunanin su ya basu kamar da alaƙa? Saboda tsabar kamar Kuwailat da suka gani a fuskar Kuwailat da ta wacce ta zama rayuwa gare su. *Kafin* su farga da kama ce kawai irin ta katari? Ko kuma dai kama ce dake samo asali daga dangantakar jini? Sai ga Ummu wacce ita girma da shekaru ya sa kamannin nata suka fi rikiɗewa zuwa ga na... *Hajiar su*. Ba Mama Nuriyya da Abbu ba, har da Yaya Bilal da Fa'iza duk suka zaro idanun ganin wannan kamanni na Hajia a fuskar Ummu da tsufa ne kawai ya bambamta su, amma daga farar fatar, idanun, hancin, bakin dake musu murmushi sak irin na Hajiar su, zuwa ga tsayin ƙirar ta da ƴar mulmujewar, ƙwarai, wannan Hajia ce, musamman ma Bilal da Abbu Mukhtar da suka fi sanin Hajiar tun lokacin ƙuruciya, sai suke ganin da ace mahaifiyar su ta ɓata kuma a basu kwangilar samo ta, to haƙiƙa ba mai raba su da wannan, wallahi kawai Hajiar su ce. Bayan wannan kamannin, akwai sauyawar yanayin su dake tabbatar da haɗuwar jini irin na iyaye da abun da suka haifa, hakan ne ma yasa Abbu da Mama Nuriyya kasa kawar da duban su ko da na sakan ɗaya daga fuskar ta, musamman mama Nuriyya da hawayen da suke saukowa kan fuskar ta suka sake nuna mata lallai da wani abu a ƙasa, dan hawaye ne irin masu sanyin nan ƙarau wanda ta kas dakatar da su. Aunty Fa'iza kaɗai tayi jarumtar yin murmushi ta kalli Yaya Bilal dake son ɗauke kallon shi daga matar mutane amma ya kasa kuma bai san dalili ba tace "Yayana, ka ga wani ikon Allah? Fuskar ƙuruciyar Hajia a jikin matar nan." Da sauri ya kalle ta da yanayin dake nuni da ya tafi wtat duniyar, amma samun wacce take ganin abinda yake gani yasa ya kalle ta cikin raɗa sosai yace "Ashe kin gani kema? Wannan wace irin kama ce? Kamar ƴan biyun Mamie." Mama da ta ga Mama Nuriyya na kuka sai gaban ta ya faɗi saboda tunanin da tayi, hakan yasa ta ƙaƙaro murmushi ta kalli Ummu da tsarguwa yasa tayi tsaye ta ma rasa ina za ta nufa, kallon da mutanen ke mata mamaki yake bata kuma yana neman hassalata, haka kurum mutane huɗu su tsare ta da idanu kamar mai laifi, kuma fa kowa da gaske kallon ta yake ba ko ƙyabtawa, abun takaici kuma daga matan har maza, hakan yasa suka sa ta fara tunanin to ko dai iskancin Fahad dama daga gida ya samo asali? Me ye a jikin ta da suke mata wannan kallon ƙare dangin? Wata alama suka gai da ta nuna ita wata ce? Ko kawai sun yi niyya ne dai? Dan ita dai tasan ba kyawun ta bane ya ɗauki hankalin su, dan duka matan biyu alamu ya nuna sun yi tashen kyau girma ne kawai, amma hakan ma bai ɓoye kyan su da tsari da kuma kula da jikkunansu ba, haka kuma tasan ba hasken fata bane, dan Mama Nuriyya jajir take wacce kana gani ka ga buzuwa ta asali, sauran ne ma duka suke da duhun fata, shima ba irin wanda ya munana ba. Da fara'a Mama tace mata "Ƙaraso mana Ummu, ga Kuwailat can zata kawo abun sha." Saida Ummu ta ɗan sake matsawa ta kalli fuskar Abbu Mukhtar, a wani irin sanyaye ta ji gaban ta ya faɗi haka, kamar wacce ta hango wani abu a fuskar shi sai ta ɗan tsaya jim tare da karkata kan ta tana ƙara haɗa idanu da shi... To! Idanun ta ta ɗaga ta kalli Mama Nuriyya dake kusa da shi, ita kam ta gane ta dan wayayyar mace ce da har status tana ɗora kan ta da Ahalin ta, abun mamaki... Irin yanayin da ta ji akan Dattijon nan haka take jin shi yanzu daga kallon fuskar aunty Nur, ba tare da sanin ta ba kawai ta ji ta saki murmushi, wato irin abun nan ne da ake faɗa wai *ƙauna daga kallon farko*, kafin sakannin yanzu tsarguwa take ji da haushi haushi na kallon wuce ƙa'ida da suke mata, amma yanzu sai ta ji wata ƙauna da ba ta taɓa sanin tana ma aunty Nur ba da mutumin dake kusa da ita wanda ta fi tunanin mijin ta ne. Ƙara takawa Ummu ta yi da niyyar zami kusan Mama, amma sai Mama Nuriyya da ita kawai zuciyar ta da ƙwaƙwalwar ta ke ta faɗa mata ke fa *ƴar ki ce* kawai ta miƙe ta sha gaban Ummu, wani kallo take ma Ummu kamar mai shirin saka hannaye biyu ta mata irin ɗaukar nan ta jarirai, daga sama har ƙasa take kallon ta da murmushi da kuma kuka a fuskar ta, shauƙi kuma da farin ciki ya sa ta kasa cewa uffan sai ƙarewa Ummu kallo kawai take. Hakan yasa Ummu dake ta doka murmushi ta riƙo hannun Mama Nuriyya tace "Aunty Nur, dama na faɗa ai zan iya gane ki a zahiri, ina wuni?" Hawaye kaɗai ke mata zarya a kumatu, sai kuma ta juya ta kalli Abbu Mukhtar da shi ma fa idan aka bar shi cewa zai yi wannan yana da alaƙa da ita, to amma lamuri irin wannan ai bka saurin nuna kan ka, sai a maka wata fasara ta daban, hakan yasa burin shi bai wuce kar ta kwafsa musu ba, dan tunda ya ga ta tare ta yasan t ji abinda ya ji ne, dama kuma samun Aisha ya rage mata raɗaɗin rashin Kuwailat, shine ma har sai ka ga kamar ta manta da ita, to da alama dai yanzu za ta tuna, wannan kuma idan wannan ita ce ta haife ta, to zai ga yadda za'a raba su kam. A kiɗime ta kalle shi da yanayin da shi kaɗai ya gane me take nufi tace "Kan gani aboki? Wannan ba Kuwailat bace? Aunty Ummu, ke ce Kuwailat ko?" Ta ƙarashe maganar har da sake matsawa daf da Ummu, duk ƙauna da soyayyar nan da Ummu ta ji tana mata yanzun nan, da girmamawa da ganin mutumcin da take mata na haɗuwar waya, sai ta ji tana mata wani kallon anya kuwa? Me take nufi to da wannan maganganun da basu da makama? Da sauri Abbu ya taso ya kama ta ya mayar ya zaunar da ita tare da yi mata raɗa "Ki nutsu ƙawata, kar ki sa muji kunya dan Allah, neman aure muka zo, idan muka gama zamuyi waccen maganar, kin ji ko?" Dan dai ya kwantar mata da hankali ne ya faɗi haka, sai kuwa ta jinjina kai tana murmushi tace "Da gaske? To shikenan, amma wallahi wannan Kuwailat ce, baka ga kamaninin Hajia ba." Murmushi ya mata yace "Na gani, sosai ma, ke dai ki nutsu, zamuyi magana, wannan ai Kuwailat ɗin mu ce ma da gani." Murmushi tayi irin na ya yarda da ita ɗin nan har da gyara zama tana ci gaba da kallon Ummu da duk jikin ta yayi sanyi take ji abu irin dai na shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin ta da mutanen, haka ma Kuwailat da ta fito daga madafa ta aje ruwa da lemu a faranti tana sake gaishe su sannan ta shige wajen Nabila, ƙara gaisawa aka yi sosai kafin Yaya Bilal ya kalli malam Adam yace "Malam, ni sunana Bilal, ni Yaya ne ga shi Fahad mai son Nabila, wannan mai ɗakina ce Fa'iza..." Ya faɗa da nuna Fa'iza da ta yi murmushi ta sadda kan ta, sai kuma ya nuna Abbu yace "Wannan ma ƙanena Alhaji Mukhtar, ga iyalin sa nan..." Gyara zama yayi ya ɗora da "Hajia ce ta wakilta mu kan mu zo mu ba wa iyayen Nabila haƙuri kan duk abubuwan da suka dinga faruwa, duba da rayuwar da yaran nan sukayi, amma bamu taɓa zama muka tattauna dan dawo dasu hanyar da ta dace ba, to daga bisani sun yanke shawarar aure sai kuma su iyayen namu suka nuna ƙin amincewar su, sun ce mu faɗa muku ba komai yasa suka ƙi amincewa a wannan lokacin ba sai dan rashin sanin niyyar tasu ta yin auren, sannan kuma basu san ko suna da ƙudirin shiryuwa ba, wannan kawai shine dalilin da ya sa suka ce a'a, bayan rsuwar mahaifin mu ƙanin shi ya zauna da mahaifiyar mu sun yi magana sosai, anan suka fahimci ai ita Nabila har ma shi Fahad ɗin ya umarce ta da ta yi istibra'i, hakan ne yasa suka janye makamai su suka kuma yarda su auri junan su tunda suna so." Numfashi ya ja sannan ya sauke su ya sake kwantar da murya yace" Abu mafi mahimmanci da ya kawo mu ne shine bayar da haƙuri, takaba da Hajia ke yi yasa ta ce mu mu zo, ba dan haka ba da kan ta za ta zo, dan Allah muna baku haƙuri akan abinda ya faru, sannan ku taya mu ba wa ita yarinyar haƙuri, dan mun san ba'a kyauta mata ba, mu ma kuma ba yadda zamuyi ne tunda su suka haife mu, amma magana ta gaskiya bamu ji daɗin abinda suka ma Nabila ba." Gyaran muryar da malam Adam yayi alamar zaiyi magana yasa Mama kallon shi, ita ba ta da damuwa idan ya ce sun haƙura kuma sun yafe, amma dai ba ta so yayi gaggawar amsa buƙatar su, gaskiya ta ji ba daɗin abinda Nabila ta faɗa mata sun mata, kuma yanzu ta gasgata tunda gashi har suka yi tattaki da kan su suke neman a yi haƙuri, sun san basu kyauta ba kenan? To a yafe ɗin, amma dai amincewa buƙatar su sai an ji ta bakin Nabila ba gaskiya. Kan ta na ƙasa ta ji malam Adam yace "Wannan ai ba komai bane, shi dama sha'ani na yara ya gaji haka, kuma tun farko da mu manya mun shiga maganar, ina ga da duk abun bai kai ga haka ba, kuma laifi ba naku bane ku kaɗai har da mu, dan ni kaina dake aminin mahaifin ta ina ga da shi mai iya neman ku ne dan kuyi maslaha tsakanin su, dan haka mu dai daga gare mu ba komai wallahi, fatan mu dai Allah ya ƙara shirya mana su, idan kuma har akwai wani abu da ubangiji ke nufi da tarayyar su tun farko, to Allah ya bayyana mana alkairin da ke ciki." Da ameen ɗakin amsa har da Ummu da ta ɗan kawar da fuskar ta, wallahi duka mutanen nan kallon ta suke ta yi har yanzu, ba ma kamar aunty Nur dake ta mata murmushi ba ta ko san kawar da duban ta daga gare ta, Abbu Mukhtar ne ya gyara zama shima yace" Alhamdulillah, gaskiya mun ji daɗi da wannan karamcin da kuka mana, yanzu buƙatar mu gare ku bata wuce amincewar ku wajen ƙulla alaƙa tsakanin Fahad da kuma Nabila." Shiru aka yi na sakanni, malam Adam da bai san me ye ra'ayin mahaifiyar Nabila kan haka ba ya kalle ta, haka Yaya Luƙman ma Mama yake kallo dan bai san matsayar su kan haka ba, Ummu kuma da tasan yadda aka yi cikin nutsuwa da ladabi duba da ita ce ƙarama a duk taron ta dube su da fara'a a fuskar ta tace "Zamuyi farin ciki da hakan, sai dai zamu ji ta bakin ita Nabila, dan a baya tayi ƙorafin ba zata yi aure yanzu ba, dan haka zamu so muji yadda ta yanke." Yaya Bilal ne yayi murmushi, wallahi sak maganar ta irin a nutsen nan yadda Hajia ne take yi, shiyasa fa Hajia ko faɗa ba ta ma yara irin mai hargagin nan, ya salam! Wannan kama jama'a? Da tsufan shi da komai amma yarinyar nan ta gane irin kallon da yake mata, kar dai tayi wani tunanin a kan shi ma? Da ƙyar dai ya saita nutsuwar shi yace "Wannan ai ba matsala bane, dama dole ne mu ji ra'ayin ta akan haka, ba damuwa." Miƙewa Ummu tayi tace "Bari na kira ta." Mama Nuriyya da Abbu ne suka bita da kallon da har Yaya Luƙman saida ya tsare su da idanu da yanayin jin haushi, dan dama duk abin da ke faruwa ai suna lura da komai, an ɗauki minti biyu kafin Ummu ta fito Nabila a bayan ta, zunbulelen hijab ne jikin ta da ya mata kyau, kanta na ƙasa idanun ta a kan ƙafafun ta har ta ƙarasa ta zauna ƙasa kusa da ƙafafun Ummu, a taƙaice kawai ta iya furta "Ina wunin ku?" Dukan su da fara'a suka amsa mata da "Lafiya lau Nabila, ya gida?" Ba Ta amsa ba sai sadda kai da ta ƙara yi, hakan yasa malam Adam faɗin "Nabila, waɗannan sune shaƙiƙan saurayin ki Fahad, sun zo ne su baki haƙuri akan abinda ya faru, sannan kuma su sake jadadda neman auren ki." Shiru ɗakin ya ɗauka saboda lokacin kowa Nabila yake kallo, amma fa ban da Mama Nuriyya da idanun ta ke kan Ummu tana kallon duk wani motsin ta, a lokacin ita tama manta me ya kawo su gidan, ƴar ta kawai take hangowa gaban ta. An ɗauki lokaci kafin Nabila cikin sanyayyar murya tace "Ba komai, ni dama ban riƙe su ba, saboda alkairi suka min, dan sanadin abinda ya faru ne na gane gaskiya, dan haka ma ni godiya zan musu." Da jin daɗin haka suka mata godiya tare da saka mata albarka, sannan daga bisani malam Adam ya ɗora da "Sai kuma buƙatar su ta gaba, suna so su samu amincewar ki dn à ɗaura muku aure ke da Fahad, ya kika gani? Kin amince da haka?" A hankali ta ɗaga kai ta kalle shi, sai tayi murmushi a nutse ta sake sunkuyar da kan ta tace "Abba, ni dama na jima da faɗawa Fahad aure ni da shi bai kamace mu ba, bare kuma yanzu da aka nuna min ban dace da shi ba, Abba, istibra'i nake jira nayi, akwai dayawa masu son aurena, zan duba ɗaya daga ciki wanda zai yi daidai da ajina na aura." Tana gama faɗin haka ta miƙe tsaye ta juya da sassarfa ta koma ɗakin ta, da kallo duk suka bita har da Mama da Ummu, saida suka ga ɓacewar ta Ummu ta kalli Yaa Bilal da ta ga ya fi mata rangwamen kallo tace" Abba, kar ku damu da abinda Nabila tayi, in sha Allah zanyi magana da ita, nasan ranta ne ya ɓace na abinda ya faru, amma wannan ba damuwa bace in sha Allah." Murmushi Yaya Bilal yayi yace" Ba komai *ƴata*, tana da gaskiya ai, zamu ƙara kwana ɗaya dan jiran jin abinda zaku tattauna." Murmushi Ummu tayi ta sunkuyar da kai, duk haramar miƙewa sukayi, hakan yasa Mama Nuriyya kallon Abbu Mukhtar ta riƙe hannun shi tana kallon Ummu tace" K ce zamu yi maganar nan, ƴata ce fa." A nutse ya tallabota ta tashi tsaye cikin rarrashi yana faɗin "Kinga nutsu, na sani ƴar ki ce, kinga yanzu aiken da Hajia ta mana bamu samu amincewar ya..." Girgiza mishi kai tayi irin ba fa zata ƙara yarda da shi ba, sannan ta juya ta kalli inda Ummu take, da ƙarfi ta so fincike hannun ta da ya riƙe amma ya ƙi sakin ta, hakan yasa tayi azamar kamo hijabin Ummu ta riƙe gam har saida Ummu ta kalle ta a ɗan tsorace, cikin fitar hayyaci take kallon Ummu tana cewa "Aunty Ummu, ai kin san bamu taɓa ganin juna ba ko sai yau? Ban taɓa jin abinda nake ji a kan ki game da wani ba, ina ji a jikina muna da alaƙa, dan Allah ki saurare ni aunty Ummu, n..." Rufe mata baki Abbu Mukhtar yayi, sannan ya shiga ƙoƙarin raba hannun ta da hijabin Ummu, cikin nutsuwa Ummu ta kalli Abbu Mukhtar ɗin tace" *Abbu*, ni ban san akan me take magana ba, dama aunty Nur bata da lafiya ne?" Yaya Bilal ne yayi saurin faɗin" A'a, lafiyar ta ƙalau, ƴata, damuwa da ɗimuwar rashin ƴar ta ne ya mayar da ita haka, ta rasa jaririyar ƴar ta da ko kamannin ta bata gama shaidawa ba saboda son zuciya na wasu mutane da dalilin su marar tushe na son ɗaukar fansa akan yarinyar da ko iskan duniya ba ta gama karɓa a jikin ta ba, basu warke dga wannan raɗaɗin ba suka sake samu wata ƴar, amma ita ma sai tsohuwar matata ta ɗauke ta tayi nesa da ita saboda ita tafi so a ce ita ta fara haifawa ahalinmu jika ba wata ba, bayan wannan shekarun yau mun ga kamannin mahaifiyar mu a fuskar ki, wataƙila kin kula da kallon da dukan mu muke yi miki, ba na komai bane face ganin fuskar Hajia a fuskar ki har ma da murmushin ku iri ɗaya da kuma taushi da sanyin maganar ku, ba ita da take jin ta haife ki ba, ko ni da za'a bani kwangilar nemowa mahaifiyata ƴan biyun ta ko kuma nemo ƴar ƙanina da ta ɓata, to shakka babu ke ɗin nan ke zan kamo musu a matsayin wacce suke nema." Murmushi Ummu ta sake yi ta kalli Mama Nuriyya sannan ta nuna mata inda Mama ke tsaye tace" Aunty Nur, ni kinga mahaifiyata nan, ita ce ta haife ni, nan kuma shine gidan mu kuma ahalina, shekarata talatin a duniya yanzu, sha bakwai daga ciki Mamana ce ta kula dani tun daga cikin tsummana har ta aurar da ni, daga sha takwas kuma zuwa talatin ni nake kula da kaina, dan haka a wannan rayuwar tawa yanzu dai bana buƙatar sanin su waye suka haife ni, bare ma nasan dalilin da yasa basu neme ni ba duk wannan shekarun, da izinin Allah shekarun da uka rage min ubangiji zai tsaya min ya kuma kula da lamurana." Abbu Mukhtar da ya fi kowa fahimtar kalaman ta ya fahimci wani abu, _a yanzu ba ta buƙatar sanin su waye suka haife ta_? Me take nufi to? Hakan na nufin dai ba wannan ɗin ta haife ta? Magana fa tayi da hausa, duk da ba asali bahaushe bane amma yana gane hausa ƙwarai. Ummu da ta ci gaba da magana ne yasa shi maida hankali gare ta, Mama Nuriyya ta kalla tana cewa "Aunty Nur, ban san shekarun ki sun ruɓanya nawa ba, duk da hotunan ki da na gani ba su nuna haka ba, amma dai dana dinga kiran ki da sunan *Maama*, dan Allah mu ci gaba da zumuncin mu kamar yadda muke yi, ni kuma saina ɗauke ki uwa." Jan majina tayi saboda hawayen da suka taho mata kan kumatu, kallon su tayi dukan su sannan tace" Allah maida ku gida lafiya." Daga haka ta juya da sassarfa ta shige ɗakin Nabila ta rufo ƙofar, da wani irin sauri Mamie Nuriyya ta so fincikar hannun ta da niyyar ta bi bayan Ummu tana faɗin" Ka ji ko, wallahi ƴata ce, ke..." Ta faɗa tana kallon Mama da tashin hankalin ta ya fi na kowa tace" Ki faɗa min wannan ƴata ce, ki gaya mata gaskiya ba ke kika haife ta ba, wall... " Abinda ba taɓa faruwa ba duk shekarun nan ne ya faru, dan kuwa Yaya Bilal ya ga zata ɓallo musu ruwa daga zuwa neman aure, dan haka ya kama hannun ta da ƙarfi sannan ya shiga jan ta zuwa waje yana faɗin" Kuyi haƙuri dan Allah da abin da ya faru, in sha Allah zamu dawo gobe dan jin matsayar Nabila." Da sauri Fa'iza da Abbu suka bi bayan su. Mama da ta gama hango komawar Ummu wajen iyayen ta na gaskiya, dan kuwa ba zata ci gaba da ɓoye musu ba, duk son ta da Ummu da ƙaunar da take masa saboda tsantsar ladabin ta da biyayyar ta da haƙuri dole ta rabu da ita, dole ta haƙura da Ummu dan yanzu kam ta ga zahirin ɗimuwar da mahaifiyar ta take ciki na rashin ƴa, abu ɗaya kawai da ba zata iya kare kanta gare su ba shine idan suka ga mijin Ummu, ta san Alhaji Kabir yayi jika da Ummu, kuma sun yi ƙoƙarin su akan hana ta aure shi amma ta ƙi fahimtar su, tana tsoron kar iyayen ta na asali su ɗauka ta aurar da ita gare shi ne dan ba ita ta haife ta ba, amma ba komai, ta rabu da Ummu ma bare laifin da zasu tuhume ta akan shi, za ta iya jure komai duk wahala kuwa. *Alhamdulillah.* 15/08/2023, 20:15 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *50* Kamar an tura Mama faɗawa tayi kan kujera inda ta tashi ta fashe da kuka mai tsuma zuciya tana rufe da fuskar ta, da kulawa Yaya Luƙman ya zauna kusa da ita sai malam Adam da ya bi bayan su Abbu yana musu ban kwana, cike da tausayawa Yaya Luƙman yace "Mama, lafiya ? Me aka yi na kuka kuma?" Ɗaga kan ta tayi ta kalle shi cikin kuka tace "Me aka yi kuma? Kai baka ga abinda ya faru bane?" Sai ta sake haɗa tafukan hannayen ta da fuska tana kuka tana faɗin "Allah! Ya Allah! Hasbunallah wani'imal wakil, ashe dama tarayya Nabila da Fahad sanadin haɗuwar ƴa da uwa ne? Ashe tarayyar su za ta zama alkairi ga dubbanin mutane?" Da sauri Yaya Luƙman yace "Mama, ya zaki faɗi haka? Dan sun nuna sun san ta ai bai zama lallace ƴar su bace, basu da hujjar da zasu tabbatar mana ita tasu ce, Mama kawai mu manta da maganar nan, wallahi Ummu ƙanwata ce, kuma babu wanda ya isa ya rabamu da ita." A hankali Mama ta ɗaga kan ta tana duban shi da murmushi a fuskar ta tace" Luƙman, Ummu ƴar su ce, suna da hujja, kuma shekaru tara da suka wuce na san da haka, amma..." Sai kuma ta sake fashewa da kuka sosai har da haɗa kanta da hannun kujera tana faɗin" Luƙman gara na rasa ku, gara na rasa ku kai da Nabila da na haifa da na rasa Ummu, ka sani ina ƙaunar yarinyar saboda babu wanda ya kai ta ƙaunata a cikin ku, sannan Ummu tana son ku fiye da yadda ni da na haife ku nake son ku, ta ya zan jure rabuwa da ita bayan duk wannan shekarun, Mama take kirana, ba zan iya ba, ba zan iya ba Luƙman, dole na faɗa musu gaskiya, amma ba zasu raba ni da ita ba." Rasuwar mahaifin shi kawai ta saka shi kuka, bayan haka ba wani abu da ya sake saka shi zubar da hawaye, amma sai gashi yanzu yana zubar da su wanda ya ma kasa tantance yana kuka ne dan mahaifiyar shi tana yi? Ko kuma yana kuka ne dan tunano abinda ke neman tunkaro su? Ba fa zai iya rabuwa da Ummu ba shima, ya fi so ta ci gaba da zama da su anan matsayin ƙanwar sa wacce ya fi so, Ummu da ko saɓani ya samu da iyalin sa ita ke musu sulhu, kuma ko shine bai da gaskiya kai tsaye take faɗa masa gaskiya Yaya baka kyauta ba, ba zai juri rabuwa da ita ba gaskiya. *Duk* wannan bidiri da aka yi Sa'ad na waje cikin mota yana jiran su, dama ya ce ba zai shiga ba tunda kai tsaye ba neman auren bane, har yana musu raha da idan yarinyar ta amince to zai fara zuwa zance wajen ta kafin angon ya zo, hakan yasa har Yaya Bilal ya ranƙwashe shi a kai yana cewa _"Yarinyar Baban ka ce fa."_ Shi kuma yayi dariya yace _" Ai bana ɗaukar Fahad Baba, sai dai Abbu."_ Abubuwan da suka faru yasa sun ma manta tare da shi suke, bare su ce a kawo masa ruwa ya sha da abun taɓawa da aka kawo musu. Bi saki hannun Mama Nuriyya ba saida ya shigar da ita mota Abbu ma ya shiga baya ya zauna sannan ya ce Sa'ad ya tafi shi kuma shiga ɗaya motar. Ba ta masa gardama ba, amma ji take kamar ya hanata ganin ƴar ta ne, saida suka fara tafiya S'ad na tambayar Abbu ya ya? A taƙaice kawai ya ce mishi "Zamuyi magana daga baya." Jin haka kamar da ita suke sai ta fashe da kuka da iya ƙarfin ta, hakan yasa da sauri Abbu ya jawo ta jikin shi yana daddaɓata da faɗin "Shiiiiiii! Ya isa haka mana ƙawata, ba gobe zamu dawo ba? Zamu dawo gobe ki tafi da ƴar ki." Ba Ta saurare shi ba sai kukan nan da take yi, Sa'ad da duk ya ji ba daɗi ne ya tambaye su "Abbu lafiya? Me ya faru dan Allah?" Jim Abbu ya yi kafin ya kalle shi yace "Wata muka gani sak Hajia a ciki, komai nasu iri ɗaya da Hajia bayan shekaru da suka bambamta su, mtsss!" Sai kuma yayi ɗan gajeren tsaki ya kalli Sa'ad sosai yace "Sa'ad, naji a jikina kamar akwai wani abu tsakanin mu da yarinyar nan, Allah kaɗai ya fi mu sanin sirrin dake ɓoye, amma da wuya a ce wannan ba haɗa jini da ita ba." Shiru Sa'ad yayi yana nazarin maganar sa, basu sake magana ba sai kukan Mama da suke ta saurare har suka isa masaukin su wanda da gidan Sa'ad ɗin suka so zuwa dan su duba Eesha da ya ce bata da lafiya, amma halin da suke ciki ya sa ma ba wanda yayi wannan maganar. ******************** Saida kowanen su ya ci kukan shi kafin Mama ta wanke fuskar ta ta ƙwanƙwasa ɗakin Nabila cikin dakusashiyar murya tace "Ummu, fito yamma tayi sosai ki wuce gidan ki, maza fito daga ɗakin nan kafin na sa a ɓalla min ƙofar." Cikin waa irin murya Ummu dake kwance ta amsa da "Ina zuwa Mama." Saida ta sai ta nutsuwar ta tare da gyara jikin ta sannan ta fito, fitowar ta kuma daidai da shigowar Yaya Luƙman, yana ganin ta yace "Yawwa Ummu, Alhaji ne ya kira ni yanzu ya ce muje na sauke ki gida." Da mamaki ta kalle shi tace "Kai kuma Yaya? Amma ai da mota ta na zo, kuma ya sani." Ba alamar wasa yace "Haka dai ya faɗa, kuma kinsan mai gidana ne dole na kaiki gida." Raɓa su Mama tayi ta wuce tana faɗin "Maza ki shirya to ki tafi." Jiki a sanyaye ta shiga haɗa nata-ya nata dan tafiya gida, saida ta gaa shiryawa Kuwailat ta fito suka ma Mama sallama suka tafi Yaya Luƙman ya mayar da su. Ƙofar gida suka same shi daf da magrib, Ummu shigewa sukayi shi da Luƙman kuma suka gaisa kafin yace mishi "Kayi mamaki da na ce ka kawo ta ko? Duk da ta tafi da motar ta." Murmushi Luƙman yayi yace "Ban yi wannan tunanin ba Alhaji, kawai nayi abinda ka ce ne." Murmurmshin jin daɗi yayi yace "Luƙman, dama ina son magana da su Mama ne, da ni naso zuwa da kaina, amma sai na ga rashin dacewar na je gidan akan wannan maganar, shiyasa nace ka zo dan ka min alfarmar sanar da su, idan zai yiwu har da malam Adam, saboda yana ɗaya daga cikin wanda suka bani auren Ummu." Kallon shi Yaya Luƙman yayi yace" Allah dai yasa lafiya?" Murmushi yayi har da dafa kafaɗar shi yace" Kar ka damu ba komai, kai dai ka sanar da su." Jinjina kai yayi yace" Shikenan, amma kamar wane lokaci zan faɗa musu?" Saida ya sauke ajiyar zuciya yace" Idan zai yiwu ko zuwa anjima ma." Sake jinjina kai yayi yace" Shikenan, in sha Allah zan sanar da su." Murmushi ya masa tare da yin godiya sannan sukayi sallama shi ya nufi masallaci shi kuma dan komawa, sai dai jikin shi a sanyaye yake yana jin kamar ba lafiya ba. Tana zaune dai ne kan salayya, azkhar ɗin da ta saba yi yau tunani ya sa ta kasa kammala su, tunani ne barkatai ke zuwa mata kwanya na abinda ya faru, gaba ɗya ma ta manta da tana da damuwa, lallai ita kanta sha'awa kwanciyar hankali da ƙoshi ke kawo ta. Tana wannan halin Alhaji ya sallamo ɗakin ta, da mamaki ta kalle shi tare da amsa sallamar, kwana huɗu kenan rabon da ya leƙo ɗakin nata, daga ganin fuskar shi kuma ba wannan jarababben hushi yasa ta fara jin kamar akwai salama tare da shi. Sai dai nata yanayin ita ma ya addabe ta, dan haka ta sadda kanta ba ta ce mishi komai ba sai ma azkhar din ta da ta fara yi dan ya gane ba haka kawai take zaune ba, zaune yayi bakin gado yana kallon fuskar ta da fara'a yace "To ya? Baƙin sun samu karɓuwa a wajen Nabila kuwa?" Kallon shi ta sake yi, hakan na nufin ya huce kenan? Ƙwarai kuwa, tunda ai da ko kallon inda take ba ya yi, cikin nutsuwa tace "Har yanzu dai, amma zanyi magana da ita, in sha Allah za ta amince." Cike da gamsuwa yace "Allah ya aminta, gwara ta amince kam, kinga ai sai na ɗaura mata aure, matsayina na mijin auntyn ta." Murmushin jin daɗi tayi tace "Gaskiya ne, in sha Allah ma zata amince, kawai aji ne take so ta ja musu." Murmushi yayi bai ce komai ba, shiru ne ya ɗan biyo baya na daƙiƙu kafin ya sake kallon ta yace "Ki tashi kiyi wanka ki fito falo, akwai hirar da zamuyi." Kallon shi ta sake yi, sai kawai farin ciki yasa ta jinjina kai tace "To." Miƙewa sukayi a tare ita ta nufi ban ɗaki bayan cire hijabi da tayi shi kuma ya fita daga ɗakin yana jin hakan kawai shine maslaha. A falo ma shi da Kuwailat suka dinga hira har sallah isha'i Ummu bata fito ba, saboda kwalliyar da ta tsaya tsarawa duba da yau ya daina hushi da ita, kuma dai ai ta iya hausa sosai, da ya ce tayi wanka tasan me yake nufi, dan haka tana fatan ganin sauyi akan komai, indai har sauyin nan ya tabbata to zata nemi izinin shi ta bar ƙasa na wata ɗaya ta huta kafin ta dawo. Saida tayi sallah isha'i sannan ta fito ita ma, Kuwailat na idar da sallah ta kalle ta tace "Mamie, nifa yunwa nake ji, me zamu ci?" Kallon ta tayi tana zama tace "Kin dai ga ban dafa komai ba, amma abinda zki ci zaki faɗa min." Wani irin zama tayi cike da sangarta tana faɗin "Mamie indomie da kifi." Girgiza kai Ummu tayi ta kama hanyar madafa, amma ƙarar wayar ta yasa ta dakata tare da dawowa ta ɗauki wayar, *Aunty Nur*, shine sunan da ya bayyana, kawar da kai tayi da yanayin an fara takura ta, ƙin ɗagawa tayi sai da kiran ya tsinke sannan tayi saurin buɗe wayar t sauke layukan nata tare da aje wayar ta ƙara nufa madafa... Sallamar Alhaji da kuma muryar Mama da ta ɗauka yasa ta dakatawa da ɗumbin mamaki tana kallon ƙofar, ai ko sai ta ga suna shigowa da ɗaiɗaya, Mama, malam Adam, da kuma Alhaji Sagir da shi kan shi Alhajin, mamaki dai kam bai barta ba gaskiya, tunda biyun ai basu jima da rabuwa ba, to kuma me ya kawo su yanzu? Musamman ma Mama da gaba ɗaya zuwan da tayi gidan nan nata ƙidayayye ne. Haka dai ta tarbe su ba tare da ta ɗauko hijabi ba, dan dukan su iyaye ne a wajen ta har shi Alhaji Sagir ɗin, saida dukansu suka zauna ta miƙe tace "Bari a kawo ruwa, amma Mama wani wajen zaku je ko?" Da sauri Alhaji ya dakatar da ita da cewa "Ki bar ruwan nan, zo ki zauna." Kallon shi sai taji gaban ta ya faɗi, jiki a sanyaye ta koma ta zauna ƙasa kusan ƙafafun Mama har tana dafa guiwar Maman da tashin hankalin ta ya fi na Ummu, tunanin ta ɗaya shine ko iyayen Ummu sun biyo ta hannun shi ne? Inda Ummu kuma tunanin ta ya fi raya mata matsalar auren Nabila ce, saida duk aka yi shiru kowa yana jiran ya ji daga bakin Alhaji da ya tara taron, sai suka ji yana ce ma Kuwailat "Auta, tashi ki je wajen Hajiar Khamis ina zuwa." Da ladabi ta miƙe bayan ta amsa mishi da to ta fita, zuba masa idanu Ummu tayi, ta fara hango wani abu na daban yanzu, anya kuwa ba ƙarar t zaiyi wajen Mama ba akan gamin da ta masa wajen Alhaji Sagir? Ya kuwa san Mama? Nan fa tana iya gyara zama ta tsinke ta da mari? Anya Alhaji kuwa tsufa bai fara gigita shi ba? Kallon su Mama yayi cikin nutsuwa ya fara magana "Kuyi haƙuri da taraku da nayi akan abinda nasan ba zai muku daɗin ji ba, sai dai ya zama dole na sanar da ku dan maslaha muke nema, sannan ina so daga ƙarshe ku min kyakyawar fahimtar da ko kun ji hukuncin da na yanke, to ina so mu ci gaba da zumuncin mu da kuma mutumta junan mu kamar yadda muke a baya, Hajia..." Ya kira Mama yana kallon fuskar ta, ɗaga kai Mama ta sake yi ta kalle shi da nutsuwa tana sauraren shi, ɗorawa yayi da" Wata matsala ce ta ɗan kunno mana kai zamantakewata da Ummu, lokacin da ta fara min ƙorafi akan rashin samun yadda take so, sai nake kallon ta marar haƙuri ba kamar sauran matan nawa ba, to amma jiya zuwa yau sai na sake yin nazari kan matsalar, sai naga ai shekarun Ummu duk bata wuce ƴa a gurin matan nawa ba, sannan idan ƴata ce a wannan halin gudun kar ta faɗa halaka zan iya neman alƙali a da ya raba auren ta, wannan yasa nayi dogon tunanin kafin na yanke hukuncin da na taraku dan ku ji, kuyi haƙuri dan Allah kuma kar ku ƙullace ni, ban kira ku dan na ci fuskar ku ba, kuma ba na kira ku dan kawai ku shaida bane, amma na kira ku ne saboda girman da kuke da shi a idanuna, sannan ina so ku fahimci abun kamar yadda na fahimceshi nima, duk da sirrin mu ne wanda ban so fitar shi ba, amma dai nasan ku ma kun san daga ganin zamana da yarinya kamar Ummu kun san akwai cutarwa, a yau ɗin nan dana zurfafa tunani, na ji nayi nadamar auren ƙaramar yarinya kamar Ummu, wallahi tallahi na ji ina ma ina iya dawo da hannun agogo baya? Da ban yarda na auri Ummu ba, amma tunda haka ta faru mu bar shi a matsayin rabon haihuwar Kuwailat ne ya haɗa ni da ita, dan haka..." Sai kuma ya kalli Ummu da ta zuba mishi idanu hawaye har sun fara ɓata kwalliyar da ta caɓa saboda shi, murmushi ya mata ba tare da ya daina kallon ba yace" Kiyi haƙuri Ummu, ke yanzu kamar tsuntsuwa ce, ba zai yiwu na ci gaba da riƙe ki ba, ni ban barki kin tashi ba kuma ni ban tashi tare da ke ba, ina son ki Ummu, zan iya ce miki tsakanin ke da Hajia Luba ban san wacece ta fi yi min alkairi a rayuwata ba, amma dai nasan idan magana ake ta so, to ke ce ƙaramar su a shigowa gidan nan, kuma babbar su a filin zuciyata, ina son ki, kuma ina son zama dake na har abada, burina bai wuce ki zauna tare da ni har ki min takaba ba, sai dai bamu san yaushe hakan za ta faru ba, dan haka nake so na sama miki ƴanci, dan ba zan so kaina dayawa haka ba, Ummu, abu mafi muni da girma da zaki iya zuwa min da shi nan gaba shine zuciyar ki ta ci gaba da ƙawata miki wasu fuskokin, ba zan so haka ba, gwara nasan ko da kinyi haka to ba saɓo kika aikata ba, dan haka Umm..." Ummu da kuka ya ƙwace mata da sauri ta girgiza mishi kai, ƙafar Mama ta riƙe gam cikin tashin hankalin da bata ɗauka zata samu kan ta a ciki ba wai dan Alhaji Kabir na neman rabuwa da ita, rabuwa mana, tasan abinda yake shirin yi kenan, cikin kuka mai siririn sautin dake ratsa duk mai sauraro Ummu tace "A'a Abban Kuwailat, in dai nice wallahi na haƙura, kar ka mayar da ni *bazawara* dan girman Allah, wallahi tun ranar da naga kayi hushi ma na cire wannan abun a raina, na roƙeka Alhaji kar ka tona min asiri, ka barni na rayu da ƴata a gidan nan a ƙarƙashin kulawar ka, wallahi zan haƙura nima na maka biyayya." Kawar da duban shi yayi daga gare ta, sadda kan shi ya yi ƙasa sosai yana girgiza kai, cikin nutsuwa yace "Kiyi haƙuri Ummu, adalcin da zan iya yi miki kenan a rayuwa, Ummu, *na sake ki saki ɗaya*, idan kika samu miji kiyi aure, ina miki fatan..." Wani irin abu zuciyar shi ke yi, ƙarfin hali ne kawai shima ya yi, ga shi yadda ta rushe da kuka tana ƙamƙae jikin Maman ta ya ƙara tsuma zuciyar shi, kamar ya ce su basu wuri ya rarrasheta ta hanyar rumgume ta jikin shi, kasa ɗaga kan shi yayi saboda shima ƙwalla yake ji a idanun shi, Ummu kuma sai cakumar jikin Mama take tana kuka, Mama tayi suman zaune daddaɓata kawai take, ba ta taɓa tunanin zata iya kallon Alhaji Kabir ta mishi maganar da yanzun take ciciyar ta, amma haka ta kalle shi cikin dakakkiyar murya tace "Alhaji, kuma babu wata mafita sai wannan?" Bai ma ɗaga kan shi ba bare ya kalle ta, gashi kuma yayi shiru bai ce komai ba, Alhaji Sagir ma kunyar iyayen Ummun ta sa ya ƙi ɗaga kai ya kalle su sai girgiza kai da yake yi, hukuncin ya masa daɗi gaskiya, tunda ba zai iya ba idan ya riƙe ta kuma wani abu mummuna zai faru, ita kan ta Ummu za ta san gata ya mata amma nan gaba. Malam Adam ma ya fahimci zancen sosai da sosai, dan haka shima bai ga laifin Alhajin ba, hasalima matakin da ya ɗauka ya masa daidai, duk da dai Ummu ta fi birge shi, dan ba duka mace ke iya kallon mijin ta ta faɗa masa bata gamsuwa ba, mafi aksari ƙawayen su ne suke sanin haka, shiyasa sai ka ga ba'a samawa matsalar mafita ba sai mace ta ƙara durmiyawa wata babbar matsalar, a haka sai a rabu a wulaƙance ana zargin juna. Dake yana kusan kujerar Mama ne, ɗan matso da kan shi yayi kusan kunnen ta ya raɗa mata "Kar ki damu zamuyi magana, ki rarrashe ta kawai ta tashi muje." Tallabo fuskar Ummu tayi dake ta son duƙar da kan ta, hakan ya ɗan hassala Mama tace "Ke! Dube ni nan, kiyi haƙuri mana aka ce, ba zaki ɗauki *RUBUTACCIYAR KI* a yadda ta zo miki bane? Rufe min bakin nan." Ta ƙarashe har da hararen Ummu, asali Alhajin take so ta harara, ita dai koma yana kan daidai ai bata ga anfanin ya kira ta ya zaunar da ita sannan ya sakar mata ƴa gaban ta, ya san yadda uwa ke ji kuwa? Ya san me take ji a halin yanzu? Ya yi tunani da kyau kafin ya yanke hukuncin nan? A hassale ta miƙe tare da cicciɓa Ummu ta kama hannun ta suka nufi ɗakin Ummun da lokacin shasheƙa kawai take kamar ranta zai fita, suna shiga ta saki hannun ta tace "Haɗa min abinda zaki iya anfani da shi na tsawon lokaci, daga baya kya zo ki ɗauki sauran." Madadin tayi abinda Mama ta ce, sai kawai Ummu ta faɗo jikin Mama ta sake fashewa da kuka, runtse idanu Mama tayi saboda suya da zuciyar ta ke yi, a hankali ta sa hannu tana shafa bayan Ummu, tun ita ma kukan da Ummu ke yi yasa ta zubar da hawaye tana faɗin "Kiyi haƙuri kin ji, kiyi haƙuri Ummu, in sha Allah ba zaki tagayyara ba, Allah yana tare d ke, ki ɗauki rabuwar ki da shi ita tafi zama alkairi, kiyi ta addu'a Allah ya musanya miki da mafi alkairi, kin ji ko ? Yo shiru daina kukan bana so." Cikin matsanancin kuka Ummu tace" Wanene zai fi Alhaji Kabir alkairi Mama ? Wanene zai fi min shi a rayuwata? Mama mai yasa baiyi tunani ba kafin yanke hukunci? Shekarar mu goa sha uku a ce mun rabu? Dama ni ce baya so a cikin matan shi?" Da sauri Mama ta ci gaba da daddaɓa bayan ta tana faɗin" Mutanen arziƙi ai dayawa suke, in sha Allah zaki samu wanda ya fi shi, ke dai kiyi ta addu'a, kuma na gaya miki bana son kukan nan, ai ba shi kaɗai ne namiji ba, maza share hawayen hado min kayan ki." Yadda Mama ta haɗe fuska yasa dole Ummu ta nufi wajen kayan nata ba tare da ta tsagaita da kukan ba, Mama na tsaye ta riƙe haɓa tana kallon ta zuciyar ta sai harbawa take, ina ma tana da ilimi? Ina ma ubangiji zai sanar da ita ilimin da ke cikin abubuwan da suke faruwa ɗin nan? Da ko ba komai zata samu nutsuwar zuci na sanin abinda zai faru gaba. *Alhamdulillah.* [16/08 à 19:35] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *51* Sun jima nan Ummu na ta haɗa kaya cike da ƙunar zuciya n abinda bata taɓa tsammanin zai faru da ita ba, saida ta cika jaka uku manya sannan ya ɗauki hijabin ta da tayi sallah ta saka, jaka biyu Mama ta jawo mata suka fito ita kuma tana jaye da guda. Dama tunda suka shiga nan malam Adam ke ta hira da Alhaji Sagir, motsin fitowar su yasa Alhaji ɗaga kan shi, yana ganin su da kaya ya miƙe tsaye har suka ƙaraso, da kulawa cikin raunin murya yace "Ummu, ban sake ki dan ki tafi gida yanzu ba, ki zauna ɗakin ki kiyi idda, haka shari'a ta ce." Cikin ajiyar zuciya da ya samo asali daga kukan da tasha ta kalle shi tace "Nagode da kulawar ka, amma ba zan iya zama ba gaskiya, dama kana sona ne zan iya zama, ko ba komai zaka kalle ni da mutumci." A raunane yace "Ba haka bane Ummu, ina ƙaun..." Da sauri Mama ta kalle shi tace "Zan tafi da ita ne dan bana son kukan nan nata, idan tana cikin tashin hankali kuma bata kulawa da kan ta." Shiru yayi na sakanni, sai ya jinjina kai yace "Hakane, na sani nima, idan bata cikin yanayin daɗi ko cikin ta bata damuwa da shi." Taɓe baki Mama tayi tare da juyawa ta kalli Ummu tace "Muje." Jan jakunkunan tayi tana ayyana dole ne mana, daga Ummu har Nabila ai babu mai iya ci idan ran su ba ya musu daɗi, kuma hakan ya samo asali ne daga ita, ita ma haka take, yanzu bata san wa zai kwaɓi wani kan su ci abinci ba? Shiyasa ma ai ta rame lokacin damuwar Nabila. Har sun fara tafiya Alhaji ya bi Ummu da kallo yace "Kuwailat fa? Kin san babu wanda ta saba da shi sama da ke?" A gigice Ummu ta juyo cikin hassala tace "To sai me? Ba ka san da haka ba ka sake ni, Kuwailat nan gidan uban ta ne, za ta iya rayuwa duk yadda ta zo mata, ni ma kuma zan je gidan tawa uwar na rayu duk yadda rayuwar ta zo min, idan kun kasa riƙe ta ka kasheta mana." Cikin rashin jin daɗi ya girgiza kai yana kallon ta kawai, ya san ranta ne ya ɓace, amma ya zata yi da ya wuce haƙuri, har suka fita ba wanda ya sake cewa komai, malam Adam daga baya ya musu sallma ya bi bayan su, Yaya Luƙman dama shi ya kawo su, bai shiga bane saboda ya san hirar tsakanin su ce, ko da ya gan su da jakunkuna kam ya san dama akwai abinda zai faru, haka ya ja su ko tambayar su bai yi ba saboda kuka da Ummu ke ta yi har da rashin ban kwana da Kuwailat, kuma ba ta so ma ta ga zata tafi ɗin, shiiyasa bata yarda sun haɗu ba. *Har* cikin falo malam Adam ya raka su ɗauke da jaka ɗaya, kan kujera Ummu ta zauna kusa da Nabila da suka samu tana karatu, tuni hankalin Nabila ya tashi ganin akwatinan Ummu ga ta kuma ta dawo bayan tafiya ɗazu sannan tana kuka, rumgumota tayi jikin ta tana faɗin "Aunty Ummu, lafiya ? Me aka miki? Me ya faru? Ina Kuwailat ?" Ba wanda ya iya ba ta amsa har Mama ma da ta zauna sukuku da ita haka ma Yaya Luƙman, daga baya ne malam Adam ya zauna yana kallon Mama yace "Aminatu, da alama ranki ya ɓace game da abin nan da ya faru, amma ni ban ga abun ɓacin rai ba?" A ɗan kausashe Mama ta kalle shi tace "Ba ka ga abun ɓacin rai ba? Haba malam, ta ya dan zai sakar min ƴa sai ya kira ni na zauna sannan ya danƙara mata saki ɗaya, kuma wai yana bani haƙuri? Haka ake yi? Kawai dan muna ƙasa da shi?" Murmushi malam Adam yayi yace "Ina ga baki fahimci abinda yake nufi bane ko?" Nabila da Yaya Luƙman da abun ya zo musu bazata kusan a tare suka maimata kalmar "Saki fa?" Sai dai ba wanda ya kula da su saboda malam Adam da ya ɗora da "Aminatu, ƴar ki fa wani hali take neman shiga saboda rashin samun biyan buƙata, aminin nashi Alhaji Sagir ya ƙara min bayani ai, ga Ummu nan ki tambaye ta har ƙarar Alhajin ta kai wajen shi Alhaji Sagir, shin hakan bai isa ya sa ki fahimci girman hukuncin da ya yanke ba? Dattijo kamar shi y zauna gaban mu yana furta kalmar so ga yarinya kamar Ummu, ai kin san dole ce zata sa ya rabu da ita, yau fa da ya ci gaba da riƙe miki ƴa, gobe kika wayi gari kika gan ta a halaka, shin hakan zai miki daɗi ne? Dan fa ki fahimci haka ya ce ki je, amma ki taso kina hushi da shi? Yau da milyoyin maza suna ɗaukar irin wannan matakin, da ba za'a samu dayawa masu zina ta kowace irin siga ba, kina ina wasu matan ke kai mzan kotu dan a raba su? Kina ina wasu matan ke yin tsaye kan sai miji ya sake su? Amma mazan su dage kan ba zasu sake su ba saboda tsabar mugunta, sannan kina ina dubbanin mata ke susucewa saboda sun kai kukan su ga iyayen su sun ƙ sauraren su, sannan mazan ba wanda zasu zauna su fahimci juna bane, wata a haka sha'awar ta zata dakushe har ta kai bata jin buƙatar namiji, wata garin biya wa kanta za ta kamu da ciwon sanyin da zai addabi rayuwar ta, ke wasu ma kusan halaka mazajen su suke yi garin nemawa mazajen maganin da zai ƙara musu kuzari... To yanzu shi yayi namijin ƙoƙari ya sama musu maslaha, sai a ga laifin shi kan haka?" Girgiza kai yayi tare da miƙewa tsaye ya sa hannu aljihu ya ciro check ya miƙawa Mama yace" Gashi ki bata, shine ya ce a bata saboda haka shari'a ta faɗa idan ka sallami mace to ka mata ihsani dan ta kula da kan ta kar ta tagayyara." Amsa mama tayi jiki a sanyaye sai Luƙman da ya miƙawa hannu yace" Ni zan koma gida, tun yamma da na fito ban sake leƙawa ba, sai anjiman ku." Yaya Luƙman ma miƙewa yayi ya kalli Mama yace" Bari nima na wuce sai na aje ku daga nan, Mama saida safe, dan Allah kuma ta daina kukan nan haka." A sanyaye Mama ta amsa da" Saida safe, Allah ya yi albarka." Da haka suka fita suka bar su, Nabila ce ta ɗauki kayan Ummu ta kai ɗakin ta, haka suke zaune shiru sai shasheƙar kukan Ummu kawai dake ta tashi, sun jima nan kafin ta miƙe ta fita ta ɗauro alwala ta dawo ɗakin, tana ɗaukar hijabin ta ta kalli Mama tace "Saida safe Mama." Ba ta jira cewar ta ba ta shige ɗakin Nabila, da kallon tausayawa suka bita, Mama ma na ganin haka ta ce ma Nabila "Idan kin shiga ki buɗe kayan nan nata ki ware mata su, idan akwai wuri a drower ki ki saka lata wasu a ciki." "To Mama." Nabila ta faɗa tana miƙewa, saida Mama ta rufe gidan ta kashe wutar falo sannan ta shige nata ɗaki ita ma. ********************* Duk da bata jin daɗin jikin ta, amma abinda ya faru a tafiyar ta iyayen nata ya sa dole Eesha mirtsikewa ta zo masaukin nasu dan duba Maman ta, ta ɗauka Maman ta ta daina damuwa da ƴar uwar ta da ita ma bsu san inda take ba, amma yau ta tabbatar lallai maman su kawai tana taushewa ne dan ba yadda ta iya, irin kukan da take yi da hargagin kiran sunan aunty Ummu ya sa ba ta jin haƙurin da suke ta bata da rarrashi, cikin tausayawa Aisha tana rumgume da Maman nata tace "Mamie, ba dai aunty Ummu ƴar ki bace, wallahi zan dawo miki da ita, ni da kaina zan je gidan gobe ko ta ƙarfi ne sai ta zo gare ki, dan Allah Mamie ki nutsu, kinsan damuwar ki tashin hankalin mu ce." Cike da tabbaci Mama Nuriyya ta jinjina kai tace "Ƴata ce, haka naji a jikina, kuma ita ma bata musa ba, Maman ta tana kallo ai, ta ya za'a ce ba ƴata bace dan Allah? Ta ya?" Cikin kulawa dai Aisha tace" Hakane Mamie, su ma ina ga basu gane bane, ta ya zasu ƙi yarda dake? Basu san mun jima muna neman ta bane?" Haka ta ci gaba da shafa bayan ta tana rarrashi har bacci ya ɗauke ta, ba wai dan ta shirya ba sai dan kukan da ta ci da kuma samun jikin Aisha tana sauke shasheƙa, ganin baccin Maman ya sa Aisha kallon Sa'ad da su ke zaune sun buga tagumi tace" Abbu, dan Allah ka min izini da safe na je gidan aunty Ummu muyi magana da ita?" Da sauri Abbu Mukhtar ya kalle ya yace" Ki je ki ce mata me Eesha? Zato fa kawai muke, amma bamu da wata hujja ko makama." Kallon shi tayi tace" Ina da hujja Abbu, zan kuma gano hakan da yardar Allah, ko iya abinda kuka ji daga haɗuwa da ita kawai ya isa ya zama hujja." A hankali Abbu ya girgiza kai yace" A'a Eesha, hakan abu ne da zai iya faruwa ga kowa, wataƙila kawai jin..." Da sauri Aisha ta katse shi da" Abbu ya fi ƙarfin haka, kawai ku amince naje na ganta muyi magana." Jinjina kai yayi a kasalance yace" Shikenan, ga mijin naki nan ai." Kallon Sa'ad tayi da bai ce komai ba har lokacin, dan shi tunanin shi daban ne akan wannan matsalar, shi so yake ya shiga lamarin ta hanyar bincike, ba kawai ta haka kowa ya dage ƴar sa bace, tana kallon shi ya lumshe idanu a tausashe yace" Ba damuwa, Allah nuna mana goben." "Ameen." Ta faɗa har da sauke ajiyar zuciya, haka ta ci gba da shafa maman ta dan bata so ma ta farka ta sake ɗora musu rogimar nan tamkar wata jaririyar goye. *WASHE GARI* Tsatsaye suke yana dafe da kafaɗar ta, ita kuwa sai faman share hawaye take, Alhaji da hankalin shi na kan Khamis ne ya sake duban ta yace "Yi shiru mana auta, na gaya miki Maman ki fa tana gidan su Nabila, kuma ga Khamis zan sa ya aje ki can, kinga sai ki wuni a can tunda yau juma'a dama ba karatu." Ba ta ce komai ba sai share hawaye da take yi, Khamis da har yanzu bacci ne a idanun shi tun komawar da yayi bayan sallah asuba yace" Abba, can gidan su Nabilan zan kaita? To a can aunty Ummu ta kwana ne?" Kallon Khamis ɗin yayiya ɗaga masa kai yace" E, dan Allah maza ɗauko makulli ka kai min ita." "To." Ya faɗa yana kallon Kuwailat da idanun ta sukayi jajir yace "Haba auta, shikenan daga aunty bata nan sai kuka? Kamar ba kowa a gidan, ba naga wajen Hajia kika kwana ba?" Kallon ta Alhaji ke yi yana juran ya ji amsar da zata bashi amma shiru, hakan yasa Khamis nufa ɗakin nasu, sai kuma yana bada baya Aliyu na shigo tare da Aisha a bayan shi da tayo sammako, saida suka ƙaraso Aisha tayi sallama Alhaji ya amsa suka gaisa sosai kamar sun san juna, ita bata yi tsamanin shine mijin aunty Ummu ba, a tunanin ta surukin ta ne ma'ana wanda ya haifa mata miji. Dan haka suna gama gaisawa cikin rusunawa Aisha da nutsuwar ta dake kan Kuwailat mai kama da fuskar Hajia tace "Abba, dama na zo ganin aunty Ummu ne." Gyara tsayuwa Alhaji yayi, haka ma Aliyu dake son ya ji amsar da zai bayar, ya shiga ɓangaren Ummu dan gaishe ta kamar yadda ya saba, amma sai Kuwailat dake shiri tace Mamie bata nan, ina taje da safe haka? Shiyasa da matar take tambaya nan ne ya ce e ta shigo kawai, cikin nutsuwa Alhaji yace "Gaskiya Ummu bata nan, ta fita ne, amma idan son ki da ganin ya na ujila ne to ga ƴar ta nan yanzu can ta nufa, zaku iya tafiya tare." Faɗaɗa murmushi Aisha tayi, ƙaunar yarinyat lokaci guda yana tsarga mata tamkar ɗaya daga cikin yaran ta, hannu ta miƙawa Kuwailat da kulawa tace" Zo mana ƴan mata." Duk da Kuwailat an zama ƴan mata, amma haka ta turo baki ta matsa kusan Aisha, dafa kan ta tayi tana kallon Alhaji tace" Zamu iya tafiya? A mota nake." Kallon ya shima Alhaji yayi yace" Yayan ta ne zai kaita, ya..yawwa gashi nan ma zuwa." Jinjina kai tayu tace" Ba damuwa, ni sai na bar mota ta a nan, idan muka dawo na ɗauka." Girgiza kai Alhaji yayi yace" A'a, kuje da ita, sai ya muku jagora." Ta ji daɗin hakan ƙwarai, dan haka Khamis na zuwa Alhaji ya faɗa mishi yadda zasuyi, riƙe yake da hannun Kuwailat har suka fita Aisha na godiya, Aliyu na tsaye gaban Alhaji yana masa wani kallon tuhuma yace" Abba, me aunty ta je yi gida tunda safe? Kuwailat ta ce min wai a can ma ta kwana? Lafiya?" Juyawa Alhaji yayi yna kallon ɓangaren na Ummu yace" Ba komai, lafiya lau." Cike da rashin yarda duba da jiya ai gaban su ya share ta kuma tana kuma yasa shi komawa inda yake fuskantar Alhajin yace" Abba, dan Allah ka faɗa min me ke faruwa? Naga kamar akwai damuwa tsakanin ku." Kallon shi Alhaji yayi fuska haɗe cikin kaushin murya yace" Mun rabu da Ummu, na sake ta." Yana faɗin haka kawai ya kama hanyar zuwa ɓangaren Hajia, haɗewa sukayi da Hayat hakan yasa shi faɗin" Ka ce Maman ka ta same ni ɓangaren Hajia Luba, har da Maman Aliyu ma, yanzu yanzu." Da ladabi Hayat ya amsa ya koma ɓangaren na Maman shi da ya fi kusa da shi. Aliyu da ya bishi da kallo saida ya ji kan shi ya sara, hankalin shi ya tashi sosai, zuciyat shi ta gagara fahimtar komai, rabuwa Abba da Ummu? Akan wane dalili? Me ya yi zafi haka da Abba ba zai yi haƙuri ba? Yana ganin wannan hukuncin yayi daidai kenan? Gaskiya bai ji daɗi ba ko kaɗan, kuma ba zai kasa faɗawa Abban nashi ba. A ƙofar gida Khamis ya sauke su yace ma Kuwailat "Auta ki gaishe min da aunty, anjima zan dawo na ɗauke ku." Kuwailat bata kula shi ba, dan ita bata ga dalilin da ya sa Maman ya kwana ba a gidan Baban ta ba, Aisha ce kawai ta masa godiya sosai kafin ta bi bayan Kuwailat su shiga. Tsakar gida suka samu Mama tana gyara abin da za su karya, har ƙasa Aisha ta duƙa saboda Mama zaune take suka dinga gaisawa da fara'a, kafin Mama ta dubi Kuwailat tace "Ke kuma lafiya kike ta jan idanu?" Murmushi Aisha tayi tace "Ai kuka take ta yi wai Maman ta." Da mamaki Mama ta nuna Kuwailay tace "A haka ɗin ganɗanɗan dake? To Allah ya kyauta." Murmushi Aisha ta sake yi tace "Ameen Mama, aunty Ummu ɗin tana ciki? Nima ita na zo gani." Kallon fuskar ta Mama tayi, cikar kamala da haiba yasa Mama faɗin "E tana ciki, ku wuce ciki, tana nan bacci take." Har Aisha zata miƙe sai kuma ta dakata ta dubi Mama tace "Na san baku gane ni ba Mama, sunana Aisha, ƴar Alhaji Mukhtar Yaya ga uncle Fahad, jiya ai sun zo ni ban samu zuwa ba saboda ban ji daɗin jikina ba." Da kulawa sosai Mama ta sake kallon ta tace "Allah sarki A'ishatu, ƙwarai kuwa hakane, ai ko Nabila ma dan ta tafi islamiyya da kun haɗe, nagode sosai, ku wuce ciki tana nan." Da jin daɗi Aishata miƙe ta shiga, ɗakin da ta tabbatar nan Kuwailat ta shiga ita ma ta shiga dan tana jin kamar sautin kuka, tana shiga ko ta samu Kuwailat a ƙirjin Ummu da shigowar Kuwailat ɗin ta farka daga bacci saboda kwana da tayi tana sallah kan ubangiji ya kawo mata mafita cikin lamarin ta, dan haka ƙala ma bata ce ma Kuwailat ba saboda yadda ta faɗo mata a jiki tana kuka, daddaɓa bayan ta kawai take yi har Aisha ta shigo, a sakanni ƙalilan suka kalli juna, amma take irin ƙaunar nan da ake cewa *daga Allah* ta tsargu tsakanin su, ga kuma kowa da yake ganin kamannin wani a fuskokin junan su, Aisha na ganin kamannin Hajia da aka bata labari, Ummu kuma na ganin kamannin dattijon nan (Abbu Mukhtar) a fuskar matashiyar da duk ƙibar ta bata sa Ummu jin wannan ba zata gaza yin ƙanwa da ita ba. Sallamar da Aisha tayi ta amsa a tausashe, kafin ta gyara zaman ta sannan ta daddaɓa Kuwailat tace "Kukan ya isa haka, yanzu je ki ban ɗaki zuba min ruwa nayi wanka." A kunyace Kuwailat ta miƙe tana rufe fuska saboda kunya, sai Ummu da ta miƙe tana nuna ma Aisha gadon ta zauna duk da bata san ta ba amma tana jin tana da alaƙa da mutanen jiya, a tausashe tace" Bismillah zauna." Da fara'a Aisha ta zauna tana murmushi da cewa" Nagode." Saida ta zauna Ummu ta sake duban ta tace" Muna lafiya?" Kallon ta Aisha tayi tace" Ina kwana aunty Ummu. " Da jin sunan aunty Ummu ta sake gasgatawa, haka suka gaisa sosai har Kuwailat ta fito, shiru sukayi saida ta raɓa ta fita daga ɗakin sannan Ummu tace" Duk da dai ina son sanin da wa nake tare? Amma ki ɗan gafarce ni, ba zan iya komai ba idan ban watsa ruwa jikina ba, amma ba zan jima ba." Da murmushi Aisha tace" Ba damuwa aunty, ki ɗauki lokacin ki." Murmushi Ummu tayi tare da nufa madafar tana ji koma menene ya kawo matar nan gidan su to yana da alaƙa da sambatun da aunty Nur ta fara yi jiya cewa wai ita ƴar ta ce. *Alhamdulillah.* [18/08 à 12:27] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *52* Ta jima zaune ita kaɗai har Kuwailat ta dawo ɗakin da abun kari ta aje mata ta ce in ji Mama, tayi ftain cikin karammata da sukayi, amma abin da ke tafe da ita da taradaddin tabbacin karɓuwar da zata samu ya sa ruwa kaɗai ta kurɓa dan ko a gidan ta bata samu ta sha ba kafin ta fito. Ƙarar buɗo ƙofar baɗaki yasa ta ɗga kai ta kalli ƙofar, ganin Ummu ɗaure da towel wanda ya sauko mata har kan guiwa, da kuma wani ƙarami a kan ta har zuwa kafaɗun ta saita saukar da kan ta, Ummu da fara'a tace "Na barki ke kaɗai ko? Yi haƙuri." Murmushi Aisha tai tace "Ba komai aunty." Hakan yasa Ummu zaunawa bakn gadon ta ba Aisha baya ta fara goge ruwan jikin ta kafin ta fara shafa mai, saida ta kammata tsaf ta shafa kulaccar ta sannan ta miƙe dan saka kaya, a drower ta nemo riga da siket din da ta yi niyyar sakawa, saida ta fara saka siket ya zauna maya daidai tare da janyo jigidar ta wacce ta shige ƙasan siket ɗin hakan kuma baya mata daɗi, sannan ne ta fara kiciniyar saka riga bayan ta sassauko da towel ɗin dake kan ƙrjin ta, hakan yasa tun rigar bata gama sauko mata ba towel ɗin ya zame ya faɗi ƙasa. Aisha da tunda ta ga Ummu ta fara saka kaya ta ɗauki wayar ta tana dannawa ba dan wani abu muhimmi take ba, sai dan kar wani abu ya ɗauki hankalin ta, zamewar towel din yasa ta ɗan saurin ɗago kan ta ta kalli ɓangaren, fahimtar abinda ke faruwa ya sa tayi saurin kawar da duban ta. To amma wani abu da ya ɗan ɗauki hankalin ta yasa ta saurin maida kallon nata ga ƙugun Ummu, hakan ya sa gaban ta wata irin dokawa, bata san ta saki wayar ta ba ƙasa ta miƙe tare da yaye mayafin data naɗiɗiye kan ta da shi, gaba ɗaya ta aje gyalen kan gadon tare da ɗaya rigar zanen dake ɗaure jikin ta, ƙibar ta tasa saida ta ja cikin ta sannan tayi nasarar jawo jigidar dake ƙugun ta, kafin ta haɗu da iyayen ta bata saka jigida, har saida suka haɗu tayi aure ma tana da cikkn ta na fari Maman ta ta zo garin, nan take ta mata faɗa kamar ba mace ba, ba sarƙar ƙafa dan ado, duk da ma zamani ya sa yanzu ko kana son sarƙar ƙafa dole kake haƙura da ita, amma kuma hannayen ta ba awarwaro, yatsun ta ba zobe ko na wasan yara, haka dai Mama tayi ta faɗa, shine bayan haihuwar ta su aunty Mardiyya za su zo ta taho mata da jigida dozin, sai kuma wata wacce Maman ta ce ta fi bata mahimmanci saboda su ma iyayen su ne suka bata ita da aunty Mardiyya, ita aunty Mardiyya nata suna nan a ƙugun ta, ita ce dai bata da ko ɗaya duk ta ba wa ƴaƴan ta. Ba komai ya sa Aisha jin wani abu game da haka ba sai dan Maman ta faɗa mata duwatsun ba gama gari bane, mafi yawan wanda aka yi jeren a ƙarƙashin ruwa ake samun mu, sai kuma murjani da aka ƙara ƙawata jihidar da shi, da sauri Aisha da ta jawo jigidar ta tana kallo ta kalli ƙugun Ummu da take shirin sakin rigar ta, da gudu gudu Aisha ta ƙarasa bayan Ummu da bata san me take ba. Tana zuwa bayan Ummu kamar daga sama ta sa hannu a ƙugun ta tare da jawo jigidar ta Ummu dake irin zaren nan ne na roba dake jawuya. A tsorace Ummu ta juyo tana ƙarasa sakin rigar ta ta zuba ma Aisha wani irin kallo mai tattare da mamaki da al'ajab da jin cexa _"To, ke kuma haka kike?"_ Dan abu ɗaya da ya zo mata a rai shine matan nan ne dake neman ƴan uwan su mata, hakan yasa ta ja baya tana ci gaba da yi mata wannan bhagon kallon, Aisha ko jigidar ta dake hannun ta ta nunawa Ummu fuskar ta fal murmushi tace" Aunty Ummu, kin gani ko? Irin tawa ce, a ina kika samu wannan jigidar? Kin gani ko?" Sai lokacin Ummu ta kalli jigidar, ita kan ta saida ta ji jikin ta ya amsa, tak tak iri ɗaya ne, amma sai ta basar ba ta ce komai ba, hakan yasa Aisha ɗan hasala ta sake matsawa kusan Ummu ta saki jigidar ta, riƙo hannayen Ummu tayi cikin kaushin murya tace "Wai me yake damun ki ne aunty *Kuwailat*? Ke fa ƴar uwata ce, wannan jigidar Mamie ce ta saka miki ita da hannayen ta, idan ke ba jinin su bace, ta ya kika samu wannan? Me yasa kika kasa fahimta ne wai? Me yasa ba zaki fahimci hawayen mahaifiya bane? Ke ma fa uwa ce, kina ganin duk inda ƴar ki zata shiga zaki kasa gane ta ne?" A nutse Ummu ta janye hannayen ta daga na Aisha cikin nutsuwa tace" Kinga baiwar Allah, ni ban ma san wacece ke ba? Jiya wasu haka suka zo min da maganar nan, ki gane mana kema, rayuwa bayan wannan shsekarun kawai wasu su nuna min kansu wai sune iyayena, to me ya hana su nema na? Sai kawai da *RUBUTACCIYA* ta haɗa Nabila da Fahad, sai ya zama silar haɗuwata da nawa iyayen? Kina ganin an min adalci kenan? Da ba'a zo nema wa Fahad auren ƙanwata ba, da kenan ba zamu taɓa haduwa da su ba? Kinga, ni ban damu da sai nasan su wa suka haife ni ba, mahaifiyata gata can waje kin baro, ina da kyakyawan ahali anan, ina gudanar da rayuwata yadda ya kamata, dan haka ban buƙatar matsala, ina so naji da wacce ke gabana yanzun haka, dan hka ku rabu dani dan Allah, bana buƙatar arziƙin ku ko wata alfarma taku." Raɓata Ummu tayi za ta wuce, rai ɓace saboda Aisha tana da ƙarancin haƙuri ta sake riƙo damtsen Ummu, a wani zafafe ta kalle ta tace" Ba dan nasan ke ce a gaba dani ba, wallahi da na tsinka miki marin da zai sa ki dawo hayyacin ki, me ya toshe kan ki? Kina tunanin akwai uwar da zata iya mantawa da abinda ta haifa ne? Ko da kuwa ta mummunar hanyar ta same shi? Kin san shekarun da suka kwashe suna neman mu? Kin san milyoyi nawa suka kashe kawai domin a yaɗa labaran ɓatana ni da ke? Ko kin san da iya wanda ya san wani wanda ya san inda kike kawai sun saka kyautar kuɗi har milyan biyar, ba ma ga wanda ya nuna musu mu ba? Mutumin da ya kamo hannun iyayena ya kawo su har gidan da nake a gabana suna bashi cakin (check) na milyan sha biyar, duk da haka a shirye suke da su tuɓanya ninkin ba ninki akan ki, saboda ni sun same ni kuma sun san yadda nake, amma ke basu san a ina kike ba? Wace rayuwa kike yi? Me kike yi? Ya kika zama?" Sassauta murya sosai Aisha tayi hawaye na zarya a kumatun ta tace" Saida mutane suka fara kiran mahaifiyar mu da mahaukaciya, saboda ɓatan mu ya zautar da tunanin ta, mahaifin mu kuma yana fama da hawan jini, idan kika gan su shi da kawu Bilal, zaki ɗauka Abbu shine gaba da kawu saboda tsufan da yayi gaggawar cimma sa saboda damuwa da zulumi, amma kuma bayan kawu Bilal har aunty Murjanatu ta shiga tsakanin su, Ummu ko na sakan ɗaya ne ki rumgumi jikin iyayen ki, ta nan zaki fahimci gaskiyar da ake faɗa miki, dan soyayyar wacce ta ɗauki cikin ka wata tara sannan ka fara shan nonon ta, da wacce ta shayar da kai daga baya bata taɓa zama ɗaya, saboda wannan *mahaifar*, wacce sunan ta ma a larabce *tausayi* yake nufi, kuma wallahi haihuwa ba wasa bace, kin yi ta kin san me ke ji, ki roƙi Maman ki ta faɗa miki gaskiya, in har ba wata manufa ce akan ki ba na ƙin son ki san iyayen ki, to za ta sanar dake ba ita t..." A mugun zafafe Ummu ta nunowa Aisha yatsa tana zaro idanu da faɗin" Kar ki kuskura, kar ki ce zaki fara faɗawa mahaifiyata maganar banza, idan..." Mama da ta shigo falo dan karyawa ne ta ji wannan tashin muryoyin, hakan yasa ta aje kwanon hannun ta da sauri ta shigo ɗakin, abinda ta riska ne yasa ta gaggawar yi ma Ummu tsawa, shiru duk sukayi suna kallon ta har ta ƙaraso, tana zuwa ta kalli Aisha a nutse tace "Dan Allah, zan iya ganin iyayen ki?" Murmushi Aisha tayi tace "Me zai hana Mama, zaku iya." Jinjina kai tayi tace "Muje ki kaini ida suke dan Allah." Da sauri Ummu tace "Mama, me zaki je ki musu?" Kallon ta tayi ta nunota da yatsa tace "Kar na kula jin bakin ki a maganar nan." Tana gama faɗa ta juya zata fita, hakan yasa Aisha kallon Ummu sannan ta wuce ta ɗauki gyalen ya da wayat ta har da jakar ta sannan ta bi bayan Mama, saida suka kai ƙofa Mama ta juyo ta kalli Ummu tace "Ki saka hijabin ki, tare zamu tafi." Kallon Maman tayi sosai, sai kawai ta jinjina kai tace "To Mama." Juyawa tayi ita ma ta fara neman hijabi, tana ɗaukowa ta fito ta samu har sun fita tsakar gida Mama na faɗawa Kuwailat ta ɗauko hijabi ita ma zasu fita sai a rufe gidan, hakan kuwa aka yi tsaf suka tafi tare babu kowa gidan. Babu mai hira a motar dan kowa da abinda yake saƙawa a ran shi, haka suka isa masaukin baƙin, sai dai tun daga bakin ƙofa mai gadin wurin ya leƙo ta madubi yna faɗa ma Aisha "Barka da zuwa Hajia, yanzun nan ko su Alhaji suka fita." Da mamaki Aisha tana kallon shi tace "Suka fita kamar ya ya? Ina suka je su kuma?" A taƙaice ya bata amsa da "Asibiti." Dukan su na motar saida duka kalle shi har da Kuwailat dake maƙale a kafadar Ummu, Aisha ce tayi gaggawqr faɗin "Asibiti? Me ya faru? Wa ye ba lafiya cikin su?" A nutse yace "Wallahi dai Hajia na ga sun tallabo an saka ta mota sun fita da ita, farar matar nan mai ɗan tsayi..." Bai ƙarasa ba Aisha ta furta "Mamie, inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un !" Sai kuma ta kalle shi a gigice tace "Wane asibiti suka kaita?" Da kulawa yace "E to, ban sani ba gaskiya, amma dai tare da Alhaji Sa'ad suka tafi." Jin haka da sauri ta ciro wayar ta daga jaka ta fara kiran lambar Sa'ad ɗin, jim kaɗan ya ɗaga hakan yasa ta gyara zama tace "Abbuna, ina Mamie ? Ya jikin nata? Wace asibiti kuka je?" Cikin nutsuwa daga ɓangaren Sa'ad yace "Ki fara kwantar da hankalin ki, babu abinda ya samu Maman mu, jinin ta ya hau kawai, amma Alhamdulillah yanzu haka an mata allurar bacci tana hutawa." Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, duk da ya san zata iya faɗa masa haka dan ta kwantar da hankalin ta, amma dai ta san da sauƙi ɗin, dan haka a nutse tace" Wane asibiti ne? Gani nan zuwa." A nutse yace" Hanyar da muka biyo dake da zamu taho, akwai alllon shaidar asibitin na nan da kin karya kwana." Tuni ma Aisha ta kama hanya dan ta gane asibitin. Tunda aka ambaci asibiti gaban Ummu ya yanke ya faɗi sosai, hatta tsigar jikin ta duk saida ta tashi tana jin ba daɗi sosai, amma dai haka tayi shiru ba ta ko nuna abinda ke ran ta ba, tana jin Mama dake gaba tana ta jajanta abun da Aisha ita kuma tana ƙara faɗa musu ai tun jiyan nan dma kuka kawai take ta ƙi cin komai, hakan yasa Mama sake ɗaurar niyyar yau sai ta sada Umm da iyayen ta, dan gaskiya ta tausaya musu sosai da sosai. Basu sha wahalar samun ɗakin da aka kwantar da ita ba, ƙwarai da gaske Abbu yayi mamakin ganin Aisha tare da Ummu, gaisawa sukayi kafin Mama ta kalli Abbu a raunane tana riƙo hannun Ummu tace "Alhaji, dan Allah ku gafarce ni abisa ɓoye muku wani babban al'amari da nayi shekaru tara da suka wuce, na gane kuskurena daga sa'ilin da naga irin kiɗimewa da tashin hankali da mahaifiyar..." Sai kuma ta kalli Ummu da ita ma take kallon ta tana son ta ji me zata aikata tace" Ummu, da gaske *Ummu Kulsum ƴar ku ce*, ƴar ku ce halak malak." Faɗin irin yanayin da dukan su suka tsinci kawunan su ma ɓata lokaci ne, farin ciki mai saka kuka, jin daɗi marar misaltuwa, da kuma mamakin ya haka ta faru? Ummu ce kawai takamaiman yanayin ta bai bayyana ba, ita dai ta kalli Mama da ke ci gba da ba wa Abbu haƙuri, sai kuma ta kalli Abbu da yake kallon ita ma Ummu. Ta jima haka kafin wasu zafafen hawaye su sauka kan kumcin ta, kallon Mma tayi dake kuka sosai tana sakin hannun Ummu da niyyar fita ta bar asibitin, da sauri Ummu ta riƙota suka kalli juna, cikin dakusashiyar murya Ummu tace "Me yasa Mama? Kin fa san halin da nake ciki, yanzu ke kawai nake da buƙata, ina so ki rarrashe ni da kan ki ne Mama, sai kuma ki damƙani hannun waɗanda basu damu dani ba." Girgiza mata kai Mama tayi tana kuka tace "Ummu, ta ya wai kike wannan banzan tunanin? Iyayen ki suna son ki fiye da komai, kuma sun damu dake sosai Ummu, ki gane mana, har yaushe zaki bari mahaifiyar ki ta ci gaba da kukan rashin ki? Kina neman rahama kuwa?" Wasu sababbin hawaye ne suka gangaro mata, hakan yasa cike da tausayin kan ta ta faɗa jikin Mma tana rera wani sabon kukan, daddaɓata Mama ta dinga yi a tausashe tana faɗin" Kiyi haƙuri mana Ummu, kin san bana son kukan ki ko? Ki daina mana, ki je sau ɗaya ki rumgumi iyayen ki, ina tabbatar miki zasu rarrashe ki fiye dani." A hankali Mama ta ɓamɓare Ummi daga jikin ta, juyawa tayi za ta fita Aisha ta riƙe hannun ta tana girgiza kai tace" Mama, kin bami abu mafi daraja, bai kamata ki tafi haka ba." Kuwailat da ta ga Mama na kuka sosai ne tayi saurin matsawa kusan ta suka rumgumi juna, hakan ya sa Aisha fuskantar Ummu dake share hawaye tayi murmushi tace" Aunty, kinga maganata ko? Na faɗa miki ke ƴar uwata ce." Sai kawai ta sake fashexa da kuka ta jawo Aisha jikin ta suka rumgumi juna sosai suna kukan farin ciki dukan su. Muryar Abbu ce ta daki kunnuwan su ya furta" *Kuwailat*." Kasancewar Ummu ta ji Aisha ta kira ta da sunan ɗazu, hakan yasa ta ɗago kan ta da sauri haka ma Aisha, sai Kuwailat ƙarama da ita ma tayi saurin juyowa ta kalle shi, a hankali Abbu ya buɗe hannayen shi alamar ta zo gare shi, nauyi da kunya ya sa Ummu sunkuyar da kan ta, dan gaskiya a dai al'adar malal bahaushe bata taɓa gani ido da ido ba, sannan tana ganin ai tayi girman da ya kamata ma ace ta wuce haka. Cike da zumuɗi Abbu ya sake cewa "Zo mana, zo *ƴata*." Da bata yi niyyar zuwa ba saboda jin abun wani iri, amma sunan ƴata da ya faɗa yasa Ummu har da takawa a guje tana rushewa da sabon kuka kawai ta shige ƙrjin mahaifin ta luffff tana ci gaba da kuka. Wani irin sanyi ne mai kama da an cire maka wani dutsin dake cikin zuciyar ka ta ji, haka saida jikin ta ya amsa sakamakon haka, wani irin ƙamshi ne take ji a jikin mahaifin ta wanda duk da akwai na turare amma tana jin wani ƙamshi na daban wanda zata iya cewa kamar alaƙa ce ta janyo take jin hakan, hakan yasa ta gyara tsayuwa ta sake yin ruffff tana ƙara ƙamƙamo bayan mahaifin nata da shima dole tasa yake wasu irin hawaye masu tsada na tsantsar farin ciki, abu ɗaya kawai take jin yana faɗa "*Allah na gode maka, Allah na gode maka, ko yanzu ka ɗauki rayuwata na gode maka, tunda ka nuna min wannan ranar da na sake rumgume jaririyar ƴata da ta ɓata shekara talatin..." Duk da ya kai ƙarshe, amma da sauri Ummu ta ɗago tana girgiza kai tace "A'a, a'a *Abbu*, ba zaka tafi yanzu ba, gwara a ce ni na tafi." Sake danna kan ta yayi a ƙrjin ji yana girgiza mata kai, ba wanda bai musu hawaye ba a wurin har Sa'ad ma, sai Yaya Bilal da ya share hawaye yace "Ni ba za'a rumgume ni ba?" Ɗagowa Ummu tayi, hakan yasa tayi dariya saboda kallon fuskar Yaya Bilal da har da turo baki, a hankali ta taka gaban shi, irin rumgumar nan ce sukayi ta gefen jiki kawai tare da dafa kan ta yace "Allah ya miki albarka, mun jima muna kewar ki Kuwailat." Sakin ta yayi ta ƙarasa wajen aunty Fa'iza nan ma suka rumgume junan su, kafin Aisha ta nuna mata Sa'ad tace "Wannan shine Abbu, mijin ƙanwar ki." Dariya maganar Aisha ta bata tana kallon Sa'ad, shi kam cike da shaƙiyanci ya rusuna a mugun ladabce yace ma Ummu "Babbar Yaya uwa, ina kwana ? Da fatan ba zaki ce ban miki ba, dan gaskiya ba mai raba ni da ƴata a wannan shekarun da nayi ina rainon ta tsakani da Allah." Duk dariya aka yi, sai Aisha da ta harare shi ta turo baki, Yaya Bilal ne ya dubi Kuwailat da ita ma tayi dariya yace" Wannan ƴar ki ce ?" Kallon Kuwailat tayi sannan ta sada kai cike da kunya tace" E." Da hannu ya ma Kuwailat alamar ta zo, matsaxa tayi tana zuwa ta raɓa ta jikin shi yna faɗin" Ya kike? Ya sunan ki?" Murmushi Kuwailat tayi ta sunkuyar da kai, ta ji suna kiran Maman ta Kuwailay, dan haka ta rasa to ya za ta ce? Hakan yasa Yaya Bilal cike da tsokana faɗin" Ke, ni fa mijin ki ne, yau aka ɗaura mana aure ko? Tunda yau na san ki, dan haka faɗa min ?" Cikkn ƙyalƙyala dariya Kuwailat tace" Kuwailat." Da mamaki sukayi kallon kallo kafin Yaya Bilal yace "Kuwailat kuma? Da gaske sunan ta ne?" Ya tambaya yana kallon Ummu, jinjina kai tayi tana murmushi tace "... *Alhamdulillah.* [19/08 à 11:19] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *53* Jinjina kai tayi tana murmushi tace "E Abba, sunan ta Kuwailat, mahaifin ta ya saka mata sunan, saboda malamin da yake matuƙar sauraren wa'azin shi ya ce ba'a cika saka sunan Kuwailat ba, hasalima ni ban taɓa jin sunan ga wata ba sai akan ta." Da mamaki Yaya Bilal ya sake rumgume Kuwailat yana ɗago haɓarta suka kalli juna yace" Ikon Allah! Da aka haifi mahaifiyar ki Kuwailat aka saka mata, sai gashi da ta ɓata an canza mata wani sunan, amma abu na Allah sai ƴar ta taci sunan." Cikin tsokana kuma Yaya Bilal yace" To, yanzu dai ai kina sona ko? Dan fa ba zan bari wani ya kuma ƙwace min ke, kai kuma Mukhtar..." Ya faɗa yana kallon Abbu dake ta doka murmushi mai ban ƙayatarwa yau ga shi da duka ƴaƴan shi, shi kam me zai ce da ubangiji sai godiya, Yaya Bilal ɗorawa yayi da" Ka haƙura da wannan ka samo wata, ko ka ci gaba da zama da Nurriyar ka, wannan dai tawa ce." A nutse Abbu ya zura hannu ya kamo hannun Kuwailat, tallabo fuskar ta yayi da hannayen shi biyu suna fuskantar juna, murmushi suke ma junan su cikin nutsuwa yace" Kuwailat, zaki bar ma ƴata wannan sunan? Ko kina son shi na bar miki?" Da fara'a Kuwailat cike da kunya tace" Na bar wa Mamie." Jin daɗi yasa shi sumbatar goshin ta sannan ya sake kallon fuskar ta yace" Kina kama da Maman ki sosai, ita kuma tana kama da Mamata, kenan dukan ku da wa kuke kama?" Saida Kuwailat ta ɗan waina idanu tace" Mammie, ko?" Murmushi ya sake faɗaɗawa ya sake sumbatar goshin ta sannan ya kalle ta yace" Ni kuma fa?" Daga bakin ta yake so ya ji, dan haka da Kuwailat ta furta" Grandpa." Ya rumgume ta tsam a jikin shi kamar zai mayar da ita ciki, cikin jin daɗi yace" Na fi son wannan sunan, dan Yaya Bilal ya riga da ya ƙwace min *amaryata*." Dariya duk sukayi, Mama n ba gefe ta tsagaita kuka ta ɗan yi murmushi tace" Daga yau ba ni ba ƙawance dake, tunda kin ƙwacewa ƴaƴana majazensu." Nan la dariyar suka sake yi, sai Ummu da ta tausasa murya tana kallon Abbu tace" Abbu, ina *Mamie*." Da sauri Aisha tace" Oh ! Autyn ki? Ina ga suna nan ciki." Ta nuna ɗakin da tun shigowar su nan ta ga aunty Fa'iza ta fito. Murmushi Ummu tayi ta kai w Aisha duka a damtsen ta dake cike da nama tace" Bana son iskanci, kar ki tsokane ni mana bayan yanzu na san ina da ku." Cike da farin ciki Aisha ta riƙo ƙgun Ummi ta kama ta suka nufi ɗakin tana cewa" To na daina *aminiyata*, muje na fara yi wa ƙawata albishir." Da kallo Abbu ya bisu, sai ya ji hawaye sun sake saukowa a kumatun shi, yaran shi biyu mata da suka sha wahalar rayuwa, suka rabu tsawon shekaru ba tare da su ba, yau ga su ubangiji ya haɗa musu su dukan su, gashi har yana kallon su suna rumgume da juna suna nufa inda mahaifiyar su take, shi kam yana so ya ga farin cikin da zai bayyana a fuskar ta, yana so ya ga hawayen da zata zubar saboda ganin haka, duk da dai yasan bacci take mai nauyi, amma dole ta farka ko dan ciwon ta ya ƙare, haka ma wannan daskararren *ciwon* da ya jima *a zuciyar ta*. A nutse da kuma sallama suka shiga, kwance take tana bacci abun ta da ƙarin ruwa a hannun ta, ƙarasawa sukayi inda Aisha tana tsaye Ummu ta zauna bakin gado, cikin nutsuwa ta kama ɗaya hannun Maman nata tana kallon fuskar ta cike da so da ƙauna da kuma tausayawa, a hankali ta kai ɗaya hannun tana shafa goshinta da gashi ya ɗan sauko mata, ƙara matsa kan ta tayi ga fuskar ta cikin raɗa tace " *Mamie*." Shiru ba alamar za ta farka, hakan yasa Aisha zaunawa ta ɗaya ɓangaren ta ɗan daddaɓa Maman, girgiza mata kai Ummu tayi tace "A'a, ki barsu suyi baccin su, ai ba guduwa zanyi ba." Da raha Aisha tace "To naji shikenan, amma dai ya kamata ta farka, dan tana ganin ki ciwon nan zai ƙare mu koma gida." Murmushi kawai Ummu tayi tace "Da alama ƴar ƙiriniyar ƙanwa na samu." Dariya Aisha tayi ta turo baki tace "Kema aunty haka za ki faɗa? Abbu fa haka yake cewa." Da tabbaci Ummu tace "Ni ma da yanzu muka haɗu na faɗi haka, bare kuma Abbu da ya haife ki." Da sauri Aisha ta girgiza kai tace "Um um, ba Abbun mu, mijina nake nufi, Sa'ad." Da mamaki Ummu ta game fuska tace "Shine Abbun? Lallai daɗi miji." Dariya Aisha ta sake ƙyalƙyalewa da ita tace "Ba haka bane aunty, na saba ne wallahi, saboda lokacin da ya taimaka min ina kallon sa ne kamar uba, hakan yasa nake kiran shi Abbu, sai kuma ya zo ya ce yana so, to dake nima ina son abuna sai kawai mukayi aure, shine kuma na kasa daina kiran shi Abbu." Da fara'a da kuma irin gargaɗi Ummu tace" Eesha." Cike da kunya Aisha ta rufe idanu tana dariya tace" Na daina aunty, amma fa kema zaki zama kamar ni, saboda kinga ƙawata gaba take saka mutum sai sunyi hira ko baya so." Da mamaki Ummu ta kalli maman da Aisha ta nuna ta kirata ƙawa tace" Ƙawa kuma?" Jinjina mata kai tayi tace" Haka take kirana, ni ma kuma ta ce ai ƙawata ce, dole na saba mue ƙawance, saboda an ce uwa ta samu kusanci da ƴaƴan ta mata sosai." Jin daɗin hakan ya sa Ummu faɗaɗa murmushin ta ta sake kallon fuskar Maman, ita wai da ta rayu a gidan share ka zauna, suka rayu da yunwa, sai an fita an nemo za su ci, wata rana ma ba'a samun na cin, ta yi karatu a makaratun gwamnati saboda babu halin yin na kuɗi, yau ita ce ta wayi gari a wata sassauƙar safiyar *juma'a* da ta shiga tarihin ta a rayuwa, ta haɗu da uba wanda ya haife ta, sannan ga ta ga uwa wacce ita ce ta haife ta, ga kawun ta wanda a baya bata da shi, dan ƴan uwan margayi baban ta basa wani ɗaukar ta da mahimmanci kasancewar ba shi ya haife ta ba, Mama kuma fulanin jeji ne da ba wani babban ahali bane sannan ba mazauna kusa da ita ba, hakan yasa dai rayuwar ta ta daga ita sai Mama sai su Nabila, sai kuma mijin ta... *tsohon mijin ta* da ƴan uwan shi suka zama ƴan uwa gareta, da suna girmama ta da bata darajar ta, sai kuma abokanan arziƙin da ita ta ma kan ta su. Yau kuma, ita Ummu Kulsum ɗaya ce a ciki ahali *Ahlan*, ahalin da ko a mafarki bata taɓa hango wata alaƙa ta nesa tsakanin ta da su ba bare ta kusa, yau ita ma ƴa ce ga wannan gida... Murmushi ne ya suɓuce mata, jiya jiya ta rabu da mijin da take ganin shine gatan ta a duniyar nan, tayi kukan rashi Alhaji saboda yarda da tayi cewa shine makomar ta, gatan ta, rumfar da ta fake, ƙashin bayan da ya taimaka mata ta tsaya, abu alfaharin, masoyin ta sannan kuma uban ƴar ta. Haka ta kwaa tana faɗawa Ubangiji damuwar ta, tana rarrashin shi da yi masa kirari kan ya kawo mata mafita, sannan ta ƙara da bata son mafitar da gaggawa, alkairi kawai take nema, sai gashi safiya na wayewa ta samu iyayen ta, wanda ta san ba zata sake yin kukan maraici ba, ba zata sake tunani akan yadda za ta ci ko tasha ba, duk da dai ma Alhaji ya mata ihsani na rabuwa, dan kuwa milyan biyar ya bata cif tare da takardar da ta gani yaa shaida mata da yana sake tabbatar mata mallaka motar ta duk da dama shi ya siya mata, Alhamdulillah, ta ji daɗin kyautar dan akwai abinda ta hango zata yi da kuɗin, ta ji ina ma maza zasuyi koyi da shi, da mace ba ta tagayyara ba dan auren ta ya mutu, da ba zata yi wani abu ba wai shi *zawarci*, da zata fi ƙarfin komai har ubangiji ya sake damƙata hannun wanda ya zaɓa mata. Yadda tayi nisa a tunani ya sa har bata ji sanda Aisha take ci gaba da tayar da Maman ba, saida ta ji tana faɗin "Yawwa, Mamiena, tashi ga aunty Ummun ki na kawo miki, nayi yaƙi na ƙwato miki ita, kuma yanzu ta yarda ke mahaifiyar ta ce." Kallon Aisha tayi da irin yanayin nan na _"Oh Allah !" Sannan ta kalli Mamie da ta riƙe hannun Ummu gam tana shirin tashi da wani irin maɗaukakin zumuɗi tana faɗin "Aunty Ummu, da gaske ke ce? Ke ce a gabana?" Ɗan riƙe ta Ummu tayi tana fara'a tace "Ni ce, ni ce da kai na *Mamie*." Rarako idanu tayi alamar mamaki ta kalli Aisha tace "Mamie? Ƙawata kin ji me ta ce? Wai Mamie? Ni ce Maman ta?" Dukan su murmushi suke, kafin Ummu ta sake cewa "E mana, *Mamana*, ke fa mahaifiyata ce." Ƙurawa fuskar Ummu idanu tayi, hakan yasa Ummu sadda kan ta tana jin kunyar wasu abubuwa da suka faru tsakanin ta da Maman, daga kan sunan *aunty* da take kiran ta, zuwa kan hirarrakin da suke yi wasu lokuta a grp ko a pc, Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! Ita ga gwana iyayya ƴar masani, komai da ruwan ta komai ta sani, ashe duk hirar nan da take yi wacce ta shafi mata da maza duk Maman ta na jin ta? Ita kam ya za ta yi? Mama Nuriyya kuma ko ko a kai wannan tunani bai zo mata ba, to ita bata ɗauki hakan a wani abu ba, hasalima alfahari za ta yi da ƴar ta ta kasance mai sani dayawa akan abin da ya shafi mace da namiji, kuma take da sanin maganin wasu matsaloli da dama, ita kawai tunanin ta wai jaririyar da aka ɗauke mata a cikin tsumma, ita ce zaune haka gaban ta? Tayi tsayi sosai, tayi jajir da ita, tayi kyau, fatar ta a kwance alamar hankalin ta kwance a gidan mijin ta, ga haƙoran makka dake nuna ta sauke farali, ita wannan abu ina za ta saka kan ta dan farin ciki? Daga wannan kallon kuma sai ta fashe da kuka, hakan yasa suka rumgume juna suna kukan tare Aisha na rarrashin su. *A* ƙanƙanin lokaci labarin samun jikanyar margayi Saheeb Ahlan, ga makusanta wannan ahali tuni suka ga fuskar Ummu, dan zumuɗi ya sa suka kasa haƙura, take wasu kira suke ta WhatsApp kuma hoto mai motsi dan su ga fuskar da aka ce tana kama da Hajia sak. Ita kan ta Hajia saida ta zuba ruwa tiles ta sha dan murna, ta gode Allah, tayi murna tayi juyi duk da tsufan ta, haka kuma Abbu ya kira ta ta ɗauka aka bata Ummu suka dinga kuka da murnan ganin juna, abu ɗaya ya sa farin cikin su raguwa sanda Hajia take ce ma Yaya Bilal "Kar dai ku kuskyra ku dawo min nan ba da ita ba, ku nema mata izini wajen mijin ta, ina so na gan ta." Take Ummu da Mama da har lokacin take nan suka kalli juna, shiru ɗakin ya ɗauka kfin Ummu ta kalli Hajia ta wayar tace "Granny, ba zan iya zuwa yanzu ba, amma za ki ganni bayan wata uku in sha Allah." Da mamaki Hajia ta kalle ta tace "Bayan wata uku kuma? Me yasa sai bayan wata ukun?" Saida ta sauke ajiyar zuciya ta ɗan kawar da duban ta daga fuskar Hajia sannan tace "Saboda ina *idda*." Da Mamie da Hajia da kuma Yaya Bilal ne suka maimaita kalmar "Idda?" A tare, sai Aisha da tace "Aunty, wai kun rabu da Abban Kuwailat ne?" Saida ta sauke ajiyar zuciya sosai kafin ta kalli Hajia tace "Zamuyi magana daga baya, labarin mai tsawo ne." Dan ta kawar da hankulan su sai tace ma Hajia "Ba wannan ba yanzu, Granny ya haƙurin rashin jigon ahalinmu?" Ai ko dubarar tayi aiki dan take aka koma jimamin abinda ya faru na rashin Alhaji da aka yi. Ganin jikin Mama kam yayi sauƙi da gaske har ma an sallame su saboda bata son zaman lokacin da zasu tafi Abbu ya kalli Mama yace" Hajia, dan Allah muna neman wata alfarma?" Da kulawa Mama tace "Ba damuwa, ku faɗi duk abinda kuke so." A nutse yana kallon Ummu yace "Muna so ne dama idan Kuwailat ta kamalla iddar ta taje mana ziyara?" Shiru Mama tay tana nazarin wannan kawaici da aka mata, kafin ta kalle shi tana murmushi tace "Alhaji, na kawo muku Ummu ne yau ba dan na koma da ita ba, daga jiya zuwa yau na fahimci raɗaɗin da kuke ciki na rashin Ummu, na san ba zamuyi nesa da juna ba, dan haka na kawota ne dan ta zauna da ku matsayin ku na iyayen ta." Da sauri Abbu ya girgiza kai dan shi sai ya ga kamar irin tayi zuciya ne ya kawo musu ƴar su kenan, dan haka yace "A'a Hajia, ba zamu taɓa raba ki da Kuwailat ba, ƴar ki ce, a ƙalla mu dai yanzu mun samu nutsuwar zuci tunda mun san mu muka haife ta, amma Kuwailat, ta ki ce ai." Ummu ma dake sauraren su kallon Mama tayi tace "E Mama, ba zamu rabu da juna ba, ke Mamata ce, ina so na zauna tare da su, amma ba haka kwatsam ba, idan na gma idda zan je na kwana tare da su." Cike da gamsuwa Yaya Bilal yace "Hakane, hkan yayi, Allah nuna mana ranar." Sai kuma ya kalli Kuwailat ƙarama yace "To amma, za dai a barmu mu tafi da Kuwailat ƙarama ko?" Kallon Kuwailat ɗin tayi kafin tace "Abbana, ba zan iya cewa E ko a'a ba, saboda tana hannun mahaifin ta ne, kuma yanzu na hutun makaranta, idan zata iya neman izinin shi zan fi kowa farin cikin aje wa da Hajia da ita." Aunty Fa'iza dake manne da Kuwailat ɗin ce tace "Ga Eesha ai tasan gidan, sai muje tare da ita mu nemi izinin nashi, dan gaskiya ina so mu tafi da ita." Abbu dake zaune bakin gado Mama Nuriyya na riƙe da hannun shi ne yace "Bai san mu ba, bamu san shi ba, kamata yayi muje dukanmu sai mu nemi izinin nashi." Cike da gamsuwa Mama ta jinjina kai tace "Hakan ya yi, sai dai Dan Allah ina mai ƙara baku haƙuri akan auren Ummu ɗin, har ma da sakin nata, dan ji nake kamar ni ce silar komai." Lokacin da Abbu ke kallon Maman yana nuna mata ba fa komai, ko gaban su take ai haka zai iya faruwa, a lokacin Kuwailat ta matsa kusan Maman nata ta faɗa jikin ta kamar za ta yi kuka cikin raɗa tace" Mamie, me yasa Abba ya sake ki? Yanzu shikenan ba zaki sake zuwa gidan mu ba? Ni kaɗai zan yi ta zama can?" Tausayin yarinyar ya sa Ummu rumgume ta tana rintse idanu ita ma cikin raɗa tace" Karki damu Kuwailat, komai da kika ga ya faru haka Allah ya tsara mana tun kafin wanzuwar mu, kar ki saka damuwar rashina a gidan mahaifin ki, ya riga da ya yanke hukunci cikin hushi ba yadda na iya, amma ko yanzu ya ce na koma ɗakina zan koma ba tare da jayayya, dan ba zaniya rayuwar farin ciki ba tare da ke da shi ba, amma dai ki sa a ran ki Maman ki tana tare da ke, Allah ba zai barki kiyi maraicin rashina ba." Ƙara ƙamƙame ta Kuwailat tayi tana kuka cike da tausayi, Mama Nuriyya na kallon su ita ma kamar ta musu hawayen, dan ita tsarin nan na brin Ummu a nan bai mata ba gaskiya, tana so ƴar ta ta kasance tare da ita, su shaƙu da juna kamar yadda sukayi da Eesha, duk da ta san zaman ba mai jimawa bane, dan tana samun miji ita ma aure zata yi, amma dai ko yaya ai zasu zauna, sai dai ba zata faɗawa kowa abinda ke ran ta ba dan kar a kalle ta marar godiyar Allah, a tafi a haka ma dai. ********************* Hankalin Aliyu bai gama tashi ba da yarda ko mahaifin shi tsufa ya fara gigita shi saida ya zo shiga falon Hajia babba ya ji abinda ke faru, ya tara iyayen su duka wai har da Hajia babba yana tambayar a cikin su idan har akwai wacce ta san tana da sauran buƙatuwa ga namiji har yanzu? To ta faɗa mishi shi kuma ya sawaƙe mata, dan baya son shiga haƙƙin kowace a cikin su, ba kuma ya so wata matar ta kai shi wuta, dan haka ya tsare su da wannan tambaya, inda su kuma suka shiga zare idanu suna mamakin shi, to su wace buƙata ce da su saboda Allah akan wannan lamari? Har gwara ma Hajia Atika da ta ji da shekaru goma zuwa takwas da suka wuce ne baya yayi wannan tambayar, to shakka babu da ta amsa mishi sai dai ya ga butulcin ta, amma zuwa yanzu ta haƙura kam ba ta jin wani abu mai kama da hana bawa bacci ita dai, dan haka tana nan har sai tayi takabar sa daga nan a bata nata kason bayan ta karɓi na yaran ta ma. Lura da yada suke kallon shi kamar wanda ya sha giya yasa yace musu "Kar kuyi mamakina, yanzu haka Ummu bata gidan nan, tun jiya na sake ta saki ɗaya, saboda na fahimci ci gaba da riƙeta a gidan nan zai azabtar da ita, tunda ita tana da buƙata, shiyasa kuka ji na muku wannan tambayar, amma shirun da kuka yi ya nuna kuna son ci gaba da zama dani, dan haka Allah ya muku albarka." Wani irin masifaffen daɗi ne ya kashe Hajia Atika da Hajia Asiya, musamman da suka ji ya ambaci suna san ci gaba da zama da shi, da kuma albarkar da ya saka musu, sai suke tunanin ko dai Ummu ta zo mishi da alfasha ne a gida? Shiyasa har haka ta faru? Hajia Atika a ranta ta ayyana "Allah raka taki gona." Inda Hajia babba kuma saida ta zabura ta kalli ɓangaren da yake cike da rashin jin daɗi tace "Subhanallah! Alhaji wannan wane irin ɗanyen hukunci ne? A shekaru 74 na rayuwar ka 13 da yarinyar nan ka yi su, me yasa zaka ɗauki wannan matakin?" Kallon su Hajia Atika yayi ya musu alamar su tafi, hakan ya baƙanta ran su sosai har Hajia Asiya na raya _"Dama da tsohuwar nan ka haɗa ka tura waje."_ Sun ji haushi sosai dan sun san labarin abinda ya faru zai bata, gashi ya kora su ba zasu ji ba, to a ina zasu samu labarin yanzu? Bayan na sakin ma basu sani ba tun jiya sai yanzu da shi yake faɗa. *Jin* suna tahowa ya sa Aliyu ɓuya dan yana nan har lokacin, yana jin irin baƙaƙen maganganun da suke ta faɗa akan mahaifin nashi da Ummu har sukayi nisa, wani sabon takaici ne ya kama shi, dan ko ba komai ya sa mahaifin su yayi rashin mata ta gari, tabbas Hajia Asiya ita ta haife shi, amma ba zai ce tana kan daidai ba gaskiya. A ƙalla dai da Ummu tana nan zata zama abokiyar hirar shi, abokiyar dariyar shi ko kukan shi, zai ci mai kyau da daɗi, zai samu nutsuwa da hutu, ba zai yi kaffara ba idan ya ce zama da Ummu ne yasa mahaifin shi ya rage yawan ciwukan da a baya kafin auren ta yake yi. Dawowa ya sake yi ƙofar ɗakin, murya ƙasa sosai ya ji Alhaji na faɗin "Hajia, kin san me yasa na auri Ummu Kulsum?" Girgiza masa kai tayi alamar a'a, ɗorawa yayi da "Akwai ranar da wani likita ya bani shawara kan hqwan jinin da nake fama da shi, ya faɗa min dole na dinga samun hutu, sannan na samu wanda zai dinga kula da abincina, ya faɗa min na dinga fita ƙasashen waje tare da wani ko wata wanda na fi so ko son gani a kusa dani, hakan zai taimaka min sosai, dan hawan jinina yawan damuwa ne da rashin hutu da kuma rashin tsari ga abinci, a wautata sai naga bari na auri ƙaramar yarinya, dan gaskiya ba zan iya yawan tafiye tafiye ba tunda iyali gare ni, bayan na yanke wannan shawarar ne na ga Ummu, duk da rashin amincewa da iyayen ga sukayi a farko, daga ƙarshe dai sun amince sun bani ita." A nutse ya ci gaba da faɗin" Hajia, bayan aurena da Ummu na samu canji sosai, kiyi haƙuri ko da kin ji ba daɗi, amma gaskiyata nake faɗa miki, kinga tana min wauta, tana min shirme, tana min hauka, tana min yarinta, tana min ƙiriniya, tana...ta dai ɗaukeni tamkar abokin rayuwar ta, sannan ga ƙoƙarin iya girki da kula ƙoƙarin dafa min duk abinda likita ya ban shawarar na dinga ci, a taƙaice ta dai zama maganin ciwona, idan ina tare da ita bana zama shiru, dan ko abu zata yi wandq nake ganin bai kamata ba na hanata sai tayi min kukan shagwaɓa, Ummu fa ko fita za ta yi na ce a'a sai tayi hawaye, wannan birgeni yake, saboda a gurina wani irin nishaɗi ne na musamman da tun a shekarun ƙuruciyata dake na gan shi, sai dai Hajia Luba, Ummu mace ce mai sha'awa, ba wai irin masu tsananin sha'awa da ake kira harijai ba, a'a, kawai dai ni ne da jikina yayi rauni har ta kai ga bata samun yadda take so, tun tana haƙuri har ta gagara ta sanar wa da Alhaji Sagir da tunanin zai iya yin wani abu a kai..." Jin yayi shiru na sakanni da sauri Aliyu ya bar bakin ƙofar yana istigfarin laɓen da yayi akan hirar da bata shafe shi ba kuma ba'a kasa da shi ba, sai dai da kyakyawar niyya yayi da tunanin idan ya ji bakin zaren sai yayi ƙoƙarin sake haɗa wannan dangantakar, sai dai zywa yanzu ya fahimci komai, ya gane abinda mahaifin nashi yayi shine daidai, kuma wata irin ƙaunar mahaifin shi da tausayin shi suka kama shi, ƙwarai bai da aure bare ya san ya abun yake, kuma Jabir ya fi shi sani sosai akan abinda ya shafi zamantakewar aure, dan ya karanci fanni sosai kuma yanzu haka yana da burin zama a gaban babban malami Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa dan sake sanin wasu bubuwan da suka shafi zamantakewa, amma a nashi sanin abinda Abba yayi ya kyauta, dan ci gaba da zaman cutuwa ce da zalinci, dan haka ya koma ɗakin shi yana ta yi mishi addu'ar samun rahamar ubangiji akan wannan namijin ƙoƙarin da ya yi, dan rabuwa da wanda kake so ba tare da kuma wani ya saka ka ba babban jarumta ce, sannan wani abu da zai iya sake cewa akan haka shine mahaifin shi *so na gaskiya* yake wa Ummu, tunda ya sadaukar da farin cikin da yake samu a zaman shi da ita saboda nata kwanciyar hankalin, wannan ko ai ita ce *sadaukarwa* ta gaskiya. *Alhamdulillah.* [21/08 à 09:24] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *54* *Lokacin* da abubuwa ke ta faruwa anan, Jabir da mahaifin shi sun sauka lafiya gurin su Anna, sun samu tarba yadda basu yi tsammani ba, sai dai kuma Jabir ya lura da yadda mahaifin shi kunyar abubuwan da suka faru a baya tasa bai haɗa idanu da Alka da kuma Anna ba, haka suma sun kasa haɗa idanu da shi kuma har da Jabir musamman ma Anna, suna cikin matsananciyar yunwa duba da yaron da suka ƙi tausaya ma ne yau gaban su cikin kamala da haiba irin na babban mutum. Haka dai aka nemi juna gafara da fatan a manta duk abinda ya faru a baya, dan ƙara rikitasu da nuna musu ya manta komai Jabir ya zub musu tilin tsarabar da a hanya ma ya yi siyayyar. Bai manta da matar Kakan nashi ba wato Mardiyya, dan haka baiyi ƙasa a guiwa ba wajen son ya ganta, sai Anna ta faɗa mishi ai tana gidan ƙanwar ta Nuriyya da sirikin ta ya rasu, dake ita Nuriyya bata nan kuma danginsu na zuwa yi musu ta'aziyya, sai ita Mardiyya ta je zata yi kwana biyu kafin su dawo ita ma sai ta dawo, duk da ya ji abinda ya kai su ɗin bai yi wani tsananta ba bare har ya gano wani abu, sai dai alkairin da matar ta mishi wani zuwa da yayi wanda ko kakar shi da ya zo wurin ta bata mishi ba, ta sakar masa fuska, bata yarda ya zauna da yunwa ba, sannan da zai wuce Niamey ta mishi tsaraba sosai wanda shi a lokacin yarintar shi tasa ya ɗauke ta a abu mafi daraja, dan haka ba zai manta da ita ba. Take ya faɗawa Anna a haɗa shi da wanda ya san gidan ya same ta can, baya so sai ta zo ta same shi, gashi kuma kwana biyu zasu yi su wuce Niamey, ba wanda ya mishi musu haka suka mishi kwatance kuma ya ce ya gane sosai, dan da ƴan mata suka so haɗa shi shi kuma baya so dan haka ya zaɓi tafiya shi kaɗai. Dake rasuwar nan da aka yi tasa ana barin shiga babu ƙwaƙwaran tsaro, buɗe mishi ƙofa sukayi ya wuce shi da motar shi bayan sun gaisa, da kuma jagorancin wata mai aiki ya isa har falon Hajia inda nan Mardiyya take tare da ita. Akwai mutane sosai a falon, amma inda aka nuna mishi Mardiyya tana zaune daga ita sai Hajia da wata tsohuwa ce a ɗan corridor, dan haka ya shiga takawa a nutse har ya isa wurin, yana zuwa ya durƙusa yana gaishe su, salayyar dake kusa da Aunty Mardiyya ta warware ta shinfiɗa ta ce masa yaa zauna, duk da kuwa dukan su kallon son sanin ina suka san shi suke? Musamman aunty Mardiyya da yake mata fuskar Aghali, wato autan Anna wanda aka ce yana kma da Fatime maman Jabir, dan ita kafin auren ta da Alka Fatime ta rasu, dan haka ba ta san ta ba gaskiya. A nutse ya zauna kan shi a ƙasa kafin ya ɗan ɗago ya kalli aunty Mardiyya da shi ba zai iya manta ta ba yace "Mammie, na san baki shaida ni ba, ni ne Jabir, ɗan margayiya Fatime." La'ilaha ilallah ! Wani irin farin ciki da ta nuna a fuskar ta mai tafe da cikar ƙwalla a idanun ta ya saka shi tsura mata idanu, duk da dai har da kunya a tare da Anna, amma shi bai ga haka ba gaskiya, wani irin farin ciki ne ya bayyana gare ta tana faɗin "Lahhhh ! Jabir ? Kai ne haka? Jabir, yaushe ka zo?" Murmushi yayi mai birgew cikin taushin murya yace "Yau muka zo Mammie tare da Abba, na tambaya aka ce ba ku nan, ni kuma ba zan iya jira sai kun zo ba, shiyasa na zo." Cike da ƙaunar yaron wanda haka kawai take jin ta ta matso ta ɗora hannun ta na dama a kan shi tana shafawa tana faɗin "Allah sarki Jabir, baka manta da ni ashe? Gaskiya na ji daɗi sosai da ziyarar nan taka, ya kake Jabir? An sha karatu?" Saida suka sake gaisawa kafin ta nunawa su Hajia dake kallon su tace "Hajia, ɗan Fatime ne babbar ƴar mijina wacce ta rasu bayan haihuwar sa, ya jima rabon shi da nan sosa, shine sai yau suka zo." Cike da dattijantaka Hajia ta miƙa mishi hannun ta da murmushi, da gimmawa Jabir ya miƙo mata nashi hannun, ɗan jinjinawa tayi tana faɗin" Jabir, Allah ya maka albarka, gashi kuma kai ka baro Maraɗi yaran nawa kuma duka suna can wani muhimmin abu." Cikin nutsuwa yace" Ameen Ya Allah, nagode sosai, Allah ya ƙara muku lafiya da nisan kwana, Allah kuma ya jiƙan Alhaji da rahama." Ya ɗan jima suna hira da aunty Mardiyya kafin ya yi haramar tafiya yana faɗin" Tsarabar ku tana gida, naga rashin dacewar zuwa muku da ita nan, sai idan kun koma in sha Allah." Da mamaki aunty Mardiyya tace" Kenan ba zan same ku ba? Ina so mu sake zama Jabir muyi hira sosai." Ya ji daɗin haka, dan haka ma yace" Ni kaina ina son haka aunty, dan akwai abinda nake so dangina su yi min, to kinsan Anna yadda take, bata sakar min jiki yadda zamu tattauna ba." Cike da bawa maganar sa mahimmanci tace" Na sani Jabir, ka ci gaba da haƙuri kai dai, ni kaina ina so ne muyi hirar bayan rabuwa, musamman akan ɓatan ka da aka dinga jita-jita, ina so naji gaskiyar lamarin, amma dai ba zaku koma ba har sai na zo ko?" Jinjina kai yyi yana murmushi yace" Zan yi ƙoƙarin ko da kwana ɗaya ne mu ƙara har ku dawo." Da farin ciki ta amsa da" Yawwa, nagode sosai Jabir, in sha Allah sai na zo." Su Hajia ya kalla ya musu sai anjima, cike da tsokana Hajia da son mutumta baƙon na Mardiyya tace" To Jabir, sai kwana biyu, duk da dai naji kafi son kakar ka Mardiyya akan ni Maman ka, dan ita kaɗai ka kawowa tsaraba." Dariya ce ta kubce mishi saboda murna ya rusuna yace" Tsaraba ba zata haɗani da Mamana ba, in sha Allah zan sake dawowa na kawo muku taku tsarabar da ta fi ta kowa." Dariya Hajia tayi tace" To Allah ya yarda, a ƙalla dai ko baka dawo dan kawo min tsaraba ba, ka dawo dan na sake ganin kamilalliya kuma kyakyawar fuskar ka." Murmushi yayi sosai cikin taushin murya yace" Nagode, kamar yadda zan iya dawowa ko dan na sake ganin ainahin dattijanka." Duk dariya sukayi kamar waɗanda suka jima da sanin juna, saida aunty Mardiyya ta raka shi har inda ya aje mota suna ci gaba da sai anjima kafin ta juyo shi kuma ya bar harabar gidan. *WASHE GARI* Tunda ya kira Alhaji bai ɗaga ba ya koma kiran Aliyu, duk da ya san ko lokacin da yake nan suna barin wayoyin su gida ne idan zasu tafi masallaci, amma kuma duba da lokacin da suke dawowa yayi sai ya sake kira, kira uku ya ma Aliyu ba'a ɗaga ba, dake yana da riƙo da aƙidar idan ka kira mutum sau uku bai amsa ba to kar ka sake kira, kamar dai yadda aka ce ka koma idan kayi sallama gidan mutum sau uku ba'a amsa maka ba. Yana da yaƙinin idan Aliyu ya gama uzurin da ya hana shi ɗagawa zai kira shi, duk da yafi tunanin kawai ba ya kusa ne, dan ko me yake yi idan ya kira ko bai ɗaga ba to zai tura masa da gajeran saƙon *zan kira ka*, dan haka suka ci gaba da zaga dangi shi da Abban shi ana ta nuna musu Jabir dai, wanda kowa yayi watsi da shi saboda dalili marar ƙarfi. *Bayan* ya shigo ɗakin ya tarar da kiran Jabir uku, maida mishi kira yayi nan take yana zama bakin gado, ba jimawa Jabir ya ɗaga, daga ɓangaren Aliyu ya fara faɗin "Alaramma barka, ka kira ina waje." A sanyaye Jabir kamar wanda ke rowar muryar sa yace "Umm! Me kake yi?" Cike da takaici Aliyu yace "Kana min magana kamar kana yi da budurwar ka, to ba abinda nake, me yasa ka kira ni kai?" Nauyayyar ajiyar zuciya Jabir ya sauke, sai ya ji kamar Aliyu faɗa yake masa ko wani abu mai kma da hka, dan haka kawai yace "Ba komai, sai anjima." Aliyu ma da ya fahimci me Jabir ɗin ke nufi da abinda yake shirin aikatawa, wato ya yi hushi kenan? Waina idanu yayi da sauri yace "Dakata." Ɗan saurarawa Jabir yayi, sannan ne Aliyu ya shiga jero numfashi, abinda ya ji ne yake ta masa yawo a tunani, gashi kuma ba yadda zai yi, shiyasa duk ranshi ke jagule yake jin haushin kowa da komai, amma dake basa samun saɓanin dake wuce awanni ma da Jabir ɗin yasa yace "Ina jin ka, ya Abba?" Take Jabir ya fahimci akwai damuwa, dan dama da ka ji ɓacin ran Aliyu musamman baka san hawa ko sauka ba, to tabbas wani abu ya ɓata masa rai ko yana cikin tunanin wani abu dake caza masa kai, saɓanin shi da ya ƙware wajen shanye damuwar sa, zaka iya msa laifi sau ɗaya ya maka uziri, sau biyu ma haka, to idan kayi na uku ne zai iya maka magana shima a nutse, amma idan ka maimata bayan haka? To fa nan zakuyi ba daɗi. Cike da kulawa Jabir yace da shi "Me yake damun ka?" Shiru Aliyu yayi yana lumshe idanu, sai kuma ya saki murmushi saboda jin daɗin yadda Jabir ya fahimta duk da bai ga fuskar shi ko yanayin shi ba sannan yace "Maganar tana da mahimmanci, kuma akwai buƙatar mu zauna sosai ni da kai, dan haka bai kamata muyi ta a waya ba, zan jira har ka dawo." Jabir mutul ne mai sauƙin kai da fahimtar mutane da kuma rashin son shiga rayuwar wasu, duk da ya tabbatar wa kan shi akwai matsalar, amma kuma tunda ga shi yadda ya ce, sai kawai ya masa uzuri yace" Shikenan, Allah ya datar damu." A ake Aliyu ya amsa da" Ameen, ya Abba ? Ya kuma su Anna da kowa da kowa?" A nutse shima yace" Kowa lafiya lau, ya Abbana yake? Na kira ba'a ɗaga ba, da fatan suna lafiya?" Saida Aliyu ya feso iska daga baki kafin yace" Lafiya lau Abba, yanzu ma na baro shi falon Hajia babba." Cikin jin daɗi Jabir yace" Na ji daɗi, zan sake kiran su zuwa anjima." Cike da tsokana Aliyu ya gyara zama yace" To ya? Anna bata maka mata a can ba? Ko dai ka rantse sai ƴar garinmu za ka aura?" A daƙile Jabir yace" Idan na nema ka hana ni, sai anjima malam." Dariya Aliyu yayi yace" Da alama ma ka samu buzuwa acan ko? Dan naga daga yin maganar kana neman kashe min waya." Cike a gargaɗi Jabir yace" Aliyu." Inda Aliyu ya amsa da tsokana" Na'am, Jabir." Kafin kuma Jabir yace wani abu sai yace" To kaga, idan kai baka so ni ka sama min wata kyakyawar buzuwa, ka dai gane kyawun da nake nufi ai?" Shiru Jabir yayi, kyakyawa da Aliyu yace yana nufin, yar babban gida, mai tarbiyya ƴar dattawa, wannan shine burin su akan mace, idan ubangiji ya basu kyakyawar zasu karɓa suyi godiya, amma dai addini suka fara sakawa a gaba. Sallama sukayi daga haka inda Aliyu ya tashi ya shiga wanka dan ya shirya ya fita sabgar shi da ta Jabir da ya bar mishi sallahun dubawa kafin ya zo,komai Alhamdulillah komai na tafiya daidai sai san barka. ******************** A ɗan lokacin da ya gabata na rayuwar ta bata jin akwai wani wuni da ta gabatar da ya kai mata wannan da take gudanar da shi da iyayen ta yi mata daɗi, Abbun ta, Mamien ta, sun saka ta tsakiya suna ta shafar jikin ta, Yaya Bilal kuma da aunty Fa'iza na gefen su zaune suna ta hira cikin nishaɗi, sai Aisha da har kan ƙafafun Ummu ta zauna ta rumgume wai ita ba zata yarda a barta baya ba, daga ƙarshe kuma da Sa'ad ya zo tare da yaran su duka da suka sauko daga islamiyya sai ta samu wata kujerar ta zauna. Fahad da ƙarara Abbu Mukhtar ya fahimci kamar abun ya fi yi masa daɗi, dan wannan kiran da yayi yanzu haka suna kallon juna shi da Abbun na biyar ne, kuma Ummu yake cewa a bashi dan Allah ya sake ganin ta, ashe dai ƴar sa ce ita? Ashe ƴar sa ce Ummu? Ashe duk shekarun da sukayi da Nabila Ummu jinin sa ce bai sani ba? Sai kuma wata kalma da ya taɓa faɗa akan Ummun lokacin da Nabila ta zo da maganar za ta bata magani ta ba mijin ta, yana jin kunyar hakan, musamman da sukayi magana da Nabila ma akan gano Ummun da aka yi, har saida ta tuna masa ita ma da cewa "Ka gani ko? Amma kai ga ɗan duniya har da faɗin wai a ara maka ita na d..." Bai barta ta ƙarasa faɗa ba ya shiga bata haƙuri da alfarmar ta manta da wannan maganar, shi kanshi yana jin kunya da kuma takaicin kan sa. Bayan Abbu ya ba wa Ummu wayar sun sake gaisawa ne Ummu ke faɗin" *Abbuna*, kafin na san ka haushin ka nake ji saboda soyayyar ka da kuke yi da ƙanwata, amma yanzu, sai..." Katseta yayi da sauri yana dariya yace" Yanzu sai nake birge ki ko?" Dariya tayi ita ma tace" Ba haka ba, sai dai nake ji a jikina dama kun haɗu ne kawai dan ku haɗamu, *RUBUTACCIYA* tasa sai abinda ya faru ya faru kafin zamu haɗu." Jinjina kai Fahad yayi cike da gamsuwa yace" Hakane, dan ubangiji da ya bayyana mana ke tun a waccen lokacin, da aure na so Nabila tun haɗuwar mu, amma sai sheɗan ya rinjaye mu muka shiga wata rayuwa ta daban, da ubangiji ya so mu haɗu tun lokacin, da iyaye sun shiga maganar mu da gaggawa, kinga kuma ta haka za'a gano abinda aka gano yanzu." Murmushi Ummu tayi tace" Hakane, ina alfahari da kai Abbuna." Kafin ya bata amsa Yaya Bilal ya taɓe baki yace" Wai Fahad take cewa Abbu bayan tsaran ta ne, shekarar ku ɗaya fa." Fahad da ya ga basu ganin juna shi ma taɓe baki yayi yace" Haka kawai mutum sai ya ji yana baƙin ciki da ci gaban ka, kai ma dake Yayan Alhajin (Abbu Mukhtar) ta kira ka Abbu bare ni dake ƙane gare shi mafi soyuwa." A kausashe Yaya Bilal yace" Ina jin ka, ina jin me kake faɗa marar kunya kawai." Da sauri Fahad ya ɗaga ma Ummu hannu yace" Sai anjima ƴata ta gaban goshina, zamu sake waya idan kowa yayi bacci." Ummu dai dariya take ita da sauran mutanen ɗakin har da shi kan shi Yaya Bilal ɗin, Abbu Mukhtar kuma shi tunanin Hajia ne ma ya zo masa a rai da ta fara ikrarin za ta zo garin nan saboda ta ba Mama haƙuri da kan ta, dan lokacin da sukayi wayar kuka take na tuna abinda ya faru, ta ci mutumcin Nabila, ta tozarta ta, ta ƙyamace ta tare da yi mata korar kare. Ashe yarinyar nan ƙanwa ce ga jikanyar ta, ashe yarinyar da take ganin fitsararriya ce marar tarbiyyar da iyayen ta suka kasa riƙe ta, ashe mahaifiyar ta ita ta riƙe musu ƴar su har ta aurar da ita? Ƙwarai ta yarda da Fahad ya ce iyayen ta dattawa ne, kuma suna ƙoƙarin su kan tarbiyyar ta, kawai dai hali ne na ƴaƴan zamani da aka ce ka haife shi baka haifi halin shi ba, gashi yanzu tana jin kunyar kallon mahaifiyar Nabila, uwa uba kuma Nabilan da take ganin ba zata sake iya haɗa idanu da ita ba har abada. Dan haka take so ta zo, duk da tana takaba, amma ai abun nan da ya taso muhimmi ne da zai iya fitar da kai waje, dan haka gobe za ta taso ta zo, idan har ta samu yafiyar su to zata sake jadadda neman auren Nabila g Fahad, idan ta samu amincexar su ba zata bar nan ba sai an saka musu rana da yardar Allah, hakan da suka tattauna ya sa Abbu rusa maganar tafiya gidan mijin Ummu dan nemo izinin tafiya da Kuwailat, sun jira har sai Hajia ta zo sai ta su tafi ko ina tare. Dare na yi Ummu ta ce zasu koma gida ita da Kuwailat Mama ta nemi fashewa da kuka, dan haka hankali tashe Ummu ta kama hannun ta tace "A'a Mamie, shikenan fa tunda ba kya so, na fasa tafiyar, anan zamu kwana, shikenan?" Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi sannan tace "Nagode aunty, ina so ne na kwana tare da ke na yau kawai." Murmushi Ummu tayi tace "Mamie, ba aunty ba dan Allah, Ummu Kulsum." Maƙale kafaɗa tayi tace "Um um, ban da kunya aka ce miki da zan dinga faɗin sunan ki kuma gaban ki? Ki barni da aunty kawai." Murmushi Ummu tayi tace "Shikenan, tunda hakane nima zan ci gaba da kiran aunty kawai." Da yanayin raha Mamie din tace "E ba zan ji haushi ba, ki kirani aunty ɗin, na fi son haka ai." Cike da farin ciki suka rumgume junan su, tsawon dare, ko na ce raba dare sukayi a falon nan suna hira, yadda Ummu ta fasa tafiya haka Aisha ta buga kai ga ƙasa ta cewa Sa'ad ba inda zata je tana ganin Maman ta da ƴar uwar ta, ba kuma yadda bai yi ba dan su tafi amma ta ƙi, sai da dai Yaya Bilal yace la Sa'ad ɗin "Wai Sa'adu me zata maka a gidan da ba zaka ƙyale ta nan ba? Ba fa gutsirar maka mata zamiyi ba." Shafa kai yayi yana satar kallon Aisha yace "Kawu, kai dai ka barni da ita kawai, Allah kaɗai yasan wahalar da ƴar tahlikar nan take bani idan dare yayi, ka san ba bacci take yi ba saboda mugayen mafarkai?" Taɓe baki Aisha tayi tana murmushi tace "A dai dinga jin tsoron Allah wallahi." Haka dai cikin raha y tattara yaran suka tafi Aisha ta yi zaman ta, su huɗu suka fara kwantawa kan gadon, Mamie, Ummu, Kuwailat da kuma Aisha, sai kuwa ga Abbu ya shigo, Mamie ce ta fara tashi zaune dan tasan me yake nufi, amma ganin gadon ba zai ishe su ba sai ya zauna gefe yana kallon su, lura da hakan Ummu ta tashi zaune ta tankwashe ƙafafu, haka yasa dukan su sukayi yadda tayi sannan suka ce Abbu ya zo ya zauna, da farin ciki kuwa ya zauna yana fuskantar Ummu, duk da dai tana jin kunya da yin wani abu, amma da ta fahimci su wayayyu ne da babu ruwan su, har ta kai bata jin nauyi ma yanzu, dan haka da Abbu ya tambaye ta ya rayuwar ta kafin yau? A hankali ta shiga sanar da su tun daga ƙuruciya har girman ta da kuma rayuwar auren ta. A duk labarin da ta basu sun fahimci mijin da ta aura babban mutum ne mai mata, sai dai basu iya ƙiyasto shekarun sa ba, duba da akwai matasan da suke ɗaukar aradu a kai su tara mata dan birgewa ko ra'ayi, babban abinda ya musu daɗi fahimci shi ɗin adali ne kuma ta rayu da shi cikin aminci, duk da dai bata faɗa musu komai game da rabuwar su ba, sai kawai ta ce dai basu taɓa samun saɓani mai tsanani har jiya da auren su ya ƙare. *Alhamdulillah.* [21/08 à 23:50] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *55* Alƙawarin da Jabir ya ma Hajia na tsaraba shi ya zo cikawa, har ga Allah ita ta saki wannan magana, hasalima ta manta da ta haɗu da shi, amma shi tunda ya ambata bai manta ba kuma ya zo cikawa, abinda ya saka ta jin daɗi kenan duk da bata san me ye a farar kyakyawar ledar da ya bata ba, tayi murmushi sanda ta kalli fuskar shi har tana ayyana _"Ina ma tana da ƴa? Da ta ba wa dattijon yaron nan ita."_ Da ace Kabil mace ce ai da ba abinda zai hana ta miƙawa Jabir ita, amma duk da haka ta mishi godiya sosai, saboda fatan ɗorewar zumuncin su kuma har sukayi musayan lambar juna tana faɗin" Zamu dinga waya in sha Allah, sannan idan na dawo daga tafiya da zanyi zan kira ka mu sake zama mu sha hirar mu kyakyawan dattijon." Bai san soyayyar kakani ba, haka kuma bai san wasar kaka da jika ba, dan haka yake ɗaukar Hajiar a matsayin kakar sa, babban dalilin da ya sa ma kenan ya sake dawowa. Cike da kulawa Jabir ya tambya" Tafiya *annashuwata* za ta yi? Shine ban sani ba sai yanzu?" Wata irin dariya Hajia tayi cike da jin daɗi tace" Yi haƙuri *yarima*, tafiyar ba mai jimawa bace, shiyasa ma bana shelan zan tafi." Murmushi yayi yana kallon fuskar ta yace" To Allah ya kaiku lafiya ya kuma dawo min daku lafiya." Tana cikin amsawa da" Ameen." Aunty Mardiyya ta shigo da abun taɓawa da ta kawo ma Jabir ɗin, kusan shi ta zauna tana faɗin" Jabir, kun ganni jiya ma shiru ko? Wallahi dawowar tasu ne aka ɗan ƙara ɗagawa, dake kasan akwai babbar ƴar gidan nan da ta ɓata tun tana jaririya?" Da gamsuwa Jabir ya jinjina kai yana faɗin" Ƙwarai, na tuna, na ga hakan da jimawa a yanar gizo tun muna Saudia." Ɗorawa tayi da" Yawwa, shine fa aka gan ta jiya, to kafin ma ita yarinyar ta yarda an ɗan sha wahala, dan har Nuriyya ta kwanta asibiti, to Shiyasa aka ɗan samun tsaiko." Sosai Jabir ya taya su murna da nuna musu farin cikin shi da yi musu addu'a, kafin Hajia ta ɗora da" Shine zan je dan ƙara yi musu godiya akan abinda suka mana, sannan mu basu haƙuri akan wani abu da ya faru a baya, sai kuma autana da zan nemowa auren ƴar gidan." Nan ma addu'ar fatan dacewa ya mata da sauka lafiya kafin ta miƙe ta basu wuri shi da aunty Mardiyya, tana fita auntyn ta kalle shi a tsanake tace" Jabir, nayi mamakin yadda daga haduwar farko Hajia ta saki jiki da kai har kuka fara'a haka, kamar dama can kun san junan ku." Murmushi yayi kan shi ƙasa yana wasa da yatsun shi, a ranshi ya furta _" Darajar Alƙur'ani kenan."_ A bayyane kuma sai yace" Gamon jini kenan." Jinjina kai aunty Mardiyya tayi tace" Gaskiya kam, dan ban taɓa ganin haka ba." Sai kuma ta nuna mishi kayan dake gaban shi tace" Bismillah Jabir, ci wani abu." Jinjina kai yayi alamar to, kafin ya sake ɗagowa ya kalle ta a nutse yace" Aunty, wata alfarma nake nema a gurin ku? Saboda Abba ya ce yau zamu bar garin nan, gashi har yanzu bamu zauna ba." A tausashe tace" Hakane Jabir, kayi haƙuri, ni ma na so mu zauna da kai, amma ba damuwa faɗi ina jin ka." A nutse ya fara fadin" Aunty, lokacin da kuka sami labarin na gudu na bar gida, tabbas guduwa nayi saboda wahalar mahaifina, a lokacin da ban gudu ba wataƙila furucin sa na sai ya ga bayana yayi tasiri a kaina, na fita daga gida a wannan lokacin da burin shiga duniya ne, amma take *RUBUTACCIYATA* ta karkata akalata zuwa ga hanyar dattijon arziƙin da yanzu ya zama uba gareni, aunty, Alhaji Kabir ya min komai a rayuwata, komai aunty ina nufin komai, abu mafi daraja da ya bani shine dalilin shi na samu ilimin addinin da na san yadda zan bautawa ubangijina, sai kuma tallafin da ya bani yanzu haka akan kasuwancina wanda shila ban san ranar daina cin moriyar shi ba, to Abbana ya je ya mishi godiya akan haka, sai dai gaskiya godiyar Abbana ta min kaɗan, Anna da mijin ku kuma ba zasu iya barin garin nan saboda wannan ba kawai, ni kuma kimar sa ta kai na iya neman arziƙi na shekara ɗari dan kawai na tura a masa godiya, a can wajen Abbana kuma Mama ma nasan ba zata iya ba, saboda tana da faɗa sosai da rashin fahimtar mutane, bayan dogon nazari da nayi sai naga aunty ke kaɗai zaki iya yi min wannan, shiyasa nake roƙon da ki samu izini, ni zan baki kuɗin da duk zaki buƙaci wani abu dan kije ki sake yi masa godiya, dan a halin da ake ciki yanzu ina tunanin sun gama magana da Abbana akan zai bani autar sa, sai dai ban san yaushe suka yanke ba." Cike da bashi ƙwarin guiwa aunty Mardiyya tace "Gaskiya shawara ce mai kyau, duk da dai girman abubuwan nan daka lissafa ya maka ya fi ƙarfin a masa godiya, addu'a ce kawai zaka iya saka masa da ita ko nace zamu iya, dan ba kaai kaɗai ya taimka ba har da mu, amma yi masa godiyar ma daga wajen ahalin ka zai ƙara nuna masa girman alkairin da ya yi mana a rayuwa, in sha Allah Jabir zan je, sai dai kuma ni zan ma Alka magana kan zamu tafi tare da Annan taka, dan gaskiya zai so ganin jinin ka a tafiyar nan, duk dai nasan irin mutanen nan ba lallai ya ji daɗin hakan da zamuyi ba, dan nasan ko me ya maka dan Allah ya maka." Jinjina kai Jabir yayi cike da gamsuwa yace" Shikenan aunty, tunda kin ce haka ba zan musa ba, kuma Gaskiya ne abinda kika faɗa, amma yanzu yaushe zaku saka ran tafiya?" Ƴar dariya tayi tace" Jabir, ai kai zaka bamu lokacin da ya kamata mu tafi." Murmushi yayi shima yace" A'a aunty, ku da sai kun nemi izini, sannan ku da tafiya ni da saka muku lokaci?" Girgiza kai tayi tace" Kar ka damu Jabir, ka saka lokacin kawai." Shima girgiza kan yayi yace" Aunty kawai ku saka rana da kan ku." Murmushi ta sake yi sannan tace" Shikenan to, zan fara magana da Kakan naka, yadda duk mukayi zaka ji ni, yanzu fara bani lambar wayar ka." A nutse ya shiga zayyana mata lambar tashi tana kwafewa, take ta kira shi ya ga lambar ta shima ya ɗauka ya saka suna, kafin nan sukayi sallama ta mishi Allah kiyaye hanya. ******************** Ya so yayi kara game da lamarin na Kuwailat, sai dai da ya ga an kwana har an tashi kuma an doshi sallah azahar ba wani labari, sai zuciyar sa take raya masa ko dai Ummu ta riƙe ta ne tunda sun rabu kuma da alama ran ta ɓace yake game da shi? Khamis ya tura ya ɗauko ya ne, nan ne fa suka samu labarin abinda ke faruwa na bayyanar iyayen Ummu na asali, sai ga Alhaji Kabir da farin ciki kamar ma zai fi Ummu murna, duk da yasan suna hushi da shi dan zahirin su ya nuna basu ji daɗin abinda yayi ba, amma baiyi nadama ba, dan yasan gata ya ma Ummu da sai nan gaba zasu gane me yake nufi, sai dai yana takaici na rashin mata kamar ta. Bai yi ƙasa a guiwa ba bayan sallah la'asar haka ya je gida wajen Mama, da Nabila ya ci karo ta dawo daga maƙotan su, gaisawa sukayi a mutumce yana mamakin canzawar Nabila, kafin ya gaya mata Mama yake son gani? Ba jimawa ta dawo ta mishi iso har cikin gidan. Bayan sun gaisa yake sanar da ita abinda ya kawo shi, murna ya taya su da kuma yi musu fatan alkairi, dake Mama ta fahimci abinda Malam Adam ya gaya mata sosai, ta daina hushi da Alhaji Kbir da jin bai kyauta ba, hakan ma ya sa ta saki jiki har suka jima suna hira tana bashi labarin abinda duk ya faru. Daga ƙarshe da mamaki suka rabu yana nanata kalmar _"Dama Ummu ƴar Mukhtar Ahlan ce?"_ Sai kawai ya jinjina kai yace _"Wani hani ga Allah kenan."_, A cewar Mama yanzu haka za ta je masaukin ne dan ta duba jikin Maman Ummu duk da dai ta ga da sauƙi, amma za ta je ta duba ta ta dawo, nan ya buƙaci ko zasu iya tafiya tare dan ya ga iyayen Ummu su gaisa? Ba damuwa, shine abinda ta faɗa mishi kafin ta ƙarasa kimtsawa suka kma hanyar tafiya. ******************* Dake tafiya ce ta masu hannu da shuni, a awa da bata kai biyu ba suka iso a jirgi, tare suka zo da Alhaji Abbas sai ɗaya daga cikin masu kula da sashen ta, ita din ma ta zo da ita ne saboda idanun dake ɗan sako ta gaba musamman idan dare yayi. Ganin juna da aka yi shi ya sa aka sake shiga wata sabuwar murnar aka manta da an yi a waya, haka suka jima suna ta farin cikin ganin junan su har bayan la'asar. Tuni da sun bar gidan, sai dai dake tafiya ce da ta fi mutum biyu, sai gashi an ɗauki lokaci, dan Ummu ma ta ce zata bisu ne daga nan ta zauna wajen Maman ta, haka ma Kuwailat da ta ce zasu tafi tare sai ta sa ko Nabila ta rakaya gidan Baban ta, ga kuma Mama Nuriyya da taji har da Ummu sai take ganin kamar zasu rabu kenan, hakan yasa ta ce zta bisu sai su dawo tare, to fa kafin a shirya ne har Mama ta shigo gidan ta kuma faɗa musu ai tare da tsohon mijin Ummu suke ya zo ya gaishe su sannan ya musu barka da ganin juna. *Tunda* Alhaji ya shigo suna gaisawa mutanen da basu san shi ba suke ta kallon junan su, jira suke suga wani matashi ko dattijon da bai kai wannan shekaru ba, amma sai suka ga shiru ba alamar wani zai biyo bayan shi, sai dai duk da haka basu sare da zasu ga wani a matsayin mijin Ummu ba sai da Kuwailat na fitowa da sauri ta nufe shi ta zauna daf da shi tana riƙo hannun shi tana faɗin "Abba, sannu da zuwa? Ina wuni?" Murmushi ya mata ya shafa kanta ya amsa da "Autana, lafiya lau, kina nan kin manta da Abban ki?" Dariya tayi ta ɗora kanta a damtsen shi tace "A'a Abba, ban manta ka ba, ai yanzu gida zmu tafi." Murmushi kawai ya mata ya kalli Abbu Mukhtar da aka shaida mishi shine surukin nasa yana murmushi yace "Kuna ta shan ƙiriniyar auta ba, ina ce dai kuna zane ta? Dan sai ta saka muku ciwon kai." Abbu da shi dai abun yake ta masa yawo a kai, yana ta mamakin yadda aka yi ƴar sa Ummi ta auri mutumin da tsf zai iya cewa tsaran Abbun su ne da ya rasu, to fa gaba ɗaya Abbun su Bilal shine babban ɗan sa, ta ya ya jama'a? Dama wannan ne ta aura? Shine har da mayar mishi ƴa bazawara? Taɓɓ ! Ko da yake gaskiya hakan ya fi zama alkairi, dan shi dai lokaci ɗaya ya gama fahimta ko ta ji daɗin zama da shi ta ko ina, ta auratayya dai kam zata samu naƙasu. A zahiri kam murmushi yayi sosai kmar ba komai dake ranshi yace "Wannan amaryar Yayan nawa bata taɓuwa, dan da kowa yana iya yin yaƙi akan ta." Yaya Bilal d shima abinda ke ranshi kenan game da Alhajin haka ya daure kamar ba komai yace "Ƙwarai kuwa, ai ba ma za'a fara ba, a bar min kayata tayi ƙriniyar ta." Alhaji kam murmushin jin daɗi yake na yadda suka karɓe shi, sai Mama Nuriyya da take jin anya? Anya shine mijin Ummu? Wannan tsohon da ko ita za ta iya cewa ya mata tsufa? To ita gaba ɗaya har yanzu Abban su 64 gare shi, amma fa wannan shekarun ba kaɗan ba da alama, to ta ya ma auren su ya yiwu ne? Kuɗi mariƙan Ummi suka bi? Ko ita Ummun ce ta bi kuɗin? Dan ba sai an faɗa ba akwai su daga yadin dake jikin shi, irin wqnda nata mijin ke sakawa ne har tana ganin yana ɓannar kuɗi dayawa. Ta jima da fahimtat abinda ke ranta shine ran dukaninsu, dan hka ta wayance kamar kowa ta hanyar faɗin "Ni kam da na samu bulala zane tan zanyo, dan tunda ta zo kaina ya ƙ ya daina ciwo." Da fara'a Alhaji ya kalli Kuwailat dake hangen Mama Nuriyya tana maƙale kafaɗa yace "Kin ji ko? Kina ba wa Hajia ciwon kai, ki daina ƙriniya auta. Dake a kwana ɗayan nan sun saba da Yaya Bilal saboda yadda ya j ta a jiki, da sauri ta miƙe ta nufi inda yake ta zauna tana sake kwantar da kan ta ƙrjin shi tace" Nawan, ai ba zaka bari ba ko?" Riƙe hannun ta yayi a tausashe yace" Ba zan bari ba tawan, sai dai idan bayan raina ai, amma ki barsu tunda sun kasa gane matsayin ki da kike da a wurina." Mama ma dake kallon Kuwailat taɓe baki tayi tace" Ke dai baƙin jinin ki yawa ne da shi, na ɗauka ita zakiyi ƙawance da ita tunda kin rasa ni, ashe ita ɗin ma kamar ni dai." Mama Nuriyya da fara'a tace" Ba dai ni ba kam, me zan yi da ita ni? Sai dai ko ƴar uwa?" Ta faɗa da nuna aunty Fa'iza. Da sauri Aunty Fa'iza tace" A'a ba dai ni ba, macen da ta ƙwacen miji, daga jiya zuwa yau duk na kasa gane kan shi." Kallon ta Yaya Bilal yayi yace" Ba kuma zaki sake ganewa ba madam, ke ai dama idan zaki tambayi kuɗi ko fita a hana ki to sai ki ce kin rasa gane kan mutum, amma sabuwar amaryata ina so ma ta tambaye ni fitar amma har yanzu shiru kake ji." Kallon shi tayi tace" Au ! Sharri zaka min? Daga ganin amaryar ka?" Kuwailat dai bata san yadda zata tafiyar da matan ba, to dukansu babu wacce bata nuna mata soyayya da kulawa, daga wacce ta sani tsawon shekarun ta har zuwa kan waɗanda ta sani jiya zuwa yanzu, ta ga dai a ƙrjin Mama Nuriyya ta kwana, aunty Fai'za kuma da safe neman yi mata wanka tayi fa, dan saida aka raba su da ƙyar, amma a haka saida ta bata abinci a baki, amma gashi yanzu sai wani gwasale ta suke yi. Kafin Mama Nuriyya ta bata amsa Mama ta taso da leda a hannun ta ta miƙoma Mama Nuriyya tace "Ke na kawowa wannan, ko zaki iya tuna abin da ke cikin ledar?" Karɓa tayi tana buɗewa tana kuma faɗin "To, Allah ya sa zan iya tunawa." Tana buɗewa rigar dake jikin jaririyar ta ne da ta ɓata da zanin goyo har da abun tsutsar nan wanda kawai anfanin shi yaro yayi ta tsotsa ba komai, take wasu zafafen hawaye suka sauko mata, kallon Mama tayi tana share hawayen tace" Wannan kayan da ke tare da Kuwailat ne kafin rasata, kin sake tabbatar lana lallai ƴar mu ce a hannun ki, ni kam dame zan saka miki?" Da sauri Mama ta kalle ta tace" Da abu ɗaya." Duk kallon ta sukayi saboda son kin buƙatar ta gare su, Abbu ne yace" Menene shi? Ki faɗa, in sha Allah zamu miki." Saida Mama ta sauke numfashi kafin tace" Sunan da na ba ƴar ku, suna ne da nake burin sakawa ƴar da zan haifa, sai Allah ya sa na fara haihuwar namiji, amma ikon Allah sai na tsinci Kuwailat ɗinku kafin na haifi tawa macen, hakan yasa na saka mata sunan Ummu Kulsum, shi kawai, shi kaɗai nake so dan Allah *ku ci gaba da kiran ta da shi*, duk da nasan kuma soyayyar sunan tasa kuka saka mata, sannan duka sunayen masu ma'ana ne da tarihi." Hajia da ta sake ganin dattakon matar dan ita ta ɗauka ku wani abu da ya shafi dukiya zata nema, murmushi tayi tace" Amina, ke mai karamci ce, da izinin Allah sai kin zama mace abar koyi da kwatace, Allah ya miki albarka, Allah ya wa yaran ki albarka." Da jin daɗin wannan addu'a Mama ta amsa har da duƙawa ƙasa dan Hajia ai uwa ce gare ta, Abbu ne yace" In dan wannan ne ba komai, ƙwarai soyayyar sunan Kuwailat ta sa muka saka mata shi, amma tunda Kuwailat ta bamu wata Kuwailat ɗin, ina ga ba buƙatar sai anyi biyu, mun ɗauki naki sunan." Murmushi Mama tayi tace" Nagode, kuma ina ga Allah na son ku samu Kuwailat ɗin, shiyasa tun kafin ta haihi take kiran kanta da maman Kuwailat." Murmushi sukayi sai mama da tace" Mune da godiya." Alhaji Kabir dake son ya ɗan taushi zuciyar su kan rabuwar shi da Ummu duk da yasan ba lallai sun san komai ba, amma dai yasan dole sun san maganar rabuwar su yayi gyaran murya yace" Ammm! Nace ba ? Ina mai baku haƙuri kuma akan abinda kuka tarar wanda na san bai muku daɗi ba, amma idan kuka zauna da ita Ummu ta sanar da ku komai, nasan zaku fahimce ni in sha Allah, amma ina baku haƙuri dan allah, dan ba burin kowasu iyaye bane mutuwar auren ƴar su." Alhaji Abbas ne kawai ya yi amsar ban haƙurin shi da nuna masa ba komai haka Allah ya tsara, sai yaya Bilal da shima ya amsa haka ma Hajia, kafin a sake sakin zancen Abbu Mukhtar yace" Gashi ko dama muna shirin zuwa mu same ka akan maganar Kuwailat? Da tun jiya muka so tafiya zuwan Hajia ya dakatar damu." Zuba mishi idanu yayi yana son jin me kuma ya faru? Ɗorawa yayi da" Dama ita Ummu muka so tafiya tare dan ta ɗan zauna mana, to sai ta ce ba zata tafi ba sai ta kamalla iddar ta, shine muke son tafiya da Kuwailat, amma dole sai da izinin ka, da shine zamu je dan mu san juna da kai sannan mu samu amincewar ka, sai kuma ga ka." Ajiyar zuciya ya sauke, shi kam ai ba zai hana ba gaskiya, dan dama zama da ita yanzu zai mishi wahala, duba da tafi sabawa da Maman ta kan kowa, shi kuma ba mazaunin gida ba kowane lokaci, islamiyyar su kawai zai je ya sanar da malamin, kafin hutu ya ƙare ta dawo ma yana sa ran Aliyu ya kammala nashi aikin, dan haka tana zuwa sai sabuwar islaiyya in sha Allah. Nan fa ya amsa musu da ba komai, inda ya sake jinjina tarbiyya da rasa mata kamar Ummu, wacce bayan kun rabu ma zata yi ƙoƙarin kare maka darajar ka, ko da ya ji haka sai kawai ya musu sallama ya tafi, kuma abun farin ciki Abbu Mukhtar saida ya mishi rakiya har waje suna ci gaba da hirantawa. *Alhamdulillah.* [22/08 à 23:41] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *56* Fitar Alhaji ta sa Alhaji Abbas sake gabatar da kanshi ga Mama sannan ya fara bata haƙuri kan lamarin Nabila da Fahad, haka Hajia ta dinga faɗin kuskuren ta da bakin ta tana ba Mama haƙuri, har zuciya Mama ta nuna musu ba komai fa wallahi ita a wajen ta komai ya wuce, kaxai dai Allah ya yafe musu baki ɗaya. Sannan ne Alhaji Abbas yace "Sai kuma magana ta biyu da ta kawo mu, wacce ita Hajia Radiya ta yi alƙawarin ba zata koma ƙasar ta ba har sai kin amince da buƙatar ta." Murmushi Mama tayi tana sadda kai tace "In sha Allah ma babu abinda zai gagara muyi musu." Yana kallon fuskar ta ya furta "Auren Nabila take so ki ba Fahad, dan Allah ? In dai da gaske komai ya wuce." Ɗan kallon shi Mama tayi, amma haiba da kwarjini sai ta sadda kai tace "Alhaji, wallahi ban hana Nabila amincewa buƙatar su ba, amma indai ni na haifi Nabila, kuma da gaske tayi tuna na gaskiya, in sha Allah Nabila ta amince da Fahad kenan, idan na koma gida umarni kawai zan bata, Hajia sai ki saka musu lokacin da ya dace." Ba wanda bai yi farin ciki da wannan magana ta mama ba, wacce ta ce ita idan a so samun ta ne bayan kammala istibra'in Nabila da sati ɗaya a ɗaura musu aure abun su, take Mama ta amsa ta yarda da hakan, hakan yasa aka yi ta murna sai Ummu da suka kira wacce tunda Mama tace tare da Alhaji suke ta shige ciki basu haɗu ba. *A GURGUJE* Mama ta cika musu maganar ta, dan suna komawa gida tare da Ummu suka saka Nabila tsakiya, dole ta amince da buƙatar su har da raha da cewa "Wallahi aunty Ummu dan dai yana ɗan uwanku ne, ba dan haka ba bani ba shi." Ummu dariya tayi ta amsa mata da "To mun gode a haka ma." Amma kuma sai ta ce ba fa za'a ɗaura mata aure a kai ta wani gari ba tare da Ummu ba, dan haka ma Ummu ta sake jadadda "Gaskiya fa ba zan saɓa umarni ubangiji ba, an ce mace mai idda ta killace kanta, ba zan ta yawo sakaka ba alhalin ina idda, ke dai Allah baku zaman lafiya." Ita ma cike da tabbaci tace "Wallahi tallahi Mama na yarda zan auri Fahad, amma fa sai bayan auntyna ta gama idda, idan bata raka ni ba waye zai raka ni? Dan haka in ya musu to, in bai musu ba su ƙara gaba." Dole dai suka bar ta a haka, da suka sanar da Hajia ta ce ba damuwa, da yau da gobe da bayan wata uku ai duk kamar gobe ne wajen Allaj ba wuya, dan haka su Hajia suka tattara tare da Kuwailat da saida ta je ta ɗauko kayan ta tama su Hajia sallama sannan suka tafi dukan su a mota. *Bayan sati ɗaya* da haka kuma aunty Mardiyya ta zo, ita kawai suna waya da Ummu ne da sunan zata sauka gidan su, na farko ita ma taga Ummu sannan ta isar da saƙon Jabir wajen Alhaji, ba ta san cexa Alhaji Kabir shine mijin Ummu ba, ita dai sun zo ita da Anna Ummu da Mama suka tarbe su yadda ya dace. *Washe gari* da sassafe suna tsaka da shiri Ummu ta kawo musu abun kari, gaisawa sukayi sosai kafin tace "Mamma, ga abincin ku." Aunty Mardiyya dake shafa mai ta amsa da "Ok ina zuwa, bari na saka kaya." Kallon su tayi daga yadda suke shiri tace "Mamma ko fita zaku yi?" Amsa mata tayi da "E wallahi, ba na faɗa miki abu biyu zai kawo ni ba? To na ganki yanzu zamu fita gabatar da ɗayan." Da kulawa Ummu tana kallon Anna dake shafa kwalli a idanu tace "Kuma Mamma sai da sassafe haka? Har ina zaku je?" Nuna mata Anna tayi tace "Akwai babban jikan ta dake nan, to akwai wani ubangidan sa da ya msa komai a rayuwa, kusan ma kamar shi ya haife shi, to shine da ya je yace yana so mu zo mu ƙara yi msa godiya saboda dai yasan duk alkairan da yake masa muna sane kuma muna jin daɗi." Cikin gamsuwa Ummu tace" Gaskiya ne, hakan yana da kyau ai." Anna jin su kawai take, amma idan akwai abinda ta fahimta a ciki bai wuce mahaifi da ta ji an ambata ba, sam sam bata jin hausa ko kaɗan bayan gaisuwa, dan haka take shiru shiru saboda bata san da yaren da zasu gane juna ba. Suna cikin cin abinci Ummu tace "Duk da bana son na cika yawan fita, amma zan raka ku sai na kaiku, bai kamata mu bar ku ku hau adaidaita ko taxi ba." Murmushi aunty Mardiyya tayi tace "Kar ma ki damu kan ki, akwai wani ɗan gidan da yayi magana da shi zai zo ya ɗauke mu." Murmushi ita ma tayi tace "Yawwa, gaskiya hakan ya fi." Tunda Khamis ya faɗa mishi shi fa a kwatancen da ya mishi gashi ya zo kuma kwatancen gidan su aunty Ummu ya nuna Jabir ya shiga tunani da mamaki, gudun kar ya mishi kwatance ba daidai ba ya sa kai tsaye ya ba Khamis lambar aunty Mardiyya ta gaya mishi inda suke, to ya haka kuma? Aunty Mardiyya ta ce gidan ƴar ƙanwar ta da aka samu kwanan nan ne suka sauka. Amma dan ya samu tabbaci sai ya kira yace "Aunty, wai a ina kuka sauka ne?" Da mamakin tambayar ta amsa da "Jabir ina inda nace maka zamu sauka." Shi ma dai da yanayin rashin fahimta yace "To ai aunty kwatancen ne ya nuna *gidan su Maamana*, shiyasa na sake tambaya." Kamar suna gaban juna ta jinjina kai tace "Ummm! To mu dai anan kaga mai gidan sunan ta Aminatu, sai ita ƴar Nuriyyar da bata jima da dawowa nan ba saboda rabuwa da sukayi da mijin ta, sai kuma autar gidan Nabila wacce ita ce Fahad autan *Hajiarka* zai aura in sha Allah nan da wani lokaci." A duk cikin maganganun ta ba abinda ya fi fahimta da kyau ya kuma fi riƙe shi sosai a cikin kan shi sai *saboda rabuwa da sukayi da mijin ta*... Sai ya ji gaban shi ya faɗi daga jin wannan magana da bai gama tantace da wa ake nufi ba, yanayin tashin hankali da zufa suka nemi rufe shi lokaci ɗaya , da sauri ya tambayi aunty Mardiyya "Wacece ? Wacece ta rabu da mijin nata aunty?" Ba tare da tunanin komai ba tace "Ummm! Ummu Kulsum, ƴar ƙanwar tawa." Saida Jabir ya dafe kan shi saboda bugawar da yayi mishi yace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Maama, me ya faru? Ya aka yi ban sani ba?" A nutse aunty Mardiyya tace "Jabir, ka san wani abu a kan su ne?" A dake ya amsa da "Ba komai aunty, shikenan kawai." Kafin ta ce wani abu kuma ya yanke kiran ya bar ta da tunanin to ko lafiya? Ummu ma saida ta fita rakiyar su ta ga Khamis ne ya zo ɗaukar su, anan ta fahimci Jabir ne kenan jikan Anna? Sannan sun zo yi masa godiya ne wajen Alhaji? Haa dai suka rabu ba wanda ya nuna wani muhimmin abu. *Washe gari* suka dawo daga Niamey shi da Abban shi, zai iya ce wa ya fi jin daɗin zama Agadez akan Niamey, saboda ko ba komai kakanin shi sun nuna alamar damuw a fuskokin su da kunyar haɗa idanu da shi, to amma kakar shi da ta haifi mahaifin shi ita da ƴan uwan mahaifin nashi babu wnda ya nuna masa wannan alamar, hasalima zalamar su ce ta fito fili akan ganin irin arziƙin da Allah ya mishi wanda shi a wurin shi ba komai bane face kaɗan da ya ɗebo saboda su, hakan yasa bai ji daɗin zama da su ba, babban abinda ya bashi haushi sosai game da su shine yadda Kakar shi ta masa maganar wai ga ƴan mata nan cikin dangi ya zaɓi ɗaya sai ya aura, bai iya ce mata komai ba sai mahaifin shi da ya bata amsa kawai. Shi ba la wannan ne gaban shi ba, abinda ya ji jiya ne tashin hankalin shi, Abba ya rabu da Maama? Me ya faru? Me ya shiga tsakanin su? Damuwar da suke ciki har ta kai ƙadamin da dole sai rabuwa ce kaɗai maslaha? Ya Allah! Ya Allah! Me ya shiga kan Abba ne? Me Maama tayi da zafi da har mata uku da ya zauna da su basu taɓa kwatanta yi masa ba? Da wannan tunanin suka shigo kuma har ya haɗu da Aliyu, ya jima yana kallon fuskar shi da mamaki, wannan maganar ce dama ya ƙi faɗa masa a waya? Tun Aliyu na kawar da kai har dai shima ya kalle shi yace "Jabir? Me ye a ran ka? Faɗi ina ji?" Girgiza kai Jabir yayi sannan ya gyara zama ya sae kallon Aliyu da kyau yace "Maama bata gida, me ya yi zafi tsakanin su da Abba?" Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke yana duban shi cikin nutsuwa yace "Na so faɗa maka tun a waya, amma mahimmancin maganar ya sa ban yi haka ba, ƙwarai aunty da Abba sun rabu, kuma rabuwar tasu ta taɓani sosai ta yadda na so ƙalubalantar Abba, amma da naji yana sanar da su Hajia babba dalilin sa na sakin nata, sai na gamsu na kuma yarda da hukuncin da ya yanke ɗari bisa ɗari, shine daidai." Zubawa Aliyu idanu yayi cikin tashin hankali yace" Alfasha Maama ta zo da ita?" Girgiza kai Aliyu yayi yace" Ba alfasha ko ɗaya." A ɗan kausashe Jabir yace" Kuma a hakane kake ganin hukuncin da Abba ya yanke yayi daidai? Saboda me? Dan ba...." Sai kawai Jabir yayi shiru saboda abinda ya so faɗa ba lallai ya ma Aliyu daɗi ba, amma shi dai gaskiya gani yake Aliyu ya ji daɗin hakane dan ba Maman sa bace kuma ba ɗaya daga cikin ƴan uwan sa ba, ai ko me mace ta yi ba daɗi a ce an sake ta, bare shi da yake da tabbacin Maama ba zata yi abinda zai zama na ƙyama ba. Aliyu kuma kamar ya san me ya so faɗa sai yace "Hakane, nasan ba daɗi, tunda ina da ƴan uwa mata, amma kuma aunty Ummu wanan matakin shine daidai da ita, dan in ba haka ba to alfashar da ka ambaa uta za ta faɗa ciki tsumdum, ka fi ni sanin ana raba aure idan har buƙatar ɗaya daga cikin ma'aurata ba ta biya, bare kuma zamantakewar Abba da aunty da shi dai ba zai iya zama yadda take so ba, kuma ita babu maganin matsalar ta na har abada, ka fahimci Abba, k san ba zai yi haka da son ran shi ba." Shiru Jabir yayi ya riƙe haɓa yana nazari akan abinda Aliyu ya faɗa, abinda ya raba su kenan? Maaman shi? Abba ? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! Shi fa ba wanda ya fahimce shi ne har yanzu, shi fa abinda yake dubawa yanzu da suka rabu saboda Allah, *uban wa ye ya isa ya ja matar Abban shi*? Saboda Allah yanzu idan ta gama idda sai kula a ce tayi *aure*? To ta auri wa? Shi fa ba zai bari matar Abban shi ta auri wani ba? Ya yi alƙawari tsakanin shi da Allah kan zai kare mutumcin iyalin shi, to idan ta auri wani ya isa ne? Ai ko ganin ta wahala zai masa bare ma ya san damuwar ta ko akasin haka? Mtssssss ! Shi kam yana nan yana jira zai ga marar kunya kuma fitsararren da zai fito ya ce yana son ta? Buƙata ce ta fito da Maama ko? To sai dai *buƙatar ta kashe ta*, amma ba zata je ta kwanta a gadon wani zéro ba har ma ya mata maganin matsalar ta. *Har* sukayi kwana uku suka koma Anna tana jinjina ladabi da karamcin Ummu, yarinyar ta birge ta sosai yadda take girmama su, sannan ta san ita ce wacce ita a ganin ta zata iya cewa dalilin ta aka taimaki Jabir, nan ma dai zumunci ya sake ƙulluwa, hakan yasa yanzu ɓangarorin suka sake zama tamkar ɓangare ɗaya. *BAYAN WATA UKU* Zaune tayi kan kujera ƴar tsugunno ta tara hannayen ta, a nutse Kuwailat ta fara zuba mata ruwa tana wanke jan lallen data saka a hannayen ta, cikin magiya kuma Kuwailat da duka satin ta ɗaya da dawowa yau take rarrashin Ummu kan ta tafi da ita idan zasu kai aunty Nabila, amma tayi murmushi ba ta ce mata komai ba, ta san dalilin da ya sa take so ta koma, to da ta dawo kasa shaidata tayi da fari saboda yadda ƴar ta ta koma tubarkallah, Kuwailat da bata rasa ci da sha ba gidan mahaifin ta, sai gashi ta canji da kulawa ta sa ta fito wata kyakyawar budurwa ɗas da ita, hatta jar fatar ta ta sake bayyana fiye da baya. Kamar za ta yi kuka saboda yadda take ta magana amma ta ƙyale ta tace "Mamieeee?" A kausashe ta kalle ta tace "Kuwailat zuba min zuwa, ki kuma barni na sha iska." Turo baki Kuwailat tayi tana ci gaba d zuba mata ruwan tace "To Mamie zaki tafi da ni ɗin? Dan Allah Mamina." Kallon ta tayi tace "Yaushe kika dawo? Kuma nan ma ba hidimar ke akwai ba, dole sai na tafi da ke bayan kin san karatu kike? To ni ba zan sake neman izinin zuwan ki ko ina ba." Turo baki tayi irin ranta ya ɓace, hakan yasa ta shiga bulbulo mata ruwan da ƙarfi, da sauri ta kalleta tace" Kuwailat, kina gani ko?" Shigowar Nabila tare da ƙawar ta a gajiye suna zubexa kan tabarma yasa hankalin Ummu komawa kan su tana musu sannu da zuwa, amsawa sukayi da girmamawa kafin Nabila tace" Aunty Ummu, kin ga mutumin ki bai ɗinki mana duka ba ko?" Da sauri Ummu tace" Dan Allah fa ? Amma dai naki ko? Dan idan nawa ne zai ga tashin hankali." Da mamaki Nabila tace" Iyesh! Aunty ni ce amaryar fa." Taɓe baki Ummu tayi tace" Ina ruwana, ai mune zamuyi shgar biki." Ƙawar Nabila ma cexa tayi" Nima haka nace aunty Ummu, amma har da ɗaya daga cikin naki bai kammala ba." Nabila kam share su tayi tace" Wai ina Mama?" Ummu ce tace" Suna ciki, kayan ki suke gyara miki da kika barbaza musu." Dariya tayi ta tashi da sauri tana faɗin" Na shiga uku, bari naje na kama musu." Ummu na gama wanke lallen ta shiga wanka da gaggawa ta fito, Kuwailat da ta samu zaune tace ma" Ki shirya fa na gaya miki tare zamu fita, idan muka dawl daga karɓo ɗinkin ki gidan ku zan aje ki." Dama tana jin haushin ba za'a tafi da ita ba, ga kuma haushin Maman nata da take ji idan ta ce gidan su ko gidan Baban ta, bata so wallahi, amma ta ga iyaen nata basu da niyyar saje komawa zama, miƙexa tayi har da bubbuga ƙafafu tana faɗin" Kullum dai gidan Baban ki gidan Baban ki." Da kalli Ummu ya bita tana faɗin" Na faɗa din Kuwailat yanka ni, ni kike turowa baki ?" Ƙwafa tayi ta bi bayan ta ta shiga ɗakin dan shiryawa, man ta na kullum ta shfa dake karɓan fatar ta wanda ita ke haɗawa da kan ta, hakan yasa bata yrda ta nemi man kaɗanya ta tas a rayuwar ta, tana gama shafawa wani ƙaramin turare ta shafa wanda miski ne sai dai na jiki, tana shafa shi ta saka kayan ta da ta jima da turare su da daddaɗan turaren gidan Hajia Fussam, sihirtaccen ƙamshin shi ya sa take anfani da shi yanzu idan zata fita tunda ta kammala iddar ta, saboda shi ƙamshin shi yanayi da turaren wuta yake, hakan yasa idan kana anfani da shi ka shigo waje za'a juya a kalle ka, idan ka wuce ma haka za'a bika da idanu cike da ɗokin son sanin sirrin turaren ka. Cikin doguwar riga ta atamfa ta shirya da babban mayafin da ya dace da atamfar da kuma takalmi flat wanda ta fi son saka su saboda tsayin dake gare ta, babu kwalliya ko ɗis a fuskar ta bayan hoda data shafa, ba ta ɗauki jaka ba ta fito tare da saka Kuwailat gaba bayan ta ma su Mama sai anjima. *Alhamdulillah.* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *57* Aliyu dake ci gaba da kallon gidan wanda mahaifin Jabir ya siyar da filin shi ya siya mishi saboda gida ne matsakaici da ya dace da matashi kamar Jabir kuma larura ta sa mamallakin shi zai siyar da shi da sauƙi, sha'awar Jabir ya zauna tare da shi ya sa ya siya mishi dan daka fito daga gidan mahaifin kana hangen gidan Jabir ɗin, gida ne mai tsakar gidan da zai ishi bawa dai ya walala duk yadda yake so, ga kuma ban ɗaki da madafa duk a tsakar gidan, sai wata veranda ɗin da aka zagaye ta da gajeruwar katanga mai kwalliya wacce mutum har zama zai iya yi saman ta, gashi kuma da ƙofa biyu babba dan shigowar abun hawa da ƙarama dan shigowar mutane. A ciki ma ɗaki uku ne, biyu jere da juna sai ɗaya daga gefe, kuma kowane da ban ɗaki a cikin shi sai matsakaicin falo, duk da gidan sabo ne amma saida Jabir ya sa aka mishi kalar gyaran da yake so, hakan yasa aka fitar da ƙofar da zata kai mutum madafa daga falo ba sai ya fito ba, sannan aka rufe ƙofar dake wajen, hakan yasa wurin ya fi yin kyau ga fanti da aka canza tare da ƙwan fitilu da fankoki irin na zamani, sannan ɗakuna biyun duk ya sa aka saka ac a cikin su. Wani matashin yaro ya samu a unguwar dake lura masa da gidan tare da yi masa shuke shuke, hakan yasa yanzu gidan ko mai shi idan ya gan shi zai ɗan wahala kafi ya yarda shine gidan nan, dan hatta da rufin kwanl sai da aka canza ma gidan. Jabir fa ya kankaro wulaƙanci, dan tunda aka gama ginin shagon nan harkoki suke tafiya daidai, yanzu kam harka in dai ta kuɗi ce to baya jin ɗar sai dai kawai tattali da ake son ɗan adam ya kasance da shi. Bayan gama ganin wurin da nuna masa abubuwan da aka canza Aliyu ya jinjina kai yace "E lallai malam Jabir, wato duniya sabuwa zaka buɗewa kan ka ko? Yanzu Alaramma ku kuke koya mana mu ƙauracewa duniya, shine kai zaka shinfiɗa irin wannan rayuwar, to yaushe amaryar za ta tare?" Girgiza kai Jabir yayi yana kallon shi kamar mai ciwon baki yace" Aliyu na farko da na sani a rayuwata mai surutu, sahabin Annabinmu (SAW) bayan jarumta da yake da har da miskilancin da kan hanashi yawan hayaniya idan ba wajen faɗin Allah da Manzon sa bane, amma kai..." Sai kawai ya sake girgiza kai tare da juyawa zasu fita daga gidan, Aliyu dake ta dariya ya biyo bayan shi faɗi yake" To ai nima da miskilin ne, da Abba ya tashi tura min abokin zaa sai ya tura min *adunkuma*, to idan ni nayi dukum kai ma kayi ɗummm abun ka, wa ye zai tayar da wani kenan? Dole ni ai na sauke girmana da ajina kawai nake surutu abuna, dan ya fi daɗi ma wallahi, kuma ni dake fama da ɗalibai idan ban yi surutu ba to me zan koyawa yaran mutane." Juyowa Jabir yayi ya masa wani kallo ba alamar wasa yace" Na ce ka ɗauke ni aiki ka ƙ ko? Ba ka buƙatata kusa da kai ne?" Taɓe baki Aliyu yayi yana ƙoƙarin buɗe mota inda Jabir ɗin ke rufe gidan yqce" Ni ma ai nace ka min aiki kyauta, kafin na tsaya da ƙafafuna sai na fara biyan ka albashi." Bai ce mishi komai ba saida ya shiga mota Aliyu zai tayar sannan ya kalle shi fuska a haɗe yace" Ba zan yi a kyauta ba, kuɗi nake nema ni, kuma zan fara aiki a makarantar ko baka so dole ka biya ni." Kallon shi Aliyu yayi galala, sai kuma ya tayar da motar yace" To! Ina ga fa haushin Abba ya ce sai Kuwailat ta kammala karatu ya sa kake so ka fara huce haushin ka a kaina, dan yanzu tunanin ka nuna ma yake ni nake jan karatun ko?" Cike da shashantar da zancen Jabir ya gyara zama a miskilance yace" Na faɗa maka ina buƙatar ƙanwar ka ne yanzu dan raino, ku bari ta ƙara ƙwari, kwa miƙo min ita." Dariya Aliyu ya fashe da ita yana nuna kan shi yce" Alaramma ni kake faɗawa haka?" Taɓe baki Jabir yayi bai ko sake bi ta kan shi ba, shi bai san yanzu idan aka yi maganar Kuwailat ba ma gyatumar ta ce ke zuwa masa lissafi, da gaske dai zawarci take a gida, Abba yana ji yana gani zai ƙyale ta tayi abin da take so? Kwana uku yau ya je gidan gaishe da Mama wai bata nan, yawo take zuwa ko? Ita kawai Maama hali dai irin na ƙuruciya sai tayi ta aikata shi, bayan budurwa gare ta. Shi ya ma rasa da wanne zai ji ne? Kula da haƙƙin *Abba margayi*? (Baban su Nabila), ko kuma kula da haƙƙin *Abba mai rai*? Kowanen su ya masa alkairi kuma baya so ya ga wani abu ya samu iyalin su, to ita Maama ai ba zai iya yi mata faɗa ba ko? Kuma sun saka Abba gaba kan yayi haƙuri dan Allah mana su manta d komai, amma dake shima Abban baya so su yarda tsufa bai fara jigata shi ba kawai ya ce wai su bar zancen, yanzu gashi can Maama ta yi free, dan tsaf yake sa lissafi a kan shi, yau kwanan ta shida da kammala wa'adin nan, to ina daɗi irin haka fisabilillah! Kai tsaye gida suka wuce saboda Aliyu dake bada sallah magrib da subah a masallacin Alhaji yanzu, kuma sun taho tare ne dan akwai karatun da zasu tafi daga nan, ƙofar gida suka aje motar suka wuce masallaci. *Ummu* da tund suka doso unguwar ta ji bata ji muryar limami ana sallah ba sai ta ɗauka nan har sun idar da sallah, dan haka ta kawo Kuwailat ƙofar gidan ta aje, yadda take ta tuttura baki yasa ta kallon ta tace "Ke! Wai lafiya kike ta sha min magani? Me na miki?" Cikin turo bakin tace "Ba komai." "Ba komai ɗin ne kike ta turo min bakin nan?" Ta faɗa cikin yanayin faɗa, a hankali ta ɗan saki bakin amma ba duka ba, buɗe mota tayi za ta fita Ummu tace mata "Yanzu haka zamuyi sallama? Kuwailat dan nace ba zaki bini ba shine kike wannan hushin? Me yasa kike so ki katse karatun ki to? So kike Yayan ki Aliyu ya yi tunanin dan yana na gida ne za'a dinga masa haka? Kiyi haƙuri mana, idan da rai da lafiya idan Nabila ta haihu sai ki je, ko ba haka ba?" Ba dai dan ta saki fuskar ta ba tace" Shikenan Mamie, sai anjima." Murmushi Ummu tayi tace" Ina ƙaunar ki." Tana fita daga motar tace" Nima haka." Rufo ƙofar tayi ta nufi ciki Ummu na faɗin" Ki gaishe da su Hajia." Ko juyowa Kuwailat ba ta yi ba, Ummu da ta fahimci har yanzu dai bata haƙura ba murmushi kawai tayi tana girgiza kai tare da ƙoƙarin tayar da motar ta wuce tana faɗin" Allah ya shirya min ke *takwarata*." Muryar Idi mai gadi ce ta katse mata hanzari sanda ya furta" A'a, Hajiar auta ce a gidan namu?" Ba ta so zuwan kowa ba ko wani ya gan ta, saida ta rintse idanu a hankali ta juyo ta kalle shi tana murmushin yaƙe, dan Alhaji gida yake sallah magrib sai in ba ya gari, idan fa suna cikin gaisawa ya zo? Ba tare da ta saki jiki ba tace" Ina wuni Baba Idi?" Da fara'a ya amsa da" Lafiya ƙalau Hajia, ina wuni?" Ba ta iya kora da hali ba ma bare wulaƙanci, amma a gaisuwar da yake ta mata har da ɗan mata nasiha na me zai hana ayi haƙuri a dawo ko dan yarinyar nan ta takura sosai, amma haka ta daure kawai tana jin shi tana kuma amsa mishi, saboda dai ta ga ta bar wurin tace "In sha Allah Baba Idi zan dawo, abinda ya faru ma tsautsayi ne, nagode sosai da kulawa, sai kwana biyu kuma." Ta ƙara yi wa motar key kawai ta ji muryar da ta saka gaban ta wani irin tsinkewa ta faɗi cikin yanayin rashin jin daɗin haɗewa da suka yi ɗin yana faɗin" Barka uwar auta." Nan ma rintse idanu tayi ta cije leɓe ta sadda kan ta, ta ɗan ɗauki sakanni haka kafin ta buɗe motar ta zuro ƙafar ta a nutse dan ta fito su gaisa, ko da suna zaman aure ba ta gaishe shi tsatsaye haka bare yanzu wanda rabon da ta saka shi idanun ta tun daren da ya yanka mata tikitin zuwa gidan su, kuma har yanzu tana jin haushin shi na ɗanyen hukuncin da ya yanke mata, amma ba zata gagara girmama shi ba tunda dai anyi zaman amana. A nutse ta fito har lokacin bata kalle shi ba, cikin nutsatsiyar murya tace "Ina wuni?" Da fara'a Alhaji dake binta da wani irin kallo yace "Lafiya lau maman auta, ya kike? Ya kuma kwana biyu?" A matuƙar tausashe ba tare da ta kalli inda yake ba tace "Lafiya lau wallahi, dama Kuwailat na kawo, ni zan wuce." Da fara'a ya ɗora da "Da wuri haka? Ko ciki b zaki shiga ku gaisa ba?" Murmushi tayi kanta na ƙasa tace "Sauri nake, dama daga gurin karɓo ɗinkin Kuwailat muke, wani lokacin na shiga." Jinjina kai yayi yace "Shikenan, ya kuma shirye shirye? Nabila ana shirin amarcewa." Murmushi tayi a taƙaice kawai tace "In sha Allah." Ƙara buɗe murfin motar tayi zata shiga tana faɗin "Na wuce, sai anjim..." Again muryar Aliyu ce ta sake dukan kunnuwan ta wanda suke tahowa shi da Jabir, farin cikin ganin su ya saka Aliyu yin murmushin jin daɗi yace "Gaskiya aunty ni dai ban yarda da wannan abu ba, kuma ni sam ban gane komai ba." A nutse Ummu ta juyo ta kalle shi, shadda ce jikin shi da ta masa kyau irin ɗinkin zamani, sai Jabir da ya ƙara rage kuzarin tafiyar shi yana ƙare mata kallo yana ayyana _"Wato Maama an fara koyon bidi'a, tsabar a nunawa duniya yanzu ba'a tare da mariƙi shine har da saka sange."_ Ummu ko fuskar shi bta kalla ba da ta fahimci yau shigar ta shi da ta Aliyu kusan iri ɗaya ce, saida suka ƙaraso Aliyu yace" Ina wuni aunty?" Da fara'a ta sadda kai cike da kunya tace" Ina wuni Yayan yara?" Da girmamawa ya amsa da" Lafiya lau auntynmu, ya kuma kuke tsaya nan Abba?" Yayi maganar yana kallon Abba dake ta kallon fuskar Ummu, haɗe fuska yayi ya kalli Aliyu yace" A ina kake son ganin mu?" Murmushi Aliyu yayi bai ce komai ba, hakan yasa Ummu da tayi murmushi ita ma ta ƙara buɗe ƙofar mota ta ɗaga ƙafar ta ta shiga, zata zauna Jabir da tun haɗuwar su bai ce komai ba yace" Maama, ina hijabin ki kuma? Na ga da shi kike sakawa? Baki san ubangiji ya ce ku rufe al'aurar ku bane? Ke kuma gashi wiyan ki, hannayen ki duk a fili." Kamar dai yadda kasan uba da ƴar sa, sai ya ƙara haɗe fuska har da girgiza kai ya goya hannayen shi baya yace" Ki daina haka kin ji Maama? Babu kyau, kuma mu ma ubangiji zai tambaye mu saboda mun gani kuma bamu tsawatar miki ba." Narai-narai tayi da idanu, ta kalli Alhaji da shi kuma yake kallon Jabir da mamakin ƙarfin halin shi, sannan ta kalli Aliyu da shima har da karkace kai yana kallon Jabir ɗin, take taji idanun ta suna neman kawo ruwa saboda saurin kuka da take da shi, ba dan komai ba sai dan jin wai Jabir, Jabir dai, Jabir dai yaron nan ne ke kora mata wannan kashedi haka mai kama da gargaɗi, Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! Wai me yasa Jabir yake abu kamar dai bai san manya bane? Da gasken gaske harara ta watsa ma Jabir karo na farko a rayuwarta, ga idanun ta da suka cika da ƙwalla, hakan yasa Jabir dake kallon hararen da mamaki yake hango wasu abubuwa na daban a cikin idanun nata. Cikin rawar murya kamar zatayi kuka tace *"Na san da haka tun kafin a haife ka, kuma ai ba tsirara na fitowa ba, sannan wuyana rufe yake da mayafi, ban ce ka kalli can ba bare ka gani, kar ka sake min irin haka ni ba tsarar ka bace."* Shi kam sai ya ma manta da akwai wasu bayan shi da ita, ita kawai yake kallo wani sabon yanayi na sake hauhawar masa na ɓacin ran akan me za ta ƙi karɓan gaskiya? Hakan yasa shi saida ya tako kus da Aliyu ba tare da ya rusuna duban shi kan ta ba yace" *Abba ma yayi ba daidai ba zan gaya mishi gaskiya, kenan sheɗan fitsari yake miki a ka Maama? Wace sura kika karanta kafin haihuwar tawa?*" Duk dauriyar Aliyu saida ya tintsire da dariya yana rufe baki, Abba kuma kallon su kawai yake da wani sahihin murmushi a fuskar shi yana jinjina kai, da yanayin jin haushi tna jin kamar ta mare shi tace" Kai ai kasan na karanta dayawa kafin ka yi wayo, ka daina min rashin kunya Jabir." Sama da ƙasa ya kalle ta, sai kawai ya taɓe baki yace" Ni dai na gaya miki kar ki sake fita babu rufi a jikin ki, dan ubangiji zai ƙona ki, ni da Abba kuma ai ba zamu so haka ba." Sai kawai ya juya zai bar wurin ya kalli Abba dake ci gaba da kallon su yace" Abba, kai ka gaya mata da kan ka, dan gani take ta haifi kowa anan, bayan bata wuce *a zaneta ba* saboda *ƙuruciya*." Ko waiwayowa bai yi ba ya shige cikin gidan ya bar Ummu na share hawaye, Alhaji ta kalla da ya sauke ajiyar zuciya tace" Kana ganin shi ko? Dan na bar gidan ka shine zai dinga min rashin kunya?" Saida ta shige mota ta rufe ta tayar sai kuma ta leƙo ta kalli Aliyu tana ƙara share hawayen ta tace" Kuma ka faɗa masa kada ya sake kirana Maaman shi, dan ɗan baya wa uwa fitsara." Saida ta tayar musu da ƙura Aliyu ya sake sheƙewa da dariya yana kallon Abba da shima dole ya murmusa yana faɗin" Jabir, wa ya faɗa maka ana ma uwar auta haka? Ita fa ganin ta take ta haifi duniya." Da sauri Aliyu ya wuce ciki yana fadin" Bari 'a je na sanar masa da saƙon nan." Da dariya Abba ya bishi da kallo dan ya san akwai daru a gaba kam, amma kuma ya birge shi ba kaɗan ba, to ai san girman Ummu ya sa take ganin kamar Jabir bai isa ya mata magana yadda ya mata ba, bayan kuma gaskiya ya faɗa mata sannan a nutse da ladabi. Aliyu na shiga ya haɗe da Jabir tare da Hayat suna gaisawa, saida ya bari Hayat ya tafi sannan ya riƙo hannun Jabir yana kallon shi yace "Malam, ya haka wai ? Me yake damunka ne? Maaman ka ce fa yau ka wanke haka tasss?" Yatsina fuska yayi yana ciro wayar shi yace "To sai me? Gaskiya f de ba za'a faɗa mata ba ita?" Sai kuma yayi ƙwafa, wai yaro? Kuma ta ce aka haife shi? Shine za ta ce ta karanta sunan nan kafin a haife shi? Shi ɗin? Nawa take ɗauke da ita wai? Nawane duka shekarun nata? Wata ƙwafar ya sake yi ta jin haushi ya fara danna wayar shi, Aliyu kuma da murmushi yace "Na sani, amma ai sai naga kamar kana jin haushin ta kake magana, sosai fa ka cizga maama." A ɗan hassale ya kalle shi yace "Ka rabu da ni Aliyu." Taɓe baki Aliyu yayu yace "Na ji, amma ta ce in faɗa maka kar ka sake kiran ta da Maama, dan ɗa ba ya raina Maaman sa." Wani kallo ya ma Aliyu, sai kawai ya raɓa shi zai wuce yana faɗin "Ba sai ta faɗa ba ma, ni kaina ba zan sake ba, amma kafin na daina bata isa hana ni faɗa ba yanzu, wai ita me ye matsalar ta? Me take ɗaukar kan ta ne? Haihuwa tayi?" Cikin jin haush yayi tsaki tare da wucewa yana ce ma Aliyu "Muje sabgar gaban mu dan Allah." Karo suka ci da Ahaji da ya ji komai da ya faru, a taƙaice suka mishi sallama da sai sun dawo ya musu addu'ar Allah ya tsare. *Alhamdulillah.* [25/08 à 15:27] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *58* Cike da gajiya da zancen Mama ta sake riƙe haɓa tana faɗin "Yau ni naga ikon Allah ! Ke wai akan Jabir ɗin kike wannan hawayen? Dan ya ce ki daina saka gyalen?" Kallon Mama tayi tana share hawayen, ita kan ta so take su tsaya tace "A'a mama, ni ba dan ya ce na daina bane, Mama yadda Jabir ke min magana kamar wani shi ya haife ni, wai har da ce min kenan sheɗan fitsari yake min a kai? Kuma wai ni yake cewa bai wuce a zane ni ba saboda ƙuruciya, Mama Jabir fa, ke la ai kin san nan yayi wasan ƙasa a tsakiyar unguwar nan ko?" Galala Mama ta kalle ta, ko Jabir yayi wasan ƙasa, ita shekara nawa ne gare ta lokacin? Shekara fa uku ne tsakanin ta da Jabir, girgiza kai tayi ta miƙe tana faɗin" Allah ya kyauta." Ɗaga kanta tayi ta bi Mama da kallon ita yanzu ba ta ga wannan rainin wayon da ya mata ba? Shigowar Nabila da gudu gudu ɗauke da kaya ya sa Mama dakatawa tana cewa" Ke lafiya? Me ye haka za ki shigo a haukace?" Da fara'a Nabila ta kalli Mama sannan ta kalli Ummu tace" Mama, aunty Ummu kinyi baƙo a waje, ana miki magana." Da mamaki dukan su suka maimaita" Baƙo kuma?" Sai Ummu da ta ɗora da" Ni ɗin?" Da zumuɗi Nabila tace" E mana aunty, tashi kije dan Allah, wallahi babban mutum ne." Tsaki Ummu tayi tace "Kuma sai yace ni yake nema? Ke bana son iskanci?" Kallon Mama Nabila tayi tace "Wallahi Mama da gaske ne, a ƙofar gida na gan shi ya ce gidan su Ummu Kulsum yake nema." Taɓe baki tayi tana miƙewa za ta shige ɗaki tace "Ki ce masa ba zan zo ba, jaraba kawai, me zan masa? Yaushe la na fito daga gidan da za'a dame ni." Da sauri Mama ta kalle ta tace "Ke! Zo ki wuce ki ga wanene." Turo baki Ummu tayi cike sa shagwaɓa tace "Mama ban san fa ko wanene ba, kuma Kinga ma yaushe na fara zawarcin?" A tsawace Mama tace "Ke bana son iskanci Ummu, zaki wuce ko sai na raka ki har wajen?" Da sauri ta ɗauki gyalen ta data aje kan kujera ta yafa zata fita tana ta kumbure kumbure, har ta kama hanya Mama tace "Da gyalen zaki kuma fita bayan ɗan naki ya hana?" Juyowa Ummu tayi, sai taji kamar maganar Maman ta fi ma sosa mata rai fiye da ta waccen ja'irin yaron, amma sai tayi shiru tunda ai gaba da gaban ta, ficewa tayi zuwa ga wanda ke neman nata a tsanake. *Tsaye* ta samu dattijon jingine a motar shi cikin manyan kayan da suka ƙara mishi kamala, tana ganin fuskar shi ta sake tahowa a nutse tana gane inda ta taɓa ganin fuskar, tabbas shine wanda ranar suka gani zaune a shagon da suka siyo kayan kicin ɗin Nabila, a tunanin ta kuma kamar shine mai shagon duba da ranar yadda yaran shagon ke ta faman rusuna mishi. Tunda ya hange ta dama yake ta murmushi yana sake ƙare maya kallo, tun rannan dama bai ga wata makusa ba duk da da hijabi ya gan ta , da aka faɗa masa bazawara ce sai ya ji shi fa ya samu kalar matar da yake so, fara kuma doguwa sannan kyakyawa, zahiri kuma ya nuna tana da nutsuwa da hankali sosai. Ummu na ƙarasowa tayi sallama ya amsa a mutumce shima yana gyara tsayuwar sa, gaisawa sukayi sosai da girmamawa kamar sun san juna, kafin daga bisani ya sake gyara tsayuwar sa ya faɗa mata abinda ya kawo shi tare da buƙatar jin ta bakin ta. Ummu da kanta ke ƙasa, wani irin yanayi ne take ji, bata taɓa tunanin akwai ranar da zata risketa bayan Alhaji Kabir zata iya tsayuwa da wani namiji haka ba bayan ba dwan uwan ta ba, kai gaskiya Alhaji Kbir ya cuce ta, gashi kuma basu haɗu sosai ba bare ta masa ɗanyan kan da ta saba. Ba tare da ta ɗago kai ba cikin wannn nutsatsiyar muryar ta ta tace "Ban san me zn ce ba, wannan yanayin, wannan rayuwar, komai sabo ne a gare ni, amma kayi haƙuri idan ba haka ya kama na faɗa ba." Murmushi Alhaji Haris yayi yace "Ba damuwa gimbiya, ai girman ki ne hakan ma idan kikayi, ko shiru kika min ai ni nayi nasara tunda na samu ganin ki ma, bare kuma na ji muryar ki, sai dai zan so a zauna ayi tunani game da lamarina, sai a bani lokacin da zan sake dawowa dan naji amsar da gimbiyar tawa ta yanke." A hankali Ummu ta saci kallon shi, a sakanni ta gane dattijo ne da bai kai tsaran Alhaji Kabir ba, hasalima wannan bai wuce tsaran su Mama ko dai shekara hamsin haka, shirun da tayi ba ta amsa mishi ba yasa shi cexa" Sai dai kuma na manta da wani abu, ban faɗa miki ina da mata biyu ba da kuma yara takwas." Numfashi ta sauke tana sunkuyar da kai tace" Ma sha Allah, Allah ya sanya maka albarka a cikin iyalin ka, sai dai nima ya a shari'ance ya kamata kasan nima me ya fito da ni daga gidan tsohon mijina, sannan ina da ƴa mai kusan shekara sha uku zuwa sha huɗu." Murmushi yayi yace" Ba ki da matsala, idan na sake dawowa ma tattauna sosai akan haka." A hankali ta jinjina kai alamar to, dan haka ya tamabaya to yaushe zai dawo? A taƙaice ta bashi amsa da" Zuwa jibi ma." Da haka sukayi sallama, ta kuma yi sa'a yana shirin tafiya Yaya Luƙman ya zo, saida suka gaisa sannan ya tafi, to shi yake sanar da ita mutumin kirki ne shi dai a sanin shi, amma zai yi bincike a kan shi dan su san wanene shi sosai. Ummu sun ci gaba da shirye shiryen su, inda shirye shiryen ke tafiya da kyau, kuma duk abinda ke faruwa anan a can ahalin Ahlan suna sane, haka suma suna sanin labarin nasu shirye shiryen a wajen Ummu, hatta da Fahad da ke shirin tasowa dan ya zo a yi ɗaurin aure da shi. Wani abu da Ummu ba ta sani ba shine abotar da ta haɗu tsakanin Jabir da Fahad sanadin Hajia, kusan ma za'a iya cewa Jabir ne babban abokin Fahad wanda ke ta zirga zirgan tarban Fahad da abokanan shi da zasu taho, gidan su yayi niyyar sauke su madadin kama wani masauki, hakan ya sa duk da babban biki ne amma labaran komai ke yaduwa tsakakkanin su tamkar dukansu ahali guda ne. Furuncin da Yaya Luƙman yayi cewa Alhaji Haris mutumin kirki ne ya sa da wa'adin da zai dawo ya cika Ummu har tayi shirin tarban sa cikin doguwar rigar abaya da ta fito da ita tamkar balarabiya, a farfajiyar gida suka zauna ta tarbe shi da abun sha, iya haka ma kawai ya nuna masa ta amince da shi kenan, sai dai Ummu ba wai ta amincr bane kai tsaye, za ta so su ɗan fahimci junan su ta gane wane mutum ne shi? Kafin za ta yarda har maganar aure ta shiga tsakanin su. Sun ɗan jima suna hira wannan karan kafin ya gaisa da su Mama, daga nan sukayi sallama bayan ta faɗa masa za dai suyi waya, amma ba za ta ganu ba gaskiya saboda hidimar bikin ƙanwar ta. *Ranar Alhamis* Duk da Ummu ta ga dangin Mama da na Abba sun fara cika gidan saboda bikin Nabila, har ranta ba ta ji komai ba bare ran ta ya ɓace wai dan basu zo a bikin ta ba. Saboda cikar gidan da hayaniya ya sa ta shiga maƙotan su aka mata kitso da lalle, ana idawa daf da la'asar ta shiga girkin da Kawun nata Fahad ya buƙaci da tayi dan tarban baƙin shi daa zasu zo tare, suna hanya ya ce zuwa magriba suna shigowa in sha Allah, dan haka a nutse ta shiga sarrafa girki kala kala da taimakon wanda take aikin a gidan su dake akwai ƴan mata. Kai da kawowa Ummu ke yi kasancexar Nabika ba ta da wata ƙawa sai Naja'atu, sai wanda kawai yanzu ne ta yi su saboda bikin, amma duk ƙawayen nata ta raba hanya da su wasu kuma sunyi aure. Ana kiran sallah ta kammala komai ta killace shi, a lokacin suke waya da Fahad ya shaida mata sun shigo lafiya kuma zuwa bayan sallah isha'i zasu zo su gaishe da Mama da kuma amaryar shi da yake son gani, a haka sukayi sallama ana idar da kiran sallah ta shiga wanka. *Ƙwarai* Ummu tayi mamaki da Alhaji Haris ya kirata ya ce gashi a ƙofar gidan su ta zo zai bata saƙo, ba ta ji daɗi ba dan ta ga ai jiya ma ya zo, kuma ita a tsarin ta fa ba wannan shirmen da sunan hirar soyayya, ta fito ne da niyyar faɗa masa gaskiya bata son irin wannan bazatar, gashi ya katse mata falon Mama da take ma turare saboda zuwan su Fahad tunda ai anyi sallah isha'i tasan yanzu zasu zo, hankalin shi na ga waya sai ƙamshin sanyayyan humrar ta ne ya sanar da shi ta iso,dan haka ya juyo yana aje wayar tare da yin murmushi yace "Gimbiyata, barka da fitowa?" Ba tare da tayi murmushi ba ta amsa da "Ina wuni? Nayi mamaki da ka ce kana nan." Da murmushi ya amsa da "Dole ne, tunda ban sanar dake zuwana ba, amma a gafarce ni, nasan na shiga lokacin ki, dan da alama hidima kike sosai." Gyara tsayuwa tayi tace "Gaskiya kam, d..." Abinda tayi niyyar faɗa ta haɗe saboda saurin da yayi ya buɗe bayan mota yana faɗin "Dama wai tqwa gudumuwar bikin na kawo, na so na turo yaro, na ce dai bari na kawo da kaina." Ajiyar zuciya ta sauke, it dai kam da yasan hakane gaskiya da ya turo ɗin ya fi, saida ya buɗe motar gaba ɗaya sannan ya ɗan juya dama da haunin shi, cikin sa'a ya hangi wasu matasa na zaune, kiran su yayi suna zuwa ya umarce su da su ciro kayan, Ummu na tsaye tana kallo ta ga kowane matashi ya wuce da buhun shinkafa cikin gidan su, ta ɗauka shikenan bayan buhu ukun, amma sai ta ga an ɗauki jarkar mai da kwalin maggi da wasu ledoji da bata san me ye a ciki ba, saida yaran suka gama ya sallame su suna ta farin ciki sannan ya dawo wajen Ummu yace "To gimbiya, ni zan wuce na bar ki kuci gaba da hidima, sai munyi waya ko?" Da mamaki Ummu tace "Amma Alhaji, naga kayan kamar sunyi yawa, ai da baka wahalar da kan ka ba haka." Murmushi yayi yana kallon fuskar ta da yau ma dai babu kwalliya ko ɗis, kafin ya ce wani abu *motar Jabir* ta danno kai layin ɗauke da Fahad a gaba sai wasu zaratan matasan a baya su huɗu, tun yana son ya gano wacece a ƙofar gidan har saida dai jikin shi ya tabbatar masa wacce dai yake tunanin ce, a ƙuntace, a illance, a rikirkice ya ƙaraso da motar ran shi na mugun ɓacewa. Yadda ya faka motar daf da Ummu yasa ta ja baya tana kallon motar tare da yin tsaki sannan ta ɗauke kan ta ta mayar kan Alhaji, murmushi tayi tace "To shikenan, nagode, idan na shiga zan sanar wa da Mama, nasan zata buƙaci yi maka godiya, sai na haɗaku a waya in sha Allah." Shima da fara'ar yace "Ba sai kinyi haka ba gimbiyata, Nabila ai ƙanwar mu ce duka, dan na yi wannan a hidimar ta bana jin wani abu nayi na arziƙi." A haukace, a mugun zafafe Jabir da ya ga wani kallo da ta ma motar sannan ta watsar har saida ya ga kamar bakin ta yayi tsaki, sannan ta kalli wannan garjejen Alhajin tayi murmushi, murmushi fa Maama ke yi gaban wani ba Abba ba, har adon haƙoran ta (haƙorin makka) ya fito yana kallo, me yasa Maama ke yin haka wai? Saboda Allaj wannan wace irin rayuwa ce take son saka kanta a ciki? Kasa ɗauke idannunshi yayi a kanta, duba ne yake yi mata irin wanda yake fatan ta gane me yake nufi ta nufi gida a mutumce ba tare da ta saka shi ya raba wani abin faɗa ba da ita salon a ce bai da kunya, amma yarinyar nan da ita da tarin taurin kunnenta sai ta sake juyawa wajen mutumin da yake iya kiransa da Baba shi ma dan a haifen dai zai iya haihuwarsa domin shi bai ga wani bambanci tsakaninsa da Abban shi ba tana murmushi kamar wata wacce ke neman fitina. "Jabir, motar a kulle take." Fahad ya faɗa yana duban jabir ɗin shi ma ya kai dubansa wajen da jabir ɗin ya zubawa idanu. Buɗe motar yayi suka fita, amma shi ya kasa ciro ƙafarsa bare har ya iya fitowa daga cikin motar, Fahad na ƙoƙarin sake yin magana Jabir yace"Ku je Fahad ina zuwa." Yanayin muryar da Jabir ɗin yayi magana sai da ta bashi mamaki, domin tun ɗazu dai suna hirarsu ne da sakewa, amma a yanzu gaba ɗaya muryar tasa a haɗe ba sakewar nan bare walwala. Bai iya cewa komai ba suka yi gaba Jabir kuwa ya sake zubawa inda take idanu, tunda ya faka motar Alhaji ya lura da irin yadda ta kasa samun nutsuwa, tsakin da take ja ƙasa ƙasa ya fi a irga sai kuma ta ɗan saci kallon motar da ta tsaya daf da tasa ta sake watsa harara ƙasa ƙasa. Murmushi yayi cike da dattako yace" Zan wuce gimbiyata, na ga kamar abokin takarata ne ya zo?" A zabure ta kalli fuskar Alhaji Haris ido cikin ido bayan ta kasance mai ƙauracewa yi masa irin duban nan bakinta har rawa yake wajen furta" Astagfirullah! Alhaji wai waccen motar? Ɗana ne a ciki fa, yaron wajen tsohon mai gidana ne." Yadda ta yi maganar sai da ya saka shi sakin murmushin da bai shirya ba yana faɗin" Ahaf! Duk ɗaya dai gimbiyata, wannan da alama baya son kasancewata a nan, sai dai ya taki sa'a ni ɗin ma tafiya zan yi, sai mun yi waya." A dole ta kauce rai na tuƙuƙi tana duban motarsa har ya ɓacewa ganinta sannan ta juyo da nufin sauke masa nasa rabon kafin ta je gida ta sanarwa Yaya Luƙman ya je ya faɗawa Alhaji a shiga tsakaninta da fitsararen yaron nan, dan ta kula sababin darussa yake neman sauke mata. Sai da ta ja baya da ƙarfi sakamakon ganinsa jikin motar tasa ya zuba mata kakkausan idanuwan da bata taɓa tunanin zai iya wannan kakkausan kallon ba bare ta ce ta taɓa ganinsa ba. Shasheƙa ta shiga yi irin ta dannewa harshenta furucin da yake son amayarwa mai zafin gaske sanadiyar wani irin nauyi da harshen ya mata mai wahalar gaske, a hankali ta ɗanyi siriryar ƙwafa sannan ta juya da nufin tafiyarta, cikin wani irin kaushin murya ta ji muryarsa amma kuma a sanyaye yace" *Maama Kulsum*." Gabanta sai da ya yanke ya faɗi, a ɗan razane ta sake juyowa dan ta samu tabbacin kunnayenta abinda suke ƙaryatawa sai ta ga da gasken dai ita yake kallo kuma yanayinsa ya nuna shi ya yi furucin, duk da jin sunan daban a bakin shi saboda yadda ya furta sunan da sanin ma'anar sa da yadda harafin s ɗin ya ambace shi akan harshe kamar dai yadda a ƙa'idar larabci s ce da ake faɗa akan harshe, amma sai rikicin wanda ya faɗi sunan ya danne duk wannan abun da take ji. A hankali ta ƙaraso tana dubansa har da nuna kan ta da yatsa tace" Jabir, kai ne ke kama sunana haka?" Lmmshe Idanun shi yayi cike da auna rainonta a ma'auni kafin ya buɗe yana kallonta ido cikin ido yace" Dama kin rabu da Abban mu ne dan ki zo kina kula wasu mazan da ko shi na tabbata basu kamo ba? Kin san cewar hakan ba mai yiwuwa bane ba ko Maama? Menene anfanin hakan? Ko tausayin Kuwailat bakya ji? Bakya tausayin Abban mu? Shine zaki fito daga gidansa dan son rai ki zo kina ƙoƙarin fara shinfiɗa banzar aƙidar kula tsofaffin." Rai ɓace Ummu ta kalli fuskar Jabir wanda kafin yanzu hakan wahala yake mata, da matsanancin ɓacin rai tace" Saurara min haka Jabir! Nace ka saurara min haka! Ina ganin idan duniyar maza na ajiye a nan damata ce, ko shi Abban naka bai isa ya hana ni ba bare kai, maganar na fito dan na kula wasu kuwa ka faɗa masa ka kuma tambaye shi ba'asi, abinda na sani shine baku isa ku mayar dani ƙaramar bazawara ba kuma ku hana ni kula waɗanda zasu sake tara min ƙasa ba!" Saida ta nuno shi da yatsa sannan tace" Ya isheka haka na faɗa maka, ni ba tsarar ka bace." Tana gama faɗa ta juya rai ɓace ta nufi cikin gida tana mamakin wai me ye tsakanin ta da Jabir da ya fara mata wasu abubuwa haka? Sai dai shi nashi ran ya ninka nata a ɓacewa, domin shi har idanun shi ke rufewa na mugun tashin hankalin da ya sakawa ransa, mota ya shiga da nufin bari ya je ya gaya wa wanda yake ganin ya isa ya gaya mata ai, dan ko ruwa ba zai sha ba sai ya yi wa matsalar nan tufka, haka yake tuƙi ya bar angwayen ya nufi gida. Bai kula kowa ba dan burinsa ya haɗu da wanda zasu tattauna maganar ko zai iya sauke numfashinsa daidai har ya sada kansa da inda Abba yake, tunda ya yi sallama ya duƙar da kansa yana fitar da numfashi ɗaya na korar ɗaya bayan ya sanar da abinda yake tashin hankali a gareshi wanda yake da yaƙinin shi d'ansa ya ji irin wannan ɓacin ran lalle lalle Abbansu zai je ya mayar da ita ɗakin ta a wuce wajen, amma sai ya ji wata magana mai kama da almara Abban na faɗin" Jabir, ka kwantar da hankalinka mu yi magana, duba ka ga yadda kake shasheƙa?" Kallon Abban yana ayyana _" Ko bai ji abinda ya faɗa ba? Matar sa uwar Kuwailat fa ya ce tana can waje tare da wani."_ Alhaji kuma numfashi ya sauke sannan yace" Haba Jabir sakin Ummu na yi fa, shin dama an taɓa saki a kuma bi mace a ɗora mata ƙa'idar wanda zata kula, tun dai ina kauce faɗa maku dalilin da yasa na rabu da Ummu sai na faɗa? Tunda kai ba yaro ƙarami bane kuma masanin addini ne Bar ka ji, na sawaƙe mata ne dan gudun faɗawarta halaka ta damuwar buƙatuwa, shin hakan laifi ne? Haba Jabir, ka sanyaya lamarin nan a zuciyarka mu kuma bita da addu'a, ko menene ai ya zo da sauƙi tunda ba'a kai ga halaka kai ba ko?" Jabir ya lumshe idanunshi, kansa na sarawa nauyi da kunyar Abba na neman lulluɓeshi, ya Salam! Me ya yi? Ya kai har ya saka Aban furta masa abinda yake siri ne a wajensa, sai dai yana ji a ransa wata aba wai buƙata ba zata kashe UMMU ba dan ta zauna da Abbansu! Me ya sa to ba ta haƙura ba? A sanyaye ya sake duƙar da kai yace" Ka yi haƙuri Abba, in sha Allah ba zan sake ba, sai dai ita Maama ai bata ma iya jan rigimar ba, domin wanda take kulawar yanzun ma dattijon ne." Da farko kamar Abba bai ji da kyau abinda jabir ya faɗa ba har sai da ya kusa fita yace" Jabir zo nan." Jabir ya juyo ya dawo ya sake duƙawa gaban Abba, Aba ya muskuta ya miƙe da kyau yace" Kana nufin wanda ka ganin da Ummu ba mai ƙananun shekarun da basu gaza arba'in bane?" Jabir ya sake jan numfashi a hankali yace" Ta yiwu ya kai tamanin fa Abba." Kuma shi tsakanin sa da Allah ya faɗa. Sai da Abba ya zaro idanu waje yace" Tamanin fa ka ce?" Shiru Jabir yayi ya ƙi cewa komai har sai da Abba da kan shi ya sallame shi kafin ya miƙe ya shiga kai kawo yana ji kamar zai kifa dan ɓacin rai, mene? Ai bata isa ba! Ba zata taɓa auren wanda ya ɗara arba'in ba, dan kuwa ba zata fitar da damuwarta a sakata a hanyar magancewa ba ta sake afkawa wani ramin. *Alhamdulillah.* [26/08 à 00:37] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *59* Duk da ta shigo a hassale amma hayaniyar angaye a falon ta sa ta haɗe komai, tana gama faɗawa Mama ta ga kayan arzikin da Alhaji Haris ya kawo ta wuce ciki, da farin ciki tayi sallama tana kallon Fahad dake kujera ɗaya da Nabila da fuskar ta ke rufe da hijabi cike da kunya, ratsa zaratan samarin tayi tana faɗin "Abbuna, matsa min na zauna kusa da kai?" Kallon Ummu yayi yana murmushi ya kuwa gyara zaman shi yace "Zo nan ta gaban goshina, na gan ki waje ai ke da surukin nawa, shine ko ?" Murmushi tayi cike da kunya kafin ta kawar da zancen ta hanyar faɗin "Abbuna ya hanya? Ina su aunty da. Abbu?" Amsa mata yayi da lafiya lau, kafin ya kalli Nabila da fuskar ta ke rufe sannan ya kalli Ummu yace "Ta ce wai ke kika hana ta buɗe fuska, hakane?" Da fara'a Ummu tace "E Abbu, gyaran jiki nake mata, amma ai sauran kaɗan ka ganta ko?" Jinjina kai yayi ya kalle ta da kyau yace "To ya? Ni fa yunwa nake ji ta gaban goshina." Miƙewa tayi tace "Abbuna, kasan abubuwan da na dafa saboda kai kuwa? Ina zuwa?" *Jibril* tunda Ummu ta shigo ya ƙare mata kallo, duk da ba wata shaida dake nuna masa ba matar aure bace, amma dai kuma alamun na nuna mishi kamar bazawara, sai kuma Fahad ya tabbatar masa ta hanyar faɗin sunan suruki da ya yi, dan haka ya ci gaba da ƙare mata kallo da dukkan wani motsin ta. Kan teburin da ta aje abincin mai kujeru huɗu ta nufa, wanda dole tasa ta raɓa ta tsakiyar hanya da kujerar da Jibril yake, abun ka ga wanda ya san sirri' mace, wanda ya san sirrin duniyanci take ƙamshin nutsatsiyar kulacchar da take anfani da ita da kuma turaren kaya ya dokar masa kai tare da jin wani irin mugun yanayin da ya saka shi gyara zama ya ɗan saci kallon ta, garin haka kuma Ummu dake wuce tana gyara kallabin abayar ta sai kuma ya ji sautin nan na cacas cacasss! Jigida, ya san mecece jigida da kuma sirrinta a jikin mace, hakan yasa ma yake tunanin a cikin turaren da yaji a jikin ta wataƙila ɗayan daga jigidar yake fitowa? Har Ummu ta dawo Jibril na cikin wani irin yanayi na shauƙi da cin burika akan wannan santalele kuma gonar audigar, cikin farin ciki da raha angayen suka ci abinci, inda Ummi ta bar musu tare da Nabila da Naja'atu suna ta hira. *RANAR BIKI* Cike da gajiya da rashin sanin madafa ta ɗaga wayar Fahad da safiyar nan bata san kira na nawa bane ya mata, cikin kaushin murya da kuma zafi zafi Fahad yace "Kinga Ummulele, faɗa min gaskiya zaki kawowa baƙina abincin nan ko kuma a'a?" A ladabce tamkar wanda ya isa haihuwar ta Ummu tace "Abbuna kayi haƙuri, wallahi ka ga Mujittafa ne ya ke ta ce min gashi nan a hanya amma har yanzu shiru, yanzu haka gani ƙofar gida neman cikin yaran unguwar mu sai na basu kuɗin adaidaita su je su kai." Cikin ƙufula Fahad yace "Haba jama'a, tun safe ba wanda ya ci komai, gashi Jabir ne yasan can kuma sun tafi tarban wasu baƙin mu, waɗanda kenan duk baƙi ne da ba zasu iya kai kansu can ba, kuma nace zan je sun hana wai bai dace ba, to na barsu ne da yunwa?" Ɗan shiru Ummu tayi tana sauraren faɗan da yake yi, shi kam dai ai yayi sa'a a rayuwa da duk da dai shekarun su ɗaya amma Allah ya bashi girman da yake iya yi mata faɗa, ya zatayi ita kam? A sanyayr tace" To Abbu ko na zo da kaina na kawo muku? Dan ni dai gaskiya na gaji da ɓata min rai da Mujittafa ke yi." A sanyaye shima yace" Tun tuni da haka kikayi ma, sai kin zo ɗin." Da sauri jin yana neman kashe wayar tace" To Abbu ina ne gidan?" A tsanake yace" Gidan Jabir ne." Saida ta ji wani tuƙuiƙi ya kamata na takaicin da bai sake ta ba har yanzu na abinda yaron nan ya mata sannan ta taɓe baki tace" Ban san ina ne gidan shi ba, kawai ka kwatanta min." A nutse ya kwatanta mata gidan, sai ta ji ai duk tsohuwar unguwar su ne inda suka taso, kawai dai ƴar tazarar kaɗan ce, a taƙaice ita ma ta amsa da" Sai na zo." Sannan ta kashe wayar ta koma cikin gida, saida ta canza kayan jikin ta dan har ta saka wanda suka dace da manyan tukanen da zasu ɗora a wuta dan girkin rana, sannan ta saka mayafin ta tare da ɗauko kwandon abinci bayan yara sun saka mata manyan kulolin a mota da makulli ta fito da sauri da zuwa yanzu zata dawo. A kwatancen da ya mata ram ram ta iso sai gata ƙofaro gidan, daga ganin motar da ta san Jabir na hawa kwanakin nan wacce bata san Alhaji da ita ba gata kuma sabuwa ce dal ta faka ta tsaya, a nutse ta fito daga motar tana riƙe gyalen ta da kallon ƙofar gidn tana kula ayyana _"Lallai Jabir, hala Alhaji ne ya msa kyautar gidan nan? Fitsararren yaro."_ Kwandon ta ɗauka sannan ta nufi gidan tana kiran lambar Fahad, jim kaɗan ya ɗaga yace" Yane ɗiyar?" A mugun tausashe tace" Gani ƙofar gidan." Da sauri yana tasowa dan tarban ta yace" Shigo mu haɗe, ina ciki nima." Ta ƙaramar ƙofa ta shiga tana yin sallamar da ita kaɗai ta ji abar ta, amma Jibril da Yusuf dake farfajiyar ma basu ji ba, saidai suna ganin ta hankulansu suka koma kan ta, a nutse ta gaishe su suka amsa, Jibril dake ta shafar gemu yana kallon ta da fara'a yace "Ta gaban goshin Fahad namu, sannan... Ta gaban goshin duk wani masoyin Fahad." Kallon shi tayi, ummmm ! Zubin shi dai akwai kamala, kamar yadda daga kallon fuska kuma baka bambamce na ƙwarai da akasin haka, murmushi dai ta mishi saboda ganin Fahad na fitowa tace" Nagode abokin Abbu." Sai kawai ta raɓa su ta nufi Fahad da tuni ya kai hannu zai karɓi kwandon tare da cewa" Ƴar, ba dai shikenan abincin ba?" Dariya tayi tace" Abbu kuɗi fa ka bayar masu yawa a maka abinci, na baka iya wannan ai kayi shari'a dani, sauran na mota a manyan mazubai yake." Da dariya Fahad yace" Ki ce sai maza ɗauko sauran?" " Gaskiya." Ta faɗa tana jinjina kai, kwandon ya karɓa zai juya yana faɗin" Ina zuwa?" Da sauri ta riƙo hannun shi tana faɗin" Abbu dakata, na faɗawa Hajia nan fa tare da kai muke amma bata yarda, gani take ana barin ka da yunwa." Dariya yayi yana gyara tsayuwar shi da maida hankalin shi kan wayar Ummu da take saitawa tana kiran Hajia a kiran da zasu ga juna kai tsaye, ba jimawa ko Hajia ta ɗaga dan dama sun yi da ita zata kira ta, ta na ganin fuskar Hajia da ko kwalli bata shafa ba saboda har yanzu bata kammala ida takabar ta ba tace "To Hajajju, gani ga autan naki, kin ganmu ? Kin tabbata yanzu Maraɗi ba babban birnin da autan ki zai gagara haɗuwa dani bane?" Dariya Hajia tayi ta kalli Fahad tace "Autana, ya hidima? An ɗaura aure lafiya ko? Ina su Alhaji (Abbu Mukhtar)." Fahad dake murmushi yace "Duka lafiya lau Mamie, kinga zan kira ku anjima, yanzu zan kaiwa baƙi abinci, su Alhaji kuma suna ɗaya masaukin Abbu (margayi)." Da gamsuwa Hajia tace "To shikenan, ka ranƙwashe min kan matar nan ta kusan ka." Da dariya Fahad yace "Mamie ƴar tawa ? Tunda na zo nan ita ke bani abinci." Da mamaki Hajia tace "To? To ina dattijon (Jabir) da na haɗaka da shi?" Murmushi Fahad yayi tare da ɗan waiwayawa bayan shi ya kalli ƙofar ɗakin yace "Yana ciki Hajia, yanzu ya shigo, ai shi wannan oga ne akan taimakon da yake mana, saidai Rabbi ya biya shi, hatta ruwa ya wadatamu da su yadda bama nema mu rasa." Sai kuma ya jinjina kqi yace "A gaskiya Hajia ta bakin ki, Jabir dattijo ne." Taɓe baki Ummi tayi tana rayawa a ranta _"Hmmmm! Bak san halin shi bane, wai kamar Jabir ne zai dinga mata rashin kunya, kuma ya ce shi dole malami ne."_ A zahiri kuma Hajia ce tayi murmushi tace" Na san zai iya fiye da haka, shiyasa na msa godiya tun kafin ma ranar ta zo." Da fara'a Jabir yace" To Mamie, sai na kira." Sallama sukayi ya shiga ciki yana kallon su Jibril dake ta satar kallon Ummu yace" Kai Yusuf, dan Allah kuje Ummu ta buɗe muku ku ɗauko sauran abincin nan." Jibril ne ya fara faɗin" Ba damuwa." Sai kuma ya kalli Ummu da ke sallama da Hajia yace" Ran ki shi daɗe muje ko? Idan ban takura ki ba fa." Murmushi Ummu tayi ko ba komai magana da girmamawa ai tana birgeta sosai, kai ita fa ko goba zata siya ka mata magana da ladabi zata iya siye kwandon gobar, amma idan ka mata magana a gatsau haka yadda har hankalin ta bai kwanta ba, to fa gaskiya zata fasa siyan ko ɗaya ne tayi tafiyar ta, ai girmama na gaba ma daɗi gare shi, hausawa suka ce wai *bin na gaba bin Allah.*! Haka suka bi bayan ta ta buɗe musu motar suka ɗauko manyan kulolin suka shiga da su, ita kam bata sake shigowa ba a waya kawai ta kira Fahad ta shaida masa ta wuce, amma dan Allah kwanukan nan inji Mama kar komai ya ɓata, godiya ya mata ta wuce abun ta zuwa ta su hidimar. *Duk* abubuwan dake ta faruwa Jabir da bai jima da shigowa ba yana hangen su ta ƙofa, duk da akwai hayaniya a falon saboda akwai maza dayawa, amma dai hankalin shi na Allah ya sa Maama ba sai ta shigo har ɗakin nan ba, tunda dai ai gashi nan ƙarara Maama ta rage jin tsoron Allah yanzu, gashi kuma ta ƙi ma fahimtar ba daidai take aikataxa ba bare ta sabin ta imanin ta. Har ta fita yana kallon ta cikin doguwar rigar shadda kalar kore da ya ƙona sosai, sai zaren da aka mata aikin dashi kalar orange haka ma ɗan kwallin ta da takalmi, gashi yau ma dai babu kwalliya a fuskar ta dan aikin da zasu yi yasa take so da anyi sallah azahar zata tafi wajen kwalliya wacce rabon da ta shafa kwalli a idanu ma ta manta, kwalliya kuma mai sunan kwalliya da ta cika duniya zata iya cewa tun haihuwar matar Yaya Luƙman wacce yaron na nan shekarar sa uku da watanni. Tunda ya ga sun fita da su Jibril bai kawo komai a ran shi ba, sai dai yaji zafi ganin ita ce gaba su suna baya, duk da doguwar rigar ta bata bayyana surar ta ba saboda mai zubin babban riga ce ta maza, alla shi dai akan me za ta shiga gaba? Yana tsaka da wannan tunanin Fahad ya dube shi yace "Dattijo, ina zamu samu manyan farantai?" Kallon Fahad yayi ba fara'a yace "Me ya sa ba ka tambayi Maama ba?" Kallon Jabir Fahad yayi yace "E to, d..." Da sauri Aliyu ma da yau duk kai da kawon da shi ake yi yace "Kai ka kira mana sai ka sanar da ita." Wani kallo ya ma Aliyu mai kama da harara sannan ya miƙe ba tare da ya ce komai ba ya fito ya saka takalmin shi, ɗakin da matashin nan ke kwana ya buɗe dan ya san akwai faranti ko da guda ne, sai yayi sa'ar samo biyu manya kuma wanda ya san ya fi ƙarfin cin abincin mutum biyu ma, juyowa yayi zai fito kawai ya ji wata magana da ta tayar masa da hankali, Jibril ne da Yusuf tsaye ƙofar ɗakin suna hira, wanda tsabar buƙatuwa zuwa ga Ummu da ɗaukar hankali ta sa Jibril kasa haƙura ya jawo Yusuf yake mishi maganar. Tamkar wanda ya shekara bai sha ruwa ba kuma ya gansu kusa da shi yake faɗin "Wallahi Yusuf nake gaya yarinyar nan haukacewa nake idan na ganta, wata irin sha'awar ta ce ke damuna, tunda na zo garin nan fa na kasa kallon kowace mace bare ma na ɗan rage zafi, ita kawai nake gani a idanuna, sannan hancina wannan turaren nata yake jiyo min kowane lokaci, uwa uba kuma... Ya Allah, wayyo... Ahhhhhh!" Yusuf da ya san waye Jibril kallon shi yayi yace" Uwa uba kuma me? Jibril naga wannan ai kamar ba kalar kayan ka bace, sannan ka dube ta da kyau ai ba yarinya bace." Saida ya lashe leɓen shi da ya fara bushe mishi tsabar jaraba yana wani gyara tsayuwa har da ɗan riƙe hantsa yace" *Jigidar ta*, wallahi sautin ta ke mugun tayar min da hankali, wannan cacas cacass... Wow! Wallahi tsigar jikina har tashi take yi, matar nan, na san ba kalata ba ce, amma kana ganin ta kasan t..." Tsabar tashin hankali ne ya sa Jabir sakin farantin hannayen shi da ya ɗauko yana duba su, bai san idanun shi sunyi ja ba saboda ɓcin rai da tashin hankali saida ya fito yana kallon su Yusuf ya ga kowanen su da yanayin mamaki a fuskar shi, bai san duk abinda yake ji wasa bane game da Maama sai yanzu da yake jin wannan maganganun ɓatan cin a kan ta daga bakin yaro kamar wannan da bai wuce tsarar su ba ko ya ce sun girme shi da shekara biyu zuwa uku. Kallon fuskar Jibril yake da kyau da son gano kamar dukan da ya kamata ya ma fuskar shi wanda zai zubo da haƙoran shi waje, amma kuma... Ba haka Allah ya ce ba, sannan bai da dalilin fara dukan nashi tunda ba shi ya halicce shi ba. Dan haka ya gyara tsayuwa yana sake sauke numfashin da yasan idan bai fara sauke shi ba za'a samu matsala wajen fitowar amon muryar tashi, a ɗan rikice muryar shi har rawa take ya fara faɗin "Wataƙila za ka ji na shiga rayuwar ka, amma maganganun nan da kake faɗa akan mace da ubangiji ya halicce ta da daraja basu dace ba, kai musulmi ne, nasan kuma kasan aikata alfasha haramun ne, wani aikin ba sai mun aikata ba ubangiji yake bamu ladar sa ko ya rubuta mana zunubin shi, iya niyyar mu ta wadatar ta kaimi ga halaka, abubuwan nan da kake faɗa niyya ce da ka gama ɗaurata a zuciyar ka sannan kake furtawa a baki, tun kafin aje ko ina bakin ka zai bayar da shaida akan abinda ke zuciyar ka, da a ce mala'ikan mutuwa zai ɗauki ran ka a nan inda kake tsaye, za ka tafi ne da niyyar aikata babban laifin zina, bayan haka abokina, ita mace ce da ta killace kan ta take kuma mutumta kan ta, ka darajta ta ko dan kasancewar ta mace mana, dan nasan idan ƴar uwar ka ce aka ma haka ko ƴar ka ba zaka ji daɗi ba." Ɗan tsaki Jabir ya ja tare da juyawa zai bar su, kai shi har farantin ya fasa kawowa su zo su ɗauka da kan su, aikin banza kawai! To amma sai ya gano ashe dai da rabon ya huce takaicin shi inda ya dace ne madadin wanda bai san hawa ba bai san sauka ba, tunda gashi Jibril ya tari gaban shi cikin zafin kai na matasan da basu san kunya ba cikin kaushin murya yace "Kai a wa malam da zaka nemi shiga abinda bai shafe ka? Akan me zaka dinga haɗa ƴan uwana ko ƴata da wannan maganar da ni kawai ta shafa? Wa ye kai ? Ina ce tunda muka zo nan bayan gaisuwa ko kallon inda kake bana yi, to me zai sa ka shiga harka ta?" Da fa irin tashen balagar nan da son wayance abun kunyar da ya aikata ya ɗora yatsar shi a ƙirjin Jabir yana daddagawa da cewa" Dan Fahad ka zo nan nima haka, kar ka shiga rayuwata kamar yadda taka bata dame ni, dan h..." Ba tare da ya gama faɗa ba Jabir da shi ba wai abinda yake mishi bane yanzu ke ƙona masa rai kamar kalaman da ya faɗa akan Maama, Wa'iyazubillah! Har yana jin sautin abar nan kenan shima? To wai shi wannan abar me ye anfanin ta ne fisabilillah? A cireta mana a huta, amma mata da neman jaraba kala kala, duk hanyar da za'a kasa zaman lafiya sun san ta, gashi shima wannan yana jin sautin abar nan har yana faɗawa wani kuma, ya salam ! Ya salam ! Shi kam ana ɗaura masa aure sa Kuwailat ai umarni na farko shine ta cire wannan jarabar daga kumkumin ya gaskiya, dan baya son tashin hankali a rayuwa wallahi. A ɗan zafafe ne Jabir ya sa hannu ya tura Jibril da nufin ya ɗauke yatsan shi daga kan shi, kamar da wasa Jibril sai ya ji wannan hankaɗa da Jabir ya masa tamkar shirya ta yayi dama sai ko ya zube ƙasa daɓas saboda rashin sanin hakan zai iya faruwa da shi a lokacin. Sh kan shi Jabir bai yi tsammanin zai faɗi ba, amma kuma da ya ga Jibril na kiciniyar tashi a haukace da nufin a shaƙo Jabir ya buga shi ga ƙasa, dan ai gaba ɗaya suffar Jabir irin ta masu laushin nan ce dan halittar shi ma a tausashe take da tattausar tsokaci da ke rufe da tattausar fata. Amma iko na ka Allah sai Jabir ya sunkuyo kan Jibril tare da sake saka hannu ya mayar da shi zaune daɓas tare da ɗaga murya a tsawace kuma a kausashe ya furta "... *Alhamdulillah.* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *60* Da ɗaga murua a tsawace kuma a kausashe har da nuna Jibril da yatsa yace "Ka zauna a wurin nan malam, ban ce ka tashi ba magana nake maka." Sai kuma ya nuna kanshi yana ci gaba da faɗin "Babu daɗi ne irin haka ni kake suffanta *tawa uwar* da duk banzayen kalaman da suka fito daga bakin ka? Kaga ban san ka ba nima, kuma ban so sanin ka ba duk zaman nan da mukayi, kai ka fara *shiga rayuwata* saboda ka *taɓo abu mafi mahimmanci a rayuwata* da ni a wurina *tafi komai*, ta ya kyi wautar tunanin zan iya yin shiru bayan kana aibatata? Bari kaji malam, nasiha kawai na maka saboda haƙƙi ne da yake kaina a kan ka wanda ubangiji ne ya ɗora min ba yadda zan yi, *ka ɗauke idanun ka a kan ga*, idan ba haka ba *komai nake jin zan iya aikatawa a kan ta*. " Ɗagowa yayi daga sunkuyarwa da yayi tare da raɓa Jibril zai fita, a matuƙar haukace Jibril ya miƙe tsaye dan kuwa har Aliyu da wasu biyu daga ciki da suka ga abinda ya faru sun fito suna tsaye suna kallon su, wannan ya sa Jibril cin alwashi har ya bi Jabir da kallo yace "Ita a wa ɗin ka? *Budurwa*? Ko *ƙanwa*?" Cak! Jabir ya tsaya ya lumshe idanu, wani nauyayyen numfashi ya sauke yana so ya saita nutsuwar sa, a saiɓance ya juyo ya zuba idanun shi da har yanzu jajir suke akan Jibril, a wani irin daƙile yace " *Maamana ce*." Wani shaƙiyin murmushi Jibril yayi na jin daɗi sannan yace "Da kyau, to ka ji da kyau, wannan abun da ka min ya sa na ci buri akan Maaman ka, kuma burina zai cika ko ta wace hanya, kai baka san waye ni ba, amma ka je Zinder ka tambaya wa ye *Jibril MC*." Wani malalacin murmushi Jabir yayi ya ɗan kaɗan kan shi kaɗan haka sannan ya taɓe baki tamkar wanda ba ya so Jibril ɗin ya ji me zai faɗa yace" *Mu zuba mu gani*." A nutse ya sake juyawa ya ci gaba da tafiyar shi har ya fice a gidan, Fahad bai san me ya faru ba a waje, amma da ya sani wataƙila a yi ɓatacciya sosai, dan kuwa Ummu ƴar ɗan uwan sa ce, amma shi a ran shi kamar ƙanwa ko wacce aka haife su tare yake kallon ta dan shekarar su ɗaya, ya kuma san Jibril wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda yake ma nasiha da su bar abinda suke su tuba kamar yadda shima ya yi, yanzun haka ba dan sabga ce da yake buƙatar mutane dayawa ba da ba ruwan shi da Jibril da ma ire-iren shi da suka zo maa sabgar nan. Waɗanda suka gani kuma masu nutsuwa ne da basu tayar da zancen ga kowa ba face tsakanin su da suka sake tattauna abun, daga nan kuma suka bar shi kawai ya wuce a zuwan saɓani ne. *An* sha biki sosai an kuma yi lafiya an gama lafiya, an ma amarya kwalliya an ɗauke ta hotuna da ƙawayen da suka zo cika mata taro da kuma ƴan uwa da abokanan arziki, dan zuwa safiyar gobe za'a ɗauki hanya da amarya, hakane yasa tun daren su Yaya Luƙman suka gana da ƴar uwar su har Mama ma ta mata nasihar da zata iya yi mata, inda kuma Ummu da babbar Yayar su Mama da ƙanwar Baba (margayi) sai wacce ke kamar Kaka ga Nabila ta wajen uba ne zasu rakata zuwa ɗakin ta, da wannan shirin aka kwanta huta gajiyar yau da aka ɗauka kafin a shiga ta gobe. *WASHE GARI* Ƙarfe 09:20 mota uku daga wajen sj Fahad ta zo, kamar an ce wa Nabila ga motar da zata ɗauki ran ta nan sai ta fashe da wani kuka, har aka gama ɗaukar iya abinda motocin zasu iya ɗauka a bayan motar su dan tuni motar kaya masu yawan tayi gaba tun daren jiya, da ƙyar su Inna suka raba su har da Ummu wacce ita ma da shirin tafiya ta kwana biyu ne zata bar garin, sai gashi ita ma kukan take, saida Yaya Luƙman ya mata jan idanu yace "Ummu zan fa ci uwar ki, me ye haka wai? Kinga dama dan kina matar mai gidana ne bana son taɓaki, yanzu ko sai in zane ki." Ƙanwar Mama Kubra ce tace "Haba Luƙman, ka bisu sannu mana, dole suyi kuka ai." Ƙwafa yayi bai ce komai ba dan shi fatan shi ya ga tafiyar su kafin ya je kiran da Alhaji Kabir ke mishi wanda tun jiya ya ce ya zo idan baya komai, da ƙyar da suɗin goshi aka raba su kowace ta shiga mota Mama na kuka su suna kuka aka tafi cike da ɗauki da kewar junan su, inda Mama ta shiga bin su da addu'a. Ummu kuma sanin sai an yi ta koke koke yasa jiya ta sa aka maida Kuwailat gida ta ƙi yarda ta kwana, kuma ce mata tayi zata tura a ɗaukoya da wuri dan suyi sallama, share wa ne kawai ta yi idan ta zo ta ga bata nan ai ba zata ga kukan d zatayi ba bare ta ɗaga mata hankali. Hanya kam sun sha ta sosai dan har dare sannan suka shiga, sun samu tarba mai ban mamaki na abinci da sakin fuska, dan kuwa Nabila ma a cikin katafaren gidan nan aka ware mata na ta ɓangaren kamar dai yadda yake burin Alhaji, suna gama ci da sha wanka sukayi ɗaya bayan ɗaya inda Ummu ta musu sallama ta nufi ɓangaren Maman ta anan ta kwana. *MARAƊI* Da ladabi Yaya Luƙman yake zaune gaban Alhaji da shima yake kallon shi cikin dattako yace "Luƙman, kasan me yasa na kira ka?" Girgiza kai yayi ba tare da ya kalle shi ba yace "A'a Alhaji." Numfashi ya sauke sannan yace "Luƙman, shekaran jiya Jabir ya zo nan yake faɗa min ya ga Ummu da wani tsoho suna hira, a yadda ya faɗa min kamar ma ya fini shekaru, sai nake ta tunanin to ita kuma me zai kaita kula wanda ya fini? Bayan kuma ta san abinda ya rabamu da ita, kuma ina tunanin kuma kun sani, amma me ya san kuka ƙyale ta?" Da mamaki Yaya Luƙman ya kalli fuskar Alhaji yace" Tsoho kuma? A gaskiya Alhaji ban san da wani na neman auren Ummu ba bayan Alhaji Haris, kuma ina ga da akwai ko Mama ba ta faɗa min ba ita zata gaya min da kan ta." Alhaji ma kallon shi yayi yace" Wane Alhaji Haris ɗin?" A ladabce yace" Alhaji Haris dai wannan, Mado." Gaban Alhaji saida ya buga da ƙarfi, to ana nan dai, shi kam da ya bar Ummu ta auri Alhaji Harisu ai gara ya maida ita ɗakin shi wallahi, komai lalacewar shi dai zai iya soka mata allurar shi ko da bata tsikare ta da kyau ba, amma Alhaji Haris? Kallon Yaya Luƙman yayi yace "Amma kuma kai kasan da haka kuma ka ƙyale ta take ci gaba da sauraren shi?" Da ladabi Yaya Luƙman yace "E to Alhaji, dake ban san komai a kan shi ba gaskiya sai alkairi, kuma naga sun fara fahimtar junan su." Girgiza kai Alhaji yayi yace "Kayya ! Luƙman ka gaggauta dakatar da alaƙar su koda tana son haka, nasan abubuwa dayawa game da Alhaji Harisu Mado, ba zan ce maka komai ba saboda kar kuyi tunanin alaƙata da Ummu za ta sa na fara mata wannan cunen, amma ka kira Alhaji Sagir ka tambaye shi wa ye Alhaji Harisu Mado, zai faɗa maka komai da ya sani." Shiru Yaya Luƙman yayi na sakanni kafin ya jinjina kai yace" Shikenan Alhaji, nagode sosai, wallahi ban san komai ba, kuma na ɗanyi tambaya a kan shi duk maganganun alkairi ne suka fito daga bakunan waɗanda na tambaya ɗin." Suna yin sallama tun a mota ya kira Alhaji Sagir, dake dama suna gaisawa ma ta waya bai wani tsaya faɗa masa wanene ba, yadda sukayi da Alhaji ya faɗa masa komai sannan ya tambaye shi? Numfashi Alhaji Sagir ya sauke sannan yace" Luƙman, ka datse alaƙar Ummi da Alhaji Haris, a baya ban maka musun shi mutumin kirki bane, amma sama da shekara goma Alhaji Haris maganganu na yawo a kan shi cewa ana hulɗa da malaman duba wanda zamu iya kiran su da bokaye, akwai wasu abubuwa da yake yi da ya sa dole ake zargin shi da shirka ko aikata sihiri, ka ga Alhaji Haris duk kasuwancin d zaka zo mishi da shi indai anyi sallah magriba to baya kula ka koda kuwa kasuwar ta kai ta milyan ɗari, ni nan kaina na neme shi da harka da daddare amma ko wayata bai ɗaga ba, sannan matan shi dake gidan shi yanzu ba sune matan shi na farko ba, waɗannan suna zauke ne saboda dukiya, amma an tabbatar da wata mu'amula ta aure bata haɗa shi da matan shi saboda mummunar alaƙar da yake da tsakanin shi da maza matasa, dan abinda zan iya faɗa maka kenan a kan shi, amma ka sake bincike da kyau ka tabbatar." Zufa yaya Luƙman ya share yana feso iska har Alhaji Sagir ya yanke kiran bai sani ba, ya Hayyu ya Qayyum! Ka ga mutum a mutumce amma ace maka da dai sauƙi ɗabi'ar shi? Ya Allah! Dan kar ya ɗagawa Ummu hankali ya sa bai kirata a lokacin ba dan ya san suna kan hanya, amma fa *gari na wayewa* ya kirata ko tashi ba ta yi ba tana gadon Mama Nuriyya tana bacci a nutse kiran shi ya tashe ta, ya ɗauka zata shiga damuwa ne, amma sai ya ji tace "Allah ya kyauta, nagode Yaya Luda ban sakankance da shi ba, shi kuma Allah ya shirya shi idan mai niyya ne." Kwanan da bata koma ba kenan, duk da bata ji zafin rabuwa da shi da zatayi ba, amma dai halin nashi da aka faɗa abun ya taɓa ta ya kuma bata mamaki, sai take ganin yanzu duk nutsuwar nan tashi? Ya rasa wa zai nema sai maza? Ya Allah! Ƙwarya ƙwaryar walima aka sake danƙarawa a gidan saboda murnar zuwan amarya da kuma Ummu cikin wannan ahali, rana ta biyu kenan da Ummu ta sake caɓa ado na ban mamaki, sannan ta cancare a cikin riga da siket na leshi da ya karɓi jikin ta ya kuma zauna mata ɗas, biki ne dai na taya juna murna da farin ciki, amma a wajen wasu sai ya zama har da yaɗa manufar su a fili wajen babbar jikar margayi Saheeb da aka tabbatar musu zawarci take. *Larwan* ma ya kasance jika ne ga ahalin Ahlan, dan mahaifiyar shi ma ita ce babba ga su Alhaji wacce ta jima da rasuwa, gaba ɗaya shekarun sa basu fi arba'in da biyu zuwa da uku ba, yana da mata ɗaa da yara biyu kasancewar shi riƙaƙƙen ɗan kasuwa kuma mai ilimin boko, ba ra'ayin sa bane auren mace biyu, amma da ya ɗora idanun shi a kan Ummu kuma ya tabbatar bata tare da mijin ta, yanayin ta da sanyin maganar ta, kyawun ta da zubin tsarin ta duka ya birge shi, sai kawai a take ana tsaka da bikin abun ka ga ɗan boko ya sanar da Yayar shi *Nargis* akan yana son Ummu, ɗari bisa ɗari ta bashi goyon baya, sai dai kuma... Ita ta ta manufar da ta sa ta amince bai wuce yadda bata so damar auren jikar Saheeb Ahlan ta kubce musu, ta sani ne yarinyar za ta kwashi arziƙi, dan akwai abubuwa dayawa da Abbu Mukhtar ke yawan furtawa da sunan ƴar sa Kuwailat da Eesha, bugu da ƙari bayyanawa ne ba'a yi ba, amma Alhaji margayi ya mallaka wasu manyan masana'antu ga jikar sa ta farko da aka fara haihuwa wato Kuwailat (Ummu), an bar maganar ne kawai saboda ɓatan ta, amma yanzu tunda ga ta tasan za'a taso da duk wata magana ma dake binne. Haka ma a wajen Jibril da ya sake rikicewa saboda ganin yau Ummu ta saka siket ɗin da ya fito da surar ta, hakan yasa shi tsare Fahad da tambayoyi a kan ta har saida ya gaji ya kalle shi a fusace yace "Wai me ye na damuwa a kan ta? Ka tsare ni da tambaya a kan ta." Saida ya sauke nauyayyen numfashi sannan yace "Fahad, ba zan ɓoye maka ba, gaskiya ina son ƴar ka, kuma wallahi so na aure." Ƙare masa kallo Fahad yayi sannan yace "MC, ka san dai na san ka, kuma nasan komai akan ka, ita kuma ƴata ce." A ladabce Jibril dake son samun hanyar ratsa Ummu yace "Na sani Fahad, amma kuma ai kasan na jima da daina wanana harkar ta banza da ka sanni da ita, ka tambayi Yusuf da su Lawur, wallahi na daina kuma na jima da tuba, idan ka amince ka shige min gaba wajen samun Ummu, zan baka mamaki saboda canzawata." E to! A dai ɗan lokacin nan da ya zauna garin nan bai ji ko ganin shi da harkar mata ba, kuma dama ai yana aure duk da bai jima da yin auren ba, ba zai hna shi damar sake zama na gari ba, saboda yana da tabbacin abun da yayi da Nabila Jibril bai yi rabin sa ba, sai dai shi Jibril ba mace ɗaya yake bi ba, dan haka yace mishi "Ban da matsala da haka MC, kamar yadda ka ji Ummu ba yarinya bace, dan zata iya tsarar ka, sannan ƙaddara ce ta raba auren ta da mijin ta, ba yarinya bace da zan maka sharar fage, ka jaraba shigar da kan ka a wajen ta, idan ta amince da kai zan fi ku farin ciki da haɗin nan, fatan nasara aboki." Wannan magana ta sa Jibril farin ciki da ƙara masa ƙwarin guiwar tunkarar Ummu a wannan yammacin ya sanat da ita abinda yake ji a kan ta, kallon shi tayi irin sama da ƙasan nan, sai ta ga wannan yaro ai ya raina mata wayo ma? Yana tsaran ta a shekaru ne zau ce yana son ta da aure? To wane irin zama zasuyi? Me zai iya yi mata? Me kuma zai ce mata shi yanzu fisabilillah? Take a wurin Ummu ta bashi amsa da "Kayi haƙuri abokin Abbuna, ban ƙ ba, sai dai ba zan iya soyayya da kai ba saboda wasu dalilai nawa, kuma kaga ni ba ya yarinya bace dan ƴata ma na nan budurwa da ita, ko yau ta samu miji aurar da ita zanyi, kag kai kuma ba lalle ma kayi auren fari ba, idan la kayi kuma kana so na a haka nasan gidan ku la abza'a barka ba, amma dan Allah kayi haƙuri idan maganganuna sun ɓata maka rai." Kawai dariya ta bashi, to magana ce take irin wai mai shekara goma sha shidan nan ya zo neman auren ta, shi yanzu ne zata dinga faɗa masa maganganun nan? Ka ji fa dan Allah matar nan, girgiza kai kawai yayi yace" Ƴar Fahad, duka nasan da komai kuma na tunkare ki, kar ki ɗauki haɗina dake wani sabon abu ne ko kuma bai dace ba, nasan kina da ilimi da kuma sanin ta kamata, wanda ma bai kai shekarun ka ya aureka kun zauna bare kuma ni da nake kyautata zaton ba zamu girmi junan mu ba, amma zan baki lokaci kiyi tunani, duk wanda kika ga yana da mata kuma yana son ya ƙara wata to yana da hujja, haka kuma duk wacce kika ga ta fito daga gidan mijin ta, to ba'a son ran ta bane, dan haka ki zauna kiyi tunani..." Raɓata yayi zai wuce yace" Zan kira ki nan da kwana uku dan naji abinda kika yanke, na barki lafiya." Ƙwarai ya soke ta da magana ta hankali, to ya zatayi? Kawai zat yi nazarin ta gani, dan daga jiya zuwa yau ta gane wani girma da duniya da ahalin ntaa suke da shi, ta san ko dan arziƙin ahalin ta yanzu ai ba za'a hana yaro ƙarami ba ma auren ta, bare wannan da ya mallaki hankalin shi, ba tsaran ta bane gaskiya, amma dai tunda ai shekarun su ne ɗaya zata iya maleji a haka, madadin wata rana wanda bai kai shekarun shi ba ya fito mata ya saka ta jin kunyar al'umma ta kasa fita cikin mutane. *Washe gari* baƙi na ta shirin komawar su, Ummu na taya su shirin haɗa kayan su a ɓangaren Nabila suna hirar su, da sallaa Fahad ya shigo suka amsa mishi, duk da sun gaisa haka ya sake gaishe da su tare da faɗin "Ana ta shiri kenan?" Amsa mishi sukayi da "Wallahi kam." Murmushi yayi sannan ya kalli Ummu ya mata alama da ta zo, tasowa tayi ta nufo shi shi kuma ya fita verandar, tana samun shi tace "Abbuna, ina ji?" Kallon ta yayi yana ƙara matsawa daf da ita da mamaki a fuskar shi kamar wani abu ya bashi mamaki ko tsoro haa yace "Wai ƴata in tambaye ki? Dan Allah me ye tsakanin ki da dattijo Jabir?" Saida ta ji gaban ta ya faɗi saboda ita har ta manta da jadawalin shi ma, amma da ya ambaci me ye tsakanin su ya ɗaga mata hankali, da mamaki ita ma tace "Ban gane ba Abbu ? Wani abun ne ya faru?" Saida ya riƙe haɓa sannan yace "Status na ɗora a wayata na bikin nan, shine kawai ya min voice na minti uku yana ja min aya da hadisai wai hakan ba kyau, sannan idan la ɗorawa zan yi wai *na cire na Maama* gaskiya, har da faɗin wai ko bana *kishin ki ne*? Yanzu da na ɗora na san maza nawa ne zasu kalla? Sannan da wace manufar za su kalla? Ki ji fa." Da yanayin haushi Ummu ta sauke numfashi ta wulwula idanun ta sannan ta kalle shi tace" To kai me ka ce mishi?" A sanyaye yace" Ni wallahi tsoro ya bani, yo a kausashe yake magana fa da kuma bani umarni wai nayi maza maza na goge kafin a fara gani, sai kawai na goge." Da jin haushi ta kalle shi tace" Abbu kenan umarnin sa ka bi?" Girgiza kai yayi yace" Ba wani abu bane ai, ko da dai kamar ƙanena ne amma dai ai gaskiya ya faɗa mana." Ɗan tsaki ta ja ta juya zata koma ciki, da sauri ya ce" Karɓi nan ƴata." Enveloppe ɗin da ya miƙo mata yasa ta sa hannu ta karɓa yana fadin" Ki ba wa baƙin mu su sha ruwa a hanya." Ta ji daɗi sosai dan ta gane enveloppe ɗin akwai nauyi a ciki, ga kuma goma ta arziƙi da Hajia ita ma ta haɗa musu zasu tafi da shi, su da basu zo da kaya dayawa ba sai gashi suna ta gangamar kaya jaka jaka sabda abubuwan da aka haɗa su da shi. Haka baƙi suka kama hanya musamman a motar gida, inda suka bar amarya da kewar su da kuma halin ta da yi mata fatan zaman lafiya, daga nan Fahad da Nabila suka fara kalar nasu zaman mai cike da kunyar junan su da nadamar rayuwar da sukayi a baya, ilimin da Nabila ta samu a yanzun ya mata anfani sosai musaman wajen zama da mijin ta, ba ta ɗaga idanun ta akan nashi, ba ta ɗaga muryar ta fiye da tashi, ba ta ɓacin rai ga buƙatun shi, suna mutumta juna da kuma salon soyayyar su mai tsafta, sai kuma barkwanci da Fahad kan saka a zaman nasu wanda yakan ƙarawa tarayyar tasu armashi. *Alhamdulillah.* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *61* *Kwana* tara kenan yau da tarewar Nabila, kuma yau Alhaji Abbas ya zo da maganar Larwan gidan, yadda Ummu ta ga duka iyayen suke ta farin ciki da lamarin sannan ita kan ta ta ga bata da wani dalili na ƙin shi, ɗan uwan ta ne, sannan yana da mata, kula shekarun shi sun haura nata, yana da ilimi da wayewa ga kuma kyau da tsari, to me ya rage mata ita kam, sai kawai ita ma tayi amanna da shi tare da ƙara watsar da maganar Jibril wanda dama ko da ya kira ta sake faɗa masa yayi haƙuri fa, sai dai baiyi haƙurin ba yana kiran ta, idan ta ɗga zasu gaisa ya sake jadadda mata ƙudurin shi, gane hakan ya sa ma ta daina ɗaga kiran, sai dai saƙo a ƙalla yana turo mata goma ko sama da haka a wuni, tun bata kulawa har kalaman nashi ke ɗan so su kama hankalin ta. To ama da ta haɗu da Larwan da take ma laƙabi da *Yayana*, wanda komai yana yin sa ne kai tsaye musamman ma da yake ganin zai samu kulawar da ya rasa a wajen matar sa daga Ummun, hakan yasa shi kan shi yake zaƙewa wajen nuna mata kulawa da soyayyar sa. Tana kwance kan gado da wayar ta tana shan soyayyar ta da Yayan ta sai faman dariya take, muryar Mamie Nuriyya ce ta daki kunnuwan ta tana ƙwala mata kira da sunan da suka saba wato aunty, da sauri ta tashi zaune tana amsawa da "Na'am aunty." Sannan ta miƙe ba tare da ta ɗauki ɗan kwali ba saboda ta ɗauka Maman ta ce kawai a wurin, tana zuwa ta samu har da Abbun ta yana mata faɗan "Shikenan haka zaku zauna ke kice aunty ita ta ce aunty? Wa ye auntyn a ciki to? Kaga sakarcin banza." Turo baki Mamie tayi tace "To dan Allah ba ƴar farita bace? So kake na dinga kiran sunan ta gatsau ? Bayan manyanmu sun hana mu kuma." Ummu na dariya ta ƙaraso tace "Aunty gani." Kallonta Abbu yayi a tausashe yace "Haba mana babyta, faɗan da nake yi fa kenan." Dariya tayi tace "Ayi haƙuri Abbu, in sha Allah zamu daina." Kallon ta Mamie tayi tace "Kin sauke min ruwan magarya na?" Ɗaga gira Ummu tayi tace "Tun tuni aunty, na san la ya huce." Kallon su Abbu yayi sai kawai ya girgiza kai yace "Allah ya shirya ku." Da dariya kuma a tare suka amsa da "Ameen." Kallon Ummu yayi yace "Baby, Larwan ya same ni akan yana so ya turo a yi maganar auren ku, nace ya bari sai na shawarce ki tukuna, ya kika ce?" Turo baki Ummu tayi cike da shagwaɓa ta faɗo jikin Mamie tana rufe fuskar ta tana faɗin "Ni wallahi Abbu ka daina min haka." Dariya duk sukayi, sai Mamie da ta kalle shi tace "Ta fa amince, ai kawai ka ce ya turo, auntyna fa kullum mafarki take yi, gwara na gaggauta miƙata ɗakin mijin ta." Sai kuwa Ummu ta fashe da kukan shagwaɓa tana kallon Abbu tace "Abbu ka gani ko? Wallahi aunty bata so muna zaman lafiya yanzu, sai ta dinga tsokanata dan kawai na koma wajen Hajia." Zura hannun shi yayi ya kamo na Ummu ya taso da ita yana faɗin "Kinsan ai daina son ki tayi saboda ina tunanin laulayi ta fara, gani take zata sake samun wasu yaran, amma zo nan baby ki faɗa min a kunne na ji." Zaune tayi kusan shi tana wasa da hannun shi kanta ƙasa, sunkuyo kanshi yayi yace "To ya? Kin amince ɗin?" Shiru ta sake yi ba ta ce komai ba, hakan yasa shi shafa kwantaccen kan ta yana faɗin "Ma sha Allah baby, shirun ki ma magana ce, Allah ya miki albarka kin ji, sannan na miki alƙawarin damƙa miki wasu muhimman abubuwa da suke naki ne a ranar da aka ɗaura auren ki." Miƙewa Ummu tayi irin da sauri tana fadin "Ni wallahi Abbu kunya kuke bani." Da kallo suka bita inda Malie ke faɗin "Allah aunty ranar auren ki sai na kwaso shoki." Da sauri Abbu ya kalle ta yace "A ina? Ba dai a gidan nan ba." Saida ta masa fari da idanu sannan tace "A nan kuwa, za ka gani kuma." Kallon Ummu yayi dake daf da shiga ɗaki yace "Auntyn ta Mamie (Hajia) fa na kiran ki a ɓangaren ta." Da ladabi ta amsa da "To Abbu." Ta ƙarasa shiga ɗakin da niyyar ɗauko hijabin ta ta saka sannan ta nufi wqjen Hajiar. A can ta tarar da Nabila da aunty Fa'iza suna ta lissafin abubuwan da za'a yi na sadaka saboda Hajia na daf da fita wanka, tunda ta shigo Hajia ta harare ta tace" Sai da na neme ki ko? Ke wallahi ba dan kama da kike da ni ba da nayi hushi da ke." Gwalo Ummu ta mata tace" Gashi kuma na zama ƙarfen ƙafa." Zaunawa tayi kusan Nabila dake rubuta abubuwan da Fa'iza ke lissafawa tace" Me kuke yi hakane?" Harara Hajia ta sake wanka mata tace" Aiken ki zanyi ni malama." Numfashi Ummu ta sauke tace" Ina kuma?" Gefen ta ta ɗauki jaka ta buɗe ta ciro abinda Ummu na gani ta tabbatar tikitin Hajd ne ko umara ta miƙo mata, tana buɗewa har da passeport na Mama ne da aunty Kubra da Mama Jamila har da Iya da malam Adam, a taƙaice dai Mama da ahalin ta da malam Adam, cikin farin ciki Hajia tace "Mun so haɗuwa da mahaifin Nabila sanda yake da rai, sai dai ubangiji bai yarda hakan ya kasance ba, shiyasa ni da iyayen ki muka tattauna muka ga idan babu shi ai akwai ahalin shi, shiyasa mukayi wannan." Duk da Alhaji Kabir ya kai Mama aikin hadj haka ma Yaya Luƙman yasa tayi umra, amma bai hana Nabila da Ummu rumgume juna ba suna murna da farin ciki, suna cikin wannan farin ciki Hajia tace" To kune zaku mata abishir ɗin sabon gidan ta? Ko kuma ita ce zata muku?" Nan ma sake ruɗewa sukayi sai Nabila data sunkuya ƙasa tana ma Hajia godiya, tallaba ta Hajia tayi tana faɗin ba komai, ita ta musu alkairi ai kuma har yanzu basu biya ta ba. Ummu nata sharar ƙwallan farin ciki da hasaso yadda Mama zatayi Hajia tace" Ke, daina kukan nan je ki shirya zaku tafi kasuwa ke da Nabila." Da mamaki Ummu tace" Amaryar ce zaki fara aika kasuwa?" Kallon ta Hajia tayi tace" To amarya ba'a aiken ta? Kuma ni ba aikena za ta je ba, sautu dai zan baku idan kuka tafi tare, ama Nabila yanzu ai ƴar garin ce, sati kusan biyar yanzu." Turo baki Ummu tayi tace" Ke dai tsohuwar nan, to bari na je, kuma kisa dreba ya kaimu, dan ba zan yi tuƙi ba." Uffan Hajia ba ta ce mata ba har ta fita ta koma na su ɓangaren, tana shiga ta samu kira a wayar ta kiran Yayan ta har bakwai, murmushi tayi tunanin ta shine tunda yau week-end ne baya aiki yana gida kawai neman ta ne yake da fitina dan tana gaya msa bata son shiga lokacin auntyn ta, kenan ɗan dakatawar da tayi bata bashi amsa bane har ya kira ta sau bakwai haka? Dake ba wanka za ta yi ba kaya ta fara canzawa, tana cikin canza kayan ta ji an sake kira, tana zuwa ta ga shine ba ta ɓata lokaci ba ta ɗaga tana murmushi tare da danne wayar da kafaɗar ta dan ta samu ta saka zif ɗin siket ɗin ta tana faɗin "Yayana, rigima ko? Ba nace bana son shiga lokacin auntyna ba?" Wata irin gigitacciyar murya ce aka daka mata tsawa cikin hargagi da ita wnda alamu suka nuna mai muryar ko hausa bata da mai kyau a baki ana faɗin "Auntyn ubanki ne ni, ƴar iska karuwa mai bin mazan mutane, wacece ke? Me kike nema gurin mijina? Ko kinsan da zan iya hallakaki har lahira akan mijina? Kinsan da na ɗauki ranki ni ba komai bane a gurina indai akan shi ne? To bari kiji karamar ƴar iska, mijina ya fi ƙarfin ki, kula shiga gonata tamkar ki tari zakin da yayi shekaru bai ci nama bane, sannan shigowa gidana daidai da yake da kin wa ƙarbarin ki sallama, dan haka kada ki sake kira min miji, ki fita a harkar shi tun kafin nasa a gano min ke sannan na saka rayuwar ki a gararin da kafatanin danginku sai sunyi tofin Allah tsine da kika fito ɗaya daga cikin su, banza ballagaza shashasha." Ƙit ! Ta yanke kiran, hakan kuma ya sa Ummu lumshe idanun ta ta saki wayar ta faɗi, kwaram ta faɗa kan gado tana ambaton sunan Allah a zuciyar ta. Ta san yana da mata, kuma dake ita ƴar uwar sa ce ta ɗan ji labarin wai bata da kirki, bata da halaye na ƙwarai sannan ga rashin girmam shi shi kan shi, amma...amma ai bata ɗauka abun ya kai haka ba, yau ita? Ita da kan ta ce aka faɗawa wannan maganganun? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! Wani irin kuka ta fashe da shi tare da faɗawa kan gado saboda tuno wasu abubuwa dayawa, dama haka zawarcin yake cike da ƙasƙanci da tozarci? Ashe shiyasa duk munin gidan miji iyaye ke cewa ayi haƙuri dai a zauna? Ban da Alhaji Kabir ma da ya ja mata wannan buru'ubar, har wata mace ta isa ta kira ta a waya sannan ta gaya mata wannan maganganu masu zafi haka? Har ita ce ake kira da banza ballagaza shashasha? Ita ba yarinya ba ba komai ba, wacece wannan matar tashi? Wacece ita? Fatan ta ɗaya ace babbar mace ce da shekarun ta suka fi nata, dan ta hakane zata iya yin daidai da ita su gurji junan su, amma idan bata kai ga shekarun ta ko kuma tsarar ta ce, ai ta cuce ta ba kaɗan ba wallahi, kuma ba abinda zai hana ta saka Nabila ta zane lata yarinya ko Abbun ta Fahad, ai ya gaya mata ba abinda ba zai iya yi akan ta ba. Ta ji zafin maganganun nan ƙwarai da gaske, hakan ya sa ta jima tana kuka na takaici, jin motsin Mamie na tahowa tana faɗin "Aunty, wai ba Haj..." Da gudu ta tashi ta shige ban ɗaki dan bata so ta ga tana kukan nan sai ta tambaye ta dalili, ita kuma abun kunya ne ta maimaita kalaman da yarinyar nan ta mata, yo shi kan shi Yaya Larwan ɗin shekarun sa nawa da zai auri wacce ta kai shekarun ta? Ai ya faɗa mata yana son auren ta ne ma saboda shekarun ta zasu killace ta daga aikata masa aikin da kan iya saka shi firgita. Wanko idanun ta tayi sannan ta fito, tsaye ta samu Mamie tana kallon ban ɗakin da taji motsi, da sauri Mamie ɗin tace "Aunty Hajia fa jiran ku take, me kike yi ne wai?" A hankali ta sauke towel ɗin dake fuskar ta ɗan ƙarami ta kalle ta, cikin dakusashiyar murya tace "Ba komai Aunty, ina shiryawa ne kawai ture ya shigar min idanu, kinji masifar zafin." Da mamaki Mamie ta matsa kusan ta tana faɗin "Kuka kikayi aunty saboda turaren ?" Turo baki Ummu tayi ta ƙ magana, hakan yasa Mamie girgiza kai tace "Aunty, ni kal da gaske ke kika haifi Kuwailat? Ko farka ki akayi aka cirota?" Da irin son abar maganar Ummu ta buga ƙafa tace "Auntyyyyyyyy." Da sauri Mamie tayi tace "To shikenan, ama dai gaskiya taɓarar ki tayi yawa, dama Maman ki ta gaya min kina wa dattijon Hajia kuka (Jabir), ai da na so ma nace Abbun ki ya au..." A ƙagauce Ummu ta kalle ta tace "Aunty, zan ƙarasa shiryawa." Dariya mamie tayi tace "To na fita, me ye ba kya so na gani? Nonuwan? Ko uwawun?" Sai kuma ta dakata tana duban ta tace "Ke bari ma kiji, kije ki dawo ki zo ki nuna min nonuwan nan naki, aure fa zakiyi, dole muyi gyara wallahi." Irin kallon nan Ummu ta mata na _"Tofa."_ Hakan yasa Mamie yin murmushi tace" Oh ! Na manta, ashe gyaran da nake tunanin yi miki a gare ku na koye shi... Wayyo Allahna." Ta faɗa tana ƙyalƙyala dariya ta fita daga ɗakin, Ummu ma dariya tayi saida ta ga ficewar ya sannan ta kalli kan ta a madubi, kawai sai ta samu kan ta da latsa nonuwan nata, sai kuma tayi murmushi na jin daɗi, ba ta da matsala da su gaskiya ta nan fannin, to tunda ta yaye Kuwailat wa ye ya kuma jan su? Tayi gyara kamar ba gobe saboda tunanin za ta sake haihuwa, sai gashi haihuwar shiru nonuwan kuma suna nan gidir gidir dasu a tsaye kuma a cike, ƙwarai hilba ta mata anfani sosai ta wannan fanni, haka ma albasa da madara peak da zuma sun taka muhimmiyar rawa, kazalika alkama, dan haka ba abinda za ta ce musu sai godiya. *Idan kuna so zaku iya magana sai mu koyi wannan gyaran na nono in sha Allah.* Da gaggawa ta ƙarasa shiryawa ta fita ta samu Nabila, nan Hajia ta basu kuɗi mai yawa sannan ne ma Ummu ta san me za'a je siya, kayan da za'a yi wainar sadaka ne da kuma cincincin, sai gyaɗa mai suga da kuma wani ɓangare na naman zabi da zasu biya su bawa mai kawo naman shi zai biyo su da shi har gida gobe in ji Hajia. Hak suka je sukayo siyayyar nan suka kamo hanyar dawowa gida kusan bayan la'asar, suna shigowa farfajiyar gidan ta hangi motar Yaya Larwan tasan me ya kawo shi, dan haka ta haɗe fuskar ta har suka tsaya ƙofar ɓangaren na Hajia inda shima anan yake har ma ya gaisa da Haji sannan ya ɗan dakata ya jira su. A mutumce suka gaisa da Nabila sannan t shiga ciki ɗauke da wasu ledojin, inda dreba ya bi bayan ta da sauran kayan, Ummu kuma fuska tamke ta ɗan juya msa baya tace "Barka." Murmushi yayi yace "Ƙanwata, a haƙura ko na rera waƙar da aka yi dan ni da ke?" Sake turo baki tayi ba ta ce komai ba, a hankali ya taka ya fuskance ta yana murmushi, cikin tattausan murya yace "Na sani ni mai laifi ne, amma ayi haƙuri a saurari uzirina." Da mamaki ta kalke shi tace "Uzuri? Yayana wane irin uzuri da ya sa zaka ba w a matar ka waya ta zage ni son ran ta? Ka kuwa san irin maganganun da ta faɗa min? Kaji zagi da cin mutumcin da ta min wanda ba'a taɓa kwatanta yi min shi ba tun da nake a rayuwata? Sannan har wautar matar ka tasa tayi ikrarin ganin bayana." Cike da rashin jin daɗi da takaicin halin *Fauziyya* ya jinjina kai yace" Duka na ji abinda ta faɗa ƙanwata, muna magana dake na ga nayi magana amma baki ban amsa ba, sai nayi tunanin kin ɗan aje wayar ne, hakan yasa nima na tashi na shiga wanka dan ina so na fita kafin l'asar, ina wanka ne naji bala'in ta tana faɗin wai dama amanar ta nake ci? Kenan gaske ne da aka ce zan ƙara aure? Shine fa kafin na suturta jiki na fito ta rufe ni a ban ɗaki, ban ina ƙoƙarin ta buɗe ni naji tana kiran ki, na mata kashedi da gargadin kar ta kuskura amma bata saurare ni, haka ina ji tana faɗa miki mugayen kalaman nan, amma wallahi ƙanwata na ɗauki mataki a kan ta wanda bana jin gobe zata sake maimata min ɗanyen kan nan." Kallon fuskar shi tayi kamar mai son gasgata abinda ya faɗa, sai ta ji ya bata tausayi ma, kuma ai ya ce ya ɗauki mataki akan ta, dan haka ba komai, zata shiga gidan nashi idan ta je ta sace zuciyar mijin ta ita kuma ta bar ta a gantale. Cikin wata mahaukaciyar shagwaɓa da ita kan ta tasan ta wuce misali, amma da dagangan tayi saboda ta fara nuna ma matar shi iyakar ta kawai ta shiga bubbuga ƙafa tana kukan shagwaɓa tace "Uhhmm uhhhm! To shikenan naji na haƙura, amma sai an bani chocolat ɗina." Zuba mata idanu yayi yana jin kamar zai suma dan wani irin abu da yake ji tare da yin murmushi yace "Ƙanwata rigimar ki ko? To in dai chocolat ne ai zan bayar, amma kafin nan albishirinki?" Kallon shi tayi tana murmushi tace" Zuma." Dariya yayi yace" Goro ake cewa." Ita ma kai tsaye tace" To ai bana cin goro." Murmushi yayi yana cije leɓen shi yace" Ashe da wayon ki." Ɗan zaro idanu tayi tace" Yayana, shekaruna fa talatin a duniya, kaga kuwa ai ba abinda ban sani." Dariya yayi yace" Ƙanwata alamu nuna min suke kina da son girma, ke dai baki ƙi ace ni ma kin girme ni ba ko ?" Ajiyar zuciya ta sauke tace" Ba wai son girman nake ba, sai dai ina so idan ka san na girme ka to ka girmamani kawai, raini ne bana son Yayana." Ɗan sunkuyo kan shi yayi kusan fuskar ta cikin raɗa yace" Ina fata dai baki yi kuka ba da Fauziyya ta miki rashin hankali?" Ɗan gimtse fuska tayi ta kalle shi da kyau ba alamar wasa tace" Maganar gaskiya nayi kuka, musamman da na shiga tunanin ya adadin shekarun ta." Numfashi ya sauke yace" Kiyi haƙuri dan Allah, amma na miki alƙawarin share miki hawayen nan ranar da kika tare ɗakina." Rufe fuska tayi da tafukan hannun ta tace" Ni dai Yayana kunya nake ji." Dariya yayi yace" Na sani mana, na sani ai ke ba ruwan ki." Jinjina kai tayi sannan tace" To ina albishir ɗin nawa?" Cikin raɗa ya sake faɗa mata" Abbu ya ce min na turo magabatana, kuma yau zasu zo nema min auren wannan ƴar ƙriniyar, sannan na roƙe su Allah Annabi da su suka mana sati ɗaya a ɗaura mna aure." Zaro idanu tayi tace" Lahhh ! Sati ɗaya ? Wallahi babu mai ɗaura min aure a sati ɗayan nan." "Me yasa? Wani abu zakiyi ne da baki yi shi ba?" Ya tambaya yana tsare ta da idanu, jinjina kai tayi tace "Sosai ma." Da wani mayateccen kallo ya bita yace "Menene shi abun?" Saida ta ɗan matsa daga gefen shi sannan tace "Bacci a gadon auntyna." Tana gama gaɗa ta kwasa da gudu gudu ta shige falon Hajia, dan ta san halin Yaya Larwan zai iya sako mata zancen da zai sa kanta yayi nauyi, da kallo ya bita yana dariya, saida ya ga shigewar ya sannan yace "Ƙanwata kenan, to ai nima da gadajen a gidan nawa ko? Ba sai ki kwanta a can ba." Girgiza kai kawai yayi ya shiga benz ɗin shi ya bar harabar gidan cike da farin cikin haduwar shi da Ummu da zumuɗin Allah ya nuna mishi ranar da zai kwashe yarinyar nan, dan shi ya kasa yarda ma shekarun ya sun kai yadda take faɗa. Haka kuma cike da baƙin cikin halayen Fauziyya da fara dana sanin auren ta a rayuwar shi. *Da dare* kam su Alhaji Abbas da wasu dattawan suka zo nema wa Larwan auren Ummu, cikin farin ciki da shauƙin haɗa dangantaka suka saka musu sati uku mai zuwa a ɗaura aure, dan haka aka tsayar da magana kan washe gari mata zasu kawo kayan tsarabe tsaraben da suka saba, bayan su sun damƙa sadakin su da duk wani abu da ya kamata. An kawo kayan Ummu tamkar na wata budurwa, inda labari ya game duk wani wanda ya san ta ko ya san wanda ya san ta, kai har ma wanda bai san ta ba yana da hoton kayan saboda yawan su, dan harka ce sukayi ta girma da son nuna bajintar su. *BAYAN KWANA HUƊU* Fitowar ta kenan daga wanka tana ɗan cije fuska saboda gajiya da tayi sosai akan kujerar dukkhan, ƙafafun ta ta kalla da har suka mata mijirya sosai, a hankali ta ƙara gaban gado ta zauna tana ɗaukar kofin da dama ta tanadi abun ta, cokali ta sa ta buɗe babban gwangwanin madarar dake gaban ta ta zuba a kofin mai yawan, sannan ta buɗa wata ƙaramar kwalba dake ɗauke da dakakken kanunfari gari luƙui ta zuba kaɗan, haka ta zuba garin dabino shima a ciki da garin aya, ruwan dake cikin flask masu ɗumi ta ɗauka ta zuba ta gauraye, rintse idanu tayi ta kifa kai ta shanye duka sannan ta aje kofin tana sauke numfashi. Miƙewa tayi a hankali ta ƙarasa bakin ƙofa ta buɗe ta ƙwala kiran sunan Adama? Sai da ta kira sau biyu sannan ta amsa, daga nan ta tambaye ta "Ina kaskon wutar da nace ki kawo min?" Da sauri Adama ta taho tana faɗin "Gashi nan Hajia, dama jira nake ki fito." Dawowa tayi ɗakin tana takawa da ƙyar, wallahi jaraba ce tasa take wannan abubuwan, amma fa tun ranar farko data fara ta fara shiga bala'i, wannan ciwon marar nata ya dawo mata sabuwa fil, kuma wannan ma yafi waccen ƙamari saboda wannan haka take wuni kwana uku kenan, marar ta sai tayi nauyi tana yawan murɗa mata, ga kuma ruwa d take yawan fitar ta masu kauri da yauƙi da ɗumi da yake sakata canza pant duk sanda zatayi sallah. Da ladabi Adama da ta aje kaskon tace "Gashi Hajia." A hankali ta kalle ta cikin kasalalliyar murya tace "Nagode Adama." Juyawa tayi zata fita Ummu tace "Adama me kuka dafa? Yunwa nake ji." Gyara tsayuwa Adama tayi tace "Hajia ai Mamie ce ma a madafa, mu kama mata kawai muke yi, amma yanzu na sauke dambun shinkafa da tayi da cabage, s..." Dakatar da ita tayi da "Akwai salade?" Da fara'a tace "E Hajia, shi nake wankewa ma yanzu haka." Jinjina kai tayi tace "To kinga ni nafi son salade ɗin, idan kin gama ki kawo min shi kaɗai kawai." Jinjina kai Adama tayi ta juya tana faɗin "Shikenan Hajia." Saida ta rufo ƙofaro bayan fitar Adama sannan ta sake saka kaskon tsakanin kujerar tsugunno, kanunfari ta ɗauka guda huɗu dake irin na Saudia ne mai yaji ne sosai ta saka a wutar sannan ta zauna kan kujerar tare da rufe jikin ta da kakkaurar dara. Idanun ta a rufe suke tana jin yadda yake shiga jikin ta tana jin zafi, ƙara rintse idanu tayi sosai tana ayyana _"Matsalar kanunfari kenan."_ Gashi daga ya fara shiga jikin ta sai ɓaɓɓago mata da ruwa yake har tana jin suna gangara a jikin ta, sai dai bata tashi daga hakan ba tana zaune saida ta ji hayaƙin ya fara rage shiga jikin ta sannan wutar ta fara ƙauri sai ta miƙe, saida ta sake komawa ban ɗaki ta kama ruwa sannan ta ɗauro alwala ta fito. Tana zaune kan sallaya tana azkhar Mamie ta shigo da flate a hannun ta, zaune tayi bakin gado tana faɗin "Aunty kin idar ? Ga salade ɗin." Jim Ummu tayi kafin ta shafe addu'o'in neman tsarin da ta sba yi bayan kowace sallah sannan tace "Aunty, na idar." Miƙo mata tayi tana faɗin "To gashi." Karɓa tayi ta aje gaban ta sannan ta cire hijabi, a nutse ta ɗauki cokalin mai yatsu ta fara tsakuro salade ɗin da ya ji tumatir da ƙwai da kuma mayonnaise har da cucumber da dankalin turawa, tana fara ci ta kalli Mamie din dake kallon ta tana karantar yanayin ta tace "Aunty, gaskiya fa daga yau na daina yin komai." Tsura mata idanu tayi kamar mai tuhumar ta tace "Me kika daina ɗin?" Sadda kan ta tayi ƙasa tana tsakurar salade ɗin tace "Shan komai aunty, na daina gaskiya." Numfashi Mamie ta sauke tace "Me yasa?" Ɗan ɗaga kanta tayi ta kalli Mamie ɗin da kunya ta sake sadda kanta tace "Bana jin daɗi ne aunty." Shiru Mamie din tayi na wani lokaci kafin tace "Shikenan, zaki iya dainawa, amma idan aka shiga satin sai ki ƙara ko na kwana uku ne." Cike da kunya ta sunkuyar da kan ta, hakan yasa Mamie tashi zata fita, sai kuma ta dangwari kan Ummu cike da raha tace "Aunty ba dai jaraba ba, ni dai wallahi ba haka nake ba, sak abokina kika biyo." Irin taɓararren kukan nan Ummu ta fashe da shi tana sosa inda Mamie ɗin ta ranƙwashe ta amma ba tace komai ba, sai Mamie da ta kai ƙofa tace "Ki gaggauta fa kafin rana ta hantse, kin san zamu tafi siyayyar kayan baccin nan da kuma kwanuka." Da sauri Ummu ta kalle ta tace "Aunty, Abbu ya bayar kenan?" Ɗaga mata gira tayi tace "Me zai hana ya bayar? Ai baya saɓa umarnina." Dariya Ummu tayi saboda yadda Mamie tayi maganar, saida ta fice sannan ta gyara zaman ta da kyau ta maida hankali ta ci salade ɗin nan. *Alhamdulillah.* [28/08 à 11:25] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *62* Siyayyar kayan bacci da kwanuka suke ba ji ba gani, sun fi awa uku suna zaga cikin babban shagon zamanin, kafin Mamie ta nemi zagayawa wajen siyar da kayan ƙwalam, da fari Ummu cewa tayi sam ba zata siyi kayan zaƙi ba, amma sai tace "Aunty ba ni zan sha ba, Kabil ne ke so shine zan siya na tura masa." Wani kallo Ummu ta mata tace "Aunty Kabil ɗin dake ƙasar da ake sarrafa chocolat kala kala, shine zai sa a siya masa anan bayan an turo daga can?" Murmushi Mamie tayi tace "To ai ya ce can tsada ke akwai." Irin kallon nan Ummu ta mata na baka dai yarda da abun nan ba, hakan yasa tace "Da gaske, idan baki yarda ba sati mai zuwa muje New-York ɗin." Murmushi kawai Ummu tayi tare da yin gaba tace "Aunty kinsan Abbu faɗa yake miki idan kina shan kayan zaƙin nan, zan faɗa masa na ce ya sa ido sosai dan kin siyi sababbi." Kallon Ummun tayi tace "Kin ga ni kar ki haɗani da shi, daga nan muna siya zan miƙa gidan mota." Sosai Ummu ta kalle ta, sai kawai ta girgiza kai tace "Ban san mota ta fara zuwa inda Kabil yake ba ai, da tuni na sha mai a tawa motar naje." Shiru Mamie tayi dan ta kula magana ce ta faɗa mata, ƙarasawa sukayi cikin s'a Ummu ta samu kayan ƙwalam na jerin masu ciwon suga wanda basu da zaƙi, ai ko su ta matsa dole aka siya, hakan ya sa Mamue ke ta turo baki tana bata so ita ta fasa siya amma saida Ummu ta siya, sun isa wajen biyan kuɗin kenan Jibril ya shigo neman wani turare da yake aiki da shi, da fara'a ya ƙaraso yana gaishe da Mamie, kafin ya kalli Ummu da wai salo yace "Ranki shi daɗe, da gaske dai kin hanamu ganin ki." Murmushi tayi cik da jin kunyar rashin amsa mishi saƙonnin da har yau yana turo mata tace "Ina wuni?" Da fara'a ya amsa da "Lafiya lau wallahi, ya kike? Ya kwana biyu?" A taƙaice ta amsa da "Alhamdulillah." Sai kuma ya bita da kallon ki tausaya min yace "Ranki shi daɗe, idan babu so me ya kawo gaba kuma?" Ɗan zaro idanu tayi tace "Gaba kuma? Da wa? Anya ni na taɓa yin gaba ma." Murmushi yayi yace "To ba gashi ba, da na ɗaga kirana ma, amma yanzu aka daina, saƙonnin ma da nake turowa ko kulani ba'a yi fa, a ƙalla dai ranki shi daɗe ko sallama a dinga amsa min." Gaskiya kam ! Kuma ta ji ba daɗi da ko sallamar bata amsa mishi, duk da dai ai laifin shi ne dan ta faɗa mishi ma ai suna soyayya da Yayan ta, me ya hana ya shafa mata lafiya shi? Wai shi baya jin kunya ma dan Allah? Idan ta ce ta amince shi yana ganin zai iya da ita ne? Ko da yake laifin ta ne, tunda ai Alhaji Haris take ta sanar da shi yayi haƙuri alaƙar su ba mai yiwuwa bace, sannan ta gode da ƙauna da ya nuna mata da ɗawainiya, daga haka tayi bloquén shi a wayar ta har yau ba su sake magana ba, to shima da haka ta mishi ai da an zauna lafiya. A hankali ta kalle shi tace "Shikenan a gafarce ni, kuma dake kasan ana ta shirin ɗaurin aurena ne, to ni kaina bana da lokacin kaina bare ma waya." Ta faɗa masa hakane dan yaji ya kuma haƙura ya cire ta a ran shi, ai kuwa tashin hankali da damuwa da mamaki suka gani ƙarara a fuskar shi har ya ɗan tambaya a razane" Me? Aure?" Jinjina mishi kai tayi cike da tabbatarwa tace" E wallahi." Lumshe idanu yayi yana ayyana _" Shikenan hatta da alwashin da ya ci a kan ta a gaban yaron nan ustaz ya tashi a banza kenan?"_ A zahiri kuma sai ya furta" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Hasbunallah wani'imal wakil!" Fuskar shi ɗauke da damuwa ya kalle ta a sanyaye tamkar da gaske yace" Ba zan ɓoye miki ba *Nur*, wallahi ban ji daɗi ba, hasalima ban san ya zanyi ba yanzu, ban taɓa jin ba zan same ki ba wallahi." Cike da rashin jin daɗi Ummu ta ɗan kalli Mamie da ita ma tausayin Jibril ɗin ya lulluɓe ta tace" Ayya! Kayi haƙuri kaji Jibril, ni ban san akwai wani abu tsakanin ku ba ai, kayi haƙuri kaji, Allah ya baka wacce ta fita, wanda zata auta yanzu ɗan uwan ta ne na jini." Kallon Maman yayi bai ce komai ba, matsawa yayi kusan da ake biyan kuɗin ya ɗauki siyayyar da sukayi yna ɗorawa dan a lissafa musu kuɗin, ana faɗin kuɗin ya ciro kashh ya biya, Mamie saida ta zaro idanu dan fa duka siyayyar da sukayi ce ya biya, to ya zasu yi da nasu kuɗin? Ba fa zai samu Ummu ba, ya san da haka kuma ya musu wannan wahalar, yana biya kuɗin juyowa yayi kawai ya kalli fuskar Ummu yace "Nagode Nur, sai anjima." Sai ya sake ɗaure jijiyoyin Ummu, wato irin mugayen mutanen nan sun san lagon karya zuciyar mace, Jibril na tafiya ne a hankai yana wani dafe kan shi har ƙoƙarin karo da mutane yake yi da kai wa bango karo, hakan yasa Ummu da suke ya kallon shi Mama na ɗaukar kayan tare da yaran shagon tace "Na shiga uku, aunty kar ya je ya ji wa kan shi ciwo, anya zai iya tuƙi kuwa? Wayyo Allaj, wallahi ya bani tausayi." Shiru Ummu tayi dan gaskiya ita ma wani abu take ji game da yaron, wallahi... To a dai bar kaza cikin gashin ta, haka suka fito daga wurin jikin su duk a mace bayan an loda musu kayayyakin da suka siya sannan suka ɗauki hanya. Suna hanyar komawa gida Ummu ke waya da Mama, da mamaki Ummu tace "mama, da gaske zaku zo? Yaushe?" Daga ɓangaren Mama ta bata amsa da "Ban saka lokaci ba Ummu, Yayan ku nake jira ya saka min ranar, amma ni ko gobe ya ce ga tikiti to zaki ganni." Da farin ciki sosai Ummu tace "Kai! Amma Mama naji daɗi, wai har kun fara kewata haka?" Da irin bsarwa Mama tace "Ke dallah! Kewar ki ɗin ki me? Ni wajen Hajia zan zo, kinga sun fita daga wanka lafiya ban zo na musu barka ba, ga kuma godiya da nake so na zo nayi a madadin su Malam da su Kubra, dan duk sun ce sun ɗora min nauyin, sai kula ɗaurin auren ki da nake so na riska." Da fara'a Ummu tace" Lallai Mama, ki ce dai idan kuka zo sai wanda ya ga komawar ku? To gaskiya Mama Yaya Luƙman yayi maza ya sako mana ku ku dawo nan, dan ni wallahi ina kewar ki Mamana." Murmushi Mama tayi tace" Amma idan na tashi zuwa zan zo miki da ƴar ki, dan kinga dai ranar Alhaji da kan shi yarinyar nan ta taso ya zo ya kawota ana ta rarrashi, shekaran jiya kuma nake gaya miki Aliyu da Jabir ne suka zo ɗaukar ta amma ta botsare ita ba zata koma gidan nan ba, saida fa Jabir ya mata magana cikin tattausan muryar nan tashi, ja'ira yadda kika san uban ta haka ta amsa mishi ba ɓata lokaci." Dariya Ummu tayi tana kallon Mama dake tuƙi tace" Ai Mama Kuwailat har da shegantaka dan taga ba ma dukan ta, ai da zane ta kuka sa Aliyu yayi, in ba haka ba budurwa da ita zata zauna kukan Maman ta." Mama Nuriyya da ta fahimci zancen kallon Ummu tayi tace" Dan taga ita kaɗai ce a gaban ki, ki yi auren nan dai ta ga kin fara haihuwa, za ta nutsu ne ai." Kallonta Ummu tayi tace" Auntyyyy." Mama dake sauraren su cike da goyon baya tace" Wallahi hakane, ai dan ta ga ita kaɗai take wani iskancin, ni dai zan zo miki da ƴar ki." Turo baki Ummu tayi tace" To Mama karatun fa? Haka za ta gintse shi saboda son ran ta." Mama ce tace" A'a Aliyu ne ya ce wai ba damuwa mu taho tare, ni ma nace mishi a'a ya ce ba komai." Girgiza kai Ummu tayi tace" Mama, wallahi Aliyu na ji labari a wajen Zeinab baya ɗagawa yaran gidan nan ƙafa a kan karatu, kawai Kuwailat tausayin bana gidan da kuma kunyata ya sa yake ɗaga mata ƙafa, amma ku bari zan kira shi yanzu muyi magana, kun ga sai ku taho kawai ku barota, idan Eesha za ta taho sai su taho tare, dan ko jiya munyi magana da mijin ta (Sa'ad) ya ce shi fa sai ana jibi ɗaura auren zai bar ta ta zo." Cike da gamsuwa Mama tace" Gaskiya dai kam ya fi." Sai anjima sukayi da cewa za ta kira Aliyu yanzun nan suyi magana. ******************** Jabir na ofishin na Aliyu yana nazarin wani littafi sabodz ƙudurin fara rubuta wani abu da yake da, amma yana ɗan bincike a kai da ci gaba da neman sani wanda har yake tunanin tafiya Kano da haɗuwa da malami biyu rak, sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da kuma Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar lemu, a gajiye Aliyu ya shigo yana zama kan kujera tare da ɗaukar ruwa ya sha, saida ya sha sosai ya sauke numfashi ya kalli Jabir da tunda ya ɗaga kai sau ɗaya ya kalle shi bai sake duban shi ba saboda mahimmancin abinda yake yi, wayar shi ya ɗauka tare da kunna data dan ya ga me ke faruwa? Lokacin ne kuma ya kalli Jabir yace "Koyarwa da wahala, ban san ko zaka iya ba?" Ɗan kallon shi Jabir yayi a nutse yace "Me zai hana? In dai zaka biyani da kyau." Maganar biyan nan da Jabir ke yi ya fara saka shi tunanin wani abu, anya zai iya ɗaukar Jabir aiki a makarantar nan kuwa? Taɓe baki kawai yayi ya kalli wayar shi yana faɗin "Sai na haƙura d kai ɗin, dama dai a Ƙur'ani kafi ƙarexa sai kuma Hadith, in sha Allah ba zan rasa madadin ka ba." Kallon shi Jabir yayi sosai yana ɗan murmushi yace "Hakane, amma kasan an ce *ba rabo da gwani ba*..." Jinjina kai Aliyu yayi yace "Gaskiya ne, kuma na sani indai canza murya wajen ƙira'o'i ake nema aka zo kan ka za'a dakata, sai kuma..." Sai kuma ya jinjina kai da irin tabbacin nan yace "Alhamdulillah ubangiji ya baka kaifin harda wanda hakan yasa kake da sani sosai akan tasfirirrikan malamai da dama, kuma kowane ka karanta nashi tafsirin tsaf yake zaunawaa kan ka." Murmushi Jabir ya sake yi tare da furta "Alhamdulillah, nagode Allah da ya sa na zama ɗaya daga cikin rabe-raben mutane, ina da naci akan abu idan ina son hardacewa, abinda kuma ya fi saurin zauna min kai sannan na jima ban mance shi ba, shine idan na hardace shi irin bayan sallah asuba, Alhamdulillah, wannan shawarar malamina ce." Murmushi Aliyu yayi yace" Gaskiya ne, Allah ƙara ilimi mai albarka." A tausashe ya amsa da" Ameen Ya Allah." Shiru suka ɗan yi na sakanni, hakan ya ba Aliyu damar maida hankalin shi kan waya, shi kaɗai kawai yayi dariya, ba wai dan ya cutar da Jabir ko ya ji ba daɗi ba, irin dai abun nan da zai sa kayi magana kai kaɗai haka, cikin raha yana dariya yace" Fahad kenan Abbun Aunty, wato shi ina ga fa har sai an ɗaura auren auntynmu sannan zai daina ɗora status ɗin kayan nan da shelar zai aurar da ƴar shi." Da sauri Jabir ya kalle shi, ba alamar wasa, ba tare da ya san abinda bakin shi ya so faɗa ba kenan ya furta" Kuma da *hoton Maama* ya ɗora ko?" Kallon shi Aliyu yayi ya girgiza kai yace" A'a, kayan ne kawai." Wawuyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ci gaba da abinda yake yi, Aliyu kuma sai ya zuba mishi idanu na daƙiƙu kafin shi ma ya ci gba da abinda yake yi, shi fa Aliyu har ya saki maganar zancan auren aunty, amma Jabir na nan da abun a rai, ƙwarai ya gani wai Maama za ta yi aure? Wallahi dai su Maama anji kunya? A ce an fito daga gidan Abba dattijon ƙwarai saboda wai buƙata, shine aka ce ta samu matashi mai arba'in da kaɗan, to in sha Allah... In sha Allah zai mata addu'a a cikin dare, ba mugunyar addu'a zai mata ba, amma dai gaskiya bata kyauta masa ba, ba zai so idan tayi aure ta sake fitowa wai zawarci ba, ba kuma zai mata addu'ar mijin ya dinga dukan ta ba har ta fito da ƙafafun ta, amma dai zai ce tayi ta mafarkin Abban su kawai... To kuma. Jin kamar addu'ar da yake son yi mata a cikin daren bata dace ba yasa shi jan tsaki ya miƙe ba tare da ya taɓa komai daga cikin kayan da ya zube a teburin ba ya fita farfajiyar makarantar da niyyar shan iska dan yaji a cikin ofishin ma zafi da ƙuncin yanayi yayi yawa. Fitar shi ke da wuya Ummu ta kira Aliyi, bayan sun gaisa take faɗa masa ya riƙe Kuwailat makaranta ya bari zasu taho tare da Eesha, ya ɗan nuna mata ba komai fa shi daga gare shi, amma sai ta nuna mishi yayi dan mahimmancin karatun ta da kuma kasancewar shi malami kawai ba Yaya ba, hakan ya sa ya ji ƙarfin guiwa tare da ƙudurin ba zai sake ma kuwailat ɗin sako-sako ba indai akan karatu ne ko zuwa makaranta. *Ummu* kam suna zuwa gida a ɓangaren na Mamie ake faɗa mata tayi baƙuwa tana nan tana jiran ta a falo, suna shiga ma Nabila na falon tale sake sanar da ita "Aunty kinyi baƙuwa, ta jima fa zaune tana jiran ki." Ummu mamakin baƙuwar take, wacece ? Ba ta san kowa ba a nan bayan ƴan uwa, dan haka tace la Nqbila "Wacece wai ? Ta jima ne?" Tana gaba Ummu na baya tace "Gaskiya ta jima aunty, tafi awa zaune muna ta hira." Taɓe baki Ummu tayi ta ƙarasa shiga sai Mamie sake baya tana tsaye masu aiki na fito da kayan da suka siyo, suna shiga Nabila ta kalli matar da ta gaji da zama, amma abinda ya kawota ya sa ta dake ta kuma haɗe har tale sakar wa Nabila fuska tace" Yawwa aunty ga aunty Ummu." Wacce Nabila ta kira da aunty ba ta wuce tsarar Nbilan ba, ita kan ta Nabila duniya ce da kuma girmamawa yasa take kiran ya da aunty, ba wai dan ta girme ga ba. A nutse Fauziyya ta taso da fara'a sosai tana tunkaro Ummu da faɗin" Sannu da zuwa aunty Ummu, sai yanzu ? Ai na jima i..." Kafi ta ƙarasa faɗa ta kawo daf da Ummu, tana zuwa kuma cikin ƙarfin hali da rashin kunya ta jefar da gyalen dake saman kafaɗar ta, ba tare da tunanin komai ba ta ɗaga hannu sai kuwa a fuskar Ummu ta ɗauke ta da mari... Mai aikin dake biye da Umlu saida ta saki ledar da ta ɗauko, dan ita kawai tsbar tashin hankali ta hango yadda yau Abbu Mukhtar zai hargitsa gidan nan ne saboda an taɓa babynshi. Haka ma Nabila da ta juyo a haukace ta kalli matar tana ayyana _"Dama tsinanniya ce ta tarba?"_ Takaici, baƙin ciki, dana sani, al'ajab, mamaki, ruɗu da toshewar kai suka saka Ummu zaro idanu kawai ta kalli matar da bata fi tsarar ƙanwar ta ba, gata kuma bata da suffar mahaukata saboda shigar ta da jikin ta, hasalima kyakyawa da ita duk da dai bata kai Ummu kyau da haske ba. Hango kalar dukan da zata mata ne ta fara yi yasa ta saki jaka da wayar ta tare da zame gyalen ta duk ta jefar a ƙasa... Ta ɗaga hannu kenan za ta kai ga jikin Fauziyya, wace ita kuma ganin ta mari Ummu ta ci gaba a kan ta na farko kamar yadda malamin ta ya faɗa mata, sai ta fara ƙoƙarin zaro ƙaramar wuƙar data soke a siket ɗin ta da niyyar yanka wuyan Ummu idan ya so ita la a kashe ta. Sai dai kafin Ummu da ita kanta Fauziyya su aikata abinda sukayi niyya Nabila ta shiga tsakiyar su, ba wanda ya ankara sai saukar mari suka ji a kumatun Fauziyya Nabila ta wanke fuskar ta da shi, kafin Fauziyya ta gane Nabila ce ba Ummu Nabila ta sake ɗauke ta da mari, a gigice Fauziyya ta ɗago bayan tayi ihun da ya karaɗe gidan, amma sai Nabila ta kwashi ƙafafun ta ta zubar ƙasa tare da bi ta kan ta ta fara naushi kamar dama ba ciki take da ita. A nutse Ummu tayi wani shaƙiyin murmushi tareda duƙawa ta ɗauki jaar ta da wayar ta sannan ta kalli mai aikin nan tace "Ki ce Adama ta zo ta ɗauki kayan nan ta kai min ɗakina." Jiki na rawa mai aikin ganin har wasu ma'aikatan sun fara fitowa haka ma Mama ta kwaso a guje ta shigo ta amsa da to ta nufi inda za ta ga Adama, Ummu kuma kan kujera ta ƙarasa ta zauna ƙafa ɗaya kan ɗaya saboda ganin Nabila ce ke ta casa matar da bata san ta ba. A rikice Mamie ta kalli Ummu tace "Aunty me ye haka? Kina kalo za'a yi ɓatacciya?" Ƙala ba ta ce ba sai Mamie da take ta ƙoƙarin ɗago Nabila tana fadin ta daina mana me ye haka? Nabila kua yadda ka san mai aljannu fadi take "Aunty Ummun? Aunty Ummun ce zaki ɗaga hannu ki mara? Wa ya turo ki? Nawa suka baki? Ƙaramar ƴar iska." Sai da Adama da ɗaya mai aikin nan suka zo ne suka kama ma Mamie raba su Nabila, lokacin har wata mai aiki ta tafi shaidawa, ƙwarai da gaske Fauziyya ita ta zo gidan nan san tayi tijara ta ɗaga hankalin kowa, saboda ta san ahalin Ahlan ai tasan masu kuɗi ne da basu san wahala ba bare ma su iya jagaliyanci, bata san akwai ƴar daba gidan ba gaskiya da ta ɗebo zuga guda sun zo. Ana cikin kiciniyar raba su ɗin nan Fauziyya ta shammaci mutane a haukace ta sa wuƙar nan ƙarama ta yanki damtsen Nabila da lokacin hankalin ta na kan Mamie dake mata faɗan me ya aike ta wannan faɗan? Bayan ita ta ga alamun juna biyu a tare da ita, ihu Nabila tayi tare da dafe hannun ta da tuni ya fara fitar da jini. Kukan kura Ummu tayi ta ɗauke fuskar Fauziyya da marin da ya saka ta sakin wuƙar dan bata yi tsammanin zuwan wani marin ba bayan duk wannan jigatuwa da tayi a hannun Nabila. A gigice ta duƙa zata ɗauko wuƙar Adama tayi saurin ɗaukewa a haukace tana daka wata irin tsawa da tasa mutanen ɗakin kallon ta tana faɗin "Kan ki ɗaya wai? Ƴar gidan uban wacece ke?" Hakan yasa wata mai aiki rusunawa kusan kunnen Mamie ta faɗa mata "Mamie Adama bata da lafiya, idan ta rikice mun shiga uku wallahi." Kafin ma Mamie ta maida kallon ta ga Adama har masu aikin nan biyu sun riƙe Fauziyya gam tana ta kubcewar su sake ta, kallon Ummu take hankali tashe tana faɗin "Kinga wannan jinin da ya fito a hannun wannan? Wallahi sanfuri na zo takanas dan na nuna miki kalar uƙubar da na tanadar miki, nayi alƙawari ne ko zanyi yawo tsirara sai an fito da gawar ki a ranar da aka kaiki gidan mijina, idan har ban zama ajalin ki ba Allah ya haukatani a daren ki na farko da mijina." Daga kalaman ta suka gane me ya faru, Mamie kan ta sai lokacin ne ta ma gane ko wacece, hakan yasa da mamaki ta furta" Fauziyya? Ke ce wai dama?" Cike da fitsara tace" Ni ce, ni ce, da matsala ne?" Girgiza kai Mamie tayi, kafin tayi magana Hajia da Fa'iza suka shigo tare hankali tashe, sai dai suna shigowa Hajia na tambaya" Subhanallah! Lafiya? Me yake faruwa?" Shiru ba wanda ya bata amsa, hakan yasa take ci gaba da kallon mutanen ɗaya bayan ɗaya har ta kalli Nabila dake zubar da jini a hannunnta, matsawa tayi kusan ta tana kamo hannun tace" Nabila, ciwo kika ji ? Wai faɗa kuka yi ne?" Tayi maganar tana kallon baƙuwar matar nan, lokacin ne kawai ta iya kallon fuskar ta, dake da gilashin ta a idanu tar ta gane ta, dan haka tace" Fauziyya? Ke ce wai dama?" A haukace Fauziyya ta kubce daga riƙon da msu aikin suka mata tace" Nice, kula wallahi abin da kuka gani yanzu kaɗan ne idan har kukayi haukan kai wannan yarinyar gidana da sunan matar Larwan." Tana gama faɗa ta juya a fusace za ta fita, da azama masu aikin suka so sake riƙe ta da tunanin ai ya kamata ta fuskanci hukunci, sai kawai Hajia ta masu alamar su ƙyaleta, hakan yasa Fauziyya fita a jigace tana tofar da yawun bakin ta da suka yi jini ga kukkurjewa da duk fuskar ta tayi. Da ƙarfi Ummu ta faɗa kan kujera tana rintse idanu, ya Allah! Ya Allah ! Kawai take ta maimaitawa a zuciyar ta, Hajia kuma Fa'iza ta kalla tace "Dan Allah Fa'iza taimakawa Nabila, jini take zubar wa." A ladabce ta amsa da to ta kama hannun Nabila suka fita, hakan yasa Hajia kallon Mamie tace "Wai me ya faru? Yaushe ma Fauziyya ta zo gidan nan?" Cike da damuwa Mamie tace "Wallahi Hajia ban sani ba, mun dawo wannan take faɗa ma ta tayi baƙuwa, ni na tsaya a ciro kayan da muka taho da su, kawai fa sai wannan hayaniyar na ji Nabila tana faɗin wai Fa'iza ta mari aunty." Irin ɗan tsakin nan tayi tare da zama kan kujera tana faɗin" Gaskiya ba zan juri wannan abun ba, yaushe ma na haɗu da ƴar tawa da za'a dinga kirarin hallaka min ita? Wallahi ba zai yiwu ba." Hajia ma cike da tabbaci tace" Ba zai yiwu ba ko kaɗan, bari Mukhtar ɗin ya zo ayi wa tufkar hanci, wallahi sai dai duka dangi su ga laifina." Ummu dai na jin su, amma ita abinda ta yanke a ranya shine ko su basu dakatar da wannan auren ba ita kam ba zata iya ba wallahi, dan haka ma take sauraren su kawai haka kuma ta wuni sukuku har dare, Fahad ba irin zagin da bai ma Fauziyya ba da ya ga yankan da ta ma Nabila, inda Yaya Bilal ma hankalin shi ya tashi uwa uba kuma Abbu, hakan yasa shi girgiza kai yana kallon Hajia yace "Mamie gaskiya kuyi haƙuri, amma wannan auren bana jin zai yiwu, tashin hankali irin haka? Ba wai tsoron ta ko ba za'a iya bane, sai dai ikrarin da tayi zai iya cutar mana da yarinya ko ma ta salwantar mana da rayuwar ta ta, dan haka Mamie gaskiya na dakatar da auren Baby da Larwan." Cike da gamsuwa Hajia tace" Ka min daidai, kuma ko da baka ɗauki wannan matakin ba ma ni zan ɗauka, da Ummu ta iya masifa ne zan iya yarda ko dan ta koya mata hankali, amma ta je can da halin ta." Fahad dake ta huci jinjina kai yayi yace" Wallhi da ina nan ko? Da saidai Larwan ya zo ya ɗauki matar shi, amma ba abinda zai hana in kakkarya ta wallahi." Yaya Bilal ne yace" Ku dai a yi haƙuri yanzu komai ya wuce, zan kira Alhaji (Abbas) na sanar da shi abinda ya faru, sannan a kira Larwan ɗin a mayar masa da duk abinda ya kawo, nan da gobe a bashi kayan shi, amma zama lafiya ya fi zama ɗan sarki." Akan wannan matsayar suka tsaya Mamie kuma hatta wasu daga cikin kayan da Ummu ta fara bada wa ɗinki saida ta sa aka nemo mata irin su sak ta mayar a akwati nan, washe gari da rana tsaka Larwan ya zo dan shi la kwana sukayi a gidan shi da Fauziyya suna tashin hankali da ta faɗa masa inda ta zo har take alfaharin wai ta zo tayi kashedi, bai taɓa dukan ta ba tunda suke, amma yau da safe saida ya wanwanka mata marin da shi kan shi bai san adadin shi ba, sannan ya watso ta ƙofar gida ya ce ba shi ba ita ya sake ta saki biyu, a ƙofar gidan ya barota tana haukan ba inda za ta je, ai dan ita kawai aka yo shi, dan haka ya je ya dawo zai same ta nan. Duk yadda ya so nuna musu ɓacin ran shi da son suyi haƙuri kar maganar auren nan ta lalace abun ya ci tura, haka suka bashi haƙuri da musu fatan kowa Allah ya haɗa shi da rabon sa, ya shiga tashin hankali sosai tare da ƙara tsanar Fauziyya da ita ta jawo masa, babban abun takaicin shine yadda ya ya je dan ya roƙe su suyi haƙuri, amma sai ya ce ko shine mahaifin Ummu haka zaiyi, dan alamu sun nuna matar shi ta fi ƙarfin sa sannan ba zai iya kula da gidan shi ba, abu kamar wasa sai gashi ganin Ummu ma ya zamar masa aiki, yana so ko sau ɗaya yayi magana da ita amma ya kira wayar ta kashe, kula ta kashe ne dan ya san zai kira ta ai. *Fahad* kuma tun da safe sukayi waya da Jibril yake faɗin "Shikenan Fahad kai ma ka ƙi ni kamar yadda ƴar ka ta ƙi ni." Fahad da baya cikin yanayin daɗi ya tambaya "Ban gane ba ? Me ya faru?" A tsanake Jibril yace "Fahad na farauci Ummu ko Allah zai sa na samu, amma sai jiya muka haɗe da ita take ce min ma zatayi aure wai, ita bata faɗa min ba kai ma kuma haka." Cikin jin haushi ma Fahad yace "Kai dan Allah wannan ma tsohuwar magana, yanzu ai ba maganar aure tsakanin Larwan da Ummu, kuma kaga ita dai ba yarinya ba, dan haka har yanzu a ksuwa take, Jibril idan ka san kana son ta tsakani da Allah kuma zaka min kara ka riƙe ta amana, to ni mai baka goyon baya ne wajen sake fitowa ka nemi auren ta, idan ta amince faƙat." Labari ne ma fi daɗi a gurin Jibril, dan hakan a wurin shi kamar tabbaci ne na Ummu dai za ta zama mallakin shi, a yanzu ba wai so yake ya shiga rayuwar ta kafin aure ya gujeta ba, so yake ya aure ta saboda yadda Fahad ya mishi magana ɗin nan ya san an samu matsala babba, dan haka zai bari su sakankance dayawa har a ɗaura musu aure, sati kawai zai riƙe ta yana riƙe ƙugun ta yana bata wuta, satin nan na cika zai sallame ta shi kuma ya bar ƙasar saboda Fahad ya san zai iya masa ɗanyan kai, ba wai Ummu ba hatta matar shi da yaran shi suyi ta kan su ba bare kuma wata Ummu. *Alhamdulillah.* [30/08 à 10:44] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *63* *Kwana biyu* kenan da faruwar wannan abu da ya sa Ummu lazimtar zaman ɗaki da rage yawan magana, abubuwa ne sun taru sun mata yawa ta rasa yadda za ta yi, tana kwance dai ne tun da safe amma ba bacci take ba kuma ba abinda take sai tunani. Wayar ta ce tayi vibration wanda rashin son hayaniya ya sa ta saka ta a wannan mode ɗin, a nutse ta zura hannu ta jawo wayar daga ƙasan filo, ganin sunan Yayana yasa ta jan tsaki ta mayar da wayar ta aje, saida kiran ya tsinke sannan ta ɗauki wayar za ta kashe, kafin ta kashe saida ta duba kiran da ya mata bata ɗagawa har kira kusan ɗari da shida a kwana biyun nan, tsaki ta sake ja cike da takaici ta gyara kwanciyar ta za ta kashe wayar gajeran saƙo ya shigo wayar daga lambar shi. _"Dan girman Allah ki ɗaga waya ƙanwata."_ Shine abinda ya rubutu a saƙon, to ita wacece da za'a haɗa da girman Allah ta ƙi abun? Yana kira ta ɗaga sai dai tayi shiru kawai, ajiyar zuciya ya sauke cikin wata gigitacciyar murya yace" Haba ƙanwata, saboda Allah ko da ace abinda ya faru bai faru ba tsakanin mu, shin babu girmamawar da zata saka ki ɗaga kirana ko babu dalili?" Rashin son magana yasa a taƙaice kuma a daƙile tace" Kayi haƙuri." A taƙaice shima yace" Na yi. " Sai kuma ya marairaice yace" Ƙanwata, ke ma kin goyi bayan hukuncin da iyayenmu suka yanke? Ummu ba laifina bane abinda Fauziyya ta zo tayi, ban sani ba wallahi, ban sani ba, dan girman Allah Ummu kiyi haƙuri kar ki ce kin fasa auren nan, wall..." Katse shi tayi a saiɓance da fadin" Dan Allah Yaya Larwan, mu bar maganar kawai, mu yi haƙuri da hukuncin da suka yanke, bayan haka ni ba zan iya da wannan tashin hankalin ba, gidan da na baro mu huɗu ni ce ta huɗun, amma wallahi har yau ba zan iya gaya maka wata magana da cikin ukun nan wata ta faɗa min da ta min zafin da ta hana ni sukuni kamar yadda matar ka ta min ba, kawai ina fuskantar wariya ne da shariya a gurin su, idan kaga magana marar daɗi ta haɗa mu to suna ganin na shiga hurumin su ne, amma sai gashi har gidan iyayena, matar da ban auri mijin ta ba ta zo yi min kashedi har da marina a fuska? Yarinyar da bata wuce tsarar Nabila ba, sannan ga ikrarin ganin bayana da tayi wanda ya isa mu tsaya gaban alƙali ni da ita akan wannan furucin.... Ba zan iya ba Yaya Larwan, dan Allah ka manta da alaƙar soyayya da mukayi da kai a baya ya zama tarihi, mu ci gaba da kallon junanmu a matsayin ƴan uwa, bana so wani abu ya shiga tsakanin mu marar daɗi, sai anjima." Tana ji yana kran sunan ta da kar ta kashe wayar ta kashe ta gaba ɗaya ta aje wayar gefe, gyara zama tayi kan gadon ta ɗauki filo ta rumgume tana kallon ƙofar ban ɗaki, ta yi nisa a tunani kamar daga sama ta ji ana bubbuga ƙofar, da sauri ta dawo da nutsuwar ta ga ƙofar a tunanin ta Mamie ce dan haka ta ce "A shigo." A hankali Abbu ya buɗo ƙofar ya shigo yana faɗin "Baby." Ƙara gyara zama tayi da rigar baccin ta mai siraren hannaye tace "Abbu, ba ka fita ba dama?" Bai ce komai ba saida ya zo kusa da ita ya zauna yana kallonta yace "Ban fita ba, Mamin ki ta faɗa min yanzu ɗaki kawai kike zama, kina lafiya? Wani abun yana damun ki ne?" Numfashi ta sauke tana kallon hannayen ta tace "Abbu ba komai." Girgiza kai yayi yace "Um um! Faɗa min ke dai?" A hankali ta sauke numfashi ta kalle shi cikin sanyin murya tace "Abbu, dama haka zawarci yake tattare da ƙalubale? Abbu na fara sarewa da lamarin nan, na fara jin tsoron ko shikenan na rasa adalin namiji a cikin dubannin mazaje." Da sauri Abbu ya girgiza mata kai a sanyaye shima yace "A'a, ba haka bane *magajiya*, ta ki jarabawar ce ta zo a haka, kuma in sha Allah na san ba da jimawa ba zaki samu wanda ya dace, ai har yanzu kina samun masu son ki, kuma zaki samu wanda ya dace da ke da izinin Allah." A ladabce ta girgiza kan ta kamar za ta yi kuka tace" Abbu bana jin hakan zai faru, ni na ma fara tunanin ko butulci na ma Abban Kuwailat, shiyasa ubangiji zai jarabe ni da ra..." Da sauri ya mata alamar tayi shiru yana girgiza mata kai yace" A'a, kar na sake jin kin faɗi haka, ba kiyi butulci ba, shi ma kuma ya san da haka, sannan adalci ya miki, dan haka bana so ki sa damuwar nan a ran ki, dan Alhaji Haris da Larwan sun kubce, zaki samu wani nagartaccen da ya fi su dacewa dake, ina tabbatar miki da haka." Ɗan murmushi tayi ta jinjina kan ta tace" To Abbu, nagode." Hannu ya kai ya shafo kan ta yana murmushi yace" Ki tashi kiyi wanka ki fito, gaba ɗaya auntyn ki ta damu saboda rashin ganin walwalar ki." Murmushi tayi ita ma tace" To Abbu." Tashi yayi ya fita ita ma ta miƙe ta shiga bn ɗaki dan yin wanka. Ba ta wani jima ba ta fito, tana cikin shafa mai Adama da ita kaɗai ce mai aikin da Ummu ta yard take shigo mat ɗaki saboda ta fi samun nutsuwa da ita ta shigo ta tambaye ta a kawo mata abinci nan ne? Amsar ita ce "A'a Adama, gani nan fitowa ma, zan ci a can." Da fara'a ta ams mata ta juya ta fita, ba jimawa kam ta gam shiryaw ta fito, a veranda t samu Mamie da Nabila sun hira inda Mamie ke yankan ɗanyar miyar faku, sai Nabila dake gyaran akaihu tana faɗin "Wallahi Mamie da ba'a samo mana ɗanyar miyar nan ba ko? Ina g fa da na fita da kaina nemn ta." Dariya Mamie tayi ba tare da ta kalli Nabila ba tace "Dole ma ai mu samo ko dan sabon yariman mu." Ƙarasowa Ummu tayi dake sauraren su tace "Auntyna, ba dama mutum ya ce yana son abu ko baya so sai an fassara shi." Duk kallon ta sukayi duk da kuwa Adama ta sanar da su tn zuwa, Nabila ce ta fara faɗin "Shine fa aunty Ummu, har bana so na ce ina sh'a'war wani abun." Kallon ta Mamie tayi tace "Saboda ba ky ao a ce kina da wani abun ko?" Duk murmushi sukayi sai Ummu da ta ja kujera ta zauna, hira suka fara yi har Ummu na cewa Mamie "Aunty, ina so zan je gidan su Ammie (gidan iyayen su Mama Nur), da kuma aunty Murjanatu da ita ma tana ta ƙorafin na ƙ zuwa na mata kwana biyu." Saboda bata son ganin ta a damuwa tace "Ba matsala ai aunty, yaushe zaki tafi? Dan ki sanar da Abbun ki da wuri." Saida ta ɗan yi tunani na sakanni kafin tace "In sha Allah ko gobe ma." Jinjina kai tayi tace "Ya yi, Allah ya kaimu." Da "Ameen." Suka amsa ita da Nabila kafin suka ci gba da hira, nan Ummu sukayi waya da Mama har take sanar da abinda ya faru tsakanin ta da Larwan, sosai Mama ta ji ba daɗi dan gaskiya ta sa rai da auren Ummu da Larwan ƙwarai, haka ta danne nata rashin jin daɗin tana nuna mata tayi haƙuri komai zai wuce in sha Allah. *A* daren Yaya Bilal ya karɓi baƙuncin iyayen Jibril, dan lokacin Abbu ma muhimmin taro yake da shi da yasa bai dawo ba, amma da Yaya Bilal ya faɗa masa abinda ake ciki sai ya ce ya ji da su kawai, Ummu ƴar sa ce, idan ya basu ita ta badu fa, duk da ya ji daɗin jin haka, sai dai wani abu ɗaya da ya ji bai msa ba shine, yadda yake ji a gari ana faɗin ƴan mata ma ya aka ƙarata wajen samun masu so da aure bare wacce ta taɓa auren? To amma ga Ummu har yanzu ko wata ɗaya ba ta yi da gama idda ba sai mza ke fito mata, e ya san tana da ilimin addini, ilimin boko daidai gwargwado, sannan tana da hasken fata da kuma kyau daidai misali. Amma fa kuma Ummu tana da kuɗi, ƙwarai tana da kuɗi, mijin ta ya bata milyan biyar ihsani ga kuma mota dake can garin da ta baro, anan kuma mahaifin ta akwai kasuwancin da ita yake juya ma wanda Alhaji margayi ya bata matsayin kyauta na haifa masa jijar farko daga ɗan sa namiji, sannan Mukhtar yana da kaso mafi tsoka a cikin dayawa daga cikin harkokin da sukayi fice aka san su da su, hakan na nufin *Ummu Kulsum*, *Aisha* da kuma *Kabil* sune kawai magadan shi, Ummu kuma matsayin ta na babba zata iy jan ragamar wasu harkokin ko a yanzu. To wannan tunanin ya sa yaji abun bai ɗan kwanta masa a rai ba, sai kawai ya ce da su faɗawa ɗan qu ya nemi amincewar Ummu tunda yanzu ita ke da ikon zaɓawa kan ta abokin rayuwar ta ba su ba, ko ba komai dai su haka ya musu dan dace ce aka basu ai da ɗan su zai gwada sa'ar sa, idan yayi sa'a sai kaga ya zama magajin wannan katafaren gida da aka gina tamkar an maya za'a mutu a bar shi. Daga Abbu har kawu Bilal ba wanda ya faɗa mata abinda ya faru, da safe ta shirya tsaf ta fita fara ziyarar ta da tayi niyyar yi wunin yau, a gurin ziyarar nata ne Jibril ya addabi rayuwar ta har ma yake faɗa mata ai iyayen ta ne suka bashi damar neman amincewar ta. Abun ya fice mata a rai, tunanin za ta sake komawa wani bala'in ko kula rabuwa ya sa ta nemi yakice Jibril daga jikin ta, ta nuna masa ita tana gaba da shi amma ya ce wannan ba hujja bace, dan haka da irin gatsen nan tace "Idan na amince zan aure ka Jibril, sai dai idan ka yarda zamuyi aure a sati biyun da ya rage a sa ranar da aka yi tsakanina da Yaya Larwan?" Mai nema ne wai ya samu, kamar mai son ƙure ta sai ko Jibril yace "Na amince, wallahi Ummu na amince, ni ko yanzu kika ce zan amince, me zai hana na ƙi amincewa bayan wacce nake so ce zan samu tabbacin ta zama tawa ta har abada." Karon farko da ta ji bata sha'awar yin aure, gaskiya ba ta so a ce ta auri Jibril saboda tsaran ta ne, gaba ɗaya ma auren ya fice mata a rai wallahi, to amma ya za ta yi? Kamar fa wuƙa xe ta sa a wuyan ta kula ta bashi damar yankar ta, ba zai yiwu ta kuma sake kawo masa wani uzurin ba ko dan kar girman ta ya faɗi, za ta zuba idanu ta ga me zai faru kawai, sai dai tana ji a jikin kamar ba lallai alaƙar ta da Jibril ta yiwu ba. Dan kar ya ga kawai tana kore shi ne ba tare da dalili ba sai ta faɗa masa to ta yarda, amma fa bata buƙatar komai sai sadaki kawai, farin ciki a gurin Jibril ba ya misaltuwa saboda zai samu abunda yake so, ba tausayi ko jin wani wai bai dace ba, burin shi dai a ɗaura aure aga me zai faru, duk da ya san ahalin ta suna iya ɗaure shi kuma ya kasa ganin ko da rana, sannan yasan idan za'a bar shi da Fahad to tsaf Fahad zai kirɓa shi a turmi, amma fa haka ɗin, yayi niyya ne sai ya ga kalar zaren dake ƙugun matar nan sai dai daga baya a nemo shi a yanka. Ummu ma da tunda ta je gidan su Ammie ba ta dawo ba, duk da gida ne da ya fi nasu hayaniya da mutane, amma dai ta ji daɗi zama saboda kowa na faran faran da kai, sannan mahaifiyar Maman ta mace ce mai faɗa da zafi akan abu, tana da tsauri da kuma tsari ne da kai daga farko za ka ga takurawa gare ta, amma daga baya sai abun ya birge ka dan zaka fahimci gata ta maka. Kamar yadda zuwan Ummu na farko gidan da ta ga duk aikin gidan nan ƴaƴan kishiyoyin ta ƴan mata ne ke yi saboda ita bata da ƴan mata, sai Ummu ke ganin ai kamar tna azabtar da su ne saboda kishi da ganin ba ita ta haife su ba, sai ranar da ta ga hatta da pant ɗin su ita ke yin tsaye idan zasu wanke tana nuna musu yadda zasuyi, da kuma suka kwana ita da Eesha ta ga yaran komai suna yin shi ne da fara'a da sabawa da shi, ga kuma suke yi a nutse da kuma hankali, sai ta fahimci lallai *ƴa mace* duk muguntar da aka mata indai wajen aiki ne to wallahi *anfanin kan ta ne*, dan ba'a isa a ƙwace wannan abun da aka koya mata ba idan zata tafi wani gidan. *Yadda* suka saba gaisawa bayan kwana biyu ya sa yau ma Alhaji da kan shi ya kira suka gaisa har ya bashi Kuwailat suka sha hira har yana tambayar ta "Amaryar Yaya Bilal ba wani abin da take so?" Cikin shagwaɓa da turo baki Kuwailat ta amsa da "Ni zobe nake so na azurfa, yanzu garin mu shi ƴan mata da samari suke ya yi, sai kuma biscuit ɗin nan dake saka ni kumatu." Dariya Abbu ya dinga ƙyalƙyalawa yace "To ba matsala amaryar Yayana, dake ai maman baby za ta zo, idan za ta koma sai na bata ko?" Cewa tayi "Ah! To ai tare zamu koma, zuwa ne kawai za ta riga ni, amma nima na zo ɗaurin auren Mamana." Hakan yasa Abbu cewa "Za ki iya wannan yawon kuwa? Dan fa da zaren an ɗaura aure za ta tare, kinga ke kuma ba zki iya wahalar nan ba, kin zo daga Maraɗi kin je Zinder, sannan zaku ɗauko hanyar garin mu, ba fa zai wuce kwana biyu ba zaku sake juyawa zuwa Zinder ɗin." Ita Kuwailat ta ɗauka wajen komawa yake nufi, dan hka tace" Zan iya mana Grandpa, ni dai ku tanada min tsarabata, kuma Mamma (Fa'iza) ma ta min alƙawarin tsarabar da nake so." Da tabbaci ya amsa mata da" To ba damuwa, Allah ya kaimu." Da haka Kuwailat ta miƙa ma Alhaji waya ya amsa yana dariya da faɗin" Auta kenan, an girma ba'a san an girma ba, kullum cikin rigima take." Dariya Abbu yayi yace" Haka fa, to ai ta ji kuna kiran ta auta ne, dole ta baku wahala kamar yada kuka so." Dariya Alhaji yayi da irin kunyar nan yace" Gaskiya ne, amma ai in sha Allah Maman ta za ta ƙaryata mata wannan tunanin." Shima murmushi yayi yace" Allah ya aminta." Da" Ameen." Alhaji ya amsa kafin a nutse yace" Amma Alhaji, na ji kamar kuna maganar Zinder da waye waye? Dama shi Larwan ɗin a Zinder yake da zama?" Da irin ka tuno abun nan Abbu yace" Kai! Alhai wai ban sanar da kai abinda ya faru ba ko? Ai tuni aka bar magnar auren ta da Larwan, wallahi wani abu ne ya faru da ya ɗaga mana hankali dole muka janye maganar, matar sa muka kula kamar ba za'a zauna lafiya da ita ba, yanzu haka tabo na nan a hannun Nabila wanda matar ta yanke ta da wuƙa kuma har cikin gidan nan, hakan yasa na ga indai har za ta iya aikata wannan ɗanyan aiki a gidan su Ummu, to ina ga idan an kai ta gidan ta? Ya kenan? Kashe ta zatayi da gaske kamar yadda ta ci alwashi?" Cikin tashin hankali Alhaji ya dinga jajata lamarin, Abbu kuma kawai faɗa masa yake" Ba komai wallahi, ameen nagode da addu'a, ai dake ma za'a ɗaura auren a ranar da aka saka in sha Allah, wani abokin Fahad ne Jibril wallahi ya nuna sha'awar auren nata, kuma duk sharuɗɗan da ta gindaya masa ya amince, sai dai mu musu fatan Allah ya sanya alkairi." Da jin daɗin haka Alhaji yace" Ma sha Allah, Allah ya sanya alkairi, Allah ya tabbatar ya nuna mana wannan ranar." Amsawa yayi da ameen kafin su ɗan taɓa hirar kasuwa, dama suna jimawa suna waya in dai suna yi, to yanzu ma haka sun ɗan jima suna wayar kafin suyi sallama da juna kowa ya shiga harkar gaban shi. ******************* Fahad da bai san me ya faru ba shi dai Jibril ya ce ya bashi lambar yaron nan Jabir, ganin Jabir na harkar kayan maza ma'ana sutura da takalmi irin da agogo har da sauran kayan jiki dai na maza, sannan kuma sun haɗe a bikin shi sai ya ɗauka ai sun zama ɗaya yanzu dukan su, dan haka kawai ya tura mishi bai ce komai ba. Jibril kuma cike da alfahari da son ƙular da Jabir musamman ma da aka faɗa mishi ai ba ɗan tsohon mijin ta bane, kawai dai yaron shi ne da yake ɗauka kamar ɗa shima, yana kira Jabir ya ɗaga kasancewar lambar shi da har a gaban shagon shi ita ce ya saka ake neman shi da ita, dan haka ba ya ƙin ɗaga kira in ai a layin ne yayi sallama. Bai amsa sallamar shi ba, sai magana da ya fara a gadarance yace "Ni ne, Jibril, zuwa yanzu na san kasan da saura kwana shida a ɗaura aurena da *Maaman ka*, na faɗa maka dama kada ka ja dani, idan na so abu ina samun shi ne ta ko wane hali, Jabir ka ke ko? Zan auri Ummu sannan nayi yadda nake so da ita, baka isa ka hana ni ba kamar yadda ba wanda ya isa ya hana ni aikata abinda nayi niyyar aikata mata bayan buƙatata ta biya a kan ta, ina maka murna da maaman ka za ta yi aure." Yanke kiran yayi ya bar Jabir cikin tashin hankali, kifa kan shi yayi a teburin ofishin Aliyu dake ya fara yi wa ɗalibai darasi akan aure, duba da duka karatun da ake musu babu wanda zai koyawa mata da maza yadda ake zaman aure, hakan yasa Jabir ba wa Aliyu shawara a ware mata daban ana musu koya musu yadda zasu zauna da mazan su, haka sula mazan ana koya musu yadda zasu zauna da matan, to Jabir ne ke gabatar da karatun duk ranar litinin da safe. Tunda ya kifa kan shi bai ɗago ba saboda... Abun ya ma wuce kwatance, shi dai ya ji kawai duniyar tana masa zafi, wanda hakan ya sa shi ba tare da ya ɗago kai ba kawai ya lalubo wani abu dake kusan shi bai ma san menene ba kawai ya buga shi a teburin da ƙarfi. Wannan ƙarar ta sa Aliyu dake ƙofar ofishin yana magana da wata ɗaliba kamar yadda ba ya yarda suna shigo masa ofishi in dai mai aure ce yasa shi kallon matashiyar dake rufe ruf cikin shiga ta kamala da daraja yace "Ina zuwa malama?" Da sauri ya shigo ajin yana kai duban shi kan kujerar shi inda ya san anan Jabir ɗin ke zaune, ai ko anan yake ya haɗa kan shi da teburi, da sassarfa ya ƙarasa kusa da shi yana kiran "Jabir." Shiru bai ɗago ba kuma bai amsa ba, saida ya ƙara matsowa daf da shi sannan ya sa hannu ya dafa kafaɗar shi ya sake kiran "Jabir, lafiya? Kan ka ne ke ciwo? Me ya faru?" Har lokacin shiru yayi bai kula shi ba, dan haka Aliyu ya shiga waige waige har saida ya hango kwalin allin da Jabir ya tarwatsa mishi, sake duban shi yayi yace "Jabir, me yake damun ka? Idan baka da lafiya ne kayi min magana." Wani numfashi numfashi ya ji ya sauke mai kama da na mai kuka, hakan ya ɗaga hankali Aliyu ya ce "Subhanallah! Kaga tunda ba zaka min magana ba, bari na kira Abba (Abban Jabir) na sanar da shi, idan baka da lafiya ne sai ya zo muje asibiti." Wayar shi dake kan teburin gefen hannun Jabir ya zura hannu zai ɗauka, ram Jabir ya riƙr hannun shi a hankali ya ɗaga kan ya kalli fuskar Aliyu yna sauke numfashi, idanun shi Aliyu da ya kalla saida gaban shi ya faɗi, sunyi jajir jajir da su ga kuma ruwa da suka cika su alamar kuka yake yi ko kuma yake shirin yi, cikin kulawa Aliyu ya rusuna a tausashe yace "Jabir, me ya faru? Wa ya rasu? Dan Allah faɗa min?" Sakin hannun Aliyu yayi ya kawar da kai, numfashi ya sake saukewa sannan ya sake juyawa ya kalli Aliyun, cikin yanayin da shi kan shi zai iya kiran shi da baƙo, cikin tashin hankalin da bai yake mamakin yadda zuciyar shi ta ƙ bashi lafiya game da lamarin Maaman shi, murya a tausashe tamkar idan yana nasiha ga bayin Allah, ga kuma muryar na rawa rawa wanda hakan yasa maganar tashi kan ta da yake yi sai take bada wani irin kalar gagarumin tausayin wanda yake furtawa yake faɗa ma Aliyu "Me yasa Aliyu? Me ye na gaggawar? Me ya kawo ujila a cikin lamarin? Me ye na dole sai tayi aure da gaggawa? A matse take da ɗa namiji ne? Idan auren ya zama dole yanzu, me yasa ba zata aje hankalin ta tayi zaɓi na ƙwarai ba? Ta fito daga gidan Abban mu dattijon ƙwarai, sai kawai ta ɓige da auren yaron da wani abu na jikin ta ne yake so, wallahi Aliyu *sirrin ta yake so ya gani dan kawai ya tozarta ni*, me yasa? Me ya sa Maama ke ta yin wasu abubuwa kamar bata da hankali? Idan na mata magana sai ta ce ni ba tsaranta bane, amma kuma *wauta* take min kowa na gani..." Hawaye ne suka gangaro mishi a kumatu har suka sauka kan lallausan gemun shin, shiru yayi na sakanni tare da kawar da kan shi kaɗan, sai kuma ya miƙe da sauri yana sake kallon Aliyu ya ɗan kausasa fuskar shi yace" Wallahi ba zata aure shi ba, ko zan mutu, haka ita ma ko zata mutu, sai dai muyi *mutuwar kasko*, amma ba zata auri wannan yaron ba." Bai ba Aliyu damar cewa komai ba ya fice daga ofishin ko wayar tashi bai ɗauka ba da sauran abubuwan shi, da kallo Aliyu ya bishi, sai wani irin mugun tausayin shi ya kama shi saboda hango wani abu da ya ga shi Jabir ɗin ma kamar fa bai san da ya kama shi ba bare yasan hanyar da zai bi wajen sarrafa kan shi, faɗawa yayi kan kujera yana tunanin lamarin, yiwuwar shi ko akasin haka? Ya Allah! Gashi dai ba haram bane, sannan tabbas akwai ilimin da ya sa haka yake faruwa, to kenan dama akwai abinda ubangiji ke nufi zai faru ne tsakanin su? Ya Allah. *Lallai* lamarin da ya sa Jabir har ya zo babban shago yau babba ne, amma da Jabir yake faɗa mishi matsalar Maama ce, sannan dan Allah yayi ƙoƙarin fahimtar da ita yaron nan da za ta aura ba mutumin kirki bane, sai kawai ya zuba idanu yake ta karantar Jabir ɗin, idanun shi, yadda yake ta magana har shasheƙa yake, yadda yake maganaro ba tsayawa da kuma sauri sauri... Lumshe idanu Alhaji yayi sannan ya buɗe akan Jabir yana sauke numfashi, cike da gamsuwa ya ɗan zuro hannun shi ya dafa guiwar Jabir yace "Na yarda da kai Jabir, zan ɗauki mataki akan haka, ba zan sake bari ta kula kowa ba yanzu, dan naga fitina take neman mu da shi ko?" Da sauri Jabir tamkar yaron da ke neman uwar sa ido rufe ya gyaɗa kai yace "E Abba." Shima jinjina kai yayi yace "Shikenan, zan mata magana, in sha Allah *Maaman ka za ta sake dawowa gare mu*." Wani murmushi yayi ya jinjina kai yace "Yawwa Abba, ka dawo da ita kawai, kaga ba zata sake kula kowane jaki ba." Murmushi Alhaji yayi yana haɗe wasu irin yawu, ga abu nan ƙarara yana gani, tausayin Jabir sosai ya cika masa ruhi da zuciya, haka ya sallame shi ya tafi yana mamaki da tunani kan abun kamar dai yadda Aliyu ke can yana nashi tunanin. *Alhamdulillah.* [31/08 à 15:33] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *64* Suna yin sallah magriba a cikin masallaci ya tambayi malam shin ko abinda yake tunani a ranshi ya halatta? Har saida aka kira sallah isha'i bai gama yi masa bayani akan hallacin abinda yake nufi tare da nun in yayi haka ma yayi bajinta kuma ubangiji zai masa sakayya ta alkairi in sha Allah. Mama ya kira ya tambayi yaushe ne tafiyar ta tace "Jibi in sha Allah." Alhaji kuma dake gaggawa yake sai yace "Hajia, wani muhimmin abj ne ya taso da dole zai sa naje dan mu tattauna da su Alhaji (Abbu Mukhtar), to gobe nake son tafiya, idan baku riga kun ciro ticket ba me zai hana mu tafi tare da ku?" Girmamawar da take masa duk da akwai abubuwan da ta so yi zuwa goben, haka ta ɗanyi wanda za ta iya yi a daren sannan ta gama haɗa kayan ta tsaf, suna jiran wayewar gari. *WASHE GARI* Tunda ummu ta ji Mama na hanya ita da su Adala ke madafa suna ta shirye shirye, ba wanda ya san tare da Alhaji Kabir suke sai Abbu kaɗai da ya faɗa ma yna son magana da su ne mai mahimmanci da ta sa dole sai ya zo da kan shi madadin a waya ko ɗan aike. Dake motar gida ce sai ga tafiyar tasu tayi saurin da basu yi tsammanin ta ba su kan su kula ba gudu sukayi irin na wuce ƙa'ida ba. Kai tsaye ɓangaren Hajia suka sauka har da Alhaji da ko da suka haɗa idanu Ummu ta gan shi take ta mamakin me ya kawo shi? Ɗaurin auren ta? Kuma shine ya zo tun yau? Kwana biyar fa saura? Sai dai hankalin ta bai kwanta ba kawai da ganin shi, dan har gaban ta ta ji yana faɗuwar da batasan dalili ba, amma dai bai hana suka gaisa ba a mutumce ɗaya daga cikin ma'aikatan ne suka mishi zuwa ɓangaren saukar baƙi shi da dreban shi, a can aka kai musu abinci inda Mama kuma tana nan wajen Hjia ta hna ta motsawa, anan suka ci abinci suna ta rahar su har sanda lokacin dawowar Abbu ya yi. *09:27* Abbu da ya buƙaci zama da Alhaji dan ya ji me ke tafe da shi shi ma kuma Alhaji ya buƙaci haɗuwar duka mutanen gidan amma wai ban da Ummu, sanda ta ji an ce ita ta zauna sai ta taɓe baki ta ayyana _"Ba zan koma cikin sauƙi ba Abban Kuwailat, ai ba ni nace ka sake ni ba bayan ban maka komai ba, shine za'a wani zo a haɗani da iyayena ko?"_ Ƙyale su tayi suka hallara taron su, bayan Alhaji ya sake tabbatar musu lallai akwai abinda ya kawo shi mai mahimmanci, sannan bai san ta ya za su kalli lamarin ba, amma dai shi a nashi ganin shine daidai kuma taimakon wasu mutanen. Nan Abbu yace" Ba komai Alhaji, ka faɗa muna sauraren ka, ko menene zamu mishi kyakyawar fahimta." Saida ya kalli Abbu da ya yi maganar, sannan ya kalli Hajia da kuma Mamie ya numfasa yace" Na zo ne na baku shawara kan ku haɗa *auren* Ummu da Jabir." Kamar ya faɗi wata mummunar magana sai kowa ya ƙara wara idanu wajen kallon shi, inda wasu kuma ke kallon junan su, babu wanda mamakin abinda ya faɗa bai bayyana a fuskar shi sai Hajia kawai, ita kaɗai ce tayi tahmidi ta hanyat faɗin" Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhaji Kabir, ban girme ka ba, amma Allah ya wa rayuwar ka albarka bisa wannan shawara da ka kawo wacce ta jima tana min yawo a zuciya." Sai kuma kallo ya koma wurin Hajia, mamakin abinda ta faɗa suke ita ma, to amma ai ba wani abu akan haka idan ba alaƙar dake tsakanin shi Jabir ɗin da Alhaji ba, a nutse Yaya Bilal da ya hango lamarin ta wata fuska yace" Alhaji, na fahimce ka, sai dai menene dalilin ka na kawo wannan shawara?" Gyara zama Alhaji yayi da kyau yace" Na ji daɗin wannan tambayar Alhaji, dalilina biyu ne rak, na farko shine... *soyayyar* da na hango a idanun Jabir wanda shi kan shi kamar bai ma san yana cikin ta ba game da *Maaman shi*, tun rabuwar mu da Ummu sau uku yana samuna da maganar da ta shafe ta, na farko ba laifi saboda yana ban haƙuri kan koma me yayi zafi na haƙura na mayar da ita ɗakinta, na biyu da yayi na fara tunanin wani abu, lokacin da ya zo hankali tashe yana faɗin wai na mata faɗa tana kula maza barkatai kuma tsofaffi, sai naga ai ba hurumina bane, bayan faruwar haka kuma jiya sai ya sake zuwa min da magnar na dakatar da auren ta da Jibril, abun mamakin shine har hawaye na gani a idanun Jabir..." Tausasa murya yayi sosai ya ci gaba da fadin" Ya damu da ita fiye da yadda ita take damuwa da kan ta, ina da yaƙinin zai iya da lamarin Ummu, ni na zauna da ita na kuma san wacece ita, daga halayen ta zuwa son girman ta har ma da buƙatar ta, zai iya, Jabir zai iya." Shiru ɗaki ya ɗauka bayan ya dire maganar shi, sun kai minti biyu a haka kowa da abinda yake saƙawa a ran shi, musamman ma dai Mama da ta raini Ummu ta fi su sanin wacece ita, sannan ta fi su sanin wa ye Jabir ɗin kan shi. Muskutawa Abbu yayi yan kallon Alhajin yace "Kuma kana ganin hakan ba matsala? Jabir yaro ne da kowane uba zai so haɗa zuri'a da shi, to amma..." Shirun da yayi yasa Alhaji murmushi yace "Alhaji, na san abinda kuke tunani ba zai wuce yadda ni na ɗauki Jabir tamkar ɗan dana haifa ba? Karku damu da wannan, ni mutum ne mai son sauraren karatuttuka dan ƙarin ilimi, anan naji hakan ba wata matsala bace, sannan jiya na sake tambayar limamin masallacina, shima ya tabbatar min da hallacin haka." Fahad da ke sauraren su tuntuni ne ya kalli Alhaji Kabir ɗin yace" Kuma kana ganin dukansu zasu amince? Ni sai nake ganin da kamar wuya." Kallon Fahad yayi da kulawa yace" Ba wuya, idan muka nuna musu mune a gaba da su, Alhaji..." Ya kira Abbu yana kallon shi gaba ɗaya sannan yace" Bana jin Ummu za ta samu wani zaɓi da zai kai mata Jabir alkairi, yana da ilimin addini da na boko, yana da ƙoƙarin neman na kan shi, ta san shi ta san waye shi tun ƙuruciya, sannan yana girmamata da darajanta ta, bana jin idan Allah ya ƙaddara auren su Jabir zai iya ɓata ko da ran Ummu ne sabod yadda take a wajen shi, amma kamar yadda na faɗa muku shawara ce, zaku iya yin bincike akan shi yaron Jibril, idan har kun gano da gaske akwai wani mummunan nufi a zuciyar shi game da ita, ko kuma ya fi Jabir nagarta, to zaku iya ɗaura musu aure, dama ni tunanina a kan su ba wanda ya sani sai ku ɗin nan." Kallon Abbu Hajia tayi cike dattijantaka tace" Ni fa gaskiya na yarda da shawarar shi ɗari bisa ɗari, ba wai dan ban gamsu da tarbiyyar Jibril bane, a'a, kawai dai na fi samun nutsuwa da dattijo, sannan na fi gane mata dubbanin alkairi a tarayyarta da shi, sannan kunga ma-nemin ta na farko haka aka samu matsala, aka zo kan Larwan shima, wannan ma idan aka samu akasi za'a iya cire mata son auren daga zuciyar ta gaba ɗaya." Abbun da Hajia ke magana da shi ya jinjina kai a nutse yace" Mamie ni ban da matsala daga wajena, sai dai ko da mun sake bincike kan Jibril, dole ita zamu so jin ta bakinsu dukan su, dan ba zamu aurar da su ba tare da sanin su ba ai." Ƴar dariya Alhji Kabir yayi yace" Idan ko sai sun amince sa kan su, to ɗaurin auren nan ai an ƙara saka wata ranar, dan nasan zai yi wuya." Yaya Sabeer da ya fi sauran zafi ne yace" In dai mun tabbatar da wani mummunan abu akan Jibril, ai bamu buƙatar amincewar su tunda ba ƙarfin mu suka fi ba." Murmushi Alhaji Kabir yayi yace" Amma kafin nan, zan so naji ra'ayin ku game da haɗin nan?" Yaya Bilal ne ya fara bashi amsa da" To ai kusan nji kowa y goyi bayan haka, ko kuwa?" Ajiyar zuciya aunty Fa'iza ta sauke tana murmushi ita ma tace" Gaskiya kam, duk da ban jima da sanin shi ba, amma dai kmilin matashi ne da zai yi wuya samun kamar sa a yanzu." Sai Fahad da yayi saurin fadin" Ni kam da za'a ji tawa ma ai d yanzu muka ɗaura aure, ni da Jabir ya diga ba umarni na sauke hoto Maman shi a stats ɗina, dama sai da na tambyi ƴata ko dai akwai wani abu tsakanin su ne? Ta ce min a'a wai." Murmushi duk sukayi sai Mama da cikin matuƙar nutsuwa sosai tace" Idan akwai wani da ya kamata a ji ra'ayin sa anan kaine Alhaji, ka taimaki Jabir a rayuwa kamar kai khaifeshi, shin baka gani duniya zata zagi Jabir har ma a kalle shi a matsayin butulu?" Murmushi Alhaji yayi yace" Duniya Hajia dama abinda mutanen cikin ta suka fi ƙwarewa kenan a kai? Jiya malam ya faɗa min saboda irin hakane ubngiji ya haramta yin adopté (ban san haka da hausa ba), dan kuma ya tabbatar mana da bbu gado a irin wannan tarayya, sai aka fara zartan da hakan ga Annabinmu fiyayyan halitta Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Hajia, ni daga gareni wallahi har cikin raina nake son ƙulla wannan alaƙar, ban taɓa tunanin hakan a raina ba, amma dare ɗaya sai ubngiji ya saka min hakan tare da wani irin ƙarfin guiwar tunkarar kowa game da zancen, jiya banyi bacci ba wallahil'azzem ina tunanin abubuwan nan, idan kowa ya nutsu sai ya ga dam dai abinda zai faru kenan shiyasa duk abubuwan da suka faru a bya suka faru, sannn nayi sallah raka'a biyu kan abinda na ji na saka a gabana, cikin ikon Allah sai naji nutsuwa ta sake sauko min har ma naji dole yau na zo garin nan, dan sai nake ganin kamar mutuwa za ta iya shiga tsakanina da wannan abun alkairin da na ƙudurta a raina." Numfashi Mamie ta sauke tana kallon Alhaji Kabir tace "Sai na kasa tantancewa, shin Jabir ne ya fi dacewa da Ummu a yanzu? Ko kuma dai kai da ka fara rayuwa da ita tun asali?" Murmushin jin daɗi Alhaji yayi ya ɗan girgiza kai yace "A yanzi shi ya fi dacewa da ita, ni daga yanzu *uba nake a gare su*, idan har komai ya tabbata, to zan karɓawa ɗana auren ta da izinin Allah." Sabeer ne ya sake cewa "Fahad, tunda abokin ka ne, kai za sake binciko mana halayen shi da bamu sani ba, dan n..." Kallon shi Fahad yayi ya katse shi da faɗin "Gaskiya fa tsakani da Allah zan gaya muku abinda na sani a kan Jibril, amm wallahi ya ce min ya tuba kuma kunga ni ai na jima bn zauna garin nn na lokaci ba, sai nayi tunanin da gaske hakane, amma fa gaskiya Jibril ya ɗanyi harkar mata, shaye-shaye dai ne ban sani ba dan ban taɓa gani ba." Wata harara Sabeer ya watso mishi yace" Ka san da haka tun farko shine ka ƙyale mutane? Mu ai daga bayanan ka ne mukayi aiki, tunda kasan ba ɗan nan bane shi." Turo baki Fahad yayi yana kawar da kai da gungunin _" Ni fa shiyasa bana son harka da Sabeer ɗin nn, shi ya cika zafin kai, yana min irin haka kuma hayaƙin kaina tashi yake."_ A zahiri kuma bai ce komai ba shi dai yana sauraren su Yaa Bilal na faɗin kawai a kira Ummu a gaya mata? Wasu kuma na a'a a ƙyale ta har da safe, sai Mamie da tana buɗar baki tace" Ni kam na san halin auntyna wallahi da kafiya, ni kam da ɗaurawa akayi daga baya mun bat haƙuri, lokacin ba yadda zata yi ai tunda an ɗaura, amma idan aka ce sai ta amince ko?..." Sai ta jinjina kai kawai, Mama kam dariya ta fara yi tunda Mamie ta fara magana saida ta dire sannan tace" Ke da baki gama karantar ta ba kenan, ni ai ƙa'ida ne idan nace yi sau ɗayata ce a'a to sai na kusa saka hannu sannan take yin abun, idan ba haka ba ita gani take to tana babb da ita tunda ta ce a'a a bar ta mana? Kuma har yanzu haka muke da ita dan Ummu akwai wani abu wai shi taurin kai." Dariya duk sukayi, hakan yasa nan fa suka dinga shawarta yadda zasuyi tun daga kan Jibril, zuwa ga Bban Jabir da Alhaji ya ce a bar shi zai mishi magana da safe, zuwa ita kan ta Ummu da suka ce kawai a tafi a haka har a ɗaur auren ta ji daga baya saboda gudun matsala, sai kuma shi ma gogan mai gayya mai aiki wato mai taya *Abban shi kishi*, wanda yake can cike da farin cikin Abba zai dawo da Maama ya ga ta tsiyar tara maza kala kala. *Zuwa* safiya duk wani wanda ya kamata ya ji wannan abu ya ji har da iyayen Jibril wanda Yaya Bilal ne ya faɗa musu a nutse cewa hakan ba zai yiwu ba, sun sake bincike sun gano wani abu da shi Jibril ke aikatawa wanda gaskiya su basu sami tabbacin ya daina ba, ya dai basu haƙuri da kuma yi musu fatan alkairi, ɗaya a ciki bai ga laifin su ba, inda sauran ke ganin iskanci ne mana, me y hana su ce haka tun da wuri? Sai yanzu da lokaci ya matso duka kwana huɗu ya rage? Kawai dai dan sun ga Jibril bai da abinda suka tara ne, a haka dai suka rabu suna ta kumbura fuska, sai wannan ɗayan dake ta ƙoƙarin faɗa musu Jibril fa rayuwar shi yake yi a waje, amma su idan sun gamsu su bashi nasu ƴaƴan mana tunda suna da, sai kuma suka tsaya kame-kame da faɗin ai ba wannan maganar ake yi ba yanzu. Abba Jabir zuwa su Anna duk wanda ya ji ƙumewa yake da farin ciki, sai Abban Jabir ne ma da yasan sun yi magana da Alhaji akan Kuwailat sai yake mamaki har ya tambayi Alhaji "To kuma Alhaji wanda da ɗiyar ce ka bashi, kuma ka faɗa min wannan shekarar kake so ta kammala sai ayi bikin su, ya kenan kuma yanzu?" Dariya Alhaji yayi kamar yana gaban shi yace "Wannan ba wata matsala bane, kaga dama ai daga ni sai kai sai Allah muka yi wannan maganar, kuma nima wani abu ne da na gani a idanun Jabir ɗin ya sa nayi wannan shawarar, to amma da na nutsu sai naga nafi hango wannan abun a idanun shi game da *uwar* fiye fiye da *ƴar*, Abban Jabir, wataƙila dama Jabir tun yana matashin shi yana jin wani abu akan Ummu, idan ma ba ya jin komai a kan ta, wallahi Allah ya riga da ya rubuta wata babbar *RUBUTACCIYA* ce a tsakanin su, za ka gane haka daga ranar da ni ban san shi ba, shi ma ba da niyyar zuwa gidana ya zo ba, amma ubangiji ya ja linzamin sa har zuwa ƙofar gidana, Allah ya sa ni ɗin nan dana fara auren Ummu ni ne zan taimake shi a rayuwa har ya dogara da kan shi, a wannan gaɓar idan na ce ba zan bari haka ta faru ba, to kenan faɗa zanyi da ikon ubangiji? Ni na isa na ja da hukuncin Allah ne? Bayan abun nan faruwa yake tamkar tarihi ne ke maimata kan shi, hakan ya faru tsakanin Annabi Muhammad (SAW) da sahabin sa Zeid bin Haris da kuma Zeinab bintu Jahash, duk da nan an samu saɓani ɗan ne ya saka Annabinmu kuma aura, mutane kuma nasan abinda zasuyi magana a kai shine na ma Jabir komai amma auri tsohuwar matata, to sai me? Ni wanene? Kuma da Jabir ne ya sake ta ni na aure ta ba wanda zai yi magana saboda ni babban mutum ne ko? To dan haka ni amincewar ku nake nema da kuma tayani tanƙwara yaran nan biyu da nasan dole su wahalar da mu kafin amincewar su, na ji nutsuwa sosai game da wannan abun, ban sani ba ko shine zai iya zama silar shigata aljanna, ko dan sheɗan dake ta ƙoƙarin nuna min *ta ya Jabir da ka ma komai, kuma shine zai dawo ya saka takalmin ka*? Wani sa'ilin kuma faɗa min yake a kunne *ya yaron da ka ma riga da wando, shine zai kwanta a shinfiɗar da ka tashi*? Da na ji haka sai nayi gaggawar korar sheɗan, na tuna a duniya kuma matan Annabi Muhammad (SAW) ne kaɗai aka hana wani mummini ko sahabi ko waliyi ya aura bayan wafatin sa, Ummu kuma ba zan hanata aure ba dole ta yi ko ba yanzu ba, to fargaban shine ni tun da ƙuruciya na iya sarrafata, shin yanzu wani wanda za ta aura zai iya shanye matsalolin da na san ta dasu? Shin wanda za ta aura zai zama mai mata uzuri? Zai iya sakata farin ciki? Sannan zai iya magance mata matsalar da ta raba ni da ita? A ganina, gwara a ce har yanzu Ummu tana cikin ahalina, ba wai zaman ya kusa dani nake so ba, amma dai a ce yau wni ne da na san shi sosai take aure, da Jabir bai da nutsuwa ba zan yarda ya auri matar da na saka ba, amma yaro ne mai hankali da nutsuwa da halin manya, ba Ummu da na samu tabbacin zai iya ji da rigimar ta ba tun ranar da yake mata magana a gabana kuma a gadarance, ko Hajia *Luba* ni zan iya aura mishi saboda zan sami nutsuwa ta shine zai iya kula da larurorin da take fama da su, dan haka matsayin ka na mahaifin shi kawai ka mana addu'a." Cike da gamsuwa Abban Jabir ya musu addu'a ya kuma ba Alhaji damar yai magana da Jabir ɗin, murmushi Alhaji yayi yace" Na faɗawa aminin sa halin da ake ciki, na kuma saka shi ya fara share mana filin yaƙin da shi." Dariya duk sukayi kafin su shiga hira irin ta raha game da Jabir din suna hango yada zai yi tun kafin su mishi maganar. *MARAƊI* Awa biyu Aliyu ya samu kammala da ɗalibai ya nufi gidan Jabir da ya faɗa masa yau ko fita bai yi ba kan shi ne ke ciwo, saida ya siya mishi abun kari da ya buƙata da magani sannan ya wuce, cike da tattalawa da kuma neman tsokana yake mishi hidima yana dariya yana faɗin "Girman ka ne ai, zan maka komai wallahi, da girman kujerar ka *tonton Jabir*." Jabir da ya dafe kan shi yana sanye da baƙa siɗik ɗin singlet da wandon shi tree quater ya ɗan ɗago da ƙyar ya kalle shi, shi fa tun damuwar jiya ce da ya kwana da ita take ta damun shi, ya yi kuka har da marin kan shi saboda maganganun da ya tuna Jibril yayi akan ta har da ma na jiyan, amma shine Aliyu ke masa wani zancen banza kuma haka? Banza yayi da shi har ya miƙo mishi farantin sistem ɗin da cokali da bred ya ɗan fara tsakura, kujerar dake fuskantar Jabir ya zauna yana ta kallon shi sai wasar baki yake. Hakan yasa Jabir aje farantin kan teburin din dke tsakiyar su ya kalle shi murya a daƙile yace "Ya aka yi? Me kake so na yi maka Aliyu?" Ƙara faɗaɗa murmushi Aliyu yayi cike da ƙaunar Jabir ɗin da ya ga har ya fahimci akwai abinda yake so ya mishi, gyara zama yayi yace "E to, dama fassarar wata aya nake so ka ɗan tuna min?" Ɗaga idaun shi ya sake yi ya kalle shi da suka masa nauyi suka ƙanƙancewa, duk da yana jin kamar ba gaskiya bane, to amma bai isa ya ce ƙarya yake bai manta ba, dan mu'ijiza ce ta Alƙur'ani wanda yake rubuta shi ma ka ga ya wata aya a cikin wata sura da zaka ga yaro ma ya haddace ta a sauƙaƙe amma ta ɓace mishi ɓat, sai kawai ya sake ɗaukar farantin yace "Ina jin ka?" Da farin ciki Aliyu da dama ya gaa shiryo maganganun shi tun jiya a peper saboda yasan mutumin nashi yasa ya fara faɗin "Yawwa, ina faɗa kana fassarawa dan Allah, a hankali a hankali yadda zan gane da kyau, idan zai yiwu malam tafsirin ayar nake so sosai." Kallon shi kawai Jabir ke yi yana cin abincin shi sannan ya fara faɗin " A'uzubilahi mina shaiɗanir-rajim." Yana shirin ci gaba Jabir da a daƙile yake maganar saboda ciwon da kan shi ke yi masa yace" Ina neman tsarin Allah daga sheiɗan abun jefewa." Kallon shi Aliyu yayi sai ya fahimci kenan dai tafsirin zasuyi? To ba damuwa a je a haka, sai yace" Aramma, tafsirin aya ta talatin da bakwai nake so a cikin suratul Ahzab?" Numfashi Jabir ya sauke tare da aje farantin nan yana maida nutsuwar shi ga Aliyu yace " _Wa iz taƙula lillaziy an'ama-Allahu alaihi_, tuna, lokacin da kake faɗawa wanda Allah ya yi wa ni'ima, *ma'ana Zeid bin Haris da Allah ya ma ni'imar shiga addinin musulunci*, wa an'amta alaihi, _kuma kai ma ka masa ni'ima_ *daga bauta ka ƴantashi ya zama ɗa*, amsik alaika zaujaka wattaƙillah, _ka riƙe matar ka, kuma ka ji tsoron Allah_, *ma'ana lokacin da Zeid ya kawo ƙarar Zeinab bintu Jahash kan tana masa ba daidai ba*, wa tukfi fi nafsika _kana ɓoye wani abu cikin ran ka_ mallahu mubdihi _kuma Allah zai bayyana shi_, wa taksha-nass; _kana tsoron zantukan mutane_ wallahu ahaƙƙu an takshahu, _Allah shi ya fi cancanta da ka ji tsoron shi_, *a ƙarƙashin tafsirin wannan ayar akwai hadisin Nana Aisha uwar muminai dake cewa da akwai wata aya da Annabi Muhammad (SAW) zai ɓoye bai ambata ba to da wannan ayar ce*, falamma ƙada Zeidu minha waɗaran _lokacin da Zeidu ya biya buƙatar shi da ita sai ya sake ta_, zawwajnakaha _sai muka aura maka ita_ li kaila yakuna alal'mu'uinina harajun fi azwaji ad'iya'ihim, _dan kada muminai su samu ƙunci a cikin auren ƴaƴan da suke mayar ƴaƴan su_, iza ƙaduu mihunna waɗarann, _idan har sun sadu dasu bayan aure_ wa kana amrullahi maf'ula _lallai al'amarin Allah abun zartarwa ne_." Cikin nutsuwa ya sake gyara zama yace" Aliyu, daɗi ke akwai ubangiji ya ce ka yi ka aikata, ka duba wata buwaya ta Allah, Zeid ya sake ta, kuma sai aka tura shi ya nemo auren ta da kan shi, Zeid na cewa daga lokacin da Annabi y faɗi buƙatar sa ga Zeinab, wallahi sai ya ji kamar bai taɓa zaman aure da ita ba, kawai sai ya fara kallon ta a cikin jerin iyayen su muminai, wannan biyayyar ta sa sahabbai suka mana dintinkau har yau muka kasa cimmusu, lokacin da ya je ya sanar da ita rigima irin ta iyayen mu mata sai ta sa Zeinab fadin wai sai ta nemi zaɓin Allah a kai, shin Aliyu a duniya akwai wani alkairi ne bayan fiyayyen halitta? Wanda farin cikin mu duk sanadin shi ne, daga ƙarshe dai Ubangiji da kanshi ne ya ɗaura auren a sama ta bakwai kuma mala'iku ne shaida, a ganina ba wani aure da zai sa ka ji alfaharin kasancewar ka yi shi bayan wannan auren, ita kan ta Zeinab tana faɗawa matan Annabi haka lokacin da suke tsokanatar ta, kaga kenan duk yadda zaka riƙe ɗa maganar wai ɗan ka ce bata taso ba, baka da gadon shi bai da gadon ka, haka kuma zai iya sakin mata ka aura kai ma zaka iya saki ya aura, ama a yanzu wannan zamani da muke ciki idan haka ta faru za'a kira wanda yayi hkan ne da butulu, ma ci amana, koma dai menene kada zancen mutane ya damu mutum, saboda akwai misali a Alƙur'ani kuma ga shugabanmu fiyayyen halitta haka ta fara faruwa, to me zai sa kayi baƙin ciki idan haka ta so faruwa a kan ka? A zamanin nan akwai wanda yaron shi bai isa ya kalli ƴaƴan sa da sunan soyayya ba, wani kuma tunda na maka komai a rayuwa, to iyalina sun haramta gare ka daga matan har yaran, wa ye zai iya yin hali irin na magabatan mu? Ko ba irin na su sadaukarwar ba, a ƙalla dai a kwatanta yin haka." Murmushi Aliyu yayi yace" Hakane Jabir, Allah ya ƙara mana imani da koyi da su." " Ameen Ya Hayyu ya Qayyum." Cewar Jabir yana ɗaukar abincin shi, sai Aliyu kuma da yace" Sai dai fa a wannan ƙarnin la an samu wanda ya kwatanta irin hakan." Yana cin abincin yayi murmushi yace" Wa ye wannan?" Ido Aliyu ya tsura masa kafin ya furta" Abban mu ne, *Abban ka* Alhaji *Kabir Saley*, ya nema maka *auren* maaman ka Aunty Ummu." Da ƙarfi Jabir y ci birki saboda wata muguwar ƙwarewa da yayi, a gigice ya shiga yin tari ba ƙaƙƙautawa, da ƙyar ya ɗauki ruwa ya sha sannan ya ya fara kwanta masa, saida ya ɗan nutsu ya zubawa Aliyu idanu cike sa tausayin yaushe hka ta fara faruwa da shi? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! A Saudia ya haɗu da su? Ko a Misra da suka je? Ko nan Madina ne? Dama fa an ce ana kamuwa da aljannu wajen karatun nan, amma shine basu taɓa nunawa ba sai yanzu? A hankali ya aje farantin nan ya muskuta da niyyar tashi ya ɗaure Aliyun ya msa ruƙiya, ina lafiya malam guda ba lafiya? Amma sai Aliyu ya tabbatar masa da lallai fa aljanu gare shi ta hanyar rigan shi miƙexa tsaye yace "Kana ji ko? Ka riga da ka faɗi abubuwan da suka dace a fassarar da ka min yanzu, kada kayi tunanin abinda mutane zasu faɗa, ka ji tsoron Allahn ka kawai Jabir, Abba ya ga kafi cancanta da aunty Ummu, shiyasa ya je har can yayi maganar auren ku, kuma wallahi ko baka yarda ba Jabir kana *son Maaman ka*, kayi tunani da kyau sannan ka faɗa musu matsayar ka, amma ka tuna wani abu, idan ka ƙi amincewa to auren ta zai tabbata da wanda ka tabbatar jikin ta ne kawai yake so, idan kuma ka amince to ko baku son juna nasan zaku zauna lafiya dan zaku mutumta junan ku, idan ka yi shawara ka kira ni sai na kira Abba nima na sanar da shi." Juyawa yayi zai fita sai kuma ya dakata ya juyo ya sake kallon Jabir da yayi mutuwar zaune yana kallon Aliyu kawai da mamakin har haka abun yayi ƙamari wai? Ko dan sun jima basu kwana tare bane shiyasa har aka samu dandalin kafa shaiɗanci a jikin bawan Allahn nan? Cikin nutsuwa Aliyu yace "Ka da kace zaka kawo dalilin ƙin amincewar ka ta hanyar faɗin tsohuwar matar Abban ka ce, Jabir Abba ba Abban ka bane dan ba shi ya haife ka, ka da ka zama ɗaya daga cikin masu haramta halal saboda gudun zancen duniya, kar kuma kama kanka babban zalincin da ruhi ke wa gangar jiki, ma'ana hana zuciyar ka abinda take so, hakan zai jigatar da gangar jikin ka ƙwarai, amma zan iya yarda da dalilin ka idan ka ce ta maka *girma ne a shekaru* ko kuma saboda ta *haifi budurwa*." Yana faɗa ya fice daga falon ya bar Jabir da hangen bayan shi, da sauri Jabir ya ɗauki wayar shi zai kira Abba ya gaya mishi maza maza su dawo ba lafiya a gida, dan wannan haukan na Aliyu zai iya saka shi tara mutane ma a ɗaura masa aure da Hajia babba wata rana, ina dalili kai jama'a? Aliyu? Shine ke wannan maganganun da bakin shi? Astagfirullah! Astagfirullah! Gashi kuma ba cikakkiyar lafiya ba bare ya tirsasashi yin istigfari shima. *Alhamdulillah.* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *65* Abba da ya ga kiran Jabir ya ɗauka rigima ce zai masa, amma sai ya ji yace "Abba, Abba dan Allah ku dawo, wallahi Aliyu ba lafiya, yaushe zaku dawo?" Da yanayin tashin hankali Abba yace "Subhanallah! Aliyun? Me ya same shi Jabir? Jiya munyi waya ɗazu ma da safe haka, yana ina?" Girgiza kai Jabir yayi kamar yana gaban Abba yace "Abba Aliyu wasu maganganu yake ta yi alamar dai baya hayyacin shi, dan Allah ku zo sai mu kaishi wajen malamai." Cikin son ya nutsar da shi yace "Kaga Jabir, nutsu, sannan ka faɗa min me ya faru da Aliyu? Haɗari ya yi?" Ajiyar zuciya Jabir ya sauke yana istigfari na abinda bakin shi zai maimaita kafin a sanyaye sosai yace "Abba, wai Aliyu ne ke faɗin wani abu dai haka ni da Maala, to ai kaga bai da lafiya ko? Dan Allah ku dawo." Yanzu ne kaɗai Abba ya fahimci Jabir, dan haka ya numfasa a nutse sosai yace "Jabir, kenan nima idan na maimaita mka abinda Aliyu ya faɗa maka, haka zaka ɗauke ni mai aljanu?" Wata dariya ce ta kubce mishi irin ta haba ɗin nan tare da tausasa murya a ldabce yace "Abba, kayi haƙuri, na san nayi laifi saboda jiya ban kira ba naji ya kuka sauka, sannan ban kira da safe na gaishe ku ba, kuyi haƙuri dan Allah, amma kada ku hukuntani ta hanyar irin wannan wasar mai hatsari." Ba alamar wasa Abba yace "Jabir, da gaske nake maka maganar nan Jabir, na zo nan ne na nema maka auren Ummu, kuma tun daga mahaifin ka, Anna, Alhaji (Alka) da ita kanta iyayen ya duka sun amince, yanzu kaine kawai ka rage." Tsaye ya miƙe saboda jin yau dai kamar duk mutanen basu da lafiya, ciwon kan shi ne ya ji ya sake ruɓanya dan har jijiyar kan shi ya ji tana amsawa da ƙarfi, cikin yanayin tashin hankali da ruɗu Jabir yace" Abba..., Abba da gaske kuke maganar nan? Abba Maama fa? Wai me yake damunku ne yau ɗin nan? Abba ta ya kuma ni zan iya... A'a Abba, gaskiya ba zan iya ba, ba zan iya wannan abun ba idan ma da gaske kuke faɗa kenan." Jin yadda Jabir ya rikice yana magana yasa Abba faɗin" Shiiiii! Jabir nutsu ka saurare ni? Maga..." Da sauri Jabir ya girgiza kai yace" A'a Abba, Abba dan Allah ku daina wannan maganar, Abba sai anjima, kaga dama tun jiya bana da lafiya, zan sha magani na kwanta Abba." A ɗan kausashe Abba yace" Jabir, da kai nake magana fa, ka saurare ni mana." Ajiyar zuciya Jabir ya sauke mai nauyi tare da tsayawa cak daga kai da kawon da yake yi, a hankali kuma ya sulale ya zauna kan kujera yana dafe goshin shi cikin wata tikitacciyar murya kamar zai fashe da kuka a sanyaye yace" Kayi haƙuri Abba, dan Allah ka ce min wasa kake min?" Shima Abba a nutse yace" Jabir ba da wasa nake maka ba, wannan shine abinda muka tattauna, Jabir, na san kaan ba haramun bane hakan ko? Sannan kasan ba zan sa ka abinda zai cutar da kai ba, rayuwar Ummu na ga tana cikin haɗari na rashin samun wanda ya dace, shiyasa nayi bugun gaba a kan ka Jabir, yanzu in tambaye ka?" Shiru Jabir yayi sai murza goshin shi da yake yi yana jin kawai mafarki yake yi kuma burin shi shine ya farka, Abba da ya ji bai ce komai ba sai yace" Jabir, ka yarda ni uba ne a gare ka?" Shiru Jabir ya sake yi yana tunanin da irin hakane ake so a cuce shi kenan? A kanainaye shi yadda zai kasa motsawa, Maama fa suke magana? Wai me suka sha ne yau? Maama? Maaman Kuwailat da yake da burin a bashi ya raine ta? Maama dai wacce ko idanu baya haɗawa da ita? Maama dai matar da Abban shi ya saki, wandaa ya masa komai a rayuwar nan, tunda daga ilimin da ya samu har zuwa kan duniya da ubangiji ya fuwace masa yake samu, shine ake so wai ya auri... Aure fa? Ya auri Maama dai? Subhanallah! Wannan saɓo da mutanen nan ke yi yau Allah ne kaɗai zai iya gafarta musu gaskiya. Saida ya sauke numfashi mai nauyi sannan a ƙasan maƙoshi ya furta "E Abba, ban da wani uba a duniyar nan sama da kai." Kamar suna gaban juna saida yai murmushi sannan yace "Kuma zan iya umartar ka kayi indai ba saɓa shari'a ba?" Saida Jabir ya runtse idanu wasu zafafen hawaue suka taho mishi, shiru yayi saida Abba ya sake faɗin "Da kai nake Jabir?" Da sauri Jabir ya amsa da "Zan yi komai da ka umarce ni Abba, amma dan Allah..." Sai kuma yayi shiru na wasu daƙiƙu, kafin ya sassauta murya kamar mai raɗa yace "Dan girman Allah Abba *ka da ka umarce ni da kwantawa shinfiɗar da ka tashi*, ba zan iya aikata haka ba Abba ko da zaka yankani ne, gwara na bar duniyar nan kana mai alfaharin kasancewata ɗanka, ba wai na tafi kana kallona a matsayin wanda yasan wani ƙololuwar sirrin da ya taɓa zama sirrin ka ba." Yana gama faɗin haka bai jira jin me Abba zai ce ba kawai ya kashe kiran tare da wurga wayar kan kujerar dake gefen shi ya sake dafe kan shi, ya jima haka yana tunani da jin kamar ya kasa yarda da lamarin, ba'a fi minti talatin ba kiran Abban shi ya shigo waya, a wannan lokacin ya san Abban shi na aiki ne, amma abun mamaki yana ganin kiran saida ya ji gaban shi ya faɗi haka kawai, sai ya shiga tsoron ɗaga kiran wanda hakan yasa bai ɗaga ba saida kiran ya yanke, gaba ɗaya sai suk saka mishi jin tsoro da kuma wani irin ƙyama da jin haushin komai. Dama ya jima da burin son tafiya Kano dan ya ɗauki karatu gaban malamai nan guda biyu, dan haka kawai ya miƙe ya fara shirya kayan shi, saida ya gaa tsaf ya fito ya samu kira a wayar shi sosai har da Abban shi da Abba ma duk ya sake kira. Girgiza kan shi yayi yana ayyna _"Ban taɓa tunanin zaku iya kawo min haka a ran ku ba, to me kuka ɗauke ni? Ko mayen mata ne ni ina ni ina Maama saboda Allah? Shikean baku san me zakuyi tunani a kai ba, sai ku tunano abubuwan ku sai kuma ku ce dole sai an yarda saboda ba haramun bane?"_ Haka ya gama komai tare da rufe abindake buƙatar rufewa da kashe na kashewa sannan ya fice da makullin motar shi yana kiran lambar *Hassan*, yana ɗagawa yake sanar da shi gashi nan fa zai kamo hanyar Kano, da farin ciki Hasan yake faɗa masa sai ya zo yana jira, yana samun wannan tabbacin ya kashe wayar shi gaba ɗaya ya kama hanya da rana tsaka tamkar wanda aka kora daga gari. ******************* A kasalance ta farka tana buɗa idanun ta da jin jikin ta ya mata wani irin nauyi, a hankali ta kai hannu kan marar ta ta shafa sannan ta sake yaye zanin rufar ta zuro ƙafafun ta tasauko, da ɗan sauri ta nufi ban ɗaki dan yin fitsarin da take tunanin yaa fara taho mata tun a gado. Tabbas tayi fitsari, sai dai har da abun da bata yi tsammanin shi bane yanzu da safe, sai kawai ta gyata jikin ta ta ɗauki pad da sabon pant ta saka sannan ta tara wa kan ta ruwan wanka ta fito dan cire rigar baccin ta. Gaban madubi ta tsaya ta cire figar baccin, hakan yasa bras ɗin da take sakawa kwana uku yau saboda gyran nonon da Mamie ta ce wallahi sai tayi baƙa wacce ta kama ta sosai, a nutse ta ɓalle ta sannan ta cire ta aje gefe, sai ta samu kan ta da jin kunyar kallon nonuwan nata saboda ita kanta wani abu taga sun ƙara yi da ta kasa ganewa, sai take ganin su kamar ba a jikn ta ba wallahi tsbar yadda suka ƙara yin wani digir digir da su a ƙirjin nata da kuma yadda suka wani busu sai ƙyalli suke, wataƙila na man hulbar da ta shafa ne? Ko kuma dai saboda cikar nan da sukayi ne? Yatsa tasa ta ɗan latsawa ta ga da gaske dai nata ne, sai kawai ta saki murmushi tana hango... Yadda Jibril zai yi da kayan nan, jin kamar ruwan da ta tara sun cika ya sa ta nufi ban ɗaki da sauri. Wanka tayi sosai ta fito ta shirya cikin kayan da ta fi anfani da su wato doguwar riga, bayan mai da turare ba ta shafa komai ba ta fito da wayar ta a hannu tana kallon lambar Jibril da take son ta kira amma Mama ta ce mata kar ta kuskura shima sun gaya maa daga yanzu har a ɗaura auren kar ya kira ta, ita kuma bata san Mamie ta saka mata lambar Jibril a baƙin jadawalin da ko ya kira kashe za'a ce maa wayar ta bare ma ɗana kiran nan ya shigo ta ankare, falo ta samu su Mama da Mamie da Nabila suna karin kumallo, gaisawa sukayi kafin Mamie ta kalle ta tace "Aunty wannan baccin na jaraba kuma fa da kika samu yanzu da safe?" A kasalance Ummu ta girgiza kai tace "Ba komai aunty." Sai kuma ta kalli Mama tace "Mama, ina son yin magana da Jibril, dan Allah ki ce anty ta barni na kira sau ɗaya." Harara Mama taa watso mata tace "Ke ki fita idona kin ji, wallahi na ji kin kira shi sai dai Maman ki ta harare ni bayan na bada baya, amma ba abinda zai hanani zane ki Ummu." Turo baki Ummu tayi ta kalli Nabila da tayi dariya sannan ta kalli Mamie ma da tayi dariyar tace "Wa ce ni Maman aunty, mutuwa ai tana kunyar idanun mahaifi, haka na ganki fa ke da ƴar ta ki." Sai kuma ta kalli Ummu tace "Maza ki karya ki tashi ki haɗa kayan ki ku wuce, ga Nabila nan za ta raka ki sai ta dawo." Da mamaki Ummu tace "Ina kuma? Ina zan je aunty?" A taƙaice tce "Waje Mammie, saboda nan akwai baƙin da zasu fara zuwa yau, zuwa anjima gidan nan ya cika, gashi kuma akwai al'adar da muke so mu cika tunda mu yanzu a wurin mu auren fari ne zakiyi." Da yanayik damuwa Ummu tace "To amma aunty..." A taƙaice Mamie tace "Kiyi abinda nace aunty." Da sauri ta sake cewa "Amma aun..." Mama ce ta ɗauki cokalin dake cikin kofin shayi tayi kamar zata jefa mata tana faɗin "Yau ni naga iskanci, ke Ummu abinda ta ce kiyi ɗin n..." Tuni Ummu ta miƙe tana wartar bredin dake hannun Nabila ta nufi ɗakin ta tana faɗin "Na tafi Mama, na tafi wallahi." Da kallo suka bita inda take ta kunkunin _"Wai saboda Allah me yasa suke mata haka? Sai wani rainon ta suke kamar Kuwailat ce zasu ma aure? Basu san ta girma bane wai? Shekara nawa gareta saboda Allah? Sai a dinga mata abubuwa irin haka, ga ta da jikin girma ma sai sun sa ta karya ƙashin kwankwason ta wajen gudu."_ Ba jimawa ta fito a shirye da duk abinda take da buƙata tana ta turo baki, saida ta je wajen Hajia tana ta ƙorafin tana kallo z'a tura ta wani wuri? Sannan Nabila ta same ta anan suka wuce inda dreba ke jiran su. ******************** Gashi dai ya bar garin ne wai dan ya samu nutsuwa ya kuma sake yin nesa da masu kawo mishi zancen ne irin na marasa lafiya, amma abun ya ƙi fita a ran shi, shi fa har zuciyar shi yake jin sun aikata kuskure da wannan furuci da sukayi, hakan yasa gashi dai ga Hassan yana ta mishi hira, amma ya kasa sakewa saboda akwai abinda ke ran shi ƙwarai kua yake damun shi, idan ma yayi dariya ko murmushi take kake fahimtar irin yaƙen nan ne kawai. Suna shirin kwanciya bacci Hassan ɗin ya dubi Jabir yace "Da gaske gobe zaka fara zuwa wajen malam Muhammad Sani? Dan gaskiya mun fi kusa da shi sosai, kuma kaga a masallacin nake sallah isha'i kullum, idan dai ba wani uzuri ba ya kama ni kamar dai yau da bamu samu zuwa ba." Jinjina masa kai Jabir yayi yace "Ummm!" Sai kuma ya ga kamar rashin dacewar amsar sai yace "In sha Allah, abinda ya kawo ni kenan, gwara na fara da wurwuri." Jinjina kai Hassan yayi yana sak rigar filon d Jabir zai kwanta yace "Allah ya kaimu." Da "Ameen." Jabir ya amsa yana saka safar ƙafar shi irin ta baccin ne ta zallar audiga, yana gama gyara masa ya miƙe tsaye yana faɗin "Bari na faɗawa Jibril ya sanar da Hajia muna buƙatar abun kari da wuri idan Allah ya kaimu, dan ka karya kafin k fita." Sunan Jibril da Hassan ya faɗa ya saka Jabir ƙura ma Hassan idnu yana kallon shi, sunan Jibril... Ba wai ya tsani sunan bane, sai dai ya tsani wannan ɗayan mai wannan sunan, bayan tunawa da sunan shi ma sai ya tuna har abinda Abba ya faɗa mishi na cewa _"Idan bai amince da auren Maama ba, to Jibril ɗin da baya so shine zai aure ta."_ A rikice ya miƙe tsaye wani sabon tashin hankali na ziyartar shi, yada yake zaro idanu da fara safa da marwa ya sa Hassan dakatawa ya kalle shi yace" Ya dai Jabir?" Girgiza kai Jabir yayi ya kalle shi, shi ma bai sani ba, ji dai yayi yana nanata sunan Jibril da Maama? Jibril ya auri Maama? Bayan kuma ya san ƙudurin shi? Idan yayi haka ai bai kyautawa kowa ba kuma, tunda ya san manufar shi ba mai kyau bace, ita kan ta maaman bata sani ba. *To ko dai ya amince ne*? Ta hakae kaɗai zai kuɓutar da maama daga sharrin shi, dan ba zai sake magana akan maneman ta ba ya ce a maya magana, ba kula zai ce a fasa auren ba a fasa tunda dai shi ba kowa bane wajen su, amma idan ya amince da auren, to dama da zai kuɓutar da maama daga sharrin Jibril. To amma kuma maama fa? Maama zai aura jama'a? Shi ya yarda a ɗaura masa igiyoyin da Abba ya kasa iya ja? Ya Allah? Shi matsalar ba ma zai yarda a ɗaura masa su bane bare har mutane su samu abun yayatawa, ai da ya yarda an ɗaura da ya tabbatar Jibril ya cire idanun shi akan maaman shi sai ya saketa. Wannan tunani barkatai da ya jima zaune yana yi har ta sa shi bayan yayi alwala kamar yadda ya saba yayi raka'a biyu biyu har shida, sai yayi biyu daban da niyyar istikara sannan yayi addu'ar da ya inganta ana karantawa (sallah istikara tana da mahimmanci a rayuwar mu, inji malamai hatta a zaɓen wanda zai shigabance mu), daga nan kan sallaya yana ta ambaton Allah neman zaɓi a gurin shi har bacci ya ɗauke shi daga zaune bayan asuba ta fara gabatowa. Duk da a cikin bacci ne amma yanayin na masa daɗi sosai, idan ta shine ba zai farka wannan lokacin ba, amma kiran sallah da ladan yayi ya zaburar da shi daga farkawa baccin nan da ya masa mugun daɗi daga zaunen, amma abun mamaki da ya so bashi tsoro sai ya haɗa idanu da Hassan da shima yayi sallan daren ya kwanta kuma kiran sallah ne ya farkar da shi yanzu ma, mamakin Jabir yake da ya ga yana bacci amma yana ta wangalar baki yana dariya, wallaho sai ya mishi sak irin yadda yara ke yi idan suna bacci suna dariyar nan. Motsawa yayi yana gyara zaman shi da matsa wuyan shi da ya ji yana masa ciwo, idanun shi kuma akan Hassan a hankali ya firta "Ya dai Hassan? Lafiya kake zaune haka kana kallona?" Gyara zama Hassan yayi yace "Ai kai zan tambaya Jabir, kai dake ta sheƙa dariya cikin bacci kamar wani jariri." Haɗe fuska yayi, duk da Allah bai saka shi mai wani tuna mafarki ba idan yayi, amma sai na yau ya ɗan so tsaya mas a ƙwaƙwalwa shi ma ba wai duka ba, ƙwarai zai iya tuna a baccin shi yana cikin farin ciki ne da jin daɗin da ya fallasa sirrin zahiriyar fuskar shi. *Maama*? Anya kuwa, shi Jabir wai me ke damun shi? Da gaske dai ubangiji na nufin *aure* zai haɗa shi da maama? Ya yarda da istikhara ɗari bisa ɗari, hatta ginin gida da zai yi sai da yayi istikara, mota da zai siya ma haka har kasuwancin shi ma, kai ba ya komai ne kusan sai ya yi ta dan samun zɓin Allah, musamman tunda ya ji falalar ta kuma ya ga idan yayi yana samun dacewa kan abinda ya sa a gaba. Amma idan yayi istikara kuma yadda dama ƙa'idar ta take, ba wai za ka ga wani abu na musamman bane da zai nuna maka ka aikata abun da ka saka gaba, a'a malamai sunyi ittifaƙi kan zaka ji nutsuwa ne na ka yi abun idan shine alkairi, idan kula bari ne to za ka ji abun na fita a ran ka ne, sannan akwai wanda ubangiji zai saka maka wasi-wasi kan yi ko barin, to anan sai ka nemi shawarar manya da dattawa, ko kuma ka duba wanda ya fi alkairin sai kayi. *A* yau kum a yanzu da ya yi istikarar sai yayi mafarkin ga maama cikin shiga irin ta larabawa farare tasss tana ta dariya bayan idanun su a cikin na juna suke, ba wannan ba ma! Tashin hankali da tunanin da ya wuni yana yi har lokacin da yake tsaye yana sallah nan, yanzu bayan farkawar shi sai ya ji shi wani irin shaƙat haka kamar ba mai ɗauke da wannan yanayi da ya kasa tantance na baƙin ciki ne ko alhini. Bai kula Hassan ma sai ban ɗaki da ya shige ya ɗauro alwala, haka Hasan shima alwala yayi ya fito suka nufi masallaci, suna hanya Jabir na tasbihi da tahmidi har suka isa, suna kaiwa ƙofar shiga sukayi addu'a suka shiga, basu zauna ba saida sukayi tahiyatul masjid sannan suka zauna, bayan an kira sallah na biyu ma suka gabatar da salatul fijir sannan suka sake zama na daƙiƙu. Nauyayyar ajiyaro zuciya Jabir ya sauke ya lumshe idanun shi, ƙwarai nutsuwa yake ji na saukar masa daga tafin ƙafar sa har zuwa kan tsakiyar kan shi, sai kawai ya ji ya zai yi? Ba zai iya ci gaba da jan wannan rigima ba, dama kuma *wata kokawar* ta fi ƙarfin iyawar ɗan adam ko aljan, lallai a yanzu da ya nemi zaɓin Allah kula ya saka shi jin nutsuwa game da lamarin, to ya yarda shine ya rubuto musu haka, dan haka basu da tsimi bare dabara daga shi har ita Maaman, shi dai kam za yarda dan yayi biyayya ga umarnin Allah, sannan ya zama ɗaya da suka ɗaffaka sunnar da aikatata yayi ƙaranci a cikin al'umma, dan haka *daƙiƙa biyar* ba zai sake ɓatawa ba wajen sanar da iyayen shi ya yi biyayya ga umarnin su, dan bai san me suka hango mishi game da tarayyar nan ba da shi ya kasa hangowa, dan ya taso ne a rayuwar shi bai san so ba barz ya san yadda ake jin shi, duk da dai ya musa abinda Aliyu ya faɗa cewa wai yna son maama, bai san menene so ɗin ba, amma fa kuma bai yarda yana son maama ba, dan idan yana son ta ai zai gane ko ya ya n je tunda shi ba *dutse* bane. Hassan ya kalla dake kusa da shi lokacin har liman ya shigo yana haramar tayar da sallah yace "Hassan, da mun idar da sallah fa zan kama hanyar komawa, na tuna wani muhimmin abu a gida." Da mamaki Hassan ya kalle shi yace "Gida kuma? Karatun shi? Haka kwatsam? Lafiya?" Kallon shi Jabir yayi, sai dai kafin ya bashi amsa sai kawai ya ƙyale shi saboda kabbarar harama da aka fara yi, haka Hassan ya ƙyale shi har suka idar da sallah, ba yadda ya iya haka ya mishi addu'ar sauka lafiya bayan ya ɗauki jakar shi da kayan da ko warware su bai yi ba, haka ya sake kama hanya a fujajen kamar dai yadda ya taho ɗin nan, saida ya kama hanya sannan ya kunna wayar shi da ya ji shakkar kunnawa dan yasan zai samu kira da dama. *Alhamdulillah.* [02/09 à 16:19] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *66* Kiran Abban shi (mahaifin shi) da ya fi yawa shi yafi ɗaga masa hankali, gashi wai har da kiran Mama uwar marayu da Hajia da aunty Mardiyya, sai suka ma bashi dariya, wai su yanzu duk sun yarda su aura masa maama ne? Saboda Allah wannan wace irin fitina ce suke neman haɗawa? Ko da yake yayi alƙawarin ba zai sake jin auren nan a matsayin wata masifa ko mummunar *RUBUTACCIYA* ba, tunda ubangiji ma ya bashi alamar dake nuna yana bayan wannan haɗi. *Tunda* saƙo ya shiga wayoyin su na Jabir ya dawo kan sadarwa har suke riga-rigan kiran shi saboda lokacin kowa ya tashi sallah, kiran Hajia ne ya fara shigowa wayar shi, yana ɗagawa tun suna gaisawa ya ji wayar na ɗin-ɗin-ɗin, yana dubawa ya ga kiran Aliyu ne, bai mayar da wayar kunnen shi ba saida ya ga kiran Abban shi. Sauraren Hajia ya fara yi da tace "Dattijo, ya zaka min haka kuma? Bayan ina ta faɗa da ƙarfi cewa kai ɗin mutumin kirki ne har da ƙari, wanda ba zai bamu kunya ba dan mun bashi zaɓin mu." A nutse Jabir da ke tuƙi a hankali ya lumshe idanun shi, cikin wannan muryar tashi mai kama da fuskar shi yace" Ta ya kuka ga haka ya dace? Hajia Maama fa matar Abba.." Da sauri ta katse shi da cewa" Tsohuwar matar Abban ka dai, dattijo kada ka bari wannan aikin ladan ya wuce ka mana, na sani ba zaka kamo ƙafar Abban ka Kabir wajen dattako ba, dan gaskiya ko ni da nafi kowa farin cikin abinda ya aikata, ina tausaya masa da kuma jinjinawa nagartarsa, sai dai ba na so kuma ka bari Jibril ya fi ka nagarta a wajen kowa, dan iyayen Ummu sun tabbatar idan baka amince ba to zasu ba wa Jibril ita, abinda yayi a baya na neman mata kuma zasu ɗauke shi a matsayin ajizanci ne." Cije leɓen shi yayi yana ƙara damƙe sitiyari sosai, saida ya ji zafi a leɓen nashi sannan ya saki da sauri yana faɗin" Hajia ba za'a daina kawo maganar *ɗan nan* bane? Bai dace da Maama ba." Da sauri Hajia dake murmushi tace" Dan haka sai ka aure maaman ka, ko kuma kana kallo a bata wanda bai dace ba." Shiru yayi kawai yana sauraren ta, ita ma shiru tayi saida ta ji ba dai zai ce mata komai ba sannan ta numfasa tace" Jabir, kai fa kake faɗa min kana so ka sakawa Abban ka Kabir da abinda ya maka a rayuwa ta hanyar kyatatawa da riƙo da iyalin shi tamkar naka, ka faɗa min indai kna raye ba zaka taɓa bari shi ko ahalinshi wani ya zubar da hawaye ba, sannan ka faɗa min kana so ka taya shi kare mutumci da martabar iyalin shi, ka manta ne? Ka faɗa min duk waɗannan maganganun? Yanzu Jabir lokaci yayi da zaka saka masa, sai ka bijire ka watsa masa ƙasa a idanu? Jabir, Ummu tsohuwar iyalin sa ce, ya fi ka sanin dalilin da ya sa ya ce ka aure ta, idan ba kai ba wani ne zai yi, shin Jabir ba zaka taya shi kare wannan martabar da kayi ikrari ba? Ka fi so Ummu ta auri wani wanda daga mu har ita bamu san manufar sa ta son auren nata ba? Idan wani abu ya faru marar kyau da ita ba ka ganin kaima kana da kamasho a ciki? Tunda har an maka tayin auren ta amma ka ƙi, kayi tunani Jabir, ni a ganina kamar hakan ma wata hanya ce da zata saka ka ci gaba da tsare mutumcin iyalin shi, sannan ni a ganina duk da Alhaji Kabir dama mai taimako ne, amma ya sake samun azamar taimaka maka ne har ka kwana gidan shi na wasu kwanaki kafin tafiyar ka karatu saboda Ummu ta bashi labarin ka kuma ta san ka, da bata san ka ba wataƙila baka samu kulawa da gatan da ka samu a wajen shi ba, kasan mutane dubbani nawa ya taimaka a rayuwar sa? Ka san da yanzu wasu ma bai san da zaman su ba? Amma me yasa kai kaɗai kayi zarra a cikin su? Saboda kawai jinin ku ya haɗu ne? A'a Jabir, shi fa komai da ka gani a rayuwar nan wallahi akwai dalilin da yasa yake faruwa, abu zai iya faruwa shekara ɗaya baya, amma sai bayan wannan shekara ɗarin wani sanadi zai faru da za'a gano dalilin da ya faru a waccen lokacin, ni a tunanina haka tunanin Alhaji Kabir ma, kamar dan wannan ranar ne waɗancen abubuwan suka dinga faruwa da suka fito da kai daga gidan Abban ka." Numfashi Hajia ta sauke sannan tace" Zan aje waya, na ji ana ta kiran ka." Ba ta jira me ya ce ba ta yanke kiran, Jabir da duk ta ƙara saka jikin shi yin laushi ya fara saddaƙo ma duniya ya kuma fara jin yarda lallai fa kamar hakane, yana kallon kiran Aliyu amma ya kasa ɗagawa saboda tunanin da yake yi, ganin kiran ya tsinke sai ya aje wayar a mazaunin ta, take kuma kiran Abban shi ya shigo, ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗaga ya sa wayar a amsakuwa. Muryar nan ce ta daki kunnuwan shi ta Baban shi wanda ya ɗauki shekaru bai ji ta ba, wato muryar ingarman sojan nan cikin wannan zafin da ya raine shi da shi yna masa tsawar da duk da a zaune yake saida ya ji kamar zai sunkuya, cikin wani irin hargagi ne yace "Jabir dan ubanka kana ina?" Zaro idanu Jabir yayi ya taka birki saboda girman abun, yaushe rabon da a zage shi shi kam? Yanzu akan wannan abun ne ake zagin malami? Take yaji tsoron mahaifin nashi ya baibaye shi kamar dai yadda suke a shekarun baya, muryar shi na ɗan rawa rawa na son kuka da yake yi saboda wani sabon kaɗaici da kewar mahaifiya da yaji ya ɗarsun masa take a wurin yace "Abba.. in...a hany...a ne.." Cikin wata sabuwar tsawar yace "Hanyar gidan uban wa?" Lumshe idanu Jabir yayi ya ɗan lashe leɓen shi sannan ya furta "Hanyar Kano...Abba, amma ina dawowa yanzu." A hassale Abban yace "To maza ka dawo min gidan nan Jabir ina neman ka, sannan tun a hanya ka kira waɗanda kasan ya dace su halarci ɗaurin auren ka ka sanar da su da ƙarfe 09:00 na safiyar gobe malam Adam zai ɗaura auren ka da Ummu, ka fahimta?" Bai buɗa idanun shi ba ya haɗe wasu yawu masu zafi zafi sannan ya amsa da" E... Abba..." Ƙit! Abban yayi saurin yanke kiran saboda jin muryar Jabir na neman saka shi kuka. Jabir kuma haɗa kan shi yayi da sitiyari ya na hawaye, ba wai na auren da za'a masa ba, sai na yadda aka kasa samun mutum ko ɗaya ne da zai nuna ya fahimce shi sannan ya goyi bayan shi, ko da dqga baya zai nuna yana tare da sauran mutanen ne. Lallai rashin *mahaifiya* wani tabo ne babba a gurin mutum, yana da yaƙinin da tana raye wataƙila ita ta fahimce shi, idan kuma tana tare da su ne ita ma da zata rarrashe shi ne da maganganu masu daɗi, wataƙila ma har ta dinga shafa kan shi dake kan cinyar ta. Kiran Aliyu ya ɗaga dake ya san nacin Aliyu, yana ɗagawa cikin tsokana kam Aliyu yace "Tonton, wallahi ka dawo daga in da ma ka tafi, ka ganni dai na gama gayawa duk wani da nasan ka sani cewa auren ka gobe ne, kai *Mansu Sadiq Abdallah* yau yake tasowa, kasan dake akwai abun ba matsala bane a gurin shi kuɗin jirgi, ya ce dai baa za'a yi auren ka baya wurin ba, kuma ma sai ya ci tuwon amarya ya koma, dan Allah tonton ka dawo muna jira, kai mata sune ke guduwa idan za'a musu aure ba a so, na farko a rayuwata da naga namiji ya gudu, sai tonton, Allah dai ya ja zamanin ka, wallahi auren nan zai ɗauru gobe da izinin Allah." Yana gama faɗa ya kashe wayar, shi dama ba wai ya ji ina yake bane, kawai ya dai sanat da shi da mutane fa suna ankare game da auren nashi, haka zai sa ya shiga hankalin shi ya san da gaske ake masa ba da wasa ba. ******************** Shigar Eesha gidan ya sa Ummu da ita suka fashe da ƙara ta murnar ganin junan si suna rumgume juna duk da tsohon cikin Eesha ɗin da ya shiga wata na bakwai, cikin jin haushi Hajia Mammie ta harare su tace "Dallah kuna wa mutane ihu kamar ba mata ba, sai kowa ya ji muryar ku." Shiru sukayi tare da juyawa zasu shiga ciki suna ɗan turo baki da jin ita fa haka take tsohuwar nan, ita ba wani wai jika da zai ce yana da shaƙuwa da ita bare ɗa, haka kawai take ita, juyawar da sukayi ta sa ta faɗin" Ai kin san da mai lalle ke take jira ko?" Ummu da tasan da ita take juyowa tayi tace" Ina zuwa yanzu Mammie." Suna shiga Eesha ta kalli Ummu da kyau tace" Aunty, wai kinga yadda kika sake komawa? Wallahi kamar ba ke ba, har ɗaukar idanu kike." Sai kuma ta matse baki da irin rahar nan tace" Wannan idan *Jabir* ya gan ki a daren farko ai haukacewa zai yi." Haraa Ummu ta maka mata tace" Mahaukaciya, Jabir din me? Jibril yake." Da sauri Aisha ta dantse leɓen ta da ta ji ya so saka ta a uku yau, sai ta wayance tace" To ai na ɗauka duk ɗaya ne." Hararen ta ta sake yi tace" Da bambamci, Jibril kuma ya fi daɗi." Murmushi Aisha tayi tana taɓe baki, hakan yasa Ummu faɗin" Tare da wa kuka zo?" Da hannu Aisha ta fara lisafa mata" Ni da tawagata (ƴaƴan ta), da Maman Abbu (maman Sa'ad) da autar su Abbu (Leila ƙanwar Sa'ad), da wata matar aminin mahaifin Jabir, da kuma Maman Fadila (matar kawu Hisham) sai kuma Kuwailat ɗin ki." Da mamaki Ummu tace" Lallai tawaga, duk auren nawa ne suka zo wai? Kamar wani auren fari?" Taɓe baki Aisha tayi tace" To ai na farko ne mu a wajen mu, kinga shirin da Mamie take yi kuwa? Yanzu haka gida na can ɗinke da jama'a baki gani ba, na baro masu aiki na ta aikin abinci, Kuwailat ma ganin su Fauzan da Mubaraka ya sa ta ƙi biyo ni, gobe fa biki ne da aka ci masa buri, kuma kowa so yake ya ga me zai faru a bikin ƴar farin Abbun mu." Girgiza kai Ummu tayi tace" Lallai, to amma ita wata matar aminin Abban Jabir da naji kin ce, me ya haɗami da ita?" Murmushi Aisha tayi tana ayyana _" Ba zaki saka ni sakin baki ba."_ A zahiri kuma sai tace" To ke ko ai akwai zumunci sosai tsakanin su da malam Adam, kuma Abban Kuwailat ne duk ya gayyace su." Ɗan tsaki tayi tana kawar da kai tace" Wai shi Alhajin nan na rasa gane mishi, ya sake ni amma sai wani wurin zama yake nema a cikin ahalina, shifa tun shekaran jiya yana nan, ni wallahi tsoro nake kar ya hana aure na yiwuwa, in ba haka ba wa ya taɓa zuwa auren tsohuwar matar shi." Aisha dai dariya take yi kafin tace" In sha Allah ba abinda zai faru, wataƙila ma shi zai ɗaura auren." Tsaki Ummu tayi tace" Allah ya sawaƙe." "Ameen." Aisha ta faɗa suka ci gaba da hirar su, ganin zasu ɗauki lokaci ta fito aka fara yanka scoht ɗin da za'a mata lalle da shi, dan tun jiya aka mata wani irin kitso ƙanana sosai. _*RANAR LAHADI*_ Aliyu da Fahad yake kallo da suka zage suka shirya wata ƙwarya ƙwaryar walima a cikin harabar makarantar Aliyu, shi fa abun mamakin yadda mutane suka amsa gayyatar su su, kamar dai sun zo nedan su ci gba da ƙular da shi, harabar makarantar nan timjim take da matasa ƴan 25years zuwa 40years saboda karada kuma zumunci. Da gayya Aliyu da Fahad ke ta kai da kawo, shi Aliyu yna kiran shi da tonton, wato irin ga mijin auntynka nan ko? Shi kuma Fahad yaketa wani faɗin *mijin yarinya*, a ƙufule yakeda su, a cike fa yake da su wallahi, dan ya kula rayuwar shi ce suka mayar banza suke masa wasa da hankali, yaji ya yarda an ɗaura mana, amma menene na su dinga yi masa izgili? Bai yi zagi ba fa, amma wallahi daf yake da ya rurruga musu ashar yaran nan. Hular da tunda aka dawo daga ɗaurin aure ya cire ta ya aje gefe ya kalla, ƙwafa yayi yada kasan hular ta masa auren nan da yake kira *auren dole*, Aliyu da ya zo giftawa ta gaban shi yana ɗauke da lemuka a hannun shi masu sanyi zai ba baƙin da suka zo yanzun ya dakata, sunkuyowa yayi cikin raɗa yace "Tonton, dan girman Allah haba ka dinga murmushi, ka wani kama fuska ka tsume haka? Mutane suka lura ba sai ka sa a ɗauka baka farin ciki bane da auren auntyna." Irin kallon nan ya ma Aliyu, na wallahi ka kiyaye ni fa, sai kawai ya riƙe haɓa a tausashe yace" Aliyu, kuma yanzu nan kai baka jin haka kana jin kunyar hidimar nan da kake? Tunda ai kaga auren dole aka ma abokin ka ko?" Dariya Aliyu ya saki yana girgiza kai yace" Ko kaɗan wallahi bana ji." Gyara zama Jabir yayi yana girgiza kan shima yace " To kuma ba ka jin irin kunyar nan na kun haɗa ɗa da uwa zaman da bai dace ba?" Nan ma girgiza kai Aliyu yayi yana ƙyalƙyala dariya yace" Ko kaɗan, me zai sa naji kunya? Bayan nasan nan da wata tarain sha Allah wannan ɗan zai ma maaman shi ciki ne ta haihu." Wani irin numfashi Jabir ya sauke, sai kuma ya ƙura ma Aliyu idanu kamar zai haɗe shi, kallon shi ya dinga yi ba ƙyabtawa har saida Aliyu ya fahimci ya fa kaishi matakin ƙarshen nan, sai kawai ya bushe da dariya ya wuce sabgar gaban shi, Jabir kuma saida ya juya ya bishi da kallo saboda ganin kawai Aliyu dai ya zubar da ilimin shi wallahi, sannan abubuwa yake ta yi dai kamar irin na ƴan iska, in ba haka kuma Maaman? Zunubin auren ma da suka ɗaura bai ishe su ba sai sun sake raya wani a ransu da shi ya fi muni ma? Me zai aike shi tunanin kutsa hanyar da Abban shi ma ya gagara iyawa da ita? Wane kalar karen ne ya cije shi da zai saka shi tunanin shiga inda ba zai iya ba? Kai a ƙaddara ma zai iya, ta ya zai iya yi wa maaman shi wannan abun? Wallahi haramiyar shi, ba zai iya yin tsirara gaban maama ba gaskiya, ƴar tsirarar da yayi yana yaro lokacin ta gani ma ya isa ai, kuma ya san ita ma ai ba ruwan ta, ba zata yarda ta ɗauko hankalin shi da wasu abubuwa ba. Kai dakata! Duka ma zaman na kwana nawa ne zasuyi? Ai ba jimawa zasuyi tare ba, zai tafiyar shi Kano ita kuma ta koma gidan su ta samu wani daidai ita ta aura. Mansur Sadiq dake balarabe ne da yayi tattaki kawai dan wannan sabga gyara zama yayi yana kallon Jabir cikin harshen larabci yace "Ango, ya baka fara'a ne, wani abu yna damunka ne?" Kallon shi Jabir yayi, to ita wannan fara'a wai dole ce, a sa ka auri uwar ka ace dole sai kayi fara'a? Haba mana! Ɗan yaƙe ya sakar mishi yace "Kaina ne yake ciwo, ba komai bayan haka." Murmushi Mansur yayi yace "Kar ka damu Jabir *Abu Siddiƙ* (inkiyar da suke ma Jabir), ba dai kayi amarya ba, ita zata sauke maka gajiyar nan." Kallon shi Jabir yayi kamar yanzu ya fara ganin shi, Abu Siddiƙ? Ya ma manta da ana mishi wannan sunan, kafin Jabir ya bashi amsa Fahad da ya zo gilmawa yana waya ya dafa kafaɗar Jabir yace" Ango namu." Da kallo ya bi bayan Fahad, sai kuma ya kalli Aliyu da ya dawo yana kallon Mansur yace" Maƙwabci, kaga abu Siddiƙ ko?" Sai kuma ya kalli Jabir cike da son ƙular da shi yace" Ai in sha Allahu ma nasan yadda ka ci burin Siddiƙ ɗin nan, nasan maa wata na bakwai Maaman naka za ta antayo maka shi." Har ya juya zai tafi Jabir ya riƙe hannun shi gam, hakan yasa Aliyu juyowa yakalle shi da tunanin kar dai ya zabge shi da mari, tunda Jabir ai har ruƙiya yana yi ko, ya dambatu da aljanu ma shi kam ba zai iya dakuwa da shi a taron nan ba, murmushi yayi yace "Tonton ya dai?" A nutse Jabir ya miƙe sai kawai yayi gaba yana jan hannun Aliyu, bin shi yake yana murmushi har suka haɗe da Fahad da ya shigo da wasu baƙi su biyu, gaisawa sukayi da baƙin kafin Jabir ya ja hannun Fahad shima yace su zo, saida suka fito ƙofar makarantar Jabir ya saki hannayen su ya fuskance su sosai fuskar nan tashi a tamke yace "Kuna ji ko? Kunga dai nan taron da kuka haɗa ne, ku ji da sabgar ku nima ku bar ni naji da abinda yake raina, na rantse da Allah ku daina tsokanata ɗin nan, kunga dai ai Maama ba abokiyar wasan ku bace ko? Ku daina yawan ambatar ta a wurin nan bana so..." Sai kuma ya kalli Aliyu ya dafe ƙugu ɗaya yace" Da kake cewa Maala za ta haifa min Siddiƙ, Aliyu dama ni ɗan iska ne ban sani ba? Ka taɓa ganin na nemi mace ne da zan rasa wa zan nema sai Maamana? To ka daina Aliyu, bana so mu raba hali cikin mutane a zo na shiga uku dan abun faɗan yawa zaiyi a kaina, uwar Siddiƙ kuma tana nan tafe in sha Allah." Gaba yayi zai koma ciki yana faɗin" Ku zo muje." Fahad ne ya tsaya baya yana ƙumshe dariya yace" Kaje kawai, ni dama ɗaukar kazinmu da muka bayar a gasa mana za ni." Jin haka sai Aliyu ma ya dakata yace" E hakane, nima ɗaukar waccen saniyar za ni da aka bayar a yi mechouix." Kallon su yayi, ya kalle su sosai, wato dai ba zasu shiryu ba ko? Abinda ke haɗa shi da al'umma kenan fa, ba sa ji sau ɗaya, jinjina kai yayi yana ayyana _" Na barkuda halinku."_ A zahiri kuma sai ya dubi Aliyu yace" Kuma bana son sunan tonton ɗin nan." Suna kallo har kusa shigewa sai Fahad da ya ɗan biyo bayan shi yana dariya yace" To Alaramma kana nufin jingine min ƴar tawa zakayi a gidan naka? Wallahi ya zama dole ka..." Kallon da ya juya ya musu ya sa suka yi saurin barin wurin, Aliyu kula faɗi yake" Kai dallah rabu da shi, yaron da mafarki kawai zaiyi kaga yayi wanka." Jinjina kai kawai ya yi, Allah shi da ma anyi karatu yau da ya shiga wurin ɗalibai duk wanda yayi ba daidai ba ya zane shi, ina dalili jama'a mutane su suka ka gaba haka? Kawai dan anga shi maraya ne? Hmmmmm. Walima ta gudana yadda suka tsarata, an ci an sha alhamdulillah kuma an yi wa ango da amarya addu'a, har magriba matasa anan ana ta hira kafin a watse tunda babu kak amarya, saidai an tabu ne sa tunanin sai da safe dan akwai waɗanda za'a tafi da su yin godiyar ƴa da aka basu wajen iyaye. *Haka* ma a wajen amare biki da walima ne aka gabataro, bayan sallah la'asar kuma malamai mata ne suka gabatar da wa'azi, komai yayi armashi kafin sanda a ka watse aka bar Ummu da tunanin me ya sa aka ɗaga tariyar ta kuma? Amma ba ta tambayi ba'asi ba tunda dai an ɗaura auren, saidai har yau rashin yin wayada Jibril na damun ta sosai, kawai dai bata so ta fito da damuwar ta ne har a gane. *Alhamdulillah.* [02/09 à 22:16] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *67* Aisha ce ke janye da alkyabbar da ta rufe jikin ta da ita ruf, hatta kayan dake cikin jikin ta ba'a gani sosai, tunda suka shigo ɗakin ya sake sunkuyar da kan shi ya lumshe idanu, ya salam! Ya salam! Shine abinda yake ta maimaitawa, wuri Aisha ta samu tsakanin Mama da Hajia Mammie wacce Mama Nuriyya ta buƙaci ta kasance wurin dan ita zata musu maganin Ummu idan ta so yi musu hauka ta zaunar da Ummu ƙasa snnan ita ma ta samu wuri ta zauna kusa da Abbun ta. Yaya Bilal ne yayi gyaran murya yace "To Alhamdulillah, ranar da muke jira yau gata ta zo, komai dama idan aka saka mishi lokaci to ƙararre ne a wurin ubangiji, yau gashi Allah ya nuna mana an ɗaura wannan aure da muke fatan Allah ya saka albarka a ciki ya kuma albarkaci wannan ma'aurata." Sai kuma ya kalli Ummu duk da lulluɓi ne a fuskar ta baya ganin komai yace" Ummu, ke ce anan ke da buƙatar sanin wnda kika aura, shiyasa ma na ce a haɗu yanzu ba sai da dare ba kin tare saboda gudun matsala." Sunan ta ya sake kira da ya saka gaban ta sake tsinkewa ya faɗi, dan jin ya ce tana da buƙatar ta san wanda ta aura sai ta fara tunanin wani hali ne ga Jibril ɗin da ba su sani ba sai yanzu? A ƙasan maƙoshi sosai ta amsa da" Na'am." Ɗorawa yayi da" An ɗaura auren ki jiya da safe, na san kina cikin tashin hankalin son sanin me ya sa baki tare tun jiya ba, sannan me yasa ko kiran ki Jibril ba ya yi, to haka ya faru ne saboda ba da shi aka ɗaura miki aure ba, kuma ni da kaina na masa kashedin kiran ki, na kuma faɗa la iyayen sa idan ya kira ki zan ɗauki matakin da ba zai musu daɗi ba." Rintse idanu tayi sosai ta furta" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Hasbunallah wani'imal wakil!" A hankali ta buɗa idanun ta, sai dai jinin jikin ta ya ƙi tafiya daidai, haka ma kanta ya ƙi dakatawa daga sarawaro da ya fara yi mata, ba ta sake maida hankalin ta kan abinda yake faɗa mata ba a lokacin, saida ta tsinkayo muryar shi irin daga saman nan yana faɗin "Ki ɗauki *auren ki da Jabir* a matsayin abinda Allah ya hukunto, kafin muyi wannan tunanin Abban Kuwailat ne ya fara kawo mana wannan shawara, duk da Mamie ma abin ya jima a ran ta, da wannan muke fatan zaku yi masa sakayya da alkairi, ku zauna da junan ku lafiya da mutumtawa, hakan shine zai sa yayi farin ciki mu ma haka, sannan ku toshe kunnuwan ku daga maganganun da mutane zasu faɗa a kan ku, kusa kyakyawar niyya a ran ku kuji cewa ku ba haramun kuka aikata ba, Allah ya muku albarka, Allah ya albarkaci rayuwar ku, Allah ya baku zuri'a ta gari." Da" Ameen." Ɗakin suka amsa, sai dai ban da Jabir da ya tanƙwashe ƙafafun shi kan shi ƙasa cikin babban riga har da hula, duk da ba kayan da aka ɗaura aure jiya bane a jikn shi, amma dai suma sabi ne ƙalll, rashin sabo yasa yake jin takura da kayan, sannan sun ƙara mayar da shi wani dattijo, amma fa sun ƙara fito da kyawun shi da sake bayyanar da ƙaramar fuskar shi dake ɗauke da ƙananun shekaru. A ɗan rikice haka ta ɗago a hankali saboda bata tabbatar da abinda take so ta ji ɗin ba, saida ta sa hannu ta ɗan ja hular alkyabbar baya kaɗan sannan ta samu damar ganin Kawu Bilal ɗin, a nutse cikn tattausan murya duk da ta ga Jabir zaune kusa da Abban ta da kuma Alhaji Kabir, amma sai ta shafawa idanun ta toka tace "Abbu, *wane Jabir ɗin*?" Jabir dai bai ɗaga kan shi ya kalli wurin ba, sai kaxu Bilal ɗin da ya kalle ta da kyau yana murmushi yace "Ƴata, Jabir mana, gashi." Da fari galala ta kalke shi haka, sai kuma ta yi wata irin dariya mai nuna haba ɗin nan! Ɗan satar kallon Jabir ɗin ta yi wanda yau sai ta ga ya ƙara zama mata ma ƙarami a idanu, duk da dai yayi kyau kuma hancin nan uwa biro har ko bakin buta, amma ina ruwan ya da hancin shi. Ɗauke duban ta tayi ta sake maidawa kan Kawu dai Bilal da shine ta ga kawai za ta iya yi wa magana, dan bayan shi kowane anan zai iya raina mata hankali ai, murmushi ta saki irin mai ratsa zuciyar nan da ya saka kawu Bilal sauke ajiyar zuciyar an dace kenan? Ba tare da an sha wahla ba, amma sai yaji tace "Abbu, ni nake nufi wai da wa aka ɗaura min aure? Ko dai Jibril ɗin ya fasa ne?" Hajia Mammie ce ta daka mata tsawa da cewa "Ke, kalle ni, aure aka ce an ɗaura miki da Jabir, Jabir dai da kika sani gashi nan kuma gaban ki, da magana ne?" Wani irin gyara zama tayi inda tayi irin zaman sallah tana wani juya kai tana kallon Jabir, Jabir? Ka ji wani batu dan Allah? Juyawa kanta tayi ga Mama da ta tsura mata idanu tana ta addu'ar komai ya zo da sauƙi tace" Mama, wai da gaske Jabir ne mijin nawa?" Mama dake kallon ta dama ɗaga kai tayi tace" E Ummu, shine." Da wani irin yanayin hassala tace" To me ya samu Jibril ɗin? Ba shi zai aure ni ba? Idan ma mutuwa yayi ya za'a mayar dani kamar wata sakarya, a rasa wa za'a aura ma ni ɗin sai wannan *ɗan*, to gaskiya Mama ki faɗ..." Dama dai a tsakiyar Hajia Mamie da Hajia Mammie take, dan haka Hajia Mammie da tafi zafi ta kai hannun ta daidai bakin Ummu, sai kuwa ta runbusta mata shi wanda ya bayar da sautin bupppp! Da sauri ta dafe bakin ta tana kallon ta cikin wani irin yanayi na ɓacin rai, dama ita fa ba ƙaunar tsohuwar nan take ba duk da ta haifa mata uwa, bare kuma yanzu da suke neman tado mata aljanun ta ma. A ɗan hassale ta gyara alkyabbar ta tana ja baya da niyyar komawa wajen Abbun ta da ta san zata fi jik daɗi, dan Hajia Mamie ma dai ba wani gane wa juna zasuyi ba, uwa uba kuma Mama da zata iya marin ta ita ma, ganin haka ya sa Hajia Mammie ɗin nuna mata inda ta tashi tace "Ke dawo nan? Maza zo zauna nan." Haɗe fuska Ummu tayi ta girgiza kai tace "Mammie dan Allah ki ɗan dakata, Abbu ne zan tambaya, na san shi ba zai min wasa ba ai." Yunƙurawa Hajia mammie tayi zata tashi, da sauri Abbu ya musu alamar su zauna tare da kallon Ummu yace "Ummu, koma ki zauna." Ba dan taso ba ta matsa ta zauna, Abbu ne yace "Ummu, da gaske ne abinda kika ji, jiya auren ki da Jabir aka ɗaura ba da Jibril ba, ga Abban Kuwailat nan, shi ya nuna mana alfanun haɗa ku, bayan haka kuma muka gano matsalolin dake tattare da auren ki da Jabir, shiyasa muka yi hakan ba da izinin ki ba saboda tabbacin da muke da na zaki yi mana biyayya, ko ba zaki iya ba?" Kallon Abbun take yi da wani irin yanayi inda hawaye suka fara yi mata zarya a fuskar ta da babu kwalliya, girgiza kai take yi a hankali kafin tace" Abbu, ya zaku min haka dan Allah? Abbu wane Jabir kuma? Abbu ni da na yarda zan auri Jibril ne saboda kawai na tausaya masa, amma ba dan ina so saboda ya min ƙanƙanta a shekaru, ta ya kuma za'a haɗani da ƙasa da shi? Haba Abbu kun min adalci kenan? Idan Jibril yana da matsala a fasa auren mana, sai na samo wani mijin ko? Amma baa haɗani da duk wanda aka gani ba kamar dai a matse kuke da nayi aure na bar muku gidan ku, Allah yana gani ni bana son wannan auren, ƙwarai ina so na mutu ɗakin mijina, amma dai yaro kamar Jabir da kuma shi kan shi Jabir ɗin, to gwara na tabbata babu aure saboda bana son harkar raini wallahi." A ɗan zafafe Mama ta ɗaga hannu kamar za ta buge ta, hakan yasa Ummu runtse idanu amma bata gusa ba alamar ta ɗauko halin nan nata na kafuwa ba, sai kawai ta dakata dan tasan ko dukan ta zatayi yanzu zata ji mata ciwo ne amma tana nan kan bakan ta, dan haka ta sauke hannu ta a nutse tace "Ummu, magaganun ki sai suka min kama da na wacce bata taɓa zuwa makaranta ba, ya zaki bani kunya haka? Ina cike da alfaharin cexa na haɗaki da iyayen ki ban ba tare da naƙasu a tarbiyyar ki ba, amma sai ki dinga maganganu haka kara zube, me yasa? Me yasa Ummu?" Fashewa tayi da kukan da ya sa ka Jabir ɗin muskuta ƙafar shi, shi dai ayi a ƙare dan Allah ya bar wurin nan, bai taɓa sanin Maama na da wauta ba sai yau, shine take kira yaro ɗin? To me ye aure wai? Ba ci, sha, tufatarwa, kula da addinin ta, ɗawainiya yayin tashin lafiya, sai kuma saduwa ba? Bayan wannan akwai wani abu ne da take ganin ba zai iya ɗin ba? Shiyasa har take kiran shi da yaro? Hammmmm! Cikin kukan da ya saka Aisha jin kamar za ta fashe da kuka take faɗin "Abbu ku taimake ni dan Allah, wallahi ba zan iya zaman aure da Jabir ba, Jabir fa? Abbu yaron tsohon mijina ne fa, wallahi kamar ɗa yake a gurin Abban Kuwailat, to ta ya za'a ce wai shi zan zauna da shi a matsayin miji, Abbu ba zan iya ba wallahi, dan Allah ku kwance wannan auren." Hajia Mamie ce ta kalle ta tace" Hajia, ki saurare mu mana, ki dinga sanin me zaki faɗa gaban *mijin*, zo nan zamuyi magana?" Ɗaga kanta tayi ta kalli Hajia jin ta ce wai gaban mijin ta, ya subhanallah! Me yasa iyaye suke hakane? Wane Jabir wai? Yaron da Eesha ma tana gaba da shi a shekaru? Ba zata iya ba gaskiya, ga shi ɗan tsohon mijin ta, ga shi ya rainata, gashi kuma ƙanin bayan ta ne, to da wane za ta ji a cikin ukun? Ita bata da matsala dan an ɗaura musu aure bata sani ba, amma dai waɗancen abubuwa a'a. Ba zasu fahimce ta ba, dan haka ta yunƙura ta tashi tayi tako ɗaya ana biyu Hajia Mammie tace "Ke, gidan uban wa zaki je bayan magana muke da ke?" A kasalance ta kalli Hajiar murya ƙasan maƙoshi tace "Mammi ba zaku fahimce ni bane, shiyasa zan tafi, kuyi haƙuri dan Allah." Da sauri Hajia Mammie ɗin ta miƙe tsaye tana sake nuna mata wajen zaman ta tace "Zauna min nan malama, har wacece ke da zamu taru anan saboda ke amma ki tashi ki bar mu? Wato mu ga banzaye da basu da kima da daraja ko? To koma ki zauna min nan maza malama, idan ba haka ba ranki ne zai ɓace." Saida ta haɗe wni irin abu da ya tokare mata maƙoshi sannan ta kalli fuskar Hajiar tace" Mammie, k..." Abbu dake zaune ne yayi magana a kausashe da cewa" Ummu, ba magana ake miki ba? Zauna maza" Ita ai sanyi da lumanar Abbun ta kawai ta sani, da kuma riritata da shagwaɓa ta da yake, hakan yasa ta juya ta kalle shi ba tare da tayi abinda ya ce ba tace "Abbu kai ka gwada fahimta ta mana, dan girman Allah Abbbbbbbbb...." Ɗauke fuskar ta da yayi da mari ne ya sa ta yin ɗuffff bayan ta tangaɗa kamar za ta faɗi, tsananin mamaki yasa ta kalli mahaifin nata tana dafe da kunci da jinjina lamarin, yanzu akan Jabir ɗin ne aka mare ta? Mari fa? Da girman da ƴar ta da komai? Aka mare ta? Kuma ma a gaban yaron? A gaban shi ko kunya ba sa ji? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Wannan wane irin abu ne haka? Ƙiriƙiri a ɗaga hannu a marze ta gaban ƙannan ta jama'a dan kawai ta zauna da ɗan ta? Sake kallon Abbun tayi da ya sake nuna mata wurin yace "Zauna na ce." Sum sum sum ta juya ta koma ta zauna ta nutsu sosai, dan har lokacin ma kunnuwan ta basa ji da kyau, Alhaji Kabir da duk ba daɗin abun ke ta masa yawa a hankali ya kalli Abbun yace "Kayi haƙuri dan Allah, ba yarinya bace da zakuyi saurin saka mata hannu." A zafafe Abbu ya kalle shi yace "Har ita wacece da uwata na mata magana ba zata yi abun ba? Ba yarinya bace amma zamu zauna muna maimaita mata magana sau biyu, uban wa ta haifa anan? Dan kawai mun aura mata wanda muke ganin ya dace da ita, saita raina mu?" Ƙwafa yayi sai kuma ya kalli Ummun ta kwanta kan ƙirjin Aisha tana ta rirriga ta kamar yarinya tace" Ji nan da kyau, an ɗaura auren ki da Jabir jiya, kuma munyi hakane dan ina ganin na isa da ke, idan kina so ki ƙaryata tunanina da yaƙinin da nake da a kan ki to ki ci gaba da bore har kina faɗin duk abinda ya zo bakin ki, anjima za ki tare ɗaya daga cikin gidajen nan na Yaya Bilal dake kallon nan gidan, ki gaggauta gama shirin ki dan duk randa mijin ki ya zo tafiya ku bishi ku tafi tare." Ko da ya faɗi haka ya miƙe a hasale ya fita ba wanda ya dakatar da shi, Hajia Mammie ma da ranta ya gama ɓacewa miƙewa tayi tana faɗin" Allah ya baku zaman lafiya." Ficewa tayi, hakan yasa Alhaji Kabir da duk ya ji ya tsargu kuma dama dreba na jiran shi zasu koma inda suka fito yace" Kiyi haƙuri Ummu, ban bayar da shawarar wannan haɗin ba dan na cutar dake, wallahi da zuciya ɗaya nayi hakan saboda ganin dacewar hakan, amma kiyi haƙuri tunda na ɓata miki, ki yafe min dan Allah." Miƙewa yayi zai fita Ummu ta ɗaga kan ta daga jikin Aisha ta kalle shi, cikin muryar kuka har tana rawa tace" Ban taɓa ganin mugu kamar ka ba, da fari ka sake ni babu dalili ban maka komai ba, dan kar na auri wani da baka sani ba, shine ka sa yaron ka ya aure ni, dan ya sake ni a duk lokacin da ka s haka? Ba damuwa, zan zauna da shi har sanda zaka faɗa mana ya sake ni, amma idan na fito daga gidan shi ba ni ba sake aure." Murmushi Alhaji yayi yana girgiza kai, su Hajia ya kalla yace" Hajia ni zan wuce, in sha Allah sai munyi waya da ku." Addu'a suka bishi da ita har ya fita bayan Jabir ya miƙe ya bi bayan shi, Hajia Mamie ce ta kalle ta tace" Ummu, kenan ba'a isa a faɗa miki ki ji ba? Yanzu tsohon mijin naki kike faɗa ma haka kuma a gaban mu?" Kallon Hajiar tayi har da wata harara harara ta maka mata a zafafe tace" Hajia ku ba kuna kallo suka ɗaura min aure da shi ba, kun sani fa yaron shi ne da bai da kamar sa, kuma nima kun san alaƙata da shi irin ta ɗa da uwa ce, shine kawai sai a ce an aura min shi sabda ni ga wacce ta rasa masoyi, bayan gaba ɗaya Eesha ma ta girme shi a shekaru, to fisabilillah wane irin zama zamuyi? Shi ne *zai min ladabi*? Matsayina na wacce ta girme shi kuma na masa alkairi a rayuwa, ko kuma *ni zan ladabin* saboda shine mijin ni kuma matar? Ni wallahi kun cuce ni." Dariya Hajia tayi ta miƙe tana faɗin "Iyayen ki dai suka cuceki, ni dama ina bayan dattijo ne, ba dan a ce na masa tsufa ba ai da ni na aure abuna saboda nagartar sa." Da kallo Ummu ta bita tace "Oho! Kun san da haka ni kika aura min shi? Kenen ni duniyar ta zage ni?" Juyowa Hajia ta kalle ta tace "Ke, ba fa ke kika aure shi ba, shine ya aure ki." Saida Hajia ta fita kawu Bilal ya kalle ta a tausashe yace "Ƴata, ya haka? Dubi zaman da muka tara da iyayen mu amma kin watsa mana shi, mun tara zaman nan ne dan a saka muku albarka da baku shawarwari, amma kinga kin hasala kowa ya tafi ba tare da anyi wani abu muhimmi ba, Abbun ki kanshi da sai ta ɓace kake ganin ɓacin ran ki dubi yadda ya bar nan bayan ya kashe miki tafi a fuska?" A hankali ta matsa kusa da shi ko sauraren Mama ba ta yi ba dake mata nasihar ta gyara halin ta, cikin rarrashi ta kama ƙafar shi tace" Abbu, Abbu ai nasan zaka fahimce ni kai, Abbu dan Allah ya dace haka da suka min? Jabir fa yaro ne Abbu kuma k..." Irin kallon nan na hangen nesa ya mata yace" Ummu, wa ya ce miki namiji yana kaɗan ne?" Duƙar da kan ta tayi tana ayyna _" Tsoho ma ya kasa iyawa da ni bare ɗan mitsitsin yaron nan?"_ A zahiri kuma sai ta kalle shi a sanyaye tana zubo da hawaye cikin muryar kuka tace" Abbu, Jabir *ƴata* Kuwailat ce ta *dace* da shi wallahi, saboda ka ga yanzu tana sha huɗu ne, amma ni? Haba Abbu dan Allah ka duba maganar nan." Wani abu da ya gano a tare da Ummun shine, ita kamar matsalar ta ba ma wacce su suka yi ta hangowa bace, ita kamar dai shekarun Jabir ɗin ne basu mata ba ko ya ce suka mata kaɗan, in hakane zai namiji ne Jabir, kuma tunda zasu zauna bari kawai ya mata na babba da yaro, a ƙalla ya nuna mata ko kwana ɗaya mutum ya baka a duniya ya fi ka dabaroa, haka kuma ko ka ba mutum shekaru akwai abinda zai iya yi ko ya sani da kai ba lallai ka san karatun ba. Jim yayi alamar yana tunani, sai kuma ya kalli Mama dake kallon su yace "Hajia, ku ɗan bamu wuri dan Allah zan yi magana da ita." Da murmushi Mama ta miƙe tana addu'ar Allah ya shirya ki Ummu, da kallo Ummi ta bita tana ayyana _"Yo Mama ke ki aure shi mana idan ya sake ni, ai baki da miji kema, me ya hana ki aure har yanzu?"_ Saida Mama ta fita ya kalli Aisha yace" Kuna ji, sirri zamuyi da ku, zaku riƙe sirri?" Ɗaga kawunan su sukayi, inda Ummu tayi wani murmushi tare da gyara zaman ta irin ta ga mafita a matsalar ta, cikin raɗa yake ce musu" Kina ji ko? Yanzu zaku zauna cikin gidajen nan na wasu kwanaki, kiyi haƙuri ki zauna da shi kin ji? Alma da zaren kin ji ya ce zaku koma maraɗi, sai kiyi gaggawar sanar da ni, ni kuma nasan le zan yi da zai sa ya tafi ya bar mana ke nan, shikenan kun rabu, amma fa kada kowa ya ji." Cikin farin ciki Ummu tace" Da gaske Abbu?" " Ina miki wasa ne?" Ya faɗa yana mata kallon tuhula, girgiza kai tayi alamar a'a, hakan yasa yace" To yanzu tashi ku tafi, ki saki jikin ki kici gaba da harkokin ki kawai, ni na gaya miki kafin ku bar nan sai auren nan ya mutu." Cikin jin daɗi Ummu tace" To Abbu, nagode sosai, Abbu Allah ya saka maka da alkairi, kai kawa ka fahimce ni." Kallon Aisha tayi tace" Muje?" Miƙewa Aisha tayi tana kallon Ummu sororo da mmakin wai da gaske ita ce gaba da ita? To gashi dai ƙarara ya bayyana kawun nasu dabara ya mata, amma wai ta yarda kuma? Tsabar son a raba auren ne? Ko tsabar son girman ta ne ya hanata gane bata da wayo? Haka ta kama ta suka fita tanata share fuska a dole yanzu so take ta saki ran ta tund an bata garanti na rabuwar auren ta da yaron nan. *Tun* bayan sallah isha'i tsirarun mutanen da suka shirya rakata sua shiga harama, Ummu dake cikin farin cikin sirrin su da kawu Bilal haka ta zauna ana rangaɗa mata kwalliya ta gani ta yaɗawa a yanar gizo, tunda ai ya ce ta saki jikin ta kar wani ya gane wani abu, wani tsadadden material ne fari ƙal aka mata riga doguwa, haka komai aka mata shigar fari sai kwalliya da ta sake fitowa da ita. Tsaf ta zauna gaban su Mama da Mamie Nuriyya suka mata nasiha kamar yadda ake ma kowace mace kafin aka fito da ita, daga ƙofar ɓangaren su Mamie zuwa ƙofa tafiya ce mai zaman kan ta, dan haka mota aka saka ta sannan aka nufi gidan da suna kallon juna ne. Ƴan rakiya bsu jima ba suka fito daga gidan, Aisha da su Kuwailat ne suka jima dan saida Aisha ta sa yaran suka sake yin shara da goge goge suna yi suna hira kafin su baro mata gidan, a ƙafa suka taho inda Aisha ta ji daɗin tafiyar dan duk hidimar da aka yi ba'a yarda an saka ta aiki mai yawa ba saboda halin da take ciki. *Alhamdulillah.* [03/09 à 11:52] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *68* Da yana ɗaukar duk abinda su Aliyu ke yi dan su ƙular da shi ne, amma yanzu sai ya gane suna yi ne dan su lalata shi fa, so suke dole ya wa maman shi sheɗana, in ba haka ba me ya haɗa shi da kaza a wannan daren? Maaman zai ba kaza ta ci dan shi ma ta bashi ƙaniya ya ci ko me? Aliyu da ya ga da gaske b zai karɓa bane da sauri ya riƙo shi yana danna msa ledar a hannu yace "Jabir dakata kaji, wannan fa haƙƙin ta ne, kuma tun daga nan ne za'a iya gane riƙon da za ka mata, ko ba komai a ran ka a ƙalla dai ka bata tunda ana ba kowa, amma idan baka bata ba kenan zaka sa ta ji a ran ta dan ba budurwa ka aure ta." Shiru yayi yana kallon Aliyun da yake ganin kamar wayo yake so ya mishi, sai kuma ya kalli Fahad dake ta faman dariya yace" To ce ma wannan ya daina min dariya, ni wallahi ba abinda zan wa Maama." Cikin rarashi Aliyu yace" Mun sani mana, kai da kace ba ɗan iska bane kai, ko ka iskance ɗin ne? " Girgiza kai yayi yace" Um um." Tare da figar ledar yayi hanyar shiga ciki, saida safe suka dinga yi mishi har ya ɓace ma ganin su, gidan tsit ba alamar akwai mutum a ciki, gidje ne dama irin na zaman mai mata ɗaya, haka ya buɗa falon ya shiga wanda dama ba'a yi gyara ba saboda ba zama zasu yi na lokaci ba, fridge, carfet, labulaye da wasu abubuwan buƙata ne kawai a falon, sai wasu sofa masu kyau da ya ƙawata falon. Ɗaki biyu ne a ciki sai ban ɗaki dake gefen su bayan ta tsakat gida, ɗakin da ya ga hasken fitila ya nufa, ba rufe yake gaba ɗqya ba kuma ba buɗe yake ba, dan haka ya ɗan ƙwanƙwasa ƙofar tare da zuba wata irin siririyar sallama da ta saka gaban Ummu faɗuwa, duk da gidan miji take amma ta ma ɗan manta da wanene mijin nata, kayan baccin ta da aka haɗe mata da ƙananan kayan ta na ciki kawai take ta faman warewa, da sauri ta miƙe tana kallon ƙofar, sai kuma ta gyar tsayuwa tana ci gaba da duban ƙofa da son sanin lafiya kuma? Me y zo yi mata? Ba tare da ta gusa daga inda take ba irin ɗan nan ya zo wajen Maaman shi a gatse tace "Oui, wa ye?" Jabir dake baƙin ƙofa jin ta msa wannan tambayar sai ranshi ya sosu, sai kawai ya turo ƙofar a gadarance ya shigo, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kan shi, kayan da aka kawo ta da su ne bata cire ba, ƙwarai Maama tayi kyau kuma sai tayi wani irin sharr da ita kamar ƴar budurwa, musamman da babu ɗan kwali a kan ta sai ƙananan kitson nan da ya fito rass ga wani jan lalle da aka cika hannayen ta da shi gaba da baya haka ma ƙafafu. Sai dai ai maaman shi, ba zai bari sheɗan ya dinga saka shi yawan kallon ta ba gaskiya, zama da mace wuri ɗaya ai haɗari ne da shi, sheɗan kuma dama ai la'anannen Allah ne, Maaman ka ma sai ya sa ka ji wani abu a kan ta. Rusunawa yayi ya aje ledar hannun shi kan carfet ɗin da aka shinfiɗa ɗakin wanda shima gadon ɗaya daga cikin ɗakunan baƙi dake cikin gida ne wajen su Hajia aka aza musu, kuma wannan ɗakin kawai aka gyara ban da ɗayan, saboda suna ganin to ai mata da miji ne. Yana aje ledar ya juya ya fice bai ce mata ƙala ba, ita ma bata kula shi ba har ya fita sannan ta je ta rufe ƙofar tana ayyana _"Ba kaza ba? Za ka ci kaza, marar kunya, dan baka jin kunya har ni zaka kawo ma kaza, to idan na ci me zaka min?"_ Aikin gaban ta ta ci gaba da yi, inda Jabir ma da ya fita yayi mamakin ganin ba komai a ɗaya ɗakin bayan fitila da fanka sai jakar kayan shi da ya aje tun sanda suka zo, kayan baccin shi ya ciro da zai saka sannan ya cire na jikin shi amma da singlet ɗin shi da towel a wuya ya fito ya nufi ban ɗaki. Dama ban ɗakin ita ke kallon ɗakunan, hakane ya sa yana daf da isa ban ɗakin Ummu ma ta fito za ta shiga dan yin wanka ɗaure da towel amma da hijabin ta, suna haɗa idanu da sauri ta maida ƙofar ɗakin ta rufe tana maka masa hararar da ta saka shi ɗan yin tsaye yana tunanin da shi take ko me? Me ya mata to? Kar fa dan yna ce mata maama ta raina shi shima, ba ya son haka fa, shi tsaran ta ne da zata harare shi? Ka ji yarinya kai da iya shege. *WASHE GARI* A kujerar sofan dake falo ya kwana dama, da ya dawo daga masallaci ma nan ya sake kwantawa, hakan ya sa ko da Ummu ta fito saboda matsananciyar yunwa za ta shiga madafa ɗauko faranti ta zo ta ci kazar nan ya tashi zaune, wallahi ya ɗauka za ta gaishe shi ne ko ta ce masa dai ko da sannu, amma ƙuruciya irin ta Maama sai tayi kamar ba ta gan shi ba ta fita, jim kaɗan ta dawo ta wuce wqnda dole Jabir ya bi bayan ta da kallo, sai kawai yayi murmushi ya sake komawa ya kwanta. Saida ta ci ta ƙoshi ta tattare komai ta fito da farantin da leda a hannun ta, saida ta durƙusa gaban fridge ta saka sauran lemukan da ta rage sannan ta ɗauki sauran ta kai madafa ta aje ta wanko hannayen ta ta dawo. Gyaran ɗakin nata tayi ta kunna masa turaren tsintsiya da na wuta bayan ta fesa na ruwa, fitowa tayi ta shiga ban ɗaki nan ma wanke tayi tasss ta saka turare sannan ta dawo falon. Hararen shi tayi duk da ta ga idanun shi a rufe suke, taɓe baki tayi tana ayyana _"Yanzu dan fitsara Jabir ko ina kwana ba zai iya ce mata ba? Ba laifin shi bane ai na iyayen ta ne."_ Dake ba wani gyara d zata ma falon, sai kawai ta fara fesa turaren ruwa, sannan ta jona wayar kaskon turaren wuta mai aiki da lantarki, hayaƙin da ya fara tashi ne ya saka Jabir buɗa idanun shi duk da dama ya ji tana ta feshe ɗakin da wata masifar🤣, zaune yayi yana kallon ta tana kunna wani turaren kuma na tsintsiya, bai so yi mata magana ba saboda shi dai ita yake so ta fara masa magana tunda ai ita ce mata a gidan. Amma kuma wannan abun idan ya masa yawa mura yake saka shi, dan haka ya mata wani irin natkakken kallo murya ƙasan maƙoshi kamar mai rowar muryar yace "Bana son hayaƙin nan ya min yawa." Ta san da ita yake, amma sai ta ƙi ko jiyowa bare ya san ta ji shi, ama daga haka ƙusƙus take faɗin "Ɗakina ne ba naka ba, ka fita mana." Ganin bata saurare shi ba yasa a dake ya sake faɗin "Ki barshi haka, bana so ya min yawa." Ba tare da ta juyo ta kalle shi ba tace "Idan baka so ka canza guri mana." Kallon ƙeyar ta yayi, sai kawai ya jinjina kai yana miƙewa yace "Ok." Hanyar ɗakin nata ya nufa, da kallo ta bishi, ganin har ya buɗe ya shiga zai rufo ƙofar da sauri tace "Jabir." Ɗan dakatawa yayi saboda jin yadda ta wani kira shi a wani gatsaltsal haka wai Jabir, amma shi wannan shege ɗan iskan ta iya kwantar da kai idan za ta kira sunan shi ko? Har wani Jibril take faɗi? Wani arnan kallo ya mata da idanun shi nan ƙanana irin _" Ina ji?"_ Ba alamar rusunawa ko taunawa tace" Ɗakina ne nan." Cike da shaƙiyanci ya kalle ta sama da ƙasa sai kawai ya ja ƙofar ya rufe, dake nan hayaƙin ya rage sai dai ƙamshin na nan na wannan sanyayyan turaren da mace indai kikayi aiki da shi da wuya ki cigaba da son wani turare bayan su, wato *bakhoor* da kuma *fleur da coton*, turare ne da su basa buƙatar wuta, ƙamshin su ba karamin daɗi gare shi ba, sai dai idan ba ka jaraba ba kawai. Lafiyayyar shinfiɗar nan ya haye tare da jawo zanin rufar ya rufe jikin shi, cikin wata irin nutsuwa ya fara sauke numfashi a hankali a hankali. Ummu kuma ƙwafa tayi da tunanin zai fito ne ai, dan haka ta ci gaba da gyaran tsakar gidan, amma da ta kamalla ta shigo sai bata gan shi ba, rufe ƙofar falon tayi saboda tana so turaren da tayi ya jima sannan ta nufi ɗakin tana tunanin yau zai gane gaba take da shi, in ba rainin wayo ba ɗakin nata zai shiga ya kwanta? Bacci har ya fara ɗaukar shi kawai ya ji an bubbuga katifar da ƙarfi, da ƙarfi fa irin za ka tashi wanda ka raina ɗin nan daga bacci, kuma har da kwaroroton kiran sunan "Jabir.. Jabir kai...tashi ka koma ɗakin ka nim..." A hankali ya tashi yana rintse idanun shi sosai tare da danne leɓen shi na ƙasa, zuro ƙafafun shi yayi ƙasa yana ɗan dafe goshin shi, saida ya ji kan shi ya daina sara mishi saboda hargitsatsen tashin da ta masa sannan ya ɗaga kan shi ya kalli fuskar ta. Ta dafe ƙugu sai wani harare harare take yi, ai ba yarinya bace ita, kuma ta san me ake nufi da miji, shine kawai ta raina? A nutse, cike da dakiya ba alamar wasa yace "Haka ake tashin mutum a bacci?" Kallon fuskar shi tayi, ka ji yaron nan da rainin wayo? Sai kawai ta taɓe baki ba tare da ta daina kallon shi ba tace "Ka koma ɗakin ka." Ok! Kenan dai ta kasa fahimtar yaren shi ko? Dan haka ya miƙe a nutse tare da takawa ɗaya a na biyu ya kai gare ta, daf da ita ya tsaya, zai iya cewa kansu ɗaya da ita a tsayi ma, dan da zata saka dogon takalmi tsaf za ta fishi tsayi, hakan ya bashi damar kallon ta ido cikin ido fuskar shi a haɗe yace "Kinga, ba tashin hankali nake so muyi ba a zaman nan da zamiyi na ɗan lokaci, sai dai duk da haka bana so ki na yin abubuwan da zasu hassala ni, kinga jiya da na shigo na miki sallama, amma baki amsa min ba sai kika ce wa ye? Bayan kuma nasan kin san ko wa ye ɗin, na ƙyale ki muka kwana a haka, tunda safiyar nan tayi ba ki ce min komai ba, ko ba komai ki ce min ma antashi lafiya? Amma ba ki yi ba, ni na miki magana kan wannan hayaƙin da kike ta cika ɗaki da shi, amma me kika ce min? Na zo nan kuma shima ba zaki barni ba? Bana so wani abu na rashin ganin girman juna ya shiga tsakanin mu, ko haihuwata kikayi tunda yanzu *igiyoyin ki* na hannuna na cancanci a darajta ni." Sai kuma ya ɗan ja baya kaɗan yana ci gaba da kallon fuskar ta yace" Burin da na zo dashi gidan nan shine, idan na ga fuska a wajen *Maama*, to zan ci gba da gaishe ta kamar yadda nake yi lokacin tana gidan Abba, idan gari ya waye na tambayi Maama ko da abin da take so nayi mata, tun daga wanke wanke, shara, girki, komai ma, na yi shiru ne jiya da yau dan naga naki salar kamun ludayin, shin idan ni ban yi ba ke zaki nuna nagartattun halayen babban gidan da kika fito, sai baki yi ba, to ya kike so na miki? Na nuna miki tawa kalar?" A nutse yake maganar kuma a nutse ya koma ya zauna bakin gadon yana dafe kan shi yace" Nan ɗakin zan zauna, waccen ba a gyara yake ba, kuma daga ni har ke ai zaman wucen gadi ne zamuyi." Komawa yayi ya kwanta yana kallon fuskar ta dake kallon shi idanun ta sun yi ja kuma a cike da hawaye, bai damu da ganin haka ba dan bai ga abinda ya mata na kuka ba ya sake cexa" Dan Allah kar ki sake tashi na, azumi nake." Zuciya ce ta kawo wa Ummu a wuya, sai kawai ta juya da sauri ta bar falon tna fashewa da kuka, kukan kawai take tana tuna zafin maganganun da auren da aka mata da Jabir ya sa shi ganin damar ta har yake faɗa mata... Kamar busar sarewa kukan nata ke cika mishi kunne, tun yana juyi yana gyara kwanciya har dai ya ji shi fa baya son takura, kukan nan nata jin shi yake kamar a cikin zuciyar shi take yi, dan haka ya taso ya fito ya same ta zaune sai goge majina da hawaye take yi da hijabin jikin ta. Ƙarasowa yayi ya tsaya gefen ta yana kallon ta yace "Wani abu akayi kike kuka?" Ɗago kan ta tayi ta kalle shi, sai kawai ta miƙe tsaye tana aika mishi wani kakkausan kallo muryar ta a ɗan ɗage sama tace "Idan ban yi kuka ba ya kake so nayi? Jabir ni ce zaka sa gaba haka kana wa wulaƙanci? Dan kawai na ce ka koma ɗakin ka? Shikenan ku maza da an ce wannan matar ku ce shikenan sai ku kasa girmamata ku dinga kallon ta kamar yanzu aka haife ta." Jinjina kai tayi tare da komawa ta zauna tana jan majina da ƙara share idanun ta, kamar wacce ta tuna wani abu kuma sai ta kalle shi tace" Kuma da kake cewa ban gaishe ka ba, Jabir fisabilillah ni kake jira na gaishe ka dama? Ni ce fa, ni maman Kuwailat, a kawo ni gidan ka jiya amma ka dinga min ihu wai ban gaishe ka, saboda Allah maganar nan da kayi ta dace a ma'aunin hankali?" Kallon ikon Allah kawai Jabir ke yi, saida ta gama maganar ta tsaf sai kawai ya taɓe baki yace" Hmmmmmm!" Juyawa yayi ya sake shigewa ɗakin ya rufi ƙofar yana addu'ar Allah ya shirya wasu, ya kula ba wa wasu lafiya irin su Aliyu da maaman shi. Duk da tana son shiga ɗakin dan ta cire kayan ta tayi wanka, amma haka ta haƙura bayan ta daina kukan kawai ta kishiginɗa anan har bacci ya ɗauke ta ita ma. Ƙarar ruwa a ban ɗaki ne ya tashe ta, ganin ɗakin nata buɗe ya tabbatar mata wato yaron nan ke wanka ko? Tashi tayi tana cire hijabin ta ta shige ɗakin ta rufo, saida ta ƙara gyara shinfiɗar tana ta ƙwafa da tsakin ya sakar mata ƙamshin wani bahagon turaren shi da ba ta san wane iri bane, yana da daɗi dai amma ita bai mata ba, tana gama gyara shinfiɗar ta cire kayan ta sannan tayi ɗaurin ƙirji dan yin wanka. Ko da ta fito ta ji motsin shi a ɗaya ɗakin, dan haka ta shige ban dakin ita ma ta rufo, saida ta fara wanke kayan dattin ta sannan ta yi wanka ta shanya pant ɗin ta a murfin tagar sannan ta canza pad ta fito. *Ba ta* san fitar shi ba, saidai tana fitowa kan ɗan ƙaramin teburin dake tsakiyar falon dan babban an tura su yau da safe suna hanya, su Aisha na zuwa kula zasu yi gyaran ɗakin, farar takarda ta gani tana ɗauka kuɗi suka faɗo, duba takardar tayi tana kula duba kuɗin, gajeran rubutu ne daga Jabir _"Ki yi abinci iya ke, ina azumi."_ Wata irin ƴar dariya tayi tana zama tace" Ikon Allah! Nan Jabir wai kuɗin cefanai ne ya bani? Taɓɓ!" Wayar ta dake hannun ta ta fara dannawa lambar Mama kira tana aje kuɗin da takardar, Mama na ɗauka Ummu cikin shagwaɓa tace" Aunty, shine ko a kira a ji ya amarya ta tashi?" Dariya Mama Nuriyya tayi tace" Ke aunty baki sani ba, ni gidan la na so in je in gaishe ku, Abbun ki ya ce ai kawai ban da hankali, dole na haƙura fa, kula ya ce kar a kai muku abinci, ai ke ba yarinya bace za ki dafa." Numfashi Ummu ta sauke tace" Aunty ki ƙyale Abbu, ni fa ya mara a fuska saboda auren ɗana, ai wallahi ina nan zai zo mu shirya." Dariya Mama ta sake yi tace" Ai kam zai zo, dan tun jiya yake ta kallon hannun shi wai ya mare ki, har da cewa na kira ki naji kina lafiya? Ni kuma na ce na ƙi ai yana da waya." A tausashe tace" Aunty ina zaman lafiya? Bayan kun haɗani da yaron nan yna ta min rashin kunya a gida." Tintsirewa Maman tayi da dariya tana faɗin" To Allah dai ya bada haƙuri, kinga aunty bari na je su Maman ki ne ke ta shirin tafiyar su." Da sauri tace" To, saura kuma su tafi ba wanda ya zo min ban kwana." Har za ta aje wayar sai kula tace" Aunty a turo min abinci dan Allah, yanzu na tashi fa." Da" To." Kawai mama ta amsa ba tare da tunanin to me ya sa ba zata dafa da kan ta ba ko dan mijin ta? Sallama sukayi inda kowa ya shjga yin abinda ke gaban shi. Sai azahar su Mama suka zo yi mata ban kwana, saboda zasu tafi ƙarfe 03:00 dan a Zinder zasu kwana kafin da asuba su wuce, saida tayi ƙwallar rabuwa da Maman haka ma Nabila saida tayi kuka kafin su bar Maman ta tafi. *Ƙarfe 06:34* Tana zaune kan kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya tana danna wayar ta inda take sauraren wata nutsatsiyar waƙar hausa, hankalin ta ya ɗauku kan mutanen grp ɗin su da suke ta mata barkar aure da tayi wanda ita bata faɗa ba ma sun dai ji ne, hakan ya sa har ya shigo yana sallama ba ta kula ba, saida ya yaye labule ya shigo yna sake yin salama ne tayi saurin ɗqga kanta ta kalli ƙofar. Take ta maida duban ta kan wayar ta cikin daƙilewa ta amsa da "Wa'alaika salam." Ba ta sake kallon inda yake ba, a nutse ya shigo bayan ya cire takalmin shi tare da duban ta a karo na biyu, ledar hannun shi ya aje kan teburin tare da yin zaune kan kujera yana faɗin "Alhamdulillah ala ni'imatil islam." In kafin ya shigo ta san akwai wani abu a kusan ta haka yanzun ma da yake zaune, abinda ya saka shi kenan zuba mata idanu yana kallo, ba kwalliya tayi ba bayan kwalli dake ga idanun ta, amma ɗaurin da ta kashe kan riga da siket din da duk da bata miƙe tsaye ba ya san sun mata kyau, sai kawai ya miƙe ya shiga ɗakin nashi ya yo shirin watsa ruwa kafin a kira sallah. Tana ganin ya shiga ta miƙe da sauri ta shige ɗaki dan dama ta so yin haka, amma bata so ta bada baya ya kalle ta saboda siket ɗin ya kamata sosai, kuma daga yanzu za ta dinga zama da hijab kusa da ita saboda irin haka, yana fitowa bai gan ta sai bai damu ba ya wuce ban ɗaki, dan danan ya fito ba jimawa amma sai ya samu ledar da falon yadda ya wuce ya bar su. Yana shiga a gaggauce ya sanyo farar jallabiya da wasu silifas masu kyau ya feso turare ya fito, da sauri ya buɗe ledar ya ɗauko robar dabino ya buɗe, guda bakwai ya ɗauka ya wanko waje sannan ya dawo ya zauna, a nutse yayi buɗa bakin shi kafin ya fita masallaci. *Alhamdulillah.* [03/09 à 20:54] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *69* Sosai ran shi ya ɓace ganin ya dawo ya ƙara tarar da ledar nan, kenan ba ta damu da abinda ya shigo da shi ba, bayan kuma shi ɗin ya kasance malami ne dake koyar da ƴan mata da matasa samari yadda ake zaman aure, yana faɗawa matan su dinga karɓan duk abindz miji ya shigo da shi, shine shi za'a nuna masa iyakar sa kenan? Kai tsaye akalar sa ya juyar zuwa ɗakin nata, yana zuwa tura ƙofar kawai ya yi, kwance take saboda hauka irin na Maama bayan yanzu aka idar da sallah, kuma shi bai ma ga alamun ta yi sallar ba. Ko da ta kalli ƙofar a ɗan firgice saboda ba ta tsammanin zai shigo wannan lokacin, sai ta sake mayar da kallon ta ga wayar ta hankali kwance, cikin dakakkiyar muryar da saida ta kalle shi yace "Zo nan?" Daga haka ya juya ya fita, da tsananin mamaki ta kalle shi tana maimaita "Zo nan?" Sai kuma ta nuna kan ta tace "Ni ɗin? Ni ce Jabir za ka ma wannan kiran?" Zaune tayi tana cije leɓen ƙasa, sai ta jinjina kai ta gyara zaman ta, ba za ta je ɗin ba, dole akwai buƙatar ya koyi yadda zai dinga mata magana, ko dai yana mijin ta ya dace ya wani ce mata wai zo? Kuma ya juya ya fita kamar wani uban da ya haife ta, to ba zata je ba ya zo ya ɗauke ta idan ƙarfin shi ya kai. *Wato* ba za ta zo ba kenan? Minti ashirin kenan fa da ya ce ta zo, wai Maama hawan jini ne take neman saka mishi daga jiya zuwa yau ɗin nan? To ba zai yiwu ba, gaskiya shi ba zai iya haƙurin da Abban shi ya yi ba, dan haka bari yayi maganin fetsara da sheɗanancin Maaman nan marar kunya kawai. Yana shiga ɗakin da irin zafi zafin nan ya tsaya gaban ta har lokacin tana zaune kan gadon, fuskar shi a haɗe yace "Ba ki ji na kira ki bane?" Cike da ƙarfin hali irin na Ummu ta masa wani kallon sha ka tafin nan sannan ta ɗauke kan ta tace "Ai ban ɗauka da ni kake ba." Jinjina kai yayi yace "Ok, dama ba ke kaɗai bace a ɗakin nan?" A nutse ta miƙe tsaye tana aje wayar ta tana kuma kallon shi tace "Jabir, ai kasan ko ni dabba ce bai kamata ka min kiran da ka min ba wai zo nan, sannan ka tafiyar ka, ni na ɗau..." Bai so haka ta fara faruwa tsakanin su ba, bai so a ce nan kusa wani abu ya fara haɗa jikkunan su ba, to amma ya ga Ummu fin ƙarfin shi take so ta yi, abinda ya hassala shi kenan da azama cike da jarumta ya zura hannun shi ya damƙo damtsen ta tare da jawo ta jikin shi.... Yadda ta faɗa jikinshi shi kuma ya saki damtsen nata sai ɗaya hannun shi da yayi gaggawar zagaya shi ta ƙugun ta ya haɗa da na shi ƙugun dan kar ta samu damar zame masa har sai ya faɗa mata abinda yake son faɗa. *Amma* yana dora hannun shi a ƙugun nata sai saman wannan jarababbiyar *jigidar* dake rikita mutane bayin Allah... Hannun shi ne kawai ya taɓa jigidar, ya ji shatin ta tare da jin sautin ta saboda taɓawar da ya ma jigidar, wani irin tsammmm! Jikin shi yayi ya amsa har saida ya ji tsigar jikin shi ta tashi, da zafi ne ya riƙe ta dan ya kora mata nashi kashedin ta gane nashi haukan ya girmi nata fa. Amma sharrin shedan dake saka wa ɗa tunani marar kyau akan maaman shi, sai ya shiga dan shafa ƙugun nata da duka hannayen nashi biyu yana sake jin yawan jigidar a ƙugun ta. Idanun ta yake kallo ba wannan rusunawar da wani kakkaucewa, kamar yadda take kallon shi yana hango tsana da jin haushin shi a idanun nata da suka rikiɗa tsabar takaici da baƙin ciki kuma sun mata taff da hawaye. Cike da shaƙiyanci yake jan duk jigidar da ta dira a hannun yana tantance yadda suka saki ƙugun nata da kuma zaren da aka yi ɗaurun su da ita, mafi aksari zaren yana ja, bai fi uku zuwa huɗu ba da ya ji zaren su bai jawu ba sanda ya ja shi, matso da fuskar shi ya sake yi daf da ta ta, wanda hakan yasa Ummu saurin kawar da kan ta hawaye na silalo mata a kumatu. Yatsu biyu ya sa ya riƙo haɓar ta tare da juyo da kallon nata ga fuskar shi, daga leɓen ta da ta cije zuwa kan hancin ta da idanun ta dake zubar ruwa yake ƙarewa kallo, sai yake ji a zuciyar shi _"Ashe haka Maama take da kyau idan aka ƙure ta? Ashe haka jikin ta ke da laushi kamar na mage? Ashe haka jikin ta ke fitar da wani ƙamshi mai daɗi?"_ A zahiri kuma wani narkakken kallo yake mata amma muryar shi a ɗan kausashe yace" Wai ni kam *haihuwata* kikayi ne? Da komai komai nayi sai kin ce wa ye wa ye, to na faɗa miki bana son tashin hankali, idan na ce kiyi kawai kiyi ba sai na maimaita ba, yawan hayaniya ciwon kai yake saka ni, sannann...." Yatsa biyu ya sa ya kamo leɓen nata da ta cije ya ciro shi daga cikin bakin nata ya ɗan matse leɓen nata, hakan yasa bakin ta buɗewa har ya ji iskan kanunfari ya daki hancin shi da ya saka shi ƙara matsa kan shi kusa da fuskar ta sanan ya ɗora da" Kuma bana son sunan nan *Jabir*, ina dai buƙatar canji daga bakin ki, ba girmamawa bace mace ta dinga kiran sunan mijin ta babu sakayawa, kin gane?" Za ta iya rantsewa a lokacin babu jini a jikin ta bayan ruwan da suke fitowa a idanun ta, haƙiƙa yau baƙar rana ce a gare ta, kuma bata jin zata iya gafartawa iyayen ya da wuri akan abin da suka yi mata. Jabir kuma bai sake ta sai ma ƙara tambayar ta" Na ce kin fahimta?" Ƙura masa idanu kawai tayi tana kallo, hakan yasa Jabir busa mata iska a idanun nata yace" Na ce kin gane? Ko sai kin ji a jikin ki?" Kafuwa da son nuna masa shi ba komai bane ya sa ta ƙi amsawa, shi kuma dake namijin duniya ne sai ya ɗaga rigar ta tare da zura hannun ta cikin rigar ta ta, da sauri ta lumshe idanu saboda wani irin tartsatsi da taji ya dira a jikin ta saboda sanyin tafin hannun shi da ya taɓa fatar jikin ta har saida ta ja wani siririn numfashi, yanzu kam a ainahin jigidar ya ɗora hannun yna lalubawa ba tare da wani abu ya masa shamaki ba, ɗaya daga cikin jigidar ya kamo wa ce ta kasance ta zaren roba, yana kallon fuskar ta ya sake nanata "Kin gane nace? Idan baki amsa min ba da ɗaiɗaya zan cire wannan jarabar dake tayar mana da hankula." Cissssss! Jin ƙarar cirewara jigidar ta yasa ta saurin buɗa idanu ta juya inda ta ji duwatsun na zuba, a firgice ta kalle shi da idanun ta da sukayi ja har kwallin da ta saka ya fara zubowa, ganin ta kalle shi sai ya ɗaga mata gira cike da shaƙiyanci yace "Kin fahimci abinda na faɗa? Kuma za ki gyara?" Ɗan mutsu mutsun ƙwatar kan ta ta fara yi tana girgiza kai wasu hawaye na ziraro mata tace "Jabir ka daina, ka daina wulaƙantani haka Jabir babu kyau." Ciss! Ta sake jin katsewar wata jigidar, da sauri ta matse bakin ta saboda kuka ke son kubce mata irin wanda za ta buɗe bakin nan, cike da dagiya shima ya sake jan wata jigidar ta cire yana faɗin" Zan ga bayan su, sannan na koma kan ki, dan dama wannan ba abun da ya kamata na same ki da su bane idan nayi niyyar *shiga gonata*." A haukace ta kalle shi cikin tashin hankalin jin yana tunanin ita Ummu har zata iya yi masa saken da zai iya hangen gonar nan bare har ya shiga, da sauri ta ƙara ƙoƙarin ƙwacewa tana faɗin" Jab... Shikenan naji, na fahimta." Tallabo haɓar ta yayi abinda ya sa ta kenan rintse idanu saboda kunya a ce Jabir ne haka ke taɓa jikin ta, shi kuma yana kallon bakin ta dake ta saa shi haɗe yawu yace" Oya Maama! Me ye sabon sunan nawa?" Cikin jin zafin wannan rashin kunya da yake yi mata ta ɗaga murya tace" Jabir ka sake ni mana? Ya zaka m..." Yatsar shi manuniya ya ɗora kan laɓɓan ta ya furta" Shiiiiiii! Ni mijin ki ne, ba wawan d zaki iya ɗagawa murya haka ba, kin gane? Saida ta ja majina sannan ta jinjina kai alamar e dan ta kula kawai Jabir dama dai bai karanto komai ba, wataƙila Aliyu rufa masa asiri yake yi, ama dole ya ƙware a fitsara dama. A hankali ya fara sakin ta har ya raba jikin shi da nata, bai tsaya ɓata lokaci ba ya juya zai fita yana faɗin "Ina jiran ki yanzu, ko na dawo na ɗauke ki." Saida ta ga fitar shi da sauri ta faɗa kan gado tna dafe kan ta ta fashe da wani sabon kuka, tsakanin ta da Allah take kuka tana faɗin "Ya Allah, Allah kana gani, shi ɗin ƙanena ma na biyu, amma *sanadin aure* yana min rashin ladabi, Allah idan bashi da lafiya ne ka bashi, idan kuma da gangan yake min saboda raini Allah ya nesanta ni da shi, dan in haka ta ci gaba da faruwa zan iya mutuwa dan takaici." Tana cikin tunanin nan ta ji muryar Jabir irin ka haɗu da kakar kan nan da kake tsokana yana faɗin "Maama, da gaske yunwa nake ji, kuma idan yunwa ta jigata ni rikicewa nake, dan Allah ki zo ki taimaka min." Ƙwafa Ummu tayi ta taso a fusace ta fito daga ɗakin ta ma manta da bata so ya gan ta da wannan kayan, tana zuwa gaban shi ta tsaya irin ƙiƙam ɗin nan tana kallon shi cikin muryar da ta sha kuka tace" Me zan maka?" Saida ya ɗaga kan shi ya kalle ta sosai, wato Maama dai har yanzu da sauran ƙuruciya, ba zaka ce ita ta haifi budurwar nan ba Kuwailat wacce yanzu yake mata kallon *ƴa* tunda maman ta yake aure, sai kuma ya kalli ledar gaban shi yace" Wannan zaki gyara min." A fusace ta ɗauki ledar, sharrin zuciya da rabon ayi sai hannun ledar ya cire lemu orange da ayaba suka faɗo, hakan yasa shi kallon ta a ɗan fusace shima, ganin za ta duƙa ta ɗauke da sauri ya miƙe ya zagaya yana mata alama da hannu da ta bari yana faɗin "Bar shi kawai, zan iya ma." Cak ta dakata dan ya gama ɗaure ta saboda tuni ya duƙa yana ɗauke kayan shi, cikin ledar ya mayar sannan ya aje kan teburin ya miƙe zai nufi madafa sai kuma ya kalle ta yace "Sanin kan ki ne ba abinda mace za ta yi na aikin gida da ni ba zan iya ba, nima kawai neman fitina ce ta sa na ce ki min, dan bana so muyi zaman doya da man ja." Ficewa yayi ya bar ta tsaye, ɗan kumburo baki tayi irin baka da mafitar nan kuma abun bai mata daɗi ba ita ma, jin motsin shi a madafa ya sa ta juya ta koma ɗaki duk jikin ta ba karsashi. Jabir kuma da kan shi ya yanka lemu da kankanar har ma da tufa sannan ya sa gaba yana sha yana jin nutsuwa na saukar masa na yunwar da ya kwasa dan bai yi sahur mai kyau ba, madara kawai ya sha da ruwa ya kora da salatin Annabi. Basu sake ganin juna ba tunda abun nan ya faru, ya fita amma abata sani ba bata kuma san yaushe ya dawo ba, ita ma bayan ta kwashe duwatsun ta tana faɗan ya cire mata abar da tun bai da wayo take ɗaure da kayan ta, amma dai rainin wayo rana guda ya tsinka mata dan bai tsoron Allah. *Da asuba* ma da ya ji motsin alamar t tashi sai bai damu da sai ya tashe ta ba kawai ya tafi masallaci, kamar jiya ya dawo kuma bai gan ta ba ya koma ya kwanta kan sofa ya lumshe idanun shi. Yau ma bacci suka sha abun su ba mai tashin su saida ya farka dan gaban kan shi, a kasalance ya miƙe ya shig ɗakin shi kafin ya fito da shirin wanka... Har yayi ya gama Ummu bacci take da gasken gasken saboda ta jima ba ta yi bacci ba daren jiya tana tunanin yadda za ta sake kama kan ta yaron nan ya daina ganin damar ta. Madafa ya wuce dan duba me ta dafa? Ganin babu komai yasa ya dawo falon yana tunanin abun yi, gidan su zai je wajen Hajia ya ci? Ko wajen siyar da abincin zai je ya siya? Ba dai zai iya juriyar yunwa ba gaskiya, dan yanzu ulcer din shi za ta motsa ya zo kuma yana rakin ciwo gaban waccen *ƴar*, sauran kayan marmarin da ya zuba fridge ya ɗauko ya ƙara sha, yana gamawa ya koma ɗakin shi ya ɗauko kwalin madara da baya rayuwa babu ita tunda ya samu wadata, cokali ya sa yana shan saida ya ji ta isheshi sannan ya kora ruwa, hamdala yayi ga ubangiji sannan ya kalli ƙofar ɗakin ta, girgiza kan shi kawai yayi ya fita, yana so yayi koyi da manzon rahama ta hanyar shiga ɗakin ta duk asuba ya tabbatar tayi sallah sannan su gaisa, amma ba yanzu ba, dole sai sun saita zaman ta ta fara gane shine mijin ta sannan zai fara, amma yanzu idan ya fara za ta ɗauka ai dan ta girme shi ne yake mata haka. *Wunin* ranar haka suka yi shi basu wani haɗu da juna ba sai sau ɗaya, shi ma da ta fito daga madafa ne ta wanke kwanukan da tayi anfani da su ta dawo ɗakin ta same shi zaune, shine ma da za ta shige ciki ba tare da ya kalle ta ba shima yace "Zuba min abinci." Ba tare da ta kalle shi ba ita ma, kuma ba ta tsaya dan bshi gamsashiyar amsa ba kawai ta ci gba da tafiya tana faɗin "Idomie ce na dafa, kuma babu." Shiru ya mata kawai ya haɗe, dake ba baƙon yi wa kan shi abu bane tsaf ya miƙe ya shiga madafar dan wuni yayi da yunwa ta yadda ba zai ma yarda ya kwanta bai ci ba, idan kuma ya kwanta ɗin ya san dole zai tashi. Ummi na saka kayan bacci za ta kwanta ta ɗan ji kamar ƙamshin ana soya ƙwai, sai kayi tayi tunanin hancin ta ne, imma kum Jabir ne dai ohon mishi, ita dai ba zata masa wahala ba gaskiya dan kar yaji a ran shi ita matar sa ce bare har ya ci gaba da yi mata abinda ya ga dama, so take kafin ma kawu Bilal ya aiwatar da shirin shi shi ya haƙura da ita ya sake ta, tunda ai ta san shi bai da juriyar yunwa in ji Aliyu. Ƴan magana suka ce wai *wanda ya iya ya huta*, bayan ya ci ya ƙoshi saida ya rage soyayyen ƙwai saboda sahur, dan haka yana tashi ya ci abu shi ya sha ruwa yayi alwala ya wuce masallaci. *Alhamdulillah.* [05/09 à 13:58] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *70* Da wuri ya shirya zai fita saboda Mansur da suka taso shi da Aliyu kuma yau zai wuce zuwa Niamey daga nan ya ɗaga zuwa ƙasar shi, yau baki da baki yake so ya gaya mata girki yake so, dan shi haro yanzu bai ga tayi girki mai sunan girki ba, ɗakin ya wuce a nutse tare da tura ƙofar a hankali yana yin sallama, kwance ya same ya tana bacci... Ko da yake bai da tabbacin baccin take tunda ta rufe fuskar ta da filo kamar mai neman kashe kan ta, saida ya ƙarasa ya sa hannu ya ɗauke mata filon sannan ya ga idanun ta rufe bacci dai take yi, aje filon yayi yana ƙare mata kallo, riga da wando ne jikin ta, kula wandon har ƙasa yake sannan bai kma jikin ta ba sosai, sai rigar dake da siraren hannaye ta fito mata da fararen hannayen ta, garin kalle kalle ya kai duban shi kan wuyan ta dake shafe sumul fari ƙal, a hankali ya yo ƙasa da idanun shi sai kan wasu abubuwa da ya ga sun yi wani irin cirko cirko haka kamar zasu huda rigar, kamar wanda aka bashi assignement akan su sai ya shiga duban su da kyau yana so ya gane wai su ne ko dai abar nan ce da mata ke yin ciko? Tunda ai maama ita ta shayar da Kuwailat. Ya dai kasa ganewa kawai sai ya zura yatsun shi biyu ya ja hancin ta, ba wai yayi dan wata manufa bane, yayi ne kawai saboda yana sha'awar yin wasa da matar auren shi ko ba ita ba, yatsina fuska tayi ta sauke idanun ta kan shi dake tsaye, a nutse ta gyara kwanciyar ta sannan ta tashi zaune tana ƙare mishi kallo, da salon faɗa ta buɗa baki tace "Jabir wai ya kake neman maidani wata kakar ka ne? Saboda Allah ni tsarar kace da zaka dinga min abinda ka ga dama? Me ye haka wai? Shi wanda ya sa ka ka aure nin ne ya ce ka dinga min haka?" Zuba mata idanu yayi kawai yana kallo, saida ya sauko ƙafafun ta tana shafa fuskar ta ya miƙo mata kuɗin hannun shi, kallo shi tayi sannan tace" Na me ye?" A tausashe yace" Girki nake so, zanyi baƙi." Gyara zaman ta tayi irin zaka rufe ɗan ka da masifa sannan tace" Wanda ka bayar jiya ma banyi komai da su ba, kuma ina ga ai zai fi idan zaka saka ni aiki ka roƙe ni alfarma ko?" Azumi yake, amma tunda na nafila ne ba matsala, ya san wa ye shi, haka Allah ya halicce shi abun tayar da sha'awa ba ya masa kaɗan, ya san zai yi wuya idan ya taɓa jikin ta azumin shi ya ci gba da zma lafiya lau, amma gaskiya baya son rainin nan na Maama fa. Miƙewa tayi a ɗan hassale ta raɓashi ta wuce wajen kayan ta za ta ɗauki towel dan ta yi wanka kafin ta samu abinda za ta saka ma cikin ta, takon shi ta ji a bayan ta da ya saka ta saurin juyowa, sai ta ga da gaske shi ɗin ne kuma har lokacin nufo ta yake yi da yanayin da ta kasa tantancewa, dakewa tayi ba ta nuna alamar mamaki ko tsoro ba ta ɗauki towel ɗin sannan ta sake niyyar raɓa shi za ta wuce. A gadarance ya kamo hannun ta, kafin ta ankara ya haɗata da bango sannan ya matse ta ta hanyar yi mata shamaki ta kowace kusurwa da hannayen shi, inda idanun shi kuma ke cikin nata idanun dake kallon shi cike da masifa tana faɗin "Jabir na faɗa maka bana son irin haka ko? Ka daina taɓa ni dan ni ba sa'an wasan ka bace." Ba tare da ya daina kallon ta ba cikin dakakkiyar murya yace "Me ye kike so namiji ya mallaka kafin ki fara kallon shi a namiji?" Yatsina fuska tayi da sauri tana kallon gemun shi tace "Me? Ban gane ba?" Sai kuma ta gyara tsayuwar ta fuska a haɗe tace "Jabir matsa daga kaina kar na ji maka ciwo." Ɗaga girar shi ɗaya yayi yana ƙara tamke fuska yace "Jaraba." Da mamaki ta kalle shi tace "Na jaraba me?" Cike da shaƙiyanci ya kanne mata idanu yace "Ji min ciwon mana." Iska ta huro daga bakn ta tare da waina idanun ta irin ka dame ni ɗin nan sannan tace "Wallahi da gaske nake maka, matsa daga kusana Jabir, saboda Allah ko kunyar taɓa ni baka ji? Kana kirana da Maama amma kana min duk iskancin da ka ga dama, ina ce ni ɗin matar Abb..." Da sauri Jabir da ya cije leɓen shi saboda kusancin da suka samu ya sa har ƙirjin ta ke neman taɓa jikin shi, to yadda suke ta kallon shi ne ke wani tsuma shi yna zabura daga ƙasa, yatsar shi ya ɗora kan laɓɓan ta yana mata wani irin narkakken kallo, saida ya tabbatar tayi shiru daga abinda take son faɗa, da gangan, da gayya, da rashin sanin me ya aike shi aikata wannan aiki kawai ya dinga yin ƙasa kaɗan da yatsar tashi har ya shafo wuyan ta har kuma ya sauko da ita daf da ƙirjin ta da ya tsura ma idanu... Numfashi Ummu ta so ɗaukewa da sauri ta riƙe yatsan nashi tana faɗin "A'a Jabir, idan ka min haka ba zan yafe maka ba, dan Allah ka barni ka ji, bana so a ce na mari wanda yake aurena wallahi." Tsakiyar idanun ta ya kalla, sai kawai ya sake kanne mata ido ɗaya yace "Jaraba." Tunda ya ce ta jaraba ai ba za ta kasa ba, tunda nema yake ya mata lalata yaron nan, dan haka ta sa iya ƙarfin da take da shi ta tura ƙirjin shi zuwa baya, Jabir da dama ya an ba zai wuce hakan za ta yi ba tuni ya sake tabbatar da ƙafafun shi cikin ƙasa, hakan yasa da ta tura shi kafaɗar shi kaɗai ta ɗan motsa amma shi ko getsau, hakan yasa ta buɗe baki irin mamakin nan ya kashe ta sannan ta kalli ƙafafun nashi da suke mata kama da na jarirai, ai sam bai kamata a ce kamar ita ta tura yaron nan ya ƙi gusawa ba. A karo na biyu ta sake ɗaga hannun ta zat ture shi, caraf ya riƙe hannun ta ya ɗora a ƙirjin shi yana kallon fuskar ta yace "Wahalar da kan ki zakiyi Maama, ba ki san cewa ɗan ki ya girma bane?" Numfashi ta dinga saukewa a hankali tace "Na ji, matsa ka bani guri?" Wani malalacin murmushi yayi jin wani wai matsa kabai guri, kamar wani ɗan da ta haifa? Sakin hannun ta yayi amma bai matsa ɗin ba yace "Zan samu girkin, ko sai n..." Ya faɗa yana ƙoƙarin zura yatsar shi ta saman rigar ta, da sauri ta kalle shi a zafafe tace "Jabir hannun ka, ya kake neman taɓa min nonooooooo...." Giraren shi biyu da ya ɗaga yana mata wani kallo ya sa ta yin shiru tana jin kunyar abinda ta faɗa a bakin nata, ƙara muskutawa tayi a dole so take ta gusa daga nan, amma Jabir ya kakkareta ta ko ina ba hanya, tsuke baki tayi tana sauke numfashi, Jabir kuma dake ta ƙoƙarin riƙe dariyar shi da irin mamakin nan da son ƙular da ita ya ɗan saka yatsar shi saman nonon ta na hagu ya latsa yana faɗin "Shi wannan ɗin dama shine nono?" Tsaki tayi ta kwaɗa masa harara tace "Ban sani ba, sake ni Jabir ina da aikin yi." Cike da shaƙiyanci Jabir yace "Maama, duk ni ke da wannan farin idanu?" Sai kuma ya taɓe baki ya sake kai hannu zai taɓa nonon ta, da sauri ta ɗaga ƙafafun ta sama hakan yasa ta ɗan fishi tsayi, da mamaki ya kalle ta lokacin da tayi hakan, amma da ta fashe da kukan taɓara tana faɗin "Na shiga uku na lalace, Jabir kar ka taɓa min nan wurin dan ya Rasulillah, Jabir wai baka jin kunya ne? Dama lafiyaro ka ta ganin mutane ce?" A dai nan kusa zai iya cewa tunda ya zo garin nan bai yi dariya wacce ake ƙyalƙyalawa ba, amma sai gashi yau lamarin na maalan shi ya saka shi fashewa da dariya har da ƙyaƙyatawa, ba tare da y tsagaita da dariyar ba ya dube ta yace" Maama, da gaske kuma talatin kike?" Irin zazzafan kallon nan kawai ta dinga aika mishi, hakan yasa ya sake matse ta a bango har saida ta ɗauke numfashin ya dan jikin shi take ji kamar yana shafar ta, ko da yake wannan ɗin ya fi kama da hannu ke ga Jabir na uku, dan abinda take ji a riƙe yake fa sosai, irin a murɗen nan n manyan mazn da suka amsa sunan su, Jabir kuma ina? Dubi fuskar shi ma ta yara fa? Tana tsaka da tunanin nan ta ji yatsar Jabir na zagaya nonon ta na dama yana bin ta da wani narkakken kallon da shi ma bai san yana mata ba cikin wata irin yakusashiyar murya yace "Maama, ki ban nasha mana ko kaɗan ne?" A razane Ummu da ta ga lamarin Jabir ya fara neman fin ƙarfin ta tace "Me?" Ba alamar kunya ko rusunawa yace "Mammmammman mana, dama ai baki taɓa bani ba ko?" Sai kuma ya raunana murya sosai har da karkace kai yayi kalar tausayi yace "Ki ban nasha dan Allah, ban sha nonon uwa na ƙoshi ba, ina yunwar sa." Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Jabir dai? Jabir da ta sani? Lumshe idanun da tayi ya ba hawayen da suka taru a idanun ta damar zubowa, cikin raunin murya da tsorata da lamarin Jabir da ta yarda yanzu kam yana fala da shafar aljanu tace" Jabir kaine? Kai ne ke min haka? Kunya ba ka jin kunya?" Kallon idanun ta yayi yana girgiza kai yace" Um um." Da tuhuma ta kalle shi tace" Da gaske?" Ɗaga mata kai yayi yana gyara tsayuwar shi yace" E, to akan le zan ji kunyar wacce *ke aurena*." Cikin zubo da wasu hawayen tace" In dai ka yarfa ni ke auren ka, kuma kana min biyayya matsayina na wacce ta auri Abban ka, sannan shima kana girmama shi, to ka matsa daga kusa na, sannan kada ka sake gigin taɓa ni." Zubawa fuskar ta idanu yayi yana kallo ba alamar wasa yace" Ina girmama duka wannan abubuwan da kika lissafa Maama, sai dai hakan da nake miki na ɗaya daga cikin sakayyar da zan iya yi wa Abbana, tun dai kin ga..." Sai kuma ya sake rusunowa kamar zai haɗa bakin shi da nata sannan yace" Na...fa san... Abin...da...ya rabaki d..aaaaa Abban nawa." Da sauri ta kalle shi wasu hawaye masu zafi suka sake zubo mata, shi Alhajin ne ya faɗa ma wannan yaron? Kenan shiyasa yake mata kallon jarababbiya? Har ma Jabir ke mata wannan abubuwan irin na ƴan iska? Sai takaici da kunyar kan ta suka sake rufe ta, ɗan karɓan saƙon ma da ta ji tana yi na taɓa ta da yake yi sai ta ji ya tsaya cak, sunkuyar sa kan ta tayi ƙasa har ma da idanun ta. Jabir da ya kula kamar ya ɗan ɓata mata rai sai ya tallabo haɓarta yace "Girkin, zan samu?" A ƙufule, a kausashe, a tsawace tace "Ba zan yi ba." A nutse ya shiga sakin ta tare da yin baya yana yin nesa da ita, hakan yasa da sauri ta juya masa baya tana share hawayen ta da towel ɗin dake wuyan ta, cikin kausashiyar murya ta ji yace " *Idan baki yi ba Maama, za ki gane kalata, dan dole ki yarda ni mijin ki ne*." Juyawa yayi zai fita duk da ya ga bata juyo ta kula shi ya sake cewa "Allah ya sa *haukan ki* ya raya miki fara *saɓa umarnina*." Ko da taji ya rufo mata ƙofa da sauri ta juyo tana neman inda wayar ta take, tana ganin kan gado ta ɗauka da sauri ta tura wa lambar kawu Bilal kira, wayar na fara kururuwa kafin a ɗaga wani irin kuka ya suɓuce mata tuna kalman shi na ƙarshe, haukan ta, saɓa umarnin shi, fisabilillah yanzu haka ya dace? Shikenan kawai sai Jabir ya rainata da ga an musu auren dole? Ko da yake dama ya fara rainata tun kafin auren, amma wallahi ba ta ɗauka abun shi ya kai haka ba ai, haba jama'a? Wannan ɗan firit ɗin yaron ya zauna yana mata yadda ya ga dama? Kukan nan ya sa ba ta kira kawu Bilal ba, ta ci mai isar ta ta gode Allah, sai take ganin anya kuwa ba ta auri kuka ba kenan har sanda zasu rabu da Jabir? Dan daga ranar da ta san shine mijin ta zuwa yanzu ta yi ya fi a irga? Kula mafi aksari shi ne musababbin kukan nata? Kawai dan aljanu sun shafe shi sai ya dinga yi mata abubuwa kala kala? Girkin da ba ta yi ba kenan, dan ta yi niyya ba zata yi ba, idan ta fara karɓan umarnin sa tun yanzu kenan wace aka yi? Kai ita fa bata son auren nan wallahi, kawai a raba ta da shi ta huta ma ran ta. Ta jima zaune da kwance tana kuka kafin ta shiga ban ɗaki, nan ta samu tabbacin tsarkaka daga hutun sallah, dan haka tayo wanka gaba ɗaya ta fito, ƴar doguwar riga kawai ta shafa ta fesa turare sannan ta wuce madafa dan ɗora abinda za ta ci iya ita kawai, ba ta manta abinda ya faɗa ba, amma ai tayi niyya ba za ta yi, sai dai yau su nunawa junan su iyakar su, dan haka tana gamawa ta ci ta ƙoshi ta koma ɗaki ta kile kan ta tayi kwancin ta. *Tun* tana sallah azahar kiran Aisha ya shigo wayar ta, saida ta idar da sallata a nutse sannan ta maida kira dan tasan sun gama shirin tafiya ne, dan yau za su ɗaga a motar gida zasu tafi, Aisha na ɗagawa tace "Aunty, kina ina wai? Mu fa zamu wuce, Mamie ta hana ni zuwa da yaran yi miki ban kwana, wai dattijo na nan bai fita ba kar a takura muku?" Huro iska tayi cikin rashin jin daɗi tace "Bana son iskanci Aisha, kun shirya ne?" Daga ɓangaren Aisha ta furta "Mun shirya aunty." A taƙaice tace "Gani nan zuwa, bari na shirya." Aisha ta amsa da "To, mu ma dreban ne muke jifa da ya je zai sha mai." Da haka sukayi sallama Ummu ta miƙe ta cire hijabi, ruwa ta watsa sama sama ta fito shima dan tayi bacci ne dan ta wartsake sosai, doguwar rigar leshe ta saka da ta mata kyau ta kama jikin ta sannan ta yafa mayafi, wayar ta kawai ta ɗauka sannan ta saka kuɗin da za ta bawa yaran su sha ruwa a hanya sanan ta saka takalmi flat da suka dace da kayan ta, ba kwalliya tayi ba amma ta yi kyau sosai ga ƙamshi da take bazawa ta fito amaryar ta sak. Tana buɗo ɗakin ta ci karo da Jabir dake ɗan dube dube yana so ya ga inda kwanukan abincin da aka girka masa yake, jin motsi ya sa shima ya kalli wurin, kyan da ta masa a idanu ya sa ya ɗan kafe ta da idanu har ta rufe ƙofar da makulli ta fara takowa tsakiyar falon... *Ba ta* ce da shi komai ba, hasalima tun kallon farko ba ta sake duban wajen da yake ba, hakan ya ƙona masa rai sosai, musamman da ya ga ma kamar shirin fita ne ta yi, d gaske fita ne z ta yi? Zuwa ina? Wa ta faɗa ma? Da izinin wa? Shi ga sakarai? Soko? Shashasha da bai san me yake ba kenan? Dama dai tunda safen nan azumin shi ya warware, dan da ya fita kafin su yi sallah shi da su Aliyu a masaukin da Fahad ya sauke Mansur saida ya yo wanka a ɓoye, bai yarda su Aliyu suka gane ba dan ya san zai sha tsiya, dan haka yanzu ma yake jin zai kuwa sake kirta wani sabon rashin mutumcin da zai kafawa Maama tarihin da ba za ta manta da shi ba. Ganin taƙim taƙim ta kama hanya yasa shi ɗan karkata kan shi yace "Ina abincin? Zan kai wa baƙona ne." Irin juyowan nan ce tayi kamar kana tafiya saman titi a maka oda, to wannan ƴar juyawar da zaka yi ai ba'a bakin komai take gare ka ba, haka Ummi tayi tare da faɗin "Na faɗa maka dama ai ba zan iya ba." Da ƙarfi Jabir ya lumshe idanu yana ɗan tauna leɓen shi, bai buɗa idanun ba har sai da ya ji tana ƙoƙarin buɗe can ƙofar gida zata fita, da sauri ya juya sai ya hango ta daf take da fita dan har ta buɗe ƙofar, da sauri ya ɗaga ƙafar shi ya fito farfajiyar a kausashe yace " *KUSLSUM*." Har za ta fita, amma abinda ta ji ya dakatar da ita ta juyo da matsanancin mamaki tana kallon Jabir har ƙanƙance idanu take yi irin ɗan ta nan ya kira sunan ta, ta manta da wasu yaran ma suna kiran sunan iyayen da suka haife su ne duk da tana ɗaukar hakan a matsayin rashin girmamawa, amma sai ta sauke numfashi ta girgiza kai irin _"Allah ya shirya min kai."_ Ɗin nan tare da sake jawo ƙofar za ta fita, daga inda yake yana kallon ta a hassale yace" Ina zuwa?" Sake juyowa tayi a yangance tace" Gidan mu." Fuska a haɗe yace" Koa ciki, babu inda zaki je." Wani sakaran murmushi tayi tana girgiza kai tace" Jabi..." Bai bata damar faɗa masa ya fa daina yi mata irin wannan karan tsayen kawai ya ɗan tako yana faɗin" Idan na sake maimaita miki ba zaki ji daɗi ba wallahi, kuma ba zaki sa ni kaffara ba." Gyara tsayuwa tayi ta haɗe fuskar ta irin za ta yi halin nan, duk da ta ga shima fuskar shi haɗe tale sosai saboda ɓacin ran ya masa yawa, sau nawa yana cexa tayi ta na ƙin yi, dan ta nuna masa bai isa ya zaa mijin ta ba ko me? Ya umarce ya ta ƙi yi, bayan ta gaya masa da rashin kunya shine ma a gaban shi zata fita kula bai sani ba, to wallahi sai ya zane ta idan ya sake cexa ta koma ba ta koma ba yanzu, kula ba zai yi kaffara ba. Ummu dake kallon shi cike da tsiwa tace "Na gaya maka gidan mu zan je, gashi nan fa yana kallon namu gidan, su Aisha ne zasu tafi, kaga ko ai ba zaka hana ni yi musu sallama ba." Ƙara cije leɓen shi yayi yana shaƙiyin murmushi, daman shi ya kalla bai ga abinda ya so gani ba, sannan ya kalli hagun shi, nan ma dai bai ga abinda yake hasasowa ba, da ɗan sauri ya juya da niyyar komawa ɗaki, sai kuma ya tuna a aljihun shi akwai cazar wayar shi da ya fita da ita, sai kawai ya dakata ya saka hannu aljihu ya zago ta. Riƙon da ya ma cazar ya sa Ummu gyara tsayuwar ta tana kallon shi da son gane me yake nufi? A daƙile yana kallon ta ya nuna mata hanyar komawa da yatsa yace "Wuce nan, ba zan sake maimaita miki ba." Irin mamakin nan neya kashe ta, hasbunallah wani'imal wakil? Wai me yake nufi? Me yake so yayi da abar hannun shi? Ko da yake an ce wai ga wuri ga waina, bari ta ɗan masa tsayayya ta ga me zai faru, dan haka ta gyara tsyuwar ta tace" Jabir, ka tabbata ba ka shan komai? Kai yanzu ko Kuwailat ka hora da bulala bare ni uwarrrrrrrrr....Aaaaaaazaaaa." Subhanallah! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Ita Jabir ya tsala wa bulala a ƙafafu? Ihun da tayi ba ta ankara bane, sam da ta ga yana nufo ta bata ɗauka da gasken dukan ta zaiyi ba, amma sai taji saukar cazar nan a ƙafafun ta da gasken gaske da ya saka ta zabura ta juya ta sake juyawa ta shiga diddira ƙafafu tana kallon shi sai salati take yi. Duk da ya ji saukar bulalar da ihun ta a ƙahon zuciyar shi, amma sai ya share kawai dan tanƙwarata yake so yayi, sake nuna mata ƙofar yayi da ƙarfin murya yace "Wuce nace." Kukan ke son taho mata, amma take daurexa bata so ya ɗauka shi ya sakata kuka da bulalar nan, sai kawai take daurewa tana faɗin "Jabir, Jabir wallahi ka ji tsoron Allah, kag...." Ɗaga cazar ya sake yi ya kuwa tsula mata a baya tare da rintse idanun shi.. Haba wa? Ai sai Ummu ta daka tsalle tare da sakin kuɗin hannun ta da wayar ta ta kwamtsa ihu tana kiran "Wayyo... Wayyo, mama mama mama.. Aunty, auntyna..." Sai kuma ta durƙushe ƙasa a rikice ta rarrafa ta cakumo rigar Jabir tana kallon fuskar shi hawaye na zubo mata a kumatu, cikin tashin hankalin da ita duk shekarun da ta ɗauka gidan Alhaji bata taɓa riskar kamar sa ba tace" Yi haƙuri, zan yi, zan dafa wallahi, zan dafa, zan dafa Jabir, daina dukana hakanan kaji? Wallahi zan maka girkin yanzu." *Wani* irin girma ya ji kan shi ya masa da ya saka shi haɗe fuska tamau sannan murya a tsume yace" Wuce to." Da gudu gudu ta miƙe ba tare da tsayawa ɗaukar wayar ta ba, hasalima ta manta da su kawai ta wuce tana kama gyalen ta dake neman faduwa, dole tayi gudun ceton rai, dole ta ƙaurace ma Jabir, tunda aljanun shi har duka suke yi, ba shakka za ta faɗa wa su Anna su sama mishi magani, idan ba haka ba ta koma gidan su da zama, dan matsalar masu irin wannan larura kai ba zaka iya ramawa ba, kula idan sun illaya banza a banza suka illata ko alƙali ba zai ƙwatar maka haƙƙin ka ba. Shi ya ɗauki wayar da kuɗin ya kai mata falo ya aje, sannan ya zauna ya kira Fahad ya ce dan Allah shi ya taho da abincin sai su kai wa Mansur, Ummu kuma yayi niyya sai ta dafa shi, idan ya dawo anjima ya ci tunda ba azumi yake ba. A rikice ta shiga madafa ta ɗora tukunya ba tare da ta san me za ta dafa ba, saida ta ji tukunyar tayi zafi ne ta zuba ruwa kawai ta rufe ta fito, tana shigowa falon da ta gan shi zaune wallahi da gaske saida gaban ta ya faɗi, cikin sissine kai ta raɓa shi sosai kamar za ta bi bango sannan ta shige ɗakin ta, kaya ta canza kafin ta fito gadan gadan ta fara aikin, tana yi kuma tana share hawaye idan har ta tuna yau ita ce namiji ya daka, namijin ma wai Jabir, Billahillazi Alhaji Kabir lallaɓata yake yi, ita ke masa laifi kuma ya lallaɓa abar sa har ma ya mata kyauta na baki da ta turo gaba saboda hakan na birge shi, ama yanzu kawai sai a haɗata da mai iskokai, ya zo yayi ta narka a cikin gida? Yanzu da irin fitsarar nan da yake mata idan ya mata a gaban mutane fa? Shikenan darajar ta sai ta zube? Ko da yake ai ta ji an ce hantiti da jibda suna maganin iskokai ko? Wataƙila ta jaraba yi masa kafin su Anna su kawo mata ɗauki, dan wata rana kasheta zaiyiaa gidan ba wanda ya san ma aikin shi ne. *Alhamdulillah.* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *71* Nan su Aisha suka same ta sukayi ban kwanan cike da kewar junan su, duk da Aisha na mata sharrin wai dattijo ne ashe ya hanata fita tana ta faman girki, haka dai suka rabu tana hawaye cike da kewar ƴar ta duk da kuwa a jita-jitan mutane ita ma ba da daɗewa ba za ta same su can. Ana sallah la'asar ta kammala girkin ta aje kan teburin nan sannan tayi wanka tayi sallah, ta ɗauka zaiyi irin dawowar nan ta jiya, amma haka tayi ta zama a falon har magriba tayi sallah, wasa wasa sai gashi har ƙarfe 09:00 tayi bai shigo ba. Kaɗaici ne ya dame ta har ta ji zuciyar ta na raya mata _"Ya zo gidan mana ko masifa ce ma muyi."_ Sai kula ta ja tsaki tana faɗin" Ke dallah! Dukan ki fa ya yi ɗazu." Sai kawai ta tashi ta shige ɗakin ta tare da saka makulli ta rufe ta yi kwance ba dan bacci ba, ba ta fi minti biyar ba sai ta ji an murɗa hannun ƙofar, amma dake rufe take sai ba'a shigo ba sai ma aka ƙwankwasa, zaune ta tashi tace" Wa ye?" Duk da kuma ta san shine dai a wannan lokacin, shiru yayi tare da sake ƙwanƙwasawa, tasowa tayi a kasalance, har ta kawo bakin ƙofar da sauri kuma ta juya ta ɗauko dogon hijabin ta na sallah ta saka da tunanin ko da almatsutsan ke motso mishi ya dake ta da wayar ɗazu to hijabin zai rage mata raɗaɗi, tana buɗewa suka haɗa ido sai kuma ta kawar da nata tana jira ta ji me zai ce. Muryar shi ba yabi ba fallasa ta ji yace "Me ya sa kike son tambaya ta wa ye?" Ba tare da ta kalle shi ba tace "Saboda duniya ce muke ciki yanzu ba kyau, a gidan ka ma ɗauke ka ake yi." Taɓe baki yayi ya juya yana faɗin "Abinci zan ci." Inda yake tunanin wane shaƙiyi zai zo gidan shi ya ɗauke mishi Maama ne? Wato ba'a so ƙasa ta zauna lafiya kenan? Ko da yake wai me ya sa ma ya damu ne haka? Ummu kuma da kallo ta bi bayan shi, wallahi ƙirar shi ma a nutse take kamar fuskar shi da muryar shi, amma sai abubuwa yake yi wanda da zai dawo hayyacin shi a faɗa masa ya yi su sai yayi ta istigfari duk da ba laifin shi bane. To yanzu da ya faɗa mata me za ta mishi? Hmmmmm! Taɓe baki tayi tare da ƙoƙarin jawo ƙofar ta rufe in ya so a yi wacce za'a yi, sai kuma ɗisssssss! Ta tuna bulalar ɗazu, musamman ma ta biyun nan da ta hau bayan ta sosai, da sauri ta fita ba tare da ta rufe ƙofar ba saboda tunawa ai dama masu larurar nan ɓacin rai ne basu so, to za ta bishi *sau da ƙafa* har su rabu lafiya. Yadda ta same shi zaune yana danna wayar shi ya nuna mata abinci yake so ta zuba mishi kenan? Duk da ta aje komai har da lemun da tayi na lemun tsami yana frigde, a ɓoye ta girgiza kai a zuciyar ta tana faɗin _"Allah ya shirya ka shirin addinin musulunci."_ Cikin nutsuwa take zuba mishi abincin har Jabir da ya ƙurawa hannayen ta da suka mishi kyau idanu yace" Ya isa haka." Dakatawa tayi ta zuba miyar da duk wani kayan tsirfa da tayi, lemun ta ɗauko cikin jug da kofi, tana zuwa ta tsiyaya msa sannan ta kama hanyar komawa ɗakin ta, a dake yace" Zo ki zauna?" Ba musu Ummu ta dawo ta zauna ko fuskar shi ba ta yarda ta kalla ba inda take ta wasa da hannayen ta dake cikin hijabin ta, wayar shi ya dake hannun shi ya miƙo yana jawo farantin sosai gaban shi yace" *Saka min lambar ki* Maama, ba zan juri ƙwanƙwasa ƙofar nan ba kullum." Da mamaki ta tsare shi da idanu ta kasa karɓan wayar, jin shiru ba ta karɓa ba ya sa shi ɗan kallon ta, da sauri ta zura hannu ta karɓa ta saka mishi lambar sannan ta miƙo mishi, cikin wata irin nutsatsiyar muryar da saida Jabir ya kalle ta da sauri saboda rabon da ya ji amon muryar nan tun tana *gidan Abba* tace "Zan iya tafiya?" Murmushi ya sakar mata saboda wallahi sai ta kashe mishi jiki tare da bashi tausayi, wannan ita ce maaman shi, wannan ita ce maaman shi da ya sani mai nutsuwa da hankali, dan haka ya kai lomar farko bakin shi bayan bismillah yana girgiza mata kai alamar a'a, saida ya gama taune na bakin shi sannan ya kalle ta yace "Maama, abincin nan ya yi daɗi sosai, kin iya girki maama, da wannan naje ƙara godewa Allah da ya *bani ke*." Ba ta da ta cewa a lamarin na Jabir, sai dai a haka ta bishi da irin kallon hangen nesan nan cikin tattausar murya tace "Jabir, me ya sa kake min duk abubuwan nan? Bayan nasan dole akwai wata manufa a aurena da kai." Kallonta shima yayi yana cin abincin shi a nutse yace "Me ya sa kikayi wannan tunanin maama?" Cikin yanayin jin haushi tace "Da fari dai ka daina kirana da sunan nan na Maama, tunda kaga ai babu wani abu da kake yi da ya nuna kana girmamani yanzu." Murmushi yayi da har saida haƙoran shi suka bayyana har ta ɗan shagala da kallon shi sannan ya jinjina kai yace "Ok, idan na ce *ƴar ma'aiki* ya yi? Ko kuma nace *Kulsum*?" Da mamaki ta kalle shi tace "Kuma zaka iya cewa Kulsum ɗin ba tare da ka ji kunya ba?" Cike da tabbaci ya ɗaga mata kai sannan yace "Sosai ma, to ba matata bace." Jinjina kai tayi tace "Shikenan." Kallon ta ya sake yi yace "Me ya sa kike tunanin akwai wata manufa a auren mu?" Ba tare da ɗar ba tace "Saboda yadda muke da kai, da kuma yadda kuke da Alhaji, wataƙila ya sa ka aure ni ne saboda bai so na aure wani daban, amma kai idan ka aure ni zai zama ikon sarrafani yana hannun shi, sannan..." Sai kuma ta ɗan lashe leɓen ta tare da sunkuyar da kai saboda kunya, zuba mata idanu yayi alamar yana sauraren ta, saida ta ɗauki sakan din da ya fi sha biyar sannan ta ɗan ɗago tana kallon teburin dake gaban shi tace" Ka faɗa ya faɗa maka abinda ya rabamu, kenan kaga..." Da sauri tasa yatsa biyu ta share ƙwallar da ta fara gangaro mata sannan ta haɗe wani abu mai ɗaci da ya tokare mata wuya sannan tace" Ka aure ni dan ka min abinda ya kasa yi min shi, Jabir shiyasa bana son auren nan, dan ni ta wannan fuskar nake kallon shi, saɓanin iyayena da Alhaji Kabir ya nuna musu kawai hallatar auren, Jabir, ni fa ba jahila bace, na san ba'a kaina aka fara ba, aurena da kai ta ko ina hallata yake yi, ƙwarai da gaske ina son ka dinga bani girmana na wacce ta baka shekara uku a duniya, amma son girmana bai kai ƙadamin da zan kasa yi maka biyayya ba matsayin ka na *mijina*, Nana Khadija (R.A) ta girmi Annabi da shekarun da suka ninninka nawa, amma ta mishi biyayya kuma sun mutumta junan su har ta koma ga Allah, ta zama macen da Annabi ke alfahari da ita, yake kuma jin ba daɗin rasata a lokacin da addini ya tsayu kan ƙafafun shi bayan gudummuwar da ta bayar, har Nana Aisha ta ce ban taɓa ganin hushin Annabi (S.A.W) ba kamar yadda ta ga fushin shi ranar da take faɗin ya daina damuwa da rashin Khadija tunda Allah ya musanya masa da wacce ta fi ta, amma Annabi ya ce ina! Hakan ba zata taɓa faruwa ba. Jabir da zan samu tabbacin kyakyawar niyyar ka ta aure na, me zai sa ba zan so zama wacce zata kafa maka kyakyawan tarihi ba? Bayan ni na fi kowa sanin ka sannan nasan irin wahalhalun da ka sha a rayuwar ka, da zan zamar maka baiwa ne wacce ka sa kuɗi ka siya, ta ɗaya ɓangaren kuma ai anyi auren Zeinab da Zeid, shima dan ubangiji ya mana togaciya da ƙin aikata kyakyawan aikin da zuciyar mu ke muradi ne, na sani ne ba ta yadda za'ayi ka aure ni alhalin Alhaji Kabir na raye, saboda kana girmama shi kamar shi ya haife ka, to ta ya zaka aure ni kuma?" Ko da ta gama faɗin haka ta miƙe tsaye ta nufi wajen fridge ta ɗauko ruwa, ba ta kalli inda yake ba ta wuce ɗakin ta ta rufe sai dai ba da makulli ba ta sha ruwan nan sannan ta kwanya tana sauke ajiyar zuciya, ba ta yaarda da auren nan ba, ba kuma za ta yarda ba kawai ya sawaƙe mata, amma ba za ta ci gaba da zama da shi yana mata rainin wayo kala kala bayan ta san ba tsakani da Allah ya aure ta ba. *Tun da* take magana yana sauraren ta da nutsuwa har ta idar ta miƙe ta bar shi, karon farko da ya ji ta bashi tausayi game da lamarin auren su, bai ga laifin ta ba dan abinda take tunani kenan, kusan ko ma waye zai iya tunanin haka? Gashi kuma da kan shi ya faɗa mata yasan me ya fito da ita daga can, kenan dole ta ƙara gasgata abinda ke ran ta shi kuma ya rasa hujjar kare kan shi, sannan a matsayin ta na bazawara ita ke da ikon zaɓawa kan ta mijin da zata zauna da shi, amma sai suka rufe ta saboda suna ganin za ta basu matsala... Hmmmmmmm! Doguwar ajiyar zuciya ya ja ya sauke yana ɗan tsakurar abincin, haushik kan shi ya fara ji na me ya sa yayi gaggawa a lamarin ta? Me ya sa da ya jima da fahimtar wace irin mace ce ya ƙi bin ta haka su zauna lafiya? Me ya sa yau har yayi gaggawar ɗaukar matakin kai wa ga jikin ta? Hakan na nufin shi ɗin me dukan mace ne kenan? Hakan na nufin bai yi koyi da koyarwar Annabi ba, da ya kasance ma fi kyawun iya mu'amula da mace, shiiittttt! Cikin jin haushin kan shi ya ƙarasa cin abincin ba dan yana so ba sai dan kawai lafiyar sa da yasan idan ya kwanta da yunwa za ta samu matsala, yana kammalawa ya sha lemun nan ya miƙe shima, ɗakin da kayan shi ke ciki ya nufa ya cire kayan shi yayi shirin wanka ya fito zuwa ban ɗaki, har ya gama kai da kawon shi bai ji ko motsin ta daga cikin ɗakin ba, hakan yasa shi tura ƙofar ɗakin nata ya shiga. Zaune ta tashi tana ɗan kame jikin ta saboda rigar dake jikin ta iya cinyar ta ce kuma siraren hannaye gare ta, duk da ya ga yadda take ta kakkare jikin shi haka ya haura kan gadon ta hanyar tsallaka sannan ya zauna gefe yana kamo hannun ta, da sauri ta sauka daga kan gadon tana miƙewa tsaye tare da zuba mishi idanu, matsowa yayi yana murmushi har ya sauko da ƙafafun shi ƙasan gadon. Ja baya tayi za ta matsa da sauri ya riƙo hannun ta, kafin ta ankara Jabir ya buɗe ƙafafun shi ya shigar da ita tsakiyar shi sannan ya zaunar da ita kan cinyar shi ɗaya, wasu irin yawu ta haɗe masu nauyi tare da mutsu mutsu da jikin ta tana son tashi, a ƙugun ta ya rattaɓa hannun shi ya zagayo da shi, hakan ya sa ba zata iya tashi ba sai ya bata damar haka, sinne kan ta tayi cikin taushin murya tace "Jabir, me ka ke yi haka?" Hannun shi ɗaya ya sa yana gyara mata gashin ta dake kwance kan wuyan ta yana ta mayar da shi baya yna fadin "Ba komai Maama, ai kinga ɗazu na zane ki da bulala ko? Shine na zo yanzu na tayaki kwana, saboda kar a zo ki dinga mafarkin dukan nan dana miki, kuma babu kowa a kusa da ke ki firgita." Kafin tace wani abu kuma sai ya matso da kan shi daf da fuskar ta tare da saka ɗaya hannun ya la ƙugun ta sakata sosai yace" Akwai zafi dukan ɗazu?" Yadda ya matse ta har yake neman haɗa goshin su ya sa ta girgiza mishi kai alamar a'a, dan haka a tausashe yace" Ina ne ma?" Shiru tayi tana kallon shi kawai, wanda shi kuma kallon baya masa daɗi dan bbu tausasawa a cikin shi, a tausashe ya sake cewa" Na ce ina ne?" Ba wai a kausashe yayi maganar ba, amma sai taga kamar zai shiga yanayi ɗazu ne na dukan mutane, dan haka da sauri ta nuna mishi ƙafar ta da yatsa amma ba ta ce komai ba, kallon ƙafar yayi tare da shafawa da hannun shi, sai kuma ya kalle ta yace" Sai kuma ina?" Hannun da take son nuna mishi da su duk ya kare ta sosai, dan haka ta furta" Bayana." Da mamaki kamar ba shi yayi aikin ba ya ce" A baya? Amma akwai zafi ko?" Nan ma girgiza mishi kai tayi alamar a'a, dan haka ya fara shafa bayan nata yana faɗin" Bari in miki addu'a." To ya ce zai mata addu'a, dan haka ta saurara tana jira ta ji ya ma iya addu'a kuwa? Amma saboda Jabir ya bata tabbaci ƙwarai fa yana da aljanu sai kawai ta ji ya miƙe tsaye, ba wai miƙewar shi bace matsalar ko abun ɗaukar hankali.... Da ita ya miƙe fa, saida ya tallabo ƙafafun ta kawai ya miƙe tsaye da ita, ɗaujar jarirai fa yayi mata a hannayen shi biyu, ai ko ta tabbata yana da wannan abubuwan, bayan ɓacin rai ai dama suna saka wa mutum ƙarfin bala'i, in ba haka ba ina Jabir ina lailayar ta a hannayen shi fisabilillah! Juyawa yayi ya direta a kan gado, wani lamarin kuma da shima ya so fitar da ita daga hayyacin ta sai ga Jabir ya riƙe ƙafafun ta, a hankali ya fara shafa tafin ƙafar ta ta hagu, inda ɗayar kuma ba zato ba tsammani ta ji ya sumbaci tafin ƙafar, saida ta zabura saboda wani irin abu da ya tsirga mata har tsakiyar kai, lumshe idanu tayi tana ƙamƙale jikin ta. A hankali ta ji yana ci gaba da sumbatar ƙafafun nata yana yo sama yana shafa cinyoyin ta har ya kusa kawowa ga ƙugun ta, da sauri ta zabura ta tashi zaune tana istigfari a zuciyar ta ganin Jabir na neman kwanto mata kura, ina dalili Jabir na son kai ta ga halaka, ita yanzu idan ta yarda hka na faruwa ya zo ya kasa yi mata komai fa? Da sauri kuma Jabir ya tallabo bayan ta ya haɗa goshin shi da nata yace "Shiiiii!!!" Sai kawai ya kai hannun shi kan hannun rigar ta dake siriri ya ɗan fara zame shi ƙasa, hannu ta sa ta riƙe hannun nashi, ko da ya ga haka cike da shaƙiyanci ya kalli fuskar ta ya ɗaga mata gira, girgiza kai tayi ita ma tace "Um um Jabir, ka daina." Wani murmushi ya mata yace "Kin yarda dani maama? Ba abinda zan miki, ni ai ba zan iya ba." Kallon shi tayi irin bata yardan nan ba, a hankali Jabir yayo ƙasa da kan shi ya sumbaci wuyan ta, ta ɗauka wucexa zaiyi zuwa ƙasa, amma mugunta irin ta yaron nan sai ya dakata a wuyan ta, ɗumin harshen shi taji a wuyan nata yana ɗan lasawa, abinda ya saka ta kenan jin kamar an fara mata ƙaiƙayi daga can, sannan jikin ta ya fara amsawa har ta fara rufe idanun ta. Iy wuyn ta kawai sai Jabir ke neman koya mata wani sabon karatu ka rantse yau ne zata fara shiga wannan makarantar, ta sakankance ƙwarai da gaske ta ji yayi ƙas yasa laɓɓn shi yana saukar da hannayen rigar ta ƙasa... Da sauri ta kai hannu za ta rufe nonuwan ta, shi ma kuma daidai ya kai nashi hannayen dan jin yadda wannan al'amari yake, kallon juna sukayi abind ya sakata sake girgiza kai kenan tace "A'a Jabir, a'a dan Allah, ka bari." Gefen ta ya koma ya zauna, da sauri ta ja hannayen rigar ta za ta mayar ta tashi daga kan gadon, sai kawai ta ji ya fizgota gaba ɗayan ta ya ɗora kan ƙafafun shi da ya miƙe, hasbunallah wani'imal wakil, ya ƙi barin ta fa ta zauna kan ƙafafun nashi da uwawun ta, wallahi ya tallabe mata uwawu da hannayen shi sai wani murza su yake yana kallon fuskar ta, saida ta tirza sosai sannan ya jaye hannayen nashi ta zauna kan ƙafafun shi, amma kuma hannayen shi na bayan ta suna mammatsawa, harshen shi ya zuro ya kai shi tsakiyar maman ta ya lasa, cikin dubara kuma ya ƙara yin ƙasa da rigar ta hakan yasa suka sake bayyana... A rikice, cikin duburburcewa ya kalle su da kyau ya haɗe yawu, sai kuma ya kalli fuskar ta yace "Maama, maammmaaamaa, in sha kaɗan?" Kamar za ta yi kuka ta girgiza kai alamar a'a, lumshe idanu yayi a nutse ya kai bakin shi kan na daman, tana jin wannan ɗumin sai da ta zabura tayi wata ƴar ƙara, inda shima ya ƙara ƙamƙamota ya sauke wani irin nishi. *Alhamdulillah.* [08/09 à 13:08] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *73* Ƙwarai ta san karanbani tayi dayawa da har ta dinga aiki da kanunfari har ma da ɗan ƙwallon farin maganin nan duk dan za ta sake aure tana qo ta ji canji a jikin ta, sanin kan ta ne ko iya miski tayi anfani da shi yakan saka mata raɗaɗin dake nuna yana mata anfanin da ya dace, amma fa a daren da za'a zo kewayar gonar ta dole ta ji a jikin ta, a ƙa'ida kuma kanunfari a wata ba ta aiki da shi sau uku saboda yadda yake matse ta ƙwarai, sai gashi wannan ta jera kusan kwana biyar tana aiki da shi a aka a kai. Sannan tun jiya da tayi wanka take ta anfani da miski saboda tsarkaka da tayi daga jini. Ba ta yi tsammanin abun zai kai haka ba, gashi yanzu tana shan wahala kuma tana wahalar da ɗan mutane, a yanzu ma da taji ya kwanta jikin ta yana sauke numfashi duk sun haɗa zufa ita da shi sai ta sare tana ayyana wataƙila fa ta tufe wa kan ta hanyar garin neman sai ta birge a ɗauka bata taɓa haihuwa ba, tana shirin fashewa da kuka Jabir da ya roƙi Allah ya sa dai hanyar ce yake bi daidai ba shine a rashin sani na targarɗan mafari ba yake ta zurawa ba daidai ba, dan haka ya ɗan ɗago fuskar shi ya kalli Ummu dake ta sauke numfashi yace "Kiyi haƙuri Maama, zaki ji ba daɗi, amma bana so na zama rago a wajen ki." Tsareshi tayi da idanu tace "Me kake nufi Jabir?" Hannun ta ya kamo tare da kai shi ga jikin shi ya jimƙe su tare yace "Saurara kiji Maama, huci kawai take yi saboda ke, ba zata haƙura a wannan gaɓar ba." Tunda ya ɗora hannun ta a wannan abu ta ja numfashi ta liƙe idanu, numfashin ta taci gaba da saukewa tana tasbihi a ran ta, inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Bata taɓa sanin haka wannan abu take a zahiri, ko lokacin da ta fara ƴan kalle kallen nan ai ita bata ci karo da irin haka ɗin nan ba, anya kuwa? Abun ya sakata kakkarwar tsoro saboda take ta ji ta sare kan wannan abu ba zata taɓa iya shiga jikin ta ba, ya zasuyi kenan? Ya salam! Jabir? Jabir dama haka yake? Kuma ba ya tsorata kan shi? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Ita ai kar ma a kawo maganar Alhaji anan, dan ko lokacin ƙuruciya ai bata taɓa jin irin riƙewar nan ba.... Tana cikin wannan tunanin ta ji Jabir dake goga mata wannan abu a daidai ƙofar ta dake jiƙe da ruwa kala kala yana faɗin "Allahumma janibna shaiɗan, wa jannibin shaiɗani ma razaƙtana." Ta ɗauka binta ne yake ta laluma su tafi a haka har ya samu nutsuwa, saida ta saki jiki ta sakankance har ta ƙara ci gaba da ɗaukar caji, ashe zagon ƙasa Jabir ke yi mata cike da mugun ta da son nuna dole fa yau ba zai haƙura ba ya danna kan shi da bala'in ƙarfin da sai da ya zabura ya ɗago ya ƙura mata idanu.... Wata razananniyar ihun da ta karaɗe illahirin gidan tayi lokacin da ta tabbatar Jabir ya mata shigar saurin da bata ɗauka zai mata ba, bata taɓa jin zafi irin wannan ba, ko haihuwar Kuwailat ubangiji ya sauƙaƙa mata raɗaɗin, amma yanzu da ta ji abun ya ratsata haka bata ankara ba... Tafin hannun da Jabir ya sa ya rufe mata baki ta shiga kiciniyar ƙwacewa tana ture shi daga jikin ta tare da mutsumutsun ƙwacewa. Hakan ya sa ta daidaitawa Jabir zaman shi a cikin jikin ta wanda shi kuma ya ji wani irin abun da a lokacin ya kasa samun abinda zai misalta shi da shi, cikin kazari da karsashi ya gara gyarawa kan shi tsayuwa yana sauke wani irin numfashi mai kama da kuka kuka dariya dariya... Ummu da duk motsawar da zaiyi take sake jin wata azaba da wani ƙarfin bala'i ta ja baya tare da zabura ta tashi zaune... Take Jabir ya ji shi a wata sanyayyar duniyar da ta saka shi jin ba daɗi har kamar zai tuhume ta akan wani dalili za ta fito da shi duniyar waje da babu komai a ciki sai iska da sanyi? Hakan ya sa shi sake kamota da niyyar ta rufa masa asiri ya sake komawa wurin nan da baya jin zai sake fitowa waje, amma Ummu da ta gama yarda Jabir ba yaron da ta saba gani bane, Jabir ba shine wannan yaron da take gani wani lokacin da koɗaɗɗin kaya wasu ma har da yagewa, wannan shigar ƙarfin da ya mata ta samu tabbacin nan na wata magan da ake faɗa wai *namiji ba ya kaɗan*, saboda Allah ita bata san yaushe Jabir ya zama haka ba? Ko kuma dai yana daga cikin mazan nan dake shaye shayen abubuwa dan kawai su firgita tare da birge mata? A tsorace fa ta sauka daga kan gadon tana neman zillewa, a rikice Jabir ya sauko shima tare da riƙo hannun ta, da ƙarfi ta fara son kubcewa tana faɗin "Jabir sake ni, wallahi ba zan iya wannn abun ba, kaga Jabir..." Sai kuma tayi shiru tare da cije leɓen ta na ƙasa saboda wani abu da ya tsikaro tna wannan shiga da Jabir ya mata, yadda fuskar ta take nunawa alamu na ba fa zata saurare shi cikin sauƙi ba, dan haka kawai ya aje tausayin sa da imani gefe ya haɗata da jikin shi, cikin dubara ya dinga turata baya har ta manne a jikin bango, ɗan buɗa ƙafar ta yayi sannn ya sagala tashi ƙafar ya harɗe ta ta yadda ba zata iya sake kubce mishi ba... Tana jin yana sake neman hanya ta shiga zille zille sai dai ta kasa kubcewa, dan hatta hannayen sama yayi da su ya danne su a jikin bangon da hannu ɗaya, hakan yasa ma ranta ƙara ɓacewa take ta kubcexa amma sarautar Allah ta kasa ƙwatar kan ta daga riƙo matashin balagaggen ɗan nan, da ta fahimci ba za ta iya raba kan ta da shi ba, kuma hanyar sa ta ɗazu kawai yake nema, ita kula a haka ma har yanzu ciwo take ji. Sai ta girgiza mishi kai tana sako da hawaye a tausashe tace "Na roƙe ka *man*, a hankali dan Allah, wallahi yanzu bana jin baka yagani ba, dan Allah a hankali, ka ji?" Tsura mata idanu kawai yayi yana kallo haka kuma yana ci gaba da neman hanyar shi da ta sake rufewa kamar ba yanzu ya fito ba, ba tare da ya daina kallon ta ba ya shiga tsutsar ɗaya daga cikin maaman ta, a hankali ya fara danna mata da ɗan ƙarfi sabod a hankalin ai bata wuce cikin daɗin rai. A haukace ta sake girgiza mishi kai tace "Jabir ba'a tsaye ba, dan Allah mu koma kan gado, wallahi bamu taɓa yi daga ts..." Yatsa yasa a daidai bakin ta ya hanata faɗa, sai kuma ya ƙarasa zura kan shi cike da mugun ta yana mai jin wani irin zafin maganar da ta faɗa wacce har ta saka shi yo hasaso abinda ya ji yana neman ɓata masa rai... A karo na biyu ƙara ta sake yi da ta saka Jabir zura yatsar shi dake bakin nata ciki, a dole Ummu ta kama yatsar ta dantse tsammmmm bata ma ankara da hannun shi ne take ma wannan cizon masifar ba. Dakiya da jarumta ta sa Jabir duk da yana jin zafin taune masa yatsa da take yi, amma haka yake kallon ta yana wani irin murmushi tare da ɗan haƙar ta a hankali a hankali har saida ya ji ya tsayu sosai a ciki sannan ya saki ƙafar ta daya harɗe tare da matse mata ƙafafun, hakan yasa Ummu ƙara jin kamar ya ƙara liƙeta ne yadda zata dinga shan wahala duk wajen shugar shi da fitar shi. *Kuka* ba irin wanda ba ta yi ba tana ihun kiran sunan shi, ya yi a tsaye saida ƙafafun ta suka kasa ɗaukar ta, ya kwantar da ita kan gado nan ma ta gaji sosai, komai nata ciwo yake musamman ma dai ƙasan ta da bata jin zai sake anfanuwa. Neman kawo wa da yake yi ne yasa shi yi mata wata zungura a wurin da sai taji kamar da bata da shi yanzu ne ya taɓo shi, na uku kenan da tayi wata irin ihu da har saida ya ɗan zuba mata idanu da mamakin me kuma yayi yanzu? Amma sai ya ruƙumƙume ta yana son fitar da abindz ya cure mishi, jin kamar zai ɓallata ga kuma wani irin sabon raɗaɗi da take ji yasa ta ɗaga murya a kausashe tace "Jabir, cikin jikina ne fa, ka bini a hankali mana kar ka halakani." Ina! Saida abun nan ya fito kaɗai wata zufa ta kwaranyo masa sannan ya kwanta saman jikin ta, rintse idanu duka sukayi sai Jabir dake huro mata iska a wuya, cikin jin haushi ta shiga juya jikin ta tana so ta ture shi ta tashi, da sauri Jabir da ya ji zata sake kwanto masa aiki bayan wanda ya gama ya danne ta sosai ya kalli fuskar ta, kai kawai ya iya girgiza mata alamar a'a fa, amma dake bata fahimce shi ba sai ta ɗan ja tsaki tana sauke ajiyar zuciya na kukan da take ta sha har lokacin tana ci gaba da motsin, cikin lumana ya kalle ta da ƙyar ya buɗa bakin shi yace "Ina zuwa, zan ɗaga ki ai, shin idan na sake tashi zaki iya ɗaukata ne?" Da sauri ta girgiza kai alamar a'a, dan haka yace "Dan haka ki ɗaga min ƙafa na nutsu, zan ɗaga ki ai." Shiru ko ta yi tana sauraren shi saida ya ga dama sannan ya ɗaga ta ya miƙe ya nufi ban ɗaki, da ƙyar Ummu ta ja jikin ta ta gyara kwancin ta tana matso wasu sabin hawaye, wallahi wannan abu da Jabir ya mata guda ɗaya sai take jin ya shafe na shekaru da Alhaji ya mata, Jabir dai ya tabbata marar tsoron Allah kawai. Tana jin ya fito ya nufi ɗakin da kayan shi suke ciki ta yunƙura, da gaske fa jikin ta da komai nata ciwo yake, haka a daddafe ta nufi ban ɗaki da niyyar tayi fitsarin da take ji ya cika mata mara, idan ta sauke shi sai ta je ta dafa ruwan zafi masu yawa dan ta gasa jikin ta, da ƙyar ta kai ban ɗakin ƙafafun ta na rawa saboda haka Jabir ya sagar mata da ƙafafu su ba a tsaye ba su ba kwance ko zaune ba. Tana shiga ban ɗaki da sauri ta zauna kan watar dan yin fitsari, wani irin masifaffen zafi ne ta ji ya ziyarce ta tare da jin kamar wani abu zai fito ta gaban ta, tsabar zafin da ta ji ya sa take wasu zafafen ƙwalla suka ziyarce ta, haka kuma duk tsigar jikin ta ta tashi saboda abun ƙwarai ne, a razane ta miƙe tsaye saboda jin kamar tsugunnen ne ba zai gyara ta ba, tsaye tayi tana tunanin me ye kuma wannan? Sai kuma ta saje daurewa ta zauna saboda fitsarin dake neman biyo ƙafafun ta, tana duƙawa dai wannan abun ne da ya sa dole ta sake miƙewa tsaye. "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Ummu ta dinga faɗa a haukace tana daddafe bangon ban ɗakin daga tsaye kamar wacce ke naƙuda saboda jin fitsarin nan na taho mata daga tsaye da wani irin zafin da ita kam ba dan duniya ce tayi ittifaƙin babu ciwon da ya kai na naƙuda, to da sai ta ce akwai gaskiya, dan gashi tana ɗanɗana yanzu haka, abun da ya bata tsoro shine fitsarin fitowa yake irin tsir-tsir ɗin nan kamar yana tsartuwa alamar dai baya fita da kyau, kamar za ta ciji bango haka take ta matse shi, sai da ta ji zafin ya ƙaru fiye da baya da sauri ta yi niyyar duƙawa gaba ɗaya ƙasa ko wai hakan zai fi sauƙi... *Cak*! Ta dakata tana rarako idanu saboda ganin jini na biyo fitsarin ta, haba ai sai ta buɗe muryar ta ta ƙwala ƙara da faɗin "Aaaaaaaaaa! Wayyo Allahna, na shiga uku, Jabir, wayyo Allahna." Yana tsaye gaban fridge yana shan ruwa ya ji wannan ihu, da gudu ya saki robar ruwan ya nufi ban ɗakin, bai jira komai ba ya tura ƙofar, yana ganin ta tsaye ba kaya jikin ta sai kuma ya shiga ƙarewa ban ɗakin kallo da tunanin ya ga abinda ya tsorata ta, ganin ba abinda idanun shi suka gane mishi sai ya kalli Ummu da sai bayan tayi kwaroronton da kiran sunan shi ta gane ita ce fa, shi ma kuma shi ne fa, shiga yayi ban ɗakin yan faɗin "Lafiya Kulsum? Daren alhamis ɗin nan sai ihu kike min a kai, ki kasa barina nayi salati yadda ya kamata, me ya faru yanzu kuma?" Wani mugun kallo ta watso mishi tare da niyyar ƙwalla masa harara, sai Jabir yayi saurin dakatar da ita ta hanyar faɗin "Wallahi Kulsum kina hararata zan sake ɗorawa kaina wani wanka a tsakiyar banɗakin nan, kuma jaraba ki gani." Da sauri ta maida akalar duban ta wani iri tana turo baki kamar yarinya tace "To ba kaine ba..." Sai kuma tayi shiru, hakan yasa ya sake matsawa kusan ta yace "Ni ne me? Ban ishe ki ba?" Ƙasan kafafun shi ta harara tana ayyana _"Na bi ƙaniyar da gudu."_ Sannanbta girgiza kai alamar a'a, cikin muryar kuka tace" Wallahi fitsarina da jini yake fita Jabir, kuma kaga ai ni ba yarinya bace kuma ba budurwa ba, Jabir na shiga uku wallahi, gaskiya ni tsoro nake ji." Cike da kulawa ya gyara mata tsayuwar ta yana kallon ƙasan nata, e ƙwarai akwai alamar jini amma ba fa sosai ba, shine take cewa wai fitsarin fita yake tare da jini, cikin nutsuwa ya tallabo fuskar ta yace" To bari na miki wankan, sai muje asibiti ko? Dan kin ga wallahi bana fatan wani abu ya samu hanyar hutun nan nawa." A gatse ta kalle shi tace" Ban gane ba? Ka manta ka min alƙawarin ba zaka sake yi ba daga yau? Kuma ni wallahi b zan je asibiti ba." Da mamaki yace" Me ya sa?" Cikin turo baki tace" Allah kiyaye wallahi ba zan je ba." Jinjina kai yayi yace" Shikenan, yi wanka ki fito sai na miki addu'a." Har zai fita tace" Dan Allah ka taimaka min da ruwan zafi, wataƙila idan na zauna a ciki na ji sauƙi." Jinjina kai yayi yace" Angama *aunty Kulsum*, gaskiya ban ji daɗin wannan abu da ya faru ba." Juyawa yayi ya fita ya bar ta a daddafe tana jiran ya kawo mata ruwan ɗumin... *Washe Gari*:tun Ummu tana nonnoƙewa tana nuna bata yarda da sakin jikin ta gaban Jabir ba har dai da abun ya fi ƙarfin ta ta saki jiki yake kulawa da ita, da gaske har yanzu kuma idan za ta yi fitsari sai tayi hawaye saboda masifar zafi, gashi ba yadda bai yi ba suje asibiti tun jiya ta ce sam, idan ta je ta nuna shi matsayin mijin ta? A ce ma ita ta masa fyaɗe ko? Dan haka ta ƙi yarda sai da safe ne ya siyo mata maganin da ta lissafa masa, Ibu da kuma Amoxi ta ce za ta ji sauƙi, sai dai har yanzu da rana ta hantse ba wani sauyi, hakan yasa har Jabir yayi niyyar yin sallah juma'a a gida yau saboda ai sabon aure yayi shari'a ta bashi dama, da lafiyar ta ƙalau ba zai ƙi zuwa ba, amma da ya zama duk motsi sai ta ce washhh! Sai ya bata lokacin ta kawai. Yanzu haka da hannayen shi yake ƙidaya salatin Annabi da ya saba yi kafin ya tafi masallaci sau ɗari, bayan wanda yake yi daren juma'ar, Ummu na kwance kan kujerar da yake inda ta miƙe ƙafafun ta kan cinyoyin shi, hakan yasa har yake ɗan mamatsa mata ƙafafun nata, cikin shagwaɓa tana kallon shi tace "Wallahi bana so ina jin fitsari, amma kuma kamar da gayya sai zuwa min yake." Kallon ta yayi ya sauke numfashi yace "Maama, zaki barni nayi salatin nan kuwa?" Ɗan taɓe baki tayi tace "Ni kuwa me zai hana? Kamar wata arniya." Kawar da kai tayi ba ta sake cewa komai ba, hakan yasa yace "Maama, bari na shiga cikin gida na faɗawa Hajia, wataƙila ta san maganin matsalar." Da sauri ta tashi zaune tace "A'a a'a, Jabir ai kaga abin nan da ya faru tsakanin mu ne kawai, dan haka kar mu bari kowa ya ji." Kallon ta yayi kawai ya kawar da kan shi, sai kuma ya ɗauie ƙafafun ta daga jikin shi yana tashi tsaye da cewa "Me za ki ci na dafa miki da kaina?" Murmushi tayi tana sunkuyar da kan ta, hakan yasa Jabir cewa "Kulsum, ina jin ki?" Kallon shi tayi a nutse tace "Jabir, da gaske ne abubuwan da ka faɗa min jiya?" Ƙanƙance idanu yayi ya yi tsugunno na maza gaban ta ya riƙo hannun ta yace "Me yasa kika kasa yarda dani Kulsum? Duk abinda na faɗa miki abu ne da ya faru kuma yake ci gaba da faruwa, tun jiya da na shiga jikin Maamana, sannan maamana tayi bacci mai nauyi akan ƙirjina, sai duk abubuwan da nake ji suka sake ruɓanya, Kulsum, na yarda ke *ƙaddarata* ce, dan jiya bayan faruwar abinda ya sake haɗani da ke, sai na ƙudurta a zuciyata baki taɓa zma da wani ba bayan ni, ina so ke ma ki manta da rayuwar da kikayi ta baya, dan bana so ko a furuci naji hakan daga bakin ki, *ina da kishi a kan ki*, ba zan so a kirani marar adalci kuma butulu ba, nima kuma ba zan so na dinga jin wani abu mai kama da kishi da mutumin da ba dan ya sadaukar min da ke ba, to da ban san gararin da rayuwata za ta shiga ba." Sai kuma ya miƙe daga tsugunnon ya shafa kumatun ta yace" Kin gane?" Kamar gaula haka ta jinjina masa kai alamar e, dan haka ya sake cewa" Me zaki ci?" Girgiza mishi kai tayi tace" Zan dafa da kaina, ba aikin ka bane shiga madafa." Murmushi yayi shima yace" Na sani Kulsum, amma na yanzu ni nake so na dafa, saboda ai jinyar ki nake." Wayar shi ce ta shiga kururuwa ana kira, ɗauka yayi yana ganin sunan Aliyu ya furzo iska sannan ya sake duban ta yace" Ina ji Maama." Cikin fara'a tace" Duk abinda ka iya girkawa." Dariya yayi yace" Gatse kike min? Ko kuma ƙalubalantar na iya girki kike yi?" A tausashe tace" Ko ɗaya, na dai baka zaɓi ne." Jinjina kai yayi ya nufi hanyar fita yana faɗin" Za ki gani ko." Saida ya fita ya ɗaga kiran Aliyu, daga wajen Aliyu ne ya fara faɗin" Wallahi Jabir baka da mutumci, yanzu ni zan dinga kiran ka kana share ni? Shikenan dan kayi aure sai ka fara raina min wayo, ka manya gaba nake da kai ne?" Wani irin numfashi ne Jabir ya sauke a nutse sosai yace" Toh! Da fari dai Aliyu naje na maka rashin mutumcin, aure ai ba wasa zbe da zai sa ka kasa ganin canji a jikina, maganar girma kuma ina ga yanzu haka auntyn taka ma tsoron kallona take, idan kuma aljanun ta ne suka koma kan ka, Aliyu kasan tsaf zan iya ɗaureka na maka ruƙiya, dzn ba ƙarfina kafi ba dan kawai ka fini shekaru, magana ta gaba kuma faɗa min me ya sa ka kirani? Ina wani aikin lada ne nan." A amsakuwa Aliyu ya saka shi dan sua tare da Fahad ne dala sukayi niyyar ɓata masa rai, dan haka suke ta dariya kafin Aliyu yace" Duk naji Jabir, kuma nagde, amma ka sani kafin a min ruƙiya kai za'a fara yi wa, saboda kai ne tun jiya ka shige gida ɗaya da maaman ka kuma ka ƙi fitowa har rana tayi." Taɓe baki Jabir yayi yana rumgume hannu yace" Ina ce dai ai uwata ce ko? To a faɗa min me zan fiya waje nayi? Bayan nan ɗin ya fi daɗin mutum ya sakata ya walala." Fahad ne ya fashe da dariya yace" Anji kunya wallahi, ina ce dai mutum da bakin shi ya faɗa ba zai wa maama lalata ba, kuma mala'iku ma sun rubuta a littafi." Duk da Jabir na son yin dariya amma dake yayi niyyar biye musu sai yace" Aliyu, ka faɗa masa du maganar da mutum ya faɗa ba'a hayyacin shi ba Allah baya kama shi da laifin ta." Cikin dariya Aliyu yace" Jabir a yarda ka iskance ɗin kenan?" A ɗan ƙufule yace" E ɗin, ai idan ina da zunubi kuma kuna da, saboda sai da na ce muku a'a, amma kuka haɗani zama wuri ɗaya da Maama, to idan tabbacin iskancewata kake nema ka bari muje Maraɗi na baka kyautar daren farkon auntyn ka a hannun ka sai ka kai mata." Dariya suke sheƙawa kamar zasu mutum kafin Aliyu yace" Jiya Fahad yake faɗa min baka ji daɗi ba." Wallahi murya a dake kamar da gaske ɗin Jabir da ya gane ƙure shi suke son yi yace" E, ulcerta ce ta tashi jiya, da ƙyar ma mukayi bacci ni da ƴar ku." Cike da dariyar mugunta Aliyu yace" Ina fata dai bata ji a jikin ta ba, dan nasan halin ulcerka idan ta motsa na kusa da kai ya kan sha matsa." A gadarance Jabir yace" Tunda ka san haka me ye na tambaya? Ai babu abnda ya ragu daga cikin ciwona." Kafin wani cikin su ya ce wani abu Jabir yace" Ku dakata wai! Dama kun kirani ne dan kusa ni zinar baki? To Allah ya isar min tsakanina da ku, kuma Fahad na san kai ka mishi gulmata ko? Sai da na faɗa maka ni yanzu ba ƙaunar Aliyu nake ba saboda hausa ba kama bakin shi tayi ba, hakan yasa yake kamar makaho duk abinda ya zo bakin shi faɗa yake, yanzu hankalin ku ya kwanta ai kun ji komai, kuma da kunyi haƙuri ma ai nan da wata tara kune zaku siyo ragunan da za'a yanka sunan Abubakar, amma tsabar gaggawa ta ƴan adam sai da aka kira ni." Cikin dariya Fahad yace" Ba haka bane alaramma, kawai dai dan mu san ga wacce muke ciki ne, yanzu kaga da muka samu tabbaci ai sai mu fara tariyar na ragon ko." Cike da shegantaka Aliyu yace" Ai ni har asusu zanyi saboda wa'azi zamu haɗa babba mu wayarwa da jama'a kawunan su akan cika maganar su idan sun faɗa." Taɓe baki Jabir yayi yana faɗin" Hmmmm! Ka ma yi adashin gata idan kana so, kuma duk wanda ya kama sunana a wurin wa'azin zamu kwashi ƴan kallo da mutum, tunda ai ba haramun na aikata ba, kuma dan Allah daga yanzu idan ba ni na kiraku ba kar ku kirani, saboda Kulsum ta ce bata son ƙarar wayata." Fahad ne yace" La'ilaha ilallahu! Jabir mu ɗin? Yanzu zumuci za ka yanke damu? Kuma ita maaman ce yanzu Kulsum? Kuma ai naga wayar ka babba ce ko?" Cikin ƙufula Jabir yace" E na faɗa Kulsum, zo ka gaya mata mana, kunga sai anjiman ku, girki ta saka ni amma kun hana ni saboda surutu." Aliyu ne yayi saurin faɗin" Kuma kake mata ita tana zaune?" Duk da ya san Aliyu ya dai faɗa ne, amma shima sai ya ce" Kai ba zaka gane ba saboda *single* kake, amma ka tambayi Fahad ya maka bayani, idan ma mutum ya ce ba zai yi ba to tsayuwar dare fa ba zata yiwu ba, shiyasa muke ta koyi da Annabinmu manzon Rahama." Yana gama faɗa ƙit ya yanke kiran tare da soka wayar aljihu ya fara dubawa dan ya ga me zai fara da shi, su Aliyu kuma dariya suka dinga yi suna hirar Jabir ɗin da tattaunawar su yunda aka ce za'a yi auren nan, suna farin cikin da jin an ɗan samu sauyi, duk da sun san wani abun ya faɗa musu ne saboda gatse da kuma kare kan shi daga sharrin su, amma dai suna farin ciki. *Alhamdulillah.* [08/09 à 15:40] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *72* Dakatawa yayi ya ɗago ya dubi fuskar ta yana shafa duka nonuwan nata da hannayen shi cikin wata kasalalliyar murya yace "Maama, na yi ƙishin wannn ɗin, ban sha na *Mamana* na ƙoshi ba, dan Allah za ki iya ƙara m..." A hankali ta kawar da nata duban daga fuskar shi domin bakinta ya mutu, idanu ta rintse da ƙarfin gaske tare da ɗora hannunta a saman kanshi ba tare da sanin ita kanta ta aikata hakan ba, hakan da tayi kuma sai ya saka Jabir sake danna kan shi a ƙirjin ta ya shiga yi masa wata mahaukaciyar tsutsa yana gurnani kamar wani marayan zaki, hakan ya sa Ummu ta nemi mimmiƙewa tana sakin ɗayan hannun ta data rirriƙe zanin rufa haɗe da sakin wata irin ajiyar zuciya tana wata irin ɓoyayyar miƙa tana ƙara banƙaro mishi ƙirjin nata, wasu siraren hawaye masu zafi da suka gangaro kan kumatun ta ya sa ta sake ankara Jabir ne fa, Jabir dai, ɗan ture shi ta fara yi saboda bata so hakan ya fi gaba da faruwa, gashi Jabir sai wani irin abu yake yi tare da ƙoƙarin cire mata rigar ta a hauka. Tun tana nuna bata so tana ture shi, har abin ya zo ya girmi tunaninta ta mance da wa take? Ina take? Ya zamana idan ya kai hannunsa ya shafa mararta ko uwawun ta sai ta yi kamar ta kwantar da shi kan gado, domin ita kaɗai ta san abinda take ji, kunyar kanta ɗaukewa ta yi ta shiga kwaranyo ni'imar gyare gyaren da ta kwasa a jikinta wanda yake ta ƙoƙarin yaƙi da son kwantar da ita da zuciyar shi ke ta raya masa, dan a gani yake yana kwantar da ita ɗin nan to fa ba zai iya riƙe kan shi ba kuma. Wannan daddaɗan ƙamshin kuoaccha da ta saba anfani da ita, da kuma wani irin laushi da santsi da fatar jikinta ke yi shi ya fi komai bashi mamaki da saƙawa a ran shi _"Me maama taje sha? Jikin ta tamkar na jaririyar baby."_ Sake shafar fatar yake tare da latsa duk inda hannun shi ya samu, kuma har lokacin bakin shi na kan ƴan biyun yana tsutsa kuma bai ji alamar zai gaji ba saboda laushin su gasu car car suke har lokacin. Shi fa kan nan nashi da Maama ke ta faman murzawa yake sake rikita mishi lissafi, cirata yayi daga zaunen da suke ya juyar da ita ya kwantar da ita ya mata runfa, bakin shi ya kai kan nata laɓɓan a ɗan sumbata, sai kuma ya sake tsutsar bakin nata, cikin ƙwarewa ya kamo harshen Ummu da tayi saƙe tana sauraren shi har lokacin idanun ta a rufe suke, wata irin wasa ce yake ma harhen nata idan ya tsutsi harshen sai kuma ya dinga zagaya shi da nashi harshen, dole dole Ummu ta masa shiru tare da ƙudurtar ai koma menene kawai ayi, ita kam ta zubar dz makaman nan nata wallahi, Jabir dai ai *mijin ta* ne, kuma da iyyen su ai da sanin me mata da miji suke yi suka haɗata zama da shi, dan haka wallahi babu komai ayi ai na daren yau ne kawai, idn aka gama zata cnza takon ta kawai. *Gam gam gam*! Wannan sautin da suka jiyi na bugun gida ya sa Jabir saurin ɗagowa yana tunanin ko mafarki ne yake yi, Ummu m idanun ta ta buɗe saboda tunanin wa ye a yanzu? Duk da dai ta san dare bai wani yi sosai ba, Jabir ma da idanun shi sukayi jajir suka ƙar ƙanƙancewa ya kalle ta, cikin wata irin murya kamar mai koyon magana yace "Wa...ye? Maa... M.a." Cikin kunya Ummu ta kawar da kan ta bata kula shi ba kawai, ƙara bubbuga ƙofar da aka yi yasa shi ƙoƙarin sauka daga kan ta yana fadin "Bari na duba..., ina tunanin ba lafiya ba, kuma wayata na caji." Tsaye yayi a ƙafafun shi, amma sai yayi saurin dafe gadon saboda wani irin yanayi da yaji kamar zai kayar da shi, saida ya saita nutsuwar shi tare da gyara kayan jikin shi duk da dai kallo ɗaya za ka mishi ka fahimci halin da yake ciki, musamman ma ƙasan shi da abun yayi muni sosai, haka a daddafe ya fita daga ɗakin, Ummu na satar kallon shi har ya fita sannan ta miƙe da sauri ta shiga ban ɗaki dan tayi wanka bata so ya same ta, a gaggauce ta fito ta koma ɗakin ta ta rufe ƙofar da makulli sannan ta jingina a ƙofar ta rintse idanu tana sauke numfashi kamar zaki ne ya biyo ta, sannu sannu ta shiga tariyo abinda ya faru tsakanin ta da Jabir. *Yana* buɗe ƙofar ya hangi Fahad har ya fara tafiya zai koma da kwando na kwanuka a hannun shi, buɗewar da ya yi yasa Fahad juyowa ya dawo yana faɗin "Haba alaramma, ina kuke ne haka? Ai na ɗauka ba lafiya ba da na ji shiru." Wani kallon jin haushi Jabir ya dinga jifan shi da shi har ya zo ya tsaya kusa da shi, ganin bai ce mishi komai ba ya sake cewa "Lafiya ko malam? Wane abu na faruwa ne a ciki?" Cike da ƙufula Jabir ya ɗaga msa kai alamar e yace "Sosai ma, majalisi muke a ciki, me ya sa ka katse ni?" Da mamaki Fahad yace "Malam, dama yanzu kuna nan falo kuna majalisi amma kuka barni nayi ta buga ƙofa?" Cikin jin haushi Jabir yace "Akwai dokar da ta ce dole sai a falo za'ayi majalisi ne?" Sai lokacin Fahad ya fahimci abinda yake nufi, dan haka ya ƙyalƙyale da dariya yace "Kai! Subhanallah! Malam kar dai na katse maka hanzari?" Da sani irin yanayi kamar zai mari Fahad ɗin amma a nutse dan wallahi baya jin daɗin jikin shi sannan yace "Sosai ma, babban katse hanzari ma, daf nake da antayo mai sunan *sadiƙul masduƙ* duniya, amma ka dakatar saboda hassada da kake min, Fahad me na maka? Me ka zo yi mana yanzu cikin tsakiyar daren nan?" Cikin muryar dake nuna zolaya Fahad yace "Ayya! Ka gafarce ni dattijo, naji ɗazu ka nemi abinci ne da za'a ba wa Mansur, shiyasa nayi tunanin to ko dai ƴar tawa tsayayya take maka ne, shiyasa na kawo maka abincin sannan na ce ka miƙo min ƴar nan in zazabga mata mari ta gane har yanzu akwai sauran hayaƙin nan a kaina, tuba ne nayi saboda ba kyau amma halin na nan ban manta ba." Jinjina kai Jabir yayi a tausashe yace" Na ji, yanzu dai ka tafi Fahad, ina bata wani horon ne, gobe da rana ka dawo sai ka mata hukuncin, tunda ai kaga kai Baban ta ne ba zan hanaka ba." Jinjina kai Fahad yayi yana ta ƙaarewa Jabir kallo ya miƙo mishi kwandon yace" Gashi to, sai da safen." Girgiza kai Jabir yayi yace" Up um, ka tafi da shi, *ƴar albarka* ta dafa min na ci na ƙoshi, Alhamdulillah." Wani shaƙiyin murmushi Fahad yayi yana jinjina kai sannan ya juya yace" To shikenan, sai da safe." Cike da tsarguwa Jabir yace" *Siriki*." Juyowa Fahad yayi ya dawo ya tsaya, hakan ya sa Jabir cewa" Sai naga kana ta min wani kallo irin na ƴan iska, lafiya? Ko dai zargin kake ina wa ƴar taka wani abu ne a ciki?" Da sauri Fahad ya girgiza kai yace" Ah haba, wannan tunani ma ai saɓo ne, kai da na san ɗan ne ita kuma maama, ko ba haka ba." Ɗan murmushin yaƙe Jabir yayi yace" E mana, kai ai ka fi Aliyu fahimta, shiyasa na fara tsanar Aliyu, saboda kallon zan wa maama lalata yake min." Faha dake ta dariya a ɓoye ne yace" Ni ma ai na fara tsanar Aliyun nan, dan gaskiya abu yake irin na marasa tsoron Allah, to amma abun da ya ɗan ɗaure min kai dattijo, kai da bakin ka kace mahaifiyar Siddiƙ na nan zuwa amma ba maaman ka ba, to ya akayi haka kuma?" Ɗan taɓe baki yayi fuska a haɗe yace" Canza shawara kawai nayi, akwai wasy tsare tsare ne da nake ta yi akan Siddiƙ din, idan na ce na jira nan da shekara hakan zai ɗan taɓa shirin karatun da na masa, shiyasa kawai ƴar ka zata kawo min, wacce za ta zo bayan ta sai ta kawo su *Khadija* da su *Umar* in sha Allah." Da mamaki Fahad dake ta tiƙar dariya yace" Jabir, wai nufin ka ƴar tawa ba zata ishe ka bane? Ahalinmu fa akwai jatumta." Yatsina fuska Fahad yayi yace" To ai ina tsaka da fagen tantancewa ne ka katse ni ko? Mybe zuwa safe in canza shawara." Dariya Fahad yayi ya juya yace" To saida safe, Allah baka sa'ar antayo mana Siddiƙ din nan a wannan shekarar." "Ameen, nagode." Cewar Jabir yana jawo ƙofar da niyyar rufewa, sai kuma ya ji Fahad na faɗin "Allah kaimu safe lafiya, Aliyu zai sha labari." Da sauri Jabir ya dakata yace "Siriki." Juyowa yayi ya dawo inda Jabir ya fito daga cikin gidan gaba ɗayan sa, ba kamar duk hirar da sukayi yana daga ciki ba kula ya rufe jikin shi da rabin ƙofa saboda baya so ya fahimce shi, yana zuwa kusa da Fahad ya ɗan dafa kafaɗar shi yana faɗin "Kana ji Fahad? Kar ka faɗawa Aliyu, idan ya ji labarin nan uku zai saka ni, kawai ka faɗa masa da ka zo kayi ta buga ƙofa ka same ni kwance ma ulcerta ta motsa saboda yunwa, hakan zai sa ya ji tausayina ya ma ƴar ka wa'azi." Jinjina kai Fahad yayi yace "To shikenan, amma dai idan na faɗi ba daidai ba ai zunubin a kan ka ne ko?" Ɗauke hannun shi yayi daga kafaɗar shi ya kalle shi sosai yace "Fahad, ka bar ƙofar gidan nan kafin nayi shari'a da kai." Nuna kan shi yayi da yatsa yace "Ni ɗin?" Da tabbaci yace "Kai ɗin mana, haihuwata ka yi...?" Sai kuma ya juy zai shige yana faɗin "Na ma lura son girman nan asali ya samo wallahi, to ita ma tana can za ta karɓi sakamakon ta, kai kuma je gurin matar ka." Fahad dai na dariya har ya koma gida haka Jabir ma ya dawo. Ƙwanƙwasawa ya dinga yi amma Ummu tayi shiru, ta na ji amma tayi shiru tana kwance kan gado, saida ta ji yana ci gaba da bubbugawa ta taso, tsaye tayi bakin ƙofar da har lokacin yake ƙwanƙwasa mata a nutse kamar mai son saka ta bacci, jingina tayi a ƙofar sosai cikin taushin murya tace "Dan Allah Jabir ka tafi, bana son haka ta ci gaba da faruwa tsakanin mu, na roƙe ka ka tafi Jabir, sannan..." Da sauri Jabir kamar zai yi kuka ya furta "Dan Allah Kulsum?" Da sauri ita ma tace "Ka tafi Jabir, kar ka kwanta da sh'awata a ran ka, hakan zai sa na kwana cikin hushin ubangiji." Haɗa kan shi yayi da ƙofa tare da dafeta da hannayen shi yace "Ba zan iya haka ma Kulsum, ko nayi ƙoƙarin cire hakan a raina ba zan iya ba, tunda nake a rayuwata ke ce mace ta farko da na haɗa jikina da ita, kowane haɗuwar jikina da naki a ƙwaƙwalwata yake zaunawa, ba zan iya dakatar da hakan ba, dan yanzu haka jikina a bayyane yake a matakin ƙarshen da ni kaina ya fara tsorata ni, ki buɗe ƙofar Kulsum, bana so ki kwana alhalin *ni ina begen ki*, ba zan bari mala'iku su tsine miki ba, dan zan kwana tsaye ina shaidawa ubangiji yafiyata a gare ki ne, dan Allah Kulsum, ki buɗe ƙofa kin ji." Ummu ma jikin ta ne ya mutu sosai, inda ta ji kalaman shi na ƙarawa marar ta ɗaurewa, shauƙin sake kasancewa da shi na ci gaba da kamata, hakan yasa ta kama hannun ƙofar a hankali tare da murɗa makullin ta buɗe, sadda kan ta tayi ƙasa bata kalli ko da fuskar shi ba, shi ma a hankali ya dinga takowa har ya zo daf da ita bayan ya ƙare mata kallo, a nutse ya sa hannu ya shafo hannun ta sann ya tallabo haɓar ta, da sauri ta rintse idanu, cikin raɗa yace mata "Kalle ni mana maamana." A hankali ta buɗa idanun ta da suka cika da ruwa, tana buɗewa kuma hawaye suka gangaro mata, da sauri ya sake tallabo fuskar ta da duka hannaye biyu yana girgiza mata kai, sai kuma ya zuro harshen shi a nutse tana kallo ya dinga lashe hawayen nata, kafin ya ƙurawa idanun ta ido yace " A duniya *hawayen ki* su suka fi komai ɗaga min hankalina, na jima da yin alƙawarin cewa in dai ina tare da ke ba zan taɓa bari ki zubar da su ko da a wajen farin ciki ne." Da ɗan mamaki a fuskar ta na abinda ya faɗa cikin shaƙaƙƙiyar murya tace "Me ya sa?" Ɗan murmushi ya ƙaƙaro tare da ɗaga kafaɗu alamar oho! Sannan yace "Ban sani ba nima, sai dai tun *ban san wa ye ni ba* nake jin *Ummu Kulsum* daban a ƙasan zuciyata, dan zamu zama *ma'aurata ne*? Ko kawai *haɗuwar jini ce*? Ban sani ba nima." Ba tare da ya saki fuskar ta ba ya haɗa goshin shi da nata suna kallon juna cikin wata irin nutssatsiyar murya sosai yace" Kiyi haƙuri abisa dukan ki da nayi ɗazu, ba'a son raina haka ta faru ba, Maama ina so muyi zama da zai tsaya mana a zuƙatanmu dukan mu, amma kuma sai naga a dole so kike tuƙin ki ya fi ƙarfina, da fari na bi ta hanyar nasiha ne kamar yadda ubangiji ya umarce mu da muyi muku lokacin da kuka zo da abinda ya saɓa mana a cikin suratul *Nisa'i aya ta 34*, amma duk da na miki sai kikayi biris kamar baki gane yarena ba, na saka ki aiki kika baki min daidai ba, na ƙaurace miki na wuni ɗaya amma sai naga ba abinda ya canza, dole na bi matakin ƙarshe na ɗan taɓa lafiyar jikin ki, zan iya cewa na ga canji daga gare ki, amma nayi niyyar idan baki tafi yadda nake so ba, to zan bi dake ta wata hanya ne da zaki yarda ni ba yaro bane kamar yadda kike faɗa." Sai kuma ya rumgume ta ƙam ƙam yana sake raɗa mata a kunne" Ki yi haƙuri Maama, ba zan sake ba har abada, da izinin Allah." Jin ba ta ce komai ba ya sake ƙamƙame ta yana faɗin" Ki yarda dani Kulsum, ban aure ki saboda haka Abba ya so ba, na yi ne saboda ya bani dalili da hujja a ilmance, bayan duk alfanun da suka nuna min na aurena da ke, ni akwai wani da na hango wanda na yi tunanin zan samu daga gare ki...." Sai kuma ya ɗago daga jikin ta yana riƙo hannayen ta suna kallon juna yana jinjina hannayen ta yace" Na ji a jikina zan samu wacce za ta dinga bani abinci akan lokaci, Kulsum kin san irin rayuwar da nayi a gidan mahaifina kafin yanzu, horon da aka min na yunwa yayi tasiri a kaina ta yadda har na kamu da ulcer, amma da aka ce na auri Kulsum, sai naji a raina ai Maama ta iya girki sosai, dan haka ba zata sake barina da yunwa ba sai idan ba ta nan kawai, na ji tsangwama da kyara da hantara da zagi daga wajen matar mahaifina da mahaifin nawa, dubi nan ki ga..." Ya faɗa yana cire rigar shi t-shirt tare da juya mata bayan shi, da sauri Ummu ta rufe baki tana ƙurawa bayan nashi idanu, ita fa ba tabo tabon da ta ci karo da su a lafiyayar jar fatar shi bane ya bata mamaki, kamar ganin wata irin lafiyayyar ƙira da ta fito masa da tsarin zubin halitta na cikakken namiji, tare da mamakin yadda sutura ke ɓoye wannan ƙwanjin nashi da bai wuce misali ba kuma ba irin na ƴan damben nan da wasu ma ko kyan kallo baya da. Juyowa yayi tare da saka yatsar shi daidai gefen cibiyar shi yace "Kin ga nan ma? Satin dorina ne saboda kawai yunwa ta hanani dawowa gida da wuri, dan nasan idan na zo ba zan samu abinci ba, shine ya dake ni haka." Jefar da rigar shi yayi ƙasa tare da sake nuna mata ƙasan damtsen shi, nan ma wani shati ne na ban mamaki ya nuna mata yace" Wannan tabon kuma ya fi shekara ashirin, saboda kawai na zubar da wasu canji a cikin kuɗin cefanai da aka aike ni." Sai kuma ya ɗan shiga hautsina tarin sumar shi da ta zama irin ta Larabawa, hakan ya sa da ƙyar ya buɗa gashin ya nuna mata wani shati yace" Wannan, ɗaya ne a cikin cuwukan da naji a ranar da na bar gida nayi niyyar shiga duniya... Kulsum, shiyasa na yarda na aure ki saboda ke kika fi kowace mace sanina a duniyar nan, hatta da kakanin da suka haifi iyayena sun kasa riƙe ni, ke kuma na san zaki iya tausaya min ko dan rayuwar da na gani a baya, sannan *shekaru uku* da kika bani zasu iya saka ki rarrashina matsayin ki na babba a gare ni har ma ki warkar min da waɗannan tabon da suka ƙi barin jikina har yanzu." Sai kuma ya numfasa yace" Sannan na aure ki ne saboda *bana so kiyi nesa dani*, dan akwai ranar da na same ki kina kuka gidan Abbana, ranar kasa bacci nayi ina so nasan dalilin kukan ki, Kulsum, in faɗa miki gaskiya?" Yadda ya tambaya ɗin kuma ya tsare ta da idanu ya sa ta jinjina kai alamar e, dan haka ya ɗan mata magana cikin raɗa yace" Asubr wannan ranar kasa sakin jikina nayi mu gaisa da Abba, saboda kawai zuciyata ke ta raya min kamar shine musababbin kukan ki, bana ce haushin shi nake ji ba a lokacin, amma dai ina jin kamar nace mishi *me ya sa ka saka ta kuka Abba*?" Hawaye wani na korar wani a idanun Ummu, mamaki na sake kamata na gaba ɗaya komai ma da Jabir ke faɗa mata, hakan yasa cikin rikitacciyar murya tace" Jabir, a kaina? Duk kake jin haka? Me ya sa to?" Nauyayyar ajiyar zuciya ya saue tare da ƙara jawita jikin shi sosai yace" Na jima da faɗawa kaina *RUBUTACCIYATA*, *ke ce Kulsum*." Wani irin kuka Ummu ta fashe da shi tare da saka hannayen ta ta rumgume Jabir, shin tausayi ne ya bata? Ko kuma dai abinda kashe mata jikin da yake yi ne yayi tasiri akan ta? Sosai take kuka kuma take ƙamƙame shi a jikin ta, har saida Jabir ya ɗn karkata cikin kunnen ta yace mata "To za ki bani na sake tsotsa?" Irin tsakn nan tayi irin na baka son haka fa tare da gantsara masa cizo a kafaɗar shi, dake abun bazata y zo mishi wata ƙara yayi sannan ya furta "Aouchhhhh! Maama, ɗan naki?" Sai kuma ya sake rumgume ta sosai ya raɗa mata a kunne "Kulsum, za ki yarda mu ci gaba da abun nan na ɗazu?" Ɗagowa yayi dan ya gani kum ya ji amsar da zata bashi, sunkuyar da kai tayi cike da kunya, hakan yasa shi sake faɗin "Ina jin ki Maama?" Turo baki tayi tace "Ka kirani da Kulsum kawai, tunda yanzu baka jin kunyata." Ɗaga mata gira yayi yace "Me ya sa kika ce haka? Duk ƙoƙarin rusuna kallona da nake a kan ki Maama." Cikin shagwaɓa tace "To ɗazu ba rigata ka cire min ba, kuma ka taɓa min.... Nan." Ta ƙarashe da ɗan zame towel ɗin daga ƙirjin ta ta nuna nonuwan ta, take ya lashe leɓe yace "Wai maama ababen nan ba zasu iya kallon ƙasa bane? Ban san me na musu ba, amma hararata kawai suke." Cikin jin kunya tayi saurin jan towel ɗin ta tana juya mishi baya, ta baya ya rumgumota yana takawa da ita suka nufi gado yace "Mu koma kan gado Maamana." Yana shirin kwantar da ita ta tsaya car tace "Jabir, ka min alƙawari ɗaya mana?" Amsa yata yayi da "Ina ji?" Saboda tuni ya fra wasa da ƙirjin ta har ma yana son kwance mat towel ɗin, dan ta riƙe ne, ɗorawa tayi da "Ka min alƙawari daga wannan idan muka yi Jabir ba zamu ƙara ba, sannan ba zaka faɗa ma kowa ba." Da murmushi ya kalle ta yace "Maama ai alƙawari biyu ne?" A ɗan gadarance tace "Duka nake nufi." Jabir da ya riga ya zame mata yar rufar nan ta jikin ta ya kalleta a ita ɗin ta, ya ga Ummu a yanayin da Ummu ce kawai ke ganin kan ta tun bayar rabuwar ta da Alhaji, ya ga ainahin ƙirar ta da jikin ta dukan shi, tun daga ƙasan ta ya fara shinshina wani ƙamshi mai kama da na turaren wuta mai daɗin ƙamshin nan har dai ta kai su ga... 😉Sirri. *Alhamdulillah.* [09/09 à 21:10] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *74* Abun da ya birge ta da ranar juma'ar yau shine yadda Jabir ke manne da ita sallah la'asar kaɗai ya fita masallacin nan yayi, amma suna tare komai za ta yi sai ya taimaka mata ko ma ya mata da kan shi, har idan ya mata wani abun sai ta ji kamar ta ce _"Ni ba tsaran ka bace."_ Sai kuma zuciya ta raya mata _" To wane dare ne jemage bai gani ba?"_ Sai kawai tayi murmushi duk da dai bata biye mishi, amma kuma bata hana shi ko da ya taɓa ta a inda take jin kunya ne. Abinda ya sake bata mamaki game da lamarin shi ta gane shi daban ne a cikin maza, kuma ubangiji ya bata shi ne saboda yana son ta kuma ya zama dole ta godewa rahamar sa, idan ba haka ba ta godewa azabar sa, da kan shi ya faɗa mata abinda yake sha'awar ci, sai ta ce bari tayi sallah la'asar sai ta zo ta gyara nama ta fara aikin, tana watsa ruwa tayi sallah ta fito ta same shi farfajiyar gidan daga shi sai singlet da dogon wando ya yanka albasa mai tarin yawa sannan yana wanke naman ragon cikin nutsuwa ko wata mace albarka. Da sauri ta ƙaraso tana marairaicewa tace "Jabir, ba nace zan dafa maka ba? Me ya sa zaka yi wannan aikin? Dubi fa albasar da ka yanka." Wani narkakken kallo ya mata yace "Kulsum turaren nan naki ki ɗan canza shi man, kinga aiki nake so nayi kar ki ja min fitina." Waina idanu tayi tace "Ba wannan nake magana magana ba Jabir, kaga bani nan?" Tayi maganar tana durƙusawa zta kama wankin nama, da sauri ya jaye robar yace "Kar ki saka hannun ki, ki bari hannu ɗaya yayi ƙarni mana." A tausashe ta kalle shi tace "Jabir so kake a ce bana jin maganar ka har yanzu? Aikina ne fa." A tausashe yace "Na sani, wallahi kama miki kawai nake yi saboda akwai lada, a islamiyya ni nake faɗawa maza su dinga taya matan su aiki, kinga ai nima sai na dinga yi ko?" Turo baki tayi tace "Na ji to, amma gaskiya idan ma kama min zaka dinga yi, to bana son taɓa albasa da tafarnuwa da abinda ya shafi yaji da kuma ƙarni." Wani shaƙiyin murmushi ya mata yace "Ok, sai yanzu na gane ki, ai Maama bana yarda na kama ruwa bayan na taɓa albasa ba tare da na wanke hannuna da detol ko makamancin haka ba saboda tsaro, ai ke kin gane haka ko?" Cike da nata salon shaƙiyancin ta kanne masa ido ɗaya tana ɗan cije leɓen ta tace" Na ga zahiri, dan yanzu ma da na shiga ban ɗaki da ƙyar na yi bawali, kuma na tabbatar nayi ƙari." Da yanayik tashin hankali yace" Au! Kinsan kinyi ƙarin dama kuma kika ƙi yarda muje aibiti?" Turo baki tayi a tausashe tace" Wallahi ina zuwa ɗinki zasu min, kaga kula yanzu wurin baya son tashin hankali." Cike da tabbaci yace" Ai ko dole muje asibiti, mu kammala girkin." Girgiza kai tayi tace" A'a Jabir ba zan je ba, ba wani dayawa bane ba fa, da nayi aiki da ruwan ɗumi da kanunfari zai koma yadda yake." A gadarance ba tare da gamsuwa da bayanin ta ba yace" Kulsum." Sadda kan ta tayi tana turo baki gaba, hakan yas a dake ya sake cexa" Kul...sum." A sangarce ta amsa da" Na'am." Cike da bada umarni yace" Muna gama girkin ba sai nayi magana ba ki shirya muje asibiti, kin fahimce ni?" Saida ta ƙara rusuna kan ta sannan tace" Tom, naji." Miƙewa tayi tana mamakin duniya kenan, yau ita ce Jabir ke juyawa kamar waina a tanda? Haka ta kama suka fara aikin, daga yadda Jabir ke aikin sai ta fara ɗar din kar dai ma fa yaron nan ya fi ta iya girki, dan gaskiya yadda ta ga yana komai ita kan ya sai ya birge ta duk da ta iya itama kuma tana aikin ta cikin nutsuwa. Tun kafin magriba suka kammala aikin nan Ummu ta sake yin wanka tare da alwala, tana idar da sallah ta shiga shiryawa a tsanake tunda ya ce ta shirya kafin ya sake magana, duk da bata son zuwa dan tana ganin kamar tonawa kan ta asiri za ta yi, amma bata so ɗan nan ya ci gaba da wani bata umarni haka a tsatsayen nan, gwara tayi yadda yace kawai. *Jabir* kuma tun suna sallah ya ji wayar shi na vibration, yana fitowa ma ana ci gaba da kira ya ɗaga, bayan sun gaisa sosai ne sannan mutumin ke faɗa masa wanda zai haɗa msa album ɗin karatun shi ya zo, kula kwana uku kacal zai yi, shi ya sa ma a kira shi a shaida masa, dan haka Jabir ya ce gobe shima zai shigo dan aikin alkairi ne da ya sa gaba yake so ya yi, karatun shi ne tun daga Baƙara har Nass. Yana shigowa gida ya same ta a shirye, rumgumota yayi jikin shi yana kallon fuskar ta yace "Maama kin yi kyau." Kallon shi kawai tayi ita ma ba ta ce komai ba, hakan yasa ba tare da ya raba jikin shi da nata ba yace "Kin san me? Gobe fa zamu tafi?" A ɗan razane ta kalle shi tace "Ina?" Saida ya jujjuya idanun shi sannan yace "Gidanmu mana." Zaro idanu tayi ta girgiza kai tace "A'a Jabir, gaskiya ni dai na fi so mu zauna a nan ma, nan ya fi daɗi kuma kaga babu wanda ya sanni." Ɗan jan ta baya yayi daga jikin shi ya kalle ta sosai yace "Me ya sa? Ai a can dama zaki zauna." Shiru tayi tana tutturo baki, a nutse ya juyar da ita ya zamana bayan ta ke fuskantar shi, sai ya ɗora haɓar shi a kafaɗar ta ya fara takawa da ita zuwa ɗakin ta yana faɗin "Maama, na kasa manta daren jiyan nan fa, maama ko ba'ayi ɗinkin ba mutum na iya ƙarawa?" Ɗan kubcewa ta so yi daga jikin shi tana faɗin "A ƙara me? A'a Jabir ba haka mukayi ba, kaga wannan ma fa munyi alƙawarin babu wanda zai ji." Sakin ta yayi har ta juyo ta fuskance shi suna kallon juna, cike da dubara da wayo ya taɓe baki yace "Ai dama tambayar ki ne nayi ko za'a iya? Saboda yanzu na biyo wajen Hajia na sanar da ita abinda kike ji, shine sai ta faɗa min maganin." Da ɗan zumuɗi da kuma kamar dai bata yarda ba ta kalle shi tace "Da gaske?" Ɗan yatsina fuska yayi yace "Ni zan miki ƙarya ne?" Girgiza kai tayi alamar a'a sannan tace "A'a." Dan haka ya ja hannun ta zuwa ɗakin ba tare da ya ce mata komai ba, suna shiga ya maida ƙofar ya rufe sannan ya jawota jikin shi, ƙoƙarin zamewa ta fara yi hakan yasa shi faɗin "Ki dakata Maama, Hajia ta ce in faɗa miki wani abu ne da bai kamata a taɓo ba na taɓa, shine ta ce sai an sake maimaitawa kaɗai komai zai koma muhallin shi, ko ba kya so ki samu lafiya ne?" Ƙura masa idanu tayi kamar mai tuhumar sa, hakan yasa shi ɗan kawar da kai yana jin tsarguwa tare da zura hannayen shi cikin rigar ta yana shashafa jikin ta, riƙe hannayen nashi tayi tace" Ba asibiti zamu je ba?" Kallon ta yayi yace" E zamu je, amma ai zamu je asibiti saboda ƙari ne, amma idan kin fi son duka likitoci su gane matsalar shikenan, bari na je nayi wanka." Juyawa yayi zai tafi a hankali yake takawa yana jira irin ya ji ta riƙe shi ko ta dakatar da shi, amma sai ya ga har ya kai ƙofar ba ta da niyyar yin haka. Ita kua kallon shi take tana ayyna _" Da gaske Hajia ce ta faɗi haka? To kuma kawai sai ta sake yarda da shi kenan? Ko da yake ai dan ta samu lafiya ne, amma kuma wane irin wanka zai yi bayan wanda yayi ɗazu?"_ Tana cikin tunanin ta ga Jabir ya dawo da sauri kusan ta ya tsaya, zif ɗin rigar ta ya fara cire mata yana faɗin" Zamu je asibiti maama, amma ki fara ban wannan nasha, yunwa nake ji." Yadda yayi maganar kamar yaro da wata shagwaɓa yasa saida ta ji gaban ta ya faɗi a sanyaye, sai kawai ta marairaice ita ma tace" Jabir." Wani kakkausan kallo ya mata yace" Wai ni ba za'a iya daina kiran sunana bane gatsau haka?" Da sauri yana dire maganar Ummu tace" Man.. Man., ai na saka maka sunan tun jiya." Wani shaƙiyin murmushi yayi yana ci gaba da sauke zif ɗin ta ƙasa yace" Ni na cancanci haka?" Yadda yayi maganar tare da latsa ɗaya na shanun ta da ya ciro daga cikin rig yasa Ummu jin tayi wata irin zabura da sauri ta faɗa jikin shi, sai kuma ta rintse idanu tana tambayar kan ta _" Me ya sa take neman zaƙewa ne wai a wannan harkar?"_ A zahiri kuma saboda mugun ta irin ta Jabir da ya ga ya samo kan zaren sai ya ci gaba da ɗan lallatsa su dukan su, hakan yasa Ummu kai bakin ta daidai kunnen shi tana shafo kan shi har zuwa ƙeyar shi tace" Yessss! U deserve it." Kamar wani matashin zaki Jabir ya fuskanci fuskar ta ya manne bakin shi da nata, yadda ta mishi magana a kunne cikin wata sanyayyar murya mai rawa rawa na ɗaukar cajin abinda yake mata, ga kuma yessss ɗin nan da ta ja haɗe da ɗumin bakin ta da ya daki fatar kunnen nashi, sai ya sake tunzura shi kawai ya shiga tsutsar bakin ta a nutse yana kuma rabata da kayan ta. Ba ta hana shi ba, sai dai kuma tana ƙamƙame jikin ta ne dan bata so ya ce zai je can, a wahalce take har yanzu da zuwan jiya da ya mata, idan ya ƙara wani yanzu ba lallai ta kallu ba fa, magana ta gaskiya Jabir da kan shi ya zo mata ba ta hanyar ƴan aike ba, dan haka ya rubuta mata tarihi a bangon zuciya da ba zai taɓa gogewa ba. Yana cikin shafa jigidar ta da duk ta cikasu da sauti sai ta ji ya kama pant ɗin zai cire, da sauri ta daddafe hannayen shi tana girgiza kai amma ta kasa magana dan bakin ta da yake tsutsa tana jin kamar ma haƙoran ta yake ƙidayawa tsabar masifa, ba tare da ya raba bakinshi da nata ba cikin bakin nata yace "Ki tsaya mana Kulsum, gani fa kawai zan yi." Shiru tayi tana sauraren shi ya yi ƙasa da pant din nata, take shi yayi da ƙafa da nufin ta cira ƙafafun ta ko? Amma sai Maama ta ƙi yin hakan saboda bata so su wuce nan, kamar girgizar ƙasa haka ta ji Jabir ya cirata gaba ɗayan ta bai dire ko ina ba sai kan gado... Kallon fuskar ta yayi sai kuma ya dinga bin jikin ta da kallo yana shafa jigidar ta da kuma nonuwan ta, kakkarewa take ta kalle shi tace "Jabir hasken nan yayi yawa, sai fa kallona ka ke." Rusunowa yayi ya sumbaci marar ta da ke cike da jigida sannan yace "Na sani, ai matata ce ko?" Cikin wani bazawarin salo ya dinga goga mata gemun shi da ba wani yalwar gashi gare shi ma akan mara, rintse idanu tayi tana sauraren shi tana jin kamar za ta ɗauke numfashi, sannu sannu ta ji yana yin sama har saida ta ji harshen shi cikin ramin cibiyar ta yana mata wata irin lasa... Jiya kam ta sha azaba da wahala, amma yau ne take kan jin daɗin lamari saboda hatta da hanyar nan Jabir bin ta yake yana saka harshen shi, tunda ya zo shiga kuma ta ji daga bakin ƙofar bai sha wahala ba, sannan ita ma ta ji wani raɗadi ba, sai daga ciki ne kaɗai har saida ta sauke ƙaƙƙarfan numfashi lokacin da ya shiga, inda shi kuma da ya ji kamar yanzu ne ya fara shiga wurin ya sauje wani marayan numfashi mai kama da kuka, sai kuma ya rumgume ta tsam a jikin shi yana ci gaba da sauke numfashi. Dama dai sallah isha'i ta wuce su da nisa, dan haka kafin Jabir ya fito wani sanyayan bacci mai daɗin da ya zarce misali ya ɗauke Ummu saboda yau ne ta ji daɗin harkar nan fiye da tunanin mai hasashe, Jabir kan shi da ya fito ya same ta tana baccin nan yayi mamaki, amma kuma sai ya tuna shi kan shi baccin yake ji, amma sallah dake kan shi ya sa bai ma fara wannan tunanin ba har sai ya sauke nauyin dake kan shi, tsaye yayi yana ƙare mata kallo yana murmushi a fuskar shi, daga al'aurar ta zuwa ƙirjin ta ne ke rufe da yalalon zanin rufar, saida ya gama kallon ta wanda hakan ke saka shi jin sake wani mararin ya da shauƙin ta, dan shi kan shi sai yanzu ne ya fahimci idan aka bi abun a hankali ashe ya fi armashi da kuma tabbatar da nutsuwa ga ruhin ma'aikacin wannan aikin. Sunkuyawa yayi ya sumbaci bakin ta da kumatun ta sannan ya daddaɓa ta, tana buɗa idanu ta zabura ta tashi zaune tana sauke numfashi, cikin nutsuwa ya ce mata "Ki tashi kiyi wanka kiyi sallah, sannan ki fara shirin tafiya, na faɗa miki da safe in sha Allah zamu tafi." Saida ta murza idon ta ɗaya tace "Wai dama da gaske kake? Amma man ta ya tafiya haka kwatsam? Kuma Gobe da safe?" Zagayawa yayi yana ɗaukar rigar shi yace "Akwai wani muhimmin aiki da na saka gaba tsawon watanni, mai ƙarashe aikin ne ya zo kuma zai koma nan da kwana uku, kinga bamu da lokaci kenan." Nauyayar ajiyar zuciya ta sauke tace "Kuma dole sai ka halarci wurin da kan ka?" Cike da tabbaci ya jinjina mata kai yace "Dole ne." Jinjina kai tayi tana k ara kamo zanen tana rufe jikin ta tace "Shikenan, Allah ya sa alkairi." Karon farko da tayi biyayya ga umarnin sa da ya saka shi jin kamar tsarguwa sabda yadda ta amsa cike da ladabi sai ya ji wallahi ta bashi wani irin tausayi duk da kuwa ya ji daɗin yadda ta amsa mishi kuma ya ji shima fa irin mai gidan nan mai bada umarni, wannan tausayin nata da ya ji daga ƙasan zuciyar shi yasa ya bita da kallo har ta kusa ficewa yace "Ki shirya zamu leƙa su Hajia mu sanar da su, zuwa safe kuma sai muje wajen su Mammie da Anna mu musu sallama, zuwa bayan azahar in sha Allah sai mu tafi." Ɗan murmushi tayi cikin siririyar murya tace "Amma ina so naje asibiti gaskiya." Wani murmushi yayi yace "Kin yarda zaki je dan kan ki kenan?" Shiru tayi ba ta ce komai ba, amma a zuciyar ta tayi niyyaro tafiya gaskiya dan a ɗinke mata bakin ƙofar shiga duniyar ta da *man ɗin ta* ya keta, dan idan bata yi gaggawar zuwa aka ɗinke ba a gba zata yi ta buɗewa ne a banza, ita kuma yanzu a shirye take da ta ci gaba da gyaran wurin nan idan ya so a bar ta da *yaron ta* su ci gaba da cin uwar sabadar juna wallah, to me ye a cikin ido ban da ruwa? Ai da wahaa ta kashe ka gwara daɗi ya kashe ka, dan haka a ci gaba daga inda aka tsaya kawai tund ta lura shine maganin matsalar da ta rabota da gidan tsohon mijin ta, *ciki* dai ne za ta yi ƙoƙari ta ga bai shiga ba, ba wai ba zata haihu da shi ba, a'a za dai ta sa tazara kamar ta wata takwas zuwa tara haka, to kenan bayan lokacin tana iya ɗaukar ciki ba mai zargin ta da tana zuwa gidan ta sakar masa ƙaniya ya wawura. Jabir ne ya katse mata murmushin da take yi ta hanyar faɗin "Za mu je yanzu ne ko sai da safe?" A tausashe tace "Da safe dai in sha Allah." Jinjina kai yayi ita kuma ta fita zuwa ban ɗaki. ********************* Duka Hajiya ta kai mata a baya tana dariya da cewa "Wai ni Hajia tunda kika zo naga kina jin kunyata sai sinne kai kike, na ɗauka ni da ke ai ba wannan? Ko dai dattijo ya fara saita mana ke?" Wallahi da gaske Ummu kunyar haɗa idanu da su take ji, musamman Maman ta da duk sanda quka haɗa idanu sai taga kamar tana mata irin murmushin e yane ɗin nan, ga kuma zance fal bakin ta da take hangowa shima, sai Abbu kuma da tunda suka shigo ya tamke fuska ya ƙi kallon ta, wai shi a dole hushi yake da ita, bayan kuma kullum aunty na gaya mata sai ya ce ta kira ta su gaisa, sai Jabir da yake ta kallo suna gaisawa har da tambayar shi "Ya iyalin? Ba wata matsala dai ko?" Jabir kuma da iya hege saida ya kalle ta sannan yayi murmushi ya girgiza kai yace "Babu, yanzu ai Maama ta nutsu, sai abinda ba'a rasa ba kawai." Kallonshi tayi galala wai shi irin ga fa boss ɗin nan a gida, sai kuma ta ɗan kawar da kai kawai tana kallon Hajia dake faɗin "To abinda ya ragen ma ka ci gaba da yi mata nasiha da jan kunne, idan ta gagara fahimta ka zane mata jikin ta da tsumagiya, ku malamai ai ba'a rabaku da bulala." Wata ƴar gajeruwar dariya Jabir yayi cike da son hassala Ummu ya ɗan shafo ƙugun ta ba tare da kowa ya gani ba yace" Ai hakan nake ta faman yi dattijuwa." Dariya ita ma Hajia tayi dan ta kula da kallon da Ummu ke mishi kamar za ta kife shi da mari tace" To Allah ya maka albarka, ai mai kama dani yadda kasan a jinsin yahudawa aka haifota, ƙin gaskiya." Jabir dai dariya kawai yake yi, har saida Abbu ya miƙe zai bar falon dan bakin shi so yake yace *baby ya kike*? Yana ganin idan yayi haka kuma ya kwafsa, Ummu da ta ga haka da sauri cikin shagwaɓa tace" Abbu, Abbu ka yafe min dan Allah, ka daina hushin dani haka mana, tafiya ma zamuyi gobe, shine muka zo sanar da ku." Cak! Ya tsaya tare da haɗe wasu irin yawu, sai kula ya jiyo ya kalle ta ita ma tana kallon shi amma bai ce komai ba, a ladabce ta sake cewa" Abbu muna zaune lafiya, ka tambaye shi ka ji, yanzu na daina masa komai wallahi, tun jiya da ya min bulala biyu da wayar caza." Murmushi Abbu yayi yana dawowa ya zauna inda yake lokacin da Jabir ya zaro idanu ya kalle ta yace" Lahhh! Ni zaki wa sharri?" Da mamaki ta kalle shi tace" Au! Baka dake ni ɗin bane?" Hajia da Mama Nuriyya da ya ga suna ta dariya ne yasa shi kallon Hajia yace" Hajia, ba fa wani duka bane, da fa zariyar wando ne, kuma ma ban zo da kaya masu zariyar wando ba saida na aro wajen Fahad." Dariya Hajia ta ƙyalƙyale da ita yana ƙarewa shigar dake jikin Jabir ɗin, shadda ce sabuwa fil rigada wando irin ɗinkin zamani tsaf, kuma ta san dole zariyar gare su ai, amma sai ta yi shiru kawai tana ta dariya, Ummu kuma ɗan saddo kanta tayi daf da shi cikin raɗa tace "Tun da nake a rayuwata, ban taɓa ganin irin wannan faɗa ba daidan ba." Murmushi yayi yace "Astagfirullah, ai dai nufin ki ba ƙarya ba ko?" Girgiza kai tayi kawai ba ta ce komai ba, sai Abbu da ya tambaye shi da gaske gobe ne tafiyar? Nan ya sanar da su abin da zai mayar da shi ɗin da gaggawa, addu'a suka mishi sannan Abbu ya tashi ya ce yana zuwa. Abbu ya jima bai dawo ba hakan ya basu damar sake tattaunawa sosai, har Mama Nuriyya tace mata "To aunty kin gama shirya kayan da zaki tafi da su ne?" Girgiza kai Ummu tayi tace "A'a aunty, wataƙila sai yanzu idan mun koma." Jinjina kai tayi tace "To idan aikin zai miki yawa ki kirani ko Adama sai ta je ta kama miki." Ita ma Ummu jinjina kan tayi tace "To, amma bana tunanin zaiyi yawa ma, tunda kunga iya kayan jikinmu ne kawai sai kuma wasu daga kayan kitchen, dui komai naku ne ai." Cike da gamsuwa Mama Nuriyya tace "Duk da haka dai." Sun jima suna hirar nan kafin Abbu ya shigo da sallama riƙe da takardu a hannun shi, wurin da ya tashi ya sake komawa ya zauna yana kallon Ummu tare da nuno ɗaya daga cikin takardun hannun shi wanda alamu ya nuna ciro su ne yayi daga cikin enveloppe dan gata ma a hannun shi yace "Ummu Kulsum, riƙe wannan..." Ya faɗa yana miƙo mata ɗaya, miƙewa tayi a nutse ta je gaban shi sannan ta rusuna ta karɓa cikin ladabi, komawa tayi ta zauna tana sauraren Abbu da kuma kallon shi yana faɗin "Wannan takardun wata restaurant ne da Hajia da kuma Abbu Allah jiƙan shi da rahama suka baki kyautar ta tun lokacin da aka haife ki, restaurant ɗin na nan gefe da babbar asibiti mai sunan *Halal food*, tana shigo da kuɗi sosai, na san zaki zama babbar Hajia." Duk da cikin sigar zolaya yayi maganar, kuma mutanen dake wurin sun dara, amma sai farin ciki ya sa Ummu zubo da hawaye tana sake kallon takardun da kuma Abbu ɗin, shima yana cikin dariyar ya sake miƙo mata wasu takardun da enveloppe ɗin gaba ɗaya yace" Wannan kuma ƙaramin kanfanina ne dake Niamey, a ƙarƙashin kanfanin ana sarrafa abubuwa da dama wasu kuma ana shigowa ne dasu amma da sunan kanfanin wanda yake mallakin ki ne ke da Eesha, ko ita ban faɗawa ba saboda nayi alƙawarin sai ranar da na gan ku dukan ku, ranar da aka ɗaura auren ki na so yi miki wannn kyautar, amma yadda abubuwa suka zo ya sa Allah bai nufa ba sai yanzu, ana ci gaba da kula miki da dukan su, sai dai a gobe ɗin nan zan tabbatar dake a matsayin shugaba a wannan wuraren biyu, da fatan zaki kula ki kuma yi gadon Abbun mu wajen jajircewa akan abu." Hajia ce ta fara taya ta murna da mata addu'a sosai da fatan alkairi sannan Mama Nuriyya ma, haka ma Jabir da kusan farin cikin shi ya so fin na kowa a wurin tare da jero addu'o'in Allah yayi riƙo da hannun ta ya bata ikon iyawa, cikin jin daɗi Abbu ya kalli Jabir yace "Jabir, zan iya cewa aiki kai ya sama, ina roƙon da ka kama mata kula da wannan wurare ka tayata alkintawa." Cikin ladabi Jabir ya amsa da "In sha Allah Abbu, Allah ya bamu ikon gudanar da su kamar yadda kukayi a baya." Da ameen suka amsa kafin su sake taɓa hira har dare yayi sannan suka fito zasu tafi. *Alhamdulillah.* [12/09 à 12:12] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *75* Daf da ƙofar gida suka haɗu da Fahad tare da Jibril, shigowar Fahad ɗin kenan Jibril ya tare shi yake faɗa masa matsalar da yake ciki, tunda aka fasa auren shi da Ummu mahaifiyar shi ko gaisuwar shi bata amsawa, shine ya zo ya lallaɓa Fahad ya je gidan su ya faɗa mata ba laifin shi bane, amma ta ɗauki damuwar fasa auren ne ta ɗora laifin a kan shi saboda kawunan shi basu sanar da ita gaskiyar lamarin ba saboda sanin bata da lafiya cikakkiya. Bai yi tsammanin zai ga ko da Ummu ba bare ita da Jabir, tunda ya gansu ya tsura musu idanu yake ta kallon su, musamman ma Jabir da yake ma kallon tsana saboda ganin wani shaƙiyin kallo da yake mishi har ɗaga girare yake yi yana wani murmushi, saida suka zo daf da su sukayi misabiha shi da Fahad dake faɗin "Aramma, har kun fito kenan? To kenan ni raina ni kayi da ba za'a je nawa ɓangaren a gaishe ni ba." Murmushi Jabir yayi amma bai ce komai ya ya miƙawa Jibril hannu saboda bin ƙa'idar shari'a, amma idan ta shine wallahi ba zai taɓa kallo shi ba, da ƙyar Jibril ya bashi hannu suka gaisa ya na ɗan satar kallon Ummu dake magana da Fahad. Cike da son ƙularwa Jabir ya kalli Ummu tare da zagaya hannun shi ta ƙugun ta ya shafo jigidar ta ita kuwa jigidar tayi sautin dake nuna an taɓa ta, ga jikin shi ya matsota duk da tana ta sinne kai wai ita kunya, cikin nutsuwa Jabir ya kalli fuskar ta yace "Kulsum, ki gaishe da *abokina* mana?" Kallon Jibril ɗin Ummu tayi a karon farko kenan, haɗe fuska tayi saboda ita ai bata san cikakken abinda ya faru ba, za ta yi magana sai kuma Jabir yace "Ko da yake, barshi ma kawai, kin san muryar ki *sirrina ce*." Sai kuma ya saketa tare da kallon ta yace "Je ki ina zuwa." Jinjina kai tayi a ladabce sannan ta fara takawa, tuni Jabir ya maida hankalin shi kan Jibril yana so ya ga abinda zai saka shi huce haushin shi akan shi, Jibril kuma da bai san target ɗin Jabir akan shi ba sai kuwa ya bi bayan Ummu da kallo har ma da shagala da mantawa da yana tare da wasu... A wani gadarance cike da jarumta da tafasar zuciya Jabir ya shaƙo wuyan rigar Jibril da duka hannaye biyu ya dawo da kallon Jibril ɗin zuwa fuskar shi, a kausashe yake kallon shi cikin kaushin murya Jabir da har jijjiga Jibril ɗin yake yace "Ya zama na ƙarshe a rayuwar ka da zaka sake raka matata da waɗannan ƙazaman idanun naka, kayi kuskure a rayuwar ka Jibril, da ka bari na san abinda yake ranka game da *macen da nafi so* a faɗin duniyar nan, wannan zaren kuma da kake burin ganin kalar shi har ma ka taɓa, ka sani ya maka nisa saboda yanzu ya zama *abu ma fi daraja* a gare ni, ni kaɗai ne yanzu nake da dama a kan ta fiye da kowa, idan baka daina kallon ta da wannan gurɓatacciyar aƙidar taka ba, shakka babu zaka *rasa idanun ka*, kuma ka rubuta ka ajiye dan zan aikata maka hakan ba tare da nadama ko dana sani ba." A wani tsiyace ya tunkuɗa shi baya sannan ya kalli Fahad dake kallon su wallahi kamar yau ya fara ganin su, ba maganganun Jabir bane suka fi ɗaukar hankalin shi kamar yadda ya aniya jijjiga Jibril ka rantse yana gaba da shi, murmushi ya ma Fahad yace" Sai gobe, zamuyi magana." Bai ko sake duban Jibril ba ya wuce zuwa hanyar fita, cike da takaici da baƙin ciki da kuma nadamar rayuwa Jibril ya bishi da idanu, a ce lalacewar shi ta kai har wannan yaron yna masa haka akan matar shi? Gyara wuyan rigar shi yayi ya ɗanyi gyaran murya sannan ya juya a fusace ko sallama bai ma Fahad ba ya wuce, jinjina kai Fahad yayi yana mamakin dama haka Jabir yake? Kai shiyasa aka ce idan ka ga lafiya to saka mata ƙota, yanzu ɗan Jabir ɗin nan ne ke da wannan masifa haka? Da wannan mamaki ya shiga cikin gida, duk da ya samu Nabila na ta fama da laulayi, ama dake ta kula shi sai ya dinga bata labarin abinda ya faru. *WASHE GARI* Dake asibitin kuɗi za su je a nutse saida suka gama ziyarar su daga gidan su Mammie zuwa gidan su Anna, ko ina tarba suka sami tare da yi musu nasiha da su zauna lafiya, sai Hajia Mamie da ta mata tsarabar lallen hausa mai yawa da mahallabiya da miski fari da ja dan kowane da anfanin shi, sannan ta haɗa mata da sahihin iccen magarya da kuma iccen dukkhan, Ummu dai karɓa tayi tana mamakin Hajia Mammie ɗin, kafin ta ranƙwasheta a kai ta murɗe mata kunne tana faɗin "Saura idan kun je can ɗin ki zubar min da abu ɗaya a cikin kayan nan, wallahi da akan uwar ki Nuriyya zan huce, sannan ki ci gaba da kama jikin ki da kuma kula da mijin ki, ubangiji ne ya wanke ya baki dan haka ki kula, kinga dai yana ganiyar ƙuruciyar shi ne, sannan ya san falalar dake cikin ƙara aure, wallahi duk ta inda kka gaza sai dai kiji ana miki buɗa a cikin gida, dan irin su Jabir ba zasu juri ɓacin rai da horon wahala a gurin mace ba kullum, sannan kinga lallen nan? Nasan kin iya anfani da shi ta hanyoyi da dama, daga kan gyaran fata, gyaran farji, rigakafin ciwon ƙafafu, rigakafin sanyin dake shiga ta ƙafafu, sannan kuma ado ne, haka kuma wannan kan naki mai yalwar gashi ki dinga kulawa da shi, kin ji ni?" Jinjina kai Ummu tayi tana son ta sakar mata kunne tace" Naji Mammie, zan yi in sha Allah." Daga haka Mammie ɗin ta koma binsu da addu'a har ta rakosu farfajiya tana faɗawa Jabir" Da zaran ta kusa haihuwa ka kirani ka faɗa min, da kaina zan je yi mata tsaro." Kallon juna suka fara yi ita da Jabir, wallahi da Hajia tayi maganar sai yaji kunya ta kama shi, wai fa yanzu nan sai Maama ta haifa masa yara ko? Kuma idan Abba ya ji ba zai ji komai ba? Ya salam! Lallai wata *ƙaddarar* ba dan an rubuta ta saman allon dutsi ba da ba ta yadda wani abu zai iya faruwa. Ummu kuma _"Hmmmm."_ Kawai ta faɗa tana ayyana Allah ya kaisu lafiya, tana zuwa ma zata je ta ɗauki magani gaskiya, duk da a matse take da son ta ga ta sake haihuwa, amma fa ba zata iya yinta da Jabir da wurwuri haka ba. Daga nan asibiti suka wuce, a bakin ƙofa ta ce ya jirata gaskiya ba zata yarda su shiga ana masa kallon ƙannen ta ba, murmushi kawai yayi ya ɗan ƙare dafe sitiyarin shi yana jinjina kai yace "Haba Kulsum, zamu haɗu ne anjima." Dariya tayi ta shige ciki ta barshi bayan ya damƙa mata kuɗi da sanin lallai za ta buƙace su, bayan sun gaisa da matashiyar likitar da ba za su wuce tsara ba ma cikin kunya da sinne kai ta faɗa mata abinda ya kawo ta (😕Ummu take wa mata sawu kikayi fa, ke dai kawai Allah kauda ɓacin rana), cikin fara'a da sakin fuska likitar dake kallon ta tace "To kina tunani kinyi ƙarin ne? Ko tabbaci gare ki?" Ba tare da Ummu ta ɗaga kan ta ba tace "Ina dai tunani ne." Jinjina kai likitar tayi tace "Ok, kina da aure ne?" Ɗaga kai tayi ta kalle ta da mamaki, sai kula ta amsa da "E, ina da." Dariya likitar tayi dake irin sakakkun mutanen nan ne da basu da matsala tace "Ko da yake ai ga alama nan ma ta cexa amarya ce ke, wato ango ya miki halin nasu ko?" Sai kuma tayi dariya tana miƙewa tace "Muje in duba ki, amma dai tare kuke da angon ko? Dan zan so ya saka min hannu da kan shi." Kallon ta Ummu tayi tana miƙexa tace "A'a, baya nan ne." Wani ɗaki likita ta shiga Ummu ta bita suka rufe, safar hannu ta sa tana duba ta ta ɗago tana cire safar tace "Akwai ƙari ƙawata, sai dai ba wani babba bane, amma sannu sannu idan ango na ci gba da ratsaki, zaki iya buɗewa, yanzu ya kike so a yi? A miki ɗinkin ne?" Ɗaga kai Ummu tayi tana ayyana _"Yarinyar nan bata sanni bane. "_ A zahiri kuma tace" A min." Jinjina kai tayi ta nufi inda kayan aikin suke tace" Amma fa ba zi wuce a miki biyu ba gaskiya, dan in akayi fiye da haka to nan da sati zaki iya sake dawowa." Ummu dai na sauraren ta ba ta ce komai ba, tana ji tana gani da ranta da lafiyar ta kuma a hayyacin ta aka dinga tsikarar jikin ta ana ɗinkexa saboda *aikin Jabir* ɗin da ta ɗauka b zai iya mata komai ba saboda Alhaji ma ya kasa iyawa da ita. Tana fitowa ta same shi yana waya, ganin ta yasa ya yanke kiran cikin kulawa ya tambaye ta "Ya ake ciki? Har an gama ne?" Jinjina kai tayi tana yatsina fuska saboda zaman da tayi ta ji ba daɗi, sai kuma tace "An idar." Ba tare da ya ɗauke idanun shi daga kan ta ba yace "Ba wata matsala kuma? Komai daidai." A hankali tace "Babu." Sai kuma ta sa hannu jakar ta ta ciro takarda ta miƙa mishi tace "Sai wannan da ta bayar, ta ce a siya zai taimaka wajen saurin warkar da ciwon in sha Allah." Karɓa yayi yana dubawa tare da soka takardar aljihu yace"In sha Allah." Kumatun ta ya shafa cike da tausayawa yace" Da zafi ko? Hala ma kinyi kuka? Ga idanun ki sun ɗan canza." Ajiyar zuciya ta sauke tace" Da zafi gaskiya, shiyasa ma na so ta sumar dani kafin ta min aikin." Matsawa yayi gaf da fuskar ta ya sumbaci kumcin ta sannan yace" Ki gafarci *ƙanin ki aunty*, tangarɗar mafari ce." Turo baki tayi cikin shagwaɓa tace" Bana son haka fa, bayan ka kekketani." Dariya yayi suna ɗaukar hanya, sai kuma tayi saurin duban shi tace" Yawwa ka ga na so in manta, likita ta ce na faɗa maka daga yanzu har sanda ciwon zai warke fa ba abinda zaka sake min, sai nace mata ai dama akwai alƙawari tsakanin mu na uku ma ba zai sake faruwa ba, ko?" Wani wawan kallo ya mata da alamar gaskiyar shi kenan yace" Kin gani ko? Shiyasa ban cika son mu'amula da irin mutanen nan ba, ita yanzu matar nan ba dan bata shan nata magani bisa ƙa'ida ba, ya ubangiji zai hallatawa mutum ziyartar gonar shi ita ta ce sai ta saka mishi lokaci, ita ɗin wacece ita?" Da mamaki Ummu ta kalle shi tace" Jabir, abu ne fa da kowa ya sani, ba ta yadda za'a wa mace ɗinki kuma a je mata a lokacin." Taɓe baki yayi yace" Zan duba na gani." Itama ɗan taɓe bakin tayi tace" Ba wani za ka duba, hakane ma kuma dole kaima kayi haƙuri, ni fa ba katifar ka bace Jabir." Yadda tayi maganar kamar ta hassala ya sa shi duban ta yace" Kulsum, kinsan dai bana son rigima dake yanzu ta fatar baki ko? Gwara mu shiga tukara idan muka shiga filin ibada sai wanda ya fi ƙarfin wani yayi maganin shi ko, to ki kiyaye." Kallon shi Ummu tayi tace" Jabir, fisabilillah kai yanzu ko sau ɗaa ba zaka taɓa min magana da ladabi ba? Irin dai ko dan nji daɗi ɗin nan ka girmamani." Wani kallon sama d ƙasa ya mata sannan yace" Sannu Maama, Allah huci zuciyar ki *uwata*." Da mamaki ta sake kallon shi, wai jama'a dama hka Jabir yake riƙaƙƙen tantiri ne? Kaji fa wasa wasa yanzu kawai babu wani abu da yake yi dake nuna yana mutumta ta, kaji fa har da yi mata gatse, wannan magana da ya faɗa ai ba daga zuciyar shi ta fito ba. Jinjina kai tayi tana faɗin "Ba damuwa, ci gaba da yi min yadda kake so Jabir." Kallon ta ya sake yi yace "Magana ta gaskiya fa sunan nan ƙona min rai yake, wai ke baki ji ana cewa *ba faɗa da malam ba... Daren ake tsoro*? Kin san dai ba zanyi tsayuwar dare akan ki ina shaidawa ubangijina abinda kike min da bana so ba, sai dan ba zan ji whalar tsayar da mutum kan ƙafafun shi ba sannan na saka shi shasheƙa har sai an fara min kuka, dan haka ki kiyaye." Irin kallon nan ne take mishi mai cike da mamaki har tana tambayar kuma yanzu nan shi saboda Allah ya yarda shi malami ne? Yana mata abubuwa haka ɗin yake so ta yarda shi malam ne? Ko da ya fahimceta sai kawai ya taɓe baki yace" *Sorry aunty Kulsum*." Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tace" Allah ka shirya mu shirin addinin musulunci." "Ameen Maama." Ya faɗa da ƙarfin shi yana ci gaba da tuƙin shi, da haka suka isa gida suka ci gaba da haɗa abinda ya rage musu, dan tun jiya suka haɗa kayan su tsaf shi da ita ba tare da kowa ya kama musu ba dan ba wani babban aiki bane. *A gurguje* Duk da shigar dare sukayi amma Allah ya sauke su lafiya, dama kuma su Aisha da suka riga su zuwa basu tsaya hutu ba aka samu mutane aka shiga gyaran ɗaki, su kan su saida daren suka kammala komai suka nufi gidajen su. Dan haka suna zuwa gida ya musu kyau kamar ba nasu ba, ga wasu irin kaya na gani na bugawa a jarida da Jabir ya samu sun zuba a gidan, gashi duka ɗakunan ukun an gyara su kuma da gado a ciki, ai a nutse suka samu sukayi wanka Ummu kuma saida ta zauna ruwan zafi saboda fa ta sha wahala a tafiyar nan, dan ma wani lokacin Jabir ɗin na ɗan tsayawa ta koma baya ta kwanta ko ya kwantar maya da kujerar, hakan yasa ma zaman ya ɗan rage mata tsayi. Tunda suka dawo suka sake buɗa sabon shafi na raha da farin ciki da kuma sauke haƙƙoƙin dake kawunan su, Jabir dai baya jin nauyin faɗa mata kinyi kyau Maama, ko ina buƙatar ki Maama, ko wannan abun akwai haukatar da mutum, ko ya dinga wasa da jigidar ta ko kuma abubuwan da har yanzu ya ce bai san me ya sa suke son hararan shi ba. Ita kan ta Ummu yanzu tana aje kunyar ta gefe da duk wani girman kai tana mayar masa da martanin duk abinda ya mata, idan ya faɗa mata wata kalmar sai ta murje idanu ta rama, idan wani abu ya taɓa nata haka za ta rama ta ce tunda dai ya rainata, wani lokacin kuma idan tana so suyi raha ko faɗa idan ya mata abun sai ta riƙe haɓa ta ce _"Kuma yanzu nan baka ji kunya ba ko?"_ Da ta faɗi haka shi kuma sai yace _" Oh! Sorry aunty."_ Da irin haka suke gudanar da rayuwar su cikin farin ciki, haka kula babu taushe hannu game da lamarin sukuwa kan gado a wajen Jabir, kullum more rayuwar shi yake da Maaman shi da ita ma take miƙa masa wuya saboda har yanzu godiya take ga Allah da ya bata wannan yaro daje iyawa da buƙatar ta. Wani lokacin ma idan ta ga karatu ya ɗauki hankalin shi yayi dare ko kuma nazari akan wasu litattafai, tunda ta san me ke tsokano shi haka za ta sako kayan bacci ta shafo humrar ta ko kulaccha sannan ta dinga gilmawa ta gaban shi tana tako da ɗan ƙarfin da zai dinga saka jigidar ta sautin da dole sai ya kalle ta, da ya ga haka kuma sai ya aje komai ya riƙota yace _"Maama kina lalatani dayawa fa, alƙawari nayi zamu ci amarcin wata ɗaya, amma har mun haura wata kin ƙi barina na maida hankali kan karatu, kin ga fa yanzu ko wajen karatun malam na daina zama, sa'a ɗaya ma shi ɗin mai fahimtar mutane irina ne, ya ce ya min uzuri amma na tabbata satin nan na koma majalisi."_ Da ya faɗi haka sai tayi dariyar ƙeta ta marmaɗa masa idanu tace" To ni me nayi? Za'a hanani wucewa ne ta cikin falona?" Sai ya girgiza mata kai yace" A'a, amma kuma nima ba'a isa a hanani kewaya gonata ba na ga ya ta wuni." Dariya tayi tace" To ka dinga zama ɗaki kana karatun." Rumgumeta yayi a jikin shi yace" Wannan ma baki isa ba, ina zamana kije tafe kina kaɗa sautin abar nan mai rikitani, wallahi idan naji sautin nan gabana har faɗuwa yake yi." Cikin salo ta dinga zagaya gemun shi cike da son ɗaukar hankalin shi tace" To muje ciki, amma fa kar ka faɗawa kowa abinda ke faruwa tsakaninmu." Saida ya sumbaci bakin ta yace" Har yau kin ji ko ganin wanda ya nuna miki abinda ke faruwa? Ko Aliyu da ya zo ranar kinga yana mana kallon dake nuna ya san me muke aikatawa ne? Ai ni ba sakarai bane da zan faɗawa wani ina wa maamana wannan abubuwan." Dogon hancin sh ta ja suka shige ɗaki kamar yadda suka saba. Wani abu kuma dake ƙara birge Jabir game da maaman nashi, yadda take tsananin kulawa da cikin shi, yana tashi da safe zai samu abun kari marar nauyi kamar yadda yake da buƙata ya ci, idan ya fita kuma abinci dama akwai yaron da yake turowa yana ɗaukar masa idan yana shago, zata haɗa masa abinci kala kala ta tura masa, haka da dare ma zai samu abincin shi akan lokaci, baya ga haka ga abubuwan taɓawa da take faman yi kowane lokaci baa dai ai waiwayi abinda zai iya ci ya rasa ba, wani lokaci ma idan tayi masa wannan kayan maƙulashen cewa yake kar tayi girki su kaɗai ma sun ishe shi. Ba dan makulli dake gare shi na gidan ba, da ya jima tsaye yana bugun ƙofar ba ta sani ba, sai gashi ya shigo ko alamar ta ji babu bare ta san da shigowar shi, haka ya tsaya kan ta yana kallon da gaske bacci take irin mai nauyin nan idanun ta ruf sannan tana ta sauke numfashi, girgiza kai yayi a hankali saboda mamakin baccin nata, ta kwanta da wuri tun dare bai yi ba, idan tayi sallah asuba ma ta sake komawa kafin ƙarshe 08 ta farka dan shirya abun kari, ace bayan duk haka kuma ta sake kwantawa har bacci ya ɗauketa? Daddaɓata yayi ta farka, a kasalance ba dan baccin ya ishe ya ba ta tashi zaune tana ta murza idanu tana faɗin "Wai har ka dawo? Wallahi wani irin bacci ne ya ɗauke ni kamar na sha wani abu." Juyawa kawai yayi zai fita yana faɗin "Dan Allah ki gaggauta shiryawa na aje ki." Ƙeyar sa ta kalla tace "To idan sauri ka ke ka tafi mana, ni sai naje a tawa motar." Juyowa yayi ya mata wani irin kallo, sai kawai ya sake juyawa ya fice, gwalo ta mishi tana sauka daga kan gadon tace "Komai abun ka sai na fara fita ni kaɗai, zan zauna ne kullum kana kaini unguwa." A tsanake ta shirya saboda kasala dake ɗawainiya da ita kwanan nan, cikin doguwar rigar atamfa ta shirya ta ɗora dogon hijabin ta har ƙasa mai hannaye haɗe da niƙab, sannan ta saka safar ƙafa ta fito, yanzu kam ta saba da wannan shigar, dama ko da tana gidan alhaji tana ɗan yi wasu lokuta, dan haka da Jabir ya nuna yanzu a haka yake son ta dinga fita ba ta wani masa tsayayya ko shan wahala ba ta zarce abun ta. Falo ta same shi yna waya yana faɗin gashi nan tafe, yana wani abu ne muhimmi amma yana zuwa, yan ganin ta ya wurgo mata harara yace "Wallahi Maama kin raina ni, yanzu ni kika shanya haka?" Jinjina kai tayi tace "Uhummmm! Ni da kake kiran sunana gatsau ban ce komai ba sai kai za ka ce haka?" Hannunta ya kama yana janya yace "Muje dai yanzu sauri nake, munyi faɗan a cikin mota." Murmushi tayi tare da tallabo fuskar shi ta sumbaci goshin shi tana faɗin "Ɗan ƙanena kenan." Girgiza mata kai yayi yace "Ban yarda ba, ki canza kalaman ki ko muje filin ƴar ƙure." Da sauri ta bushe da dariya tana faɗin "To nji Yayana." Nan ma girgiza kai yayi yace "Shi ma ban yarda ba, a bani matsayina kawai." Janshi tayi suka fice tana rufe falon tana cewa "Rigima kake ji, muje mu dawo sai a tantance ɗin." Murmushi yayi shima ya juya yana faɗin "To, amma idan na ɗauko ki zamu biya mu gaishe da Abba." Da sauri ta juya ta kalle shi, Alhaji yaie nufi, kuma ya san ta ce ita kam gidan shi idan ba wani abu ya faru ba gaskiya ba zata je ba, musamman da Zeinab ta gaya mata irin caccakar ta da maman ta Atika ta dinga yi wai ta zagaye ta aure yaron Alhaji, su kam dama sun san ai da wani abu tsakanin ta da Jabir, haka kawai ba zai zo ba ya rasa wanda zai taimaka mishi sai Alhaji, kawai sun wanke shi ta baibai ne, Zeinab ta faɗa mata abun nan har sai da ya sa Alhaji ya ce ta tafi gidan su, da ƙyar aka lallaɓa shi a lokacin dan ƙwarai maganar ta Atika ta so tayi tasiri a zuciyar shi, dan sai yake ji da ganin ko haka ɗin nan, dan haka yayi gaggawar dakatar da abun. Saida ta gama rufe ƙofofin ta same shi mota suka fara tafiya, kallon shi tayi tace "Man, gaskiya ba zan je gidan Abban ka ba." Kallon ta yayi yace "Me ya sa?" A taƙaice ta amsa da "Kawai." Bai sake cewa komai ba haka ita ma har ya aje ta gidan Mama ya shiga suka gaisa sannan ya tafi ya bar ta, tun kallon farko da Mama ta ma Ummu ta gane kamar ciki gare ta, amma sai ta sake tabbatar mata ta hanyar cin abincin da ya fi ƙarfin cin ta a yadda ta san ta, sannan tana yin kwance sai bacci, dariya kawai mama tayi tana kallon ta tace "Allah ya raba lafiya." Kamar cikin bacci haka kamar kuma a mafarki ta ji wannan addu'ar, buɗa idanu tayi da ƙyar ta kalli mama sai tace "Mama magana kikayi?" Girgiza kai Mama tayi tace "Ban ce komai ba." Yadda Mama tayi maganar kamar da irin yanayin nan na gatse sai Ummu ta ji ta tsargu, ita ma indai kunnuwan ta daidai suka jiyo to fa ji tayi mama ta ce Allah raba lafiya, ya raba me to? Ita da mijin ta? Ita kam ai yanzu wallahi tallahi *tana son mijin ta* ba wanda ya isa ya raba ta da shi, to me ma ta masa ko ya mata? Ko kawu Bilal fa anyi lokacin da ta daina ɗaukar wayar shi saboda tunanin zai mata maganar rabuwar su, to saboda Allah yaro salihi ma irin mijin ta wa ke da shi a duniyar nan? Ba ruwan shi, ba ya mata komai, shi fa ko ɗan faɗan nan na mata da miji basa yi, da tayi ba daidai ba ranar dai zai wuni yana saka wa'azin Margayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam ne, ko kuma margayi Sheikh Albany, da dai sauraren su, ko kuma idan dare yayi akan gado ya mata nashi salon wa'azin, shikenan fa, girki ma bawan Allahn nan na safe tare suke yi, idan yana gida da yamma suyi na dare tare, kai kaɗan ne daga aikin Jabir tana farkawa a baccin rana ta same shi ya wanke musu kayan su tsaf ita da shi, ya ce shi kam zai iya bayar da kayak shi wanki, amma na matar sa ai aikin shi ne kawai, hatta ɗan kamfai yaron nan wanke mata yake, to fisabilillah shine Mama za ta ce Allah raba su lafiya? Ai ko suna kusa da daina ganin ta, dan ko zaman iskanci take dashi yake mata wannan ɗawainiya, ai ta so gama rayuwa da shi bare kum zaman aure, dan haka ba wanda zai san tafiyar su wallahi, gwara su je can wata uwa duniyar suyi zaman su. (🤔Maama, wato da shi kaɗai ne za'a miki fatan rabuwa lafiya?) *Alhamdulillah.* [14/09 à 12:34] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 *RUBUTACCIYA* 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨 _NA_ *SAMIRA HAROUNA* _SADAUKARWA GA_ *MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA* _(Allah ya jiƙanta da rahama)_ *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicé Lait de nuit Parfums désodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waɗannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃 Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94* *SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_ _Bismillahir- rahamanir-rahim._ *76* Komai na tafiya daidai a rayuwar su, kasuwancin su ma mazajen su na taimaja musu tare da haɗin guiwar ma'aikatan da tun fil'azal, arziƙi kam ma sha Allah bunƙasa yake, gashi kuma sunyi sa'ar maza da basu saka idanu akan dukiyar su ba, bare ma Jabir da nashi harkokin ke ta kara sako shi gaba, sai dai a ce Alhamdulillah. Haka a zaman auren su ma farin ciki ya fi komai yawa a ciki, dan zama ne da fahimtar juna ya samu wajen zama, hakan yasa basu cika samun saɓani ba, dan ta ɓangaren Aisha da Sa'ad ita ce ke kiran shi *Abbu*, hakan yasa tana masa komai ne da mutumtawa, yayin da tayi laifi kuma sai ta masa takwaf takwaf da fuska ta ce uba ne shi ai yayi haƙuri, sai kuma ya ɗauki halin Annabawa yayi haƙurin. Ita ma dai gyambon haka take, ba dan ma yanzu rigimar da ita kan ta tana bata mamaki da ta koya, dan yanzu kaɗan a aikin ta ne idan yana mata wani abun musamman ma ta masa ba daidai ba yana faɗa, ta ga da gaske Jabir faɗa yake mata irin dai na miji da mata ɗin nan, sai ya samu nutsuwa musamman idan ta cika mishi cikin shi sai ta riƙe haɓa tana kallon shi tace _"Fisabilillah ɗazu da kana min faɗa baka ji nauyi ba? Jabir ba dan ƙasusuwan jikin ka da suka baka haɗin kai ba har ka kamo ni a tsawo, kana ganin da yanzu ba'a can cikin ƙasa kake ba?"_ Dama da ta faɗi haka sai ta fara murmushi, dan kuwa ko kallonta ba ya yi yake faɗin _" Ki sa ƙafa ki take ni mana, kinga saina koma cikin ƙasar."_ Da ya faɗi haka sai ta kawar da kai ta taɓa baki tace _" To Allah ya shirya min kai, amma wallahi ba dan mutane ba *gafarta* da ba abinda zai hanani yanko maka form ka cike ko ka samu damar shiga jerin dakarun oga (sheɗan🤣), dan abinda kake min ba dan ina da haƙuri ba kuma na ɗauki girman na yarda wauta ba abinda ba ta sakawa, ai kaima kasan da tuni na bubbuga ka a ƙasa."_ Dariya yake yi har yana tintsirawa, kafin ya rumgumota jikin ta ya haɗa kan shi da goshin ta yace" Na sani mana Maamana, shiyasa ai naa zaɓe ki, dan ke kaɗai ce zaki iya haƙurin zama da ni, yanzu ba gashi ba, muna zaune abun mu muna ta bautar ubangiji." Jinjina kai take yi tace" Umm! Kuma gobe ma in sha Allah zamu tashi da azumi ko?" Kanne mata idanu ɗaya yayi yace" Haƙƙun, kuma Maama zata shayar dani ko?" Ita ma idanun ta kanne mishi tace" Me zai hana? Dan na san ka gwanin sirri ne ai." A tare sukayi dariya suka ci gba da hirar su, kafin Ummu ta ɗauki wayar ta tana dubawa ta ga saƙon Aisha, ganin Video da sauri ta buɗe tana miƙewa tsaye tana faɗin" Kar dai yrinyar nan ta haihu ba ta gaya min ba? Sai yanzu zata turo min hoton yaro." Kallon ta Jabir yayi yace" Idan ta gaya miki me zaki mata?" Kallon shi tayi tana faɗin" Ni nake so fa na rakata asibiti." Taɓe baki yayi yana ɗaukan tashi wayar da tunanin ya kira Sa'ad ma wallahi ya msa kashedi kar ma a fara, kai shi fa akan Maama zai iya yiwa kowa gargaɗi amma ban da mutum huɗu, na farko *Abban shi* wanda shi ya haife shi ya kawo shi duniya, na biyu kuma *Abbu* wanda shi ya haifa masa wacce ta jima da zama *rayuwar sa*, sai na uku *Alhaji Kabir* wanda shi ne ya masa gatan da babu wanda ya kwatanta yi masa a duniya, sai na huɗu kuma *Aliyu*, Aliyu: ƙwarai Aliyu halin Abban su Alhaji gare shi, ba ya da ƙyashi, ba ya da hassada, ba ya da baƙin ciki, sannan ya zamar masa komai a rayuwa, ban taɓa tsammanin Aliyu zai fahimci maganar auren shi da Ummi ba, amma sai gashi sahun farko a cikin mutanen dake son jawo hakalin shi kan ya aikata hakan, ya jima yana so ya ga canji daga Aliyu da ya ja baya da shi shima, amma wallahi Aliyu yadda kasan copie ne na shugabanmu Aliyu na asalin wato zaki, sai hakan ya ƙi zuwa a kan shi ma bare har a gani a fuskar shi, har yau har gobe Ummu yanzu kallon budurwar da suka haɗu da ita a titi yake mata suka nemi auren ta aka bsu, yana kiranta da aunty ne kawai saboda sabo, hakan yasa bai ma Aliyu shamaki da gidan shi ba, kowane lokaci ya kan iya zuwa neman sa idan yna nan, haka kuma ko yunwa yake ji ya kan gayyace shi gidan shi, dan yanzu shima burin shi shine ya saka musu da alkairi mutanen nan da halin girman su ya zarce misali. Vodeon na buɗewa Ummu ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta zauna tana aje wayar da cewa "Haba yarinya, nima zan rama wata rana, dan kinga malam nake aura ko? Kana saka kiɗa ma za'a fara maka wa'azi." Wani kallo ya mata mai kama da hagen nesa yace "Kulsum, wani lokaci abubuwan ki kamar dai irin ba ue kaɗai ba ko? Sai kina abu haka kamar dai an baki ajiyar burkutu." Ɗan hararen gefen shi tayi tace "Ai da kalansir nake kwana a ɗaki *ɗan Maama*." Jinjina kai yayi yana ɗaukar wayar ta ta yace "In ga me ye Aisha ta turo da ni ba zan iya ba ake ci min mutumci?" Kallon shi tayi tace "Kar ka sani a baki." Jawota yayi jikin shi yana faɗin "Zo nima na nuna miki tawa ƙwarewar?" Da sauri ta miƙe tana faɗin "Bari in dawo, kaga wainar flawa kawai naji ina sha'awar ci yanzun nan." Da wani irin kallon haba ɗin nan ya bita har ta shige. To fa haka rayuwar tasu take tafia gwanin ban sha'awa, ga taimakekeniya tsakanin su da su kan su har birge juna suke, dan takanas ta kano Jabir saida ya wakilceta a wani taro da aka yi a kamfanin su ita da Aisha, kuma tare da. Sa'ad ya tafi suka dawo lafiya, kamar yadda ita ma akwai ranar da ta wakilce shi a makaratar Aliyu, ba kuma wani uzuri bane ya hana shi, sai dai ya zo inda zai ɗan fayyace wani sirri ne ga matan ajin shi kuma yana ji nauyin jaka, bugu da ƙari Kuwailat ma na wannan ajin a lokacin, sai ya bata wannan awa ɗaya ɗin ta musu darasin, bata ji nauyin Kuwailat ba dan abu ne da dama tana ɗan ɗorata a hanya akan wasu abubuwan, abun mamaki su kan su ɗaliban a ranar da ya koma sai suka faɗa masa sun fi son darasin malama, dan ita mace ce sannan har fari da ido ta koya musu yadda ake yi. *Tun kwana uku* da suka wuce take ta lisafin rabon da ta ga al'adar ta, sai abun ya fara damun ta sai kuma ta wayance ta hanyar faɗin "Ibu ɗin da ta sha lokacin da aka mata ɗinki ne ya jirkita mata kwankin al'ada, Shiyasa dama bana son shan shi wallahi saboda haka yake min." Sai kawai ta basar da maganar ta shiga wata harka daban. To zuwan Kuwailat gidan yi mata hutun sati ɗaya ya sa ta gano dai da gaske ciki gare ta, Kuwailat gani tayi maman ta tayi ƙiba sannan ga cikin ta da ya taso sosai, sannan wuni take bacci ga rashin son aiki, dan ranar da ta zo ma saida ta mata sharan ɗaki da guga ta ce tun jiya ba ta yi ba ita, sannan ta ga idan tana zaune *Yaya Jabir* idan ya shigo wanda har yanzu ta kasa cnaa mishi suna daga Yaya sai ya zo yake kama hannayen ta sannan su shiga ɗaki amma ba ta iya tashi musamman idan ta gama cin abinci kenan. Shine ranar suna zaune Kuwailat tace "Mamie, idan Allah ya sauke ki lafiya ina so nayi walima ni da ƙawayena kawai, dan lokacin zai iya daidai da gam a jarabawar mu." Kallon Kuwailat tayi irin mutum yayi abun mamaki gaban kan nan, sai kawai ta kalli cikin ta sannan ta kalli Kuwailat tace "Idan na haihu fa kike nufi ko?" Da farna Kuwailat ta amsa da "E Mamie, dan Allah kada ki hanani Mamie." Sai kawai Ummu ta miƙe zunbur duk da batayi niyyar tashi ba a lokacin, ɗaki ta shiga ta ɗauko wayar ta da jakar ta da ta san akwai kuɗi ciki da makullin motar ta ta fito, hijabin ta na sallah ta yafa tace wa Kuwailat" Idan *Abbun ki* (Jabir) ya shigo dan girman Allah ce masa asibiti na tafi, gwara su gaya min gaskiya, da gaske Jabir ciki ya min ko me yake nufi?" Tayi maganar tana ficewa daga falon. Lokacik shigowar shi ne dama, hakan yasa tana fita ya shigo, a ladabce Kuwailat ta masa sannu da zuwa ya amsa sannan ya tambaye ta maman ta? Amsar ta bashi da ta tafi asibiti yanzu, duk da ta ce masa fita tayi, amma da ya tambayi Kuwailat yace "Asibiti? Yin m? Ko wani ne ba lafiya?" Sai kawai tace masa "A'a lafia lau, ina ga dai awo ne zata je yi ko gwaji." Sai kawai yayi dariya ya shiga ɗakin shi dan ya jira dawowar ta. Ta jima kafin ta dawo gidan jiki a sanyaye kuma a eikice ta shiga ɗakin nashi, ƙasa ta jefar da jakar ta tana faɗin "Shikenan, Jabir ka tona ma zaman da muke cikin ɗaki asiri, wallahi ciki ne da ni, wai likita har da min faɗa kamar uwata wai ciki wata biyar amma ban sani ba dan hauka...han." Ƙwafa tayi tana zama kan gadon, zaune yayi yna kallon ta da irin basarwa yace "Ciki fa Maama? Ke gare ki wai? Subhanallah." Kallon shi tayi tace "Wallahi ka sani Jabir, shiru kawai ka min dan dama kana so ka ga bayana." Sai kuma tayi kamar zata fashe da kuka tace "Yanzu fisabililahi ya kake so nayi? Ranar da mukayi waya Abbu Bilal ya ce min zai zo fa ya aiwatar da shirin sa a kanmu, sannan su Mammie da Hajia da Eesha, kai har ma da Nabila da uncle Fahad iskanci suke min wallahi, kai har ma fa aunty, sai ka ji ta ce idan Eesha ta haihu za'ayi kasa da kaza, duk burin ta akan hiahuwar Eesha ne, tunda ni ai Yayar ka ce ba abinda kake min, ni kuma sai nace e mana." Kamota Jabir yayi jikin shi ya matse ta tsam cikin muryar dariya yana ɗan jijjigata da daddaɓa bayan ta yace" Shikenan Maamana, ba dai cikina ne ba, ni ai ban san ya shiga ba dan bai yi shawara da ni ba, kuma kinga ai kin shaideni da riƙon alƙawari, amma ki min alfarma ɗaya, ina kewar mahaifiya, ina ji ina ma na san kamannin ta? A ƙalla da zan dinga tuna fuskar ta ko na ga mai kama da ita, hakan yasa a duniya buri ɗaya ya rage min yanzu bayan samun ki, wannan burin kuma shine *UMMU KULSUM* ta haifa min *ɗana* daga tsatson ta, na roƙe ki Maama, ki barshi ya zo duniya ba tare da tsangwamar ki ko nuna masa ƙiyayya ba, ina tabbatar miki daga shi shikenan." Ɗaga kanta tayi ta kalle shi da irin tuhuma tace" Da gaske?" Jinjina mata kai yayi yace" In sha Allah." Laɓe baki tayi cike da tausaya mishi, ai ya gama da ita kuma, yo me ye a ciki wai? Dan ta haifa masa ɗa ɗaya dai ƙwallin ƙwal? Ba komai ai dan gaban idanun ta wanzami ya kai ziyara gidan su, kai ita ma lokacin ba wayo ne da ita ba fa, dan haka zata haifo guda ɗayan mana, Alhaji ma ba gashi ta bashi ɗaya ba da yake tuna ta da ita? Shi ma zata masa hakan kawai dan ai ta fi *son sa* gaskiya akan Alhaji, e ta faɗa kam, wanda zasu yada mata magana kuma ai idan ta musu shiru ta bisu da idanu ta gama da su kawai, dan haka za ta sake shiga ɗakin yaƙin mata in sha Allah ita ma nan da wata huɗu. *Kwana biyu* da faruwar haka Aisha ta haihu, nan fa aka shiga hidimar suna inda mutanen Agadez suka taho biki, Ummu na ta kai da kawo babu zama, gashi wasu baƙin ma a gidan ta suka sauka har da aunty Mardiyya da ta ce ita bata surukuntaka da Jabir dan dama ɗan ta ne, Mama Nuriyya ce dai bata leƙo gidan ba ita a dole kunyar zuwa gidan babbar ƴarta take ji, sai bayan suna ne suna shirye shiryen komawa sun dawo daga kasuwa da yamma kwatsam suka biyo ba tare da Ummu ta sani ba. Hakan ya sa Jabir suka samu a farfajiya yana wanke kayan su shi da Ummu ita kuma tana ɓarar dankalin turawa suna hira abun su, gaisawa sukayi da Jabir sosai inda ya shiga ciki dan ya canza kayan jikin shi ya basu wuri, hakan yasa Mama cire takalmen ta ta nufo Ummu dake tsaye da shi tana faɗin "Na shiga uku ni Nuriyya, aunty dama bawa kika mayar da mijin naki? Dan kawai kin girme shi da wasu ƴan shekaru sai kike saka shi wanki." Da gudu Ummu tayi bayan aunty Nuriyya da suka tafi kasuwa tare tana faɗin "Mama ki gaya mata wallahi ba haka bane, aunty dakata kiji in gaya miki gaskiya." Dakatawar Mama tayi tace "Ina jin ki to munafuka." Ba tare da ta fito daga bayan Mardiyya ba tace "Aunty, bari ya fito ki tambaye shi kiji, Billahil'azim ban taɓa saka shi da kaina ba, kinsan ai shi mai koyi da Annabi ne." Hararan ta Maman tayi amma ba dan ta yarda da abinda ta faɗa ba, haka suka shiga ciki suka zauna Jabir kuma ya fita. Wannan zuwan ne da sukayi Ummu ke jin labarin wai Alhaji Abbas dai ƙanin margayi Alhaji ya tura su nemo masa auren Mama uwar marayu, wani irin farin ciki ne ya lulluɓe ta har da hawaye da kuma zumiɗin son jin amsar da Maman ta bayar, sun faɗa mata ta ce za ta yi nazari tunda gaskiya har da matar shi ma ta amince kuma tare suka je, wannan kam halayen ta ne na gari ke bibiyar ta. *BAYAN WANI LOKACI* Tun bayan barin ta gidan yau ne na farko d ta shigo shi, shima ba dan dalilin rasuwar Hajia babba ba da bata zo ba, tare da Kuwailat suka zo wacce yanzu ta zama ƴar gidan tun bayan haihuwar *Abubakar Siddiƙ*, Kuwailat ke goye da shi suka shiga duka ɓangaren matan ta musu gaisuwa, Hajia Atika da har yanzu bata daina ƙiyayya da Ummu ba kuma ita kan ta bata san dalili ko mafarin ƙiyayyar ba, ƙwarai ta ƙara jin hasada duba da yadda Ummu ta koma, tana baƙin cikin ta auri mijin su, da ta fara zawarci ta ɗauka zata samu wani dattijon nan, amma sai ta samu yaron da a yanzu ita ce zata tsufa ta barshi idan bata kula da kan ta ba, gashi alamu sun nuna hankalin ta kwance yake saboda wata ƙiba da tayi mai tsari da kyau, ga hasken ta da ya ƙara bayyana har wani yelow yelow tayi, ko da yake ai tana ji ga Zeinab irin ci gaban da take samu da dukiyar da ta mallaka yanzu, dan haka kawai ta yarda Ummu ta tsere mata nesa ba kusa ba. Saddiƙ kan shi da ta gani bayan Kuwailat ta sauke shi saida ta ƙura masa idanu, ba ta san ma cikin kyawawan iyayen nashi da wa yayi kama ba, Jabir ne? Ko kuma Ummun ce? Abinda zata iya cewa a taƙaice kawai shine ɗan kyakyawa ne gashi cikin ƙoshin lafiyar shi. Anan Ummu suka samu Mama ita ma bata jima da zuwa ba, dama kuma tun bayan auren ta da Alhaji Abbas bai ɗaukta daga nan garin ba saboda ya ga nan ta saba nan take da ahali, dan haka shine ke zuwa duk lokaci bayan lokaci, yanzu haka Mama rayuwa take cikin ƴanci da farin ciki saboda tana ƙarƙashin inuwar aure, sannan tana tsananin farin ciki da godewa ubangiji kan ni'imomin da ya mata a rayuwa da ba zataiya misalta su ba, dan yanzu haka Mama cike ne da ita na wasu ƙananan watanni, wanda har Allah Allah take ayi bikin su Kuwailat da aka saka rana kafin cikin ta ya fito fili. *Abubuwa* ne suka tari suka ma Ummu da Jabir yawa na wannan hidima, dan aure uku Alhaji Kabir ya haɗa zai yi, na farko shine na Aliyu da amaryar sa *Ni'imatullah* wacce ɗalibar sa ce, sai kuma auren Khamis da amaryar sa shima wacce ƴa ce ga ɗan uwan Hajia Radiya, lokacin bikin Fahad da suka kai amarya suka haɗu har soyayyar su ta ƙullu wato *Zinnira*, sai kuma auren Kuwailat da angon ta balarabe *Mansur* wanda sai bayan komawar shi yake sanar da Aliyi shi fa yana son ƴar maaman Jabir. Jabir ya zama uba ne ga amarya Kuwailat, dan duk wani abu da zai haɗa Ummu da Alhaji Kabir magana kan wannan hidima, shi suke sakawa a tsakani saboda Ummu ta ƙi yarda suyi magana, ba dan bata so ba ko dan tana riƙe da shi, kawai dai bat son doguwar mu'amula na haɗa su, gaisawa sukan yi idan sun haɗu, amma bayan haka ba komai, to ita ma, kasancewar ta na uwar amarya wannan hidimar ce ta sako ta gaba, sai kuma Jabir dake ƙoƙarin ramawa kura aniyar ta, wato irin hidima da faɗi tashin da Aliyu yayi lokacin nashi auren, ga kuma Mansur da ya masa tattaki ya zo har ƙasar nan saboda ɗaura auren shi kawai, haka kuma ga Khamis da shi ma ba baya ba wajen bada tashi gudummuwar, dan haka da kwanakin sukaa ƙarota ya zama kamar mahaukaci, ba dan Maaman shi dake saita shi a hanya ba, musamman cikin sa da bata wasa da shi, dan tasan da ya fara jin yunwa zai ruɗu ne ya fara masifa da mutane har ma da angayen. Anyi biki lafiya amare sun tare ɗakin mazajen su, inda amarya Kuwailat kuma tare wajen Maman ta sai bayan sati ɗaya zasu tafi, Alhamdulillah dai an gama hidimar lafiya kuma kowa hankalin sa ya kwanta. *Washe Gari 07:18* *Cikin* wata nutsatsiyar shigar jallabiya da ihramin ta ya fito yana ɗaura agogon hannun shi, Ummu na ganin shi tayi saurin miƙawa Kuwailat kofin haɗe sassaken ɓaure da ta tsiyaya mata tare da miƙewa, karɓa Kuwailat tayi ita ma ta miƙe ɗin tana rusunawa da kallon Jabir tace " *Yaya* fita zakayi?" A nutse Jabir shima dake kallon ta yace "Fita zanyi *autar Abba*, malam ya tafi jinyar mahaifin shi a Maroc, ni zan fara gabatar da karatu yau." Da wani sahihin murmushi mai kama da na maman ta Ummu tace "Kai, amma Yaya naji daɗi sosai, Allah ya bada sa'a." Da jin daɗi ya amsa mata da "Ameen." Har ta wuce sai kuma yace "Ya, kunyi waya da mijin naki?" Da kunya Kuwailat ta amsa da "Yaya ai kiran shi ke tashina a bacci da asuba." Da sauri ta shige cikin ɗakin ta, a nutse Jabir ya maida duban shi kan Saddiƙ dake bacci kan kujera, sai kuma ya kalli Ummu dake bin shi da wani kallo kamar n tuhuma, da alamar tambaya da idanu ya mata alamar" Ya ya?" Da jikin ta ita ma ta mishi alamar" Ba komai." Sai kuma ta taɓe baki ta sauke ajiyar zuciya, kama hannun nashi tayi ta ƙarasa maƙala mishi agogon, sannan ta fuskance shi sosai tana ƙara gyara masa hiramin kan shi tana faɗin" Abun mamaki baya ƙarewa duniya." Da idanu ya tsare ta yana aika mata da tambaya, tana cikin gyara masa ta dubi idanun shi tace" To, da fari aurena da kai ne abinda ya fi bani mamaki, sai kwatsam kuma abokin ka ya aure min ƴata, hakan ya sa na rasa kallon da zan ma Kuwailat, shin zan ce mata *matar abokin mijina*? Ko kuma *ƙanwar mijina*? Na rasa." Hannayen shi ya sa ya zagaya ta bayan ta ya riƙo ƙugun ta, hakan yasa duka hannayen shi ke kan tilin jigidar ta, cikin kafeta da idanu yace" Ke kuma da ba kya son hutar da kan ki, kin fi so kullum kina ba wa sheɗan dama yana zuwa miki da shubuha kala kala." Murmushi tayi har haƙoran makkar ta suka fito fili tana ƙara saka yatsan ta tana kwantar masa da doguwar girar sa tana faɗin" Yau zaka fara bayar da karatu, ina so ka nutsu sosai *alarammana*, dan ka dace da faɗar ubangijinmu." Jinjina kai yayi cike da jin daɗi ya amsa da" In sha Allah, nagode sosai." Sumbatar kumatun ta yayi ita ma haka sannan ya nufi wajen Saddiƙ ya sumbace shi, kallon ta yayi bayan ya ɗago yace" Sai na dawo." Har zai fita tayi saurin riƙo hannun shi ya dakata, juyowa yayi yana kallon ta, turo baki tayi cikin shagwaɓa tace" Dan Allah, dan Allah *my man* ka da ka haɗani da kowace mace a duniya, dan Allah?" Gyara tsayuwar shi yayi yana ƙarewa idanun ta kallo da suka kawo ruwa taf, tallabo fuskar ta yayi cike da tausayawa da jin sabuwar ƙaunar ta dan ko sunan da ta kira shi da shi bata taɓa ba, tana dai cewa man, amma yau na farko da ta kira shi da *nata*, cikin nutsuwa yace " Haba mana *mai ɗakina*, ni fa dake kawai nake son ci gaba da rayuwata, har yanzu ban ji akwai wani gurbi dake buƙatar kawo wata sabuwar hallita dan cike shi ba, kin gama min komai a rayuwata Kulsum, kin zama uwar ƴaƴana biyu, Kuwailat da Assadiƙ da masi zuwa nan gaba, kin zama tasirina sannan cikar kamalata, ni kam me zai aike ni da haɗaki da wata?" Sai kuma ya girgiza kai tare da sumbatar bakin ta yace" Kin manta da ke ɗin Maamana ce? Ta ya zan iya haɗaki da wata kuyi tarayya? Ai ko a aljanna ke ce shugbar su, kamar yadda anan gidan duniya bayan mahaifina ke nake burin kyautatawa dan na samu shiga aljanna..." Sai kuma ya rumgume ta tsam a jikin shi yana lumshe idanu yace" *Ina son ki Kuwailat*." A zabure Ummu ta ɗago tana zaro idanu tace" Kuwailat kuma? Ƴar tawa?" Waina idanu yayi sannan ya ɗan harareta yace" Ke Maama wai me kika ɗauke ni, wallahi zan aje hiramin nan muyi baram baram kafin na bar gidan nan, ina ce ke aka fara sakawa Kuwailat ɗin ko?" Wulwula idanu tayi ta sauke ajiyar zuciya tace" Oho! Yanzu na ji batu, to Allah baka haƙuri, kuma ai ba zan gaji da faɗa maka kana min rashin kunya ba." Jinjina kai yayi ya juya zai fita yana faɗin" Sa'ad, Fahad, Aliyu, Mansur, ke har da wannan ma ƙaramin ɗan sheɗanin da bayan sheɗan ya saki nono ya kama (Jibril) duk sun rasa yadda zasuyi da ni, bare ke maama da awa biyu kawai ke ladabtar dake." Dariya Ummu keyi ita dai ba ta ce komai ba saida ya kai ƙofar ɗaki tace" *Jabiru*." Juyowa yayi da mamaki yace" E, lallai dai ta tabbata da sheɗanu a gidan nan, ko kuma dai na uncle Fahad ne suka dawo kan ki." Kanne masa ido ɗaya tayi tare da faɗin" *Ina alfahari da kai*." Murmushin jin daɗi yayi tare da aiko mata da sumbata yace" Ni ma haka, ina son ki." Da fara'a tace" *Ni ma h...*." Sai kuma ta juya da sauri ta nufi ɗakin ta tana faɗin" Ni Allah ban yarda ba, haka kawai Jabir ka asirce ni a gidan na, gaba ɗaya fa kai kake sarrafa tunanina." Tana daf da shigewa Jabir yace" Aunty." Dakatawa tayi ta juya tana kallon shi, shima kanne mata ido ɗaya yayi cikin raɗa yace" Ki saka wannan kayan baccin farare sannan ki kashe wuta, yau wasan ɓuya zamuyi, kuma idan ba tsoro ba karki cire jigidar nan." Ɗan hararen shi tayi tace" Oho! Dan ka gano ni ko?" Murmushi ya mata alamar haka ɗin ne fa, dan haka ita ma cikin raɗa ko dan Kuwailat dake ɗakinta tace" Karka damu, yau sai dai bayan komai ya kamala ka roƙa mana gafara, amma dole zan ma gafarta rawar jigida." Wani irin yanayi ya ma fuskar shi tare da ɗan cije gefen leɓen shi alamar" Ta saurara masa mana, fita fa zaiyi." Ita ma da idanun ta da kuma bakin ta ta shiga yi masa alamar" To ka tafi mana." Sannan ta ɗaga masa giraren ta biyu ta kanne masa idanu, sai kuma ta zura hannun ta ta baya tanayi kamar zata zare zif ɗin rigar ta, hakan yasa Jabir zaro idanu yana matse baki da nuna mata" A'a fa." Saida ta zare zif ɗin sannan ta ɗan juya bayan ta dafe ƙofar ɗakin ta da hannu ɗaya, ɗayan kuma ta dafe bango, hakan yasa ta juya masa baya gaba ɗaya ya zama yana ganin santalelen bayan ta da ko bras babu sai tarin jigidar ta da ya hanga, yana kallo ta ɗan fara yin sama da ƙasa da ƙugun ta tana kuma yin gefe da gefe da shi tare da juyowa tana kallon shi... A rikice Jabir ya yo kan ta da niyyar damƙota amma sai ta juyo gaba ɗayan ta cike da salon mugun ta ta dinga wani irin motsi jigidar na bayar da sautin dake ƙara ɗaga masa hankali, yana daf da kawowa kusan ta ya shuge ɗakin da gudu ta rufo ta sa makulli. Jingina kanshi yayi a ƙofar a tausashe yace "Maama, dan Allah mana, ɗanki ne fa." Ummu na ta ƙyalƙyala dariya yace "Um um! Ka je kayi karatun ka, ai zaka same ni gidan." A tausashe sosai kamar wani mai shirin yin kuka yace "Um um maama, ban da nutsuwar karatu yanzun, zan kira Aliyu ya karɓa min, ko naje ba zan iya komai ba." Cikin fashewa da dariya tace "Alaramma ba ruwana, wallahi ba na zama silar fasa karatu ba." Murmushi yayi yace "To naji, zan tafi, amma dan Allah ki tarbe ni da kyau." Cikin ɗaga murya tace "A dawo lafiya, Allah bada sa'a, *ina ƙaunar ka ƙanena*." Dariya kawai yayi ya fice daga gidan yana mai cike da kewar Maaman shi da yi mata fatan alkairi, haka kuma yana gyara yanayin shi ko dan kar su haɗe da Aliyu ya sha jarabar tsiya, duk da dai yasan jiya shima aka ɗaura nashi auren wataƙila ya shiga tasu duniyar, amma Aliyun shi da ya sani da surutu wanda zai iya cewa shine Aliyu na farko da ya sani haka, sai ya masa tsiya inda ya gano shi. *MA SHA ALLAH, ALLAH NA GODE MAKA DA KA NUNA MIN ƘARSHEN WANNAN LITTAFI NA RUBUTACCIYA, KOMAI YAYI FARKO DAMA YAKA DA ƘARSHE, ALLAH NAGODE MAKA DA KA ARA MIN RAI DA LAFIYA HAR MUKA KAMMALA SHI, INA NEMAN AFUWAR KA AKAN KURAKUREN DA NAYI DA KUMA SUƁUL DA BAKA KAN WASU ABUBUWA, ALLAH KA GAFARTA MANA BAKI ƊAYANMU, ALLAH YAA SA A MIZANINMU.* _MASOYANA NA NESA DA NA KUSA, WANDA SUKA BANI HAƊIN KAI HAR MUKA KAMMALA WANNNAN RUBUTU, INA GODIYA A GARE KU, ALLAH YA BAR ƘAUNA DA ZAMAN TARE, HAƘIƘA KUN SAKA NI FARIN CIKI DA ZAFAFEN COMMENT ƊIN KU, NAGODE MUKU SOSAI DA ƘAUNAR DA KUKA NUNA MIN, WANDA MA SUKE GRP ƊIN AMMA BASU SAN TSIYAR DA MUKAYI BA, KU SANI INA GANIN KU KUMA KUN KYAUTA, SANNAN NAGODE DA CIKA MIN GIDA DA KUKAYI, MASOYANA NA ASALI KUMA INA SAKE GODE MUKU, INA ƘAUNARKU FISABILILLAH._ 😍 *HMMMMMM! WATAƘILA KU JI NI A KUSA KO A NESA, BA DAI ZANCE KOMAI BA GASKIYA, AMMA KU SANI IDAN KUKA NA TASO ZAKU JI NI DA WANI GIGITACCEN SALON DA ZAI HAUKATA TUNANIN KU, SAI DAI GASKIYA BA'A FREE BA🚶‍♀️😕, YASIN FREE NOVEL YAFI DAƊI SABODA WASU ABUBUWA, AMMA KUMA PAID MUTUM ZAI SHA MADARA YA CI KAZIII.*😎 _CYAMATU, YAGANA MUSSA, LUBABATUSHEHU,HAJIA ZUWAIRIYYA, UMMU HUSNA, HALIMA AHMAD, JAMILA YUSHA'U, MAMAN ABULKHAIR, ALEESA, MURJANATU UMAR, HALIMA SHEHU, MAMAN ABNA, MA NIÈCE UMMU (MOM ABBA BAZOUM), NUR, AISHATU ISMA'IL, AMINATU ABBA. Dama sauran da baa zan iya lissafaku ba duk ina gode muku abisa ƙwarin guiwarda sharhinku yake bani, da fatan idan na taso a sabuwar tafiya zaku yi haƙurin bibiyata sannu sannu._ *KWATE, KI TSARO MANA LABARI MU DIRAR MASA MU BIYU.*😉 *Alhamdulillah.*