Copied By YAYA HAYAT (admin Hayat hausa novels Group Hausa novels and fashion Group Cool novel, makeup and kitchen1 Group And WOMEN24 TV Group WHATSAPP NO:+2349030159301 [4/23, 3:59 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *F.A.S* _Shafi na 1_ { Yawan comments yawan posting ,shirun ku shize sa Nima nayi shiru d typing ,luv u oll mah fanc}😍💋😍 "Wayoo" ma'u bakya Gani ne? Shashashar banza da hofi kawai. Ayya! Mama habee ban lura bane Dan ALLAH kiyi hak'uri wlh bansan kin taho bane, wacce take bada hak'urin Tana sadda kanta k'asa. Wanan Ai Duk Yana daga cikin Aikin Rashin Nutsuwar Taki ,sbd kina Sauri Sauri Zaki Gidan D aka yankema gyatumarki cibi ko? Uwar Naci d Kwad'ayin Abin Duniya ? ALLAH ma yasa Iyakarki Boyi a cikin Gidan wahalaliya kawai Haka Zaki K'are Rayuwar Irin Ta Gyatuma ai ,Aje Ayi Abin Da aka Saba Wahala Kan Wahala ba, wacce Aka Kira d mama habee taja Uwar Tsaki Ta shiga wani Tsohon kitchen d'in da k'iris Yake Jira Y Ruso kowa ya Huta Tana zabgama *Asma'u* uwar Harara cike da Tsana. Ita ko ,Da tagama bada hak'urin Ficewa Tayi daga Gidan Ranta Duk Babu dad'i sakamakon cin Zarafin Da akama mahaifiyar Ta da ita ,duk da dai inda sabo tasaba d halin mama habee, yaranta ne kawai mutane na kowa ba mutane bane . *Asma'u* cikin Nutsuwa take Tafiya har Ta Isa Bayan layin Su da niyar Shiga Wani Katafaren Gida Mai Girma Da kayan Alatu Na more Rayuwa Iri Iri ,Wanda yasa Tun Asma'u Na k'auyanci Har Ta Fara Sabawa d Ganin Abubuwan more Rayuwar Da wayewa Irin Ta 'yan Gidan ,sbd yau d Gobe Da take Shiga Gidan Taya mumcy (hajiya babba) Aiki . Yauma Kamar Kulin wajen Motar Da kulin itace mahangar da take Fara dubawa kafin shigarta Gidan ,indai motar na Nan to lallai A d'ad'are Zata shiga Wajen Mumcy tare Da firgici Da tsoron Da ta Rasa Dalilin Shi Tun zuwanta Gidan Kuma Ta Rasa Sani Ko Tantance Mamalakin Wanan Motar ,Dan Har yau Basu Taba Had'uwa Ba Da Mamalakin Motar Dan Bata fi Sati 4 kacal Da Fara zuwa Taya mumcy Aikin ba . Kamar Kulin Kirjinta Na bugawa Ta nufi Sashin mumcyn Cikin Ladabi Da Nutsuwa bakinta D'auke Da sallama Mai Gamsar Da zuciyar Duk Wanda Ya saurara . Tana Shiga ta Sami Hajiya babba a zaune Akan hamshak'iyar Kujerar ta Mai kyau Da tsada ,ta Durk'usa Har K'asa Ta Gaishe ta , hajiya babba ta Amsa kamar Yadda ta Saba fuskarta D'auke da Fara'a . Bayan sun Gama gaisawa ,hajiya baba ta umarci Asma'u da ta Fara gyara Mata room D'inta kamar yadda ta Saba ,ta gyara bed ,tayi shara , morphine kamar yadda ta Saba , toilet ma ta k'alk'ale Mata shi tafeshi shi da Air freshner Bayan ta kunna burner tasa turaren wuta kamshin sai yafi bada ma'ana Dan Har ta windows yake fita ,ta dawo d'akin ma ta turare da kamshin turaren wutan sanan ta k'ara sa room fresh komai dai yayi acan_ acan gwanin birgewa ga duk Wanda ya kalli gyaran . Tana Shirin Fitowa daga D'akin Hajiya babba tajiyo wata murya suna musayar kalamai da hajiya babba cikin d'a'a da girmamawa ,Amman inta gareta muryar bugawar zuciya tasa ta ciki, tsabar tsoro da shayin Mamalakin muryar batare da ta tab'ayin tozali da Mamalakin Mai muryar ba . Haka tayi shahada ta fito kawai ,Tazo Ta Rusuna kusa da hajiya babba" tace na gama hajiya saura parlour" kafin Kowa yayi mgn , *FU'AD* ne ya Fara yima Asma'u Kalon Tuhuma da wasu mayun idanun sa masu rikita Wanda ake Tuhuma ko Alkali iyakacin firgicin da zaka shiga. Kafin mumcy tace komai ,yace "ke Kuma Fa Daga Ina Haka? Waya kiraki? _Dirty Girl_ Har da wuce parlour zuwa Da'ki ? Ko badaga Nan Naga ta fito ba mumcy? Itako zuciyarta ce ta Shiga tsuma ga tsoro duk ya mamayata , shi kanshi ya gano hakan. Hajiya babba ce tace "Son Zaka Fara ko? Toh! Duk inada amsoshin tmby ka . "NO" mumcy ki Bari ta Amsa min da kanta ko kurmace ? Mumcy "tace indai Kai kurmane itama kurmace " Tana Mai wani kalon gargad'i na Bata son raini . Yace "mumcy y kike had'ani da dirty girl ne Haka ? Mumcy tace,duk ba wanan ba ka tashi kaje ka Gama Shirin wucewa office zata gyara parlour ,Kuma dai wanan ba wata bace face Asma'u itace ta maye gurbin Hafeeza Mai min gyare gyare kasan tayi doguwar tafiya don Karo ilimi ,to shine ta kawo min ita Kuma nasha ganin su tare Inna fita unguwa ko idan Ina dawowa su Kuma suna dawowa daga islamiya ko idan zasu ,Abinda yasa na karbeta na yaba d hankali da tarbiyarta da Kuma tsaftar ta da Kuma duba da Rashin Karfin Su .Ina fatan ka fahimta ,banason wasu tmby daga Haka Kuma . *FU'AD* nada Abin cewa Amman Dole y Hak'ura Dan Yasan mumcy Babu Wasa inta furta mgn Tasha mur akai ,Amman duk d Haka sai d yace nidai Banga abubuwan d Kika lisafo ta dasu ba ,uwa uba tsafta Ina tsaftar anan ,nidai please mumcy ko cup d'in da Zan kurb'i juice Kar tsautsayi yasa ta tab'a ,badan niba mumcy ,indai har ta kiyaye dokokina Babu Ruwana d k'urar ta ,tunda kinji kingani keda ita kawai nidai Babu Ni Acikin duk wani Abun d zatayi ,zuwa madafa ( kitchen) ma Dan ALLAH karki barta ta Dinga shiga kibar wayayun can Su dinga Shiga kamar yadda suka Saba . Mumcy tace "to naji na iya wanan karatun mallam sai wanne Kuma? FU'AD ya Sosa Keya ya saki Wani kasalalen murmushi Mai sigar rarashi ga mumcyn sa yace tuba ne mumcy na ban furta hakan dan tab'a zuciyar uwa tagari ba ,inda sabo ta Saba d halin FU'AD na rashin son bak'anta ran kowa arayuwar shi ,Dan Haka tayi murmushi tace naji yaron kirki ALLAH yayi Albarka in Ka Gama sai ka sakko ka karya kafin Tafiya office ko? FU'AD yace "To mumcy barinje na sauko" komai ya kammalu ko? Mumcy "tace eh Mana Son" D sassarfa ya Fara haurawa matatakalar benen ,y juyo y wurgama Asma'u hararar gargad'i kafin y k'arasa Hawa. Ita ko Yana barin wajen ta samu damar Fara Aikin ta ,Babu wani dirty a parlour ,Amman Haka ta k'ara k'alk'ale shi ta feshe d Air freshner ta gogoge kayan Kallo ,ta koma dining area Dan gyarawa lokacin da yayi dadai d ta d'auki plate da spoon akai don goge wajen ,shine yayi daidai d sakowar FU'AD ya ganta Kuma ,atake yaji tsanar Plate d'in Da ta tab'a d Kuma ita kanta wacce ko sunan ta be Rik'e bama . Itako tsakaninta d ALLAH take gudanar d komai ,ko da ya gama sakowa har y nufi wajen karyawan y kalleta ya wani wurga Mata uwar harara yaji Yama tsani komai nawajen Dan Haka ya buga tsaki ya nufi room d'in momcy da niyar yi Mata sallama. Ita ko Asma'u tsintan kanta tayi da Jin zafin tsakin da ya Mata Dan ta tasani tsaki gara ka daketa daka Mata tsaki ma ,Nan ta dinga karatun zuci Akan FU'AD Tana hak'aito zamanta a gidan yazo k'arshe Dan bazasu shirya d FU'AD ba me cin zarafinta Haka d son wulakanta ta ,ai arzikin duniya bana lahira bane Kuma ma ita aikin Nan Hafeeza ce tabata Rik'on kwarya. _yanzu aka soma_ *Comments dinku shine ze bani damar typing insha ALLAH* [4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *F.A.S* _Shafi na 2_ {Comments dinku yamin kadan Gaskiya akara himma don naji karfin yin typing d post nima} *FU'AD* Bayan ya ma mumcy sallama da niyar wucewa office ,sai d ta tamby shi yayi Break ? "Kai tsaye ya Bata amsa da eh ,Godiya yake ,Al'adar sace Godiya aduk lokacin da mahaifiyar sa tamai Wani Abu ,Dan Haka batayi zargin komai ba tamai Addu'a dawowa lpy kamar yadda ta Saba ,ya amsa da Ameen uwa tagari ,yafice zuwa wajen Motar sa hanun shi Rik'e da makulin motar yanata zuba kamshi cike da kwarjini da kamala. Koda ya fito parlour ze wuce suka had'a Ido da Asma'u sai d ya wurga Mata uwar harara Mai cike da Tsana sanan yafice . Itako cewa tayi abanza man kare tunda banji duka ba ,in gidankune zanbar muku abinku Nan kusa d na Sami aron waya na Kira Hafeeza mukayi shawara. Koda hajia babba ta fito ta samu Asma'u nata Aikinta na gyara, tace in ta kammala ta kwashe kayan da FU'AD Yayi break takai kitchen awanke inkuma Mai wanke wanke ta gama to ita ta wanke Wanda yayi Amfani dasu . Da kamar baza tace beci ba sai taga to me zata wanke ? Ai ya zama Dole ta sanar Mata beci komai ba D'an Rainin wayon . Asma'u tace "hajia be tab'a komai ba yadda aka ajiye Haka kayan suke har yanzu Naga Kuma kamar ya fita da Shirin barin gidan ma . Mumcy tace son din be karya ba ya fita ? Asma'u tace "eh hajia kin gani ? Tana nuna Mata plate din da ko digon Abu ba'asa Masa ba . Don ta gaskata har Tasowa tayi ta bud'e taga komai Yana Nan kamar yadda aka ajiye shi a wajen ,tayi ajiyar zuciya ta koma ta zauna ,Bata kirashi a lokacin ba Dan ranta yad'an bacci Kar yasha ruwan fad'a shiyisa ta Bari tad'an huce tukunna . Sai Bayan ta huce ta d'auki waya ta kirashi ,cikin girmamawa ya d'aga . Tace "Son meye hujja ko dalilinka na kin karyawa ka fita ? FU'AD cewa yayi ,mumcy wlh Inna sakowa Naga wanan _Dirty girl_ d'in Tana Wasa da da plate d'in wajen Ni Kuma konaci Abinci bazan samu _peace of mind_ ba kawai na barmata kazantar d tayi,naji nama k'oshi da komai na wajen. Mumcy tace , "Weldon Son ,Bazance maka komai ba kowa Rai Yama Dad'i ai bakamar meshi ba ,ita yunwa ai Bata da hankali ,Amman kasani Akan Asma'u karka Aro wasu d'abi'u ko halaya da bansanka dasu ba ,Bata jira amasar daze Bata ba ta katse wayar . FU'AD bin wayar yayi da kallo ,Yana zargin ko Ran mumcy ya sosune ,Dan Haka atake yasake Kira ,sai d ya Kira so 3 yanajin _busy_ sai da ya sake Kira sanan ta d'aga . Cikin ladabi kamar Yana Gabanta ,yace mumcy ta ALLAH ya hucci zuciyar uwa tagari banyi hakan don tab'a Ranki ba naji kinata Danna min bussy mumcy ta ? Mumcy tace ba busy na dannama ba muna waya da yayanka ne akan maganar dawowan shi . FU'AD yace ok mumcy barin kirashi mu Gama kashe boss d'in Dan tunjiya muka Fara mgn bamu k'arasa ba ya kashe wayar cike da kewar mahaifiyar shi. Bayan Asma'u ta Kamala komai ,ta sanar ma mumcy ko Akwai wani Abu da zata Mata ? Mumcy tace Babu, zaki iya tafiya Koda wani Aikin Da zakiyi agida ,nagode inji mumcy , Asma'u tace nice da godiya hajiyar Girma ,mumcy tayi murmushi tace har canjin suna na samu Kuna son lak'abamin sunaye kala_kala , Asma'u tace Ai kin cancanci hakan ne ,na Tafi sai ALLAH ya kaimu , mumcy tace ALLAH ya nuna Mana goben muna masu lpy Kuma Rayayu , Asma'u ta amsa da Ameen ta wuce gida cike da fargabar Abin da zata tarar na masifar mama habee. Kafin Asma'u ta wuce gida sai da ta biya ta gidan su Hafeeza ta karbi number ta ,ta tafi wajen D'an Bala communication ta karbi waya ta kirashi Hafeeza ,Bata d'auki dogon lokaci ba aka d'aga ,cikin murna Asma'u tace Hafeeza y karatu ya 'yan uwanku nacan? Hafeeza ta Gane me mgn ,tace "lpy kanwata ya gida y hak'uri da Rayuwa? Asma'u tace "muna Kai ,Kar muja kud'i da yawa mgn Zan Miki Akan *RIK'ON KWARYAR* Da Kika bani dama ,wlh na fuskanci Akwai d'an rainin wayo agidan ke Kuma kince min gidan Babu matsala ta ko'ina kin nunamin basa kyamar talaka ,Naga hakan daga wajen hajia babba Amman wani d'anta Sam baze barni zaman gidan ba karkiji na ajiye Miki *RIK'ON KWARYAR* Da Kika bani kice ban kyauta ba ne yasa na Fara sanar Miki . Tunda Asma'u ta Fara mgn sai d takai aya ta tsaya wai gudun Kar aci kud'i da yawa . Hafeeza ce taja ajiyar zuciya sanan tace "k'anwata ki kwantar d hankalin ki yanzu mgn bazatayi ba Naga kina Sauri ki Bari anjima kije gidan mu Zan Kira mama nace inkinzo tamin flashing sai na kiraki muyi mgn kinji ? Asma'u taji dad'i tace to ,ta kashe wayar ta mikama D'an Bala communication wayar akan taji nawa ya cajeta ? Bayan y duba yace ,kudinki 150 ma'u ,ta ciro wata cikurkud'ad'iyar D'ari guda ta bashi tace zata ciko Mai Dan ALLAH ,duba d yanayin ta da zargin ukubar d takesha wajen kishiyar mamanta yasa shi cewa yabar Mata Babu damuwa ,Aiko tayita Mai godiya ta tafi ranta fes bame binta bashi . Tana Shiga gida bakinta d'auke da sallama ,tozali d mahaifinta da tayi yasa bugawar zuciyarta ya ragu Dan Ana Rage wani Abu daga cikin kiyayar da ake nuna Mata agidan in Yana Nan . Tana Shiga tace baba sannu da gida ,mama habee sannu da gida ,baba ne y Fara amsawa sanan mama habee ta amsa Babu yabo Babu falasa ,babane yace kinci Abinci ma'u ta? Kafin ta bashi amsa ,haidar karamin D'an mama habee yace gashican akicin barin d'auko Miki Yaya ma'u dake jinin su ya had'u da shi ,mama habee Babu bakin mgn Haka ta zuba Ido taga Wanda ze d'auko Mata Dan Bata zuba Mata ba Sam ,nata n tunkunya asandare. Aiko na Yar gwal ya d'auko ,humaira ya ajiye gaban ma'u ,takaici y rufe mama habee tayi mgn baba yace Babu banbanci tsakanin ma'u da humaira Dan Haka ta had'iyi bak'in ciki da takaicin haidar . *Muje zuwa Ruwan comments Ruwan typing*💋💋 [4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *F.A.S* _Shafi Na 3_ {Nafi son Ruwan comments ba heart,da stikers ba guys ,duk d Ina godiya d hakan ma} Bayan ma'u ta kammala cin Abincin ta rage taje ta ajiye a kitchen ta wanke hanun ta ,ta wuce tsohon d'akin mahaifiyar ta da ta shud'e . Bayan humaira ta dawo daga gantalin asarar ta ,wuf ta afka kitchen da niyar neman Abinci in Yar Aiki ta, ta gama wato mama habee sbd tsabar tausayi da imani irin na humaira . Ko da ta shiga bataga sakayayen abinci ba kamar yadda aka Saba killace Mata sai ragowar d Ma'u ta Rage sai sandarare na tukunya ,Dan Haka a fusace taje take tmby mama habee Abincin ta? Mama habee dama a sama take yau tace Yana gidan uwarki Dan ubanki gantalaliya Mara aikin fari bare na Baki ,inkinga dama ki duba tukunya in yamiki sanyi Kya d'umama . Humaira ta tab'e Baki tace mama habee y ba'a zubamin an boye min ba Dan ALLAH ? Mama habee tace Mai kafar yawo ,Wanda n Adana miki ya zamo Rabon kanwarki ma'u Dan ita ta cinye .......fuuuuu humaira zata tafi hukunci .......mama ta dawo d ita d cewa to Alkaliya sarkin hukunci kyaji yadda akayi kafin ki d'auki hukuncin ai de ko? K'aninki nee ya d'auko Mata y Bata tacinye ,kinsan haidar d imanin d bansan inda ya gado shiba , kamar kaninta uwa 1 uba 1 D'an bantan uban yaro . Humaira aka furzar d hucin takaici akace "wlh taci sa'a ,shi Kuma ze dawo naji Dani d Ma'u waye ahak'un shi sokon yaro kawai t fice ta tafi cin sandarare dan lalaci baze barta ta d'umama ba . Bayan ma'u ta huta ta share gidan ,baba y shigo tace Mai zata gidan su Hafeeza Kai sak'on da hajiya babba tabata takaima maman su hafeezar ,baba yace sai ta dawo Amman Kar ta Jima ,tace "toh ta fice zuwa gidan mamar Hafeeza Dan yin waya da hafeezar" Tana shiga bakinta d'auke d sallama ,ta tsuguna ta gaishe d mama . Mama ta amsa cikin sakin fuska ,tace "kinzo? Ma'u tayi murmushi tace "eh mama" Mama tama Hafeeza flashing ,ba'a Jima ba Hafeeza ta Kira mama taba Asma'u wayar ta fice ta Basu guri . Hafeeza d Asma'u,anata Hira akan FU'AD Asma'u ta dage barin Aikin zatayi sbd wulak'ancin FU'AD tun ba'aje ko Ina ba ,Hafeeza nata Bata hak'uri Tana nuna Mata Ribar Aikin da Kuma cewa shi Haka yake Amman Kuma yanada kirki duk Wanda ta tmby ze fad'a Mata kyawawan d'abi'u da halayar FU'AD ta gwada tmby wasu ma'aikatan gidan Kuma taji ,sosai Hafeeza ta kwantar Mata d hankali ta Bata hak'uri da dabarun yadda zasu zauna lpy da FU'AD Amman ta koya Mata dabara in yazo Mata a Wuta ita Kuma ta fito Mai a Ruwa Dan ta kashe shi Dan cin zarafi da tozarci bashi da dad'i ba kowane ze iya jurewa ba , Asma'u ta gamsu da shawarwarin Hafeeza ta Mata godiya sukayi sallama ta kashe wayar , Asma'u Tama mama sallama mama tace "ta gaishe da mutanen gidan" Bayan komawar ma'u gida ta samu humaira na cin zalin haidar ,sai take tmby dalili ,Aiko humaira ta dawo kanta d masifa,mama ta Shiga mak'ota tsegumin d ta Saba ,Tana shigowa tajiyo hayaniya ganin Ma'u ake tsigalewa yasa da bazatayi mgn ba sai ta hango haidar autanta Yana rusar kuka shine fa ta magantu ,Ma'u tace haka kawai take cin zalin karamin yaro Dan an tmby dalili shine ta dawo Kan mutum ita d Bata k'unar zaman lpy Sam. Aiko mama tace Dan ubanki me y Miki ? Humaira t turo Baki ai zagina yayi d rashin kunya ,sai baba y shigo shima y samu Ana tmby ba'asin dukan haidar d humaira tayi . Shiko haidar Yana kuka yace k'arya ne wlh wai Dan dazu n d'auko Abincin d aka ajiye Mata naba Yaya ma'u shine take dukana yanzu . Anan mama ta gano dalilin duka ,shima baba Ranshi y b'aci ya Fara yi ma humaira fad'a Yana nuna Mata d ita d Ma'u duk 1 suke a wajen shi kuma karta sake dukan Mai autan shi ,mama ma taji haushin dukan haidar d'in ta dinga zazagama humaira Ruwan fad'a har sai d tayi nadamar hukuncin d tayi . *********** Washe Gari ma'u tayi wanke wanke ta share gidan Bata tsaya jiran dumamen tuwon mama habee ba ta yima baba sallama Kan zata tafi gidan Aikinta ,ya Mata nasiha kamar kulin to ma'uta ki kula da kanki na Baki amanar kanki da kanki ALLAH ya Shiga cikin Al'amarinki ako Ina kike . Asma'u tace Ameen baba , insha ALLAH sanan ta fice Tana cema mama habee Sai na dawo mama ,ko ci kanki batace ba sai tabe Baki da tayi inda sabo ta Saba gwanda a tab'e Mata Baki ma d ace Mata wani Abu Dan cin mutunci d zagin mahaifiyar tane ze biyo baya . Yauma kamar kulin d ta Shiga harabar Gidan motar Nan me sata fad'uwar gaba tafara tozali da ita ,ta wuce tayi sallama a part d'in hajiya babba cikin ladabi da biyaya Babu kowa a parlour sai FU'AD da yake tsaye Alamar wani Abu yake jira . Da ya juyo d niyar Amsa sallamar Dan yaji sautin muryar har kwanyar shi y juyo d niyar ganin balarabiyar da tayi sallama kawai yayi tozali da wacce yafi Tsana a yanzu cikin Rayuwar gidan mumcyn shi ,kawai yayi tsaki batare da ya amsa sallamar ba ,har sai d ta Kara Bayan tasan yajita kawai baze amsa Mata bane ,sai ga Hari Mai Aikin su ta fito dg kitchen sai yace yauwa Hari Zo ki amsa sallama anayi ,ta taho d niyar bin umarnin uban gidan nata ,Abin Yama ma'u ciwo . Hari d sakin fuskarta tace , waalaiki sallam Asma'u kamar yadda sukaji mumcy na fad'a ,Aiko ma'u tace Ita dai sallama ta kowa d kowa ce kuma Lada mutum yake samu inya amsa ta . FU'AD ya juyo afusace yace " ke dawa kike"? Mema Kika ce? Sai ga mumcyn ta fito Tana ma FU'AD mgn . Ma'u ganin yadda y taho azafafe Kar Taci bugu sai tace mekaji nace ? Yalabai? Ganin mumcy ta fito sai ta juya itama tace gaishe kafa nake tayi yafi so 5 kak'i amsawa . Ya D'an zaro Ido yace kaji _dirty girl_ da lauya mgn ,Aiko mumcy tace haba Son ya mutum zeta Gaisheka har so biyar kak'i amsawa Kuma ka dinga huci ? FU'AD zeyi mgn mumcy ta dakatar dashi d cewa nasan halin d ka Aro Wanda yake ba naka ba Akan Asma'u karkace min komai ,Amman banason Haka amsa gaisuwa kawai ? Banaso kaji na fad'a ma . Ran ma'u yayi fes ,shiko FU'AD y k'ara d'ura 'yar tsama d Ma'u musamman yace sai y hukunta ta Akan Abin d tamai yau d'inan har mumcy tamai fad'a agabanta . Dan Haka Bayan y karbi takardun d mumcy ta d'auko Mai y haura sama a fusace , Mumcy ta fahimci hakan Amman ta share shi Dan batason cin zarafi d wulak'anta D'an Adam Mai kima da daraja ,shima Kuma tasan ba halin shi bane . Asama'u har k'asa ta tsuguna ta gaishe da hajiya ta amsa cikin sakin fuska , ta Bata umarnin Fara gabatar d Abin d y kawo ta ,Bayan masu Aiki sun Gama jere komai na break suka sanar ma d mumcy . Mumcy ta d'au waya ta Kira FU'AD Dan yazo y karya ,yace Mata ze karya a sama tace Bata Amince ba minti 2 ta bashi y ajiye duk abinda yakeyi inajiran ka, ta kashe wayar ,tasan sai ta Mai da gaske tunda yayi fushi . Ma'u ta Kamala d D'akin mumcy har ta share parlour tayi morphine Tana goge gogen kayan alatun parlour ya sako ya nufi dining shida mumcy ya taimaka ma mumcy Amman fuskar ba asake ba kamar yadda suka Saba break shi yake hada Mata su tea tsabar biyaya ya zuba Mata komai indai tare zasuyi break ,yauma yayi komai kamar yadda y saba Amman Babu Hira bare sakin fuska .mumcyn ma ta share shi. Ma'u nata Aikin ta kawai ,ta matso kusa dasu Tana Shirin d'aukan bunner Dan ta kunna tasa turaren wuta Aiko y daka mata tsawar d seda ta saki bunner Dan firgici ,wai zata zubo musu k'ura acikin Abinci . Ganin yadda y firgitata , mumcy tace Mai "haba Son " meye haka? FU'AD yace "mumcy bakiga Aikin K'ura takeyi ba tazo zata zuba Mana 7million deaseas acikin Abincin mu? Yana wani b'ata Rai bilhaki da gaskiyar shi . Mumcy tace ina kaga k'urar? Ita Kuma d ka firgitata har Nima ka tsoratani shi Kuma ya zakayi da hakin? To kayi gagawar neman yafiyar mu Dan babu kyau tsoratar da musulmi ka karanta Kuma ka sani . Ita Dai ma'u d'aukan bunner tayi ta Kuna Tana mamakin halayar FU'AD d kowa yake yabon shi Amman ita tsakanin su Sai kyama da kyara d tsangwama ,amman y kamata ta Fara nemanma kanta 'yanci ko hakan na nufin barinta gidan d Aiki ,lnba Haka ba Rana zafi inuwa k'una Abin ze zamar Mata ,gidan su zafi gidan hajiya baba k'una . Bayan ta gama komai aparlour tazo tacema mumcy ta gama ,me za'a Mata yanzu ? Mumcy tace Babu sai dai t tmby masu Aiki a kitchen in basuyi wanke wanke ba ta musu ,Jin zata tab'a kwanukan gidan har d Wanda yake cin Abinci kawai sai ya Fara tunanin Aikin da ze sata me wuya Wanda ze bak'anta ranta . Can ya tuno yace mumcy d taje ta tab'a Mana dishes taje ta gyaramin sama Kuma gyara me kyau harda wankin toilet zefi . Mumcy tace ,to kinji Asma'u ? Zaki iya? FU'AD ya juyo Yana hararar Asma'u yace haba meye bazata iya ba mumcy ki Bata umarni kawai , Aiko Asma'u tace zan iya hajiya ,mumcy tace toh Asma'u jeki gyara Mai . Asma'u ta haura badan taso Ba sai Dan ta faranta ran mumcy ta nuna Mai Aiki ba mutuwa bane. {Sharhin ku na karamin himma} [4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *F.A.S* _Shafi na 4_ *Nima Ina mugun yinku MASOYANA* 😍😍😍😍😍 Bayan Asma'u ta haura sai da ta gama Shan kallon ta a had'ad'en parlour d ko na macce Mai 'yanci da gata sai Haka ,sosai Asma'u ta kusa zautuwa d alatun dake dankare a parlour . Cikin kwarewa da himma d sauri sauri Dan ta kammala tabar mai parlour shi take gudanar da komai ,ta gyara ko ina har takardu d laptop din d ya baza seda ta gyare Mai komai yayi tsaf ,ta Shiga toilet ta k'alk'ale shi ta feshe d room fresh ta kulo shi ta dawo parlour taci gaba da gyara . Shiko Yana can yanason haurawa kodan ya takurata Kuma yanajin tsanarta Dan Haka yaketa tufka da warwara . Itako gyara take tsakanin ta da ALLAH Tana had'awa da sauri Kar yazo ya sameta . Tunawa da yayi wayar shi na sama Kuma zeyi waya da Yaya shurem sai ya tashi y haura Dan d'auko wayar ,kafin ya Shiga sai da kirjin shi yayi wani irin bugun da shi kanshi besan dalili ba ya Shiga parlour ko sallama Babu Dan yaga kazantar da take Mai ,Yana Shiga ya ganta tanata aikinta bil_hak'i da gaskiya ,ya wuceta y d'auki wayar shi Yana cewa Kar fa amai kazanta . Taji haushin kalamin shi ,itama sai ta Rama da cewa Adinga sallama dai shine banbancin mu dasu.......a fusace yace me kikace ? Me kike nufi ? Ganin n Babu idon mumcy tayi k'asa da murya tace Babu abinda nace fa . Yace kina nufin bakice komai ba? Tace "Ni Babu abin da nace ,illah toh .....ya katseta da cewa ki Gama gyara ko Ina ki fita min dg parlour Mara kunya _dirty girl like u_ har Zaki dinga mayar min da martani kinyi 2 kina na 3 zamu gauraya dake ,ya faki idon ta y zubar da kud'i 'yan 100 agefen gado da Kujerar shi wai Dan ko ze zama sanadin barinta gidan in aka kamata da laifin d'iban Mai kud'i in mumcy taji yasan Dole zamanta yazo k'arshe a gidan Dan shi kanwar SA Sam bazata jiku da ita ba ,sanan y fice zuwa down stairs. Itako tacigaba d gyaranta . Bayan y sako y Kira yayan nashi suka Sha Hira har mumcy y sanar musu jibi zai dawo , mumcy tace insha ALLAH gobe za'a gyara maka part d'in d'in d zaku sauka Big Son ,sunata Raha d farinciki suka Rabu . Asma'u ta gama gyara komai ta feshe ko Ina da freshner masu dad'in kamshi kusan kala 4 taga kud'in d y zubar Suma ta tatara Mai ta Adana Mai Akan gadon shi batare da sisin kwabo yayi ciwo ba ta fice dg parlour ta na zuwa ko kalon inda yake batayi ba, ta cema mumcy ta Kamala saura me? "mumcy tace taje baya ta Kira Hari suzo suje kasuwa ,ta tafi Kiran harri. Bayan ta dawo mumcy ta Basu Aiken ta had'asu da driver Dan y kaisu y dawo dasu . Bayan FU'AD ya koma parlour shi yaga ko Ina very clean ga freshner da yaketa welcoming d'in shi ga kud'in shi an Adana Mai a gefe ya d'auka y k'irga Amman duk d Haka yace na Farko ne maybe gaba ta sata . Koda ya Shiga toilet ma yaga komai very clean ya fesa wankan y fito y shirya d niyar barin gidan ,Yama mumcy sallama tamai Addu'a d tasaba ya fice . Bayan su Asma'u sun dawo ta tsaya wajen su harri Tana k'ara koyan wasu abubuwan dan sun fita kwarewa a girke2 zamani dan Haka takeson mak'ale musu kodan ta k'aru dasu . Asma'u Tana tare dasu har aka Kamala girkin Rana ta karu sosai d girkin d akayi ganin tanason harkan kitchen sai mumcy ta barta duk d tasan za'asha fama d FU'AD inya sani sai ta d'auki aniyar gyara Asma'u ta hanyar wadata ta da sutura da kayan gyara Kai duk d ita Bata tab'a hango datti ko k'azantar da FU'AD yake kiranta dashi ba Dan Asma'u Akwai kula d Kai Akwai tsafta sai dai ka hango mutuwar kayanta d tsufansu Suma saidai ka tantance ajikin hijabinta ahakan Kuma har goge hijabanta takeyi duk d sun sufa Dan Bata tab'a sa gyale tazo Aiki ba kulin cikin hijab take kamar matar liman . Bayan Asma'u sun Kamala mumcy ta cikata da su snacks tace gobe tazo d wuri zasu gyara part din yayan FU'AD ze zauna da matar shi inyazo Dan Haka harda ita za'a gyara , Asma'u tace to sai goben ,ta wuce cike d tsaraba mutum 2 take hangowa suci Abin suji dad'i baba da haidar auta Dan duk gidan sune masu k'aunarta d son farin cikin ta Dan Haka ita Bata da kamar su . Bayan ta Shiga t samu baba ya dawo cin Abincin Rana gashi ba'a Gama ba haidar ma yanata Rigima anata rarashi yaki yin shiru baba na niyar bashi kudi ya siyo ko awara ne ,tana shigowa ta same su ,sai ta Fara rarashin haidar d'in ta d'auko wani meat pei ta bashi Aiko yabar kukan y sakema baba kud'in awarar shi ya Fara cin Abinshi y Shiga ciki d gudu . Taba baba yace aa ya gode tunda dai ta kawo masalahar kukan aunta ya gode da wanan ma ,tace "Dan ALLAH baba kaci wlh tunda haidar yake kukan yunwa to anyi yamma girki ne Kuma tasan shima yanajin yunwa Dan ALLAH Kar yaki samata Albarka hajiyace ta Bata Dan ALLAH ya karba ,da kyar da magiya sanan ya karba ,taji dad'i kuwa sanan tayi d'akinta da sauran ,ta d'auko pure water guda 1 ta kawo ma baba tace ya had'a ya karba yanata sa Mata Albarka. Yana zuwa wajen humaira uwar kwad'ayi ta kamo shi zata Mai wayo ya kubce Yana baze Bata ba ,ta taso d gudu Tana Dan uwarka sai ka sammin Dan yawuna y tsinke ai babane ya siyama ,sai sukayi kacibus da Asma'u tazo kawo musu nasu ,mama habee dai gefe tayi d Kai irin batasan me akeyi dinan ba ,itako humaira karba tayi shima haruna yace Yaya humaira raba kiban nawa tunda yau so ake mu Mutu a gidan Nan . Aiko mama ta jeho Mai kofin karfe Tana Dan ubanka inkun mutu kwanan kune ya kare kwad'ayaye me Sarai da Abin wani kawai, ALLAH ya taimake shi ya goce. Humaira ma bak'ar yunwa takeji ta raba Kashi 3 taba haruna y tafi Yana gunguni d jifan d mama ta kawo Mai y goce Yana cin Abinshi Yana Santi,har y Isa wajen baba ,baba yaji dad'in yadda take Basu Suma . Koda humaira taba mama kinci tayi Dan bak'in ciki ,itako t had'a ta cinye aiko ta ci gori wajen mama . Bayan haidar ya cinye ya koma ma'u ta k'ara Mai ,harda bashi ragowar pure wata yasha yayi k'at ya koma wajen baba d donut a hanun shi Yana ci Yana Santi. Girkin Nan be sauka b sai Bayan la'asar lokacin kowa ya toshe cikin d ita sarabar ma'u sai ita uwar gayyar d bak'ar yunwa taketa Mata zak'ule a cikinta ,Aiko tace Babu ita Babu girkin dare wlh ta gama aci a rage na dare ba kowane ma yaci ba Dan ma'u kotakan garau garau d'inta Bata bi ba . *********** Washe Gari d wuri ma'u ta Kamala komai d zata Taya mama habee tabar gidan Bayan Tama baba sallama ,ya Mata nasihar da ya Saba . Cikin Nutsuwa d sallama ta Isa parlour mumcy , ta samu mumcy Zane gasu Hari da su hibba tanata Basu umarnin gyaran part d'in Yaya shurem ,Bayan Asma'u ta gaishe ta ,ta ce tayi maza suje can su Fara Aikin gaba d'ayan su. Zasu tafi FU'AD ya sako ya cema mumcy Ina zasu? Mumcy ai Bata Gama aikinta ba Zaki turata wani waje ,kamata yayi ta kammala d Nan sanan taje can ta tayasu ,meye amfanin ta Yana Galla Mata harara d nuna tsana atanun shi mugunta ya Mata . Mumcy tace to shike Nan ku kuje ku Fara kafin t Gama d Nan d'in ,su Hari suka tafi ,suko y bita d wani mugun kalo . D'akin mumcy ta Fara gyarawa ta sakar Mai Kam shi ,sanan ta dawo parlour , FU'AD ganin har t Gama d d'akin mumcy yace Anya Babu Algus cikin Aikin Nan har anyi me? Mumcy ta bashi amsa da bana son hakafa Son Bata d laifi kuwa wajen gyara ko Kai nasan ka yaba d gyaran d jiya Tama a saman ka .....kafin FU'AD Yayi mgn ... Asma'u tace har Albarka yasa min hajiya ya yaba gyara Kuma sosai . FU'AD Ido ya zaro Yana mamaki Yana cewa kuji min yarinya karama da makirci ,yace "a Ina na yaba d wawan gyaran d kikamin Wanda koni d nake Namiji sai nayi Wanda yafi shi kyau masharanciya? Mumcy d sauri ta katse shi ,tace "banason sake Jin kalmar Nan abakinka son ,nasan halinka na yabon abinda y birgeka ka yaba kawai na yadda .. Takaicin mumcy ta katse shi t hanashi cin Zarafin ta ,yasa yace ki koma yauma ki k'aramin wawan gyaran inma kinayi Dan karnace ki Kuma gyarawa to Baki Isa ba ke Zaki dinga gyarawa _as 4rom today_ tace _Weldon sir_ tana d d'aga kafad'a Tana cewa ,bani da matsala d kowane irin gyara ne ai ,ta Fara gyara parlour y daka Mata tsawa Kan cewa Kar da zuba musu k'ura shida mumcy Bata d hankali ne suna parlour zatayi shara? Ta tafi sama d fara gyara can Kuma inbeyi ba sai ta sake . Mumcy tamai fad'an tsawan d yayi Mata ,tace Asma'u jeki ki Fara gyara Mai inyaso kafin Nan mun tashi Kya gyara Nan din kinji? Asma'u tace to hajiya ,ta faki idon mumcy ta murgud'a Mai Baki ta haura sama ,batayi zaton ya ganta ba shiko Yana kalonta d gefen Ido ,yaci Alwashin hukuntata inya hau sama Dan Dole ma ya hau sama kodan yimata hukuncin akan Rainin da yake Shirin Shiga tsakanin shi da ita . *F.A.S*........😍😍 [4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *Fatima Abubakar Shu'aib* (Maman shaheed) _shafi na 6_ _Dedicate to oll Rik'on kwarya fanc_ ❤❤❤❤❤❤ Washegari da wuri ma'u ta Kama aikin gida tun kafin mama habee ta farka ta Fara yi Mata tijara Akan aikin gidan ta Kama kayanta ,duk aikin da tasan zata iya taimaka musu dashi agidan .. Bayan ta Kamala komai ,ta je ta gaishe d babanta y amsa cikin kulawa d yi Mata addu'o'in d ya Saba yi Mata . Ta koma ta fesa wankanta a rugujajen bandakin su ,da kiris yake jira y tuntsure . Bayan ta fito ,ta shafa fauda Fara Bata dauka d zafi ba ta sa man shafawa a lebenta ba wata kwaliya tayi ba Dan babu su kayan kwaliyar ma bare ta caba . Ta Ciro dogayen rigunan d mumcy ta Bata ta shiro wata dg cikin su blue Mai adon yellow ta matukar amsan jikinta data sa ,ta dinga juyi Dan gani take matsayinta be Kai na ace tasa ba ,Amman yau gashi Yar Aljanna wato mumcy ta gwangwajeta tashi ,tsakanin ta d mumcy sai Addu'a ,shiko FU'AD tsakanin ta dashi baram baram mugu Mai kinjinin talaka Mai izza d ukuba kawai, tanata k'ara yabon Rigar ta Ciro karamin hijab yellow ta saka ta fito Shar da ita ,Amman tanata deciding bazata iya fita d guntun hijab Haka ba ,gashi Bata d wani hijab d ze Shiga d rigar Wanda za a kaleta akara kalonta ,shidai wanan din dai shi yafi match d rigar ,badan taso ba tayi shahadar sakawa tunda b yawo zata ba Kuma wuni zeyi a jikinta ai ba cirewa zatayi ba . Bayan t Gama shirinta ,su mama habee d humaira sunata baccin asara ,ita mama habee t d'an farka taga alamun ma'u ta Kama aikin shine ta sake likimo tabi lafiyar yalolon gadon .. Ma'u tunawa d mumcy ta rok'eta Kan tazo d wuri yasa ko karyawa batayi ba Tama babanta sallama ,ya Mata fatan Alkhairi d nisaha ,ta nufi gidan mumcy Tana GODIYA g ALLAH d y Bata uba kamar baba.. Tana Shiga cikin sallama falon mumcy babu kowa sai masu hidima d gidan ,cikin girmamawa ta gaishe su ,suka amsa cikin sakin fuska ,suka ce mata ta Fara aikin ta yau ba'a jiran order kowa yayi abin da yaga ya dace kawai da ze faranta ran momcy .. Ma'u ta Shiga gyara falon yayi d suka nufi kitchen su Kuma suna cemata inta Gama t biyo su kitchen d'in ,Jin shiru hajiya babba ba'a fito ba ma'u tasan tabas Akwai Abin d takeyi cikin d'akinta . Cikin tsafta d Kula ma'u ta dinga gyaran falon ,Tana gyara yadda kowa yagani sai yayaba d tsarin har wasu abubu take canzama position Dan ta k'awata falon yadda za'a yaba .. Ma'u tayi nisa cikin gyaran saura k'iris ta Kamala ,taji alamun sakowar FU'AD bada komai take gane Yana sakowa ba sai d'an Aiken turaren shi Mai sanyin kamshi ,itako ma'u ta tsani kamshin sbd yadda shima ya tsaneta ,komai nashi baya burgeta sbd yadda yake Mata ,Dan Haka d gudu gudu sauri sauri tabar falon ta shige kitchen cikin masu Aiki ,Dan ko had'uwa batason suyi . Tana Shiga t wayence ,ta Kama musu iya Abin d zata iya sunayi suna Hira . Koda FU'AD ya sauko falon y Fara kalo shide bega munin falon ba sanan be yaba da aikin ba ,Dan Haka room din momcy kawai ya nufa ,Bayan mintuna 5 Naga sun fito tare suna mgn jirgin safe yayan FU'AD d'in zasu biyo Dan Haka dole komai ya zama ready kafin isowar su ,shine tace Bari ta lek'a kitchen taga meke wakana. Shi Kuma FU'AD d'in y zauna a falo Yana jiran momcy shi . Momcy d sallama ta Shiga kitchen d'in t Fara tmby break y Kamala afara Basu suyi kafin su fad'a aikin matafiya? Ma'u ce tazo d himma ta durk'usa har k'asa ta Fara gaishe d momcy ,Aiko momcy ta saki fara'a tace ah Asma'u kece ? Ai ban gane kiba nazata bak'uwa mukayi ,Ashe ta wajenace . Ma'u taji kunya tace ,Kai hajiya Ina Abin da zesa ki kasa ganenin, tun d'azu nazo Naga kina hutawa ne yasa banje n kwashi gaisuwa ba ,sai n gyara falo na dawo Nan tayasu kafin nazo d'akin ki shima na Mai fes . Momcy tayi dariya tace ,oh hankali shine gani ban luraba d gyaran falon ,ma'u tace ko Dan ban fesheshi d turarukan freshner bane d zakisan angyara Dan shine y rage Mai kawai sai Abin d beyi ba kice na gyara d gagawa Zan gyare Miki shi hajiyar mu Tana murmushin girmamawa Nan nata . Momcy tace to sai naje na gani tukun yanzu ku kawo Mana break falo nida son ,hajiya na cewa son ,kirjin ma'u ya buga da k'arfi Tana addu'ar Kar ace ta Kai musu ko k'unar tozali Da FU'AD batason yi wlh .. Sauran masu aikin ne suka amsa d toh hajiya gamunan .. Koda akama ma'u tayin Kai musu cewa tayi Bari ta karasa wani Aiki ,ganin zata Bata lokaci kawai harri ta tafi Kai musu ta kwashi gaisuwa wajen FU'AD ya amsa sama sama ya amsa Dan attention d'in shi Naga phone d'in shi Suna cikin karyawan ,harri ta sake fitowa ta kawo musu wani abincin ,momcy tace y Isa amayar Amman Tama Asma'u mgn tazo ta sa musu turare a falon .....Bata rufe Baki ba FU'AD yace wai har mayyar yarinyar Nan tazo d uwar satiyar Nan ? Momcy tayi banza dashi don taji ciwon kalmar mayya d ya jefi ma'un dashi . Ya sake cewa ,momcy d kun barta yau Baki zamuyi fa ,Amman _dirty girl_ D'inan sai d Kika Mata izinin zuwa d ta shawara nane d bazata Zo ba wlh ,zata Bata Mana happiness d'in mu kawai ... Momcy ta Harare shi tace ,ni nace tazo uban mutane Kuma wlh ka fita hanyar yarinyar Nan ,babu Ruwan ka da ita ,zamana take Kuma Aiki na take banason mu samu sabani akanta da Kai kaji na gayama Tana d'aga mai murya da k'arfi .. Shi Kuma Abin d ya b'ata Mai rai kenan har yayi fushi be gama break d'in ba ya mik'e zai tafi "momcy tace au Akan mgn Nan Dana ma shine kayi zuciya d break d'in ok,fi Ruwa gudu cikin ka wlh bazan lalab'aka ba tafi d'in.. Cikin kufula FU'AD ya tafi Yana mita dama nasan kin Dena ji dani momcy Akan wata kucaka har kina barina da yunwa , ALLAH y kawo min yayana lpy y haura sama Ranshi a b'ace tsakanin shi d ALLAH . "Cikin Ranshi yanata hak'aito irin abinda zema ma'u Koda zesa tabar gidan ne kuwa" Maman shaheed ce dai👌🏻 [4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *F.A.S*...... _Shafi na 5_ Mumcy na barin parlour ta Shiga d'akinta , FU'AD y haura yin hukunci . Koda y Tura K'ofan Ya Shiga Babu Sallama wai Bata Kai yamata sallama ba, shida parlour shi a irin Rainin d yake ganin abin . Y sameta tanata Had'amai Kan Takardun shi d y watsar ,ko kallon inda yake batayi ba bare tasan ya shigo . Yaje ze giftata y kamo kunenta da yake cikin hijab da hanun hagu Dan mugunta Yana cewa uban wa kike murgud'ama baki dazu? Waya Miki Kama d sa'anki duk gidanan ?Yana wani hucci d zare mata idanu . Sai d tasaki 'yar k'ara tace , ALLAH y baka hak'uri Ni konayi ma bansan Nayi ba Tana turo Baki . Yace Aljanune dake ko me da zakiyi Rashin kunya kice bakisan kinyi ba ? Ta samu ta fizgi kunnen ta da kyar ta shek'a d gudu tayi hanyar fita ,tace "eh sune Dani masu gyarama mutum zamansa wanda be so azauna lpy ba , ta bugo Mai k'ofar parlour ta seta benen atamanin Tana hucci. Shiko FU'AD mamaki yake yaushe ta samu dama d saken mayar Mai d martani Haka? Tab! Lailai Dole y gyara Mata zama yarinya 'yar ficiciya ta iya Rashin kunya haka ,oo no duk mumcy ce taja min yarinya har cikin gida har parlour na tamin Rashin kunya ,tab ! Yarinya kin Tab'o Zaki,hmmmm dirty girl ko gyaran Bata Gama ba tayi Rashin kunyarta ta gudu . Itako Tana sauka taga mumcy tayi saurin gyara nutsuwar ta ,tazo tace hajiya na Kamala d saman saura parlour , mumcy tace Zo ki gyara barin Shiga d'aki inkin Gama ki kirani na dawo parlour Dan mu karya d Son , Asma'u tace to hajiya . Asma'u gudu gudu sauri sauri take Kar FU'AD y sako tayi saurin shara tayi morphine Tana Kan goge goge FU'AD y sakko ganin ita kad'ai ce a parlour gashi sai wani hucci yakeyi yana sake b'ata Rai yaci magani kamar be tab'a dariya ba ,ya nufota d niyar zalintar ta ' Aiko Tana ganin niyarsa d gudu ta saki Abin goge TV ta Ruga D'akin mumcy ,kafin ta Shiga t seta nutsuwar ta ,ta Shiga d sallama tace mumcy na kammala . Shiko FU'AD kwafa yayi da Tamai gudun wuce sa'a ,Amman zasu gauraya ne ,Dan Haka dining y nufa Yana jiran mumcy shi . Tare suka fito d Hajiya ,wani mugun kallon gargard'i y wurga Mata ,itako ta k'ara murgud'a Mai Baki Karo na biyu ,Abin ya tsaya Mai A zuciya shikenan kucakar 'yar Nan ta Raina shi? Yama Rasa meze Mata Dan ya bak'anta Mata ,Sai y Tuna Bata K'arasa Gyara Mai takardun Parlour ba ya zaburo ta, ta gudo ,Dan Haka cikin izza yace Wuce kije ki Gama Aikin ki na sama da Baki Gama ba . Mumcy tace ,au Bata Gama ba Daman? Asma'u tayi karfin halin cewa , mumcy na gama komai shima sheda ne ,muje da wani agani inbangyara komai ba . Jin Haka mumcy ta gano kodan 'akwai 'yar tsama ne tsakanin su d ta Rasa Dalilin tsana da tsangwamar da FU'AD yakema Asma'u ,Dan Haka tace to jeki ki karya sai kije ki Taya su harri Aikin part d'in yayan FU'AD . Asma'u tamai wani irin kallo sanan ta tafi zuciyar ta fesss. Cikin kad'uwa da Tsarin part d'in ta dinga k'arema komai kallo ,ta Shiga cikin su Tana tayasu Aikin sunata hirar yayan FU'AD d'in da Bata sanshi ba ,sai yau d Tasha lbr shi harma d wasu kyawawan d'abi'u da halayar FU'AD d hajiya ,ita dai ta yadda d halayen hajiya managarta Amman FU'AD Kam Babu abinda zata d'orar sai kinjinin marashi a tunanin ta,shiko yayan sai yazo zata d'orar da nashi salon. Bayan sun kammala gyaran komai yayi k'alk'al suka turare ko 'ina da turaren wuta d na freshner sanan suka Rufo suka dawo part d'in mumcy . Kusan wuni Ranar Asma'u tayi agidan Dan har kasuwa ta Raka hajiya babba sukayi siyayan kayan d za'a tari bak'in gobe sanan suka Shiga store ta siyama Asma'u ,dogayen Riguna kala 5 da k'ananan hijabai daidai kafad'a masu flawowi da stones ajikin su kala 5 Suma sai flate shoe 3 sai atamfa kala 3 sanan tasai Abinda take buk'ata suka koma gida da taimakon driver d ya kaisu ,shi y d'auko kayan gaba d'aya y shigoma d hajiya babba da taimakon Asma'u . Bayan ankammala komai na gidan ,hajiya babba taba Asma'u umarnin tafiya gida d yamma lis ,ta d'auko ledar dogayen Rigunan ta Bata tace natane t Bata kyauta ,Aiko Asma'u anmata kyautar d tun zuwanta duniya Babu Wanda ya tab'a Bata ,Aiko ta Dinga yima hajiya Addu'a da godiya d Addu'a ALLAH yajikan iyayenta ,hakan ba k'aramin faranta Ran mumcy yayi ba duniya tanason ayima iyayenta d suka Rasu Addu'a har sadaka takeyi Don hakan . Asma'u zuciyarta fes ta Isa gida Bata samu kowa tsakar gida ba ,tanata sallama mama habee na d'aki tanaji tak'i ko kulata ,Dan Haka taje ta Adana kayanta d niyar sai anjima zata bude ta gwadasu in ta nunama mahaifinta . Asma'u muryar mama habee ta jiyo tanata kiranta wai tazo ta kwashe tuwo tunda baiwarta ta gama miyar . Asama'u ta fito ta nufi kitchen d'in ta had'o kwanuka ta duba taga tuwon be Isa a kwashe ba ma gashi Babu wuta sosai ,Dan inda sabo ansaba musu d'anyen tuwo agidan ,sai ta gyara with ta rufe tuwon Dan ya k'ara silala kafin ta kwashe kodan cikin mahaifinta ta gyara tuwon badan su humaira ba . Tana cikin kwasa baba y shigo hanun shi Rik'e d na auta haidar ,d gudu haidar y shigo kitchen d'in Yana cewa yau zamuci tuwo Mai dad'i tuwon Yaya ma'u ,Aiko mama habee ta danno Mai Ashar tace sai ka fad'i Wanda Babu dad'in Dan uwarka Dan nema samamme kawai ,Aiko baba y Fara Mata fad'an zagin d takema haidar ta d'inga gunguni kamar zata zageshi ,sanin Hali yafi sanin kama yace ALLAH ya shiryeta . Bayan Asma'u ta Kamala taci nata ita d haidar ta kaima baba nashi ,ta yi hanyar d'akinta ta d'auko kayan d Hajiya ta siyo Mata ta nunama baba agaban mama habee ,baba yasa Mata Albarka y k'ara yi Mata nisiha da tuni Akan halal d bin Rayuwa sannu a hankali ,sanan t Mike t nufi mama habee zata nuna Mata d sauri mama habee ta dakatar d ita Tana cewa "me Zan gani akayan sata baze wuce satowa kikayi ba anyo gado har Gyatuma ta kwanta dama ai sana'ar ta kenan ,Abin ya Sosa Ran Asma'u idon ta ya ciciko da Ruwa. baba yace tashi ma'uta kije Abinki nine Wanda zanbada sheda Akan mahaifiyar ki ko tsinke Bata tab'a d'auka d sunan sata ba ,a cikin gida ko mak'ota Kuma ita ta huta don tata tayi kyau yanzu mu ta Bari cikin cakwakiyar duniya shi Kuma iya Ruwa ai fidda Kaine . Mana habee ta Fara masifa Tana cewa "waye kakema fatan tasa kartayi kyau Ni ,to walh saidai bakin ka y fad'ama tsohon gidan Nan naka d k'iris yake jira y Rugurguje muga ta fad'i sauro y kada cizo Tana jaraba kamar adamar kamaye ta cikin dadin kowa . Baba yace sede kiyi d wani habee kulin Addu'a shiriya nake Miki ,bazan fasa ba . Asama'u ta koma d'akinta d kayanta ranta fess Dan baba y yaye Mata k'uncin d mama habee ta k'unsa Mata ,zama tayi tanata gwada kayanta Tana juyi Tana murna Tana ganin kyawun da kayan suka Mata gashi kamar an gwada ta ba k'aramin dad'i taji ba ta ware Wanda zata sa Gobe Dan ta fuskanci goben ta musammance ga kowa na gidan hajiya baba harsu masu Aikin ba'a barsu baya ba ,Dan Haka itama zata k'ure adakarta gobe tafito Shar d ita . *F.A.S*.......... [4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *FATIMA ABUBAKA SHU'AIB* ( Maman Shaheed) _shafi na 7_ ```Comments Dinku Na Bani Karfin Gwuiwar Yi Muku Typing ,Dafatan Ana tsintar Darusan Dake Tatare Da ilimintarwa Dake cikin labarin```👌🏻👌🏻 Bayan haurawan FU'AD Sama ,mumcy badan Taso ko taji dad'i Aranta ba Son D'in nata yayi zuciya da break ba ,sai Dan tayi Adalici kawai, Bata rufe Ido ta goyi Bayan karya Alhalin ga gaskia Tana kallo muraran ba,Dan haka ta yi kokarin danne Abin cikin zuciyarta. Bayan ta kammala ,Ma'u tazo ta k'arasa gyara komai na falon ta Kuna turaren wuta masu dad'in Kamshi suka baibaye falon ta ko Ina . FU'AD wayar sa ya d'auka ya Fara latsawa Yana kale kale ,can ya buga uban tsaki yayi kwafa ,sanan ya Mike ya Shiga bathroom d'in shi ya feso wankan kwalisa irin na 'yan bana7 ya fito sai kamshin turarukan wanka yake Yana goge Kan shi da towel. Gaban dressing mirror ya nufa Dan shafe jikin shi da cream din shi Mai kamshi ,Bayan ya janyo stool ya zauna ya Fara shafe jikin shi da Mai ahankali kamar Mai tausayin jikin nashi ko wata macen Bata lalab'a jikinta haka ,ya feshe jikin shi d body spray Mai kamshi ya Gama ya nufi cllothset ya ciro wasu k'ananun kaya masu tsada da kyau Yana sawa Yana bad'e kayan da jikin shi da turaruka kusan kala 3 har su Bayan kunen shi seda ya samu rabon kamshi ,Dan FU'AD Akwai sani lungu da sakon da ya kamata ace turare ya ziyarta Dan har yafi wata macen sanin Haka . Ganin _Time be_ k'arasa ba na zuwa d'auko big bro d'in shi dg _Airport_ yasa ,ya zauna ya Shiga _thinking to what he do to Ma'u_ _dirty girl_ da har zata ji zafi tabar gidan _before her big bro_ jirgin su ya landing.... Can ya tuno da wani wulak'anci da ze Mata ,sai ya d'au phone nashi ya dailing numb momcy shi ,Bayan ta d'auka ranta har ya d'an Mata wasai ,tayi shiru tace ya akayi son? Yayi ajiyar zuciya ba yadda momcyn zata jiyo ba ,yace "momcy yau ko Arzikin gyaran samana ban samu ba kinata big bro kin barni cikin dirty ? Murmushi tayi ,kamar Yana kalon ta ,tace barin turo Ma'u ta gyara ma , _if u like it?_ Da izza d mugunta a ranshi yace toh ! Turo wawiyar ....ya kashe Kiran. Jin furucin shi na karshe yasa momcy _deciding_ inta bar Ma'u zuwa Mai gyara ita kad'ai _definitely something must be happing wihch is embarrassing_ da ze fito from FU'AD to Ma'u Dan Haka atunani da sanin ya kamata irin na momcy sai ta deciding sake Kiran shi don ta bashi umarnin sakowa kasa Don ma'un taji dad'in Aikin ta hankali kwance ... Koda momcy tace y sako ,sai cewa yayi tazo tayi aikin ta shi Yana wani abune a sama _which is important_ yanzu sai ya Kamala zai sakko . Momcy tace toh ,gata Nan ,yayi kwafa ya cigaba da duba wata tablet dake hanun shi . Momcy Kiran Harri tayi da ma'u tace suje su gyarama Son sama Dan ALLAH tare in sun kammala su sakko su cigaba da Abin da sukeyi ,babu musu ko shayin komai Amman dai Ma'u ba Haka taso ba ,Amman ganin harda Hari Kuma babu mutsu ko gardama tsakanin ta da hajiya babba sai kawai ta amsa suka nufi saman nashi .. Suna zuwa ,ma'u tayi sallama ,harri Kuma ta kwankwasa ,Jin muryar Ma'u yace " _dirty girl_ asamu shigowa Dan nasan ba wani _come in_ ma Kika sani ba yadda kike _empty head_ d'inan .... Suko Jin furucin shi beba kowa daga cikin su dama Shiga falon ba sai kallon kallo da sukema junan su kowa na tunanin dashi ake ,ita dai ma'un tasan da ita yake Dan har ranta taji zafin furucin nashi amman sannu Bata Hana zuwa sai dai adade ba'aje ba ,Bataso ta Fara mayar Mai da martani a matsayin yadda take a gidan su . Jin shiru yayi yawa ,ya wani daka Mata tsawa dallah in bakiga Daman wanke toilet d'in bane ki koma ki sanar ma wacce ta turo ki ,kina taremin hanyar kofan falon ... Ganin ze cinye su d'anye babu shawara kawai Harri ta Fara Shiga Bayan ta bud'e falon bakinta d'auke da sallama ,sanan ma'u ta Rufa Mata baya ,kafin ma'un ta taho yimai Aikin sai da ta kirma wani yabud'odon hijabin ta mara galihu ta cire k'aramin Mai kyau ta ajiye sanan ta kirma wanan hijabin da ya b'oye kwaliyar ta . Ganin Harri sai beji dad'in furucin d ya musu ba Kuma yaji haushin zuwan harrin Dan ta tare Mai wani mugun wulakancin d ya tanadarma Ma'u ... Harri ce ta Fara gaishe shi ,sanan ma'u Yana hararta ma ya amsa tare da kwafa ,fuskar Nan kamar besan meye _smile_ ba arayuwan shi . Ma'u har tayi hanyar _toilet_ Harri tace Bari na wanke Mai karki b'ata rigan ki Ma'u ,sai ma'un ta dawo Tana murna cikin ranta ,ga fargaban irin harara d mugun kallon da FU'AD yake Mata lokaci zuwa lokaci. Karema rigan kallo yake ita Bata sani ba ,rigan d ake cewa karta Bata ,Bayan shigan Harri _toilet_ yace jari bola kenan wai karkiyi datti ,to meye marabar ki da dattin shi kanshi ? Ki Fara Abin d yake gaban ki ba abubuwan munafukai d kikeyimin Shiba yanzu ... Ma'u babu musu ranta ab'ace ta Fara gyara falon ta kasa furta ko uffan Dan fargaba daga ita sai shi a falo... Tanata aikin ta ,ta jiyo shi Yana waya d wani abokin shi cikin nutsuwa d Kamala kamar wata macce ,Yana cewa shi ai babu abin d ya tsana a duniya sama da *kuliya* Sam beson ko ganin ta acikin dabobi ita yafi tsana shi yasa ko inda take baya nufa itama Bata zuwa Dan ze iya kirga iya ganin shi d ita a duniya ... Ma'u duk Tana jin shi ,tanata kisima wani Abu cikin ranta da koni bansan meye ba ,har suka Gama hirar d abokin shi ya kashe wayar . Aikin ta yazo inda yake zaune Dan ,Haka cikin girmamawa tace yallab'ai Zan gyara wajen kanta a k'asa .. Ya wani bita d kallon tuhuma ,waye yallab'an naki ? Me ? Yallab'ai , barin Miki gargad'i na farko Kuma na k'arshe ko a wawan mafarkin ki karki sake tsautsayi yasa ki k'ara gigin kirana d wanan sunan ,only ma'aikata nane kawai suke kirana da shi ,keko Ina Kika Kai matsayin yimin Aiki bare ki kirani da sunan ? Baki Kai ba bazaki Kai ba Kuma ,Ni wlh bansan meyasa momcy ta _accepting d'in ki as_ Mai taimaka Mata ta wani b'angaren ba wlh , kawai kiyi aikin ki, ki fice min da gani Yana wani jifanta d wawan kallo....ya Mike y Shiga bedroom d'in shi hannun shi rige d _phone da tablet_ d'in shi . Ma'u taji zafin kalaman shi ,ta sake k'aryata maganar hafeeza da tace wai yanada saukin Kai da kirki da iya mu'amala ,atake tace wlh ko 1 baida shi _totaly_ ma beyiba a Rayuwa besan hakkin d'an Adam ba sam ,ahakan yakeda ilimin addini sosai? Aiko indai yasan ayar da ALLAH yake cewa ya karama bani adama ko almajirin gidan Nan beze wulakanta ba bare ita d ba bara tazo ba Dan ta wuce bara duk da tasan ita ba wata bace ,Dan Haka ilimin shi baya amfanar shi Kuma ma itafa aikin Nan *RIK'ON KWARYA* Ne agareta Da Mai shi ta dawo zata sakar Mata abinta ta koma zaman ukubar gidan mama habee, can Kuma ta tuno da azabtuwar d tijarar mama habi sai Taji Rana zafi inuwa Kuna kenan duk d Haka gwanda gidan hajiya babba matsalan ta FU'AD ne kawai ,can ko harda su humaira ,sai d idon ta yayi yunkurin zubar da Ruwa ,sai Jin mgn harri tayi Tana cewa yi maza mu k'arasa mu sauka Ma'u ,da sauri ta mayar d kwalar ta amsa Mata suka Kama aikin hanu bibiyu kafin kace me sun gyare Mai ko Ina sai kamshi ne yake safa da marwa a falon d ko Ina ,besan sun sauka bama Yana bedroom d'in shi . Ko da suka sakko Kan aikin su suka fad'a kad'an y rage a Kamala girkin ma Dan fin Rabin ya kammala . FU'AD sak'on kamshine ya kaimai yasa shi fitowa falon yaga duk babu su y tabatar sun Gama ne ,Dan Haka ya zari makulin mota ya nufo k'asa batare d ya yabi gyaran ba ,acewar sa baze yabi gyaran ta ba Dan Bata Kai ba ,Yana sakkowa ya nufi inda momcy take zaune ya zauna Yana ce Mata saukan su Yaya kawai yake jira Amman kamar zuwa zeyi kawai jirgin y landing a gaban shi Dan Haka ya tafi d'auko Mata _first son_ d'inta ta musu fatan dawowa lpy ,cikin murmushi d iya zama da kowa da bama kowa hakkin shi tace adawo lpy ALLAH ya kaika lpy, su Kuma ALLAH ya kawo su lpy ku iso min gida cikin Aminci , FU'AD yace Ammen uwa tagari ya fice zuwa inda motar shi take .... Maman shaheed ce dai👌🏻 [4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *FATIMA ABUBAKA SHU'AIB* (Maman Shaheed) Pg 8 *Shafin Nan nakune masoyan RIK'ON KWARYA Ina mugun yinku kamar yadda kuke mugun yin RIKON KWARYA*❤❤👌🏻 FU'AD bai tsaya ko Ina ba sai _Airport_ befi minti 15 da zuwa ba jirgin su big bro ya sauka a makeken filin jirgin Aminu Kano . Su Ma'u dasu Hari suna Kamala aikin komai sai Abin d ba'a Rasa ba na shirya wajen da za'a kwashi garar girkin ,hatta sashin da su big bro d'in zasu zauna an sake gyarawa an bade shi da turaruka masu dad'in Kamshi aka rufo musu . Mutane nata sakowa daga jikin jirgi wasu turawa ,wasu bakar fata Amman da ka gansu kasan hutu d Jin dad'i ya ratsa su ,kamar yadda na hango big bro d'in FU'AD da hutu da Jin dad'i ya Gama canja Mai fatan shi,shida matar shi Mai kyau hanun su cikin na juna suna sakowa suna Hira cikin nishad'i da birgewa da salon soyayya Mai k'ayatarwa ... Bayan sun karasa sakowa ,ya ciro waya da alamun yin Kira kenan yaga k'anin shi FU'AD yazo fuskar shi d'auke da fara'a da Jin dad'in Yana cewa gani Ina ta jiranku ai ,da sauri suka rungumi juna suna sakin wani murmushi na matsanaicin zumunci da ganin su kasan suna son junan su matuk'a. FU'AD ne ya kalli matar big bro d'in yayi murmushi yace matar Yaya sannu da isowa kasarmu ta gado ,dafatan bakiyi fushi ba da na Fara kula big bro d'ina kafin ke? Murmushi ta Mai ,sanan tace "ai wata kusan tafi wata kusan ,wariyar launin fata ka nunamin tun a Airport Tana kallon mijinta Tana wani narkewa kamar zatayi Mai kuka , kafin mijinta yayi mgn FU'AD yace "tuba nake banyi Haka don son Kai ba kema ai Tamuce munma fi ji dake Dan kamar canji akayi kece tamu, tace ba wanin Nan zakamin dad'in Baki ko? Cewa yayi " yanzu aimin afuwa Yana had'e hanun sa a kirjin shi Alamar ban hakuri . Ita dai cewa tayi ,naki wayon ,sai da Mijin ta yasa Baki sanan ta hak'ura , FU'AD yace aunty rigima kenan Yaya Haka kake fama? Yayan nashi yace Mata ai sai da rarashi , FU'AD yace hmmmm musamman taka ba ,yayan yad'an daki kafad'un FU'AD yace Kai wayasan Abin da zakayi ma , FU'AD yace hmmmm Babu Ni cikin wanan aikin wahalar da Kan gaskia ,yayan nashi y dinga yimai dariya da matar tashi suna cewa irin ku sunfi kowa ma.. Kayan jakankunan su aka Gama zuba musu a motar FU'AD sanan FU'AD ya jasu sai katafaren gidan momcy. Hari da ma'u sun Kamala had'a wajen da za'aci abincin sun jere komai sun gyara ga kamshi Mai nishad'antarwa dake yawo a wajen ... Bayan isowar su katafaren gidan ,horn FU'AD yayi baba Mai gadi ya bud'e musu Yana musu barka da zuwa ,ya samu waje yayi parking ,har bakin motar baba Mai gadin yazo Yana kwasan gaisuwa ga yayan FU'AD din da matar shi cikin girmamawa ,shima ya amsawa baban har yamai kyautan kud'i yanata GODIYA da murna ya dinga yima mahaifin su Addu'a kuwa da ALLAH yamai Rasuwa tun wasu shekaru da suka shud'e ,suka dinga amsawa da Amin ,Dan suna Jin dad'in ayima mahaifin su Addu'a... Bayan shigan su falon momcy bakin FU'AD d'auke d sallama Yana tsokanan momcy ,momcy na hakince a kujera ,tozali da tayi da yayan FU'AD din sai murnar ta ta k'aru ,Amman ganin surikarta sai ta Fara cewa"Zo Nan surikar kirki taho kusa Dani kiyi masauki anan ,ta tafi kusa da Momcy ta rungumota ta had'ata da jikinta Tana Mata oyoyo ,ita ko ta zauna ta Fara yaba karamci irin na surikar tata da nuna kulawa tun Bata Sami ko mintuna 5 ba acikin gidan . Bayan sun gaisa ,momcy nata tmby y suka baro jama'ar can kasar da iyayayen sirukar tata, tanata nuna musu kulawa ,Bayan sun hutane momcy ta umarci da suje suci abinci kafin suyi masauki a sashin su don su huta .... Jama'ar momcy ne suka halara gaba d'ayan su ,su hud'u awajen cin abincin surikarta na kusa da ita shima FU'AD na kusa da yayan shi sunata Hira Mai cike d nishad'i suna Hira suna raha mahaifiyar tasu na nuna musu kulawa ,ahaka har suka Kamala cin abincin kowa na yaba irin girkin d aka shirya musu Haka kala kala.. Bayan sun Gama momcy tace suje su huta a sashin su ,ta Kira Ma'u akan taje ta bud'e musu sashin Dan d'azu a hannun ta akabar makuli ... Jin furucin momcy yasa FU'AD Jin wani iri wai Ma'u akaba makulin sashin yayan shi? Shi besan inda momcy takeson ajiye _dirty girl_ d'inan ba ,ya fad'a cikin zuciyar shi,Dan Haka ya maka Mata wata uwar harara Mai Tatare da gargad'i yace ta bashi makulin waya gayace ta sashin ma tukunna da har hannun ta ya samu ma'adanar makulin sashin? Ta mik'o Mai kenan,jikinta a sabule, sai momcy tace "son kafita idona na rufe ,Ni na gayaceta na Bata umarni Kuma yanzun ma itace zata bude ta cika umarni na "abinda hukunci ya biyo baya kazo kamana nida ita ,wuce kije Asma'u ... Abin da momcy tayi y kular da FU'AD ,itako matar Yaya murmushi tayi tace suna Mai dad'i shine akayi _short cut_ d'in shi wai Ma'u ,momcy tace ai Haka kowa yake kiranta Amman Banda Ni ,shidai yayan FU'AD d'in cewa yayi mu tafi nidai na gaji hutawa kawai nake bukata ,sai ko FU'AD y garoma Ma'u akwatin big bro d'in nashi wai gashi tunda momcy ta zab'ar maku abokiyar rakiya Ni bazan jera da ita ba Yana mita Yana kallon momcy ta gefen ido ... Momcy kuwa cewa tayi ,sai me Abin da ba kaje kayi ba ,ma'un zata iya ai ,zuwanka d rashin zuwanka babu abin da zai k'ara kamar yadda babu abin da zai rage ,Ina dalilin wanan al'amarine ka aro Halin d ba nakaba ka k'ak'aba ma kanka .... Yayan shine yace , gaskiya Kam Nima ban sanshi d wanan sabon halin ba ,maza kayi watsi dashi kabar halinka managarta Abin koyi ... Momcy tace ka tayani dai tunda kaga zahiri yanzu kaima .... Jin anmai yawa y haura sama ranshi Babu dad'i Yana mita ,Yana Kara Jin haushin Akan wata kazama aka Mai Haka? Ya zama dole yayi maganin ta wlh. Ma'u tabi umarnin momcy ta rakasu har sashin su ta bud'e musu kofar ,ta Kira me yima momcy wanki da guga ya dibi akwatunan su ya Kai musu sashin su , momcy ta umarci Ma'u da takai musu wani abinci da ko tabawa ba'ayi ba atunanin ta ko kunya surikar tata takeji ... FU'AD tunda y haura sama be sako ba sai da ya samu Kiran gagawa daga office ,Dan yau dama yace ranar ta yayan shi ce ,gashi Ma'u ta Shiga Mai cikin ranar ta b'ata Mai Dan Haka y sakko ,yana ma momcy sallama yace ya samu Kiran gagawa ne , momcy atunanin ta duk fishin ne yasa zebar gidan ,Dan haka Taki kulashi bare rarashi ,sai Addu'a sauka lpy d tamai.... Bayan ya fita ,ya samu ma'u naba baba Mai gadi abinci ,sai FU'AD ya shirya Mata mugunta Bayan ta gama bashi ta juyo Tana tafiyar ta hankalin ta kwance batasan ma ya fito ba kawai , FU'AD yayi kanta da mota ze kad'eta gadan gadan k'iris ya rage be tab'ata ba badan tasa ihu ta koma bayaba ,Aiko ta bugi gate d'in gidan sai da hanun ta yayi wani irin k'ara kanta ya bugu alamun kamar taji ciwo ,hatta baba Mai gadi sai da Abin y tsorata shi ,itako ajiyar zuciya kawai takeyi atunanin ta FU'AD besan me ya aikata ba,sai kawai taga Yana ba baba Mai gadi Umar nin bud'e Mai gate ,ita Kuma Yana Mata wani mugun kallo na irin kad'an Kika gani d'inan .... Bayan an bude Mai ya Cinna hancin motar y tafiyar sa batare da y saurari Abin d y aikata na yunk'urin kisan Kai ba ,yasa ta dinga ajiyar zuciya d k'ara yadda tsanar d y Mata har ya Kai ze iya kashe ta? To aikuwa ko tabarmai gidan su kafin yayi ajalinta ko tayi damarar fafatawa dashi a filin daga, matukar karfin ta yakai na rike makaman yakin da zata iya yak'ar shi ..... Maman shaheed ce👌🏻 [4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *Fatima Abubakar Shu'aib* (Maman shaheed) _shafi na 9_ _Dedicate to oll Rik'on kwarya fanc_ ❤❤❤❤❤❤ 🥰🥰🥰🥰🥰🥰 😍😍😍😍😍😍 Bayan baba Mai gadi ya Gama jajantama Ma'u ,jikinta a salub'e ta koma ciki Amman Tana Dan Jin zafi a kanta da hanun ta inda ta bige ta had'u da gate d'in ... Haka ta koma ciki suka d'an tab'a Hira da su Harri sukaci Abinci ,.. Yaya da matar shi suna sashin su sunata huta gajiya . ************* Kici Abinci inzakici ke kulin sai ansha fama dake wajen cin abinci ,kici Kisha magani in Kuma kukan kikafi so to in kin Gama na dawo na Baki maganin .... Wanan furucin na fitowane daga bakin wata ma'aikaciyar jinya ta masu tabuwar kwakwalwa ( mahaukata) Tana ta tursasa wata baiwar ALLAH Akan taci abinci Tasha magani .... Ita dai wanan matar Bayan wasu shekaru da suka shud'e ne wani atajiri ya bigeta da mota sakamakon ganinta d yayi a yanayin hauka yasa yaayi gidan mahaukata da ita Don yanada Halin talafama Rayuwar ta Dan Haka ake kuka da ita da maganin ta da Abin da take ci ,maganin ake Mata Amman fa kullin jiya iyau Abin kamar zeyi sauki sai ya Kara tashi ,yayi cigiyar Yan uwanta har ya gaji ,matar shi da mahaifiyar shi sun shawarce Alh malan akan agwada Mata na gargajiya yace Sam ba zeyiba asibiti ma sunayin komai shi irin Yan asibiti akida d'inan Nan gidan shi ba'a Shan jik'e jik'en gargajiya ko wasu abubuwan da ya shafi malamai a cewar sa duk 'yan tsubbu sunfi yawa yanzu da masu maganin karya ,kowa ka gani shine Mai gaskia Mai bada maganin kowacce cuta Karin Abin takaici su fito kafafen sadarwa kamar su ,gidan rediyo,talabijin,suta talata kansu ,da wanan ya kafa hujja yasa duk ya musu kud'in goro baya harka dasu Sam Kuma iyalan shima Basu Isa ko ab'oye suje ba bare azahiri ,Dan ganin yadda bayaso yasa hajiya Ramatu ta hak'ura hatta hajajju makkatu wato mahaifiyar sa ta sallama dake gidan su d'aya ya dawo da ita kusa dashi sashinta da ban ,zaman su kadaran kada han da surikar ta da jikokin ta ,shidai Yana matsanaicin kula da mahaifiyar shi ... Bayan ma'aikaciyar jinyar ta gama ma matar sababi taje ta dawo ta Bata abincin ta karba ta Bata maganin kamar yadda suka Saba kullin sai sunkai Ruwa Rana kafin Tasha maganin inda sabo har sun Saba .... **************** Momcy ce ta umarci Ma'u da taje sashin su yayan FU'AD ta fito da kayan Abincin da suka kammala ,cikin girmamawa da bin umarni Ma'u taje bakinta d'auke d sallama har ta k'ara yi musu ban gajiya ,suka amsa d gajiya tabi lpy taga matar yayan ta Kara canja Kaya daga Wanda tazo dasu zuwa wasu masu masifar kyau Dan sai d ta birge Ma'u .... Wani Abu ,da kyar Ma'u ta d'ibo kayan Abincin zuwa kitchen din mumcy Tana Gama ajiyewa ta dinga shafa hannun ta Tana "wash ALLAH"! Haka ta sake komawa ta d'ebo sauran dauriya kawai takeyi Amman hanun ta na Mata zafi tabas kawai dauriya takeyi ... Bayan wasu awanni da yamma sosai Bayan an Kamala girkin dare , momcy ta umarci Ma'u da ta kaima su yayan FU'AD nasu sashin su harda tacacen lemukan da aka hada musu don Susa a firinji don yayi sanyi kafin su buk'ata ... Koda Ma'u ta d'auki jug din don Fara Kai musu hanun ta kasa d'auka yayi jug din tintsirewa yayi ya zube ,momcy da Harri sukace lpy Ma'u kalau kike? Ma'u yatsina fuska tayi tace wlh hanun tane taji baze iya d'aukan jug din ba . Momcy tace meya Sami hannun ,Hari tayi saurin cewa badai tun dazu ba d kikace kin bige ? Ma'u tace tun shi wlh kawai daurewa nakeyi . Momcy tace kufito min a mutum? Meya samu hanun? Nan Ma'u ta saya Mata abinda ya faru ,kawai tace bigewa tayi da taje kaima me gadi abinci dazu shine hanun yaketa ciwo har yanzu ga zafi da nauyi ko motsa hanun banason yi sai dole .... Momcy ta tab'a hannu Ma'u tace "wash ALLAH na da zafi" momcy tace sannu Harri babu inda ake gyara d Kika sani kuje aduba kafin ta tafi gida inyaso inkunje daga can sai ta wuce gida ta huta nasan Ma'u da son ganin babanta da bin umarnin shi tun dazu na fuskanci son tafiya gida takeyi ,ko ba Haka bane Asma'u? Inji momcy. Ma'u tace hakane babu kunya Dan duk ta k'osa ta tafi gidan taga baban ta da haidar autan su . Suna cikin Haka suka jiyo sallamar FU'AD ya shigo ,da fara'a ya shigo ya nufo inda mahaifiyar shi take ,Amman ganin Tana tab'a hannun Ma'u Tana Mata sannu sai y rage fara'a ... Momcy ta dubeshi tace son andawo? Yace na dawo uwa tagari batare d y sake kalon inda suke ba ,yace abinci nake buk'ata momcy dafatan ya kammala ? Y na Shirin zuwa inda aka tanada Dan can abinci , momcy tace eh Bari a taimakama da su plates d spoons,yace harmu nawane zamuci d naji kina jam'u momcy ... Momcy tace ba sai ka zuba iya naka kabar sauran ba? FU'AD yace "toh" momcy ta ,Amman Kar ki turo min wanan abun ta gabanki Dan Tana zuwa na hak'ura da abincin ... Momcy ta Galla Mai wata uwar harara ,tace dallah ita hannun Tama ciwo yakeyi Bata da lokacin taimakama da Kai wani ne da ka taimaka musu suje adubata ... FU'AD yayi saurin cewa "what"? Tab Ashe baza'a dubata ba momcy wanan abun? Momcy ta Harare shi tace "waye abun? Asma'u? "Yace eh Mana momcy" Momcy tace Kar na k'arajin kace Mata wanan abun acikin gidan Nan ,kaji menace? FU'AD ya dago yasan Babu Wasa atare da momcy, yace "Amman Zan iya fad'a a wajen gidan Nan ,acikin gidan na bar fad'a sai a waje" Momcy tace son kashiga hankalin kafa wlh ,umarni nake baka matukar na Isa a ko'ina karka k'ara kiranta da wanan abun kwata kwata na Hana ,kaji me nace? FU'AD har mamaki Abin ya bashi sai d Yama momcy wani kallo na Anya momcy Baki rage Sona da k'aunata ba kuwa? Sanan y amsa d angama uwa ta gari ,Nima Kuma ta dinga kiyaye dokokina a gidan Nan ta Dena zuwa Inda abincina da Shana yake ... Momcy tace kana nufin har gyaran saman ka ta Dena yimaka? FU'AD yace aa wanan shine Aikin ta ma ai ,tafi dacewa d wankin _bathroom_ ta d'ora daga inda ta tsaya ,meye amfanin ta? Momcy tace hmmmmm ,aikin kawai d sai kadin gayi da kanka ai Ashe tanada Rana ... Momcy Bata k'ara sauraran FU'AD ba tace Harri kuje kinji duk abinda na Gaya Miki direba ya kaiku , ALLAH ya sawake Asma'u kinji kin d'auki ledar da nace ki d'auka? Ma'u ta girgiza Kai Alamar a'a sai momcy tace "Hari d'aukan Mata ki rik'e Mata , Harri ta amsa da to hajiya suka nufi kitchen Ma'u ta gama shiryawa ta cire birmemen hijab tasa karamin da taimakon Harri sanan suka dawo sukama momcy godiya da sallama suka fita .. FU'AD Baki ya tab'e Yana cewa waya Bata aron Kaya ? _dirty girl_ kamar Ma'u ,Yana cin abinci yanajin haushin ma'u Akan yadda momcy take Mai a kanta Abin d ko a mafarki momcy Bata Mai fad'a Haka iya tsahon zaman su da mahaifiyar shi ,Dan gaka babu shi babu Ma'u ,shifa dole momcy ta gane jinin sune kawai be had'u ba . Bayan Harri sun Isa wajen Mai gyara ,kafin Nan hanun Yama Ma'u tsami har kwalla tayi da ake gyarawa Ashe ta d'an samu matsala a hannun ,Bayan an Gama ta share hawayenta yasa Mata magani ,Harri ta rakata har gida da ledar ta har suka gaisa da baban ma'un ,Jin ma'un taji ciwo Abin har cikin ran baban ya dinga Mata sannu ,harrin ta k'ara jinjina so da k'auna irin na d'a da mahaifi ,sanan ta musu sallama tama ma'un ALLAH ya k'ara sauki sanan ta koma gidan momcy .. Ma'u da d'aya hannun ta fito da su abincin da kayan cincin d'in d momcy ta cika Mata leda dasu taba babanta tace yaci ,yace" ta Fara ci ,tamai k'aryar ai ita taci kad'an zata k'ara ,sanan ya karb'a ya Fara tmby garin Yaya taji ciwo ,ta sake labarta Mai yadda ta tsara ba ainahin Abin da ya faru ba ....baba y Mata sannu yace taje ta huta ,tace "toh ta tafi da sauran Abin dake cikin ledar ta nufi tsohon d'akin d take kwantar d hak'ark'arinta ... Bayan ta d'iban ma mama habee Abin d tazo dashi ta tafi Kai Mata ,koda tayi sallama ta Shiga ta Bata ,sai tabe Baki mama habeen tayi tace batacin Abin d Bata da tabas akanshi ,ko satowa akayi ko me akayi aka samu Bata sani ba ,Abin Yama Ma'u ciwo Amman inda sabo ta Saba ,ta mik'e zata tafi haidar ya shigo d gudu Yana cewa Yaya Ma'u Ashe ciwo kikaji? Wayoo ALLAH sannu Yaya Ma'u ,mama habee tace agarin satar ne inajin aka kwad'eta wata ranama ajalinki Zaki sato indai Baki canja Hali ba .... Haidar yace ,wlh Yaya Ma'u Bata sata Yana turo Baki ,Aiko mama habee ta makomai duka d Kofi ya kauce k'iris ta fama ma Ma'u ciwon ta ,tayi saurin barin d'akin kafin ta mayar Mata d Abu sabo ... Bayan Ma'u ta koma d'akinta ,kwanciya tayi Akan yaloluwar katifar ta ,Tana ta tunani da Jin rad'ad'in Abin d FU'AD ya Mata ,gashi ko abincin kirki ta kasa CI , gashi yanzu ya barta da ciwo Mai tab'a zuciya Dan har ranta take Jin ciwon harfa kuka tayi ...... Haidar ne yazo y katse Mata tunani d cewa ,Yaya Ma'u humaira tace kibani abinda Kika ba mama habee Taki karb'a ,Amman tace Kar bace ita ta turo Ni wlh sai d ta murd'emin kunne ,karki Gaya Mata kinji Yaya Ma'u ? Ma'u ta saki murmushin dole tace "kuda wajen kwad'ayi za'a mutu" ta dib'o ta bashi tace shima yaci da yawa fa ,ya tafi Yana murna Yana cewa kad'an Zan Bata ,Ma'u tayi murmushi ta koma tunanin ta .. Cikin ranta Tana cewa Anya zata sake komawa gidan su FU'AD kuwa ,yaufa d yazo d tsautsayi d y kashe ta ,Kuma Taji ciwo ta dalilin abinda y mata Amman Yana sake binta da sharri , gaskia y Kanata tabarmai gidan su .... Washe gari Ma'u Bata samu Taya mama have aikin gidan ba ,Aiko ta dinga sababi harda cewa Dan kartayi Aiki yasa taji ciwon ,yanzu haka ma ciwon karya ne, sai d baba ya ma mama habee da gaske sanan ta saurara kad'an ,Amman duk d haka mama habee sai d tace Bari nagani ko zataje aikin boyi boyin d ta Saba shine ze tabatar d k'aryar ciwon , bud'ar bakin Ma'u tace wlh babu inda zani Ina gida har gobe har jibi har ......d sauri baba y dakatar d Ma'u da cewa sbd Ma'u ta? Ma'u tace wlh baba hanun namin ciwo Kuma kaga Aiki zanjeyi Kuma karfin aikin da hannu ne ,Kuma kaga yadda hanun ya zama . Sanan baba yace eh ba fahimce ki ,sannu kinji ALLAH y k'ara sauki d lpy. Ma'u tace Ameen baba ,ngd..... Mama habee d humaira sukace uhummmmm munafurcin dodo dai ,sai d baba y harari humaira sanan ta shiga hankalin ta tayi shiru ,itako rasa'u Bata fasa jifan Ma'u da miyagun kalamai ba . Maman Shaheed ce👌🏻 [4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *Fatima Abubakar Shu'aib* (Maman shaheed) _shafi na 10_ *FU'AD kaga ta Kanka da makaranta ,ku fahimce shi Mana jinin sune kawai bai had'u ba da ma'u*👌🏻👌🏻🤷🏼‍♀ Gari har ya K'ara wayewa Rana ta fito Ma'u babu niya bare haramar tafiya gidan momcy ,Kuma tanata fama d Shan bak'ar magana daga mama habee Abin karayar ta na safe ma a wulak'ance aka Bata shi ,dama Bata Gama cinye Abin cin da momcy ta jido Mata ba ,Dan Haka Babu d'umame ta Kama cin abincin ta Dan jiya dama zafin abinda FU'AD da Rad'ad'in ciwon ne yasa Taki cin abincin,yau ko yunwa ta sa ta kama ci haidar na tayata ..... Momcy ganin lokacin zuwan ma'un ya wuce, yasa ta Fara tunanin ALLAH yasa lpy tajita shiru ko Kuma hannun ne y hanata zuwa ? Tun Tana mgn da zuciyar ta har sai d ta fito fili ta farayi da ma'aikatan duk sukace ALLAH dai yasa lpy ,momcy tace "Ameen" Bayan wasu Awanni matar big bro ta shigo ta gaishe da momcy ,momcy cikin kulawa da yabawa ta amsa shima big bro d'in ya gaishe ta ,Bayan sun gaisa yake tmby FU'AD ! Momcy tace Yana sama Yana baccin lalaci dake yau Asabar CE Babu Aiki ,da azama yayan nashi y haura sama y same shi yanata bacci hankali kwance , bubuga bayanshi yayi ,FU'AD ya d'an bud'e ido tozali da yayan shi da yayi ya saki wani murmushi Mai k'ayatarwa yace " morning big bro" big bro d'in yace "morning junior " hw was ur night? Yace fine big Yaya ,Ashe har kun tashi ? Ina aunty tawa na kwashi gaisuwa kafin n Kuma Mata laifi ,Dan tace ranar d kuka diro k'asar Nan na Fara Mata laifi ,yayan yayi murmushi y d'an daki kafad'un shi yace Tana k'asa tare d surikar ta ,nasan ko break bakayi ba so ka tashi ka gyara kazo kayi break ji room d'inka ma gyara yake buk'ata Yana k'arema ko Ina kallo . FU'AD y yatsine fuska yace eh _dirty girl_ d'inan d momcy ta rakibo zatazo ta gyara Dan amfanin ta kenan ,yayan nashi yace wa kenan? FU'AD yace wata me Kama da mayya ko Ma'u ko me'u sunan ta oho naji momcy dai na cemata ko Asama ohon Ni dai ,yayan nashi yayi dariya yace K'anina ka fa canza daga yadda na barka na Kuma Sanka _why_? FU'AD yace kaima ka Fara yadda d mgn momcy wlh Ina Nan kamar yadda nake kawai fahimta fuskane bansan meyasa momcy takemin lak'abi da canja Hali ba ,Ni har mamaki nakeyi , yayan nashi yace ko ma dai meye Zan gani Nima kafin muje Abuja Dan Akwai wani aki da zamuje muyi na 6months da Zan bar madam anan ita da surikarta Amman tace gwanda mu tafi tare ,so nake muyi shawara d momcy Abin da tace shi za'ayi .... Aiko FU'AD ma yace kawai ka tafi d matar ka ai bazata sake damu ba nake gani tunda Bata Saba ba damu ba sai ahankali ,Amman yadda kuka Gama shawarar dai ,barin Shiga nayi wanka n fito gaba d'aya kafin Nan na harbo yarinyar Nan ta gyara min falon yau har d'akin ma zata gyara wancan ne kawai bazata gyara ba Dan ba sosai nake Shiga ba ,big bro yace sai ka sakko ... Bayan yayan y sakko ,y zauna suka hau fira da momcy ,amaryar yayace ta Fara cewa Ina wanan _cuty girl_ d'in ta tayani gyaran sashin mu momcy ? Momcy ta gane Asma'u take nufi ,sai tace "Asma'u? Tace "eh Asmah ita, sai momcy tace wlh Bata Zo ba yau Ina kyautata zaton hannun tane y hanata zuwa ,lokacin da yayi daidai d sakowan FU'AD ya katse musu hiran ta hanyar gaishe d momcy da amaryan yayan shi cikin raha d sakin fuska , sai momcy taci gaba da cewa , "tunda har takai yanzu Bata Zo ba Akwai dalili Mai k'arfi ,Amman Zan sa Harri taje ta dubo min ita be kamata a barta ba Kuma anji shiru tunda Bata tab'a yin hakan ba tunda hafeeza tamin canji da ita ,sai ko FU'AD yace ... "Wai yarinyar Nan kin zuwa tayi naji kunata dogon tataunawa akanta ? Momcy tace eh ,kawai t Rabu dashi , sai ko yace dama tsintacen mage baya mage ne ko meye Inji hausawa ,Haka kawai kika rakib'o Mana ita momcy Ni gwanda karta k'ara zuwa ma karki sa kowa ya bita please momcy. Kafin momcy tayi mgn yayan yayi saurin cewa , FU'AD wai me kazama ne ? Ina Ruwanka momcy tafika sanin dalilin d yasa ta karbeta ba taimaka Mata takeyi ba? Baka Jin dad'in taimakon d takema mahaifiyar Kane? Kuma yanzu kasan dalilin d ya hanata zuwa ne Ana cemaka taji ciwo Ana tunanin ciwon ne ya hanata zuwa ,Yana d kyau a tabatar ai ko? Kuma yanzu Naga kaima Tana amfanar ka ko acikin gidan? FU'AD Yana Kai Loma Dankalin turawa soyaye da kwai har ze kware ya kurbi tea kakaura ,yace yaya Dame take amfana na a gidan Nan? Wlh babu amfanin d ta tab'a min ko zatamin anan gaba ...yayan y katse shi d cewa Amman FU'AD bakai ne FU'AD d'in momcy da muka Gama Hira d'azu ba Koh? Waye yace ze Kira Asama take kowa? Ta Mai gyaran falo da d'aki ? Ba Kai bane? FU'AD yace oh wanan nine Mana to ai Daman aikin tane ,ba wai taimakona zatayi ba ,aikin tane Daman ,da ta samu na barta ta haumin sama ma batayi arziki ba ,yarinya kamar aljana ga gulmar shiru shiru ko had'a ido da mutum Bata yi sbd gulmanta fa ,hmmm can tagane . Amaryar yayan CE tace ,is good ai hakan means tanada halaye masu kyau Bata tsatsare mutum da ido irin n rashin Tarbiya Kuma respect ne ai take baka ,Kai K'anina akwai Wanda ze iya maka kuwa? Ko ka yadda ko kak'i Tana maka Amfani har momcy ma dole ma ka yadda ,kowa ya amsa da kema Kya fad'a ,shi ko FU'AD yace Sam bazaku gane bane kawai abar zance wanan Abun , da sauri momcy ta wurgo Mai tambaya mekace son? Cikin tunawa da mgn da sukayi a baya yace oh no sorry momcy wlh mantawa nayi Asama take ko ma'ule , ALLAH y huci zuciyar uwa ta gari na tab'a Yar Aikin ta Mai yi Mata hidima _double sorry momcy_ Yana sake loman abincin shi ... Momcy kwafa kawai tayi ,itako Amarya Abin dariya y Bata d sha'awa yadda yaran ke girmama mahaifiyar su itama take jansu ajiki sabanin tata mom d'in Dan ita mahaifinta yafi janta ajiki . Yayan FU'AD d'in ne yace ,Haka ka zama ko ,yanzu kayi laifi ka wanke laifin ka ,momcy tace ka manta da son ne ? Halin shinan na dabara Yana Nan har yanzu ,duk suka sa dariya ,ya b'ata ma ya wanke ma ,duk shi kad'ai ... Momcy ce ta Kira Harri tace taje ta Taya Amaryar yayan FU'AD gyaran sashin su ,in ta gama Kuma zataje ta dubo Mata lpy Ma'u ,Harri ta amsa da to hajiya ,suka nufi sashin ita d matar yayan . FU'AD ko cewa yayi yanzu dole sai kin aika ? In ta damu ai zatazo d kanta ,Dan ALLAH Kar ki ........be k'arasa ba momcy tace son kafita idona na rufe wlh zaka jama Kanka zuwa dubiya ko Aiken dole Dan umarni Zan baka zazzafa ,wlh zakaja na dawo da Aiken Kanka na umarce ka da kaje ka dubo min ita , in Kuma ban Isa ba sake furta kalmar A Akan Asma'u na shayar da Kai Ruwan mamaki yanzunan ... Aiko FU'AD ya zaro ido ,har Yana sa yatsun sa yana Kama bakin shi yasan kad'an daga aikin momcy in ta d'au zafi Akan Abu ,Dan Haka y kame bakin shi ,be k'ara cewa ufan ba ,har yayan shi na tsokanar shi Amman yak'i cewa komai sai murmushi d nuna Mai momcy da yatsan shi ,yayan ya dinga Mai dariyar mugunta momcy tayi maganin shi ... Anan yayan FU'AD d'in yake gayama momcy zeje wani aiki a Abuja na wata6 ya take ganin za'ayi zai tafi da madam ne ko ya barta anan? duk Abin d tace shi za'ayi Yana nuna girmanta a gare shi . Shidai FU'AD nashi kunne , momcy tace da d'an uwanka ya girma ya kawo min surika ai da ya isheka shawara to be sa niyar girman ba bare ya zama abokin shawara in yayi hankali sanadin Auren ,..... FU'AD yace hmmmm momcy yanzu a Mara hankali Ashe kiketa d'auka na? Ya taso daga inda yake karyawan y zauna kusa d yayan shi yace ai shi kenan ,Ni ban yi girman da Zan ajiye mace ba bawai Dan Banda Abin d Zan ciyar d ita ba ,in Mata 4 ne Zan iya ciyar dasu Dan dai Basu shinkafa,taliya,doya ,sai musu atamfa,shadda duk Zan iya kawai matar ce batazo ba sai tazo tukunna Yana wani shagwaba .. Momcy ce tace duk Abin d zakayi dai kayi kana sani ,sakon daga Alhaji ubayyu Zan baka da ya bani , yayan mahaifin ka duk ranar da ya diro k'asar Nan to da mgn aurenka ze Zo ko kazaba ko ya zab'ar ma ,kuma sai an d'aura zai bar k'asar ,Niko kasan bazan iya tijarar shi ba ,na gama Shan takaicin su tun Rasuwar mahaifin ku in Kuma so kake ka dawo min da abun da ya wuce ne toh ,ayanzu duk wata burga da tijara da zasu min be wuce akan Auren ka ba inaganin aurenka shi ze bani kariya da katanka Mai k'arfi ta karshe daga duk wani tuggun su ko tijarar su yazama na anyi na farko anyi na k'arshe Dan babu wani abun magana daga Haka nasan ,ka ajiye wanan a ranka shi yisa na sanar maka be fad'i watan zuwan shi ba Amman kasan zai Zo d'in tun da y furta Dan kasan yafi kowa rashin son zaman lpy. Duk sai da FU'AD d yayan shi suka tuno wasu abubuwan da suka shud'e tun Kan Rasuwar mahaifin su har Bayan Rasuwar mahaifin su Wanda hakan ya gadar ma da momcy hawan jini shiyisa har yau suke gudun Abin da ze b'ata Mata Rai .. Yayan FU'AD ne yace kaji ko ,sai kasan Abin yi ,in kana gudun b'acin Ran mahaifiyar ka in baka manta tak'addamar da akasha Akan Aure na ba...shiko FU'AD cewa yayi ku Rabu dashi can ya gane masifafe kowa baya Jin dad'in ka a family har Abin d ka Haifa ,in ya mutu kafin zuwan shi mu maje ta'aziya da buhuhunan shinkafa da lemuka kala kala Yana fad'a Yana b'ata Rai ... Ganin tsakanin shi d ALLAH yake magana yasa ,momcy Bata balbale shi d fad'a ba ,Amman sai tace in beyi mutuwar ALLAH ba sai kaje ka kashe shi ai kuje da buhuhunan shinkafar kwa had'a har d na gero ,kai Kuma kayi gadin duniyar tun da Kai bazaka mutu ba ... FU'AD yasan momcy magana ta Gaya Mai Dan Haka be k'ara furta komai ba ,gudun sake b'ata Mata Rai. Shi ko yayan shi cewa yayi , FU'AD yaro man kaza ,Amman komai yarintar ka Haka zamu aurar da Kai ko ga yarinya ne kuje kuyita yarintar ku ,shi dai bai cemai ufan ba y shiga b'acin ran maganar Alh ubaiyyu .. Har su momcy suka Gama shawara ,momcy ta umarci yayan y tafi d matar shi yace amgama Haka za'ayi , har Harri tazo Bayan sun Gama gyaran sashin ,momcy ta aikata gidan su ma'un dubo ko lpy , FU'AD bai k'ara cewa uffan ba sai Danna wayar shi d yake tayi .... Bayan Harri taje t dawo ,ta zayyane ma momcy komai na jikin Ma'u ne babu dad'i ga hanun ya samata zazzab'i shine ya hanata zuwa ,kowa sai d ya tausaya Mata Amman Banda FU'AD ..... Maman Shaheed ce👌🏻 [4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *Fatima Abubakar Shu'aib* (Maman shaheed) _shafi na 11_ *Wanan shafin nakune kuyi yadda kuke so dashi* _Namcy ummu Qaseem_ _ummi Abeeha_ _mmn Ameer_ _Mrs sulaiman_ _daugter ummu ammar_ _maryam bello_ _mmn hafeeza_ _mmn sadiq_ _Aisha_ _mrs nuur_ Kunada yawa💋💋 Teemah namcy team FU'AD😀😉 Washe gari ma Haka ma'u Bata samu zuwa gidan momcy ba ,sai momcy ce ta sake tura Hari don dubo jikin ta har da kayan dubiya tace, amata sannu . Ma'u taji dad'in tubiyar da momcy ta Aiko ,Tana k'ara girmama momcy da darajata Dan irin su Basu da yawa a Halin yanzu ,tace amata godiya sosai da sosai ,sanan Hari ta tafi . Baban Ma'u akai akai yake tmby jikinta da hannun ta in be dawo gida d kanshi ba to zai Aiko haidar ya dubata da jiki Dan ko ya Aiko Aminu Mai bima humaira ma yasan ba zuwa zeyi ba Dan Halin su guda d su humaira d su mmn habee. Ma'u nata kula da hannun ta ,Bata biyema habaici da Gori tare d wulak'ancin da take Sha wajen su humaira d mama habee indai ma'u taji sasauci to babane ya dawo gidan ko Kuma haidar yazo y d'ebe Mata kewa ,da baba Yana bada wani Abin kaiwa Baki akawo ma mama habee nata Dana ma'u daban ,duk d Haka mama habee sai ta ragi na Ma'u wani lokacin ma ahanata gaba d'aya adaki haidar Akan wai in ya Gaya Mata sai anmai duka ,shiko sai ya fad'a ko zasu yanka shi ,Ma'u sai dai ta barsu da ALLAH . Yanzu ko abinci da kyar a wulak'ance ake Bata sbd ba'a morar ta ta hanyar aikatau acikin gidan Dan Haka wulak'ance sai Wanda ta gani .. Wata matace tayi sallama kyakyawa da ita kana ganin ta kasan hutu ya ratsa ta ,tayi sallama ta shigo gidan mama habee . Cikin girmamawa mama habee ta karb'e ta ,ta Bata wajen zama da sakin fuska atunanin ta bak'uwar tace hank'oron ta Abin d zata samu daga wajen matar Dan duk jikin ta gwala gwalai ne ... Matar ce bayan sun gaisa da mama habee ta Fara tmby mama habee d cewa Niko Ina husnah ? (Asma'u) Yar aunty na nuwaira Mai Rasuwa?.. Sai ko mama habee aka rage fara'a ,da kyar tace gata can cikin d'aki ko uwar me takeyi oho tayi ta zaman d'aki kamar sabuwar Amarya .....tun daga Nan bak'uwar ta fuskanci Akwai matsai d takura cikin zaman Asma'u a wajen uwar goyon tata ,Dan Haka tace Bari taje ta ganta ... Mama habee Kar Ayi wani Abu bataji ba yasa tace aa ta Bari a kirata su zauna Anan Mana ,Amman matar tace aa Bata tsaya jira ba ma ta wuce d'akin da aka nuna Mata ,ran mama habee bai so ba .... Matar na Shiga d'aki ta Fara k'arema kallo ,itako Ma'u tanata aikin tunani batasan ma an shigo ba ,sai d matar ta k'are Mata kallo sanan ta Mata sallama Dan dawo da ita hayyacin ta ,d sauri ma'un ta amsa sallamar Tana cema matar bisimillah ! Matar ta zauna a wata kujera da ta gaji da duniya .. Bayan Ma'u ta gaishe da ,matar tace "Asma'u Baki gane ni bako? Ma'u tace "eh wlh" Matar tace "ni Yar uwar mahaifiyar kice 'yan uba muke d mahaifiyar ki tun tasowar mu jinin mu ya had'u da ita ,Nasha duka tsangwama akan maman ki aunty nuwaira awajen 'yan uwana d mahaifiyata Auren d akama mahaifiyar ki aka kawo ta garin Nan gidan Mahaifin ki shine rabuwar ,Nima daga baya akamin Aure ko zama bamuyi ba anan da mijini muka wuce indiya ,gaskia inason Jin lbr mahaifiyar ki Amman Abu y gagara ko sak'o na bayar abata baya samun ta Dan Haka na hak'ura ma daga baya gaba daya zuwana k'asar Nan befi so 3 ba shekara 18 da aurena ,Dan Baki fi shekara da haihuwa ba akamin Aure Kuma yanzu so 1 na taba kawowa mahaifiyar ki ziyara sai yanzu na biyu Dan ko Rasuwar ta da jimawa kafin nazo k'asar Rasa sanin Wanda zanma gaisuwar ta yasa d nazo last banko Zo gidan kuba sai yanzu ... Ma'u da matar duk atare suka nisa ,Sanan matar tace Naga kamar kina zaman hak'uri ne acikin gidan Nan ko? Ma'u tace aa ,matar tayi murmushi tace karki b'oye min Ni Naga wasu abubuwa, sai Ma'u tace babu komai wata Rana sai lbr ,matar tace Amman Baki d matsala d mahaifin ki ko Akwai? Ma'u tace wlh babu duk duniya bani da Mai Sona kamar shi ,ma'un na kalon k'ofa Tana rage sautin maganar ta , matar ce tace "lpy naji kinayin k'asa k'asa d mgn ki ? Sai ma'un ta nuna Mata k'ofa ,tace ,Ana Mana lab'e ne, Haka akeyi indai Zan keb'e da wani ,matar ta sake tausayama Asma'u ,ta d'ako kud'i ta Bata sanan tace zata dawo Rana ita yau Ana gobe zata koma Dan ta kusa tafiya , ALLAH yajik'an mahaifiyar ki" duk d ban yadda da Mutuwar ta ba , mgn ta fito ne batare da matar tayi tunanin anji ba,Amman ALLAH yaji kanta zamuce kawai .... Sai gaban Ma'u yabada Rass! Tace me kikace ? Sai matar tayi saurin cewa aa Babu komai kinji karki sa komai a ranki ,ki kasan ce Mai yi Mata Addu'a a Koda yaushe ,muma munata binta dashi har kushewar ta ,ita dai ma'un shiru tayi Amman ta Adana kalaman matar cikin ranta ,itama matar k'asa k'asa take mgn ,har ta mata sallama ta tafi ,Ma'u har waje ta rakata... Mama habee lif tayi a d'aki bayan ta gama Jin wasu abubuwan da suka tatauna akai ,daga d'aki ta amsa sallamar da matar tayi Mata ma.. Bayan Ma'u ta dawo ta Adana kud'in ta cikin ganamost go d'in ta tasa kwad'o ta had'e bakin zif d'in Tana tunano amfanin da kud'in zai Mata Akan kudirinta na makaranta .... Bayan mama habee taci wuya da itacen ta Mai hayak'i ta Kamala musu girkin Rana ,ko hutawa batayi ba Aminu ya shigo Yana cemata yunwa yake ji ,sai ga humaira ta dawo daga yawon bin gidan kawayen ,itama ta dawo da yunwar ta ,haidar ma ya shigo karban ma baba nashi ,sai ga ma'u ta fito ta zauna ita da batayi mgn bama sai tata tafi zafi ,ai ko ta Fara surfa musu ruwan ashar da masifa wai su ciki suka kawo duniya babu shegen d ya iya Mata sannu sai gyara bakin ci Dan ubansu d shima harda dogon aike baiwar d ya Gina ta Kamala ko? Ma'u duk tafi Jin zafin mgn da aka jefi mahaifin ta dashi ,can Kuma tace ita da ALLAH ai ,su humaira sunsha masifa kafin aka basu abincin ba Wanda ya kulata Dan sun San kad'an daga aikin ta ta hanasu kwatakwata ,aka zuba wani d'an kad'an aka jefi ma'un da shi akace mayya kafin ki had'iye Ni ..... Ma'un ta d'auka ta nufin d'akinta ,ta zuba Danbun Naman d momcy ta aiko Mata cikin shikafar d kamar jik'ata akayi ta samu ta d'anci badan ya ishe ta ba ,Bata Isa ta nemi k'ari ba Kuma ,da Danbun Naman ta sake ciko ta Sha rogowar pure watan ta ta Shiga nazarin Rayuwar ta ..... Maman shaheed ce👌🏻 [4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *Fatima Abubakar Shu'aib* (Maman shaheed) _shafi na 12_ *Ina bukatar Addu'ar ku fanc next week Zan Fara exams ba lalai kujini ba ,ina godiya da kulawa da yabawa*👏🏼👏🏼😍 _Dedicate to oll Rik'on kwarya fanc_ ❤❤❤❤❤❤ Ma'u ta Jima Tana nazari ,Akan hiran su da matar da tace Mata k'anwar mahaifiyar tace ,ga Kuma tarin tmby da ta Adana Wanda ba a bakin da take sauraron amsoshin su zai a bakin mahaifinta baba (mlm usmanu) Dan haka dawowar shi kawai take jira ... Ma'u Basu had'u da baba ba sai dare ,mama habee d sababin ta ya Hana Ma'u ganawa da mahaifin ta Dole ta hak'ura zuwa gobe ... FU'AD ne ya zako k'asa cikin shigar sa ta tafiya _office_ shigar shi ta burgewa da Kamala yanata zuba kamshi ,ya Shiga d'akin momcy ya tsuguna har k'asa ya gaishe ta da girmamawa "ta amsa cikin kulawa Tana tmby y ya kwana? Ya Bata amsa da "lpy Lau " Tace "Masha Allah" anfito za'a tafi nasan wanan Shirin tafiya Aiki ne wanan ,Amman Bayan kayi break ko? FU'AD yace "yes my mum "Addu'a ki kawai nake jira Bayan mun Gama break d'in . Momcy tasowa tayi suka tafi wajen karyawa... Bayan sun Gama , FU'AD y d'auki jakar sa ,yace momcy saura Addu'ar ki? Momcy tace "ALLAH y kaika lpy ya dawo min dakai lpy har gidan Nan ,Kuma akula d hakkin mutane da kanka. FU'AD yace toh momcy ,Ameen insha ALLAH Zan kula ,ngd. Har yayi hanyar waje y dawo yace ,yauwa momcy idan wanan Asama din Taki tazo ta gyaramin sama gyara Mai kyau Mai tsafta kice Mata momcy kinsan yarinyar ,she is dirty girl sai Ana jadada Mata ... Momcy ce tace "ka Gama ? Uban mutane? To batazo ba Bata da lpy kace Bata da Amfani agareka Amman kana morar lpyr ta ,to yau sai kayi Abin da takema ai ,Dan batazo ba har yau ... FU'AD yace ,Kai momcy ya kike hakane ,kawai dama malalaciya ce ,dg ta d'anci ciwo sai ta fake dashi take kin zuwa yi Miki hidima ,Ni badan gyaran bama meze had'a ta da zuwan min ko k'ofan falo be bare har ta shigar min falon zuwa room ma ? Kawai ma danke Kika Fara aikata da izinin ki ta Fara shigar min ... Momcy ce tace"suda sarkin lbr ka wuce ka tafi yaudai ba Mai maka gyara ,in Kuma gidan su Ma'u zaka ka d'auko ta toh da zefi maka wanan dogon turancin Mara dalili ,Dan Banga meyima gyara ba yau d'inan tunda babu Asma'u. Tun lokacin da momcy tace ko zeje gidan su Ma'u .......ya kafeta d ido Yana tuhumar mezeje yi, itako momcy ko kalon inda yake batayi ba har sai da ta gama maganar ta . Aiko ,Yana ganin ta dire mgn ta yace "haba momcy Ni gidan su _dirty girl_ like Asama take ko wa ma? Me yayi zafi da gemu zai ci wuta momcy? Tasha zaman ta har sarkin zama yazo ya sameta wlh ... Momcy tace "kamar yadda saman ka zesha zaman shi da kazanta har mahadi ya bayyana ba indai ma'u Bata Zo ba ,Kuma nida Kai a gidan Nan matuk'ar baka canja halinka ba da ka aro .. FU'AD cewa yayi ,Ni momcy bansan meyasa Kika cewa na canja ba ,Ni nama tafi sai na dawo ,barin lek'a mu gaisa da big bro ,Yana mita Akan Ma'u .. Momcy tace , ALLAH ya kiyaye adawo lpy. Ma'u nata son mgn d baba ,da kyar t samu baba habee ta Shiga mak'ota da sanyin safiya wai ta tafi sama wata Mai jego ruwan wanka ,ita Kuma humaira ta tafi siyo awara wani gidan ... Ma'u ce ta gaishe d babanta ta ,Fara da cewa ,baba Niko kasan wata k'anwar mama ,wacce take Aure a *India*? Baba yayi ajiyar zuciya yace "Ma'u a Ina Kika samu wanan lbr? Ma'u tace ,zuwa tayi shekaranjiya , baba ya nisa Sanan yace "eh nasanta huwaila sunan ta ai " Kuma mutumiyar maman kice 'yan uba suke ,dake mamanki ita kad'ai ce wajen mahaifiyar ta sakamakon Yan uwanta da suke Rasuwa d an haife su babu wanda ya zauna araye sai ita .. Baba yayi shiru alamun tunanin wani Abu yake ,Ma'u tace baba cigaba Ina sauraron ka na Jima Ina buk'atar wanan Rana ta tarihin Rayuwar manana da dangin ta Koda yaushe nama mgn sai kace nabar wanan mgn Dan ALLAH baba karka ki bani lbr komai ... Baba yace ,ma'uta ,wai me matar ta Aiko ki ki tmby Ni ? Wanan ba tunanin ki bane , Ma'u tace "wlh baba babu abin d ta turo Ni in tmby ka ,nice dai nake son sanin wani Abu kamar yadda ta shigo rayuwata kwatsam . Baba yace Ma'u ,banaso kisa komai aranki ,mamanki dai ba Yar Nan bace ta taso cikin Yan uwanta kamar yadda n Gaya Miki babu masu k'aunar ta in Kika cire mahaifinta da mahaifiyar ta sai wanan huwaila Dan sauran Yan uwanta duk tsangwamar ta sukeyi ,Nasha wuya kafin n Sami aurenta ,babu Mai zuwa wajen ta sai huwaila itama ba'a sani ba take zuwa ,tun Bayan aurenta ta Dena zuwa Dan ban k'ara ganin ta ba ,nadai San zuwanta so 1 ,sai lbr d ake cewa Tana yoma mamanki aike aki Bata ,to tun Bayan Rasuwar maman ki sai yanzu a bakin ki na sake Jin lbr ta . Ma'u tace baba kamin tsalake cikin lbr ... Baba yayi murmushi yace Ma'u ta karki k'ureni Mana, me kikeson ji Kuma? Ma'u tace cigaban lbr ,Ina kakata da kakaba yanzu? Baba yace ,sun Rasu tun Bayan Rasuwar mahaifiyar ki sakamakon hatsarin mota ,wacce ta rage yanzu kishiyar kakar ki wacce tafi kowa tsanan mamanki a Nan duniyar ,ko inda maman ki ko kike Bata tab'a kallo ba ,kuma Tana Raye gidan ko dama ita ko wani nata be tab'a zuwa Nan gidan ba ,suka tatara gado suka cinye ,mahaifin ki da mahaifiyar ki dama ba wani dangi ne dasu anan ba sosai ,ita mama ki iyaye ta Y'an yamen shiko kakan ki d'an Mai duguri Ne ,bansan wasu dangin mamaki ba sosai shiyisa nacigaba da ganin ki da tatalin ki da rik'e amanar ki tamkar yadda na rik'e amanar mahaifiyar ki shine sakamakon da Zan Mata na nuna soyayya ga Abin da ta Bari tun Bayan Rasuwar ta ... Ma'u tayi narai narai da ido kwala na son fitowa ,tace "toh baba bani lbr raduwar mahaifiyata ? Baba sai da wani mumunan fad'uwar gaba ta ziyarce shi ,ma'un ma ta gano yanayin d y Shiga yace "Ma'u mamanki ta rasune tun Bayan haihuwar ki da shekara 1 akamakon mutanen b'oyen ta (aljanu) da suka tashi ta fita cikin dare ta barki ,taje mota ta bigeta shikenan ta fad'i atake Rai yayi Halin shi Bata ko shura ba ,baba ya fashe d kuka ,itama ma'un kuka takeyi sosai ,sai taji ta gamsu da bayanin mahaifin ta Amman zuciyar ta nason k'aryatawa adole ta hak'ura da son k'aryata baba da zuciyar ta keson yi .. Sai d suka k'oshi d kukan babu Wanda y rarashi wani sanan baba ya rarashi ma'u da kalamai masu dad'i har Yana cewa shi zai zamar Mata jigon Rayuwar ta matuk'ar Yana Raye bazatayi maraici ba duk d yasan Tana cikin maraicin kodan azabtuwar d takeyi awajen mama habee ,to tayi hak'uri ta jure wata Rana sai lbr Yana iya k'ok'arin shi ,ta d'auka hakan shine jarabawar ta ta Rayuwa ,babu Wanda zai ji dad'i d'ari bisa d'ari mahaifiyar shi ko mahaifin shi baya gida sai k'alilan azamanin yanzu sai Wanda yayi kyakyawan Dace da mariki na ALLAH ... Nasiha sosai baba Yama Ma'u ,taji Kuma ta d'auka ,daga baya ma'u take cemai ,aunty huwaila k'anwar mamanta tace zata dawo ta Mata sallama yau saura kwana 5 ,baba yace indai tazo ko Yana wajen siyar da hatsi ta kirashi ,Ma'u tace toh baba ... FU'AD bai tashi sanin Mata suna Aiki ba ,sai d ya dawo yaga da gaske momcy take ko tsinke Bata bada umarnin a d'aga daga saman Shiba ,duk d komai kamar yanzu aka siyo shi ga tsafta irin ta FU'AD Amman komai Yana son gyara ,don kwaliya Tana biyan kud'in sabulu ,komai a tsaftace yafi dad'i da sa nishad'i ,... Har y nufi momcy d k'orafin don me ba'a sa wani y gyara Mai saman shi ba ,duk ma'ai katan gidan kusan 4 ,sai kuma y tuna indai momcy ce tunda har Bata Aiko ba toh da Shirin d tayi ,kawai y kawar d Abin d zai iya kawar wa ya barma gobe sauran ... Don Haka ya rage kayan jikin shi yabar short niker ya Shiga gyara kafin kace me wai har y gaji , toilet d'in d ya wanke d kanshi ma gani yayi bai fitar Mai yadda yake so ba ,Amman y zeyi Haka ya hak'ura y k'arasa Yana mita ,Yana cewa Dole y Nemo sabuwar Mai Aiki Amman girman shi yafi ace yau first time in history yayi gyaran saman shi d kanshi duk ma'aikatan gidan d matsayin shi wajen momcy shi Amman wata banzar yarinya nason kawo Mai sab'ani tsakanin shi d momcyn shi abar Alfaharin shi uwa ta gari agare shi ? Ya sake cewa "in ALLAH y yadda ma'u ma ta bar gidan kenan da aikin........ *Maman shaheed*👌🏻 [4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *Fatima Abubakar Shu'aib* (Maman shaheed) _shafi na 13_ FU'AD yayi mita kamar ba gobe ,ya k'ara tsanar Ma'u da ba ita ta kar zomon ba ,ya Gama jagwalgwalon shi ya barshi Haka ,yayi wanka ya saka k'ananun Kaya marasa nauyi ya sauka k'asa . Yana sakkowa ya Sami momcy da su yayan su da matar shi sunata Hira cikin Jin dad'i da fahimta ,da ya sako da d'an takaicin shi ganin ba Wanda ya tmby shi d sani me ya aiwatar a saman yasa shima ya saki Rai da Fuska ya shiga hiran anata Raha Ana dariya ,har suka ci Abin cin dare gaba d'ayan su ,amaryar (sa'adiya) Yaya dai yanata mgn Akan Ma'u ,momcy na cewa zata aika gobe ak'ara dubo Mata jikinta insha ALLAH. FU'AD ko wani abune yaji ya tokare k'irjin shi ,Amman yasan Yana furta wata kalma momcy zata mayar Mai d martani wata k'ila ma yafi nashi zafi ,don Haka yayi shiru ya ci gaba da Hira da yayan shi ,Suma sukaci gaba da tasu har suka kammala ... Sunjima suna Hira har sallah anan sa'adiya tayi ,sai d sukayi isha'i sanan suka koma sashin su ,shima FU'AD sama ya koma wai zaiyi Aiki a *lap top* d'in shi na office,Amman zai dawo yi ma momcy sai da safe ,tace "asako lpy son" Ma'u dai anrabu da takaicin FU'AD Amman anata karb'an na iyalan mama habee ,awajen baba kawai take samun sauk'i ,hanun ta Kuma yayi sauki sai Abin d ba'a Rasa ba . Washe gari mumcy ta Aiko duba Ma'u baba Yana Nan ,har yaji harin nacewa mumcy tace in hanun har yanzu beyi sauk'i ba ko gobe tazo kuje asibiti indai kinajin da saura har yanzu? Ma'un tace aa hannu yayi sauki ba sai munje asibiti ba .....baba ma yace ai to sai kiyi k'ok'arin zuwa taga lpy hannun tunda Kinga tanata aike _wanda ya damu da kasuwa shike Mata sautu_ Dan Haka ko gobe ne sai ki lek'a kinji ma'un baba? Ma'u Bata zab'in da ya wuce na cewa toh! Dan baba ya ari bakinta yaci Mata Albasa tare da Bata umarni Kuma a gaban Hari Dan Haka tace "agaishe da hajiyan Kuma Gobe zatazo ta nuna Mata hanun ,Haka Hari ta Mata sallama ta Bata sak'on momcy ta tafi ma da momcy gamsashen bayani daga ma'un. Ma'u Bataso komawa ba gidan yanzun ma cewa tayi d momcy taga hannun ta zata dawo Kuma bazata koma ba sai Abin d Hali yayi .. Washe gari ma baba sai da ya k'ara yima Ma'u mgn tafiya gidan hajiyan badan kwad'ayin Abin hanun su ba sai dai kawai Wanda duk ya darajaka kaima ka daraja shi ,Kuma a yadda ya lura Basu da kyamar talaka ahalin gidan Kuma Yana ganin ma'un na samun sauk'i ta hanya biyu intaje Aiki gidan ,farko takan biyama kanta bukata d Dan abun d ta samu Dan ko sisi be tab'a karb'a daga ma'un ba ,na biyu Tana hutawa daga tsangwamar mama habee da wulak'ancin ta intaga baya gidan ,Dan Haka ya dinga Mata nasiha d y fuskanci kamar Bata son zuwa ,taji nasihar Kuma tayi naam da ita ,tace Bari taje ta shirya ma ,baba yace "ALLAH ya Mata Albarka tayi sauri su fita tare Dan d wuri ze fita yau. Bayan ma'u ta shirya cikin wata tsohuwar atamfa Riga d zani da tsohon hijabin ta daya gaji da duniya ,ta fito suka Fara Shirin fita d baba .. Aiko mama habee ta dinga Yar musu da habaici Tana ,uba zaije bikon yarsa ,waya sani ma sammaci aka kaso muku kuketa b'oye b'oye ,in tayi wari maji ,Amman ai munsan banza Bata Kai zomo kasuwa ,Haka kawai baza a gurgud'e hanu a banza ba ,da baba zai mayar Mata d martani ,sai Ma'u tace Dan ALLAH ba karkace komai ba yadda mama habee zata ji ba ,Dan inta ji wata sabuwar jarabar ce zata biyo baya . Ahanya baba da Ma'u suka Rabu ,Ma'u ta nufi gidan hajiya babba ,Tana Shiga ta samu Mai gad'i suna mgn da FU'AD gabanta ne yayi mumunan fad'uwa ,da kyar ta iya karfin Halin gaishe da baba Mai gadi sanan ta gaishe d FU'AD badan taso ba , FU'AD k'in amsawa yayi sai d Mai gadin yace yallab'ai Ana gaishe ka ,sanan yace "lpy nake " Yana Mata wani kallon gargad'i ,sanan ya Gama ba Mai gadin sautun in Mai wanke motar ya k'araso ya wanke Mai farar ya kaimai office ya dawo da jar gida ,baba ya amsa da "to yallab'ai angama insha ALLAH. FU'AD ya juya Yana tafiya yaji ,baba nacewa sannu ya hanun naki ? Daftn kinji sauki ko ? Ma'u tace "eh yayi sauki haun Alhmd na suna arziki buk'atar Mai yi Bata biya ba ,ngd baba , FU'AD sai ya Fara tmby me _dirty girl_ d'inan take nufi d kalamanta ? Ganin y Gaza gano manufarta yace "ita ta sani " yayi gaba Abin shi zuwa Gama shirin shi na tafiya office... Yana Shiga Fallon ,Ma'u ma ta shigo ,momcy sai ta saki Fuska Tana ma ma'un murmushi fiye da yadda ta sakar ma FU'AD d'in ,Aiko FU'AD sai ya Fara mamakin momcy da kishin Ma'u lokaci d'aya ,wajen break y wuce ya Fara yanayi Yana tunanin k'untatama Ma'u kafin yabar gidan ... Ma'u har k'asa ta tsuguna ta gaishe da mumcy ,momcy cikin sakin fuska ta amsa Tana nuna Mata wata kulawa ta musamman , FU'AD na daga gife Yana cizon yatsa .. Momcy har hannun ma'un sai d ta tab'a don tabatar da gaskiyar lpy hannun wai Kar Ma'u ta b'oye Mata , Ma'u tace "wlh hanu Alhmd har Ina iya d'aukan Abu dashi ,don momcy ta gwada ta tace toh taje wajen Hari ta karb'i break d'in su Yaya FU'AD takai musu sashin su tanata tmby ta tajita shiru , Ma'u tace "toh momcy Bari ki gani " ta tafi ta karb'o kayan Karin duk d hanun d sauran d'an zafi kad'an da yake Mata ,Amman ta daure ,ta d'ibi kayan ta Kai musu Bayan ta Shiga amaryar yayan ta Fara samu ,ta gaishe ta Tana tmby hanun ta ,tace "yayi sauki wlh "ngd ,tace Babu komai dama Akwai wasu Kaya d nake son Baki karki tafi bakimin mgn ba kinji Asmah? Ma'u tayi murmushi tace toh ngd ,sunan d take kiranta dashi ji take kamar iyayi ne da tsabar gayu Dan Haka ma'un takejin suna wani Abu Daban. Bayan Ma'u ta gama Kai musu komai ,momcy tace"toh yaushe Zaki dawo Aiki? Ma'u sai taji nauyin hajiyar "tace ko yaushe ma ,yanzu me Zan Miki na Miki shi ? Sai momcy tace ,aa ki Bari hannun y k'ara warkewa gaba d'aya karki takura kanki Asma'u ,sai ma'un tace "Babu komai hannu Alhmd fad'i ko meye na Miki kawai hajiya . Kafin momcy tace ufan , FU'AD ya wurgo mgn ,haba momcy ma'aikaci yasan aikin shi Yana buk'atar ki bashi ke Kuma sai hanashi kike ,Alhalin shi hangen wata yayi ya karbi Albashin shi Mai kyau yakeyi ,Ni taje ta gyara min samana Kuma gyara Mai kyau banason k'azanta a tsaftace min ko Ina da komai ....momcy ce ta amsa da son ka dinga tsaftace kalamanka Ina sake tuna ma ,Ma'u Kuma ko tamin Aiki ko bata min ba ihsani yakan iya Shiga tsakani na da ita ko ba Dan tamin wani hidima ba ,aikin samanka Kuma sai Abin da tace ,in taga bazata iya ba Babu Mai tursasa ta ,sanan sai ta gyara min falo kafin ,intaji ta gaji bazata iya aikin saman naka ba ,sai kowa ya hak'ura . FU'AD ya Shiga mamakin kalaman momcy ,yace "itafa tace Miki taji sauk'i momcy ,ita ta nuna kwad'ayinta da aikin ,wai Ni aikin nata gaba d'aya na nawa ne nayi cinikin shi ta zama Mai hidimar samana kawai agidan Nan nawa takeson a biyata ta fad'a ko nawa ne ,ganin momcy ta tafi tunani......sai kawai yace ke _dirty girl_ nawa kike son abiyaki ai kinji bayanina dake nake bada wani ba duk kin tsare mutane da mayunwatan idanun masu fad'arma da mutum gaba indai yayi arba dake ,Dan Haka bana had'a Ido dake sosai ....ina jinki .. Ma'u dai ko kallo FU'AD be ishe taba ,Momcy tace ,son , Asma'u ba kwad'ayin tarin dukiyar dake gidan Nan ne ya kawo ta ba ,hasali ma ita aikin Nan sunan shi *RIK'ON KWARYA* a wajen ta Dan hafeeza ce tab'ata shi amatsayin *RIKON KWARYA* Kuma kusan Dole hafeezar tayi mata in baka sani ba yau ka Sani ba hajaran majaran tazo neman shi ba ..... FU'AD yace ,Amman ai Tana son tukwauicin Aikin don.......momcy ce ta dakatar tashi ,barni na sauka .. Da kake ne man na sadaukar ma da ita,ko siyarwa ,kasani batayi arahar Haka ba ,aikina takeyi a gidan Nan bana kowa ba ,Kuma kamanta furucin ka na ta tsaya a iya hidimata da ka tab'a cewa? Ina tuna ma ,sai dai ka Nemo wata ai kanada Abin da zaka iya biyan ta ko miliyan nawa ne to kaje ka nema in kaso ma ka tafi k'asar fararen fata ka Nemo nasan Arzikin ka yakai Haka koma yafi Amman Asma'u tawace in kayi biyaya ne Zan taimaka ma itama ta taimaka ma d wani abun ,Albashin ta Kuma acikin jakata Zan dinga biyanta Daman ban tab'a cewa ka bata Albashi ba ko na tab'a? FU'AD dai ya Gama zuwa wuya momcy ta gama dashi a gaban _dirty girl_ Haka ,Amman Dole ya fanshe haushin shi akanta .. FU'AD tashi yayi yace momcy Ni yanzu basan matsayina bama a wajen ki,Yana mita Yana Hawa saman shi ,momcy tace kana Nan a *Son* d'inka Abin Alfaharin momcyn shi autan ta Babu kowa bayanka ,har ya kure hawan matatakalan ya juyo ,yace aa momcy Ina kokwanto sai munyi zama harda big bro gaskiya ... Ma'u ji tayi ranta fess kamar FU'AD be tab'a Mata laifin komai ba ,gaskia momcy ta cika uwa ta gari Abin Alfaharin kowa ,itama inama ace tata na Raye taga gata Haka? Momcy CE ta dawo da inta dg tunanin d ta Lula ,tace tashi ki gyara falon Nan Asma'u ai zaki iya ko? Ma'u,"tace ba Dole ba yadda Kika faranta min momcy ,tace eh , Ma'u ta mik'e ta Fara Aiki . FU'AD y sako fuskar Babu walwala sai kamshin turaren sa dake tayima kowa murmushi ,yayi hanyar waje zai fice ,momcy tace "son" ko sallama Babu yau Addu'a tawa ma ba'abar nema bace ? Sanan ya dawo ,yace afuwan wlh na manta ne ,momcy tace sbd na tab'ama ranka ko? Yace aa ,tace to kasaki ranka dai kayi Aiki lpy cikin farincikin da Aminci ,momcy nama fatan zuwa lpy da dawowa lpy ,Kar kasa komai ranka kaji autan hajiya ? Sanan ya d'anyi murmushi yace toh ,uwa ta gari ,ya juya ya wurgama Ma'u uwar harara da kwafa ,sanan yayi niyar ficewa ,momcyn ma tashi tayi ta Shiga d'aki Bayan FU'AD ya fice ... Ma'u nata gyaran ta ganin Babu kowa a falon harda cire hijabi ,tanata Aiki batayi aune ba sai shigowar FU'AD ta gani Babu ko sallama ,afirgice t rarumo hijabinta a kafar benan da zai hau ,d tazo gab d shi ,y kamo kunnen ta d k'arfi Yana hucci yace "wlh ki kiyayi gamuwar mu ,Kuma wlh idan nadawo Baki gyara min samana ba ,wlh sai kin yabama Aya zak'in ta _dirty girl_ kawai y dungure ta sai d kanta y d'an had'u da karfen benen ,taji zafi tace wash ALLAH na ,da taga ya haura sama Yana Shirin kulewa tace , ALLAH dai ya Hana zalunci ,yajita Sarai ,Amman a tunanin ta tunda taji yayi shiru be ce komai ba to be jiba ..Dan Haka taci gaba d aikin ta Tana cewa Dole ta kwaci 'yancin ta wajen mugun Nan kafin ya ilata ta. Da ya sakko ,ya nufota ,Yana cewa Maimaita Abin da kikace d'azu ? Ganin Babu Mai kwatan ta ,ta Fara ja da baya har seda y rutsata jikin bango taga Bata da Mai ceto ,tace "Ni wani Abu nace? To mema nace ? Ni Babu Abin d nace ,Yana Shirin yi Mata wata muguntar yaji momcy na Shirin fitowa da sauri y rankasheta y barta a wajen yayi hanyar waje Yana wlh zata sani ne har Yana Shirin tuntub'e ... Ma'u tace dama ,mutum y fad'i ,mugunta ai fitsarin fak'o ce ,tasan ya jita ,taci Alwashin Dena saurara Mai Kuma tunda tanada mumcy Mai bin Bayan gaskiya... Maman shaheed ce👌🏻 [4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *Fatima Abubakar Shu'aib* (Maman shaheed) _shafi na 14_ *Ma'u na Miko gaisuwa masoya ,har FU'AD din ma ,🤪Wanda duk bai Amsa gaisuwar FU'AD ba yayi missing*🤪🤣🤣 Ma'u da wuri ta Kamala komai da niyar barin gidan taje ta huta a gida ,har saman FU'AD d'in ta gyara Mai Dan ALLAH badan shi ba . Ta ma momcy sallama zata tafi ,momcy tace toh! Amman intaga goben d matsala basai tazo ba ta huta ,Dan lpy uwar jiki ce ,ma'un tace Babu komai naji sauki ma zanzo insha ALLAH indai Ina Halin lpy Zaki ganni . Momcy tace to Asma'u ki gaishe min d jama'ar gidan ,tace to zasuji insha ALLAH ,Tana Shirin fita sa'adiya matar Yaya t shiko da wata k'atuwar leda Mai kauri irin wace ake bayarwa wajen shopping na kasashen waje ,ta mik'ama ma'u . "Tace yauwa Asmah ga sak'on d nace kizo ki karba ,nayi tunanin kin tafi ne ma na kawo momcy ta ajiye Miki zuwa gobe najiki shiru ,wasu Yan suturu ne Babu yawa ki saka ,sbd Jin dad'in yadda kike hidima d momcyn mu muma . Momcy tayi murmushi tace Masha Allah, Asma'u na godiya ,ma'un ma tace "ngd ngd sosai aunty ALLAH ya saka da Alkhairi ,hajiya Kinga Abin arziki daga Aunty babba ta mik'a Mata ledar . Momcy ta tatab'a acikin ledar tace ,nagani Ina tayaki godiya . Sa'adiya tace la Babu komai kunfi Haka awajena ,momcy ko kare Kika nunama kulawa muma zamu kula dashi bare mutum Mai girman daraja . Momcy tayi ajiyar zuciya tace abinda nakeso son y fahimta kenan ,da yanada wanna fahimtar Amman yanzu y rik'id'e zuwa wani Abu daban ,bansan meyasa ba wlh . Sa'adiya tace indai ba Haka yake ba zai canza daga halayen aro zuwa nashi managarta kamar yadda naji yayan shi na fad'a karki sa wani Abu aranki ko ki takuramai da yawa momcy insha ALLAH zai yi yadda kike so . Momcy taji dad'in kalaman sa'adiya tace ALLAH yasa ,Ma'u da sa'adiya sukace Amin atare . Ma'u ta k'ara yi musu godiya ta yafi murna fal cikinta . Bayan awa biyu da kwata da tafiyar Ma'u , FU'AD ya shigo Yana Mai sallama d nuna alamun gajiya Tatare da shi . Momcy ta Mai sannu d zuwa ,yace Bari yaje sama y watsa ruwa Yana sakowa yanzu . Bayan y haura y Fara mita momcy n jiyo shi ,hmmm ALLAH yasa _dirty girl_ d'inan batayi abinda n bata umarni ba laifinta ya doubling kenan harda rashin kunyar d tamin d'azu ,Yana bud'e k'ofan Fallon shi wani sasanyan kamshine ya Doki hancin shi gami d sanyin easy dake mak'ale a yalwatacen Fallon ,Kuma yaga ko Ina very clean and neat ,Amman Haka be bashi damar yabo ba sai ma sukar wadda tayi aikin ya sake kutsa Kai bedroom ko zai gano Abin k'orafi ,shima sai tashin kamshi yake ,sanan ya koma bathroom zai taking bath shima sai kyali da kanshi ,Mai makon godiya sai kwafa d tsaki da yayi Yana ayyana ,dama batayi ba d ta karbi gwagwab'an hukunci harda rashin kunyar d tamai ga bijirema umarnin shi ,amman hakan ma tanada hukunci Mai tsoka na fitsarar d tayi Mai . Bayan y watsa ruwa y saka k'ananun Kaya ,ya feshe jikin shi d turaruka masu dad'in Kamshi n saudiya ,ya sakko k'asa .. Yana zuwa ya kwanta kusa d momcy ya d'ora kanshi Kan cinyan ta ,momcy tace toh yau Abin ya motsa shagwab'ar ta taso . FU'AD ya yamutsa fuska yace ,yaushe rabon d kimin tayin cinyan ki uwa tagari Mai Albarka ,Sam kin dai na ji Dani sai wani fad'a ma da kike min a kwanakin Nan . Momcy tace inaji da auta na ,fad'a Kuma In kaga bayi maka Akan gaskiya nayima , Kai Kuma yanzu Naga ka canza bakason fad'an gaskiya ,amman son aduniya Wanda y Rasa Wanda zai Mai fad'a yayi kuka ,fad'an ma gata ne . Sai ko FU'AD yace yauwa momcy ,Kan mgn Alhaji babba ,wanan shirmen d yazo Miki dashi nifa wlh sai dai y aurar d wanan bushashen yaron nasa Amman bani ba ,Dan ban Isa rik'e iyali ba . Momcy tace yayan mahaifin nakane yake shirmen? Son , FU'AD yace ,toh momcy inba shirme ko takura ba tun dady na Raye Basu barmu mun huta ba har ALLAH y karb'i rayuwan shi suka dawo kanki ,daga baya suka sako Yaya Jamil agaba sai da yayi Aure suka hakura sanan yanzu ze dawo kaina me muka tare musu a Rayuwa ne? Momcy tayi ajiyar zuciya tace ,bamu tare musu komai ba . FU'AD yace duk dady ne y ki kwatan Mana 'yancin mu ,Bayan ya Rasu Kuma zamu kwata d kanmu Kika dakusar damu ,shine har yanzu abun yak'i karewa ....Ni wallahil Azeem.......momcy tasa hannu ta toshe Mai Baki . Son bana son Jin wata kalma Mai had'e da Rantsuwa Kuma tsakanin ka d Alhaji mala biyaya matukar bece karkabi ALLAH da manzon sa ba,ka zuba Mai Ido Akwai shirina Nima na k'arshe Akan shi ,inace Auren ka shine final? Babu wani Abu d zasuce Kuma? FU'AD yace tunda sun Saba sunacin bulus ba'a tab'a musu komai ba ,Bayan Auren nawa ma sai sun billo d wata fitinar wlh momcy ... Momcy tace na maka Alk'awari daga Auren ka anyi na farko Kuma anyi na k'arshe ,biyayya iya biyayya munyi musu . FU'AD yace toh Ni momcy ai ban Isa ajiye iyali ba ,banma San me Auren ke nufi sbd yarinta ta ,momcy sai da ta Dara sanan tace "son kenan autan momcy wato Auren ma baka San manufarshi ba tunda yazo kanka? Bare kasan ma'anar iyali ,ga yaro sabon mutum Wanda aka Haifa yanzun Nan ko? FU'AD ya fututuke yace ,eh Mana Ni yaro ne wajen uwa ta gari Abin share kukana . Momcy tace Kai dai kayita Addu'a ,idan Auren yazo Meka Rasa ? Mahali? Aikin yi? Ko Arzikin bikin? Babu ko d'aya fa ,wani ma yanzu zaka iya aurar dashi ka bashi muhali da jari acikin Arzikin ka da ka gada da Wanda kake nema na kanka yanzu son ,kawai dai tsarin Auren ne Babu shi a gabanka yanzu . Da sauri FU'AD yace ,yauwa azo wajen momcy hakane ban shirya ba gaskiya . Momcy tace Kuma Aure Dole afareka ko cikin shiri ko ba cikin shiri ba ,don Naga Alamar kaima ba lokaci zaka Samar ma kanka ba ko anbarka zuwa gaba . FU'AD yace ,sbd me zakice Haka momcy? Tace "yanzu kamar Nan d yaushe kake ganin zaka iya Auren? FU'AD sai d yayi nazari sanan yace "Nan da 15 years haka . Momcy ta zaro ido ,tace "kaji shirmen ba? Lokacin jikoki sun cikamin gida insha ALLAH in ina Raye ,wlh bana tare da Kai a wanan tafiyar nidai kaji abinda yayan mahaifinka ya sanar maka ,Ni Kuma itace damar d Zan Gama Basu ta k'arshe a Shiga sha'anina d iyalina . FU'AD cewa yayi badai shi za'ayima Auren Dole ba ,momcy tace shidai y Fara Nemo Mata in ba hakaba yace d kowa ma zai iya had'a shi . Sun Jima suna tataunawa ,in momcy ta b'illo ta Nan FU'AD ya b'ille ta can ,har ya tashi y tafi masallaci . Washe gari , Ma'u bataje Aiki ba sbd baba bayajin dad'i tun da taga baze fita itama ta hak'ura d nata aikin ,Mana habee ta dinga Yar Mata d mgn wai munafuka kamar ta fita iya jinya ,itako humaira ta bad'ad'a yawon ta wai Kai d'inkin wani anko da wani saurayinta suka tafi . Koda momcy taji shiru ,sai tayi tunanin ko jikin ma'un ne ,Dan Haka bata saka komai cikin ranta ba ,shiko goga FU'AD harda barin sak'on inta Zo ta gyara Mai shi fiye da gyaran jiya (samun waje tusar asuba) momcy ta mik'o Mai hannu tace a nawa? FU'AD yace ta fad'i ko nawa ne in wata yayi zai bata kudin boyin ta ,momcy tace tafi k'arfin boyi ,Ni taimako ne tsakani na da Asma'u son ,ta taimaka min Nima n taimaka Mata . FU'AD yace ,Kai momcy bansan matsayin d kike son Kai _dirty girl_ d'inan ba ,nidai nasan ke kike taimaka Mata kawai ,nidai t gyara min ,na tafi uwa ta gari . Momcy ta bar zancen ganin Yana sauri tace "adawo lpy ,sai d y biya yama Yaya Jamil sallama kafin y tafi . Ma'u taji dad'in kayan d aunty sa'adiya ta bata duk kayan English wears ne masu kyau d tsada wasu d skirt wasu dogayen riguna har d Mai wando ma ,kusan kala 10 Bata nuna ma baba ba wai sbd kunyar kayan takeji saidai d Baki d ta fad'a Mai ,ya musu Addu'a . Kafin magriba baba yayi dama dama Dan har ya fita sallah ,Ma'u tafi kowa Jin dad'in ganin baban ahaka . Bayan FU'AD y dawo Koda y shigo falon Babu kowa y haura saman shi ,yaga yadda y bar komai Haka ya dawo ya same shi don Haka ,wanka kawai yayi ya sako Jin ba'asi . Koda ya had'u da hari ya tmby ma'un tace yau Bata Zo ba ,sai y fasa masifar da zeyi ,Yana shakar ya ce wani Abu akanta a gaban momcy don yasan baze Sha ba ,don Haka shi yasan me ya danadar Mata Gobe inta Zo Dan bada wuri ze fita ba Gobe . Washe gari Ma'u ta shirya zuwa gidan momcy Aiki tasa Riga d skirt da sa'adiya ta bata Babu laifi tayi kyau duk d ko fauda Bata shafa ba ,hijabin ta Wanda yad'an fi dama dama tun Daren jiya ta wanke ta goge duk d ya tsufa amman gugar sai ta kankaro Mai mutuncin shi ,tasa tayi wajen Aiki ,tare suka fito d baba suka rabu a hanya. Bayan ta shigo ta gashe da momcy ta gaishe da masu aikin da ta taradda su harda Harri . Ta samu sunata tak'a dama Akan wani k'adan gare d ya shigo kitchen anata korar shi yak'i fita kodan yaga matane ,momcy ma na fitowa ta samu Ana budirin ,Aiko sai ga FU'AD ya sakko cikin Shirin tafiya office ,Yana arba d Ma'u da jikinta yaketa rawa na tsoron k'adangare tanata rab'ewa a bango sai y wurga Mata uwar harara tare da alakoron mugun kallo Mai cike da gargad'i ,yace meye Haka kikeyi kamar me Jin wani abu ? Ki gyara min samana harda aikin d bakiyi na jiya ba ,kuma ki sani kinacin abinda b hakin ki ba matuk'ar Zaki dinga tsalake kwana bakizo Aiki ba ,don kamar Alkhawari Kika d'auka Kuma abaki cikaken Albashi kisa wanan hannun naki ki karb'a jiki na rawa ,sai kin Rama aikin jiya da bakiyi ba Kuma . Aiko Ma'u ta murgud'a Mai bak'i tace Ni ban tab'a cin Abin d bai zama halalina ba ,k'asa k'asa yadda shi k'adai yaji Aiko ya taho azafafe da niyar Jin da gaske shi ta mayar ma da martani ,ta kwasa ta k'arasa kitchen din d sauri ,ya Shiga kitchen din. Ganin shi a zafafe ,momcy tace yauwa son Zo ka taimaka musu Dan ALLAH ,nasan kajiyo budurin d akeyi na k'adangaren ,Kora musu shi ko ka Ciro shi a wajen gas d'inan gashi Nan yak'i fita inajin ma dashi muka kwana ,Aiko sai su Hari suka Fara matsawa da baya .. Ma'u tace to dama ga maza Mata me zasu iya? Taga kamar tsoro yake son ji ,Kuma furucin ta yasa yaji karya kasa agaban _dirty girl_ kawai yayi shahada ,yace "bani wanan k'azamin hijabin tatan kokon naki na d'auke dashi . Ma'u zaro ido "tace mezai kaika tab'a k'azamin Abu ? Kllin sarkin fidda datti,ya wurga Mata want mugun kalo ,Ashe momcy ta gani tace ,have son hijabin ta d mutuncin shi zaka cire Mata k'adangare dashi ,wlh ka cire Mata dashi ko shakka Babu sai ka siyo Mata sabo wlh ayau d'inan . Ma'u taji dad'in kalaman momcyn ,sai ta tab'a ta Bayan shi yadda zai jiyo mgn ta ,tace ko na m'iko maka hijabin ? Ya juyo zeyi mgn momcy tace ga tsuma a hanun Hari cire sukama aikin da zasuyi Dan ALLAH son. Shiko ji yake kamar ya shak'o Ma'u ya had'a kanta d na k'adangaren dan ya fuskanci tsoron shi takeji ,kuma tamai rashin kunya kusan Kashi 3 be d'auki mataki ba ? Karta samu k'ofa fa ? Don Haka Yana huccin yasa tsunman ya damko wuyan k'adangaren ,shima a tsorace yake shahada kawai yayi ,Aiko da yaji k'adangaren zai fito ta Bayan hanun shi da sauri a razane ya wurgama Ma'u jikinta ,batare da yayi shawara ba ya koma gefe shi be d'iba da gudu ba kamar yadda su Hari wasu suka fita ta k'ofan waje na kitchen wasu kuma suka shiga falo momcy ce kawai Bata bar kitchen d'in ba ,itako Ma'u wani uwar k'ara da ta saki ,sai sumewa da tayi wajen ko numfashi batayi . Momcy ce tayi kanta da sauri ta d'agota Tana Asma'u ,son kaga Abin d kaja Mana ko zaka kashe Yar mutane? Baba Mai gadi ne ya shigo shida Hari ,ya fitar d k'adangaren ,saiko FU'AD yace abinda y kamata kuyi kenan kuka tsaya jiran Wanda be Saba ba ,Ni natafi office ,ko ya tsaya yabi takan Ma'u atunanin shi ai dama ta k'ular dashi yayi maganin Mara kunya ta sake yimai rashin kunya ,azahiri Kuma bada niya yayi ba kawai shima tsoron tsoro ne ,sai Abin yazo dadai Kan ma'un . Asumen ya fice ya barta ,momcy ce ta dinga yimai masifa Tana cewa wlh yayi gagawan Kiran _family doctor_ d'in su yazo da gagawa in ba haka ba wlh zai gamu d fushin ta ,Jin furucin momcy yasa shi Kiran Dr din ya fice Yana cewa wai Yana zuwa . Sa'adiya Jin hayaniya yasa ta shigo sashin ita d Yaya Jamil Bayan FU'AD y bar gidan . Ma'u dai Ana kanta anata k'ok'arin ceto ranta Kuna Dr bai k'araso ba kowa hankalin shi atashe Banda Wanda ya asasa Abin Yama tafi aikin shi . Hankalin momcy yafi na kowa tashi . *Maman shaheed ce*👌🏻 [4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *Fatima Abubakar Shu'aib* (Maman shaheed) _shafi na 15_ *shafin Nan sadaukarwa ne ga masu jajantama Ma'u ,Ma'u nayinku irin wujiga wujiga d'inan har Adana bayanan ku takeyi* ❤💚❤💚❤💚 Hankalin momcy yafi na kowa tashi ,Dan Haka sai da ta sake Kiran FU'AD ta Fara Mai Ruwan fad'a ,sai ga _family Dr_ su ya zo . Bata Gama sauraron Abin d FU'AD yake cewa ba ta katse wayar ,ta Fara yimai mgn daga anmaida ma'un falo Kan doguwar kujera , FU'AD biyo Kiran momcy yayi Tak'i d'agawa ,ya Kira yafi so nawa Amman Tak'i ko kalon wayar . Shiko Dr ya Fara aikin shi na duba Ma'u yanata Bata taimakon gagawa ,Jin momcy Bata d'aga wayar shi ba yasa shi ,canja hanya ya Kira Yaya Jamil ,momcy na Jin ringing ta d'ako ta kalli Jamil tace "indai son ne ya kiraka ban baka izinin d'aga wayar ba,daga Haka tamai d hankalin ta ga Dr da yake cukucukun ceto Rayuwar Ma'u . Sai da aka kwashi kusan minti 30 sanan Ma'u tayi ajiyar zuciya Mai k'arfi d kusan kowa na wajen yaji ta ,su momcy da sa'adiya suka d'auki Hamdala suna godema ALLAH musamman yadda suka ga hankalin momcy ya tashi . Momcy ta Kira sunan ta "Asma'u y meke damun ki ? Ma'u ta kalle su sosai sai ta tuno da abin da ya faru sai ta duk'unk'une momcy Tana cewa Dan ALLAH ku cire min shi banason shi . Momcy taga Alamar afirgice take tace ,sannu Asma'u Babu komai ajikin ki Kinga ma Babu hijabin ai y sauka anfita dashi ma ,sannu kinji ,badan dg bakin momcy taji furucin ba d k'aryatawa zatayi Dan ta tsorata sosai d k'adangaren. Sanan ta tashi ta zauna ,momcy tace ma Dr Babu wani abudai ko ya dubata da kyau ? Yace kawai firgita ce kawai normal Babu komai gashi har kina Mata mgn Tana amsawa ai Alhmd! Momcy tamai godiya Abin yazo da sauki ,ya tafi Yana musu ALLAH ya Kara kiyayewa. Jamil Kam har silent yasa wayan sbd Kiran d FU'AD yake tayi Mai ,ga momcy ta Hana d'aga wa. Bayan Ma'u taci abinci ta k'oshi momcy tace ko zataje gida ta huta? Ma'un kamar kad'an take jira tace toh ,momcy ta had'a Mata su fruits ta cika Mata leda tace ta gaishe da mutan gidan , ALLAH ya kiyaye gaba ,Ma'u tayi Mata godiya ta tafi cike da zulumin k'iyayar da ke tsakanin ta da FU'AD Haka? Koda ta Shiga gida mama habee ta ganta ta dawo da wuri sai ta Fara cewa ,anyi d'an Halin ? Naga kamar wacce aka Koro ,Suma da jarabar naci sai kace Dole su salamaki daga gidan Abu yaci tura ,Ni banyi zaton zaku Jima Haka bama ,gida kamar gidan hajiya babba Amman ta yadda take zaune dake kalan ki bad'a Mata kwarkwata ,ko bashin tsamin ki ma Bata ji ,ke naci suma naci maga Mai saki dai . Ma'un dai ba maganganun mama habee babe a gaban ta ,sai wucewa tayi kawai ,Tana ce Mata bana Jin dad'i ne wlh ,mama habee tace hannun ne ya dawo? Ko shawarar ce ta motsa? Sai ko ma'un tace aa kawai kaina ke ciwo . Mama habee tace banza bata Kai zomo kasuwa ,inkinyi wanke wanken can Kya huta kafin lokacin d'aura na dare Dan ciwon Kai ai baze Hana aikin gidan uba ba . Ma'u tabita da kallo tace to barin ajiye hijabi na fito , ta nufi d'aki Tana Dana sanin dawowanta gidan,Amman ya ta iya haka zatayi Dole. Bayan ta Kamala wanke wanken ,ta koma daki ta Dan ci ayabar ta sakamakon rashin Gama abincin Rana d ba'ayi ba har to 3 ,har Tasha lemun ta ma ta danji cikinta yad'an d'auka sanan ta fad'a dogon nazari ta inda zata Rama Abin da FU'AD ya Mata koda hakan na nufin barinta gidan. FU'AD yaji Babu dad'i da momcy tak'i d'aga wayar shi ,yasan Tana Nan Tana ciki dashi ,don haka Dole ya Nemo ruwan sanyaya zuciyar momcy shi yau . Yamma lis FU'AD ya taho ma da momcy wata sasanyar fura da ake damata da su ayaba da su inibi da Madara ta had'u sosai momcy nason furar ga gasashiyar hanta gashin Ruwa Ruwa Mai dumi duk na toshiyar bakin momcy ne . FU'AD da d'an k'arfin shi ya shigo gidan ya ki Hawa sama ma don yau so yake ya wanke lefin da be d'auke shi laifi ba ,Amman yasan ya zama laifi a wajen momcy don Haka maganin zaman lpy kawai y nuna Mata shifa bada niya yayi ba . Ya mik'o ma momcy ledar yace momcy ga hantar Nan Kar ta huce nafi son kici da duminta Dan ALLAH kinji uwa ta gari ,ta k'arba babu wani walwala ,tamai godiya ta bud'e ta Fara ci ya tashi d kanshi ya d'auko Mata _glass cup_ ya zubo Mata furar ya m'ik'o Mata ta k'arba Tana cewa ALLAH yayi Albarka ,hankalin FU'AD a kwance yace "Ameen momcy in ban Miki ba wa zanyima? Dole nane na Miki momcy ... Hankalin FU'AD kwance gani yake ya Gama cinikin momcy da hanta da furar shi Mai sanyi ,ya mik'e zai haura saman shi momcy tace "dawo ka zauna cinikin be yiwu ba ,wanan toshiyar bakin sunmin kad'an da har zasusa naki fad'ama gaskiya son. FU'AD ya dawo ya zauna ,Yana cewa hmm momcy Babu mantuwa na sani ai Daman,azuciyar sa ,afili Kuma yace ,momcy nifa ........ta dakatar dashi da cewa. "FU'AD meyasa ka Aikata Abin da kayi d'azu kakuma nuna Halin ko in kula Kan lamarin ,kamar amanace agareni fa ,inda yazo da k'arar kwana kasan komai zai iya faruwa? FU'AD yace "momcy ki yadda Dani wlh banyi da manufa ba karyewa ne yazo daidai gab'a ,Amman banyi Ina sani ba ,Nima kaina naje ceto Dan kinsan bana son k'adangaren Nima momcy ,fitowa zaiyi y tab'ani na tsorata na sake Mata a Kai bawai don Ina sani ba wlh,Naga kin d'au zafi , ALLAH y huci zuciyar uwa tagari . Momcy tace ,na yadda sbd rantsuwar d kayi ,Amman ka rage Mata tsananin Nan bana so ,kaji na Gaya maka. FU'AD yace" za'a kiyaye insha ALLAH . Momcy tace ,akiyaye inba hakaba zamu sa kafar wando guda da Kai wlh . Sanan FU'AD y haura saman shi y rage kaya ,Yana mamakin yadda momcy take Mai Akan Ma'u . Itako Ma'u duk tunanin ta bai wuce Dame zata Rama Abin d FU'AD y mata ba ,inta barshi ma tace ta hak'ura da Aiki a gidan ,shine yaci blus Kuma ita tayima kanta Dan ba momcy ce ta koreta ba ,Kuma b hafeeza ce ta dawo ta karb'i aikinta ba ,kawai ta nemar ma kanta mafita ,Amman ta Yaya hakan ze yiwu ? Zuciyar ta tace sai kin cire tsoron shi da nuna Mai kema mutum ce kamar shi,girman shi da tsoron Nan duk ki ajiye ku goga Wanda yaji tsoro ya hak'ura. Washe gari ,shine ranar da k'anwar mamar Ma'u tazo ,Dake da wuri tazo Ma'u ko Aiki tak'i fita ,saima aikawa da tayi baba yazo su gaisa ,dake mama habee an lek'a mak'ota tsegumi ,Dan Haka ma'u ta sake da aunty tata har baba ya shigo mama habee ba'a dawo ba . Bayan sun gaisa da huwaila da baba ,tamai gaisuwa suka dinga hirar yaushe gamo ,sun Jima suna Hira har hirar k'iyayar da mahaifiyar su takema mahaifiyar ma'un Bata canja ba har yau da ta canja d ma'un ta dinga Kai musu ziyara ta dinga Jin dad'i itama tanada Kaka a kusa d ita ,Amman Inna baza ta karb'eta a jika ba ,watakila sai zuwa gaba ... Baba da aunty huwaila sun Jima suna tataunawa ,mama habee ta dawo ,wani ya mutsa da b'ata Rai ta dingayi Tana Harare Harare ,Haka dai Ma'u da su baban suka fita harkar ta . Bayan baba sun Gama gaisawa ,ta d'auko kud'i taba baba yak'i karb'a sai da ta dinga had'ashi da ALLAH sanan ya karb'a mama habee Ashe Ana lab'e sai ji sukayi tace asara yawun bacci ,girma ya fad'i Rak'umi ya shanye Ruwan 'yan tsaki ,Dan Haka aka dawo ai ,duk sun jita Kuma sun gane manufarta ,itako azuciyar ta haushi taji anba baba Abin da ta dinga sa rai ita ta samu sai gashi ya tsalaketa ,baba ya mata godiya da fatan Alkhairi yace zai wuce kasuwa ALLAH ya maida ita gida lpy ,Amman duk d Haka ta rok'i baban Kan Ma'u ta kaima hajiyan su ziyarar bazata ko ta Rana 1 ce ,inta karb'eta a jika to inbata k'arbe ta ba sai su fawalama ubangiji su barta da halinta , da kyar baba y amince Akan wata Rana Ma'u zata insha ALLAH ,sosai huwaila taji dad'i don Tana son farfad'o da zumuncin su ,taso ace a k'asar take Aure da tafi kula da Ma'u . Bayan tafiyar baba ,aunty huwaila ta dinga ma Ma'u tmby Akan karatun ta da matsayinta yanzu duk ma'un ta Gaya Mata tunda ta gama junior section Bata samu taci gaba ba ,islamiya ma kud'in term ne ya hanata zuwa har na term 2 sai ta magriba da take zuwa tunda ita kud'in laraba kawai ake biya . Aunty huwaila ta d'auko kud'i ta Bata har da wata jaka Mai d'an girma tace situru ne aciki harda gyale da hijabai ta k'ara ta dinga Amfani dasu ... Sun d'auko jakar sun bud'e Ana dudu ba kayan ,sukaga alamun Ana musu lek'e ,har aunty tace ko abari sai ta tafi ta duba ,ma'un tace ai ko kin tafi innatafi Aiki za'azo Amin bincike gwanda yanzu a Gama gani afi kyaleni na huta ,sanan suka Gama bud'e kayan gaba d'aya ,Kaya basuji jiki ba masu kyau da tsari har da takalma set 5 masu kyau ,ma'un nata godiya Tana Mata Addu'a. Sun Jima aunty huwaila na Mata nasiha da ta kula da kanta ,aikin nata ma ta rik'eshi da daraja ta rike mutuncin ta Kuma ,karatu kuma ta dage ko da kud'in aikin ne ta dinga taimakon kanta ,duk ta d'auka tamata godiya Kuma taso ace ciki d'aya aunty huwaila suka fito da mahaifiyar ta tasan da batayi maraici ba ,Amman ahakan ma ta godema ALLAH. Sai daga baya aunty huwaila tace zata tafi , Ma'u badan Taso ba ,ta tafi rakata har bakin hanya sanan ta dawo kud'in da ta Bata Yana soke ajikin ta. Koda Ma'u ta koma da sauri taga an Shiga d'akin ta ,koda ta Shiga humaira ta gani Tana d'ad'aga kayan da aka Bata , sai ta zuba Mata ido kawai ,da sauri humaira ta juyo Jin motsi a Bayan ta ,suna ido hud'i da Ma'u sai ta saki kayan Tana inda inda , ma'un tace ya akayi Yaya humaira ? Sai humaira tace ,dama murna nazo tayaki kayan sunada kyau wlh ,ki bani aron wanan doguwan rigan naci bikin afifa baby dashi Dan kinsan doguwan Riga za'asa a Arabia night din ,Ma'u tace d'auki Yaya humaira kima ajiye a wajen ki kafin jibin ,humaira gwuiwa Babu kwari ta karb'a ta fice ,itako Ma'u ta Mata hakane don ta saurara karkuma ta sake zuwa Mata bincike don ta Mata Abin d in itace bazata iya mata ba .. Humaira na Shiga ta cillar d doguwan rigan a gadon mama habee da yaketa neman agajin a gyara shi ko yayi hankali,mama habee tace kyauta ta Baki? Humaira tace aro dai kamani tayi fa Ina Mata bincike ,shine na wayance da aron rigar ,Kuma wlh Akwai kayan d sukafi doguwan rigan kyau Amman na tsaya a ita ,shegiya wlh ta samu Kaya masu kyau da tsada ,mama habee tace Yar banza ba Dole ta Baki wasu ai Naga wata Riga da wando ma cikin d'akin jiya zasufi dacewa dake ,kice ta Baki intak'i kimin mgn sai na tursasa shegiya ,humaira tace toh ,mama habee tace kema kece Mai tsinannen Baki duk wani kud'inki ciki yake tafiya acici mala'ikun tauna kinba kwad'ayi da had'ama dama ,shiyisa Baki da Abin arziki sai na tsaiya , humaira ta turo Baki tace "Zaki Fara Kuma ko mama? Mama habee tace ai gaskiya na fad'a ... Ma'u ta gama kaiwa k'arshe akan tunanin Abin da zata ma FU'AD da zaiji har ransa kamar yadda taji itama ,sai tsoron abinda zai je yazo da takeyi ,Amman t k'udiri aniyar aiwatar da niyar ta inba Haka ba bazata huce ba ...... *Maman shaheed ce*👌🏻 [4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *Fatima Abubakar Shu'aib* (Maman shaheed) _shafi na 16_ *AFUWAN INADA EXAMS GOBE DA JIBI SO BAZAKU GA POST NA RIK'ON KWARYA BA SAI MONDAY ZAKUJINI INSHA ALLAH* *INA BUK'ATAR ADDU'A KU AKAN EXAMS DIN DA ZANYI ABIN ALFAHARINA FANC*👏🏼👏🏼 Washe gari Ma'u ta saka wata doguwan Rigar atamfa ya d'an Mata yawa Amman ba sosai ba ,ta zabo hijabi cikin kayan dai da aunty huwaila ta Bata ,ta zura ,ta Adana kayanta a jaka tasa kwad'o ta rufe ta tafi da can akulin ta saboda tsaro badan tsoro ba ,dama ta gama ragema mm habee wani aikin,sanan tayima baba sallama ,ya mata fatan samun nasara atafiyar ta da dawowar ta ,sanan Tama mm habee ,Aiko tace "ba ya Miki Addu'a ba shi Wanda kike zaman shi ? To ai ba sai na Bata Baki ba absnza da wofi ,ajuri dai zuwa Rafi wata Rana tulu zai fashe ,Ma'u Bata ce komai ba ta ficewar ta haidar na Mata baibai Yana jikin baba . Bayan fitar Ma'u fad'a baba y Fara yima mm habee ,Amman ta Fara tsagalgale shi ,dake tace ne sai yayi Mata shiru danma yanada addini yasa wani aikin intayi baya Kama shi ,shida yarsa Ma'u da ta tsole musu ido ,Amman mama habee ba a zaune take ba .. Ana d'an kunge kunge ,Dan ko mahaifiyar Ma'u Tasha fama sosai . Ma'u cikin Kamala ta d'au hanyar zuwa gidan momcy ,Koda tayi tozali da motar FU'AD taji fad'uwar gaba matuk'a Amman Haka ta k'arasa falon cikin sallama da nutsuwa ,Babu kowa sai motsi d tajiyo a kitchen nasu Hari Dan Haka kawai sai ta nufesu don su gaisa . Bayan sun gaisa Tana ta tayasu d wani aikin ,can sai ta jiyo motsin momcy a falon ta fito sai ta tafi Dan kwasan gaisuwa ,har k'asa tsuguna ta gaishe da hajiya ,hajiya ta amsa fuska asake Tana tmby y jikin ta ,sai ga FU'AD sakko cikin Shirin tafiya office Yana ma momcy mgn cikin sakin fuska da Kamala . Ma'u ce ta gaishe shi ,Amman sai yayi kamar beji ba Kuma yaji ,sai momcy tace "haba son bakaji ne Ana gaishe ka ko ta daina ne ? Sai y yatsuna fuska yace "Ni banji bama attention d'ina Yana ga uwa ta gari ,lpy shike Nan Yana kallon wajen da aka jere Mai break d'in shi ,sai ya doshi wajen Yana cewa momcy kizo muyi breakfast pls Kar na makara ,itako momcy mamaki ne ya Kama ta sai d tace "son" yace "naam? Sai tace "Zo" da yazo ta nuna Ma'u tace haba kamar ba d'an musulmi ba Kuma Dan hajiya ko ka tmby yarinyar Nan jikin ta? Bayan kaine ummul'aba isin sakata cikin yanayin Koda bada son ranka bane ai ta cancanci ka Mata sannu duk d ta samu sauki . Sai yace ,ayya n manta ne ,Zan kiyaye gaba momcy ,sai ko yasa Kai zai tafi ,momcy tace "son wlh inbaka ma yarin Yar Nan sannu da jiki ba wlh sai ranka ya bacci ya Ina nunama annabi kana runtse ido ,musulmai muke fa ba kafirai ba ,haba ne ? Banason wanan Halin beyi daidai da naka ba Sam ka sake ,kabi umarni Kuma ko kaga Aiki d cikawa yanzun Nan.....itako Ma'u kanta a k'asa tanajin dad'in yadda ake tursasa FU'AD akanta . Ganin momcy da gaske take ,sai y Bata Rai yace "ke sannu ,y kinji sauki ai ko? KO tsayawa yaji amsar da zata bashi beyi ba ya wuce zai haura saman shi . Ma'u tace , Alhmd naji sauki ,Tana Mai dariya cikin ranta .. Momcy ce tace son Ina zaka? Yace sama Zan d'auko jakana ne ,sai momcy tace "oh Dan nama gyara shine kayi fushi da breakfast? Sai y Kama inda inda zai wayance ,sai momcy tace "Zo nan mu karya in kaci ka fita ka amayar dashi kaji ko ? Zo ka wuce ,Dole ya dawo ya wuce wajen kayen abincin ,momcy tace "ma'u taje ta gyara Mata d'aki ,da sauri Ma'u tabi umarni . Momcy ce ta dinga lalab'a FU'AD Tana Kuma k'ara Gaya Mai gaskiya ,sai cewa yayi "shifa Abin d y sa shi Jin Babu dad'i fad'an d ta dinga Mai gaban kazamar Nan ,kamar wani yaro menakon abayan idon ta ? Ai sai ta rainani momcy ,momcy tace yo to raini na nawa tunda baka Jan girman ka Kuma Tana baka girman ka ,kabi ka tsaneta Kuma ta sani ,sanan tsautsayi yasa ka sumar da ita kace Mata ya jiki kawai bazaka iyaba ,bansanka d wanan Halin ba wlh ,indai baka gyara ba zamu dinga kwasan 'yan kalo gaskiyar mgn . FU'AD yace ,to Zan gyara ,Amman duk kuskuren da zanyi Kar ki min fad'a agaban ta Dan ALLAH ,Ni dake sai kimin fad'an ,Amman .....momcy tace "meze Hana ka kiyaye duk Abin d zesa namaka fad'an ? Yace "Zan kiyaye ,itama ta daina Shiga sha'ani na ta dinga bin umarni na ,momcy tace "Ana jika dai , ALLAH ya kyauta ,kayi sauri ka Gama ka tafi ,yace ,Ni nama Gama ,kice ta gyara min sama Kar na Mata mgn kice nayi wani abun ba daidai ba ,barin d'auko jakana ..... Ma'u cikin lokaci k'ank'ani ta kammala komai ta dawo falo ,shima ta gyara ,momcy tace ta gyara saman FU'AD ,shima ta tafi ta gyara .. Sa'adiya ce to shigo ta gaishe da momcy ta umarci Ma'u tazo ta tayata gyaran sashin ta ,momcy tace to Asma'u Babu komai Zaki iya ko Harri taje? Sai Ma'u tayi murmushi tace Zan iya hajiya ,sanan suka tafi . Sosai Ma'u ta saki jiki da sa'adiya ,suna Aiki suna Hira kamar sun Jima da sabawa ,har aikin nasu yak'i sauri don duk rabi Hira sukeyi kawai ,har sa'adiya tayi amai take cewa ma'un Bata Jin dad'in sai ta ziyarci asibiti yau ko gobe ,har ma'un take cewa gwara kije yau lpy ai itace uwar jiki ,aunty sa'adiya tace insha ALLAH zata Bari Jamil ya dawo .. Ansha Hira tsakanin Ma'u da sa'adiya sosai har ta d'an d'ebe Mata kewa ,don da kasala da lalaci duk sun baibayeta Amman hirar d sukayi da Ma'u duk sai ta d'anji dama dama ,gashi tafiya aikin Jamil yanata gabatowa befi saura wata1 ba su tafi . Kafin FU'AD y dawo Ma'u ta tafi gida . Koda y dawo k'alk'al ya Sami komai na saman nashi . Washe gari da safe Jamil y d'auki sa'adiya suka tafi asibiti Bayan sunyima momcy sallama ,tanata yima sa'adiya sannu Bayan hasashen ta y Gama sanar Mata da sakamakon rashin lpy sa'adiya . Koda sujaje asibiti hankalin Jamil a tashe ,Bayan 'yan gwaje gwaje aka sanar Mai da jiki ne da ita sati 6 murna kamar yayi me , sa'adiya ce ta hanashi Kiran momcy Amman d tun a waya zai sanar Mata . Ma'u tuni tazo ta Fara aikin ta har tayi nisa kafin suka dawo ,Jamil wajen momcy y nufo Gaya Mata sakamakon ,itako sa'adiya kunya tasa ta wuce sashin su ,tace atura Mata Ma'u kawai . Koda Jamil yazo ,ya sanar ma momcy ,itama murna tayi da Addu'a ALLAH y rabasu lpy , har FU'AD yazo y samu big bro nata fara'a ko da y tmby shi dalili ,sai ya d'aki Bayan shi Yana Mai wasa yace ,auta ka kusa girma ,aunty ka zata baka baby soon ,momcy tace shi ba yace be Isa ba ,jikokina ne Ni kad'ai ka barshi kawai ,Aiko sai FU'AD yayi murna da d'an ihu Yana cewa wlh baby nane mace ko namiji ,Hana momcy karkimin Haka Mana yaron big bro ai Babu Mai iko dashi duk duniya kamar Ni ,suka saka dariya duk farin ciki ya Kama su . *Maman shaheed ce* [4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *Fatima Abubakar Shu'aib* (Maman shaheed) _shafi na 17_ *Ina Jin dad'in comments din ku ,team FU'AD anmuku wayo fa Yan team Ma'u suna nema su muku zarrah meyasa*?😉😀 *Ina Godiya da Addu'a ku ga exams din da nake ,still Ina k'ara neman Addu'ar ku bangama yanzu aka soma exams din*👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼🥰 Ranar momcy,Yaya Jamil, FU'AD duk cikin murna suke ,momcy ta tura Ma'u ta gyara ma sa'adiya sahin ta ,sanan ta dawo ta gyara na FU'AD tanata mita Dan wulak'anci hatta short niker shi a k'asa yau ya barshi gashi Ma'u nason tayi shara ta gyara d'aki ,gashi kyamar tab'awa wai take ,duk d Bata tab'a ganin Haka ba sai yau ,don har ta hak'ura d gyara d'akin ,tasan inya dawo mita zeyi masifafe kawai ,sai d ta gama gyara falon ta dawo d'aki ta d'ako sandar Morpher ta d'auki short niker ta sak'ale Mai a jikin windon shi kamar anwanke anshanya ya bushe d'inan ,tayi Haka ne don ya gani in be sani ba gaba ya kiyaye in Kuma Yana sane gaba Abin da yafi Haka ma zata Mai ,Dan kwanaki ma singlet d'in shi ya Bari a k'asa itako d tazo shara ta turata k'asan gadon shi ,sai d yazo d'aukan Abu ya gani ya dinga Mata mita a zuciyar shi Yana ta rainashi waya Bata ikon ganin irin wad'anan kayan nashi ma,ai matsayin ta be Kai ba ,sai gashi yau anbar oga kwata kwata na maza ,Dan Haka ta sak'ale Mai taci Alwashin ko me ze mata saidai yayi Amman sai ta nuna Mai ba a ko 'ina ake ajiye su ba indai mutum yasan darajar Abin shi . Bayan ta gama gyara ta fita tabar Mai d'akin shi .... Bayan ta koma k'asa suka Fara Hira dasu Harri sunayi Tana tayasu Aiki Tana k'aruwa dasu sosai Akan wasu abubuwan da Bata iya ba... *GIDAN MAHAUKATA* Matar Nan d ake fama d ita wajen cin abinci yauma kamar kullin sai d rarashi ta karb'a tanaci Tana hawaye Tana wani Abu kamar Mai dogon nazari , Alhaji d y bigeta ya ajiye kud'in maganin da da Mai kuka da ita ,matsalar sa guda har yau yak'i yadda a Mata taimakon ko maganin gargajiya ko na malamai su taimaka Mata ,yace Sam kawai shi antabatar Mai matsala ta Yana cikin kwakwalwar ta ne don Haka na asibiti za'ayi maganin hauka Kuma Ana jimawa kafin aga sauk'in sa ,hope d'in da yake dashi ma da akecewa Akwai (progress)alamun nasara aciki don Haka yake cigaba da taimakon ta har nasarar tazo ko ta warke . FU'AD da wani abokin shi a office d'in su Mai suna b2k sunata Hira akam yarinyar da wani abokin su zai aura ,kwankwarariyar Yar boko Kuma ta girma kafin yanzu ze aureta Dan anci biro ansha ruwan karda tsabar boko , FU'AD ma shi mgn isar sa tayi ,yace "ALLAH y Basu zaman lpy y nuna musu lokacin lpy Ayi kowa ya huta Dan wanan inba aurar dashi akayi ba ze iya aika aika Dan shi ya yunk'uro,suka sa dariya ,b2k yace shima Dan be samu wacce yake muradi bane da ya bada himma Kar ya zama baba na soro ,kanin shi yayi Aure ga 1 Yana Shirin yi har sun fara jamai mgn wajen hajiyar su , FU'AD yace sai ka bada himma mudai da saura ba shine a gaban mu ba yanzu ,b2k yace wlh kaima dai kayi Mai yiwuwa Dan lokaci tafiya yake Kuma kwana k'arewa suke momcy na buk'atar ganin iyalin ku yadda nasan big mansion d'in naku Babu motsin yara Dole ta so, sai ko FU'AD yace ai gashi Nan Yaya Jamil zai Bata . B2K yace "kana nufin big bro har ya ba Yar mutane ruwan wake Tasha Ina ganin shi so silent Haka Ashe........be k'arasa ba FU'AD yace "Kai karka min iskanci fa Yaya Jamil d'in nawa zakayi ma d'an biki agaba na ,to Dan uwarka dutse kake so ya zama? Da beyi ba ba se muyi tunanin ko Babu lpy bane Amman yanzu ai munsan lafiyaye ne ,D'an Air kawai zakamin shirmen banza .. Aiko sai b2k yace "shike Nan me Yaya Jamil ,Ni kak'i ka gayamin kalar matar d kake cewa _ur choice_ Dana tayaka neman ta awuce gurin ko baka shirya ba man FU'AD . FU'AD y wurgo Mai uwar harara ,yace ALLAH ya kareni da in Baku cigiyar Mata ,Ni ko ita bamuyi arahar Haka ba ,nifa Babu Rana Dan ma kaji ,yi ta kanka nayi ta kaina d'an air . Sai b2k yace , wlh k'arya kake munafuki kana ci kana k'oshi kace ........ FU'AD ya doshe Mai bak'i yace wlh Kai mugun d'an air ne ,nidai bani lbr wacce kake muradin na tayaka samowa ... B2K y dinga Mai dariya Yana cewa ka hanami mgn ko ?Ni ai nafi kowa sauk'i Dan ban d'au duniyar Nan d zafi ba ,yarinya nake nema _so silent, gentle, beautiful,Mai good character s_ Kai ko daga k'auye ta fito indai tanada abubuwan d nakeso bani da case ,Kuma Koda ace ba wata bace ita Kuma ba Yar kowa ba ,kawai nafiso na koyar da ita komai by my self Dan mu dinga _making good luv_ na shayar d ita madarar k'aunata mu dawwama a son junan mu da k'aunar junan mu ........ FU'AD ya dakatar dashi d cewa "Kai ai wanan matar taka tafi kowa araha ,gasunan kamar janfa ajos sunfi kowa sauk'in samu ma .......da sauri b2k yace a Ina ka sansu ko ka ga irinta pls? Sai FU'AD yayi dariyar mugunta ya kalle shi ya watsar ,can yace "Akwai wata _dirty girl_ ma da momcy ta d'auko _as house girl_ Naga zata iya Hawa bayanan ka sai kaje ku daidai ta na d'auki nauyin hidimar biki da kayan d'aki , FU'AD Yana dariyar mugunta Yana fad'a ..... Sai ko b2k yace ya tab'ata Abin da ya fad'a? Amman wani hanzari naji kace Yar Aiki kaifa Dan Wulak'anci ne Yar Aiki nace ma Ina nema? Kawai intayi kace gobe n kawo ma momcy ziyara . FU'AD yace Kai dai Akwai ,wani bi tacan in ka ganta wata k'ila Tama yadda kake tutiyar baka d'au duniya da tsanani ba ai ,Amman kazamace Dan bana shiri d ita Sam jini na yak'i had'uwa da nata ,har koyawa kaina nake naji na rage tsanar ta Abu ya gagara kodan momcy . B2k yace Dan ALLAH mubar mgn duk ka Gama zaginta da tsine Mata shine zaka had'ani d ita Kuma _house girl dirty girl_ kafi kowa sanin yadda na tsani k'azanta ,kawai mubar mgn barinje na dawo tare zamu Zo d ango anjima in bamu Zo ba ko gobe zamu had'u ,Amman fa Zan Ware Rana t musamman don zuwa gaishe da momcy insha ALLAH! Sai ko FU'AD yace zakazo bara d rok'on iri dai na _dirty girl_ sai b2k yayi dogon tsaki yace "wlh zakasa na fasa zuwa wanan mgn Babu ita mubarta tabi Isa ,Ni nama tafi ...... FU'AD y bishi da dariyar mugunta..... Bayan Ma'u ta gama komai sun Sha Hira d sa'adiya sosai ga tafiyar su nata gaba towa saura sati 2 ga sa'adiya ciji Babu kwari gashi tanason bin mijinta shima yanzu yafi son tafiya da ita ... Bayan Ma'u ta koma gida ,ta tarar da mama habee d humaira anata fad'a Amman suna ganin Ma'u komai ya tsaya don Kar ta samu Abin fad'a Basu San ko ajikin ta ba ,haidar ne y bita d'aki ya dinga Gaya Mata yadda fad'an ya somo ,tanata musu Addu'a shiriya gaba d'ayan su . FU'AD na dawowa ya ga Babu kowa a k'asan ,ya k'arasa d'akin momcy ya sanar d ita dawowan shi "ta Mai sannu da zuwa da huce gajiyar office"sanan ya haura sama y rage kayanshi tun afalo Yana shak'ar kamshin falon Mai dad'i ko bai fad'a ba gyaran ya Mai yadda yake so da kamshin falon ,sai d ya huta y Shiga d'akin don Adana kayan da ya rage a jikin shi Dan saka jalabiya don fita sallar magrib in lokaci yayi ... Yana Shiga yayi tozali da Short niker na we'll coming d'in shi a window ,Aiko sai ya k'arasa wajen Ciro ya dinga jijuyawa Yana tunanin ai ba wankewa akayi ba ,to meya kaishi jikin window ? Wanan aikin Yar k'auyen Nan ne _dirty girl_ to meya kaita ma tab'amin ,zuciyan shi na tmby shi ... Can Kuma yace ,Kash! Girmana ya fad'i yarinyar Nan ta gane min shorty ,to inyi Mata mgn ma ya zama ,na nad'e tabarmar kunya da hauka ! Kawai na kiyaye gaba ,Kuma na sake tsare gida Kar ta Raina Ni ..... Washe gari Ma'u tazo ta gama aikin ta sun had'u da FU'AD Amman be ce Mata uffan ba ,har ta dinga cewa Ashe karyar banza kake na gama da Kai ai .... Sa'adiya fama takeyi da laulayi sosai komai taci sai ta amayar gashi Bata iya tab'uka komai sadai Ma'u tayi Mata ga tafiya saura sati 1 ,Yaya Jameel ya rasa yadda zeyi ,don Haka ya shawarci momcy yadda za'ayi sai ko tace ko da Ma'u zasu tafi Amman fa sai in iyayenta sun yadda sun amince da dakaina zanje neman muku Alfarma ,Amman ka tmby sa'adiya kaji,sai ko yace momcy ai amincewa zatayi ita d za'a taimakawa Kuma Kinga tasu tazo d'aya ma ,momcy tace "toh yanzu Zan shawarci ma'un na Fara ji daga gareta in Babu matsala ,kafin na doshi gidan su ,Jameel yace toh "ALLAH yasa muji Alkhairi. Koda ya gayama sa'adiya dad'i taji ko Babu komai ta dinga d'ebe Mata kewa in jameel Ya tafi Aiki . Washe gari Ma'u na zuwa momcy ta Mata bayanin yadda suka shawarta ,Ma'u tanason tafiya Tana tunanin baban ta batason nisa dashi ,Amman Tana son nisa d su mama habee ,gashi ta Saba da momcy ma Bata son barinta ,amman wata k'ila baba ya amince in momcy taje d kanta ,Kuma itama t huta d wanan mugun fu'aduuun .... Ma'u da momcy sun yanke shawarar yau zasu tmby baba ko ze amince . Da yamma momcy tasa ma'un a mota Mai numfashi Basu tsaya ko Ina ba sai gidan mama habee d gudu haidar yaje y sanar ma mama habee ga aunty Ma'u da wata Mata da wata arniyar mota Mai kyau ,itako humaira taba tsaye a waje d wani saurayi taga ma'un da wata hamsgak'iyar Mata can ta gano hajiya babba Ashe ta k'ara tabbatarwa lalai hajiya babba ta kwanta cikin arziki da wada Sam batasan Babu ba . Koda hajiya da Ma'u suka Shiga ,idon mama habee idon Mai kud'i da sauri ta amsa sallama ,tunanin ta abata kawai kamar ta bada ajiya , harda shimfid'a akama hajiya ,Bayan sun gaisa aka mik'o Mata wani pure wata guda 1 2 da aka siyoma humaira zataci Fara da manja ,hajiya suna gaisawa ita Kuma Ma'u ta Aiki haidar Kiran baba . Ba'a jimaba baba da haidar suka taho . Bayan baba sun Gama gaisawa ,hajiya babba ta Koro Mai jawabi da Alk'awarin rik'e Ma'u Amana insha ALLAH tare da neman amincewar shi Babu alamun tirsasawa ko iko da dukiya . Mutuncin ta ,kimar ta ,darajar ta ,shigowa ta gidan ma kawai Abin Alfahari ne ,Bata da girman Kai Amman ba'a fiye ganin ta a irin gidajen wajen ba , gashi tamai Alk'awarin riketa amana ,da tunanin zataji dad'in tafiyar fiye da yadda mama habee take galaza Mata don Haka ya amince yace shidai indai an rik'e Mai Ma'u Ammana bashi da matsala ,sosai momcy taji dad'in karamcin da baba ya nuna Mata . Mama habee kuwa kamar ta had'iyi zuciya ta mutu Dan bak'inciki zata tafi Abuja taji dad'i da humaira aka Basu duk d shegiyar humaira girman Kai baze barta tayi aikin ba ,Amman da zasu amince ko da bala'i da masifa da sai ta tursasata tayi ... Sosai momcy Tama baba godiya ,ta Ciro wasu kud'ad'e taba baba kamar tasan Halin shi na girma ba lalai ya karb'a ba ,ta Shirin 10k only Dan Koda yak'i karb'a taba waccan da taga tanata lek'a Mata jaka jikinta nata rawa na abata kawai , sai ko baba yak'i karb'an kud'in ,yin duniya d magiyar momcy Amman yak'i karb'a Dan Haka ,sai tace "to ke gashi asai ma su haidar biscuits ,hannu na rawa mama habee aka fuzge kud'i sai godiya ake Ana ma momcy Addu'a .. Baba ya koma wajen sana'ar sa da Jin haushin karb'an kud'in da zalamamiya ta karb'a ,Ma'u ma ta raka momcy har mota taba CE Mata sai Gobe zata Zo ,momcy tace ALLAH ya kaimu lpy. FU'AD duk besan anshirya tafiya d Ma'u ba ,atunanin momcy tunda ya tsaneta in ta barmai gidan ai shikenan Dan Haka ba sai anyi shawara ko hirar dashi ba ,Dan Haka su kad'ai suke Shirin su ,gashi saura kwana 5 su tafi ,yadai San da tafiyar yanata cewa Dana Kar suce sun Saba da yayan nashi iya dawowar shi dinan . Wata Rana Ma'u nama momcy Aiki FU'AD sai hararar ta yajeyi ,ko ta kanshi Bata bi ba ,tazo fitowa daga d'akin momcy ya kusa gwara Mata Kai da bango ,Amman wai ya kama Mata masifa wai Bata gani kamar makauniya,itako tace kokuma shine makahon ba ai ya ganta sarai ,ran FU'AD ya sosu ya Fara Gaya Mata kaifafan kalamai masu tsayawa a zuciya Yana huci kamar zai mareta ,sai ga momcy ta taho ta Fara yimai fad'a sbd kalaman shi taji marasa d'ad'i ga duk bawan da aka fad'ama ,momcy ta jashi d'aki tamai fad'a tunda yace Adena yimai fad'a agabanta ,sosai momcy ta Mai nasiha ,amemakon ya gyara sai ma haushi da yaji ... Itako Ma'u dama momcy ta umarce ta da taje d gyara Mai saman shi ,Dan Haka sauri sauri gudu gudu don tayi ta gama ta sakko kafin ya Zo ya sameta ,kafin ta Kamala har y bar wajen momcy y hauro saman , ma'un tayi lakwaf aikin ta kawai takeyi Tana tsoro ,ya harareta yace wa d'azu take mayarma da martani? Ganin y rutsata kartaci bugu afita da gawar ta Dan ta rad'a Mai mugu Mara tausayi ,yasa tace Ni ai ba dakai nake ba! Yace "Ni Zaki Raina ma hankali wlh ko ki fad'i gaskiya ko na lahira ya fiki Jin dad'i ganin Kar ya cuceta ,tace "toh Allah baka hak'uri" ya sake cewa Ni sa'anki ne? "Tace to nace ALLAH baka hak'uri ai" yace wa kikeson rainawa? "Tace wai ba na baka hak'uri ba "ALLAH baka hak'uri nace " ta ajiye Abin da take goge falon Tana Shirin arcewa ,shiko duk ya gano manufarta guduwa zatayi ya Gama d'ana Mata ,ta ajiye kenan zata gudu ya sa Mata k'afa ya tad'o ta ,har kusan fad'o Mai tayi Amman FU'AD ya koce wai Kar ya had'a jiki da _dirty girl_ Dan Haka ta fad'a Kan wani lalausan carpet dake malale a falon ,har k'asa ta fad'i ganin ta ak'asa yasa shi fita harkar ta ya nufi bedroom d'in shi ,itako tayi ta maza ta mik'e tace "wlh bazan k'arasa gyaran ba mugu ban yafe ba Kuma wlh " ta zura da gudu ta sauka ,afusace ya dawo kafin ya cafkota ta fece....... *Maman shaheed ce* [4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *Fatima Abubakar Shu'aib* (Maman shaheed) _shafi na 18_ ```Na Gode Da Kulawar Ku Sosai My Fanc ,ngd Kwarai Da Kulawar Ku Gareni , ALLAH Ya Bar So Na tsakani Da ALLAH```👏🏼😘🥰😍 Tun da Ma'u ta Sha da kyar daga hanun FU'AD ,har yabar gidan Basu sake haduwa ba ,itako ta cigaba da aikin ta dasu Hari ,har taje ta Taya sa'adiya Aiki suka d'anyi Hira ... Kafin Ma'u tabar gidan taji mumcy na cewa Gobe FU'AD bazeje Aiki ba hutawa zeyi a gida wai ,Ma'u najin Haka cikinta ya duri Ruwa tasan Akwai takun sak'a Dan Dole ya takura Mata itako ta gaji d wanan ta Kura Dan Haka Dole ta Nemo makamin tunkarar wulak'ancin shi ko ta Nemo yadda zata mayar Mai d raddi ,da wanan tunanin ta bar gidan hajiya babba ... Bayan Ma'u ta gama k'arban wulak'ancin mama habee d gorin da ta Saba Mata ta shareta ,Bayan babanta y dawo ta Sami sasauci ,ranar kwana Ma'u tayi Tana dogon nazari Akan FU'AD burin ta koyaya ya Shiga bacin Rai daga gareta ,da kyar ta samo masalaha ,Aiko ta dinga Addu'a ALLAH ya Bata nasara Akan FU'AD gobe ,da farin ciki fal ranta ta kwanta .. Washe gari Bayan ta taimaka ma mama habee d aikin gidan kusan ta gama komai har dumamen tuwon gidan ita ta musu ,suna d'aki suna Jin ta ko su lek'o Dan sun San ta Kama aikin ,Dan Haka ,Tana ganawa ta shirya tayi tafiyar ta dama baba ya rigata fita ... Ma'u nagani da kwalin indomei a hanun ta Tana Shirin Shiga gidan mumcy baba me gadine ya bud'e Mata yake cewa Ina zata d kwali Haka? Tace sak'on mumcy ne ,yace toh babu matsala a mik'amai gaisuwa ga hajiyar ,Ma'u tace in Sha Allah ..... Ma'u na zuwa inada ake Adana motocin gidan ta ajiye kwalin Nan cikin firanin da suka gewaye gidan ta Shiga Haka ita kad'ai Ko da ta doshi kofan Shiga ,ta samu k'ofan Fallon a bud'e alamun wani ne ya Shiga ko ze fito ,Ashe FU'AD ne yazo fito y koma d'auko Abu ,y sake fitowa ,har Ma'u tasa Kai zata Shiga cikin falon,k'amshin turaren FU'AD ya sanar Mata d Yana nufo inda take ,d sauri ta Adana sallamar da take Shirin yi ta koma cikin furanin da sukayi k'awanya a tsakar gidan masu dad'in kallo d kamshi ta shige tayi luf kamar Babu mutum jiki.... Aiko Tana lab'e cikin firanin FU'AD y fito ya janyo k'ofan falon y doshi motan shi ,duk Ma'u na lura dashi har fitowa tayi taga yanata dube dube a cikin motan da alamu wani Abu yake nema yanata dubawa duk y bud'e k'ofofin motan ,Abin be Mai ba y Shiga ciki y zauna a wajen Mai zaman banza ya d'ebo wasu takadu Yana duba wacce yake nema ... Ma'u na hango tayi 'yar shewa da k'wafa ,daga bisani tsoro da rawar jiki ya kawo Mata ziyarar bazata yayin da ta doshi wajen kwalin d ta shigo dashi gidan ,ta Jima Tana shawara d zuciyar ta Akan Abin da take Shirin aikatawa ,tsoro nata yawo a k'irjin ta ,tunawa da suman d ya tab'a sata tayi Wanda taci Alwashin ,bazata yafe Mai ba har sai tamai kwatankwacin Abin da ya aikata Mata sanan zata yafe Mai shima sai taga irin Halin d ya Shiga sanan ,Dan Haka a fusace ta bud'e kwalin ta fito da kuliyar (mage) dake ciki wata me gashi kamar na yaron Kura ,ta sid'ad'a gabanta na fad'uwa tasan indai ya ganta aikin ta tabbas yazo k'arshe Amman tayi shahada Taki hak'ura ta sunkuya ta Isa bakin motan ta k'ofar baya ta saki kuliyar a cikin motar ,jikinta na rawa ta lalab'a ta koma har k'ofan falon hajiya baba da rarafe sai d ta Isa bakin k'ofan sanan ta mik'e ta Shiga bakinta d'auke da sallama ,Babu kowa a falon sai motsin mutane d tajiyo a kitchen,Bata k'arasa ba sai d ta tataro nutsuwar ta ta dasa a jikinta da zuciyarta tukunna ta doshi su Hari ,ta gagaishe su ,suka amsa cikin sakin fuska har ta Kama wani aikin kafin ta Fara nata na falon .. Shiko FU'AD hankalin shi kwance yake Yana duba takar dun shi ,Aiko kuliyar Nan ta kamo seatbelt ta d'ane kujerar da FU'AD yake Kai Tana dube dube can ta saki wani kuka irin na maguna .... Jin kukan a kunen FU'AD besan lokacin da ya kusan sakin fitsari a 3kwatan shi ba ,a sukwane ya juyo don ya tabatar ba wani bane yake tsokanan shi? Aiko suka k'ara 4eyes da kuliyar Nan ,beyi aune ba ta fad'o jikin shi ,dabara ko azacin nutsuwa yayi yunk'urin tureta duk basu zoma FU'AD ba sai ma da ta sa faratan ta tanason haurawa fuskar shi ,anan yasa ihun da be tab'ayi ba a Rayuwar shi sai gashi a sume cikin mota kuliyar Kuma Tana jikin shi ... Baba Mai gadine ya jiyo ihun y taho a razane Yana cewa yallab'ai lafiya? Sai tozali yayi d yallab'ai a sume ga kuliya a jikin shi ,da sauri y talabo shi Yana Mai mgn ganin Babu numfashi atare dashi yasa shi rikicewa ya nufi falon hajiya babba a rikice ,Yana Shiga y Fara Kiran hajiya ! Hajiya!! Yallab'ai fa Babu lfy kizo ... Da sauri mumcy ta fito daga kitchen har su harin ma ganin yadda me gadi ya shigo musu , mumcy ce tace wane yallab'an? Murya na rawa me gadi yace auta dai naki Yana farfajiyar gidan acikin mota baya numfashi ........kafin y karasa mumcy ta fice a zuwa wajen motar Tana Ina zeje shida yau baida zuwa office ,yaushe ma ya sako k'asan? Da sauri suka nufi motar tashi ,ganin FU'AD Babu alamun numfashi a tare dashi yasa , mumcy rabza salati da salalami Tana Akira Mata jameel yazo y tayata ganin bak'ar Rana yau ,da sauri Ma'u ta tafi jikinta sai rawa yake kuka kuwa tuni ya kwace Mata da take isar ma da Jameel sak'on mumcy tsabar tausayi da nadamar Abin da ta aikata da ba kowa ne ya sani ba ,sosai take kuka tsakanin ta da ALLAH ta ,da gudu Jameel d sa'adiya suka Zo ,suka bar Ma'u a baya Tana kukan nadama , Jameel ne y karb'i FU'AD a hannu mumcy da ta takabo shi Yana jijigaji Yana Mai mgn ,Bayan yayi Yan gwaje _gwajen shi ya razana can Kuma yace Ina k'anina baze mutu yanzu ba ,baze mutu ba mumcy ,Ina driver yazo muje asibiti d gagawa ,Aiko Mai gadi yace Bari amai waya dazu ya tafi gida wai kanshi namai ciwo .... Jameel a fusace y d'auki key d'in motan FU'AD din d ya gani a k'asa ya ma mumcy umarnin Shiga motan gidan gaba ,ya mayar d FU'AD baya ya kwantar dashi ,suka doshi asibiti........ Suna Isa aka Fara ,ba FU'AD taimakon gagawa jikin mumcy sai rawa yake tanata jarumtakar jero adu'o'i Kar autan ta ya mutu ,shima jameel sai kai komo yakeyi Yana buga hannu.... Ma'u kamar tabisu taji Amman Ina Babu Hali ,tunanin ta in FU'AD mutuwa yayi fa? Shi kenan ta Shiga uku itakam tasan sai ankama dangin ta Kam yadda su mumcy sukeda masu fad'a aji (kud'i) Nan ,can kuma tace to ai Babu Wanda ya sani ,sai ta sake cewa kisan Kai fa ,wlh fad'a zanyi na gwamaci kunyar duniya da na lahira ,sai ji su sa'adiya d su Hari sukaji ta k'ara wani uban kuka Mai ratsa zuciya kamar wacce akama mutuwa ,kowadai a tsorace yake ,Amman na Ma'u daban ne da na kowa ,sbd suna cikin Alhini shiyisa Basu tsaya tunanin dalilin tsananta kukan ta ba ,sai danganta abun d sukayi da yarinta ko tsantsar tausayi d Babu Abin d baya sawa ..... Sa'adiya d Hari NE suka dinga ratashin ta .... Asibiti......da kyar FU'AD y farfad'o da Addu'a y farfad'o Yana neman tsari da kuliyar ,Yana runtse ido Yana cewa su d'auke Mai ita ,sai a lokacin mumcy da Yaya Jameel suka dawo d tunanin su kan kuliyar d Yaya Jameel din d hannun shi ya fitar da ita a motar d zasu taho asibiti ,don suna cikin tashin hankali ne yasa Basu tmby meya kawo kuliya gidan ba har Kuma motar FU'AD ,sai a lokacin mumcy ta tuna ai tayi manakin ganin kuliyar ,yanzu ta sake tabatar d itace sanadin shigan autan ta Halin da yake ciki a yanzu ,Amman burin su yanzu lpy FU'AD .... Mumcy tace Dr yayi duk Mai yiwuwa y dawo Mata d nutsuwar d'anta sanan tanaso abar shi y huta yad'an samu bacci ,Bataso y cigaba d surutun da yayi yanzu .... Dr yace insha ALLAH komai yazo da sauki ,kawai zamu samai ruwane sakamakon firgita da yayi sanan Wanda ze zauna tare dashi yayi k'ok'arin faranta ransa muma zamuyi namu k'ok'arin wajen kawar da razani da tsoran dake zuciyar sa .... Mumcy ce tace Jameel yaje gida ita zata zauna da shi ,Jameel yace aa shi zai zauna ita ta tafi ,ganin zasuyi ja'in ja dai ,sai mumcy tace to Bari Naga yanayin jikin sai na tafi ,Jameel yace to ... Sa'adiya ce ta Kira Jameel Tana tmby jikin FU'AD ,ya sheda Mata d sauki Yama farfad'o Amman a razane d alamun kuliyar Nan ce ta firgita shi ,acema baba Mai gadi yayi gagawan fitar da ita daga gidan , sa'adiya tace to ,ta aika aka sanar ma da Mai gadin ... Duko sunji dad'in farfad'owar FU'AD musamman Ma'u harda doguwar ajiyar zuciya tayi ...... Su Hari ne sukaje suka shirya lafiyayen abinci aka ba Mai Aiki takai musu ,sai suka taho da mumcy gida .... Mumcy duk Bayan minti talatin sai ta Kira Jameel taji jikin FU'AD ,shiko Jameel Yana kwantar Mata da hankali ... FU'AD dai ya samu kansa da kyar Amman har yau inya tuna da kuliyar Nan sai yaji Babu Dadi ,sanan ya Kara tsananta tsana da kyamar kuliya yanzu ,sosai ya Rasa kuzarin sa ,da taimakon Jameel y samu yaci abinci ya Sha magani yayi sallah ,har ya samu yayi waya da mumcy Dan hankalinta ya kwanta sosai ,taji dad'in Jin ya samu lpy kuwa sosai ... Ma'u dai jiki Babu kwari ranar ta gama aikinta har yabar gidan sai ma momcy ce take cemata ta saki jikinta ai ya samu sauki ,Tana alakanta firgitar Asama'un da Mai tausayice shiyisa duk tashiga wani Hali ,Amman shi FU'AD ya tsani yarinya Haka kawai ,gata ita Tana tausaya ma Halin da ka Shiga ,kaiko lokacin d ka tsoratata ko d'igon tausayinta bakaji ba , ALLAH dai ya cirema tsanar yarinyar Nan son ..... FU'AD dai a asibiti y kwana shida Yaya Jameel , mumcy kusan kwana tayi Tana waya dasu,shima jameel Yana Kiran sa'adiya akai akai Don yaji lpy ta .... Ma'u kwana tayi Tana tausayin FU'AD Tana mamakin kamar FU'AD Yana tsorata har d Suma Haka? Wani sashin zuciyar ta kuma yace kema Haka ai yasa ki ,kawai sai ta samu kwarin gwuiwar itama ta Rama yanzu abun ya wuce a zuciyar ta ,Amman duk da Haka Tana Jin babun dad'i Aranta ..... Washe gari Ma'u batazo Aiki d wuri ba ,har mumcy ta fita asibity ita d sa'adiya sukaje wajen FU'AD don ganin shi d Kuma in an sallame shi su dawo gida ... Bayan Ma'u tazo ta kammala duk wani Aiki d tasan natane har saman FU'AD sai d tamai k'alk'al ,Bayan ta gama ta Shiga kitchen Tana tayasu suna hiran rashin lpy FU'AD ,itadai Ma'u tayi shiru Tana jinsu ,sai mumcy ta Kira wayar Hari wata k'arama da mumcy t siyamata don Kira irin Haka ,take tambayar ta Asma'u tazo kuwa? "Tace "eh" mumcy tace ta gyara ko Ina ? Harri "tace eh Mumcy "tace bani ita" Harri ta mik'ama ma'un waya,ma'u ta k'arba ta gaishe da mumcy , mumcy tace tayi k'ok'ari ta gyara saman FU'AD yanzu ,sai Ma'u "tace ai na gyara tun d'azu ,sai mumcy tace to ,Suma gasunan dawowa an bashi sallama ,sai cikin Ma'u y d'uri ruwa ji take kamar ya gano ta ,ta Rasa dalilin d yasa ta tsorata take tunanin gamuwar su al'halin Babu Wanda yasan shirinta ....... [4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *Fatima Abubakar Shu'aib* (Maman shaheed) _shafi na 19_ *Wanan page din sadaukarwa ne ga duk wata Mai suna ASAMA'U ,Ko Ma'u ko Asmy ,Duk dai* kawayen ga fejin kunan kuyi yadda kuke so dashi🥰😍❤ Ansallami FU'AD dg asibiti har sun dawo gida .... Ma'u cikin shirinta n zuwa wajen Aiki gidan mumcy ,wata zuciyar na karanto Mata rashin kyautuwa Abin d Tama FU'AD ,wata kuma na ganin dacewar hakan ,cikin kwarin gwuiwa dai ta k'arfafi zuciyarta tace itama ai ramawa tayi ,Dan Haka Haka tace ,ai Rama cuta ga macuci ibadane ,yanzu munyi 1,1 inya sake mun Nima sai na Rama , Ma'u d wanan tunanin ta siyi katin mtn na 200 ta nufi gidan manan hafeeza k'awarta da ta b'ata *RIK'ON KWARYA* Aikinta don ta saka a wayar mama su gaisa ,Tana Shiga ta korama mama bayani ,mama nata Mata dariya Tana cewa in Banda abinda har sai ta wani siyo Kati ,ai ko flashing akama hafeezar zata Kira , Ma'u dai tace babu komai mama so nake muyi Hira sosai mun kwana biyu bamu gaisa ba , Ma'u ta karbi wayar tasa katin ta Kira k'awarta ,sunjima suna Hira Tana Bata lbr gidan hajiya babba d karamcin ta har tafiyar da zasuyi d Yaya Jameel d matar shi , Ma'u na k'ara kozanta rashin kirkin FU'AD ,Amman hafeezar na kare shi ,Haka dai har ma'un tabarma mama sauran canjin a wayar ta Mata godiya d sallama ta tafi gidan mumcy don Aiki.... Cikin kwarin gwuiwa Ma'u ta Shiga falon ,musamman d taji alamun falon cike yake da mutane ,bakinta d'auke da sallama , mumcy d wasu tsiraru na falon ne suka amsa Banda FU'AD d ko samun darajar kallo batayi ba a gunsa ,dama itama batasa Rai ba ,Dan Haka wajen mumcy ta nufa har k'asa ta gaisheta sanan ta gaishe d Yaya Jameel sanan aunty sa'adiya ,sai FU'AD ,Yana Shan k'amshi ya amsa shima don mumcy ta jefeshi d kallon tuhumane ,Yana amsawa ,ta sake cemai ya k'arfin jiki? A dak'ile yace lpy ta qalau ko Baki gani ba? Mumcy ta katse Al'amarin d cewa "Asamu Kinga har Harri ta gyara falon ke jeki ki gyara saman FU'AD yanzu sai ki dawo dakina kinji? Ma'u ta amsa d toh, ta mik'e zata tafi mumcy tace "Asma'u ko Zaki Fara karyawa? Bud'ar bakin Ma'u tace "laaa mumcy wlh Alhmd na karya ai baba baya barina na fito ban karya ba , FU'AD ko cewa yayi kamar gaske y d'auke wuta kamar bashi y furta hakan ba Kuma kowa yaji shi , mumcy tace jeki to anjima Kya k'ara, Ma'u ta haura Tana mita ai me Hali baya fasa Halin shi ,gwanda d nayi maganin ka ,aikin banza yasani asarar mage Haka kawai anbani ita Don nayi kiwo na kawo don na Rama Abin d yamin yasa anfitar min d ita ,Ni ba Abin nayi tmby ba na jama kaina Ruwa ,Dan rainin hammata kawai .....Tana tafiya Tana mita har ta Isa falon. K'alk'al ta gyare Mai saman ,Yana zaune anata Mai sannu ,kowa na ji dashi awajen musamman Yaya Jameel .... Bayan Ma'u ta gama gyaran ta sakko k'asa ,ta Shiga d'akin mumcy don gyare Mata shi .... FU'AD ne yace ze haura sama don ya huta ,duk d mumcy da Yaya Jameel suna mgn tafiyan su ne ,Amman FU'AD sai yace duk Abin d aka tatauna a ajiye Mai inya tashi a bacci a gayamai , sa'adiya na tsokanan shi tace angama ,k'aramin megida *Na mage* lokacin da yayi daidai d fitowar Ma'u daga d'akin mumcy shi Kuma FU'AD Yana Hawa k'afar bene ,Aiko y juyo yace haka Kika samin ko matar Yaya? Tayi fari d ido tace "yes" Aiko yayi kwafa alamun sunan bemai dad'i ba ,itako Ma'u murmushi da Jin sunan d aka rad'a Mai ...... Suko su mumcy dariya sukayi ,sukace sunan ya Dace da Kai , gashi har y kaika ga kwanciya a asibiti ..... Har ma'un tayi hanyar Shiga kitchen wajen su Hari ta jiyo hirar su ,Aiko sai Yaya Jameel yace "Ma'u kike ko Asma'u kin Gama shiryawa ko don tafiyar mu ta kusa Ana bani update Nima Zan sanar Miki don anrage lokacin .... Ma'u Kai ta gyad'a Mai Alamar eh ,sai mumcy tace "magana zakiyi Asma'u " sanan tace "eh insha ALLAH" sanan sukace taje sai taji kira,tace "toh"... Ma'u Tana murna da tafiyar wani b'angaren Kuma tanajin Babu dad'i zata zauna na wani lokaci d mutanen d Bata Saba dasu ba ,zata bar babanta Abin share kukanta gatanta na duk duniya tunda ta Rasa mahaifiyar ta ,dg baya ma tayi watsi d tunanin tace "Rayuwa dama ai ta gaji Haka , ALLAH y tabbatar Mata d abin da zefi zama Mata Alkhairi a Rayuwar ta .... B2k ne da wasu daga cikin abokanen su FU'AD sukazo duba shi ,Bayan sun Gama cacafkewar su zasu tafi sunaya tsokanar shi wai ya zama *na mage* Yana ce musu sunyi biyu Haka ma wifyn Bros tace Mai ,wlh ze karta musu RM in Basu Bari ba ,Aiko suka sa dariya suna cewa kabada maza wlh ,yace "eh yaji d'in don Basu San meya faru dashi bane a zahiri su yanzu bar'ini suke ji ,har zasu fita a falon ,B2k yace "ya Ina bara gurbin kamun da kace kamin ne d'an iskan abokina? FU'AD be furta komai ba sai ga mumcy d Ma'u na biye d ita ,sai ko mumcy tace "aah badai kunfito ba ? B2k ne yace "eh wlh zamu koma wajen Aiki mumcy munga jikin d sauki ma mutumin namu ya fito daga tarkon kuliya ,sai wani a cikin su yace "hhhhh dakyar Nasha yafi dakyar aka kamani ,Amman Kai baka Sha ba don kamuwa kayi wlh ,Aiko sai aka dinga darawa Ana dariya har mumcy , Ma'u ma batasan lokacin d murmushi Mai sauti ya kwace Mata ba ,Aiko sai a idon FU'AD ya had'e Rai yace _dirty girl_ waye sa'anki anan? Da har Ana magana kike k'ok'arin ......... mumcy ce tace "bana so son" ba ruwanka d ita ,sanan B2k yace oh itace Yama FU'AD alamu d ido ,sai ko FU'AD y Harare shi ,shi ko B2k yace ,Abin yayi fa FU'AD yaushe zamuyi magana? Sai ko FU'AD y Harare shi y d'aure fuska y fahimci me yake nufi ,y fice y barsu a falon irin in bazaku fito ba kuta zama d'inan ,sai ko sukace mumcy mun tafi ALLAH y k'ara sauki ,suka fice ...... B2k na son tsokanar FU'AD ,Amman yaga yaci magani ,sai y kyale kawai ,suka Mai ALLAH y k'ara sauki suka tafi ...... Bayan FU'AD y dawo daga rakiyar su ,sai y Sami Ma'u a falon ita kad'ai y k'arasa wajen ta y zuba Mata rankwashi akanta Mai lulub'e da hijab ,batare d tasan y shigo ba atsorace tace ,mena maka? Yace "tambayata ma kike? Bakisan Shiga sha'anin mutane da kikayi ba dazu sai kace dake ake? Tayi nesa dashi Tana Jin zafin rankwashin Tana sosawa tace au to ,Ni din Aljanace da bazan Shiga sha'anin mutane ba? Yayi yunk'urin k'arasowa inda take ,sai ko ta k'ara nesa dashi tace ,Naga dai Nima mutum ce kamar kowa ,afusace FU'AD y biyo ta, ta afka kitchen d sauri ganin Kar taci bulus be hukuntata b y bita kitchen din Yana Shiga yaga harri sai y wayance d cewa ke kawo min Ruwa d juice yanzu Nan ,sai ko Harri tace yi maza Ma'u ki kaima yallab'ai ruwa juice Yana Miki magana ,jiki Babu kwari tace to ,ya harareta sanan ya fice Yana jiranta a falo , Ma'u nata nuk'u nuk'u ta kasa Kai Mai ganin Harri Kar ta gane tsoron fita takeyi sai kawai tayi shahada ta fita ,ta Kai Mai jiki na rawa zata ajiye Mai ta gudu yacce in ta ajiye wlh sai y hukuntata ,sai ta mik'a Mai tace "toh gashi ,sai yasa hanu y d'auki juice d'in ya bud'e bakin ,zata ajiye Mai Kan center table ta gudu kenan duk'awar ta keda wuya ya watso Mata juice d'in ajikinta har fuska yace "ko Dan gaba da glass cup ake hadoma da mutum ba a bashi Haka ba ,Kuma acikin minti 2 ki gyara wajen wlh ko hukunci ya biyo baya _dirty girl_ kawai ,wani k'ululun bak'in ciki ne ya turnike Ma'u gashi duk y Bata Mata hijab ,tace "toh ai nata ko su turawan na kasashen duniya ma bana k'asata 9ja ba ,suna Shan Ruwa da bakin roban da shi lemon ba hadisi bane ko aya da za'ace lalai sai anzuba a Kofi kafin ya Shiga Baki ba ,su da sukafi mutum wayewa kenan .......Tana Shirin guduwa y kamo gefen hijabin ta ,ta kusa fad'uwa ya Kama kunnen ta acikin hijabin yace Ina gargad'an ki da ki guji mayar min d amsa ayayin da na Miki magana ,wlh don mumcy na barki a gidan Nan d tuni na k'ara Miki wuta wlh ,Naga alama Baki da kunya wuyanki y fara kauri ko? Ya sake Mata kunne kenan ze rankwashe ta sai ta gudu Tana cewa "ai dama ko a lahira wani nacin Albarkacin wani kaima wataran bakasan ko nawa zakaci ba "ta shige da gudu Tana cewa *na mage* kawai FU'AD kasa gaskatawa yayi furucin daga bakinta ya fito ko ba daga bakinta ba ,cikin Isa da izza yayi k'ok'arin binta har kitchen d'in domin tabatarwa , mumcy ce ta fito ta dakatar dashi ta hanyar yimai magana Akan tafiyar yayan shi Jameel ,sai ya had'iyi hak'uri Akan Abin d y k'udiri aniyar yi ,ya zauna Yana huci suna Hira d mumcy Amman be Bari ta fahimci Halin d yake ciki ba ,.... Ranar Ma'u har tabar gidan Bata Bari sun had'u d FU'AD ba . Washe gari , Ma'u batazo Aiki ba ,sbd babanta ba lpy ,sai washe gari taje ,koda mumcy ta tambayeta sai ta fad'a musu dalilin rashin zuwantan ,suka Mata ALLAH ya bashi lpy,ta amsa d Amin. . Tafiyar su sa'adiya d ma'u tazo , mumcy har ta Fara kewar ta don mumcy na yabawa da aikin ma'un d'ari bisa d'ari ,Amman ya zatayi tunda sa'adiya d lalura Haka zata hak'ura , mumcy d kanta ta fad'ama ma'un ,sanan Jameel y d'auki sa'adiya sukaje suka sanar ma da baban ma'un har da ranar da zasu tafin ,suka Mai Alkhairi da kyar baban Ma'u y karb'a sai da sukata bashi Baki sanan .... Saura kwana 3 su tafi Sam FU'AD besan d Ma'u zasu tafi ba don be tab'ajin anfad'a ba ,don Haka yanata kulama Ma'u irin mugun kamun da zai Mata .... FU'AD yanata cema yayan shi zeyi kewan shi ,sun Jima suna Hira a falon don saura kwana 2 ya rage musu ... Ma'u nata Shan sabon wulak'anci wajen mama habee akan maganar tafiyar ta da baba ya Gaya Mata wai zata yawon neman mazan Abuja dai don ta kawo ma ubanta kud'i to su sani kwayar cutar side (k'anjamau) Tana Nan Tana neman Rai ankasa samun Mai kashe ta ,baba yace ALLAH y tsari ma'uta daya dukan Sharin Abin ki da Abin Halitta ,mugunji mugun gani ALLAH ze tsareta ,mama habee a zahiri ta sake bayanama baba tsanar da Tama Ma'u akan tafiyar Nan Don da Tana b'oye Mai wani Abu ,baba ma yanata mamaki ,ma'un ma tanata neman tsari da jafa'in mama habee ,sosai mama habee ta k'ara jefama Ma'u Karan tsana da takura ,Ma'u nata jurewa don tasan ta kusa samun Isa badan baban ta ba da bazata taso dawowa ba ma ... Ana gobe su Jameel d sa'adiya d ma'un zasu tafi , mumcy d yaranta sun Jima suna hirar zumunci , FU'AD da jameel sunata kewar juna ,Ma'u ma tayi kewar mumcy sosai mumcy ta fahimci hakan atare d Asama'un , Asma'u ce ta cema mumcy Inna Miki wani Abu hajiya ki yafeni ,mumcy tace bakimin komai ba Asma'u , ALLAH ya kaiku lpy ,Naga kinason karatu zansa a samo Miki me koya Miki darasi a gida don ki taimakawa karatunki da ya kwanta kinji ,sosai Ma'u taji dad'in,ta dinga ma mumcy godiya ,ranar d wuri Ma'u tabar gidan Bayan Tama mumcy da su Harri sallama ,ta wuce gida don k'arasa shirinta ga Kaya da mumcy ta siya Mata harda jaka Mai kyau ta zuba kayan tafiya ... Tunda Ma'u ta shigo d jakar mama habee take Mata habaici da Gori wai zata yawon ta zubar shegiya me Halin uwarta Ana musu magana suna shiru kamar sunfi kowa hak'uri a duniya ,Ma'u dai ko ufan batace ba ... Haidar ne yaketa cewa Yaya Ma'u karki tafi wlh kamar na biki ,sai ma'un ce ta dinga bashi hak'uri ,da kyar ta Shawo kanshi da d'ari 200 tace ya kaima dije Mai awara yace Mata kulin zezo ya dinga karban ta ishirin har kud'in ya k'are da gudu da murna ya fita zeje Kai kud'in ,humaira na Kiran shi ma yak'i ko sauraranta ,tace sheke me Kama da d'an rik'o ,Aiko mama habee ta wurgo Mata muciyar da take talge tako sameta a kusa da Baki ,humaira tasa ihun da sai d Ma'u da baba suka fito daga d'aki suna tmby lpy ? Humaira dafe wajen tayi ,itako mama habee cigaba d sababi tayi wai ita Bata haifi shege ba da zata sheganta Mata yaro Kuma ita ba rik'o aka Bata shi ba .... Baba ne ya harareta yace ,toh ai barewa bazatayi gudu ba d'anta yayi rarafe don duk daga wajenta takejin kalaman tun Tana yarinya har gashi ta haddace ,sai ko ta koma kanshi ,yace Ni bazakiyi Tani ba Kinga ficewata yayi tafiyar shi masalaci don Kiran sallah d yaji anayi ,sai t dawo Kan Ma'u ,to uwar munafukai d ankunshe a d'aki Ana had'a kayan d za'a ji dad'in bin maza dasu ,Amman garorin maza daga Jin ihu anfito tsugudidi ,munafukai wacce take Shirin gujema talaucin d ubanda ya gada ,kije duk yawon duniyar ki indai talauci ne da aka buga muku hatimin shi Yana Nan manne daku kamar fatar dake jikin ku in ALLAH ya yadda kije ki Gama yawon naki ki dawo Mai don wlh sai kin dawo Mai Koda da *kiranye* ne.......sum sum Ma'u ta koma d'aki Tana me mamaki da Jin furucin mama habee *kiranye*? Me take nufi ? Dama mama habee nabin bokaye? Kiranye ai inajin kamar a wajen bokaye akeyi ko wajen malamai kamar naji ance Kuma ,koma dai menene ta Kara bani tsoro a Dole na k'ara tsare kaina da Addu'a don tserema sharinta .... Ma'u ta gama had'a kayanta tsaf Gobe har gida zasuzo su d'auketa su wuce ,sosai ranar Ma'u suka kusan raba dare suna Hira d babanta da haidar har yayi bacci a cinyar baba ,mama habee nata habaicin ta sukaba banza ajiyar ta ,Abin ya kular d ita... Washe gari d sasafe FU'AD ya shirya wai zasuyi meeting ne kafin ya Shiga office ,don Haka gudu gudu sukayi sallama da yayan nashi da sa'adiya Diya yace sai sunyi waya Kuma ai zai kawo musu ziyara Abujan ,suka rungume junan su suna kewar juna ,daga baya suka rabu sukama juna fatan Alkhairi ,har wajen mota Yaya Jameel y raka FU'AD har sai d yabar harabar gid'an d mota sanan y wuce sashin su suka Kamala shiri suka fito tsaf suka nufi falon mumcy ,suna Gama karyawa ,Suma suka mik'e sosai momcy tayi musu Addu'a da fatan sauka lpy da tuk'i ahankali don baby, dake cikin sa'adiya taji kunya ,har haraban gidan mumcy d su Harri suka rakasu suka fita suna kewan juna ,Basu tsaya ko Ina ba sai k'ofan gidan su ma'un ... Bayan sa'adiya ta Shiga don fito d ma'un shikin Shiga Mai tsari d tsafta tun ba'aje garin su buharin ba har naso na kasa gane ta ,tun a wajen d ma'un takema mama habee da humaira sallama , sa'adiya ta fahimci wacece mama habee Aiko ta kashe bakinta da wasu 'yan kud'ad'e har da karb'a Tana godiya ,Amman Basu Sami arzikin Addu'a ba har suka bar gidan dama ba ita suke jira daga gare su ba ..... Har wajen baba sukaje suka Mai sallama ,yayi ta kwarara musu Addu'a ,har Jameel zeba baba kud'i ya fasa Kar yaga kamar cinikin yarsa sukayi inyaso daga baya y Aiko abashi ... *Yaya jameel*, *Aunty sa'adiya* , *Asma'u* Ma'u sundau hanyar Abuja ......................... [4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITERS ASSOCIATION*💥 Pg 20 Su Ma'u sun sauka lpy ,suna Isa gidan suka nufi sashin su aka nunama Ma'u masaukin ta ,d'aki ne se bandaki aciki ,aunty sa'adiya ta umarce ta da ta Shiga d kayanta ta watsa Ruwa ta huta sanan suci abinci da sukayi take away d'in shi tun daga hanya . Suma kowa d'akin shi ya tafi ya watsa Ruwa suka sake shiri sanan ,sa'adiya ta kaima Ma'u abincin ta Suma suka zauna sukaci nasu ,Yaya Jameel nata ciyar d sa'adiya abaki Mai d'auke da gudan jinin shi ,lalabata yake sosai . Ranar haka ma'u ta kwana batare da ta aikata komai ba ,Amman zuciyarta cike da kewan babanta d haidar har da kewan hajiya babba inta tuna d Rayuwar FU'AD acikin gidan sai taji ALLAH ya rabata da wahala na muguntar shi ... Washe gari FU'AD gudu gudu sauri sauri ze tafi wajen Aiki ,yake ba mumcy sautun cewa in ma'ule take ko wa intazo ta gyara Mai saman shi gyara Mai kyau Kuma ,mumcy ta manna Mai ta amsa da toh uban ma'ule ....sai FU'AD ya Sosa keya ya fita Alamar ya gane magana mumcy ta Gaya Mai Akan Ma'u ,ita ko cewa tayi ba sai ka ganta ba ... Washe gari jameel ya fita yabar su a gida don ganin ma'aikatar da aka kaishi ... gyaran gidan gaba daya Ma'u ce tayi da aunty sa'adiya ta Fara gyarawa sai ma'un tace "ta barshi zatayi" Sosai aunty sa'adiya kejin son Ma'u da son saka Mata da irin kyautatawar da take Mata kodan ta fito d ita don ta fuskanci yarinyar lulub'e take da wata baiwa da Baki baze iya furtawa ba ,Dan Haka sa'adiya ta Kira Ma'u Bayan ta gama komai suna Hira ta tambayeta lbr rayuwarta ,ma'un Bata b'oye Mata komai ba nadaga Rayuwar ta ,sosai sa'adiya ta tausaya Mata tayi Alwashin kunna nutso cikin Rayuwar ma'un don tuni ta goge Mata Ma'u ta koma kiranta *Husna* sosai Ma'u takejin sunan , sa'adiya taji Ma'u ta iya wasu hadisai d litattafai Kuma ta wuceta a Qur'ani ,sai sa'adiya tace "Ma'u ta dinga koya Mata Arabin (karatun addini) ita Kuma ta koya Mata English (karatun boko) duk da dai ta iya Kuma Tana ganewa ,duk sun yadda da Haka .... Sosai Ma'u ta Fara Hawa hanya d'od'ar Amman fa duk inda zata Shiga a gidan da hijabinta karami ko gyale take yawo Dan kunyar su takeji gaba dayan su,har yanzu Bata saki jiki dasu ba . Bayan FU'AD y dawo yaga angyara Mai komai k'amshin d'akin ba kamar yadda ya Saba ji ba beyi magana ba ,Haka washe gari ya Kuma gayama mumcy agyara Mai saman shi,kusan sati biyu kenan Yana bada umarni Ana bi ,ahaka ba tare da yasa Ma'u a idon shi ba ,sbd dama ba agaban shi take ba ko damuwa beyi da seya ganta ba... Ma'u sosai takejin dad'in zama da su Yaya Jameel d matar shi gashi duk taba Ma'u Kaya masu kyau harda Wanda Bata sa ba ,Ma'u dai Ashe kyakyawace ,ta zuwa party ,ta gaban mota ,wacce in aka jera Mata dubu Wanda zasuyi gasar kyau ko shakka Babu in batazo ta 1 ba zata Zo ta 2 ,kyanta ya Fara bayyana damma Bata kwaliya sosai ,tanayi Amman sama sama ,koni da kyar na gane ta ,gashi sa'adiya Tana koya Mata abubuwa da yawa sosai na rayuwa da wayewa ga karatun su ya gagara sakamakon yanayin d take ciki na juna2 sai malami sa'adiya tasa Jameel ya d'ako Mata yake koya Mata a gida Kuma sosai take fahimta har malamin yake Basu shawara da takai tsawon wani lokaci in suna karatun tas zata iya zana WAEC Dan kwanyar ta Tana ja sosai har mamaki take bashi d iyayen gidan nashi ,Yaya Jameel yace ta dage ya Mata Al'k'awarin biya Mata kud'in WAEC DA NECO indai tayi k'ok'arin dagewa da karatu ,sosai ta musu godiya da tabbatar musu da cewar zata dage insha ALLAH. Tafiya nata tafiya cikin aunty sa'adiya yanata girma ,Ma'u ce Mai komai agidan ,wata Rana har fita sukeyi yawon Shan iska da siye siye ,Jameel nata aikin shi ,sosai suke waya d FU'AD Yana ce musu zezo har yau shiru ... FU'AD ya kwana biyu baya ganin Ma'u Yana so ya tambayi mumcy Kuma sai ya tuna meye hujja shi na tambayan meya had'a da ita ,shi d ya rabu da ganin kazama ma ALLAH ya taimake shi meye zeyi da ganin ta ,Dan Haka ya share ko bi takanta be sake ba sai ma sabgogin shi daya fuskanta tunda Tana gyara Mai saman shi ai shikenan , mumcy ko Jameel ko aunty sa'adiya Babu Wanda ya sanar Mai Ma'u Tana tare dasu ..... Itama ma'un hankalin ta kwance kamar Bata tab'a gamuwa da mugu FU'AD ba ...... Mumcy na zaune sunata Hira da FU'AD sai yayan dadyn su ya Kira ,Tun da yaji mumcy tace "ASSALAMU ALAIKUM" Alhaji Yaya ,sai FU'AD yasan me Kiran Wanda ayanzu Babu Wanda ya tsana kamar shi ,Bayan sun gaisa sai yace Mata Yana Nan zuwa k'arshen wata Nan Kuma in yazo da maganar bikin FU'AD zezo asanar Mai kafin yazo Kuma da iyalin shi zasu Zo ,be jira cewar mumcy ba ya kashe wayar shi . FU'AD tuni ya kufula , musamman da mumcy ke Kora Mai jawabi Abin da yace , FU'AD ko magana beyi sai had'e gurar sama da ta k'asa da yayi ,mumcy ce ta dinga Mai nashiha da tausar sa da bashi shawara Akan inyanada wacce yake so ya kawo in Babu ya Nemo ko adangi ne har ta dinga lisafo Masa matan da suka dinga nunawa suna sonshi Amman ko 1 be tab'a kulawa ba ,Amman FU'AD ko ufan be ce Mata ba sai ma tashi da yayi ya Fara Hawa bene ze tafi d'akin shi ,Yana cewa in yazo yaga Babu matar ya hak'ura ya barni ai , mumcy sai ajiyar zuciya tayi Tana Addu'a akan zabin ALLAH ,ta Kira Yaya Jameel ta sanar Mai Akan ya Kira FU'AD ya tataushe shi y bashi Baki ...... Kwanci tashi Babu wuya saura kwana 10 zuwan Alhaji yayan baban su FU'AD ,hankalin FU'AD a kwance Amman na mumcy atashe da Yaya Jameel Dan har sun Rasa yadda zasuyi da taurin Kan FU'AD sun zuba Mai ido ..... Ma'u ta samu an samo Mata number baban ta da ta hafeeza k'awarta ,don sa'adiya ta Bata wata Nokia wacce Babu number kowa sai ta mumcy da babanta da hafeeza da aunty sa'adiya kawai ...... Tanata karatun ta ta k'ara kyau ,cikin aunty sa'adiya ya fito dodar don ta Shiga watan haihuwar ta ma ............. [4/23, 4:00 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AB* (Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg 21 *SADAUKARWA GA MASOYAN MA'U MUSSAMAN NAME SAKE UMMU QASEEM*😍🥰 Mumcy ,Yaya Jameel suna cikin fargaban zuwan Alhj Yaya ,shiko FU'AD ko ajikin shi an tsikari kakausa .... FU'AD Yana zaune a d'akin shi Yana latsa wayar sa ya Shiga IG ,ya fita y koma WhatsApp sai ya Fara viewing status na fanc can y ga na aunty sa'adiya be fiye viewing status na kowa da kowa ba ciki harda na matar yayan shi ,Amman yanzu sai y tsinci kanshi da bud'ewa yayi tozali da pic d'in ta da ita d wata matashiyar budurwa d'anya sharaf Mai asirtacen kyau ,azahiri tamai kwarjini Amman ji da Isa da tak'ama ya Hana ya gazgata zuciyar shi bare shed'an yamai wasiwasi a tunanin shi,Dan Haka y banzatar da Abin ,Bayan y Gama viewing status d'in har k'arawa yayi ,gudun Kar zuciyar shi ta bijiro Mai d wani Abu kawai ya fita ya koma duba sak'onin da suke ta shigo Mai . Yaune Ma'u da sa'adiya sun fita suna tataki Tana d'an tatakawa saboda ance ta dinga motsawa Dan haihuwa zata iya zuwa Mata koda yaushe ,shine suke fita da Asma'u ,sun fita lpy a hanyar su ta dawowa kafan aunty sa'adiya ta rik'e d'akyar ta samu ta d'aga sun Fara tafiya k'afan ta sake rigewa ko d'agata ta kasa yi sai zama da tayi Kan wani kwalbati dake bakin wani link d'in unguwan su ,Jin abun na kamari gashi Ma'u sai subo Mata ruwan sannu take tun Tana amsawa har ta gagara ,da Ma'u ta rikice har cewa tayi ko ta goya ta? ,Ita dai sa'adiya waya ta mik'a ma ma'un tace ta Kira Mata Yaya Jameel ,cikin sauri da himma Ma'u ta lalubo number d taimakon sunan d sa'adiya ta fad'ama ma'un kamar yadda tayi saving sunan dashi ,bugu 1 ya d'aga ya Fara tsokanan ta wai sai yaushe zata haihune suci hanji ,Jin Haka Abin Yama ma'un banbanrakwai taji nauyin mayarmai da amsa sai tasama sa'adiya wayar a kunne ,sai sa'adiya ta Fara Mai mgn Tana cicijewa ,yanajin Haka yace "Bata da lpy ne ? Tace eh yazo suje asibiti kawai ,da sauri ya tambaye su inda suke ,suka kwatanta Mai Basu da nisa da gida sosai Dan Haka yace gashi Nan zuwa shima yanzu ya Shiga gida Dan Haka zai taho da baby bag din da suka had'a na haihuwar ya kashe waya y tafi a tamanin .... Su Ma'u basuyi aune ba sai ganin Yaya Jameel sukayi a gaban su ,da sauri yazo ya Suri sa'adiya Tana cijewa yasa ta a mota Ma'u ma ta Shiga sai asibiti .... Suna Isa aka Shiga d ita labour room aka gwada cm dinta akaga har ya Kai 5 ,Nan da Nan kuwa ciwon ya tashi da gaske ,su Jameel d ma'un nata Mata Addu'a sauka lpy had'e da Kai komo ... Bayan kusan awa 1 da rabi ,aka sanar musu ta haihu ta Sami yarta mace ,murna harda bada goron Albishir Yaya Jameel yayi ,ya nemi ya ganta akace ya Bari a Gama gyara baby itama a canja Mata d'aki ,Ana Gama wa aka fito da ita har wani runguma ya Kai Mata ,sai d ta ture shi tace "zai balla ta ita Bata d kwari ,ya manna Mata kiss a goshi Yana Mata sannu ,sanan suka tafi d'akin da aka kaisu Dan ta huta ,Ana Shiga ya karbi babyn ya Mata huduba da Ameena suna mumcy ,murna fal cikin Ma'u da Jameel ,da sauri y d'ako wayar shi ya sanarma FU'AD ,sanan mumcy ,Suma sunata murna da Addu'a samun lpy ita da baby .... Ma'u ma sai murna tanata yi Mata sannu ,Bayan 24hr aka sallame su ,suka tafi gida ..... Aranar mumcy d FU'AD suka Kira sa'adiya suka Mata barka, shiko FU'AD cewa yayi a d'auki pic d'in babyn atura Mai ,Aiko Yaya jameel y tutura Mai kusan 10 harda Wanda na Ma'u ta rik'e babyn fuskarta Bata fito sosai ba saboda Tana murmushi Tana kalon baby Tana sanye da wata marun din doguwar Riga ta yane kanta da gyalen shi tayi kyau Dan koni ban ganeta ba ,har a lokacin da yaga pic d'in sai yaji kamar yace ta juyo yaga fuskarta Dan ya gane wacce ya gani ne a status d'in aunty sa'adiya ,Amman ya basar girman Kai ya cuso cikin lamarin shi na har yanzu bega maccen da ze ma kallo 2 ba daga 1 ya Gama duk had'uwarta ko mulkinta kuwa .... Washe gari k'anwar sa'adiya tazo daga Ghana Dan asalin su su 'yan Ghana NE sunan ta Aishat ,tazo don ta dinga Taya Ma'u Aiki Kar aikin ya Mata yawa ,Aiko Ma'u taji dad'in zuwanta ta samu abokiyar Aiki Kuma abokiyar Hira don Haka tare suke komai Nan da Nan suka Saba da junan su ,suna Aiki suna Hira ,Ana suna saura kwana 3 mumcy ta biyo jirgin yamma tazo Abuja ganin baby da nik'i nikin kayan arziki na baby da uwar baby ,ranar murna wajen ma'u kamar tayi me har Yaya Jameel d sa'adiya ma sunyi murnar ganin ta ,ranar mumcy tare suka kwana room d'aya da Ma'u da Aisha ,Ma'u nata jinjina rashin girman Kai d Isa da nuna Halin arziki irin na mumcy har ta yadda suka iya kwana d'aki d'aya badan Babu wani d'akin ba a gidan sai don tanason tana son su kwana tare kawai ,sun Sha Hira kuwa har mejego kafin ta tafi ta barsu Dan da wuri zata tafi gobe ,kowa sai cewa yake meya Hana FU'AD biyota su taho ,sai cewa tayi "yace ze Zo Amman ga kayansa su Fara isowa kafin shima yazo ganin mamin shi don shi ya zabi lak'anin sunan d za'a dinga kiranta Dan Yaya Jameel shi yaba zab'i kowa yayi naam d hakan kuwa ... Ma'u da Aisha kace sun shekara ne sunyi mugun sabo har Aisha naba Ma'u wayarta ta Kali hotuna ko video irin na chats har ta dinga chat a gabanta Tana Bata labarin media ,har take cewa ya kamata ace tanada waya don yanzu duniya Kan kowa a waye yake kodan saurayi ka rik'e babbar waya ,dake Aisha tafi Ma'u wayewa da d'an rawar Kai ,Ma'u dai sai cewa tayi Ni 'yar gidan saurayi ,rufamin asiri ban Isa ba saurayina karatuna ,sosai Aisha ta dinga yima Ma'u dariya harda rik'e ciki ,sai ta Mata uziri da ta gano rashin wayewa ta duniya atare d Ma'u ,sai cewa tayi "lokaci ne ,Zaki ce na fad'a Miki rashin bakisan waye ke bane bakisan me duniya take ciki bane bare kisan waye namiji suwa so da k'auna da ALLAH yake sawa tsakanin mace da namiji ,kema na tabata Dan Baki bada had'in Kai bane ga mazaje Dan baxakice Babu Wanda ya tab'a Yana kyanki ko Miki tayin soyayya bane da kin samu Wanda ra'ayin ku yazo d'aya da duk wanan furucin bazakiyi shi ba ,Amman Bari ki fad'a tafkin son wani kiga yadda labarin zai canja ki rubuta ki ajiye ,Nan gaba kibani labari..... Ma'u dai gajiya tayi da dogon hirar da Aisha take Mata wacce ta Mata kama da sakin layi a ganin ta ,Dan ta Mata maganar soyayya ,aganin ta wama ze sota har ya aureta ? Abinda babanta ma ko kud'in d ze Mata kayan d'aki bashi dasu sai rufin asirin ci da Sha ,ko saurayin ma Kai kafin aje ga kayan d'akin ,ta kawar da tunanin ta fad'a na mahaifiyar ta ,ganin canjin yanayi atare d ita , Aisha ta tambayeta ko lpy? Da taso b'oye Mata ,Amman takura da nacin Aisha dole sai da Ma'u taba ta labarin komai na daga rayuwarta Bata b'oye Mata komai ba ,sosai Aisha ta tausaya ma Ma'u taji yanzu ma ta Kara sonta don in da son ta take to yanzu harda tausayin ta ,don Haka taji Tana son Bata gudumawa iya k'arfin ta ,daga hirar tausayawa har bacci yayi gaba dasu kowa da gadon shi a d'akin .... Yau suna FU'AD ya gagara zuwa ganin baby , sa'adiya nata Mai Gori Yana Bata uzirin shi ,Yaya Jameel Yama ma'un d'inki kala 3 masu kyau har anko ya musu da Aisha ,me jego ma an zuba Mata nata din kunan kusa set 10 ,mutum 5 sukazo daga Ghana dangin sa'adiya ,sai 'yan uwan Jameel na wajen mumcy da sukazo kusan mutum 20 wasu ma duk a gidan hajiya jumai suka kwana kawar mumcy ce dasafe suka k'araso gidan sunan .. Taron suna yayi kyau anci ansha Jameel ya yanka ma mejego raguna 2 da sa 1 ,anci an k'oshi sosai haka aka wuni Ana bidiri su Ma'u an bayanno da kyakyawan kyau don Mai kwaliya ta k'ara fito da ita ba Yaya Jameel ba hatta sa'adiya da Aisha sai d sukayi mamakin Haka dama Ma'u take ? Dama tuni sa'adiya da Aisha sun Dena kiranta wata Ma'u ko As'ma'u husna kawai abirnance ,Dan Haka yau Ma'u a husna ta fito kyau ya bayyana be buya ba ,Haka ita da Aisha suka dinga karb'an Baki ,sunsha hotuna a wayan Aisha ,Mai hoto ma ya kasta musu da yawa ,wuni akayi ranar cikin farin ciki da ado Mai kayatarwa ..... Da dadare ma Hira suka kafa Daren sunan don mutanen Ghana ma washe gari zasu koma don Haka aketa hirar rabuwa kusan kwana sukayi suna Hira ,sosai Ma'u ta Saba dasu Suma suka Saba da ita kamar Kar su rabu ... Washe gari aka cikasu d kayan suna ,Haka ma mutanen mumcy Suma aka musu shatara ta arziki kowa ya tafi ,sai Ma'u da Aisha da Mai jego da baby Mami , mumcy karama ..... Jibine zuwan Alhaji Yaya mumcy nata lisafi shiko FU'AD ko ajikin shi ,yau Babu Abin da ya tasa agaba ma sai kallon statun na Yaya Jameel Yana ganin baby can ya koma ganin na aunty sa'adiya don ganin wanan yarinyar da zuciyar shi Taki yadda ita yake gani wai shi baby Mami yake gani gudan jinin Bros d'in shi ,sosai ya ga wanan fuskar yau ta waku iya wankuwa gata ga matar yayan shi harda wata wato Aisha sunyi kyau kamar a tsamo su ahoton ,Wanda baya kallon macce so biyu sai gashi da kurema hoto kallo ,Amman yaki yadda ita yake kallo wai yarshi yake kallo ,sai da ya kurema status d'in kallo harda maimaici duk hoto sai ya tsamota aciki Kuma ya karyata kanshi .... Yaune isowar su Alhj Yaya daga Egypt shida iyalan shi hajiya hafsa da yaran shi 3 sanaya itace babba sai uzaifa sai mufida karamar su duk sun girma wai ya Gama haihuwa dake d'an boko akida ne yara 3 sun ishe shi zaman duniya tunda ba noma zasu Mai ba ,acewar shi ,yaran sun taso cikin sangarta da tabara Babu Wanda ya Isa ya hanasu abinda ransu keso sukeyi Dan Haka da zasu iso ya Kira Jameel da mumcy yace sun taso in sun sauka a Abuja zasu branch a gidan Jameel tunda yanzu Yana Abuja , mumcy da Jameel sukace ALLAH y kawo su lpy ... Koda suka k'araso Bayan jirgin su ya sauka ,ya Kira Jameel yaje ya d'auko su Bayan sun gaisa da su sa'adiya da Aisha,da Ma'u ,an saukesu da Abin arziki abinci da kayan Sha sai da suka Bari kowa na murna da ganin su har an Basu masauki kowa yayi naam ,sai ko sanaya da uzaifa sukace su gaskiya bazasu iya kwanan gidan ba kawai dady ya Kama musu hotel ,mamyn su hajiya hafsa ta Fara lalabasu suna wani yamutsa wai su bazasu iya ba gaskiya ,Aiko Babu shiri Alhaji Yaya ya cema Jameel yazo ya kaisu hotel Mai kyau tunda sunfi son can ,Jameel yasan Hali dama ko kulasu beyi ba ya zari key din mota a fusace , sa'adiya ta yi yunk'urin dakatar dashi don ta Basu Baki ko zasu yadda ,shima ya dakatar da ita ,ta Fara musu magiya da rok'o ya haneta da idanun shi Akan ta barsu kawai ,dole ta zubama musu ido ,Ma'u da Aisha sai kallon Abin mamaki Suma sukeyi ,sanaya ko sai hararar Aisha d ma'un takeyi ,Bayan jameel ya fita "Alhajin yace Nima tare Zan kwana dasu acan inke kina Nan to ,Jin za a Mata wariyar launin fata hajiya hafsa tace Nima muje can din gwanda mu had'u waje guda ai ta d'auki jakar hannun ta ta d'auki gyalen ta itako sanaya dama ashirye take har tayi bakin k'ofa ma ,Abin ya ba k'aramar k'anwar su haushi mufeeda don Haka tace ita Babu inda zata anan zata kwana sai kace ba 'yan uwansu ba ai ba kulin mutum yake samun yadda yake so ba kuje duk Abin da zai cinyeni don na kwana anan ya halakani ,dady yace ,bafa hanata kwana zeyi ba in hankalinta ya kwanta da wajen Kar ta cuci kanta shi Yana son duk Abin da kowanen su yakeso in ra'ayi ya banbanta Kuma kowa yabi ra'ayin sa ,tace toh su tafi ita Tana Nan ,don Haka suka tafi suka barta ,sanaya nata mita yarinya sai shegen kicifi da nuna ita kowa nata ne Bata da wani ra'ayi aduniya komai ta nuna ita Bata da tsanani akai dole kowa ya Raina ki ai ta buga Mata tsaki suka fice ,sa'adiya ta jata suka zauna taji dad'in kin binsu d tayi don Haka ta Sami wani tambarin girmamawa azuciyar su dukan su har jameel din ... Har hotel din y kaisu yaso settling bill d'in su ,da yaji haushi ma ya fasa ,ya rabu dasu ya dawo gida ,itako mufeeda har ta zama 'yar gida sunata Hira da su Aisha dake kansu d'aya har da hotuna sukayi a Daren . [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AB* (Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg 23 FU'AD kasa dago kansa yayi shi Jin Abin yake ma kamar hauka Dan ya kasa gaskata zancen kwata kwata ... Mumcy da hajiya hafsa mamaki ya Gama kashe su ,ita mamy na tunanin had'in be Dace ba saboda tasan indai har sangartaciyar yarsu Bataso ba to tabas zata iya aikata komai ciki kuwa harda kunyata mahaifin ta .... Itama mumcy Tana ganin angama cutar Mata da son matuk'ar aka had'a auren shi da yarinya irin sanaya wacce sukayi baram baram da Tarbiyar da kamun Kai ,Dan tasanta farin sani zuwanda d mumcy ta tab'ayi don ziyara da takai musu ,Tasha ganin ta suna gaisawa da namiji harda had'a kafadu da maza tundaga Nan ta tsani Rayuwar can ta gama tir da Tarbiyar irin ta Alhaji Yaya Dan yasan komai ,yanzu ace ita zata zama surikarta , gaskiya da sake dole ta magantu Akan wanan lamarin.... Don Haka mumcy tace , Alhaji Yaya kana ganin Babu cutarwa ko tirsasawa acikin lamarin? Ta duka b'angarori biyu? Ita sanayan da shi FU'AD d'in? Sai ko mamy tace zancen ki hak'un adai duba lamarin Kar aahiga hakkin yara gaskiya .... Tana direwa ,Dady ya d'auka ku har tunani ne daku Mata da har zaku had'a tinanin ku da nawa? Hukuncin da na zartar kuke son yima kwaskwarima? To wlh ahir d'in ku duk na Isa daku ,Bari ma kuji rantsuwar d'an musulmai wallahi billahilazi Babu gudu Babu Jada baya sai na d'aura Auren FU'AD da SANAYA sai dai idan Rai be kaini ba ,Kuma duk cikin su duk Wanda yace bayayi daidai nake da iskancin shi daga FU'AD din har ita 'yar lelen ......Afusace ya wuce sashin da aka bashi don sauka ...... FU'AD a razane ya d'ago don Jin furucin mugun yayan mahaifin shi ,yanzu y tabbatar ba mafarki yake ba Kuma yaga sabon sallo yima namiji Auren dole ko Auren cushe zai ce ,k'afe mumcy kawai yayi da idanu masu neman agajin gagawa Yana Shirin raunana zuciyar shi ,da ido mumcy take rarashin d'an nata da ya k'arfafa zuciyar shi ,tanada masalaha da mafita kodan bak'anta ran Alhaji yayan da nuna ikon ta amatsayinta na uwa ga FU'AD ,tunda yayi rantsuwa tasan Kuma baze karya ba duk da cikin jahilci yayi rantsuwar don da yasan ta da beyi saurin furtata ba ,Amman itama dole abi maganar da zatazo dashi ..... Mamy ma sai taji tausayin 'yarta kawai Banda shi FU'AD d'in ,suna cikin zaman jugun jugun kamar an Aiko musu da zancen mutuwa sai ga sanaya ta fito hanun ta rik'e da waya Tana latsawa Tana tsotsan sweet ,Tana hura hanci kamar gidan u banta ..... Ganin mamy da mumcy da shi FU'AD d'in ,hakan ya tabbatar Mata da wani Abu Yana faruwa koma ya farun Dan yanayin su ,alamu ne na damuwa . Sanaya ta tambayi mamyn ta lpy mamy meya faru Kuma ,cikin Alhini da nuna tausayama 'yar Tata tace "daughter dadyn ki yayi kyautan ki ga FU'AD" a razane sanaye tace "mene mamy ? Kinsan me kikace kuwa? Kyauta ga wani FU'AD ko fuuu wa ma kikace? Kodai wancan yarinyar Mai sanyin Hali kike nufi Mai shigewa jikin kowa wacce Bata Taran kowa ? "Mami tace " ke dai yace Kuma yayi rantsuwa babu fashi nida ya gayamin Abin da zeyi kenan a 9ja da be kwaso mu kamar awaki ba ya kawo mu ya tozarta mu ba" Sanaya zubewa tayi jikin mamy Tana karema mumcy da FU'AD kallo can ta d'ago ta ma FU'AD wani kallo sai akaci sa'a shima ya d'ago Yana kallon ta da idanuwan shi masu alamun gargad'i izuwa gareta ,itako zuciyar tace ta Fara yaba Haifa da sura da kyau uwa uba kwarjini irin na FU'AD ganin zuciyarta na Shirin shagaltar da ita Kar ta Bari ta yadda da auren ikon da aka Mata sai tayi saurin kawar da yabon da take Mai ta Mai wani irin kallon raini "tace Kai kace amaka Aure Dani? Kai kayi kuskuren zabana amatsayin matar ka? Dama baka da Mata aka kwaso mu akace bikin ka zamuzo ? ..... Takaici da b'acin Rai duk sun Hana FU'AD zagin ta ji yake kamar ya mareta ma ,sai harara daya maka Mata ya mik'e Yana cewa taje ta tambayi Wanda ya kawota inda yake shine Mai amsar tambayiyinta Amman bashi ba da zeje shiryo nashi tambayoyin da zai amsa min Bayan ya Gama amsa naki keda ya Haifa ....... mumcy ce ta dakatar dashi taga Yana neman wuce gona da iri ,ta Mai ummarnin da ya haura zatazo ta sane shi ...........har ya Fara tafiya Kan steps sai wayar shi tayi ringing ganin sunan b big Yaya ya fito a screen d'in wayar ya San Yaya jameel ne yake Kiran shi ,don Haka dawowa baya yayi ya kawoma mumcy wayar ya koma ya haura saman shi . Mumcy wayar ta karb'a tayi d'akinta Tana tambayan masu jego , tace Jameel Alhaji Yaya ya wargazamin farinciki yau d'inan ya wargaza na d'an uwanka ma Dan kasa d'aga wayar Kama yayi ,cikin tashin hankali Jameel yace abashi FU'AD d'in , mumcy tace kasan inyayi fushi koni sai namai uziri Yama tafi yabar wayar ,sai ko Jameel yace mumcy Dan ALLAH karki b'oye min komai daga Abin da ya faru ki sanar Dani , mumcy tace maganar boye_boye Babu ita ,gaba d'aya ta zayyane ma Jameel komai ... Jameel Baki na rawa yace , mumcy ku kwantar da hankalin ku in ALLAH ya yadda ,yayi na farko yayi na k'arshe gwanda ko baram baram muyi dashi mungaji da mulkin Kama karya da Yaya Alhaji yake Mana wlh yau d'inan zanzo ko amu ko ashi cin kashin yayi yawa ku jirani Ina hanya insha ALLAH ,be jira cewa mumcy ba ya kashe wayar ya koma gida daga office..... Mumcy jin Jameel ya fusata Dan dama Akwai zafi Dan yafi FU'AD fad'a Dan bashi da wasu k'annen ne ba'a gane fad'an shi ,Amman ko ita sai yace zema fad'a in Banda ta ginasu da tsarkakakiyar tarbiya Mai yado har zuriyar su ta Nan gaba ,don Haka ta kirashi don ta bashi Baki ,da kamar baze d'auka ba don yasan tatsuniyar gizo Bata wuce ta kok'i don yasan hakuri zata bashi da gargad'i akan kudirin shi .... Haka kuwa mumcy ta Fara bashi hak'uri Akan karyayi rashin tarbiya subi komai cikin nutsuwa itama ta gaji da Halin Alhaji Yaya Dan Akwai k'udirin ta da takeson aiwatar wa, Amman tanaso ya sasauta zuciyar shi da Aiki da ilimi da hankali atahowar shi har agaban Alhaji Yaya ma inya Zo ,jameel ce mata to kawai yayi yace sai ya k'araso Dan jirgi zai hau ,tamai fatan isowa lpy .... Sanaya da mamy sun koma masaukin su suka Sami mufeeda suka sanar Mata ,itama ta tausaya musu da had'in rashin sani da za'a musu ta kowanne b'angare Tana ganin Basu Dace ma da juna ba Dan tasan FU'AD zesha wuya da aunty ta shi tafi tausayama ma ,itako sanaya harda kuka Tana cewa wlh dady ya yaudare ta d tasan cushen da ze Mata kenan wlh da Bata biyo su ba ,Kuma wlh ya musu k'arya ....uwar dake uwar doya ce Bata kwab'i 'yar ba akan cewa da tayi uban ya musu k'arya ,sai mufeeda ce take cewa ,aunty dadyn ne mak'aryaci yau? Mahaifin namu da ya Gama Mana komai a duniya? Cikin kuka da tsiwa sanaya tace Ni be Gama min komai ba wlh meyamin ? Had'ani da wancan d'in da yayi shine koman? Wlh ya zalince Ni da auren da yamin Babu shiri da Wanda ya bani Kai wlh Ni ban amince bama sai dai idan dady bashi ya Haifa Ni ba .......mamy ce ta ture ta tace Dan ubanki uban waye to ya Haifa ki Dan uwarki Ana d'oraki kina sauka sai kinemo ubanki ,nidai nasan nida shi muka haife ki ba Kuma dashen ki akamin ba ba aron ki aka bani ba bare kice asibiti mukace aka siyar min dake ,kaji Mara kunya ,fitsarar yau kanmu zata dawo? Kinga Ana Miki duk abun da kike so? Turo Baki sanaya tayi Tana mita da kunkuni ..........mufeeda ko cewa tayi ai inkana rashin mutunci inbakayima kanka ba baka cika ba ,cikin zuciyarta Dan Bata Isa ta furta suji ba ....... Alhaji yaya ya Gama yanke hukunci ,daga baya ma fita sukayi da wani abokin shi da yazo ya d'auke shi don zaga gari ,shi kanshi Yana jin wani iri Akan in sanayan tace batason FU'AD d'in fa ,to Amman atunanin shi zama taso shi yaro kyakyawa Mai ilimi da aji ,ga uwar kadarori da kud'i ya mallaka ta ko Ina bashi da makusa ,Kai kodan ya k'untata Mai ma dashi da uwarshi Mai gadon arziki ya aura Mai sanaya ko ze mutu itama dole tayi hak'uri Koda ransa baya so kuwa shida yake mahaifinta ... FU'AD ko tun Yana tunani irin Abin da zeyi Akan al'amarin har Abin ya nemi ya zamar Mai damuwa Dan Haka kawai ya tatara komai ya watsar ya kirawo baccin dole don ya Sami sasauci aranshi da Rayuwar shi ta yau .... Koda mumcy ta haura saman shi ta sameshi Yana bacci lakadan Bata tashe shi ba sai ajiye Mai waya da tayi a kusa dashi ,tamai Addu'a Dan Al'adar mumcy ce har da girman su Tana musu Addu'a ta tofa musu ko gaisgeta sukazo yi hakama inta gansu suna bacci . Jameel tun da ya koma gida ya sanar ma sa'adiya halin da ake ciki ,ta jajanta Abin ya nuna Mata zeje ,ganin ranshi ya matuk'ar b'aci ta dinga kwantar Mai da hankali da bashi hak'uri Akan yabi komai ahankali ta shirya Mai kayan shi set 4 a k'aranar jaka Tana Mai fatan ALLAH ya kaishi lafiya , yasa suyi nasara shi da su mumcy ,sosai yaji dad'in Addu'a Tata ya Mata sallama ya tafi dama ya booking flight ..... Bayan tafiyar Jameel sa'adiya taje ta Sami su Ma'u da Aisha da suka zama 'yan uwan juna ,take sanar musu Abin da ya faru ko yake son faruwa , Ma'u najin Auren bazatan da za'ama FU'AD batasan lokacin da wani mugun fad'uwan gaba ya gawo Mata ziyarar bazata ba , da kyar ta iya magana Akan lamarin Bayan tayi namijin k'ok'arin kawar da yadda taji cikin ranta da ta Rasa dalilin Akan wani mugun FU'AD da ya hanata zaman lafiya a gidan su shi d'an masu gida , ALLAH ya k'ara ma gwanda su aura Mai ita ta koya Mai hankali na mage kawai ,had'in ma yayi ,sai Ma'u ta tsinnci Kan ta da Jin dad'in had'in ,duk da zuciyar ta na bijiro Mata da tausayin FU'AD d'in kawar wa Kawai takeyi .... Sun jima suna tatauna batun sunajin dama agaban su za'ayi wanan cakwalkwalin cakwakiyar , sudai sukabi Abin da Addu'a ..... Koda jameel ya sauka be tsaya jiran FU'AD ya d'auko shi ba ,bema San zezo ba ,driver kawai ya Kira yaje ya d'auko shi ,Yana zuwa ya shige d'akin mumcy Dan Babu kowa a falon , mumcy na ganin shi ta Fara murna ta Fara tambayar shi lpy su sa'adiya da baby da su Ma'u 'yar amana ,duk yabata amsa da lpy suke suna gaisheta ma ,Aiko y Fara tambayar Ina gwanin hukuncin? Mumcy ta Fara tsawatar Mai Tana nuna Mai mudin yayi wani abun ALLAH yayi wadai ,to zata zaci daga Tarbiyar da ta bashi ne don kowama Haka zeyi zaton dama and cewa yaran mace acikin dangin mijin duk da basa gari d'aya Amman bita da k'ulli be k'are ba , tadinga Mai fad'a Akan ya risina harshen sa da tausar zuciyar sa, daga baya ya tambayi mumcy meye k'udirin ta Akan na Alhaji Yaya ,sai ta f'ad'a Mai ,Yaya Jameel yayi murna sosai da jun Abin da ta yanke don baza'a k'untata ma FU'AD ta ko Ina ba ,burin su ALLAH yasa yayi naam da hukuncin su ,Dan Haka ma bazasu sanar dashi ba sai agaban Alhaji Yaya .. FU'AD ya farka a baccin ya tashi yayi sallah ,Yana zaune sai yaji anyi sallama an shigo jin muryae Yaya Jameel yasa yayi saurin d'ago da Kai ,sukayi ido 4 da sauri FU'AD yaje ya rungumi yayan nashi Yana murna matuk'ar murna Yana cewa "haba Yaya zuwa Babu bayani " Jameel yace Ina zakasan zanzo wani yazo ya b'atamin ranka Haka kawai ,duk yasa kana fushi damu ,sai FU'AD yayi dariya yace "haba fushi daku nasan da da shawarar ku hakan baze faruba Yaya ,Amman Babu komai nazubama sarautar Allah ido ,Akwai ALLAH "Yar tasa kawai ta Isa ta wargaza Abin Dan itama baso take ba ,ban Yaya Jameel ya dinga ratashin shi Yana bashi hak'uri Yana nuna Mai Auren ba lalai ya d'ade ba don wanan yarinyar Mara tarbiya bazata iya zaman Aure ba ,sosai hankalin FU'AD ya d'an kwanta Amman Yana mamakin ya za'amai Aure a k'ank'anin lokaci irin Haka shi harma ya Rasa da wanne suna ze Kira Auren ..... Mmn shaheed ta [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AB* (Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg 22 Ma'u ,Aisha,mufeeda sai bacci b'arawo ne ya sace su badan sun shirya Mai ba ... Sanaya da mamy su d'akin su 1 uzaifa da dadyn shi d'akin su 1 ,duk da ba Haka sanaya yaso ba ... Washe gari da safe su Ma'u da Aisha suka Fara dorama aunty Mai jego ruwan wanka da hidimar Dora Abin karyawa ,ganin sunata Aiki ,mufeeda ta yi k'ok'arin Taya su ,suka hanata ita Kuna tace zatayi duk da bayi takeyi a gida ba don 'yan hutu ne na bugawa a jarida ,wani abun ma sai dai ta tambayesu ya akeyi har abubuwan suka Fara birgeta yadda suke komai cikin salo da kwarewa ,Haka dai tayi Abin da zata iya har suka kammala gyaran gidan da girkin gidan Suma suka tsala wankan su suka Sanya suturun su Masu mugun kyau ,ba kace Ma'u ta saje cikin yaran masu dashi ba Haka sun d'auko Mami sunata d'aukan ta wanan yaba wanan Haka suke tayi kowa sha'awa take bashi ,mamanta ta tafi wanka ..... Mumcy tun safiyar take fama da FU'AD Akan ya hak'ura d fita yau saboda zuwan Alhaji Yaya ,shi ko FU'AD sai cewa yayi "ai da wuri zai dawo har ze dawo ma kafin su iso tunda shi kitse ne bayason Rana ta tab'a shi yasan sai yamma zasu ka'raso , mumcy tayi murmushi tace baban naka ne kitse? FU'AD yace "to mumcy baya Shiga Rana gudun Kar ya narke " mumcy tace kawai dai hutu ne ya ratsa shi , FU'AD yace "muma fa muna hutawar Nan Amman hakan be hanamu Shiga tsaleliyar Rana mu Nemo Abin kaiwa Baki ba , mumcy tace "sai kace wani magidan ci wai Abin kaiwa Baki irin Mai iyalin Nan ,ko da yake iyalin suna hanya tunda kakijin shawara wlh kaida Alhaji Yaya bazan iya da jarabar shi ba gwanda yazo ayita ta k'are .....fuuuu Rai a bace FU'AD ya Mike zai koma saman shi , mumcy ta raka shi da cewa "kardai ka Jima ka sakko katafi inda zaka don ka dawo da wuri nafison yazo ya sameka a cikin gidan Nan ,har da zece wani Abu sai kuma ya fasa Dan har ya tsaya ya juyo da niyar magana .... mumcy ce tace "fadi karta kashe ka ,inajin ka " kawai sai ya gyad'a Kai ya tafi ..... Tsaf FU'AD ya shirya Yama mumcy sallama ya fice agidan Yana mita cikin zuciyar shi .. Sanaya Bata farka ba sai da Rana ta Fara yi tayi wanka ta shirya ta canja Kaya ,mamyn ta ko dama tuni tayi wankan ta ,sai mamyn ta Fara cewa ya kamata dadyn ku ya fito mubar hotel d'inan don tafiya inda muka dosa ,sai ko sanaya ta yamutsa fuska tace "kinsan dady ba Abin da yafi tsana kamar fitar Rana kamar d'an d'ako ko Mai siyar da rake ,Nima nafison sai sakaliyar la'asar sai mu tafi garin yafi Dadi da sha'awa awanan lokacin ,Jin furucin sangartaciyar 'yar tasu ,sai ma tayi tsaki tace sai ki zauna ai inkin ga wajen zaka ke ,kawai sai ta Kira dadyn nasu a waya ta labarta Mai ,irin furucin da sanaya tayi shi ya Fara zayyano Mata shima ,haushi da takaici yasa ta kashe wayar ta ma ,sanaya ta dinga Satan kallon ta Tana murmushi irin tasan za'a Rina ai ..... FU'AD tare da abokin shi b2k ,sai yake tambayar FU'AD Ina budurwar shi house girl d'in su? Sai FU'AD yace "banza baka da m ,Tana can Mata Ni yaushe rabona da tozali da _dirty girl_ da kamar ma tsotse Ni takeyi da wanan mayunwatan idanun nata masu dafi aciki , sai ko B2k ya bushe da dariya yace kafa matsa Mata da yawa fa mutumina zanci tarar ka Ni inason sake ganin ta ma bako hoton ta a wayar kane? Sai ko FU'AD ya mako Mai uwar harara yace itace sukutum a d'akina ba hoton t awaya ba Mara m kawai ,B2k yace Mai da wukar Nima wasa nake ma ,Amman zaku aramin ita innai Aure ta dinga ragema matata Aiki ko? Sai FU'AD ya Harare shi yace "Dan Air kawai sai dai tazo a matar taka kawai " sai B2k yace "dalla wanan in taji gyara ko Kai bazaka iya barmin ita ba wlh sai ka nemi halakani ma akanta Dan yadda kake d'inan hmmmmm,sai ko FU'AD ya fusata yace "kaifa wani lokacin baka da Kai kamar sigari ,wlh inajin kaci Kai ,me zanyi da wanan abun ko a masu aikin gidana bare wai ..,ya kasa karasawa ma don takaici........sai B2k d'inne ya talabo kafadun shi yace abokina inajinka muyi magana Akan da Abin da ya had'amu anan ...... FU'AD Bayan ya furzar da wata iska Mai huci sanan yace ,hmmmmm wani yayan abban mu ne yazo zai min Karan tsaye Akan Aure ,wai ko na Nemo Mata ko ya samo min da kanshi ,kaf ya Gama ba B2k labarin ..... B2k yace ,ta kwana gidan sauki tunda baka da ita a hannu ko ince baka shirya mallakar ta ba ayanzu ,Amman fa da Isa Aure ko ajiye yara ya Isa har kana Shirin wucewa ma ,Ina ganin kawai ka rabu dashi kaga gudun ruwan shi ,ai baze maka tilas ba , in Kuma kaga zai ruguza maka duk wani tsarin ka da ka tanada kawai sai ka bashi hak'uri kace zaka Nemo Nan da wani lokacin ,Amman fa kaima kayi k'ok'arin kodan mumcy abokina badan wani Abu ba ... FU'AD ajiyar zuciya yayi ,yace "bazaku gane bane abikina ,Kai dai ALLAH yasa mudace kawai ,shi Kuma ALLAH ya kawo shi lpy bazan yadda da mulkin Kama karya ba Sam , Nan B2k ya Gama bashi shawara masu Amfani , FU'AD yaji Amman sam yace baze yadda da maganan wani Aure a yanzu ba ,sun Jima tare .... Mufeeda da ta Kira dadyn su ,ya sanar Mata sai yamma Jameel zai kaita hotel din su tafi airport don tafiya ,sai taji dad'i kodan Kara samun awanni da zatayi tare da su Aisha Tana k'ara samu garabasa daga Rayuwar su masu cike da ababen koyi Dan sun Gama birgeta matuka ta kowacce siga Basu da makusa sosai take k'aruwa da su ... Yamma lis Yaya Jameel ya d'auki mufeeda tare da rakiyar su Aisha da Ma'u don shima ya fiskanci sabon da sukayi sosai ,itama mufeedan kamar Kar ta barsu ... Bayan sun Isa hotel d'in ya Kira dadyn su mufeedan don sanar Mai ya kawo ta ,duk suka fito da niyar tafiya ,sai su Ma'u da Aisha suka fito suka Shiga kwasan gaisuwa wajen mamyn su day dadyn su mufeedan kowa cikin sakin fuska ya amsa musu sabanin sanaya da uzaifa masu Hali iri d'aya ,sai Jameel yace su Shiga mota su tafi dake siyanan abokin shi mak'ocin shi ya karb'a yasan tashi ta musu kad'an ,dady a gaba mamy da uzaifa da uwar rigima sanaya a tsakiya sai su mufeeda da Aisha da Ma'u a baya ,tirya tiryan har Airport ya kaisu bayan angama musu booking flight d'in yamma ,sosai Ma'u taji dad'in zuwa da ita da akayi ko banza tabama idon ta abinci first time in history arayuwar ta ,bankwana sukayi tsakanin su ukun kawayen juna sabanin sanaya da ko takanta basa bi Suma ,sukama dady d mamy sallama da fatan sauka lpy ,Kuma agaishe da mumcy ,musamman Ma'u da ta shagala wajen bada sak'on gaisuwar nata ga uwar d'akinta suturar ta wacce ta rufama rayuwarta asiri ,sai ko sanaya ta hantari Ma'u Tana hararar ta ,Tana cewa "waye yaron ki duk cikin mu da kike wani jero almajiran sak'on nin ki marasa gaba bare baya? Wa kike aika acikin mu ? Wa Kika Raina ma tukunna? .....duk wad'anan tambayoyin na Ma'u ne da hsushi ya hanata amsa ko 1 mamy da dady d su Yaya Jameel duk suna jinta sunsan Abin d Tama Ma'u be Dace ba wasu haushine y hanasu magana Amman dady gani yake hakan daidai ne agun shi ,sai mufeeda ce tayi caraf tace ,aunty sanaya bafa dake take ba Dani take " sai sanayan ya wurgoma k'anwar Tata ido tace "oh kece 'yar Aiken nata? Sai mufeeda tace "eh Mana ,meye aciki sak'o na kisa ne? Daga bada sak'o ,Dani take Kuma naji Zan isar da sak'on ta insha ALLAH ,Jameel sosai yaji dad'in kalaman da mufeeda ta mayar ma yayar Tata ,don shi ya Gama kufula Daman shi yisa yayi shiru da yayi magana da bataciya za'ayi ,sai ko sanaya tace "wai ke me aka bakine a 9ja Naga in only 1 kina neman ki rikid'a ki canja daga mufee zuwa mufee 9ja? Kanki 1 kuwa? Sai ko mufeeda tace 1 ne ko nawa Kika gani aunty fad'amin gaskiya kinsan Ni ba gani zanyi ba sai dai aganin mun ....a fusace sanaya zatayi magana mamy da dady suka dakatar dasu har suna hada Baki ,suka umarce su da su wuce zuwa inda suka nufa ba shirme ba ,uzaifa da su Aisha da ko kallon su kawai sukeyi ..... Bayan sun yi sallama da mufeeda ,suka wuce zuwa mota mufeeda nata d'ago musu hannu ,Jameel ma Yama dady sallama da mamy da mufeeda ko takan sanaya da uzaifa be bi ba ya wuce ,sanaya ta wurge shi da harara tace "Kai ka sani ,uzaifa ma hararar ya Kai Mai suka tafi ..... Bayan su Jameel y dawo dasu gida ,suka koma d'aki suna yaba halaya irin ta mufeeda suna kushe Halin sanaya da uzaifa..... Isar su dady keda wuya ,ya Kira mumcy Akan sun Isa azo a d'auke su, mumcy da gagawa ta umarci driver yaje ya d'auko su ,ta dinga Kiran FU'AD a waya Tana Mai gargad''in Kar ya Bari Alhaji Yaya ya rigashi shigowa gidan ,sosai FU'AD ya k'ulu da maganar mumcy y Rasa dalilin da yasa take Abu kamar Tana tsoron mutumin Nan Bayan Babu abun da ya Isa ya Mata sai Abin da ALLAH ya Mata ,in anyi magana tace gudun magana ,kwana da lafiya yafi kwana da kud'i ,yadai tabatar Mata da zai dawo Yana hanya ,al'halin ko hanyar be gau ba ,har akaje aka d'auko su suka shigo main parlour...... Sosai mumcy ta sa aka shirya musu lafiyyayen abinci kala kusan 6 da juice kala kala da snacks ...... Alhaji Yaya FU'AD ya Fara tambaya don yayi mamakin da bashine yaje d'auko su ba ... Mumcy murya na rawa tace "baya gidan ne ,Amman ta same shi a waya gashinan zuwa " shiru kawai yayi Mata sai mamy da suke ta gaisawa da mumcy ,sai sanaya da uzaifa da suka gaishe da mumcy ,sai mufeeda a k'arshe har take ba mumcy sakon gaisuwar Ma'u ,mumcy sosai ta tuba da Asma'u taji dad'in sak'on Kuma ,hakan ya bak'anta ran sanaya sai tab'e Baki da tayi .... Suna zaune gaba d'ayan su su 3 uzaifa ya tafi masaukin su da aka sauke su ,sanaya ma da mufeeda sun tafi nasu ,su Kuma sunata magana Kan matar d FU'AD d'in ze aura , mumcy tace ya Bari in FU'AD d'in yazo yaji daga bakin sa .......sai ga FU'AD ya shigo .... FU'AD da yayi tozali da Alhaji Yaya ji yayi kamar ya koma ,Amman Ina ya Riga ya shigo sunyi ido 4 dashi ,kawai karasawa yayi ya kwashi gaisuwa ... Nan Alhaji ya Fara Mai maraba da tambayoyi zafafa Akan maganar matar da ya fitar ze aura ,da kyar FU'AD ya iya furta Babu ,Bayan gumin da yake shirin keto Mai yau ya tabbatar da gaske ake maganar ga wani mugun kwarjini da yayan mahaifin nashi yau ya Masa ji yake baze iya musu da duk Abin da ya yanke Masa ba a yau gani yake bashi da tacewa ,barawo a hanun Mata ya gamar sadak'arwa da duk wani zabi ko hukuncin da ya zartar Mai don Haka ya San cewa yau sunan shi ,sai yadda ALLAH yayi .... Alhajin ne ya dawo dashi hayyacin shi ,da bashi minti 2 kacal ya Gama tunani da Nazari Akan matar Aure in ba hakaba yau zemai Mata gobe atashi da d'aurin Aure a gidan .....ba mumcy ba FU'AD d'in kanshi sai da hankalin shi ya tashi ..... Kusan mintuna 4 FU'AD Babu labari mumcy nata Mai magana da ido ,Akan ko adangi ne ya zaba amma Ina FU'AD tunani ya tsaya cak ya Gama sadak'arwa .... Afusace Alhaji Yaya yace to ya shirya Gobe ze d'aura Mai Aure Ana sakowa daga masalacin juma'a Babu fashi matuk'ar numfashin su yakai Gobe gaba d'ayan su .... FU'AD kasa d'agowa yayi ,sai mumcy da ta iya tambayar Yaya wa zaka aura Mai Ni da inada shawara .......dakatar da ita FU'AD yayi Akan tayi shiru ,sai ko Alhajin yace ko baka dakatar da ita ba ,Bata da hurumin yin magana Akan wanan batun Mara kunya fitsarare ,ko babanka ALLAH yayi Mai rahama na fad'a baya tankawa kasani kaima Kuma ko Yana Raye Zan iya zartar da Abin da nake shirin zartarwa kasani itama ta sani ,gyada Kai mumcy tayi Alamar hakane ,Bata hak'ura ba ta sake tambayar to wa zaka aura Mai kenan? Cikin nuna Isa da gadara da Gaya Mata Dan kowa ya sani Yana hura hanci kamar botorami yace " *SANAYA* k'anwar shi ................mumcy da mamy atare sukace *SANAYA KUMA*? ........... Shiko FU'AD ba'asan a duniyar da yake bama ........... Maman shaheed ce dai💃🏼 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AB* (Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg 24 *NA GODE DA ADDU'O'EN KU*👏🏼 *Shi Kuma mamaci Allah ya Haskaka kabarin sa ya Raya Abin da ya Bari ,Allah ya shafe lefukan shi ,da mamatan da suka Rasu nacikin motar Baki daya,Allah ya lulub'e su da Rahamar say yasa Aljannah ta zama makoma agare su ,intamu tazo Allah kasa mu cika da imani*😭👏🏼👏🏼 Jameel be Bari wata damuwa ta cigaba da baibaiye FU'AD ba duk inda yayi Yana tare dashi har mumcy da ta ji su shiru saman ta haura don ganin Halin da suke ciki ,Tana zuwa ta gansu kamar wani Abu na rashin Jin dad'i baya Shirin faruwa a gidan musamman yadda ya sama d'an uwan nasa farin ciki ,sosai tayi Hira dasu ta jadada musu yin biyaya Ga ummarni shi . Yara masu biyaya sun amsa ,Amman FU'AD ji yake bana fa kamar ze kauce ,kawai dai ALLAH ya tsare . Sanaya tanata dambarwar akan Auren da dadyn ta ya kirkirar Mata Tana cewa bazata auri FU'AD ba ,Dan Babu ruwanta da Abin da zuciyarta ta Fara hango mata na nagartan shi bere har ta yaudari kanta ta amince dashi maysayin zabin dady kamar wata Yar k'auye ko Almajira Dan kusan sadakanta yayi ko za'ayi biki na kece raini ma kuwa ,ganin wanan duk ba mafita bane ta d'auki wayanta ta Fara Kiran dadyn nata ,sai da takai Kira 5 sanan ya d'aga ,kafin tace komai ya katse ta da Yana tare da abokin shi ,yakusa dawowa gidan ,Dan yasan tatsuniyar gizo baya wuce na kok'i ,akufule ta jefar da wayar ,mufeeda Tace "sorry big aunty sai an had'a da hak'uri shi biyaya ga iyaye ALLAH ne ya bada umarni ,bin iyaye Kuma wajibine don mutum zega daidai arayuwar shi .......Bata k'arasa ba ,sanaya ta wulo Mata wani takalmi dake kusa da ita ,Tana cewa "Dan ubanki ke ai sai ki Aure shi laraba imani ayi canji dake uwar biyaya munafuka ,in kin haufu Dan ALLAH ki bigi kirji kice ya mayar da auren kanki ,karyar banza harni zakima wa'azin k'adangaru ,Tana yunk'urin tasowa ta duketa Dan ta kufula sosai . mufeeda cew tayi , ALLAH ya Baki hak'uri ban furta hakan Dan Bata ranki ba , yi yadda kikeso ,Amman fa ki tuna daga k'in gaskiya sai kauce hanya tabar musu d'akin ,a zafafe sanaya take Shirin bin mufeeda ,Amman mamy ta Hana ta hanyar kamota ,Aiko sanaya aka saki kukan takaici ,mamy kinaji tanamin rashin kunya da wa'azin k'arya Amman Baki hanata ba sai Ni da zan Mata hukunci? Mamy ,toh inbanda sanaya meye ta fad'a Wanda ba gaske ba duk cikin maganganun ta? Kiyi hak'uri ki Bari dadyn ku yazo muyi magana ta fahimta ,sanan sanaya taji sanyi na wucin gadi ya ziyarci zuciyar ta , Alhaji Yaya ,Yana dawowa ya Fara da Kiran sanaya ,Tana fitowa ta fad'a jikin shi ,Rayuwar turai Tana tabara da shagwaba ,sai kuwa ya cireta a jikin shi don yasan yanzu zasuyi bataciya don ya Gama yanke hukunci ba tare da amincewar ta b. Sanaya "dady wai tatsuniyar naji ne ko GASKIYAR labari? Cikin himma da dabaru ya Fara Shirin birneta ta hanyar rarashin ta ,Yana Mata bayani Akan zumunci yakeson su k'arfafa gudun Kar rasuwan k'anin shi yasa zumuncin ya lalace ,Aiko Bayan ya Gama yimata bayani sanaya ta dire tace ita Sam bada ita za'ayi wanan zumuncin ba ,ya be Gaya Mata manufar shi ba tun kafin su bar Egypt sai yanzu kawai Dan yaga anzo ? Atake ta saka Mai kuka ,ganin tanata surutu bakinta har Yana Shirin furta zafafan kalamai ga dadyn nata ,yayi saurin tsawatar Mata da nuna Mata cewa Aure fa Babu fashi ta rungumi k'addara kawai ,Mara kunya tace "ita Bata Santa ba Dan ko hanya Basu had'a da k'addara ba ,Dan haka......Bata k'arasa ba mufeeda Tace haba bis aunty kisan kalaman da Zaki dinga firtama mahaifinki Mana? Sanaya harara ta doka Mata ,sai shi dadyn ne yace "barta mufeedan dady so take taga b'acin Raina ,Kuma ba Abu Mai wuya bane ,mamy sai yanzu ta sako musu Baki , gaskiya hukuncin Nan anyanke batare da dogon nazari ba fa ,ya kamata aduba fa ,Ni yarinya ta ......Bata idar ba dady yace "dallah rufema mutane Baki bazaki yayafama wuta Ruwa ba sai K'ara izata ,in Baki da Abin cewa kimana shiru Akan Auren Nan Zan iya batawa da kowa wlh ,in nace kowa Ina nufin ke,ko ita ,ku kowa ma kawai ,Dan Haka kowa ya karb'i Abin hannu bibiyu kawai ,Dan Haka Gobe Akwai meeting misalin goma na safe ba Akan kowa bane Akan Auren ne zansa date kad'an Kuma Zan sa ,ya fice ya bar su .... Jameel ko takan Alhaji yayan bebi ba ,Haka shima FU'AD din kwanciyar su kawai sukayi Bayan sun Gama Hira da mumcy,itama ta tafi ta kwanta .... Sanaya kuwa ranar kwanan bak'in ciki tayi tana tuna samarin ta na k'asar su ,in ta tuna wai FU'AD ne ze zama miji agareta Amman shima ai ya cancanci taso shi da gagawa take kawar da zancen ,Tana ganin Auren ma gaba d'aya be Dace da ita yanzu ba ,ranar kwana tayi Tana gaba da kowa .... Washe gari, Bayan an karya an had'u a parlour anyi zaman sauraren Alhaji Yaya ,cikin Isa da tak'ama yake magana ,ya yanke Auren FU'AD da sanaya Nan da sati Mai zuwa kacal ,ya d'an k'ara ne don su fahimci juna ,na yanke hukunci Kuma Babu gyara tun da ya Rasa matar da ze nuna amatsayin wacce yakeso har sak'o nace abaka ,Amman ka nuna ban Isa ba Kai da mahaifiyar ka ...... Fu'ad ko motsi kyakyawa ya kasa ,sai Jameel ne ya iya cewa ,to dady abashi iya satin Mana ya Nemo wacce yakeso .....be idar ba dady yace kunyi kad'an wanne ubanne ze bada 'yarsa cikin sati a garin Nan ,Nima tsananin zumuncin dake tsakanin mu da k'aninane yasa Dan Bata da masaniya itama sanayan hak'uri tayi . Mamy ce tace ,hak'urin dole ba ,Amman itama da anbata zabi da ta fito da mijin da takeso Wanda ya Dace da ita ,sai ko dady yace hafsa d'an d'an uwan nawane be Dace da 'yar da na Haifa ba? Da sauri mamy tace ba Haka nake nufi ba ,ganin ya harzik'o....mumcy ce ta katse zancen da cewa nidai Alhaji Yaya Abu d'aya nakeson kamin Wanda ze tabbatar min da inada hakki Akan FU'AD Wanda nakeson zartarwa batare da ka k'i karbar Abin da nazo dashi ba ......Bata idar ba yace "jeki daidai zancen ki ,meye buk'atar ki Naga kinason cewa wani Abu ,inajin ki . Mumcy tace "amatsayina na mahaifiya ga FU'AD na Amince da auren da kamai na gata da nuna so da k'auna ,Nima don in k'ara tabbatar da gata da nuna so ka k'auna ga FU'AD d'in Zan k'ara Mai Mata amatsayin tukwuicin biyaya da ya Mana inyaso a d'aura Auren tare Dana sanaya ........ FU'AD arazane ya d'ago ya kalli mumcy Yana cewa mumcy Mata biyu? Lokaci d'aya ? Noma zasu min ko me? Haba mumcy.....be k'arasa ba mumcy tace son kayi biyaya Kan wacce ka Saba yimin Dan ALLAH kasan dai bazan cutar dakai ba ko? To banaso kace komai sai k'arb'an Abin da Nima nazo dashi ,Mata biyu karsu saka cikin fargaba namijine Kai ,ka d'auki Haka matsayin rabo Mai Amfani , ALLAH ya bama Mai sa'a sa'a kawai . Sosai Alhaji yaji maganar mumcy tamai banbarakwai ,Amman tun farko ta gama danne shi da godiya Akan Auren da ze hada na sanaya da FU'AD d'in ,don Haka bayaso Amman ya hak'ura yasan babu yadda za'ayi a aura Mai wacce takai sanaya kyau,ilimin boko,wayewa,martaba da dukiya ,Kuma ze dinga juya FU'AD d'in son ransa daga baya ma ze iya sawa asaki wacan d'in 'yarsa ta zauna ita kad'ai agidan FU'AD d'in ,da wanan tunanin ya hak'ura ya karb'i buk'atar mumcy,itako mamy nason magana Tana tsoro ,sanaya takaici ne ya hanata motsi gani take kamar ba gaske bane Abin ta Shirya yima dadyn ta tijara Bayan sun tashi daga meeting din Dan Basu suka had'a Abin ba da su zata ma tijarar ,Dan Haka ta zama kurmar dole ,mamyn ta ko nata Jin haushin shirun da tayi Alamar ta amince da auren harma da wata kishiya amatsayin tukwuicin yadda da auren da tayi tirkashi...... FU'AD mik'ewa yayi ze koma saman shi sakamakon tsaka me wuya da mumcy ta k'ara sakashi don dogon nazari Kan wa mumcy zata k'ara jona Mai Kuma ? Alhaji ne ya tambayi mumcy wa zata bashi matsayin ta biyun? Bud'ar bakin mumcy sai tace "wata Yarinya ce Asma'u ,insha ALLAH nasan zasu zauna lpy ,sosai sunan ya d'aki kunnen FU'AD Amman Yama Rasa gane me sunan ya kasan tantance wace ma Asma'u da mumcy ta k'ara Mai da ita ba tare da shawara da shi ko iyayenta ko ita ba ,shidai ya Shiga shekarar sa'a aure uku duk Babu Mai so duk Auren Cushe da had'in dole ,Kai Abin yamai yawa ,Yana Shiga ya wuce room d'in shi ya fad'a gado da ribda ciki kansa yamai wani nauyi Yama Rasa ta Ina ze Fara .... Sosai mumcy taji dad'in k'arb'an Auren Asma'u da Alhaji Yaya yayi don shine masharin hawayen da take zaton zai share hawayan dayake ambaliya a kyakyawan fuskar FU'AD insha ALLAH Dan tamai zabi nagartace Dan baze dawama da bak'in ciki ba matuk'ar Yana tare da ita ,ita Kuma sanaya ta k'araci rashin Tarbiyar ta ....... Sanaya ma da kuka tabar wajen da sauri dady ya bita Yana rarashi ,har d'aki ya shiga Yana cewa haba shalelen dady meye acikin Auren santalelen yaro kamar FU'AD d'an uwanki? Ko meye acikin kishiya irin ta 9ja ? Kucaka duk da Baki ganta ba ,nasan kin Mata zarra ta ko ina kin yaga Mata kina sama da ita Auren ma sai kin zaba naki kikeso a Fara d'aurawa ko na wacan d'in kenaba zab'in da ko shi FU'AD d'in be Isa na bashi ba ,ishiru shalelen dady muyi magana ki fad'amin duk Abin da kikeso na Miki Al'k'awarin shi Ni Kuma ......sanan ta rage kukan tace ,afasa Auren ,Nan dadyn yace nanfa d'aya Banda wanan Dan Babu fashi ,masifa ta Fara yima dadyn Tana gayamai maganganu na rashin tarbiya harda ya yaudareta da ya kawota 9ja ya kyautar da ita ze gudu k'asa mafi 'yanci ya barta da jagajaga ai zalinci ne wanan ,ko rashin Jin dad'i beyi ba da tace Mai zalinci ne wanan tsabar lalacewar tarbiya Koda yake daman ba'a bada ita ba bare asameta ,cigaba tayi da nuna rashin tarbiya ta tsaurara lafuzanta ga mahaifinta ......be tsawatar Mata ba sai da yaji ta Fara sauka ahanya sosai kamar Tana neman zagin shi har ta Fara cewa wlh bazata aure shi ba sai dai duk Abin da zeyi yayi ,shine fa ya Fara Mata masifa sosai har sai da ya mareta ,Kuma ya tabbatar Mata ko mutuwa yayi in Bata auri FU'AD ba be yafe Mata ba ,ya fita ya bar Mata d'akin yayin da mamy ,mufeeda,uzaifa, suka taho da gudu jin Anaya musayar muryoyin tsakanin dady da sanayan da ta karb'i la'adar Mari Kuma ta rushe da wani wawan kuka,afusace ya wuce su ,su kuma suka Shiga d'akin suka Sami sanaya ta rik'e kumatu Tana kuka Mai cin Rai ,ta gama amincewar dady baya son ta ya Kuma tozarta ta yau Dan Haka neman mafita kawai takeyi .... Mumcy ce tace Jameel yaje ya ganin Mata Halin da d'anta yake ciki ,da sauri Yaya Jameel ya tafi . Mumcy tanata tunanin yadda zata bulloma lamarin Taya zata doshi gidan su Asma'u da maganar Auren asma'un? Tunanin me mutane zasuyi da iyayen Asama'un , itama Asma'u zata Amin ce kuwa ? Kai Akwai matsala fa ,kodai ta janye had'in Auren ? Sosai jameel yake rarashin k'anin nashi da Shirin korar Mai duk wata damuwa da ta baibaye shi ,atake ya Kira su sa'adiya ya sanar Mata Halin da ake ciki sosai taji b'acin ran abun tayi tir da Halin Alhaji yayan ,shi Kuma ta tausayama k'anin mijin nata ,da ze auri Mata har 2 Kuma ba zab'in ransa ba ,gashi taci buri a Auren shi inya tayi yi yanzu komai nata ya wargaje don inta nuna murnar ta sai aga kamar Bata damu da abinda ya faru ba ,sosai suka tatauna da junan Kan maganar . Tunda sa'adiya ta sanar ma da Aisha da Ma'u maganar sai hankalin Ma'u yayi mugun tashi Wanda ta Rasa dalilin hakan ,ta Kuma tausayama FU'AD sosai ,daga baya saboda rashin sanin dalilin tausaya masan da haushin Abin da taji ,dole ta k'irk'iro Jin dad'in da bekai zuciya ba tace gwanda amai hakan ai mugu d'ayar matar ma Babu Wanda yasanta shi ya sani gwanda abashi koma waye can ya gane ,be kamata na tausaya Masa ba ma ,su sa'adiya da Aisha suna ta magana Kan Auren amman Ma'u ta kasa cewa komai tadai janjanta da nuna tausayama FU'AD d'in afili gabansu ,Amman zuciyar ta najin wani iri game da lamarin ta kasa gano komai Kuma ....... 👏🏼Allah kasa mu cika da kyau da imani😭 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AB* (Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg 25 Sosai Ma'u ta saka batun Auren FU'AD a ranta da kyar take yaki da zuciyar ta wajen kawar da wasu tunanuka akai ,Amman Abu yaci tura ,ta Kuma kasa gane dalilin hakan . FU'AD Yana Jin d'aci da k'unar Rai inya tuna da auren sanaya da aka lik'amai ,da ya Kuma tuna Wanda mumcy tamai na huce takaici sai ya rasa inda zesa Kan shi ma ,har tambayan kanshi yake,wacce mumcy ta ke Shirin huce Mai haushi da ita ,inma makauniya ce ko kuturwa ko gurguwa ita dai mumcy ta jona Mai hankalinta kwance Bata tunanin Halin da ze Shiga ? Shidai yanzu har Yama rasa Abin yi..... Number B2k ya Kira ya Fara cemai Kai abokina nifa Ina Ruwa, B2k yace kamar ya ? "FU'AD yace hmmmm banma San ta Ina Zan Soma ba ,kawai dai Kar kuji Abu kamar saukar aradu shiyisa Zan sanar ma yanzu ,nifa angama Dani Dan Babu saurana , B2k yace abokina ninkeni kake baibai ,futo min a mutum pls"FU'AD yace ,hmmmmm anyi gunduwa gunduwa Dani an rabama wasu Mata Ni ,dayar ma ko sanin ta ban samu Halin yi ba dayar ma karkayi tunanin Dan na Santa ko da amincewa ta ne ko inaso ,kawai dai anbadani garesu ,in baka tab'ajin Auren gagawa ba to yau ga Auren katsaham ,wai ni za'ama Aure Kuma har Mata biyu ,pls Kaine mayen Auren kazo ka fanshe su a sadaka ma Ni dukan su har sadaki zanma wlh na maka Al'k'awari ...... B2k ya bushe da dariya ,yace abokina nasan baka Shan komai sai su easy da juice da su Ruwa nine ma sheda da sai nace ko kafara kurb'e kurb'e ne ko kana afa morijiwana da sauran su kasan me kake fad'a kuwa ? FU'AD tsaki yaja yace Kai fa wani lokaci kamar kaci Kai ,kawai ya kashe wayar shi . B2K ya Kuma bushewa da dariya sai da ya gama darawa sanan ya Kira abokin nashi yasan ranshi y b'aci ,kin d'agawa FU'AD yayi har sai d B2k ya tura Mai sak'on karta kwana na ban hak'uri sanan ya samu ya kirashi ya amsa wayar ,sosai FU'AD ya ma B2k bayanin komai , B2k ma ya fahimce shi ya Mai Al'k'awari zuwa gidan Kuma insha ALLAH. Mamy nata fama da sanaya itama Tana lalab'ata Dan taso bijirema Auren ta hurema sanayan kunne Kuma wata magana da dady ya fad'a Mata shine yasa ta d'an hak'ura har take ba sanayan Baki Kan ta bi umarnin dadyn ta shine biyaya da sakamakon gatan da ya nuna Mata Kuma yake Kan nuna Mata ,ita dai sanaya gidan tarbiya rashin kunya ta dinga yi har Tana cewa Suma Auren cushe aka musu? Ai na soyayya aka musu danme ita zasuci amanar ta Haka kamar siyota sukayi a kasuwa , mufeeda da haushi d takaici ya Gama cikata duk fitsarar yayar ta anrasa me fasa Mata Baki sai Kuma lalab'ata da sukeyi kamar tsoron ta sukeji ,ita wlh tafi tausayin mijin da za'a bata ma wlh ,Dan zega abubuwa ,har mamaki take ya akayi Halin su ya bambanta Dana yayar ta? Kuma iyaye guda ne suka haife su suka Basu tarbiya Kuma a hanun su suka taso tun k'uruciya har kayau ,lallai ta yadda da kalmar mlm bahaushe ta ALLAH d'aya gari bamban, halayar kowa Kuma daban Amman duk d Haka me Hali madai musamman yake , ALLAH ya shiryeta da gagawa inba hakaba za'asha fama a gidan miji . Mumcy ce taje wajen baban Ma'u ita da Yaya Jameel batare da sanin FU'AD ba ,sun tafi Kan maganar Auren FU'AD da Ma'u ,sosai baba yaji dad'in maganar Auren Ma'u ,inda matsalar take beyi maraba da Abin ba ,da akace FU'AD ne ze aureta hamshakin matashin Mai kud'i kamar FU'AD Sam be shirya siyama yarsa wulak'anci da cin mutunci ba ,talaucin shi be Kai Haka ba Dan Haka baba fir yace be amince ba Sam , mumcy d yaya jameel suka kad'a suka Raya Sam yak'i ,sai da mumcy ta dinga bashi Baki tace Mai Kar ya musu Haka Mana suda suka dogara da ALLAH da Kuma shi wajen samun amincewar Ma'un don shine tal zai taimaka musu da taimakon shi ,don shi yisa Basu sanar Mata ba don su bashi ikon shi da k'arfin shi da ALLAH ya bashi a matsayin shi na uba ga Asma'u ,Kuma sunmai Al'k'awari rik'e Asma'u da Amana Kuma Babu wulak'anci ko tozarci tsakanin su fa Asma'u, Kuma basuyi Haka don nuna ikon arzikin su Akan su ba ,basu yi haka don Raina talaucin su ba ,hasali ma sunyi hakan ne don girmamawa da ganin mutuncin juna da yabawa da tarbiya da Halin datako na gidan nashi . Sosai maganganun mumcy suka Shiga baba ,Amman duk d Haka Yana dogon nazari ,ya Kuma yaba Hali irin nasu na d'aukan duniya sannu ahankali Basu d'auki kansu maysayin da wasu masu arzikin suke Kai kansu ba ,yaji Dadi sosoi ya amince musu yace Amman da sharad'in bazema Asma'u dole ba wanan shine sharad'in . Babu ja'in ja suka Amince suka Mai godia , Yaya Jameel ze Mai wata dunk'ulaliyar kyauta don Jin dad'in Abin da ya musu , mumcy ta yi gagawan hanashi da ido da Mai nuni da hannu ,ya fasa suka Mai godiya suka tafi ,amota mumcy take sanar Mai ai zaka sa kwab'ar mu tayi ruwa ,wanan d kake ganin shi jajirtacen datijo ne Mai kudin duniya ,ai duk wani kyautatawa da bajinta da zamu Mai abari sai Bayan bikin FU'AD da Asma'u wanan shine ze zama tukwuicin yaba kyauta ,Amman ba yanzu ba gudun Kar abata rawar da tsalle ,Ina fatan ka fahimta ko ? Sosai jameel ya fahimci manufar mahaifiyar tashi . Baba Yana Shiga y kasa sanar ma da mama habee maganar gudun maganganun da zata jefi Ma'un tasa dasu ,shima Kuma be tsira ba ,dama kulin cikin jifan ma'un da jafa'i take wai ita da dawowa sai ta kawo musu tsarabar yawon ta zubar wato d'an shege take nufi ,baba saidai ya nema wa ma'un tsarin ubangiji yace bakinta ya sari tulun Kashi ,y fasa fad'a ya bar gidan ma . Barin Kashi aciki baya maganin yunwa ,Haka baba yayi shahada yasa audiga ya toshe kunnen shi ya fad'ama mama habee Amman be bayana Mata Wanda ze auri ma'un ba ,masifa da bala'i da mugayen maganganun da take jefo musu ya Hana baba bayyana Mata ko waye mijin da Ma'un zata aura atunanin ta wani Sha katafin ta samu a Abujan ,shiko baba Jin masifar na neman harzuk'ashi ya fice ya bar Mata gidan cikin daren gashi ya gaji Yana son hutawa don Haka baba yace dole shima ya k'ara aure ya gaji da masifa d bala'in habee tin tanayi a b'oye yanzu a bayyane take yi,in yayi Auren ma raba musu gida zeyi ALLAH yagani baze Rasa yadda zeyi ba sai ya samo ko wacce Bata haihuwa ne ko datijuwa Mai Halin kirki ko ya mutu cikin sutura ta mutunci . Da ma'un ta Kira babanta suka gaisa Yana son sanar Mata Yana tunani ya Kuma yadda kamar yadda sukace Bata sani ba yaga alamun hakanne ,don Haka yace Mata ,ze Mata wani Abu amatsayin shi na mahaifi agareta dafatan zata karb'i abun hannu bibiyu bazata bashi kunya ba saboda tasan baze cutar da ita ba inko tak'i karb'an abun to ta d'auka tamkar ta tozartashi gaban mutanen dake cikin duniya ne ,ya samu k'arfin gwuiwar furta hakanne sakamon munanan kalaman habee da nuna bak'in ciki k'arara Akan lamarin shi yisa ya amince yakeson yima ma'un umarni da amincewa itama ,sosai hankalin ma'un ya tashi burin ta baba ya fad'i buk'atar shi tamai ko menene Dan tamai Alk'awarin hakan ,baba dai kasa fad'a yayi sai cewa yayi ze sake kiranta Amman kartasa komai cikin ranta ,Yana diya da irin yarinyar da ALLAH yamai kyauta da ita ,sosai Ma'u ta gano baban najin nauyinta ne ko nauyin fad'an maganan ,Dan Haka ma'un tabashi hak'uri ta k'arfafa Mai zuciya har ya fad'a Mata maganar ,Amman ya nuna Mata Akan wanine yakeson aurenta Kuma iyayen shi sun Zo ,ya Kuma yi bincike akansu sunada nagarta da datako ,sosai Ma'u taji abun kamar saukar aradu Amman bin ummarnin da Tama baba Al'k'awari ya zama dole Bata da zabi ko neman shawara atake ta amsa da sanyayiyar zuciya tanata danne damuwarta Kar baban ya fuskanta ,Jin ta amsa sai Addu'a yake Mata da shi Mata Albarka ,sanan yace ta kashe wayar shima ze kirata yaji ko Tana lpy ,Bata iya amsawa ba ta kashe wayar jikinta a macce sai kuka ya kwace Mata Kuma ...... Aisha ce ta shigo ta sameta Tana rabza kukan sosai take rarashinta Tana tambayan ta ,ganin Taki shiru Kuma tak'i fad'a Mata kawai Aisha ta kwalama aunty sa'adiya Kira ta shigo suka Fara tambayanta gaba d'ayan su .... Sosai ma'un take kuka ta Gaya Mata duk yadda sukayi da baban ta Bata b'oye musu komai ba ,sosai Suma suka tausaya Mata ,aunty sa'adiya Tana cewa "oh keda FU'AD irin k'addarar da ta fad'o muku kenan? Gaban ma'un ne yayi mumunan fad'uwa k'irjin ta na bugawa da k'arfi da k'arfi ,batare da tasan manufar hakan ba ....... Kukane ya sake kwace Mata ,sai su sa'adiya da Aisha suka koma rarashin ta da Mata umarni da bin mahaifinta in ALLAH ya yadda zataga daidai arayuwar ta ,tayi hak'uri da yadda rayuwa tazo Mata da sannu zata cinye jarabawar ubangiji ,sosai ta samu hankalinta ya kwanta da taimakon nasihohin su ga wani kulawa ta musamman da suke Bata tamkar ciki guda suka fito . Sa'adiya Kiran Jameel tayi ta sanar Mai tashin hankalin da ma'un ma take ciki Bata rufe Mai komai ba murmushi Jin dad'i yayi Amman sai ya nunama sa'adiya ya tausaya Mata ,Amman su cigaba da rarashin ta da nuna Mata bin iyaye wajibine da sannu zataga sakamako Mai kyau,shi Kuma ze zame Mata uban d'aki nagari a cikin Auren insha ALLAH,sosai sa'adiya tamai godiya ta kashe wayar tanajin dad'i har ranta ,ta sanar ma husna yadda sukayi da jameel ,taji dad'i sosai don dama shine fargabanta na farko inda za'a Sami kud'in da za'a Mata Abin da ya samu na Auren , Aisha ma tayi k'ok'arin kawar Mata da damuwa ta hanyar d'ebe Mata kewa da labarin fan dinta na social media. B2K sosai yake rarashin FU'AD da nunamai mahimmancin bin iyaye Yana bashi hak'uri ta tausan shi da rarashi ,da nuna Mai ya d'auki hakan matsayin k'addara Mai kyau sai ALLAH yaga niyar shi ya jefa Mai Albarka cikin Abin , sosai FU'AD ya fahimci abokin nashi ,Amman daurewa kawai yakeyi shi kad'a yasan ya yakeji Aran shi , B2k sai da ya shafe wasu awwanni tare da FU'AD seda yaga Yaya Jameel yazo sanan ya barshi ya tafi don Shirin angon cin abokin shi me Mata 2 lokaci 1 Dan FU'AD yace Babu Abin da zeyi Wanda ango yakeyi na farin ciki da auren da zeyi don Haka B2k ya d'auki nauyin yin wasu abubu bawai na bidi'a ba kawai irin Ayi party ko 1 ne sai kayan da zesa na angwancin da duk wasu abubuwan daze buk'aka tare da taimakon Yaya Jameel Dan sunyi magana kafin ya tafi . Gudun rigima Yaya jamee yace abar ma'un acan gidan aunty sa'adiya ,Amman mumcy tace dole ta dawo gidan su don bama mahaifinta hakkin shi na uba agareta Kar suyi Aiki da Kai Mana ,don Haka jibi su Ma'u da sa'adiya duk su taho in Kuma Kai zaka je ka taho dasu to ,kaga gatana ne d'aurin Auren in sun dawo washe gari za'a daura Auren ranar jama'a .. Sosai B2k da Yaya Jameel suke shiri sun shirya lefen amaren biyu duk da komai cikin gagawa akeyi ,komai iri daya ake sa musu sai banbancin kala in ansama wanna green sai asama wanan red Haka ake zuba musu uwar Kaya cikin setunan akwatunan nasu ,ita sanaya cikin gidan aka kawo nata akaba mamy ,itako ma'un mumcy ta Adana nata har sai baba yace akai in Ma'u ta iso garin . Ma'u ta Kira hafeeza ta sanar Mata d Auren d za'a Mata har take Mata jajen barinta gidan mumcy da Aiki sosai itama ma'un takejin abun Amman Babu yadda zatayi ,sosai hafeezar ta rarashi ma'un ita . Sanaya Ana nuna Mata lefenta da yaci uwar kud'i sai wani yatsuna takeyi Tana gwasale kayan wai ankarya darajarta ,kayan lefen ta had'in 9ja ba England ko Germany,ko India ba ko Yar Dubai d'inan da tazama Gama gari ita wlh ancuceta batason lefen aba almajirai masu buk'ata ,mamy da Taji haushi tace to ko amayar ma da uwar mijin naki? Da rashin kunya tace eh ace Mata nagirmi had'in 9ja wlh ,sai ko mufeeda tayi dariya ciki ciki tace ai aunty Sana d'auka zakiyi ki kaimusu abinsu ganinan biyo ki da wani Nima ,sai ko ta mik'e Tana turo Baki ta d'auki wani kit Tana Jan wani trolly wai zata mayar sai ko mamy tace ke Dan ubanki goyon gwauro ce ke? Baki da tunani Ashe kunya ta Miki k'aranci? K'anwar takice zatace kiyi Abu kiyi ? Sai ko mufeeda Tace mamy ki barta tunda batasan gatse ba,da gudu ta biyo mufeeda Tana setaci ubanta ita zatama gatse ? Mufeeda ta sunale ta Bayan mamy ta gudu ta bar musu d'akin a 360 ,sanaya kamar ta mutu don bak'in ciki ,kifewa tayi Kan gado Tana kukan shagawaba Tana cewa wlh in kuka auramin shi kun siyamai wahala don banayin shi wlh ...mamy tace Aiko saidai kiyi Kuma bakin alk'alami ya bushe ,sanaya cikin kukan tace to wlh ku tanaji kotun yin shara'a Mai suna *day to day court* tare da manyan alk'alai .......mamy tace wanan Kuma mun Jima da tanadar su yarinya ta fice ta barmata d'akin ta tafi wajen dady . Ta same shi Yana son fita Yana tsoron Rana wai bayason Rana ta tab'a shi Kuma wajen abokin shi zeje suyi maga Kan bikin Dan shine waliyin sanaya gwanda ya bashi girma yaje kafa da kafa don ya sanar mishi ga Rana na Shirin Mai cikas ,haushi da takaici ya kama mamy tace Ni bansan ranar da zaka canza ba Akan sababen akidan Nan naka kamar ba cikin ranar ka taso ba ka girma inda Tana kisa ma da bamu had'u ba ,sai kuyita wasan b'uya Kai da ranar .......da fad'a ya dakatar da ita nace ki dinga sanin lafazin da Zaki gayamin ko kin San banason Ana dawo min da Abin da ya gabata ko? Har zakice cikin ta na taso Amman ba tare aka haife mu ba ,kice ki tambayi masu ilimi akanta kisan irin illar da take Mana a jikin mu da fatocin mu kafin ki Shiga Abin da Babu ruwanki ,Tace bansan ilolin ta ba nadai fi sanin amfanin ta musamman irin na hantsi da kariyar da take bama jikin d'an Adam ,Bata k'arasa ba yace wanan Kika sani? Je kiyi k'ok'arin sanin ilolin sai Kika wanne yafi rinjaya ,kawai malama Zaki b'ata min Rai inaji da son fita Rana tak'i rusunawa Dan wanan ranar ko easy na kunna sai ta shinshinani ko Babu yawa wlh sai ta buys Zan fita duk nacin ki tuna ba aikena kikayi ba Kuma ba d'andako ko Mai wulbaro nake ba ,in abun buk'ata ne kinsan na Tara bani da matsalan komai ko Egypt Kuma kinsan da ba 9ja bane ko can innaga ta kaleni kinsan buya nakeyi bare 9ja da da kamar tasu ta daban ce ,mamy tace karde ashiga hurumin Mai komai dai wato ALLAH shi yayita dai asan matsaya Kar harshe yayi subul da baka baruwan wani da ALLAH bame Shiga tsakani ,sai ko ya Fara jaraba wai wa'azi zata Mai ? Ganin ya hassala sosai ta sulale ko Abin da zata fad'amai Bata fad'a ba ta barmai d'akin . Washe gari Yaya Jameel yaje ya kwana a Abuja don taho da su sa'adiya . Abu ya kusa saura kwana 2 d'aurin Aure ........ Allah kayi Mana kyakyawan karshe👏🏼 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AB* (Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg 26 _kuyi hakuri da jina shiru abubuwane suka min yawa_ Bayan Yaya Jameel ya Isa Abuja ya sanar ma su aunty sa'adiya dasu Ma'u har Aisha suyi shiri Dan gobe zasu tafi ,basuyi mamaki ba domin ya sanar musu tun a waya . Ma'u jiki Babu kwari take Shirin tare da taimakon sa'adiya da Aisha suka samu ta shirya ,ranar dai ba wani baccin kirki ta samu ba ... Shima FU'AD b'acin Rai ne fal zuciyar shi duk da abokanen shi suna bashi hak'uri Akan ya bama zuciyan hak'uri ya karbi kaddarar da tazo Mai yayi fatan hakan yazamo mafi Alkhairin k'addara agare shi , yaji shawarwarin su Kuma ya amsa ,Amman cikin zuciyar shi Abin ba yaka yake ba. Sanaya ma har ji take kamar ta gudu tabar k'asar don ji take ta tsani 9ja da jama'ar ta gaba d'aya ,kullin cikin Bata Baki mamy take ,itako mufeeda nuna Mata matsayin bin umarnin iyaye take don samun tsira ,suyi fad'a Amman mufeeda ko damuwa batayi don tasan gaskiya take Gaya Mata. Washe gari su Yaya Jameel suka kamo hanya by road Dan Haka mumcy ta umarci Yaya jameel da ya wuce da Asma'u gidan su Kar yayo Nan da ita ,yace "to" suna zuwa ko ya Fara sauke ta gidan su da Mata Al'k'awarin aunty sa'adiya da su Aisha na Nan zuwa su debe Mata kewa , Ma'u taji Dadi sosai yace Mata inda wani Abu Kuma ta sanar ma aunty sa'adiya ta sanar Mai , Asma'u tace toh insha ALLAH ,tagode da Abin da suka Mata ta Shiga gida ,Yaya Jameel be wuce gidan mumcy ba sai da biya ta wajen baban Ma'u suka yi wata magana Mai mahimmanci ,sanan ya wuce dasu gidan mumcy. Sosai mumcy tayi murnar ganin su sa'adiya ,ta musu tarba Mai kyau tanata farin ciki ,mufeeda ma sosai tayi murnar ganin su Aisha da ta Kuma yi. FU'AD ma bayan ya dawo gida yaga su aunty sa'adiya yaji farinciki sosai da yaga Aisha sai ya dinga tambayan kanshi itace a pic d'in da ya gani kuwa? Can dai yace ba ita bace to Ina wacan din ya suke da aunty sa'adiya ? Meye alak'ar su? To ma me zeyi da alak'ar su ko sanin wacece meya had'in shi da ita ,da gagawa ya kori tambayoyin ya Shiga Hira Mai mahaimmanci da Yaya jameel da mumcy .... Tsakanin FU'AD da sanaya Babu wani so ko k'auna ,hirama Bata Shiga tsakanin su gashi Gobe ne da'a daura musu Aure ,sosai suke Jin wai tayaya Auren ze gidana a tsakanin su ,sude Dan anfi k'arfin sune kawai da hakan be faru ba. Aranar da Ma'u ta dawo baba ya umarci Ma'u da taje gidan aminin shi malam kalla don ganin lefen ta ,taso yimai gaddama Amman ya Bata hak'uri da yi Mata nasiha Akan tabi umarnin shi da sannu zataga Alkhairin Abin ,Babu musu taje don ganin kayan sosai mama hinde ta dinga Mata nasiha da tayi hak'uri ta karb'i Auren hakan ze zama yayewar wahalar Rayuwar ta da yadda Allah ,sosai Ma'u taji Kuma ta d'auki shawarwarin ta ,don ta jima cikin gidan ma kafin ta koma gidan mama habee gidan masifa da bala'i don tun dawowar ta mama habee take Yar Mata da kalamai marasa dad'in sauraro ,harda za'a fake da Aure Bayan an Gama yawon ta zubar sanan aka dawo da ita wai za'amata Aure da wani Mara rabon.....ita dai Ma'u Bata tab'a tankawa ba ,sai ma kukan rabuwa da baba da takeyi da hangoma kanta wata irin rayuwa da zatayi a gidan Wanda ze zamo miji agareta da batasan ko waye ba . Cikin gagawa Yaya Jameel ya bigo invitation card suka Shiga rabo Wanda ya samu ya samu Wanda be samu ba shikenan ya bisu da Addu'a saboda k'urewar lokaci ,anba Alhaji Yaya nashi ,aka tambayi sanaya ko Akwai wani occasion da takeson yi? Cikin bacin Rai da takaici tace ALLAH ya sawak'e Mata kaf cikar 9ja bataga inda ya Dace da tayi shagali ba ,mussaman da Bata fatin ciki da wanan Auren Dan Haka Babu wani abun farinciki agareta su je su k'arata ,Yaya Jameel yace Mata Bata buk'atar kud'i a hanun FU'AD? Tace baida Abin da ze Bata ,tafi k'arfin kud'in hannun shi ,Yaya Jameel yayi murmushin irin batasan waye yaro da kud'i ba wato FU'AD da ta sani bazata furta hakan ba ,Amman tunda babanta ya sani ai ze Bata labari ko wata Rana ,ganin bazasu Toya wainar arziki ba da sanaya yasa ya rabu da ita ,Dan da FU'AD d'inne ma Bata Isa ya saurareta ba ,shima dama karambani yayi ,bangaren FU'AD kuwa, mumcy ce ta tilasta Mai bama Asma'u wasu kud'ad'e don ko zata buk'ata ,Dole ya d'auka ya bayar ,Yaya Jameel ya kaima baba yace abata ace Inji angon ta ,baba ya raba kudin gida biyu ya ajiye rabi ,ya fito da rabi ya nunama su Ma'u da mama habee yace sai suyi shagalin biki dashi ,gani kud'i mama habee ta d'an saki ranta tace sai Ayi ko 'yar walima ce agayaci mak'ota Kar suji wai wai ,baba yace Babu laifi indai baza asamai kid'a a gida ba ,da sauri humaira tace iya Mata ne sai na rakata kasuwa yau mu buga iv da siyayan Abin da za'a ci da na rabarwa ma ,baba da Ma'u murmushi sukayi baba Yana cewa wato dake kunga kud'i zakuyi yadda kukeso har kunyi naam ,Allah ya shirye ku ,acikin zuciyar shi ,ma'un ma hakan take a zuciyar ta ,Nan da Nan suka shirya da tirsasawar mama habee da na humaira sukasa ta shirya suka tafi kasuwa jakar kudin na hanun Ma'u anba mama habee wani Abin don hidimar gida ,dake humaira tasan takan kasuwa kamar wacce akayi nakudar ta tsakiyan kasuwa ,atake suka siyo kayan da Ma'u zata sa Gobe suka bada d'inki express aka d'inka musu suka bugo iv suka siyo takeaway da kayan rabo su snack ma order suka bayar Akan zasuzo Gobe da safe su karb'a ,ganin kudin banza har wurin gyaran jiki takai Ma'u duk Abin da aka caje su sai humaira tace ma'un ta lisafo abasu dake taga kud'i kamar na banza ,adaren suka Gama rabon iv duk yawanci ma kawayen humaira aka kaima sai Yan uwan mama habee sai kawayen Ma'u da humaira na islamiya d makarantar dare akayi sa'a adaren hafeeza ta dawo hutun karatu ,Nan suka dinga hirar yaushe gamo ita da Ma'u ,da tirsasawar hafeezah Ma'u ta amince zataje gidan kishiyar kakarta gidan su aunty sha'awa wacce ta tab'a zuwa wajen ma'u wacce take Aure a India ,cikin fargaba da tsoro don tun k'iyayar da sukema kakar Ma'u shine yazo har Kan mahaifiyar Ma'u har ya dawo Kan ma'un ,Koda su Ma'u suka Isa ,Haka aka karbesu Babu yabo Babu falasa ,da Ma'u suka bada katin gayyatan bikin ,a wulak'ance aka karb'a kishiyar kakarta tace zata duba tagani in Bata da Abu Mai mahimmanci Gobe ,ko Ruwa ba'a Basu ba har suka tafi ,da aunty sha'awan ta Kira hajiyar su ,sai hajiyar take sanar Mata da auren Ma'u har gayyace su Amman Babu inda zasu ,Nan aunty sha'awan ta dinga ba hajiyar Baki da hak'uri Akan taje da kyar ta amince zata .. Gida yad'au harama su humaira anga kud'in banza har da k'rkiro kamu a Daren aka feshe Ma'u da turare wai anmata kamu aka gayyato makota kawai ,aka raba musu kaskon wuta da turare ,. Washe gari ranar daurin Aure ,tun asuba mama habee suka tashi da gyaran gida ,da gari ya waye mak'ota suka shigo don tayasu aikin girki ,aranar bikin aka kawo ma baba dinkin shi da aka bayar jiya Ma'u ce ta bayar itama mama habee dasu humaira anyi sabun dinkuna kusan kala 3 3 har haidar ma anyi Mai ,sosai gidan ya dinke da masu Taya Aiki ,misalin karfe 10 na safe k'ofar gidan su ma'un fal yake da jama' a 'yan daurin dake karfe 11 za'a d'aura Auren a masallacin layin su ma'un inda baba yake kamsu salawat , Ma'u ko inbanda zuciyar ta da take bugawa Babu Abin da takeyi da taimakon hafeeza take samun nutsuwa . FU'AD da kyar Yaya Jameel ya sashi yayi wanka da taimakon B2k da na wasu abokanen shi suka samu yayi wankan yasa Kaya da yace bazeje d'aurin Auren ba sai da mumcy tamai da gaske yaga ranta ya b'aci sanan ya shirya suka fice . Alhaji yayane ya ke tambayan sanaya Akan Auren wa takeso afara d'aurawa,nata Kona d'ayar da Basu San ko wace ba? Yana lalamin ta Yana cewa sai ta zab'a ,wani kallo tamai tace ita ohooo suyi duk yadda sukeso ita ai basa neman zab'in ta ,cikin Jin haushi yace ke Kika sani ,sai ko mamy tace abari a d'aura nata daga k'arshe tasama Amarya ,sai ko yace to ,ya sani doguwar malummalum ya tafi ,sai ya d'auki Yaya Jameel suka Fara zuwa gidan su ma'un don afara d'aura nata adole aka tirsasa FU'AD zuwa can din fuska Babu yabo Babu fallasa . Mumcy ta gayyaci jama'a duk da ba sosai ba ,Amman yayi komai agurguje. Wake ya dinke ya cika da jama'a ,cikin nasara aka Fara d'aura Auren ma'un da FU'AD daga baya aka koma aka d'aura na sanaya da FU'AD , Ma'u uwargida sanaya Amarya ,sosai waje ya d'auka aka dinga yima FU'AD ALLAH ya sanya Alkhairi ,shiko sai yake kawai yake yi. FU'AD ne ya Sami mumcy ranshi duk Babu dad'i yace Mata"shifa ba yanzu zasu tare daatan da aka k'ak'aba Mai ba sai Nan da sati 2 ,ya tashi yayi hanyar ficewa , mumcy ta dawo dashi cikin fad'a ,wlh son bazaka watsamin k'asa a ido ba ,wajen ajiyesu ne baka dashi ko Abin da zaka ciyar dasu ? Sai ko Yaya Jameel ya shigo dama duk yaji me akecewa ,sai ya dafa kafad'un FU'AD yace "k'anina Rabin Raina ,kayi hak'uri kowacce ta tare Nan da sati 1 kacal kaji karkace komai kaji Rabin Rai na? Sai ko FU'AD Yama yayan nashi kallon k'auna irin na d'an uwa da d'an uwa ,Yana ayyana yayan shi yafi mumcy fahimtar shi ,sai ya kalli mumcy ya kalli Yaya yafice a d'akin da alamun ya amince da maganar yayan. Sosai Yaya Jameel da mumcy suka tatauna Akan Auren ,sun Jima kafin Yaya Jameel ya tafi wajen sa'adiya ,suko Aisha da mufeeda suna tare sunata tataunawa Akan Auren da akama Asma'u da k'ananan shekarun ta har suna shirya gobe za a rakasu suje su dubota ... Maman shaheed😍😘 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AB* (Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg 27 Sosai FU'AD yakejin b'acin Rai akan Auren da akayimai da Mata har biyu duk Babu zab'in ranshi shi . Shiko Yaya Jameel da kanshi ya nemi Alhaji Yaya Akan maganar sai Nanda sati 1 FU'AD ze tare da matan shi inyaso sai Ayi ko waleema ce ranar don ahad'asu gaba d'ayan su ,sosai Alhaji Yaya yaso bijirema maganar Jameel sai da Jameel ya fito ya Gaya Mai gaskiya akan Kar aja da Abin da FU'AD d'in yace inba hakaba Abin bazema kowa dad'i ba ,yayi k'ok'ari na bin umarnin su shi FU'AD d'in Dan haka ya kamata shima abashi damar shi Babu Abin da ya rage fa da yau da gobe duk 1 ne wajen ubangiji ,sanin da Alhaji yayi FU'AD yafi Jameel kafiya da taurin Kai yasa yace" to abarshi zuwa satin ,sanan Jameel ya tashi ya fice ,yanajin duk Babu dad'i aranshi Akan Auren d akama k'anin nashi. Bayan dady ya gama sanar ma d su sanaya da mamy Abin d FU'AD yace ,sanaya ce ta Fara Jan dogon tsaki tace "be birgeta ba da Bari yayi sai Bayan shekaru biyar masu zuwa ,afusace dady y juyo zai mareta ,mamy ce ta dakatar dashi Tama janye shi daga d'akin suka koma wani ,sai ta Fara koramai jawabin kalamin da sanayan ta farayi Kan Auren ,taji Tana cewa ko abita a hankali ko tayi duk Abin da zatayi Dan har barin 9ja zata iyayi ko da sanin mu ko Babu sanin mu Dan kiris take jira ,kaga inhar muka k'ureta komai ze iya faruwan Kar akai matakin da bazamu iya Shawo kanta ba tunda ta yadda an d'aura mubita ahaka shima mubi shi zuwa satin ,Amman ka Dena yink'urin dukan ta Kar Abin ya Mata yawa ga mari ga tsinka jaka ,sosai yaji shawarar mamy yace su Fara shiri sun kusa komawa Egypt bayaso oder shi ta rigashi Isa Egypt ,sai ko mamy tace Nima duk nagaji da k'asar wlh ,Amman Kuma kasan Akwai rigima in zamu tafi ko wacce zamu fuskanta daga sanaya ko? Yace banni da ita na shirya Mata ,tafiya Nan kusa tazama dole in baziki tafi ba sai ki zauna ki dinga d'ebe Mata kewa ,mamy tace Nima tafi dolece agare Ni ,yace to ki gayama su mufeeda su Fara shiri bance kuyi yadda sanaya zata sani ba Kuma nafison sai Ana saura kwana 2 sai na sanar Mata,mamy tace "toh".. Aunty sa'adiya batasan waye mijin Ma'u ba Haka zalika batasan matar FU'AD ta biyun ba sai da ta Fara k'orafi akan ba'ama FU'AD adalici ba da aka zab'amai sanaya matsayin Mata ga shi basuyi tarayya a abubuwa da dama ba ,ganin tanata sababi ,har Tana cewa ALLAH yasa d'ayar ta zamo sanyin idanun shi duk da hakan baze zamo lallai ba Dan itama ba zab'in shi bace zab'in kuce ,sai Jameel ya fito Mata amutum ya Mata bayanin da ya gigita tunanin ta daga baya ya seta Mata tunanin ta da sata cikin farinciki , Amman duk da Haka gani take FU'AD beze so Ma'u ba, yadda taga basa ga muciji ,sosai jameel ya Mata bayanin komai da dalilin da yasa ya b'oye Mata ,ta Kuma fahimce shi dake Akwai ta da fahimta . Da sa'adiya ta gayama Aisha sosai ta Taya ma'un farinciki , sa'adiya ta haneta da sanar ma ma'un ,tayi Al'k'awarin bazata sanar mata ba . FU'AD kullin Kulawar mumcy Dana yayan shi Jameel yake samu harma Dana sa'adiya ta ninka Kulawar da take Mai da ,shiko Yana k'ara takaicin Auren d suka Mai ,ko an tambayeshi Ina matan shi sai yace "suna inda suke sosai wasu daga abokanen shi suka San baya farin ciki da auren".. Sanaya ko had'uwa tayi da FU'AD babu maganar da take had'asu ,Kuma mamy ta Mata fad'a ta nuna Mata yanzu Mijin tane ,shima FU'AD ko takanta baya bi . Koda dady ya tambaye FU'AD inda zasu zauna sai cewa yayi atambayi Yaya Jameel ,dady beyi k'asa a gwiwa ba ya tambayi Jameel ,Yamai bayanin da mumcy tamai Akan wata ta zauna a part d'in dake waje wata Kuma ta zauna a sama inda yake kwana ,in Kuma hakan be Mai ba ya koma tagwayen gidajen shi da suke gefen GRA sai kowace ta zauna a 1 tunda iri 1 ne sak ,sai ko dady yace hakan yayi . Sosai mama habee taci uwar sabada taga kudin banza ,sukasha shagalin su ta ciki Tana ciki Tana bak'in ciki Tana farin ciki har Tana Addu'a ALLAH yasa d'an mafiya akaba ita ,duk da Bata Gama sanin asalin kudin d akaba baba ba tadai ji ance basai ankaita da komai ba shine take Addu'a tafad'a mugun hannu ,ita da humaira. Ma'u taci kuka kamar babu Gobe ,kishiyar kakarta tazo bikin da kyar Bata koyi awa 1 ba tatafi Kuma Babu Abin d ta sinanama Ma'u ,sai ma Ma'u da ta cikasu da Abin rabo Dan tasan sune dangin mahaifiyar ta duk da Babu mutunci tsakanin su ,Kuma tayi farinciki zuwan Basu ,sai dangin baba d Suma ta kwashi kayan rabo da kanta ta Basu ,sunata Mata Addu'a ,Bayan sako ya iso gareta daga angonta zuwa babanta da yake sanar Mata sai Bayan sati 1 zata tare ,taji dad'i sosai ,suko su mama habee masu tsinin Baki cewa suke anzo wajen maye yayi Amarya , ALLAH ya raka Taki gona,itako ma'un ko ajikin ta Dan tanada yak'inin baba baze bada ita ga Wanda ze cuceta ba duk da biyaya Tama Auren kawai ,sosai kawayenta na makaranta suka d'ebe Mata kewa duk da Babu wani walwala atare da ita ,Bayan baba y sanar Mata d tarewar Tata sai tace ALLAH yasa Haka shine mafi Alkhairi , baba yaji dad'in furucinta yayita Mata nasihohi da Addu'a . FU'AD da sanaya kamar abokanen gaba sai da dady d mumcy suka musu fad'a shi FU'AD yaji sama sama ,itako sanaya yashiga Amman ya fita ,in agaban mutane ne zata Mai magana in Bayan mutane ne ta share shi , FU'AD ko dama gidan ta tarar Bata gaban shi ma,Dan ma aunty sa'adiya namai nasiha Kuma Yana d'an shigar shi . Akwana atashi har yau ce ranar da aka ambata ta tariyar su sanaya ,hankalin FU'AD ya mugun tashi besan ya zema kowacce ba Dan ko keb'ewa bayaso suyi da wata amatsayin matar shi gashi kamar ansami kwallo neman garashi akeyi ,da taimakon abokanen shi d Yaya Jameel d nasihar mumcy da aunty sa'adiya y Fara seta nutsuwar shi d zuciyar shi Mai k'ak'aro Mai jarumtaka ,sosai mumcy ta had'a lafiyayen liyafa na tariyar tagama aikama Ma'u da komai har da dank'areriyar waya Dan suna waya tab'ajin lafiyar ta ,baba ya amince duk lokacin da sukeso suzo su d'auki ma'un tunda kowa ya sheda and'aura Mata Aure da FU'AD ,sosai mumcy ta Mai godiya tace zata turo da mota sai ad'auke su "yace to" Ma'u komai na hannun ta Wanda zata sa da dabara aunty sa'adiya da Aisha suka zage sukaje wajen ma'u ,wai bama Susan Tana gida ba sunzo arakasu gidan tane sai suka ganta ,sai ko ta sanar musu da komai Akan tariyar ta yau d'in ,Dan Haka aunty sa'adiya ta dage ta shiryata shiri Mai kyau ita da Aisha sosai Ma'u tayi kyau ta gaji da had'uwa cikin doguwar rigar amare ya kasance ta gama shiri ,har ta dinga rok'on su Dan ALLAH su Bari aje dasu suyi Mata Kara , Aunty sa'adiya tace Mata Babu damuwa , Ma'u har Tana musu godiya ,suko dariya suke Mata cikin ransu ,misalin 5:00pm akazo da motoci d'aukan su ,anata afito da Amarya cikin Ma'u ya ba da wani irin k'ululu,sai da su aunty sa'adiya sukata Bata Baki ganin firgitar da tayi ,shima baba har d'akin yazo ya Kara Mata nasiha ,sosai yasata kuka ,mama habee nata zumburar Baki wai munafurcine yasa take kuka ,su humaira sai anga kwal uwar daka da tace bazata Kai Ma'u ba Kar aci kanta itama ,sai da taga kawayen su zasu wasu masu rawar Kai su 5 sanan tace zata ,mama habee ta hanata Amman humaira tace wlh sai taje ,mama habee tace itama zata humaira tace wlh bazata ba Dan Kar ta b'ata show yin duniya humaira ta hanata zuwa Dole ta hak'ura ,da kyar su sa'adiya suka fita da ma'u agidan da taimak'on su hafeeza da mamanta da matar abokin baba wacce aka ba ajiyar akwatin Auren ma'un ,motocin na Alfarma mumcy da su B2k suka kawo na d'aukan Ma'u wata rantsatsiya Mai numfashi bak'a akasa Ma'u da hafeeza da aunty sa'adiya da Aisha su kad'ai sai sauran mutane akace kowa shi kad'ai ze Shiga motar da yakeso ganin an Raina yawan su day sunfi Haka da anfison Haka ,kowa ya Shiga tashi Mai numfashi Banda humaira da kayan cikinta suka kusa yowa waje atake tunanin hak'ura da zuwa yazo Mata Dan yanzu ta gaskata maganar mama habee na anba Ma'u d'an fashi babba ko d'an mafiyan ,yin duniya tace ta hak'ura ta koma gida Tana ba mama habee labari ,Mana habee harda ajiyar zuciya wai ALLAH Yana son su shiyisa suka fasa rabon Basu Gama Shan Ruwa a duniya ba ,mama habee har da fita ta Gaya ma kawayen su humaira da Ma'u masu Shiga motar Kar ashanye jinin su ,Koda ta fito har sun tafi sai k'urar motar su sai baba da yaketa binsu da kallo da Addu'a ,sai ko mama habee tayi k'wafa tace shikenan Ma'u sai wata bake ba ,ta Harare baba ta dawo ciki.... Maman shaheed ce😘 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AB* (Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg 28 Humaira tsiru a gida ita daama habee Tana tunanin Ma'u da masu kaita ,mama habee ta dawo gida Tana Addu'a ALLAH yasa acinye kayuwan masu gulma da gani kwaf ,da Abin ya Mata dad'i ,ita lo Ma'u dama haka taso azuk'e jininta kowa ya huta ma . Ma'u sosai take kuka Wanda ya k'unshi abubuwa da dama ,ga rabuwa da baba ga Auren umarni ga rashin 'yanci ga na Rashin uwa ko danga managarta komai ma Tana tunanin ta Rasa itakam arayuwar ta ,Kuma farin ciki ta 1 tal wato baba ,gashi yau da hannu ya bada ita ga inda Bata sani ba wanda tamai suna da auren umarni ,Wanda ta Jima Tana tunani da sak'a2 akai da ace mama habee ce ta Mata Haka da ko shakka Babu ta kwammaci barin gidan akan ta zauna ta mutu da b'acin Rai ,to gashi babane da kanshi ,biyaya kawai tayi ko ALLAH zesa k'arshen wahalanta yazo , hankalin ta baya jikinta har aka iso gidan anata Kiran sunan ta Amman Ina Ma'u batasan anayi ba wai kunu a Wani gida ,sai da Aisha ta jijigata sanan tayi firgigit ta dawo duniyar mu ,ta sa k'afa zata fito ta d'aga ido Tana so taga inda ALLAH ya kawo ta sai kuma tayi turus ,ta Fara tambayan kanta meya kawota gidan mumcy? Ko dai babane ya bada umarnin akawo Ni in Mata sallama? Kai hakane ma Inji sashin zuciyar ta ,Dan Haka da k'arfin gwiwar ta ta fito Tana Amman ankyauta Mata gaskiya ,tanason tambaya ko zata samu k'arin bayani Amman tayi shiru Dan ance Amarya ran aurenta Bata fiye magana ba ,sai kawai ta mik'ama Aisha da hafeeza hannu kamar yadda suke mik'o Mata akan ta Zo su Shiga ,Bata da zab'i ta mik'a musu suka Shiga falon mumcy .. Acike suka Sami falon da tsirarun 'yan uwan mahaifin su FU'AD wasu daga dangin Alhaji Yaya sai wasu masu yawa daga dangin hajiya babba Wanda suka ninka wad'ancan yawa ,anata ci Ana Sha ,Ana ganin anshigo da Ma'u suka Fara gud'a da murna ,atake hankalin Ma'u ya Fara tashi ga tarin tambayoyi ta Rasa Wanda zata kusanta dasu bare ya amsa Mata ,anata ga uwar gida ga Amarya can Kuma ango d'an gata gaba da baya ,sai ko Ma'u ta sake cewa meya kawo canjin bayani kuma sabanin Abin da aka Gaya mata? Baba dama yace Mata tanada uwar gida ,to Amman meya kawota Nan ko dai Yar uwar mumcy ce,Kuma Amarya naji kamar ance kodai tuntub'en harshe ne? To Babu mamaki b'arin zance ne dai, Kai tanada tarin tambayoyi ya kamata ta Nemo Mai amsa Mata ,Bata Gama tunani ba ,aka d'auketa aka kaima mumcy don tayi Mata fad'a .... Dama sanaya na can ba'a Jima da kaita ba tanata zumburo Baki cikin gyalen da aka rufe Mata har fuska . Ma'u kusa da sanayan aka ajiyeta ,sosai wata yayar mumcy datijuwa ce to manyanta ta Fara musu nasiha Tana musu fad'an su zauna lpy suyima mijinsu biyaya Kar su Bari munafukai su Shiga tsakanin su ,nasiha ta musu Mai ratsa zuciya ,daga baya ta rufe da Addu'a da sa ma Auren Albarka ,aka Kira dangin Alhaji Yaya wata datijuwa autar mahaifiyar su Alhajin ta yi nata nasihar tasa musu Albarka ,sanan akace sanaya ta zaba inda takeso kakar yadda Alhaji Yaya ya bada umarnin sai sanaya ta Fara zaba ,Aiko a yatsuna fuska da rashin ta ido tace part d'in waje zefi Mata Dan Bata gaji hayaniya ba ,sosai kowa yaji maganar har ma'u da zuciyar ta take Mata luguden tarwatsewa Tana tambayan shin waye mijin su ita da wanan Mara iya maganar? Badai iro Mai wanki da gugan gidan ba Dan tasan shine Mai alak'a ta zumunci irin na iyaye da kakanni irin nada dasu mumcy da har ake d'aukan shi Dan gida? In ba Haka ba to waye mijin su agidan ,itakam anemo me amsa Mata tambayoyinta kafin zuciyar ta, ta tarwatse ...... Sanaya aka Fara d'auka aka Kai part d'in wajen dama angyara an Kuma gyara benen saman FU'AD ,sai ko , mumcy tace ita Kuma kuyi sama da ita ai ta kwana gidan sauk'i ,k'irjin Ma'u ne ya k'ara bugawa da taji Ana cewa ta taso ,ta zata bada ita akeyi ba ,da kyar ta iya rik'e kanta Tana tafiya da kyar ,saman akayi da ita ba'a direta ko Ina ba sai d'ya daga cikin maka makan d'akunan ,wani Mai Italian bed white nd brown me kyau da shek'i ,'yan kawota aka cikasu da Abin ci na Alfarma dama tun zuwansu suke zuba kyauyan ci suke Mata murnar samun Aljannah duniya , hafeeza ma gani tayi yanzu gidan yafi k'ayatuwa ,sai Aisha itama da take ganin lalai gidan surukan aunty sa'adiya sunci sun Tara ma'udan dukiyar da har jikokin jikoki zasu iya gado dama ta sani Amman yanzu ta k'ara tabbatar wa , hafeeza ce takema Ma'u kuskus wai nifa bangane waye angon ki ba ,wani aka samu a gidan Nan sabon yaron gidan ko me da aka Mai Auren gata da ko ke baki sanshi ba kamar yadda Kika fad'amin. Ma'u tayi raurau da murya tayi doguwar ajiyar zuciya tace "kawata Adana tambayar ki har na samu amsoshin nawa Ni kwanyata ma ta jirkice ,ki taimaka ki Nemo min aunty sa'adiya matar Yaya Jameel na kaimata takardar tambayoyi na ko na fito daga duhun da aka tura ni Dan ALLAH Tana Shirin kuka ,sosai hafeeza ta rarashe ta tace to sign bansanta ba , Ma'u tace "ki tambaya za'a nuna Miki ita ,ba'a Jima ba hafeeza ta dawo tace sun had'u wai Tana zuwa . Koda aunty sa'adiya tazo , Ma'u murya na rawa take cemata "aunty nifa bansan inda nake ba ke kad'ai ce Zaki iya sanar Dani inda nake Kuma na gamsu,murmushi Mai cike da ma'anoni sa'adiya tayima ma'un ,tace"kibani wasu mintuna barinje na sallami wad'anda suka kawo ki ,sunata cewa zasu koma shine mumcy tace Nasa amayar dasu, ma'un tace toh inajiranki aunty na . Sosai su shamsiya ,hauwy da sauran su suka Zo sunama ma'u ALLAH ya bada zaman lpy Bayan ancikasu da takeaway da tsarabar biki ,anata musu godiya ,har mota aka rakasu ,sai ma'un taji kamar Kar su tafi hafeeza ce kawai ta rage tace sai taga kwal uwar daka ,daga Ma'u Amarya sai hafeeza sai Aisha suka rage a saman sai masu zuwa wai suga saman uwar gida sunata sake jefa Ma'u dogon nazari . Bayan wasu lokuta sai ga aunty sa'adiya da rakiyar Mai Aiki da kayan abinci na su ma'un ,Bayan sunci sun k'oshi Ma'u ta Fara watso ma aunty sa'adiya tarin tambayoyi ta hanata amsa ko 1 sakamakon jero su da takeyi kamar alokaci 1 takeson a amsa Mata , Aunty sa'adiya murmushi tayi tace "to wanne kikafi so na amsa acikin su? "Ma'u tace waye mijin da akace an auramai Ni? Me gadin gidan Nan ko direba? Ko iro Mai wanki? Idon ta cikin na aunty sa'adiya tanason sanin waye acikin su? Sai sa'adiya tace "Husna duk ki wuce tunanin su da sanin su ke ai matar manya ce ,da namiji Mai 'yanci da kima Kika Dace ,Suma bawai Dan ba mutane bane aa ko 1 kowa dai da abokin Rayuwar shi Suma zasu iya Auren macce Mai daraja Kuma a zauna lpy babu yadda ALLAH baya yi,Ma'u dai saurare take taji amsoshin tambayoyinta can ,sai sa'adiya tace "nasan kinfi zak'uwa da son sani waye aka Baki matsayin mijin ki ? "Da sauri Ma'u ta gyad'a Kai alamun eh bakin ma be samun damar bud'uwa ba ,sai ko sa'adiya tace "Ma'u ki yi Amfani da damar da ALLAH ya Baki wajen d'orewar farin ciki da kwanciyar hankalin ki Dana duk wani masoyinki ko Mai tausaya Miki musamman baba , FU'AD shi ALLAH ya zab'a Miki matsayin miji Haka shima ya tab'a mafarki be tab'a ba ? Kece amatsayin matar shi matsayin uwar gidan shi Kuma Dan Auren ki aka Fara d'aurawa , nasan zakiji maganganu na kamar Ina watsa Miki ruwan batir ,ki bani nutsuwar ki kifahinci manufar mu Akan wanan had'in ,wacce ta asasa had'in Nan itace mumcy ,in tambayeki Zaki iya sadaukarwa ga mumcy kuwa Akan komai? Jiki Babu kwari Ma'u ta sake gyad'a Kai ,Bayan mamaki ,tsoro ,tashin hankali ,fargaba da duk suka dirar Mata tunda akace FU'AD ne mijin ta ,Tama Rasa Abin yi ko fad'a , sa'adiya taci gaba da cewa toh ashawarce Babu wani abun sadaukarwa ko sakaya ko farantawa da zakima mumcy da ya wuce karb'an kyautar da ta zab'o ki ta Miki ,Dan zab'o ki tayi ta had'aki da gudan jinin ta da take so ,kin taba tunanin Zaki auri FU'AD ? Da sauri Ma'u tace aa wlh ko amafarki yanzun ma ban Gama tabbatar wa ba wlh Tana Shirin yin kuka .... Sa'adiya ce ta share Mata hawaye tace to Zaki tabbatar ranar da Kika ganshi agaban ki ,afirkice k'irjin ta ya bada daram tasa hannu ta rufe fuskar ta kamar Yana gabanta ,Tana ayyana irin tozarcin da ze Mata ,sai jin muryar sa'adiya tayi Tana cewa ,wani da Zai sa ki k'ara dagewa wajen faranta ran mumcy shine juriya da duk wani Abu da zai dinga bijiriwa daga FU'AD zuwa gareki na ,ki daure ki share matuk'ar babu cutuwa ko tozarci ,Dan shima irin biyayar d kikayi ita yayi aka had'a Auren ku,Kinga ko shi namiji ya hak'ura ma balle ke mace? Sai ko Ma'u tace au dama Auren Dole aka Mana gaba d'ayan mu ? Sai Jin muryar sa'adiya tayi ,nasan Zaki ce Auren Dole aka muku kenan? Sai ko Ma'u tace shikenan Abin da nakeson sani har ta hango kodai aunty mayyace? Sai sa'adiya taci gaba da cewa ,duk gaba d'ayan ku da FU'AD d'in da sanayan da ke duk umarni kuka bi kuka bi zab'in da iyayen ku suka muku ,Nan taba Ma'u labarin da Bata sani ba Kan Auren sanaya duk da tasan wani wani Kuma Bata sani ba sai taji tausayin kansu duk su 3 ya Kama su.... Sa'adiya taci gaba da d'ora Ma'u ahanya Tana nuna Mata sai tayi juriya da hak'uri insha ALLAH zataga ribar Auren ,Kuma Bata da matsala tunda har mumcy ce ta zab'e ta matsayin surikar ta ,Bayan ta gama Mata hud'ubar Aure da rayuwa ta koma wajen mumcy . Aisha ta d'orama Ma'u da nata hud'ubar da hafeeza suka dinga sata ahanya Mai b'illewa ,sosai Ma'u take fahimta sai tsoro da shakkar aikatawa da takeyi ,zuciyar ta fal da mamaki da tunanin ya zasu zauna matsayin ma'aurata da FU'AD? Sanaya ma tsirarun dangin dady sun tasa ta gaba sunata Mata tasu hud'ubar ,Yana Shiga Yana fita ,sosai akayi Mata iya nasihar da zasu iya da ban Baki ,mamy duk Tana Jin su . Mufeeda tun da ta gano Ma'u kishiyar aunty sanah sosai taji dad'i ,Amman ita sanayan Bata sani ba ,Dan har ziyara ta Kai Mata suka had'u da Aisha ,sunata hira Abin su. Itako sanaya Banda takaici Babu Abin da takeji gashi samarinta na Egypt sai Kiran ta suke wai ya zata musu Haka sunga k'awarta summy tasa a statun wai Ashe rabon aure ne yakai sanah 9ja . Tun Sana na k'aryatawa Tana Basu amsa har abun ya Fara kular da ita Dan Haka ma ta kashe wayan ta ta jefa jaka kawai taji da zafi 1 ..... Mamy dai lalab'ata takeyi Tana tambayan ta abubuwan da take buk'ata amata ko ta hak'ura tayi zaman Auren da kyau duk da mamyn ma k'arfin ta dady yafi ta hak'ura da auren ,duk irin lalamin ma mamy ta Mata tak'i fad'an son ranta sai kalamai masu kaushi da take fesarwa ga mamy da dadyn nata Akan Auren ,sai dabara ne ya fad'o ma mamy tace "yauwa baby wane mota kwanaki kikace dadyn ki ya canza miji ma fad'amin model d'inta insa asai Miki ,sai ko sanah ta juyo ayatsune tace hmmmm a 9jan za'a zamu motan mamy ,Tana Mata kallon tuhuma da rashin kunya , "sai mamy ta Mata dakuwa tace "Dan uwaki dan ubanki me Kika d'auki tushen iyayen naki ko kin manta ne na tuna Miki? Sai ko sanaya ta yarfar da hannu take aa mamy ban nema ba ,ban nemi sani ko ji ba Wanda na sani abayama is ok ,nidai ba 'yar 9ja bace jibiyana na foreign country ,Kinga tushen mu daku da banbanci ,sai ko mamy tace Dan ubaki aidai Wanda suka haife ki kike fad'ama Haka wawiyan yarinya kawai duk motan da kikeso Akwai anan bana son karya mutunci k'asa ,ki fad'amin sunan ta Nasa dadyn ku ya siya Miki sanan in kina da ra'ayin fita Aiki sai kiyi magana anema Miki Mai kyau Wanda Rana beze dinga dukanki ba Inji dadyn ki ba injini ba ,muna sauraren ki ,mamy ta tashi ta fice Bata jira amsar sanayan ba . Sanaya tunani ta Shiga yi Akan siyan motan da yin aikin ko barin shi ,daga baya tayi tunanin bazata Sha wuyan banza ba Akan wasu 'yan kud'ad'en da befi Tasha Mai amotan ta ba a wata amatsayin Albashin ta ba ,Dan Haka babu aikin da zatayi kawai asai Mata motan ko Shan iskan ta dinga fita da motan da su zuwa saloon .... FU'AD sunata magana da B2k Akan ya zeyi da Mata biyu yanzu gashi kowa ta d'auki part d'inta sai ya raba musu kwana ,sai ko FU'AD ya Galla Mai harara yace ,Kaine kwanan ai me zanyi da kwanan balle na raba shi ? Abarshi a had'e Mana shi kwanan Yana Jan wani gajeren tsaki ,sai ko su B2k suka bushe da dariya ,sukace wlh Dan air ne Kai abokin mu ,Dole fa kaba dakai bori ya hau ahaka zaka samo Mana jikokin Wanda mumcy zata kalla taji dad'i? Sai ko ya kale su yace "Aiko bazata zamu ba Dan bani nace su jona min kowa ba acikin su ,ko suba kansu babin har Mata 2 sai kace noma zasu min . Sai ko Ahmada abokin shi yacce eh Mana noma zasuma da taimakon ka ....be karasa ba FU'AD ya dakatar dashi yace d'an air Banda time d'in batawa Akan wanan Auren ki rabu Dani ,badon sun so ba sai Dan ganin FU'AD ya fututuke ,suka canja Hira . Yamma tayi gari ya Fara duhu Babu FU'AD Babu labarin shi sai Yaya Jameel ya Kira shi a waya da kamar baze d'auka ba sai dai ya d'auka ,Dan bayason Ayi Mai magana Akan matan da aka aura Mai ,sai ko Jameel yace Yana son ganin shi da gagawa a gida Dan yaga alama kunya yakeson Basu , FU'AD tunda yace Yana zuwa be k'ara cewa komai ba ,sai da ya k'ara awa 1 da rabi shima sai da yaga Kiran mumcy sanan ya ,daga be Bari tace komai ba yayi saurin cewa gab yake da shigowa gidan ya kashe wayar Yana mita Akan Auren. Su B2k nata bashi shawara da hak'uri da karb'an Auren da hannun Alkhairi . Bayan ya dawo gida ,sukayi magana da su mumcy Akan tafiya wajen matan sa ,yin duniya yace shi fa sai satin da mumcy tace zatayi gagarumin taro Akan bikin sanar shima ze ziyarci d'akin matan , mumcy masifa ta Fara Balbale shi dashi sai da Yaya Jameel ya Bata hak'uri yace abarshi zuwa ranar ai duk takusa kare wa duk abinta ,yanzu ya kakeso ayi tukunna a ina zaka kwana ma? Jameel yake tambayan shi ,sai ko yace a part d'in ku tunda kun koreni yau a sama ,Jameel yace toh jeka kwanta ganinan zuwa , FU'AD ya tashi ya fita , mumcy Dan haushi ko kallon shi batayi ba,sai Bayan ya fita ta rufe Jameel da fad'a Akan Yana sangarta FU'AD da nuna mai sai dai subishi badai shi ya bisu ba? Jameel Bayan mumcy ta gama yace "ba binshi muke ba ,kowa ya kamata abashi hakkin shi ne uwa ta gari ,kin bashi umarni ya bi kin tursasashi ya amince bafa Dan baze iya bijire Miki ba ,kawai biyaya ce tasa Haka ,to Damme kema bazaki iya Mai wasu alfarmomi ba da Basu Gaza ikon ki ba? Ki tuna fa abu biyu kike d'auka Akan mu nida shi kece uwar mu kece uban mu ,shi ko FU'AD Ina Mai hakane don in dinga tuna Mai da gata da yanayin k'aunar da Alhajin mu yake nuna Mana kafin k'asa ta rufe idon shi ,kinsan duk Abin da mukeso shi yake Mana hatta Abin da zamuci sai mun zab'a in ban manta ba munsha zab'an Miki kayan da zakisa ajikin ki don yagani yaji dad'i muna yara ,duk wanan besa mun lalace ko zama sangartatu ba saboda gata ,to damne bazamu dinga tunashu ba? Da yin d'abi'u irin nashi ba,shima fa Yana kewar shi kamar yadda ni dake mukeyi ,Kuma Yana buk'atar Kulawar mu ,yamana biyaya iya biyayya ,da wanan zamu saka Mai muma ,sai ko mumcy tace shi kenan na fahimce ka , ALLAH ya nuna Mana ranar lpy .... Kwayen Ma'u da humaira sun koma gida da su hafeeza da mamanta ,kawayen su humaira sun korama humaira labarin gad'uwar gidan Ma'u da irin daular da ta samu ,sai ko mama habee da humaira suka tsure mama habee ba'cin Rai ne ya turnuk'eta Amman Tana sake Mata Addu'a ALLAH yasa d'an mafiya ne ,tun da suka tafi humaira take zirgilon son zuwa ,gashi Basu sanar Mata da gagarumin taron da hajiya babba zatayi ba ,sai k'arya da sukama humairan ma sukace "Akwai manya manyan karnuka agidan ,Kuma in Basu tab'a ganin mutum ba yagalgalashi sukeyi Suma sai da aka nuna Mai susanan suka Shiga ,ga sojoji marasa mutunci har pant dinki sai sun caje Kuma gate 4 a gidan ,ke gidan fa Abin tsoro ne duk suka tsorata humaira Dan sun gano hassada karasa atare da ita da Babar ta da sukema ha'un ,Aiko sosai humaira ta tsorata mama habee ta sake tabbatar wa Dan yankankai akaba Ma'u [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* _RUBUTAWA DA TSARAWA_ BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AB* (Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg 29 Sosai humaira ta tsorata da gidan Ma'u dama gata kura ga tsoro ga ban tsoro ,Amman tanaso taga shin da gaske ne Ma'u ce tayi Dace Haka? FU'AD ko takan wasu matan shi be bi ba ya Shirin kwanciyar bacci ,sai yaya Jameel ne yaje yayi sallama dasu , Ma'u da aunty sa'adiya da Aishat zasu kwana kamar yadda mumcy tayi umarni , Ma'u har kunyar had'a ido take da mumcy ga godiya da takeson Mata na rashin kyama da ta nuna Mata ta had'ata Aure da d'anta mafi soyuwa a gareta ,duk da ita Ma'u tanajin zaman su bazeyi armashi ba Dan har yanzu kallon mugu azzalumi take Mai ,sanan Kuma Tana ganin intayi ma mumcy godiya kowa ze zata Tana farin ciki ne da aka Bata FU'AD matsayin miji zasuga kamar nunawa take tafi kowacce macce sa'a a duniya ,dad'i ne yasa ta fito har take godiyar ma ,Dan Haka ta Adana godiyar ta zuwa lokacin da ya Dace . Su Harri Aiki ya musu yawa sunata d'auki zuwa ganin Ma'u matsayin surika cikin gidan hajiya baba Abu kamar a mafarki ,tunda labari ya same su suketa jijuya lamarin har me gadi da masu wankin gidan da duk wani ma'aikacin gidan . Ko da Harri ta kawo musu abinci sukayi tozali da Ma'u sai murna take yima ma'un da ,itako Ma'u har tallabo Harri takeyi Tana tambayan ta sauran ma'aikatan gidan ,duk Harri tace suna Nan lafiya suna tayata murna zama surikar mumcy ,murmushi ma'un kawai tayi ,suka d'an tab'a Hira da Harri kafin Harri ta koma aikin ta. Sosai su aunty sa'adiya suke d'ora Ma'u Kan hanyar samo Kan FU'AD ,suna nuna Mata k'iyaya ko gani Bata Isa zama matar shi ba duk ta ajiye tayi biyayar Aure kawai , inhar tayi da sannu zataga ribar Abin ,tunda abune Babu Wanda ya kwana da sanin shi ,ko ita mumcy bawai ta had'a don dama can da Abin Aranta bane ,zuwa yayi kawai batare da kowa ya sani ba ,Dan Haka Dole ku d'auki na anabawa hak'uri ,kubi umarnin Wanda suka had'a Abin ,sosai Ma'u take sauraron aunty sa'adiya wani abun Tana ganin zata iya wani ko Tana ganin Ina badai ita ma'un ba ,Haka har bacci yayi gaba dasu . FU'AD dai ya tare wajen yayan shi kamar yadda mumcy ta maida sa'adiya wajen ma'u Haka mufeeda take Taya sanaya kwana a part d'in ta Dan dama Akwai komai gyara wasu abubuwan akayi ,kwanaki sunata tafiya har gobe ake Shirin gagarumin taron biki da mumcy ta had'a don Taya d'anta Aure duk da ba Haka taso bikin yazo Mata ba yadda taci burika a Auren autan nata ,Amman Babu yadda ta iya yanzu ma Dole ta nuna farin ciki ta Dan tabada umarni Kuma ambi ,Dan Haka ta gayyaci mutane sosai ,duk wani Abu da za'aci ko asha ko na kyauta ta gama dasu Dan order ta bayar . Washe gari da safe ranar taron ,Wanda FU'AD d sanaya har ma'un ba wani matsanaicin farin ciki ,kowa yak'e yakeyi . Tun safe aunty sa'adiya tasa Husna tayi wanka ta turare ta da turaren wuta na jiki Mai dad'in kamshi dazo ta turare Mata kayan da zata saka wani leshi da mumcy ta siya musu har sanaya Amman Akwai bambancin kala sanan ,ta Bata wasu turaruka Dana jiki Dana Kaya tace ta feshe jikinta dasu sanan tasa kayan ,d'an kwalin kuwa ta Bari Aisha tazo ta nad'a mata,sosai Aisha ta gyara Husna ta fito cas da ita ,sukaje suka kwashi gaisuwa wajen mumcy ,Sana da rakiyar Aisha sukaje gaishe da mamyn sanaya har wajen sanayan sukaje batare da sanaya taga fuskar Ma'u ba ta amsa gaisuwar a wulak'ance suka koma part d'in su Yaya Jameel don gaishe su ,Yaya jameel kawai suka gaisar FU'AD ko tashi abbaci beyi ba Dan Haka suka koma saman da suka baro . Biki yayi biki FU'AD Dan Dole ya shirya da taimakon su B2k ya saka wani arnen yadin shi Mai tsada da laushi yamasa kyau kamar danshi akayi yadin ga hular shi da ya kafa tangaran ta had'u da yad'in sai basarwa yake irin bikin ba akanshi yake ba da Ayi da Kar ayi duk 1 gara ma Kar ayin badan mumcy ta dage ba . Sanaya ma da masifar dady da na mamy ta samu tasaka leshin da mumcy ta d'inka musu ,ba wani kwaliya tayi ba Dan tace bataga Abin kwaliya a Auren ba ,dama ba gwanar kwaliya bace ,Amman kayan sun amsheta duk da dama tanada kyanta dadai nata . Sosai gidan ya d'inke da jama'ar mumcy da ta gaytata ciki har da su hafeeza da kawayen su Ma'u da humaira da suka zage jiki suka dawo don aci uwar sabada da su ba tare da sanin humaira ba Dan da sai ta biyo su . Sosai suka gwabji arziki sukaci suka Sha harda guziri suna k'ara yaba sa'a da Ma'u ta tabka . Ma'u sai da ta canja Kaya kusan set 5 sanaya ko d'akyar ta canja 2 sai da mamy ta dinga had'ata da dadyn ta sanan. FU'AD ma da taimakon su Ahmed da masifar da Yaya Jameel ya Mai yasa ya canja kala 3 .... Sosai akasha taro da su gabatar wa har had'a ango da matansa sai da akayi fuskar Nan ta FU'AD Babu annuri Sam acikin ta ,sanaya ko fuskarta fes take kallon kowa duk da Babu ko alamun murmushi itama , Ma'u ko Babu Mai ganin fuskarta ma bare yacce idon ta k'iri da muzu Akan jama'a ,Dan Haka mutane suka dinga Mata shedar tafi amaryar kunya da kamun Kai ,karaf a kunnen mufeeda da mamy Dan Haka mama tayi saurin yima sanaya sakwan karta kwana a wayar ta Akan da bi al'ada ta rufe fuskar ta ,Amman Sana tayi burus da maganar mamyn ,sai magana mamyn take Mata da ido harda nuni da hannu ,sai ta mayar Mata da itafa zafi take ji weather Akwai dumi na 9ja bazata takura kanta ba ,Haka Dole mamy ta rabu da ita . Sosai bikin yayi armashi don anyi nasiha anyi jawabi Akan zaman Aure da biyaya cikin Auren , mumcy tasa FU'AD yima mutane godiyar Dole na hallartan taron da sukayi na shi shida matan shi daga k'arshe ya musu fatan komawa gidajen su lpy badan yaso hakan ba sai Dan bin umarnin mumcy Dan yaga ranta ya baci sosai ne . Sosai taro yayi armashi ar mutane suka Fara watsewa mumcy nata Basu Abin da ya sawak'a da musu fatan Isa gida lpy . Su Kuma kowacce ta koma inda yake mallakin ta amatsayin ta na matar FU'AD . Kowa ya watse gida ya rage daga 'yan ciki sai tsirarun bak'in mumcy . K'arshen tika tik yau dai ta faru ta k'are ,yau ne FU'AD ya d'auki Al'k'awarin karb'an sanaya amatsayin matan shi ,Dan Haka ranshi yau yafi na Koda yaushe b'aci gashi babu gudu babu Jada baya ,Dan Haka tun wuri mumcy da Yaya Jameel suka Fara Mai tuni uwa uba Alhaji Yaya da Yamai magana shima ,sai ko FU'AD yace ya sani .... Mamy ce taje tace ma sanaya y takeso a raba kwana? A Fara da ita ko afara da Husna kamar yadda taji suna Kiran ta? Sai ko sanaya tace suje can su k'arata Ni ko bezo ba daidai ne agareni sai ko mamy ta rufeta da fad'a Tana cewa ya zata dinga maida kanta ba duk Abin da ya biyo baya ita ta sani Kar tayi kuka dasu sunyi iya yin su wajen kwato Mata 'yanci Amman har yanzu tak'i ganewa ,Dan Haka saura ya rage nata ,ta fice taje tacema mumcy FU'AD ya Fara Shiga d'akin Husna kawai ,sai ko mumcy tace toh ,cikin ranta tace dama ai ita aka Fara d'aura mai Aure da ita Dan Haka daga kan uwar gida za'afara raba kwana ba Amarya ba Amman sai ta bita da toh kawai. Mumcy ce tasa aka Kira Mata FU'AD ta gagauta bashi umarnin kaima uwargidan shi ziyara ,da gargad'i Mai zafi Akan kartaji Kar ta gani ya wulak'anta ta ko ya tozarta ta ,ya d'auketa matsayin umarnin ta ,bin umarnin ta gareshi Kuma biyayace da sakayyar da ze nuna Mata Akan reno da Tarbiyar da tamai tun haihuwa shi har kayau ,iya tukwicin daze Bata shine karb'an kyautar da takai na auramai Asma'u ,sosai tamai fad'a Akan yin adalci tsakanin su ,Yaya Jameel ma ya k'ara Mai da rarashi da ban Baki da nasihohi masu shiga jiki ,sanan ya tafi wajen sa'adiya . FU'AD ya tashi zai fita jikin shi duk Babu kwari Kuma ya kasa tofa ko ufan ,har ya fita falo ,besan mumcy Tana biye dashi ba taga yayi hanyar waje alamun ze fita cikin dare ,sai ko mumcy tace Ina zuwa Kuma? Cikin alamun na rashin gaskiya yace "zanyi waya da su B2k ne ,sai ko mumcy tace dawo Nan kayi wayar dasu sanan ka haura sama ina gani in Kuma sallama zakaje kayima sanaya to ? Da muryar takaici yace ai na Mata sallama , mumcy tace "ka kyauta " ba shi da zab'i Dole ya d'aga waya ya Kira B2k Yana lek'awa yaga ko mumcy ta koma yaga Bata da niyar tafiya ,sai ko B2k ya Fara cemai Kai abokina yaufa ranar kace sai inda ka zab'a meye na kirana Ni ban dameka ba Kai zaka dameni Kar kasa matanka su Fara tsana ta fa suce na Shiga hakkin su "FU'AD ne ya katse shi da cewa dalla mallam Ni ka kawo min sak'on Nan Ina jiranka yanzunan ,sai ya kashe wayar ,shi kanshi besan wanne sak'o B2k ze kawo Mai ba ,Haka shima B2k tunanin duniya ya Rasa wanne sak'o ze kawo ma FU'AD d'in can dai yace Dan iskan abokina kodai k'unshin da ango yake shigar ma Amarya dashi yake nufi Dan tun d'azu nake Mai magana Yana basarwa to yanzu ya kasa shigane inaga ,barin juya mota na taimaka ma Daren angon cin shi Dan ALLAH da Amarya badan shi ba ,mutumin kawai ,abaka Mata biyu zuk'a zuk'a asauk'ake Amman ka tsaya kana yawa kana waskewa ,mutumin kawai . Cikin sauri B2k ya faka motar shi inda ake Gaza dakwalen kaji masu kyau da tsada ga dumi komai yaji atare da su ya siyi gud'a 2 ya hada musu da fresh milk Mai sanyi sanan ya nufo gidan su FU'AD" mumcy dai ta kafa ta tsare Tana jiran sak'on FU'AD ko zuwa ya karb'o Bata yadda da hakan ba Tana jira B2k ya shigo har ciki ya kawo Masa ya juya shima ya nufi wajen baccin shi ,sun d'an Sha jira ba laifi sai ga B2k shima be wahalar da kanshi ba wajen tsayawa Kiran FU'AD cikin gidan ya shigo kawai yayi sallama mumcy ta amsa sai B2k yaji kunyar ta da nauyin ta ya har'iye tsiyar da zema FU'AD d'in ,ya k'ara gaishe da mumcy yaba FU'AD sak'on yace shi ze wuce sai sunyi waya ko? FU'AD Yamai godiya duk da besan me B2k ya kawo Mai a matsayin sak'on k'aryan da yayi ba . Sai ko mumcy tace "maza ka haura sai da safe , ALLAH ya tashe mu lafiya ,bashi da zab'i Dole yaja Leda ya tafi saman ledar da yaso barinta ma a wajen Dan Kar yasake jama kanshi magana ne yasa ya tafi da ita duk da baya tunanin Akwai amfanin da zata Mai . Sai da mumcy taga ya bacema ganin ta har tajiyo k'arar bud'e kofa sanan ta koma nata d'akin . Koda FU'AD ya Shiga da sallama Dan Al'adar shice ko Babu mutum ciki yakanyi sallama in ze Shiga ,yaji ba'a amsa ba yasa Kai ,yaga Babu mutum a falon Dan Haka yasa Kai zuwa d'akin shi ya ajiye ledar ya fad'a gado cike da tarin tinani kala kala ,sai can ta d'an shafo ledar da B2k ya kawo Mai sai yaji dumi ,sai yace "baringa Abin da Dan rainin hankalin Nan ya kawo min ,Koda ya duba yaga dakwalen kaji namai disko ,sai ya ja gajeren tsaki ,yace "Dan iskan banza Abin dai Yana ranshi ya Gama nacin naki kulashi shine da tsautsayi yasa na kirashi shine ya aiwatar da manufar shi? Jan ledar yayi ya nufi kitchen ya d'auki 1 kazar yasa a plate y d'auki fresh milk 1 yabar sauran a ledar ya nufi inda yake hasashen anan amaryar mumcy take ,ko da yayi sallama cikin wata zazak'ar murya yaji an amsa ,har ga ALLAH muryar ta d'aki kunnen shi har zuciyar shi ,Kuma Yana tunanin kamar ya tab'a Jin irin muryar ,Amman gajartan lokaci be bashi damar tuna inda yasan ko ya tab'ajin muryar ba kawai ya Shiga ,yace kina lafiya amaryar mumcy? Ma'u ta jinjina Abin Aranta ,amaryar mumcy Kuma? Shine sunan da kamin d'an rainin wayo? Hmmmm sai tace "lafiya Lau nake mijin Mata biyu ,shima sosai ya Jin jina sunan ,zece wani Abu Amman lokacin bana tatauna wani Abu bane balle su kaiga sa'insa Dan Haka ya mik'a Mata leda yace gashinan sai da safe ,har yace bakin k'ofa ta ce "ALLAH ya bamu Alkhairi ya Kuma kaimu muna masu kosashiyar lafiya, hankalinta kwance ,sai muryar ta dinga Mai gizo yaso ace yaga fuskarta kafin yabar d'akin ,Amman in ya tuna da yadda akayi Auren sai ya fasa ,ya fice kawai zuciyar shi fal tunani ..... Maman shaheed dinku ce👌🏻 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg 30 Sosai muryar Ma'u Ta Dinga dawoma FU'AD adodon kunen shi ,gashi ya k'aryata kinen shi da cewa muryar zak'i tamai ,sai ma neman kushewa da yayi Kuma cike da son ganin fuskar mama lakiyar fuskar ,da kyar ya samu yayi watsi da tunanin da yake neman addabar zuciyar shi ,ya samu ya kwanta. Bangaren sanaya ma ,ba wani damuwa tayi da ganin FU'AD d'in ba ,sai ma k'ara tsanar shi da takeyi kamar shi yace amusu Aure tare ,sai taso tsage gaskiya sanan take Jin haushin dadyn ta da ya b'oye Mata gaskiya ,ya Kuma had'ata da FU'AD d'in kuma suke Shirin barin ta a 9ja ,wanan Abu Yana Bata takaici ,Dan Haka ma Taki Dena charting da abokanen karatun ta maza da Mata da samarinta na Egypt ,hankalinta kwance Kuma take waya dasu . Har yau mufeeda ce take tayata kwana ,'yan aikin mumcy suke Mata komai na buk'ata girki ma duk su suke Kai Mata Wanda aka girka a kitchen d'in mumcy . Ma'u ma hankalinta kwance ta kulle d'akin ta Bayan ta gama dogon nazari da waiwaye Kan Rayuwar ta da zamanta a gidan mumcy matsayin 'yar Aiki da ta karb'i *RIK'ON KWARYA* a wajen hafeeza ,har 'yar tsama ta Shiga tsakanin ta da FU'AD ,wai yau shine matsayin mijinta gata a d'akin shi matsayin Mata ba Mai yi Masa hidima ba Yana kyarata ,Tama Rasa me zatace ,Babu tunanin da batayi ba daga baya ta tashi ta canja kayan da aunty sa'adiya ta Bata ,da kyar ta saka wata doguwar Riga iya gwiwa ta zura hijab ta kwanta Bayan tayi Addu'a ,misalin 3 na dare kuwa ta tashi ta d'auro alwala tafara sallah ,Tana neman ALLAH buwayi ya Shiga lamarinta da FU'AD ya tabbatar Mata da Abin da yake Alkhairi tsakanin ta dashi ,in Babu Alkhairi Kuma ALLAH ya had'a kowa da rabon shi ,sosai ta jima Tana Addu'a Akan aurenta sanan ta koma Kan baba tamai Addu'a sanan mahaifiyar ta da su mumcy ma duk sun shigo Addu'a Tata . Sanan ta d'an kwanta akan sallayar Bata farka ba sai da taji Ana Kiran sallah asuba ta farka cikin idon bacci ta sake d'auro alwala tayi sallah asuba sanan ta koma bacci . Washe gari , mumcy ta bada izinin Ayi girki kala kala na karayar safe akai duk inda aka Saba kaiwa Amman afara kaiwa saman FU'AD sanan akai sauran guraren atambaye shi ma inda abun da yake buk'ata ma ya fad'a adafa Mai "Harri ta amsa da toh ta had'a komai ta tafi aiwatar da umarnin mumcy. Harri nata buga kofa sai da tayi kusan so 4 Tana Shirin juyawa taji motsin bud'e k'ofa sanan ta tsaya . Sai ga FU'AD ya bud'e d'aki ya fito don ganin ko waye inda yayi daidai da bud'e k'ofar Ma'u itama taji bugun ,sosai Ma'u da FU'AD sukayi ido da ido atake kowa ya shagala da kallon d'an uwan shi ,shi Yana Mata kallon tuhuma da son gano inda yasan fuskar ,ita Kuma Tana Mai kallon raini da tsoron karya gane ta ya Fara kafta Mata rashin mutunci da ya Saba Mata Dan Haka ta tsare shi da nata idanuwan Dan taci Alwashin k'in ragama wulak'ancin shi ,sosai suka shagala da kallon juna Basu ankara ba sai da suka ji anyi sallama an bud'e k'ofan dama FU'AD tun fitar shi sallah asuba be rufe k'ofan ba ,Jin an shigo ne ya dawo dasu hayyacin su kowanne ya sauke idon shi Akan Wanda ya shigo ,sai ko Harri ta sunkuyar da Kai Alamar girmamawa ta Fara gaishe da FU'AD ,cikin sakin fuska ya amsa Mata ,sanan ta koma gaishe da Ma'u Tana murmushi ..... Ma'u .....da FU'AD yaji Harri tace anan k'irjin shi yabada daram daram Yana tambayan inama ya tab'a jin sunan? Ganin tunanin nashi bashi da tushe balle makama Kuma baida lokacin tuna inda ya tab'ajin Mai irin sunan sai ya basar ya ma Ma'u wani irin kallon ya nemi waje ya zauna a kujera . Harrin tayi hanyar Kan dining zata ajiye Mai kayan karayar safen sai yace "ta kawo Mai Nan kawai " ta kawo ta ajiye tace "Akwai wani Abu da hake buk'ata? Ma'u ko ta k'ame a tsaye jira take Harri ta tafi ta gaishe shi ta koma d'akin da ta fito " FU'AD cewa yayi akawo Mai kayan tea kawai ,da sauri ta fita Dan kawo Mai ,sanan Ma'u ta samu Baki da damar ce mai "Ina kwana? Sai da ya Gama Shan k'amshin shi kafin y amsa lpy amaryar mumcy ,taji haushi Amman ta dake ta doshi hanyar d'ak'i zata Shiga "FU'AD ya dakatar da ita da cewa inada maganar da Zan Gaya Miki ,da kamar bazata dawo ba sai ta tuna Ashe fa wai mijin tane Dan wai zatace har yanzu gani take kamar ba gaske ba sanan tazo ta zauna nesa dashi kanta a k'asa tace "gani mijin Mata biyu" sosai ya d'ago ya kalleta da wani irin siga Mai isar da ma'anoni na gargad'i da tsare gida yaga ma gaba d'aya hankalinta da idanuwanta harma nutsuwar ta ba atare dashi suke ba Dan Haka ya maida kanshi k'asa Yana zuba abincin da zai CI sosayyen dankali da kwai da had'in salat Wanda yaji komai na had'i . Harri ce ta shigo bakinta d'auke da sallama ta ajiye Mai komai da ya buk'ata Wanda ta kawo Tana saurin fira daga d'akin Dan tabar amare su gurji amarcin su Kar ta shiga sha'anin su . Har yanzu Ma'u Bata d'ago ta kalle shi ba kanta na k'asa. Yaga Bata da niyar d'ago kanta gashi ta d'an Mai kwarjin Dan Haka kawai ya Fara cewa "inaso naja kunen ki Akan wasu abubuwa a zamana dake Auren mumcy kina saurarona ? Sai ko "tace kunuwa na natare dakai mijin Mata biyu" sai FU'AD ya Mata wani mugun kallo lokacin da yayi daidai da ta d'ago Kai "yace gargad'in farko ya Fara fito wa ,kiyi gagawar janye kakmar Nan ko sunan da kike gayamin tun shigowar ki gidanan ya zama na farko Dana k'arshe in bazaki Kira ni da sunana na gaskiya ba ki hak'ura kawai "sai ma'un tace sai dai na hak'uran" sai ko ya d'ago a sukwane yaga Bata ma kallon shi yace wanan yarinyar za'asha fama ya Mai da kanshi Kan tea d'in da ya had'a Mai zafi yace da yafi Miki" Jan kunne na gaba Ina Gaya Miki da babbar murya Kar ki sake ki fitar da duk wani Abu na Nan saman Kar naji Kar na gani Ina fatan kin san ta yadda akayi Auren ko? "Ma'u tace kamar Yaya karna fitar da komai ? Ina so nasan shi koman ,meye komai ? "Yana kurban tea Yana cewa komai Mana in kin gane kin gane inma Baki gane ba ya rage naki tunda dusane acikin kanki ko Kuma da wani yaren nake magana ba hausa ba nidai na gargad'e ki in kina son zaman lafiya Dani da Kuma mahaifiyata acikin gidan Nan ,Dan Haka na sallame ki in kina buk'atar wani Abu Zaki iya tambaya na buk'atar yau da kullin tundaga naira miliyan 1 har sama da Haka . Ma'u zatayi magana FU'AD ya dakatar da ita yace lokacin magana ko k'orafi ya wuce Dan Haka ta tari gaba . Sosai Ma'u ta jinjina wulak'ancin FU'AD wato sab'on game yakeso su Soma? Taci Alwashin winning a game d'in indai da ita zai gabza Dole ta aro ko k'irk'iro rashin tsoro ta jajirce Dan fafatawa da FU'AD a filin daga sanan ta tashi ta tafi Tana cewa ALLAH ya ba Mai rabo sa'a. FU'AD kamar ya dawo da ita don tamai bayanin me take nufi sai ya fuskanci Kar ta Fara Raina shi tun yanzu Bari yaja linzamin mutuncin shi wajen yarinyar Dan Haka ya rabu da ita . Bayan FU'AD ya kammala ya koma d'akin shi ya shirya ya fito cikin shiri da niyar tafiya office hankalin shi kwance ya sauka wajen mumcy ya gaishe ta yanata fara'ar Dole . Mumcy ta amsa da sakin fuska har Tana tambayan shi kwanan surikar ta? FU'AD ya Fara kame k'ame "yace Tana lafiya "mumcy tace da fatan ta karya dai ko? "FU'AD yace aa tace sai anjima bacci takeyi ma na fito banaso na tashe ta shiyisa na barta anjima wani ya haura ya tasheta don ta karya . Sai ko mumcy tace kamar ya zaka barta da yunwa Amman Kai ka karya amanace fa aka baka akace in kaci taci itama ko har ka Fara manta ginshik'an Auren? "FU'AD ya Fara Sosa k'eya Yana Shirin magana ...... mumcy tace tukunna ma Ina zaka? FU'AD kanshi tsaye yace "office " "Sai ko mumcy ta sakko daga gado ta dawo bakin gadon tace "o.....me? Au Ina kurin da kakemin kwanaki na inkayi Aure bazaka fita office ba sai ka huta Bayan hutu har alakoron zakayi? Au ko nunama duniya zakayi auren ki akama? Me kake nufi son Ni zaka tozarta a idon duniya? Daga tarewar ka jiyan Nan shine har zaka fita kabar gida yau da safe don ka sheda musu ba Auren soyayya kayi ba Dan kajamin magana ? FU'AD ya Fara inda inda Yana son yin magana don ya kare Kan shi ,ya Fara kenan mumcy ta dakatar dashi da cewa "to wlh Babu inda zaka muna Nan da Kai in Kuma ban Isa ba ga hanya Nan jeka Tama mik'e ta fice tabar Mai falo ta tafi karyawa itama . FU'AD ne ya biyota Bayan ya Gama d'acin ran shi,ganin ta hassala sosai sai da ya Bata hak'uri yace to Bari yaje su gaisa da Yaya da aunty . Sai mumcy tace ka Fara zuwa ka gaishe da dadyn ku sanan mamy sanan yayan naka sai sanaya amaryar ka kaga ta tashi lafiya sanan ka dawo ka koma ka tashi Yar mutane ta karya indai kanason farin ciki na kabi matakan da na jero ma mumcy ta jigaba da cin abincin ta . FU'AD bashi da zab'i Dole ya bi umarni Bayan ya gaishe da kowa ya nufi d'akin sanaya ranshi a dagule sai da ya buga kusan so 4 sanan mufeeda Tana bacci ne ma Amman ta taso ta bud'e Mai itako hakimar Tana ji latse latsen wayar ta kawai takeyi Kuma Tana falon . Bayan y shigo cikin girmamawa mufeeda ta gaishe shi da sakin fuska ya amsa ,da sauri mufeeda ta bar musu falon suna kalon ta wai irin tabar Amarya da ango su tatauna d'anan . Sanaya ba'a gaji gaisuwa ba sai shine yace "Tana lafiya? Ta amsa a Dole normal nake Dafatan Babu wani Abu ko? Tace na maka Kama da mabuk'aciyar wani Abu na hannun ka ko na rayuwa Kai ko na Kulawar ka ma? FU'AD yace hmmmmm da sannu dai ,sanaya tace da sannu me? "FU'AD yace in tayi wari zakiji Ni nabarki lafiya nazo dubaki ne dama bisa umarni "sai ko tace ka sanar ma Mai baka umarni ya Dena wahalar da kanshi ya barka a mazaunin ka yafi maka sauki . Sosai FU'AD yaso tanka Mata to ganin Kar ya sake ballo ma kanshi Aiki ko baccin Rai awajen mumcy gashi be Gama magance wancan ba sai ya rabu da ita kawai Amman da k'udirin seta Mata tunani da lafuza yabar d'akin ta . Bayan fitar FU'AD sanaya ta bishi da gajeren tsaki ,zuciyar ta nata hango Mata zallah kyau da cikar Haifa irin ta FU'AD Amman duk kiyayar Auren shi tasa duk Bata gani ,sai ta k'ara Jan wani tsakin ta d'auki wayan ta Kira mufeeda Tana cemata munafuka uwar magulmata sai ki dawo ai "mufeeda dariya tasa Tana ce mata to kin sallami angon naki kenan ? Sai sanaya tace ban sani ba uwar mutane sai ke kizo ki sallame shi ta kashe wayar ta batare da tajira Abin da mufeedan zata ce ba. Babu shiri FU'AD ya koma saman shi da niyar hak'ura da fita dama neman magana ne ,ya kwankwasa k'ofan d'akin Ma'u bisa umrnin mumcy yace ki tashi ki karya Inji wacce ta aura min ke in kin tashi ruwan ki in kin cigaba da kwanciya kaman Ruwa ke Kika sani nadai isar Miki da sako "ma' u Dan ta k'ular dashi sai cewa tayi to naji Dan aike " FU'AD a kufule da zai tura k'ofan d'akin ya Shiga ko ya mayar Mata da amsa sai kawai zuciyar shi ta rarashe shi Akan karka kulata kuyi sa'in sa har ranshi ya b'aci wajen mumcy Dan haka ya rabu da ita yayi kamar beji me tace ba sai ma barin wajen da yayi ya koma d'akin shi . Sai da Ma'u ta tabbatar Babu alamun motsin mutum a falon sanan ta fito Dan tasan Dole zata buk'aci abinci ,tayi sa'a ta gansu dama ita suke jira ta bubud'e taga Wanda zata iya ci taci ta k'oshi sanan ta gyara falon yayi tas sanan ta koma bathroom d'in dake falon shima ta gyare shi ta feshe da kayan k'amshin band'aki sanan ta koma nata d'akin ta gyara FU'AD da Ma'u kowa na d'akin shi in anga sun fito motsi sukaji a k'ofar falo alamun wani ze shigo ko in sunji sallama ,Amman Babu wata Hira tsakanin su Haka har wani dare ya sake yi . Yau kwanan FU'AD 3 da Aure Amman tsakanin shi da matan shi kadatan kada han ,su dady Kuma sun Gama Shirin komawa Egypt sanaya nata tsula iskancin ta sai dady ne yake zazabirar ta da masifa Akan Babu inda zata bisu da aurenta Kuma wlh yaji wani mumunan labari ranta ze b'aci ,sanaya ranar kwana tayi Tana mita adakeka a hanaka kuka Haka kawai to wlh itama zata musu Abin da bazasu so ba . Maman shaheed😍😘 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* (Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg32 Tunda FU'AD ya Shiga d'aki be fito ba sai da ya tabbatar sanaya ta bar falon Dan tun Tana mita har ta hak'ura har dadyn ta ya kirata tadinga Mai shagwaba Yana ratashin ta ,har ta gaji ta tafi kwanciya itama . FU'AD futowa yayi ya samu Abin da ze sama cikin shi ,Bayan ya k'oshi yayi Kat ya koma d'aki duk tunani ya dabaibaye shi ,ya Rasa gane wanne irin Aure yayi ko Dame zai Kira Auren da kyar ya samu bacci yayi gaba dashi ,bai farka ba sai da ya tashi ya ji Ana Shirin Shiga sallah asuba da gagawa yayi alwala ya fice masalaci don sallah cikin jam'i baya wuce shi sai da dalili. Da safe da suka had'u da sanaya shi yace Mata kin kwana lpy ? Dan yasan ba gaishe shin zatayi ba sab'anin kwanan da yayi a wajen Husna be tab'a rigata gaishe shi ba ,cikin Isa da mulki tace kalau na tashi ,Kai fa? Yayi murmushi yaji sabon salon gaisuwa" shi ma yace yadda Kika ganni ,atunanin ta ko zata gyara sai kawai yaga ko ajikin ta ,yace ALLAH Mai mutane ya wuce dining don breakfast sai da yayi Kat sanan yace "ita taci ne? "Tace lokacin karyawan ta da sauran awa 2 don Haka Kar ya damu da ita " yace shi kenan ai ba feeding d'in ki za'ayi ba " ta Harare shi tace ko za'ayi ma ai ba kowane ke iyawa Dani ba sai Wanda yakai " ko kallon ta beyi ba ya koma d'akin shi be nuna mata beji dad'in maganar ba ma ,yayi wanka ya shirya ya ce tazo suje su gaishe da su mumcy . Uwar taurin Kai tace yaje zata Zo ya tafi ya barta yaso tursasata sai ya fasa gudun Kar tun yanzu ace ya Fara takura Mata ,Amman tabas Halin sanaya Akwai gyara akansu . Bayan ya Isa ya gaishe da mumcy sun zauna suna Hira , mumcy tace yaje yaga lafiyar Asma'u sai ya sakko ya cigaba da hirar ,zece wani Abu yaga mumcy Tasha mur ko damar k'orafi be samu ba Dole ya Gama nok'e nok'en shi ya tashi ya haura sallama yayi batare da ya jira an amsa ba yasa Kai Abin shi ,Yana Shiga Husna ta tashi da sauri alamun zata gudu saboda Babu gyale ko hijab a jikin ta har tayi hanyar Shiga d'aki ya dawo da ita da cewa "Ina Zaki Kuma ba kwana nazo yi ba yanzu Zan koma nazo ganin lafiyar kine kamar yadda aka umarce Ni . Sai ko ta dawo ,tazo ta d'an rusuna tace "Ina kwana? Yayi murmushi Yana sake bambance Hali irin na Asma'u da na sanaya ,yace Lafiya ,kin tashi lafiya? "Tace lafiya Lau ya matarka? Wani murmushin ya k'ara sakewa yace Lafiya Yana sake tunanin Akan Abin da sanayan Bata tab'a yi ba kenan ,sai yaji kamar ya zauna su d'anyi Hira Yana son fahimtar yarinyar da dalilan da yasa mumcy ta aura Mai ita matsayin aure share hawaye ,sanan yanada tarin tambayoyi Kan yarinyar Wanda masu amsawar ma sun kasu Kashi Kashi ,Yana nazartan halayen ta sosai ,ganin kamar ta takura tak'i sakin jiki ta sunkuyar da Kai sai yayi tunanin Bari ya tafi ya barta ko ta Sami nutsuwa da sakewa ya Mata sai anjima har Yana tambayar ta ko Akwai wani Abu? "Tace Babu yace to sai anjima in ya lek'o "tace ALLAH ya kaimu agaishe da ita" ya juyo yace wafa? "Husna tace matar ka ta shige d'aki abinta " Murmushi yayi yace Zan sanar Mata d sak'on ki in ta karb'a to ,ya sauka wajen mumcy . Bayan ya dawo sosai mumcy ta sake Mai fuska sukayi Hira har aunty sa'adiya da Yaya jameel sukazo gaishe da mumcy ,Aisha nata tambayan Husna ,Jin tambayan yayi yawa FU'AD yace wait Ina kikasan Husna Haka ne keda ba Yar k'asar Nan ba? Sai ko Aisha da aunty sa'adiya suka kalli juna ,sai Aisha ta Fara inda inda Tana cewa a Nan gidan Mana ,sai aunty sa'adiya tayi murmushi irin ALLAH ya taimake ta d'inan ,duk FU'AD na lura da su ,yayi murmushi yace hmmmm Akwai ayar tambaya aunty na . Kafin mumcy tace wani Abu sai Jameel yace kasan fa Mata basu da wiyan sabo a mota ma suka had'u sai kaga kamar tare aka haife su . FU'AD yace da wanan Dan wanan Amman badan ya yadda ba . Ita dai Aisha cewa tayi Bari naje muyi Hira da husna ko na sakko da ita ,ta haura saman aunty sa'adiya na Mata dariya . Sosai Aisha da Husna akasha Hira har taba Bata labarin yadda sukayi da FU'AD d'azu ,Husna ta dinga dariya Tana cewa itama fa Tana so tasan danme za'a b'oye Mai Dan bazata d'auki wulak'ancin da ya Mata ba a baya , Aisha dai tace kedai kibi komai sannu a hankali Dole ma ai ze sani komai zai dedeta ,Amman fa kinyi sa'a miji k'awata wlh FU'AD na daban ne kin Gama d'auke jarumin jarumai a cikin 9ja ,Husna dai keb'e Baki Tana cewa hmmmm wai sa'a Auren da Babu shawara ko tambaya kawai had'amu akayi gaba d'ayan mu Babu so balle k'auna ? Duk Ni aka ma son Rai ma Dan ansan baze Soni ba kuma bamu da komai wlh da annemi shawarata da nace Kar....... Da sauri Aisha ta toshe Mata Baki tace "karki k'ara furta irin wanan kalaman kina nufin godiyar da zakima mumcy kenan da wanan kalaman Zaki saka Mata? "Husna ta girgiza Kai " Aisha tace takayar da Zaki Mata kenan ? Don ita ta had'a Auren ki da d'anta Abin soyuwa agareta baran Tana k'in ki ba Kuma Tana so ku had'a jini da zuriyar su Bata Miki daidai ba da ta zab'o ki cikin Mata dibu? "Husna tace aa ba Haka nake nufi ba ,Baki fahimce Ni ba Aisha " "Aisha tace bazan fahimta ba kuwa indai Akan hakane ,ashawarce karki Kuma ko kusa ko Alamar sake furta Haka akan Auren Nan ki kasance Mai fad'an Alkhairi ko kiyi shiru zakiga Abin mamaki cikin aurenki da FU'AD insha ALLAH ,wace zata zamu kamar FU'AD tafara k'orafi ko Auren Dole aka Mata dashi ? Tab jarumin jarumai ne fa? "Husna hmmmm kema dai ALLAH ya Baki jarumin jaruman Nan " da sauri Aisha tace na Ghana ba" suka sa dariya "Husna tace itama matar tashi ai ko damuwa dashi batayi ba kamar yadda be damu Dani da itan bama kina hango Mana zama na soyayya ko na k'aunar juna ko Nan gaba ahakan? Aisha tace Kwarai ma kuwa da yadda ALLAH ki rubuta ki ajiye mahak'urci mawadaci ,maganar matar shi Kuma ki ajiyeta gefe iya Ruwa fidda Kai ,nifa banason firta maki wasu abubuwane Dan Ni fa Akan kishi ko kishiya inada k'azamin kishi har Addu'a nake ALLAH ya yaye min ,keko Naga Abin naki da sauki ,kuma hakan nada kyau Dan mazan yanzu sai dai abarsu wlh ,Amman nidai nafiso ki nemi soyayyar mijin ki da k'arfin ki da 'yancin ki da kanki basai wata uwar miji ko wani yazo ya karb'an Miki ba ,wallahi ki tashi tsaye zakice na Gaya Miki , ALLAH ya kashe ya Baki ba kud'in da yake dashi bane Abin dubawa ko so ba dukiya daban so da k'auna daban in takai ce Miki ma Babu Abin da yafi kulawa da zaman lafiya dad'i acikin sha'anin Aure ba duk da banyi ba Ina tare da wad'anda sukayi Kuma suke Jin dad'in hakan ,Dan Haka hajiya ta ki dage ki karb'i soyayyar ki kawai ,husna dai dariya tasa Tana cewa ALLAH yasa mu Dace to" Aisha tace Amin . Bayan sun Gama Hira suka sauka k'asa suka samu sai mumy da Yaya Jameel da FU'AD ,aunty sa'adiya ta koma sashin sanaya wai zata tayata Hira Kar ace basa kula da amanar da aka barmusu , mumcy dai murmushi tayi tace hakan nada kyau ,su Aisha na Jin Aunty sa'adiya na wajen sanaya Suma suka tafi , mumcy tayi murmushi tace ALLAH ya tabbatar min da dawamamen zaman lafiya cikin ahalina Wanda ze zamar min matsana ALLAH ya nisan tamu dashi " su FU'AD suka amsa da Amin. Husna , Aisha da sallama suka Shiga part d'in sanaya anuty sa'adiya na zaune Tana Taya sanaya Hira Tana amsawa kamar Dole tanayi tana danna wayar ta Alamar charting takeyi . Tun da ta d'ago suka gaisa da su Husna Bata k'ara kallon su ba ,sai da Aisha ta gaji da zaman shirun sanaya ta barsu yasu yasu suna hirar su sai tace "aunty Sana ke mukazo tayawa Hira fa Amman kin barmu munatayi mu k'adai ? Sai sanaya tace " ayya sorry wallah mutanen Nan ne suke d'auke min hankali sorry Ina zuwa ,ganin Abin bana k'are bane sai Aisha ta tashi ta k'arbi wayar sanayan Tana cewa mugansu suwaye ne suka Hana 'yan uwa hirar zumunci bakije wajen mumcy anyi dake ba mun biyo ki nanma kin barmu munatayi mu kad'ai ,suna cikin haka sai ga FU'AD ya shigo bak'in shi d'auke da sallama da sakin fuska yasan su aunty sa'adiya na d'akin ,Yana shigowa Husna tace Aisha muje ko ? Sai ko FU'AD yayi Mata wani irin kallo Mai sigar rarashi Dan yaga su aunty sa'adiya "yace Ina zaku ? Tayi shiru ta sunkuyar da Kai " sai yace kuyi zaman ku Nima Ayi hirar Dani ya nemi waje can gefe shi kad'ai ya zauna Yana kallon makeken TV dake manne a falon Aisha rik'e da wayar sanaya sai cewa tayi laaa ,aunty ai Baki da enough charge ma? 43% fa? Barin sa miki ,ko amsa Bata tsaya jira ba ta tafi ta saka Mata wayar a caji ta dawo ta Fara janta da Hira sunayi suna kalon TV ,sanaya a Dole ta Fara amsawa Aisha hirar duk ta Haka tanayi tana Shan qamshi . Shi ko FU'AD sai Satan kalon Husna da sanaya yake , Aisha na kalon shi ,suko Basu San ma yanayi ba ,ita dai Aisha ta Rasa me yakeson hangowa atare dasu tanata kalon shi ,shima besan Tana lura dashi ba . Sanaya adole take hirar har aunty sa'adiya take cema sanaya Bata Jin wani iri da zaman kad'aicin da take? "Sai sanaya tace aa ai ta Saba indai itace Bata son damuwa wani lokacin ,suko mutane indai zaka zauna acikin su wani lokacin Akwai damuwa a tare dasu " sai ko maganar ta tsayama Husna a Rai tace au yanzu mu damuwa ne kenan da mukazo tayaki Hira? Ita kanta Husna batasan ta furta hakan ba . Tambayar Tama kowa daidai har FU'AD yace yauwa Ashe kinada zurfin tunani karamar cikin su ,sai ko sanaya ta dafa kafad'un Husna tace "ayya sorry ba nufi na kenan ba ,banyi Dan ku ba ,bakiji ba nace wasu kema kinsan Akwai irin wad'anan mutanen ai kiyi tunani Akan magana ta ,sai ko Aisha tace hakane ,Amman Nima nayi tunanin ko mune damuwar ,Yaya Jameel ne ya musu sallama yace sa'adiya tazo mami na kuka ,da sauri Aisha ta mik'e Tana cewa ayya my daughter Zo in ji dalilin kukan" sai ko Jameel yace ai Tana wajen mumcy " da gudu Aisha ta tafi d'aukan ta " Jameel d'in yabi bayanta ,sanan sa'adiya ma Tama sanaya sallama ta tashi ta tafi Tana cewa uwar Mami kamar tanada Abin Bata ,suka bar sanaya da Husna da mijin su . Sai Bayan sun fita Husna taji me ya hanata rigasu fita? Ji take kamar k'asa ta tsage ta nutse Dan kunya da nauyin FU'AD har sanayan ma ji tayi tana Jin kunyar ta ,sosai FU'AD ya Sami damar k'are musu kallo ,tun ma'un na d'ago ido su had'a ido har ta daina d'agowa ,shi kanshi yasan kalon yayi yawa Amman shi yabarma kanshi sanin dalilin kalon . Sanaya ce ta mik'e taji wayar ta na ringing ,ganin mufeeda ce take Kira da sauri ta d'aga tace ,sis nayi fushi dake dady be Gaya Miki ba? " Mufeeda Dace ayya double sorry blood sis ,dalilin Kiran kenan Dan na wanke kaina ma ,so ya kike ya 9ja ? Sai sanaya ta yamutsa fuska gata munata hak'uri har hak'urin namu na neman k'arewa , daga FU'AD har Husna sai da kowa ya saci kalon ta , itako ko ajikinta . "Mufeeda tace to ya mumcy yasu FU'AD ? " Sanaya gashi can " sai mufeeda tace Kai aunty Yana lafiya na tambayeki fa? Sai sanaya tace uwar tsari lafiya Mana yake tunda kikaji nace Haka" sai mufeeda tace Masha Allah" Ina Husna fa? Atsorace ta tambaya "sai ko sanaya tace gata Kar kice itama ban Baki amsar da ya Dace ba ki tambayeta lafiyan ta da kanki kin hutar Dani tafinta ,sai ta karama husna waya a kunne tace ga mufee na magana . Husna fara'a ta d'anyi tace mufee ya kike ya su dady da mamy? Cikin Jin dad'i da farinciki mufee tace lafiya suke wallahi. Husna tace ki gaishe min dasu Dan ALLAH . Mufee tace insha ALLAH. Husna ta ba sanaya wayar ta Tana Shirin tashi zata gudu sai FU'AD yace "Ina zuwa ? Da sauri tace wajen mumcy" sai yace barin raka ki ya taso yace ma sanaya Ina dawowa " hannu kawai ta d'aga Mai alamun toh saboda Tana waya . Tun lokacin da Husna take waya har Tana tambayan su dady sai yaji ta gama birge shi duk da har yanzu haushin dadyn yake ji ,sanan itama bawai Dan ALLAH yake son rakata ba Dan ya tambayeta inda tasan mufeeda har suka San juna Haka yake son ji daga gareta. Suna Fara tafiya yayi murmushi yace ya take sauri? Tace Babu komai " sai yace Husna a Ina Kika San mufeeda Haka har Naga kun zama 'yan uwa? Sai ko tambayar tazo Mata a bazata ,Amman ta dake "tace a Nan gidan Mana kasan mu Mata bamuda wuyan sabo " FU'AD yace hmmmm najima inajin wanan" cikin kwana kalilan har kuka Saba daga zuwanki gidan? Sai ko tace eh Mana Kuma ai na tab'a Jin labarinta wajen mumcy ,yace hmmmm ALLAH ko? "Husna taga alamun be yadda ba Dan Haka take sauri su Shiga falon mumcy ko ta huta da tambayoyin FU'AD. Gab da zasu Shiga ya cemata wai ma ya alak"arki da mumcy ne Asma'u ko Husna wanene na gaskiyan ne? Sai ko jikin Husna ya Fara rawa tambayar 2 zuwa Mata tayi , kafin ta bashi amsa sai ,Yaya Jameel ya fito ya tare shi Yana Mai magana ,da sauri sauri Husna ta samu ta gudu ,gudun Kar ya Kuma ritsata da tambayar shi ta zauna wajen mumcy tasan be Isa yaci gaba da tambayar ba . [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg33 Bayan Yaya Jameel d FU'AD sun Gama hirar da zasuyi ,sai suka koma wajen mumcy gaba d'ayan su ,suka sami Husna sunata Hira , FU'AD yanata Satan kallon ta ,itako ko kalon inda yake Batayi ba sai Hira suke da mumcy. Abin ya ishi FU'AD yaga mumcy taba Husna nutsuwar ta sunata Hira "sai FU'AD yace mumcy nifa bakimin bayanin Kan Asma'u uwa tagari da yadda muke alak'a ko nasaba ......be karasa ba , mumcy tace kaji daga baya Kai dai ka kula da matanka kasani amanace su agareka ,sai mumcy ta k'ara da yimai wa'azi Mai ratsa jiki da Haka ta bagarar da zancen ... Sanaya ta zauna Tana ta latsa wayar ta , FU'AD ya shigo ya Mata sallama ,ta amsa sama sama ya zauna ganin hankalin Yana ga wayar ta ,ya tashi ya barta y koma d'akin shi . Wasa Wasa sai da FU'AD ya shafe sati 2 shi a gida da matan shi tare da tursasawar mumcy . Dan Haka yau da wuri ya shirya ya Fara Shirin tafiya office Dan har wani farin ciki yake yi ,Haka Bayan ya Gama shiri Yama sanaya sallama be jira amsawar ta ba ya nufi inda mumcy take ,ya gaishe ta yace ze tafi office da sauri da zumud'i ,har ya fita yayi hanyar waje mumcy ta dawo dashi da cewa yaje su gaisa da Asma'u ,a Dole yaje suka gaisa yake tambayar ta lafiyar da ,ta amsa da Babu matsala yanayi Yana Satan kalon ta har yabar dakin har yabar d'akin . Bayan ya fita Asma'u ta koma wajen mumcy suka Sha hirar su . FU'AD ya koma fita office yanata aikin shi hankali kwance ,matan Kuma ya raba musu kwana kowacce Yana Mata kwana 2 . Aunty sa'adiya da Aisha suna yawan zuwa suyi Hira da Asma'u ,suna d'an lek'a sanaya ba sosai ba Dan har yanzu tak'i sakin jiki da su . Da FU'AD yayi biris da son sanin wacece Asma'u ,Amman ayanzu da gaske yake son sanin asalin ta da alak'ar da ke tsakanin su musamman inya ga Tana Mai Kama da wacce ya tab'a gani a status d'in aunty sa'adiya ,Abin haushin shi ya Rasa dalilin da yasa be ajiye hoton ba da ya tantance ayanzu ,sanan Tana Mai kama da wata wacce be San kowace ba har yanzu . Yau kwanan Husna ne Dan Haka kafin kowa yaje ya kwanta FU'AD ya Kira Husna yake tambayar ta asalinta da yadda suke da mumcy ,sosai Husna ta kasa Mai bayani ,da ya matsa Mata tace "yace ya tambayi mumcy ze samu amsoshin tambayoyin shi ,shi Kuma yace ai yasan da mumcy yake tambayar ta Dan hanka ya zama Dole ta fad'a mishi . "Ita Kuma tace be zama Dole ba indai a bakin ta yake son sanin ko ita wacece ,ganin da gaske yake ta ci Alwashin ko me zai Mata bazeji komai a wajen ta ba ,badan Tana tsoron yasan ko ita wacece bane saboda ji take ayanzu ta Kuna Bata tsoron kauri Dan ji take ta shirya ma duk rigimar FU'AD ko Dame yazo itama tazo da nata zalon ,Haka suka Kai wajen 11 dare suna Abu d'aya tak'i gayamai shi Kuma ya nace sai ta Gaya Mai ,ganin bata da niyar fad'a yace in kin shirya zama Dani Dole ki fad'a min in ba Haka kuma.........sai ya kasa fad'a yayi shiru ..... Sai Husna tace inaki fad'a Kuma me? Barin je na sanar ma mumcy gwanda ka bayyana k'udirin ka tun yanzu tun zaman mu beyi nisa ba ta sani kowa ma ya sani na gidan . Ya wurga Mata wani mugun kalo ,ta kawar da idon ta ,daga baya ma ta mik'e zata sauka k'asa alamun gayama mumcy zatayi ,da sauri yace "Ina Zaki? " "Tace wajen mumcy in sanar Mata Abin da kace tayi gaba abinta ,yaga da gaske take zata tafi ,da sauri yasha gabanta "yace Kar ta sake ta sauka ko da Wasa ,yaga Bata da niyar komawa ta tsaya Yana ta Mata magana Tana Jin shi ,yasa hannu ya kamo kafad'un ta yayi kujera da ita yace ta zauna ko taje ta kwanta ,da ya rik'eta sai da wani spark ya shige shi bayare da yayi aune ba da sauri ya dagwarar da ita Yana tunanin al'amarin . Itako Yana zaunar da ita ta tashi ta sakeyin hanyar barin falon da niyar tafiya Tana cemai kabari naje na sanar Mata Mana .....da zafin sa da nuna Isa ya daka Mata tsawa ,ta tsorata amman ta ki Bari ya gane ,yayi sauri ya saka Mata k'arfi ya kamota ,yana ji wani Abu na ysirga Mai Amman be sake ta ba sai da ya tabbatar ya kaita d'akinta ya zaunar da ita abakin gadon ta "yace wlh inta sake ta sauka a yau d'inan wallahi ranta zai mugun b'aci zata San waye FU'AD ,Yana tafiya Yana magana ,cikin k'aramar muryar da batayi zaton zeji ba tace "waye Kai Banda mugu kawai" da sauri ya juyo don Yana son tabatarwa itace tayi furucin ko kunnen sa ne Yamai k'arya ? Sai yaga bakinta kamar ba ita tayi maganar ba ,duk da Haka be yadda ba sai da ya ce mata "me naji kince"? "Tayi mursisi tace Ni? Babu Abin da nace ,ko kaji nace wani Abu? "Kwafa yayi ya fice ya rifo Mata k'ofar zuciyar sa fal da tunanin furucin da yaji kamar tayi sai ya tuna da Ma'u _dirty girl_ sosai abubuwan ta suka dinga dawo Mai har yake neman gaskata cewa tabbas muryar ta yaji Babu shakka ,ya Jima Yana tunanin yadda zai bullo ma da mumcy maganar son sanin wacece Asma'u? Amman Yana tunanin Kar ya balloma kanshi Ruwa . Washe gari da safe Ma'u ta rigashi tashi Dan ya makara ,ta kwankwasa Mai k'ofan d'akin shi ,Bata jira fitowar shi ba ko amsawar shi ta tafi k'asa Taya su Harri aikin break ,tashi yayi ya Shiga bathroom yasan itace ta tashe shi ko magana beyi ba ,sai Bayan ya watsa Ruwa ya shirya tsaf don tafiya office ya fito yanata zuba kamshi Mai dad'in ji ,ya sauka ya gaishe da mumcy itako dama yasan Tana k'asa ,Dan Haka a k'asa suka had'u ta kasa Mai magana sai Satan kalon shi da takeyi shima Yana Satan kalon ta Yana Mata kalon gargad'i ,itako so take ta gaishe shi Amman Tana tsoro Kar mumcy tace meya hanasu gaisawa duk asama sai yanzu ,shima Dan Kar mumcy tayi zargin wani Abu yasa ya kasa Mata gargad'in da yakeso ya Mata ,Haka mumcy ta saka su a gaba har dining don suyi breakfast tare har ita ,ta aika a Kira sanaya ,sai aikowa tayi da cewa ita ba yanzu zata karya ba , FU'AD har ya tashi zeje ya Mata magana mumcy ta Hana shi ,badan yaso ba ya zauna ya rabu da ita Yana mita aranshi . Tsakanin FU'AD da Husna sai kalon kalon sukema junan su duk mumcy Bata sani ba har FU'AD ya Gama ya ma mumcy sallama ya ma Husna sallama itama tamai Addu'a wacce ba mumcy ba har shi yaji dad'in Addu'a,ya amsa da Amin ya fice mumcy na cemai Kar ya sake ya fita be lek'a yaga lafiyar sanaya ba ,yace to ya tafiyar shi ko bi takan sanayan beyi ba Dan ta k'ular dashi akan kin zuwan da mumcy tasa Ayi Mata Taki zuwa wato ta Raina Mai uwa tagari Dan Haka yaki zuwa inda take shima . Sai Bayan sun Gama har Asma'u ta koma saman ta ta gyara Rana ta farayi Bayan su aunty sa'adiya sunzo sun gaishe da mumcy sun tafi sanan sanaya tazo kwasan Tata gaisuwar wajen mumcy , mumcy nata janta da Hira don ta nuna Mata kulawa da son nuna Mata itama Yar tace ,Amman sanaya sai Shan kamshi take Tana nuna ba hirar takeso ba daga baya ma ta nuna k'osawar ta da hirar da mumcy take Mata har tace zata tafi don ta huta in ta gama karyawa ,har mumcy take Mata fad'an Akan ta daina Bari Rana Tana Mata Bata karya ba saboda ulcer ,sanayan tace to kawai bawai Dan ta gansu da bayanin mumcy ba ta koma sashin ta . Da Rana ma su aunty sa'adiya da su Husna a wajen mumcy suka wuni Amman sanaya ko ta lek'o har FU'AD ya dawo da yamma duk Husna na tare da mumcy da su Aisha ,ganin Husna Bata da niyar haurawa ta Sami FU'AD ,sai aunty sa'adiya tace Mata ta tashi taje tamai sannu da zuwa Mana ta rubuta Mata a wayar ta ta turo Mata Tana cewa Kinga hoton d nake Miki magana Husna ,sai Husna ta karb'a ta karanta ta kalli aunty sa'adiya Tana murmushi alamun ta gamsu Kuma zata ,sai ko mumcy tace"ya kamata a canja Miki waya kema Asma'u Bari zamuyi magana da FU'AD d'in . Sai Husna tashi Tana ce musu Tana zuwa sai ko mumcy tace "in FU'AD d'in ya huta kice Mai Ina neman shi ,da girmamawa Husna tace "to hajiya"ta haura saman bakinta d'auke da sallama ta Shiga ta same shi ya baje a kujera alamun hutawa yakeyi . Ta Mai sannu da zuwa "ya amsa Babu yabo Babu fallasa ,ita Kuma ta d'auko Mai Ruwa Mai sanyi ta bashi ,ya karb'a Yana cikin Sha tace mumcy nason ganin ka Inka Gama hutawar . Har Yana Shirin kwarewa yace me? Tace hajiya nason ganin ka ,yace me kikaje Kika ce mata ? Wani abun Kika Gaya Mata ya Mata kalon tuhuma ,itako tayi mirsisi ,ya taso kamar zai damk'eta yace ba magana nake Miki ba?taga da gaske yake sai ta seta hanyar fita Tana cewa in kasan ka firta wani Abu kazo da Shirin amsa tambaya in kasan baka shirya ba Kuma kazo hankalinka kwance ta fice ko jiran Abin da zece Mata batayi ba ta fice ta sauka k'asa wajen su mumcy . Kwafa yayi kawai Yana mamakin rainin da take Shirin Shiga tsakanin shi da yarinyar Nan ,Bayan ya canja Kaya da zeje masallaci ya sauka k'asa yace ma mumcy ya wuce masallaci yaji kiranta Yana Nan dawowa cike da fargaban Abin da akaje akace ma mumcy Dan Yana zargin kamar Husna ta furta Mata wani abune . Bayan ya dawo har ze haura sama dake mumcy Bata wajen sai Husna sai aunty sa'adiya Dan Haka yakeson gujema Kiran mumcy , sai Husna tace "ba dai ka manta Kiran mumcy ba? Yadda kowa zeji lokacin da yayi daidai da fitowar mumcy daga kitchen wajen su Harri ,sai ko FU'AD "yace oh na na manta uwa tagari gani ,Yana nufan inda take Yana hararar Husna da gargad'i Mai zafi akan Abin da tamai ,itako cikin ranta Tana Mai dariyar mugunta . Koda mumcy tace muje ta nufi d'akin ta ,sai ya saddakar yana cewa yarinyar Nan badai ta sanar da mumcy Abin da mukayi jiya ba ,har suka Isa d'akin Yana tunani . Bayan sun Shiga yaji mumcy namai magana Akan yabi sanaya ahankali ya bi komai sannu a hankali sanan ya Kama ya siyama Husna waya Mai kyau ta zamani kodan ta dinga gaisawa da mutan gidan su ,da yaji inda bayanan mumcy suka dosa sai yace to zeyi yadda take so Insha ALLAH,yaso Mata maga Akan Husna da labarin ta Amman ya kasa Kar ya b'allo ma kanshi Ruwa sai ya fasa suka d'anyi Hira da mumcy ya tashi ya fice ya tafi wajen Yaya Jameel don zasuyi magana Akan komawar shi Abuja shi kad'ai Dan aunty sa'adiya tace ba yanzu zata koma ba abarta a Nan yaje ya dawo weekend . [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg 31 Dady ya siyama sanaya mota Mai kyau da tsada duk Dan ta samu nutsuwa ta zauna a 9ja ga kud'i da ya watsa Mata a account d'inta ,shine tad'an samu ta saki ranta kad'an ba yadda zasu gane ba ,mamy ce ta tsara tafiyar Akan sai Nan da kwana 4 Ranar da FU'AD zai koma d'akin sanaya sai subar k'asar ,dady yayi naam da hakan . FU'AD dai Bata matan shi yake ba burin shi ya za'ayi mumcy ta barshi ya koma Aiki ,duk hanyar da zebi yabi karshe ma tace inya sake ya koma Aiki ba tare da ya Gama hutun 2weeks a gida tare da matan shi ko wacce ya Bata 1week ba ransa zeyi mummunan b'acci ,shine ya hak'ura ya zauna adole Yana ganin takurar tayi yawa Dan Haka ko wani dogon Hira baya had'ashi da matan . Kamar kullin Ma'u ta tashi tayi wanka ta gyara ko Ina duk da Tana matsanaicin Jin kunyar mumcy da jama'ar gidan ,ta sakko ta nufi d'akin mumcy ta duk'a har k'asa ta gaishe ta ta amsa cikin sakin fuska da fara'a Tana tambayan ta lafiyan ta da yadda ta tashi , Ma'u ta sanar Mata lafiya Lau ta tashi ,sai ga FU'AD ya shigo bak'in shi d'auke da sallama ,har k'asa ya durk'usa ya kwashi gaisuwa ga uwa ta gari ,ta amsa cikin fara'a Tana tambayan shi lafiyar shi da ta Amarya "sai FU'AD yayi sub'utar Baki yace gata Nan ai ,sai ko mumcy "tace me kace FU'AD? Da gagawa ya Ankara don yaci Alwashin b'oyema mumcy zaman da zeyi da Mata a bad'ini sai dai tasan na zahiri Dan Haka da gagawa ya saki fara'ar Dole yace lafiya Lau muka tashi da ita mumcy yanzu har Ina cemata ta jirani mu sako tace ita sai tazo da rigani gaishe ki shine na barta ,sai ko mumcy taji dad'in kalaman da FU'AD ya tsara Mata ,har tasa musu Albarka ,suka amsa da Ameen gaba d'ayan su . Atare mumcy ta umarce su day suje su gaishe da dadyn su da many har ma da sanaya . FU'AD badan yaso ba ya Fara gaba , Ma'u tabi shi a baya suka tafi Babu yabo Babu fallasa zungwi zungwi Tana bin shi a baya har d'akin dady da na mamy har suka karasa wajen sanaya in sunje wajen mutane sai su saki fuska,Koda suka Shiga wajen sanaya ciki ciki ta amsa musu sai mufeeda da take sakar musu fara'a har Tana tsokanar Ma'u har ma'un na dariya Bata yi shiru ba sai da sanaya ta sakar Mata wata muguwar harara sanan Kuma duk sun ganta Dan Haka FU'AD ya ce in Babu wani Abu zamu koma sama "a yamutse tace Babu " suka koma part d'in su suka Sami mumcy a zaune a falo Dan Haka FU'AD yaji nauyin komawa saman sai suka zauna a falon kawai gaba d'ayan su ya Fara Jan mumcy da Hira ,itako Ma'u tashi tayi ta Shiga kitchen Tana cema mumcy Bari ta gaisa da su Harri sai ko mumcy tace hakan yayi kyau. Sosai Ma'u ta saki jiki dasu Harri suna Hira har Tana neman tayasu Aiki Harri ce ta Hana shine ta hak'ura ,sai ma'un ta koma falo ta Sami su Yaya Jameel da Aunty sa'adiya sun shigo suka gaisa gaba d'ayan su sa'adiya na tsokanar Husna Tana cemata "uwar gida ran gida in Babu ke Babu gida " sanan ta koma Kan FU'AD Tana cemai "ango uwar gida da Amarya ya Naga Mata naka suna shining ne me kake Basu sukeci Haka Nima yayan ka ya siyo min Dan na k'ara kyalli ,sai ko FU'AD yasa dariya yace ki tambayi yayan nawa ai ya fini sanin abubuwan da duk ya Dace dake sai ko sa'adiya tace kaidai fad'i gaskiya ,na tambayi Asma'u dai "sai FU'AD yace to tambayeta gata Nan ,Mena Baki ? Sai Ma'u Taji kunya ta sunkuyar da Kai. Sai Yaya Jameel yace Kar ku takurama k'anwata fa kunsa ta kasa magana ,cikin barkwanci da tsokana suke ta Abin su har suka d'an tab'a Hira ,mamy na fitowa ita da k'anin sanaya sai ta zauna suka gaisa da mumcy sai ko tace yaje ya Kira sanaya Ana Nan Ana zumunci ita Tana can da mufeeda duk su Zo yanzunan ,da sauri ya tafi ya dawo yace gasu Nan zuwa ,mufeeda ce kawai tazo wai sanaya tace bacci yafi mata wanan hirar ,afusace mamy ta tashi zata Mata masifa mumcy ta Hana cikin dabara da nuna Maya maybe ta gaji ne ko Tana buk'atar hutawa abarta wata Rana ma ai basai ance tazo ba zata saki jiki ne insha ALLAH,a badan mamy taso ba ta hak'ura tabar sanayan itama daga baya ta tashi ta bar mufeeda da su aunty sa'adiya sunata hirar su hankali kwance sosai FU'AD yake noticing husna da mumcy take Kira da Asma'u ai irin sunan da take Kiran ma'ule wato _dirty girl_ dashi ne ,sanan Kuma kamar yarinyar da ya gani a status d'in aunty sa'adiya ne ,to Amman aunty sa'adiya Bata nuna Mai Tana da alak'a da wanan husnan ba sanan mumcy ma Bata Mai bayanin wacece Asma'u ba da Abin da ya shafi dangin ta ,ya zama Dole ya tambayi mumcy har aunty sa'adiya don yasan alak'an dake tsakanin su sanan shima Tana Mai Kama da wata da ya sani Amman ya Rasa gane inda ya Santa ,Amman Kuma in ya nemi sanin ta da son sanin dangin ta mumcy ko wasu zasu zata ya Fara son tane da har ya keson Jin asalin ta ko wani Abu da ya shafi dangin ta gwanda ya Bari har sai wacce ta aura Mai ita ta Mai bayani da kanta ,da wanan shawarar ya hak'ura da son Jin wacece Husna ? Wacce yaji su Yaya Jameel na kiranta da shi, mumcy Kuma na kiranta da Husna ,Amman duk da Haka zeyi maga Kan _dirty girl_. Kwanci tashi gobe su dady zasu koma Egypt Dan Haka dady ya sake damk'a amanar sanaya hannun mumcy da umartan ama sanayan duk Abin da take so duk Yana hakane da sigar rarashin sanayan ,su ko su Yaya Jameel da FU'AD takaici ne ya turnik'e musu zuciya wato ita husna ba 'ya bace tasa ce 'ya , mumcy na lura dasu togaciya take ta musu da ido ,har ya Gama bayanin shi mamay ta k'ara da nata duk suna Jin su ,taro ya watse kowa ya koma sashin da yake Banda aunty sa'adiya da mufeeda da Aisha da Husna da Yaya Jameel da FU'AD , Jameel na Hira da FU'AD ,Suma suna hirar su . Washe gari da za'a raka dady da su mamy airport wajen rabuwa sanaya harda kukan shagab'a wai Kar su barta a 9ja sauron 9ja da weather 9ja su halakata ,mamy da dady sunata Bata hak'uri suna nuna Mata 9ja ma gidane Kuma ta fad'i duk matsalanta da Abin da take buk'ata k'ofa a bud'e take ,da kyar mumcy ta rabasu ta sa sanaya a mota suka tafi , mufeeda ma tanata kewan aunty ta da su Husna da Aisha k'awayen ta har mumcy Mai kirki injita da fad'a ,sanan suka shishiga mota sai gidan mumcy cike da kewan iyayenta da ganin sun Mata ba daidai ba Dan Haka suna dawowa ta wuce part d'in ta mumcy taso tazo falon ta don suyi Hira su d'ebe Mata kewa Amman tak'i Dole ta hak'ura ta rabu da ita . Su ko suna falon mumcy wasu na Hira FU'AD ko charting yake da su B2k yanata Mai tsiya Yana tambayan shi ya Aure yake Akwai dad'i? FU'AD yanata kaucewa Yana zagin B2k shiko yanata yi Masa dariyar tsokana . Ganin sanaya shiru har yamma lis Bata fito ba , mumcy ta Kora Mata FU'AD Akan yaje ya d'ebe Mata kewa Kar yabar Yar mutane ita kad'ai ,yaso yin gardama Amman ganin mumcy da gaske take Dole ya shige ya tafi Yana matar irin Auren da aka Mai . Ko da ya Mata sallama d kyar ta amsa ya nemi waje ya zauna shiru Babu Mai magana har sai da Harri ta shigo kawo musu abincin dare sanan tace ya fito suje masalaci inji Yaya Jameel sanan ya Mata sallama da niyar zai dawo inyayi sallah ya fita . Bayan sun idar ya dawo ,yaga zaman kurumta Yama yawa sai y kunna TV sai ta Fara Mai magana ita zata kulle d'aki ya tashi ya tafi ,sai yayi murmushi Yana ayyana yarintar ta ,sai da ta maimaita so 3 sanan ya kaleta yace "Nima turo Ni akayi wai na tayaki kwana " sai tace to ka koma nagode " sai FU'AD yace Wanda ya turo Ni yanada dubun daraja a wajena bana iya ketare umarnin shi ,na barki Zan Shiga d'aki ya wuce d'akin da aka ware Mai " Yana jiyota Tana mita ita wlh bazata kwana da Kato ba kamar FU'AD " shi ko murmushi ya dingayi Dan dariya ma ta bashi . Maman shaheed😍 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) Pg34 Bayan komawar FU'AD sama ya Sami Ma'u ,ya kalleta wani irin kallon Mai isar da ma'anoni tare da tuhuma "yace karata Kika Kai wajen mumcy ? Cikin mamaki da fargaba Husna tace " me kake nufi kamar ya nakai karar ka me kayi da Zan Kai karar ka ? Ko kayi wani Abu ne? Cikin huci yace eh Mana Baki Kai bane? "Cikin Jin haushi tace nakai " ya juyo yace me Kika ce mata ? "Tace Abin da aka Gaya maka " "Yace ke ki San dawa kike magana fa ,Kar Kigya na sakar Miki ki zata na yi arahar da Zaki dinga sa'insa Dani ,ki San dawa kike magana kinji na Gaya dirty girl like you,be zata maganar ta fito ba har yadda zataji ,Aiko sai akunnen ta ,cikin zuciyar ta tace "Kai Kuma sarar ka Haka take? Halin ka beje ko Ina ba a baka gana ganeni ba Ina matarka tun yanzu ka Fara kirana da sunan ta nafi tsana da na sabaji a bakin ka ? Tace naci Alwashin duk Abin da kamin sai na Rama Nima ,Dan haka ta tashi ta nufi d'aki tace" wani na mage da Kai" ta shige d'aki tanayi Tana tsoron Kar ya biyo ta ,Bata Ankara ba taga ya kusa kamo ta ,da gudu ta fad'a d'akin ganin inta tsaya saka key a d'akin zai kamata Dan har wani huci yake tsabar takaici ya kasa furta komai Kira yake ta Shiga hannun shi ya Mata hukunci Dan Haka take son tserema muguntar shi . Tana ganin tazarar su befi taku 5 ba sai ta fad'a bathroom Dan har ya Kai Mata cafka a zafafe sai ta fad'a ta rufe ,Aiko ya ji matsanaicin haushi "yace me kikace? Sai kin maimaita Abin da kikace ,har raini ya Shiga tsakani na dake? Har ma ke wacece da Zan fad'a ki mayar min ,to wallahi ki fito ayita ta k'are Dan sai nasan wacece ke da alak'ar dake tsakanin ki da mumcy yau d'inan ,tab yarinyar Nan kinma Sami waje wallahi ,Ina jiranki ko kwana zakiyi a Bathroom d'in . Husna ido ya Raina fata tanata danasanin Bata fad'i sunan ba ,gashi Bata Dame tare Mata yau ya zatayi gashi bazata iya bashi hak'uri ba ,sai ma cewa da tayi Kai ai ka Fara Nima ramawa ai nayi . "Ya mayar Mata da cewa Zaki rame kuwa yau Dan sai kin fito kin lashe amanki da kikayi yau d'inan ,Dan daga yau nakeson datse wani raini da yake Shirin Shiga tsakani na dake yau d'inan ba tare da Ankara kwana ba. "Cikin Bayan gidan tace Aiko zaka kwana anan " "Ya mayar Mata da zadai ki kwana anan tare da hukunci Mai tsanani " Husna dai kusan mintuna 30 tak'i fitowa ,akazo 50 shiru har awa d'aya Bata fito ba "can sai tace ai nasan kana Nan bazan fito ba " Sai ko yace Ina Nan Kuma zanyi maganin taurin kanki yau batare da ankai wani dogon lokaci ba . FU'AD dai ganin Husna da gaske take gashi anyi sallah har kiranshi akayi ya amsa waya kusan so 3 gashi lokacin sallah na neman wucewa sai ya fita ko rufe mata k'ofa beyi ba wai Dan Kar taji ta fito so yake in yaje ya dawo ya dawo ya sameta Dan yau ba kwanan ta bane na sanaya ne . Itako taji fitar shi Dan Haka yana fita ta samu ta fito ta rufe falon ta da key ta koma d'akin ta rufe aciki tayi alwala tayi sallah Tana ta tunanin ya zasu k'are da FU'AD in suka had'u . "Har FU'AD ya dawo daga sallah ya Zo Yana kwankwasa Mata k'ofar tak'i budewa har ya gaji ya sauka k'asa Yana huci ,sama sama sukayi Hira da mumcy sanan ya tafi sashin sanaya ,fitar shi mumcy tasa aka hairana da Asma'u abincin ta sama kamar ta sani ,Ma'u najin maganar harrin ta bud'e k'ofar ta karb'a ta koma ta sake rufe k'ofar ,so 3 Yana dawowa amman shiru Dan har sai da mumcy taji dad'in yadda taga Yana zirya a saman ma'un Dan Bata tab'a ganin Yana zirya Haka ba Dan Tana kula dashi da duk wani shige da ficen shi . Washe gari da safe ma haka sukayi sab'ani da FU'AD ko had'uwa Bata Bari sunyi ba ,da FU'AD d'in ze tafi office mumcy tace Mai sun gaisa da Asma'u ? "Sai yace Mata eh Dan Kar ta fahimci wani Abu " Asma'u Bata sakko k'asa ba sai da ta tabbatar Babu motsin FU'AD a gidan Dan sai da ta tambaya . Yamma nayi da ta fiskanci lokacin dawowar shi ta kusa sai ta haura sama Tama mumcy sallama ,har mumcy nacewa lafiya kwana biyu inta haura Bata sakkowa? "Sai tace wai kanta ne yake Mata ciwo kad'an ,sosai mumcy taji wani iri har taba cewa ko akaita asibiti a dubata ko a Kira likita har gida ya dubata ? "Tace aa ze sauka ne insha ALLAH , mumcy tace ALLAH yasa Amman indai bai sauka ba ta Mata magana , Asma'u tace toh. Bayan FU'AD ya dawo ya Shiga wajen mumcy ya gaisheta sai ya tafi wajen sanaya Bayan mintuna k'ad'an ya dawo ,ya haura saman Asma'u ya buga k'ofar shiru tak'i bud'ewa sai da tayi tambaya "yak'i amsawa ya sake bugawa " ta sake tambaya sanan ya tace inkaine ma bazan bud'e ba yadda ka kuddiri wata aniyar acikin k'ok'on ranka Nan ,Ni ka tafi bana nemanka na yafeka ma ,Dana ba tsinanamin kakeyi ba jeka na yafe Mani ,ji yayi kamar ya b'alla k'ofar ya Shiga yanata mita Yana cewa zakiyi bayani ne yarinya zanyi maganin tsiwar kine yarinyar kawai kanki kamar na mutane kawai . Dole ya sauka k'asa ya had'a game da Harri yace ta kaima Husna abinci da drink Mai sanyi sama yanzunan shima gashi Nan zuwa ta had'a har dashi shima ze hauro ,da himma Harri ta haura . FU'AD sai da ya ga Harri ta haura ya faki idon mumcy yayi sauri ya haura yanaji Tana kwankwasawa har Tana bayanin kanta Tana bud'e Mata ta Shiga dai ya k'arasa haurawa ya shige falon ,Husna batayi aune ba sai ganin shi kawai tayi ta Rasa yadda zatayi gashi bakinta da jikinta sai rawa suke kamar mazari ,gudun Kar Harri ta fuskanta ta d'an dake ,Harri ta ajiye ta juya zata fita "Husna tace Dan ALLAH ki kawo min ragowar farfesun Nan na d'azu in Akwai ragowar" sai ko tace toh ta sauka . Shiko oga dodon Husna a yau ya kafa ya tsare jira kawai yake tazo gudu ya shad'ileta ta fad'i Dan Yana kujerar da zata sadata da Shiga d'akin ta gashi Babu Halin sauka tasan baze barta bama fad'a yajeji da ita yau ta gama fuskantar Alo tsiya Alo danja ,sai ko FU'AD ya wurgo Mata wani mugun kallo ,ganin Tana niyar guduwa d'aki zatayi zagaye ta Bayan kujera yayi kamar baya ganin ta kamar hankalin shi na Kan wayar shi ,sai ko ta zagaya tanayi Tana fak'on shi ,tazo gabda Shiga ya wani irin mik'ewa kamar wani mayunwacin Zaki ya kamota da hannu 1 ya had'ata da bango Yana ce mata haba yaushe aka haife ki ? Yaushe kikazo duniyar kici bashina ki zauna lafiya yarinya kararama kanarki ? Sai ko ta Fara Jan d'an kwalinta Tana Shirin rufe k'irjin ta sai ko ,ya Harare ta da ya fahimci manufarta yace see u wata _kwaila_ dake me Zaki tare dama kin cika ne sai ki min shamaki ko katanga to ki say ranki inuwa da sauranki kwailis . "Sai ko Husna tace eh naji mijin kwaila kawai ta murgud'a Mai Baki irin tsiwar Nan " yako shak'e bakinta yace kina hannu kina cigaba da tsiwa yarinya wai ke karamar kwaila ko? Sai Harri ta Fara kwankwasa k'ofa sai ko , FU'AD yaje ya bud'e Mata hannun shi rik'e da na Husna gudun Kar ta gudu ,tace "ka sakeni naje na bud'e Mata kaji ko mallam? Sai ko ya dungure Mata Kai yace karki kaini inda bazan fito ba ,Dan mallam sai su gafaka alagahwarta mallam ,yaje ya bud'e ma Harri ya karb'a be Bari taga rik'on da Yama Husna ,ya karb'a ta tafi ya dawo ya ajiye a Kan table . "Yace ke jiya me kikace ko ki maimaita ko kisan waye FU'AD yau " ta sunkuyar da Kai k'asa tabata k'ok'arin rufe k'irjin ta ,sai ko ya tsaya Yana k'are Mata kallo yace kin Gama rufe abun da Zaki rufe? Ko na tayaki ? Sai ko ta Harare shi tace Ni ka sakeni me nace jiyan ? Ya kalleta yace Baki sani ba? Ko tuna Miki kikeso nayi? Kina wani Jan wani d'ankwali kina son rufe wani jikin ki ke ma Kika d'auki kanki da har Zaki dinga wani kare kare, ki Bari sai kin zama mace tukunna haka batama kanki lokaci kikeyi ,ya sake shak'eta yace bazaki fad'amin ba kwailis ? Sai ko tace Zan shayar da Kai ruwan mamaki Dan d'an hakin da ka Raina ......Taki k'arasawa ,yace me kike nufi da hausar Nan,tace oho shafa kaji intayi wari ka fasa tanayi Tana tsiwa ,Aiko yace Ni kikema rashin kunya kina had'ama kanki laifufuka Baki sani ba ko ,sai da ya had'ata da bango yace bazaki fad'amin ba? Sai da Husna taji wiya tace ,abinda kaji nace Mana ,ya sake matseta duk da yanajin wani yanayi me wuyar kwatantuwa Amman yanajin baze iya saketa ba dan so yake ya magance Mata taurin Kan da yake tatare da ita ,tun kafin ta Raina shi ,ya sake cewa a Ina kikaji sunan Nan? Tace oho ka sakeni nidai ,yace sai kin fad'a min ,sai ko tace ai ko zamu kwana anan Dan baxakaji ba .....Bata rufe Baki ba ya matse bakin Yana cewa bakin Rashin kunyar Zan ragargaza inga Wanda zeyi Amfani Gobe ,sai ko ta fuzge bakinta . Ya k'ara had'ata da bango Yana cewa bazaki fad'amin ba uwar masu taurin Kai ? Tana Jin zafin Amman Taki fad'a ,sai da ya k'ara had'ata da bango ta fahimci mugunta yake Shirin mata ,sai tace oho nace maka mugu kawai Tana Shirin yin kuka ,yace waima ke wacece tukunna? Ki fad'a min Dan yanzu ya k'ara tabbatar da zargin shi Akan yasan me irin muryar da salon maganar Ganin Bata da niyar yin magana ,ya cillata Kan kujera Dan Abin da yakeji Yana nema ya kasa controlling kanshi yace wallahi in Kika sake rufemin kofa sai ranki ya b'aci Ina dawowa yanzunan wajen mumcy zani .......fuuuuuu ya wugarda da ita kujera ,ya sauka wajen mumcy. Yana sauka ya samu mumcy na d'aki ya Fara tambayar harri kitchen cikin rashin fara'a Yana cemata me ta sani game da Husna ? Tayi shiru sai da ya sake cemata nace me Kika sani Kan Rayuwar Husna Kuma wallahi in Kika fad'a min ba daidai na had'a da Wanda ta fad'amin na gaskiya zamu samu sab'anin da bamu tab'a samu dake ba ,Dan ta fad'amin gaskiya Kuma har tace na tambaye ki ,Jin Haka sai taji abun yazo Mata gidan da sauki tunda har Husna ce ta Fara gayamai tasan hajiya babba ma ta Gaya Mai Dan Dame bataga Amfani ko hikimar b'oyewa ba Dan Haka tace Mai " to ai Babu wani abun da zance maka tunda sun Gama bayani ,kawai dai itace wacce ka sani Ma'u wacce ta zauna anan kasan ,tun Bayan tafiyan ta Abuja bamu had'u ba sai da aka kawota gidan Nan a matsayin matarka wallahi kaji nama rantsuwar musulmi .... Sosai FU'AD ya fusata yana hucci yabar kitchen d'in ya tafi a fusace ......... [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg35 Sosai FU'AD ya fusata yana hucci kitchen d'in ya tafi a fusace ya doshi wajen mumcy fuskar Nan ko annuri babu. Yana zuwa k'ofar d'akin ya buga kafin ta bashi izini ya Shiga Yana Shiga mumcy ta ga yanayin shi da hanzari da nuna kulawa ta Fara tambayan shi ko lafiya ta ganshi Haka? FU'AD shiru ya Mata sai goron numfashi da yake saukewa gami da hucin takaici. Sai da mumcy ta sake Mai magana ,sanan yace "mumcy ya za Amin Haka Dan ALLAH Dan Annabi ,wanne laifi na aikata mafi girma da hukuncin shi yayi daidai da Abin da akamin irin Haka batare da Yana kallon idon mumcy ba bare ya ji shayin amayar da Abin da yake cin shi Aran shi. Mumcy d'agowa tayi Tana cewa ,son lafiya meya faru ko ince me akayi? Ban fahimci inda kasa gaba ba. FU'AD sai da yayi wata doguwar ajiyar zuciya sanan yace "mumcy Dan ALLAH karki ce min Baki fahimce Ni ba uwata gari me share hawayena ,Dan ALLAH me na Miki Kika hukuntani da Abin da nafi ki wane laifi mafi Muni na aikata Miki Haka uwa ta gari? "Mumcy cewa tayi nifa ban fahimci inda kasa gaba ba ,in bazaka min magana da yaren da Zan fahimta ba ka Adana kalaman ka inajin zasu maka Amfani wajen warwarewar matsalar ka ,tama tashi Tana niyar ficewa a d'akin ,maganar da FU'AD yayi ne ta dawo da ita. Mumcy kin San wacce Kika had'ani Aure da ita kuwa? Kina sani kikamin Haka uwa abar Alfaharin 'ya'yanta ko kema a rufe aka baki kamar yadda aka bani? Sai da mumcy taji k'irjin ta ya mumunan bugawa sai da tayi da gaske ta iya aro mazantaka ta d'aura a zuciyar ta ta Sha mur Babu alamun Wasa ko sasauci tace "wafa kake nufi ? FU'AD yace mumcy wanan _dirty girl_ d'in da Kika manna min take neman zamemin kaska rabi me jini Asma take ko wa da kuka canja Mata sunan ta kuka zamanan ta da shi wai husuna ko me su matar Yaya suke ce Mata , mumcy yanzu Ni aka hada Aure da kazamar Nan mumcy kuma house girl d'inki fisa illilahi mumcy an kyauta min ? Da ita Kika min huce takaici Yana fad'a idon shi a gefe bayason ko hada ido da mumcy don Kar ya kasa amayar da ta cikin shi ,Dan Haka Yana fad'a Yana bayyanar da rashin Jin dad'in shi da lamarin. Fad'a da gaskiya tsoro ne Inji wasu masu iya maganar Dan Haka tayi ta maza tace "son duk Abin da zakace kace Amman kasani banyi ko ban taba wani Abu Dan na cutar da Kai ba sai Dan neman maka masalaha da samun nutsuwa da kyakyawan nufi Akan Auren akan Auren da na maka Wanda kamai suna da auren huce takaici tunda baka d'auki Abin da nama da hannu bibiyu ba da kyakyawan nufi ba,son kasani banyi Dan na cutar da Kai ba ......... FU'AD ne yace katse ta da cewa mumcy meyasa Baki tambayi raayi na ba Kika aura min wanan yarinyar? Mumcy...........ce ta karbi maganar da cewa meye illar ta ko aibun ta ko Kuma tsanar ce kawai ka Mata ba tare da tarin hujoji ba? Ran FU'AD a b'ace yace mumcy yarinyar da take Miki Aiki fa mara kunyar Nan fa wacce kike goyon bayanta idan tamin rashin kunya da har ta Fara Shirin rainani Kuma kike goyon bayanta haba ? Mumcy Dan kun barni da Zan Nemo wacce Zan aura Nan da wani lokaci ai ,Amman har arufe min sanin wacce aka bani a matsayin Mata fisabillilahi ki duba fa mumcy kiga wanan lamarin andakeni Kuma ace bazanyi kuka ba? Hakan anyimin adalci kuwa mumcy ? Mumcy ce tace ,ahangen da nayi wanan shine adalci aganina ,Amman in Kai kana ganin hakan a rashin adalci to ,yarinyar Nan har yanzu baka fad'amin illar ta ko aibun ta ba ,ko kana ganin kafin k'arfin aurenta ne? Dan suna talakawa? A iya tunani na bansanka da izgilanci ko kyama ga talaka ko talauci ba ,ldan kasa hak'uri a Rayuwar Auren ku da yarinyar Nan zakaji dadinta da yadda ALLAH ,kusan jihadi kayi Akan Auren Asma'u ........ mumcy Bata rufe Baki ba .......... FU'AD yace Ni ai jihadin nawa yafi na kowa ga wacan Abin da Alhaji ya k'ak'aba min ga naki na wanan yarinyar da kuka rufe min ita duk Kuma har yanzu bakiga anmin rashin daidai ba ...........fuuuu ya mik'e ze tafi ranshi a b'acce sai wani fitar huci yake , mumcy ce tace Zo ka zauna tunda aka Fara da Kai sai an Kai k'arshe ,yanzu ya kake so Ayi ? Ina sauraron ka. Ana cikin Haka sai ga Yaya Jameel ya shigo ,yatana kwankwasa musu k'ofa basuji ba sai muryar su mumcy da take jiyo wa ,sai ya bud'e ya Shiga Baga bakin shi d'auke da sallama Yana cewa uwa da d'an ta me ake tataunawa ne? Sai ko FU'AD ya wurgo Masa uwar harara da Jan ido ,sai ko Yaya Jameel yace k'anina me akayi ne? Me ya faru naganka a wani yanayi? FU'AD kasa magana yayi ,sai mumcy ce tayi ma yayan bayanin Abin da FU'AD yake kalubalantar ta akai . Yaya Jameel yayi ajiyar zuciya ya dafa kafad'ar FU'AD yace "k'anina kasani duk duniya bamu da kamar mumcy Kuma itama Bata da kamar mu bana mafarki ko tunanin yanzu ko Nan gaba Akwai Abin da mumcy zatayi Dan ta cutar damu ba ,ba'ayi maka hakan ba sai Dan maye maka gurbin b'acin ranka da Abin da ze iya zama farin ciki a gareka , FU'AD k'anina d'an uwa ta gari ,ka yadda ka karb'i auren ka da Husna matsayin k'addara Mai kyau duk Abin da baba ya hango yaro baze hango shi ba ....... FU'AD ne a fusace ya Fara cema Yaya Jameel ai har da Kai akamin Abin da akayi Yaya nayi imani da kasan komai Amin Auren cushe na nuna k'ina kun had'u kun bani Baki kunganni k'arami kamar Mara 'yanci sanan kukazo ban Gama da wancan b'acin ranba kuka sake turani cikin wani da auren da babu shawara ta ko sanin asali ko nasabarta da mumcy banyi ba na karb'a kuka sake harbani cikin wani yanzu ,ya kukeso nayi da Raina ? Ya za'amin haka Dan ALLAH ,yarinyar Nan ma Kuma Dan ALLAH arasa wacce zata zama Mata ga FU'AD sai kazamar yarinyar Nan ? Har ma a b'oyemin Abu daga gareta Alhalin na Santa ,haba mumcy haba Yaya Dame kukeso naji? Auren cushe ko Auren huce haushin ko b'oye nasaba ko asali ? FU'AD mik'ewa yayi Yana hucci ranshi a b'ace Yana cewa Ni gaskiya Abin da akamin anunamin kamar ba d'an gidan bane da Alhaji na, na raye da ba'amin Haka ba nasani Kuma Kai Yaya har da Kai akamin Haka Kai ai matar da kakeso ka aura duk da a k'uraren lokaci ka samota amman ai Kai ka nemota da son ranka ,Nima ku saka acikin ranku Dole na Nemo wacce nakeso wacce zanyi Auren ra'ayi da it's wacce nake so take Sona Dan shafe Abin da akamin bada ra'ayina ba fuuuuuu ya nufi k'ofa zai fita ranshi a b'ace ..........har Yaya Jameel ya bud'e Baki zai Mai magana sai mumcy ta dakatar dashi . Sosai ran mumcy ya b'aci duk da Tana hango gaskiyar FU'AD akan lamarin ,Amman hakan be Isa yasa ya samu lasisin fad'an magana son ranshi ba ,ganin ranta ya b'aci sai Yaya Jameel ya Fara tausar ta Yana nuna Mata irin Halin da FU'AD yake ciki Dole sumai uziri yaro Mai hakuri da kawaici kamar FU'AD ya dinga magana irin Haka Dole su bashi damar shi yayi yadda yakeso shima tunda sun Mai yadda suke so, mumcy dai Jin shi kawai takeyi Amman kalaman Basu Gama Isa kwanyar ta ba. ********* Mama habee labarin gidan Ma'u da had'uwar sa da matsayin Wanda ta aura ya Zo Mata daga majiya Mai tushe duk hankalinta ya Gama tashi ta gama tsurewa Dan aduniya Tana son alak'a da Mai shi a matsayinta na marashi Dan ta Gama tunani da zataye dangin ta tace duk matsiyata ne Dan Haka ita da arziki sai dai su samu abokanen arziki a duniya Dan Haka burinta kullin ya za'ayi taci Karo da Mai arziki ya zama gatanta ya zame Mata jini da tsoka ,sai ga shi yanzu ta Sami labari da sanin asali na dangi da mahaifan Wanda Ma'u wacce tafi tsana a duniya yazo Mata ta tabbatar Kuma Dan Haka suka kullar suka shirya fito na fito da farin ciki da daular da Ma'u take ciki burin su yanzu ya za'ayi su datse ta ? Mama habee tace ko zata yi yawo tsirara sai ta datse ma Ma'u da babanta farin cikin da suke ciki Dan Haka ya tabbatar Mata da kin nuna damuwar baban Ma'u Akan Auren Ashe yasan inda ya kaita shiyisa hankali shi ya kwanta . Harri taga alamun Akwai Abin da ya faru ko yake son faruwa Dan ta jiyo magana da FU'AD yakeyi da mumcy duk da ba wani Abu taji ba Amman tasan tabbasa maganar nada alak'a da tambayar da FU'AD ya Mata Akan ma'un Dan Haka da hanzari ta tafi jikinta na rawa ta sanarma ma'un duk yadda sukayi da FU'AD har dabarar da barazanar da ya Mata Bata b'oye Mata komai ba ,Tana nuna rashin Jin dad'in Abin da ze farun ,jikinta duk yayi sanyi tanata ba Ma'u hak'uri Tana cewa karta zama silar faruwar wani Abu cikin Auren su .....sai ma'un ce tace babu komai ta kwantar da hankalin ta tayi tafiyar ta kawai , ma'un Bata nuna ta firgita da al'amarin ba sai Bayan harrin ta tafi sosai ta tsorata Tana sauraron Abin da kunuwanta zasuji. Maman shaheed dinku na godiya da comments [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg36 Mama habee da humaira sosai suke shiri akan zuwa gidan Ma'u Dan ganin ra'ayil ayn Akan Abin da sukeji na wai wai ,suna son zuwa humaira na tsoro ,sai da mama habee ta zazage ta tayi Mata tas tukunna humaira ta Fara tunanin zuwa ganin irin gidan da Ma'u take ciki. Ma'u dai jikin ta sai rawa yake gashi tanata k'ok'arin ta aro dakiya da rashin tsoro ko shayi ta dasa ma zuciyar ta ko ta iya fuskantar FU'AD da barazana ko hargitsin da yake Shirin tinkarota Dan tasan tabas Yana Nan gabato ta. FU'AD ko sai da yaje part d'in sanaya ya shige d'akin shi batare da yace Mata komai ba Amman ran Nan nashi adagule ,ko da sanaya ta ganshi sai cewa tayi can da yawar ka inkaso ma ka fashe muga karshen kumbiri can da yawar ka. FU'AD ko ya dawo part d'in sanaya ne ko ze samu sukuni yadda yakeji cikin ranshi Dan yadda ranshi ya dugunzuma ji yake ze iya aikata komai ,Amman duk da hakan sai yaji kamar ran nashi ma Kara baci yakeyi Dan Haka ya fusata ya bar d'akin ya nufi inda Husna take Yana tafiya Yana fitar da hucin d'acin Rai har ya Isa k'ofar falon ko sallama be samu damar yi ba har sai da ya tabbatar Yana cikin falon Aiko ranan a bacce yake furta ke _dirty girl_ zonan ,yaji shiru Bata fito ba da alamu Kuma Tana d'akinta ne ,Husna ko da Tana falo tanajin motsin k'ofa ta rufta d'akinta da sauri sauri ,Jin Yana kiranta da sunan da tafi tsana har kusan so 3 sai ta fito gwiwa a salub'e batace Mai komai ba Tana Shirin zama a kujera. Gigitaciyar tsawar da FU'AD ya Mata ne ta dakatar da ita daga zama a kujerar da take Shirin yi ,Yana cewa ke wai har dake za'a yaudare Ni? Arasa Abin auramin sai ke a matsayin huce takaici ? Basusan yin hakan daidai yake da ilata rayuwata ba? Ke Kuma Kika amince? "Husna ta girgiza Kai alamun aa" "FU'AD yace to ke kikace kina son aurena Amman tun da haka kawai ba'a k'ak'abamin ke ba wait matsayin Mata wacce zanyi Rayuwar Aure da ita ,tir da wanan had'i wallahi ,ke inaso yanzunan ba anjima ba kije kicema mumcy wallah ajanye wanan tarayyar Taki Dani Sam bamu Dace ba Kuma wallahi ya matso ya kamo kunnen ta Yana cewa ba shawartan ki nake ba umarni na Baki yarinya ,sanan ya sake Mata kunne ,tayi hanyar Shiga d'akin ta d sauri ya damk'ota Yana cewa gidan wa Zaki ? Bakiji karatun da na biya Miki bane? "Tayi yunk'urin kwacewa daga rik'on da yayi Mata Amman Ina komai na babba yafi na yaro ta kasa ,sai cewa tayi eh to ka sakemin hannu naje na idar da sak'on ka Kuma yadda ka biyamin Haka Zan boyama Wanda kakeso sak'on ya Isa garesu ,Kuma Ni d'in akace ma na tab'a mafarki ko tunanin zama matar mugun mutum Wanda besan hakin Dan Adam ba kamar ka? Ko tinani ko sha'awa bantab'a d'aya daga cikin su ba ,Ni in kanaso ka birgeni muje ka maimaita kalaman ka a gaban hajiya inkamin Haka ka Gama min komai sarki zalimu kawai ta murgud'a Mai Baki .......Aiko FU'AD ya saki hannun ta ya kamo bakin zai murd'e ta zille ya sake cakumo ta Yana laluben bakin har hannun shi yayi karambanin zuwa inda be shirya ko tab'a zuwa ba a Rayuwar sa da sauri ta bige hannun Tana cemai Allah ya isana mugu kawai sarkin cin zali kawai ,shiko da sauri ya d'auke hanun shi ya mayar Kan bakinta ya matse Yana cewa Mara kunyar banza me zanyi dake Baki isheni sakace ba bare k'oshi wata kazama dake fitsarariya kawai ke har kina sa kanki sahun Mata ? Ta kwace bakinta daga rik'on da yayi Mai ,tace ai Ni har nafi wasu matan da kake ganin su cikakun matan lokaci shi ze tabatar ma Kuma wallahi in baka Dena kirana da kazama ba bazan Dena kiranka na mage ba mamugunci kawai muryar ta na rawa Dan k'arfin Halin mayar Mai da martani kawai takeyi ,Dan ta Sha matsa a wajen shi ,Aiko FU'AD ya sake had'ata da jikin shi ya matse ta Yana cewa bazaki bar min rashin kunya ba ko yarinya wallahi da rabon asibiti suyi bak'i Dan wallahi inna Miki wani abun sai dai asibiti inda rabo su ceto ki. Husna tace ohooo kafin ka kaini Ni na Fara kaika ai ,sai ko FU'AD ya kamo bakin ya k'ara murd'ewa Karo na 3 yace me kike nufi uwar fitsararu ? Yimin bayani ko ki kwashi kashin ki a hannu yanzu ,sai ko tace ohooo Ni ka sakeni Tana k'ok'arin waskewa Kar yasan ita tayi sanadin zuwanshi asibiti da gasken kamar yadda sub'utar Baki ya kaita furtawa batayi tunanin Abin da zaije yazo ba ,ganin da gaske yake son Jin Abin da take nufi da bayanan ta sai ko taga sai ta Fara had'awa da kirsa a tsakanin ta da FU'AD Dan Haka da ya k'ara matse Mata Baki ta Fara Shirin kuka muryar ta ta raunana Tana fitar da sautin azabtuwa daga cutarwar FU'AD d'in. FU'AD cigaba yayi da Mata tambaya Yana sake matseta da bango sai kawai ta Fara kuka Tana cewa ,mugu ka sakeni muje wajen hajiya na fad'a Mata sak'on ka Nima na gaji da muguntar ka mugu kawai ,tanata yunk'urin kwacewa daga rik'on da yayi Mata Aiko sai FU'AD ya tsaya cak Yana cema to tayi sauri ta kwace in zata iya ,yin duniya Husna ta kasa kwacewa daga rik'on FU'AD,sai ko FU'AD yace kin Gama sai ya saketa Dan kanshi da gudu ta zuba zata sauka kasa Tana Shirin cewa wani Abu yayi saurin shak'ota yace wallahi idan kikaje Kika maimaita Abin da nace a wajen mumcy ba tare da kince ke Kika ga dacewar hakan ba wallahi sai kin fuskanci Abin da yafi na yanzu in kin Musa kije ki fad'a ,ya tureta har ta kusa fad'uwa. Sai da taga takai bakin k'ofan fita tace sarki zalimu kawai Kuma sai na fad'a inyaso ka kasheni abirne gawata mugu ,tsoratata yayi kamar ze biyota da gudu ta sauka Tana haki ALLAH yasa babu Kowa a falon ,sai d ta zauna ta huta ta goge fuskarta numfashinta ya dawo kafin ta nufi kitchen ta Sami su Harri ta Fara tayasu Aiki suna hanata Tana cewa babu komai ai d'aya suke zuciyarta fal tunanin yadda zata kaya tsakanin ta da FU'AD gashi yau a d'akinta yake har mumcy ta shigo ta same su taga Asma'u tsamotsamo a cikin su tanata Aiki mumcy ta musu sannu ta Kira Asma'u zuwa falo. Sun jima suna Hira tsakanin mumcy da Asma'u , mumcy nata tausan zuciyar Asma'u akan FU'AD Tana rok'on ta da tayi hak'uri dashi na wani gajeren lokaci sanan babu hallacin d zata Mata kamar na rufe sirinta ko tsakanin ta da FU'AD shine iya sakayyar da zata Mata a rayuwa batan ta biyata Alkhairin da tamata arayuwa ba ,sosai maganganun mumcy suka ratsa zuciyar Husna ta Mata Al'k'awarin insha ALLAH zatayi iya Abin da zata iya ,so 2 FU'AD na niyar sakowa daga sama sai ya koma a tunanin shi ko Husna na gayama mumcy Abin da takeson sanar Mata ne daga baya dayaga Abin yaki ci yaki cinyewa kamar cin Kwan makauniya sai ya fito da k'arfin gwiwar komai ma ya faru Dan ya shirya b'ata ran kowa akan Husna ayanzu ba sanaya bace matsalar shi Husna ce damuwar shi Dan itace abar fafatawar shi Dan sanaya baya sata a lissafi ayanzu. FU'AD d ya sako sannu da hutawa Yama mumcy zai wuce sai Husna ta Harare shi ta murgud'a Mai Baki ,ya mayar Mata da mugun kallo ,sai mumcy ta Kira shi ,sai da yaji bugun zuciya Amman ya dake "yace naam uwa tagari" ya zauna kusa da ita ,sai mumcy tace "kunyi magana da yayanka kasan gobe ze tafi Abuja tare zasu tafi da aunty sa'adiya k'arshen wata zasu dawo ,sai ko FU'AD yaji hankalin shi ya kwanta ya samu kwarin gwiwar cewa yanzu wajen shi zani muyi magana sai mu tatauna Akan maganar. Sai ko mumcy tace yayi kyau hakan ,har ya Mike zai fita sai mumcy ta dawo dashi tace wai Ina wayar da na maka magana ta Asma'u Naga banganta ba a hannun ta da ka siyo Mata nasan da ta nunamin yadda nasan Asma'u dai ko ummarnin nawa ne bazakabi Ni naje na siyo Mata? Sai ko FU'AD ya Harare Husna sai Akan idon mumcy batare da yayi tunanin zata iya gani ba ,sai ko mumcy tace Ni zaka harara ita meye nata a ciki? Sai FU'AD ya wayen ce nifa ba hararar ta nayi ba ,Zan siyo Mata ko zuwa gobe ne Kinga yau bazan fita office ba sai gobe inban manta ba ,sai ko mumcy tace Inka manta sai jibi ko gata ko? To yau d'inan zaka siyo Mata insha ALLAH Kuma tare zaku tafi ta zaba umarni ne ba shawara ba gaba d'ayan ku na baku ,duk har sun bud'e Baki zasuyi magana maganar mumcy ta hanasu k'arasawa , FU'AD to kawai yace ya tafi wajen Yaya Jameel , mumcy ko cema Husna tayi taje ta shirya tazo sutafi,ta aika Akira Mata sanaya , Anci sa'a ba'a Jima ba tazo ta gaishe da mumcy Babu yabo Babu fallasa , mumcy ta amsa ,sai mumcy take cemata ta shirya suje FU'AD ya canja musu waya ita da Asma'u intana ra'ayin hakan yanzu ma Asma'u ta tafi shiryawa ne shima yanzu zai dawo sai driver ya kaisu ko ya kaisu da kanshi sai ko sanaya tace "aa Bata buk'ata ta hannun Tama ta isheta ita kawai so take asashi ya Mata Visa zuwa Egypt ta kaiwa su mamy ziyara shine Abin da tafi buk'ata ko baze biya Mata ba kawai Tana son ta Sami izini a wajen shine Dan tanada uwar kudin ta badan Tana tsoron Kar dady ya korota ba da sai dai suji ta a Airport ma tuni ,duk wanan maganganun surikar ta take labartama mumcy batayi mamaki ba Dan tasan daganin kura dama zataci mutum Dan Haka tace zata duba ta gani in Haka zai yiwu ,babu godiya bare girmamawa ta tashi zata tafi sai mumcy ta dawo da ita da cewa to ki haura saman ki gayama Asma'u ke bazaki ba suyi tafiyar su Kuma Daman Baki tab'a haurawa Kinga wajen zaman abokiyar zaman Taki ba Kinga Kya jefi tsintsu biyu d dutse 1 ko ? Da kamar bazata ba sai ta juya zuwa Hawa matatakalar da ze sada ta da falon Husna ,Koda ta ita ta kwankwasa kusan 3 har tayi tsaki zata tafi sai Husna taji kamar ba irin bugawar da FU'AD yakeyi bane Dan Haka tazo ta bud'e ranta fal tsoron FU'AD gashi an had'ata futa dashi tasan yau yankata zeyi ya watsar da gawarta a waje yadda yakejin tsanarta Haka ,sai ko sukayi ido biyu da sanaya da sauri ta saki fara'a ta Mata sannu da haurowa ta kamo hannun ta har kujera tanata jera Mata sannu ,da sauri Husna ta d'auko Mata juice ta zuba Mata suka gaisa babu laifi sanaya tad'an saki fuska Rana ta farko da ta saki fuska ga Husna ,suna cikin Haka FU'AD ya shigo yayi sallama ganin su a tare dama mumcy ta sanar Mai har kin zuwan da sanayan tace bazata ba d kudirinta na son tafiya Egypt shima cewa yayi zai duba yagani. Husna ce kawai ta amsa sallamar da yayi ,ya Harare ta ,itama ta murgud'a Mai Baki duk sanayan batasan sunayi ba ma ,sai yace ke kince bazaki ba ko? Sai da ya maimaita so 3 sanan Husna tace dake fa yakeyi sis sanaya , sai ko sanaya ta d'ago tace oh ban saniba ai naji be Kama suna ba kowa anan Kuma yanada sunan shi ,sai ko Husna tace da gaskiyar ki 'yar uwa kowa da sunan shi Kam koni iya Abin da zanyi kenan ,sosai FU'AD yaji haushin had'e Kan da suka Mai ayanzunan ,yace kwaji da gulmar ku ,ya shige d'aki yaje ya Gama shiryawar Dole da mumcy tasa shi ya fito yanata zuba kamshi ,sai Bayan ya fito ya gansu sai yaji haushin kanshi Yana tambaya Wana ya fesa ma turare? Husna ko sanaya ko Dan zasu fita da Husna har ze wani Mata kwaliya harda fesa turare Mai tsada da k'amshin dad'i ? Sai zuciya ta shawar ceshi da yaje ya zura jalabiya kawai ya fito su tafi basai ya fesa komai ba ya cire kayan da yasa ,har yayi hanyar Shiga d'aki wayar shi ta Fara ringing Ashe mumcy ce ,Yana d'agawa tace ya sakko yanzunan ta kashe Bata tsaya jiran meze ce ba . Dole ya sauka ,Yana cema sanaya ,sanaya kike ko wa maganar tafiyan ki sai na duba na gani ,Bata Bari ya Gama fita ba ta mayar Mai da cewa Ashe inada suna ,sai ko Husna ta kwashe da dariyar k'eta Tana cewa bama Dole kiyi suna ba ,afusace ya juyo ya harareta da mugun kallo da ya jefeta dashi ,sai ko a idon sanaya ,Bata yi shayi ko tsoro ba tace meye nata ba ita takar zomon ba ai ,rataya aka Bata ,har zai dawo masifa Kan me uwa da wabi sai ya tuna babban Kiran da uwa tagari tamai yaga beze iya had'ashi da komai ba Dan Haka yabar Abin matsayin bashi ya rabu dasu ya tafi Kiran mumcy. Sosai Ma'u tayi tariya mussaman da taga Abin ya tab'a ran FU'AD ,itako sanaya ko dariya Abin be Bata ba sai sanaya ta mik'e Tana cewa Bari taje sai sun dawo ,sai ko Husna tayi saurin binta k'asan dama gyalenta na jikinta Kar ya dawo ya rutsata a saman ita kad'ai ta kwashi kashin ta a hannu tare suka sauka suka ci Karo dashi Yana Shirin haurawa fuskar a murtuk'e ,sai mumcy ta gansu sun sakko sai tace "Ina zaka Kuma son ? Kazo ku tafi ,sai ya Rasa me zece ya Fara kame kame ,sai can yace key Zan d'auko a sama sai mumcy tace meyake damun kane son ba yanzu Naga key a hannun ka ba ? In Kuma na farar motanan kake nema ba Yana wajena ba da jiya ka bani ? Sai ko yace au na manta kinganshi a aljihu na ,sai ko mumcy tace son ka ragema kanka Aiki fa ka samu ka dinga hutawa sosai banason tsanaita komai arayuwa kaji ko ? Kama yayi ka samu ka huta yau tunda babu office ,sai ko karyewa tazo Kan gab'a yace to ahak'ura da fitar mumcy sai na kwanta ,sai ko mumcy ta gano shi taje ban lamunce ba me neman kuka anjefe shi da kashin awaki ko ,to kuje ku dawo inyaso sai ka kwana kana baccin ,sai ko yaji Babu dad'i hak'on shi bai cimma Ruwa ba yayi hanyar fita Yana cewa sai kizo mu tafi Inkin shirya. [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA D TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg38 Aiko humaira 2500 ta kaima iliya Mai kantin ta dawo tace ma uwarta ta Kai Mai ta kalmashe 500, Bayan baba y dawo aka sanar Mai da bakuwar da tazo har da Al'k'awarin Gobe za'a kaita gidan Ma'u kamar yadda buk'ata ,baba bayaso kowa yaje inda Ma'u take gudun faruwar matsala musamman su mama habee da wani nata ko kawayen ma'un ba kowa yakeson yaje ba inda ALLAH ya taimaka ma ba wasu kawayene da ita ba sai tsiraru humaira ce tsarkin kawaye kare da doki har biri duk nata ne ,Amman Jin huwailace zataje wajen ma'u beyi takaici ba sai murna ma Dan yasan wace huwailar sai takaicin shi da humaira ce uwar rakiyar Dan har sai da ya nuna bayason humaira tayi rakiyar ya wayen ce da ai batasan gidan ba abari shi ze mata kwatance da kanshi ,Aiko mama habee ta Fara kumfar Baki wai zumunci ALLAH ze raba da bayason humaira taje taga mazaunin Yar uwar ta tun da ranta ya Shiga tsakanin su inaga in kasa ta rufe idon ta Bata tsaya Nan ba har da cewa dama yafison Ma'u ya tsani nata yaran ta sani ,Jin ta doshi wani babin yasa shi amincewa da humairan ta raka ta ,har da kanshi ya Mata kwatancen gidan murna fal cikin humaira da mama habee har ALLA! ALLA!! Suke gari ya waye suje kwaso gulma da tsugudidi. Washe gari humaira ko cangal batayi ba agidan dama sai taci zagi da Gori takeyi tun tafiyar Ma'u ake mata Gori har yau ba'a fasa ba ,yau ma kin komai tayi da mama habee tayi magana sai tace Kar ta Fara bakuwa tazo sai tace wanka ma zatayi tayi wanka tasa kayanta kure adaka. Ba'a jima ba aunty huwailan ta k'araso cike da tunani fal cikin ranta in ka ganta Dole zaka fahimci kamar Akwai Abin da yake damunta ,Ashe tunjiya ne ta taho ta wani gidan mahaukata tazo wucewa sai wasu sukazo shuka tare ta suna tambayar ta bataga wata Mata Mai matsalar kwakwalwa ba ta fito daga cikin gidan da gudu yanzu daga fito da ita Dan ganawa da wani Mai lura da ita sai ta samu ta kwace ta fito su Kuma suna can suna tataunawa akan abubuwan buk'atun ta basu San ta fito ba ,sai ko tace tabbas taga wata ta gifta ta wajen ginin can Amman Bata ga alamun rangwamen hankali atare da ita ba ,sai ko suka kwasa da gudu ita Kuma ta tsaya tausaya musu da jimami sai ko gasu har sun samota tanata tafiya cikin nutsuwa Tana hawaye suka kamota suka dawo da ita Tana cewa Dan ALLAH su barta kawai Amman Inna sai k'ok'arin mayar da ita gidan suke furucin da take cikin muryar kuka da kunjin tausayi ya d'aki dodon kunnen aunty huwailan har ya haifar Mata da mumunnan fad'uwan gaba matar na Basu hakuri Amman Haka suka Shiga da ita gidan batare da aunty huwailan ta samu ganin fuskar matar ba Wanda bataso hakan ba ,adole taja motar ta tayi gaba dake intazo k'asar motar kanin ta musbahu take d'auka Dan sunfi kowa saukin Kai acikin yaran hajiyar su sune masu k'aunar mamar Ma'u su kad'ai ,toh shine abun yake damunta har yau Kuma ta kasa hirar da kowa. Bayan sun gaisa da mama habee ta nemi Mai rakata yazo su tafi ,da sauri humaira ta fito cikin shiri anci uwar kwaliya fuskar Nan taf da kwaliya mama habee tanata musu adawo lafiya harda cewa agaishe Mata da ma'un ta,aunty huwaila tace toh gami da wani murmushi me cike da ma'anoni suka tafi a motar da tazo dashi suka tafi humaira na Kara jinjina Mata cewa Mai katshin arziki ce. Isarsu keda wiya humaira ta gane tabas shine gidan da baba ya kwatanta Mata Dan Haka da k'arfin gwiwanta tace su Shiga kawai ,humaira nata kici_kicin bud'e mota zata fita su Shiga gidan tsabar rawar Kai da d'oki "aunty huwailan ce tace "Ina kuma Zaki ki Bari abude mu Shiga Mana ko suna Hana Shiga ne? Humaira tace aa da k'arfin gwiwanta ,sai aunty huwaila tayi horn Mai gadi ya wangale gate tamai sannu ta kutsa ciki da motar ta batayi nisa ba Tama motar masauki gefen wasu furanni masu kyau da kamshi ,sai ta tmby humaira inane part d'in ma'un ? Nan fa idon humaira ya bayyana sunan ta na mak'aruaciya ganin Bata da mafita sai kawai tace na manta ko can nne ko Nan nadai manta Amman inajin babban can nne ,aunty huwailan ta fahimci inda tasa gaba batabi takanta ba ta koma zata tambayi Mai gadi sai ga aunty sa'adiya ta fito da baby mami ahannun ta ,sai ta k'arasa suka gaisa tace "Dan ALLAH Ma'u fa Tana Nan? Sai ko tace " eh Husna ko? Sai humaira tace aa ma'u dai ma'un baba ,ganin ta dage zata musu shirme sai aunty huwaila ta katse humaira tace yi shiru Bari a kaimu wajen Husna duk sunanta ne ai ,sai ko aunty sa'adiya tace "yawwa 'yar gari bisimmillah ku! Kuzo na kaiku ...... Suna Shiga suka had'u da mumcy ,Bayan anuty sa'adiya ta gabatar musu da mumcy sosai humaira ta zak'u Dan taga Ma'u bataso aka b'ata lokaci wajen mumcy ba ,itako aunty huwaila sanin daraja da kallon da Tama datijuwar na girma yaza ta Bata girman ta sosai sukayi gaisawar mutunci daga bisani aka nuna musu saman Ma'u ,sosai mumcy taji dad'in ganin wani daga dangin Asma'u yau Dan Basu taba zuwa ba duk da tasan wani Abu Amman yau takeson sani wasu abubuwan Dan ta shirya magana ta fahimta da gaskiya da gaskiya da aunty huwaila Dan ta yaba da hankalinta da Halin girman ta Dan Haka take jiran fitowar ta Dan su zanta Akan gaskiya da gaskiya. Hawa sukayi saman suka kwankwasa kofar cikin nutsuwa da hankali aunty huwaila ce ta kwankwasa Dan humaira tuni taja gefe ganin tsaruwar k'ofar Dan taji ance gidan masu arzikin Nan k'ofofin su ma da numbers ko remote ake bud'ewa gudun Kar tayi k'auyanci tabar 'yar gayu ta bud'e sai taga ta tab'a wani Abu sai 'yar wak'a ta fito Bayan ta kwankwasa a farko. Ma'u na tambaya waye ? Aunty huwaila "tace nice " Da sauri Ma'u tazo bud'ewa Dan ganin waye ,Tana bud'ewa taga aunty huwaila ,da sauri da murna Mara misaltuwa ta taho ta Ringumeta Tana Mata oyoyo aunty nayi missing d'inki wallahi ko takan humaira Bata bi ba,sai da ta rungume aunty ta kaita har Kan wasu luntsuma luntsuman kujera sanan ta dawo ta rungumi humaira Tana ce Mata "Yaya humaira sai yau? Humaira sosai taji dad'i Ma'u dama Akwai ba mutum girman shi ,humaira kanta ya k'ara fasuwa na ma'un Bata manta dasu ba ,tayi fari da idanu tace Ina Zan manta da k'anwata Ma'u ko wa sabon sunan da aka sake Miki a Nan gidan sai naji ma yafi Wanda baba ya rad'a Miki wallahi . Aunty huwaila ce tace "to ai ba rad'a Mata sukayi ba dama nata ne Asma'u ,Husna duk sunan ne keda Baki sani ba? Humaira tace wallahi ban taba sani ba sai yanzu da Kika wayar min da kai. Aunty huwaila nasaon suyi hirar sirri da Ma'u Amman Tana tsoron rediyo me jini 'yar rahoto Dan ta gama zargin su zarginta Kuma na neman zama gaskiya. Itama Husna so take suyi Hira sosai Amman ta Rasa Abin yi saboda humaira ,Bayan husnan ta Basu kayan motsa Baki sunci sun k'oshi sai dabara tazo ma aunty huwaila tunda tafi Husna hankali da sanin Kan duniya sai tace ma humaira "ga wanan ta zaro 'yan dari bibiyu sababi fil Bata k'irga ba ma Amman ba zasu wuce 5k ba tace ki hau napep ki koma Kar aga kin Jima kinji nagode ki gaishe da maman naki ,da sauri humaira aka amshe kud'i aka mik'e jiki na rawa ta zari gyalen ta Tana neman tafiya ma'au har tayi hanyar d'aki aunty huwaila ta dawo da ita da hannu da Mata magana da Ido Akan taje ta raka humaira ta tafi ,husnan ta d'auki umarnin da aunty ta Mata ,har k'asa ta rakata suka samu mumcy na zaune na jiran su. Husna ce tace "mumcy ga yayata fa kungaisa ai ko? Mumcy tace eh har da k'anwar mamarki ma badai tafiya zasuyi ba ? Sai Husna tace eh Yaya humaira ce zata tafi ,sai ko mumcy ta d'ako wata k'aramar Leda da turare da sanulai aciki tace gashi ki gaida gida ko. Humaira jiki na rawa aka karb'a Ana cema Husna ki tayani gldiya ,nagode hajiya ,Husna ma gldiya ta k'ara yima mumcy sanan ta raka humaira har harabar waje ta dawo , mumcy ta tambayi Husna wanna ce kuke baba d'aya ko? Husna tace eh ta haura sama Dan suyi Hira da antyn ta ,itako aunty huwaila nata Jin dad'in korar humaira da tayi. Bayan Husna ta dawo ,sosai sukayi hirar yaushe gamo da aunty Tata har da exchanging numbers sukayi , Ma'u Bata ra'ayin chart Amman yau aunty ta umarce ta ta nuna Mata hanyar Amfani da babbar waya ta hanya Mai kyau ta nuna Mata yadda zata gujema gurbataciyar hanya ta ce mata zasu dinga chart inta koma India shine husnan ta k'ara Jin dad'i dama Aisha nata Mata nacin zata bud'e Mata Taki yadda wai Dan su dinga chart in itama ta koma Ghana to gashi yanzu zataga amfanin abun aunty sa'adiya ma tace da bud'e saboda Koda FU'AD in baya k'asar sa dinga magana through chart duk da Bata d'auki wanan shawarar ba Amman ta yadda da gaisawa da aunty huwaila da Aisha dai. Aunty huwaila bata bar gidan ba sai da ta bud'e Mata whatsApp,insta, Telegram,imo......tayi Mata sub kuma. Sosai sukayi Hira ta Jin dad'i Husna ta yadda aunty huwaila gatace agareta ta sheda Mata daga yanzu duk wata matsalar ta karta b'oye Mata ko Tana India ne zata taimaka Mata iya iyawarta ,Dan Husna Bata b'oye Bata komai game da irin Auren da aka Mata da FU'AD ba ,Amman aunty huwaila ta yabama hajiyar tasan zeyi wuya tabar husnan ta wulak'an ta mussaman ta dinga Shan cikin husnan Akan zamansu da FU'AD har ta gano komai Wanda it's husnan batayi tunanin komai akai ba ,Dan Haka aunty ta kudiri aniyar karban number mumcy ko ba yau ba ko a wajen husnan ne ,Bayan sun Gama hirar su tace ma husnan ta bud'e account ta tura Mata da number Amman da izimin mijinta inya Hana ta rabu dashi ita dai Tana Mata nasiya da tabi umarnin shi matuk'ar be Saba shari'a ba,Husna tace to zakiji yadda mukayi aunty nagode naji dad'in kasancewa ta 'yarki kin isheni rayuwa aunty Abin da kikamin ALLAH ya ninka Miki ,aunty huwaila ta toshe Mata Baki tace "Mana Miki keda ki tayani Addu'a Zan zamarmiki bargon da izimin ALLAH , ALLAH dai ya karemin ke Kar naji ko ganin kin sake zuwa gidan hajiyar mu banji dad'in Abin da sukayi a bikin ki ba Dan Haka ki rabu dasu ki manta dasu ko had'uwa kukayi da wani acikin su karki nuna musu muna tare su Kuma ALLAH ya ganar dasu kinji? Husna Tana share guntun hawaye take toh aunty insha ALLAH zanyi yadda kikace suka sauka zata rakata ta tafi. Suba sakowa suka had'u da mumcy , mumcy ta fara Jan huwaila da Hira har ta Fara shigo Mata da tambayoyinta Tana Bata amsa har ta fahimce ta sosai sukayi Hira harda labarin zaman da su mumcy suka tab'ayi a Indiya kafin su koma Egypt Dan tare suka zauna da baban sanaya shi Alhajin su FU'AD ya dawo 9ja da zama shida kasashen waje sai dai yaje Dan kasuwanci ko ziyara dan shi yafi dadyn sanaya kishin k'asar shi ta haihuwa shiko dadyn sanaya tunda yaje yaga wajen zama Yana bak'in cikin amai maganar dawowa 9ja ma ,sosai Hira Mai ma'ana ta b'arke tsakanin huwaila da mumcy har mumcy nama huwaila Al'k'awarin Suma sunan Nan zuwa India Dan bana acan takeson zuwa hutawa in tafiyar ta yiwu sa taho da Husna in mijinta ya lamunta ,sosai huwaila tayi murna Tana cewa ALLAH yasa ya Amince da ya Gama min komai kema zanyi murna ranar da na gangu a k'asar ,Dan ALLAH ya taimaki marainiyar Nan ya tayamu Bata farincikin da ta Rasa na rashin gatan uwa ya taimakemu mu maye gurbin mahaifiyar ta ,sosai mumcy taji dad'in kalaman huwailan tace "Zan mishi magana insha ALLAH indai ya Bari tare zamuzo ki kanta ku zauna ku k'ara shak'uwa da juna Kona satikai ne ,bani number ki ma ,karyewa tazo Kan gab'a dama kunya taji ta kasa karb'a , huwaila ta karanta Mata tasaka ta Adana ama'adanar sunaye. Tana Shirin fita Bayan sunyi sallama da mumcy Akan in tasamu lokaci zata dawo inkuma tafiyar ta tazo gab bazata samu dawowa ba Amman zata Kira waya suyi sallama ,sai ga FU'AD ya dawo daga Aiki , mumcy ce ta dawo da huwaila da cewa to ga surikin naki da Rabon ku gaisa Ashe , mumcy tace ma FU'AD ga k'anwar mahaifiyar husna wacce take India da zama ,sai ko yad'an ji kunya ya rusuna hark'asa da girmamawa Yana gaishe ta ,Tana amsawa Tana yima Husna magana da Ido Akan ta karb'i jakar hanun shi Mana Bayan ta gama karanta Mata dabarun mallakar miji ko Tana nufin wanan baya ciki ne ? Ganin ta tsanan ta yasa Husna zuwa ta rusuna tamai sannu da zuwa Tana Mai mik'a hannu Akan ya Bata jakar hannun shi ,ya amsa ,ya mik'a Mata jakar hakan sai ya birge mumcy ,shiko gani yayi husnan tazo Mai da wani sanabe yau da besan me ze kirashi ba Dan baze kirashi da kulawa ba ,itako tun da ya Bata ta rataya jakar sai aunty huwaila tace to ta tafi mumcy ce ta Bata wata katuwar leda ,taso Taki karb'a Amman mumcy ta nuna Ina Dole tasa ta karb'a tayi godiya ta fice Koda Husna ta tafi rakata basuyi nisa ba tace ta dawo Tana sake tuna Mata dabarun zama da miji. Da Husna ta dawo ta samu FU'AD nata tambayan mumcy Akan aunty huwaila ,Yana cewa bayason jajibe jajibe ne inko Basu da alak'a ta jini gwanda Yama tufkar hanci tun wuri ,Husna ko azuciyar ta cewa aunty na tafi k'arfin jajibe jajibe Dan kasani gwanda mun ita da Kai tazarar da Nisa bazaka tab'a kamota ba ,ta k'arasa shigowa ta musu sannu shida mumcy ta haura sama abinta Tana tunanin inda zata wular Mai da jakar shi da tayi dakon ta d'akin shi takai Mai Dan Bata buk'atar ya zauna Mata ma a falon ,har ta ajiye Mai zata fito sai taga d'akin babu gyara sai ta dinga tunano hud'ubar aunty huwailan ,ta sake tunowa dama itace Mai gyara Mai saman matsayin 'yar Aiki to yanzu gata matsayin iyalin shi itace da Alhakin gyarawan dai Dan Haka ta Fara gyara Mai cikin sauri sauri wai Kar yazo ya sameta ta Bayan gida ta Fara sama_sama ta dawo gado ta kad'e ta gyara zuwa su tsakar d'akin komai ta gyara ta feshe da turare Tana Shirin fitowa sukayi kacibus har sai jinta tayi a k'irjin Abin ma tsoro ya Bata Dan bataji motsin shiwan shi falon ba bare d'akin Dan Haka ta gama mutuwar tsaye sai ta kwalara k'ara a razane ,batare da ta bud'e idon taba ,ganin zata Tara Mai mutane da sauri ya rungumota ya rufe k'ofar ya maida ita cikin d'akin bayan yasa hanun shi d'aya ya toshe Mata Baki da shi ,Yana cewa ke karki Tara Mana mutane matsoraciyar banza ,dodo Kika gani ko me? Sai da ta dawo hayyacin ta ,ta jiyo sautin muryar shi ta samu damar d'agowa ta kalle shi ,shima zuba Mata ido yayi Yana kalon ta sai kalon kalo ya Shiga tsakanin su ,ita Tana kisima zallar cikar haiba da ALLAH ya huwace Mai shima Yana gano tsagwaron madarar kyau da kwarjini da ALLAH ya Mata baiwa da su ,Amman azahiri kowa yak'i gaskata hakan ,sai da taji Rik'on da ya Mata ta takura shima ya farajin wani sako na gauraye duk illahirin jikin shi ,sanan suka rabu da jikin juna atake ,musamman ita Dan har hular kanta sai da ta fita gashin ta ya bayyana Mai kyau da shek'i da laushi Bata da yawan gashi irin har gadon baya Amman tanada na zaman falo daidai ita Kuma Tana kuka da abinta Kuma sosai ya d'auki hankalin FU'AD duk da baya son ko k'aramar yarinya ce yaga kanta abud'e saboda tsanar da Yama gashi amman sai yaji na Husna yau Yamai dad'in kallo ga wani kamshin wasu sinadarai da suke tashi Wanda bazaka iya tantance da man da take gyara kanta ba ,ganin yadda yadda yadda zuba Mata ido ,gashi jikinta duk yayi la'asar sai tayi yunk'urin barin d'akin da sauri .....tsugunawa yayi ya d'auko Mata hular da batasamu damar d'auka ba yace ungo ki rufe min wanan kazamin gashin naki ,Kuma me kikemin a d'aki? Da kamar bazata karb'i hular ba ,sai Taki tambayar da ya Mata yasa ta dawo ta karb'i hular Tana sawa Tana cewa ,jakar ka nazo ajiye ma mezanma a d'aki kuwa ,me ka ajiye da zanzo gani ko d'auka? Hannu ya d'aga mata kawai Yana cewa jeki karki min rashin kunyar Nan Taki nayi maganin yarinya Yana duba yanayin d'akin kamar an gyara shi Dan ba Haka ya Saba fita ya barshi ba ,Husna cewa tayi hmmmmm ta fice a d'akin. Shima ko'ina ya k'arema kallo ya tabbatar an gyara d'akin Dan ya tabbatar har Bayan gida ya duba ,sai ya dinga mamakin waye ya gyara yace Husna Ce zuciyar shi ta karyata yace sai dai in mumcy ce tace wani yazo ya gyara. Bayan ya sauka kasa cikin hikima yake tambayan mumcy waye ya gyarama Husna samanta yau ,sai mumcy "tace Babu Wanda yaje don Mata gyara ai tafi sati da cemin Adena tura kowa yi Mata gyara da kanta zata dingayi tafi ganewa ganin ta rok'eni Alfarma tace ai shine kawai aikinta harda had'ani da ALLAH sai na Amince Mata Amman da sharadin duk Abin da ya gagareta tayi magana a tayata ,tace min Kuma to. Me ka gani ko Tana buk'atar wani taimako ne? FU'AD cewa yayi aa shima tamai wanna bayani ya Hana Amman ta dage shiyisa ya rabu da ita ,ya tashi ya koma sama Yana ayana dama tafi dacewa da Mai Aiki ai Dan Haka it's zata dinga gyara Mai d'akin shi tunda Haka ta zab'a Dan wai ya k'untata mata. Bayan ansako contact abincin dare sosai mumcy ta dinga shi Mata Albarka Tana cemata FU'AD yanata yabon gyaran da takeyi Mai a d'aki Dan ko ita tasan gyaranta babu ha'inci aci ba FU'AD ba kawai ,hakan ya faranta ran Husna tayi Al'k'awarin cigaba dayi tunda har hakan yasa mumcy nishad'i da Jin cewa Tana kula Mata da d'a,shi Kuma Mai gulma da girman Kai Ashe ya yaba Amman yaketa fad'in Rai aikin banza kawai Dan ALLAH zanci gaba dayi da mumcy badan Kai ba wani na mage da Kai kawai.......duk Abin da take fad'a atunanin ta azuci take fad'a batasan afili ta ke fad'a ba ,sai ko ji tayi FU'AD ya Kama kunnen ta Yana cewa uwar marasa kunya maimaita Abin da kike cewa yanzun Nan ko nayi k'asa k'asa dake yanzun Nan. Jikin Husna NE ya d'auki rawa ,tace me nace Ni? Ta samu ta kwace kunnenta da karfi sai ta Ari na kare sai k'asan mumcy Tana cewa mugu na mage kawai. 😘😍 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* (MAMAN SHAHEED) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg 37 FU'AD na gaba Husna na binshi cikin wata shigar doguwar Riga Mai bala'in kyau ta rolling kanta da d'ankwalin Rigar ,ganin bazata iya fita a Haka ba saboda kunya sai ta d'akko wani gyale kalan beats din jikin Rigar ta yafa a kafadunta ,ita kanta bason tafiyar take ba umarnin mumcy ne kawai bazata iya k'etarewa ba , Haka uban tafiyar umarnin mumcy kawai yabi ,Yana Isa jikin motar ya shige mazaunin driver ya hakince Yana hangota ta jikin madubin motar sai yaga rashin dacewar ta bishi a Haka babu hijab tunda cikin hijab ya Saba ganin ta har ya k'udiri aniyar yi Mata magana Kan ta koma ta sako hijab sai yaga meye bashi aciki inma tsirara zata tafi meya shafeshi Dan Haka ya Adana kalaman shi ya had'iye. Husna na zuwa ta Shiga gaba kusa da mazaunin driver tasan Yana iya Gaya Mata magana in ta Shiga baya ,Ashe gudun gara tayi ta haike zago "a tsawace FU'AD yace tayi gagawan bacewa daga kusa dashi ta koma baya shi sa'atane da zata zauna kusa da shi? Iya haushi da k'uluwa Husna tayi Amman sai ta shanye burinta suje lafiya su dawo lafiya ta fito ta koma gidan baya batare da ta furta komai ba ,sai da ta Bari ya tada mota har me gadi ya bud'e Mai gate ya cinna hancin motar titi ya Fara tafiya cikin kwarewa da sarrafa karfen nasara sanan tace "in bamu zama sa'a Ni ba ka zama driver Dole ai ciki ciki ta furta hakan Amman yajita Sarai yak'i kulata ,sai da sukayi nisa yace ke Mara kunya me naso naji kina cewa? Husna tamai shiru kamar bada ita yake yi ba ,sai da ya juyo yace wata rashin kunyar kike sake d'orawa Kan wacce kikayi ?ko bada ke nakeyi ba? "Sai ko Husna tace banyi tunanin Dani kakeyi ba Dan banji sunan da baba yasa min ba sai shi yisa kaga ban tamka maka ba. FU'AD wata muguwar harara ya wurga Mata yace hmmm yaro besan wuta ba sai ya taka da sannu Zan setaki _dirty girl_ zakisan waye FU'AD. Babu Wanda ya sake magana sai da Husna taga ya Adana motar shi wani wajen da aka tanada Dan Adana motocin da sukazo siyaya wani katafaren wajen Saida wayoyi masu nunfashi ,Bayan ya adanata sai ya fito Yana Shan kamshi Yana bin Husna da wani mugun kallo ,Wanda yasa ta yunk'urin fitowa azaton ta magana yake Mata ta fito bakin be samu bud'uwa ba ,Tana Shirin fitowa taji muryar FU'AD na cewa "Ina Zaki ayawo? Waya kiraki ko kinyi ajiyane da zakije d'akowa? Sosai ran Ma'u ya bacci ,sai cewa tayi banyi ajiya ba sai aike da nayi na gagawa Wanda ya zama Dole ga Wanda na aikan ,afusace FU'AD yace ke Ina Wasa dake ne? Na Miki kama da sa'an ki ? Me kike nufi? Ganin kamar zai cakumo ta sai tace "Ni me nace , ALLAH ya baka hak'uri ban fad'a da wata manufa ba ,tsaki FU'AD yayi badan ya gamsu da Abin da ta fad'a ba ya nufi hanyar Shiga kata faren shagon siyar da wayoyin , iPhone 11 ya dankaro Mata ya biya ya had'o Mata da layi gud'a 2 ya fito a shagon batare da b'ata lokaci ba ,ko da ya dawo sai ce Mata yayi ke fito Nan yaci magani kamar me Shirin yin dambe ,Husna har ta Fara tunanin wanne irin tozarci ze Kuma yi Mata Kuma? Jikin ba kwari ta fito ,sai ya nuna Mata gaba yace ki zauna anan bawai Dan kin Isa ko Dan kin Kai ba Dan ma karki yaudari kanki ,sanan ga wayar da akasa na sai Miki ALLAH yasa kyauyancin ki ze barki ki iya Amfani da ita ya cillo Mata Kan cinyar ta ,sai ko tasa hannu ta d'auka zuciyar ta fal murna a zahiri Kuma Babu yabo Babu falasa sai dai godiya da Addu'a da ta Mai ,Tana cikin yimai godiya ne ya dakatar da ita yace kije kima wacce kikaci Albarkacin ta Amman bani ba Wanda d yinki da Bari duk 1 har gwanda ki Bari. "Sai ko Ma'u tace wanan ai farilla ne Tata ta musammance ai ,sai yace ke Kika sani kidai tsaya iya Haka karki zarme Kuma wallahi kisan irin maganar da Zaki dinga mayarmin Inna Miki Abu inba Haka ba Zaki Gabe shayi daga Ruwa yake. Husna Bata cemai uffan ba ta rabu dashi sai da suka kusa Isa gida yace Kuma aikwai sauran tamu dake Dan tsuguno be k'are ba sai kin amsa min wasu tambayoyi ,toh! Kawai tace Mai ta cigaba da kallon hanya har suka Isa gida wata magana Bata k'ara had'asu ba ,sai da y shigo harabar gidan ya ajiye mota a ma'ajiyar ta ya bud'e yayi ficewar shi yace Mata intaga wajen zama tayi ta zama shidai yayi gaba ,itama yunk'urawa tayi ta fito Tana cewa Bata min Kama da wajen zama ko yin wani abun nishad'i ba nida nakeda abinyi ,karaf akunnuwan FU'AD afusace ya juyo Yana tambayan ta Ni kike mayarma da martani tunda na Gama Miki komai na siya Miki wayar da ko mafarki Baki taba tunanin rik'ewa ba karshen ta har ki k'are rayuwarki ta gidan duniya Baki Isa rik'eta ba badan arzikin mumcy da ta had'ani dake ba ke kinsan karyar ki kice Zaki mallaketa shine zakimin rashin kunya a matsayin tukwicin wayar? Ganin Yana nufota sai tayi baya tayi nesa dashi Tana Shirin canja hanya ,shima k'ara nufota yayi ,sai ALLAH ya Aiko da aunty sa'adiya ta dawo daga wajen Mai yi musu guga ,sai ko tace ango da uwar gida outing Akan d'an fita ne? Sai FU'AD ya sakar Mata fara'ar Dole ,a aunty daga Ina kike Haka? Sai ta sanar Mai daga wajen Mai guga take ,sai FU'AD ya gaishe ta ,sai Husna ma ta gaishe ta Tana cemata wlh wai munje siyan waya ne Kinga wayar da akamin kyautan ta kitayani godiya aunty na ta mik'a Mata tanayi Tana kallon FU'AD ta wutsiyar ido ,shiko ya d'auke Kan shi har ya Fara tafiya ya tsinkayo muryar aunty sa'adiya ,lalai angwangwaje k'anwar tawa godiya mara'adadi angon Husna da sanaya Sha alwashi kabada kanka asare kaje gida kace ya fad'i na sanaya da Asma'u bada mamaki ,murmushi yak'e yayi yayi gaba kawai ya rabu dasu ,itako Husna har part d'in aunty sa'adiya ta k'arasa suka gaisa da Aisha ta d'auki baby Mimi dake Aiahan ta kusa komawa k'asar su ta ghana saura sati2 ba wani jimawa yayi ba ta koma part d'in mumcy Dan nuna Mata wayar da d'anta ya siya Mata bisa umarnin ta ,Tana Shiga ta sameta ita kad'ai FU'AD har ya haura sama,Husna na Shiga ta ma mumcy barka da gida ta mik'a Mata kwalin wayar Tana ce mata hajiya wayar Nan tayi kud'i da yawa Ni da me k'aramin kud'i ya siyamin ma ta ishe Ni amsa Kira dai ba wani Abu ba hajiya ? Sai mumcy tayi murmushi tace "Banda abinki Asma'u shi yaga ze iya tunda ita ya shiya Miki kema sai ki Shiga yayi kawai , ALLAH ya Baki ikon Aiki da ita ta hanyoyin da suka Dace ALLAH yasa Alkhairinta ya rinjayi sharinta agareki ,Dan ita wayar Nan da kike gani Akwai sharuka atare da ita Akwai Alkhairi yadanganta game sarafata ,Akwai Amfani Akwai akasin shi atatare da wayar zamanin Nan sai dai mu daure mudinga Abin da ya Dace da ita ba sab'anin Abin da ya Dace ba ,jeki abinki kinji Yar Albarka ,sai ko Husna tayi Tama mumcy godiya da Addu'a ALLAH ya jik'an mahaifan hajiyan da mijinta baban su FU'AD ,sosai mumcy taji dad'in Addu'a ,Dan Haka take k'ara son Asma'u Akwai nutsuwa da sanin ya kamata . ********** Mama habee na zaune taji anyi sallama da kamar bazata amsa ba sai dai ta amsa ,sai sukayi ido biyu da wata mata da tatab'a zuwa wajen ma'u tace ita 'yar uwar mahaifiyar ma'un ce wacce take Aure a India ,ganin ta da maik'o yasa mama habee fad'ad'a fara'ar ta kamar mayyar da taga nama, Tana Mata iso zuwa shifid'ar da tayi na wata tsohuwar tabarmar da kamar gadon ta taciyo wajen kakar kakar ta tsabar datti da tsufa ,sai ko ta kundumo ma humaira uwar ashar kamar wacce ta had'a nasaba da matuzawa wai ta kawo Mata dadumar baban su wacce yake zuwa sallar juma'a ,ganin rawar jikin mama habeen yasa humaira sauri ta d'ako ta shin fida Mata har ta Fara zama ma aka dakatar da ita ,Bayan sun gaisa take Kara Mata bayanin kanta inta aunty huwailan Dan da mama habee Bata Gama gano ta ba tadai sheda fuskar ,Jin wacce ake nema ya sa tad'an rage fara'a tace ta zab'i Aure ai Akan zaman gidan mahaifinta Tana can tabi namiji tabar babanta yanata fama da bak'in talauci ,sai ko aunty huwailan tace Aure ma'un? Humaira tace sosai ma kuwa Tana can da wani Wanda ko sanin asalin shi ba'ayi ba ko d'an mafiyane ko waye ohon Mata ita tace Taji ta gani ,sosai aunty huwailan ta fahimce zancen su akwa shagube da son Rai gami da hassada aciki ,Amman bazata tabbatar ba har sai taje sunyi magana da Ma'u Dan Haka tace a rakata gidan Ma'u , humaira har ta kusa sub'utar Baki tace Suma Basu San gidan ba ,sai mama habee ta Mata magana da Ido tace Basu sake zuwa gidan ba tun kaita da sukayi itace ta k'ular dasu har yau batazo ta gaishe da mahaifin taba har Yana gab da yafeta ,sai ko aunty huwailan tace ba'ayi Haka ba ,yanzu dai ya za'ayi nace wajen ma'un na Mata tasa Dan tayi Aure har ta Fara wofantar da mahaifinta Haka ya zama Dole na Mata wankin babban bargo Tana musu dabara Dan su kaita gidan ,sai ko sokwayen sukaji Dadi mama habee tace ki Bari Gobe sai a rakaki ,sai aunty huwaila tace ALLAH ya kaimu goben barin tafi ,mama habee tace sai goben inkinzo ,sai ta zaro 5k taba mama habeen ta karb'a hannu na rawa ,ta Mata godiya ,Bayan ta fita aka zageta wai matsiyaciya ta Rasa Abin bayarwa sa dubu biyar kacal sai kace wacce ta d'aurawa tsiya zani ,sai ko mama habee tace meyasa ma na karb'a ne ,ungo mayar Mata da kayanta ko ruwan leda tasa shegiya ,sai ko humaira ta karbi kud'i zata Mike ta Kai Mata ,sai Mama habee ta wafce ta bige hannun humaira ,ke bakisan gatse ba Dan ubanki memakon ki hakurtar Dani kin barni sai balok'ok'o nakeyi har da karbanki Zaki Kai Mata tunda Baki da tunani Dan jakar uwarki ,Yar kundun uba Banda bashin da iliya Mai kanti yake bin mu da kin mayar Mata da kyaci bantan ubanki muga ko ubanki zamu siyar mu biya Dan kinsan uban ki ba biya zeyi ba zece ai ba'ayi shawara dashi ba wajen ciyowa ,sai ko humaira ta keb'e Baki tace "bake kikace na mayar ba ai da Amfani zanyi dashi Dan bazanga samu Naga Rashi ba mama ,sai ko mama habee tace macuciya to bazakici sisi ciki ba tashi ki kaima iliya dubu uku ciki mu Fara rage Mai ta wurga Mata tace wanan ma biyan bashi zanyi ,humaira ta Suri kud'i ta fice Tana cewa wallahi 2500 Zan bashi Dan said naci wani Abu Nima ,sai mama habee take me kike cewa Dan ubanki kike magana ciki ciki meye Kuma wani tufayin? Fadi da hausa Dan kanuwar ubanki ? Humaira tayi waje tanama ta dariyar wai tufayin matsalar kyauye kenan...... [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg39 Mumcy Bata falon ganin Husna Bata samu mafaka ba tanajin motsi a kitchen sai ta fad'a." FU'AD biyota yayi yaga Babu kowa a falon yayi zaton wajen mumcy ta shige Dan Haka be tsaya bi takanta ba yayi part d'in sanaya Dan tun d'azu tace tanason magana dashi, be Bata dama ba sai yanzu ya tuna shine ze je." FU'AD bakin shi d'auke da sallama ya Shiga Bata falon Dan Haka ya Mata sallama a k'ofan d'akinta "yace gashi yazo tazo ta fad'i matsalar ta" Sanaya dake jikin dressing mirror Tana gyara kanta sai cemai tayi "ka shigo Ina d'an wani Abu ne please" Jin ta ambaci kalmar ban hak'uri yasa shi shiga. Yana Shiga yayi tozali da gashin kanta yanata walkiya yaci uwar Mai anata ciyar dashi da mayuka masu tsadar kud'i ,hankalinta kwance ta nuna Mai wata 1seater a d'akin wai ya zauna. Ganin besan manufarta ba Kuma Yana son sani sai ya biye Mata ya zauna, yace " Ina jinki Amman in magana zakimin ki rufe wanan abun tukunna Dan ba kasafai nafiye son ganin tsaraicin gashi ba,infa kina son na saurare ki kenan. Sanaya cewa tayi "gashin ma wata duniya ne? Meye acikin gashi ? Sai gani tayi FU'AD ya mik'e ze fice babu ko magana fuskar Nan kamar be tab'a dariya ba. Sai sanaya tace "Ina zaka kuma ko duk akan gashin ne? Kalon ta yayi ta gefen ido yace "bana maimaita magana in kin Gama Ina falo .......... Be fita ba sanaya tace "toh na rufe Zo muyi magana ta fahimta Tana Mai sakaya gashin ta da gyalen After dress. FU'AD cewa yayi "Ina sauraron ki ? Sanaya sai cewa tayi ,so nake na tafi Egypt Nan da 1week Kuma so nake ka Fara sanarma dady sanan duk yadda dady zai tambayeka karka nuna Mai nice nakeson zuwa bisa ummarnin ka ne nakeson zuwa zaka cemai kaji? FU'AD wani kalon shek'e k'e ya Mata Yana Mai tashi Yana tafiya cikin nutsuwa ya d'auko wani Abu a farar leda da wasu Akan takkada Fara ya dawo ya zauna Yana cemata "wanan Amman umarni kike bani ko ba shawara ba ko neman Alfarma? Far sanaya tayi da Ido Tana ce Mai "babu ko 1 kawai magana mukeyi tsakanin Ni da kai" FU'AD yace "aa umarni dai Dan yafi Kama da umarni" Sai ko sanaya ta harzuk'a tunda Haka kace "eh shi ne Kuma aikatashi ya zama Dole nifa autenka ko Kai basa gabana kasa anzo antakura Ni a Nan 9ja ko a gidan yarin Egypt iya kacin takura da matsin da Zan Shiga be Kai Wanda kukamim ba Kai da dady,Tana magana kamar zatayi kuka kuma cikin gatsali take maganar Tata." FU'AD sai da ya Gama k'arema Abin da ya d'ako kallo ya dubeta yace "meye wanan kike sawa a hannun ki? Sanaya harara ta wurga Mai ,tace ohon maka da ka d'auka sai abin ya baka amsa Tana turo Baki Tana d'auke kanta daga kalon shi. FU'AD mik'ewa yayi Yana Mai Shirin tafiya dashi,sai sanaya tace "Ina zaka min da Abu bafa a lefenka aka sako ba impact ga lefenka can ka d'ebe bana so bana buk'atan su Ni ka barni naje Naga iyayena kaji ko malam? Juyowa Yana jifanta da wani mugun kallo Yana cewa "ALLAH ya shirye ki haramun ne saka farce gashin ma ALLAH yasa bana doki bane Dan Naga lamarin ki da gyara Kuma Babu inda Zaki matuk'ar Ni Zan taimaka wajen tafiyar ki ,maganar tafiya Kuma kifi Ruwa gudu ke Kika sani yasa Kai Yana Shirin barin d'akin." Da sauri ta biyo shi Tana cemai "see u! 9ja man kawai ungo kataba kaji wuce na is natural from God ,ba'a tab'a ganin gashi ba angani an tsure shafi arziki Kar ka tafi baka dangwala ba ,sosai sanaya ta Sha gaban FU'AD Tana tura Mai kanta . Kad'an ta buge Mai fuska ,sai tureta yayi Yana cewa ,matsa can kazama Ina abun yake? Farce Kuma karna k'ara ganin kinsa ki dinga sanin hukunci ALLAH aduk Abin da zakiyi Kar Rayuwar wasu a waje ta Rud'e ki ko kasashen wajen ma ba kowane Mara tarbiya ba ke zuwa kikayi ma wajen muko haifar mu akayi acan ma inkin manta na tuna Miki inbaki da labari kije asanar Miki keda kaiki akayi daga baya ma har wani felek'e zakiyi muku 'yan can ne munada takaddun mu keko duk daga baya aka Miki ki Kama kanki karya gudu ya barki yarinya,ya fice yabar Mata falon. "Sanaya sai cizon yatsa takeyi da mita kamar tayi ihu take ji ,can tace inkasan wata bakasan wata ba wlh sai na maka sharri wajen gyatumar ka wallahi kuma sai nabar k'asar Nan Koda tsiya Koda arziki. FU'AD komawar shi part d'in mumcy ya had'u da mumcy da Husna sunata hira cikin nishad'i da birgewa har ze haura sama Bayan Yama mumcy sannu ,sai mumcy ta Kira shi ta tambaye shi lafiya ? Sai yayi gagawar sake fuskar shi yace "Mata lafiya Lau" tace Mai "yau bazashi office bane? Sai FU'AD yace "mata eh wata unguwa zasu da B2k abokin shi zezo gida ya d'auke shi" Sai mumcy tace "toh shikenan ALLAH ya kawo shi lafiya" FU'AD yace "Ameen" Mumcy da Husna anata Hira FU'AD na tsomo Baki sama_ sama yanayi Yana galama husna Hara ra itama Tana mayar Mai duk ba tare da mumcy tasan sunayi ba har B2k ya shigo bak'in shi d'auke da sallama. Yana Mai k'ok'arin rusunawa ya gaishe da mumcy fuskar shi d'auke da fara'a, sa'anan tun shigowa shi yake kalon Husna FU'AD ma ya lura da haka. sai ko FU'AD ya Harare shi Yana Mai cemai dalla malam ka fad'o ma mutane cikin iyali Babu neman izini gwauron banza kawai." Sai ko B2k ya juyo yace Mai "iyeee yaushe akayi Abu da har........Bari dai nayi shiru Yana sake tambayar shi Kai abokina tambayar ka zanyi Dan ALLAH seriously babu zancen Wasa wanan ba itace Dan girl ba babu Kama suna nasan ka fahimta Dan hoton ta baze taba bace min ba, please kace min itace abokina? FU'AD ya Fara hassala , mumcy ma ta Fara gano hakan lamarin ya Mata dad'i sai tace sandar da wani ya Raina ,wani ita yake nema ya samu ta duka ai,ta tafi d'aki Tana cema Husna tasa akawo ma B2k Ruwa. Husna da sauri ta amsa tana Mai niyar zuwa su gaisa da B2k da biyu ta nufi inda yake. Batayi aune ba sai muryar FU'AD ta tsinkayo Yana cemata ke Ina Zaki? Ci gaba tayi da tafiya Tana cewa ,zamu gaisa ne da abokin ka,sai yace dalla malama bazaku gaisan ba,shima B2k yace aa gaisuwa dai abokina ? Kar muyi Haka dakai Ina wuni Asma'u kamar Haka naji mumcy tace ko? Asma'u gyad'a Kai tayi tace hakane sunan , FU'AD yazo iya wuya sai tasowa sukaga yayi Yana cewa "wallahi kina k'ara amsa Mai ranki ze b'aci wacce batasan mutuncin kanta ba kawai,bace min anan. Husna d sauri ta nufi kitchen da aiwatar d umarnin mumcy ranta fes har da ita ake tusawa FU'AD haushi. Bayan shigar Husna kitchen FU'AD masifa ya farama b2k har ma'un ta fito da kwalin juice da glass cup a hannun da Harri Kuma na biye da ita a baya suna nufan inda B2k yake sai k'ara murmusawa yakeyi , FU'AD ya Gama zuwa iya wuya ganin Harri ne kawai yasa shi tsayawa da surfa musu masifa Amman Husna nata karb'an uwar harara da mugun kallo. Husna ce tace abokin mu ga Ruwa kasha ko? Ita Kuma harrin ta ajiye ta fita ,sai ko FU'AD ya shak'o Husna Yana cemata a gidan uwar wa k'ato ya zama anokin ki? Kema wuyanki ya Fara kauri ko yaushe kikaci Kika k'oshi da har Zaki goge bakin ki? B2K ne ya taso Yana cemai "haba abikina ba'a rik'e mace Haka Mata rarashin su akeyi." Sai ko FU'AD ya juyo Yana cemai wallahi karka karaso inda muke balle ka rik'e matar mutane Dan ihun gardi Zan maka Naga gama nema Shiga gonar da ba taka ba har ka zarme." B2K dai cemai yayi "naji Amman dai saketa daga mugun Rik'on Nan naka ,kamin Kuma bayani yadda Zan fuskanta shin wacece ita awajen ka a yanzu? Amman tabass wanan itace matar da kamin kyauta.........be k'arasa ba ...... FU'AD yace Kar ka k'arasa wallahi kana k'arasawa Ina maka wulak'ancin da baka tab'a tsammami ba ,tambayar ka akayi? Suda sarkin labari? Aku kuturu..... B2K dariya kawai ya Fara yima FU'AD. Sai FU'AD ya koma kanshi ya sake Ma'u ,Yana cemai Kai Zo kabar Min gida na fahimci tada zaune tsaye kazoyi har cikin gida na fita inzo in sameka, Yana nuna Mai hanyar waje da hannun shi." Ma'u na kwacewa tayi d'akin mumcy Tana murguda ma FU'AD Baki da hararar shi Tana cema B2k ,abokin mu ka gaida gida sai gani na biyu ,a zafafe FU'AD ya biyota ta k'arasa d'akin mumcy da sauri, B2k cewa yayi "to madam sai gani na biyu sai kin ganni" Yana matana FU'AD na tura shi waje Yana cemai malam na fasa fitar Dan Isa kawai ,Kai sai nayi shari'a ma dakai Dan iskan banza. FU'AD ya juya ze Shiga falo , B2k yace "To tafiyar Tamu fa? Sai ko FU'AD "yace bazanje ba" B2k yace Dan ALLAH kazo mu tafi kasan Ana jiran mu" FU'AD cewa yayi "akwana Ana jira Mana Kai namaka ta mahaukaci wallahi bazanje ba sai gobe inaga da Hali yau tsare gida na zanyi saboda tsaro badan tsoro ba ,yayi hanyar shigewa falon. FU'AD jiyo muryar B2k yayi Yana cemai ,lailai mutumina ka shak'a da yawa ,kayi hak'uri goben muje nazo gida mu tafi ko na jiraka? Harara FU'AD ya juyo ya wurga Mai yace ,ka jirani Kar ka k'ara zuwarmin gida inba haka ba ihun barawo zansa amaka." Ya shige falo ya turo k'ofa da k'arfi. B2K cewa yayi Kai ,na Tabo abokina fa da yawa wai ya suke da yarinyar Nan ? Yanzu ya kashe Mana fitar mu ? Dole na bada hak'uri kenan ince sai gobe zamu Zo in yaga dama? Ya zanyi Dole na nayi hakan ya d'aga kafad'a ya d'auki motar shi yayi waje Yana ma FU'AD muguwar dariya har da gyaran Kiran waya FU'AD har ta tsinke FU'AD be daga ba. Share And Comments [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* (Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg40 *Special thanks to all my Fanc*❤ # ONE LOVE# *SON SO FISABILILLAHI*🥰😍😘........ FU'AD ya fusata iya fusata ,hankalin shi be kwanta ba sai da yaga fitar B2k daga gidan. Yana shigowa falo ya Fara muzuran inda zai gano Husna kawai yake ,ganin babu halamum ta a falo ya haura sama a zafafe ,saman ma Bata Nan ko Ina ya duba Dan Haka ya sakko har kitchen ya duba sai su Hari da ma'aikata. Zama yayi a falo Yana fitar da iskar takaici Yana cewa "munafukar yarinyar Nan Tana wajen mumcy atunaninta ta tsira batasan karama kanta lefi tayi ba ,Dan Banga me hanani hukuntata ba wanan karon. FU'AD Yana zaune har mumcy ta fito Husna jiki na rawa yadda mumcy bazata gane ba ta biyo bayanta , mumcy ce ta Fara cema FU'AD. "Dama kana zaune Son ? FU'AD cewa yayi "eh mumcy" Mumcy cemai ta k'arayi "ya Ina B2k ya fitar ko kun fasa ne? "Ko d'agowa ya kalli mumcy beyi ba sai ma wayancewa da yayi da latsa wayar shi Yana ce Mata "eh mun bar fitar zuwa gobe ne" Mumcy daga Haka Bata k'ara cemai danme ba ,sai tace "ALLAH ya kaimu" Ciki ciki yace "Ameen" Husna ta kasa katab'us ,Amman ko yadda ta had'a ido da FU'AD batayi ,a zahiri Tana nuna Mai batayi lefin ba a cikin ranta Tana tsoron Abin da ze biyo baya." Har aka Kira magriba duk suna zaune sai Hira jefi jefi da yake Shiga tsakanin mumcy da Husna FU'AD Kam ya d'inke bakin shi sai ma'aikata dake Kara k'aina a tsakanin su." Ganin FU'AD kamar baida niyar zuwa masalaci sai da mumcy tamai maga sanan ya tafi Yana jifan Husna da harara Mai cike da gargad'i Mai zafi ,itako tasan za'a rina ,ko kalon shi takiyi burinta ya kauce inta haura samanta sai safe ita da sakowa Dan da biyu tamai haka tasan ba a d'akinta yake ba." Husna cema mumcy tayi Bari ta d'ibi abincinta ta haura Dan kanta ciwo yake da tayi sallah isha'i magani zata Sha ta kwanta." Mumcy tace Mata" to Allah ya sawake ki tabata kinsha maganin in bai saukaba ki sanar Dani da wuri inyaso ko asibiti FU'AD ya kaiki" Husna zaro ido tayi a hanzarce tace" Asibiti da FU'AD? Batasan maganar ta fito ba har mumcy tajiyo ta. Sai mumcy tace "eh meye Naga kin razana? Ko da matsala ne? Inda matsala ki sanar Dani Asma'u kinji? Da hanzari "Husna tace "a mumcy babu matsala Razana nayi da Kika Kira asibiti saboda tsoron Allura nakeyi,Amman Babu komai hajiya." Murmushi mumcy tayi kafin tace "toh ai in Banda Asma'u kamawa takeyi ai a d'aure Alkali ,inta Kama Dole amiki ,Amman Ina Miki fatan Samun Sauki ma insha ALLAH kinji? Da murmushi "Husna ta amsa da to nagode hajiya barin je na d'iba tayi hanyar kitchen. Bata tsaya Hira d su Hari ba gudun Kar FU'AD ya dawo ya sameta ta d'iba ta haura sama ,Tana Shiga falon ta tayi wata ajiyar zuciya na ta tsira daga hannun Zaki FU'AD. FU'AD be shigo gidan ba sai da yayi sallah isha'i sanan ya shigo sai da ya lek'a part d'in sanaya yaga tanata cika tana batsewa yasan akan maganar tafiyar da yaki Amincewa ne inya zauna ma fada zasuyi Kuma ga Abin fada can ya baro wato Husna, Haka ya fito yazo hukunta Husna kafin ya kula sanayan." FU'AD na shigowa yaga mumcy ita kad'ai ya tambayeta Husna" tace ta haura yin sallah Amman ba lalai ta sakko da wuri ba Dan ta d'ibi abincin tama kanta ne yake Mata ciwo. FU'AD sai cewa yayi a gaban mumcy barin haura in duba ta "mumcy tace to ka k'ara Mata sannu, yace" toh" FU'AD buga k'ofar ya dinga yi Yama Rasa wanne irin bugawa zeyi Dan ta bud'e ,ya buga yafi so 5 Amman Babu niyar bud'ewa , sai cewa yayi munafuka tasan Abin da tayi Tana jina har da haurawa sama wai ita munafuka me ciwon Kan k'arya ya Jima Yana bugawa kafin ya tafi Yana takaicin Abin da ta aikata Mai b'acin Rai Kan b'acin Rai. Yana sakowa wajen mumcy ya dawo yake cemata "ta Jima d haurawa ne? Mumcy tace "eh tun tafiyar ka masalaci" Azuciya FU'AD yace "tasan me ta aikata ,sanan afili yace "to har yaci ace tayi bacci na buga yafi so 5 Bata bud'e ba? Mumcy sai cewa tayi "Ina Jin tayi baccin. Sai FU'AD ya Mik'e zai Tafi Yace Sai Da Safe Mumcy , Mumcy tace "Allah ya bamu Alkhairi" Har FU'AD yaje k'ofa ya dawo yace ", mumcy bani phone d'inki na d'auki number aunty murja Dan naji kunya da ta kirani shekaranjiya ban Gaya Miki ba Kuma yanzu na Rasa gane number ta Dan na samu Kira daga mutanen da bani da numbers d'in su da yawa ,bani nayi saving Kar ta sake Kira naji kunya taji dad'in yimin tsiya Dan tace Tana Nan zuwa ma. Mumcy wayar ta mik'a Mai Tana cewa "ato gara da Tama Haka , ALLAH ya kawota lafiya. FU'AD ya Jima Yana laluben number da yafi buk'ata ayanzu Dan aiwatar da wani k'udirin shi ,be Gama tabbatarwa ba ya d'auki number sanan ya d'auki ta aunty murjan daga baya ya tafi Bayan Yama mumcy sallama ta 2." FU'AD da sallama ya Shiga part d'in sanaya ,cikin Kin haushin me sallamar ta amsa ta Mai Maraba da harara tare da oyoyo da kalon banza ,neman waje yayi ya zauna yace "ba akawo Mana dinner bane? Sanaya cewa tayi sun kawo Yana inda ka Saba ganin shi ,kazo ka baje a kujera kace kana neman girki? FU'AD beja magana ba ya nufi Kan dining sai da ya cika tunbin shi sanan yace ,mutum ko yaci abinci Dan ya Kori yunwa ko Kar yaci duk d'aya ,ita dai yunwa Bata da hankali inji yaran malam Dan har targad'e takeyi ,kulin bazakici abinci ba in ankawo Amman hakan baya sa nakasa Jin motsi tsakar dare ,Ashe ba'a fushi da ciki dasafe ma Ina duba Naga an wawiki wani sashi na abincin. Sanaya ta gama zuwa wuya da gugar zanan da FU'AD yake mata,sai cewa tayi ,maganar ciki ai ba magana bace afito fili agaya Mana tsoro ya hana. FU'AD sai cewa yayi kowa yayi zagi a kasuwa ai yasan da wanda yake yi ,ganin laushi ai baze Hana Tankad'e ba yarinya ,ya tashi ya nufi hanyar d'akin shi Yana Mata wani kallon raini." Yana Shiga ya rage kayan jikin shi ya Shiga bathroom ya watsa Ruwa ya fito yanata kamshi ya Fara duba wasu takaddu sai kawai al'amarin Husna da B2k ya dawo Mai ,atake ranshi ya b'aci sai kawai ya cafko wayar shi ya Fara laluben number da ya sato a wayar mumcy ya Danna Kira..... Ringing 1...2....3...sai aka d'aga cikin Sasauk'ar murya Mai Amo Mai dad'in sauraro yaji ance, "ASSALAMU ALAIKUM" FU'AD da ya Fara tantama anya ya samo number daidai kuwa? Can yaci an sake cewa waye Dan ALLAH? Anan ya ji kamar itace ,yayi k'arfin Halin cewa ,shine Kika gudu ko Baki iya neman gafara ba sai guduwa kina ganin hakan tsira kikayi? Jin anyi shiru ba'ace komai ba sai FU'AD ya Fara zargin Kar fa ba number husnan da yake zargi bane? Yana cikin tinanin katse wayar ma ,sai yaji ance "Ni ai ba guduwa nayi ba kainane yake min ciwo." Wawan ajiyar zuciya FU'AD ya sake kafin yace "karya kike ba gashi kin iya d'aga waya ba Amman so nawa na buga Miki d'akin Baki bud'e ba sai kace da kudinki aka Gina min Fallon ? Husna sai cewa tayi "to ai bacci nayi Kiran wayar nanne ya tashe ni,Kuma Ni Babu ko sisi na cikin Gina maka benen ka me nakedashi ,sai dai kawai nasan inhar da Rai da rabo." Da sauri FU'AD yace " karya kike makaryaciya ,Kuma karkimin Rashin kunya Dan me tarin lefice ke" Husna tace "Ni ba makaryaciya bace Kuma lefin me nayi maka?" FU'AD sai cewa yayi "yi Rashin kunyar ki son ranki kafin na had'u dake Gobe ,sai kinyi Dana sanin zamanki a gidan Nan ma gaba d'aya Zaki gayamin in B2k ne ya kawo ki gidan Nan ba mumcy ba" Budar bakin Husna sai cewa tayi "nifa Banga Dalilin kishi a Kan Abin da mutum be damu dashi ba,kafito a mutum sak kawai ko....Bata Gama ba FU'AD ya katse ta. Ke waye yake kishi? Ina Abin yake? Meye Abin kishin? "Husna sai cewa tayi to Babu Rami me ze kawo Rami? FU'AD be Bata amsa ba sai Jin sanaya yayi ta shigo d'akin babu sallama Tana cemai" wallahi baka Isa ba kazo d'aki ka tasa waya da 'yan matanka sanan Ni ka kuntatamin ka rabani da kowa nawa kazo kana enjoyment d'inka da wasu banzaye acan wallahi baka Isa ba........ Duk Abin da sanaya take fad'a Husna najin ta tayi tsuru tanajin drama ta cikin waya.......... FU'AD ko a zuciye ya taso yace "ke uban waye yake shashancin da 'yan matan? Tukunna ma waye banzar? Matar tawa ta sunna da shedu suka sheda aurena da ita kamar yadda tsiraru suka sheda naki ? Get out of my room now....... Ya nuna mata hanyar waje. Ya sake cewa I said get out ......... nonsense kawai ..... Sanaya fita ta farayi Tana cewa "wallahi talihi wether u like it or not wallahi sai na tafi Egypt wether u agree or.......Bata k'arasa ba FU'AD ya turata waje ya rufe k'ofa Yana Kara wayan shi a kunne Yana cewa." Kina Nan ,kijirani da safe kin k'arama kanki laifi.......be k'arasa ba........yaji Husna tace Ni ka rabu Dani kaje kaji da matarka Kar ka karbi hukunci yau.....Bata jira me zece ba ta katse wayar." FU'AD mamaki tare da Tambayoyi ya tsaya yi ,Ashe taji shirmen sanaya? Kuma me take nufi da Kar na karbi hukunci? Karfa tayi zaton kishinta nakeyi? FU'AD yace "Kai Ina" me zesa tayi wanan zargin ma bare takai ga ta gaskata Tama San bazan taba kishi akanta ba har mezanma kishi? Sosai kwanyar FU'AD ta Shiga lugude da kid'a,ga tunanin Abin da sanaya tamai da ya d'auka a matsayin shirme ,Yana sake tambayan kanshi meye hakan tayi kishi kenan ko hauka? FU'AD ya Jima Yana tufka da warwara Kan abubuwan da suka kawo Mai farmaki na hargitsin B2k da Husna ga sanaya itama. Husna ko tinani ta dingayi Akan kalaman FU'AD ,taso ta gaskata ya Fara kishinta duba da Abin da ya faru tsakanin ta da B2k ga yanzu ma da taji wasu kalamai daga gare shi duk da ba afili ya furta ba Kuma sanaya ce ta sashi yin hakan amatsayin ta na me kishi akan FU'AD d'in,Amman Tana karyata kanta wani lokaci na cewa FU'AD baya sonta Kuma baze sota ba Tama sani. Sanaya sosai taci kukanta ta k'oshi kafin ta samu tayi waya da mamynta ta tsara Mata yadda zata billomai ,taji ta d'auka tace zuwa gobe zata aikata sai taji daga gareta. Sosai charting da aunty huwaila ya gusar ma da Husna duk wani tunani Mai kyau da Mara kyau da yake cunkushe a kwanyar ta ,taji dad'in hirar tasu har aunty huwaila take nuna Mata yadda zata zauna da su mama habee ta Kuma sheda Mata jibi zata koma indiya bazata Sami Daman dawowa ba saboda Akwai Abu Mai mahimmanci da zata gabatar Gobe ,sosai Husna ta Mata fatan Alkhairi tace ALLAH ya dafa Mata akan Abun da tasa a gaban. Aunty huwaila Bayan ta wuce a mota ta koma gida kwana tayi Tana wasu mafarkai Akan matar da take cewa su Taimaka Mata Tana Kuka ,da safe da ta tashi cewa tayi Dole seta je taga matar Haka kawai taji Tana son Taimaka Mata inda Hali hakan atare da ita Dan Haka taje har gidan mahaukatan ba tare da kowa ya San taje ba daga gidan hajiyar su ,ta Jima Tana kwatance da dogon bayani kafin suka gano matar ,sai da Tasha Tambayoyi Tana basu amsa da Alkhawarin Taimaka mata kafin aka Bari zata gana da maralafiyar Mai rangwamen hankali." Tun da aka Taho da maralafiyar k'irjin aunty huwaila yake luguden bugu har aka kawota gabanta be Dena ba ,sosai aunty huwaila ta kad'u hantar cikinta ta kad'a da tayi tozali da da maralafiyar Dan sai da ta zabura ,ma'aikatan sukace ko ta Santa ne wani lokita (Dr Junaid)da wata mace ? Da kyar aunty huwaila ta seta nutsuwar ta tace "A kawai tausayi matar ta Bata har ta karajin Tana so ta taimaka Mata." Sukace kuma matsalar ta ba babba bace sai dai Akwai tsanani cikin matsalar ta gami da sark'ak'iya saboda ba hauka takeyi tuburan ba ga kuka da take yawan yi maganin akeyi babu fashi Amman sai aga ta Fara samun lafiya sai aga Abin ya dawo har daga waje Ana kawo Mata magani Ana Mata afmani dasu Amman har yanzu sauki be Gama zuwa ba ga wani hamshakin Mai Arziki da yake Taimaka Mata Yana k'ok'ari da Aljihun shi da jajircewar shi duk Akan ganin lafiyar ta Amman har yanzu. Sai aunty huwailan tace "ya suke da Wanda yake Taimaka matan? Sai likitan da yake kula da ita yace "babu wata alak'a tsakanin su shima bigeta ya kusayi da mota ALLAH ya rufa Asiri shine yaji Yana son ya Taimaka Mata ,shine yake Mata magani da dukiyar shi har yanzu da kina Nan ma jibi zai Zo akan maganar maganin ta......likitan be Gama magana ba wayar shi ta d'auki k'ara ya fita Dan Amsawa." Sai Aunty huwaila takai dubamta wajen matar da suke tare da Dr ma'aikaciyar gidan da take Bata labarin har daga waje Ana kawo Mata magani da sa hanun babban su na gidan ,sai ko aunty huwailan tace"Nima Zan iya kawo nawa maganin abata? Sai ko matar Tace ,ai baza abari a Bata ba ,sai aunty huwaila tace saboda me? Sai matar Tace "saboda dokar gidan ,Aunty huwaila sai cewa Tayi keko ki Taimaka min daga india Zan Aiko dashi ko ta hanun ki kinsan Haka kawai bazan cutar da ita ba me tasani ma da wanne zata ji da har zanyi mumunan kudiri akanta? Sai matar Tace badaga mu bane Haka dokar gidan take Kinga Kuma a hakan suna haukan wasu sunada mumunan kudiri akansu saboda tsabar son duniya anyi case a gidan Nan har so ba adadi ,wasu ne suke kashe wasu inda da Hali kiyi hak'uri kawai duk da na yadda dake. Sai aunty huwaila ta Fara Bata Baki Tana Mata Al'k'awarin kyauta mafi tsoka ,har ta Shawo kanta Akan in ta koma zata Aiko da magani daga india adinga Bata insha ALLAH zata samu lafiya. Matar Taji kyauta ta Amince ,har sukayi exchanging na number waya su matar tace sunan ta hindatu ,aunty huwaila ma tace sunan ta huwaila a India take Aure zata Mata magana idan zata Aiko da maganin sai taje Airport ta karbo ta Mata Amfani dashi. Sosai aunty huwaila ta sake kurama Mara lafiyan ido duk son ta da tagano Abin da takeson ganowa ta kasa Dole ta hak'ura ta tafi Bayan Tama hindatu d'an ihsani. Washe gari FU'AD da wuri ya bar sashin sanaya ya koma nasu mumcy Dan hukunta Husna ,Koda yaje sai mumcy ya samu ze haura mumcy tace Dan ALLAH ya kyaleta ta samu isashen bacci tunda ta kwana da ciwon Kai jiya yanzu Haka bacci ta samu inajin kawai ka Mata waya anjima." FU'AD badan yaso ba ya hak'ura ranshi Babu dad'i ,Harri ya Kira yace ta kawo Mai break din shi Nan ta kaima sanaya nata anjima shi da wuri ze fita ,har aka kawo Mai sunaci suna Hira har ya Gama yanata Saran ko Husna zata sako shiru har Yama mumcy salama tamai fatan dawowa lafiya ya fita." Husna Bata sakoba sai da ta tabatar FU'AD yabar gidan ,har k'asa ta durk'usa ta gaishe da mumcy , mumcy ta amsa Tana tambayan ta jikin ta? Husna ta amsa da "da sauki" Mumcy tasa tayi break tare da nuna Kulawar ta ga husnan tasa aka kaima sanaya nata kamar yadda FU'AD ya Basu umarni. Bayan Husna ta koma sama tayi wanka ,sai ga aunty sa'adiya da Aisha da sauri Husna ta karbi Mami Tana Mata Wasa ,sai Aisha take cewa kifin Rijiya kizo ki Rakamu store yanzu zamu dawo Amman in man d'in ki ya barki." Sai Husna tace dama duk na gaji da zama waje Dayan kamar kin Sami ,sai aunty sa'adiya tace kizo muje je ki Tambayo k'anin nawa ,sai Husna tace "ai ya tafi office" Sai Aunty sa'adiya tace meye amfanin phone d'inki? Sai Husna tace toh barin Kira naji bataso Susan Akwai wani Abu tsakanin su Dan Haka kirjinta na lugude a zahiri shahada kawai zatayi sai ta kirashi Tana Addu'a cikin Ranta." Yana D'agawa yace "Uwar Marasa kunya inajinki? Sai Husna tayi ta maza tace "Dama Dan ALLAH aunty sa'adiya ce tace na Rakasu store......Bata Gama fad'a ba ya katse ta da cewa bazaki ba me kafar yawo zaman gida Baki Fara Shiba ma tukunna.......Husna d'auke wuta tayi na wani lokaci sai ta wayence da tari Mara sauti .....sai aunty sa'adiya tace bani k'anin nawa Naga ke soyayya zaku gabza Mana bani mu kashe boss d'in ta karb'i wayar .... Sallama Tama FU'AD ,jin muryar ta FU'AD ya saki fara'ar Dole yace maman mami kun Gama shiryawa ne? Aunty sa'adiya tace eh kanina ,Husna kawai muke jira idan ka amince in baka amince ba ta zauna muje mu dawo. FU'AD yasan da kunya ya Hana Rakiyar sai yace To kuje Mana Babu damuwa na Baki amanarta sai kun dawo." Aunty sa'adiya tace "insha ALLAH na d'auka ,nagode sai mun dawo. Sosai Husna tayi farinciki ta karb'e wayar ta katse Kiran. Atare suka fita Bayan Husna ta gyare baby Mami ta feshe ta da turare masu sanyin kamshi ta rik'eta sukaje yima mumcy sallama dama ashirye take fad'uwa tazo daidai da zama. Mumcy ma fatan dawowa lafiya ta musu , mumcy nata ma Mami takwarar ta Wasa itako tanata bangala dariya ,har suka fita Mami na hannun Husna. Sosai suka siyoma Aisha kayan tsara da zata tafi Ghana dasu Dan saura 3days ta tafi ,a store d'in Aisha ta had'u da wani Gaye Mai Aji da kwarjini da kyar ya samu ta kula shi har wasu siyayan ya Kara mata ,cikin girma ya gaishe da su Husna da aunty sa'adiya duk ya kirasu da Aunty's. Bayan sun dawo gida sukaba mumcy Abin da suka siyo Mata na tsaraba a falon mumcy suka baje anata cin kayan kwad'ayi da suka siyo sukaba Harri takaima sanaya nata tunda batason Shiga cikin su sunjata Taki Shiga cikin su har sun Rabu da ita. Husna nata tsokanar Aisha Mai new catch." [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION* Pg41 Sosai suka Sha Hira da mumcy kafin suka ci abinci aka Kira sanaya Taki zuwa ,sukaci nasu aka Kai Mata nata ,sanan su aunty sa'adiya suka koma part d'in su Husna ma ta haura saman ta. wajen yamma lis sanaya tazo wajen mumcy kamar tazo Hira da itane Ashe tatace ta kawo ta. Sanaya ce ta dubi mumcy "tace Dan ALLAH tasa Baki akan matsalanta da FU'AD na cewa bazataje Egypt ba Kuma da ya amince har Yana cewa ita da zuwa sai Nan da shekara da shekaru Dan tsabar ya kuntata Mata har da cewa Kam gidan Nan babu Wanda ya Isa ya sashi ko ya hanashi Akan maganar tafiyar ta ,har inace Mai har mumcy? Ya budi bake zece eh ,na dakatar da shi nace karyayi kuskure Dan uwa uwace ,sai sanaya ta barke da kuka irin na tausayi sai da ta tabatar su Husna da Aunty sa'adiya basa nan. Sosai ran mumcy yad'an sosu a kalaman Husna na k'arshe ,wani bangaren Kuma Tana zargin FU'AD baze furta hakan a gareta ba ,Amman intayi tunanin yadda bayason Auren har yanzu biyaya kawai yakeyi sai taga ze iya firta hakan ko cikin fushine. Ana Haka sai ga ,mamyn sanaya ta Kira mumcy daga Egypt d'in, mumcy D'agawa tayi suka gaisa kowa na girmama kowa ,sanaya na sauraron su ta gane mamyn take ta kira,sai mamy ta gama Dora mumcy Akan maganar zuwan sanaya Egypt ta gama zazago Mata k'arya da gaskiya ,wani mumcy taji Bata yadda ba wani kuma tayi ta kokwanto akai ,akarshe dai taga masalaha kawai sanayar taje Egypt d'in taga uwar da zatayo insun rik'eta ma sun hanata dawowa shi kenan huta roro waken gizo yaki 'ya'aya ,Amman saboda mumcy ta nuna musu ba umarni suka Bata ba Kuma shawaraga da iko na wajen ta ,tace zatayi tunani akai zata Kira inta yanke shawara su jira wayar ta ,sanan mamy tace sai Taji daga gareta ta katse wayar ta. Sanayan ma da guntun hawayen ta ta mik'e Tana Kara cema mumcy ,nidai tafiyana Yana hanun ki hajiya , mumcy tace to sai kin jini Zan nrmeki Akan maganar ,sanaya tace to ta fita Tana goge hawayen ta na makirci Dan kukan a iya idon ta ya tsaya ba har ranta ba Dan ta Gama tsara tafiya Koda yadda FU'AD ko babu sai tatafi Koda zaduyi baram_batam da dadyn ta kuwa. Gab da magriba FU'AD ya dawo gida ,wajen mumcy ya Fara zuwa tamai barka da dawowa sanan ya koma wajen sanaya yaga tanata cika Tana batsewa ya fita harkar ta tunda yaga lafiyar ta ,sai ya haura saman husna yaga Tana Shirin fitowa ta sauka wajen mumcy da hannu ya maida ita Yana Mata muzurai ta juya zata koma ciki da sauri ya figota har Tana fadowa jikin shi yace "gidan uban wa Zaki? Wa Kika rains? Keda Mara mutunci Nan da ya kiraki 'yar uwarsu ,to in ma 'yar ubansu ce nayi mahanin shi yau saura ke ,Dan yau yasan yayi da d'an halak FU'AD Mai nasara Dan wallahi ko agidan Nan na k'ara ganin shi sai anmana shara' a Haka kema ko a filin arfa Kika hadu dashi ko ta cikin mafarki Dan nasan Baki da ranar zuwa bare shekara ,Kika sake Kika ko Kali inda yake bare kimai magana sai kin gane kuren ki walahi na Gaya Miki . Kuma in Kika sake magana da wani ma bashi ba irin maganar da Kika Mai sai kin sani wallahi ,ke ko bako akayi ma namiji a gidan Nan Kika k'ara gigin kawo Mai Ruwa sai na barar daku keda Abin da Kika kawo Mai d'in ,ai ba aikin ki bane ki rik'e aikin ki .....be rufe Baki ba ta kwace daga Rik'on d ya Mata tace. To Ni ka kyale Ni meye damuwarka da Ni ,Dan ya Fara min magana na amsa Mai ,wai Kai to meye hakan kakeyi? Ni sunan Abin nakeson sani? Ka fad'amin da bakinka ? Bata rife Baki ba ya matse Mata Baki Yana cewa ke Ni sa'an kine ? Ina fada kina bani amsa? Har wacece ke acikin mata da zaki titsiye Ni kina min tambaya ? Ke martabar Aure fa kawai nake karewa da barin ki zanyi ki tafi sakaka kamar tunkiya ,Dan bakya gabana dake da oho duk daya kuke a wajena ,sai ko Husna tace bakai zaka Fadi hakaba lokacine ze nuna. Sai ko FU'AD ya k'ara matse ta yace da wa kike? Lokaci ne ze nuna me? Me kike nufi? Yana matse Mata Baki da k'arfi ,yasa d'an k'ara tace eh Mana Inna bar hanun ka ko nabarma gidanku ai lokaci ya nuna kanshi na huta da zalincin ka ,sai FU'AD ya tureta da yaji manufarta yace ,sai me inkin bar gidan daidai ma kenan dirty girl kawai Yana dosan d'akin shi. Husna ta juyo tayi hanyar nata d'akin tace ,Nima Haka nakeso ai na mage kawai ,ya biyota a sukwane ta afka nata d'akin ta rufo Tana haki da ajiyar zuciya. D'akin shi ya koma Yana k'wafa da y kamata da ta Mai bayani ,Yana Shiga yaga gyaran da akama d'akin Yana Mai oyoyo sosai tsari da k'amshin d'akin suka d'auke shi Amman halaya ta mazantaka ko Halin wasu mazan sai be yaba ba Yama tab'e Baki ya d'auki hakan matsayin Dole tayi ai aikinta tunda dama tanan tafi kwarewa da rashin kunya ma Naga yanzu har dgree take Shirin yi Akan fitsarar tata,toh yarinya kin had'u da me hukunta ki. Husna Bata fito ba sai da Aisha ta hauro saman taga FU'AD ta tambaye su yace Tana d'aki dama taji shigowa Aisha sanan husnan ta fito kamar ba buya tayi ba ,suka sauka kasa FU'AD nata jifanta da hararar gargadi ,daga Nan ma part d'in aunty sa'adiya suka tafi suna Taya Aisha had a kayanta na barin gari,sosai suka Sha Hira kafin Husna tabaro part d'in ta dawo nasu ,a kasa wajen mumcy ta had'u da FU'AD ,Tama mumcy sannu ,sai mumcy ta tambayi Husna "Ina Aisha me zumudin barin gari? Sai murna take ,sai FU'AD yace . Aisha tafiyar tazo ne? Sai Husna tayi saurin cewa eh Mana bana gayama ba? Sai mumcy tamai wani irin kallo tace zaka Fara Halin naka na mantuwa ko? Sai FU'AD ya wayance yace kinsan abubuwanne da yawa mumcy ita Kuma Bata tunamin ba ,Yana mamakin yarinya karama tasashi yin karya yanzun Nan tasa ya sake kwai na karya ,sai Husna tace kad'ai manta Amman na tuna ma ,sai mumcy tace kyale shi Asma'u nasan Halin kayana fa. Yauwa FU'AD bikin gidan Alkali za'ayi wanan satin Dan Haka dakai da matanka duk zamuje har sa'adiya ma Dan Haka ka shirya zamuje _mother's day zamu dinner_ karkace ban fada maka ba. Yauwa aunty huwailan Nan ta India k'anwar mahaifiyar Asma'u ta Rokeni Alfarmar ka Taimakama Husna ta bud'e account zata Aiko Mata da sako taba babanta Kar naji wani magana kuma Dan nasan baze gagara ba ko zuwa gobe ne ka d'auketa kuje Ayi a wuce wajen , ALLAH yayi Albarka kaji. FU'AD dai kallon mumcy ya tsaya yanayi ,Yana ayyana ta dakeshi ta hanashi kuka ,ta sharemai hawaye da Addu'a,ya ya iya Haka ze cika umarni kodan wanan Addu'a,iyakaci in yarinya tamai kauyanci ya bibigeta. FU'AD be Mike ba mumcy ta Dora Mai da cewa ,yauwa son muyi magana ta fahimta ka bani aron nutsuwarka Nan ,kabar sanaya taje taga iyayenta kaji zeyi magana yaji mumcy nacewa inda rabon Taki dawowa ma kaga shikenan ,Jin haja yasa FU'AD cewa "Toh" Amman yarinyar naso sai na ladabtar da ita kafin Dan har nuna Mata nayi baza'ayi tafiyar ba ko meze faru,sai ko mumcy tace "au Ashe dai gaskiya ta fad'a har nake karyatata" Sai FU'AD yace wani Abu tace Miki ? Me Dame tace Miki mumcy ? Sai mumcy tace "abar wani tashin tashina tunda ka maimaita yanzu a gabana kace komai ze faru baza'ayi tafiyar ba daidai yake da kalmar da ta furtamin, FU'AD yace "wacce kalma mumcy? Mumcy tace "kawai magana ta wuce ,taje inta dawo falillahil hamdu in ata dawo ba shikenan. FU'AD yace ALLAH yasa ma karta dawo cikin zuciyar shi besan maganar ta fito ba ,sai ko mumcy tace "ba Amin ba" ta d'auke kanta kamar ba itace ta bashi amsa ba ,sai Fu'ad ya juyo yace "wai kinji ne? Sai mumcy tamai wani irin kallon tace as cikin k'irjin ka nashiga na tsaga zuciyarka na jiyo abun da kace,sai Fu'ad ya Sosa k'eya yasan bak'a mumcy ta Gaya Mai ,sai ya haura saman kawai. Bayan anfama cin abincin dare ,Husna ta haura zata kwanta FU'AD ya rutsata ,Yana kalubalantar ta Akan cewa ita tace a bud'e Mata account ko? Da Taki kulashi Kuma ita ta had'a Abin da mumcy Dan Abin yafi tafiya bisa umarnin mumcy ,ganin ya dinfarota ze bige kamar sauro sai ta magantu ,Tana Shirin ja da baya Tana cewa "Ni to Ni ko zancen ma ban sani ba sai yanzu a bakinka , FU'AD ya harareta Yana cewa mak'aryaciya rantse ? Sai Husna tayi fari da Ido tace "na rantse " yace "Haka ake rantsuwa a kauyen ku? Sai tace "ai Dan babu kyau rantsuwane Dan ita rantsuwa icen kabarice Amman da na rantse ,Amman Ni bansan maganar ba ma ,sai ya dungure Mara Kai har ya wuce ya dawo ya Fara cewa saura Kiki shiryawa gobe da wuri Dan zankaiki bisa umarnin uwa tagari ki bud'e na dawo dake saura kimin kyauyanci walahi tun acan Zaki gane kurenki. Husna dai azuciya ta dinga Mai dariya Tana Dole akaini a dawo Dani driver. Washe gari Bayan sun breakfast ,Husna tashirya cikin wani material Mai matuk'ar kyau d'inkin buba yaji adon duwatsu masu kyau da d'aukan ido tayi simple makeup abinta ,ta fito da mayafinta kalan flat shoe d'inta Mai kyau farare masu d'aukan ido shi Kuma material d'in Orange ne da fari ,ko da ta sauko ya harareta Bayan ya had'u da mumunan fad'uwa gaba adadai lokacin da ya kalli Husna kalon farko , mumcy ma husnar ta Mata kyau tace "Asma'u anfito zoki karya sai ku wuce ko? Husna cikin girmama a taje ta zauna kusa da mumcy tasa FU'AD a gefenta ,har mumcy ta gama tabar FU'AD awajen Tana cemai yayi sauri su tafi shida ze wuce office. Bayan FU'AD yanata jifan Husna da wani kallo da ya Rasa dalilin yinshi sai can yace "ke malama ko Baki gamaba ki tashi mu tafi Dan ba yaron gidanku bane Ni. Sai Husna tace toh ,nama Gama ,yasa Kai dak'in mumcy Yana cemata mumcy asa wani ya gyara sama Dan ALLAH kafin mu dawo ,sai ko Husna na Bayan shi zatama mumcy sallama itama sai tace ai na kammala da komai babu abinda ban gyara ba har d'akin ka ,sai mumcy tace sannu uwar k'ok'ari ALLAH ya bada zuriya d'ayiba ALLAH ya Baki me Miki ,Husna rufe fuska tayi Tana amsawa Dan ita sai yau ta tuna ko hankalinta ya tab'a tunano Mata Ashe fa wata Rana zata Sami yaro na k'ashin kanta? To yaushe ne? Tab! Shekarun Amman ai da yawa ,da tunanin a ya Fara haurawa Kan to dawa zata samu yaron? Sai tayi saurin gusar da tunanin ta Dan har ta Fara Jin kartayi sab'o .....da sauri ta bar d'akin. Shiko FU'AD ya cukule Rai da fuska har me take nufi Ana Mata Addu'a samun zuriya Tana dariya Mai nuna Jin Dadi? Har Tana tunanin zata haihu dama? Sai ya sake tambayar kanshi to da wa zata Sami yaran? Sai zuciyar shi ta amsa Mai da Kai Mana ,ta sauri yayi a'uzubillah! Kamar yaga shed'an Yana ayyana hakan ko amafarki baze faru ba har me akayi akayi Husna? Da ze malaketa a matsayin Mata? Har ta haifarmai yaran da zeyi alfahari da cewa nasa ne matar so ta haifar Mai ,Kai Ina...... FU'AD ma fitowa yayi ranshi fal wasi_wasin kalaman mumcy akansu hankalin ta kwance. Shiga mota yayi Yana jira Husna ta shigo ,sai ta tambayeshi ta window mota Tana cewa "gaba ko baya Zan Shiga? Sai kawai ya juyo yace sama Zaki hau ko boot d'in motan sai ki zab'i 1 ciki ya d'auke kanshi ,Abin be bama Husna haushi ba tasan za'a runa Dan dole ta fuskanci abubuwa sai dai tayi hakuri har ALLAH ya dawo dasu gida. Sai kawai ta marairace murya tace ,Dan ALLAH Yaya FU'AD ,har ilahirin jikin shi yaji sautin sunan da Husna ta kirashi dashi a yau dama Bata taba kiranshi ba,sai ya tsinci kanshi da Satan kalon ta ,sai ta Kama shi sai kawai ta sake cewa Bari na zauna a baya Dan Naga hankalinka yafi kwantawa na Shiga Bayan ,sai ta Kama marfin k'ofar baya zata bud'e sai kawai yace "malama ki dawo gaba" murmushi ta sakar Mai tace "to Yaya FU'AD nagode" sai ya Fara tambayar kanshi godiyan me take Mai? Ko da yake d'abi'ace Mai kyau ,koma dai meye ita tasani dai. Tunda FU'AD yaja mota be tsaya ko Ina ba sai danja inda traffic ya tsaida su ,anan ya hango want mutum Mai shirgegen ciki Yana karema Husna kallo ,idon FU'AD yakai kanshi ,har harara ya maka Mai (harara a duhu inji masu iya magana) sai da aka basu hannu ya fizgi mota sai da Husna ta tsorata Dan kiris ya bigi Bamba wani mota ,sai da tace "hazbinallahu .....tafi a hankali Yaya FU'AD , ALLAH ya tsare ku da tsarin karfe ,Kalonta yayi ya ce bake Kika ja Mana ba. Husna tamai wani kallo tace "da nayi me? Sai ya wayence da cewa "Ameen" ya amsa Addu'a da tamai yaki Bata amsa. Bayan sun Isa bank d'in ya Kira wani abokin shi yace sun iso ,Tana zaune aka Mata komai sai Abin da ba'a Rasa ba aka cike meta har form ATM aka Bata ta cike Abin da Bata gane ba shi FU'AD din ne yake Mata ko ya Gaya Mata ,yanata cewa taci sa'a Bata mishi kauyis ba ,suna Shirin tafiyane shi FU'AD d'in sun tsaya suna Hira da abokin nashi sai wani had'ad'en Gaye ya kawo ma Husna farmaki da tayin soyayya shi ,tanata basarwa har juyawa tayi Dan ya rabu da ita ,Tana sane Taki cemai matar Aure ce ita Dan tasan da FU'AD suke tare ,har sai da FU'AD ya hango su babu sallama ya bar abokin ya saki Baki Yana zuba kamar laya ,yazo ya same su ya Fara cema gayen ,lafiya malam? K'anwar kace? Ko yayarka? Shire Nd Comments [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIKON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION* Pg42 Gayen kafad'a yad'aga ma FU'AD yace ko d'aya kawai dai waje na gani shine nakeson isar da sako Dan na Raya furena da kyau.....be rufe Baki ba FU'AD yace furen uban agidan uwar wa zaka Raya furena da matar Aure? Ko agarin mahaukatan ku Haka ake yi ? Ke Baki Gaya Mai ke matar Aure bace? Husna hankalinta kwance tace ,Ina Shirin Gaya Mai ne kazo ka same mu. Sai ko FU'AD yace ,to mahaukaci da aurenta ka aikata haramum aje Ayi istigifari,ya Kama hannun Husna ko sallama bema abokin ba sai waje ,suna fita ma yaci Karo da wani Yana kallonta har kamar Yana Mata murmushi ma sai Fu'ad ya Harare shi ya sata a mota Yana cewa "kinsan mumcy ta aurar dake in Kuma kin gaji da auren da ta Miki ne kiyi gagawar sanar Mata ,Amman ba kizo kina d'aukan hankalin mazan waje ba. Ran FU'AD a b'ace ya ajiye Husna ya cilla Mata ATM card d'inta ya fice zuwa office ran Nan babu dadi. Shigar shi harabar office din keda wuya B2k ya hango motar dama yazo yanata jiran shi ,da sauri ya k'araso wajen shi da yaga ya fito daga motar. FU'AD ya ganshi Amman ya d'auke kanshi ,sai da B2k yasha gabanshi tukunna FU'AD ya kalle shi yace "malam bashi ko Tara? B2K yace ko d'aya Amman ya zama Dole ka tsaya muyi magana ,Kar 'yan baka su samu Abin yi Mana ,dama suna neman sugammu a rana suji dad'in yimana dariya da shewa, sai Fu'ad yace to waye ya jawo sai me Dan sunyi kamawa hakan tayi ,sai B2k yace Bata kamaba abokina ka saurare ni ,sai Fu'ad yace bani da lokacin ka yanzu Dan Kai da kanka kasan ba iyanzu nake zuwa office ba na makara Bari na k'arasa mayi magana in kaso yin hakan letter. FU'AD Yana tafiya B2k na biye dashi har office d'inshi dake Hawa na biyu , office had'ad'en sai na'urar sanyaya waje da take bada sauti ga wani uban kamshi komai dai yaji na Alfarma , FU'AD zama yayi sanan ya kalli B2k ya watsar ya d'auke kanshi Yana Shirin zama a kujerar milkin shi in Yana Kan Aiki. B2K cewa yayi ai ba bak'on zafi bane nid'in ,in yau ba'a bani masauki ba ai abaya anbani barin zauna muyi magana. B2K yace "FU'AD lafiya naganka sai Hawa kake kamar Akwai Abin da ya faru dakai na baccin Rai ALLAH yasa ba Akan wanan pretty bane.......be rufe Baki ba FU'AD ya d'aki table d'in gaban shi yace "karka maimaita min Abin da kamin Ni fa banga amfanin bita da kullin da kake min ba ,Ina ruwanka da baccin Raina ko kunci na meya shafeka computer sarkin naxari? B2K sasauta murya yayi sanan yace "ALLAH ya huci zuciyar abikina cool ur mind ,duk Bata Kai Haka ba manta da komai please ,I don't mean 2 hut u guy , ALLAH ya baka hak'uri komai ya zama pass tens ,Amman ya kakata ka min dogon bayani akanta Dan na kiyayi gaba Dan Naga da an tabota kake fita a giya.......be rufe Baki ba FU'AD yace "naji jeka latter will talk about her ,not right now,Yana nuna Mai hanyar waje alamar ya fita. B2K ne yace "ok" nabarka lafiya ,in Mai kasancewa ta kasance dai ka yafeni in na hurting d'inka Dan ........bai k'arasa FU'AD ya bar inda yake ya k'araso inda B2k yake ya kamo kafad'un shi yace meye Haka abokina? Kasan banason irin wasan Nan ko? Mutuwa dama ai tunda mu musulmai ne muminai mun yadda da ita Kuma mun San Dole ce Amman kafi kowa sanin banason irin wasan Nan kasani Kuma. B2K ne ya saki murmushi ciki ciki sanan yace bacin ka Bari na gano lagon ka acikin zuciyar shi Dan tun da wani aminin su ya tab'a Mai irin Haka sai ko Abin yazo akan dadai ALLAH ya karb'i ranshi suna Rabuwa da FU'AD da B2k Bayan ya Gama musu maganar mutuwa duk sun d'auki Abin Wasa ko minti talatin Basu samu a tsakanin su ba ya gamu da hatsarin mota ya mutu a take tundaga Nan FU'AD ya tsani wasan mutuwa Dan ji yake kamar hakan ze farune babu makawa bawai mutuwar yake tsoro ba tashin hankalin lokacin yake tsoro. Dan Haka B2k ya tuno Mai duk da bada gayya yayi ba sai Dan ya Rasa hanyar Shawo Kan abokin nashi sai da dabarar hakan ta fad'o Mai yanzu gashi har ya sakko. FU'AD cemai yayi ka dawo ka zauna muyi magana ,sai B2k yace kace na dawo letter ,ka Bari when u are free sai muyi magana ,sai Fu'ad yace eh naji Amman ka zauna ko kallon ka nayi 4more 30mnts ma sai ka tafi ma had'u anjima ,sai B2k ya zauna Yana cewa banaso nayi jayaya ne da bazan sake ko 1mnt ba , FU'AD yace eh naji dai shegen abokina ,shi Kuna B2k yace Dan iskan abokina dai sai e ya k'ara cewa a ka manta d'an guguwan abikin ka dai tunda har iska tayi d'a guguwa ma zata d'a sai suka sa dariya dukansu har fira jifa_ jifa ya Shiga tsakanin su. Shigar Husna keda wuya ta Sami mumcy sunata Hira da su Harri itama ta zauna anayi da ita anata nishad'i , mumcy ta tambayi FU'AD Husna tace yace ace Mata ya wuce office, mumcy tamai Addu'a dawowa lafiya. Bayan hirar husna d aunty huwaila a waya ta sanar Mata FU'AD ya bud'e Mata account d'in ,har ta tura Mata account number, sosai aunty huwailan Taji dad'i har Tana sama FU'AD Albarka ,Husna har ranta taji dadin musamman da ta Mata Addu'a samu albarkar Aure wato haihuwa ,Amman daga baya tace wama yasan lokacin koma mutuwa zanyi bazan samu masu yimin Addu'a ba , ALLAH masani nidai ganinan banma sani ba ,jin Shirin yayi yawa ne Aunty huwailan ta dawo da Husna daga duniyar shirmen da takeyi ,suka cigaba da hirar su tanata d'orata Akan hanyar mallakar miji ta tsaftataciyar hanya Kuma a sauk'ak'e. Bayan FU'AD ya dawo gida sosai ya titsiye Husna Yana surfa Mata ruwan masifa da dikoki Akan mazan waje ,Husna ta dinga turo Baki Tana cewa to Inka sakeni ai acikin sune wani ze aureni ko ka manta kace jona maka Ni akayi inkaga Dana zaka Kara min wuta NE naje na karata kaima ka d'auko 'yar luv wacce take type d'inka ka manta da wanan batun naka? In kamanta Ni na adanashi a kundun Adana mahimman baya naina Kuma Akwai Randa mumcy zata Mana Alkalanci akai.......Bata karasa ba taji saukar wayar hanun FU'AD Akan bakin nata atake ta tsuguna saboda wani azabar zafi da ya ziyarci bakin ,Tana bud'e hannu Tana jini ,shima yazo d'aukan wayar shi Yana Shirin rufeta da masifa yaga aikin da ya Mata sai yayi saroro ,Husna tasa kuka tayi hanyar sauka Tana cewa wallahi tun yau d'inan ma mumcy zata Fara Mana alkalancin ba sai mun d'auki dogon lokaci ba har ka Fara Shirin illatani ? Cikin kakausar murya FU'AD yace ke karki sake ki sauka k'asa. Husna tace sai na saukan so kake nayi mushe a saman ? Tana Shirin sa kafarta a kofar FU'AD yace "bakiji ba wallahi in Kika fita ......be k'arasa ba Husna tace wallahi ko me zakamin sai na fita Haka kawai ka dakeni ka hanani kuka.....tasa Kai ta fice sai Fu'ad ya bita da sauri saurin ba d'aya ba ya kamota yayi_yayi ta dawo tace wallahi bazata dawo ba ,ganin Bata da niyar komawa d'akin ga jini na zuba a bakinta ga hawaye da takeyi sai Fu'ad ya sungumeta kamar jaririya Tana dukan shi ta kirji ta kanshi Amman bema San tanayi ba sosai ya rik'eta ya had'a da k'irjin shi be ajiyeta ko Ina ba sai d'akin shi ya direta a gadon shi ,Tana tureshu Tana cewa Ina zaka kaini Ni ka rabu Dani wallahi. Ganin ta a gadon da sai dai hanun da su Kai yau itace a kwance male_male ga k'ato a kusa da ita yasa k'arfin zakin shi ya danneta Yana Shirin Ciro Abu a karkashin gadon sai kokuwa cirowa yakeyi da hannu 1 sai ko Husna tace "ka rabu Dani wai me zakamin wallahi in ja cutar Dani ALLAH baze barka ba me kake Shirin yimun ne a banzan gadin Nan mugu Mai Shirin aikata .........sai ya toshe Mata bakin ya sako first aid box Kan gadon ,Tana gani tadan samu sukuni daga Abin da take Shirin firtawa ga FU'AD ,Tana tirjewa Yana saka k'arfin da ALLAH ya bashi Yana sarafata har ya Gama gige Mata ya sa mata magani inda taji ciwon ma kad'an nne ba kamar yanda yayi zato ba shi yisa hankalin shi ya tashi shima ,sai ce mata yayi uwar raki ji dan Abin ,Mai arahar jini kawai tashi kiban waje Ni ,sai alokacin ya sake ta daga Rik'on da ya Mata ya bar kusa da ita gaba d'aya ma ,sai ko borin kunya ya Hana Husna tashi sai cewa tayi,ai kawoni akayi sai a mayar Dani inda aka d'aukoni ..... FU'AD gadan_gadan ya taho Yana cewa Bari na nuna Miki karyar rashin kunya fitsarariyar yarinya kinji gado Mai taushi Zaki more to Baki Isa ba Baki da mahali acikin shi ,Yana Shirin tab'ata ,ta gice da sauri tace zanma tashi muguntar da kamin ma ya Isa ,ta Mike jiki Babu kwari ga tarin kunya da taji duk ta lulubeta ,da sauri ta fita Tana cewa , ALLAH dai Yana kallon ka , FU'AD yace ke baya kallon ki kin buya a gidan mumcy Yana Shirin Shiga bathroom din d'akin shi. Husna batayi tunanin fita ba yanzu ,d'akinta ta nufa Dan taga yadda aka Mata da Baki Dan taji yad'an canja Mata , dressing mirrow ta duba taga Ashe fashewar Babu yawa kamar yadda Wanda yayi aikin ya fad'a Amman jini ya zuba ,sai ta canja hijab ta nufi kasan mumcy Gam taji alamun FU'AD ya rufe ya kuma tafi da makullin ,k'wafa tayi da tsaki ta koma d'akinta Tana tunanin muguntar FU'AD har take auna yama zece Yana kishin ta ko zuciyar ta zata karanta Mata k'arya wanan Sam ba gaskiya bane . [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg44 Bayan dawowan su mumcy kowacce tayi part d'in ta Bayan mumcy ta yad'a FU'AD da sanaya ta yi musu nasiha d togaciya ,shi Akan kula da hakkinta ko d Tana can irin su kiranta yaji lafiyan ta ,itama irin tasan tanada Aure tabar mijinta ta kula da kanta duk sunji sun d'auka kamar gaske daga baya ta musu Addu'a akan sai goben su aunty sa'adiya sa rakata Airport d'in Kuma har da FU'AD d'in za'aje. Yau FU'AD a d'akin sanaya yake yayi k'ok'arin zama a falonta Yana kalo Yana Amfani da wayan shi sama_sama Yana Hira da ita ,itama Tana bashi amsa sama_sama Har yake cemata yaushe Zaki dawo ? Ta yatsuna fuska tace "za muyi waya kasan tafiya itace da Kai ba Kaine da ita ba" FU'AD kalon ta kawai yayi yace "hmmm" Sai Tana tashi tace "Bari taje ta k'arasa had'a kayanta. Shiru_shiru Bata fito ba kusan awa 1 Dan said kawai ya tashi ya wuce d'akin shi. FU'AD kwana yayi Yana tunanin wasu abubuwa game da Husna sanan ya dawo da tunanin shi Kan sanaya a tunanin shi tasan meye Aure tunda ta girmi Husna Kuma idonta yafi na Husna bud'ewa Amman tayi buris da komai kamar yadda yakeso shidai har Rasa yadda ze Kira Auren shi yake,ya Jima Yana tunani da dogon nazari kafin ya ajiye komai ya kwanta. Washe gari da asuba ya tashi sanaya akan tayi sallah ya wuce masalaci ,Amman har ya dawo Bata tashi ba sai da ya tsaya akanta sanan ya samu tayi alwala tayi sallah. Bayan sund'an koma bacci Basu tashi ba sai da Harri ta kawo musu break d'in su ,Bayan FU'AD yaci ya barma sanaya nata Dan so 2 kacal suka tab'a Break tare ,ya tafi Dan ya samu yayi wanka. Bayan ya fito yace ta gama shiryawa Kar azo Ana jiranta Dan babu yaron ta a duk gidan be jira amsawar taba ya fice yayi part d'in mumcy. Tare da Husna ya same su suna breakfast suna Hira ta surika da surika ,shi kanshi Abin ya birge shi Amman be nuna ba, a fili sai ya gaishe da mumcy har k'asa ,ita kuma Husna ta gaishe shi cikin girmamawa da Ladabi ,sai Fu'ad yace kun shirya ko? Dan bazan jira kowa ba nasan matar bro Bata da case ,sai ko mumcy tace "itama Asma'u ai Haka Akwai cika Al'k'awari yadda na Santa,sai ko Husna ta keb'e Mai Baki irin yauwa kaji? D'inan taji an yabeta" Sai FU'AD yace "Kai mumcy kamar kece lawyer ta" sai mumcy tace waya sani baka da wata maganar ta Isa daga Haka? Inci gaba da kareta. Husna har murmushi tamai gami da fari da Ido ,abun Yama FU'AD wani iri Amman yaki yadda yadda yadda kirashi da kyau Kuma har ji yake kamar ta Kara yi Dan ya gani. Husna ya harara yace tashi kije ki cema ammyn mamy ta gama shiryawa? Sai ko mumcy tace "haba son meyasa kake hakane? Bata da suna ne? Sai kayi gaba sai ka dingayin baya ,yau ka canja gobe ka koma Ruwa. Sai yace "Kai uwa ta gari toh husuna take ko Asuma'uu tashi kije ki Tambayo Ina magana kunata bin mutum da Ido. Jin ya dai Kira sunan ko Yaya sai Husna ta mik'e ta tafi fad'a mata. Bayan tafiyar husna fad'a mumcy ta dinga yima FU'AD har da nasiha Tana nuna Mai Jan matan shi a jikin shi ta yadda inya samu zuriya dasu zasuji dadin shi ,shi ko FU'AD cream yayi a zuciya tab wai zuriya a Ina Kar kima Sarai mumcy Dan Banga lokacin ba yara daga muna mace sai Mai over wayewa da nuna Isa Ina Mata a Nan dama_dama muna macen ma ita husunan Kai ko itan ma Ina abun yake Kai can ta gane Banga yadda za'ayi ba da har zanyi tunanin samun yara daga gareta ko ita sanayan. Sai da mumcy ta sake maimaita magana sanan ya dawo daga duniyar tunani da ya lula. Bayan Husna ta dawo tace "aunty sa'adiya ta gama shiryawa hanun ta d'auke da mamy tanata Mata Wasa" FU'AD ido ya zuba musu Karo na farko da yaji yanason yaro sai Husna da mamyn suka bashi sha'awa Amman ya fizge ,sai mumcy ce tace sakwarata Zo mu gaisa. Sai husna ta mik'a Mata Tana cemata hajiyar mu sakwara fa kikace takwara dai ko kice namcyn ki kawai zamufi understand ,sai ko FU'AD ya juyo ya kalli Husna Yana tunanin dama tasan wani Abu daga cikin harufan turanci? Sosai mumcy takema mamy Wasa itako tanata dariya dama Akwai fara'a musamman in taga Husna Dan ta saba da ita sosai. FU'AD tun Yana basarwa akan birgewar da Husna da mamy suka Mai sai da takai yace kawo min me sunan uwa tagari mu gaisa ,har ta yunk'ura zata kawo Mai sai yace Bari ma nazo na d'auketa ,sai ya k'arasa yasa hannu ze d'aketa sai hanun su ya gauraya Dana Husna sai da wani kyakyawan sak'o ya samu matsuguni a illahirin jikin su ,ita dai Husna ta fassara shi da oho koma meye,shiko FU'AD fassara Yamai kala_kala Dan sai da Yama Husna wani kallo da shi kad'ai yasan ma'anar shi ,da yaga mumcy na kalon su sai yaji wani iri sai ya d'auki mamyn ya Fara Mata wasa Yana cemata dadyn ta ya kusa dawowa ,itako many Taki Mai dariya kamar tasan be Saba d'aukanta ba ,sai ya sake canja salon wasan nashi Yana ce mata yarinya me fiskar mamanta me kyawun babanta Dan sauran abubuwan duk namune ,mamy sai ta Fara keb'e Baki alamun kuka ,sai ya lakato Mata kumatu Yana cewa bazakimin dariya ba kodan Kinga bana samun lokacin renon ki ingaya Miki babanki tare da mumcy sukayi renina Nima naso yin renon ki Dan dai ba anan aka haife ki bane yanzu Kuma da kukazo Mana naso yin hakan Aiki NE baya bani dama ,bazakimin dariyar da Naga kinama su mumcy da aunty Nan Taki ba? Sai ki mamy ta rushe da kuka kamar wacce aka bigeta sai Fu'ad ya hau salati Yana cema Husna "ungo rik'eta jijigata Dan ALLAH kiji yarinya" Husna na karbanta ta jijigata ta Fara Mata Wasa sai tayi shiru , mumcy nata mai dariya ,shiko cewa yake mumcy ko kyuya ta Fara? Be Gama tambayar shi ba yaga ta Fara bangalama Husna dariya sai ya dawo kusa dasu Yana cewa laaa kuji yarinya Ni zakima Haka? Yana tab'a kumatunta ,sai ko mumcy tace "kaga banbancin salon wasan mace Dana namiji ko? Kai duk a wasanka baka Kama hanyar da zata ma dariyar ba sai kanayi kamar labari kake Bata ,itako Husna tsokanar ta takeyi Tana sata nishad'i zauna kayi course indai kanaso ta Saba dakai nidai barinje nayi sallah walha inkayi biyaya Husna ta koyama yadda ake Reno kafin naku yazo. Sai FU'AD ya harari Husna ,Bayan mumcy ta shige d'akinta sai Fu'ad yace ke ya kike Mata take dariya ? Ina magana kina sauraron mutum. Sai Husna tace kunuwana fa abud'e suke ba atoshe ba ,sai Fu'ad yace "rashin kunyar Zaki min? Ya dungureta Yana cewa ,Zo mamy na ,sai ko ta manne ajikin Husna, FU'AD yace Kai kuji sai kace itace mamanki, sai Husna tayi wani fari da Ido tace to Ni d'in da ba mamanta nake ba? Yatace halak malak aunty da Yaya sun bani ,sai ko FU'AD yace matsani Mara kunya kidai haifi naki wanan ta mutane ce sai Husna tace kaide ka haifo naka Ni ai Rai dai ,Kuma ko ayanzu an haifo min ,sai Fu'ad yace fitsarariya sai a haifan Miki Kam Dan ke Babu Abin da Zaki iya akace Miki yara iriki ne zasu iya haifan yara masu kyau Haka? Dallah bani Yar mutane ya kwakwumeta a jikin Husna Yana cewa nine babanki yarinya Zo kiji inkin girma Ni Zan d'auki dawainiyar ki ,Yana karbanta ta Fara kuka da sauri yace ma Husna Zo kimata Wasa Dan tayi shiru ,Husna na Fara Mata wasa tayi shiru har da dariya ,suna Haka sai ga aunty sa'adiya ta shigo hanun ta d'auke da hulan mamy ,sai tace inyeee iyayen mamy Ana Shan luv ne da Yar taku? Sai a yanzu FU'AD ya lura yaga yadda sukayi daf da juna shida Husna har kayansu na gogan na juna sai kunya ta kama shi ,sai ya ajiye mamy a cinyan Husna batare da tayi aune ba Yana kamo hannun t Yana cewa rik'eta da kyau barin ma sanayan magana ta fito mu tafi. Dariya aunty sa'adiya ta dinga Mai Dan ta gano shi . Bayan sun taho dashi da sanaya tanata rangaji kamar iska na kad'a bishiya ,sai ta fashe su lokaci na farko da bakinta ya Fara gaishe su ,har d'aki ta Shiga ta ma mumcy sallama ,tare suka fito da mumcy Tana Mata fatan sauka lafiya Bayan ta cikata da tsaraba ,uwar iyayi harda cewa ta barshi sai da mumcy tace ai ba ita taba ba su mufeedan ta zata kaiwa ,sai ko sanaya tace hmm mufy ta kowa da kowa kenan ,sai aunty sa'adiya ta mayar Mata da martani ai halinta daban yake awaye take kowa natane ta iya mu'amala ,sai jikin sanaya yayi sanyi Amman taso mayarma da sa'adiya martani sai Fu'ad ya taho Yana cewa kufa nake jira Ina mota . Sai sukama mumcy sallama ,har bakin mota mumcy ta rakasu suka fice daga harabar gidan. Isar airport jirgin su ya kusa tashi ta musu sallama suka Mata fatan sauka lafiya sukayi bankwana ta shige ,shiko FU'AD ko nuna Mata wata irin kulawa irin ta miji da Mata be tsaya yi ba sai kawai cewa da yayi sai munyi waya ya wuce mota abinshi, su Husna sukabi Bayan shi Husna na gaba da mamy sai Wasa sukeyi aunty sa'adiya na baya. Bayan isarsu gida duk wajen mumcy suka tsaya kafin lokacin tafiyan su biki yayi su koma Dan yauma zasu sake komawa. FU'AD ko zuwa yayi yad'an kwanta ya k'ara hutawa kafin ya tashi. Da yamma lis ya d'auki su mumcy bisa ga umarnin mumcy ya kaisu wajen biki. Da dare yayi ma shi ya koma ya d'auki su ya dawo dasu gida. Yau kwana biyu da tafiyar sanaya , FU'AD ya dawo d'akin Husna har zuwa dawowar sanaya ,sai Husna take cemai Dan ALLAH tanaso taje ta gaishe da mahaifinta Dan tayi kewar shi ya Mata Alfarma Dan ALLAH . Sai yace toh zeyi tunani akai. Shiru shiru har kwana biyu da maganar bece Mata komai ba sai ko ta sake tuna Mai "sai yace ya manta amman ze Mata magana ,Husna tace Dan ALLAH ya fad'a Mata a lokacin ta Matsu da son ganin shi ,ganin inya hanata be kyauta ba inya barta taje da Rana ma shima duk be lamunta ba sai yace ta shirya yau ze kaita amnan bazata wuce minti 30 ba inta yadda to in Bata yadda ba shikenan. Husna tace ya zanyi samu yafi iyawa ,zani ,amman Dan ALLAH zanje ATM indan Ciro sak'on da aunty huwaila ta turo tace na bashi ,sai ko FU'AD yace Babu inda zata indai sak'on kud'ine ze Bata ta bashi Amman ita da k'ara zuwa bank ko ATM babu Rana indai agidan take Dan shi yasan darajar Aure . Sai Husna tace to duk da bataso hakan ba. Husna murna ta wuni tanayi ,har dare yayi dama FU'AD ya sanarma mumcy husnan ma ta Gaya Mata , mumcy taji dad'in hakan sosai. Suna Isa baba na dawowa daga sallah sosai baba yaji dad'in ganin ma'un shi cikin farinciki abi da yake Mata fata kulin ,tun da tazo su mama habee da humaira aketa zumburar Baki haidar kuwa sai murna yakeyi sosai ma'un tamai tsaraba ko su humairan Bata barsu a baya ba sunsha nasu tsarabar da FU'AD ya Bata ta Basu . Bayan ta musu sallama ,ta dunkulle wasu kud'i da FU'AD ya Bata ko kirgawa batayi ba tace gashi yayi Amfani dasu kodan bunkasa sana'ar awon shi ,sai ko baba ya bud'e Baki Yana mamakin yawan kud'in sai yace ma'uta Bata sana'a na turaki ba zaman Aure na kaiki ko rok'on su kikayi? Duk da nasan sunada arziki kija takaucin mu yadda ya Dace Kar kijawo Mana Gori kinji ? Husna tace baba wlh Ina kiyaye duk umarnin da kamin Kuma Ina Nan a yadda nake ban canja ba daga ma'un ka ,kayi Amfani da kudin Nan hankalinka kwance aunty huwaila da FU'AD su suka bani Ni Kuma na baka Dan ALLAH baba Kar ka sake cewa komai in har ka yadda Dani. Sai ki baba yace to shikenan ,muje na gaisa da FU'AD din kamar yadda kikace ai basai ya shigo ba . FU'AD na hango futowar baba da Ma'u ya bud'e mota ya fito yazo ya d'an duk'a ya gaishe shi gaisuwa na girmamawa ,baba yanata shimai Albarka da Addu'a,Bayan sun Gama suka wuce shi da Husna baba nata sha'awar zaman nasu. Mama habee kuwa bakin ciki kamar ta mutu inda takema humaira data ace Ma'u ce aciki? Aiko da sake anba me kaza Kai Sam Dole tasan abinyi kafin ta mutu da bakin ciki tunani ta farayi kafin wani lalausan murmushi ya bayanna a fuskarta Mai ma'anoni da yawa. Bayan komawar su gida ,Husna godiya tama FU'AD ,yace "ta meye godiyar? Tace na sadani da mahaifina farinciki na da kayi ALLAH ya saka maka da mafifucin Alkhairi, FU'AD sosai ya fahimci irin farinciki da yasa husnan ,amemakon ya amsa ko ya nuna Mata Jin dad'in shi shima sai yace "ki godema ALLAH da mumcy badan ita ba da Babu inda Zan kaiki,sai Husna tace "dama ai mumcy ba godiya kawai ba har Addu'a nake Mata a kulin Dan ta cancanci fiye da Haka a guri na........duk da kalmar shi Bata Mata Dadi ba ,sai ya katseta da cewa ba Dole ki Mata Addu'a ba tunda ta had'aki Aure da Wanda mafarkin ki be tab'a Baki ba kinyi dare_dare kin bararaje ba.......a fusace Husna tace matsayi_matsayi ne aman daraja kowa nada shi Dan kowane d'an Adam me daraja ne dukiya ko wani milki Kuma duk aduniya ake samun su Kuma duniya zamu barsu Kuma bawai zana ALLAH yakeyi ba ......Bata rufe Baki ba ya janyo gyaketa ze zalinceta akan gaskiyar ta dama Bayan sun shigo Fallon mumcy ne ,ya Kai hannu ze rankwasheta sai ga mumcy ta fito daga d'akin ta ......... Zuwa gobe insha ALLAH🤦🏼‍♀ [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* (Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg43 Sosai FU'AD ya ke dariya akan Abin da husnan tayi yau karon farko a iya zaman shi da ita. Bayan ya Gama shiri ya fice tare da yima mumcy sallama tamai Addu'a kamar yadda ta Saba kulum. Husna bata sakko ba sai da ta tabbatar da taci baccinta ta k'oshi Kuma dama tasan tuni FU'AD ya fice Dan ta duba agogo. Bayan ta tashi ta gyara d'akinta taje d'akin FU'AD ta gyara Mai ta feshe da turarukan kamsasa d'aki da falo ta rufo Mai ta sauka k'asa ,suka danyi Hira da mumcy daga baya ta wuce sashin aunty sa'adiya Dan gobene tafiyan Aisha. Sanaya dawowa tayi wajen mumcy Kan maganan tafiyan ta ,ko da ta Fara ma mumcy magiya sai mumcy tace "Kar ta samu damuwa ta shirya baze gagara ba insha ALLAH. Sosai sanaya tayi murna karon farko da Tama mumcy godiya ,tace to yaushene tafiyan nayan nata? Mumcy tace "ke yaushe kike ganin Zaki tafi? Da so nake ki Bari muje wani biki da za'ayi in angama sai ki tafi ko kina ganin da matsala? Sai ko sanaya tace "Dan ALLAH abasu hakuri sahun giwa ya take na rakumi nafi bukatan tafiya ta da bikin duk da bansan matsayin bikin awajen ku keda FU'AD ba am sorry to say........sai mumcy ta dakatar da ita da cewa ko Fara bikin ne za'ayi dake inyaso sai ki tafi ko ana tsaka da bikin kiji ko? Ran sanaya be so ba Amman tace to ya tsarin bikin yake? Sai mumcy tace kinga yau muna laraba to Gobe Alhamis za'a Fara bikin Dan Haka ko program din goben sai ki samu inyaso sai ki tafi juma'a ko asabar yadda Kika gani dai? Sanaya cewa tayi "toh zani goben sai na tafi Friday kawai. Mumcy tace to ALLAH ya nuna Mana ya kaimu da Rai da lafiya, mumcy ta Kara cewa"goben event din na yamma ne around 5:30pm sai ki shirya da wuri Abin da kike bukata Wanda Zaki bikin dashi sai kimin magana inyaso sai atanadeshi tun yau ,wai mumcy tana Mata duk Dan tayi adalci ,sai ko sanaya tace Bata da Abin buk'ata da ya wuce tajita a Egypt ,Koda FU'AD baze Mata komai ba na tafiyan tanada kudin da zatama kanta komai Kar su damu. Sai mumcy tace "Aiko lalacewar FU'AD Bata Kai haka ba ,yama wani ma bare Wanda suka had'a wani Abu? "FU'AD ya wuce yadda kike zato kedai ki Adana kudinki ya Miki magani Kinga ko tsaraba kyayima kannenki ran mumcy fes tunda ta Bata amsa daidai maganar ta . Sanaya tashi tayi kamar Mara gaskiya ta wuce part dinta. Sosai su Husna sukayi Hira da Aisha sunata Wasa da baby mamy tanata bangala musu dariya. Bayan sunci abincin Rana ma sun Jima a wajen mumcy har mumcy tabama Aisha wasu tsadadun turaruka da shadoji da atamfofi tace tayi tsaraba , Aisha da aunty sa'adiya nata godiya har Husna ma tayasu godiyar tayi da yamma lis suka koma part d'in aunty sa'adiya. Bayan FU'AD ya dawo mumcy take gayama FU'AD Gobe su Husna zasu raka Aisha Airport Kuma zasu biki Gobe Dan Kar ya dawo gida yaga ba Mata ya tafi filin cigiya da sanarwa Dan haka ta sanar Mai tunda yasan da zancen. Sai ko FU'AD yace ko Baki fad'a ba ai kin isane Ina muku fatan dawowa lafiya ,sai ko mumcy tace"ALLAH yasa bada biyu kake zancen Nan ba. Washe gari da sasafe FU'AD ya Gama Shirin tafiyar shi office har yayi sallama da mumcy Yama sanaya sallama har ya Shiga mota ze tafi sai ya tuna da gargad'in da zema Husna sai ya fito a fusace y nufi d'akin ta ,Yana haurawa ya sameta a falo Tana Shirin fitowa sai da ya karema inda ya jimata jiwo kallo sanan yace "ke saura in Zaki fata kiyi wanan shigar kisan dai Akwai auran da mumcy tasa aka d'aura Miki akanki duk abunda kikayi Akwai me kallon ki ,ke kimayi duk Abin d zakiyi ki gani nasan zaku rakiya keda aunty sa'adiya kuma kisa hijab wata Yar ficiciya dake Amman kin iya hada fitina da kin saka hijab kinji na Gaya Miki,Yana Mai Kama kunnen shi irin alamun gargadi dinan. Husna abun sai yamata wani iri sai tace "wai wanan ne ya dawo dakai? Sai FU'AD yaga Tana neman ta rainashi daga tambaya sai yace "wanan din banza ke har kin Isa ki dawo Dani Abu nazo yi , dole ya wuce d'akin shi badan Yana son d'auko wani Abu ba ko yin wani Abu ba Haka ya fito salin alin ya fice Yana hararar ta. Bayan FU'AD ya Isa office ,tunanin yadda take kasancewa tsakanin shi da Husna ya Fara a'iya atunanin shi ya Rasa gane hakan me yake nufi yayi imanin Kuma ba kishinta yakeyi ba to Amman Damme ze dinga Jin haushi in wani ya kulata? Yana cikin tunanin wani abokin aikin shi ya shigo ya tsayar Mai da tunani cak. Bayan Husna tayi wanka ta shirya sauka tayi kasa Dan zuwa rakiyar Aisha Airport ,ganin mumcy Bata kasan sai ta wuce part d'in aunty sa'adiya ta samu Suma sun Gama shiri Ana shirya baby mamy ,sai ko Husna tace kawota na karasa Mata ,aunty sa'adiya ta mik'a Mata komai nata . Aisha ce take cema Husna "Ashe matar mijin ki tafiya zatayi ? Sai Husna tace au haba? Ina zata? Sai Aisha tace "k'asar su ta gado Mana *Egypt* jiya aunty ta tursasani wai sai naje na Mata sallama saboda Hakin musulunci shine fa take cemin itama gobe zata bar k'asar har taso muyi Hira akan 9ja da matsalolinta nace Mata Ni bani da matsala da 9ja Dan babana d'an Ghana ne Amman mamana 'yar 9ja ce kimga ko 9ja ta gama min komai ,shine fa tayi shiru ,yanzu dai tanata murna zata koma k'asar gado ,sai suka bushe da dariya aunty sa'adiya ta jiyo su take cewa wacce gulmar akeyi wanan irin kyakyatawa..... Aisha ce tace no! Aunty wanan hirar muce cigaba da soyewarki awaya da angon nesan ki tunda baya kusa ,sukaci gaba da dariyar su. Husna na zaune taji alert ya shigo wayanta na 50k sai ta duba taga daga aunty huwaila ne sai murna ta kamata duk da Bata da abinyi ko buk'atar kud'i ayanzu saboda ta godema ni'imar da ALLAH yayi Mata ma ahaka na zama karkashin mumcy da FU'AD Bata nemi komai ta Rasa ba Dan Haka Bata da bukatar kud'i ,Amman tayi murnar ganin kudin ,Bayan sun gama shirya baby mamy sai suka fito. Gaba dayan su suka jema mumcy sallama Dan har Airport zasu rakata har mumcy ta Basu sak'o a cam in suna dawowa ,driver Daman su kawai yake jira Bayan ya Gama saka duk wani Abu a motar Wanda Aisha zata tafi dashi,sai suka Shiga Suma sai tafiya. Sosai Husna da Aisha akaji Rashin dad'in Rabuwar su ,sukayi bankwana ta tafi suka wuce wajen sakon mumcy daga Nan suka juyo gida. A falon mumcy suka zauna suka huta suka Sha hirar su har suka ci abinci Rana Bayan sun Harri sun Kamala. Yamma nayi Bayan la'asar mumcy ta umarce su day su shirya Dan tafiya wajen bikin ,Husna tayi sama aunty sa'adiya ta wuce part d'inta Dan nata Shirin ,Bayan sun shiryo sun fito ,sai aunty sa'adiya taja Husna samanta tace wanan kwaliyar da gyara ta mata makeup Mai kyau ta gyara Mata ko Ina ita kanta Husna sai yau ta yadda Ashe ita Mai kyau ce Dan anfitar da komai babu algus acikin kwaliyar zallar madarar kyawuntane ya bayyana tsirara ga d'auri da ta kashe ta dashi Mai steps ta had'a Mata komai perfect match suka sakko kasa Ashe mumcy nata jiransu Dan sanaya Bata fito bane da ta aika Suma su fito ,Dan ta aika Harri ta Kira sanayan su tafi. Sanaya nacan na Shirin tafiya Egypt ba'ason ranta ta sake ba ta canja Kaya Babu wani mugun kwaliya wai Tana alfahari kyawunta is natural ,batasan in kanada kyau to ka Kara da kwaliya ba Inji mlm bahaushe ta sake abinda takeyi ta fito Dan su tafi. Mumcy ma taga zallar kyawun Husna yau sosai ta birgeta ,sai sanaya ma da ta karaso taga Husna sai da kirjinta ya buga amman Bata d'auki hakan komai face kodan ita ba ma'abociya kwaliya da fente fuska bane, Amman dai kyawunta yaso firgitata sharewa kawai tayi ,ganin su had'u sai mumcy tace su tafi ,Husna ta karbi mamy Tana hannun ta ko amotar. Bayan isa su wajen bikin aka dinga tarban su sanin wacece mumcy yasa suka Kara samun tarba Mai kyau wajen su day ban da irin abun da aka tarbesu dashi ba irin na wasu da dama bane ,aunty sa'adiya da Husna sun saki jiki da kowa Banda sanaya da taketa Shan kamshi wasu in sun tambaya akace musu a egy ta taso sai su Mata uziri wasu ko sadai ta Kara kular dasu ma su d'auketa matsayin Yar wulakanci ,su aunty sa'adiya ko kowa jansu yake da Hira da tsokana dama Basu taba had'uwa Haka ba a taro ayanzu mumcy ta dinga nuna musu kowa sosai suka Saba da, FU'AD sai da ya Kira Husna a waya Yana Mata gargad'in wai saura tayi rawa saboda Halin yarinta "Husna tace aa fad'i wani abun Amman ba wanan ba ,Ni ka tabaji ko nama Kama da Karishma? To fad'i wani abun Amman wanan be samu mahalli ba ,sai ko FU'AD ya fusata "ke Rashin kunyar ki Tana Nan ko? To Zan sauke Miki ita wallahi _dirty girl_ kawai ,kafin ya kashe yajiyo ta itama Tana cewa ,na mage kawai, har ya kashe ya sake Kira" ke me kikace? Husna tace "wa ni ba abinda nace ,sai ya kashe wayar Yana cewa zanyi maganin Mara kunya ai. Sosai akasha hotuna da mumcy da jama'a Yan uwanda da abokanen arziki sai surukanta da akayi dasu Suma har wayar Husna aunty sa'adiya ta karb'a ta dinga musu hotuna da su mumcy da aunty sa'adiyan har sanaya duk nokewarta sai da aunty sa'adiya tasa sukayi da Husna ta janyota cikin su har da mumcy sai da sukayi mutane Bayan an Gama komai suka ma kowa sallama mumcy tasa su a gaba suka nufi gida anata Kiran sallah magriba. FU'AD ya dawo gida duk yaji gidan babu Dadi ,wai Dan mumcy Bata Nan..........lol saura kuce😝 Maman shaheed Comments dinku na karamin karfi💃🏼💃🏼 Stikers na sani murmushi🥰 Addu'o'inku na sani nishadi😍 Acigaba da *kaftawa*👌🏻🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀ [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg46 Bayan su mama habee sun tafi Husna ta Adana turaren a d'akinta tanata murnar canjawar mama habee. FU'AD Bayan ya dawo gida yaci abinci ya fita wai zashi wata unguwa ,tunda ya tafi be dawo ba sai around 9:30pm by d time d'in Husna ma ta Shiga d'aki ta kwanta har bacci yayi awon gaba da ita Dan har sai da ya lek'ata yaga tanata bacci sosai wani Abu ya dinga Mai yawo a kwanyar shi ahaka ya rufe Mata k'ofa ya koma d'akin shi. Washe gari FU'AD be fita Aiki da wuri ba sai da yasha bacci kafin ya shirya Kuma yace da wuri ze dawo Dan yau Yaya Jameel ze dawo da yamma zai je ya d'ako shi a airport. Sosai aunty sa'adiya ta dage ta Shiga kitchen Ana shiryama abban mamy girki lafiyaye na taryar shi Husna na tayata da ma'aikata Akwai kitchen a part d'inta Amman tafi so tayi anan saboda Akwai masu tayata ,cikin kwarewa da birgewa suka kammala komai aka Adana Ana jiran me ci. Mamy kusan yau a hannun Husna ta wuni har da FU'AD ya dawo gida ya k'ara shiryawa ya tafi d'akko Yaya Jameel yanata ma mamy Wasa ya fita wai so yake Dole ta Saba dashi. Bayan ya dauko Yaya Jameel su dawo ,Yaya Jameel sai da ya Fara zuwa yaga mumcy har rugumarya yayi na kewarta da yayi sanan suka gaisa da ma'akatan gidan sai Husna da ta sakko suka gaisa hannunta rik'e da mamy ,Yaya Jameel ya mikamata hannu Yana murna ze d'auketa Taki zuwa wajen shi mumcy da FU'AD sunata Mai dariya wai ta manta shi Dan Haka sai yayi sabon shiri wajen sabawa da ita ,Dole ya hak'ura da d'aukan ta ya tafi wajen Aunty sa'adiya. FU'AD karb'an mamy yayi ya haura sama Yana Mata Wasa ,husna kuma Tana k'asa ,mamy ta Fara gajiya ga FU'AD be iya wasan da takeso ba sai ta fara Shirin kuka ,sai ya d'aga waya ya Kira Husna Tana D'agawa yace Zo ki karbeta kin koyamata kin mutane ya kashe wayar be jira me zata ce ba. Husna dariya ta dingayi har mumcy ma da Husna ta Gaya mata Abin da FU'AD yace ,Tana haurawa ta Sami yanata rarashin ta ,sai Husna tace kawota sai ta karb'eta ta Fara mata Wasa Tana rarashinta har tayi shiru ta Fara ma dariya , FU'AD yazo kanta Yana lakace mata hanci Yana cewa an koya Miki kin mutane ko mamyna,sai Husna ta kalleshi ,sai Fu'ad yace "ya da kallo ko da magana ne? Ko karya nayi Baki koya Mata ba? Husna dai kincemai komai tayi ,sai murmushi da ta sakar mai. Sai FU'AD yace "Rashin kunya tayi sanyi kenan" Washe gari Bayan FU'AD ya tafi office ,Yana zaune Yana Aiki sai yaga sakatariyar sa tazo tace yanada bak'uwa ,Koda yabada izini Akan bakuwar ta shigo ,ba wata bace bak'uwar sai humaira ,tana shigowa ta Fara karema office din kallo ,shiko FU'AD ko d'agowa beyi ba bare yasan wace bak'uwar Dan yasan baida appointment da kowacce mace,Bayan ta gama kalon ta seta nutsuwarta tace "Assalamu Alaikum ina gajiya ya Aiki? FU'AD d'agowa yayi yace , waalaiki sallam,sai wacce ya kamata na amsa ? FU'AD cewa yayi "daga Ina? Humaira fari tayi da Ido kafin tace "nasan bazaka ganeni ba tunda ba'a maka bayanin wacece Ni ba Dan Haka nakeson sanar maka da kaina ,Ni yayar matarka ce baiwar ALLAH Ma'u ,Husna ba ,nice yauarta ita take Bina nazo mu gaisa ne Dan ita ta bani address d'inka tace wata Rana na leko mu gaisa idan nayi hanyar bama so nake ba ta dinga had'ani da ALLAH ,shine fa na samu na leko mu gaisa. FU'AD kare Mata kallo yayi ,azuciyar shi yace to kaza kanki da motsi, afili kuma yace "sannu yayar Ma'u kinyi k'ok'ari nagode yanzu na sheda ki. Humaira sai cewa tayi Bari na tafi Dan so nake dan napep d'in da ya ajiye mu ya wuce damu nida mama kasan Tana waje ko zakazo ku gaisa? Sai FU'AD yace wacce mama Kuma? Sai humaira tace "laaa mama habeen maman tamu nida Husna ko kazata watace? Sai FU'AD ya wayance yace oho na fahimta duk ya gaji da gani da sauraron humairan sai Fu'ad yace ok muje na gaisheta ,tare da humaira FU'AD ya sakko duk inda ya gifta sai an girmama shi Ana barka dai oga Ana Mai jinjina wanna abun sai ya karama humaira girman Kai taji kanta yayi girma Tana ji kamar ma ita ake girmamawa har suka sauka k'asa ,har suka fito wajen company din ,acikin adaidaita ya hango mama habee anata Hira da Mai adaidaita ,sai ko ta fito daga ganin humaira da FU'AD ,ita ta Fara gaishe da FU'AD duk da humaira bataso ba ,taso mama habeen ta Bari a bata girmanta Amman Taki sai can tace toh zamu wuce sai wani lokacin ,sai Fu'ad yace "au Zaki Kara dawowa kenan ,sai yace mata a fili to ku gaida baba Dan ALLAH,ngd ya mik'ama humaira wasu kud'i masu kauri yace sa biya Mai adaidaita ,sosai mama habee ta wage Baki tanata godiya kamar me neman dad'i ,itako humaira ji take kamar ta toshe bakin mama habeen ,sai cewa tayi mungode FU'AD Mai adaidaita ja mutafi ,awajen suka bar FU'AD yanata mamakin abun kamar a mafarki.... Yana tunanin har yaushe Husna tasan wajen aikin shi da har zata turo yayarta? Kai Akwai ayar tambaya a lamarin Naga kamar Akwai bambancin tarbiya tsakanin su first ya kamata nasan ya suke kafin nasan Abin yi ...... ********* Mamy dai da kyar ta Sha Kan dady har yabar sanaya ta d'an zauna Dan said da suka Kai Ruwa Rana dashi da ita kafin itama sanaya sai da ta dinga kuka da rok'o da magiya kafin ,chart Kuma a waya sai Fu'ad ya Mata magana sai taga dama take amsa Mai shima sai ya fita harkan ta in Bata amsa ba. Bayan FU'AD ya komo gida be cema Husna komai ba sai da suka kammala komai suka hauro sama zasu kwanta har zata tafi d'aki sai ya kirata ta Zo. Sai yace ke wace humaira ma ya kuke da ita ? Sai Husna tace "yayata ce" "Sai ya sake cewa dukanku mama habee ce ta haife ki? Sai husna tace "eh " agajarce alamun ta Fara k'osawa da tambayoyin shi ,sai Fu'ad ya sake cewa karki b'oye min komai tambayar da na Miki tanada mahimmanci agareki inkika min karya Zan had'a da Abin da mumcy ta gayamin kin gane ai ko? Sai ko Husna tace hakane ,barin gayamai gaskiya Dan bazan karyata mumcy ba ,sai tace mama habee ita ta haifi yaya humaira Ni mamana ta Rasu tun Bayan da ta haifeni ,wani abune? Sai FU'AD yace "hmmmm biri yayi Kama da mutum ,da zakimin karya" Amman Baki da matsala dasu ko? Husna tace eh babu duk ta b'oye mai,sai yace to jeki ... Sosai FU'AD ya Fara hassaso wani Abu. FU'AD yaki fad'ama Husna ne saboda ganowa da yayi Bata da masaniya da zuwansu ,Dan Haka yabar zancen. Washe gari ,Haka ya tafi office tare suka fita ma da Yaya jameel Dan Akwai aikin da zeyi a company dinsu suna Hira ta d'an uwa da d'an uwa har suka Isa. Bayan wasu kwanaki Husna tayi wanka taci kwaliya aka buka Mata k'ofa taje ta bud'e Ashe mamy aka kawo Mata Tana zuwa ta karbeta ta dawo d'aki zamansu keda wuya sai ga FU'AD yazo ya karbi many shima Yana Mata Wasa Yana dagata sama sai tamai tumbudi ta Bata Mai Riga da sauri yace Husna ta d'ako Mai tissue ta goge Mai ,tayi sauri ta d'auki ta Miko Mai tace kawota sai ka goge sai ya harareta yace malama ki goge mun ko ,Bata da zab'i sai ta Fara goge Mai ahankali takeyi sai Fu'ad ya daka Mata tsawa yace dallah malama meye Haka kamar kina Susan kwarkwasa wani ahankali ki goge min sosai ,Dole ta saki jiki ta Kama rigar da kyau ta goge Mai tas ta je ta zubar da tissue taje d'aki ta dauko turaren da mama habee ta Bata wai ita zatayi gwaninta sai tace ga turare ka fesa a wajen nasan ku maza bakuso tunbudi ,zata fesa Mai kenan ta seta bakin turare sai yace "aa barshi banaso nasan irin warin turaren naki wata Kila kwanda warin tunbudi ma dashi da gani ma kamar d'an duri turaren,sai ko Husna taji haushi tace ai dama gwaninta be karbi kareba ,in halinane na sake..... Sai FU'AD yace me kike cewa ? Sai Husna tace " cewa nayi me Hali baya fasa Halin shi halinka nanan Babu inda yaje" Sai ko FU'AD yace rashin kunyar na Nan kenan ? Kinyi ya isheki karki wuce gona da iri kuma. Sai Husna tace oho dai. Suna cikin Haka sai mamy ta Fara kuka sai husna ta jefar ta turaren a kujerar to Tana cewa kawo ta ,ya mik'a Mata Yana cewa uwar Reno sata tayi shiru. Ya wuce d'aki ma abinshi ,Husna nata rarashin mamy har tayi bacci sai ta kaima aunty sa'adiya ita akan akwantar da ita ta dawo falonta ta wuce d'akinta ta manta turaren a falon. Washe gari Bayan FU'AD ya shirya ya sauka kasan mumcy ya karya sanan ya dawo sama ya d'auki kayan shi ze sauka sai yaga wanan turaten a kijera kawai ya d'auka Yana cewa Akan wanan turaren jiya akemin fushi Dan ban Bari anfesa min ba har akemin rashin kunya barin fesa naji kamshi da yakeyi ,kawai sai ga Husna ta fito, sai Fu'ad yaji kunya yayi sauri ya ajiye ,sai Husna tace me zakayi da Abin da kafi k'arfin shi ? Dai FU'AD yace me kike nufi ? Sai Husna tace eh Mana ka girmi turaren Ina nufin girman kanka ya wuce kayi Amfani da turaren da ya fito daga hannun fakiriya kamar Ni ,sai Fu'ad yace "Kar ki sake cewa inada girman Kai " Sai Husna tace wallahi kana dashi inda baka dashi da ka fesa lokacin da nazo na sameka kana Shirin fesawa da ka ganni ai girman Kan motsawa yayi sai ka fasa fesawa ,wallahi kana da girman Kai ,sai ko FU'AD ya d'aki turaren ya fesa ajikin shi Yana cewa Kashi na karya ransuwarki Dan Haka azumin kaffara ya Kama ki muga karyar Mara kunya .... Husna mamaki abun ya Bata FU'AD ya Gama fesa turare kenan ze fita har yakai bakin k'ofa sai kanshi yayi wani mumunan sarawa sai kawai ya juyo Yana cemata Kai wanan wani irin turare ne Haka ,kafin Husna ta bashi amsa sai jiri ya fara diban FU'AD da sauri Husna ta taho wajen shi Dan taga idon shi na canja kala Husna na karasowa dab dashi batayi aune ba sai ji tayi FU'AD ya fad'o jikinta assume...........Husna ihu tasa kafin ta lalubo salatin annabi Tana yi........ 🙆🏼🤦🏼‍♀😢 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg45 FU'AD waskewa yayi sai ya canja salo , mumcy ta ganshi Ras Amman ta basar kamar bataga meyake Shirin yi ba sai cewa ma tayi "FU'AD da Husna kun dawo? FU'AD da sauri yace eh mumcy ,Husna ma ta k'arasa tace eh hajiya baba yace agaishe ki ,sai mumcy tace"muna amsawa dafatan lafiya kuka baro su? Husna tace "lafiya Lau suke. FU'AD sama ya haura Yana cewa ,Bari naje muyi waya da babban yayana na kaina, mumcy tace asha waya lafiya ,tasan in suka Fara waya kamar bazasu kashe ba Dan Haka ta samu damar Jan Husna d'akin ta Tana tambayanta dazu FU'AD dukanta yayi? Husna tace aa , mumcy tace Amman da niya ai,Nan ma Husna tace aa ,ganin dai b'oyewa takeson yi sai tace "hmm nagani fa ko be aikata ba ya kusa aikatawa" karki b'oye min komai Asma'u FU'AD ya tab'a dukanki? Husna tace "aa" mumcy tace "nifa uwace agareki in be tab'a ba baze yi niyar yi ba dazu na ganshi kawar da kaina nayi kawai inaso ki saki jiki Dani ki sanar min da duk wani Abu da FU'AD yake Miki na rashin Jin Dadi ko kumtatawa? Husna Kara sunkuyar da Kai tayi Tana cewa "babu abin da yamin ko yake min ko yauma har kud'i yaba baba da yawa" Sai mumcy tace ,wanan ai ba sabon Abu bane aikin shine Daman Yama wasu bare sirikin shi? Nasan Halin FU'AD nada nasan Wanda ya aro ya k'ak'aba ma kanshi ,kin b'oye min wani Abu Amman Ni zangano inda wani abun ai ,Naga har yanzu kamar be Gama ammana da auren ba Amman aure kuma Haka zecigaba da hak'uri kamar yadda kuma kuke hak'urin tunda duk aura muku shi akayi shi da yake jin kamar an aikata Mai zunubi. In yasan wata besan wata ba , mumcy ta fad'a a zuciyar ta ,tace Husna ta tashi ta tafi,Husna ta mik'e ta tafi saman ta. Husna na Shiga ta samu FU'AD a falo yanata waya ,yanata Mata magana da hannu da Ido akan tazo ta bashi remote da ruwa Yana mata nuni itako tamai banza tayi kamar bata gani ba ta wuce d'akinta Dan ya kular da ita. Ganin Bata fahimce shi ba sai ya mik'e ya Shiga d'akin shi Dan d'aukan ruwanshi Akan center table d'in d'akin ,Yana Sha Yana Jin dad'in yadda d'akin yake kamshi yasha gyara Karo na farko da ya yabi aikin Husna ,Yana cewa ta horu da aikin ,har suka Gama waya da Yaya Jameel k'ara birgeshi d'akin yakeyi. Kusan sati biyu kenan da tafiyar sanaya tanata sharholiyan ta da abokanenta ta waya Dan basu had'u ba sai friendship d'in da sukeyi a waya kawai,yaune Kuma dadyn ta ya dawo daga China ,yaje duba wasu kayanshi da sukaso samun matsala sai da ya Gama clearing komai har tsahon sati uku acan sanan ya dawo yau. Yana shigowa yayi tozali da sanaya ,Aiko ya Fara sababi Yana tambayar ta ita da wa tazo?? Baki na Rawa take cemai "Ni kad'ai nazo na gankune bisa yadda mamanshi da shi ......Bata karasa ba dady yace maza had'a kayan ki ko hutawa bazanyi ba Zan saki a jirgi ki koma har ban Isa ki sanar Dani zuwanki gida ba ? Yayi wuri ace har kin Zo Egypt .......be rufe Baki ba ganin da gaske yake sai sanaya ta sakar Mai kuka Tana cewa dady Ni bazan koma da gagawa ba Haka infa aka matsamin Zan yafe Auren nashi Banda biyayan da nayi abun aga k'ok'ari na Amman sai ganin laifina ma .... Afusace dady ya k'araso gaban sanaya Yana huci .....da sauri mamy tasha gaban shi Tana cewa "aa dadyn yara babu sabo ko kuskure cikin kalaman sanaya fa da gaskiyar ta wanan Abin da zaka'aikata ba maslaha bane kamar ba sanayan mu ba banga Abin da tayi na ba daidai ba ta kareta ta ko Ina. K'wafa dady yayi yace "ku jirayi hukuncina gaba d'ayan ku ya wuce master room d'in shi. Mufeeda ganin abun Yana neman zama wani iri ,nasiha ta Fara yima su mamy da sanayan sai sanayan ta Fara zagin ta Tana cewa "shegiya muguwa kizo ki koma gidan FU'AD d'in amadadina na bar Miki Auren da 9ja" Mufeedan dariya tasa Tana cewa "haba aunty Sana a Ina Kika taba ganin Haka a wanne film ko novel? Ai ba Ayi FU'AD nakine d ALLAH ya Baki Nima nawa Yana zuwa Tana sake tuntsira Mata dariya . Sanayan harara ta maka Mata Tana cewa "au da anfara akanki ai ,wallahi zanyi maganin ki kin rainani da yawa fa, mufeeda cewa tayi Am sorry sistoo na,ta had'e hanuwanta waje guda daga baya ma tabar musu wajen,mamy da sanaya sukaci gaba da tataunawa Akan yadda zasu billoma dady Akan karya korata. ******** Aunty huwaila ta Aiko da magani ta hannun wanan malamar jinyar Mai rangwamen hankalin Nan duk da Alhj da yake taimaka Mata Yana iya k'ok'arin shi har yanzu. *********** Mama habee ita da humaira da wuri sukayi wanna suka kintsa sukasa kayan su na can k'arshe akwati ajin k'arshe Dan yau unguwa zasu Mai mahimmanci ,Koda aka gayama baba yin duniya su fad'amai inda zasu sunki kawai dai sunce unguwar Mai mahimmanci ce Dan Haka basai kowa ya sani ba ,baba ya rabu dasu yadai ce musu adinga Aiki Ana sanin hukuncin ALLAH acikin Aikin daga Haka be k'ara kokai ba suka fice dake Ana cewa da hukuncin ka kakeso asani, dake yau ba da wuri ze fita ba. Bayan sunje wani waje da suka dawo sai suka biya ta gidan Husna , mumcy suka samu a falo har k'asa mama habee ta gaishe da mumcy tanata yank'are hakora kamar gonar kashi, cikin fara'a da sakin fuska mumcy ta tarbe su dake ta sheda humaira ,Harri aka tura ta Kira Husna ,Husna na sakowa da k'arfin gwiwanta tayi tozali da su humaira sosai gaban Husna yayi mumunan fad'uwa tace "shikenan sunzo su gutsire guntun Auren Dan Mana habee tauraruwace Mai witsiya ganin ki ba Alkhairi ba" atake ta canja yanayin fara'ar ta har mumcy sai da ta lura da hakan,daga baya ta k'arasa sakowa Tana cewa "sanin ku mama habee Yaya humaira sanunku da zuwa ,mama habee sai tallan hakora take Tana yauwa Yar sutura sanun dai ,atake jikin Husna yayi wani iri tace "yau Kuma harda canja min suna ? Wato da can baya 'yar tsirara nake yanzu na koma 'yar sutura tunda arziki wasu ya lulube Ni? Husna Bata Gama tunani ba mumcy ta tsayar Mata dashi ,ta hanyar cewa ki kaisu Sana ko sai Harri ta biyo su da Ruwa ,Husna tace to hajiya Mama have kuzo muje ,zungwi_zingwi suka bita , mumcy na dogon nazari akansu. Husna bataso kaisu saman ba Amman dai ta kaisu bisa umarnin da Amincewar mumcy. Mama habee kamar ansamu cenima kallo kawai takeyi na k'auyanci ,can tayi narai_narai da ido Tana Shirin fitar da kwalla Tana cewa "Ma'u ki d'auki komai ba komai ba duk Abin da ya faru ki barshi a baya ki kalli gaba ,ki zauna lafiya a gidanki ki rik'e mijinki da surikar ki ,abun da ya faru baya kiyi afuwa nasan ke me afuwace sai mama habee aka Fara kwalla har Tana zubowa har Ana cewa "ALLAH yajikan mahaifiyar ki" mahaifinki Kuma ALLAH ya barku tare ,ga 'yar uwarki kisata Addu'a ki ALLAH ya fito Mata da nata mijin ko kwatan_kwatan nakine ma'ana ko Wanda bekai naki ba gata Nan ki dinga Mata fad'a Naga kinfita nutsuwa da hankali .....sai ko humaira ta juyo a zabire ,mama ma'unce ta fini hankali da bakinki kike fad'a? Itako Husna abun sunata Mata yawo a kwanya shin gaskene ko ba gaske bane? Kai gaskene harda hawaye fa ALLAH sarki mama habee ta dawo hanya,humara tana cewa nidai wallahi wata Ma'u bance tasani a addut ba Kuma banga hankalinta ba da har zata fini,sai ko mama habee tace ta fiki sai dai Kiki ALLAH ,humaira aka sunkuci Baki. Mama habee ta inda ake Shiga Bata Nan ake fitaba ta gama cikama Husna Kai da karatun ta ,sunayi suna taba Abin da aka cika musu gaba dashi har da kaji Dan takansu ma suka fara, cikin hirar mama habee Tama Husna dabara Dan suji inda company d'in su FU'AD yake ,har da office d'in shi inda yake ,Husna tace Ni dai wallahi ban sani ba Amman naji suna cewa a sultan road yake office d'in ko a second floor ne ko 3rd ne nadai manta ,mama habee Bayan ta gama ji tace to shikenan ma barshi ba buk'atar sani nakeyi ba,sosai suka ci suka k'oshi harda guziri da zasu tafi mama habee taba Ma'u want turare Mai kanshi wai tayi Amfani dashi har humaira zata fesa Mata mama habee ta daka Mata tsawa Tana cewa uwar azarbabi da rawar Kai ce miki tayi bata iya fesawa ba? Dallah bani ungo jiki ki Adana abinki,Husna karb'a tayi ta tafi Tana murnar canjawar mama habee lokaci d'aya haka. ........ loading.........🖊 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg47 Wani uban k'ara Husna ta sake lokacin da taji FU'AD ya fad'o jikinta rigijib ,badan taimakon kujera Mai laushi da suka fad'a Kai ba da zeyi wuya wanin su beji ciwo ba,Husna ce a kasa FU'AD a samanta ya sakar Mata nauyin shi da ALLAH ya bashi,gashi ba ahayyacin shi yake ba ,sai da kyar ta iya karanto salati da su hailala Tana Shirin kuka Tana neman agajin Wanda ze kawo Mata doki wajen daga Mata Fu'ad ta samu ta mik'e. Da kyar Husna ta samu ta jirkitar da FU'AD ,ta dinga jijiga shi shiru ,sai ta sake sakin uwar k'ara a firgice Tana na Shiga uku FU'AD ka tashi Dan girman ALLAH meya sameka ? Kafin kace kwabo idanu da kumatun Husna sun Gama jikewa da ruwan hawaye ,maganar duniya FU'AD ko numfashi bayayi,da gudu Husna ta bud'e k'ofan falo tayi k'asa wajen mumcy, a firgice mumcy ta ganta tace" lafiya Asma'u ,waye ya mutu? Husna babu Baki ,nuna saman su kawai takeyi Tana cewa FU'AD ne ,sai mumcy ta saki wayar hanun ta Tana cewa shine ya mutun? Arazane sai ga Yaya Jameel ya shigo falon ,sai mumcy tace "Jameel Zo Nan" muje Asma'u ,da sasarfa suka haura Saman Suna Shiga sukaga FU'AD wanwar a kujera kafafun shi a kasa ,sai ko mumcy d Yaya Jameel sukayi kanshi a firgice ,suna jijigashi suna Kiran sunan shi. Ganin baya motsi , mumcy ta juyo tace Asma'u me Kika Mai? Husna ta kasa furta uffan Dan ita har tunani da maganar ta sun d'auke gaba daya Tama Rasa meye abinyi yanzu in FU'AD ya mutu ,Tana wanan nazarin Yaya Jameel ya daka Mata tsawa "ke meya Sami d'an uwana ,me Kika Mai? Husna sai fanfon hawaye takeyi Tana nuna turaren da ya fesa ,a fusace da k'unar Rai Yaya Jameel yace "wai ba akiyi magana ba musan abinyi? Wanan duk baze kaimu ba kina ganin ko numfashi bayayi sai , mumcy tace Jameel mu tafi dashi asibiti da gagawa aunta be mutuba Yana Raye ya za'ayi ya tafi ya barni a cikin duniyar Nan? Sai a lokacin bakin Husna ya bud'u tace "in ALLAH ya yadda be mutu ba Kuma baze mutu ba Dan ALLAH mu kaishi asibiti. Yaya Jameel ne ya d'auke shi ya yo kasa dashi da sauri Husna ta Suri hijab jikinta na rawa idon ta nata ambaliyar hawaye take bin Bayan mumcy da Jameel , mumcy ma hijab ta samu ta d'auko da wayarta suka nufi wajen Adana motocin gidan. Jameel ya manta da matar shi ma sai da ya ganta ta fito tajiyo hayaniyar ma'aikatan gidan suna tambayar meya same shi ,babu Wanda ya samu damar Basu amsa sai mumcy da tace "ku kula da komai zamu asibiti Dan sanin meke faruwa muma bamu sani ba ,sai aunty sa'adiya tace "toh ALLAH yasa muji Alkhairi Dan ALLAH da kunje ku kiramu Dan zaku barmu a Rud'ani ,Yaya Jameel yace to insha ALLAH sudai tayasu da Addu'a ,shi yasa FU'AD a mota , mumcy da Husna suka Shiga sai Asibiti ...... Suna Shiga aka Fara ba FU'AD taimakon gagawa sosai wani likita ba indiye ya tsaya akanshi yanata bincike ,yanatama Yaya Jameel tambayoyi akan Abin da ya faru har ya Shiga wanan yanayin ,ganin baida amsar su sai suka Kira Husna sukace tayi bayani. Husna cikin kukan da ta Rasa me rarashinta ta Fara cewa ,wlh nidai lafiya Lau yake ze fita Bayan ya Gama Shirin tafiya sai Mike d'an takkadama Akan wanan turaren Dana nuna muku ,ya karb'a ya fesa Yana fesawa ko minti 2 ba'ayi ba Naga ya Fara wani Abu sai ya fad'i Naga idon shi nata wani Abu ,shine nazo na Gaya Miki daga Haka wallahi bansan komai ba. Sai likitan yace ko yanada Asma ne? Da sauri mumcy tace ko d'aya ,sai likitan ya sake cewa baida wani ciwo bayananne da yake tashi Mai? Atare da Yaya Jameel suka had'a Baki "sukace babu" Likitan sosai ya Gama gwaje_gwajen shi kafin yace da ranshi Amman inaganin ya shaki turaren nne over har Yana nema Yama huhunshi illah ,zamu Mai scanning Bayan mun samai Ruwa min Mai wasu allurori sai muga abun da za mu iya Akan matsalar shi. Sosai hankalin mumcy d yaya Jameel ya dugunzuma ya Kara tashi ,har Husna da take cewa nice sila inya mutu na Shiga uku afili take fad'a batare da tasan Tana fad'a ba ,sai ko mumcy ta juyo tace "me kike cewa Asma'u? Da sauri Husna ta toshe bakinta azaton ta a fili ta fad'a har mumcy Taji? D sauri tace "mumcy FU'AD baze mutuba insha ALLAH Zaki rayu da d'anki bazan zamo silar rabaki da jininki ba Kuma wallahi ki yadda Dani bansan komai ba....... Bata rufe Baki ba mumcy tace "kin San komai Asma'u ,ki kuka dakanki matuk'ar wani Abu ya Sami auntana ki fad'amin Abin da Kika sani ko kike b'oye min? A Ina aka samo turaren da ya fesan? Siyowa kikayi ko nashine ? Ko Baki akayi? Husna mumunan bugawa kirjinta yayi ta kasa fad'an inda turaren ya fito gani take inta fada har babanta zasu shiga uku ba mama habee da humaira ba kawai ita Kuma da babanta ya Shiga mummunan yanayi gwanda ta mutu cikin mumunan yanayi indai babanta ze tsira. Mumcy ce ta sake cewa "Asma'u duk lokacin d Nagano kinada hannu a faruwar matsalar FU'AD ,saki fuskanci fushi na Mai tsanani agareki fa ,Dan kin nunamin ke Yar Adam ce ,tun wuri ki gayamin musan abinyi. Sai Husna tace "turare nane na kayan lefe na Amman yau na Fara Amfani dashi" Mumcy cewa tayi "hmmmmm ALLAH ka dawo min da d'ana hayacin shi. Yaya Jameel Yana ta waya da aunty sa'adiya Yana ce mata ankusa Shawo Kan matsalan su cigaba da musu Addu'a ,Yana Raye ya kashe wayar. FU'AD har dare besan waye akanshi ba ,har abokanen aikin shi d sakatariyar shi suka dinga Kiran wayar shi sai dai Yaya Jameel ya d'aga yace bashi da lafiya Yana asibita Amman jikin da sauki har wasu sukace zasuzo asibitin ya basu address ,ya hanasu ta hanyar kwantar musu da hankali wai su jira jikin nashi da sauki ,Dole suka hak'ura badan sun so ba. Dare yayi anma FU'AD scanning sun kasa gane ainahin matsalar ko Abin dake damun shi ,ganin zasu Sha wuya kuma maybe suta kashe kud'i abanza ,sai likitan yace su Bari agama Mai iya taimakon da zasu bashi in ba'a samu Abin da ake so ba sai ya musu transfer zuwa India ya had'asu da wani kwararen likita a asibitin kwararu na Delhi a India zuwa jibi a fita dashi Dan Shawo Kan matsalar da gagawa. Ranar Husna wunin kuka tayi , mumcy dai jira take kawai ta sani da sa hanun Husna a rashin lafiyar FU'AD ko babu kafin ta d'auki mataki. Bayan isha'i su mumy da Husna suka tafi tare da aunty sa'adiya dake ita ta kawo musu abincin dare ita da driver. Bayan komawar su gida Husna ta kasa aikata Abin kirki sai ma mumcy ce take karfafa Mata gwiwa sanan ta samu tayi sallah tasata ta had'a lafiyayen tea da yaji had'i ta sata gaba ta shanye kamar magani Haka Taki tea din. Husna a falon mumcy ta kusan kwana sai da mumcy ta fito ta ganta sanan ta tasheta ta koma saman su ,duk sai mumcy ta Fara Jin tajsayinta. Bayan Husna ta koma tanaso ta sanarma aunty huwaila Tana tsoro Kuma sai kawai ta fasa. Turaren Husna ta d'auka ta dinga kallo Tana Kuka Tana kiranshi da bakin turare Wanda ya bakanta ran mutane da dama ,to ma meye acikin shi ? Mama habee kece kike Shirin tarwatsamin farin ciki? Wallahi Baki da gaskiya a turaren Nan ,har anan ma Baki barni ba? Sanin da na Miki bakya bin malaman tsubbu ko bokaye duk da bansan gaskiyar ki ba Kuma hankaka kike gabanki fari bayanki Baki ,yanzu in wani Abu ya Sami FU'AD fa ? Duk da badan shi kikayi ba kinyi ne Akaina Mara galihu da nayi Amfani dashi inajin da yanzu na sheka barzahu .........kuka ya ci k'arfin Husna Tana maimaita ALLAH ya Isa tsakani na dake nida yadda dake har gaban aba in Akwai kin kasheni da Raina wallahi badan baba ba sai na Toni asirinki makira nabar Miki gidan ma ban tsira ba ,sosai Husna take kuka a kujera ta kwana idonta fal hawaye idanun duk sun kumbura. Ana Kiran assalatu ta farka a gigice ta d'auro alwala ta yi nafila sanan ta dinga Addu'a har aka Shiga sallah tayi sallah. Bayan ta idan a dadumar bacci batawo ya saceta ta d'an runtsa,Tana cikin baccin ta farka a tsorace taba tashi bathroom kawai ta fad'a tayi wanka da zata tsaya gyaran d'aki sai taji Bata da k'arfi ko kuzarin da zata iya wani Aiki ,Dan haka wanka kawai tayi ta zura doguwar Riga ta zura hijab tayi kasa wajen mumcy. Mumcy na Kan salaya Tana jira sai tayi sallah walha kafin ta mik'e sai taga Husna ,Husna har k'asa ta duk'a Tana gaishe da mumcy yayin da hawayen da take a adanawa yaki b'oyuwa sai da ya shatato kumatunta ,ganin ta cigaba da kukan mumcy ta rarasheta duk da Tana ayyana matuk'ar ta sameta da hannu cikin rashin lafiyan FU'AD tabbas zata ji babu dad'i. Bayan mumcy tayi walhan ta Shiga band'aki tayi wanka ta saka doguwar rigar leshi ta d'auko hijab tasa da safar kafa ta riko carbinta ta d'auki Jakarta sai tace ma Husna tazo su koma asibiti hankalinta yak'i kwanciya kwana tayi cikin zulimi da fargaba,Husna ma cewa tayi wallahi Nima hajiya mu tafi Dan ALLAH. Ko aunty sa'adiya sun manta basuma magana ba sai sako suka bayar abata ,ma'aikatan gidan nata musu Addu'a ALLAH yaba FU'AD lafiya Mai d'orewa,cikin kuka Husna take amsawa da Amin. Suna Isa asibiti ,suka nufi d'akin da aka kwantar da FU'AD d'in Yaya Jameel y taso ya taresu , mumcy burinta taga FU'AD da sanin abinda yake ciki. FU'AD ya dawo hayyacin shi yadan bud'e ido ,yanzuma kamar yaji muryar mumcy motsi sukaji a farayi Yana bud'e ido kad'an_kad'an har ya bud'e ido , mumcy kamo hannun shi tayi Tana Kiran sunan shi yayi shiru dai baya ko iya magana ,Husna nacan yanata kuka ,can FU'AD ya juyo sautin kukanta waigawa da zeyi ya hangota sai ya runtse idon Yana Mata nuni da hannu Akan ta fita a d'akin,sosai suka fahimci abinda yake nufi Yaya Jameel d mumcy ,Husna k'ara rushewa tayi da kuka Tana wallahi FU'AD banma komai ba wallahi ......Bata karansa ba FU'AD ya Kara runtse ido Yana dafe k'irjin shi Yana sake Mata nuni da ta fita kawai baya San ganin ta. Mumcy ce ta ce ta fita Dan ALLAH hankalinta a tashe ,Husna taso Taki fita Amman yadda yaya Jameel ya hayayak'o Mata kamar zai turata Dole ta fita Tana shatayar hawaye. Sai da mumcy ta dinga lalaba FU'AD da mishi tambayoyi Akan Husna Dan ta kafa hujja da kyau ,duk tambayoyin da take Mai amsa yake Bata kawai ko ya fahimta ko be fahimta ba ji yayi ya gaji da tambayoyin Aiko ran mumcy ya sosu fita tayi ta Sami Husna "kikace Baki da masaniya a matsalan FU'AD ? Husna ta bud'e Baki Tana cewa "wallahi tallahi hajiya bansan..... mumcy tace "Asma'u Adana kalamanki kawai ki sani in FU'AD ya Sami matsala kin samu kema ya akayi baya son ganin ki? Kuma na tambayeshi kinada masaniya Akan samuwar matsalar sa yace min eh" Dan Haka Husna kije gida kawai har sai mun nemeki ,Husna zatayi magana mumcy ta d'aga Mata hannu kawai kiyi abinda nace muma barin k'asar zamuyi Dan Nemo lafiyan shi ta tafi tabar Husna a wajen tanata kuka. Mumcy na komawa Yaya Jameel yace , mumcy husnace sanadin rashin lafiyan k'anina ,abinda yarinyar Nan zata Mana kenan? Mun suturtata mu zatama tsirara a kasuwa? Ki barni naje na hukuntata Kuma sai na mayar da ita gidansu a yau tare da kashedi Mai zafi da Zan Mata akan k'anina da mayakin Auren su fuuuuu Yaya Jameel yayi hanyar fita ....... Mumcy ce tayi saurin dakatar dashi "haba yayan aunta wanan da Mata yafi dacewa Kai da zaka seta nutsuwarka ,da hangen mafita ,ka rabu da ita Nima nace taje gidan su har sai muje India mun dawo kafin duk da banso hakan ba Amman Babu yadda zanyi ,yanzu mu fuskanci matsala da lafiyan son kawai kaje kaga Dr Khaner sai ku shirya komai Gobe a fita dashi kawai banason jira. Jameel kwafa yayi ya fita , FU'AD ko shiru yayi gashi yanajin wasu abubuwa Amman baze iya mayarwa ba shi kad'ai yasan me yakeji duk da ba wani ciwo yakeji a jikin shi ko gabobin shi ba Amman jikin nashi Babu dad'i. Husna Tana Kuka ta koma gida ,sashin aunty sa'adiya ta nufa Tana Kuka Tana gayamata yadda komai yake har cewar da hajiya tayi ta tafi gida ,sosai sa'adiya ta tausayama husnan har da tayata kukan Abin ya tab'a zuciyan ta ,shawara da hak'uri yaba Husna tace taje gidan komai zai daidaita insha ALLAH yanzu suna cikin Jin zafin faruwar lamarinne Amman zasu huce ,Amman karta tafi ta Bari sai zuwa gobe in zasu tafin in sun sake cewa tabar gidan sai ta tafi. Aunty sa'adiya ta shirya ta tafi asibitin ta duba jikin shi sosai ta tausaya Mai ,taso tayi magana Akan abun gudun Kar tata tayi zafi sai ta fasa. Husna wuni tayi a gidan su Harri na aikin rarashi ,har su mumcy suka dawo da FU'AD d yamma likis. Yaya Jameel Yana tozali da Husna ya Fara cemata" me kikeyi ne har yanzu Baki tafi ba ? Tsugunawa tayi zata bashi hak'uri ya juya baya Yana cewa baze saurareta ba kawai ta tafi gidan su sai yazo. Husna mikewa tayi tace su Mata alfarmar magana da FU'AD ko so d'aya ne Dan ALLAH.......Basu Bata izini ba ta tashi taje gaban FU'AD tace Dan ALLAH FU'AD kayi hak'uri ko kiyashi bantaba cutarwa ba bare Kai kayyada Dani wallahi Nina kaina a daure yake kabud'e Baki kayi magana ka fitar Dani daga zargin da su mumcy sukemin inkamin Haka kagama min komai sai na tafi nabarma gidan ku ,kayi magana FU'AD Dan ALLAH Tana had'a hannun ta biyu a goshinta tanata rabza kuka, sanan kaima ka amince na tafi? FU'AD d'aga Kai yayi Yana kawar da Kai gefe ,zaro Ido Husna tayi ,tace nagode da katamcin ku gareni bazanmanta wanan ba ko zanbar duniya dashi Zan tafi acikin Raina..... Sai mumcy tace tashi kije driver ya kaiki je ki d'auki kayanki ,Husna cewa ta sakeyi na tafi ko FU'AD? Da hannu ya Mata nuni da eh ta tafi baya son ganinta,husna na kuka ta tashi ta haura sama ,aunty sa'adiya ta bita tanata Bata hak'uri suka rungumu junan su ,aunty sa'adiya ce ta tayata had'a kayanta a wani akwati me kyau da tsada ,har ta d'auko wani kud'i ta Bata har bakin mota rakata Tana cemata zasuyi waya ,Husna na kuka tabar gidan duk da mumcy Tana Jin babu Dadi a ranta Amman Babu yadda zatayi lafiyar FU'AD yafi Mata komai ayanzu. Husna Bata gane Tana cikin matsanaicin tashin hankali ba sai da taga anfaka a gidan da take farinciki lokacin da ta barshi yau gashi ta dawo Mai inta tuna da cewa da babanta zatayi rayuwa a gidan sai tad'an samu nutsuwa ta fito a mota ta ja akwatin ta da sasanyar sallama ta Shiga gidan jiki Babu kwari. Mama habee na ganin ta tace ,me ya dawo dake Nan keda kike cikin aljannar duniya har kina hurama mutane hanci? Husna kukane yaso kwace Mata ta nufi d'akin da ta Bari ,sai ko humaira Tasha gabanta ke Baki da matsuguni a gidan Nan mun yafe ki Nan dakina ne waje road ........Tana nuna Mata hanyar waje Husna ajiye akwatin tayi tace Ina babana? Mama habee tace uban wa Kikaba ajiyar gyatumin naki? Husna cikin kuka ta fice a gidan ta nufi wajen sana'ar shi ta awo ,tun kafin ta k'arasa taga shagon a rufe ,da zata juyo ganin ko zama anyanatayi a gidan ubanta sai ta k'arasa wajen mak'ocin shi taga ma ba Wanda ta sani bane ,duk da Haka tamai sallama ta gaishe shi ta tambayeshi babanta ,yace wallahi Suma cigiyar shi suke yau satin shi kusan na 3 kenan be bud'e shagon ba sun aika gidan ance wai ba'asan inda yake ba ,salati Husna tasa yayinda kuka yaci k'arfinta ta nufi gida. Tana Shiga ta sake tambayan su Ina babanta ne wai ,mama habee tayi shewa tace ya bacce Suma neman shi suke in ta ganshi ta turo musu shi humaira nata taunar cingam. Husna kuka tasa Tana ta Shiga uku ,mama habee tace ko d'aya back shiga ba sai kin ganni a titi Zaki kwana karti sunyo kanki Nan Zaki San cewa kin Shiga uku dumu_dumu Dan wallahi bazaki kwana cikin gidanan ba in Kuma kina musu zauna kisha mamaki ,Husna kuka tasa Tana ba mama habee hak'uri Amman ta turo Mata d'an kwali ma alamu babu sani babu sabo rashin mutunci zallah. Husna d'ankwalin ta ta shimfida zata zauna sai humaira ta tare wajen ta nad'e Mata d'an kwalin ,sosai duniya Tama Husna zafi Nan ta sake tabatar da cewa Akwai mugun k'ulli da sukayi cikin turaren Nan Dan Haka ta taho dashi. Haka suka Gama abincin Rana suka cinye a gaban Husna ,sai da suka Shiga d'aki ta d'auki buta ta kama Ruwa tayi alwala ta shimfida d'ankwalin ta tayi sallah ta dinga rok'on ubangijinta. Tana idarwa ta mik'e ta karkad'e d'ankwalin ta tafice a gidan suka bushe da dariya suna cewa Rana zafi inuwa k'una bakiga komai ba shegiya Mai k'ashin arziki Kuma cikin tsiya aka haife ki aciki nakeson ki mutu ba a wadata ba ,ko kin bar gidan ba a Haka zanbarki ba muzuba mugani...... Husna gidan su hafeeza ta nufa wacce ta Bata *RIK'ON KWARYA* Aikinta tana kuka take sanarma da maman hafeezar komai har k'arshe ,maman hafeezar ce tace ta barmusu gidan ta nemi wani daga 'yan uwanta ta koma wajen su , ma'un tace ai Bata da wajen zuwa ita ko Akwai ma kanta ya kulle yanzu ,suna cikin Haka sai wayarta ta Fara ringing husnan ma bataji ba maman ce tace "bake ake Kira ba? Sanan Husna ta d'aga wayar a kasalance batare da ta duba me Kiran ba muryarta fal kuka ,Tana Jin muryar aunty huwaila taji kukan na neman tsayawa ,aunty huwaila ce tace meke faruwa ta Gaya Mata ? Husna Bata b'oye Mata komai ba ta fad'a Mata Tana Kuka kamar ranta ze fita,aunty huwaila cewa tayi ta share hawayenta ta kwantar da hankalinta matsalar ta tazo k'arshe bak'incikin ta ze yaye da yadda ubangiji ,ta jirata Akwai magana Mai mahimmanci da zasuyi ta jira wayar ta anjima.......... Sharing........... Comments.......... Urs maman shaheed😍 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg49 *AISHAN Maman AISHA Wanan Pg Din Kyauta Na Baki Shi Kiji Dadinki Keda kawarki Husnan FU'AD Dftn Kuna Tare A India*🙃🥰🤣 Husna Bata Sami matsala da baiwar ALLAH Nan ba har ya landing ,Koda suka sauka Husna nata k'ok'arin yadda zata sanarma da aunty huwaila isowarsu ,tanata neman yadda zatayi agarin waige_waigen ta tahango aunty huwaila da wata sun nufo ta da murna suna Mata sannu da zuwa. Dad'ine ya Kama Husna batare da Tasha wiya ba ta samu aunty huwaila Ashe Tana jiran su, aunty huwaila sai da ta Fara rungume wanna baiwar ALLAH kafin ta dawo Kam Husna Tana Mata sannu da hanya ya ce ma matar da suka taho tare ta d'auki akwatin su ta saka cikin mota. Koda suka Gama Shiga motar Basu tsaya ko Ina ba sai a katafaren gidan aunty huwaila da iyalanta irin tsarin wasu gidajen India komai aciki har d'akunan koda ace family house ne. Suna Isa aka Kai Husna masaukinta itama baiwar ALLAH d'akinta daban sai wanan wace suka taho tare akace itace Mai kula dasu kome suke buk'ata sumata magana,Husna tace "toh aunty" Bayan su Husna sunci abinci ankaima matar nata ,sai Husna take cema aunty huwaila ya naji gidan Babu kowa ? Sai anty tace " Affan Yana wajen Aiki sadeeq Kuma ya tafi shop muhibat Kuma Tana makaranta Asma'u Husna takwarar ki da take gidan wani abokin abban su Gobe za'a dawo da ita su Kuma duk Nan da anjima Zaki gansu. Sai Husna tace "ayya Ashe inada takwara a gidanan" Sai aunty tace "ai tunda naji yaya tasa sunan naji inason sunan da na samu muhibat abban ta yaki yadda asa da na sake samun macce Dole ya amince akasa.......aunty Bata rufe bakiba Husna tace yauwa aunty meyasa aka raba Mana d'aki da matar can? Da kinbar mu tare zan iya rayuwa da ita Sam bana Jin kyamarta ko tsoronta na Rasa meyasa. Sai aunty huwaila tace "hakane na raba mukune kawai kowa da d'akin shi a gidanan" muhibban da Husna ne kawai suke d'aki daya Amman ko Affan da sadeeq kowa d'akin shi daban, itama bana raba muku bane Dan Ina kyamarta ,inda Ina kyamarta bazan daukota na kawota k'asar da nake zaune ba Kuma har cikin gidana har na Bata d'aki ba da a wajen zan Bata d'aki kusa da papashango , Akwai Abin da hakan yake nufi ,in kin lura rashin lafiyanta Mai tsafta ne babu duk'a Babu zagi Babu jifa bare surutai babu dariyar rashin nutsuwar Nan Dan nni banma taba d'aukanta a Mara hankali ba sai Mara lafiya zuwa wani lokaci Kuna Ina Mata fatan samun lafiya da izinin ALLAH Dan yanzu Abin da nasa agaba kenan Nemo mata maganin warakar ta indai kud'i da jajurcewa suna Aiki kema ki tayani Addu'a. Husna cewa tayi "ALLAH yasa mudace , ALLAH y saka Miki da mafificin Aljanna aunty irin ku Basu da yawa aunty ,sai aunty ta rungume ta Tana cewa" inaso kifini kekuma in kin taso da naki d'abi'un Dan mamanki ta fini kyawun Hali da kirki da tausayin na kasa da ita acikin halinta befi rabi nakedashi Dan ita ranta fansa ne Akan Dan uwanta na jini kema Kuma ai jini tace. Sai Husna tace "Toh ALLAH ya bani ikon koyi da Halin ku da d'abi'un ku" yauwa aunty wai matar Nan meye ita a wajen ki Ina nufin kunada alak'a ne? Kafin aunty taba Husna amsa sai da taji daram a kirjinta ,sanan ta daure tace "bamu da alak'a ta kusa ko ta nesa kawai dai na kwadaitu da son taimakon ta ne kinsan na Gaya Miki yadda na Fara ganinta Kuma gani nayi matsalanta ba wata babba bace irin shine in ba'asamu kulawa da dagewa Kan maganin su se matsalar ta zama babban ko tabi jiki har a Rasa maganin ,in kin kula matsalan ta Yana buk'atan Addu'a Kuma Kinga ai bani daya keson taimaka Mata ba harda wani bawan ALLAH bawai Dan tafi kowa buk'atan taimakon ba. Sai ko Husna tace "Haka fa Dan mun had'u dashi ma har yabada number shi wai in Ana neman temakon shi ashirye yake da ya taimaka Kuma yanaso a dinga bashi update na rashin lafiyan ta. Aunty huwaila tace "babu damuwa adanata in Zan kirashi sai na karb'a wajen ki yanzu kije ki huta kafin Yan uwanki su dawo abban su dai bai gari ya tafi Germany jiya da asuba 1week kawai zeyi ya dawo. Husna tace "ALLAH ya dawo dashi lafiya " Aunty tace "Ameen 'yata" Bayan Husna ta Shiga d'akin matar tanata janta da Hira Dan son Kara gano kalan Rashin lafiyanta matar sai ta k'urama Husna ido sai ta d'auke babu um Babu um_um duk yadda Husna taso matar tace wani Abu Taki furta komai Dole Husna ta karanto Addu'a ta tofa Mata ta fice zuwa nata d'akin ,Tana Shiga ta kwanta a gado tunanin FU'AD da su mumcy ya dawo Mata arai sosai tayi Nisa cikin kogin tunanin Halin da suke ciki Dan ita bataga laifin su ba Dan sun koreta ta cancanci fiye ma da Haka yanzu in FU'AD ya samu matsala fa? Waye sila? Ai nice ba kowa ba sosai ta k'ara tausayama kanta tana Addu'a ALLAH yasa Abin duk da akayi Dan ita akay Banda wani Dan matsalar tazoma FU'AD da sauki. Yamma lis gab da magrib su Affan da sadeeq suka dawo ita Kuma muhibat ta wuce gidan da Husna take ace tazo ta kwana washe gari sai su koma gida tare shine ta sanar ma ammyn su aunty huwaila ta waya Kuma dama itama sun kirata kafin suka Kira muhibat din Dan dakyr aka Bari sukaje gidan Dan basa yawo. Bayan Affan ya dawo da sadeeq sai cewa suke"wai Ina bakin nasu? Ammyn su tace suzo suje wajen matar da take Gaya musu Tana son taimaka Mata ,ko da suka Shiga d'akin affan dake shine babba gabanta yaje Yana gaisheta yaga ta kalle shi batace komai ba ya sake cewa ammy Bata magana ne? Ammyn girgiza Kai tayi alamar a tace " tanayi Amman zuwa zuwa,sai ko sadeeq dake gefe yanata karantar matar sai ya gano wani Abu sai yaca "ammy nifa ganin Kama nakeyi a tsakanin ki da matar Nan,Kai Yaya bayya baka gani ba? Sai Affan yace wai Kai ka rainani sai bayya ya amsama ,sai ammy tasa musu dariya Tana cewa "tunda yace maka yafi son Yaya shi Dan 9ja ne k'asar India zuwa mukayi sai ka dinga Kiran shi da Abin da yafi so. Sai sadeeq yace to bayya au double sorry Yaya ALLAH ammy suna yanayi da baiwar ALLAH Nan baka lura ba ? Sai Affan yace " Ni ban gani ba kaima inajin a karatun ka ka hango hakan, jin sadeeq ya dage sai ammyn tace wanan kuma Kai kaga hakan muje na Kira muku Husna. Bayan sun fito suka zauna a main parlour ,sai ga ammyn su da Husna ,Bayan ta gabat musu da ita ,itama ta gabatar Mata dasu ,sosai suka gaisa da juna cikin mutunci da son junan su ,har dare suna tare a parlour anata hira da ciye_ciye Mai Aiki nata hidima dasu time to time suna zuwa duba baiwar ALLAH Nan dasu da me aikin da take kula da ita ,anan ne sadeeq yake cewa Akwai wani ogan shi Kuma malamin shine zemai magana in ya Bamu appointment sai muje mu ganshi a hospital d'inshi,sai ammy tace "yauwa yamai maganan. Bayan dare yayi kowa ya tafi ya kwanta Husna tunanin Yaya FU'AD yake ko ya dawo hayyacin shi ? Kashi bataso asan inda take bare ta Kira aunty sa'adiya. Mumcy angama shirya tafiya Akan gobe jirgin su ze daga zuwa India ,aunty sa'adiya ce tazo take gayama mumcy massage din da Husna ta turo Mata Tana cewa _taba mumcy hakuri Bata da laifi itama turaren Bata akayi Akan tayi Amfani dashi ita Kuma Bata Kai ga Amfani dashi har FU'AD ya d'auka ya fesa wallahi da tasan da wani Abu da bazata Bari ya fesa ba Dan Bata da riba a cikin cutar da wani bare FU'AD wallahi ALLAH shine shedanta Kuma ze fitar da ita_ _Kun kini Waze soni Ina muku fatan Alkhairi inda rabon mu sake haduwa to in Babu ku gafarceni nagode da Alkhairin ku gareni_ Ma'salam. Ana Gama karantama mumcy tace Akira Mata ita ta Fadi lefin waye? Aka dinga Kiran number Husna a kashe ,sai cewa mumcy tayi abari zuwa da safe a sake gwadawa,sun Jima suna tataunawa akan maganar har Yaya Jameel yazo ya same su suna maganar ,shima yaso sanin laifin na waye har number ya karb'a ya gwada Kira shima ya akashe da ya gaji da gwadawa sai ya hak'ura zuwa da safe ,dama adare mumcy ta nemi akawo ma FU'AD taimako na Addu'o'e da maganin musulunci Wanda zasu tafi dashi can adinga hadawa dashi Ana hadawa da na asibitin. Mumcy kwana tayi da Husna a zuciyar ta sai take ganin tayi gagawan bin ra'ayin FU'AD da ta hanyar nuni da yake Mata akan tafiyar husnan. Washe gari su mumcy sun Gama shiryawa tsaf ,aka sake gwada number Husna shiru ankira yafi so 20 Amman zancen dai akashe yake sai hak'ura sukayi, mumcy ta barma sa'adiya sak'on tacigaba da gwadawa Dan ALLAH a wunin yau in Bata kunna wayar ba watakila fishin zuciya tayi tayi barar zuwa gidan su ta tambayeta,aunty sa'adiya tace toh insha ALLAH zatayi hakan. Bayan sun Gama shiryawa har ansha kayansu a mota driver ze kaisu Airport tare da Rakiyar aunty sa'adiya,suna Isa sukayi sallama da aunty sa'adiya mumcy nata jadaddama sa'adiya tafa je intaji shiru sai ta kirata ta sanar Mata yadda akayi. Ba'a Jima ba jirgin su FU'AD ya shilla sarararin subuhana inda ya nausa k'asar lndia. *Nagode da Addu'o'e ku gareni da my son Muhammad Mai babban suna jikin mu da sauki,but now Alhamdullilah* *Kumin sorry inbakuga post ba Gobe kumin uziri*🤦🏼‍♀ *Kuyi hak'uri da wanan*🙃 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg48 Maman hafeeza cema Husna tayi taje ta d'auko kayanta ta zauna a gidan kafin komai ya daidai ta Amman Kar ta nunama su mama habee a gidan zata zauna. Husna na kuka takema maman godiya ,fita tayi taje ta d'auko kayan mama habee nata jifanta da munanan kalamai Tana cewa ta ALLAH zata kasance lokacin da yayarki zata maye tabi gurbinki agidan attajiri indai Ina Raye ,kekuma wuya da taskun rayuwa bakiga komai ba wallahi ,Husna Tana Kuka take cemata mama habee duk Abin da zakiyi ki dinga sanin hukuncin ALLAH acikin shi .....Husna sai saukan Mari taji humaira ta sakar Mata ke Dan uwarki b'ataciya kina nufin mamance Bata tsoron ALLAH kome? Kina sake furta wata kalma zanyi k'asa_k'asa dake inkin Musa kice Tak! Husna shiru tayi tasan kad'an da aikin su sumata daron dangi haka ta fita ko haidar Bata samu damar gani ba tun zuwanta gidan, wani layi tabi Dan Kar su gane inda ta nufa Dan kad'an da aikin mama habee tasa abiyota ,Aiko sai da tasa humaira ta bita abaya wai taga inda tayi ,aka samu akasi badan ta canja layi tayi shataletale ba da zasu had'u ,har Husna ta Isa gidan maman hafeeza humaira Bata ganta ba tanata bilayi a unguwar d ta gaji ta koma gida. Sosai Husna takeson tuno wata kalma da taji humaira ta ambata Akan mahaifiyar ta Dan tayi fashin Baki akai ,Amman wayar da aunty huwaila ta sake Mata ita ta tafi Mata da wanan tunanin ,jiki na rawa husna ta d'aga wayar"murya na rawa tace "Assalamu Alaikum aunty" Aunty huwaila tace "Husna kibani nutsuwarka Nan kinji ko komai yazo k'arshe da yadda ALLAH yanzu ki shirya a yau d'inan kije gidan masu tabin kwakwalwanan dake unguwar chiroma ki Ce nuna Miki aunty tanni to ita zata had'aki da wacce zata Miki bayani ta nuna Miki wata baiwar ALLAH wacce nakeso kuzo Nan India tare da ita na muku buking flight Gobe da Rana around 2:00pm ki kula kinji Akwai wani Yusuf ze kiraki yanzu shi ze shige muku gaba na komai da komai kinji har tasowar ku in kun iso sai ki kirani a waya ,kafin haka ma Zan k'ara Miki bayani da yadda komai ze tafi anjima da dadare in muna chart kinji ,yanzu kije can d'in na Gama magana dasu...... Husna kuka ta fashe dashi Tama Rasa kukan dad'ine kona meye Tama Rasa ,da sauri ta kashe wayar ta Fara yima maman hafeeza bayani ,da maman hafeeza taso su tafi tare Dan shige Mata gaba ta Bata kariyar da inda ace mamanta nada Rai zata samu fin Haka Amman sai aka bugo Mata waya Akan zatayi bako Dole ta hak'ura ta umarci Husna da tayi wanka ta kintsa ta tafi ,Husna Dan sauri_sauri da bazatayi wankan ba gani take lokaci ze k'ure sai da maman tace haba keko kinsha kuka kin k'oshi ga Rana da Zaki d'iba Banda Wanda Kika d'ebo daure ki watsa kiyi ki fito kije ki dawo kafin lokaci ya k'ure maki...... Bayan Husna ta fito ta canja Kaya zuwa Riga da skirt na atamfa da hijab ta fito Tana maman sallama ,maman ta mik'o Mata d'ari biyar daga cikin kud'in masu adashe tace gashi ze isheki kuwa kiyi na mota? Sai husna tace ,laa ki barshi mama da kud'i a wajena ,sai maman tace toh yi sauri karki zauna Dan ALLAH. Bayan Husna tabi wani layi duk Dan ta gujema ganin wani daga gidan mama habee Tana cikin tafiya ta samu nape ya d'auketa ,kafin ta Isa gidan Yusuf ya kirata ya Mata bayani Akan sai gobe su had'u a gidan marasa lafiyan na laying chiroman Dan daga can zai kaisu Airport d'in ,Husna tace toh ta gode zata kintsa komai zuwa gobe ze sameta acan insha ALLAH. Husna na Isa ta samu wani ta tambayeshi aunty lantana ,aka had'ata da ita ,sai ta Mata bayani itama ta kaita wajen babban likitan da yake kula da maralaiyan ya Mata bayani sosai har akaci sa'a Alhajin da yake d'aukan nauyin kula da ita yazo Dan ya samu Kiran gagawa daga hukumar gidan ,yazo suka Mai bayani ,yanzuma suka Kara ma Husna da Alhaji bayani Akan zasu Mata transfer zuwa India bisa sa hannun hukumar masu kula da masu tabin kwakwalwanan na India bisa sahanu da taimakon aunty huwaila an turo musu da komai ta Gmail sun gamsu Dan Haka suka amince ,Alhajin ma fatan Alkhairi yayi Akan ALLAH yasa su Dace har ya karbi number Husna Akan ze dinga Kira yaji lafiyar ta tunda yaga tare zasu tafi,duk wanan abun da akeyi Husna bataga matar ba har yanzu k'arshe Mai sai cemata akayi Tana bacci ba'aso a tasheta Kuma sai dai ta l'ek'a ta window ta ganta kafin goben tazo tafiya da ita ,ta window ta ganta kuwa Bata wani rarabe da kamanninta ko kalar ta ba bak'ace ko farace Sam Bata gane ba tadai Mata fatan samun lafiya ,har ta k'osa ta tashi taga irin rashin lafiyar da take ciki. Bayan Husna ta musu sallama ta koma gidan maman hafeeza. Da dadare Husna na d'akin hafeeza nada tanata charting da aunty huwaila da aunty sa'adiya harda Aisha Ghana tanata Mata jajen Abin da ya faru ,itama aunty sa'adiya nata Bata hak'uri Tana tambayanta taba gidansu ko ? "Eh" kawai Husna tace Mata Dan gajarta maganar ,itama aunty huwaila tanata Mata bayanin yadda goben ze kasance da Kuma Mata tambaya Akan yadda sukayi da masu duba baiwar ALLAH Nan ,Husna nata Mata bayani har da sanar Mata Basu had'u bama amman ta lekata ta window sai gobe zata ganta sunata ma kwantar min da hankali wai haukanta ba na duk'a ko surutai bane tsabtataciyar haukane duk yadda kakeson sarafata zakayi indai ka iya bida ita kawai dai Tana son labarin ban tausayi ne ayadda suka Gama lura da ita Nan zakaga har hawaye take in tausayin ya tsananta ma harda kuka Dan Haka suke hango alamun nasara a rashin lafiyan ta gashi karamin Abu Wanda suke ganin zai Zo da sauki ya gagara zuwa da zauki sai yayi sauki sai yayi tsanani .......aunty huwaila tace ,hakane duk sun min wanan bayani ki kwantar da hankalinki lafiya zakuzo har inda nake da yadda Mai duk'a burina da fatana naganku a kusa Dani sai burina ya cika. Sosai Husna take godema ALLAH da ya sako aunty huwaila cikin Rayuwarta da babu Mara gata kanarta a duniya Dan da babu Abin da ze Hana a nad'a Mata sarautar Mara gata da sa'a aduniya ,godiya da kuka ta dinga yima aunty huwaila ta hanyar tura Mata da vn da emojis da ,aunty huwaila nata rarashin ta da nuna Mata babu komai. Ranar Husna kasa bacci tayi kusan kwana tayi online. Washe gari da asuba ta tashi tayi wanka ta gyara ma mama gidanta ta tayata had'a Abin da zasuyi Karin kumallo , ATM taje ta Ciro wasu kud'i acikin kud'in da aunty huwaila ta turo Mata ,sai da ta kusa kuka da ta tuna da drama da akayi da FU'AD ranar da ya bud'e Mata account ,tuno da wulak'ancin da suka Mata har Yaya Jameel da mumcy yasa taji Tama tsanesu ji take kamar ta share babinsu a Rayuwarta ,can Kuma zuciyarta tace "karki zamo Mai son kanki" yanzu kinsan Halin da FU'AD d'in yake ciki ? Kuma a sanadinki hakan ya faru dashi fa? Sai wani sashin zuciyar nata yace "toh ba korata sukayi ba ai da nida matsawa daga kanshi har sai Naga ya dawo hayyacin shi ,Amman yanzu ni takaina nakeyi tunda kowa son kanshi yake. Bayan ta Ciro kudin ta dawo gida sosai sukayi Hira d mama tanata karanta Mata rayuwa da irin mutunci da hak'uri irin na mahaifiyarta ,sosai Husna taso Jin irin mutuwar da mahaifiyarta tayi a bakin mama amman sai mama tace ke yarnan barni na mutu maza su kaini ba mata ba ,ki dage da Mata Addu'a kedai kinji duk girman gona Akwai kunyar k'ashe ,duk ta inda Husna ta bulloma da mama da tambaya sai mama ta toshe ko ta zille k'arshe dai ta umarce ta da ta tashi ta shirya Kar yaje Yana jiran ta. Bayan Husna ta gama shirnta tsaf cikin doguwar Riga Mai kyau da tsada ta yane kanta da gyale tayi kyau matuka ,Yusuf ne ya Mata waya yace gashi Nan ze taho itama tace Tana hanya insha ALLAH. Sosai mama ta Fara sabawa da Husna taji dad'in zama da ita , Addu'a da nasiha ta dinga yi Mata Tana cewa sai tajisu a waya ta dinga kiranta Dan ALLAH dama tun jiya Husna ta karbi number mama,husna har kyautan 15k taba mama da kyar mama ta karb'a Husna ta tafi .... Husna ta Riga Yusuf Isa wajen sai da ta cike wani form kafin akace a d'auko Mata matar Bayan sun Gama waya da aunty huwaila. Matashiyar datijuwa rashin lafiya be safe kyanta ya gushe ba ,sai dai ka tausaya Mata Dan rashin fahimtar Abu da batayi ,Amman yau wanka da shigar da aka Mata na Musamman ne Dan kayanta masu kyaune da tsada an saka Mata hijab anfeshe ta da turare komai nata tsaf gashi yau kamar batason magana Taki cewa komai tun tashin ta befi so 5 tayi magana ba ,yayin da suka k'araso gaban Husna da matar ,Husna na tozali da ita taji kirjinta ya buga atake jikinta ya Kama rawa ,aka zaunar da matar kusa da Husna ,matar tun da ta kalli Husna ta kau da Kai Bata k'ara kallonta ba sai da Yusuf yazo shima aka bashi wata takkada ya ceke yayi signing ,suka tafi Husna na gaba kusa da Yusuf matar na baya tayi shiru. Har suka Isa Airport din Husna na waya da aunty huwaila har taba Yusuf wayar suka Gama magana. Duk wani Abu daya Dace Yusuf ya musu iya yinshi sosai ,Husna take son ganin aunty huwaila saboda tarin tambayoyin da suke dunkulle a zuciyarta da bakin ta. Jirgin da su Husna zasu hau ya landing ,Ana musu screening .......... Yusuf sosai ya musu fatan sauka lafiya ,be bar airport d'in ba sai da yaga tashin jirgin su Husna sosai ta seta nutsuwarta duk da ko ganin jirgi Bata tabayi ba bare zuwa kusa dashi yau har itace a ciki , Addu'a kawai takeyi su sauka lafiya ba tare da kowa ya gane matar da suke tare tanada matsala ba. Bayan Yusuf ya gayama aunty huwaila su Husna sun taso ,sosai take shirye_shiryen tarban su day kyakyawar masauki. Kafin Husna ta kashe wayarta sai da tama aunty sa'adiya text massage ta sanar Mata da komai sanan ta kashe wayarta gaba d'aya *********** Su mumcy tafiyar su sai gobe ita da FU'AD da Yaya Jameel ,sosai takejin kamar ta aikata zunubi Akan hukuncin Husna ,har magana Tama Jameel Amman yace a rabu da ita ta cancanci fin Haka ma, mumcy dai hankalinta be kwanta ba Dan dai tafiya na gabanta ne Amman kamar taje ta dawo da ita har ta yanke hukuncin zata shawarci FU'AD inya amince ta dawo d'akinta ko Bayan tafiyar su ne ,inyaso sai sa'adiya taje ta dawo da ita. FU'AD Yana kwance babu umm babu umm_umm take Mai zancen Husna ta dawo ya girgiza Kai alamar aa , mumcy tace kamata uziri mubi komai sannu a hankali ,ta dawo? Ya sake girgiza Kai har da nuni da hannu ,sai ko Jameel yace Dan ALLAH ki hak'ura mumcy shifa yasan Abin da ya faru ,Dole mumcy ta hak'ura ta barshi Amman Husna na ranta ,Suma sun Gama shiri tsaf gobe sai India ......... Sharing Nd Comments 🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀ [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` By *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman Shaheed/ 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg50 Su FU'AD sun sauka lafiya ,har sun huta Dr ya fara duba FU'AD akan matsalan shi. Bayan sun huta sosai mumcy ta sake Kiran sa'adiya ta tambaye ta maganar zuwanta gidan su Husna ko ta sameta a waya? Sa'adiya tace Bata samu fita ba wayar Husna Kuma akashe take har lokacin ,Amman gobe insha ALLAH zataje , mumcy tace"toh" Washe gari sa'adiya ta shirya ta tafi gidan su husna cikin girmamawa ta gaishe da mama habee ,mama habee ta dinga Mata wani irin kallo, ganin sa'adiya ba Abin da tazo yi kenan ba sai tace " mama Dan ALLAH Ina Husna? Sai humaira tace "Ma'u dai" Sai sa'adiya tace" eh itafa Dan ALLAH Tana Ina sauri nake? Sai mama habee ta yamutsa fuska ta kebe Baki tace "wacce kike nema dai Bata Nan tazo gidan Nan Ina tambayanta mijinta da mutan gidan ko amsa bata bani ba band'aki ta Shiga ta fito ta had'a inata_inata Kinga Yar uwarta na Kamata Tana fizgewa wai barin garin zatayi babu yadda bamuyi Taki zama gashi mahaifinta baya nan, Arazane sa'adiya tace "kuka barta ta tafi Dan ALLAH? Mama habee tace " to kamata zamuyi mu daureta a turke? Mukasan Abin da ya korota? Sai sa'adiya tace "a Amman Dan ALLAH Basu San inda zata sameta ba? Mama habee tace bamu sani ba ,kije can ki nemeta. Sa'adiya zata k'ara magana sai ,mama habee tace "ke Yar Nan nagaji da amsa tambayoyin ki kamar a kotu ki Adana kalaman ki zasu Miki Amfani Amman ni babu Amfani da zasu min,ki tashi kiyima tafiyar ki kije ki nemeta inda Zaki sameta Ni bani da damuwa da tatiyarta ko dawowarta shima Wanda ya auretan ai yasan kowa yasai rariya zata zubda Ruwa shi ya jiyo. Sa'adiya bataji dad'in kalaman mama habee ba ,sai ta Mike Tana cewa "Da yaddar ALLAH Zan ganta Kuma ko me yake a b'oye ALLAH ze bayana shi ,Dan da walakin goro a miya " tayi hanyar waje. Sai ko mama habee tace goro a uwar Miya ma har Ni Zaki gayama magana kizo har kida na da kin tsaya kiga karyar rashin kunya kudin banza keda Ma'u ko uban da ya haifi ma'un na tanaji amsar bashi bare ku karar kara Miya da kuka ganta a bagas, sa'adiya ko kulata batayi ba har ta fita ta ga haidar na tahowa ze Shiga gidan Daman tasan labarin shi awajen Husna sai ta kirashi ,yaje tace Mai "lna yayar shi ma'u? Sai haidar yace "tayi Aure Tana wani gida har yau su humaira Basu kaini na ganta ba ,Kuma baba yace ze kaimi wataran ,Amman abokina yace min jiya ya ganta da akwati a bakin titi zata tafi danazo gida na tambayi su mama Ina Yaya Ma'u Sai suka dinga zagina wai nabasu ajiyanta ne? Inata tunanin Zan ganta har yanzu ban ganta ba. Sai sa'adiya tace "toh Ina baban yanzu? Sai haidar yace "yayi tafiya Amman ya kusa dawowa, Sa'adiya ta d'auko 200 zata bashi sai ta tuna Halin mama habee Kar ta dakeshi sai ta mayar ta Ciro 20 ta bashi tace ya sai biscuit yace "ya gode ya koma da baya ya fasa Shiga gidan yayi hanyar kanti yanata murna" Sa'adiya dai gidan mumcy ta koma tanata tunanin inda Husna take karfa ace ta Shiga uwa duniya ? Da ba'a kyauta mata ba kuwa gashi ba kowa nata suka sani ba sai matsiyatan Marasa mutunci su humaira da basa Bari ayiaganar arziki dasu ,babanta ma baya Nan ,amman Bari su jira dawowa baban ko zasu Sami wani gamsashen bayani daga wajen shi. Sa'adiya na Gama dogon tunani ta Kira mumcy ta sanar Mata da babu Husna bare labarinta ,sosai hankali mumcy ya tashi ta dinga salati da salalami Tana cewa Dan ALLAH acigaba da gwada number ta har itama zataci gaba da gwadawa. Sa'adiya tace "toh agaishe da FU'AD da jiki" mumcy tace "zeji insha ALLAH tin zuwanmu likitoci suka had'u akanshi matsalan a numfashin shine insha ALLAH Kuma Kinga inata Mai Addu'a da malam yace in dinga Mai yace har sauka zasuyi yau dinan in sun Gama Zan kiraki sai Ayi sadaka kamar yadda yace. Sa'adiya tace "toh sai najiki hajiya" ************* Sosai sabo da shakuwa ya Fara Shiga tsakanin Husna da Affan yaron aunty huwaila ,Dan yau da wuri ma ya dawo gida tunda ya biya ya d'auko su mihibbat ya dawo dasu gida da yamma be koma wajen aikin Shiba ya zauna dasu a gida dake tunda suka ga Husna suka dinga murna duka makale a wajenta sunata Mata Hira da labari a Dole ta saki jiki dasu tun kafin su kwana tare Dan akwaisu da son mutane gasu sun girma Dan muhibat da zama budurwa Husna ce ma bata Gama zama budurwar ba tafi muhibat shigema Husna ma Tana cewa ai namcyn tace, Aunty huwaila dai Abin birgeta yayi taji dad'in yadda suka karbi Husna Dan dama tasan Bata da matsala dasu Dan Haka ko bayanin tanada Aure Bata taba musu ba Tana de ce musu akwar Yar yayarta da ta Rasu a wajen babanta Tana tausayin yarinyar sai kawai tace yarinyar zatazo ta zauna dasu na wani lokaci,daga baya tace ita da Mara lafiyar da takeson taimaka ma zasu taho, Suma su muhibat da sukaga Mara lafiyar sai da suka tausaya Mata suka dinga mata Hira sai dai ta bisu da ido. Ranar kwana su mihibbat da Husna babba da karama sukayi Ana Hira da kyar suka tafi d'akin su ,washe gari da suka tashi da wuri suka Gama komai na Shirin tafiya makaranta muhibat na jami'a ita Kuma Husna na secondary yayan su Affan ne ze kaisu daga Nan ze wuce da su Ammyn shi da Husna d Mara lafiya wajen likitan da sadeeq yake magana in sun Isa zasu Kira sadeeq din ya karaso su Kuma za'a ajiye su a makaranta. Bayan sun Gama karyawa ,sun fita gidan sai masu Aiki da masu kula da gidan ,Husna aka Fara ajiyewa sanan muhibat sai suka wuce ganin likitan ,suna Isa suka Kira sadeeq be Jima ba ya taho." Babu b'acin lokaci likita ya buk'aci a kawo Mai Mara lafiyan aunty huwaila ce ta kamata da sadeeq suka Shiga da ita taso tirjewa Amman dake aunty huwaila Akwai iya dabara ta lalab'ata suka Shiga tace Husna ta tsaya tare da Affan dake Yana jiran su sugama ya mayar dasu gida kafin ya wuce wajen aiki. Affan tsare Husna da tambayoyi ya dingayi ,tin daga Kan karatun ta na islama har na turanci da matakan da ta tsaya duk tamai bayanin komai babu Abin da ta b'oye ,ya Mata Al'k'awarin ze Mata lesson na tsawon sati4 da kanshi sanan ya mayar da ita makaranta anan indiyan,sosai Husna taji dad'i tamai godiya, sun Jima suna Hira kafin su sadeeq suka fito da Mara lafiyar suka nufi mota da ita aunty huwaila nace ma Husna da Affan mu tafi da yadda ALLAH za'a Dace Dr nada Kai sosai,affan da Husna atare sukace "ALLAH yasa adace" sadeeq ya amsa da Amin ,ai sananne ne ko jami'ar India ta bashi award...... Bayan komawar su gida shi sadeeq dama acan suka barshi ,Affan da ze tafi sai da yace ma Husna me ze taho mata dashi? Tace babu komai ita Ina tasan irin Abin cin india ,yasa dariya yace ko a TV bakya kallo? Tace "Ina kallo ba sosai ba Amman Dan ba ma'abociyar kallo bace Ni ,Kuma ma ai bana rik'e sunan su......su aunty huwaila da Affan din suka dinga Mata dariya ,aunty huwaila tace yadai siyo Mata Abin da zata iya ci kawai,yace to ya tafi ranshi fes da nishad'i. ********** FU'AD Yana asibiti karkashin kulawar wani kwararen babban likita inda aka farama FU'AD check up a iya ganowar su da iya sakashi a na'ura Mai kwakwalwa da suka dingayi suna sakewa kawai suna ganin an poisoning d'in shini ta hanyar Abin da ya shak'a Haka sukace Dan Haka zasuyi duk Mai yiwuwa Dan dedeta Mai numfashi da bashi maganin da ze dawo Mai da komai cikin brain din shi ba tare da ya tab'a tunani cewa ya tab'a loosing memory shi ba ze warke kamar ma beyi ba ,aka musu bayanin adadin ma'udan kudin da zasu biya atake sukace sun amince su Fara aikin su kawai, Akaba Yaya Jameel takarda yasa hannu suka Fara bama FU'AD magani na tsawon kwana 3 kafin a mishi Abin da za'a mishi na gaba. *********** Kullin wani shakuwane yake Shiga tsakanin Affan da he Husna itade iya Kama kanta tanayi dan tafi kowa sanin ita wacece Amman a tunanin ta aunty Bata sanar musu da hakikanin matsayin ta na matar Aure ba ayyada ta lura da yadda suke d'aukan ta matsayin budurwa ,Dan Haka itama Bata sanar musu da gaskiya ba a tunaninta batasan dalilin yin hakan da aunty tayi ba wata Kila ta fita hujja duba da yadda batasan ma matsayin Auren nata a Halin yanzu ba ,shin FU'AD ya yadda Bata da sa hannu a Kan cutar dashi? Ko kuwa har yanzu Yana zargin ta? Shin Auren su ma Yana Nan ko ya datse igiyar Auren sun? Bata da masaniya Dan Haka itama Bari ta fuskanci abubuwan dake tunkarota na cigaba kawai. ********* Sanaya da dadyn ta kulin cikin Mata mita yake ta shirya ta koma ga mijinta sai tace yayi hak'uri ta kusa komawa FU'AD ne yace ze Gaya Mata ran da zata dawo kulin Haka take gayama dadyn sanan fita takeyi any how abinta Bata kilace darajar aurenta har da saurayinta sun fita batare da sanin kowa a gidan ba inda yayi nasarar rabata da mutuncin ta batare da yaddan ta ko amincewar ta ba ,tayi takaici da nadama tayi kuka kamar ranta ze fita tamai taijara da zagi na tsamen nama dake a juice ya zuba Mata Abu Tasha ,shi Kuma a tunanin shi wani ya kwace Mai ita a 9ja har ya Santa a mace kafin shi da yakeson ta da Aure shine yasa yace shima sai ya nuna Mata son da yake Mata ta hanyar Jin ta ,sai gashi ya sameta a matsayin shine mutum na farko da yasanta yayi takaici Koda Abin ya faru da yasan hakane da be ci zarafin ta ba Dan yasan Tana son shi kenan tunda ta k'are Mai kanta har yanzu ,shi yisa da take ta zagin shi da Mai masifa be iya Mata komai ba sai hak'uri da ya dinga Bata da cewa Haka baze Kara faruwa ba da Mata Al'k'awarin ko a yanzu ze iya aurenta in ta amince zata rabu da mijin 9ja." Tana Kuka take sanar mai Ashe yanaso dady ya yafe ta ,daga Nan suka dingama junan su alkawaririka na yadda da juna da cewa hakan baze sake faruwa ba." Gajiya da dadyn yayi yasa ya d'aga waya ya Kira FU'AD din da kanshi don yaji shin gaske ne abin da sanayan ta fad'a Mai ,ya gwada number agaban sanayan yafi so 6 Amman baya tafiya,sanayan ko sai godiya takema ALLAH da murna." Kafin dady ya rigata samun FU'AD a waya tayi saurin guduwa d'aki Dan ta Kira FU'AD ta rokeshi ya rufa Mata asiri wajen dady , Itama Taji wayan a kashe ,ta gwada na mumcy shima a kashe ,ta Rasa yadda zatayi sai can ta tuna Ashe AISHA ta taba samata number sa'adiya Tana cemata ko mu bakiyi zumunci damu ba kyayi da aunty ki matar yayan mijinki ,to sai yau ta lalubota Dan ko da Wasa Bata taba gwadawa ba babu kunya ta kirata Kai tsaye ," Aunty sa'adiya ta d'aga cikin sallama da tambayan waye? Sanaya sosai ta Mata bayanin kanta , Sai sa,adiya tace "yau an tuna damune Haka? Sai sanaya ta Bata hak'uri tace Dan ALLAH mumcy fa na kirata number ta baya tafiya? Sai sa'adiya tace Ashe dai Kiran da dalili , mumcy na India" Sai sanaya tace ,toh FU'AD fa Dan Allah? Sa'adiya tace "hmmmm wai Baki da labarin bashi da lafiya ne? Sai sanaya ta yamutse fuska tace dama mutuwa yayi azuciyan ta ,afili kuma tace wallahi babu labari meya sameshi? Sai sa'adiya tace ,bashi da lafiya ne barin turo Miki number da ake samun su dashi ki Kira kiji Karin bayani." Sai sanaya tace" to turo min txn"ta kashe wayar ta babu ko sallama. Sai sa'adiya ta bi wayar da kallo tace "matar asara bama kisan mijinki Halin da yake ciki ba tsawon kwanaki" Wanan Akwai banza. Sanaya fita tayi tace "dady wai FU'AD Babu lafiya munyi magana da matar wanshi Nan ,so ga number ka kirasu." Sai dadyn yace bani naji meke damun wanan yaron ,yaro ya Tara uwar kud'i Haka daga Kai sai wanka sai uwarku ku kanku bakusan iyakacin Abin da kuke dashi ba ba Dole in asara tazo muku un_ respected ki samu h attack ba,bani naji asarar trillion nawa akayi? 🏃🏼‍♀ [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg52 Baccine ya Mai nauyi ya d'auke FU'AD be farka ba sai da Yaya Jameel yazo ya tashe shi Jin shiru be sakko ba. Masu aikin gidan da mutanen arziki sunata ma mumcy murnar samun lafiyar FU'AD ,a Yanzy hankalin mumcy sosai ya kwanta Dan ganin FU'AD Yana walwala Al'amarin inda zataga Husna da ya tsaya Mata arai. Har gidan su Husna suka koma akan ko ta dawo Amman sai wulak'anci da suka fuskanta daga mama habee sosai mumcy take dogon nazari Akan mama habee." Yau kusan satin su guda da dawowa Amman FU'AD indai aka gyara Mai d'akin shi ko falo sai yaga gyaran ba irin Wanda Husna ta Saba yi Mai bane ,yanaso ya ga Husna sosai kodan gyaran da take Mai Amman su mumcy sunce ance Bata gida toh Ina taje da auren da mumcy tasa aka musu akanta ita a garinsu haka akeyi? Sai wata zuciyar tace Mai "kaifa kuka nemi ta bar muku gidan ta Bari kuma neman me kuke Mata? Sai wata zuciyar tace Mai "gaskiya be kamata ace tabar gidan ba tun farko gashi da amincewar shi tabar gidan. FU'AD d Yaya Jameel d mumcy a falo suna zaune suna magana Akan Husna da inda za'a ganta ,sosai mumcy take nuna damuwarta Akan rashin sanin inda husnan ta ke da Kuma inda za'a ganta ,Yaya Jameel ne yabada shawarar anemi babanta aji daga gareshi mumcy tace "ai sa'adiya tace baya gidan Kuma mama habee Taki fad'an inda yake da Abin yazo da sauki ,sai mumcy tace " gaskiya hakin yarinyar Nan Yana kanmu wallahi ita sai yanzu ta Kara ganin kuskure cikin Abin da suka aikata alokacin idon su ya rufe Suma suka dada asassa tafiyartan Musamman Kai FU'AD da Daman baka d'auketa matar da kakaso ba kana ganin aurama ita nayi......sai FU'AD yace "mumcy nifa bansan lokacin da nace ta tafi ba." Sai mumcy tace "ai ba da Baki kace ta tafi ba nuni ka Mata da umarni wallahi alokacin naso tsayar da ita Amman idona Kai kawai yake hangowa Dan Haka na kasa tsayar da ita.......Yaya Jameel ne yace wallahi Nima Abin duk ya dameni gashi anbi number ta yaki tafiya har yau Ina tunanin ko zata Kira sa'adiya a waya ma Amman shiru har yau Bata kirata ba ita kanta Abin na damunta. Mumcy cewa tayi ko cigiyar ta zamu bayar ? FU'AD yace aa hakan ze zama tozarci kawai abari intaga dama duk lokacin da ta dawo shikenan. Mumcy tace "wanan ai ba magana bace son ALLAH dai ya dawo da ita lafiya zakuce hankalinta ya juyo Kan aurenta a duk inda take ,kuma ALLAH yasa Tana Halin lafiya shine fatanmu. FU'AD sai da yaji idin shi na neman rufewa alamun bacci sosai sanan ya haura ya haura sama ya kwanta yasa tunani a gaban shi ,wanin sashin zuciyar shi na cewa to meye na tunanin Husna ai kawai kayi baccin ka ka rabu da tunanin ta,sai kawai yabi shawarar zuciyar shi har bacci ya d'auke shi. Bayan FU'AD ya k'ara kwana 5 a gida su B2k duk sunzo sun duduba shi har gida ko yau sai da B2k ya sake duba shi har ya musu Al'k'awarin Gobe ze shigo insha ALLAH shima. Jin FU'AD zeje office mumcy da Yaya Jameel sunso hanashi Amman ya nuna musu Babu matsala ze iya zuwa Kuma ba dad'ewa zeyi ba. Washe gari da sassafe FU'AD ya tashi yayi wanka ya shirya ya sakko Yama mumcy sallama , mumcy ma tamai fatan Alkhairi har Yaya Jameel. Bayan awa 2 da zuwan FU'AD office jama'ar sa nata zuwa Mai ya k'arfin jiki ,Bayan mutane sun Dan sarara sai ga sakatariyar shi tazo tace Mai wata nason ganin shi ,kamar baze bada damar ace ta shigo ba amman sai yace "ace ta shigo" Fuska FU'AD na kallon wasu files har aka shigo, be d'ago ba sai muryar humaira yaji Tana Mai sallama ,a sukwane ya d'ago Yana tuhumar meya kawo ta me tazo yi yau Kuma? Sai tace" ko Zan iya zama? Sai FU'AD ya d'ago yace "tsaya a inda kike ma ya Isa ,ya akayi da wacce Kika Zo? Sai humaira tayi fari da Ido tace "dama tambayar ka nazo yi akan Yar uwarta ko ta dawo? Sai FU'AD yace "daga Ina ta dawo? Sai humaira tace ba nemanta aketayi ba muma nemanta mukeyi ko Ina bamu ganta ba shine Mama tace nazo naji ko anganta? FU'AD shiru yayi na wani Dan lokaci kafin yace "malama ALLAH ya bamu Alkhairi Husna Bata dawo ba shikenan na amsa tambayar ki? Humaira zata sake magana yace "ke fitamin a office ranshi a bacce ,sata sake magana duk da ta tsorata da korar da ya Mata ,da ya daka Mata wata uwar tsawa sai da ta Rasa k'ofan fita a gigice ta fice Tana mita wallahi mama habee zata turo Mai. Da taje gida karya da gaskiya ta kitsama mama habee da ta turo ta ,mama habee gyale ta d'auka suka koma office din FU'AD din Koda sukaje baya Nan har yabar office din ya koma gida. Be jima da Shiga gida ba ,ya Kira wani a company sai yake sanar Mai wata Mata da budurwa sunzo neman shi ,har FU'AD ya tambaye shi yaa fasalta Mai yadda suke atake FU'AD ya fahimci wacce take tutiyar ita maman Husna ce ,sai cemai yayi toh shikenan ya fad'a Mai sak'on da zai fad'a Mai ya kashe wayar yana me dogon nazari Akan mama habee da humaira." Ranar FU'AD kusan wuni yayi a sama Yana tunani Akan su mama habee da Husna da son sanin Wanda yaba husna turaren da ya fesa har ya Shiga cikin wanan Halin sanan ya zama Dole ya datse igiyar da takema su humairan jagoranci na zuwa office din shi daga ita har mayaifiyar ta." Sosai FU'AD ya Kara matsuwa da son ganin Husna Dan Mata tambayoyi sosai yake kewar ayukanta na gidan atake kishin Auren shi ya sake motsawa Akan waima a Ina take da take yawo da igiyar Aure akanta meya hanata waigowa gida? Ko Tana nufin ta hak'ura da auren da mumcy ta musu? FU'AD ba karamin tashin hankali ya Shiga ba akan son sanin inda Husna take ,burin shi tazo ta amsa Mai tambayoyin shi sai ta koma duk inda taga damar zuwa indai ya samu gamsasun amsoshi daga gareta, ya Jima a falo har gani yake kamar ze ganta ta fito daga d'akin shi Amman shiru. *********** Aunty huwaila ta jajirce ba itaba ba sadeeq ba akan maganin baiwar ALLAH Nan ,Husna nata katatun ta tana son Kiran aunty sa'adiya Tana tsoron wani yasan inda take wani lokacin har gwada Kiran takeyi sai zuciyarta ta gargad'eta sai ta fasa,sosai ta saki jiki da mutanen gidan har abban su Affan dake mutum ne Mai barkwanci da son mutane ,gashi muhibat d Husna karama suna yawan zuwa d'akin matar Nan Mara lafiya suna d'ebe Mata kewa da Mata Hira ko su dinfayin hirar su a gabanta amman batare da suna hayaniya ba sai Dan haka likitan da yake dubata yace musu adinga Mata ,yauma kamar kullin sunata Hira a d'akin matar ta k'urama Husna ido ko kiftawa batayi har Abin ya tsorata Husna muhibat ma ta gani da sauri ta fita ta Kira aunty huwaila ,aunty huwaila da ta gani tace ALLAH yasa hakan na nufin wani abu. Husna ta tambayeta me take nufi da Haka? Sai tace "Ina nufin ALLAH yasa sauki ne yazo Mana ta haka" su Husna sukace ALLAH yasa Amin. Affan sosai ya Fara nunama Husna ra'ayin shi Dan baya tsoran kowa ya gane ma yanzu Dan har aunty huwaila ta Fara fuskanta alokacin da ta Fara zargin hankalinta ya matuk'ar tashi duk da taga husnan na baya_baya dashi ,Amman sai aunty huwaila ta sake tsananta zargin ta Dan ta tabbatar shin hakanne sai take sama Affan Ido sosai Dan gano gaskiyar zargin ta. ********** Washe gari da FU'AD ya tafi office , still Mama habee ta sake dawowa , FU'AD ya Mata fata fata har bakin gate din company ya rakota Yana Mata gargadi me tsanani yanama masu gadin company da sakatariyar shi gargadi Akan karsu sake barinta ko yarta su Shiga Mai company inba hakaba abakin aikin su Dan ya nuna musu b'acin ranshi sosai,cike da nazari da tunani kala_kala ya koma office ,mama habee nata tsine Mai Tana cewa ya rabu da Husna kenan rabuwa na har abada asarare me zuciyar tsiya kana attajiri ka makalema matsiyaciya Dan rashin sanin darajan arziki, Indai nice kayi da 'yar halak Kuma zamu gauraya ne. Bayan FU'AD ya koma gida da damuwa fal a fuskar shi in an tambaye shi yace "babu komai" FU'AD sosai yake son ganin Husna ko sanin inda take ,ya kirata har ya gaji ya Mata massage yafi so nawa Amman Babu reply yau har gidan su sukaje d Yaya Jameel ,suka yi suka dinga tambayar mutane makotan shi sai aka kwatanta musu wajen shagon shi sukaje suka tambayi mak'ocin shi yace wallahi baida labarin shi dayan Kuma yace shima sabone a wajen ,Suma har gidan shi sukaje suji ko lafiya Amman matarshi ta musu hauka suka kyaleta shine har yau babu Wanda ya sake komawa." Sosai su Yaya Jameel suke neman Wanda yasan inda baban yake ko Husna komawa sukayi sukaje unguwar akace su nemi wani abokin shawarar shi a Bayan layi wata kila yanada masaniyar inda yake,suka rankaya aka rakasu. Bayan sun gaisa suka tambaye shi inda baba yake ko ya sani? Atake yace gaskiya be sani ba ,su FU'AD har suna Shirin tafiya Bayan sunmai godiya da sallama sai ya kirasu yake tambayar su ko su suwaye? Sai Yaya Jameel yace "wanan mijin yarsa ce ni Kuma yayan shine" Har zasu sake tafiya mutumin ya sake cewa , mijin Ma'u kenan? Sai Jameel yace "eh" Sai FU'AD yace "Yaya tashi muje kawai" Sai mutumin yace "Dan ALLAH ko Zan iya sanin dalilin neman shi da kukeyi ? A fusace FU'AD yace "babu mutafi Yaya kawai" Sai mutumin yace "haba yaro fushin fari ba naka bane matam bayi baya Bata,inda Rai da rabo ku gayamin ko Akwai temakon da Zan iya muku ,baban Ma'u amini na ne nasan sirin shi yasan nawa ku gayamin ko Zan iya taimaka muku? FU'AD ya Gama hassala gani yake mutumin Bata musu lokaci kawai zeyi ,sai jameel yace "dama baban muke nema Dan munaso musan ko Husna Tana tare dashi? Sai mutum ya firgita yace "meya Sami Ma'u badai Bata tayi ba" FU'AD a fusace yace "ba Bata tayi ba nemanta dai muke" Sai Jameel yace "eh nemanta muke munga baban ma baya Nan shine muke zaton ko duk inda yake suna tare Dan hankalin mu ya kwanta" Sai mutum yayi ajiyar zuciya yace "ki gafarce Ni kaima abokina ka gafarce Ni kace karna gayama kowa amman Dole na fada Dan Abin ya shafeka ma'un ka ake nema Inna b'oyema zakace ban kyauta maka ba." Dai FU'AD ya juyo Yana cewa "me kake cewa? Sai mutumin yace "shi yace karna Fadi inda yake Amman Dole na muku jagoranci duk da bansan gidan ba Nima sai kwatance da ya bani ,Dan Yana kyauyen karmanje masifa da bala'in matarshi yasa ya tafi yabar Mata garin Dan yadda yace min badan haidar da Ma'u ba da yabar su kenan baze dawo ba duk da can din duk Yan uwansa sun mutu sai wasu kalilan ,Amman fa da tafiya inkun shirya ko yaushe ne sai kuzo muje ko ALLAH zesa mu Dace. FU'AD wani wawan ajiyar zuciya yayi gani take anma Dace kawai ,sai Yaya Jameel da ya Riga FU'AD magana toh Gobe sai mu tafi da safe Babu matsala? Sai mutumin yace babu insha ALLAH, FU'AD ba haka yaso ba beki a tafi alokacin ba ,Amman sai yayi shiru tunda Yaya ya Gama magana ,sukama mutumin sallama suka tafi , FU'AD nata ayyana rashin kirkin da zema Husna inta Bari suka had'u tasa Ana ta wani nemanta kamar 'yar gwal wata dirty girl da ita badan tsoron Kar ALLAH ya tambaye shi ba da babu wani neman ta da ze Bata lokaci yanayi tunda babu Abin da take tsinana Mai ,dai gyaran d'akin da k'oshi ze iya Abin shi ita baga tuwo ba bare Miya sai dai adafa tashi yanzu kawai ta tafi daga Mata gatse kamar dama jira takeyi ta tashi hankalin uwa tagari kawai. *Maman shaheed*👌🏻 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` By *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman Shaheed/ 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg51 Hannun dady na rawa ya dailing number d sanaya ta bashi ya mayar wayar shi, Kira 1,2......aka d'aga cikin nutsuwa mumcy tamai sallama." Dady sai cewa yayi meya Sami FU'AD d'in ance min bashi d lafiya har anfita da shi dafatan ba struck y samu ba ko? Mumcy ajiyar zuciya tayi da ta fahimci me maganar sanan tace "ALLAH ya raba FU'AD da wani Abu me Kama da Haka ma , FU'AD dai kawai baida lafiya ne da izinin ALLAH Kuma ya kusa samun sauki." Sai dady yace "toh bani shi" sai mumcy tace "ai baya iya magana" Sai dady ya sake cewa "kince matsalar karamace gashi yaro karami Yana neman zama wani iri akan wani lisafe_lisafen shi ,ki gayamin gaskiya Akan Abin da ya Sami Dan d'an uwana? Sai mumcy tace "kawai turare ya shak'a over sai yazo Mai da matsala shine aka turo mu Nan India Kuma mun Fara ganin nasara da yadda ALLAH." Sai dady yace "toh ashaa Aiki ya b'aci Abu beyi Dadi ba ,Zan kawo Mai matarshi don tayi jinyar shi jibi INSHA ALLAH muna hanya...... Mumcy ta katse shi Akan base sun Zo ba ,dady ya Fara fada Yana cewa Dole fa matar shi tazo taga Halin da mijinta yake ciki Dan tunda taji labari hankalinta ya tashi har yanzu be kwanta ba Dan Haka zuwa kamar tazo ta ganshi kibar Bata bakin ki ma Tana iyalin shi guda. Dole mumcy tace "toh ALLAH ya nuna Mana sai kunzo" Jameel yaji haushin zuwan da dady ya dage sai yayi ,sai da mumcy ta dinga Mai fad'a sanan ya hak'ura ya kyale su. Tun da mumcy taji labarin rashin samu ko ganin Husna hankalin ta yake a tashe,ko da yaushe Tana sake sawa a binciko Mata Halin da Husna take ciki Amman shiru har yanzu. *********** Sosai aunty huwaila ta dage akan matar Nan da duk wani Abu na kula da lafiyar ta tare da taimakon sadeeq da su Husna. Affan ma ya Fara koyama Husna karatu sosai ya fahimci kwanyar ta tana ja ,wani lokacin su muhibbat na hira su Kuma suna lesson din su. ********* Gobe dadyn sanaya zasu Zo shida sanaya ,ya Gama tursasa sanaya sosai Dan sai da ya Mata wuta_wuta kafin ta amince zata je Amman ba ason ranta ba. Washe gari kuwa suka zuba tafiyar su ta sarararin subuhana jirgin su be tsaya ko Ina ba sai India suka Kira Yaya Jameel yazo ya tafi dasu yanata mita a zuciyar shi." Tunda sanaya taga FU'AD sai ta d'anji tausayin shi kad'an,shiko dady cewa yake meye result din da suka bayar babu hawan jini kuwa? Adai duba da kyau. Sai ko Yaya Jameel cikin Jin zafin kalaman dady yace "Babu wani alamu ko hawan jini atare da d'an uwana,kawai tsautsayine ya same shi ta hanyar shak'ar turare Dan Haka ya samu matsala ,Amman ankusa gano matsalar shi insha ALLAH. Sai dady yace ,toh Alhmd fatana ya dawo hayyacin shi ni inajin gobe Zan koma na barku da me dak'in shi ta tayaku jinyar shi Dan Haka ku kula da lafiyar shi da kyau. Ranar dady bema tsaya a asibitin ba wasu harkokin shi kawai ya tafi sai dare ya dawo musu , mumcy da sanaya suka tafi hotel suka kwana shima dadyn ya tafi hotel din d ze kwana Yaya Jameel Yana tare da FU'AD a asibitin. Washe gari dady da wuri yazo ya musu sallama ya bar kasar yanata ma sanaya hudubar banza Bayan ya kirata gefe. ******* Affan sosai yake Bata lokacin shi Akan Husna da koyar da ita ita hushan duk ta d'auki hakan matsayin 'yan uwantaka da k'aunar juna kamar yadda su muhibbat suke Mata Dan ji suke kamar su shige jikinta Dan nuna kulawa da k'aunar juna ,suna janta jikin su sosai itama ta saki jiki sosai da su ,ita Kuma ammyn su Bata fahimci wani Abu ko zargin wani Abu ba tsakanin su." Affan kulin da tsarabar da zema Husna har su Husna karama dake al'adar shi ce dama can shi yisa kowa be kawo komai ba a ranshi haka sadeeq ma gaba d'ayan su yake sai musu Abu. Wasa_wasa yau kwanan sanaya 7 a India tuk jinta take a takure burinta ta koma Egypt har ta gaji da jinyar ,da ta buya take ma dady waya akan zata dawo Egypt ita sai cewa yayi indai har ta sake tabar India to tayi hanyar 9ja d'akin mijinta tunda ita ba yarinyar share hawaye bace Yar cikar buri Dan Kar ta dawo Mai Egypt ya Abu ya kusa fadawa zata har gitsa Mai komai ,be tsaya jin me zata ce ba ya katse wayan shi y barta da turo baki da buga kafa. Sosai FU'AD ya Fara samun sauki Yana gane kowa a yau Yana magana kadan_kadan bame tsayi ba farin ciki ya cika mumcy da Yaya Jameel shiko FU'AD burin shi su koma gida 9ja ya sa anemo Mai Husna Dan ta amsa Mai wasu tambayoyi Akan mugun turaren da yasa shi a mumunan yanayi Dan d'aukan mumunan mataki Akan kowaye. Sosai FU'AD yake Kara samu sauki har sun Fara neman sallama ,Dr yace ba yanzu ba se sunga jikin zuwa Nan da sati 1 sanan zasu sake dawowa ko Bayan ansallame shi Dan Mai check up, mumcy ma nason komawa Dan ta dage da neman Husna da kanta ko zata ganta. ******* Aunty huwai nata shirye_shiryen tarban abban su Affan Dan yau ze dawo Dan Haka yau kowa murna yakeyi a gidan har Husna da ta ara ta yafa wai Dan ta tayasu farin ciki ,aunty huwaila da kanta ta Shiga kitchen tare da taimakon Husna suka kammala komai sai muhibat da ta d'an tayasu aka jere kokai Ana jiran oga kwata_kwata head of d house. Affan da sadeeq ne sukaje d'auko shi. Suna zuwa Husna taje da gudu ta hugging abban ta ,sai muhibat tamai nata sannu da zuwan sanan husnan FU'AD ma tamai sannu da zuwa cike da girmamawa ,shima cike da yabawa da kulawa ya amsa Yana tsokanar ta dafatan ta Saba da india zuwa yanzu dai ko? Husna tace eh babu laifi kam k'asar Akwai dad'in zama ,sai yace Amman ba kamar mahaifar mu ba ko? Sai Husna tace "gaskiya tafi mahaifar mu kawai dai sai de ace zamuyi kishin k'asar mu ta haihuwa Haka babu laifi ,sosai anty huwaila ta dinga musu dariya Tana ta nan_nan da mijinta kamar ta goyashi Dana wanan ba sabon Abu bane agare su. Affan ya d'an ja baya da Husna tun dawowar mahaifin shi daga tafiya Dan yasan Babu Wasa atare dashi ko sake Akan yaran shi da Abin da ya danganci tarbiyar su." Bayan aunty huwaila ta gabatar da Husna ga mijinta da wanna baiwar ALLAH sosai ya zaro Ido Yana mamakin ganin matar sai aunty huwaila tamai nuni da karyace komai ta dinga Mai magana da Ido ,ya hadiye Abin da yakeson furtawa,su Affan sun lura da hakan Dan sadeeq sai da ya tambaye shi da sauri ya waske Akan mamakin ganin nitsuwarta yayi gashi ance Bata gane komai har an kaita gidan mahaukata Amman karsu damu kowa yaje yayi Abin da ya Dace tunda dare yayi shima zeje ya huta,sai kowa yabi maganar abban su muhibbat suka tafi da Husna d'akinta,su sadeeq ma kowa ya tafi nashi d'akin. Sosai aunty huwaila Tama abban su Affan bayani yadda ze fahimta ,ya fahimce ta sosai." FU'AD Yana ta samun sauki hankalin mumcy sosai ya Fara kwanciya har Yaya Jameel din ma ,sanaya ko Babu yabo Babu fallasa Amman takan nuna kamar ta damu da rashin lafiyan shi ga bin didigi da takeyi na son sanin Abin da ya faru da FU'AD har yakai ga Shiga wanan Halin,sai su mumcy sukace komai dai ya faru ya wuce fatan samun lafiyan FU'AD shine Abin da zasuyi kawai." Sanaya badan taso ba tabar zancen kullin Tana makale da usee a chart Yana d'ebe Mata kewa." Duba da yadda FU'AD ya samu sauki yaji dad'in jikin shi har likita yana Shirin sallamar su sukoma gida After 4weeks sai ya dawo asake duba shi. Mumcy har take cewa da Haka kawai ne a Halin lafiya suka shigo India da ta nemi aunty husna kodan su sada zumunci Amman yanzu Ina ita Ina dosan aunty husna inta tambaye ta Husna wacce amsa zata Bata? Ta Mata k'arya? Inta gano fa Nan gaba? Girmanta ya fad'i? A Bata da idanun ganin huwaila Dan Haka tama bar zancen zuwan burin ta inta koma 9ja tasa anemo Mata Husna aduk inda take . Sosai FU'AD Yana magana Yana cin abinci Yana gane komai kamar bashine mara lafiya ba ,har yanzu mumcy Bata ce abar Mai Addu'a ba Dan yau za'amai saukar al_Qur'ani na k'arshe ma Akan lalurar da ta same shi Dan yau sun jima sunata Hira da mumcy d yaya Jameel har sanayan da take sako Baki jefi_jefi." FU'AD ya Sami sauki sosai har an sallame shi daga asibiti yau ,Dan Haka sun koma hotel suna hutawa gobe ma zasu Dan zagaya a k'asar India shi da Yaya Jameel ya danga gari sai jibi su koma 9ja, sanaya ko gobe zata koma Egypt acewarta Bayan 2weeks zata biyo su 9ja , mumcy tace "ALLAH ya nuna musu tare da taimakon Yaya Jameel ya Gama Mata komai Akan Gobe zata tafi su Kuma su Shiga gari. Washe gari suka raka sanaya ta tafi suka Shiga gari sosai FU'AD yaji dad'in jikin shi har , mumcy ma suka fita gaba d'ayan su da yammah tad'anga wasu gurare cike da nishad'i farinciki family ya dawo gobe sai 9ja. Sa'adiya tanata musu shirye_shirye da tarban mijinta da tayi missing,dama so take kawai mumcy ta dawo Susan Abin yi Akan maganar husna Dan kanta ya Fara kullewa Akan al'amarin." Washe gari da safe suka dau hanyar 9ja ita da iyalanta, FU'AD ko da burin ido biyu da Husna ya nufi 9ja Dan amsa Mai tarin tambayoyin da yakeson sanin amsar su daga gareta kafin ya zartar da komai." ************** Karatun Affan da Husna yanata tafiya har Affan ya siya Mata layin can ya sa Mata a wayarta ,su muhibbat nata nuna Mata wasu abubuwan, har yawo suka kaita da amincewar aunty huwaila kusan kwanan su 3 suna fita da ita. Husna ta saki jiki da kowa na gidan ta Fara ja baya da Affan sakamakon wani kallo da yake tsareta dashi Wanda Bata gane Mai ba ,sosai ya Fara fahimtar hakan shima Amman be nuna mata ya fahimta ba. ********* Sanaya Tasha masifa wajen dady akan dawowanta Egypt wai danme bazata koma d'akinta ba sai da mamy tamai da gaske har suka Sami matsala sanan ya fita harkan su yace su zuba Ido suga Abin da ze biyo baya. Su mumcy sun sauka lafiya ,sun Sha tarba wajen mutanen gidan ,tunda FU'AD y maida layin shi ake Kira Ana dubashi daga baya sai kashe wayar yayi ya haura saman shi Dan ya huta ,Yana Shiga ya fara gane tabbas babu mutum a d'akin uwa uba da ya Shiga bathroom d'in shi Sam yasan ba irin gyaran da aka Saba yimai bane ko kadan gyaran be birge shi ba. [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg53 Washe gari su Yaya Jameel da wuri suka fito Dan tafiya k'auyen da baba yake ,ko mumcy Basu sanar ma ba acewar su so suke su surprising nata. Bayan sunzo sun d'auke shi Yana nuna musu hanya tirya_tiryan har k'auyen wajen neman gidan ma da kwatancen baban sun Sha wuya FU'AD nata b'acin Rai Yana ayyana akan wata dirty girl fa suke kwasan wanan ranar, har gajiya sukayi da tambaya sai abanza suka Sami inda baban yake ,aka kaisu Yana gindin bishiya yanata Hira da wasu cikin kwanciyan hankali da nishad'i. Baba na ganin aminin shi da sauri ya mik'e Yana taro shi ko su FU'AD be sheda ba ma ,sai da aminin yace "tare muke da Baki fa surikin ka da wanshi" Atake baba yaji mumunan fad'uwar gaba ,yace "sanun ku da zuwa bisimillah ya matsa musu sai abokanen nashi guda 2 suka gaisa da su Yaya Jameel sukace Bari a Nemo musu Ruwa irin na Yan birni wato ruwan leda (pure water) Bayan sun huta ankawo musu Ruwa da take ferare Mai kyau wankanke ga abinci shinkafa da wake da yaji da manta babu su salad Dan Basu damu dashi ba baban Ma'u nata cewa Dan ALLAH suci.... Bayan sun gaisa baba yace ALLAH yasa lafiya ba wani Abu bane ya Sami ma'uta ko wani abun tayi na laifi duk da ban taba samunta da hakan ba iya samunta da nayi a Rayuwarta? Ajiyar zuciya Yaya Jameel yayi kafin yace "baba kana nufin bakwa tare da ita anan? Sai baba ya zabira yace kamar Yaya? Sai aminin baban yace "nemanta Suma sukeyi shine sukaje gida ankasa basu bayanin takamaimai inda take shine suketa nemanka kaima babu tartibin inda kake da kyar suka sameni da naso b'oye sirrinka kamar yadda mukayi da Kai ,Amman ganin Abin da ya shafi Ma'u ya shafeka shi yisa na sanar musu inda kake har suka nemi na rako su na rakosu sauran bayani kaji daga garesu. Sai baba ya juya yace "Dan ALLAH kumin bayani Ina Ma'u ta Shiga? Yaya Jameel ne yace "wallahi muma nemanta mukeyi Dan wani abune yad'an faru babu Abin da zamu b'oyema ,suka Mai bayanin komai Basu b'oye komai ba. Sai baba yace "bawai son Ma'u bane ya rufe min Ido ,Amman kunyi kuskure kunmin ba daidai ba duk da ta wani fanin banga laifin ku Amman in hankali ya Bata tunani ke Nemo shi da kunyi Aiki da lura da Haka Bata faru ba ,Ni a iya nazari na da tunani na duk wanan Aiki baze wuce algungumar da ta raboni daga can bane ta shirya Kuma take Shirin cin nasara Dan zaman Nan da kukaga nayi anan gajiya nayi da mugun halinta da abubuwan da takemin ga wasu mafarkai da suka tasoni gaba Akan marigayiya mahaifiyar ma'un shine na bar Mata garin nazo Nan Dan na huta nasan inzan shekara bazata boyo Ni ba ,Kuma zaman da nake har Addu'a aketa min da tsari Akan sharrinta da ake bani,Amman yanzu komawa yazama min Dole kodan sanin inda bakin zaren yake Dan bazan fitar da komai ba sai naji daga gareta me yiwuwa tanada sa hanu a barin Ma'u gidan Dan yadda nasan Ma'u bazata taba tafiya ko Ina ba sai gida. Sosai hankalin baba ya tashi ,sai da Yaya Jameel da aminin baba suka dinga kwantar Mai da hankali sanan ya samu ya hak'ura ya shiryo yayi sallama da mutanen akan ze dawo inya samu nutsuwa. Bayan sunyi sallah suka dau hanya sosai aka musu tsararbar rake aka gyara aka zuba musu a mota suka d'au hanya FU'AD ya kasa cewa komai. Bayan sun Isa gidan baba suka tsaya baba ya Shiga gida da gudu haidar ya taho yamai oyoyo yanata murna ,mama habee ko a razane take Mai magana sai cewa ma tayi "shine dawowa babu bayani ? Harara baban ya wurga Mata yace" ba wanan ba ma'u tazo gidanan ko Bata Zo ba? Mama habee tace "batazo ba" Sai ko haidar yace wallahi naji kuna magana da humaira kunce tazo Kun koreta ai naji ku wallahi Kuma abokina me kanti yace ya ganta danaje siyo biscuits da wata aunty ta bani kud'i na siya. Sai ko baba ranshi ya b'aci Yana huci yayi kutufoli da roban da mama habee take diban kulin Dan wake Tana wurgawa cikin tukunya akan wuta da sauri mama habee ta mik'e Tana cewa "malam k'onani zakayi ne? Humaira ko da sauri ta saki turmin da take daka yajin da zasuci Dan waken taja haidar d'aki Tana zagin shi Tana cemai munafiki. Baba wuyan mama habee ya shak'o Yana cemata ,bazaki fad'amin gaskiya ba ? Da mama habee taji shak'a sai tace "wallahi ba laifi na bane mijinta ne ya Fara korota sai ta dawo Tana tambayar ka nace bansan inda kakake ba inta damu da son ganin ka taje ta Nemo ka shine tun da ta fita Bata dawo ba atunani na ta koma gidan mijinta ne Bayan Haka bansan komai ba. Sai baba yace "k'arya kike wallahi ki rubuta ki ajiye watan tashin hankali da rashin kwanciyan lafiyan ki ya kana wallahi inhar banga Ma'u ba ki saka aranki komai ze iya faruwa innace komai Ina nufin koma meye yanzu ba da bane" har yayi hanyar fita ya koma wajen su FU'AD sai ya jiyo kukan haidar da magana k'asa_k'asa cikin d'aki ya dawo ya nufi d'akin yaga humaira ta kama kunen haidar,haidar nata matsar kwallah ...... A fusace baba yayi kanta ya d'auketa da gigitacen Mari Bata Gama fahimtar ya shigo ba ya sake aika Mata da wani a sukwane ta fito Tana ihu ya biyota ya rufeta da duk'a Yana masifa Akan ya fad'i aika_aikan da kukayi shine kike Mai hukunci ku Abin da kukayi in hukunta ku za'ayi da duka ai ko k'ashin ku baza'a gani bama sosai idon baba ya rufe yake dukan humaira da wata igiyar Taya labceciya da haidar ya shigo da ita Yana wasa da ita ,sai ko ta gudu wajen mama habee ,sai mama habee tace Dan ubanki ki gudu kafin ya illata min ke Dan Naga a haukace ya dawo bazan iya tare Miki ba babanki yau babu sauki ,da gudu humaira tayi hanyar waje ta sheka makota Tana hawaye su FU'AD nata binta da kallo suna mamakin meya korota ko gyale babu sai gunjin kuka Haka? Baba sai cewa yayi haukar da nazo da ita bakuga komai ba ma ku jira na dawo na koma kanki,yayi waje wajen su FU'AD.... Yana fita aminin shi yace "ya dai lafiya Naga Yar wajenka a guje kamar wacce mayunwacin Zaki ya biyota? Sai baba yayi tsaki da furzar da iska Mai zafi yace "hmmmm da nine wallahi Basu da imani suna da sa hannu a barin Ma'u gidan Nan ita da uwarta su fad'amin gaskiya Kuma sunki su min magana d'aya. Sai aminin baba da Yaya Jameel sukace "ka bisu a hankali har su fad'a fushin fari ba naka bane Kar ka biye musu" Sai baba yace "anamiman sunki fad'a ai Kuma Zan iya fito na fito da kowa akan gudan jinina Ma'u na Rasa uwarta macce 'yar halak me biyaya itana nazo na Rasa ta wallahi baze yiwu ba bada son Raina nabar gari ba da Haka bazata faru ba inda Ana ganin idona Abin da yasa ban kawo komai a Raina ba nasan Ma'u ba zuwa Nan take yi ba Dan tasan bamasu sonta bane su da nasan Akwai Rana irin ta yau da ko da Wasa bazan tafi na barta dasu ba,baba Yana fad'a fuskar sa na nuna matuk'ar b'acin rai. Tun da aka Fara FU'AD bece uffan ba sai yanzu "kawai in Basu fad'i inda take ba ku barni dasu da inspector sani gume Zan had'a su ya dealing dinsu Dole su magantu suyi bayani. Sai aminin baba da Yaya Jameel sukace basai takai ga Haka bama zasu fada asaukake. Sai baba yace "hmmmm bakusan taurin kansu bane kamar mutanen farko suke sai sunji wuya zasu fad'a ,sai Fu'ad yace ku barni dasu nace Gobe Nan zamuzo dashi in sun sassauta ma kansu suyi bayani a Nan gida inko sunyi taurin Kai muyi gidan kwalawa dasu. .....haka dai aka tsaida magana su FU'AD suka nufi gida baba da aminin shi aka barsu anan. ******** Husna Tana Kiran maman su hafeeza a waya su gaisa ta tambayeta labarin babanta sai tace Bata da labarin shi Amman tasan Yana Halin lafiya insha ALLAH. Affan ko yacigaba da nunama Husna kulawa fiye da tada har sadeeq ya Fara fahimtar shi su muhibbat ko Basu fahimta ba sun zata irin son da suke matane Suma Dan kullin cikin k'ara sonta da shak'uwa da ita suke. Abin ya Fara damun aunty huwaila Dan ta Gama harbo jirgin Affan ta Rasa Abin yi ta Kuma kasa gayama Abban su ,sai ta yanke shawarar Kiran Affan tamai magana Akan Kar zarginta ya zama gaskiya. Koda ta kirashi ta Gaya Mai ,yaso b'oye Mata sosai ya nuna ba haka bane da yaga ta fututuke Mai sai yace "eh sonta yake Kuma da Aure shi yaga mata..... Sosai hankalin aunty huwaila ta tashi ,Amman ta daure ta bashi hak'uri ta nuna Mai tun dare be Mai ba ya cireta a ranshi Dan Akwai matsala Kuma bataso ya tsananta tambaya bataso taci gaba da ganin alakar da a tsakanin su ,ze Mata magana ta koreshi. Sosai Affan ya zurfafa a tunani da son gano matsalar da ammin tashi take fad'a Sam ya kasa ganowa ,Dan Haka yaci gaba da neman zabin ALLAH ,Abin na damun shi har hirar sukayi da sadeeq , sadeeq yace "tunda ammin su tace Haka yayi hak'urin tanada huja Dan Kar ka manta tanason duk wani Abu da muke so uwa uba mu kammu ji take babu kamarta a duniya da tayi sa'ar samun yara kamar mu ,muma Haka muke gani babu Mai sa'ar uwa kamar mu kaga ko tun tasowar mu ahaka muka ginu Aiko Dole mu karbi Abin da duk tazo Mana dashi indai mun sheda bazata cutar damu ba Dan Haka Ina shawartan ka kayi yadda takeso Akwai fa'ida ko hujjar yiu hakan bayyah au d'an uwana sai ko Affan ya kawo Mai duka ya goce Yana dariya. Affan yad'an ja baya da Husna ita kanta ta fuskanci hakan ,Kuma hakan ya Mata dad'i sosai,Amman fa Tana Nan a makale a zuciyar shi. Sosai baiwar ALLAH Nan take samun sauki tare da kulawar su sadeeq har wajen wani musulmin ba'indiye ake kaita Yana Mata magani Kuma suna hango nasara a cikin maganin da yake Mata. ********* Bayan su FU'AD sun koma gida basu b'oyema mumcy komai ba , mumcy ta dinga mamaki ,daga bisani tace ya zama Dole su mama habee suyi bayanin inda Husna take Dan har da ita wajen wucewa gaba akaisu Kara ga hukuma ,sai Yaya Jameel yace "haba uwa ta gari ki huta barmu dasu ma mun ishesu Gobe zamu koma ai, mumcy tace "toh shi kenan ALLAH sarki Asma'u baiwar ALLAH ko Tana Ina oho ALLAH ya dawo min dake cikin ahalina lafiya. Bayan FU'AD ya haura saman shi ,ya jima Yana tunanin ta inda Husna zata billo sanan yanata mamakin makircin mama habee ayanzu ya Fara zargin ba mama habee bace taba husna turaren Nan da yayi Amfani dashi ba kuwa? Yanzu ya sake yadda da Abin da take fad'a batayi da wata manufa ba Kuma wallah Bata da masaniya akan komai,ya jima Yana tunani kafin ya Kira abokin shi sani gume ya karanta mai komai suka tsara yadda zasu yi. Washe gari kafin FU'AD yaje office sani gumel ne ya Fara zuwa suka wuce gidan su mama habee da sukayi kwanan jugum_jugum ita da baba ,sukayi sallama da baba ya fito ya musu tarba Mai kyau ya musu iso zuwa zauren gidan ya koma cikin gidan. Mama habee tabata yanka dumamen tuwo Tana jefawa cikin tukunya Tana wak'arta me cike da habaici ,sai baba yace ki Adana wak'arki kizo Nan yanzu ,sai ta kalleshi ta d'auke kanta ta cigaba da wak'arta ,sai ko baba ya Shiga kicin d'in ze damk'ota sai mama habee tace "tsaya! Tsaya!! Karka k'onani Naga wani salo ka dawo dashi kamar wani shago dambe kakeji karka jefani cikin tukunyar tuwon Nan barin fito ,sai ko ta fito yace da Kinga yada ake Kama Abin banza. Sai tace wai Ina zani? Sai baba yace zaure magana zamuyi. Sai tace ko dai surikin nawa ne yazo me neman Auren humaira kasan wani ya fito yanata son ku gana ko ya samu labarin dawowarka ne? Sai baba yace "shine ai ya k'araso gwanda kizo Ayi komai dake" Sai mama habee ta Shiga d'aki Tana cewa, a madallah da zuwan suriki barin sauya zani da d'aukan hijab wankanke Kar ya Fara rainani tun yanzu ,ta d'auko ta fito baba na binta a baya har zauren ,taba zuwa tayi tozali da FU'AD sai ta Fara juyowa Tana cema baba "aa abokin wanan attajirin ne ma ashe? Sai baba yace eh ,sai isfeta sani gumel ya mik'o Mata handcuff Yana cewa bani hanun ki Nan ,sai mama habee tayi hanyar komawa Tana cewa baban humaira kaga iya shege gun surikin Nan Ni ba barauniya ba ba Mai laifi ba ze mik'o min wanan abun tada hankalin? Tayi hanyar komawa gida kenan baba ya hankad'ota ya dawo da ita Yana cewa ,bakiga ta komawa ba ,ki musu bayanin inda ma'uta take ko wallahi suyi caji ofis (police station) dake. Sai ko inspector sani gumel ya zaro Mata mugayen idanuwan shi Yana ce mata "ko ki bamu had'in Kai muyita anan ko na saka Miki wanan ankwar ko na harbe kanki kowa ya huta Yana nuna Mata bindiga, ki kalleni da kyau bani da mutunci Zan iya aikatawa inkina mamaki kimin gardama yanzunan Ayi jana'izarki acikin gidan da kike tutiya nakine ,sai ko mama habee Baki na rawa tace "tabas da ganin Kira ai ansan zataci mutum" toh wallahi ALLAH Ni bansan inda Ma'u ta tafi ba,sai ko sani gumel ya daka Mata tsawa ,bazaki fad'a ba ko? Sosai jikin mama habee ya d'auki rawa Tana cewa na Rantse da Wanda yayi ne tazo dai na koreta bisa tsautsayi nace ubanta ma bansan inda yake ba alhalin nasan inda yake Dana fad'a Mata da zata nemeshi Amman wallahi tallahi bansan har yanzu Ana nemanta ba wallahi ku Kira humaira kuji an ta Fadi badaidai ba kumin komai ,sai ko ga humaira ta dawo daga yawon siyo awarar safe ,baba ya gurfabar da ita aka rutsata ta Fadi gaskiya ko atafi da ita caji ofis a bainar jama'a ,sai ko humaira ta Fara ransuwa tana fad'an gaskiyar ta,sai ko FU'AD yace be yadda ba shiryawa sukayi. Sai mama habee tace wallahi ko Al_Qur'ani Zan iya dafawa Akan hakan. Sai FU'AD bama su baba labarin zuwansu office d'inshi da duk abin da ya wakana ,ran baba ya bacci dajin Abin atake yace ya saketa Kuma ta jira Abin da ze biyo baya inbega ma'un shi ba sanyin idanun shi ,atake mama habee ta Fara ba baba hak'uri da humaira Tana Kuka Tana cewa yayi hak'uri ya mayar da maman ta ..... FU'AD ne ya tsayar dasu da cewa ,Bayan tiya Akwai wata cacar ,me kikasa a cikin turaren da Kika ba Husna ? Mama habee ta zabura zatayi musu , FU'AD yace musawa zakiyi Bayan ita husnan nan CE ta Gaya min? Wallahi in Kika Musa sai munshiga shari'a dake Dan har gidan yari sai kin ziyarta Bayan munyi shari'a." Sai ki mama habee tace "wallahi ba wani Abu bane sosai a ciki kawai Dan Addu'o'e ne da mallam me fukafukai ya bani banyi Dan na cutar da ita ba...,......babane ya d'auketa da Marin da yasa ta had'iye sauran kalamanta Yana cewa"munafuka muguwa meson raba sunnar ma'aiki. Sai FU'AD ya harareta yace kenan can Kika koma wajen shi ya harba Husna tashiga uwa duniya? Sai kuwa mama habee tace a wallahi ban da masaniyar inda ta tafi na rantse da kabarin .......baba ya tsayar da ita da tsawa ,jahila Ana rantsuwa da kabarine? Kidahuma wallahi Zaki girbi Abin da Kika shuka. Mama habee na kuka take cewa in Baku yadda ba Zan iya dafa Al_qur'ani Akan ban Mata komai ba. Sai FU'AD ya fice a cikin bacin Rai daga zauren ,sai sani gumel ya sake firgita su mama habeen har Yana sa musu bakin bindiga kafin ya fito yabar su ,da gudu mama habee da humaira suka shige gida. Babane ya fito Yana cema FU'AD insha ALLAH tana hannu nagari. Sai FU'AD yace Kuma baka tunani zata wani gari ko wani guri? Sai baba yace gaskiya Babu inda zata ,Amman Akwai aminiyarya wacce ta Bata aikin da takeyi a gidan ku kuzo muje na tambayi mahaifiyarta ko tazo. Suka dunguma suka je k'ofar gidan maman hafeeza,akayi sallama da ita ta fito ta gaishe da su baba cikin kulawa. Baba ya tambayeta ko tanada masaniyar inda Husna take? Tace eh "tazo Amman ta tafi tace min zata dawo Dan suna waya da wata ko aunty huwailan ta fita Amman bansan wani Abu ba Bayan Haka. Sai ko FU'AD yace "Anya Bata tare da aunty huwaila ? Sai baba ya zaro Ido ,India fa kace? Ko garin Nan ma'u Bata tab'a Bari ba bare k'asar ,tab nasan huwaila inhar zata d'auketa sai da yadda ta Kuma tanada hankali da tunani kamar 'yar uwarta bazata d'auketa tasan tanada Aure ba wanan magana ma kubarta bama ze faru ba ko a mafarki kaji FU'AD kuje gida mucigaba da Addu'a ALLAH ze bayyanata insha ALLAH. FU'AD tafita sukayi da sani gumel ya ajiye shi a station d'in su shima ya wuce office ranshi duk Babu dad'i har Yana tambayar kanshi wai meye Haka yakeyi wai sonta yakeyi ko me? Zuciyar shi tace "ko d'aya kawai Auren da yake kanta nake tatali da Kuma mahaifinta da yakeson ganinta yanzu Amman Ina Abin so ga dirty girl like Husna ko Asma'u ne oho mata. Bayan FU'AD ya koma gida ya sanar ma Yaya Jameel da mumcy da aunty sa'adiya duk Abin da ya wakana sunata ma mama habee dariya ,atake mumcy tace bazan ki tataka ba Bari na Kira huwaila na tambayeta , mumcy ta Kira suka gaisa kafin ta gabatar da tambayar ta ,aunty huwaila ta rigata da tambayar yasu husnan ta take? Jiki a sanyaye mumcy tace "Tana lafiya "aunty huwaila tace Masha ALLAH Haka nakeson ji har suka Gama wayar mumcy jikinta a sanyaye ta kasa gayama huwaila komai. FU'AD ne yace "ai da kin tambayeta" sai jameel yace haba k'anina Kar idonka ya rufe Mana hankalinta tashi zeyi daga yanayin bayanin mumcy kasan ita auntyn tata batasan husnan Bata Nan ba meye ribar d'aga Mata hankalin yanzu ta hanyar sanar Mata da mumunan labarin Nan? Mucigaba da Addu'a kawai , mumcy dai kasa magana tayi tana tausayana Husna da FU'AD taga duk ya damu. Suna cikin hakane dady ya Kira FU'AD a waya yafi ko 3 yak'i D'agawa har mumcy na Mai fad'a da Yaya Jameel ,sai da ya gaji da Kiran FU'AD sai ya koma Kan mumcy ,kafin ta tsinke ta d'aga babu gaisuwa babu komai ,ya fara cewa ,ya Kanata yaron Nan yazo ya d'auki matar shi Kar ya wuce kwana 3 bezo ya d'auketa ba. Sai mumcy tace Aiko FU'AD tafiyace a gaban shi cikin satin Nan har Wanda zamu Shiga Akan wasu ma'aikada da zasu bud'e shida yayanshi Jameel Dan Haka Zan Mai magana ya buking Mata flight gobe ko jibin . Sai dady ya Fara washe Baki Yana cewa "toh madallah siyan kadara ai tanada amfani sucigaba da hakan,sai ya Mata babu damuwa sai ta taho kawai ta dawo d'akin su , ALLAH ya basu zuriya Mai Amfani. Mumcy tace "Amin sai naji zabinta gobe ko jibin" Sai dady yace "zuwa jibin ma ai is ok Tana da wani zab'i ne Bayan Wanda muka Mata kawai ya shirya Mata" Mumcy kashe wayar tayi Tana cewa "Haka kawai kasani yin k'arya da girmana agaban yara" Sai sa'adiya da Jameel sukayi dariya ,sai Fu'ad yace "toh uwa ta gari ai karyar raba gardama kikayi Dan ta hallata a girl na" Sai mumcy tace dake na kare ka ko? Sai FU'AD yace "ai wallahi da ba inda zanje Ana maganar mutane ze zo ya damemu da wata yarsa me Jin kowa be Isa ba da ya barta ta Kara hutawa ma ai ,sai mumcy ce ta Mai fada Akan matar shi ce fa batason irin haka,k'arkashin zuciyar ta Kuma Tana Jin dad'in ya Fara k'arb'an Auren share hawayen da tamai ko a iya yanzu tasan ya amince Dan Haka take Addu'a ganin Husna Tazo suyi zaman Amana da k'aunar juna da son autan ta. Sai daga baya FU'AD yake Gaya musu zuwan mama habee company su har office d'inshi ,har da maganar turaren da ya Mata dabara yaji Ashe itace taba Husna tayi Amfani dashi Dan ta cutar da ita tsautsayi ya fad'a min ,muguwar matace fa Dan Haka ranar na Mata fata_fata na Hana asake barinta Shiga company ma gaba d'aya. Mumcy salati ta Shiga yi Tana mamakinta ,da firgici take tambayar FU'AD wai Ina turaren ne ma? Tun Bayan dawowar su daga indiya take bilayin nema Bata ganshi ba. Sai FU'AD yace "Nima banganshi ba atunanina husnan Ce ta tafi dashi" Sai ko hankalin mumcy da aunty sa'adiya ya tashi kowa na Addu'o'e da yazo Mai Kan ALLAH yasa bazatayi Amfani dashi ba asamu Abin da ake nufinta da turaren. Sai FU'AD yace "waya sani ma ko tayi amfanin dashi to bagashi ba anata nemanta anrasa ,tana gani ya cutar da wani inba yarinta ba meye nata na d'auka Kuma? Sosai suke Mata Addu'a kariya daga sharrin mama habee da kaidinta. Bayan Haka suka tab'a Hira kowa ya koma inda yafi wayo. ********** Affan ya kasa hak'ura da Husna Dan haka ya dawo da nuna Mata kulawa wacce ta ninka ta baya wai ya kasa bawa zuciyar shi hak'uri ..... Dan rik'e madogara da makamin kare kanshi wajen aunty huwaila ,ya yanke shawarar fad'ama Husna kawai yaji me zata ce. Ya kasa fad'a Mata sosai Abin yake Mai nauyi,yanata cigaba da Bata gudumawa Kan lesson d'in da yake Mata har sadeeq ma Yana tayashi sanar da ita wasu subjects din in be dawo da wuri ba zaman su gwanin sha'awa sai Affan da ya dawo da Halin da yake nuna Mata a baya Dan Haka yanzu tafison suyi karatu da sadeeq sosai aunty huwaila ta fahimci hakan sai ta sake saka matakan tsaro nason gano ko Affan d'in yaci gaba da nuna Mata so ne? Ta Kuma shirya Bata Mai ranshi Akan hakan sosai inhar ta gano. Shiko 'yar k'asa yakeyi yadda bazata tab'a fuskanta ba sai dai ita wacce akeyi domin ta. Gashinan na muku 2pg in 1😝🤣😅👌🏻 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg54 Aunty huwaila ta Kira Husna ta Gaya Mata mumcy ta Kira Tana tambayanta, Husna ji tayi har jijiyoyin jikinta ko Ina sai da ya motsa atunanin ta ko za'ace FU'AD ya mutu Dan dashi take kwana dashi take tashi ga matsalar Mara lafiyar Nan Tana damunta sosai ji take wani shak'uwa na Shiga tsakanin su sosai kawai Bata taba gayama kowa bane. Sai Husna tace" ma tace Miki aunty? Sai aunty huwaila tace "hmmm wai nemanki sukeyi ko inada labarin inda kike? Ajiya zuciya Husna tayi kafin tace "toh ALLAH dai yasa FU'AD d'in ya Samu lafiya Kar na zamo silar faruwan wani Abu cikin family hajiya babbah. Sai aunty huwaila tace ,ai naji kamar ya samu lafiya duk da Bata gayamin ba kuma Kinga bana nuna Mata na sani ba ,tunda kika ga suna nemanki kinsan hankalin su ya akwance yake tunda har ya dawo kanki. Sai ko Husna ta tsinci kanta cikin matsanaicin farin ciki ,tace "Allah yasa Haka Amin aunty Amman wallahi banason komawa ma Ni" Sai aunty huwaila tace "Auren Kuma fa kiyi Yaya dashi? Yata rik'e igiyar Auren shi ahannu shi ko yaba mumcy tunda yace aurenta ne inya tashi fada Haka yake cewa inji husnan. Sai aunty huwaila tace ,hmmmm in Auren shine ko na mumcy yanzu komai ze bayyana ba karamin dad'i najiba da Kiran wayar da sukayi shi ya tabbatar min da cewa kina da Amfani acikin su Amman idon su ya rufe. Bayan aunty huwaila sun Gama magana da Husna ta tafi wajen mijinta ,ita Kuma Husna wajen Mara lafiya ta tafi Tana kare Mata kallo Tana nazarin wani Abu agame da ita ,Bayan sun Gama k'arema junan su kallo sai matar ta Fara fitar da hawaye Tana kalon husna,sosai hankalin Husna ya tashi ta matsa kusa da ita ta na tambayanta dalilin kukan, bud'e Baki tayi kamar zatayi magana Amman firta komai ya gagara agareta sai damk'e hannun Husna da ta sakeyi ,Husna cigaba tayi da Mata magana Tana so taji ko harafin "A" ta firta Amman Abin ya gatara ,atake Husna taji itama hawayen ya Fara Shirin zubo Mata har yaci nasara zubowan ,har Husna k'arama ta shigo Tana sallama ba Wanda ya jita ganin kukan da suke gaba d'ayan su sai ta tafi wajen aunty huwaila ta tana fad'a Mata ,atare suka dawo da aunty huwaila. Aunty huwaila Kama kafadun matar tayi Tana cewa lafiya Yaya? Sai Husna ta juyo Tana cewa Yaya Kuma aunty? Sai huwaila ta dawo hayyacin ta tayi gagawan had'iye hawayen da yake Shirin zubo Mata ta Tana cewa "eh Husna shawara na yanke Zan dinga kiranta Yaya duba da ganin cewa ta girme ni, Husna ji tayi Amman bawai Dan ta yadda ba Dan Bata tab'a cemata ba acan baya sai yau Kuma ta fuskanci itama kamar taso yin kukan,Amman Husna sai ta basar Tana cewa"aunty kuka hawaye takeyi Kuma tanata kalo na shine Nima bansan lokacin da hawaye na suka Fara zubowa ba Dan tausayinta da ya shigeni tun ranar da nayi tozali da ita har ka yau da muke tare. Sai huwaila tace "ayya Haka ikon ALLAH yake kuci gaba da tayamu da Addu'a muna ganin alamun nasara Akan matsalar ta jiya ma mutumin da yake kula da ita ya Kira na Nigeria Nan Yana tambaya nace Mai Akwai alamun nasara insha ALLAH yace suna tayamu da Addu'a. Husna tace "munayi muma Amman zamu k'ara insha ALLAH , huwaila tace toh tashi muje bana son kuka da kukan Nan Abin bazemin dad'i ba yanzu sadeeq zezo ya dubata yaga yanayinta Dan yasan yadda zema Dr dake dubata bayani gobe in ALLAH ya kaimu in mun koma Dan bada ita zamu ba goben. Bayan sun fita ,suna zaune a falo anata Hira cikin fara'a da raha kowa na Fallon Banda Affan." Affan na dawowa yaje d'akin shi ya canja Kaya zuwa k'anana Bayan y watsa Ruwa ya dawo Fallon ya umarci Husna da ta kawo Mai abinci ,badan taso ba ta tashi ta kawo Mai ,ta ajiye ya sake cewa ta kawo Mai drink ta tambaye shi zab'i yace "ko wane kawai" ta kawo Mai ta ajiye ta tafi ta zauna ,Bayan ya Gama ci ya dawo ya zauna yanata k'are Mata kallo ,Abin har ya Fara k'ular da ita sosai aunty huwaila take kula dasu ,daga baya ma ya tashi ya dawo inda ze dinga kalon ta sosai ,ganin bazata iya jurewa ba sai ta tashi ta bar falon ta koma d'akin matar Nan da ta zama yayar aunty huwaila jiya. Ba aunty huwaila ba har abban su Affan ya kula da Abin da ya faru Dan Haka ya Kira huwaila ya Fara Mata magana Akan Abin ,Bata boyemai komai ba tace ta fuskanta har ga Abin da tacema Affan d'in ,Amman taga alamar be yadda ba,sai Abban yace "toh yadda kikayi ne Kika Kara asasa matsala kiramin shi mu fito Mai a mutum yadda zefi fahimta babu b'oye_b'oye ,zatayi magana ........Abba ya dakatar da ita,Dole ta tafi ta Kira Affan d'in. Bayan Affan yazo baban shi ya mishi bayanin ya fahimci Abin dake tsakanin shi da Husna ,ze Musa aunty huwaila ta hanashi ,sai baban ya gayamai tanada Aure fa." Sosai Affan ya girgiza dajin maganar ya razana sosai sai da kyar ya iya furta ,haba ammy shine dalilin da yasa Kika Shiga tsakanina da ita ta wata siga? Huwaila rarashin shi ta Fara yi tana shigar Mai da buk'atar ta Akan tanaso soyayyar da yake nuna ma Husna ya riked'e zuwa na 'yan uwan taka Dan ya zama Mata Yaya cikin Rayuwarta me kare Mata mutunci da hakkin ta irin Wanda duk wani wa ze iya k'arb'an ma k'anwar shi." Affan sosai yaji d'acin kalaman ammyn shi ,Amman Abban shi ya dinga rarashin shi damai nashiha da bashi hak'uri ,itama huwaila ta dinga bashi hak'uri da rarashi ta kuma fad'amai komai akan Rayuwar Husna har aurenta da FU'AD har take cemai badan Auren FU'AD d'in da ya musu shamaki ba da zatafi so ya aureta Amman bazata ki wani taso nata ba ,hakuri shine mafi a'ala ALLAH ze bashi wacce ta fita insha ALLAH,sun Jima suna Mai nasiha kafin ya yadda ya tashi ya tafi ranshi Babu dad'i Yana mamakin ya akayi ta zama matar Aure da har be sani ba ,ko da yike lefin Ammyn shine da bekai ga sonta ba da ta sanar dashi da wuri." Affan kwana yayi Yana tufka da warwara ta yadda zeyi ya rabu da son Husna ,Dan ko had'uwa Basu sake yi ba har ya tafi bacci." Bayan tafiyan Affan Abba fad'a ya yima huwaila Akan ya kamata ta mayar ma da FU'AD matar sa in har sun tabbatar da ya samu lafiya tunda har suke neman ta ,Dan be Dace tayi ta zama da auren wani akanta ba ,yanzu ga irinta har d'ansu ya kamu da son ta Akan wani dalilinta Wanda ita kad'ai ta sani ,Amman fa ba korar ta yake ba darajar Aure yake dubawa ya tabbar Kuma itama tana son mijinta Kar ta Shiga hakkin su." Huwaila cemai tayi "bafa rahasu zatayi ba kuma ta fahimce shi kawai tanaso Susan sunyi kuskuren Koran ta sanan suzo bikonta da kafan su akuma lokacin da sukasan tanada mahimmanci a cikin su ta hanyar nuna kulawa gareta da damuwa da ita da mijinta zeyi duk takeson sanin Haka ,Dan Bayan tiya Akwai wata cacar ,Amman Bayan wanan bani da wata manufa Akan rik'e Husna a india. Sai Abba yace "toh ai sunso Ayi sulhu kikaki Basu fuska ta hanyar cewa bakisan inda take ba,Kika barsu haka" Sai huwaila tace "wanan ai be wadatar ba Kuma ba wani neman kirki suka Mata ba da zasuso su gayamin Bata tayi ko Abin da ya faru ka fahimci zance na fa Abban su Affan" Sai yace da gaskiyar ki Kuma Dan wanan Amman dai nasan zasu sake nemanki in Hali yayi Dan ALLAH karki wahalar da shari'a ki Basu ita ko yanzu nasan suna kewarta. "To "kawai tace mai. ************ Sosai baban Ma'u yake ma su mama habee tijara duk sun zabura hankalin su atashe Musamman humaira da yasa ta fitar da miji da gagawa ko yayi kyautan ta, mama habee cewa tayi be Isa ba wallahi ,shiko yace zega Wanda ya Isa a gidan. Mumcy da FU'AD hankalin su ko da yaushe nakan Husna ga komawar su india saura kwana 3 ita da FU'AD d'in kawai zasu koma Dan Yaya Jameel zasu je Abuja su d'an kwana biyu sai wata k'anwar mumcy da aurenta ya mutu tazo zata zauna agidan." FU'AD ya kasa b'oye maganar husna har su B2k ya fad'ama , B2k ya dinga Mai dariya kafin yace komai,har FU'AD ya hassala yace "bana son iskanci fa Ina gayama Abu kamar na kawo ma wani Abin dariya ,matsalaka kenan na manta d'an adawa nake gayama ,har ya tashi ze bar office d'in sai B2k ya tashi ya kamo shi Yana cewa yi hak'uri abokina am so sorry ,I don't mean to hurt u,banji dad'in faruwar lamarin ba Amman ga shawara.... Sai FU'AD ya dawo ya zauna Yana cewa tame? Sai B2k yace Kun dubata ko Ina duk wani me alak'a da ita Kai har k'awa ma? Sai FU'AD yace "duk anje duk da Bata da wasu 'yan uwa Kuna kawarta d'ayace Kuma munje babu wani labar har wajen wata aunty ta aka tambaya Amman tace bata ma da labarin ta kwana biyu ,bama tasan nemanta ake ba dake gaskiya badani sukayi wayar ba da mumcy sukayi." Sai B2k yace "Ina ganin da Kun Mata bayani sosai Dan aji ko tanada shawara ko mafita,Amman ko anan ma ku tsanaita bincike batanta da ban mamaki Kuma ku ci gaba da tsorata marikiyar ta ko tanada Abin cewa ,Amman inama jaje gashi Naga kamar ka fad'a gaba d'ayan ka......sai Fu'ad ya Harare shi Yana cemai Ina na fad'a zaka Fara ko? Sai B2k yace "wallahi love kanaso ko baka so ,shawara dai kawai kaci gaba da kishinta kamar yadda kakeyi dinan Dan Ni ganau ne ,sanan ka nuna Mata so na hak'ika in Kun had'u Dan kun mugun dacewa ba Zan maka Dole wajen gyara kuuren ka ba har sai in ka zauna Kama kanka karatun ta nutsu da kanka tunda kace zab'in mumcy ce." Sosai Abin da B2k ya fad'ama FU'AD ya Shiga kanshi Amman Ina be yadda da kalaman ba saboda zuciyar shi ta karyata hakan in gangar jikin shi ta amsa,har suka rabu Yana dogon nazari..... ********** Washe gari Affan ma be Bari suka had'u da Husna ba duk ya kasa gane ma kanshi da ak'ar shi da ita ,shin tsanar ta zeyi ko d'aukanta matsayin k'anwa, ko ya fita harkarta kwata_kwata? Be Gama shawara ba Dan Haka yake wasan b'uya da ita. Husna ta so fahimtar kamar Akwai wata ak'asa Amman ganin ba'a sanar da ita ba Kuma batasan ko meye ba sai ta bar komai Amman ranta fal da tunanin su FU'AD. Sosai ammyn su Affan ta kula da d'auke wutar da FU'AD Yama Husna Dan Haka ta sake kiranshi tamai nasiha da nuna kulawa Akan damuwar shi da janshi ajiki da nuna Mai soyayya ta d'a da mahaifiya har take cemai mayar da Husna 'yar uwa agareshi kamar su muhibbat shine ze tabbatar Mata da ta Isa dashi Kuma ze iya Mata biyayya ko Bayan ranta,sosai Affan ya Bata hak'uri ya nuna Mata ze gyara Kuma ya hak'ura ya barma ALLAH komai daga yau Husna Bata da wani da ya wuce shi har ya rok'i ammin shi da Kar ta sanar Mata da Abin da ya faru Dan dama be tab'a Gaya Mata ba abar Abin a Haka kawai ,tamai Al'k'awarin bazata sanar Mata ba ta sama Rayuwar shi Albarka. Komai ya koma normal tsakanin shi da Husna sosai yake Mata lesun tare da nuna Mata shi yayan tane k'ofa a bud'e take Akan duk wani damuwarta ko matsalar ta tagaya Mai sai inda k'arfin shi ya k'are,sanan ya dinga siyo Mata Kaya na kyale_ kyale gashi kusan kullin sai ya fita dasu Yana nuna Mata wajaje na wayayun mutane sosai Kan Husna ya k'ara bud'ewa ta waye dressing babu Wanda batayi daga name na hausa har na larabawa zuwa Kan turawa har indiyawa da take ganin su yanzu sari babu Wanda Bata sawa cikin lokaci k'an'kani ta k'aru da abubuwa sosai komai ta iya ci duk inda zaka ganta da su muhibbat zaka ganta hankalin ta a kwance ta k'ara cikowa komai nata yayi bul_bul tayi haske har wani shek'i takeyi gashi kowanne dressing tayi sai ya Dace da ita babu gatan da Bata samu Kama daga Aunty huwaila abban su Affan ,sadeeq Dan Haka takejin kamar tafi kowa gata a yanzu take k'arama ALLAH godiya Kan ni'imomin da ya Mata ,lokaci zuwa lokaci Tana Kiran maman hafeeza tana sawa wani k'anin su Yana dubo Mata baba da lafiyar shi Dan Haka takejin hankalinta na k'ara kwanciya. ********* Yaune tafiyar su FU'AD bakuwar da zata zauna musu da a tun daren jiya ta is mumcy ta gama karanta Mata komai da nuna Mata ma'aikatan gidan itama ta gabatar musu da ita amatsayinta na kanwarta aunty karama suke ce Mata Amman sunan ta haule,sosai aka dinga musu fatan sauka lafiya ma'aikatan gidan,Yaya Jameel da sa'adiya ne suka rakasu har Airport dake su sai gobe zasu dawo,agoben Kuma sanaya zata duro itama...... Su FU'AD sun tashi lafiya har sun sauka lafiya cikin Aminci ALLAH. Basu je asibitin ba sai washe gari wai in sun huta. Washe gari kuwa da wuri sukaje sukaga likita,Bayan sun Gama ganin likitane ya duduba shi yaga jikin da sauki sai alamun tunani ko nazarin wani Abu dayaga kamar FU'AD d'in nayi ta hanyar tambayoyin da yamai ya gano hakan da ya tambaye shi damuwar shi sai yace "babu" Dr yace Mai Akwai ya fad'a Mai gaskiya ,sai Fu'ad yace "kawai sai dai ko damuwar wajen Aiki Bayan shi babu komai,sai Dr yace "ya Rage Dan Haka ba baze koma ba sai Bayan sati 1 amemako 4dys , FU'AD ze nemi Alfarma Dr yace dikace kawai yabi haka ya karb'a ya hak'ura kawai yace ya dawo Bayan kwana3 ya sake dubashi, suka wuce wajen cin abinci mumcy take cema FU'AD sai dai ya taho Mata da nata ,haka kuwa akayi , Husna da su muhibbat sun zama Yan Shan iskar gari har zumud'i fitar da akeyi dasu sukeyi sun k'ara shak'uwa da junan su. FU'AD da mumcy sukan Dan fita ganin gari so 2 mumcy nacema FU'AD su kaima aunty huwaila Husna ziyara daga Nan sa sanar Mata da Halin da ake ciki sai Fu'ad yace "aa Dan ALLAH base ta sani ba shi baya son gani wani na Husna har sai ta bayyana agaresu,sai mumcy ta hak'ura. Yauma sun koma asibitin ,likita ya duba jikinshi yace "da sauki sosai" daga can suka wuce gidan wani abokin FU'AD acan ma suka had'u da sadeeq yaje wajen shi shima Ashe abokin shine awajen Aiki Amman ya girme shi sosai suka gaisa suka mutunta juna har aka d'an Saba daga baya sadeeq ya tafi yabar su a gidan. Ana sauran kwana 2 su FU'AD su koma ,sun tafi siyayya wani k'aton supper market Mai kyau da girma , FU'AD na saman bene ta window kamar ance Mai ya l'ek'a yayi tozali da wasu Mata 3 biyun kansu d'aya sai karamar su da bata kaisu ba,a zuciyar shi yake cewa wad'an Nan matan sunyi kama da 'yan 9jan mu ,kamar ance su juyo yayi Tozali da wata zankad'ed'iyar budurwa komai nata gwanin birgewa Koda ya k'ure Mata kallo sai idon shi yake tambayar zuciyarshi da kwanyar shi "wai baka gane fuskar ba? Sai da yayi gajeren tinan da nazari sai ya bada amsa da cewa "Kai kamar Husna ta? Sai zuciyar shi ta tambayi kwanyar shi "husnar ka? Waya baka? Kai da take cewa Auren mumcy ce? Da sauri ya Kori wanan sakaran tinanin ta hanyar gaskata idanun shi da suka Fara tsegunta Mai ,eh wallahi itace ,Kai Aiko sai cema mumcy yayi Ina zuwa mumcy yanzu Zan dawo cigaba da zab'an abin da kikeso , mumcy na tambayar shi Ina bejira me zatace ba ya d'au hanyar sauka har Yana had'a steps...... Wajen dai ya k'araso Yana cewa "Ina kukayi Kuma? Wallahi ba gizo bane ,Dan ya gaskata wani Mai sai da Ice_cream ya tambaya bega wasu Mata 3 ba yanzu hannun su da bag? Mutumin ya sheda Mai ai tare suke da wani Yama d'auke su suntafi har Yana nuna Mai inda suka bi har da Mai bayanin kayan da suka sa Nan FU'AD ya gaskata itace ,da sauri ya koma wajen mumcy yace "ta taho su tafi ganin yanata Abu wuta_wuta ta fara tambayan shi sai cewa yayi ta taho ze Mata bayani,Bayan an cajesu Abin da suka siya ya biya sai suka nufi masaukin su." Ganin ya kasa samun nutsuwa sai mumcy take tambayar shi ,sai yake Gaya Mata yaga Husna fa a k'asar Nan Dan Haka ta taso suje gidan aunty ta kawai." Mumcy sai cewa "tayi bana son Wasa da shashanci karya zatama da ta nuna Bata gidan ta? Kuma ma Babu inda zamu Dan so kusan3 inacema muje ko gaisheta muyi ka hanani zuwa Ni kuma Dan banaso na barka na hak'ura sai yanzu da mafarkin ka ya gayama k'arya zaka tasheni a tsaye kace muje Babu inda zani." Magiya FU'AD ya farama mumcy ,atake mumcy tace wallahi yau d'inan Babu inda zata Dan ya sani,sai cewa yayi "to bani address d'inta Ni nace.....be rufe Baki ba ta sake cewa wallahi kaima ba inda zaka ka zauna ka huta kamar yadda Dr yace." FU'AD ji yayi ranshi duk ya dagule kamar mumcy ta aikata Mai wani zunibi sai cizon yatsa yajeyi Yana tunanin ko ya tafi ne ya nuna Mata kamar ze fita Shan iska ne sai ya tafi yawon nemota .......... 🙃 *Naga Kunji Dad'in 2 in 1pg din dinan ga wani ma*🤭🤣🙊🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀ [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` By *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) Pg56 Da sauri mumcy ta kwace hannun FU'AD d'aga wuyan Affan ,tana daka Mai tsawa Tana cemai "kana haukane FU'AD wanne irin shirme ne kake aikatawa Haka? FU'AD ya bud'e Baki zeyi magana ........ mumcy ta dakatar dashi. Duk Abin da akeyi aunty huwaila na zaune Tana hakaito kishin da FU'AD yakeyi Akan Husna a bayyane amman Yana nuna kamar be damu da ita ba, shi yisa batace komai ba har yanzu." Sallama sukaji ta Abban su Affan shida sadeeq , mumcy komawa tayi ta zauna shima FU'AD ya koma ya zauna ,shi ko Affan gyara wuyan riganshi kawai yayi ya taso yanama Abban su sannu da zuwa Sadeeq da FU'AD kallon kallon suketama junan su kowa nason Tino inda sukasan juna sai daga baya sadeeq ya tuno agidan da suka had'u ,shima FU'AD ya tuno inda suka had'un ,atake sadeeq ya mik'oma FU'AD hannu Yana cewa Ammi bak'i mukayine Haka? Aunty huwaila da fara'ar ta sai da tama mijinta sannu da zuwa kafin ta amsa tambayar sadeeq "eh bakin Husna ne damu duk'a" Abba shima cewa yayi sannun ku da zuwa sun biyota kenan? Aunty huwaila tace "eh toh sun biyota zumunci ya biyo dasu sai suka taradda ita ,wanan surikar Husna ce sai mijinta gashinan FU'AD ,Ashe Bayan Abin da ya faru indiya suka kawo shi aka dubashi suka koma yanzu Appointment din da aka basune yayi sanadin zuwansu Ashe rabon zamu had'u zasuga Husna ne." Sai Abba yace "Masha ALLAH jiki dai babu matsala ko surikina ko ince d'ana Danni d'a na d'aukeka kamar yadda husnan take 'yata,ai fushin zuciyane ya hanamu neman ku gaskiya kamar yadda Kuma shi yasa kuka koreta duk anyi ba daidai ba sai ayafi juna agujema gaba ...... Mumcy da fara'a tace "hakane Munfi kowa lefi ai daga baya abin be Mana dad'i ba munyi nema muna Kai Ashe Tana Nan kun sabinta Mana ita..... Abban cewa yayi Amman zaku barmana ita tad'an kwana biyu ko ta taho daga baya sai Fu'ad ya kalleshi Yana son yin magana ganin mumcy da kowa shi yake kallo Kuma yake saurare sai ya kasa cewa komai. Sai Abban ne yace "fad'i Abin da zaka fad'a abinka duk mun zama d'aya , FU'AD k'eya kawai ya Sosa Ido sunmai yawa ,sai Abba yace "na gane kana nufin abaka matarka kawai babu laifi ku Gama magana da ita kanada iko da dama sai naji yadda kukayi da ita ya shigo inda katafaren d'akin shi Mai had'e da wani falo yake. Sadeeq d Affan ma tashi sukayi sukayi ciki suna Hira kasa_kasa..... Huwaila ma zuwa tayi ta Kira Husna tace takai FU'AD d'akin bak'i sanan ta kaimai duk Abin da ya Dace ko tasa masu Aiki sukai Mai" Bayan ta samu ta fito da kyar Husna na tura Baki Tana hararar shi tace "muje batare da kowa ya ganta ba bak'in cikinta keb'ewar dazasuyi su biyu Kar hakan ya bashi Daman cin zarafinta." Mumcy tataunawa sukayi Akan gobene tafiyar su ga Husna tak'i amincewar Tana ganin ko FU'AD din ya tsaya ya taho da ita lokacin da yashawo kanta ita ko tafiyarta zatayi gobe Dan gidan babu kowa duk da kishiyar husnan ta koma jiya Amman Nima gara na koma. Huwaila tace "toh shikenan tunda shi ze tsaya babu damuwa..... Bayan Husna tasa an cika FU'AD da kayan bawa 'ya'yan hanci me gishiri da me siga be tab'a komai ba sai wani kallo da yake tsare Husna dashi a cewar shi kallon tuhumane d gargad'in.... Husna gajiya tayi da kallon tace "lafiya mallam? Bafa nason kallo Dan inyayi yawa cuta ne in cuta tayi yawa Kuma maganine in magani yayi yawa Kuma mutuwane...... FU'AD mamaki ya farayi ya akayi _dirty girl_ tayi Baki haka? Kuma ta Dena shakka shi ? Sai yace "Koh Aku? Ko nace magana jari? Kin mantani ne Amman zan tunasheki.... Waye Affan a wajenki tukunna? Meye tsakanin ki dashi? In Kika min karya wallahi Zan gane kuma Zan hukunta ki tun a Nan k'asar babu ruwana kinfi kowa sani..... Husna wani irin kallo tamai Tana bud'e wani sweet Mai kyau da kamshi ta wurga a bakinta sai da ta tsotsa sanan tace"Affan wani jigone a cikin Rayuwata Kuma jininane tunda d'an uwanane Dan yayana ne........Bata karasa ba taga FU'AD ya taso har yazo gabanta Yana huci Yana cewa"Kar ki rainamin hankali ba amsar da nakeson ji ba kenan inma k'ashin awakai ne ku ke dashi ta shafa ,ce Miki nayi meye a tsakanin ku? Husna ta sake cewa"ha'a mallam to ai shi nake fad'ama ka katse Ni kawai yayana ne, FU'AD sai cewa yayi gafaka ne ba mallam ba in Kika sake kirana mallam Zaki sani naka kin k'aro wulak'ancin har kinkai ki dinga wulak'anci da Rai? Yayan ki na kwanannan? Husna da Isa tace "eh Kuma na har abada" FU'AD har yakai hannu ze buge Mata Baki ya fasa yace wallahi kinci sa'a innace Zan dakeki b'abb'allaki zanyi da kinga yadda ake maganin rashin kunya ke da Kika samu ragowa ma..... Sai ki Husna tace ai da ka dakeni kasan yanzu ba da bace dakeni Dan ALLAH ta d'an matso gaban shi kamar zata shige jikin shi sai Fu'ad yaja da baya Yana cewa yarinya Akwai Abin da kike buk'ata abokin mutuwa kike nema ,amman zanyi maganin ki dake da wulak'ancin da Kika k'aro ,Abin da nakeso ki sani ki shirya dake zamu koma goben Nan." Husna cewa tayi wallahi bazan koma gobe ba Tana Shirin kuka Kai da ka koreni in kaganni a 9ja wanjen babana naje..... FU'AD ne ya katseta da cewa Toh Daman yarinya can za'a taimaka Miki Akaiki dan shima nemanki yakeyi Amman Ina ruwan wani dake waya damu dake? Sai Husna tace "ALLAH sarki baba zanzo gareka da nayi fushi da k'asar Amman kodan Kai Zan dawo insha ALLAH Amman ba jimawa zanyi ba ,Bayan ta d'an zubar da hawaye FU'AD nata Mata kallon mugunta irin ya Fara gano bakin zaren ,sai ta share hawayen tace "wallahi fa bazan tafi Gobe ba kamar d'aukan Rai tafiya katsaham bama tare zamuba hanyar jirgi daban na mota daban Kai Ni da su Yaya Affan ma zamu...... Bata k'arasa ba FU'AD yace "karki sake min maganar wani Affan ko wa yarinya ke kika sanayi gulmamiya da dashi kikazo? Sai Husna tace ,Ni ba gulmamiya bace Kuma ko banzo dashi ba ai Zan koma dashi ,Kai d'in tare mukazo? Sai FU'AD yayi subuta kallam yace "Ni ai mijin kine Kuma da aurena akanki Naga ke sai anmiki da gaske .... Sai Husna ta juyo da mamaki Tana kallon shi tace "barin gyara ma Auren mumcy dai ba naka ba in ka manta na tuna ma" ka taba kirana matar ka ne can ka nemi sanaya itace matarka ba wacce mumcy Tama Dole ba..... FU'AD Rasa yadda zeyi yayi yau ga Husna Tana cin tuwo akanshi Dan taga bayason Kai hannu jikinta ,Amman da ta k'ure shi zai mangareta,sai ya canja zancen da cewa "ke nutsu kiji Ni da kyau ki Kuma bani amsa daidai da tambayar da Zan Miki kinsan k'a'idata bana son k'arya,waya baki turaren Nan danayi Amfani dashi? Nan da Nan Husna ta nutsu jikinta yayi sanyi ta saisaita murya ta zauna a kujera , FU'AD ko dariyar mugunta ya Fara yimata cikin zuciya Yana cewa Mara kunyar karya... Husna cewa tayi "wallahi ALLAH na ranste da Wanda Raina yake hannun shi mama habee be silar faruwar komai sai daga baya na gane duk makircin da suka shirya har yaudarar da tamin Akan cewa na yafe musu sun Gane cewar sun Jima suna muzguna kin Ashe tuban muzuru sukayi wallahi bansan Dan acutar Dani ko wani akayi ba da bazan Bari wani ya gani ba bare ma kayi Amfani dashi.... FU'AD sai cewa yayi ,meyasa kikayi karyar na lefenki ne? Meyasa Baki Fadi gaskiya ba da duk wasu abubuwa Basu faru ba? Husna sai cewa tayi wallahi tsoro naji Kar baba na ya Shiga cikin Abin Dan in aka kamata ko tozartata gani nake kamar baba aka yima sai daga baya na gane baba daban mama habee makira daban..... FU'AD yaga Husna duk tayi laushi dama Haka yakeso sai yace "mubar wanan maganar har mu koma 9ja Amman Tana Nan fa sanan abunyi yanzu shine kije ki Gama shiryawa gobe zamu tafi na kaiki wajen baba da hannu na umarni na Baki ba shawara ko zab'i ba.... Husna cewa tayi "duk naji Amman yadda na maka rantsuwa banga Abin da zesani azumin kafara ba Gobe tafiya tamin kusa ban kwana da shiri ba bazan tashi da shirnta ba ko sallama da yafar juna bamuyi ba su Yaya Affan ya sadeeq muhibat,Husna..... FU'AD sai cewa yayi wai ke Baki da Abin magana ne sai Affan! Affan!! Me Affan!!! D'inan ya Miki arayuwa ne aikin banza aikin hofi mutuwa zakiyi da sai kinyi bankwana dasu Dan wulakanta Kai da Aure ma sunan shine a farko bama a k'arshe ba? Husna ta fahimci tsagwaran boyayen kishi ne da yake bayyana shi atunanin shi asirtawa yakeyi sai cewa tayi ,toh Kai meye tsakanin ka da shi waya tab'a kashe ma? Naka kamar kana nema ka tsane shi ko ince ma ka tsane shi meya tab'ama a rayuwa? Shin ma ka tab'a ganin shine na sama da awa 24 ? FU'AD baida amsa Dan da wuri zata Kama shi inyaci gaba da magana ya fahimci yarinyar yanzu ta zama banban Kai yadda ya Santa ada yanzu ta wuce Haka sai kawai yace "toh mumcy kisamin duka sai na fad'a Miki kinji mumcy? Husna baki ta bud'e da mamaki Tana cewa bankai ba nama barma d'akin Naga Abin naka sai anbarka ka huta ,amman Ina sake sanarma bazan tafi Gobe ba ko ka nemin kamun k'afa wajen Abba da aunty kuwa in ka Musa gwada sa'ar ka kaga iko da Isa da mulki a masarautar Husna da ka shigo da k'afafuwan ka,ta fice tabar FU'AD da mamakin yadda Husna ta canja Haka...... Bayan fitarta , FU'AD dogon nazari ya fad'a daga bisani ya yanke shawarar sai dai mumcy ta tafi Dan seya gwadama yarinyar Nan ya fita taurin Kai duk bala'in rashin kunya ta sai ya mayar da ita 9ja. *********** Tunda sanaya ta koma take chart da saurayinta Wanda yasan mutuncin ta Yana Mata magani ganun banza itace ya Dena Bata so sai shi yace "baze Dena ba har sai ta dawo gareshi Dan Tana kashe aurenta ze Aure ta suji dad'in Rayuwar su Dan ta birgeshi da Bata siyar da mutuncin ta ha FU'AD ba Dan Haka ko dar nayaji Akan wani mijinta gani yake babu wani Abu daze faru, ita Kuma Tana cemai "ya jira yaga Abin da zatayi Wanda ko dady ne ya gani ko yaji labari ze so a raba Auren su day gagawa sai ya dawo suyi Auren su,sosai yaci gaba da Mata kalamai na batsa har takejin kamar bazata iya Kama kanta ba ganin karta shiga wani Hali sai ta hak'ura da chart d'in ta fad'a gado tanata dogon nazari Akan FU'AD....... Tsakanin sanaya da k'anwar mumcy gaisuwa kawai Amman Babu Hira taja ta har ta gaji Dan Haka ta rabu da ita sai umarnin mumcy da takebi na cewa akai Mata duk Abin da take buk'ata." ******** Da in FU'AD ya Kira sanaya sai taga dama take d'auka Amman yanzu da ya Kira take D'agawa ,yau har da kanta ta kirashi Bayan Husna ta fita yana cikin dogon nazarin shi Bayan ya d'aga sun gaisa yake tambayan ta ko Akwai matsala ne? Tace "eh Akwai" Yace "Yana sauraron ta tafad'a yaji ,har Husna ta shigo ta samu suna wayar Yana amsawa a kasalance kamar Dole aka Mai,itako Husna sai hakan ya nuna Mata kamar wayar Ce Mai mahimmanci shiyisa ya tatara nutsuwar shi Akan wayar har ta shigo be fasa ba Kuma ya ganta,sai ma cewa da yayi fad'i Mana karkiji komai duk Abin da kikeson fada ki fad'a ashirye nake da na Miki komeye? K'irjin Husna ne yayi wani mumunan bugawa ,komeye? Komeye fa yace? Wace wanan ? Ko sanaya ce ko wata ya samu? Husna ji tayi zuciyarta na neman tarwatsewa gashi ta kasa tantancewa kishine ko me har ta juya zata fita yasa hanun shi ya kamota ya rik'e Gam ,zatayi magana ya mak'ale wayar a kafad'ar shi Yana cemata shhhhhhh yasa yatsan shi a Baki alamun tayi shiru kartace komai...... Husna tsayawa kawai tayi Tana tunanin Yama rainata Yana waya da wata banza shine har zece tayi shiru Kar maganarta ta fito ,kici kicin kwacewa takeyi ta kasa ,sai cewa tayi "Ni ka rabu dani kaje ka Gama wayar da take gabanka ,murmushi FU'AD yayi Karo na farko da tun shigewar shi gidan beyi ba gashi murmushi namai kyau gashi da wahalar yi in suna tare Amman yanzu yayi sai Abin ya birge Husna har ta Fara yabon shi da kyan da yayi taji yaci gaba da wayar Yana cewa "ko sai na dawo mayi maganar Naga kamar maganar nada nauyi a harshenki ko? Sai Husna ta ji wani Abu ya tsikareta a zuciyarta ta sake cewa ka sakeni mallam,Jin wanan kalmar FU'AD besan sanda ya katse wayar da sukeyi da sanaya ba ya kamo bakin Husna Yana cewa wanan kalmar in nasake jinta a bakin ki sai na yanke Baki Kuma ki fuskanci hukunci, Husna sai tamai wani irin kallon tuhuma wace kalma Kuma? Sai FU'AD yace kalmar da Kika furta masu harufa 8 in bakisan kin furta ba na ankarar dake ,sai ko Husna ta tuna Yana nufin kalmar da tace _ka sake ni_ toh ai Bata wata manufa ta fad'a ba Tana nufin ya saketa daga Rik'on da yayi Mata,Tana ayyana au har ka d'aukeni Mata bakason sakina yanzu? FU'AD ne ya Mata magana"ke me kike tunawa? Husna sai ta kwace hanun ta ,Tana cewa Ina ruwan wani ,kaci gaba da wayar ka nabar maka d'akin dama mumcy ce tace na kiraka in ka Gama ka fito tayi gaba da sauri ya biyota Yana cewa meye hakan kikeyi yi ? Ko kishine ne? Yarinya ta Fara girma har tasan kishi tab! Husna harara ta wurga Mai Tana cewa "ALLAH ya sawak'e meye Abin kishin kayi waya da Mata dubu ma meya yayi tsalle ya tsalla min Mari ,k'arshe ma ka auresu har su haifama taron idi k'arshe yawa ...... FU'AD sai cewa yayi tabbas alamun girma sun bayyana har kina iya maganar haihuwa yanzu ,yarinya zakiyi bayani ne ..... Husna sai da yayi magana sai ta tuna Abin da tace duk da ita Bata d'auki maganar wata Abu ba kawai shi Yama maganar fassara ,sai tace Ni ai na wuce yarinya.... FU'AD cewa yayi tabbas nine sheda nagani Kuma naji irin kalaman bakin ki ai,Amman lokacine ze nuna hakan...... Husna gaba tayi Tana cewa kanka akeji har suka Isa falon , mumcy da ammin suna zaune sai mumcy tace son Kaine zaka zauna ku taho da Husna ko Ni ,Dan beyi daidai ba ace daga ganin ta yau_yau ace Gobe Dole atafi da ita ba Dole Ayi komai cikin shiri.... FU'AD atake yace "kedai Zaki tafi uwa ta gari tunda gida babu kowa Ni na taho da ita Kar na koma baba ya tambayeni Ina na baro Mai 'ya. Husna da aunty huwaila suna ayyana rainin hankalin FU'AD wai baba bama shi ba ..... Sai mumcy ta raba gardama da cewa ,baba ko FU'AD shi baba ai tashi Mai sauki ce da yaji hanun da take hankalin shi kwanciya zeyi Kaine Abin ji kana fakewa da guzuma kana Harbin karsana ka fito a mutum sak..... Sosai FU'AD yake Jin cewa mumcy ta bada shi a gaban Husna har wani kallo take bin shi dashi sai kawai yace "haba mumcy baba Ni nafi tausayama kinfi kowa sanin Halin da ya Shiga .... Husna da aunty huwaila sai cewa sukayi a zuciyar su Dole sai ya doje ..... Mumcy ko cewa tayi "naji Ade barshi a hakan" kana nufin dai kwa taho tare? FU'AD hararar Husna yayi ya kalli mumcy yace "eh kawai" Sai anty huwaila tace" toh shikenan Bari na Kira Abban su kuyi sallama tunda kinki kwana anan kince FU'AD ma baze yadda ba... Bayan Abban su Affan yazo sun Gama magana da mumcy , mumcy nata Mai godiya ,shima yanata jadada Mata amanar Husna ,sukayi sallama ya Mata fatan tashi da sauka har Isa gida lafiya cikin Aminci ALLAH.... Da Affan da sadeeq ne suka raka su mumcy Dan har hotel d'in zasu kaisu ,Husna ma sallama Tama mumcy da Addu'a ALLAH ya kaita gida lafiya har FU'AD na cewa nifa bazakimin Addu'a ba? Dan ya k'ular da Affan yasan bazataki yi ba kodan idon mutane ,sai tace "to kaima ALLAH ya kaita gida lafiya" Sai yace "gida ko hotel? Sai tace "toh hotel shi kenan" Da gayya yace "Ameen" Affan ko ajikin shi duk da yanajin rashin Dadi inya tuna da ya Rasa Husna Amman sai ya nemi zab'i Awajen ALLAH mafi Alkhairi." Aunty huwaila d su muhibbat byebye suka dinga yima mumcy har sadeeq yaja motar ya fitar da ita daga gida...... *Kuyi sorry da wanan maybe Saturday and Sunday baxakujini ba maybe fa in Kuma kunga update to nayi typing* *Inajin dad'in sharhin ku sosai* *Ina godiya da Addu'a* *Dan Allah kusa mijin k'anwar mamana a Addu'a ALLAH yamai Rasuwa jiya* اللهم اغفره ورحمه أمين يا الله👏🏼 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman Shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg55 FU'AD hak'uri yayi kawai badan yaso ba, mumcy duk tana lura da yanayin shi taki kulashi Dan so take ta sake gaskata damuwar da FU'AD ya Fara nunawa akan Husna duk da ba abayyane gani take Yana zargin Husna na wajenta ne,Kuma Abin na damun shi amman afili Yana nuna be Dame shi ba." Bayan wasu d'an awanni sai mumcy ta Fara yima FU'AD magana Akan komawar su indiya." Washe gari....... FU'AD cewa yayi toh aitana Nan Amman Akwai wani abokin shi daze gani yau ko be Dan haka anjima ze fita, Mumcy tace "agaishe da sabon abokin Dan naga alamar kamar Baku Jima da had'uwa ba . FU'AD zeyi mgana mumcy ta tashi ta Shiga d'aki Tana Mai adawo lafiya. FU'AD shiryawa yayi ya fita yanata mita Yana ayyana hukuncin da zema Husna inya ganta Dan ta wahalar da mutane shi bega abin da suka Mata ba,Yana tafiya Yana tunanin zuci..... Store d'in d ya ganta ya sake komawa ya kusan awa 1 Yana duba masu Shiga daga gefe da masu fita ko zeganta Amman shiru ya Shiga ma ya sayi wasu Kaya y kusan kwashe awa aciki Amman shiru babu ita babu labarinta,y hak'ura ya fito. Bayan ya fito yanata tunanin yadda ze billoma mumcy sai yaji wayar shi Tana ringing ya duba yaga Ashe B2k ne ya kirashi ,sai ya d'aga sukayi magana Yana tambayar shi komai normal ko? FU'AD yace Mai "eh wallahi ,Bayan sun Gama magana har sunyi sallama sai Fu'ad ya Fara gayama B2k labarin ganin Husna da yayi Amman Kuma kamar ba itaba ,sai ko B2k yace "ba aunty ta tana Nan ba kace min? FU'AD yace" eh" B2K yace "toh gaskiya ka binciketa agidan kafin ku dawo Dan komai ze iya faruwa." FU'AD cewa yayi "ai Nan nake hari yanzu matsalana yanaga mumcy ,kasan wancan lokacin da mukazo aka kawo Ni Bayan na samu kaina tace muje mu gaisa nanuna kin amincewana itama na hanata zuwa still zuwan mu dinan ma na hanata zuwa d ta sake bijiro min da son zuwan ,yanzu Kuma d nake zargin Tana gidan shine nakeson zuwa sai mumcy tace baza'aje ba kasan uwa ta gari babu wasa har Ina neman kasa Shawo kanta wallahi." Sai B2k yace "gaskiya ka lalabata auta da ita ya Kamata aje ma Ina Nan Ina tayaka Addu'a daga Nan." Bayan sun Gama waya sai ya yanke shawarar zuwa wajen mumcy Dan ya samu ya lalab'ata su samu suje gidan aunty huwaila." Mumcy na ganin shi da fuskar shi Mai Kama da ta me neman yafiya , mumcy tace son da wacce akazo ne? FU'AD Yana Sosa k'eya yace "mumcy tafiyar Nan fa gobe Tana Nan ,Amman kiyi hak'uri muje mu gaishe da aunty huwaila duk da Ni naki adacan yanzu Naga dacewar hakan Dan ALLAH karki datse igiyar sada zumuncin da nega cancantar shi a yanzu uwa ta gari Abin Alfaharin kowa." Sai ko mumcy tayi murmushi Tana cewa "hmmmm auta kenan" sai ko FU'AD yace "mumcy karki bijirema buk'atata Dan ALLAH ki tashi muje . Sai mumcy tace "da zafizafi Haka? FU'AD yace "eh uwar ta gari" Sai mumcy ta shirya ta saka hijabin ta Mai kyau da tsada har k'asa ta d'auko Jakarta me had'e da takalmi masu uban tsada tace toh na shirya me ziyarar bazata Dan ko Gaya Mata banyi ba sai mun Isa unguwar sai na kirata. FU'AD yaji dad'i har cikin ranshi Amman Babu alamu afuskar shi har Yana cema mumcy kawo jakar namiki dakon ta,sai mumcy tace"haba auta na hutashe ka muje kaidai" Bayan su mumcy sun Isa unguwar Tana bin kwatancen da ta Bata har gidan ,sai ta kirata a waya Kira har so 3 ba'a daga ba sai mumcy tace no answer son ko mu koma? Sai FU'AD yace "a mumcy mu gwada Shiga daga gate man din zamu gane in gidan ne ze gaya Mana ,suna Shirin Shiga Bayan sun kwankwasa tamfatsetsen gate din katafaren gidan da fad'en tsaruwar sa ma Bata bakine ko Alkalamin rubutun........ Sai ga wata k'atuwar mota Mai numfashi ta danno Kai da alamun gidan zasu Shiga ,sunata horn...... Da sauri me gadin gidan ya taho ya bud'e k'ofa bayan ya lek'o ya ga motar... Mumcy da FU'AD sai da motar ta shige suka bita da kallo sai suka ga alamun kamar ba indiyawa bane cikin motar Amman me gadin gidan ba'indiye ne." Suko Yan cikin motar ,Affan shike tuk'a motar sai Husna a gaba kusa dashi sai Husna a baya babu muhibbat Sam basu ga fuskokin su mumcy ba Bayan su suka gani Husna Kam ma Danna wayarta taketa dannawa Bata lura dasu ba duk da ta ji wani irin bugu da k'irjin ta yayi lokacin da suka dai dai k'ofar gidan memakon ta kalli k'ofan gidan sai ta runtse idonta ta Fara karanto Addu'a Tana Addu'a ALLAH ya tabbatar Mata da duk abin da yake Alkhairi agareta Bata bud'e Ido ba har sai da taji Affan ya tsayar da motar alamun sun Isa inda ze adana motar." Husna k'arama ce ta Fara fitowa yayin da mumcy ma suka shigo da FU'AD cikin gidan mumcy na niyar tambayar Husna ko nanne gidan huwaila...... Sai ga Affan ya fito yanata dariya har da kyakyatawa sai ga Husna itama ta fito Tana nata dariyar har Tana rufe Baki irin tmdariya tayi armashi d'inan Tana nuna Affan da yatsa Tana magana ........ Caraf a idon FU'AD Amman da mamaki Yana son ya nuna rashin daidain hakan ,Amman Yana tsoron Kar yayi Abin kunya a inda Basu Gama tabbatarwa inda suke nema bane ,Dan yaga husnar ta gama zama cikakiyar mace cikin k'ank'anin lokaci komai nata ya cika ta zama babbar yarinya Mai cikar hallitu shine yafi bashi mamaki Dan yasan Husna da yake nufi wato _dirty girl_ ba... FU'AD na tunanin Nan, mumcy Kuma na magana da Husna k'arama a yayin da Husna FU'AD ta jiyo a sukwane tayi tozali da mumcy , mumcy ma tayi tozali da Husna ,kowa mamaki ganin kowa yakeyi...... Husna kasa k'arasawa tayi sai da mumcy ta k'araso gareta Tana cewa "wai Asma'u tace? Sai Husna ta k'araso da gudu ta fad'a k'irjin mumcy atake muryar ta tafara rawa Tana cewa" nice hajiya"...... FU'AD tun da ya tabbata Husna ce y gani da wani k'ato sunata dariyar Jin dad'i sai tsanar Affan ta dirar Mai Yama manta da murnar ganin husnan da ya kamata yayi sai aikama Affan da uwar harara yakeyi har Affan ya Fara tsarguwa... Affan ne ya k'araso yace my Husna bak'in mu ne? Daga Ina suke?...... Husna cemai tayi "eh mu Shiga dasu daga ciki yau aunty tanada bak'i" Affan cewa yayi "toh bisimmillah ku mu shiga ciki" Yana nuna ma su FU'AD hanya ... Duk da yanayin Affan ya canja Dan ya Fara zargin FU'AD shine mijin da ya kwace Mai Husna Dan biri yayi kamada mutum ga sak'onan Yana aiko min ,inbeyi Wasa ba be bini ahankali ba sai namai akuya,Dan ya samu na hak'ura anshawo kaina da kyar ma......k'wafa kawar yayi yayi gaba suka bishi. Husna k'arama kuwa tuni tayi gaba Tana bama Aunty huwaila labarin ga 'yan uwan aunty husna Nan sunzo dama sunsan gidan? A tsorace aunty huwaila ta biyota tana cewa "su waye 'yan uwan nata muje nagansu sai sukayi kacibus a hanya.... Aunty huwaila ce ta bud'e Baki alamun mamaki sai , mumcy ma ta mayar Mata da murmushi gad'i da cewa ga bakin katsaham bakin da Basu nemi izinin zuwa ba..... Bata k'arasa ba aunty huwaila tace "Kai karkice haka sanun ku da zuwa sanun ku naji dad'i sosai da fara'a ta kaisu masauki anata musu sannu da hanya." Tsakanin FU'AD da Husna sai kallon kallo har yanzu basuyi magana da juna ba nashi b'angaren kishi ya turnik'eshi acewar shi ba kishi bane haushin ganin ta a India ne Ashe Nan ta gudo har ta fetsare? Itana taba tunanin har yanzu Halin shi nanan da Halin ko in kula da son zalintar ta ga girman Kai Yama ganta ya d'auke wuta har yanzu Yana Kan bakanshi na korar ta kenan tasan mumcy ce ta tursasamai zuwa gidan gashi sai hararan d'an uwanta Abin sata farin ciki shida iyayen shi da sauran 'yan uwanshi yakeyi Dan Tana kallon shi Dan Haka itama ta share shi taci Alwashin inhar be mata magana ba bazata Mai ba." Bayan sun zauna! Aunty huwaila ta Fara gaishe da mumcy cikin kulawa da mamakin ganinta a india, mumcy ta amsa cikin fara'a. FU'AD ma ya gaishe da aunty huwaila ,cikin sakin fuska ta amsa ,sai sukayi shiru na d'an wani lokaci kowa na neman Abin zewa ,aunty huwaila na zargin ko Husna suka biyo to ya akayi suka San Tana Nan? Mumcy ma nata tunanin ta inda zata soma. FU'AD ko yanzu baida abun sani kamar alak'ar dake tsakanin Husna da Affan Dan har yanzu yak'i sakin ranshi gashi a gaban shi suka shige Yana Mata magana Tana amsa Mai da girmamawa.... Can dai mumcy tayi magana ,nasan zakiyi mamakin ganin mu a India har zuwanmu inda kike yanzu batare da na sanar Miki ba kafin muzo? Sai aunty huwaila tace "eh kwarai kuwa" Sai mumcy tace "nama Rasa ta Ina Zan Fara sakamakon ganin Husna da nayi tare dake Dan banyi zato ko tunanin Tana Nan ba in Baki manta ba har kiranki nayi na tambayeki Kika nuna min Bata Nan,Ni Kuma ban zurfafa neman ba kamar yadda bakiso Jin meyefaru ba har muka ajiye wayar." Aunty huwaila take " hakane kwarai" Mumcy ta sake cewa"kawai dai abubuwa da dama sun faru sakamakon faruwar nasu ne in husnan Bata b'oye Miki komai ba,dalilin hakan ne ya kawo mu India ALLAH yasa muka Dace har Fu'ad ya dawo hayyacin shi muka koma suka bamu appointment na dawowar mu Dan amishi check up shine mukazo har andubashi muna Shirin komawa ma Naga dacewar na kawo Miki ziyara nakuma sanar Miki Halin da ake ciki Dan muyi magana Baki da Baki Dan kamar zefi shine fa nazo nayi tozali da ita Asma'u..... FU'AD yaji dad'in kwanar da mumcy Tasha da batace shi ya nuna son azo ba Dan Kar yarinya ta rainashi wato Husna marainiyar wayon shi." Bayan mumcy ta gama bayanin ta sai aunty huwaila tace "hakane Husna ta fad'a min sanan Kuma naji dad'in ganin FU'AD haka Dan tunda tamin bayanin faruwar lamarin hankalin mu yake atashe Abin da yamin zafi korar ta da kukayi gaskiya bazan b'oye muku ba naji zafin hakan ba inda kuke tunanin zata Suma suka koreta Dan Haka na Mata Visa zuwa India ,ganin annuna rashin damuwa da Halin da take yasa nayi biris da maganar ku Nima Dan na bincika Bata da laifi ko masaniya Akan Abin da ya farun ,Kuma ku kunada Hali da yadda zaku neman ma d'anku lafiya aduk k'asar da kuka buk'ata fad'in duniyar Nan kamar yadda ta faru yanzu gaku a India, itako Bata dashi sai babanta sai ALLAH sai Ni da na kunna nutse cikin Rayuwarta da yanzu wani labarin ake ba wanan ba Dan da dukan baza zusan inda ta Shiga ba Dan babanta baya Nan su Kuma azzaluman gidan sun koreta...... Aunty huwaila zata cigaba da magana..... mumcy ta tsayar da ita da cewa "hakane Dan kuskure munyi shi itama tayi shi da Abin ya faru ta tabbata acikin turaren matsalar take sai tayi bayani asan yadda za'a Shawo Kan matsalan, Kuma na damu kwarai da son ganin ta da dawo da ita cikin ahali na nayi wayar na tura har gidan su hatta su FU'AD mijinta gashi Nan a zaune sune sanadin Nemo mahaifinta da ba Wanda yasan inda yake bala'in muguwa kanwa uwar gami ya koreshi har k'auyen da yake sukaje suka bayyana Mai Halin da ake ciki,Jin matsalar shi tafi shafa yabar k'auyen suka dawo tare..... Husna na labe Tana sauraron duk maganganun su tuni hawaye suka Fara sintiri a kumatun Tana tunanin da yanzu Tana wani Hali na wulak'anta da ita ta amfana da turare Mai mugun kud'irin mama habee..... Sosai mumcy ta keba aunty huwaila hakuri akan Abin da ya faru da godiya da d'aukan Husna da tayi.... Bayan ankawo musu Abin ci da Sha , FU'AD ya kasa furta komai har yanzu Bayan godiya akan k'ok'arin da aunty huwaila tayi yaja bakin shi ya d'inke. Lura da yanayin FU'AD yasa aunty huwaila kiran Husna ,Bayan tazo ta umarce ta da tataunawa da mumcy da mijinta Tama tashi tabarsu Bayan ta Mata bayanin duk Abin da suka tatauna akai. Husna sosai ta dinga Jin son mumcy uwar datako FU'AD ko be ce mata komai ba. itama Bata ce Mai ba , mumcy nata mamaki da Halin da ya nuna kamar ba Wanda ya Gama Mata magiya Akan zuwa ba yamaga husnan memakon murna sai kunci da yaketayi har yanzu be cemata komai? Ko dayake itama ta birgeni da Taki kulashi Naga ta sake samun wayewa da sabuwar rayuwa ma ai bazan shiga maganar ku ba har sai ka magantu sai ta dinga Jan Husna da Hira kawai ,Husna nata tambayar su aunty sa'adiya..... Bayan aunty huwaila ta dawone sunata Hira da su mumcy muhibat da su Husna karama da Affan sukazo suka gaishe da mumcy Affan hannu ya mik'ama FU'AD ,da kamar baze bashi ba sai kawai suka gaisa adole... Husna ce ta Fara gabatar ma da mumcy Affan matsayin yayanta sai sadeeq Wanda baya Nan sai muhibat Yar uwart sai husana autar su takwarar ta Kuma. Sosai mumcy ta Nuna Jin dad'in ta tana sa musu Albarka cikin Rayuwar su." FU'AD ne ya Fara tsokano maganar cewa Husna ta shirya tare zasu tafi Gobe zasu koma.... Husna tayi tsallen Albarka tace ita ba Gobe zata koma ba ,ganin zata Mai gaddama shi Kuma yace dolenta ba Aure ne akanta ba? Aunty huwaila na sane Taki saka Baki , mumcy ma da biyu Taki magana ,su Affan ma ganin manya basuyi magana ba Suma sukayi shiru..... Ganin sunki saka Baki ga Affan da yaketa binta da kallo Yana so ta dago ta kalle shi ya Mata magana da Ido Akan tabi mijinta ta koma dakinta, Amman Taki d'agowa.... Hakan ya k'ara k'ular da FU'AD yace sai fa kin tafi Gobe in har da igiyar aurenki a hannuna kiji na gaya Miki Kuma Dole ki Amince,sai ko Husna ta d'ago ta kalli Affan ya dinga rarashinta da Ido ,Amman Husna ta kalli FU'AD tace wallahi bazan tafi Gobe ba Tama fashe da kuka ta mik'e da sauri ta nufi d'akin ta ,muhiy d Husna suka bita da sauri suna Kiran sunan ta." FU'AD ko shak'o wuyan Affan yayi Yana huci Yana cewa me son Rana sunna me ka Gaya Mata da Ido? Eye Meka gayamata nace........? Da sauri mumcy ta Mike ta nufi inda suke Tana Kiran sunan FU'AD da k'arfi............... 😍😍😍🥰🥰 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg57 Bayan su Affan sun sauke mumcy ,sun dawo gida suka samu Ammin su nata ma Husna nasiha akan bin mijinta Husna nata kuka Tana nuna batason binshi a yanzu tafison zuwa wani lokaci Amman ba yanzu ba sanan bataso tayi Nisa da Yaya matar da batasan ko wacece ba Amman jikinta na sanar da ita matsayinta Dan yanzu sun shak'u Dan har abinci take Bata a Baki gashi wani lokacin Tana yunk'urin yi Mata magana bakin ne kawai baya bud'uwa sai ta hak'ura. Affan da sadeeq ma hak'uri suka dinga ba Husna da mata Al'k'awarin duk Abin da ya dameta tayi gagawan sanar musu ko menene zasu Mata maganin shi iya k'arfin su ba Akan FU'AD ba kawai ko Akan waye ma har uwar Rik'on ta mama habee ,sanan zasu iya zuwa har 9ja su dawo da inta indiya daga yanzu ta saka acikin ranta family ta suna indiya in 9ja ta k'iki indiya na mararin ki..... Wanan maganganun sun sanyaya ran Husna ,Kuma sun k'ara Mata karsashin Jin ta shirya kwatoma kanta 'yanci a wajen FU'AD da duk wani da yakeson kawo turnik'i cikin Rayuwarta inko har abun yafi k'arfinta da gudu zata sanar musu kamar yadda suka buk'aci hakan. Muhibat da Husna sunata nuna rashin Jin dad'in Rayuwar da zasuyi da Husna ,sanan yanzu Basu da wajen Hira sai dak'in Yaya matar Nan cikin nutsuwa da nuna rashin hayaniya har hirar tafiyar Husna suke ,matar ta zuba musu ido kamar Tana fahimtar Abin da suke cewa ,daga baya ma tasa musu kuka Husna ce taje ta dinga rarashin ta tana tanbayarta meyasa take kuka ? Ci gaba tayi da kuka babu magana ganin bazata ce komai ba inda sabo ta Saba yasa Husna ta samu ta zame jikinta da kyar ta d'ebo Mata abinci ta dinga Bata abaki Tana ci ta Bata ruwa Wanda akayi Addu'o'e aciki ta Mata bissimillah tasha.... Husna ido ta zuba Mata Tana tambayan kanta dalilin da yasa takejin wasu abubuwa game da ita ? Rashin samun gamsasuiyar amsa yasa tabar d'akin ta koma falon Tana kallon tv tare da su Husna da muhibbat Dan sun fito sun barta aciki." Suna zaune ne har Affan ya fito ya zauna suna Hira Yana tsokanar Husna wai matar boss ,Husna ta Harare shi tace "ai bada ita yakeyi ba" Affan yace "eh da wata nakeyi dama bance dake nakeyi ba" Sai ga sadeeq ya fito shima ya zauna kusa da Husna Yana cewa "ya k'anwar mu medame kike buk'ata ne na tsaraba ko Abin amfanin ki mu Fara tanadar Miki kafin zakin mijinki yazo tafiya dake Dan wanan gani nake baze barki ki wani Jima batare da ya tasa k'eyar ki zuwa 9ja ba" Husna kalon shi tayi kafin tace "har da Kai ya sadeeq ,Ni fa kubarni ba yanzu Zan barku ba Kuma ma kozan tafi bana buk'atar komai Inna rik'e tsaraba ne na ma baba tsaraba bayanshi Banda kowa a 9ja sai 'yan mutunci kawai." Affan dariya yayi kafin yace 'yan mutuncin dama yake nufi Kuma dai ki zama cikin shiri kinsan Ammi Bata Isa ta hanaki bin mijin ki me........sai Ammi tayi saurin cewa me me? Tana Shirin zama nesa dasu,zaka farane? Sai Husna karama tace "Yaya Affan ya koma me tsokana sai tsokanar namcy na yake kamar wata abokiyar wasan shi ya mayar da ita ,sai ko yace "in ban tsokaneta ba k'anwar wa kukeso na tsokana? Duk suka saka dariya Banda Husna .... Washe gari FU'AD har Airport ya Kai mumcy ya Mata fatan sauka lafiya , mumcy nata Mai fad'an yabi komai ahankali ya kwantar da Kai batason Halin Nan da ya aro in yasan bazeyi Abin da ya Dace ba ya batta ta zauna ta taho da ita shi ya tafi yanzu." FU'AD sai cewa yayi " haba mumcy wanan ai ba akin ki bane ke ai kin Gama naki sauran nawa ne" mumcy tayi murmushi tace toh Ina sauraron ka naji yaushe zaku taho kasan sanaya Tana can itama jiranka take a matsayinta na matarka Dan Haka Kar ashiga hakinta Ayi maza a dawo ,a fili FU'AD sai cewa yayi to ace Mata Ina hanya insha ALLAH ,a zuci kuma yace wai hakki Ni na Gama Bata hakkinta babu Abin da babu a gidan in kud'ine tamin magana na Mata transfer ko nawa take buk'ata... Bayan jirgin mumcy ya tashi FU'AD ya koma hotel duk sai yaji zaman hotel d'in babu dad'i Dan Haka ya Kira Yaya Jameel sukayi magana sosai Akan Husna Yaya Jameel ma jamai kunne ya dingayi har Yana cemai kodai yazo su tafi gidan su k'ara Basu hak'uri? FU'AD yace aa ya Bari ai angama komai tahowa ma zasuyi , Jameel yamai fatan Alkhairi da Mai nasihar rik'e matan shi da aka aura Mai da kyau." FU'AD har ya kwanta ya sakejin duk babu dad'i ya fita ya shiga gari ya nemi wani abokin shi da suka tab'a karatu tare da Yama manta dashi sai yanzu ya tuna yaje gidan shi suka Gama Hira har yake cemai shima matarshi Tana Nan be boyemai komai ba ya Gaya Mai ,abokin nashi me suna musbahu kingkhan yace ya Kama ya karbi matarshi su tafi ta hanyar soyayya da nuna kulawa in ba hakaba wallahi zata iya bijirewa tace bazata bishi ba inya matsa Tana iya cewa Bata son Auren shi tafison d'an uwanta ...... Musbahu kingkhan be rufe bakiba FU'AD ya Fara huci Yana cewa yabar maganar Haka ,Dan bama ze tab'a faruwa ba ,musbahun yace Mai kana sonta kenan yanzu? FU'AD yace "ko Ina sonta ko bana sinta hakan ko sanin hakan ba abun da ya shafeka bane ,kawai kazo muje kamin rakiya sanan karka wuce makad'i da rawa Dan nasanka tun muna school Nima Kuma kasanni ,toh ban canza ba nine dai FU'AD basaraken da kuke min lak'abi da naci ubanku kuka goge sunan da kyar........ Dariya sosai musbahu yayi harda rike ciki ,Yana cewa "Kai abokina sunan fa ya Dace da Kai halinka dai Wanda yasanka kumafa baka canza ba wallahi kana Nan yadda nasanka , FU'AD ma yace "Haka zalika kaina kanari sarkin surutu halayenka duk suna Nan na tsallake gona da iri...... Bayan su Gama komai musbahu ya d'auki mota Yana tak'i FU'AD na gefen shi sunata hiran school life d'in su har suka Isa gidan... Jin ance FU'AD ne Ammin su Affan tace "amai iso ya shigo har parlour ya shigo ,ya gaishe ta shida musbahu cikin girmamawa,tasa aka cikasu da Abin tsa Baki ,sanan tasa aka Kira Mai Husna ita Kuma ta tashi ta Basu wuri." Husna abokin ta Fara gaisarwa kafin FU'AD Abin ya k'ular da FU'AD Amman ya basar ,gashi tun da ta fito ko fara'a tak'iyi , musbahu ko ya saki Baki ya dinga zuba kamar bakin indararo har sai da FU'AD ya dakatar dashi sanan ya tsaya ,Husna nata Mai dariya a zuciyarta." FU'AD ne yace "ya maganar tafiyar mu kin Gama shiryawa? Husna cewa tayi aa da saura ,sai Fu'ad yace sauran me ? Husna tace" Akwai abin da nake jirane" Sai FU'AD yace "shi Abin bashi da suna ? Sai musbahu yace kaima kamar bakasan Mata ba shirinsu baya k'atewa sai su d'au tsawon lokaci suna shiri hatta powder shafawan su sai su zagaye store suna nema sucema Basu samu type d'in su ba....... FU'AD ne ya tsayar dashi da cewa ,toh ita cemaka tayi Tana daga irin wad'an Nan matan ? Sai ko Husna tace kasani Nina ai mace ce" Sai FU'AD ya harareta ke kinsan dai nasanki ko karki biyema wanan kimin karya ko Halin Nan naki ya k'arasa maganar da Mata nuni da tashiga hankalinta,ta kalleshi ta watsar tana cewa nidai a bani isashe lokaci ingama komai a tsanake Ni ji nakema fa kamar Kar na koma........ Bata rufe Baki ba musbahu yace.... Kaji ko? Kaji magana ta ko? Sai ko FU'AD ya kulu Dan musbahun nema yafi k'ular dashi yace "me naji da maganarka da guntun Kashi duk d'aya ke Kuma wallahi Baki Isa ba kuma ya zama Dole mutafi tare ko kingama shiri ko Baki Gama ba inkika k'ara ganina a gidan Nan kisani nayi zuwan k'arshe Dole ki biyoni mu tafi Zan ga Wanda yakeda iko dake Bayan Ni....... Afusace FU'AD yace "Kai Kuma sai ka taso uban hasashe in Kuma kaga waje sai kayita zama , musbahu cewa yayi aa abokina muyi tsiya muyi dad'i zikaji banaso ka tafi kana fushi Dani ko ita Zo muyi maganar fahimta ya dawo da FU'AD d'in.... Yace ,baiwar ALLAH matar abokina ,Kinga dai komai ya faru bisa kuskure Dan ALLAH komai ya zama tarihi kibi mijinki ku zauna lafiya Kinga da auren shi akanki ,shima ya amsa ya Kuma karb'a yasan da aurenki akanshi ya Kuma shirya Baki kulawa fiye da ta baya da ya Baki Dan ze shayar dake zumar so zallah Mara sirki........ FU'AD yaji kingkhan na sakin layi sai yace "Kai kafa tsaya matsayinka karka fad'i Abin da be fito daga gareni ba toma wai Kai waya aikeka can inda ka nufa ? Kawai ka Gama fad'an Abin da zaka fad'a maganar ka har ta k'are ka Fara had'awa da shifcin gizo kawai nadai Gaya Mata ta zama cikin shiri konawa tare Dole babu shawara babu lalab'awa sai umarni ya mik'e ya saka Kai ..... Kingkhan ne ya dinga rarashinta Yana Mai k'aryar Yana sonta wallahi Kuna ze kula da ita kawai dai tayi gagawan karantar shi da sanin mulkin shi da sanin waye shi inta San Haka ta gama dashi ya Mata sallama ya bi abokin nashi FU'AD waje...... Bayan Husna tabar wajen FU'AD d'akin matar Nan ta shiga ta fad'a jikinta tanata kuka Dan da Tana tsoronta da d'ari_d'ari da ita yanzu ko ta Dena ,Husna na kuka Tana cewa wallahi Ina tunanin komawa hanunka FU'AD duk da nayi imani da mumcy bazata barka kacigaba da min Abin da kamin a baya ba Amman Naga kamar ka sake k'aro wulak'anci inko hakane Dole Nima na Shiga kasuwar Rashi mutunci dan siyo kalan nawa wulak'anci kana gabzamin na mayar maka da martani da naji zaman bazemin ba na dawo india abuna Dan Naga 'yan uwa masu sona nikam nagama maraishin dangi insha ALLAH." Husna sai ji tayi matar na rarashin ta ta hanyar jijigata da hannun ta tana hawaye itama... Husna da sauri ta d'ago ta kalli matar sai ta sake saka hannunta Tana sharema Husna hawaye ,Husna hanunta ta Kama Tana murmushi cikin kuka Tana cewa ,wai kinji abinda nake fad'ane? Ido kawai matar ta zuba Mata ,Husna sake Mata tambayar tayi Tana kamo hannun matar ,shiru matar tayi Tana k'arema Husna kallo,har sai da Ammin ta shigo ta samesu a Haka sai da Ammin ta kusa minti 3 Tana kallon ikon ALLAH tana mamakin tsak'uwar da ke tsakanin su day wasu abubuwa da ita tabarma kanta sani kawai sai can tace...... "Husna Ina mijin naki kiketa kuka keda yayan da ba jinki takeyi ba? Husna d'agowa tayi Tana cewa "dama kin shigo ammi? Tana share hawaye ,sai cewa Ammin tayi Dena share hawayen ki yi abunki Kya Kori rad'adin da kikeji a zuciyar ki kukan ma ai da amfanin shi , in na mamakin yadda yaya take tayaki kuka Akwai shak'uwa a tsakanin ku da ta bijiro kwanan Nan Haka ALLAH yake ikon shi ..... Sai Husna tace "me kike nufi Ammin? Sai Ammin tace "Ina nufin jinin kune ya had'u kawai" [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg58 *Wanan page din gaba dayanshi na namcy nane wato ummu Qaseem*❤😍🌹 Sai Ammi tace "Ina nufin jinin kune ya had'u kawai" Husna bawai Dan ta gamsu ba tabar maganar ne kawai. Koda Ammi ta tambayi Husna FU'AD cikin Halin ko in kula tace "sun tafi" Ammi Kiran Husna tayi gefe a cikin d'akin tanata rarashin ta da Bata hak'uri akan FU'AD da Mata Al'k'awarin bak'in ciki da b'acin ran da Tasha a baya da izinin ALLAH yazo k'arshe duk wani Abu daze faru tsakanin ta da FU'AD indan na sirrin sune tayi k'ok'arin shanyewa da adanama cikinta Dan ciki badan abinci kawai akayishi ba' Sanan duk Wanda take buk'atar shawara k'ofa abud'e take ,Wanda Kuma zata iya magance shi da kanta tayi k'ok'arin magancewa batare da ta nemi agajin kowa ba zaman Aure ya gaji Haka,sosai Husna ta d'auki nasihar aunty huwaila tayi naam dashi Kuma. *********** Mumcy ta Isa k'asar mu ta gado wato Nigeria lafiya, Tasha tarba wajen k'anwarta balaraba da ma'aikatan gidan sanan su Jameel da sa'adiya suka Mata nasu bangajiyar ta waya dake suna Abuja. Sanaya Bata Zo ba sai da akaje Kai Mata abinci akace Mata mumcy ta dawo, shine ta d'ebo 'yan matan kafafuwanta tazo Dan ta tambaya akace Banda FU'AD suka dawo ,shine tazo Jin dalili? Bayan ta gaishe da mumcy ta yi shiru sai mumcy ce tace "karkiga FU'AD be dawo ba tare zasu dawo da Husna kinsan Tana can indiya taje wajen aunty ta huwaila shine zasu dawo tare duk da ba tare suka tafi ba ,Dan mumcy Bata tab'a Gaya Mata b'atan Husna ba. Sanaya yak'e tayi tace "toh babu komai ai ,Amman bazasu wuce Nan da 5dys ba Koh? Mumcy "eh toh banace ba Amman bazasu wuce hakan ba insha ALLAH" Sanaya "toh ALLAH yasa" ta tashi zata koma sashin ta ..... Sai mumcy ta dawo da ita "nikam sanaya bakya gajiya da zama ke kad'ai d'inan da kikeyi? Ko wani cikin ma'aikatan Nan kinki sakin jiki dashi bare abokiyar zamanki inaganin zaman kadaitan Babu dad'i ...... Sanaya"a ai inda sabo na Saba some times ban fiye son hayaniya ba nafi son naganni Ni kad'ai nayi bacci na tashi nad'an rik'e phone d'ina mugaisa da fanc sai fita outing in Ina sha'awa,is normal ai na Saba karki damu" Mumcy "ok ba'a kwacema yaro garma ai ,u are mature basai na forcing d'inki ba Akan Abin da ba ra'ayinki ba" Sanaya "karki damu fa innaga Ina sha'awar hakan zanzo na nemi wata da zatayi daidai da ra'ayina ko nasa anema min a waje Dan Akwai wata aunty k'awana inason Kai Mata ziyara ma a Nan take ko ita sai insa ta Nemo min" Mumcy "toh ai shikenan babu matsi ko takura dai ga ahalin gidan Nan kema sheda ce" Sanaya "no banfa ce kin matsa min ba wallahi na fahimce ki Nima ki fahimce Ni Dan ALLAH? Mumcy "nasani yo Kya Fara cewa na matsa Miki ma? Kawai dai Ina tuna Miki Abin da Kika sani ne. Sanaya "eh hakane nagode barinje ,Kinga ko yanzu ma mun d'an tab'a Hira ai natafi bye. Mumcy binta tayi da kallo Tana murmushi. Baban Ma'u ,tun dawowar shi mama habee ta Dena ganin walwalar shi da fara'ar shi ,Kuma da ta Fara hayayak'o Mai ze juye Mata kwandon fad'a har sai ta rusina ,Abin na matuk'ar Bata mamaki Akan yadda ya samu dama yake Mata haka. Humaira kuwa cikin samarin ta tanata laluben Wanda zata shak'e amusu Aure kafin abata kwashikwaraf d'in da baba yace kowa ya samu tasan ze aikata tunda mama habee ta Fara laushi Dole itama tayi laushi ,Dan Haka taketa lalube Kuma wai me d'an kyau ko k'asa da FU'AD d'in Ma'u ne ,sanan med'an abinyi na rufin asiri Dan itama Auren zefi Mata ta gaji da soyayar shafi muleran da takeyi (soyayyar Shan minti) gwanda taje taji d'an gasken shafi muleran...... Maman hafeeza nata murna yau hafeeza zata dawo daga karatun da tatafi wajen k'anin ta a manbila ,Dan Haka har Dan girke_girke tamata da toye_toye tanata jiran saukarta, Bayan awa 1da Rabi kuwa hafeeza ta sauka, Bayan ta huta sunyi Hira da mamanta take tambayan ta ina kuwa Ma'u zun kwana biyun basuyi waya ba ko ta kirata ma Bata samunta Dan Haka takeso inta huta taje gidan hajiya babba taji ko lafiya? Maman hafeeza Bata labarin duk abun da yafaru tayi tace Kuma "Taki sanar matane saboda Kar ta batama Ma'u shiri na barin k'asar Dan tasan halinta zata iya Bata hak'uri tace ta hak'ura ,ita Kuma tanason yin nesa dasu Musamman ma da zata bar musu k'asar ,har zuwan su baba gidan neman Ma'u sai da mama taba hafeeza labari. Hafeeza ajiyar zuciya tayi tace , ALLAH sarki k'awata ta ga tashin hankali ,Amman da yadda ALLAH komai yazo k'arshe ,zanje gidan baba kuwa Dan jin labarin ko yasan inda take innaga tashin hankalin shi a bayyane gaskiya Zan sanar Mai inko Naga ya dangana Zan kyale shi ,sanan har gidan hajiya baban zani naji ko sun Sami labarinta ,hmmmm maman humaira fz Daman kamar Babu ALLAH aranta wallahi Bata da imani mama Akwai abubuwan da takema ma'un idan na tuna Abin tsoro da mamaki suke bani..... Mamace tace "hmmmmm ke Wanda Kika sani kenan ,Ni Akwai wani zargi ma da nake Mata Akan mutuwar mahaifiyar ma'un bantaba gayama kowa ba kema ki barta anan inhar zargina gaskiyane komai Nisan dare gari ze waye Kar dad'in Hira ya debeki ki gayama Ma'u nasan surutun ki...... Hafeeza murmushi tayi Tana cewa "haba mama babu meji , ALLAH ya shiryeta. "Amin" Inji mama, Washe gari hafeeza taje gidan su ma'un ta gaishe da baba,humaira da mama habee nata hararar ta, Jin baba bece Mata komai ba sai ita tace Mai "baba har yanzu shiru labarin Ma'u ko? Sai baba yace "eh hafiza Amman da yadda ALLAH jikina na bani nakusa tozali da ita insha ALLAH tana hannu nagari yadda zuciyata take min shakku akanta yanzu Sam na samu nutsuwa, Hafeeza "toh baba Nima Ina ganin insha ALLAH ta kusa juyo mu" Baba "hafiza yaushe Kika dawo? Hafeeza "jiya baba Ina dawowa mama take bani labari har zuwanku gidan nemanta shine nazo naji ko ta dawo Ashe haryanzu" Baba "eh har yanzu Amman muna cigaba da nemanta insha ALLAH" Hafeeza Tama baba sallama ta fice..... Kafin hafeeza ta wuce gida sai da taje gidan hajiya babba ,Tana zuwa suka gaisa mumcy nata murnar ganinta ,har take sanar mata da Abin da ya faru ga FU'AD da Ma'u har ta tabbatar mata da sun kusa dawowa insha ALLAH. Labarin Yama hafeeza dad'i sosai ,da murna tabar gidan. Bayan hafeeza ta koma take ba mama labari mama taji dad'in yadda sukasan inda husnan take.... Maman ce take ma hafeeza magana Akan neman Aiki idan sakamakon ya fito na diploma da tayi in Kuma *RIK'ON KWARYA* Da taba Ma'u zata karb'a toh? Hafeeza "ahaba mama bawai girman Kai ba ,Amman gwanda na samu wani Abin da Zan dogara dashi ,ita Kuma Ma'u Ina Mata fatan wajen ya zama sanadin share hawayen kukan da ta jima tanayi Wanda hakan ya bayyana insha ALLAH. Mama ta Mata fatan samun abinyi .... Sanaya tun Bayan faruwar Abin da ya Shiga tsakanin ta da me sanyinta wani lokaci sai taji Tana son sake kad'aituwa dashi Abin na dawo Mata har ta rasa yadda zatayi Musamman yanzu da ta dawo 9ja gashi FU'AD Bata d'auke shi kokai ba da ko dashi ta rage zafi Amman Tana sha'awar kyan shi da kwarjinin shi Dan intace be had'uba ma tayi k'arya gashi Abin ya Fara cin k'arfinta.... ********** FU'AD tun barin su gidan su Husna kingkhan yake Mai nasiha da gyara kuren shi ta hanyar nunama matarshi kulawa da so da k'auna , FU'AD nata kawo nashi hujjan Wanda bazasu karbu ba da kingkhan yaji hauashi ma tafiya yayi yabarshi. FU'AD komawa yayi hotel ,be jima ba Yaya Jameel ya kirashi a waya Yana jadada Mai karfa ya aikata ba daidai ba Akan Husna yayi k'ok'arin sanin kimar matarshi Kar ya cigaba da nuna Halin ko in kula irin na da,duk cewa Toh kawai FU'AD yake..... Bayan FU'AD yayi bacci ya tashi ,yaji gaba d'aya ya gaji da India gashi ya kasa Shawo Kan Husna Kuma bayajin ze iya tafiya yabarta a india Dan Haka yayi shawara da zuciyar shi Akan gobe ze koma gidan aunty huwaila yayi magana da mijinta baban wanan wawan da yake sa matar mutane farin ciki wato Affan. A dadafe FU'AD ya kwana yanata burin ganin wayewar gari yaje ya kashe boss din shi da Husna.... Husna ko shiri Bata Fara ba sai aunty huwaila cema take tayata shiri ta had'a Mata kayanta da wasu abubuwan da zata buk'ata.... FU'AD na zuwa gidan aunty huwaila be Bari yayi tozali da kowa ba ya nemi ganin megidan ,ba'a jimaba kuwa yamai iso ,Bayan FU'AD ya gaishe shi ya Fara zuwa Mai da buk'atar shi Akan tafiya da Husna Dan wani Abu yazo Mai na gagawa a company d'in shi." Abban su Affan "toh babu matsala ai Babu Abin da ya rage da ya wuce ta wuce ku tafi ,sai dai inaso na Kara tunama matsayin Amana take a gareka Dan tunda ka aureta take Amana agareta Ina nufin Kar ka sake Wasa da damar ka yanzu ma badan na lura na Kuma yadda da irin son da kake Mata ba da bazata koma ba Dan zuwanta dinan har ta samu Mai sonta tun kafin ya tunkareta da maganar akace Mai tanada miji Dan ko ita har yau batasan maganar ba." FU'AD "hmmm wai ya lura da son da nake mata waya gayama inason ta? Kuma baze wuce munafikin d'anka bane yake sonta mayen Mata kawai ya zama Dole tabar gidan ma kodan shi.....Yana mita cikin zuciyan shi. Bud'ar bakin FU'AD sai yace "za'a kiyaye faruwar hakan agaba insha ALLAH ,yanzu dai nafison kasa min ranar da zanzo na d'auketa mu tafi Dan Kar nayi asarar abubuwa da dama saboda jiranta sanan Kuma kaga har yanzu hankalin baban ta atashe yake sakamakon baida labarin ansan inda take ,nafison na surprising d'in shi yadda Zan maye gurbin damuwar shi ta baya da farinciki in ya ganta a zahiri ba wai_wai ba. Sai ko Abba yace "hakan ma kayi tunani mekyau kodan hakan bazan Bari Abin ya sake d'aukan kwanaki ba kamar yaushe kake ganin zaku tafi? Da sauri da zumud'i FU'AD yace "ko jibi ma Gobe ta gama komai jibi sai nazo mu tafi,dad'in June bayanan Abba FU'AD har number shi ya karb'a yamai godiya,Yana cewa ze iirashi yaji yadda ake ciki ya tafi batare da yasa husnan a idon shi ba duk ta idanun shi nason ganin ta Amman ya Hana zuciyar shi. Aranar da daddaren ranar Abban su Affan ya Kira Husna ya Bata umarnin shiryawa zuwa gobe Dan jibi mijinta zezo su tafi kodan a cirema babanta shakku asaka Mai farin ciki be tsaya jin Abin da zatace ba ya maye gurbin kukan da take Shirin yi da yi Mata Addu'a da shima Auren su Albarka.... *Sharhin ku nasani nishad'i*💃🏼🌹💃🏼 *Addu'o'e Kuna karamin k'aimi Ina godiya*👏🏼😍 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg59 Bayan Husna ta karbi maganan Abban su Affan Abin be Zo Mata a yadda taso ba Amman ya ta iya Dole tamusu biyayya shida aunty huwaila ,Amman taci Alwashin tsatsafema FU'AD aduk lokacin da yaso wulakanta ta ko cin zarafinta Dan ta Gama jurema tozarcin shi." Sosai Husna ta fara Shirin tafiya 9ja duk da asanyaye takeyi Babu kwari a jikinta ,su muhibbat ne ke tayata had'a kayan." Ranar Affan y d'auketa da su Husna k'arama y dinga yawo dasu a stores Dan ta zab'i Abin da takeso ,iya gata ya nuna Mata ita Yar gata ce ,Amman duk Abin da FU'AD yake Mata Tana zargin kamar Yana son tane ,itako Bata tabajin Koda sata iya son shi ba Dan so Tana son Affan batasan Tana son Shiba sai da tayi nesa dashi ada Tana tunanin yafi k'arfin ta sai daga baya ta gane Ashe shine daidai da ita Dan asoyayya Babu fin karfi ko Dan so d'ayane Tak yakan Burma duk zuciyar da yaso asanda yaso kamar yadda son FU'AD y afka Mata duk da Tana zargin shi din cushenta akamai ,Amman ayanzu ko ya yadda ko yaki yacigaba da girman kansa da izzar sa ,tasani Kuma ta amince Yana sonta ko ya Fara sonta Koda ace Dole aka Mai kuwa ,inko har haka lokaci yayi da inhar ya bada Kai bori ze hau Dan ita zata zama borin a nuna Mai kulawa inhar shima ya amince Yana sonta Kuma Yana nuna Mata kulawar. Bayan Husna ta gama dogo zuzurfan tunani komawa tayi wajen Yaya Mata lafiya Tana kare Mata kallo Tana kewan sunzo tare zata tafi ta barta gashi Tana Jin ta kamar want sashin jikinta ,kallon be Mata ba ta matsa kusa da ita ta d'auki wayarta ta dinga masu selfei ,matar kamar ta sani sosai ta tsaya akayi hoton Kuma ta fito d'od'ar ,Husna Tana kalla Tana Jin dad'i har muhibbat tazo ta same su itama ta Shiga akayi hoton da ita ,har Husna tace yauwa "bani phone d'inki na tura pics d'in da mukayi a fitar da mukayi , muhibbat mik'a Mata tayi ta tutura suka d'ora da Hira har aunty huwaila tazo ta same su itama akayi hoton da ita daga baya ta zauna aka Fara hirar da ita itama ,matar kamar zatayi magana sai ta kasa sosai abun yaba su husna mamaki har suka Mata rumfa sunata tofa Mata Addu'o'e ,duk yunk'urinta da son tayi magana gashi a zahiri magana takeson yi Amman Abu yaci tura Dole ta hak'ura ta fashe musu da kuka Mara sauti...... FU'AD ko ji yake ya Gama da case d'in Husna Dan ya Mata Dole ,Dan Haka hankalin shi yad'an kwanta har ya Fara waya company shi Akan ya kusa dawowa ,ya Kira mumcy ya sanar Mata jibi zasu dawo , mumcy nata musu fatan isowa lafiya ,sanan tamai umarni da ya Kira sanaya ma ya sanar Mata zeyi gardama mumcy ta dakatar dashi Dole yace "toh" FU'AD Kiran sanaya yayi ,ya Saba sai ya Mata Kira biyu kafin ta d'aga Amman yau Kira 1 ta d'aga beyi mamaki ba ,suka gaisa ta tambayeshi yaushe ze dawo ,ya sanar Mata jibi ,tace "ALLAH y dawo daku lafiya" yace "Amin " Kafin ya kashe wayar sai da ya tambayeta "ko kinada Abin buk'ata a India? Sanaya "a komai kawai Mai kyau da Aminci Wanda ya Dace Dani ka taho min dashi ,in kasiyo Wanda be min din bama babu damuwa Zan iya kyauta dashi Dan ra'ayin mu ba lalai yazo d'aya ba nasani" FU'AD har zece wani Abu sai ya fasa yace Mata "toh hakima" be tsaya jin me zatace ba ya kashe wayar y fita siyo Mata Abin da yaga ze iya har Husna ma.... ********** Sanaya sosai take cikin buk'atuwa dacan da wani Abu be tab'a Shiga tsakanin ta da wani d'a namiji ba Bata da matsala Amman yanzu tun da taji maza duk da bama iya tantancewa tayi ba Amman Tana son sake Jin ya Abin yake ne gashi batason had'a jiki da wani ,sai zuciyar ta tabata shawarar ai Babu Wanda ze iya Mata wanan aikin sai Fu'ad cikaken namiji Mai kwarjini kanarsa inhar Bata amfana dashi a lokacin buk'atuwar ta ba kafin su rabu ta koma ta auri Wanda takeso sai yaushe? Aiko ta mutu da yunwa kawai kiyi Amfani da damarki kafin ta guje Miki ,atake ta amshi shawarar zuciyarta Amman ta wacce hanya? Wani dogon tunani tayi kafin ta d'auko wayar ta ta duba sunan wani magani ta Fara tambayan inda zata samu through online ....... Husna ta Gama shiri tsaf babu Abin da takeso sai ganin babanta Amman ba wai Dan ta koma gidan FU'AD d'in ba ,sosai FU'AD d sadeeq suka cikata da abun arziki Bayan sun Mata Al'k'awarin duk wani buk'atun ta kartaji d'ar wajen sanar musu. Sosai Husna ta musu godiya harda kuka , muhibbat ce to dinga share Mata hawaye Tana nuna Mata ai sun zama d'aya ,yauce ranarta ta k'arshe a india har se in ALLAH ya sake kawota ,Dan Haka kukanta ya sake k'arfi ,su duk sun zata kukan rabuwane ,ranar Affan d sadeeq ko Aiki Basu fita ba ganin Husna duk a takure sai suketa d'ebe Mata kewa da kutsawa cikin walwalarta har suka d'auketa suka fita harda aunty huwaila akafita yau dasu husna sunata zagaye gari Dan su saka Mata farin ciki Dan ta bark'asar batare da wani baccin Rai a zuciyarta ba.... FU'AD ma ya Gama shiri Dan har ji yake kamar yaje gidan Dan ya tabbatar Husna bazata bijirema tafiyar ba ? Amman tunawa da cewa abban ba k'aramin mutum bane Kuma sunyi waya Akan insha ALLAH tafiyar Tana Nan da yazo zasu tafi shi yisa ya d'an hak'ura Amman yanason zuwa yaji daga bakinta Kuma Yana tsoron ballo liki Dan yasan kusan Dole aka Mata." Su Husna ba'a dawo ba sai yamma lis Dan sai da abban su Affan ya dawo ya kirasu a waya yace "ya dawo" sanan aunty huwaila ta bashi hak'uri tace "sun fita da Husna ne Amman yayi hak'uri gasunan zuwa" Bayan sun dawo gida still suna parlour anata Hira Ana dariya cikin raha da k'aunar juna tuni Husna ta manta da komai Amman lokaci zuwa lokaci Tana tashi taje d'akin matar Nan Tana dubawa sai taga tanata bacci....... Har dare babu Wanda ya tafi kwanciya tun aunty huwaila d Abban su Affan na kyale su suna cewa suna Taya Husna Raya Daren Ne har suka ga Abin nasu bana sauki bane suka musu magana suna nuna musu ko Husna ta tafi Akwai waya fa ba rabuwa akayi ba Kuma baza'a rabu ba Ni nayi muku Al'k'awarin Husna zata kawo muku ziyara inhar na samu amincewar mijinta FU'AD zatazo kusake ganinta itama ta ganku hakan ya muku? Duk sukace "yes our dady" Musamman Husna k'arama da ta rungume Husna babbah suna dariya da murna sosai Abin ya birge su Dan sun saka musu farin ciki aransu yanzunan uban su Affan kenan Wanda ya iya tafiyar da iyalin shi." Sanan suka tashi kowa ya tafi makwancin shi ,husna d muhibbat d Husna small d'akin su guda Hira suka sake kafawa raba dare sukayi suna hirar rabuwa. FU'AD ma kusan a matse yake ,burin shi kawai yaga Gobe tayi yaje ya d'auki Husna ya kaima su mumcy d baba ita ya Shiga harkokin office d'in shi. Washe gari FU'AD da wuri ya tashi yayi sallah asubahi ya shirya cikin shigan suit Mai tsada da tsari dama ya Gama had'a kayan shi komai ya musu buking flight d Husna Dan jirgin safe zasu bi...... Su Husna Kam tun tashin ta da asuba tayi sallah tayi Addu'o'e ta tasake koma Dan ji take tafiyar kamar ba gaske bane ,su muhibbat ma suka rufa Mata baya Dan dama baccin ba isarsu yayi ba.... Da gari yad'an waye ne har masu Aiki sun Gama breakfast Ana Shirin taso su husba,sai wayar Abban su Affan ta d'au k'ara ganin sunan FU'AD ya bayyana Abban y d'aga ya mishi sallama ,shima ya amsa Mai ,yake sanar dashi lokacin da jirgin su ze tashi Dan asanar ma Husna, Shi Kuma ze Zo kafin lokaci Ana sauran awa daya da rabi. Abban Affan d'in yace Mai" toh sai kazo kafin lokacin ta Gama insha ALLAH" FU'AD yamai godiya ya kashe waya....yanaso ya koma bacci Amman ji yake kamar inya koma ze makara ko husna zata guje Mai." Abban su Affan ne ya tura Ammin su Affan ta taso su don suyi break su samu suyi wanka su shirya da wuri Kar yazo Yana jiranta Dan tafiya ita takeda Kai bakaine da ita ba. Ammin cewa tayi "toh" ta tafi d'akin su muhibbat ta Shiga bakinta d'auke da sallama.... Husna k'arama ce ta Fara farkawa sanan muhibbat Husna babba kuwa bil'hakki baccin ta takeyi ji tayi kamar karta tasheta ,Amman ya zama Dole ta taso ta kodan ta samu ta shirts a tsanake." Bayan ta tashe su , brush suka farayi suka wuce dining Dan break Koda suka Isa sun samu su Affan da sadeeq sun Fara cin abincin su. Husna ce to Fara gaishe da Abba har k'asa, sanan muhibbat sai Husna auta ,sanan suka gaishe da Ammin su sai suka koma Kan su Affan ,cike da walwala suka amsa musu suna masu sakar musu fara'a." Suna karyawa suna Hira cike da nishad'i har da tsokanar muhibbat sadeeq yakeyi , bayan sun Gama Husna ta tambayi Ammi Ina abincin Yaya? Mara lafiyan nan,sai Ammin tace " pretty ta Kai Mata tun d'azu nace ta kula da ita har ta cinye kinsan yansu Bata son cin abinci sosai Amman inda kulawar wani a wajen takanci da yawa Musamman ma inkece a wajenta. Murmushi Husna tayi tace "barin duba su na gani" har ta Mike zata tafi sai Abba yace "yauwa Husna kiyi k'ok'arin shiryawa da wuri kinsan jirgin safe zakubi Dan ALLAH Kar ki Bari yazo Yana jiranki nasan Shirin ku na Mata sai ahankali tun yanzu ki Fara shiryawa saura awa 4 yazo ku tafi kinji? Husna tsayawa tayi ,Bayan ta Gama sauraron Abin da abban ya sanar Mata tace "to Abba insha ALLAH" cikin ranta tanajin kamar tace ta fasa ko ta saka ihu" Bayan ta amsa ta tafi cikin kamala sadeeq da Affan na yabawa da biyayya irin ta husna ga mahaifin su.... Husna na Shiga ta samu Ana ta rarashin ta akan ta cinye abincin ko tea d'in ma Tasha ,Husna ce ta karbi cup d'in tea Tana Mata magana cikin nutsuwa Tana Bata tana Sha har ta shanye har abincin ma taci yafi rabi ,Abin mama yaba pretty ma..... Bayan awa 3 su Kowa na parlour anata Hira sai ga Aike ya iso wai FU'AD Yana sallama a d'ayan falon da suka fi had'uwa su zauna ,sai Abban yace ace Mai ya shigo Nan duk suna Nan ...... Ba'ajima ba aka Mai iso zuwa inda suke Husna ko agogon wayarta ta duba taga ai da sauran awa 2 kafin tafiyar su kamar yadda fad'ama Abba,Amman meya kawo shi yanzu? Bata Gama tunani ba har FU'AD ya shigo bakin shi d'auke da sallama ,Affan da sadeeq sunata Mai sannu da zuwa kowa na bashi wajen zama , FU'AD yaki tayin Affan ya wuce wajen sadeeq ya zauna ya Fara gaishe da Ammi.... Bayan sun Gama gaisawa kowa ma ya gaisa da FU'AD Banda Husna sai da Ammin ta Mata kallon tuhuma sanan tace " barka da zuwa" fuska a sake d fara'a Dole ta ganin idon su Abba yace "yauwa Husna dafatan kin Gama shiryawa ko? Husna sai cewa tayi "eh Amman bamuyi wuri ba yanzu? Naga da sauran lokaci... Sai FU'AD yace hakane ,Amman Kinga lokaci shi baya jira sai dai a jirashi yanzu ko zuwana har naci Rabin awa Kinga kafin ki fito yanzu mu tafi har da isarmu maybe mucinye awa 1 Kinga kuwa befi muyi zaman 30mnts ba." Abba ne yace eh hakane lissafin FU'AD hakane jeki ki fito gasu yayanki Affan Nan har can zesu rakaku.... Husna Bata da zab'i fakar idon kowa tayi ta harari FU'AD ,ya ganta sarai Amman ya basar a zuciyar shi Yana cewa hmm yarinya Zaki gane ne... Husna k'ara gyara kanta da fuskar ta tayi tare da taimakon muhibbat ta Mata kwaliya simple bawai Dan husnan Bata iyaba sai Dan kawai Dan ta birgeta sosai Husna ta k'ara fitowa tayi masifar kyau komai nata ya cika ta goge ta k'ara wayewa ba yadda za'ayi kace waccan ma'un ce ko Husna da Dan sosai india ta karb'eta. Sai da muhibbat ta Gama kasheta da hotuna kafin suka fito muhibbat ta dinga fito Mata da Kaya tare da taimakon Manisha harimar gidan ,itako Husna wucewa yayi d'akin Yaya ta rungumeta Tana son yin kuka Tana cewa "Zan tafi na barki Amman Zan cigaba da Miki Addu'a samun lafiya Ina kewarki nasan shakuwar mu abune min indillahi ,itama k'ank'ame Husna tayi kwalla na fito mata.... Sallama huwaila sukaji ,da sauri tayi wajen su muryarta na rawa takeba kowanen su hak'uri Tana janye Husna da kyar tayi nasarar rabasu da juna tayi waje da husna... Sai da Husna ta sake komawa d'aki ta gyara fuskarta sanan suka fito da Husna k'arama da take manne da ita." Bayan sun fito sai da FU'AD yayi suman wucin gadi Dan gani yayi kamar ank'ara yimata halita gani yayi kamar anja komai har girma da kwarjini ta k'ara yimai ganin zuciyar shi nason tonamai asiri da sauri ya k'aryata ta har da d'auke kanshi duk da ya kwad'aitu da sake son kallon ta. Husna gaban Abba d aunty huwaila taje tanata musu godiya ,aunty huwaila ta d'agata Tana cewa itama yarsuce d'aya suke da Affan muhibbat Dan Haka karta sake cewa komai , ALLAH ya Mata Albarka taje su tafi ,shima Abba Addu'a ya musu ita da FU'AD d Addu'a sauka lafiya .... Bayan angama fita da komai na Husna sai Abba yace zasu biya ta hotel d'in FU'AD ya sauka ze d'ibi kayan shi sai su wuce Airport ,toh sadeeq yace. Husna kuka tasa aunty huwaila ma kukan takeson yi Abba ya janyeta suka koma ciki... Affan na kusa da driver sai sadeeq da FU'AD a tsakiya sai su Husna da Husna da muhibbat a baya ,har hotel aka Isa d taimakon ma'aikatan hotel d'in da driver har d sadeeq suka saka kayan a boot d'in motan Dan Affan ba sosai yake shigema FU'AD ba Dan ya lura da zafin kishin da yake d'iban shi akan Husna ya Kuma cancanci yayi hakan Dan Husna ta dabance shi yisa baya shige Mai shima. Basu jimaba suka Isa Airport ,suka iso a daidai jirgin da zasu hau ya kusa tashi saura minti 20 Dan Haka su Husna da muhibbat anata bankwana harda kukansu da hawaye sai da Affan ya musu magana suka d'an saurara , sadeeq ya janye su muhibbat zuwa mota Bayan sun yi sallama da FU'AD .. Shima Affan sallama sukayi da Husna yanata rarashin ta Fu'ad ya Gama cika , Affan ne ya mik'a Mai hannu yamai sallama, adole FU'AD ya bashi hannu Yana cin magani ,sai Affan yace haba abokina sai kace kububuwa wanan irin tashi sama Haka? Ai komai yazo k'arshe ,kasana ranka sallama ,Kuna k'anwata Amana gata Nan ,in ka kasa rik'e amana sai kaba masu rik'ewa waje na barka lafiya,Affan ya wuce yabar FU'AD na huci yaso mayar Mai da martani wayarsa ce ta dakatar dashi har Affan ya b'ace Mai... Bayan ya Gama amsa wayar mumcy ya sanar Mata suna hanya har mumcy taba sanaya wayar sukayi magana da FU'AD ,itama yace suna hanya sai ko sanaya ta mayarma mumcy wayarta ta koma sashinta da kyakyawan shiri Dan ayanzu Abin da takeji yafi na ko yaushe ma." Umarta Husna FU'AD yayi da su Shiga jirgin ,toh kawai tace Mai ta d'auke kanta..... Bayan sun Shiga sun zauna ga kujerar ta gata FU'AD , FU'AD nata kallon ta ,har Husna ta gaji ,tace "ya da kallo mallam ko naji ma bashi ne? Sai ko FU'AD ya saki wani kasalallen murmushi yace "kwarai kuwa Kuma Zaki biya soon Mara kunya Mai Hali ai baya fasa Halin shi" Suna Haka aka sanar musu da jirgi ze tashi ,yako tashi ya Lula sarararin subuhana inda ya harba k'asata tagado Nigeria Abin Alfahari na.......... Wash!🤦🏼‍♀ 😍😍 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* (Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg60 *Wanan Pg d'in sadaukarwa ne ga masoyan RIK'ON KWARYA Musamman 'yan RIK'ON KWARYA FANC*..........😍😍😍😍😍😍😍😍😍 Gidan mumcy ko Ina ya d'au gyara da kamshi Musamman mumcy tasa aka gyarama Husna samanta aka feshe da fresheners masu dad'in kamshi masu wajen kawai ake jira.... Sanaya ma t Gama shirinta tsaf da duk wani abun da takeson aikatawa Dan hak'urinta ya k'ure da Tana mamakin kanta da kanta sai taga ai she's mature.dan ta buk'ata ba laifi bane Tama yi hakuri over. Around 2:45pm jirgin su FU'AD y landing a Aminu Kano Airport. Suna fitowa FU'AD ya Kira mumcy yace "sun iso a turo driver d wuri ya d'auke su" Mumcy da murna tasa driver ya tafi d'auko su,taba su Harri umarnin cika musu dining da kayan da aka girka domin su. Driver na Isa ya hango FU'AD a gefe da alamun ya Fara k'osawa da jiran ,da sauri ya k'arasa Yana cewa"Afuwan yallab'ai Ana fad'amin wallahi komai banyi ba na taho d'aukan ka affuwan Dan....... Be k'arasa ba FU'AD yace"ba wani Abu kwashi jakankunan Nan muje,ya juya Yana cema Husna "taso muta tafi malalaciya kamar akafa kikazo Naga kamar kin ga kamar kin gaji. Husna kallon shi tayi tace"bada kafa nazo ba Amman kasan nayi sammakon tashi ai? Kuma duk Kai kaja min. Sai driver yace"ah wai hajiyace ? Tab Amman india ta mugun karb'anki ai sai anyi da gaske ake sheda ki badan naji murya ba zata zanyi wata ce. Hararar shi FU'AD yayi cikin takaicin maganar shi yace "toh da ka zata wacece? Had'a kasa rabawa ko wani Auren kaji labarin na sake? Da sauri driver yace"a yallab'ai ko d'aya ai nasan su biyu ne kawai dai can dinne ya k'arb'eta..... Be k'arasa ba FU'AD yace"toh zabiyi muje in ka Gama,har ka San yadda take dah da yadda ta canza yanzu,muna zaune Kuna kalle Mana mata Kuna Gane janzawar su ya fad'a ciki_ciki Yana tafiya. [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg62 Kota FU'AD ya koma mumcy nason magana dashi be Bata attention d'in shi ba sai da ya l'ek'a Husna yaga baccinta takeyi bilhaki da gaskiya sanan ya dawo wajen mumcy. Mumcy fad'a ta Fara Mai Akan Husna Tana nuna Mai inyaci amanar ta ALLAH baze barshi ba sanan ya rik'e sanaya ma kowacce ya dinga Bata hakkin ta. FU'AD amsa Mata yayi Yana cewa "insha ALLAH" Har ya mik'e ze tafi mumcy tace "ka kiramin Husna Inka haura, FU'AD har ya amsa sai ya tuna a cikin condition d'in da ya barta sai yace "au namanta batajin dad'i Tama kwanta" Sosai mumcy ta gano kame_kame yakeyi ,sai cewa tayi"lafiyar ka kuwa auta yanzunan kamin magana biyu? Sai Fu'ad ya Sosa k'eya yace ai na manta ne wai kanta ne yake Mata ciwo shine na Bata magani Tasha ta kwanta Kuma ko yanzu da na koma baccin take yi. Sai mumcy tace "ka tabbata ka Bata magani son nasan halinka fa ko naje na Bata da kaina ko ka kiramin ita Nan ,ya d'aga dawowarta zata gara rashin lafiya batare da ta samu kulawa daga gareka ko Ni ba kafin kowa sanin irin wuyar da akaci kafin ta dawo. FU'AD da sauri ya Mata rantsuwa akan ya kula da ita Kuma ya Bata magani agaban shi Tasha. Mumcy ta yadda Dan ta Fara gano canji sosai atare dashi Akan Husna ,sai ta sake gwada shi tace "son Ni inaganin har yanzu baka Gama karban Husna matsayin Mata ba da namaka zab'i Dan Haka Gobe da kaina zan kaita gidan su tad'an zauna na wani lokaci inyaso in ka yadda da ita a matsayin matar ka da zaka iya Rayuwa da ita ko Bayan babu Raina kaje ka dawo da ita inbaka karbeta ba sai ka barta gidan su nasan bazata Rasa Darin masoya masu son Auren ........sai ko FU'AD ya zabura ya ma mumcy wani mugun kallo me gad'e da tuhuma irin me kike cewa? D'inan" Yana cewa haba mumcy ai kodan zuwanki gidan da Kuma dawo da ita da aka Bari nayi ta dalilin ki da Abin d ya faru a baya ai na karb'i auren kodan ranki yayi fari. Mumcy murmushi tayi a zuciyarta ita kanta tanason dasama d'an nata wani Abu azuciyar shi na k'aunar husnan Dan Haka ta rutsashi yanzu Dan Fara yimai gwajin farko da alama ze cinye Amman yak'i bin hanyar da ta Dace,sai tace Mai"au Dan farin cikina ne ma Banda Kai? Dan Haka nace Zan mayar ma da babanta ita gobe tashi ka tafi mun Gama maganar. FU'AD cewa yayi "haba mumcy ki fahimce Ni Dan ALLAH ki saurare Ni ,in Kika barta a gidan Nan kinsan kasheta matsiyaciya Mata Nan zatayi haka kike so? Mumcy cewa tayi "nasan babu me kasheta babanta na Raye sanan Kuma bazata Rasa me aurenta ba Dan masoya zatayi kodan kyawawan d'abi'un ta uwa uba tarbiya da iya mu'amala da mutane. FU'AD da rawar Baki yace "me kike fad'ane mumcy ? Da aurena na fa akanta kike had'ata da wasu kartin mazan da ba'asan ma ko suwaye ba haba mumcy Abin da wani zeyi amai hukunci kikeyi da kanki? Mumcy cewa tayi "eh Nima ai ban wuce hukuncin ba a wajen ko waye ,sanan kaima fa kaji Abin da kace ,sanan har yanzu baka amsamin ba kana nunawa kamar adole kake zaune da ita irin babu so ko k'auna tsakanin ka da ita d'inan na jima Ina sane da wanan abun kyaleka kawai nakeyi ,yanzu ko bazan zuba Ido hakan yaci gaba da gudana ba... FU'AD zeyi magana mumcy ta dakatar dashi "kawai kaje Abin ka na Gama iya maganar da Zan fad'a gibo Husna sai gaban babanta kad'ai sanni Akwai fad'a da cikawa. Duk yadda FU'AD yaso Yama mumcy bayani Taki sauraran shi Dole ya hak'ura ranshi babu d'adi ya haura saman da niyar tashin ta Dan yamma tayi sosai. Bayan FU'AD ya shigo ya Kai kusan minti 5 kafin yad'an bubuga gefen gadon ahankali Yana Kiran sunan ta. Husna da Addu'a ta farka a bakinta ,Tana bud'e ido taga FU'AD ta had'e Rai ta wurge shi da harara. Husna "me kazo yi d'akina Kuma? Inji ta. FU'AD "tashin ki Dan yamma tayi sosai yanzu zakiji Ana Kiran sallah magrib.inji Fu'ad Husna"toh naji" Injita ta d'auke kanta daga kallon shi. FU'AD tashi yayi har yaje bakin k'ofa yace "ya zazzabin naki muje asibitin ko kinji sauki? Husna kamar bazata amsa ba sai can tace "da saukin musulunci dai" FU'AD "har yanzu dai kenan in munyi sallah maje asibitin" Inji shi. Husna ,babu inda zani fa sai gidan babana Kuma Inna tafi ba tare zamu dawo ba Dan ma ka sani. FU'AD a sukwane ya juyo ya kalleta ,sai yace hmmmm naji Amman mu Bari Bayan sallah isha'i maje ko muna idar da sallar inkin k'ara Shan maganin ki. Husna "toh " tace kawai. Bayan FU'AD ya fita d'akin shi ya koma yanata tunanin hirar su da mumy ga Abin da Husna tace Mai itama. Dan Haka kawai ya yanke shawarar ya Kira likita ko maganin bacci ya bashi Dan tayi bacci Akan da tayi sallah bacci yayi gaba da ita Dan Kar suje gidan har sai gobe inta sake samun karfi ajikinta. Dr tambayoyi yamai Akan dalilin shi na so ya Bata maganin bacci bada sanin ta ba ,karya FU'AD yamai Dan yace baze Gaya Mai sirrin shi ba ,Dan Haka Dr ya hanashi ya bashi shawara , FU'AD yaji ya hak'ura da kudirin shi. Yana zaune ya dinga tunani Akan mafita ,can sai ya tuno da abokin cin mushen shi wato Wanda suka Saba tsiya da dad'i ,ya kirashi a waya Yana D'agawa ya Fara tsokanar shi aggo_ aggo kasha k'amshin. Sai FU'AD yayi tsaki kaifa banza ne wallahi Zan kashe wayata,sai B2k yace toh kashe Mana base nazo gidan ba dama ai zuwa da Kai yafi sako. FU'AD sai cewa yayi Dan iss_iss dallah ka zama mutum muyi magana Akan Abin da ya kunno min Kai a yanzu.... FU'AD komai ya kwashe ya gayama B2k sai k'alilan da ya rage. "hmmm abokina kace aruwa kake Amman Bari na taimaka ma kafita da kanka,Inji b2k. Da kabari Gobe Tama da zuwan da kace zaka kaita da kanka da cewar mumcy zata kaita da kanta ,masalaha da shawara gwanda ka kaita Daren yau hakan ze faranta ranta ita amaryar Dan yau amarya Zan kirata tunda kaci wasan,sai FU'AD yace zaka Fara ko? Bani da ikon yin magana ta serious da Kai Koh? "A abokina Dole Zan Dan d'ana kaima ka sani ,Amman maganar gaskiya kuje yau k'asata farin ciki da mayaifinta sanan kaima zaka samu nutsuwa ta bangarenta ,ita Kuna mumcy ka barni da ita gobe ai kana gida ko zanzo sai mu k'arasa aikin da Kai ba inda zata da ita Bari sai nazo zaka gani. FU'AD sai cewa yayi toh ,Amman kar kazo da wuri nasanka da sammako kamar me Kama Fara,sai B2k yace "au Ni d'in ko? Na gide kana angwanci baka so zuwana ba ai nama fasa zuwan asha angwanci lafiya Husna Amarya kuma uwargida ayi amarci lafiya kabi Yar mutane a...... Be k'arasa ba FU'AD yace "munafikin ALLAH kaji da gulmar ka Kuma wallahi baka Isa kaki zuwa ba in kazo kamin iskanci kuma wallahi agaban mumcy da Husna zamu raba Abin fad'a. B2K cewa yayi "ai mun Saba indai agaban Husna ne ai da sauki ko kamanta in tuna ma? FU'AD sai cewa yayi "Kai dallah share Kai baka mantuwa ne ,lokaci ze bani damar Rama Abin da kake min fa. B2K sai cewa yayi ALLAH ya nuna Mana Kai inda na biyema ai da kowa ya Kama gaban shi ,wai Kaine yanzu har da neman shawara Akan mace? Macen ma Husna ....... Be k'arasa ba FU'AD yace "ya isheka Haka Kuma kayi na mutunci neman shawara be zama iskanci ko tone_tone ba ,Kai yanzu gani kayi na mutu akanta? Nafa Gaya maka duk yadda Abin ya faru ,Kar kamin fassara Kuma wallahi badan inajin tausayinta ba ko kallo Bata ishe Ni ba Dan Kar kaga k'ofa kace zaka zak'e da yawa. B2K cewa yayi hmmmm gaskiya fa sarkin taimako uban gajiyayu baya goya marayu me ubanma se ka goya ,zanga ranar da zaka amsa Dan wallahi adaidai wajen kake bansan wanne irin kafiya bane da Kai abokina Abu yes kawai ka tsaya kaki amsawa, I see fa sai fa su taimako taimakon ne ya kaika kogin tunani da ka Bari mumcy ta kaita gidan su gibe ai ,acan baza a Rasa Mai taimakon ta ba ai....... FU'AD cewa yayi kaifa mutumin banza ne ga kin yadda da Abin da na Gaya ma dallah Ni tafi kabar min kunena ya huta goben dai Ina juranka, B2k yace anki azo goben sai mumcy ta kaita kaje Biko Dan rainin wayo kawai sai ya kashe wayar. FU'AD wayar yabi da kallo ,Yana cewa Dan wulak'anci kamar shi ya kirani ,sake Kiran shi yayi amman B2k yaki D'agawa ,sai FU'AD yayi murmushi yace shegen Kaya Bayan nasan Kai nawajena ne Akwai fad'a da cikawa anjima mayi magana. FU'AD masallaci ya tafi yayi sallah ,Bayan ya idar ya dawo ya Sami mumcy a falo ,ya Mata sannu ze haura sama ,tace "ya Kira Husna taci abunci ,har yace "Bari ya d'iban Mata ya tafi Mata dashi" Sai mumcy tace "wai hanata sakkowa kayi ne ,ko Bata iya tafiyane da kafafun ta banfa Gane nufin ka ba? Jin mumcy na son ballo Mai Ruwa sai yace" toh barin kirata" FU'AD sama ya haura.... Yana Shiga ya Sami Husna ta idar da sallar Tana ninke sallaya ,sai yace "mumcy tace kizo kuci abinci" Husna yamutsa fuska tayi "Ni ko yunwa fa banaji nafison ganin baba da komai" Sai FU'AD yace nace zamu ai ko ke meyasa kikeda son maimaita magana ne? Husna kallon shi shi tayi Tana Shirin kuka tana cewa "toh fad'a zakamin sai in tafi wallahi Ni kad'ai kasan Zan aikata ko kana musu? FU'AD cewa yayi ,naji bance kimin kuka ba me arahar hawaye ,muje mumcy jira take Kar ta gaji ki taho da Shirin ki ,sai Husna tace "Ni nagana shiri na hijab zansa Dan sanyi nakeji har yanzu" Sai FU'AD yace "toh ki hak'ura zuwa gobe yau ga naci" Husna sai ku tace "Ni wallahi yau zani ko sarafi nakeyi" FU'AD cemata yayi "toh dakko mutafi da mungama sai mu tafi,sanan ki sani Naga kina wani Abu kamar wacce kwai ya fashema aciki ki karfafa kanki inba hakaba mumcy tasan Baki da lafiya bazata Bari na kaiki ba. Husna zaro ido tayi ta fada kujera jagwab Tana Shirin kuka . FU'AD har ya tsorata yace "meye hakan Kuma? Sai Husna tace "kace mumcy tasan bani da lafiya kamin mugunta ka kwashe kaje ka sanar Mata da wanne Ido ka iya kallon ta ka Gaya mata sanan Nima da wanne zata kalle Ni ,gaskiya namiji baida ta Ido....... Bata k'arasa ba FU'AD yace "ke karki yi b'arin zance ,Ni ban nemi dogon bayanin Abin da ya shud'e bisa kuskure ba ,ce mata nayi kanki na Miki ciwo kuma zakici tace Miki ya Kan naki,na fad'a Miki ne Dan Kar kiyi Abin da zata Gane zazzabi ne a jikin ki. Sanan Husna tayi ajiyar zuciya ,tana cewa "hmmmm ai da ka fad'a Mata mugun abun da kayi"Tana mik'ewa Tana gyara hijabin ta. FU'AD murmushin Dole yayi Yana cewa kuji kuri ,yanzu ai sai ki Gaya Mata in munje ,sai Husna tace "Ni nayi ? Sai FU'AD yace "wayi sani Abu duhu" Husna cewa tayi hmmmmm ai ALLAH ze saka min. FU'AD cewa yayi "bazaki Dena fad'an Haka ba ko? Kinsan kina aikata zunubi ai ko? Sai Husna tace "eh ai bani kad'ai ce nayi zunubin ba Kaine me babban zunubi ma ai" FU'AD yace "da na aikata me? Husna "da ka aikata Abin da ka aikata min" FU'AD "hmmmmm" kawai yace,sanan yace kizo mu tafi nadai Gama Miki gargad'i inba Haka ba mumcy ta Hana fita. ALLAH sarki Husna ta yadda da zancen shi ,batasan kanshi yakeson gyarawa ba, Yana gaba taba baya har suka sauka. Husna wajen mumcy ta nufa ta zauna kusa da ita , mumcy na ta kallonta Tana cemata sannu Husna ya Kan? Husna tace "da sauki hajiya" Umarni mumcy taba wata me musu Aiki akan tazo ta zubama Husna abinci ,har FU'AD yake cewa nifa hajiya? Mumcy kallon shi tayi tace "wa yake takai" dariya me aikin tayi tace "mu muna tashi nasan Dan Asma'u Bata Jin dad'ine ma da ita zata zuba Mai. Bayan sun Gama ne FU'AD yayi ta maza yace mumcy Zan Kai Husna taga baba ki hankalin ta da nashi ze kwanta da ya Rasa yadda zeyi ya sanar Mata Kar tayi zargin shi ta shirya hakan. Mumcy ma tayi zargin Shirin shine kuwa ,sai tace ma Husna "wai haka Husna? Sai tace eh hajiya naso na Bari sai gobe sai Naga nakasa hakuri ,sai mumcy tace "bakiga bakya Jin Dadi ba? Sai Husna tace "ai da sauki Dan ya ragu sosai da FU'AD yaban magani Dan da dazu ne ma ko sakkowa bazan iya ba,Amman yanzu Alhamdullilah! Sai mumcy tace "toh a gaishe shi nana zamu sake komawa dake ai insha ALLAH. K'irjin FU'AD sai da ya bada daram,Amman be Bari mumcy ta gano shi ba ,sai ya mik'e Yana ce mata muje ko, mumcy sai mun dawo har Yana sakin fuskar Dole wai Dan mumcy tace ai ranshi yanaso ze kaita Kuma ya Fara canjawa. Bayan sun fita FU'AD na gaba Husna na biye dashi ita kanta tasan k'arfin Hali takeyi kuma rigima ce kawai Amman Dan Kar tabar FU'AD ya zauna lafiya shima kamar yadda yadda yadda hanata kwana lafiya a ranar da tazo 9ja shiyisa shima ta dage sai taje, tabbas ta San yanzu ya Fara damuwa da lamarinta koma tace ya Fara son ta Amman b'angaren shi har yanzu Akwai ragowar girman Kai Wanda takeson sauke Mai. Bayan sun Shiga mota FU'AD yace minti nawa Zan baki? Husna tace "kamar ya? FU'AD yace "kamar yadda kikaji na fad'a kinsan ba dadewa zamuyi ba ai Kuma kinji Abin da mumcy tace Kar mu Dade mu dawo ko? Sai Husna tace "to ai Ni nace ma acan zaka barni da ka Gaya Mata ai,sai FU'AD yace "meya hanaki ke ki Gaya Mata? Husna tace "toh ai Daman Kai zaka fad'a Mata" FU'AD cewa yayi "toh mu koma Mana ki sanar Mata waka abakin meshi zatafi d'ad'i ai ko? Husna turo Mai Baki tayi Tana cewa"ai Dan munriga mun fito ne muje mu dawo gobe na tafi Inna had'a kayana ma" sai FU'AD yace "au Ashe Abu gangan ne ko kayan ma babu yanzu Amman kike neman rigima hmmmm yarinta kenan" Husna hararar shi tayi tace "wallahi na wuce yarinya ka dubeni da kyau" FU'AD murmushi yayi ya jefeta da wani kallo samfirin harara a duhu Yana kunna mota yayi hanyar waje Dan tuni gate man ya bud'e Mai gate Yana cewa hmmmmm Ni kuwa nasan kin girma Amman lokacine ze sake tabbatar min da gaskiya" Husna cemai tayi "kamar Yaya? FU'AD cewa yayi "in Dan Hali ko lokaci yayi Zaki sani" Husna Bata sake cewa komai ba Dan Kiran FU'AD akayi a waya ya d'aga ,daga Jin wayar kasan abokanen aikin shine har Yana ce musu baze Zo office ba Gobe. Suna Isa FU'AD yace ki Shiga kafin komai kimin sallama da baban. Husna "toh" kawai tace ta fice Tana tafiya cikin nutsuwa. Sallama tayi a cikin gidan duk babu Wanda ya d'auki muryar ta sai haidar Dan da gudu yayi kutubar da tuwon dawar da yake mai cin Dole ya taso Yana cemata Yaya Ma'u...... Husna cemai tayi "haidar kanina" Rungume shi tayi shima Yana murna Yana tuhumar ta Ina taje tabarshi baya ganin ta? Mama habee da humaira mutuwar zaune sukayi Musamman mama habee. Husna k'arasa Shiga tayi duk da babu Wanda ya Bata izinin hakan Amman tasan ko bulon k'asa d'aya ne tanada gado agidan Dan Haka Tama kanta matsuguni. Husna Bata tsaya bi takan su ba sai cema haidar tayi "haidar baba fa? Haidar cemata yayi ,Yana masallaci tuwo yace nazo naci na koma ,Bari naje na Kira shi ,da sauri haidar ya tafi sai Husna tace "Zo ka wanke hannu kaji? Sai ya dawo ya tunjima hannun shi cikin tukunyar tuwon da aka kwashe aka jik'a da ruwan kwasan be tsaya ko Ina ba sai wajen baba a masallaci. Husna fita tayi ta samu FU'AD a cikin mota tace Mai "baba Yana masallaci Amman antafi Kiran shi,har zata tafi FU'AD yace "toh Amman kinsan kin Fara cin lokacin ki ko? Ki gajarta duk Abin da zakiyi Dan mu koma gida mumcy ta sake min waya wai kar mu dade. "Toh" kawai Husna tace Mai ta koma ciki. Bayan Husna ta shigo ta samu humaira nama mama habee gulmar wai da FU'AD muka zo har anleka angani. Husna zama tayi agefen tabarma ,tace "mama Ina wuni? Mama habee sai cewa tayi lafiya keko Ina Kika makale har aka dinga nemanki kikaso jazama mutane masifa da bala'i? Bud'ar bakin humaira dai cewa tayi ,Tana can yawon tazubar d'inta Mana bakiga ta cika ta tinbatsa ba waya sani ma ko ta kunso......... Bata k'arasa ba taji baba yace "shashasha wawiya wacce Bata iya kalami ba, bazanga wanan fatan ba yarinya Tana gidan mijnta tare da samun kulawar al'umma masoyanta na gaskiya. Humaira shiru tayi ta had'iye sauran maganar ta. Sai baba yace "ma'un baba yanzu Naga mijinki mun Fara magana dashi nace ya Bari na Shiga na fito Dan burina nayi tozali dake kawai ko hakan ze zama Abu na k'arshe a Rayuwata. Sai Husna ta saki murmushi Tana cewa ,aa baba insha ALLAH ba yanzu zaka mutu ba, baba Ina wuni? "Lafiya ma'un baba" Baba ya komai da komai da fatan komai lafiya baba? Eh Ma'u ko ba lafiya ba ai yanzu lafiya tunda ga ma'un baba tare da baba. Ashe kina wajen huwaila a k'asar India? Husna tace eh wallahi baba ai tun korata da sukayi na kirata na sanar Mata sai gashi tamin komai har muka Isa wajenta nida wata Mara lafiya. Baba cewa yayi Yar uwarta ce? Husna sai cewa tayi aa kamar yadda tace ai aunty huwaila tayi Nisa wallahi taimakon ta kawai tayi har yanzu Tana can Tana ta neman Mata magani acan. Baba yace" ALLAH sarki ai Akwai kirki halinta daban Dana kowa a d'akin su har hajiyar su" Mama habee sai zungurar Baki takeyi harda habaici. Husna ko sai Hira sukeyi da baba ,can baba yace "Ma'u Bari naje mu Gama gaisawa da yaron Nan Kar yace na nuna Mai 'yan ubanci. Mama habee sai cewa tayi ,yo na nawa Kuma ance da kuturu a Gama lafiya. Har baba ze tanka Mata sai Husna tace "Dan ALLAH baba kayi shiru" Sai humaira tace "munafuka Ina ruwanki manya na magana kinasa Baki" Baba ne yace "kece munafuka ai Kuma wallahi ki rik'e lisafi na kusa sadakar ki Dan ko kolo ko me kwalabe ne Baki zanyi lokaci nake jira Kisha mamaki. Can d'in batayi arahar Haka ba ,Inji mama habee. Baba be kulata ba ya fice ,sosai baba sukayi Hira da FU'AD haidar na mak'ale a hannun FU'AD yanata zuba Mai zance. Husna ko musayar kalamai suka dingayi da su humairan da mama habee na tare ma yarta ,Dan Husna tace ta Dena raga musu. Bayan baba ya shigo sukayi sallama da Husna ya dinga sa Mata Albarka Yana Mata Addu'a Yar mama habee taji haushi, har waje ya raka ta ,mama habee Tana cemai za'aje maulan ne Allazi wahidin? Dan tanan kafi kauri Dan Haka kayi cinikin ta ka dangin attajirai Amman kake kirarin ba kolo tawa Yar to da izinin ALLAH itama Mai danshin zata aura Wanda zeyi daidai da lokacin ka da ka d'ibar Mata uban hotiho. Husna taji ciwon Abin da mama take gayama baban Amman Dole ta hak'ura ta danne Dan ba fitina bane ya kawo ta gashi da FU'AD suke bare ta biye musu su raba Abin fad'a. Babayan baba ya rako su ya musu fatan Isa gida lafiya , FU'AD cema haidar yayi jibi ze dawo ya kawo Mai sweet's da su biscuits haidar ya dinga murna, FU'AD da Husna suka tafi ran Husna fal farinciki. *Maman shaheed ce*👌🏻 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg61 *Husna tace duk Bata gaishe ku Dan..............*🙊🤭🤣🤣 Mumcy na fitowa daga d'akinta taga sanaya ta shigo Fallon asukwane Dan ko zarafin sallama Bata samu ba. Mumcy Abin mamaki ya Bata yanayin da taga ta Shiga,Amman sai t cire shakku tace "lafiya sanaya? Sanaya babu kunya Dan a wani yanayi take Mara misaltuwa ,sai cewa tayi Fu'ad fa hajiya yasa injirashi ya Shanyi shine nazo naji ko lafiya? Sai mumcy tace ai ko Yana sama ya haura ya d'an ci abinci ya watsa Ruwa.... Atake ran sanaya ya sosu Bata tsaya mayar ma mumcy amsa ba sai ta haura saman Dan Ayi duk wacce za'ayi. Da ta haura sai ta Fara buga k'ofan bugu na rashin nutsuwa ,sai da tayi kusan so 5 ba'a bud'e ba kuma babu alamun za'a bud'en. Mumcy ce ta aika Harri Akan ta Kira sanaya ta sakko maybe ya kwanta ne Dan yace kwanciya zeyi. Ko da Harri ta isar da sak'on mumcy sai cewa tayi "toh naji muje" tanayi Tana hararar k'ofan Falon. Bayan sun sako ne , mumcy take cemata "yayi bacci fa tunda har kikaji shiru. Sanaya Rai a bacce tace "Amman sai ya shanya Ni ai ya kirani ko awaya ,Bata jira me mumcy zatace ba ta fice Tana hucci ta tafi d'aukan wayarta ta kirashi ko magiya tamai Dan ya fitar da ita daga sammatsin da take ciki in ba Haka ba komai na iya faruwa. Mumcy binta tayi da kallo Tana tunanin ko lafiya take yau? Mumcy batasan Tasha ya fi k'arfinta bane. Sanaya na Isa ta sungumi wayarta ta Fara dannama Fu'ad Kira sai da tamai Kira 8 be d'aga ba tayi jifa da wayar a kujera Tana Kama marar ta tana tsinema Fu'ad da Husna Tana cewa"uwar me sukeyi da sukaki bud'e k'ofa har da ita munafuka da ake ganinta Haka ,Aiko wallahi ze fuskanci fushina da rashin mutunci in ita ya juyewa had'ina Dan wallahi sai yasan yamin Haka Dan Isa banza da ya samu ma Zan rage zafi dashi inbadan inason sake jin yanayin baya ba mezanyi da wani FU'AD bare buk'atuwa dashi. Tana rik'e da mararta ta d'auki waya ta nufi d'aki ta fad'a gado ta Shiga social media ta Nemo blue film ta Fara gani Tana ragema kanta zafi ko ta samu ta samu sasauci ta dawo hayyacin ta , FU'AD da Husna Kam sun Sha tsinuwar Husna yau. FU'AD kasa had'a ido yayi da Husna ,Husna ko kuka kawai takeyi ji tayi ya sake tabbatar Mata da shi mugune yau atake ta karajin ta tsane shi , FU'AD dai Yama Rasa me zeyi kunya ce ta rufe shi da kokwanto yakeyi Anya shine kuwa? Ganin ga shi ga Husna a shimfida d'aya yasa ya gaskata ga wani kuka Mai cin Rai da takeyi ,yanaji sanaya ta dinga buga k'ofar yaki bud'ewa Dan ko mumcy ce baida kuzarin mikewa ya bud'e bare yasan sanaya ce. Haka Yana gani ta dinga jera Mai Kira shima yak'i D'agawa,ga kukan Husna har ranshi yakeji ,ba tare da ya juyo ya kalleta ba yace "kibar kukan Nan Haka Mana ni ya kamata nayi kuka bake ba" Husna da takaici da haushi suka d'ebeta tace "da na maka me? Ka kusa kashe Ni Amman kace Kar nayi kuka? Toh Bari nace wajen mumcy na sanar Mata sai ta bambance Mana Wanda ya fi dacewa da kukan...... Husna da kyar take motsi Amman k'arfin Hali ahaka ta Fara k'ok'arin sauka daga gadon zata tafi har ta zura kafarta bakin gadon ta sauke daya zata sauke ta biyun FU'AD ya fuzgota ta fad'o jikin shi Yana cewa "ke yanzu sai kije? Husna da gunjin kuka tace eh wallahi zuwa zanyi mugu kawai Kuma bar maka gidan Nan zanyi kasan wacce zaka dinga zalinta ......toshe Mata Baki yayi da hannu. Kiciniyar kwacewa takeyi Tana ka barni naje na Gaya Mata ,ya rik'eta ya matse a k'irjin shi ,ze sakko daga gadon ta samu ta kwace ta nufi k'ofa abinka da tafiyar Mara sauri har ta fita daga d'akin ya biyota ya kamota. Kwacewa taso yi Amman ta kasa ,sai kuka takeyi Tana dukan shi har da mintsini Amman ya matseta a k'irjin shi atake wani tausayinta ya dinga ratsa zuciyar shi sai ya Fara rarashinta Yana shafa Mata baya sosai yake Bata hak'uri da Al'k'awarin baze k'ara ba Kuma bada niya ya Mata ba inya sake ta fad'ama mumcy. Cikin kuka Husna tace "ka tabbata? FU'AD da sauri yace "eh indai Zaki daina kukan Amman" Bayan yayi fama da ban Baki da rarashi ya zaunar da ita a kujera sai ya Fara rarashinta ta Akan taje tayi wanka shima zeje yayi da kyar ya samu ya lalab'ata har ta yadda yadda yadda had'a Mata ruwan kusan kala biyu ma ,Bayan ya kaita d'akinta har bathroom d'in ya rakata Amman ya tsaya a bakin k'ofa......har ya juya ze tafi sai yace "kin iya wankan ko? Husna wata uwar harara ta wugo Mai da idon ta Mai cike da hawaye babu bakin magana FU'AD ya kashe shi. Hak'uri ya Bata yace "afito lafiya" FU'AD na Shiga d'akin shi ya wuce bathroom Yana jikin shower Yana tunanin aika_aikan da yayi ga wani kinyar yarinyar da yake lulub'e shi sai yaji inama kasa ta tsage ya shige. Iya tunanin shi da be gano musababin faruwar hakan ba ,sai da ya tuna da Abin da sanaya ta bashi Aiko ji yayi kamar ya fito yaje ya sameta yaci Mata mutunci ,Amman ya Adana rashin mutuncin da ze Mata zuwa wani lokaci Dan yanzu yafi son ya Gama rarashin Husna Dan har yanzu tausayi take bashi.... Husna ma wanka takeyi Amman tanata tunanin meya Sami FU'AD ko ya Fara shaye_shaye ne ? Dan kamar ba ahayyacin shi yake ba San da ya mata hakan. Dan Haka daman ya dinga nacin taho dani? Mugu kawai wallahi bazan Kuma yadda ka cutar dani haka ba ,dake yasan ya zalince ni ai har hak'uri ya dinga bani ya sauke girman Kan nashi Ashe karyar banza ne jinkan da kakeyi. Husna dai da tunani kala_kala ta samu tayi wankanta ta fito ta Fara murzama jikinta mayuka masu tsada da dad'in kamshi da turarukan jiki duk da tabajin jikinta babu kwari,ta d'auko wata atamfarta Mai kyau d'inkin Riga da skirt peach color tayi masifar kyau d'inkin ya karb'eta Bayan ta Gama shiryawa sai ta koma gadonta tayi kwanciyarta ta juya baya ta rufa da bargon dake gadon Dan ji tayi kamar zazzabine yakeson rufeta. Bayan FU'AD ya fito ya shirya cikin wata jalabiya Mai kwaliya da shek'i ,yanaso yaje ya duba Husna Yana tunanin da wanne Ido ze kalleta? Yarinyar da ya Raina yake d'aukanta kazama wai itace yau me afkuwa tasa ya afka Mata? Ta dalilin wanan Mara mutuncin Yar iskar da tanemi halaka shi ALLAH yasa ma akanta na tsaya ,itako me ze hadashi da ita tunda Abin da takeso kenan Aiko bazata taba samu awajen shi ba wawiya kawai waya sani ma ko ta Saba ne inba Haka ba ya mace zata buk'aci namiji? Banza maybe tayi irin Halin na wasun su masu zama a kasashen waje marasa ji irinta, inma tayi ita tasani,daga yanzu Kuma Zan dinga kiyaye duk Abin da ta bani insha ALLAH. Ganin zaman d'akin da tunanin ba shine yafi dacewa dashi ba ga Husna can besan Halin da take ciki ba yasha Jin labarin irin Haka in ta faru da abokanen shi wasu har sai andangana da asibiti ko Kiran likita toh shima ya kamata yasan ahalin da take ciki Dan nema Mata lafiya tunda nine da alhakin hakan duk da bada son Raina bane. Haka ya samu ya fita ya nufi d'akinta,Yana Shiga bakin shi d'auke sallama ya shiga. Ciki_ciki ta amsa cikin fushi. FU'AD sai cewa yayi " kin ci abinci? Be damu da ta juyowarta ba , Husna"a" tace Mai kawai agajarce. FU'AD "toh ya kamata ki tashi kici naje na zubo Miki? Husna "a nifa nakoshi nace" FU'AD sai cewa yayi "toh tashi muje wajen mumcy" sai cewa tayi"nifa Banda lafiya sanyi nakeji bazan iya zuwa ba Tana turo baki Kuma ta juya Mai baya. FU'AD sai cewa yayi toh tashi muje asibiti ko Akira likita? Husna sake cewa tayi "Dan ALLAH ka rabu dani Kuma Ni Babu inda zani sanan karka kiramin kowa Dan wallahi bazan kulashi bama Tana Shirin yimai kuka Dan muryarta ta raunana sosai. FU'AD har ranshi yaji ta Fara bashi tausayi sai yace "toh ke wacce irice Ana Gaya Miki Abin da ya Dace kinama mutane gardama Haka ko a kyale ki ne? Husna a fusace ta juyo Tana zubda hawaye Dan ta Gama gajiya da maganar da take amsa Mai "eh ka rabu dani din tunda ka cimma manufarka mugu naka na amsa ma Abin da hukunci ya Kama kamin kaji ko zazzabine ajikina da wanne zanji da zalincin ka zanji ko da Abin da yake damuna mayaudari har kana cewa Dan baba ka taho Dani Ashe Dan mugun kudirinka ka taho Dani........ Bata k'arasa ba FU'AD ya d'agota Yana cewa ke uwar tsiwa karki tsallake iyakarki ba lalab'aki nakeyi ba shawartan ki nakeyi...... Be Gama fad'a ba ,Husna tace "nice shedar ba lalab'ani kakeyi ba Dan nagani acikin zalincin da kamin ta dunkulle hannu ta buga Mai a k'irjin Tana sake cewa Kuma wallahi wajen baba na Zan tafi ,ta kwace daga Rik'on da ya Mata dama ba wani sosai ya rik'eta ba ,ta nufi wajen da hijabanta suke Tana Shirin d'auko wani...... FU'AD zuwa yayi ya kwace da ta d'auko wani ,Yana cewa "me zakiyi ke bakida lafiyan zaki fita? Ido cike da hawaye tace "eh gwanda naje gaban shi nayi mushe yafi min zama da mugu irinka Wanda kanshi ya sani kawai" FU'AD kamota yayi ta kwace ,ta sake d'auko wani hijabin Tana zurawa Tana Shirin tafiya , Fu'ad yace "ke wai bazakiji me nake Gaya Miki ba? Ni ba mijin ki bane? Husna cewa tayi "yanzu ne kasan Kai miji na ne? Wallahi sai na tafi Ina ruwana da wani Auren ka ai Auren ma ai kace ba naka bane na mumcy ne ko ka manta na tuna ma? FU'AD rariyace taso kwace Mai yadda ta tsare shi da idanun ta da sukaci ubansu ,sai had'iye dariyar yayi ya kamota ya na cemata , naji ki Bari Gobe sai na kaiki da kaina ya Miki? Husna take Tana cewa "wallahi ban yadda ba yau zani ina mutu kafin goben fa yadda ka d'auko Ni ai ba haka kace min ba" Kafin FU'AD ya Gama shiryama rigimar Husna yaga har ta nufi k'ofa alamun da gaske takeyi ,Aiko zuwa yayi ya taro ta Yana cewa "toh tsaya kiji Al'k'awarin da Zan Miki shine Zan kaiki Amman anjima idan munyi sallah magrib hakan yayi? Jin ya amince ya sakko da wuri Haka sai tace "naji Tana hararar shi Tana Shirin komawa gadon, FU'AD yace kafin Haka taso muje ki karb'i paracetamol Kisha sanan kid'an ci wani Abu sai kizo ki kwanta ki huta" zatayi wata magana ya dakatar da ita da cewa banason musu kawai barin kawo Miki. Tafiya yayi ya dawo d'auke da tea Mai kyauri da zafi da magani sai snacks a plate ,taso Taki ci Amman yasata a gaba Yana cewa taci sai ta kwanta Dole ta Dan ci sanan Tasha maganin ta kwanta Tana hararar shi. FU'AD murmushi ya sakar Mata kafin yace ALLAH ya Kara lafiya Ayi bacci lafiya , Husna murgud'amai Baki tayi tace "mamugunci kamin dariya Mana shi yafi cancanta Dani ai ,shine tukwici na.... FU'AD har ya Isa d'aki Yana Mata dariya cikin ranshi Yana jinjina tsiwa da rigimar ta ga k'arfin Hali da takeyi ..... Sanaya Bayan ta Gama gumarzon ta wani bacci me nauyi ne ya d'auke ta...... Bayan FU'AD ya l'ek'a yaga Husna ta samu bacci sai ya sauka k'asa wajen mumcy ya d'auko ma Husna akwatin kayanta ,Nan mumcy take Gaya Mai sanaya tazo neman shi ,sai yace "eh yaga kiranta yanzu zeje yaji" mumcy tace Mai "ya kamata Kam"Inji mumcy. FU'AD part d'in sanaya ya nufa ko sallama babu ya bud'e k'ofa ya Shiga yaga Bata falo, D'akinta ya wuce ya sameta tanata fama da wani nanauyan baccin da ko sanin yazo ma batayi ba. Sai da ya Gama hararar surar ta da takaicin Abin da ta aikata Mai ya Gama yima kanshi murna dabe afka Mata ba da har ya mutu baze manta wanan ranar bakin cikin ba.......a zuciye ya d'aki had'ad'en gadon da ta baje akai ,Yana cewa "munafuka hakan ki be cimma Ruwa ba tashi neman me kike min? Sanaya ji tayi kamar daga sama ,ahankali ta Fara bud'e ido ,ganin kamar FU'AD ne akanta sai tayi yunk'urin tashi ta samu ta mik'e ,Tana mik'ewa ta ci kwalar jalabiyar shi tana cewa"macuci kura da Shan bugu wani da kwace kudin wallahi zakasan ka aikata ba daidai ba indai sanaya ce Tana janyo shi kamar zata kwantar dashi agadon. FU'AD ganin Tana k'ok'arin kifar dashi a gadon ta turmushe yayi sauri fincike hannun ta ya wurgar gefe "banza Naga har yanzu ba a daidai kike ba abokin mutuwa kike nema sai dai kiyi da wani badai FU'AD din mumcy ba gantalaliya mabuk'aciya kawai,ya juya ya fita Yana cewa inkin dawo hayyacin ki na Kora Miki gargad'in da nazo Miki Dan yanzu innayi ma a banza ba a setin ki kike ba.ya fice Abin shi,itako kifewa tayi tanata kukan takaici. [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg63 Bayan tafiyar su FU'AD da Husna ,har FU'AD yayi hanyar gida sai ya juya akalar motar ya d'auki wata hanya. Husna kasa hak'uri tayi tamai magana "Ina Kuna zamu haka? FU'AD yace "wani waje zamu bazamu Jima ba" Sai Husna tace "Dan ALLAH mu wuce gida na gaji wallahi bacci nake sonyi" FU'AD ko kallonta beyi ba yace "hmmm wato buk'atar maje hajji sallah sallah ko? Tunda Taki buk'atar ta biya kawai atafi gida ,to Nima anada Abin da Zan d'anyi sai mu wuce gidan" Husna "hummm kawai tace" ta fita harkan shi. FU'AD a *suya sport* ya tsayar da motar shi yace ma Husna "Ina zuwa" be tsaya jiran amsawar ta ba ya fice ya nufi inda dakwalen kaji suyan 'yan birni sunata gad'a a madafarsu ga wani maik'o da sheki da suke zubawa duk Wanda yayi tozali dasu. FU'AD cewa yayi a bashi masu kyau d dumi guda 3 azuba mai komai yaji a zuba guda guda biyu a waje d'aya asaka 1 daban, Haka kuwa aka Mai yaka bashi a wata k'ayataciyar leda ya biya ya wuce inda ake sai da juice masu dad'i da sanyi ya zab'i masu kyau da fresh milk masu sanyi ya biya kud'in ya tafi yanata sauri y samu Husna a mota suka tafi gida. Bayan sun Isa ya Adana motar a inda ya Dace ,suka nufi sashin su ,suna Shiga sukaga mumcy Bata Nan Tana d'akin ta sai FU'AD yace ta haura da ledan sama Bari ya dubo mumcy. Husna haurawa tayi ta ajiye Mai ledan shi a falo ta shige d'akin ta Tana Shirin canza kayan jikinta zuwa na bacci. FU'AD sai d ya jira mumcy ta idar da shafa'i da wutiri kafin tayi Addu'a ya tayata shafawa ya sanar Mata sun dawo baba yace agaishe da ,d sakin fuska mumcy ta amsa har take tambayan lafiyan su , FU'AD ya tabbatar Mata da lafiya suke,sanan y Mata sallama , mumcy tace ya gaishe da Husna amata sai da safe. Bayan FU'AD ya haura yayi zaton zega Husna na jiranshi ko y ganta a falon ,Amman Babu ita sai ledar shi ,Kiran ta yayi Amman Jin Bata amsa ba yasa shi kutsa Kai d'akin ta babu sallama atunanin shi tana jinshi kin amsawa tayi Dan yana sane har yanzu haushin shi takeji. FU'AD na Shiga yayi tozali da Husna Tana canja Kaya d'auke idon shi yayi daga inda take Yana cewa" kina jina dama na sani" Husna ta'awuzi ta Fara "a'uzubillah babu sallama ne? FU'AD sai cewa yayi ,ban koya ba kizo Ina jiranki karkimin Rashin kunyar d Kika Saba,Kuma karki k'ara yimin ta'awizi tunda ba shed'ani bane Ni. Husna cewa tayi ,Amman ai ka iya fad'oma mutane babu sallama Dole nayi ta'awizi Naga k'ato babu shiri ai......Bata k'arasa ba ya juyo d niyar dawowa Yana Mata mugun kallo Yana cewa "waye k'aton? Husna shiru tayi Tana bashi amsa d ido amemakon Baki ,Dan Abin da ze sake had'a fatanta da FU'AD ma bataso bare hannun shi ya tab'a jikinta. FU'AD ganin alamun Taki tsoro sai yace ,da yarinya tayi magana Mana? Fita yayi Yana cewa inkinga dama kizo yanzu. Zama yayi a falon Yana b'ud'e ledan d ya siyo drinks Yana rabawa gida biyu. Husna Bayan tayi shigar bacci sai ta fita zuwa Kiran FU'AD ,batare da tace komai ba FU'AD yace "ga ledan Nan d'auki kije da ita Naga kin barta Baki cinye ba Yana mik'ewa da nashi ledan Yana nufan room d'in shi. Husna d'auka tayi ta tafi tana son sanin meye aciki da har ake Mata gargad'i kamar wata babyn shi. Bayan Husna ta Shiga ta bud'e tayi tozali da masu maik'o da kyalkyali har seda ta had'iye yawu Dan sha'awar da suka Bata,gashi karyewa tazo Kan gab'a Dan ji take kamar seta d'an k'ara abinci kafin ta kwanta. FU'AD ma zama yayi yaci nashi yabaci Yana chart da B2k akan zuwan shi na goben. Husna ma zama tayi Tama kazar Nan cin ALLAH ya tsine uwar Mai k'arya ta k'oshi ta Kira da milk sanan ta tatara ragowar Tana mita Akan ai ba jaka bace ita da zece ta cinye tas. Bayan ta d'an huta ta samu ta kwanta tanata mitar Akan Abin da FU'AD d'in ya mata na gwada Mata kalan imanin shi da tunanin FU'AD bacci yayi gaba da ita. Washe gari Bayan gari ya waye sunyi Karin safe , FU'AD nata Addu'a ALLAH yasa mumcy Kar ta sake tsokano maganan tafiyar husna gida Dan besan da wanne Ido ze kalli baba ba datijo Mai Halin kirki kamar shi. Bayan wasu awanni suna zaune a falo sai ga wayar B2k ta shigo wayar FU'AD. FU'AD da k'arfin gwiwa ya d'aga Yana cemai ya shigo Mana ya tsaya a wace ko sallon munafurci ne yau yazo dashi. Mumcy ce take dinga yimai dariya Tana cewa munafircin ma harda salo? Sai FU'AD yace ,toh mumcy kinsan fa shigowa yakeyi Amman yau ya mak'ale a waje Yana jiran izini na besan Nima katawa nakeyi a gidan ba Dan ba nawa bane yanayi Yana kalon mumcy da Husna ,ita Husna kallon shigarta yakeyi Kar B2k ya ganta a wani yanayi sai yaga Ashe da gyale ajikinta Kuma ya rufe Mata jiki. Mumcy ta katse Mai tunanin Husna da shigarta da cewa "gidan ne ba naka ba harda rabawa kakeyi? Sai FU'AD yace "eh Mana yanzu inza'ayi kwatance ko da Alh yake Raye da gidan ki ake kwatantawa gashi fa shi ya Gina gidan Amman gidan hajiyar Alhaji ake cewa ,Kai Mata Akwai kace basai mutum ya mutu ba da ranshi ake Mai kwace yanayi Yana murmushi. Mumcy sai cewa tayi "hmmmm yau Ni kakema biki ko? Sallamar B2k besa mumcy ajiye maganar ba ,Bayan ta amsa tamai sannun da zuwa tacigaba da cewa "kaima Nan da wani lokaci zakaji Ana gidan su Husna da sanaya yanzu ma saman husna ake cewa Dan ya tashi daga na Fu'ad. Sai ki Fu'ad ya gaisa da B2k Yana cewa kaji ko abokina da Raina an mallakama wata sashi na tun ban mutu ba. Sai ko mumcy tace Aiko ma'aikatan gidan Nan saman husna suke cewa wajen sanaya ma suce sashin sanaya sai sashin sa'adiya ma ace nata bana Jameel ba. Husna dariya tayi Mara sauti Bayan sun gama gaisawa da B2k. Sai ko FU'AD yace "shi kenan na zama d'an rakiya? B2K yace "tunin mah" FU'AD cewa yayi "a da sake anba me kaza Kai" B2K mumcy ya gaisar sanan ya cigaba da Hira Yana sako hirar taho da Husna da FU'AD ya tsaya yayi har akazo gabar da mumcy ta magantu da fadin cewa husnan ma ai tafiya zatayi gidan su Dan FU'AD har yanzu be d'auketa Mata ba...... B2K ke ne ya Shiga tsara mumcy da nuna Mata irin so da nuna alhinin rashin ganinta da ba'ayi ba akazo aka ganta yaki barin ta har sai da ya sakota gaba wanan kad'ai ya Isa ya ba me son sanin inda aka kwana amsa ,Dan Haka kowa ya zuba Ido yanzu wasan ze Fara. Mumcy taso ta tirje Amman B2k ya dinga haska Mata hanya da bayanin shi masu kashe zuciya duk da FU'AD yanaji kamar duk B2k duk ya Gama bada shi agaban Husna ,da kyar B2k yace a bashi only 4 months in anga yanayin zaman kamar na bayane sai mumcy tayi hukunci da Abin da ta gani ,da kyaru mumcy ta amince Albarkacin B2k. Bayan anyi Yar Hira mumcy ta Aiki Husna wajen su Harri Dan ta kula da girkin da suka d'ora ita Kuma ta tafi d'aki. FU'AD cema B2k yayi sannu baba uban zance ,fad'i ba'a tambaye ka ba har da sakin layi a bayanen naka... Sai B2k yace "au wanan shine godiyar da zakamin? Ko tun da na Gama maka komai ko? FU'AD sai cewa yayi haba mutumina tamu Bata bacci ,share kawai kaidai kayi jihadi ladanka Naga ALLAH.yanzu muje mud'anci wani Abu sai mu fita mu lek'a office Amman fa ba jimawa zamyi ba Dan inaso na dawo na turk'e Mara mutuncin yarinyar can naji uban da ya sa ta gabzamin magani na afkama Yar mutane Haka kawai...... B2K ne yace "have abokina ka share kawai ka manta Ni hakan dad'i yamin wallahi Dan yanzu nasan kayi Aure Kuma da Abin ya tsallake kanta ba k'aramin nasara bane gareka da Husna ita Kuma ai tayi kwanan wuya da wanan kawai ka barta tasan babu nasara a lamarin ta, please Kar ka d'aga hankalinka bare kuyi hayaniyar har yakai ga mumcy ka zamo namijin duniya Mai rufe asirin gidan shi Mai warware matsalar iyalin shi ta sauk'ak'iyar hanya kaji ko? FU'AD cewa yayi ,kasan dai bazan bar wanan yatafi a banza ba Dole na tauna tsakuwa Dan Aya taji tsoro don akiyaye gaba inba hakaba tayi gaba Dan nama gaji da auren ta. B2K bud'e Baki yayi Yana cewa"Kai mutumina yaushe akaci talatar bare laraba ,daga abinan sai kace .......hmmmmm har ka Fara sanin dad'in Auren kana nufin Husna har ta gamsar dakai kanajin da ita kawai ma zaka'iya rayuwa har anzo wajen da gagawa haka? FU'AD wani mugun kallo ya bi B2k dashi Yana cewa "Dan is .....Mai tashen bakagar tsuntsaye baka da m Meka d'auke Ni? Ni cema nayi na fahimci wani abuma Abin da mutum yayi bada niya ko shiri ba Kai nifa har yanzu yarinyar Bata gabana kawai dai matsalar ta k'arama ce absa ta sanaya ,Dan ita ko banza Ina amfanuwa da ita ta gyaran d'akina sanan Tana d'ebema mumcy kewa Kuma Tana son duk Abin da ze faranta ran mumcy shine kawai Amman har yanzu bawai sonta nakeyi ba ko ince wai Ina sha'awar Kara jin ya take ba wacan ma na dalili ne da me ze kaini wanan aikin Kai Abin ya dama shegen gayen abokina Dan iss..iss...kwai! B2K dariya ya dinga yi Yana cewa "hmmmm wallahi Zan tunama kalaman Nan naka Kuma ko ka amince ko kaki anzo wajen Kuma wallahi u fall in love with husna. Sai B2k yace "Ni muje office Kar ka cikani da Abin da nasan ba gaskiya bane. Bayan sun Gama FU'AD Yama Husna da mumcy sallama suka fice shida B2k. Husna lalabawa tayi ta gyara saman ko Ina har d'akin FU'AD Koda mumcy ta Aiko da me gyara cewa tayi "ace Mata ta gyara ma" Sanaya Shirin cima FU'AD mutunci kawai takeyi ,wani sashin Kuma zuciyar ta na rarashin ta Akan tayi hak'uri ta lalab'a ta samu biyan buk'atar ta. Mama habee tun zuwan Husna gidan abubuwa suke damun ta ga canji da ta gani atare da Husna bak'in ciki kamar ya kashe ta Dan haushi sai ta Kira humaira Tana zagin ta wai ta fito da mijin kece raini wallahi inba hakaba zata cire hanun ta a maganar ta tabarta da baban ta ko d'an bakwal ya samu ya hadasu. Humaira kunkuni tafarayi Tana cewa tafi k'arfin Dan bakwal wallahi ,Ade bari Gobe za'ayi bikin kawarta sajida girman Kai tasan abikin za'a kwantale sanan bikin sugars dadys ne Dan wani sakin gara ta samu datijo Mai shekaru da tsufa ga arziki Wanda Yan Mata wayayu suke Kira da aureni ka wuce kabarmin dukiyar, inyaso tayi duk me yiwuwa ta samo d'aya ta manne Mai har ta Aure shi. Sai ko mama habee tace "toh sai ki tabuka Abin kirki ko aron Kaya kiyi ki samu ki Mai kamu kazar kuku ki fizgi hankalin shi ko bada son ranshi ba Ni Kuma in yaso ki barmin sauran aikin Dan babu Abin da zansa gaba banci nasara ba na barshi ,duk da na had'u da karfen kafa wanan shegiyar yarinyar Ma'u Dan bansan me ta rik'e haka ba da har na kasa galaba akanta naci nasara Kan uwar da ta kawo ta duniya ma bare ita? Sai humaira tace "yauwa mama kince Babar Ma'u ma kamar Bata mutu ba ko? Toh Tana Ina? Mama habee ce ta zabiro ,Dan ubanki uwarki zaka Mata Ana ga yaki kina ga kura ban tabatar da Tana Raye ba mafarki nace Miki nayi mafarki Kuma gaba d'ayan shi karya ne ki min shiru da maganar Nan in tana rayema ai ita da ganin wani nata ma ai har abata bare ta mutu har abada. Sai humaira tace "ance mafarki na tabbata fa" Mama habee cewa tayi Dan ubanki sai ki tabbatar min tashi Yar Mai naci da kafiya da taurin Kai ,ki kashe wutar gabanki inba Haka ba ki zama matar bakwal cikin kwanakin Nan Aiki ne ja agabanki bezo ba be k'are Mikiba ba Shiga shirgin wasu ba. Humaira turo Baki tayi "Ni nafikarfin zama matar Mai k'aramin k'arfi ma bare ogan me bakwal" Mama habee "zagina kike Dan k'anwar ubanki? Fita humaira tayi ta tafi Jin bayani Akan bikin sajida girmai Kai Dan tasan irin Shirin da zatayi. Husna sunsha waya da su aunty huwaila d su muhibbat har Husna ta tambayeta labarin jikin Yaya ,sosai aunty huwaila ta sanar Mata da sauki. Bayan FU'AD ya dawo da yamma lis ,be Shiga wajen su mumcy ba sai da ya Fara zuwa sashin sanaya ,Yana Shiga ya sameta Tana cin abinci ,tun da ya shigo ko kallon inda yake batayi ba bare ta amsa Mai sallamar. FU'AD ne yace "hmmmm me Hali baya fasa Halin shi ai ,uban wa ya Baki damar cutar Dani ta hanyar wawan planning d'inki Mara cimma gaci? Shiru ta sake Mai ,ya sake d'agowa ya tambayeta Karo na biyu ,shima babu amsa sai da yayi na 3 shima ba amsa ,dakan table d'in da take cin abincin yayi Yana huci Yana furta" ke badake nakeyi ba? Wato ga mahaukaci na haukan shi ko? Yana niyar shak'ota tayi saurin mik'ewa tayi baya Tana cewa" ban sani ba ,namijin hoto kawai wai sunan kana namiji babu Abin da kake tsinanawa a gidan Auren inba k'addara ba me ze had'a dutse da kwai? Wallahi sai k'addara da tursasawar dady. FU'AD cewa yayi ,toh kice bakyayi Mana? Ko ance kiyi Dole ne jarabus banna Kuma da Abin da aka dawo kenan ,wanan 'yanya ma ba hoto aka aura min ba? Sosai gaban sanaya ya fad'i Dan ta fahimci manufar shi,Amman ta dake tace "Kaine hoto wallahi Amman bani ba Dan zanyi manage da Kai ma kaci sa'a? FU'AD kasalalan murmushi yayi yace "hmmm babu Rami meya kawo Rami? Ta Ina kikasan wani Abu irin hakan inba sabawa kikayi ba ? Toh Nan gani Nan Bari sai lokacin da nayi niya Dan wani tuggun ki babu Abin da zemin gwada kibini a hankali ko ashekara Kya samu round innaji tausayin ne ma fa keda kikace babu amfanin da zanmiki a iya zamana dake ko kin manta? Sanaya ta Tama zuwa wuya ,kuka take Shirin yi Tana Shirin tafiya d'aki "wawa Mai sharri zakasan kayi da sanaya Kuma wallahi bashi kaci na duk rashin mutuncin da kake min ,Wanda besan mutuncin wani ba bare nashi Mai girman Kan tsiya duk kauda kanka wallahi nasan kanaso munafuki ai ba waliyi bane Kai Dan daganin ka za'asha fama dakai macce 1 bazata isheka ba hakan yasa aka had'ama biyu lokaci guda ,Ni Kuma nayi Al'k'awarin kurema gudu..... FU'AD nufarta yayi ,da sauri ta goje tace Abin ya motsa Nima ban shirya ba zaka fake da Kai hannu jiki ba ko ka k'oshi Dan daganin ka a yunwace kake sai dai kaje wajen waccan badai Ni ba ban naso Nima ,ta wuce d'aki ta bugo Mai k'ofa. FU'AD mutuwar tsaye yayi Yana mamakin kalaman sanaya ,Amman ta Gama dashi Musamman dabe Bata amsa ba ,barin falon yayi ranshi a bacce atunanin shi ta Gama cimai mutunci yau Kam. Maman shaheed😍 Comments and share👌🏻ku rik'e stikers din ku😝🥰 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` By *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* (Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg66 Bayan FU'AD ya rufe k'ofar shi y barta, itama tafiya tayi Tana Mai mita. Washegari da FU'AD suka had'u d sanaya wani kallon shek'ek'e tamai ta watsar,shima bebi takanta ba sai tambayanta lafiyan ta da tambayan Tana buk'atan wani abune? Sanaya ko kukashi batayi ba ,saima cewa da tayi me Zan buk'ata a tare da Kai? FU'AD murmushin takaici ya jefeta dashi sanan ya fice ya barta ,wani irin mugun kwafa sanaya ta sake me cike da manufofi da yawa. Bayan FU'AD ya fita wajen mumcy ya nufa ya gaishe ta ya haura ya duba Husna y tambayeta ko Akwai abin da takeso ,tace "babu " ya sauka ya wuce office. Yau ne ranar zuwan su Yaya Jameel tun safe suka Gama shiri d baby Mami su suka taho by road ,sunma su mumcy tsaraban kayan marmari da yawa masu kyau ,Haka mumcy tasa aka shirya musu lafiyayen girki kamar yadda aka Saba,Husna ma murna takeyi d zuwan su Dan Sam Tama manta dalilin zuwan nasu da Abin d Yaya Jameel ya Mata Dan tamai uziri duk da abin bataji dad'in shi ba. Kafin azahar su Yaya Jameel suka iso ,sunsha tarba daga ma'aikatan gidan da su mumcy har Husna , mumcy ta aika a sanarma sanaya d zuwan nasu Dan har tazo ta musu sannu d zuwa suka gaisa Babu yabo Babu fallasa,da aka raba tsaraba aka Kai mata ta karb'a har ta ci Abin d takeso aciki. Bayan sun huta FU'AD ma ya dawo gida a d'akin mumcy Yaya Jameel yake ba husna hak'uri Akan akan abinda ya assasa aka Mata agaban kowa. Husna cewa tayi"babu komai Abu ma ai ya wuce duk anyi kuskure ALLAH ya yafemu Baki daya. Mumcy tace "Masha ALLAH , ALLAH ya yafemu Baki daya, FU'AD ya amsa da Amin, mumcy ta musu Addu'a da sa musu Albarka cikin Rayuwar su da Abin da zasu Haifa Nan gaba. Bayan sunci sun k'oshi ,Hira ta samu guri tsakanin aunty sa'adiya da Husna sosai suke Hira cikin birgewa da k'aunar juna Husna nata renon Mimi Shan nono ke maida ita wajen aunty sa'adiya kawai. Kwanci tashi babu wuya yau kusan watan Husna 3 da dawowa daga indiya sosai baiwar ALLAH Nan ta samu sauki hankalinta da duk tunaninta ya dawo taci kuka kamar ranta ze fita da tayi tozali da k'anwarta har ta fahimci itace silar dawowarta hayyacin ta sanan tayi farinciki da ta rike Mata Husna kamar yarta ta cikin ta taso Dan badan husna ba ji tayi ta tsani Nigeria ma batason asake Mata maganar tashi kirikiri huwaila ta hanata magana da yarta Husna akan hujjarta ta son ta shayar da ita ruwan mamaki Dan taji Dadi sosai. Baba ma ya cigaba da uzirama humaira Akan miji da kyar ta samu ta shawo Kan wani Alhj birni ya yadda ze aureta matan shi 3 itace ta 4 humaira taso ki ,Amman mama habee ta zugata Akan ta yadda inba Haka ba ta auri kolo ko Dan bakwal Dan babu ruwanta da tijarar ubanta Dan taga alamar ya fita agiya. Humaira ta turoshi har sun gana da baba ,baba yace ya bashi akasa ranar Aure wata 3 kacal shima Dan ya Gama shirye_shirye ne mutum yace ze Mata komai basai baba yayi ba yanaso arage bikin da kyar baba yace ya Rage wata 1 kacal saura wata biyu biki,Aiko mama habee ta dinga surutu yarta humaira ta samu miji na bugawa a jarida Dan Haka taron biki zatayi na kece raini mutane tun kafin bikin yazo asanar dasu da Baki ance su Fara lissafi. Husna da sanaya babu wata Hira dake guda atsakanin su sai gaisawa shima sai in sun Hadu, su aunty sa'adiya tuni sun koma Abuja,hafeeza takan kawoma Husna ziyara tare da karatun iya zama da miji Dan itama yanzu ta samu wani da yake sonta har sun tsaida maganar aure Husna nata murnar zatayi bikin kawarta. Sosai FU'AD ya yake kishin Husna Amman a fili baya nuna Mata tsantsar so da k'auna Dan ya hanata saka hoton ta a dp ko status d'inta sai ya fake da babu kyau sanan wani lokaci intasa hoton ta astatu sosai yake mayar da hoton abin kallon shi Yana cin ta hadu Amman sai zuciyar shi ta hure Mai kunne ya ki yabon kyan nata ahalin yanzu Abin ya Fara fizgar shi da son canja shi. Ganin Husna ta Dena sa hoton ta sai takesa nasu Aisha Ghana k'anwar aunty sa'adiya da su muhibbat d Husna ta taba saka nasu Affan d sadeeq sai da sukayi fada da ita shara'a har gaban mumcy , mumcy ta musu sulhu abun ya mata Dadi Dan ta gano tsagwaron kishi tare da autan nata Amman ta musu fada na tsakani da ALLAH sai ma Affan da tafi ba rashin gaskiya Bayan yayi fushi ya tashi ta sakena Husna nata nasihar Akan ta daina sosai Husna ta fahimci manufar mumcy. Ayanzu Husna Tana masifar son FU'AD yanzu ta Gane namijine na nunama sa'a Tana tunanin bazata iya Rayuwa da kowanne namiji bama sai shi ,Tana yin duk yadda zatayi ta birge shi da Jan hankalin shi Dan kwaliya ta Fara biyan kudin sabulu indai tayi kwaliya yata binta da kallo kenan ga wasu mayun turaruka da take Amfani dasu masu masifar Jan hankalin FU'AD din badan Jin Kai irin na Fu'ad ba da tuni yabada Kai bori ya hau Amman dai da sanu_sanu inji masu iya magana,Dan ko baida Abin ce Mata in adakinta yake ze kirata falo yata sata Aiki har d'auko Mai Abu a d'akin shi ko ba amfanm zeyi da su ba kawai bayaso tayi nesa dashi. Yawan ganin hoton Aisha Ghana a status d'in Husna da ganin kawancen su yasa FU'AD yayi k'ok'arin hada B2k da ita ko ze zamo silar Auren su , B2K be watsa Mai kasa a Ido ba ya amshi tayin shi har hoton ta ya tura Mai yamai ciko da kyawun halinta Dana yayarta Dan sun zauna na wani lokaci,ganin B2k ya karni Abin da mahimmanci FU'AD ya dinga tsokanar shi Yana cemai munafuki dama kayi tsatsa badan Kun rabu da wanan joker ba nasan d tuni ka kawota daga ciki yadda kake dinan....... B2K dariya ya dingayi Yana mayar Mai da martani Yana cewa kaima dai naka kamar baka aikin da aka baka Mata biyu har yanzu babu wacce ta taba ko batan wata Dan nasan abokina ba juya bane Haka suma. FU'AD naushin shi yayi da Wasa Yana cemai"ka tabbata su ba juyoyi bane? Kanata sheda? B2K mik'ewa yayi Yana dariya Yana cewa ,Ni ba inda ka nufa naje ba ,Banda sheda Dan iskan abokina mubar maganar Kar kamin iskanci,yanzu dai akarbo min number my A dinan mu Fara cacafkewa Dan tun da wuri Zan Gama gini na na shige no time to play kafadi duk Abin da zaka fad'an Dan is...is... Suna dariya suka rabu , FU'AD yamai Al'k'awarin turo Mai number batare da sanin Husna b Dan bayaso ta sani sai kumai yayi nisa game d'in ya Gama fadawa sai ta sani yadda zataji Dadi itama. Dady Egypt Abu ya Fara kaishi mak'ura ganin hak'anshi baze cimma Ruwa ba ga wasu miliyoyin kud'i da yake buk'ata dan zuba wani hannun jari ga shi kudin hannun shi baso ya Ya kwashe ya zuba Dan sune uwar kudin shiyisa yake neman wasu daban,gashi bayaso ya ankarar da su FU'AD Akan manufar shi hada Auren shi da sanaya da yayi Dan Haka ya Fara sababi zaman sanaya ya Isa Haka babu da babu jik'a bare tayi k'ok'arin Shiga cikin duniyar su FU'AD Kota hanyar kasuwanci ne Dan komai ya dawo hannun ta,maman ma ta goyi Bayan shi sai mufeeda da ta Fara nuna musu rashin halkacin abun Aiko Tasha zagi. Dady da kanshi ya Kira sanayan ya Fara Mata magana Akan manufar sa taso bijirewa Amman yadda taga da gaske yake ta amshi maganar nashi Amman bawai Dan tayi naam ba ,ita burinta da ban Akan FU'AD sai ya dinga kusantar ta Koda niyar sa ko babu Dan Haka ma yanzu ta k'are Mai wani shiri da tanadi Dan ta rantse sai tayi rushe Mai tanadin shi na girman kan da yake damun shi. Tun Abin da sanaya Tama FU'AD baya sakewa yasha ko ruwan da fito daga hannun ta. FU'AD ya Gama kwana 2 shi yau ya koma d'akin sanaya har yaci kwana 1 yau ze cinye na 2 kamar yadda aka Saba Nan sashin aka kawo Mai kayan abincin shi Yana zaune aka shigo da Mai da komai harda kunun Aya Mai Madara Wanda yaji Zuma da kwakwa da dabino FU'AD da kamar baze Sha ba sai ya tuna daga inda yafito sai ya kurba ya sake Dan yaji abun yayi matuk'ar Dadi sosai yasha yaci abinci har ya tashi bega sanaya ba gashi dama beci abincin ba sai Bayan isha'i yasan ita taci nata Dan yaga plate din da taci ma ,Bayan ya gamacine yaje yama mumcy sallama ya haura Yama Husna sallama suna had'a Ido da Husna yaji tsigar jikin shi ta tashi da sauri ya kawar da idon shi ya sake kallon ta ya sake tsintar kanshi dajin yanayin da yaji dazu Dan haka be d'auki abun komai ba ya Mata sallama ya wuce sashin sanaya. Yana Shiga ya Fara tunanin me yasa yaji wani iri a lokacin da ya kalli Husna? Da sauri ya kawar da abun daga ranshi Dan Yana tunsni Yana sake Jin bak'on yanayin,ya kunna kallo ma ya kashe ya tafi bacci d'akin shi. Shigar FU'AD d'aki keda wuya sanaya ta fito cikin sanda ta nufi k'ofan falo ta saka key ta cire ki din ta tafi dashi d'akinta ta b'oye ta dawo Fallon ta kwanta cikin wata iriyar shigar rashin mutunci ta baje a kujera kanta ko dankwali babu dama ta Gama Shirin Kota kwana. FU'AD Kam zuwa yanzu Abu ya Fara kankama ya rase meke Mai Dadi hoton Husna da buk'atuwa da itane kawai a tare dashi Dan Haka ma ya kasa samun nutsuwa ya saka jalabiyar shi Dan zuwa sashin su Husna ko inya ganta ze samu sasauci Yana fitowa yayi tozali da sanaya Sanaya ma taji fitowar shi Amman sai tayi kamar bacci takeyi ,ganin hankalinta baya kanshi k'ofa ya nufa cikin wani yanayin buk'atuwa ya bud'e yajita a rufe da key y duba yaga jikinta babu key y koma d'akin shi y dinga laluben spire key be gani ba hankalin shi atashe yazo y Sami sanaya y tasheta Yana mata masifa ta bashi key Dan y Gama tunanin ita ta cire key din falon. Tashi tayi cikin siririyar murya Tana cewa batasan inda yake ba ,ganin Abin nata yazo da rainin hankali tureta yayi Yana Shirin mirdeta ya duba hanun ta yaga tanata b'oye Abu. Yana had'a jiki da ita yaji karuwar yanayin da yake ciki ,sosai y cigaba d murdeta y samu ya bud'e hannu da ta dunkule Ashe babu komai ciki wata sigace t tayi don Jan hankali da yaudarar shi ,tashi ta sakeyi ta tafi d'akin ta binta yayi Yana Shirin makureta Akan ta d'auko Mai makullin ko yaci mutuncin ta,Yana Shiga tayi Kan gado Tana wani ajiyar zuciya kin Hawa gadon yayi hannu y Mika y kamo kafafunta y janyota Yana Mata magana cikin zafi_zafi da yanayin b'acin Rai a lokacin har ya fita hayyacin shi k'arfin Hali kawai yakeyi Dan jikin shi y rawa ,samu tayi ta turashi gadon kafin ya taso ta bushe fitila Yana tureta Tana Mai naci da k'arfin tsiya ta Fara k'ok'arin yin aikin da ba ita yakamata ace tayi ba. 🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀👌🏻 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg64 🎂🍾🎂🍾🎂🍾 🎂🍾🍾🎂 🎂🍾🎂 🎂 *Happy birthday to you HAYATU BABA ZUBAIRU*🎂🍾 *Allah ya Karo shekaru masu Albarka da lafiya da Nisan kwana Mai Amfani Yaya hayyat Admin of Admins*🥰 🎂🎂🎂🎂🎂🎂 Bayan ya Gama sauke goron numfashin takaici ya fice yabar Fallon. Husna watsa Ruwa tayi ta sake gyara d'akinta ta feshe da turarukan kamsasa waje ta fesa kwakiyarta sanan ta sauka k'asa wajen mumcy suna hira, FU'AD ya shigo wani irin kallo yabi husnan dashi Yana mamakin girmanta da wayewarta lokaci 1 ganin zuciyar shi nason ta kaishi inda be shirya ba yayi saurin kawar da zancen. Sannu da gida yama mumcy ya nufi saman shi ,Husna ma sannu da zuwa tamai cikin zazakar murya ,amsawa yayi da sakin fuska har da d'an murmushi Dan mumcy ta kafe shi da Ido. Can zuwa wani lokaci sai ga FU'AD ya sakko kunnen shi manne da waya da alamun waya yakeyi da Yaya Jameel. Can sai yace "eh lafiya duk suke ko na baka Husna? Yaya Jameel cewa yayi "a kabari zamuzo a satin Nan ai kunyan ta nakeji sai nazo na wanke Kai har sa'adiya sai ta tayani bada hak'uri aikata laifi bisa rashin sani son k'anina ya rufe min Ido. FU'AD cewa yayi "toh shike Nan , mumcy fa ita? Sai yace "abata" Bayan mumcy ta karba sun gaisa yake sanar Mata zuwan su Dan zuwan na Husna ne ma gaba d'aya , mumcy take cewa ya kamata Kam. FU'AD zama yayi aka d'anyi hirar dashi daga baya ya wuce masallaci Husna Kam a wajen mumcy tayi sallah sukaci abinci. Bayan FU'AD ya dawo ma yaci nashi abincin y sake taba Hira kafin ya haura sama. Husna ma haurawa tayi badan Kar mumcy tace wani Abu ba da sai kwanciyar bacci ze maida ita saman. Bayan ta haura zama tad'anyi a falo ganin FU'AD baya Nan ,Tana cikin kallon wani film a zee world sai FU'AD ya dawo falon Jin motsin TV ,sai ya kalleta yace "inace kinje kin kunshe kanki a dakinne kamar kosai a takarda. Husna kallon shi kawai tayi ta saki murmushi Mai bayyanar da amsar tambayar shi. Zama yayi kusa da ita Yana cin Cookie's ya m'ik'o Mata Kar ki jamin ALLAH ya Isa acikin zuciyan ki ban Miki tayi ba. Husna wani kasalalen kalo ta bishi dashi kafin tace "nama k'oshi ni" FU'AD sai cewa yayi "nadai fita hakkin ki ,ummmm Amman yayi dad'i yanaci Yana latsa wayan shi Yana sakin murmushi alamun abun da yake kallo ya kayatar dashi. Husna duk atakure tajita Dan Bata Saba ba gashi ji take kamar ya matsota da yawa duk da tazarar dake tsakanin su mutum biyu ko uku sirara zasu iya zama Dan Akan 3seater suke kuma kowa na gab da k'arshe ne. Husna ce tace "yauwa inaso gobe ko jibi zanje gidan su hafeeza in duba mamanta ba lafiya duk da karya tayi tasan inba Haka tayi ba bazeyi saurin amincewa ba hakan ma Bata da tabbas. FU'AD yi yayi kamar be jita ba ,tasan ya ji me tace Abin ya k'ular da ita ta sake cewa "nasan fa kajini Ina magana" FU'AD ko ya kalle ta bare ya amsa ,sai Husna ta k'ara kukewa ta mik'e Tana Shirin Shiga d'aki Tana cewa "gobe na nemi izini wajen hajiya nasan ita bazatamin shiru ba sai dai ma tamin rakiyar ingaishe su,har ta kusa Shiga d'aki tajiyo FU'AD na cewa "saboda mumcy ce take Auren ki ko? "Husna dawowa tayi kad'an Tana cewa"ai dama zamanta nake aurena Kuma ai natane ko ka manta? Tayi gaba ta barshi da mamakin maganar. Shiru_shiru FU'AD zega Husna ta fito Amman har ya tashi Bata fito ba. Bayan shigan Husna sallah tayi ta rage kayan jikinta Bayan ta fito daga wanka ta kwanta zuciyar ta fal tunanin FU'AD da rainin hankali irin nashi. Waahe gari Fu'ad ya fito cikin Shirin tafiya office Yama mumcy sallama Dan tun d asuba da ya tashi Husna sallah bata Bari sun Kara had'uwa ba sai a wajen mumcy yanzu ,Musamman da yaga tayi wanka taci kwaliya shine yake zargin ko unguwar zata tambayi mumcy taje Dan Haka yafara cemata "Kar ki fita har sai nadawo in da yiwuwa na kaiki da kaina ko driver ya kaiki" Husna da bazata amsa ba ,sai ganin mumcy yasa ta amsa da "toh" Sai mumcy tace fita zatayi da? Sai FU'AD yayi sairin cewa "wai gidan wata ko hafeeza ko me zatajeyi nama manta" Husna d'agowa tayi tana Mai kallon rainin hankali ,Shima mayar Mata yayi da "eh na fad'a din" Sai mumcy tace "Aiko hafeeza ta wuce wata wajena bare Husna ita da kawarta ko yar'uwarta Dan kawancen gaskiya Kan rikid'e ya zama 'yan uwantaka. Sai FU'AD yace ,toh ta Bari har na dawo dai mumcy na tafi Kar na makara Akwai meeting da zamu d'anyi kafin na Shiga office. Mumcy da Husna suka Mai adawo lafiya ,sanan ya amsa ya tafi. Bayan Rana ta Fara fitowa , mumcy ce tacema Husna taje su gaisa da sanaya. Husna amsawa tayi ta nufi sashin sanayan cikin girmama umarnin mumcy. Husna bakinta d'auke da sallama ta Shiga sashin sanayan ,taci sa'a Tana falo kuwa ,zama tayi cikin sakin fuska Tana gaishe ta ,cikin sakin fuska sanayan ta amsa ,har take cemata mufida tace a gaishe ta,Husna take Tana amsawa. Bayan husana ta koma samanta ta nufa ta Kira Aishan Ghana suka Sha Hira sai ta Kira su muhibbat indiya suka gaisa. Bayan FU'AD ya dawo da yamma ,Husna sake Mai magana tayi Akan zuwa gidan su hafeezar a gaban mumcy ,ganin mumcy Tana kallon shi sai yace ta shirya Bari ya watsa Ruwa Amman baze wuce minti goma shabiyar ba. Husna" toh" tace ta Mike ta tafi gyarawa. Bayan ta shirya ta sako Tana jiran shi ,shima ya Gama Yana Mata wani irin kallo na kinfiye naci yace mu tafi to,tace "toh mumcy muntafi" Mumcy har tsaraba taba husnan Alaina mmn hafeezar Dan da amana tsakanin hafeeza da mumcy. Bayan sun Shiga mota FU'AD yace "kin nace sekinje to munti gima Zan baki in Kika wuce zan tafi" Sai Husna tace "kace minti 15 Kuma ? Sai yace "toh naki karki wuce dai" Bayan sun Isa gidan yace kiyi sauri kinsan bame gadi bane Ni ko? Husna cewa tayi "toh" Husna na Shiga bakinta d'auke da sallama ,Aiko hafeeza har ta d'auki muryar ta ,da sauri tazo ta rungume ta sunata murnar ganin juna,Husna take cewa karki kadani ni,sai hafeeza tace qau to ko munkaru ne barin ja baya Kar na matse ma yarona hanci. Sai kuwa Husna ta tabe Baki Tana cewa "banza kece yarinyar ai Yar air kawai zaki Fara iskanci naki ko? Sai hafeeza tace ,eh Kuma bazan fasa ba muje ki gaisa da mama sai muje na zuba Miki hadda Dan so nake kiyi sauka cikin kankanin lokaci Dan ba ga kina buk'atar karatu duk da Baga kin dau ganya Amman da sauranki wlh. Bayan husna sun gaisawa da mama ,sai hafeeza ta janye ta suka shige d'aki tanata karanta Mata dabarun yadda zata zauna da FU'AD da nuna Mai tsagwaran so da kulawa ta karbi mijinta sosai kartayi Sanya. Husna murmushi ta dingayi Tana cewa toh taji,hafeeza tace wallahi inkinji kin d'auka to da kanki Zaki bani labari Nan gaba inkin zauna kiga zaunau bare Naga har kishiyace dake duk da Naga kinfita fada to kiyi k'ok'arin gyara masarautar ki maganar wata kunya ki ajiyeta agefe kiyi bautan ubangiji ,Husna dariya ta sakeyi ,sai hafeeza ta sake cewa hmmmm wallahi zakigane amfanin baya nai na Nan kusa ki rubuta ki ajiye. FU'AD ne ya Danna ma husna horn har so 2 ,sai hafeeza tace ga makale Mata can Yana magana naji kina cema mama tare kuke ,tashi ku tafi Ina Nan zuwa Nima. Husna turo Baki tayi Tana cewa kyale shi Dan ALLAH ya tafi mana,sai hafeeza tace wallahi sai kin tashi inba Haka ba na hadaki da mama,sai Husna ta Mike tace munafuka kawai muje na Mata sallama. Bayan Tama Mama sallama sai hafeeza ta rakata suka gaisa da FU'AD da har yaci kunu ganin hafeeza sai ya Dan saki ranshi suka gaisa ya Bata kud'i yace akaima mama ace Yana dubata ,ta karb'a tayi godiya Tana cewa zataji. FU'AD komai be cema Husna ba sai da suka kusa Isa gida sanan yace jibi zamu unguwa dake bance Kuma ki tsaya tambayar inda zamu ba. Husna cewa tayi hmmmmm k'arfin Hali azuciyar ta afili kuma tace "indai ba gidan yanke wuya zamu ba ai da sauki" Fu'ad yajita Amman yamata shiru har suka Isa gida babu Wanda yayi magana. Wash🤦🏼‍♀kuyi hak'uri da wanan🥰 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg65 Bayan shigan Husna da FU'AD gida suka tsaya wajen mumcy daga baya FU'AD ya haura ya watsa Ruwa. Washe gari FU'AD ya koma d'akin sanaya ji yake kamar Kar ya kwana part d'in nata duk ji yake yafi samun nutsuwa da kwanciyan hankali a part d'in da ya Saba kodan mumcy Bata Mai wuyan gani ne oho Dan acewar shi saboda mumcy yafison kwana da hutawa a b'angaren. Tun safe bayan tafiyar FU'AD office Husna ta Shiga d'akin shi ta gyara Bayan ta Gama gyara nata ta feshe d turarukan freshners masu kamshi da tsada ,tazo zata gyara falo ,taji Ana kwankwasa k'ofa ko da ta bud'e suka gaisheta cikin girmamawa ta amsa da sakin fuska ,suka sanar Mata da umarnin mumcy na Aiko su su gyara Mata saman da tayi,Husna batason jayaya da mumcy sai ta Basu izinin gyara Fallon kawai ta kulle d'akunan ta Bayan ta sanar musu ta gyara su Dan su 2 ne. Bayan Husna ta Gama komai ta shirya tsaf ta sauka ta gaishe da mumcy ta zauna ta karya a kasan. Da yamma Bayan FU'AD ya dawo sai da ya Fara zuwa wajen mumcy ya dubata sanan ya haura sama ya Dan ganin lafiyar Husna Amman sai yace wai Abu ze dauka daga Nan ya bige da taje kasa tasa akawo Mai wani Abu daze d'anci ,cikin ladabi Husna ta tafi kasan da kanta ta had'o Mai abincin ba wani me yawa ba Dan tasan cin sa me kama da na gulma. Bayan ta kawo Mai ,ta ajiye Mai komai da ya kalla cikin tren gwanin birgewa da kayatarwa Amman sai ya basar ya Fara cin abincin Yana tambayan ta "Akwai Abin da take buk'ata Dan mumcy tace duk Abin da takeso ko buk'ata ta dinga fad'a" Husna a cikin Ranta tace "hmmm wato mumcy ce ma tace har yanzu halinka na Nan" Afili kuma tace "Bari na gayama Mumcy in Ina buk'atar wani abun kamar yadda tace ma. Sai FU'AD ya kalle ta yace "toh ai ba ita Zaki gayama ba Dan ba ita take Auren ki ba ,Kar naji kince Mata komai game da buk'atar ki" Husna murmushi tayi tace "toh in inadashi na fad'a Amman yanzu Kam babu Kuma nagode" Sai FU'AD yace "da akayi me kike godiya? Husna tace"da kulawar mumcy" FU'AD au ta mumcy ce ma? Sai Bayan ya furta Kuma sai yaji Kar ta Raina shi yasa ta Fara Jin ita watace" Husna "eh ko kulawar kace? FU'AD da mumcy kike magana ko danta? Husna da danta ,toh nagode d kulawa" hakan Yama ? FU'AD kunya yaji Amman ya basar sai tsare gida da ya k'arayi ma. Sosai FU'AD yaji kamar Kar ya koma wajen sanayan gashi harda kwana ,yanata son Jan Husna da Hira Amman Taki sakin jiki suyi sosai duk da shima da salon jinkai yake Mata hirar,ita Kuma so takeyi ta sauka wajen mumcy,ganin bashi da niya sai kawai tace Mai ita Tana wajen mumcy. FU'AD cewa yayi ki Bari mu sauka tare. Husna tace"toh" Ganin yanata yanga d cin abincin Kamar bazeci ba sai ta Mike Tana cewa "Ni na tafi sai ka sakko Naga ba yanzu zaka Gama ba" FU'AD wani irin kallo ya Mata Yana cewa "haka Kika koyo a India? Husna da bazata ta kulashi ba ,Amman tace "ai da Haka na koyo da baka samu ganuna ba bare har kaci nasarar taho Dani ,kasani India da wandanda nakedasu a can sunmin komai kamar yadda sukama Dan Albarkacin su kaci na biyoka muka dawo Dan Haka ka gode musu,Musamman ma yya Affa......Bata k'arasa ba FU'AD ya dakatar da ita Abin ya motsa. Dakata ba tambayar ki nayi ba ke kuka sani keda shi da ya hanaki zuwa ai ko yanzun ma yazo ya maidake sai nafi Gane cewar shi yake saki ko hanaki ko Baki umarni,fuuuuu Fu'ad ya bar abincin yayi hanyar waje batare da ya jira su sauka taren ba. Bayan shi tabi Tana Mai dariya karkashin zuciyar ta ,Bayan sun sauka kasa , mumcy tace Kai Kuma fa Naga kamar me jin bacci? Kafin ya Bata amsa da kanshi ke ciwo ,Husna tayi saurin cewa "wai bacci d gajiya ne suka tarun Mai shine nace yaje ya huta a inda ze kwanta ko hajiya? Mumcy hakan ya birgeta Dan dama tasan Husna Bata da matsala da sanaya ,sai tace "hakan yayi kyau" Shi ko FU'AD harara da mugun kallo kawai yake bin Husna dashi ,yanzun Nan ta gilla karya har ya Rasa tacewa? Dole sai ta nuna tafa girma ta Fara sanin takan duniya da salon zama da mutane? Ficewa yayi Yana ma mumcy sallama ,Husna sai itama tace"ahuta lafiya a mik'amin gaisuwa ga madam" FU'AD yi yayi kamar beji me tace ba ,sai da mumcy tace "son bakaji me Husna take cewa ba? Sai FU'AD yace na amsa batare da ya juyo ba ya ficewar shi. Husna gwalo Tama Bayan shi ,ta daukema mumcy hankali da Hira. FU'AD sashin sanaya ya Shiga beganta afalon ba ya wuce d'akin shi kawai. Can sanayan ta fito Tana daga murya waye ya shigo babu kwakwarar sallama bare ya l'ek'a ya duba mutane? FU'AD shiru ya Mata can dai ta gaji ta l'ek'a k'ofar d'akin shi ,mallam unguwa zani anjima ,sai FU'AD yace dalibar malam a makarantar marasa tarbiya da mutunci babu inda Zaki har sai anladabtar dake shika shikan koyan yadda ake tambayar fita unguwa. Sanaya murmushi tayi sanan tace "hahaha wai koyan tambayar fita toh Kai har ganin ka kake kakai wani namiji tsayaye agidan shi Wanda ya amsa sunan shi? FU'AD sai cewa yayi "ban Kai ba Amman ahakan akaso yimin fyad'e ai ,babu inda Zaki waya sani ma ko irin uzirin zakije ki gabatar acan inda zakin ya karasa acikin zuciyar shi. Sai ko tace "me kace banaji yi yadda zanji Kar kaji tsoro ko shakka kaji amsa son ranka" FU'AD harara y jefa Mata yace nace babu inda Zaki Kuma wlh Kika fita Zaki gane waye FU'AD ayau dinan in kina Wasa ki gwada. Ya rufe k'ofar d'akin shi ma yabarta awajen. Zuwa gobe insha ALLAH🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀ [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg67 FU'AD dai Mai afkuwa ta afku, azuciye yayi wani yunk'uri yayi wancakali da ita idanun Nan jazur ya Mike Yana surfa mata masifa ya fice daga d'akin Yana ALLAH wadai d Hali irin naki Kuma zakisan kin aikata min wanan aikin da kikayi abaya wanan shine kuskure mafi Muni da Kika aikata agareni da rayuwa Aure na dake y wuce d'akin shi Yana huci. Sanaya ma yunk'uri tayi d taga haikan fita zeyi Bata damu da furucin tozarcin da yake Mata ba ta sake kamo shi ,y tureta y rufe k'ofar y wuce d'akin shi. Komawa sanaya tayi ranta abace Tana Jin wani irin Abu game da FU'AD din d kuka ta fad'a gadon Tana Jin babu Abin da yafi wulak'ancin d Fu'ad y Mata a yau ta bashi kanta Amman zagine tukwici ta? FU'AD tun shigar shi d'aki y fada gadon yanata wani irin Abu Mara misaltuwa Addu'a samun daidaiton nutsuwar shi d illahirin gabobin shi ya dingayi ,sosai yayi dauriya a yanayin d yake ciki. Sanaya d ta Gama kukan g dare y Rana duk d ta samu biyan buk'atar ta Amman Babu Abin da ta fahimta aciki Dan Haka t Mike ta d'auko key din falon d na d'akin duka biyun ta fita ta mayar d na jikin k'ofan sanan ta ajiye Mai na d'akin shi a center table ta koma d'aki ta rufe kanta tanata takaucin taurin Kai da hali irin na FU'AD gashi Tana bala'in son ya kusance ta duk da Taki yadda yadda Fara kamuwa da son shi. FU'AD kwanan wuya yayi kusan kasa bacci yayi sai d yajiyo Kiran sallah asubahi y samu yayi wanka ya dauro alwala sanan ya fito d niyar dosar d'akinta ko a tsiya ko a Dadi, har y nufi d'akinta sai yayi tozali da makulin dake center table d'in Rai a b'ace ya d'auka y nufi k'ofa ze zura sai yaga na jikin k'ofar k'wafa yayi ya bud'e kawai ya nufi masallaci. Bayan y shigo gidan ya nufi sashin su mumcy sai ya tuna ai Basu bud'e ba har ze koma sashin sanaya sai yaji beki ace yabar sashin Bari na har abada ba Dan Haka dama d wayar shi ya fito sai ya Kira Husna a waya har ta katse Bata d'aga ba sai d ya sake Kira sanan ta d'aga cikin maganin bacci cikin murya Mai kamada rada Fu'ad ya umarci Husna d tazo ta bud'e Mai k'ofa Kar mumcy taji Kuma,zata Mai magana ya kashe wayar ,Husna d Ido tabi wayar da kallo. Bayan husna ta bud'e Mai sai taga mutum ya Kama hannun ta ya cire daga k'ofan d take Shirin rufewa ya rufe ahankali ya sake kamota suka haura sama kamar mara gaskiya har sai da suka Shiga falo sanan y sake ta ,Yana raba jikin shi da nata yaji Abu ya dawo Mai sabo a take ya Kuma Shiga wani yanayi. Husna na tambayan shi lafiya koroshi akayi? FU'AD be samu damar Bata amsa ba ya wuce d'akin shi a zaton shi ko ze samu sasaucin Amman Ina abuma sai gaba_gaba yakeyi Dole ya d'aga waya ya Kira Husna ,Bayan ta d'aga umarnin zuwa d'akin shi y Bata be tsaya ta tambaye shi ba ya kashe wayar. Husna da har tayi biris da umatnin nashi ,Amman sai ta mik'e da kayan bacci ta yafa siririn gyale ta Shiga d'akin bakinta d'auke da sallama , FU'AD kasa amsa sallamar yayi yanaya murkususu a gado alamu Akwai matsala. Husna Jin shiru be amsa sallamar ba ,Abin har ya k'ular da ita ta fusata zata fice Tana cewa" shikenan dama Haka kawai aka Kira mutum babu dalili tunda sallama ma Babu damar a mansa maka har ta Kama k'ofa zata fita" sai FU'AD yace "waalaiki sallam" cikin wata kasalaliyar murya Mai rauni da neman agaji ,Husna Abin tsoro ya Bata Dan Bata sanshi da irin muryar ba ,d sauri t dawo ganan gadon ta Kira sunan shi Tana tambayan shi "lafiya kuwa? FU'AD nuni ya Mata da bedside d murya raunaniya "dubamin wani magani a ciki ki taima kamin d Ruwa" D sauri Husna ta d'auko ruwan roba t lalubo wani magani Tana cewa" gashi tashi kasha" FU'AD hannu y dinga Mika Mata ,itama mikamai ta dingayi ganin hanun su Taki kaiwa sai ta d'an hau gadon ,ruwan kawai ya karb'a Yana cemata "kamani na tashi" Husna tsakani da ALLAH ta Fara kiciniyar kamashi ta bud'e| ruwan ta ballo maganin Tana Shirin samai a Baki Tana Shirin bud'e Ruwa FU'AD ya goce ya Fado kanta ,Husna kiciniyar kwacewa ta Shiga yi Amman Ina FU'AD ya mak'aleta ta ko Ina sai sambatu da kalamai yake zuba Mata ,tureshi ta dingayi Tana cewa" mugu Mara cika alk'awari Ni zakama dabara" Duk yunk'urinta Husna kasa kwayan kanta tayi daga hannun FU'AD sai da ya cimma burin shi sanan ya Sami sukuni. Husna taci kuka tayi magiyar tayi ban hakuri Amman har sai d kuka ya rinjayi maganar ta. Bayan FU'AD y dawo hayyacin shi ,Husna na ta kuka tana Shirin tafiya d'akinta FU'AD ya kamota daga rarashi da bada hak'uri sai ya sake nausawa birnin karaye sosai Husna da jigata , FU'AD nata aikin rarashi da magiya. Husna taci kuka kamar ranta ze fita , FU'AD yayi rarashi kamar ze Ari Baki sosai yake rarashin ta Amman Ina ta zuciya gashi gari ya waye sai yanzu yake kunyar Kar mumcy ta ankara Yana sashin tayi zargin me ya kawo shi? Jin kukan Husna ya mantar dashi tuhumar mumcy kawai ya koma d'akin Husna ya dinga Bata hakuri nuna Mata bada niya ko sa kanshi hakan ya faru ba ,Husna tsawa ta daka Mai Tana cewa" Daman ka Saba Haka ka fad'a kwanaki ma" FU'AD d kyar y samu husna ta Dena kuka,da aka umarci me Aiki ta Kira Husna su karya da mumcy "FU'AD sai cewa yayi akawo Mata sama a had a harda shi yanzu y shigo a gayama mumcy,komawa akayi aka idar da sak'on oga FU'AD. Mumcy mamaki ta dinga yi daga baya ganin cewar matar shice Kuma ya Fara damuwa da son ta duk da yaki yadda sai kawai ta share zancen. Bayan ankawo musu ,d kyar FU'AD ya Shawo Kan Husna tad'an ci wani abun yanata ji kamar ze giyata Dan yasan yau ta taimake shi ayaune kawai ce iya cewa tamai hallaci a rayuwa Dan ya manta wacan lokacin. Husna Abin har mamaki yake Bata ,Amman in ta lura da yadda yake Mata ayanzu Bayan ya cucewata sai taji ai badan ALLAH yake Mata hakan ba sai tayi watsi da Jin dad'in kulawa da tarairayar da yake Mata. FU'AD ya Gama yanke shawarar yau ko Aiki baze fita ba ,har mumcy Kiran shi tayi awaya sai ya nuna Mata bayajin dad'in jikin shine ,ta umarci da yaje asibiti ko likita yazo ya duba shi ,sai yace Mata ai gajiyace kawai ya sani ze warke insha ALLAH kuma Yana samun kulawar husna, mumcy cewa tayi toh shikenan sai na ganku in bakuzo ba Ni nazo dubiya,sosai FU'AD yaji kunya Bayan ta amsa yabata fargabar Kar ta hauro din da gaske. Husna ma Abin duk nauyi y Mata yau ta kasa sauka kasa ,ko tayi k'ok'arin sauka sai FU'AD ya hanata ta hanyar tambayar ta Abin da take bukata Abin har mamaki ya koma bata. FU'AD d Husna Basu suka sakko ba sai azahar shima Dan FU'AD ze fita masallaci ne ya lalaba Husna suka sakko Kar mumcy ta tambaye ta Dan yasan Dole Ayi Haka.... Sanaya dai Abin duniya ya Fara isarta mamanta Tama waya Akan itafa zata taho Egypt ta gaji da auren d suka Mata naki Dan ......sai ta kasa fada Tana gudun Kar zargi ya biyo Bayan bayannan ta. Maman ce tace"Dan mme fada min duk matsalolin ki inbaki fad'amin ba wa Zaki fad'ama a matsayina? Sanaya cire kunya tayi tace ,Daman baya bani hakin Auren d kuka Mana ne jiya har neman shi nayi yaki kulani kuma ma..... Bara k'arasa ba maman tace,sanaya me Kika zama har ke kike neman shi ? Ai ban taba tunanin lalacewan da kikayi a Nan yakai ki nemi namiji ba haka, wayace ki nemeshi bakisan komai ze iya faruwa ba? Ko yace Baki da tarbiya ko yace kin saba bin maza.... Sanaya kuka tasa Abin da take gudu ya afku Amman tasan Mama bazata Bari maganan ya fita ba zata kashe shi Dan Haka ta sake cewa "haba mum kekika ce na fad'a Miki kuma gaskiya na nafada Miki kinsan dai Ni ba dutse bace tun kawo da kuka girke be tab'a kulani bafa maganan da nakeson ki Gane ace banki tonamai asiri tuni ba sai yanzu Dan na fad'a har kema zakiga nayi laifi? Mum cewa tayi ehtoh kema kince wani Abu kinyi daidai kinyi ba daidai ba koma dai meye kawai wanan maganar kartaje ga dadyn ki Amman Akwai ta inda Zan billoma lamari sanan Kar ki Kara nuna buk'atan ki gareshi kina mace Mai class Haka Dan kin banbanta da wawiyar da suka Kara aura Mai din can kinji ko? Sanan zamuyi magana kinji ki barmin komai a hanuna. Sanaya tace "toh sukayi sallama" Bayan Husna ta sakko suna Hira da mumcy FU'AD har yaje yayi sallah ya dawo ya shige cikin su Yana tayasu hirar sama_sama Husna inta kalle shi suka had'a ido sai ta Harare shi , FU'AD sai ya dauke Kai,kusan so biyu Husna na hararar shi d alamu haushin shi takeji ,sai ya fito da dabarar da ze goge haushin shi da takeji sai ya d'aga waya ya Kira B2k suna hirar office sai B2k ya sako hirar Aisha ,sai ko Abin Yama FU'AD dad'i suka dinga magana har FU'AD na Kama sunan Aisha Ghana yanayi Yana Satan kallon Husna tanajin sunan tayi wani iri har kusan tsare Fu'ad tayi da kallo batare da ta sani ba fal tambaya a tare da ita ,har FU'AD ya ajiye wayar Husna neman Karin bayani take daga FU'AD din Dan tanason gaskata bayanan dake fita daga bakin FU'AD Akan Aishar da take zargi. Bayan FU'AD sun Gama wayar sai yafara cewa"hmmmmm kunsan mutumin nawa ya kusa zama ango Yar gida zamuyi insha ALLAH. Sai mumcy tace wakenan? Kuma dawa za'ayi Yar gidan? Itako Husna da Ido take tuhumar shi idon ta kir akanshi Taki daukewa Dadi hakan yamai ko banza ya samu attention d'inta yanzu sai yace"B2k ne soyayya ta kullu tsakanin shi da Aisha k'anwar matar Yaya Jameel wacce ta zauna da ita d'inan ko nace kawar Husna Dan kufi ganewa wacce sukayi rayuwa tare a Abuja. Husna mamaki tayi har batasan lokacin da tace Aishan? Da B2k naka? Mumcy ko cewa tayi "Masha ALLAH" ALLAH yasa yin na ALLAH ne Abu yayi Dadi ai tanada hankali gwanda ta dawo kusa da Yar uwarta. FU'AD sai da ya amsa Addu'a mumcy kafin ya amsa tambayar Husna da cewa sudai Kinga kawar ki zata dawo kusa daku sai kawancen ku ya Dora. Husna murmushi Mai kayatarwa tayi da ya sake bayyanar da kyanta yayi gagawar korar haushin Fu'ad , FU'AD ma Dadi yaji yayi hamdala da dabarar Nan d yayi na sanyata cikin Nishad'i. Kiran wayane ya shigo wayar mumcy ,Bayan ta d'aga sai take cewa ai na shafa'a da maganar taron Nan Amman insha ALLAH zanzo ko ba Akan lokaci ba zuwa anjima Kar ku damu ai aikin mune munsaba. FU'AD tun da yaji Tana maganar ai aikin sune yasan maganar foundation dinsune na talafawa marayu da gajiyayu da nakasasau Yana tausaya Mata akan zirga_zirgan da takeyi itako Bata tausayin Kan yayi_yayi akan ta wakilta wasu ta wakilta din Amman duk da Haka Tana Kai musu ziyara d zuwa dubawa abubuwan dake gudana in shi ko Yaya Jameel sunyi magana tace hakan yanada kyau su bazasu Gane bane tunda har mahaifin su be hanata ba toh Suma Dole su kyeleta acewar ta ai ba Aiki take ba kawai nata shawara ne da ziyarar gani da Ido talafin ta ta account d turawa abayar suke zuwa ba ita da kanta take bayarwa ba akanme zasu hanata. Bayan ta Gama wayar , FU'AD ya bud'e Baki zeyi magana , mumcy tayi saurin dakatar dashi da cewa "Fu'ad inace mun Gama wanan maganar? Bana son Jin komai sanan umarni ba shawara ba yau da Husna zamu Dan inaso zamu biya ta gaishe da hajiya karima Dan nagaji da zubama ido duk d kasan yadda nake da ita Amman baka tabamin karar kace zakakai wata daga cikin matanka ba Dan Haka Ni yau zankaita da kaina. FU'AD Babu yadda ya iya da hukuncin mumcy Dole yayi shiru ,Yana sauraron mumcy na cema Husna ta shirya Bayan la'asar zasu fita zasu *HAJIYA BABBA FOUNDATION* daga can zasu biya gidan kawarta su gasheta, sai d mumcy ta gama sanarma Husna,Husna ta amsa da "toh hajiya" FU'AD ganin babu fashi cikin tafiyar Kuma yau harda Husna ,ganin bashi da ikon hanawa sai kawai ya fito da dabarar cewa ze kaisu da kanshi. Mumcy murmushi tayi Mai tarin ma'anoni sanan tace ma Husna "kinji Abin da yace kin amince? Ko driver y kaimu kawai? Tambayar a wata iri tazoma Husna Amman ganin kamar da biyu mumcy take tambayar sai tace"eh hakan ma yafi sauki ya samu ladanki ma hajiya" FU'AD wani irin kallo Yama Husna Yana ayyana gaskiya ta samu fada da yawa a wajen mumcy sanan ya Fara tunanin karfa ta Raina shi Dan taga ya sakar Mata kawai yayi hakane Dan......sai ya kasa k'arasawa kamar wani najin shi alhalin shida zuciyar shi suke magana,sai kawai ya kawar da kallon shi daga Kan Husna zuwa wayar shi. Bayan la'asar Husna ta shirya cikin wani leshi Mai Baki da ja Mai kyau da tsada ya karbi jikinta dinkin Riga da zani da gyalenta Baki da Jakarta da takalmin ta duk bakake tayi kyau tayi kwaliya ba Mai yawa ba tasa turarenta masu dad'in kamshi tunda da FU'AD zasu fita da ita kad'ai ce da humra zata sa. Bayan ta sakko tayi masauki wajen mumcy Dan FU'AD ya shirya su yake jira Dan mumcy shi ta farama magana ,tunda Husna ta k'araso Fu'ad ya kafa Mata Ido yanason magana Yana kallon mumcy ,gashi mumcy ta gama shiri tafiya zasuyi Dan ta d'auko komai d zata Shiga d'aki da ya samu damar amayar da ta cikin shi ,da zasu fitane sai mumcy ta l'ek'a kitchen tab'ama su Harri magana suna Mata adawo lafiya ,shine Fu'ad ya samu damar cema Husna ,kinsan cikin mutane zaku Shiga Kika yafo gyale ko? Sai tace "toh me Zan saka? Naga tare da hajiya zamu bafa biki ko wani shagali zamu ba. Suna cikin haka har hajiya ta fito taga FU'AD ya tsatsare Husna da Ido alamun magana yake Mata Akan wani Abu sai tunanin ta ya Bata ko takurata yakeyi....... Shiko FU'AD ganin mumcy sai yayi saurin cemata ,kije ki sako hijab yasha mur kamar bashi ya furta ba. Mumcy d himma ta k'araso kafin Husna tabi umarnin shi ,sai mumcy tace ya akayi Kuma? FU'AD cewa yayi "babu komai" Sai mumcy tace "toh mutafi" Fu'ad din Dan takaicin katse Mai hanzari da mumcy tayi sai yayi gaba ya barsu. Husna Dadi taji ta karbi jakar hanun mumcy suka bishi a baya. Har sukace FU'AD na kula da motsin Husna har ya kaisu gidan hajiya karima har ya dawo dasu gida har ya tsaya ya siya musu fura a Rufaida Dan mumcy nason fura da nono sanan ya dawo dasu gida. Bayan sun dawo gab d magrib, Bayan sun idar da magriba Husna taci abinci ta k'oshi ta haura tacema mumcy ta gaji ta Mata sai da safe ta shige d'akinta ta rufe tanaji FU'AD ya dinga bigawa tamai shiru adole tayi bacci. Washe gari Fu'ad y koma sashin sanaya ze d'auko wasu takardun shi ,ta ganshi ta Fara Mai rashin kunya ,yayi kamar ze mareta ta goce ta cigaba da Mai ya tusa Mata haushi da mumanan kalamai ya fice ya barta. Takun saka ne ya dinga Shiga tsakanin sanaya da FU'AD. Husna ma nesa takeyi d FU'AD Dan ba sosai take sakewa dashi ba in suna zaune a falo suna Hira ,shiko ya fahimce ta sai yayi kamar besan me take nufi ba. Aisha sunyi hirar B2k da Husna ta through chart sosai tanata nuna Mata farin ciki ta. Aunty sa'adiya ma tanata murnar dawowar Yar uwarta kusa da ita Dan tafi kowa Jin dad'in Haka. B2K Yaya Jameel ya wakilta Akan ya shige Mai gaba wajen neman Auren Aisha Dan har anshirya zuwa gaisuwa da rok'on iri zuwa Ghana dama aunty sa'adiya zata ganin gida ,tafiyar kuma da Yaya Jameel d B2k da FU'AD d sa'adiya da Husna za'aje sa'adiya ce ta had'a tafiyar harda Husna Dan Fu'ad yaso ta zauna agida Amman ganin mumcy tasa Baki sai ya hak'ura badan yaso ko yayi Amman da hakan ba. Maman shaheed😍 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIK'ON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* 💥 *ROMANTIC WRITER'S ASSOCIATION*💥 Pg 68 Tafiyar su Yaya Jameel Ghana saura sati biyu Husna nata murna ,Aisha ma daga can tanata murnar tozali da Rabin ranta B2k da kawarta d yauarta aunty sa'adiya. Mama habee bikin humaira ya matso saura sati 3 shiri sukeyi sosai Alhajin birni nata sauke musu kabakin arziki na kwalam da ma kwalashe yanzu Kuma na kud'i duk da ba wani uban kud'i bane Kuma kudin abanza yake tafiya Dan ci banza ci wofi sukeyi da kudin sai Abin da ba'arasa ba, baba dama Husna ta bashi waya sai ya kirata yake Gaya Mata Akan karta ji labarin bikin Yar uwarta humaira duk da su Basu d'auketa Yar uwa ba,zatayi Aure Amman ya shawarce ta Akan karta damu inbata samu damar zuwa ba ta bisu da Addu'a Dan Akan su habee duk abin da tayi musu daidai ne. Sosai Husna tayi mamakin bikin ta musu fatan samun zaman lafiya tace ma baban Tana Nan zuwa Daman Dan zatayi tafiya da su FU'AD zuwa Ghana zatazo sanar Mai intazo sai ta musu fatan Alkhairi Dan watakila Bata Nan za'ayi bikin duk da batasan yaushe zasu dawo ba,baban yace toh ALLAH y kawota lafiya. *INDIA* Sosai su Affan da sadeeq sukayi mamaki yadda ammin su huwaila ta b'oye musu cewa Husna Yar Yaya ce wacce take jinyar ta Amman ta b'oye musu har husnar da take matsayin 'ya agareta ,Nan suka dinga tambayar hujar yin hakan? Aunty huwaila bayani ta musu yadda zasu fahimta agaban Yaya mahaifiyar husnan take musu bayani ,sosai bayanin Amin nasu ta gamsar da su muhibbat kowa na murna na gidan burin kowa Kuma be wuce yaushe zasu saka Husna cikin farinciki ba Dan tasan cewa wacce takejin wani Abu Mai kama da shak'uwa tsakanin su itace mahaifiyar ta,Nan sukayi shawarar yadda zasu sanar Mata ta hanyar Kai ta har 9ja tare da Rakiyar Affan da sadeeq Daman bawan ALLAH da yake taimaka Mata ya samu labarin warkewarta yanata so ya ganta. Tafiyar su Husna saura sati 1 inda bikin humaira saura sati2 har sun Fara rabon invitation card. FU'AD najin Husna ayanzu ta zama wani sashi na jikin shi Amman har yanzu zuciyar shi Taki gaskatawa Kuma baya k'aunar ta kaurace ma ganin shi. Sanaya sunyi mamana da mum dinta ta Bata dabaru duk yadda zatayi ta mallaki FU'AD da Abin da suke dashi na duki ta hanyar samun ciki dashi Wanda ita da dadyn sanayan suka zauna suka kirkiro wanan dabarar ,sanaya taji ta Kuma d'auka Dan yanzu babu Abin da takeso da ya wuce Fu'ad ya kusance ta Dan Haka ta karbi shawarar su ,Amman inda gizo ke sakar ta Ina zata same shi har da guziri Wanda yake ikirarin cewa na Rasa shi har abada Kuma abakar zuciyar shi tasan ze aikata Dan Haka yazama Dole ya karbeta matsayin matar shi Koda tsiya Koda arziki Dan Dan yanzu ma ta Fara buk'atar shi. Yau su Yaya Jameel zasuzo Dan jibine tafiyar su Ghana insun huta agidan mumcy. Bayan isowar su Yaya Jameel Husna d muena ta d'auki baby Mami ta Shiga aikin renon ta har FU'AD ya dawo Shan nono ke maida ta hannun mamanta. Adaren ranar kusan kwana sukayi suna Hira gaba d'ayan su har sanaya sai da mumcy ta takura Mata ta fito ta Shiga cikin su badan taso ba tsakanin ta da FU'AD sai yake kawai ,kowa na Hira da farinciki Amman Banda sanaya sunci sunsha kafin kowa ya tafi hutawa. Gobene tafiyar su Yaya Jameel Ghana sunsai musu tsaraba Banda Wanda mumcy ta Basu sun Gama Shirin su akwatin kayan Fu'ad d Husna daya kamar yadda na Yaya Jameel d sa'adiya yake guda sai baby bag din Mimi, B2k sai gobe ze bugo musu sammako. Washe gari d asuba mumcy tasa aka shirya musu komai na kumallo sai da suka had'u sanan suka karya suna cikin karyawa B2k ya taho , Fu'ad yanata Mai tsiya wai shi angon kwanan Nan,Bayan ya gaishe da mumcy ya gaishe d su Yaya d sa'adiya kafin suka gaisa da Husna FU'AD Yana cewa "Bari kuga Mara mutuncin Nan baze gaishe niba fa" sai B2k yace "Waze gaishe ka kauce buba Yana Mai gwalo. Bayan sun Gama ansa musu Kaya a mota driver ze kaisu Airport. Da tirsasawar mumcy FU'AD yaje yama sanaya sallama ,sai da ya kusa mangareta kafin su rabu Dan har macuci tace Masa,ya fice ya rabu da ita. Har bakin mota mumcy ta rako su Tana musu Addu'a sauka lafiya ,sunata amsawa Yaya Jameel a gaba FU'AD d B2k a baya sa'adiya d Husna a gidan Bayan su d Mami. Bayan jirgin su ya d'aga zuwa Ghana,Suma su Aisha Ana can anata faman Shirin tarban jama'ar ta Dan ta Gama musu tanadi. Su humaira anata ahagali Aure wani satin angama tsara komai mama habee taso aje aga gidan angon yace ba sai sun wahala ba sudai Amarya kawai zasu kawo Akwai komai,mama habee aka buga shewa da guda aka Fara sakar ma baba habaici Ana cemai ya rik'e gadon bonon da yake shirin tozarta humaira dashi kamar yadda aka Kai Husna zikau ta dangwali arziki itama humaira haka zata tarar Dan haka basa buk'atar komai nashi. Baba murmushi ya sakar musu Mai Kama da gargadi ,kafin yace ,ba girin girin ba dai tayi Mai,kuyi yadda kuke so habee ALLAH ze nuna Miki aikin ki tun aduniya kafin ki shude. Mama habee d masifa d tsiwa tace ,zatayi Mai har da naso bakinka ya sarin bangon gidan ka, Kuma wlh babu wani aikina da zangani. Baba bar Mata gidan yayi Yana Mata fatan shiriya. *INDIA*........ Aunty huwaila ta Gama shiri tsaf akan yayar ta ga wani shak'uwa da yake Kara Shiga tsakanin su har suna Jin kamar Kar su rabu gashi sunaso su had'asu da Husna yarta kodan samun farinciki Husna d yayar ,Dan jiya d Husna ta kirasu zata musu sallama tafiyar su Ghana sai da sujaji kamar su Gaya Mata Amman aunty huwaila ta fasa Dan tafison tayi tozali da ita har baba da tafiyar iya Affan da sadeeq ne Amman yanzu tafiyar har aunty huwaila d su muhibbat d Husna Dan ba zuwa sukeyi ba Dan Haka zuwan nasu ya Kara Nisa Amman Nan d sati 1 zasuzo daidai da bikin humaira. Matafiya sun sauka lafiya sun Sami tarba na girma,Aisha sai sunkuyar da Kai takeyi na kunya aunty sa'adiya kuwa ta saki jiki sai murna ganin iyaye da Yan uwa takeyi. Bayan sunci sun Sha aka Basu masaukin da zasu huta har kwana kafin suyi abin da ya kawo su. Sosai suka dinga Jan Husna Akan ta saki jiki dasu,sun sanar ma mumcy saukan su lafiya ta musu fatan huta gajiya. Bayan sun huta aka musu iso zuwa gun baban su aunty sa'adiya suka gaisa yanata farinciki da zuwan su kafin FU'AD da B2k suka ba Yaya Jameel d baban nasu waje Dan isar da sak'on abokin FU'AD din. FU'AD ne ya umarci Husna d ta kirama abokin nashi sahibar shi,Husna har Fallon Tama Aisha iso suna ganawa da masoyin nata shima FU'AD acan nesa da su Yana hirar Dole da Husna Dan gani yake kamar antakura shi gashi kwanan Nan sai ya dingajin wani Abu game da husnar sai yayi kamar ze bayyana Mata tsagwaron son ta sai zuciyar shi ta Hana shi ta nuna Mai faduwar mutuncin shi da darajar shi ne ze billo baya sai ya Adana zuwa lokacin da Hali zeyi. Husna ko sosai ta saki jikinta Tana Jan shi da Hira Yana amsawa Yana Mata tambaya Tana bashi amsa itama sunayi suna kallon dacewar da B2k da Aisha da sukayi ,can Husna take ba FU'AD labarin zuwan su aunty huwaila 9ja da ahalin ta har matar da ta bashi labari Mara lafiyar Nan Amman yanzu ta Sami sauki ,sai Fu'ad yace "Amman zasu kwana biyu har zamu koma mu same su ko? Husna "eh" tace Mai. Husna fata Fara Gane Fu'ad Yana son ta ya damu da ita ba sai da ta nuna Mai rashin Jin dadinta na halartan bikin yayarta humaira da bazatayi ba. FU'AD futitikewa yayi Yana Mata fad'an rashin sanin ciwon kanta mutanen da suke son ganin bayanta da zasuga ranta da zasu d'auka Amman ita Tana damuwa dasu,ganin yadda yake bilhakki da gaskiya yasa ta fahimci sai ka damu da mutum kake tatalin lafiyar shi Dan Haka yace ko sun koma babu inda zata zeje har gida Yana baba hak'uri da uzirin yin hakan. Suko su B2k da Aisha anata zuba luv ,sai da aunty sa'adiya da Yaya Jameel suka shigo suka raba tsakanin masoyan hudu. Aunty sa'adiya ce ta shawarce su da fita Sudan ga gari ,ta had'asu da wani k'anin ta saurayi Amaduu su sai gobe sai su fita gaba d'ayan su suyi ziyara gaba dayan su. Basu dawo ba sai gab da magrib ,su Husna anata hirar soyayya da Aisha. Bayan sunje masallaci sunyi sallah dawo aka kawo musu abincin suka Dan taba Hira gaba d'ayan su zuwa Bayan Isha kowa ya nufi masaukin da aka bashi Dan kwana. FU'AD ko Abu zai tambayi Husna sai ya kirata a awaya su Aisha sunata tsokanar ta wai ta zama rik'e wuyan Fu'ad Amman ya dinga basarwa Bayan mun sani. Kusan kwana sukayi suna Hira. Washe gari da safe har d Husna aka Shiga kitchen aka shirya girki maman su Aisha nata yabon kirki irin na Husna har suka kammala suka kaima su Yaya Jameel nasu Suma sukaci nasu kafin sukayi wanka suka shirya Dan ziyara zasu yau da ganin gari. Bayan sun fito cikin Shirin driver ya d'auki mota Yaya Jameel ne agaba dai matan na baya su FU'AD na tsakiya suka nufi gidan yayan mahaifin su aunty sa'adiya,isar su aka tarba Mai kyau da girmamawa. Bayan sun fito suka nufi gidan kakanin su aunty sa'adiya ,kusan ziyarar Nan Tama sa'adiya da Yaya Jameel Dadi Dan be tab'a wanan ziyarar ba sai sanadin neman ma B2k Aure,kusan hakanne ga Aisha Dan ko yanzu dangin ta sunsan wa zata aura. Sosai sukayi ziyara suka zaga gari sunga gari daga k'arshe sukaje wani wajen shakatawa kowa da wyfin shi Husna ma da FU'AD har bakin Ruwa sukaje gab da bakin ruwan ne wani irin jiri ya dibi Husna tatafi luuuu kamar zata afka ruwan badan Fu'ad yayi sarin rikota Yana tambaya ta lafiya ba da ta fada. Runtse ido tayi d sauri hankalin su aunty sa'adiya d su Aisha y dawo kansu FU'AD da Husna, gefen ruwan ya zaunar da ita Kan wata kujerar da ika yita ta gini Mai ban shaawa yayi Yana tambayar ta meya sameta? Bud'e Ido tayi d kyar tace "babu komai ji tayi jiri ya dibeta kawai Amman lafiya Lau take" Duk sun gamsu da bayanan ta sai Sanu! Sannu!! Suke Mata Bayan sun Dan taba Hira Awajen ganin walwala ta Dan kaura daga fuskar Husna sai Fu'ad ya nemi da su koma gida kawai,sai Yaya jameel yace "toh muje mudan Sha ko juice ne sanan sai mu tafi,duk acikin wajen ne dai ,da taimakon aunty sa'adiya sukaje wajen. Wani abokin Yaya Jameel ne ya kirashi a waya Wanda ta sanadin shi suka had'u da aunty sa'adiya har ya aureta yake sanar Mai ya dawo gari insun shigo su nemeshi Dan ALLAH. Sai Yaya Jameel yace "sun shigo har suna Shirin komawa jibi Amman gone zasu kawo Mai ziyara dafatan yanada masaukin bataliyar Baki Dan sun kusa su d'ari,dariya Abdulmalik yasa yace "ko su million ne yanada masaukin su ko shekara zasuyi Yana maraba dasu shida me d'akin shi" Yaya Jameel yace toh gobe zasu Zo insha ALLAH,sanan y kashe wayar. Bayan sun koma gida Husna duk jinta take wani iri Taki gayama kowane sai k'arfin Hali da takeyi kawai. Ranar aunty sa'adiya da Aisha kusan kwana sukayi suna Hira Amman Husna tuni tayi bacci Dan ko wayanta a silent tasa FU'AD ya kirata kusan so 3 Amman bataji ba bare ta d'aga,Dan yad'an kula da yanayin ta ba kamar yadda sukazo ba ,Amman ganin ba ita tafad'a Mai da bakin ta ba sai ya kyaleta shima. Washe gari suka dunguma sai gidan su Abdulmalik sunga tarba daga gareshi da Matar shi anty ayna sun Sha Hira sosai Husna ko sai yake kawai takeyi. Basu bar gidan ba sai yamma lis sunso kowama a washe gari Dan adaren ranar Jameel ya nemarma B2k izinin neman Aisha aka tsaida magana da niyar manya zasuzo asaka ranar bikin Nan bada jimawa ba Amman anbashi Aisha Albarkacin Jameel ,da kyar mahaifin su aunty sa'adiya suka ce su Bari sai jibi sai sutafi ,ganin sun gaji tarbiya Basu Saba jayaya da manya ba suka hak'ura zuwa jibin. Washe gari wuni sukayi a gida sai su aunty sa'adiya d Husna d Aisha da suka Shiga kasuwa suiayi siyaya,Bayan sun koma gida maman su aunty sa'adiya taba Husna kyautan setin tukunyar Ghana Mai kyau da tsada da Kaya kirar Yan Ghana har da takalman su masu Aminci har mazan akaba har da tsarabar mumcy ,adaren ranar suka Gama had a komai nasu da niyar zasu wuce gida gobe. Sosai alamun gajiya suka baytana ajikin Husna in antambayeta sai tace gajiyane kawai sai amata uziri Dan ansan Bata Saba zirga_zirga irin hakaba rabanta d irin wanan zirga_zirgan tun kafin ta samu yancin zama matar Dan mumcy wato Fu'ad Dan Haka ta wahala sosai aganin su. Yauma da wuri ta kwanta Bayan sunyi waya da FU'AD taje ta karbi kayan shi tazo ta had'a musu cikin akwatin da sukazo da kayan aciki, B2k ma Hira akasha da Aisha ta bankwana Bayan sun rabu ya koma wajen Fu'ad yake cemai shifa anan zasu barshi Dan yaga waje inze tafi yabar Rabin ranshi a Ghana? FU'AD dukan kafadan shi yayi Yana cewa "baban soyayya to kace adaura kawai ka wuce da ita mana Naga har kana nema kafi masu Auren ma sanin makamar aikin" B2K "bance ba komai lokacine Suma masu Auren asirin su insha ALLAH ya kusa tonuwa munafircin banza sukeyi sunaso suna kawaiwa kasuwa Bayan anyi walkiya mungano komai Sanu sannu Bata Hana zuwa sai dai adade ba'aje ba,da sannu haske zai haska,Inji b2k. FU'AD sai cewa yayi "kaji dashi munafiki hasken inya haska har kyauta zanmaka ka tunanin Inna manta Kai zakasha kunya yaro" B2K dariya yasa yace, Zan tunama kuwa Dan kaikeda Jin kunya Dan nasan ba dutse bane Kai........Yaya Jameel ne ya shigo cikin su suka bar maganar suka koma wata hirar daban. Washe gari kowa na dokin kowa Musamman Husna da takejinta wani iri Amman aunty sa'adiya ji takeyi kamar su barta anan tasan ma jameel baze yadda ba Dan Haka Bata Fara tambaya bama. Bayan sun Gama shiryawa tsaf aka Debi motoci guda 2 da kayan su na tsaraba har Airport baban su aunty sa'adiya yasa aka kaisu sunata musu godiya da fatan Alkhairi ga Auren kowannen su har Aisha akayi Rakiyar d kyar suka rabu da B2k da rarashi. Yau mutanen India ma suke Shiga Nigeria. Bayan isar su gida wajen fitowa daga jirgi Husna sai da jirin Nan ya sake dibanta ga Mimi a hannun ta d taimakon Fu'ad da aunty sa'adiya suka samu Bata Kai kasa ba ,da kyar ta lalab'a ta Shiga mota Dan tuni motar da mumcy tasa adauke su take zaman jiran su tasan FU'AD baya son jira. Acikin mota FU'AD yake cema Husna Akwai Abin da yake damunta sa'adiya ma Haka tace Amman Husna ta kafe babu Abin dake damunta ,sai Yaya Jameel da B2k ne sukace gaskiya ya kamata ko Bayan anhutane taga likita FU'AD yace babu wani Abu Bari mu Isa gidan. Bayan isar su gidan anata raha Bayan anmusu tarba Mai kyau ,a wajen mumcy suka Sami sanaya a yatsune ta musu sannu da dawowa ta Mike tabar falon mumcy sai sawa tayi aka bita da tsarabar ta. Tun shigowar su mumcy ta kula da canjin yanayin Husna Amman ganin tanata walwalarta sai batace komai ba har akaci abinci Amman Tana gamaci yanayinta ya canja da sauri ta haura sama duk Abin da takeyi Fu'ad na kula da ita da sauri yabi bayanta Yana zuwa yaga Bata falo d'akinta ya nufa yaga Bata Nan sai gyalenta a Kan gado sai kakarin amai da yake jiyowa a bathroom dinta. Sai da ta Gama ta gyara ko Ina ta wanke fuskar ta sanan ta fito Tana Nishi ta tafi zata fada gado irin ta huta dinan sai tayi tozali da FU'AD hannun shi a harde a k'irjin shi. Ganin ya tsareta da ido alamar tuhuma be hanata kudirin kwanciya ta huta ba kwantawar tayi ta juya Mai baya. FU'AD dawowa yayi inda tasa fuskar ta Yana cemata "ke bakida lafiya Amma kinata cema mutane lafiyan ki Lau ko? Meke damun ki? Husna yatsuna fuska tayi alamar gazawa da tambayar shi "babu komai nace ma" FU'AD Ido ya kura Mata kafin yace so kike kijamin magana wajen mumcy? Toh ki Dan huta anjima muje asibiti zatayi magana yace "banason Jin komai na Gaya Miki kawai" ya fice ya koma d'akin shi ya watsa Ruwa kafin ya sake lekota yaga Tana kwancen har yanzu sai ya koma kasa. Bayan ya sauka B2k yake cewa ze tafi ya gode da karamcin su gareshi yaya Jameel d mumcy suke cewa Yama Dena wata godiya Dan daya suke dama can. FU'AD ne ya rakashi yasa driver ya kaishi har gida kafin ya dawo. Sai da kowa ya koma sashin shi Dan ya huta , mumcy take tambayar FU'AD Husna yake cemata gani yake kamar Bata Jin Dadi Amman zasu asibiti zuwa anjima , mumcy da tausayawa tace ai basai anjima ba yanzu ya kamata kuje amai karar da ruwan jiki yake kaga Tana aman Amman kazo kayi zamanka anan amanar da ka karbo daga indiya kenan? FU'AD d bin umarnin mumcy yayi yaje ya Sami Husna da matsawar shi ta samu ta shirya itama taji yanayin ya girmin sanin ta tanaso tasan meke damunta ta zumbulo hijab suka sauko sukama mumcy sallama suka nufi asibiti. Su aunty huwaila sun iso cikin fargaba da tashin hankali ta doshi wajen hajiyar su da maman Husna Dan ta San da tsananin tsanar da ta Mata kamar da ita suka had'a kishin ,da murna aka karbe su a gidan ganin maman Husna sai fara'ar hajiyar ta d'auke ta Fara tuhumar ta dalilin zuwanta gidan matar da akace ta haukace ta shigo Mata da mahaukaciya gida......Ana cikin haka sai ga wani babban yayan su hajiyar Kuma Daman tanajin maganar shi dama aunty huwaila ta Gama shirya komai sai da tamai wayar sun iso shine yazo Dan Ayi komai agaban shi ,Aiko hajiyar ta dinga sababin sai tabar Mata gida ,yayan natane ya Shiga maganar maman Husna nata kuka da kyar da sidin goshi aka Shawo kan hajiyar su huwailan da lalami da wa'azi da nuna Mata ALLAH da mutuwa da ranar k'arshe da nuna Mata Ina wadanda suka gadasu yanzu a Raye? Da mahaifin su wato mijin hajiyar baban su aunty huwaila d mahaifiyar da kishiyar tata da ta had'a kishi da ita wato mahaifiya ga maman Husna? Duk ta bada amsa da basa Nan sosai wa'azi da farakarwa sukayi tasiri akanta ta wa'azantu ta nemi yafiyar maman Husna har aka tsaida cewa jibi zasuje gidan mijinta wato baban Ma'u lokacin da yayi daidai da ranar daurin Auren humaira. FU'AD sun Isa asibiti da kyar Husna ta iya Shiga asibitin da taimakon Fu'ad ganin yadda jikinta yayi FU'AD ya nemi da adubata da kyau amata duk Abin da ya kamata ,Dr Yana ganin ta Bayan gwaje_gwaje da tambayoyi da ya Mata yace test zasu Mata kafinan Tana buk'atar Ruwa a jikinta Fu'ad da gagawa ya bada umarnin su saka Mata atake aka admitting Husna aka saka Mata Ruwa FU'AD atake ya Kira mumcy ya sanar Mata sosai Husna takejin jirin na damunta Dan tunda ta rufe idonta ko budewa ta kasa. Bayan awa 1 Dr ya shigo ya sake dubata fuskar shi d'auke da fara'a adaidai lokacin mumcy da Yaya Jameel d aunty sa'adiya suka shigo d'akin sai ji sukayi Dr yace ma FU'AD "congratulation Abokina"............ Afuwan kunsan in aski yazo gaban goshi👌🏻🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀saura 2 insha ALLAH👌🏻 [4/23, 4:01 PM] Hayat: *RIKON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) _SECOND TO THE LAST PAGE_👌🏻 Pg 69 FU'AD kasa fahimtar Dr yayi Dan ko Alamun fara'a babu a fuskan shi. Su mumcy ko tuni fara'a ta baibaye fuskokin su kafin Dr ya karama FU'AD cikaken bayani tuni sun hau hamdalah suna karasa shigowa bakin aunty sa'adiya d'auke da sannu k'anwata. FU'AD binsu yayi da kallo Dan kanshima ya kulle be Gama fahimtar su ba sai da ya tsinkayo aunty sa'adiya nacewa"ALLAH ya inganta ya rabaki dashi lafiya k'anwata Mami ta kusa kani ko kanwa" FU'AD be Gama fita daga mamaki ba ta sake cewa FU'AD Ina tayamu murna Baki daya ka kusa zama father. Wani kyakyawan murmushine ya kubcema FU'AD batare da ya shirya zuwan shi ba,sai ya gimtse ganin idon mumcy akanshi Yana cema Dr muje inason muyi magana yabi Bayan Dr suka fice. Husna tun da taji kalaman Dr da maganganun aunty sa'adiya sai tayi lamo kamar me bacci cikin ranta ko cewa take "na Shiga uku wanima cewa zeyi da sanina hakan ya faru ,sashin zuciyar ta na karfafa Mata gwiwa Yana cemata "toh ai Daman kinsan da kwanan Haka duk macce me aure ai zata haihu Kuma yara Abin so ne ,in Zaki shirya zama da mijinki da samun zuriya to ,in ba Haka ba sanaya ta haifo Mai Dan kinsan bake daya bace " Atake tsana da kishin sanaya ya bijiro Mata lokaci na farko ta taji kishi akanta ,tayi damarar fatatawa a filin zuba kuri'ar son FU'AD da lashe zaben. Da kyar aunty sa'adiya ta tashe ta tabata abinci aka samu taci kadan. FU'AD da kyar ya iya shigowa d'akin be tab'a tunanin Akwai ranar da zeji kunyar mumcy d Husna ba sai yau ,ganin babu yadda zeyi sai ya shigo kawai Yana susukuyar da Kai. Wayar Husna ce ta dau Kara alokacin Tana hanun FU'AD ,ganin ko d'agowa batayi ba bare ta bukaci abata wayar sai FU'AD ya d'aga ganin sunan mamana ta indiya ajiki yasan huwaila ce. Da sallama ya amsa wayar ta amsa Mai Tana tambayan shi Husna ,sai yace wallahi bada Jin dad'ine suna asibiti ba ,yanayin maganar ta da tambayoyin da take Mai yasa ya gane cewa ta firgita da Jin rashin lafiyan husnan ,sai ya samu yace Mata "da sauki ma ai jikin tana bacci ne yanzu Amman zata kiraki inta farka. Su mumcy Basu bar asibiti ba sai kusan goma na dare ,akabar Husna da FU'AD Dan Dr yace da ruwan ya k'are zataji k'arfi a jikinta zata iya tafiya in Kuma zasu kwana toh babu matsala ,da mumcy tace su kwana sai ,shi Kuma FU'AD yace "aa indai zata iya tafiya komai dare zasu taho gida" mumcy tace "to ALLAH ya Kara lafiya Asma'u sai najiku" Daman Yaya Jameel yazo shi zemai dasu gida yanata tsokanar FU'AD ,shiko FU'AD sai kunya yakeji. FU'AD nason Kiran B2k ya sanar Mai Amman Yana tsoron surutun shi yasan inya fada Mai kamar ya sanar ma duniya ne Musamman da yake ganin zece hasashen shi ya tabbata shegen Gaye kamar me duba? FU'AD kin Kiran shi yayi yanata jinyar Mara lafiyar da Bata um bare um_um dan wani irin matsanaicin kunyar juna sukeji ,Amman da ta motsa ze Fara cemata sannu! Sannu!! Sannu!!! Inane yake Miki ciwo? Batare da ta kalle shi ba take cemai babu sai tashin zuciya kawai. FU'AD hankalin shi da nutsuwar shi nakan ruwan da yake samun matsuguni a jikin Husna burin shi ya k'are su tafi gida. Bayan awa 1 da Rabi kuwa ya k'are da kanshi ya cire Mata ruwan ya taimaka Mata ta tashi yace tayi tafiya intaji zata iya zuwa gida su tafi. Husna cemai tayi zata iya tafiya Daman batason kwanan asibitin ,Dan Haka FU'AD Kiran Dr da aka harashi dashi yayi Dan wancan ya Gama dutyn shi ya tafi gida yazo ya sallame su ya Bata magunguna da taimakon FU'AD Husna tashiga mota ya jata zuwa gida mamaki da farinciki fal karkashin ran FU'AD wai shine yake Shirin zama uba? ALLAH sarki Ashe farinciki na Yana kunshe a abun da nafi tsana nake Kira kazama ? Wa'iyazu billah! har banason tunowa,toh yanzu da wancan mayyar ne na samu baby da ita da ya kenan? Tab! Da nagama yawo mezanyi da Abin mahaifanta gwanda husnan duk da na tozarta ta tahakura da duk wani wlakanci na gashi yanzu Ashe itace me Shirin bani happy family? FU'AD na cikin tunani ya iso gida ya Shiga ya taimaka Mata suka nufi sashin mumcy yayi Amfani da spire key din shi Bayan ya Shiga ya kulle yasan mumcy tayi bacci tunda yajita shiru Dan ya kwantar Mata da hankali sosai. Har sun Fara Hawa steps ,suka tsinkayo muryar mumcy nacewa ,sannu ku da dawowa ,Husna jikin da sauki ko? Husna na mak'ale jikin FU'AD tace "eh mumcy nagode" Mumcy ta sake tambayan ta Bata buk'atan komai? Husna tace eh Akwai malt a sama Zan dansha kafin na kwanta. Sai mumcy tace"yauwa toh sai da safen mu" Atare da FU'AD d Husna suka amsa da "ALLAH ya tashe mu lafiya" Suna Shiga falon FU'AD ya nufi d'akin shi da ita ya rud'e har sun kusa Shiga Husna ta tirje tace "d'akina dai" Sai a lokacin FU'AD ya fuskanci inda ya dosa da ita ya koma hanyar d'akin ta da ita. Gyara Mata shinfidar yayi Yana cewa ko Zaki rage kayan jikin ki ? Husna cemai tayi "eh " Ganin baida niyar fita sai ta Debi kayan ta nufi bathroom dashi taje ta canja , FU'AD nata Mata dariya Yana cewa yarinya meya rage Kuma kibada Kai mu Gina sabuwar rayuwa mu Kori duk wata gaba da kiyaya da fadace_fadace mu manta baya mu Gina rayuwa Mai inganci da Aminci mu Mori Rayuwar mu,duk cikin ranshi yake biya wanan karatun. Bayan ta dawo tayi sallah duk Yana zaune. Sai da zata kwanta take cemai "kaje ka kwanta dare yayi fa" Agogon tsintsiyar hanun shi ya duba kafin yace "to babu damuwa nabarki ke kad'ai duk da Baki da lafiya? Husna cemai tayi "eh zata iya kwana ai" FU'AD yace "hakan ya Miki? Ta sake cewa "eh" Hadi da nuna k'osawa da tambayar tashi. Ficewa yayi Yana cemata sai da safe inda buk'atar wani Abu da takeji Yana sauraron ta ko yaushe ne. "Toh" kawai tace Mai ya fice. Itama kwanciya tayi tanata zuba tunani wai itace ke d'auke da cikin FU'AD? Ashe zata haihu Kuma da FU'AD shifa Daman Haka abun ALLAH yake" Toh yanzu FU'AD Ya Dena tsanar ta ko har yanzu Yana d'aukan ta matsayin kazama, Yar Aiki,wacce mumcy ta aura Mai ala tilas? Ze karbi Dan kuwa? Kasan zuciyan kuma tace"eh Mana bakiga wani kulawan Musamman da ya Fara Baki ba? Shima yanason yara fa ko kin manta ne? Ai kulawa har sai kince ta ishe ki"ALLAH yasa Inji zuciyar ta" afili Kuma ta amsa da Amin. Sosai bacci ya d'auki Husna cikin baccin tayi wani irin mummunan mafarki wai ga mama habee ta biyota da tukunyar wuta ahanun ta tana gudu babu me ceton ta tanata tsala ihu har sai da ta Fadi kasa ,sai matar da aunty huwaila take taimaka ma tazo da sauri ta hankada mama habee Tana cemata" anan dai Kam Baki da nasara Nima ta ALLAH ba takiba" Agigice Husna ta farka da hailala Mai k'arfi har sai da FU'AD ya jiyo ta Dan ba wani bacci Mai nisa yayi ba Daman da sauri ya nufo d'akinta. Yana Shiga da sallama Yana tambayar ta lafiya? Yaga gumi duk ya fito Mata tanata waige_waige Tana Addu'a. Ganin batace Mai komai ba ya hauro gadon ya tallabo ta k'irjin shi Yana cewa menene? Husna kuka tasa Mara sauti sanan tace "wani mafarki nayi Mai sarkakiya ka kiramin aunty huwaila dan ALLAH na tambaye ta" FU'AD sake rungumeta yayi Yana cewa ,dare fa yayi karfe 3 dare ki Bari zuwa gobe ,Kuma mafarki ai ba gaskiya bane. Sai Husna tace"na sani Amman mama habee nagani ta biyoni da tukunyar wuta fa sai Mara lafiyan gidan aunty huwaila ne ta taimakeni fa Ni kaina ya kulle. Sai FU'AD yace toh kiyi hak'uri zuwa gobe ,kuma watakila bakiyi Addu'a ba Kika kwanta Koh? Husna eh tace babu musu. FU'AD yace "kin gani ko? Ai karki dinga sakaci da Addu'a Musamman yanzu. Husna cikin kuka tace"kamar ya Musamman yanzu? FU'AD Babu kunya yace "Ina nufin yanzu da kike d'auke da .........sai ya kasa iarasawa. Husna ma runtse ido tayi Daman Tana jiran ya karasa. Sai yace "kawai kiyi bacci Zan tayaki kwana sanan Zan sanar ma mumcy atayamu Addu'a Akan wanan algungumar matar baban Dan bazan sake yadda da ita ba muguwace babu ALLAH aranta kema karki sake amincewa da ita na Gaya Miki. Husna tunani ta dingayi akan mafarkin. FU'AD ne yace"ki kwanta anan sai kiyi Addu'a Nima Zan Kara yi Miki Kinga kina buk'atan hutu kisamu kiyi bacci ya ishe ki. Husna kwanciya tayi, sai da FU'AD yaji hanun Husna cikin nashi ta damke kamar Wanda ze gudu ya barta sai yace Mata"ko natafi d'akina? Da sauri Husna ta k'ara damke hannun shi tana cewa "aa Dan ALLAH" dariya yayi cikin ranshi Yana ayyana tsokanar da ya Mata. FU'AD dai a d'akin Husna ya karasa kwanan shi har makara yayi be samu sallan asuba a jam'i ba Abin da baya wuce shi. Bayan y tashi yayi sallah ya tashi Husna itama tayi ,yaga ta nufi fridge ta d'auko malt ta bud'e Tana Sha yace in yunwa takeji taje kasa tanada umarnin a dafa Mata wani abun Mana? Husna cemai tayi wanan ma ya isa. Bayan sun koma bacci sun tashi sukayi wanka Husna nata samun kulawar FU'AD suka sauka kasa suka tarar da aunty sa'adiya da mijinta d mumcy,suka gaisa anata ma Husna ya jiki tanata amsawa ciki_ciki Dan kunya tanata sunkuyar da Kai Bayan sun Gama karyawa FU'AD da Yaya jameel suka tafi unguwa. Da Rana Husna ta kasa jurema mafarkin da tayi ta Kira aunty huwaila ta sanar Mata ,aunty huwaila tace gata Nan zuwa gidan taga jikinta. Bayan awa 1 sai ga aunty huwaila da matar Nan dasu Yaya sadeeq su Affan d muhibbat d Husna sun tafi gidan kanuwar huwailan ta haihu. Suna isowa mumcy ta dinga karema matar kallo Tana hango Kama da Husna atare da ita Bayan sun Gama gaishe da mumcy ta musu umarnin su haura sama husnan na sama. Shigar aunty huwaila Husna da sauri ta taso ta rungumeta da murna farinciki far ranta da fuskar ta. Can taga matar Nan Mara lafiya ,sai taji wani irin faduwar gaba Amman hakan be hanata rungumeta ba Tana Mata sannu da jiki. Cikin Jim Dadi da ganin samun lafiyar matar Husna ta dinga janta da Hira Tama manta da su sadeeq .....suko kallon ikon ALLAH kawai suka tsaya yi suna ayyana tsakanin uwa da 'ya sai ALLAH. Aunty huwaila ce ta dawo da Husna daga mafarkin ta da cewa "Husna kinsan kuwa cewa mahaifiyar ki Bata mutu ba? Mafarkin ki daidai yake da amsa ta. Husna cikin kaduwa da razana ta Fara kallon aunty huwaila Tana cewa "Ammin su muhibbat kice min baiwar ALLAH da kike Kira Yaya itace mamana Kuma Yar uwarki? Huwaila tsayawa tayi Tana Mata kallon mamaki. Can Husna tasa kuka Tana Kama hannun huwaila Tana cewa Dan ALLAH kice min itace kafin zuciyata ta tarwatse na sake fahimtar hakane ta mafarkin da nayi da Kuma shak'uwa da nakeji akanta tun zamana daku a India. Huwaila rikota tayi Tana cewa "eh Husna itace yayata mahaifiyar ki amaryar baba kishiyar anamimiya mama habee. Da gudu Husna ta tafi ta rungume ta tana Kuka,itama kukan takeyi Tana cewa "ALLAH sarki Asma'u ta Ashe Zan sake ganin ki ,nasan kinsha gwagwarmayar rayuwa hanun habee wacce babu ALLAH aranta Amman naji labari komai yazo k'arshe awajen k'anwata tilo wacce samun kamarta sai antona ta Mana gatan da ba kowane ze Mana ba bamuda kamarta har mu gushe bazamu bar Mata Addu'a ba. Sosai kowa ya tausaya musu ,da sauri Husna ta sauka ta Kira mumcy tazo taga mayaifinta ,da sauri hajiya babba ta hauro har aunty sa'adiya akama waya tazo itama suka dinga tayata murna duba da Jin labarin asiri aka Mata ta hanyar hayaki aka kashe ta har aka sallace ta aka birne ta duk da sun Rasa yadda akayi ta dawo da ranta matsayin me rangwamen hakali kuma. Huwaila ce tace wanan amsar habee ce zata iya amsawa idan muka Mata diran mikiya Dan bazanbar Abin ya tafi abanza ba Dole ta girbi tashin hankali yayin da take Jin taci bulus. Sai Husna tace "ya kamata Kam aunty Amman abari sai Bayan bikin humaira Dan Gobe za'a daura Mata Aure. Sai huwaila tayi wata she was kafin tace "shine daidai ta girbi shukar da ta bama Ruwa ,alokacin da take cikin farinciki lokacin zamu tarwatsa Mata shi naji dad'in labarin nan,maman Husna zatayi magana huwaila ta dakatar da ita da cewa"nifa duk Wanda ze dakatar Dani daga kudirina kamar ya hanani cimma burina ne kawai aunty kiyi shiru inbaki da gudumawa. Aunty sa'adiya ma tace "gaskiya Kar a saurara Mata dari bisa dari tabada goyon baya rafiya yakin Nan ma da ita za'ayi. Mumcy ma tace ya kamata a nuna Mata annabi ya faku Kam Amman ta hanyar lumana Dan ALLAH,huwai toh kawai tace. Sadeeq ma yace "Dole tasan tayi babban tabargaza akuma gyara Mata atanar da batayi tunanin Akwai me gyara matan ba. Bayan sun Gama maganar huwaila d sadeeq d maman Husna suka tafi da niyar gobe zasu hadu a gidan baba suka bama junan su lokaci. Mumcy d sa'adiya cike d mamaki suka dinga tatauna maganar a kasa wajen mumcy. Bayan FU'AD ya dawo Husna ta rokeshi Akan zata gidan su baba ta gaishe shi , FU'AD cewa yayi bazata ba gidan muguwar matan Nan ita da Bata da lafiya ma? Jin suna takaddama a falon mumcy ,sai mumcy ta fito tashiga maganar har takema FU'AD bayani Akan samun mayaifinyar Husna da Kuma zuwan da sasuyi gobe har tamai umarni da ya barta taje. FU'AD badan ranshi yaso ba ya hak'ura ya sake kafa huja da matarkin Husna , mumcy hakuri ta bashi sanan tace Akwai ALLAH da Addu'a za'adage insha ALLAH alkadarinta ya karye. Ranar ma FU'AD a d'akin Husna ya kwana yanata bata kulawa. Washe gari gidan mama habee ya dinke anyi party jiya yau daurin Aure angon ma be samu zuwa ba wai yayi tafiyar gagawa. Gidan mama habee ancika antunbatsa baba yaba wani walicin Auren humaira andaura Aure kowa ya sheda aka dinga raba alewa da goro. Aranar za'akai Amarya ,Amarya sai rawar Kai takeyi ta Gama hada kayanta tsaf na barin gidan zuwa gidan Alhajin birni taci kaza ta kora da juice ta gaji da cin tuwon datsan mama habee. Su aunty sa'adiya d Husna sun shirya Dan anti sa'adiya tace kallo baze wuceta ba,suna jiran wayar su aunty huwaila. Su aunty huwaila ma sun shirya tsaf suna Shirin fita suka Kira Husna sukace su hadu acan. FU'AD ne ya kaisu ganin su aunty huwaila Basu karaso ba Husna tace su Fara zuwa gidan su hafeeza sa gaisa da mama, FU'AD dai yace ma Husna kome ake ciki ta Kira shi ta kula da kanta Dan B2k ne yake ta takura Mai da Kira tunda FU'AD ya Kira shi yace zasuyi magana Kuma Daman Aisha ta Fara kyasa Mai zancen Dan itama ta Kira Husna tanata tsokanar ta. Bayan su Husna sun gaisa da mama da hafeeza har Husna take gayama mama makasudin zuwansu ,Aiko mama tace "na kwana da sanin wanan ranar zatazo hafeeza ga amsar tambayar da na haneki da nanata min nasan wallahi tuggun habee ne yasa mamanki tabar gidan Dan ko a wajen wanka ba ita aka wanke ba Dan Ni ganauce ba kiyau ba ko sheda Zan iya bayarwa,hankalin Husna ne ya Kuma tashi da mamaki fal fuskar ta. Kiran huwaila ne ya tsayar musu da komai ,Suma sun kataso ,fita Husna da sa'adiya sukayi har hafeeza mama ma tace gatanan biyo Bayan su. A k'ofar gidan suka had'u da su Husna ,maman Husna fuskarta lilube da nikab suka Shiga gidan. Suna Shiga suka dinga gaisawa da mutane masu zumden Husna nayi wai humaira ma ta samo nata Attajirin Kar amusu karyar azziki. Mama habee na ganin Husna d su huwaila atunanin ta husna ta kawo Mata kabakin arziki ne tasan ta da hanun kyauta bare taga dangin su FU'AD sa'adiya wai sanan ga mutanen India. Hakori ta dinga washe musu Tana musu sannu da zuwa ,Tana cewa Kai Amman kinma Yar uwarki kara ,itama kinji ta samo Attajirin miji ko gashi dai kunzama daya sai ku zauna lafiya agidajen mazajen kuyi yadon yabanya Mai kyau ta 'ya'ya. Tir suka dingayi da Hali irin nata da baya boyuwa. Gaishe su ta dingayi daya Bayan daya har tazo Kan maman Husna ,amsawar da taji har ta d'auki murya sai tace "wace wanan ku kuke ganin mu bamu muke ganin ku ba,Kya cire kodan Kisha iska ai kekuwa" Tana fad'an Haka sai maman Husna ta cire nikabin ta kalli mama habee Ido cikin Ido Tana Mai karanto Addu'a neman tsari da mallam ya Bata. Mama habee zabura tayi Tana cewa ke wacece wanan din? Banason lalata waya dawo min da abar Nan? Mik'ewa tayi atake gumi ya Fara keto Mata ta tuge dankwalinta Tana firfita dashi. Can maman Husna tace ,habee y taro? Mama habee sake cewa tayi taron uban wa ke daga Ina sai mama habee ta Fara soshe_soshe Tana cewa ke dawowa kikayi? Waya dawo dake Daman seda akace Kar na Yar dake na Bari abirne ki nayi kardama nace nafison gawarki ta wulakanta a bola ko jeji Ashe hakan ze haifar min da gagarumar matsala wallah sai kingoma kabari Zo na birne ki......da gudu Tayo Kan maman Husna zata cakumota aka tareta Dan a lokacin hankalin mutane tuni ya dawo Kan mama habee d kalamanta Dan kamar Tama zare. Yunkuri take zata Kama maman Husna Ana dakatar da ita ,mama habee dariya ta dingayi Tana cewa wallahi sai kin koma kabari Dan ban shirya mutuwa yanzu ba. Sallati gidan bikin ya d'auka da gudu akasamu magulmacin da yaje ya sanarma baba da gudu har baba na tuntube sai gashi cikin Mata tsamo_tsamo. Baba na tozali da maman Husna ya Fara godiya ga ALLAH da Addu'a girmamawa ga ALLAH Yana murnar yadda ALLAH ya karb'i Addu'a shi Dan ya Jima Yana mafarkin ta yasan Akwai boyayen Abu cikin mutuwar ta. Mama habee Tana cikin wani Halli take tonama kanta asirin aikin da tayima maman Husna. Malam ALLAH wadai da halinta ya dingayi ,Yana ya saketa muguwa macuciya. Labari da yaje wajen humaira amakota sai kuka takeyi na Bata Mata show da mama habee tayi na bikinta wai me makon ta Bari sai ankaita sai ta haukacen ita wallahi zuwa gidan Alhaji babu fashi ta bita da Addu'a , amman bari taje ta ganta. Humaira na zuwa taga Abin ya fi k'arfinta ,kuka ta dingayi Ana cikin Haka aka dinga cewa motocin d'aukan Amarya sunzo Ashe humaira da kawayenta ne suka Kira angwaye wai suzo akai Amarya kawai tun yanzu shine suka turo da motoci. Mama habee hauka ta kankama anata yage yagen zani Tana tonama kanta asiri Abin yazamar ma su Husna wani irin Dan mamaki sun Rasa mema zasuyi ,maman hafeeza d shigowar ta kenan sai cewa tayi ALLAH ya Toni asirin ki , ALLAH y shirya masu Hali irin naki. Gidan biki ya koma gidan gulma da tsugudidi anata gulmar uwar Amarya ta haukacen asirin da Tama kishiyarta ya koma Mata. Baba ko ji yake kamar ya rungume maman Husna macen rufin asirin shi. Humaira ko sai cema wata kanwar mama habee tayi su rik'eta su kaita d'aki da ta Isa gidanta zata Fara Shirin samo kudin da za'a Mata magani ,itama aunty hafsun dake uwar son Abin duniyace tace ai Tana Nan har ta warke taji abun samun kud'i. Aunty huwaila had'a Kan su Husna ta dingayi Tana cewa su tafi tunda kaikayi ya koma Kan mashekiya Kai Kuma mijin Yaya in kanason magana da ita ka biyomu gidan hajiyar mu ,baba d maman Husna har seda sukaji kunya gashi Basu samu sunyi magana ba. Humaira Kam ita ta dinga tataro Kan mutane Tana cewa suje su Shiga mota su tafi kar angwayen su fahimci me ake ciki ,mutane nata mamakin yadda matsalan uwarta baya gabanta. Husna d sa'adiya wucewa gida sukayi cike da murna da farin ciki. Mama habee Kam an sata a d'aki anata bunka Mata hayaki wai na temako sai suritai takeyi. Su aunty huwaila Suma gidan bawan ALLAH Nan da ya dinga taimakawa maman Husna suka nufa Dan kaimai ita yaga Halin da take ciki na samun lafiya daga can sunifi gidan hajiyar mu suka wuce cike da murnar tonuwar asirin mama habee ayau. Sanaya ta fahimci cikine da Husna ganin yadda aketa Mata sannu da jiki Kuma mumcy ma ta Mata magana Akan ta Mata ya jiki Dan bataji Dadi ba ,hankalin sanaya inyayi dubu ya tashi wato itace FU'AD baya kulawa? Tana Kuka ta Kira mamanta take Gaya Mata sai ko dady ya kwace wayar ya dinga zaginta Yana cewa itama inbatayi ciki a satin ba ze yafeta daga yaranshi sokuwa wacce batasan Abin da ake nufi da itaba, Yana ajiye wayar gumi ya dinga keto Mai Yana tunanin meye abinyi akan FU'AD komeye ma zeyi Dan cikar burin shi. *Saura fejin k'arshe insha ALLAH*😍😍 [4/23, 4:01 PM] Hayat: **RIKON KWARYA* ```RUBUTAWA DA TSARAWA``` BY *FATIMA ABUBAKAR SHU'AIB* ( Maman shaheed) _The last page_.............The end_👌🏻 *Special Thanks to All my Fanc I really appreciate your caring,ddu'ah, support,nd follow m bomba to Bamba*👌🏻😀😍😍 Pg70........🔚🔚🔚🔚 Bayan sanaya ta ajiye waya ,ta rabza ihu Tana mitan y dady zece sai ta samu ciki d mutumin da kamar besan meye Aure ba akanta Ashe munafuki Yana can Yana Abin da yakeso ko Dole uwarshi take Mai Amman ai yayi din ai Dan Haka itama Dole ta tirsasa Mai. Tun Bayan isar su aunty huwaila gidan Mai taimakama maman Husna yayi matuk'ar farinciki ganinta cikin sahun masu gamsashiyar lafiya har iyalin shi sosai sukayi murnar ganin ta da lafiya. Itama godiya tamai sosai ,har aunty huwaila ma ta tayata yimai godiya daga bisani suka wuce gidan hajiyar mu. Su Husna na Shiga gida FU'AD ya kirata Yana tambayan ta komai lafiya dai ko? Cemai tayi "lafiya sun koma gida ma" Hakan Dadi Yama FU'AD kafin yace "toh ta zauna ta huta shima ya kusa dawowa" Husna Bata samu bakin amsawa ba sai samun sararin mamakin canjawar FU'AD farad d'aya Haka ,kodan Yana tunanin Akwai jinin shi a jikinta? In ta fahimce shi badan ALLAH ya canja ba kenan? Sashin zuciyar ta cemata yayi "nd so what? Hakan ma ai yanadaga cikin so da nuna damuwa Kuma sai kanada kima mutum zai hada jini dakai har ya baka lokacin shi nawane ake had'a jini dasu din Amman Babu wani nuna kulawa ko damuwa da Halin da suke ciki? Kawai kobada Kai bori ya hau kema" Bayan sun huta mumcy ta tirsasama Husna cin abinci Dan ji tayi batason cin komai gudun Kar tayi amai a gaban mumcy. Da kyar ta samu taci kadan ,Jin Yana taso Mata tayi saurin tashi tace zataje ta kwanta asama , mumcy tace toh ,Nan tabar aunty sa'adiya naba mumcy labarin dramar gidan mama habee. Bayan tafiyar husna sama amai take ta kwarawa kamar zata amayar da yayan hanjin ta sai da tayi me isarta ta wanke fuska da Baki tafito ta fad'a gadon Tana dogon numfashi. Bayan ta samu ya lafa Mata kamar bacci na Shirin d'aukanta ma sai tajiyo sallamar FU'AD kamar a matarki. FU'AD kusa da ita yazo Yana Mata magana Akan ta tashi taci fruit din d ya kawo mata. Badan taso ba ta bud'e fuska d Ido da kyar tamai sannu da zuwa ta karbi ledan ta ajiye. Ganin baci zatayi alokacin ba sai FU'AD yace "kici Mana nasan kinyi Mayan Aman Nan ki samu kici". Zatayi gardama , FU'AD ya bud'e ya d'auko banana ya Fara bare Mata Yana Miko Mata har sai da ya Bata kusan 3 ta cinye ya d'auko Apple shima sai da ta cinye 1 da Rabi lemu ma Tasha guda 1 Tana cikin Shan na 2 sai Amman ya dawo kafin ta Mike gaba d'aya ta wanke FU'AD da Aman sai sauran d ya mak'ale abakinta ta samu t rarafa d kyar tayi toilet. FU'AD haushi d takaici nee Kama shi gani yayi kamar da gangan tayi Dan Haka kawai besan lokacin d ya Fara balbaleta da masifa ba har Yana cemata baze d'auki wanan kazantan ba da wawancin wallahi. duk da ta fito a wahale a galabaice Yana gani Amman be fasa fad'an ba gashi Abin d ya Kara k'ular dashi Bata gyara Mai jikin shi take bama kwanciya tayi gashi ko hakuri Bata da niyar bashi sai wani Abu takeyi kamar me Shirin barin duniya,wani dogon tsaki ya ja Mata kafin ya saki ledar fruit din ya Mike Yana cewa sai ki karaci kazantan ki y fice daga d'akin ranshi babu d'adi yanata kyaman jikin shi. Husna takaicine ya turniketa batasan lokacin d kuka ya kufce Mata ba tana cikin yine FU'AD ya shigo ya d'auki wayar shi d ya manta a wajen d ya zauna ,Jin gunjin kukan ta sai ya sake kuluwa Yana cewa"au keda lefi keda kuka Dan shagwaba? Ba amiki komai ba Amman Zaki zauna kina kukan santarta ? Wayar shi y d'auka yace kitayi har sarkin kukan yazo ya same ki ya sake ficewa yabar d'akin. Husna sake gunjin kukan tayi Tana takaici Akan Halin FU'AD Ashe Yana Nan babu inda yaje ,yanzu hukuncin ta kenan baya lura da Halin da take ciki?. Besan ya takeji dama yaudarace ya nuna kamar ya sakko? Har d wani siyomin kayan marmari Ashe ya siyone Dan ya cimin mutunci ta sanadin su? Alwashi taci Akan bazata sake cin komai da ze Bata ba Kuma baze sake zama Mata a d'aki ba sanan baze gara ganinta ba a yau har sai gobe Dan Haka d kyar ta samu ta Mike ta saka key a d'akin ta gyara wajen d ya b'aci d kyar ta koma ta kwanta Tana tunanin rayuwa cikin Halin d take tunanin FU'AD ya canja Ashe be canja ba yaudarace kawai. ...........Bayan shigar FU'AD d'akin shi kayan y cire Yana wani ajiyesu a yamutse sai d y Gama ciresu yanata tsaki kafin ya samu ya fad'a bathroom ya fesa wanka y Gama jikinshi d turarukan wanka masu dad'in kamshi kafin ya fito ya janja Kaya y sake feshe jikin shi d turare Dan gaske. Kiran Yaya Jameel ne ya shigo wayar shi yace yazo Yana part d'in shi suyi wata Yar magana. Yawa amsawa ya ajiye wayar ya tafi Kiran d yamai,a falon mumcy y bar mumcy d aunty sa'adiya kafin y nufi Kiran Yaya Jameel din. Bayan yayi sallama y shiga y sameshi a zaune Yana kallo daga bisani ya dawo d nutsuwar shi Kan k'anin nashi y Fara Mai bayani Akan hakuri d zaman Aure d hakuri da me ciki Dan zuciyoyin su a kusa yake b'acin Rai baya musu wuya gasu d kayan takaici wasun su Amman Dole Ayi hakuri Ayi k'ok'arin Basu farinciki har ya bigamai misali da aunty sa'adiya har yaji ta tabayi akan tamai amai ajiki ya Mata fada ba karamin wuya yaciba kafin ya samo kanta tundaga Nan ya kiyaye ya Fara lalab'ata ba Kuma yadda zata sangarce ba haka sukata hakuri da juna suna renon kyautan da ALLAH ya Basu har ya Isa haihuwa Dan haka Yana shawartan shi da yayi hak'uri ya ajiye zuciyar Nan tashi har zuwa Husna ta haihu lafiya ya ninka kulawar da yake Bata Kuma". Tunda Yaya Jameel y Fara magana FU'AD ya nausa duniyar tunani sai yaga kamar ya fahimci meya faru ma badan yasan Husna bazata gayamai ba da sai yace itace ta sanar Mai. Jin yayi shiru Yaya Jameel din y cigaba d bugs Mai misalai d yanayin ciki ga wasu matan d ya samu labarin su a wajen abokanen sa wasu Abin tausayi wasu Abin dariya akarshe dai ya nuna Mai tsananin buk'atuwar kulawar d ya Dace aba masu dauke d juna biyu Dan samu su haife lafiya cikin kishin lafiya batare d uwa ko Dan ya fad'a cikin gararin matsala ba. Sosai kalaman Yaya Jameel suka ratsa FU'AD ya samu sauyi a lokaci guda so da k'aunar Abin da za'a Haifa Mai tun besan meye bama atake yaji nadamar Abin d ya aikata ma Husna dazu Dan ji yayi harma ya kosa da tunasarwar Yaya Jameel din. Bayan sun Gama magana suka tatauna akan sanaya Yaya Jameel din Yana Mai fad'a Akan ya dinga Bata hakkin ta , FU'AD y amsa d Yana iya k'ok'arin shi yarinyar ce Akwai wuyar sha'ani Amman ze Kara k'ok'arin wajen kulawa d itan. Atare suka koma Fallon mumcy Yaya Jameel ya zauna Ana hirar dashi FU'AD Kam ba'a bashi zama ba haurawa yayi wajen Husna. D'akinta ya nufa yaji ansa key ,yayi mamaki Amman sai yayi tunanin ko bacci take har ya Fara bugawa sai ya fasa y koma d'akin shi Dan ya rage wani aikin. Bayan kusan awa daya y sake dawowa buga k'ofan ya farayi Amman Babu niyar budewa Dan Haka ya d'auki waya ya kirata kusan so 3 kafin ta d'aga bisani ta d'aga cikin muryar tausayi. Ji yayi tausayinta d wata kaunarta ya Kama shi sai yace "Zo ki bud'e min k'ofa". Sai tace "me zakama kamaza?. Ko zakazo ne tsautsayi yasa na maka amai ka sake cin zarafina? "Kayi zamanka tunda babu tausayi da jinkai a tsakanina da Kai ko ganinka banason yi Kuma barma gidanka zanyi Inna haihu na kawo ma danka Amman na Gama Rayuwar wulak'anci bazan sake jure Mata ba ta fashe da kuka" FU'AD yanajin kukan har ranshi yanata Kiran sunan ta Amman Ina kuka yaci k'arfinta maganar duniya da magiya Taki amsawa. FU'AD wani irin yanayi ya Shiga Mara misaltuwa Yana cikin wanan Halin B2k ya kirashi a wayar shi d kamar baze d'auka ba sai ya d'auka de. Bayan sun gaisa sai suka Fara maganar company sai FU'AD yace "ka Bari anjina mayi magana" Sai B2k yace "mutumina lafiya kuwa najika kamar a wani yanayi fa?. FU'AD yaso b'oye Mai Amman B2k d magiya d lalami har sai d FU'AD y bashi labarin komai tundaga samuwar cikin Husna d abun d ya faru yau,atake B2k yaba yaba FU'AD rashin gaskiya y nuna Mai inhar yanasin gaskiya d son zaman lafiya d happy family sai ya zubar da makaman shi na baya ya fuskanci Rayuwar Aure Mai cike da tatali da nuna kulawa ga iyalin shi ya manta komai ya fuskanci gaba yasan cewa Husna wata kyautace Kuma tsarin ALLAH a gareshi Dan su tsara rayuwa Mai inganci ,duk yadda FU'AD ya bullowa B2k sai B2k ya toshe ya Gina Mai hujja Mai k'arfi Wanda Dole ya yadda Haka har B2k yaci galaba akan FU'AD ya yadda bashi da abar so da kauna samada _dirty girl_ sunan da bayason ko tunawa yayi yanzu , B2k be kashe wayar ba sai d Yama FU'AD tunin kyautan da zezo karb'a na maganar su ta baya da yake cemai kamar me duba ,sai ko FU'AD ya dinga dariya Yana cewa maye me gani har hanji sai kazo Ni barinje in gyara Abin da na Bata. B2K cemai yayi ako kayi sauri Dan inba hakaba a haifo ma d'a da tabon b'acin Rai ajikin shi Yana cewa sai nazo karb'a. FU'AD da kakarfar zuciyar shi ya sake komawa wajen Husna yin duniya Taki bud'e k'ofan y sake kiranta Yana mata dabara Akan ta fito taci abinci tace "Bata ci" Abin duniya Yama FU'AD zafi ,Dole sai da yaje ya nemi taimakon aunty sa'adiya batare da mumcy ta gano ba. Tun zuwan aunty sa'adiya da Husna ta fito take ALLAH...... ALLAH....ta tafi kafin FU'AD ya hauro Tana cikin tunanin hakan FU'AD yayi sallama ya shigo auwar harara Husna ta wurga Mai ya gani Amman yayi kamar be gani ba ,aunty sa'adiya cewa tayi Bari tatafi tunda ga FU'AD dama tazo ta d'ebe Mata kewa ne taga jikinta Kuma,Husna godiya ta mata. Bayan tafiyar aunty sa'adiya Husna har ta dau hanyar komawa d'aki FU'AD yasha gabanta Yana cewa" wai Ina zakine haka? Husna cemai tayi "inda na fito ko Akwai Abin da zanma ne? Ko kauanka da na batama Zan wanke ma? FU'AD cemata yayi "eh shi Zaki wanke Ayi mutum Mai gardama anaso afahimtar dake Abu kin kasa bada lokaci ki fahimta" "Wani irin kallo ta wurgamai sanan tace "mezan fahimta ka fahimtar Dani din malamin fahimta" "Dariyace taso kubcema FU'AD Yana cewa hmmmm gafa aikin masu cikin duk ya Fara bayyana atatare da yarinyar Nan dama Akwai gaddama Amman kamar ta Kara ninkawa Amman Bari na bisa ahankali Albarkacin jinina dake damfare ajikinta ko na samu ta fahimce ni,Afili Kuma sai yace "me kike da buk'ata yanzu love me zakiyi? Cemai tayi "Ni bana buk'atan komai daga gareka nagode ka rik'e komai naka na barka lafiya ta karasa kulewa d'aki,...... Kafin ta turo k'ofa batayi aune ba sai ganin FU'AD tayi kawai aciki ya harde hannayen shi biyu a k'irjin shi Yana kare Mata kallo. Haushi Abin ya Bata sai kawai ta juya zata fita ya rikota Yana Shirin had'ata da k'irjin shi,kwacewa tayi Tana cewa" mekake Shirin yi? FU'AD cewa yayi "zanji dumin baby na da ko hallita ba'agama Mai ba sanan ki nutsu ki fahimce Ni nasan fishi kikeyi Dani ko? Batare da ta kalli inda yake ba tace "sai ka Bari inyazo duniya kaji dumin nashi inyaso ka had'a harda sanyin shi kaji ba dumi kawai ba,ka Gama kwance min zani a kasuwa yanzu mun dawo gida zakace zaka daura min bazan yadda da milkin Kama karya ba wallahi ayanzu ko ada na hakurane saboda wasu dalilai yanzu kuwa bazan iya d'auka ba gara nabar gidan naje inda ake nemana" FU'AD d sauri yace "nine na kwance Miki zanin ? Kuma nine me miki mulkin kama karyan? Shin a Ina ake nemankin wane buk'atar ki ahalin yanzu da ya wuce Ni? Batare da ta d'ago ta kalle shi ba tace"eh duk Kaine kake min ,Akwai mayaifinta ahalin yanzu d su aunty huwaila sunfi kowa buk'ata ta" FU'AD d sauri ya tuno d hirar su d aunty sa'adiya sai yace "na sani Nima Ina tayaki murna da son Jin dumin ta da bakiyi ba shekaru masu tsayi Amman kibi komai ahankali ki nutsu ki fahimce Ni Zan tayaki yakin Nemo kuri'a da lashe zaben kaunarta gareki Wanda Kika Rasa a shekarun baya da suka shude Amman inaso ki bani Aron lokaci d nutsuwarki kiji da Abin da nazo Miki. Kalaman FU'AD sun Fara karya lagon Husna sai ta kwad'aitu da son Jin manufar sa Amman duk da Haka Tana tunanin bazata yafe cin zarafin d ya Mata ba,sai tace inajinka ai kunne ne yake sauraro mezaka gayamin d ban sani ba? FU'AD Rasa yadda zeyi yayi Dan yama Rasa ta inda ze Fara Amman sai yayi shahada kawai yace "husna ki cire komai aranki Yana Mai kamo hannun ta Yana murzawa ahankali Dan bayanan shi Sufi saurin ratsa zuciyar da illahirin jikinta,yaci gaba da cewa"ki manta duk wani Abu da ya faru abaya kawai mu fuskanci gaba.........be dire maganar shi ba Husna tace "kana nufin duk abubuwan Nan sun tafi abanza? FU'AD sake kamo hannun ta yayi yaci gaba da cewa "haba ya kike maida gaba baya ne? Ko sai nace kiyi hak'uri haka kikeso? Toh kiyi hak'uri Akan abinda ya faru Dan ALLAH? Husna d'agowa tayi tana kallon FU'AD Tana mamakin shine yau yake Bata hak'uri? Y kamata ta saurareshi taji Dame yazo zaman lafiya ko yafiyar abubuwan da ya aikata Mata a baya Dan Haka sosai ta maida nutsuwarta gareshi tace inajinka me kakeson sanar Dani Wanda ban sani ba? Cikin kwarewa da salo FU'AD ya dinga bama Husna hakuri har ya Fara tuno Mata da abubuwan da suka faru baya Akan jarabawace wacce bazasu iya tsalake Mata ba Musamman shi da ya dinga Mata abubuwa Wanda faduwar su yanzu bata lokaci ne Abin da gaba zata haifar kawai ya kamata su fuskanta wato kula da Abin da yake tare da ita nadaga jinin shi. Husna Baki sake take cewa "kana nufin ka aminta d Auren mumcy ? Ka janye daga jingina shi da mumcy da kakeyi? *FU'AD da sauri yace eh Auren shine bana mumcy ba Kuma wallahi zata sameshi me Bata kulawa da tatalin da babu wani miji da ya tab'a mafarkin bama matarshi bare a farke kawai ta tayashi kula da cikin dake jikinta Dan ALLAH! Husna farinciki ya lulubeta Tama Rasa me zatayi murna ko mamaki yau ga FU'AD Yana Mata magiya Yana rokonta yafiya Akan Abin da ya gabata ya Kuma shirya zaman Aure da ita matsayin matar shi d ya aminta da ita? Yau tafi kowa farinciki aduniya Amman bazata tabbatar da hakan ba sai tagani a zahiri da aikace sanan zata gaskata zancen shi da nadamar shi. Washe gari su Affan, sadeeq , muhibbat,Husna suka kawoma Husna ziyara sosai mumcy tasa aka shirya musu lafiyayen girki na saukar Baki masu mahimmanci a saman husna aka baje musu kolin abincin FU'AD Yana Nan sukazo yakan saki jiki da sadeeq Amman har yanzu Akwai takun saka tsakanin shi da Affan duk yadda yaso ya goge Abin ya nuna Mai babu komai aranshi Amman ya kasa sai ma ji da yakeyi yanzu ya Fara kishi da duk Wanda ze ketare Mai ta gona. Husna sunsha Hira sosai da Yan uwanta kamar bazasu rabu ba daga baya su Affan d sadeeq suka tafi suka bar su muhibbat zuwa dare FU'AD yace ze maida dasu ko yasa amayar dasu sosai hakan ya faranta ran Husna Dan wata sabuwar walwalace da Jin Dadi suka sake mamaye ran huana. Humaira dai yadda Alhajin birni ya zugaga Mata labari harda cewa gidanta daban Tana zuba Ido a jibgeta a hadaden gida Mai yalwa da kayatuwa sai taga an direta a family house Bata sake dorar wa ba sai da aka ajiyeta aka Shiga k'aton gidan kafin ta Fara cewa wani Abu sai taga anyi wani waje da ita wajen yafi na kowa tsaruwa a gidan sai wata tafara cewa ba Nan bane ciki zakuyi da ita daga cikin matan gidan,sai dayar wata Mai tsiwa ta Fara cewa a ki Bari ta lasa kamar yadda aka Saba Mana canne sashinta ku direta acan sannun ku da k'ok'ari kudai d kirsa d makircin matar aka dire humaira a sashin komai Akwai tunanin da yake zuwama kowa arai shine Nan fa yafi kama da sashin megidan Amman Babu Wanda ya firta. Bayan an dire humaira dama taron kwado da hamane suka kawota ba Wanda yayi tunanin kaita wajen iyayen gidanta Dan abada amanarta Dan Haka Nan sukazo aka gagaisa ,Bayan ansaukesu d kaji da lemuka Basu Gama ci ba aka Fara cewa su fito Dan ajuya dasu Aiko wasu suka dinga guziri suna diba suna fita da sauri Dan Akwai tazara tsakanin gidan su mama habee d gidan humaira Dan sabuwar unguwace gashi ance har yanke Kan mutane anayi indare yayi Dan Haka kowace hantar cikinta ta Gama kadawa kowa ya watse akabar Amarya ba kowane ma ya samu zarafin Mata sallama ba. Itama Daman babu Wanda take buk'atar gani sama da Alhajinta Dan yace kyautar ta ta farko motace adaren ze mallaka Mata Kuma Dan Haka ta daukaki Daren. Babu jimawa Alhaji ya shigo d ledar shi yanata baza hanci kamar gajeren wando yanata fadin Rai ,yaso nuna Mata mazauninta tun adaren Amman dokin kwasan amarci da zeyi yasa y kasa sai yace Bari ya Bari sai gobe Dan Haka dama Akwai karancin sani sallah d ake gabatarwa ma shi ya yafeta Dan Haka ya cillo Mata ledar kazarta su humaira kamar jira ake ta hauta da yaga tanaci Tana korawa da drink shiko goga yana gefe Yana jiran mayinwaciyar kaza ,Tana ganawa kuwa ya ajiye babbar rigarshi y umarceta da takaimai d'aki Tana Shiga yabi sawunta. Bayan wasu mintoci kamar 40 sai tashin Zaki da cin mutunci tsakanin ango da Amarya Yana ALLAH y Isa ancuce shi yayi asarar kudinshi ya banzatar dasu abanza wallahi bazata Sabu ba Dan Haka adaren zata barmai d'aki kafin washe gari ta koma gidan me dattin hula da dankwalinta. Humaira kuka ta saki Tana bashi hak'uri Tana ya rufa Mata asiri ya Mata aikin gafara ya tuna da kauna ya barta ko zuwa wani lokaci kokai ze dedeta wallahi batasan ya akayi Haka ta kasance ba. Alhaji masifa y Shiga surfa Mata Yana wlh zati 1 kacan ze Bata shima Dan Baki su Gama komawa ne Amman Dole ta koma gida Dan besan asara y d'auka ba,humaira magiya d kuka harda majina Tana bashi hak'uri d kyar y hak'ura Amman da Al'k'awarin gobe d asuba zata barmai sashin shi t karasa kwana 6 da suka rage Mata acan. Bayan magriba Husna ta umarci FU'AD da ya taimaka amayar dasu muhibbat gida daga Nan itama zataga mamanta Dan ALLAH! FU'AD yaso cewa driver ya kaisu Amman ganin Yana k'ok'arin canjawa daga FU'AD din baya zuwa na yanzu sai kawai ya amsa ,ya umarci d su taho su tafi Husna d murna suka tafi har gidan hajiyar mu Tana Shiga ta Fara rungune aunty huwaila sanan mamanta tanajin wani shaukin sonta ba shigarta sanan hajiyar mu ta bud'e hannu Tana cewa"nifa bazakimin oyoyon ba? Kodan ban nuna Miki kulawa da so irin na jik'a d kaka ba? Ki d'auka komai y wuce sai sabon babi na rayuwa Kuma wallahi inasonki kamar sauran jikokina kisa haka aranki kuka na Shirin zuboma hajiyar mu d gudu Husna taje ta rungumeta Nan Abin Yama kowa Dadi" Hajiyar mu ce ta cema Husna "kije ki shigo min da me gidan nawa inkuma Rowarshi akemin toh" sai Husna tace "karfa kimin kwace Dan naki ya jima da tunkuyar birji " sai ko mamanta ta Mata dakuwa aunty huwaila tasa dariya su muhibbat ma suka tarena husna anata dariya, sadeeq ne yaje ya shigo d FU'AD yazo ya kwashi gaisuwar surikai anata Wasa da dariya Ana raha kafin su tafi ma har baba ya lalabo yazo husna murna kamar tayi Yaya Kai tsaye hajiyar mu ta bada shawarar mayar da auren maman Husna da baba amman a gidanta zata zauna Dan Akwai gidanta na gado da hajiyar mu da ta cinye Mata Dan Haka aka tsaida magana Nan d sati 2 za'a mayar musu da auren su baba d maman Husna sunyi murna sosai ,Husna ma kusan tafi kowa murna harda kukan Dadi ta sakar musu aunty huwaila d hajiyar mu suka dinga rarashinta d su Affan , FU'AD ji yayi kamar yaje ya rarashe ta sai d aka Gama magana sanan FU'AD ya d'auki baba ya mayar dashi gida adaren kafin ya dawo ya d'auki Husna suka tafi d rarashi Dan shagwabace ta motsa abinka da dacan babu Wanda za'ayima sanan tabi FU'AD d Al'k'awarin FU'AD ze sake kawota. Washe gari FU'AD ya Shiga wajen sanaya Tana ganin shi ta gaishe shi y amsa ya wuce d'akin shi yayi Abin da zeyi ya fito sai ya sake fita wanan fitar ce taba sanaya damar Kiran mamyn ta suka dinga gulma tana kashewa dady y kirata Yana Mata bayanin planning din d ya shirya Akan FU'AD Dan ya Gama tsara yadda kidnappers zasu daukeshi su bukaci biliyoyin kud'i inyaso ko gayyar Auren ta watse yaci riba ya cimma manufar shi g uwar bashi Ana binshi. Sanaya bataso ba ta Fara nuna Mai illar hakan Dan yanzu d gaske takeson FU'AD Aiko dady ya dinga surfa Mata bala'e harda zaga Yana cemata ta cire soyayyar shi maza Dan babu Wanda ya Isa ya hanashi cika birin shi inba hakaba wallahi zatayi takaba ko tabi umarnin shi duk abinnan da suke tataunawa FU'AD Yana bayanta Yana sauraro tare da recording a wayan shi batare da ta sani ba tabbas ya fahimci akanshi ake magana Kuma da mumunan manufa Dan Haka ya fito da dabara salon jiyar da sanaya daga dabarun shi Dan ya samu ya karb'i wayar ta ya Danna recording Dan ya zamar Mai evidence. Cikin sanda ya har gab da ita ya sakalo hannun shi ya Kama kugunta Yana Mata wani kalon so da shak'uwa ,muguwar firgitace ta kawoma sanaya ziyara idon ta na nuna salon razana Amman sai FU'AD ya manna Mata wani mugun kiss da ya tafiyar da mamaki da tsoron da taji har tayi shiru da wayar FU'AD ya Mata nuni da tacigaba da magana ya Mata dabarar karban wayar Bayan y juyar da ganin ta y kunna wayar ya Danna recording yace taci gaba da magana Yana rungume da ita yanata kasheta da salon da Bata tabaji ba har wani yawo yake Mata da hannun shi a jikinta kusan shidenawa sanaya tayi yau ga FU'AD a banza Dan Haka ta saki jiki dashi sai magana da take taunawa kafin ta mayar ma da dady amsa Dan da yaji yanayinta ya canja har tambayanta yayi ke kad'ai ce Kuma kina fahimtar bayani na? Da sauri tace" eh dady duk yadda kace Haka za'ayi" Jin ta amince sai ya cigaba da Mata bayanin yadda komai ze wakana tunda a d'akinta yake tabar k'ofa a bud'e cikin dare za'azo a tafi dashi a nisanta shi d garin har sai anbiya kudin fansa ko a kashe shi Dan yasan ma zasu iya biyan kudin , FU'AD d Ido da sallon shi yake sanar ma sanaya tayi waya babu komai Kar ta damu yasan akanshi ake maganar,ita Kuma sokuwar ta zata ya dawo gareta ne ta saki jiki tanata jin Dadi har gado ya kaita ya zaunar da ita a cinyar shi tabata nishad'i Tana waya,d dabara d salon FU'AD Mai jiyar da sanaya Dadi har suka Gama waya da dady Tana cemai zata kirashi kafin ta dire waya FU'AD yayi gagawar karban wayar ya rungumeta yanata Mata wani salon dabarun gyarana recording dinshi zama wayar na hanun shi yanata yaudarar ta harda hurt kiss ya dinga Mata sai da ya Bari takai kololuwa a zaucewa sai ya Fara tambayar ta dawa take waya? Still y sake Danna recording a wayar shi Yana d'aukan bayanin da zata Mai ,sai sanaya ta Fara barin Baki jikinta na rawa Tana bashi labarin manufar dadyn ita Kuma ganin kamar FU'AD din ya canja sai take cemai wallahi Daman bazatayi Abin d dadyn yakeso wallahi ya yadda da ita tanason shi wallahi bazata Bari acutar da shi ba Tana had'a hannu Tana bashi hak'uri Akan ya yafe Mata Kuma ya yadda da ita. Dabara FU'AD ya Mata ya nuna ya gamsu da baya Nan ta Kuma ze duba yagani in Akan kudine ai ko ba'abi hakaba shi me iya bayarwa ne ,sai ko wawiyar tace shikenan ma sai ka bashi mucigaba da Rayuwar mu tana sake makalkalo FU'AD jikin ta shiko k'ok'arin yakiceta yayi Yana cewa Bari yaje ya dawo sai sucigaba ,sikuwar yadda tayi gashi ya tafi d wayarta da tashi. Dakinshi ya Shiga ya mayar d recording din wayar shi y goge na wayar ta sanan ya d'auki wayarta y mayar Mata tanata yaudarar shi ya rungumeta Yana cewa tayi hak'uri Yana zuwa mumcy ce ke kiranshi Amman baze jima ba Yana Bata hak'uri ganin be tab'a Mata saukin Kai irin Haka ba sai ta yadda dashi. Bayan FU'AD y tafi sashin mumcy Kiran Yaya Jameel yayi sukayi magana sosai Akan matsalar suka fito da dabarar zuba jami'an tsaro yau agidan Dan tabbatar da hujja. Mumcy d husna duk basusan me ake ciki ba har suka gana magana d jami'an tsaro. Sanaya dai FU'AD ya Gama tsara Mata karta gayama dady komai ta ,sanaya ta yadda ta amince Tana zuba idon ganin Abin da FU'AD zeyi gashi ya Fara k'ular da ita sai ja Mata Rai yakeyi Dan Haka har ya Fara Bata haushi ma damma Yana nuna Mata kulawa har awaya Yana kiranta ya Bata hak'uri Akan gashinan zuwa gareta Dan yau a d'akinta ze kwana murna d Dadi kamar su kashe sanaya. Husna ma ta Sami kulawar FU'AD a ranar Amman ba sosai ba Dan hankalin ya tashi da Jin kudirin dady mumcy ma nata ba Husna kulawa. Humaira Bayan asuba Alh y watsota sashin d yace zata koma cikin sauran matan shi ,Aiko aka dinga Mata habaici da yaba magana Abin duniya Yama humaira zati jira take ta Shawo Kan Alhaji ya hak'ura su zauna haka da tuni taje ta dubo Halin d mama habee take ciki Dan tun samuwar tashin hankalinta a gidan da take rawar kafan akawota hankalinta y koma Kan uwar. Mama habee ko anata fama babu sauki cikin al'amarinta tanata tonama kanta asiri ,shiko baba yanata murna matarshi abar doyuwa a gareshi zata dawo gareshi. Hafeeza bikinta ya matso taje gidan Husna sun Fara shirye_shiryen bikin danma Tana fama da cikin da yake tare da ita. B2K ma d Aisha manya sun Shiga ankusa bikin saura kadan. Bayan FU'AD sun Gama komai dare yayi FU'AD sai dare yabar wajen Husna yanata nuna Mata kulawa itama ta saki jiki dashi sosai takejin ya zama jigo arayuwar ta ,hakan ba karamin faranta ran mumcy yakeyi ba Dan hankalinta ya kwanta yanzu burinta ya hak'ura ya karb'i sanayan ma a matsayin Mata sai ya gyarata yadda yakeso Dan yanzu yakin dedetasu zatasa a gaba Dan ya zama adali acewar mumcy. Bayan FU'AD yabar mumcy y Mata sallama Yama Husna ma y Gama waya da jami'an tsaro har baba me gadi yasan planning din su FU'AD din har aunty sa'adiya ma tasan meze wakana kusan kasa bacci sukayi ita da Yaya Jameel Amman FU'AD d Jameel sukanyi ma junan su magana ta sak'on karta kwana Dan Jin Halin da kowa yake ciki. FU'AD dai babu yadda ya iya da jarabar sanaya gashi yanason cimma manufarshi Dan Kar yaki Bata hadinkai ta fahimci wani Abu Dole ya dinga biye Mata Yana Jan al'amarin burin shi kafin komai ya wakana bakin da dady ya turo su k'araso jami'an tsaro suyi ram dasu sai wasan ya Kare tsakanin shi da sanayan. Sanaya ta Gama mutuwa Akan FU'AD yau ga FU'AD Tana saraffashi yadda takeso Dan Haka tafi kowa sa'a ayau yanata sakin jikin Dole da ita Ana cikin Haka yaji motsi a falo lokacin da sanaya take gab da cimma burinta akan FU'AD har sai d su kidnappers din suka shigo suka doshi d'akin shi Dan Haka aka Basu damar suyi Basu San ya canja wajen kwana ba ,duk shigowar su gidan a idon Jameel d sa'adiya ta window sa'adiya ta tsure Jameel ne ke kwantar mata da hankali da sauri sak'on karta kwana ta gauraye wayoyin su d jami'an tsaron da FU'AD din da kowama Wanda yasan da Abin Husna ma ta farka duk sai taji ta kasa bacci alamun wani Abu na Shirin faruwa. Bayan kidnappers din sun shige d'akin FU'AD sukaga kud'i a zube a gadon suka fada Kai suna kwasa kafin su nemi Wanda sukazo domin shi dake mayunwatan kudinne d sauri jami'an tsaro suka shigo suka arresting din su Kowa Baki sake cike da mamaki aka Fara fito da kudaden dasuka jida aka kwace bindugogin su Ana cajesu anaka saka musu handcuff kowannen su aka fito dasu falo Jin Ana gunjin ihu da ban hakuri FU'AD ya kwaci kanshi da kyar daga wajen sanaya ya fito falo Yana hamdalar yasha a wajenta batare da burinta ya cika ba,itama bayanshi ta biyo Tana Mai magiya sai sukayi cirko_cirko suna mamakin yadda akayi hakan ta faru. FU'AD tafi ya farayi Yana tafama jami'an tsaron Yana yabana aikin su ,Yaya Jameel ya Kira da sauri sai gashi harda aunty sa'adiya Bayan an Gama magana aka tasa keyar su a motar jami'an tsaron su 6 sukayi ofishin su dasu cikin Daren hajiya baba tajiyo alamun da matsala Amman ta window ta fahimci wani Abu kamar barayi aka Kama Jameel ta Kira a waya d sauri yazo y saneta Dan yaji alamun hankalinta y tashi ,Husna ma dama tun tashinta Bata koma ba Jin motsi a falo sai ta sakko duk taji Abin dake faruwa,suka dinga salati har su harri sai da suka fito suma. Sanaya kuka taketayi Yaya Jameel sunata bayanin Wanda yasa Ayi hakan mamakine bayyane a fuskokin kowa na gidan sanaya tashi tayi d gudu ta koma sashinta jikin Daren ta kulle kanta a d'aki tanata kuka. FU'AD ko d su Husna d su mumcy kusan anan falo suka karasa kwanan su Kowa ya kasa komawa anata tatauna yadda za'ayi d safe. Da gari y waye sanaya ta Kira dady ta sanar Mai da komai hankalin Dadi y tashi y rude y dinga surfa Mata zagi da masifa Yana cewa ya yafeta Yana Gama waya da ita ya kashe wayoyin shi yasa Mami ma ta kashe nata jami'an tsaron nata neman numbers dinshi shiru dake kidnappers din sunci gabza da kansu suka fada suka bada number shi ganin ba'a sameshi ba aka karbi na Mami itama shiru Dan Haka suka San Akwai Shirin da aka kula Wanda suna zargin sanayace ta sanar musu Dan Haka FU'AD ya nemi Husna da tabashi number mufida k'anwar sanayan ta bashi aka Kira ta d'auka akace tasa a speaker yadda dady d Mami zasuji aka Mai razanarwa Mai tsauri Akan sanaya da karamin company shi dake 9ja suna hanun jami'an tsaro inya kawo kanshi a yau ya nemi sulhu inko be kawo ba ya tabbatar suna cikin garari wata uwar ashar dady ya sakarma mufida Akan tabar waya a kunne har ankirashi za'aci zarafin shi har da duk'a ya bita , jami'an tsaron sukace a rabu dashi ai sako ya Isa su bashi yau zuwa gobe. Bayan su FU'AD sun koma gida ne suka mayarma d mumcy duk Abin d y faru tsakanin su day dady. Dady kuwa tunda yaji asirin shi ya tonu ya Shiga garari d tashin hankali har mamy ,da kyar mamy t lalabashi Akan su taho 9ja akashe case din su taho d sanaya ,d masifa ya Shiga surfa Mata Yana cewa duk ita tabata Mai shiri Kuma ai ta sani shi kawai zejene saboda company shi ,mamy amincewa tayi tace suje din inde zeje. Mufeeda ko cewa tayi bazata bisu ba Dan bazataga Abin kunyan d yayi ba Amman sai ta fake da katatun ta ita d kanin sanaya Dan shima y Gane gaskiya Dan Haka fumeeda ta koma gidan wani abokin dady su Kuma suka dunguma zuwa 9ja k'asar gado. Da zuwansu a hotel suka sauka basufi awa 1 da sauka ba suka amsa gayyatar ofishin jami'an tsaro aka Kira su FU'AD da har hajiya babba ma sai da taje har sanaya da Ido ya raina fata taga samu taga Rashi na FU'AD. Ganin abun na Shirin zama babban case sai mumcy tace abarsu suyi sulhu Amman komai arubuce ze kasance kowa ya yadda Amman abokin FU'AD jami'in tsaton da kyar ya amince Dan yace Abin ba na Wasa bane. Dady ko sai hura hanci yake aka fito da kidnappers din aka musu tambayoyi duk babu Abin da suka karyata sai dady d ya musu taurin kai. K'arshe dai aka kare da dady yasa hannu Akan duk Abin da ya sake faruwa da ahalin mumcy shine Kuma se ankamo shi a duk inda yake ,da kyar yace ya amince . Aka tambayi su FU'AD sun yafe mishi asake shi? Dan mumcy ce to bada umarnin Haka FU'AD yace "eh sanan ya sawakema sanaya Auren shi dadyn ta ya tafi da Yar shi ta jari hujja da ya bashi aurenta" Salati mamy tasa sai sanayan ma ta fad'a jikin mamyn ta shiko dady uwar harara kawai yake jifan FU'AD dashi k'arshe aka Gama komai a rubuce aka sallame su day niyar sanaya d jami'in tsaro zasuje ta kwado komai nata a gidan mumcy. Mumcy ma taja iyalanta suka tafi kafin su tafi sai d mumcy ta zubarma da dady kalamai masu Sosa zuciya kamar ya kasheta Dan bakin ciki hotel suka wuce suna zaman jiran sanaya Dan yace gobe zasu koma Dan bayaso Yan uwansu na Nan Susan me ake ciki gwanda ya gudu kafin labari ya Isa garesu. Sosai sanaya ta dinga kuka d zata bar gidan Tana ba FU'AD hak'uri d mumcy. Mumcy dai tace ta yafe Mata FU'AD Kam cewa yayi ALLAH ya yatemu Baki daya na rabu da kidnappers. Ranar gidan mumcy wuni akayi Ana murna da mamakin faruwar al'amarin ma gaba daya. Bayan sati guda FU'AD yakai Husna gidan hajiyar mu Dan acan za'a daura Auren maman Husna da baba harda FU'AD d Yaya Jameel da B2k aka d'aura auren. Baba kuwa bakin shi har kunne d abokanen shi wajen dai ya cika kamar manya akema Auren ba. Itama maman Husna taji kwaliya anata tsokanan ta husna sai narkewa takeyi Tana musu shagwaba aunty huwaila nata lalab'ata hajiyar muma nata bata kulawa sun Gama fahimtar ciki ne da ita basa barinta tayi komai kuma duk Abin da takeso Bata sukeyi. Sai d aka daura Auren su FU'AD sunci sun Sha sanan suka tafi gida d niyar sai dare zezo ya d'auki Husna, Yaya Jameel ne ya kawo su mumcy ,su hafeeza ma duk sunzo d mamanta d abokanan arziki har kawayen mumcy ma sunzo sosai bikin gyatumai yayi armashi har kowa ya washe ya koma gidan shi aka mayar da mumcy gida aunty sa'adiya kuwa Husna ta hanata tafiya wai su Bari akai Mata mamanta gidan babanta kafin sai sukoma Dole ta hak'ura. Dare Bayan i'sha aka d'ebi motoci da Amarya d komai nata da hajiyar mu d taimakon FU'AD d aunty huwaila suka gyarama baba d maman Husna gidan su yayi kyau aka kaisu FU'AD ne yakai su Husna daga can yayi gida dasu baba ko takan mama habee bebi ba sai sauti yaba k'anwar ta me jinyar ta da zuwa yanzu ta Fara gajiya yace ze tafi gidan Amarya Dan matarshi amaryar shi ta dawo wacce sanadin dawowarta ne habee ta fad'a wanan Halin na k'aikayi koma Kan mashek'iya. Kafin ya fice sai ga humaira afujajan Ido duk hawaye Tana Kuka ta shigo sai ko k'anwar mama habee ta Fara tambayar ta lafiya? Baba da mamaki ya cikashi sai ji yayi tana cewa ,wai na dawo gida har sai ya nemeni wallahi bashi da mutunci Dan akuyane Ashe .......Bata k'arasa ba baba yace "ko Kuma kece Yar akuyar ba " da ganin Kira ai Daman zataci mutum. Kanawar mama habee sai cream tayi ai tunda Auren rawa yake Zo ki kula d mamar ki Dan ko da take da lafiya ba dadinta mukaji ba tausayi da Imani yasa nake zaune a wajenta ,sai ko humaira tasa kuka ta kamata Tana Bata hak'uri Tana cewa"ta Mata Rai wallahi ta San komai ,baba ficewa yayi ya barsu a wajen Yana zumudin gidan amaryar shi sabuwa. Bayan sati 4 humaira duk ta fita hayyacinta d jinya baba so 2 kawai yaje ya duba su shima kayan abinci yakai musu da zuwa d'aukan haidar Dan samamai makaranta Mai kyau ,haidar nata murna baba ya tafi dashi Dan yanzu tsarin kayan abinci yake bayarwa buhun hunna ya tashi daga awo duk wanan taimakon FU'AD ne Dan husnan ma Bata sani ba. Husna tazama Yar dangi ji take tafi kowa Jin Dadi da farinciki ayanzu taje taga babanta da mamanta taje gidan kakaninta duk inda taso zuwa dai yin duniya zata ta dubo humaira d mama habee ,Amman FU'AD ya hanata Dole ta hak'ura. Su aunty huwaila sun koma da farinciki d tsaraba jibgi da FU'AD d Husna suka musu Dan FU'AD ya sakar Mata bakin aljihu sosai takeyin duk Abin da taso Dan mumcy ta zaunar dasu tamusu nasihar rik'e juna da Amana Musamman FU'AD din da cire komai arai Dan sun zama abokan arzikin juna hakan yasa FU'AD ya dinga ba Husna hakuri Akan abubuwan da suka dinga faruwa yake sake ninka Mata kulawa da so da k'auna ,gashi kowa na gidan son Husna yake Dan saukin kanta da iya mu'amala da kyauta ga kowa ya kwalafa Rai Akan cikin jikinta. Kwanaki sun shude ,satikai sun tafi,wattanni sun ja yau cikin Husna ya cika wata Tara Dan har anyi bikin B2k da Aisha ,anyi bikin hafeeza ma da mijinta Isa duk lokacin Husna babu bayani anata faman da ciki. Baba yakan kaima su humaira kayan abinci da Abin buk'ata da taimakon mama Dan Yama saki mama habee Dan bega ranar zama da ita ba humaira ma takardar ta har gida ta biyota Dan Haka tayi kukan tayi takaicin har ta hak'ura Dole. Yaune Husna ta tashi da nak'uda sama_sama tun Tana daurewa har sai da FU'AD ya ganota ,tace Mai babu komai har murmushin k'arfin Hali takeyi ,shide yace be yadda ba ya sauka ya sanarma mumcy da sauri ta hauro ta Mata tambayoyi ta Bata amsa sai mumcy tace suje asibiti alamunta ne sai fatan ALLAH ya Bata da sauki. FU'AD a rikice ya d'auki makulli ya d'auki aunty sa'adiya suka nufi asibiti. Bayan andubata akace alamunta ne ba'a Kara awa 1 ba Husna aka dinga gumurzo sai ga yarta macce katuwa Mai Kama da ita kyakywa. Murna wajen FU'AD Abin Babu misali tun a asibitin ya dinga rashin kunya agaban kowa Husna nata rufe fuska sai aunty sa'adiya ce take tsokanan shi tana cewa Daman Mai kunya inya falle sai ankauce Mai ya dinga cewa yaji din gudan jinin shi duk da ta biyuce dai Mami ce ta farko. Bayan ansallameta FU'AD ya dinga sanarma mutane duk Wanda bezo barka ba ya Shiga uku wajen FU'AD. Bayan suna da aka zubar da naira baby taci sunan aunty huwaila da aunty huwaila zasuzo ma Amman FU'AD ya hanata yace Suma sunan zuwa da baby tayi kwari zasuje kusan k'asa5 harda india d saudiya..... Sosai kowa yake kula da Dan uwanshi tsakanin FU'AD da Husna sanan suyi tarayya wajen bama baby huwaila kulawa gami da so da k'auna. Komai na tatiya yadda akeso baby huwaila takai 5months FU'AD ya Gama musu komai sukama mumcy sallama da kyar FU'AD yabar Husna taje taga humaira da mama habee ta musu Alkhairi humaira nata kuka tana rok'on ta yafiya taje gidan hafeeza ma Dan Basu da nisa da unguwar ta Mata Alkhairi sosai sanan taje gidan maman hafeeza ma ta Mata Alkhairi sai ta wuce gidan hajiyar mu Suma ta musu Alkhairi sanan ta wuce gidan B2k ta musu sallama tanata tsokanan Aisha Mai ciki Dan har y fito sai ta wuce gidan mama d baba ta musu nasu kabakin arzikin cike da kewa da kulawa suka rabu FU'AD ya d'auketa sukayi gidan mumcy. Washe gari sukama mummy sallama suka Kira aunty sa'adiya ta waya suka musu sallama Dan ta tafi wajen Jameel tafi Gane ta dinga zuwa Tana dawowa basa son barin mumcy ita kad'ai Musamman Dan barin Mata Mami da akayi tunda aka yayeta aka barma mumcy ita. India su FU'AD suka Fara sauka da tsaraba Mai yawa sunsha tarba tsakanin FU'AD da Affan an gyarota sai shiri ma yanzu da suke sosai kowa ya dinga murna da ganin su anata d'aukan baby huwaila suna nuna Mata tsantsar so kin yadda sukayi su FU'AD su sauka a hotel. Daga Nan suka dinga zuwa kasashen da zasu saudiyace ta k'arshe sukayi umrar su suka koma gida Bayan sun shafe wata 5 har Aisha ta haihu d'a namiji. FU'AD da Husna aka Dora daga inda aka tsaya sosai suke morema Auren su da kula da junan su FU'AD da wuri ake dawowa daya wajen Aiki ,Husna na kula da Mami da baby huwaila sosai sanan Tana kula da mumcy da Haka ta sake narkewa cikin zuciyar FU'AD d Yaya Jameel d mumcy kanta ga motar ta d Fu'ad ya siya Mata me kyau da tsada duk yadda takeso haka akeyi rayuwa ta sauya sai Jin dad'i da Jin dad'i kawai tsakanin masoyan biyu. *TAMMATBIHAMDULLAHI* ```Anan na kawo k'arshe littafi a me suna RIK'ON KWARYA Abin da na fad'a daidai ba iyawata bace da yadda ALLAH nayi Abin da nayi kuskure ajizancin Dan Adam ne ALLAH yasa sakona yaje inda ya kamata na gyara a gyara na badaidai ba akauce``` *Kuyimin Afuwa typing error s Dan basamu nayi editing ba Cox pg din Akwai tsayi*🤦🏼‍♀ Sai mun had'u Bayan sallah cikin sabon novel Dina me suna..................🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀🏃🏼‍♀ Urz Maman shaheed😍 Shire And Comments Copied By YAYA HAYAT (admin Hayat hausa novels Group Hausa novels and fashion Group Cool novel, makeup and kitchen1 Group And WOMEN24 TV Group WHATSAPP NO:+2349030159301