[6/19, 11:42 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 1/2 Da farko dai sunana safiya Al-hassan sani ni haifaffiyar garin kaduna ce asalin mahaifina su mutanen zaria ne momallawa ne, babana yana da mata uku. Ta farko sunan ta Hajiya Atika y'ar garin makarfi sannan matarshi ta biyu Hajiya Maryam mahaifiyata kenan itakuma Asalinta y'ar garin kebbi ce a zuru matarshi ta uku itace Hajiya Hauwa'u ita kuma asalinta y'ar katsina ce a huntuwa. Gidanmu mun kasance mu ashirin da biyar ne y'ay'an babanmu amman uku Allah yayi musu rasuwa, mu ashirin da biyu muke raye acikin yaran gidanmu nice ta sha tara, a dakinmu kuwan nice ta shida, matar babanmu ta farko Hajiya Atika tana da takwas haihuwarta tara amman takwas ne a raye daya ya rasu, mamata kuma haihuwarta goma amman takwas ne suke raye biyu sun rasu,matar shi ta uku kuma 'ya'yanta hudu ne kacal a gidanmu, amman ta taba yin aure ta haifi wasu y'ay'an sannan auren ya mutu ta auri mahaifina. Muntaso nida kanwata Firdausi wadda take bimin tare muka taso dukda na girme ta da y'an watanni amman kasancewar babanmu idan yaran shi suka taso tare koda daya ya girmi daya to tare zai kaisu makaranta, a haka muka taso akasani ni da Kanwata Firdausi a nursery school tare da wasu daga cikin yaran unguwa kasancewar Babanmu mutum mai jama'a da son taimako yasa yake daukar yaranshi da na masu karamin karfi ya kai school shi yasa yake da jama 'a, tare muke zuwa tare muke dawowa saboda school din yana bayan gidanmu ne . Kasancewar gidanmu akwai mata to dole za'a samu y'an kace nace wanda muka taso muka ga anayi , zasuyi rigimarsu tsakanin su amman mu yara babu ruwanmu don bamasa baki, Mahaifiyata mace ce mai kawaici da hakuri wanda duk abinda zasuyi bata sa yara aciki don haka, muka taso da kaunar y'an uwanmu, don munga suna rigima bama sa kanmu aciki muna mu'amala da kowaccen su da zuciya daya, bama taya Mamanmu kishi abinda bamu sani ba su sauran y'an uwanmu basa kaunarmu don suna taya iyayensu kishi. Haka dai muka taso tare ni da Firdausi dukda cewar na girmeta amman haka nake binta tamkar itace yayata, Abinka da yarinta duk lokacin da na bita muka fito wasa sai tasan yadda tayi ta hadani da sauran yaran unguwar sunyi min dukan tsiya, a kullum babu ranar da zata fito ta fadi banci dukansu ba, ni kuma ban iya fada ba don bana iya ramawa sai dai nayi kuka, hakan yasa tun abun bai damun mamana har ya fara damunta, In nashigo ina kuka tayi ta min fada wani lokacin ta karamin wani dukan tace, "Don me bazaki ramaba, saidai ki shigo kina baremin baki" Hakan baisa na koyi ramawa ba, wata rana daga cacar baki nida firdausi baiwarAllahr nan ta dauki abu ta makamin agoshi take kuwan ya kumbura, amman budar bakin mahaifiyarta sai cewa tayi: "Allah ya kara bake ba ce babbar banza duk inda ta shiga kina biye da ita maimakon ita ta biki" Mamanmu ba tace komai ba ta kamani tasa huta ta lailayamin har ya wartsake ta lallasheni. Haka rayuwar take tafiya muka gama nursery Babanmu ya kaimu L.E.A kabala tare da sauran yaran unguwar mu,nan muka fara daga primary one harzuwa primary six. Nayi matukar wahala don abu kadan zai hada ni da Firdausi su taru suyi min duka a kan hanyar dawowa gida, bata ma tuna cewar ni y'ar uwarta ce wadda muka hada jini daya wato mahaifi. Insha kuka na na share hawayena na dawo gida in fadawa mamana duk abinda ya faru sai tace inyi hakuri, wani abu daya karamin bakin jini a gurinsu shine Allah ya dorawa Babanmu sona fiye da sauran y'an uwana, don inada farin jini a gurin jama'a, komai akayi za'a ce safiya mutanen unguwarmu suna yawan yabo na komai dai safiya! Safiya!! Ashe hakan yasa y'an uwana da kishiyoyin Mamana kullata ta. Duk abinda Firdausi take min bantaba fushi da ita ba haka gobe zan kara binta koda zata sa ayimin wanda yafi wannan, a haka har muka gama primary muka tafi secondary nan ma ajinmu daya nida Firdausi, a wannan lokacin Firdausi ta kasance mace mai tsananin zuciya da fada don baka isa ka nunata da yatsa ba kuma ka maidashi lpy ba, musamman ma ni da ban tsiraba a gurinta tamkar kanwarta shi yasa na rage shige mata duk abinda zatayi saidai nasa mata idanu in kalleta . Shigarmu secondary school sai Allah ya hadani da mutane masu sona daga classmate dinmu har senior dinmu, A wannan lokacin duk wani alamu na cikar hankali (balaga) ya fara baiyana a jikina, hakan yasa tun a lokacin samari suka fara yi min tururuwa gida da makaranta. Alokacin da muka shiga jss2 wani saurayi ana kiranshi Nazir a cikin school yake haka a gida akwai wanda yake matukar sona, Abubakar A school kasancewar Naziru senior dinmu sai aka bashi Amir, ashe Firdausi taji haushi don me Amir din makaranta Zai kasance saurayin *Safiyya* . # Vote #Comment #share Maman Ihsan ce😍 [6/22, 3:15 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 3/4 Hankalin firdausi yayi matukar tashi da wannan abun saboda kishina take yi saurayina shine Amir, da yake haka akeyi a MSSN za'a bawa namiji Amir mace kuma Amirah. Wani ikon Allah Ana tashi daga school Firdausi da y'an unguwarmu suka tare ni tashiga tambayata "Me ya kaiki Mssn da har Amir ya ganki yace yana sonki ? " Da mamaki na kalleta nace, "Ni bana zuwa mss " Daya daga cikin gangs dinta Fati tace, "Lallai ma firdausi ki tambayeta da yaren da zata gane ki mareta zata fada miki duk kulle kullenta " Raina ya baci idona yayi ja cikin bacin rai nace , "Wallahi kar ki kuskura ki mareni karki fara na fada miki" Ta kalleni da mamaki tace, " kar na fara fa kikace ? " Kaina tsaye na amsa mata da "Eh" tace, "Toh saina mareki sai naga ubanda ya tsaya miki sai naga karshen kurinki" Tana kaiwa karshen maganar ta ta daga hannu zata zabga min mari da sauri na rike mata hannu raina bace nace, "Wlh bazaki kuma duka na ba daman can ina kyaleki ne to yau kam baki isa ba" Nan take kawar ta ta yunkuro zata mareni itama na rike hannun ta tare da zabga mata lafiyayyun mari guda biyu, ai kuwa sai suka tarar min abinka da mai hakuri idan ranshi ya baci bai iya fushi ba, na hada kansu na gwara na fara kai musu duka tuni kawarta ta gudu ita kuma ta tsaya don a tunanin ta zata iya yimin duka. Nan nayi mata dan banzan duka duk na ji mata ciwo muna cikin fada sai ga teacher din mu Firdausi tana ganin shi ta gudu don tasan bata da gaskiya yace, "Safiyya me ya hadaki da 'yar uwarki keda nake yabonki baki da fada" Nayi shiru ina sauke ajiyar zuciya nan ya bani hakuri tare da ja min kunnen na daina fada da kanwata. Firdausi kuwan direct gida ta nufa taje ta fadawa mahaifiyarta karya da gaskiya nan ta shiga sababi tana zage zage, don daman ita fadanta a fili yake sabanin uwargidan wadda take boye nata sai dai taje gurin wannan tayi gulmar wancan, kai kuma gobe ta kai taka gulmar gurin dayar, shi yasa yawanci ita ke hadasu fada a yau din ma tana zaune batace komai ba ballantana ta bada hakuri. Ina shiga gidan mahaifiyar firdausi ta tareni da masifa tana zagina tana cewa, "Don mugunta kinkama kanwar bayanki kin dake ta saboda cin zali ko da yake kin sha a nono ba laifin ki bane amman don uwarki yau sai na fadawa ubanki don bazan saki baki ba ki lahanta min yarinya domin nasan ciwonta ehe" Mamana tana zaune amman batace komai ba ta tashi ta ahige daki،saida abun ya isheta ta leko tace, "Haba maman Garba bai dace kiyi ta fada akan yara ba da zaunar dasu kika yi kikaji ta bakinsu sannan sai ki yankewa mara gaskiya hukunci " Nan fa fadan ya koma na mamana saida mama tayi mata tas sannan tayi shiru. Ashe shirun nata iya nan ne sai da dare taje tasamu Babanmu da zancen tace, "Alhaji kana ganin Safiya yadda take musgunawa firdausi tun ina shiru yanzun na gaji don haka ka shiga tsakanin su kowa yayi harkar shi" Babanmu ya aika aka kiramu ya tambayemu abinda ya hada mu, tas na fada mishi duk abinda ya faru, ya tambayi firdausi hakane tace "Eh hakane" Yace, "me yasa kuke fada a tsakanin ku alhalin kuna y'an uwa ? " Ni kuma nace, "Ai fati ce take zugata wai ta mareni" "Ta mareki fa ? " Ya fada cike da mamaki na gyada masa kai yace, "Firdausi kin manta safiya yayarki ce da har zaki daga hannu zuwa marinta ? " Tayi tsuru tsuru yace aje akira mashi Fati, tana jin kiran taki zuwa har sai da yace idan bata zoba zaije da kanshi ya daukota babu shiri tazo a tsorace don kowa yasan baban mu yana da zafi sosai musamman idan ranshi ya baci yace, "Ke me yasa kike hada y'an uwa fada ? " Tayi shiru ta kasa cewa komai nan yayi mana fada sosai ya kuma ja kunnen mu kar mu kara yin fada Baba ya dauko mana..............✍ Alkalumman: Maman nurul huda 👄 Maman ihsan😍 Comments please [6/22, 4:22 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 5/6 Dedicated to my forum Gorgeous Writers Forum Allah ya kara hada kanmu ya kuma daukaka mu Ameen Sai baban mu ya dauko takarda yace, "Toh kowa ga takarda ya karanta " Ni nafita kokari a boko, ita kuma tafi kokari a islamiyya, dukda nima ina kokarin amman tafini sai yace mu karanta. Kasancewar bokone sai na karanta ita kuma ta kasa nan yayi mata fada yace ta ringa zuwa gurina ina koya mata, don itama ta iya a daina yi masa asarar kudin shi. Ashe taji haushin zancen tana fita ta fashe da kuka, ta sanar wa mahaifiyarta abinda ya faru nan fa wani sabon masifar da bala'in ya barke a cikin gidan, ta fara cewa, "Daman baka sona baka kaunar y'ay'ana a kullum sai ka nuna mana kiyayyarka kafi son hajiya Maryam da y'ay'anta to wlh ahir dinku ku dukka don nafi karfinku kuma Allah zai saka mana" Nan tayita ruwan bala'i baji ba gani har cewa takeyi ya saketa ta huta, ganin haukan nata yayi yawa ya shuri takalmansa yayi waje yana mai yi mata addu'ar shiriya. Haka nan rayuwar ta ringa tafiya yau dadi gobe akasin hakan, har gobe uwargidan babana tana kulle kullenta shi yasa basa kwana biyu sai sunyi fada. Acikin wannan lokacin Naziru ya kammala karatunshi ya bar makarantar, tunda ya bar makarantar sai firdausi ta sarara min da bakaken maganganu da yimin sharri a gida. Ana haka Abubakar ya kara bude huta gurin kafa soyayyar shi a zuciyata, shi lallai da gaske yake aurena zai yi babu wanda yasan da maganarshi a gidanmu sai Firdausi,muna ta soyayyarmu duk da babanmu ya nuna bazai yi mana aure ba har sai mun gama makaranta saboda shi mutum ne mai son karatun boko sosai. Tun muna soyayya a boye har dai avun ya bayyana yana rakani makaranta haka idan an tashi yaje ya tarbeni, hakan yasa duk y'an unguwarmu sunsan muna soyayya amman banda mutanen gidanmu idan kika cire Firdausi, yayanmu wanda suke uwa daya da firdausi ana kiranshi *Musa* suna hira a majalisa sai yake tambayar *Abubakar* yace, "Abubakar wai ina kake zuwa ne da safe bana ganin ka haka kuma da rana ko ka samu aikin yi ne ? " Budar bakin Abubakar sai cewa yayi, "Ai Kanwarka safiyya ce muke soyayya shi yasa da safe nake rakata makaranta haka da rana sai naje mu dawo tare" Murmushin mugunta musa yayi ya gyara zama don ya bugi cikin Abubakar yace, "Da gaske kake kana sonta kuma zaka aureta?" "Eh mana sonta nakeyi kuma ina fatan ta zamo matata ku taimaka ku bani aurenta" Sai musa yayi dariya yace, "In dai auren safiyya kake so to mun baka sai ka shirya" Cike da farin ciki Abubakar yace, "Don Allah da gaske kakeyi?" Musa yace, "Eh mana da da gangan nakene? Ko ana wasa da maganar aure?" Abubakar yace, "Nagode dole na turo manya ayi magana" Musa yana tashi daga gurin gida ya nufa har dakin mamana budar bakinshi sai cewa yayi, "Nazo gurinki ne goggo maryam kuma nazo sanar miki wani mummunan labari" Mamana ta dafe kirji tace, "Mummunan labari fa kace Musa wannan wanne labari ne?" "Wallahi goggo Maryam sai kin mike tsaye inba haka ba zaa lalata miki rayuwar y'arki" Da mamaki ta kalleshi tace, Bangane za'a...................✍ Alkalumman: Maman nurul huda👄 And Maman ihsan😍 Comments is needed pls [6/23, 4:50 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 7/8 "Bangane za'a lalata min rayuwar yarinya ba ?" Yace, "Kwarai kuwa don kinga safiya din nan taki ta taso da farin jini a unguwar nan kowanne saurayi ya taso sonta yake yi kinsan mene babbar matsalar?" Cikin jimami da takaici tace, "A'a sai ka fada min" Yaci gaba da cewa, "Duk samarin da suke cewa suna sonta ba don Allah bane, suna yaudarar ta ne kawai don su lalata mata rayuwarta" Atake gaban maman mu ya fadi ta fara fadin "Innalillahi wa'inna inna ilaihir raji'un" Taci gaba da cewa, "Lallai kam wannan mummunan labarine dole in hana safiya fita" Yace, "Kwarai kuwa dole ki hana ta fita kafin a rabata da darajar ta tare da tarbiyyarta" Ya mike zai fita sai kuma ya koma yace, "Kuma duk wanda yazo yace da gaske sonta yake to wallahi karya ne ba son ta yake yi ba zai yi muku wayo ne yayi duk abinda yaso da ita" Nan mamana ta shiga yi masa godiya tana cewa, "Nagode musa lallai ka cika dan uwa kuma mai kaunar kannen shi insha Allahu zan kula da ita sosai Allah ya taya mana" Yayi murmushi ya fice a dakin. Tundaga wannan lokacin Mamana tasa min ido fiye da da duk wani motsina akan idonta yake haka tana sane da duk lokacin tafiya da dawowata daga makaranta, Nan mamana duk ta canza min idan na sake yaran gidan suka rigani dawowa sai tayi ta hantarata tana fada hakan yasa na fara shiga damuwa babu wani fuska ga y'an uwana haka ga mahaifiyata. Wata rana na dawo daga makaranta muna tafe nida Abubakar sai ga Mamana ta dawo daga unguwa, ta kallemu suka gaisa ita da Abubakar da fara'ar ta ta wuce gida. Aikuwa ina isa gida na cire kayan makaranta na kenan sai gata da bulala ta fara tambayata, "Me ya hadaki da Abubakar da har kika jera tare da shi kuna tafiya?" A take kirjina ya fara dakan tara tara don nasan bani da gaskiya na fara kuka ina bata hakuri kar ta dokeni. Amman ina sai da Mamana tayi min dukan kawo wuka har saida ta gaji don kanta tun ina kuka da ihu har muryata ta dishe ina bata hakuri. Tace dole sai na rabu da Abubakar Amman na kasa furta mata zanyi don ina matukar son Abubakar kamar raina kuma nasan bazan iya rabuwa da shi ba. Babu wanda yayi yunkurin bata hakuri a gidan mu sai ma dariya da wasu suke yi mana. Dukan da mamana tayi min bai hanani kula Abubakar ba don ban ma fada masa ba ballantana na bukaci ya rabu dani, don a tunani na mama bazata sani ba tunda tana gida don bansan ana kai mata gulmata ba. Ashe ranar da aka dakeni Yaya Musa yana nan yana cikin daki yana kallinmu ta window. Wata rana ya shiga dakin uwargidan baban mu suna hira sai yake cewa, "Ai in fada muku safiya ta lalace ta zama y'ar iska don Abubakar take bi" Suka hada baki gurin cewa, "Wanne Abubakar din?" Yace, "Abubakar na unguwar nan mana wanda muke zama tare a majalissa" "Tab lallai yarinyar nan ta bata wayonta"daya daga cikin su ya fada. Musa yace, "Ai don baku sani bane amman iskanci ko babbar karuwa Albarka don ance har hotel yake kaita bata zuwa makaranta, idonta ya riga ya gama budewa" "Ko shi yasa goggo Maryam tayi mata duka kwanaki?"yaya Rabi'u ya tambayeshi, yace "Eh mana dalilin dukan kenan bata fada bane don kar zancen yaje kunnen babanmu" Kadan kadan magana ta fara zaga cikin gidanmu cewar na zama y'ar iska daga yayyena mata har kanne aka fara janye su daga jikina wai kar na lalata su, ko tambayar su wani abu nayi sai iyayensu su bata rai su kirasu. Haka a unguwa ma..........✍ Alkalumman: Maman nurul huda👄 And Maman ihsan😍 Pls your comment is needed [6/25, 4:42 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 9/10 Haka a unguwa ma kowa kallon y'ar iska yake min, amman ni bansani ba kowacce uwa tana janye diyarta daga gareni wai kar na lalata musu y'ay'a. Shi kuma Abubakar kanwar mamanshi gurinta yake da zama kuma makotanmu ne, da ta samu labari sai tace ya daina tsareni a hanya muna hira ya ringa kirana cikin gidanta muna hira domin ita Allah ya dora mata kaunata tamkar y'arta kuma tana farin ciki da alakarmu tsakanina da dan yayarta dake wajenta wato Abubakar. A lokacin mahaifinmu duk cikin gidanmu yafi son aike na musamman da safe inje in siyo masa kayan breakfast, sai dai in ba na nan sannan ya aiki wani cikin y'an uwana, Kuma kanwar Maman Abubakar itace take saida kosai, da yake har tasan na nawa yake siya sana je zan tarar ta zuba ta ajiye mishi, shi yasa idan naje siyan kosan sai na tsaya muyi hirar mu ni da Abubakar sannan in dauko cooler kosan in tawo gida . Kullum haka nakeyi tun babanmu baya fahimtar na dade har ya fara ganewa rannan dai ya tambayeni yace, "Safeeya wai me yasa y'an kwanakin nan idan na aike ki ki ke dadewa? Bakya kawo min kosai na akan lokaci?" Nan fa duk na rude da kyar na fizgo magana nace, "Kayi hakuri Baba insha Allahu bazan karaba, zan ringa dawowa da wuri" Na fadi haka ne kawai don na kare kaina tunda ni nasan inda nake tsayawa wato hira da saurayi. Da yake Maman mu ma'aikaciya ce, sai na bari sai ta tafi gurin aiki sai na fice a gidan muje mu hadu ni da Abubakar a wani gurin muyi hirar mu. Abinda bamu sani ba musa yafi kowa sa mana ido don ko mamana bata kaishi samin idoba don tun kafin tafiya tayi nisa ya gane ina fita idan mamanmu ta fita, shi yasa duk inda muke zuwa muyi hira ya sani duk wani AP din da muka hada sai yasan yadda ya bugi cikin Abubakar ya fada masa inda zamuyi hirar. Shi kuma Abubakar kwata-kwata bai gane manufar Musa ba, don yana mishi kallon mai son alakarmu tunda yana nuna ya bashi goyon baya 100%. Hakan yasa ya dauki dabi'ar kiran mamana ya fada mata cewar na fita tare da Abubakar, ita kuma tana dawowa zatayi min matsiyacin duka kuma hakan bai hana ni fita ba na rasa wa yake fada mata duk randa na fita. Kullum sai naci duka saboda Abubakar tamkar jaka, babu ranar da zata fito ta fadi banci duka ba a gurin mamanmu, hakan yasa y'an gidanmu suka gasgata cewar ni din y'ar iskace tunda kullum sai an dakeni, don su basu san dalili ba bayan wanda musa ya fada masu. *Ina son nayi amfani da wannan damar gurin tunanatar da y'an mata har ma kananan zawarawa cewar su daina saurin shigewa namiji da zarar ya furta yana son su don basu san cikin shi ba wata kilama ba sonki yake ba musamman idan iyayenki sun nuna basa sonki da shi ki daure kiyi hakuri ki fawwalawa Allah tare da kai kukanki sai kiga komai yazo da sauki amman ga y'an matan mu ba haka bane su gani sukeyi iyayensu basu waye bane tunda basu san soyayya ba, wlh duk namijin da ya san cewar iyayenki basa son alakar ku kuma ya ki kyaleki ba masoyinki bane akwai abinda yake nema a gurinki, wani gayen ma dan karya har turo miki abokinshi zai yi yace bashida lafiya saboda sonki hawan jini ya kamashi kaji karyar banza yo iyaye suka mutu ma aka hakura ballantana budurwa pls y'an mata kuyi wa kanku karatun ta nutsu Allah ya tsaremana y'ay'anmu daga sharrin guys Ameen* Duk wahalar da nakesha amman na kasa rabuwa da Abubakar, hakan yasa harda makirci ake hada min duk lokacin da mamana ta kusa dawowa daya daga cikin kishiyoyin ta zai aikeni kasuwa, idan ta dawo ta tambayi ina nake sai suce su basu san inda naje ba ai tun fitar ta na fita ban dawo ba har yanzun,ai kinsan inda y'arki take zuwa tunda ta balaga ta fara bin samari bata hanani ba ai gashi yanzun tana gani da idonta abun ya ruka ko tsoro banayi in dawo yadda nakeyi da kafin ta dawo, yanzun zamana nakeyi saboda nima inajin kaina. Ita kuma ina dawowa ta rufeni da duka tamkar An aikota ba tare da ta tambayi ina naje ba. Sry fans Alkalumman: Maman nurul huda 👄 And Maman ihsan😍 Comment please [6/27, 9:20 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 11/12 Kullum abun baya canzawa na zamo tamkar jaka a gurin mama, bata taba tambayata akan zancen ba. Wahala tayi wahala dole na fara tunanin barin Abubakar tare da soyayyarshi domin kuwa bazan iya jure wannan dukan ba kar naje wata rana mamana tayi min baki. Ai kuwa na sameshi da zancen nace, "Abubakar bawai bana sonka bane ba wlh ina sonka amman wannan rayuwar ta wahala bazan iya ba mu rabu kawai don ina gudun bacin ran mahaifiyata" A take ya rude ya fara rokona karnayi haka yana cewa, "Yanzun duk soyayyar da kike min iyakacin ta kenan zaki iya rabuwa dani saboda wahala alhalin ni duk wuya duk runtsi ina tare dake babu wata wahalar rayuwa da zata sa na rabu dake, ina tare dake safiya har muddin rai ke din tsokar da ke kirjina ce idan babu ke hakika babu Abubakar, ki tausayawa bawan Allahn nan kar ki rabu da shi domin zai iya rasa rayuwarshi, kece ni safiya nice ke kar ki gujeni ni naki ne ke kadai" Nan dai yayi ta zuba kalaman soyayya har sai da yayi nasarar janye zuciyata naji shi din rabin jikina ne bazan iya rabuwa dashi ba a take nayi masa Alkawari nace, "Nayi maka alkawari Abubakar ko kasheni za'ayi bazan rabu da kai ba ina tare da kai, da soyayyar ka zan rayu" Murmushi Abubakar yayi yanamin godiya nan muka ci gaba da hirar mu. A lokacin da muka shiga js 3 sai mamana ta fara hanani fita in kuwa fitar ta zama dole to sai dai na fita da kanina namiji wanda yake bina mai suna Abulkhairi ko autarmu Nabila,amman ni kadai ban isa na fita ba saboda kar naje gurin samari nake zuwa a tunanin mamana da sauran mutanen gidan. Alhalin ni kuma banida wani saurayi bayan Abubakar, kuma shima din don naga yana sonane tsakani da Allah kuma nima ina sonshi. A wannan lokacin ne yayata wadda nake ba zatayi aure sai miijn nata ya siyo mata waya ash motoroller da ake yayi a lokacin dayake tanada wata wayar sai ta ce na dauketa tunda ta samu sabuwa. Kaf cikin yaran unguwar mu daga maza har mata wadanda suke tsakanin shekaruna ni na fara rike waya. Tabbas waya tana bata tarbiyyar yara da matasa waya a wannan lokacin itace ja gaba gurin gurbata dukkan reshe mai kyau. A lokacin da na samu waya sai naga ai wata damace aka bani wadda zamuyi communicating da Abubakar a duk lokacin da muka so zamuji muryar juna harma mu tsara inda zamu hadu, Dagani har Abubakar munji dadin samun wayar nan sosai Mamana da kanta ta saimin sim tasamin, domin bata kawo komai a ranta ba. Abinda bata sani ba kuwa shine ta kara bamu gudun mawar gudanar da soyayyarmu yadda muke so domin waya bata yankewa a tsakanin mu kullum muna waya. Idan ya kirani sai muyi awa biyu zuwa uku muna waya ba tare da na gaji ba, kuma koda mutum yana zaune a gurin bai isa yaji me nake cewa ba saboda ina rage murya sosai . Irin dai yadda y'ammata suke waya lol Muci wayarmu sosai don yana turomin kati shi yasa baya yankewa a waya. _Bake kadai ba safiya nima hakane fah🤣_ Yau da gobe akace sai Allah sannu sannu maman mu ta fara fahimtar cewar ban rabu da Abubakar ba, Wata rana bansan yadda akayiba kawai mama ta rufeni da duka bayan tsayin lokacin da ta dauka bata dake ni ba. Kuma ta amshe wayar hannuna ta mika min sim tace, "Ga shinan sai kiyi kira da shi sim din" Haka nan na share hawayena kewar Abubakar ta dameni na dauko sim din nayi ta juyawa wani lokacin harda hawaye na. Wani dare da zan kirashi daren bakin ciki wanda bazan taba mantawa da shi ba yayana Musa uba daya ni da shi.............✍ Alkalumman: Maman nurul huda 👄 And Maman ihsan😍 Vote and comments pls [6/29, 7:40 AM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 13/14 Wani dare da zan kirashi daren bakin ciki wanda bazan taba mantawa da shi ba a rayuwata yayana Musa wanda muke uba daya ni da shi, ya shigo dakina ya tashe ni a barci na mike ina kallonshi da mamaki duk da banji a raina cewar nemana yazo yi ba tunda a ganina yayana ne dole ko yayane akwai so yayya da tausayina a ranshi a matsayina na kanwarshi yace, " Safiya kinsan ko me ya kawo ni ? " Na girgiza kai har lokacin ina ta tunanin me ya kawo shi nace, "A'a yaya Musa sai ka fada" Yayi wani murmushin gefen baki yace, "Matso kusa in tabaki safiya" Jikina ne ya dau rawa muryata tana rawa nace, "Yaya Musa ka tabani fa kace, ban gan ka tabani ba ? " Yace a dan tsawa ce "Eh ki zo nace na taba kiiiii" Nan fa muka shiga gardama ni naki bashi hadin kai shi kuma ya nace sai na yarda ana cikin haka sai ga Mamana ta fito yana ganin ta ya chanza akalar zance yace, "Wai safiya ba cewa nayi ki saka min tuwo inci ba ? Kika tsaya kina kallo na" Jikina har lokacin yana rawa nayi saurin dauko kwano ina cewa, "Kayi hakuri don Allah yanzun zan zuba maka" Na zuba mishi tuwon na mika masa ya amsa sai mamanmu tace, "Wai daman tuwo yace kisa masa kika ki kika tsaya baki zuba masa ba ? " Na girgiza kai alamar A'a, ta wucewarta daki bayan Musa ya fita. Washegari bayan sallahr isha'i kowa ya dawo gida gashi an dauke nepa gidan dundum yana shigo a tsakar gida ya tarar dani ina zaune sai yace, "Ke safiya zo nan" Na mike na nufe shi naje har inda yake sai yace, "Maza ki cire kayanki ki daura zani ki biyoni bayi" Shi fa duk a tunanin shi Abubakar yayi disvirgin dina, na kalleshi da mamaki nace, " Wanne irin in cire kaya na biyoka bayi" Na yi tsaye ba tare da na tafi zuwa cire kayanba ai kuwa ranshi ya baci yace, "Wai safiya ba dake nake bane da kika yi tsaye kika sani a gaba" Rigar jikina daman jacket ce kunsan yadda jacket take tana bayyana saman Albarkatun kirjin mace ban an karaba kawai sai ji nayi ya kawo hannu yana taba min kirji ai a zabure na buge hannun shi nace, "Wallahi kul ka kuma taba min jikina bana son iskanci me ka maidani ina matsayin kanwarka ne fa wallahi bazan dauki wulakanci ba" Ashe dayan yayan namu sunusi yaga abinda ya faru ya hade rai yace masa, "Kai lafiya ? " Nan ya daburce ya fara kame-kame yana cewa, "Abu nagani shine nake kakkabe mata" Da mamaki ya kalleshi yace, "Ya za'ayi cikin duhun nan kaga abu a jikin ta maza fada min abunda ka gani kuma ka nuna min shi" Nan ya kuma rikicewa yace, "Ai ni daman bayi zanje ba wurin ta nazo ba" Ya dauki buta ya wuce bayi abinshi yaya sunasi ya ja tsaki ya wuce dakin Maman shi wato uwar gidan. Yana jin tafiyarshi ya fara kirana yanacewa, "Ke Safiya kikawo min ruwa ina bayi" Nace, "Wallahi bazan kawo ba ! Bazan kawo ba !!! " Sai yayi shiru ya dade a cikin bayi sannan ya fito ya sameni a zaune lokacin ba kowa yace, "Ke dallah y'ar iska waye bai san halinki ba to abunda kike bawa Abubakar yana ci shi nima nake so ki bani naci" Sai kace wani abinci🤭 Sai nace, "Malam wallahi ni ba y'ar iska bace ni ba karuwa bace abinda kuke tunanin inayi da Abubakar wallahi ba haka bane hasalima bai taba neman hakan a gurina ba, kuma kai da ka nema bazan baka ba na hana babban kwabo kawai mts" Naje na samu mamana in fada mata duk yadda akayi gudun kar taji zancen a waje tayi zaton ko bani da gaskiya washegari ta daukeni ta kaini gurin kanwarta ta fada mata duk yadda mukayi da musa. Kanwarta tace, "Kin gani tunda kinsan yaron nan Abubakar yana son safiya ki kyalesu suyi soyayyarsu" Mamana tace, "Wallahi bazan bari ba ai nasan duk wanda zai ce yana son safiya a yanzun to ba sonta yake ba wayo zai yi mata ya rabata da darajarta" Kanwarta tace, " Daman ni shawara ce na baki don karki manta a yanzun Ss 2 zata shiga a ganina don ta tsaya da saurayi ba wani abu bane" Mamana tace, "A'a ita fa bata yarda da hakan ba a dole kanwarta ta kyaleta tayi min fada sosai akan na cigaba da kame kaina, nayi mata godiya muka nufo gida ni da mamana. Haka rayuwar taci gaba da juyamin a kullum sai an shirya labari an fadawa mamana ita kuwa daman ba ruwanta da bincike zata nada min duka ne kawai. Kuma babu mai kwata na agidan duk yawan gidan. Daga baya ma mamana da kanta ta koreni daga dakin ta tace bazata zauna dani a daki guda ba, uwargidan Babana ita tace, "Ai baza'ayi hakaba ki dawo dakina ki zauna ai nima uwace" Na tattaro kayana na koma dakinta da zama kwata-kwata mamana ta fita har kata ta cireni a gabanta bata ma san Allah yayi ruwana a gidan ba, rayuwarta kawai take yi bata da damuwa don bata kaunar naje gurin ta. Shekara ta zagayo kowa mahaifiyarshi tayi masa dinkin sallah amman banda ni kuma ga uwata a raye ubana a raye amman saboda Abubakar na rasa su tare da duk wata hidimarsu gareni. Babbar matsalar Mamana rashin bincike komai aka fada mata ta zauna a kanshi kenan bata la'akari da halayyar mutum zai aikata ko bazai aikata ba, duk abinda akace mata y'arta ko danta yayi a gurinta ya aikata ne kawai bazata tambayeshi ba zata yanke hukunci. Haka nan akayi sallah kowa yasa sabon kayansa ni kuma na wanke tsohon kayana nasa abina. Haka nan nacigaba da rayuwar kunci a gidan mahaifina, ga kuma firdausi ta dawo da halinta a kaina ganin bana tare da mahafiyata tasani gaba, ta ringa hadani da jikokin hajiya rabi har sai da mukayi fada sosai hakan yasa itama ta koroni daga dakin ta tace, "Bazan iya ba na taimakeki amman kina fada da jikokina ki koma dakin uwarki mai bakin hali kawai uwarki ta koreki ma ballantana ni" Na kwashe kayana ina kuka na nufi gidan kanwar mamana na fada mata duk abinda ke faruwa mamaki tayi sosai ta kuma ce na dawo gidanta na zauna, na koma gidanta. Wata na biyu a gidanta sannan ta samu ta shawo kan mamana ta hakura na koma gidanmu. Alkalumman: Maman nurul huda👄 And Maman ihsan😍 Pls share and comment [6/30, 2:05 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 15/16 Na dawo gidan naci gaba da zama cikin kunci da matsi kowa ya tsangwameni magana daya biyu safiya yar iska. Wata rana ina fita naje makotanmu a ranar banma hadu da abubakar ba amman mamana tana dawowa akace mata wai anganni da Abubakar yana latse ni, a take muna haduwa mamana ta dauramin wani gigitaccen mari wanda yasa na dauke numfashin wucin gadi na fara ganin juwa tana daukana, Nan mama tayi min duka zancen duk ya karade unguwarmu dama family house dinmu dake zaria kasancewar y'ay'an hajiya Rabi sunfi rayuwa acan shi yasa suka kwashe karya da gaskiya suka fadawa dangin mu, cewar nazama y'ar iska bin maza nakeyi na zama karuwa harda ciki nayi aka zubarmin hakan yasa duk sukaja kunnen y'ay'ansu akan su daina mu'amala da ni. Duk family din mu babu inda zanje na samu salama saboda anbata min sunana ako ina kowa gudu na yakeyi, Kaf din yaran gidanmu mata babu wadda babanmu ya taba daga hannu ya daketa sai ni saboda makiya na da magulmata na da kuma *Sharrin y'an uba* sai da aka zigashi yayi min dukan tsiya. Hakan yasa na fara kokarin cire Abubakar daga zuciyata duk da irin son da nake yi masa na fara ja baya daga gareshi. A lokacin da na shiga Ss 3 sai kuma farin jini na ya karu masu kudi suna yawan zuwa gurina har gidanmu duk da bawai ni ke nuna musu gidanmu ba tambaya suke yi. Nan fa zance yakara bin gari yanzun iskancin nawa ya karu gashinan harda alhazai masu motoci ke biyoni har gida. Duniyar ta kara yimin kunci, ada ina tunanin idan na rabu da Abubakar za'a sakarmin mara nayi fitsari ashe ba haka bane, wani ballin daban ne zai kunno kai. Babban wana ya kamani yayimin dukan tsiya, na zamo tamkar jaka wannan ya daka wancan ya daka kullum cikin duka duk iya kokarin da nakeyi don na fahimtar dasu amman sun kasa fahimta ta. Haka nan nayi ta rayuwata mahaifiyata bata bani fuska ba ballantana na sanar da ita damuwata ba har na gama secondary school, acikin yayyena mata wadanda suka yi aure yayarmu babba mace a dakin mu ita kadai ce take tausayamin. Nan ta fara cewa inje wurin ta inyi mata hutu sai inje sati daya nake yi na dawo bazan dade ba zata kuma neman nazo, tana son zama dani don bani da k'iywar aiki domin a unguwarsu basu da ruwa sai kayi tafiya kafin kaje inda ruwan yake haka zan kwashi bokitai na tafi na debo mata ruwan. Don nafi son zaman gurinta akan gidan mu duk da ina mata aiki amman nafi sakewa akan na zauna gurin da kullum ina cikin cin duka. Kullum sai naje dibar ruwa hakan yasa na fara sabawa da mutanen unguwar muna dan gaisawa a tsakanin mu, wata rana naje dibar ruwa na dawo sai aka aiko ana sallama da ita sai ta fita don ganin wake kiranta. Tana fita sai taga police a tsaye bayan sun gaisa yace, "Don Allah yarinyar nan da take dibar ruwa kullum 'yar aikin ki ce?" Sai tace masa "A'a ba 'yar aikina bace kanwata ce mamanmu daya da ita baban mu daya tazo hutu ne" Nan yayi mata fada akan don ba ita tahaifeni ba shi yasa kullum take aikana dibar ruwa, ta kalleshi da mamaki tace, "Malam yarinyar nan fa kanwata ce uwa daya uba daya kuma bani da ruwan nan mene aibu don ta debo min ruwa?" Sai yace, " wannan ne kawai matsalar?" Tace masa "Eh "yace, "Toh ni zansa a ringa kawo muku ruwa amman ta daina zuwa dibar ruwa" Tace, "Toh" tare da yi masa godiya yayi tafiyarshi, Haka ake kawo ruwa kura daya kullum, rannan ta fita unguwa sai wasu samari a unguwar suka gaidata tare da tambayarta "Kwana biyu mun daina ganin kanwarki tana zuwa dibar ruwa " Sai tayi dariya tace, "Ya akayi kukasan kanwata ce?" Sai sukace, "Ai daga ganin ta ansan kanwarki ce ba sai an fada ba" Tayi murmushi tace, "Tana gida" Sai suka ce," don Allah muna neman Alfarma a gurin ki?" Tace, "Ina jinku Allah yasa bata fi karfi na ba" Sukace, "Dibar ruwan da takeyi muke so ta daina zamusa mai ruwa yana kawo miki ruwan" Abin ya bata mamaki ya kuma daure mata kai tayi musu godiya ta je ta dawo ta sameni tace, "Safiya daman irin farin jinin da kike dashi kenan? Gaskiya dole ki samu matsala a gida saboda ba lallaine aganki da irin wannan farin jinin ba ba tare da anbiki da mugun abu ba" "Kinsan me yasa kika ga na daina turaki dibar ruwa?" Na girgiza kai nace, "A'a" tace , "Rannan wani police ni ban ma san a inda yake ba shine ya dauki nauyin kawo mana ruwa kuma gashi yau wasu samari suma sunce na daina turaki dibar ruwa zasu sa a kawo mana" Washegari na shirya zanje gida domin inje inga gida sai tace tare zamuje, Muka je gida tare suna hira take cewa, "Goggo Ki daina dukan safiya akan samari domin ba yin kanta bane Allah ne ya yita mai farin jini duk inda ta shiga saita samu masoya" Nan mamana ta rufeta da fada sosai tana cewa, "Karki kara fada min wannan maganar don kuwan safiya ta riga ta lalata kanta" Ta fada mata cewar, "Wallahi goggo ada ni nake zuwa na debo ruwa da safiya tazo sai na fara aikenta inta kaice miki yanzun kurar ruwa biyu ake kawo min kullum saboda safiya kuma bata san wadan da suke kawo waba" Mamana ta kafe sam bata yarda ba wai hada baki mukayi ni da ita tazo tana mata dadin baki. A bisa kaddara sai kariyar arziki ya samu mijin yaya Aisha da yake gidan haya suke sai aka koresu ta dawo nan gida dakin mamana ta zauna. Kaf din gidan nan ita kadaice ke kwata ta a hannun mamana ta bata hakuri idan tana dukana kuma tayita lallashina. Ana haka itama yayata wadda nake binta ta dawo gida nan itama ta matsamin tayita min fada har sai yayarmu Aisha ta tsawatar mata, don maman mu ko daga kai batayi ballantana ta nuna tasan abunda muke yi. Ana nan sai naga zaman haka bazai yi min ba sai na fara hada sitati irin wanda ake sawa a shadda ina siyarwa duk yin da nayi saina saida kuma ina samun riba sosai na fara tara kudina don inason in yi waec saboda shekara ta zagayo ban samu nayi ba. Ana cikin wannan lokacin irin y'an siyasar nan masu campain suka biya mana neco mukayi lesson sannan muka zana neco. Allah ya taimakeni na fito da credit uku English, geograph da government amman bani da maths. Yanzun kishiyoyin mamana sun kara matsa mata da gangan zasu kirkiri tafiya garuruwansu su kime mata aikin gida ga kuma tana zuwa gurin aiki hakan yasa ta fara sarara min tana dan sakewa dani wani lokacin har muyi hira. A kwai wata sallah babba dayake baban mu ita yake dorawa akan aikin naman sallah haka zasu tsame hannun su su barta da aiki kuma in anzo rabon nama a shiga bala'i ana cewa duk ta handame naman daga ita sai y'ay'ata babanmu ne yake bata hakuri. Wata rana muna hira take cemin, "Safiya inda zakiyiwa kanki fada ki shiryu irin haka da yafiye miki" Nayi murmushin takaici nace, "Goggona" ta amsa da "Na'am"nace, "Wallahi tallahi ni ba y'ar iska bace ko hannu na ban taba yarda wani namiji ya taba ba, amman ana hadani dake alhalin ni ko yawo bana zuwa" "Munafuka ni zaki yiwa dadin baki ne zaki lallameni ko?" Ta fada a fusace nace, "Shikenan goggo Ina addu'ar Allah ya bayyana gaskiya kuma ko wane ne munafikin sai Allah ya sakamin" "Safiya fito fili kice min Allah ya isa tunda ni sa'ar ki ce" Ta fada a fusace tare da rufeni da duka naci kuka na nagodewa Allah. Nawawoo this story make me cry sometime ooo, the star of this story i say sorry to you 😢 Allah is with you Alkalumman: [6/29, 7:40 AM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 13/14 Wani dare da zan kirashi daren bakin ciki wanda bazan taba mantawa da shi ba a rayuwata yayana Musa wanda muke uba daya ni da shi, ya shigo dakina ya tashe ni a barci na mike ina kallonshi da mamaki duk da banji a raina cewar nemana yazo yi ba tunda a ganina yayana ne dole ko yayane akwai so yayya da tausayina a ranshi a matsayina na kanwarshi yace, " Safiya kinsan ko me ya kawo ni ? " Na girgiza kai har lokacin ina ta tunanin me ya kawo shi nace, "A'a yaya Musa sai ka fada" Yayi wani murmushin gefen baki yace, "Matso kusa in tabaki safiya" Jikina ne ya dau rawa muryata tana rawa nace, "Yaya Musa ka tabani fa kace, ban gan ka tabani ba ? " Yace a dan tsawa ce "Eh ki zo nace na taba kiiiii" Nan fa muka shiga gardama ni naki bashi hadin kai shi kuma ya nace sai na yarda ana cikin haka sai ga Mamana ta fito yana ganin ta ya chanza akalar zance yace, "Wai safiya ba cewa nayi ki saka min tuwo inci ba ? Kika tsaya kina kallo na" Jikina har lokacin yana rawa nayi saurin dauko kwano ina cewa, "Kayi hakuri don Allah yanzun zan zuba maka" Na zuba mishi tuwon na mika masa ya amsa sai mamanmu tace, "Wai daman tuwo yace kisa masa kika ki kika tsaya baki zuba masa ba ? " Na girgiza kai alamar A'a, ta wucewarta daki bayan Musa ya fita. Washegari bayan sallahr isha'i kowa ya dawo gida gashi an dauke nepa gidan dundum yana shigo a tsakar gida ya tarar dani ina zaune sai yace, "Ke safiya zo nan" Na mike na nufe shi naje har inda yake sai yace, "Maza ki cire kayanki ki daura zani ki biyoni bayi" Shi fa duk a tunanin shi Abubakar yayi disvirgin dina, na kalleshi da mamaki nace, " Wanne irin in cire kaya na biyoka bayi" Na yi tsaye ba tare da na tafi zuwa cire kayanba ai kuwa ranshi ya baci yace, "Wai safiya ba dake nake bane da kika yi tsaye kika sani a gaba" Rigar jikina daman jacket ce kunsan yadda jacket take tana bayyana saman Albarkatun kirjin mace ban an karaba kawai sai ji nayi ya kawo hannu yana taba min kirji ai a zabure na buge hannun shi nace, "Wallahi kul ka kuma taba min jikina bana son iskanci me ka maidani ina matsayin kanwarka ne fa wallahi bazan dauki wulakanci ba" Ashe dayan yayan namu sunusi yaga abinda ya faru ya hade rai yace masa, "Kai lafiya ? " Nan ya daburce ya fara kame-kame yana cewa, "Abu nagani shine nake kakkabe mata" Da mamaki ya kalleshi yace, "Ya za'ayi cikin duhun nan kaga abu a jikin ta maza fada min abunda ka gani kuma ka nuna min shi" Nan ya kuma rikicewa yace, "Ai ni daman bayi zanje ba wurin ta nazo ba" Ya dauki buta ya wuce bayi abinshi yaya sunasi ya ja tsaki ya wuce dakin Maman shi wato uwar gidan. Yana jin tafiyarshi ya fara kirana yanacewa, "Ke Safiya kikawo min ruwa ina bayi" Nace, "Wallahi bazan kawo ba ! Bazan kawo ba !!! " Sai yayi shiru ya dade a cikin bayi sannan ya fito ya sameni a zaune lokacin ba kowa yace, "Ke dallah y'ar iska waye bai san halinki ba to abunda kike bawa Abubakar yana ci shi nima nake so ki bani naci" Sai kace wani abinci🤭 Sai nace, "Malam wallahi ni ba y'ar iska bace ni ba karuwa bace abinda kuke tunanin inayi da Abubakar wallahi ba haka bane hasalima bai taba neman hakan a gurina ba, kuma kai da ka nema bazan baka ba na hana babban kwabo kawai mts" Naje na samu mamana in fada mata duk yadda akayi gudun kar taji zancen a waje tayi zaton ko bani da gaskiya washegari ta daukeni ta kaini gurin kanwarta ta fada mata duk yadda mukayi da musa. Kanwarta tace, "Kin gani tunda kinsan yaron nan Abubakar yana son safiya ki kyalesu suyi soyayyarsu" Mamana tace, "Wallahi bazan bari ba ai nasan duk wanda zai ce yana son safiya a yanzun to ba sonta yake ba wayo zai yi mata ya rabata da darajarta" Kanwarta tace, " Daman ni shawara ce na baki don karki manta a yanzun Ss 2 zata shiga a ganina don ta tsaya da saurayi ba wani abu bane" Mamana tace, "A'a ita fa bata yarda da hakan ba a dole kanwarta ta kyaleta tayi min fada sosai akan na cigaba da kame kaina, nayi mata godiya muka nufo gida ni da mamana. Haka rayuwar taci gaba da juyamin a kullum sai an shirya labari an fadawa mamana ita kuwa daman ba ruwanta da bincike zata nada min duka ne kawai. Kuma babu mai kwata na agidan duk yawan gidan. Daga baya ma mamana da kanta ta koreni daga dakin ta tace bazata zauna dani a daki guda ba, uwargidan Babana ita tace, "Ai baza'ayi hakaba ki dawo dakina ki zauna ai nima uwace" Na tattaro kayana na koma dakinta da zama kwata-kwata mamana ta fita har kata ta cireni a gabanta bata ma san Allah yayi ruwana a gidan ba, rayuwarta kawai take yi bata da damuwa don bata kaunar naje gurin ta. Shekara ta zagayo kowa mahaifiyarshi tayi masa dinkin sallah amman banda ni kuma ga uwata a raye ubana a raye amman saboda Abubakar na rasa su tare da duk wata hidimarsu gareni. Babbar matsalar Mamana rashin bincike komai aka fada mata ta zauna a kanshi kenan bata la'akari da halayyar mutum zai aikata ko bazai aikata ba, duk abinda akace mata y'arta ko danta yayi a gurinta ya aikata ne kawai bazata tambayeshi ba zata yanke hukunci. Haka nan akayi sallah kowa yasa sabon kayansa ni kuma na wanke tsohon kayana nasa abina. Haka nan nacigaba da rayuwar kunci a gidan mahaifina, ga kuma firdausi ta dawo da halinta a kaina ganin bana tare da mahafiyata tasani gaba, ta ringa hadani da jikokin hajiya rabi har sai da mukayi fada sosai hakan yasa itama ta koroni daga dakin ta tace, "Bazan iya ba na taimakeki amman kina fada da jikokina ki koma dakin uwarki mai bakin hali kawai uwarki ta koreki ma ballantana ni" Na kwashe kayana ina kuka na nufi gidan kanwar mamana na fada mata duk abinda ke faruwa mamaki tayi sosai ta kuma ce na dawo gidanta na zauna, na koma gidanta. Wata na biyu a gidanta sannan ta samu ta shawo kan mamana ta hakura na koma gidanmu. Alkalumman: Maman nurul huda👄 And Maman ihsan😍 Pls share and comment [6/30, 2:05 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 15/16 Na dawo gidan naci gaba da zama cikin kunci da matsi kowa ya tsangwameni magana daya biyu safiya yar iska. Wata rana ina fita naje makotanmu a ranar banma hadu da abubakar ba amman mamana tana dawowa akace mata wai anganni da Abubakar yana latse ni, a take muna haduwa mamana ta dauramin wani gigitaccen mari wanda yasa na dauke numfashin wucin gadi na fara ganin juwa tana daukana, Nan mama tayi min duka zancen duk ya karade unguwarmu dama family house dinmu dake zaria kasancewar y'ay'an hajiya Rabi sunfi rayuwa acan shi yasa suka kwashe karya da gaskiya suka fadawa dangin mu, cewar nazama y'ar iska bin maza nakeyi na zama karuwa harda ciki nayi aka zubarmin hakan yasa duk sukaja kunnen y'ay'ansu akan su daina mu'amala da ni. Duk family din mu babu inda zanje na samu salama saboda anbata min sunana ako ina kowa gudu na yakeyi, Kaf din yaran gidanmu mata babu wadda babanmu ya taba daga hannu ya daketa sai ni saboda makiya na da magulmata na da kuma *Sharrin y'an uba* sai da aka zigashi yayi min dukan tsiya. Hakan yasa na fara kokarin cire Abubakar daga zuciyata duk da irin son da nake yi masa na fara ja baya daga gareshi. A lokacin da na shiga Ss 3 sai kuma farin jini na ya karu masu kudi suna yawan zuwa gurina har gidanmu duk da bawai ni ke nuna musu gidanmu ba tambaya suke yi. Nan fa zance yakara bin gari yanzun iskancin nawa ya karu gashinan harda alhazai masu motoci ke biyoni har gida. Duniyar ta kara yimin kunci, ada ina tunanin idan na rabu da Abubakar za'a sakarmin mara nayi fitsari ashe ba haka bane, wani ballin daban ne zai kunno kai. Babban wana ya kamani yayimin dukan tsiya, na zamo tamkar jaka wannan ya daka wancan ya daka kullum cikin duka duk iya kokarin da nakeyi don na fahimtar dasu amman sun kasa fahimta ta. Haka nan nayi ta rayuwata mahaifiyata bata bani fuska ba ballantana na sanar da ita damuwata ba har na gama secondary school, acikin yayyena mata wadanda suka yi aure yayarmu babba mace a dakin mu ita kadai ce take tausayamin. Nan ta fara cewa inje wurin ta inyi mata hutu sai inje sati daya nake yi na dawo bazan dade ba zata kuma neman nazo, tana son zama dani don bani da k'iywar aiki domin a unguwarsu basu da ruwa sai kayi tafiya kafin kaje inda ruwan yake haka zan kwashi bokitai na tafi na debo mata ruwan. Don nafi son zaman gurinta akan gidan mu duk da ina mata aiki amman nafi sakewa akan na zauna gurin da kullum ina cikin cin duka. Kullum sai naje dibar ruwa hakan yasa na fara sabawa da mutanen unguwar muna dan gaisawa a tsakanin mu, wata rana naje dibar ruwa na dawo sai aka aiko ana sallama da ita sai ta fita don ganin wake kiranta. Tana fita sai taga police a tsaye bayan sun gaisa yace, "Don Allah yarinyar nan da take dibar ruwa kullum 'yar aikin ki ce?" Sai tace masa "A'a ba 'yar aikina bace kanwata ce mamanmu daya da ita baban mu daya tazo hutu ne" Nan yayi mata fada akan don ba ita tahaifeni ba shi yasa kullum take aikana dibar ruwa, ta kalleshi da mamaki tace, "Malam yarinyar nan fa kanwata ce uwa daya uba daya kuma bani da ruwan nan mene aibu don ta debo min ruwa?" Sai yace, " wannan ne kawai matsalar?" Tace masa "Eh "yace, "Toh ni zansa a ringa kawo muku ruwa amman ta daina zuwa dibar ruwa" Tace, "Toh" tare da yi masa godiya yayi tafiyarshi, Haka ake kawo ruwa kura daya kullum, rannan ta fita unguwa sai wasu samari a unguwar suka gaidata tare da tambayarta "Kwana biyu mun daina ganin kanwarki tana zuwa dibar ruwa " Sai tayi dariya tace, "Ya akayi kukasan kanwata ce?" Sai sukace, "Ai daga ganin ta ansan kanwarki ce ba sai an fada ba" Tayi murmushi tace, "Tana gida" Sai suka ce," don Allah muna neman Alfarma a gurin ki?" Tace, "Ina jinku Allah yasa bata fi karfi na ba" Sukace, "Dibar ruwan da takeyi muke so ta daina zamusa mai ruwa yana kawo miki ruwan" Abin ya bata mamaki ya kuma daure mata kai tayi musu godiya ta je ta dawo ta sameni tace, "Safiya daman irin farin jinin da kike dashi kenan? Gaskiya dole ki samu matsala a gida saboda ba lallaine aganki da irin wannan farin jinin ba ba tare da anbiki da mugun abu ba" "Kinsan me yasa kika ga na daina turaki dibar ruwa?" Na girgiza kai nace, "A'a" tace , "Rannan wani police ni ban ma san a inda yake ba shine ya dauki nauyin kawo mana ruwa kuma gashi yau wasu samari suma sunce na daina turaki dibar ruwa zasu sa a kawo mana" Washegari na shirya zanje gida domin inje inga gida sai tace tare zamuje, Muka je gida tare suna hira take cewa, "Goggo Ki daina dukan safiya akan samari domin ba yin kanta bane Allah ne ya yita mai farin jini duk inda ta shiga saita samu masoya" Nan mamana ta rufeta da fada sosai tana cewa, "Karki kara fada min wannan maganar don kuwan safiya ta riga ta lalata kanta" Ta fada mata cewar, "Wallahi goggo ada ni nake zuwa na debo ruwa da safiya tazo sai na fara aikenta inta kaice miki yanzun kurar ruwa biyu ake kawo min kullum saboda safiya kuma bata san wadan da suke kawo waba" Mamana ta kafe sam bata yarda ba wai hada baki mukayi ni da ita tazo tana mata dadin baki. A bisa kaddara sai kariyar arziki ya samu mijin yaya Aisha da yake gidan haya suke sai aka koresu ta dawo nan gida dakin mamana ta zauna. Kaf din gidan nan ita kadaice ke kwata ta a hannun mamana ta bata hakuri idan tana dukana kuma tayita lallashina. Ana haka itama yayata wadda nake binta ta dawo gida nan itama ta matsamin tayita min fada har sai yayarmu Aisha ta tsawatar mata, don maman mu ko daga kai batayi ballantana ta nuna tasan abunda muke yi. Ana nan sai naga zaman haka bazai yi min ba sai na fara hada sitati irin wanda ake sawa a shadda ina siyarwa duk yin da nayi saina saida kuma ina samun riba sosai na fara tara kudina don inason in yi waec saboda shekara ta zagayo ban samu nayi ba. Ana cikin wannan lokacin irin y'an siyasar nan masu campain suka biya mana neco mukayi lesson sannan muka zana neco. Allah ya taimakeni na fito da credit uku English, geograph da government amman bani da maths. Yanzun kishiyoyin mamana sun kara matsa mata da gangan zasu kirkiri tafiya garuruwansu su kime mata aikin gida ga kuma tana zuwa gurin aiki hakan yasa ta fara sarara min tana dan sakewa dani wani lokacin har muyi hira. A kwai wata sallah babba dayake baban mu ita yake dorawa akan aikin naman sallah haka zasu tsame hannun su su barta da aiki kuma in anzo rabon nama a shiga bala'i ana cewa duk ta handame naman daga ita sai y'ay'ata babanmu ne yake bata hakuri. Wata rana muna hira take cemin, "Safiya inda zakiyiwa kanki fada ki shiryu irin haka da yafiye miki" Nayi murmushin takaici nace, "Goggona" ta amsa da "Na'am"nace, "Wallahi tallahi ni ba y'ar iska bace ko hannu na ban taba yarda wani namiji ya taba ba, amman ana hadani dake alhalin ni ko yawo bana zuwa" "Munafuka ni zaki yiwa dadin baki ne zaki lallameni ko?" Ta fada a fusace nace, "Shikenan goggo Ina addu'ar Allah ya bayyana gaskiya kuma ko wane ne munafikin sai Allah ya sakamin" "Safiya fito fili kice min Allah ya isa tunda ni sa'ar ki ce" Ta fada a fusace tare da rufeni da duka naci kuka na nagodewa Allah. Nawawoo this story make me cry sometime ooo, the star of this story i say sorry to you 😢 Allah is with you Alkalumman: Maman nurul huda 👄 And Maman ihsan😍 Love you fans please what can i say next 🤔 Oo Please share, comment and pray for us [7/2, 3:33 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 17/18 Dedicated to Rayuwar safeeya fans duk da dai bakwayin comment sosai pls ku gyara. Yawan dukana da akeyi yasa na fara sabawa da shi don nayi laifi ko dar banaji saboda nasan dukane kawai kuma ko banyi ba za'a yi min makircin da zai janyo a dakeni hakan yasa za'a iya yi min mugun duka amman ko ajikina ana gamawa zan share hawayena na yi tafiyata daga karshe ma ko da za'a yi min dukan mutuwa bana kuka saboda ya riga yabi jikina tamkar icce ake duka. Kudin sana'a ta inata tara su domin bana kashewa wata yayarmu diyar Hajiya Aisha tana karatu a zaria data zo hutu ta sameni tace min "Safiya naga kina son karatu kuma baba yaki biya miki mai zai hana kizo zaria dubu biyun ki ya sai miki form ki fara karatun ki tunda kina sana'a" Nace mata, "Wallahi inaso kuwan kuma ina da kudi a ajiye" tace, "Toh kiyi shawara" na amsa mata da toh. Naje na samu maman mu da zancen na sanar da ita inason karatu tace, "Toh Allah ya bada sa'a yasa karatun ya zamo silar shiryiwarki" na amsa mata da Ameen. Shima babanmu na sameshi nayi masa bayani cewar inason naci gaba da karatu kuma a zaria zan sayi form yace, "Toh safiya ni dai gaskiya bani da kudin daukar karatun ki saboda yanzun ba kamar da bane" Nace, "Insha Allahu Allah zai hore daga yanzun zuwa lokacin da admission zai fito" yace, "Toh safiya amman a ina zaki zauna don bana son ki zauna a hostel don na riga nasan halinki" Nace, "Wallahi baba zan iya zama a hostel kuma zan kare mutunci na" A take ya kafe akan sam shi bazai yarda na zauna a hostel ba sai dai na nemi wani gurin, Ina fitowa na samu yayar nan tamu iklima na fada mata yanda mukayi dashi tace, "Toh ince masa zan zauna a gidan da take zaune gurin yayarta suwaiba" Naje na sameshi na fada masa sai yace, "Ina bazaki iya zama da suwaiba ba domin tana da zafin rai nasan halinta sarai tana da mugunta da bakar zuciya baza taso ki rabeta ba har ki zauna kiyi karatu a gurinta ba domin ko anan gida bata shiri da goggonki baxai yiyu ba ki canza shawara" Nace masa Toh har na mike ya kirani yace, "Ga ma babban yayanku tunda shima yana zaria kuma yafi kusa FCE bari na kirashi" Ya dauki waya ya kirashi ya sanar dashi komai sai yace, "Ai kuwa nan da wata biyu admission zai fito kuma matata taje ganin gida katsina idan lokacin yayi sai ta zo babu damuwa" Cikin ikon Allah kafin watannan biyu mun fara jituwa ni da Mamana muna zaune muna kallo sai gashi an kirata a waya ta daga wayar bayan gaisuwa akace, "Hajiya Maryam kina ina ne ?" sai tace, "Bana gida ya akayi ne ?" Kuma alhalin tana zaune a daki tare da ni sai akace, " Ga y'arki safiya nan da wani a lungun bayan unguwarku yana lalata da ita" tace, "y'ata fa safiya kace?" yace, "Kwarai kuwa gata nan ina kallonsu bata san na gansu ba don suna ta aikata masha'ar su" Tace masa, "Na gode Allah ya biya insha Allahu zan sake kira" sai akace, "A'a ba sai kin kiraba ni daman ina son na fada miki ne don kiyi mata nasiha" Tace toh tare da kashe wayar tayi shiru bata ce komai ba ta zuba tagumi hakan da nagani sai hankalina ya tashi nafara jera mata tambayo yi ina tambayarta lafiya ko mutuwa akayi sai tace, "Lallai akwai wani abu da yake faruwa" Na kalleta da mamaki nace, "Goggo wanne abu ne kuma meke faruwa?" Ta gyara zamanta ta fuskanceni tace, "Ina son in tambayeki kuma ina fatan gaskiyace zata fito daga bakin ki ina kike zuwa kuma wane abokin shashancin ki" Nayi shiru take hawaye suka wanke min fuska nace, "Wallahi goggo ban zuwa ko ina kuma ni ba y'ar iska bace" tace, "Kar kiji tsoro na ina son ki fada min gaskiyar inda kike zuwa"nace mata, "Wallahi babu inda nake zuwa bayan gidansu Abubakar shima yanzun na daina zuwa gidan kuma har yanzun muna tare da shi sai dai ba kamar da ba in an aike ni ne muke tsayawa muyi hira amman bama dadewa kuma ni bana kula kowa bayanshi" Tayi ajiyar zuciya tace, "Toh ki sanar dani ko sau dayane wata mu'amala mara kyau ta taba hadaki dashi?" nace, "Wallahi ban taba yin wani abu mara kyau da shi ba" Hawayene ya wankewa mamana fuska taringa kuka tana cewa na yafe mata jikina yayi sanyi bantaba tunanin zuwan wannan ranar ba mamana tana kuka tace, "Kiyi hakuri safiya na zalunceki na dau alhakin ki duk abinda aka fada min akanki bana bincike nake zartar da hukunci tabbas na dau alhakin ki" Mamaki da tsoro ne ya rufeni nashiga tambayar ta meke faruwa tace, "Bazan iya fada miki ba sai yayarku tazo" Ta kira yayarmu dake tudun wada tace tana son ganin ta cikin gaggawa tace toh Bayan tazo ne take tambayar Mamanmu abin da ke faru a take ta sanar damu komai tun daga farko har yanzun yayarmu wadda nayi zama gidanta tace, "Daman na fada miki kika gwale ni kina ganin ban isa na fada miki gaskiya ba yanzun wa gari ya waya Allah ya taimakemu ta tsare kanta wahala bai sa ta saida mutuncin ta ba " Nan mamanmu ta ringa yi musu Allah ya isa kwando kwando don sun cutar da tunanin ta ita kuma ta cutar da y'ar ta bataji bata gani ba. Maman mu ta samu baba ta fada masa komai duk yadda akayi yace ta kirani nazo, yace, Alkalumman: Maman nurul huda 👄 And Maman ihsan😍 Pls comments and share [7/2, 5:56 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 19/20 "Ki fadamin gaskiyar duk abinda ke tsakanin ki da Abubakar a ranar da na dake ki?" nace, "Wallahi Alhaji a ranar an aikeni siyan madara sai na gamu da Nura dan gidansu Abubakar ya bani kudi yace na siyo masa zobo a gurin goggo Aisha shine na amshi kudin shi na kai mata a tunani na zai aiko a amsar masa shi yasa ban je na kai masa ba na Whigs harkokina sai da yamma aka aiko inzo inji Abubakar wai yana jiran sakon Alhalin ni ba Abubakar bane ya aikeni nura ne kuma tun lokacin da akaje aka fada maka ka dakeni nace maka bansan wani sako ba" Yayi ajiyar zuciya yace, "Kiyi hakuri safiya ki yafemin a lokacin ban tsaya na fahimceki ba" nace, "Wallahi babu komai Alhaji nasan ka isane da ni shi yasa kuma ni ban rike ka ba don ka dakeni bazanyi fushi ba" Nan sukayi ta samin Albarka tare dayimin addu'o'in neman tsari daga makiya. Tun daga ranar Mamana ta fara jana a jiki mukayi wata shakuwa mai karfi nida ita duk wanda ya kawo mata labarina zata zaunar dani ta tambayeni gaskiyar zancen in nayi sai nace mata nayi in banyi ba kuma nace banyi ba. Ganin mun shirya nida mamana sai sauran y'an uwana na dakin hajiya Rabi da kuma y'an dakin su firdausi suka tsangwameni babu dama na zauna tare dasu kuma suka fara yayatawa a gari Wai yanzun iskancin nawa yaci gaba don mamana ta daure min gindi ina kawo mata kudi shi yasa bata yimin komai idan an fada mata sai dai tayi ta jana ajiki. Wata biyu yana cika babban yayan wanda zan zauna gidanshi yazo da zuwan shi mamanshi tace wa matar shi ai bazata iya zama dani ba saboda ni y'ar iskace zan lalata mata diya na bude mata ido da yawon iskanci, Hakan yasa ina zuwa na gaidata naga ta kalleni sama da kasa ta watsar tare da jan tsaki da kyar ta amsa gaisuwata, shi kuma yayan namu yace naje na hadu kayana mu tafi naje mamana ta tayani na hada kayana, Mamana ta kirani na amsa tace, "Kin ga dai Murja matar yayanki ce toh inason ki dauketa tamkar uwa kiyi mata biyayya kar ki saba mata ta hanyan kin bin umarnin ta idan kuma kika aikata Allah ya isa tsakanina dake" A take jikina yayi sanyi kalau nayi shiru vance komai ba ta je gurin murja tace mata "Murja ga amanar safiya nan na baki ki dauketa tamkar y'ar ki ki ringa gyara mata kuskuren ta ki ringa yi mata fada idan tayi ba dai dai ba" Ta amsa da Toh muka shigo mota ni da ita babu wanda yayiwa wani magana har muka isa garin zaria muna isa na kira Abubakar na fada masa kasancewar mamana ta bani waya ta sai yace, "Wato safiya bakya jin magana sai da nace miki karkije makarantar nan amman kika nace sai da kika tafi ko ki ka barni baza mu ci gaba da soyayyar mu ba kenan" nace, "Kayi hakuri idan Allah ya rubuta soyayyar mu tabbatacciyace to sai munyi aure haka idan Allah ya rubuta babu aure a tsakanin mu dole ne mu hakura mu rabu da juna duk kuwa yadda muka kai da son juna don haka kayi hakuri nayi karatuna lokaci zuwa lokaci zamu ringa waya" Yace "Toh shikenan" Haka na fara rayuwa da Murja ni nake yin girki ita sai dai tazo ta kunna min gas gaba daya ta mikamin girkin gidan bata yin komai har wanke wanke hakan bai dameni ba don nasan rakwafci nake yi idan na gama girkin ita zata zuba min abincin babu ruwanta ya isheni ko bai isheni ba haka zan dora da ruwa. Shiru shiru admission bai fito ba shida yayi wa babana Alkawarin nemamin admission sai yaki zuwa ya kirani yacemin ranar Monday naje FCE, na ansa masa da toh Ni ban taba zuwa FCE ba ban san hanyar da zan bi naje ba amman ya turani, ranar monday na shirya na fita bakin titi nayi tsaye bakin titi ina raba ido don ban san inda zan nufa ba can naga wani dan mashin na tsayar dashi nace, "Malam FCE nake son zuwa amman bansan ta inda zanje ba don ban taba zuwa makarantar ba" yace, "Ai babu nisa Naira talatin ne hau in kaiki" Na hau ya ajiye ni a kofar makaranta na kira yayan nawa nace masa gani a kofar makarantar, Yace in shiga in tambaya haka dai nasha bakar wahala gurin neman admission babu wanda ya taimaka min kullum sai na fita. Fitar nan da nake yi ashe yayata iklima tana kiran murja tace mata wai ta ganni tare da maza muna ta yawo a cikin makaranta tin kafin ma na fara karatun. Ita kuma ta kara matsamin da ayyukan gida da hantara ina ji da wahalar neman admission ina ji da wahalar gidan, duk office din da zakaje maza ne kuma da kaje zasu fara neman hadin kan ka, wani ma gada ga ya fito fili yace min "Ga ki y'ar fara kyakkyawa mai kyan sura kin tsaya kina wahalar neman admission ban gishiri in baka manda akeyi a rayuwar nan in kina son admission zan fada miki inda zamu hadu sai ki biya min bukata ta ni ma na biya miki taki don kuwa ki kaddara kamar kin samu admission ne kin gama " Na kalleshi da mamaki nace، "Bawan Allah kaga nayi maka kama da y'ar iska ?" yace, "Toh ba daga kaduna kika fito ba ai daman ku y'an matan kaduna wayayyu ne idonku ya riga ya bude " Na girgiza kai cike da takaici nace, "Kayi hakuri malam ni ba irin wadannan y'an matan bace'' Na fito na bar masa office din shi ina fitowa na hadu da wani dan uwanmu ni ban gane shi ba shine ya gane ni yace, "Ah ah wannan ba safiya bace?" Nace masa "Ni ce" yace, "Nan kike karatu? " nace masa a'a admission nake nema na free MC" yace, "Muga takardun naki" Na mika masa ya duba yace, "Ai takardun ki bana free MC bane ko zaki shekara kina neman admission bazaki samu ba amman ki tafi zan gyara miki" Na tafi bawan Allah nan shi ya gyara min yayi min komai ya kawo min har gida yace gobe naje makaranta na same shi. Washegari na shirya naje makaranta wani tsautsayi..................✍ Daga Alkalumman: Maman nurul huda 👄 And Maman ihsan😍 Pls comments and share[7/4, 2:25 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 21/22 Washe gari na shirya naje makaranta wani tsautsayi ina shiga na kirashi yayi min kwatancen office din shi, naje Akan hanya na gamu da wata mata ashe y'ar lesbian ce tun shigata ta zuba min ido tana kallona tamkar taga nama ta nufo ni da zuwa ta fara yabani tana cewa, "Wallahi kin hadu y'an mata ga kyau ga fari ga kira ni dai kin yimin na kuma gani ina so ya za'ayi mu ringa haduwa gashi ni na kusan tafiya America me kike karanta ne?" nace mata, "Ban fara karatu ba admission nake nema" Ta bude ido da mamaki tare da kama bakinta tace, "Duk wannan kyawon naki amman kina zaryar neman admission ai yanzun ba marks ake dubawa ba iyawarka da kyawon mutum ne yake bashi damar cigaba da karatu ki bani hadin kai ki gani kowanne irin karatu kike so a makarantar nan zan nema miki shi cikin sauki " Ni kam murna na ringayi don har a lokacin ban fahimci manufar ta ba, ganin yadda nake murna sai ta zubamin ido tana kallona ta sani na juya taci gaba da kallona. . Duk sai jikina yayi Santiago ina mamakin me yasa take kallona Alhalin ita mace ce y'ar uwata da na fito sai wannan dan uwan namu yace min, "Safiya kar ki kara zuwa makarantar nan kiyi zamanki a gida zan nemomiki admission saboda bana son ki kuma haduwa da matar nan" Mamaki ne ya kamani nace, "Saboda me baka son na kuma haduwa da ita ?" Ya numfasa sannan yace, "Daman nasan baki fahimceta ba don kuwan matar nan da kika gani y'ar lesbians ce kuma idan tasa daliba a gaba bata gyaleta sai ta cika burinta ta lalata mata rayuwa kuma bana fatan hakan ya kasance akanki" Nan jikina ya fara rawa na tuno tambarin da akayi min na y'ar iska atake na shiga addu'ar Allah ya tseratar da ni nace masa, "Insha Allahu bazan kuma dawowa ba " Shi yayi ta min wahala ni kuma ina gida kuma yayan nawa bai sani ba na samu ko ban samu ba tun ranar da ya turani bai kuma yi min zancenba. Dakyar dan uwan nan namu wato Nazir ya sama min admission, sannan mukayi screening anan ne fa suka kafe cewar waec dina printing ne dole sai naje kaduna na dauko original din kuma gashi bani da ko ficika . Naje gida na samu yayanmu na fada masa nan ya rufeni da fada son me zan tawo karatu na bar documents dina a gida nace masa, "Ai ni bansan suna da amfani ba secondary school na gama bansan yadda abin yake ba ballantana nasan abinda ake bukata a jami'a ba" A take yace shi bashida kudin da zai bani na hau mota hakan yasa na kira mamana na fada mata ina son zuwa gida don naje na samu papers dina tace, "Zansa kanin ki ya amso miki su dukka kafin kizo" nace, "Toh goggo kudin mota fa don ni bani da kudi a hannuna kuma bana son na takurawa yaya" Sorry fans😴 . Daga Alkalumman: Maman nurul huda 👄 And Maman ihsan😍 Pls comments and ahare [7/5, 4:14 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 23/24 Sai tace min "Kanwata tana nan kusanku zanyi mata magana sai ta baki dari biyar " Na amsa mata da Toh ana gobe zantafi gashi wato weekend sai na samu murja nace mata "Aunty murja gobe zanje kaduna" Nan ta fara balbaleni da masifa tana cewa, "Kenan tun yanzun zaki fara zaryar yawo zuwa kaduna ko?" Nan nayi mata bayanin muhimmancin zuwana sai ta tabe baki tace, "Allah raka taki gona sai kin dawo" Naje gurin kanwar mamana nayi mata bayani tayi mamaki cewar ina kaduna nan tayimin addu'ar Allah yasa na kammala a sa'a ta bani kudin motar dari biyar. Na hau mota muka isa kaduna aka ajiyeni a NDA gashi bani da kudin motar da zan karasa kuma da nisa zuwa unguwarmu na dabi sayyada har gida na amso result dina kuma ban fadi cewar yaya bai nemomin admission ba har na koma zaria. Muka fara karatu gadan gadan a duk ranar da na fita makaranta sai naji sunana ya harba har gida cewar naje yawo daga makaranta. Ina shiga zata fara balbaleni da masifa wai yawo nake zuwa gashi ko kudin mota basa bani ballantana kudin abinci in wuni da yunwa in dawo da yunwa in naci sa'a ina da naira ashirin shine zanci garin kwaki nan fa ulcer ta sako ni gaba har saida na kwanta a school ne nake zuwa ake bani magunguna, Abinda ban saniba ina tafiya makaranta Aunty iklima take zuwa ta fara tsarawa murja tana cemata bamuda lecture ranar yawona kawai nake zuwa daman tunda kuka tawo da ita nasan ta samu lasisin gantali kafin na dawo ta tafi. Wata rana dai Allah ya hada mu ina shirin shiga gida sai gata tana sauri zata fito na kalleta nace, "Aunty iklima kece yau a gidanmu?" Nan ta shiga kame kame tana cewa, "Yau na gama lecture da wuri ne shi yasa na zo nace bari na gaida Aunty murja" nace, "Amman ai mun hadu a masallaci shine baki fada min ba sai mu tawo tare?" sai tace, "No ai lokacin banyi tunanin zuwa ba sai daga baya don lokacin muna da lecture teacher din ne bai zo ba" Nan dai ta gama kame kamenta mukayi sallama. Ina shiga na iske Aunty murja ta murtuke fuska ta hade rai na gaidata na wuce kitchen tsaye nayi da mamaki ganin dan abincin da aka ajiye min wanda inda za'a bawa yaro dan shekara uku tsaf zai cinye ya tashi watakil ma yace bai koshi ba amman wai shine abinci na. Haka nan naci dan abincin nan kuma da dare ba'a tashi abinci ba sai tara tace na dafa indomie. Haka nan dai nake tare da su da dadi ba dadi har muka tafi wani dogon yajin aiki tsayin six months nayi nayi su barni naje gida suka hana ni dole na zauna ina musu bauta gashi kullum diyarta sai tayi fitsarin kwance nike yi mata wanka na wanke kayan na shiryata ke duk wata hidimar su nice daga wanki har guga da shara da mopping duk ni kadai yadda kikasan jaka amman dole nake jurewa saboda mamana ta riga tayimin fada. Idan nayi musu maganar xuwa kaduna sai ayi ta min fada wai ban isa naje kaduna ba ko gidan kanwar mamana sun hana ni zuwa balle naje na huta dole zan zauna tare dasu ina musu bauta. Ni zanyi girki amman dana zubo abincin zanci zata fara yada min magana, "Uhm su safiya an cika ci babu aiki saina cika ciki" Ta ringa complain kenan wata rana har kuka nakeyi wani lokacin kuma nayi murmushi don gani nakeyi da kanta take don kuwa ita ke cin abinci tayi chatting tana gamawa ta hau barci. Ashe ciki ke gareta ni bansani ba don kuwan ita irin matannan ce mai kiba kuma bata laulayi shi yasa ban sani ba don inba ita ta fada maka ba bazaka ganeba kuma ya girma. Cikin lokaci kankani wahala tasa na fige na rame inkikaganni sai kice nice y'ar aikin gidan nan ba kanwar miji ba. Ga y'an uwanta suna yawan zuwa daga katsina kuma ni ke hidimarsu su baje suyi ta barci ni kuma inata aikin gida tare da dora musu ruwan wanka. Kadan kadan wani kanin ta da ya dawo daga maleysia ya ringa jana ajiki tun bana sakewa har na saba dashi muyi ta hira lokacin nan inya tambayeni me na karanta sai nace masa English geography. Nan fa ya samin suna *English geography* na nuna mata ina son inje islamiyya da kyar suka sani islamiyya na dora daga inda na tsaya a gida da yake daman mun kusan yin sauka lokacin saukar makarantar mu ya kai na ce musu zanje kaduna zamuyi sauka tunda nima na hade karatun nawa anan. "Aw wai daman ke kinsan Allah har da sauka amman kike da shegen son maza kina aikata alfasha" Nan dai tayi min tas da kyar suka barni naje kaduna mukayi bikin saukarmu na dawo gidan bauta. Sati biyu da yin saukarmu Abubakar ya kirani cewar yana zaria inyi kokari mu hadu kafin ya wuce kaduna don tare yake da y'an uwanshi, na tambayeshi inda yake yacemin, "Ina kofar doka gurin gidan mai" Nayi mamaki nace masa "Ai kaf kofar doka babu gidan mai, sai dai ko makarantar Alhudahuda nan ne akwai gidan mai ko gidan yari kake nufi" Yace sam shi gidan mai na kofar doka yake na amsa masa da toh ina zuwa, naje gurin Aunty murja na shirga mata karya nace, "Aunty anyi wa Jamilar nan ta unguwarmu rasuwa kakarta ta rasu shine suka zo ina son inje inyi mata gaisuwa" tace, '' Ayya wannan matar da take aikomana kosai ko?" na amsa mata da Eh tace, "Toh ga naira dari kije kiyi mata gaisuwa motata babu mai da nima naje don matar tana da kirki" Na amsa nayi mata godiya na shirya na fita na kira shi nace masa ganinan zuwa Cikin sa'a na hadu da wani dan uwanmu ya rage min hanya zuwa kofar doka muka zagaye kaf kofar doka banga ko kyallin abubakar ba nace masa ya ajiyeni a round about na kofar doka tunda kaduna zasuje dole zasu bi ta nan. Bayan na sauka na kirashi na fada masa inda nake wai sai ya shiga yimin fada me yasa naje round about sai dai in dawo baya naje dai dai kofar dokan. "Haba Abubakar yanzun ya zanyi na tsallaka wannan makeken titin kai fa hanyar ku ce ka biyo mu gaisa sai na wuce gida" Nan ya kafe sai dai na tsallaka na tarar dasu haka na hakura na tsalla titunan nan naje na samesu ya wani hade rai kamar wanda akayiwa sakon mutuwa muka gaisa da y'an uwanshi cikin mutunci sukayita yabona suna cewa ya dace ya samu kyakkyawa, Shi ko kokim bai ce ba har suka shiga mota sannan ya yi tsaye jikin motar na kalleshi nace, "Abubakar lafiya naga ranka a bace?" Ya wani kauda kai yace, "Ba komai yanzun ina zaki ?"nace "Ni daga nan gida zanje " Daga cikin mota 'dan uwanshi yace, "Tunda gida zakije ki shigo mu rage miki hanya" nace, "Ku da zakuje kaduna sai in maidaku baya kuma kuyi tafiyarku zan hau mashin" Nan dai suka kafe akan lallai sai na hau sun kaini sai na hau suka kaini har unguwar kaya na sauko shima ya sauka muka tsaya a jikin motar ya fara fada, "Haka zaria ta koya miki safiya ki ga y'an uwana ki wulakantamin su " Na rike baki nace, "Yanzun bakaga kokarina ba kenan kai da ya dace kaje inda nake bakaje ba na dauko kafa na biyo ka ka wani hade rai kuma wai har kana da bakin yimin korafi" Suna jin abinda mukayi daya ya leko yana cewa, "Abubakar kaji tsoron Allah yanzun baka ga kokarin yarinyar nan ba kenan ta tawo gurin mu amman ka ringa yi mata fada, kar ka manta a bakin titi muka tsareta fa" sai yace, "Babu ruwanka malam ba dakai ake ba ka rufe glass din motar nan" Ya zuge glass din na girgiza kai nace, "Haba Abubakar yanzun har dan uwanka ya fika sanin gaskiya" yace, "Ba wani nan ke dai kinyi samari a zaria kin manta dani" nace, "Ni yanzun gida zanje kar a koma jirana" sai yace, "Toh tunda tafiya zakiyi kiyi kissing dina sannan" Mamaki ne ya kamani bakina yana rawa nace, "Wanne irin kiss kuma Abubakar tunda nake na taba yi maka ne da zaka wani ce nayi maka kiss? Ko kunya baka ji ga y'an uwanka kuma akan titi don rashin tsoron Allah ya za'ayi na aikata wannan abun?" Pls kuyi hakuri bazan iya posting sau biyu ba. Daga Alkalumman: Maman nurul huda👄 And Maman ihsan😍 Please comments and share [7/6, 7:27 AM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 25/26 "Wanne irin kiss kuma Abubakar tunda nake da kai na taba kissing dinka da zaka wani kwasojiki kace wai nayi maka kiss? Ko kunya bakaji ga y'an uwanka kuma akan titi don rashin tsoron Allah ni bazan taba aikata wannan aikin ba" Nan dai na shiga yi masa masifa ta inda na shiga ba tanan nake fita ba don kwata kwata banyi tsammanin haka daga gare shi ba, ina yin shiru yace, "Kenan bazakiyi min ba ko?" na amsa masa da "Eh bazan yi ba" sai yace, "Kenan kin gwammace mu rabu muna fada ko?"nace, "Ina ruwana mu rabu muna fadan mana ni ba damuwata bace, tunda rainin hankalin ka ya fara yawa" sai yace, "Ah lallai zaria ta bude miki ido ni d'in da ko tsinke na ajiye bakya tsallakawa sai da umarni na amman yanzun daga tambayar simple kiss kin hayayyakomin ko?" nace, "Na hayayyako maka din kuma ko gobe ka kara haka zanyi maka ni kaga tafiyata" Na kwankwasa musu nace ni na wuce ganin raina a bace suka ringa bani baki nace musu ba komai rayuwa ce. Na wuce ko takanshi banbi ba na tsallaka na hau mashin zuwa gida ina isa gida ko kaya ban cire ba sai ga wayarshi ya kira ni ni kuma sai nayi zaton ya gane kuskuren shi ne sai na daga wayar inacewa, "Ya dai malam da kira kuma?" sai yace, "Wallahi yau kin kunyata ni kuma kin shayar dani mamaki" nace, "Dana yi maka me kuma?" sai ya shiga fada nayi saurin katse shi ina cewa, "Malam kyaleni da hayaniyar nan kar ka janyo min ciwon kai daga dawowata ko hutawa banyi ba ka fara min da bala'i" Nan ya kara hura huta yana kumfar baki yana cewa, "Safiya nine bala'eh'ehn kenan ko? Wawiya kawai sakarai dabba akuya y'ar kauye kawai bagidajiya" Mamaki ne ya sandarar dani dakyar nace masa, "Abubakar ni kake fadawa wannan maganar?" sai yace, "An fada miki din ke mece ce inba wawiya akuya jahila ba" Raina ya kara baci nan ni ma na rufe ido na fara maida masa ina cewa, "Ba'a wawiya daya sai dai wawaye, ba'a dabba daya sai dai dabbobi ba'a akuya daya sai dai akuyoyi kuma ba'a jahila daya sai dai jahilai kuma ka sani ko da tare aka haifemu kamar kashin awaki to na rabu da kai kenan har abada ballan tana daman anan cikin duniya na sameka yadda na bar cikin uwata haka a yau na rabu dakai har abada" Dariyar rainin hankali yayi yace, "Ke dince zaki iya rabuwa dani ke da kike makale dani kamar chewing gum yadda kike sona nasani ko me zanyi miki bazaki iya rabuwa dani ba" Murmushin takaici nayi ta yadda na bata lokacina akan Abubakar da yadda na ringa bijirewa iyayena akan shi nace, "Ni Safiya diyar hajiya Maryam daga yau na rabu da kai Abubakar har karshen numfashina ko da sonka zai kasheni ne, kuma yadda kaci fuskata wallahi kaima sai anyi maka idan ka zalinceni Allah sai ya saka min ina rokon Allah ya hadani da masoyi na gaskiya wanda zai soni don Allah babu yaudara" Na katse wayar tun daga ranar muka raba jaha da Abubakar na shafeshi a babin rayuwa ta na cigaba da karatu na kuma a yanzun Alhamdulillahi ina kula saurayi idan naga yana da nagarta. Akwai wani tun ina jss yake sona amman a lokacin saboda Abubakar ne akai na ban wani bashi fuska ba sai a wannan lokacin ya kuma dawowa neman aure na. Kadan kadan yakan kirani mu gaisa bana wani sakewa dashi Sosai amman Ahmad bai damu ba ya cigaba da lallabani. A wannan lokacin bikin Aunty iklima ya gaba to ga kuma Aunty murja ta haihu, nan fa abin ya kara yimin yawa don kuwa anan zaria ake bikin ga aikin jego ga hidimar biki abin ya taru yayi min yawa da kyar nake samu nayi barci zuwa goma na dare karfe shida na tashi. Nan fa na kara ramewa na bushe hakan yasa mutane suyita bugar cikina don na fada musu halin da nake ciki amman bana fada sai dai nace "Lafiya klau muke " A she hakan yana bawa y'an ubana haushi a zaton su abinda na fada musu gaskiya ne bata wahalar dani basu san cewar ni kadai nasan damuwata. Tunda muka fara waya da Ahmad bai taba zuwa gidan mu ba sai rannan ya kirani yace min, "Insha Allahu a satin nan zan shigo zaria" nace, ''Ah ah daman ba a zaria kake da zama ba ne?" yace, "Eh a lagos nake ina aikine a CBN" Nayi mamaki nace, "Wanne CBN din ?" Nan yayi mun bayanin aikinshi wato su na buga kudi duk dai yayi min bayanin aikin nashi har na gamsu, yace, "Don Allah ina so na ganki idan naje ko zan samu a ware min wani dan lokaci" Shiru nayi ina tunanin kamar Ahmad yafi karfina haka dai nayi masa kwatancen inda nake yace ai yasan unguwar don ksnwar mamanshi tana aure anan " Haka kuwa akayi daya zo zaria yana isa unguwar mu ya kirani nayi masa kwatancen gidan ya zo na fito da yake bansan fuskarshi ba na ringa dube dube amman ban ganshi ba, Dayake ni da wata y'ar uwarmu sumayya ne muka fito tunda duk sunzo gurin biki na fada mata cewar ban san fuskar wanda yazo gurina ba ashe ita tasan shi abokin saurayin tane tace, "Tawo muje na nuna miki shi" Muna dan tafiya sai ta nunamin shi na rike baki nace, "Lah har fa ta gabanshi na wuce amman ban gane ba" yace, "Ai dan baki lura bane ina tsaye ina miki dariya don na fahimci baki gane ni ba" Nan dai muka gaisa ya fuskanceni yace, "Safiya zaki aureni?" Mamakine ya kamani don banyi zaton maganar aure daga haduwar mu ba nayi shiru ina nazarin abinda zance masa don gaskiya ya kwanta min don haka na daure a kunyace nace, "Eh zan aureka" Nan yayi farin ciki tare da yi min godiya yace, "Ki sanar a gida zan turo don bana son muyi ta zama ahakanan" Nan dai mukayi sallama muna zuwa gida sumayya ta samu Aunty murja ta fara bata labari naje zance gurin saurayi nan dai ta fada mata karya da gaskiya. Muna komawa gida naga Aunty murja ta wani hade rai tana wani cin magani Daga Alkalumman: Maman nurul huda👄 And Maman ihsan 😍 Please share and comments [7/6, 4:12 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 27/28 Tunda naga ta hade fuska na sha jinin jikina ina tunanin wanne irin cin fuska da rashin mutunci za'a yimin ina kammala aikina ta kirani naje sai cewa tayi, "Wane ne kika je gurin shi har kika tsaya da shi?" nace, "Sunanshi Ahmad yau muka fara haduwa da shi kuma yace na fadawa yaya cewar zai turo magabatanshi don aurena zai yi" Tana bude baki tace, "Alhamdulillah! Alhamdulillah!!!! Allah ya takaita min wahala zan rabu da kajaga ai gwanda kiyi auren kowa ya huta da bala'i da masifar son mazan ki Allah yasa kar ya janye ya dai tabbatar miki zai aureki ko?" Na share hawayen da ya wanke min fuska nace mata, "Eh da gaske yake sai dai babanmu bazai bari ba tunda yace sai na kammala karatu" Ta wani ja baya a zabure tana cewa, "Ai dole ma zai barki kiyi auren baban nusaiba zan yiwa magana ya lallaba shi a samu a mika ki kin karasa karatun a can insha Allahu december mai zuwa an tattaraki anyi bikin ki an mikaki muma mu huta don wallahi ni na gaji da zama da ke inda ina da hali da tuni na koreki kin barmin gida na" Ina hawayen bakin ciki na mike na koma dakina ina kuka. A ranar ko ta sanarwa Yayan mu zancen ya amsa mata da toh zai yi bincike akan yaron. A bangaren Abubakar kuwan tuni ya bar unguwarmu saboda labarin abinda yayi min ya karade unguwar sai wasu daga samarin suka fara hantarar shi a dole ya tattara kayan shi ya bar unguwar. Wani abu kuma da yake kona min rai kullum na fita naje makaranta sai an zazzage min jakata na rasa me ake nema acikin jakar makaranta ta, ni a tunanina yara ne suke min haka amman daga baya na fahimci ba su bane tunda kullum sai hakan ya faru kuma wani lokacin nakan ajiye jakar inda yaron bazai iya dauka ba amman still sai an zazzage. Wani abin haushi ko ince na dariya ana zazzage jakana ne don a gani ko akwai condom a ciki tunda ansan y'an iska da yawo da condom saboda gudun ko ta kwana. Ban taba korafi ba saboda nasan ina da gaskiyata rannan dai abun ya ciyo ta da kanta ta fadi kanta. Ta ringa fada wai ita bata yarda dani ba" ba kya dawo wa gida da wuri kina famar bin maza a titi wallahi kicigaba dai ga HIV nan tana yawo a gari" Ranar naci kuka ba kadanba daga karshe na lallashi kaina na fawwalawa Allah lamurana, ana haka muka fara exams mai zafi lokacin barcina na ke ajiyewa nayi karatu saboda da rana bani da lokacin da zan dauko littafi, Rashin barci ya sako ni gaba duk jikina ya daina yi min dadi ga babu isashshen abinci, in wuni a school in dawo gida na tarar da ayyuka suna jirana. Wata rana paper hudu mukayi har sai da nakai magriba bamu gama ba kuma bani da credit a wayata bamu taso ba sai 7:30pm ga hadari ya hado yayi baki kirin kuma banida kudin mashin ballantana na samu na isa gida da wuri. Ina cikin tafiya ruwa ya tsuge da karfi har wayata sai da ta fadi screen ya dagargaje nayi sauri na dauka ina sauri in isa gida da wuri don hanyar bata da kyau idan dare yayi har raping din y'ammata ake yi ko kuma wani lokacin a tsinci gawar mutum an yanka shi. Haka na daure ina addu'a nabi hanyar nan ina sauri don Allah Allah nakeyi na isa gida ruwa yayi min dukan tsiya da kyar a tsorace na isa gida. Ina shiga gidan tun daga tsakar gida ta tsayar dani tana cewa, "Kar ki kuskura ki shigo min daki har sai kin fada min daga inda kike gidan ubanwa kika je?" nace, "Wallahi Aunty daga makaranta nake kuma wayata babu kati shi yasa ban kiraki ba, kuma wayar ta fashe" Sai tayi kwafa tace, "Humm Ki fadawa wanda bai san hali ba amman ni kam ko duk jikina kunne ne bazan yarda ba idan yayanki ya dawo kyayi masa bayani" Na cire kayana na nufi daki na shanya takarduna na koma kicin tsaye nayi ina kallon kular abincin da dan abincin da ke ciki bai fi cokali daya ba. Gashi na kwaso yunwa tun tea din safe ne a cikina haka nan na lomace dan abincin na side hannu na, naje nayi alwala nayi sallah na kwanta. Washe gari haka yayana ya tsareni da tambaya shima yadda nace mata haka nace masa yace, "Toh wallahi zanje na bincika idan na ji akasin haka ranki sai yayi mugun baci don na fara gajiya kullum ke sai an kawo karar ki anganki anan an ganki acan" Na shaki kukana na shirya na wuce makaranta, a ranar aka sanar damu sai bayan sati biyu result zai fito, naje na fadawa Aunty murja sai tayi murmushi tace, "Allah ya nuna mana don result dinki shine zai baki lasisin zama kici gaba da karatu a gidan nan ko kuma akasin haka" Na ja jikina na koma daki ina addu'ar Allah yasa naci exams din. Sati biyu yana cika naje ganin result abun farin ciki five point na samu nayi murna sosai da fara'a ta na nufi gida naje na nuna mata ita da kanta sai da tayi mamaki don bata zaci haka ba. Daga Alkalumman: Maman nurul huda👄 And Maman ihsan 😍 Please share and comment [7/9, 1:09 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 29/30 Shiru tayi tana mamakin result din sai juyawa takeyi tana tabe baki tace, "Ah lallai uwayen yawo sunci exam amman nayi mamaki kwarai da gaske wanne lokaci kika samu kika yi karatun har kika samu wannan result din ko da yake ba abun mamaki bane" Ni dai murmushi kawai nayi bance komai ba, yayana yana dawowa ta nuna masa shima yayi mamaki sosai don cewa yayi, "Ni lokacin da nayi karatu kaf department dinsu babu wanda ya fito da five points Lallai yarinyar nan Allah ya taimake ki ashe dai kina karatun zan tsaya miki kici gaba " Nayi masa godiya sosai Mamana ta kirani tace, "Safiya zan biya miki jamb kiyi sai ki zo nan kaduna kicigaba da karatun" nace, "Ni ba ma jamb bane yafi damuna illah WAEC don bani da maths kuma kinga dole sai na canza ko five credits ne in samu" tace, "Hakane kuma to Allah ya baki sa'a yasa ki samu" Na amsa da "Ameen" Mamana ta biyamin kudin waec naje na samu Aunty murja nayi mata bayani kawai sai ta hauni da fada tana cewa, "Wanne waec kuma kawai dai kice kina son tafiya gidane kije gurin samarin ki toh babu inda zaki je" Har tayi shiru ban tanka ta ba na je daki na kira mamana a waya nace, "Goggo kiyiwa Aunty murja bayanin zanje kaduna gurin jarabawa" Ta amsa min da toh ta kirata ta fada mata bata nunawa mamana komai ba tace, "Ai ba komai Allah ya kaimu lokacin" Ranar da zan tafi kaduna nasha habaici kala kala dole na naji nayi kamar banji ba harda mugun fata wai " Allah yasa na fadi a waec din inje inta biye maza tunda bin mazan nafi kwarewa" Ni dai bance komai ba haka na nufi kaduna naje nayi jarabawa ta abin farin ciki dukka papers din naci illah Accounting shi kadaine na samu pass na dawo zaria da farin cikina. Ban dade ba kuma da dawowa lokacin jamb yayi nace mata zan koma nan ma da kyar ta barni kuma ta bini da mugun baki. Kuma ta hanani kudin mota alhalin tana da shi gurin classmate dina na ari dari biyar da magriba na tafi kaduna karfe takwas na isa kaduna. Haka na samu nayi jarabawar nan kuma Alhamdulillahi shi ma jamb din naci. Nan Mamanmu tace za'a mai dani ABU amman yayana da Aunty murja suka kafe akan sam tunda na fara FCE to sai dai na hakura nacigaba anan, Haka suka sa mamana asarar biyamin jamb tunda bazanyi amfani dashi a FCE ba mamana ta bani hakuri tace nacigaba anan din ba komai. A wannan karon yayana ya dan taimakamin tunda ya biyamin wasu kudi da aka bukata lokacin neman admission babanmu bai ma sani ba. Duk da hakan na wahala sosai don baije da kanshi gurin neman admission ba ni nayita fafutuka sai da aka fara karatu na samu. Kuma yaki biyamin kudin registration mamana ce ta aikomin da rabi babana ya biya rabi, ga kuma kudin register makaranta shima bani da shi naci kuka na na koshi. Daga baya na yanke shawarar kiran yayata wadda take tudun wada nayi mata bayani tace, "Wallahi safiya nima bani da kudi naira dubu biyar kawai zaki samu a gurina don duk kudin hannuna na tattara na biya kudin cs dasu " Na yi mata godiya nace, "Nagode Aunty zama su isheni Allah yasa ayi miki cs din a sa'a ubangiji ya baki lafiya " Ta amsa da ''Ameen" ai kuwan ta turomin dubu biyar din nan naje nayi registration na cikin maka ranta na samu canjin dubu biyu da dari uku. Tsautsayi mun gama lecture sai na manta jakata a class kafin naje har na samu wata ta zare kudin ta barmin dari takwas kawai gashi ko handout ban siyaba kuma bani da wani kudin. Har semester din nan ta kare ban samu kudi ba ballantana na siya handout sai da exam tazo a lokacin mun saba da wani classmate dina shi nake bawa kudin photocopy yayi min daga baya da ya fahimci banida kudin sai ya fara siyan guda biyu sai dai kawai naga an bani handout nayi masa godiya wani lokacin harda hawaye nakeyi a boye. A wannan lokacin da karatu yayi zafi idan kikaga yadda kafata ta tsattsage saboda tafiyar kafa wallahi sai na baki tausayi amman ko daga kai Aunty murja da yaya basa yi ballantana nasa ran za'a bani na ocada, haka zan tafi a kasa na dawo a kasa kuma idan ban dawo da wuri ba masifa ga aikin gida a gefe guda. Idan na samu na siya takalmi ko wata biyu bayayi ya lalace saboda tafiya, ina cikin wannan halin kuma ciwo ya sakoni gaba Daga Alkalumman : Maman nurul huda👄 And Maman ihsan😍 Please share and comment [7/9, 3:59 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 31/32 Ciwo ya sakani gaba wato appendix daman na taba yinshi tun ina secondary amman yanzun yafi takuramin don inya rikeni bana iya motsawa sai in ya sakeni. Nan fa Aunty murja tace batasan zancen ba don bata ragemin aiki ko daya ba haka ina cikin aiki zai tashi na sandare a gurin ina hawaye ko kallona bazatayi ba ballantana na samu arzikin sannu ko ta ragemin aiki ba. Sai dai ta shiga fadan naki nayi sauri nayi mata aikinta ita babu ruwanta da wani karyar ciwo da nakeyi kuma dole kiyi aikin nan. Tun in ya tashi daga tsaye nake sandarewa har ya kai inya tashi dole sai na kwanta a gurin ko inaso ko bana so, gashi a lokacin mamana ta tafi saudia na kira mamana na sanar da ita halin da nake ciki. Tace na amshi kudi gurin yayata da take tudun wada inje aaibiti don ayi min scanning, na amsa da toh haka kuwan akayi na kira yayartawa na fada mata ta aikomin da kudi naje gurin scanning. Ashe inda naje basu iya scanning ba domin cemin sukayi su basuga komai ba, na koma gida ina zuwa Aunty murja ta amshe result din ta duba sai cewa tayi, "Ai daman nasan karya ne babu wani ciwo a jikinki kawai salon ki barni da aiki ne" Ina hawaye nace mata "Wallahi Aunty inajin ciwo a jikina don ni kadai nasan azabar da nake sha idan ya tashi" sai tace, "Me kike nufi kenan ko cewa zakiyi shima scanning din karya ne, ni dai nasan ko wanne ciwo gareka idan kayi scanning za'a gani matukar ba karya bane" Ganin bazata fahimceni ba yasa na tashi na bar gurin. Bayan sati biyu naji ciwon yaki ci yaki cinyewa sai na kara kiran mamana na fada mata cewa "Nayi scanning sunce basu ga komai ba kuma ni banida lafiya har yanzun" Tace ''toh bari zan kira Auntyn taki" Da dare mamana ta kirata tace mata, "Ina son safiya taje kaduna don nayiwa wani doctor magana zai duba min lafiyarta" Ta amsa da toh, ai kuwa da safe ta fara sababi kamar me tana cewa, "Eh kinji dadi burinki ya cika mamanki tana makka taje sauke farali kina ta faman kiranta kin tada mata hankali sai da kika sata kashin kudi saboda karyar ciwonki ki kyaleta tayi ibadarta lafiya amman kinki to ke kika sani ba dai kaduna ba Allah ya raka taki gona" Gashi a lokacin mun fara exams dole na tsaya domin kar nayi missing a haka nake shiga aji bana iya yin komai sai dai nayi zaune ina jinyar kaina classmate dina kemin exams sai a mikomin nayi submit kamar ni nayi. Washe garin ranar da muka zana last paper na kama hanyar kaduna lokacin kuwa babbar sallah ta kusa. Tun zuwana kaduna na fara ganin doctor kadan kadan lafiya ta fara zuwarmin don a farko ance sai anyi min aiki sai naci sa'a maganin da aka bani yasa na fara warkewa. Lokacin sallah ya zo tun ranar Arfa kishiyoyin mamanmu suka sakomu gaba da dariya da habaici wai naman da muke ci duk shekara bana bazamu samu kamar shi ba. Shiko babanmu duk yayi sanyi don ya saba duk shekara mamanmu ke shugabantar aikin sallah har a gama amman wannan shekarar bata nankuma duk kishiyoyin ta sunja baya babu wadda ta kula da shi. Ranar sallah Akayi yanka suka kime naman nan ko y'ar hantar da mamanmu take dafa masa bai samu ba don babu wacca tayi tunanin dafa masa har karfe biyu na rana ba 'a fara aiki ba. Yaran gidan sai tsaki sukeyi suna cewa "Inda goggo maryam tana nan da tuni munci naman nan amman yanzun ko fara gyaranshi ba'a yi ba. Yayan mu ya shigo yana ta fada " gida duk y'ammata amman ko wacce ta makale a daki kamar daddawa don karkuyi aiki" Caraf uwargida hajiya Atika tace, "Ai yau ba girkina bane girkin Amarya ne sai ta fito ta fara aikin ta" Amman maman firdausi ko tari batayi ba ballantana asa ran zatayi, yayanmu ne ya takurawa y'anmatan dole suka fito suka wanke naman suka hasa wuta suka dorashi tare da zuba maggi da Albasa kowacce ta kara tayi gaba, tana zuba tsaki ni kuma suka ce naje na gasa nama abawa mazan gidan. Suka hanani magi naje na tambaye su suka hanani ni kuma nace, "Wallahi bazan dauki magginmu na gasa muku nama ba don haka ko ku kawo maggi ko naje na gasawa babana nama shi kadai" Dayake lokacin bakina ya fara budewa naje na gasawa babanmu nama shi kadai na kai masa yayi ta shi min albarka ya cinye tas. In kikaga gidannan sai ki rantse ba babbar sallah bace, aka bar nama akan wuta yana ta dahuwa ba a motsa ba, babanmu ya kira maman firdausi yace ta duba naman nan sai ta tabe baki tace, "Allah ya kiyaye na zauna nayiwa kato aikin nama yaci toh wallahi ba da ni ba" Ina zaune a gurin nayi murmushi nace, "Allah ya jikan goggo maryam ba don ta mutu ba nasan inda tana nan da tuni naman nan ya zama tarihi kuma aci ana cewa nata yafi yawa" Ai kuwa ta hayayyakomin kamar zata cini danya nace, "Ah ah fa ni ba dake nake ba yadda kikayi maganarki nima nayi" Taja tsaki ta koma daki tana fadan nayi mata rashin kunya Nawa wo Wai shin ya za'ayi da naman nan ? Zai lalace ko kuwa? Ni dai nace da sun bani in kaiwa y'an *gorgeous writer forum* nasan su da cin nama da kuma iya aikin shi masamman...............ba ruwana wlh kar tayi min duka Daga Alkalumman: Maman nurul huda And Maman ihsan Please share and comments Comments yasa nayi typing biyu yau😃 [7/10, 2:56 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 33/34 Haka aka bar naman nan akan wuta kowacce shige da ficenta takeyi babu wadda take da niyyar kula naman. Ganin naman zai lalace sai na dauko wayata nasa kati na kira yayata na ce mata, "Wallahi Aunty za'a bar naman sallah ya lalace baba yayi asarar kudin da ya siyi dabbar gashi nan an dorashi kan wuta ko juyashi ba'ayi ba ballantana a soya shi" Sai yayartawa tace gata nan zuwa don daman ta gama nata aikin mijinta bai yi yanka ba wanda makota suka bata ne kuma ta soye shi. Cikin mintuna ta iso tana zuwa na kama mata muka fara aikin, tana dago naman gurin juya shi kasan ya dafe ya daddage kuma babu gishiri ballantana maggi sama kuwan danye kwata kwata bai dahuba sai uban maggi da gishiri da ya dan kale, Haka tasa karfinta tayi aikin nan tsaf ni kuma ina tayata, ta soye naman nan ta ajiye, da yake kwana zatayi bata bar aiki ko daya ba, Tana tafiya aka fara tsegumin tazo ta kwashe nama ta kai gidan mijinta, kuma fa ba ita tayi rabo ba su suka raba da kansu. Matasan gida ko suma sai gunguni sukeyi an basu nama kadan ba kamar yadda mamanmu take basu ba, don daman mazan wadanda sukayi aikin yanka sai ta cika musu samira amman wannan shekarar cikin ledodi suka basu. Haka dai akayi sallahr nan kowa yana tsegumi bayan sallah na koma zaria gurin karatuna don Alhamdulillahi naji sauki sosai. Haka nan lokaci yake ta tafiya nima inata karatuna da dadi da babu dadi ina hakuri, wani hutu da muka samu sai mukaje katsina garin su Aunty murja y'an gidansu suna sona don har munyi sabo da su babu mai tsangwama ta. Bayan mun dawo Aunty murja ta kwanta ciwo mai tsanani ni nake hidimarta da hidimar gida da kuma karatuna amman wadannan da suke zigata ko dubiya babu wanda yazo. Ni din dai da take wahalarwa take wulakantawa ce a kanta da dukkan bukatun jinyarta daga nan fa jikinta ya fara sanyi ganin ban taba gajiyawa da hidimaeta ba nan fa ta fara tunanin "Anya maganganun da ake fada a kaina gaskiya ne? Ko dai ana fada mata ne don ta cutar dani?" Haka tayi ta sake sake a ranta, har ta samu lafiya a wannan lokacin ne na koyi hada room freshener. Daman yanzun ina dan samun kudi gurin Ahmad ya kan aiko min kudi dubu daya biyu har zuwa uku, to a lokacin ya aiko min dubu biyu na dauki dubu biyun nan na fara hada room fresh dashi. Maganar Aurenmu da Ahmad tayi karfi don har manya sun shigo zancen, nan fa mahasadana wato y'an ubana suka kara tsangwama ta ganin Ahmad ya fito daga babban gida suna ganin zan shiga gidan hutu, suka takuramin sosai don ko Aunty murja batayi niyyar yi min abu ba sai sun sata tamin. Ina fara room fresh din na bawa Aunty murja na dauki wasu na kaiwa kanwar mamana. Kwana biyu da bata room fresh ta duba bata gani ba sai ta hau bala'in wai na dauke roomfreshener na kaiwa kanwar mamana. Ina dawowa daga makaranta ta tareni da tambaya "Ina kikaje?" nace, "Daga makaranta nake banje ko ina ba" tace, "Ba naji kina cewa nusaiba zakije gidan kanwar mamanki ba?" Na dafe kirjina nace, "Ni ? Wallahi bance ba kuma banje ko ina ba kinsan idan zanje guri dole sai na fada miki ban taba zuwa wani guriba ba tare da na sanar miki ba" "Toh naji ina airfreshener din" ta fada tana ballamin harara Na dauko mata na nuna mata wanda na dauka zan kaiwa kanwar mamana, tayita y'an kame kamenta ta fice, Bansan wa ya kawo mata gulmar karya ba wai an ganni na je yawo, matar nan ta daina yimin magana ko gaidata nayi bata amsawa sai da na rufe sati guda ba'a bani abinci a gidannan, biscuit shine abinci na da yake ana rabawa yara biscuit malam nasiru kuma yayana wato mijin Aunty murja malamin makaranta ne shine yake kawo mana sauran ya raba mana ni da nusaiba da mai sunan babanmu, Biscuit din nan shi zanci da safe da rana da dare, ni kuma na fita hanyarta banje na tambayeta me nayi ba kuma ban bata hakuri ba. Ranar ta sameni a daki ta zageni tsaf tare da cimin mutunci wai naki zuwa na bata hakuri ni kuma nace, "Wanne irin hakuri kuma Alhalin ni nasan banyi miki komai ba inda nasan nayi laifine" sai cewa tayi "Toh shi kenan sai kiyi hakuri nasan na horaki da yunwa je ki dibi abinci ki ci" Tun daga ranar ta sassautamin daga horon yunwa, daya ke yanzun ina samun zuwa gurin kanwar mamana har nayi sati kadan kadan ta fara fahimtar halin da nake ciki sai cemin "Safiya ba wai zugaki zanyi ba amman gaskiya abinda matar yayanki take miki yayi yawa tunda dai ba uwarki bace karki sake yi mata kuka idan tayi miki ki rama idan kikaga tana miki fada akan laifin da bakiyi ba kar ki kara bata hakuri idan kuna Parlour to ki koma daki ki kyale ta kiyi banza da ita karta kuma ganin fushin ki" Na amsa mata da toh na dauki shawarar ta idan tana masifarta ko daga kai banayi na kalleta ballantana na bata hakuri kuma bana nuna fushina ballantana kuka. Haka muka ringa rayuwa kadan kadan sai ta fara canzawa idan aka kawo mata gulmata zata tambayeni idan na amsa toh idan ban amsa ba ta sa zancen a kwandon shara. Zaman mi ya fara dadi muka fara fahimtar junan mu, muna mutunci sosai. Tsautsayi rannan ta fita sai dawo da ita akayi tayi accident muka shiga tashin hankali ni nake jinyarta har ta warke wannan karon ma magulmatan ta ko leke ballantana tasa ran wata hidimar su. Bayan ta samu sauki ta sameni ta bani hakurin duk abinda tayimin nace, "Wallahi ni ban rike ki ba don kallon uwa nake miki tunda mamana ta mikani gareki don haka komai ya wuce Allah ya bamu hakurin zama da juna" A lokacin sauran shekara daya na gama karatu sai aka fara maganar auren mu da Ahmad. Nan fa tsegumi ya tashi sabo yayyena maza da zasu jagoranci hidimar duk suka janye jiki da kyar aka samu aka lallaba su harda rokon Allah Aka hada sannan zancen nan yasassauta. Daga Alkalumman: Maman nurul huda👄 And Maman ihsan😍 Please share and comment [7/10, 3:46 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 35/36 Akasa ranar mu ni da yayanmu na miji, kannen mamana suka sameta akan zancen tace zata yiwa yayyena magana tukunna gaba da gaba yayyenmu suka ce su baza suyi min kayan daki ba don basu sani cikin lissafin kannensu wadanda zasuyiwa kayan daki ba. Mamana har kuka tayi ta kira kanwarta ta sanar mata yadda akayi nan ta kwantar mata da hankali akan zasuyi min komai. Haka kuwan akayi kannen mamana su sukayi min komai na daki har kitchen, lokacin da aka kawo kayan lefena kaf mahassada na saida suka rude don kaya ne nagani na fada wanda akeyiwa y'ar gata. Nan aka fara zagin Aunty murja wai da ita aka hada baki aka nemomin miji mai kudi ankawo lefen da babu wacce aka taba kawowa irin shi a gidan. Nan fa suka yi fada uwaka ubanka ita da su ta tona musu asiri tsaf "Duk hakkin yarinyar nan da kukasa na dauka bai yi muku ba so kukeyi bikin ta ma na nuna mata bakin hali to wallahi baku isa ba daman don ban san halinku bane amman yanzun anyi walkiya na ganku munafukai kawai mahassada wallahi sai na tona muku asiri na fadi duk abinda kuke fada min tsaf" Lokacin biki yazo akaje ganin gidan Amare gidana yafi na yayarmu wadda za'a yimana aure tare kyau nan suka tuburewa mijin dole irin gidana zaiyi hakan yasa zancen auren ya watse aka fasa don shi bashi da kudin Ahmad don Ahmad iyayenshi ma masu kudine ballantana shi kanshi. Nan fa maganar aurnta ya watse aka mai da masa kudin shi akayi nawa bikin ni kadai. Munyi walima da yini don ba wasu kawaye gareni ba sai aboka nan karatu na Da Aunty murja akayi hidimar nan har da hawayenta tana bani hakuri tare da fada min duk abinda aka dhirya min Nace, "Aunty ki daina damun kanki don komai ya wuce a gurina don kin tallafeni kika bani gurin zama har nayi karatuna na gama ba abinda zance miki sai godiya" Haka dai daga mun kebe Aunty murja zata ta bsni hakuri har abin ya fara damuna na fadawa mamana tayi mata magana ni komai ya wuce bana son yawan bani hakuri da takeyi Mamanmu ta kirata tayi mata magana tare da nuna mata mun riga mun zama daya yanzun. Aka mikani gidan Angona kuma masoyina Ahmad ina kukan rabuwa da y'an uwana da kuma mahassada na domin na riga nayi imanin hassada ga mai rabo taki ce. Bayan y'an kawo amarya sun watse aka barni ni kadai inata share kwallah cikin farin mayafin da aka rufe min fuska, Can na jiyo zazzakar muryar angona yana yimin sallama na amsa a sanyaye ya karaso bakin gadon yana doka murmushi bakinshi yaki rufuwa yace, "Alhamdulullahi the game is over now you are my wife my halal thank you god" Ni dai shiru nayi ina raba idanu a cikin mayafin domin ina tare da tsoron nan irin na amare😉 Ya yayemin mayafin yana kallon fuskata cike da shauki farin ciki yana kara mamaye shi a yau gashi ya mallaki sarauniyar zuciyarshi. Ya umarceni da na taso nayi alwala mukayi alwala tare da yin nafila raka'a biyu ya dafa goshina yayi min addu'a sannan ya fara jefomin tambayoyi game da addini na tsaf na amsa masa. Sannan ya gabatar min da kazar amarci tare da freshmilk, girgiza kai nayi aikuwa take ya hade rai yadebo ya nufo bakina da shi a kunyace na bude bakina na amsa tare da taunawa a nutse. _Maman nurul huda ya da hadiyar miyau kuma mu da muke dauko labari ko so kike a ganmu ? Ta harareni tace, Lallaima Maman ihsan din nan nasan ko kema ranki ya biya da kazar nan kallifa ko kashi babu a cikin ta tsoka zallah lol_ 😂 Bayan ya gama ciyar dani sai shima ya ci a hankali na zame na nufi dakina nayi wanka na dauko kayan barci nasa riga da wando iya gwiwa saboda tsaro na kwanta saboda ina tare da gajiya _wai ita wayo safiya kenan🤭_ Can cikin barci na ji an rungumeni sosai kamar zai maidani ciki dif nayi kirjina yana dakan uku uku don tsoro a hankali ya ringa yawo da hannun shi a sassan jikina tuni notikan jikina suka kunce don sun fara amsar sakonnin shi. Saida naga ana neman ciremin security sannan na nemi hanawa amman habibty yace bai san zancen ba dole na hakura ina y'an hawayen wahala da farin ciki Ahmad yayi nasarar mai da ni cikakkiyar mace, Na sha wahala sosai shi kuma yasha sun batunshi don bazan iya lissafa alkawarurrukanshi ba da kuma shi min albarka da akayi tare da ambatar inasonki matata. _Toh y'an mata sai a kula a rike mutunci domin budurcin ki mutuncin ki naga wani post yana yawo a media wai babu budurci mazan hausawa fyade suke yiwa mata shi yasa to wallahi karya ne zancen nan sai dai ko wacce macce da yanayin halittatta wata jini na zuba yayin fitar yanar budurci wata kuma babu jini amman mijin ta zai san budurwa ce wallahi babu maganin matan da zai dawo miki da budurcinki don haka kar kwadayi ya kaiki ya baro_ *Nasiha ce daga maman ihsan* Bayan komai ya lafa barci ya kwashe ni hakan yasa yaja blanket ya lullubemu shi kam dakyar yayi barci don farin ciki, domin lokacin da yake neman aurena ansha tarar shi ace masa bin maza nake yi. Tausayina ne ya cika shi sosai ya kuma dau damarar duk wanda ya kuma aibatani sai inda karfinshi ya kare. Fans ku kawo ruwan zafi mu taya Ahmad gashin sahibar shi💃🏻 Daga Alkalumman: Maman nurul huda👄 and Maman ihsan😍 [7/12, 12:12 PM] MAMAN IHSAN 😍: *RAYUWAR SAFIYAH* *True life story* Story by : Maman Nurul Huda👄 Written by: Maman Ihsan😍 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ! 🌟GORGEOUS WRITER FORUM🌟 🌟G. W. F🌟 Home of gorgeous intelligent and expert writers, we are the best among the rest. Page 37/38 *Barka da juma'a y'an uwa Allah ya Hadamu da Alkhairin wannan rana Ameen* ⬅🔚🔚🔚🔚🔚🔚 Sosai Ahmad yayi ta tattalina tamkar kwai ni ko ina zuba shagwabata son raina ina kuma kara godewa Allah akan ni'imar miji na gari da ya bani. Bayan wata hudu wasu barayi suka shiga gidana suka sacemin kayan lefena kaf,mutane suka yita zuwa gurin yi min jaje amman y'an ubana ko sau daya basu tako gidana ba sai rade raden magana naji wai suna ta cewa Allah ya kara ba ina ta murna na samu miji mai kudi ba. Sai da naje gida sannan suka tasa ni da tambayar wai sunji anyi min sata nace musu eh, Wasu sukace "Allah ya kyauta" wasu sukace "uhmm" ni dai ban kulasu ba don nasan hassa da ce take cin su. Na samu farin ciki a gidan aure na wanda a da bantaba tunanin samu ba babu abinda na nema na rasa komai mijina ya tsaya min don har mota ya siya min kaya kuwan mahassada na sai dai su gani a jikina suyita bakin ciki. *NASIHA DAGA SAFIYA* Yaku y'an uwana musulmai ina mai fatan kun karu da darussan da ke cikin rayuwata kuma zakuyi amfani da shi. Idan zama ya hadaka da mutum kar kayi masa hassada acikin al amuran rayuwar shi ka rayu da shi da zuciya daya domin duk wanda kayi wa hassada karshe shine a sama kai kuma a kasa kaga kenan tamkar ka zuba masa taki ne a gonar rayuwar shi, idan ka kalli labarin rayuwa ta zaka fahimci hakan yadda y'an ubana suke nunamin y'an ubanci a fili da badini kuma gashi duk cikin su na fisu dace da miji na gari kuma mai arzikin da zai daukemin dukkan bukatuna. Sannan kira ga iyaye da ma y'an uwa wadanda da zarar an sanar dasu magana zasu hau su zauna akai ba tare da sunyi bincike ba sai dai kawai su shiga yanke hukunci idan kika duba mamana da kuma Aunty murja a zahiri da badini su din masoyana ne amman makirai da magulmata sune suka shiga tsakanin mu wanda yanxun zance Alhamdulillah tunda sun ajiye dukkan dabi ar daukar zuga a gefe pls jama'a idan aka kawo muku zance ku danne zuciyar ku kuyi bincike sannan kafin hukunci. A yanzun bani da abokiyar shawara bayan Aunty murja domin duk sirrina itace haka itama mun koma tamkar uwa daya uba daya. Haka ban garen mamana da y'an uwana wadanda muke uwa daya komai ya dai daita a tsakanin mu. Amman y'an ubana har yau sunki saduda don har yanzun basu bar yi min hasssada ba kuma kullum ni ce a sama. Anan zan tsaya da baku tarihin rayuwata ina fatan zaku amfana da sakon da yake ciki. Toh safiya mun gode da labarin rayuwarki da kika mika mana domin isar dashi ga Al umma ina mai godiya ga Allah da ya bani ikon sauke wannan nauyin fata Allah yasa mu amfana da darussan da yake cikin rayuwarki a madadin daukacin y'an Gorgeous writer forum da sauran fans muna miki fatan Alkhairi a rayuwarki ta gaba na barki lafiya. *Alhamdulillah* Daga Alkalumman : Maman nurul huda👄 And Maman ihsan😍 Please share masu rowar comment yau dai na kar kare muku buk din 🤪masu comment ana mugun tare😘 Maman nurul huda 👄 And Maman ihsan😍 Love you fans