Copied By YAYA HAYAT (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion Cool novel, makeup and kitchen1⃣ Cool novel, makeup and kitchen2⃣ AND Cool novel, makeup and kitchen3⃣) WHATSAPP NO:+2349030159301 [10/26, 9:21 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RAYUWA* page1⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM* *INA GODIYA GA ALLAH SWA DAYA BANI IKON RUBUTA WANNAN LITTAFIN. SALATI DA AMINCI SU KARA TABBATA GA ANNABI MUHAMMAD SAW, ALLAH YA KARA MANA SON SA AMEEN.* *NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN DUNGURUNGUM GAREKI MASOYUYATA AYSHA ALIYU GARKUWA. ALLAH YA KARA BASIRA DA DAUKAKA, ALLAH YA RABAKI DA SARRIN MAI SARRI YA TSAREKI DAGA DUKKAN MAKIYANKI. YA ALLAH INA ROKANKA KA DAUKAKA AYSHA ALIYU GARKUWA KASA TAFI KARFIN DUK WANI MAKIYINTA AMEEN* *INA TAYAKI MURNAR KAMMALA LITTAFINKI BANDIRAWO DA KIKAYI ALLAH YA SANYA ALKHARI YA KARA BASIRA DA BAIWA MAI TARIN YAWA AMEEN.* Kauyan *katsalle*wani karamin kauye ne dake cikin kauyen *bunkure* dake jahar *kano*. Malam Mukhtar da iyalinsa na daya daga cikin mazauna cikin kauyen. Matan malam Mukhtar biyu lami itace uwargida sannan Aysha amarya. Tun auran malam Mukhtar da lami shekara goma allah bai basu haihuwa ba hasalima ko bari lami bata taba yi ba. Malam Mukhtar ya damu kwarai da rashin haihuwa da bai samu ba, wannan dalilin yasa shi Karo aure. Allah ya hadashi da Aysha yar mokocinsu ya aureta, bakaramin tashin hankali lami ta shiga ba jin wai mijinta zai Karo aure sannan kuma yarinya karama zai aura wadda bata fi yar cikinta ba, wannnan dalilin yasa lami shiga ta fita na ganin ta hana wannan auran amma sam abu yaci tura duk wajen malamin da taje magana iri daya suke fada mata dole ne sai yayi wannan auren, Wannan dalilin yasa ta hakura da bin malaman ta daura damarar yiwa malam Mukhtar da Aysha tijara da rashin mutunci Sam ta hanasu sukuni da kwanciyar hankali kullum cikin neman masifa take. Wata tara da auran Aysha da malam Mukhtar allah ya a zurtasu da 'ya mace kyakykyawa sak ta dauko kamannin Aysha, kasancewar ita Aysha kyakykyawace tamkar balarabiya. Haihuwar da Aysha tayi ya kuma daga hankalin lami, ranar da akayi haihuwar ta wanke kafarta ta tafi gidan aminiyarta delo ta fada mata abinda ke zuciyarta ba bata lokaci delo ta zari mayafi suka kama hanyar gidan bokansu. Suna zuwa suka fada masa bukatarsu nan ya bata kullika da wanda zatayi turare dana tsarki da wanda zata zubawa malam Mukhtar a abinci ya tsani Aysha da 'yar ta ta. Bayan ya gama yi musu bayanin kumi lami ta kunce gefen zaninta ta kunto kudi ta zubewa boka sukayi godiya suka tawo cikinsu fal murna. Tun daga wannan ranar malam Mukhtar ya juyawa Aysha baya, baya shiga dakinta ko magana ma bayi mata yakeyi ba saidai idan lami ta zugoshi yazo ya balbaleta da fada, KO sunan jaririyar ma ita ta sama mata *HIBBATULLAH* _gift of Allah_. Haka rayuwa ta juyawa Aysha da 'yarta cikin lokaci kankani, shekarar Hibbah daya allah ya bawa lami 'ya mace so kuga rawar kai wajen malam Mukhtar da lami, tunda lami ta haihu Aysha takoma tamkar yar aiki komi ita takeyi wankin kashi kirki komai ita keyi. Ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar lami wato Rahmatu, akasha shagalin suna duk da kauyene amma malam Mukhtar ya kashe kudi. Rahmatu ta taso cikin sangarta da shagwaba sabanin Hibbah data taso cikin tsangwama da kyara da tsanar da mahaifinta yake nuna mata. _wannan kenan_ "Ke Hibbah! Hibbah ina kike ne? kina jina ina kiranki ayeh?" Lami dake zaune a tsakar gida ta fada tana karasa jera abincin siyarwarta a faranti, Rahmatu na taya ta. "Na'am Inna gani nan zuwa" Hibbah ta fada tana fitowa daga wani dan karamin daki rike da hijjab dinta a hannu tana kokarin sakawa. A hankali ta karaso ta tsugunna a gaban Inna lami tare da cewa "gani Inna". Murfin dake hannun innan ta kwada mata aka tana cewa "ubanki kikeyi a dakin kina jina inata a kwada miki Kira amma kikari burus kika k'i amsawa koh? Saboda kin rainani koh?" Cikin tsantsar masifa da daga murya take magana. Da sanyin murya tace "Dan allah Inna kiyi hakuri wallahi hadda nakeyi,gobe malam zai ansa hadda kuma duka zaiyi idan ban iya ba...........". "Ni zaki fadawa karatu don ubanki ko don ba waccan tambadaddiyar uwar taki bace take kiranki, ayeh?" Cikin masifa da bala'i ta katseta. Kasa Hibbah tayi da kanta ta kuma cewa "kiyi hakuri inna" "Bazanyi hakurin ba shegiya munafuka sai anyi magana kice ayi hakuri da hakurin ta mutu sadakar nawa kika bada? Nace sadakar nawa kika bada? Kuma wallahi wannan makarantar gaf kike da daina zuwanta don bazai yuyu ba ki dinga yimin cikas acikin Sana'a taba tashi ki dauka ki fitar min dashi kuma saura ki dawo min da saura kiga yarda zanyi lasalasa dake a gidan nan". Magana takeyi ko numfashi bata saukewa. Matsawa tayi kusa da farantin ta dauka ta Dora a kanta data Fara tafiya taji Rahmatu Na cewa "wallahi Inna bakin cikin Hibbah take miki, kullum sai sale driver yace takai masa amma taki ta Kai masa, tun rannan dayace zai siye duka shine tace bazata saida masa ba." Rike baki Inna tayi tanajin Rahmatu sannan cikin tsantsar masifa tace "ke Hibbah zonan yar bakin ciki" jikinta ne ya fara kyarma ta juyo cike da tsoro ta tsugunna a gabanta. Wata maka Inna ta kaimata a fuska tace "bakin ciki kike yimin kar a siye kwantai kike so nayi? To wallahi kika dawo min da kwano data wallahi sai naga mai kwatarki a gidan man shegiya Mai zubin aljannu, tashi ki bar min gaba." Tashi tayi hawaye nabin gefen fuskarta tayi hanyar zaure da niyyar fita ji tayi an dafa kafadarta ta San ko wane hakan yasa cikin sauri ta goge hawayenta, sannan ta kakaro murmushi ta juyo Umma ce a gabanta wadda a gabanta akayi komai, dauke da murmushi a fuskarta tace "kiyi hakuri hibbatullah wata Rana sai labari kiyi ta hakuri *RAYUWA* mai canji ce wata Rana ma bama duniyar baki daya." Murmushi tayi tace "wallahi Umma babu komai a raina nasan haka allah ya kaddara min tawa *RATUWAR*" Umma ta shafa gefen fuskarta tace "yauwa Hibbah allah yayi miki albarka". "Ameen "Hibbah ta fada tana kokarin fita daga gidan. "Hibbah" Umma ta fada tana karasowa kusa da ita. Juyowa tayi tare da cewa "na'am Umma" kuma dafa ka fadarta tayi tace "don allah Hibbah....." Katseta... *Idan kuna bukatar Na cigaba sai naga comments naku ta wannan number 07088301840* *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:21 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RAYUWA* 2⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Masoyana na samu sakonnin ku kuma in allah ya yarda zan cigaba da wannan littafin na gode da kauna da kulawa da kuka nunamin.* Katseta Hibbah tayi da cewa "na kula da kaina karna kula kwayan banza, karna biyewa wani namiji muyi hira kuma na zama mai kamun kai da nutsuwa a wajen sana'ata na girmama mutane, duk wanda ya zomin da wata magana dabai dace ba karna kulashi ko ba haka ba Umma?" Hibbah ta jero mata wadannan kalaman. Umma kuwa tsayawa tayi tana mamakin yarda d'iyar tata tasan abinda take son fada mata. Cikin mamaki dauke a fuskar Umma tace "ya akai kika san abinda zan fada miki kenan Hibbah?", murmushi Hibbah tayi tace "Umma ai kullum idan zam fita sai kin yimin wannan fadan shiyasa na rike". Cikin jin dadin kalamanta umma tace " to shikenan dan allah kiyi amfani da fadan danayi miki kinji Hibbah, kije Allah yayi miki albarka, ya kare minke daga dukkan sharri ya kuma bada sa'a kinji Hibbah". Take taji wani happy ya lullubeta cikin jin dadi da manta duk wata damuwarta tace "ameen ummana saina dawo" ta fada tana fita daga gidan. Umma tace "allah ya dawo min dake lafiya". Tsakar gida umma ta koma ta nufi bakin murhu tana iza wutar da take girki da ita. Muryar lami taji dab da ita tana cewa "munafuka annamimiya ai dama nasan duk abinda Hibbah takeyi a gidannan kece kike kitsa mata komai, to wallahi gara ma tun da wuri ki daina kitsa mata bakin hali irin naki idan ba haka ba......." Tayi kwafa "kema kinsan sauran, haba shiyasa naga kullum idan zata fita saikin kirata kin kitsa mata muggan kalamai to ni naci dubu sai ceto wallahi." Lami ta fada tana nuna umma cikin tsantsar masifa har wani girgiza jiki take yi. Ita dai umma bata tanka mata kasancewarta mace mai hakuri da juriya saima ce mata tayi "allah ya baki hakuri Yaya" Cikin masifa lami ta hayayyako mata "ai dama ke kullum haka kike sai kin kulla munafincinki kizo kina bawa mutane hakuri, wallahi bara malam yazo ni gaskiya na gaji da ganinki a gidan nan yazo ya sauwake miki kawai." Umma ta tsorata kwarai dajin furucinta don tasan tsaf zatasa ya saketa din murya na rawa tace "Yaya kiyi hakuri wallahi addu'a kawai nayi mata banda wannan bance Mata komai ba." Tabe baki lami tayi ta juya tana tafiya tare da cewa "kyaji dashi don zamanki a gidan ya kusa karewa eyeeh! Gara ki tattara ki tafi" Tsugunnawa umma tayi a gaban murhun tana mamakin wannan *RAYUWA* da sukeyi a cikin gidan tamkar wasu 'yan aiki ko kuma bare. Hannu ta daga sama tana addu'ar Allah ya kawo musu dauki. Ita ko lami kofar dakinta taje ta zauna tana girgiza kafa cike da masifa, Rahmatu ce ta fito daga daki duk tayi wani dige dige a fukarta tazo ta kwanta akan cinyar lami cike da shagwaba tace "inna nifa yunwa nake ji" ta fada tana zunburo baki. Lami tace "a'a Rahmatu ai na ajiye miki abinci gashi can a roba kije kici" kuma zumburo baki tayi "ni wallahi bana cin wancan abincin" Rahmatu ta fada tana kuma narkewa a jikin lami. Lami cikin bala'i tace "to karki ci din cikin waye?", Burgima Rahmatu ta shiga yi tana cewa "ni wallahi bazan ci wannan abincin ba". Lami nasan Rahmatu fiye da kowa cikin sauri ta dagata tana cewa "haba Rahmatu ya zaki dinga burgima akan wani abinci, uhumm?" Cikin shagwaba da sangarta tace "to ni ki bani kudi na siyo alala a wajen Abu don bazanci wannan abincin ba". Cikin lallashi lami tace "don wannan ai mai sauki ne " ta kunto kudi a jikin zaninta ta bata "ungu jeki ki siyo kinji" karba tayi ta ruga da gudu tabar gidan. Bangaran Hibbah kuwa tana fita ta nufi kasuwa dake can take kaiwa, bayan taje ta zauna a mazauninta mutane suka fara zuwa siye. Sale driver ne yazo yana........... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:21 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RAYUWA* page 3⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Na sami dukkan sakonku masoyan A.A Garkuwa, kuma in allah yarda zan cigaba da rubuta wannan littafin.* Yana wangale baki ya karaso kusa da Hibbah zai zauna da sauri Hibbah ta mike tsaye tana binshi da wani mugun kallo tare da nunashi tace "Kai sale mene haka baka da hankaline zakake kokari goga jikin ka da nawa?", Kallon ta yayi yana kuma wangale baki yace "haba Hibbah mene waike yaushe ne zaki gane nufina to mene don na hada jikina danaki." Mugun kallo ta buga mai tare da daukar farantin ta zata bar wajen. Hijjab dinta ya janyo da karfi, baya tayo sosai tare da farantin hannunta hakan yayi sanadiyyar subucewar faranti daga hannunta. Ya kife sauran abincin rabi ya zube a kasa rabi kuma a jikinta, Rahmatu da a gabanta akayi komi ta tsaya tana dariya don tasan koba komai yau Hibbah saita nadu a wajen inna . Ita kuwa Hibbah iya kuluwa ta kulu zuciyarta tana mata wani irin radadi cikin zafin nama ta juyo tana binsa da mugun kallo tare da cewa "wallahi kaji Na rantse sale sai ka biya kudin abincin nan daka zubar don bazan dauki asara ba, don nima idan na koma ba afuwa Inna zata min ba bazaka jamin duka a banzaba wallahi" cikin zafin rai take magana. Dariya sale yasa yace "ai nasan da haka kudin abincinki zan biyaki na nawa ne?" Kallon shi tayi a kaiksice tace "Na murtala shida da rabi ne", Hannu ya zura a aljihunshi ya ciro Dari biyar ya mika mata, kallon shi tayi cikin tsiwa tace "mene na wani bani dari biyar bayan kasan bani da canji." Juyawa yayi yaga hankalin mutane baya kansu ya kalli Abu kawar Hibbah yaga bata kallonsu. Hibbah ta kalleshi duk yayi yanayin mara gaskiya sai wani waige yake tace "malam ni ka samu canji ka bani kudi na ka wani tsaya kana waige waige." Murmushin mugunta sale yakeyi yana kallonta yace "karbi kudin da daddare zanzo dandali cin gyda kafin nan kin samu canji saiki bani." "Ni ban yarda ba kuma bazan karba ba kawai kaje ka samo ka bani ina zaune anan" Hibbah ta maida mai da amsa cikin sauri. "To yanxu ya kike so nayi kinsai dai babu wanda zai bamu canji a kasuwar nan koh?" Sale ya fada yana kallon kirjin Hibbah yana lasar lebe. Tsaki Hibbah taja "kaje ka samo ina jiranka a wajen Abu " tana gama fada masa ta tsugunna ta kwashe robobin da murafi tare dayin gaba, wajen da Abu ke zaune ta karasa ta zauna. Da gudu Rahmatu ta kwasa tayi hanyar cikin gari. Da ido Hibbah ta bita cike da tsoro don tasan tana zuwa gida zata fadawa inna. Abu ta kalleta tace "Hibbah ni a ganina dama ki karbi kudin kamar yadda yace da daddare idan mukaje dandali saiki bashi". Hibbah tayi shiru kafin tace "wallahi Abu ina tsoran sale ne kwata kwata na tsameshi na tsani halinshi bana son yana kulani KO kadan, shiyasa fa bana son ya dauki abincina, kina gani kullum don kar magana ta hada mu yasa bana karbar kudin abincinsa amma shi ki duba yarda kullum yake wani shige min." Ta fada cike da damuwa, "Don kin tsane shi bazai hanaki karbar hakkinki ba a wajensa, sannan ki duba fa kigani kullum sai Inna lami ta dakeki akan bakya cika mata kudinta, gashi yanxu Rahmatu taga lokacin da ya zubar da sauran abincin na tabbata saita fadawa Inna kuma idan baki karbi kudinnan ba baki da wata sheda ta kare kanki a wajenta gwara kawai ki amsa." Shiru Hibbah tayi tana nazarin kalaman Abu tabbas gaskiya ta fada mata gwanda ta karbi kudin nan data komawa Inna gida ba sauran kudi. Kuma tasan tunda Rahmatu ta ganta tasan saita fadawa Inna. Hibbah tace "to idan na karba yazo da daddaren kuma ba canji fa?" Abu tace "karki damu saina anso mana wajen gwaggo nasan tana da canji" Hibbah tace "to shikenan idan zamu tafi na amsa" mikewa Abu tayi tare da cewa "tashi mu tafi alalan ya kare ai" mikewa Hibbah itama tayi ta dora farantinta aka sannan ta karasa kusa da inda sale yake tace "Zan tafi gida ka samo canjin?", "ban samu ba gashi na amsa ko gobe ne idan yau banzo dandalin ba" sale ya fada yana kuma kallon girjinta tare da miko mata kudin. "Ni dai wallahi babu ruwana idan na kaiwa Inna kudin tace baza ta bada canji ba" ta karba kudin, shi kuwa sale ya sha'afa da kallon lips dinta, jin bai amsa ba ta kalleshi tace "kadai ji Na fada" sale yace "ai ba komai saina fanshe" kallon mamaki Hibbah tayi masa tace "ka fanshe da me" cikin sauri yace "a'a ina nufin bakomai idan ma ta hana canjin." Juyawa tayi taja hannun Abu suka tafi, muryar sale sukaji yana cewa "saina zo" basu waiga ba suka yi............. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:21 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RAYUWA* page6⃣to7⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *الله اكبر الله اكبر الله اكبر* *لااله الا الله، الله اكبر الله اكبر ولله الحمد* *الله اكبر كبيرا* *والحمد لله كثيرا* *و صبحان الله بكرة و اسيلا* _*Ina bawa mabiya littafin RAYUWA hakuri kasancewar yau zan dakata da yin typing sai bayan sallah idan Allah ya kaimu zan dora, allah yasa muyi sallah lafiya mugama lafiya.*_ _*Au na manta da sakon Aunty na ban fada muku ba, Aunty AYSHA ALIYU GARKUWA tace bayan sallaha karku manta ku tawo mata da nata naman😜.*_ Haka Hibbah ta yini tana kuka da tunanin yarda zata cigaba da *RAYUWA* a gidannan cikin wahala da ukuba. Sallah ce kawai ta tasheta daga inda take, alwala tayi tai sallar azahar sannan tayi la'asar kasancewar taji anata kiraye kirayen sallah bayan ta idar ta zauna ta rika kwararo addu'a tana kaiwa mai sama kukanta, addu'a take yi amma hawaye na zuba a idanunta. KO abinci ranar bata iya ci ba saboda tsantsar damuwar dake damunta na rabata da mahaifiyarta gatanta da akayi. Umma kuwa suna zuwa gida Yaya Habu ya fadawa su gwaggo komi, sun firgita kwarai dajin kazafin da akayiwa 'yar tasu, ko kadan saki bai daga musu hankali ba saboda sunsan yanayin halin da 'yar tasu take ciki a gidan mijin nata. Kuma sun goyi bayan Yaya Habu daya tafi da ita cen Bunkure din zatafi samun nutsuwa sannan data gama iddarta idan Allah ya kawo miji tayi aurenta. Nan sukayi musu sallama suka huce. Da daddare bayan sallar isha'i Hibbah na kwance a dakin ummanta zazzabi ya rufeta sai rawar dari take yi. Rahmatu ce tashigo dakin tana cewa "ke Hibbah kije sale driver na kiranki, cikin rawar baki Hibbah tace "Dan allah Rahmatu anso masa canjinsa wajen Inna, zazzabi ya rufeni bazan iya tashi ba." Harararta Rahmatu tayi "lallai ma ni zaki aika? Shima din abinda yasa kika nazo kudi ya bani amma badan haka ba babu inda zani, mtwss" ta karasa maganar dayin tsaki tayi ficewarta. Tana fita dakin Inna ta shiga tana shan rake bako sallama ta haye kan gadon innar ta cigaba da shan rakenta, inna ta kalleta tace "me sunan baba me kike shane haka?" Shiru Rahmatu tayi bata amsa ba ta cigaba da shan raken. Inna ta kalleta tace "au saboda kar nace ki sammin shiyasa kikayi min shiru koh Rahmatu?" Cikin gajiyawa da maganar Rahmatu tace "ai dama nasan sai kince na sammiki bayan kuma kena fara cewa ki bani kudi na siya kika hanani" ta fada tana kuma gyara zamanta akan gadon innar. Cikin yanayin lallashi Inna tace "haba me sunan baba ai ina baki kina siya, ki sammin kadan zansha." Turo baki Rahmatu tayi tare da mika mata tace "to gashi nan karki sha min dayawa, inkika sha da yawa allah saikin sai min wani," inna ta amsa tana cewa "bazan ma sha da yawa ba." Bantara tayi tasha zata kara, Rahmatu tayi saurin cewa "wallahi inna kika Kara saikin sai min sabo" mika mata inna tayi tana cewa "ai raken nakine akwai zaki, wa ya baki kudi kika siya?" Bata kalli inna ba tace "Sale direba ne yazo wajen Hibbah, shine zan shigo ya ganni yace na kira masa ita nace bazani ba shine ya dauko hamsin ya bani." Inna ta gyara zama tace "wai mene a tsakanin su ne dazuma kince ya bata Dari biyar a kasuwa, don ya barar mata da abinci kuma nidai nasan abincin dana dora mata na dari uku ne. Kinga kudin ma data zo tana ta uwarta bata ma yimin bayani ba ta bani kudin duka." Rahmatu tace "toni ina Zan Sani ni dai nasan kawai yana yawan kulata ko kuma yace zai tabata ita kuma ta haushi da masifa." Tana gama fadin haka ta mike tare da cewa "ni na tafi dandali" inna tace "sai kin dawo amma kafin ki tafi ki shiga ki kira min wannan shegiyar yarinyar tana nufin dan uwarta tabar gidan shine yau bazata fitar min da gyadata ba." "Inna tana can bata da lafiya" Rahmatu ta bawa inna amsa tana fita daga dakin. Murmushin mugunta inna tayi tare da bin bayan Rahmatu. Shi kuwa sale ganin Hibbah bata fito ba yasa ya zauna zaman jira don yasan dole zata fito da gyada. Yana nan zaune yaga Rahmatu ta fito ya kalleta yace "Rahmatu ina Hibbah din?" Kallon shi tayi adan wulakance tace "tana ciki wai bata da lafiya" tana fadin haka tayi gaba. Shiru yayi yana nazarin koya shiga cikin gidan, yana kuma tsoran kar a kamashi don yasha alwashin yau dinnan saiya dan dani zumar Hibbah. Inna ce ta katseshi da cewa "sale Kaine a kofar gidan namu?" Dan sosa keya yayi ya shiga gaishe da inna tare da cewa "nazo karbar canjina ne a wajen Hibbah na dazu dana bar mata". Inna jin anyi batun canji yasata murtuke fuska ta fara masifa "wane irin canji kuma?" Dan sunkuyar dakai sale yayi tunda yasan shi yake nema yace "eh dama dazune na zubar mata da abinci a kasuwa kuma na bata Dari biyar babu canji shine nace zanzo Na amsa." Dariya inna tasa harda tafa hannu tace "hmm yaro man kaza sale mene na boye min ni mai taimaka maka ne ka samu abinda kake so a wajen Hibbah, nasan komai kuma Zan taimaka maka ka samu Hibbah a Daren nan ma idan kana so amma da sharadi." Wani irin happy ne ya rufe sale cikin sauri yace "wane sharadi ne xan bishi matukar zan sami Hibbah" dariya inna ta kumayi tace "sai naji dumus a hannu" ba musu sale ya dauko 'yan dari bibbiyu ya irga guda shida ya bawa inna, inna ta amsa ta irga wani kallo ta bugamai tace "dubu daya da dari biyu ne fa kana tunanin wannan yakai darajar abinda zaka samu?" Cikin sauri ya kuma irgo guda hudu ya mika mata. Karba tayi tana ganin hudune cikin zafin nama ta warce sauran na hannunshi ta hada. Tace "kazauna anan idan kaga malam ya shigo sai kabi bayansa zakaga wani karamin daki dayake kallon dakin dazai shiga amma yayi nisa sosai da wanda zai shiga to tana ciki saika shiga." Sale cikin happy yace "to amma ummanta fa?" "Ummanta bata gidan" tana kaiwa nan tayi shigewarta cikin gidan cike da murna. Ya kalli Hibbah yana dariyar keta, ita kuwa mugun tsoro ya bata cikin Sauri ta tashi zaune tana ja da baya. Binta ya shigayi shima, mikewa tayi dakyar ta shiga yin baya batason tazo bakin gadon ba sai ji kawai tayi ta fada kan gadon. Murmushin mugunta sale yayi yace "kin rage min aiki." Hawaye ne ya fara sintiri a fuskarta tana yin baya har taje karshen gadon. Hayowa gadon yayi yana murmushi, cikin kuka tace "don allah sale kayi hakuri karka rabani da muyuncina darajata don allah ka kyale...." Dariya yasa yace "wallahi Hibbah yau ba mai hanani kusantarki garama ki nutsu mubi komi a hankali idan ba haka ba kuma zanyi ta karfi Wanda ni zanfi son hakan." Kifa kanta tayi a tsakanin cinyoyinta tana karanto kowacce addua tazo bakinta. Kayan jikinsa ya cire ya wurgar daga shi sai trouser ya tunka rota............ *by* *MAMYN NAJMAH* [10/26, 9:21 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RAYUWA* page 4⃣to5⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *الله اكبر الله اكبر الله اكبر* *لا اله الله، الله اكبر الله اكبر و لله الحمد* *الله اكبر كبيرا* *والحمد لله كثيرا* *و صبحان الله بكرة و اسيلا* Sukayi tafiyarsu suna hira Hibbah tace "Abu wallahi akwai wani abu da yake bani mamaki da tsoro" kallon mamaki Abu tayi mata tace "wane abune wannan Hibbah?." Numfashi Hibbah ta danja tace "Abu kusan kullum sai nayi wani mummunan mafarki, wai Inna tasa baba ya kori umma daga gidan ni kuma ta biyoni da gudu da wuka a hannunta zata kasheni, sai wani balarabe Wanda ban taba ganinsa ba ya kwaceni a wajenta. Ita kuma ya jefata cikin wani katon rami me dubu idan ya jefata sai naga baba yaxo ya rumgume ni yana cewa na yafe masa" ta karasa maganar cikin tsananin damuwa. Abu tadanyi shiru tana nazarin kalaman Hibbah kafin tace "idan har hakan zai kasance gaske toda munfi kowa murna, mafarkin ki yana nuna nan gaba wani zai taimakeki ya ceto baba daga sharrin Inna. Amma abinda bangane ba shine korar umma da kikace Inna tayi daga gidanku." Cikin damuwa Hibbah tace "Abu nima abinda nake ta tsoro da wannan mafarkin da nakeyi kenan kar fa ya kasance gaskiya." "In allah ya yarda bazai kasance gaskiya ba, Umma tasan kina wannan mafarkin?" Abu ta tambaye ta, girgiza kai tayi tare da cewa "a'a bata sani ba" Abu tace "yakamata ki fada mata wata kila ita ta fimu fahimtar mafarkin naki" "hakane idan na koma zan fada mata" Hibbah ta fada. Suka cigaba da tafiya suna dan hira jefi jefi. Farantin kantane ya subuce ya fadi kasa robobin suka tarwatse, bata damu da faduwar da sukayi ba sai kirjinta data dafe da hannu saboda bugun da yake yi mata. Kallon mamaki Abu tayi mata tace "lafiya Hibbah?" Cikin tsantsar tashin hankali Hibbah tace "wallahi Abu ji nayi gabana yayi wata mummunar faduwa kirjina na bugawa da Sauri sauri," Abu tace "to allah yasa lafiya," Hibbah tace "ameen" tare da sigunnawa tana tattara robobin Abu na tayata. A can gida kuwa bayan umma ta sauke tukunyar daga kan murhu ta dauki tukunyar takai kofar inna tare da cewa "Inna gashinan na gama." Inna Na cikin daki bata ce mata komi ba tayi banza da ita. Umma ta saba da hakan don haka bata damu ba taje daki ta dauko roba ta ajiye a kusa da tukunyar. Buta ta dauka ta shiga bayan gida ta fito ta daura alwala ta shiga daki, sallah tayi bayan ta idar ta zauna tana kaiwa ubangiji kukanta, bayan ta shafa ta zauna ta cigaba jan carbi. Muryar malam taji yana kwalla mata kira cikin fada "ke Aysha, Aysha ina kike fito munafika maci amana." Cikin sauri Umma ta fito tana cewa "malam lafiya.........?" Bata Ankara ba taji saukar yatsun malam a fuskarta. Rike kuncinta tayi tace "malam me nayi don Allah ka fada.........." Kuma katseta yayi da wani gigitaccen mari Wanda yayi sanadiyyar faduwarta kasa, binta yayi ya cigaba da dukanta baji ba gani yana binta da muggan kalamai "Allah ya isa tsakanina dake Aysha bazan taba yafe miki ba, kin cuceni kuma sai kinga sakayya, ki rasa dame zaki saka min saida bin maza" yaci gaba da dukanta. Lami wadda taji duk abinda ya faru tana daki tanata dariya domin kuwa tarkonta ya kama malam, da gudu ta fito daga dakin ta karaso kusa da malam tana cewa "haba malam dukan mace kamar wani mara hankali me tayine malam?" Bai saurareta ba ya cigaba da bugunta. Itako Aysha ganin babu mai cetonta yasa dakyar ta mike ta koma dakinta da gudu. Yana kokarin binta malam Habu wan Aysha daya shigo ya tareshi da sauri "haba malam Mukhtar me yayi zafi haka dukan matarka da hannunka? Da hankalinka kake dukan mace ai fada ya dace kayi mata ba duka ba." Mugun kallo malam Mukhtar yayi masa yana cewa "eh ai dama dole kace nayi mata fada tunda kanwarka ce koh? Kuma na tabbata kasan irin tarbiyyar da kuka bawa 'yarku don haka kadau keta ku tafi na saketa." Ba malam Habu kadai ba har umma dake daki saida ta tsorata, ta fito a rikece tana kallon su malam Habu yace "saki fa kace malam Mukhtar me yayi zafi haka? Ai idan tayi maka wani laifi ni ya kamata kasamu sai mu magance matsalar a sasanta komai, bawai kadinga dukanta ba daga karshe kuma kace ka saketa ba" malam Mukhtar ya kalleshi cikin bacin rai yace "a sasanta me? Ai babu a abinda za'a sasanta kawai ka dauki fasikar kanwarka ku barmin gida" cikin mamaki Umma ta dafe kirji tace "fasika fa kace malam, Inna lillahi wa Inna ilaihirra ji'un allahumma ajirni fi musibati wa akhlifnii khairan minha." Umma ta fada cike da damuwa, malam Habu ya kalleta ya kalli malam Mukhtar yace "Mukhtar fasika fa zina fa kenan, ka nufin matarka na aikata zina? Ka ganta da idanunka ko kuwa zargi kakeyi Mukhtar?" Cikin hayayyakowa malam Mukhtar yace "eh ai dama baza kaga laifinta ba tunda kanwarkace jininka ce, ni dai na gama magana ka dauki kanwarka Ku barmin gida". Lami data nuna damuwa a fuskarta a badini kuwa ta shiga tsananin farin ciki tace "fasika malam gaskiya bazan boye maka ba don ko jiya naga inuwar wani katon mutum da daddare ni wallahi dana ganshima ba karamin tsoro naji ba ashe gurinta yake zuwa" malam Habu kallonta yake cikin mamaki yake kallonta, ita kuwa umma rushewa tayi dawani kuka mai ban tausayi tana cewa "wallahi malam sharri akayi min tunda nake ban taba aikata zina ba kayi bincike kafin ka yanke hukunci......." Katseta yayi da cewa "wane bincike zanyi bayan gashi nasan gaskiya babu wani bincike da zanyi kawai ki fitar min a gida na sakeki......." Furucin malam yayi daidai da shigowar Hibbah, sallama tayi amma babu wanda ya amsa ta kallesu dukansu basa cikin nutsuwa. Lami tadanyi murmushi tace "malam Saki nawa kayi mata?" Malam yace "saki daya nayi mata" saki daya kuma malam fasika ce fa koka manta, kenan zaka dawo da ita nan bada dadewa ba." Lami ta tareshi da fadin haka. Malam yace "wa? Allah ya tsareni da kuma zama da ita, dama can saboda ban samu haihuwa bane yasa Na aureta yanxu kuwa allah ya azurtani. Ni ina ma shakku Anya wannan yarinyar jini nace kuwa?" Cikin tsananin kuka umma tace "wallahi 'yarkace malam jininka ce" ta juya ta kalli lami cikin kuka tace "Yaya kiji tsoron allah ki rinka tunawa da mutuwa da kwanciyar kabari, kinyi min sharri akan abinda ban aikata ba kisani sai allah ya bi min hakkina akan abinda kikayi min..........." Kukane yaci karfinta. Hibbah ce ta matso kusa da umma itama hawaye na bin fuskarta, ta shiga sharewa umma hawayenta, rumgume ta umma tayi tana cewa "ya allah ga amanar 'yata nan, Allah ka kareta daga dukkan sharri na mutum kona aljan Allah ka tsareta daga dukkan abinki kasa tafi karfin makiyanta" ta fada cikin kuka. Malam Mukhtar yace "ai da 'yarki zaki tafi baza ki barmin ita a nan ba" cikin sauri lami ta katse shi "a'a malam ka barta a nan kanaso tajene ta kwaso irin halayenta?" Malam yace "ai bana zaton 'yata ce shiyasa gara ta tafi da ita kawai" "a'a malam gara ka barta anan koba komai zaka tserar da ita daga halakar fadawa zina" Malam Habu ya kalli Umma da Hibbah yarda suka kuma kamkame juna suna kuka sai yaji sun bashi tausayi, yace "Aysha taso mu tafi gida kiyi hakuri kinji" cikin kuka mai ban tausayi ta kalleshi tace "Yaya tayi min sharri ta rabani da farincikina Hibbah, yanxu kowa a garin nan kallon fasika zai rika yimin alhalin ni ban taba zina ba......." Wani kukan ta kuma saki tana kuma rukunkume Hibbah. Hibbah kuwa hankalinta ne yayi mugun tashi ta shiga tunani _zina? Umman nawace ke aikata zina? Me yasa Inna lami bazata taba kaunar ummana ba? Me tayi mata a *RAYUWA* da har ta tsaneta haka_ Malam Habu ya katse mata tunani da cewa "kiyi hakuri Aysha ki saka aranki wannan itace kaddarar da allah ya aiko miki kiyi kokarin cinye wannan jarrabawar, *RAYUWA* ce wata rana sai labari kinji? Kuma maganar mutanan gari kuma dama ni na yanke shawarar zan tafi dake can bunkure ki zauna, yanxu idan mun shiga gida nayiwa su gwaggo bayani sai mu huce" Kai ta daga masa sannan ta mike tana kallon Hibbah. Murmushi ta kakalo tace "Hibbah zan tafi nasan zaiyi wuya na dawo nan kusa, Dan allah ina rokonki Hibbah ki kula da kanki ki zamo mai hakuri da juriyar duk abinda zaayi miki. Nasan zaman daza kiyi a gidannan sai yafi na baya kunci da wahala, nasan kina da hakuri to ki Kara akan wanda kike dashi kinji allah yayi miki albarka yasa kifi karfin makiyanki ya kareki daga dukkan mugun mutum." Rike hannunta Hibbah tayi cikin kuka tace "Umma Dan allah karki tafi ki barni wallahi idan kika tafi Inna kasheni zatayi don allah ki zauna" ta kuma fashewa da kuka. Umma cikin hawaye tace "kiyi hakuri Hibbah mahaifinki yana zargina da aikata zina, sanadiyyar haka ya sakeni kuma koda bai sakeni ba aure da zargi bazai yuyu ba. Ki hakuri Hibbah Zan tafi amma zan rinka zuwa dubaki." A hankali umma ta zare hannunta daga na Hibbah sannan tace "kirike addu'a itace makamin mumini, karki manta da azkar na safe da maraice sannan alwala kafin ki kwanta kamar yarda kika saba, da yardar allah saikinfi karfin duk wani mai nemanki da sharri." ahankali Umma ta rinka ja da baya tana tafiya, da gudu Hibbah tazo ta rumgume ta tana rokonta karta tafi. "Kiyi ki barmin gida kafin nadawo", malam Mukhtar ya fada yana fita a gidan. Ita kuwa lami guda ta Saki tace "saika tattara kanwarka Ku kara gaba ai dama duk wacce tayi gigin hada miji dani sai taga abinda yafi haka", ta fada tana kuma shekewa da dariya. Mamaki da al'ajabin abin ne ya hana malam habu magana ya kalli Umma yace "kiyi hakuri mu tafi yamma nayi." Haka suka rabu su biyun duka suna kuka. Bayan fitar su umma haka Hibbah ta zauna tanata rusa kuka mai ban tausayi, lami ce ta kalleta ta tabe baki tace "ni bani kudin sana'ata, gara ma ki daina yi mata kuka don kema kin kusa barin gidannan." Mika mata kudin tayi, fizgewa lami tayi tai gaba. Ita KO Hibbah saboda tashin hankali tama manta bata fada mata akwai canjin sale ba............. *by* *MAMYN NAJMAH* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page 8⃣to9⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *ina neman afuwarku na kuskuren danayi a last page na, fatan za'a yimin uxuri* *Ina mika sakon barka da sallah ga dukkan masoyan aunty na _AYSHA ALIYU GARKUWA_. Ina kuma baku hakuri na jina kwana biyu da banyi typing ba, abubuwa ne sukayi yawa don ko na happy sallah bansamu damar yi muku ba. Masha Allah yanzu komai yayi normal kuma insha allah zaku cigaba da jina. ~Aci gaba da gashi~.* Tun karota yayi gadan gadan ya hayo gadon tare da fizgota ta fada cijikinsa, ya shiga shashshafata. Jikin ta ne ya dauki rawa tamkar mazari saboda taji bokon abu, kokarin kwace kanta ta shiga yi duk da bata da wani karfi saboda zazzafan zazzabin da take fama dashi. Cikin kwarewa yake bin gabbanta yana shafawa hannunsa ya dora kan dukiyar fulaninta, jin hannunsa a kan kirjinta tayi cikin zafin nama ta hankadashi ya fado kasa da sauri ta duro daga gadon ta nufi hanyar fita. Fizgota yayi tare da cewa "ke kin isa na shigo dakin nan ba tare dana biya bukata ta ba, wallahi tunda na bawa waccen matar kudina kema saina fanshe a kanki." Ya fada yana janyota jikinsa tare da shafa fuskarta yace "kina da kyau baby, me yasa baza ki yarda dani ba? Uhum? Kibani hadin kai mana." Banza tayi dashi tana cigaba da kiciniyar kwacewa. Ganin zata bata masa time yasa ya ja wuyan rigarta tare da ketawa, take rigar ta yage dukiyar fulaninta ya bayyana. Rikicewa yayi ganin yarda suke a tsaye gwanin sha'awa, hannunshi yake kokarin dorawa tasa bakinta ta kafa masa wani mugun cizo. Da sauri ya saketa yana yarfe hannu, ita kuwa mikewa tayi zata bar dakin yasa kafa ya tade kafarta kamar an wurgata ta bugi kofar dakin akwai wata b'ula a jikin kofar, ta saitinta ta fada karfen jiki ya yanketa a goshinta ta zube a kasa jini yana kwararowa taa fuskarta. Rarrafowa yayi ya karaso inda take yana dariyar keta, Hibbah kuwa bayan ta fadi karfen da suke tare kofa take laluba da hunnunta, cikin sa'a kuwa tajishi. Janyoshi ta rikayi a hankali, shi kuwa sale tuni yayi mata rumfa yana sumbatarta ta ko ina. Janyo karfen tayi tare da dagoshi ta kwada mai a keyarsa. Dagata yai yayi gefe yana layi ya fada gasa yana ta juyi. Ita kuwa jin ya dagata ta samu da kyar ta mike tana dafa bango ta bude kofar tare da fita itama cikin layi ta fito daga dakin KO gabanta bata gani ji tayi ta bugi mutum, jirin da yake dibanta yasa tayin baya, cikin sauri Abu ta rikota tana tambayarta lafiya? Kokarin k'wace jikinta take yi tana nuna mata cikin dakin, kuma riketa Abu tayi tace "mene Hibbah? Kiyi min magana mene a dakin." Cikin rudu tace " na kashe shi yana ciki ya mutu." Sai kuma ta fashe da kuka ta rike hannun Abu sosai tana cigaba da kuka. Kallon goshinta Abu tayi inda ta yanke tadan waro ido tace "Hibbah meya sameki a goshi? Kuma waye ya mutu?" Bata amsa ba ta cigaba da kuka tana cewa "Abu ya mutu wallahi bada niyya na kashe shi ba." Abu ta kasa fahimtar waye ya mutu, kawai taja hannun Hibbah zuwa cikin dakin, K'ara Hibbah tasa tana cewa "wallahi idan naje dakin nan fyade zaiyi min, Abu kashe ni zaiyi ki kyale ni?." Ta kuma fashewa da kuka tana ciccijewa. Tsayawa Abu tayi da janta tace "ki nutsu Hibbah kiyi min bayanin komi," Abu ta fada cikin kwantar da murya. Shiru Hibbah tayi ta kasa magana, kallon ta Abu take yi tace "Hibbah ki fada min mana musan abinyi kafin Inna lami tazo." Jin an ambaci Inna lami yasa ta fara bawa Abu labarin abinda ya faru. Mamaki ne ya bayyana karara a fuskar Abu tace "fyade? Zai ai kata indai sale ne, Ai dama tun da naga yarda yake miki a kasuwa nasan akwai abinda yake nema" ta danyi shiru sannan taja hannun Hibbah tana cewa "ki nutsu Hibbah, mu shiga dakin muh gani idan yana motsi sai musan matakin dauka. Idan kuma ya mutu musan nayi," cikin tsoro Hibbah tabi bayanta suka shiga dakin. Sale suka gani a baje a dakin yana ta mutsu mutsu jini duk ya b'ata dakin. Kara sowa sukayi cikin dakin kallon shi Abu tayi taga yana motsi ta kalli Hibbah tace "ki kwantar da hankalinki Hibbah bai mutu ba yana motsi" Hibbah dai har yanxu hankalinta bai kwanta ba tace "to Abu kice ya fita daga dakin nan, kinsan idan Inna lami tasan yana dakin nan na shiga uku dukana.........." Katseta sale yayi cikin muryar data ji jiki yace "wallahi baxan fita ba idan har kinga na fita daga dakinnan to na samu abinda nazo nema." Ya mike zaune yana tallafe da keyarsa ya cigaba "Hibbah kisani bugamin karfen nan da kikayi shine *babban kuskuren da kika tafka* don kuwa kinsa naji dole na kusanceki kota halin k'ak'a." Dayake Hibbah tana daga bakin kofar dakin cikin tsiwa tace "aniyarka ta bika mugu kawai," murmushin yak'e sale yayi yace "wato kin samu bakin magana koh?" Murguda Mai baki tayi tare da jan tsaki tace "Abu yanxu mene abunyi kindai ji abinda ya fada koh?" Jan hannunta abu tayi suka fito daga dakin, bangaren su Inna lami suka nufa da sauri Hibbah ta kalli Abu tace "me kike shirin yine Abu?.'' Abu bata kalleta ba tace "ke dai ki biyo ni kiga me zanyi," "na biyoki Kamar ya? Ke kinsan halin Inna lami, babu yarda za'ayi mu fada mata wannan matsalar, memakon ta warware mana ita saidai ta kuma hargitsa abun." Tsayawa Hibbah tayi tana kallon Abu tace "allah Abu kije ke kadai nidai bazan jeba." Kallon ta Abu tayi tace "nifa ba fada mata zanyi ba kedai kizo muje" kuma gyara tsayuwa Hibbah tayi tace "wallahi kinji na rantse bazani ba". Jin ta rantse ya kuma tabbatarwa da Abu Hibbah bazata karasa inda take so suje ba. Shi kuwa sale ganin sun fita su biyun yadan ji tsoro karfa su Tara masa jama'a don yasan halin Abu tsaf zata aikata, cikin ransa yace _Anya kuwa bazan hakura da k'uduri na ba? Karfa nazo ayimin duka tunda kowa a kauyen nan yasan halin yarinyar nan_ mikewa yayi yana dafa bango. Su kuwa su Hibbah suna tsaye Abu sai magiya take mata amma ita tace tsoron abinda Inna lami zata mata take. Abu ganin Hibbah na bata musu time kar sale ya gudu yasa cikin ihu da daga murya yarda su Inna lami xasuji ta shiga cewa "wayyo allah kwarto jama'a kwarzo wayyo!" Saida ta fada sau uku ta tabbatar su Baba sunji sannan tayi hanyar waje tana ihun kwarto. Da gudu Hibbah tasha gabanta tana cewa "haba Abu wannan ai tonan asirine, kina so mutanen k'auyen nan Susan abinda ya faru Dani ne?" Kallon ta Abu tayi "to mene idan sun sani, naga dai kowa yasan halinki kuma kowa yasan waye sale, to don sun sani har wani abune?" Ta fada tana kaucewa daga inda Hibbah ta tsaya. Muryar Inna lami sukaji ta tawo da gudu rike da muciya tana cewa "ina kwarton yake?" Kallonta Abu tayi tad'dan nuna yanayin tsoro tare da nuna mata cikin dakin, da gudu Inna ta shiga dakin. Shi kuwa sale jin Abu na ihun kwarto yasa tsoro ya kuma dirar masa cikin tsoro ya xura kayansa ya nufi kofar fita cikin sauri. Kicib'is sukayi da Inna lami tana kokarin shigowa, baya yayi da sauri ya zaro ido waje ganinta da muciya. Murmushi tayi masa tace "ka kwantar da hankalinka na rik'e wannan muciyar ne kawai saboda tsaro, kaima kayi sakaci wai ya akai haka ta farune?" Kallon sale yake tsoro ya bayyana a fuskarsa b'uru b'uru yace "Zan miki bayani daga baya ni dai yanxu matsa na huce kinga yaran cen zasu tara min......." D'aga labulen da akayi ne ya katse masa magana, baba ne ya shigo yana kallonshi cikin tsana. Bayason baba yaga fuskarsa, Cikin zafin nama sale ya hankad'e Inna lami yabi ta gefen baba ya fita da gudu daga dakin, yana fita tsakar gida yaga su Abu da k'awayen su rik'e da sanduna, da wani mugun gudu ya gifta ta kusa dasu don karsu same shi amma duk da haka saida Abu da kharime suka kwad'a masa........... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page1⃣2⃣to1⃣3⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *wannan page d'in naki ne ~sweety~ _SADNAF_ Allah ya kara basira🙏* Cikin dare Hibbah ta farka saboda zazzabin dake nuk'urk'usarta ga kuma ciwon kai, tashi tayi daga kwanciyar datayi ta zauna tare da ruk'unk'ume jiki tana ta rawar dari hakk'oranta suna ta bugar juna. Kuka take yi a hankali Mara sauti. Cikin barci gwaggo taji gunjin kuka yana tashi a hankali, lalubar touch light dinta tayi ta kunna ta haska. Hango Hibbah tayi a zaune ta dukunkune tana kuka k'asa k'asa. Daga gadonta ta sauko ta k'araso kusa da Hibbah tace ''y'ar nan lafiya cikin tsakiyar dare ki tashi kina kuka?" Cikin muryar da bata fita sosai tace "gwaggo sanyi nake ji kaina kamar zai fashe, gwaggo sanyi sanyi nakeji," ta karasa maganar tana kuma k'amk'ame jikinta. Janyota jikinta gwaggo tayi taji yarda jikinta yayi zafi sosai tace "yi hakuri Hibbah bara na kawo miki ruwan raidore Dana tafasa dazu kisha insha allah zaki ji sauki kinji?" Kai kawai ta d'aga Mata. Zame jikinta gwaggo tayi daga na Hibbah a hankali ta tashi ta dauki touch light dinta ta fita tana haskawa, a bakin murhu ta bude wata tukunya ta tsiyayo ruwan a kwano ta rufe tukunyar ta dawo d'aki. Tana shiga d'akin ta k'arasa kusa da Hibbah D'agota tayi ta kafa mata a baki, bismillah ta fara sha, ba laifi tadan sha da yawa ta kauda kai. Gwaggo ganin ta kauda kai bata takurata ba ta ajiye kwanon, tare da maida ta ta kwanta ta rufa mata zanin data rufa dashi tace "kiyi hakuri insha allah yanzu zazzab'in zai sauka," kallon ta Hibbah tayi tace "gwaggo kaina fa?" Sannu gwaggo tayi mata tare da mikewa tace "ina zuwa," bayan kofa ta nufa tadauko ruwan zafi a buta da take ajiyewa ta zuba a roba ta sirka dana sanyi ta kawo gaban Hibbah ta ajiye taje gaban buhun bakkonta ta dauko dankwalin kayanta sabo. Kasancewar ita bata daura dankwalin atampa. Ta rabashi biyu ta karaso kusa da Hibbah ta zauna ta janyo robar ruwan ta tsoma dankwalin a ruwan ta matse ta d'ora a goshin Hibbah ta shiga gogewa a hankali. Haka tayi tayi mata har wajen daya kunbura yad'an koma Hibbah sai raki take mata. Bayan ta gama ta dauko d'ayan d'ankwalin ta daure mata wajen dashi sannan ta kuma kwantar da ita. Gwaggo ta d'auki ruwan robar takai bakin kwata tace da safe zata zubar itama tazo ta kwanta a hankali barci yayi awon gaba dasu. Baba kuwa koda ya koma d'akinsa shiru yayi yana ta tunani yarasa meke masa dad'i kuma ya rasa tunanin me yake yi da haka shima barci ya d'aukesa. B'angaren Inna kuwa koda ta ja Rahmatu tana zuwa cikin dakin ta shiga zakinta ta inda take shiga bata nan take fita ba. Ita kuwa Rahmatu ko a jikinta tace "to amma Inna me yasa wai baki k'aunar Hibbah ne, nifa gaskiya abinda kike yi mata Sam bana jin dad'i kawai dai ina boyewa ne kawai kita wani sata wahala haka kawai?" Inna kallon ta take cike da mamaki wata dabara ce ta fado mata tace "ke wai bakya kishin yarda kowa yake yabonta ke ba'a yabonki kuma baki ga tafiki kyau da farin jini ba ko a wajen k'awayenku?" Shiru Rahmatu tayi can tace "eh wallahi nima fa shiyasa wani lokacin nake ji bana sonta, amma kuma me yasa kikayi mata sharrin nan kika sa baba ya koreta?" Inna tayi murmushi tace "ai duk saboda ke nayi, ke kin damu da *RAYUWA*rta ne bayan ita bata k'aunarki ta tsaneki ke kuma kina nan kina tausayinta," ta karashe da tsaki. Rahmatu tad'an zaro ido waje tace "dama bata sona?" Inna tace "ina zata soki bayan uwarta ta tusa mata tsanarmu shiyasa nayi waje da uwar itama kinga gashi ta tafi, kinga yanxu dana yi haka ai sunanta ya b'aci a gari kinga yanxu kowa zai tsaneta, saboda abin kunyar da tayi sannan ke kuma su dawo sonki" Dariya Rahmatu tasa tare da ihun dad'i tace "Kai amma naji dad'in haka inna Ashe itama bata sona shiyasa d'azu da ina tambayarta meya sameta tayi banza dani, to nima na tsaneta inna." Inna cikin happy tace "yauwa y'ar gari" daga haka suma sukayi bacci. *Dan allah kuyi hakuri da wannan, muna biki ne bansamu time nayi typing dayawa ba.* *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page1⃣0⃣to1⃣1⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Da hanzari baba ya fito daga dakin cikin bacin rai da tsana yake bin Hibbah da mugun kallo, Hibbah ta tsorata da kallon da yake mata. Abu ta matso kusa da ita ta kunce Dan kwalin kanta ta mika mata tana cewa "rufe k'irjin ki da wannan," karb'a Hibbah tayi ta daura shi a k'irjinta. Cigaba baba yayi da binta da mugun kallo yana karasowa kusa da ita hannunsa ya daga ya yarfa mata wani gigitaccen mari, kafin ta dago ya kuma dagota da dayan b'angaren, cikin kakkausar murya yake magana "ni zaki wulak'anta ki batawa suna a gari Eye? Wato kinyo gado koh?" Ya cigaba da dukanta. Inna lami cikin kissa tazo ta shiga gaban baba tana cewa "haba malam kaima kasan barewa bazatayi gudu d'antq yayi rarrafe ba, taga uwarta nayi itama dole tayi." Cikin muryar kuka har tana sarkewa Hibbah take cewa "wallahi baba fyade zai yi min bani na gayyato shi ba, kaga rigata ma ya yaga min saboda naki bashi hadin kai." Abu ce taje gaban baba ta tsugunna tana bashi hakuri "kayi hakuri baba, da gaske ne ba ita ta kawo shi ba shi ya kawo kansa kuma wallahi baba fyade yaso yayi mata." Kallon Abu yayi yace "me kika sani? A gaban ki akayi?" Girgita masa Kai tayi tace "a'a baba ba agabana akayi ba," dauke kansa baba yayi daga gabanta yace "kinga kenan kema baki da tabbacin ba ita ta kawoshi ba, tunda baki da wata sheda daza ta tabbatar min da hakan." Cikin daga murya da b'acin rai ya nuna Hibbah dake gefe a tsugunne tana ta rusa kuka yace " baza ki maida min gida bariki ba ki tattara kayanki ki barmin gida!!" Furucin baba ya tsorata kowa dake wajen, cikin rudu Hibbah ta taso da gudu ta rike kafafun baba tana kuka tace "don allah baba kayi hakuri wallahi bantaba aikata abinda kake zargina dashi ba, fyade zaiyi min baba idan nabar gidan nan ina zani baba babu inda nasani." "Kibi uwarki kema ki shiga duniya!" Muryar inna lami sukaji tana bada amsa. Kallon ta su Abu sukayi, cikin tsana Abu take hurga mata harara ta kalli baba tace "Baba ina da sheda," "mece shedar taki?" Baba ya tambaye ta. Karasawa tayi kusa da Hibbah ta tallafo fuskarta tana nuna goshinta tace "Baba kalli koshinta inda ta yanke," Baba ya kalli goshin nata tare da kawar da kai. Abu ta cigaba"saboda taki bashi hadin kai ne ya buga mata Kai da kofar dakin ta yanke, sannan ga rigarta ma inda ya yaga Mata duk saboda bata bashi abinda yake so ba. Na tabbata Baba da ita ta gayyato shi baza ta bari ya yaga mata sutura koya ji mata ciwo ba. Da kuma shima bazata............" "Malama wannan duk zancen banzane!" Inna lami ta katseta cikin fada. Shiru baba yayi yana nazarin kalaman Abu ya kalli inna lami yace "lami lamarin yarinyar nan fa akwai k'amshin gaskiya," cikin fada Wanda ya zame mata jiki inna lami tace "eh dama dole ka fadi haka kai ga mai 'ya koh? To wallahi ni bazan zauna da mazinaciya fasik'a a cikin gidan nan ba idan ita bazata bar gidan nan ba toni saina tafi," ta fada tana girgita jiki saboda tsabar masifa. Kallonta baba yayi yace "a'a lami wai da a duba lamarin kafin........." "A duba lamari koh? To bari kaga idan na tafi gidan mu Kai saika zauna da mazinaciyar," ta fada tana yin hanyar dakinta. Ita kuwa Hibbah kuma fashewa tayi da kuka tana karanto _inna lillahi wa inna ilaihira ji'un_, su Abu karime da dije ne suka karaso kusa da ita suna lallashinta. Shi kuwa Baba da sauri ya Sha gabanta yace "haba lami ai ko bata aikata komi ba kikace tabar gidannan saita Bari," ya juyo ya k'araso kusa da inda Hibbah take ya nuna ta "ki tashi ki barmin gida tun kafin na b'ab'b'allaki," Hibbah ta kalleshi hawaye na bin fuskarta tace "Baba idan na bar gidan nan ina zani yanxu ga dare, baba baka tsoron wani abu ya cutar dani?" Baba yace "ni dai kawai nace ki barmin gida!" Ya kuma d'aga murya. Rahmatu wadda ta shigo yanxu ta kalli Hibbah yarda take kuka kamar zata shid'e, sai taji ta bata tausayi duk da rashin kunyar Rahmatu tana son 'yar uwarta kawai bata nunawa ne saboda tasan halin Inna. Karasowa tayi kusa da Hibbah tace "Hibbah meya faru? Me kika yiwa baba yace kibar masa gidansa? Mene a goshinki?" Kukane yaci k'arfinta ta kasa magana, daga cen suka jiyo muryar inna lami tana cewa "karuwa ce mazinaciya fasik'a har gida take kawo su, yarda taga uwarta nayi." Zaro ido waje Rahmatu tayi tace "karuwa fa kikace Inna?" "Eh karuwa ce da kwarto aka kamata," inna ta bata amsa. Shiru Rahmatu tayi ta kalli Abu tace "Abu a gabanki akayi?" Da Abu batayi niyyar amsata ba, amma kanin yarda ta damu da Hibbah yasa ta Girgiza kai tace "a'a nazo dai na ganta ta fito da gudu daga dakin a gigice," Rahmatu tace "kinga kwarton?" Hibbah kallon ta takeyi da mamaki saboda Rahmatu bata tab'a nuna damuwarta akan Hibbah ba, ba Hibbah kad'ai ba harsu Abu da inna lami mamaki take basu. Abu ta kalleta tace "eh na ganshi," da sauri Rahmatu tace "waye?" "Sale direba ne," "sale direba?" Rahmatu ta maimaita tana kallon inna wadda yanayinta yad'an sauya tace"Anya inna baki da masaniya akan wannan abun kuwa?" "A gidan uwarki nake da masaniya?" Inna ta fad'a tana yi mata dak'uwa tace "malam yarinyar nan idan fa bazata bar gidannan ba ni Zan tafi" baba yace "kafin na irga uku kibar min gida" Rahmatu da sauri tace "allah baba kayi bincike naga fa inna dazu da sale a kofar gida." Gaba d'aya kowa ya waiga yana kallon Rahmatu, da sauri inna ta k'araso kusa da Rahmatu ta buge mata baki sannan ta fara janta, ciccijewa Rahmatu ta shigayi tana cewa "wallahi sai na fadi gaskiya, baba kayi bincike kafin ka yanke hukunci, da sa hannun inna a cikin wannan abun....." Kuma buge mata baki inna tayi tare da cewa "wallahi malam idan na kuma maimaita Hibbah ta bar gidannnan to ni zan barshi." Jin haka yasa baba da hanzari yazo gaban Hibbah yana masifa "ki tashi ki fita nace koh?" Cikin sark'ewar murya Hibbah tace "baba ka tsaya kayi bincike....." "Bazan yi ba d'in mai bak'in hali ki fita," ya buga mata kafa "baxa ki tashi ba so kike ki kashe min aure?" Ya kuma Kai mata duka. Ganin yana shirin ji mata ciwo yasa su dije da Abu suka d'agata don ta kasa tashi. Dak'ar take takawa har suka je bakin k'ofar fita juyowa tayi ta kalli baba taga ashe shima ita yake kallo, cikin murya mai rauni tace "baba me yasa zaka yankemin hukuncin barin gidanka koda ace lefin da kake zargina dashi na aikata? Baba ka rabani da mahaifiyata mai k'aunata, yanzu kuma ka rabani da gidanka bayan kuma idan na barshi babu inda zani nan d'inne kawai muhallina, me yasa baba kake son kuntata min? Me yasa kake son na rayu cikin kunci da kad'aici? Kafison *RAYUWA*ta ta lalace? Me yasa baba? Me yasa.........." Kukane yaci k'arfinta. Shi kuwa baba jikinshi yayi sanyi bakinshi kuma yayi nauyi ya kasa ce mata ta dawo. Su Abu ne suka jata suka bar gidan a k'ofar gidan Hibbah taja tunga ta tsaya tana kallonsu d'aya bayan d'aya hawaye na sintiri a fuskarta tace "yanxu Abu ina zanje da wannan daren me yasa baba bazaiji tausayina ba?" Abu ta dafa kafadarta tana goge mata hawaye tace "kiyi hakuri Hibbah ba lefin baba bane saboda baya hayyacinsa, yanxu kizo muje wajen gwaggo ( mahaifiyar Aysha, umman Hibbah ) kawai." _gwaggo kaka ce a wajen su Abu da Hibbah, Abu 'yace awajen malam Habu yayan Aysha. Tunda aka kawota yaye bata koma gidansu ba_ Dije tace "tabbas nan ne kawai zakije Hibbah," kallonta Hibbah tayi tace "kuna ganin babu matsala?" Karime tace "haba Hibbah kema kinsan KO kowa ya zargeki gwaggo bazata zargeki ba." Hibbah tace "shikenan nan muje." Kai tsaye gidan gwaggo suka nufa, abakin kofar gidan sukayi sallama dasu karime. Su kuma suka shiga cikin gidan, dakin gwaggo suka nufa lokacin ma har tayi barci Abu ta tasheta. Tashi tayi zaune tana kallon Abu da Hibbah tace "lafiya kika tasheni ina barci? Ke kuma Hibbah me yasa kika biyota baki ganin dare yayi?" Abu tace ina fa lafiya gwaggo? Baba ne ya koreta daga gidan," cikin mamaki gwaggo tace "ya koreta to saboda me?" Nan Abu ta fada mata duk yarda akayi. Tattafa hannu gwaggo ta shigayi tana sallallami tace "ai dama nasan za a rina matar da bata bar mahaifiyarki ba balle ke" Baban su umman su Hibbah ne ya lek'o yana cewa "lafiya ne naji kina sallallami?" Gwaggo tace "ina fa lafiya........." Nan ta shiga labarta masa komi kamar yarda Abu ta fad'a mata. Shi kanshi baba yaji ba dad'i amma sai yace "to ai shikenan sai tayi zamanta anan din tunda bata da inda zata." Yana gama fadin haka ya koma dakinsa. Gwaggo ta kalli Hibbah tace "ki kwantar da hankalinki kiyi zamanki a nan kinji? Kuma karki kuskura ki zargi mahaifinki don bashi da lefi baya hayyacinsa ne, *RAYUWA* ce wata rana sai labari kinji?" daga Mata kai Hibbah tayi tace "insha Allah gwaggo" gwaggo tace "yauwa 'yar albarka allah ya muku albarka" sukace amin. Tashi sukayi suka dauro alwala suka kwanta................ *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page1⃣4⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Washe gari Hibbah bata tashi ba sai wajen k'arfe 9 na safe, bayan tayi sallah asuba data koma abinda bata tab'a yiba kenan barcin safe, shima tayi ne saboda jiya da dare bata samu tayi isasshe ba saboda zazzabin daya rufeta kuma alhamdulillah yanxu ya sauka don garau take jinta. Bud'e ido tayi tare dayin salati tayi addu'a ta kalli gwaggo dake zaune kan sallaya tana jan casbaha tace "ina kwana gwaggo?" D'aga mata kai gwaggo tayi saboda bata magana idan tana lazimi. Tashi tayi ta wanko fuskarta da bakinta tare da d'auro alwalar sallah walha ta koma daki tayi sallah bayan ta idar ta jima tana kaiwa Allah kukanta akan matsalolinta kafin ta shafa. Bayan ta idar inna ta ajiye mata kwanon koko da k'osai ga kuma na d'umame a gefe wai taci wanda take so rabon da Hibbah taci irin wannan cimar har ta manta, kokon da k'osai taci taji harma ta k'oshi. Inna lami kam gari na wayewa ta zari mayafi tayi gidan Inna delu aminiyarta, bayan sun gaisa Inna lami cikin happy tace "uhumm albishirinki aminiyata," itama Inna delu cikin zumud'i tace "Kai muguwa nasan wata muguntar kika shirya tunda har kika kasa jurewa kikazo gidana, to goro bani nasha." Inna lami tace "hmm ai kedar bari, yafa saketa," gud'a delo tasa tace "Kai lami gaskiya kin iya mugunta to ita kuma waccen aljanar 'yar fa?" Lami tayi murmushin mugunta tace "itama a jiyan da daddare uban yace tabar mai gidansa," da zumud'i delu tace"ita kuma me kika yi Mata," shewa lami tayi ta shiga fad'a mata duk abinda ya faru sannan ta d'ora da cewa "shima da uban naga kamar yana jin tausayintaa na fututtuke nace zan bar masa gidansa ba shiri yace ta tafi." Delu ta kalleta tace "gaskiya lami kin fini iya tuggu amma fa kinyi kuskuren korar yarinyar nan daga gidan" cikin alamar tambaya lami tace "kamar ya kuskure bayan itama zata kawo min matsala idan na barta a gidan, saboda idan na barta kinga itama fa tana da gado banda gidan ma ga kuma gonakinsa fa," murmushi delu tayi tace "ai ke baza ki gane ba ai cikin salama zakiyi komi batare da kowa ya zargeki ba". Inna lami tace "kamar ya?" Kuma murmushin mugunta delu tayi tace "ai kawai aikatau zaki turata birni, kinga kin samu riba biyu kenan ga kudin aikinta gashi kuma ta bar miki gida cikin salama," cikin happy inna tace "Kai delu shiyasa fa nake sonki amma kuma yanxu lokaci ya kure ya kenan?" Delu tace "a'a aminiya lokaci bai kureba, yanxu ita Hibbah tana ina?" Cikin nuna rashin damuwa lami tace "ya huce gidan kakarta tana da inda yafi nan ne?" Delu tace "yauwa kinga ya kwana gidan sauki, kawai turawa zakiyi kice tazo nasan tunda yarinyar nan na sonki babu abinda zai hana ta zuwa." Inna lami tace "Kai delu kin yi dabara to yaushe zaki kaita kenan?" "Ai dama in anjima zan shiga garin kano, Zan anso kudin wata yarinya kinsan wata ya kare," delu ta bata amsa. Lami tace "to kuma kudin nasu yana kaiwa nawa?" Delu tace "eh to ya danganta da yanayin gidan da aka kaita da kuma yanayin aikin da take musu," lami tace "Kai amma fa zan cafki kud'i" delu tace "kodai zamu cafka?" Lami bata amsa ta ba tace "yafa kamata mukoma wajen boka don kar fa malam ya kawo min cikas a lamurana, kamar yarda na fada miki jiya ma fa yaso ya kwafsa," delu tace "bakya sanya lami baki da sauk'i da kinga ya fara warewa saiki kuma d'aureshi" dariya inna lami tayi tace "ina fa zanyi sanya, yanzu dai yaushe zamu je?" Delu tace "eh to muje yanxu, bara na k'arasawa Musa d'umamencan sai mu je?." Lami ta d'an yatsina fuska tace"nikam musan nan idan wani yaji yarda kike masa saiya zata shine mijin naki ai," dariya delu tayi tare da cewa "kamar yarda kike yiwa Rahmatu ba," "ai gara ni macece kuma idan nayi mata ma ai koya mata nake," lami ta maidawa delu. Delu tace "oho dai nima koya masa nake yi" ta fada tana mikewa. Bakin murhu ta nufa taje ta sauke tukunyar takai d'akin Musa, sannan ta zaro mayafinta suka nufi gidan boka. Wani daji suka nausa canciki sunma fita daga kauyen *katsalle* sun shiga dajin k'auyen *Gomma* wani dogon dutse naga suna hawa saida suka hayeshi tas, sai kuma suka cire mayafansu da d'an kwalayensu da takalma suka fara tafiya da baya da baya baya har suka k'arasa bakin wata bukka. Zagi suka shiga yi sai ga wani mummunana gardin mutum ya bayyana a zaune a wajen yana dariya yace "halakarku kun zo ku kuma halaka?" Ya k'alk'ale da dariya, lami ce tace "yauwa boka dama........" Katseta yayi da cewa "na sani! kamar yarda aka Saba ga wannan," ya mika lami wani kullika yace "kici gaba da tsarki dashi, wannan a abincinsa wannan kuma turare," ya kwashe da dariya. Karba tayi tana godiya, yace "wannan yarinyar daza ku turata aikatau karku bari ta kuma waiwayar k'auyen nan don idan kika bari ta dawo gida da akwai matsala gagarima. Ku tashi ku tafi na sallame ku." Yana gama fadin haka ya b'ace, kallon kallo suka shigayi kafin su tashi subar wajen, kayansu suka d'auka suka sa sannan suka sauka daga dutsen kowacce da abinda take sakawa musamman ma lami. Bayan sun shiga cikin k'auyensu lami ta kalli delu tace "me kike ganin zamuyi akan abinda boka yace?" Delu tayi shiru kafin tace "mafita d'aya ce kawai idan na kaita gidan nace basai ta rink'a zuwa ganin gida ba zan dinga zuwa ganinta." Lami tace "kina ganin hakan ba matsala" delu tace "babu wata matsala ai nace zan dinga zuwa dubata kuma su gidan gaba ta kaisu." Lami tace "Hmm to shikenan bara na huce gida saikin zo." Delu tace "ai kawai mu shiga ki aika a kirata mu huce don ba lallai na dawo ba," murna fal cikin lami suka shiga cikin gidan. Suna shiga gidan sukaci sa'a Rahmatu na nan, delu tace "shikenan nan ma Rahmatu nanan kinga saita shiga ta kirata koh," kallonta lami tayi tace "toh allah yasa taje kema kinsan halinta." Delu dai batace komi ba suka k'ara cikin gidan. Kujera delu taja ta zauna hakama lami amma ita tata kujerar kusa da Rahmatu ta kaita tare da kwantar da murya tace "yauwa Rahmatu Dan allah shiga gidansu Abu ki kira min Hibbah kice tazo yanxu." Kallon ta Rahmatu tayi a wulak'ance tace "tab ni wallahi na gaji babu ida zani" matsowa lami ta kumayi kusa da ita tace "haba autar inna kije mana don Allah" Rahmatu ta zumburo baki "wai me zakiyi mata ne bakince ta bar gidan ba, kuma kince ta tsaneni to me kikeso kuma tayi mana a gida?" Lami tace "aike baxaki gane ba aikatau za'a kaita birni kinga kenan duk kudin da aka bada na aikinta namu ne daga nan ma saina saimiki wayar da kikace kina so koh?" Daga Kai Rahmatu tayi cikin happy tace "eh wallahi inna ammafa kinyi dabara bara naje" ta fada tana mikewa da gudu tabar gidan. Lami tace "oh ni lami naga Randa Rahmatu zatayi hankali" delu tace "gaskiya kam." *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page1⃣5⃣to1⃣6⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.Z.W.A Su Hibbah suna zaune a tsakar gida suna gyara waken alala ita da Abu da gwaggo, sai gay Rahmatu ta shigo gidan kamar an wurgota ko sallama babu ta kallesu d'aya bayan d'aya, sannan ta maida kallonta ga Hibbah tace "ke zo inna na kiranki," tana gama fadin haka ta juya ta fita abinta. Tsorone ya bayyana k'arara a fuskar Hibbah ta kalli Abu tace "Abu kinji wai Inna naje ni wallahi tsoro nake ji." Abu tace "kuma ke zuwa zakiyi? Kika sani ma ko wani muguntar ta kuma had'a miki kawai zaki kwashi jiki kice zaki," gwaggo tace "ke inna ruwanki kika sani KO uban ne yace ta dawo?" Abu tace "tab, gwaggo kin dai fimu sanin halin matar nan wallahi ko yace ta koma sai tayi yarda tayi tace karya maida ta." Murmushi gwaggo tayi tace "hmmm Ku yara ne bazaku gane ba, ai zata maida tane don ta ci mata gaba da tallanta, ko kuna tunanin wannan mara kunyar 'yar tata Rahmatu zata daukar mata talla?" Hibbah wadda tayi shiru tana sauraronsu tace "wallahi gwaggo nima abinda nayi tunani kenan," ta mike tsaye tare da cewa "bara naje naji gwaggo," "waike yanxu xuwa zaki yi?" Abu tayi saurin katseta, Hibbah cikin damuwa tace "to ina da wani mafita ne banda naje d'in?" Abu ta tab'e baki tace "tab wallahi da nice baza ni ba," gwaggo tace "kinga karki biye mata yi maza kije kiran innarki kinji." Daga kai Hibbah tayi tace "to." Ta fice a gidan. Gidansu ta nufa tana shiga taga inna lami tare da aminiyarta inna delu suna hira harda shewa, wani yawu ta had'i kut, zuciyarta ta fara bugawa tasan tunda taga inna delu a gidan to wata muguntar ta had'a. A hankali ta k'arasa cikin gidan da sallama babu Wanda ya amsa mata saima mugun kallon da innar ta bita dashi tare da cewa "kefa a taki k'aramar k'wak'walwar kinyi tunanin na dawo dake gidan nan ne KO?"ta Saki wata dariya suka tafa da delu ta cigaba"ni Neman kud'i zanyi dake don haka ki tashi kije ki had'o tsummokaranki kizo zaku tafi da delu." Da sauri Hibbah ta d'ago kanta tace "ina inna?" "Gidan ubanki nace gidan ubanki kujimin yarinya da rashin kunya dole sakinji KO ina ne, ki tashi ki hada kayanki nace, kuma wallahi saura idan ankaiki kice zaki zo ganin gida wallahi saina kasheki kinsan halina sarai Zan iya kasheki." Jikin Hibbah na rawa ta tashi ta shiga d'akinsu kayanta tashiga had'awa hawaye na sintiri a fuskarta cikin ranta take tunanin wannan *RAYUWA* tata a raba ka da mafiyarka da mahaifinka yanxu kuma zaa rabaka da danginka da kowa naka akaika can wani waje kayi *RAYUWA* ba tare da kasan kowaba acan. Wani hawayen ya kuma gangaro mata Ta share da bayan hannunta ta karasa had'a kayan nata da basu fi kala biyar ba duk dun kod'e ta k'ulle a d'an kwali ta fito, taje gaban inna ta tsugunna tace "inna na had'a kayan." Inna ta watsa mata harara "kindai ji abinda nace kika kuskura kika dawo k'auyen nan saina kashe ki wallahi tashi ku tafi," hawaye ne yake gangarowa daga idonta tasa hannu tana sharewa amma duk da haka bai daina zuba ba. Rank'washi inna ta Kai mata aka tace "kujimin da munafukar yarinya annamimiya uwarki nayi miki daza ki Sani a gaba kina yimin kuka? Uban me nayi miki? Daza ki daina arhar hawayenki ma daya fi miki don wallahi, kinji na rantse babu Wanda ya isa ya hanani kaiki aikatau birni, shegiya mai bak'in hali." Ta fad'a tana kuma kwad'eta. Kuka ta kuma Saki harda magina ta kalli inna delu wadda sai murmushi take kana gani kasan na mugunta ne tace "meye kike kallona da wad'annan mayun idanun naki mayya kawai, ni tashi dallah mu tafi kina b'ata min lokaci ina da wajen zuwa da yawa." Cikin shashshek'ar kuka Hibbah ta kallesu tace "inna dan Allah kuyi min hakuri ku barni a cikin 'yan uwana da dangina, karku rabani da mahaifata don Allah wallahi bana so.........." Wani wawan mari inna t Kai mata "don ubanki har kina da bakin magana, ki kalli tsabar idona kice wai na barki cikin danginki? Ina kike da dangin? Shegiyar yarinya zatayi min bak'in ciki tun wuri gara ki fidda ran zaki kuma *RAYUWA* cikin danginki har abada!" Sun kuyar dakai Hibbah tayi tana kuka sosai. Inna delu ta mike tace "keh! Tashi mu tafi," ta kalli aminiyar tata tace "to lami zamu huce sai kuma na kawo miki albashin nata kuma duk wani alheri da aka bata a gidan naki ne." Cikin happy lami take washe baki tace "to shikenan sai na jiki allah ya kiyaye hanya, ke kuma" ta nuna Hibbah "kindai ji abinda na fada miki kika kuskura kika dawo k'auyen nan kinji dai furucina tam," mikewa Hibbah tayi tana share hawayen dayake tayi Mata sintiri ta kalli katangar su Abu ta tuno nan ne kad'ai yanxu ya ragemata kuma gashi suma an rabata dasu, Dama a dangin babanta bata san kowa. Abu ta hango tana lek'o gidan, kallonta ta tsayayi kafin ta d'auki k'ullin kayanta tabi bayan inna delu. Har bakin zaure inna lami ta rako su suna shirin fita daga gidan saiga su Abu da gwaggo sun shigo. Gwaggo ta kalli Hibbah tace "ina kuma zaki da kaya haka?" Daga gefe inna lami tace "aikatau zan kaita birni saboda ni na maidata tamkar jari ne, Neman kud'i zata je tayi a dinga aikomin kuma na fad'a mata karta kuskura ta waiwayi k'ayen nan koda wasa eyyeh." Kallonta gwaggo tayi cikin mamaki tace "tabbas Abu maganarki ta tabbata, yanxu lami bakya gudun yarinyar nan ta fad'a mugun hannu ko kuma su gidan a ka kaita su koreta ina zata dosa wata Sani acan? Da zakice karta kuskura ta waiwayi mahaifarta?" Inna lami cikin rashin kula tace "oho ita ta sani ni KO karuwanci zatayi taje tayi nidai kawai ta kawo min kud'i. Ai ita 'yar kishiya jarice baka saurin illata ta nima sai yanxu naga kuskurena na korarta danayi jiya shiyasa nace Rahmatu ta kirata." Harara Abu ta bugawa lami tace "to wallahi babu inda zata saboda ba 'yarki bace shine zakice zaki wani turata aikatau, ai kema kina da 'ya macen ki turata mana." Cikin masifa inna tace "keh Abu ki shiga hankalinki ko wannan kakar taki bata isa ta hanani Kai Hibbah aikatau ba balle wata ke 'yar ciki dallah kauce min da gani." Gwaggo tace "ke Abu babu ruwanki Karna k'ara jin bakiki," ta kalli inna "lami don allah badon ni ba kiyi hakuri karki tura yarinyarnan aikatau, kodan gudun b'acin tarbiyyarta........." "Wallahi Zulai babu Wanda ya isa ya hanani aikata birni," cikin tsantsar masifa lami ta katse gwaggo. Ba Hibbah da Abu ba harta gwaggo tayi mamakin yarda inna ta fadi sunanta kai tsaye batare data sakaya ba. Da mamaki gwaggo tace "lami zulai kai tsaye ba sakayawa?" Da masifa tace "to ba sunanki bane koba sunanki Zulai ba?" Girgiza kai gwaggo tayi tace "lallai lami," Hibbah ce ta k'araso kusa da gwaggo tace "gwaggo kiyi hakuri nasan ni haka tawa k'addarar *RAYUWA*r take na karb'eta hannu bibbiyu, Zan tafi aikatau birni na bar dangina, gwaggo ki kwantar da hankalinki nasan kina tsoron kar tarbiyata ta lalace ne. Insha Allah babu abinda zai canzani kedai kiyi tayi min addu'a nima inanan Zan cigaba dayi." Gwaggo taji dad'in kalaman Hibbah sosai cikin dauriya tace "to shikenan Hibbah allah ya miki albarka," Hibbah tana kallon Abu tace "ameen gwaggo," lami tace "mukuma allah ya tsine mana koh?" Babu Wanda ya kulata, Hibbah tace "Abu zan tafi nasan ni daku mun rabu har abada kiyafe min 'yar uwata kinji." Abu batasan danda hawaye ya zubo Mata ba tace "baki yimin komi ba Hibbah ni ya kamata na nemi yafiyar ki," cikin shashshekar kuka Hibbah tace "nima bakimin komi ba Abu." Suka had'a Kai suna kuka lamarin dayasa gwaggo itama hawaye. Kallonsu inna lami da delu sukayi suka tabe baki delu tace "gaskiya lami lokaci na tafiya fa." Da zafin nama ta fincike Hibbah daga jikin Abu tace"dallah ki huce ku tafi." Haka Hibbah tana ji tana gani suka rabata da y'an uwanta, haka suka rabu da Abu kowacce na zubda k'alla tare da d'agawa juna hannu har suka bacewa idanunsu. Tashar babura sukaje saida suka hau babur ya kaisu tashar *Bunkure* sannan suka nemi motar garin Kano, cikin sa'a kuwa suka samu motar data rage saura mutum uku ta cika. Kwandostan ya nuna musu motar, wajen motar suka k'ara delu ta kalli Hibbah tace "dallah ni shiga muje," Hibbah bata tab'a hawa mota ba shiyasa batasan yarda ake hawa ba. Tsayawa kallon delu tayi tace "aya zan hau?" Wani mugun kallo ta bita dashi tare da bangajeta ta shiga motar. Tsayawa tayi taga yarda ta shiga sannan itama ta shiga duk a tsorace take, wani mutum aka samu shine cikon na ukun. Yana shiga driver yaxo ya tashi motar jin mota ta fara tafiya Hibbah gabonta ya tsananta fad'uwa kuka ya kuma taso mata kanta ta tusa a tsakanin cinyoyinta ta shiga rera kuka marar sauti, batasan sanda barci ya kwashe ta ba............... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page1⃣7⃣to1⃣8⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Sun iso garin kano ta dabo tunbin giwa koda me kazo anfika. A tashar unguwa uku motarsu ta yada zango, mutanan motar suna ta fitowa, delu dake kusa da Hibbah ta kalleta a wulakance cikin daga murya tace "ke! Tashi mu tafi!" Allah sarki Hibbah tana can duniyar bacci bata Masan tana yi ba, ita kuma delu ji take duk salon barin gidan datayi ne yasata yin banza da ita. Cije lebe tayi tare da Sakin wani murmushin mugunta, mayafinta ta yaye ta daidaici tsakiyar bayanta ta buga mata gwaiwar hannunta. Kamar a mafarki taji saukar wannan dukan tasaki wata gigitacciyar k'ara a firgice ta d'ago kanta har hawayen azaba ya fara bin fuskarta, gefenta ta kalla inda delu take tana kallon ta. Ruwan pure water mai sanyi dake hannun delu ta fetsa Mata a fuska tace "dallah malama tashi mu tafi kin wani zauna kina yiwa mutane bacci a waje," delu ta fad'a tana bin Hibbah da mugun kallo. Hibbah bata da bakin magana sai hawayenta data goge tabi bayan delu suka sauka daga motar. Fita sukayi daga tasha suka nufi bakin titi, Hibbah sai kalle kalle take yi garin ya burgeta sosai wani titi data gani a sama motoci nabin takai ne yafi tafiya da hankalinta. Delu ta tarar musu adaidaita ta fada masa ya kaisu unguwar Rijiyar zaki,yace to suka shiga gani tayi sun nufi wannan gadar saman ihu tasa tace "malam Dan allah karka bi damu tanan mutuwa zamuyi." Me a daidaita da dariya ta taso masa yace "yarinya ki kwantar da hankalinki ba mutuwa zakiyi ba yanxu zakiga mun sauka ai hakan ma wani cigaba ne," delu tace " ke ki nutsu kina cikamin kunne, Dan allah kaima malam rabu da wannan yarinyar bata da hankali kasan Dan kauyen mutum", ita Hibbah bata Masan sunayi ba don gaba daya ta gama tsorata ta k'ankame jikinta sosai ta rufe idanunta k'am jikinta sai rawa yake. Mai adaidaitan ne ya juyo ya kalleta yaga yarda ta takure, sai hakan ya kuma Bashi dariya cikin dariyar yace "y'ammata ki Saki jikinki mun huce wajen," ko kulashi batayi ba saima kuma k'ankame jikinta datayi. A kofar wani madaidaicin gida adaidaitan yayi parking jin da tayi adaidaitan ya tsaya shine ta samu damar bud'e idanunta ta fito daga ciki ta tsaya tana ta kallon unguwar, kud'in me adaidaita delu ta bashi sannan tayi gaba Hibbah nabinta a baya. K'ofar gidan suka k'arasa delu tar k'wank'wasa, wani dattijo ne ya lek'o yadan washe baki tare da bud'ewa yace "a'a delu kece tafe da rana haka?" Delu tadan yi murmushi tace "nice wallahi kasan karshen wata yayi," ta kalli Hibbah, Hibbah tace "ina yini?" shima yana 'yar dariya yacer "lafuya lau, eh fa kin kawo wata ba'kuwar kenan?" "Eh wallahi allah yasa hajiyar na nan," delu ta tambaya. "Eh to wacce daga ciki?" "Hajiya Zainab mana" " tana ciki" delu tace "bara mu karasa ciki." Ta fada tana shiga cikin gidan, binta Hibbah tayi tamkar wata jela tana kuma kallon cikin gidan tana mamakin wannan gidan. Fili ne fatal sai wani bangare da aka ware don Adana motoci saida sukayi yar tafiya sannan suka kuma shiga wata k'ofar nan ma da 'yar tazara sai kuma taga k'ofofi guda uku. Ta bangaren daman taga delu ta k'wank'wasa, wata matace ta fito ta bude musu wacce bazata huce sa'ar delunba itama da fara'a tace "delu kece tafe?" Delu tai yake tace "eh wallahi hajiyar dai na nan koh?" Delu ta tambaya, da sauri Hibbah ta ce "ina yini?" Matar ta kalleta tace"lafiya lau," ta kalli delu "Eh tana ciki, amma dai wannan ce wadda kika kawo mata a madadin dije koh? Don jiya ma saida tace na duba Mata anan wajen mu wai tajiki shiru, ashema kina tafe, yarinyar kuwa mai hankali," delu tace "eh wallahi bara mu shiga," Ciki suka shiga nan fa Hibbah ta kuma baza ido tana kalle kalle, parlor ne babba an tsarashi da kujeru na zamani, babu wani tarkace a parlor'n, kayan kallone na zamani sai center carpet din dake shinfid'e a tsakiyar parlor'n da wani table da aka d'ora a kanshi, sai daining area. K'ofofi biyu ne a parlor'n wata 'yar hanya sai kuma bene dake can gefe. Hibbah ta shagala da kallon tsarin gidan sai ji tayi ta yi tuntub'e ta tafi kamar zata hantsila tai saurin ja baya, da rawar jiki ta shiga bashi. Shi kuwa janye kafarsa yayi yana murmushi baice komi ba ya maida hankalinsa ga TV da suke kallo. Mugun kallo delu ta bita dashi tana zama a k'asa tace "wai ke baki da hankali ne? Ace mutun don ya rayu a k'auye sai ya zama marar hankali? Dan allah Faruq kayi hakuri" wanda aka kira da faruq din yace "babu komai baba, dole ai ta nuna bak'unta." Ita dai Hibbah batace komi ba sai sunkuyar dakai da take yi ta zauna itama a rakub'e, sauran yaran dake parlor'n suka gaishe da delu a dak'ile, 'yammata ne su biyu wanda baza su huce sa'annin Hibbah ba sai kuma wani k'aramin yaro dabazai huce shekaru shida ba. Kan Hibbah na k'asa ta shiga gaishe su, 'yammatan suka amsa a dak'ile Faruq ya amsa yana kallonta kafin ya mike yabar parlor'n Wanda yayi daidai da saukowar wata budurwa daga benan parlor'n kana ganinta kasan 'yar uwar Faruq ce da sauran yaran don suna tsananin kama, amma kana ganinta kasan ta girme musu. Wayarta data bari a parlor'n ta d'auka tare da komawa zata hau benan Faruq yace "Aunty Aysha pls dan kira musu momy sun dan jima da zuwa suna jiranta," wadda aka Kira da Aunty Aysha tace "suwa fa?" Don ita batama Lura da su delu ba. Faruq yace "wannan wadda take kawo mata 'yan aiki ce, gata nan a zaune," kallon inda ya nuna mata Aunty Aysha tayi tace "lah baba delu ina yini Ashe zakizo har momy ta fidda rai da zuwanki," ta fad'a tana k'arasowa kusa da su delu, delu tai murmushi tace "lafiya lau Aysha wallahi ina tafe ina momyn taku?" Aunty Aysha tace "tana sama bara na kira miki ita," ta kalli Hibbah tace "wannan ce yarinyar? Kyakykyawa tubarkallah ga kuma hankali" Delu tace "hmm itace ina wani hankali anan daga zuwan mu har ta fara rashin hankali," Aunty Aysha tace "me tayi na ganta nutsatstsiya," "ina nutsuwa anan, daga shigowarmu ta taka Faruq dake zaune." Delu ta fada tana hararar Hibbah. Faruq har yakai k'ofar shiga d'akin su yaji delu na fad'ar ta taka shi, ya waigo yace "Aunty Aysha bata sani bafa," yana gama fad'in haka yayi shigewarsa. Kallon Hibbah aunty Aysha tayi wadda duk ta kuma takurewa tace "ya sunanki?" Hibbah cikin sanyin murya tace "Hibbah!" Aunty Aysha tace "wow nice name dama ana samun irin wannan sunayen a k'auye?" Delu ta tab'e baki tace "uhumm ita dai gashi nan" Aunty Aysha ta kalli goshinta da aka nannad'e da k'yalle tace "me ya sameki a goshi?" Kallonta Hibbah tayi lokaci d'aya taji tana burgeta ganin yarda take ba girman kai, gata da saukin kai tace "yankewa nayi." Tace "ayya allah ya sauwak'e, bara na kira muku momy din." Ta fada tanayin hanyar hawa benan. Su kuwa 'yan matan suna ganin Aunty'n tasu tabar parlor'n d'aya daga cikinsu tace "Saudat kinga matsalar Aunty Aysha koh, ta maida 'yan aikin gidan nan kamar wasu 'yan uwanta." Wadda aka Kira da Saudat tace "ai kedai bari Safiyya ni kaina ina jin haushin wannan abun." A tare suka juya suka watsawa su delu wani mugun kallo suka ja mugun tsaki suka cigaba da kallon su. Karan saukowa sukaji Wanda ya basu tabbacin momy'n suce take saukowa, kyakykyawar macece Fara take saukowa cikin shiga ta alfarma ta k'aso cikin parlor suka gaisa da delu Hibbah ma ta gaisheta. Momy tace "ai da ji nake baza kizo ba har na bawa Hadiza cigiya ta samomin wata," delu cikin girmamawa tace "wallahi hajiya bansami yarinyar da wuri bane," hajiya ta kalli Hibbah tace "to Allah yasa ba irin halinsu d'aya da dije ba, dan banji dad'in aikin dije ba Sam." Delu ta kuma duk'ar da kai cikin girmamawa tace "ba halinsu d'aya bama insha Allah, kuma ita wannan na kawota ne zatayi zama dindindin anan, don ko ganin gida ma baza ta dinga zuwa ba." Da mamaki akan fuskar momy tace "to saboda me delu?" Delu ta k'ak'aro murmushi tace "ai haka iyayen nata suka ce," momy tace"to Allah ya taya mu rik'o kenan sai aurene zai rabamu da ita." Delu tana yak'e tace "ai kuwa." K'walawa Hadiza kira momy tayi, saiga wannan Matar data bud'e musu kofa nan ta shigo da hanzari ta durkusa a gaban momy tace "gani hajiya," momy ta kalli Hibbah tace "Hadiza gatanan ki kaita d'akin ku, sannan ki nunnuna mata aikinta."Hadiza cikin girmamawa tace "to hajiya" ta kalli Hibbah tace "taso muje" mikewa Hibbah tayi tabi bayanta. Wata 'yar hanya sukabi ta parlor'n suka b'ulla wani dan fili daga gefe kuma d'akine, Hadiza na gaba Hibbah na binta a baya suka shiga ta nuna mata inda zatasa kayanta, suka fito suka nufi kitchen dama Hadiza girki take nan Hibbah ta shiga taimaka mata da yanke yanke. Su delu kuwa sun dan taba hira kafin delu ta tashi zata tafi aka Kira Mata Hibbah sukayi sallama ta huce............ *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page1⃣9⃣to2⃣0⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Komawa kitchen d'in tayi suka k'arasa girkin, bayan sun gama Hadiza ta zuba a kula tace Hibbah ta d'auka sukai parlor. D'auka tayi suka shiga parlor'n lokacin ma babu kowa a parlor'n, tsayawa tayi Hadiza tayi gaba ita kuma tabita a baya dinning area suka nufa Hadiza ta jere kayan akai tacewa Hibbah"ki rik'a lura da abubuwan da nakeyi don wannan duk aikin kine," Hibbah ta d'aga kai tare da cewa to. Haka suka k'are jera abincin akan dinning suka koma kitchen suka d'auki nasu Wanda Hadiza ta ware musu, d'akin da hadiza tace nasune suka koma Hadiza ta zuba musu sukaci tare. Hibbah sai taji matar ta burgeta yarda take janta a jiki ba kyara bare hantara, Hibbah tayi shiru tana tunani da tana k'auyensu da yanzu ta dawo daga islamiyya inna ta d'ora mata tallah, sai kuma ta tuna ashefa ta bar gidansu tana gidan gwaggo. Tana can duniyar tunani ta tsinci muryar Hadiza cikin d'aga murya tana cewa "Hibbah! Wai me yake damunki ne? Tunanin me kikeyi?" Numfashi Hibbah ta sauke tace "ba komai baba," Hadiza ta kalleta tace "a'a Hibbah da akwai wani abu, kinga fa abincin da kike ci kin dena, kin tafi tunani fa kuma hawaye a fuskarki ko dai kewa gida kike yi?" Da sauri Hibbah ta d'aga kai, Hadiza tace "ai sai hakuri a hankali ma zakiga kin saba da nan d'in musamman ma kika rik'e dokokin hajiya zaki zauna da ita lafiya don hajiya bata da wata matsala, sai dai yaranta wannan 'yammatan su biyu sune masu matsala, suma idan kika bi duk abinda suka ce miki suma baki da matsala dasu." Hibbah ta girgiza kai cike da gamsuwa tace "to baba na gode, amma menene dokokin hajiya da 'ya'yan nata?" Hadiza tace "gaskiya hajiya macece mai son tsafta bata son k'azanta ko kadan, sannan tana son mutum mai gaskiya da rik'on amana, tak'i jinin rashin kunya tana son taga kana mutuntata da yaranta, idan kikayi haka sai kiga hajiya na sonki wata k'ilama tasa ki a makaranta kamar yadda tayiwa dije gata tasa ta a makaranta ta d'auketa tamkar 'yar cikinta daga baya dije tazo tana yi Mata d'auke d'auke, har yakaita da d'aukar sarkar hajiya ta gold." Zaro ido waje Hibbah tayi tace "sata?" Hadiza tace "wallahi kuwa, shiyasa ma hajiya ta koreta," Hibbah ta girgiza kai tana mamakin wannan lamari can tace "insha allah zanbi duk dokokin hajiya kuma Zan kula da dukkan ayyukana." Hadiza tace "Allah yasa," "ameen" Hibbah ta fad'a tana mikewa ta d'auke plate d'in dasukaci abinci takai kitchen tare da wanko hannunta, Tana shigowa d'akin Hadiza tace "kizo kiyi wanka ki canza wad'an nan kayan, sannan wannan kanma ki wankeshi kizo nayi miki kitso na gaya miki hajiya fa bata son k'azanta," Hibbah tace "to" a zuciyarta kuwa cewa tayi baba Hadiza bakisan *RAYUWA*r danayi bane shiyasa kike ganin k'azantata, towel Hadiza ta d'auko mata sabo tace "ga wannan dashi zaki rika wanka" Hibbah ta amsa tare daa godiya. Kayanta ta shiga cirewa ta d'aura towel d'in da Hadiza ta bata ta shiga band'akin, tsayawa tayi kallon band'akin ya tsaru kamar ka kwanta, ta gama k'arewa toilet d'in kallo itadai bata ga ta inda ruwa zai fito ba sai wata 'yar tukunya data gani Fara da ruwa a kwance a wajen kuma wannan bata ga ta inda mutun zai tari ruwa ba. Hakan yasa kawai ta juya ta fita daga toilet d'in, ta nufi kitchen ta Kira Hadiza ta nuna mata yadda zata yi. Hanyar kitchen d'in ta nufa cikibis sukayi da Faruq ta sunkuyar da kanta tare da matsa masa ya huce ji tayu shiru mutum bai huce ba hakan yasa ta d'ago kanta don ganin me ya tsayayi. Gani tayi ya sha'afa yana kallon ta, kallon idanun sa tayi sannan ta kalli jikinta gani tayi Ashe kirjinta ya k'urawa ido yana kallo. Sai a lokacin ta tuna ashefa towel ne a jikinta kuma shima tsayinsa bai huce iya gwaiwarta ba da sauri ta juya zata koma d'akinsu, shima Faruq cikin sauri ya janyo hannunta ta fad'a jikinsa wata gigitacciyar k'ara ta saki wanda hakan yayi sanadiyyar fitowar Hadiza da sauri daga kitchen tayo dakin nasu inda anan ne taji k'arar. Aunty Aysha ma da take parlor a zaune tajiyo k'arar itama cikin sauri tayo wajen. Tsayawa Aunty Aysha da Hadiza kukayi suna mamakin yadda Faruq ya rukunkume Hibbah suna kokawa, yana kokarin zare towel d'in dake jikinta. Kasa jurewa Aunty Aysha tayi ta buga masa wata muguwar tsawa, da sauri Faruq ya cika Hibbah, Hibbah wadda hawaye kebin fuskarta da sauri tayi d'akinsu. Aunty Aysha ta karasa kusa dashi ta yarfa masa Mari tace "Faruq baka da hankali ne daga kawo yarinya zaka nuna mata halinka, da kake kiciniyar k'wace mata towel din jikinta fyade kakeson yi mata kome? Tambayarka nake ka bani amsa." Hadiza data ke gefe tace "kiyi hakuri Aysha ki daina d'aga murya kar hajiya taji," "ai gara taji baba hadiza " tana gama fad'in haka tabi bayan Hibbah. Aunty Aysha na shiga taga hango Hibbah acan k'arshen katifar dake d'akin ta kifa Kai da gwaiwa tana ta rera kuka, k'arasawa kusa da ita Aunty Aysha tayi ta zauna a kusa da inda take tare da d'ago kanta tace "kiyi hakuri Hibbah don Allah," Hibbah cikin kuka tace "Aunty Aysha ki daina bani hakuri don allah ni nasani ahaka zan k'are *RAYUWA*ta, ko wanne namiji burinshi kawai yaga ya yaga min rigar mutunci....." Ta kuma sakin kuka Aunty Aysha tana lallashinta tare da bata hakuri. Hadiza ce itama ta shigo ta zauna a gefen katifar tace "haba Hibbah mai yasa zaki fita da wannan d'an towel d'in a jikin ki?" D'ago kanta Hibbah tayi tace "wallahi baba Hadiza banyi hakan da niyya ba ni shaf nama manta da abinda ke jikina nafito na tambayeki yarda ake kunna famfo d'in band'akin bansan yarda ake kunnawa ba." Hadiza ta kalleta yarinyar ta bata tausayi tace "kiyi hakuri Hibbah wannan ma tsautsayi ne kinji?" Aunty Aysha tace "ba wani tsautsayi baba hadiza, tun yaushe yake wannan halin? Ni wallahi nayi tunanin Faruq yabar wannan halin tuntuni ashe be daina ba. Kiyi hakuri Hibbah yanxu zanje na fad'awa momy komi don yaga yanxu daddy baya zama shiyasa kenan ya cigaba da halinsa." Murmushin takaici Hibbah ta k'ak'alo tace "babu komi fa baba Hadiza Ku daina bani hakuri, aini haka tawa k'addarae take kuma na karbeta hannu bibbiyu, kuma don allah aunty Aysha karki fad'awa kowa" ta mik'e tare da cewa "Dan baba Hadiza kunna min famfon bansan ya ake kunnawa ba." Hadiza ta mike tare da cewa "to", tare suka shiga ta nuna mata yarda zata kunna sannan ta fito, koda ta fito ma ba zama tayi a d'akin ba ta fita tabar Aunty Aysha ita kad'ai a d'akin tana tunanin furucin Hibbah. Tana nan zaune Hibbah ta fito daga wanka ta wanke kanta, gashin duk ya barbaxu a fuskarta ruwa sai d'uga yakeyi. Kallon Aunty Aysha tayi tace "au Aunty Aysha kina nan har yanzu?" Murmushi Aunty Aysha tayi tace "ina nan Hibbah akwai abinda nake so na tambaye ki ne," Hibbah ta kalleta da d'an mamaki a fuskarta tace "wace irin tambaya zakiyi min Aunty Aysha?" "So nake don allah ki bani tarihinki, kuma don allah karki boyemin komi," shiru Hibbah tayi ta ta tsaya da shafa man datake yi. Aunty Aysha tace "kiyi hakuri Hibbah kiyi wani furucine Dana kasa fassara shi shiyasa nake bukatar jin labarinki," hawayene ya fara kwaranya a fuskarta tace "haba aunty Aysha wai me yasa kike bani hakuri? A k'asanki fa nake zan baki tarihina yanxu." Nan ta shiga karanta mata labarinta. Aunty Aysha ta tausayawa Hibbah ta kalleta da hawaye a fuskarta tace "Hibbah insha Allah daga yau kinbar kuncin *RAYUWA*, kuma ba wani namiji dazai keta miki haddi na kyaleshi koda kuwa Faruq d'in ne wallahi sainayi Shari'a dashi. Kema yanxu kinzama 'yantacciya don na d'aukeki tamkar su Safiyya" Hibbah taji dad'in kalaman Aunty Aysha cikin happy ta rumgume ta tana godiya, Aunty Aysha tace "ke 'yar uwata ce Hibbah munzama jini d'aya ni dake" cikata Hibbah tayi tana murmushi, Aunty Aysha tace "tashi kisa kayanki." Mikewa Hibbah tayi ta jawo k'ullin kayanta ta d'auko wata kod'add'iyar atampa zatasa Aunty Aysha tace "baki da wasu kayan ne Hibbah wannan ai sun lalace," kasa Hibbah tayi da kai tace "Aunty Aysha duk cikin kayana wannan ne masu kyau." Tashi aunty Aysha tayi tace "jirani ina zuwa." Sama Aunty Aysha ta hau ta nufi d'akinta ta d'auko wasu kaya dasukayi mata kad'an ta had'a zata bayar, ta dawo d'akin su Hibbah ta bata tare da cewa "gwada su mu gani," wani baby pink material ta bata ta gwada ai kuwa sai gashi skirt d'in yayi mata rigar take k'okarin sawa Aunty Aysha tace "Hibbah ina bra kuma a haka zakisa rigar?" Rufe fuska Hibbah tayi tace "bani fa da ita Aunty." Dariya Aunty Aysha tasa ta kuma fit............. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page2⃣1⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* D'akinta ta kuma komawa ta d'auko mata bra ta Nuna mata yarda zatayi amfani dashi sannan ta bata waje ta saka, tana fita Hibbah tasa kayan saiga Hibbah ta dawo kamar ba ita ba. Tana gama saka kayan ta taje gashinta da kum d'in kan dressing mirror ta cureshi waje d'aya kamar yadda ta Saba ta daura d'ankwalin kayan ta tsaya a gaban dressing mirror tana k'arewa kanta kallo gani take kamar ba ita bace. Ita kuwa Aunty Aysha tana fita ta nufi bedroom d'in momy, da sallama ta shiga, momy ta amsa mata zama tayi kusa da momy tayi shiru ta rasa ta inda zata Fara, littafin da momy take karantawa momy'n ta ajiye ta kalli 'yar tata tace "Aysha fad'a min me kike so?" Da d'an mamaki Aunty Aysha tace "momy ya akai kika gano abinda ke tafe dani?" Murmushi mommy tayi tace "haba Aysha nifa uwace hak'k'i nane na fahimci duk wata matsalarku, kuma dukkannin ku idan kuna cikin matsala ina ganewa don haka meke damunki fadamin pls ina sauraron ki," kasa Aunty Aysha tayi da kanta tace "momy dama wata alfarma nakeso na rok'a a wajenki dan Allah," kallonta mommy tayi na fahimta tace "wace irin alfarma kenan Aysha?" Shiru Aunty Aysha tayi nad'an dak'ik'u kafin tace "momy akan wannan yarinyar Hibbah da aka kawo miki aiki yau," "to me kike so ayi mata?" Momy ta tambaya, Aunty tace "momy Dan allah so nake kisata a school both boko da islamiyya, na tausayawa yarinyar momy ta taso cikin k'iyayyar kishiyar uwa da kuma ta uba, ta rabata da uwarta yanzu mafa ita ta turota aikatau kuma ta gargad'e ta karta sake ta koma k'auyensu," momy cikin mamaki tace "kamar ya bangane ta rabata da mahaifiyarta ba, kince kuma ta taso da k'iyayyar mahaifinta, kiyimin bayani yadda zan fahimta" nan aunty ta fara bata labarin Hibbah kamar yadda Hibbah ta fad'a mata sannan ta d'ora da cewa "wallahi mommy yarinyar ta bani taudayi sosai, na tausayawa *RAYUWA*RTA shiyasa ma na d'aukarwa kaina alkawari kula da ita, najiyar da ita dadin *RAYUWA* koda ta hanyar bata ilimine momy pls ki taimaka min, ki bani k'arfin gwuiwa," momy tayi shiru tana jinjina hali irin na wasu matan komene ribarsu don sun sa uba ya tsani 'yarsa daya haifa? Mene amfanin ma bin bokaye da 'yan tsibbu? Ta kalli Aysha tace "bake kad'ai ba Aysha nima Zan bada gudun mawa wajen ceto yarinyar nan," d'ago Kai aunty tayi cikin happy ta kalli momy tace "da gaske momy?" D'aga mata Kai momy tayi itama tana murmushi. Aunty tace "na gode momy sosai allah ya k'ara girma da tsawon rai mai amfani," momy taji dad'in addu'arta tace "amin Aysha, in anjima idan malam Jamil yazo ki turata wajensa itama ya dinga yi mata lesson d'in kuma yaji izunta nawa, sannan bangaren boko kice masa ya Fara Mata daga faro," momy ta d'auko purse d'inta ta zaro dubu biyar ta mikawa Aunty Aysha tace "ga wannan idan yaxo ki Bashi kud'in nan yayi Mata komi harda uniform zai kawo mata, ita kuma makarantar bokon kinga yanxu suna hutu kuma kinga idan sun komai zasu shiga third term ne sannan kuma Hibbah tayi girma da primary, za'a barta har wannan term din ya k'are yana yi Mata lesson idan anshiga new session sai musan abinyi." Aunty Aysha shiru tayi tana mamakin momy bata tab'a tunanin haka ba batasan sanda rumgume momy ba tana ta zuba Mata addu'a mommy tace "abin alkhari be yin hakan Aysha, sannan ita delu tunda muguwace baza mu Nuna Mata muna kula da Hibbah, sannan zansa Hadiza ta samo min wata mai aikin tunda ita Hibbah karatu bazai barta tayi aikin ba inyaso ita ko da daddare ko a weekend ne idan aikin ya taso sai ta dinga yi." momy ta tashi daga kan gadon ta bud'e wardrobe ta d'auko wasu kaya daba'a d'inka ba atampa ce guda hud'u, leshi uku, materials kala biyar sai wasu abayoyi masu shegen kyau guda biyu ta ajiye a gaban Aunty tace "gashi ki kaiwa tailor'n Ku ya d'inka mata," ta kuma zaro wasu kud'in ta bata tace " ga wannan kisiya mata inner wears da kuma 'yan kayan kwalliya, da turaruka." Aunty Aysha cikin mamakin yawan kayan tace "momy dama kina da kayan daba'a d'inka ba ajiyayyu haka?" Momy tayi murmushi tace "a'a Aysha last week ne da hajiya Rukayya ta kawo min sune, ni kuma da kunya nace bazan amsa ba shine na amsa da ajiye," d'aga Kai aunty tayi alamar gamsuwa, nan aunty Aysha ta kuma yiwa momy godiya ta kwashi kayan ta sauko k'asa dakin su Hibbah Sam bata fad'awa momy abinda Faruq yayi ba. Aunty Aysha ta shigo da kaya nik'i nik'i ta k'araso kusa da Hibbah ta zube kayan hannuta a kan katifa, ta juyo da Hibbah suna fuskantar juna tace "kai Hibbah kinyi kyau masha allah," hunnu biyu Hibbah tasa tan rufe fuska dashi tace "Kai Aunty na gode," aunty taja hannunta suka zauna a bakin katifa ta kalli Hibbah tace "albirishinrinki," Hibbah tana murmushi tace "goro Aunty." Aunty tayi murmushi tace "na fad'awa momy komai game da *RAYUWA*rki, tatausaya miki kuma tace zata taimakamiki," Hibbah cikin tsantsar happy tace "da gaske Aunty? Amma gaskiya na gode na gode Aunty allah ya k'ara girma da d'aukaka" Aunty tace "amin" ta zaro kudin da momy ta bata tareda janyo kayan tace "Hibbah wannan kud'in momy ta bayar tace a yi miki komai na makarantar islamiyya, akwai Wanda yake yiwa su Saudat lesson kema zaki dinga zuwa yanayi dake, makarantar boko kuma sai wata shekarar zaa kaiki, wannan kuma tace a siyo miki kaya kwalliya." Farin ciki ya hana Hibbah magana wai yau itace ta samu wannan gata har ta samu 'yancin yin karatu, katse mata tunani Aunty tayi da cewa "wannan kayan kuma badawa tayi tace a d'inka mikinsu," Hibbah cikin tsantsar happy ta shiga godiya sosai tacewa Aunty" don allah Aunty rakani wajen momy nayi mata godiya," aunty tace "to tashi muje," Hibbah ta mike suka bar d'akin. Saman suka hau nan Hibbah ta kuma ganin abubuwa iri iri sunje tayiwa momy godiya, mommy ta nuna Mata ai babu komi ita dai fatansu Hibbah tarik'esu da amana kamar yadda suma zasu rik'eta cikin aminci. Hibbah taji dad'in kalaman momy nan ta kuma yiwa momy godiya suka sauko. Da suka dawo Hadiza na d'akin Hibbah cikin happy ta nuna mata kayan da aka bata, Hadiza tayi ta yaba kyahun kayan. Aunty ta kalli Hibbah tace "taso muje ki rakani wajen tailor mu kai masa kayan" Hibbah tace to tare da mik'ewa ta d'auko hijjab d'in data zo dashi zata sa Aunty tace "haba Hibbah karki badani mana kinyi kwalli kuma zaki d'auki wannan hijjab d'in kisa, bara na d'auko miki mayafi a kayana kisa taso muje d'akina." Binta tayi kamar jela suka kuma komawa sama, wannan karan d'akin Aunty'n suka nufa direct wardrobe d'inta Auntyn ta nufa ta d'auko mata mayafi fari da wani ta kalmi me dan tudu shima fari tace "gwada wannan mugani zaiyi miki," sawa Hibbah tayi sai gashi yayi mata amma kuma yad'an yi mata yawa, Aunty tayi dariya tace "tab Hibbah kin fini karamar k'afa." Dariya Hibbah tayi tace "ai kuwa dai gashi ammafa kamar yayi min tsayi Anya zan iya tafiya dashi?" aunty tace "gwada tafiya dashi muga" Hibbah tad'an fara tafiya dashi ad'an tsorace, aunty ta kwashe da dariya tace "ki saki jikinki kiyi tafiya," a hankali take takawa dashi tana zagaye d'akin har ta d'an saba idan kaga yadda take tafiyar sai ka rantse yanga takeyi. Aunty ce ta ja hannunta suka karasa gaban gadonta, tana cewa "zo na gyara miki wannan d'aurin d'ankwalin ba haka ake d'aurawa ba," kunce mata d'aurin tayi taga ta cure gashinta girgiza kai Aunty tayi ta dauko kum da man kitso ta shafe mata kan dashi ta taje ta d'auko ribbon tayi mata packing gashin sannan tayi mata d'auri mai kyau ta shafa mata powder da lipstick ta bata kwalli tasa, dana kalli Hibbah saida na kuma kallon ta don wani mugun kyau danaga tayi Masha Allah ashe komai nason gyara. Aunty ta kalleta tace "Hibbah kin ganki kuwa yadda kikayi kyau Masha Allah kamar baki tab'a *RAYUWA* a k'auye ba," ta fada tana dariya. Murmushi Hibbah tayi na jin dad'i tace "Auntyna bani da bakin yi miki godiya na gode Allah ya saka da alkhari na gode," hannu Aunty ta d'ora akan lips d'inta tace "shiiit bana son yawan godiya Hibbah, tashi muje yamma nayi," da haka suka fita sukayiwa momy da Hadiza sallama gidan saiya zama shiru ba kowa dayake su Safiyya duk sun tafi islamiyya, suka fito daga gidan Adamu driver Aunty tayiwa magana ya fito da mota suka wuce. A mota Aunty take tambayar Hibbah tace "Hibbah a k'auye izunki nawa?" Hibbah tace "izzuna goma sha bakwai," d'an zaro ido Aunty tayi tace "dama k'auye karatunsu yana sauri haka?" Girgiza kai Hibbah tayi tace"ba'a makaranta kawai muke karatu ba ummana ce take yi min k'arin karatu idan ta biya min yau gobe zan kawo mata hadda," Aunty ta girgiza Kai alamar gamsuwa tace "kenan duka bakwai d'in yana kanki yanzu," d'aga kai Hibbah tayi alamar eh. Bangaren Faruq kuwa yana komawa d'aki ya fad'a gado takaici da mamaki duk ya rufeshi ya soma tambayar kansa wai me yake damuna me na gani a jikin yarinyar nan da har na kasa jurewa na kasa saita kaina, juyi ya kumayi yace yarinyar dabaza ta huce sa'ar Saudat ko Safiyya ba at least baza tafi 13 or 14 years ba amma duk nabi na rud'e a kanta bayan ga manyan babies nan a gari dasuke kawo min Kansu ba wadda na rud'e akanta sai wannan 'yar yarinyar, murmushin mugunta yayi yace kin janyowa kanki Hibbah don kota halink'ak'a saina d'and'ani wannan dirin naki kafin na koma hutu tunda kikasa har Aunty Aysha ta gane halina na nan. Janyo pillow yayi ya rumgume siffar Hibbah na kuma tariyo masa cikin kwanyarsa, yace yarinya k'arama amma ta had'a abubuwan da wasu manyan babies din ma basu dashi duk da cewa yanxu suka fara tasawa abubuwan nata, amma tana da diri mai kyau da d'aukar hankali, ya tuno yadda ya ganta d'aure da towel sai ya kuma matse pillow gam a jikinsa, haka yayi ta tunaninta har dare ba mafita daya rufe idanunsa ita yake gani ga wata muguwar kasala da sha'awar kasan cewa da mace data saukar masa kasa jurewa yayi, ya tashi ya shiga toilet ya sakarwa kansa ruwa na wani lokaci kafin ya fito ya tsala wanka cikin k'anan kaya ya feshe jikinsa da turaruka masu kamshi ya zari key din motarshi ya nufi club. Su kuwa su Hibbah sunje sun kaiwa tailor d'inkunan yace nanda kwana biyar zai kawo, daganan Aunty tace zasu wuce super market zasuyi siyayya, wani babban shop na kayan mata suka shiga Aunty ta yiwa Hibbah siyayya ta had'a da kud'in hannunta duk tayo mata siyayya haka suka d'auko hanyar gida da kaya nik'i nik'i. Suna shigowa gida ana kiraye kirayen sallah don haka kai tsaye Aunty tabi Hibbah bangarensu suka ajiye kayan anan ma sukayi sallah sannan Aunty ta shiga nuna mata yadda zatayi amfani da komi har pad tace mata wannan idan kina al'ada shi zaki dinga amfani dashi ta nuna mata yadda ake sakawa. Sai bayan isha'i malam Jamil yazo bayan sun gaisa dasu momy ya tashi ya nufi d'akin da suke karatun a ciki, su Saudat suka mike kowa ya d'auki kayan karatunsa suka bi bayansa dayake hadda sukeyi a wajensa suna zuwa suka shiga Bashi hadda. Aunty tazo tayi kiran Hibbah suka tafi d'akin, bayan sun gaisa da malam Aunty tayi masa bayanin komai yace "ba matsala Aysha insha allah za'ayi yadda kikace kuma gobe in allah ya kaimu su tafi tare dasu Safiyya makarantar sai ayi mata komai zan karbi sunanta yanzu", Aunty tayi masa godiya ta koma ciki. Su Saudat sai harararta suke yi suna jin haushin yayar tasu wai akan me zata dinga had'a su da 'yar aiki. Malam Jamil ya kalli Hibbah yace "mene sunanki?" Hibbah tace "sunana *Hibbah Mukhtar Muhammed*" malam ya girgiza Kai alamar gamsuwa yace "izufinki nawa?" "Izufina sha bakwai" Hibbah ta Bashi amsa yace "hadda kikayi ko kuma biye?" Hibbah tace "hadda nayi," malam ya kalleta yace "zaki iya karanto min naji?" Kai ta d'aga, ya kalli Safiyya da take shirin fara Bashi haddarta yace "kiyi mana hakuri Safiyya bara ta biyamin naji," Safiyya tace "to malam" ya kalli Hibbah yace "bismillah" nan Hibbah ta shiga biya masa har ta gama yayi mamakin karatunta yarda take da tajwidi take fidda kowane hukunci ya jinjina mata, ya kuma yi mata k'arin karatu, saida ya tambaye ta shafi take so ko rabin shafi tace yadai biya mata kawai shafi d'aya ya biya mata, saida yaji ta iya sannan ya k'arbi haddar Safiyy........... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page2⃣2⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Idan kaji ana a marmatsa giwa ce ta iso, gaba dai gaba dai uwar gayya karo da karo sai rago waye zai bada tauranshi _AYSHA ALIYU GARKUWA_ ke kad'ai kike baki da sa'a.* *D*a haka malam Jamil ya gama biya musu karatu ya tafi. Hibbah tana zuwa d'akinsu tayi ta bibiyar karatun batayi bacci ba sai da ta tabbatar ta haddace sannan ta samu tayi bacci mai dad'i cike da mafarkin ummanta, tunda take bata tab'a yin barci akan abu mai taushi ba kamar nayau don katifar tana da taushi. Ta Saba k'arfe hud'u da rabi take tashi, haka yauma ta tashi, ta d'auro alwala tazo ta rik'a jero nafilfili tana godiya ga allah bisa wannan ni'ima dayayi mata. Kiran sallah assalatu ne ya d'agata daga wajen ta tada sallar asuba, bayan ta idar ta tashi Hadiza tayi itama sallah bayan ta idar ta zauna tana jan carbi, ita kuwa Hibbah karatunta ta bibiya sannanta d'ora da azkar na safiya dayake ta haddace su. Sai gari ya fara haskr suka fito da Hadiza ta nunnuna mata inda zata share bayan tagama shara ta nuna mata yadda ake mopping da goge kayan kallo, ita kuma ta shiga kitchen don had'a breakfast. Bayan ta gama gyara ko ina ta koma nasu d'akin ta gyara ta wanke toilet, Hadiza ta bata turaren wuta tace tasa a parlor kafin su tashi ta gyara musu can saman, Hibbah ta amsa tasa tuni parlor ya d'auki k'amshi. Kasan cewar yau weekend ne da wuri yaran gidan ke tafiya islamiyya don k'arfe takwas na safe suke tafiya, hakan yasa bayan sun gama breakfast suka shirya zasu tafi. Hibbah tasan tare zasu tafi don haka tayi wanka da wuri ta shirya, powder ta shafa tasa kwalli kamar yadda taga jiya aunty tayi mata, bata da hijjab d'in sakawa, ta d'auko nata tasa ta fito tayiwa Hadiza sallama. A parlor taga aunty Aysha dayake yau sunday bata da lectures, a zaune tana kallo, taje tace "aunty barka da safiya kin tashi lpy?" Murmushi aunty tayi tace "lafiya lau Hibbah ya kwanan bakunta?"murmushi Hibbah tayi tare dacewa lpy aunty" gani tayi aunty tad'an harareta tace "kinyi kyau amma kin bata kwalliyarki da wannan hijjab d'in, cireshi kizo muje sama na baki wani," tana gama fad'in haka taja hannun Hibbah suka hau sama Hibbah na binta a baya, Saida suka Fara zuwa ta gaishe da momy sannan aunty ta bata wani Hibbah Mai hannu tasa yayi mata mugun kyau, sannan ta sauko suka tafi. Safiyya tayi gaba tace "nifa wallahi bazan jera da 'yar k'auyen nan ba haka kurin ajina ya zube," Saudat tace "ai kuwa adai yanayin dressing d'in datayi babu Wanda zaice Mata 'yar k'auye, kuma ni wallahi ma k'awance zamu kulla da ita naga tana ja," kamar wadda aka zabura Safiyya tace "ke dawa zaku kulla k'awancen?" Saudat tayi dariya tace "da Hibbah mana" tsaki Safiyya ta buga tare dayin gaba abinta. Su Hibbah kuwa suka jero da Saudat, Hibbah ta rikee Hisham suna tafiya Saudat tana ta janta da hira har suka isa makarantar. Anyiwa Hibbah komai kuma an kaita ajinsu Saudat, ta Fara d'aukar darasi. Haka *RAYUWA*r Hibbah ta cigaba a gidan su Auntyn tata cikin kulawar Auntyn ta, mommy da kuma Hadiza. Sosai take jin dad'in zama a gidan, malam Jamil ma ya Fara koya Mata karatun boko kuma yaga kwazonta don idan ya biya mata nan da nan k'wak'walwarta take d'auka, makarantar islamiyyar tasu malamai nata yabon k'wazonta. Yau saura kwana biyar Faruq ya koma school, kuma yau ya kama ranar Friday, gidan ya kasance babu kowa sai Hadiza da Hibbah. Wannan al'ada ce tar 'yan gidan duk ranar Friday suke tafiya family house nasu dake zoo road, tun safe suke tafiya basa dawowa sai dare, Aunty Aysha kuwa bata zuwa sai yamma saboda yanayin karatunta. Da misalin k'arfe hud'u na yamma bayan sallar la'asar kenan Hibbah da Hadiza sun shiga kitchen zasu fara had'a dinner dayake tare sukeyin komai na girki kuma alhamdulillah Hibbah tana k'ok'ari wajen ganin ta fahimci komai, Faruq ne ya shigo fuska a tsuke sai wani muzurai yake kamar gaske ya kalli Hibbah wanda tunda ya shigo jikinta ya Fara kyarma, yayi mata duban wulakanci yace "keh!!" Da sauri ta kalleshi a tsorace tayi tsuru tsuru, ya cillo mata key d'in d'akinshi yace "kije ki gyaramin d'aki," abinda ya fada kenan ya juya yayi ficewarsa. Hibbah ta kalli Hadiza tace "wallahi baba Hadiza Faruq tsoro yake bani shiyasa mafa banason fitowa parlor saboda kar mu had'u dashi, sau tari ina jiyo dariyarsa dasu Saudat amma nake k'in fita gashi yanxu kuma ya Sani wai gyaran d'akinshi." Dafa kafardarta Hadiza tayi tace "Hibbah Faruq d'in da kika Sani da Bashi bane yanxu, Faruq ya sauya ko lokacin da abin nan ma ya faru tsautsayine kawai don tuni Faruq ya sauya halinshi tun sanda Alhaji yayi masa fad'a ya nuna masa bacin ransa, don haka ki kwantar da hankalinki kije kiyi aikin daya Saki." D'aga Kai Hibbah tayi tare da fita daga kitchen d'in ta nufi d'akin Faruq d'in badon ranta yaso ba. Tana zuwa ta bud'e d'akin tare da shiga kallon d'akin tayi babu wani datti, tsarin d'akin ya burgeta babu wani tarkace, ta d'aga kanta hotunansa ne iri iri duk a kafe a jikin bangon d'akin, wasu ya rik'e ball a hannunsa wani kuma yayi tsalle kamar zai kamo ball d'in wani kuma ya k'ame da alama ma suna taken Nigeria ne aka d'aukeshi a hoton, a zuciyarta tace "kenan Ya Faruq d'an k'wallone," yayi kyau sosai kaminninsa da momy sun kuma fitowa, don duk 'ya'yan momy kamansu d'aya da ita babu Wanda ya d'auko kamanin daddy duk da bata tab'a ganin daddy'n nasu ba. Ta shiga toilet d'insa, ta fara dirza saidata wankeshi tas sannan ta saka air freshener ta turo toilet d'in sannan ta dawo d'akin. Blanket d'in kan gadon ta shiga linkewa ta ajiye gefe ta gyare gadon, sannan ta share d'akin tas ta fito da sharar ta debo ruwan mopping tayi ta goge masa wardrobe, tana cikin gogewa Faruq yaH shigo tare dasawa d'akin key ya zare key d'in ya zura a aljihun jeans d'insa, kallonsa tayi ta d'auke kanta duk da zuciyarta na cike da zoranshi, ya k'araso kusa da ita yana d'an murmushin mugunta yana jifanta da wani irin kallo. Batasan yazo dap da ita ba sai numfashinsa data ji daf da ita, da sauri ta d'ago kanta tana kallonshi kanne mata ido d'aya yayi, baya ta fara yi yana binta ji tayi ta zo bango, ta kalleshi idonta ya circuko da k'walla baki na rawa tace "Ya Faruq kayiwa Allah da manzonsa ka k'yaleni don allah," sai kuma ta saki kuka. Dariya ya saki saida yayi mai isarsa har ta fara zargin anya Faruq yana cikin hayyacinsa kuwa irin wannan dariya haka, sai kuma ya tamke fuska kamar Bashi ba ya nunata "Hibbah kinsani abinda bantab'a yiba wato tunanin 'ya mace, na Saba duk yarinyar datayi min kuma naji inada sha'awarta direct nake zuwa na biya buk'ata ta. Amma ke kin hargitsa min shiri tundana Saki a idona zuciya ta ta kwad'ata da wannan durin naki," cikin kuka Hibbah tace "wai mene a jikina me nake dashi da maza suke son b'ata min *RAYUWA*?" Faruq ya Saki dariya yace "ashe muna da yawa bani kad'ai bane, idan su sun k'yale wannan durin ni bazan k'yaleshi ba wallahi yau ko ana muzuru ana shawo saina d'and'ani wannan durin," bata Ankara ba ya fincikota tare da buga kanta da bangon d'akin k'ara ta saki ya wurgata kan gadon. K'arar data saki yayi dai dai da shigowar Aunty parlor zabura tayi cikin sauri tayi d'akinsu Hibbah bata ganta ba sai Hadiza kawai ta gani, a hargitse take kallon Hadiza tace "baba Hadiza ina Hibbah?" Hadiza bata kawo komai cikin ranta ba tace "Faruq yasa ta gyran d'akinsa tana d'akin.........." Kallon mamaki aunty tayi mata tace "Faruq?" D'aga mata kai Hadiza tayi. Aunty cikin tashin hankali tace "baba kina me har yasa ta aiki bayan kinsan k'udirinsa a kanta?" Hadiza itama da yanayin damuwa tace "wallahi Aysha gani nayi ya gyaru yanxu ya........" Aunty bata ma tsaya sauraronta ba ta fice daga d'akin. Shi kuwa Faruq bayan ya wurgata kan gadon binta yayi tare da hawa kanta yayi mata rumfa yana kiciniyar fidda rigar jikinta. Duk da cewa Hibbah kanta ya bugu amma hakan bai gusar da hankalinta ba, don tare suke kiciniya dashi hawaye nabin fuskarta. Ihu takeyi tana kiran sunan Hadiza da Aunty Aysha suzo su ceceta, Faruq yasa hannunsa ya toshe mata baki da hanci kamar zai mata k'amshin mutuwa cikin sa'a ya zuge zip din rigarta, ita kuwa Hibbah ganin yana k'ok'arin kasheta ba shiri ta sakar masa kanta, tasa hannunta akan nasa tana k'ok'arin cire hannusa daga bak'inta cikin sa'a k'aramin d'an yatsanshi ya shiga bakinta ita kuwa ta gantsara masa mugun cizo, cika mata bakin yayi yana yarfe hannu. Yunk'urin tureshi ta Fara yi, shi kuwa kamar cingam sai kuma manne mata yakeyi, tuttureshi takeyi tana kuka mai sauti tana kiran ummanta, mari ya shiga zuba mata ta ko ina, Aunty tana fita tayi d'akin Faruq tana zuwa taji ansawa d'akin key, da gudu tayi hanyar stairs direct d'akin momy ta shiga ta nufi wata k'aramar wardrobe inda momy take ajiye spare keys ta janyota ta dudduba babu su babu alamarsu, hankalinta ya kuma tashi ta janyo ta biyun suma basa nan, ata ukun ne ta gani cikin azama ta kwasosu duka. Da gudu ta sauko daga stairs a matattakala ta k'arshe wani key ya fad'i, ta kalli k'asan bata ganshi ba kawai tayi gaba tana zuwa jikin k'ofar taga Hadiza itama duk ta rud'e, suna jiyo ihun Hibbah tana kiran sunansu dana ummanta tazo ta taimaketa, jikinta har b'ari yake ta shiga gwada keys d'in, hankalinta ne ya kuma tashi jin Hibbah ta saki wata gigitacciyar k'ara gashi kuma gaba d'aya keys d'in sunk'i yiwa d'akin. Allah ne ya bawa Hibbah sa'a ta hankad'e Faruq daga kanta ya fad'i k'asa tayi hanyar fita da gudu ya fizgota ta fad'o kansa, stool d'in dake kusa dashi ya dinga buga kanta dashi har saida yaga ta fita hayyacinta sannan ya d'auketa yayin gado da ita. Ya zubeta shikuma ya shiga cire kayan jikinsa, har wani b'ari yake duk ya k'osa ya kusanceta. Parlor Aunty da hadiza suka koma suka shiga duba k'ark'ashin stairs ko zasuga key d'in amma shiru kakeji gashi hankalin Aunty duk ya tashi, Hadiza ce ta hangoshi k'ark'ashin kujera hannu ta zura ta d'auko tace "Aysha ga mukullin nan," da sauri aunty ta waiwayo tare da amsa tayi d'akin Faruq tana zuwa tasa key d'in kuwa ya bud'................. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page2⃣3⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Masu cewa kirarin dana yiwa AYSHA ALI GARKUWA yayi yawa, to kuyi hakuri ba laifina bane k'aunace tasa na fad'a da babbar murya AYSHA ALI GARKUWA GAGARA BADAU CE BABU KAMARTA.* *A*unty tana bud'e k'ofar ta danno kai cikin d'akin abin da ta gani ya d'aga mata hankali, Faruq ne akan ruwan cikin Hibbah daga shi sai trouser ita kuwa ya cire mata Riga bra ce kawai a jikinta sai skirt d'inta dake manne a k'ugunta, kukan kura aunty tayi cikin b'acin rai ta hankad'e shi ya fad'i k'asa. Ta d'ago Hibbah a gigice take kiran sunanta amma Hibbah ko motsi batayi, hankalin aunty ya kuma tashi ta kalli Hadiza dake tsaye gefe tana kallonsu duk jikinta yayi sanyi bata tab'a kawo Faruq da wata manufa yasa Hibbah ta gyara masa d'aki ba, Aunty tace "baba Hadiza dan allah bani ruwa yarinyar nan suma tayi," gaban fridge d'in Faruq ta daje ta bud'e tare da d'auko gorar ruwan faro ta bud'e ta mik'awa Aunty. Da azama Aunty ta amsa ta tsiyayo a hannunta ta shafawa Hibbah a fuska, wata sanyayyar ajiyar zuciya Hibbah tayi tare da bud'e idanunta a hankali karaf ta zubesu ana Faruq, wata zabura tayi cikin rud'u ta mik'e zaune tana k'ok'arin sauka daga gadon, rik'ota aunty tayi tana Mata sannu. Bata saurari Auntyn ba sai cigaba da k'ok'arin kwace kanta da takeyi tana nuna mata Faruq cikin muryar data sha kuka har ta fara dashewa tace "Aunty Dan Allah ki taimakeni, Faruq kasheni zaiyi wallahi Faruq Bashi da tausayi," ta tusa kanta a tsakanin cinyoyinta ta cigaba da kuka, murmushi Faruq yayi Wanda kana gani kasan na mugunta ne donshi ko damuwa baiyi ba towel ma ya d'auko tare da d'aurashi a k'ugunsa yana shirin shiga wanka, Aunty ta sauko daga gadon cikin tsananin b'acin rai take yi masa wani mugun kallo ta k'arasa kusa dashi tare da fizgoshi yayi baya ta shiga marinsa da Kai masa duka ta ko ina, cikin zafin nama ya rik'e hannunta b'acin rai kwance a fuskarsa yake bin Aunty da kallo, itama Auntyn kallon fuskarsa take abinda ta hango a cikin idanunsa ne yad'an sa zuciyarta tad'anyi rawa, da wata murya yake magana"Aunty Aysha kin tsaneni kin takurani bakya k'aunar kiga farin cikina ko kad'an, me nayi miki kika tsaneni? Gashi yanzu lokaci d'aya kin har gitsamin shirina kin fifita bare 'yar aikitau a kaina" cikin bacin rai yake maganar. Fizge hannunta Aunty tayi itama cikin zafin rai tace "ban tsaneka ba Faruq halinka na tsana, amma tunda kace na tsane ka to na tsane ka d'in, kuma ina kaunar Hibbah a zuciyata fiye dakai bakayi k'arya ba na fifita Hibbah fiye da Kai saboda ta fika halaye kyawawa, kuma wallahi kaji na rantse sai na fad'awa momy duk abinda ka aikata," murmushi yayi ya d'aga kafad'a yace "I don't care kuma ki rubuta ki ajiye wallahi saina kusanci wannan yarijyar kota halin k'ak'a," yana gama fad'in haka yayi hanyar shiga toilet, aunty tace "to mugu mai bak'ar zuciya yanzuma kazo ka aikata k'udirinka akanta ta Allah ba taka ba, ya d'aga kafada alamar ku ta shafa ya shige toilet. Shiru aunty tayi kafin ta kalli Hadiza tace "baba Hadiza pls kamamin ita mu fita da ita bata da karfin takawa," Hadiza tace to" tare da k'arasowa suka kama Hibbah suka fita da ita, tana rik'e da kanta inda Faruq ya buga Mata har ya fashe jini na d'isa d'is d'is. A parlor aunty ta d'auki mayafinta ta kalli Hadiza tace "bara na kaita asibiti ayi mata treatment kinga jini na zuba," Hadiza tace "eh gaskiya nima Bari na d'auko mayafina mu tafi tare," girgiza Kai Aunty tayi tace "a'a baba ki barshi, kije ki k'arasa aikin ki kinga yamma nayi bara muje mu biyo sai mun dawo," aunty ta fad'a suna fita daga parlor'n,Hadiza ta rakasu tare da binsu da addu'a. Suna fita Aunty ta yiwa Adamu driver magana yazo ya kaisu asibiti, jiki na rawa Adamu ya fito da motar suka nufi asibiti, direct asibitin da suke zuwa suka nufa suna zuwa doctor yayi mata treatment d'in wajen ya basu magunguna sukayi godiya suka tawo. A hanyarsu ta dawowa momy ta kira wayar Aunty take tambayar ta har yanzu bata zoba, aunty tace "wallahi momy da akwai matsala ne a gidan shiyasa banzo ba yanzu ma muna kan hanya mun dawo daga asibiti," cikin d'an hargitsi momy tace "matsala? Wace irin matsala Aysha? Waye ba lafiya?" Aunty ta kalli Hibbah dake gefenta tace "wallahi momy Hibbah ce ta samu rauni a goshinta amma da sauki ma" "a garin yaya Aysha?" Momy tayi tambayar cikin nuna damuwa. Aunty tace "ki kwantar da hankalinki momy ba wani ciwo bane, magana a waya bazai ba," momy tace "to shikenan allah ya bata lafiya, muma da anyi sallah zamu tawo" aunty tace "allah ya dawo daku lafiya," momy tace "ameen" tare da kashe wayar. Ta kalli Hibbah tace "sannu kinji Hibbah, babu abinda ya isa yayi miki Wanda Allah bai miki shiba, zan fad'awa momy da daddy duk abinda yakeyi nasan sai daddy yad'au k'wak'wk'waran mataki akansa," juyowa Hibbah tayi suna fuskantar juna tace "Aunty dan allah karki fad'awa kowa wannan abun, mu musilmi ne kuma ko wane bawa akwai k'addarar da Allah yake jarrabtarsa da ita, nasan ni wannan itace k'addarar da Allah ya d'oramin ta *RAYUWA*, ni na yarda da ita. Aunty a sharad'an imani yarda da k'addara yana ciki kuma imanin musilmi bazai tab'a cika ba har sai ya yarda da k'addara mai kyau ko mara kyau, don haka na yarda da wannan a matsayin k'addarar *RAYUWA* ta." Aunty ta kalleta k'aunarta na dad'a shiga ranta yarinya ta bata tausayi tace "Hibbah nasani wannan k'addara ce amma ki sani bafa a kanki Faruq ya fara wannan abin ba, Faruq har night club yake zuwa saida yaga daddy ya bud'e masa wuta sanan ya daina ashe ba dainawa yayi ba don kafin Ya Faheem ya tafi saida ya fad'a min bai daina ba amma nak'i yarda ashe kuwa bai daina ba d'in," Hibbah tace "Aunty waye kuma Ya Faheem?" Aunty tayi murmushi tace "baki sanshi ba Hibbah shine babban yayanmu, kafin kizo da sati d'aya ya koma abroad zaiyi wani cause yana da aure matarsa d'aya Kausar da yaronsa Nawaz anayin arba'in d'in Nawaz ne ma suka tafi." Girgiza kai Hibbah tayi tace "Dan allah karki fad'awa kowa Aunty" aunty tace "to naji bazan fad'awa kowa ba amma in one condition," Hibbah yanxu tana d'an fahimtar turanci ba laifi shiyasa ta fuskanci me Auntyn ta fad'a, Hibbah tayi murmushin jindad'i tace "to mene sharad'in?" Aunty ta kalleta tace "kiyi min alk'awarin zaki kwantar da hankalinki baza kisawa kanki damuwa ba," Hibbah tace "don wannan to nayi miki Aunty," "yauwa Hibbah na ammafa zan fad'awa momy saboda kinga na Fara fad'a mata ta waya," Aunty ta fad'a tana kallon Hibbah. Hibbah tad'an had'e rai tace "a'a aunty itama banaso taji pls," girgiza Mata Kai aunty tayi tace "Hibbah kina so nayiwa momy k'arya?" Girgiza kai Hibbah tayi tare da cewa "a'a Aunty" Aunty tayi murmushi tace "to indai ba so kike muyiwa momy k'arya ba to mu fad'a mata." Hibbah ta d'an turo baki tace "to a fad'awa momy amma dan allah kice mata itama karta fad'awa kowa har daddy." Aunty tayi murmushi tace "to shikenan babu wanda zaiji." Hibbah cikin jin dad'i tace "yauwa Auntyna na gode," aunty ta d'an harareta tace "na fad'a miki bansan yawan godiya ko," rik'e bakinta Hibbah tayi tace "to na daina, amma Aunty inason na tambaye ki," aunty tace "you are free ina sauraronki," Hibbah tad'an muskuta tace "uhmmmm Aunty kiyi hakuri da tambayar da zanyi," aunty ta kalleta sosai tace "kiyi tambayar ki Hibbah matambayi baya b'ata" shiru Hibbah tayi tana jin nauyi tambayar tana kuma ganin kamar ta zak'e da yawa idan tayi tambayar tace "Aunty shikenan ma kawai ba sainayi tambayar ba," harararta Aunty tayi tace "ai kuwa baki isaba saikin fad'amin, fad'i ina sauraronki," kallon aunty tayi taga ta b'ata rai sai taji bataji dad'i ba tayi k'asa da kanta tace "Aunty wai momy tana da abokiyar zama ne?" Aunty taji tambayar a wani iri ta kalli Hibbah sosai tace "me kika gani Hibbah?" Kuma sunkuyar da Kai Hibbah tayi tace "kiyi hakuri aunty idan maganata ta b'ata miki rai, naga gidan ku babba ne kuma b'angare uku ne a gidan." Dariya aunty ta d'anyi tace "baki b'ata min ba Hibbah, kuma bara na fahimtar dake, wannan b'angarorin da kika gani kowanne dame shi, kinga da bangaren mu dana Abba da kuma na hajiya kaka. Haka daddy yayi tsarin ginin, daya gama kuma hajiya kaka tace ita baza ta zauna ba shine ya bawa Ya Faheem part d'inta, shi kuma b'angaren Abba sai yazo kano yake zama a ciki da iyalansa a Abuja yake aiki," Hibbah ta girgiza Kai alamar gamsuwa, a ranta tace ko waye Abba d'in? Aunty ta kalleta tana dariya tace "bara ma fad'a miki waye Abba don nasan zaki iya tambaya, Abba abokin daddy ne sosai tare suka taso tun suna yara, iyayensu ma aminan junane hakan yasa wasu suke tunanin ko 'yan uwane, amincin dake tsakanin su ne yasa suka zama tamkar tagwaye, d'aya baya tab'ayin abu saida d'an uwansa, sannan matar Abba ma k'anwar daddyn mu, Kausar ma matar Ya Faheem ma 'yar Abba ce, Abba yana da yara biyar Ya Haisam shine babba sa'an ya Faheem ne, sai Kausar wadda sa'a tace, sai Usman, Mubarak sai autar su Janan, yanxu kin fahimta?" Hibba ta d'aga Kai. Da haka suka k'ara gida suna ta hirarsu kamar babu abinda ya Faru. Da daddare bayan su momy sun dawo lokacin ma har sun gabatar da dinner d'insu, momy ta Kira Aunty bedroom d'inta take tambayarta mene ya faru a gidan, aunty bata boye mata komai ba ta fad'a mata tun sanda Hibbah tazo gidan har kawo yanzu abinda ke faruwa tsakaninta da Faruq. Momy ta girgiza k'warai dajin k'udirin Faruq akan Hibbah, wayarta ta zaro ta shiga dialing number Faruq saida ta kusan katsewa ya d'auka yana karawa kunnansa yaji momy tace "kazo sama ina son ganika," ta kashe wayar. Yasan aunty ta fad'awa momy komai shiyasa ko d'ar baijiba. Saman ya hayo ya nufi bedroom d'in momy ya shiga da sallama ya samu waje ya zauna, momy cikin fad'a ta fara magana"yanxu Faruq abinda kayi ka kyauta kenan dama baka canza halinkaba?" Nan momy ta shiga yi masa fad'a sosai ta inda take shiga ba tanan take fita ba, sai da ta wanke shi tas sannan ta Fara yi masa nasiha mai ratsa jiki saida ta tabbar nasihar ta ratsasu sannan ta sallame shi, babu Wanda yayi tunanin Faruq zai kuma magana saboda yadda ya nutsu. Yana tashi yace "ai dama nasan gidan nan babu mai sona daddy ne kawai da Ya Faheem ke sona suma yanxu gashi basa nan, k'iris ake jira nayi laifi to gobema zan koma hutu kuma yasin na tafi sai kun ganni don bazan kuma dawowa ba saina gama," ya fita yana 'yar mita momy tace "allah ya shiry............ *# JUMMA'AT MUBARAK TO YOU ALL😍* *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page2⃣4⃣ *NA* *Mamyn Najmah* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Gagara tarkon mahassada AYSHA ALI GARKUWA ki shige gaba muna binki abaya sawun giwa ya take na rak'umi farin gani farar aniya dashe daga rabba idan zaki yai kuka baza a tsaya ba, Allah ya barmu tare cikin so da k'aunar juna🤝😍* Washe gari da sassafe Faruq ya had'a kayansa ya huce Abuja gidan Abba wai acan zai k'arasa hutunsa, sai bayan ya sauka ya huta ma sannan wajen k'arfe d'aya na Rana ya Kira momy yake fad'a mata yana Abuja, daya fad'awa momy tad'anyi mamakin wannan tafiyar tashi babu sallama amma daga baya sai ta rakashi da addu'a da fatan samun nasara. Washe gari Hadiza ta kawowa momy sabbin 'yan aiki mata biyu, saidai su ba kwana zasu dinga yi ba suna gama aikinsu da dare yayi zasu tafi, momy taji dad'in zuwan 'yan aikin nan ba kamar ma aunty don ita bata so taga Hibbah na aikatau shiyasa tayi murna sosai da zuwan 'yan aikin. Kwanci tashi babu wuya a wajen ubangiji yau gashi har Hibbah tayi wata bakwai a gidan su Auntyn ta, wanda tayi *RAYUWA* a cikinsa mai tsafta da ganin gata tamkar itama 'yar gida ce, babu wanda zai kalli Hibbah yanzu yace itace Hibbah 'yar k'auye, don ta waye sosai jikinta yayi kyau fatarta ta kuma laushi sai sheki take, gashinta ya kuma samun gyara yayi kyau. Ita dai babu abinda zata cewa Auntyn ta da momy sai godiya da fatan alkhari dan duk sanadinsu ta samu wannan gatan, bata da wata matsala yanzu ta *RAYUWA* tasamu gatan da bata samu a wajen iyayenta ba ga ilimi na addini Dana zamani, bata tab'a tunanin zata samu wannan ilimin ba sai gashi ta sanadiyyar aikatau da aka kawota birni yanzu she can speak english for more than 5mnts. Yau ya kama ranar Monday kuma ayau ne d'alibai suka koma makaranta ciki kuwa har dasu Saudat bayan hutu da sukayi na k'arshen zangon karatu, yanzu sun shiga new session a ranar ne za'a kai Hibbah makaranta. Da wuri Hibbah ta shirya saboda tasan da yau za'a kaita makarantar boko shiyasa taketa zumud'i har Saudat na tsokanarta wai indai school d'insu ne da k'afarta zata gudu dan idan suka taxi tun safe baza su dawo ba sai shidana yamma", ita dai Hibbah saidai tayi murmushi a ranta tace kaida ka samu gata da dama har zakayi karatu ina kake da k'afar guduwa saidai kayi fatan allah ya shige maka gaba. Bayan su Saudat sun tafi aunty ta shirya da kanta zata rakata don ansai mata file anyi mata komi, dayake makarantar islamiyyarsu ce kuma basu da nisa a bakin layinsu take da k'afa ma suke tafiya. Bayan sunje makarantar Aunty suka gaisa da malaman direct office d'in principal suka huce bayan ta gaishe shi ta fad'a masa Hibbah itace sabuwar d'alibar dama da aka kawo, sannan ta buk'aci sannin class d'in daya bata, yace "ai bata da takardun primary bamuga sakamakonta ba, JS 1 kawai zamu kaita," nan aunty ta shiga Neman alfarma a kaita SS 1 ajinsu Safiyya, principal yak'i yarda, dake abune na kud'in tana cikashi da su dak'ar principal ya yarda za a kakta JS 3, nan akayi mata komi suka bata uniforms Kala Kala, aunty ta kalleta cikin kulawa tace "Hibbah nasan kinada k'ok'ari da hazak'a pls karki bani kunya, ki mai da hankali akan duk abinda ake koya miki babu ruwanki da k'awaye karatu kikazo yi kuma shi zakiyi, ki kula da kanki Hibbah makarantar nan makaranta ce da take cud'anya da maza kuma 'ya'yan masu kud'i zasu iya rud'arki da abubuwa da dama don haka ki kiyaye, duk da nasan Hibbah na bamai kwad'ayi bace tana jin magana," Hibbah taji dad'in kalaman aunty sosai tace "insha allah aunty zan kiyaye kuma bazan watsa miki k'asa a ido ba, zan maida hankali sosai kan abinda ya kawoni, ke uwa ce a gurina ya zamemin dole nayi miki biyayya," Aunty ma furucin Hibbah yasata farinciki, ta janyo Hibbah ta rumgume ta da d'an wani lokaci kafin suyi sallama aunty ta tafi don itama tana d lectures. Principal da kanshi ya kai Hibbah class lokacin da suka je da malami acikin class d'in dan saida malamin ya dakata principal ya gabatarwa da students ita as a new comer, ya mik'a amanarta a hannun class rep mace kuma yayi mata mazauni a kusa da class rep din. Ta maida hankalinta ga malamin suka cika cigaba da d'aukar darasi, sai bayan ya fita class rep d'in ta mik'awa Hibbah hannu cikin harshen turanci tace "barkanki da zuwa bak'uwar mu ni sunana Fauziyya Usman Aliyu zaki iya kirana da fauzy," ita ma Hibbah ta mik'a mata hunn cikin harshen turanci tace "naji dad'in had'uwa dake ni kuma sunana Hibbah Mukhtar Muhammad, fatan zaki rik'e ni amana kamar yadda nima Zan rik'e ki" fauzy ta girgiza kai tace "sunanki na da dad'i kuma zan rik'e amana insha allah," Hibbah tace "na gode kema sunanki yayi dad'i," da haka sukayi ta hira sauran students suka zo suna yi Mata sannu da zuwa da haka wani malamin ya shigo. Haka Hibbah ta cigaba da zuwa makaranta tana fahimtar abubuwan da ake koya mata, Wanda ya shige mata duhu bata fahimta ba takan tambayi malamai ko fauzy, idan a gida ne kuma sai ta tambayi Auntyn ta idan bata nan ta tambayi Saudat bata tambayar Safiyya saboda babu fuskar tambayar. A haka har su Hibbah suka k'are zango karatu na farko tare da fito da result d'in data bawa kowa mamaki, ta d'auki 5th position a class. Aunty tayi murna sosai da result d'in hakan ya kuma bawa Hibbah k'arfin gwaiwa tare da d'aura d'amarar cigaba da farantawa Auntyn tata, satinsu d'aya dayin hutu Abba ya turo a ka d'auki su Safiyya, gidan sai ya koma shiru gashi Hadiza itama ta tafi ganin gida, sai gidan ya zama daga Hibbah sai momy sai kuma 'yan aiki shiyasa Sam Hibbah bata jin dad'in gidan sai dai idan aunty ta dawo. Ganin yarda Hibbah take takura yasa Aunty ta nemi shawarar momy akan sukai Hibbah gidan kawunta inda ummanta take tayi hutu a can. Ranar asabar da daddare Aunty suna zaune da Hibbah a d'akinta, dayake Hibbah ta koma d'akin Auntyn tun sanda Hadiza ta tafi ganin gida, aunty ta kalli Hibbah tace "Hibbah ni kuwa akwai wata shawara da muka yanke ni da momy ban Sani ba ko zaki bamu had'in Kai," Hibbah da take duba wani littafin makarantarta ta kalli Aunty tace " Aunty bani da bakin yin jayayya daku duk abinda kukayi a kaina dai dai ne, nasan bazaku tab'ayin abinda zai cuceni ba," aunty taji dad'in furucin Hibbah tace "Hibbah kalamanki da sanin ya kamatanki sune suke kuma dasa k'aunarki a zuciya ta, dama shawarar da muka yanke da momy cewa mukayi tunda gidan nan ya zama ba kowa sai ke kad'ai kuma kema bajin dad'in zaman kike yi ba, shine nace ko zamu kaiki gidan kawunki can wajen ummanki ki k'arasa hutun a can." Da sauri Hibbah ta d'ago kanta tana kallon Aunty sai kuma ga hawaye tace "aunty ina tsoron zuwa wallahi nasan halin inna lami zata iya kasheni, dan allah ki barni a nan d'in," Aunty ta janyota jikinta tace "ki kwantar da hankalinki Hibbah ai Umma da inna lami kince min ba k'auyensu d'aya ba kuma mu iya kacinmu k'auyen da Umma take kawai zamuje," Hibbah ta goge hawayenta "aunty na gode allah ya k'ara d'aukaka, ni dama inna lami nake jin tsoro amma nima inason naga ummana," aunty tayi dariya tace "Hibbah na kin cika tsoro da yawa, ki shirya gobe da safe zamuje don bani da lectures goben," Hibbah ta kuma ruk'unk'ume Auntyn tace "na gode Auntyna allah ya k'ara d'aukaka ya barki da Uncle d'ina," ta fad'a tana tusa kanta jikin Auntyn nata wai kunya taji. Auntyn tayi murmushi tace "ameen Hibbah, tashi mu had'a kayan tafiya." Mik'ewa sukayi suka shiga had'a kayan. Washe gari k'arfe tara na safe suka d'auki hanyar Bunkure cike da tsaraba, Hibbah tana nunnunawa driver hanya har suka isa gidan, driver yayi parking a k'ofar gidan suka fito. Da sallama suka shiga inna (babar Abu) tana iza wuta a bakin murhu ta k'araso kusa dasu tana yi musu sannun, ta shinfid'a musu tabarma suka zauna ta d'ebo musu ruwa Aunty tana gaisheta ita sam bata gane Hibbah ba saida ta gaida ta da taji muryarta sannan ta ganeta ido ta zuba mata tare da rik'e hab'a cikin mamaki tace "Hibbah kece haka? Ai ni Sam bangane ki ba lallai birni ta karb'eki kinga yarda kika koma tubarakallah kinyi kyau," Hibbah ta rufe fuskarta da mayafinta, ita kuwa Aunty murmushi tayi, inna ta d'ora da cewa "ai a wajen malam (mahaifin Abu) nake jin wai lami ta turaki birni aikatau kuma ta horeki karki kuskura kizo ganin gida, bayan sharrin da tayiwa Aysha kema tayi miko saida ta rabaki da 'yan uwanki, Kai wannan Mata allah ya rabamu da sharrinta." Aunty tace "Amen, inna dama munzo wajen ummanta ne na kawota zatayi hutu anan, tunda can an hanata zuwa." Inna tayi murmushi tace "allah sarki Hibbah kinyi dacen iyayen gida, amma fa saidai kunyi rashin sa'a don ummanta tana gama allah ya kawo mata wani Alhaji a birni, ubangidan malam yace yana sonta aka d'aura musu aure bayan bincike da malam yayi ya tafi da ita birni," Hibbah ta d'ago da sauri ta kalli inna ta kalli aunty. Aunty ta d'an gyara zama tana kallon inna tace "inna a birni wane gari suke?" "Ai a nan garin kano suke da zama," inna ta bawa Aunty amsa, aunty tace "wace unguwa a birnin," inna ta d'anyi shiru kamar mai tunani can tace "wallahi 'yar nan na manta sunan unguwar amma da sa'idu zaizo daya fad'a muku sunan unguwar don jiya ma yaje ya kai mata sak'o," Hibbah tace "inna zai jima ne bai dawo ba?" Girgiza kai inna tayi tace "a'a don naga bai d'auki kayan aikinsa ba, yanxu zaki Ganshi ya shigo, bara na k'arasa iza wutar can," ta fad'a tana tashi, shiru sukayi can saiga sallamar sa'idu kallon su Hibbah yayi alamar rashin sani ta gaida Aunty, Hibbah ta gaishe shi itama saida tayi magana ya ganeta nan, inna ta k'araso tana cewa "yauwa sa'idu dama Hibbah ce tazo take son ka rakata gidan ummanta idan baka komai," sa'idu yace "ba matsala dama baba ya aikeni kasuwar su muje kawai," aunty tace "a wace unguwa take a kano d'in?" Sa'idu yace "a wai goran dutse," "ok" aunty ta fad'a tare da mik'ewa Hibbah ma ta mik'e, nan dai suka yiwa inna sallama aunty ta zube mata kud'i tayi ta godiya suka tafi. Garin kano suka koma, unguwar goran dutse suka nufa sa'idu yana yiwa driver kwance har suka isa gidan, kallon gidan Aunty tayi da mamaki ta kalli driver tace "Adamu wannan ba gidan Alhaji Sani bane?" Adamu driver yace "eh shine hajiya.............. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page2⃣5⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Wannan page d'in naku ne DA BAZARMU WRITERS allah ya k'ara had'a kanmu cikin k'aunar juna* Mamaki fal a fuskar Aunty ta b'alle murfin motar suka fito Hibbah ta kalleta tace "Aunty kinsan gidan ne?" Aunty tana kallon gidan tace "gidan Alhaji Sani ne, shine babban yaron daddy," Hibbah ta kalleta Auntyn ta kawai bata ce komai ba, aunty ta cigaba "idan har Alhaji Sani shine mijin ummanki, to ta more don Alhaji sani mutum ne mai kirki shekarun baya matarsa ta rasu da d'ansa guda daya mallaka sanadiyyar accident da sukayi a hanyarsu ta dawowa kano daga Abuja, shi kuma a lokacin sunyi tafiya da Abba," Hibbah ta karyar da kai yanayin jin tausayi tace "allah yayi masu rahma." Suka nufi gidan, gida ne madaidaici, mai gadin ya gane sa'idu don haka ya barsu suka shiga dayake ma irin almajiran nan ne yara, direct parlor'n gidan sa'idu yayi dasu suka shiga da sallama Umma tana zaune tana kallon sunnah TV suka shigo. Umma ta kalli k'ofa da sauri ta mik'e tsaye tare da zaro ido waje tana nuna Hibbah tace "Hibbah? Kece ko mafarki nake," Hibbah tana murmushin farincikin hawaye nabin fuskarta ta k'araso kusa da Umma ta rumgume ta, sai kuma ta saki kuka Umma ma hawaye nabin fuskarta, bata tab'a tunanin zata had'u da Hibbah a nan kusa ba. Ta d'agota daga jikinta tana share mata hawaye tace "kiyi shiru Hibbah ki daina kuka kinji," ta d'ago ta kalli Umma sannan ta maida kallonta ga Aunty tace "Umma ga Auntyna ita ce ta gyara min *RAYUWA*, inna lami da inna delu sunso b'ata ni sai allah ya taimake ni kuma aunty da momy suka taimakeni," Umma tana murmushi ta k'arasa kusa da Hibbah tana cewa "Auntyn Hibbah kiyi hakuri ban tare ki ba koh? Wallahi murnar ganin Hibbah ne yasa," ta k'araso ta rik'o hannun Aunty suka shigo cikin parlor'n aunty tace "lahh babu komi Umma ai tsakanin d'a da haifi sai Allah," ta zauna a kusa da Hibbah tace "Hibbah na yau sai kwana tare da Umma ko," Hibbah ta rufe fuska tana gyad'a kai. Shi kuwa sa'idu dama suna shiga ya nemi wajen zama. Umma kuwa kitchen ta shiga ta d'ebo musu dangin su snacks da drinks ta cika musu gaba dashi, suka d'an ci suna ta hirar yaushe gamu, Hibbah ta Saki jiki sunata hira da umma ita kuwa aunty mamakin Hibbah take yadda ta Saki jiki tana ta zuba surutu tana bawa Umma labarin abinda ya faru tun bayan tafiyarta har taimakon dasu aunty sukayi mata. Aunty ta kasa jurewa tace "Hibbah wai dama haka kike da surutu?" Hibbah ta tad'an rufe fuska tace "Kai Aunty," aunty tace"eh mana gashinan sai hirarki kike da ummanki," Hibbah tayi murmush. Umma ta kalli aunty tace "mun gode Auntyn Hibbah allah ya saka da alkhari, gaskiya naji dad'in abinda kuka yiwa Hibbah bamu da bakin yi muku godiya Allah ya bar zumunci." Aunty tace "ameen Umma dama na kawota ne zatayi hutunta anan idan sun koma zan turo driver ya d'auketa," Umma tace "to shikenan nan auntyn Hibbah Allah ya kaimu," aunty ta mik'e tana d'aukar jakarta tace "Umma ni Zan tafi sai yazo d'aukar Nata" ta kalli Hibbah tace "Hibbah ni Zan huce sai Adamu yazo d'aukarki idan kuma na samu time zan zo" Hibbah ta mik'e tace "to aunty na gode allah ya saka," aunty ta d'an harareta. Umma tace "mun gode fa Aysha kiyiwa momyn naku godiya kafin muzo, ki gaida gida allah ya tsare" umma ta rakota har bakin k'ofar parlor tana ta yi mata godiya Aunty har ta Fara jin nauyi ma. Har wajen mota Hibbah ta rako Aunty, sannan sukayi sallama cike da kewar juna. Hibbah ta koma suka cigaba da hira shima sa'idu yace zai tafi, umma ta Bashi kud'in mota ya tafi. Da umma zatayi girki ma tare sukayi da Hibbah, umma tayi mamaki Gannin yarda Hibbah ta iya girki haka. Lokacin da mijin umma ya dawo Alhaji Sani ya taya umma murnar ganin Hibbah kuma yace zai d'auketa ya rik'eta tamkar 'yar da ya Haifa. Haka Hibbah ta cigaba da zama wajen ummanta, kullum cikin bawa ummanta labarin gidansu aunty take, har umma taji bazata iya karb'ar Hibbah a hannunsu ba, dan sunyi shawara da Alhaji akan zasu karb'eta yace zai rik'eta, a haka har hutun Hibbah ya k'are aunty tazo ta d'auki Hibbah tare sukaje da umma tayiwa momy godiya. ***** *RAYUWA*r Hibbah ta canza daga k'unci ta koma farinciki, Hibbah ta kuma gogewa ta waye, ta kuma zama budurwa idan kaga Hibbah sai ka rantse tafi shekaru sha bakwai, ta kuma cika ta ko ina ta zama cikakkiyar budurwa. Yanxu suna shirin shiga SS 2, Hibbah ta kuma maida hankali akan karatunta don tana cikin d'aliban da malamai keji dasu a makarantar. lokacinne kuma aunty ta kammala makarantar ta *BAYERO UNIVERSITY KANO*, zata tafi service d'inta, da farko Enugu state aka turata, sai da Abba ya shiga ya fita suka dawo da ita arewa inda aka tura Aunty Abuja, taji dad'in turata Abuja da akayi don a gidan Abba zata zauna. Matsalarta d'aya Hibbah bata so tabar Hibbah a gidan saboda tasan any time Faruq zai iya dawowa kuma tasan k'udirinsa akan Hibbah, idan kuma tace zata tafi da ita Abuja momy bazata ji dad'i ba ga kuma karatunta zata fara lalata mata shi. Haka Aunty Aysha tayi ta tunanin mafita daga baya ta yanke shawarar kaita gidan ummanta, ta fad'awa momy shawarar data yanke kuma momy tayi na'am da hakan, Ana gobe zatakai Hibbah, Hibbah ta tattara kayanta suka tafi gidan umman nata, aunty ta yiwa umma bayanin komai sannan ta tafi suka rabu cike da kewar juna. Kafin aunty ta tafi saida ta bawa Hibbah waya wai su dinga gaisawa. Haka Hibbah ta cigaba da zama a wajen ummanta cikim kula irin ta uwa tare da taimakon mijin nata Alhaji Sani, umma ta samo mata mai adaidaita da yake kaita makaranta yana dawo da ita, da haka har aunty ta dawo daga service d'inta lokacin da ta dawo ana hutun makarantu shiyasa bata je d'auko Hibbah ba kuma bata fad'a mata ta dawo ba. Sai Ana saura one week su koma school da yamma aunty taje ta d'aukota, tun a bakin gate Hibbah ta fara ganin taron Jama'a amma mafi yawansu mata ne, ta kalli Auntyn ta tace "Aunty me akeyi a gidan naga taron mutane," aunty tayi murmushi tare da cewa babu komai Hibbah," ita dai Hibbah bata yarda ba duba da k'unshin dake hannun Auntyn, driver ya shiga cikin gidan tare da yin parking, suka fito duk harabar gidan 'yan mata ne 'yan gayu masu ji da Kansu gefe guda kuma ga manyan mata a zazzaune akan fararan kujeru. Suna doso cikin gidan 'yammatan suka shiga ihun Amarya Amarya, kan Hibbah ya kuma d'aurewa ta kalli Auntyn ta sai taga ta kawar da kai tana murmushi taja hannunta suka shiga cikin gidan, a parlor ta kuma ganin tawagar wasu matan ta kuma gani nan ma suna shiga suka shiga yi mata ihun Amarya, daga can gefe ta hango Saudat, Safiyya da wata da bata Santa ba sai wani yaro da bazai huce shekaru uku ba d'an kyakykyawa yana ta wasansa. Ta gabansu suka zo hucewa zasu hau stairs taji wannan Wanda bata sani d'in ba tana tambayar aunty "Aysha wannan kuma wace naga bansanta ba," aunty ta d'an kalleta tace "k'anwata ce," tana gama fad'in haka suka hau stairs, Safiyya ta tab'e baki tace "uhhmm aunty Kausar 'yar aiki ce fa aunty ta maida ta kamar wata 'yar uwarta, wallahi abinda aunty take yiwa Hibbah komu bata yi mana," Saudat ta harareta tace "nifa banga wani abu ba don ta taimaka mata, to ke ina ma ruwanki dan ta d'auketa a matsayin k'anwa?" Rama hararar Safiyya tayi tace "aike dama sam baki da kishi wallahi, ni haushinki nake ji ki rasa dawa zakiyi k'awance saida 'yar aiki" Kausar ta rik'e baki "y'ar aiki? Itace ta koma haka kamar wata 'yar wani da wata, ni wallahi ji nake ma k'anwar Sagir d'ince," safiyya ta tab'e baki tace "hmm ni fa aunty abin da yake kuma bani haushi school d'in mu fa aunty ta kaita allah ya taimakeni ma ba class d'in mu aka kaita ba amma islamiyya ajinmu d'aya wallahi ga yarinyar da shegen farin jinin tsiya" Kausar ta zaro ido waje "har ta samu wannan matsayin, lallai da matsala" "to wai ku ina ruwanku," Saudat ta fad'a tana mik'ewa tabar wajen, Safiyya ta tab'e, Kausar tace "gaskiya Aysha bata kyauta ba 'yar aiki ta maida haka, to me momy tace," Safiyya ta d'auki wayarta ta fara dannawa tace "ai duk bakinsu d'aya," Kausar ta jinjina kai. Aunty kuwa suna hawa d'akinta suka nufa a bakin gado suka zauna ita dai Hibbah so take ta tambayi aunty me akeyi a gidan, ta d'an sunkuida kai kar k'asa tace "aunty dan allah ki fad'a min me akeyi a gidan nan naji anata ce miki Amarya, ko bikin ki akeyi aunty kike b'oye min," aunty ta k'araso kusa da ita da wata Leda babba a hannunta ta zube a gado tare da zama a kusa da Hibbah ta rik'e hannun Hibbah tace "kiyi hakuri my Hibbah abubuwa ne sukayi yawa shiyasa banma zo da wuri na d'auke ba kuma baki Sani ba, amma kiyi haku..........." Hibbah tayi saurin rufe mata baki da hannunta tace " haba aunty hakuri fa kike bani ni wace? Wallahi ni aunty ba laifi kika yi min ba ai abin farin cikine, yau aka fara bikin?" Girgiza Kai aunty tayi tace "a'a Hibbah d'azu aka ma d'aura aure nima da k'yar momy ta barni nazo d'aukarki shima saida nayiwa sagir waya na tambaye shi," Hibbah ta d'anyi kalan tausayi "amma aunty shine baki zo kin d'auke ni ba," aunty tace "kiyi hakuri Hibbah abubuwa ne sukayi min yawa wallahi ko zama bana samun damar yi shi kanshi Adamu baya zama shiyasa ban turo shiba, amma ai yau za'ayi dinner amma sai an Fara kai Amarya tukunna," Hibbah tace "to shikenan nan aunty Allah ya sanya alkhari," "ameen" aunty ta fad'a tare da janyo ledar ta shiga fito da kayan, material da lashe sai kuma atampa had'ad'd'u anyi musu d'inkin zamani a goge suke sai wani abin d'auri kalar kayan yayi Kyau, sai takalma da pulse duk kalar abin d'aurin. Hibbah ta shiga d'agawa cikin happy tana ta yiwa aunty godiya, aunty ta kalleta cikin nuna tausayi tace "Hibbah kiyi hakuri na yanke wani hukunci ba tare da saninki ba," Hibbah ta ajiye kayan ta juyo tana kallon aunty "aunty ai duk abinda kikayi daidai ne ni a wajena, kuma komai kikace nayi zanyi miki shi aunty ke uwace a wajena," aunty ta shafa gefen fuskarta tace "kalamanki Hibbah suna sani nishad'i," Hibbah tayi murmushi aunty ta d'ora "Hibbah kinga yanzu aure zanyi kuma ni bazan iya barinki a gidan nan ba saboda kinga Faruq ya kusa dawowa kuma nasan halin Faruq tunda yace saiya kusance ki nasan zai aikata. Ya Faheem ya dawo daga abroad wata biyar dasuka huce kuma ya koma gidansa dake Nasarawa GRA, yana samun matsala da Kausar matar sa, aikin banki take idan ta fita tunda safe bata dawowa sai dare Bashi da wanda yake kula da gidan kullum cikin yawon restaurant yake yana ciyo abinci, ga yaronsa Nawaz babu mai kula dashi saidai kullum idan ya dawo daga school a wuce dashi gidan k'anwar Abba," aunty ta dan numfasa "shine ya nemi shawarata akan yadda zaiyi donshi ya gaji, ni kuma kawai nace masa ya d'aukeki nasan zaki kula masa da gida, Hibbah amma idan na takura ki barshi." Hawayen farinciki ne ya zubowa Hibbah ta rumgume aunty tana cewa "nayi dacen uwa mai kaunata, aunty zaki bar gidan nan ki tafi gidan mijinki amma ke tunaninki yarda zaki tserar min da mutuncina, wallahi aunty bani da kamar ki a duniyar nan banda bakin gode miki na gode allah ya Baku zaman lafiya, kuma aunty nayi miki alk'aqarin kula masa da gida." Itama aunty rumgume ta tayi tana mata godiya sund'au lokaci a haka, momy ta shigo take cewa aunty ta shirya za'a tafi da ita, nan ta mik'e tayi wanka tana fitowa tace Hibbah ta shiga ita kuma aunty ta shiga shiryawa wata atampa ta fito musu da ita iri d'aya tayi musu da Hibbah, bayan Hibbah ta fito itama ta shirya sunyi kyau sosai. Mammy (mahaifiyar Kausar) itace tazo ta fita da aunty, hannun aunty rik'e Dana Hibbah har fito harabar gidan a mota aka sa Aunty su mamy suka shiga. Mamy tacewa aunty "Aysha wace aminiyar taki tazo mu tafi," aunty da kanta ke rufe tace "mamy Hibbah ce Hibbah zaku Kira min," aunty ta fito daga motar ta kalli Hibbah tace "kece Hibbah ko?" D'aga mata Kai Hibbah tayi, mamy ta bud'e mata kusa da driver ta shiga, driver yaja sai gidan Amary........... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page2⃣6⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Sis shema allah ya bada zaman lafiya ya barku tare har mutuwa cikin so da k'aunar juna, nan da wata tara muzo suna, allah kawo k'azantar d'aki ammafa bata rashin shara ba🤣🤣.* Gida ne me kyau kana gani kasan gidan Amarya ne su daddy sun zuba dukiya a cikinsa, ita Hibbah sai kalle kalle takeyi tsarin gidan ya burgeta. Bedroom d'in aunty kai tsaye akayi da ita mamy da wasu 'yan uwanta sukayi mata fada akan zaman aure dake su daddy tun sanda aka d'aura aure sukayi mata nasu, saida 'yan Mata wanda zasu wajen dinner sukazo sannan su mammy suka tafi. Wata budurwace tazo kusa da aunty ta yaye mata mayafi tare da cewa "Aysha ki tashi kiyi sallah kukan ya isa haka, kinga takwas ta kusa kuma wannan make up d'in yana da cin lokaci," aunty da idanunta sukayi jajazir ta kalli gefenta tace "ina Hibbah?" Wadda tai maganar tace "sun fita da Saudat da k'anwata fauzy," aunty tace "Dan Allah surry d'an sa a kirata ki fara yi mata kafin nayi sallah," surry tace "ok bara na Kira fauzy," aunty ta girgiza kai tare da mik'ewa ta nufi toilet d'in d'akin. Surry ta shiga dialing number fauzy, bugu d'aya ta d'auka "hello sis kun gama ne?" Fauzy ta fad'a a yayin da ta d'au wayar, surry tace "a'a Hibbah zakice mata tazo inji Aysha," "to kuna ina?" Fauzy ta tambaya, muna sitting room d'inta" fauzy tace "ok to bara na fad'a mata" fauzy ta kalli Hibbah tace "y'ar gidan aunty kije aunty na kiranki wai suna sitting room," Hibbah tai murmushi tace "au kema haka zaki ce?" Saudat da suke ta aikin make up ita da fauzy dayake su duk sun iya har kit ne dasu tayi karaf tace "to ba 'yartan bace," ta kalli fauzy "ai fauzy jelar aunty ma zakice mata ai, ga wanan na Aunty ne kayanta ne ta bari a d'akinta shine momy tace na tawo mata dashi," suka sa dariya Hibbah ta mik'e tare da d'aukar kayan ta nufi sitting room d'in, a lokacin su Hibbah har sunsa ankonsu na sisters baby pink yayi mata kyau sosai. 'Yan matane a zaune a parlor kowacce na kintsa kanta sunsha wani material sky blue sunyi kyau, ta k'arasa ciki inda yayar fauzy surry take tace "Yaya surayya gani" surry tace "zauna Hibbah Aysha tace a Fara yi miki," tace "to" ta zauna aka fara yi mata a zuciyarta tana jin k'aunar Auntyn ta na ratsata. Aunty ma alwala ta d'auro tazo ta tada sallah saida ta fara gabatar da maghrib sannan tayi isha'i, ta kalli inda Hibbah take tayi murmushi ganin yarda Hibbah tayi kyau bata ce komai ba, saida aka gama yiwa Hibbah aka d'aura Mata d'ankwali tayi kyau kamar itace Amaryar sannan aka Fara yiwa Aunty, Hibbah ta sunkuyo da kanta daidai kunnan aunty tace "aunty ga kayanki nan inji momy, kuma aunty na gode Allah ya saka da alkhari ya barki da uncle sagir." Aunty taji dad'in add'arta a zuciyarta tace ameen a fili kuwa hararar Hibbah tayi, Hibbah cikin sauri tabar d'akin ta koma wajen su fauzy ba jimawa ma akace su fito ga motoci nan. Motar wani abokin Sagir d'in suka shigaa akwai shi da surutu, ita kuwa Hibbah tunda ta shiga motar batai magana ba tana dai ta Danna wayarta ta bud'e pulse d'in da aunty ta bata kud'ine sababbi 'yan hamsin bandir d'aya tayi murmushi a ranta tana yiwa aunty godiya, ta cigaba da sauraron duk hirar dasuke yi shida su Saudat da haka suka k'arasa wajen dinner d'in,waje yayi kyau an k'awatashi. Su Hibbah akace karsu shiga har sai Amarya tazo, suna nan a jikin wata mota saiga Amarya da angonta cikin shiga ta alfarma suka shiga da su, kowane sit na mutum hud'u ne dan haka su Hibbah suka samu d'aya daga ciki suka zauna. Suna zaune wannan Wanda ya kawosu d'in yazo ya zauna yana cewa "na zamo cikon na hud'un kenan," ya kalli Hibbah yace "y'ar beauty waike bakya magana ne?" Ta kalleshi tace "sannu ka," ta d'auke kai, ya kalli Saudat yace "Saudat 'yar beauty nan bata magana ne?" "Tana yi mana, ai indai kaga tana magana to tana tare da aunty shiyasa ma nake ce mata jelar aunty," suka sa dariya ita da fauzy. Hibbah ta harareta, shi kuwa murmushi yayi yace "mene sunan beautyn tawa ne," Hibbah ta maimaita a ranta beautyn tawa? A ina na zama tashi? Fauzy ce ta katse mata tunani, ji tayi tace "sunanta Hibbah," da murmushi a saman fuskarsa yace "Hibbaaaaahhh!" Ya wani ja sunan tare da sakin ajiyar zuciya ya kalli Hibbah yace "Hibbah sunanki yana da dad'i kamar yadda kema kike da kyau sunan ya dace dake," Hibbah tace "na gode," yace "da farko dai sunana Jabeer ni abokin sagir ne, kuma ba maganar b'oye b'oye tunda na ganki naji kin shiga zuciya ta Hibbah," Hibbah ta mik'e tace "to na gode da sonda kake min" ya kalleta yace "ina zaki kuma Hibbah? Ina son muyi magana ne," Hibbah ta Fara tafiya tace "inason zanje nayiwa Auntyna lik'i ne," ta fad'a tare dayin gaba. Jabeer ya kalli su fauzy yace "wallahi da gaske nake Saudat ina son Hibbah tun dana ganta kuma aurenta zanyi" Saudat ta mik'e tace "Ya Jabeer indai kana son ka samu Hibbah cikin sauk'i to ka kama k'afa da aunty" yace "allah ko Saudat" fauzy tace "wallahi ya Jabeer don aunty ce kad'ai zata iya fad'awa Hibbah taji," suka kalli wajen rawa, Hibbah suka hango tana ta zubawa Auntyn ta kud'i, Jabeer yayi murmushi tare da yin wajen rawar su fauzy ma suka mara masa baya. Yana zuwa ya shiga zubawa Hibbah kud'i yana mata lik'i, ta d'ago Kai ta kalleshi yayi mata murmushi ya cigaba da yi mata lik'in, kallo sai ya koma Kan Hibbah, su Saudat mazari tuni aka fara rawa ta rik'e hannun Hibbah wai sai tayi rawa, ita kuwa Hibbah ba gwanar rawaba ta dai tsaya tana kallon yadda suke ta rawar su. Haka yayi ta mata lik'i daga baya aka tashi daga wajen dinner ango ya d'auki amaryarsa suka huce, abokan ango suka kwashe 'yammatan suka huce dasu. Ita kuwa Hibbah tana ganin zaa tashi taje ta cewa Adamu driver ya kaita gida tayiwa Aunty sallama, aunty ta jata gefe tace "Hibbah dan allah kiyi hakuri da duk abinda Kausar zata yi miki nasan kina da hakuri ki k'ara akan na da, kuma nasa Adamu d'azu yakai miki kayanki duka gidan saina gobe dazaki sa kawai ya bar miki suna d'akina," Hibbah ta share hawayen daya zubo mata "insha allah aunty na gode," da haka sukayi bankwana, aunty ta kawar da kanta don bata son Hibbah taga hawayenta, Hibbah itama ta huce tana share hawaye don ta shaku da aunty fiye da kowa, Adamu ya tafi kaita. Shi kuwa Jabeer shida su Saudat sai nemanta suke yi daga baya suka gaji ya d'auki Saudat ya kaita gida ita kuma fauzy driver'n su ne ya kaita. Hibbah tana zuwa taga gidan babu kowa duk 'yan bikin sun watse sai su aunty Kausar da safiyya a zaune a parlor suna maida gajiya, Hibbah ta shigo da sallama babu Wanda ya amsa Kausar ta bita da wani mugun kallo tace "'yar aiki kawai.............. *kuyi hakuri da wannan, muna asibiti ne 'yar hatsaniyar da taa faru a fagge ne ta ritsa da nephew na yanzu haka ma muna asibiti bashi da lpy, ina bukatar addu'ar ku pls🙏.* *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page2⃣7⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Wannan page d'in nakune MASOYA RAYUWA GROUP na gode da k'aunar da kuke nuna min Ana mugun tare🤝😍.* *Fans na gode da addu'o'in ku Allah ya saka da alkhari.* Hibbah ba tace komai ba ta nufi stairs da niyyar hawa, fincikota Safiyya tayi tana mata wani mugun kallo tace "haba madam da kenan kafin aunty tabar gidan nan, yanzu baki da 'yancin hawar mana stairs ba tare da izinin mu ba don haka kisan nayi," Hibbah ta d'ago ta kalli Safiyya sannan ta kalli Kausar ta juya da nufin ta fiya taji muryar momy, "Hibbah hayowarki ki rabu dasu don Aysha ta bar gidan nan hakan ba yana nufin na daina kula dake ba kenan," Hibbah ta juyo ta kalli momy tana daga sama take magana momy tayi mata murmushi, hawa Hibbah ta shigayi direct ta huce d'akin Auntyn ta. Momy ta wurga musu wani kallo tace "ke Safiyya ki kiyayeni wallahi ki fita a ido na, naga kanki yana rawa ko zan daidaita miki shi zan d'auki babban mataki akanki, ke kuma Kausar saboda zubda girma har dake ake yiwa yarinyar nan rashin mutunci ko? Ku cigaba," Kausar tayi k'asa da kai Safiyya tace "kiyi hakuri momy," harararta momy tayi tare da yin ciki. Safiyya ta kalli Kausar, Kausar tace "Safiyya dafa matsala kalli yadda momy take mana fad'a kan waccan banzar," Safiyya tace "hmm ai sainayi maganinta," Saudat ce tayi sallama ta k'araso kusa dasu ta xube a kujera tace "wash Allah wallahi na gaji, Safiyya kun jima da dawowa kenan," Ta fad'a tana kallon Safiyya, Safiyya tace "eh tun kafin Aunty su huce muka tawo," Saudat tace "kuna nan a zaune tunda kuka dawo?" D'aga mata kai Safiyya tayi tace "eh mene kike tambaya?" Saudat tad'an kishingid'a tace "kunga shigowar Hibbah? Tun d'azu da aka tashi muketa nemanta amma bamu ganta ba," harararta Kausar tayi tace "Saudat wannan wane irin maganar banzane, kinga munyi miki kama da masu gadi ne daza kizo kina tambayar mu wata banzar 'yar aiki," Saudat taji haushin furucin Kausar dama kuma ba shiri suke ba, Saudat tace "kinga dai aunty Kausar bada ke nake ba kiyi hakuri kiyi min shiru," Safiyya ta kalleta tace "ai gara ita ta tanka miki ni kina tunanin zan tanka miki ne yarinyar da a kanta momy tayi min fad'a, kuma ki fad'a mata tunda tasa momy tayi min fad'a sai tayi data sanin zuwanta gidan nan" Saudat ta buga tsaki tare da mik'ewa ta kalli Safiyya tace "aikin banza don momy tayi miki fad'a saiki huce a kanta? To bismillah," ta kalli Kausar data d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana karka d'awa, Saudat tace "a shawarce da zaki daina biyewa wannan daya fiye miki, kinfi kowa sanin halinta matarda ko gidanta bataso aje shine kike mak'ale da ita, duk soyayyar da zata miki a gaban su momy ne kina zuwa gidanta zakiga bambanci ," tana gama fad'in haka ta hau stairs, binta da ido sukayi musamman ma Kausar tayi mamakin Saudat, kuma ta kasa cewa komai, suka kalli juna Safiyya a ranta ta yarda da kalaman Saudat don kafin aunty tayi aure saida tazo tana fad'awa momy. Ita kuwa Saudat d'akin aunty ta nufa donta duba ko Hibbah ta dawo, shiga d'akin tayi da sallama ta k'arasa kusa da Hibbah tana murmushi tace "shine kika gudo koh? Mukaje can muna ta nemanki." Hibbah tayi dariya tace"wallahi gani nayi wannan mutumin yana neman takurani ne shiyasa," Saudat ta d'an matso kusa da ita tace "Hibbah baki fahimci Ya Jabeer bane yana da halaye masu kyau ki tsaya ki fahimce sa," Hibbah ta d'an kalleta tace "kinga Saudat nifa bacci nake ji ki rabu Dani da halin mazan nan duk Wanda yazo wajenki buk'atarsa d'aya ce ya nemi jikin ki," "a'a Hibbah karki yanke hukunci" Saudat tayi saurin katseta, Hibbah tayi murmushi tare da mik'ewa ba tace komai ba ta nufi toilet ta d'an watsa ruwa ta d'auro alwala sukayi sallama da Saudat, tayi addu'o'in ta ta kwanta. Kamar yadda ta saba tashi haka yauma ta tashi, ta d'auro alwala ta zo tana ta nafilfili tana rok'on allah ya k'ara mata juriya da hakurin zama da Kausar, tana nan zaune har akayi assalamu ta tashi ta gabatar da sallah, ta d'auko Qur'anin aunty ta shiga karantawa, bayan ta idar ta d'ora da azkar har gari yayi haske sannan ta ajiye ta sauko k'asa ta nufi kitchen. Hadiza ta gani tana kiciniyar had'a breakfast, ta gaisheta suka shiga had'awa tare. Suna ta hira har suka gama suka kai dinning Hibbah ta jere kayan, Hadiza dama ta ware nasu daban ta koma sukaci sunata hira. Sama Hibbah ta koma tayi wanka ta shirya cikin wani material Orange tayi masifar kyau ta gyara fuskarta, wayarta ta d'auka tanata game har wajen sha d'aya sannan taji motsin 'yan gidan. Tana zaune wajen sha biyu Hisham ya turo k'ofa ya shigo, ya k'araso gaban Hibbah yace ""aunty Hibbah kizo inji daddy'n Nawaz," ji tayi gabanta ya fad'i duk da bata sanshi ba, mayafinta ta d'auka tasan tafiya zasuyi k'irjinta na bugawa ta fita. A parlor'n k'asa taga 'yan gidan a zazzaune harda su momy ita da mamy amma banda aunty Kausar da alama tana tare da mijin nata ko kuma tun jiya ta huce ta gaishe da su, momy tace "yauwa kije yana waje yana jiranki, ki kula da kanki Hibbah ki d'auke kanki akan duk abinda za'a yi miki, can yana da bambanci da nan kinji?" D'aga mata kai Hibbah tayi k'aunar momy na kuma shiga ranta, tace "na gode momy allah ya saka da alkhari," momy tace "ameen Hibbah," mamy ta kalli su Safiyya tace "ku tashi Ku rakata mana," Saudat ce ta fara mik'ewa taja hannun Hibbah suka fita, ita kuwa Safiyya dama danna wayarta take yi data fito ma cigaba tayi da abinta. A mota suka tarar dashi motar a bud'e shi kuma ya zuro kafarsa d'aya waje yanayiwa Nawaz wasa, suka k'araso wajen inda yake suka gaishe shi ya amsa tare da d'agowa ya kalleta, ji tayi gabanta yayi wata muguwar fad'uwa ganinsa tayi kamar Faruq komai nashi irin na Faruq bambancinsa da Faruq kawai girmane amma hatta maganarsu ma iri d'aya ce. Ya kalli Nawaz yace "boy shiga mota mu tafi gida," yaron d'an kyakykyawa yace "to daddy," ya kalli su Saudat yace "Aunty Saudat wace wannan?" Saudat tayi murmushi tace "sunanta aunty Hibbah," ya kalli Hibbah yace "aunty Hibbah," Hibbah ta kalleshi tana murmushi. Ya kuma kallon Saudat yace "aunty Saudat aunty Hibbah tana murmushi don na Kira sunanta," Faheem ne ya katseshi da cewa "Nawaz ka shiga mota mu tafi mana," da sauri yaron ya juya ya bud'e motar tare da shiga yana yiwa su Hibbah murmushi, Saudat ma ta bud'ewa Hibbah gidan baya ta shiga sukayi sallama, Faheem ya tashi motar suka huce. Safiyya na ganin sun tafi ta komawarta gida dama ita Danna wayarta take. A mota Nawaz sai surutu yake tayi shi kad'ai, yace "daddy aunty Hibbah gidan mu zamu da ita?" Faheem dayake tuk'i yace "eh Nawaz ita zata dinga zama tare da kai idan ka dawo daga school, tayi maka wanka ta koya maka homework ta dafa mana abinci," Nawaz jin ya ambaci homework yasaki ihun murna "yeeeh daddy nima na samu aunty," ya juyo yana kallon Hibbah yace "aunty Hibbah har unguwa zaki dinga zuwa dani momy na bata zuwa unguwa dani wai nayi girma, ai banyi girma ba ko aunty?" Hibbah ta d'aga masa kai tana murmushi tace "eh Nawaz zan dinga zuwa dakai," lokaci d'aya taji k'aunar yaron ta shiga ranta, shi kuwa Nawaz cigaba yayi da wasanshi har suka k'araso gidan Mai gadi ya bud'e gate d'in gidan yana yiwa Faheem sannu dazuwa. A parking lot ya ajiye motar suka fito, Faheem yayi gaba shi kuma Nawaz ya zo ya rik'e hannun Hibbah suka parlor yana ta yi mata surutu. Suna shiga suka tararda Faheem a parlor yana k'ok'arin kunna TV, bai kallesu ba ya kunna TV ya dawo ya zauna yana kallon labarai, a k'asa Hibbah ta zauna Nawaz yana kan cinyarta, Faheem yad'an kalleta kad'an ya kawar da kansa yace "Hibbah sunanki ko?" Hibbah ta d'aga kai "eh" yace "Hibbah aikin ki a gidan nan shine girki, gyaran gida sai kular min da Nawaz pls ki rik'e amana," Hibbah tace "insha allah daddy," Faheem ya cigaba da kallo yace "sannan maganar zuwa school d'inki idan kika gama aikin da wuri sai kije yanzu dai samo min wani abu naci," Hibbah ta mik'e ya kalli Nawaz yace "son nuna mata d'akin da zata zauna da kitchen," Nawaz ya mik'e ya rik'e hannun Hibbah ya kaita har d'akin dayake yasan suna extra daki ta ajiye mayafinta, sannan ya kaita kitchen. Gaskiya ta raina tsaftar matar gidan kitchen duk yayi datti kaya duk a barbaje komai a wulakance yayi kaca kaca, nan ta shiga gyara kitchen d'in ta d'auke kayan ta wanke ta share tayi mopping kitchen din yayi fes, sannan ta d'ora girkin.......... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page2⃣8⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYAHA ALIYU GARKUWA* *Ina taya duk musulman duniya murnar shiga sabuwar shekarar Muslunci, allah ya bamu alkharan wannan shekara ameen.* *Ina kuke DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION FANS wannan page d'in nakune muna godiya da k'aunarku.* Nan da nan gida ya d'auki k'amshin girki, ta had'a lemon kwakwa, bayan ta gama ta juyo shi a kula ta kai dinning ta ajiye ta koma d'auko lemon ta tawo da plates da spoons sai kuma cups tazo ta ajiye akan dinning d'in, ta zubawa Faheem daban ta zubawa Nawaz shima nashi ta rufe ko wanne da wani plate d'in. Ta dawo parlor ta tsugunna a gaban Faheem tace "daddy na gama ga abincin can a dinning," ba tare daya kalleta ba yace "ke kin d'ibi abincin?" Ta girgiza kai alamar a'a yace "kije kici" "to" ta fad'a tana komawa wajen dinning din, ta d'ebo a plate d'in tazo zata huce Faheem yace "ina zaki?" Tace "daddy a d'aki zanci," ya d'aga kai tare da mik'ewa Nawaz na biye dashi suka k'arasa dinning. Yana bud'ewa wani daddad'an k'amshi ya daki hancinsa ya lumshe ido tare da kai lomar farko bakinshi, kuma lumshe ido yayi gaskiya yaji dad'in abincin rabon dayaci irin wannan abincin tun yana gidan momy, ya kuma kai wata lomar bakinsa tare da kurbar lemon, Subhanallah ji yayi ya kuma rikicewa gaskiya yarinyar nan ta iya girgiki abinda yake fad'a kenan a ranshi. Nawaz sai da ya gama wasansa sannan ya fara cin abincin yana ci yace "daddy abincin aunty Hibbah ba irin wanda kake siyo mana ba," Faheem yayi murmushi yana shafa kan Nawaz yace "haka ne Nawaz abincin Hibbah yayi dad'i, amma kaci abincinka banda surutu kar ka kware kaji," yace "to daddy amma kullum ita zata dinga yi mana abinci ko?" Faheem ya d'aga masa kai, ya cigaba da cin abincin har suka gama, suna gamawa Nawaz ya ruga d'akin Hibbah lokacin itama ta gama ci, ya shigo yana cewa "Aunty Hibbah abinci da dad'i daddy ma yace da dad'i," Hibbah tayu murmushi taji dad'in furucin Nawaz tace "Nawaz idan aka shigo d'aki sallama ake fara yi kafin ayi wata magana," Nawaz ya d'an karyar dakai "to kiyi hakuri aunty abincin ne yayi dad'i," Hibbah tayi murmushi tace "to naji amma tashi kaje kayo sallama tukunna," Nawaz ya mik'e ya fita yaje yayo sallama, ta amsa masa sannan ya shigo ya zauna akan k'afae Hibbah yace "aunty Dan Allah ki cigaba da yi mana irin wannan abincin yayi dad'i," Hibbah ta kalleshi tace "da gaske daddy yace girkina da daddy Nawaz?" Nawaz ya d'aga Kai "eh aunty yace da dad'i," tace "Nawaz ai dole na cigaba da yi muku irin wannan abincin," Nawaz yayi ihun murna "yeeeh zamu dinga cin abinci me dad'i," Hibbah ta d'anyi dariya tana kallon yarda yake murna tace "daddy ya fita ko yana parlor?" Nawaz ya mik'e "bara na duba," ya fita jimawa kad'an ya dawo "aunty baya nan ya fita," Hibbah tace "yauwa Nawaz," ta mik'e zata fita Nawaz yace "aunty ina zaki?" "Zan wanke kayan aka b'ata ne Nawaz" "Aunty idan kin gama zaki yimin assignment d'ina ran Monday zamu koma school," ta d'aga kai tare da fita. Ta had'o kayan ta wanke ta gyara ko ina parlor ma tasa turaren wuta sai k'amshi ke tashi ta koma d'akin nata taga Nawaz ta tattaro littattafansa na makaranta ya barbazasu, tana zuwa ta shiga nunnuna masa yaron akwai k'ok'ari nan da nan yake fahimta, bayan sun gama Nawaz ya dinga yi mata shirme tana biye masa, yaje ya d'auko mata wani hotonsa ya ajiye mata a gefen gadonta wai yabata haka dai yayi tashirmensa har yamma. Bayan tayi sallar la'asar ta shiga kitchen tayi musu dinner, ta koma d'akin tayi wanka ta canza kaya tana nan zaune akayi kiran sallar maghrib ta tashi tayi sallah. Shi kuwa Nawaz yana gani ta shiga kitchen ya fita wajen iliya mai gadi yana ball. Sai bayan sallar maghrib suka shigo da daddyn shi, suka nufi dinning suna cin abincin Kausar ta shigo da sallama ta ajiye Jakarta akan kujera itama ta zube a kan kujerar tace "wash Allah, daddyn Nawaz yau har ka yo take away d'in kenan," Faheem bai kulata ba saida suka k'araso inda take da yake sun gama cin abincin ya zauna a d'aya daga cikin kujerun parlor'n yace "a'a aini yanxu na wuce wannan wajen, Aysha ce ta bani shawarar kawo mai kula min da gida ta kular min da yaro tunda ke kin zab'i aikinki akan mijinki da iyalanki," maganar ta yiwa Kausar zafi "haba daddy'n Nawaz kaima fa kasan yanayin aikina, kayi min uzuri mana," "wane uzuri zanyi miki Kausar? Bayan hakurin zaman da nake yi dake yanxu," maganganunsa sun fara yi mata zafi ta kalli Nawaz a tsawace tace "Nawaz kira yarinyar da tazo Kace ta kawo min abinci," Nawaz ya kalleta a d'an ta yace "to momy bara na k'arasa kallon wannan film d'in," "dallah ka tashi kaje ka kira min ita," Kausar ta fad'a tsawace da gudu Nawaz ya fita duk ya tsorata. Faheem ko kallon ta baiyi ba sai wani cika take tana batsewa, Nawaz ya dawo Hibbah na biye dashi suka shigo parlor'n da sallama Faheem ne kawai ya amsa ita kuwa ko kallonta bata yi ba tace "ke zubo min abinci," Hibbah tace to" ta nufi dinning ta zubo mata abincin ta kawo gabanta ta ajiye, tana shirin tafiya Kausar tace "keehh" Hibbah ta juyo ta kalli Kausar tace "na'am aunty," cikin mamaki Kausar ta mik'e "ke meya kawoki gidana?" Ta kalli Faheem "badai wannan ka kawo min a matsayin 'yar aiki ba," yayi mata kallon gefen ido "a ina kika ganta? Ina ce a cikin gidan nan kika ganta kuma na miki bayanin ai ko?" Tace "haba Faheem ya ina tambayar ka kana yi min magana a duk'unk'une," bai kulata ba ya kalli Hibbah yace "tashi kiyi tafiyar ki," "ke dawo karki sake ki koma min cikin gida mayya kawai," cikin masifa Kausar take mata magana, cikin tsawa Faheem ya d'aga mata hannu "ya isheki Kausar baki isa ki hana Hibbah zama a gidana ba, ni na kawota cikin gidannan kuma ko kinaso ko bakyaso dole ne ta zauna," ya kalli Hibbah yace "ki tafiyarki ciki babu Wanda ya isa ya hana ki zaman gidan nan," Hibbah ta nufi cikin d'akinta. Kausar kuwa takaici ne ya isheta tasan halin Faheem sarai yanxu zai dizgata a gaban yarinyar nan, ta suri jakarta tana ta mita ta shiga ciki. Faheem ko kallonta baiyi ba ya cigaba da kallon news, Nawaz ya kalli daddyn shi yace "daddy ni yau a wajen aunty zan kwana," Faheem ya kalleshi "a'a Nawaz zakaje ka takurawa Hibbah ne da surutu ne kawai," "daddy bazan yi mata surutu ba," "to shikenan kaje ka canza kayan naka sai kaje Ku kwanta," Nawaz ya tashi yana murna yaje ya canza kayanshi ya tafi d'akin Hibbah, ya shiga da sallama waya yaga tanayi tace "aunty kiyi hakuri zanzo amma ba yanzu ba, saina daina xuwa islamiyya tukunna," daga can aunty tace "yaushe ne zakuyi walimar ne Hibbah?" "Next week Sunday," Hibbah ta hawa aunty amsa, "to Allah ya kaimu," "ameen Aunty," Nawaz ya matso kusa da ita "aunty bani mu gaisa da momy Aysha,," Hibbah ta mik'a masa wayar suka gaisa da aunty sannan sukayi sallama ta kashe wayar. Ta kalli Nawaz tace "Nawaz daddy ne yake Kira na?" Ya girgiza kai "a'a aunty nazo mu kwana tare ne," "ok to zo muyi alwala sai mu kwanta," suka mik'e suka d'auro alwala suka yi addu'a tare da kwanciya. Da safe Hibbah ta tashi tayi duk wani aikin gidan sannan tayi wanka tayiwa Nawaz ta shiryashi sukayi breakfast ta wanke cups d'in, da rana ma haka tayi musu girki hakama da dare. Haka Hibbah ta cigaba da yi musu bauta a gidan amma Kausar bata tab'a yi mata koda kallon aizik'i ba balle ta samu godiya daga wajenta. Da haka har ranar walimar su Hibbah tazo, aunty da umma sunyi bajinta kwarai don duk wani abu da akewa 'yar gata da walimarta haka sukayi wa Hibbah ta fito kamar ba ita ba, haka taro ya tashi aka sallami 'yan sauka aka basu allon su tare da kyaututtuka. *** Watan Hibbah d'aya agidan har ta Saba sosai kullum sai tayi komai na gidan take tafiya school, daddy kuwa Nawaz yake aikowa ya kai mata kud'in motarta. Ranar lahadi Faheem yana gida da wuri Hibbah ta gama komai ta kira Nawaz tace "Nawaz jeka fad'awa daddy zamuje gidan Aunty," Nawaz yace "nima zani gidan momy Aysha," tace "to jeka fad'awa daddy kazo mu tafi," ya juya cikin happy ya tafi wajen daddyn nashi dake harabar gidan yaje yace "daddy wai inji Aunty Hibbah zamuje gidan momy Aysha," Faheem yaji dad'in yarda Hibbah ta bashi girmansa ya zaro kud'i a aljihunsa ya mik'awa Nawaz "ka kaimata Ku hau mota kuce ina gaishe da Aysha," Nawaz ya amsa ya kawo wa Hibbah kud'in. Hibbah ta shirya cikin wata atampa yellow da ratsin royal blue tayi kyau sosai ta shirya Nawaz suka fito titi Neman adaidaita. Da k'yar suka samu suka nufi gidan Aunty. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:23 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page2⃣9⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHS ALIYU GARKUWA* Sun isa gidan aunty inda ta tarbe su cikin farin ciki suka rumgume juna suka zube kan kujera suna gaisawa, Aunty ta cika musu gaba da abinci kala kala sunaci suna ta hira har lokacin sallah yayi suka tashi suka gabatar da sallar. Ba wani aiki auntyn take yi ba a gidan daga gyaran d'akin mijinta sai girki don haka suka kuma zama a parlor suna ta hira, sallamar su sagir ce ta katsesu suka amsa musu, Hibbah ta gaishe da sagir dana bayan shi dan bata ga fuskarsa ba. Jabeer ya saki sassanyar ajiyar zuciya tare da amsawa muryarshi data jini ne ta gane wanene ta d'ago kanta duka kalli juna, Jabeer ya sakar mata wani murmushi mai cike da ma'anoni. Ta kawar da kanta kefe suka cigaba da hira da aunty ita kuwa aunty ta fahimci abinda ke tsakaninsu, ta taya Hibbah murna sosai ta kuma yi farin ciki da hakan ta mik'e ta nufi d'akin mijinta ta had'a masa ruwan wanka tare da fito masa da kaya marar nauyi, shima sagir biyota yayi donya watsa ruwa. Parlor'n ya rage daga Jabeer sai Hibbah sai kuma Nawaz daya ke ta wasanshi jikinta, Jabeer ya kalleta yana murmushi "Hibbah ba magana," ta sunkui da kai "ai na gaishe da ku," "Hibbah gaisuwa daban maganar da bake so kiyimi da ban," ta d'ago tad'an kalleshi ta mayar da kanta k'asa don bata da amsar bashi, gani take yi kamar zai yaudareta tana yiwa maza kallon halinsu d'aya shima hankali zai buk'aci jikinta. Ta kuma yin k'asa da kanta yace "Hibbah ki yarda dani wallahi inna k'aunarki kuma ni auranki zanyi pls ki karb'i buk'atata," Hibbah dai bata ce komai ba sai wasa da take yi da zuben hannunta, Jabeer yayi suru kawai yana kallonta, ita kuwa Hibbah duk a takure take dan bata son yawan kallo yana takureta. Aunty ta dawo parlor'n tana dawowa Hibbah tace "aunty bara mu tafi yamma tayi," aunty ta harareta "me kike nufi? Wai yanxu zaki tafi?" Hibbah ta d'an karyar da kai "aunty daddy fa yana nan kinga bazai so kukai dare ba, ga girki ma da zanyi yanzu idan na koma," aunty tayi murmushi "to shikenan na karb'i uzurinki," Hibbah ta d'auki jakarta Nawaz ma ya mik'e "aunty zamu huce sai munyi waya," "to shikenan Hibbah na gode ki gaida min da Yaya," Jabeer yayi zaraf "Aysha mai zai hana na kaita tunda da mota a hannuna," da sauri Hibbah ta d'ago Kai ta kalleshi, aunty ta kalli yanayin Hibbah duk ta rud'e tace "ai kuwa da ka kyauta, kasan yanzu kafin ta samu mota ma aikine tunda yamma tayi," Hibbah ta kalle Aunty tayi narai narai da ido. Jabeer yaji dad'in furucin aunty jiki na rawa yafita, Aunty tayi murmushi tace "Hibbah Jabeer yana sonki so na hak'ik'a me yasa bazaki karb'i tayinsa? Kullum idan yazo gidannan Bashi da zance sai naki," Hibbah ta kalli Auntyn ta "aunty bana k'i karb'ar tayinsa bane kawai ni inajin tsoran maza ne," "a'a Hibbah ba duka aka taru aka zama d'aya ba, kinga yanzu yana jiranki a mota, kaso mai sonka kinga shi aurenki zaiyi da kin k'arasa school amma dai kiyi tunani." Hibbah tace "to shikenan aunty na gode," aunty ta bata wata leda bak'a cike da kayan kwalliya ta amsa tayi godiya. Aunty ta rakota har bakin motar ta bud'e mata kusa da Jabeer ta shiga suka tafi, a mota Jabeer sai janta yake da hira ita dai ba magana daga uhmm sai a'a, dayaga haka sai yayi ta jan Nawaz da hira har suka shigo unguwar nan ne ma dai tayi ta nuna masa hanya. A bakin gate d'in gidan yayi parking Hibbah kanta na k'asa tace "na gode," Nawaz ya bud'e motar ya fita da gudu ya shiga gida. Jabeer ya kalleta yace "Hibbah maganar mu fa?" "Sai na fad'awa aunty," ya kalleta "nasan Aysha zata bani da yardar Allah," "Allah yasa," ji sukayi an bud'e k'ofar ya janyoh hannun Hibbah tare da sinka mata mari "uban me kikeyi a motarsa?" Hibbah ta d'ago kai ta kalleshi, cikin tsoro ta furta " *Faruq* kaine yaushe ka dawo?" "Bansani ba, me kikeyi a motarsa nake tambayarki," Jabeer cikin zafin yace "kai dallah ya isheka kawai daga ganin yarinya muna tare sai ka shiga dukanta," "na daketa d'in, ta maka waye ni a wajenta ta fad'a maka matsayinta," ya kalli Hibbah dake rik'e dakuncinta yace "ke ki fad'a masa matsayinki a gidan mu," Hibbah tayi shiru wasu zafafan hawaye nabin fuskarta "tunda ke baxaki fad'a ba ni bara na fad'a, Hibbah ba kowa bace a gidan mu face 'yar aiki kuma baiwa!!!" Kalmar tayiwa Hibbah zafi da gudu tayi cikin gida tana kuka. Jabeer ya cilla masa wani mugun kallo "ba baiwa ma ko wace Hibbah ina sonta ina kuma k'aunarta a hakan Zan aureta," yana gama fad'in haka ya shige motarshi ranshi a b'ace ya figi motar. Faruq kuwa ya kasa nutsuwa yana tunanin koya bita cikin gidan sai kuma ga koma motarsa ya had'a kansa da sitiyarin motar. Yana mamkin meya kawo ta gidan ya Faheem. Hibbah kuwa tana shiga gida d'akinta ta nufa ta zube a kan gado ta shiga rera kuka, tana mai jin zafin abinda Faruq yayi mata ace a gaban saurayinka yayi maka wannan rashin mutuncin wannan wace irin *RAYUWA*ce? Ta kuma rushewa da kuka tana kuma tunano *RAYUWARTA* ta baya. Nawaz ne ya shigo rik'e da chocolate a hannunsa yana sha ya mik'o mata "Aunty kinga uncle ya bani chocolate," da sauri ta goge hawayen ta tana murmushi tace "to jeka sha Nawaz nima bara na shiga kitchen," ta mik'e ta nufi kitchen ta had'a musu dinner ta gyara kitchen d'in, tana gamawa taji ana kiraye kirayen sallah tayo alwala tazo ta gabatar da sallar, ta d'ebo abinci ta zauna suna ci ita da Nawaz sai shirme yake mata ita kuwa duk abin da Faruq yayi mata ne yake damunta har ta kwanta tana tunanin abin. Washe gari Monday ta tashi da ciwon kai sakamakon kukan da taci jiya da dadaddare, ta tashi tayiwa Nawaz wanka ta shirya shi school bus na zuwa ya tafi, ita kuwa bata da niyyar zuwa saboda ciwon kan dake damunta don tana gama shiryashi ta koma ta kwanta sai wajen sha d'aya ta tashi tayi duk ayyukanta tana cikin yin mopping taji motsin mutum a bayanta tana waigawa taga Ashe Faheem ne tace "barka da safiya daddy" bai ma jita ba dun ya sha'afa wajen kallonta tunda suke zaune da ita sai yaune ya tab'a k'are mata kallo lokaci d'aya yaji wani abu a zuciyarshi, hazak'ar Hibbah da ayyukanta suna burgeshi sam bata nuna gajiyawarta akan duk abinda Kausar zata sata ga d'awainiyar da take yi masa da yaro. Ta kuma cewa "daddy barka da safiya," ya d'anyi firgit ya kalleta "lafiya" ya huce d'akinsa ya shiga ya d'auko takardun daya manta ya huceta, ita kuwa ko a jikinta ta k'arasa aikinta tayi wanka ta shirya tsam kamar mai fita wajen party ta shiga kitchen ta d'ora musu abinci yana yi ta juye ta jere a dinning ta koma d'aki ta d'an kwanta a hankali bacci yayi awon gaba da ita. Cikin barci kamar a mafarki taji ana shafata taji kamar an danneta a hankali ta bud'e idanunta wa zata gani Faruq ne a kanta wani wawan ihu ta saki tare da tattaro k'arfinta ta tunkud'eshi ya fad'i k'asa da gudu ta ta fito parlor kicib'is sukayi da Faheem daya dawo hannunsa rik'e dana Nawaz da gudu ya rumgume ta, ita ma ta rik'eshi sai zare ido take yi. Faruq ya fito yana binta da mugun kallo, Nawaz ya k'arasa kusa dashi "uncle yaushe kazo?" "D'azu nazo Nawaz," ya kallo d'aya yayiwa Faheem ya fice abinsa. Faheem Wanda ke tsaye yana kallonsu kamshi ya d'aure me ya kawo Faruq gidanshi yanxu bayan yasan baya gidan, mene a tsakaninsa da Hibbah kodai itama tana biye masane? Da Sauri ya girgiza kai a'a Hibbah tana da halaye masu kyau, ya kalli Hibbah cikin b'acin rai yace "me kike aikata min a gida?" Da sauri ta girgiza Kai "a'a daddy wallahi bansan ya shigo ba ina kwance naji shi.......," nauyin k'arasawa tayi sai ta saki kuka. Tsayawa yayi kallon ta zuciyarshi ba dad'i sam baya son wannan kukan, ya d'aga mata hannu "tashi ki tafi bana son hayaniya," mik'ewa tayi ta nufi d'akinta tana kuka akan gado ta zube tana ta kuka yanzu shima zarginsa zai d'ora a kanta abinda ta tsana kenan Faheem yaga laifinta shiyasa take jure duk wani wulakanci da Kausar zata yi mata, tashi tayi ta d'auro alwala tayi sallar la'asar a wajen ta zauna tana addu'ar allah yasa Faheem kar ya zargi wani abu tsakaninta da Faruq, kuka ta cigaba dayi Nawaz ya shigo "aunty yunwa nake ji," ta mik'e ta nufi dinning ta zubo masa a plate ta kawo masa gabansa ta tura masa ta koma gefe tayi jugum tana tunani yace "aunty ke baza kici ba?" Ta k'ak'alo murmushi "nak'oshi Nawaz," "aunty dama kinci kafin na dawo ko?" "A'a Nawaz na k'oshi ne," bai kuma yi mata magana ba don shima wani lokacin kisan halinsu d'aya da daddy'nsa haka yaci abincinsa yana gamawa ya fice parlor. Faheem ya gani parlor ya k'arasa kusa dashi yace "daddy aunty Hibbah tak'icin abinci sai kuka take," Faheem ya kalleshi "kuka kuma Nawaz," "eh daddy tun d'azu take yi," ya mik'e ya nufi d'akinta yana zuwa ya tura k'ofar d'akin ganinta yayi a zaune akan sallaya ta kifa kanta. "Hibbah saboda me kika k'i cin abinci saboda abinda ya faru?" Da sauri ta girgiza kai, "to menene kisani ni bana zarginki akan komai, amma ki sani babu Wanda zai ganku a d'aki Ku biyu gida kuma ba kowa bai zargi wani abu ba, ki fita harkar Faruq fatan kin fahimce ni," ta gyad'a kai. "Shikenan ni bana son b'atawa mutum banson na ganki kina damuwa don haka ki samo abinci ki ci kinji ko?", ta kuma gyad'a kai to. Ya rufe k'ofar, sai ta samu kanta tana bin umarninsa, ta d'ebo abincin tana ci sai taji ta samu nutsuwa hankalinta ya kwanta, Nawaz yasa ta a gaba Allah sarki shima ya damu yace "Aunty Hibbah daddy bai tab'a dukana ba kema bazai dake ki ba," tayi dariya yaro yaro ne, ahankali ta wantstsake har tayi musu girkin da dare. Washe gari da wuri ta tashi tayi komai don zata je skul. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:23 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page3⃣0⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Facebook groups ina ganin sak'on nin ku da k'arfin gwaiwr da kuke k'ara min ako da yaushe kuma ina godiya Allah ya saka da alkhari ina k'aunarku har cikin raina.* Yau da yamma ta gama komai da wuri tana zaune a d'aki taji wayar ta na ruri ta d'auko dan ganin wake kiranta bak'urar number ta gani da kamar karta d'auka sai kuma ta d'auka a tsorace "hello!" Ta furta a hankali. Daga d'ayan b'angaran taji yace "Hibbah bak'on ki ne gani nan k'ofar gida ina jiranki," ta dafe k'irgi "wai wa kenan ban gane mai maganar ba," yayi murmushi mai sauti "ai baza ki gane ba tunda ban tab'a kiranki ba, Jabeer ne wannan mutumin mai nacin nan, kiyi min hakuri Hibbah kar kice baza ki fito ba don Allah," Hibbah ta d'anyi shiru sai can tace "to ganin fitowa" ta kashe wayar. Ta sanya wata abaya bak'a mai mugun khair gami da lullub'e kanta da mayafin rigar, ta shafa powder da lipstick ta feshe jikinta da daddad'an turarukan da aunty ta bata, ta rik'e hannun Nawaz d'an kad'afi duk inda ta cire k'afa ya maida sawunshi, shiyasa suke kuma shak'uwa. Yana zaune cikin motar ya kasa d'auke idanunsa daga kanta ashe duk ganin da yake mata bai gama ganin baiwar da Allah yayi mata ba, tayi masa kyau shi dai yana k'aunarta a ransa, tak'i goguwa a zuciyarsa wani d'an sataccen murmushi tayi masa, ikon allah sai yaji ta tafi dashi gaba d'aya. Ya fito ya jingina da motar komanta ya burgeshi ya rik'o hannun Nawaz yana kallon kyakykyawan yaron, a kunyace ta gaisheshi don itama d'in yau ta k'are masa kallo. Bak'ine kyakykyawa wato irin black beauty d'in nan hancinsa dogo har baka shi ya dad'a fito da sigar kyansa ga shiga da tsari, yana sanye da wani laushashshan boyel yayi matuk'ar kyau ga nutsuwa da allah ya bashi. Ya kalleta da murmushi a fuskarsa yace "Hibbah naji dad'in ganinki da baki fito ba bazanji dad'i ba sai na tafi zuciya ta tana wasi wasi kina jin sak'ona wajen Aunty Aysha na dameta da batunki, Hibbah ki godewa Allah dan ba k'aramin so nake miki ba," tayi murmushi "uhm to na gode itama tana fad'amin," ya kuma murmushi "Aunty sarkin yak'ina ce koda yake itama tasan irin son da nake miki so ne na tsakani da Allah, gashi kuma rowar magana kike yi min so nake naji muryarki dad'i take yi min," ta d'an kalle shi "to me kake so nace?" "Hibbah kenan nidai fatana ki amince min muyi aure, amma fa ban b'oye miki ni mutum ne magidanci mai iyali da mata na da yara na uku ban miki tsufa ba dai ko?" Ta kuma murmushi "aure nufi ne na Allah," "nasan hakan kina nufin kin amince kina so na kuma zaki aure ni?" Tayi shiru, ya karyar da kai yace "hmm Hibbah kinyi shiru har cikina ya d'uri ruwa fa," tayi dariya "sai kace wani mai lefi?" "Ai gara ace lefi nayi zuciyata ta kasa nutsuwa," tad'an sauke ajiyar zuciya "to ka bari sai naje na fad'awa ummana." Ya dubeta a nutse "shikenan iyaye sune gaba da komi Hibbah na baki dama Amman dai ki tausayawa bawan Allah nan, Zan Kira ki a waya naji yarda kukayi," ya bawa Nawaz kud'i "Nawaz rik'ewa Auntyn ka ko?" A daidai sanda motar Faheem ta sanyo kai ko kallonsu baiyi ba ya shige cikin harabar gidan, 'yar hantar ta saida ta motsa sukayi sallama da Jabeer ya huce sukuma suka tawo gida. B'angaran Faheem kuwa yana shiga ya zauna kan gado gami da jefar da takardun yayi jim zuciyarsa zafi take da tana tafasa sai yaji gumi ta kowanr kofofin gashinsa kamar Mai had'iyar wuta, ya kasa sanin wannan abu ciwo ne ko lalura ne ya rasa meke masa dad'i, ya huro iska mai d'umi a bakinsa zafi dad'a k'aruwa yake a ko ina na jikinsa, mik'ewa yayi ya shoga toilet ya sakarwa kanshi shower snyin ruwan ya ratsa shi had zuciyaarsa, bai san iya lokacin da ya d'auka ba sannan ya fito ya kunna AC ya kwanta ya d'ora kansa bisa pillow ya lumshe idanunsa. Yana tunanin wai shin me yasa ya damu kansa da yarinyar nan? Shi fa ba sabgarta yake shiga ba don me yake jin zafo don ya ganta da wani ina ruwanshi da sabgarsu? Don me zai tunzura haka don ta fit a bada izininshu bane ko kuwa metayi masa ya b'ata ransa har hankalinsa ya tashi haka? Ji yayi anyi masa kiss gami da shafo sajensa, juyowa yayi ya rumgumota yayi ajiyar zuciya, ya lalubo abinshi duk lefinta ne da bata tarairayarsa bare ta kwantar masa da hankali in ya shiga damuwa. Juyowa tayi suna kallon juna abinda ta gano a idanunsa ya tabbatar mata akwai rikici wani abu ya tab'o mata shi. Ta kuma k'ura masa ido "dear me yake damunka ne naka ka sauya ba kamar yadda nake dawowa na sameka ba," bai fad'a Mata abinda me zuciyarsa ba sai dai yace Mata wai baijin dad'i tunaninta da kewarta suke damunsa, nan ta shiga yi masa kisses masu zafi don k'ok'arin mantar dashi dan tasan lefin tane Sam bata bashi kulawa kullum ita tana wajen aiki kamar agogo.. *** Hibbah na zaune a d'aki taga mutum kawai a gabanta a karo na biyu ya kawo mata ziyarar bazata yunk'urun guduwa tayi ya kuwa yi azamar cafkota kamar 'yar tsana ya rik'e ko motsi bata iyawa, tasa kuka mai ban tausayi yau ta gamu da gamonta kashinta ya bushe in dai kisa ne yau Faruq ya karta. Ya tallafo hab'arta ya juyar da kanta gefe, tsananin bugun zuciyarta yasa taji zata fad'i don dai ya rik'eta ne amma da tuni ta fad'i. Shi kuwa Faruq tamkar wata sabuwar halitta yake ganinta d'an hakin da ka rain a shike tsone maka ido, wai Hibbah ce macen da ya kasa jimiri da dakewa akanta so guda ne kamar Hibbah babu abinda yake buri fiye da ita a *RAYUWA RSA*, duk tsarinsa ya wargaje d'aya bayan d'aya abin har mamaki yake bashi ya tashi hankalinsa idan yana zancen zuci sai ya fito fili yaji yana sambato. A yau tausayi take Bashi a yau ji yake ba mace mai k'imarta, a yanayin sonta da yake addabarsa, don't me why not baisan dalili ba? Ya sassauta murya "Hibbah why? Why Hibbah? Me yasa nake son ki wallahi babu dad'i akwai wani abu ne daga Allah, ni fa na haukace akanki Hibbah ke baza ki Sani ba har sumbato nake idan sonki da tunaninki sukayi min zabi, ranar dana ganki da wannan guy d'in kasa barci nayi Hibbah, son nan shu'umi ne ya canzani Hibbah ya canza min manufa a kanki ki manta da baya daya kasance kuskure ne don a da can ban iya tantance sha'awar da nake miki yanxu kyauta kika mallaka min kanki bazan iya yi miki komai ba sai Allah yasa aure a tsakanin mu Hibbah bud'e idanunki ki dubi masoyinki." Hawaye ne yake zuba a idanunta, yasa hannu ya lakuto hawayenta ya shanye kuma sassauta murya yayi "Hibbah kina sona kuwa?" Saura kad'an ta fad'i yayi saurin tarota kanta yayi gingirim. "Hibbah" ya fad'a da rad'a, wani abu ke taruwa cikin idanunsa, tsorone yasa ta gyad'a mishi kai alamar wai tana sonshi don tasan Faruq sarai baida tausayi da imani kwanda ta bishi su rabu lafiya. Ya kafeta da ido can kuma yayi murmushi "matsoraciya ban yarda da wannan amsar ba ki bud'e bakinki naji muryarki kiyi magana da yawunki," "uhmm ina sonka" muryarta a sark'e ta fad'a. Ya shiga tsantsar farin ciki "are you sure? Kin tabbatar alk'awari ne fa," ta rufe bakinta da hannunta yadda zuciyarta take bugawa zai iyasa jininta hawa saboda tsoro. Ya ja da baya "ina k'aunarki Hibbah zan tabbatar miki da hakan idan kin samu nutsuwar zuciyarki, don Allah ki daina jin tsorona ki amince dani," ta gyad'a kanta, Nawaz ya k'ank'ame shi "uncle kullum kazo sai kasa aunty Hibbah tayi kuka saina fad'awa daddy na." Bata san sanda ta zube k'asa ba ta had'a kanta da gwaiwa, ya shafa kan Nawaz ya zare masa ido tare da d'ora hannunsa a kan leb'ensa yace "shiiit! Keep quiet surutunka yayi yawa parrot, tafiya zanyi gobe zan kawo maka ice cream da ball," Nawaz yayi dariya ya kad'a kansa. Ya kashe bakin surutu tunda zai kawo toshin baki ya d'aga mishi hannu "uncle bye sai gobe," yayi murmushi tare tare da fita daga parlor. Nawaz dafa bayanta "Aunty Hibbah uncle dukanki ko? Saina fad'awa daddy shima ya dukeshi," bata kulashi ba yace "kinji," Sallamarshi ta katse Nawaz ta kasa d'ago kanta bare yayi masa sannu da zuwa, ta runtse idanunta bugun zuciyarta ya tsananta, sai kuma taji wani sanyi yana kad'ata wani abune ta kasa fahimtarsa a duk sanda taji Faheem, bata san ya dinga ganinta da wani lefi, mutum ne mai k'ima a idonta. Ya rumgume me Nawaz suka zauna hankalinsa yana kan Hibbah kome yake sata yawan damuwa? Nawaz ya kalli daddy'n nasa "Daddy, uncle ne ya so shine............." Nan take fuskarshi ta canza kamar an fad'a mishi sak'on mutuwa, d'if komai ya tsagaita a kwanyarsa, wani abu ke faruwa dashi fiye da wanda yaji ranar dayaga Hibbah da Jabeer, dole Faruq yafi tada masa hankali idanunsa sun sauya. Bai sake kallon ta ba, ta mik'e ta shige d'aki ta fad'a kan gado, wani bak'in ciki ya addabeta ya zatayi da *RAYUWARTA*, shiru ma magana ce a wajen Faheem tun a karo na farko yaja kunnanta da gargad'inta akan Faruq gashi ya kuma jin Faruq yazo wajenta dole ya zargi da yawunta da sanint Faruq ke zarya a gidan, haka tayi ta jin haushin Faruq zuciyarta sam bata jin dad'i. Tun daga ranar basu k'ara had'uwa da Faheem ba, sun shiga wasan b'uya naushi ya kuma k'aruwa. Shi kuwa Jabeer ko yaushe yakan tuntubeta a waya yaji wai yaushe zai zo ya ganta, ita kuma ganin Faheem baice da ita komai ba sanda ya gansu da Jabeer yasa bata damu ba ko kad'an tunaninta Aunty Aysha ta fad'a masa komai game da Jabeer, don haka ta bashi damar cigaba da mu'amalarsu. Kamar kullum da yamma rana tayi sanyi ya shigo saidai bai samu damar shigowa harabar gidan ba saboda tsaro daya samu an canza wani mai gadi, kuma ya sanar dashi cewa Mai gidan ya kafa dokar shiga gidansa. Waya ya zaro ya kira Hibbah ringing biyu ta d'auka yace "na k'araso ina bakin gate d'in," "to" ta fad'a tare da kashe wayar ta fito. Tana sanye take da da atampa green light da ratsin baby pink ta lullub'o baby pink mayafi a waje ta iskeshi ta k'arasa suka yiwa juna murmushi, ya rik'o hannun Nawaz yana da san yara sosai yace "Hibbah kina jin dad'inki kullum kike min, ya batun mu kinsan rana bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya," ta sunkui da kanta "ai nace na amince, munyi waya da Umma tayi farinciki," yayi dariyar jin dad'i "to Hibbah na gode da karb'ata da kikayi, ni kuma sainaga abinda ya turewa buzu nad'i dan Zan turo manyana su gana," "kamar ya ban fahimta ba," wani kallo yayi mata harsaida taji kunyarshi "to ina neman izini zan turo manyana wajen iyayen mu, za'a ga Alhaji ko? Hibbah aurene ya kama ceki zaki fi samun nutsuwa hankalinki ya kwanta ki samu wadataccen 'yan ci" Shiru tayi cikin nazarin jawabinsa babu shakka gaskiya ya fad'a domin har yau a rakub'e take gidan mutane matsayin mai aiki, amma in d'akin aurenta ne fa alfarmace da darajarta, ta kalleshi "bazan b'oye maka komai ba kamar yarda kaji a bakin Faruq ya fad'i matsayina a gidansu ni 'yar aikinsu ce, Aunty Aysha ita ce ta taimakawa *RAYUWATA* ta bani kulawa da ilimin da nake yi, dan haka kai tsaye bazan amsa maka ba har sai nayi shawara da Aunty dan bani da wadda ta fita a duniyarnan sai Umma," yayi d'an murmushi "naji bayananki kuma na gamsu, nidai na ganki nace ina son ki, ra'ayi nane na gamsu dake Hibbah don allah nake sonki," "na fahimce ka, kuma ka kuma bani dama dai na sanar da aunty," yayi dariya "kina son Auntyn nan da yawa," "ba doleba masoyinka ai masoyinka ne," ya kuma yin dariya "to na gode sai kuma yaushe?" D'as d'as k'irjinta ya data gano motar Faheem, a d'an sace ta kallo shi ko inda suke bai kalla ba, mai gadi ya bud'e k'ofar tare da d'aga masa hannu "barka da dawowa," hon yayi masa ya shiga ciki............. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:23 PM] Maman Najma Author P1: Yana mamkin meya kawo ta gidan ya Faheem. Hibbah kuwa tana shiga gida d'akinta ta nufa ta zube a kan gado ta shiga rera kuka, tana mai jin zafin abinda Faruq yayi mata ace a gaban saurayinka yayi maka wannan rashin mutuncin wannan wace irin *RAYUWA*ce? Ta kuma rushewa da kuka tana kuma tunano *RAYUWARTA* ta baya. Nawaz ne ya shigo rik'e da chocolate a hannunsa yana sha ya mik'o mata "Aunty kinga uncle ya bani chocolate," da sauri ta goge hawayen ta tana murmushi tace "to jeka sha Nawaz nima bara na shiga kitchen," ta mik'e ta nufi kitchen ta had'a musu dinner ta gyara kitchen d'in, tana gamawa taji ana kiraye kirayen sallah tayo alwala tazo ta gabatar da sallar, ta d'ebo abinci ta zauna suna ci ita da Nawaz sai shirme yake mata ita kuwa duk abin da Faruq yayi mata ne yake damunta har ta kwanta tana tunanin abin. Washe gari Monday ta tashi da ciwon kai sakamakon kukan da taci jiya da dadaddare, ta tashi tayiwa Nawaz wanka ta shirya shi school bus na zuwa ya tafi, ita kuwa bata da niyyar zuwa saboda ciwon kan dake damunta don tana gama shiryashi ta koma ta kwanta sai wajen sha d'aya ta tashi tayi duk ayyukanta tana cikin yin mopping taji motsin mutum a bayanta tana waigawa taga Ashe Faheem ne tace "barka da safiya daddy" bai ma jita ba dun ya sha'afa wajen kallonta tunda suke zaune da ita sai yaune ya tab'a k'are mata kallo lokaci d'aya yaji wani abu a zuciyarshi, hazak'ar Hibbah da ayyukanta suna burgeshi sam bata nuna gajiyawarta akan duk abinda Kausar zata sata ga d'awainiyar da take yi masa da yaro. Ta kuma cewa "daddy barka da safiya," ya d'anyi firgit ya kalleta "lafiya" ya huce d'akinsa ya shiga ya d'auko takardun daya manta ya huceta, ita kuwa ko a jikinta ta k'arasa aikinta tayi wanka ta shirya tsam kamar mai fita wajen party ta shiga kitchen ta d'ora musu abinci yana yi ta juye ta jere a dinning ta koma d'aki ta d'an kwanta a hankali bacci yayi awon gaba da ita. Cikin barci kamar a mafarki taji ana shafata taji kamar an danneta a hankali ta bud'e idanunta wa zata gani Faruq ne a kanta wani wawan ihu ta saki tare da tattaro k'arfinta ta tunkud'eshi ya fad'i k'asa da gudu ta ta fito parlor kicib'is sukayi da Faheem daya dawo hannunsa rik'e dana Nawaz da gudu ya rjn [10/26, 9:24 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page3⃣1⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Jabeer yad'an fahimci wani abu akan fuskarta amma bai son yi mata bin k'wak'k'wafi ya d'auko wata leda a cikin mota ya bata don Nawaz tuni ya tafiwajen daddy'n shi. Tayi masa godiya sukayi sallama ta shiga ciki, bata iske kowa a parlor'n ba ta shige d'akinta tare dayin 'yar ajiyar zuciya. Labarin zuciya a tambayi fuska tana tsoran Faheem in dai ya ganta da wani jikinta yakan bata wani abu Wanda ta kasa tantance komene shi, tana son ko sau d'ayane su gaisa da Jabeer don ya fahimci irin manufofinsa, don d'an mutunci ne aurene ya kawoshi ba wai wani shashanci ba. Ta yunk'ura ta bud'e ledar wani k'amshi ya daki hancinta mai dad'i, wani material ne marun mai shegen kyau da mayafinsa da takalmi sai turare da mayuka da kud'i dubu biyar, wani card mai hoton zuciya yafi tafiya da hankalinta, ta d'akko ta bud'e kalaman k'auna ne taci karo dasu Wanda suka sanyaya mata zuciya, karo na farko da taji ta gamsu ta amince da auran Jabeer, don miji ne na k'warai ta lumshe idanu, hak'ik'ashi d'in ne take gani Jabeer yana da kirki yana Mata so na tsakani da Allah. Faheem yana shiga d'aki yayi wurgi da jakar hannunsa ya d'ora kansa a pillow rikitaccen abun yana da rikirkita tunani da wahalar fahimta, zuciyarshi ta Gaza sarrafuwa yana da juriyar gaske akan duk abinda ya jarrabtu gareshi amma me yasa ya kasa daurewa? Allah mai iko ya dafe zuciyarsa abinda yake ji a cikinta bazai iya fad'a fatar baki ba, ya runtse idanunsa shi bai tab'a samun irin wannan matsalar Mai zafi a cikin zuciyarsa ba, ya lalubo wayarsa tare da earpiece yasa a kunnensa k'ira'ar sudais ne ke tashi harshensa nabin surar tiryan tiryan ya haddace ayoyin nutsuwa ya samu da yak'inin wani abu ba makawa zai iya kasancewa dashi. *** Su Hibbah suna ta kiciniyar fara exams (WAEC) ta maida hankali tuk'uru wajen karatunta dan ganin result d'inta yayi kyau, sabon malami aka kawo musu don yi musu lesson d'in waec, ranar wata laraba kamar yadda suka Saba ita da fauzy suna zaune a cikin ajinsu suna solving wani physics dayake babu malami a cikin ajin, wata yarinya ce ta shigo tare da neman excuse tace "wai Hibbah Mukhtar Muhammad tazo inji uncle Sadeeq," suka kalli juna ita da fauzy sannan ta kalli yarinyar "kice masa ganinan," ta fad'a tana mik'ewa, direct office d'inshi ta nufa da sallama ta shiga ya amsa ta gaisheshi, bai amsa ba sai nuna mata d'aya daga cikin kujerun office d'in. Ya dubeta yayi mata murmushi "barkanki da safiya 'yar kyakykyawa muryarki tana da d'an karan dad'i," ita dai Hibbah batace komai don a d'osane take akan kujerar, kanta a k'asa tana murza zoben hannunta shi kuwa ya zuba mata idanu ta tsargu da kallon da yake mata. Matashi ne dogo siriri fari idanunsa a tsatstsaye suke irin na mashahuran 'yan duniyar nan, inyana kallon mace dole gabanta ya fad'i gashi kamar maye idan ya k'ullawa mace. Uncle Sadeeq shu'aibu kenan tunda yazo ya k'ella ido akan Hibbah ya kasa nutsuwa duk da yaga yarinyar bata hannu bace, amma idan ya k'ullawa mace saiyasan yadda yabi ya yaudareta, balke mace irin Hibbah ina zai iya bari, ai kota wane hali sai ya bi harta sallama masa don yaga kamar tsoranshi take ji. Ya dubeta "Hibbah kenan gaskiya kina da baiwa dan nidai ban tab'a con karo da irinki ba gashi muryarki akwai sanya mutum kasala," yana wani murmushin k'eta irin nasu na salon yaudara, ya janyo take away d'insa dankali ne da k'wai sai k'atuwar kaza ya Fara ci, "bismillah, ko na baki ne a baki? Kinsan ke ta dabance" ta kalleshi mamaki yake bata sosai "na gode ni Zan koma class," "haba Hibbah me yasa? Ko kin gaji da hirar tawa? D'auko min maltina a fridge," haushi taji kawai tasan d'an iskane ba mutumin kirki bane ta mik'e ta nufi fridge din. Ya k'urawa bayanta ido dama hikimarsa kenan idan ta tashi ya k'are mata kallo duk da hijjab d'inta yayi masa garkuwa amma hakan bai hanasa bin k'wak'wk'wafi ba. Ta ajiye masa zata tafi yayi saurin cewa "no no baby zauna tukunna ban gama ba ai," ta kuma had'a rai don dai babu yadda zatayi ne da tuni ta ci masa mutunci. Yayi dariya "smile mana Hibbah akwai lefi don nace ina sonki kinyi min ne, naga har yanzu a tsorace kike Dani ki saki ranki, ina sone mu more *RAYUWA*rmu, abinda za'ayi yanzu zan baki address d'ina ko?" Waro ido waje tayi tace "uncle me kake fad'a haka gaskiya ni ba 'yar iska bace," ta kuma bata rai tayi tunananin zaiji haushi yace ta tafi sai ma taga yayi dariya "no problem mai sonka shi yake binka don haka ni idan abu yayi min bana damuwa kiyi min kwatancen gidanku ni zanzo," ta kuma zaro ido wai ita awa takai wannan gidan Faheem ai ta shiga uku, to tamayi me da d'an bariki, "akwai dokoki da yayana ya kafa a gidansa ni bana tsayawa da kowa," ya fashe da wata muguwar dariya, da sauri ta fita tana tunanin kodai tab'ab'b'ene, ya bubbuga table d'in dake gabansa yace "ta yaro kyau take bata k'arko idan kinsan wata ai bakinsan wata ba." A tsorace ta isa class d'in fauzy ta kalle "Hibbah lafiya na ganki duk a tsorace," murmushin k'arfin hali ta k'ak'aro "ba komai fauzy," "to me un Sadeeq d'in yace miki?" Hibbah ta d'auko physics textbook d'in tana cewa "kawai wani aiki ya sani," "uhhmm Hibbah kenan kina k'ok'arin b'oye min wani abu ne, amma ki sani Uncle Sadeeq ni ya fara kira akan batun yana sonki bai samu dama bane shine ya rabu Dani," Hibbah tai mata kallon mamaki "amma shine baki tab'a fad'a min ba" "to ai gani nayi ba wani abun bane tunda mun rabu da shi akan ya hakura, amma ke me yace miki?" Hibbah ta kwashe duk yadda sukayi ta fad'a mata, fauzy tace "dama fa malamai suna ta fad'a wai d'an iskane don school d'in daya baro an tab'a kamasa da wata d'alibarsa," Hibbah ta gingina kai "tab' ai kuwa nan bazai samu matsuguni ba," "ai kuwa dai kuma wallahi ya kuma kiranki sai mun had'ashi da principal" fauzy ta fad'a da masifa, haka sukayi ta tattauna maganar har aka tashe su. Da yamma Nawaz yana zaune wajen Isah mai gadi suna wasa don Isah akwai barkwanci, ya lek'o yace "soja" don haka yake kiran Nawaz don yaga Nawaz akwai son wasa da bindiga sai ya saita Isah yana cewa "fire". Isah yace "Nawaz jeka cewa Hibbah tayi bak'o na fad'a masa dokar Alhaji shiyasa bai shigo ba," da gudu ya shiga cikin gidan "Aunty Hibbah uncle Jabeer," bata yi mamaki ba don wasu lokutan akwai matsalar network sai kayi ta kira yaki shigowa. Wani leshinta ta d'auko purple ta sanya tayi kyau ta fito, tayi zaton sabuwar mota ya canza sai da tayi tozali dashi ta tub'une fuska kamar kashin shanu, tana tunanin ya akayi mutumin nan yasan gidan nan don bak'in naci. Wannan nataccen murmushin nashi yana kan fuskar shi, idanunsa k'uru k'uru a kanta ya lashi leb'ensa tare da had'iyar wani miyau k'ut, ashe hijjab d'in nan yana hanasa ganin kaya, shi duk abinda yake nema a wajen 'ya mace ya gano shi gun yarinyar nan. Ta k'araso gami da kawar da kanta gefe shi kansa yasan bai samu masuk'i ba a wajen ta, ko kad'an baiji ba shi sai burge shi ma da take yi, "Hibbah baby bana son ki shan kunu da cin magani, sonki ne ya ingizo k'eyata tiryan tiryan na biyo ki har gidan ku, banga lefin mai gadinku ba don a kan aikinsa yake shi yasa na tsaya anan to amma mu shiga mota don ina buk'atar yin sirri da ke kin gane?" Ta tsuke baki "ina baka hakuri, saboda na fad'a maka yayana bai barina na fito don inada mijin aure," yayi dariya "na fahimce ki babyna bani da damuwa da mijin da zaki aura, ai nima ina da aure kawai dai inason mu k'ulla k'awance ne cikin sirri, babu wanda zai sani idan kina so ma sai mu dingaa fita Abuja ko Lagos mu killace acen ba mai sanya mana idanu muyi soyayyarmu a cikin weekend, idan kina so ma a jirgi zan dinga killace ki don bansan kisha wahalar mota," wani taikici ya tokareta a wuya "wannan ba harkata bace ni 'yar mutunci ce kamar yarda ka gani a siffance sai kaje ka nemi dai dai dakai k'warya tabi k'warya," "haba baby sone yake d'awainiya dani in banda haka da tuni nabar wajen nan" ta kalleshi "to ka bari mana ni na rik'e maka k'afa ne?" Da gudu motar Faheem ta huce su, uncle Sadeeq nata yi mata surutu kamar aku, Sam bata fahimtar abinda yake fad'a hankali ta nakan Faheem. Faheem ya k'urawa inda suke ido a hargitse zuciyarsa ta tunzura zafi take yi masa, shi kanshi mamakin kansa yake yaushe ya samu wannan zafin ran? Wannan abida yake yi harara cikin duhu ne iskace take wahakar da mai kayan kara don yarinyar bata ma san yanayi ba ga kwashe kwashe data tsira suyk tacin karansu babu babbaka, to mema ya kawo Sadeeq Shu'aibu nan wajen? Ya sanshi cikakken sani don tare sukayi secondary school, amma irin abotar nan da batayi nisaba, irin alak'ar makaranta ce da angama kowa ya kama gabansa sai dai idan wani dalili ya had'asu a gaisa da juna. Amma hakan bai hanasa sanin halayyar Sadeeq ba don yanajin labaran a wajen abokansu na neman mata, shiyasa Faheem bai fiya son mu'amala dashi donshi duk abinda zai zubar masa da mutunci da k'imarsa a wajen Jama'a bai sonshi, shiyasa duk macen daka ganta da Sadeeq dole ka zargi wani abu a tsakaninsu. Da k'yar ya shiga gidan ya kasa zama a parlor kamar yaje ya gargad'I Sadeeq kar ya sake ganinsa da Hibbah, to amma in b'era da sata daddawa ma da wari, ita ta bashi daman zuwa yasan tun sanda suke tare? Ko sallama basuyi ba ta kamo hanyar gida, tana shigowa tayi tozali da wani kallon tuhuma da yayi mata wani burki taja tayi tuntub'e da fushinsa dan ta gani yau a fuskarsa ta nuna. Jikinta sai rawa yake hantar cikinta ta yamutsa yau karon ba dad'i, saboda zabar b'acin rai har fuskarsa ta canza kamar fuskar Faruq idon zaici zalinta. Cikin sand'a sad'af sad'af zata wuce, yace "zo nan...............," *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:24 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page3⃣2⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Sautin muryar data ji yasa cikinta wani irin hautsinawa, ta durk'usa kanta k'asa tana sauraron hukuncinta may be taji saukar mari ko kuwa rufeta zaiyi da duka. "Don me kike kawo min irin wad'annan 'yan iskan gidana an fad'a miki dandalin bariki ne? Tun yaushe ma kike mu'amala da shi?" Ta kasa cewa komai sai k'asa da ta kuma yi da kai, "to bazan amince da wannan iskancin da rashin mutuncin ba da kin jawo Faruq yau kuma kin janyo wani har kin Bashi dama yazo min gida saboda nan ne matattarar 'yan bariki ko? Ki sani bana d'aukar nonsense na kuma fad'a ak'idata d'aya ce banazanjawa, na tsani munafinci gara ki nuna kanki kawai nasan inda kika dosa ba Wanda zaiyi tunanin idan an sa miki yatsa a baki zaki gatsa, kin bani mamaki kin bani kunya kisan yadda za kiyi da wannan kwashe kwashen banzan naki koki kama gaban ki!!" Wasu zafafan hawaye ne suke sauka a kuncinta, Kalmar k'arshe itace take dawo mata "koki kama gabanki!" Me wannan kalmar ke nufi kenan yana yi mata Kora da hali ne ko yaya? Garam! Ya buga k'ofar har tsakiyar kanta ta rintse idanunta da gudu ta shige d'akinta, wani abu yana mata yawo a cikin zuciyarta ta rasa gane menene wannan bak'in cikin zuwan uncle Sadeeq ne? Ko kuwa na mummunan zargin da Faheem ke mata ne, abin da take gudu shiya faru shikenan mutuncinta daya ke gani ya zube a idanunsa, dama shirun da yake yi mata tarata yakeyi yau ta cika masa ciki shiyasa yake mata kora da hali, ita duk cikin su Jabeer ne kad'ai take so, Jabeer mutumin kirkine yana da halaye masu kyau shiyasa ma tabar kyakykyawar alak'a ta shiga tsakaninsu, kuma shine dai yake zuwa da yardarta, amma Faruq ba ita ta kawoshi ba hasali ma baisan zai ganta a gidan ba, balle Wanda ya janyo fitinar uncle Sadeeq. Nawaz yazo ya kwanta akan cinyarta "aunty Hibbah kije kicewa daddy yayi hakuri naje yace baya son hayaniya," ta shafa kansa "to Nawaz ka bari ya huce ya daina fushin sai muje na bashi hakuri," ya gyad'a kansa kawai. Ranar har dare bata da wani sukuni maganganun Faheem ne kawai suke dawo mata, cikin tsakiyar dare ta kasa barci sai faman juyu take yi abin ya dami ranta bata son b'atawa mai kyautata, kallon mutuniyar banza Faheem ke mata baza ta iya goge wannan bak'in fentin ba, gashi yanzu yana yi mata hannunka mai sanda koda bazai kuma yi mata magana ba zaiyi ta tarata ne rana d'aya ya fad'a mata b'uru b'uru, da wad'annan maganganun ta kwana. Da safe gudanar da komai yadda ta saba saidai batayi sammakon fita ba yadda ta saba, bayan sun fits gaba d'ayansu ta d'auko Jakarta, yau ko school baza ta jeba don gidan su Umma kawai zata koma ta dubi hoton Nawaz dake bedside table yayi matuk'ar kyau tun ranar da tazo Nawaz ya bata shi, ta d'aukon ta rumgume wasu k'walla suka d'iso mata, baza ta iya kwatanta shak'uwarsu da Nawaz ba, ko ya zaiji idan ya dawo ya nemeta bai ganta ba, batason rabuwa da shi amma babu yadda zatayi. Ta mayar da hoton ma'ajiyarsa, bata da number Faheem data yi masa text message ta fad'a masa. Ta bud'e Jakarta a zaro paper da biro don rubuta sak'on da zata bar masa sai taji hannunta na rawa, a hankali ta fara rubuta masa sak'on _daddy ina neman afuwa, nayi abinda yake lefi ne a wajenka d'an Adam ajizi ne mai kuskure ne a koda yaushe, nasan akwai rashin fahimta da kayi min daddy bansan yadda Zan goge lefina a wajen ka ba, amma kayi hakuri Allah ya huci zuciyarka, mutunci madarane nasan nawa ya zube a idanunka kuma bazai tab'a kwasuwa ba to amma bincike da tuhuma wajibine akan mai lefi kafin a zartar masa da hukunci. Gaskiya d'aya ce daga k'inta sai bata nima ina da buk'atar ta inada dalilai daya sani tilas zanbar gidan nan, ba wai don ka nuna min kuskure na ba, bani da Kalmar yabo da godiya a wajenka na gode da kyautatawar da kayi min allah ya saka da mafificin alkhari. Ka bawa Nawaz hakuri ka rarrasar min shi Nina zanji ciwon rashin Nawaz!" "Bissalam, daga Hibbah._ Ta goge hawayenta ta ninke takardar ta ta shiga d'akinsa don baya kullewa saboda kullum sai ta gyara mishi d'akin, ta d'ora akan pillow, ta fito tare da kulle gidan. Ta doso gate d'in ta hango Isah yana washe baki ya k'araso yana cewa "yau tafiya zakiyi kenan wato kinyiwa wazirin naki wayo, amma fa yau mai gida zaisha fama," tayi murmushi "ai bazan dad'e ba kwana biyu zanyi kawai," "to Allah ya kaiki lafiya bari na d'aukar miki jakar," ya d'auki jakar suna tafe suna hira har suka yi nisa ta juyo ta sake kallon gidan, ko zata kuma zama a gidan ko kuma kallon k'arshe take yi masa, kai bata jin zata kuma sake dawowa gidan ko da wata rana ne, ta goge k'walla don kar Isah ya gani, ya tsaida mata adaidaita sukayi sallama ta d'auko dari biyu ta bashi yayi ta godiya, yana d'aga mata hannu "a sauka lafiya," Da rana tunda Nawaz ya dawo Isah ya tareshi suna zaune a benci yana ta janshi da wasa shi kuwa duk ya shiga damuwa yana ta damun Isah wai har yanzu aunty Hibbah bata dawo ba, haka Isah yayi ta biye masa har Faheem ya dawo da yammaci lik'is yayi mamakin ganin Nawaz a bakin get da uniform a jikinsa. Da gudu yaje ya rumgume shi tare da zubar da jakarsa, yana ajiyar zuciya cikin murya mai sanyi yace "daddy aunty Hibbah bata dawo ba har yanzu," ya dube shi a nutse kamar ya sokeshi da mashi "bata dawo ba?" Ya nanata a cikin ransa, tuni ya soma wani zargin ya d'auki jakarsa yana lallamin Nawaz "karka damu my son yanzu zanje na d'aukota a wajen aiki," ya gyad'a masa Kai. Isah ya rugo da gudu ya kawo masa mukulli, ya karb'a ba tare da yayi magana ba. Ya bud'e gidan suka shiga m, tsit parlor'n babu motsin Hibbah daya saba ji da k'amshin girke girkenta, lallai mutum ma a guri rahama ne, tun anan yaji wata kewarta da kad'aicin Hibbah, Wanda ko Kausar matarsa bai tab'a jin hakan ba akanta ba, ko dan ta horesu ne da rashinta oho. Ya dafe goshinsa ga mamakinsa sai ya rasa meke masa dad'i babu shakka Hibbah tafiyarta tayi tunda har ta bada ajiyar mukulli, don bata tab'a tafiya wani wajen ba tare da izininsa ba, sai dai ko idan Jabeer ne yazo kuma idan ya dawo yakan iskesu a waje, to amma me yasa bai tab'a d'aga hankalinsa ba kamar na jiya kodan ya ganta da wannan d'an iskan Sadeeq ne. Ya shiga d'akin yana bin ko ina da kallo babu wata alama da zai nuna tana nan ba tafiya tayi ba, yayi ajiyar zuciya, ashe Hibbah bata da hankali tana nufin ta bar gidan kenan ita mai zuciya saboda 'yan iskan samarinta, sai taje a sauka lafiya shi dai ba zai iya d'auka ba. Ya shiga toilet ya watsa ruwa sanyin ya ratsa shi, ya fito ya shirya ya d'an kwanta yana d'ora kansa a pillow yaji wani abu a Kai, ya lalubo takarda ce ya k'ura mata idanu shi dai yasan bai ajiye takarda ba, ya bud'e yana nazari. Lumshe idanu yayi daya kai k'arshe, Hibbah, zuciyarshi tana bugawa komai ya rikice masa, Hibbah abin har yana Bashi mamaki da al'ajabi, ya fito waje ya yafito Isah, da sauri ya taso. "Ranka ya dad'e," "am yaushe yarinyar nan ta tafi ne?" "Bayan kun fita ne tace min kwana biyu zatayi harma ta bani d'ari biyu ranka ya dad'e," ya kad'a kai "shikenan kawai dama bansan da tafiyar bane." Ya shiga motarsa tare da barin gidan, wai meke damunsa ne? Duk ya rasa nutsuwarsa, yanzu ina tafi neman Hibbah bayan ta yankewa kanta hukunci, kawai kalamanta ne suka karya masa zuciya, haka kawai zai dami kansa sai kace Wanda yasha k'awa? Yayi tsaki tare da juya kan motar ya koma gida. Ita kuwa Hibbah tunda taje gidan Umma bayan sun gaisa ta kasa komai bata da wata nutsuwa, Umma ta fahimci hakan a tattare da d'iyar tata, "Hibbatullah ganinki nayi tafe da kayanki, ko dai wani abune ya faru hankali na ya tashi," ta maida k'wllar da ta tawo mata don kar Umma ta gani tace "ba komai Umma sunyi tafiya ne su duka shiyasa nima na tawo nan, Umma Jabeer da gaske yake fa," ta fad'a mata yadda suka yi dashi. "Wannan aniyace mai kyau Allah ya tabbatar mana da alkhari zan fad'awa Alhaji, kuma kije ki shawarci Auntyn ki don mai k'aunarka har a bada ya gama yi maka komai kuma ta b'angarenta yaron nan yazo ta san komai game dashi," wayarta ce tayi ringing Jabeer ne sai taji zuciyarta tad'anyi sanyi ta mik'e tana satar kallon Umma, Umma tayi dariya "wayar sirikin nawane dai na sani" ta fita tana murmushi ta kara wayar a kunne "tunaninki nake yi na k'osa muyi aure wallahi, yaya alkawarinmu kun tattauna da Umma?" "Uhm yanzu maganar da muke yi kenan da ita ta sanya albarka amma tace zata fad'awa Alhaji," ya d'anyi murmushi "naji dad'i kuma nasan insha Allah akwai nasara zasu bani goyon baya, Hibbah in dai na sameki burina ya cika ki saurare no da yamma zanzo," "to amma ina gidanmu bara zanyo maka text message na kwatancen unguwar," "ok na gode ki gaishe da Umma," da haka sukayi sallama. Tana ajiye wayar kiran fauzy ya shigo tana d'agawa ta fara yi mata masifa "haba Hibbah dama kinsan bazaki je school ba yau kuma jiya kika k'i bari mu k'arasa wannan physics d'in," "no fauzy ba haka bane ina cikin matsala ne ni kaina bansan bazan zo ba, yanzu haka ma ina gidan Umma," ta maimaita "kina gidan Umma? Mai ya faru?" Nan Hibbah ta kwashe komai ta fad'a mata, fauzy tace "amma wannan mutumin anyi d'an iska, kinsan Allah ya taimake mu ba jiya bane don yau aka kamasa da wannan d'alibar tasa Dana ke fad'a miki yanzu maganar da nake miki ma an mik'ashi kotu gobe za'a fara Shari'a," Hibbah cikin razana tace "garin yaya fauzy?" "Hmmm ai in fad'a miki zuwa yayi school d'insu d'aukota, ashe vice principal yaga lokacin da suka fito da ita a mota, suna fita yaje ya fad'awa principal shine fa suka d'auko masa police suka biyoshi ana zuwa office d'inshi aka gansu suna aika aika," "tab to allah ya shirya" fauzy tace "ameen ya goben amma zaki shigo ko?" "In allah ya yarda" "To shikenan nan ki gaida su Umma," da haka sukayi sallam.................. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:24 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page3⃣3⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Wannan page d'in naki ne Surbajo tawa ban manta dake ba kina raina Allah raba ki da mak'iya, kinfi k'arfin duk wani mai hassada💪* Yayi d'an tsaki ya ture plate d'in gefe, cikin kwanki biyar kacal da yajin aikin Hibbah ya ritsa da kowa na gidan komai ya tsaya cak, sai mutum baya nan ake sanin amfaninsa, shi yafi kowa sanin mahimmancinta a gareshi, gashi nan gidan yau kwana biyar kenan ba'a share ba bare a goge k'ura, to waye ma gwagin yin aikin shi ko Kausar. Matar da take fice warta aiki kuma ko tana nan baza ta iya ba, basu gane rashin Hibbah gib'ine a gidan ba sai a wajen girkinta babu abincin nan Kala Kala na yay daban na gobe daban, yau gashi kwana biyar kenan kullum abinci d'aya sukeci ba canji har ta gundire su. Babban matsalar da ta tashin hankalin Faheem bame kular masa da Nawaz, ya rasa yadda zaiyi da damuwa Nawaz ya daina cin abinci har yayi 'yar rama, ga damunsa da kuka da yake yi shi dai a kaishi wajen Aunty Hibbah zai je wajenta, abubuwan da ta saba mishi sun shiga jikinsa ya shak'u da ita sosai fiye da uwar data haife shi. Da daddare baya barinsa yayi barcin kirki dan rigima yake masa shi wai dole wajen Hibbah za'a kaishi. Ashe ko kare ne da ranarsa ita kanta Kausar duk da ba kulata take yi ba to amma ta Saba da abincinta sannan ga d'awainiyar da take yi Mata da yaro har sun shak'u, bata da wata fargaba da wahala hankalinta kwance yake tasan Hibbah zata kula dashi. Kwana biyu da bata ganta ba sai ta dinga yiwa Faheem k'oeafi tana tambaryarsa ina Hibbah ta tafi bata sanar da ita ba, haushine ya cika shi yace "tayi tafiya," a ganinsa duk lefinta ne, ita ta tab'arb'ara jin dad'in gidan, da tana tarairayar su da menene zai dame su. Shi bama damuwarsa kan Hibbah tayi yawa bawai don tabar kula masa da gida ba, kad'aicinta ya danganta da babban al'amari ahi kad'ai zai iya sanin abinda ke damunsa, baisan abin ya shahara haka ba saida ya daina jin motsinta a kusa dashi, yaje bakin k'ofar d'akinta ya kasa kunne ko zaiji motsinta amma shiru ya bud'e d'akin ya lek'a babu kowa a ciki d'akin har yayi k'ura, Anya kuwa zai iya hakuri? Ya zaro wayarsa har ya dannan layin Aunty Aysha yayi saurin katsewa, karfa Aysha tayi tunanin wani abu don bata San Hibbah bata nan ba, bai jin dad'i Sam a ransa yasani yayi rashin wani abu mai mahimmanci wadda ya rasa yadda ya kasa sarrafashi. Ya sauke ajiyar zuciya, ya kalli Nawaz dake jikinsa, Bashi da lafiya tun jiya da daddare da yaci wani farfesun kifi ya sashi amai da ciwon ciki, shiyasa yau ko shirin makaranta baiyi masa ba. Nawaz ya fara juyi ya rik'e cikinsa yana murk'ususu, hankali tashe Faheem ya d'agoshi ya rumgume shi "Nawaz menene?" Yasa kuka "daddy cikina ciwo," "oh God sannu sannu kaji," ya d'auko maganinsa na jiya ya bashi, sannan ya d'aukeshi ya kaishi toilet yana masa wanka Nawaz ya shiga kwararo amai, habawa duk hankalinsa ya kuma tashi don ko k'uda baya son ya tab'a Nawaz tilon d'ansa d'aya daya mallaka don Kausar ta hana kanta haihuwa sai nan da wasu shekaru. Ya gama yi masa wanka ya saka masa kaya ya Bashi tea nan ma ya amayar ya kasa jurewa ya d'aukeshi suka nufi asibiti. Suna zuwa doctor ya dubashi yayi masa test d'in fitsari da jini yasa aka dauki hoton cikinsa duk babu wata gagarumar matsala, kawai dai cikinsa ne baison abinda yaci shiya b'ata masa ciki. Doctor ya sanya mishi ruwan don jikinsa yayi sanyi sosai, saida Nawaz ya samu barci sannan ya kira Kausar ya fad'a mata komai. Hankalinta a tashe ta shigo ta ganshi yana barci ta zauna tana shafa sumarsa tayi ajiyar zuciya cike da tausayin d'an nata wani mummunan tunani ya fad'o mata _yanzu idan Nawaz ya mutu yaya zanyi?_ ji tayi k'irjinta tayi mugun bugawa. Ta dubi Faheem yana rik'e da hannun Nawaz da aka Sanya mishi k'arin ruwa don kar ya motsa ya goce, kamar yasan abinda take tunani wani abu ta hango a cikin idanunsa tsabar damuwa ce kawai, Faheem yana son yara sai dai babu yarda zaiyi ne yabar abin a zuciyar shi. In banda yahudanci da sab'awa Allah, bawa yace shi zai zab'awa kansa yaran da yake son ya Haifa wannan ai halaka ne, ka manta Allah shi ya halicceka shiyake da hurumin zab'a maka komai na rayuwa, kuma yarda yaso haka za'ayi don haka tun anan imanin mutum yayi rauni kenan. Ta kewaya hannunta a bayanshi ta sunkuyo ta gefen kunnanshi da sigar lallashi "dear menene ka damu da yawa zaiji sauk'i insha Allah, baka walwala cikin kwanakin nan meke saka damuwa ne haka uhmm?" Ta janyo kujera ta zaune suna fuskantar juna, "kinfi kowa sanin damuwata, dole ne na damu don ni bansan dad'in mace ba, saboda bamu da mahimmanci a gurinki aikinki ya fimu a wajenki baki da lokacin iyalinki, duk wani hakuri nayi a kanki gashi nan saboda ciye ciyen restaurant yaro na ya samu matsala cikinsa ya gurb'ace, kullum ni kenan yawo gidajen abinci sunan ni magidanci ne ina da mata, wani abin bana k'ate bane nifa na gaji mafita zan samawa kaina," ta d'ora kanta akan cinyarsa don tasan ta tab'oshi kuma ya fita gaskiya "kayi hakuri naji lefina na d'auka zansa momy ta nemo mai dafa masa abinci," yayi shiru maganar ta kuma Bashi haushi wato ita dai baza ta zauna ta kula da gidanta ba kenan. Nawaz ya farka yace "Daddy" ya rik'oshi yana shafa kansa "Nawaz sannu cikin ne?" Ya girgiza kai, "zaka sha yogurt?" Ya kuma girgiza kai yace "aunty Hibbah" suka kalli juna, tsaki taja "har yanzu bai manta wannan yarinyar ba sai kace mayya ko kurwars ta kama ne, haba abin yayi yawa," bai kulata ba ya zubo mishi yogurt a cup yana bashi amma surutun Hibbah yake tayi musu, Kausar ta kama mita don haushi taji wai duk kwashe kwashen Faheem ne da Aysha sai da ta nuna rashin amincewarta akan zaman Hibbah a gidan k'ila ma mayya ce. Yayi murmushi "hmmm ki Sani ita zuciya nason mai kyautata mata shi yake sanya shak'uwa har mutum ya ji bazai iya rabuwa da mutumin nan ba domin rashinsa wani gib'ine a rayuwarsa, kinga d'anki ma kenan k'aramin yaro yasan mai tarairayarsa mai k'aunarsa har rashinta ya sakashi damuwa, ina tabbatar miki da kece bakyanan bazai damu haka ba don bai saba ganinki a gida ba bare ki rumgume shi ya shak'u dake kamar ko wace uwa da d'anta, 'yan awoyi kad'an kike bamu sauran duk na aiki ne agogo sarkin aiki, to idan mafarki kike ki farka don wallahi kinji na rantse na kusa sama mana mafita," Kausar taji zafin kalaman Faheem ta wurga masa wani kallo tama kasa magana sai huci take ta warto jakarta ta fita fuuuu babu ko sallama. Ya tab'e baki, ya cigaba da kula da Nawaz yana ta biye masa suna surutu har bacci ya d'auke shi ya gyara mishi kwanciya. Washe gari da sanyin safiya ta shigo tana cika tana batsewa, sai da taga jikin Nawaz da sauk'i ta d'anyi saki ranta, doctor ya shigo ya dubashi ya d'an jinkirta Bashi sallama don a cewarsa karsu tafi wani abu ya faru saiya tabbatar da lafiyarsa. Dak'ar Kausar tayi masa magana tana wani kumbure kumbure ta tambayi lafiyar Nawaz, shima a ciki ya amsa mata don ganin wajen aiki zata tafi, azaton shi yau dai zata zauna ta kula da d'anta domin lafiya tafi kud'i, mai makon ma ta dafo wani abu da tasan mara lafiya zai buk'ata ta kawo musu sai tazo musu k'iyau miyau. Sai takardu a hannu sai kace wadda zata kadance kundin ilimin duniya, shi yasan duk wannan aikin da take yi d'anta ya fishing daraja a matsayinta na 'ya mace bata da abinda yafi d'anta mahimmanci a wajenta. Ta dubi agogo "Zan wuce wajen aiki su momy suna zuwa da abinci munyi waya da Safiyya," ko kallon ta bai yi ba "basu da hakkin bani abinci wannan aikinki ne ba nasu ba kuma baki damu ba zaki tafi uzurinki, akwai ranar k'in dillanci, shiyasa wasu 'ya'yan sam basa tausayin iyayensu kuma ba komai ke janyowa ba sai irin wad'annan abubuwan, baka san wahalar d'an daka haifa ba, shi zaiji k'anka bayan ke ba haka iyayenmu suka yi miki ba," ta d'aga mishi hannu cikin hayayyak'owa "bafa tsoranka nake ji ba da zaka dinga fad'amin abinda kaga dama, ka fad'amin ayar da tace don ka aure ni na ciyar dakai cewa akayi a ciyar dani, kuma ni haka tsarina yake bazan canza ba," "ke kuma akace kimin biyayya don ki samu aljanna to idan na nemo abinda Zan ciyar dake yana cikin biyayyar aure ki dafa min, to don haka ki kiyaye yimin ihu aka kinsan ni ba sa'anki bane sannan a k'ark'ashi na kike kin gane koh?" A fusace ta fita, ya cije leb'e wato yayi shi kad'ai ita bazata saurareshi ba. Duk iyalan gidan sunzo momy, daddy yake yana gari da Faruq su Saudat suna makaranta shiyasa basu zo ba, suna zuwa Faheem yace zaije ya d'an kintsa a gida, momy tayi mamaki da Faheem yace mata wai Kausar ta tafi aiki. Da yamma ya kasa jurewa ya nemo number Aysha, ringing biyu ta d'auka bayan sun gaisa tace "Dan Allah yaya kayi hakuri ina tafe an jima zan shigo ya jikin boy d'in nawa?" "Karki samu damuwa da sauk'i sosai," "to harna ji dad'i Allah ya k'ara sauki, yauwa yaya don Allah ina son ganin Hibbah zamu d'an tattauna akan maganar Jabeer wallahi ya dameni yana so a yi auren nan kasan wajen aikin mu d'aya," Gaba d'aya ji yayi wani abu mai Kama da bugun guduma a tsakar kansa, ransa babu dad'i yayi ajiyar zuciya wani abu na nuk'urk'usar zuciyar sa, "yaya kana jina dai ko?" "Hmmm ina sauraronki, bata nan taje gida ne kwana biyu bata dawo ba bansani ba ko lafiya, bani address d'in gidan nasu," "Oh to Allah yasa lafiya don nima ban nemeta ba kwana biyu, ai gidan Alhaji sani ne gidan nasu fa," "Alhaji sani dai wanda na sani?" Faheem ya tambaya "eh shine yaya," sukayi sallam. Sai ya samu kansa da............ *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:24 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page3⃣4⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* ```Tabital pulaaku group ina kuke? Wannan wannan page d'in d'ungurungun nakune, Allah ya barmu tare cikin so da k'aunar junanmu.``` Sai ya samu kansa da kasa samun nutsuwa sai yaje gidansu Hibbah don gaskiya yana so yaga Hibbah, dayake har lokacin momy na nan sai yace mata yana zuwa ya zari key ya fita, direct gidan Alhaji Sani ya nufa, Alhaji Sani ya tare shi suka shiga cikin parlor babu kowa cikin mutumci suka gaisa sosai Alhaji yana tambayarsa ya iyali, suka d'anyi shiru na wasu 'yan dak'ik'u Alhaji yana mamakin zuwan Faheem gidan sa ko Alhaji ne ya turosa ya kasa jurewa yace "Faheem Alhajin ne ya turo ka?" "A'a dama ina sone mu gaisa da Umma tana nan ne?" Alhaji yayi murmushi "to to naji dad'i bara nayi mata magana tana d'aki," Alhaji ya mik'e ya shiga d'aya daga cikin d'akunan cikin parlor'n, jim kad'an sai ga su sun fito shi da umman, Alhaji sukayi sallama da Faheem don shi fita zaiyi. Faheem ya zamo daga kujerar da yake zaune ya durk'usa har k'asa ya gaishe da Umma ta tambaye shi Kausar da Nawaz (ta tab'a ganinsa ne a hoto da Aysha ta nuna mata shi). Yace "wallahi kinga ma shiya taso ni nazo don baijin dad'i ne, kuma ya damu da Hibbah don ciwon da sauk'i akan damuwar," Umma tayi murmushi "Allah sarki bamu sani ba ai da anje an dubo shi Allah ya Bashi lafiya, bawan Allah haka so yake gamuwar jini, badai abinda zamuce muku sai fatan alkhari, Allah ya biya da aljannah," yayi Jim wani abu ya tab'o zuciyarsa yaji dad'in kalaman Umma, yana son ta tashiga ransa sai yaji don me bazai fad'a mata damuwarsa ba damin a maganarta ya fahimci bata da masaniya akan abinda ya faru har Hibbah tayo musu yaji. A nutse ya fad'awa Umma komai abinda ya kasance har yajin da Hibbah tayi musu na tawowa ba tare da saninsa ba, Umma ta kad'a kai "ikon Allah wallahi bansani ba ni nan b'oye min tayi bata fad'a min ba cemin tayi kunyi tafiya ne ni kuma nasan bata iya k'arya ba kuma Allah bai nufa munyi maganar da Alhaji ba, kai amma banji dad'i ba kuma bata kyauta ba. Ita d'in me tafi k'arfin ayi mata fad'a ne idan tayi badai dai ba ka tsawatar mata wannan shine tarbiya, wato tasan idan ta fad'a zanyi mata fad'a shiyasa b'oye tak'i fad'a min, don Allah kayi hakuri," Faheem sai yaji wani iri kamar Umma da girmanta da k'amarta ta dinga Bashi hakuri "a'a Umma babu komai wallahi," wadda take yiwa Umma share share ce tazo d'aukar abu Umma tace ta turo mata Hibbah, sai gata kuwa tana ganinshi tayi turus, zuciyarta tana bugawa kamar zata tarwatse ko a mafarki bata tab'a tsammanin shi ba, ta zube "ina yini Daddy," ya dubeta ya had'e fuska "bazan amsa ba Hibbah tunda nayi fad'a kikayi fushi har kika tawowarki gida bako sallama, kin bani girma kenan? Gashinan kinsa yaronki rashin lafiya yana asiiti kin kyauta kenan?" Ta dubeshi a razane hantarta har ta kad'a ta had'iyi miyau dak'ar idanunta sun cicciko hawaye, Nawaz Allah sarki dama tasan za'a rina bata yi masa adalci ba, ita ma tana nan har d'an zazzab'i tayi shak'uwarsu tayi yawa ita da Nawaz, Allah sarki sak taji tausayin yaron da k'aunarsa na kuma shiga ranta. To yaya zatayi idan ba ta barwa Faheem gidansa ba don yayi mata hannunka mail sanda. Umma kuwa ta rufe ta da fad'a "ni ban san sanda kika koyi k'arya ba halin hofi Hibbah don me baza'a fad'a miki kinyi ba dai dai ba kinfi k'arfi a tank'wara kine, to ki shiga hankalinki idan ka rasa mafad'i a duniya ka shiga uku, wad'annan mutanen sunan k'aunarki mutunan da suka d'aukekan tamkar d'an uwa na jini suke d'awainiya dakai, tun wuri ki sauya tunani ni ban goyi da bayan ki raina na gana da ke ba d'an halak baya manta alkhari, wallahi kar na kumaji kinyi irin wannan shirmen kuma ki d'auki kayanki ki koma, ki bashi hakuri yanzu," Zuciyarta tayi rauni jinkinta yayi sanyi ganin ran Umma ya b'aci sosai gashi tana ta yi mata fad'a abinda bata tab'a yi mata ba, da k'yar muryarta tana rawa tace "daddy kayi hakuri bazan k'ara ba, Allah ya huci zuciyarki Umma," ta fad'a tana share hawaye. Tausayinta yaji sosai ko da yake yaji dad'i umman ta burgeshi don shi mutum ne Mai son a bashi girma da girmama na gaba dashi don haka bai son reni ko kad'an shi yasa Hibbah ta shiga ransa don tana da biyayya da ladabi Sam bata kiransa da Yaya kamar yarda k'annansa suke kiransa saidai tace masa Daddy kamar yadda taji Nawaz yana fad'a. Ta tashi ta d'auko Jakarta, ya ajiyewa Umma kud'i ba yadda batayi ba ya d'auke abinsa amma yak'i yaji dad'in karramawar da akayi masa da sanin ya kamata irin na iyayen k'warai, suka yiwa Umma sallama suka fito. Ya bud'e mata gaban motar don yasan halinta sai ta zauna a baya, ta kalleshi gani tayi ya had'a rai babu alamar wasa a tattare dashi shiyasa ba musu ta shiga. Ya dad'e bai ji annashuwa ba kamar a yanayin nan ya kunna wakar Celine Dion yana sauraron baitukan wak'ar, yana tuk'i cikin nutsuwa, Hibbah ko numfashi bata yi k'wak'wk'wara ji take yi tamkar ta nutse, kunya ce nauyi ne rashin sabo ne, duk sunyi Mata dabaibayi don basu tab'a had'uwa haka gata gashi ba. Ya dubeta a nutse domin duk damiwarsa babu ita ashe Hibbah ce ta hana zuciyarshi nutsuwa, "Hibbah ta Nawaz ya kikayi shiru ne na takuraki ko? Banji dad'i bane akan abinda ya faru ashe fushi ne dake haka, ki sani nayi miki fad'ane don kawai na damu dake ina kishinki tamkar k'annena su Safiyya ya d'auke ki badon haka ba babu ruwana da ra'ayin wani, ina data dai kin huce ko?" Bata ce komai ba, ya dubeta idanunta sunsha kuka kuwa, zata kuma iya ci gaba da yinsa idan har ya takurata sai yaji maganarta don a takure take ya Sani, shi kuwa so yake ta saki jiki dashi ta daina jin tsoranshi haka don haka ya rabu da ita, da haka har suka k'arasa asibitin. Yana gaba tana binsa a baya, sama suka hau basuyi wata tafiya ba suka isa d'akin, suka shiga ta gaishe dasu momy lokacin Nawaz yana barci momy ta mik'e zata tafi wai dama shi take jira ya dawo yamma tayi sukayi sallama tayi masa fatan samun sauk'i suka tafi. Jimawa kad'an Nawaz ya tashi yana ganinta ya mak'aleta yana k'yalk'yala dariya kamar zata sake gudu ta barshi, ta shafa kansa tana dubansa yayi 'yar rama ta share k'wallar data taru a idanunta. Nawaz ya rik'e hannayenta "aunty Hibbah shine kika gudu wajen Ummanki kika barni kinga inda doctor yayi min allura," ta tab'a wajen "sannu Nawaz Allah ya baka lafiya," "Aunty Hibbah nima zan biki wajen Umma." Ta gyad'a Kai "to naji amma sai ka ji sauk'i zamuje," ta ja hannunsa suka fice barandar suna kallon titi dayaga abinda ya bashi sha'awa sai ya dinga nuna mata suna dariya, yana ta bata labarin abinda ya faru bayan tafiyarta. Yana tsaye ya hard'e hannayensa a k'irjinsa yana kallonsu sun burgeshi da Bashi tausayi "Hibbah" ya ambata a zuciyarsa sunan mai dad'i, ga mamakinsa ashe maganar ta fito fili har tabi iska ta isa kunnenta kawai gani yayi tad'an juyo ta kalleshi, suka had'a idanu cikin wani yanayi a hankali ta d'auke kanta, wani sanyi take gani cikin idanunsa sai taji abin yana mata yawo a k'wak'walwarta. "Hey! My boy," duk suka dubeshu, yayi zanzaro da hula Hana sallah a kansa, da siririyar sark'a tana k'yalli a wuyansa har taso ta shak'e sa, "Yaya ya jikin boy d'in?" "Alhamdulillah yaji sauk'i sosai," hankalinsa yana kan Hibbah bai ko damu da ganin Faheem ba, ya d'auki Nawaz ya rumgume shi tare da yi masa kiss a kumatunsa, shi kuwa ya mak'ale hannayensa a wuyansa tare da zagaye k'afafunsa a jikinsa, Faruq kenan yana k'aunar Nawaz shiyasa shima Nawaz yake k'aunar uncle d'in nasa. Hibbah kuwa kallo d'aya tayi masa ta d'auke kanata don har yanzu tsoransa take ji............... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:25 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page3⃣5⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.A.W *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Ya kalli inda Faheem yake a tsaye bashi ba dalilinsa, ya matso kusa da ita abinda bata so kenan, shi a wajensa ba wani abu bane don ji yake kamar ya rumgume ta, wutar k'aunarta yana faman huruwa a zuciyarsa duk sanda ya d'ora idanunsa a kan idanunta baya iya sarrafa kansa, ya matso sosai kusa da ita, bata da niyyar kulasa, "Hibbah kinsan kuwa irin sonda nake miki? Kada ki maida hannun agogo baya bana so ki dinga tuna baya ban tab'a tsintar kaina a irin wannan love d'in ba Hibbah." Ya dafa kafad'arta, a taorace ta kalleshi suka k'urawa juna kallo na d'an wani lokaci abinda ta gani a idanunsa tad'an tsorata don tabbas binda ke zuciyarsa ya fad'a, ta ture hannunsa. Yayi murmushi "wannan gangar jikin mallakina ce sai nayi yadda nake so da ita in munyi aure, don haka ki dena guduna , ni d'in nan zan baki mamakin yadda zaki yi dadi indan na zama mijinki," murmushi tayi don ita a ganinta wauta kawai yake tace "abinda kamar wuya, naji zancen kamar almara ta Yaya zaka aure ni? Ka tuna fa kaso k'unsa min b'ak'in cikin da har na mutu bazan manta shi ba, kuma badon komai ba kawai don zalinci da son Kai, karma ka Fara yaudarar kanka don yarda ba yadda za'ayi dakai wai kai masoyina ne, don Allah na rok'eka saboda girmanasa ka k'yale ni ka k'yale min rayuwa haka." Ya kad'a kanshi "duk abinda kika fad'a gaskiya ne ni kaina ina cikin mamaki da tuhumar kaina Yaya akayi na samu kaina cikin sark'ak'iya har na fad'a tarkon sonki, banji haushi ba ai na fad'a miki kyauta kika sadaukar min da kanki wallahi zuciyata bazata iya daure wani abu dake ba matuk'ar ba aure mukayi ba," "ni kana bani mamaki to wai taya zamuyi aure? Wannan shirmen tunani ne abinda bazai yiwu ba." Yaji zafin maganarta ya take k'afafunta da takalmin k'afarsa, ta runtse ido saboda zafi, Faruq mugune yasan takan mugunta. Ya tallafo tallafo hab'arta yana wannan murmushin nasa na k'eta "dube ni sai na aure idan yaso in na aure ki ki hak'a rami ki binne ni da raina ko kuma kii gunduwa gunduwa da nama na saboda tsabar k'iyayyar da kike min," ya k'ura mata idanu tak'i bud'e idanunta, ji yayu tamkar ya lashi kumatunta, ya hurawa idanun iskar bakinsa duk da a rufe suke. Ta bud'e idon tana dubansa shed'anin mutum kenan gani take kamar baya hankalinshi, Anya ma Faruq baya shan k'waya don abubuwan da yake yi kamar bashi da tunani a k'wak'walsa, duk inda ake neman namiji mai kyau Faruq ya kai sai bashi da hali. Ya lakuce mata hanci, ya matso da kansa kusa da ita sosai ya sassauta murya "ke d'innan yadda kika shiga raina, ni sonki nake Hibbah kamar nayi hauka don Allah me kika yi min ne?" Ta juyar da kanta gefe, ya sa dariya "kin mai dani dodo ko Hibbah?" Yayi k'wafa "wata rana sai kin rumgume ne kinmin kiss, ni kuma shagwaba zan tayi miki," ya d'an ja da baya "ki samu cikin addu'a Allah yasa muyi aure." Ta gyad'a kai cike da mamaki don ita wasa ta d'auki abin "aure? Wani banbarakwai nake jin abin na fad'a maka abin da kamar wuya taya ma hakan zai faru?" "Insha Allah za'ayi, ki fad'a min *I love you* zanji dad'i," kamar ta kurma ihu take ji ta rasa wanda zata cewa tana so sai Faruq. "Kinsan halina sai na rumgume ki a nan ni babu ruwana gara ki fanshi kanki kawai kiyi abinda nace," tasan halinsa sarai zai aikata "amma ko na fad'a ka sani tursasani kayi kar kayi tunk'awo dashi *I LOVE YOU*" ya tuntsire da dariya, haushi yasa idanunta sukayi narai narai ya rik'o hannunta ta fizge don zuciyarta zafi take, da sauri tabar wajen yana ta shek'a mata dariya babu abinda yake so kamar yaga yasa Hibbah a gaba har tayi kuka, sai yaji wani sonta da k'unarta na shigarsa. Ranar ya nace mata yak'i tafiya ko zama zaiyi saiya dawo kusa da ita sai ya waske yana yiwa Nawaz wasa, shareshi take yi don bata son Faheem ya fahimci suna wani d'asawa ne da Faruq. Ya shigo fuskarsa a had'e kamar bai gansu ba, gani tayi Faruq ya daina rawar kai, "Faruq Ku had'a kayan nan mu tafi gida sun bamu sallama," Faruq ya kalleta "mene kike wani d'ari d'ari nifa bana jin kunya a gaban Ya Faheem sai na miki kiss kinga daya ga haka sai yasan yadda zai nema min aurenki, su bani abuna ko kuma na ja musu maga na b'allo ruwa." Ta marairaice "ka tabbatar min ka tsaneni shiyasa kake bin duk wanda nake da k'ima a wajensa kake zubar min da mutunci, Allah sai ya saka min," maganar ta shige shi ya janyo Nawaz ita kuma ta had'a kayan suka fito. A nota suka iske shi yana danna ways Sam ya rasa mai yake masa dad'i ransa a b'ace yake, Faruq ya bud'e motar yana sa kayan, Nawaz ya shige gaban motar. Ya kalleta "muje ga mota ta mu tafi tare" ta dalla mishi wata harara ta tsuke baki, ya Sosa sumarshi yana dariya ciki ciki, ta rasa wanda zata bi don tana matuk'ar jin nauyin Faheem d'azu ma da k'yar take numfashi a cikin motarshi, amma da ta hau motar Faruq gara ta hau gara ta tafi a k'asa, gani tayi Faheem yayi tafiyarsa. Faruq yaji wani dad'i a ransa shi yasa Faheem yake burgesa akwai jan girma yasan abu ya gani amma sai ya basar kawai don shi baison shiga sabgar yara. Ta k'urawa danjojin motar idanu har suka b'ace a duhun daren, hannunshi taji cikin nata "my dear," a fusace ta k'wace hannunta ta soma tafiya ko waiwaye bata yi har ta d'anyi nisa don zuwa bakin titi daga asibitin da d'an nisa. Faruq ya shiga motarsa yana biye da ita "Hibbah mene haka wai kinsan halina idan kika b'ata min rai," ko kallon shi bata yi ba, kwatsam sai ga wash d'irka d'irkan karnuka sun sharp a guje suna haushi, turus tayi ta ci wani mugun burki zuciyarta tana harbawa ta k'ame babu abinda tafi tsoro kamar kare, sai kace zakuna haka suka tunkarota ta kasa gaba ta kasa baya, gashi sun nufota gadan gadan ai batasan sanda ta bud'e motar ta rufe ba, ta tusa kanta tana ambaton Allah. Faruq ya kwashe da muguwar dariya mai ban haushi yana kad'a kai don wak'ar Machel Jackson yake saurara yana ya fara tuk'insa cikin nishad'i, ya d'ago kanta "my baby kin fiya tsoro, idan munyi aure da kin b'ata min rai police dog zan d'auko su yayyaga ki" tayi banza dashi "Hibbah" ya Kira sunan a hankali, ta kalle shi "gaskiya kin fa tashe ni daga aiki wai sai kimin shiru kin mai dani mahaukaci wato nayi ta sambatun sonki ni kad'ai, ki tausayamin wallahi da gaske nake aurenki zanyi" ta mishi kallon nutsuwa sai yanzu taji zuciyarta ta gamsu da gaske yake amma kuma yafi buk'atar jikinta akan komai, Allah mai yadda yaso gata dai a hannun Faruq duk abinda yaga dama yayi da ita. See Sweet suka iso yayi parking ya fita yaje ya siyo ice cream da fresh milk yana tahowa ta k'ura masa ido handsome bakinta ya furta, ya k'araso cikin motar. Ya mik'a mata ledar, ta kalle shi "gaskiya ba zan karb'a ba na gode in don nice da bakayi asarar kid'inka ba," ya had'a rai ya jefa mata jikinta "sai ki jefar tunda baki so," ya tashi motar bai sake magana ba har suka gida, ta fito ta bar masa kayansa a mota. Ya d'auko ya bita da shi, Faheem yana ta lallab'a Nawaz yayi barci ya dameshi bashi kansa ciwo yake masa. Hibbah tayi sallama yana jinta ya tashi, Faruq ya shigo ya zauna yana kallon news, yana tambayar Faheem kanun labaran Nawaz ya haye jikinsa yana tambayarsa me ya kawo musu a leda, ya mik'a masa wai ya kaiwa Hibbah. Hibbah kuwa kitchen ta nufa tana zuwa ta hango Kausar tana aiki a ciki "aunty sannu da aiki," tayi mata wani kallo dama tana jin haushinta a dalilin tafiyarta yaronta ya samu matsala har ta kaisu ga yin 'yar hatsaniya da Faheem don har yanzu basu shirya ba, "Kama aikinki donni bazan iya ba dama na gaji" tayi ficewar ta. Taji babu dad'i abinda Kausar take yi mata yayi yawa ka d'auki d'an Adam kamar dabba a wulak'ance, ta duba abincin ashe ma indomie ce take dafawa sai kuma dankali da ta soma ferayewa, ragowar mata shikenan abincin da ta iya. A bayanta ta ji shi ta juyo suna kallon juna, surarta ta ja hankalinsa duk da ba yau ya fara ganinta ba, ta juya amma ta kasa ci gaba da aikin don ita bata son kallo da takura. Nawaz ya shigo "aunty yunwa nake ji" ta zobo masa indomie dayake tayi ta bashi, Faruq ya kuma matsowa "Hibbah yaya zan kwatanta soyayyarku da Nawaz ne, gashi shi kad'ai ne a wajen ya Faheem daya bamu shi nasan bazai bamu ba don shi yana son yara, amma wannan Matar tashi ta fini yahudanci wai bata son haihuwa" ita dai feraye dankalin take bata ce masa komai ba "kin San abinda na tsana kenan kiyi min shiru ina magana ko?" Tayi shiru, kawai yatsunsa taji a gefen cikinta yana mata cakulkuli, wata zabura tayi ta zille gefe tasa kuka "Wallahi zanje na fad'awa Daddy'n Nawaz wannan wulakanci da kake min ya ishe ni," "ni d'in mahaukaci ne zaki k'yale ni ina magana ni kad'ai?" Kausar ta shigo tana wani muzurai "ke dalla ki bawa mutane abinci muna jin yunwa" taja tsaki, Faruq yayi mata wani kallo ya had'a rai, sim sim ta fita tana mita don tana shakkar Faruq. Yayi tsaki "stupid kawai 'yar rainin hankali ce matar nan, sai Yaya ya dinga min wa'azi ga rubbish nan a gidansa ya kasa sarrafata, dama ina ciki da ita" "to kai ina ruwanka da shiga tsakanin miji da matar sa haka yake son matarsa don gani yayi zai iya zama da ita" ya harareta "Allah ko uwar iyayi kin fini sanin hakan ko?" Tayi d'an murmushi "kaima ai ba kanwar lasa bace" "Wai ni na rasa girman lefina da ake gani har kuna hangen nauyin zunubi na bazai kankaru ba, ba'a shiga tsakanin Bawa da ubangijinsa ni bana aikata manyan aiyuka bana shan giya bana sata, kisa bare fashi da makami, to menene a ciki kawai don mutum yayi rayuwar da yake ra'ayi tajin dad'i sai ace ya sab'i Allah? Ina sallah, azumi da bin iyayena to menene saura kuma?" "Haka ne to amma ina batun b'angaren Mata naji ka keb'ance shi ko shi baya cikin manyan lefuka? Ba wani inkari da zakayi don kai Gwani ne ta wannan fannin" ya sosa k'eta "kin gane Allah gafurur rahim ne, wannan va wani abu bane kawai lokaci ne daga na aure ki zan daina, don nasan zaki gamsar dani bani da lokacin bin wasu matan" ta dubeshi "hali zanen dutse, a duniya babu abinda nake k'yamata kamar miji mai neman mata, kai kuwa ya zame maka jiki duniya ma ta shaida haka, to saboda me ni kuma zankai kaina ga halaka?" Wani abu ta gani a idanunsa da alama maganarta ta tab'ashi sosai, bai ce komai ba ya fita, tayi d'an murmushi ta k'arasa aikinta. Yana parlor bai tafi ba ta ajiye musu abinci ta koma d'akinta ta gyara don da bata nan yayi k'ura, saboda tunda ta tafi Nawaz ya koma wajen daddy'nsa da kwana. Tayi sallah a gajiye take ta kwanta cikin tunani daban daban, tun daga sanda Faheem yaje gidan Umma, tana jiyo kalaman Umma ko ya ta d'auki Faheem? Lallai yana da k'ima da girma a gunta bata tab'a yi mata maganganu masu zafi haka ba................ *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:25 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page3⃣6⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Washe gari da safe ta shirya zata tafi school taga Nawaz bai tafi ba yama cire uniform tace "Nawaz ina shirin makarantar?" "Aunty Hibbah daddy ne yace yau bazan je ba uncle d'in mu ya bani hutu sai gobe," tayi murmushi "to haka ake so Nawaz Allah ya k'aro sauk'i, ni kuma zan tafi school saina dawo" "aunty Hibbah ki tawo min da chocolate" ta shafa kansa "a'a Nawaz doctor ya hana shan zak'i saboda ciwon ciki" tana rik'e da hannunsa suka fito har bakin gate suka gaisa da Isah, yana tsaye a wajen Isah ya d'aga mata hannu "Aunty Hibbah bye bye sai kin dawo," ita ma ta d'aga masa hannu gami da fita daga gidan, ta soma tafiya har ta k'arasa bakin titi. Ta jima a tsaye bata samu mota ba, duba agogo tayi taga ta kusa latti ta soma tafiya ko zata samu a gaba. Hon don haka ta kauce ta basu hanya, "Aunty Hibbah" juyowa tayu don jin muryar Nawaz, shine da Daddy a motar, sanye yake da T shirt ta d'an d'ame shi, sai ya koma mata kamar Faruq don shi bai saba d irin wannan shigar ba yafi sabawa da shigar manyan kaya. Nawaz ya fito ya bud'e mata baya, dak'yar ta shiga tace "daddy barka da safiya" "lafiya lau Hibbah, wane school kike ne? Ko kema kina inda su Saudat suka gama?" Tace "eh" Shiru ya ratsa sai Nawaz dake ta suruntunsa, Hibbah kuwa zancen zuci take tana mamakin Faheem wane irin mutum ne shi Wanda ta kasa saboda dashi har yau. Sun iso makarantar ya ajiyeta a bakin gate, tana k'ok'arin fita taji yace "k'arfe nawa zaki tashi?" "K'arfe biyu ne" "ok ki jirani" a sanyaye ta fita daga motar, ta kasa shiga school d'in tabi motar da kallo. Ji tayi an dafata ta d'an tsorata ta waiwayo Fauzy ce tana mata dariya "Hibbah me kike jira ko har kin fara duty ne yau?" Hibbah tayi dariya "a'a Fauzy ai kema kinsan bana fara duty da wuri, yanxu fa nazo" fauzy taja hannunta "zo muje class da labari fa su momy sun amince da Ya Nazeef" Hibbah tana murmushi tace "da gaske?" "Wallahi kedai muje na baki labari," suka k'arasa class. Ranar wani yanayi ne mai dad'i a ranta kawai tunanin Faheem ya tsaya mata a rai haka komai nashi take gani harta yarda yake yin tuk'i a nutse da kalamansa masu saka nutsuwa, Allah mai iko wai har takai matsayin da zai kaita school bayan ba komai bace ita sai 'yar aikinsa, Anya kuwa zak'ewar batayi yawa ba, ko da yake Faheem da Aunty halinsu iri d'aya ne sun d'auke ta ne a matsayin 'yar uwa ne ba 'yar aiki ba, kuma yana girmamata gashi akwai kunya da nauyinsa da take ji don bata iya hawa motarsa don dai bata iya yi masa musu. Wani tunani tayi, yanzu idan Kausar ta gano tana shigar mata motar miji ai ta shiga uku, Anya kuwa bazata gudu ba idan yazo yaga bata nan ai zaiyi tafiyyarsa, kuma tunda ba wata magana suke yi ba bazai tambaye ta ba. Ana tashi kuwa tayi sauri ta had'a komai nata suka yi sallama da Fauzy, tana fitowa gabanta ya fad'i ras, mamaki take yi kamar a mafarki anya Faheem ne kuwa? Ikon Allah, tasan ya ganta babu maganar tserewa. Yana kallon ta ta cikin glass ya Gaza d'auke idanunsa, magana yake a waya amma duk hankalinsa yana kanta sai yaji maganar ma tana neman gagararsa, ya had'iyi wani abu sai kace sihiri ya manne mishi kamar mayan k'arfe. Kamar ta nutse Sam ta kasa dubanshi tunda ta shiga motar ai gara d'azu da Nawaz shi yana gaba ita tana baya, wai wannan wane irin nauyi ne da kunyar Faheem Allah ya d'ora mata. Haka sukayi shiru a motar tamkar kurame, Faheem akwai shi da nutsuwa da lafazi a tausashe "Hibbah" ikon Allah saura kad'an numfashinta ta d'auke, shima sautin muryarsa ya sauya. "Ina son muyi wata magana kin shirya saurare na?" Muryarshi tayi sanyi duk sai yasa ta wani yanayi da bazata manta shi ba a ranar, "nafi son ki bud'ame baki kiyi min magana tunda nima mutum ne kamar ke ki daina wani d'ari d'ari Dani, ni na d'auke kine tamkar 'yar uwata" yayi murmushi dayaga ta d'an Saki ranta "mene a tsakaninku da Faruq? Ki fad'amin gaskiya kinsan dai Faruq k'anina ne ke kuma amana ce a hannuna Hibbah" shiru tayi, "Hibbah bakice komai ba" "daddy shine yake zuwa........." "Nasan shine yake zuwa ma'ana maganar daya shafi soyayya" ta d'anyi shiru "gaskiya batun wannan bansan a muhallin da zan iya ajiye Faruq ba, shidai a cewarsa wai zai aure ni...." " kin tabbatar kina sonshi?" Zuciyarta ta shiga harbawa a ganinta cin fuska ne tace bata son d'an uwansa ciki guda. Ya sauke ajiyar zuciya "baki ce komai ba hakan na nufin kinason shi kenan?" Ji tayi gabanta yayi mugun fad'uwa tace "Daddy magana ce mai nauyi zan fad'a amma ba'a wannan lokacin ba" yay d'an murmushi yaji dad'in wannan furucin nata. Yayi parking a wani babban shop ya shiga ya d'an jima a ciki kafin ya fito, tunda ya fito ta k'ura masa ido ta glass d'in tana kallon sa da yake glass d'in a rufe yake kuma mai duhu ne, tabbas wani abu take ji yana ratsa zuciyarta ko mene wannan d'in? Yabshigo motar k'amshinsa kawai yana mata dad'i mutum ne gentle, ya ajiye ledojin a kujerar baya suka tafi. Nawaz yana ya biyo su, yana gama parking ta shige gida ta barsu anan. Tana shiga tayi wanka ta sauya kayanta tayi sallah ta nufi kitchen, tana cikin aiki Nawaz yace Daddy na kiranta. Ta iske shi zaune yana kallon MBC 2, taje ta durk'usa a gabansa yace ta kawo mishi ruwa, yaso su had'a ido amma kunyarta tayi yawan gaske, ta kawo masa ruwan a cup ya karb'a yasha. "Hibbah" ya furta, yau dai furucin nan yana tsumata, "d'auki wannan kayan naki ne" mamaki yasa ta kasa godiya d'auka tayi ta nufi d'aki. A kan gado ta zazzage, atamfofi ne guda uku da dogayen riguna biyu da hijjabai biyu sai riga da skirt kala biyu, masu daraja don duk 'yan waje ne, da mayuka da turarukan Mata, ta lumshe idanunta tunanin Faheem take da alkharinsa tun sanda suna mota take tuno irin k'amshinsa da kalamansa, Hibbah yadda yake furta sunan a tak'aice a harshensa, wani abu zuciyarta ke zargi don me Faheem yake yi mata wad'annan tambayoyin? Bata yi mamakin wad'annan kayayyakin ba, duk da bai tab'a yi mata kyautar kaya masu tsada kamar wad'annan ba amma dama ya saba yana yi mata kyauta. Ta d'auko takarda da biro, ta soma tunanin me zata rubuta,kawai sai ta fara rubutun. _Daddy_ _Bani da kalmomin godiya a gareka, na gode Allah ya k'ara girma da bud'i na alkhari ya barmu da Nawaz._ _Hibbah._ Ta kira Nawaz ta bashi ya kai masa, yana kwance a parlor ya haye kansa "Daddy gashi inji Aunty Hibbah" ya karb'a ya bud'e ya karanta, yayi nazarin kalamanta wani d'an murmushi yayu yarinyar ta shiga rayuwarsa, yayi ajiyar zuciya yau saboda da ita ne kawai yaji bai son fita ko ina yana hutawarsa. Allah yasa ta fahimci manufarsa, ko tama sanu take sharewa don yayi mata hannunka mai sanda oho, ai ita mai hankali ce zata gano shi a hankali matsalarta dai rashin son sakewa a gidan indai yana gidan, sai tayi ta nuk'u nuk'u bata son ko ganinta yayi har abin ya zame mata tsoro. Da yamma ya samu ya fita don anyi masa waya ana nemansa, yana fita Jabeer yayo mata waya yana waje, nan ta shirya ta ja hannun Nawaz suka fita. Bayan sun gaisa Jabeer yace "Hibbah banji inda shawarar ku ta tsaya ba akan sa ranar nan, sauraronki nake yi na samu Aunty Aysha naji bakinku yazo d'aya itama tace wai zata tattauna da Umma, abinda yasa na dame ki ni mutum ne mai d'aukar abinda nake so da mahimmanci ban son shiririta a al'amurana, idan kina ganin abin bazai yiwu ba ki fad'a min gaskiya kawai kar ki b'oye min" tayi d'an murmushi "kasan ba nike da kaina ba kuma nayi maka bayanin komai bani zan aurar da kaina ba, amma ka samu Alhaji Ku tattauna kaji ta bakinsa," "to naji dad'in hakan, kar kiga zak'ewata ina sonki da yawa shi yasa nake nuna miki damuwata kuma nasan kema kina sona, zan sameshi in Allah ya yarda." Faheem ya dawo ya huce su, Nawaz ya bishi don taryarshi, al'adarsa kenan komai yake yi da yaji motar Daddy'n shi ya dawo to saiya taro shi, Faheem ya saba mishi da hakan yakan ji dad'i aranshi sosai. Tayi ajiyar zuciya Faheem mai sata cikin rud'ani in dai ta ganshi sai komai ya sauya mata in a parlor take ta gudu d'aki, in tana tafiya ne taji kamar anyi mata dabaibayi dole take tsayawa sai ya huce sannan ta cigaba, ya katse mata tunani "ina son mu gaisa da yayan nan namu amma naga kamar bai da son mu'amala da mutane, a k'alla ya sha wucemu anan yasan kuma ina zuwa wajenki ne don na aureki amma ko duban inda muke baya yi bare ko hannu ya d'aga min, ni kuma inason mu gaisa dashi ya sanni sosai don yasan shima yana da ruwa da tsaki a cikin maganar aurenki tunda a hannunsa kike zaune" "gaskiya ne kuma mutumin kirki ne, kawai dai allah ne bai nufa zaku gaisa d'in ba sannan na fahimci bai da wani ra'ayi akan shiga maganar aure na tunda bai tab'a yin magana akan hakan ba, amma nasan idan lokaci yayi zai yi." Ya gyada kansa "shikenan Allah ya tabbatar da alkhari na gode" ya bata wani k'unshi a rufe a takarda. "Kai baka gajiya yau da gobe sai Allah," "Ana gajiya da masoyi ne?" Mutuminta ne ya huce su a mota, Faruq d'an rikicin duniya da da inda zata je data gudu sai ya tafi saita dawo domin zai sa ta a gaba ne kawai sai ya sata kuka. Sukayi sallama ta shigo gida, ta huce shi a cikin motar kamar bata ganshi ba, ya dad'a k'uluwa kishi ke cinsa kamar masifa, wai wannan Jabeer da jaraba tsiya yake duk yadda ya tozarta Hibbah a gabansa bai hakuri ba. Ya fito yana take mata baya ya janyo mayafinta ba shiri ta yo baya kamar zata fad'i ranta a b'axe ta kalleshi zallar masifa ta gani a idanunsa yau ta tab'o Faruq, mai cin zalinta a bulus bare da dalili. Ya nannad'e mayafin a hannusa tana ja ta kasa k'wacewa, ya kuwa murd'e hannunta ta rintse idanunta ji tayi kamar zai b'allata tayi wata 'yar k'ara "wayyo Allah na!" Abinda ta tsana kenan wannan rashin mutuncin da Faruq yake yi mata tana d'aukarsa tsabar tsana ce da rashin galihu. "Zan nuna miki mahaukacin kishi na akanshi zan iya komai tunda kika jawo mutumin nan duk da irin tozarcin da nayi miki a gabansa ashe tsugunno bata k'are ba, matuk'ar na k'ara ganinki dashi sai na miki rashin mutuncin da baki tab'a zato ba, don ji nayi kamar nasa bindiga na harbi k'ok'on kansa." Faheem ne ya fito yaji kuma furucin Faru$q sarai amma yayi kamar bai san su ba yayi wucewarsa, wani bak'in ciki taji ya k'ulleta kamar ta fad'i ta mutu wajen. Babu mutumin da a duniya bata son mutuncinta ya zube a wajensa kamar Faheem tana ganin girmansa, gashi a yau yaji ya gani hujja ce da zai d'ora zarginsa akan gaskiya tana mu'amala da Faruq bawai iyakar soyayya ba, wani tunanin zai yi don Faruq dai bashi da halin k'warai akan 'ya mace, gashi ya rik'e hannunta gam bata da wani sauran mutunci a idanun Faheem, wannan wace irin *RAYUWA* ce............... *#JUMMA'AT MUBARAK TO YOU ALL😍😍🤝* *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:25 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page3⃣7⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Wani sambatun banza yake yi mata ta tureshi a fusace "Allah ya isa cin zalina da rashin mutuncin kake min, k'arewar tsana k'in jini ka kashe ni ka huta, babu mutumin da na tsana a duniya irin ka.........." Kuka ya shak'eta, maganar ta shige shi domin alwashin ya daina mata irin wannan abun amma why? Why yaji kishinta haka? Kishinta ne ya tursasashi don abinda yafi wannan ma zai iyayi sai dai duk abinda za'a yi masa ayi masa, ta shige gida, a cikin d'akin ta watsar da kayan ta kwanta kan gado gami da kifa kanta a kan pillow, ta gaji da wannan wulak'ancin da cin zarafin na Faruq wai me ta tsare masa ne a duniya? Burinsa ya sata kuka ya zubar mata da k'ima da daraja a idanun mutanen da suka d'auketa mai mutunci, to ina k'iyayyar da ta huce wannan ina zata kai k'ararsa ne don a k'watar mata 'yancinta. Faruq ya shigo ya rufe k'ofar yana kallon ta, sai yaji wani haushin kansa kai zuciya bata yi ba, sai ta ingiza ka kayi abinda zaka zo kana shiga damuwa, sam baiji dad'in kalaman Hibbah ba duk ta rikitashi har yaji ya tsani kansa. "Hibbah" ya sunkuyo kanta, wani d'an tsaki yayi kukanta take yi, "oh my God! Wai Hibbah ya za muyi da juna?" Ya tsugunna nan ya d'ago kanta, fuskarta sharkaf da hawaye, ya maida kan nata kan filo tare da kifa nasa shima, "ni dai babu yadda zanyi da k'aunarki Hibbah tunda kince kin tsane ni to ko guba ce ki bani nasha na mutu na huta da wannan azabar sonki Hibbah, wallahi zan iya yi miki kuka a yau don ki tabbatar da ina k'aunarki ba tsanarki nayi ba, ki sani ni gwarzon namiji ne babu abinda zai iya sani kuka amma saboda ke nace zan iyayi haba masoyiyata Hibbah" zunbur ta matsa daga inda yake ta koma can k'ashen gadon "zo na rareasheki Hibbah baki san yadda nake ji a zuciyar nan tawa ba." "Allah yayi min tsari dakai shad'anin mutum irin ka, kai ba masoyina bane babban mak'iyi nane Wanda yak'i jini na, burinka nayi kuka raina ya b'aci na rasa kwanciyar hankali, shikenan farin cikinka me na tare maka?" Ya daki pillow'n da hannunsa yana huci idanunsa sun kad'a, cikin wata irin murya yace "ni ne shad'anin mutum zan tabbatar miki da hakan yanzu." Yayi wata zabura zai rik'ota ta tashi da gudu tayi hanyar fita yayi saurin cafkota, jikinta ya d'auki rawa badon ya rik'ota ba da tabbas zata iya fad'uwa saboda tsabar tsoro da fargabar mai zai faru, ya tsura mata idanu yadda yake ji a zuciyarsa yasan Hibbah ta kaishi k'arshe, so jarraba ne baya jin zai iya yi mata komai amma badon haka ba da yau saiya nuna mata shad'ancinsa. Yayi murmushi "Hibbah ina sonki da yawa furucinki ya fusata ni, fushina akwai wahala don bani da dad'i komai aka yi min saina rama, haka nake sai dai idan ni nayi niyyar yafiya ke kad'aice mace ta farko data sauya akalar ra'ayi na, kin ganni kamar tab'ab'b'e dubeni" saita bi umarninsa, don a cikin tsoro take, suka k'urawa juna ido. Sai yayi dariya ya ja hannunta suka koma parlor suka zauna ya shiga goge mata hawayenta "kin yave min? Wallahi nayi miki alkawarin bazan kuma b'ata miki rai ba, sai dai idan abisa kuskure na aikata, yanzu me kike son nayi miki?" Ta dube shi a nutse "Dan Allah karka sake kulani bare ka shiga harkata shikenan abinda nake son kayi min, kabar rayuwata ta huta abinda kayi min na yafe," "kina nufin baza ki aure ni ba?" Dam gabanta yayi wata mummunar fad'uwa zuciyarta ta shiga bugawa wai shi da gaske yake? "Aure fa kace Faruq kasan mene ma'anar aure? Taya aure zai k'ullu tsakanin mak'iya biyu? Ni fa abokiyar gaba ka d'auke ni, wace irin rayuwa zamuyi bayan nasan halayenka babu abinda ya sauya, ka kaga wuyanka sarka ce, kana nan akan batunka nason b'ata min *RAYUWA* saboda bani da galihu Allah ne gata ne." Ga mamakinta sark'ar ya tsinke ya jefar "wallahi tunda bakya so daga yau nayi miki alk'wari na daina sakawa, bazan iya daina sonki ba Hibbah sonki zai iya kashe ni, ni ban iya son abu ba idan ina son abu ina sonshi ne da dukkan gaskiya ta ko da zan rasa raina, Hibbah da kin aure ni zan zubda duk wasu d'abi'u na da bakya so zan daina su" "to kai baka la'akari da matsayina ne da naka, ka manta ni 'yar aiki ce a gidan Ku, ka duba matsayinka na d'an masu kud'i ni kuma ba 'yar kowan kowa ba, ka shahara da farin jini a football ga farin jinin mata. Kaga wannan Jabeer d'in shine ya dace dani shine mai min soyayya tsakani da Allah, a gabandmsa ka tozartani da bayyana masa matsayina na 'yar aiki a gidanku, amma hakan bai hanashi k'aunata ba kuma idan Allah bai wulakanta ka ba babu mai tozartaka a duniya, a cewarsa koda yawo nake ina tsinyar abinda zanci, zai aure ni ballantana don ina aikatau a gidan ku ai ba sata nake ba ba maita ba, shine yasan darajata yake sona don Allah," idanunsa sun kusan rufewq saboda tsabar b'acin rai "kinsan yadda nake jin zafin maganganunki nan gara ki caka min wuka mai dafi, Hibbah ina ta fahimtar dake irin son da nake miki kin kasa fahimta ki daina tunanin matsayinki wai waye waye ni zan samu Ya Faheem na fad'a masa," ta waro ido waje "Daddy'n Nawaz ma fa yasan da batun Jabeer ya zanyi dashi kayi hakuri kawai," ya d'ora hannunta a kan k'irjinsa "Hibbah kiji yadda zuciyata bugawa idan kina min zancen wani zata iya bugawa ki kashe ni ki huta." Ta zame hannunta "ni dai ka daina tab'ani ban so" "saboda ni kuturu ne ko, idan ban tab'aki ba wa kike son na tab'a kawai ki yi hakuri da halina duk abinda kike tunani yanzu kin huce haka a wajena, idan kuma nayi niyyar kusantarki sau nawa ina ritsaki a d'aki, kawai ni so nake kafin na tafi Germany a d'aura auren mu," ta tsorata da kalamansa ita gani take kamar Faruq baya hayyacinsa, ta tashi ya rigata yana dariya "nasan kina sona gulmace irin taku ta mata kina so kina kaiwa kasuwa, da munyi aure zan bud'e miki idanu na koya miki yadda zaki soni har ma kiji idan baki ganni ba na d'an wani lokaci ki kasa sukuni, dama wand'annan idanun na kuka ne abu kada'an kiyi ta kuka." Tayi murmushi "kaji dashi dai ni aiki na zanje nayi," "muje na tayaki kinsan ni bana barin macen da nake so cikin damuwa ko yaya take shiyasa nake miki naci zaki ji dad'in rayuwarki dani" ta girgiza Kai "a'a na gode ka tafi kar Daddy'n Nawaz ya dawo" ya tab'e baki gami da yarfar da hannu "to meye a ciki, zan fad'a masa ma aurenki zanyi ai yasan komai tunda yana gani na tare da ke, kawai dai yana sharewa ne, ni bani number ki bazan iya barci ba sai naji muryarki" ta tsaya kawai tana kallonsa wai ita Faruq yake furtawa Kalmar so anya wannan ba salon yaudara bane, idan tayi la'akari da kalamansa na wannan jikin mallakinsa ne, jikinta kawai yake so ko da zai aureta daya gama cin muriyar jikinta zai yada ita ya koma har kokinsa da mata. "Magana nake miki kin wani tsare ni da wannan idanun naki masu saukarwa da mutum kasala, idan kina kallona tsumani kike yi ina ji ina k'ara sonki, idan kika cigaba da kallona kema kinsan abinda zai faru," tayi dariya "Kai fitina ne da kai na gaji da fad'a maka bazan iya ba" "gara ma tun wuri ki sama mana mafita don karshen watan nan nake so a d'aura aure idan ba haka ba za'a haifi d'an da ba ido" ta shige d'aki ya bita da kallo gaskiya yarinyar nan ta tafi dashi da yawa, ga manyan babies nan a gari amma duk basu burgeshi ba sai Hibbah. Ita kuwa Hibbah tana shiga d'aki ta shiga tunani tabbas Faruq jikinta kawai yake so ba wai yana sonta tsakani da Allah bane, da sunyi auren yana samun abinda yake so shikenan zai koma duk wasu d'abi'unsa, gara tun da wuri karta sake ta yarda ayi wannan auren, to amma mene mafita? **** Faheem kuwa cikin dare ya kasa bacci, da k'yar ya kalli agogo dare yayi sosai tsit kakeji sai haushin karnuka daga cen nesa isaka ke kad'owa. Kamar yasha abin maye, jirim jirim yake jin kansa tunani yayi masa yawa zuciyarsa ba dad'i yayi wani d'an tsaki me yake kawo masa ciwon Kai ne, ya juyo ya dubi Kausar barcinta take hankali kwance irin mai dad'in nan don ta kwaso gajiya, babu ruwanta da irin damuwar da yake ciki Anya wannan macen ita ta dace da ya zauna da ita, sam bata damu dashi ba bare ta san damuwarsa har ta kwantar masa da hankali. Ya shafa kanta yana son Kausar saidai rashin kulawar da bata yi masa ya dakusar da son da yake mata, a ganinsa duk mace burinta ta tarairayi mijinta ta kula dashi donta mallakeshi amma ita banda ita aikinta yafi masa mahimmanci. A hankali ya shiga kiranta a cikin kunnenta "Kausar" saida ya tashe ta ta karanto damuwa tsantsa a cikin idanunsa, babu abinda yake buk'ata a yanzu kamar ta sanyaya mishi zuciyarsa har ta huce ta daina yi masa wannan rad'ad'in da yake ji. Ita kanta ma ta damu da kewarsa tasan tayi missing mijinta tasan dole ya damu bata tsinana mishi komai tana dawowa datayi sallah taci abinci sai barcin gajiya, da safe kuma kafin ya fita ma ta fice, lallai ta jinjina hakurin Faheem wasu lokutan yakanyi fad'ansa da mitarsa ya hakura, ita kanta tasan ya fita gaskiya amma saita take don ita aikin nan jinsa take a jininta. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page3⃣8⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Haka Kausar tayi k'ok'arin faranta masa a wannan daren fiye da yadda yayi tsammani har ya ma manta da wata matsala da take damunsa, sai yaji ina ma haka Kausar zata d'ore, mace mai neman albarka ita ke faranta ran mijinta a duk sanda ta ganshi cikin damuwa sai tayi k'ok'arin kawar masa da wannan damuwar. Bayan komai ya lafa yaji wannan abun dake tsaya masa a zuciya ya dawo, ikon Allah wato wannan abun bazai k'aye sa ba kenan. Washe gari ya kama juma'a yayi wankan juma'a cikin wata rantsatstsiyar shadda mai mugun kyau, yayi kyau da sosai ya fito tamkar saurayi baza ka tab'a cewa Faheem yana da aure ba, Faheem akwai iya kwalliya da k'yale k'yale kamar mace. Ya fito da alama masallaci zashi, "Daddy" ya juyo don sautin yad'an tab'oshi, ta cigaba "dama Aunty tayi min waya wai zanje nayi mata kwana biyu don bata jin dad'i" d'if yayi abinda yasa ta dubanshi kenan ashe shima itan yake kallo, ya dawo ruwa tsundum wai shifa ya yanke shawarar zai dake bazai k'ara bari wannan abun ya dawo masa ba, yana k'ok'arin dak'ile shi k'arfi da yaji to amma bayin kansa bane abin yana fitowa ne a duk sanda zai d'aga idanunsa ya kalli Hibbah ko kuma ya ganta da wani tana mu'amala dashi, ko kuma idan bai ganta ba yana jin shi kamar ya rasa wani abu muhimmi ne a rayuwarsa, tun jiya har yanzu wannan abun yana jinsa a zuciyarsa gashi ita kuma yanzu Aysha na k'ok'arin nisanta shi da ita, anya kuwa zai iya jure rashin Hibbah a kusa da shi? Da k'yar ya nemo abinda zai fad'a mata don kada ta zargi wani abun "ki Bari ni zan same ta basai kinje ba" yana gama fad'in haka ya fita. Haushi ne ya kamata bata so ya hanata fita ba ita saidai ta zauna tana yi musu gadin gida kenan, ita kenan bata da 'yancin kanta gaskiya gara tayi aurenta ta huta da wannan mulkin mallakar. Bai nemi Aysha sunyi maganar ba donshi shaf ma ya manta sai da yamma ya fita ya tuna, ya sassauta gudun da yake yi ya nemi Aysha ta waya, bayan sun gaisa yace "me ya faru ne wai yarinyar nan zata zo me zata yi miki?" "Yaya bana jin dad'i ne shine nake so na karb'i ajiyata dana kawo" "hmmm amma dai kinsan idan ta tafi akwai matsala a gidana, ina mai miki aiki?" Tayi dariya "ba komai tana nan dama nafison ta dawo hannuna tunda maganar aurenta ta taso, ya kyautu itama da ta k'arasa jarrabawarta tayi aure tunda ta samu miji, Jabeer ya takura min da maganar Sanra rana shiyasa nake son ganinta, na yaba da hankalinsa kuma bata b'oye masa komai ba akan dangantakar dake tsakaninmu da ita, to shine nake son naji ta bakinta asa ranar yanzu ne ko kuwa a bari saita k'arasa kammala WAEC d'inta don muma musan irin gudunmawar da zamu bada ko?" Ya taka burki don hakan shine kawai zaifi samun nutsuwa don maganganunta sun Sanya shi cikin wani yanayi, kai shi dama baiyi mata wayar ba don kalamanta sun sanya shi cikin wani tunani. "Yaya kana jina kuwa naji kayi shiru" bai ce komai ba ya kashe wayar, gorar ruwan faro ya d'auko yana sha kad'an kad'an sanyin ya ratsashi har cikin zuciyarsa, yayi ajiyar zuciya yana ganin kiran Aysha ya k'yale don bazai iya cigaba da jin wad'annan maganganun nata ba zasu iya kaishi emergency yanzu, zurfaffan tunani ya tafi mai zai hana yayiwa kansa k'iyamul laili me yasa zai haramtawa kansa abinda ya yarda yana yiwa tsarkakakkyan so, gaskiya zai k'wari kansa wajen nuna kawaici da nuna nauyi baki anya zai iya cigaba da hakuri har ya sadaukar da irin wannan son, zai iya haifar masa da ciwon zuciya. Yaso yaji ta bakinta akan mu'amalarta da Faruq don baison alak'arta dashi amma tak'i fad'a masa da alama Faruq zai zame masa k'adangaren bakin tulu. "Uncle" d'ane bayansa yana k'yalk'yala dariya, yana son Nawaz don yashiga ranshi sosai, tayi murmushi Faruq, Faruq duk shigar da yayi tana yi masa kyau kamar Faheem, sun iya shiga mai tsari kodai a jinin su hakan yake kamar gaske wuyansa yau ba sark'a. Ya dubeta "masoyiyata kinyi min kyau yau fiye da kullum" ta dubi kanta material ne yellow anyi mishi d'inkin Riga da skirt yayi mata d'as a jikinta, ya matso yana k'ok'arin tab'ata taja da baya ta kawar da kanta gefe, "bana son abinda kake min donni a wajena hakan ba waye bace saboda irin tarbiyyar da aka koyar dani hakan bai dace ba" "to ya kike so nayi Hibbah, so ba abinda bai sawa kinsan yadda sonki yake a rayuwata kuwa kawai kiyi hakuri dani, bara kiji wallahi saboda ke na dad'e banyi mu'amala da mace ba na tada kaina harsai ranar auren mu" "Duk sanda zakayi abu kayi shi domin Allah, kajo tsoran Allah bawai saboda ni zaka daina mugayen ayyuka ba kabari domin Allah na sani shiriya ta Allah ce, don haka fad'in hakan bazai sani nayi wasarere da jikina ba domin mu ba muharramai bane, shed'an shine zai shiga tsakanin mu" "to amma ki sani so gundarinsa kansa mutum ya canza koda baison canzawa kuma shiriya ta Allah ce, amma komai yanada sanadi kuma zanso ace kece kika ja ra'ayina zuwa halaye masu kyau, Hibbah na k'agu muyi aure" ta numfasa "ni har yanzu zuciya ta bata yarda da mutum irinka ba, ban yarda wai k'aunata kake tsakani da Allah ba shiyasa nake ganin bamu dace da juna ba, kuma bazan b'oye maka ba Jabeer yayi magana da Aunty Aysha akan sanya ranar auren mu kaga bai kamata mu dinga yin abinda bazai yuwu ba." Fuskarshi ta canza ta soma jaja jaja, sauke Nawaz dake goye a bayansa ya rik'o hannunta da kyau, ta shiga kiciniyar k'wacewa. Ya zaro idanunsa waje "Hibbah saboda ina sonki shine kike yi min wannan wulakanci kin sani Allah ne kawai yayi min wannan jarrabin amma matsayina ya wuce ajinki bawai ina lallaminki bane ni mace bata juyani ko tirsasani akan abinda baya cikin ra'ayina, sai na aureki zaki gwammace kid'a da karatu sai kinyi nadamar abinda kikayi min zaki san kin auri d'an bariki!" K'wallar data taru a idanunta ta d'igo a kumatunta don ganin Faheem ya dawo ya fito daga motarsa, yayi shigewarsa ko kallonsu baiyi ba yayi wucewarsa. Faruq yana ta sambatun surutunsa don a cikin zafi yake baima damu da ganin Faheem ba. Hibbah duk hankalin ya tashi bata so ko kad'an Faheem ya ganta da wani bama Faruq kawai ba. Faheem yana shiga parlor ya dafe kansa dake sara masa jagab ya zauna akan kujera ya rufe idanunsa zuciyarsa tana bugawa, anya wannan abin nashi zai d'ore kuwa anya bazai je doctor ya duba lafiyarsa ba kuwa don yanaji kamar akwai wani abu dake damunsa. Ta shigo idanunta cike da hawaye kamar kullum Faruq ya saba sata kuka, ranta a b'ace yake don baram baram suka rabu da shi, taya ma zasuyi shiri da Faruq harma suyi wai aure, bayan kullum cikin fad'a suke. Tayi turus kamar tayi tuntub'e sai kace sai kace wadda aka yiwa dabaibayi ta dad'a shiga rud'ani ya dubeta cikin idanu wani abu data gani ya kuma sata rud'ani wani yanayi taji kamar ta fad'i a wajen, abin ya cigaba da zagayeta sai kace sihiri, a hankali taja k'afarta da tayi nauyi ta wuce d'aki ta rufo k'ofar gami da jingina a bayanta a jikin k'ofar, ta goge hawayenta cikin wani rashin jin dad'i da rud'ani meke damunta ne Faruq ya b'ata mata rai, tare da tasirin wani abu dake faruwa da ita. To amma Faheem fa me yake damunsa kamar ba shi ba, wai meke damunsa a yadda ta gansa kace kace cikin damuwa, duk sai take jin kanta ba dad'i sam ta kasa sukuni, to wai mene nata da shiga damuwa don Faheem yana cikin damuwa ita da ba matarsa ba. Faruq yana fita daga gidan Faheem cike da b'acin rai ya nufi gidan Aunty Aysha, bayan yayi parking ya nufi cikin gidan yayi knocking mai aikinta ta bud'e ya shigo ya zauna a kan kujerun d'akin. Ta shigo "barka da zuwa yau kaine a gida na?" Yayi murmushi "to ya zanyi dake nayi fushina na gala ba zan iya gaba da ke ba, d'an uwa baya fushi da d'an uwansa" tayi dariya "Umar Faruq kenan yaya halinka? Ka canza ko har yanzu kana nan dashi?" "Ki bari dai kawai Aunty yanzu ma tawa ce ta kawo ni domin kece jagoraba don nasan zaki sharemin hawaye na," ya sassauta murya "Aunty aure nake son yi a cikin wannan lokacin kafin na tafi Germany, ki bani shawara kisa albarka kuma kiyi addu'a" tayi shiru tana nazarin maganar Faruq lallai Faruq yayi hankali ya nutsu tunda har ya yanke shawarar yayi aure, "to naji bayaninka kuma shi aure alkhari ne Allah yasa albarka yasa hanyar shiriyarka kenan ka dena wad'annan d'abi'un, nasan hali dai zanen dutse amma in da nauyin iyali a kan rusuna koma a daina gaba d'aya, yaushe ne za'a Fara shirye shirye, ka sanar da momy da Daddy da kuma Ya Faheem ya sani shima ko?" Ya sosa sumarshi "hmmm basu Sani ba tukuna, manta da Ya Faheem kinsan shi tsarine dashi zai iya kawo suka cikin lamarin don bana tunanin zai goyi baya" "to ai kuwa Ya Faheem shike da ruwa da tsaki a maganar aurenka shine yake wakiltar Daddy tunda ba zama yake yi a gari ba kuma kaga Abba ma bai fiya zama ba, kasan ance babban wa uba ne ko?" Ya yamutsa fuska "ai kin gane ni na fahimci baya son alak'ata da yarinyar, labarin zuciya a tambayi fuska, kawai dai bashi da yadda zaiyi ya rabani da abinda nake so" Aunty ta girgiza kai "a'a shi dai yana duba halayyarka ne saboda me zaik'i son abinda kake so shi zaifi kowa farin ciki da aurenka, a kullum burinsa Faruq ka shiryu ka bar kaza da kaza wannan abin da kake yana zubar maka da k'imane fa," "Nifa ina mamakin wannan wane irin hali ne nawa kuke ta aibatani, ni ba kisan kai nake ba, ba fashi da makami ba ba shan giya ba, ba kuma na ta'ammali da miyagun aiyukan ta'addanci, men's a cikin rayuwar dana keyi bai hanani bautawa mahaliccina ba, na lura gani kuke ki kamar na kafirce ko bansan Allah ba ko nauyi zunubi na yakai Allah bazai yafe min ba ku daina shiga tsakanin bawa da ubangijinsa domin shi gafuru rahim ne." "Gaskiya ne to amma babu Wanda ke son yaga nasa ya lalace in baka gyarashi ba duniya zata gyara maka shi, in baka fashi da shan giya amma kamannin mutum ake dubawa a gane yaya halayyarsa take care banzane kona kirki, kuma banji kayi lissafi da neman mata ba ko ita bata cikin manyan ayyuka zina fa, dole ne Faruq na fad'a maka gaskiya nasan da d'aci da ciwo amma ina tausayin wadda zata aureka, ina tunanin rayuwarta a hannunka domin idan neman mata ya damk'i mutum masifa ne, don barinsa ba k'aramin jihadi bane......" Ya d'aga mata hannu ransa a b'ace "kin gani ya isa kawai bana son wani k'wak'ule k'wak'ulen maganganu ina ruwanki da harkokina don sa ido irin naki ai kowa da tashensa lokaci ne idan ya wuce ai shikenan kuma aure ne sai nayi" tayi murmushi "Umar Faruq kenan to a ina yarinyar take nasanka da lek'e lek'e da gane gane, zanso ganin wannan yarimyar dole na kirata mai sa'a don ta ciri tuta tunda har zata auri k'anina" yayi dariyar jin dad'i "yauwa mutuniyata ai 'yar gidan ki ce ba wata bak'uwa ba, yarinyar nan ce Hibbah" ji tayi kamar gini ya ruso Mata rigigim! Ta zaro idanu "wace Hibbah? Badai tawa ba?" Ya gyad'a kansa "Hibbah dai da kika Sani.................." *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page3⃣9⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Aunty hankalinta yayi mummunan tashi "yaushe har ka yaudareta ka hure mata kunne kuka k'ulla soyayya tayi k'arfi haka?" "Ni ina sonta kuma itama tana sona duk da miyagun halayena, bata ganin aibuna kuma tace bazasu hanata aurena ba" cikin b'acin rai ta nunashi da yatsa "wannan shirin ka ne ni nasan k'aryane, yaudararta kayi don magana ce wannan da k'wak'walwata ta kasa d'aukata ba sonta kakeyi tsakani da Allah ba, ka tuna ka kusa illata yarinyar nan tun da ka d'ana mata tarko Allah ya tserar da ita, shine ka b'ullo ta wannan sigar to babu kai babu auren Hibbah 'yar mutunci bata cancanta da kai ba, kawai kaje ka cuceta da zalincinka na 'yan bariki, nasan bazata soka ba koda bata fito k'arara ta nuna maka k'iyayyarta ba don tana jin nauyi a matsayinka na k'anina, bazan goyi da bayanka ba don nasan daka gama cin moriyar gagga zaka yarda k'wauronta, tayi miji mai sonta don Allah Jabeer iyayenta sunsan da maganar auren bazan tab'a yadda ka dagula zancen ba wallahi, babu kai babu ita zan ganta itama sai naci ubanta shashashar banza kawai bata San inda yake mata ciwo ba, wato ita bata tausayawa kanta bata nemawa kanta 'yanci." Ya mik'e yana wani irin huci iyakar fusata ya fusata fuskar nan tayi jawur "Ashe ke mak'iyiyata ce a yau na tabbatar ni ba jininki bane ai hannunka baya rub'ewa ka yanke ka zubar duk lalacewata ni naki ne, kince ni d'an iskane uban bariki ne ni ba d'anta ba, wallahi saina auri Hibbah idan yaso ki dinga yankar naman jikina kina k'onawa ko kuma ki fad'i ki mutu don bak'in ciki. Wallahi zamusa k'afar wando d'aya dake koda zamu k'ulla gaba ta har duniya ta nad'e, aurena da Hibbah ba fashi don ra'ayi nane kuma babu abinda kika isa kiyi." Yayi awon gaba da center table d'in dake parlor'n glass cups d'in dake kai suka fad'o suka farfashe, ko juyiwa baiyi ba yayi tafiyarsa don ya d'au zafi. K'ofar fita sukayi karo da Sagir mijin Aunty Aysha saida ya gogi kafad'arsa, yaja baya yana kallon Faruq da mamaki, gaba yayi ko waigowa baiyi ba bare ya kula sa, ya kad'a kansa ya shiga ciki yana mamakin Faruq, ya zauna tayi masa sannu da dawowa. Ya gano tana da damuwa cikin sigar rarrashi ya matsota "haba amarsu na kiyi hakuri nasan fad'a kukayi da d'an uwan naki, kinsan su sai ana hakuri dasu a hankali zai canza" ta numfasa "kayi hakuri naga har bangajeka yayi, Faruq fitinannen yaro ne ya damu family'n mu, kullum bama shiri jituwa dashi sai fad'a don na fad'a masa gaskiya ni kuma bazan fasa fad'a masa ba sai dai muyi ta fad'a dashi" Ta fad'a mishi abinda ke faruwa. Yayi murmushi "ku mata wani lokacin tunaninku kamar na k'aramin yaro yake, Aysha ai ba'a fad'in abinda ba alkhari ba a lamarin aure idan ita kuma yarinyar tace shi take so sun had'a kansu fa, yaya zakiyi sai kiji kunya kuma har abada zai ta kallonki da wannan abin tunda bake kika haifeta ba na dai gane abinda kike hango mata, kina sonta kuma ke kin fita sanin halin d'an uwanki amma kamata yayi ki nuna goyan bayanki ki tayashi murna, ba yadda zakiyi dashi naka nakane saidai kiyi masa ta masa add'a da fatan auren ya zama sanadiyyar shiryuwarsa." Aunty ta numfasa "my dear abinda ka fad'a hakane amma karka manta fa akwai maganar aure a tsakanin yarinyar nan da Jabeer kuma har manya sun shiga sa rana kawai za'ayi sai yanzu zasu zo min da maganar banza daga ita har shi, ai itama zan sameta ne saina ci mata mutunci" "kibi abin a sannu, kum idan ita Hibbah tace bata son Jabeer ai dole ya hakura ko zakiyi mata dole ne?" Ta girgiza "to kingani kawai saidai muyi fatan Allah ya zab'a abinda yafi alkhari" "to ameen muje ka watsa ruwa ko?" Suka mik'e a tare suka shiga ciki. Faruq kuwa yana fita daga gidan Aunty cikin b'acin duk inda ya wuce sai an dube shi kamar mai shirin barin garin, gudu yake sosai a mota bai tsaya a ko ina ba sai a night club, idanuwannan a hargitse banda masifa babu abinda yake ji ransa a mugun b'ace yake ji yake kamar ana tsigar gashin kansa, tabbas da yana da bindiga da sai yayi gangancin harbin Aunty Aysha mene amfanin mak'iya a duniya ya tabbatar yanzu bashi da makiyi kamarta. Kid'a ne yake tashi kamar zai tsaga ginin wajen, ya zauna yana muzurai kamar wani kumurcin maciji, ya d'auko sigari ya kunna mata wuta wai ko zai rage zafin abinda yake ji, ya dubi mashaya barasa kala daban daban yakanji a wajen abokansa wai giya na gusar da mummunan tunani da kauda bak'in ciki ga d'an karan dad'i amma shi bai tab'a sha'awar Shanta ba, ya kansha ganye da wasu kwayoyin shima tun lokacin yana secondary school tare da tak'adiran abokansa da suke kiran kasu bad boys, amma tuni ya manta dasu shidai burinsa yaga macen da yake ra'ayi kawai yayi mu'amalarsa da ita. Hankalinsa ya kasu biyu ya kalli barasar yana kwad'ayin lasawa ya wurga idanunsa yana kallon kangararrun matan dake shawagi wurin duk baiga Wanda ransa ya biya ba don haka ya yafito hadimin wajen da hannunsa. Da harshen turanci ya gaisheshi cikin ladabi "barka da dare me kake buk'ata" ya mik'a mishi wata takarda da jerin nau'ikan barasa, ya karb'a yana d'an nazari sai ya yatsuna fuska "kowanne ka kawo" don bai san wanda xai zab'a ba. Ya dire tray da manyan kwalaban giya masu sanyi, ya d'auki guda d'aya idanunsa sun shige ciki ya k'ura mata idanu, yana tunani zuciyarshi yasha ko karya sha, ya sha kawai koya huce zuciayarsa ta raya masa. Yana kaiwa bakinsa ta karb'e kwalbar, ya cira ido da k'yar ya dubeta, siririya ce doguwa Fara Sol, tana sanye da wani bulun skirt iya cinyarta da wata 'yar figigiyar riga data manne a jikinta. Ta zauna gami da rik'o hannayensa da wani asirtaccen murmushi akan fusakarta tuni tayi awon gaba da tunaninsa, Rita kenan yana son yarinyar don tasan ta kanshi sosai da ranshi ya b'aci zata sauko da fushinsa. Ya kewaya hannunsa a k'ugunta suka mik'e suka hau sama don cin karensu babu babbaka. **** Bak'in hadarin daya taso da wata iska mai k'arfi, sannan ruwan ya sauko yana tarwatsewa bisa glass d'in motar yana sauraron wak'ar Dr Mamman shata, yau dai yana cikin annashuwa yana tunanin maganganun Umman Hibbah sun sashi farin ciki har yana hangen wata *RAYUWA* a gaba da zasuyi dole ne yayi azumin godiya ga Allah daya cika masa burinsa ya mallaka masa abinda yake matuk'ar so,shikenan ta zama mallakinsa. "Karka damu komai nufi ne na Allah, nayi farin ciku da jindad'i tsakaninku da yarinyar nan amanace, wannan ita ce k'auna domin Allah sai addu'ar alkhari, Allah ya tabbatar da alkhari zan fad'awa Alhaji yanzu daya shigo ayi komai a yau d'in nan a gama." Yayi ajiyar zuciya ya tuna maganganun masu dad'in sauraro, wannan wani sirri ne daga shi sai Allah sai kuma Umma data share masa hawayensa, tura ce takai bango har yaji bazai iya zama da kashi a ciki ba don baya maganin yunwa, don haka ita kad'ai tasan maganar ya dad'e da gamsuwa da halin dattako irin nata, don yasan zata taka rawar gani ta magance masa matsalar data addabeshi shi, shiyasa ya kai mata ziyarar gaisuwa da rok'on iri kamar uwa ya d'auketa ba suruka ba. Yana parking ya k'ura mata idanu ta cikin glass d'in motar, tana rik'e da lema tana tarar ruwan saman a wani bokitin roba shi kuma Nawaz yana Tara nashi cup d'in yak'i taruwa, ta dinga yi masa dariya ya shammaceta ya ture nata bokitin ruwan ya zube, sai ya hau shima yi mata dariya harda tsalle yana k'yak'yata mata dariya k'ya k'ya k'ya. Ta lura da motar Faheem don basu ji shigowarsa ba saboda ruwan da akeyi a tunaninta bazai fito ba saboda ruwa karya jik'asa, ga mamakinta fitowa yayi abinsa, Nawaz ya dinga d'aga masa hannu "Daddy Daddy ruwa zai dokeka ka gani ya jik'a ka" ya karb'e lemar daga hannunta yana kallonta, ta sunkui da kanta "Hibbah" wannan lafazin na Faheem sai taji.muryar tashi ta canza "baki kawo min lema ba kin Bari ruwa ya jik'a Daddy'n Nawaz." Ya ilahi, ita dai wani abu take ji tamkar zata fad'i k'afafunta suka d'auki rawa, ya zuba Mata idanu kawai yayi nisa ya tafi da yawa ikon Allah haka so yake Allah ya had'aka da Wanda baka tab'a tunani ba. Kamar bata motsi kunya da nauyinsa sun rutsa da ita. Shi da kansa ya samu damar da yake jira yasa Hibbah ta fad'a tarkonsa yau k'wauron baki ya k'are zai fasa k'wai. "Hibbah" da sauri ta juya da gudu cikin gida, yayi d'an murmushi yana Mai jinjina wannan irin kunyar ta Hibbah. D'akinta ta shiga ta d'ora kanta a bisa pillow zuciyarta kamar tana harbawa idanunta Faheem kad'ai take gani kamar cikin cikin film wannan abu yak'i goguwa nauyi ne tsoro ne ko kuma kunya me yasa haka? Faheem dodo ne? Tsabar cika ido da kwarjini ne ta bawa kanta amsa. "Hibbah" yadda yake futawa take tunawa a tausashe sai taji kamar yafi kowa iya furtawa. "Aunty Hibbah kizo inji Daddy" zumbur ta tashi zaune ta kad'a kanta "to ina zuwa" Ta jima tana sak'a da kwancewa me ya hanata fita kiran Faheem don fa ya rud'ata nauyinsa ya k'aro. Ya bud'e k'ofar ya shigo, ta dubeshi ya jingiba bayansa da k'ofar ta saci kallonshi wata k'atuwar rigar sanyi sanyi ya Santa mai taushi kamar gashin jikin mage, ya cire hular jikin rigar daga kansa gami da Santa hannayensa cikin aljihun rigar. "Hibbah" sai da ta kad'u sassanyan kiran ya ratsa zuciyarta "Hibbah ni gani nazo tunda na aiko ki zo kin k'i fitowa ni d'in............ *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page4⃣0⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* "Hibbah ni gani nazo tunda na aiko ki so kink'i fitowa ni d'in abin tsoro ne? Ni fa mutum ne kamar ki idan kuma kunya ce gaskiya tayi yawa" tayi shiru ta kasa magana "ok to ki saurareni ina so ne muyi wata mahimmiyar magana, kinsan so wani abu ne dake faruwa da mutum ba tare da zato ko kuma tsammani ba, munyi amanna da fad'ar Allah ta'ala shike jefa so a tsakanin d'ayanmu, na tsinci kaina a cikin wani hali mai wuyar fad'uwa may be ma kin fahimce ni kika basar, na nuna miki alamomi da dama ke mai hankali ce kinsan me nake nufi. Ina nufin kalma guda aure, idan banda shi bani da wata manufa a gareki, ni zan aureki amma da sharad'in abu biyu kina sona kuma kina ra'ayina don wad'annan abubuwan suke Gina aure." Saura kad'an numfashinta ya d'auke wani abu taji ya harba a zuciyarta, duk lissafinta ya wargaje , wata sabuwa inji d'an caca ko da wasa bata tab'a tsammanin wannan furucin daga bakin Faheem ba, ikon Allah wai ita Hibbah 'yar aikin gudansa ba kazar kowa ba ita yake so? Ta yarda wani wajen Ana gudunka ana tsanarka wani wajen kuma sonka da k'aunarka ake yi, duk mutumin da ake yiwa hassada da k'yashi sai hassadar ta zama kamar taki ake barbad'a masa Allah abin godiya wai ita ke da matsayin da Faheem yace yanaso tabbas idan Allah bai wulakanta ka ba babu mai wulakantaka a duk fad'in duniyar nan, Inna lami taso lalata rayuwarta amma da yake Allah gafuru rahim ne sai yayi hanyar zuwanta birni don wasu su gyara mata *RAYUWA* mai makon a lalata, Allah ne ya bata wannan baiwar bamai iya ja da ikon sa. "Ni zan aureki" kalmomin da suke mata yawo kenan, to me za tace abubuwa sun sark'e, "Hibbah" ya katse mata tunani, sai taji kamar ta fita da gudu don bayyana son nata gareshi zai dad'a nauyi da kunyarsa a tare da ita "Hibbah ya dai sai kin bani amsa ko muyi ta zama anan" Ya rud'a mata k'wak'walwa ta rasa Kalmar da zata d'orata a harshenta. Ya zauna gefen gadon nan fa taji daddad'an k'amshin dake manne a jikinshi ya kuma tsumata, a yanayin da take jin Faheem ranta shi d'inne tsagwaronsa kamar yadda take ji a yawan lokuta idan sun had'u abin na yi mata yawo, ko me kenan? Zata iya fassara shi da kalmar "so" to amma anya wannan so ne, idan sone me yasa bata jinsa ga Jabeer ko Faruq, tunda suma suna sonta kuma dasu ne ta Saba mu'amalar soyayya musamman ma Jabeer. Yau dai gata ga Faheem mutumin da take d'ari d'ari dashi, hanyar da yabi ma bata so ta bi don kar suyi arangama saboda mutuncinsa da k'imarsa da take gani fiye da kowane mutum a rayuwarta. "Haba Hibbah nifa bana son nayi ta magana a k'yale ni ni kad'ai bana jin dad''i, na jima a cikin k'alubalen sonki nayi k'ok'arin barin abin saboda wasu dalilai amma Hibbah na kasa jurewa, ba irin wannan son bane ake dak'ileshi yafin k'arfin hakan, na yarda da shi na kuma daina wani inkari cewa zan iya hakuri dashi domin ya wuce tunani na. Na sani kina ganin k'imata da girmana inason mu tafi a haka ki cigaba da ganin mutunci na, don ni hakan bazai hanani nuna miki k'auna ta zahiri ba tunda bawai wasa nake ba magana ce ta gaskiya ta aure, lokaci na k'urewa ko yaushe na k'ella ido na ganki sai abin ya tab'o min zuciya, bai kamata na b'oye miki ba don sai da amincewarki za muyi aure, kinga kuwa dole na nemi had'in kanki." Yayi murmushi gami da tsagaitawa ya maida numfashi "hmm Ana min rowar eyeball d'in nan har b'oyewa kikeyi don karna gani, Hibbah kinsan saboda ke nake dawowa gida da yamma, ko muryarki kawai naji sai hankali na ya kwanta, to ina zankai sonki bazai yuwu na iya daurewa ba ko kuma na cigaba da k'wauron baki ba, kinsan halayena nasan naki abinda na sani tuwo na maina za'ayi ki auri mai gidanki bana son tsaiko ki tare nan da sati biyu" ya dubeta "zuciyarki ta gamsu dani da shawarata?" Ta rufe idanunta da hannayenta magana dashi tana mata wahala. Hmm shidai ya sani akwai sanshi a tare da ita, sai dai ta kasa fahimtarsa ko ta san itama tana sonshi d'in domin kunyar da take mishi ai alamune na akwai wani abu a can k'asan zuciyarta dake tirsasa jin kunyar. "Hmm amma dai Hibbah nan zansha wahala dake wannan kunyar taki tayi yawa amma akwai lokacin da zan rad'a miki wani abu sai kin manta da komai banda ni d'in nan" ya mik'e "inason tuwon masara da k'ashin rago miyar kukan nan, ga wannan ki bawa Isah ya siyo miki abinda kike da buk'ata." Kud'i ne ya ajiye a gefen gado. "Zan fita ne tunda ruwan ya tsagaita" ya d'anyi murmushi ya kad'a Kai wannan yanayin bazai manta shi ba don a yanzu Hibbah ta zama mallakinsa, ya fice. Ta k'urawa kud'in idanu har yanzu k'amshin Faheem ke mamaye a d'akin, wani murmushi da bata san dalilin yinsa ba ya sub'uce a leb'enta, wannan shine k'auna da so Wanda yake daga Allah ne, ta dad'e tana son bincike da bin k'wak'wk'wafin abin amma sai zuciyarta ta dak'ile zargin, domin abune da take ganin har abadan bazai faru ba taya ma Faheem zaice yana sonta har ya aureta. Wannan ikon Allah da yawa yake, surar Faheem ta fara hango wa sai taga kamar abinda wuya cikakken mutum mai mutunci wayayye, shi komai nashi a tsare yake ta duba tsarin gidansa da yadda yake tafiyar da rayuwarsa. Ko Kausar matarsa ta isa ta firgita 'ya mace, idan banda ita da ta zauna da su ta karanci tsarin Kausar akwai abubuwa da dama data kuskure su bata kuma damu data gyara ba, wai kuma cikin ikon Allah ita d'in dai yake ra'ayi to me take dashi daya ja hankalinsa. Kausar da Faruq sune k'adangaren bakin tulu, ita dai baza ta iya auren mijin Kausar ba kuma Yayan Faruq, don haka batun Faheem fa sai hakuri. Hibbah lallai Allah ya bata baiwa, wasu lokutan tana ganin Kausar takai k'arshe a sawun had'ad'd'un mata, wai me mace 'yar gayu irin Kausar yaya za'ayi ita ta burgeshi. A shirmen tunaninta kenan Allah sarki Hibbah rashin sani yafi dare duhu soyayya had'uwar jini ne, Faheem shi yaga abinda ya burgeshi harya yamutsashi da rud'ashi akan 'yar budurwar daya kira Hibbah. Sark'a Mai rikitaniya ya ta iya da Faruq idan yaji labari ga kuma bawan Allah Jabeer da ya mik'a wuya magana tayi k'arfi don kowa yasan dashi, furucinsa ya shiga ranta. " _Hibbah ba zan tab'a wulakantaki ba har abada ni nasan darajarki, a yadda na ganki kinyi min kuma in sonki kamar raina shiyasa nake so muyi aure donki samu 'yancin kanki, Hibbah kina da daraja da baiwa amma sai mai hankali da nazari ne zai gane nasan ke baki san haka ba_" Tana jin fitarsa saita samu........... *Ga wannan ba yawa, banjin dad'ine ina barar add'ar Ku* *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page4⃣1⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Fans naga dukkan sak'onninku na gode da addu'o'in ku Allah ya saka da alkhari, ya k'ara donk'on k'auna🤝* Taro ne na mutane hud'u kacal don tattauna muhimmiyar magana domin kowanne a cikinsu zai bada gudunmawa da kuma taka rawar gani. Ya gyara xama yana kallonsu d'aya bayan d'aya don sun bada dukkan hankulansu don sauraronsa "kin bani mamaki Aysha zumunci fa babban abune Wanda zai iya Kai mutum aljanna ina so ku zama tsintsiya d'aya mad'aurinku guda dole ne ka sowa d'an uwanka abinda zaka soma kanka shine cikar imani, abubuwa suna ta faruwa ba akan idanuna ba saboda ni ba maxauni bane. Amma banji dad'in abinda kikayi ba Aysha kinsani komai lalacewar Faruq naki ne koda d'an ta'adda ne mai kisan mutane don haka ni d'innan zan tirsasaki dole kiso abinda yake so koda ke baki sonshi, indai har kinason ki gama da ni lafiya, ni banga dalilin zak'ewarki ba don Hana ruwa gudu kice bazai auri yarinyar da yake so ba, ke ba Wanda kike so muka amince kika aure shi ba? Waya hanaki? Haka ake rayuwar duniya idan jifa ya wuce kanka ya fad'a kan ko waye ko? Wato ke kinsamu shiya rasa. To bara na fad'a miki matuk'ar kina son shiri dani to karki sake saka baki a cikin maganar indai ba alkhari xaki fad'a ba wannan shine dalilina na Tara Ku anan gobe insha Allah zanje mu gana da marik'in yarinyar Alhaji Sani, Kai Faheem kai zaka wakilceni ka jagoranci komai babu shakka nasan baka da wata matsala. Next week zanyu tafiya kuma sati biyu zanyi insha Allah, kayi k'ok"arin gama duk wani shirye shirye za'a d'aura aure ne kafin Faruq ya tafi Germany Inda zaiyi contract d'insa bazai wuce wata biyu ba zai dawo idan ya dawo sai ayi binkin, shikenan idan babu Mai magana zaku iya tafiya" Aunty Aysha ta girgiza kanta don ranta ya b'aci d'aci take ji a ranta tamkar ta rushe da kuka don bak'in ciki shikenan ta faru ta k'are, gashi Daddy ya d'ora mata laifi don shi daman a duniya babu abinda yak'i jini kamar ka tab'a Faruq to fa bashi da mak'iyi kamar kai, Faruq baya laifi a gurinsa duk abinda akace yayi zai k'aryata ya dinga bad'an da bashi da dalili wai ansa mishi yaro a gaba, wannan shine sanadiyyar lalacewar Faruq. Ya ilahi, babu tsimi babu dabara sai daga Allah, kansa kamar ya rabe biyu ga zuciyarsa data tsananta bugawa bai tab'a shiga tashin hankali irin na yau ba, ya rasa a wane hali yake ciki sai dai hakuri, don Faruq k'aninsa ne kuma babu yadda zaiyi don tuni ya yanke hukuncin sadaukarwa da Faruq soyayyarshi, sai dai son Hibbah ya illatashi ainun don allah ne kad'ai yasan yadda yake matuk'ar son Hibbah a ransa, ji yake inama bai furtawa Hibbah Kalmar so ba ya barsa cikin ransa, dominzata zama Matar k'aninsa kuma dole akwai abinda zai had'asu yasani tunda son gaskiya yake mata duk sanda suka had'u dole ne wani abu ya motsa zuciyarsa. Sai yaji wani abu marar dad'i domin yaci burin *RAYUWA* da Hibbah. Ya katse masa tunani "baka ce komai ba Faheem" bai yarda sun had'a idanu da Daddy ba don zai iya fahimtar yanayinsa ya sauya, har shima ya ja masa bak'in layi kamar yadda ya yiwa Aysha yanzun nan, ya d'anyi gyaran murya don yawun bakinsa ya bushr akan harshensa "insha Allah babu matsala Allah ya tabbatar da alkhari" "ameen Faheem Allah ya yi muku albarka, ka gaishe min da abokina Nawaz" yayi murmushin k'arfin hali yayi musu sallama. Faruq ya bishi da kallo yana wani tunani akwai abubuwan da ya jima yana nazari da son ganosu akan Faheem ya sanya mishi ayar tambaya, labarin zuciya a tambayi fuska ya gano Faheem baya son mu'amalarsa da Hibbah, yana ganin wani yanayi a tattare dashi a duk sanda ya gansa da Hibbah sai dai kawai bai tab'a fitowa k'arara ya nuna da'awarsa ba balle ya tofa wata kalma Mara kyau. Aunty Aysha ce 'yar Hana ruwa guru saidai ta manta gaba da gabanta shima shiyasa ya kawo k'ararta wajen Daddy inda ko tak'i ko taso dole tabi, ko d'an shaid'an ne shi ba d'an bariki ba saiya auri Hibbah. Ba k'aramin dad'i yaji ba shiyasa yake k'aunar tsohun nasu mutum ne mai jajircewa akansa baya k'aunar b'acin ransa, Daddy ya dafa kafad'arsa fuskarsa da murmushi, tunaninsa ya katse yayi dariya "na gode Daddy banson me nayiwa Aunty Aysha ba bata sona yanzu." "Ya isa banson wannan ba kaga nayi mata barazana da fad'aba kace zaka kawo mata raini babu ruwanka kabar ni, ni da ita tunda duk ni na haifeku kuma nasa albarka a cikin wannan aure nayi addu'a, Allah ya albarkaci lamarin ka kwantar da hankalinka idan kaga ba'ayi ba to Allah ne bai k'addara za'ayi ba. Amma ina Jan hankalinka ka nutsu ka gyara halayenka don shi aure nauyi ne da hak'k'insa zai d'oru a kanka ka gyara zuciyarka ka zama cikakken mutum ka duba misali akan d'an uwanka Faheem mana abin kwatancena da alfaharina a ko ina za'a girmamashi." Ya gyad'a kansa "insha Allah Daddy Allah ya k'ara girma" "ameen" Faruq ya mik'e shikam tafi nono fari don farin ciki ya cika zuciyarsa a yau. K'wak'walwa ta hargitse ya fad'a motarsa gwuiwoyi a sab'ule, kamar an doke idanunsa sun k'ank'ance kansa yayi nauyi ya rasa meke masa dad'i a duniya yau zuciyarsa ta tunzura ta ya mutse "Hibbah" ya furta cikin wata iriyar murya ikon Allah abu biyu ne rak a kowane jarrabi na *RAYUWA* samu ko kuma rashi, nasara ko rashinta, amma rashin cikar abinda kake so yafi tada maka hankali don zakaji kamar ka rasa wani sashe na ruhinka. Wace irin rashin sa'a Gare shi wane irin so yake yiwa Hibbah gashi kuma ya sameta ta zama mallakinsa amma zai salwantar da soyayyarta don faranta ran mahaifinsa da d'an uwansa. Anya ma zai iya tuk'in nan kuwa? Aunty ta bud'e motar ta zauna, waya fi jin bak'in ciki tsakanin ita da Faheem, sam bata ji dad'i ba Faruq yayi nasara, gabanta ya cigaba da harbawa ta had'iyi yawu dak'yar cikin damuwa, nazarinta da tunaninta baika ga fahimtar Faheem ba ganinta ta fishi bak'in cikinda shiga damuwa da tana da yadda zatayi to tabbas da saita hana wannan auren, kawai abinda ta d'auka Faheem baya jin dad'i ne. "Baka jin dad'i ne naga yanayinka gaba d'aya ya sauya? Naga yanzu muke tare lafiya lau, ni maganar shashashan yaron nan ta dame ni" yayi shiru, hakan ya dad'a bata tsoro "Yaya karka tada min hankali wani abin ke damunka?" Ya sunkui da kansa shi kad'ai yasan me yake ji a zuciyarsa. Ya cira idanu ya dubeta saida gabanta ya fad'i ragagas, cikin razana ta fiddo ido tana mamaki bata tab'a ganinsa cikin wannan halin ba. Ya dafa saman kujerar da take zaune " Aysha babu Wanda zai iyayi min maganin fitinar da nake ciki sai Allah na shiga mawuyacin hali Wanda ni da kaina tunanina da hangen nesa na bai tab'a hango min shiba, domin zuciya ta ta Gaza sarrafuwa naso dak'ile tasirin al'amarin amma baud'ad'd'ene a yanzu lokaci ya k'ure min, saidai ni da kaina ina tausayawa kaina zanyi k'ok'arin hakuri Allah ya bani jimiri." Ya dubeta cikin idanu "ina son Hibbah son da bazan iya misalta miki shi ba na fahimci na fahimci hakan saboda abubuwan da suke faruwa tsakaninta da Faruq shiyasa na kasa samun nutsuwa nasa Hibbah gaba na tambaye ta don ina son gano abinda ke tsakaninta da Faruq, amma bata nuna min akwai wata alak'a a tsakaninsu mai k'afi ba kamar yadda na sani dai shike zuwa wajenta, na sanya idanu da tsaro don sanin halin yaron nan bawai yana sonta tsakani da Allah bane, da ita yarinyar zatayi tunani bai kamata ta kuma sauraronsa ba ko don abinda yayi mata, tsoron kar wani abu ya faru na kasa b'oye abinda ke zuciyata da farko na gana da Ummanta d'ari bisa d'ari ta bani goyon baya kafin nace zan aureta, a lokacin tace na kirawo waliyina a d'aura mana aure saboda son da nake yiwa Hibbah ya rufe min idanu, ban kawo komai a raina ba na Kira Abba na fad'a mishi komai Allah ya taimake ni a lokacin yana gari, a ranar da yamma aka d'aura mana aure da Hibbah a masallacin unguwarsu. Bana son abinda zai b'ata ran daddy Aysha shiyasa na yanke shawarar zan barwa Faruq Hibbah ni zan hakura!" Ya had'iye bushshshen yawu "Aysha ki kaini asibiti wani abu yana tab'o min zuciya" ta runtse ido ga mamakinta hawaye ya zubo mata saboda tausayin d'an uwan nata. "Haba Yaya wane irin hukunci ne wannnan ka yanke ma kanka, kai ne kawai is dace da aurenta domin kai mutum ne dana tabbatar baza ka tab'a wulakanta mace ba har *Abadan*, duk wani jin k'ai da tallafi zaka yiwa Hibbah a matsayin matarka saboda kyawawan halayebka haka matsalolin gidanka sun dakushe, amma Hibbah tasab komai kuma zata magance su da tafiyar da al'amuran iyalanka. Ta saba da Nawaz ta jashi a jiki tana tarairayarsa me yafi wannan kwanciyar hankali, gata mai ladabi kuma tana baka girmanka dayi maka biyayya bata tab'a tsallake maganarka, wallahi na tabbatar Hibbah xata amince da auren nan ko musu baza tayi ba, ko da ace bata ra'ayin aurenka maganar gaskiya kawai idan su dadday sukaje sukaji tana da aure sai mu fad'a musu kaine mijin, amma zancen sadaukarda soyayya ma bai taso ba." Ya numfasa "Aysha kinfi kowa sanin halayena bana son naga ko kad'an na b'atawa su daddy rai, kinsan yadda yake ji da Faruq kina ganin dai maganganun daya fad'a miki don kawai kince bazai aureta ba, to ina kuma ni Dana aureta gaba d'aya? Gobe idan sunji tana da aure a goben zan bar masa ita insha Allah, Aysha karki manta komai nufin Allah ne ki rik'e min wannan banason kowa ya sani sai gobe zan fad'a musu da kaina, Faruq d'an uwana ne banason hanashi auren Hibbah ina k'ausa sosai zan iya sadaukar mishi da komai." Ta goge hawayenta tana girgiza kai "Yaya wata kusan tafi wata bazan iya had'a 'yan uwantaka ta dakai da shi ba, bazan iya jayayya da kai da mahaifinmu ba inda wani bare ne da saina hana yuwuwar abin amma tunda Kai ka yanke hukunci da kanka, Allah ya tabbatar mana da alkhari, muje na kaika kaga doctor." Ya yamutsa fuskq "ba komai kawai ki rakani gida bazan iya tafiya ni kad'ai bane, kinsan tuk'i saida nutsuw................ *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page4⃣2⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* "Uncle" ya d'ane jikinsa, d'agashi yayi cak yana juya shi suna dariya, tana tsaye kallonsu kawai tayi saita koma kitchen ta cigaba da aikinta. Ya sauke Nawaz ya bi bayanta kitchen d'in, ya tsunkule ta a gefen cikinta tayi zillo gefe fuskarta a d'aure "bana son abinda kake min bai kamata ba wannan ai wulakanci ne" idanunta suka ciko da k'walla ya ritsata yana yi Mata murmushi, idan da abinda ta a duniya to isgilancin da Faruq yake yi mata a duk sanda yazo gidan sai yaga hawayenta hankalinsa yake kwanciya, ya lakuce hancinta ta juya kai gefe "albishin na kawo miki Hibbah, wannan duk gangar jikin nawane nan da sati biyu za'a d'aura mana aure, iyaye sunyi magana kinga na zama naki kin zama tawa har *Abadan* maganar da akayi jiya kenan, Yaya mutum ne mai zurfin ciki na sani bazai fad'a miki ba ko da yake ke ba abokiyar hirarsa bace, nasan bakwa wata mu'amala idan banda ta gaisuwa tunda shi ba shiga harkar mutane yake yi ba, ni shiyasa ma zuciya ta tak'i yarda dashi har na d'ora wani zargi a akansa to amma na kasa gano gaskiya." A razane take kallonsa "Faruq idan mafarki kake to ka farka don wannan maganar shirmene irin naka, ta yaya ma ni zan aureka? Wani irin zama zamuyi dakai? Nasha fad'a maka iyayena Jabeer suka sani baza kuma su canza ra'ayi ba don hakan nuna k'aranta ne" ya had'e girar sama da k'asa to zaki gani kuwa ni zan tsone miki ido idan kuma baki yarda ba kije ki binciki labarin don haka bakin alk'alami ya bushe ni dake mutu ka raba," ta matsa gefe ya dings k'yalk'yala mata dariya mai ban haushi, hangar cikinta tana kad'awa "Allah ya tsare ni da aurenka saidai a kai maka gawata Faruq don bana sonka bana k'aunar halayenka" "to ai kuwa za'a Kai gawar taki gidan nawa ko kuma muyi mutuwar kasko ki k'one mu gaba d'aya saboda k'iyayya" Bata san sanda ta sa kuka ba don bak'in ciki, ya rik'o hannunta ta k'wace da k'arfi d'aki ta nufa da gudu ta kulle hankalinta yayi mugun tashi, number Aunty ta shiga kira, tana d'agawa cikin rawar murya "Aunty........" Da sauri Aunty ta katseta kinga ni babu ruwana, bani ba ke Hibbah kuma kanki kika cuta, Faruq ba kanwar lasa bane d'an uwa nane amma bazan b'oye miki ba ina cikin masu da'awar wannan aure, Faruq jikinki kawai yake so daya samu zai yarda k'wallon mangoro ba fata nake miki ba." Ta fashe da kuka "Aunty wallahi tallahi bana sonshi basan ya k'ulla wannan k'aryar ba nima yanzu yazo yana fad'amin" tsawa Aunty tayiwa Hibbah donhaushinta take ji "dalla ni rufe min baki ni kin bani mamaki da kunya, Dana san kina son shi da tun farko ban d'aukoki daga gidan ba na k'yaleki yayi miki abinda zaiyi miki, wallahi Hibbah ina tausaya miki a hannun Faruqna fad'a miki badon Allah yake sonki ba" cikin kuka Hibbah tace "Auntyna kiyi min rai na tuba wallahi gaskiya na fad'a miki, na shiga uku Aunty kiyi hakuri wallahi bazan iya auran Faruq ba," "to ni me zan yi miki ai ta faru ta k'are tunda har iyaye sun shiga maganar saiki d'auki k'addara haka Allah yaso, fatana Allah yasa ki bashi guzurin shiriya ki dunga sashi a hanya ta k'awarai" Aunty tana kaiwa man ta kashe wayar don ba k'aramin haushin Hibbah take ji ba, gani take da Hibbah bata amince da Faruq ba da bazai ce sun daidaita ba, kuma da gani take Hibbah tana son Faruq don da bata sonshi baza ta dinga sauraronshi ba, da wata ce yadda yayi barazanar lalata Mata *RAYUWA* ai da ko kallo bai isheta ba. Hibbah tayi wurgi da wayar ta kifa kai ta saki wani irin kuka, ita dai ta shiga uku haka *RAYUWARTA* zata kasance cikin k'unci, kuka take sosai tana shashsheka kamar zata shid'e numfashinta har wani sama sama yake yi. Ji tayi an bud'e k'ofa ga zatonta Nawaz ne, wani mugun kallo tayi masa don ita tayi zaton ma ya tafi. A hankali ya zauna kusa da ita, ta zubura ta koma gefe don yanzu bata k'aunar ganinshi ko kad'an, ya d'aure fuska gami da d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana kad'awa cikin k'asaita yana wurga mata harara, wanj murmushin mugunta dake saman fuskasa yake jifanta dashi. Wata muguwar sha'awarta yake ji kuma yanason aikata k'udirinsa don ya tabbatar mata da ta zama tashi, surarta mai kyau yake gani, kafin ta ankara ya fizgo hannunta "haba baby Hibbah aini mijinki ne na rantse miki bazan wulakantaki ba inason ki ki yarda da ni" Wani bak'in ciki ya tokareta ta yaya zuciyarta ma zata amince da Faruq bayan ba sonta yakeyi tsakini da Allah ba, illa da wata muguwar manufa, burinsa kawai ya lalata Mata rayuwa, ta tuna maganar Aunty Aysha data ce _jikin kawai yake so daya samu shikenan zai yarda k'wallon magoro,_ tabbas haka ne gashi nan yanzu ma bashi da burin daya huce yaga ya tab'ata. Faruq ya tashi daga kusa da ita kamar Wanda zai fita daga d'akin, ita tayi tunanin ko haushi yaji zaiyi tafiyarsa, saidai taga sab'anin haka kulle k'ofar yayi ya zare mukullin ya jefa a aljihunsa yana dariyar mugunta. Kan gadon ya turata da k'arfin tsiya ya mak'ureta, Allah sarki Hibbah sai ta kuma sakin kuka. Cikin kuka take magana kanaji kasan cikin ranta babu dad'i "matuk'ar ka cimma mummunar manufarka akaina wallahi sai kayi nadama a rayuwarka, kuma aurenka ne bazanyi ba, bazan hanaka aikata k'udurinka ba tunda bakaji tsoron Wanda ya halince ka ba kana aikata abinda baya so." Bai ma san tanayi ba don shaid'an ya kad'a masa ganga yau dai yana k'ulaficin yarinyar nan wannan masifa dame tai kama. "Sai na fad'awa iyayenmu abinda kayi min domin su sani aure ya jagule, kuma su sani kai bak'in kumurci ne azzalumi" Ya rufe mata baki da hanci kamar zaiyi mata k'amshin mutuwa. Da k'arfi aka bugi k'ofar zubur ya d'agata yana harar k'ofar a k'ufule yake saboda burinshi bai cika ba, da gudu ta tashi zata fita ya rik'o hannunta ya murd'e ta saki k'ara ya toshe mata baki "ki nutsu ki kama kanki matuk'ar kikayi yunk'urin tona asiri na to kamar kin fasa k'wai ne don Daddy bazai yarda da zancen ki ba, koda zaki rantse da Qur'ani, kuma ina tabbatar miki mutuwa ce kawai zata hana wannan auren Hibbah saidai idan na mutu ko ke kin mutu. Ina tabbatar miki wannan gangar jikin mallakina ne kin zama tawa iyaye sun shaida kuma kafin wannan lokacin saina aiwatar da nufina yanxu an b'ata min shirina amma ki saurari gamonmu a gaba sai nayi kaca kaca dak............." Bugun k'ofar ya katse shi "Aunty Hibbah, Aunty Hibbah" yayi tsaki Nawaz ne amma yaron nan ya kwafsa masa ya doki iska da hannunsa, ya dubeta kuka take sosai kome ya tab'o zuciyarsa ya tallafo hab'arta "Hibbah sone sanadi ni kaina saina miki wani abin zanyi nadama ke kuma kiyi ta yimin gardama, to mene abin damuwa sirrin mu nefa ni dake babu Wanda zaiji. "Ubagiji ya sani wannan gub'atacciyar soyayya ce domin babu Allah cikin lamarinka, kana aikata k'udirinka aure ya lalace sai anyi istibra'i don tsarkake aure, Faruq kaji tsoran Allah ka tuna kana da k'anne idan akan yi musu haka baza ka ji dad'i ba" "ke ki share wannan wa'azin naki, abu ne na da yanzu zamani yazo da irin wayewa to menene ni na k'addara ke matata ce to meya rage, ai Allah mai gafara ne, ni ba ruwana da wannan surutun banzan ni saina yi abinda nake so." "Sai kayi laifi kace Allah mai gafara ne bayan yace kar kayi kai kuma kace sai kayi, a hakan Allah zai yafe maka bayan kak'i bin umarnunsa, Allah ya tsare ni da kai wallahi Kai babban mak'iyi nane" ya fashe da dariya "zan naushi wannan bakin mai tsiwa zaki d'and'ani kud'arki gamona dake ba kyau, gaskiya kinyi sa'a ina sonki Hibbah" ya lakuto hawayenta yana murmushi, ya tusa hannunsa a aljihu ya zaro mukullin ya bud'e k'ofar sannan ya dubeta yana murmushi yasa kai ya fita. Ta zauna dirshen tana kukanta mai zafin zuciya ta kuma yiwa Allah godiya tasan shine yake tserar da ita sharrin Faruq, tsabar rashin mutunci ne da rashin tsoran Allah, Faruq bashi da tausayi da imani dole idan y k'udurce mugun nufinshi sai ya aikata abinda yake so, baya fargaba shakkar uban kiwa Anya kuwa Faruq bashi da matsala a k'wak'walwarsa. Nawaz ya katse mata tunani ya kwanta akan ciyarta "Aunty Hibbah Daddy na bashi da lafiya yana................. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page4⃣3⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* A razane take kallonshi "me ya same shi? Tun yaushe ne bashi da lafiya?" Kausar ta lek'o fuskarta babu walwala "wato ke yanzu iskancin naku har sai kun shigo d'aki kun rufe kanku a ciki ko? To wallahi ba'a nan gidan ba don zan sanar da Faheem kwashe kwashen banzan da kike yi, dama tsintacciyar mage bata mage, kizo ki had'a min tea inason nasha kafin na koma asibitin" wasu hawaye suka zubo mata masu zafi tabbas dole ne kowaye ya d'aura zarginsa a kansu tunda suna d'aki ita dashi kuma su ba muharraman juna bane, amma wulakancin da Kausar take mata ya isheta haka itama yau basai gobe ba insha Allah zata bar musu gidansu zata kira Aunty t bata hakuri don gaskiya ta gaji da rashin mutuncin da Faruq da Kausar suke yi mata gara ta tattara ta bar musu gidan su........... "Dalla ki huce ki kawo min tea nace, ai abinda yafi kuka ma sai kinyi shi badai kwad'ayi kika zab'arwa rayuwarki aba" Hibbah t goge hawayenta ta jinjina kai tare dayin hanyar kitchen. Ta had'o mata tea d'in ta kawo mata ta karb'a tana yatsina fuska ba madalla bare na gode ta Saba da wannan wulakancin na Kausar don wai bata isa ba ma tayi mata godiya. Hibbah ta d'anyi k'asa da Kai "Aunty a wane asibiti Daddy'n Nawaz yake zanje nayi masa sannu?" Ta wurga mata harara tare da jan tsaki "b'ace min da gani bansani ba stupid kawai" tamkar an kwad'a mata gora a tsakar kanta, wannan wulakanci dame yayi kama? Koda mutunci ne kawai a tsakaninta da Faheem ace bashi da lafiya yana kwance a asibiti ai ya dace taje tamai sannu bare mutumin da ya zame Mata kamar uba ya rik'eta amana. A sanyaye ta wuce d'akinta Nawaz zai biyota Kausar ta buga masa tsawa ya koma ya zauna, ta shiga d'aki zuciyarta a dagule ta janyo wayarta tana tunanin ko ta Kira Aunty Aysha tana kuma tsoro karta kirata tak'i d'aukar wayar don tasan haushinta take ji, tana mason ta fad'a mata ma jiya ta gama exams d'inta amma tana jin tsoro, number Aunty ta shiga dialing zuciyarta cike da tsoro. Sai da ta kusan tsinkewa sannan ta d'auka "me kika kira kuma ki fad'a min?" Cikin sanyinta tace "Aunty da rana, kiyi hakuri ki saurare ni" "lafiya ai kema kinsan laifinki dole ne nayi fushi dake wato kin had'a kai da Faruq kin bashi goyan baya, Hibbah bazan b'oye miki ba ina tausaya miki Faruq ba cikakken mutum bane don baki fini saninshi ba, d'an uwana ne amma bashi da halin mai kyau kuma halin kirki shine cikar mutum, Hibbah idan har kika auri Faruq to baki yiwa kanki adalci ba ki duba irin rayuwar da kika taso a cikinta karki manta fa har yanzu bakiyi 'yancin kanki ba a k'ark'ashin wasu kike kina musu aiki, idan kika duba sam Faruq bai dace da rayuwarki ba, kamata yayi ki samu mijin da yasan daraja da k'imarku Wanda zai gyara rayuwarki ya ingantata, yanzu na gano nice kad'ai kishinki da tausayinki ke sam ba kya tausayin kanki, rashin zuciya ne irin nawa da nake ta k'orafi akan maganar" Hibbah ta fashe da wani irin kuka "Aunty yaya kike son nayi da raina kina d'ora min laifi babu abinda baki sani ba tsakani na da Faruq ke kika ceco rayuwata daga hannunsa, ni dai nasan wannan k'addara ce ta Allah amma babu sa hannuna akan duk abinda Faruq yake aikatawa tun farko na fad'a masa ni ina da wanda zan aura, kuma yace su Daddy yau zasu je wajen Alhaji zasuyi magana, yanzu nasan Alhaji bazai Hana su Daddy ni ba saboda ya d'auke ni kamar 'yarsa idan nace banaso zaiga kamar don bashi ya haifeni ba Aunty ni addu'arki kawai nake nema." "To ma fahimce ki Allah ya zab'a abinda yafi alkhari amma nidai auran Faruq bai kwanta min ba, yanzu ki shiryowa Yaya abinci kar kisa gishiri yana asibiti bashi da lafiya." Taji dad'in yadda Auntyn ta sauko "Aunty me yake damunsa ne haka?" "Ba komai sai dai kinzo d'in zakiyi mamaki idan na fad'a miki ciwon dake damunsa" ta rausayar kai "to Allah ya bashi lafiya yana wane asibiti?" "Nan dai asibitin da suke ganin likita" "to shikenan insha Allah ina tafe" sukayi sallama ta ajiye wayar tare da nufar kitchenta had'a masa abincin da marasa lafiya tayi wanma ta shirya ta nufi asibitin. A hankali ta shigo sanye take da bak'ar abaya tayi kyau sosai ya dubeta zuciyarsa ta harba, matuk'ar zai k'yalla idanu yaga Hibbah to dole saiyaji wani abu a zuciyarsa ko wanne abu Allah ne yake sashi amma akwai silarshi ko shakka bayayi itace silar wannan ciwon nasa. Bata yarda sun had'a idanu ba ta gaishesu da tambayar ya jikin nasa ta ajiye kayan abincin. Aunty Aysha tana kallonta da nazarin wani abu alamar tausayi "Hibbah ya shirye shirye banji kince komai ba ga Yaya ba lafiya" ta dubeta da mamaki me kuma ya kawo rashin lafiyar Daddy a ciki? "K'warai kuwa abinda kikaji na fad'a shi zaiyi ruwa yayi tsaki a d'aura auren nan don Daddy zaiyi tafiya, kuma nasan halin Faruq sarai bazai yadda a d'aga auren nan ba" ta had'iyi wani yawu ita kam ta shiga uku yanzu ba za'a fasa d'aurin auren nan ba. Faheem yana jinsu bai ce komai ba. Aunty ta kalleta duk tayi wani iri kamar ba ita ba tace "Hibbah ina sauraronki kinyi shiru bakice komai ba, alkawarin dana yi miki yana na nan bazan fasa ba zan bada gudumawata mai tsoka mu siyo abubuwa da ita." Maganganun Aunty sun sata rud'ani da rashin nutsuwa ta mik'e zata fita "Hibbah! Ya haka yaya muna magana zaki fita?" Ta tsaya Jim sai kuma had'a idanu dashi wasu hawaye suka zubo mata zuciyarta ta cushe da wani abu marar dad'i, kawai ta fice. Suka kalli juna da da wani yanayi mai ban mamaki, Aunty ta d'anyi murmushi tace "Yaya yarinyar nan ka yarda bata son auren nan da laifinta nake gani amma na gano wani abu k'ulli ne kawai Faruq yayi mata" ya yamutsa fuska "meye dalilinki na fad'ar haka? Kina da tabbacin abinda ke zuciyarta? Idan tana so zata yarda ta amince ne?" "Hmmm Yaya kenan har yanzu baka fahimci Hibbah ba, Hibbah yarinyace mai kawaici da alkunya tana da biyayya da zurfin ciki, nasan halayenta ni kaina sai tura takai bango nake sanin wani abu nata, matsin da Faruq yayi mata lokacin tana gida badan tana da hakuri ba da zata iya barin gidan don ba kowace macece za'ayi yunkurin rabata da kimarta ba kuma ta cigaba da zama a inda ake barazanar aikata mata wannan mugun abin, yanzu Yaya wanda yaso aikata wannan b'arnar ace yana son ta tsakani da Allah ni nasan k'arya ne yayi haka ne don comma wata manufa. Hibbah bata b'oye min sirrinta d'azu data kirani take fad'a min bata son Faruq lokacin idona ya rufe da fushi nak'i sauraronta daga baya nayi tunani mugunta ce kawai irinta Faruq don karya barta ta auri Wanda take..........." Wayarta ce ta katseta ta lalubo wayar a cikin jakarta sunan da ta gani ne a kan screen d'in wayar yasa zuciyarta bugawa ta kalli Faheem, yace "waye yake kiranki?" Tayi ajiyar zuciya bata amsa sa ba ta d'aga wayar don taga ta kusa katsewa. Bai ma Bari tayi magana ba ya hauta da fad'a "kun kyauta Aysha wato saboda bakwason Faruq ya auri yarinyar da yake so shine kuka had'a baki keda Faheem kuka k'ulla tuggunku yaje ya aureta kafin naje nema masa ko, to kuzo yanzu Ku sameni a gida ina jiranku," "kayi hakuri Daddy Allah ya huci zuciyarka, amma Daddy wallahi bawai don bama son Faruq ya aureta bane dama tuntuni Faheem yake sonta kuma yaje ya sami mahaifiyar yarinyar ta bashi ita.........." Cikin fad'a Daddy ya katseta "rufe min baki munafukan banza kiyiwa shi Faheem d'in waya kuzo tare tunda ni na kirashi yak'i d'auka" Aunty ta kwantar da murya "kayi hakuri Daddy ba k'in d'auka yayi ba muna asibiti ne bashi da lafiya kuma na kira Abba da su mamy na fad'a musu" "ba wata rashin lafiya da yake yi duk k'arya ne kuzo yanzu ina jiranku idan ba haka ba ranku zaiyi mummunan b'aci" yana gama fad'in haka ya kashe wayar. A sanyaye ta sauke wayar daga kunnenta, Faheem ya kalleta "me Daddy yace miki?" Ta sauke ajiyar zuciya "Yaya Daddy yak'i saurarata yace muje yanzu yana nemanmu, na fad'a masa muna asibiti baka da lafiya yace k'arya ne idan bamu zo ba ranmu saiya b'aci" Faheem ya yunk'ura ya tashi zaune "kije ki Kira min Dr Umar yazo ya sallame mu muyi sauri muje," "a'a Yaya baka jin dad'i fa har yanzu ka bari ni naje ni kad'ai" ya kalleta "haba Aysha so kike na sab'awa su Daddy ne? Ai rashin lafiyata ba komai bace akan sab'a musun da zanyi don haka kiyi abinda nace ki Kira min Dr" ta kalleshi tana tausayawa Yayanta, lallai ba k'aramun so yake yiwa Hibbah ba a dalilinta ya samu ciwon zuciya, gashi kuma ya d'aukarwa kansa hukuncin barinta. Ta mik'e da niyyar zuwa kiran Dr sai gashi ya shigo, suka gaisa ya shiga duba Faheem d'in bayan ya gama yayi 'yan rubuce rubucensa ya juya zai fita, Faheem yace "Dr inason ka sallameni yanzu pls" da mamaki sosai akan fuskar Dr Umar yace "saboda me? Kasan illar ciwon da kake tattare dashi kuwa? Kayi hakuri ka zauna a nan zaka fi samun kulawa" Faheem yad'an dubeshi "kayi hakuri Dr Daddy ne yanzu yayi min waya yana son ganina da gaggawa, pls ka taimaka ka sallameni yanzu karna sab'a umarninsa" Dr yayi shiru yana yaba biyayyar Faheem ga jyayensa "to shikenan Aysha biyoni office" Ya fita Aunty tabi bayansa suka je office ya bata takardar sallama da ta wasu magunguna da ake buk'ata tayi masa godiya ta dawo d'akin ta had'a kayansu suka fito daga asibitin. Wata bak'ar mota ce mai bak'in glass tayi parking a gabanta aka bud'e gidan baya tare da fizgota cikin motar aka rufe motar ta fita a 360. Cikin tsoro Aunty ta kalli Faheem tace "Yaya wannan ba Hibbah bace?" "Itace yi sauri mubi bayan motar" da sauri suka shiga motar Aunty ta figi motar a 360 suka bi bayan motar sai dai ina motar................... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page4⃣4⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Motar tuni ta b'ace suka kalli juna ita da Faheem wanda hankalinsa ya mugun tashi, ta karyar da kai "Yaya pls ka kwantar da hankalinka kaga baka da lafiya, insha Allah ba abinda muke zargi bane zai faru da Hibbah" ya gyad'a kai "muyi sauri Daddy yana jiran mu" Aunty ta juyar da kan motar suka nufi gidansu. Babu kowa a babban parlor direct parlor'n Daddy suka nufa Faheem ne a gaba Aysha tana biye dashi suka shiga cikin parlor'n, dukkanin ilahirin gidan ciki manyan gidan iyayen nasu kenan. Faheem ya shigo da sallama Abba da su momy da mamy ne suka amsa Daddy ko kallonsa baiyi ba yana zagaye parlor'n, Faheem ya gaishesu Aunty ma haka nan ma Daddy bai kallesu ba. Faheem ya matso kusa da inda Daddy yake "don Allah Daddy kayi hakuri wallahi bani da niyyar.............." Katse shi yayi ta hanyar yarfa masa wani mugun mari cikin fad'a ya fara magana "Faheem ni zaka wulakanta ka nuna ban isa da kai ba, saboda kuna yiwa d'an uwanku bak'in cikin karya auri yarinyar da yake so shine kuka zage kai da Aysha kuka k'ulla makircinku har ka aureta ko? To baka isa ba tunda shima ya rasata dole kaima ka rasa, aikin banza da wofi yara sai bak'in cikin tsiya ni banma yarda da wannan auren ba tunda shi Abban Janan shine walilinku kuma ba zama yake yi ba za'ayi aure ne babu waliyyi?" Faheem ya sunkui da kansa yanaji rad'ad'i mai zafi a zuciyarsa baya so yaga ran iyayensa ya b'aci sam. Abba dake zaune ya kalli Daddy cikin kwantar da murya yace "Daddy'n Faruq ka tsaya kayi bincike akan abinda ya faru kafin ka yanke hukunci, ni d'innan nine nayiwa Faheem waliyyi aka d'aura auren nan, ya kirani a waya yake fad'amin damuwarsa nasan Faheem akwai shi da zurfin ciki tunda har ya fad'amin damuwarsa to abin ya dameshi, ni na bashi shawarar yaje wa mahaifiyar yarinyar da maganar Allah bashi nasara daya fad'awa mahaifiyarta ta bashi aurenta a lokacin tace a d'aura, ya kuma kirana a waya ya fad'amin cewa ta amince kuma tace ya turo yanzu a d'aura auren Allah yasa ranar na shigo kano naje aka d'aura auren, don nima ina sauri ban ma shiga mun gaisa nayi mata godiya ba saidai na barwa mijinta sak'on gaisuwar. Bayan an d'aura auren mai makon naga Faheem yana farin ciki sai naga ya shiga damuwa na tambaye shi menene kuma yake damunsa, yace min yana tunanin yadda zaka d'auki zancen k'aro auransa bada saninka ba ga kuma Kausar da yayowa itama abokiyar zama ba shiri, na nuna masa karya damu indai Kausar ce, kai kuma zanyi maka bayanin komai Allah bai bani ikon kuma dawowa kano ba sai jiya da kayi min waya mukazo yau. To kaji abinda ya faru Daddy'n Faruq tun kafin ka fad'a min Faruq nason yarinyar nan Faheem yake dakon son ta a dalilin maganar da kayi musu jiya shi kuma ya yankewa kansa hukuncin sadaukarwa da Faruq ita bayan irin son da yake yi mata, sonta ne da fargabar rabuwa da ita ga kuma dakon sonta da yayi yasashi kamuwa da ciwon zuciya" daddy yayi shiru yana sauraronsa yace "naji kuma na fahimta amma yarinyar nan Faruq ya shaida min shi take so kuma ita ta amince da aurensa, don haka ke Aysha kece mai number ta ki kirata yanzu tazo ta shaida mana wa take so a tsakaninku, oya Aysha kirta kisa muna ji" Abba ya kuma kallonsa "haba Daddy wai sai yaushe ne zaka daina nunawa yaranka bambanci? Ka dinga yi musu adalci mana" "kayi hakuri Abba ka kyaleshi ai dama yayi niyyar barwa d'an uwan nasa ita to Dan nace a kirata ta zab'i zab'inta ai ba lefi bane" Abba ya gyad'a kai kawai dama su momy da mamy basu saka baki ba. Aunty Wanda tunda suka shigo data zauna kanta yake a k'asa tana zubda k'walla tana tausayawa halin da Faheem zai shiga na rashin Hibbah a hankali ta d'auko wayarta a jaka ta shiga kiran Hibbah ta saka a speaker kowa yanaji tana fara ringing Hibbah ta d'aga cikin tashin hankali da tsoro ta Fara magana "Aunty ki taimake ni kasheni zaiyi ya kuma lalata min *RAYUWA* Faruq ya sato ni ya kawo ni wani waje zaiyi lalata dani Aunty don Allah ki taimaka......" D'if wayar ta d'auke. Aunty gaba d'aya ta tsorata da fargabar abinda Faruq zai yiwa Hibbah ta kalli kowa na parlor'n duk sun firgita suke ta kalli Daddy jikinsa yayi sanyi don tagumi ma yayi, ta maida dubanta ga Faheem gani tayi ya mik'e ya dafe kansa yana tangad'i zai fad'i kafin tayi wani yunk'uri har yazube a wajen. Da gudu ta k'arasa kusa dashi ta shiga tana kiran sunanshi saidai ina baya ma hayyacinsa, su Abba suka k'araso kusa dashi suna tattab'ashi sam baya motsawa daddy duk hankalinsa ya tashi ya zaro wayarsa daga aljihu ya shiga kiran layin Dr Umar. Ba jimawa ya d'auka Daddy baima jira sun gaisa ba yace "Umar kana asibiti ga munan zuwa Faheem ya fad'i" shima Dr Umar ya d'an ji tsoro saboda yanayin ciwon nasu ba'ason mutum ya dinga damuwa balle har takai ga ya fad'i "ina nan daddy garin yaya" Daddy bai tsaya bashi amsa ba ya kashe wayar. Abba da Daddy ne suka kamashi suka shiga dashi mota, Aunty da Abba suka shiga motar, Daddy momy da mamy kuma suka shiga wata motar. Suna zuwa nurses har sun fito masa da gado aka d'orasa a kai suka shiga dashi Dr Umar yabi bayansu wani d'aki suka shiga. Dr Umar ya kai kusan 1hour a ciki sannan ya fito daga d'akin, su Daddy da sauri suka nufoshi suna tambayar jikin nasa ya kasa magana yace "daddy kuyi hakuri muje office" yayi gaba suna binsa a baya har suka isa office d'in nashi, suka zazzauna akan kujerun office d'in. Dr Umar ya dubi su Abba, dasu momy da hankalinsu ya gama tashi don a rikice suke, balle kuma Aysha da taketa kuka mai ban tausayi, yace "munyi k'ok'arin ceto rayuwarsa cikin ikon Allah Daddy gaskiya rayuwar Faheem tana cikin had'ari sosai zuciyarsa tana gab da bugawa, matuk'ar ba'a daina b'ata masa rai ba akwai abinda yake matuk'ar so a zuciyarsa amma kuma ana yunk'urin hanasa wannan abun, matuk'ar ana buk'atar rayuwarsa to Dan Allah Abba ayi yunk'urin yi masa wannan abun. Nan 4hours zai iya farkawa yana buk'atar hutu baza ku iya ganinsa ba" gaba d'ayansu sun kasa magana Abba ne kawai yayiwa Dr godiya suka nufi d'akin da Faheem ke ciki suna lek'ensa ta window har ya d'an fad'a duk tausayinsa ya cika musu zuciya. Sagir mijin Aunty Aysha ne ya shigo cikin wajen ya k'araso kusa dasu ya gaishe dasu Abba da tambayar mai jiki, shima ya lek'a ta window yaga yanayin jikin Faheem d'in ya tsorata ya kalli Aysha "Aysha wai mene sanadin wannan ciwon" Aunty Aysha tasa kuka tama rasa me zata ce masa, hankalinta ya kasu biyo tana tunanin rayuwar d'an uwanta tana kuma tunanin rayuwar Hibbah a wajen Faruq, Daddy ne yayi k'arfin halin ya bashi labarin duk abinda ya faru ya d'ora da cewa "nayi nadama sagir nayi Dana sanin sangarta Faruq da nayi na lalata masa tarbiyya, na b'ata masa rayuwa sam bana ganin laifinsa idan yayi gashi yanzu yaya neman lalata Matar Yayansa Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un nayi nadama" ga mamakin kowa hawayene yake zuba a idanun Daddy. Sagir yace "kayi hakuri daddy kabar min komai a hannuna ni da kaina yau zan fara binciken inda ya kaita yanzu zanyiwa yarana waya daga asibitin nan bazan je ko ina ba zan fara bincike akan Faru................. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page4⃣5⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *a gurguje pls* Sagir mijin Aunty Aysha inspector ne shiyasa yayi ruwa yayi tsaki a kwana uku suka damk'e Faruq ta hanyar amfani da company'n Layin da yake amfani dashi don gano inda yake, sun sameshi ne agidan gonar Daddy dake wajen gari inda yake yunk'urin raba Hibbah da mutuncinta. Bangaren Faheem Allah ya taimaka ya farka sannan su Abba suna bashi kulawa daidai misali, anyiwa Kausar waya ita hankali a tashe ta nufo asibitin, kwana ukun da yayi alhamdulillah ya samu lafiya musamman ma Daddy ya tabbatar masa da aurensa da Hibbah babu fashi tana nan a matsayin matarsa, tuni Faheem ya watstsake ya samu sauki don shi a yanzu ji yake babu wani abu da yake damunsa duk wata matsala yashi ta kau. Su momy ne suka zaunar da Kausar suka yi mata nasiha mai sanyaya jiki kafin su fad'a mata abinda yake faruwa, ta girgiza sosai dajin a dalilin aikin da take yi mijinta zai k'aro aure sannan kuma 'yar aikinta zai aura gaskiya wannan aikin bata ga amfaninsa ba tunda bata da lokacin Bawa mijinta kulawa. Da bata d'auki hakan wani abu ba sai yanzu, sai yanzu take ganin illar wannan aikin nata na bank ga 'ya mace tunda ta gani a kanta wace irin kulawa ce Faheem baya bata duk da ta fifita aikinta akan zaman aurenta hakan baisashi ya daina bata kulawa ba, babu abinda ta rasa a wajensa ga d'anta Nawaz data k'wallafa rai akansa shima sam bai Saba da ita ba yafi sabawa da Daddy'nshi da kuma Hibbah, ita kama shikenan bakin alk'alami ya bushe, me yasa bazata bashi kulawa kamar yarda yake bata ba? Me yasa ta zab'i ta k'untatawa iyalanta ta fifita aikinta akan mijinta da d'an? Lallai ta tafka babban kuskure wanda baza ta tab'a iya gyarashi duka ba tunda gashi a sanadin haka mijinta zai auri 'yar aikinta wadda tafi tsana. Ranar da aka damk'e Faruq suna kamashi suka yiwa su Aysha waya suka fad'a mata ita kuma ta fad'awa su Abba, Daddy have su huce dashi yanzu zasu zo su amshesa, don sunyi shawara da su mamy sun yanke hukuncin kaisa gidan mari su kuma cigaba da yi masa addu'ar Allah ya shiryesa. Faheem ba k'aramin farin ciki yayi ba da aka samo masa Hibbarsa, ya kuma hi dad'i da hukuncin dasu Daddy suka yanke don hakan shine daidai. A lokacin Daddy da Abba suka je suka amshi Faruq suka wuce dashi gidan mari, yayin da inspector Sagir ya kawo ta asibitin wajen su Aysha bama su had'u da su Daddy ba, dama kuma bata tab'a ganin ko d'aya daga cikin daddy ko Abba ba. Inspector Sagir yasha godiya da addu'a wajen su Aysha da su momy har ma da Hibbah d'in, yayin da Faheem yayi masa kyauta mai tsoka tare da yi masa godiya. Tunda Hibbah tazo bayan Sagir ya koma bakin aikinsa su Aunty suke ta tambayarta abinda ya faru, Hibbah ta numfasa tace "Aunty Allah abin tsoro ne, sai ka jima kana shirya abu amma matuk'ar bai nufin hakan da faruwa ba babu Wanda ya isa yasaka hakan ya faru, Aunty ashe Faruq ya jima yana shirya hakan yayi amafani da Kalmar so wajen ganin ya aikata nufinsa a kaina ashe duk yaudarace yana sone ya aure ni daya samu abinda yake so sai ya rabu dani, don yaga bani da gata bani da galihu yanson ya wulakanta min rayuwa don kawai ya cika burinsa akaina." Sai kuma ta fashe da wani kuka mai ban tausayi, Aunty ta janyota jikinta "Hibbah kiyi shiru Allah yana tare dake shine gatan mu kuma nima ina tare dake" da hawaye tab a kan fuskarta ta d'ago tana kallon Faheem dasu mamy sannan ta dubi Aunty "na gode Aunty da kulawar da kika nuna min Allah ya saka da alkhari, Aunty wai da gaske ne Daddy ne mijina yaushe aka d'aura auren?" "Waya fad'a miki Hibbah?" Ta d'anyi shiru "Faruq ne ya fad'a min, don Allah Aunty idan da gaskene ki rok'a minshi ya sake ni don wallahi Aunty bazan iya auren mijin Aunty Kausar ba kuma na d'auki Daddy kamar uba taya zan iya zaman aure da mutumin da nake jin nauyinsa nake bashi girma fiye da kowa a duniyar nan Aunty kuyi hakuri don Allah bazan iya zaman aure bashi ba" maganar Hibbah ta d'aga hankulansu duka musamman ma Faheem da yaji wani abu ya tokare shi, Aunty ta dubeta duk tayi sanyi "Hibbah ki tausayawa rayuwar d'an uwana wallahi Yaya yana sonki sosai wannan rashin lafiya da kika ganshi duk a sanadinki yake yi saboda Daddy yace lallai saiya rabu dake......" Nan Aunty ta kwashe komai ta fad'a mata, Hibbah ta kafa ta gumi ta ma kasa cewa komai tana tunanin wannan hukuncin na ubangiji, wato abinda baka tab'a zato ba saikaga ya sameka, matsayin da baka tab'a tunanin zaka taka ba sai Allah ya baka shi. K'ofar aka bud'e Kausar ce rik'e da kwandon abinci Saudat ta rik'o hannun Nawaz ita da Safiyya suna biye da ita, da gudu Nawaz yaje ya rumgume ta "Aunty kinga daddy bashi da lafiya baki zo kin dubashi ba kin gudu gidan ummanki, Aunty nima bazan kuma zama a wajen momy ba idan zaki tafi ki tafi dani zan biki" ta k'ank'ame Nawaz tana shafa kansa tace "Nawaz ba inda zan kuma kowa ina tare da kai" yayi tsallan murna "da gaske Aunty Hibbah?" Ta gyad'a masa kai ya kuma rumgume ta. Kausar ta ajiye kayan ta tsaya tana kallon su cike da tausayin kanta tabbas tayiwa kanta da yanzu duk wannan soyayyar da Nawaz yake yi Mata da ita zai yiwa. Ta kalli Faheem shima kallonsu yake yi yana murmushi, yaji dad'in kalaman Hibbah hakan na tabbatar masa data amince zata zauna dashi kenan, su Aunty ma dasu momy sai murmushin jindad'i sukeyi. Hibbah kuwa ta kasa d'aga ido ta dubi Kausar saboda nauyinta da take ji, kuma bazata iya kallon idanun Aunty tace bata son d'an uwanta ba hakan zai zama kamar butulci da cin fuska shiyasa bata da wani zab'in daya wuce ta amince da auren, ikon Allah kenan wai akanta har Faheem yake da ciwon zuciya gashi a gadon asibiti a kwance yana ciwon so. Saudat ta k'araso kusa da Hibbah tana murmushi cikin sigar tsokana tace "Aunty Hibbah matar Yaya" dukansu suka sa dariya banda Kausar da duk abin duniya ya isheta duk danasani da nadama ta addabi zuciyarta, yayin da Safiyya take bak'in cikin faruwar wannan abun take kuma jin tsanar Hibbah a zuciyarta sai wurga mata harara take yi. Hibbah tayiwa Saudat hararar wasa, Saudat tayi kamar bata gani ba ta cigaba "mamy da Aunty nasan kune akan komai don momy ba shiga zatayi ba, yanzu yaushe ne zamu sha bikin babban Yaya kusan mune manyan k'awaye" wani bak'in ciki ya tsayawa Safiyya ji take kamar taje ta doki Saudat, Hibbah tayi k'asa da kanta cike da kunya da kuma jin wani iri don gani take kamar cin fuska ne abinda Saudat take yi, tana yi ne saboda Kausar wanda ita tana ganin rashin dacewar hakan. Aunty tace "Kai Saudat irin wannan zumud'i haka ki bari su Daddy su dawo sai su tsaida mana rana" Saudat ta gyad'a kai "sai mu fara shiye shirye kenan." Tsayuwa ta gagareta ta samu gefen gadon Faheem ta zauna kanta a k'asa tana tunani yanzu shikenan Faheem ya zama nasu su biyu, ta d'ago kai ta dubeshi shima ita d'in yake kallon yana tausaya mata don yasanta akwai zafin kishi yayi mamaki ma da bata wani tashi hankalinta ba sosai yayi mata murmushi, ta kawar da kanta gefe. Su Abba ne suka shigo da sallama suka amsa musu tare da yi musu sannu da zuwa, Abba ya dubi inda Hibbah take Nawaz yana zaune akan cinyarta kanta yana k'asa yana murmushi yace "surikarmu ki d'ago fuskar taki mu gani mana kinsa mana yaro kwanciya ciwon so, naga ma ya samu lafiya saboda ya ganki" cikin sigar barkwanci Abba yake maganar saboda Abba akwai shi da barkwanci, Hibbah ta kuma k'asa da kanta cikin kunya, su Daddy dasu momy sai murmushi suke yi Faheem kuwa shima k'asa yayi da kansa don jin nauyin maganar Abba. Saudat tace "surikar su Abba ki d'ago kanki su ganki" ta fad'a tana mata dariya, mamy tace "kai Saudat kin takurawa surikata fa, zan fara rama mata" momy tace "gaskiya kam Saudat kin takurata da yawa ke a haka ake Matar Yayan?" Daddy yayi dariya "nifa na k'osa naga fuskar wannan mai sa'ar data sace min zuciyar Faheem haka har ya kasa nutsuwa saboda rashinta" su aunty suka kwashe da dariya. Gaban Hibbah ne ya shiga fad'uwa jin muryar da bazata tab'a mantawa ba zuciyarta ta shiga harbawa da sauri ta d'ago kanta don tabbatar da muryar da taji, a hankali ta d'ago kanta ta zubasu akan Daddy cikin mugun hargitsi da rikici ta tashi tsaye tana kallon daddy murya na rawa tace "baa.......baa? Baba kaine?" Jin muryarta ya hargitsa Abba muryar da yafi so a duk duniya kuma bazai tab'a manceta ba har *Abadan* ya jiyo cikin fargaba yace "Aysha....." Hibbah ganin fuskar Daddy yasata zubewa a k'as............... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page4⃣6⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Aunty ce tayi saurin tarota ta fad'o jikinta, Faheem besan sanda ya diro daga gadon ba yayi wajenta da sauri yana ambaton sunanta su momy ma suka matso suna jijjigata, mamy ce ta d'auko ruwa ta fara shafa mata a fuskarta. Abba kuwa da hanzari ya fita ya kira Dr, suna shigo Hibbah tana farkawa Dr ya k'araso ya shiga dubata ko da wata matsala, ya gama dubata ya tabbatar musu da lafiyarta sannan ya fita. Hibbah tayi shiru kawai kallon Daddy take yi tana son ta gano wani abu game da Daddy tana kuma tambayar kanta, me ya kawo babanta birni dama babanta yana da aure a birni amma bai tab'a gayawa su Inna ba kuma akace bai tab'a haihuwa ba sai akanta idan haka ne su Aunty Aysha kuma 'ya'yan waye? Bata da amsoshin wad'an nan tambayoyin nata ya zame mata dole ta tambayi daddy don shi kad'ai ne zai iya amsa mata wad'annan tambayoyin. Daddy da Abba sun shiga tunani Daddy ya tafi wani tunanin akan Hibbah yana son yasan wani abu game da wannan razanar da tayi ta ganinshi don ta bashi tsoro, yayin da Abba kuma ya tafi tunani wacece wannan mai irin murya da kamannin k'anwarsa Aysha kodai 'yar Aysha ce? Ya tambayi kansa sai kuma ya girgiza kai a'a, a iya saninsu Aysha tun tana k'arama ta b'ata kuma baya tunanin yanzu tana raye, lallai ya zame masa dole yasan ko wacece ita. To amma me ta sani game da Daddy da har zata suma don tagansa mene a tsakaninsu? Dukkansu su biyun basu da amsoshin tambayar su don haka Daddy ya d'ago Kai ya dubi Hibbah dake kwance itama duk tunani ya dameta. "Hibbah ki fad'a min mene dalilin da yasa don kin ganni kika tsora har kika suma?" Hibbah tayi shiru tana nazari kenan baba bai ganeta ba kodai ba babanta bane kama ce? Ta dubi su momy duk jira jira sukeyi tayi magana, cikin yanayin tsoron da bai saketa ba tace "Baba, baba baka gane ni ba Hibbah ce fa, Hibbah 'yarka daka kora" sai kuma hawaye ya fara bin fuskarta. Daddy cikin yanayin nuna damuwa yace "Hibbah kiyi hakuri bani bane Wanda kike fad'a" Hibbah ta rik'e kanta don ya fara mata nauyi wannan wace irin *RAYUWA* ce ka haifi 'yarka amma ka kasa gane ta? Me ta canza da baba zai kasa ganeta? Faheem dake kusa da ita ya dubeta cikin kulawa "Hibbah kiyi mana bayani yadda zamu fahimce ki, kinsamu a cikin hargitsi" Hibbah hawaye nabin fuskarta damuwarta ta k'aru "babu komai Daddy zan cigaba da rayuwata ba tare da babana ba dama tun tasowata nafi sabawa da ummana akan babana saboda baya sona bai damu da rayuwarmu ba........." Sai kuma ta saki wani irin kuka. Daddy ya kasa fahimtarta ya kasa gane maganganunta, balle kuma Abba da idan tayi magana yake jin gabansa yana bugawa. Faheem kam wannan kukan da take yi jinsa yake har cikin ransa, Aunty ta janyo Hibbah jikinta tana rarrashinta. D'akin yayi tsit sai sanyin AC dake ratsa d'akin, Abba ne ya katse shirun da cewa "Hibbah dukkanmu nan bama gane abinda kike fad'a, amma ko zaki fad'a mana sunan mahaifin naki may be mu ganeshi," da kamar ba zatayi magana ba saboda kukan da yaci k'arfinta, dak'ar ta iya rage kukan cikin muryar kuka tace " *MALLAM MUKHTAR MUHAMMAD*" da hanzari Daddy ya nunata "kina nufin kice min Mukhtar yana raye!?" Daddy ya fad'a cike da rud'ewa, kansa ne ya fara juya masa a hankali ya kama gefan gadon ya zauna yana jin k'aunar d'an uwansa tana kuma ratsa zuciyarsa. Abba ma gefen Aunty ya zauna yana kuma tuno rayuwarsu ta baya gefen zuciyarsa kuma cike yake da rud'ani don ya k'osa yaji wacece Hibbah so yake yaji asalinta don kamar da suke yi masa da Aysha k'anwarsa ta b'aci. su mamy da momy ma suna cike da rud'ani ashe Hibbah'yarsu ce basu sani ba. Faheem, Aunty, Kausar dasu Hibbah sun kasa fahimtar komai game dat abinda yake faruwa, Faheem cikin damuwa ya dubi su Daddy "Daddy don Allah kuyi mana bayanin abinda yake faruwa mun kasa gane abinda kuke nufi" Daddy yayi shiru k'aunar d'an uwansa na kuma ratsa zuciyarsa ya dubi su Faheem "Faheem yau zan bayyana muku komai game da rayuwarmu." Kowa ya maida hankalinsa kan Daddy, ya cigaba da cewa "Kamar yadda kuka taso a garin kano muma a cikinsa muka taso iyayenmu mu uku suka haifa sab'anin yadda kuka sani, nine babba sai mai bina Mukhtar sai kuma mamynku Rukayya, mun taso cikin so da k'aunar iyayen mu sun jajirce wajen ganin sun inganta rayuwarmu ta hanyar bamu ilimi na duka b'angarorin. Ni da Abbanku mun taso tare kamar tagwaye komai tare mukeyi, haka ma Mukhtar da abokinsa Ibrahim sam ba'a jin kan d'aya daga cikinmu, muna level 4 a jami'ar bayero university kano inda muke karantar business administration dukanmu, Allah yayiwa mahaifinmu rasuwa mutuwar data gigitamu dukkannin mu, munyi kukan rashinsa sanadiyyar mutuwarsa ya janyowa hajiya hawan jini. Bayan rasuwar mahaifinmu duk wata d'awai niya ta gidan ni da Mukhtar ne muke yinta da yake dama mahaifinmu kafin ya rasu ya d'oramu akan kasuwancinsa da yakeyi a kwari sai muka cigaba da juya dukiyar. Shekarar mahaifinmu d'aya da rasuwa muka kammala degree d'in mu, hajiya kuma ta matsa mana akan muyi aure dama duk muna da wad'anda muke so yayinda Abbanku kuma yake son Rukayya, ba'a d'au wani dogon lokaci ba akayi bikinmu. Auran da mukayi sai Allah ya kuma hab'b'aka arzik'in mu, don haka hajiya tace mu raba gadon da Alhaji ya bar mana idan yaso kowa saiya tada jarinsa munyi na'am da abinda hajiya tace don haka aka raba gadon aka bawa kowa hakkinsa muka cigaba da juyawa. Kafin shekara arzik'in mu ya kuma burink'asa amma duk cikinmu Mukhtar ya fimu iya business don a lokaci k'ank'ani yayi suna a cikin garin kano har ya fara fita k'asashe babu wanda baisan *Alhaji Mukhtar Muhammad shagari* ba kowa ka tambaya zai nuna maka. Shekarar mu d'aya dayin aure Allah ya azurta matanmu nida Abban Ku da samun haihuwa kuma duk maza, sab'anin Mukhtar da matarsa Aysha Allah bai basu haihuwa ba. Ranar suna nasawa Faheem Muhammad sunan mahaifinmu kenan shima Abban ku yasa sunan haifinsa Ishaq shine suke kiransa da Haisam. Haka yaran suka taso cikin kulawa musamman ma Aysha da Mukhtar sunfi kowa basu kulawa. Cikin ikon Allah shekarar su Faheem uku allah ya azurta Aysha da samun ciki, kowa ya tayata murna sai d'auki akeyi da murnar wannan cikin, cikinta yana da wata shida Rukayya ma ta kuma samun nata rabon, a lokacin ne kuma Ibrahim abokin Mukhtar yayi aure. Kasuwanci yana cigaba da bunk'asa yayinda mak'iya suke yiwa Mukhtar bak'in ciki da d'aukakar da Allah ya bashi. Ranar wata laraba da bazan tab'a manta wa ba a rayuwa ta rana mafi muni a garemu ranar dana rasa d'an uwana na kuma rasa mahaifiyata ga kuma Aysha matar Mukhtar itama mukayi rashinta. Mun saba kullum da daddare bayan sallar isha'i muna zama da iyalanmu mu tattauna matsalolinmu, ranar tunda muka zauna Mukhtar yake cewa kansa yana masa ciwo Aysha ta kawo masa magani ta bashi yasha duk da cewa a lokacin tayi nauyi, bayan d'an wani lokaci kawai muka ga Mukhtar yana yi mana wasu abubuwa tamkar wani mahaukaci lokaci d'aya ya canza ya koma yana yi mana hauka tuburan sam ya fice a hankalinsa, hankalinmu ya tashi duk muka hargitse musamman ma Aysha wadda tsabar tashin hankali a lokacin nak'uda ta kamata, hajiya kuwa hawan jininta ya tashi muka rasa ya zamuyi kawai nida Abban ku muka samu dak'yar muka tura Mukhtar d'aki muka kulleshi hankali a tashe mukayi asibiti dasu hajiya. Muna zuwa cikin gaggawa aka karb'e mu sakamakon wahalar da Aysha ta sha wajen nak'uda yasa ta rasa duk wani k'arfinta suka ce saidai ayi mata aiki, a lokacin lafiyarta kawai muke da bukata ba tare da tunani komai ba na saka hannu, Ana shirin yi mata aikin ta haifo 'yarta sai dai tana haihuwa Allah ya karb'i ranta munyi kukan rashinta don Aysha macece mai kirki da sanin darajar d'an Adam, don haka Ana kawo yarinyar nayi mata hud'uba da sunan mahaifiyarta. Hajiya kuwa dak'yar likitoci suka samu hajiya ta farfad'o har ta d'an ware likitoci suka bamu damar shiga mu dubata, hajiya tayi murna da ganin yarinyar da Aysha ta haifa, ta tambayemu lafiyar Aysha da munyi niyyar b'oye mata saboda yanayin ciwonta amma Faheem yayi caraf ya fad'a mata Amminsa ta rasu don haka suke kiranta. Nan fa jikin hajiya ya kuma tashi Dr da yaga jikinta ya dinga fad'a itama a lokacin tace ga garinku nan. Nan fa muka kuma shiga damuwa Rukayya da momynku suka fad'i a wajen a sume hankalinmu ya kasa kwanciya nida Abban Ku. A tak'aice dai haka ranar muka yini cikin zulumi da rud'ani, washe gari muka tawo da gawawwakinsu hajiya gida abinda muka samu a gida yasa nima saida na ziyarci asibiti don nima ban tab'a tunani zan kuma rayuwa ba don zuwa mukayi kuka tadda Mukhtar ya b'alle k'ofar ya bar gidan. Abbanku shine yayi k'arfin zuciya yasa akayi musu sallah aka kaisu makwancinsu, ni kuma yasa aka kaini asibiti shi kuma ya zauna da sauran dangi suna karb'ar gaisuwa. Bayan na samu sauk'i munyi cigiya a gidan radio dana TV amma bamu samu Mukhtar ba haka muka hakura muka mikawa Allah lamarin, abinda ya bamu mamaki ko da wasa Ibrahim bai zo mana gaisuwa ba balle yayi mana jajan rashin d'an uwanmu. Ni na d'auki Aysha yarinyar Mukhtar na cigaba da rik'onta." Daddy yasa tissue ya goge hawayen daya zubo masa, sauran matan ma duk kuka sukeyi musamman su mamy ji suke mutuwar ta dawo musu. Cikin kuka harda majina Hibbah tace "Daddy wace Aysha da Ammi ta bari?" Daddy ya d'ago ya dubi duk 'yan d'akin "kuyi hakuri yauzan bayyana duk wani sirri da muke b'oyewa, Hibbah Ayshan da aka haifa ba kowa bace illa............. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page4⃣7⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Ba kowa bace illa Auntynku Aysha, itace wadda amminku ta rasu ta barta, ni kuma na d'auketa momynku ita ta shayar da ita kuma babu Wanda zaice ba Zainab bace ta haifi Aysha, gashi ta d'auko kamannin Zainab tunda Aysha da Zainab uwa daya uba daya ne" duka 'yan d'akin sun firgita da jin wai Aunty Aysha ba 'yarsa bace, Aunty ta janyo Hibbah ta rumgume ta suka saki kuka duka su biyun mai ban tausayi sun jima a haka babu Wanda yayi yunk'urin rabasu kowa tausayinsu yake ji a zuciyarsa musamman ma Hibbah da ta taso cikin wahala da uk'ubar *RAYUWA*. Hibbah ta d'ago daga jikin Aunty suna kallon juna "Aunty dama ashe ke 'yar uwata ce shiyasa kike tausaya min kika inganta rayuwa ta ki jiyar dani dad'in rayuwa aunty bani da kamar ki na gode Allah ya saka miki da.........." Aunty tayi saurin toshe mata baki "ko a da Hibbah babu godiya a tsakanin mu balle yanzu da muke *jini d'aya* ni dake, Allah za muyiwa godiya da har ya nufe mu da sanin gaskiya" Hibbah tayi murmushi tare da yiwa Allah godiya, ta dubi su momy sai murmushi suke yi ita da mamy. Mamy tace "zonan Hibbah inji d'umin jikin d'an uwana" a hankali Hibbah ta k'ara kusa da mamy, mamy ta rumgume ta tana jin k'aunarta na ratsa jikinta, ta b'anb'areta daga jikinta tana kallonta "Hibbah yanzu ina d'an uwana yake? A ina yanzu yake *RAYUWA*?" Hibbah hawayen farin ciki nabin fuskarta "mamy yana wani k'auye a cikin k'auyukan Bunkure" mamy ta kalli su Abba da suke ta bin Hibbah da kallo cike da k'auna tace "Yaya yaushe zamuje mu gansa?" Daddy fuskarsa cike da farin ciki "ai yau za'a sallami Faheem tunda k'auyen ba nisa ne dashi ba sai muje yau Donni na k'osa naga d'an uwana" Saudat ta mik'e da sauri "bara naje na kira Dr yazo ya sallami Yaya mu tafi" Aunty tasa dariya "kai Saudat kin fiye zumud'i ki Bari yanzu ma zaki Ganshi ya shigo" "ai Aunty na k'osa ne muje wallahi" Faheem yayi murmushi yana yiwa Hibbah wani kallon "Ashe dai ke k'anwata ce shiyasa na rud'e a kanki na kasa sukuni saboda bana son wani ya b'ata miki *RAYUWA*" "ba wani nan dama can kai kana sonta kana tsoran kar ayi maka k'wace ka rasata yasa har ka kwanta a asibiti wai ciwon zuciya" Abba ya fad'a cikin sigar tsokana duka suka sa dariya banda Kausar da Safiyya da sunma kasa had'a idanu da Hibbah saboda tsantsar kunyarta da suke ji. Safiyya tafi Kausar kusanci da Hibbah don haka ta matso kusa da ita ta rik'e hannayenta "don Allah Hibbah kiyi hakuri ki gafarce ni wulakancin da nayi miki" Hibbah tayi murmushi "habba Safiyya wallahi ni baki yi min komai ba" Safiyya ta rumgume ta tana share hawaye cike da Dana sani tace "na gode sis Hibbah" Hibbah ma ta rumgume ta tana yiwa Allah godiya a zuciyarta ashe itama tana da gata haka, Saudat dake gefe cikin tsokana tace "lallai Safiyya wato yau Hibbah har ta samu matsayin sister" ta fad'a tana dariya Safiyya ta harareta "to ina ruwanki gulgul." Kausar ma ta matso kusa da ita ta zauna a gefenta "Hibbah na sani na wulakantaki nayi miki rashin mutunci iri iri na d'aukeki kamar wata baiwa a gidana, yanzu gani a gabanki ba don ni ba don Allah kiyi hakuri ki yafe min" Hibbah ta shiga girgiza Kai "Aunty Kausar ni ya dace na baki hakuri ba ke ba, don kuwa a matsayina na 'yar aikin gidanki na aure miki miji kiyi hakuri Aunty wallahi babu laifina a ciki ban ma san da auren ba" Kausar tayi murmushi "haka Allah ya k'addara Hibbah hakan shine sanadiyyar kawo zaman lafiya a gidan Allah ya bamu zaman lafiya" Hibbah tayi k'asa da kai cike da kunya, don tunda akace ita matar Faheem ce take tsananin jin kunyar Kausar da kuma Faheem d'in. Momy tace "alhamdulillah naji dad'in wannan al'amari Allah ya had'a kanku" suka ce amin. Dr ya shigo don duba lafiyar Faheem ya tadda Faheem a zaune yana ta murmushi kamar ba shine Mara lafiya ba, dr cikin mamaki yace "a'a Faheem yana ganka haka garau dake kamar ba Kaine Mara lafiyar ba?" Aunty tayi caraf "dr ba dole ka ganshi haka ba tunda ya samu abinda yake so ai dole ya watstsake" Faheem ya harareta "Dr ba wani nan Allah ne ya kawo sauk'i" "to Allah ya k'ara sauk'i" "amin suka amsa. Dr ya mik'a masa takardar sallama da kuma ta wasu magunguna da zai cigaba da amfani dasu, ya amsa sukayi masa godiya ya fita, Daddy yace "kuyi sauri Ku had'a kayan mu tafi, ni so nake kawai naga Mukhtar" Hibbah ta dubi Daddy idanunta taf da hawaye zuciyarta cike take da tsoro tana tuna furucin Inna *_kuma wallahi sauran idan an kaiki kice zaki zo ganin gida wallahi saina kashe ki, kinsan halina zan aikata,_* ta kuma tuno lokacin da gwaggo tace *_yanzu lami baki tsoran yarinyar nan ta fad'a mugun hannu ko kuma su gidan da aka kaita su koreta, ina zata wata sani scan da zskice karta waiwayi mahaifarta? Inna tace oho ni ko Karuwanci zatayi tayi ina ruwana._* Hawayen fuskarta ya tsananta zuba gaskiya bazata iya zuwa k'auyen nan ba don tasan halin Inna lami tsaf zata iya kasheta, ji tayi an dafa kafad'arta da sauri ta waiwaya Kausar ce tace "Hibbah me kike tunani muna ta magana?" Ta share hawayenta ta girgiza kai "ba komai Aunty" Nawaz ya kwanto a jikinta "Aunty me yasa ki kuka?" Aunty tace "haba Hibbah ya kina kuka kuma kice babu komai don Allah ki fad'a mana me ya saki kuka me kike tunani?" Hibbah ta k'ara goge hawayen dake zuba a idanunta,"Aunty kuyi hakuri wallahi ina tsoran komawa k'auye ina tsoron Inna lami nasan halinta zata iya kashe ni, tunda tayi min gargad'in karna kuma waiwayar garin" Hibbah ta fad'a hawaye na bin fuskarta. Faheem yana daga can gefe "karki damu Hibbah babu abinda ta isa ta yi miki Wanda Allah bai nufa zai same ki ba ki tuna baya taso ta lalata miki *RAYUWA* ta tozar taki amma da yake Allah ba azzalumin sarki bane sai ya hana faruwar hakan sannan ta turoki birni don ki zama k'ask'antacciya shima hakan sai ya zame miki alkhari don haka ki cire wannan tunanin daga ranki, mu duka nan muna tare dake Allah na tare dake babu abinda ta zai sameki da yardar Allah" Hibbah ta gyad'a kanta cike da gamsuwa ta kuma ji dad'in kalaman Faheem, "Kai Aunty Hibbah kin fiye tsoro da yawa" Saudat ta fad'a tana dariya, Hibbah tayi mata hararar wasa Safiyya tace "ai tsoro halal ne kuma kema kina yi Aunty Hibbah nima ina bayanki ki cigaba da jin tsoro wallahi mutumin da yace zai kasheka kuma kasan halinsa zai aikata ai dole kaji tsoransa" Abba yace "haka ne amma Hibbah ina son nasan wani abu game dake, don ni har yanzu zuciya ta tana raya min wani abu game dake kuma inajin wani abu a tattare dake" dukkan ninsu suka maida hankalinsu kan Abba, ya cigaba "Hibbah tun d'azu dana ji muryarki nake jin zuciyata na harbawa danaga fuskarki kuma k'irjina ya tsananta bugawa idan kika yi magana kina tunamin wani mummunan abu daya faru a baya, kina tuna min k'anwata Aysha da nake matuk'arso" Hibbah ta kasa fahimtar inda kalamansa suka dosa "Abba ni wallahi ban fahimce abinda kake fad'a ba" Abba yayi d'an shiru yana tunani, su Daddy dasu momy kuwa duk so suke suji abinda ya faru da Abba mene shi kuma had'insa da Hibbah? Abba cikin murya mai nuna tausayawa yace "Hibbah Aysha da kike kama da ita k'anwata ce iyayenmu d'aya mu biyu ne a wajen iyayenmu, mahaifimu d'an kasuwane tare suke kasuwanci da mahaifin Daddy'n ku. Ranar juma'a da rana bayan sallar juma'a su Alhaji da hajiyarmu zasu yi tafiya zuwa k'auyukan dake zagaye da garin kano, Alhaji ya saba duk juma'a yakan je k'auyuka ya kai musu tallafi, sun saba da Aysha suke tafiya ni kuma a barni a gidansu Daddy lokacin Aysha tana da shekara biyar a duniya. A hanyar su ta dawowa ne daga k'auyen suka had'u da 'yan fashi........... Inna lillahi wa inna ilai hirra ji'un" Abba ya fad'a hawaye yana bin fuskar sa yasa tissue ya goge hawayen sanna ya cigaba "suka buk'aci kud'i daga wajen su Alhaji lokacin Alhaji babu kud'i a wajensa don haka ya fad'a musu cewa babu kud'i a wajensa, babu ko imani suka harbeshi a k'irjinsa suka hajiya ma tare da driver'nsu amma basu harbi Aysha ba ogansu yace su k'yaleta. Haka suka barsu a k'asa a kan titi suka tafi da motar, Aysha ta zauna a wajen tana ta kuka daga baya kuma ta tashi ta shiga cikin garin don shaida musu abinda yake faruwa tun daga nan ba'a kuma ganinta ba. Bayan an kawo gawawakinsu na irin Neman da ba'a yiwa Aysha ba amma ba'a ganta ba. Naji mutuwar iyayena nayi kukan rashin Aysha, daga lokacin ne Alhajin su daddy ya d'auke ni ya cigaba da rik'eni." Abba ya kuma share hawayensa yana kallon Hibbah yace "shiyasa zuciyata take raya min ko Aysha tana raye ke 'yarta ce" Hibbah da itama hawayen take yi na tausayawa Abba tace "Abba saidai muje wajen Umma a tambaye ta amma ni nasan a k'auyen mu Ummana ta taso don iyayenta ma suna raye har na baro k'auyen" Daddy shima cike da tausayi yace "babu matsala sai muje muji ta bakinta, ku tashi mu tafi" Nan suka shiga had'a kayayyakin suka zuba a mota suka huce gidan daddy............... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page4⃣8⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Suna zuwan wanka sukayi kawai suka shirya Faheem da Kausar kuwa saida zukaje gida suka kintsa a can Kausar ta tawowa da Hibbah kayanta, Aunty ma saida taje gidanta anan ta kira Sagir mijinta take fad'a masa abinda yake faruwa yayi mata izinin zuwa kuma yayi mamaki ashe su *dangin juna* ne shiyasa Allah ya dasa musu k'aunar junansu. Su Aunty suna dawowa Daddy yasa Adamu ya fito da mota Daddy da Abba suka shiga baya, yayin da motar Faheem kuma Kausar ta karb'i tuk'in shi kuma yana gefenta mamy momy da Hisham suna baya. Motar Aunty kuma Hibbah tana kusa da ita Nawaz yana kan cinyarta sai Safiyya da Saudat a baya, sai hira suke cike da k'auna a haka suka k'ara gidan Alhaji Sani. Sunyi sa'a yana gida don shigowarsa kenan daga masallaci motocinsu sukayi parking a gidan, yayi mamakin ganin zugarsu haka da yawa amma duk da hakan bai hanasa tarbarsu cikin karamci ba yayi musu iso cikin gidan direct ya shiga dasu har parlor. A parlor suka tadda Umma ita kad'ai kana zaune tana sauraron karatu Wanda kana shigowa parlor'n zakaji yana tashi. Tana ganin su Aunty sun shigo ita dasu Hibbah, Saudat, Safiyya da Kausar ga kuma mamy da momy ta tsayar da karatun ta taresu da murna suka zazzauna akan kujerun parlor'n tana ta yi musu sannu da zuwa. Ta cika musu gaba da abinci kala kala ga lemuka sannan suka shiga gaisawa, anan su momy suke fad'a mata basu kad'ai bane tare suke da mazajensu amma su suna tare da Alhaji zasu shigo daga baya Umma tace to shikenan dama da hijab d'inta a jikinta ita a lokacin ta idar da sallah. Sun d'an tab'a abinci suka shiga hira kamar sunsan juna, karb'ar da umma tayi musu ta burge su sosai sunji dad'i, suna cikin hira su Abba suka shigo da sallama suka amsa musu, kallonta Abba ya tsaya yi zuciyarsa na harbawa da k'arfi tabbas babu tantama wannan itace Aysha k'anwarsa don ga muryarta nan ga kuma kamanninta nan sak dana hajiyarsu. Ya ilahi! Ikon Allah kenan dama ashe zai kuma sanya Aysha a idanunsa, suka zauna ta kawo musu abubuwan tab'a baki, sai binta da kallo yake tabbas itace ga tafiyarta nan ma. Kallon da Abba yake mata ya fara b'ata mata rai don duk inda tayi saiya bita da kallo don haka lokaci d'aya umma ta had'e rai. Bayan sun d'an huta Alhaji Sani ya fad'a mata wajenta suka zo ba wajensa ba umma ta mayar da hankalinta kansu tana son jin meke tafe dasu don ita tayi tunanin ma akan maganar auren Faheem da Hibbah ne. Daddy ne yayi gyaran murya ya gyara zama ya shiga bata labarin abinda ya faru ya kuma tabbatar mata da cewa Hibbah 'yarsu ce basu sani ba. Umma hawayen farin ciki ya sauko mata "alhamdulillah naji dad'in wannan al'amari ikon Allah kenan ashe 'yar kuce shiyasa Allah ya sanya k'auna a tsakaninku har kuka inganta mata musamman ma Aysha yadda kike kula da Hibbah babu Wanda zaice ba 'yar uwarki bace ita ashe k'anwarki ce jinin Ku d'aya" Daddy ya d'ora da cewa "bayan batun Hibbah akwai wani dalili mai k'arfi da ya samu zuwa gidan nan" ya mik'a mata hotunan da Abba ya d'auko nata da su Alhajinsu, ta amsa tana gani cike da tsantsar mamaki tabbas wannan suna Kama da ita lokacin tana yarinta don baza tace Hibbah bace don dad'ewar hoton amma kuma ita tunda take bata tab'a sa irin wad'annan kayanba. Ta dubi Daddy cikin nutsuwa tace "Alhaji gaskiya wannan bani bace don banma tab'a saka irin wad'annan kayan ba da na tab'a saka su to babu tantama nice" Daddy yayi murmushi "tabbas kece a jikin hoton nan Aysha" nan Abba ya bata labarin duk abinda ya faru. Umma ta sunkui da kai tana tunani ita dai tasan tabbas a k'auyen katselle aka haifeta, ta yaya zasu zo su bata wani labari daban bayan kuma ga mahaifanta nan a raye baba da gwaggo. Ta dubi su Daddy "kuyi hakuri gaskiya wannan labarin ma ba ni bace a cikinsa don ni iyayena suna nan a raye basu mutu ba" Daddy ya kuma murmushi "Umman Hibbah kina nunawa kamar baki yarda da mu ba ko? To idan ba damuwa ki shirya yanzu muje wajen su iyayen naki na k'auye mu tambayesu zasu fad'a miki gaskiyar abinda yake faruwa, mun tambayi Alhaji ya amince mu tafi tare yanzu kawai shiryawa zakiyi mu tafi." Umma tayi shiru tak'i tashi daga wajen balle taje ta kintsa, Hibbah ce ta matso kusa da Umma ta rik'o hannayenta "Umma don Allah ki tashi muje don tabbatar da abinda su Abba suke zargi, Umma Abba yana son 'yar uwarsa yana sonki a kusa dashi ki taimaka masa don Allah" Umma ta kalli 'yarta ta "naji na amince zan biku" "yauwa Umma mun gode" Umma ta mik'e ta shiga d'aki ta d'auko duk wani abu dazata buk'ata ta fito suka nufi k'auyen katselle. Motarsu tayi parking a k'ofar gidan su Hibbah don Daddy ne ya rok'i alfarma su fara tsayawa k'ofar gidan d'an uwansa don yana son ya fara ganinsa. Yara suka zo suka baibaye motocin, suka fito daga ciki suna kallon yanayin k'auyen Daddy ya kalli Hibbah "Hibbah shiga ciki kiyi mana iso" ta dubi Daddy duk yanayinta ya koma na tsoro sai k'ifta idanu take "Daddy tsoro nake ji inajin tsoron Inna lami wallahi" Aunty ta dafa kafad'arta "tawo muje babu abinda ta iya tayi miki" Hibbah ta gyad'a kai Saudat tace "nima zani" Safiyya da Kausar har suna had'a baki "ku tsaya ni" suka tsaya suka k'araso suka shiga gidan hannun Hibbah yana cikin na Nawaz. Sukayi sallama Rahmatu ce ta amsa musu tana zaune a tsakar gida tasa turtsetsan cikinta a gaba, ta nuna musu tabarma suka zauna ta gaishesu ita sam bata gane Hibbah ba tace "kuyi hakuri yanzu innar zata dawo ta fita ne" Hibbah tace "ba komai ai zamu jirata sai dai bamu kad'ai bane akwai iyayenmu mata da maza a waje suna son ganin baba, ya dawo ne?" Rahmatu ta tsaya tana kallon Hibbah tana son gano wani abu tattare da ita, bata gane fuskarta ba amma muryar tana ta tunanin ko Hibbah ce amma kuma tana mamaki anya Hibbah ce. Hibbah ta katseta "wai Rahmatu aure kika yi ne na ganki da ciki?" Rahmatu ta zaro ido "Hibbah kece kinga yadda kika koma kuwa, Hibbah ki yafe min kinga yadda *RAYUWA* ta mai dani ko hausawa sunce idan zaka gina ramin mugunta ka Gina shi kajere wata Rana kai zaka fad'a, gashinan Inna taso lalata miki rayuwa Allah bai bata iko ba sai Allah ya dawo mata da abin kaina Hibbah ba aure nayi ba....." Sai ta saki kuka ta rik'o hannun Hibbah "Hibbah ki yafe min don Allah Inna ta b'ata min *RAYUWA* garin son kud'i Inna ta sani na koma karuwar k'arfi da yaji gashinan yanzu sun b'ata min rayuwa sun guje ni, cikin nan da yake ni kaina banson na waye ba a tsakanin sale direba ko kuma Musa d'an Inna delu. Hibbah kowa ya guje ni Inna kullum a cikin hantarata da kyarata take, duk son da baba yake yi min yanzu ya daina k'awaye na sun gujeni kowa a k'auyen nan k'yamata yake yi, Hibbah nayi nadama nayi Dana sanin biyewa Inna dana yi gashinan yanzu na lalata rayuwa ta" Hibbah ta shiga share mata hawaye itama hawayen na bin fuskarta "baki yi min komai ba Rahmatu na yafe miki duniya da lahira Allah ya yafe mana" "na gode 'yar uwata na gode, su waye wad'annan?" Hibbah ta dubi su Aunty "y'an uwan mu ne danginmu ne su bamu sani ba" "danginmu kuma kamar ya dama muna da 'yan uwa a birni?" Rahmatu ta tambaya cike da mamaki. "Eh Rahma kuna dasu mana muma bamu sani ba sai yau d'innan" Aunty ta bata amsa, Rahmatu sai taji sunan wani iri don ba haka ake kiranta da shiba, Aunty ta shiga bata labarin duk abinda ya faru. Rahmatu tayi mamaki sosai "Hibbah ashe rabon kije birni ki samo mana dangin mu ne yasa Inna ta turaki can ikon Allah, to ku shigo dasu ai ba'a barsu a waje ba ko?" Wayar Hibbah tayi k'ara ta duba bak'uwar number ta gani, da kamar bazata d'auka ba sai kuma ta d'aga "hello my heart desire ya ake ciki ne kun barmu a waje" ai Hibbah suman zaune tayi jin furucin Faheem ta kasa magana yace "hello kina jina?" "Ammm.....dama......dama yanzu zanzo na shigo daku" ta fad'a cike da in ina ta kashe wayar, Aunty tace "keda waye kike masa in ina?" "Ba kowa Aunty Daddy'n Nawaz ne yace sunji shiru" Saudat ta kwashe da dariya "to ai saiki tashi kije kar kisashi ya kuma ziyartar Dr" Hibbah ta kai mata duka suka sa dariya. Ta fita ta shigo dasu Rahmatu ta kuma shimfid'a musu wata tabarmar suka zauna ta gaishe su, Hibbah ta gabartar mata da kowa a cikinsu, Rahmatu ta nuna Umman Hibbah "Hibbah kardai kice min wannan Umma ce?" "Itace Rahmatu" Rahmatu ta zube a gaban Umma tana neman yafiyarta ta fad'a mata duk abinda ya daru da ita. Umma tace "babu komai Rahmatu ni baki yi min komai ba ina innan taki?" "Ta fita amma yanzu zata dawo...." Kafin ta rufe baki Inna lami ta shigo tana kallonsu da mamaki................ *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page4⃣9⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* ```Wattpad@mamyn_najmah2222``` Mamakin ta ita dai rasan bata da kowa a birni to me ya kawo 'yan birni gidan kuma ta gani har da manyan mutane bayan jerin motocin da ta gani a k'ofar gidan. Ta k'araso tana wangale musu baki "sannunku da zuwa" dukkan ninsu kallonta suke da mamaki yayin da Hibbah zuciyarta cike take fal da tsoran Inna, Daddy ne ya amsa mata da yauwa, ta gaishe su ka amsa ta dubi Rahmatu cikin fad'a kamar ba Rahmatu 'yar lelen Inna ba "ke Rahmatu kina gani anyi bak'i ba zaki kawo musu ruwa ba, kuma baza ki lek'a gidan delun ki kirani ba" Rahmatu tayi shiru tare da yin k'asa da kanta Inna ta mik'e "bara a kawo muku ruwa ko?" "A'a ki barshi mun gode" Faheem yayi saurin dakatar da ita donshi ko me za'a yi masa bazai iya cin wani abun daya fito daga hannun lami ba. Abba yace "wajen mai gidan muka zo gashi ance baya nan zai iya kaiwa zuwa yaushe kafin ya dawo?" Inna ta kuma washe baki "ayya ai yanzu zaku ganshi ya dawo ba jimawa zaiyi ba" Abba ya jinjina kai "to shikenan bara mu jira sa" Hibbah sai b'oye kai take kamar munafuka, su kuwa su momy dasu Saudat su Aunty duk mamakin inna sukeyi yadda take ta wani washe baki kamar gonar auduga. Suna nan zaune har wajen k'arfe hud'u saura malam bai dawo ba duk sun k'osa ya dawo musamman Daddy, Faheem ya kalli inna dake ta son jansu da hira "anya kuwa zai dawo yanzu ga la'asae har ta gabato ko dai muje mu dawo ne?" "Eh to ko zakuje ku dawo d'in amma idan sak'one Ku bayar a ajiye masa" duk suka kalleta da mamaki, ita kuwa ko a jikinta ta mik'e ta d'auko wata bak'ar buta wadda rabon da a wanketa har anmanta ta d'ebo ruwa a ciki ta kawo musu "ga ruwan alwala naga lokacin sallah yayi" Faheem ya mik'e "a'a mun gode muna da ruwa a mota" ta dube shi ta d'an b'ata rai ya fara bata haushi "au k'yamarmu kake yi 'yan k'auye ba mutane bane?" Daddy shima ya tashi yana bawa inna hakuri "kiyi hakuri baiwar Allah ba k'yamarki yake yiba, bara muje zuwa anjima zamu dawo" ta kalli su momy da suka kasa ma magana don matar mamaki take basu "ku tashi mu k'arasa can in anjima ma dawo." Suka mik'e zasu tafi Hibbah sai b'oyewa take a bayan su Saudat ita kuma Umma mamaki ne tab ya cikata ya akai Inna bata ganeta ba meta canza. Har k'ofar zaure inna tayo musu rakiya sai surutu take yi musu sudai basu kulata ba sukayi gaba. Ta koma cikin gidan tana ta d'auki ta dubi Rahmatu "ke yanzu haka ake tarbar bak'i musamman ma wad'annan 'yan birni dasu kina ganinsu kinsan kud'i ya zauna musu ai ko baza su shaba sai ki kawo musu ruwan, ni wannan d'an gayun ne yafi bani haushi sai wani iyayi yake yimi" sai kuma ta washe baki "Kai Allah mun gode maka may be sunzo tafita ne da malam can birnin shikenan zamu bar zaman k'auye" ta saki gud'a. Su Daddy kuwa suna fita suka ce su sallah zasu fara yi su matan su shiga gidan su Umma idan yaso su daga baya zasu shigo. Haka kuwa akayi Umma tayi musu jagorancin shiga cikin gidan suka shiga da sallama lokacin gwaggo tana sallah bata amsa musu ba. Umma ta shigar dasu d'akin gwaggo ta shimfid'a musu tabarma suka zauna ta dubesu da murmushi a saman fuskarta "Hibbah tashi kije ki amso musu ruwan alwala mun mance ba'a amso ba" momy tayi saurin tare ta "a'a idan akwai a nan zuba mana muyi dashi" "zaku iya kuwa amfani dashi karya ja muku matsala tunda ba sabawa kukayi ba?" Mamy ta mik'e "nuna min inda ruwan yake ni na d'iba don naga kamar kina tsoro ne" "a'a bara na d'ebo muku" Umma ta tashi ta d'auko butocin gwaggo sababbi guda uku ta zuba musu ruwan a ciki, momy da mamy da kuma Aunty suka d'auka. Suna fita gwaggo ta idar da sallar ta dubesu "sannunku da zuwa kunsha tafiya ya hanya?" "Yauwa alhamdulillah" "kunzo lafiya?" "lafiya lau mun same Ku lafiya?" Nan suka shiga gaggai sawa, Nawaz da Hisham suka gaishe ta. Hibbah ta kalli gwaggo cikin shagwaba "wai gwaggo yanzu don Allah wai baki gane ni ba?" Gwaggo ta tsaya kallonta tana mamaki fara tattafa hannu tana salati "Hibbah Kece? Alhamdulillah Allah kaine abin godiya Hibbah dama ashe zan kuma ganinki?" "To ba gashii kin ganni ba, ni fa ba mun b'ata da wannan tsohuwar tunda bata ganeni ba" Hibbah ta fad'a cike da shagwaba "ayya Hibbah ba haka bane ni ban tab'a tunanin zan kuma ganinki ba, na d'auka tunda lami tace karki kuma dawowa bazaki dawo d'in ba." "To ba gashi yanzu na dawo ba ina Abu?" "Gaskiya naji dad'i da zuwan nan naki, Abu tuni tayi aure Hibbah har da 'ya'yan biyu ma" Hibbah ta zaro ido "gwaggo Abu ce ta haihu har yara biyu?" "Eh mana Hibbah kema da kina nan da yanzu da naki, wad'annan su waye? Ko a wajensu kike aikin?" Gwaggo ta tambaye ta. Gyad'a Kai tayi "eh gwaggo a gidansu nake aiki sune suka inganta min rayuwa suka tallafa min suka ni a makaranta sun d'auke ni tamkar 'yarsu" "Allah mai iko mun gode da wannan kulawar da kuka yi mata Allah ya saka da alkhari ya k'ara bud'i mun gode" Kausar tayi murmushi "babu komai gwaggo" su mamy suka shigo suka gaggaisa da gwaggo suma gwaggo tayi musu godiya. Su Hibbah suka tashi don zuwa suyi alwala Saudat ta kalli Hibbah tana murmushi tace "Hibbah banji kincewa gwaggo kinyi aure ba" Hibbah ta harareta gwaggo ta rik'e baki "au Hibbah kema kinyi aure shine ba'a fad'a mana ba" "gwaggo k'arya take fa" Saudat tasa dariya "wallahi gwaggo tayi aure amma bata tare ba, munzo wajen baba ne" Hibbah ta kai mata duka tare da fita ta d'auki buta Nawaz ya biyota wai shima alwalar zaiyi. Su Safiyya ma suka fito Saudat tana ta yiwa Hibbah dariya, suka yi alwala suka koma d'akin. Bayan sun idar da sallah su momy suka shiga hira da gwaggo kamar sunsan juna anan suke fad'a mata tsakanin su da Hibbah kuma sun tabbatar mata da cewa Hibbah da gaske tana da aure d'an uwanta ma take aure amma bata tare ba, gwaggo ta bayyana murnarta sosai suna cikin hira Daddy ya kira layin momy ya fad'a musu sun dawo. Momy ta fad'awa su Umma taje ta shigo dasu, gwaggo ta fito da manyan tabarmi aka shimfid'a a k'ofar d'akin su Daddy suka shigo a tare da malam (mijin gwaggo) suka gaggaisa dasu gwaggo, sukayi musu godiya da kuma yi musu murnar ganin d'an uwansu da sukayi. Bayan sun gama gaggaisawa gyara zama ya fad'a musu abinda ya kawo su ya d'ora da cewa "to shine muka zo don mu tabbatar amma ita Umman Hibbah tace wai ba ita bace ita a nan aka haifeta kuma wai iyayenta basu mutu ba suna raye" malam da gwaggo suka yi shiru kamar ruwa ya cinyesu babu wanda ya iya magana, malam yayi k'asa da kai yana tunanin dole yau ya bayyanawa Aysha cewa ba sune mahaifanta na asaliba don ranar wanka ba'a b'uyan cibi. A hankali ya d'ago kai ya kalli duk su Abba da suka maida hankulansu a kansa ya dubi Umma yace "tabbas Aysha ba mune asalin mahaifanki ba" a razane Umma take kallon sa da alamomin tabbaya k'unshe a fuskarta. Malam ya cigaba "bamu muka haife ki ba kuma da dukkan alamu wad'annan mutanen sune 'yan uwanki da mukayi ta nema bamu samu ba, yau zan baki labarin yadda akayi muka same ki" "Ranar wata juma'a da yamma na dawo daga gona na hango ki kinata............... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page5⃣0⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* ```wattpad@mamyn_najmah2222``` "Ranar wata juma'a da yamma na dawo daga gona na hango ki kinata gudu kina kuka abin tausayi na tsayar dake da k'yar kika tsaya kinata kuka kamar zaki shine, na tambaye ki meye saki kuka? Cikin shashshek'ar kuka kina magana da k'yar kika ce min 'yan fashi ne suka harbi iyayenki suna can a bakin titi. Naji tsoro sosai shine naja hannunki cikin zulumi da tsoro muka tafi bakin titin amma abin mamaki babu kowa akan titin saidai jini dake ta gudana ta wajen. Na tambaye ki ina suke kikace kema anan kika barsu sai na shiga tunanin ko wasu mutanan ne suka zo wuce suka d'auke su, banyi k'asa a gwaiwa ba naja hannunki muka je wajen mai gari na shaida masa komai, shi da kansa yasa a cigirta ko za'a ga iyayenki na barki a hannunsa n dawo gida inna bawa zulai labarin abinda ya faru ta tausaya miki sosai. Zawon sati guda ana cigiyar iyayenki ba'a samu ba, da mai gari ya ce a kaiki cikin birni wajen 'yan sanda ko zasu ga danginki ni na bashi shawarar ya barki kawai a wajensa duk lokacin da 'yan uwanki suka natsu suka dawo hayyacinsu zasu buk'ace ki, mai gari yace nayi hakuri bazai iya rik'e ki ba amma ni idan naga zan iya k'ofa a bud'e take sai na d'auke ki. Nace masa to amma bara naje nayi shawara da iyalina, na dawo gida na shaidawa zulai komai mutuniyar kirki sam bata nuna komai ba a ranta sai ma murna da tayi ita da d'anta Habu. Na koma wajen mai gari ya bani ke amana muka tawo tun daga ranar na rik'eki tamkar d'ana Habu sam bansan naga hawayen ki ko kad'an saboda amana ce ke a wajena." Malam ya d'anyi shiru "Aysha tunda yanzu ga danginki sunzo nemanki to ya kamata ki koma garesu musamman ma shi da yake son rayuwa dake" Umma wadda hawaye ya gama wankewa fuska ta d'ago tana kallon malam "baba dama ashe da gaske ne maganar da yake fad'a? Don Allah baba kace min ba haka bane kace min kaika haifeni ba wasu daban ba" "haba Aysha keda ya dace kiyi farin ciki da murna kinga danginki sai kuma ki rik'a wasu maganganu daban?" Gwaggo ta tareta da fad'in haka. "Gwaggo ba farin ciki ne banyi ba tabbas nayi farin ciki amma bansan a ce baku ne iyayena ba" Abba shima da hawaye suna zuba a idanunsa yasa tissue ya goge yace "Aysha k'anwata hak'ik'a yau ranar farin ciki ce a gare mu ranar mai cike da alkharai ranar da Allah ya bayyana mana fuskokin mu, ki kwantar da hankalinki domin kuwa har yanzu su malam suna nan a matsayin iyaye a gareki" Gwaggo tace "alhamdulillah naji dad'in zuwan wannan rana naji dad'i da Allah bai karb'i rayukan mu ba har ya bamu aron wannan Rana da zamu damka ki a hannun d'an uwanki," "tabbas zulai haka ne, yau zamu maida amanar da aka bamu sai dai kash mai gari da ya bamu ke Allah ya amsa abunsa, duk da haka yau zan Bawa yayanki amarki." Ya kalli su Daddy "ga amanar 'yar uwarku nan da aka bamu yau na dawo muku da ita" Daddy cikin jin dad'in lafazin tsohon yace "mun gode daamanar daka rik'e mana bamu da abinda zamu saka maka dashi anan duniya, Allah ya saka muku da alkhari" suka amsa da amin kowa murna yake. Daga haka suka shiga hira sosai sai can Daddy yace "don Allah malam ina rok'on alfarma a wajenku don Allah Ku yarda ku bimu birni mu zauna a can" malam yayi murmushi yana girgiza kai "a'a kuyi hakuri baza mu iya binku birni ba Ku barmu anan kawai" nan fa su Aunty suka shiga rok'on su da k'yar ya yarda zasu koma amma shi bazai zauna a can ba sai dai gwaggo ta zauna nan sukayi ta godiya daga nan suka shiga hira har akayi kiran sallar magrib mazan suka tafi masallaci su kuma matan suka a yi gida. Suna dawowa daga masallaci Daddy yace su taso suje gidan su Hibbah don sun ganshi yanzu ya shiga gidan. Haka suka d'un guma zuwa gidan su Hibbah. Kamar yadda suka shiga d'azu matan ne suka fara shiga suka tadda baba a k'ofar d'aki a zaune yayi shiru k'irjinsa sai bugawa yake yi dama yau tunda ya tashi yake jin k'irjinsa yana yi masa nauyi zuciyarsa tana harbawa gashi haka kawai sai ya dinga jin gabansa yana fad'uwa ko kuma ya zauna yayi shiru ya rasa me yake tunani yana son tuna wani abu amma saiya kasa tunawa. Su Saudat sukayi sallama suka shigo baba sai binsu d'aya bayan d'aya yake da kallo k'irjinsa na bugawa da yake akwai sauran hasken gari. Mamy ta k'ura masa ido cike da tausayin d'an uwan nata hawaye na shatata akan kumatunta tasa hannu ta share, baba yace "ku zauna ga waje" suka zauna suna gaishe shi ya amsa, Hibbah da Umma dai ba suyi magana ba. Bugun zuciyar baba ya tsananta a lokacin da sukayi ido hud'u da mamy da Sauri ya kawar da kansa gefe ya danne bugun da zuciyar tasa take yi yace "kune kuka zo nemana d'azu?" Momy cikin k'arfin hali da tausayin d'an uwan mijin nata kuma mijin k'anwarta tace "eh mune amma bamu kad'ai bane akwai mazajenmu da suke waje sune ma suke son su gana da kai" "ahh to ku shigo dasu mana ya zaku barsu a waje?" Aunty ta kalli Hibbah da tayi tsuru tsuru duk tsoro ya cikata tace "haba k'anwata ki nutsu mana ai komai yazo k'arshe da yardar Allah" Hibbah kawai kad'a kai tayi don gani take ko ya tayi magana Inna da baba zasu iya ganeta numfashinta ma a hankali take yi wai kar su ganeta. Aunty ta dubi Safiyya tace "Safiyya kije ki cewa su Abba su shigo"Safiyya tace "to" ta mik'e tai waje. Tana fita Inna na fitowa daga d'aki ta dubesu tana washe baki rik'e da fitila a hannunta "sannunku kun dawo?" Kausar ta yarfa mata harara Aunty tace "eh mun dawo" Hibbah ta kuma k'amk'ame Aunty ta fara kuka k'asa k'asa don a rud'e take sosai. Umma ta kalleta ta d'anyi k'asa da murya "Hibbah mene na kuka kuma babu abinda ta isa tayi mana Wanda Allah bai nufa zai same mu ba ki kwantar da hankalinki kinji?" Hibbah ta gyad'a kai Aunty ta janyota jikinta tana rarrashinta. Baba kuwa k'irjinshi da zuciyarshi ne suka tsananta bugawa gabansa ma ya shiga fad'uwa da sauri sauri. Ba jimawa su Abba suka shigo da sallama tabarmar da baba yake kai suka nufa zasu zauna, baba wanda tuni ya mik'e tsaye jin muryar da bazai tab'a mantawa ba ya shiga nuna Daddy yana girgiza kai yayin da kanshi yayi masa nauyi wani duhu ya halarci idanunsa tuni yayi taga taga zai fad'i da hanzari Daddy da Abba suka taro shi. Hibbah tana ganin baba ya fad'i ta k'walla k'ara tare da cewa "baba!" Ta dubi su Aunty suma duk sun rud'e tace "Aunty baba ya fad'i kar wani abu ya same shi" sai kuma tasa kuka. Gaban Inna ne ya fad'i jin muryar Hibbah cikin rud'ewa ta mik'e tsaye tayo kan Hibbah Wanda itama tuni tayi kan baba da masifa take magana "muryar wa nake ji kamar ta Hibbah me ya dawo dake garin nan baki ji gargad'in da nayi miki ba ko?" Kausar dake gefenta tace "itace Hibbah ce kuma ta dawo ne don ceto rayuwar mahaifinta daga hannun azzalumar mace irinki" cikin d'aga murya Inna tace "ke Kama kanki ki nutsu ban kasa dake ba da zaki d'auka" ta kalli Hibbah da tayi tsuru tsuru ta fizgota ta d'aga hannu zata mareta Faheem ya rik'e hannun "karki sake ki tab'a min mata, kina tab'ata sai dai a kwashi gawarki" "idan ba'a kwashi gawata ba za'a kwashi gawarta yanzu ba sai gobe ba, wallahi alkawarin da na d'auka saina cika shi na indai Hibbah ta dawo garin nan sai na kasheta" Faheem ya tura Hibbah kusa da Inna "gata nan don Allah ki kashe ta ki kasheta nace" Inna ta buga mai wani mugun kallo "ku jirani nan da mintuna kad'an" ta zari mayafinta ta fita tana masifa. Hibbah ta kuma saka kuka Kausar ta janyota jikinta "kiyi shiru Hibbah babu abinda Bawa ya isa yayiwa d'an uwansa Bawa wanda Allah bai nufa zai same shi ba ki kwantar da hankalinki babu abinda ta isa ta yi miki" Rahmatu dake d'aki jin fitar Inna ta fito don Inna hanata fitowa tayi ta d'auko kwano cike da ruwa ta mik'awa su Abba, Abba ya amsa ya d'iba a hannunsa ya safa a fuskar baba, baba baiyi motsi ba ya kumayi nan ma shiru har sai da yayi sau uku baba bai motsa ba nan hankali su ya mugun tashi har sun yanke shawara d'aukar shi zuwa asibiti sai kuma.............. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page5⃣1⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Kulawarku da damuwa da littafina ya sani cikin farin ciki na gode sosai, masu kirana a waya basu samu ba da masu min magana ta what's up kuyi hakuri ina busy ne.* Sai kuma baba ya ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya a hankali ya fara bud'e idanunsa ya sauke su akan na Daddy shima da Daddy kallon sa yake zuciyarsa duk ta karaya hawaye na zuba a idanunsa. A hankali baba ya d'ago hannunsa ya d'ora a saman fuskar daddy ya shiga goge masa hawayen yana masa murmushi "ka daina kuka d'an uwana ban Sonka da zubar hawaye" Daddy ma murmushi yayi "ai dole ne Mukhtar munyi kewar rashinka munyi kuka har mun gaji munsa a ranmu ka rasu sai yanzu muka sami Labarin kana raye kaga kuwa dole mu zubda hawaye farin ciki" baba yayi murmushi yana kallon duk mutanan wajen babu Wanda ya Sani a cikinsu banda momy da mamy sai kuma Faheem da yake ta kallo yana son gano waye? Ya dubi momy da mamy da suke ta matsar k'walla "autar hajiya da matar Yaya ku daina kuka Dan Allah ku matso gare ni" a hankali suka matsa kusa da baba ya rumgume su tamkar yara suka fara kuka yana d'an bubbuga bayansu. Baba ya d'ago kansa yana kallon Abba suna yiwa juna murmushi da kuma hawaye a fuskokinsu, baba ya d'an saki su momy ya kuma duban Abba "babban Yaya wai wad'annan duk 'ya'yana ne?" Abba ya d'aga masa Kai "naka ne duka Abban Aysha" mamaki ne ya bayyana a fuskar baba yace "Abban Aysha wace Aysha? Ni banga Aysha ba da hajiya suna ina?" Da sauri daddy ya d'ago kansa jin mutanen da k'anin nasa yake tambaya hawayensa suka tsananta zuba, Abba shima hawayen yake yi yace "kayi hakuri Abban Aysha sanadin cutar da ta sameka a wannan daren Allah yayiwa hajiya rasuwa sanadiyyar hawan jininta daya tashi, Aysha kuma tashin hankali ne yasa ta nak'uda a lokacin ta haifo 'yarta mace shine aka saka mata sunan Aysha saboda ita ma Aysha bata rayu ba." Inna lillahi kawai baba yake furtawa zuciyarsa na masa zafi a sannu rayuwar da sukayi da mahaifiyarsa da matarsa ya Fara tunowa sai kuma hawaye suka fara sauka a saman fuskarsa yasa hannu yana gogewa yana mai yi musu addu'ar samun rahamar ubangiji. Su Kansu su daddy hawayen suke yi saboda tuno mutuwar da sukayi sai filin tsakar gidan yayi shiru sun d'auki wasu lokuta a haka kafin baba ya katse shirun da cewa yana murmushi "wace Ayshan a cikinsu? Duk sun d'auko kama iri d'aya" daddy ya dubi Aunty "Aysha matso Gare shi zo ga mahaifinki" Aunty ta taso ta zo wajen baba, shi kuwa baba cikin happy ya rumgume ta k'aunarta na ratsa duk ilahirin jikinsa ita kuwa Aunty kuka take ga k'aunar mahaifinta na shigarta sun d'auki lokaci k'amk'ame da juna baba ya d'ago yana kallon su Kausar "yarana ku matso gare ni kuzo naji d'umin jikin yarana" ya fad'a yana bud'e hannayensa, matsowa su duka suka yi banda Hibbah dake gefe kusa da Umma tana ta kuka zuciyarta cike take da tsoron abinda inna ta fita yi shima Nawaz bai tashi ba yana jikin Hibbah yana goge Mata hawaye wai tayi shiru . Su Saudat kuwa baba had'asu yayi ya rumgume su yana mai jin k'aunar 'ya'yan 'yan uwan nasa na ratsa shi, sun dauki lokaci kafin ya sakesu ya kalli Faheem "babban Yaya kar dai kuce wannan ne Faheem nawa" da murmushi Abba t?yace "shine Abban Aysha" baba ya dubi Faheem yana dariya "lallai na dad'e rabona da ku dubi fa yadda ka zama babban mutum, ina Haisam kuma?" "Haisam yana Abuja acan yake aiki" "to Allah ya bada sa'a ina dai fatan yanzu kun ajiye iyali ko?" Faheem ya d'an Sosa k'eya yana duban Abba. Cikin dariya Abba yace "ka fad'a masa mana" Faheem ya kuma sunkui da kai daddy yayi dariya "duk sunyi aure dashi da Haisam d'in shi ya auri k'anwarsa Kausar da ka tafi Rukayya na da cikinta har ma da d'ansu Nawaz yanzu kuma ya kuma k'aro wata a sanadiyyarta ne muka gano inda kake." Baba ya dubeshi da mamaki "wace ita?" "Hibbah ce 'yar wajenka" mamaki ne ya kuma bayyana a fuskar baba gumi ya fara keto masa "Hibbah ina kike matso gare ni kiyi min afuwa ki yafe min muzgunawar dana miki ke da mahaifiyarki, kinga Rahmatu yadda mahaifiyarta ta cutar mata da *RAYUWA* ko?" Hibbah ta matso kusa da baba Nawaz ya biyota tace "baba baka yi min komai ba na yafe maka" "ina Ummanki Hibbah?" Ta nuna masa Umma. Ya yunk'ura zai tashi daddy ya ruk'oshi, baba yayi murmushi don ya gane dalilin rik'eshin da daddy yayi "nafa samu sauki babu inda ke min ciwo" daddy ya sake shi ya k'arasa gaban Umma "kiyi hakuri Aysha ki yafe Min lefin da nayi miki don Allah" "nasan ba lefinka bane na yafe maka Allah ya yafe mana" baba yaji dad'i tace "na gode Aysha" ya dubi Nawaz "wannan ne abokin nawa?" Ya fad'a yana janyo Nawaz jikinsa ya kalli Faheem dake ta sunna Kai "Faheem wai kunyata kake ji ne? Ni ba surukinka bane fa" Faheem yayi murmushi yana kuma k'asa da kansa. Baba yayi murmushi yana mamakin yadda Faheem shi bai yadda ba kunyar shi yake ji. Abba ya d'anyi gyaran murya "k'aramin k'anina (haka yake kiranshi) ka taya ni murna nima naga Aysha k'anwata" farin ciki ne ya bayyana a fuskar baba da kuma mamaki "a ina? Wace ita? Me yasa baku tawo tare ba?" Tambayoyin baba sun basu dariya Abba yace "mun tawo da ita mana" "tana ina? Ya baku shigo da ita ba?" Daddy ya kuma dariya saboda yadda k'anin nashi yake ta wani zumud'i "gata nan a gabanka, ai ba bak'uwa bace Umman Hibbah ce" "Umman Hibbah?" Baba ya tambaya cike da mamaki "eh ita ce" Abba ya bashi amsa sannan ya shiga bashi labari kamar yadda malam ya basu. Baba ya jinjina kai ya dubi Hibbah " ikon allah kenan, Hibbah kinga *RAYUWA* ko? Kinga sanadin kaiki aikatau da lami tayi kin nemo danginki ko?" Hibbah ta d'ago tana kallon baba da murmushi tace "haka ne baba amma ya akayi kazo k'auyen nan?" Aunty ta kalli Hibbah tana dariya "shine kika rigani tambaya" Saudat tace "ai gara da ta tambaya aunty don na k'osa naji yadda akayi" baba yayi murmushi, Hibbah ta tsaya tana kallon fuskar baba tana mamakin yadda baba yau yake yawaita murmushi, ko dan yaga 'yan uwansa ne oho. Baba ya katse mata tunani "ni kaina bansan yadda akai nazo nan ba nima kawai na tashi daga bacci ne na ganni a gidan su lami sai daga baya mahaifinta yake fad'a min a halin da ya since ni na hauka. Mahaifin lami shahararran malami ne a cikin k'auyen nan shine ya cigaba da bani magunguna har na samu sauk'i ya bani kud'i yace na koma garin mu saboda na bashi labari na. Kasa komowa nayi saboda gaba d'aya ji nake na tsaneku bana son kuma rayuwa daku na fad'a masa ni bansan komawa cikin dangina ya tambaye ni dalili na fad'a masa cewar ni kawai bansan komawa bai takurani ba ya barni a gidansa na cigaba da zama. Ya koya min sana'ar da yake yi nima na shiga taimaka masa, Allah sarki malam shehu shekarar mu d'aya dashi Allah ya karb'i ransa kafin ya rasu saida ya rok'eni da na auri 'yarsa d'aya daya mallaka Fatima wato lami na amince masa duk da tarbiyyar lami sam bata yi min ba don sun shagwaba ta sam bata da kamun kai amma bazan iya bud'e baki nace masa bana son jininsa ba haka na hakura aka d'aura aurena da lami ya bani wannan gidan da muke ciki. An d'aura aurenmu da sati d'aya malam Shehu Allah yayi masa rasuwa munyi kukan rashinsa. Ni na cigaba da Kular masa da dukiyarsa da matarsa baba mairo mata Mai mutunci da karamci, shekaramu d'aya da aure itama baba mairo Allah ya karb'i rayuwarta sanadiyyar ciwon cikin da tayi ta fama dashi. Tunda mukayi aure da lami bata tab'a haihuwa ba shine sanadiyyar auren Aysha da nayi har ta Haifa min Hibbah amma abin mamaki na kasa kula da su hasali ma tsanarsu nayi sam bana son ganinsu, sai gashi kuma Aysha tazo tana cin amanata. Ina kasuwa malam Haruna mijin k'awar lami yazo yana fad'amin cewar Aysha fa tana ta rayya da maza don ganin idanunsa shi shaida ne na zo gida Sam babu bincike na saki Aysha ashe tuggu lami ta had'a ita da kawarta delu, sai daga ba malam Haruna yazo yana neman yafiya ta ya fad'a min cewar sharri suka yiwa Aysha" baba ya d'ago ya kalli Umma da Hibbah "Ku yafe min don Allah" "na yafe maka ni tuntuni" "baba ni baka yi min komai ba" B'an garan Inna kuwa tana fita gidan delu ta nufa delu tayi mamakin ganinta da daddare tace "lami lafiya?" "Ina fa lafiya Hibbah ta dawo tare da wasu manyan mutane 'yan gayu masu kud'i har d'aya daga cikinsu yana ikirarin wai Hibbah matarsa ce," delu ta zuba Mata idanu cike da mamaki "Matar sa? Kice zama bai Kama mu bai kama mu ba" "ai dama na sanki aminiyata shiyasa na garzayo wajenki" delu ta janyo mayafinta tace mu tafi wajen halakakke" suka fito suka nufi wajen boka basa ko tsoran dare suka hau dutsen da yake kai suka cire takalmansu da d'ankwalayen su da mayafai suka doshi inda yake zazzaro ido sukayi waje cike da tsoro suka.......... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page5⃣2⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Aunty Garkuwa Allah ya baki lpy ya kuma yaye miki wannan ciwon idon da kike fama da shi ameen.* Suka dubi juna a hargitse lami tace "delu huta ce fa take cin jikinsa duba fa kiga" "na gani lami ai kuwa muma muyi maza mubar wajen" delu ta fad'a tana jan hannun lami suka sauko daga kan dutsen duk a tsorace suke. Lami ta kalli delu tace "wai yanzu mene abin yi ne?" "Bamu da wata mafita kawai ki hakura kina gani halakakke yana ci da wuta kinga ba wani aiki fa da zai iya yi mana" lami ta jinjina Kai haka ne amma ke baki San wani ba da zai yi mana aikin?" Delu tayi shiru tana tunani can tace "eh.....to akwai wani boka a can k'auyen gomma zai yi miki aiki kuma zaki ji dad'in aikinsa amma ke baza ki iya da aikinsa ba don na sanki" "mene matsalar tawa kema kinsan komene yau zan iya aikata shi matuk'ar Hibbah zata wulakanta a duniya" lami tayi saurin tare ta da fad'in haka. Delu ta dubeta "dole ne zai kwanta dake kafin yayi miki aiki kin yarda muje?" Ba tare da tunanin komai ba lami tace "Muje kawai indai zan samu biyan buk'ata" Nan suka d'auki hanyar gidan boka zulk'ulle dake k'auyen gomma, suna zuwa suka fad'awa boka buk'atarsu yace sunsan sharad'insa suka ce eh yace to ita lami ta tashi su shiga ciki ba ko tsoro a zuciyarta suka shiga ita dashi yayin da delu tana k'ofar wajen tana zaman jiransu. Can gidansu Hibbah kuwa bayan sunyi sallar isha'i zama sukayi suna ta hira cike da barkwanci da nishad'i kowa cikin farin ciki yake jinsa Hibbah har ta mance da wata Inna. Saudat ta dubi Hibbah "wai ni Aunty Hibbah ba'a zuwa dandali ne a k'auyen nan?" Rahmatu dake gefe da k'aton cikinta tace "zuwa kai kina son kije ne?" Cikin zumud'i Saudat tace "eh don Allah Aunty Hibbah kuzo muje naga yadda dandalin yake" Hibbah cikin tsokana ta kwantar da kanta akan cinyar mamy tace "tab kije ke kad'ai ni dai bacci nake ji". Saudat tayi kalan tausayi "Kai Aunty Hibbah don Allah ki tashi muje" "a'a karki takurata ki k'yaleta tayi baccinta" momy ta fad'a tana shafa kan Hibbah. Saudat ta dubi Hibbah tana k'arya kai kamar zata yi kuka, Hibbah tayi mata gwalo ta kuma gyara kwanciya a jikin mamy. Safiyya da Kausar me zasu yi inba dariya ba Safiyya tace "wallahi Aunty Hibbah karki je kiyi baccinki ita idan tana son abu dole sai anyi mata" Saudat ta kai mata duka ina "ruwanki yarinya sai rainin tsiya don kinga Ana miki wasa ko" Safiyya ta DA dariya "to tsakanin mu shekara nawa ne d'aya ne fa kuma shima akasi aka samu da baza ki girmemin ba, kuma dandali ne baza'a ba" "eh naji na dai baki shekarar ai ko 1 minute na baki na dai girmeki kuma dandali ne kar aje d'in ai kema kina son zuwa bani kad'aice ke son zuwa ba" Safiyya tayi dariya "kuma fa haka ne nima Allah ina son zuwa" Aunty ta kalle su cike da sha'awa idan suna wannan fad'an nasu burgeta suke yi tace "au ke Safiyya da bak'in ciki zaki yiwa Saudat d'in kenan?" "A'a Aunty nasan Aunty Hibbah da Saudat ne ba'a jin Kansu shiyasa na fad'i haka nasan koda tace baza ta je ba zata dawo ta je d'in" Hibbah dake kwance tana game da wayarta tace "nifa babu inda zani" Umma ta dubeta "tashi maza ki raka su suje don kinga suna rok'on ki shine kike cewa wani baza kije ba" Hibbah ta d'an d'aga ciyar mamy ta dubi Umma "wallahi Umma ciki nane yake min ciwo har banson na zauna ma balle na tashi nayi tafiya" Daddy da suke can d'ayan tabarmar dasu Abba da baba yace "a'a ku rabu da ita tunda bata da lafiya ko zuwa dandalin dole ne" baba cikin kwantar da murya yace "a'a baza ayi haka ba ta tashi ta lallab'a ta raka su tunda suna so" Saudat cikin murna tace "yauwa baba" ta yiwa Hibbah gwalo "to ai saiki tashi mu tafi" Saudat ta mik'e tana gyara mayafinta. Ganin haka Faheem ya d'auki wayarsa yanata hello hello ya fita daga gidan baba yace "sai hakuri ina jin gidan ba service" Hibbah kuwa ba don ta so ba ta tashi ta yafa mayafinta ta gyarawa Nawaz kwanciya don yayi bacci Safiyya ma ta mik'e suka fita, su Aunty da Kausar daau momy suka cigaba da hirarsu. Saudat ce agaba sai Safiyya a tsakiya sai Saudat dake binsu a baya tana ta mita. Ji tayi an fizgota ta fad'a jikin mutum tana k'ok'arin bud'e baki tayi ihu ya toshe mata baki da hannunsa tare da mannata a jikinsa ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya, ita kuwa Hibbah sai tureshi take tana son k'watar kanta a hankali ya lalubi kunnenta yace "ki nutsu a jikin mijinki kike" ita dai Hibbah bata kula shi ba ta cigaba da kiciniyar k'wace kanta. Kuma matseta yayi a jikinsa ya tura hannunsa k'asan cikinta yana shafawa a hankali cikin rad'a yace "meya sami cikin naki ni dai nasan banyi ajiya a cikin nan ba ko?" Ita dai bata kula shiba tayi lamo a jikinsa don bata da k'arfin ture shi ganin yadda ya k'amk'ameta, ya cigaba da shafa cikin nata "ki fad'a min me yake damun cikin ko saina duba da kaina?" Tayi masa banza ita duk kunyarsa ma take ji ga kuma mamaki wai daddy ne yake yi mata wannan abun, bata yi aune ba taji yana yi mata tafiyar tsutsa a jikinta sai jin hannunsa tayi a kan breast d'inta. Zazzaro ido tayi waje "daddy....." Tama kasa magana sai rik'o hannunsa da tayi tana girgiza masa Kai, murmushi yayi duk da a duhu ne yace "ai dubawa zanyi tunda ke kink'i fad'a min" da sauri tace "wallahi Daddy k'arya nake kawai don kar na raka su ne" dariya ta bashi sosai yace "my hrt desire dama kin iya k'arya?" Shiru tayi tana k'asa da kai ya kuma murmushi ya rik'e bakinta ya d'an matsa "ni ki daina maidani tsoho kina cemin Daddy idan kuma ba haka ba......" Yayi k'wafa ganin yadda ya kuma matseta da sauri tace "to na daina." Saudat ce ta lek'o "Hibbah ina kika tsaya ne ki fito mu tafi" Hibbah ta kuma zaro ido da k'yar tace "takalmina ne ya mak'ale gani nan zuwa" "to ki haska mana ba da waya a hannunki ba" Hibbah tace "gani nan fa" ta kalli Faheem "daddy su Saudat na jira na" ya had'e rai "baki ji ba ko nace ki daina cemin daddy zan d'au mataki fa" "Allah ya baka hakuri na daina" ya cikata "to jeki ko nazo nayi rakiya?" Da Sauri ta girgiza kai, yayi dariya "matsoraciya" da gudu ta fita ganin ya sake ta, shi kuwa dariya ta bashi ya shiga cikin gidan yana murmushi yana kuma mamakin kansa yadda yaso ya kasa saita kansa don kawai ya manna jikinsa dana wannan yarinyar, ya d'anyi tsaki a zuciyarsa yace duk laifin Kausar ne wallahi ba don haka ba da ba zai susuce akan wannan 'yar yarinyar ba. (Ni kuwa nace eh akan yarinyar ka kasa nutsuwa har ka kwanta a asibiti saboda ciwon zuciya😏) Ta fito suka tafi dandali Saudat tana ta yi mata mita suna ta fiya ita dai bata kulata ba don duk abinda Faheem yayi mata yak'i goguwa a kwanyarta da haka suka k'arasa dandalin Ana ta kad'ekad'e 'yammata suna ta rawa wasu kuma sunata zuba tad'i. Suka k'arasa wajen suna ta kallon matan masu rawar, Saudat ta kalli Hibbah cikin tsokanar tata tace "Auntyna ke baza ki shiga kiyi rawar ba, da fa har dake ake yi ko?" Hibbah ta harareta bata ce komai ba, Saudat da Safiyya suka kwashe da dariya Saudat tace "kuma wad'annan k'olawan ne samarin Ku?" Saudat ta fad'a tana dariya har da rik'e ciki. Hibbah ta buga mata duka tana cewa "wallahi tashi mu tafi dama don kiyi min wulakanci ne yasa kika ce zaki zo ko?" Safiyya ita ma dariyar take tace "haba Aunty Hibbah ai ko da kina k'auyen nan kinfi k'arfin wad'an nan k'olawan" itama ta fad'a tana dariya, Hibbah ta tashi ta fara tafiya "idan kun gama dariyar ku same ni a gida" "ki tsaya mu mana Auntyna" Saudat ta fad'a cikin dariya banza Hibbah tayi dasu ta fara tafiya. Ji tayi an dafata ta baya ance cikin yanayin mamaki "Hibbah dama zaki dawo k'auyen nan?" Da sauri Hibbah ta juyo jin muryar kharime tace "kharime" "na'am Hibbah yaushe kika zo?" Farin ciki ne ya lullub'e Hibbah tace "yau nazo kharime ina dije?" "Dije suna tare da salahu, Hibbah kinga yadda kikayi kyau kika koma 'yar gayu kamar dama a birni aka haife ki" Hibbah tayi Mata hararar wasa "kai kharime kin fiya tsokana" "Allah da gaske nake, kinsan Abu tayi aure kuwa?" Hibbah ta janyo hannunta suka zauna akan wani benci tace "eh gwaggo ta fad'a min ke yaushe ne naki?" "Ai idan zaki kai wani satin a garin nan to dake za'ayi" "da gaske?" Hibbah ta tambaye ta cike da zumud'i kharime tace "Allah kuwa" Su Saudat suka k'araso suka gaisa da kharime, Hibbah an samu aminiya tuni suka zauna suna ta zuba hirar yaushe gamo, dije ce ta k'araso tana ta mita "wallahi kharime halinki saike gara ma ki canza hali gidan wani zaki" kharime ta kalleta tana dariya "Amaryar salahu me nayi kuma?" "Wato sai da kikayi yadda kikai kukayi magana da wad'annan 'yan birnin ko?" Dariya kharime ta kuma yi "Hibbah ce fa" "wace Hibbah karki raina min hankali mana" "Allah da gaske nake nima ta muryarta na ganeta" dije ta zubawa Hibbah ido lokaci d'aya kuma ta gane kamannin Hibbah, da sauri suka rumgume juna suka zauna Ana ta zuba hira. Su Saudat kuwa zuba musu ido sukayi suna ta sauraron hirarsu, sun jima suna ta hira badon sun so ba haka suka hakura suka rabu akan gobe idan su Hibbah basu tafi ba zata zo su je gidan Abu. Haka suka koma gida aka cigaba da hira kamar baza'a daina ba, ita kuwa Hibbah duk kunyar Faheem take ji shiyasa ma ta kasa sakewa a haka har dai suka yi bacci. Inna lami kuwa sunkai wajen 3hours a ciki ita da boka kafin............. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page5⃣3⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* ```watpad@mamyn_najmah2222``` Kafin su fito ya had'a musu wasu k'ullika ya bata "ga wannan ki barbad'a a wajen da kika tabbatar zata tsallaka daga yanzu da kika amsa karya awa d'aya baki yi amfani dashi ba sannan da kinje gida ki barbad'a tana tsallakewa da mintuna biyar ki share, karki karya k'a'ida ko guda d'aya idan aka samu matsala d'aya a cikin mu zai mutu ko ni na mutu ko ke ki mutu" babu ko d'ar a zuciyar Inna lami ta amsa suna k'ok'arin zube masa k'ud'i y katse su "wannan aikin naku yana da had'ari ku bari sai aiki yayi kyau sai ku kawo" nan suka tashi sukayi godiya suka tafi. Suna tafiya suna ta hira a kan maganin da bokan ya basu, sunzo tsallaka wani d'an k'aramin titin da zai sadasu da k'auyen katsalle da yake titi guda d'aya ne sai ji kake k'uuuuuuuuuu wata k'atuwar dab tayi shoki da su delu ma'ana tayi sama dasu a take suka zube a wajen. Can gidan kuwa ana kiraye kirayen sallah dukkanninsu suka tashi mazan suka nufi masallaci yayin da matan sukayi a gida bayan sun idar kuma suka shiga tattare gidan don Daddy yace yau zasu koma gida, suna shirin d'ora girki sai gashi gwaggo ta aiko musu da breakfast mai rai da lafiya. Nan suka amsa tare da godiya aka zauna aka nad'i girkin gwaggo bayan sun gama kuma sukayi wanka Ana ta shirin komawa birni. Ita dai Hibbah bata so komawarsu ba taso zuwa gidan Abu kodan suka juna ta kuma fad'a mata abinda yake faruwa tasan abu zata tayata murna. Haka ba don tana so ba suka gama shiryawa suka nufi gidan gwaggo don d'aukota su tafi sannan su yiwa malam sallama, da suka je ma itama ta shirya suka kuma yiwa malam godiya suna shirin fita saiga Abu ta shigo ta gaishe dasu momy sannan ta rumgume Hibbah tana murnar ganinta ita ma Hibbah cikin d'auki da murna ta rumgume Abun, Abu tace "na tayaki murna Hibbah naji dad'in wannan al'amari ashe dama rabon kiga dangi ne ya kaiki birni" Hibbah ta kuma k'amk'ameta sai dai taji bata rumgume Abu sosai ba don wani abu ya tokare tsakaninsu Hibbah ta d'an saketa ta d'an matsar da ita daga jikinta tana son ganin mene abun da ya hanasu had'a jiki sosai. Ido Hibbah ta zaro da mamaki tana kallon Abu tayi k'asa da murya tace "Abu me nake gani ciki?" Abu ta d'an buge kafad'art "ni har kin bani tsoro wallahi ji nake wani abun ne, to cikin bashi bane ribar aure" Hibbah ta rik'e baki tana mamaki wai Abu ceda ciki kenan itama dole ne ta k'unshi nata?" Ta girgiza Kai Anya kuwa zan iya? Abu ta dafata "tunanin me kike yi?" "Ba komai waya fad'a miki nazo garin nan?" Hibbah ta tambaye ta "Abban Amina ne ya fad'a min" kallon ta Hibbah tayi da mamaki "waye kuma Abban Amina?" Abu tace "au a shefa baki santa ba, 'yar da na Haifa ce ta rasu" "au wai kina nufin wannan cikin bashi ne na farko ba? Tab kina k'ok'ari" "k'ok'arin me?" "K'ok'arin d'aukar wannan cikin" dariya ma Hibbah ta Bawa Abu tace "kema zaki d'aukane" Saudat dake gefensu tana jin duk abinda suke cewa tace "tab har na hango Hibbah da k'aton ciki nan kina tafiya da k'yar" ta kuwa kwashe da dariya. Hibbah ta harareta bata ce komai ba, Saudat ta cigaba "kinga dama Daddy yace nan da sati biyu zaki tare kinga kenan nan da wata tara zamu so suna" Abu ta kalli Hibbah da mamaki "au Hibbah kinyi aure kema?" Da Sauri ta katseta "k'arya fa take yi" Saudat tayi zaraf "wallahi da gaske nake sanadin auren ne ma yasa muka zo garin nan kuma ki tambayi su gwaggo" "na yarda ma wallahi, to ke Hibbah ai ba'a b'oye abin alkhari" ita dai Hibbah bata ce komai ba sai hararar Saudat da take yi. Suna nan zaune sukaji sallama babban mutum ne wai baba yake nema, baba ya tashi ya fita abinda ya gani ne ya sashi juyowa gida da sauri ya shigo duk a hargitse kallon mamaki su Abba duk suke masa suna tambayar lafiya? Yama kasa magana waje kawai yake nuna musu ganin ya kasa magana yasa suka mik'e suka fita don ganin abinda ya rikita baba. Inna lillahi kawai suke kira duk sun firgita da abinda suka gani, Inna lami ce da delu a kwance a k'ofar gidan inna k'afafunta sun cire fit babu hannaye ga idanunta ba duk bata gani sai surutai take yi "wallahi Hibbah saina ga k'arshenki dama saida boka halakakke yace karna sake na bari ki dawo k'auyen nan idan kika dawo akwai mummunan al'amari da zai faru kuma na gargad'eki karki dawo amma sai da kika dawo gashi nan munje wajen bokan mun tadda shi yana ci da wuta don haka kema sai na k'onaki" sai kuma tasa wata muguwar dariyar da ta tsorata su duka wajen ga 'yan k'auyen duk sun zagayeta. Sai da tayi mai isarta sannan ta tsagaita dariyar "na tsaneki Hibbah bazan iya barinki kiji dad'in rayuwa ba shiyasa muka tafi wajen wani bokan yayi amfani dani ya bani wasu k'ullika yace ina komawa gida na barbad'a miki kar na huce awa d'aya ban barbad'a ba, kuma idan na barbad'a miki kina tsallakewa na share kar yayi mintuna biyar ban share ba idan ba haka ba ni ko shi d'aya a cikinmu zai mutu, mun tawo akan hanyar mu ta dawowa mota ta bigemu........" Sai kuma tasa wata muguwar dariya can kuma tasa kuka kamar yarinya wai ciwo jikinta yake mata "wayyo malam jikina ciwo" sai ta kuma sa dariya "malam kaima nice nayi maka asiri don karka koma garinku saboda inasonka bayan nayi maka asiri ne na fad'awa baba shine ya aura maka ni. Kuma nice na rabaka da Aysha da Hibbah nasa ka tsanesu nayiwa Aysha sharrin zina nasa ka rabu da ita Hibbah ma nice na tura mata kwarto d'akintaaaaa!" Sai ta kuma fashewa da da dariya. Gaba d'aya jikinsu yayi sanyi sai kallonta suke yi hauka take sosai tana ta fad'in abinda ta aikata, delu kuwa dake can gefe ko numfashi bata yi da alama ma ta mutu. Rahmatu da Hibbah sun had'a Kai sai kuka suke yi Rahmatu wani zugi take ji a zuciyarta ace mahaifiyarka na aikata shirka yanzu kuma ta haukace a wajen bin bokayen nata gashi ba hannaye ba k'afafu ba idanu wannan kad'ai ya ishi masu yi isara. Mijin delu dake gefe ya dubi baba "malam Mukhtar kaga *RAYUWA* ko kaga aikin bin bukaye ko wallahi nayi danasanin kasancewarta mata a wajena Allah ya isa tsakani na dake delu bazan yafe miki ba" daddy yayi saurin kace shi "a'a malam ba'ayi haka ba ba'a bin mamaci da mummunar addu'a kayi mata fatan rahmar ubanjgiji kawai" mijin delu ya gyad'a kai zuciyarsa na k'una yace "Allah yayi miki rahma" Baba kuwa ya kasa magana su momy kuwa al'ajabin abin ya hanasu magana sai fatan allah ya bata lafiya suke. Haka dai suka d'auko hanyar garin kano bayan an kai delu gidanta na gaskiya, inna lami kuwa acen suka barta a gidan cikin hauka don baba cewa yayi baza su tafi da ita ba da Abba ya buk'aci su tawo da ita saisu kaita gidan mahaukata amma fafur baba yace aa a barta abinda ta shuka take girba. Sun dai tawo da Rahmatu da take ta kuka tana yiwa mahaifiyarta fatan samun lafiya don hannunka baya rub'ewa ka yanke ka yar. Haka suka iso garin kano direct gidan Daddy dake rijiyar zaki suka huce anan suka yada zango, bayan sunyi wanka suka ci abinci aka zauna zaman hutu. Ba jimawa Umma tace ita zata huce gidan mijinta, baba yayi mamaki don shi a tunaninsa Umma bata yi aure ba yana shirin mai data d'akinta sai kuma yaji ashe tana da aure, sai kawai ya kawar da tunanin yana addu'ar Allah ya zab'a masa wadda tafi alkhari. Daddare duk suka watse Aunty ta koma gidan mijinta da tace da Hibbah zata tafi momy tace a'a ta barta anan tayi zamanta. Kausar ma Faheem d'aukarta yayi suka huce yaso ya d'auki Amaryarsa Hibbah amma Daddy ya hana haka badon yaso ba suka tafi shi da Kausar suka bar mata Nawaz a wajenta don cewa yayi shi a wajen Aunty Hibbah zai zauna. Rahmatu kuwa da gwaggo sunsha gata da tarairaya gata iri iri. A daren Rahmatu ta haifi 'yarta mace amma 'yar bata zo da rai ba. Tun dawowar su daga k'auye aka shiga shirye shiryen bikin *Hibbah* da *Faheem* sosau su momy suka shiga kintsa Hibbah da sabulai maya mayai na gyaran jiki Dana sa laushin fata ga turaruka kamar Ana b'arin turare a jikinta ko hucewa tayi ta kusa da kai sai k'amshin ya jima bai baje ba, ga wasu had'i da ake bata kamar me har su Saudat ma sha suke yi don suma an tsaida maganar aurensu, Saudat kuwa sun daidaita da Usman d'an Abba ita kuwa Safiyya wani saurayinta ne Yusif. Faheem kuwa duk ya k'osa a kawo masa matarsa baya iya jure rashin ganinta a kusa dashi shiyasa kullum yana hanyar zuwa gidansu don ganin abar k'aunarsa. Momy da mamy har gwaggo sun gane take takensa shiyasa suka kuma d'aura d'amarar gyara Hibbah. Su Aunty ma sun fito da anko kala biyar wai bikin 'yar gata za'a yiwa Hibbah, mamy ce ta had'o mata lefe na gani na fad'a........ *#Juma'at mufeedah to you all my fans😍❤🤝* *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page 5⃣4⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* ```wattpad@mamyn_najmah2222``` *wannan page d'in d'ungurin gum na sadaukar dashi gareku masoyan littafin RAYUWA ina son Ku ina jinku a zuciya ta, Kuyi hakuri bakwa jina kwana biyu wallahi bana samun time ne.* Daddy ya baiwa baba duk wata dukiyarsa da take wajensa da da farko baba yak'i karb'a yace ya barsu ya cigaba da juyawa amma daddy yace ina kawai ya amsa, haka badon baba yaso ba ya amsa. Part d'in da Faheem ya zauna nan daddy ya mayar na baba. Kwanansu uku da dawowa daga k'auye, suna zaune kamar kullum don tunda suka dawo kullum da yamma zasu zauna a parlor ko a garden suyi ta hira, mai gadi ne ya shigo da hanzari yayi musu sallama suka amsa yace "Alhaji dama wani ne ya bada sako a kawo maka" ya mikawa daddy takardar dake hannunsa yace "kuma yace don Allah idan yanzu kana gida idan ka karanta sakon dake ciki ka hanzarta zuwa asibitin" daddy ya kad'a kai "to shikenan zaka iya tafiya" mai gadin ya juya ya koma bakin aikinsa. Daddy yana rike da takarda yana zulumin abinda zai gani a cikinta yana tunanin to daga k'ark'ashinwa wannan takardar tazo sannan waye a asibiti? Su Abba da sauran mutanen dake zaune kuwa kowa da abinda ke cikin ransa tunda sukaji an ambaci asibiti. Da k'yar daddy ya iya bud'e takardar ya karanta sak'on da ya gani ya d'aga masa hankali ya d'ago ya dubi su baba da duk shi suke kallo yana furta Kalmar Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un yace "Ku tashi mu tafi asibitin murtala" a gigice suke kallonsa waye ba lafiya baba yace "waye bashi da lafiya" Daddy da har ya kai kofar fita yace "kuyi hakuri ba lokacin bayani Ku tawo kawai mu tafi" haka su momy suka d'augo hijjabansu suka fito, motoci suka shiga kai tsaye asibitin murtala Muhammad suka nufa, bayan sun gama parking suka nufi cikin asibitin d'akin da aka yiwa Daddy kwatance suka nufa Daddy ne yake jagorantarsu har suka isa d'akin. Da sallama suka shiga yarinyar da take jinyar tashi ta amsa masa, Wanda baba ya gani yana jinyar ne ya sashi karasawa kusa dashi cikin hanzari "Ibrahim Ibrahim me ya sameka garin ya wannan Abu ya faru?" Baba duk ya rude sai tambayoyi yake masa. Su momy kuwa sai sannu suke masa, Alhaji Ibrahim dake kwance a gadon na asibiti ya rame yayi bak'i kasusuwansa duk sun bayyana kamar mai cutar Ebola ga hannunsa d'aya babu k'afa ma babu guda d'aya bakinsa kuma ya karkace ya rik'o hannun baba "Mukhtar ka yafe min kaji k'aina nayi nadamar yadda na rusa amincin mu ta hanyar cin amanarka, wallahi nayi dana sanin san duniya irin nawa" ya ja numfashi da k'yar baba ya kuma k'amk'ame hannun nasa "Mukhtar kaga k'arshena ko? Kaga k'arshen zab'ar duniya akan lahira da nayi ko? Kaga illar cin amana ko? Sannan ga uwa uba shirka da nayi da ubangijinmu, Mukhtar duk wani hali da ka shiga a baya wallahi nine sila ni nayi maka sammun da aka zautar maka da tunani ni nasa a lalata maka k'wak'walwa, kaga k'arshena ko Mukhtar kowa ya gujeni hatta 'ya'ya sun gujeni matata ma haka wannan yarinyar nurse ce ita kad'ai ce take jinyata don Allah ka yafe min wallahi nayi nadama....." Ya karasa maganar hawaye na bin fuskarsa sannan ya soma wani irin tari kamar zai amayar da hanjinsa. Allah sarki baba shi duk tausayinsa yake ji sashen zuciyarsa kuwa na mamaki irin wannan san zuciya na mutane ashe har Ibrahim zai iya yi masa wannan rashin imanin? Da sauri ya girgiza kai nima ina da lefi da ina bawa kaina kariya da Neman tsari wajen ubagiji da bazaiyi tasiri a kaina ba, baba ya kuma rik'e hannun Ibrahim yace "na yafe maka Ibrahim Allah ya yafe mana" murmushin k'arfin halin Ibrahim d'in yayi bayan ya tsagaita tarin ya dubi su Abba dasu momy da su Hibbah masu arhar hawaye har amfara ambaliyarsa yace "don Allah Ku yafe min" daddy ya dube shi "ba komai ni na yafe maka Ibrahim Allah yana son masu yafiya" suma su momy su Aunty duk sukace sun yafe masa. Sai kuma ya dinga wani tari sosai ba k'ak'k'autawa har numfashinsa na d'aukewa, yarinyar dake jinyarsa ta fita da sauri don kira doctor shi kuwa baba dake kusa dashi sai maimaita masa Kalmar shahada yake amma ina ya kasa kamawa a haka har numfashinsa ya d'auke gaba d'aya (to dama Wanda yayi shirka ina zai cika da Kalmar shahada). Dr ya shigo tare da budurwar ya shiga duba shi lokaci daya ya gano cewar ya rasu ya lullub'a masa zanin dake jikinsa ya dubi su Daddy "Alhaji sai dai hakuri Allah yayi masa cikawa" su baba dama tuni suka gano hakan sai suka bishi da addu'ar samun rahma wajen ubangiji don ba'a shiga tsakanin Bawa da ubangijinsa. Haka suka d'auko gawar suka mata sutura aka kaishi gidansa na har abada, sannan aka nemi iyalinsa aka fad'a musu. An kashe kudi a bikin Hibbah da Faheem don ko wajen events d'in kawai da aka gabatar kawai kud'insa ya isa ballantana azo ga irin dukiyar da su Abba suka kashe mata a kayan d'akinta dana kitchen, gaskiya su Daddy sun sunyi rawar gani don kuwa Hibbah ta zama 'yar gata ta ko wane b'angare. Wani tank'ameman gida aka shigo da Hibbah ko a iya get d'in gidan kawai kasan gidan ya tsaro mamy data rik'o hannun Hibbah na dama yayin da aunty ta rik'o d'ayan hannun nata gaba d'aya Hibbah a rumgume take a jikinsu fuskarta a lullub'e tana ta kuka k'asa k'asa, mamy ta rad'a mata "my Hibbah nemi tsarin Allah ki yi add'u kafin ki shigo ki shigo da k'afar dama kiyiwa aurenku addu'a da sa masa albarkar ubangiji" duk da kuka take hakan bai hanata yin addu'a ba ta kuma shiga da k'afar dama. Haka su mamy suka shigo da ita cikin k'aton gidan nata dake ta zuba uban k'amshi mai dad'i direct bedroom d'inta suka huce da ita inda suka sauketa a kan gadonta, nan mamy ta kuma yi mata nasiha sosai a k'arshe ta rufe da kuma koya mata wasu dabarun zama da miji kafin kuma su tafi. Haka 'yankai Amarya suka tafi suna ta zuba santin gidan, aka bar Hibbah ita kad'ai sai Saudat Safiyya da fauzy da aka bar mata suma suna gama gyara inda 'yan kawo Amarya suka b'ata suka ce zasu tafi Saudat tace "Aunty Hibbah mu dai mun tafi kar ango yazo ya bubbugemu, ni dai da safe zanzo gashi" fauzy tace "lallai kam ni dai kazar za'a ajiye min" Safiyya tace "auntyna mudai mun tafi" suka fita suna dariya adamu driver ya kaisu gida. Haka suka bar Hibbah ita kad'ai duk tsoro ya cikata ga kuma kunya tana tunanin da wane ido zata kalli Faheem a matsayin mijinta? Tunaninta ne ya katse a lokacin da taji k'arar bud'e k'ofa da sauri ta kuma yin k'asa da kanta zuciyarta na harbawa da sauri sauri. Faheem ne ya shigo shi da Haisam dake rik'e da leda a hannunsa shima da k'yar Faheem ya yarda ya rakoshi wai ai ba auren fari bane kuma Dan d'an uwansa ne bashi da yarda zaiyi. Suka k'araso da sallama a zuciyarta ta amsa, suka k'araso suka zauna Haisam ya ajiye ledar dake hannunsa yana cewa "Amaryarmu k'anwarmu sannu ya gajiyar biki" Hibbah tayi shiru bata ce komai ba, Haisam yace "too k'anwata yau kuma rowar magana ake min? Ko da yake ba laifinki bane Amarya ce ke" ya fad'a yana murmushi "to tunda na rako miki angonki bara na tafi" sai kuma yau d'an fara yi musu nasiha kafin ya mik'e Faheem ya raka shi har bakin get sannan ya dawo. A inda ya barta anan ya dawo ya sameta, a hankali ya hayo kan gadon ya yaye mahafin dake lullub'e a fuskarta tare da shafo fuskarta ruwa yaji a hannunsa da sauri ya juyota suna fuskantar juna ya shiga goge mata hawayen ya d'anyi k'asa da murya "haba my hrt desire kuka kike yi gidana fa aka kawoki gidan yayanki kuma mijinki mai k'aunarki to mene naki na kuka kuma Uhumm?" Ita dai Hibbah bata ce komai ba tayi k'asa da kanta saboda tsananin kunyar Faheem. Faheem yayi murmushi ganin yadda ta wani yi k'asa da kai "nifa gaskiya wannan kunyar yau a ajiyeta a gefe don baza ta k'ware ni ba" ina ai Hibbah ji tayi kamar k'asa ta tsage ta shige ciki. Hannunsa ya d'ora a kan cikinta yana d'an dannawa "my hrt desire hidima ta hanaki cin abinci koh? Gashinan cikin ya kuma matsewa taso muje na baki" ai hankali kanta a k'asa tace "naci abinci na k'oshi" "a'a banyarda ba tashi maxa muje muyi sallah mu godewa Allah sai na baki wannan d'an cikin ne yaci abinci" ya fad'a yana jan hannunta suka sauko daga kani gadon ya zaunar da ita a kan carpet, ya fita kitchen ya d'augo plate da cup ya ajiye lokacin ita har tamayo alwala, shima ya shiga yayo kafin ya fito ta d'auko hijab d'inta yana zuwa yaja su sallah, nan suka gabatar da sallar bayan sun idar ya shiga kwararo addu'o'i kafin ya dafa kanta yayi mata addu'a, bayan ya gama ya shiga yi mata tambayoyi a take duk ta bashi amsoshinsa wanda dama yasan za'a rina. Ya janyo place d'in da cup ya juye kazar a plate d'in ya tsiyaya mata madarar a cup sannan ya zauna tare da janyota jikinsa ya gutsuro ya kaishi dai dai bakinta a hankali ta bud'e bakin cike da kunya ta amsa tana taunawa kamar bata so. Ya d'auko madara yasa mata a baki ta kurb'i kad'an ta kawar da kai, ya kuma gutsurowa zai sa mata ta kawar da kai "daddy na koshi fa" ya d'an had'a rai "wannan cikin naki yana bukatar abinci kuma kina cemin wani kin k'oshi ki amsa ko kuma na miki d'ura" haka badon taso ba ta bud'e bakin ya saka Mata, haka yayi ta bata har sai da ya tabbatar ta k'oshi sannan ya daina bata shi kuma ya shiga ci. Shima saida ya k'oshi sannan ya d'auke gayan daga wajen ya gyara, ya dubeta gyangyad'i ma ita take yi ya d'auketa cak ya d'ora bisa gado. Firgit ta tashi ya dubeta yana murmushi "bacci ko my hrt desire?" Ta d'aga masa kai yace "to ina zuwa" ya mik'e ya fita. Ta ganin ya fita itama ta tashi ta cire kayan dake jikinta ta d'aura towel ta Shiga wanka da alwala. Ta fito ta mulke jikinta da wani mai da Aunty ta bata mai tsananin k'amshi ga kuma turarukan da Aunty da mamy suka ce idan zata kwanta ta shafa sai kuma Wanda gwaggo ta bata, haka ta d'auko duk tayi amfani dasu sai k'amshin ya had'e ya bada daddad'an k'amshi. Ta d'auko wata rigar baccinta iyaka gwaiwa samanta net ne daga wajen k'irjinta sai kuma k'asan yadi mai taushi da silb'ine hannun kuwa na bra ne ta saka sannan ta kashe fiyila ta koma kan gadon ta karanto suratul mulk da iklas, falaq, nas sai ayatul kursiyyu ta tofa a tafin hannunta ta shafe jikinta sannan ta kwanta a b'arin hannunta na dama ta karanta بسم كاللهم اموت و احيا sannan ta kwanta zuciyarta cike da tsoro. Ta Fara bacci kenan taji mutum a kusa da ita yana shafa jikinta a hankali tayi firgit ta tashi ta juyo Faheem ta gani a cikin bargon shi ko a jikinsa yana cigaba da shafata, ta dubeshi a marairaice "Daddy bacci nake ji" wannan daddy da take kiransa dashi yana b'ata masa rai a zuciyarsa yace yau zan bambance miki tsakaninki da Nawaz don ya kirani Daddy kema saiki ki fad'amin hka. A fili kuwa yace "kiyi baccinki my hrt desire ni dai zan samawa Nawaz k'annene a wannan Daren mai albarka" sai kuma ya shiga aikata mata sak'onni wanda lokaci d'aya Faheem ya fara fita hayyacinsa kamar ba mai mata ba😏. To Faheem Hibbah asuba ta gari ni nayi nan🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page5⃣5⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* ```wattpad@mamyn_najmah2222``` 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 Hibbah yau dai an zama cikakkiyar mace an shigo sahun manya don Faheem bai gyaleta ba sai da ya mayar da ita cikakkiyar mace. Sai bayan komai ya lafa Faheem ya janyo Hibbah ya rumgume ta yana ta samata albarka gami da lallashinta, ita kuwa sai kuka take saboda shiga bakon abu da tayi ga kuma kunyar Faheem data rufeta ta rasa inda zata sa kanta. Haka dai Faheem yayi ta rarrashinta har ya samu tayi bacci, jinshi yake kamar wannan ne aurensa na farko don Hibbah ta dabance sam ni'imarta ta bambanta data Kausar jinshi yayi yafi samun gamsuwa da ita fiye da Kausar. Haka yayi ta tunanin abinda ya kasance a tsakaninsu daga baya ya mik'e ya shiga toilet yayi wanka sannan ya d'auro alwala yazo ya dinga nafila yana godiya ga Allah. Satin Hibbah biyu a gidan Faheem har ta ware duk wannan kunyar tashi ta sauketa ta tsaya tana kula da mijinta yadda ya kamata. Shi kuwa Faheem kamar ba shiba yadda yake yiwa Hibbah wani lokacin har kunya take ji, daidai misali yana k'ok'ari wajen kwatanta adalci a tsakaninsu. Faheem ya had'e Kausar da Hibbah a gida d'aya sakamakon Daddy ya kirashi yace ya had'e matansa waje d'aya don su kuma shak'uwa a matsayinsu na *jini d'aya*. Had'e sun da yayi sai suka kuma shak'uwa sosai Hibbah tama fi son haka saboda kullum tana tare da Nawaz d'inta, ita ma Kausar taji dad'i amma wani lokacin sai ta shiga d'aki tayi ta kuka tana da ta sanin rashin kula da mijinta da tayi aikinta kuwa tuni ta rubuta takardar ajiye aiki. *3 month later* Hibbah na gaban dressing mirror tana k'ok'arin sanya wani pink ashoke da aka nad'a Mata shi ta gama kwalliya sanye take cikin wani material mai shegen kyau gashi yayi mata matuk'ar kyau. Faheem dake jikin k'ofar d'akin ya zuba mata idanu yana kuma jin k'aunarta na ratsa duk ilahirin jikinsa ya k'araso gaban mirror ya karb'i ashoken ya saka mata da kanshi sannan ya juyo da ita "Masha Allah my hrt desire kinyi kyau sosai Anya kuwa zan barki kije wajen dinner d'in nan kuwa" Hibbah ta marairaice fuska "my boo kar muyi haka dakai Dan Allah ka barni naje, bikin Saudat da Safiyya ace banje dinner ba" ya girgixa kai "a'a my hrt desire kiyi zamanki kawai zansa a d'auko miki duk abinda aka gabatar a wajen" Faheem baiyi aune ba sai ganin hawaye yayi a fuskar Hibbah cikin kuka tace "Dan Allah my boo ni zan iya ma wanke kwalliyar Allah, kuma fa kace zaka dinga kaini kullum wajen bikin tunda kace bazanje na kwana ba" da sauri ya janyota jikinsa yana rarrashinta "ai zaki b'ata kwalliyar wasa nake miki" ya shafi cikinta "anya yarinyar nan ba ajiyata a jikinki kuwa naga fa sai wani haske kike yi kuma na Lura yanzu kina yawan ka sala, kwama biyun nan dana kusanceki fa naji kin canza" Hibbah ta rufe ido cike da kunya don itama ta lura da hakan kuma watanta biyu kenan bata ga al'adarta ba ga yawan tashin zuciya ga kasala amma sai ta dangana hakan da kawai janjin yanayi ne wai don da tana budurwa ne yanzu kuma tana da miji. Ta karyar da kai "my boo ni bani da komai fa" "a'a gobe zamuje Dr ya duba min ke don ni ban yarda ba akwai ciki a jikinki" ya fad'a yana shafa cikinta. Hibbah ta ja hannunsa "mu tafi lokaci na k'urewa fa" Haka suka wuce wajen dinner d'in su biyu don Kausar tana can ita da Nawaz, wajen ya k'ayato wuta a wajen kamar rana sai sautin kid'a dake tashi a wajen. Faheem ya samu waje yayi parking ya kai hannunsa kan cikinta yana dubanta yace "ni zan koma idan anjima zan dawo na d'auke ki, ki kularmin da ajiyata" ta kawar da kanta gefe "babban Yaya baza ka zauna a wajen ba" "a'a ai Ku kun wakilce ni" Hibbah ta bud'e k'ofar zata fita "to saina kazo" ya janyota "a hakan zaki fita baki bani sak'ona ba" tayi murmushi tare da yi masa Kiss a kan leb'ensa sannan sukayi sallama. Ta k'arasa cikin wajen lokacin ma amaren basu zo ba, wajen su Aunty ta nufa suka shiga gaggaisawa sannan suka zauna ana ta hira Aunty itama da cikinta. Sai can mc yake sanarwar amare da angwayensu zasu shigo amare da angwaye sunyi kyau matuk'a sun kuma dace da juna, Hibbah da aunty suka tashi suna yiwa amare lik'i har suka k'araso wajen da aka tanadar dominsu suka zauna aka shiga hotona kafin kuma a shiga kad'e kad'e. Aka buk'aci angwaye da amare su fito filin rawa bayan sun fito Hibbah ta tashi ta shiga yi musu lik'i tana d'an rausayawa a hankali, hakan da takeyi sai ya janyo hankulan wasu samari abokanan ango su uku, d'aya a cikinsu yace "Salis kunga wataj had'addiyar baby da idanuna suka hango?" Dayan yace "ai ni tun shigowarta na ganta yanzu ma zanje na sameta" dayan da baice komai ba yace "ai ku naku wasa ba'a sanya a irin wannan bash Ku tashi muje" suka mik'e suka nufi filin rawar suka shiga yiwa Hibbah lik'i. Faheem dake tsaye yana kallonsu ranshi a mugun b'ace ya nufi cikin gilin rawar, Hibbah tana hangoshi gabanta ya shiga fad'uwa don ganin yanayinsa gaba d'aya ya sauya. Yana zuwa ya d'auketa tamkar jaririya yayi waje da ita, waje kuwa ya d'auki ihu ana ta tafi wai babban yaya yana koyawa amare yadda za suyi soyayya, Kausar kuwa wani Abu ne ya tsaya mata a rai tama kasa cewa komai a hankali hawaye ya shiga mata sintiri. Mota Faheem ya bud'e yasata sannan ya kunna motar suka nufi gida bai ce Mata komai ba har suka isa gida itama bata yi magana ba don a tsorace take. Yana gama parking ya bud'e ya fita tare da banko k'ofar, da sauri itama ta fito ta biyo bayansa a parlor ta iskashi yana zaune ya d'aga kansa sama. Ta k'araso ta tsugunna a gabansa "don Allah my boo kayi hakuri wallahi ni bansansu ba banma san suna min liki ba" ya dubeta yama kasa magana kawai ya kawar da kansa gefe Hibbah ta kuma matsoshi jikinsu na gogar juna tace "my boo kayi hakuri Dan Allah......" Sai kuma tasa kuka hawayenta na d'iga a k'afafunsa. Ya d'ago da sauri ya d'orata kan cinyarsa yana goge hawayen fuskarta "my hrt desire kinsan ina da kishi akan iyalina amma kika shiga filin rawa a gaban gartin maza kina rawa har wasu suna hiran zasu sameki ku daidaita" ta shafo wuyansa ta baya tare da had'a bakinsu don tasan haka ne kawai zai sanyaya masa zuciya hot kiss take masa cikin k'warewa sun jima a haka don har Faheem ya fara fita hayyacinsa, sannan ta zame bakinta daga nasa "kayi hakuri Dan......" Bata k'arasa ba ya d'auketa ya nufi d'aki da ita don ya kasa jurewa. *6 years later* "Asra baza kizo mu tafi ba zamu tafi mu barki fa" Nawaz dake tsaye a bakin k'ofar d'akinsu Asra d'in, yanzu yana da shekara 12 kenan sanye yake da wata shadda anyi masa d'inki irin na samari sai zuba k'amshi yake. Wadda ya Kira da Asra d'in ta fito yarinyace da bazata wuce shekaru biyar ba daka ganta kaga Hibbah don tsananin kamannin da suke da juna sanye take cikin wata riga mai hannun vest da wando jeans kanta anyi mata wata kalba mai shegen kyau an zubo mata dashi ta k'araso kusa da Nawaz d'in, cikin 'yar muryarta irinta Hibbah tace "kayi hakuri Ya Nawaz naje d'aukowa Uncle sweet din da Daddy ya siyo min jiya ne saboda bani da abinda zan bashi idan ya dawo" ta k'arashe maganar tana marairaicewa kamar zatayi kuka. Nawaz ya janyo hannunta "to sarkin 'yan kuka tawo mu tafi su momy suna jiranmu a mota" suka k'araso Asra ta nufi gaban mota don ita take zama anan don ko wani ya shiga sai ya fito bazai zauna ba. Faheem ya dube su "Nawaz me kuka zauna yi ne a ciki?" "Daddy Asra ce ta tsayar damu" Faheem ya kalli Asra "me kika zauna yi a ciki ne Mamana? (Sunan momy ne da ita Zainab)" ta d'an had'a rai "Daddy ni ka daina cemin Mamana kace min Asra yafi dad'i" yayi murmushi don yasan bata son sunan yace "to Asra baby" tayi dariya "yeeh daddy sunan yayi dad'i" ta dubi Hibbah "Aunty mama bani Asrar na rik'e shi dan Allah" Nawaz yace "a'a salon kawai ki muntsine shi anki a baki d'in" Asra ta juyo ta harareshi "to ina ruwanka Daddy ka Ganshi ko?" Faheem ya kalli Nawaz "a'a Nawaz babu ruwanka, ke kuma Asra bana hanaki yi masa rashin kunya ba oya tell him sorry" ya fad'a yana kallon Asra data turo baki tace "sorry" faheem ya kalleta haka ake bada hakuri?" Ta juyo ta kalli Nawaz tare da had'e hannayenta waje guda "am so sorry I won't repeat it" Faheem ya kunna motar suka nufi gidan Daddy, yana gama parking Asra ta bud'e k'ofar ta fito da gudu ta nufi cikin gidan tana kiran uncle Faheem ya girgiza kai su Hibbah suka fito Kausar tana rik'e da Asrar suka shiga cikin gidan. Tana shiga ta d'ane jikin Faruq, ya d'agata sama yana "oyoyo my Asra ina Nawaz?" Tace "yana mota yanzu zasu shigo dasu Daddy" ya sauke ta ta mik'a masa sweet d'in dake hannunta "happy birthday uncle" "Tnx my Asra wannan ne gift d'in nawa kenan to na gode" tayi murmushi "mention not uncle you deserve more" ta fad'a tana hawa saman momy tana kiran k'walawa Saida 'yar wajen Aunty don sa'anni ne. Su faheem suka shigo suka gaisa Faruq ya karb'i Asrar yana masa wasa sai k'yak'yata dariya yake Faruq ya kasa duban Hibbah don har yanzu kunyarta yake ji duk da tun wancan satin daya dawo ya nemi yafiyarsa kuma ta yafe masa amma har yanzu yana daya sanin abinda ya aikata a baya. Bayan azahar duk ilahirin family suna zaune a parlor Ana ta hira cikin rah da k'aunar juna, Daddy yayi gyaran murya "to abinda yasa na tara mu anan don na sanar muku da abin farin cikin daya samemu bayan godiya ga Allah daya shirya mana Faruq har yanzu yake Neman aure kuma insha Allah ranar juma'a za'a d'aura auren" gaba d'ayansu duk mamaki da farin ciki ya cika su har suna had'a baki wajen fad'in "wacece amaryar daddy?" Daddy yayi murmushi "ai tun zuwansa suka daidaita da Rahma" Hibbah dake kusa da Rahmatu tace "amaryarmu shine baki fada min ba" Haka dai sukayi ta hirar yadda bikin zai kasance. Ranar juma'a da yamma aka d'aura auren Faruq da Rahma Wanda dubun nan mutane suka halarci d'aurin auren musamman Faruq dayake da masoya kasancewarsa d'an k'wallo ada. To Rahmatu dai ta tare a gidan mijinta Faruq bayan gyara da tasha a wajen su gwaggo, sunci amarcinsu sun more. Shekararsu d'aya da aure Rahma ta sambad'o yaranta 'yan biyu duk maza masu Kama da Faruq sak ansha shagalin suna aka sawa yara sunan baba da Abba wato Mukhtar da Umar, ana kiran Mukhtar da Hammad shi kuma Umar Hammam. Sati d'aya da suna Kausar ta haifo itama 'yarta aka sa Mata sunan mamy wato Rukayya suke ce mata Hooriya. Haka *RAYUWA* ta cigaba da tafiyarwa wannan family cikin farin ciki da kaunar juna. *Fahibbateam💘* *SUBHANAKALLAHUMMA WABI HAMDIK ASHHADU ALLA ILAHA ILLALLAH ASTAGFIRUKA WA A TUBU ILAIH, ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH* *NA GODEWA ALLAH DA YA BANI IKON KALLAMA WANNAN LITTAFIN* *GODIYA TA MUSAMMAN GAREKI AUNTYNA AYSHA ALIYU GARKUWA* ```YABON GWANI YA ZAMA DOLE AUNTY AYSHA ALI GARKUA ALLAH YA KARO BASIRA DA HAZAKA YA KAREKI DAGA MAK'IYANKI.``` *GODIYA GAREKU K'AWAYEN ARZIK'I BAZAN* _EYSHART NA GODE DA K'AUNARKI_ _Sweetie Safiyya Dandada_ _uktee Lessy_ _Teemah nuhu_ _bestie Muneerah_ _Merry jay_ *BAN MANTA DA KUBA* Kuna bani k'warin gwaiwa _Hassana danlaravawa_ _kadeey pinky_ _ummu Fatima_ _Muneera_ _feenerh baby_ *Jinjina gareku* *Masoya novel group* *Mamyn Najmah fans* *Aysha Ali Garkuwa fans* *Tabital pulaaku* *groups din Facebook, da duk wani group da nake ciki ina mik'a godiyata a gareku na gode sosai Allah ya bar k'auna ana mugun tare🤝😍* ```Ina yiwa masoyana albishir da littafaina masu zuwa, amma saidai ku zab'i guda d'aya da zan fara yi muku a cikin guda biyu da zan bada zab'i kuma dukkanninsu true life story ne``` *WATAN UWAR MIJI* *DA* *WANI GIDA* _sai Ku zab'i guda d'aya a ciki_ *labarin WATA UWAR MIJI labari ne daya kunshi yadda wata uwar miji take gallazawa surikarta har take kishi da ita, Ku dak biyoni kuji abinda ke cikin wannan labari* *labarin WAMI GIDA labari ne daya kunshi wasu 'Ya'ya da suke yiwa mahaifinsu rashin mutunci da rashin kunya saboda bashi da kudi kuma sun samu koyarwarne daga wajen mahaifiyarsu, gefe guda kuma ga wata d'iyace da ta lalace a sanadiyyar rashin aurar da ita da kakarta ta Hana ayi* _Ku dai Ku biyoni a cikin wad'annan littattafai, kafin nan kuma sainaga zab'in Ku Wanda zab'insa yafi yawa shi za'ayi._ *sai na ji Ku BISSALAM* *by* *Mamyn Najmah* Copied By YAYA HAYAT (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion Cool novel, makeup and kitchen1⃣ Cool novel, makeup and kitchen2⃣ AND Cool novel, makeup and kitchen3⃣) WHATSAPP NO:+2349030159301