======🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ Tsit wajen ya yi babu wanda ya iya motsawa almost 3 mins for silent. A hankali Smart ya ja doguwar numfashi tare da saukewa, sannan ya juyo da kallonsa a kan iyayen nasa da suka kasa motsawa daga in da suke, yau ga abin al'ajabi. Muryar Smart na ɗan sarkewa ya ce. "Mommah dama kina da wani yaro ne bayan ni?"..... Sai a lokacin ta ja dogon numfashi alamar ta dawo cikin hayyacinta ita ma, tsayar da kallonta a kansa ta yi, tamkar mai raɗa ta ce. "Kai nike shirin yiwa wannan tambaya, waye shi? Daga ina ka ɗauko shi? Meyasa yake kama da kai?". Tamkar ba ita ta yi maganar ba, da kyar ta iya motsa bakinta. "Momma i don't know him, kawai ganinsa na yi ya shigo bedroom ɗina zai ɗauki ƴar tsana na dakatar da shi"........... A ɗan ruɗe Mommah ta ce. "Omerish ya za'ayi kace baka san shi ba? A ɗakinka fa muka gansa, please before zuciyata ta shiga wani hali tell me who's he?". King dai tamkar ruwa ya cinyesa, saboda a duniya babu wani sarki da ake tsoro biyun Black Tiger, ya san labarinsa sosai, amma bai taɓa sanin face ɗinsa ba, yana jin labarin King Lucian wanda akewa lakabi da Black Tiger, so kun san baban Black Tiger shi ma da Black Tiger ake kiransa a da, to shi King Zuhair labarin baban yake ji, bai san Black Tiger can ya mutu yanzu ɗansa bane. Ace sarkin da ake mutuwar tsoro, wanda bashi da tausayi bashi da imani, ga bala'in karfin sojojin yaki wai ace yana kama da ɗansa Smart, abin ya yi matuƙar jijjiga shi!. Zubawa face ɗin Black Tiger idanu Mommah ta yi, a cikin ranta take ji wlh wannan ɗanta ne, jininta ne, sai dai tambayar da take yi wa kanta a nan shi ne ta ya aka yi ya zama ɗanta? Tasan dai Smart shi ne ɗanta na farko! Kuma wannan ba zai yiwu ace kanin Smart bane, sai dai su zo mate, kenan da shi da Smart identical twins ne tamkar Omaid and Obaid?. Lokaci guda ta ji kanta ya sara mata, saboda yadda tinaninta da kaifin ƙwaƙwalwarta ya bata wannan amsa, tabbas wannan tinani nata shi ne gaskiya. Dafe cikinta saitin mararta ta yi, a hankali ta ɗan yi taku step biyu baya, murya can ƙasan makoshinta kamar wacce take a cikin maye ta ce. "Tabbas ɗana ne, idan har na canka dai'dai twin brother ɗinka ne". Dawo da kallonsu King and Smart suka yi a kanta. "Mommah me kike faɗe ne haka? Do you mean wannan ɗan uwana ne?". Ya yi maganar tare da yunƙurawa zai miƙe. "Tabbas abin da nike nufi kenan, wannan ɗan uwanka ne Omerish, dama ni nasan ba yaro ɗaya na haifa ba, dole akwai abin da ya saɓa, daddyn Zunaira idan baka manta ba a lokacin da nike da cikin Omerish ko an mun scanning ba'a ganin cikin, anyi gwajin duniya ba'a gansa ba, da farko ma cewa aka yi babu cikin, daga baya aka ce ruwa ne kawai ya cika mun cikina shiyasa ya yi girma, har Dubai mun je amma ba'a ga Omerish a cikin cikina ba, kuma da aka zo za'a mun aiki a cire ruwan da yake a cikin cikin nawa sai suka ce basu ga ruwan ba kuma! Ka tina bamu taɓa ganin abin da yake a cikina ba har muka haifesa?". Ta jefawa King tambayar tana kallonsa, idanunta sun cika tab da kwallah. Jinjina kai King ya yi kallonsa dai a kan Black Tiger, saboda al'ajabi ya hanasa dai'na kallonsa. Sai a yanzu ya tuna tabbas cikin Smart ya zo da gargada da babban matsala mai tafe da abubuwan al'ajabi, babu ma wanda ya zaci Mommah zata kai labari, sun sha fama wanda kuma har suka haifi Smart bata huta ba, tabbas akwai wata a ƙasa, sun yi scanning ya fi sau a kirga, amma ba'a iya ganin ainahin abin da yake a cikinta, and sama da sau biyar tana bleeding da cikin Smart, bayan haka ya fi sau a kirga cikin yana yunƙurin fita, amma ALLAH ya hukunta sai ya zo duniya, dik yadda aka yi Black Tiger ko Smart akwai wanda yake da wata nasaba da baiwa, kuma hakan na daga cikin dalilin da yasa ALLAH ya taimaki Mommah cikin bai fita ba, tabbas akwai gagarumin matsala!!. ME KUKE TINANIN ZAI IYA ZAMA WANNAN GAGARUMIN MATSALAR?. Ganin abin ya zama wani case daban yasa Smart ya ji kwarin gwiwar miƙewa tsaye da kyau yana fuskantar iyayen nasa, abin mamaki abin al'ajabi, wai a haka dan ma Smart bai ji ainahin tarihin azabar da aka sha kafin ya zo duniya ba, Mommah ta auna arziki gaskiya!. A yayin da hakan ke faruwa sojojin yakin Black Tiger suna can suna gyara barnar da suka yi tamkar yadda Smart ya basu umarni, cikin ƙanƙanin lokaci suka kakkawar da manya-manyan abubuwa daga hanya, abubuwa na ɓarnar da suka yi, suka hau gyare komai!. Luluƙawa duniyar tinani King ya yi, kenan idan har Mommah twins ta haifa ya aka yi waɗan da suka karɓi haihuwarta a lokacin basu sani ba? Maman Chuchu ita ce ta tsaya wajen jagorantar waɗan da suka karɓi haihuwarta a lokacin, ita take a tare da ita, to how comes bata san twin's aka haifa ba?. A lokacin Mummyn Chuchu bata da lafiya, tana fama da laulayin ciki, so bata je wajen ba, tabbas akwai abin da ya saɓa, basu da hujja, amma tabbas yanzu a kan Mamah ya ɗaura zarginsa!. "Daddyn Zunaira ka yi magana mana, ka faɗa mun cewa wannan ɗana ne! Dan bani da kanwa bani da ƴar uwa mace balle in ce ko ɗanta ne ya yi kama da Smart, Yah Muhammad bai taɓa haihuwa ba, su Yah Omar (Abu Abdussalam) dik narigasu haihuwa, na rigasu yin aure bare in ce ko ɗansu ne!". Cewar Mommah da gabaɗaya a rikice take!. Matsawa King ya yi ya ɗan rungumota, cikin mamaki da tashin hankali ya ce. "Tabbas Rahilarh wannan ɗanki ne, jini ba wasa ba, ni da nike matsayin uba na ji a jikina ɗana ne bare ke da kike matsayin uwa, tabbas twin brother ɗin Omerish ne". Wani irin ajiyar zuciya da Mommah ta sauke sai da hawayen da suka cika idanunta suka gangaro saman kumatunta. Sake King ta yi ta fara takawa a hankali tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki ta nufi in da Black Tiger yake kwance. Uhmm ni ko na ce lallai ba shakka duniyar shaiɗanu sun saki Black Tiger, da wlh yanzu wani labari ake yi ba wannan ba, ace Smart ya daki Black Tiger har ya suma duniyar shaiɗanu basu ɗauki mataki nan take ba! Ai kuma kun san yanzu zaki ya yi lafiya fa!. A daidai saitin fuskar Black Tiger ta tsugunna, hannunta na kerma ta kai ta shafi lallusan kumatunsa. Lokaci guda ta lumshe idanunta tare da dafa saitin kirjinta da ɗayan hannunta, a hankali ta ce. "He's my son, tabbas jinina ne, ɗana ne wlh, har cikin rai'na na ji hakan". UHM UWA KENAN!. Matsawa King ya yi kusa da ita, a dab ita ya durkushe gwiwowinsa shi ma, shoulders ɗinta ya riko, cike da al'ajabi da tunane-tunane a ransa ya ce. "For sure he's our son!"....... Smart dai bin iyayen nasa da kallo kawai yake yi, lokaci guda tsananin kaunar Black Tiger ya narku a zuciyarsa, a hankali ya ce. "No wonder sau da dama nakan ji tamkar ana amfani da jikina, ashe we're identical twins wanda yasa nike jin tamkar ba ni kaɗai bane!". A hankali kyawawan ƴatsun hannun Black Tiger suka fara motsawa. ALLAHU AKBAR!!. Ya ji hannun mahaifiyarsa a jikinsa, har sai da zara-zaran eyelashes ɗinsa suka ɗan motsa, sanyin hannun uwa yasa zuciyarsa ta koma bugawa normal yadda yake wanda hakan ya yi sanadiyar farfaɗowarsa. Slowly ya waro dara-daran eyes ɗinsa da suke jajir tamkar wuta wanda sai da ya razana Mommah yasa ta yi gaggawar ɗauke hannunta daga saman face ɗinsa. Kafin su ankara sai ganinsa suka yi a tsaye a kan kafafunsa. A tare suka yi gagawar ɗaga kawunansu suka kai kallonsu a kansa. Dik karfin hali da dakiyar zuciya irin na King sai da ya sha jinin jikinsa a lokacin da suka sauke kallonsu a kan face ɗin Black Tiger, saboda babu annuri ko tausayi bare imani, ran maza a ɓace yake, har wasu siraran jijiyone suka fito a cikin idanunsa, huci yake saki tamkar wanda yake shirin kamawa da wuta. Idanunsa kai tsaye a kan Smart ne kawai babu ko kyaftawa, kun san ya iya ɗaukar tsawon lokaci yana iya kallan Sweetie ba tare da kyafta ido ba, to haka ya yi wa Smart a yau!. Miƙewa Mommah ta yi da nufin ta yi mashi magana, ta zaci tattausa ne wanda zata iya tausarsa kamar Smart, bata san wannan ko King Abdul Malik ya bashi hanya ba, dan bama za'a gwada taurinsa da King Zuhair ba, sai dai wanda King Zuhair ya gado daga wajensa!. Mommah na shirin buɗe baki sai gani ta yi ya ɗaga Smart sama ya yi jefa da shi a saman sofas da suka yi kaca-kaca da shi ɗazun, tsabar zafin nama bata ga time da Black Tiger ya nufi Smart ba, sai gani ta yi ya yi jifa da shi. Ai a miliyan ta waro idanunta, tsabar tashin hankali jikinta tsananta kerma ya fara yi. Kamar walkiya haka ta sake ganin Black Tiger a bayyana a gaban Smart, lamarin da ya sanya King Zuhair ya yi zafan shiga tsakaninsu yana san rabasu, sai dai kuwa, cikin tsananin ɓacin rai Black Tiger ya damki wuyansa da karfi ya shake. A halin da yake a cikin yanzu kome ta shiga gabansa zai iya taketa ya bi ta kanta ne ya wuce, baya ji kuma baya gani!. Ai Smart bai san yana kaunar King fiye da kansa ba sai yau, dan kuwa a miliyan ya miƙe tsaye tare da tattaro dikkan sauran karfinsa ya kaiwa Black Tiger naushi a bayan kunne wanda yasa dole ya saki King. Domin duka a bayan kunne komai taurinka sai ka jisa, yana kai mutum lahira nan take, ko kai da kanka ka sanya yatsa ka matsa bayan kunnanka sai ka ji azaban zafi bare a kai maka duka a wajen. Ai wani irin ɗago kai da Black Tiger ya yi sai da yasa King Zuhair yin baya baya kamar zai faɗi, shi kansa Smart sai da ya razana, Mommah kam yau ta ga bala'in da bata taɓa zatan zata gani ba. Kamar walkiya haka Black Tiger ya sake dawowa gaban Smart ya kai hannu ya shaki wuyansa. Tsabar tashin hankali Mommah bata san lokacin da ta isa gabansu ba, King na ƙoƙari dakatar da ita dan kada Black Tiger ya yi mata illah, amma ina, kafin King ya kai ga dakatar da ita har ta isa wajen. Cike da tsananin tashin hankali ta kai hannunta zata zare hannun Black Tiger dake wuyan Smart tana faɗa mashi ya bari kada ya kashe ɗan uwansa. Ai a wani irin zafa ya juyo zai shaketa ita ma, sai dai kuma yana sauke idanunsa a kanta ya ji kamar wanda aka cakawa allura, kamar an watsa mashi ruwa mai sanyi a zuciyarsa, bai santa ba, bai taɓa ganinta ba sai yau, amma ya tsinci kansa da shakkar yi mata wani abin, zuba mata idanu ya yi yana kallonta har cikin ido ba tare da kyafawa ba, ita ma kallonsa take yi, sai dai tana cigaba da bubbuga hannunsa a kan dan ALLAH ya yi hakuri ya sake mata ɗanta kada ya kashesa . Saboda sanyi irin ta uwa. Uwa ta fita daban, wlh bai san time da ya zare hannunsa daga wuyar Smart ba, sai gani suka yi Smart ya durkushe kasa yana faman tari. Da sauri King ya yi kansa yana yi mashi sannu. Shi kuma Black Tiger cikin zafi ya nufi in da Pretty take a kwance ba tare da ya dai'na bin mommah da kallo ba, a cikin ransa yake jin kamar yana da alaƙa da ita, har can kasar zuciyarsa ya ji face ɗinta ya kwanta a ransa, ya ji dik duniya babu wani abin da yake da ƙayatarwa da daɗin kallo kamar face ɗinta, har ji ya yi kamar ya yi ta kallonta kada ya dakata. Sai dai kuma dik da wannan, da suka ce mashi su ne iyayensa, kada ya je ko'ina, sai ya ce babu wannan magana, bai san su ba, shi ubansa ɗaya ya sani a duniya, kuma ya mutu, bayan shi bashi da wani Uba, dan haka kada su kuskura su kawo mashi wata maganar banza a nan, ransu ne zai ɓaci!. Da suka ga ba zai taɓa yarda shi ɗansu ne a yanzu ba, sai suka ce su kyalesa zuwa wani ɗan lokaci, su bibiyu al'amarin a hankali domin su je mashi da hujojin da dole ya aminta ɗansu ne shi, saboda ba ta yadda za'ayi su kasance abu guda da Smart kuma ace shi ba ɗansu bane, da ma a iya kamar kawai ta tsaya to da sauki, amma ace fingerprint ɗin Smart ya buɗe nasa sannan ya ce shi ba ɗan su bane? Ko ciki ɗaya kuka fito da mutum fingerprint ɗinka ba zai taɓa buɗe nasa ba sai twins, twin's ɗin ma ba kowanne ba sai identical, sune harta DNA ɗinsu ma iri ɗaya ne, komai nasu ɗaya basu da banbanci, dan haka dole Black Tiger twin brother ɗin Smart Tiger ne, babu wata kwana-kwana. Amma da yaki yarda sai Mommah ta ce su rabu da shi sai sun yi bincike sun tara hujojin da ba zai iya musawa ba. Shi dai ko sake kallon in da suke bai yi ba yasa hannu ya saɓi Pretty a saman shoulder ɗinsa yana nufar hanyar fita da ita. Cikin zafa Smart ya tare gabansa tare da kai hannu ya rike Pretty. A tsorace Mommah ta ce. "Omerish lafiya? Ka kyalesa ya tafi nace maka". ALLAH sarki, bata son taga suna faɗa ne, dan tasan su ɗin abu guda ne!. Ba tare da Smart ya kalli in da suke ba ya ce. "Mommah tafiya da ita fa zai yi"....... Cikin sanyin murya Mommah ta ce. "Ka kyale mashi ita ya je da ita, in har ɗanane, jinina ne, a cikina ya kwanta tabbas ba zai cutar da ita ba, dan haka ka kyalesa ya je da ita".......... Dik da tasan Smart yana bala'in son Pretty, amma ta ce ya sakewa Black Tiger ita domin gudun irin ɓarnar da Black Tiger zai iya yi masu idan aka hana shi burinsa! A yadda ta gansa bata ga alamar sauki a tattare da shi ba!. Cike da mamaki Smart ya juyo da kallonsa a kan Mommah, tinani ya shiga yi a kan how comes zai barwa wani ƴar tsanarsa ya tafi da ita? Dik da yana jin tsananin kaunar Black Tiger a ransa, amma baya jin zai iya ɗaga mashi kafa a kan matarsa. Cike da damuwa ya dawo da kallonsa a kan King wanda yake ta famana binsu da kallo, shi burinsa ɗaya shi ne Black Tiger ya bar masarautar, idan ba haka ba hankalinsa ba zai taɓa kwanciya ba, saboda ɓarnar da ya yi masu ta wuci misali, shi ya yarda ɗansa ne, amma yana ganin kamar a yanzu Black Tiger ba shi kaɗai yake ba, dan haka barinsa Kingdom ɗin shi ne mafi alkhairi a garesu!. "Omerish ka sake mashi ita ka ji?". Mommah ta sake faɗa a karo na biyu. Shi kansa Black Tiger baya son dukan Smart, domin tin da ya shigo cikin ɗakin ya ɗaura idanunsa a kan Smart yake mamakin kamannin dake a kan tsakaninsu, shiyasa kuka ga ya tsaya shiru yana karewa Smart kallo a lokacin da ya shigo ɗakin, he was very shocked ne na ganin irin wannan kama, dole tasa yake jibgan Smart, amma ba wai dan zuciyarsa tana so ba, sai dan kawai ya shiga tsakaninsa da bukatarsa ce wato Pretty. Shi yanzu Black Tiger ma ba wai lallai saboda Spender zai ɗauki Pretty, e akwai bukatar Spender a ciki, amma yanzu saboda ya kaita wajen Sweetie ya ga kyakkyawan murmushin dake bayyana a kan face ɗin Sweetie ɗin a dik lokacin da ta samu wani abin farinciki ne yasa ya ji ba zai iya barin Pretty ba, a takaice dai son Sweetie ta yi farinciki har ma ta yi mashi murmushi yasa zai ɗauki Pretty!. Ba don Smart ya so ba ya sake mashi Pretty, sai dan umarnin Mommah, ita kuma Mommah da biyu ta ce a bar Black Tiger ya tafi da Pretty!. Yana sake mashi ita ya wuce ba tare da ya sake waiwayarsu ba, amma ta magic eyes ɗinsa yana ta kallan Mommah da baya jin zai iya gajiya da kallonta, haka ya nufi waje ya je ya tattare gabaɗaya warriors ɗinsa da ko kaɗan basu jiggata ba kuma basu gaji da yaki ba. Farko kenan a tarihinsa da ya taɓa zuwa yaki ba tare da ya shafe labarin masarauta a doron duniya ba ya koma empire ɗinsa, yau dai bai shafe su King Zuhair ba, ya tattari warriors ɗinsa suka wuce, kuma dik saboda Mommah yasa bai tsaya karisar da yakin ba, matar ta tsaya mashi a rai, sai yake jin kamar ma ya ɗauketa ya tafi da ita empire ɗinsa, ya je ya ajiyeta ya yi ta kallonta. Amma haka ya wuce. Yana tafiya Smart ya yi gaggawar ficewa daga ɗakin saboda tsananin bakincikin da ya taso mashi. Kallon juna Mommah da kin suka yi, a lokaci guda suka sauke nannauyar ajiyar zuciya. Dikkansu babu wanda ya ita cewa ɗan uwansa uppan, King ya wuce ya fita izuwa fada dan su tattauna kan batun ɓarnar da aka yi masu, ko in ce ɓarnar da ɗan cikinsu ya yi masu, ita kuma Mommah ta koma underground domin tattaro kan su Jaish. Uhm Black Tiger yana kaunar marayu har ma yana renonsu, baya taɓa barin rayuwar maraya ta tagayyara, su Angela gabaɗaya marayu ne ya rena bawan ALLAH, kazalika kingdom of power suna ɗaukar marayu da daraja, saboda Mahnoor marainiya ce yasa suka bar aurenta da Jaish, A nan kun fahimci daga in da Black Tiger ya yi gadon renon da jin kan marayu?. Uhm ƴaƴan Mommah dikka they're gifted, Black Tiger yana da kaifin ƙwaƙwalwar da ku dubi yadda yake tafiyar da birninsa, ku dubi yacce ta gwammaci kasarsa ta mallaki komai a kan su fita waje suna saya, kuga yacce ya gyara birnin, common motoci a kampaninsa na Black Tiger auto motors ake kyarawa, kuga yacce yake da manya-manyan jiragen sama masu ɗauke da tambarin sunansa. Yana da sani a kan mulki sosai!. In short sai da kingdom of power ta ɗauki almost 2 weeks suna gyare-gyare kafin su iya shawo kan ɓarnar da Black Tiger ya yi masu a kasa da awa biyu kawai. A lokacin da su Zarina suka samu labarin abin da ya faru da kingdom of power sun so zuwa su karisar da su kawai su huta, sai dai basu samu labari da wuri ba, sai hayan farfaɗowar kingdom ɗin ne suka samu labari, wanda hakan sam-sam bai yi masu daɗi ba. Sai dai basu wani damu ba, sun daure sun cigaba da gagarumin shirinsu na tinkararsu su yi masu kwaf ɗaya, sun haɗe sojojin yakinsu gabaɗaya a empire ɗin Zarina suna kara tsananta masu horo dan suna son yi wa Zuhair duka ɗaya ba tashi kenan!. UHM YA KUKE TINANIN SU KING ZASU YI BLACK TIGER YA YI ACCEPTING ƊINSU A MATSAYIN IYAYENSA? ANYA ZASU SAMU WATA HUJJAR DA ZASU RIKA WANDA ZAI SANYA DOLE YA YARDA DA SU KUWA? MEYAFARU A LOKACIN CIKIN SMART TIGER AND BLACK TIGER? MEYASA AKA RIKITA MOMMAH? META AIKATAWA MUTANE? HMMM BLACK TIGER YANA TA FAMAN SHAN WAHALA A KAN SPENDER BA TARE DA YASAN CEWA DAMA SPENDER MALLAKINSA BANE, E MANA MALLAKINSA NE TIN DA YANZU SHI NE BABBAN YARON KING ZUHAIR, SPENDER KUMA NA KING NE, KUNGA SU NE MASU GADONSA! AKWAI CASE, DOMIN BLACK TIGER BA ZAI TAƁA YARDA SU IYAYENSA BANE HAR SAI BABANSA DA YA MUTU YA DAWO YA FAƊA MASHI NA SHI YA HAIFESA BA, WAI MA TA YA AKA YI YA BAR KINGDOM OF POWER? WAYE YA SHIRYA DIKKA WANNAN RASHIN ADALCIN WA KOMMAH? MUJE ZUWA KU DAI! WANNAN KENAN A ƁANGARE CROWN OF POWER, BARI MU LEƘA WANI ƁANGAREN DAN JIN HALIN DA SUKE A CIKI!. 🔥🔥CROWN OF JUSTICE🔥🔥 Bayan sallar isha'i, yau a gidan Papa su Hoorain suka yi buɗa baki, a can kuma suka yi sallar magrib. Ko da suka dawo Hoorain bai nemi su Ude ba, ya wuce yabi bayan Rishan izuwa bedroom ɗinsa, saboda baya son ganin su Ude, sun yi tattaunawa mai muhimmanci a tsakaninsa da Papa. Dama Papa ya jima yana zargi Ude ba shi ne King Omerish na ainahi ba, amma saboda rashin hujja yasa ya ja bakinsa ya yi shiru. A tare suka yi zama da Abdul Mutallab, a gabansa aka haifi su Omranish, ya yi mamakin sauyawar Omranish ɗin zuwa bakin azzalumi daga mutuwar Abdul Mutallab babu jimawa, wannan ya ɗarsa zargi a ransa. A tattaunawar da suka yi a yanzu da Hoorain ya faɗa mashi cewa ya rinƙa nunawa su Ude kuskurensu ta hanyar nuna masu fushinsa, ma'ana a cikin dabara Hoorain ya rinƙa ja baya da su, ya ce mashi idan yana nuna masu fushinsa a matsayinsu na iyayensa waɗan da suke tsananin kaunarsa suka kuma shafe shekaru ba tare da shi ba zasu canza abubuwa ko dan farincikinsa, dan haka idan sun yi ba daidai ba ya rinƙa nuna masu ya yi fushi. Hoorain ya ɗan ji wani irin da waɗan nan shawari na Papa, hakan yasa da suka kamo hanyar dawowa gida ya ce. "Uncle meyasa Papa zai ce in rinƙa yin haka ga su Dad? Hakan sai nike ganin kamar yana san in rinƙa janye kai'na daga garesu ne". Ba tare da nuna wata damuwa ba sadauki Rishan ya ce. "Kada ka damu my son, ka yi dik abin da Papa ya faɗa, dan bayayin abu haka kawai, watakila akwai abin da ya hanga ne yasa ya ce maka hakan". Da yake Hoorain yaro ne mai biyayya tin ainahinsa, kun san warriors da biyayya ai, sannan yana da natsuwa yasa ya amince da batun uncle ɗin nasa ba tare da wata ja ba, sai dai a cikin ransa yana mamakin wasu abubuwan da suke faruwa, kowa sai ya ce mashi ya yi hankali kuma ya kula, shi kansa commander Zafar da ya dawo yau sai da ya ja mashi kunne a kan ya kula da kansa sosai, saboda sarauta ta wuci dik yadda yake zata, ya kula da kansa sosai, abin har ya fara sanya mashi shakku a ransa!. Cike da tinani kala-kala suka shiga ɗakin sadauki Rishan. Suna shiga ya zauna a saman sofa yana faɗin. "Uncle ina son yin wanka?". Kallo mai cike da tambayoyi Rishan ya wurga mashi kafin ya ce. "Wai kai baka da bedrooms ne? Ya zaka zo ka takura mun a nan? Ta shi ka wuce naka ka je kayi wanka a can". Ɗan tsuke fuska ya yi kafin ya yi ƙasa da kansa, a kunyace ya ce. "Kai uncle, nasan Hoonairata ta yi wanka yanzu, bana san in koma bedroom namu ban yi wanka ba, shiyasa zan yi a nan"........ Rishan dake ƙoƙarin rage kayan sarautar dake jikin ne ya ce. "Zama ka dawo hanya ne, ni ban taɓa ganin angon da zai ce ya tsaya jiran amaryarsa ta girma ba sai kai, wato so kake ka yi shiri daga nan ko? Da ka je shikenan babu ɓata lokaci". A wannan karon tafukan hannunsa yasa ya ɗan rufe face ɗinsa yana faɗin. "Kai uncle ka bari mana, ni fa ba haka nike nufi ba, babu abin da zan yi mata ko na je face in bata abinci, dan nasan bata ci ba tana jirana". Gyara tsayuwarsa sadauki Rishan ya yi da kyau yana fuskantarsa, sannan ya ɗan ɗaga mashi gera guda kafin ya ce. "Ko?"........ Kai ya gyaɗa alamar haka ne. Ɗan girgiza kai Rishan ya yi. "My son baka san me ake cewa mace bace shiyasa zaka ɓata lokacinka a shirme, but shaaa soon zaka sani, domin......" Sai kuma ya dakata ya ki karisar da maganar, dama cewa zai yi domin matarka ba irin macen da ake iya gani a kyale bane, ta wuci nan, dan haka da kanka zaka je in da ake so ba sai kowa ya ce ka je ba, tinawa da ya taɓa son Zunaira a baya yasa ya katse magana a kanta bai ƙarisa ba, dan baya son ya rinƙa yin magana a kanta sam-sam. Wato idan Rishan da Hoorain suna hira sai sun baku mamaki sun kuma hurgeku, hira ce ta natsuwa da mutuntawa, sannan dikkansu zasu yi magana tamkar ba su suka yi ba, babu alamar fara'a a kan face ɗinsu, zakunan warriors ne suke magana, ba zaka taɓa cewa sun san menene murmushi ba a rayuwarsu. And magana one by one. "Uncle da gaske Zunaira yarinya ce, shiyasa dik yadda na kai ga sonta zan hakura sai ta girma, nima ina son babys kuma ina son.......". Ƙasa ƙarisa maganar ya yi saboda nauyi da ta yi mashi a baki kuma yana jin kunyan uncle ɗin nasa, dama cewa zai yi kuma shi ma yana son ɗanɗana zuman Zunairarsa. HAKA KAWAI SADAUKI RISHAN YANA NEMAN CIRE MANA KUNYAR OUR HOONRAIN YA MAYAR DA SHI MARA KUNYA, KUN GA HAR YA FARA SANYA SHI SAKIN LAYI!. Da yake Rishan babba ne kuma yasan kan duniya sai ya fahimci me ɗan nasa yake son faɗe ya gagara karisawa dan haka sai ya ce. "Ummmmm to je ka yi wanka kazo in shiryaka shiri na musamman". Ya kai karshen maganar tare da zare kayan jikinsa gabaɗaya, ya rage daga shi sai short. Miƙewa Hoorain ya yi ya nufi cikin toilet, da kallo Rishan ya bisa yana mamakin hali irin na Hoorain, wai Auta ta yi karama, a ransa ya ce da matarsa ce ai yanzu in bata da ciki to fa ta saba da raund 4 a kowani dare, shi ai ba zai iya wani ɗaga mata kafa, kyakkyawa kamar Auta yarinyar da tamkar ita ta yi kanta ɗin ne yana ganinta a ɗakinsa kuma saman bed ɗinsa zai ɗaga mata kafa? Tab ba dai shi Rishan ba, sai dai wani gaskiya. NI KAM NA CE TO KOMA WACECE WACCE ZATA ZAMA MATAR RISHAN TA YI GAGARUMIN SHIRI!. Zama ya yi a gefen bed tare da jawo wayarsa ya shiga latsawa yana tinanin a gaskiya lokaci ya yi da zai yi aure, dan yana tsananin buƙatar mace, sai dai kuma a ina zai samu matar? Shi da ba kula kowa yake yi ba, a ina zai samu koda rabin Zunaira ce ya lallaɓa da ita?. A wannan hali Hoorain ya fito ya same shi, yana ɗaure da towel a waist ɗinsa, yana riƙe da ɗaya kuma yana goge kyakkyawan golden white hairnsa dake ta faman kyalli tin ba'a gyara ta ba. Binsa da kallo Rishan ya yi kafin ya miƙe ya shiga wajen clothes set ɗinsa. Jim kaɗan ya fito hannunsa ɗauke da wani cartoon. Miƙawa Hoorain ya yi yana bin gashin kansa da kallo. Lokaci guda ya ji gabansa ya faɗi a time da ya tuna mahaifiyarsu haka gashin kanta yake, golden white, wato Hoorain and Sweetie suka ɗauko irin gashin nata. Uhm my people's shin kun san da cewa mahaifiyarsu Rishan tana a raye ko baku sani ba? Ni Queen of surprise na ce ku karɓi wannan. Mahaifiyarsu tana a raye a in da basu sani ba, kuma ba kowa bace face Ammo ta babyn baby, wannan dattijuwa ita ce mahaifiyarsu Rishan, matar King Abdul Mutallab, kakar su Hoorain kenan wacce ta haifi King Omranish. QUEEN MOTHER NA CROWN OF JUSTICE. To me ya rabata da ƴaƴanta har haka? Kada ku manta irin rayuwar da suka yi ita da baby a baya na wahala kafin ALLAH ya aiko baby ya taimaka masu, uhm Ammo Queen mother of CROWN OF JUSTICE, ita ce ta kare a gantali a titi, me ya ja hakan?. Nasan zaku ce dik sharrin su Zarina ce, to a nan dai aikin KING ZUHAIR ne ya haɗa da ita, King fa ya yi taɓargaza bawan ALLAHN nan, ku dai mu je zuwa kawai. Another one surprise shi ne wacce zata iya banbance King Omranish and Ude tana a kingdom of power, wai cakwakiya kenan, to wacece? Muje zuwa! ----------------------🔥 Karɓar kayan Hoorain ya yi Rishan ya koma gefen bed ya zauna. Cike da jin kunya ya ɗaura kayan a saman bedside drawer ya wuce izuwa gaban mirror. A gaggauce ya shirya saboda yana son zuwa wajen Auta, dan ya tabbata bata ci komai ba. Lokaci da ya ware kayan barcin da Rishan ya bashi sai da ya ji tsikar jikinsa ta tashi. Slowly ya ɗago da kallonsa a kan Rishan, sai kuma ya ga uncle ɗin nasa ya miƙe ya nufi dressing room. Kallan kayan ya dawo da idanunsa ya hau yi, a hankali ya ware kayan gabaɗaya, kusan irin kayan ranar ne da ya bashi, sai dai na yau rigar net ce, shara-shara ce sosai ta yadda za'a ce kusan da ita da babu dik ɗaya ne. WATO DA RISHAN DA RISHMA SUN RANTSE SAI SUN HAƊE WAƊAN NAN MASOYAN SUN MANNESU. A natse ya hau saka kayan yana tinanin ai ranar Zunairarsa ta ji daɗi da ta gansa da irin wannan shiga, dan haka ko dan ta yi farinciki zai sanya. Haka ya hau sakawa yana tinanin yadda zai sameta........... Ya ilahi, ya yi fitina a cikin waɗan nan kaya, ya yi tsantsar kyau. Yana tsaye yana bin kansa da kallo sai ji ya yi uncle ɗinsa ya hau tattare mashi gashi ta baya, ɗan rage tsawonsa kaɗan ya kara yi domin ya baiwa uncle ɗin nasa damar gyara mashi gashin da kyau, dan kusan tsawonsu ɗaya da Rishan ɗin. Kamar wani ɗan yaro haka Rishan ya mayar da Hoorain a yau, da kansa ya gyara mashi gashi ya feshesa da tsadaddun hair perfumes masu kamshin daɗi, yana gyarasa yana faɗin. "You're our Prince, ba zan zuba maka idanu ba, saboda na ga kai baka ɗaukar abubuwa serious". Shi dai ya ɗan yi kasa da kai, kamar mai tinanin wani abin. Sosai Rishan ya gyara mashi gashi ya ɗaure a tsakiya kamar yadda al'adar Koreans take, sannan ya ja jelar gashin ya murɗeta ya kewaye ɗaurin da ya yi mashi da ita, a karshe ya sanya pil ya kame gashin da ita!. Ya sake binsa da perfumes masu kamshin kwantar da hankali. Shi kansa Rishan yasan Hoonaira ya yi fitina a yau, dole Zunaira ta ruɗe. Wani kyakkyawan Rose Rishan ya bashi haɗe da wani karamun box of chocolate kafin ya ce. "Good night my son". Ya faɗa tare da nufar toilet dan ya je ya yi wanka shi ma. Har zai shiga toilet ɗin sai ya ji Hoorain ya kira sunansa. Juyowa ya yi yana ɗaga mashi gera guda alamar lafiya?. Da sauri Hoorain ya nufosa, yana zuwa ya tungumesa kafin ya ce. "I really love you my one and only uncle"..... Shafa bayansa Rishan ya yi haɗe da cewa. "Love you to my first son my first love". Ya kai karshen maganar tare da raba jikinsu, sannan ya ce da Hoorain ya je yunwa na damun Auta. Da sauri ya juya yana mai jin tsananin kaunar uncle ɗin nasa, ya nufi waje. Yana fita suka ci karo da Rishma, dama shi ta zo nema, dan Auta dai taki cin komai, ta ce sai ya dawo zasu ci abincin a tare, shi ne ta zo duba shi. Cikin girmamawa ya ɗaga mata gaisuwa kafin ya tambayi ina Auta, a natse ta amsa mashi da tana ɗaki tana jiransa. A dai'dai wannan lokacin shi kuma Ude yana can yana kai komo a cikin bedroom ɗinsa, ya gama tsuma, surar jikin Auta ne kawai ya tsaya mashi a rai, ya kwaɗaitu da ita ainun, faɗi yake yi ko ta wani hali ne sai ya sami Auta, ko da rayuka zasu salwanta, sai ya ɗanɗani yarinyar nan!. Tinani yake yi ta yadda zai je mata ta aminta da shi ba wata gardama, can wata zuciya ta ce ya tsafeta, ya sanya zuciyarta a kwalba zata yarda da shi. Kai ya girgiza alamar wannan shawa bata yi mashi ba. Shiru ya ɗan yi, ya sake natsawa cikin tinaninsa. Can kuma wani ɓangare na zuciyarsa ya ce to me zai hana ya shiga siffar Hoorain ta tsafi, hakan zai sanya ta yi balai'n aminta da shi, zai samu sex mai daɗi da ita, dan zata zaci Hoorain ne sai ta sallama mashi kanta. Na'am ya yi da wannan shawara, dan haka sai ya fara tsara da wani lokaci zai je mata?!. Shi kuwa Hoorain sallama suka yi shi da Rishma, ta wuce ciki wajen Rishan shi kuma ya nufi bedroom ɗinsa. A natse yake takawa, gabaɗaya a matse yake da son ganinta, amma dik da haka sai da ya fara zuwa in da Kamran ke kwance yana jinya ya duba shi kafin ya nufeta. Tana tsaye a jikin window, ta yaye curtain tana kallan harabar kingdom ɗin, sanye take da wani figaggen riga wanda ya tsaya mata a iya gwiwowinta, rigar ya yi bala'in yi mata kyau, ga shi very silky haka, yau sarauniya Rishma da kanta ta je ta yi mata sayayyar kaya sosai, daga ciki ne ta sanya wannan sleeping dress ɗin, ta yi fitina a cikin kayan. Ɗan dakatawa ya yi a tsakiyar bedroom ɗin yana kallonta cike da zallar kauna, ko kaɗan bata ji shigowarsa ba, hankalinta ya yi nisa wajen tinanin ina ya tafi to? Ga shi daga ita har shi babu waya a hannunsu, and bata san number Rishan ba bare ta kirasa ta tambayesa ina yake ko da wayar waye ne. Sai dai ta ji bugawar zuciyarta alamar yana kusa kenan!. Wani musulmin ajiyar zuciya ya sauke, hankali ya kwanta ya ɗaura idanunsa a kanta. Takowa ya yi step biyu, sai kuma ya ɗan dakata ganin tana ɗan ɗaga kai kamar zata juyo, ƙamshin perfume ɗinsa ne ya daki kofofin hancinta shiyasa ta ɗan ɗaga kai tana shaka. Ganin bata juyo bane yasa ya kara lallaɓawa a hankali. Unexpected ta ji saukar hannunsa a saman shafaffen cikinta game da kwanto da kansa a saman shoulder ɗinta, kamshin dake jikin dogon arabs hairnta ya fara shaka yana ɗan lumshe idanu. "Sai yanzu zaka dawo?". Ta faɗa tana turo baki. Juyo da ita ya yi suna fuskantar juna tare da gyara tsayuwarsa, ya tsaya da kyau kafin ya ce. "Sorry my Hoonairata". Ya yi maganar yana ɗaura hannunsa ɗaya a saman mazaunanta ta baya. Ture shi ta yi game da cewa. "Ban hakura ba, kuma fushi nike yi da kai". Ta kai karshen maganar tare da wuce, ta raɓa gefensa izuwa saman bed. Binta da kallo ya yi yana jin wani irin musulmin yanayi na shigarsa, yadda take tafiya tamkar bata son taka ƙasa, kai ka ce da gangan take yi mashi irin wannan tafiya, dik tasa ya rasa natsuwarsa. Hayewa saman bed ta yi tare da jawo pillow ta ɗaura a saman lap ɗinta, ba tare da ta kalli in da yake ba ta kifa kanta a jikin pillown. A ransa ya ce kome ta yi kyau yake yi mata, dama idan mace bata da rigima ai namiji ka auro ba mace ba, har cikin ransa ya ji wani musulmin daɗi ta lulluɓesa na rigimar da ta yi mashi, mace da rigima aka santa. A natse ya taka izuwa in da take domin yin rarrashi. Yana zuwa ya zaune a gefen bed ɗin. Yatsun hannunsa ya kyasta mata wanda hakan yasa ta ɗago da kanta, slowly ya kwantar da nasa kan a in da ta ɗaga nata, a saman laps ɗinta kenan, yana kallon face ɗinta yacce take faman turo baki. Ƙasa sosai ya yi da murya, cikin wata iriyar murya da bai taɓa yin magana da ita ga kowa ba a rayuwarsa ya ce. "Ba zan ce Hoonaira ta yi hakuri ba, amma zan ce ta yi mun purnishment ɗin da ya dace dani, saboda nasan ban kyauta ba, yakamata ace na dawo da wuri domin in bata dinner, amma na barta da yunwa". Yana magana yana kallan face ɗinta. Cikin dabara take satar kallon kayan jikinsa, bata san yana kallonta ba, kayan sun yi matuƙar yi mashi kyau over, sai ta ji dik wani fushinta ya gudu, dama rigima ce kawai irin tata. Hannunta ta ɗaura a saman massive chest ɗinsa dake buɗe. "Zan kuwa baka purnishment sosai, dan ni ba zan hakura ba". Ɗan limshe idanunsa ya yi jin saukar hannunta a wajen, slowly ya sake warosu a kan face ɗinta. "Kowani purnishment in dai daga Hoonairata ce, zan yi farincikin yinsa". Ya faɗa yana juyo da jikinsa gabaɗaya gareta. Slowly ta ɗan yi mashi kamar tafiyar maciji da hannunta daga kirji zuwa wuya zuwa face ɗinsa, lallausan kumatunsa ta ɗan shafa kafin ta ce. "Ka yi kyau sosai my hero, kayan sun yi maka kyau and........... ". Sai kuma ta yi shiru. While shi ma shiru ya yi yana sauraronta, sai a lokacin kuma ya tina ya bar rose and chocolate da Rishan ya bashi a ɗakin da Kamran yake. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Saboda ke na sanyasu, and ke kaɗai na yiwa kwalliyar, and menene kuma? Karisa faɗi in ji". Ya faɗa muryarsa na ɗan sarkewa, saboda yadda take taɓa shi har cikin ransa yake ji!. Siririn murmushi ta yi kafin ta ce. "A'a babu komai, ka dai yi kyau".......... "Please my Hoonaira, and menene?". Cike da matsuwar san jin amsar da zata bashi, tabbas ya karanci kasan harshenta, so take yi ta ce and lips ɗinsa sun yi bala'in yi mata kyau yanzu, amma sai ta fasa faɗi, sam bai ji daɗi ba, ya so ta faɗa, dan shi ma dai ba laifi yana son bawa flowers ruwa in dai da ita ne!. "Kai my hero, in kana son in faɗa ka dai'na kallona to"....... Slowly ya rufe idanunsa yana faɗin. "Na dai'na kallanki. Faɗa mun to". Uhm kalaman Risham ne suka dawo cikin kunnenta, na cewa kada ta taɓa jin kunyarsa tin da mijinta ne, tana tsananin sonsa, kuma shi ma yana sonta, kada ta yarda da wani kauyanci wai jin kunyarsa, ta kula da abinta ta yadda zata kara gina soyayyarta a ransa ba wai ta tsaya kunya da shirme ta rushe ginin soyayyar da ya yi tun farko ba, dayawan mata daga wannan waje suke ruguje ginin soyayyar da mazajensu suka yi masu tun farko, a maimakon su karawa ginin ƙargo sai shirmensu yasa su rushesa su kuma dawo suna danasani!. RISHMA BATA SAN DAMA ITA AUTA ƳAR LOVE BACE, TANA SON HOORAIN, KUMA BATA TAƁA ƁOYEWA A KO'INA TANA SON SHI, TO TIN DA TA TSUGUNNA A GABAN GABAƊAYA FAMILY TANA RIƘON KING TANA FAƊA MASHI TANA SON HOORAIN AI DAGA NAN YAKAMATA KUSAN BA KARAMUN SO TAKE YI MASHI BA WANDA BATA IYA ƁOYEWA! KO A GABAN WAYE ZATA IYA FAƊA!. Cool smile ta saki ganin yadda ya datse idanunsa. A natse ta rakwafo da kanta a kansa, sumbata ta fara kai mashi a lallausan kumatunsa kafin ta ɗan shafi lips ɗinta da babban yatsanta, dab da bakin nasa ta kawo nata, kamar zata yi kissing ɗinsa sai kuma ta dakata, cike da zolaya ta ce. "My Hero buɗe idanunka ka gani". Ta kai karshen maganar tana ɗan goga lips ɗinta a saman nasa cikin salo. Haba lokaci guda ya ji tamkar wanda aka jonawa lantarki, gabaɗaya ya ji ta ko'ina jijinsa ya amsa, a hanzarce ya juyo da kyau ya rungumeta gam a jikinsa, tana ƙoƙarin ɗage kanta daga kansa ya yi gaggawar riƙota, tongue ɗinsa ya tura a cikin ɗan bakinta yana wani limshe idanu tare da sakin numfashi mai nauyi. Kyakkyawan wuyansa ta shiga shafawa tana mayar mashi da martanin hot kiss da yake bata. Ai bai san time da ya miƙe daga kwanciyar ba, sai dai ganinsa kawai ya yi ya yi mata rumfa da faffaɗar kirjinsa, ita fa Auta sam bata jin tsoronsa, saboda ta yarda da shi ɗari bisa ɗari, ta yarda tin da ya ce mata ta saki jiki babu abin da zai yi mata ta aminta da hakan, saboda tin da take da shi bai taɓa saɓa maganarsa a gareta ba. UHM SAI DAI ITA YARINYA CE, BATA SAN WANNAN FAGEN BAYA JIN KOWANI YARE BA BARE WANI ALKAWARI!. Ya ɗan ɗauki lokaci yana kissing ɗinta kafin ya zame ɗan bakinsa ya mayar saman wuyanta, kamar zai kwantar da kansa a wajen sai kuma ya fasa ya fara yi mata raɗa a kunne, izininta yake nema, ta bashi dama ya yi wasa da kirjinta, ya kara yi mata alkawari a kan ba zai yi mata komai ba a yanzu. Ta yarda da shi sosai, cikin shagwaɓa ta ce mashi ai nashi ne, ba sai ya nemi izininta ba. Wani irin Musulmin daɗi ya ji ta rufesa, da kyar ya iya cewa. "ALLAH ya yi maki albarka". Wuyansa ta saƙalo da hannunta ɗaya tana amsawa da Amin. Hannunsa ya tura ta kasan rigarta insert of ta sama, ta ɗan ji shock, amma sai ta dake ta cigaba da wasa da harshenta a saman lips ɗinsa, hakan ba karamun kara tsuma shi take yi ba, sai dai yana iyaka bakin kokarinsa kada ya yi loosing control ɗinsa har ya karya alkawarin da ya ɗauka mata. Ai bata san lokacin da ta kara ƙanƙame wuyansa ba da ta ji saukan hannunsa a saman mararta, shafa wajen a hankali-hankali ya fara yi, cikin natsuwa ya ce. "Yaushe Hoonairata zata girma ta fara period?". Da kyar ya yi maganar. Uhm saboda ta ce mashi bata fara al'ada bane yasa yake kara yi mata kallon yarinya sosai, bai san abin ba daga shekaru bane, yana bin yanayin jiki ma sosai. "Kai my hero nima fa ban..... Sani.... Ba". Muryarta na rarrabewa ta yi maganar. Saboda saukar hannunsa a saman tula-talanta da ta ji, lokaci guda ya sauke wani irin sanyayyar ajiyar zuciya a bayyane sosai. Zuba mata idanu ya ɗan yi yana kallon face ɗinta, ita kuma sai ta yi gaggawar limshe nata idanun. Slowly ya fara shafa tula-talan nata tare da kwanto da kansa saitin kunnenta. Can ƙasan makoshinsa kamar mai raɗa ya ce mata. "Yanzu wannan nawa ne my Hoonaira? Kin zama tawa?". Yana magana yana ɗan shasu a hankali. Da sauri ta juyo ta shige jikinsa tana murmushi tana ɓoye fuska. Kara janyota jikinsa ya yi ba tare da ya cire hannunsa daga matsa breast ɗinta da yake yi ba, sai ma ya haɗe bakinsu waje guda, domin wani irin abin da yake ji a jikinsa. Hannu tasa ta zame pil da Ude ya kama mashi gashin kansa da shi, ta saki gashin ta hau wargaza mashi shi. Nan fa suka shiga faranta ran junansu babu kakkautawa. Sun shafi 20 mins a haka, gudun kada ya karya alkawari yasa ya rabu da ita ba dan ya kwantar da tarzomar da ya tayar wa kansa ba. Dole ya daure ya saketa tare da ce mata ta tashi su je su yi dinner. Ta shige cikinsa ta ƙanƙamesa taki yin magana. Hakan yasa ya dawo da kallonsa a kan face ɗinta, idanunta jajir kamar wuta. Can ƙasan makoshinsa ya ce. "Menene?". Kai ta ɗan girgiza mashi alamar babu komai. "Hannunsa ya ɗaura saman mararta, yana kallon face ɗinta ya ce. "Ina burin ganin ranar da za'a ce mun akwai babyna a kwance a nan". Ya kai karshen maganar yana ɗan shafa mararta. Ta ganosa, so yake yi ya yi ƙasa da hannunsa, amma tamkar yana tsoron wani abin, bata san cewa yana tsoron kada ya isa can ya ƙasa control ya rike kansa bane yasa yake shakkar kai hannunsa wajen ba dan komai ba!. "Zamu haifi baby's In Sha Allah, kuma ina fatan samun twins kaman su Akka da King Badeen, kamansu Yah Omaid". ALLAH SARKI ITA BATA SAN TWINS ƊIN MA SUNA DAYAWA BA, DOMIN GA BLACK TIGER AND SMART TIGER, GA KUMA KING ABDUL MALIK DA KAKANSU BOBO, SU AI SUN GAJI TWIN'S NE MA SOSAI A FAMILYN SHIYASA. Hannunsa na ɗan rawa ya yi kamar zai yi ƙasa da hannun nasa, sai kuma ya yi sama da ita cikin gaggawa tare da ɗan raba jikinsa da nata yana faɗin. "In Sha Allah zaki haifama". Ya faɗa tare da miƙewa. Da ka gansa kasan a hannu yake, amma ya daure ya miƙe tsaye, ƙasa ya sauko yana faɗin ta sauko su je su yi dinner. So yake yi su ci abinci, idan sun ƙoshi sai ya je ya ɗauko abin da Rishan ya bashi ya barosa a wajen Kamran. Saukowa ta yi jikinta dik a mace, da kansa ya yi serving ɗinsu ya kuma bata a baki har sai da ta ci ta ƙoshi. Sannan ya miƙe ya ce mata yana zuwa, bedroom na Kamran ya koma. Tana zaune a bakin bed ya dawo da rose da chocolate ɗin, a maimakon ya bata sai ya ɗaura a saman mirror drawer, saboda ya ga tana hammar barci, wato saboda shi soyayyarsa ta natsuwa ce sosai har yasan tin da tana jin barci ko ya bata gift ɗin ba zata yi farinciki sosai ba, kuma ajiyesa kawai zata yi ba zata bi ta kansa ba, dan haka zai bari sai da safe lokacin da take garau ya bata, a nan ne zata ji daɗi har ya samu tsarabar kiss da rumguma. Wajenta ya dawo, a natse ya ce mata. "Mu kwanta ko?". Kai ta gyaɗa mashi. "Okey to kwanta ina zuwa". Ba musu ta karisa hayewa saman bed ɗin. Shi kuma ya koma wajen da suka ci abinci ya tattare komai, dan ita bata iya ba. Ya fitar da kayan abincin, dan baya son wata baiwa ta sake shigo masu ɗaki, shiyasa bai kirata ta zo ta tattare ba. Kwance ya iskota har barci ya kwasheta, hayewa saman bed ɗin ya yi tare da jawota jikinsa sannan ya ja masu bargo game da kashe wutar ɗakin. ASUBA TA GARI!. Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ======🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ Da yake bedroom ɗinta ne, already tasan komai da yake a ciki, sai ta wuce ta nufi toilet ba tare da ta yi mashi magana ba. Bayanta da kallo ya bi, shi dai wlh yana son dirin Khadijah, kun fa san su fa basu da boobs and al'amura, Khadijah kuma so Masha ALLAH, tana da diri mai kyau da ɗaukar hankali, goodbye a cike welcome a tsaye. Sai da ta shige cikin toilet ya ƙarisa saman sofa ya zauna yana sauke ajiyar zuciya, gabaɗaya da ka kallesa zaka san a matse yake, kaman kuma ya takura kansa, da alama yana son ya ga Khadijah na farinciki sosai, amma bai san ta yaya zai bi ya sanyata ba, shiyasa yake ta waɗan nan kame-kamen..HAR YA BAN TAUSAYI. Yana zaune a wajen har ta fito sanye da white bathrobe ɗinsa, dan iskanci irin na Khadijah kuma sai ta ɗauki nasa ta saka, kai wato idan kaga an yiwa ɗan Nigeria wani abin ya yi shiru bai ɗauki mataki ba fa shi ya ga dama, shi ya yi ra'ayi, amma wlh duniya dik ya shaida mu daban muke, we're gifted in all har da ƴan iska, ta sanya kayansa ta fito kuma bata ko kalli in da yake ba. Da kallo ya bi kyawawan ƙafafunsa da bathrobe ɗin bai kammala rufewa ba yana haɗiyar yawu, uhm kafin ta haifi baby Ahmad ma ya ji sha'awarta mai karfi haka bare yanzu da ta haihu ta kara cikowa da tsantsar kyau, hankalinta ya kwanta sosai a kingdom of power ɗin nan, ta yi fresh, ai dole ma Bobo ya rasa sukuninsa. One thing, ita fa Khadijah tana son shi sosai, kuma ba wai bata san tana son shi ba, ta sani, kawai abin da ya yi mata ne yasa ta ɗaura ɗamayar hora shi, sannan bata da tabbacin a matsayin me suke a zaune yanzu! Shin zina ne? Ko dai mata da miji na sunnah? Tana buƙatar wannan amsa kafin nan ta san kalar hukuncin da zata yi mashi! Dan ta ci alwashin ba zata rabu da shi ba, ya je ya ɗaukota a ranar da mahaifinta ya rasu, kuma a ranar babu tausayin halin da take a ciki ya yi dis virgin ɗinta, ta yi kuka bai taɓa rarrashinta ba, sai ma wahala da yake kara mata na kowani dare sai ya zo ya biya buƙatarsa, ba hira mai daɗi, ko mara daɗin ma bata samu ba, babu abin da ya iya sai ikon bala'i, to wlh yanzu dai bai isa ba, zai san da jinin arewacin Nigeriya yake yi!. A gaban mirror ta tsaya ta gama shafe-shafen manta dikka. Tana yi tana satar kallonsa, ya tsareta da waɗan nan dara-daran idanun nasa tamkar zai cinyeta da ido. Da ta ɗan ɗaga bathrobe ɗin zata shafa mai ta ɗan saman cinyoyinta tana ganinsa har wani irin yawu ya haɗiye, sai da ƙashin makogwaransa ta motsa da ɗan karfi!. A ranta ta ce sai ma na tabbatar matsayin me muke zaune zaka gane shayi ruwa ne, sai ka biya kuncin da ka sakani a ciki. Sai dai kuma kafin ta iya tabbatar da irin zaman da suke yi dole sai shi ɗin zata tambaya, dan bata jin akwai wanda zai iya bata wannan amsa idan ba shi ba!. Tsabar neman magana irin tata ta jima tana shafa mai a cinyoyinta kafin ta koma kan hannayenta. Shi dai bai ce mata ko uppan ba, dan ya lura kamar bata a cikin mood mai daɗi, da alama yanzu ya fara iya tantance a wani hali take a ciki! So ya fara gane lokacin da yakamata ya yi mata magana da akasin haka. Da yake tasan tana da kaya a gidan sai ta wuce closet ɗinsu. Ta sha madarar mamakin ganin yadda side ɗinta yake nan ba'a taɓa komai ba, sai ma uban tulin kayan da aka karo mata, hakan na nufin tana a cikin ran mai ɗakin, kullum tana a cikin tinaninsa. Uhm kun tina time da ya je gidan Smart ya sameshi a ranar da zasu fita yawo da su Pretty? Ai wannan rana ɓata ran da yake yi dik sabosa ita ne, damuwa da tinanin ina take ne ya yi mashi yawa, baku ji Smart yana ce mashi komai zai wuce ba, to kullum su suke rarrashinsa, dik kuma a kanta, shiyasa nace maku yana sonta, iskanci ne ta yi mashi yawa, yo iskanci mana, ai tin da Smart ya iya rarrashin ƴar tsana babu wanda ba zai iya kula da mace ba sai dai in iskanci ne ya cika mashi kai. Yana dai zaune har ta fito shirye cikin wandon jeans and shirt, daka ta saman wandan ya kamata ya fitar mata da shape sosai, daga ta kasa kuma kafan wandan ya buɗe sosai, rigarta kuma mai ɗan dogon hannu ne wanda bai ƙarisa kai mata karshen hannunta ba, kuma rigar da kaɗan ta wuce cibiyarta, irin shigarsu dai na wajen shi ta yi, kuma dikka kayanta dake a cikin wajen irinsu ne kawai ya saya mata. Ta ɗaura boyfriend Jacket a saman kayan, sannan kafafunta na sanye da safa ash color, ta yi kyau sosai, true beautynta ne ya ƙara bayyana without make up. Ai malam Bobo kara rikicewa ya yi, ALLAH ya gani yana kewarta sosai, zuba mata idanu ya yi sosai, ita kuma ta ɗaure fuska tamau tana wani basarwa ta nufi waje. Har zata fita ta tsinkayo voice ɗinsa a sanyaye sosai yana faɗin. "Ina zaki je kuma?". Tamkar ba da ita yake yi ba, ta wuce abinta bata amsa ba. Wani irin yawu mai karfi ya haɗiye sai da makogwaransa ta yi sama ta sake yin kasa, har sautin haɗiyar yawun sai ka ji, tamkar ba lafiya ba!. Kasa ta sauko, su mom suna nan a zaune yacce ta barsu. Ba tare da ta ɗago ta kallesu ba ta karisa gaban mom, cikin girmamawa ta mika mata hannu a kan ta bata baby Ahmad zata je ta yi mashi wanka!. Wani irin mugun kallo mom ta bita da shi, matar nan babu kunya bare tsoron ALLAH a ranta wai bata son Khadijah ta taɓa mata jika, yau ga ikon ALLAH, uwa da ɗanta wai ba za'a bata shi ba, har da wani cewa da ga yau ba zai sake shan nonon Khadijah ba, wanda ya sha a baya ma bata yafe ba da Khadijah ta shayar da shi, shi ba kalar Khadija bane, dan haka yanzu madara zai cigaba da sha. Abin dai is like mom bata da cikakken hankali, yo idan ba rashin hankali ba saboda kin tsani Khadijah sai ki ce yaro ba zai sha nono uwarsa ba? Haka ake rayuwa? Karfi da ya ji zaki raba shi da uwarsa saboda ke gaki uwar mugaye!. Siririn tsaki ciki-ciki Khadijah ta ja yanda ba za su jita ba kafin ta ce. "Mom bana son irin wannan wasa, and sauri nike yi, ina son kwanciya in huta gajiyar wahalar da ni da ɗanki ya yi na kawoni nan". Ta kai karshen maganar tare da sanya hannu ta karɓi baby Ahmad da ɗan karfi. Wato Khadijah ta karo walaƙanci, sai ta nuna tamkar bata san nufin mom ba, ta mayar da abin wasa kawai ta karɓi ɗanta...... AKWAI CASE A WANNAN GIDA!!. Sake baki cike da mamaki mom ta yi tana kallonta, amma bata tanka mata ko ta yi ƙoƙarin kwace Ahmad daga gareta ba, saboda Bobo yana nan, ta kuma san halinsa, idan ya birkice masu ko mahaukacin zaki albarka, baya ji baya gani in ransa ya ɓaci, and tasan irin balai'n son da yake yi wa Khadijah, a kanta zai iya yin komai, lokacin da ta ɓata haukace masu ne kawai bai yi ba, dik wani security na gidan sai da ya ɗanɗani azaba, shi kenan kullum yana zarya a tsakanin Nigeria da Paris dan nemanta, ya rasa dik wani sukuninsa, har ciwo ya kwanta, dan haka tasan komai, ta kuskura ta yi wa Khadijah wani abin yana nan asirinta ne zai tuno, Bobo zai gane ita ta sanya aka mayar da Khadijah Nigeria, dan haka gara ta ja bakinta ta datse har zuwa lokacin da Bobo zai fita ya basu waje. Ita dai Khadijah upstairs ta nufa da baby Ahmad dake ta zuba barcin. Da ido su Pinkish suka bita da kallo, suna son ɗaukar Ahmad amma suna shakkar mom, sai suka yi jugum-jugum. Lokacin da ta dawo ɗakin Bobo ya shiga wanka, hakan yasa ta shinfiɗesa a saman katafaren bed ɗinsu ta wuce izuwa wajen closet ɗinsu. Manya-manyan towels guda biyu masu laushi farare tas ta ɗauko, ta dawo cikin room ɗin, a kusa da baby Ahmad ta kwanta tana daka hamma, barci sosai take ji. Jiransa take yi ya fito sai ta yi wa baby Ahmad wanka su ji daɗin yin barci. After 25 mins da kwanciyarta sai ga shi ya fito sanye da wani bathrobe ɗin, fari kal tamkar wanda ta sanya ɗazun, a lokacin barci ya yi awon gaba da ita. Bai lura da ita a saman bed ɗin ba, da yake bedroom ɗin yana da girma sosai, toilet na da nisa da in da bed yake. Closet ya nufa dan shiryawa. Jim kaɗan ya fito sanye da hoodies milk color a jikinsa, saboda sanyin da ake yi, ya yi bala'in kyau a cikin kayan, ya zura hannunsa a cikin aljihun wandan kayan, sannan ya sanya hular hoodie ɗin a kansa, sai tashin fitinannen kamshi yake yi. Tsakiyar room ɗin ya tsaya, tin da ya kyalla ya ganta shinfiɗe a saman bed ɗinsa ya kafeta da kallo babu ko kyaftawa. A hankali ya taka zuwa wajen bedside drawer, a natse ya zauna a wajen idanunsa gabaɗaya a kan shape ɗinta, ga shi irin kwanciyar da ta yi a miƙe hakan ya baiwa komai damar bayyana, barcin unexpect ne ya ɗauketa. Wani irin yawu ya haɗiye har sai da makogwaransa ya harba, ya yi sama ya kuma yin ƙasa. Ɗan limshe idanunsa ya yi, almost one year ake nema yanzu rabonsa da ya jita a jikinsa, gaskiya ya yi kewa kuma ya yi hakuri da juriya. Ɗan rankwafowa kanta ya yi kamar zai haɗe fuskokinsu, sai kuma ya tsura mata idanu yana mai cigaba da haɗiyar yawu. Da yake barcinta bai yi wani nauyi ba sai ta ji saukar numfashinsa a saitin in da tata yake fita, hakan yasa numfashinsu ya gauraya, tana shakar nasa shi ma yana shakar tata. Jin hakan yasa ta waro idanunta waje a razane. Ai tana ganinsa a miliyan ta yunƙura zata miƙe tana wani ɗaure fuska. Cikin zafa yasa hannunsa ya mai da ita dole ta kwanta, ba don ya yi niyar hayewa kanta ba ya miƙe ya yi mata runfa da faffaɗar kirjinsa, sai ya haɗe hannayenta dikka biyu ya rike da hannunsa ɗaya bayan ya mayar da hannayen nasa ta saman kanta. Ai a fusace ta ce mashi. "Ni ka sakeni, kuma kada ka sake taɓani!". Tana magana tana ƙoƙarin fisge kanta daga garesa haɗe da binsa da wani mugun kallo......... Ɗan bakinta ya bi da kallo, idanunsa ne suke kara rikiɗewa sosai izuwa jajir tamkar wuta, murya tamkar wanda yake a cikin maye ya ce. "My wife, why are you avoiding me? Don't you know that i love?". Yadda ya yi maganar sai ka zaci ba shi ya yi ta ba. Cak ta dakata da ƙoƙarin kwace kanta da take yi, lokaci guda ta dalla mashi wani irin hararar da bata san ta yi ba, kamar zata cinyesa da ido saboda kallo ta ce. "So kuma ni kake yi wa? Ka je dai ka nemi wacce kake so, amma ba ni Khadijah ɗiyar Ahmad ba". Ta kai karshen maganar tana fisge riƙon da ya yi mata da karfi. Ya gama fahimtar yanzu kam bafa zata saurare shi ba, ta yi nisa gaskiya, zuciyarta ya rigada ya bushi a kan abin da tasa a gaba. Ya yi nisa a cikin tinanin da yake yi sai ji ya yi tasa karfi ta turesa gefe. Da karfi ta miƙe zaune, kafin ya farga ta diro ƙasan bed ɗin, ranta a matuƙar ɓace ta ce. "Kada ka sake taɓani, saboda bana sonka, na tsaneka! Idan kuma ka sake taɓani, to ka sani cikin biyu abu ɗaya zai faru, ko dai na bar maka gidan, ko kuma na kashe kai'na na huta da balai'nka tin da dik in da naje ba zaka rabu da ni ba". From the button of her heart ta yi maganar, babu wasa ko karya, zallar gaskiyarta ta faɗa mashi!. Ta kai karshen maganar tare da matsawa ta saɓi baby Ahmad a saman shoulder ɗinta ta nufi toilet. Ai mutuwar kwance ya yi yana binta da kallo, dik zafin ransa da faɗansa yau Khadijah tana faɗa mashi son ranta har tana kafa mashi sharruɗa amma ya gagara furta word, lallai ba shakka yana mutuwar kaunar yarinyar nan ba kaɗan ba, to yanzu me mafita a garesa kenan? Ya jefawa kansa tambayar. Tabbas ba zai iya hakura ya rabu da ita ba, saboda yana sonta, and kuma ya yi mata farin sani, yasan dik abin da ta faɗa zata iya aikatawa, tsab zata iya kashe kanta ko ta bi dare ta gudu, kun san mai hakuri bai iya fushi ba. Bugu da kari shi wlh yanzu a hannu yake, yana son kasancewa da ita, ba zai iya cigaba da hakura ba, menene mafita a garesa kenan?. Ya natsa cikin tinanin mafita ta fito ɗauke da baby Ahmad da ta ƙudundunesa a cikin towels guda biyu da ta ɗauko, ya lafe a saman shoulder ɗinta yana ɗan lumshe idanu alamar barcin bata ishe shi ba. Ganin still Bobo yana kwance a saman bed ɗin ne yasa ta ɗauki pillow guda ɗaya zata nufi saman sofa su kwanta. Cikin sanyin murya game da natsuwarsa ya ce mata. "Zoki kwanta a bed ɗin ba sai kin je wani waje ba". Ya faɗa tare da saukowa ƙasa ya basu waje. Fuskarta a ɗaure tamau, ko kallon in da yake bata yi ba ta juyo ta koma saman bed ɗin ta haye. Da kallo ya bita yana jin tamkar ya fisgota ta zo jikinsa ya ji ɗuminta, sai dai ina, ba zai yi abin da bata so ba a yanzu, dan shi ma kada ya ga tashin hankali. MY PEOPLE'S KU ZO MU TARU MU FAƊAWA KHADIJAH GASKIYAR CEWA BOBO BASHI DA LAIFI, WLH BASHI DA MASANIYAR ABIN DA MOM ƊINSA TA YI MATA, TA DAURE TA YARDA DA SHI TA YAFE MASHI, KADA TA YI ASARAR NAMIJI ƊAYA TAMKAR DA DUBU, ZATA YI DANASANI, DAN YANA SONTA, KUMA WLH TA TAKI BABBAN SA'A A RAYUWARTA NA SAMI PRINCE KAMAN BOBO, AMMA ZATA YI WA KANTA TSAKIYAR DA BA RUWA! KU ZO MU FAƊA MATA IRIN WAHALAR DA YA SHA WAJEN NEMOTA, TA TAUSAYA MASHI TA YADDA DA SHI! IYA WAHALAR NEMANTA DA YA SHA MA KAWAI YA ISHESHI BA SAI TA KARA MASHI BA. Kwanciya ta yi tare da kwantar da baby Ahmad, ta kasan ido ta saci kallon Bobo, sai ta ga ya tsareta da waɗan nan dara-daran eyes ɗin nasa, so take yi ta baiwa baby Ahmad nono dan ya mayar da barci, amma bata son yin hakan a gaban Bobo. Da dai taga bashi da alamar matsawa daga in da yake ko ya dai'na kallonta sai ta jawo bargo ta shige ciki. Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyin gaske kafin ya juya ya nufi waje, jikinsa dik a mace tamkar wanda aka zarewa laka. Parlour ya sauko, nan ya isko Pinkish and beauty suna zaune suna hira, mom ta haura sama. Cikin sanyin murya ya ce. "Come and escort me". Ya yi maganar ba tare da ya dakata da tafiya ko ya kalli in da suke ba. Ai da gudu suka miƙe, har suna rige-rigen rufa mashi baya. Kai tsaye parking lot na gidan ya nufa. Da gudu wani security ya ƙariso in da yake, nuna mashi motar da zai hau ya yi, take securityn ya fito da key ya fito da motar. Gidan baya ya shiga shi da su Pinkish, da gudu security ya ja motar, basu zame ko'ina ba sai wani katafaren shopping mall. Kayan baby dayawa ya je ya lodowa baby Ahmad, dan ya ga naɗosa a towel kawai Khadijah ta yi, babu kaya a jikinsa, hakan na nufin bashi da kaya a gidan kenan. Su Pinkish dai sai kwasan abubuwan da suke so suka hau yi, shi kuwa da kansa ya zaɓanwa baby Ahmad irin kayayyakin da yake so, sannan ya zaɓowa Khadijah nata ita ma, dikka very sexy kaya ya ɗauko mata, masu zafa da ɗaukar hankali, wandunan jeans ɗin nan irin sexy and crazy ya jido mata, yana son ta rinƙa saka masa irinsu, ga shi basa shiri, yanzu in ta saka ma sai dai shi ya kare da kallonta makogwaransa yana sama yana ƙasa saboda haɗiyar yawu, dik ta tashi hankalinsa. Ita kuwa Khadijah barcinta ta hau yi ita da baby Ahmad, basu da wata damuwa abinsu. Ko da Bobo ya dawo da kayan sai ya tadda sun yi barci, bai tashesu ba, kawai ya zube masu kayan a saman carpet, ya koma saman sofa ya kwanta kamar wani maraya ko mara gata. Da yake a gajiye yake shi ma, yana kwanciya ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi. Ba shi ya farka ba sai bayan sallar magrib. Miƙewa ya yi ya nufi toilet. Ga mamakinsa sai ya ga su Khadija har lokacin suma suna barci, bai dai tashesu ba ya shiga toilet. Jim kaɗan ya fito ya nufi closet ɗinsa. Jallabiya ya zura a jikinsa ya zo ya shinfiɗa dadduma. Sai a lokacin ya biya bashin sallolin dake a kansa, ɗazun shap ya sha'afa. Da ya idar da sallah ya duba time lokacin sallar isha'i ta yi, nan fa ya gabatar da sallarsa kafin ya miƙe ya nufi waje. Dinner yasa su Pinkish suka ɗauko suka kawowa Khadijah room ɗinsa, lafiyayyun abinci masu kara kuzari da lafiya. Daga haka ya komo cikin bedroom ɗin nasa, nan ya isko Khadijah ta tashi ta shiga toilet, su Pinkish sun haye masu bed suna ta kallon baby Ahmad tamkar su lashesa saboda so. A tinaninsa idan Khadijah ta fito zata yi masu faɗa tin da ta nuna bata son shi, sai ya ga akasin hakan, domin kuwa da fara'a ta tarbesu har tana ce masu to su ɗauki Ahmad ɗin mana. ALLAH sarki ai bai san time da ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ba, ya ji matuƙar daɗi, yana da daɗi a nuna ana son danginka fa. Ta ƙasar ido ta saci kallonsa jin ya sauke ajiyar zuciya, kara ɗaure fuska ta yi kafin ta wuce izuwa closet zata yi shirin yin sallah. Wucewa shi ma ya yi izuwa balconynsa, ya zauna a saman ɗaya daga cikin sofas dake a wajen, sannan ya ciro wayansa. Number Zash ya kira domin ya bashi shawara, saboda yasan Zash ɗan love ne, Smart dai shiru ne, babu wata shawara da zai bashi in ma bai ce ya rabu da Khadijah ɗin ba tin da bata sonsa, shiyasa ya nemo Zash asirinsa a rufe ko. Lokacin da kiran ta shigo wayar Zash yana a kwance saman katafaren bed ɗinsa yana ƙoƙarin kiran layin Bobo ɗin domin ya ce ya haɗa shi da Pinkish ko kuma ya turo mashi num ɗinta kenan call ɗin Bobo ya shigo. Yau tin da Zash ya tashi da safe tinanin Pinkish yake yi, shiyasa ya ce bari ya nemeta su gaisa, ya shirya cikin sleeping dress ɗinsa, yanzu ba jimawa ya fito daga ɗakin Mama Haulat, ko in ce Gimbiya Haulat, ya barota tare da Leesharh, ALLAH sarki Leesharh ta samu sauki sosai, sai bala'in kewan mijinta da take yi, kunya da kawaici yasa ta ƙasa iya karɓar wayar yayan nata tasa numbersa ta kirasa, da shi a ranta take kwana take tashi, kome take yi tinaninsa take yi. Da farko ta ce ba zata sake kula shi ba, saboda abin da ya yi mata, amma da Mama Haulat ta rinƙa bata baki tana kara tuna mata wannan abin da ya faru a tsakaninsu fa dole dama sai ya faru, kuma ta godewa ALLAH da ya nuna mata wannan rana, miliyoyin mutane suna san ganin wannan rana a rayuwarsu amma basu samu dama ba, dan haka ta godewa ALLAH ta rungumi mijinta, yana sonta sosai, da lallashi da lallami mama Haulat ta shawo kanta ta aminta har take neman ta yadda zata samu damar jin muryansa. Mama Haulat dai ta zage sai gyara yarta take yi, gabaɗaya Leesharh ta canza tamkar ba ita ba, ta yi fresh tana wani glowing, na tabbata Ramish idan ya ganta sai ya susuce. --------------------------🔥 Picking Zash ya yi, cike da kaunan juna suka gaisa kafin Bobo ya bashi labarin dik abin da yake faruwa da shi. Ba tare da nuna wani damuwa ba Zash ya ce mashi. "Irin wannan fushi idan mace ta yi bata saukowa da wuri, dan haka ka nemi abin da take tsananin kauna ka yi mata shi, ta hakan ne zaka fara shawo kanta, sannan ka yi kokarin sanin menene burinta wanda take ganin yana da matuƙar wahala ya cika, sai ka yi ƙoƙarin cika mata shi, kana yin wannan ina tabbatar maka zata zub da makaman yaki ta rungumeka". Cike da jin daɗin kalaman Zash ya ce. "Are you serious my guy?"......... Jinjina kai Zash ya yi haɗe da cewa. "Yeah, ka gwada zaka bani labari, yanzu dai bawa sisterta waya, yau tin safe da tinaninta a rai'na na tashi, kwana biyu ba'a mun shagwaɓa na yi rarrashi ba". Cikin zolaya Bobo ya ce. "Anya Zash babu wata a ƙasa kuwa? Me kuke kullawa kai da ita?". Gyara kwanciyarsa Zash ya yi kafin ya ce. "To idan ma da wani abin ina ruwanka ni da sisterta? Babu ruwanka in ma muna kulla wani abin, kai dai je ka ji da rigimammiyar matarka ka samu damar shawo kanta, ni kuma ka bani sisterta in ji voice ɗinta ta mun shagwaɓa ko zan samu damar yin barci". Shiru Bobo ya ɗan yi, lokaci guda a cikin ransa ya ce ALLAH yasa abin da yake tinani shi ne yake faruwa a tsakaninsu, zai fi kowa farinciki idan Zash ya auri Pinkish, saboda yasan halin abokin nasa, mutum ne da kowa zai zo haɗa jini da shi. "Wai ba zaka bata wayar bane? Kasan halin da nike ciki na son jin muryarta kuwa?". Ya faɗa yana jawo bargo saboda sanyi da ta fara yi mashi yawa. Miƙewa Bobo ya yi ya nufo cikin room ɗin yana faɗin. "Idan ta yi tsami dai zamu ji koma me".......... "Oho dai, ku bari ta yi tsamin sai ku ji, yanzu dai ba zaku ji komai ba". Zash ya faɗa. Ɗan girgiza kai Bobo ya yi, dai'dai lokacin ya ƙariso cikin ɗakin, nan ya iskosu suna cin abinci a tare da Khadijah, ba ƙaramin Musulmin daɗi bane ya rufesa, a ransa ya ce ashe Khadijah tana da kirki sosai haka? Tana kaunar ƴan uwansa! Kai wannan abin ya yi mugu-mugun yi mashi daɗi, dole ma ya kara kulawa da ita sosai. A fili kuma waya ya miƙowa Pinkish yana faɗin. "Ga shi"......... Tana rungume da baby Ahmad ta ce. "Waye ne Yah Bobo?"...... Gabaɗaya kallansa a kan Khadijah ya amsa mata da. "Zash ne". Ai Pinkish bata san lokacin da ta saki wani ƙayataccen murmushi ba, kara wayar a kunnenta ta yi, tana jin voice ɗinsa ya ce. "My rigimammiya". Haba sai ta saka mashi kuka wanda sai da Khadijah ta ɗago tana kallonta, da yake bata saba da halin Pinkish ba sai da bushe da kallonta, ita kuwa beauty da ta saba ai ko ɗagowa bata yi ba, ta cigaba da cin abinci tana faɗin. "Yah Bobo ka zo mu ci abinci a tare". Kamar tasan abin da yake so kenan, aikuwa bai ki ba, ya zauna a tsakaninta ita da Khadijah, kusa da Khadijah kenan. Da sauri beauty ta kara masu abinci a cikin plate ɗin, da yake a plate guda suke ci. A hanzarce Khadijah ta ajiye spoon ɗin hannunta zata miƙe. Satar kallan beauty ya yi, sai ya kalli bata kallonsu, hankalinta na a kan Pinkish dake ta kukan shagwaɓa wa Zash. Ƙasa sosai ya yi da murya wajen cewa. "Please don't let them to know wani abin". Harara ta dalla mashi ba tare da ta yi magana ba, dai'dai lokacin beauty ta juyo da hankalinta a kansu, fuska a ɗauke da murmushi ta ce. "Aunty ki ci abincin mana". Dole ba dan Khadijah ta so ba ta ɗauki spoon ɗinta suka cigaba da cin abincin, har cikin ransa ya ji wani irin daɗi ya lulluɓesa, ko ba komai ya ci abinci da ita yau. Ita kuwa Pinkish ajiye spoon ɗinta ta yi tare da miƙewa ta koma balcony tana cigaba da zubawa Zash shagwaɓar nan tata dake kara rikita shi, ya wani matse pillow a kirjinsa yana rarrashinta. Cike da yarinta ta fara bashi labarin kyan baby Ahmad, har da ce mashi. "Yau tare da shi zamu kwana, ba zan bawa mom ɗinsa shi ba, ka gansa ma a hannuna, Yah Zash ya fi Yah Bobo da Aunty dikka kyau, like angel". Uhm da yake Zash ɗan love ne sai ya ce. "Kada ki damu, idan kina son baby's ai zan baki dayawa waɗan da suka fi baby Ahmad kyau"....... Murmushi ta saki, dik da ta gane nufinsa saboda wayayyiya ce sosai kuma ita ma yar love ce, amma sai ta yi kamar bata gane ba, a ɗan shagwaɓe ta ce. "To Yah Zash yaushe zaka zo ka bani babys ɗin". Kamar mai raɗa haka ya ce mata. "Dik time da kike so zan zo in yi wuff dake"...... Wani irin Musulmin daɗi ta ji ya rufeta, dama ta jima tana son shi, kawai bata son faɗa mashi ne, ta fi son shi da bakinsa ya faɗa mata. "Yah Zash ni fa a shirye nike, ko yanzu ka zo". "Are you sure?". Da sauri ta gyaɗa kai tamkar tana a gabansa....... Wani irin daɗi shi ma ya ji, ƙasa yin ƙasa sosai da murya ya yi kafin ya ce. "To a fara canza mun zuna tukun nan!". Ita dai tana son da bakinsa ya furta yana sonta shiyasa take wani kauce-kauce dan haka yanzu ma sai ta ce. "To Yah Zash wani irin suna kake so in saka maka?".... Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Sunan love dai haka mai daɗi". Ai saboda tsabar jin daɗi bata san time da ta sumbaci baby Ahmad a kumatu ba, sannan ta ce. "To Yah Zash ai iya masoya ne kawai ke sanyawa kansu sunan love, ba yaya da kanwa ba". Yasan ta gane nufinsa, kuma yasan so take ta ji wannan kalma daga bakinsa kai tsaye, dan haka sai ya ce. "To ni ba'a sona kenan?"....... Tana murmushi sosai ta ce. "A'a ana sonka mana, amma matsayin yaya, sai dai kuma akwai wanda ake so matsayin masoyi daban". Ai bai san lokacin da ya zabura ya miƙe zaune ba, muryarsa har tana haɗewa wajen cewa. "Mekika ce?". Tamkar zata kwashe da dariya jin yacce ya yi maganar, amma sai ta ɗan dake tare da maimaita abin da ta faɗa, wato tana da wanda take so. Hannu yasa yana ɗan tausar zuciyarsa, sai da ya yi shiru na tsawon 3 mins ya rasa abin faɗe, har juya mashi sai da kansa ta yi, bai taɓa zatan sonta a ransa ya kai har haka ba sai yau da ta ce tana da wanda take so, ya girgiza. Ita ma shiru ta yi tana ta murmushi tana sauraron yacce yake ta faman sauke ajiyar zuciya. Slowly ya koma ya kwanta tare da kawo pillow, muryarsa har ƴar dashewa ta yi, in a cool way sosai ya ce. "Sorry na yi shiru ko?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e. "Wani abin ne ya zo mun bakatatan unexpected shi ya ja wannan shirun, but yanzu mu cigaba". Da kyar ya iya kai karshen maganar. "Ayya to shikenan, baka tambayi waye nike so ba, nasan kai zaka so shi, kaga sai ka tayani faɗawa Yah Bobo ina son shi ko? Nasan Yah Bobo zai ji maganarka". Tin da ta fara magana baya wani gane me take faɗe, saboda gabaɗaya hankalinsa ya yi nisa wajen tinanin yacce zai yi da soyayyarta dake cikin ransa, ba abin da ya iya ganewa a zancenta face cewa da ta yi bai tambayi waye take so ba. Sai da ya ɗauki a kallah 1 min kafin ya iya cewa. "Wani mai tsananin saa ne wannan?". Miƙewa tsaye ta yi saboda baby Ahmad ya ɗan fara motsawa alamar yana son fara kuka, jijjigasa ta ɗan fara yi kafin ta ce. "Wani ne kyakkyawan gaske kamar kai, kuma shi ma skin ɗinsa chocolate color, and daga royal family yake...........". Bata karisar da maganar ba ya ce mata. "Beb amma kin katsani dayawa, but babu komai zan rama ne". Dariya ta ɗan saki mai ɗan sauti kafin ta ce. "Gaskiya Yah Zash sai dai ka rame ba dai ka rama ba, wai ba zaka bari in ƙarisa zayyano maka haɗuwan beb da nikeso ba?". "ALLAH Pinkish kin sha da rabona ba zan kyaleki ba, gobe dole in zo dan ramawa"..... Kara faɗaɗa murmushinta ta yi, cikin shagwaɓa sosai ta ce. "To Yah Zash kai ma ai ka bani wahala ne shiyasa na rama". Ɗan zaro idanu ya yi!. "Wahalar me kuma na baki?"....... "Ba kai ne ba, kasan kana sona kuma ka barni ina fama da dakon sonka kaki faɗa mun da wuri, da gaske har kasa na kusa bawa wani dama, dan ina ganin kamar baka sona". "Tab ki bawa wani dama fa kika ce?". Kai ta gyaɗa tana faɗin. "E wani ne a school ɗinmu, na kusa fara soyayya da shi, dama ya jima yana neman hakan"........ A takaice ya ce. "Da kuwa na datse harshensa na furta maki love ɗin". Wani irin daɗi ta ji ya lulluɓeta, zata yi magana baby Ahmad ya fara kuka yana jin yunwa. A hanzarce ta ce. "Yah Zash zan kiraka ta wayata". Da yake ya ji kukan baby Ahmad sai bai yi magana ba, ya jinjina kai kawai game da katse kiran. Da sauri ta dawo cikin room ɗin. A lokacin sun kammala cin abinci kenan basu bar wajen ba. Ai Bobo da Khadijah har suna rige-rigen miƙa hannu zasu karɓi Ahmad. Ganin ya miƙo hannu yasa ta janye hannunta tare da mikewa ta koma saman bed. Karɓar Ahmad ya yi ya nufi waje da shi bayan ya karɓi phone ɗinsa. Ita kuma Khadijah ta mike ta koma saman bed, masu aiki beauty ta kira suka gyara wajen kafin ta fito ta nufi bedroom ɗinsu. Ita ma Pinkish cike da zumuɗi ta koma bedroom ɗinsu dan ya je ya kira Zash a waya su cigaba da hira. Garden Bobo ya wuce da Ahmad suka zauna, ya rinka kallan yaron nan cike da zallar so da kauna, shi ma yaron ya yi tsit, ya lafe jikin babansa. Sai around karfe 10 Bobo ya dawo dashi cikin room ɗinsu. Nan ya isko Khadijah ta jima da yin barci, a kusa kusa da ita ya kwantar da Ahmad, sannan ya ja masu bargo, ya rage gudun Ac. Ji yake yi tamkar ya rungumeta ko ya samu sauki, amma tina kalamanta yasa fasa, ya wuce saman sofa ya kwanta zuciyarsa cike da tinaninta, gangar jikinsa cike da kwaɗayin nata, da kyar ya samu barci ta iya yin awon gaba da shi. ASUBA TA GARI!. BLACK WORLD.🔥 Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ======🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ BLACK WORLD.🔥 Dik wani shirinta ta kammala shi, Ronnie har da sayo mata rose dayawa dan tarban Pretty, sai dai shi ya saya mata ne ba dan ta bawa Pretty ba, sai dan ta yi wa Big Bro godiya da shi. Tana tsaka da ɗouki tana kallon rose ɗin fari kall mai shape of heart, an jerasu shape of heart sun yi fitina, ga wani ratsin gold a jiki, sai santin kyan rose ɗin take yi, dan ba karya ya yi kyau kuma bala'in tsada ne da shi. Tana shirye cikin wani dandatsetsen doguwar riga mai bala'in kyan da ya kara fito da kyanta, kun san dressing na birnin gabaɗaya zaku samu rigar irin mai cuff of breast, kamar weeding gown haka, gata fara tas rigar kuma pich da ratsin gold, sai ta kara tsantsar kyau na ban mamaki, ta sanya siririn silky headband a kanta ta yadda ta samu damar warsa jelar golden white hairnta a gadan bayanta, tamkar ka saceta ka gudu saboda tsantsar kyau. While shi kuma Ronnie yana sanye da Three-piece suit masu bala'in kyau da tsada kalar kayan jikinta, anko suka yi, yacce kuka san ango da amarya haka, ga shi gobe suna da party na H-S day ɗinsu da suke ta magana a kansa tin tuni, a yi farinciki da rana ayi kuka da daddare, kai wara tsiyar sai Black Tiger wlh!. ------------------🔥 Tasa Ronnie ya tsaya a tsakar bedroom ɗinsa, ta miƙa mashi rose ɗin fuska a ɗauke da fara'a tana faɗin. "Welcome my lovely sis". Karɓar rose ɗin Ronnie ya yi yana ɗan murmusawa kafin ya ce. "Bari in nuna maki wani abin, tsaya irin tsayuwar da Big Bro yake yi bari in yi maki wani abin". Ba tare da nuna wata mamaki ko kawo wani tinani a ranta ba ta fara ƙoƙarin kwatanta irin tsayuwar Black Tiger yadda yake a buɗe, ta wani buɗe hannu, tana nan ƴar siririya sai ta yi kamar balbela zata tashi sama, wai ita nan ta buɗe kirji yacce Black Tiger yake. Ai Ronnie bai san time ɗin da ya kwashe da dariya ba, cikin dariya ya ce. "Kin ganki kamar wata shamuwa da aka jiƙa a cikin ruwa, ji ƴan siraran hannunki kamar sandar snooker". Ya kai karshen tare da kara kwashewa da dariya har yana dafe ciki. Ɗaure fuska ta yi, yanzu dik irin ƙoƙarin da ta yi wajen kwatanta tsayuwar Big Bro shi ne zai yi mata dariya, gaskiya bai kyauta mata ba. A kufule ta rarumo pillow daga saman bed ta fara kai mashi duka, shi kuwa yana cigaba da tikar dariya, wlh irin yacce ta tsaya ta wani bubbuɗe hannu ne dole sai ta sakaka dariya, ga wani ɗan guntun ga wani uban gown ɗinta da hannunsa na net ne kusan za'a ce bashi da hannu, hakan yasa siraran hannun nata suka kara bayyana, kun san Koreans fa basu da kiba, ƴan shafal suke Ganin yaki dai'na dariya ne yasa ta kama kunnansa ta murɗa da karfi game da jefar da pillow. Da ɗan karfi ya furta. "Wash! Sis wannan fa mugunta ne, kuma kin san ALLAH ya hana mugunta"...... Sake kunnan nasa ta yi ta kama dogon gashin kansa ta ja da karfi tana faɗin. "E ai ba mugunta na yi maka ba, ramako ne". KUN SAN ME YAKE BURGENI DA MUTANEN BLACK WORLD? SUNA KOYI DA ANNABI ISA SOSAI, MATSALAR ƊAYA SHI NE MALAMANSU SUN KI GASGATA MASU ZANCEN ANNABI ISA DA YA CE SHI BA ALLAH BANE BAWAN ALLAH NE, MALAMANSU SUN ƁOYE MASU WANNAN, AMMA TIN DAGA KAN YANAYIN SHIGAR MAZANSU, BARIN DOGON GASHI DA MAZANSU SUKE YI DIK IRIN YACCE ANNABI ISA YAKE YI NE, KUN SAN ANNABAWAN ALLAH BASA ASKIN GASHIN KAI, HASALI MA ASKE GASHIN KAI AYI KWALKWAL YAHUDANCI NE, YAHUDAWA NE SUKE YI, BARE ANNABI ISA SHI DA YA FI KOWA TARA GASHI MAI TSAWO SOSAI HAR BAYA, SHIYASA ZAKU GA DAYAWAN STARS ƊINA GASHINSU YANA DA TSAWO SOSAI HAR GADAN BAYA, TO KOYI DA SHI SUKE YI, AND HAKA RIGUNANSA SUKE MASU MAƊAURI A TSAKIYA SAI YA YAFA MAYAFI, DO MUTANEN BIRNIN BASA YAFA WANNAN MAYAFIN DA ANNABI ISA YAKE YAFAWA, AMMA IRIN RIGUNANSA SAK SUKE SAKAWA. NIMA WANNAN DALILIN YASA NIKE SON NAMIJI MAI BARIN DOGON GASHI SOSAI A LITTATAFAINA, SABODA KOYI DA ANNABAWAN ALLAH, WLH TIN ZAMANIN DA YAHUDAWA SUKE ASKE KAI BA MUSULMI BA, NI NASARA DAGA INA MUSULMAN YANZU SUKA SAMO BATUN ASKI KUMA.....😅 DO INA KAUNAR ANNABI ISA DA TARIHINSA, SHIYASA DAYAWAN LOKUTA NIKE SON SHIGO DA ABUBUWAN DA SUKA SHAFI RAYUWARSA A BOOKS ƊINA, KAMAR RAYUWAR MUSULMI DA KRISTA A KITTAFINA, INA SAN IRIN TUFAFINSA DA IRIN MU'AMALANSA DA MUTANE, YACCE BASHI DA YAWAN MAGANA, BAYA SHIGA CIKIN MUTANE DAN YIN HIRA, YANA DA KAƊAICEWA DUBA DA YACCE YA TASO CIKIN TSANANIN TAKURA DA WAHALA, ANA JEFANSA DA KALMAR MARA UBA, SO YA YI RAYUWAR KUNCI, BABU WALWALA BAYA FARA'A, BAYA MAGANA DA SAURANSU. SHIYASA WANI LOKACI IDAN NA YI RUBUTU A LITTAFI ZAKU GA KAMAR BABU IRIN WANNAN MUTUMIN A DUNIYA, AKWAISU, AMMA A ZAMANIN ANNABAWA, A ZAMANINMU NE DIK BABUSU SUNA CAN SUNA NEMAN KUƊI,🤭 KAZALIKA INA SON ZAFIN ZUCIYA IRIN NA SAYYIDINA OMAR DA SAYYIDINA ALI GADANGA BUSAR YAKI!, INA SON SANYI HALI IRIN NA SAYYIDINA ABUBUWAKAR, INA SON KOMAI DA KOMAI NA MANZON ALLAH SAW!. BA ZAN TAƁA RUBUTUN LITTAFI BABU WASU DAGA CIKIN DABI'U DA HALAYEN MANZANNIN ALLAH BA, DOMIN A KARA YIN KOYI DA SU MATUƘA! --------------------------🔥 Turo baki ya ɗan yi kafin yasa hannu ya riƙo waist ɗinta. Ai a miliyan ta sake mashi gashinsa tana dalla mashi harara. Cike da zolaya ya ce. "Kayan yayana fa na taɓa da kike wani zabura haka". Harara ta kara dalla mashi game da ɗan taɓe baki. "Ni ɗin ce kayan yayanka ko waist ɗin nawa?". Cikin rashin fahimtar nufinsa ta yi maganar........ Siririn murmushi ya saki kafin ya ce. "Dikkanki, yanzu dai ba wannan ba, yi tsayawa mai kyau ki juya baya irin like Big Bro yana tsaye a tsakiyar room ɗinsa ko kuma yana a gaban mirror". Ya faɗa yana gyara rose dake a hannunsa. Tana turo baki ta juya mashi baya tana ɗan gyara tsayuwarta irin na dakewan nan. "Kome zan yi kada ki yi magana, acting like Big Bro zaki yi" . Ya faɗa kallansa a kan kyawawan gashin dake kwance a bayan wuyanta, sai sheki yake yi. Kai ta jinjina mashi game da ta kara dakewa. Step ɗaya ya taka ya matso in da take, slowly ya kwanto da kansa a saman shoulder ɗinta kafin ya zuro hannunsa ta gaba haka, sannan ya kawo mata rose ɗin saitin face ɗinta, muryarsa kamar wanda yake a cikin tsananin shaukin soyayya ya ce. "Thank you so much my Big Bro, na yi farinciki sosai da ka haɗani da ƴar uwata, and na jinjina maka, ba zan taɓa mantawa da kai ba da ka zama sanadiyar na samu ganawa da sister ɗita ɗaya tilo a duniya, this rose is yours, saboda farincikin da ka sanyani a ciki ban san da me zan biyaka ba, amma ga wannan karamar kyauta daga gareni". Ya kai karshen maganar yana raba jikinsa da nata, sannan ya dawo ta gabanta. Miƙa mata rose ɗin yayi. Tana ɗan murmusawa tasa hannu ta karɓa. Matsawa ya yi ya bata sumbata a kumatu kafin ya ce. "Wannan ma karin wani tukuici ne, nagode sosai kuma na ji daɗi". Ya faɗa yana tsai da kallansa a kan idanunta. Lokaci guda suka sakarwa da juna murmushi kafin Sweetie ta yi mashi bodi da rose ɗin, ta yi kamar zata harbesa da shi ya ɗan sunkuya yana kara faɗaɗa murmushi. "My bro na gode da shawararka, da farko kwata-kwata ban yi tinanin in yi wa Big Bro godiya ba idan ya kawo Pretty, amma sai ga shi ka ankarar dani a kan abin da ya dace". Binta da kallo ya yi, a ransa yana saƙa yacce Black Tiger zai ji daɗi idan ta yi mashi abin da ya ce mata, komai taurin zuciyar mutum tana son mai kyautata mata, dan haka dole Black Tiger zai ji sanyi a yayin da zata furta mashi waɗan nan cool words ɗin. A ɗayan ɓangare na zuciyarsa kuma yana murna sosai, saboda yasan wanna abin da zata yi ba ƙaramin gyara tsakaninsu zai yi ba, zai sanyata ta shiga zuciyar Big Bro. Da gudu ta ɗaura rose ɗin a saman bed ta nufi views na ɗakin, da sauri ta yaye curtains na wajen ta fara leƙa tsakar empir ɗin, saboda ta ji karar jirage, a tinaninta su Big Bro ne suka dawo. "Lafiya dai ko?". Ronnie ya tambaya yana nufota....... "I think su Big Bro ne suka dawo, kasan ya ce mun yau zai dawo ba zai kwana ba". Tana magana tana murmushi. A kusa da ita ya zo ya tsaya idanunsa a kan jiga-jigan jiragen dake shawagi a sararin samaniyar empir ɗin. Gabaɗaya jiragen da tambarin sunan Black Tiger a jikinsu, sannan da hoton bakin damusa. A sanyayye ya ce. "Waɗan nan ai ba droms na yaki bane, jirage ne da suka ɗauko solar + hydrogen wato cibiyoyin wutar lantarki mai tsaftar da kuma karfin da wuta ba zata iya yankewa a new palace ɗin Big Bro ba, sai kuma self-healing materials, wato karafa da ke iya daidaita yanayi, irin ko iska, ruwa, zafi or sanyi ake yi a birnin cikin empeir na Big Bro zata kasance da daidaitaccen yanayi, so kayan kara ƙawata new empeir ɗinsa ne". Face ɗinta ne ya ɗan canza, ta so ace sune suka dawo, amma ba komai zata yi dakon jiransu. Cike da farinciki a ranta ta ce. "Bro kasan me?". Juyo da kallonsa a kanta ya yi kafin ya amsa mata da bai sani ba. "Wannan new empeir ɗin na Big Bro bana jin akwai irinsa a duniya, ka duba girman ginin fa, gold ya yi kuka a wannan gini, kalli yacce yake wani irin kyalli yana ɗauke idanu, dik glasses da aka yi amfani da su wajen wannan gini ban taɓa ganinsu ba sai a kan wannan palace ɗin, gaskiya ya yi karshen haɗuwa sosai". Idanunsa a kan kyakkyawan face ɗinta ya ce. "I wish wannan palace ɗin ya ci sunan Omaish red diamond palace tin da kinga da red diamond ɗin nan aka yi kusan rabin ginin". Zaro mashi idanunta ta yi har sai da ya ɗan rage nasa, kara faɗaɗa murmushinta ta yi game da cewa. "Ba dai Omaish ni ba, wane ni, na ma san sunan da za'a saka mashi bai wuce Black Tiger new palace ba". Nisawa ya ɗan yi kafin ya ce. "Uhm wannan empeir da muke ciki ita ce Black Tiger new palace ai, old one da muka baro kuma gold palace sunanta, dan haka ina fatan canjin sunan da za'a samu a sabon nan ya zamana sunanki ne, kai sunanki ne ma In Sha ALLAH". Saboda bata son su ja maganar ya yi tsawo yasa ta ce mashi tana zuwa. Ta kai karshen maganar tare da wucewa tana sakin curtains na views ɗin. Ya gane waskewa maganar take son yi, dan haka sai ya rabu da ita ya bita da idanu kawai. Waje ta nufo, kai tsaye ta wuce bedroom na Black Tiger. Tana zuwa ta shigar da password ɗinsa ta buɗe kofar, tana sanya kai sai da ta sauke wani sanyayyar ajiyar zuciya, take wani Musulmin daɗi ya lulluɓeta, dama tin ɗazun kewarsa kamar ta yi ihu, yanzu da ta shigo side ɗinsa sai ji ta yi tamkar shi ta gani. Wucewa saman swang sofas dake a ɗakin ta yi, luntsama saman ɗaya ta yi ta zauna tana tinanin rayuwar duniya. Gabaɗaya sai ta ji ta damu da baya nan, a ƴan kwanakin nan bata cika yin tinanin Kamran ba, saboda a yanzu soyayyar Black Tiger ya ci karfin zuciyarta, idan ba shi ba bata tinanin kowa!. Ta jima zaune a wajen kafin barci ya fara ɗauketa, da kyar ta iya miƙewa tana zabga hamma ta koma saman dogowar sofa ta kwanta, tana kwanciya babu jimawa barci mai nauyin gaske ya ɗauketa. Shi ma Ronnie kasancewar sun kammala shirya komai da zasu tarbi Pretty, hayewa bed ɗinsa ya yi ya kwanta yana tinanin a wani halin yayansa yake ciki a yanzu!. .......... AFTER SOME MINUTES. Can cikin barci ta ji tamkar an ɗagata sama, sai kuma ta jita a jikin mutum wanda hakan yasa a razane ta waro idanunta. Ai tana warowa kai tsaye sai saman kyakkyawan face ɗinsa da ta karayin very fresh, sai dai kuma alamar yana a cikin damuwa, domin fuskar ta fi ta kullum tamau. Ai a miliyan ta yi blinking eyes ɗinta domin ta tabbatar ba mafarki take yi ba. Aikuwa shi ɗin ne, yana sanye da black pj's a jikinsa, kayan sun yi masifar yi mashi kyau kasancewarsa fari tas cikin bakin abu. Zabura ta yi zata kwace kanta sai ji ta yi ya shinfiɗeta a saman katafaren king bed ɗinsa ya juya tamkar ba shi ba, ya nufi in da Pretty take kwance a balconynsa, yau a tsananin natse yake tafiyarsa fiye da kullum, tamkar jikinsa dik a mace. Lallai barci mai nauyin gaske ne ya ɗauketa, domin kuwa yacce jirage suka rinƙa shawagi a sama kusa-kusa suna kukan nan dik bata ji ba, yacce empeir ɗin ta ɗauki tashi ta ko'ina dik bata ji ba, ko'ina sai da ya amsa Big Bro ya dawo, amma dik bata ji ba, saboda daren jiya bata samu ishasshen barci ba, dik saboda zumuɗin dawowar Pretty, shiyasa barci yakamata mai nauyi. A miliyan ta diro kasan bed ɗin, da gudu ta bi bayansa tana faɗin ina yar uwarta? Ko sannu da dawowa bata yi mashi ba, ita dai yar uwarta kawai. Shi kuwa yana dawowa ya kwantar da Pretty a balcony ya wuce toilet, sai da ya yi wanka ya canza kaya, ya buƙaci abincin da zai ci, sannan ya dawo zai wuce wajen dining area ɗinsa ne ya hangota zata faɗi ƙasa, barci ya yi daɗi har ta kusa faɗuwa bata sani ba, shi ne ya yi gaggawar zuwa ya ɗauketa zuwa saman bed ɗinsa!. Zama ya yi gefen Pretty bayan ya ɗauko bottle water kenan. Da gudu ta ƙariso wajen, idanunta a kan Pretty dake kwance, jikinta har kerma yake yi, tamkar mai tsoron yin magana ta ce. "Pretty ɗita ce wannan?". Ta tambaya tana dawo da kallonta a kansa. Kada ku manta tun Pretty tana da shekaru bakwai Sweetie tazama makauniya, dan haka bata san ainahin kamannin Pretty ba, shekara bakwai ai kunga ita ma ba wani wayau ke gareta ba, so banda kamannin da suke yi matsayinsu idencial da ba zata iya gane Pretty ba!. Yana ƙoƙarin ɓalle robar ruwan ya ɗago da kallonsa a kanta, sai a lokacin ya fara kare mata kallo, ta yi fitina a cikin kayan jikinta, har cikin ransa sai da ya ji wani irin sanyi ganin haɗuwar da ta yi, kamar zai ce wani abin sai kuma ya fasa game da kawar da kallonsa daga kanta, ruwa ya tarbo a hannunsa ya shafa a face ɗin Pretty yana jin wani irin musulmin daɗi da kuma sabon yanayi yana kara shigarsa........ Dik wannan bidiri Ronnie yana can shi ma yana ramakon barci!. Kun san tin da duniyar shaiɗanu suka bar jikin Black Tiger ya koma so sillent over fiye da da can baya, da idan ka mashi magana sau biyu zuwa uku zai amsa, amma yanzu ka yi ta magana ba ya amsawa, magana mugun wahala take yi mashi, wato yanzu ne ainahin siffarsa ta bayyana, ga jinin sarauta dake guda a jikinsa, sai abin ya taru ya yi mashi yawa! Ya zama miskili ajin farko, kallo da ido kawai ya wadatar!. Nannauyar ajiyar zuciya Pretty ta sauke kafin ta waro idanunta a natse. Kai tsaye sai kan face ɗinsa, a karo na biyu ta sake sauke ajiyar zuciya, dan a tinaninta Smart ɗinta ne. Lumshe idanunta ta yi zata fara yi wa Smart iskancin da ta saba. A hankali ta ɗago da kanta ta koma jikinsa, a saman Lion chest na Black Tiger ta kwantar da kanta, ita ta manta a ina take ta suma, kawai zata fara rashin M da ta saba. Hannu tasa ta fara dukan kirjin nasa a hankali, cikin shagwaɓa sosai ta fara faɗin. "Ni ka tashi muje ka rakani in ci abinci, yunwa nike ji". Ai daga Black Tiger har Sweetie babu wanda ya iya kwakkwarar motsi, Sweetie ta yi suman tsaye ganin yacce ƴar ɓul-ɓul ɗinta ta kara kiba da cika, gurun wuyarta so Masha ALLAH. Shi kuwa Black Tiger ji yake tamkar Sweetie ce a jikinsa take yi mashi wannan shagwaɓa, haka kawai zuciyarsa ta ayya mashi ina ma ace Sweetie ce ta iya shagwaɓa yacce Pretty take yi, ai da sai shiru. Jin bai amsa mata bane yasa ta sake cewa. "Ya na ji kirjinka ya kara tauri da girma?". Tana magana tana mashi iskancin da take yi wa Smart, wato tana bin sassan jikinsa da shafa, har zuwa kyakkyawan wuyansa, wanda shi kuma gabaɗaya ya mayar da abin kamar Sweetie ce take yi mashi hakan, kun san ita ma ta iya mashi tsiya har da sumbata wani lokaci!. Lokaci guda abin tamu ta mata ya motsawa Sweetie, wato kishin da bata san shi ba, kun san shi kishi ko ka san shi ko baka san shi ba idan ta motsa maka sai ka yi, abin a jininmu yake, dan haka wlh ita Sweetie bata ma san tana son Black Tiger ba, bata san menene kishi ba, kawai dai ta ji zafin irin yacce Pretty take shafe mashi jiki ne, hakan yasa ta ce. "Omnish lafiyarki kuwa? Kin san shi ne?". A wani irin miliyan Pretty ta waro idanunta waje, domin ko mutuwa zata yi ta dawo muryan Sweetie ba zai taɓa ɓace mata ba. A zabure ta juyo da kallonta izuwa ta in da ta ji maganar. Tamkar a mafarki haka ta ga Sweetie, ai bata san lokacin da ta bar jikin Black Tiger ba, sai ganinta a gaban Sweetie kawai ta yi, ashe muryarta garau yake iskanci ne yasa take magana a shagwaɓe, da karfi ta ce. "Sweetie na?!!". Jinjina mata kai Sweetie ta yi, ai bata san lokacin da ta zunduma wani irin ihu ta daka tsalle ta haye jikin Sweetie ba, da yake Pretty ta fita kiba da nauyi sai suka yi baya gabaɗaya suka zube a ƙasa, ina Sweetie ba zata iya ɗaukar Pretty ba. Binsu da kallo cikin tsantsar farinciki Black Tiger ya yi, farincikin dake a kan fuskar Sweetie it make his day wlh, dik da baya murmushi kuma fuskarsa bata nuna alamar ya ji daɗi ba, amma daga ta ciki ya ji daɗin ganinsu suna farinciki, sai ya ji ya samu gamsuwa da karin natsuwa, har lokacin da Pretty ta haye Sweetie suka tafi zasu faɗi ƙasa tamkar shi ne zai faɗi har ya ɗan zabura kamar zai taresu, sai dai kuma sun rigada sun kai ƙasa, hakan yasa ya mayar da hannunsa da ya buɗe zai taresu izuwa saman kansa, ya ɗan shafa kyakkyawan arabs hairnsa yana binsu da kallo!. (I wish Big Bro ya yi murmushi a wannan lokaci, amma yaki ya yi, fuska tamkar bai taɓa sanin me sakin fuska bama bare murmushi, wai a haka kuma ya ji daɗi, abin da ba zaka gane hakan ba saboda yacce face ɗin take a ɗaure tamau.) Dariya dikkansu suka kwashe da shi Pretty ta sake haye jikin Sweetie tana ambatar sunanta. Cikin tsantara farinciki Sweetie ta ce. "Haba mana my lutiya, kece fa babba, kuma kin fini kiba, ki bari mana ni in haye jikinki, amma sai ki hayeni zaki karyani, ko kin manta kece babba a kai'na ne?".. Kuma kun manta cewa Pretty ce babba ko? To dik wannan iskancin nata ita ce nan babba, in baku manta ba mai black hair aka fara haifa, mai bakin kuka kuma acici ba, wato Pretty, Sweetie ita ce wacce taki yin kuka time da aka haifeta, shiru-shiru yanzu gabaɗaya Ronnie ya mai data rasa kunya ɓeran tanka!. Kara hayeta da kyau Pretty ta yi tana faɗin. "Ai sai ki bari in ji ɗumin jikin naki kafin nan, ko kin manta kema mom ta ce ki kula dani ne?". Rungumeta Sweetie ta yi tana faɗin. "Ban manta ba, shiyasa ai kullum kike rai'na, kuma na cika magamar mom tin da na kula dake dik da bani da ido a wancan lokaci!". Ai a zabure Pretty ta raba jikinta da nata tana faɗin. "You means yanzu kina da ido?". Kai Sweetie ta jinjina mata tana miƙewa tsaye. A karo na biyu Pretty ta miƙe game da daka tsalle ta hayeta tana faɗin. "Wlh ALLAH shi kaɗai ne abin godiya, ni kam yau a ina zan sanya rai'na in ji saukin tsananin farincikin da nike ji ne?". A wannan karon da Pretty ta hayeta ɗin ma sake yin baya-baya suka yi zasu faɗi ƙasa kamar walkiya haka Black Tiger ya taresu. Sweetie ba karfi sai baki da iyayi game da rashin kunyar da take yi wa Big Bro!. Gabaɗayansu suka tafi suka faɗa jikinsa. Da sauri suka kai kallonsu a kansa, take Pretty ta canza murya izuwa na shagwaɓa da ta saba yi wa Smart, a sanyaye ta ce. "Ni kam wai yanaga ka canza dayawa ne? Ka kara haske da kyau sosai kamar ba mutum ba". (Kun san Black Tiger baya fita rana, kai ko inuwa ma baya fita yana ciki kullum, so dole skin ɗinsa zata banbanta da ta sauran mutane, dole su rinƙa ganinsa kamar ba mutum ba, kyansa zata banbanta da kowa, infact dole ya fita daban!!) In baku manta ba ita Pretty bata san fuskar Black Tiger ba, a lokacin da ta suma akwai mask a face ɗinsa, so bata ga yana kama da Smart ba shiyasa yanzu ta ce Smart ne. Dawo da kallonta a kanta Sweetie ta yi kafin ta ce. "Kin san shi ne dama?"...... Kai ta shiga gyaɗawa a kan e ta san shi. A maimakon Sweetie ta tambayeta a ina ta san shi domin su warwarewa juya cewa mutum biyu ne masu kama ɗaya, sai zumuɗin ganinta yasa bata tambaya ba, ta bar zancen tare da cewa ta zo su je ta shirya mata abinci. Ta kai karshen maganar tare da barin jikin Black Tiger, ta ja hannun Pretty suka yi waje.... Yanzu Pretty tana yi wa Black Tiger kallon Smart Tiger ne, ga shi dikkansu basu san mutum biyu ne masu kama ɗaya ba, me kuke tinanin zai faru? Ga Sweetie da kishi, Pretty da son jiki da shagwaɓa!. Sai a lokacin Pretty ta fara bin ɗakin da kallo, mamaki ne ya kamata ganin irin wannan Daula da bata taɓa gani ba, kamar zata tambayi Sweetie ina ne nan, sai kuma ta fasa suka wuce kawai, kun san bata son yawan magana. Da kallo Black Tiger ya bisu da shi har sai da suka kurewa ganinsa, ajiyar zuciya ya sauke a hankali, lokaci guda tinanin Mommah ya faɗo cikin ransa, a fili ya furta. "Meyasa matar nan ta tsaya mun a rai?". Ya yi maganar tare miƙewa ya koma dining area ɗinsa. Ji yake yi tamkar yasa a ɗauko Mommah, yana tinanin Smart sosai, amma ya fi tina Mommah da dalilin dayasa yake kama da Smart over haka, shi da kansa yanzu zuciyarsa ta fara gasgata cewa su ne iyayensa, sai dai kuma ya yi ƙoƙarin ignoring hakan, yaki aminta. Zama ya yi saman chair, take robot suka hau zuba mashi abinci. Cikin natsuwa ya hau ci, yana ci yana tinanin Mommah. Bai wani ci dayawa ba ya miƙe ya koma saman bed ɗinsa, zama ya yi a maimakon kwanciya, a ransa yake faɗin daga wannan sai wannan, shi da ya je neman Spender ya haɗu da abin da ya jefa zuciyarsa a tinani yake neman ɗauke hankalinsa daga kan burinsa na mulkar duniya, shin wai me yake damunsa ne? Dama ya ɗauko Pretty ne dan ya kawota ya bata farinciki ko kuwa dan ya kawota ta bashi Spender? Bai taɓa zatan zai dakata a kan neman cikar burinsa dede da second ɗaya ba a rayuwarsa, sai ga shi abubuwa biyu sun yi mashi kutse cikin burin nasa a lokaci guda, mutanen da suka yi kutse a rayuwarsa da sunan iyaye, da kuma burin da zuciyarsa take yi na son ganin Sweetie tana farinciki ko da shi ba zai yi ba, a dalilin haka ga shi ya gagara koda yi wa Pretty tsawa kan ta bashi Spender, dik saboda zuciyarsa taki aminta ya yi abin da zai sanya Sweetien kuka. WAI YA NE ZUCIYAR BIG BRO? YA KIKE NEMAN KAWO MANA WASU AL'AMURRA A LOKACIN DA MUKE GAB DA SAMUN CIKAR BURINMU NE? NA CE YANE? SWEETIE YANE? KI YI GAGGAWAR FITA RAYUWARMU DAN MU CIKA BURINMU NA MULKAR DUNIYA FA!!. Ya jima zaune yana tinani kafin ya gyara ya kwanta, da kyar barcin huce gajiya ta yi awon gaba da shi. Ba shi ya farka na sai karfe 8 na dare, da kyar ya iya waro idanunsa, zuciyarsa cike tab da tinanin Mommah har yanzu, jikinsa dik a mace ya miƙe ya ƙarisa gaban mirror ɗinsa. Take ya juya magic eyes ɗinsa ya fara ƙoƙarin samo CROWN OF POWER ko zai kalli Mommah ya ɗan ji sanyi a ransa. Sai dai ya yi iyaka ƙoƙarinsa bai iya gano in da take ba a cikin kingdom ɗin, dan haka sai ya ce bari ya yi wanka ya watsake ya sake gwadawa ko zai iya ganinta. Toilet ya nufa zuciyarsa tana tinanin ina Sweetie yau sam bata leƙosa ba, saboda ta samu ƴar uwarta, da haka ya shiga wanka. Ita kuwa Sweetie tana can, sai ɗurawa Pretty abinci take yi, tana barin bedroom ɗinsa kai tsaye ta wuce zuwa ta tashi Ronnie daga barci, sai murna take yi tana tsalle. Ai Ronnie sai da ya ji shocked lokacin da ya kalli Pretty, har ga ALLAH yaga kamarsa da ita, da alama jininsa ya fi karfi da ita a kan Sweetie. Lokaci guda a ransa ya ji ya yi mata, tin da yana sa rai da fatan yayansa ya yi wuff da Sweetie, shi kuma ai sai ya yi wuff da Pretty, shikenan su haɗesu waje guda. (Ni kuma na ce team Smart zaku yarda kuwa? Ronnie zai yi wuff da ƴar tsana, kun fa san Ronnie ya fi Smart iya love, dan haka zai iya sace zuciyarta🤸) Hannu ya baiwa Pretty da nufin su gaisa yana sakar mata murmushi, kun san an ce blood is thicker than water, pretty bata taɓa yarda kowa ya taɓa jikinta ko da sunan wasa, amma sai ga shi tashi ɗaya ta baiwa Ronnie hannunta suka gaisa tana murmushin da a baya bata yi, ko Smart bata yi mashi murmushi, sai gata tana yi wa Ronnie, lokaci guda ta ji zuciyarta ta gamsu da shi, tamkar yacce ta yi saurin sabo da Kamran, haka ta ji Ronnie a ranta, sai take ganinsa kamar Kamran, kun san dik kamannin guda ne, Koreans ne!. Ɗan rungumanta Ronnie ya yi yana kara yi mata welcome, cike da zolaya ya ce da Sweetie. "Sis ɗinmu ta fiki kyau, gashin kai kawai kika fita mai kyau da ɗaukar hankali". Muguɗa mashi baki ta yi kafin ta ce. "Ashe dai akwai abin da na fita kyau ɗin da shi? To wannan gashin da kake gani mom ta ce shi ne kalar gashi mafi tsada a duniya, shi kaɗai ma arziki ne, faɗa mun abin da take da shi mai arzikin rabin gashin nawa?". Tana magana tana wurga mashi hararar wasa. Raba jikinsa dana Pretty ya yi tare da kai hannu zai capkota ya samu damar matse bakin da take murguɗa mashi ɗin nan, sai dai ina, ai yana kawo hannu ta watsa da gudu sai waje tana dariya mara sauti!. Hannun Pretty ya riƙo yana faɗin. "Zo muje in baki abinci, rabu da sis ɗin nan bata ji, kullum haka nike fama da ita". Cike da mamakin kyawawan halayen Ronnie Pretty ta ce. "Amma kana da hali irin na Yah Omar ɗinmu (guyson)". Hannunsa yasa yana cire password na door ya ce. "ALLAH sarki, to ki ɗaukeni a matsayin shi ne kawai". Kai kawai ta jinjina mashi ba tare da ta sake yin magana ba, da haka suka sauko ƙasa, nan ta ga wata sabuwar duniyar da ta gagara hakura har sai da ta tambayesu ina ne nan? Wai dan ma ba ta glass way kuma bata escalator ya biyo da ita ba, elvator suka biyo wanda shi ta saba shigarsa a kingdom of power, ina ga da ta glass way ya biyo da ita wannan mayyar tsoro ba zata taɓa hawa ba, dan zata ce zata faɗo kasa ko kuma ta ce glass ɗin zai fashe ta faɗa kasa, tana ganin kasa da nisa ai yaseen ba zata hau ba. A dining room suka isko Sweetie ta gama zubawa kowa abinci tana jiransu. Pretty sarkin ci take ta hau ci abinta, bata bar kanta a duhu ba, sai da ta ƙoshi cak sannan ta sake tamnayarsu wai ina ne nan?. Dikkansu sai suka rasa ta yacce zasu yi mata bayani, dan haka sai suka ce mata Big Bro royal palace kawai. Kasancewar tasan su Aneesa suna kiran Smart da babban yaya, sai ta zaci shi ne Big Bro ɗin ai, dan haka sai ta bar zancen a haka kawai ta hau yaba kyau da tsaruwar wajen. Ita dai Sweetie yanzu hankalinta gabaɗaya ya yi kan Big Bro, sannan tana son su keɓe da Pretty ta tambayeta ina Spender ina kuma Kamran, tana san samun waɗan nan amsoshi guda biyun! Sai dai kafin samunsu sai dare ta tsala idan Ronnie ya yi barci, sai su haura sama su tattauna, dan haka sai ta danne tambayoyin a ranta suka cigaba da hira har zuwa lokacin sallar magrib, yau saura kwanaki biyar sallah!. A ɓangaren shi kuma Big Bro, shirye cikin wasu irin mahaukatan kayan barci masu bala'in kyau ya fito, wando ce dogowa har ƙasa, sai kuma rigar zuwa gwiwarsa, rigar a buɗe take sai maɗauri a tsakiya, rigar dai zubin bathrobe take da, sai dai kuma kayan silky ne, ya yi fitina a cikin kayan, and ya ɗaure dogon gashin kansa har tsakiyan bayansa, yacce dai gashin gabaɗaya mutanen birnin suke, su fa hakikanin kiristoci ne masu ɗaukar abubuwa da muhimmanci ba kiristoci masu sunan kiristoci kawai ba. Dan haka shi ma yana da dogon gashi sosai har tsakiyar baya dan koyi da Yesu, yau sam bai ɗaure gashin ba, kun san Annabi Isa baya ɗauke gashin kansa, haka yake zubosa side by side, shiyasa suma mutanen birnin basa taɓa ɗaure gashin kansu, sai su rabata gida biyu su sakota side by side, so shi Black Tiger yana ɗaurewa gaskiya, ba zaka taɓa sanin yana da dogon gashi sosai bama sai ya warwareta, gashin nasa bata da cika ne sai tsawo, kun san gashin larabawa ai, ga shi bakinkirin yana sheƙi. Yau ya fito a ainahin kiristoci masu ƙoƙarin koyi da Yesu ɗin da ya saki gashin, ban taɓa sanin yana da wani dandatsetsen cros a wuyarsa ta zallar zinari ba sai yau, da alama ba kullum yake saka cross ɗin ba, idanunsa nan sun kara tura kala alamar akwai abin da yake damunsa, sai tashin fitinannen kamshi yake zubawa. A gaban mirror ya tsaya domin cigaba da gwadawa ko zai iya kallan Mommah. Ɗan limshe idanunsa kaɗan ya yi tare da sake warosu jin alamar an taɓa kofarsa, ajiyar zuciya ya sauke, domin ko bai juyo ba yasan Sweetie ce. Ita kuwa sai lallaɓawa take yi a hankali wai irin kada ya jiyota ɗin nan. Tana sanye da sleeping dress irin na jikin Ronnie, ta baiwa Pretty ma kala ɗaya ta sanya, ta baro Pretty da Ronnie suna hira ta ce masu bari ta je parlourn kasa tana zuwa, ta yi dabara ta ɗauki rose ɗinta ta fito. Shi Ronnie sarai yasan ba wani parlon ƙasa da zata je, Pretty ce bata san karatun ba. Cigaba da binciko Mommah ya yi yana jin takun da take yi na nufosa har cikin ransa. Unexpected ya ji ta kwanto da kanta a saman bayansa, yacce Ronnie ya ce ta yi haka ta yi mashi, ta kawo mashi rose ɗin gabansa, cikin sanyin murya ta ce "Thank you so much my Big Bro, na yi farinciki sosai da ka haɗani da ƴar uwata, and na jinjina maka, ba zan taɓa mantawa da kai ba a rayuwata da ka zama sanadiyar na samu ganawa da sister ɗita ɗaya tilo a duniya, this rose is yours, saboda farincikin da ka sanyani a ciki ban san da me zan biyaka ba, amma ga wannan karamar kyauta daga gareni, please kada ka ce ba zaka karɓa ba ka ji?". Ta kai karshen maganar tare da dawowa ta gabansa tana cigaba da miƙo mashi rose ɗin. To shi tin da yanzu ba dutse bane kuma babu duniyar shaiɗanu, sannan shi ɗin lafiyayyen namiji ne tuni ya ji wata shaukin mai musulmin daɗi ta lulluɓe zuciyarsa, ai bai san sadda ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ba, tin da ya baro kingdom of power yake jin ɗacin rai, bai samu natsuwa gamsasshe ba sai a yanzu, wani irin yanayi ya ji tana ratsa shi. Ya shagala da jin yanayi mai daɗi unexpected ya ji saukar sumbata a saman lallausan kumatunsa, kwata-kwata bai ji time da ta sanya hannunta ta saƙalo wuyansa ba, sai dai ya ji haɗaɗɗen sumbatar da ta yi nasarar karasa jefa zuciyarsa cikin wata iriyar shaukin da tin da ya zo duniya bai taɓa jin irinsa ba, lokaci guda ya jisa tamkar a sararin samaniya, ya ma gagara iya fasalta yacce yake jin kansa. Ganin bai yi mata kuma ko kallon face ɗinta bai yi bane yasa jikinta ya yi mugun sanyi, kamar wacce kwai ya fashewa a ciki haka ta juya gane da ɗaura mashi rose ɗin a saman mirror, a fili ta ce. "Dama na san ba zaka kulani ba bare ka karɓi kyautata, amma please ko ba zaka karɓa kyautar nan ba ka ajiyesa a tare da kai kuma a waje mai muhimmanci, na gode da taimakonka a gareni". Cikin sanyin murya da karyewar zuciya ta yi maganar. Ta kai karshen maganar tare da ɗan matsawa kaɗan zata raɓa gefensa ta wuce. Da ido ya bi kyakkyawan face ɗinta zuwa kan haɗaɗɗen gurun wuyarta, har ta ɗan wucesa kaɗan tana nufan waje, unexpected ta ji saukar hannunsa a saman waist ɗinta, ya jawota ta dawo gabansa, ba tare da ya cire hannunsa daga waist ɗin nata ba ya ɗan rankwafo kanta, kallansa gabaɗaya a kan ɗan bakinta, kamar zai yi magana sai kuma ya ɗan yi shiru. Kallan tsantsar kyansa a kurkusa ta tsaresa da yi, ji take yi tamkar ta sumbaci ɗan bakin bawan ALLAH'n nan, yau ya yi wani fitina, yacce ya saki gashin kan nan nasa sai ya ruɗa mai kallansa, ga gashin na larabawa mai tsananin laushi da sheki, bata taɓa zatan shi ma yana barin gashi irin na mutanen birnin ba sai yau, kuma ya yi bala'in kara fito da tsantsar kyansa. While shi ma abin da yake ji a ransa kenan. In a cool way sosai bai san time da ya furta. "You're so kind, sexy and adorable". Ya yi maganar ne ba tare da bakinsa ta hana abin da zuciyarsa take ayyanawa fita fili ba, ya tsareta da idanu zuciyarsa na ta yaba kyanta shi kuma yana ƙoƙarin dojewa, shi ne dai maganar ta fito fili. Mamaki tamkar ya kasheta, wai yau ita ce Big Bro yake cewa tana da kyau? Abin da mamaki, gabaɗaya hankalinsa a kan kyakkyawan ɗan bakinta da take ɗan motsa shi a hankali-hankali, kamar yana kerma saboda mamaki da kuma ta ɗan fara tsorata na irin kallon da yake yi mata, kuma tin da ba dutse bane lafiyayyen namiji ne tini idanunsa suka fara canza launi, alamar abar gadan ta motsa, jikinsa har tsuma yake yi. Uhm a kan Sweetie ya fara sanin feeling bayan rabuwarsa da duniyar shaiɗanu, kunga kuwa dole idan ya ganta sai komai ya motsa mashi. Sai a wannan lokacin kallanta ya sauka a kan kyakkyawan cross dake ɗaure a wuyansa, take ta ji babu daɗi, bata so hakan ba, amma a zuciyarta ta kuduri niyar rabashi da ita, dama addinin nasa gabaɗaya. Hannunta na rawa ta sanya ta ɗan taɓa kyakkyawan arab hairnsa da ya ɗan zubo ta saman shoulder ɗinsa zuwa kirjinsa, ɗan janye gashin ta yi domin ta samu damar ganin cross ɗin da kyau, dama gashin ya ɗan lulluɓesa ne, dan tabbatarwa yasa ta janye gashi. Wani irin kamshi ne ya kara dukan hancinta na mayukan gashinsa, babban yatsanta na rawa ta ɗaura a saman cross ɗin ta ɗan shafo a hankali. Slowly ya lumshe idanunsa tare da sake warosu a kanta, zuciyarsa ta so ace Sweetie ta iya shagwaɓa kamar Pretty, saboda babu karya ɗazun Pretty ta tafi da shi yacce take ta zuba mashi shagwaɓa. Muryarta na ɗan rawa ta ce. "Big Bro wannan cross ɗin fa? Please zaka iya bani tarihin wanda yake a jikin cross ɗin a tsaye?". Kun san hoton Annabi Isa suke sawa in da suke ikirarin an kashesa an buga kutsa a hannaye, to so take yi ko ta wace hanya su yi muhawarar addini tsakaninta da shi, dan tasan hujojin da zata bashi wlh sai ya musulunta babu shiri, amma shi kuma sam yaki, shiyasa ta ɓullo mashi ta wannan hanya, ta nuna kamar bata san ma'anar cross ba. Sai dai kuma ita ta yi tambayarta kuma ta ji kayanta ita kaɗai, dan shi gabaɗaya hankalinsa ya yi nisa wajen wani tinani, yacce ta motsa lips ɗinta ta yi maganar cross ɗin nan ba karamun kara birkita mashi lissafin ƙwaƙwalwa ya yi ba. Slowly ya ɗan matso da face ɗinsa dab da ita tamkar zai haɗesu, sai kuma ya dakata yana ɗan shakar kamshin perfume ɗinta. Sosai ta tsorata, bare ma da ta tina abin da ya faru rannan a toilet, gabaɗaya sai ta ji jikinta ya hau kerma, a tinaninta wani abin zai yi mata. Ƙasa-ƙasa can ya ce. "Meyasa kika cike neman faɗa and baki da karfi ko na iya ɗaukar Omnish?"....... A tsorace sosai take da shi ta amsa da. "Saboda ina da kai da kuma Ronnie shiyasa bana damuwa zan nemi tsokana a dik in da nike so dan zaku tsaya mun tin da ban da karfi". Ya ilahi ya lillahi wannan magana ta huda zuciyar Big Bro, like wow, wai saboda tana da shi da Ronnie, kenan ta saddakar su ne garkuwa a gareta? Ashe haka ta ɗaukesu da mahimmanci sosai? Wow. Ai gagara yin magana ya yi, saboda bai san me zai ce ba, an burge Big Bro a nan matuƙa. Zame hannunta daga kan Cross ɗin ta yi, tana ƙoƙarin sake yin magana mirrorn bayansu ya ɗan yi kara, hakan yasa ya yi saurin kai kallonsa wajen. Like wow, Mommah ce bayyana a cikin mirror tana zaune saman bed ɗin King suna tattaunawa, bai taɓa zatan jujun tsafin nasa zasu iya ɗauko mashi ita ba, har ya fidda rai sai kuma gata ta bayyana. Ai bai san time ɗin da ya jawo Sweetie ta faɗa jikinsa ya samu damar ganin mirrorn da kyau ba. Ai daga ita har shi sai da suka ɗauke wuta na wucin gadin, a gaggauce ya raba jikinsa da nata saboda wani irin shock da ya yi har tsakiyar kansa, hankalinsa a kan Mommah ya koma yanzu. Da sauri ita ma ta juyar da kallonta izuwa kan mirrorn, lokaci guda ta zaro idanu waje, har voice ɗinta yana sarkewa wajen cewa. "Big Bro wacece wannan kyakkyawar mata mai kama da kai ɗin? Ka ganta kamar sis ɗinka? Wlh tana da kyau sosai". Kun san Mommah na da kyan jiki ba zaku taɓa zatan cewa ita ta haifesu ba, kun ji Sweetie ta ce sister ɗinsa. Dawo da kallonsa kanta ya yi, in a cool way ya ce. "Are you serious tana kama dani?". Kai ta shiga gyaɗa mashi kafin ta ce............. Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ======🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ Dawo da kallonsa kanta ya yi, in a cool way ya ce. "Are you serious tana kama dani?". Kai ta shiga gyaɗa mashi kafin ta ce. "Kuna kama sosai, amma ta fika kyau ma fa, kalleta tamkar ita ta yi kanta, wannan daga gani tana da zuciya mai kyau duba da yacce lokaci guda ta shiga zuciyata kuma kalli yacce face ɗinta yake kyalli alamar mutuniyar kirki ce". Ta kai karshen tana juyowa da kyau ta karewa Mommah kallo. (Kun san masu bin ALLAH da Manzonsa wlh har wani Musulmin kyalli zaku ga face ɗinsu yake yi suna wani walwali na imani, ga su da saurin shiga rai, ki daure ki zama ta kirki domin ki ribaci duniya da lahira, ba zan gaji da kwaɗaita maku zama na kirki ba, saboda ina son mu haɗe daku a aljanna, ina son ganinku cikin rahama) Har cikin ransa ya ji wani irin Musulmin sanyi ta kara ratsa zuciyarsa yacce Sweetie ta faɗi kyawawan kalamai a kan Mommah, bai san dalilin da yasa ya ji Musulmin daɗi a kan hakan ba, kawai dai ya yi farinciki over to over. Kun san aka ce jini ba wasa ba, jini ne kawai dake fusgar tsakanin Black Tiger da mommah, amma dai basa wani kama, ita dai Sweetie ganin kamar kawai ta yi, uwa ba wasa ba ai kun sani!. Shiru wajen ya yi for almost 5 mins, suna sauraron hirar King da Mommah, do shi Black Tiger baya jin larabci, ba tsaginsa bane wannan, ita kuma Sweetie ai kun san da yaren da suke magana kenan a forest, dan haka tana jin dik abin da suke faɗe. In a cool way sosai ya ce. "Kina jin abin da take faɗe ne?"........ Kai ta jinjina mashi alamar e idanunta a kan King dake bin Mommah da kallo, lokaci guda ta rikice, sai ta ga kamar da King da Mommah ɗin ai dik kamanninsu ɗaya, in baku manta ba Mommah ai ƴar uncle ɗin King ne, dik jini ɗaya ne, so ko ba kama ta fuska akwai ta jini da shi ne ma yafi rinjaye da sanyawa aga kama. Binta da ido ya yi alamar yana jiran ta fassara mashi, amma bai yi magana ba, ta gane nufinsa sosai, dan haka sai ta ce. "Cewa ta yi daddyn Omerish tin da abin nan ya jagule har haka, just kawai ka fito ka faɗa mana dikkan abubuwan da suke faruwa, zamu yi maka uziri, sannan nasan Omerish zai fahimceka". Cikin harshen turanci ta fassara mashi. King ne ya yi magana don baiwa Mommah amsa, nan ma dawo da kallonsa a kanta ya yi yana son ta fassara mashi. Cikin natsuwa ta ce. "In Sha ALLAH zan faɗa maku komai, yanzu ki kira mun Omerish idan kin fita, saboda ina son yin magana da shi, sannan ki haɗa mun kan ƴaƴana maza da mata dikka daren yau ina da zama da su, daga karshe dole mu nemo ta yacce aka yi ɗan uwan Omerish ya bar hannunmu, wace kuyanga ce a lokacin take tare da Aleenarh?". Shiru Mommah ta ɗan yi kafin ta ce. "In dai har ɗan cikina ne da gaske, to babu buƙatar mu nemo hanyar da zamu bi domin dawo da shi gida, da kansa zai dawo, yanzu ma ai ba mu muka kawosa nan ba, ALLAH ne ya kawo mana shi ya nuna mana yana raye, dan haka ina da yarda dubu bisa dubu a kan ALLAH! Na tabbata ba zai taɓa bani kunya ba! Domin dik wanda ya yarda da shi baya taɓa bashi kunya! Saboda haka ɗana zai kawo kansa gareni In Sha ALLAH!!". Tin da Sweetie ta fara fassara mashi ya tsare ɗan bakinta da kallo, a ransa yake mamakin irin karfin hali da yarda da UBANGIJI da Mommah ta yi, lokaci guda a cikin ransa ya ce meyasa dik waɗan da suka yarda da ALLAH suke da confidence a kan komai ne?. NI KUWA INA DAGA GEFE NA BASHI AMSAR CEWA DIK DUNIYA ALLAH NE KAWAI ZAKA YARDA DA SHI BA ZAI TAƁA KUNYATAKA BA, SHI NE KAWAI ZAKA BAIWA AMANA YA RIKE MAKA HAR ILLAH MASHA ALLAH, SHI NE KAWAI ZAI BAKA YAU GOBE KA ROKA YA SAKE BAKA, JIBI MA KA ROKA YA BAKA YA KARA KARA MAKA, BAYA TAƁA GAJIYA DA TAIMAKA MAKA MUDDIN KA YARDA SHI KAƊAI ZAI BAKA, KUMA BAYA DA ROWA, GA SHI GAFURURRAHIM KUMA ALIMUL AZIM, SANNAN RAHMANURRAHIM, DAN HAKA MU DA MUKA YARDA DA ALLAH SHI KAƊAI NE DA CONFIDENCE ƊINMU MUKE KOMAI A KAN KOMAI BA TARE DA SHAYI KO DAR-DAR BA BARE SHAKKA BA!!!!!!. Ya kalli yacce Sweetie take da karfin hali ne, bata da tsoro ko shakkar faɗar abin da ta yi niyya ko a gaban waye, kallo yacce ta kare da su Father's a church, karfin halinta yana burge zuciyar Big Bro, abin yana tsuma shi matuƙa, yanzu kuma ya ga Mommah ita ma da karfin hali wai ta yarda ta yi imanin zai kai kansa gareta, abin sai ya yi mashi wani iri, ga shi zuciyarsa ta gagara iya musa maganarta, yana jin kamar da gaske ɗin zai iya yarda suna da alaƙa da shi, ya gagara karyata zancen da zuciyarsa take yi na sune iyayensa. NI KUMA NA CE KAƊAN KA GANI DAGA KARFIN YARDA DA ALLAH, AI IDAN MUTUN YA YARDA DA ALLAH MAGANA IDAN YA YI MA MUTANE BASU ISA MUSA MASHI BA! SABODA ALLAH BA ZAI TAƁA BASHI KUNYA BA! DOLE A YARDA DA SHI! DAN HAKA KO KASO KO KAKI DOLE ZUCIYARKA ZAI YARDA DA MOMMAH CE MAHAIFIYARKA, TA RIGADA YA BAWA ALLAH WANNAN BATU!. Tamkar mai raɗa haka ya ce. "Idan zan tambayeki me kike tinanin yake a tsakanina da waɗan nan mutane me zaki ce?". Ya faɗa yana mai da kallansa kan Mommah. Shiru Sweetie ta ɗan yi na ƴan sakanni kafin ta ce. "If I guessed it right zan iya cewa wannan mutumin daddynka ne, and wannan mata kuma sister ɗinka ce"......... "Your reason?". Ya faɗa game da ɗan satar kallanta ta wutsiyar ido. Nan ma shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Gaskiya wannan mutumin ya yi a matsayin daddynka, ina jin hakan a jikina duba da yacce fuskokinku yake, and wannan mata kuma kaga tana kama da shi, which means ƴarsa ce, kila yarsa babba ce sai kai second born, dik yacce aka yi dai kuna da alaƙa mai karfin gaske" Tin da ta fara magana ya kurawa ɗan bakinta idanu, har cikin ransa yanzu ya ɗan gasgata maganganun su Mommah, da Sweetie ta yi magana yanzu ya shaida, but ya yi ƙoƙarin hana hakan tasiri a ransa, sai dai mother no be wasa oooo, uwa ta wuci nan, dan haka zuciyarsa ta fi karfinsa a wannan gaɓa da dole yasa ya fara ƙoƙarin bincikar gaskiya a kan babansa da ya renesa a nan. Dawo da kallonsa a kan Sweetie dake ta faman kallon Mommah ya yi, dai'dai lokacin ita ma ta juyo da kallonta a kansa, kafe juna da wani lallausan Musulmin kallo mai kwantar da hankali suka yi ba tare da sun san sun yi hakan ba, wani irin kallo mai wuyar fassaruwa ya rinƙa binta da shi, while ita ma kallan da take mashi mai cike da fito da tsantsar abin dake a cikin zuciyarta zuwa kwayar idanunta. Almost 5 mins suna a haka, bai san lokacin da ya matsar da kansa kusa da ita ba, sai ji ya yi numfashin da suke shaka ya gauraye waje guda, ɗan limshe idanunsa ya yi yana sauke ajiyar zuciya, har ga ALLAH Sweetie tana caja ƙwaƙwalwar Big Bro. Can ƙasan makoshinta murya na rawa saboda tsoronsa yadda ya matso kusa da ita ta ce. "Zan iya tafiya Big Bro?". Ya subhanallah, yacce ta motsa baki wajen yin magana sai ya ji tamkar ba zai iya dakatar da kansa daga kissing ɗinta ba, do kun san koma me zai yi mata su ba zasu ɗauki hakan a matsayin laifi ba, dan ba addinin da ya haramta hakan yake bi ba, amma kun san meyasa ko da wasa bai taɓa kwatanta kissing ɗinta ba? Saboda a cewarsa bai ga wata macen da zai yi hakan da ita ba, and baya son raini, sarki yake mai karfin iko, babu ruwansa da mace mai raunin halitta, shi ne yasa almost sau huɗu yana jin kamar ya yi kissing ɗinta amma yana fasawa. Ganin bai amsa mata ba kuma bai motsa ko ya ɗan ja baya da ita bane yasa ta sake cewa. "Big Bro ina jin bar.......". Bata iya ƙarisa maganar ba sakamakon yatsansa da ya yi gaggawar ɗaurawa a saman lausasan lips ɗin nata, yacce take magana a kurkusa da shi baya jin zai iya shanye wannan rana ba tare da ya karya maganarsa na shi bai ga macen da zai yi irin wannan abin da ita ba, shiyasa ya dakatar da ita daga yin magana a kusa da shi haka. Saboda tsoronsa ita kuma yasa gabaɗaya jikinta ya fara ɓari, laɓɓan nata suka fara kerma hakan yasa ya yi gaggawar ɗauke hannunsa daga kansu, saboda wani irin shocked da ya ji ta ratsa shi. Ganin kamar matsala zata iya faruwa ne yasa ta yi saurin raɓawa gefensa ta wuce, ko kaɗan taki yarda ta juyosa wai irin kada ma ya ce ta dawo, har da haɗawa da ɗan saurinta. Slowly ya juyo da jikinsa gabaɗaya yana kallanta, ya jingina bayansa da jikin mirror drawer. Like wow yacce surar jikinta yake motsawa a hankali a cikin wannan kayan barcin nata yasa ya ji ba zai iya barinta ta tafi ba, ya zuba mata waɗan nan idanun nasa da ya canzasu izuwa magic eyes a yanzu. Tana buɗe kofa zata fita kenan sai ganinta ta yi a saman kirjinsa, ko kaɗan bata san ya aka yi ta dawo cikin ɗakin ba. Zaro mashi idanuwanta ta yi tana kara kare mashi kallo cike da mamaki, dik da tasan da magic ɗinsa, amma bata yi zatan zai jawota garesa a yanzu ba. Mayar da idanunsa normal ya yi kafin yasa hannun slowly ya ɗan janye kyakkyawan golden hair ɗinta da ya zubo mata ta saman face ɗinta, wato dan ya samu damar ganinta da kyau kenan. Ganin ta tsaresa da ido kamar wacce ta sume mashi ne yasa ya ɗan hura mata iska mai sanyi daga bakinsa zuwa face ɗinta. Slowly ta lumshe idanun nata tare da ɗan yin baya kaɗan, sai ta yi kamar zata faɗi, hannunsa ɗaya yasa ya tallabo bayanta ya maidata saman Lion chest ɗinsa. Har cikin ranta tana jin yacce zuciyarsa ke harbawa da karfi-karfi, dan kunnuwanta sun kwanta a dai'dai saitin zuciyarsa ne, gabaɗaya bugun numfashinsa ya canza sosai. A hankali ta ɗago kanta da kallonta a kansa, ya fara yi mata irin wannan kallo nasa da zai ɗauki lokaci sosai bai kyafta idanu ba. "Big Bro ina jin barci ne fa! Please ka barni in tafi mana". Take zuciyarsa ta tinano mashi maganganun Pretty a ɗazun, yacce ta yi su cikin shagwaɓa mai ɗaukar hankali, da alama yana son shagwaɓa fiye da yacce ake tinani, dik yacce aka yi halinsa ɗaya da Smart sosai ba iya kamanni suke yi ba, saboda shi ma Smart shagwaɓar Pretty ya ja shi gareta, in zata kwana ta wuni tana yi mashi shagwaɓa ba zai taɓa gajiya da sauraronta ba, to da alama dikkansu kanwar ja ce. Ya so a ce yacce Pretty ta yi magana a ɗazun haka Sweetie ta yi mashi a yanzu, da babu abin da zai hana bai ki yi kissing na ɗan bakin nan nata ba, sai dai ita bata iya magana mai kara motsa sha'awa ba, yacce take magana da Ronnie a koma ina haka take magana. (To ni ya za'ayi ma in bar Sweetie ta yi mashi shagwaɓa?🤔🤭ai dik sanda ta sake ta yi mashi shagwaɓa sai dai ku ji wata labarin ba wannan ba, yo me ya kaini mu da muke da'awa ace ga can malamar da'awar King yana..........🤫 To shiyasa Sweetie dai ba zata iya shagwaɓa ba.🥱 Da'awa muke yi a birnin fa ba love ba!.) Kun san da cewa jinin Smart da Black Tiger abu ɗaya ne! Dan haka Black Tiger zai yi wuya ya iya cin amanar Smart ya ce zai yi kissing na Pretty saboda shagwaɓa da take zuba mashi, ba abanza Mommah ta ce da Smart ya sake Pretty in dai Black Tiger jininta ne to ba zai cutar da Pretty ba, dole Black Tiger zai kula da dik abin da Smart yake so ko ya ki ko ya so, zuciyarsa ce zata tursasa mashi, saboda su ɗin idencial ne, ko da sauran ƴan uwa zasu iya cutar da junansu ban da su gaskiya! Za dai ta burgesa, amma a iya burgewar zata tsaya!. "Yanzu ba zaka barni in je in kwanta ba?". Ta faɗa tana ɗan dafa Lion chest ɗinsa ta gyara tsayuwarta da kyau. Shiru dai bai amsa mata ba, yana cigaba da kallon wuyanta har ya gangaro da kallonsa izuwa saman kirjinta, ga shi ita dai ba bra take sanyawa ba, gabaɗaya kana iya kallan shatin nipples ɗinta a cikin kayan. Ganin bashi da niyar amsa mata kamar wanda aka sassaƙa ne yasa ta sake cewa. "Big Bro na gaji da tsayuwa fa, kafafuna suna mun zafi, please in tafi?"... Sai a lokacin ya nisa tare da ɗan lumshe idanunsa, ya ga tula-talanta gabaɗaya hankalinsa ya kara tashi, kada ku manta shi ma fa jinin Akka ne, kun ga kuwa ya gado abar. Jin cewa ta gaji ne yasa ya ɗagata cak ya ɗaurata saman kirjin nasa alamar ma bai shirya ta tafi ba kenan, wato tin da ta gaji shi bai gaji ba ai. Kwanto da kanta a saman shoulder ɗinsa ta yi, ko kaɗan zuciyarta bata yi danasanin zuwanta wajensa ba, sai ma farinciki da ta tsinci kanta a ciki wanda bata san dalili ba. Slowly ta kai hannunta saman dogon arabs hairnsa dake kwance har tsakiyar bayansa, ɗan shafa gashin ta yi haɗe da bayansa, kamar mai raɗa yacce take kwance a saman shoulder ɗinsa ta ce. "Big Bro gashin nan ya yi maka makurar kyau, ban taɓa sanin kana da shi ba sai yau, amma meyasa ku mutanen birnin nan dikka gashinku yake dogo har tsakiyan baya? Father's na church ma na su har ya zarce tsakiyar baya". Ajiyar zuciya ya ɗan sauke kafin in a cool way sosai ya ce. "Saboda Yesu haka yake"..... Bata yi expecting zai bata amsa ba, sai ga shi ya amsa. Hakan yasa ta kara jin wani mugun daɗi ya lulluɓeta, dama ita tin daga kan yanayin shigarsu ta gane cewa koyi suke yi da Annabi Isa, amma saboda ta ja shi da magana yasa ta tambaya. Kun san da ni namiji ne irin shigar da zan rinƙa yi kenan! Irin na annabawan ALLAH. Riga mai maɗauri, takalma mai maɗauri, yafa mayafi daga kai zuwa jiki, barin dogon gashi mai kyau da tsabta, karatu da rubutu, waɗan nan sune shigar dikkan annabawa except Annabi Adam da ya kasance mai sanya ganye a jikinsa shi da Nana Hauwa'u kafin tufafi su iso. A cikin Alkur'ani da hadisan Annabi (SAW), babu wani bayani kai tsaye da ke nuna cewa wani Annabi bayan Annabi Adam (A.S) ya yi amfani da ganye don rufe tsiraicinsa kamar yadda Annabi Adam da Nana Hauwa'u suka yi bayan sun ci itacen da aka hana su a Aljanna. Wannan labari na amfani da ganye domin rufe tsiraici ya kebanta da Annabi Adam da matarsa Nana Hauwa'u ne kawai, kamar yadda Allah ya ce a cikin Suratul A'raf, aya ta 22. Sai ya ruɗe su da makircinsa (Shaiɗan kenan). Da suka ɗanɗana itacen, sai tsiraicinsu ya bayyana gare su (wato ALLAH ya maidosu duniya ya fitar dasu daga aljanna), suka fara liƙa ganyen a jikinsu. Wannan liƙa ganye don rufe tsiraici ba a ambace shi da wani Annabi ba bayan su Adam. So a lokacin sauran annabawa, mutane sun riga sun samu tufafi da sutura, na so kawo maku tarihin, but yanzu dai babu isasshen lokacin, idan da rabon ku ji tarihin kafin in kammala RAWANIN ZALINCI zaku ji ko a gaba, in kuma babu rabo ku tara a next book ɗina In Sha Allah. ------------------------🔥 "Big Bro to ka barni in je in kwanta ka ji?". .... Tamkar wani karamun yaro haka ya girgiza mata kai alamar a'a shi ba zai barta ta je ta kwanta ba, ya yi hakan tare da ɗaura hannunsa a saman bayanta, tamkar mai ɗan jin tsoron wani abin ya haurar da hannunsa sama, kun dai san yacce yake balai'n kaunar kalar gashin kanta, yana mugun tafiya da imaninsa. Kamar yana tsoro da shakkarta haka ya kai hannunsa saman gashin nata. Ai bai san time da ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ba, slowly ya fara cusa hannun nasa cikin gashin nata, ba karamun razanata ya yi ba, gabaɗaya ta ji tsikar jikinta na wani mimmiƙewa, a gaggauce ta zame hannunta daga cikin nashi gashin ta fara yunƙurin sauka daga jikinsa. Ganin tana ƙoƙarin sanya shi karya maganarsa na cewa ba'a yi macen da zai yi irin hakan da ita bane yasa ya yi gaggawar sakinta shi ma, da sauri ya datse idanunsa dan ma kada ya kara ganta ya gagara jurewa. A hanzarce ta nufi waje ba tare da ta sake waigosa ba. Tana samun damar fita ta watsa da gudu sai bedroom ɗinta. Nan ta isko Pretty kwance har ta yi barci, shi kuma Ronnie ya wuce bedroom ɗinsa, ya jima yana hira da Pretty har sai da barci ta ɗauketa sannan ya rufa mata bargo ya wuce room ɗinsa. Tana shigowa ta wuce toilet, alwalar barci ta ɗauro ta dawo cikin ɗakin. Saman bed ta haye ta kwanta, cikin bargon ta shige, sai dai a maimakon ta yi barci sai ta fara tinanin abin da ya faru tsakaninsu a yanzu, wani kyakkyawan murmushi ta saki wanda ya kara sanyayya zuciyar Big Bro dake tsaye gaban mirror yana kallanta, har cikin ransa yake ji idan ta yi murmushin nan. Ya jima yana kallonta har sai da barci ya ɗauketa sannan ya wuce saman nasa bed ɗin ya kwanta. Sai dai shi ma ya jina kafin ya samu barci, dan tinanin Mommah and Sweetie da Smart sun hana shi sakat, da ya ga abin zai iya kawo mashi matsala sai ya yi amfani da magic ɗinsa ya share tinanin Mommah and Smart a ransa, ya cigaba da tunano murmushin Sweetie da yacce ta rinƙa magana a kurkusa da shi har barci ya ɗaukesa. Sai dai yau a wannan barci ya yi abin da bai taɓa zata ba, domin kuwa yacce ya hana kansa karɓar shawarin zuciyarsa wajen yin kissing ɗinta, dole ya karɓi hakan a mafarkinsa ba tare da ya shirya ba, baya jin ya taɓa mafarkin wani abin da ya shafi jinsin mutane sai kan Sweetie. A hankali ya rinƙa kissing ɗinta cikin mafarki yana kara rungume pillown dake kusa da shi a zuwan ita ya runguma, har yana laluɓar pillown a zuwan jikinta yake yi wa hakan, a mafarkinsa ya damki tula-talanta, a zahiri kuma ya damki pillow. Shiru Ronnie dake zaune kusa da shi ya yi, dan Ronnie ya zo room ɗin ya yi sallar asuba ne, around karfe 6 na safe ne lokacin da ya fara yin mafarkin, Ronnie yana son tashinsa daga barci ne, ya haye saman bed ɗin zai tashesa kenan ya ga yana wani daddamke pillow yana sakin numfashi mai nauyi. Kun san yau ranarsu ce ta Happy and Sad day, shi ne ma yasa Ronnie zai tashesa daga barci domin su shirya. Da farko ya zaci wani magic ɗin yayan nasa yake yi, sai da ya kasa kunne da kyau sai ya ji Black Tiger na sambatu can ƙasa-ƙasa, hakan yasa ya matsar da kunnensa kusa, tsabar gulma irin na Ronnie ma dan ya ji da kyau har da kwantar da kansa a saman pillow ɗin da kan yayan nasa yake. "I really like this your ball and your sexy lips, please hug me tight, play with my nipples really hard, Omaish you're so sexy and sweet". Kaɗan daga cikin sambatun da yake yi Ronnie ya jiyosa. (Saura wata ta yi wa Big Bro dariya, bafa laifinsa bane🙌🥱 mafarki ne, kuma kun san a zahiri ba zai yi hakan ba ai.🥱) Wato da ya daure daren jiya yaki rage zafi da ita ya zubarwa da kansa girma a gabanta ne, shi ne yarinyar nan taki barinsa, ta zo mashi a mafarki zata lalatawa autan ruhohi tarbiyar da tsawon 34 years ake yi mashi!. Haba ai Ronnie yana jin sambatun da sunan Sweetie bai san time ɗin da ya daka tsalle ya haye jikin yayan nasa yana wani irin dariya ba, wannan shi ne mission done! Ya cika aiki tin da ga shi har mafarki ake yi da sunanta ana yi mata sambatu. Dik tinanin Black Tiger a mafarkin ne Sweetie ta faɗo jikinsa, dan haka sai ya damko Ronnie ya fara shafe mashi jiki yana cigaba da sambatu cikin wata iriyar murya mai ɗauke da zallar sha'awa mai karfin gaske. Cikin sauri Ronnie ya rungumesa yana faɗin. "Big Bro you made my day today". Jin sautin muryarsa yasa ya gane bafa mafarki bane yanzu kam, hakan yasa ya waro idanunsa da suke jajir kamar wuta, gabaɗaya gumi yake haɗawa, da sauri ya miƙe zaune yana bin Ronnie da kallo, miƙewa shi ma Ronnie ya yi. Ɗaure fuska sosai Black Tiger ya yi kafin ya ce. "Meyakawoka nan?". Irin ba wasannan. Dariya Ronnie ya kwashe da shi tare da faɗawa jikinsa, bai damu da ya ɗaure fuska ba, cikin shagwaɓa ya ce. "Big Bro please kada ka ce komai, ni tashinka na zo yi ka shirya karfe 7 ta kusa bugawa". Tamkar Black Tiger zai kai mashi duka saboda yacce ya hana shi shigar Sweetie a mafarkinsa, ya gama latseta tsab zai yi mai gabaɗaya Ronnie ya rusa plan, amma haka ya daure game da cewa. "To yi waje tin da ka tasheni ɗin". Ɗago kai daga kirjinsa Ronnie ya yi, sumbata ya bashi a kumatu, a shagwaɓe kamar Pretty ya ce. "Love you my Big Bro". Sumbata shi ma Black Tiger ya bashi, ƙasa-ƙasa ya ce. "Love you too my pleasure". Da gudu Ronnie ya diro ƙasan bed ya nufi waje, yana farinciki ya ce yau da kansa zai shirya Sweetie ta yi kyau over ta kara rikita lissafin ƙwaƙwalwar yayansa, dan kullum ya rinƙa mafarkinta. WATO RONNIE BAYA JIN MAGANA SAM-SAM, BA ZAI BAR BIG BRO YA SAMU PEACE BA KENAN!. Ɗan dafe gefen cikinsa Black Tiger ya yi, saboda wata iriyar murɗa mashi da take yi, mararsa ce ta fara yi mashi ciwo a hankali-hankali, ɗan rintse idanunsa kaɗan ya yi kafin ya juyo game da zuro kyawawan ƙafafunsa kasan bed ɗin. Da kyar ya iya miƙewa tsaye, haba bananarsa tana tsaye zat cikin wandan barcin nasa, ashe dole ma mararsa ta yi ciwo, gaskiya Ronnie bai kyauta mashi ba da bai kyalesa ko da a mafarkin ne ya samu damar zubar da wannan al'amari ba. Toilet ya nufa wasa-wasa mararsa na kara tsananta ciwo. Shi kuwa Ronnie kai tsaye bedroom nasu Sweetie ya hufa. Babu ko sallama saboda tsabar murna, yana afkawa ciki ya yi kanta, tana tsaye gaban mirror ɗaure da towel mai ɗan girman da ya rufe mata har gwiwa, Pretty na zaune a tsakiyar gado tana turo baki wai yunwa take ji, yanzu fa ta tashi daga barci. Ita kuwa Sweetie har ta yi wanka zata fara shiri. Jin an shigo room ɗin yasa ta kai kallanta wajen door. Tana ganin yacce ya shigo yana dariya bata san time da ta juyo da gabaɗaya jikinta tana kallonsa ba. Cike da mamaki ta ce. "What a wonderful surprised that me you......". Bata kai karshen maganar ba ya yi gaggawar zuwa ya riko hannayenta dikka biyu, take ya fara juyi da ita a tsakiyar room ɗin yana murmushi game da tsalle kaɗan kaɗan. Ai sake jiki ta yi ta hau biye mashi suna tsalle suna murmushi. Da kallo Pretty ta fara binsu, lokaci guda suka yi mugun burgeta, sai ta ji tamkar ta yi joining nasu. Cikin ɗan ɗaga murya Ronnie ya ce da ita. "Pretty kunna mana sauti a tvn nan". Yana magana suna cigaba da juyi. Pretty da ba abin da ta iya sai shagwaɓa da cin abince ne ta ce. "Ni ban iya kunnawa ba". Sake hannayen Sweetie ya yi, da sauri ya kunna masu kiɗa suka hau tikar rawa, da karfi da ya ji ya janyo Pretty cikinsu, dole ya sanyata yi. A dai'dai lokacin shi kuma Black Tiger yana can yana fama da mararsa dake ta faman tsananta ciwo, har ya fara tinanin kiran dr Ronnie ya zo ya duba shi, saboda tsananta ciwo sosai yake. Sai da suka tiki rawa mai isarsu sannan Ronnie ya zauna saman sofa yana mai da numfashi. Ita kuma Sweetie ta jingina da jikin mirror, Pretty ta koma saman bed, sai a lokacin Sweetie take tambayarsa wai menene yake faruwa ya sanya shi farinciki har haka?. Kashe mata ido ɗaya ya yi, a natse ya ce. "Zuwa dare zan faɗa maki, yanzu dai zo ki shirya ki yi fitina cikin kayan nan bari in kara dubawa an gama ƙawata hall ɗin nan ne! Kin san ina son ki fi kowa kyau over ne a wajen gasar da za'a gudanar yau". Faɗaɗa murmushinta ta yi kafin ta nufi closet tana faɗin. "Zan fi kowa In Sha ALLAH, yanzu zan shirya". Dawo da kallonsa a kan Pretty ya yi, yau ji yake yi tamkar ya zuba ruwa a kasa ya sha saboda daɗi, shi ko kaɗan baya tausayawa Sweetie, burinsa kawai shi ne yayansa ya sota saboda ya musulunta, a tinaninsa idan ya so Sweetie dole zai musulunta, burinsa ɗan uwansa ya kuɓuta daga hanyar halaka zuwa ta tsira. "Pretty ya ke baki yi wanka ba? Yau fa muna da gagarumin shagali". Tana turo baki ta amsa da. "Ni yunwa nike ji, sai na ci abinci zan yi komai". Ɗan zaro idanu ya yi. "Zo mu je in baki abinci". Ya faɗa tare da miƙewa. Wato ita fa Pretty ko kaɗan bata yi kawar Smart ba, ga dikkan alamu Pretty bata san so ba, kuma bata damuwa da abubuwa, har da yin barci abinta ba tare da ta nemesa ba, yanzu kuma ta tashi kunga ta abinci ma take yi ba ta shi ba, kai Pretty sai shirin ALLAH, shi kuwa yana can tamkar zai yi hauka, a daddafe ya kai wannan sati biyun, kome yake yi tunaninta yake yi, yanzu haka bincike yake yi a kan ina ne Daular Black Tiger yake,dan ba zai iya zama babu ita ba, dole ya je ya ɗaukota ya kuma dawo da yayansa gida, dan ba zai iya rabuwa da Black Tiger ba tin da ya gano yana a raye. Hannunta Ronnie ya riko suka nufi waje dan su je ya bata abinci. Ita kuma Sweetie ta cigaba da shiryawa tana tinanin yacce zata dakatar da su daga yin wannan party na dare da zasu yi dan nuna alhini da koke-koke a kan mutuwar mahaifin Black Tiger, dole ta dakatar da hakan ta koya masu cewa addu'a ake yi wa wanda ya mutu ba wai a shirya party sai an ci an sha sannan ayi koke-koke na ƴan awanni daga nan a sha giya a bugu a hau tikar rawa, mata da maza suna zinace-zinace a bainar nasi, maza da maza suna liyawa wato luwaɗi mata da mata suna les, dole ta dakatar da wannan babbar ɓarna, to amma ta yaya zata faro? Wannan shi ne tinanin da ya tsaya a ranta tin kwanaki uku da suka wuce. ME KUKE TINANIN ZAI FARU A WANNAN RANA?. PARIS.🔥 Lokaci da Khadijah ta farka da safe bata sami Bobo a room ɗin ba, miƙewa ta yi ta shige cikin toilet, wanka ta fara yi kafin ta yi wa baby Ahmad, ta tsara mashi kwalliya cikin ɗaya daga cikin kayan da daddynsa ya saya mashi. Ya yi matuƙar kyau sosai tamkar ka sace shi ka gudu da shi. Da kanta ta gyare ɗakinta tsab, ta zuba perfume na ɗaki kala daban-daban masu daɗin kamshi, ita ma cikin ɗaya daga cikin kayan da Bobo ya saya mata jiya ta shirya, wani kafurin crazy ne wanda ya yi matuƙar fito da surarta, cinyoyinta tamkar zasu fasa wandan, ga shi cinyoyin wandon dik a ɗan tsastsage kana ganin kyakkyawar lallausan fatar santala-santalan cinyoyinta, sai wani kara glowing yarinyar nan take yi abinta, tana tafiya tana juya mazaunai suna kara rikita hankalin Bobo! Bayan sun shirya tsab sai tashin kamshi suke yi ne ta saɓo baby Ahmad a saman shoulder ɗinta ta nufo waje, fuskarta a ɗaure tamau alamar babu mutunci, yau ta ci alwashin tambayarsa wani irin zama suke yi, shin zaman aure ne ko na zina dan ma ta san a wani matsayi take!. Kasa ta sauko, nan ta isko mom zaune saman sofa tana shan green tea. Ba tare da ta kalli in da take ba ta ce. "Good morning". Ta yi maganar tana nufar waje gabaɗaya. Ai mamaki tamkar mom zata natse cikin ƙasa, sai ta rasa bakin magana, wai Khadijah ce yau ko kallon in da take bata yi ba? Kai abin da mamaki gaskiya, yarinyar da dik abin da za'ayi mata bata fasa ladabi da biyayya, har kasa fa da take tsugunawa gaida mom, ni ko na ce kece baki san ya fushin mai hakuri yake ba, ai tama yi maki da sauki dan akwai ɓirɓishin soyayyan ɗanki a ranta, ba dan haka ba zaki yabawa aya zakinta ne, ki godewa ALLAH ma ba da Zee aka zo ba, da kin gane Annabi Isa ba ɗan ALLAH bane Manzon ALLAH ne!. "Ke zo nan". Mom ta faɗa a gadarance. Ba musu Khadijah ta juyo ta zo, dan uwa uwa ce ko a ya take, kuma dik lalacewar uwarka idan aka yi mata ba daɗi har cikin ranka ba zaka ji daɗi ba. A saman sofa Khadija ta zauna don nuna mata girmamawa, bata tsaya a kanta ba. "Gani nan mom, oh ko da yake last time kin ce ke ba mom ɗita bace kada na sake kiranki da mom, to sorry for that, ya sunan da kike son in kiraki da shi?". Bala'in can, ai mom kusan rasa abin faɗe ta yi, eyeeeee lallai Khadija ta zo da walaƙancin da ya sha gaban tinaninta, to dama mu Nigeria ai kada mutum ya so ganin fuskarmu ta walaƙanci, dan ba zata yi mashi kyau ba, a ganmu dai a mutumcin da muka fi shahara!. "Miƙo mun ɗan nan ki tashi ki bani waje". Mom ta faɗa saboda rashin abin faɗe, dama ta kirata ne dan ta ci mutumcinta, to sai taga babu fuska, ba Khadijah ɗin da ta sani a baya bane. Miƙewa Khadijah ta yi. "Wannan shi ne dalilinki na mun kiran ƴan tasha?". Ta faɗa tana ɗan sauko da baby Ahmad. Mom bata amsata ba, ta dai bita da kallo. "Baki buƙatar yi mun kiran ƴan tasha ko kiran nuna iko a kan Ahmad tin da kinga ke ba mom ɗita bace kamar yacce kika faɗa, dan haka ba zaki nuna mun iko ba, and ni ba zan hanaki Ahmad ba, saboda jininki ne kuma first jikanki kenan a duniya da bashi da madadin". BALA'I MAGANA FA KHADIJAH TA FAƊA MATA, WATO KO ZATA MUTU KO ZATA YI RAI AHMAD DAI FIRST JIKANTA NE DA DIK WANDA ZAI ZO DAGA BAYA MA SAI DAI YA BIYO BAYANSA, E LALLAI KHADIJA TA KARO WALAƘANCI! Ta kai karshen maganar tare da miƙo mata baby Ahmad. "Ga shi nan ai, dama shi ma yana son jin ɗumin jikin kakansa a dai'dai wannan lokaci, kin ga safiya ne". Ai mom ji ta yi tamkar kada ta karɓesa, saboda wani irin kululun bakinciki da ya taso mata, ƙoƙarin cusawa kanta tsanar Ahmad ta yi, sai dai ta manta bawa baya ɗaurawa kansa soyayya ko kiyayya, dan haka baby Ahmad jininta ne so dole!. A kufule ta kai hannu ta fisgo Ahmad da karfi, a hanzarce Khadijah ta sake mata shi tana faɗin. "Ba fa sai kin saka karfi ba, kowa ya gansa ya san jikanki ne, saboda dake ma yake kama, kunga no need ki nuna power wajen karɓarsa, dan dole a baki kayanki". Tashin sense, magana cikin magana kenan, mom ta shaki takaicin wannan ma, dan ta rama sai ta ce. "Sunan jikana ba Ahmad ba ne, sunansa Alex, ba zai taɓa zama musulmi mugun iri kuma ƴan'tadda ba". Cike da nuna isa ta yi maganar, wai dan ta shakawa Khadija takaici. Sai dai ko kaɗan Khadija bata nuna ta damu ba, dik da tana tsoron hakan ya kasance, dan tasan mom zata iya rabata da Ahmad kuma ta mayar da shi krista, amma bata nuna kamar ta ji wani abin ba, muryarta a ware sosai ta ce. "To ai wannan ba wani abin bane, zaki iya saka mashi dik sunan da kika yi niyya, bakina kuma bakina ne baki isa ki umarcesa da sunan da kike so ya kira ba, ki kirasa a Alex ni kuma Ahmad, kin ga ai ba komai ko?". Sosai mom ta ji bakincikin yacce Khadija bata ji haushi ba, dan haka sai ta ce. "Ba zai taɓa yin musulunci ba idan ina da rai"...... Siririn murmushi wanda ya fi kuka ciwo Khadija ta saki, sannan ta nufi hanyar barin parlon tana faɗin. "Ai ba wani abin bane, kada ki damu, ba dai kin yarda ɗan da ya kwanta cikin musulma kuma bakar fata jikanki bane? Kuma kin yarda ubansa yana tare da musulma! To ai dik abin da zai biyo baya nafila ne". WATO SAI MAI BASIRA ZAI GANE KALAMAN KHADIJA, BAKA KIRIN TA GASAWA MOM. Ta kai karshen maganar tana ficewa waje abinta, burinta ta sanya mom ta fara ja baya da ɗaukan mata yaro, kuma da alama zata yi nasara, domin mom ta ji tsananin bakinciki na kalamanta na karshe cewa Ahmad ya kwanta cikin musulma kuma har ma ya sha nononta, dan haka sai ta dakawa Khadija tsawa a kan ya zo ta ɗaukesa ko kuma ranta ya ɓaci. Wani irin Musulmin daɗi ne ya lulluɓe Khadijah, dama ta yi mashi wanka ne domin ta kaisa ga daddynsa su gaisa sai ta samu damar tambayarsa wani irin zama suke yi, dan haka ranta ya yi fari tas da mom ta ce ta zo ta karɓesa. Da sauri ta juyo ta dawo, tana zuwa tasa hannu ta karɓesa, da ɗan karfi mon ta dungura mata shi. Bata damu ba ta karɓesa ta wuce waje. Kai tsaye garden na gidan ta nufa, dan tasan Bobo yana wajen, bawan ALLAH damuwa ce ta yi mashi yawa ya koma can ya zauna ko zai rage abin da yake ji. Ƙasa ƙasa ta yi sallama kafin ta shigo. Yana zaune saman ɗaya daga cikin lutsuma-luntsuman sofa's dake wajen karkashin wata kyakkyawar runfa ta shan iska. Ai tin da ya hangota ya kafeta da ido tamkar ya tashi ya je ya rungumota yake ji, amma sai ya daure ya bita da kallo har ta iso shi. Sallama ta sake yi mashi, a maimakon ya amsa mata sai ya ɗaure fuska sosai, cikin harsh voice ya ce. "Haka kika fito kika keta gabaɗaya masu aikin gidan nan kika zo nan?!". A tsawa ce ya yi maganar, kun san fa kishi a jininsu yake, jikin King Abdul Malik basa ɗaga kafa fagen kishi. Ganin yacce ya ɗaure fuska ne yasa ta sha jinin jikinta, dan tasan muguntarsa, idan ransa ya ɓaci baya duba in da yake nufa. Kasa ta yi da kai bata amsa ba. Wani irin tsawa ya daka mata wanda ya sanyata razana ta ɗan yi baya har tana ƙoƙarin faɗuwa ƙasa. Miƙewa tsaye ya yi yana binta da wani irin kallo mai wuyar fassaruwa, ba dan yana tsananin sonta kuma yana neman sulhu ba da babu abin da zai hana bai tattakata a wajen ba. Jikinta ne ya hau kerma, gabaɗaya ta ji harshenta ya yi mata mugun nauyi ta rasa bakin yin magana, takowa ya yi step biyu ya iso gabanta yana kara daka mata tsawa, take ya rikiɗe tamkar ba shi ba, yana wani huci. Baya-baya ta fara ja tana ɗan girgiza mashi kai. Cigaba ya yi da takowa yana dalla mata wani irin kallo mai kama da harara yana jiran ta bashi amsa. A haka har suka kure wall ɗin wajen, tsayuwa ta yi tana tsuru-tsuru da eyes tamkar an tare ɓera a tarko. Hannunsa ɗaya yasa ya dafa wall dake bayanta, da yake ya ɗan fita tsawo sai ya ɗan rankwafo kanta. "Ba zaki amsa mun ba sai na yi ball dake?". Ya faɗa babu alamar wasa a tattare da shi!. Ita kuwa ji take yi tamkar idan ta bashi hakuri ta faɗi, hakan yasa ta ja bakinta ta yi shiru, abin da ya kara kona mashi rai kenan, cikin fusata ya ɗaga hannu zai dalla mata mari, saboda yana ganin wannan shirun da ta yi mashi ai raini ne. Sai dai kuma yana ɗaga hannu ta yi gaggawar sanya baby Ahmad a tsakaninsu ta kare face ɗinta da shi tana sakin ƴar karamar kara. Aikuwa shi ma baby Ahmad fashewa ya yi da ihu wanda ya sanya daddynsa dakatawar dole, da wlh ya yi niyyar sauke mata wannan mari saboda bala'in kishi irin nasa!. Hannu yasa ya karɓi baby Ahmad ya rungume a kirjinsa, take ya ɗan ji sanyi a ransa, harara ya dallah mata kafin ya juya ya koma saman sofa ya zauna yana ɗan jijjiga ɗan nasa dan ya yi shiru. Ita kuwa turus ta tsaya a wajen tana tamkar koma cikin gida, amma tana son samun amsar abin da ta zo tambaya, lokaci guda idanunta suka cicciko da kwallah, da ta tuna ya ɗaga hannu zai mareta sai hawayen suka fara zubowa da karfi. Sake jikinta ta yi ta durkushe a wajen ta fara ruwan hawaye, shi kuma yana can yana aikin jijjiga baby Ahmad ya yi shiru. Ban fa yi editing ba na yau tom, idan kun samu typing errors sorry. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️ Sake jikinta ta yi ta durkushe a wajen ta fara ruwan hawaye, shi kuma yana can yana aikin jijjiga baby Ahmad ya yi shiru. Tamkar a mafarki haka ya tsinkayo shasshekar kukanta a kunnansa, ai bai san time da ya ɗago da kallonsa a kanta ba. Lokaci guda ya ji zuciyarsa ta yi sanyi, dik zafin kishin da wani huci da yake yi ta gudu. Nisawa ya ɗan yi, a hankali ya ciza laɓɓansa kafin ya miƙe ya nufota, ba shi da zaɓin da ya wuci rarrashi a yanzu. A gabanta ya tsugunna tare da mai da Ahmad saman shoulder ɗinsa yana ɗan shafa bayansa a hankali. Hannu ya kai ya ɗan share mata kwallah dake zuba, in a cool way sosai ya ce. "Am so so sorry". A hanzarce ta ɗago da kallonta a kansa, bata yi zatan zai taɓa ce mata sorry ba a rayuwarsa, saboda bai taɓa kwatantawa ba, ALLAH sarki zuciyar mace mai rauni, take ta ji ya bata tausayi. Hannu yasa yana cigaba da goge mata hawaye dake zuba sannan ya kara binta da sorry. Wlh bata san time da hawayen nata suka dakata da zuba ba, sai gani ta yi ya miƙe ya riko hannunta, miƙar da ita ya yi, sakin hannunta ya yi ya riko shoulder ɗinta, kaɗan ya ɗan rungumota a jikinsa tamkar yana tsoron haɗa jiki da ita, ba komai ne yasa hakan ba kuma face gudun masifarta. Lokaci guda ya sauke wani Musulmin ajiyar zuciya na jinta a jikinsa bayan tsawon lokaci. Bata kwace kanta ba, domin tana san samun amsoshi daga garesa, sannan ita kanta daurewa kawai take yi, amma tana kewarsa over to over. Saman sofa ya wuce da ita, a hankali ya kwantar da baby Ahmad a gefe, sannan ya zaunar da ita a kusa da baby Ahmad ɗin, bai yi magana ba ya cigaba da binta da idanu yana kallon yacce take murza yatsun hannunta. A karo na biyu ya sake cewa. "Am so sorry". Kai kawai ta iya jinjina mashi ba tare da ta furta word ba. Zama ya yi a ɗayar sofar yana kallanta cike da tsantsar sha'awarta game da kauna. Almost 10 mins for silent sannan ta ɗan gyara murya kafin ta ce. "Ina son tambayarka in babu damuwa". Kai ya ɗan jinjina mata. "You can go ahead". Ya faɗa yana ciro wayarsa daga aljihunsa saboda yar karar da ta yi alamar shigowar sako. "Zaka iya faɗa mun matsayin me muke zaune ni da kai?". Ta yi maganar tare da ɗan ɗagowa ta kallesa. "Whyn't?". Ya faɗa yana kunna screen light na wayar. "To ina son sani ne". Kai ya ɗan jinjina mata, hankalinsa a kan wayar ya amsa da. "Zaman mata da miji mana". Ɗago kallanta gabaɗaya a kansa ta yi, with full surprise ta ɗan waro idanunta game da cewa. "I didn't understand"..... Cak ya ɗan dakata daga ƙoƙarinsa na latsa wayar, slowly ya ɗago da kallonsa a kanta mai gabaɗaya, idanunsu ne suka sarke a cikin na juna, gabaɗayansu tsananin kewar juna suke yi, sannan ga kaunar juna dake kwance a cikin kwayan idanunsu. Da kyar ya iya controlling kansa, ya daure wajen fara magana a natse sosai. "Ke matata ce mana, don't you know that?" Kai kawai ta iya jinjina mashi alamar e bata sani ba, ta gagara yin magana, kazalika ta gagara cire idanunta daga kansa, taga ya kara tsananin kyau, zuciyar mace kenan, wai tausayawa ƴar ramar da ta ga ya yi take yi, mu mata kullum da raunin zuciyar nan tamu ake amfani a cutar damu!. "To idan baki sani ba yau kin sani, you're my sunnah wife". Ɗan kara zaro mashi idanu ta yi, lokaci guda kuma ta sauke ajiyar zuciya, tamkar mai tsoron yin magana ta ce. "Waye ya baka aurena to?". Kai tsaye ya amsa mata da. "Your Dad". Ai a miliyan ta wani irin zaro idanun da sai da suka ɗan bashi tsoro, tamkar kwayar idanun nata zasu faɗi ƙasa, muryarta na rawa, word ɗinta na sarkewa ta ce. "My....... My dad.......... kuma?". "Kina tantama ne?". Kai ta shiga gyaɗa mashi tamkar ba zata dakata ba. Ya fahimci ta ruɗe dayawa jin cewa babanta ya bashi aurenta, dan haka sai ya gyara zamansa, cikin natsuwa ya fara magana kamar haka. "Akwai wani lokaci da muka je Africa buga wani wasa, so i visit one of my friend in Nigeria, Kano state bayan mun gama buga wasan a South Africa kenan, if i could remember around 3 to 4 o'clock, mun fita ni da wannan friend ɗin nawa da sunan zai kai ni yawo in ga Kano state before jirginmu ya ɗaga, dan a ranar zan koma, in that day I saw you and your sister lokacin da muke tafiya, ban damu ba, so a time ɗin ma ban ganki da kyau ba, sai da muna dawowa, mun sake biyowa ta arearku, kin zo zaki tsallaka titi saura kaɗan mu bugeki, i think you abused us also a wannan time ɗin, saboda lokacin da muka wuceki na juyo ina kallonki, i saw this your small mouth like you're shouting abusing us, do na so dakatawa a wannan rana na yi magana da ke, kasancewar muna sauri zan koma time na fly ɗina ya yi ne yasa na wuce". Ɗan dakawa da yin maganar ya yi lokacin da ya kawo wannan gaɓa, sakamakon kara zaro mashi idanu da ta yi, dan tabbas ta tina wannan rana da ya yi magana, nasan dayawa daga cikinku kuma kun tina a ranar da ta fita sayawa daddynta magani, har wasu motoci suka kusa bugeta, to a ranar yana a cikin motocin. Gera guda ya ɗaga mata alamar lafiya? Ɗan lumshe idanu ta yi tana girgirza mashi kai wato babu komai, mamaki take yi yacce aka yi ya fahimci ta zagesu a ranar, dan fa ta zaga ɗin kam. "So if I could remember bayan na koma cikin ƴan uwana mun baro Afirka mun dawo nan Paris, this your beautiful face and small mouth for abusing people's ɗin ya tsaya mun a rai, komai nike yi i was thinking about your face, abin har ya fara fin karfina, hakan yasa na fara bincikan who're you? Through that my friend I got all information that I want, hakan yasa na ware lokaci special na yi wa Nigeria zuwan bazata, ban nemi ganinki ba, kai tsaye na sami daddynki a kasuwa, ban ɓata lokacina wajen faɗa mashi abin da ya kawoni ba, da farko bai yi accepting ba saboda ya ce ya yi maki miji". "A farkon na dawo ba da karfin gwiwa ba, after some days na sake komawa Nigeria saboda na ji ba zan iya hakura ba, a karo na biyu tare da Zash muka koma domin ya tayani bawa daddynki hakuri kan ya bani ke, sai dai mun taki babban sa'ar da ban yi expecting ba, saboda muna zuwa ya ce ya amince ya bani ke bisa wani sharaɗi, bai nemi sanin waye ni ba, hakan ya yi matuƙar bani mamakin da yasa na yi binciken meyasa ya bani ke kai tsaye bai nemi sanin waye ni ba? Sannan ya ce sharaɗinsa shi ne sai dai a ɗaura mana aure a wannan rana amma ba zan ɗaukeki ba sai bayan wani lokaci da zai faɗa mun idan lokacin ya yi, na yi mamaki sosai, sai dai da na yi bincike sai na ga ya yanke wannan hukunci ne saboda bashi da zaɓi, and baya son ya ganki cikin kunci, baya son aura maki ɗan uwanki da kakanku ta matsa a baki dan baki son shi, wannan ne dalilinsa na gaggawar bani ke ba tare da sanin waye ni ba, and kuma ya kafa mun sharaɗin dole a ɗaura auren a wannan rana". "Na yi accepted hannun bibbiyu, dan dama burina kenan, Zash ya zama waliyina, abokan daddynki a kasuwa suka zama shaida, a wannan zuwa ta biyun aka ɗaura mana aure, sai dai ya hanani tafiya dake, amma ya ce zan iya zuwa in ganki ba tare da kin sani ba, baya son mu haɗu a lokacin, hakan kuma aka yi, na je har school ɗinku na ganki, amma ke baki gannin ba, daga nan muka dawo Paris ni da Zash, kullum sai na kira daddynki, na damu sosai a kan ya bani matata, bcos i really love you". Dakatawa ya yi da ya zo wannan gaɓa, saboda ya fito mata da sakon zuciyarsa da yasa sai da ya ji wani irin sanyi ta ratsa shi. Kai Bobo ya so Khadija, soyayyar gaskiya yake yi mata, sau ɗaya fa ya ganta, kuma yana cikin mota, kawai ta kwanta mashi a rai, ya tsallake gabaɗaya matan Paris ya zo ya ɗauketa, lallai ba shakka bai cancanci wani hukunci daga gareta ba face soyayya, saboda ya taimaka ya rabata da Haidar, uhm gaskiya ya yi namijin ƙoƙari. Cigaba ya yi da cewa. "Ban taɓa rokan wani abin a rayuwata ba sai a kanki, kullum sai na roki daddynki da ya barni in zo in ɗaukeki ko kuma in zo in ganki, sai ya ce mun a'a tukun nan in jira, so the thing made me very angry over, bcos i love to much Khadija, I has your pics alot in my phone wanda kuma daddyn naki da kansa ya tura mun su, kullum ina shiga tashin hankali idan na ga hotunanki kuma bakya tare da ni, before in yi barci sai na yi ta kissing wayata saboda hotonki, kice a kan dp, wallpaper da ko'ina a wayata, na yi haukar sonki matuƙa". Ya yi maganar game da nuna mata wayarsa yana kunna wutar screen ɗin. Uhm hotonta tin tana school, sanye da uniform a jikinta, hoton ne a home screen ɗinsa. "Bani da zaɓin da ya wuce in turo a ɗauka mun ke, saboda hakurina ya kare, wannan dalilin yasa na turo aka ɗauko mun ke, and I knew that I made I big mistake na hakan da na yi, bcos daddynki bai cancanci haka daga gareni ba, ya bani ke ba tare da sanin waye ni ba, ya tsallake ɗan uwansa na gida ya bani ke, wannan dalilin yasa na ƙasa yarda in haɗu da shi, dik time da zan je Nigeria bana bari mu haɗu, saboda i did wrong to him, wannan shi ne gaskiyar abin da ya faru". Ya kai karshen maganar yana kashe wutar screen ɗin wayarsa, ya ajiye a gefensa. Slowly ya ɗago da kallonsa a kanta. Me zai gani? Ai sai ruwan hawaye ya gani ya gama wanke mata fuska. TO KUKAN ME TAKE YI. Zaro idanu waje ya yi, gently ya miƙe ya iso gabanta, tsugunnawa a wajen ya yi game da sanya hannu ya riƙo hannayenta dake saman laps ɗinta, muryarsa a sanyaye ya ce. "For give me Khadija, for give me please". Kuka mai karfi ne ta ji ya zo mata, abubuwan sun cushe mata a makogwaro, yau ya dawo mata da mutuwar babanta sabo, wato shi fa bai ma san babanta ya rasu ba, idan an barshi wai ɓoyewa baban yake yi idan ya je Naija, ALLAH sarki, sai yanzu ta tabbatar da cewa Bobo bai cancanci walaƙanci daga gareta ba, saboda shi ne zaɓin babanta, ko dan babanta yakamata ta so shi ta kuma kyautata mashi, sannan ashe mijinta ne na sunnah, ALLAHU AKBAR!. SAI DAI BA ZATA RAGAWA MOM BA!. Shi kuwa a tinaninsa kukan abin da ya yi mata take cigaba da yi, hakan yasa ya cigaba da bata hakuri yana tausanta. Gagara jurewa ta yi, da sauri ya miƙe, yana ƙoƙarin riko hannunsa da kyau ya hanata motsawa, sai dai bai kai ga yin hakan ba ta watsa da gudu ta nufi hanyar fita tana sakin kuka mai sautin gaske. Ɗan dafe kansa ya yi, cikin wani irin yanayi na damuwa ya miƙe, da kyar ya iya kai hannu ya ɗauki baby Ahmad da ya mayar da barci abinsa. A saman shoulder ɗinsa ya saɓa Ahmad, sannan ya nufi bin bayanta. Mom na zaune a parlon Khadija ta zo ta wuce da gudu tana kuka, taɓe baki mom ta yi tana dallah mata mugun harara, sannan ta miƙe ita ma ta yi sama tana jan tsaki, su Pinkish dai tana can manne da waya tana karyawa da love words daga Yah Zash, beauty dai da bata da masoyi tana ta zuba barci abinta. Mom na haurawa sama ya shigo cikin parlon, kai tsaye bedroom ɗinsu ya wuce. A natse ya yi mata sallama, tana zaune saman sofa tana murzan kukanta. Saman gado ya wuce ya kwantar da baby Ahmad sannan ya dawo in da take zaune. Kasa saman carpet a kusa da ita ya zauna, kaman ɗazun ya kai hannu ya riko hannunta cikin nasa, muryarsa na ɗan sarkewa a sanyayye sosai ya ce. "Khadijah, I knew that I made a big mistake, and I hot you more, please for give me, i will correct my mistake In Sha ALLAH". Hawaye tamkar an buɗe tap, kai ta shiga girgiza mashi, da kyar ta iya cewa. "Babu wani mistake da ka yi, idan ma akwai mistake to bai wuce rashin faɗa mun gaskiya da wuri da kuma ranar da na fi buƙatar kasancewa tare da iyayena ka ɗaukeni ba, a wannan rana da ka ɗaukeni na ji zafin da har yanzu zuciyata ciwo take yi, domin a wannan rana ne mahaifiyata take buƙatata sama da ko yaushe, bayan haka baka yi wani mistake ba". Idan baku manta ba ita tin daga wannan rana bata sake ganin mamansu ba, bata ga gawar babansu ba, kunga dole ta ji zafin ɗaukar tata da ya yi, shi kuma bisa rashin sani da zuciya yasa ya ɗauketa, ya yi ta yi wa babanta magiya a kan ya bashi damar zuwa ya ɗauketa, amma yakiya, shi ne yasa zuciya ta ɗebesa ya turo aka ɗauketa, sai kuma ya yi a ranar da bata dace ba. "In dai har da gaske ban yi wani wrong thing ba to please ki daina kukan nan kin ji? Bana son ganin kina yi". Kai kawai ta shiga girgizawa. "Kukan ne sun ki tsayawa, ba zasu tsaya ba, just ka barni in yi kawai". Slowly ya kwanto da kansa a saman laps ɗinta, cikin tattausar murya ya ce. "Kin bani dama in dakatar da kukan?". ....... Kai kawai ta iya gyaɗa mashi alamar e, hakan ba karamun daɗi ya yi mashi ba. Miƙewa ya yi tare da kai hannu ya ɗauketa cak, bai direta a ko'ina ba sai a saman bed ɗinsu. Shinfiɗeta ya yi tare da hayewa, ya yi mata rumfa da faffaɗar kirjinsa, abin nema yau ta samu, nan ya matsar da face ɗinsa dab tata, tongue ɗinsa yasa ya fara lashe hawayen nata. Cikin wani irin yanayi ta sanya hannu ta kankame kirjinsa tana cigaba da kukanta. Hawayen nata ya cigaba da lashewa har ya gangaro da tongue ɗinsa dai'dai saitin ɗan bakinta, zira harshen nasa cikin ɗan bakin nata ya yi, at the same time suka ja doguwar numfashi tare da saukewa a hankali, kara ƙanƙamesa ta yi tana sakar mashi numfashi mai nauyi, while shi ma ya kara ƙanƙameta da kyau yana cigaba da wasa da harshensa a cikin bakin nata, kan kace me sun birkicewa juna. Take ya fara huce haushin jira na tsawon lokaci. BABY AHMAD NA BARCI IYAYENSA ZASU SAMO MASHI SISTER OR BOTHER 🙌🥱 🔥🔥 *CROWN OF POWER* 🔥🔥 Zaune yake a saman sofa a parlonsa, gabaɗaya ya yi rama sosai tamkar ba Ramish yaron Mamarsa ba, yanzu sam baya shiga cikin family, su mama sun dai'na ganin walwalarsa, amma dik da haka matar nan babu alamar nadama a tattare da ita, wato koma me zai faru sai dai ya faru ba zai zauna da Leesharh ba kenan! Yanzu yana yin kwana biyu bai je ya gaida mama ba, dan baya son shiga in da take sam-sam. Wayarsa dake ɗan gefensa ne ta fara ruri alamar shigowar kira, at the same time kuma message ya shigo cikin wayar. Massage ɗin ya fara buɗewa ya duba, sakon Smart ne in da yake ce mashi anjuma ya same shi a room ɗinsa. Nisawa ya yi kafin ya bi private number da ake kiransa da shi da kallo. Bai yi picking ba har kiran ta katse, dan bai san mai kira ɗin ba. Yana ƙoƙarin mayar da wayar ya ajiye kenan kiran ya same shigowa, still kamar ba zai ɗaga ba dai, amma sai ya daure ya ɗauka tare da karawa a kunnensa. Shiru ya yi yana sauraro ya ji waye ne, sai dai shiru ba'ayi magana ba, hakan yasa shi ya ce. "Hello............. wanenne?". Sanyayyar ajiyar zuciyar da ta sauke saboda jin voice ɗinsa ne yasa ya iya gane wacece, domin kuwa shi ko a cikin duhu yana iya gane kalar sautin numfashinta. Slowly kamar wanda yake a cikin duniyar almara ya ce. "Aesh!". Ya yi maganar tare da miƙewa tsaye, a ƙagare yake da son jin ta amsa ya ji daddaɗar voice ɗinta. "My best amount the best's". Ta faɗa game da rushe mashi da kuka mai ɗan sauti. Ai a take ya ruɗe, kukan ya fi komai ɗaga mashi hankali, muryarsa har tana sarkewa wajen cewa. "Please Aesh ki dai'na wannan kukan kin ji?". Cikin kuka ta ce. "My Yah Ramish dole in yi kuka, i missed you over to over, please zaka iya zuwa in ganka?". Ai bai san time da ya amsa mata da zai zo ba, shi dai burinsa kawai ta yi shiru. SOYAYYA ZATA SANYA RAMISH ZUWA MASARAUTAR MAKIYA, KAI WATO LOVE FA HEGIYA CE, TASA KA KA JI TAMKAR KANFI KOWA KARFI A DUNIYA......😅 "For sure Aesh zan zo gareki, zan zo in ɗaukeki, please ki kula mun da kanki kin ji?". Ya faɗa yana aikin kai komo a cikin parlon, kamar ba lafiya ba. Ɗan tsagaita kukan nata ta yi kafin ta ce. "Zan kasance mai dakon ganinka, please Yah Ramish kada ka jinkirta wajen zuwa, domin akwai zuciyar da bata san komai ba face sonka a kan gaɓar mutuwa wanda kai kaɗai ne zaka iya cetarta". Ba ƙaramin daɗin kalamanta ya ji ba, dan haka sai ya ce. "Tabbas zan zo in ceci wannan zuciya ba tare da ɓata lokaci ba, ki faɗawa mama Haulat cikin satin nan zanzo". Ƙasa sosai ta yi da murya, kamar mai raɗa ta ce. "Idan ka zo zaka ɗaukeni in kasance tare da kai?"......... "Kina son hakan ne?". Ya faɗa yana zama saman sofa. Kai ta gyaɗa tamkar tana a gabansa, tana daga kwance saman bed ɗinta, wayar Zash ta ɗauka ta ɓoye number, dan bata son ya san da number da ta kirasa, sannan bata son Zash ya san ta kira, shi ne ta ɓoye number a zuwan idan sun gama waya zata goge kiran in ya zo kada ya gani, ta gagara jure rashinsa ne, hakurinta ya kare yau. "E ina son kasancewa da kai, ka zo kawai ka ɗaukeni". Cikin zolaya ya ce. "Amma kuma ba da kuka kike mun har da cewa ke mama zaki bi ba zaki zauna da ni ba?". Tamkar tana a gabansa tasa hannu ta rufe fuska tana dariya ƙasa-kasa. "Kai Yah Ramish kai ma ai kasan miji daɗi ne da shi, kuma musamman ma mijin da ake so kuma yake sonka, ya fi komai daɗi a duniyar nan". Lokaci guda kalamanta suka saukar da Musulmin daɗi a zuciyarsa, amma sai ya ce. "Meyasa kika ce hakan?". Cigaba da ɓoye fuska ta yi kafin ta amsa da. "Saboda kai zaka bani abin da su mama ba zasu iya bani ba and soyayyar miji da mata dake kaunar junansu wani abu ne da babu irinsa a duniya, ai ha a banza ALLAH ya ce miji ya fi uba ba, muddin mace ta yi aure to mijinta ya fi mahaifinta, kuma mama ba za........". Ƙasa karisar da maganar ta yi saboda nauyi da ya yi mata, shi kuwa tin da ta fara maganar daɗi ya lulluɓesa, ya rasa abin faɗe, yau Leesharh na neman dawowa wajensa, lallai ba shakka UBANGIJI baya taɓa yin ba dai'dai ba, ba banza ya fifita miji kan uba bayan aure ba. ANYA JIKOKIN AKKA NAN BABU WATA AYAR TAMBAYA KUWA, DIK MACEN DA SUKA KASANCE DA ITA BATA IYA RABUWA DA SU, KU DUBI MAHNOOR DA JAISH, ITA DA TA CE YA YI YAJI ZATA KOMA WAJEN BAPPA, JAISH NA SANYATA A ƊAKI KUN SAKE JIN BATUN YAJIN NAN KUWA? GA CHUCHU HAR KIRAN WAYA TAKE YI A ZO A BATA AL'AMURRA. KAI KUZO MU JE AKKA TA FAƊA MANA ME SIRRIN, KUN JI LEESHARH NA NEMAN DAWOWA GIDAN MIJINTA DA KANTA, AMMA FA BAN GA LAIFINTA BA, HAKA KAWAI TANA CAN WATA TA YI MATA WUFF DA SHI, DAMA GA SHI GUYSON YA CE MATA MASU SON YAH RAMISH SUNA DAYAWA!. Cike da kaunarta ya ce. "Dole in zo in ɗaukeki Aesh ɗina, saboda na ga alamar za'a iya samun matsala idan ban zo ba". Harshen damo ya yi mata a magana, wato daga ƙarƙashin harshenta ya gano tana sha'awarsa ne, amma bata san hakan ba, gara ya je ya ɗaukota kada a samu matsala, to sai dai matsalar ta yaya zai iya shiga kingdom ɗinsu lafiya ya fito lafiya? Uhm akwai cakwakiya dai kam. ---------------------🔥 Zaune Mahnoor take a saman sofa a parlonsu, Jaish ya tafi office yau, tana rike da ɗayar wayarsa tana buga game, Mahreen ta tada kai da cinyarta suna hira na tsakanin ƴan uwa, cikin zolaya Mahnoor ta ce. "Gajin bappa kema fa yakamata ki yi aure, kinga Yah Jaish ya ce zamu je Jimeta kwanannan, to ki samu mijin da zaki je Jimeta da shi a ɗaura aure in ba haka ba a baiwa Hamma Faisal ke a cika alkawarin". Tab kamar Mahnoor ta sani, dan kuwa bappa ya tabka alkawari wa Faisal cewa ya bashi Mahreen, yanzu jira ake yi kawai su je, sai aurenta da shi, shi ma Faisal ɗin yanzu ya saduda ya karɓi Mahreen ɗin, dan yasan ya rasa Mahnoor kenan. "Tab ni me zan yi da wani Hamma Faisal, kinga Adda Mahnoor ki dai'na bana so, wai baki ji Aunty Chuchu ta ce ni matar manya bane? Shi kuma Hamma Faisal ai yaro ne". Uhm Faisal fa ya girmi guyson amma take ce mashi yaro to shi kuma guyson jariri ne kenan a gabanta, Chuchu dai ta kara lalata Mahreen da ta ce lallai matar manya ce ita, ita kuma bakauyar ana nufin manya masu daloli a hannun ta tsaya tana duba shekaru, ko uban me zata ci da shekarunsu?. Mahnoor zata sake yin magana Mahreen ta rigata da cewa. "Adda Mahnoor kin san me wancan uncle Taheer ɗin ya ce mun jiya?". Kai ta girgiza mata kafin ta ce. "A'a ban sani ba sai kin faɗa". Ta yi maganar tare da kashe wutar screen ɗin wayar ta ajiye a gefe, sannan ta dawo da hankalinta a kan Mahreen ɗin, yaran nan dik sun saje da larabawa, sun kara kyau abinsu, Mahnoor sai kara kiba take yi wuya na cikowa, Jaish na bata abin da ya dace ga kulawa ziryan da take samu, madarar soyayya babu mix, ita ma Mahreen ta ɗan murmure kaɗan. "Wai jiya ne da zan je part ɗin su Aunty Chuchu na haɗu da shi a hanya, shi ne ya ce in zo, da na tsaya na ce mashi ni ba zan zo in da yake ba dan bappana ya hanani zuwa wajen maza, shi ne ya ce ai aureni ma zai yi gabaɗaya dan bayan Auta babu macen da ta kwanta a ransa sai ni". Da sauri Mahnoor ta zaro idanu, cike da zolaya ta ce. "Bappa ya hanaki zuwa kusa da maza amma kike zuwa kusa da Yah Omar ko?". Mahreen duniya kuke ji, kai tsaye ta ce. "Yah Omar ai yaro ne, bappa kuma manyan maza ya hanani, kuma shi ma Yah Omar ɗin ai bana zuwa kusa da shi sai idan kwalliya zai yi mun" Ɗan girgiza kai Mahnoor ta yi, Mahreen akwai shegen son girma da rai'na mutane, yanzu Omar ɗin ne yaro, kai wannan yarinya sai shirin ALLAH. "To yanzu ke kina son uncle Taheer ɗin ne?". Mahnoor ta jefa mata tambayar tana shafa kyakkyawan gashin kanta da ya sha gyara sosai. "E kinga ai shi babban mutum ne, kamar yadda Aunty Chuchu ta ce ni matar manya ce, kin ga yana da girma". A hanzarce Mahnoor ta ce. "A takaice dai kina son shi ko?". Zata yi magana sallamar guyson ya karaɗe kunnuwansu, fuska a ɗauke da fara'a Mahnoor ta kai kallonta kansa, ita ma Mahreen fuska ba yabo ba fallasa ta yi mashi sannu, kada ku manta yanzu ana bashi girma dan ya iya make up. Hannunsa rike da kwalin sabuwar waya dal ya kariso in da suke, saman sofa ya zauna yana faɗin. "Good evening Aunty Mahnoor". Kallansa gabaɗaya a kan Mahreen. Ita kuma Mahnoor tana kallonsa, a ranta tana jin guyson son Mahreen yake yi, yaki fitowa ne kawai ya faɗawa kowa, dan haka ta kuduri niyyar faɗawa Jaish yau, dan in dai yana son Mahreen to ba zata barta ta fara son uncle Taheer ba!. Amsa gaisuwar tasa ta yi tana cigaba da kallonsa, ko kaɗan ya kasa kawar da kallonsa daga kan Mahreen, ga shi ta yi kyau cikin riga da wandonta, kan dai babu ɗankwali, "Mahreen wajenki fa na zo". Ya faɗa yana ɗan yi ƙasa da kai, wai kunyar Mahnoor yake ji. Da sauri ta miƙe zaune, binsa da kallo ta yi kafin ta ce. "To gani nan". Shiru ya ɗan yi ya gagara yin magana, saboda kunyar Mahnoor. Ta fahimci hakan dan haka sai ta miƙe ta nufi bedroom ɗinsu tana faɗin. "Ina zuwa". Tana tafiya ya yi gaggawar dawowa kujerar kusa da Mahreen ɗin, muryarsa ƙasa-ƙasa sosai ya ce. "Zaki zama kawata please?". Ɗan zaro mashi idanu ta yi. "Kawa da namiji kuma?". Kai ya ɗan gyaɗa mata. "Kin ga ni dake ai yaya da kanwa ne, so zaki iya zama kawata kamar yacce su Auta suke kawayena". Shiru ta ɗan yi kamar mai wani tinani, can kuma sai ta ce. "Iskanci dai ba kawa ba, ka taɓa ganin mace da namiji sun zama kawaye ne idan ba iskanci ba?". Ɗan zaro idanu ya yi, a bakin Jumma ta ji zancen wannan iskanci fa, amma har ta rike. "Ba iskanci bane ga na gida, ga na waje ne iskanci, ni ba yayanki bane?". Harara ta ɗan wurga mashi kafin ta ce. "Bafa ka fini da wasu shekasu masu yawa ba, dan haka kai ba wani yayana babba bane". Jinjina kai ya yi, cikin sanyin murya ya ce. "Les say ni kaninki ne ma, ba zaki iya yin abota da kaninki ba?,". Jin ya ce mata kaninta ne shi yasa ta saki murmushi har sai da kyawawan fararen hakwaranta suka bayyana. "To idan zaka rinƙa ce mun Aunty Mahreen zan yarda mu yi abotar tun da ni auntynka ce kai kuma kanina". Da sauri ya ce. "Na yarda Aunty Mahreen, zan rinƙa faɗa, yanzu ki yi alkawarin mun zama abokai?!". Ya kai karshen maganar tare da ware mata tafukan hannunsa ɗaya. Da sauri ta ɗaura nata tafin hannun saman nasa tana faɗin. "E mun zama abokai kanina". Murmushi ya yi har sai da dimples ɗinsa suka lotsa. "To Aunty Mahreen ɗita rufe ido in baki wani abin". Haba ai wani Musulmin murmushi ta saki jin ya kirata Aunty, wayyo daɗi kasheta. Da sauri ta datse idanunta. Kwalin wayar hannunsa ya buɗe ya ciro wayar, hannunta ya kama ya damka mata wayar yana faɗin buɗe to. Da sauri ta waro idanunta, ai tana ganin wayar bata san time da ta daka tsalle game da cewa. "Yanzu wannan waya ta ce?". Jinjina kai ya yi. "Kwaraikuwa Aunty Mahreen". Uhm kuruci dangin hauka, wani ihu ta kurma game da dakata tsalle ta yi sama ta sake faɗawa saman kujerar tana dariya. Da gudu Mahnoor ta yo waje, dan a tinaninta wani abin ne ya faru. Mahreen na ganinta ta diro kasa da gudu ta yi kanta tana faɗin. "Yah Omar ya saya mun waya, kin ganta sabuwa". Mayar da kallonta a kan guyson Mahnoor ta yi, sai sakin cool smile yake yi, hankalinsa ya kwanta tin da ta yi farinciki, sai sauke ajiyar zuciya yake yi. Yanzu Mahnoor tagama gasgata cewa guyson son Mahreen yake yi, lallai akwai case kuwa. Sallamar Jaish ce ta dawo dasu cikin natsuwarsu dikkansu, da gudu Mahreen ta yi kansa tana yi mashi oyoyo, buɗe hannu ya yi ya rungumeta gabaɗaya kallansa a kan Mahnoor ɗinsa, kun san yanzu ya dawo cikin tinaninsa, so ya koma yacce suke da Mahreen a Jimeta, tana zuba mashi shagwaɓa yana lallashi da nuna kauna. Lallaɓawa guyson ya yi ya gudu, dan yasan Mahreen sai ta faɗawa Jaish ya saya mata waya, kunya yake ji shi kuma. Aikuwa yana fita ya jiyo muryarta tana faɗawa Jaish ga sabuwar wayarta, da yake gabaɗaya hankalinsa na'a kan beb ɗinsa, dan shigarta ya tafi da shi, tana sanye ne da riga da wandon jeans kusan irin na jikin Mahreen, ta yi kyau sosai, ga shi dik wasu albarkasu na jikinta sun bayyana, sai gabaɗaya komai ta motsa mashi. Hankalinsa baya a kan Mahreen sosai, sai ya amsa mata da to ta je ta nunawa Momma. Ya faɗa tare da raba jikinsa da nata, aikuwa da gudu ta yi waje ta nufi part ɗin Mommah. Shi kuwa gera guda ya ɗagawa Mahnoor alamar ya ne?. A natse ta tako izuwa in da yake, tana zuwa ta faɗa jikinsa tana faɗin. "Sannu da dawowa". At the same time suka sauke sanyayyar ajiyar zuciya, rungumota da kyau ya yi yana shafa mazaunanta a hankali. Take yanayinsa ya canza, ƙasa da murya sosai ya yi wajen cewa. "Me tauraruwata ta ajiye mun?". Ba tare da ta yi magana ba ta riko hannunsa cikin nata, ɗan raba jikinsu ta yi game da ɗan yin gaba, bayanta ya bi suka nufi bedroom ɗinsu. Suna shiga ciki ta sake faɗawa jikinsa, cike da tsananin kaunarsa ta ce. "Me habibi ya yi tsammanin samu daga noor?". Sumbatar goshinta ya yi kafin kai tsaye ya ɗaura hannunsa a saman kirjinta da suke kara cikowa sosai kullum, saboda ya iya wasa da su sosai. (Kun san idan har namiji ya iya wasa da kirjin mace to the way yake wasa da su the way suke kara girma sosai, ba dan kunya ce da ni irin naq Hoorain ba ai da na faɗa maku wata sirri, amma na barwa kai'na kayana.🥱) Ɗayan hannunsa kuma ya ɗaura saman mazaunanta. "Habibi yana tsammanin samun waɗan nan abubuwa daga noor". Ya faɗa yana fito da tongue ɗinsa waje, kai tsaye ya ɗan lashi wuyarta kaɗan. "Za'a bani ne?". Ya tambaya yana ɗan lumshe idanu tamkar wanda yake a cikin maye, ko da yake yana cikin mayen love dole ku ga hana. WAI NI INA BATUN JAWAD YA ZUBAR MASHI DA MUTUNCI NE? YANZU KENAN YA GANE MATA BA'A YI MASU WANNAN GARAJEN KENAN! "To ai dama mallakinka ne". Ta faɗa tana sanya hannu ta fara balle botiran rigar jikinsa, wato shi ma Jaish sai da ya koyar da Mahnoor wannan jaraba ta su, ko da yake dole ma ai ta koya, irin wanna alamari haka, da yamma ma ba za'a hakura ba, da safe ayi, dare ayi, rana ayi, Jaish sai shirin ALLAH, ai dik wanda zai auri jikokin Akka sai ya shirya. Wani irin mayen love ce ta ɗebesa ya ɗan matsa tula-talanta kaɗan, ya hanata sanya bra, ya ce zata matsa mashi, ya fi son koyaushe ya kai hannu ya taɓasu kai tsaye. Kara narke mashi ta yi da ya ɗan matsa tula-talanta, a lokacin ta gama cire botiran rigansa, sai ta raba shi da kayan ta ɗaura saman sofa dake kusa da sh. Hannu tasa ta zuge zip na wandansa kasa, bayan ta raba shi da wandon sai ta tura hannunta cikin short ɗinsa, already bananarsa ta miƙe zat, kai tsaye ta kamota tana ɗan shafawa, da ɗan karfi ya furta ash kafin ya kara matsa mata tula-talan nata da karfi. Ita ma kara matsa bananarsa ta yi wanda hakan yasa ya ɗauketa cak sai saman bed, ya shinfiɗeta game da hayewa, nan fa ya fara abin da ya saba, kafin kiftawa da bismilla ya rabata da komai na jininta ya hau sarrafata!. --------------------------🔥 "My Aesh to mu yi video call in ganki mana". Ya faɗa game da miƙewa ya koma cikin bedroom, dan ya ji daɗin murza kalaman love ɗinsa, yayin da Mommah and King suke can suna tattaunawa kan mafita da kuma gaskiyar abubuwan da suka faru a baya, ƴaƴansa suna nan suna bawa flowers ruwa, ita kuma Zarina sai gagarumin shiri suke yi. Wlh shirin da suka yi ba'a taɓa yin mai girma irinsa ba a tarihin yaki, dik sun tsara yacce zasu shafe kingdom ɗin, kuma wlh yadda suka tsara bana jin block guda ɗaya zai iya raguwa a kingdom ɗin in suka iso. Akwai case fa, shi dai Smart yana can yana shirin tafiya Black World, shiyasa ya nemi ganin Ramish, dan shi kaɗai zai sanarwa tafiyar tasa!. "Yah Ramish to in kiraka da number mama sai mu yi video call ɗin?". Kamar zai tambayeta wannan number waye ne, sai kuma ya fasa ya ce ta kirasa yanzu da number mama. YAU ZAI GA AESH BAYAN TSAWON SATITTIKA!. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 Cike da zumuɗi ta katse kiran, goge call ɗin ta yi ta mayarwa Zash wayarsa bedroom ɗinsa, sannan ya zo ɗakin Mama ta karɓi nata wayar, da yake mama Haulat macece mai saurin fahimta sai ta gano me zata da wayar, amma bata yi mata magana ba, ta kyaleta. Komawa bedroom ɗinta ta yi, sai murna take yi ta hau gado ya kwanta, a hanzarce ta shigar da numbersa tare da yin saving da ainahin sunansa tin da ba wayarta bane, hijabinta ta ɗauko ta sanya a jikinta game da hayewa saman bed. Kai tsaye ta danna mashi video call. Wani irin cool ajiyar zuciya ya sauke kafin ya yi picking. Hannu tasa ta rufe fuskarta tana murmushi tana binsa da ido. Ɗan limshe idanunsa ya yi, cikin taushin murya ya ce. "Alhamdulillah ya ALLAH na, na gode maka da ka mallaka mun wanna zinariya ɗaya tamkar da dubu". Ajiyar zuciya ta sauke ita ma kafin ta ce. "Na fi kowa dacen miji a duniyar nan". Waro idanunsa a kanta ya yi, tamkar mai raɗa ya ce. "Aesh please cire mun hijab ɗin nan dan in ji daɗin kallan matata da kyau". Har cikin ranta ta ji sanyin kalamansa, amma sai ta dake da cewa. "Ni kam ummm". Gera guda ya ɗaga mata alamar menene?. Ɗan juya idanunta gefe ta yi kafin ta ce. "Mama fa tana nan, tana jinka". Da sauri ya ɗan zaro idanunsa, sai kuma ya ce. "To ai matata ce ke, mallakina ce, dan haka ni dai a cire mun hijab ɗin nan kawai". Ya faɗi hakan ne dan yasan mama bata nan, saboda in tana nan Leesharh ba zata yi waya da shi ba, ita da take jin kunyar amsa kiransa a gabansu Auta ma bare mama. "Ni Yah Ramish kawai mu yi hira a haka". Tana magana tana kallan ƙasa. "Okey to look into my eyes first". Ya faɗa cikin wata iriyar siga mai tsananin kwantar da hankali. Make mashi kafaɗa ta yi alamar ita dai a'a. "Please Aesh". Ya faɗa tamkar mai raɗa. Slowly ta ɗago da kallonta a kansa, take suka kafe juna da wani irin kallo mai cike da sirrika da kuma kewar juna. "Please cire hijabin". Ya yi maganar ne da alamar motsa laɓɓa kawai!. Ai bata san lokacin da ta zare hijabin ba, saboda yagama tasan kanta. Wani irin daddaɗar ajiyar zuciya ya sauke, take ya fara bin dik sassan jikinta da kallo yana wani haɗiyar yawu, kawai gano kake makogwaransa tana sama tana ƙasa. "Aesh i can't control my self idan ina kallonki, please ɗan yi mun kasa da rigar nan kin ji?". Da sauri ta waro idanu, sai kuma ta ɗauke kallonta daga kansa, a ɗan shagwaɓe ta ce. "Yah Ramish abin da ka mun fa har yanzu ban gama warkewa ba, ni dai a'a". Kamar mai raɗa ya ce. "Da gaske har yanzu baki gama warkewa ba?". Kai ta ɗan jinjina tana shagwaɓe fuska. Cike da zallar kaunarta ya ce. "Nuna mun in ga ɓarnar da na yi, zan gyara kayana ai". Da sauri ta zaro idanu waje, sai kuma ta shiga girgiza mashi kai kafin ta ce. "Ni dai a'a". "Please my Aesh, gani kawai zan yi". Tamkar yana a cikin maye ya yi maganar, giyar sha'awarta ne kawai take ɗebansa. "ALLAH ni dai Yah Ramish a'a, idan kana son gani to ka zo da kanka". Wani idin dogon numfashi ya ja, da alama magana ma tana neman ta gagaresa ne, dan abin ta yi mashi yawa. "Ba shawara ba, umarni a mun ƙasa da rigar nan in ga kayana ko zan samu sassaucin abin da nike ji". Ya faɗa yana gyara kwanciyarsa a saman bed ɗinsa, dan gabaɗaya yana jinsa a sama jannaty. Dole na ɗan ta so ba ta hau ɓalle botiran kayan barcin jikinta, tana yi tana turo baki kamar zata yi kuka. Shi kuwa wani daɗi ne ta lulluɓesa, dan haka ya kurawa kayansa idanu, sai kawai ta matsar da face ɗinsa daga gaban screen ɗin. Shi kuwa ya kura masu idanu, ga su tula-tala tamkar an hura balo-balo, ji yake tamkar ya cakumota ya tumurmushe kayansa amma babu hali, wani irin yawu mai sauti ya haɗiye kafin ya ɗan limshe idanunsa yana juyawa ya kifa a saman bed ɗin yana wani jan dogon numfashi a hankali-hankali. Ita ma dai gyara kwanciyarta ta yi yana jin wani irin zazzafar kauna da sha'awarsa a ranta yana kara ratsata. Haka suka ƙasance cikin farinciki, daga baya Leesharh ta daure ta fara zuba mashi kalaman da za su kara motsa mashi sha'awa har ya ɗan samu natsuwa, sai dai fa da kyar ya samu wannan natsuwa, sai da suka shafe awa suna abu ɗaya, daga karshe ya ce mata cikin satin nan dole zai zo ya ɗauketa babu fashi, dan ba zai iya kwanciya ya kifu ya kuma rungume pillow ba. Sun jima suna hira kafin su yi sallama cike da kewar juna da begen san ganin juna. --------------------🔥 Gefe guda kuma ga can Smart yana ta shirin tafiya Black World, bai sanar da su Momma ba, yanzu ta batun dawo da ɗan uwansa gida yake yi, baya ta batun King ya faɗa mashi mamar Ramish!. Dik wannan bidiri da suke yi shi dai Dr Raj yana can ya gama kame zuciyar Zee, while ita kuma gabaɗaya hankalinta yanzu ya koma kan ina Khadijah? Aunty MieMie ce ke ta ƙoƙarin kwantar mata da hankali, sannan ta ce mata kada ta damu zata yi magana da Smart ta ji waye Bobo kuma daga ina yake and ina ya kai Khadijah. Hakan ne yasa hankalinta ya ɗan kwanta. -----------------------🔥 Sai da suka murji juna son ransu, ya bata a jikinta har da kuka, sannan ne ya kyaleta ya hau rarrashi, da yake yanzu ta saba, sai ta faɗa jikinsa tana cigaba da yi mashi kukan. Bargo ya ja masu hannayensa gabaɗaya a kan tula-talanta, cike da sabuwar sha'awarta tamkar bai rage komai, kamar ba yanzu ya gama tumurmusheta ba ya ce. "Noor wannan kyau da kike kara kullum ɗin nan anya kuwa ban samu baby ba?". Tana yi mashi tafiyar tsotsa da tongue ɗinta a wuyarsa ta amsa da. "Kai baby kuma?". Har lokacin tana mashi kukan shagwaɓa da iya shege tana ɗan shafa kyakkyawar sagensa dake kwance da hannunta ɗaya. "Kin manta a Jimeta kin ce zaki haifa mun ƴaƴa kyawawa ne? Ko dai kin fasa ne?". Ɗan ɗago kanta daga saman shoulder ɗinsa ta yi kafin ta ce. "Niko nike so, dama ranar zam ce maka wai ya aka yi ni har yanzu ban haifi baby ba, sai kuma na manta". Ɗan matsa tula-talanta da ɗan karfi ya yi har sai da ta ce wash, sannan ya ɗan sumbaci bakinta. "Ina sa ran yanzu mun samu baby, saboda yacce kika kara kyau sosai ɗin nan". Ya kai karshen maganar tare da matsar da bakinsa dab kunnanta. "Bayan kyau kuma kin kara daɗi sosai, dan yau ba dan kin yi mun kuka ba ban da niyar barinki". Ɗan bakinsa ta sumbata, lokaci guda ta saki cool murmushi tare da cewa. "Na tina lokacin da muke Jimeta Mahreen take sanya maka miyar kuka a kumatu". Ɗan lumshe idanu ya yi. "Mahreen ta mun son ranta, kuma har yanzu tana mun son ranta, ina ga sai na aurar da ita zan huta". Ai da sauri Mahnoor ta ce. "Yauwa dama akwai abin da zan faɗa maka na mance". Kura mata ido ya yi yana maidota saman kirjinsa da kyau dan ya ji daɗin cigaba da murza tula-talan nata da kyau. "Okey faɗi ina jinki". Hannunta ta ɗaura saman nipples ɗinsa ita ma ta shiga murzawa a hankali kafin ta ce. "Yah Omar yana son Mahreen fa, kuma so na gaskiya". Ai Jaish bai san lokacin da waro idanu waje ba, a hanzarce ya ce. "Omar nawa ne yake son Mahreen ɗita?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e. Lokaci guda Jaish ya fashe da dariyar da bai taɓa yi ba, har da ɗan sauti dariyar. Mamaki ne ya kama Mahnoor, bata taɓa ganin yana dariya ba, dan haka sai ta zuba mashi idanu tana kallonsa tamkar zata cinye shi da ido. Har sai da ta sanya ya dakata da yin dariyar, iska ya hura mata a fuska kafin ya ce. "Kallan fa?". Ajiyar zuciya ta sauke, sannan ta ce. "Yau ka fi kyau kyau da ka yi dariya, amma menene ya saka mun wannan habibi da baya dariyar yi a yau?". Girgiza kai ya yi tare da mai da hannunsa saman bayanta. "Uhm ba zaki gane haɗin Omar da Mahreen bane sai abin ya tabbata, dole ki ga na yi dariya, da akwai abin da ya fi dariya tabbas yau zan yi shi, Omar Mahreen, tab ki ce mu shirya raba faɗa har cikin dare, uhm akwai babban aiki, tab wai yaushe Omar ya girma har ya san soyayya ne ma? Kuma ke waye ya faɗa maki ya ce yana sonta?". "Yah Jaish me zai sanyasu yin faɗa hat cikin dare, kuma ni shi ne nan ya nuna yana sonta a gabana". Ta faɗa tana ɗan turo baki. "Ba zaki gane faɗar ba, ke dai ALLAH ya tabbatar da alkhairi kawai, amma akwai aiki babba, kin ga zuwa Jimeta ya kamamu, ni dai na bawa Omar ita, ban san ra'ayin bappa ba". Shiru ta ɗan yi tana tinanin me zai sanya Omar and Mahreen faɗa kuma dan sun yi aure? Da alama akwai abin da Jaish ya ɓoye mata dangane da guyson, kuma da gasken ne akwai abin da ya ɓoye ɗin ko in ce akwai abin da yake ɓoye wanda gaba zaku sani!. Ganin ta lula duniyar tinani ne yasa Jaish ya miƙe tare da ɗaukarta suka nufi toilet dan yin wanka yana faɗin. "Muje in yi maki wanka mu ci abinci ko?". Daga haka suka shige toilet abinsu. ------------------🔥 CROWN OF JUSTICE.🔥 Wayewar garin yau dai sun wayesa cikin tsantsar farinciki da annashuwa, sai dai kuma Hoorain yaki yarda ya haɗa idanu da Zunaira, wai kunyarta yake ji saboda jiya ya taɓa mata tula-talanta, gabaɗaya sai yake jin kamar ba shi ba, suna tashi da safe ya yi gaggawar shiryawa ya fita zuwa fada, dan in baku manta ba ya ce yana buƙatar kundin dokokin masarautar, so yana son duba komai a natse, shiyasa tin kafin Zunaira ta farka ya yi gaggawar ficewa abinsa, amma dik da haka sai da ya zo ya manna mata hot sumbata a kumatu kafin ya fita. Sai around 10 na safe ta farka, bata yi mamakin ganin baya nan ba, dan tasan da wuya dama ya zauna, tasan mijin nata da kunya mai tsabta, shi Hoorain wlh kunyarsa ma abin burgewa ce, cikin natsuwa da kwantar da hankali, ga ban sha'awa da tsabta. Miƙewa ta yi ta tsaro wankarta, ɗaya daga cikin haɗaɗɗun kayan da Rishma ta sayo mata ta fitar, ta shirya a cikinsu, ta yi fitinannen kyau, sannan ta ɗauko alkyabbar da Mommah ta bata ta sanya, take tsantsar kyanta ya kara bayyana sosai. Waje ta fito ta kira kuyangub dake hidima a part ɗinsu a kan su zo su gyara masu ɗaki, dan ita kam ko bed bata iya shinfiɗawa ba. Bayan ta sanar da su ne ta wuce izuwa in da Rishma ta yi mata kwatanceb ɗakinta yake, dan tana son zuwa lambu ta sha iska, so bata san in da yake ba, shi ne yasa zata je ɗakin Rishma ta nuna mata. Tana tafiya tana tinanin yacce za'ayi a yi gwajin jini a kingdom ɗin nan domin ta tsiratar da mijinta. Da taimakon ALLAH ta isa bedroom na Risham, nan ta iskota zaune saman massage machine yana matsa mata jiki, ga kuma kuyangu guda biyu a gabanta suna wanke mata kyawawan kafafunta dake a cikin ruwa cikin bowl nai ɗan gidama. Ai tana ganin Auta ta saki ƙayataccen murmushi tana welcoming ɗinta, da sauri Auta ta zo ta rungumeta tana mayar mata da martanin murmushin ita ma. Cikin girmamawa waɗan nan kuyangu biyun suka risinar da kai suka gaisheta, fuska ba ya bo ba fallasa ta amsa, sannan ta wuce ta zauna saman bed ɗin Rishma tana kallon irin gyaran kafa da ake yi mata. Haka suka cigaba da hira Auta bata je lambun da take son zuwa ba har lokacin sallar azahar ya yi, a tare suka yi sallah da Risham sannan suna zauna auntyn tata ta shiga kara mata karatu kan yadda zata rike mijinta da kyau. Shi kuwa yana can yana fama da soke dik wasu dokokin da suka saɓa da tsarin addinin Islama, ciki har da dokar kwana da amarya da Ude yake yi, Hoorain bai yi wata magana ba ya yage paper wannan doka ya yi gutsi-gutsi da ita, kun san gadan mulkin nasa ne ba na Zarina ba, dama ita mai rikon kwarya ce kawai, tin da ya bayyana ai sai ta bashi kayansa, ba shi da sha'awa ko niyyar sarauta, amma duba da yacce dokokinsu yake gabaɗaya na zalunci yasa ya ce zai karɓi mulkinsa, ai ba wai bai iya mulki bane, ya iya, dan haka zasu bashi kayansa. Ba karamun tashin hankali suka shiga ba, nan take Ude ya ce. "A'a my son, ka yi ƙanƙanta da mulki yanzu, ba zaka iya karawa da abokan gaba ba, tin da baka son second mom taka a kan kujerar mulki ni zan koma kansa zuwa ka kara girma, dama a baya saboda wasu abubuwa da suka sha kai'na ne yasa na ce na bar mata kujerar mulkin, yanzu zan karɓa". Ba dan komai Ude ya yi wannan magana ba sai dan in suka kuskura Hoorain ya shiga fada, ya zauna kan gadan mulki, to dik wani abin da suke rufewa sun san zai bankaɗa wa duniya, kuma dik wani wahalar da suka sha tsawon shekaru da suke sa ran fara mora yanzu zai tashi ne a tutan babu. Bugu da ƙari dama shi Ude ya jima yana son hayewa kan wannan kujera, dan ya nunawa Zarina iko, amma ina bai samu dama bane yasa ya cigaba da laɓewa bayan Zarina, to yanzu ga dama kuna tinanin zai bari ne?. Ai tuni ya yi tsalle ya ce zai koma kan karagar mulkinsa yanzu. Cikin girmamawa Hoorain ya amsa da okey amma dai gaskiya akwai wasu dokikin da za'a soke su, carap Ude ya amsa da ya amince a ciresu. Tamkar Zarina zata tsoma baki a wajen, sai wani huci take yi, amma ta daure ta yi shiru dan kar asirinta ya tonu, tana ji tana gani Ude ya karɓi karagar mulki wanda tsananin ɓacin rai yasa ta yi gaggawar ficewa daga fada, shi kuwa Hoorain cigaba ya yi da zaƙulo dokikin da suka saɓa da addinin islama yana sokesu, Ude bai taka mashi birki ba, dan faɗat sunkuru zasu yi, ba gaba da gaba ba, dan in suka ce gaba da gaba ne lallai ba shakka sun san Hoorain ya fi karfinsu. Bayan ya kammala cire dik dokokin da basu yi mashi ba, sannan ya ce da daddyn nasa. "Dad ina da shawara". Zuciyar Ude bakincikin tamkar bakin leda, while fuskarsa tana ƙaƙalo annashuwar dole, ba dan ya so ba ya ce. "Wace iriyar shawara kenan son?". Hoorain dake zaune saman kujerarsa ne ya ɗan kara gyara zama kafin ya fara magana a natse. "So nike ka bani dama akwai wasu dokoki da nike son ɗaurawa a kan wannan masarauta bisa experience da nike da shi kan mulki". Cike da nuna goyon bayar lallai yana tare da shi ya ce. "Wani irin dokiki ne waɗan nan?". Kara tattara hankalinsa waje guda da kyau Hoorain ya yi kafin ya ce. "Zuwa gobe ko bayan mun sha ruwa zan faɗa maka idan na gama tsarasu, na tabbata zasu ciyar mana da masarauta gaba, sannan zasu yi matuƙar tallafa mana, zasu tallafawa talakan da muke mulka". Jinjina kai Ude ya yi, sannan ya ce. "Na tabbata dik abin da zaka kawo mai kyau ne, kuma zamu yi maraba da shi". Sosai Hoorain ya ji daɗin kalaman mahaifin nasa, hakan yasa ya ce. "To Dad ina son shirya liyafa ta shan ruwan buɗa baki da talakawa a cikin gidan nan gobe". Babbar magana, ai gabaɗaya fada ta koma wannan ya kalli wannan wannan ma ya kalli wannan, abin da ba'a taɓa yi ba tsawon tarihi, wai su zauna da talakawa su sha ruwa da su, tab lallai Hoorain ya zo da babban. Shi kuma Hoorain yanzu a tinaninsa Zarina ce take sanya daddynsa yin wasu abubuwan mugunta, shi ne yasa ya ɗaura ɗamarar yaki da ita, aka ce rashin sani ya fi dare duhu, bai san Ude ya ci uban Zarina a makirci ba!. "Dad ka yi shiru baka ce komai ba". Cewar Hoorain kenan. Gudun kada Hoorain ya ji ba daɗi ko ya zargi wani abin yasa ya ce. "Dan liyafa kawai ai ba komai zaka iya shiryawa". Tsabar farinciki Hoorain bai san time da ya sauke ajiyar zuciya ba, sannan ya ce. "Thank you Dad". Jinjina kai kawai Ude ya yi alamar to. Kallon sarkin gida wato mai kula da shige da fice Hoorain ya yi, a natse ya ce. "Ka bada sanarwa cewa gobe ina gayyatar kowa da kowa ya zo mu yi ifter a nan". Cikin girmamawa sarkin gida ya amsa da to sannan ya miƙe ya nufi waje. Dai'dai lokacin gabaɗaya hayaniya ta karaɗe harabar kingdom ɗin, a take mayakan dake fada suka zare takubansu suka kara kewaye saman stage da ya kasance mallakin sarki da familynsa. Miƙewa Hoorain ya yi yana faɗin bari ya duba menene. A hanzarce waziri ya ce. "A'a ranka ya dade bari mu samu labarin menene kafin ka fita, kada ace abu mai haɗari ne da zai iya cutar da kai". Cikin mutumtawa Hoorain ya ce. "Horon Abbona ne ni fa, kada ka damu waziri babu abin da zai faru........". Bai kammala rufe baki ba wani dakakken mayaki ya shigo cikin zafa tare da tsayawa ta bakin kofa, sannan ya risinar da kansa ƙasa, cikin girmamawa ya nemi izinin yin magana. Kai Ude ya jinjina mashi alamar an bashi izinin yin magana. Kara risinar da kansa ya yi kafin ya ce. "Dama wasu mayaka ne daga Crown of Power suka yi mana kutse sai muka kamasu". A take Ude ya ce. "Ku kashesu kisa mafi muni". Da sauri Hoorain ya ce. "No Dad, su dakata bari in ga su wanene? Saboda ni nasan mayakan King Zuhair basa laɓewa su yi leken asiri, basa zuwa ta baya su yi cuta, su gaba da gaba suke fuskanta, in har mayakan dad King Zuhair dole akwai ƙwaƙƙwaran abin da ya kawosu, bari in dubasu please Dad". A ɗan fusace Ude ya ce. "Bama zaka fita ba bare har ka je dubasu, dan bana son wani abin ya sameka". Ya yi maganar cike da nuna yana kaunar Hoorain ɗin. "No Dad babu wani abin da zai faru, ni nasan dangerous warriors, nasan ya suke in and out". "My son kai baka san sarauta bane, yanzu haka ina da yakinin turosu aka yi su kasheka tin da ka juyawa kingdom ɗinsu baya". Kai ya girgiza game da cewa. "No Dad, ina mai imani da ALLAH dad King Zuhair ba zai taɓa turo mutane su kasheni ba, da zai kasheni tin lokacin da na je ɗaukar Hoonaira zai sanya a kasheni, amma ya barni na fita da rai'na, wlh dad yana sona sosai, ni naga hakan a cikin idanunsa, kawai rashin jituwarku ne ma yasa ya nuna wani abin, amma ina da tabbacin King Zuhair ba ragon namiji bane da zai sanya a biyo a kasheni dan na bar kingdom ɗinsu, shi ɗin namijin zaki ne da in ya ga dama har cikin palace ɗin nan zai zo ya kasheni kuma kai kasan babu wanda ya isa ya taka mashi birki". Ya kai karshen maganar tare da dimfaro stage ɗin zai sauko ƙasa, take warriors dake wajen suka buɗawa namijin zaki hanya, dan basu ga alamar wasa ba. Lokaci guda Ude ya ji tamkar shi Hoorain ya cakawa magana yadda ya ce King Zuhair zaki ne baya tura mayakansa su yi leken asiri, sannan mayakansa basa laɓewa suna leƙe, su gaba da gaba suke zuwa, gabaɗaya sai Ude ya ji ai wannan da su Hoorain yake yi, dan su ne kolaye masu tura ƴan leken asiri, lallai kuwa akwai matsala!. --------------------🔥 Waje Hoorain ya nufo cike da ƙagara ya ga su wanene daga kingdom of power zasu zo leƙan masarautarsu. Yana fitowa ya yi tozali da Ansar da Anwar, sun jigata sosai, saboda mayakan Zarina sun basu wahala, sai da suka sanya ragar kama zakuna kafin su iya kamasu, saboda a lokacin da suka shigo kingdom ɗin kai tsaye suka shigo babu wata kwana-kwana, shi ne mayakan Zarina suka nemi hallakasu saboda tambarin zaki dake kan hulunan kansu, sun san kingdom of power ce kawai take da tambarin zaki, to su kuma domin kare rayukansu suka zari takuba, nan fa karamun yaki ya kaure a tsakaninsu har suka kashe mayaka biyar, da dai warriors na Zarina suka ga ba zasu iya kamasu ba, sai suka sakar masu ragar kama zaki suka samu damar kamasu, suka ɗauresu da sarka shi ne suka yi masu dukan mutuwa, dik sun jigata da kyar ma suke numfashi. ALLAH sarki sun kasa iya zama a kingdom of power ne saboda babu Hoorain, suna kewarsa sosai shi ne suka zo ganinsa, wai irin su zasu nuna jarumta ya narke ya haɗe da jinin jikinsu shi ne babu ko shakka bare tsoro suka afko kingdom ɗin kai tsaye kawai. Ai Hoorain yana ganinsu bai san lokacin da ya dakawa warriors da suka rirrike sarkan da aka ɗauresu tsawa ba. Cikin zafa ya kariso wajen, dik suna cikin sarka, yana zuwa ya sake daka masu tsawa a kan su yi gaggawar kwance mashi su. Zarina na tsaye a sama jikin window ɗinta tana ganin dik abin da yake faruwa, kazalika shi ma sadauki Rishan yana tsaye a saman jikin window yana kallonsu. Da yake warriors dake kula da prison na Kingdom ɗin ne suka kamasu so basu san Hoorain ba, sai suka ce ba zasu sake su Anwar ɗin ba, su umarnin Zarina and Ude kawai zasu bi. Ai cikin wani irin ɓacin rai Hoorain bai san lokacin da ya sanya kafa ya takesu ba, su uku ne a tsaye suna jere dikkansu sai da suka zube ƙasa, ya ji zafin dukan da suka yi wa su Anwar, zaro takubi daga waist na warrior dake kusa da shi ya yi da nufin ya sare wanda ya ce ba zasu kuncesu ɗin ba, dan da alama shi ne shegen da ya jagoranci dukan su Anwar ɗin. "A'a my son dakata". Cewar sadauki Rishan dake sama. Dakatawa Hoorain ya yi yana wani irin huci, a duniya kun san bashi da aminai biyun su Ansar, yana jinsu tamkar ƴan uwansa. Dai'dai lokacin su commander Zafar suka kariso wajen da sauri. Jin sautin muryan sadauki Rishan yasa gabaɗaya warriors dake wajen suka zube gwiwowinsu a kasa alamar girmamawa. Da sauri commander Zafar ya matsa ya rungumo Hoorain yana ɗan bubbuga bayansa alamar ya huce haka. Kasa sadauki Rishan ya sauko cikin sauri, kara risinar da kai warriors suka yi. Yana zuwa ya bada umarnin a kwance su Anwar. Warrior da ya yi magana ɗazun ne cikin girmamawa ya ce. "Ranka ya daɗe suna da mugun haɗari, da kyar muka iya kamasu, sai da ma muka sanya masu ragar kama zaki sannan muka iya kamasu, sun kashe mana mayaka har guda biyar, kana ganin kamar sun jigata, ana sakesu ɓarna zasu sake yi mana........." Bai kai karshen maganar ba sadauki Rishan ya ɗaga mashi hannu, a natse ya ce. "Kwancesu!". With harsh voice ya yi maganar!. Cikin zafa gabaɗaya mayakan suka miƙe tare da zare takubansu suka yi gaggawar kewaye su Hoorain da su wai dan basu tsaro, dan su fa suna bala'in tsoron ɓarnar mayakan King Zuhair, dan sun san ɓarnarsu dayawa yake. Wanda ya yi magana ɗazun shi ya miƙe cike da tsoron abin da su Anwar zasu iya aikata masu dik da sun kwace takubansu, haka yasa makulli ya buɗe kwaɗon sarkokin da suka ɗauresu. Ai suna buɗewa Anwar and Ansar suka ɗan girgiza jikinsu wanda hakan yasa gabaɗaya warriors na wajen suka sake yi gaggawar ready da takubansu. Da sauri Hoorain ya keta tsakiyar warriors ɗin ya isa gabansu Ansar, suna waro idanunsu suka yi tozali da shi, ai cikin zafa suka rungumesa suna murna, rungumesu shi ma ya yi yana mai basu hakuri a kan abin da aka yi masu. Anwar ne ya ce. "Ai tin da mun samu ganinka komai ya wuce". Kara rungume juna cike da murna suka yi, commander ne ya matsa kusa da su yana ce masu sannu da zuwa. Ai suna ganin commander suka yi gaggawar sakin Hoorain tare da risinawa suna faɗin. "Abbo mun yi kawarka sosai". Kara matsawa ya yi ya ɗagosu ya rungume yana faɗa masu shi ma ya yi kawarsu sosai. Rungumo hannayensa a saman kirjinsa sadauki Rishan ya yi yana tsananin farincikin ganinsu, sun burgesa sosai, dik yacce aka yi aminan juna ne da suka taso a tare. Haka ne kuma, a tare suka yi wasan ƙasa, shiyasa basa iya jure ɗaya ya yi masu nisa. Wani irin farinciki Zarina ta ji, domin kuwa ta ga mayakan King Zuhair suna ta guduwa su dawo masarautarta, abin ya yi mata mugun daɗi, NI KUWA NA CE KI JIRA KI GA ABIN DA UDE ZAI YI MAKI TIN DA YANZU BURINSA YA CIKA YA HAYE KUJERAR MULKI, MY PEOPLES AKWAI CASE FA SOSAI A WANNAN KINGDOM ƊIN. Yau tsabar farinciki tamkar Hoorain ya zuba ruwa a kasa ya sha, da kansa ya kai su Ansar katafaren masaukin manyan baki dake kingdom ɗin, kuma ya zauna tare da su, suka yi wanka, yasa aka kawo masu kaya masu kyau suka sanya, ya bada umarnin a kawo masu abinci, nan suka shaida mashi da suna azumi, shi a tinaninsa tin da sun kama hanyar zuwa sun ajiye azumi, ashe ba su ajiye ba, dan haka sai ya yi umarnin a shirya mashi liyafa mai kyau a lokacin buɗa baki a kawo masu. Nan suka zauna hirar bayan rabuwa har lokacin sallar la'asar ta yi, tare suka je suka yi sallah suka dawo, sam Hoorain ya ki komawa wajen Auta, dan yasan tana a tare da Rishma, so sai ya sake zamansa da su Anwar suna hira. Cike da zolaya Ansar ya ce. "Ina gimbiyarmu? Ko dai ka ɗirka mata ciki ka barta da laulayi ne? Dan nasan halinka dama a hannu kake". Harara ya wurga mashi kafin ya ce. "Ni matata yarinya ce, sai ta girma". Anwar ne ya ce. "Eyeeeeee e mun yarda kuma zamu zuba ido". Yana harararsu ya ce. "Kada ku fito da mata kuma ku yi aure, ku zauna sa ido, sai watarana kun saka ido a abin da ya fi karfinku"......... A gaggauce Ansar ya tari numfashinsa da cewa. "Eyee wato yanzu ka yi aure shi ne har da yi mana gori ko? To kaima yaushe ka yi auren dika-dika?". Miƙewa tsaye ya yi kafin ya ce. "Koma dai yanzu na yi aure ai dai na yi, kuma na auri zaɓin rai'na, dan haka ni kunga tafiyata ma wajen matata farincikina, dik wanda ya ji haushi shi ma ya yi aure a yau, sai da safe tuzurai, amma kila in dawo in duba ku, za'a kawo maku komai da ya dace da gauraye". Ya kai karshen maganar tare da yin zafan barin kusa da su, dan a tinaninsa zasu kai mashi duka yacce suka saba wasa a kingdom of power, sai ya ga akasin haka, ya ɗan yi mamaki, amma bai ce komai ba. Bai san cewa yanzu mugun girmama shi suke yi matsayinsa na Prince ba, ba dan ya jawosu a jiki ya nuna masu ɗaya yake da su ba ma ai sun zo ne da niyar yi mashi hidima, dan haka yanzu wasan da suke yi da shi da sun ja baya sosai da sosai wanda shi kuma bai ji daɗin hakan ba, kuma bai so ba, dan yana son rayuwar da suka ta so suke yi gwanin birgewa. Haka dai ya wuce part ɗinsu, ga mamakinsa da ya je bai samu Auta a bedroom ɗinsu ba, duba time ya yi karfe biyar na yamma ta yi. Cike da jin kunya ya wuce part nasu Rishma dan ya dubata. Kwance ya isko Rishma a saman bed tana latsa waya. Tana ganinsa ta miƙe zaune tana yi mashi barka da shigowa. Cikin girmamawa ya amsa mata, sai kuma ya yi shiru, ya ji kunyar ya tambayeta ina Auta, tin da ya ga bata ɗakin. Ta ganosa dan haka sai ta ce. "Mutuniyar taka tana lambu, ta ce tana san zuwa nasa kuyangu suka kaita, da alama macece mai son yanayin soyayya sosai, yana da kyau ka mayar da hankali ko dan farincikinta". Cike da jin kunya ya ce. "In Sha ALLAH zan yi kokari, ta inane lambun?". Kwatance ta yi mashi, cike da kaunarta ya yi mata sallama ya fito. Kai tsaye ya nufi in da ta kwatanta mashi, dik in da ya wuce sai warriors sun risina sun gaida shi. Yana zuwa ya afka ciki, can ya hangota tamkar wata cikin taurari, ta yi wanka ta canza kaya zuwa na sarauta, ta sanya alkyabba mai shegen kyau a jikinta, tana zauke saman shinfiɗu na alfarma wanda aka yi su da gashin jimina, ta ɗaura hannunta saman kyawawan throw pillows dake kusa da ita, a karkashin bishiyar tuffa take zaune. Ga wasu kuyangu zaune a gefe-gefenta suna tayata hira, da alama sun ji daɗin kasancewa da ita, duba da yacce suke ta murmushi. Ai wani irin musulmin farinciki ne ya lulluɓe zuciyarsa. Komawa da baya-baya ya yi, kwari da baka ya karɓar a hannun ɗaya daga cikin warriors dake tsaron lambun, sannan ya komo ciki, lallaɓawa ya yi ya ɓuya bayan wasu bishiyoyin gwaiva da suka nuna sosai, sannan ya ciro kifiya ɗaya ya saita tuffa dake saitin gabanta, ya ja da karfi ya harbi tuffar guda uku a jere. Take suka faɗo a gabanta saman shinfiɗar da take. Ai wani irin ihu ta kurma tare da miƙewa a zabure. Sam ko kaɗan bai yi zatan zata tsorata ba, ya yi tinanin zata ɗauki tuffa ɗin ne, sai dai ta razana, kun san abu ya faɗo gabanka unexpect dole ka razana ai. Razanar da ta yi ya sanya shi yin gaggawar fitowa, cikin zafa ya taka zuwa in da take, gabaɗaya kuyangun sun miƙe tsaye suma. Yana zuwa ya jefar da kwarin hannunsa ya rungumeta a jikinsa yana faɗin sorry. Ƙanƙame shi ta yi tana saka mashi kukan shagwaɓa. Zubewa ƙasa gabaɗaya kuyangun suka yi domin kwasan gaisuwa. Bai bi ta kansu ba ya hau rarrashi. Sai da ta yi shiru sannan ya faɗa mata shi ya harbi tuffa ɗin suka faɗo suka razanata, dogon kyakkyawan hancinsa ta ja tare da cewa. "Zaka biya tsoron da na ji". "Zan biya sosai ma, da me ake son in biya?". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Zan faɗa maka bayan ifter, yanzu dai faɗa mun ina ka je tin safe? Sannan meyasa baka dawo gareni da wuri ba? Tin fa kan in tashi barci ta fita". Ɗan raba jikinsa da nata ya yi, ba tare da ya ga in da kuyangun nan suke ba ya ce. "Zaku iya tafiya tin da na zo". A hanzarce suka miƙe suka nufi waje. Ɗan matsawa step biyu baya da ita ya yi, sannan ya juya mata baya, in a cool way sosai ya ce. "Kunyar haɗa idanu dake nike yi"...... Dama tasan za'ayi hakan tin da ta farka bata gansa ba, a natse ta tako garesa, a saman faffaɗar bayansa ta kwantar da kanta tare da zuro hannayenta ta saman flat tummynsa, cike da shagwaɓa ta ce. "Saboda me kake kunyata kuma?". Wani musulmin ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juyo ya rungumeta da kyau. A kunne ya raɗa mata. "Babu komai, kawai dai da safen nan ne ina jin nauyin haɗa ido dake".. Ɗago kai ta yi suna fuskantar juna. "Saboda ka yi wasa da halak ɗinka daren jiya ko?". Kai ya ɗan gyaɗa mata sama alamar e tamkar karamun yaro. "Kai kam halinka iri ɗaya da Yah Jaish na kunya, amma shi Yah Jaish baya kunyar Aunty Mahnoor ɗinsa". Ajiyar zuciya ya sauke, a ransa ya ce. "Uhm ai dik ranar da ciki ya bayyana a jikinki bani ba haɗa ido da Mommah ko King har sai kin haihu". A fili kuma sai ya ce. "Nima zan dai'na kunyar Hoonairata soon, yanzu dai dik bama wannan ba, yaushe yakamata mu kaiwa su Mommah ziyara?". Yatsarta ɗaya ta ɗaura a saman kyakkyawa kuma lallausan lips ɗinsa dake kara ɗaukar hankalinta, ɗan shafa lips ɗin ta yi sannan ta ce......... Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 Yatsarta ɗaya ta ɗaura a saman kyakkyawa kuma lallausan lips ɗinsa dake kara ɗaukar hankalinta, ɗan shafa lips ɗin ta yi sannan ta ce. "My Hero laɓɓanka sun bushe sosai". Yana satar kallan kyakkyawar fuskarta ya amsa da. "Saboda azumi ne ai, amma ko zan samu a jiƙa mun su?". Hannayenta ta zura ta bayansa, ta harɗesu tana kallan cikin kyakkyawan idanuna da yaki kallan saitin nata, kafin ta ce. "Awa nawa ya rage a sha ruwa?". Ɗan yin shiru ya yi kafin ya ce. "Awa ɗaya da rabi"......... "Uhm ina fargabar karya maka azumi ne, amma da na jiƙa maka su kuwa, yanzu dai bar batun jiƙasu zuwa anjuma mu yi maganarsu Mommah". Hannunta ɗaya ya riko suka koma saman sunfiɗar tata, zama suka yi suna fuskantar juna, in a cool way sosai ya ce. "Yaushe zamu je wajen su Mommah ziyara?". Tana kallan face ɗinsa sosai ta amsa da. "Ba yanzu ba, sai Dad ya kara hucewa sosai, sannan sai mu je". Ya ji daɗin maganarta sosai, dama wayau ya yi mata ya bugi cikinta domin ya ji shin tana damuwa a kan halin da suke ciki ne ko kuwa, yanzu ya gane cewa ta fawwalawa ALLAH komai kenan, ya ji daɗin hakan sosai. Gyara zamansa da kyau ya yi game da ware kafafunsa, ya miƙesu, slowly ya kwanto da kansa a saman laps ɗinta yana mai ɗago da kallonsa a kansa. Wani irin Musulmin daɗi ya ji da suka haɗa idanu, ai mancewa ya yi da wata kunya suka kafe juna da kallo, take idanunsu suka sarkafe, kallo mai cike da sirrikar dake ɓoye a cikin zuciya suke aikawa junansu. Hannu tasa ta fara shafa kyakkyawan Koreans hair ɗinsa dake kyalli sosai yana ɗaukar ido kasancewarsa golden white. Slowly ta ɗan shafo kyakkyawa kuma lallausan kumatunsa dake ta faman glowing. "Ina sonka sosai mijina, ina sonka soyayyar da baki ba zai iya faɗanta ba, nasan kana sona, dan wani lokaci ina mamakin irin son da kake yi mun, sai in ga kamar bana yi maka ko kwatansa, ban ta shi sanin ka yi haukar sona ba sai lokacin da na shiga ɗakinka baka nan". Ɗan zaro Koreans eyes ɗin nan nasa ya yi kafin ya ce. "Dama kin taɓa zuwa room ɗina bana nan ne?". Kai ta jinjina mashi before ta ɗaura da cewa. "E na taɓa zuwa, babu kowa a ciki, na kuma yi sa'a kofar a buɗe, nan na shiga na fara binciken ɗik abin da kake ɓoye mun, hotunana tin ina jaririya, abin hannuna da ya taɓa tsinkewa a garden, harta rigarka da ka taɓa ɗaure mun hannu da shi sai da ka yi mashi ajiya mai kyau saboda jini dake jiki, dik wani abin da ya shafeni ajiya na musamman kake yi mashi, ni kam nasan idan na ce na fi kowa dace ma bai faɗi cikakke yadda ya dace ba, baki ba zai iya faɗar girman son da kake mun ba, abu ɗaya zan iya cewa shi ne ALLAH ya bani ikon faranta maka har karshen rayuwarmu". Ai bai san time da ya riƙo hannunta ya ware tafin hannun nata ya manna a kumatunsa ba, a sanyaye sosai ya ce. "Matata ban san me zan yi dan sakaki farinciki ba, komai na yi sai in ga kin wuce hakan nesa ba kusa ba, please ki faɗa mun me kike so yanzu in yi maki?". Tana kallan tsakiyar kwayar idanunsa ta ce. "Kunyata nike son ka dai'na ji, saboda ina son mu yi soyayya kamar na Yah Jawad and Aunty Chuchu, kai kuma sai ka ce kana jin kunyata". Shiru ya ɗan yi, a ransa yake faɗin. "Ina jin kunyarki, amma ba yacce kika zata har can sosai ba, kawai dai ina tsananin tausaya maki ne yasa ko da wasa bana son haɗa ido dake ko wani abin da zai tayarmun da hankalina ya sa na gagara controlling ɗin kai'na a kanki, bana son baki wahala a yanzu, saboda nasan kin yi ƙankanta, abin da nike gudun maki kenan ba wai ina jin kunyarki sosai har haka bane, amma tin da ke da kanki kika nemi da na ajiye kunyar, In Sha ALLAH na ajiyeta, dik kuma ranar da na gagara rike kai'na to bani da bakin furta sorry ma kam". A fili kuma ce mata ya yi. "Na yi alkawarin na cire kunyar daga yau"......... Uhm rashin sani ya fi dare, cike da murna ta ɗan ja dogon hancinsa tana murmushi, sunkuyowa kansa kaɗan ta yi game da manna mashi sumbata a kumatu, ɗan limshe idanu ya yi ya sake warosu a kanta. "Ba dan ina azumi ba ai da yanzu na ce muje ɗaki dan ki tabbatar da na dai'na jin kunyar". Kara faɗaɗa murmushinta ta yi, hannu ta kai ta fara ɓalle botir na wuyar rigarsa. "Yanzu fa ni a gida ba kowa ya san fuskar mijina ba, saboda tin tasowanka baka buɗe fuska, na kamu da sonka ban san face ɗinka ba, kai my Hero kai ɗin na daban ne". "Kamar yacce kike ta daban ba, mai soyayyar gaskiya, kin kamu da san mutumin da baki sani ba, mutumin da yakasance mai tsaronki, bodyguard ɗinki da baki san ya yake ba, gaskiya kece ainahin ta daban, garani ina kallan face ɗinki tin kina jaririya, amma ke ko sauɗaya baki taɓa ganina ba har ALLAH ya mallakamun zuciyar zinarin nan. Tana jin daɗi sosai a dik lokacin da mijin nata yake yaba mata, sanyi na ratsa zuciyarta sosai. Haka suka ƙasance cikin tsantsar farinciki har lokacin buɗa baki ya yi, miƙewa ya yi ya ɗauketa cak a kan su shiga ciki, kuka ta saka mashi kan lallai ya sauketa tana jin kunyar su Ude, sai dai bai kulata ba dan ya san ba zai haɗu da su a hanya ba, sai da ya kaita bedroom ɗinsu, a saman bed ya zaunar da ita, sannan ya zauna a gefenta, can ƙasan makoshinsa ya ce. "Lokacin buɗa maki ya yi, zan so fara buɗa baki da hot kiss ɗinki a maimakon ruwa". Yana fuskantarta ya faɗa. "To rufe ido". Ta faɗa tana matsawa kusa da shi. Slowly ya rufe idanun nasa, a hankali ta matsa dab da shi ta ɗan saƙalo wuyarsa kafin ta haɗe fuskokinsu, cikin salo mai jan hankali ta fara bashi hot kiss mai kara rikita ƙwaƙwalwa. Ai bai san time ɗin da ya kara matsawa ya mannata da jikinsa sosai ba, yasa hannu ya tallabo bayanta game da ɗan ɗaga kanta kaɗan ya shiga bata hot kiss mai zafi. Take ya fara fita daga hayyacinsa, da kyar ya iya jurewa ya raba bakinsa da nata, sannan miƙe da sauri dan lokacin kiran Sallah ta yi, toilet ya nufa, a gurguje ya watsa ruwa ya fito, shiryawa ya yi cikin jallabiya mai kyau da tsada, yana nufar hanyar fita ya ce. "My Hoonaira sai bayan sallar isha'i zan dawo, zamu tsaya yin jam'i da su Papa". Tana ƙoƙarin saukowa kasan bed ɗin ta amsa mashi da. "ALLAH ya tsare mun kai da tsarewarsa a dik in da kake, ALLAH ya cika maka burinka na alkhairi, ALLAH ya dawo mun da kai lafiya". Ba dan lokaci ya kure ba da sai ya dawo ya bata hot kiss saboda daɗin wannan addu'a da ta yi mashi, amma ya yi alkawarin bata idan ya dawo, yanzu dai sai ya amsa da Amin ya yi gaggawar ficewa. Kasa ta sauko ta shiga toilet dan yin wanka, a gaggauce ta yi ta fito, kaya ta ɗauko daga close ɗinsu ta zo ta hau shiryawa. Sai da ta fito fes sosai, sannan ta sako alkyabbarta dan gabatar da sallah. Sai dai tana fitowa tsakiyar ɗakin nata a wutsiyar ido ta kalli mutum a tsaye, a hanzarce ta juyo da kallonta a kansa. Lokacin guda ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, a shagwaɓe sosai ta ce. "My Hero ka bani tsoro, me ya dawo da kai bayan ka tafi masjid?". Cool murmushi ya sakar mata kafin ya ce. "Na gagara tafiya ne yasa na dawo, ba zan iya barinki ba, kewarki ya dawo dani". Tin daga kan murmushin da ya yi ta fahimci ba shi bane, saboda tin da take da Hoorain bai taɓa murmushi ba ko da wasa, ko abokansa na wasan kasa su Ansar basu taɓa ganin murmushinsa ba, to su ma basa murmushin bare shi, kun tina lokacin da take damunsa ya yi murmushi ya ce mata bai iya ba? To ko da wasa, komai farincikin da zai shiga bai taɓa murmushi ba, hakan ya sa ta shiga mugun shakku game da ɗan zaro idanu tana karewa fuskarsa kallo. Cikin ƙanƙanin lokaci ta zaƙulo abubuwa ɗai-ɗai har guda goma da ya banbanta shi da Hoorain, ciki har da kyakkyawan lips da ta yi wa kiss yanzu, na Hoorain ya fi nasa ƙanƙanta nesa ba kusa ba, kuma ya fi nasa kyau nesa ba kusa ba. Ai wani irin razana ta yi, a take jikinta ya fara kerma, kun santa akwai kaifin basira, dan haka sai ta yi amfani da ƙwaƙwalwata bata nuna mashi ta gane ba Hoorain bane, dan tasan idan ta nuna hakan cutar da ita zai, ga shi Hoorain and sadauki Rishan sun ta fi gidan Papa, sun yi nisa kenan. A kaifin ƙwaƙwalwa irin nata da kaifin tinaninta sai ta ga babu abin da ya dace da ita a wannan lokacin face ta ja shi da shiririta har zuwa lokacin dawowar su Hoorain. Wannan yana ɗaga daga cikin wasiyar Manzon ALLAH a garemu, Annabi ya ce a dik lokacin da musifa ta tasowa muminai, lokacin da wata bala'i ta afko masu, to kada su tashi hankalinsu, su natsu domin su san ta in da yakama su fara, natsuwarsu shi zai basu damar tinanin mafita mai kyau, amma idan suka tashi hankalinsu zasu iya zuwa su afka cikin musifar ba tare da sun sani ba. Akwai watarana da Manzon ALLAH suna cikin gida sai suka ji wata kara mai karfi a bayan gari, hankalin mutane ya tashi, sahabbai dik suka firfito dan su je su ga menene? Sai dai kun san me? Suna hanyar zuwa duba menene suka ci karo da Manzon ALLAH har ya je ya duba menene yana hanyar dawowa, sun yi mamaki sosai, yana tafiya cikin natsuwa da kamala babu wani tashin hankali a tattare da shi, so natsuwa a koma ina ne yana daga cikin wasiyar Manzon ALLAH a garemu mu musulmi, ALLAH ka bamu ikon koyi da shi!!. Ta tsorata ainun, amma ta yi ƙoƙarin dakewa, muryarta har yana sarkewa ta ce. "Amma ai daje ka yi sallar ai sai ka dawo mai gabaɗaya ko?". Takowa ya fara yi yana nufota sannan ya ce. "Gagara yin hakan na yi ai, ba zan iya yin sallah a cikin natsuwa ba shiyasa gara in dawo in samu natsuwa daga wajenki kafin in yo sallah".. KUNA JIN MAGANARSA KUN SAN BAI ƊAUKI SALLAH DA MUHIMMANCI BA SHAIƊANI, HOORAIN KUWA AI KUNGA YA ƊAUKI SALLAH DA MUHIMMANCI OVER TO OVER. Tin daga kan yanayin tafiyarsa ta kara tabbatarwa da bashi bane, saboda Hoorain cikin tsananin jarumta yake tafiya, kuma a buɗe sosai yake, sannan kafafun Hoorain dikka basa taka kasa idan yana tafiya, wajen karshen kafarsa bata taɓa kasa in yana taku, bugu da kari tafiyar bahago daban yake, dan ya fi raja'a ta gefen hagun. A gabanta ya matsa dab, tana tsaye bata motsa ba, sai dai daga ta ciki saura kaɗan ta saki fitsari a wando. Hannayensa ya kai cike da marmarinta zai riko nata hannayen ta ɗan yi saurin janyesu baya, a ɗan shagwaɓe ta ce. "Kai my Hero, ka je ka yi Sallah ka dawo akwai wani abin da na tanada maka". Sosai ya ji zafin yacce ya janye hannunta daga garesa, amma sai bai nuna hakan ba, ya makale murya haɗe da cewa. "A bani koda kiss ne sai in tafi". Kai ta shiga girgizawa kafin ta ce. "Bari ma in duba karfe nawa ne yanzu da kaki tafiya masallacin, nasan yanzu ma anyi sallah". Ta faɗa tare da wucewa wajen bed ɗinsu, wayar Rishma ta laluɓa a wajen da sunan zata duba time, jikinta ne ya fara kerma a lokacin da ta fara neman number sadauki Rishan a wayar, tana da basira sosai sai taki danna mashi kira da ta ga number, sako hawai ta hau rubuta mashi. Uncle Rishan ka ce my Hero ya yi gaggawar barin dik abin da yake yi ya dawo gida yanzu akwai matsala. Shi ne abin da ta iya rubutawa a sakon, jikinta na kerma tana ƙoƙarin turawa kenan ta ji an kwace wayar, a zabure ta ɗago da kallonta a kansa, yana tsaye gabanta ya ɗaure fuska tamkar hadari, yanzu ya fahimci ta gane ba Hoorain bane shi, saboda yadda ya ga jikinta na kerma a yayin da ta rike wayar, shiyasa ya zargi ta ganesa, dan yasan in har bata gane ba babu dalilin da zai sa ta tsorata har jikinta ya hau kerma haka. Pretending ta fara yi, tana kallonsa ta ce. "My Hero lafiya? Abu fa nike yi ka bari in gama sai mu yi magana". Cikin wata iriyar kakkausar murya ya ce. "Izuwa yanzu nasan kin gane ba shi bane". A zabure ta ja baya da shi, take jikinta ya tsananta kerma. Shi kuwa cikin zafa ya yi kanta tare da kai mata wani irin damka a waist ɗinta, ya janyota jikinsa da karfin tsiya. Ihu ta fara yi tana turesa tana kai mashi duka a jiki, sai dai ina karfi ba ɗaya ba, ta fagara ko kwatanta kwace kanta. Da karfi ta ɗagata ya yi jefa da ita a saman bed dake kusa da su. Wani ihun ta sake kurmawa mai sauti take da yunƙurawa a miliyan ta diro ƙasan bed ɗin, da gudun gaske ta nufi kofar fita daga ɗakin, sai dai ina, magic eyes ɗinsa yasa ya datse kofar gam, tana zuwa ta hau bugu da karfi-karfi amma ina babu mai jinta, dan Rishma ma dai tana can tana Sallah a ɓangarenta. Tana tsaka da buga kofar sai ji ta yi ya damki gashin kanta, da karfi ya jata izuwa gaban mirror ɗakin, tsaidata ya yi a gaban mirror, cikin tsawa ya ce. "Ki natsu ki sa idanunki a kan mirror ɗin nan". A miliyan ta waro idanunta a kan mirror, take ta hango Hoorain and sadauki Rishan a cikin mota, suna zaune a gidan baya suna ɗan hira jefi-jefi. Kara zaro idanu ta yi tana kallonsu, sai dai kuma wannan mummunar muryar tasa ce ta sake dakar dodan kunnuwanta da cewa. "Ko ki natsu ki bani haɗin kai a kan abin da nike so, ko kuma yanzun nan in saka wannan motar ta yi accident gabaɗayansu su kone kurmus!!". Jikinta ne ya kara tsananta kerma, take ta ji duniya na juya mata....... "Zaki bani abin da na zo nema ko kuwa in kashesu a gabanki kina gani?". Muryarsa ta sake karaɗe kunnuwanta ba tare da ta farfaɗo daga wancan magagi da ya jefata ba!. "Me kake so daga gareni?". Cikin tsananin tashin hankali ta yi maganar, har muryarta na rawa. Ko kunya bai ji ba ya ce. "Kanki, ke kawai nike so". DUM!!! DUM!!! DUM!!!. Haka ta ji kirjinta ya bada bugu, cikin sanyin murya ta ce. "Zan iya yin komai a kan my Hero". Da jin wannan kalamai Ude ya fara sakin murmushi, sai dai lokaci guda ta canza mashi murmushin izuwa bakinciki, domin kuwa cigaba ta yi da cewa. "Zan iya yin komai a kan my Hero, amma ba wai hakan yana nufin zan iya yi har da saɓon ALLAH ba! Ko kan iyayena ba zan iya saɓawa ALLAH ba, dan haka ba zan aikata zina saboda cetan ransu ba, sannan ba zan iya bada kai'na da na yi ƙoƙarin killacewa na kare mutumcina tsawon shekaru domin in kawowa mijina mutumcina wa wani ba, dan haba bayan my Hero to wlh na gwammaci mutuwa da na bawa wani, kuma da kake maganar kashesu ai ba kai ka riƙe rayukansu ba, ALLAH da ya haliccesu shi kaɗai yasan ranar da zasu mutu, kai baka isa ka kashesu ba, idan kuma kana da ja da maganata ka kashesu ni ma ka haɗa da ni, dan wlh da na baiwa kare irinka kai'na gara na mutu mutuwa mafi tsanani da azaba!". Cike da confidence ɗinta na jinin Modarawa ta yi maganar, har cikin ranta da ta yarda ta yi zina da shi gwara ya kashe su Hoorain ɗin ya haɗa da ita, dan tasan ba shi ya rike rayukansu ba, idan ALLAH ya rubuta yau zasu mutu to ko ta yi zinar da shi sai fa sun mutu ɗin, dan haka babu batun bada kanta. Kalamanta sun yi bala'in kona ransa, dan haka sai ya juyo da ita suna fuskantar juna, da tsannin karfin gaske ya dalla mata wani gigitaccen marin da sai da ta ji komai ya ɗauke mata diff, sannan ya yi jifa da ita saman gado, tana ƙoƙarin miƙewa ya damki kafafunta a in da ya janye kayan jikinta ya fata kiciniyar yagesu, ita kuwa da iya karfinta ta fara kiciniyar kare mutuncinta. Sai dai ina, ya yage mata kayan gabaɗaya ya dire shi, ya rage daga ita sai wannan ɗan vest da take sanyawa a ciki da kuma kara mub pant. Ganin hakan yasa ta dakarkare da iya karfinta ta rarumo lamp ta buga mashi a kai wanda yasa ya ɗan ja baya da ita, da gudun gaske ta sake miƙewa ta diro kasan bed ɗin. Kai tsaye ta nufi toilet ta banko kofar ta murza key. Sai dai kuma me? Yana zuwa duka ɗaya ya yi wa kofar toilet ɗin ta ruguje ƙasa, ai wani irin ihu mai sautin gaske ta saki, yau ta ga tashin hankalin da bata taɓa gani ba, ta shiga bala'i da ruɗani fiye da tinani. Da gudu ta yo waje ya biyo bayanta, rasa ina zata nufa ne yasa ta yanke shawarar da dai wannan tsinannen kafuri ya keta mata haddi gwara ta faɗa ta window kawai ta kashe kanta, ba tare da zurfin tinani ko tina cewa wanda ya kashe kansa wuta zai tafi ba, a lokacin tashin hankali ya zarce tinani a ranta, kawai ta buɗe window, bata ji bata gani ta afka ƙasa, ga shi suna sama can da nisa. INNALILAHI WA INNA ILAHIR RAJIUN, UDE YA YI SANADIN AUTA. MY PEOPLE'S ME KUKE TINANIN ZAI FARU NE WAI? ME ZAI FARU IDAN HOORAIN YA DAWO YA TADDA GAWARTA TA FAƊO DAGA SAMA? KAI NI BARI IN JE BLACK WORLD KO ZA'A ƊAN SAMU SASSAUCI A CAN!. ----------------------🔥 BLACK WORLD 🔥 Wani irin kwalliya da Sweetie ta tsantsara bata taɓa yin irinsa ba, kuma dik Ronnie ya goya mata baya, shi ya tsaya kai da fata ya tsara mata yadda zata ƙasance, an shirya komai su kaɗai ake jira, shi ma Ronnie ya yi shiri cikin wannan white suit ɗin nasa, Pretty ta sanya ɗaya daga cikin kayan Sweetie, sun yi bala'in kyau tamkar ka sacesu ka gudu, jama'a sun hallara sun cika hall ɗin tab, robot sai rabon drinks a cikin manya-manyan tsadaddun glass cups suke yi. Abin ba'a magana. Sai tashin fitinannen kamshi suke yi, cike da zumuɗi Sweetie ta ce tana zuwa bari ta riga kowa ganin kwalliyar Big Bro. Sai a lokacin ne Pretty ta ce. "Sweetie ina wancan mutumin ne na jiya?". Kun san ita fa Pretty saboda tabbatar sakalci da shashanci ko sunan Smart bata sani ba. Ba tare da Sweetie ta amsa mata ba ta ce. "Ki jirani ina zuwa, bari in je". Bata jira amsarsu ba ta yi gaggawar wucewa waje. A ranta kawai tana tina irin yadda suka kasance daren jiya, sai take jin wani irin tsantsar farinciki na wuce misali. Tana zuwa kai tsaye ta shige cikin room ɗin nasa. Ya subhanallah, ai mutuwar tsaye a bakin kofar ta yi tana kallan cikin room ɗin game da zaro idanu. Ba ta san lokacin da a fili ta furta. "Tsarki ya tabbata ga UBANGIJIN da ya yi wannan halitta". Jin voice ɗinta yasa ya juyo, dama yana tsaye a tsakiyar ɗakin yana ƙoƙarin gyara hannun suit ɗin jikinsa, ya bawa kofar shigowa baya, my people's na ce wai kun san daga ina guyson ya gado ɗaukar wanka kuwa? Gaskiya Black Tiger karshe ne, kuma ga shi dik irin wankan da zai ɗauka sai kayan sun hau da jikinsa, sai ya yi wa kayan makurar kyau, shi fa shi yake yi wa kaya kyau ba su suke yi mashi kyau ba, tamkar wata cikin taurari, kun san idan wata yana waje gabaɗaya disashe hasken taurari yake yi, haka Black Tiger idan ya shiga waje. Wlh ya yi fitina a cikin wanna kaya, sai dai da kallo ɗaya zaka yi mashi kayan jikinsa a mace take, dik baya cikin mood mai kyau, kun san Ronnie ya katse mashi jin daɗi mafarkinsa, bai barci ya kai babban sashe ba. Yana juyo da kallonsa a kanta a wani irin slow ya zame hannunsa daga ƙoƙarin gyara hannun rigar tasa da yake yi, kayan jikinsa da na Ronnie kusan iri ɗaya ne, fararen suit kal masu bala'in tsada, sai wasu kwalliyar duwatsun gold daga kirjin rigar wanda suka kara haskaka kayan over, yana sanye da wasu kafuran covers da tin da nike a kafafunsa kawai na taɓa ganinsu, sun yi fitinar kyau. Kafeta da kallo ya yi da waɗan nan idanun nasa masu kaifin bala'i, shi yana ganin tsantsar kyanta ita ma tana ganin tsantsar kyansa. Almost 2 mins for silent, da kyar ya iya zare kallansa daga kanta tare da ɗan juya mata baya yana mai da hannunsa a saman hannun rigar, botiran dake wajen yake son gyarawa ya sanya. Yana ƙoƙarin buɗe wajen botir ɗin bai ankara ba sai ganin ƴan kyawawan hannunta a saman wajen ya yi, sam bai ji takowanta ta zo garesa ba. Bai san time ɗin da ya sakar mata hannun rigar ba, idanunta a kan fuskarsa ta buɗe wajen botiran ta sanyasu, shi ma cikin idanunta yake kallo tamkar zai cinye da ido, lokaci guda mafarkinsa na ɗazu ya dawo cikin brain ɗinsa. Kamar wanda aka tsirawa allura ya ɗan sauke ajiyar zuciya kafin ya ce. "Today you looks more beauty than everyday". Wlh bai san ya faɗi waɗan nan words ɗin ba, sai da ya kalli ta zaro mashi idanu ne ya fara tinanin wai ma me ya faɗa ne. "Idan ana maganar kyau, daga kanka an rufe kofa, idan ana maganar iya gayu daga kanka ba'a sake kiran wani suna, idan ana maganar haɗuwa ne daga kanka sai shiru, kai makura ne da ita kanta kyau sai da ta jinjina maka". Ta faɗa tana zame hannunta daga hannun rigar tasa, ya gama sanya mashi botir ɗin. Yadda suka tsaya a tsakiyar ɗakin nan sai sun yi makurar birgeka, tamkar wasu mata da miji da suka mallaki juna, sun haska sosai. Hannu yasa ya ɗan tallabo bayanta kaɗan, sannan ya juya magic eyes ɗinsa, lokaci guda ya canza mata chain da ɗankunnen dake kunnanta, ya zuba mata diamonds one's masu bala'in kyau, yake ta kara haskawa tana wani sheki sosai. Zubawa ɗan bakinta da ta motsa a yanzu idanu ya yi, a duniya Black Tiger yana mugu-mugun sha'awar ɗan bakin nan nata, first thing da yake balai'n ɗaukar hankalinsa a tattare da ita, sai dai shi da kansa ya matsawa kansa ya hana kansa da kansa jin daɗin rayuwarsa wai baya son raini. Slowly ya ɗan saketa yana kawar da kallonsa daga kanta. Da hannu ya nuna mata kofar fita, can ƙasan makoshinsa ya ce. "Ki je kawai". Saboda tsabar neman magana irin na yarinyar nan sai ta matsa dab da shi, kamar mai raɗa haka ta ce. "Matso ka ji wani magana". A dai'dai wannan hali baya iya ja da maganarta, saboda yana cikin wani irin hali, yadda take magana kurkusa da shi sai mai tsananin juriya zai iya daurewa, dan haka sai ya rankwafo da kansa a kanta kaɗan kamar yadda ta buƙata. Ɗaga ƴan kafafunta sama ta yi, ta mance da akwai red jambaki a hakinta, haka ta manna mashi sumbata a saman lallausan kumatunsa wanda sai da ta sanya shi limshe idanunsa yana wani jan dogon numfashi game da saukewa a hankali. Shatin ɗan bakinta ne ya fito zat a kumatunsa, ga shi fari tas ga jan janbaki ai kunga dole ya bayyana sosai, shi bai yi zatan janbakin da ta saka mai iya fita a sauki bane, dan haka sai bai san ya shafu a face ɗinsa ba. Slowly ya waro idanun nasa a kan kyakkyawar face ɗinta, kasa ta sauke kafafunta tare da juyawa zata bar wajen tana faɗin. "Take care bye-bye..........". Ai bata kai karshen maganar ba sai jinta ta yi a saman Lion chest ɗinsa, haba ai ta tsokano, dama ya lafiyar kura, ga mafarkinsa bai ƙarisa ba, sannan ya yi tozali da kyakkyawar face ɗinta, yana ƙoƙarin kame kansa ta zo ta bashi sumbata kuma ta zaci zai kyaleta ta tafi a banza? Ina ai bata isa ba. Hannu yasa ya riƙo waist ɗinta a hankali, rankwafo da kansa sosai a kanta ya yi har suna iya shakar numfashin juna. A gaggauce ta datse idanunta gam ganin yadda ya yi dab da ita, idanunsa su yi mata kaifin da ta ji ba zata iya ganinsu a kurkukusa ba. Bata ankara ba sai jin saukar lallausan lips ɗinsa a saman tata ya yi, ai wani irin zabura da ta yi har bata san lokacin da ta furta. "Na shiga ukuna ba". Da ɗan karfi ta yi maganar tare da janye kanta baya da shi tana zaro idanu waje. Shi kuwa ya rigada ya sanyawa ransa sai ya ɗanɗani ɗan bakin nan nata yau, saboda abin ya zo mashi har wuya da ba zai iya shanyewa yau ba. Da ƴar gudunta ta juya zata nufi waje, sai kuma me? Ai sake ganin kanta a saman Lion chest ɗinsa ta yi, muryarta ne ya hau yin rawa, da kyar ta iya cewa. "Please Big Bro ka yi hakuri ka ji?". Kai ya ɗan girgiza mata kamar karamun yaro, alamar ba zai hakura ba, daga haka ya sake haɗe fuskokinsu waje guda, ai wani irin kankame jikinta da ta yi sai da ta bashi mamaki, shi kun san bai ɗauki kiss matsayin haramun ba duba da yacce suke. Kurawa ɗan bakin nata idanu ya yi, sai a lokacin ya yi realayzin kamar janbakin da ta saka mai iya shafan wa mutum ne. Dan haka sai ya fito da tongue ɗinsa ya ɗan lashi lips ɗin nata dan ya gani, yana da dogon harshe sosai. Ai tamkar zata saki fitsari a wando yadda ta ji saukar tongue ɗin nan nasa saman lips ɗinta, bata san lokacin da ta kai hannu ta ƙanƙame suit ɗin jikinsa ba, gabaɗaya jikinta ne ya hau kerma saboda wani irin tsoro da shauki da suka mamayeta a lokaci guda. Tamkar zata yi kuka ta shiga cewa. "Please Big Bro for give me, ba zan sake ba". Ai yadda ta yi maganar kara haukata shi ta yi, kuma tana buɗe baki unexpected tongue ɗinsa ta shige cikin bakinta shi da ya zo lasar jambaki ya gani. Yana jin tongue ɗinsa cikin bakinta bai san lokacin da ya kara ƙanƙameta da kyau a jikinsa ba, ya matseta sosai, slowly ya shiga juya tongue ɗin nasa a hankali-hankali yana ƙoƙarin capko nata. Gagara jurewa Sweetie ta yi, ai bata san lokacin da a miliyan ta sanya karfinta ta ture shi baya ba, da yake bai wani kame kansa ba, ya saki jiki yana wasa na harshen nasa a cikin bakinta, sai ta iya samun damar turesa, kirjinta ne yake wani irin dukan uku-uku da karfi, da gudu ta juya ta nufi waje. Slowly ya ɗago da kallonsa ya bita da ido, bai iya dakatar da ita ba, saboda shi kansa bai so yin abin da zuciyarsa ke ingiza shi ba, yana ganinta har ta fice, wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya wuce ya fito shi ma. Ita kuwa tana fita bedroom nasu ta koma, da gudu ta faɗa ciki, tana zuwa ta faɗa saman bed, babu kowa a ɗakin, dan su Pretty sun fita. Shiru ta takure jikinta waje guda tana jin wani irin shock da bata taɓa ji ba a ranta, babu abin da ranta yake tinano mata face yadda ta ji tongue ɗinsa a cikin bakinta, tsabar giyar soyayyarsa na ɗibarta wai bata taɓa jin abu mai daɗin ɗanɗano biyun tongue ɗinsa ba, ba dan tsoron kada ya zarce gona da iri ba wai da zata barshi ya cigaba da wasa da tongue ɗinsa a cikin bakin nata, saboda daɗinsa, ga shi cikin wani irin salo mai matuƙar tafiya da imani yake yi, abin ya yi matuƙar gigita notikan ƙwaƙwalwarta. OH SU SWEETIE AN FAƊA TARKON KAUNAR BIG BRO BA'A SANI BA, HAR DA CEWA TONGUE ƊINSA YA FI KOMAI DAƊIN ƊANƊANO, WATO SOYAYYA FA ZATA IYA SANYAKA FAƊOWA DAGA JIRGIN SAMA, KAI LOVE LOVE BA ZAN DAI CE KOMAI BA. Ta jima kwance saman bed ɗin tana tinaninsa, tin daga kan abubuwan da suka faru jiya, da yadda ya tallabota yanzu, yadda ya haɗa bakinsu, a maimakon ya yi kissing ɗinta sai ya zura tongue ɗinsa a bakinta kawai, salonsa ya gama rikita tinaninta gabaɗaya. Da kyar ta iya miƙewa ta sauko kayan bed ɗin, sai a lokacin ne kuma ta fara tinanin to ina su Pretty kuma?. Waje ta nufa dan dubasu. Tana fita babban parlor unexpected suka ci karo da wani robot mai ɗauke da glasses da suke shake da drinks kala-kala zai fita dasu wajen taro, hakan yasa gabaɗaya drinks ɗin suka yi mata wanka, kyakkyawan kwalliyarta da ya ɗauki hankalin Big Bro ya ɓaci, ta ji matuƙar takaici sosai, haka ta juya ta koma sama domin ta canza shiga tana tinanin irin tsara kwalliya da zata sake yi. Shi kuma robot ɗin ya hau gyata wajen, ya kwashe gabaɗaya glasses ɗin. Yana gama tsabtace wajen sai ga Big Bro ya shigo parlon daga waje, sanye yake da Black suit, a zahirin gaskiya idan ka gansa zaka ce Big Bro na gaske ne, kowa haka ya ɗauka, amma kuma ni da ku da yake mun san su biyu ne, sai muka gane Smart ne ba Big Bro ba, dan yau Big Bro namu wankan white suit ya yi. Robot ɗin nan na ganinsa ya risina ya kwashi gaisuwa kafin ya fita. Tsayawa a tsakiyar parlon Smart ya yi yana mamakin yadda kowa ya ɗauka Black Tiger ne shi, cikin girmamawa kowa ya rinƙa gaishesa, shiyasa ma suka bashi hanya babu wata tantama, cikin girmamawa. Dama already sai da ya yi bincike a kan empeir ɗin kafin ya zo, dan haka ya san ainahin in da parlon Black Tiger yake shiyasa na nufo kai tsaye. Bin parlon da kallo ya fara yi yana mamakin irin tsaruwa da tsananin kyansa, ya kuma yi mamakin matuƙa na ganin yadda suke wadaƙa da gold, dan yadda su kansu kujerun palon suka sha kwalliya da gold abin sai ya baka mamaki matuƙa. Ya shaga da kalle-kalle yana mamakin irin ɗinbin dukiya da ALLAH ya yi masu, dik wayewansa sai da ya jinjinawa empeir ɗin Black Tiger, dan bai taɓa ganin gini mai tsaruwar wannan ba. "What brought you here?". Daga saman staircase ya ji murya mai kama da tasa ta yi mashi wannan tambayar, ko bai ɗago ba yasan ɗan uwan nasa ne saboda muryar. Fuskar Black Tiger yadda kuka san an aiko mashi da saƙon mutuwa, a ɗaure tamau, babu alamar wasa, lokacin da Smart ya ɗago ya kallesa sai da ya ɗan jin shock na ganin fuskar ɗan uwan nasa, amma sai ya dake da cewa. "Ɗaukarka na zo yi mu koma gida". Ya yi maganar yana kallan cikin idanunsa cike da tsantsar kaunarsa. Datse idanunsa gam Black Tiger ya yi, dan ya tsani jin kalmar da Smart ya faɗa, baya son yana dangantasu, dan shi ba zai yarda su ƴan uwa bane. Da hannu ya nuna mashi hanyar fita game da cewa. "Get out before!". With harsh voice ya yi maganar. Gyara tsayuwarsa da kyau Smart ya yi. "I can't go anywhere without you my blood". Sake datse idanunsa ya yi ya sake warosu a kan Smart ɗin, take black heart ɗin ta motsa mashi, gadan-gadan ya sauko ƙasa. Yana zuwa bai yi wata wata ba ya shake Smart, cikin fusata ya ce kada ya sake dangantasu, dan shi ba jininsu bane. Shi kuma Smart da shi ma ransa ya fara ɓaci ne ya ce. "You're my blood, ko kaki ko ka so, idan ka musanta hakan ka cire kamanninka dake kan fuskata ko ka zo mu je ayi gwajin jini". Buga Smart da jikin bango da karfi ya yi tare da kara shake mashi wuya, sannan ya ce. "Bani da wata haɗi da ku, wannan shi ne last maganata!". Shi dai Smart tin da ya san Black Tiger yayansa ne baya jin zai sake yin gigin ɗaura hannunsa a jikinsa bare har su yi faɗa, domin kaunar Big Bro ta ratsa jini da jijiyarsa gabaɗaya, dan haka bai yi niyar ramawa ba, kawai ya tsare shi da ido. Dai'dai lokacin Ronnie ya shigo parlon, ai ruɗewa Ronnie ya yi ganin yacce fuskoki biyu suka zama ɗaya, yayansa da mai kama da shi, murza idanunsa ya shiga yi yana son tabbatarwa da shin abin da yake gani gaske ne ko dai almara ne?. Ganin gaske ne kuma ga shi suna faɗa ba halin ya tambayi yayansa yasa ya watsa da gudu ya yi sama. Jim kaɗan sai ga Sweetie ta fito da saurinta, shi kuma Ronnie ya wuce neman Pretty, dan ita ma ta zo ta ga abin al'ajabin da ya gani. A saman staircase in da Black Tiger ya tsaya ɗazun Sweetien ta tsaya, baya iya ganin face ɗin Smart saboda ya bata baya, tana dai iya ganin Black Tiger ya shake mutum. Ɗaga hannunta sama ta yi ta kyasta ƴan yatsunta da basu wuce a kama a kakkaryen nan ba. Hakan yasa gabaɗaya suka kai kallonsu a kanta, ta wani tsaya kamar wata babbar mace, hannunta ɗaya ta riko waist ɗinta da shi tana dallawa Black Tiger wani irin kallo mai kama da harara, yacce kuka san faɗa suke yi ko wata mai jin haushinsa, ko da yake tana jin haushin abin da ya aikata, shi kwata-kwata bashi da hakuri kuma baya tsayawa ya fahimci abu, ni kuwa na ce gaskiya baya tsayawa ya saurari abu, dan ai koba komai zai tsaya su yi magana ta fahimta da Smart, amma kawai ya shakesa yana neman kashesa ba tare da ya yi mashi laifin komai ba. Wato hajiya Sweetie Aunty Babba ta zo raba gardama, kai wlh Sweetie kamar wata renon tsofaffi, sai iyayi da son girma!. Slowly Black Tiger ya zare hannunsa daga wuyar Smart yana kallonta, lokaci guda kuma ya yi kamar mai acting ɗin rashin gaskiya, kamar kuma yana shakkarta, sai ya ɗan yi ƙasa kaɗan da kai yana satar kallonta. Shi ma Smart ita yake kallo da mamaki, dan a tinaninsa Pretty ce, bai lura da kalar gashin kanta ba, da yake ma ta sanya siririn silky headband a kan nata, amma dik da haka gashin nata a waje daga ta tsakiya, shi dai kawai yana kewar Pretty sosai ne yasa ya yi mata kallon ƴar tsana!. Ta yi fitinannen kyau a cikin kayan da ta sauya, irin Malesian gown ɗin nan ne wanda ya bi jikinta ya lafe, ya fito da tsantsar surar da ALLAH ya yi, wannan dalilin ya sanya Black Tiger zame hannunsa daga wuyar Smart babu shiri, dan kyan da ta yi yanzu ya ninka na ɗazun nesa ba kusa ba Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 Ai juyowar Smart ke da wuya ta yi balai'n ruɗewa, take ta fara wuwwuga eyesball ɗinta, ta kalli Black Tiger ta juya ta kalli Smart Tiger, kanta ya yi mugun shiga duhu da ruɗani, ta zaro eyesball tamkar zasu faɗo ƙasa, karfin hali irin nata yasa bata gudu ba ta daure, saboda Black Tiger yana a wajen, tasan koma menene ba zai bari a cutar da ita ba, amma dik da haka ta yi balai'n girgiza na ganin su biyu masu kama ɗaya. Ba dan Black Tiger ya fita daban ba, dan ko a cikin irinsa miliyan Sweetie zata iya zaƙulo shi, ba dan haka ba da ta gagara gane wane shi na ainahi, amma yanzu ta gane kasancewar ga shatin ɗan bakinta a kumatunsa na janbakinta, sannan ga lips ɗinsa sun kara bala'in ja saboda haɗe bakinsu da ya yi ɗazun, janbakinta ya kara tura kalar lips ɗin nasa, and da ta zuba masu ido sosai sai ta ga Black Tiger ya fi haske fata sosai, fatar jikinsa ma ta bambamta da na Smart sosai, tsabar bin kokkofi irin na Sweetie sai ta gano idanunsu yana da ɗan bambanci kaɗan, na Black Tiger ma ya fi girma da kaɗan. Dik da haka yarinyar nan bai ishata ba, cigaba ta yi da kare masu kallo tana tantance ƴan bambance-bambancen da ba kowa mutum ne zai iya gani ya banbantasu ba, sai mai kaifin ƙwaƙwalwa. Almost 5 mins for silent, tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta fara tako saman staircase ɗin a hankali-hankali, kai tsaye ta tinkarosu idanunta a kan Black Tiger babu ko kyaftawa. While shi ma ita yake kallo from head to toe. Tin daga kan yanayin tafiyarta Smart ya sha jinin jikinsa cewa ba Pretty bane, saboda Pretty bata yi wayon tafiya cikin yanga da yauki yadda Sweetie take yi ba, Sweetie ai kunga ta fi Pretty wayewa da sanin abubuwa sosai, ita kuma Pretty ta fita iya shagwaɓa da shegen son jiki. Ko da yake bama za'a haɗa ba ai, Sweetie har school ta shiga ga Ronnie na yi mata lesson a gida, dole ta fi Pretty wayewa sosai!. Sai da ta kusa karisa saukowa daga staircase ɗin Smart ya sake tabbata wa kansa ba ƴar tsana bace, dan ko yanayin surar jikinsu akwai banbanci, renon Black world da kingdom of power ba ɗaya bane ai, cimarsu ma daban-daban, dan haka harta soft skin na Sweetie ya ninka na Pretty kyau nesa ba kusa ba, da ta matso ma sai ya kara gane cewa Sweetie ta ɗan fi Pretty tsawo, ita kuma Pretty ta fita garin jiki, wato ta fita ɓul-ɓul. Da yake staircase ɗin yana da tsawo, escalator ɗinsu ne fa, yau ba'a kunna shi bane kasancewar yanzu gari ya waye, kunga kuwa yana da tsawo sosai, dan a kallah step dake wajen takawa ka hau ya kai step 35 zuwa 40 haka, shiyasa bata sauko ƙasan da wuri ba, ga wani tafiyar yanga da take yi, ashe daga bayanta ba doguwar rigar tana ja mata har ƙasa. Ai bata karasa ruɗewa ba sai da ta sauko ta tabbatarwa da kanta fuskoki biyu masu kama ɗaya take gani, har lokacin bata yarda mutum biyu bane, a ɗan nesa da su ta tsaya tana cigaba da rarraba eyeballs ɗinta a kansu, lokaci guda ta shiga kyafta idanunta tana sake buɗewa, dik bai isheta ta gasgata abin da take kallo ba, hannu tasa ta fara murza idanunta tana girgirza har da cewa. "Burrrrrrrrrrr ba gaskiya bane, kawai shashatau ne, kai ina a'a wasa da hankalina Big Bro yake son yi". Lokaci guda kuma ta ce. "Cool down Sweetie cool down, wasa da brain ɗin Sweetie kawai Big Bro zai yi ya raina mata hankali, dan haka ba zan yarda da shi ba, mutum ɗaya ne, mutum na biyun ni kaɗai nike ganinsa na tabbata, dan shashatau ne, cool down Sweetie". Wata iriyar dariya ta saki kamar zararriya kafin ta fara takawa izuwa in da suke, ta yarda manna mata hauka Black Tiger ya yi, har da cewa da magic ɗinsa ya yi amfani wajen kirkirar mai kama da shi dan ya wasa ƙwaƙwalwarta, dan haka ta ganosa har da cewa zata yi maganinsa kuwa. A gabansa ta dakata tana kallon cikin idonsa, shi dai Smart kusan suman tsaye ya yi saboda yacce ya fahimci ba ƴar tsanarsa bace, idan kuwa haka ne to wacece ita? ALLAH MAI IKO! TANA MAMAKINSA SHI MA YANA MAMAKINTA. Jin sai wani irin huci mai bala'in zafin gaske Black Tiger yake fitarwa tamkar zai kama da wuta ne yasa ta kara matsawa kusa da shi. Hannu ta ɗaura saitin Lion chest ɗinsa, kamar zata taɓa saitin zuciyarsa sai kuma ta ɗan fara shafa wajen, in a cool way sosai ta fara faɗin. "Cool down our Big Bro, cool down please, zafin ya yi yawa, yi sanyi haka kada zuciyar nan ta fashe, bamu son wannan black heart ɗin Big Bro, yana wahalar mana da kai, please ka kwatanta yakicesa ka gefar ka ji?". Cikin sigar rarrashi ta yi maganar, tana cigaba da shafa saitin zuciyarsa. Lokaci guda suka ji a bayyane ya sauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya almar black heart ɗin ta fara sauka kenan, da gaske ya fara cooling down ɗin fa, ALLAH mai iko mai yin yadda ya so, yanzu da a baya ne kuna tinanin Sweetien ta isa tasa black heart ya yi cool? Ai da tana nufo shi da ita dik zai haɗe ya turmushe. Smart dai yanzu kamar kansa ta kulle kamar kuma bata kulle ba, ya ma rasa gane a wani hali yake a ciki kuma me yakamata ya yi?. Cigaba Sweetie ta yi da shafa kirjinsa tana faɗa mashi cool words masu kwantar da hankali, ita sam bata gasgata Smart gaske bane, ta barsa matsayin almara ko shashatau shiyasa bata bi ta kansa ba. Almost 5 mins sukena haka kafin Black Tiger ya sake sauke wata nannauyar ajiyar zuciya mai sauti sosai alamar ya sauka gabaɗaya, hannunsa ya kai ya riƙo nata dake a saman kirjin nasa, bai iya ce mata ko uppan ba, ya ƙanƙame hannunta kamar zai mayar cikin nasa.... ALLAH YA FI GABAN WASA, ALMOST 2 YEARS SWEETIE TANA ADDU'A ALLAH YA SASSAUTA BLACK TIGER AI DOLE MA YA YI SAUKI, ADDU'A BATA FAƊUWA KASA BANZA SAI DAI JINKIRIN AMSAWA!!. Da dai Smart ya ga waɗan nan ba kula shi zasu yi ba sai ya ce bari shi ya kulasu, sun tsaya sun tsare juna da kallo ko kaɗan basu iya kyafta idanu, dan suna ganin kamar da zarar sun kyafta idanu za'a nemi ɗaya daga cikin a rasa, wato za'a ɗauke ɗaya, shiyasa suka mace da ganin juna babu kyaftawa. Yanzu Smart ya gama fahimtar cewa Sweetie tana da alaƙa mai karfi a tsakaninsu da ɗan uwansa da kuma ƴar tsanarsa, sannan ya gano cewa idan har ana son nasara a kan Black Tiger to fa a haɗa hannu da Sweetie, kun san mutanen da kaifin basira, a cikin idanun Black Tiger ya karanci cewa Sweetie tana da mahimmanci a wajensa, kuma ya gani a zahiri yadda ta taushesa cikin lokacin da bai fi minti goma ba ya sauko, abin ya ɗan sanya Smart a kokwanto da tinanin wacece ita?. Gyaran murya ya ɗan yi masu wanda yasa dikkansu suka yi saurin janye idanunsu daga cikin na juna, a hanzarce Black Tiger ya zame hannunsa daga riƙon da ya yi mata yana wani ɗan dojewa kamar yana jin kunyar Smart kamar kuma ita yake jin kunya, yana wani ɗan sunkuyar da kansa ƙasa. Ita kuma zabura ta yi game da matsawa kusa da Smart ta kara kusanci da Black Tiger, a razane tana zazzaro idanu ta ce. "Big Bro ka cire mun wannan almara da ka saka mun ɗin, saboda yana bani tsoro, kamansa da kai yana gigitani". Words ɗinta gabaɗaya haɗewa suke yi a lokacin da ta yi wannan magana. Slowly ya ɗago da kallonsa a kanta, in a cool way sosai tamkar mai raɗa ya ce. "You means that kema kina ganin kamata da tasa? Kenan ba saka kamannin ya yi dan ya shiga rayuwata ba?". BALA'IN WATO SHI BLACK TIGER YA ƊAUKA KAMANANNIN FUSKARSA SMART YA SAKA DOMIN YA YI KAMA DA SHI YA SHIGA RAYUWARSA, LALLAI BLACK TIGER BAI SHIRYA KARƁARSU MATSAYIN ƳAN UWA BA MA KENAN, TAB ƊI JAM!!. "Big Bro wannan ai sak kai ne, ALLAH kuwa babu wani banbanci, please ka ɓatar da almarar mana, ban son ganinsa, yana rikitani sosai dan ban taɓa gani kama irin haka a zahiri ba". Tana gama rufe baki sai ga Pretty da Ronnie, ya je ya kwakulota a kan lallai ta zo ta ga mai kama da yayansa, wato Ronnie fa ruɗewa ya yi, ya ga abin da bai taɓa gani ba, sai ya rasa me zai yi shi ne ya je ya kirasu. Ta sha kwalliyarta cikin irin kayan da Sweetie ta sanya a farko kafin robot ɗin can ya ɓata mata kayan, ta yi bala'in kyau. Ai tin daga kan yadda ta bar gashin kanta a buɗe Smart Tiger ya gane ga yar tsanarsa, tana wani turo baki ita a dole Ronnie ya ɓata mata rai da ya sanyata fitowa, da kyar ya samu ta zo, dan ta ce ita barci zata yi ba zata fita ba. Nan fa shi ma Smart ya ɗan ruɗe ya shiga rarraba eyeballs ɗinsa a kan face ɗinsu, ya kalli Pretty dake a saman bene ya wurga ido ya kalli Sweetie dake a gabansa tana korawa Black Tiger bayanin irin kamar dake a tsakaninsa da Smart. Yanzu Smart ya gama fahimtar kamar yadda yake da Black Tiger haka ita ma ƴar tsanarsa take da wannan mai golden white hair ɗin, take ya ji hankalinsa ya yi wani irin Musulmin kwanciya, da a tinaninsa ai juyar mashi da hankalin ƴar tsana aka yi ta mance da shi, sai yanzu ya gano gaskiya. Ai Pretty na sauke kallanta a kan Smart ta zaro idanunta waje, dan kunga bata iya wani banbantasu da Black Tiger, in baku manta ba ta ɗauka ma Black Tiger shi ne Smart, so bama ta mayar da hankali a kan Black Tiger da Sweetie dake tsaye a wajen suna magana ba, tana zuwa kawai a kan Smart ta sauke kallonta. Ai da gudu ta fara tattaka staircase ɗin game da ɗan ɗaga rigarta dake jan kaya. Tana saukowa da gudun gaske ta yi kansa tana turo baki na shagwaɓa, juyowa gareta da kyau ya yi, ya buɗe mata hannayensa, tana zuwa da gudun gaske ta faɗa jikinsa. Wani irin lumshe idanunsa ya yi tare da ɗagata sama ya manna da Lion chest ɗinsa yana sauke sanyayyar ajiyar zuciya mai Musulmin daɗi. Da sauri Sweetie and Big Bro suka wurga eyesballs ɗinsu a kan Pretty da Smart, Sweetie bata san lokacin da ta zaro idanunta waje ba, a razane ta ce. "Ke Pretty kina iya ganinsa ne? Kin san shi ne?". A matuƙar rikice ta yi maganar. Ɗago kai daga jikin Smart Pretty ta yi, cike da shagwaɓa ta ce. "Wannan ai shi ne mutumin da na baki labari jiya, wanda na ce maki ya hanani yi wa Kamran ɗin mu magana". A wani irin miliyan Sweetie ta dawo da kallonta a kan Black Tiger. "Dama ba almara bane? Dama gaske ne?". Kai ya jinjina mata, lokaci guda ta ɗauke wuta diff ta yi sumar tsaye saboda razana, ita dai Pretty yarinya kamar mai motsi a kai, wlh ko a jikinta da ta ɗago ta kalli Black Tiger, ba wani razanar da ta yi, bai yi mata kamar ta ga wani abin mamaki bama, kun fa san mutuniyar abin da yake a gabanta kawai take yi, babu ruwanta da shiga wani hurumin, dai haka sai ta mayar da kanta saman gefen wuyarsa wajen shoulder ɗinsa ta kwanta. Shi dai Ronnie ya tsaya a saman bene yana kallon ikon God yau, kansa ta kulle da wanna alamari. Slowly Big Bro ya ɗan motsa lips ɗinsa tamkar suna yi mashi ciwo, can ƙasan maƙoshinsa ya kira Sweetie da wani sunan da su Smart basu iya jin me ya faɗa ba, ni kai'na ban ji me ya ce ba, tinani ma nike yi wai dama ya san sunanta ne ko dai da bai san sunanta ba sai ya raɗa mata wani nashi daban?. Shiru bata motsa ba, kamar gunki take tsaye idanunta a kan Smart. Lokaci guda Black Tiger ya ɗan ji wani abin ta tsikari zuciyarsa, hannu yasa ya jawota jikinsa yana cigaba da ambatar wannan suna da ya ki buɗe murya kowa ya jisa. Smart ne ya dawo da kallonsa a kansu, cikin sanyin murya ya ce. "I think suma fa ta yi, bakaga bata breathing bane?". Wani irin harara Black Tiger ya dalla mashi har sai da Smart ya ji makoshinsa ta bushe yana buƙatar shan ruwa, ba tare da Black Tiger ɗin ya kalli in da yake ba cikin natsuwa sosai tamkar baya son yin magana ya ce. "Me kuma zaka ce mun bayan kai ka nuna mata wannan fuskar taka kasa ta suman?!". Maganar Big Bro ta sanya Ronnie dake a tsaye murmushi, wato Black Tiger na daban ne, ga iya yin magana a dunkule, ga shi muryarsa mai shegiyar tsada ne da in ya yi magana har tsayawa ake yi ko zai kara yi, sai ayi magana goma bai amsa ɗaya ba, bugu da ƙari muryar tasa shegen daɗi ga sanyi da matsuwa a cikinta. Ajiyar zuciya Smart ya sauke, ba karamun daɗi ya ji ba na yadda Black Tiger ya yi mashi magana, bai taɓa mashi magana a tausashe haka ba, infact bai ma saurarensa ai...... gaskiya a yau da Sweetie da Ronnie sun shiga ruɗani sosai. Amma kuma yadda Big Bro ya yi wa Smart magana a yanzu fa kamar zuciyar Big Bro ɗin ta fara saduda tana ƙoƙarin rungumar kaddararsa. Shi dai Smart koba komai ya yi murna yau ɗan uwansa ya bashi amsa a natse da taushi. "Ba laifina bane ai, amma amun afuwa ba zan kara razana maka Heartbeat ba, bari ma in samo ruwa..........". Smart bai iya kai karshen maganar ba sakamakon wani irin kallo da Black Tiger ya jefa mashi wanda ya sanya shi haɗiyar sauran zancen, ba komai yasa ya yi mashi wannan kallo ba kuma face yadda ya kira Sweetie da heartbeat ɗinsa, sai ka ce ya ce mashi hakan take a wajensa. Shi kuma Smart ya yi duba ne da yadda zanen ɗan bakin mace ya fito a kumatun Big Bro na sumbata, ga lips ɗinsa ma da alamar janbaki kamar ya yi kissing mace, sannan irin janbakin shi ne a bakin Sweetie ɗin, bugu da kari a gaban idanunsa ta zo ta rarrashi Big Bro kuma ya hakuri zuciyar ta sauka, ai dole ya kira Sweetie da sunan da ya fi heartbeat ma ga ɗan uwan nasa, dan yaga abin is too much a ce babu wata alaƙa. "Please my blood ka yarda da ni mana". Cewar Smart da ya yi maganar yana tattare gashin Pretty da ya rufe mata idanu. Ba karamun burge Black Tiger wannan haɗi ya yi ba, dik da cewa bai san a wani matsayi ya ɗauki Sweetie a cikin ransa ba, amma for show ya ji daɗin ganin yadda Smart ya ɗauki Pretty, sannan ya ji daɗin zuwan Smart sosai, dama haka kawai ya tsinci kansa da kewarsu sosai tamkar sun saba rayuwa a tare, har yana tinanin sanyawa a ɗauko mashi Mommah a kawota birnin, but zuwan Smart ya ɗan rage mashi kewar Mommah ɗin. Ko sannu Black Tiger bai sake ce mashi ba, bai ma sake kallan in da yake ba, ya ɗan rage tsawonsa ya ɗauki Sweetie cak sai saman shoulder ɗinsa, sannan ya nufi staircase da ita. Shi dai Ronnie yana tsaye ban da murmushi babu abin da yake saki, a ransa ya ce koma wanene Smart shi dai ya yi farincikin ganinsa kuma ya ji sonsa a ransa duba da yadda yake kama da yayansa. Dab da Black Tiger zai cire kafansa daga benen ya ƙarisa haurawa sama kenan muryar Smart ta katse shi da cewa. "Please my blood ka yarda da ni, trust me and zan baka hujja". Ko kaɗan Black Tiger bai sauraresa ba ya wuce izuwa bedroom ɗinsa. A fili Smart ya ce. "Idan baka yi taurin kai bama ai ba Abdul Malik bane kakanka, baka da maraba da daddy! Kun san gaskiya amma bakwa son bi, ina da tabbacin kasan gaskiya ko kuma zuciyarka ta aminta da ni, kawai wannan balaƴaƴan taurin kan naku da jin kai ɗin ne ba zai barka ka amsa ka aminta da ni ba, ni dama na shiryawa dik wani taurin kanka zan jure har sai na mayar da kai gida, ai dama in baka yi wannan taurin kai da kafiya game da zafin zuciya ta jinin Modarawa bama sai in ce fuska irin tawa kawai aka sanya maka bamu da alaƙa, amma wannan taurin kan yasa na kara yarda kai jinina ne na haƙiƙa!". Tin da ya fara magana idanun Ronnie a kansa har ya kai karshen maganar, sannan ne Ronnie ya ce. "Idan zan iya canka dai'dai kai ɗan uwan Big Bro ne ko?". Dawo da kallonsa Smart ya yi a kansa, kamar ba zai amsa shi ba, amma sai ya tina idan har yana son yin nasarar komawa da ɗan uwansa gida to fa dole ya taushi zuciyarsa ya bi matakai biyu domin nasara, na farko ya samu jituwa tsakaninsa da makusantar Black Tiger, dan zasu taimaka mashi sosai, na biyu kuma ya shiga jikin ɗan uwan nasa su yi sabo sosai ta yadda ko Black Tiger ɗin yaki yarda ya bisa to wannan shakuwa zata sanya idan ya tafi Black Tiger ya gagara samun natsuwa da kwanciyar hankali har sai ya biyosa. Yin wannan tinani yasa Smart sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da cewa. "He's my twin brother". Wani irin ƙayataccen murmushi Ronnie ya saki bawan ALLAH kowa nasa ne, shi fa yana son kowa. Dama shi Ronnie kun ga bai san komai dangane da mahaifin Black Tiger ba, dan haka kome aka ce mashi yanzu zai iya gasgatawa ne. "Na ji daɗin jin wannan zance, zo mu je in kaika ɗakin Big Bro ɗin". KAMAR BLACK TIGER YA CE MASHI YA KAISA ƊAKIN, KAWAI SABODA ZUMUƊI NE. Sosai Smart ya ji daɗin maganar Ronnie, saboda dama burinsa ya shiga jikin Black Tiger sosai, nufo saman bene ya yi yana kara gyarawa Pretty kwanciya a kirjinsa da kyau, ta wani lafe luf abinta. Gaba Ronnie ya yi suka rufa mashi baya, kai tsaye ya kai su bedroom na Black Tiger, sai bin ko'ina da kallo Smart yake yi yana kara jinjinawa karfin duniyar da ALLAH ya yi wa wannan birni. Lokacin da suka shigo cikin ɗakin dikkansu sai da suka ja birki suna kallon waɗan nan kyawawan furannin, tamkar wata da tauraruwa Zahra. Zaune take a saman sofa ta farfaɗo, idanunta suna ciccike da kwallah, yana a zaune a gefenta ya ɗan juyo suna fuskantar juna, ya riƙo hannayenta cikin nashi, da alama magana mai muhimmanci suke yi. Magana suke kan yadda Smart ya yi kama da Black Tiger over, ta kafe a kan lallai ya yarda da Smart ɗan uwansa ne saboda kamannin, ba komai ne yasa ta yi hakan ba kuma face a yadda ta ga Smart ta ga Mommah tasan musulmai ne, to burinta kawai shi ne Black Tiger ya karɓi musulunci, a tinaninta tin da kowa nasa musulmai ne shi ma zai musulunta, tausarsa da take ta faman yi kenan tin da ta farfaɗo, shi kuma ya kafe mata a kan bashi da alaƙa da su. Shi ne idanunta suka cicciko da hawayen yaudara zata yaudarar mana zuciyar Big Bro ɗinmu, zata fara kukan namu na mata mai karya zuciyar namiji dik taurinsa, har da wani nuna damuwa a kan fuskarta ta wani marairaice mashi a siffar tausayi. Already ya faɗa mata yadda suka yi da Smart and Momma a CROWN OF POWER. Shi ne ya riƙo hannunta yana kallan fuskarta, so take yi ta yaudaresa ta yi mashi wayan da ta saba, har da ƙaƙalo kuka tana ce mashi. "Ko ba dan shi ba (Smart) ka duba mahaifiyarku, uwa ce fa, ita ta sadaukar da rayuwarta ta kawoka duniya, please Big Bro kada ka yi avoiding ɗinsu, suna tsananin sonka, kalli yadda ya bar kowa ya biyoka, idan har basu da alaƙa da kai me zai sa su damu kansu da kai? Nasan kana da kaifin basira da tinani, domin dik mutumin da zai iya tafiyar da birnin nan kan tsari mai kyau da cigaba kamar yadda kake yi ya tabbata kaifin brain ɗinsa ya zarce yadda ake tinani, nasan kana da basirar da cikin ƙanƙanin lokaci zaka iya gano gaskiya, please our one and only Big Bro ka daure ka duba wannan lamari". Ta kai karshen daɗin bakin nata hawayenta na zubowa a kan lallausan kumatunta. Kurawa hawayen nata idanu ya yi na ƴan sakanni. Can ƙasan makoshinsa ya ce. "Wannan ba hawayen gaske bane, na yaudara ne, dik time da ke kanki kika gaskatatu har kika yi hawayen gaske i will think about them". Babbar magana, wato idan ta yi hawayen gaske ne ma zai yi tinani a kansu, da kyau Big Bro. Ya gano hawayen yaudara Sweetie take yi mashi, hege Big Bro akwai ƙwaƙwalwa kam. Dama ku daga ganin irin kaifin ƙwaƙwalwar Smart da yadda yake fama da nuclears ai daga nan yakamata ku fara tinanin ƴan biyu ne ko kuma ƴan uku or quadruple ne shi, dan sune suke da baiwa na musamman da bakowa yake samun irinsa ba. Girgiza kai ta shiga yi, muryarta na rawa ta ce. "Big Bro da gaske na gasgata su, kuma na yarda they're ur blood, please kada ka ki yarda, zan iya aminta cewa hawayen na ƙaƙalo shi ne domin in nuna maka yadda na yarda da su, amma har cikin zuciyata na yarda da jininka ne". Sake hannayenta ya yi zai miƙe ba tare da ya sake yin magana ba, da sauri ta kai hannu ta riƙo nasa. "Please Big Bro, zan yi kome kake so in har zaka jaraba yarda da su ko da na kwanaki ne". Dawo da kallonsa cikin kwayar idanunta ya yi, while ita ma shi take kallo. "Komai nike so zaki yi?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e. "Komai fa?". Ya sake faɗa can kasan maƙoshinsa ta yadda su Smart dake tsaye a bakin door ma basu iya jiyo me ya faɗa ba. Shiru ta ɗan yi, sai ta ji shakka da tsoron amsa cewa komai zata yi, saboda ta san yanzu yana jin feeling, tin da ya zura tongue ɗinsa a cikin bakinta ɗazun hakan na nufin yana sha'awarta, kada ta je ta amsa zata yi komai kuma ya zo da buƙatar ta bashi kanta dan su hakan ba wani abin bane a garesu, abin da kuma ba zai taɓa yiwu ba, dan haka sai ta shiga ruɗani da tinani. Miƙewa ya yi, gently ya ce. "Idan zuciyarki ta dai'na rawa ta natsu waje guda sai ki yi magana". Yana kai karshen maganar ya wuce ya nufi siririn staircase da zata sada shi da sama. Da kallo su Smart suka bishi, a ransa Smart ya ce wannan da alama ko daddy ya baka hanya a taurin kai, ga hujja karara amma saboda taurin kai da kafiyar bala'i ka ce ba haka ba, dole dole sai ka karyata abin da yake a matsayin gaskiya?. "Pleasure waye ya ce ka kawo mun su nan?". Black Tiger ya faɗa a yayin da ya tsaya saman step na farko na staircase ɗin, idanunsa a kan Ronnie ya sauke kallansa yana kara ɗaure fuska over to over. Siririn murmushi Ronnie ya saki, sai yanzu ya lura da janbakin Sweetie dake manne kumatun Big Bro, ganin babu alamar wasa a kan fuskarsa yasa Ronnie ya natsu tare da cewa. "Big Bro please mana, shi fa ya ce yana son zama tare da kai, pl............" Wani irin fusataccen kallon da Big Bro ya wurga mashi ne yasa shi haɗiye sauran maganar tasa. Wucewa ya yi yana nufar sama ba tare da ya sake yin magana ba. Yana taka step na uku kenan muryar Smart ta katse shi da cewa. "Na aminta da kai cewa bamu da alaƙa da kai, amma please ina neman wata alfarma guda ɗaya". Bai dakata daga tafiyar da yake yi ba, kuma bai amsa masu ba, yana tafiya tamkar wani mayunwacin zaki zai nufi nama, kamar ransa ta ɗan ɓaci. Binsa da kallo Smart ya yi har ya karisa aurawa bai tankasu ko ya kalli in da suke ba. Ajiyar zuciya suka sauke gabaɗayasu at once, har Sweetie, sannan ne Ronnie ya ce. "Big Bro yana da sauki kai kuma yana da wuyar sha'ani, sannan idan ka iya zama da shi sai ka fi kowa farinciki, ku karisa ciki ku zauna". Ya kai karshen maganar tare da nuna masu saman sofa. Sauke Pretty Smart ya yi, sannan ya nufi staircase da Black Tiger ya haura. Ɗan zaro idanun Ronnie da Sweetie suka yi, cike da tashin hankali Ronnie ya ce. "Am please kada ka bisa, nasan waye shi, nasan ya tsani a yi mashi kutse a abin da bai ɓukaci kowa ba, zaku iya samun matsala fiye da a yanzu". Sai dai dik a banza, Ronnie ya gama sambatunsa Smart bai kulasa ba, ya gwada mashi shi ma ɗan zafin kai ne, ya wuce abinsa. Wlh sai da Smart ya ɗan firgita da ya isa wannan wajen na linƙaya na Black Tiger, kun tina wannan dream palacen ɗin nasa wanda Ronnie ya ɗaurewa Sweetie face da hanki ya ce su yi wasan kama mutum a cikin ruwa? To wannan dai waje, tin da Smart yake yawace-yawacensa a duniya bai taɓa ganin haɗuwar waje irin BLACK TIGER EMPIRE ba wai nan ma bai ga sabuwar da gold ke magana a cikin ba, da sai yaya kenan. Gaskiya wannan wajen linƙaya ya yi mugun tafiya da imanin Smart. Bai kara jin sha'awar wajen sosai bama har sai da ya sauke idanunsa a kan tabkekekn ƙayataccen pool dake wajen, sai tiriri ruwan ciki yake yi, da alamar Black Tiger yana son ruwa mai zafi sosai. Kurawa kyakkyawan face ɗinsa idanu Smart ya yi, take ya ji wani irin kaunan ɗan uwan nasa ya lulluɓe mashi zuciya, ya sunduma cikin ruwan har zuwa saman Lion chest ɗinsa, ita kansa kawai ya bari a waje, sannan ya datse idanunsa gam tare da ɗan ɗaga kansa sama, da alama daɗin ruwan na ratsa shi. Kai Big Bro akwai shegen iya shan kamshi da fiskilanc. Almost 5 mins Smart yana tsaye yana karewa fuskar ɗan uwan nasa kallo, unexpected ya ji cool sexy voice na ɗan uwan nasa ya ce. "What brought you here?". Smart ya ɗan yi mamaki ganin cewa Black Tiger idanunsa a rufe, ta ya aka yi yasan mutum ya shigo wajen?. Yana cikin wannan tinani ya sake katse shi da cewa. "Already I told you that bani da wani relationship with you, so get out of my life, I don't want to see you again". Still bai buɗe idanunsa ba ya yi maganar. Kun san wani abin mamaki ne, dik in Smart ya matso shi sai zuciyarsa ta harba, amma saboda kafiyar bala'i da taurin kai yaki yarda, jikinsa da zuciyarsa kawai sun ishe shi hujja, amma bawan ALLAHN nan yaki ya yarda. A natse Smart ya tako zuwa gabansa, a dai'dai saitin face ɗinsa ya tsugunna, hannu ya kai cike da so da kauna ya ɗan shafi kyakkyawa kuma lallausan kumatun Big Bro, har cikin ransa Black Tiger ya ji, amma bai nuna alama ba, cigaba ya yi da lumshe idanunsa. "Ina neman alfarmar da ka ɗaukeni a matsayin bakonka na tsawon sati guda, na yarda bamu da wata alaƙa, yanzu ina matsayin bako ne da ya kawo maka ziyara, ina fatan zan samu karramawa?". Cewar Smart kenan. Shiru Black Tiger bai tanka mashi ba, sosai Smart ya cigaba da yi mashi magiya amma bai kula ba, daga karshe Smart ya miƙe ya fito daga wajen, nan ya isko Pretty zaune saman sofa tana jiransa, Sweetie da Ronnie kuwa tuni sun fice daga ɗakin, a gefen katafaren bed ɗin Black Tiger Smart ya zauna yana kara kurawa gadon kallo, bai taɓa ganin haɗaɗɗen bed irin wannan ba, ji yadda gold suka yi mubaya'a a jikin headboard na gadan. Da gudu Pretty ta miƙe ta dawo jikin Smart, cikin shagwaɓa ta haye jikin nasa tare da saka mashi kuka a kan bata ci chocolate ɗinta na wancan rana ba, kuma yanzu shi take so. Kallon tsab ya yi mata kafin yasa hannu ya matse ɗan bakinta, cikin sanyin murya ya ce. "Wannan ɗan bakin ba zai canza hali ba, da ace na aikata wani abin a gareki sai in ce kila na ajiye baby shiyasa kike wannan kwaɗayi, amma ina shegen son zaƙi ne kawai". Buge hannunsa daga saman bakinta ta yi tana kara turowa, cikin shagwaɓa sosai ta ce. "Ni ka dai'na murɗe mun baki, dan kawai kaga ya fi naka kyau shi ne zaka zalinceni"...... Harara ya dalla mata kafin ya ɗan kara matseta a jikinsa. "Bakina dai ya fi naki kyau, kuma kinga wannan gida nima bakone ban san ko'ina ba, dan haka ba shan chocolate". Kuka ta saka mashi tare da shiga bubbuga kirjinsa tana faɗin ita dai ALLAH ba zata yarda ba, koma ta halin yaya ne ya kawo mata chocolate kawai. Sam basu ga saukowar Black Tiger kasa ba, sai suka ga mutun a gabansu sanye da wasu shaggun Three-piece suit masu bala'in kyau waɗan da suka fi wanda ya cire, mamaki ne ya yi mugun kama Smart a kan yaushe bawan ALLAHN nan ya sauko kasa har ya je ya shirya. Shakar daddaɗan ƙamshinsa Smart ya yi yana kara jin kaunarsa. Wani irin mugun kallo Big Bro ya shiga binsu da shi yana wani ɗan limshe idanu, kamar mai jin barci. Da gangan Smart ya zauna mashi a gado domin ya fara takura mashi yana shiga rayuwarsa har su saba. Wucewa balconynsa Big Bro ya yi ba tare da ya ce masu komai ba. Da sauri Smart ya yi gagawar miƙewa ya bi bayansa, yana zaman ɗaya daga cikin lutsuma-luntsuman sofa's dake wajen Smart ya iso ɗauke da Pretty a saman kirjinsa. Kujerar kusa da Big Bro ya zauna suna fuskantar juna, cike da kulawa game da kaunar ɗan uwan nasa ya ce. "Big Bro muna son shan chocolate, my wife tana son sha". Ya yi maganar yana ɗan hararar Pretty da take mashi aikin da ta saba, wato shafe mashi jiki. Banza da su Black Tiger ya yi har sai da Smart ya sake yin maganar, sannan in a low voice sosai ya ce. "Kamar yadda ka umarni Robot ɗina suka dakata da aikin da na sakasu ka umarcesu su kawo maku". Sosai Smart ya ji daɗi, miƙewa ya yi ya dawo cikin ɗakin, laptop ɗin Black Tiger dake saman table na books set Smart ya ɗauko tare da cewa Pretty ta zauna bari ya nemo mata chocolate. Shi kuma Black Tiger duba time ya yi saura 30 mins a fara party da murnar white day. Dai'dai lokacin da yake duba wannan time ɗin ita ma Sweetie tana tsaye gaban mirror ɗinta tana duba time, dan ta yi alkawarin hana Black Tiger fita, ta kuma ci alwashin wargaza wannan taron party ɗin, dik shirinta Ronnie bai sani ba, yana can yana fama da practicing na irin rawar da zai tika a yau. Ganin saura 30 mins ne yasa ta yi azaman karisa dik abin da zata yi, sannan ta nufo bedroom ɗinsa, a lokacin saura 10 mins. A gaggauce ta afko cikin ɗakin kamar ba lafiya ba. Ta wutsiyar ido Smart ya kalleta yana a zaune gefen bed yana bincike a laptop na ɗan uwan nasa, ya bawa robot umarnin da yake so, sai kuma ya kama shi mashi kutse. Kamar zai yi mata magana amma sai ya share, dan a tinaninsa matar ɗan uwansa ne, so yana son tambayarta me yake a tsakaninsu. Cikin girmamawa ta ce. "Sannu da hutawa". Kai ya jinjina mata yana ɗan mamakin canzawar kaya da ta yi cikin ƙanƙanin lokaci, ta shirya cikin wata iriyar kaya, doguwar riga ce golden color, rigar tana da roba a jikinta, hakan yasa ta bi jikinta ta lafe, gabaɗaya ta fitar mata da coca colar shape ɗinta, jikin rigar sai wani kyalli yake yi yana ɗaukar idanu, ta saki gashin kan nan nata da ya sha gyara yana ta sheki, tamkar ka saceta ka gudu, still dai red lipstick ne a bakinta, hannunta rike da cup mai bala'in kyau golden color, sai kyalli yake yi. Sosai Smart ya ji ta burgesa yacce take yar gayu sosai, ta iya ɗaukar wanda, dik kuma wankar da ta ɗauka sai ya zauna ɗas a jikinta, a ransa ya so a ce ƴar tsana ta iya gayu haka, amma ina, ban da wanka da canza kaya babu wani abin da ta iya, sai uwar shagwaɓa cike da kai. Ko kun lura da cewa Pretty tana burge Black Tiger saboda shagwaɓarta, ga shi shi kuma Smart Sweetie tana burgesa saboda wayewarta da iya ɗaukar wankanta, me zaku iya cewa a kan wannan al'amari?. Kamar zata haura sama ta duba shi, sai kuma ta yo kasa, cikin sanyin murya ta ce. "Am dan ALLAH ina Big Bro?". Ta yi maganar tana kallan Smart. Pretty na kwance a gefensa saman gadan Big Bro tana kallan celling. Da hannu Smart ya nuna mata balconynsa ba tare da ya yi magana ba. Cikin gaggawa ta afka nan, har mamakin yadda take sauri Smart ya yi. Tana shiga dai'dai lokacin Black Tiger ya ɗago dara-daran eyes ɗinsa da nufin ya saci kallan Smart, da yake glass door a wajen, unexpected ya sauke idanunsa a kanta. Ɗan tsareta da ido ya yi yana kallan yadda take tafiya. A ransa ya ji bata da gaskiya, dan in dai wajensa ta zo bata sakin murmushi hawa kawai har sai in zata yi mashi wata tsiyar, to ko murmushin me take yi a yanzu? Ya jefawa kansa tambaya. Dai'dai in da Smart ya tashi ta ƙarisa ta zauna, cike da salo mai jan hankali ta ce. "Big Bro barka da hutawa". Ta yi maganar muryarta na ɗan sarkewa saboda wani irin kyan da ya yi. Lokaci guda ta ga makoshinsa ya yi sama ya kuma yin ƙasa, gabanta ne ya faɗi, dan the same abin da ya faru da safe ne kafin ya yi kissing ɗinta. Daurewa ta yi wajen cewa. "Big Bro wutar kyau, kaga kyan da ka yi kuwa?". Ta yi maganar tare da kai cup ɗin hannunta ɗan bakinta, a zahiri kamar ta ɗan yi sipping na abin dake a ciki, amma batu na gaskiya bata sha ba. Shi dai ban da wannan kallo babu wani abin da yake binta da shi, kuma ko kyafta idanu bayani, har yau gagara iya gano dalilin da yasa idan yana kallonta ita baya kyafta idanu, komai tsawon lokacin da zai ɗauka yana kallanta ba zaku taɓa ganin ya kyafta idanu ba. Miƙa mashi cup ɗin hannunta ta yi tana faɗin. "Ka tayani sha ya mun yawa". Sweetie akwai shegen wayau, maganin barci ta zuba mashi a ciki, wai so take yi ya yi barci sai ta samu damar watsa wannan taro. Bai ko motsa ba tamkar wanda aka sassaƙa a wajen, kallansa dai a kan ɗan bakinta dake ta faman kerma a hankali-hankali. Wani irin shagwaɓe murya da bata taɓa yin irinsa ba ta yi a yau wajen cewa. "Ba zaka tayani sha ba? Ko baka son abin hannuna ne?". Still tana miƙa mashi cup ɗin ta yi maganar. Tsabar yadda yake kaunar shagwaɓa bai san lokacin da ya ce. "Huuuuuuuuu". Tare da furzar da isa mai ɗan ɗumi daga bakinsa ba, still bai motsa idanunsa daga kanta ba. Turo mashi cup ɗin dab da shi ta yi tana kara shagwaɓe fuska. Hannu ya kai ya karɓa ba tare da ya kyafta ido ba. Wani irin Musulmin daɗi ne ya dabaibaye zuciyarta, burinta kawai ya sha. Sai dai kuma abin mamaki, bata san ya aka yi ba kawai sai ganin kanta ta yi a saman kirjinta ya saita mata cup ɗin saitin ɗan bakinta ba tare da ya yi magana ba, wato alamar ta sha kenan, da alama ya gano me ta aikata a cikin green tea ɗin zata zo ta yaudaresa, kai Sweetie sai shirin ALLAH. Smart da gulma yana bincike a laptop yana satar kallonsu ta cikin glass door ɗin, dan rabi a buɗe yake. Shiru ta yi tana tinanin in har bata sha ba, to tabbas daga yau Big Bro zai yi wuya ya kara yarda da ita, zai ce cutar da shi take san yi, in kuma ta sha, to fa ita zata yi barci ba shi ba. Slowly ta ɗago da eyes ɗinta a kan face ɗinsa, ya ɗaure fuska tamau kamar hadari, babu alamar wasa a tattare da shi, ɗan shan jinin jikinta ta yi, take ta luluƙa duniyar tinanin mafita. After kamar one minute sai ta saki wani irin cool murmushi tare da buɗe ɗan bakinta ya zuba mata green tea ɗin. A maimakon ta haɗiye sai ta kunshe a bakinta tare da sanya hannu ta saƙalo wuyansa, slowly ta ɗago da kansa suna fuskantar juna, ziciyarta tamkar zai fasa kirjinta ya fito saboda tsoro da fargaba, amma a haka ta daure dan cinwa burinta, matso da face ɗinta dab da nasa ta yi, yana kallanta babu ko kyaftawa, kai tsaye ta haɗe fuskokinsu, kafin ya yi wani kwakkwarar motsi ta haɗe bakinsu waje guda. TASHIN HANKALI!. Ai Smart dake cikin ɗaki bai san lokacin da ya dakata da danna laptop ɗin da yake yi ya tattara gabaɗaya kallonsa ya mayar kansu ba, he wish Pretty ce ta iya love haka, dan a tinaninsa soyayya suke yi. Saboda zafin bugun da zuciyarta yake yi ne yasa ta kara ƙanƙame wuyarsa, a hankali ta fara shan yawunsa tana tura mashi green tea dake bakinta. NA CE BA! WAI KUNA GANIN BIG BRO ZAI IYA TSALLAKE WANNAN TARKO YA GAGARA HAƊIYE GREEN TEA ƊIN NAN KUWA? WANI IRIN YANAYI ZAI SHIGA, KAI WATO FA AKWAI SHOW A WANNAN EMPIRE ƊIN GASKIYA, UHM KU DAI MU JE ZUWA. Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 Saboda zafin bugun da zuciyarta yake yi ne yasa ta kara ƙanƙame wuyarsa, a hankali ta fara shan yawunsa tana tura mashi green tea dake bakinta. Bai san time da ya haɗiye ba, saboda ko kaɗan bai ma ji ɗanɗanon me yake sha ba, tin lokacin da ta haɗe fuskokinsu ya nemi natsuwarsa da control ɗinsa ya rasa, so bai ma san me ta tura mashi a baki ya haɗiye ba. Ita ma dai sai da kaɗan ya shiga cikinta, amma na shi ya fi yawa. Ai bai san time da ya saki cup na gree tea ɗin ta faɗi kasa ta fashe bama. Bayan ta gama tura mashi dikka sai kuma me? Gagara raba bakinta da na shi ta yi saboda irin daɗi da laushin ga wani sirri na musamman dake tattare da lips ɗinsa, bata san ya aka yi ba ta tsinci kanta da sanya tongue ɗinta tana ɗan tattaɓa lips ɗinsa na ƙasa tamkar ba lafiya ba, kamar tana san kissing ɗinsu amma kuma da alamar shakka da tsoro a tattare da ita, jikinta har ya fara kerma. Yadda kuka san sassaƙa Big Bro akayi a wannan waje, kwata-kwata bai motsa ba, kuma ko kusa ko alama bai kyafta idanunsa ba. Lokaci guda sai ga shi ya lumshe idanunsa bayan tin da ta zo wajen bai kyafta su ba, ba komai yasa ya lumshesu ba kuma face capko lips ɗinsa na kasa da ta yi ta ɗan tsotsa ta saki. Har tsakiyar kansa ya ji hakan. Tamkar wacce aka tsikara sai ta yi gaggawar zare bakinta game da yunƙurawa zata bar jikinsa sai ka ce dama ita ta kai kanta, ta manta da cewa shi fa ya kawota. Ko da ta yunkura ta gagara miƙewa, hakan yasa ta yi gaggawar ɗagowa ta sauke eyeballs ɗinta kan face ɗinsa, lokaci guda ta yi wani irin razana na ganin yadda idanunsa suka kaɗa suka yi jajir da su tamkar wuta, lokaci guda ta sha jinin jikinta, a tsananin tsorace murya na rarrabewa ta ce. "Big Bro...... Am..... In...... Dama zan je......... Ka yi hakuri....... Dan ALLAH kada ka yi mun komai..... Na tuba.... Kuma k....". Cak ta daga ta yin maganar tana wani irin haɗiyar yawu mai wuyar wuce maƙoshi, ji kake gwad yawun ya wuce, ba komai ya ja hakan ba kuma face yadda ya ɗan karkato da kansa yana kallanta, idanunsa sun kara birkicewa, kamar wanda yake a cikin maye. Smart dake kallonsu gabaɗaya yanzu kansa ta kulle, ya gagara gane a wani irin yanayi suke a ciki, sannan ya fara shakka da mamakin ɗan uwan nan nasa, a ransa yake jin kamar ba lafiya Black Tiger yake ba, abin ku da idencial, kun san idan ALLAH ya yi maka arzikin kama daga kan twins har zuwa irinsu nipples da sauransu, so irinsu in dai ba'a kaddararsu ALLAH ya riga ya rubuta masu abu zai samesu ba, yana da matuƙar wahala ko asiri ne su ya kamasu, suna da baiwa sosai musamman idencial, ko asiri aka masu bata kamasu, an ko wani abin cutarwa ne bata shigarsu, na faɗa masu sai in tin farko ALLAH ya kaddaro masu ne, amma dik yin mutum sau ya barsu nan, ina da tabbacin wannan baiwa tasu ta rikita duniyar shaiɗanu har suka ɗauke Big Bro, da alamar hakan, dan ba banza ba. Kada ku manta sama da shekaru 33 yana rufe cikin ɗaki ko parlour baya fita, saboda ance shi ba irin sauran mutane bane, fitarsa a cikin mutane akwai matsala, UHM 33 YEARS YANA KILLACE A CIKIN ƊAKI BABU FITA WANNAN AI SUN ZALUNCESHI MA. Hannu ya kai ya riko wuyarta ta baya, gabanta ne ya yi wani irin mummunar faɗuwa, zazzare mashi ido ta shiga yi, laɓɓanta suka fara kerma, idanunta suka fara ƙoƙarin ciccikowa da kwallah. A wani irin slow ya rankwafo kanta, sai da ya shaki kamshinta ya ɗan lumshe idanu kafin ya kara matsawa, kamar zai haɗe bakinsu sai kuma ya kauce game da mayar da bakin nasa gefen wuyanta, ya ɗan kwanto da kansa a saman shoulder ɗinta. "Meyasa kika cika neman fitinane?". Cikin raɗa a kunnanta ya yi maganar, daga kan yadda ya yi maganar zaka fahimci yana a cikin yanayi matuƙa. Ɗan juyowa ta yi suna fuskantar juna. "Na tuba ba zan sake ba, yanzu ma tafiya zan yi........". Bata iya kai karshen maganar ba ta ji saukar tongue ɗinsa a saman lallausan fatar wuyanta, wani irin zazzare idanu ya shiga yi, a take ta ji tamkar wadda aka buɗewa dik wasu kofofin iska dake jikinta, sai ta fara jin wani irin sanyi mai ratsa kashi zuwa ɓargo yana ratsata. Wani irin numfashi ya shiga sakar mata mai nauyin gaske, hankalinta ne ya kara ɗugunzuma ya tashi, idanunta suka shiga rawa, balls ɗin suna wani sama da kasa kamar ana jujjuyasu, yatsun hannunta sai ɓari suke yi, tana wani mammatse yatsun kafafunta, ji take yi tamkar suna yi mata ciwo ne. Shi dai Smart shiru ya natsu yana kallonsu, mamaki yake yi, kuma ƙwaƙwalwarsa tana ɗaukar karatu daga Big Bro, wai yau sai ga wanda ya shafe shakaru 33 zuwa 34 yana yawace duniya shi ne yake ɗaukar darasi daga wanda ya kare rayuwarsa a cikin ɗaki baya taka ko parlor, abin mamaki da al'ajabi, lallai ya tabbata da gaske Big Bro ɗan baiwa ne na gasken-gaske dan shi babu wanda ya koyar da shi, dik iliminsa shi da kansa ya koya ta hanyar da babansa ya ɗaura shi a kai, sai kuma wanda babansa ya kara mashi kafin ya mutu. Tana a cikin wannan ruɗani da tashin hankalin unexpected ta ji saukar hannunsa a saman shafaffen cikinta, ya kara tallabota da kyau da ɗayan hannunsa. Slowly ya dawo da bakinsa saitin tsakiyar wuyarta ta gaba kenan, dai'dai makogwaronta ya tsayar da tongue ɗinsa, kamar yana neman wani abin haka ya shiga ɗan motsa tongue ɗin nasa a wajen, idanunsa a limshe tamkar mai barci. Haba jin abin da yake yi mata a wuya ya kara ɗauka hankalinta daga hannunsa dake saman cikinta, ta shiga ruɗani sosai, jikinta sai wani tsuma yake yi, bata taɓa jin irin wannan yanayi ba, ga shi ta gagara kwakkwarar motsi, ban da ɓari da yatsunta suke yi babu abin da zaka iya gani. Tamkar saukar aradu haka ta ji saukar hannunsa a saman kirjinta, bata ji lokacin da ya haurar da hannun nasa ba, sai kawai ta ji yana laluɓar kirjinta yana cigaba da sauke mata numfashi mai nauyi, sai wani langwaɓar da kansa yake yi tamkar wanda yake a make da kayan maye. Wage baki ta yi, ta dakarkare zata zunduma mashi ihu, cikin wata iriyar zafa ya tushe mata bakin da nasa, a miliyan ta kwalalo idanu waje, tamkar zasu faɗi ƙasa, gabaɗaya ilahirin jikinta yanzu kam kerma yake yi, bai cire hannunsa daga saman kirjinta ba, bai kuma yi kissing ɗinta ba, ya dai toshe mata baki ne kawai. Slowly ya cigaba da laluɓar kirjinta yana kara sakin wani irin numfashi mai nauyi kuma mai ɗumi, wani irin uwar birki ya ja lokacin da hannunsa ta kai saman tudunsu, ita kanta wata iriyar zabura ta yi tamkar zata tashi sama, sai dai kash babu halin gudu. Hannu bibbiyu tasa tare da daƙarƙarewa da karfi zata turesa ta gudu, sai dai ina, ko motsa shi ta gagara. Bubbuga jikinsa ta fara yi da hannunta tana son ko bakinta ne ya sake mata ta bashi hakuri, sai dai ina, ko kusa ko alamar babu niyar zai saurareta. Lokaci guda hannunsa ta ɗan fara kerma tamkar yana tsoron karisa haurar da hannun nasa sama. Ganin babu sarki sai ALLAH, babu mai iya watarta, it's better for her da ta natsu ta kwaci kanta a natse, in ba haka ba ita zata wahala, dan karfinta ko hannunsa ba zai iya ja ba. Natsuwa ta yi ta dai'na mutsu-mutsu da tinanin kwace kanta, cikin wata iriyar salo mai tafiya da imani ta capki tongue ɗinsa ta fara tsotsa tana wani limshe idanu, ai take ya kara birkicewa, ya maida hannunsa saman bayanta ya kankameta da kyau, sai dai kuma me? Ta yi matuƙar mamakin jin bai ƙarisa haurar da hannunsa saman tula-talan nata ba ya zaresu, bata yi expecting ɗin haka ba. Uhm kun san meyasa yaki taɓa mata su? Kun tina ranar da ta shiga toilet ɗinsa zuba mashi wannan maganin? Kun tina me ya faru a ranar ai? Ba ta kaurace mashi ba? Ai kunga ya shiga damuwa sosai, to hakan yake gudu yasa ya zame hannunsa, bai san ya aka yi ba tsinci kansa da gudun abin da zai ɓata ranta ba, baya son ko haɗa hanya da abin da zai sanyata kunci, dan ma dai yanzu abin ta kawo shi har wuya ne yasa yake kissing ɗinta, badan haka ba ba zai yi ba, dan yasan zata yi fushi ne. Jin ya zame hannunsa daga bayanta yasa ta yi ƙoƙari raba bakinta da nasa, bai hanata ba, sai dai ya bita da kallo kawai. Da sauri ta zare bakinta daga na shi, jikinta na ɗan saisaita kerman da yake yi ta yunkura zata miƙe. At the same time suka fara daka hamma ita da shi. A wannan karon bai hanata tashi ba, saboda dik jikinsa ya mutu alamar yana jin barci, har ɗan wani jiri yake gani. Miƙewa ta yi tare da juyawa da gudu zata bar waje. Sai kuma me? Wata iriyar kara ta fasa wanda sai da ya sanya shi wato sexy eyes ɗinsa game da ɗan ciza roman lips ɗinsa ya ɗan ɗago kai. Ta tsaya cak a wajen tana wani irin numfashi, take hawaye sun wanke mata fuska, da mamaki yake kallonta yana son yin magana amma tongue ɗinsa ta yi mashi nauyi. Sai da ta sake zunduma ihu a karo na biyu ne ya ɗan nisa, a natse ya ce. "Menene?". Da hannunta ta nuna mashi kafafunta tana faɗin. "My legs Big Bro". A wani irin slow ya kai idanunsa kasa. Ganin jini yasa ya ɗan kara buɗe eyes ɗinsa da kyau, da sauri ya yi gaggawar kai hannu ya ɗauketa tare da miƙewa, matsawa daga wajen suka yi izuwa kujerar dake gefe, glass cup da ya fashe ne ya farfasa mata ƴan kafafun. Saman sofa ya zaunar da ita, a gabanta ya tsugunna tare da kai hannu ya riko kafafun nata, kafa ɗaya ne ya ji ciwo, ɗayan lafiya lou yake. Hannu yasa ya zari kwalbar dake a cikin kafar tata, datse idanunta ta yi tare da fasa wani ihun. Can ƙasan makoshinsa ya yi wata magana wanda ita kanta bata ji me ya ce ba, kuma ko da ta sake tambayarsa me ya ce shiru ya yi mata bai amsa ba. Miƙewa ya yi hannunsa rike da kwalbar tata ya nufi bedroom ɗinsa, ko kaɗan bai kalli in da Smart yake ba ya wuce ya nuri T-room dan ɗaukar abin da zai iya gyara mata kafar da shi. Jim kaɗan ya fito rike da su a hannunsa. A in da ya tashi ya koma ya tsugunna tare da riƙo kafafun nata, wani ruwa a cikin ɗan ƙaramin kwalba ya buɗe, kaɗan ya zuba shi jikin cutton sannan ya fara goge blood dake wajen. Ai wani irin azabar da ta ji ya ziyarce har bata san lokacin da ta kai hannu ta damko kyakkyawar gashin kansa ba. Sai da ta ga ya ɗago da kallonsa a kanta yasa ta farga da abin da ta yi, da sauri ta sake shi tana ciza laɓɓanta tamkar zata farfashesu. Tsab ya gyara mata wajen kafin ya miƙe da nufin ya nufi fada, wato wannan taro dai ba za'a fasa ba, ta watsa mashi barcin da ya fara ji ɗin ba. Ta so hana shi fita, ta tsayar da shi da shiriritarta, sai dai kash, babu dama, dan ga kafarta ma ciwo yake yi, dole tana ji tana gani a wannan rana aka yi wannan shagali da party wanda sam bata ji daɗin hakan ba, ranta ya kuntata sosai. Ta wuni sukuku cikin rashin daɗi, Smart ya so ya yi magana da ita dan ya ji wacece ita ga ɗan uwansa, sai dai kuma bai samu yin hakan ba, dan tin da ta koma ɗakinta bata fitoba sai da ta yi sallar isha'i, nan ma abin da ya fito da ita ba komai bane face ta yi ƙoƙarin hanasu taruwa dan yin wannan koke-koken, ta kuma hanasu partyn da za'ayi da misalin karfe ɗaya na dare. Tana shirye cikin kayan barcinta mai kyau da ɗaukar hankali, ta sanya silky headband a kanta, kai tsaye ta nufi room ɗinsa, tana fitowa daga ɗakinta Pretty na shigowa, kallon tsab ta yi mata kafin ta ce. "Barci kike ji ne?". Kai Pretty ta gyaɗa mata game da cewa. "Zan kwana a tare dake ne". Taɓe baki Sweetie ta yi. "To dama in ba dani ba da waye zaki kwana? Ko dama a wani waje kike kwana ba room ɗina na?". Cike da mamaki ta yi maganar. Wuceta Pretty ta yi bata bata amsa ba, dan a cewarta ba zata biyewa Sweetie ba, irin ita babban nan ya za'ayi Sweetie ta tsayar da ita da tambaya? Kun gane ai. Da ido Sweetie ta bita tana mamakin iskanci irin na Pretty, sanka-sanka ta iya. Wucewa ta yi tana ɗan ɗingisa kafa har ta kai room ɗinsa. Tsaye yake a gaban mirror yana bin kansa da kallo, kariwa wajen ta yi har zata fara yi mashi magana kenan sai ta lura ba shi bane, Smart ne, ya shirya cikin sleeping dress na Big Bro, sai ya kara fitowa sak shi. Ganin ba shi bane yasa ta ce. "Barka da dare". Ɗan juyo da kallonsa a kanta ya yi, a farko ya zaci Pretty ce dik da yasan ita dai ba zata ce mashi barka da dare ba, kuma yanzu suka rabu ta ce mashi da Sweetienta zata kwana. Shiru bai amsa mata ba ya kawar da kallonsa daga kanta. Ganin hakan yasa ta wuce zuwa balconynsa ko yana wajen, baya nan, dawowa cikin room ɗin ta yi, ga mamakinta sai taga Smart baya a ɗakin, bata wani damu ba ta nufi sama mai gabaɗaya ta wajen gym ɗinsu, dan tasan da wuya idan baya a wajen. Tana haurawa ta tsaya a bakin wajen tana kallonsu. Black Tiger yana zaune a saman sofa yana latsa laptop ɗinsa, kaya yake oder wa BLACK TIGER AUTO MOTORS daga kasar China, hannunsa rike da cup mai bala'in kyau yana shan hot tea mai zafi. Shi kuma Smart a lokacin ya iso wajen, yana ƙarisawa kusa da ɗan uwan nasa ya zauna saman sofa dake fuskantar Black Tiger tare da miƙa hannu ya karɓi cup dake hannun Black Tiger ɗin. Ta ƙasan ido Black Tiger ya saci kallansa kafin ya cigaba da aikinsa bai ce uppan ba. Sipping na tea ɗin Smart ya yi, sai ya ji wani irin daɗi ta kaiwa maƙoshinsa karo, ɗagowa ya yi ya kalli Black Tiger. "Dalilin kenan da yasa skin ɗinta ta fi nawa haske ko?". Ya yi maganar yana nuna mashi cup ɗin tea ɗin, wato irin abubuwan da yake sha kenan yasa ya fisa kyau, Smart akwai neman magana. Wani irin kyau suka yi wa Sweetie, kayan jikinsu kusan iri ɗaya, tamkar waɗansu taurari, gaskiya sun yi bala'in haskawa. Sai ta tsaya ta shagala da kallansu. Ganin Black Tiger bai tanka mashi bane yasa Smart ya ɗan kara sipping kafin ya miƙo mashi cup ɗin. "Ga shi kada na shanye maka". ......... Tamkar babu Big Bro a wajen, ya cigaba da abin da yake yi kawai. Saboda neman magana irin na Smart sai ya kawo mashi cup ɗin saitin ɗan bakinsa, slowly Black Tiger ya ɗago da ido ya kallesa, ya yi niyar yi mashi mugunta, dan ya so juya magic eyes ɗinsa yasa tea ɗin ta yi wa Smart wanka a jiki ta kona shi, amma suna haɗa ido sai ya ji ba zai iya cutar da shi ba, dan haka sai ya mayar da idanunsa kan laptop ɗinsa. Smart bai san komai ba, bai san abin da ya yi niyar yi mashi ba, dan haka sai ya sake matsar mashi da cup ɗin yana faɗin ya sha please. Bai san ya aka yi ya tsinci kansa da buɗe ɗan bakinsa ba, a hankali Smart ya zuba mashi. Ai da ɗan karfi ya sauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya, sai ya ji tamkar Smart ya karawa tea ɗin ɗanɗano na musamman, daɗinsa ta ninku. Mayar da cup ɗin bakinsa Smart ya yi ya ɗan yi sipping kafin ya miƙowa Black Tiger. Haba a wannan karan sai ga Big Bro da buɗe baki kai tsaye aka zuba mashi. Ba karamun daɗi Smart ya ji ba, dan haka sai ya cigaba da sha yana bashi har suka shanye tea ɗin dikka a tare, wannan abin ya yi matuƙar ƙayatar da zuciyar Big Bro, sai yake jin tamkar sun kwashi shekaru aru-aru a tare, yana jin tamkar wani ɓangare na jikinsa ne Smart. Shi kansa Smart ɗin ya ji daɗin da bai taɓa ji ba, sai yake ji tamkar ya haɗe jikinsa da na Black Tiger su zama abu guda. Sweetie dai ta mayar da su tv, sun yi mugum burgeta, bata ankara ba sai jin motsi daga bayanta ta yi, a hanzarce ta juya, wani robot ne mai ɗauke da plate dake ɗauke da wani kyakkyawar glass tea pot da one cup, matsa mashi a hanya ta yi, kai tsaye ya nufesu. Yana zuwa ya ɗaura masu a saman table dake a tsakaninsu. Kallon Black Tiger Smart ya yi da mamaki, sai kuma ya ji wani musulmin daɗi ya lulluɓe zuciyarsa, wato Big Bro ya ji daɗin tadda suka sha tea a cup guda, shi ne ya bawa robot umarni da ya kawo masu wani tea ɗin kuma da cup guda ɗaya, wato dai su sake sha a cup ɗaya, Smart ya ji sanyi sosai har da sauke ajiyar zuciya, sannan ya kai hannu ya ɗauki tea put ɗin, ya zuba masu cikin cup. Kamar ɗazun haka ya fara, ya yi sipping ya baiwa Black Tiger ma ya yi sipping. Sweetie ta jima a tsaye a wajen tana kallonsu cike da farinciki, tana son zuwa hana shi yin wannan party na daren, amma kuma tana son barinsa su more wannan dare shi da ɗan uwansa. Barinsa da ɗan uwansa ya fi mata, dan haka sai ya juya zata sauka ƙasa. Unexpected ta ganta a saman kirjinsa har sai da shi kansa Smart ya tsorata ya saki cup ɗin hannunsa ta faɗi ƙasa, saboda bai ga Sweetie ba kawai ya ga mutum kwance saman kirjin Black Tiger ai dole ya razana. Ita kanta ta razana matuƙa, dik da ta saba yana jawota jikinsa a dik time da ya so, amma yau bata yi zatan ya san da tsayuwarta a wajen ba, shi ne yasa ta razana sosai. Slowly ya ɗago da kallonsa a kan Smart da ya saki cup ta yi ƙasa. "Kana namiji kana tsoro". Ya faɗa yana binsa da kallo mai kama da harara. Ajiyar zuciya Smart ya ɗan sauke, e yanzu kam Black Tiger ya fara zarce yadda yake tinani. "Ba dole in ji tsoro ba, abu unexpected haka, ai da sai ka faɗa mun cewa heartbeat ɗinka tana zuwa in baku waje ba sai kun kureni ta hanyar razanani ba.........". Bai iya ƙarisa maganar ba sakamakon wani harara da Black Tiger ya dalla mashi. Cikin zolaya ya ce. "Mayar da wukar, daga na ce ku sallameni a mutumce ba sai an razanani ba sai harara? Menayi to ni?". Black Tiger bai ce komai ba ya cigaba da dalla mashi harara. Still cike da zolaya ya ce. "Wai ma meyasa kake hararana ne? Idanunka zasu faɗi fa". Kunyar Smart tamkar zata shige cikin kasa, hakan yasa ta fara ɓoye kanta a kirjinsa tana ɓoye murmushi. Da hannu Black Tiger ya nuna mashi hanyar barin wajen kafin in a cool way sosai ya ce. "Zaka iya tafiya". Saura kaɗan yau Black Tiger ya sanya Smart murmushi, sai kuma ya dake, cike da zolaya sosai ya ce. "Saboda heartbeat ɗinka ta zo ne zaka koreni? To nima dai ina da tawa, kuma tawa ma ai ta fi ta.........". Bai iya kai saboda wani irin capka da Black Tiger ya yunkura zai kai mashi a wuya kenan ya zabura ya miƙe da sauri. "Wai kai baka hajiya da jibgar mutane da harararsu ne? To dai ka sani yanzu idan ka dakeni beb ɗita ba zata kyakeka ba, zata rama mun ne". Da jin haka sai Black Tiger ya juya magic eyes ɗinsa tare da janyo Smart gabansa. Smart bai san ya aka yi ba kawai ya tsinci kansa a gaban Black Tiger. Hannu Black Tiger ya sanya ya kamo kunnan Smart, da ɗan karfi ya murɗe mashi. Ƴar kara Smart ya saki, mamaki kamar zata kashesa ta yadda aka yi ya tsinci kansa gaban Black Tiger dab. Kara murɗe mashi kunne sosai Black Tiger ya yi har sai da Smart tsugunna ƙasa yana faɗin wash. Sweetie ta ɗauka da gaske zafi Smart yake ji sai ta sa hannunta a saman Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 Kara murɗe mashi kunne sosai Black Tiger ya yi har sai da Smart ya tsugunna ƙasa yana faɗin wash. Sweetie ta ɗauka da gaske zafi Smart yake ji, sai ta sa hannunta a saman na Big Bro, a hankali ta fara ƙoƙarin ware yatsunsa da ya rike kunnan Smart da shi. Ta wutsiyar ido ya saci kallanta yadda take ɗan tsuke baki alamar bata jin daɗin abin da yake yi wa Smart kuma kamar ita ake yi wa har da tsuke fuska. Bai saki Smart ba, sai ma ya kara murɗewa da karfi har sai da Smart ya ce. "Please Big Bro tuba nike yi". Sannan ne ya sakesa yana riƙo hannun Sweetie da ta ɗaura a saman nasa, ya ɗan fara matsa yan yatsun nata a hankali-hankali. Dafe kannansa da ta yi jajir Smart ya yi, abinku da farar fata, harara ya ɗan dallawa Black Tiger, cikin zolaya ya ce. "Nasan meyasa ka ja kunnena, saboda kawai na ce tawa ta fi taka, amma ai ban karisar da maganan ba, dik da haka ban tsira ba, but shaaa zan rama wani lokaci, kuma na kara faɗa tawa ta fi taka". Ya kai karshen maganar tare da wuce da zafa dan ma kada Black Tiger ya kara kamo shi, bai san cewa dik saurinsa idan Big Bro ya yo niyya kafin kyafta idanu zai dawo da shi gabansa ba. Amma a wannan karan Black Tiger ya kyalesa saboda abin da Sweetie take yi mashi a dogayen yatsun hannunsa ya tafi da hankalinsa da tinaninsa, ta zauna sai murzasu take yi a hankali tana mamakin irin yatsun nasa, wlh idan ka kalli skin ɗin Big Bro sai ka yi zatan bashi da jini a jikinsa saboda yanayin haskensa, abin yana baiwa Sweetie mamaki sosai, ko ita da take koreans skin ɗinta bai kai nasa zama tamkar madara ba. KUMA KUN SAN DIK RASHIN FITAR NAN NE TA HAIFAR MASHI DA HAKAN, FITA MA FA WATA RAHMA CE TA DABAN DA ALLAH YA YI WA BAYINSA!. Smart na tafiya ta yi gaggawar yunƙurawa ta bar jikinsa, bai hanata ba, ya cigaba da abin da yake yi, a in da Smart ya miƙe ta koma ta zauna, cikin sanyin murya ta ce. "Big Bro please magana nike son mu yi ka ji?". Sai da ya ɗauki almost 5 mins kafin ya jinjina mata kai alamar ya ji ba tare da ya yi magana b, nan ma da kyar ya iya jinjina kan, saboda wani irin jijjiga daga ciki da jikinsa yake yi, tin bata faɗi abin da ya kawota ba ya ji ya tsani wannan abin, har jikinsa na jijjiga ta ciki a kan hakan, yana jin wani irin a ciki black heart ɗinsa, yana wani irin harbawa da karfi-karfi. Bata lura da yanayin da yake a ciki ba, sai ta kara natsuwa waje guda, cikin sanyi da tausasawa ta ce. "So nike yi dama in yi maka ta yin....... Am...... In...... Dama...... Ina son ka ...... Gwada karɓar addinin....... Musulunci". Da kyar da suɗin goshi ta iya kai karshen maganar, gabaɗaya tongue ɗinta rawa yake yi wanda ya ja maganar tata bata iya fita da kyau. Wani irin uban dogon numfashi ta ja a lokacin da ta kai karshen maganar, ta haɗiyi yawu mai bala'in karfin wanda sai da maƙoshinta ya ce gwad!!. A ɓangarensa kuwa, tana furta wannan kalma wani irin juya mashi da kansa ya yi sai da ya ji tamkar an rotsa mashi glass a jiki, tsananta jijjiga daga ciki jikinsa ya yi, daga waje kuma wani irin tsuma ya fara yi, take jikinsa ta haɗa wata uban gumi mai rikitarwa, idanunsa suka kaɗa jajir tamkar wuta, tsabar jijjigar da yake yi ta ciki har yasa hannayensa suka fara kerma ya shiga daddanna laptop ɗin da karfi-karfi tamkar zai fashe glass dake wajen keyboard ɗin, dan irin laptop ɗin nan ne mai full screen wanda kai da kanka zaka fidda keyboard ɗinsa ka kuma lankwasa laptop ɗin gida biyu. Bata lura da halin da ya shiga ba, sai ta sake cewa. "Musulunci akwai daɗi sosai...... Kuma zai taimaka maka..... Sannan zaka.......". Maganar da bata iya ƙarisawa ba, cikin wani irin azama ta ja wata uwar birki game da haɗiye sauran maganar, ba komai ya ja hakan ba kuma face yadda ya ɗago da kallonsa yana zaro mata idanu. Kafin ta yi wani yunkuri ya daka wata uwar tsawa da wata murya ta daban wadda bata taɓa jinsa da irinsa ba. Bata farga ba sai gani ta yi ya yi watsi da table dake a gabansa, ya yi jifa da laptop dake hannunsa ta faɗi ƙasa ta yi watsa-watsa, lokaci guda dogon gashin kansa ya warware tamkar wanda aka sanya hannu aka warware mashi, haka ta tarwatse ta watso mashi har ta gaban fuskarsa, gabaɗaya ilahirin jikinsa wani irin jijjiga yake yi, yadda kuka san wani shaiɗanin aljani haka ya rikiɗe lokaci guda. TO FA DAGA MAGANAR MUSULUNCI?!. Cikin wata iriyar dakakkiyar muryar dake bada amo tana amsakuwa mai razana zuciya ta rikita ƙwaƙwalwa ya ce. "Ke karamar halitta!! Kin jima kina tsallaka iyakarki muna zuba maki idanu saboda muhimmancin da ya baki a cikin zuciyarsa, ki sani yau you have been cross ur line know, babu wanda zai iya kuɓutar dake daga hannunmu a yanzu!!". Tsabar zaranar da ita da wannan murya ya yi ai bata san lokacin da ta kai hannayenta ta datse kunnuwanta dan ƙwaƙwalwarta ba zai iya ɗaukar wannan murya ba, karfi da amonsa zai iya hautata, ga shi yana bada wani irin amsakuwa. Take Big Bro ya rikiɗe ya zama tamkar wani bujumin zaki mai firgitarwa, cikin wata iriyar zafa da jijjigar da jikinsa ke yi yasa kafa ya take sofar da take a kai, bata san ya aka yi ta miƙe tsaye ba, shi kuwa sofar ya gangara can nesa. Dogayen hannunsa yasa ya capki wuyarta da karfin gaske, ji kake yi kas-kas-kas kasusuwan yatsun hannunsa suna wani irin amsawa. Lamarin ya girmewa shekarunta, ai bata san time da ta saki fitsari a wajen ba, saboda azaba, jikinsa tamkar wani nau'i na wuta mai azaba ne, tsabar zafin da yake a jikinsa kawai ya isheta azabtar da ita ba sai ya haɗa mata da shaƙa ba, ga nails na yatsunsa wasu dogaye da su, bata taɓa shiga bala'i irin na yau ba, gabaɗaya kanta har juyewa yake yi tana ganin wani irin duhu-duhu mai ɗauke da hayaniyar wasu abubuwa dake gilma mata. DIKKA WANNAN FA SABODA TAYIN YA SHIGA MUSULUNCI NE KAWAI YA YI WANNAN BIRKICEWAR!! BABBAR MAGANA!. Cikin wata iriyar zafa ya fara taku mai amon amsakuwa, dik in ya taka sai kasa ta amsa, da wuyanta ya ɗaga sama ya nufi karshen wajen da ita. Gabaɗaya ta fita a hayyacinta saboda azaba, zafin dake jikin hannunsa kawai yana azabtar da fatan wuyanta, ga shaƙa da ya yi mata. A karshen waje ya tsayar da ita, cike da tsananin tashin hankali ta kalli ƙasa da wutsiyar ido kafin ta sake kallon cikin kwayar idanunsa da suka canza daga ainahin nasa. "Ke a su wa da zaki shiga huruminmu? Wacece ke karamar halitta?". Wannan murya dai mai amo ta sake faɗa, dan ba muryar Big Bro bane sam-sam. "Wannan ruhi ba'a haliccesa dan ya zama irinku ba, ba'a haliccesa dan ya musulunta ba, dik da yake ya fito daga tsatson musulmai, amma shi ba irinku bane ba! Na mu ne shi! Ba kuma zai taɓa kasancewa kamarku ko naku ba har abada!!". Ya sake faɗa cikin ɗaga murya. Lokaci guda ta ga face ɗinsa ya canza, fuskar wani mutum kyakkyawan gaske tamkar wani rafani ya bayyana a kan nasa fuskar, ya yi wani irin canzawar da ba zaka taɓa ganewa ba! Dik da bata a cikin hayyacinta sosai, ba shakka ta taɓa kallon wannan fuska da ta bayyana a kan nasa yanzu, bata da natsuwar da zata iya tinanin a ina ta taɓa kallan fuskar, amma ba shakka ta taɓa kuma a kurkusa ma kuwa. Slowly idanunta suka fara rufewa tamkar ranta na barin jikinta, ta dai'na jiyo sautin komai a cikin kanta. "Babu wani mahaluki a duniya da ya isa ya canza mana dokoki ya zauna lafiya! Kin shiga huruminmu dayawa! Kin mana ɓarnar da zamu ɗauki lokaci kafin mu gyara cikin ƙanƙanin lokaci da bayyanarki, kin rusa mana dayawa daga cikin burikanmu! Harke wacece?!!!!". Ya faɗa da karfi tare da wujijjigata tamkar yana karkaɗa leda. Ina idanunta sun rigada sun gamasa rufuwa ruf, sai dai har lokacin tana breathing. "Yanzu lokacinki ne na ɗanɗanar kuɗarki! Dole ki karɓi hukuncin ɓarnar da kika yi mana!!". Ya sake faɗa tare da kara jijjigata da wani irin karfi na fitar hayyaci, sannan ya sake wuyarta tare da riƙo kafarta da hannu ɗaya, ya juyata kanta a kasa ƙafafunta a sama, cikin wata iriyar bakar mugunta ya sake jijjigata zai wurgata kasa kenan daga bayansa aka rike hannayensa dikka biyu, sannan aka juyo da shi. Wasu jiga-jigan robot ne daga cikin ma'aikatansa, Smart ya basu umarnin su karɓi Sweetie daga hannunsa. Tun lokacin da Black Tiger ya daka tsawar farko Smart ya ji shi, hakan yasa ya hauro saman, ganin abin da yake faruwa ya sanya shi komawa ya zaɓo robot manya guda biyu game da basu umarnin su karɓi Sweetie daga hannunsa, dan a yadda yaga Black Tiger ya san ba shi kaɗai bane, dan haka zamar lafiya ta fi zama ɗan sarki, gwara mashi ya sanya robot da ya je Black Tiger ya kakkarya mashi kasusuwan jiki.........😅 Cikin wani irin fusata Big Bro ya juyo da idanunsa a kansu, da yake fuskarsa ta sauya robot basu ganesa ba, kai tsaye suka ɓanɓaro hannunsa daga riƙon da ya yi wa Sweetie, suka karɓeta. Cikin zafa Smart ya matsa ya karɓeta daga hannunsu, da gudu ya sauka da ita ƙasa. Big Bro da bai san robot bane a lokacin, baya ji baya gani, hannu yasa da karfin gaske ya cakumo robot ɗaya, da karfi ya ɗagasa sama, jefa da shi gefe ya yi, to kun dai san su robot karfe ne, to me zasu ji? Ai kome Big Bro zai yi masu a banza wai an yakushi kakkausa. Kokawa suka fara yi gadan-gadan cikin zafa, tamkar wasu mayunwatan zakunan da suka ɗauki tsawon shekara babu ci babu sha yanzu suka ga abinci, gwabzawa suke tamkar na za'a mutu ba. Sai jifa da su Big Bro yake yi suna kara miƙewa su nufosa. WANNAN SHI NE FAƊAR ALJANI DA ROBOT. Wani irin shaƙa da robot ɗaya ya yi wa Big Bro sai da ya ji kamshin lahira, da karfi ya yi jifa da shi saman glasses dake wajen wanda Smart ya fasa cup da kuma na laptop and table da Black Tiger ɗin ya fasa. Saman glasses ɗin ya faɗa, take suka sossoke mashi damatsan hannu jininsa ya fara koranya. Dai'dai lokacin Smart ya hauro wajen, ya kai Sweetie wajen Ronnie a ɗakin su, ya kuma gargaɗesu a kan kada su fito, shi ne ya dawo domin ya kwantar da wannan tarzoma, dan ya san waɗan nan robot idan bai dakatar da su ba zasu iya hallaka Big Bro. Cikin wata iriyar zafa Big Bro ya miƙe yana wani irin huci tamkar zai kama da wuta. Robot ɗin ne suka nufesa a tare da nufin su takeshi su jefasa kasan benen, dan a tinaninsu mugu ne zai yi zalunci kashe shi zasu yi. Gab zasu taɓa shi Smart ya ce masu a'a bai yarda ba, cike da bada umarni ya ce su ɗaure mashi shi dai, kada su kuskura su sake taɓa lafiyar jikinsa. Cikin girmamawa suka karɓi umarnin, sannan suka amsa da okey. Da sauri Smart ya ɗauko masu sarka suka ɗaure shi, amma fa da kyar suka iya ɗaure shi ɗin, sai da suka sha fama. Umarnin Smart ya yi masu da su kai mashi shi bedroom ɗinsa, haka kuwa suka yi, suka kwashesa sai cikin bedroom ɗin bayan sun ɗauresa, a saman bed suka kwantar da shi. Gefensa Smart ya zauna yana kallan cikin idanun ɗan uwan nasa, lokaci guda wani irin mugun tausayi ya kama shi, bai taɓa jin tausayin wani abu kamar yadda ya ji tausayin Big Bro a yanzu ba. Shiru Big Bro ya yi tamkar abubuwan sun lafa mashi, sai dai kuma ga wanda ya san idanunsa zai fahimci sam basu lafa mashi ba, domin kuwa idanunsa ba su koma dai'dai ba. Lokaci guda Smart ya tsinci kansa da tinanin bari ya tofa mashi addu'oi ko za'a sami sassauci. Hakan kuwa aka yi, a hankali ya fara karanto ayoyi goma na farkon suratul baƙara, kun san dik shaiɗancin shaiɗani yana mugun shakka da tsoron suratul baƙara da yaseen. A cikin zuciya Smart ya fara karantowa har ya kai karshe. Slowly ya ɗan matsa dab da Big Bro ya fara tofa mashi. Ai yana tofa na farko wani irin jijjiga da Big Bro ya fara yi, take wasu irin hasumiya na wasu muryoyi kala daban-daban suka fara tashi a cikin ɗakin, tamkar bed nasa zai ɓaɓɓalle haka ya fara yi, yana wani irin daddamke jikinsa yadda kuka san ana cizgar namar jikin nasa ne, gabaɗaya jijiyoyinsa sun mimmiƙe sun fito raɗo-raɗo, idanunsa ya koma bakinkirin babu ɗigon fari a ciki, ga wasu jijiyoyi da suka shararo mashi a gaban goshinsa, yadda kuka san ana zare ran bakin shaiɗani. Idan hankalin Smart ya yi dubu a wannan lokaci ya tashi, take zuciyarsa ta karaya da karanto addu'ar, kirjinsa na bugawa da karfi-karfi, ALLAH sarki bai san komai ba, kun ga da kamar Sweetie ce ta san da matsalar dama, da zasu san abin yi. Tinawa da ya yi cewa dik karfin sharri addu'a na ruguzasa ne yasa ya cigaba da karanto suratul baƙara ɗin. A karo na biyu ya tofa mashi. Haba ai wani irin ihun da Big Bro ya kurma sai da gabaɗaya empire ɗin ta amsa, hakan kuma ya yi sanadiyar farfaɗowar Sweetie dake sume, Ronnie ya ɗaura kanta a saman cinyarsa yana tofa mata addu'oi, Pretty dai tana zaune sai ruwan hawaye take yi tana ta faman ambatar sunan Sweetie. Tana waro idanunta waje ta fara tari mai sautin gaske. Cikin wannan tari take faɗin. "Ina Big Bro bro ina Big Bro?". Ta yi maganar idanunta a kan Ronnie dake kallonta. "Sis menene yake faruwa? Ke zamu tambaya ina Big Bro? Sannan me ya sameki? Meyasa twin brother ɗin Big Bro ya ce kada mu sake mu fita?". Da jin haka ta zabura ta miƙe zaune a tsakiyar gadon. Fuska jaga-jaga da hawaye Pretty ta rungumota tana faɗin alhamdulillah Sweetie ta farka. Ita kuwa tana zazzare ido ta zare Pretty daga jikinta. "Yazama dole in ga Big Bro a yanzu". Ta faɗa tana yunƙurin saukowa daga gadon. Da gudu Ronnie ya riketa yana girgiza mata kai, cikin natsuwa ya ce. "Twin brother ɗin Big Bro ya ce kada mu fita". Ya faɗa yana kara ƙanƙame hannunta. Ai ina fisgewa ta yi, da sauri ta diro ƙasa, ƙafafunta suna kerma, da kyar take iya taka ƙasa, amma saboda dauriya da jajircewa na son cikar burinta haka ta nufi wajen. Kafin Ronnie ya diro kasa ya rikota tuni ta buɗe kofa ta fita. ---------------------🔥 Smart yana tofa mashi wannan addu'a a karo na uku, wani irin kururuwa mai doɗe kunne da ya zunduma har sai da yasa Smart ya ji kamar ya gudu. Lokaci guda ya kara kame jikinsa tamkar wanda ake zuba mashi wuta, da alama azaba yake ji sosai daga ta cikin jikinsa, yana wani irin numfashi tamkar gurnanin zaki, yana kara mimmiƙewa, daurewa Smart ya yi ya kara tofa mashi a karo na huɗu. Haba sai ga Big Bro ya yi watsa-watsa da sarkar da aka ɗauresa da shi ɗin, ya yi wani irin kururuwa ya tsinke sarkar. Kafin Smart ya ankara sai ganin mutum ya yi tsaye a kan kafafunsa a tsakiyar bed ɗin, a wannan lokaci babu mahalukin da yake iya ganin fuskar Big Bro, saboda arab hairnsa da ya rufe mashi. Wani irin razana da Smart ya yi har bai san time da ya miƙe tsaye ba, sai dai bai gama farfaɗowa daga razanar ba Big Bro ya diro a gabansa. Gabaɗaya addu'a ce ta kwace daga bakin Smart, ya ji tamkar an shake mashi makogwaransa, dai'dai lokacin su Sweetie suka turo kofar suka shigo. Zaro idanu Smart ya yi yana kallonsu, cikin ɗaga murya ya ce. "Ku juya ku gudu tin kan ku rasa rayukanku". Girgiza mashi kai Sweetie ta yi, cikin muryarta dake ta faman sarkewa ta ce. "Kada ka gudu kuma kada ka ji tsoro, saboda shaiɗani baya haɗuwa da ayar ALLAH, ni nasan ko su waye ne, saboda na yi mashi addu'a kwanaki na shiga tsakaninsu shi ne suka fusata, shi ne yanzu suka san ta hanyar da suka bi suka dawo jikinsa suna cutarsa da sunan wai shi nasu ne, tabbas zamu yi addu'a ba zamu gudu ba, kuma da izinin mai iko da ni da su, wanda ya halicceni ya haliccesu sai sun rabu da shi, sai ALLAH ya yi mashi katangar karfe tsakaninsa da su". Da kyar ta iya kai karshen maganar!. Zuba mata idanu Smart ya yi yana mamakin jin waɗan nan kalamai nata, kenan dama already ɗan uwansa ya jima da wannan matsala? Lallai kuwa lokacin rabuwarsa da su ya yi In Sha ALLAH. "Ronnie Pretty ku kare kanku ta hanyar karanta addu'oi dan kada ya iya tinkararku". Sweetie ta faɗa hawayen da suka cika mata idanu suna gangarowa, a wannan karan duniyar shaiɗanu sun dawo a fusace, sun ji haushin abin da Sweetie ta yi masu, dama sun tsaneta tun time da ta ji mashi ciwo ta fitar mashi da jini a jiki, sai ya haɗe dikka suna son ɗaukar fansa. Jin kalamanta ya karfafawa Smart gwiwa a in da ya dage ya cigaba da addu'oi babu kama hannun yaro, take Big Bro ya kara rikice masu yana wani irin gurnani mai ban tsoro. Sun tsorata matuƙar tsorata, amma suka daure suka haɗa baki wajen cigaba da karanto addu'oi da karfi-karfi cikin ɗaga murya. Lokaci guda Big Bro ya fara wani irin jijiga, kafin su farga sai ganinsa suka yi a jikin bango ta wajen balcony ba ta in da suke ba. Har Smart zai bi bayansa Sweetie ta ce mashi. "A'a kada ka je, ka cigaba da addu'a, in ka je zasu lahantaka ne.........". Bata rufe baki ba sautin buga kansa a bango ya dakatar da ita, da karfi ya hau buga kansa da jikin bango yana wani irin ihu haɗe da gurnani. Sosai hankalin Smart ya tashi yana jin ba zai iya jure ganinsa a cikin wannan mawuyacin hali ba, amma ya sai datse idanunsa yana cigaba da karanto addu'oinsa. Dikkansu datse idanunsu suka yi saboda halin da Big Bro yake a ciki ya kazanta ba zasu iya gani ba. Sai dai kuma a lokacin guda suka waro idanun nasu sakamakon jin sautin karar glass ya tarwatse a kasa da suka yi, a miliyan suka buɗe idanunsu. Bawan ALLAH buga kansa da jikin door glass da zai sadaka da balconynsa ya rinƙa yi sai da glass ɗin ta tarwatse, gabaɗaya goshinsa ta fashe rugu-rugu jini na ta malala tamkar an buɗe tap, har lokacin jikinsa na wani irin jijjiga mai matuƙar ruɗarwa. Ai Sweetie da take cewa kada su je in da yake bata san lokacin da ta watsa a miliyan ta isa gabansa ba, dai'dai lokacin kuma ya zube kasa cikin glasses ɗin da suka yi rugu-rugu ɗin ya faɗi baya numfashi. Ihu mai sauti ta zunduma tare da kwala mashi wani irin kira tamkar maƙoshinta zai ɓalle. Da gudu su Smart ma suka yi kansa, da alama abubuwan sun sake shi sun gudu, hegu sun ji addu'a. Kuka sosai Sweetie take yi tasa hannun tana tattare arab hairnsa da ya jike sharkaf da jinin da ya rinƙa gangarowa daga goshinsa, cike da tashin hankali take faɗin. "Koma meyafaru ni na ja maka, da ban yi maka maganar addini ba da dik baka azabtu haka ba, nina zama sanadin wanann ciwo da ka ji, dan ALLAH ka tashi kada ka mutu, ni na yarda zamu zauna da kai a haka ko babu addini". Cikin fitar hayyaci take sambatun nata. Shi ma Ronnie kuka yake yi sosai tamkar ransa zai fita, saboda kun san dai yadda yake son yayansa tamkar ransa. A natse Smart ya ce. "Ku yi shiru yanzu zai samu lafiya ai". Ya yi maganar tare da gyara hannunsa, yasa karfinsa da kyau ya cicciɓi Black Tiger sama, ya ɗaura saman shoulder ɗinsa ya wuce da shi sai saman bed, gabaɗaya bawan ALLAH ya ji wa kansa uban ciwo, jini ne yake ta zuba daga jikinsa kamar an buɗe tap. Da gudu su Sweetie suka biyosa kan gadan, Ronnie ya ce bari ya kawo kayan aiki ya yi treating na yayan nasa, ita kuma Sweetie a saitin kansa ta zauna ta cigaba da karanto addu'oi tana tofa mashi. A tare Smart da Ronnie suka taimaka mashi wajen gyara mashi fuska da ya ji ciwo da damatsan hannunsa, sannan suka bashi allurai. A daren wannan rana dai babu wanda ya rintsa a cikinsu, a zaune suka kwana, batun party kuma dai ba'ayi shi ba, Ronnie ya dakatar da shi saboda halin da suka shiga. Wasa wasa har tsawon kwanaki uku Big Bro bai farfaɗo ba, kuma suna bashi kulawa sosai, ga zuciyarsa na bugawa dai'dai, amma shiru bai farfaɗo ba. Likitoci sun yi iyaka yinsu, sai dai suka zubawa sarautar ALLAH idanu. A ranar na uku da sumansa ne wasu jiga-jigan jiragen sama suka dira a birnin, Smart ya ji saukarsu, to da yake bai san komai dangane da birnin ba sai bai wani damu ba. Bayan sauran jirage da kamar minti 20 Ronnie ya isko Smart zaune a balconyn Big Bro yana dube-dube cikin ɗaya laptop na Big Bro ɗin, sallama ya yi mashi a natse kafin ya kariso ciki, da kallo Smart ya bisa yana mamakin irin raman da Ronnie da Sweetie suka yi a sanadin kwanciyar Big Bro. NI KUWA NA CE DAN BAI SAN IRIN SHAKUWAR DAKE A TSAKANINSU BANE, BAI SAN IRIN SON DA SUKE YI WA BIG BRO BANE DA BA ZAI YI MAMAKIN RAMANSU BA!!. Saman sofa Ronnie ya zauna, a natse ya ce. "Babban yaya Big Bro ya yi baki". Fuska a ɗan ɗauke da mamaki Smart ya ce. "Baki kuma?". Kai Ronnie ya jinjina kafin ya ce. "Ka duba wayarsa ko laptop ɗinsa ina da tabbacin zaka ga appointment ɗinsu, dan Big Bro baki basa zuwa mashi haka kawai, sai ya basu izinin ganinsa da kuma dik abin da ya dace". Jinjina kai Smart ya yi kafin ya bukaci da ya kawo mashi wayar Big Bro, a hanzarce ya tashi ya ɗauko mashi, da fingerprint ɗinsa ya cire lock na wayar ya shiga ciki ya fara bincike, nan ya tarar da zancen bakin, ya ɗan yi mamakin ganin waɗan da suke da zama da shi, ciki harda his excellency na Us, abin ya ɗan sanya Smart shakku a kan me suke son ganin ɗan uwansa? Sannan girman Black Tiger ya kai har su iya takowa zuwa wannan birni? Tab abin babba ne. Ga wakilin sarkin England ma har da shi. Miƙewa ya yi tare da cewa. "Ku yi masu iso zan gansu a matsayin shi dik da ban san a kan me zasu tatauna ba". Ronnie bai ji komai ba, dan yana ganin abin da ya yi Smart shi ya yi Black Tiger, dan haka sai ya miƙe ya nufi waje. Toilet shi kuma Smart ya nufa, amma kafin nan sai da ya kara duba Black Tiger, bawan ALLAH har yau bai motsa ba. Wanka ya yi a gurguje tare da zuwa ya shirya cikin ɗaya daga cikin mafiya tsada da haɗuwan suit a cikin kayan Big Bro, sannan ya yi amfani da wayar Big Bro ɗin ya kira daddynsa na Paris ya sanar da shi cewa ga kawayensa fa sun kawowa Black Tiger ziyara, kun san France, England da America kawaye ne, kada ku manta daddynsa na Paris kuma shi ne his excellency mai ci a yanzu. Ba tare da nuna wata damuwa ba daddyn nasa ya ce. "Nasan sun je wajen, amma su sun ɓoye mun basa son in sani, but ka bar wayarka a kunne bari in saurari abin da ya kaisu". Jinjina kai Smart ya yi tare da ciro wayar daga kunnensa. Kasa ya sauko, already daddynsa na Paris ya san waye Big Bro, Smart ya faɗa mashi komai. Wlh idan ka kalli Smart ba zaka taɓa cewa ba Big Bro bane, ya fito sak shi. Time da ya sauko ƙasa Sweetie na zaune a saman sofa ta yi shiru tana tinanin Big Bro, ta yi rama sosai, dik wannan ƙayataccen murmushin nata ya kau, ta zama wata iriya da ita, kullum tana a cikin bad mood. A zabure ta miƙe tsaye dan a tinaninta Big Bro ne, sai da ta kura mashi idanu har ya kara matsawa kusa da ita, sannan ne ta gane Smart ne, komawa ta yi jiki a sanyayye sosai ta zauna, tamkar zata yi kuka ta ce. "Babban yaya sannu da fitowa". Sosai ta baiwa Smart tausayi, shi fa har yau ƙalilan matar Big Bro yake yi mata, shiyasa ma yake tausaya mata sosai. "Kin sha maganinki ne?". Smart ya faɗa yana nufota, ita ma magani take karɓa saboda azabar da ta ci ranar da kuma rashin lafiyar Big Bro da ya haɗe mata, satin nan dikka bata je school ba. Kai ta jinjina mashi. "E na sha". "To ya kike jin karfin jikin naki?". Ƙasa ta yi da kai kafin ya amsa da. "Alhamdulillah". "Masha ALLAH, UBANGIJI ya baku lafiya yasa kaffarace". Da amin ta amsa tana jin zuciyarta na kara yi mata zafi. "Zai tashi In Sha ALLAH, ki cigaba da tayasa da addu'a". Ya faɗa yana wucewa zai nufi kofar fita. "In Sha ALLAH ba zamu taɓa gajiya da addu'a ba". Kai kawai ya jinjina mata tare da ficewa. Kai tsaye ya buƙaci Ronnie da ya kwatantana mashi room na tattaunawa da manyan baki na Big Bro. Har wajen Ronnie ya rakasa, sai dai dab da zai shiga wajen Ronnie ya ce mashi ai Big Bro kullum da mask a face ɗinsa yake tattaunawa da baki. Wani irin Musulmin daɗi Smart ya ji, dan dama yanayi tinanin yadda za'ayi abokan daddyn nasa ba zasu ganesa ba, dik da dama ba wani saninsa suka yi, amma in baku manta ba a baya nemansa suke yi dan aikinsa, amma yaki ko in ce daddynsa yaki basu shi. Juyawa ya yi suka koma Ronnie ya fito mashi da mask na Black Tiger, ya sha mamakin ganin irin mask masu ɗauke da zanen bakar damisa, lallai yanzu Smart ya kara jinjinawa karfin ikon Big Bro, ashe ya kai haka? NI KO NA CE SAI MA KA JI ME YA KAWO MUTANEN TUKUN NAN, AI BIG BRO YA WUCI NAN! SARKI NE MAI KARFIN IKO!. Da shigowar Smart cikin room ɗin sai ya iskosu a tsaitsaye basu zauna ba. Ba karamun mamaki Smart ya sha ba na ganin irin haɗuwar wannan ɗaki na tattaunawar, gabaɗaya tsala-tsalan kujerun dake cikin room ɗin da ɗanyar gold aka yi su, sai wai kyalli suke yi, ga sofarsu mai bala'in laushi, ɗaki ne wanda yake da views guda biyu ta ɓangaren hagu da dama, sai kuma curtains masu bakain kyau, a tsakiyar ɗakin wani katan gold table wanda tsala-tsalan chiar guda 24 suka kewaye shi, daga can jefe luntsama-luntsan sofas ne masu bala'in haɗuwa da ɗaukar ido, ga wani fitinannen kamshi dake tashi sosai. Gaskiya Big Bro na daban ne, komansa cikin tsari da ɗaukar hankali, ga tsantsar madarar natsuwa. Jiga-jigan bodyguards har huɗu ne suka rako bakin cikin room ɗin, baki uku ne dikkansu fararen fata tas, dikkansu kuma Smart ya sansu, ya gane fuskokinsu. Ko da bai san a ina Black Tiger yake zama idan ya yi baki ba, kujerar Big Bro da kanta ta bashi amsa, domin kuwa tsarinta daban yake, kwalliyar saman kayin kujerar ma ta suffar damisa ce. Dan haka wajen Smart ya wuce ya zauna yana binsu da kallo, dama yasan jira suke yi ya zauna kafin suma su zauna, dik da bodyguards ɗinsu sun caje masu kujerun dama ɗakin bakiɗaya babu wani abin cutarwa, amma basu yarda su zauna ba har sai mai wajen ya zauna. Yana zama suka zauna, cikin mutumta juna suka gaisa kafin wakilin Sarkin England ya korawa Smart bayanin abin dake tafe da su, wato sun zo ne kan kasuwanci da suke san kullawa da birnin, har da cewa zasu zuba makudan kuɗaɗensu, suna son haɗa alaƙa mai karfi a tsakaninsu da birnin, daga ƙarshe suka yi alkawarin karawa kasar kafin soji da tsaro na ban mamaki idan Big Bro ya yarda da su!.. Smart ya yi matuƙar mamakin jin wannan abin, a ransa ya ce lallai dole wannan birni tana da wani abin da ba kowa yake da shi ba. Sai dai gudun kada ya ɓata ran ɗan uwansa yasa ya c masu zai yi tinani a kan buƙatarsu, idan ya yanke hukunci zai sanar masu, ya yi masu hakan ne kuma saboda baya son yi wa Black Tiger kutse a cikin al'amurransa, bai sani ba ko ɗan uwan nasa yana da ra'ayin karɓar turawan yamma a birninsa ko akasin haka, kun ga kada ya je ya yanke mashi hukuncin da zai ja Black Tiger ya yi ta jin haushinsa a banza, dama ya ya lafiyar giwa? Dama basu samu ya aminta ya karɓesu bama. A kan wannan matsaya suka rabu, Smart ya dawo sama, nan fa ya fara binciken me birnin nan ta mallaka da turawa suke son yi mata kutse har haka?. Ba ƙaramin razana Smart ya yi ba a lokacin da ya ga irin ɗinbin dukiyar da ɗan uwansa ya mallaka, yanzu ya yane cewa dole ne turawa su yi tururuwan kutsowa cikin al'amurransa, lallai ya mallaki abin da dole ne ma ayi mashi ca a kansa, wow bayan zallar gold da birnin ta mallaka, ga crude oil, bugu da kari ga kuma red gold, suna da aluminum kala-kala, ai lallai in kuwa haka ne dole Big Bro ya yi gagarumin shiri, ashe gara da bai basu amsa ba ya yi shiru, tab akwai case.. -------------------------🔥 CROWN OF JUSTICE.🔥 Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 No editing 🤗😇 CROWN OF JUSTICE.🔥 Kafin ta kai ƙasa ya yi amfani da magic ɗinsa wajen dawo da ita, Auta bata san ya aka yi ba sai ganin kanta ta yi a saman bed, ihu ta shiga kurmawa da karfin gaske wanda bata san cewa babu in da ihun nata yake zuwa ba, dan ita kaɗai take jin ihun, dik yadda ta kai ga waje baki babu mai jiyota. Ƙoƙarin tashi daga saman bed ɗin ta yi sai dai ina, tamkar an ɗaɗɗaure mata jiki, ko motsawa ta gagara yi. Ganin haka yasa ta tina babu mai kuɓutar da ita UBANGIJIN da ya halicceta ya halicce shi, ya halicci aljani da shaiɗanu, dan haka sai bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen fara kwaranyowa kanta addu'ar neman tsari daga shaiɗanin aljani dama shaiɗanin ɗan adam. Shi kuwa ya tsaya sai ƙoƙari zare kayan jikinsa yake yi, gabaɗaya fuskarta ya yi wani irin jajir da shi saboda kukan da ta rinƙa sha, hancinta kamar an goga mata manja, fararen idanun nan nata dik sun kara jajir da su. Gabaɗaya ya koɓe kayansa ya yi tsindir a gabanta yadda take a kwance, datse idanunta ta yi tana cigaba da ambato sunan ALLAH subhanahu wata'ala da ya kawo mata agaji. Gadan-gadan Ude ya haye saman bed ɗin nan domin farmata, sai dai kuma yana ƙoƙarin kai hannunsa jikinta ya ji ana murɗa handle ɗin door. Kasancewar yasan ya datse kofar da magic ɗinsa sai abin ya yi mugun bashi mamaki kan wanene wannan da zai iya shigowa? Koma wanenen lallai na daban ne. Bai ankara ba sai gani ya yi anturo kofar za'a shigo, ai a wani irin miliyan ya ɓace daga ganin mutane ɓad, amma bai fita daga ɗakin ba, ya kuma saki Auta da ya girke a saman bed ɗin. Bakinsa a ɗauke da Musulmin sallama ya shigo cikin ɗakin, da alamar gajiya a tattare da shi, har wani lumshe idanu yake yi tamkar yana jin barci. Sai dai kuma yana sako kafafunsa cikin ɗakin ya yi wani irin wastsakewa saboda kukanta da ya dira a cikin dodan kunnuwansu. A miliyan ya zaro idanu waje. Ganin da gaske ita ke zaune tsakiyar bed tana rera kuka ne hasa shi yin zafan ƙarisowa wajen, saman bed ɗin ya haye tare da riko shoulder ɗinta, a ruɗe ya fara faɗin. "Hoonairata lafiya? Meyasame kike kuma? Waye ya taɓaki? Ina Aunty Rishma?". Yana magana yana goge mata hawaye da ɗayan hannunsa. Ja baya ta yi daga rikon da ya yi mata, saboda dik da ta ji bugawar zuciyarta, bata yarda shi bane, ALLAH sarki an rigada an tsorata ta ne. Baya ta ja sosai tana bin fuskarsa da kallo, haba ai tana gane cewa shi ne na gaske ta yi wani irin zafan faɗowa jikinsa tare da saka mashi kuka mai sautin gaske, kara ruɗewa sosai ya yi, ya rungumeta sosai yana ƙoƙarin tambayarta me ya faru?. Ude yana tsaye jikin bed ɗin tsirara yana kallonsu, amma su basa iya kallansa, ya sha madarar mamakin ganin yadda Hoorain ya shigo cikin ɗakin, bai san cewa dik karfin tsafi banza ce a idanun addu'a, yaron mamma fa daga masallaci ya fito, ga shi azumi suka wuni da shi, ya yi sallah ya yi karatun Alqur'ani mai girma, sannan ya yi askar, ai dole nema ya iya buɗe kofar nan ya shigo. Cikin kuka Auta ta fara bubbuga kirjinsa tana faɗa mashi dik abin da ya faru da ita daga farko har zuwa yanzu da take rungume da shi. Ude ya so toshe bakinta a kan kada ta faɗa, sai dai ya gagara yin hakan saboda tana jikin Hoorain yaro jiki dik addu'a, dole yana ji yana gani ta faɗi komai. Tin da ta fara magana gabaɗaya yanayin Hoorain ya canza, to me zai faru? Wai kun manta Hoorain da zafin kishi ne? Jaish da yake matsayin yayanta ma ranan da ya mareta ba shakesa ya yi a cikin fada gaban kowa ba? Kun manta yadda ya tsawatarwa uncle Taheer rike hannun Auta? Kun manta yadda ya kare da wancan guy da ya biyo Auta a lokacin walimar da mummyn Chuchu ta haɗa? Mutumin da tin bashi da tabbacin kai baima sa a ransa zai mallaketa ba yake tsananin kishinta haka bare kuma ace ta zama matarsa, tana cikin ɗakinsa sannan wani ya zo ya ce zai keta mutumcinta ku yi tinanin Hoorain zai barsa? Tab ai ina ga ko ubansa na gaskiya ne ba zai raga mashi ba bare na boge. Tsabar ɓacin rai wani irin kerma jikinsa ta fara yi, gabaɗaya tsuma yake yi tamkar ya haɗiyi zuciya ya mutu haka yake ji, idanunsa a take suka canza launi suka yi jajir kamar wuta, tsantsar ɓacin rai ne ya bayyana a kan fuskarsa, shi da aurenta da Abdussalam ma ya kasa shanyewa sai da ya tambayeta Abdussalam ya taɓata ko? Bare yanzu! Ai rabata da jikinsa ya yi, ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, cikin wata iriyar murya wadda da ka jita zaka san da kyar aka ƙaƙalota za'ayi maganar da ita. "Ya taɓaki ne?". Ya faɗa yana mai da kallonsa ƙasa, dan ya fahimci ta razana sosai da ganin yanayinsa, so kada ya ƙara ɗaga mata hankali cikin wanda take a ciki. Girgiza kai ta shiga yi. "A'a bai taɓani ba". Ta faɗa tana wani irin shessheka. "Wanene shi?". TASHIN SENSE. Ita kam waye zata ce tin da bata san kamanninsa na ainahi ba! A suffar Hoorain ya zo mata, bata san wanene bane, kai ta shiga girgizawa kafin ta ce. "Ban san shi ba, amma koma wanenen matsafi ne sosai, saboda yadda ya fito a siffarka ya zo nan". Shiru Hoorain ya yi, lokaci guda ya tina da abin da ya faru dashi a ranar da kuma in da ya ɗauko Fanan, dan haka koma wanene yana da alaƙa da wannan waje da ya ɗauko Fanan kenan. Sake Auta ya yi tare da yunƙurawa zai sauko ƙasa ya nufi waje, dan ya yi alkawari koma uban waye, ko wuta yake tauna ya haɗiye dan bala'i yau babu mai kwatarsa daga azaban da zai yi mashi, ba zai ɗagawa kowa kafa ba. Ihu Auta ta zunduma mashi da karfi tare da cewa. "My Hero ina jin tsoro, kada ka tafi ka barni, wlh zai sake dawowa, na shiga ukuna ni kam". Tamkar ba zai tsaya ya saurareta ba, dan idan ransa ya kai miliyan to ya ɓaci, amma tinawa da ya yi cewa ga yadda ta rabu da iyayenta da ƴan uwanta dik saboda shi, sai ya ga bai kamata ya barta tana kuka ba, kuma ya yi mata alkawarin ba zai bari ta yi kuka ba, wannan dalilin yasa ya dakata tare da zuba mata ido yana sauke wani irin huci tamkar zai kama da wuta. A karfi ta faɗa jikinsa tana kara sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Dik zafin da ya ɗauka sai ya ji kukanta na neman wanka mashi, dole ya danne zuciyarsa ya hau rarrashinta, tin tana kuka da karfi har ta koma yi a hankali-hankali, daga karshe ma sai ta yi shiru tana daka hamma alamar barci. Cikin magagin barci can ƙasa ƙasa ta ce. "My Hero barci nike ji sosai, dan ALLAH ko na yi barci kada ka fita ka barni ni kaɗai, ka zauna a tare da ni". Kyakkyawan arab hairnta ya shafa yana gangarowa har tsakiyar bayanta kafin ya ce. "Babu in da zan je in sake barinki har sai ranar da takobina ta sauke kan wanda ya niyyar zaluntarmu, sai na raba kansa da gangar jikinsa kafin nan ne nima zan iya barci". Lokacin da ya yi wannan magana har barci ya yi awon gaba da ita, dan haka bata ji bare ta amsa, shiru ya yi yana cigaba da shafa bayanta a hankali yana ɗan yi ƙasa har zuwa kan mazaunanta, tinani ya luluƙa a kan wani mai karan kwanan ne yake neman shiga gonarsa? Lallai dole ya binciko, kuma koma wanenen dole ya kashe shi in ba haka ba zuciyarsa ba zata yafe mashi ba. Ya jima a haka yana tinani kafin ya dawo da kallonsa a kan hannunsa, bai ma san yana ta shafe mata mazaunai ba, hankalinsa ya yi nisa. Wani irin ajiyar zuciya ta sauke cikin barci, hakan yasa ya kai ɗan bakinsa ya sumbaci forehead ɗinta, a fili ya ce. "Kin wuci na bar idanunki su rinƙa zubar da kwallah matukar bana farinciki ba, ba zan taɓa barin dik mai shirin cutar dake ya zauna lafiya ba!" Ya kai karshen maganar tare da kwantar da ita a hankali saman bed ɗin, ya kwaso pillows ya sassaka mata a gefe-gefenta, ya ja duv ya lulluɓa mata, a ransa ya hau tinanin bata ci abinci ba fa. NI KAM NA CE WANNAN UWAR WAHALA DA TA SHA TA TSIRA DA KYAR INA WANI BATU NA CIN ABINCI? AI SAI DA SAFE KUMA. Sam bai ji daɗin hakan ba, matso da ɗan bakinsa dab da nata ya yi, sumbata ya manna mata tare da ƙoƙarin ɗagowa kenan ya ji tasa hannu ta rungumoshi mai gabaɗaya, cikin magagin barci ta ce. "Ka kwanta a jikina my Hero, bana son ka matsa". Gefe guda na zuciyarsa ne ta lulluɓa da farinciki, ya ji daɗi sosai har da sauke ajiyar zuciya, gyarawa ya yi ya kwanto a jikinta, a hankali ya juyo da ita ta dawo jikinsa shi kuma ya koma saman mattress, ya ja masu duv ya lulluɓa masu. Dik Ude yana tsaye yana kallonsu, takaici tamkar ya kashesu dikkansu, saboda yadda yake tsananin katse yana buƙatarta, ya so ace shi ta runguma haka yadda ta yi wa Hoorain, a ransa ya ce da ta samu gata fiye da yadda tsammani zai iya tsammata. Da kyar Hoorain ya laluɓo remote na light ɗin ɗakin ya kashe wutar ya kunna dim light, sannan ya hau tofa masu addu'oin barci yana ɗan shafe jikinta dan ya rage zafi. Ganin sun kashe wutar ɗakin ne yasa Ude ya fice ya basu waje, dan ya ji ma suna karanto addu'oi yasan ba nasara zai yi ba, sai ya kwashi tsummokaran kayansa ya yi gaba yana ciza laɓɓansa bai samu abin da yake so ba. Tin yana iya shafeta kaɗan-kaɗan har barci ta yi awon gaba da shi mai gabaɗaya, suna manne da juna, wannan shi ne hanta da jini. ---------------------🔥 Komawa ɗakin tsafinsu Ude ya yi, nan ya isko Zarina a tsaye tana jiransa, saman waɗan nan jajayen sofa ya zauna yana binta da wani irin kallo, dama cike yake da takaicin bai samu abin da yake so ba, ga Zarina ta zo zata kawo mashi wani ciwon kai. Tana a tsaye kan kafafunta tana wani irin huci, da alama a fusace take. Yana zama ta dalla mashi wani irin kallo, in a cool way sosai, dan ita wlh baka taɓa jin ta ɗaga murya a magana, ba karya tana da sanyin murya sosai, can ƙasa ta ce. "Amma dai kasan tin ɗazun kai nike jira ko?". Yana ta hucin takaici ya ce. "Ni kike jira kamar ya? Me zan yi maki?". Sosai ya yi shocked da jin maganarsa, dan ko da wasa bai taɓa yi mata magana irin haka ba, amma sai ta daure da cewa. "Yanzu me abin yi? Ta wace hanya zamu ɓullowa yaron nan domin in koma kan kujerar mulkina......". Bata karisar da maganar ba ta dakata saboda idanu da ya zaro mata, muryarsa a ɗan dishashe ya ce. "Tab kina tinanin sake komawa kan mulki kenan? Ban kara tabbatarwa ƙwaƙwalwar kifi ne dake ba sai yau!". Zaro idanu ita ma ta yi da jin kalamansa, kai ta ɗan girgiza kafin ta ce." Ban gane me kake son cewa ba!". Miƙewa tsaye ya yi, cike da gadara ya tako zuwa in da take, sai da ya zagayeta sau biyu kafin ya tsaya a gabanta suna fuskantar juna. "Ba zaki gane me nike son cewa ba ai saboda na faɗa maki ƙwaƙwalwar kifi ne dake, idan ban da dakikanci da jakanci har zaki yi tinanin komawa kan mulki bayan ina raye? Kina tinanin yanda na zauna a saman kujerar da na fi sonsa fiye da komai na fara jin daɗinsa ina moransa sai kawai in sake tashi in bar maki waje ko?". Zazzaro idanu Zarina ta yi tamkar kwayar zasu faɗo ƙasa. Bai bata damar yin magana ba ya sake cewa. "Ai aikinki ya rigada ya kare, dama ita rayuwa ka ci amana ce kai ma a ci naka, ka yi kirki kai ma ayi maka kirki, dik abin da ka yi shi za'ayi maka, dan haka kin ci amanar Omranish, kin kashesa da hannunki yana matsayin miji a gareki wanda bai rageki da komai ba, kika ci amanarda kika kashesa, to a yanzu kema zaki ɗanɗani ɗacin da ya ji a lokacin da ya waro idanunsa ya ga ke kika ci amanarsa, yanzu kema ki waro idanunki ki ga ni Ude Ranveer Abdul mutallab ni na ci amanarki, na karɓi mulki wanda dama shi ne burina, na ɗale kan kujerar da na taso da tsananin yunwansa, dan haka yanzu zaɓi biyu ne suka rage maki, ko ki durkusa a gabana ki yi biyayya in cigaba da yi maki alfarma, ko kuma ki ja da ni ki kare a ƙaskantacciyar baiwa wadda zata zama karya ga bayin dake cikin prison ɗin Kingdom ɗin nan, ke kanki kin san yadda suke mu'amala da mata a ciki, wlh in sa a jefaki ciki, ki kare rayuwarki a hannunsu suna yadda suka so dake suna rage zafi, dan haka zaɓi ya rage gareki". Ya kai karshen maganar yana sanya hannunsa ya ɗan shafi fuskarta ya gangaro zuwa bakinta, ɗan matse bakin nata ya yi kafin ya gangaro da hannunsa zuwa kirjinta, ya gangaro da shi zuwa saman ƴan kananan breast ɗinta, sannan ya ce. "Komai ya kare daga albarkatun jikinki, na karar da komai, babu abin da zan yi dake, masu lafiyayyun kaya nikeso a yanzu, ke yanzu sai irin bayi ko tsoffin mayakan da suka yi laifi aka jefasu prison, su ne zasu kwasheki, ni babu abin da zan yi da yamutsastsun abubuwan nan". Ya kai karshen maganar yana matse mata kirji da karfi. WATO UDE ƊAN ISKAN MAI RAI NE NA GASKEN-GASKE. Mamaki ya hana Zarina motsawa, dan jin abin take yi tamkar a mafarki, sai da Ude ya matse mata breast ne ta farga ba mafarki take yi ba, dan haka sai ta ce. "Ni kake faɗawa haka Ude?". Kara matse mata kirji da karfin gaske ya yi har sai da ta datse idanunta, sannan ta ciza laɓɓanta alamar zafi. "Ki kirani da suna mai daraja wato King, kuma ki rinƙa tausasa harshe a kai'na kina kirana a daraje!!". Ya sake faɗa yana cigaba da murɗe mata breast guda ɗaya. Hannunta tasa ta ture shi da karfi, sai dai ina, ko motsawa bai yi ba, sai ma kara murɗe mata ƴan abubuwan nata da ya yi da karfin gaske wanda hakan yasa ta saki kara tare da durkushen kasa a wajen. Wani irin jan dogon numfashi ya yi game da saukewa a hankali. "Ki koyi ladabi ga manya in ba haka ba jikinki ya fi tsamiya tsami!". Yana kai karshen maganar ya yi gaggawar wucewa ya nufi hanyar fita. Tamkar a mafarki ya isko muryarta tana faɗin. "Karya kake yi karamun ɗan iska, Thomas family sun wuci a ci amanarsu, ko ka manta nike rike da karfin ikon na tsafin da kake tunkaho da shi ne?". Ta faɗa tana miƙewa tsaye. YAU FA AKE YINTA!. Ba tare da ya juyo ba, ya cigaba da tafiyarsa ya amsa mata da. "Kin manta da cewa ni na koya maki tsafi har na baki karaga da ikon juya komai ɗin ne?". Yana kai karshen maganar ya yi gaggawar ficewa abinsa. DUM!! DUM!! DUM ta ji gabanta ya bada bugu, da gudu ta mike ta haura wannan ɗan siririn staircase ɗin domin ta haura sama ta je ta duba gambun murza tsafin nata, ta tsorata da ya ce ai shi ya koya mata kuma ya yi niyyar bata damar juya komai, dan haka a yanzu hankalinta ya yi mummunar tashi. MY PEOPLE'S ME KUKE TINANIN ZAI FARU? YA FAƊA ZATA KAYA A TSAKANINSU? MACIYA AMANA BIYU ABU YA KWAƁE MASU, AKWAI KALLO FA GABA!!. ----------------------------🔥 BLACK WORLD.🔥 Bayan ta yi sallah isha'i ne ta shirya cikin kayan barcinta tamkar yadda suka saba, Smart ne ya tasasu a gaba dikkansu uku ya ce sai sun ci abinci sun ƙoshi a kan idanunsa, dan yaga ramar tasu ta yi yawa sosai, yana zargin basa wani cin abinci, sai dai su ɗan taɓa kada yunwa ta yi masu illah. Kuma hasashensa gaskiya ne, dan kuwa basa cin abincin, idan sun ji yunwa zata yi masu illah sai su ɗan tuttura sama-sama, wani lokaci ma Sweetie bata yin breakfast, sai dare in yunwa ya nemi kaita ƙasa sai ya ɗan sha green tea, to shi ne fa yau Smart ya tasasu a gaba. Ya zauna a saman chair yana kallonsu dikkansu uku ya ce su ci. Yadda kuka san suna cin dissa haka suke ta faman kwaɓe fuska tamkar an yi masu dole. Dai dai ya ga ba zasu ci ta arziki ba sai ya yi masu jan ido a kan in basu ci ba sai ya saɓa masu, wannan dalilin yasa suka ware suka fara turawa suna runtse idanu dan abincin basa jin ɗanɗanonta sam-sam. Ba shi ya kyalesu ba sai da ya tabbatar sun yi nak, sannan ne ya miƙe ya nufi bedroom na Big Bro, shi kansa Smart ɗin baya cin abincin fa, domin ya shiga damuwa sosai, ga shi babu wanda ya san halin da Big Bro yake a ciki, hakan yasa yake mulkar birnin a matsayin Big Bro, dan ma Ronnie yana highlighting ɗinsa a kan wasu abubuwa dan gane da birnin wanda bai gane ba. A cikin kwanaki ukun da ya yi a kan mulkin ɗan uwansa mutanen birnin nan sun samu canji da sassaucin rayuwa fiye da tinaninku, kuma a cikin kwanaki ukun nan mata almo 8 ne suka haihu a birnin, amma da yake Smart bai san da batun ɗaukan ƴaƴansu maza ba, sai bai karɓe masu ba, mata 6 dikka maza suka haifa, da ya ji labari babban kyauta ya shirya aka kai masu, ya basu maƙudan kuɗaɗɗen da kusan har su kammala rayuwarsu ba zasu cinyesa ba, har yasa mata dayawa suka ji sha'awar haihuwa. Sai dai kuma sun shiga shakku da mamakin yadda aka yi Big Bro ya yi masu irin wannan kyauta bai kuma karɓi ƴaƴansu ba! Do sun san yana da kyau over to over, wannan ɗabiarsa ce, amma kuma batun karɓar ƴaƴa ya yi mugun ɗaga hankalinsu da bai karɓa ba. Amma sun yi shiru suka cigaba da zubawa sarautar ALLAH su ga ko ya canza tsarin ɗaukar ƴaƴan nasu ya mayar da su sojojin yakinsa ne!. A kwanaki ukun nan ba ƙaramin tasiri sunan Big Bro ya kara a birnin ba, ya ja gabaɗaya a ko'ina sun manna hotunan bakar damisa suna nuna alfaharinsu na kasancewarsa sarkinsu, sun ji bala'in daɗin canzawar mulkinsa a kwanaki uku, harta sojojin yakinsa sun ji daɗi matuƙa, dan ya sassauta irin horon da yake basu, ya basu freedom sosai ba kamar yadda Big Bro yake azabtar da su da horo ba tare babu rana tamkar wasu jakuna ba. Wani irin daɗin da Ronnie ya ji na ganin yadda mutanen birnin nan suke murna suke jin daɗi game da yabawa yayansa da alfahari da shi, ya yi fatan idan Big Bro ya farfaɗo ya yi continuation daga kan in da Smart ya tsaya, sai da kuma bamu san me zai faru ba, mu jira tashin nasa tukun nan. --------------------------🔥 Bedroom ɗinsu suma suka koma, Pretty na ƙoƙarin kwanciya a saman gado Sweetie ta ce. "Ni kam ke kam Pretty yaushe zaki yi hankali ne?". Harara Pretty ta dalla mata kafin ta kwanta, sai da ta gama shan kamshinta sannan ta ce. "Wai Sweetie ni sa'arki ce zaki rinka mun magana haka?". IRIN ITA BABBAN NAN!. Sanin hali yasa Sweetie sassauta murya, cikin sigar rarrashi ta ce. "ALLAH ya baki hakuri, ni ba faɗa nike nema ba, amma dan ALLAH Pretty ki gyara abin da kike yin nan, kina dai ganin kowa ya ci abinci a gidan nan amma ban da Yah Omerish, amma ke ko a jikinki, kuma kin faɗa mun mijinki ne shi da na ce ki dai'na zuwa wajensa, kin ce ya ce ke matarsa ce, amma meyasa baki son kyautata mashi?". Harara ta sake galla mata tamkar idanunta zasu faɗo ƙasa. "Ai da nace maki shi mijina ne ban ce maki ina son shi ba! Ni Kamran nike so, da shi kawai nike son rayuwa, dan haka babu ruwana da wani Omerish!....." Bata iya ƙarisa maganar ba sakamakon zaro idanu da Sweetie ta yi, muryarta na rawa sosai ta ce. "Kam....... Kam..... Kamran kike so?". Kai ta jinjina mata alamar tabbatarwa. Dafe saitin kirjinta Sweetie ta yi, can kasan maƙoshinta ta ce. "Na shiga uku ina son abin da sisterta take so! Kamran take so? Ni ma shi nike so, ya zanyi da rai'na kenan?". Ganin tana magana ƙasa-ƙasa yadda ba'a ji ne yasa Pretty ta ce. "Akwai wani abin ne naga kin shiga wani yanayi daga batun Kamran?". Yadda kuka san babbar mace haka take magana. "Babu komai, amma please Pretty kina Sona?". Tana kallon tsakiyar idanunta ta ce. "Wace iriyar banzar tambaya ce wannan? Ina da wacce nike so biyunki a duniyar nan ne?". Kai Sweetie ta girgiza alamar a'a babu, sannan ta ɗaura da cewa. "To dan ALLAH idan har kina son farinciki na ki tashi ki je ki lallaɓa Yah Omerish ya fito ya ci abinci, dan ALLAH kada ki kara cewa komai kawai ki tashi". "Amma dai kin san nice babba kike mun magana kamar kina bani umarni ko? Kin san kuma bana son haka, bana son a rinka nuna mun wani ɗagun kai!". On a serious note ta yi magana. Ɗan yake kafi kuka ciwo Sweetie ta ɗan yi kafin ta ce. "Na ji Aunty Pretty, ALLAH ya huci zuciyarki jinin King Abdul Muxxalib, ai in baki yi haka na ba daga gidan sarauta kika fito ba, yanzu dai muna neman alfarman a je a rarrashin mana yaya ya zo ya ci abinci". Harara Pretty ta cigaba da dalla mata tamkar idanunta zai faɗi ƙasa ba tare da ta yi magana ba. "Aunty Pretty, dan ALLAH mana, na tuba kuma daga yau Aunty sama Aunty ƙasa zan rinka ce maki muddin zaki kula mana da yayanmu, please ki yi mashi salon kauna ta yadda zai ci abinci dayawa!". "Idan na yi mashi hakan me zaki bani?". Pretty ta faɗa tana yaye bargon da ta rufe jikinta. "Mekike so ƴar tsanar Yah Omerish?". "Wai ni Sweetie kin rainani ko?". Da sauri Sweetie ta toshe baki tana faɗin. "Na isa in rena princess Omnish? Ai wane ni! Yanzu dai please yayanmu yana jin yunwa na sani". "To idan na je na sa ya ci abinci na dawo zan faɗa maki me zaki bani kin ji?". Ta faɗa tana miƙewa zaune. "E na ji kuma na yarda, jeki ɗin dai". Tana turo baki ta miƙe ta fito daga ɗakin ko ɗankwali bata ɗauka ba. Kai tsaye ta nufi escalator tana cigaba da turo baki. Da sauri Sweetie ta biyo bayanta ta laɓe a jikin kofa tana leƙanta, so take taga ta jawo Smart sun baro bedroom na Big Bro dan ita kuma ta je ta yi mashi addu'oin da ta saba yi mashi kafin ta kwanta, tana jin kunyar zuwa ta samu Smart a cikin ɗakin, dik da baya hanata yiwa Big Bro dik abin da take so, amma tana jin nauyin ya ga kullum tana zuwa wajensa har cikin dare. Shi dai Ronnie yanzu ya dai'na hira, da ya ci abinci zai koma bedroom ɗinsa ya yi barci da wuri dan ya tashi around 2 ya fara nafilfili yana yi wa Big Bro addu'ar ALLAH ya tashi kafaɗunsa. Bakinta a ɗauke sallama ta shiga cikin ɗakin. Yana zaune saman sofa yana duba yanayin tsarin makarantun birnin da hospitals ɗinsu, jin sallamarta yasa, a natse ya ɗago da kallonsa a kanta kanta. Kura mata idanu ya yi har ta iso gabansa. Tana ƙarisowa ta faɗa jikinsa ba tare da ta yi magana ba. Musulmin ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Beb menene kuma?". Tamkar ba yanzu ta gama cewa ba shi take so ba, ta sanya hannu ta hau shafa kwantaccen bakin sajensa dake nan luf da shi. "Yah Omerish ka tashi mu je in baka abinci a baki ka ci ka ji?". Tana magana tana kara shafe mashi saje har izuwa wajen soft lips ɗinsa da suka ɗan kara red sosai. Ya sha mamakin kalamanta, dan banda zancen chocolate and tea babu wani canza dake haɗasu sai in rashin kunyarta na kusa idan ya yi magana ta bashi amsa ba respect. Addu'a ya yi a cikin zuciyarsa ALLAH yasa ta sauya ne yanzu, ALLAH yasa ta koyi kyawawan halaye daga ƴar uwanta. Bai dawo daga duniyar tunanin da ya afka ba sai ji ya yi ta sake cewa. "Da kai'na fa zan baka abaki, please ka tashi ka ji?". Idanunsa a kan ɗan bakinta ya ce. "Da gaske?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e. "Waye ya koya maki wannan karatun?". Turo baki ta yi game da ɗaure fuska sosai, ta yunkura zata bar jikinsa tana faɗin. "Oh kenan ni komai sai an faɗa mun zan yi maka ko? To shikenan mun ɓata". A hanzarce ya riƙota kafin ya ce. "Sorry to, mayar da wukar sarkin saurin fushi da tsiwa, ko dan na ji ya ɗanɗanon abincin da zaki bani a baki yake dole in ci yau, muje to". Ya yi maganar tare da miƙewa da ita a jikinsa. Kwanto da kanta a saman shoulder ɗinsa ta yi tana jin wani irin daɗi yana kara lulluɓeta, da haka suka nufi waje. Ai Sweetie tana ganin giftawarsu sun wuce ta yi saurin fitowa ta haura sama. Bata ɓata lokaci wajen afkawa ciki ba, a hanzarce ta rufo kofar tare da juyawa ta nufi bed ɗinsu. Hayewa ta yi ta matsa dab da Big Bro. Yana kwance tamkar gawa, tana jinjinawa kokarin irin na Smart da har wanka yake yi mashi ya canza mashi kaya, hakan yasa zuciyarta ta yi wa Smart kyautar waje mai muhimmanci, shiyasa kuka ga ta damu har ta rarrashi Pretty da ta je ta sanya ya ci abinci, yana da muhimmanci a wajenta ne dan yana kula mata da masoyin da bata san tana son shi ba!. Zubawa face ɗinsa idanu sosai na tsawon mintoci ta yi, ya kara haske da kyau sosai, sai wani irin sheki face ɗinsa take yi, matsawa dab da face ɗin nasa ta yi, a hankali ta fara kwaranyo mashi addu'oin da ta saba tana tofa mashi har tsawon mintuna 20, ko kaɗan bai motsa ba. Bayan ta kammala ta kara matsawa ta ja mashi bargo zuwa saman Lion chest ɗinsa ta lulluɓa mashi, sannan ta rankwafo kansa kamar mai san sanar mashi da wani abin na sirri. A wani irin slow ta ɗaura face ɗinta a saman nasa, muryarta can kasan maƙoshinta ta fara sambatu kamar haka. "Meyasa? Meyasa zaka ɗauki tsawon wannan lokaci ba tare da ka farka mun ganka kai ma ka ganmu ba? Muna kewar komai naka, muryarka kallan da idanunka suka mana mai cike da kyau da ɗaukar hankalin nan dik muna kewarsa, ka yi sauri ka tashi tin kan Omaish ta yi hauka, dan na kusa yi, in har baka tashi na zan zama zararriya, please our one and only Big Bro, wai don't you know that we love you over to over ne? Da gaske nike yi idan har baka tashi ba to zan zama zararriya ne, kuma ba zan...........". Bata iya ƙarisa maganar ba jin sautin muryarsa ya daki dodan kunnuwanta da cewa. "Ba zan taɓa bari ki zama zararriya ba ai, dan ni zan wahala". A razane ta raba fuskarta da nasa tana zazzare idanu, ko kaɗan bai motsa ba kuma lips ɗinsa ma basu motsa ba, sai dai kuma wlh zata iya rantsuwa ainahin voice ɗinsa ce ta yi wannan magana! To ta yaya kenan?. (Da na yi niyyar dasa aya a nan, amma saboda na ce zan dai'na dakatawa a wajen da yake da daɗi zan rinka gotawa kaɗan yasa zan ɗan gota.) Tana zazzare idanu sosai. Tamkar zata watsa da gudu ta bar ɗakin, sai kuma ta dake tana karanta addu'oi a cikin ranta ta kara matsawa kusa da shi sosai, ƙasa-ƙasa ta ce. "Big Bro ka dawo garemu ne?". Shiru ba a amsa mata ba. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Ashe gizo ne". Ta kai karshen maganar tare da ɗan kwantowa a jikinsa kaɗan, tasa hannun ta shafi lallausan kumatunsa tana kallan face ɗinsa sosai. "Kana da kyau over to over, komai naka kyau ne da shi, bakinka gwanin ɗaukar hankali, kamar in sumbaceka nike ji". Unexpected ta ji ya ce. "Zan ji daɗin hakan". Zabura ta sake yi, a wannan karon bata san lokacin da ta nufi sauka kasan bed ɗin a miliyan ba, sai dai kuma tamkar daga sama ta ji ya sa hannu ya damki hannunta. Da karfi ya fisgota ta faɗa jikinsa, still idanunsa a rufe ruf. Ai tsabar tsorata bata san lokacin da ta wage baki zata zunduma mashi ihu ba, kawai sai ji ya yi ya sanya hannu ya toshe mata baki tare da kara matseta gam a jikinsa. Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 Zazzare idanu ta hau yi, jikinta ya fara kerma, take ta tina da mafarkinsa da ta yi daren jiya, ta ji tsoro sosai, hankalinta a tashe ta fara faɗin. "Big Bro please kai ne?". Yadda ta yi maganar abin tausayi kuma abin dariya, a tsorace wai kai ne, (A'a bashi bane, ni ne Fatima Zahra😒) Wato kenan tasan na wancan rana dai bashi bane. Ya jima rungume da ita haka ta kasa motsawa kafin daga bisani ya ɗan sassauta riƙon da ya yi mata, slowly ta ɗago da idanunta ta sauke a kan kyakkyawar fuskarsa da ta sha gyara wajen Smart and Ronnie. "Please our only Big Bro ka yi mun magana mana! Ka buɗe idanunka in ganka". Ta kai karshen maganar tana gimtse bakinta cip. Almost 5 mins da yi mashi maganar kafin ya ɗan motsa lips ɗinsa, slowly ya furta. "Wanenen kuma Kamran?". Ya yi maganar tare da waro idanunsa gabaɗaya a kan fuskarta. Ai tsabar razana saura kaɗan ta saki fitsari a wando, idanunsa sun koma yadda suke, amma sun kara girma sosai wanda kuma shi ne ya razanata. Bata san dama can haka idanun suke da girma sosai ba, baya warosu ne kawai, kullum suna ɗan lumshe. Ya farfaɗo cikin lafiyarsa kuma cikin hayyacinsa sosai. "Am..... In...... Dama shi ɗin..... Am wani ne..... A'a a'a yayanmu ne ..... A'a dai abokinmu ne...... A'a ɗan uwanmu ne....... Ummmmm mijin sisterta ce". Tun da ta fara kwaɓa mashi wannan karya words ɗinta na haɗewa ya tsare ɗan bakinta da kallo, sai da ta kai karshen da for almost 5 mins kafin ya ɗan motsa lips ɗinsa wajen cewa. "Omaish meyasa kike karya bayan kuma ke kike ƙoƙarin hanawa a baya? Faɗa mun alaƙarki da shi da har kika tsorata dan Omnish ta ce shi take so ba Omerish ba?". BABBAR MAGANA, WATO KENAN YANA JINSU DIK ABIN DA SUKE YI! YA JI HIRANSU A CIKIN ƊAKI KAFIN TA FITO! TAB TO TA YAYA?. Ganin da gaske shi ya farfaɗo, kuma lafiya lou yake sai ta ɗan saki jiki, sannan kuma ta nemi waskewa, kwantowa a gefen jikinsa ta yi, can kasan maƙoshinta ta ce. "A da can da shi muka yi rayuwa a forest, shi yake kula da mu, shi yake kawo mana fruits har ma ya ɗaukemu mu je yawo........". Zaro mata idanu da ya yi ne ya sanyata dagatawa da yin maganar. Kallonta ya cigaba da yi alamar bai da niyyar yin magana. Hakan yasa ta fara ƙoƙarin cigaba da yin maganar tana ɗan in-ina. Dik yadda suke da Kamran ta kwashe ta faɗa mashi. Ai damko gaban rigarta da karfin gaske ya yi, wajen wuya kenan, da karfi ya fiagota ta faɗo jikinsa, har sai da ta buga kanta da wannan lion chest ɗin nasa mai kama da dutse, ɗan tsuke fuska ta yi saboda wani irin zafin da ta ji ya kai mata karo, a hankali cike da fargabar abin da zata tarar ta ɗan ɗago kan nata suna fuskantar juna, ita yake ta faman kallo kamar zai cinyeta da ido. Ita ma zuba mashi ido ta yi tana jin tamkar ta sumbaci lips ɗinsa. Unexpected daga bayansu suka ji tapi rap-rap-rap. Da sauri ita ta juya, shi kuma Big Bro yadda kuka san sassaƙasa a wajen aka yi, bai iya motsawa ba, ita kawai yake kallo babu kyaftawa. Smart ne rike da hannun Pretty suka shigo cikin ɗakin, shi ne ya saki hannun Pretty yana zubawa waɗan nan taurarin biyu tapi. A zabure Sweetie ta yunƙura zata bar jikinsa tana wani kara zazzare ido. Bai dakatar da ita ba, sai harara da yake bin Smart da shi. Ciki Smart ya ƙariso yana faɗin. "E yanzu kam ta tabbata ka nuna mana wariyar launin fata, wato sai da heartbeat ɗin taka ta zo ta dawo da bugun zuciyar sannan zaka farfaɗo ko?......" Bai ƙarisar da maganar ba sakamakon pillow da Big Bro ya rarumo ya harbesa da shi a fuska. Capke pillown ya yi tare da rungumowa a kirjinsa yana cigaba da zolayarsu. Da sauri Sweetie ta nufi barin gadon, ta wutsiyar ido Big Bro ya kalleta while shi kuma Smart ya kalli irin kallon da yake yi mata, take Smart ya gane Big Bro baya son ta tafi ne, amma kuma saboda miskilanci irin nasa ba zai iya buɗar baki ya dakatar da ita ba. NI KAM NA CE AI DAMA SHI BIG BRO BAI TAƁA DAKATAR DA SWEETIE BA, INA AI BAYA NEMAN WANNAN ALFARMA, SAI DAI YASA KARFI WAJEN DAWO DA ITA DA MAGIC!. Yau da alama baya jin yin amfani da magic ɗin ne, sai ya zuba mata ido, har cikin ransa baya son ta fita, dan yana son yi mata wasu ƴaƴan tambayoyi, bai san meyasa yake jin zafin cewa da ta yi tana son Kamran ba, zuciyarsa ta yi zafi sosai tun farfaɗowarsa, dan ya farfaɗo ne a dai'dai lokacin da suke yin wannan magana ita da Pretty, waye Kamran? Wannan suna ta tsaya mashi a ransa sosai, haushin jin maganar tasu ma tasa yaki buɗe idanu, dan yana jin tamkar zuciyarsa zata kone saboda ɗaukar zafi. "Heartbeat ɗinmu ba sai kin sauƙa ba, kin ga bashi da lafiya, bari in sanya a kawo mashi abinci sai ki taimaka mashi ya ci ko?". Cewar Smart, yana magana yana kallon ɗan uwan nasa, dan ya lura ko kaɗan Big Bro baya son Sweetie ta matsa daga kusa da shi, shiyasa ya yi mata wannan dabara. Cikin sanyin murya ta amsa da okey. Hannun Pretty Smart ya riko tare da jefawa Big Bro pillown hannunsa a saman fuskarsa shi ma kamar yadda ya yi mashi, sannan ya ce. "Bari muje mu sa a kawo maku abinci". Ya faɗa yana juyawa. Yana fita Sweetie ta dawo da kallonta a kan Big Bro, already shi dama ita yake kallo, sai suka ɗan yi shiru kamar wasu masu tinanin wani abin. Can ya ɗan motsa hannunsa wajen yi mata alama a kan ta zo. Matsawa dab da shi ta ɗan yi, sai ta ga lokaci guda ya ɗan canza haka, kamar wanda bashi da lafiya, ya ɗan yi so sillent haka kamar ba da karfinsa ya farfaɗo ba, ya zama mai rauni yanzu!. Abu biyu ne suka kashe mashi jiki wanda bata san da su ba, na farko ɗacin dake cikin zuciyarsa wanda shi kansa bai san ya aka yi ya tsinci kansa da jin wannan ɗaci ba, dan kawai ya ji ta ce tana son Kamran, so jikinsa ta yi sanyi mara dalili, dan a yadda yake gani wannan ba dalili bane. A ɓangare guda kuwa so yake yi yasan wanenen Kamran ɗin da yazama sisters dik suke son shi?!. Sun ɗan shagala da kallon juna sai ji suka yi motsin buɗe door. Shi dai bai motsa idanunsa ba, amma ita ta kai kallanta wajen. Robot masu kawo mashi abinci ne suka shigo ɗauke da manya-manyan try masu shake da kayan abinci kala-kala, kun san Big Bro da kaunar farin kala, gabaɗaya abincinsa harta spoons fararene, su cooler da sauransu. Zasu nufi dinning area ta yi gaggawar dakatar da su, ta ce su kawo saman carpet dan bashi da kwarin jikin da zai iya nufar saman dinning, ya ɗan yi mamakin jin hikima da hankali game da sanin yakamata irin nata, ya kara jinjinawa yarinyar nan sosai. Sai dai kuma Robot ɗin sam-sam basu kulata ba, dan sun karɓi umarnin Smart da ya ce su kawo abinci, kuma su sun san a in da suke ajiye abinci. Ganin basu kulata ba zasu wuce dining area ne yasa ta yi gaggawar dawo da kallonta a kansa, har lokacin bai kyafta idanunsa daga kallon da yake yi mata ba. Ɗan marairace mashi fuska ta yi ba tare da ta yi magana ba!. Ɗan gyaran murya Big Bro ya yi wanda ya ja hankalin Robot ɗin gabaɗaya suka juyo kansa. In a cool way sosai ya ce. "Kubi umarninta a koda yaushe". Yana gama faɗar hakan suka juyo da kallonsu a kanta, suna jiran jin me zata ce masu, su fa a tinaninsu da Smart da ya fita ya yi masu magana a yanzu, da Big Bro mutum ɗaya ne, sun ɗauka Smart ne ya dawo ya kwanta, kun san babu wanda ya taɓa ganinsu a tare sai Sweetie, Pretty and Ronnie, shiyasa kowa yake ɗauka Big Bro ne kawai. "Ku kawo abincin saman carpet". Ta sake faɗa tana ɗan sakin murmushi, ta ji daɗin matsayin da ya bata, ya ce Robot su rinƙa bin umarninta, wannan abu ya yi mata sugar, a ranta ta ce lokacin neman tsokanar kowa ya yi, Robot zasu tsaya mata ba mai cutar da ita, dama gudun kada a kakkarya mata kasusuwa ne yasa ta ɗagawa su Father's kafa kwana biyu bata je church da'awar ba, to yanzu dole gobe ta je da bodyguards guda huɗu kuma dikka Robot. Tina hakan yasa ta tuntsure da dariyar da bata san ta fara yi ba, ta kuma manta in da take, dariya sosai ta shiga yi kamar zararriya, dan ba abin da take tunawa face irin shakiyanci da rashin mutumci da ta tana da masu, in suka ce zasu taɓata Robot dai ba ruwansa da su Father's ne, sama-sama da su zasu yi, sai sun nunawa iska da rana su sannan su maka da ƙasa ato. Tsabar dariya har da buga jikin mattress ɗin tana faɗin. "Is my time now". Ta faɗa cikin dariya tana dafe ciki. Unexpected idanunta suka sauka cikin nasa, ai a wani irin miliyan ta haɗiye dariyar tata game da haɗe natsuwarta waje guda, sannan ta ce. "Sorry Big Bro". Ta faɗa tare da sauke ajiyar zuciya. "Zo ka ci abinci ka ji?". Ta sake faɗa tana kallon yadda yake ɗan limshe idanu yana wani ɗan ciza laɓɓansa irin ga samu ga rashi haka, ba wai ciza laɓɓa na ɗaukar zafi ko ya fusata ba, irin dai ya ji sha'awar wani abin kuma ya rasata. TO ME KENAN?. Hannunsa ya miƙa mata alamar ta kama ta taimaka mashi ya miƙe. Hannunta ta sanya ta riko nasa, da kyar ta fara jansa, sai dai a maimakon ta jasa ya miƙe, sai ta tafi gabaɗaya ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa, golden hairnta gabaɗaya ya rufe mashi fuska, ƙoƙarin ɗagowa ta yi sai kuma ta kasa, hakan yasa ta saki jiki ta kwanta tana mayar da numfashi sama-sama tamkar waddan ta ci gudu ta ƙoshi. Hannunsa ya ɗaura a saman bayansa, yasa ɗayan hannun nasa kuma ya tattare gashinta dake kan fuskarsa, cikin sanyin murya sosai ya ce. "Ina Kamran ɗin yanzu?". Mamaki ne ya dira a ranta, har yanzu bai manta maganar ba, ALLAH mai iko, kome yasa ya riki zancen a ransa? Ta jefawa kanta tambayar!. Ya yi maganar shi kuma yana watsa mata jelar gashinta a bayanta, yasa hannu ya ɗan ɗago kanta daga kirjinsa. "Kamran ni ma ban san in da yake ba, shi muke ta nema tsawon lokaci". Ta faɗa tana sake ƙoƙarin miƙewa, ga mamakinta sai ta ga a yanzu ta miƙe tsaɓanin ɗazun da ta gagara motsawa, da alama dai ɗazun shi ya riketa. A bayyane ya sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin ya yunƙura da ita a jikinsa ya miƙe zaune. A hankali ya ɗan juya tare da zuro kyawawan ƙafafunsa dake cikin bargo kasan bed, sannan ya zuba mata ido ba tare da ya yi magana ba. Da sauri ta bar jikinsa dan ta gane nufinsa, miƙewa ya yi tare da zare bargon ya yi jifa da shi a saman bed ɗin, miƙewa ta yi ta ƙarisa wajen da Robot suka ajiye abincin. Shi kuma toilet ya nufa, ta yi mamakin ganin yadda yake tafiya normal kamar ba yanzu ya gama nuna mata bashi da kwarin jiki ba, wato dai yana da shi, da gangan dama ya ce ta zo ta taimaka mashi ya miƙe. Bin bayansa da kallo ta yi a ranta tana kara jinjinawa kyan halittarsu shi da Smart. Ta yi nisa cikin zurfin tinani ya fito sanye da white bathrobe wanda ya tsaya mashi har gwiwa, kansa na nannaɗe da towel, fuskarsa ta kara wani irin haske na musamman, ya kara kyau sosai. A gaban mirror ya karisa ya tsaya tana kwance igiyar bathrobe ɗin. Sake baki ta yi tana kallan yadda ya tsaya a wajen, a tinaninta lotions zai shafa sai ta ga akasin hakan, domin bincike-bincikensa ya hau yi. Ta tsammaci ko ya manta da abincin ne, dan haka sai ta miƙe a natse ta karisa gabansa, a kusa da shi ta ɗan gefe ta tsaya ta jingina da jikin mirror drawer ɗin tana bin face ɗinsa da kallo. "Big Bro abincin fa?". Bai tanka ba, hasali ma bai yi kamar yasan da tsayuwarta a wajen ba. Bata yi mamaki ba, idan da sabo ta saba. Gyara tsayuwarta ta yi tana cigaba da kura mashi idanun. Unexpected idanunta suka sauke a saman faffar kirjinsa, kada ku manta ya kwance igiyar bathrobe ɗin, Lion chest ɗinsa a buɗe. Zubawa chain guda biyu da cross cikon na uku da suke wuyarsa ido ta yi, a mamakinta da ta yi wa cross ɗin kallon kurillah sai ta ga alamar abu a cikinsa, sannan akwai alamar hoton fuska mutum a cikinsa, dan design na cross ɗin nasa ya banbanta dana kowa, yadda wajensa yake kamar glass, cikin kuma baka iya gane me a ciki, sannan yana da kauri da ɗan faɗi. Kara zaro ido ta yi tana kure kallonta a kansa, shiru ta ɗan yi tana tinanin a ranar da wancan abin ya faru, lokacin da ya shaketa ya ɗagata sama ɗin nan tabbas ta yi ido biyu da wannan cross ɗin, tabbas a wannan lokaci wani irin koren wuta cross ɗin yake bayarwa yana wani juyi daga ta ciki. To meyasa a dik time da Big Bro yake lafiya cross ɗin take fara tas har da kyalli? Amma da zarar ya shiga wani yanayi cross ɗin zata koma koriya shar?! Abin ya yi matuƙar ɗaure mata kai, sannan bugu da kari yanzu ta tina cewa fuskar mai kama da wanda ta gani suke hira da Mommah ta cikin mirror ɗinsa (King Zuhair) shi ta gani a face ɗinsa ranar da abin can ya faru, to waye waɗan nan mutane a cikin rayuwarsa? Yana da matuƙar kyau ta san da hakan!. Ta yi nisa cikin tinani sai ji ta yi ya hura mata iska mai ɗan ɗumi daga bakinsa izuwa saman fuskarta. Ɗan firgita ta yi, a hanzarce ta dawo da kallonta a kan face ɗinsa, da ido ya yi mata nuni da mirror ɗinsa. A wani irin slow ta juyar da kallonta cike da fargabatar abin da zata iya cin karo da shi. Lokaci guda ta ɗan zaro idanunta tare da sake juyowa ta kallesa. "Su waye su?". Ta jefa mashi tambayar lips ɗinta suna ɗan kerma, saboda a jikinta ta ji cewa wannan guy da ta kallah shi ne Kamran, kerma da lips ɗinta suke yi kuma shi ne kada ace wani abin Big Bro zai yi mashi! Da ta tabbata cikin takaici kuwa. Sai da ya gama shan kamshinsa for almost 5 mins, sannan ya ce. "Shi ne Kamran ɗin naku". Ai a miliyan ta sake juyar da kallonta a kansa, yana zaune saman sofa, ya farfaɗo, Hoorain na zaune gefensa yana bashi tea a baki, ga sadauki Rishan a gefensa ɗaya yana tura mashi abinci hannunsa rike da spoon, Alhamdulillah Kamran jiki ta yi kyau sosai, har ƴar kiba ya yi a maimakon rama, sai dai yau kwanansa biyu da farfaɗowa, ban da sunan Pretty babu wata suna da yake iya faɗa, yaki yarda ya yi magana da su Hoorain, akwai shi da bala'in zuciya kun sani, to fushi yake yi da Hoorain dik da bai san wanenen shi a gareshi ba a yanzu, kada ku manta Hoorain ne ya jibgesa kuma ya hanasa kama Pretty, shi ne har ya suma ya sha jinya haushin Hoorain na ransa. SAI DA KAI YARON MAMMARSA, KAWAI A BAKA PRETTY, SHI NE KAMATABLE, RASHIN BAKA ITA KUMA SHI NE RASHIN KAMATABLE, KO YA KUKA CE MAGOYA BAYAN DAMISAN MAMMARSA?!!. "Kin san wanenen Kamran a gareku?". Big Bro ya jefa mata tambayar. Ta kafe Kamran da ido tamkar ta kirasa ya amsa take ji, ya tafi da imaninta sosai, sai dai ga mamakinta sai ta ga gabaɗaya daga shi, har su Hoorain, Ronnie da su sadauki Rishan dik yanayin fuskarsu guda ne, dikkansu Koreans ne, bata ma kara ruɗewa ba sai da ta kalli Hoorain da kyau, shi ai hatta gashin kansa iri ɗaya ne da nata babu wani banbanci, like abin ya yi mugun bata mamaki, ta shiga ruɗani, sai dai bata gama fita ba ta ji cool sexy voice ɗinsa yana faɗin. "Ɗan uwanki ne na jini, babanku ɗaya da shi........". Bai kai karshen maganar ba ya dakata sakamakon sauke idanunsa da ya yi a kan Auta da ta shigo cikin ɗakin a yanzu, hannunta rike da bottle na ruwa ta zo ta zauna kusa da Hoorain. Lokaci guda Big Bro ya ji zuciyarsa ta amsa, a ransa ya ce wacece wannan mai kama da su haka? Domin samun amsa sai ya shiga bincike a kanta da Hoorain da ta zauna a kusa da shi tana miƙa mashi bottle na ruwan, sai tambayarsa Sweetie take yi ya aka yi Kamran ya zama ɗan uwansu. Amma bai bi ta kanta ba ya hau bincike kan Auta kawai, a nan ne ya ci karo da abubuwa da dama masu ban mamaki da al'ajabi, nan ne ya samu labarin Auta ai ƴar Autar King Zuhair ne, kuma ƴar Mommah, which means kenan Auta Autar idencial biyun nan ne, Autar the two Lions of Mommah kenan!. (Wato Autar su Smart Tiger and Black Tiger Tiger.) Ɗan shiru ya yi kamar mai tinanin wani abin, sai kuma ya koma ya fara bincike kan mutumin dake ikirarin shi ne mahaifinsa, wato King Zuhair. Ita dai ya barta da kumfa a baki ya ki zayyana mata ta yadda aka yi suka zama uba ɗaya da Kamran, ya shiga wani aiki nasa. Wannan bincike da ya yi ta jawo mashi abubuwa da dama a rayuwarsa, ya yi mamakin ganin yadda rayuwar King Zuhair take dabaibaye da ruɗani ga uban tarin makiya tamkar a kansa aka fara yin sarki mai adalci da gaskiya, ta ko'ina basu barshi ba, ya gano shirin su Zarina na neman mallake masarautar King Zuhair su shafesa a doran duniya, ya kuma gano akwai tarin makiya da munafukai dake kewaye da King Zuhair, wannan abin ya jijjigasa sosai, haka kawai ya tsinci kansa da jin tsananin zafin abin da ake shiryawa King Zuhair bawan ALLAH, domin dik rashin imanin Big Bro ya shaidawa kansa King Zuhair adalin sarki ne kuma bawan ALLAH wanda ya sadaukar da abubuwa da dama da yake kauna a rayuwarsa domin farincikin al'ummar da yake mulka, lallai sarki irin wannan bai cancanci a barshi ya faɗi ƙasa ba. SAI DAI KAI BIG BRO NAMU NA AMANA!!. Yanzu amsa ɗaya yake son sani shi ne meyasa sauran masarautun nan suke gaba da King Zuhair? Amsar da yake son sani kawai, wanda shi kansa Smart ita yake son sani! Dani da ku masu karatu ma dik ita muke son sani, dan ita ce tushen komai!. Ya yi nisa cikin abin da yake yi sai gani ya yi Sweetie ta juya zata bar wajen cikin kunan rai, dan ya fi baki goma tana yi mashi magana bai amsa ba, shi ne ranta ya ɓaci zata wuce ta bashi waje. Hannunta ya riƙo ba tare da ya yi magana ko ya juyo ya kalleta ba, ya cigaba da abin sa yake yi na bincike-bincikensa, rafanan tsafin nasa suna bashi information kan yadda birnin nan ya canza gabaɗaya. Zaro idanu ya yi yana kallan yadda jama'arsa ke yabonsa suna nuna kauna a garesa, nan ya shiga binciken menene dalili, yana rike da hannunta bai saki ba har ya binciko me yafaru a birnin da suke zuba mashi ruwan albarka haka. Shiru ya yi yana mamakin ganin abubuwan da Smart ya canza cikin kwanaki uku kawai. DAMA SAI WANI ABIN YA FARU WANI ABIN YAKE BAYYANA, A LOKACIN DA WANI ZAI KWANTA A LOKACIN KAI KUMA ZAKA TASHI, A LOKACIN DA WANI YA ƁATA A LOKACIN KAI KUMA ZAKA SHIGO HASKE!. WANI SANADI KE KAWO WANI, DOMIN KUWA BIG BRO A CIKIN RANSA YA FARA TINANIN YA CIGABA DA KYAUTATAWA MUTANENSA KAMAR YADDA SMART YA YI A CIKIN KWANAKI UKUN NAN, YANZU YA FAHIMCI ZAFI DA ZALUNCI A KAN AL'UMMA BAYA HAIFAR DA SOYAYYA SAI DAI SU YI MAKA BIYAYYA DAN DOLE BA DAN SUNA SO BA, KUMA HAKAN BA KARAMAR ABU BANE, DAN DIK RANAR DA SUKA SAMU WATA YAR DAMA ZASU YI MAKA BORE NE HAR SU FARMAKA MA, DAN HAKA SAMUN SOYAYYAR MUTANE YANA SAMUWA NE DAGA LOKACIN DA KA KULA DA SU KULA MAI TSAFTA, YA SAMU KARIN HASKE SOSAI, BA SHAKKA ZUWAN SMART BABBAN HASKE NE A GARESA. (Yanzu kun gane dalilin da yasa Big Bro ya sume tsawon 3 days? Kuna tinanin a lokacin ɗaya in bai ga aiki a aikace ba zai yarda ya dai'na zaluntar mutanen birninsa ne? Kuna tinanin zai dai'na kwace masu ƴaƴa ta karfi da ya ji ne? Wannan dalilin yasa muka yi amfani da ƙwaƙwalwa wajen jinginesa ya suma na ɗan lokaci, sannan yanzu kunga zai ji daɗin kasancewar Smart a tare da shi har ma ya yi alfahari, wannan plan ta yi kuma ta mun sugar.🥱) Yanzu ya gama fahimtar komai, kuma ya ji yana son taimakawa King Zuhair. Ajiyar zuciya a bayyane ya sauke kafin ya juyo da kallonsa a kanta. "Dogon labarin ne alaƙarku da Kamran, but sooner or later zan faɗa maki". Ya kai karshen maganar tare da sanya hannu ya ɗan matsar da dogon gashin da ya zubo saman face ɗinta yana hana mashi ganin kyakkyawar face ɗin nata da kyau. Bafa ya gajiya da kallon yarinyar nan ko kaɗan, kome ta yi burgesa take yi, wata ƴar karama da ita a gabansa. "To shikenan, yanzu mu je ka ci abinci". Yarinya mai hankali, bata jayayya da maganar manya, dik da a matuƙar ƙagare da son jin alaƙarta da Kamran da take yi, bata ja da maganarsa ba da ya ce ko ba jima ko ba daɗe zai faɗa mata, ta hakura ta taushi zuciyarta. (AMMA AKWAI SHEGEN NEMAN TSOKANA 😺) "Kina son in ci abinci ne?". Da sauri ta gyaɗa mashi kai. "Ke kinci ne?". Nan ma kai ta gyaɗa mashi kafin ta shiga bashi labarin yadda Smart ya tsaresu sai da suka ci abinci suka ƙoshi sannan ya kyalesu. Lokaci guda ya kara tsintan kansa cikin wani irin farinciki na musamman, dan yadda Smart ya kula mashi da su ba karamun daɗi abin ta yi wa zuciyarsa ba, gaskiya an burge zuciyar Big Bro. Sai kawai ya tsareta da ido. Ganin haka yasa ta riko hannunsa ta jasa suka wuce wajen abin cin, ba musu ya bita izuwa wajen. Bai saba cin abinci a ƙasa ba, dik sai abin ya yi mashi wani banbarakwai, amma dai haka ya daure ya karɓi abincin ya fara ci a natse, ta zubawa ɗan bakinsa idanu tana ta aikin kallon yadda yake motsasu, ji take yi tamkar ta yi kissing ɗinsa. Yana kallonta sarai, kuma yasan yadda ɗan bakin nan nasa yake ɗaukar hankalinta, ya yi niyyar bata mamaki wani lokaci, yau ya tsinci kansa a cikin farinciki har kala uku, na farko farincikin jin cewa ubanta ɗaya da Kamran, na biyu abin da Smart ya yi ya jawo mashi soyayya ta girmama mai tsabta a birninsa, na uku.......... Bai bayyanawa kowa ba!. Sai yake jin tamkar yau ya kashe mata kishinta na san kissing ɗinsa da take yi tsawon lokaci, amma bai nuna mata alama ba, ya cigaba da cin abincinsa tana kallonsa. -------------------------🔥 Zaune suke a sama wajen da Big Bro yake yawan zama, Smart na zaune saman sofa ita kuma ta kwanta tare da kwanto da kansa a saman laps ɗinsa, sai zuba mashi shagwaɓa take yi tana aikin shafe mashi jiki, shi kuma ya ɗan yi shiru yana tinaninsu Momma jikinsa na karɓar sakon beb ɗin tasa. Sai magana dake yi mashi amma yaki kula ta, hakan yasa ta sanya mashi kuka yana turo baki, tasa hannu zata dafa laps ɗinsa ta miƙe ta bar jikinsa tin da yaki kulata, wai ita ta yi fushi. Ai tana sanya hannu sai saman bananarsa dake tsaye zat. Wani irin zabura ya yi ita kuma da tsabat sakalci sai ta ce mashi. "Me ka tura a cikin wandanka haka kamar itace?". Ta yi maganar tana cigaba da tattaɓa wajen, ta manta tashi zata yi kuma ta manta fushi take yi da shi. Da farko ya yi yunƙurin hanata taɓawa, amma sai ya rabu da ita tare da rankwafowa kanta kaɗan, cikin wata iriyar murya tamkar wanda ke a cikin maye ya ce. "Bulala mai koya maki hankali ki dawo cikakkar macece a wajen". Harara ta dalla mashi kafin ta ce. "Kenan mahaukaciya ce ni yanzu?". Kai ya ɗan girgiza mata. "Ba mahaukaciya bace ke, sai dai sakalcinki ya yi over, amma one day one time wannan bulala zai dawo mun dake kan hanya, ki natsu ki kimtau tamkar sister ɗinki". Ya kai karshen maganar yana faɗin shiiiiiiii saboda yadda take ta tattaɓa mashi bananar tasa tana kai mashi duka har tsakar ka. "To fito da bulalar in ganta, dan i dai nasan babu wani abin da zai sanya ni in zama kamar Sweetie, ban fita bane? Kanwata fa". Ta faɗa tana hura kumatu, cike da yarinta wai ita nan babba. Shiru bai iya amsa mata ba sakamakon ta rufe mashi baki, dik tasa jikinsa har wani tsuma yake yi, a wannan gaɓa ba zai iya yin magana ba. Hannunta ta ɗaura saman zip ɗin wandansa tana faɗin bari ta fito da bulalar ta gani, har da cewa zata karya shi ta zubar sai ta ga da me zai zaneta ɗin. Zuge zip ɗin kasa ta yi tana kokarin tura hannunta ciki. A cikin zafa ya damki hannun nata yana wani irin numfashi, idanunsa a limshe, can ƙasan makoshinsa ya ce. "Please ki bari kin ji ko?". Yana kai karshen magana ya ɗaura ɗayan hannunsa a saman mazaunanta. Make mashi kafaɗa ta yi game da cewa ita sai ta gani. Ta faɗa tare da kwace riƙon da ya yi mata, hannun nata ta tura ciki, hakan ya ja ya yi wani irin matse idanunsa gam saboda wani irin daɗin da ya ji ya daki ƙwaƙwalwarsa, da karfi ya capki mazaunan mata yana wani numfashi mai nauyi. Saboda tsabar rashin ji irin na yarinyar nan tura hannu can ciki ta yi, tin daga farkon bananarsa ta fara taɓawa tana san riƙo kan, kuma fa yadda kuka san mai aljanu a kan, gabanta na faɗuwa amma haka take cigaba da yi kamar ba ita ma. Ai bai san time ɗin da ya girgiza kansa game da furta. "Wuuuuuuuuuu". Cikin ɗaga murya ba, dai'dai lokacin ta kai hannunta saman kan bananar tasa, sai a lokacin kuma ta fahimci a jikinsa wannan bulala fa take, ai zabura ta yi zata zare hannunta ya yi zafan damke hannun nata manne da bananar nasa, da kyar muryar ƙasa-ƙasa ya ce. "Ai sai kin ƙarisa abin da kika fara". Kai ta shiga girgiza mashi, tamkar zata yi kuka ta ce. "Dan ALLAH Yah Omerish ka yi hakuri, na tuba ba zan sake ba". "Yau babu tuba, dan yau sai na yi maganin mara jin magana". Ya kai karshen maganar tare da ɗan matsa hannunta da ya riƙe. Girgiza ta cigaba da yi, idanunta suka ciko tab da kwallah, can ƙasan makoshinsa ya ce. "Idan kika kuskura kika mun kuka babu abin da zai hanani miƙawa Tiger ke, kuma ki buɗe kunnanki da kyau ki saurareni in ba haka ba kin san saura". Take ta natsu tana ƙoƙarin shanye kukan nata, sai ta zama abar tausayi. "Kada ki kuskura ki cire hannunki daga in da yake, wasa zaki fara yi mun da wannan bulala har sai san da na ce ki bari, kuma kina yin kuka Tiger kai tsaye, tin da baki ji yau zaki fara ji ne, maza fara aikinki tin yanzu, kuma komai na yi maki kema ki mun da ɗayar hannunki, kin ji ko?". Cikin serious ya yi maganar, babu wasa a tattare da shi ko kaɗan. Kai ta gyaɗ mashi alamar to, sannan ya zame hannunsa daga riƙon da ya yi mata, a ransa ya ce yau sai ta yi kukan gaskiya kila ya samu da ɗan natsu. Tana turo baki tamkar zata yi kuka ta ce. "Ni Yah Omerish ai ban iya wasa da shi ba". Sai a lokacin ya waro rinannun idanunsa a kan fuskarta, lokaci guda ta ɗan bashi tausayi, ALLAH sarki ko ma'anar penis bata ma sani ba, to dama girman forest yaushe zakata san wani abu shi penis, ga rashin uwa a tattare da su, ai fin haka ma zai gani. Amma sai ya dake bai nuna kamar ta bashi tausayi ba, saboda yana jin daɗin wannan wasa da ta faro da kanta. "Fito da shi waje zaki yi ki fara shafa mun shi kina wasa da shi kina sumbatarsa". Idanunsa a cikin nata ya yi maganar. KAM BALA'I ASUWAY SMART ƊAN IKKAN MAI RAI NE! WAI HAR DA TA FITO DA SHI WAJE, WATO ABIN NA BASHI SUGAR. ALLAH sarki, tana san yin kuka ba hali, haka ta danne ta zarota waje, ai bata san time da ta zunduma ihu ta zabura zata bar jikinsa ba. Kun fa san abin nan na maza mugun kwarjini ne da shi, uhm barema na su Smart ni dai bari in yi shiru. Cikin zafa ya capko hannunta ta sama, jawota jikinta ya yi, gabaɗaya ilahirin jijinta kerma yake yi, hawaye sun gama wanke mata fuska sosai, kai ta cigaba da girgizawa, ta gama rikicewa. Kalamanta suna harhaɗewa ta shiga fadin. "Yah Omerish tsoro nike ji, ba zan iya ba, na tuba ba zan sake ba, na shiga uku na, Sweetie ki zo ki ceceni". Kara ƙanƙameta ya yi kafin ya ce. "Shiiiiii! ya isa haka to, natsu waje guda". Ƙanƙame rigarsa wajen Lion chest ɗinsa ta yi, tana cigaba da girgiza mashi kai. Rungumeta ya yi ya hau shafa bayanta a hankali-hankali alamar rarrashi, ya ɗan yi nadamar razanata da ya yi, in bai yi sa'a ba yanzu zata fara jin tsoronsa ta dai'na kwanciya a jikinsa tana zuba mashi shagwaɓar da ta saba ɗin nan, ga shi wannan shagwaɓa tata ba karamun tafiya da imaninsa yake yi ba, yana sanya shi manta dik wata damuwa da ya taɓa shiga. Rarrashi ya hau yi har sai da ta yi shiru, daga haka barci ta yi awon gaba da ita, ajiyar zuciya ya sauke, a fili ya ce. "Sorry my beb, amma gaskiya ba zan iya cigaba da jira ba, i really love you more, and ina cutuwa wajen controlling kai'na a kanki, kin kai ni makura yau beb, dole in kau da kai'na in yi abin da ya dace". Ya kai karshen maganar yana sanya hannunsa ya tattare gashinta da ya sauko ya rufe fuskarta, yadda ta kwantar da kan nata a saman kirjisna sai gashin nata ya rufe mata fuska. Zuba mata idanu ya ɗan yi kafin ya ce. "I really love everything about you, komai naki abin burgewa ne". Kallon juna Sweetie da Big Bro dake tsaye a bakin shigowa wajen suka yi, tin ɗazun suka hauro, tin time da Pretty take kuka yake rarrashinta, sun burgesu ne sai suka tsaya suka kallonsu, ya kammala cin abinci ya shirya cikin tsadaddun sleeping dress ɗinsa. Gabaɗaya Sweetie sai ta ji ta nemi natsuwarta ta rasa, sun yi mugun burgeta, sai ta yi ƙasa da kai tana satar kallon Big Bro, while shi ma ita yake satar kallo, gabaɗayansu sai suka ji suna da bukatar irin wannan farincikin. Slowly ta ɗago idanu zata kara kallonsa, karaf suka haɗa ido, dan shi ma ita yake kallo, bata san time ɗin da murmushi ya kubce mata ba. Wannan murmushi ba karamar jan zuciyar Big Bro izuwa gareta ya yi ba, sai ya ji tamkar ya sallama mata kansa. Bai san time da ya miƙa mata hannunsa a kan ya zo ba, kun fa san idan ana soyayya kusa da ku ji kuke yi tamkar kuma a cikinta kuke, kada ku ga kaifinsu. Ita ma dai bata san lokacin da ta miƙo nata hannun ba, sai ji ta yi ya fisgota ta faɗa saman Lion chest ɗinsa. A tare suka sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin yasa hannu ya fara shafa wannan haɗaɗɗen gashin nata dake bala'in ɗaukar hankalinsa. Zura hannunta ta baya ta yi a in da ta harɗe hannayen nata cikin na juna a saman bayansa, uhm shi da ya ce bari ya zo ya sha iska na 30 mins ya koma ɗaki ya kwanta, sai ga su dikka sun ɓige da love daga ganin bawan ALLAH Smart yanayi. Bata san ya aka yi ba, sai jinta ta yi gabaɗayanta a saman Lion chest ɗinsa, sai kawai ta kwantar da kanta a gefen wuyansa tana sauke ajiyar zuciya. Natse ya taka da ita suka ƙarisa wajen. Ɗan zabura Smart ya yi, san bai yi expecting ɗin ganinsu a wajen ba. Saman sofa Big Bro ya zauna da ita a jikinsa, sannan ya dawo da kallansa a kan Smart. Dik tinanina ni Princess Teema zai ce wa Smart ya gode ne, sai na ga akasin hakan, domin kuwa ɗaure fuska ya yi, cikin nuna ɓacin rai ya ce da Smart a kan me zai gudanar mashi da mulkinsa ba yadda ya tsara ba? Bai duba kundin dokoki bane?. Hakuri Smart ya bashi, dan baya son yin ja in ja da shi ko kuma ya ja dogon magana, saboda yana cikin tsananin sha'awa sosai. gabaɗaya Big Bro sai ya ji jikinsa ta yi sanyi na hakurin da Smart ya bashi, amma sai ya dake saboda tsabar taurin kai da zuciyar bala'i. Miƙewa Smart ya yi ɗauke da Pretty a jikinsa, kai tsaye ya sauka ƙasa, ta wutsiyar ido Big Bro ya bisa da kallo har ya sauka, ta karfi da ya ji wani irin azabbabben so da kaunar Smart yake shigarsa, abin har ya fara fin karfin zuciyarsa bawan ALLAH. Smart na sauka kasa ya nufi wani bedroom ɗin bana Big Bro ba, dama ya ce yau ba zai bar Pretty ba, sai ya tafi ɗaki daban. Shi kuma Big Bro zama suka yi a wajen ba tare da wani abin ba, a tsanake ya shiga jera mata tambayoyi a kan mom ɗinsu, dan yana son tantance shin wacce take hannunsa ita ce mahaifiyarsu ko dai kama ce kawai! Har around 12 na dare suna wajen, sai da ya gama tabbatarwa da ita ce mom ɗinsu, sannan ya miƙe yana cewa Sweetie ta je ta kwanta, ta so ya faɗa mata meyasa ya yi mata waɗan nan tambayoyi, amma ina bata samu amsa ba, haka ta hakura ta wuce bedroom ɗinsu. Lokacin da ta shiga Pretty bata ɗakin, sam bata damu ba, ta wuce ta kwanta abinta, addu'a ta kwararowa kanta kafin ta ja bargo, yau cikin farinciki ta kwanta, shi kuma Ronnie yana saman dadduma bai san yayansa ya farfaɗo ba. WASHEGARI 🌅 Sai around 10 Sweetie ta farka daga barci mai daɗin da ya yi awon gaba da ita tin bayan sallar asuba, cike da farinciki ta tashi, yau tsabar murna linƙaya ta ce zata je yi a pool, dan haka toilet ta wuce ta yi brush, sannan ta fito ba tare da ta yi wanka ba, ta shiga wajen closet ɗinta. Jim kaɗan ta fito sanye da swwiming wear, riga ce mai haɗe da kamar short ba pant ba, tana da masu haɗe da pant ɗin, amma ta zaɓi zaɓi mai ɗan short zuwa santala-santalan cinyoyinta. Ta saki gashi har baya, sai ta ɗauko white bathrobe ta ɗaura a saman kayan ta fito ta nufi katafaren pool dake ta baya can in da mutane basa zuwa sai ita da Ronnie, kamar dan su biyu aka yisa. Tana zuwa sai da ta kunna na'urar ɗumama ruwan saboda akwai ɗan sanyi. After some times ta kashe na'urar tare da dawowa bakin ruwan ta tsaya, Ronnie ne ya koyawa yarinyar nan linƙaya a ruwa. A hankali ta warware igiyar bathrobe na jikinta, sannan ta kwaɓesa, a saman ɗaya daga cikin chairs dake wajen ta ɗaura rigar tata. Ai wani irin dogon numfashin da ya ja sai da ya ji tamkar zai jan ye numfashinsa gabaɗaya ne, tin da ta zo wajen dama ya tsareta da waɗan nan idnaun nasa, dik ta tashi hankalin bawan ALLAH, yana daga sama ne, ya tsaya yana bin birnin nasa da kallo kawai ya hangota a wajen. Ai tana cire rigar saman ya nemi dik wata natsuwa tasa ya rasa, ga shi shi ma sanye yake da white bathrobe, yanzu fitowarsa daga wanka ko kaya bai sanya ba. Yadda kuka san tasan akwai wansa take rikirkitawa tinani daga gefe, sai ta sanya hannu ta wani watsa wannan golden white hair dake kara ɗaukar hankalinsa over, ta watsa gashin sosai kafin ta mai da hannayensa saman waist ɗinta, ta tsaya a bakin ruwan. Tsalle ta daka ta afka cikin ruwan. Ai ji ya yi tamkar a cikin zuciyarsa ta afko, take ya ɗan ɗauke wuta na ƴan sakanni, slowly ya lumshe idanunsa ya sake warosu a kanta. Ta ɗan ɗauki ƴan sakanni a kasan ruwan kafin ta ɗago da kansa sama gashin kanta ya yi sama ya kara watso mata ruwa a fuska, ɗan girgiza kanta ta yi ruwan gashin nata ya watsu mashi a fuska, slowly ta waro idanunta kai tsaye sai kan fuskar mutum dake dab da ita. Wani irin zabura ta yi, ko da wasa bata ji shigowarsa cikin ruwan ba, zazzaro idanu ta yi tana kallonsa, a lokacin shi kuma ya lumshe idanunsa sakamakon ruwan jikin gashinta da ta karkaɗa mashi a fuska. UHM LAMARIN SWEETIE DA BIG BRO SAI SHIRU, TO MU HAƊE DAKU BAYAN SALLAH IDAN MAI DIKKA YA KAIMU!. Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 Zazzaro idanunta waje ta yi, daidai lokacin shi kuma ya buɗe nasa idanun waje, ta tsorata matuƙa da ganinsa a haka, amma sai ta dake tare da ƙoƙarin guje mashi, dan a cewarta lokaci ya yi da zata fara ja baya kaɗan da shi, saboda yadda ta ga ya fara sauyawa alamar sun ɗan yi nasara, dik da cewa da sa hannun Ronnie take wasu abubuwan, amma ita ma ta kara da nata gudunmawar dan sama mashi rahma. Ta ɗan yi nisa cikin tinanin da take yi unexpected ta ji saukar hannunsa a saman waist ɗinta daga ta cikin ruwan. Kara zazzaro mashi idanu waje ta yi, sai kuma ta ɗan ja baya kaɗan tana kallonsa. Lokaci guda taga kaman ba shi ba, ita fa kanta na ɗaurewa sosai a kansa, dik lokacin da zaka ɗaura idanunka a kan bawan ALLAH'N nan sai ka ga sabon abu a tatare da shi, abin yana mugun ɗaure mata kai over. Jawota jikinsa ya yi, can kasan makoshinsa in a cool way sosai ya ce. "Wacece Nufaysah a gareku?". Ai bata san lokacin da ta karisa kwalalo idanun nata waje ba, tamkar kwayar zasu faɗi kasa. Muryarta na rawa ta ce. "Am..... Mom ɗinmu ce, a ina take dan ALLAH? Ka san in da take ne? Please help us". Tin da ta fara magana idanunsa a kan ɗan bakinta har ta kai karshe. Shiru bai amsa mata ba, Big Bro akwai iya shiru ya gindayar da mutane. Ai tsabar farinciki bata san lokacin da ta kai mashi wani irin capka a waist ɗinsa ba shi ma, sai da ta ga ya ɗan lumshe idanu ne ta gane ashe akwai abin da ta yi mashi. Da sauri ta zame hannunta a wajen, dik ƙagara da son jin gaskiya tamkar zai kasheta, amma bawan ALLAH'N nan babu ma alamar zai amsa mata, ya wani kafeta da idanu. Sai da suka ɗauko good 3 mins a haka kafin nan ya ɗan yi kasa da kansa, kaman mai tinanin wani abin, can Kasan makoshinsa ya ce. "Kada ki sake mun tambaya a kanta, sannan kada ki sake tsallake rana guda baki je school ba!". On a serious note sosai ya yi maganar, babu wasa a kan fuskarsa. Ta sha jinin jikanta sosai yadda ta ga ya yi maganar, amma kuma ta ji tsananin zafin yadda yaki yin magana a kan mom ɗinsu bayan kuma shi ya fara kawo zancen, to meyasa ya ce kada ta sake yi mashi maganarta?. Uhm uwa uwa ce ko da a kan bola take, wani irin kuka ne mai karfi ta ji ya zo mata, bata san lokacin da ta fara wani irin shessheka tana sauke ajiyar zuciya ba. Kan ka ce me hawaye masu zafin gaske sun gama wanke mata fuska, tamkar an buɗe tap, tana yi tana wani irin cika tamkar zata fasa ihu mai sauti. Uhm shi da bai iya rarrashi ba, sai kawai ya zuba mata idanu yana karewa yadda lips ɗinta suke kerma kallo, yana jin jikinsa na wani irin tsuma, ji yake tamkar ya kamata ya mayar da ita cikin cikinsa saboda yadda yake ji. Almost 5 mins for silent, bayan shesshekar kukanta babu wani abin da yake ta shi a wajen. Da dai ta ga ba fa kula ta zai yi ba, bashi da wani sauki na tausasawa mutum idan yana kuka ko yana cikin wani hali, wato shi kamar yadda yake a siffa ɗaya kullum haka yake ɗaukar kowa. Abin ya kara kona mata rai over da har tana kokarin fita hayyacinta. Wani irin kuka mai karfi ta saki tare da juyawa zata bar cikin ruwan, sai dai kash, ta mance da yana rike da waist ɗinta, dan haka tana juyawa ya kara jawota jikinsa. Mannesu ya yi sosai, slowly ya rantwafo da kansa a kanta, kamar zai yi mata raɗa a kunne, sai kuma ya dawo da bakinsa dab lallausan kumatunta. Banza da shi ta yi, saboda ranta ya kai kololuwar ɓaci, tin da take babu wanda ya taɓa yi mata maganar mom ɗinsu sai shi yau, sannan ya ce kada a sake yi mashi maganar! Uwa fa ake magana! Ko dan shi bai san daɗin uwa bane yasa yake ɗaukarsu a matsayin abu guda babu wata banbanci. TO OUR BIG BRO, UWA DABAN TAKE DA KOMAI, DOLE RAN SWEETIE YA ƁACI, IDAN KAI BAKA DA SHAUKIN UWA TO SU SUNA DA SHI!. Kura mata idanu sosai ya yi, yau ya ga tsantsar bacin ran da bai taɓa ganin ko kwatansa a kan fuskarta ba, gabaɗaya sai ya ji babu daɗi. Da karfi ta yi kokarin fisge rikon da ya yi mata, sai dai kuma ina, ta gagara. Shiru shi kuma ya yi bai yi magana ba, kamar yana son cewa wani abin kuma. Almost 5 mins suna a haka, sai dalla mashi harara take da faman yi, tamkar ta rufesa da duka haka take ji, ga idanunta sun yi jajir da su. Tin tana kuka da ɗan sauti har kukan nata ya daina fita gabaɗaya, daga karshe ma ta yi shiru tsit, shi dai ko ci kanki bai iya ce mata ba, babu ma abin da yake tunawa irin zazzafar tsana da mom twis ta yi mashi, har ikirarin ɗaukar fansa ta yi a kansa, dan tana da bakin zuciya na gasken-gaske kaman Mammar Kamran haka take, a lokacin da yake gana mata azaba ya buƙaci da ta buɗi baki ta faɗa mashi a ina spender yake, ya azabtar da ita fiye da tinaninku, sai dai kuma a dik lokacin da ta buɗi baki cewa take yi. "Dik ran da na samu dama nice zan zama ajalinka, ba zan taɓa barin azzalumi irinka a doran duniya ba, nice mai kawo karshenka! Ka rubuta ka ajiye, na yi rantsuwa da ALLAH ɗaya in har na samu damar kuɓuta daga hannunka sai na ga bayanka!!". TASHIN HANKALI! Gabaɗaya yanzu kalamanta ne kawai suke ta yi mashi yawo a kansa, bai san time da Sweetie ta kwace kanta daga rikon da ya yi mata ba, sai ganinta ya yi tana barin wajen, kansa ta ɗan dauki zafi yana buƙatar hutu idan ba haka ba kuma a samu matsala gagarumi. Dan haka sai ya fito ya wuce sama shi ma, da alama jikinsa dik ya yi mugun sanyi sosai. CROWN OF POWER.🔥 Tin da King ya yi furucin zai sanar da Smart gaskiyar abin da yake faruwa ya shiga tashin hankali da damuwa, gabaɗaya ya zabge ya rame kamar bashi ba, ga ciwon zuciya da yake fama da shi, da kallo ɗaya zaka yi mashi ka fahimci yana cikin mawuyacin hali, Mommah ta shiga damuwa na wuce misali, ka zalika mummyn Chuchu ma dai tana cikin damuwa matuƙa, sai dai kuma ita Mama ko a jikinta, bata wani damu ba, kokari ma take yi na neman hanyar da Ramish zai maye gurbin babansa, so gabaɗaya hankalinta ba'a kansu yake ba. A yayin da shi kuma Ramish yana can yana ƙoƙarin shirin zuwa ɗauko Leesharh, sai dai ya ɗan dakata da kudurin nasa sakamakon ganin halin da king yake a ciki, tafiyarsa zai iya kara tada hankalin King har yasa ciwon ta karu su da suke neman ya samu lafiya, dan kun san yadda halin king yake a kan makiyasa, yana jin Ramish ya je Evil Crown zuciyarsa ce zata karisa bugawa kowa ya huta, dan haka Ramish sai ya ɗan dakatar da kudurin nasa, amma ba wai ya fasa bane. A ɓangaran Momman kuwa matar nan tana cikin tsananin damuwa na wuce misali, gabaɗaya walwala ya kauracewa kan fuskarta, har rama ta yi sosai, mom ɗin Smart ta sake zuwa bayan komawa da ta yi kafin ayi yaki, yanzu ta zo tana a tare da Mommah tana kwantar mata da hankali, amma ina Mommah hankali ya ki kwanciya, burinta kawai Smart ya dawo, dan har ga ALLAH ko barci bata iya yi tin da ya tafi, kwana kan dadduma take yi tana kwararo masu ruwan addu'ar ALLAH ya ɗorasa kan ɗan uwansa ya yarda dasu ya dawo gida. NI KAM NA CE KAMAR ABU NE WANDA BA ZAI YIWU BA BLACK TIGR YA DAWO GIDA, AMMA DAI ZAMU GANI, BA ZAI IYA RAYUWA A CROWN OF POWER BA, SABODA GANI YAKE YI TAMKAR KURKUKU NE KO KEJIN KAJI, DAN DIK GIRMA DA DAULAR CROWN OF POWER KO RABIN DAULARSA BASU KAI BA, KADA KU MANTA DA ƊANYAR GOLD AKA YI GININ ROYAL PALACE ƊINSA FA, UHM ZAI RAINA TATTALIN ARZIKINSU NE, BASU MA DA QUALITIES ƊIN DA ZASU IYA JANSA YA ZAUNA A CIKINSU, AMMA KILA YA IYA YARDA SU SUKA HAIFESHI IDAN SUKA BASHI HUJJOJI, BARI DAI MU GA ME ZAI FARU, AMMA KU ME KUKE TINANI?. ---------------------🔥 Yau ta kama Monday, CROWN OF POWER tana nan yadda take, tana cigaba da guda kamar yadda take a kullum karkashin umarnin da kaddamarwar King Zuhair, bisa tallafawar Uncle Abbas kasancewar King bashi da lafiya, so yana tallafa mashi. While Aunty MieMie ita ma tana iyaka nata bakin kokarin, shi ma uncle Jahiz haka, Akka ma dik da bata da lafiya tana bada nata gudunmawar sosai, a haka dai suke lallaba rayuwar. Gabaɗaya ƴan'matan King suna a zazzaune a katafaren main parlor, ciki har da Sareena da bata san Smart ya dankara mata red card na saki uku ba, dan Momma ta mance bata isar da sakon ba. So har yanzu tana ɗaukar kanta matsayin matar Smart ne, nan gagarumin shiri suke ta faman shiryawa na yadda zasu shawo kan Smart ita da su Omaid. Ta yi wa su Omaid alkawarin matuƙar suka tallafa mata ta samu kan Smart, to za su huta ne, har da ce masu zata sanarwa da Smart kada wanda ya saka masu ido, sanan su ci karansu babu babbaka babu mai horasu, wannan alkawari yasa suka zage dantse wajen ganin sun sama mata hanyar da zata mallaki zuciyar Smart, su dai damuwarsu su yi ta shaiɗancinsu kada a hukuntasu ko a takurawa rayuwarsu. Su Mahreen dik suna parlon, kowa dai yana wajen, sai wani harare-hararen juna suke yi tamkar ba ƴan gida guda ba, bare ma Sareena da ta matsawa Mahnoor da harara tamkar ta tsare mata wani abin, abin mamaki kuma shi ne har yau dai babu wanda ya nemi Fanan. Zee ta zuba uban tagumi tana ta tinanin Khadija, dik da Aunty MieMie ta faɗa mata Khadijah na lafiya, amma hankalinta yaki kwanciya ko kaɗan. Unexpected suka ga anturo kofar parlon daga ta waje. Gabaɗayansu suka wurga eyesball ɗinsu a kan kofar dan ganin mai shigowa, Mahreen da shegen gulma har da wani zazzaro ido waje tana wani wuwwurgasu, ta wani kwanta saman sofa tana wani shan kamshi ita a dole ta yi kwalliya. Almost 1 min da turo kofar wata kafa ta tako ciki, ai tin daga kasa suka fara ganinta har zuwa sama. Sanye take da wannan shiga tasu ta masu jajayen kunnuwa, hannunta rike da echolac tana ja, ta saki gashi tamkar wadda ta yanko daga kudancin duniya, ga wata uwar glass kamar babban yaron Smart mai suna Robert ne ya bata aro. HELEENA. Wani irin matsiyacin kallo suka fara binta da shi tamkar za su cinyeta da ido, bare ma Sareena da tin da ta ɗaura idanunta kanta ta ji ta tsaneta sosai, a gefen ita ma Heleena tana ɗaura ido kan Sareena ta ji yarinyar bata yi mata ba sam. Tamkar yadda suke binta da wani irin matsiyacin kallo haka ita ma take binsu da shi daga cikin glass, basa ganin idanunta ne yasa basu gane ba. Ko sallama bata yi masu ba hakan yasa gabaɗaya ransu ya ɓaci sosai, sai suka ɗauke kansu daga kallonta. Ganin haka yasa ta tako cikin nuna ita mai ji da kanta ce, ta nufo in da suke, a tsakiyar parlon ta dakata tana binsu one by one da kallo, da hannu ta yi pointing na Sareena kafin ta ce. "Da alama kece babba a cikinsu, baku iya girmama manya bane?!". Yadda kuka san bango Heleena ta yi wa magana ba su ba. Suka baiwa banza ajiyarta, kun san mutanen akwai ji da kai ga izzar balai, basa wulakanta mutum haka kawai, amma basa ɗaukar raini, idan ka mutumtasu ka kama kanka zasu baka mutumci, idan kuma ka nuna ji da kai zasu nuna maka gidanta ka zo. BATU NA GASKIYA BA WASA BA, WLH DIK MAI WULAƘANTA ƊAN ADAM KU BINCIKA AINAHINSA MATSIYACI NE, DIK WANDA YA TASO CIKIN DUKIYA CIKIN DAULA WLH BAYA KULAKANTA MUTANE SAM-SAM, KU LURA KUMA ZAKU CE NA FAƊA MAKU, AINAHIN MASU ABIN BASA WALAƘANCI!!. Ganin sun bawa banza ajiyarta ne yasa ranta ya ɓaci sosai, cikin fushi ta ce. "Ba daku nike magana ba wai?". Nan ma dai banza yaran nan suka baiwa ajiyar Heleena. Ji ta yi tamkar ta rufesu da duka, amma bata da karfin yin hakan, dan haka sai ta yanke shawarar ta kira ɗaya daga cikin bodyguards da ta zo da su ya zane mata su, ta ɗauka fa nan Paris ne, bata san gidan sarauta take ba, kuma shi gidan sarauta basa ɗaukar wargi da wani shashanci!. A ƙaida ta gidan sarauta wani daga waje bai isa ya keta izuwa in da family part yake ba idan ba King bane ya bashi izini, warriors dake tsaron gate na shigowa ma ai basa karɓar maganar kowa face na King, dan haka babu wanda ya isa ya wuce gate ɗin ba tare da King ya umarcesu da su bashi hanya ba, sai kuma Mommah, ita ce Princess da ake ji da ita, tana da damar aran bakin King a wasu wuraren, sarautar Crown of power na faɗa maku tsagwaran sarauta ce mai tsari da kuma bin dokoki, basa ɗaukar wargi ko wasa!. Har ta juya zata fita sai kuma ta tina ashe bodyguards ɗin nata ma basu samu damar shigo family part ba, ita kaɗan aka baiwa hanya bisa yarjewar king, mommah ce ta sanar mashi da zuwanta, shi ne ya yi umarnin a bata hanya bayan an cajeta tsab. Tuna cewa babu bodyguard ɗin da ya biyota yasa ta jan dogon tsaki, sannan ta ciro wayarta ta hau laluɓar number mom Smart tana wani dallawa su Sareena uwar harara tamkar idanunta zasu faɗo ƙasa. NI DAI NA CE IS TIME FOR GAME!!. Cigaba suka yi da yar hirar da su ke yi sama-sama tamkar basu san da mutum tsaye a wajen ba. Daidai wannan lokacin mom Smarta ta shigo parlon, Heleena na dalla masu harara ta nufi wajenta, hannunta ta kama suka wuce ciki, ba dai wanda ya ce wa wani uppan. Suna tafiya sai ga Dr Raj ya shigo cikin parlon bakinsa a ɗauke da sallama. Har suna haɗa baki wajen amsa mashi. Yana sanye cikin arabs jallabiya, ya yi kyau sosai, tin da ya sako kafafunsa idanunsa a kanta, ta buga tagumi bata ma san ya shigo ba. Cikin girmamawa kannen nasa suka hau ɗaga mashi gaisuwa. A taƙaice ya basu amsa ɗaya still kallonsa a kan Zee, cikin sanyin murya ya ce. "Ina son yin magana dake Zee". Jin muryansa yasa ta ɗan zabura tare da kai kallonta a kansa. "Lafiyarki kuwa?". Cike da mamaki ya yi tambayar. "Babu komai beb". Ta faɗa game da yin suɓutar bakin kiransa da Beb a gaban kannensa, ta manta ma a in da take. Haba nan take kallo ya koma kallon kallo a parlon, lokacin guda su Aneesa aka canza fuska, da wani irin matsiyacin harara suka hau bin Zee. Shi kuwa Dr wani irin Musulmin sanyi ya ji ya lulluɓe zuciyarsa, Zee bata taɓa ce mashi beb ba, infact bata ma taɓa kama sunansa a magana ba, bata taɓa nuna tana son shi ba, ya tabbata kubce mata yanzu ma ya yi, abin da yake a cikin zuciyarta ne ya fito fili, so shi ya ji daɗin hakan matuƙa. "Zo to sarkin tinani, ina da magana dake". Ya faɗa yana ɗan ɗage mata gera, da alama daɗin ta kirasa da beb yasa ya mance da kannensa dake a wajen. Ba musu ta miƙe ta nufesa, dan ta yi kewarsa sosai ita ma. Cike da mamaki suka saki baki suna kallon ikon ALLAH. Tana karisawa gabansa ya riko hannunta cikin nasa yana faɗin su je. Abin ya kara jirjizasu sosai, bare ma ita Aneesa da ta saki baki tana kallonsu, ta dai san yana son Zee, amma bata ɗauka abin har ya kai da su rike hannun juna ba, lallai dole su gyarawa Zee zama. BA DAN SABODA SU ZEE ƳAƳAN TALAKAWA NE YASA SU ANEESA BASA SONSU BA, KO KAƊAYA, BASU DA MATSALA SA ƳAƳAN TALAKAWA, SU MATSALARSU A NAN SHI NE LAUNIN FATA, BATU NA GASKIYA AYI TA DA WANDO KO BA HAKA BA, KASO TAMANIN CIKIN ƊARI NA LARABAWAN WANNAN ZAMANI SUN TSANI BAKAKEN FATA FIYE DA YADDA TURAWA SUKA TSANEMU, WANNAN SHI NE GASKIYA, FATARSU ZEE YASA SUKE NUNA KYAMARSU A FILI! SAI DAI SHI KUMA ALLAH BABU RUWANSA DA WANNAN, A DIK LOKACIN DA YA SO ZAI IYA JARABTAN BAWA DA SON ABIN DA YA TSANA, GA SHI DAI YA JARABCI RAMISH AND DR RAJ DA SON BLACK BEAUTYS JININ NIGERIA! KUMA BABU WANDA YA ISA YA CIRE SONSU A RANSU, DAN DAMA BA WANI NE YA SAKA BA!! Suna fita Aneesa ta yi gaggawar cewa. "Wlh ba zai yiwu ba!". "Har sai kin ma rantse?". Cewar Sareena da ta wani uban cukule fuska tana wani hura hanci. Chuchu da tin ɗazun ta tada kai da laps na Mahnoor ne ta yi gaggawar cewa. "Gaskiya wannan yarinyar ta yi local dayawa, ku ji fa har wani baby take kiransa". Da sauri Sareena ta ce. "Dama ƴan bakaken fatasuna da hankali ne? Ita bata ga kalarsa bane? Ai tasan ya fi karfinta, kawai jakanci da jahilci ne yake damunta, amma zamu nuna mata banbancin ta hanyar da zata gane". Ta yi maganar tana kallon Mahnoor, da alama da biyu ta yi maganar. Ai wani irin miƙewa zaune da Mahreen ta yi sai da ta razanasu, kamar wadda aka jefo daga sama, ta ji zasu ci mutumcin ƴan kasarta abin alfaharinta, kun san fa akwai jiƙaƙƙa a tsakaninta da Sareena, ga shi ta sake zagan mata ƴan kasa da mutanen ciki. ME KUKE TINANIN ZAI FARU? NI KAINA INA ALFAHARI DA KASATA, BA FA ZAN BAR DIK MAI CIN MUTUMCINTA BA, DAN HAKA INA TARE DA MAHREEN!. One by one ta bisu da kallo kafin ta ɗan girgiza kai tana ɗan ciza laɓɓa. Sareena ta ɗan sha jinin jikinta ganin yadda Mahreen ta miƙe, amma sai ta dake kamar babu komai. Ko uppan Mahreen bata ce masu ba ba kamar yadda suka zata ba, sai ma miƙewa da ta yi ta nufi part na Momma, ko kaɗan bata waigosu ba har ta fice daga parlon. Tana fita Sareena ta sauke wani wahalallen ajiyar zuciya wanda kana jinsa kasan na tsoro ne. Sai da Mahnoor ta ɗan saci kallonta, a ranta ta ce Mahreen ta zama abin da ta zama, yarinya har tsoro da shakkarta ake yi. Sai satar kallon kofar shigowa Sareena take yi, dan bata yarda da cewa Mahreen ta tafi ba, a ganinta wani abin ta je shirya masu ta dawo, dan tasan halin mutuniyar. Sai dai ga mamakinta shiru Mahreen bata dawo ba, abin ya yi wa Sareena daɗi har sai da ta sake sauke ajiyar zuciya, dik sun lura da ita, amma babu wanda ya yi gigigin yi mata magana, dan sun san masifarta. A ɓangaren ita kuma Mahreem kai tsaye bedroom da ya kasance nasu ita da Zee ta nufa, dik da cewa Zee a wajen Aunty miemie take idan ta zo family part a nan take zama. Saman gado ta haye, a tsakiya ta zauna kamar wata yar bori, a fili ta fara ayyana yadda zata koyawa su Sareena hankali, yadda zasu gane cewa su fa ƴan Nigeria kyautar ALLAH ne ga duniya, dan billahil lazi babu abin da babu a kwakwalwar ɗan Nigeria, uhm rashin samun wadatatcen kula ne, amma wlh babu in da ɗan Nigeria zai shiga bai zamo na farko ba, kai kusan Africa gabaɗaya, Nigerians we're gifted wlh, daban muke duniya ta shaida da hakan! Musamman arewacin Nigeria, daban muke! Idan zan tsaya zayyana baiwar da ALLAH ya zuba a kwakwalwar ɗan Nigeria wlh ina iya rubuta littafi guda complete, dan baiwarmu yawa ne da shi!!. Ta yi nisa cikin tinanin da take yi sai ganin mutum ta yi zaune a gabanta yana wani irin lumshe idanu, da alama yanzu ya taso daga barci, yana sanye da sleeping dress masu zubin pj's launin ligh ash, arabs hair ɗin nan nasa tamkar an kifa mashi hula, har gaban goshinsa, sai wani glowing yake yana kwailin, ga wani fitinannen kamshi dake tashi. Shakan kamshinsa ta yi ta ɗan lumshe ido ta sake buɗewa a kan kyakkyawan fuskansa. "Me zaka wani shigo mun ɗaki without my permission?". Tana wurga mashi harara ta yi maganar. Murya irin na mai barci ya ce. "Sorry, mafarkinki na yi shiyasa na zo ganinki, meyasa jiya kika ki bari in ganki?". Ya yi maganar yana waro idanunsa da kyau a kanta. "Ban yi ra'ayin ka ganni ɗin bane, kuma yanzu ma ka tashi ka fita mun a ɗaki tin ban tayar maka da guguwar kukan dake kaina ba". Ya sameta a kan tsi ne, wato tana tsaka da jin haushin su Sareena, shiyasa ta zata sauke a kansa. "Ki yi hakuri, amma waye ya taɓaki kike faɗa haka? Kuma kin manta now we're best friends ne? Kin manta ni kaninki ne ke aunty ta? Kin manta am ur besty?". Wani irin sanyi ta ji a ranta jin ya kirata da aunty, hakan yasa ta ɗan sassauta murya. "Na manta kai kanina ne shiyasa na yi maka tsawa, kada ka damu ka cigaba da ce mun aunty zan daina yi maka tsawa". Ta kai karshen maganar tana sanya hannu ta shafi lallausan arabs hair ɗinsa, wai irin tana rarrashin yaron nan, gabaɗaya Mahreen ta gama raina guyson son ranta, yadda kuka san ana rarrashin yaro ɗan shekara biyu, har da wani shasshafa kansa izuwa saman lallausan kumatunsa. "Dik wanda ya taɓaka ka zo ka faɗa mun zan rama maka ka ji kanina?". Ta yi maganar hannunta a kan lallausan kumatunsa. Wani irin musulmin daɗi ne ya rufesa, jinsa ya yi a sama, har ya ɗan lumshe idanu ya sake warosu a kanta. "Da gaske zaki tare mun faɗa?". Ya faɗa yana mayar da kallonsa kan ɗan bakinta. Da sauri ta gyaɗa mashi kai. "Sosai ma, ka san na iya faɗa, kada ka damu dik wanda ya rainaka zan ɗaukar maka fansa". Jinjina mata kai ya yi kafin ya ce. "To zo mu je gym mu ɗan motsa jiki, daga nan sai in faɗa maki waɗan da suke raina mun wayau a gidan nan". Jin zai faɗa mata masu raina mashi wayau yasa ta amsa da to, wai irin ita so take ta gwada mashi jaruma ce ita, shi ne har da wani amsawa da nuna ƙasaita. Kasan bed ɗin ya sauko, sannan ya nufi hanyar fita, da sauri ta diro ta bi bayansa suka nufi gym suna ɗan hira. Hannunta ya riko cikin nasa kasancewar zasu fita idon mutane, wai baya son kowa ya kalleta, idan ya rike hannunta yasan ko warriors ba zasu ɗaga idanu su ganta ba. KISHI A JININ KING ZUHAIR YAKE!. Sai dai yana riketa ta yi kokarin kwace kanta tare da juyowa cikin zafa. "Meyasa zaka rikeni?". Ɗan marairaice fuska ya yi. "Ni ba kaninki bane?". Jinjina kai ta yi. "Kuma haka ne, amma ni yakamata in rikeka ai ko?". Kai ya gyaɗa mata yana kara jin tsananin sonta a ransa. Juya hannu ta yi ta rikesa suka karisa gym ɗin zuciyarta cike da tinanin irin fansan da zata ɗauka a kansu Sareena a daren wannan rana, ta yi alkawarin ba zata bari gari ya waye ba tare da ta harhaɗa masu jini da majina ba, dan ma nan gaba su san Nigerians fa ba sa'an yin su bane, mun wuci nan!! A hankali ya fara koya mata yadda zata motsa jikinta da sauran abubuwa, dik abin da yake yi ya shiga koya mata a natse cike da kulawa, yana yi yana kare mata kallo cike da zallar madarar kaunarta bawan ALLAH. Ita kuwa ta zage wai zata kara karfi. CROWN OF INJUSTICE.🔥 Ɗakinsu ta faɗa ta murji kukanta son ranta, har barci ɓarawo ya yi awon gaba da ita. Tana tsaka da barci Ronnie ya zo ya dubata, amma bai tasheta ba, ya kyaleta tare da ficewa. Ba ita ta farka ba sai around 2 na rana. A hankali ta fara motsa idanun nata da suka yi mata nauyi, kun san kuka tasha kafin barci, so idanunta sun yi nauyi sosai. A hankali ta warosu waje tare da miƙewa zaune a tsakiyar bed ɗin, dik jikinta tsami ta ji ya yi mata, tinani ta fara yi a kan yadda za'ayi tasa Big Bro ya yi magana kan mom ɗinsu, tasan tin da ya faro maganar to ba shakka yasan wani abin dangane da ita, dole ta nemo hanyar sanya shi ya buɗe baki ya kora jawabi ko yaki ko ya so. Da wannan tinani a ranta ta miƙe ta nufi toilet dan yin wanka. A gurguje ta shirya cikin wata shegiyar doguwar riga mai bala'in kyau zubin Italians, ta yi fitinanen kyau, perfumes ta zuba a jikinta kafin ta fito ta yi niyyar sallah, dama suna da agreement na zuwa shopping ita da Ronnie wanda Smart ne ya basu izini, shiyasa ta yi wannan shiga. Bayan ta idar da sallah ta zuba addu'oi sosai kan ALLAH ya ɗaurata bisa wuyar Big Bro ya faɗa mata ina mom ɗinsu take, ta na shafa addu'ar ta miƙe ta nufo waje. ALLAH sarki, sam zuciyarta bata iya yin fushi da shi, kai tsaye room ɗinsa ta nufa tana wani kwaɓe fuska tana turo baki. Buɗe kofar ta yi ta shigo, wani irin musulmin kamshi da ya daki kofofin hancinta ne yasa ta ɗan dakata da tafiyar tana wani irin shaka. Har da lumshe idanu na ƴan sakanni ta sake warosu waje, kai tsaye sai a kan kyakkyawan face ɗinsa dake a tsaye a tsakiyar ɗakin yana ƙoƙarin sanya botir na rigarsa, da alama yanzu ya kammala shiryawa shi ma, daga bayansa Smart ne yake tsaye a gaban mirror yana gyara gashin kansa, sun yi shiga iri ɗaya, komai nasu iri ɗaya, sai suka kara fitowa a identical ɗin nasu da kyau. Kurawa juna ido suka yi, zuciyar Big Bro sai jinjinawa kyanta yake yi. Shi ma kuma ya yi matukar burge zuciyar Omaish Omranish. Sai suka mace da kallo juna, a wannan karan ma sai da Smart ya fara yi rapka masu tapi rap-rap-rap sannan suka ɗan farga, a hanzarce Big Bro ya zare kallansa daga kanta game da wucewa ya nufi dining area ɗinsa. A kunyace sosai ta ce. "Yah Omerish ina wuni?". Ba tare da kalleta kai tsaye ba ya amsa da lafiya, sannan ya bi bayan Big Bro izuwa saman table dan cin abinci. Sai da ya kusa isa wajen ya ce. "Bismillah ki zo mu ci a tare, ƴar uwarki tana barci". Cewar Smart kenan. Kamar zata ce a'a, amma sai ta tina yanzu fa yakin sanya Big Bro ya faɗa mata ina mom ɗinsu zata yi, dan haka dole ta je kusa da shi. Da sauri ta bi bayan Smart, ga mamakinta sai ta isko Ronnie zaune a wajen, da sauri ta karisa kusa da shi ta zauna tana sakar mashi cool smile. Shi ma abin da yake ta faman aika mata kenan, tana zama ya kai hannu zai shafi kyakkyawan golden hair ɗinta kenan unexpected idanunsa suka sauka kan na Big Bro, lokaci guda Black Tiger ya dalla mashi wata uwar hararar da bai san ya yi ba. Zaro idanu Ronnie ya yi, dan ko da sunan wasa Big Bro bai taɓa harararsa haka ba, sai ya kasa karisar da hannunsa izuwa kan Sweetie, ya tsaya cak yana son fahimtar ma'anar wanan harara da yayan nasa yake aiko mashi. Shi kuma Big Bro ganin ya zaro mashi idanu ne yasa ya farga da ashe ya hararesa ne, ɗan kara ɗaure fuska ya yi tare da kawar da kallonsa daga kansu izuwa kan Smart wanda tin da suka zauna yake kallonsu, a kan idanunsa aka yi wannan dirama dikka, ya gama gano cewa Big Bro ma dai akwai wannan ɗan banzar kishi na jinin modarawan a jininsa, dan haka dole ya yi taka tsantsan da shi. Ganin su Smart yake kallo yasa ya kara ɗaure angry face ɗin nasa tamau, sannan a natse sosai ya ce. "Kallan fa?". Smart yana kokarin jawo plate na abinci da robot suka kammala zuba mashi a yanzu ya ce. "Laifi ne dan na kalli ɗan uwana abin da na fi kauna a rayuwata kuma bugun zuciyana?". Hararar Big Bro ya wurga mashi kafin ya ce. "Bana son kallo, idan ka cigaba kuma zaka rasa idonka ne"........ "Baka son kallo, amma kana son kalle mana sister ko? Kuma baka gajiya da kallonta, sannan ita baka gajiya da ko zata shekara tana kall.......". Bai iya karisa maganar ba ya dakata sakamakon wani irin damka sa Big Bro ya kai mashi a arab hair ɗinsa, da karfi ya ja gashin har sai da Smart ya yi yar kara game da cewa. "Am so sorry mafaɗaci kawai". Kin sakesa Big Bro ya yi har sai da ya sake cewa. "Am so so sorry my pleasure". Sannan ne ya sakesa yana mai da hannu ya ɗauki spoon. Yana sakinsa Smart ya ce. "Kai dai ka canza hali da saurin fusata". Sweetie da Ronnie dai sai kallonsu suke yi suka faɗaɗa murmushinsu. Ko kallon in da yake Big Bro bai sake yi ba ya fara cin abincinsa a natse. "Na zauna da mutanen nan naka da suka zo mun kuma tattauna". Cewar Smart, ya yi maganar yana kallon fuskar ɗan uwan nasa. Ɗagowa Big Bro ya yi ya tsaresa da ido ba tare da ya yi magana ba, alamar yana jiran karin bayani. Kora mashi jawabin yadda suka kare da masu jajayen kunnuwa Smart ya yi, daidai lokacin da ya kai karshe Big Bro ya ɗebo abinci a spoon zai kai ɗan baki, ai bai san time da ya yi wani irin jifa da spoon ɗin ba, a fusace ya sa hannu ya daki table ɗin har sai da gabaɗaya plates ɗinsu ya girgiza, cups na ruwa wasu suka faɗi, bottle na ruwa ma haka wasu suka faɗi, take fuskarsa ta canza kala, ya kara ɗaureta tamau, idanunsa sun kaɗa jajir cikin lokacin ƙanƙani, with harsh voice sosai ya ce. "Da can ubansu ne yake bawa birnina tsaro da za su ce zasu bani tsaro in basu haɗin kai? To ni sai dai in basu tsaro ba dai su bani ba!! Na fi karfin wani ya taimaka mun! Dan haka kada su bari in kara ganin kafafunsu a birnina, idan ba haka ba, labarin karshen rayuwarsu ba zai yi daɗin bugawa a mujallu ba!!". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa zai bar wajen, cikin gaggawa Smart ya miƙe ya tari gabansa, zuciyarsa na bugawa da karfi, dan yana mugun shakkar ɓacin ran ɗan uwan nasa, amma ba zai iya kyalesa bai ci abinci ba. Sweetie da Ronnie dik sun sha jinin jikinsu, hankalinsu ya tashi sosai, a zabure suka mimmike suna zare idanu. "Gaskiya ne sai dai ka basu tsaro, ni kaina na shaida hakan, but please my pleasure calm down ka zauna mu yi lunch a tare, zamu yi farinciki da hakan, kada ka bari wasu su ɓata mana wannan moment ɗin, we really like it". Ɗago ido ya yi ya kalli cikin kwayar idanun Smart, ban da zallar kaunarsa babu abin da ya gani kwance cikin kwayar idon ɗan uwan nasa, yana wani irin huci tamkar zai kama da wuta ya ce. "Ni bana neman taimakon kowa, na fi karfin hakan, dole ma in gwada masu ni ba'a sa'an yinsu bane!". Smart ya gama fahimtar cewa shi da Big Bro ya tsani ace ya gaza ko kaɗan ne, wato shi ya tattare dik wani ji kima da isa ta jinin sarauta, wato sai dai ace wasu sun gaza ya tallafa masu. SAI DA KAI LAST BORN OF EVIL WORLD, KUMA KING OF BLACK WORLD!. "Tabbas ba zaka taɓa neman taimakon kowa ba In Sha ALLAH, sai dai ka taimaka masu, kuma ka fi karfin neman taimako, muma mun shaida, su ɗin banza". Kalaman Smart sun sanya ya ɗan ji sanyi a ransa, har da sauke ajiyar zuciya, da alama yanzu Smart ya fara gano yadda zai zauna da ɗan uwan nasa. Shiru bai amsa ba, yana cigaba da huci a hankali-hankali, Smart ya fahimci cewa lallai Big Bro mutum ne mai wuyar mika wuya a kan abu, wato yanzu ya hakura har ciƙin zuciyarsa ɗin ma ba zai yarda ya hakura ba, ba zai koma ya zauna ya nuna masu ya hakura ba, dik wuya mika wuya kai tsaye ne ba zai yi ba saboda balain taurin kai, dan haka sai Smart ya riko hannunsa ya mayar da shi ya zaunar yana kara tausansa ta hanyar zuba mashi kalamai masu sanyaya zuciya. Da haka suka samu ya ci abincin nan da kyar, suna gamawa ya miƙe ya koma cikin room ɗinsa, kallon Sweetie Smart ya yi, a natse ya ce. "Idan kun dawo daga shopping ina son yin magana dake, da farko na ce ba sai na nemi taimakonki ba, amma yanzu na gano matsalolin ɗan uwana suna da mugun yawa sosai, dole sai mun haɗa hannu, yanzu ku je shopping ɗin ku dawo". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya bar wajen. Kallan Ronnie Sweetie ta yi, a tare suka sakarwa juna murmushi tamkar ba lafiya ba, sannan a tare suka miƙe suka nufi room ɗin. Big Bro baya a cikin ɗaki, kallon Ronnie ta yi kafin ta ce. "Lovely bro ina zuwa, bari in yi wa Big Bro sallama". Kaman Ronnie zai dakatar da ita, dan yasan ba lallai Big Bro ya kyaleta ba tin da kwanaki ya roki alfarman ya barsu su ke yaki, amma sai ya daure yana addu'ar ALLAH yasa kada ya hanasu. Cike da zumuɗi ta wuce balconynsa, yana zaune a saman sofa yana latsa waya, sai huci yake yi, alamar magana yake yi da bakinsa masu jajayen kunnuwa. A kusa da shi ta zauna, ganin yadda yake huci tamkar zai kama da wuta ne yasa ta tattara dikkan natsuwarta da hankalinta a kansa, cikin sanyin murya ta ce. "Calm down our one and only Big Bro". Ta yi maganar tare da kai hannunta saman lion chest ɗinsa, a hankali ta fara shafa wajen tana cigaba da cewa. "Cool down our only Big Bro". Tin baya ta ita har bai san lokacin da ya sauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya ba, sannan ya juyo da kallonsa gabaɗaya a kanta. Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 Tin baya ta ita har bai san lokacin da ya sauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya ba, sannan ya juyo da kallonsa gabaɗaya a kanta. "Ka cika saurin fusata our Big Bro, do you know that Yah Omerish yana sonka fiye da kansa? Kasan irin tashin hankalin da ya shiga a dalilin ciwonka kuwa? Ka san damuwar da ya tsinci kansa a ciki kuwa? Kasan ko abinci baya iya ci? Please Big Bro ka so Yah Omerish ko da rabin son da yake yi maka ne ka ji?". Ta kai karshen maganar tana kallon kyakkyawan face ɗinsa. Almost 5 mins shiru ban da kallonta babu abin da yake yi, sai da ta ɗan yunkura zata sake yin magana can kasan makoshinsa ya ce. "Soyayyarsa ba'a kan fuska take ba, soyayyarsa tana cikin jijiyoyon jinin dake manne da zuciyata ne, ban san meyasa nike jin tamkar in babu shi zuciyata ba zata iya ci gaba da bugawa ba". Tin da ya fara magana ta tsaresa da ido tana kallon ɗan bakinsa yadda yake motsasu tamkar lips ɗin suna yi mashi ciwo. Abin da dikkansu basu sani ba shi ne, soyayya a tsakanin Big Bro da Smart fa wata aba ce da tin basu san juna ba akwaita a zuƙatansu, zuƙatansu a manne da juna yake, harta bugawar da zuƙatansu ke yi a lokaci guda yake yi, ai dole yanzu tin da sun ga juna soyayyar ta bayyana a fili kowa ya gani, na Smart dai ta bayyana, shi kuma Big Bro da ya kware wajen iya kasancewa a siffa ɗaya shiyasa tasa bata bayyana ba! Amma tana jijiyoyin jinin dake gudana a zuciyarsa, ba zai taɓa iya rabuwa da Smart ba, shi ne kawai yake zancensa na cewa ba zai yarda ba, wuyarta Smart ya ce zai koma ne, a nan ne zai gane ba fa son wasa yake yi mashi ba!. Ɗan zaro mashi idanu ta yi, dik da bata fahimci kan zancensa na cewa soyayyar ɗan uwan nasa a jiyoyin jini dake zuciyarsa take ba, amma ta fahimci yana son Smart, dan haka sai ta ce. "Kenan yanzu ka aminta da cewa shi ɗan uwanka ne?". Cike da zumuɗi ta yi maganar. Da sauri ya girgiza mata kai. "Kawai ina jinsa a raina ne, amma ba zan taɓa yarda ina da alaƙa da su ba!". Ya faɗa in a cool way sosai. Mamaki ne ya kara kamata, ba ita ba har Smart dake cikin room ɗin yana sauraronsu sai da ya kara jinjinawa taurin kai da kafiyar balai irin na ɗan uwan nasa, wai jinsa a rai kawai yake yi, wato ma a kawai ya ɗauki hakan, kai gaskiya Smart ya fara sarewa a kan Big Bro zai iya musulunta, a da yana sa rai, amma yanzu yana jin kamar hakan ba zai yiwu ba, dan kafiyarsa ta wuci yadda ake tinani!. Smart ya gama fahimtar cewa lallai akwai buƙatar su yi gangamin saukewa ɗan uwansa Alqur'ani, saboda ya fahimci dik ranar da ɗan uwan nasa ya yi kaman zai yarda da shi to fa sai wani abin ya gifto a tsakaninsu ya kara jagula zuciyar Big Bro yasa shi faɗa da sauransu, ranar da ciwonsa ta tashi a sama, tabbas a wannan ranar ya so yin na'am da Smart, amma sai aka birkita shi har ya yi suman kwanaki uku, a yanzu kuma a dining area, har wasa Big Bro ya yi da shi yana ja mashi gashi, ganin kamar zai aminta da shi ne yasa aka yi gaggawar jagula mashi zuciya ya birkice har da buga table wai dan masu jajayen kunnuwa zasu bashi tsaro, sam ya lura ba'a son magana mai daɗi ta shiga tsakaninsu, dole wanda yake da sa hannu a cikin wannan al'amari dikka yana kallosu, idan baya kallonsu ya aka yi yake birkita masu lissafi? Dole koma wanene yana a kusa da su!. JAMA'A KU TAFAWA SMART, DAN SAI MAI KAIFIN TINANI ZAI IYA GANE CEWA DA GANGAN AKE BIRKITA ZUCIYAR BIG BRO A SANYA SHI HASALA WANI LOKACI, TABBAS BA'A SON YA YARDA DA SMART, TO WAYE YAKE WANNAN AIKI? WAYE SHI?!! Ya yi nisa cikin tinanin da yake yi, su kuma Sweetie ta zauna tana ta kokarin forcing ɗinsa ya aminta da Smart, sai dai daga karshe da ta matsa abin ya kusa yi masu babu daɗi, dan har cire hannu ya yi zai dalla mata mari kenan ta yi gaggawar faɗawa jikinsa tana bashi hakuri, ta ɓoye fuskar tata da zai mara ɗin a cikin kirjinsa tana tausansa da sanyayyan kalamai. Izuwa yanzu ita ma ta fara karaya da cewar Big Bro zai iya musulunta, saboda yadda yake da balain kafiya, kaifi ɗaya ne shi na gasken-gaske kuwa, hakan yasa ta shafawa kanta lafiya tare da cewa. "Big Bro zamu je shopping da lovely bro". Ta yi maganar tana shafa lion chest ɗinsa. Hannun da zai mareta da shi ɗin ya ɗaura a saman bayanta, sannan yasa hannunsa dake rike da waya ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna. "Close ur eyes". Ya faɗa yana ɗan kawar da kallonsa daga kan face ɗin tata. Ba musu ta datse idanunta tana wani ƙaƙalo murmushi. After like one minute ya ce. "Buɗe". Da sauri ta buɗe, a tinaninta wani abin zata gani, amma sai bata ga komai ba, da mamaki ta kallesa, sai ta ga ya ɗan kara ɗaure fuska kafin ya ce. "Sai kun dawo". Ya faɗa tare da zame hannunsa dikka biyu daga jikinta. Kanta ne ya yi wani irin ɗaurewa, to me yake nufi? Me ya yi mata? Meyasa yau ya yi saurin aminta da su je shopping? Waɗan nan sune tambayoyin dake a cikin ranta. Kasancewar babu mai bata amsa yasa ta miƙe jiki a sanyayye zata bar waje, haka kawai a kumatunta ta ji tamkar an ajiya mata hot sumbata ne! Har cikin ranta ta ji hakan, har da ɗan lumshe idanu, da sauri ta warosu a kan fuskarsa, ya yi kasa da kai yana latsa waya, a cikin ranta ta ji tabbas shi ya sumbaceta, dan ta ji alamar lallausan lips ɗinsa a kan kumatunta. Shi dai yadda kuka san gunki haka, bai ɗago ba tamkar bai san shi take kallo ba. Juyawa ta yi ta fara takawa ta nufi barin waje, lokaci guda ta saki cool smile, wani irin sanyi ta ji ya ratsa zuciyarta. Har ta kai wajen kofa zata shiga cikin bedroom ɗin sai kuma ta juyo da gudu ta dawo, kai tsaye ta faɗa jikinsa. A natse ta manna mashi wani zazzafan sumbata a kumatu. Wani irin lumshe idanunsa ya yi ya kara warosu a kanta, can kasan makoshinsa ya ce. "Da alama baki shirya zuwa shopping ba". Ai yana faɗar haka ta zabura ta miƙe, da gudu ta bar wajen, dan ta fahimci kenan hanata zuwa zai yi idan ta cigaba da zama a jikinsa. Da ido ya bi bayanta har ta fice daga wajen, wani irin ajiyar zuciya ya sauke. Daga in da yake bai motsa ba har ya ji tashin motocinsu a kasa, alamar sun tafi, ajiyar zuciya ya sake saukewa a bayyane kafin ya yunkura ya miƙe tsaye. Ba komai yasa ya bari su tafi shopping ba face dan ta kara shagala ta mance da batun mom ɗinsu, sam ɗazun bai ji daɗin kukan da ta rinƙa sha ba, shiyasa ya yarda su je, bugu da kari yana son su tafi ya duba mom twins ɗin. WAI KUN LURA BIG BRO YANA SHAKKAR ƁACIN RAN SWEETIE? BA ZAI JE DUBA MOM ƊINSU BA SAI BATA GIDAN, WATO YASAN MA SUNA GINI GUDA KENAN! UHM KANA ABIN DA KA GA DAMA BIG BRO, AMMA MUJE ZUWA, ZAKA YI BAYANI NE! SAI KA KOYI LARABCI DAN BAN HAKURI! KO DA YAKE BAMU SAN AINAHIN YAR WACE YARE BACE MOM TWINS, BUT SHAAA ZAKA KOYI KOMA WANNENE DAN KAKARKA AKKA MAI RAN KARFE!. Kasa gabaɗaya ya nufo, tamkar zai hau wannan glass way ɗin sai kuma ya fasa ya bi wata siririyar staircase dake wajen wacce ta yi sama, da farko Smart ya so dakatar da shi, amma sai ya lura kamar abu important ne zata fitar da shi, dan haka sai ya rabu da shi. Ya ɗan yi tafiya mai nisa a wannan hanyar bayan ya haura sama ta staircase, wata doguwar corredor ce a wajen wanda ta huda har cikin wata katafaren bedroom na alfarma. Kofar ya nufa, kamar sauran kofofin empire ɗin yake, dikkansu da ɗanyar gold aka yi su. A dab kofar ya tsaya, gabaɗaya wajen dim light ne, babu haske sosai, slowly ya kai hannunsa zai murɗa handle na kofar, sai kuma ya dakata game da kasa kunnansa a jikin kofar. Wani irin tari mai tsananin karfi ne yake fitowa daga ciki, ga wani irin numfashi dake fitowa da karfi-karfi tamkar numfashin gajiyayyar sa. Shiru ya ɗan tsaya na a kallah 1 min yana sauraron wannan tari har sai da aka daina yi, kafin daga bisani yasa hannun ya murɗa handle ɗin, a hankali ya tura kofar ya shiga daga ciki, sannan ya mayar da kofar ya rufe. Gabaɗaya dim light ne a ɗakin, amma kana iya ganin irin kayan alatun dake a ciki, dan gold dake jikin kwalliyar headboard na bed ɗin gabaɗaya yana wani irin kyalli ne, dik in da akwai gold a ɗaki da dim light ɗin nan ya ɗan haska shi kyalli yake yi. Kai tsaye wajen bed ɗin ya nufa, a side drawer ya sanya hannu ya ɗauko remote, kunna wutar ɗakin ya yi, lokaci guda haske ya gauraye ko'ina. Wow! My people kun ga ɗakin nan kuwa? An zuba kayan more rayuwa fiye da tinanin mutum, king bed dake cikin ɗakin kawai abin kallo ne, harta carpet dake a cikin ɗakin wani irin laushi ne da shi, kana takawa kafarka na lumewa cikin lausasan gashin jiki, tamkar ɗaki wata yar sarki wacce ake ji da ita kamar Auta kenan, haka ɗakin nan ya haɗu. Wuwwurga eyesball ɗinsa ya shiga yi yana nemanta, dan ya ji tarinta before ya shigo, kuma tabbas yasan ita ce, dan ita kaɗai take rayuwa a wannan waje. Shiru ya natsa cikin tinanin ina ta yi to? Kamar wanda ya yi yunkurin zai cigaba da ta fiya, ya taka step ɗaya gaba, sai kuma ya yi wani irin juyawa bayansa da karfin gaske tare da capke glass dake hannunta wanda ta yi yunkurin caka mashi a wuya. Saboda irin damka da ya yi wa glass ɗin yasa ta fasa mashi hannu sai jini ya fara malala. Sai huci take yi tamkar zata kama da wuta, tana wani irin binsa da mugun kallo da idanunta da suka yi jajir tamkar wuta gwanin ban tsoro, bakinta da hancinta dik jini suke zubarwa, tarin da take yin nan ne ya haifar mata da zubar jini daga baki da hanci, alamar rashin lafiya mai tsanani ne a tattare da ita, ko kaɗan babu kuzari a tattare da ita, dan sai wani tangal-tangal take tamkar zata faɗi kasa, tana wani irin jujjuya idanu, kamar suma take son yi amma tana kokarin kame kanta dan ta cutar da shi ta ɗauki fansa, dik ta galabaita over, da alamar fitar hayyaci a tattare da ita. Muryarta na rawa sosai, tamkar tana a cikin maye, da kyar ta fara faɗin. "Ni ce ajalinka, ba zan taɓa bari ka rayu ba, bakin shaiɗani azzalumi mara imani! Ko na mutu sai ƴaƴana sun ɗauka mun fansa a kanka! Kuma burinka na mulkin zalunci a duniya ba zai taɓa cika ba, dan a kullum gaskiya ita ke nasara, karya rugujewa take, faɗuwarka na gab da zuwa.........". Bata iya kai karshen zazzafar sambatun nata da take yi ba kawai idanunta suka karisa rufewa ruf, lips ɗinta dake ta faman kerma suka tsaya cak, take ta sakar mashi glass ɗin da suka rike ta sulale kasa a wajen. Ko kaɗan bai ji zafin yankar dake hannunsa ba, sai ya yi jifa da glasa ɗin gefe guda, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ɗan rintse idanunsa, can cikin kwakwalwarsa ya fara tina irin azabar da ya gana mata, bai yi tinani zata kawo yanzu ba tare da ta samu matsala a kwakwalwa ba, dan ya yi ta tsoratata da abubuwan tsoro kala daban-daban, ya sanya mata maciji a jiki, ya haɗata kwana da kunamu amma basa cizonta, ya razanata ta hanyar wurgata kasan bene, kafin ta isa kasa ya dakatar da ita da magic, ya turo ruhanan tsafinsa su zo zu hanata barci suna gana mata azaba da razanarwa, dik wannan kyan ɗakin na banza ne, dede da minti ɗaya bai taɓa barinta ta huta ba, amma dik da haka bata taɓa jin ta sare zata bashi spender ba, saboda tsabar taurin zuciya da taurin kai irin nata, ga kafiyar balai ita ma. Har mutuwa ya nuna mata ido da ido, amma ta ce sai dai ta mutu ba dai ta bashi spender ba, dan shi ɗin azzalumi ne, tana ganin irin zaluntar mutanen birnin da yake yi ta window, tsabar zalunci ya taɓa kulleta cikin wani ɗakin duhu shekara guda bata samu ganin haske ba, ga shi ɗakin ba wajen kwanciya, a tsaye take ko ta tsugunna a kan kafafunta, amma babu kwanciya, ALLAH yasa tana da sauran kwana a gaba, da wlh matar nan ta jima da mutuwa!. Tsugunnawa ya yi a gabanta, ya kurawa fuskarta idanu, dik da su Sweetie basa wani kama da ita sosai, amma akwai blood sosai. Kurawa ɗan bakinta irin na Sweetie ido ya yi, dik bakin nata ya bushe sosai, ya kuma ɗan tsastsage. Almost 5 mins yana kare mata kallo kafin ya miƙe tsaye, yasa hannu ya ɗauketa cak, daga in da yake tsaye ya yi jifa da ita kai tsaye sai saman bed ɗinta, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya ya fita, har ya fita ɗin sai kuma ya juyo ya dawo, wajen bed ɗin nata ya nufa, yana zuwa da hannu ɗaya ya saɓata a saman shoulder ɗinsa, ya nufo waje da ita. Kai tsaye ya nufi sauka kasa. Kun tina wannan ɗaki da ya taɓa kai Sweetie zai cire mata ƙwaƙwalwa? To nan ya kai mom twins a yanzu, saman wannan gado da ya kwantar da Sweetie, a nan ya kwantar da ita, sannan ya kira drs daga cikin robot ɗinsa guda biyu ya basu umarnin kula da lafiyarta, dan ya lura tana cikin ciwo sosai over, daga haka ya fito ya koma bedroom ɗinsa. Zaune a tsakiyar bed ɗinsa ya isko Smart yana rike da ɗayar wayarsa, kamar video call yake yi. Zama ya zo ya yi a gefen bed ɗin hannunsa na cigaba da zubar da jini kaɗan-kaɗan, amma Smart bai lura da hakan ba. "Tashi mun a bed zan yi barci". Ya faɗa yana kara ɗaure fuska, kuma bai kalli in da Smart yake kai tsaye ba. Ba tare da Smart ya lura da hannunsa ba ya ce. "Dik sauran filin nan bai isheka ba?". Harara ya dalla mashi ba tare da ya yi magana ba. "Cool dawn in ji heartbeat ɗinka, to ni dik ba ma wannan ba, Please ku gaisa da familyna, my mom and my dad, sai my uncles guda biyu". Ya kai karshen maganar tare da juyo mashi da screen ɗin wayar. Da gangan Smart ya ce iyayensa bai ce iyayensu ba, dan yana so su gaisa, yasan idan ya ce iyayensu to fa Big Bro zai saka gardama wanda daga karshe zai ki gaisawa da su, shiyasa ya yi mashi hakan. Kara ɗaure fuska Big Bro ya yi, kamar zai ce a'a sai kuma ya ɗago, da kyakkyawar fuskar Mommah ya fara cin karo, lokacin guda ya wani irin jan dogon numfashi, slowly ya sauke, ɗan kura mata ido ya yi na ƴan mitocin da ba zasu gaza 3 ba, sai kallansa Smart yake yi. "Barka da rana ɗana". Mommah ta faɗa fuska babu yabo babu fallasa. Shiru bai iya amsa mata ba, saboda gabaɗaya ya ji tongue ɗinsa ta yi mashi mugun nauyi tamkar an ɗaɗɗaure mashi . Ganin hakan yasa Mommah ta miƙawa King wayar, nan ma dai Big Bro bai ce ko uppan ba, kallonsu kawai yake yi, da king ya ga bashi da niyar yin magana sai ya miƙawa uncle Abbas wayar dan a tinaninsa haushinsu Big Bro yake ji shiyasa yaki yi masu magana. Zama suka yi suna tattaunawa a kan Big Bro da Smart ɗin, Smart ya ce su fara gabatar masu da adduoi na musamman saboda ya fahimci matsalolin ɗan uwansa suna dayawa, dan haka suna buƙatar addu'a sosai, to shi ne suke wannan zaman sai ga kiran Smart ya ratso wayar Mommah. Karɓar wayar uncle Abbas ya yi tare da kawota saitin fuskarsa yana faɗin. "Wanene yaya?". Ai wani irin zaro ido da Big Bro ya yi sai da dara-daran idanunsa suka razana uncle Abbas ya saki wayar nan ta faɗi ƙasa. Da karfi Big Bro ya furta. "Dad!!!!". Ya faɗa tare da miƙewa rike da wayar a hannunsa. Da sauri shi ma Smart ya miƙe yana tambayarsa lafiya kuwa? Sai dai ina, babu amsa, sai ma cigaba ya yi da ambatar Dad cikin ɗaga murya, abin da ya yi mugun ɗaurewa dikkansu kai kenan! Uncle Abbas ɗin ne daddynsa? Kun dai san me Daddy yake nufi a wajen Big Bro, kuma kun san mutum ɗaya yake cewa daddy, wato daddynsa na Black World, wanda ya renesa kenan, shi kaɗai yake kira da wannan suna kuma ya aminta da cewa shi ne mahaifinsa. BABBAR MAGANA KENAN, TO FA , HOW COMES UNCLE ABBAS ZAI ZAMA DADDYN BIG BRO NA BLACK WORLD? HOW? TA YAYA WAI?!!. TO NI KAINA CAKWAKIYAR RAWANIN ZALINCI TA FARA SAKANI ZAZZAƁI DA CIWON KAI, UNCLE ABBAS KUMA? TAYAYA NA CE WAI?!!!! HABA MANA! RAWANIN ZALINCI KU BAR KWAKWALENMU SU SARARA PLEASE 🥺 WANNAN SARKAKIYA DA SANYA CIWON KAI YAKE! DAGA WANNAN SAI WANNAN! KAN PRINCESS TEEMA YA KULLE FA MY PEOPLE'S, A KAWO MUN AGAJI 🥺 Ɗaukar wayar king ya sake yi tare da juyo da screen ɗin a kan fuskarsa yana faɗin. "Abbas lafiyarka kuwa naga ka jefar da qayary?". Daidai wannan lokaci network ta yanke, gabaɗaya call ɗin ya katse, hakan yasa Big Bro ya sake kokarin kiransu, amma ina hakan bai yiwu ba, bata shiga, wani irin jifa da wayar ya yi ta daki views na room ɗin ta faɗi ƙasa, take ta yi raga-raga. Cikin wani irin zafa ya damko wuyar rigar Smart da karfi, a fusace with harsh voice ya ce. "Dama kasan daddyna yana a raye? Dama kasan da cewa yana nan shi ne ka ɓoye mun? Me haɗinku da mahaifina? Ka kira shi yanzu ko kuma in kasheka!!". BABBAR MAGANA!! Zazzaro mashi ido Smart ya yi. "Waye daddyn naka daga cikinsu?". Wani irin zazzafar mari ya sakarwa Smart a kumatu har sai da Smart ya ga wasu taurari sun gilma ta cikin idanunsa. "Kafi kowa sanin waye ne, meyasa zaku ɓoye mahaifina ku musanya mun shi da wancan da kuke ikirarin shi ne babana? Dama nasan cutar dani kuke son yi shiyasa kuka yi kutse a cikin rayuwata, dan haka ko ka kira mahaifina yanzu ko in kasheka!!". Yana magana yana wani irin huci mai firgitarwa, tamkar zai kama da wuta. Smart ya gama hasala ya zo har wuya, saboda bai san me Big Bro yake so da shi ba kuma, dik wani abin da yakamata ya yi mashi ya yi mashi, to bai san me kuma yake so ba yanzu, ga shi abin takaicin ma bai san waye Big Bro ɗin ya gani ba da yake ikirarin shi ne mahaifin nasa ba, sannan ga shi ya ragargaza wayar bare ya sake kiransu ya ji da waye Big Bro ya yi magana last ko fuskar waye ya gani last. Wani irin shaƙa da Big Bro ya yi masa ne yasa ya ji tamkar ana zare ransa, hakan ba karamun fusata shi ta yi ba, da karfi yasa hannu bibbiyu ya hanƙaɗe Big Bro, sai dai ko motsawa Black Tiger bai yi ba, ba ƙaramin fusata zuƙatansu dikkansu biyu ya yi ba, sun yi mugun harzuƙa, cikin fushi shi ma Smart ya damki wuyan Big Bro, cikin tsananin zafa ya ce. "Who the hell you are da zaka rinƙa mun abin da ka ga dama ina shanyewa?! Kamar yadda kake ji da kanka kowa ma haka yake ji, do you think that ina tsoronka ne yasa nike binka a yadda kake so? Ko ɗaya, just kaunarka nike yi ba tsoro ba, shiyasa nike lallaɓaka, but ba zan cigaba da jurar abin da kake mun ba, you say that zaka kasheni ba, okey do it now!! Kill now if not ni zan yi abin da kake ikirarin in kasheka kowa ya huta, ka hana mun iyayena kwanciyar hankali, ka jefa mun su cikin zulumi da damuwa, dik kai kaɗai, who are you?!!". Cikin tsananin fushi Smart ya yi maganar! Da alama yau ran maza ta kai kololuwar ɓaci!. Shiru Big Bro bai yi magana ba, sai wani irin huci da yake yi, sai da Smart ya kai aya, sannan ne ya dakarkare ya ɗaga Smart sama ya yi jefa da shi sama bed ya mirgina ya faɗi kasa. "Where's my father? Dik surutun da kake yi ba shi ne damuwata ba, ka kira waɗan nan iyayen naka su dawo mun da daddyna if not sai na tashi gabaɗaya masarautarku, kuma idan ko kwarzane ya taɓa jikin daddyna sai na karar da dikkan zuri'arka, ba zan bar ko guda daga zuri'arku ya cigaba da shakar numfashi ba!!". Ya yi maganar tare da nufo Smart gadan-gadan. A wannan karon da yake Smart ma ya kai kololuwa wajen ɓacin rai, sai ya miƙe cikin fushi ya nufo Big Bro. Faɗa suka fara gwabzawa tamkar wasu mayunwatan zakuna, babu imani babu tausayi suke jibgar junansu tamkar ba jini guda ba ne su. Big Bro yana tambayar ina mahaifinsa, Smart ya fitar mashi da mahaifinsa, shi kuma Smart yana faɗin waye mahaifin nasa a cikin uncle's ɗin nasa?. Dik kansu dai babu wanda ya saurarawa ɗan uwa, dik suka jiwa kansu muggan raunika, sannan dik suka yi watsa-watsa da ɗakin, dik wasu glass sai da suka ruguje shi, gabaɗaya sun yage kayan jikinsu, sai wani huci suke yi suna wani irin buga kirazansu yadda kuka san ba mutane ba. Harta bed na Big Bro basu bari ba, suka watsa komai, yadda kuka san yakin badar aka yi a cikin wannan ɗakin, harta curtains sai da suka ɓaɓɓale suka zubar, yau Smart ya yi alkawarin idan Big Bro bai bada kai ba shi ma ba zai bayar ba, sai dai su kashe kansu, saboda ya zo har wuya, ga shi babu mai rabasu, Pretty tana barci, su Ronnie basa nan, abin dai ya munana matuƙa, dan Smart ya samu rauni a wuya na glasa da Big Bro ya caka mashi a gefen wuya, ta fasa wajen sai jini ke malala, shi kuma Big Bro a gefen ciki Smart ɗin ya caka mashi glass ɗin, shi ma jininsa nata malala, abin dai ba kyan gani sam-sam. Wlh yadda kukan duwatsu ne jikinsu ba tsoka da jini ba, haka suke jibgar juna. WA KUKE TINANIN ZAI IYA RABA WANNAN FAƊAR? UHM NI DAI NA JUYA GABAS DA YAMMA KUDU DA AREWA BANGAN SA BA! AMMA BARI IN JE CROWN OF JUSTICE IN DAWO KILA MU YI DACEN SAMUN MAI RABA WANNAN BALAIN FAƊAR!!. CROWN OF JUSTICE.🔥🔥 A firgice ta farka daga barcin nata game da zunduma wani irin ihu mai sauti wanda ya sanya shi gaggawar juyowa, dama yana tsaye ne a gaban mirror yana gyara kyakkyawan hairnsa irin na Sweetie, ya fito daga wanka ɗaure da towel white a waist ɗinsa. Cikin zafa ya nufeta, hayewa saman bed ɗin ya yi tare da rikota yana faɗin. "Hoonaira lafiya kuwa?". Bata yi magana ba sai kuka da take yi tana wani jan dogon numfashi da karfi-karfi. Ya fahimci mummunar mafarki ta yi, hakan yasa ya rungumeta sosai a jikinsa, a natse ya fara karanto addu'oin tsari daga shaiɗanu yana tofa mata. Tin tana ihu har yazamana ta koma kuka a hankali-hankali, daga karshe ma sai ta yi tsit alamar ta samu natsuwa. Ajiyar zuciya ya sauke, can kasan makoahinsa ya ce. "Hoonaira are you okey now?". Tana daga kwance a kirjinsa ta gyaɗa kai alamar e, sai kuma ta ce. "Meyasa ka tafi ka barni?". Cikin muryar kuka ta yi maganar. "Am so sorry, amma ban je ko'ina na barki ba, ina a tare dake". Cikin kuka ta ce. "Ka tafi mana ka barni, ba ga shi wannan Udey ɗin ya zo zai kasheni ba". Wani irin zaro idanu waje ya yi, da sauri ya maimata sunan. "Udey! Kuma ya zo zai kasheki? For what reason?". Mafarki ta yi a kan laɓen da ta yi ranar tana jin hiran Udey da Zarina in da suke cewa basu bane iyayen Hoorain, kun tuna wannan rana? To shi ne ta yi mafarkin wai asirinta ya tonu Udey ya ganota shi ne ya biyota zai kasheta. JAMA'A KU CE ALLAHU AKBAR, WATO IDAN KA YARDA DA ALLAH KA HUTA, YANZU GA SHI CIKIN RUWAN SANYI ALLAH YA SANYA TA KAMA SUNAN UDEY A BAKINTA, WANDA HAKAN ZAI SA SHI KANSA HOORAIN YA FARA ZARGIN UDEY KO DA BAI BAYYANA A ZAHIRI BA, KUNGA DAGA NAN ZAI FARA SAKA MASU IDO. Zabura ta yi ta buɗe idanunta da suke jajir saboda barci da tsoro. "Mafarki na yi wai ka tafi ka barni shi ne na bika da gudu, ina sauka staircase na haɗu da Udey sai ya kamani wai zai kasheni tin da na ji sirrinsu, kuma ni ban ji komai ba". Tin da ta fara magana zuciyarsa ya shiga zargi da tinani, yasan Zunaira bata karya, bugu da kari tana da hankali sosai, me zaisa ta yi mafarkin Udey, dik da yasan mafarki ba gaskiya bace, kuma tana zuwa a kowacce siga, and kawo sittin cikin ɗari ba gaskiya bace, amma akwai mutanen da ALLAH ya zaɓa bayan manzanni waɗan da yake gwada masu ayoyi a cikin mafarki. Tabbas akwai wata a ƙasa. Amma sai ya basar da cewa. "Sharrin mafarki ne kawai, jeki yi wanka ki zo ki shirya mu je mu yi breakfast". Ya yi niyar yi mata dabara ta faɗa mashi wani sirri nasu ta ji, amma sai ya ce bari ya kyaleta zuwa dare idan suna cikin yanayin farinciki zai mata dabara, dan a ransa yasan wlh ba haka kawai ta yi mafarki Udey ba, dole ta shiga gonarsu ne, akwai abin da ta sani, lokacin guda ALLAH ya jefo mashi tinanin matsa mashi da take yi a kan ya buɗe tsohuwar fada, shiru ya ɗan yi, yanzu ya fahimci Zunaira ta san wani abin, kawai ɓoye mashi take yi, amma soon zai gwada mata fifikon shekaru!. "Ni dai my hero ba zan iya zuwa toilet ni kaɗai ba, ina jin tsoro, sai dai muje a tare". Cike da tsantsar sonta a ransa yasa hannu ya fara shafa kanta. "Kin yarda in rakaki ɗin?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e, dik a tsorace take, tana wani irin haɗa uban gumi tamkar wadda ta yi tsere da dawakai a cikin tsakiyar rana mai zafi. "Amma fa idan na rakaki fitowa zan yi ko?". Cikin zolaya ya yi maganar. Da sauri ta girgiza mashi kai. "A'a zaka tsaya sai na gama wanka". Ɗan leƙo fuskarta ya yi. "Da gaske ba za'a ji kunyata ba?". Kai ta gyaɗa mashi kafin ta ce. "Da wando a jikina zan yi wankan ai". A shgwaɓe ta yi maganar. "An taɓa yin wanka da wando ne?". Kai ta jinjina mashi kafin ta ce e. "To shikenan tashi muje". Make mashi kafaɗa ta yi. "Ni dai ka ɗaukeni da kanka ka kaini". Cikin zolaya ya ce. "Bani da karfi fa". Duka ta kai mashi a damatsan hannunsa. "Wannan fa menene?". Ɗan rankwafowa kanta ya yi, a kunne ya yi mata raɗan da ya sanyata zabura ta miƙe zaune tana fuskantarsa. Da sauri ya yi kasa da kansa yana faɗin. "Iya wannan karfin nike da shi ban da na ɗaukarki". "My hero an lalata mun kai, yanzu ka dawo baka da kunya sosai". Ta faɗa tana turo baki. Bai yi magana ba kawai ya yunkura ya sauko kasa, sannan yasa hannu ya ɗauketa cak suka nufi toilet. A tsakiyar toilet ɗin ya sauketa tare da nufar Jacuzzi, ruwa mai ɗumi sosai ya haɗa mata, ya zuba dik wasu perfume da kayan wanka da suke amfani da shi, sannan ya dawo in da take a tsaye. Ta tsaresa da ido, dik wani motsinsa a kan idonta, kyakkyawan surar jikinsa kawai take ta faman kallo tana santin kayanta, ga shi daga shi sai towel. Yana zuwa ya sunkuceta sai gab da jacuzzin ya direta, bai yi mata magana ba ya hau ɓalle botiran kayan jikinta. Binsa da kallo kawai take yi, sai da ya cire botiran gabaɗaya, can kasan makoshinsa, muryarsa har wani sarkafewa yake yi wajen cewa. "To cire rigar ki shiga ciki bari in jiraki ta bakin kofa". A takaice ta ce. "Ban iya ba, kuma hannun da ya cire botir ɗin shi zai cire rigar". Ɗan ɗago kai ya yi ya saci kallonta, ganin ta tsaresa da ido ne yasa ya sanya hannunsa slowly ya sauke rigar daga ta saman shoulders ɗinta izuwa kasa. Bai san time da ya ɗan lumshe ido ba ganin tula-tulanta suna yi mashi welcome. Tana ganin dik wani motsin da kyawar idanunsa yake yi a kan tula-tulanta. Da kyar ya iya zame rigar tata gabaɗaya saboda yadda ya tsinci kansa a cikin yanayi na daban. Da kyar ya iya cewa. "To sai a shiga ciki ayi wankan ko?". A karo na biyu ta sake make mashi shoulder, ɗago ido ya yi yana kallonta yana jiran karin bayani. "Saura wandan baka cire mun ba". Ta faɗa kamar zata yi kuka. "Ke da kika ce da wando zaki yi wanka". Ya faɗa yana daurewa ya zare kallonsa daga cikin nata. "Da pant nike nufi ba dogon wando ba". Ta bashi amsa tana guntse dariya, yau so take ta kuresa. Satar kallonta ya yi kafin ya ce. "Please my Hoonaira, ba zan iya jurewa ba, ki shiga haka". Da kyar ya iya idasa maganar!. Turo baki ta yi tare da wucewa zata shiga cikin ruwa. A gaggauce ya damko waist ɗinta ta baya, da karfi ta juyo hakan yasa ta faɗa sama kirjinsa. Kusan a tare suka sauke nannauyar ajiyar zuciya. "Meyasa za'ayi fushi da ni?". Ya faɗa yana ɗan ciza laɓɓa saboda wani irin azababben shock da ya ji tin daka tsakiyar kansa har kasan kafafunsa saboda haɗewar tula-tulanta da massive chest ɗinsa. "Ni ba fushi na yi ba, kawai na barka ne tin da ba zaka cire mun ba". A shagwaɓe sosai ta faɗa, hakan ba karamun tada mashi da hankali ya kara yi ba. "Sorry......." Shi kaɗai ya iya faɗa yana ɗan kwanto da kansa a saman shoulder ɗinta, slowly ya zura hannunsa ya damki igiyar wandan, warwareta a hankali ya yi tare da sukurkurtata. Da yake kayan is very silky sai wandan ya yi kasa, ɗage kafafunta ta yi ta cire wandan gabaɗaya. Kara matseta a jikinsa ya yi, slowly ya ɗaura hannunsa a saman mazaunanta, ya kara kwantar da kasan a gefen wuyanta yana sakin wani irin numfashi mai nauyi. Ashe dai dik tsokanar tata na karya ne, sai ga shi ta fara tsorata da yanayin da yake a ciki, kirjinta ta ji yana bugawa da ɗan karfi-karfi, amma sai ta daure saboda tana son kayanta. Bata ji lokacin da ya sanya hannunsa a jikin pant ɗinta ba, sai ji ta yi ya zame pant ɗin ya yi kasa, haba kara tsorata ta yi, muryarta na rawa ta ce. "My hero bari in yi wankan". Yadda ta yi maganar tsab zaka fahimci ta tsorata, yar kaniya ta ga ya yi mata tsirara ai dole zuciyarta ta amsa da karfi. Wani irin dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, wani iri ta ji a jikinta jin ɗumin nunfashinsa dake sauka a wuyanta, a natse ya damki towel dake waist ɗinsa ya warwareta, ya zareta tare da jifa da ita gefe. Slowly ya ɗan rage tsawonsa, bata ankara ba sai ji ta yi ya ɗaketa cak, gabaɗaya ya shige cikin ruwan da ita tsulundum, ya manneta da jikinsa sosai, gabaɗaya ta birkice mashi, tana wani irin sakin numfashin tsoro. Matsar da bakinsa dab da kunnanta ya yi. "Kada ki ji tsoro, wanka kawai zan yi maki". Da kyar ya iya faɗin hakan, saboda ya ji jikinta na kerma ne yasa ya faɗa mata hakan, dan ta ɗan samu natsuwa. Aikuwa ya samu, dan tasan baya karya, dan haka ta saki jiki har da sauke ajiyar zuciya. Sai dai ta yi mamakin ganin yadda yau bai ce a bashi izinin taɓa tula-tula ba, Unexpected ta ji saukar hannunsa a kansu, a hankali ya shiga shafesu yana ɗan matsatsu. Saboda wani irin shock da take ji bata san time ɗin da ta sake shigewa jikinsa da kyau ba, shi kam hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mashi ba, sai ya ji daɗin kara matseta sosai. Wasa da ita ya fara yi tin yana iya sanin me yake taɓawa a jikinta har ya fara fita hayyacinsa, kukan da ta saka mashi ne ya sanya shi dawowa cikin hayyacinsa, da kyar ya iya bata haluri tare da rabata da jikinsa, a ransa ya ce yana tausayin ranar da zai iya share kukanta ya iya daurewa dan kawar da kishinsa, saboda ya zo har wuya, but shaaa zai san me zai yi a kai. Wanka ya yi mata, sai kuma ya gagara iya fitowa da ita, saboda babu towel a jikinsa ba zai so ta gansa a haka ba kada ta tsorata da shi. Shiru ya yi for almost 5 mins, sannan ya yanke shawarar fitowa da ita a jikinsa, hakan zai sanya ba zata iya ganinsa ba. Na'am ya yi da wannan shawara, sai ya miƙe rungume da ita a jikinsa suka fito, bai saketa ba har sai da ya isa wajen towels dake jere a hanger, guda biyu ya ciro, ya ɗaura ɗaya a jikinsa kafin ya ɗaura mata ɗaya daga kirjinta. Sannan ya duƙa ya ɗauketa cak suka komo ɗaki. Kai tsaye saman bed ya direta, yana kokarin hayewa suka ji an turo kofar ɗakin an shigo. A tare suka kai kallonsu waje. Ɗaya daga cikin kuyangun dake yi mata hidima ne, ɗaure fuska sosai ta yi, a kufule ta ce. "Ke baki da hankali ne zaki shigowa mutane ɗaki kai tsaye haka? Waye ma ya ce ki shigo?". AUTA SARKIN KISHI!. Zubewa kasa a kan gwiwowinta yarinyar ta yi, murya a sanyaye ta ce. "Kiyi hakuri ranki ya daɗe, na zo gyaran ɗakin ne". A tsawace Auta ta ce. "Waye ya ce ki zo ki gyara ɗakin?". Ta yi maganar tare da juyo da kallonta a kansa, ya tsare ɗan bakinta da kallo yana mamakin yadda take masifa, shi bai taɓa sanin ta iya faɗa har haka ba. "Dama yallaboi ne ya ce in zo in gyara". Yarinyar ta faɗa murya na rawa. Zaro ido a kansa Auta ta yi. "Kai ka ce ta zo ta gyara mun ɗaki?". Babu wasa ko fara'a a kan fuskarta ta yi maganar. Kai ya jinjina mata. "Ni ne, dama fita zan yi, ke kuma kina barci, sai na ce ta zo ta gyara ɗakin ta kuma zauna dake zan je wajen uncle in dawo......". Bai kai karshen maganar ba saboda wata uwar tsawa da ta dakawa yarinyar. "Futa mun a ɗaki kuma kada in kara ganinki a arear nan!!". Ta faɗa tana huci. Shi da ya san zafin kishin kayansa sai ya ce. "A lafa haka nan, yi hakuri". Tana huci ta ce. "ALLAH ba zan hakura ba, ina ruwanka da ita da zaka je ta ga fuskarka har ka yi mata magana wai da sunan ka kirata ta zo ta gyara mun ɗaki? Ni na ce maka ina so ne?!". Shiru ya yi bai amsa mata ba, ita kuwa yarinyar a razane ta zabura ta yi waje da gudu. Kuka mai tsuma zuciya Auta ta fashe da shi, faɗi take yi. "Kuma kai ka je ka yi magana da ita har ta ji muryarka? Ka kulata? Ka mata magana cikin wannan natsuwa taka mai ɗaukar hankali?". "Ni nace ka kirata ne? Ko ni ban iya aiki bane?". Shi dai shiru ya zuba mata ido yana kallonta for almost 5 mins, sannan ya ɗan yi gyaran murya zai fara magana kenan ta zabura ta sauko kasan bed ɗin, kafin ya farga ta nufi toilet. Ɗan dafe kansa ya yi, da sauri ya bi bayanta, sai dai yana zuwa ta datse kofar da key, knocking ya shiga yi yana ambatar sunanta, amma ina taki buɗewa. Ya shari 20 mins a tsaye yana kiranta yana buga kofar, amma taki kulasa, daga karshe ya bar wajen ya nufi closet ɗinsa. Kaya ya fitar ya shirya a ciki, sannan ya fito ya sake dawowa bakin door ɗin, knocking ya cigaba da yi, amma taki kulasa, kuma yana jin kukanta, zuciyar modarawar ne ta motsa yau. A ransa ya ce in baka auri mace mai rigima da kishi ba ai baka more aure ba, bari in duba su Ansar da uncle in dawo in yi shirin yin frog jump, dan nasan ba za'a yafe mun ba yau sai na karɓi hukunci. Da wannan tinani ya fita ya nufi wajensu Ansar dan ya ga ya suka kwana. NIMA NA HAƊA KAYANA SAI IN MAI DIKKA YA KAIMU. Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 -------------------------------------------🔥♥️ ZABUWAR DUNIYA STEP ONE!.🔥🔥🔥 Gabaɗaya sun jigata, amma babu wanda yake da niyar risinar da kansa ya baiwa ɗan uwansa hakuri, yadda kuka san babu zuƙata a kirazansu, shi Smart mai hakurin ma yau babu alamar za ɗaga kafa, dan kada ku manta kamar yadda suke identical haka komai nasu yake iri ɗaya sai ɗan banbanci da ba'a rasa ba, wannan banbanci kuma ita ce hakurin Smart, ya fi Big Bro hakuri, da alama Smart hakurin Mommah ya ɗauko, shi kuma Big Bro rashin hakurin King, Dan dai King kam mun san bashi da hakuri kuma baya yafe gaba! Kun tina King Al-Mustapha da ya tako har zuwa Kingdom ɗinsu ya yi mubaya'a ya bada hakuri? Amma me King ya ce? Ba zai hakura ba, baya yafewa abokin gaba kuma baya manta gaba! Ko ba haka aka yi ba? So shi King bashi da hakuri ga saurin fusata, in ya fusata kuma baya saukowa da wuri, kusan Big Bro ɗin dai, sai dai aka ce ɗan nagada ya fi ɗan na koya, shi ne kawai yasa Big Bro ya dame King a iya rashin mutumci. -----------------------🔥 Wani irin shaka dikkansu biyu suka yi wa junansu, Big Bro ya shake Smart shi ma kuma ya shakesa, babu alamun zasu iya sake juna. Unexpected daga bayansu Ronnie ya kwararawa Big Bro wani ruwa daga cikin bokiti da ya shigo da shi a hannunsa. Gabaɗaya jikin Ronnie kerma yake yi, idanunsa sun yi jajir, ga hawaye masu ɗumi na tausayin yayan nasa da ya gama wanke mashi fuska! ALLAH sarki!. Ai wani irin kururuwan ihun da Big Bro ya zunduma sai da yasa gabaɗayansu suka yi gaggawar sanya hannu suka toshe kunnuwansu. A take Big Bro ya rikiɗe ya koma siffar Uncle Abbas sak, wanda hakan ba karamun girgiza Smart ya yi ba, sai a yanzu ya gane cewa waye Big Bro ya gani yake ikirarin shi ne mahaifinsa? BABBAR MAGANA!!. Jikin Big Bro take ta fara wani irin girgiza, kan kace me wani irin abu ya fara fita daga kowa sassasa na jikinsa, tamkar hayakin wuta tamkar kuma turɓayar ƙura, haka jikinsa ya rinƙa fitar da wannan hayaki yana wani irin huci, idanunsa sun kaɗa jajir, wani irin jini ya taru a kasan idonsa, kai ka ce wuta aka kwantar mashi a wajen. Gabaɗaya babu wanda bai razana ba, harta Sweetie dake tsaye ta bakin kofa rike da hannun Pretty dik sun razana suka wani irin kankame juna, ji suke tamkar su juya da gudu su bar ɗakin, amma suka daure. A kan Sweetie Big Bro ya tsayar da jajayen idanunsa masu firgitarwa, cikin wata iriyar murya mara daɗin ji ya ce. "Tin yana karami a babin kaddararsa na san da akwaiki! Kece his destiny! Nasan labarinki tin ranar da Omranish ya yi cikinki, na yi tinanin zan iya canza kaddararsa in hanaki shigowa cikin rayuwarsa, shiyasa ban kasheki tin kina ciki ba, ashe na yi ganganci, na yi gangancin barinki ki rayu, amma dik da haka ban sare ba, na faɗa mashi ke zaki kawo karshensa domin in kin shigo rayuwarsa ya kasheki da hannunsa, sai dai kuma kash, kin ɗaure shi kin kuma saka hijabi a tsakanina da shi ta yadda ban san me yake faruwa ba, kafin na farga na san abin dake faruwa a tsakaninki da shi kin rigada kin yi nisa a cikin rayuwarsa, kin rabani da ɗana, kina tinanin zan barki kenan? Kin yi babban kuskure da dole ki karɓi hukuncin mutuwa mafi muni!!". KARIN BAYANI, YA SO HANA SWEETIE SHIGOWA RAYUWAT BIG BRO, AMMA YA GAGARA YIN HAKAN, SABODA ALLAH YA KADDARA ITA ZATA SHIGO RAYUWARSA TA CECESA DAGA HANNUNSU, SANNAN DA YAKE IKIRARIN ITA CE KADDARAR BIG BRO ZATA CUTAR DA SHI, WANNAN CUTARWAR BA KOMAI BANE FACE CETONSA DA ZATA YI, RABA SHI DA SU DA ZATA YI SHI NE SUKE IKIRARIN CUTARWA NE WANDA KUMA MU MUN SAN TAIMAKO TA YI MASHI. "Ba zan taɓa bari ki cigaba da rayuwa ba, zan dawo gareki, sai mun ɗauki fansa ki shirya!!". Yana kai karshen maganar ya yanke jiki ya faɗi kasa, yana faɗuwa ya koma ainahin siffarsa na gaske, take wasu irin bakaken kamar hucin wuta ya rinƙa fita daga jikinsa, a daidai wannan lokaci dik wani abin da ya danganci duniyar shaiɗanu ya fita daga jikinsa, kuma ya shafe daga ƙwaƙwalwarsa, dan ya yi mai kankat, ya rabu dasu gabaɗaya, harta fuskar baban nasa ya shafe daga kwakwalwarsa, sai dai magic ɗinsa tana nan, dan ita ba a duniyar shaiɗanu ya koyeta ba, a Black World ya koya, amma dik wani abin da ya danganci shaggun can ya fita daga jikinsa, yanzu ya zama sabon mutum cikakke mai cikar kamala, fuskar Uncle Abbas ya goge daga kwakwalwarsa, sai dai ALLAH da hikima da basirarsa sai da ya nuna wa su Smart uncle Abbas nada sa hannu kafin hakan ta goge daga kwakwalwarsa, yanzu Smart ya ga fuskar uncle Abbas, sannan ya ji Big Bro ya ce shi ne daddynsa, kunga dole zai tuhumesa ko? Akwai dai case. Da gudu suka yi kansa, ALLAH sarki har shi Smart ɗin da gudu ya yi kansa suna ambatar sunansa, sai dai ina shiru bai motsa ba. A KARSHEN PAGE ƊIN NAN IDAN BAN MANTA BA ZAN FAƊA MAKU ABIN DA SUKA ZUBA MASHI A BOKITI YA RABU DA SHAIƊANUN NAN, RANAR MA AKWAI ADDU'AR DA NIKE SON RUBUTA MAKU A WANI PAGE NA MANCE, TO ZAN RUBUTA MAKU A KARSHE DA YADDA SUKA HAƊA ABIN DA SUKA ZUBA MASA ƊIN, DAN DIK GIRMA DA SHAIƊANCIN SHAIƊANI KO WANI SIHIRI KO ALJANI DA AKA YI MAKA SAI IN BAKA YI WANNAN HAƊI BA, TAKE ZAKA GA AIKI DA CIKAWA, DAN KO MAI BAKIN SHAIƊANCIN ALJANI SAI YA SHAFA MAKA LAFIYA, A MILIYAN ZAI YI WAJE, WAƊAN DA SUKE ZARGIN AN YI MASU SIHIRI TO KUMA GA DAMA TA SAMU DAN WARWAREWAR MATSALARKU DA KANKU, MATA MASU ZARGIN ALJANU A JIKIN ƳAƳANSU DIK A KARSHEN PAGE ƊIN NAN ZAKU SAMU MAGANIN BI IZININLAH. "Yah Omerish kasa a gyara ɗakin nan, dan in Big Bro ya tashi zai taso ne a sabon mutum, kuma ba zai san su waye iyayensa ba sai wanda mu muka gabatar mashi, kada ka bari ya taso ya ga ɗakin nan watsa-watsa haka, shakku da tinani zata fara shiga zuciyarsa wanda kuma hakan ba zai yi mana daɗi ba!". Cewar Sweetie yarinya mai hankalin manya!. Jinjina kai Smart ya yi, sannan ya miƙe tsaye, ya sanya hannunsa ya zare kwalbar dake wuyansa ya yi jifa da ita, ALLAH yasa bata shigesa har can ciki sosai ba, waje ya nufa yana dafe in da ya ji ciwon. Su kuma suka cigaba da tofawa Big Bro ayoyin Alkur'ani da addu'oi sunai mashi fatan tashi cikin koshin lafiya!. After some minutes, Smart ya dawo tare da wasu manya-manyan robot masu ji da karfi, umarni ya basu a kan su gyare ɗakin nan cikin ƙanƙanin lokaci, cikin girmamawa suka karɓi umarni, ba tare da ɓata lokaci ba suka hau aiki. Shi kuma Smart ya daddage ya ɗauki Big Bro ya nufi balcony da shi. A saman sofa ya kwantar da shi, sannan ya ce Ronnie ya zo ya yi mashi treatment na wuyansa da kuma gefen cikin Big Bro. Da sauri Ronnie ya kwaso kayan aiki ya zo ya hau gyara masu. Pretty and Sweetie kuma suka koma saman sofa suka zauna suna cigaba da addu'a, har lokacin Ronnie bai daina ruwan hawaye ba. Sai misalin ƙarfe 4 na yamma robot suka kammala aikinsu tsab, sun shigo da sabbin kaya, sun gyara ko'ina tsab, ba zaka taɓa zatan cewa an yi faɗa a cikin ɗakin nan ba, shi kuma Ronnie ya gyarawa ƴan uwan guda biyu raunikan da suka ji, sai kuka Pretty take yi tana cewa Smart sannu, ya bata tausayi ne, and Pretty tana da wani abu ɗaya, tana bala'in tsoron jini, har juwa ne yake ɗebanta idan ta ga jini, shiyasa take kuka da ta gani a jikin Smart. Sai rarrashinta yake yi, a ransa ya ce ALLAH yana sonsa da rahama shiyasa jiya ya dasa mashi tausayinta a ransa over, yasa ya kyaleta bai yi abin da ya yi niyya ba, da abin ya kwaɓe masu over yau, da anyi ɓatacciya over. Bayan sun kammala gyaran ɗakin ya yi tsab, sun zuba tirarruka masu daɗin kamshi ne suka sanarwa da Smart sun kammala aikin nasu, a lokacin ya yi wanka ya yi sallar la'asar, su Sweetie ma dik sun yi sallar la'asar ɗin. Karfi ya sanya ya cicciɓi Big Bro sama ya wuce da shi cikin room, a saman bed ya kwantar da shi yana bin ɗakin da kallo, ya jinjinawa kokari irin na robot ɗin nan, da sauri su Sweetie suka biyosu ciki, tana sanye da doguwar riga wanda ya kara fito mata da coca cola shape ɗinta sosai, ta yi bala'in kyau, sai dai kana ganinta zaka san hankalinta a tsananin tashe yake, ta shiga damuwa over. A gefen bed ɗin ta zauna, daidai saitin Lion chest ɗinsa tana cigaba da karanto addu'oi tana tofa mashi. Smart kuma yana sanye da pjs na Big Bro, ya yi kyau over, ya riko hannun Pretty dake ta faman damunsa zata ci abinci, ya rikota suka nufi waje. Shi ma Ronnie saman bed ɗin ya haye suka cigaba da yi wa Big Bro tofin addu'a har around 5:30, sannan ne suka ɗan dakata da yin addu'ar suka zubawa yayan nasu ido suna ta kallonsa. -----------------------🔥 A hankali ya fara motsa idanunsa da suka yi mashi tsananin nauyin gaske, cikin wata iriyar natsuwa ya waro idanun nasa waje, kai tsaye sai a kan fuskar heartbeat ɗinsa in ji Smart, ta tsaresa da ido tana kallonsa. Kura mata idanu ya yi tamkar wanda ya ga bakuwar halitta daga wata duniya. A natse ta ɗan motsa bakinta wajen cewa. "Big Bro barka da tashi, akwai wani wajen da yake yi maka ciwo ne?". Shiru bai amsa mata ba, tamkar babu shi ma a wajen, kallonta kawai yake yi. Da sauri Ronnie ya matsa dab da shi, cike da kaunarsa sosai ya ce. "Big Bro in kawo maka tea ne?". Lokaci guda ya gyaɗawa Ronni kai alamar e, dan wani irin hatsabibin yunwa yake ji. Da sauro Ronnie ya sauka ya nufi waje dan ya kawo tea ɗin. Kurawa juna ido shi da Sweetie suka yi har sai da ta gaji ta zare idanunta, dan shi dai ya ki dainawa kuma babu alamar zai yi magana. A tare da Smart Ronnie ya dawo cikin ɗakin, hannunsa a ɗauke da hot green tea, Big Bro baya shan tea da milk, sai dai black tea ko green tea kawai, ko coffee bai wani so sai in yana cikin tsananin farinciki yake ɗan sha kaɗan. A ɗayan gefensa Smart ya zauna, a tausashe sosai ya ce. "Sannu da farkawa". Dawo da kallonsa a kan Smart ya yi, da kyar ya iya motsa ɗan bakinsa, in a cool way sosai ya ce. "Da kuke ta mun sannu na ce maku na gaji ne? Ko akwai abin da ya faru ne?". Kada ku manta dik abin da ya shafi duniyar shaiɗanu ya goge a cikin kwakwalwarsa, hakan na nufin bai san faɗar da suka yi da Smart a yanzu ba, ya goge a kwakwalwarsa, shi ne yasa yake mamakin sannun da suke ta faman ce mashi. Tina abin da Sweetie ta ce na zai mance komai ne yasa Smart ya yi gaggawar cewa. "Babu abin da ya faru, ka jima kana barci ne tin safe shiyasa muke yi maka sannu". "Omerish karya bata yi maka kyau, kuma baka iya bama". Ya faɗa tare da yunkurawa zai miƙe. Kallon juna Smart da Sweetie suka yi, karo na farko Big Bro ya kira sunan Smart, wato dama ya san sunansa kenan! Kai wannan guy ɗin yana abin da yake so, Big Bro duniya. Gagara miƙewa ya yi saboda ciwon dake gegen cikinsa da kuma zafi da dikkan gaɓɓansa suke yi mashi, sun ki bashi haɗin kan ya miƙe, hakan yasa ya koma ya kwanta tare da rarraba eyesball ɗinsa a kansu alamar yana jiran karin bayanin me ya hana shi tashi ya riƙe mashi gaɓɓan jiki?. Kallon juna a karo na biyu Ronnie, Sweetie and Smart suka yi, sun rasa me zasu ce da Big Bro, shi dai bai yi masu magana ba, ya hau binsu da kallo kawai. "Am..... Bari Yah Omerish ya taimaka maka ka tashi sai in baka tea ɗin, mun hutassheka". Cewar Sweetie, ta yi maganar ne cikin wata iriyar sigar da ba zai iya ce mata a'a ba. Da sauri Smart ya gyara ya taimaka mashi ya miƙe zaune, sai ya sanya mashi pillow a bayansa, idanunsa gabaɗaya a kan ciwon dake wuyar Smart da ta sha bandeji, yana son tambayar me ya ji mashi ciwo, ya ji kuma bakinsa ta yi nauyi, ya gagara, sai ya ɗan shanye, amma har cikin ransa ya ji zafin wannan ciwo da ya gani, sai yake ji tamkar a jikinsa ciwon take. NI KAM NA CE KAI MA NAKA CIWON NA NAN AI, BARI KA WARE ZAKA GANSA NE!. Miƙawa Sweetie cup na tea ɗin Ronnie ya yi, Smart ya sauko kasa yana cewa Ronnie ya zo su je yau da kansa zai shiryawa ɗan uwansa abin da zai ci, ya zo su je kitchen ya koya mashi yadda ake girki. Smart bai san Ronnie ma bai iya ba, sai dai su je robot ya basu recipes. Waje suka nufa, Big Bro ya bisu da ido har suka fice, slowly ya dawo da kallonsa a kanta, while ita ma shi take kallo. "Meyake faruwa Omaish?". Ya faɗa in a cool way sosai. "Meyasamu Omerish a wuya? And nima meyafaru dani a jiki na ji yana mun zafi?". Ya sake jefa mata tambaya. Kawo mashi cup na tea saitin ɗan bakinsa ta yi, cikin salo mai jan hankali ta ce. "Bama nan, ka manta mun tafi shopping ne, yanzu dawowarmu, so bamu san me ya faru ba". Ta faɗa tana kara tura mashi cup ɗin. Kaɗan ya ɗan yi sipping tare da cire bakinsa, bai sake cewa komai ba ya tsareta da kallo kawai. "Kallon fa?". Ta faɗa tana kara mai da mashi cup ɗin a bakinsa. "You looks more beauty than everyday". Ya faɗa can kasan makoshinsa ta yadda ko kaɗan bata ji me ya ce ba, ganin bakinsa ta ɗan motsa alamar ya yi magana ne yasa ta yi gaggawar sake tambayarsa me ya ce, sai dai yaki yi mata magana, ya cigaba da kallon kyan da ta zuba yau kawai. Bata damu ba, dan ta saba da halinsa na kin maimaita abu, sai ta cigaba da bashi tea ɗin yana sipping a hankali-hankali har ya kusa shanyewa, sannan ne ya ce mata. "Is okey". Jinjina mashi kai ta yi tare da ajiye cup ɗin a saman carpet na kusa da bed ɗin, sannan ta juyo ta tsaresa da kallo. Ita dai yake da kallo shi ma. "Our Big Bro Ina neman wata alfarma please". Cikin marairaicewa ta yi maganar. Ko kaɗan bai motsa baki ba, sai kallonta da yake yi alamar yana jinta. "Please ka taimakemu ka nemo mana mom ɗinmu, wlh Ina sonta, zuciyata ta gagara masun natsuwa tin safe, ji nike tamkar in yi kuka, please, nasan nemota a wajenka karamun aiki ne wanda kafin ƴan mintina zaka yi hakan, ka taimakawa maraicikinmu". Idanunta cike tab da kwallah ta kai karshen maganar. Shiru babu niyar zai iya amsa mata, hakan ba ƙaramin bakanta mata rai ya yi ba, zafafan hawayen da take kokarin dannewa ne suka kwace mata, ga shi abin takaicin shi Big Bro ba'a nuna mashi zafa, idan kana son yin galaba a kansa ma ai dole ka bisa a hankali da hikima da tausasawa, idan ka ce da zafa zaka zo ai pata-pata zaku yi, dan shi zafa ma tsoronsa take ji. Yana ganin tana ruwan hawaye amma bai ce mata ko uppan ba, bashi da niyar yin magana kuma, hakan yasa ta ji zuciyarta ba zai iya juraba, sai ta miƙe da gudu zata nufi waje. Cikin zafa ya sa hannu ya riko waist ɗinta ta baya, slowly ya jawota ta faɗo saman Lion chest ɗinsa, wani irin nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ɗan ciza laɓɓansa saboda wani irin shock da ya ji a jikinsa. Sai a lokacin ta samu damar rushewa da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Shiru dai bai yi magana ba, da alama kukan bata tsuma zuciyarsa ba sam-sam. Almost 20 mins tana kuka bai iya ce mata uppan ba, har ta gaji dan kanta ta rage sautin kukan, a gaskiya shi bai san me zai ce mata bane, saboda wlh a halin da ake ciki yanzu ba zai iya nuna masu mom ɗinsu ba, shi kansa da bai san daɗin uwa ba ya ji tausayinsu ya kamasa bare su, ya ji ba zai iya haɗasu da mom ɗinsu a halin da take a ciki yanzu ba, dan zasu iya shiga mawuyacin halin da gwara ɓoye masu da ya yi. Tin yana iya jiyo shesshekar kukan nata har ya fara jiyo sautin numfashinta mai nauyi irin na mai barci, alamar barci ya yi awon gaba da ita, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Ba zan iya haɗaku da mom ɗinku ba Omaish". Ya faɗa yana ɗaura hannunsa ɗaya a saman kyakkyawan golden hair ɗinta. Unexpected muryar Smart ta katse shi da cewa. "Me ka yi wa sister ɗinmu take irin wannan shesshekar kuka haka?". Harara ya dallawa Smart kafin ya ce. "Kana da alaƙa da kukanta ne?". Kai Smart ya jinjina tare da takowa ya kariso gaban bed ɗin. "Sistermu ce, ina da alaƙa da kukanta, ka faɗa mun me ka yi mata ko kuma in ɗauka mata fansa". A karkashin zuciyar Smart so yake yi ya gwada ɗan uwan nasa ya ga shin zai yarda da su mommah a yanzu tin da ya rabu da waɗan can azzaluman? Ko dai har yanzu ba zai yarda da su ba, sannan yana son fahimtar ainahin abin da yake a cikin zuciyar ɗan uwan nasa yanzu, amma bai san ta ina zai fara mashi ba!. "To zo ka ɗauka mata fansar in gani". Cikin nuna iko Big Bro ya yi maganar. "Awww nuna mun zaka yi heartbeat ɗinka ce? Wato zaka nuna mun ka fini kusanci da ita kenan?". Shiru Big Bro bai amsa mashi ba, ya dai bisa da harara....... "To shikenan kawota in kwantar da ita tin da ta yi barci, kada ta fama maka ciwo". Smart ya faɗa tare da matsawa kusa da su da niyar ya ɗauki Sweetie. Wani harara da Big Bro ya dallah mashi sai da ya sanya shi cin wata uwar birki. "A jikinka take kwance ne ko ciwonka zata fama?". Big Bro ya faɗa yana ɗan ɗaure fuska. Ɗan ɗaure fuska Smart shi ma ya yi. "Daga taimako sai a mun gori? To na barku, dama a tare na ganku". Cike da zolaya ya kai karshen maganar tare da wucewa ya nufi balcony. "Zo ka faɗa mun abin da ya ji maka ciwo nima kuma ya ji mun". Big Bro ya faɗa yana binsa da ido. Dakatawa Smart ya yi tare da juyowa ya dawo, a kusa da ɗan uwan nasa ya zauna, babu ɓoye-ɓoye ya zayyane mashi dik irin faɗar da suka gwabza, daga karshe ya rufe mashi da cewa. "Yakamata ki kira Mommah ka ce mata sorry ka jiwa shalelenta ciwo". Mamaki sosai Big Bro ya yi, cike da mamaki ya ce. "Ni na ji maka ciwo?". Kai Smart ya gyaɗa mashi kafin ya ce. "Kwarai kuwa, shiyasa na ce ka kira Mommahta ka bata hakuri dan ka jiwa shalelenta ciwo". Smart ya yi mashi wannan zolayar ne dan ya fahimci ya yake jin su mommah a ransa, sai dai ya yi matukar mamaki game da girgiza da jin amsan ɗan uwan nasa, domin kuwa Big Bro cewa ya yi. "To ai nima ka ji mun ciwo, sai ka kirata ka bata hakuri domin ka jiwa first love ɗinta ciwo, ba kai kaɗai ta haifa kuma take so ba ai". Wani irin daɗi da Smart ya ji har bai san lokacin da ya kai hannu ya riko hannun ɗan uwan nasa ba, cike da farinciki a ransa ya ce. "Kana nufin ka aminta Mommah ita ta haifeka?". Jinjina kai Big Bro ya yi kafin ya ce. "Bani da wasu iyaye biyunsu ai". Kamar Smart zai ce to kenan ya yarda daddynsa na nan ba shi ya haifesa ba, sai kuma ya fasa yin tambayar gudun kada ya ɓallo wata ruwan, tin da ALLAH ya ɗorasu kansa, addu'a bata faɗuwa kasa banza, ya aminta su Mommah ne iyayensa, to bai kamata a ɗauko tsohon zance ba, kada a lalata shirin kuma. Matsawa ya yi ya rungumo Big Bro a jikinsa, har hawaye idanunsa ta kawo saboda farincikin Big Bro ya aminta da cewa shi ɗan uwansa ne, shikenan komai ya zo karshe a wannan rikicin kuma, amma fa an sha fama, sai dai daga karshe ya yi nasara, addu'ar mommah da nasa ta karɓu. Hannu Big Bro yasa ya ɗan shafi arab hair ɗinsa kafin ya ce. "I really love you my blood". Wani irin musulmin daɗi ne ya kara lulluɓe Smart. "Love you too my blood". Yanzu ta tabbata dama duniyar shaiɗanu ne basa son Big Bro ya yarda da su Mommah. Shikenan yanzu ya aminta. Cike da farinciki Smart ya ce. "Kenan yanzu zamu iya komawa gida?". Kai Big Bro ya girgiza mashi alamar a'a kafin ya ce. "Ba yanzu ba, zuwa next week zamu je gida, amma zuwa zan yi in ga iyayena kawai". Ba dan Smart ya so ba ya amsa mashi da okey, sai dan baya son su ja magana wata matsala ta sake faruwa, dan yana ganin kamar Big Bro bai gama samun lafiya ba, da yana da tabbacin ya samu lafiya ba zai yarda da cewa zai je ya ga su mommah ne kawai ya dawo ba, amma ba komai su je gidan, ya tabbata ba zai iya dawowa ya barsu ba, zai zauna da su ko da na ɗan lokaci ne!. Sun jima rungume da juna ta gefe guda while Sweetie tana kwance a kirjinsa ta gefe guda, kafin daga bisani Smart ya raba jikinsa da na Big Bro yana faɗin. "Bari a shirya maka lunch ɗinka dan nasan kana jin yunwa". Ya yi maganar yana shafa lallausan fuskar Big Bro. Hannu Big Bro yasa ya shafi nasa kumatun shi ma kafin ya ce. "Lokacin cin abinci ya kure, bari kawai mu yi dinner anjuma". Ba haka Smart ya so ba, ya so ɗan uwan nasa ya ci abinci, amma tin da ya ce a bari bari su bari ɗin kawai, dan haka sai ya miƙe ya zauna a gefen bed ɗin suka cigaba da hira jefi-jefi cike da kaunar juna. Ya dai ki barin Sweetie ta rabu da jikinsa, ya ƙanƙameta gam, shi Smart dik tinaninsa suna da aure ne shiyasa sam baya yi masu shamaki a tsakaninsu. A haka Ronnie da Pretty suka shigo suka samesu, suma saman bed ɗin suka haye, Pretty ta matso jikin Smart ta kwanta, yanzu son kayanta take yi tin da Sweetie ta faɗa mata cewa Kamran yayansu ne, sai ta rungumi mijinta tana kula da shi. YANZU SUN CURE SUN ZAMA ONE FAMILY!. Shiru Ronnie ya zauna yana binsu da kallo, ya kalli Big Bro yana shafa kyakkyawan gashin Sweetie, ya juyo kuma ya kalli Smart da yake ta faman biyewa Pretty tana kashe shi da shagwaɓa. Lokaci guda tinanin budurwa ta faɗo mashi a rai, amma har yau bai iya sake tuna Floris ba, da alama yayansa ya yi mashi wani abin a kanta ne. Sai ya ji sha'awar budurwa, ya ji yana son samun budurwa shi ma, da wannan tinani a ransa ya yunkura zai sauka daga bed ɗin kenan Big Bro ya riko hannunsa, ya jawosa jikinsa ya haɗesu da Sweetie ya rungume a kirjinsa, yana jin wani iri a ransa, wani irin tsananin so na musamman yake yi wa waɗan nan halittu biyun, dan sun nuna mashi kauna over, basu taɓa nuna sun gaji da halinsa ba, almost 2 years da wani abin yana a tare da Sweetie, dik azabar da ya ganawa yarinyar nan bata taɓa nuna ta gaji da halinsa ko ta nuna ta tsanesa ba, tana da hakuri da juriya, shi kuma Ronnie kome zai faru yana nuna mashi zallar kauna kuma yana goyan bayansa, dede da second ɗaya bai taɓa juya mashi baya ba, waɗan nan mutane biyun sun cancanci fiye da haka daga garesa. MY PEOPLE'S YA KUKE GANIN WAƊAN NAN FAMILY ZASU KASANCE? DA SAURAN KALLO FA, YANZU WASAN ZAI FARA ASUWAY, GA LOVE GA WAR! YANZU ZA'AYI ASALIN YAKI! MUN SHIGA RAWANIN ZALINCI ZABUWAR DUNIYA STEP ONE, AKWAI STRUGGLE FA!!.🤸 CROWN OF POWER🔥 "Kasan me?". Kai ya girgiza mata alamar a'a bai sani ba. "Daga yau kullum zamu rinƙa zuwa gym ɗin nan kana koya mun, sannan mu je ka nuna mun masu raina maka wayan in haɗa masu jini da majina". With her full confidence ta yi maganar. Shi dai wani lokaci mamaki Mahreen take bashi, sometimes yana rasa ta ina take zaro magana, wai ta haɗa masu jini da majina, kai ALLAH abin godiya, gata kuma kamar a hure wlh, ba auki sai baki. "Kada ki damu, sai zuwa gobe ko da daddare zan kaiki in da suke rainani in nuna maki". Jinjina kai ta yi tana wani ciza laɓɓa kamar wata yar daba, ita a dole zata tare mashi faɗa. Hmmm bata san guyson bane, wlh yaron nan da balain zuciya, ga karfi da zafin rai, ciwon cikinsa da yake yi wa kuka abu ne da ya shafi iska da dole ya yi kuka, azabansa ta wuce yadda ake tunani, wlh ba dik kai ba zai iya shanye ciwon guyson, abin ba na wasa bane, ku baku yi mamaki ba, almost 20 years yanzu sauki taki samuwa, wai baku ga baya tsoron aljanu bane? To shi da kansa aljanin kansa ne, shiyasa ranar ya zage aljanar can, ai tare da su yake kwana, kune baku san labarin ciwonsa ba, amma a hankali zaku fahimci makasudin ciwon, da dalilin kukansa idan yana ciwon da kuma meyasa zuciyarsa ta ɗan zama mai rauni a yanzu, wlh da yana asalin Omar ɗinsa na tin farko in aka zo faɗa ko Jaish ba zai sha a hannunsa ta daɗi ba, baku yi mamakin meyasa Jaish yake dariya da aka ce Omar yana son Mahreen ba, ai gagarumin maganace a kasa, shi Jaish yasan Mahreen zata iya tunzura guyson har ta tayar da abin da aka sha wahalar kwantarwa, uhm abin babba ne, muje dai zuwa. Bai sake ce mata komai ba har suka kammala gym ɗin, ya riko hannunta suka dawo ciki, ya koma bedroom ɗinsa ita ma ta wuce nata, basu sake haɗuwa ba sai karfe 9 na dare, ya zo nemanta sau ba adadi baya samunta, tana can ta ci uwar kwalliya tana lambu, ta zauna sai hotuna uncle Taheer yake yi mata, saboda ya ce ta yi kyau, yaba kyanta yasa ta ɗan saki jiki da shi, bata ita ta dawo cikin gida ba sai can mangariba, a can ta yi sallar azahar da la'asar. Ko da ta dawo cikin gida bedroom n Mahnoor ta wuce abinta, bata koma nasu ba, hakan yasa guyson ya yi ta jelen nemanta har ya hakura. Karfe tara ɗin ma yana zaune a bedroom ɗin nasa cike da tinanin ina take? Ya kira wayar da ya saya mata baya shiga. Yana zaune a tsaiyar bed ta shigo bakinta a ɗauke da sallama. Da sauri ya miƙe, muryarsa a raunace ya ce. "Ina kika je yau?". Tana yamutse fuska ta ce. "Zuwa da safe zan faɗa maka yanzu dai zo ka bani jallabiyarka fari guda ɗaya". Ya ɗan yi mamaki amma sai ya ce. "Okey amma zaki zauna mu ɗan yi hira ko?". Ka ta ɗan girgiza. "Akwai abin da zan yi, amma kila zan dawo bani da wuri". Kamar zai sake yin magana, amma jin ta ce a bata da wuri yasa ya diro kasa ya nufi closet ɗinsa. Sabuwar jallabi fara kal ya ɗauko mata, yana miƙa mata ta karɓa da sauri ta juya, bayanta ya bi da kallo yana ɗan mamakin me zata yi da jallabiya kuma?. A gaggauce ta yi waje, bata zame ko'ina ba sai room ɗinta, tana shiga ta cire kayan jikinta dikka, ta wate jallabiyar tasa ta sanya a jikinta, ya yi mata tsawo sosai, dan guyson yana da tsawo sosai, hannun ma ya mata yawa, amma dik bata damu ba, ta wuce gaban mirror ta zauna. Ai zama ta yi ta fito da kanta a siffar aljana sak da farin hoda da kwalli, ko daga ina ta samosu oho mata, ta fito gwanin ban tsoro, ta ɗauko wani farin kyalle tas mai laushin gaske ta yi rolling kanta da shi, wlh ko mai jarumtarka ka ganta sai ka razana, ta banbaɗe fuska da farin hoda, ta wani mulka bakin abu a baki ya yi bakin kirin, har gemunta baki, ta ja gera har wajen sajenta, kasan idanunta ta ƙawata shi da bakin kwalli, yadda ta zana kwallin ta yi raun ɗin idanun nata, ta damɓarasa da kyau, sai gula-gulan idanun farare tas zaka iya hangowa a fuskarta, ga uban rolling da ta yi, jallabiya na jan kasa, haka ta kammala shirinta tsab ta ɗauki kwalbar turare ta tura a cikin aljihun jallabiyar tata, sai ta ɗauko wayar cazar waya, shi ma ta nannaɗe ta tura a cikin aljihu, sannan ta nufi waje. Cikin sanɗa ta fara takawa ta nufi sauka ƙasa, ta bene ta bi. Kasa ta sauka ta nufi part ɗin uncle Abbas, sai ta bi ta kofar baya gudun kada warriors su ganta, ta saci hanya, ALLAH da ikonsa har ta shiga part na uncle Abbas kuma babu wanda ya ganta, da yake ta san ɗakin Sareena ta taɓa zuwa da Chuchu, sai kai tsaye ta nufi wajen. Kun sa basa rufe kofa, dan haka a buɗe ko'ina yake, tana zuwa ta afka ciki, ta haye sama abinta, kai tsaye sai ɗakin Sareena. A hankali tura kofar ɗakin Sareena, kamar wata ɓarauniya haka ta shigo. Tana kwance bisa gado ta yi ɗaiɗai tana danna waya, wutar ɗakin a kashe, chat take yi da su Omaid suna kara shirya mugunta. A hankali ta fara takawa har ta isa gaban bed ɗin ba tare da Sareena ta jiyota ba. Cikin sanɗa ta duƙo a ta kan gadon gefen side drawer tare da leƙo da kanta tana kallon screen na wayar da Sareena ke rike da shi, irin dai kana latsa waya aljana ta kawo maka jiyara haka. Ai jin kamar mutum na kallon screen ɗin yasa Sareena ta juyo a wani irin slow. Ai tana juyowa babu abin da ta gani sai fararen ido gulu-gulu. Wani irin ihu ta zunduma tare da zabura a miliyan ta yi jifa da wayar gefe. Miƙewa tsaye Mahreen ta yi tare da cewa. "Idan kika motsa sai kin mutu". Na rantse yadda ta yi magana ba zaka taɓa zatan ita bace, saboda muryar gardawa ta yi. Ai wani irin wiki-wiki da ido Sareena ta yi, a zuciyarta tana ambato sunan ALLAH, makoshinta sai sama yake yi yana kasa alamar tana haɗiyar yawu da kyar. Laluɓar remote na lamp Mahreen ta yi ta kunnasa, take haske ya ɗan gauraye kusa da su, hakan ya baiwa Sareena daman ita ganin aljanar cikin fararen kaya. Ai wani irin tsorara ta sake yi, jikinta ya hau kerma, ta gagara ɗago ido ta kalli fuskar aljanar saboda tsoron abin da zata gani. Tsabar razana har fitsari ta saki a wandonta a wajen, idanu dik sun raina fata. Dariya ne cike tab a cikin Mahreen, amma ta dake tare da cewa. "Ku bil adama bakwa jin magana sam-sam, musamman ma ku fararen fata da kuke nuna kun tsani bakaken fata, yanzu dik farinki kin kaini haske ne?". NI KUWA NA CE KE DA KIKE DA FARIN HODA YA ZA'AYI TA KAIKI HASKE FISABILILLAH?😸 NA RATSE MAHREEN ƳAR DUNIYA CE NA WUCE MISALI, KAI JAMA'A, YARINYA TA SANYA SAREENA FITSA A WANDO. Jiki na ɓari, murya na rawa Sareena ta ce. "A'a ban kaika haske ba". Tana magana hawaye suna tsere a kan fuskarta. Jinjina kai aljana Mahreen ta yi. "To mu jinnu da muka fiku haske kunga muna tsanar ku ne? Ku ku baku........ Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 -------------------------------------------🔥♥️ ZABUWAR DUNIYA STEP ONE!.🔥🔥🔥 Jinjina kai aljana Mahreen ta yi. "To mu jinnu da muka fiku haske kunga muna tsanar ku ne? Ko ku baku san mun fiku haske bane?". Tsabar kerman da jikin Sareena yake yi yasa ta gagara yin magana, ga dai fitsari nan ta malala ta jika mattress da jikanta sharkaf. "Bari ki ji in faɗa maki wani abin da baki sani ba, bakaken fata sun fiku daraja, ko baki san uban kowa baki bane? Baki san farkon halitta Annabi Adam (AS) baki bane ko? Ke kanki baka ce, yanayin weather ya canza fatarki izuwa fara, ko baki san haka bane?". Ta faɗa tana zaro mata idanu. Gagara magana Sareena dai ta yi, baki ya rufe ruf. Sake gyara tsayuwarta Mahreen ta yi, wai irin ta gwada ita hegiyar nan, ta ƙara kausasa murya kafin ta ce. "Daga rana irin ta yau! Girmamawa na musamman zaki rinƙa yi wa bakar fata, dan ta fiki daraja, kina jina? Kuma ƴan Nigeria da kike gani babu irinsu a duniya, su kaɗai ne, kyautar ALLAH ne su, ki san da cewa sun fiku komai, yanzu maza ki faɗa tare da ni cewa bakar fata sune gaba da kowa kuma sune farkon halitta". Ta kai karshen maganar tana zaro wayar chaza da ta sanya a aljihunta kafin ta fito. "Ba zaki faɗa cewa bakar fata ita ce gaba da kowa ba!". Ta faɗa a tsawa ce. Ai da sauri Sareena murya na kakkarwa ta fara in da in da tana kokarin tattaro kalmar da zata haɗa wajen cewa bakar fata ita ce gaba da kowa, sai wani irin uban gumi da take haɗawa tamkar wacce aka tsamo daga cikin ruwa, ta yi sharkaf, idanu duk sun raina fata, ta zama abin tausayi. Hegiya Mahreen ban da dariya da take kokarin dannewa babu wani abin da take yi, ba komai yake bata dariya ba kuma face tana tina irin zane Sareena da zata yi yanzu. "Ba..... Ba ..... Baka...... Ken .... Fa fa fata...... Sune a sama..... Da kowa". Da kyar waɗan nan words suka iya samun damar kubcewa daga bakinta suka fito, saboda tsananin tsoro. Mahreem kuwa gyara tsayuwa ta yi tare da yin wani irin girgiza ta ɗaga kai sama, wai ita nan sarkin shaiɗau. "Sunana Falcama ƴar sarkin aljanu, babana na ji dani, ki sani dik in da zaku shiga a duniyar nan ina iya ganinku, idan na kara ganin kin wulaƙanta wata bakar fata ko da harararta kika yi sai jikinki ya gaya maki! Ƴan Nigeria sun wuce da saninku, ba sa'an yinku bane! Yanzu ma ki kwanta ki mike flat, ki datse idanunki, ko me zai faru kika kuskura kika buɗe ko kika yi ihu mutuwa ta wajaba a kanki!".. Tuni cikin Sareena ya kara ɗurar ruwa, ta yi danasanin nuna kiyayya ga su Zee, yau ta ga bone. Mahreen dai ko a gefen kafarta, so take ta zaneta ko bulala biyar wai dan ma kada Sareena ta ɗauka wasa take yi mata. "Dan ALLAH kada ki kasheni, wlh zan rinƙa son bakaken fita har gaishesu zan rinƙa yi". Sareena ta faɗa cikin in da in da. "Ai sonsu dama ya wajaba a kanki tin daga yau, yanzu ni ba kasheki zan yi ba, amma da zarar kin sake aikata wani kyara ga yan Nigeria nan ne zaki mutu!!". Babu wasa a tattare da Muryar gardawar da ta yi, da gaske take yi!. Kara yin tsuru-tsuru da ido Sareena ta yi, tsawa Mahreen ta sake daka mata a akan ta yi gaggawar kwanciya kafin ranta ya ɓaci. Ai ba shiri Sareena ta kwanta flat tare da datse idanunta tana wani irin kuka mai ban tausayi. Mahreen ba tausayi babu imani yarinyar nan ta ware wannan igiyar chaza ɗin ta daddage ta tsulawa Sareena a gadan bayanta. Wani irin azaba da Sareena ta ji ne yasa ta sanya hannu ta toshe bakinta, saboda wani irin kuka da ya so kubce mata. Ko kaɗan Mahreen bata damu ba, ta sake daddagewa ta tsula mata, zafafan hawaye Sareena ta shiga yi, har wani jijjiga jikinta yake yi saboda azaba. Amma Mahreen bata kyaleta ba sai da ta shinfiɗa mata bulalu goma daidai, dik jikin Sareena ya yi ruɗu-ruɗu ya yi jajir abinku da farar fata. A walaƙance Mahreen ta ce. "Da bakaken fata ne yanzu jikinsu lahiya lou yake saboda sun fiku qualities, tashi ki fara frog jump yanzun nan". Ta faɗa tana zazzaro mata idanu. Ba shiri Sareena ta miƙe tamkar zata mutu yarinyar nan, sai hakuri take baiwa aljana Mahreen amma yarinyar nan taki sauraronta, ta ce ta yi frog jump kafa dubu yanzu a nan. Sosai Sareena ta rinƙa gamata da girman ALLAH a kan ta yafe mata, amma Mahreen ta ce idan bata yi kafa dubun nan ba zata mutu. Jin haka yasa Sareena ta daddage ta tattaro dikkan sauran karfin da suka rage mata ta fara frog jump ɗin nan babu kama hannun yaro, sai da Mahreen ta barta ta juyo daga wajen kofa ta nufi wajen toilet sai ta lallaɓa ta fice waje da gudu abinta ta bar Sareena sai frog Jump take yi tana cauting, ita a dole zata yi kafa dubu, idan bata yi dubu ba zata mutu. Tana fitowa daga ɗakin ta baro part ɗin abinta, bata zame ko'ina ba sai family part, ta so zuwa ɗakinsi Chuchu dik da take auntynta mai goya mata bayan, amma da ita aka zagi ƴan Nigeria, so ta so haɗawa da ita ta ɗauki fansa, sai dai kuma ta tuna Jawad yana nan, ba kowani namiji bane mai tsoron aljanu, kada asirinta ya tonu, dan haka sai ta ce bari ta je wajen Aneesa kawai, ta yafewa Chuchu tin da dama bata zagi ƴan Nigeria sosai ba, kuma ko ba komai bata nuna tana kyamansu ba, kunga ita take yi wa Mahreen ɗin ma kwalliya wani lokaci, ita ta koya mata wasu abubuwan ta wayar mata da kai. Mahreen and Mahnoor fararen fata ne, but kowa yasan hasken Nigerians da waje akwai banbanci, dik hasken ɗan Nigeria idan ya shiga cikin masu jajayen kunnuwa baki yake zama, shiyasa suke yi masu kallon bakake. Zata wuce part na Mama wajen Aneesa sai ta hango door nasu Omaid a buɗe yake, nan ta tuna cewa sun taɓa yi mata rashin mutumci, dan haka yau ranar ɗaukar fansa ce, dik wanda ya yi mata ba daidai ba yau zata ɗauki fansa, hakan yasa ta ce bari ta fara shiga wajensu. Kai tsaye babu ko tsoro ta nufi room ɗin. A hankali ta shige ciki. Ga mamakinta sai ta ga mutum ɗaya ne a kwance a saman bed ɗin yana barci, bata iya banbanta su, hasalima ko sunayensu bata sani ba, dan haka bata san wanene daga cikunsu bane, shin wanda ya ce sai ya kakkaryara ranar ne ko ba shi bane, wato Obaid kenan, kun san shi ne mai saurin ɗaukan zafi kuma shi ne ya ce sai ya kakkaryata Omaid ya ce ya yafe mata. Aikuwa bata sani ba Obaid ɗin ne yake kwance yake barcin, Omaid yana can garden yana hirar soyayya da wana school mate ɗin nasu. Kashe wutar ɗakin nasu ta yi sai ta kunna masu lamp dan tsabar kokari irin nata. A dede kayin bed ɗin nasu ta zo ta tsaya ta yadda Lamp ɗin nasu zai haskata da kyau su ga aljana. Perfume dake aljihunta ta fito da shi ta fara fesa mashi a kan fuska. Da yake basu da nauyi barci shi da ɗan uwansa, hakan yasa yana jin saukar abu a kan fuskarsa ya ɗan motsa tare da fara kokarin waro idanunsa waje. Ai daddagewa ta yi ta canza murya. Tamkar saukar aradu haka ya ji ta ce. "Manrabbuka"....... Haba ai da yake ya yi karatu yasan su waye zasu yi mashi irin wannan tambaya a kabari, a miliyan ɗari ya zabura ya waro idanunsa waje, sai ya ga ko'ina duhu except ɗan gefensa, sannan ga mutum fari tas a tsaye a kansa, take ya fara tinanin ko ya mutu ne yanzu yana cikin kabari mala'ika ya zo yi mashi tambayoyi. A addini yasan idan mala'ika ya tambayeka a kabari baka amsa ba guduma zaka sha, dan haka gudun ya ci azaba yasa ya ce. "Rabiyallahul lazi kalakani". Ya faɗa yana zazzare ido, take ya haɗa wata uwar zufa yadda kuka san daga cikin gidan bread ya fito, jikinsa na wani irin kerma, gabaɗaya ya yi mugum tsorata bawan ALLAH. WLH DA ZAI SAN MAHREEN CE INA GA IN BAI KASHETA BA DA WUYA TA SAKE MORUWA, YARINYA TA SANYA HATSABIBI JIN TSORO. Sake daddagewa ta yi ta ce. "Mahdinuka?". Izuwa yanzu ya fara rasa wasu daga cikin kuzarinsa, tsoro ya baibayesa, amma gudun kada ya gagara iya amsa tambayar kabarinsa ya shiga uku yasa ya daddage ya ce. "Diniyal islam". Hegiya Mahreen bata kyalesa ba ta sake cewa. "Mahhuwan nabika?"....... "An..... An...... Annabiyi..... Huwa Muhammad...... Sallalahu....... Alaihi wa...... Wa sallam". Da kyar da suɗin goshi ya iya bada wannan amsa, saboda tsabar kerma da rawar jiki da muryarsa suke yi, wlh ya kai kololuwa wajen tsorata, numfashinsa sama-sama yake fita gwanin ban tausayi. Sai wani ƙoƙarin danne dariya take yi ita kuma, saboda yadda yake muzurai da ido a gaskiya ya girgizata sosai kuma ya bata dariya, bata yi zatan yana tsoron Mala'iku har haka ba, ashe karamin ɗan iska ne shi, ta faɗa a ranta. NI KAM NA CE DAN KEMA YARINYA CE SHIYASA KIKE GANIN KAMAR MALA'IKUN KABARI BA ABIN TSORO BANE, HMMMM ALLAH DAI KA BAMU WUCEWA LAFIYA, AMMA BAWA YANA CIKIN TASHIN HANKALI! Tsabar tsorata bai iya tina cewa Mala'ikun ALLAH babu baki a kan fuskarsu kamar da ta zana baki ba, shi dai ya firgita ya tsure. Shiru ta yi tana kokarin danne dariyarta, dan kada ya ganota, dariyar na neman cin karfinta ne, ga shi yadda ya gagara ko motsin kirki, yana kwance flat bawan ALLAH. Da kyar ta iya shanye dariyar tata kafin ta ce. "Dik da ka amsa tambayoyinka daidai sai ka ɗanɗani azaba, saboda yadda ka rinƙa cin zarafin ƴan adam bayin ALLAH a duniya, ka tozarta mutane!". Ta faɗa da kyar saboda yadda idan ta ga yana zazzaro ido dariya ke shirin kubce mata. ALLAH sarki Obaid bai san time da ya shiga rawar jini sosai ya fara faɗin. "Wlh bani bane, Omaid ne yake shirya komai, ni bana cin zarafin mutane, ALLAH na tuba, wlh na tuba, kuma kullum idan muka yi laifi muna tuba, dan ALLAH kada ku gana mun azaba, na shiga uku mommah na, kullum Yah Jaish sai ya ce mana muji tsoron ALLAH irin wannan rana zata zo, amma muke banza da magarsa, dan ALLAH ku mayar dani duniya in faɗawa ɗan uwana ya daina zalintar mutane dan kada ya sha azaba shi ma, ina son ɗan uwana ban son ya sha azaba". Tun da ya fara magana Mahreen ta daddage ta toshe baki tana matse kafafu, dan wlh har fitsari ta ji yana ƙoƙarin zubo mata saboda balain dariyar da ya bata, bawan ALLAH ya zaci a lahira yake, wai a mayar da shi duniya ya sanar da Omaid ya tuba, ALLAH sarki yana son ɗan uwansa. UHM MU YI AIKIN ALKHAIRI, IDAN BA HAKA BA, YADDA OBAID YA KWATANTA DANASANI MARA AMFANI HAKA WANDA BAI KOMA GA ALLAH BA ZAI YI A LOKACIN DA BASHI DA MADOGARA BABU MAI CETANSA A LOKACIN, BA'A KARƁAR TUBA KUMA BA'A SAURARON BAWA. --------------------🔥♥️ "Yanzu ina Omaid ɗan uwan naka yake?".( KUN JI ISKANCI, YO MALAIKA YANA TAMBAYAR IN DAWANI YAKE NE IN BANSA MAHREEN DA IYA SHEGE BA) Shi kuwa ya fara fita a hayyacinsa ya amsa mata da cewa. "Yana garden, wlh na yi danasani, kuma na yi nadama, na tuba ba zan kara ba". "Danasani bata amfani a nan, kuma ba'a karɓar tuba, dole ka girbi abin da ka shuka, ka kuntatawa mutane dayawa, dan haka walakiri ku kama shi ku fara ɗanɗana mashi azaban wuta tin daga yanzu kafin ranar hisabi ya ji mai gabaɗaya daga wajen UBANGIJINMU". Ta faɗa tana ɗaga hannun riga sama alamar tana kiran su walakiri. Ai wani irin zabura Obaid ya yi sai ga fitsari a wando malala ta fara zubowa, ya ji za'a gana mashi azaba, fitsari sosai ya tsula a wando fa, KAI GASKIYA MAHREEN TA WUCI TINANINA, ALLAH YA CECEKI RANAR DA OBAID ZAI SAN KE KIKA YI MASHI WANNAN ƊANYEN AIKIN, UHM AKWAI CASE. Wannan zabura da ya yi ya saki fitsari a wandon ashe numfashinsa ta ɗauke, diff ya sume a wajen, bawan ALLAH yana da ilimin addini, yasan me ake kira da wutar jahannama, yasan hell fire yaro. "To idan kana son a sassauta maka hukunci abu biyu zaka yi, kai wannan yaron ma baka ji, babu abin da ya fi kona mana rai irin wannan baiwar ALLAH Mahreen da ka takurawa har da cewa zaka daketa ranar a duniya, yarinya baiwar ALLAH saliha bata tarema komai ba wai zaka daketa, amma ba komai zan yi maka sassauci". Ta faɗa tana wani irin jan numfashi. KAI JAMA'A WAI MAHREEN BAIWAR ALLAH, NI KAM MY PEOPLE'S YA ZAMU YI DA MAHREEN NE? DAN TANA NEMAN FIN KARFINA!. Jin shiru bai amsa mata bane yasa ta sake yin magana, nan ma shiru bai amsa mata ba. Ɗan leƙo fuskarsa ta yi, sai ta ga idanunsa a kakkafe suna kallon sama, ita da bata san suma ba sai ta zaci ya gagara yin magana ne ya tsorata, dan haka sai ta ciro igiyar chajin dake aljihunta, ta hau zuba mashi a jiki. Sai dai har ta zuba mashi sau uku bai motsa ba, hakan yasa ta razana ta hau zazzare ido. A tsora ce ta ce. "Na shiga uku, kar fa ace ya mutu ne da gaske saboda tsorata?!". Ta faɗa tana leƙo fuskarsa. Daidai wannan lokaci ita ma Sareena dake ɗakinsu tana frog jump ta sulale kasa sumammiya, ta ji azaba, bata iya frog jump sosai ba yau ta koya, dan dole ta yi kafa 200, kafafu dik sun kumbura, kuma dik a tinaninta aljanar tana a ɗakin shiyasa bata dakata da yi ba, bata san ga Mahreen kam a nan tana shuka wata tsiyar ba ko in ce ta shuka wata tsiyar. Ai ganin baya motsi yasa Mahreen ta zabura, a miliyan ta nufi waje, kuma tsabar rashin ji bafa ta yi nadama ba, daga karshe ma garden ta nufa wajen Omaid dan shi ma ta yi mashi aljanar karya, har da cewa daga Omaid sai Aneesa da Heleena, wai Heleena ma ta harareta, yau ranar ɗaukar fansa ne a kan dik wanda ya yi mata laifi. Fitowa harabar gidan ta yi, ta nufi garden da sauri tana addu'ar ALLAH yasa Obaid ba mutuwa ya yi ba, amma kuma bata sare da abin da ta yi niya ba. Daidai zata wuce wasu flower dake shuke kafin ka isa garden ɗin sai ganin mutum ta yi a gabanta yana nufota, daga garden shi ma ya fito, sanye yake da white jallabiya irin na jikinta. Da kallo ɗaya ta yi mashi ta gane wanene dik da babu wadataccen light a wajen, hakan yasa ta canza tafiya ta koma irin na horori tana wani ɗage kafafu da kafaɗu sama wai dan ta bashi tsoro. Daga garden ɗin ya fito shi ma. A tsananin natse yake tafiya cikin kamala da natsuwa. A daidai tsakiyar flowers ɗin suka haɗu da ita, wani irin canza murya ta yi ta ce. "Kai bil adama zo nan". Juyowa ya yi yana kallonta kafin ya ce. "Oh ranar da na ce ba zan tsorata bane yau kuma kika dawo ko? To wlh yau zaneki zan yi, wai ma uban me kike yi mana yawo a cikin gida ne da daddare? Uban waye ya aikoki kuma wajen waye aka aikoki da kika ishi mutane?." TO JAMA'A ALJANAR KARYA TA HAƊU DA NA GASKE, DAN DAI GUYSON KAM RABI MUTUM NE RABI ALJANI.........😸 Mamaki ne ya kamata, a ranta ta ce kenan ya taɓa haɗuwa da aljanar gaske? Balain can, lallai wannan ya kai namiji, kai ko tsorata bai yi ba. Bata karisa tinanin nata ba ta ji ya damko wuyar rigarta yana jijjigata da karfi yana faɗin. "Faɗa mun uban da ya aikoki ko kuma yanzu in ga bayanki". Tsuru-tsuru ta yi da ido, ga shi bata son asirinta ya tonu. "Idan kina cigaba da zazzare mun idanun nan naki sai na kwakwalesu, zaki faɗa mun wanda ya aikoki cikin family ɗin mu ne ko sai na canza maki kamanni yanzu?". Yana magana yana kara jijjigata. Jin hakan yasa ta sake daddagewa ta canza murya wajen cewa. "Ka yi hakuri yanzu zan tafi, kuma ba zan sake dawowa ba". "Ba zan hakura ba yau kam, dole ki faɗa mun uban da ya aikoki gidanmu, saboda in ci mutumcin koma wanene ya aikoki". Cike da mamaki ta ce. "Kana da karfin cin mutumcinsu ne?". Ɗan zaro mata dara-daran eyes ɗinsa ya yi kafin ya ce. "Kina tantama ne? To bari in gwada maki kaɗan daga cikin karfina". Yana kai karshen maganar da hannu ɗaya yasa ya ɗagata sama kamar ƴar tsana, ya nunawa sama ita kafin ya ce. "Ko kwatan karfina baki gani ba, hannu ɗayana ya fi karfinki, amma bari ki ga yadda zan yi dake". Ya kai karshen maganar zai yi jifa da ita ya makata da jikin bango. Ai a miliyan ta ware muryarta wajen cewa. "Yah Omar Mahreen ce fa". Yar ƙaniya ta ji zata sha kasa waɗan nan siraran kasusuwan hakarkarin nata su kakkarye tini ta dawo kan saiti, wai Mahreen ce. A miliyan ya sauko da ita kasa, kurawa fuskarta idanu da kyau ya yi, sai kuwa ya ga ita ɗin ce da gaske, da sauri ya ce. "Ke meyasa kika yi irin wannan shiga?". Turo baki ta yi kafin ta ce. "Ka yi alkawarin rufa mun asiri zan faɗa maka dalili". Yana kallonta cike da kauna ya ce. "Na yi alkawari". Nan ta zayyana mashi dik abin da ta yi, ko abu ɗaya bata ɓoye mashi ba. Ai bai san lokacin da ya watse da dariya ba, zuba mashi idanu ta yi tana kallon tsantsar kyan da ya kara a lokacin da yake dariya. Shi kuwa dariya har da rike ciki tare da tsugunnawa kasa. Tana ta kallonsa har sai da ya yi mai isarsa sannan ya ce. "Wlh kada ki kuskura ki bari Obaid ya rikeki, ina ga dik Kingdom ɗin nan babu wanda zai iya kwatarki a hannunsa, ai yazama dole in rufa maki asiri, in ba haka ba ai ba zaki saura ba, dan dukan mutuwa zasu yi maki, amma Mahreen bakya ji ko kaɗan, to yanzu dai wuce mu je ciki". Tana turo baki ta ce. "Ai ban ɗauki fansa a kan Omaid ba, bari in ɗauka in zo ka ji?". Ta faɗa tana kokarin juyawa. Da sauri ya riko hannunta. "Omaid ba irin Obaid bane, wlh yana da saurin tinani da ɗago abu, shi Obaid kin ga akwai kaifin kwakwalwar amma bashi da saurin ɗago abu, ALLAH tsab Omaid zai iya ganoki, in kuma ya ganoki shikenan asirinki ne zai tonu, har Obaid sai ya san kece kika yi mashi haka, daga nan kuma kin san me zai biyo baya, ALLAH idan baki yi sa'a ba sai kin shiga prison na masarautar nan kin sha horo ko na wata biyu ne, dan haka ki hakura hakan ya isa ki zo mu je ciki". Jin asirinta zai iya tonuwa ne yasa ta ce. "To amma ta yaya zan ɗauki fansa a kan Omaid da Aneesa and Heleena?". A marairace ta yi maganar. "Ki yafe mashi mana, ALLAH yana son mai yafiya fa". Shiru ta ɗan yi tana kallonsa, can kuma sai ta ce. "Ka taɓa ganin aljana ce?". Ta yi maganar tana kallon cikin kwayar idanunsa. Kai ya jinjina mata kafin ya bata labarin yadda suka kare da aljanar ranar. Dariya ita ma ta watse da shi tana faɗin. "Kai ma ashe ka iya karya, yanzu aljanar zaka ce wai ka zaga kuma ta barka?". Shiru ya yi yana kallan yadda take dariya gwanin birgewa. "ALLAH kai kam ka iya maganar banza, yanzu aljanar ce mai ido kamar kuliya kuma sai ta barka? Ban taɓa sanin kai shararren makaryaci bane sai yau". Ɗan nisawa ya yi tare da riko hannunta, ya jata suka nufi cikin gida, ko uppan bai sake ce mata ba har suka isa kofar room ɗinta, saketa ya yi, fuskarsa babu alamar wasa ya nuna mata cikin ɗaki da hannu ɗaya. "Idan kika kuskura kika sake fitowa a daren nan sai ranki ya ɓaci". Ya faɗa with harsh voice, muryar da bai taɓa yin magana da ita ba. Ta ɗan sha jinin jikinta, kuma ta ji shakkarsa ya kamata, bare ma yadda ta ga ya cukule fuska, sai bata ja magana da shi ba ta yi gaggawar wucewa ciki tana ɗan waigosa, yana tsaye bai motsa ba har ta haye saman bed ɗinta, sannan ne ya sauke ajiyar zuciya tare da janyo mata kofa ya datse. A natse ya wuce room ɗinsa yana ta faman sauke ajiyar zuciya, da alama yau ransa ta ɗan sosu. Haka ya haye bed ɗinsa ya kwanta, sai ƙoƙarin dannar zuciyarsa yake ta yi, da haka har barci ta yi awon gaba da shi. Ita kuwa sai da ta je ta wanke fuskarta tsab, sannan ta haye gado ranta fes ta tsorata tantiran gidan har da fitsari a wando da suma. Tana kwanciya ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita. ASUBA TA GARI. MY PEOPLE'S YA KUKE TINANIN ZA'A WAYI GARI A KINGDOM ƊIN NAN? OBAID ZAI CE SAM YA GA MALA'IKAN MUTUWA, SAREENA KUMA IDAN TA TASO DAGA JINYA TA CE TA GA ALJANA, KAI MAHREEN AKWAI ƳAR DUNIYA!!. CROWN OF INJUSTICE.🔥🔥 "Ki tsaya in gyara maki kwalliyar". Sweetie ta faɗa tana ɗan gogewa Pretty gefen kumatunta da wani white hanky. Sun yi fitina cikin sleeping dress iri guda dake a jikinsu, sun kara wani irin kyau, Sweetie ta gyarawa Pretty black koreans hair ɗinta, ya kara tsananin kyau yana wani irin sheki na mussamman, ita ma ta gyara nata har wani ɗaukar ido yake yi. Riga mai dogon hannu da wando shi dogo very silky mai zubin pj's ne a jikinsu, launin kayan white color ne, ɗaya daga cikin kayan da suka yi shopping ɗazun ita da Ronnie ne, sun yi sallar mangariba da ishai a tare, shi kuma Smart a tare da Ronnie suka yi sallah, Big Bro dai ko da wasa bai yi kamar zai yi sallah ɗin ba, da Smart ya ce mashi ko zai gwada sai ya ce a'a baya so bata bashi sha'awa ba. Da yake Smart yana ganin kamar bai gama komawa normal ba sai ya rabu da shi bai takura ba. Sun kammala shirinsu tsab sai tashin kamshi mai kwantar da hankali suke yi. Rike da hannun juna suka fito, bedroom na Ronnie suka fara nufa dan duba shi. Nan suka iskosa yana kokarin fitowa, shi ma irin sleeping dress ɗinsu ne a jikinsa, nasa off milk, ya yi kyau yana wani kyalli tamkar tauraro. Sai suka haɗe suna wani irin kyalli kaman taurari. Tana sakin cool smile ta ce. "Lovely bro ka ganka kuwa?". Kashe mata ido ɗaya ya yi. "Sis kin fini kyau ai, Aunty Pretty sarkin izza me kike tinani?". Ya yi maganar tare da shafa kumatun Pretty da ta tsaresa da ido. Ɗan turo mashi baki ta yi. "Tinanin su Zunaira nike yi, tana can Hoorain ya tafi da ita". ALLAH sarki basu san Hoorain ɗin yayansu bane....... Ronnie zai sake yin magana Sweetie ta rigasa da cewa. "Kaga rabu da ita da waɗan nan mutanen nata, ba ganewa zamu yi ba, ni yunwa nike ji mu je mu yi dinner". Cike da zolaya ya ce. "Yunwa ko kuma ana zumuɗin son ganin yayana?". Ɗan cukule fuska ta yi. "Waye kuma yayanka?". "Eyeeeee a lallai kin fi karfina, to shikenan bari mu je dining in ga kin kallesa ki ga yadda zan yi dake". Ya faɗa yana dalla mata hararar wasa. "To ai ni ban san shi ba ma bare har na kallesa idan muka je, kawai ni dai mu tafi, na yi alkawarin babu ma wanda zan gani". Jinjina kai ya yi. "Aunty Pretty ki zama shaidar cewa babu wanda zata gani". Da sauri Pretty ta ce. "Shaida kai, ta kuskura ta ga wani idanunta zamu kwakwale". Kasa-kasa ta ce. "Ku taɓani ku jawa kanku". Yadda ta yi maganar basu iya jin me ta faɗa ba, sun dai ga ta motsa baki, sun kuma sake tambayar me ta ce ta yi masu shiru. Girgiza kai Ronnie ya yi tare da wucewa gaba suka rufa mashi baya. Dik Sweetie ta zaƙu ta ga Big Bro, tin da suka rabu da yamma bata sake ganinsa ba, kada fa ku ga laifinta ato. Sama suka haye Ronnie na cigaba da zolayarta har suka kai bakin door na Big Bro. Suna zuwa Sweetie ta cire masu password na door suka shiga daga ciki. Ai suna shiga sai da dikkansu suka ja birki, gabaɗaya sake baki suka yi suna kallon yadda waɗan nan taurari guda biyu, sun yi balain haɗuwa, suna tsaye a gaban mirror, Smart yana tsaye a gaban chair dake a gaban mirror, while Big Bro yana zaune a saman chair ɗin, gyara mashi dogon gashin kansa Smart yake yi, ya ce mashi ya yanke gashin ya rage mata tsawo, da buɗan bakin Big Bro ya ce haka Jesus yake barin gashinsa, dan haka shi mabiyi yesu ne, bai ga dalilin rage gashinsa ba, Smart ya so ce mashi to ai in dai haka ne yakamata ya musulunta tin da yesu ma addinin Musulunci yake yi ba Christanci ba, amma sai ya kyalesa, baya son abin da zai ja Big Bro ya ce ya fasa zuwa Kingdom of power next week, so yake sai sun je gida su haɗu da mommah su yi forcing ɗinsa ya musulunta. So yana gyara mashi gashin kan nasa ne, shi already ya gyara nasa, Big Bro zai gyara nasa ne ya ce bari ya taimaka mashi, shi ne yake gyara mashi. Suna sanye da sleeping dress iri ɗaya, very sexy sleeping dress, kayan wando ne zuwa gwiwowinsu, sai riga doguwa zuwa gwiwa mai zubin bathrobe, sai dai suma nasu very silky ne haka, and rigar tasu ma tana da maɗauri a tsakiya kamar bathrobe, and kirjin rigar a buɗe take sosai. Lions chasts ɗinsu a wajen. Sun yi balain kyau over, sun fito identical ɗinsu over. Cike da farinciki a kan fuskarsa Ronnie ya ce. "Wanene Big Bro wanene Yah Omerish a cikinku?". Ya yi maganar yana rarraba idanunsa a kansu. A tare Smart da Big Bro suka juyo, Big Bro yana miƙewa tsaye dan Smart ya kammala gyara mashi gashin. Ya ilahi, wai kun ga taurarin mommah ɗin nan kuwa? Haɗuwa iya haɗuwa, abin ba'a magana. Pretty ce ta ce. "Bro ba zaka iya babantasu bane?". Cikin zolaya Ronnie ya ce. "Zaki banbanta mun su ne?". Ya iya banbantasu sosai, dan Big Bro na faɗa maku hasken fatarsa ta fita daban, ga gashin kai da ya kara banbantasu, zolayarsu yake yi yasa ya gwada bai ganesu ba. Kai tsaye dining area Big Bro ya nufa, shi kuma Smart ya tsaya yana kallonsu. "Ai ko dan yadda Big Bro ya wuce dining area kai tsaye bai kulamu ba daga nan zan iya banbantasu Aunty Pretty". Ya faɗa yana kallonta. "Yah Omerish ya fi Big Bro saukin kai". Cewar Ronnie again. Wucewa Sweetie ta yi ta bi bayan Big Bro, da sauri Ronnie ya rufa mata baya, ita kuma Pretty ta tsaya tana dallawa Smart harara da waɗan nan dara-daran idanun nata. Gentle ya tako ya iso gabanta, hannu yasa ya ɗan shafi lallausan kumatunta. "Kin yi kyau sosai my happiness, amma waye ya yi maki wannan dressing ɗin?". Hannu ta dunkule ta kai mashi duka a kirji kafin ta ce. "Ni ba zan taɓa yin abin kaina ba kenan sai in wani ne ya mun?". Yadda ta yi maganar ya fahimci abin ya ɓata mata rai. Ƙoƙarin rungumota ya yi dan ya bata hakuri, amma sai ta zulle mashi ta wuce dining area ta barshi a tsaye a wajen. Da sauri ya juya ya bi bayanta. A kusa da Ronnie ta zauna, robot suka yi serving ɗinsu, sai satar kallon Big Bro Sweetie take yi, ya yi balain kyau. Bayan Robot sun kammala zuba masu, spoon Big Bro ya ɗauka tare da ɗubo abincin zai kai ɗan bakinsa, da sauri Sweetie ta yi bismillah tare da matsar da ɗan bakinta ta cinye abincin bata bari ya kai bakinsa ba. Ta wutsiyar ido ya ɗan saci kallonta, har ajiyar zuciya a hankali ya sauke ganin irin kyan da ta yi. Ronnie ne ya ce. "Sis ya muka yi dake kafin mu zo nan a kan kallon yayana?". Hararar wasa ta wurga mashi kafin ta ce. "Ya kuwa muka yi?". Ta yi maganar tana taunan abinci. Ɗebo nasa abincin Smart ya yi zai kai baki kenan Sweetie ta sake matsawa zata cinye nasa Pretty ta yi gaggawar kai nata baki zata hana Sweetie kenan Smart ya janye spoon ɗinsa yana faɗin. "Sweetie kawo bakinki in baki, dan Pretty daman fushi take yi dani, ba zata ci mun abinci ba". Harshe Sweetie ta fitar ta ɗan yi wa Pretty gwalo kafin ta matsa kaɗan, Smart ya kawo mata spoon ɗin, zata cinye abincin kenan hannun Big Bro ya shiga tsakanin bakinta da spoon na abincin, hakan yasa ta sumbaci hannunsa maimakon ta ci abinci. Ai Ronnie bai san time ɗin da ya furta wow da karfi ba, idan ka ga Big Bro at the first place ba zata taɓa zatan yana kallonsu ba, zaka yi zatan abicinsa kawai yake ci, ashe yana ganinsu, ga shi ya hanata ci. Da sauri Smart ya ce. "Wai menene haka blood? Meyasa kake shiga tsakanina da sis ne?". Shiru Big Bro bai amsa masu ba, sai wani irin harara da ya dallawa Sweetie wanda ya sanya bata san lokacin da ta ja baya daga yunkurinta na cin abincin Smart ba, ta koma saman chair ɗinta da kyau ta zauna tana turo baki, ita a dole ya ɓata mata rai. Ita kuma Pretty miƙewa ta yi a fusace zata bar wajen. Sai dai kafin ta tafi sai da ta zago ta in da Sweetie take, ta ɗaga hannu zata kwala mata rankwashi a kai kenan hannun Big Bro ya sake shiga tsakaninsu a karo na biyu, hakan yasa ta rankwashi hannun nasa, yana dai duke da kai yana cin abincinsa bai ɗago ba. A karo na biyu Ronnie ya sake furta wow, abin ya ƙayatar over. Juyawa Pretty ta yi tana wani irin gunguni ta nufi waje abinta, ajiye spoon ɗin Smart ya yi da sauri ya miƙe ya bi bayanta yana hararar Big Bro kamar shi ya saka mashi ita ta yi fushi. Shi dai Big Bro abincinsa kawai yake cigaba da ci bai ce komai ba. Lokaci guda Sweetie ta saki cool smile na ganin yadda ya tare mata Pretty bata rankwasheta ba, abin ya yi mata daɗi over. Spoon ɗinta ta ɗauko ta ɗebo abincin, sai ta kaiwa Big Bro saitin ɗan bakinsa, cike da kulawa ta ce. "Na cinye first spoon ɗinka, to ni ma ga nawa ka ci". Shiru bai amsa mata ba, babu alamar zai karɓa ya ci ma, ganin hakan yasa ta ɗan haɗe fuska tare da janye spoon ɗin daga gabansa, zata kai bakinta kenan Ronnie ya ce. "Bani in ci sis". Kakalo smile ta yi kafin ta miƙo mashi, da yake yana da left side na Big Bro ita kuma tana ta right side ɗinsa kusa da Smart kenan, yadda suka zauna ɗin shi ne Ronnie da Sweetie sun saka Big Bro a tsakiya, and Sweetie tana kusa da Smart, Pretty tana kusa da Ronnie sannan Sweetie and Pretty sun saka Smart a tsakiya, haka suke. Kasancewar Ronnie yana ta left side yasa dole ta gaban Big Bro zata miƙo mashi abincin, haka ta miƙo mashi, ya buɗe baki zai karɓa Big Bro ya tare bakinsa, slowly ya kai ɗan bakinsa ya cinye abinci yana kallanta ta wutsiyar ido. Wani irin kyakkyawan murmushi ta saki har sai da dimples ɗinta suka lotsa. Shi ma Ronnie murmushi ya yi, da sauri ta maida spoon ɗinta ta ɗebo abincin ta hau ci tana farinciki. Suna kammalawa Ronnie ya miƙe ya bar wajen, ita kuma sai ta juyo da kallonta a kansa, cikin natsuwa da tausasawa ta ce. "Big Bro baka yi magana a kan mom ɗina ba". Tamkar zata saka mashi kuka ta yi maganar. Miƙewa tsaye ya yi tare da nufar hanyar fita, har ya kai bakin kofa ya ɗan dakata ba tare da ya juyo ba ya ce. "Zan kawo maki in soon". Wani irin zabura da ta yi, da gudu ta miƙe, cikin tsantsar farinciki ta tafi ta faɗa saman faffaɗar bayansa tana wani uban murmushi tamkar bakin ba zai rufu ba, tasan tin da ya ce zai kawota tamkar ya kawota ɗin ne ya gama, baya magana biyu. Tsalle ta daka ta manna mashi sumbata a wuya, sannan ta sake shi tare da raɓawa gefensa da gudu zata yi waje dan ta je ta sanar da Pretty mom ɗinsu ta kusa bayyana, zasu ganta. Sai dai tana raɓawa gefensa ya yi zafan sanya hannun ya riko hannunta, da karfi ya fisgota ta faɗo jikinsa, har sai da ta ce wash dan ta buga kai. Kura mata idanu ya yi na ƴan sakanni kafin ya ce. "Ina zaki je bayan kin sumbaceni?". Da sauri ta ɗago kanta daga kirjinsa, zazzaro mashi ido ta ɗan yi a kan fuskarsa. "Pretty zan je in faɗawa......". Bata kai karahen maganar ba ya............ Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 -------------------------------------------🔥♥️ ZABUWAR DUNIYA STEP ONE!.🔥🔥🔥 Da sauri ta ɗago kanta daga kirjinsa, zazzaro mashi ido ta ɗan yi a kan fuskarsa. "Pretty zan je in faɗawa......". Bata kai karahen maganar ba ya ɗaura yatsarsa ɗaya a saman ɗan bakin nata, kallonsa a cikin idanunta babu ko kyaftawa. Tana kallon cikin nasa idon, slowly ta mai da kallon nata saman ɗan bakinsa. Kara jawota jikinsa da kyau ya yi, yasa hannunsa ɗaya ya dafe bangon dake kusa da su, sai ya ɗan rankwafo da kansa a kanta kaɗan. Zazzare ido ta shiga yi tana rarraba kallanta daga kan kwayar idanunsa zuwa ɗan bakinsa da yake son motsawa kamar yana son faɗin wani abin. Yadda suka tsaya sun yi kyau ace mata da miji ne kuma masoyan juna sosai, sai dai kash babu aure a tsakanin namijin da ba musulmi da mace musulma, sai dai macen da ba musulma ba da namiji musulmi. Shi fa Big Bro dik abin da zai yi wa Sweetie gani yake yi daidai ne, dan addininsu ba wai ya hana masu bane kun sani, ita kuma Sweetie idan tana a tare da shi rasa control ɗin kanta take yi, kai tana ma da kokari fa, kuma ta yi namijin kokari gaskiya, ta taso a makauniya, ga rashin uwa, amma dik da haka ta yi kokarin kare kanta har ta kawo yanzu, kun ko ga ta yi kokari, yanzu sharrrin soyayyar Big Bro yake ɗebanta shiyasa ko ya taɓata bata iya hanasa, bama zata iya hanasa ba, saboda shi abin da ya yi ra'ayi kawai yake yi, sannan ita yarinya ce under age wanda a yanzu zuciyarta yake a buɗe sosai, a kan abin da zuciyarta yake so babu abin da ba zata iya aikatawa ba, dan yanzu bata wani san ciwon kanta ba!. --------------------------🔥 "Big Bro idan kana kallona haka kana rikita mun tunani". Ta faɗa muryarta na ɗan rawa. Shiru bai amsa mata ba, kuma bai zare kallonsa daga kanta ba, sai ma kara rankwafo kanta da ya yi, gabaɗaya ya yi mata runfa ya rufeta ruf ba'a iya ganinta, dama gata yar karama a gabansa. NI KAM NA CE MOM TWINS TA WARKE TA ZO TA ƊAUKE YARTA TIN KAN BIG BRO YA LALATA MATA ITA!!..🥱 "Ni ka daina kallona kana bani tsoro da irin wannan kallonaka mai kama da mutum ya mutu ya bar idanunsa a buɗe, ko kyaftawa baka yi, kamar idon gunki, kana ɗaga mun hankali". A shagwaɓe sosai ta yi maganar, bata ma taɓa yin magana cikin wannan sigar ba. Ai malam Big Bro tsintar kansa ya yi a wata duniyar da ko a mafarki bai taɓa zuwa ba, wani irin iska mai ɗumi ya furzar daga bakinsa kafin ya rankwafo mai gabaɗaya a kanta, slowly ya kwanto da kansa a saman shoulder ɗinta wajen gefen kyakkyawan wuyanta. Ɗan tsorata ta yi tare da kara zaro idanu. Hannunsa dake sama waist ɗinta ta baya ya ɗan motsa shi kaɗan izuwa kasa wajen mazaunanta. Lokaci guda ya ja wani irin dogon numfashi tare da saukar mata da shi a hankali, har cikin ranta ta ji ɗumin numfashin nan nasa. Can kasan makoshonsa cikin wata iriyar muryar da bai taɓa magana da irinta ba ya ce. "Maysh meyasa bakyaji ne?". Ya faɗa yana wani irin goge lausasan lips ɗinsa a sama wuyanta. Dik a tsorace take, amma sai ta daure game da cewa. "Menayi kuma? And ka manta sunana Omaish ne ba Maysh ba!". Ta kai karshen maganar tare da ɗan juyo da kanta gefen da yake tana kallon yadda yake shakan kamshin hair spray ɗinta mai shegen daɗin kamshin dake tsananin kwantar da hankali yana wani lumshe ido. Shiru bai amsa mata ba, sai jin saukar hannunsa ɗayar ta yi a kanta, kan ta farga ya zare pin da ta tsoke jelar gashinta da shi dan kada ya warwaro. Take gashin nata ya watse har kusa da mazaunanta tsawonsa. Sama ya kara yi da hannun nasa ya tura cikin gashin nata. Tamkar wanda ya fita hayyacinsa ya fara faɗin. "I really like this ur hair, so cute". Yadda ya yi maganar zaka rantse wanda ya yi tatul da giya yake a cikin maye. NI KAM NA CE BA DOLE KA SO GASHINTA BA, SABODA KALAR GASHIN SWEETIE KO MAKIYINTA YA GANI YASAN YA HAƊU BARE, SAI MA IN YA SHA GYARA GOLDEN ƊIN NAN TA KARA FITOWA SOSAI, SAI KU GA TANA WANI IRIN ƊAUKAR IDANU, ABIN BA'A MAGANA, KO ITA BATA BURGEKA BA DOLE GASHIN NAN NATA YA BURGEKA, GASHI MAFI TSADA ADUNIYA DA BA KASAFAI AKA FIYE SAMU BA, YANA DA WUYAR SAMU SHIYASA MASU IRINSA A MANYAN KASASHEN DUNIYA SUKE FITA NA DABAN A CIKIN AL'UMMA!. Dik da tana a tsorace da yanayinsa bai hanata ta ce. "Na gode, amma ai kaima naka yana da kyau, ya yi baki sosai har yana ɗaukar ido". Shiru bai amsa mata ba, sai kara tura hannunsa da ya yi a cikin gashin nata. A hankali ya gangaro da lips ɗinsa zuwa saitin ɗan bakinta, kamar zai yi kissing ɗinta kenan ta yi gaggawar sanya hannu ta daddage ta ture shi da karfi sakamakon motsin da ta ji alamar mutum yana shigowa arear. Gabaɗaya ya fice a hayyacinsa ya hau binta da kallon mayen sha'awarta da take neman zautar da shi a daidai wannan lokaci, idanunsa dik sun rikiɗe sun yi jajir, har wasu siraran jijiyoyi ne suka bayyana a gaban goshinsa, tamkar wanda aka zarewa laka, jikinsa dik ya mutu bashi da wani kuzarin kirki, har yar zufa ya fara haɗawa, irin mayen kallon da yake binta da shi sai ku zaci ba shi bane. Ai tana ganinsa a wannan yanayi ta watsa da gudu zata bar wajen kenan Robot suna shigowa dan tattare kayan abinci su gyara wajen. Karo ta ci da robot dake a gaba, take ta yi baya-baya zata faɗi tana sakin yar kara saboda yadda ta buga kanta a wannan kirjin nasu na karfe wanda yasa har wani siririn jiri ta gani. Cikin zafa yasa hannu ya tarota tare da jawota ta faɗa jikinsa, cikin zafan da bai san ya aka yi ya ɗauki zafi hakan ba ya ɗago da kallonsa a kan robot ɗin, wani irin harara ya dalla mashi wanda bai san ya yi bama. To su robot ina ruwansu ma da ana harararsu, ba sai ka kwana kana yi har idanunka su faɗo ba, abin da ba mutane bane, can maka kai ka sani, su dai wucewansu suka yi suka hau yin aikinsu. Jin tana yar kuka ƙasa-kasa ne yasa ya dawo da kallonsa a kanta, sai luguiguita gaban goshinta take yi tana turo baki. Slowly ya kai hannun nasa wajen, a hankali ya ɗan lugiguita mata tamkar yana shafa kumatun jariri. Oh ni Princess Teema, da yake tana ji da shi a ranta sai ta mance da ta ji ciwo ta hau Jin sanyi da daɗin laushin hannunsa a wajen, har da ɗan lumshe ido. Bata ankara ba ta ji hannunsa a saman wuyanta yana ɗan yi mata kamar tafiyar tsutsa. Da sauri ta waro idanun nata waje, kai tsaye sai cikin nasa da suka yi balain kara rikitata, dan gabaɗaya kwayar idanunsa sun sauya. A ɗan ruɗe ta ce. "Big Bro in son in je ɗaki in kwanta". Tamkar zata yi kuka ta faɗi maganar. Shiru bai amsa mata ba ya cigaba da shafa wuyanta a hankali yana jin tamkar ya sanya tongue ɗinsa a wajen, dik ya susuce bawan ALLAH, ya zama tamkar ba shi ba. Daɗina da sha'awa kenan, ba ruwanta da girma da izzarka, sai in bata motsa ba, tamkar yaro karami haka yake mayar da kai!. Jin bai amsa mata bane yasa ta yi kokarin yin gaggawar barin jikinsa, kafin ya yi wani yunkuri ta watsa da gudu, bayanta ya bi da kallo, kamar zai dawo da ita jikinsa, sai kuma ya fasa ya tsaya shiru yana karɓar wuta daga cikin zuciyarsa da kuma cikin wandansa. Ita kuwa bata zame ko'ina ba sai sama gabaɗaya, dan tasan Pretty na a wajen, sai dai kuma ta yi danasanin zuwa wajen, saboda manne da juna ta isko Pretty da Smart, ya haɗe bakinsu yana shanyewa sister ɗinta baki, ko da yake ita ma Prettyn yar air ce, ta yi lamo a jikinsa tana karɓar sako, bama ka iya ganinta, gabaɗaya ya rukunkumeta, shi da ya zo rarrashi ya zarce. Da gudu ta hauro dama tama zumuɗin zata faɗa mata Big Bro zai kawo masu mom ɗinsu. Ai tana ganin haka ta ja wata uwar birki, a hankali ta fara ja da baya da baya har ta sauka kasa. Kai tsaye ɗakinsu ta koma, tana zuwa ta haye bed ɗinsu ta kwanta tare da shigewa cikin bargo. Take zuciyarta ya fara tunano mata irin kyakkyawan lips ɗin Big Bro da yadda yanzu ya matsa dab da ita, ta jima tana kwaɗayin ɗan bakinsa, sai ta ji dama ita da shi ne Pretty da Smart da ta gani a yanzu, ta ji da bata rabu da shi yanzu ba, tamkar ta tashi ya koma wajensa haka ta rinƙa ji a ranta, ita kanta wani irin azabbaben sha'awarsa ne ya rufeta, sai dai karancin shekaru yasa bata gane menene bane, sai ta zaci sanyi take ji, ta wani takure jikinta waje guda tana cigaba da tinaninsa. Yanzu ta gama gane son Big Bro mai tsanani ya kamata, maganar Ronnie ya tabbata kenan, ita kaɗai ta rinƙa sakin murmushi kamar wata zararriya, da haka barci ya yi awon gaba da ita. Can cikin barci around 5 sai ta ji tamkar ana taɓa jikinta. A zabure ta waro idanunta waje, kai tsaye sai cikin nasa idanun, yana zaune saman bedside drawer, wutar ɗakin a kunne, kamar ya gagara yin barci ne bawan ALLAH, ta tsokalo mashi abin da baya jin rarrashi, dama ga shi almot 34 years bai taɓa kwatanta kawar da kishinsa ba, infact a kanta ma abar ta fara motsawa. Ya kwanta zai yi barci ne gabaɗaya barci ta gagara zuwa, ya rasa sukuninsa, idan ya rufe ido kawai lips ɗinta yake kallo suke yi mashi gizo, ga abar taki kwanciya, ya juya gabas da yamma kudu da arewa dik babu sauki, ya rasa mafita ta yadda shi kansa bai san ya aka yi ya zo ɗakin nata ba. Ya kuma yi sa'a yana shigowa ya yi tozali da kyakkyawa flat tummynta a buɗe, cibiyarta a waje, a cikin barci ta mirgina ta janye kayan nata suka yi saba wajen ya bayyana. Ai kara rasa natsuwarsa ya yi, gabaɗaya ya fita a hayyacinsa, shi ne ya zauna a wajen tare da kai hannunsa ya fara shafar tummyn nata yana wani irin sakin numfashi mai ɗumi kuma mai nauyi. Wani irin zabura ta yi ta miƙe zaune na ganinsa da ta yi, hannu bibbiyu tasa ta hau murje idanunta da suka yi jajir, wai so take ta tabbatar ba mafarki take yi ba ko? Ta murje idanun nata sosai kafin ta warosu. Sai dai kuma tana warosu sai a kan fresh face ɗinsa dab da ita, ya matsota sosai tamkar zai shige jikinta. Zabura ta kara yi tare da ɗan ja da baya, muryarta na rawa ga barci ta ce. "Big Bro are you okey? Meyahanaka barci?". Shiru bai amsa mata ba, sai kara matsawa dab sa ita ya yi. Ja da baya ta kara yi tana cigaba da blinking eyes ɗinta, dan har yanzu gani take a mafarki take ganinsa. Shi kuwa cigaba da matsota ya yi yana wani irin jan numfashi har ya hauro saman bed ɗin. Da ya ga ba zata daina ja da baya ba zata iya faɗuwa, sai ya sanya hannunsa ya riko waist ɗinta ta baya, sannan ya kwanto kanta wanda hakan yasa dole ta yi baya ta kwantasaman bed ɗin. Haba ai ya samu abin da yake so, sai ya kwanto kanta ya yi mata rumfa da lion chest ɗinsa, a saman wuyanta ya manna ɗan bakinsa ya hau bata hot sumbata a wajen yana wani irin lumshe idanu. Haba yanzu ta gama tabbatarwa kanta gaske ne ba mafarki bane, dan haka sai ta fara ƙoƙarin rabasa da jikinta tana ambatar sunansa da ɗan ɗaga murya. Sai dai ina, baya jinta. Tsoro ne ya shigeta ta fara bubbuga bayansa da hannunta dikka biyu tana cigaba da kiran sunansa. Ai bata ankara ba sai jin tongue ɗinsa ta yi a saman wuyanta yana wani irin lasheta game da sauke mata wani nannauyar numfashi mai ɗumi. Wani irin juya mata cikinta ya yi, jikinta ya hau kerma tana son yin ihu amma tamkar an rike mata makogwaro. Can kasa sosai ta ji yana faɗin. "Maysh you're too much, please don't say no to me". Yana gama faɗin hakan ya sanya hannunsa a saman kirjinta yana ƙoƙarin laluɓar tula-tulanta wanda hakan ya yi balain razanata da ɗaga mata hankali ya sanya ta daddage ta zunduma wani irin razanennen ihu wanda ya sanya Pretty dake kusa da ita razana har ta kai mata duka a gadan baya tana faɗin. "Wani irin iskanci ne kina barci kina ihu?". Jin duka da kuma muryar Pretty yasa ta zabura ta miƙe zaune tana wani irin haki da nishi ga uban zufa da take haɗawa, ashe mafarkinsa take yi ya zo room ɗinta. Zazzare ido ta fara yi a kan Pretty, wlh zata iya rantsu da ALLAH ba mafarki bane, tabbas shi ne, ya zo ɗakinta, amma to ya aka yi Pretty bata gansa ba? Kuma ya aka yi ya yi gaggawar tafiya da ta yi ihu? Wlh ba mafarki bane shi ne ya zo, tabbas shi ne. Haka ya dinga faɗa a ranta tana ƴan waige-waige ko zata ga alamarsa. Sai dai shiru. Hakan yasa ta ce. "To kila mafarkin ne da gaske". Amma zuciyarta bata aminta da mafarki bane, fatar bakinta ne kawai ya ambata hakan. Nima kuma na ce ba mafarki bane, tabbas da gaske ya zo ɗakin, kuma dik abin da kuka gani ya yi mata, kasancewar Pretty na ɗakin ne yasa ya yi magic ɗinsa ta yadda ba zata iya gansa ba sai Sweetie ɗin ce kawai zata gansa, amma tabbas shi ne ya zo. Sai da ta tabbatar wa da zuciyarta gaske mafarkinsa take yi ne ta wani irin cukule fuska tare da kai hannu ta dakawa Pretty duka a baya ita ma tana faɗin. "To ina ruwanki dani dan na yi ihu? Muryanki ko ɗakinki?". Pretty fa yanzu ta shigo ɗakin ba jimawa, daren jiya gabaɗaya tana a tare da Smart, ɗaki ɗaya suka kwana manne da juna, sai da gari ya waye, bayan ta yi sallar asuba ne, yanzu around 6 na safe ne, shi ne da Smart ya yi barci ta lallaɓa ta dawo, ita Sweetie tsabar mafarkin Big Bro ko in ce tsabar zuwa da Big Bro ya yi yasa ko sallah bata tashi ta yi ba. Wani irin ɓata rai Pretty ta yi saboda Sweetie ta daketa, a kan me zata daketa tin da ita ce babba, dan haka sai sarautar ta motsa, a kule ta daddage ta dakawa Sweetie wani zazzafan mari a kumatu tana faɗin. "Ni sa'arki ce da zan dakeki ki rama?". Sweetie ta ji zafin marin nan har ranta, domin kuwa ga shatin yatsun Pretty ruɗu-ruɗu sun kwanta a kan fuskarta, ta maru babu karya kam. Haba ita ma nan take sarautar ta motsa mata, a fusace ta ɗauke Pretty da wani gigitaccen marin da sai da ya sanya Pretty ta yi baya-baya ta faɗa kasan bed. Cikin kunar rai ta ce. "Saboda kece babba sai ki mun irin wannan dukan da ko uwata bata taɓa mun ba? Ke waye ya taɓa dukanki irin haka? Dame kika fini? Da ɗan minti biyu?". Ranta na tafarfasa sosai ta yi maganar!. Pretty da ta gama hasala har wuya ne ta rarumi lamp na side bed ta rotsawa Sweetie a kai, kan ka ce me sai ga jini ya fara malala daga kan Sweetiy. Zafi da kunan rai yasa ta yi kukan kura ta cakumi wuyan Pretty ta makata da bango, nan suka fara kokawa Sweetie ta shake wuyan Pretty tamkar zata kasheta, yadda kuka san wani bakin shaiɗani ne ya shiga tsakaninsu, yadda suke tsananin kaunar junansu tamkar su lashe juna, amma yau sai ga faɗa daga abu kalilan. Pretty ta fi Sweetie karfi, dan haka akafi cin moriyar Sweetie, Pretty ta yi mata mugun duka ta kuma zubar mata da jini a jiki, ita kuma Sweetie ta fi Pretty zuciya hakan yasa taki janyewa da faɗar, ta ce sai ta rama, hakan yasa suka cigaba da papatawa, dik abin da Pretty ta ɗauka sai ta bugawa Sweetie, tin Sweetie na iya kare kanta har ta fara galabaita ga jini dake ta malala daga kanta ya wanke mata fuska, abin ya haɗe mata over. Wani duka da Sweetie ta dakawa Pretty a gefen cikine ya matukar yi mata zafi da kona mata rai wanda hakan yasa ta zabura ta sanya hannunta ta ɓaɓɓago tv dake manne jikin bango da karfinta, in baku manta ba dik suna da magic, hakan yasa ta iya ɓaɓɓako tv ɗin, da karfi ta daddage zata bugawa Sweetie a kai kenan Sweetie ta sulale kasa bata ko motsi, saboda yadda jininta ya dinga zuba. Ai tana ganin ta sume ta zabura ta yi jifa da tv gefe guda tare da zunduma wani irin ihu da ya jawo hankain kowa a kansu, da gudu ta yi kan ƴar uwar tata tana ambatar sunanta. Kusan a tare Ronnie da Smart suka shigo ɗakin, suna ɗaura ido a kansu har suna rige-rigen nufosu, a gabansu suka durkushe. Ronnie ne ya fara faɗin. "Meyafaru haka Pretty? Meyasameta?". Tana kuka hawaye bibbiyu ta hau faɗin. "Shikenan ni na kasheta, ni na daketa na kasheta". Smart dake ƙoƙarin taɓa saitin zuciyar Sweetie ya ji yana bugawa ne ya yin saurin dakatawa cak jin cewa Pretty ce ta yi mata wannan duka, cikin zafa ya ɗago da kansa ya kalleta yana zaro ido. Kuka sosai take yi bata bi ta kansa ba, sai jijjiga kirjin Sweetie take yi tana ambatar sunanta. Cike da mamaki Smart ya ce. "Ke kika daketa? For what reason zaki yi wa yar uwarki irin wannan duka haka?". Tana cigaba da ruwan hawaye ta ce. "Ban sani ba Yah Omerish, ban san ya aka yi ba kawai ni dai ta dakeni na rama, shikenan muka fara kokawa......". Bata gamasa rufe bakiba suka ga Sweetie ta yunkura ta miƙe zaune, a kan idanunsu gabaɗaya jinin dake zuba a jikinta ya ɓata, ta dawo tamkar babu wani ciwo da ya taɓa samunta, idanunta a ɗan lumshe, a hankali ta warosu a kan fuskokinsu. Zaro ido Smart da Pretty suka yi suna kallonta, shi kuwa Ronnie da yasan waye yayansa ko kaɗan bai razana ba sai ma cewa da ya yi. "Tashi ki yi wanka ki shirya muje in kaiki school, yau sati guda baki je ba". Cike da mamaki ta fara rarraba idanunta a kansu, a natse ta ce. "Yah Omerish, Pretty me kuke yi a nan?". Kara zaro ido Smart ya yi kafin ya kai kallana a kan Pretty wadda ita ma shi take kallo, kansu ya shiga duhu, sai wani irin zazzare ido da suke yi. Sweetie zata sake yin magana Ronnie ya yi gaggawar cewa. "Tashi ki je ki shirya, babu komai". Yunkurawa ta yi ta miƙe tsaye, tana ta kallonsu cike da mamaki ta nufi toilet. Miƙewa Smart ya yi tare da riko hannun Pretty suka nufi waje, bayansu Ronnie ya bi shi ma. Komai na ɗakin ya koma yadda yake tamkar ba'a taɓa komai ba, shi kansa tv da Pretty ta ɓaɓɓako ya koma yadda yake. AFTER SOME MINUTES. Ta yi sallah ta fito shirye cikin uniform ɗinta, ta yi fitinannen kyau, wannan dark purple lips ɗin nata ya sha lips balm yana wani kyalli mai kara ɗaukar hankali sosai, kun san yadda uniform ɗin nan nasu yake da ɗaukar hankali. Ta goyo hannun guda na bag ɗinta, tana rike da jacket na school ɗin a ɗayan hannunta, tamkar wata tauraruwa haka take haskawa. Waje ta nufo tana cigaba da kokwanto a ranta na cewa anya mafarkinsa ta yi, anya ba gaske bane kuwa?. Kai tsaye dining room na parlon kasa ta nufa, nan ta isko Ronnie yana jiranta, tana zuwa ta ɗauki hot coffee dake gabansa yana sha. "Bari in yi wa Big Bro sallama in zo mu wuce, yau iya coffee zan sha". Ta faɗa tana barin wajen. Ba tare da nuna wata damuwa ba ya ce. "Sai kin dawo". Sama ta wuce abinta, dan ba sallama ma take son zuwa yi mashi ba, wai wayau zata je ta yi mashi ya faɗa mata a gaske ya je ɗakinta ko a mafarki. Babu kowa a cikin room ɗinsa, hakan yasa ta nufi balconynsa, yana a zaune saman sofa yana duba ɗayan laptop ɗinsa, kaya yake saye daga China, sabon kamfanin motoci masu kirar lambogini ya fitar da project ɗin a kan a gidana mashi a birnin, akwai special thing da yake shiryawa ta karkashin kasa wanda bai bawa kowa daman sani ba. Yana sanye da short zuwa fararen cinyoyinsa da singlet white daga sama. Fuskarsa ta yi fresh sosai, ya kara kyau, sai dai kallo ɗaya zaka yi mashi kasan yana a cikin damuwa, saboda babu kuzarin kirki a tattare da shi, wannan damuwa kuma tana da alaƙa da tsananin sha'awarta da yake yi. A kusa da shi ta zauna suna fuskantar juna, sofas ɗinsu na kallon juna, tin da ta shigo wajen yake satar kallonta ta wutsiyar ido, gabaɗaya hankalinsa ne ta kara tashi sosai, saboda yanayin uniform ɗin nasu, ga shi bata ɗaura jacket ɗin saman ba bare ya ɗan kara suturta mata jiki. "Good morning Big Bro". Ta faɗa fuska ba yabo ba fallasa. Ta faɗa kuma tana kai cup na coffee ɗan bakinta ta yi sipping. Shiru babu alamar zai amsa mata, saboda gabaɗaya ya ji tamkar an ɗaure mashi tongue. Dama tasan za'ayi haka, so sai bata damu ba, dan haka ta ce bari ta yi abin da ya kawota, ɗan ɗaure fuska ta yi kafin ta ce. "Big Bro meyasa ka zo ɗakina?". Babu wasa a kan fuskarta ta yi maganar. Ko da wasa bai motsa ba, tamkar bai jita ba, ya cigaba da abin da yake yi kawai. "Saboda ka kalli beb ɗin mom ɗinta ta yi kyau ta ci ta koshi shi ne ka je kana shafe mun jiki ko?". Ya ɗan yi mamakin jin kalamanta, amma sai bai nuna kamar ya jita ba. Ita kuma a wani video a wayar Ronnie ta kwashi waɗan nan kalaman, da yake bata ji kuma bata kaddara sai ta zo tana yi mashi. "Hada taɓa mun ɗan kyakkyawan bakina dan kaga ya fi nata kyau ko? To ko ka kyatsa ne?". IDAN ZAKA KASASHETA BATA SAN MENENE MA'ANAR KA KYATSA BA, KAWAI TA FAƊA NE JIN A VIDEON KARUWAN DA TAKE GANI A WAYAR RONNIE ANA FAƊA, KUN TUNA TA TAƁA YIN SEARCHING IRIN VIDEO ƊIN? TO KUN SAN ABIN DA KA TAƁA SEARCHING DA KA SHIGA MEDIA SHI SUKE FARA BAKA, SHIYASA TAKE YAWAN CIN KARO DA IRE-IRENSU, KUMA HAR TAKE HADDACE WASU KALAMAN DA BATA MA SAN MA'ANARSU BA. Ai tana cewa ko ya kyatsa ne sai da ya juyo a miliyan ya kalleta, nan ne fa ta fara rarraba ido tana tinanin me ma'anar abin da ta faɗa. Kawar da kallonsa daga kanta ya yi ya cigaba da abin da yake yi. Ganin hakan yasa ta ce kila ba wani abin mai zafi ta faɗa ba, sai ta cigaba da cewa. "Big Bro to ni bana so, kada ka sake taɓa mun jiki, domin jikina na mijin da zan aura ne kawai, kuma shi kaɗai yake da iko da jikina, kuskure ne wani ya taɓa mashi". Yadda take maganar nan sai ya ji tamkar ta zuba petir a cikin zuciyarsa ta kyasta ashana, ta yaya zata ce jikinta na wani namiji ne?. Ita kuwa da bata ma san yana jin zafin maganar tata ba sai ta cigaba da cewa. "Addinina ya hana hakan, kuma nima bana so, dan taɓa mun jiki tamkar cin amanar mijin da zan aura ne, so nike yi in kaiwa mijina jikina sabuwarta ba tare da wani ya taɓa ba, kuma In Sha ALLAH haka ɗin ne zai faru...........". Bata kai karshen maganar ba sai ji ta yi ya bugata da jikin sofa da take zaune, ya shake mata wuya da karfin gaske ya kuma yi mata runfa da lion chest ɗinsa, take ya fara wani irin huci tamkar zai kama da wuta, dama a kan tsini yake, sai ya kara tunzura. Zazzaro mashi idanu ta yi, jikinta na rawa sosai ta fara kokarin ture shi da hannayenta kamar a kama a karya. Kara shaketa sosai ya yi, idanunsa sun kaɗa jajir. With harsh voice sosai ya ce. "Okey dama kula maza kike zuwa yi a waje? Har ni zaki faɗawa jikinki na wani ne? Ke kin isa? To tin wuri ki faɗa mun waye a cikin ranki tin ban kasheki na fitar da zuciyarki na duba waye a ciki ba!!". Tana son ta ce ita fa bata kula kowa, amma babu halin yin magana, tana son yi mashi bayani ita fa mijin da zata aura take nufi ba wai wasu take kulawa a waje can ba, amma babu dama. Jikinsa na wani irin tsuma ya sake daka mata tsawa. "Ba zaki faɗa mun wanda kike ikirarin jikinki nasa bane?". NI KUMA NA CE TO TA YAYA ZATA FAƊA MAKA BAYAN KA SHAKETA BA HALIN YIN MAGANA?. Daga bayansa muryan Smart ya katse shi da cewa. "Blood lafiya me ta yi maka?". Ya yi maganar tare da karisowa wajensu da sauri. Yana zuwa ya sanya hannu ya fara ƙoƙarin ɓanɓaro hannun Big Bro daga wuyarta yana kara tambayar lafiya kuwa. Haba cikin fushi da zafin rai Big Bro ya ce. "Har ni zata cewa wai jikinta ba nawa bane na wani banza can daban ne! To ta faɗa mun wanene wancan ɗin in ba haka ba in kasheta in ciro zuciyarta in cire koma wanene a ciki!". Tin da ya fara magana Smart ya tsaya cak yana kallonsa, lallai yau dik zafin kishinsa ya tabbatar da ko rabin ɗan uwan nasa bai kai ba, amma kuma ya shiga tinanin cewa to meyasa Sweetie zata ce tana son wani bayan tana da aure? To ko dai basu da aure a tsakaninsu ne? Ya jefawa kansa tambayar cike da zaƙuwar son jin amsa. Sai dai kuma jin alamar Big Bro zai iya yin kisan kai ne yasa shi dakatar da dik wata tinani ya fara ƙoƙarin kwatar Sweetie yana mai baiwa ɗan uwan nasa hakuri. Sai faɗi Big Bro yake yi yana kara nanatawa wai ta ce jikinta na wani ne, a kan me zata ce jikinta na wani ne? To wlh koma wanenen take ikirarin jikinta nasa ne sai ya kashe shi. Kasa kwaceta a hannunsa Smart ya yi, da dai yaga karfinsa ba zai iya kwaceta ba sai ya ce. "Blood bafa jikinta na wani take nufi ba fa, tana nufin naka ne, irin zolayar masoyan nan take yi maka, please ka saketa da bakinta zata faɗa maka, ka saketa kada ta yi mata illah". Cikin tsawa ya ce. "Ai so nike dama in yi mata illar tin da har ni zaka kalla ta ce jikanta na wani ne!! Na wani fa! Kuma a gabana zata faɗi haka!". Cikin tausasawa Smart ya ce. "Ba nawani nace maka take nufi ba, saketa zata faɗa maka da bakinta, na shi ne kike nufi ko sister?". Ya tambaya yana kallonta yadda take zaro ido tamkar zata margaya lahira. Ai bata san lokacin da ta shiga gyaɗa kai sama haɗe da ɗaga gera sama alamar e jikinsa take nufi ba na wani ba. "Yauwa blood ka ji naka take nufi, Please ka saketa". Ya kai karshen maganar tare da sanya hannu ya fara ƙoƙarin ɓanɓare hannunsa daga wuyarta. Da kyar ya iya ɓanɓarewa, sai wani irin huci Big Bro yake yi. Ai da gudu ta yunkura zata miƙe tana wani irin tari. Cikin tsawa ya ce. "School ɗin ma ba zaki sake zuwa ba, daga yau ko wajen main parlor ba zaki sake fita ba". Ya yi maganar yana pointing ɗinta da yatsarsa. Zata gudu ita dai Smart ya yi gaggawar rikota yana faɗin. "Kada ki je ko'ina, tsaya tare da shi, kawai ki faɗa mashi cewa wasa kike yi mashi jikinki nasa ne, dan sanin kanki ne gudunki ba zai sanya ki tsira ba, dan kin fini sanin halinsa". Ya kai karshen maganar yana sakinta dan ma kada shi ma ya samu rabonsa, dan ya lura Big Bro karshe ne a kishi. Muryarta na rawan ta ce. "Wa...... Wasa nike yi, jikina ba na kowa bane face naka". Da kyar ta iya idasa maganar, tana faɗi ta juya zata bar wajen. Cikin tsawa ya kuma cewa. "Ba zaki sake zuwa school ba". Da sauri ta juyo ta sauke kallonta a kan Smart. Jinjina mata kai ya yi alamar ta ce wa Big Bro to kada ta damu. Jikinta na kerma ta ce. "Badamuwa na yarda". Murya na sarkafewa ta faɗa. Dik da haka bai huce ba, sai huci yake yi ya ce. "Da su waye kike alaƙa a school ɗin dama?". With harsh voice ya yi maganar. "Babu kowa, ni bana kula kowa". Yasan bata karya, gaskiya kullum take faɗe, amma dik da haka zuciyarsa bata yi sanyi ba, ya koma saman sofa ya zauna yana cigaba da huci. "Kawo mashi ruwa mai sanyi sis". Smart ya faɗa yana kallon Big Bro. Da sauri ta wuce ta nufi dispensar dake wajen, ruwa mai sanyi ta ɗebo ta kawowa Smart. Da hannu ya nuna mata Big Bro a kan ta kai mashi, tsuru-tsuru da ido ta yi tana tsoron zuwa. "Babu komai je ki kai mashi". Ya faɗa ƙasa-kasa ta yadda Big Bro ba zai ji ba. Nufarsa ta yi kirjinta na dukan uku-uku. Sai dai ko da ta karisa ta miƙo mashi ruwan bai karɓa ba, sai kallo da yake binta da shi mai wuyar fassaruwa. Juyo da kallonta a kan Smart ta yi, alama ya yi mata da ta zauna ta bashi ruwan a baki zai sha. Cike da tsoro ta zauna a gefensa, muryarta na rawa ta fara ce mashi ya yi hakuri ba zata sake ba kafin ta kai mashi cup ɗin sai tin ɗan bakinsa. Juyo da kallonsa a kanta ya yi, ta wani marairace mashi fuska tamkar zata yi kuka. ANYA ZAI SHA WANNAN RUWA KUWA? RAN MAZA YA ƁACI, WAI NA CE BA, IN BAN DA ABINKA BIG BRO ME NA DAMUWA DAN TA CE JIKINTA NA MIJINTA NE? ME A CIKI TIN DA KAI BAKA TAƁA CEWA KANA SONTA BA, TO NI NA FAƊA JIKIN SWEETIE MALLAKIN MIJINTA NE. NA YI NAN🥱 Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 -------------------------------------------🔥♥️ ZABUWAR DUNIYA STEP ONE!.🔥🔥🔥 Shiru ya ɗan kura mata ido na ƴan sakanni kafin ya ɗauke kansa yana sauke numfashi a hankali-hankali. Jiki ba kwari ta miƙe tsaye ta nufi sauka wajen, Smart ya so dakatar da ita, amma sai ya yi zurfin tinanin cewa ya kyaleta shi ne zai sa Big Bro ya fahimci kuskurensa, idan yazama kullum zai yi abu kuma shi za'a baiwa hakuri to ba shakka ba zai taɓa fahimtar yana yin kuskure har ya koyi gyaran kuskurensa da bada hakuri ba, dan haka Smart sai ya bi bayanta, a ɗaki ya iskota, nan ya ce mata ta ja baya da Big Bro, kada ta sake matsawa kusa da shi sosai, saboda yana son su koya mashi sanin kuskure da kokarin yin gyara. Ta ji daɗi sosai, dan haka sai ta ja baya da shi, kwata-kwata ta daina bari suna yawan haɗuwa, za dai ta je wajen cin abinci, amma ko kallonsa bata yi, yana sane da ita amma bai nuna kamar yasan fushi take yi da shi ba, shi dai tun da yana samun damar ganinta shikenan bai wani damu dan bata yi mashi magana bayan gaisuwa ba. Shi ma sai ya mayar da hankali kan shirye-shiryensa na tafiya Crown of Power da kuma tsara tsari a birnin nasa kafin ya tafi, da wanda yake son ya kula mashi da birnin kafin ya dawo, bai sake bi ta kanta ba. Daga ita har Smart sun sha mamakin ganin yadda bai nuna damuwarsa a kan fushin da ta yi da shi ba, ko ɗago ido ya kalleta baya yi, zaka rantse da ALLAH baya a empire ɗin ma gabaɗaya harkar gabansa kawai yake yi, harta Smart ya daina kula, Ronnie kawai yake kula kuma yake magana da shi. Ana saura kwana biyu zasu tafi Crown of Power ma kwata-kwata daga ita har Smart sun daina sanya shi a idonsu, kuma yana a cikin empire ɗinsa sabo, sai dai basu sani ba, sun sha nemansa a nan har suka gaji, da suka tambayi Ronnie sai ya ce masu kada su damu zai dawo, shi Ronnie yasan in da yake sarai, amma ya ki faɗa masu saboda Big Bro ya ja mashi kunne. Wai su suke fushi da shi suke ɓoye mashi sai ya gwada masu ya fisu iyawa da yake ɗan duniya ne, dik wani motsinsu a kan idanunsa suke yi, ya fisu sanin ya suke kwana ya suke tashi, dikkansu yana kula da su fiye da yadda yake kula da kansa, dan ko zamewa suka yi zasu faɗi sai ya taimaka masu, amma su basu samu damar ganinsa, dik sun shiga damuwa, harta Smart mai bada shawara ya sha jinin jikinsa, shi bai san cewa dik abin da zai faɗa mata Big Bro yana jinsu ba da ba zai bata shawarar ta juya Big Bro baya a fili ba, shi ya ɗauka sirri suka yi, to ga shi yanzu bata juya mashi baya ba shi ya ladabtar da su dikkansu biyu, suna kuka suna danasai. Ita dai Pretty ko a jikinta tin da ba Smart bane ya ɓata, dan haka ta ci ta koshi ta kwanta ta yi barci, shi ko Smart sai fama yake yi yana neman Big Bro a yayin da Big Bro yake ganinsu. Siririn tsaki ya ja kafin ya ce. "Black Tiger bai yi lalacewar da karamun halitta irinka zai shiga gonarsa ko ya ce zai iya nemansa dan ya matsa daga idon mutane ba". Ya faɗa yana shafa kyakkyawan hair ɗinsa, yana daga kwance a saman wani irin mahaukacin bed wanda zaka yi zatan ba'a kan katsa yake ba, wai wannan ma fa ba'a kammala kyara sabuwar empire ɗin ba. Da zallar gold aka yi wannan bed ɗin, sai wani kyalli yake yi yana ɗaukar idanu, ga wasu kwayayyen lantarki dake haskaka headboard ɗin suke karawa gold ɗin kyalli. Shi dai Smart bawan ALLAH ya yi sansanin wannan shawara wlh, dik ya shiga damuwa over, dik da ya kasance a ko'ina ana kiransa Smart, to fa birnin Black World da kuma Big Bro sun sa ya ji tamkar shi ɗin bashi da wani kaifin ƙwaƙwalwa, dan karamin abu yana gagararsa warwarewa a birnin nan, birnin tana da sarkakiyar da bai saba gani ba, yana shiga ruɗani wani lokaci, har yau ya rasa gane alkiblar wannan birni, shi dai ga shi nan ne yana ganinsu kawai. A daren washegarin da zasu tafi Crown of Power dukkansu babu wanda ya iya cin abinci, saboda damuwar in da Big Bro ya ɓace, shi dai Ronnie ya ci ya ƙoshi abinsa, amma sun bashi tausayi har ya ji tamkar ya sanar da su in da Big Bro yake, sai dai tina cewa ran yayansa zai ɓaci idan ya faɗa ne yasa ya daure ya kawar da kansa. Haka suka kwana da yunwa, da safe suka karisa shiryawarsu, suka tsala wanka, suka shirya cikin kayan sarauta irin na birnin wanda duwatsun jikin kayan kaf da ɗanyar gold aka yi su, covers na kafarsu kawai zata bada amsar daga Black World suka fito, saboda gold dake a jikin takalman. Shi kansa Big Bro ya shaida sun yi kyau sosai, sai dai Smart and Sweetie damuwa ce karara a kan fuskarsu, shi Smart tsoronsa shi ne kada ace Big Bro ba zai bisu ba! Ita kuma Sweetie damuwarta shi ne kewarsa, dik yana ganinsu kuma ya karanci dik tinanin dake a cikin zuƙatansu, sai dai ko a jikinsa, bai damu ba ya hau nasa shirin. Sai around 11 na rana suka kammala, sannan wasu shirga-shirgan motoci suka zo suka ɗaukesu zuwa BLACK TIGER INTERNATIONAL AIRPORT. Har suka isa airport hankulansu a tashe, dan babu Big Bro. Like wow, gaskiya Smart ya kara sarawa karfin arzikin ɗan uwan nasa, a lokacin da suka ga jiragen da zasu tafi da su Kingdom of Power sai da suka girgiza, wani dankareran jirgi ne wanda kana ganinsa kasan ya amsa sunansa, ga shi sabo fil yana ta kyalli, kun san dik jiragen birnin da tambarin Black Tiger a jikinsu ko? To haka shi ma wannan, da ɗanyar gold aka yi zanen sunan. Ga wasu kananan drones na yaki guda shidda waɗan da zasu zama tsaro ga jirgin nasu, sai wasu jet biyu da zasu wuce gaba kafin jirginsu ya ɗaga. Smart ya kara jinjinawa karfin ikon da Big Bro yake da shi, yanzu ya kara tabbatarwa da kansa ashe dole Big Bro ya yi balain ji da kai da izza, ashe dai ba ƙaramin abin ya taka ba, a dole masu jajayen kunnuwa su ɗaga mashi kafa, sai sun jira wlh. Gabaɗaya ma'aikatan airport ɗin robot ne kun sani, dan haka suka bubbuɗewa su Smart kofofin motocin suka fito, yana rike da hannun Pretty da ta sha kwalliya tamkar wata gimbiya, ko da yake ita ce gimbiyar Crown Of Power, tab Pretty gimbiya, kamar yadda Mommah take gimbiya idan King ya sauka Smart ya hau mulki fa mommah zata koma Queen mother Pretty ta zama tauraruwa da ake ji da ita, to ALLAH yasa kafin wannan lokaci shirme da yarinta ya bar kanta ta natsu ta san kasa guda ce a hannunsu. Rike da hannun Sweetie Ronnie ya fito suka nufi jirgin, an kammala komai, dan haka suna shiga basu wani ɓata lokaci ba ƙananan jet ɗin suka tashi da kamar mintuna 20, sannan drones na yaki biyu suka ɗaga kafin jirginsu ya ɗaga, drones na yaki huɗu suka rufa masu baya. Smart ya kara shiga damuwa da tsoron rashin ganin Big Bro har suka tashi, amma Ronnie ya ce mashi kada ya damu In Sha ALLAH tare zasu ce Kingdom ɗin ya kwantar da hankalinsa. Yasan yanda Ronnie yake da Big Bro, amma dik da haka hankalinsa bai kwanta ba har duka keta hazo. To mu dai sai dai mu ce a sauka lafiya, hmmmm AN ZO IN DA NIKE SON A ZO, BIG BRO A KINGDOM OF POWER, YANZU LABARIN ZAI CANZA SALO, YANZU ZAMU DAWO TAFIYA KAN MUKAKKIYAR HANYA KAN LAYI GUDA, SHIYASA NA CE MAKU MUN SHIGA SABUWAR DUNIYA, SABUWAR DUNIYAR NE DA GASKE, YANZU KOMAI ZAI CANZA, YANZU WASAN ZAI FARA, FATAN SU ISA LAFIYA AKWAI KALLO!. CROWN OF POWER.🔥🔥 Har karfe 9 na safe bata farka daga barci ba saboda jiya bata yi da wuri ba, tana a cikin barcin ta ji ana tattaɓata ana ambatar sunanta. A hankali ta waro idanunta da suka yi jajir suka yi luhu-luhu, kai tsaye sai a kan Mahnoor ta saukesu, ɗan tsuke fuska ta yi kafin ta ce. "Adda Mahnoor me haka zaki tasheni daga barci". Ta yi maganar tana miƙewa zaune. "Tashi zaki yi mu je mu duba jikin aunty Sareena bata da lafiya". Siririn tsaki ta ja kafin ta ce. "To ni ina da wata alaƙa da ita ne da zanje dubata? Ta mutu ma mana". Ta faɗa tana ɗaure fuska. "Ni kam Mahreen yaushe zaki yi hankali ne? Ta mutu fa kika ce?". Shiru bata yi magana ba, ɗan ɗaure fuska Mahnoor ta yi. "Tashi ki yi wanka mu je mu dubata, kowa yana part ɗinsu ban da mu". Tana turo baki ta ce. "To wai me ya sameta ne ma?". Har ta manta ɗanyen aikin da ta yi wai tana tambayar meyasameta. A natse Mahnoor ta ce. "Momma ta ce gamo ta yi, ba'a dai san me ya sameta ba, dan har yanzu bata farfaɗo ba, idan aka sanya mata ruwa ta farfaɗo sai ta fara ihu tana faɗin ta tuba, daga nan sai ta sake suna, an rasa gane me yake damunta, yanzu dai ankira Dr yana dubata". Sai yanzu ta tina abin da ta yi, tamkar zata watse da dariya sai kuma ta daure da cewa. "Bari in yi wanka in yi sallah sai mu je in dubata". Ɗan zaro ido Mahnoor ta yi. "Kina nufin baki yi sallar asuba ba?". Kai ta gyaɗa ba tare da ta yi magana ba, daga haka ta sauko kasan bed ɗin ta nufi toilet. Bayanta Mahnoor ta bi da kallo tana mamakin halin Mahreen, yarinya kamar rainon aljanu? Miƙewa ta yi ta koma bedroom ɗinta dan ita ma ta shirya. A can ɓangare kuwa, Obaid ne zaune a tsakiyar gadonsu yana bin ƙafafuwansa da kallo, idanunsa a kan shatin bulalar da suka kwanta mashi sun yi ruɗu-ruɗu. Da farko da ya farka daga barci ya zaci mafarkin mala'ika ya yi, ya kuma yarda a kan mafarkin ne, sai yanzu da gari ya yi haske ya ga zanen mulala a jikinsa ne ya fara tantanama a kan mafarki ne, a jikinsa yana jin wani ne ya yi mashi wannan abin. Datse idanunsa ya yi yana ƙoƙarin tuna abin da ya faru, yana ɗan shafa kafar tasa a hankali-hankali. Omaid ne ya shigo ɗakin bakinsa da sallama, da sauri ya ja wandon jikinsa ya rufe zanen bulalar dan ma kada Omaid ya gani, saboda ya ce ba zai sanar da kowa ga abin da ya gani ba. A kusa da shi Omaid ya zauna yana faɗin. "Kazo mu je duba Aunty Sareena". Wurga mashi kallo da waɗan nan shaggun idanun nasu ya yi kafin ya ce. "Love baka ji wani abin a jikinka ba?". Kallo shi ma Omaid ya wurga mashi kafin ya ce. "Na ji like an zaneni da bulla daren jiya, kuma na ji kamar kirjina yana bugawa da sauri-sauri kamar ina cikin tsoro, amma beb ta ɗauke mun hankali da yasa bai bi ta kan hakan ba, da wani abin ne?". Da sauri ya girgiza kai alamar babu, yanzu yagama tabbatarwa ba mafarki bane, dan idan a mafarki ne wlh Omaid ba zai ji a jikinsa ba, dole zahiriya ce, dik abin da Omaid ya faɗa halin da ya tsinci kansa a daren jiya kenan, ya ji tsoro kuma zuciyarsa ta yi ta bugawa da sauri-sauri, lallai wani ne ya yi mashi wannan abin, to waye? Ya jefi kansa da tambayar da babu mai amsa mashi. NI KAM NA CE GASKIYA YARAN MOMMAH GIFTED ƊIN NE DA GASKE, KUNGA WATA BASIRA! HAR YA GANO BA MAFARKI BANE! MAHREEN ALLAH YA CECEKI, DAN WLH IDAN OBAID YA KAFA RANSA A KAN BINCIKE CIKIN ƘANƘANIN LOKACI ZAI GANOKI, UHM NA DAI YI SHIRU!. Ganin ya yi shiru ne yasa Omaid ya fara binsa da kallon tsab. "Ya kamar baka yi sallar asuba ba? Kamar yanzu ka tashi ko?". Cewar Omaid, saboda ya ga ɗan uwan nasa gabaɗaya a hargitse. Kwarai yanzu ya farfaɗo daga suman, fitsarin da ta yi a jikinsa ma har ta bushe kamar bai yi ba, shiyasa ma bai san ya yi ba. "Yanzu na tashi, barcin yau ta yi nauyi dayawa, amma kai ma ya kamar ba a nan ka kwana ba?". Jinjina kai Omaid ya yi. "Ba'a nan na kwana ba, almost 4 na asuba ina garden, da na fito na wuce masjid, daga nan na wuce room na mommah na kwanta sai yanzu na tashi ne nike samun labarin Aunty Sareena bata da lafiya, shi ne na zo in yi wanka mu je dubata". Ɗan yarse ne fuska ya yi kafin ya ce. "Meyasamu Aunty Sareena ɗin?". Omaid yana miƙewa tsaye ya ce. "Gaskiya ban sani ba, amma bari in yi wanka sai mu je mu gani". Da sauri Obaid ma ya miƙe yana faɗin. "Sai dai mu yi wankar tare, dan ba zan iya jiranka ba". Uhm kuruciya za'a kirasa ne ko tsananin kaunar juna? A tare dai suka shiga toilet ɗin suka yi wanka, suka kuma fito a tare, suka shirya cikin shiga iri ɗaya, sannan Obaid ya tada sallah dan biyan asuba ɗinsa. Shi kuma Omaid ya haye saman bed dan ya jirasa. Bayan ya kammala suka tafi a tare zuwa side ɗin uncle Abbas. A can ɓangaren kuma Mahreen tsantsara shigarta ta yi cikin wandon jeans baki da riga long sleeve fara, ta ɗaura jacket mai girma zuwa gwiwarta kasancewar ana sanyi, ta sanya hular jacket ɗin a kanta, ta yi masifar kyau kam over to over. Ta fito ta nufi room ɗin Mahnoor, dama ita take jira, tana zuwa ta ce su tafi. Fitowa suka yi, suka sauko parlon kasa zasu fita kenan suna ci karo da guyson da ya fito daga ɓangaren king. Cikin sanyin murya sosai fiye da ko yaushe ya ce. "Ina kwana Aunty Mahnoor". Fuska a ɗauke da murmushi ta amsa mashi da. "Lafiya lou Yah Omar ka kwana lafiya". Alhamdulillah ya amsa mata da shi kafin ya mai da kallonsa a kan Mahreen da ta tsaresa da kallo, a ranta ta ce shi dai yana son farar jallabiya, kuma tana yi mashi mugun kyau. Nufar waje Mahnoor ta yi tana faɗin. "Mahreen baki iya gaisuwa bane ko?". Tana turo baki ta rufa mata baya kafin ta ce. "Kanin nawa zai gaisar? Shi yakamata ya gaidani tin da ni auntynsa ce, yaro ne fa karami....." Bata idasa rufe baki ba ya kai hannu ya damko hannunta, take yanayinsa ya canza, ya ɗaure fuska tamkar bai taɓa yin dariya ba. Daidai lokacin Mahnoor ta juyo zata yi mata faɗa, ai tana ganin ya damketa tasa kai ta yi waje abinta, addu'a ma take ALLAH yasa ko marika biyu lafiyayyu ya sakar mata kila ta dawo daidai, ina ba iskanci ba mutum ya baki almost 7 years ki ce wai yaro ne ƙaramin kaninki, hmmmm. Dakatawa ya yi sai da Mahnoor ta fita sannan ya ce. "Mekika ce?". Yadda ya yi magana a Omar ɗinsa ya yi ta ba guyson ba. Dik da taga babu wasa a tattare da shi hakan bai hana mata ta ce. "Kai yaro ne na ce, ba zan gaisheka ba sai dai ka gaisheni". Haba wani irin kululun bakinciki ne ya tsaya mashi a maƙoshinsa, tin da take ce mashi kaninta bai taɓa damuwa ba, amma yau da ta kirasa da yaro abin ya yi balain bakanta mashi rai, wai yaro, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, gaskiya ta kure hakurinsa yau, tinani ya shiga yi a kan me zai yi wa yarinyar nan ta san cewa akwai banbanci, wlh har wani ja idanunsa suka yi alamar ransa ta ɓaci sosai. Daidai lokacin Jaish ya shigo parlon bakinsa a ɗauke da sallama, hakan yasa guyson ya saketa tare da juyo da kallonsa a kan yayan nasa. Da gudu ta yi waje tana faɗin. "Saboda na ce maka yaro shi ne kake haɗe rai? To na faɗa yaro ne kai karami ma kuwa wanda baka wuce in goyaka ba". Haba ai wani irin yawu ya haɗiye wanda har sai da Jaish ya ji sautin haɗiyar, ido cikin ido suka kalli juna da Jaish na ƴan sakanni kafin Jaish ya ce mashi. "Ka yi hakuri". Shiru bai amsa ba, yana dai kallonsa bai kawar da ido ba. Matsawa dab da shi Jaish ya yi tare da riko hannunsa da nufin ya yi mashi magana kawai sai gani ya yi guyson ya sake mashi jiki gabaɗaya ya yi....... Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 -------------------------------------------🔥♥️ ZABUWAR DUNIYA STEP ONE!.🔥🔥🔥 Shiru bai amsa ba, yana dai kallonsa bai kawar da ido ba. Matsawa dab da shi Jaish ya yi tare da riko hannunsa da nufin ya yi mashi magana kawai sai gani ya yi guyson ya sake mashi jiki gabaɗaya ya yi ƙasa zai kwanta Jaish ya yi zafan rikosa da kyau yana kallon fuskarsa da yadda ya fito da tongue ɗinsa waje ya datseta da hakwaransa tamkar zai cire harshen nasa. Nisawa Jaish ya yi kafin a fili ya ce. "Babbar magana, aiki ya dawo baya". Ya faɗa tare da gyarawa da kyau, ya ɗan duka ya saɓi guyson a saman shoulder ɗinsa ya juya da shi izuwa part na mommah. Tana zaune a saman wannan shinfiɗa tata ta manyan ƴaƴan sarakuna kuma gimbiyoyi da ake ji da su kuyangarta dake yi mata hidima bayan tafiyar Mama Haulat ta shigo bakinta a ɗauke da sallama. A natse momma ta amsa mata, ta haɗe cikin wani dandatsetsen alkyabbarta mai balain kyau da ɗaukar ido. A gabanta kuyanga Salma ta tsugunna tare da neman izinin yin magana. Go ahead momma ta bata tana mai binta da kallo, muryarta na ɗan rawa ta ce. "Prince Jaish ne yake neman iso cikin gaggawa". Kallan hakan ta fuskar basira Momma ta yi kafin ta ce. "Yi mashi iso". Ta faɗa a cakin ranta tana fatan ALLAH UBANGIJI yasa lafiya, dan yadda ta ga Salma take zazzare ido da wuya idan ba wani tashin hankalin ta gani ba. Da sauri Salma ta tashi ta nufi waje har kamar zata kifa. Tsaye ta isko Jaish kamar yadda ta barshi bai motsa ba, a gabansa ta zube gwiwowinta kafin ta ce. "Tanai maku iso". Ai yana jin haka bai tsaya bi ta kanta ba ya yi gaggawar raɓata ya wuce ciki. Bakinsa a ɗauke da sallama ya shigo ciki, momma na ganinsa ɗauke da guyson bata san lokacin da ta miƙe tsaye tana faɗin. "Jaish lafiya kuwa?". Bai yi magana ba har sai da ya kwantar da shi flat a saman lallausan shifiɗar tata, sannan ne ya ɗago da kansa ya kalleta, a natse ya ce. "Ba lafiya ba, i think Omar ya koma Omar ɗinsa na ainahi ne, ɓata mashi rai aka yi ya yanke jiki ya faɗi, ga shi ya datse harshen nan nasa da yake yi a baya". Zazzaro ido momma ta yi a kan fuskar guyson, yana datse da harshensa a waje ya sume, take harshen tasa ta yi jajir tamkar jini ya taru a cikinsa. Kun san akwai mutane masu irin wannan ɗabi'a ta zafin zuciyar, idan zuciya tai masu yawa ko duka zasu yi sai sun fito da harshe waje su datse da hakwara da karfi, so dazarar anga sun fito da harshe waje sun datse da hakwara ma za'a gujesu saboda an san bakar zuciyar ta motsa zasu yi mugunta ne. Guyson yana da balain zuciya fiye da yadda kuke tunani, ga shi da saurin hawa, baya sauƙa ta daɗi, sannan in ransa ta ɓaci fita yake out of control, a wannan point ɗin zai iya aikata komai ba tare da ya sani ba, sai zuciyar ta sauka yake iya fahimtar ya yi kuskure. Zuciyar Omar sak na Big Bro, basu da wata banbanci, dan dai shi yaro ne kawai, sannan shi ɗaya ne ba su ƴan biyu ba, kun san ƴan biyu nasu ya fi tsanani. Tun guyson yana da shekaru biyar a duniya kakansa mahaifin momma, wato Husaini Akka King Badeen kenan, ya fahimci guyson mutum ne mai bakar zuciya sosai, baya da tsokana, amma ida ka shiga gonarsa zaka yi danasanin zuwanka duniya, ya fita daban da sauran yara, silent yake, da King Badeen ya fahimci hakan sai ya sanar da Momma cewa dik cikin ƴaƴanta babu mai irin zuciyar wannan yaron, kun san dik shi ya renesu ban da Smart da Big Bro, so yasan halinsu Omaid dikka. Nan ne ya fahimci guyson yana da banbanci da su nesa ba kusa ba, ya ce mata in aka barshi haka ya taso za'a samu gagarumin matsala, mutumin da in manya suka yi mashi faɗa saboda tsabar zuciya suma yake yi, dan a tarbiyarsa bai taso an koya mashi yi wa manya rashin kunya ba, dan haka idan suna yi mashi faɗa dole ya shanye wanda haka take iya tunzura zuciyarsa ya datse harshe waje ya sume, tin fa yana yaro ake magana, akwai lokacin da ya datse harshen nan a waje ya yi wa Omaid wata duka a bayan kunne, duka ɗaya sai da Omaid ya suma, shiysa a lokacin da sun gansa ya fito da harshe waje ya datse zasu yi ta kansu, wannan dalilin yasa King Badeen ya ce wlh za'ayi bakin mugu sosai idan aka barshi ya taso a haka, dan ma yana da tarbiya, dan haka dole a sassauta mashi wannan zuciya. Wannan dalilin yasa King Badeen ya haɗa mashi wata magani, kun san sarakuna da magunguna na 5 and 6, sun haɗa mashi maganin kashe zafin zuciya sai dai kuma zuciyar ta yi sanyi sosai, ya koma kaman rago, baya son yawan magana, za'ayi ta yi mashi abu yana shanyewa, ya zama kuma hakurin tasa ta yi yawa over to over, amma da yake karfi a jininsa take, har yau idan ya ce zai yi faɗa ba karamar fafatawa ake yi da shi ba, sai dai za'a jima ba'a ga faɗarsa ba, sai an kaisa bango an kuresa. Batu kan ciwon cikinsa kuma wani abin ne na daban wanda ya zo ya tadda kashe mashi zuciya da suka yi, sai abin ya haɗe mashi yasa har yake kukan wannan ciwo, amma da Omar na farko ne wlh dik azabar ciwon cikin nan zai iya shanyewa ba zai yi kuka ba, sai dai sun raunata zuciyarsa sosai da baya iya jurewa, bawan ALLAH. Kaɗan kenan daga abin da ya faru da Omar namu na amana a baya, mu cigaba a hankali komai zai warware. Da sauri momma ta nufi wajen dressing room ɗinta. Jim kaɗan ta fito ɗauke da wani kwalbar magani, Jaish dake tsaye ne ya miƙa mata hannu, miko mashi ta yi ya karɓa, a gaban guyson ya tsugunna tare da warware marfin kwalbar ya ajiye a gefe. Sannan ya ɗago kan guyson ya ɗaura a saman laps ɗinsa, Momma kuma ta koma gefe saman kujerar dake kan shinfiɗar ta zauna tana binsu da kallo. Sau ɗaya ake bashi maganin a shekara, da shekara ta yi karfin maganin zai mutu sai an sake bashi wani in ba haka ba ya koma asalin yadda yake. BAN SO ACE SUN SAKE KASHEWA GUYSON ZUCIYA BA TARE DA YA LALLASA MAHREEN YA KOYA MATA HANKALI BA, AMMA BA KOMAI, 99 DAYS FOR THE THEIF ONE DAY FOR THE OWNER, AKWAI RANDA ZAI KAMATA NE, SOON ZASU DAINA KASHEWA GUYSON ZUCIYA IDAN BIG BRO YA ZO, DAN KUWA ZASU GA ASHE MAI IRIN ZUCIYAR GUYSON SHI AKE SO, TIN DA GA DAI BIG BRO YA GIRMA DA IRIN ZUCIYAR BAI YI ƁARNA SOSAI BA, KUMA INA JIN A JIKINA BIG BRO BA ZAI BARI SU CIGABA DA KASHEWA ƊAN KANINSA WANDA YA GAJESA ZUCIYA BA ATO. UHM KU DAI MU JE ZUWA. Sai da suka tabbatar da sun sanyaya mashi zuciya sannan Jaish ya ɗaukesa sai saman bed ɗin momma ya kwantar da shi, yaron da tin tasowarsa ko da sunan wasa baya murmushi, amma sanadiyar wannan magani da suke bashi suka kashe mashi zuciya ya zama mai murmushi sosai, kuma ta yadda zaku san guyson ya fita daban, ko a ɓangaren karatu, ya fi su Omaid kaifin ƙwaƙwalwa da basira, ga zunzurutun zallar madarar ilimi boko da arabiya gabaɗaya ya haɗe, ɗan baiwa tamkar Big Bro ɗinsu. -------------------------------🔥 Ita kuwa Mahreen kai tsaye side na Uncle Abbas ta nufa hankalinta a kwance, nan ta isko su Mahnoor, Dr ya yi kokari Sareena ta farfaɗo daga suman da ta yi, nan fa aka hau kallon kallo ana tambayar me ya sameta jikinta ya yi zanen bulala ruɗu-ruɗu haka?. Sai dai anyi mata tambayar duniyar nan kaf bata iya bada amsa ba, tsoro da shakkar amsawar ma take yi, saboda tana ganin tamkar idan ta faɗa aljanar zata sake dawo mata again, shi ne ta ja baki ta datse gam abinta, tana wani irin kunkuni kasa-kasa. Hegiya Mahreen da ta san komai sai ƙoƙarin danne dariya take yi, sai ma da su Omaid suka shigo ɗakin, tamkar zata saki fitsari a wando saboda dariyan da ya ciyota, da ta ga Obaid babu abin da ya zo mata ranta in ba Marrabuka da ta ce mashi a daren jiya ba. Ai tana tina wannan ta watse da dariya har da ɗan dafe ciki. Sai da Mahnoor dake a kusa da ita ta taɓata ne ta farga ashe a wajen dubiyan marasa lafiya ta zo, take ta shanye dariyar ta natsu tsit tana kallonsu, su kuma suna ta faman tambayar Sareena meyake damunta? Bama su lura da su su Mahreen ɗin ba. ----------------------🔥 Tsawon kwanaki uku Sareena tana jinya kafin ta dawo normal, a waɗan nan kwanaki ukun Obaid sai ƙoƙarin gano wanda ya yi mashi wannan ɗanyen aikin yake yi, sai dai bai kai ga ganowa ba, amma yana dab da ganewa, saboda ya tina wasu abubuwa da ya gani a jikin wanda ya yi mashi, cikin abin da ya tina har da jallabiyar dake a jikanta wanda kuma in har ya canka daidai to jallabiyar guyson ne, dan shi kaɗai yake sanya irinta a gidan, tasa daban da ta kowa dama, very soft and babu design na kwalliya ko kaɗan a jikinta, su nasu akwai design, dan haka yana kyautata zatan jallaniyar guyson ne, amma yana son tabbatarwa kafin ya je kai tsaye ga next plan ɗinsa. Ita kuwa Mahreen tana can tana ƙoƙarin shirya masu wani abin, dik da ta ga Sareena ta yi laushi, amma hakan bai yi mata ba, so take ta kara mata wani azaba, yanzu Sareena bata walaƙanta su Zee sosai, sai dai bata shiga harkarsu sam-sam, ko magana baya haɗasu, da farko dai tana mutuntasu, amma tin da Obaid ya ce mata yana zargi wannan abin shirya masu aka yi, saboda ya ga zanen bulalar jikinta irin nashi, sai ya ce mata wlh su biyu aka shiryawa wannan abin, kuma ya sha alwashin sai ya nemo koma wanene ya aikata masu wannan aikin, idan ya kamasa sai dai uwarsa ta haifi wani wlh. Ta so ce mashi tana zargin Mahreen, saboda ita kaɗai ce ta taɓa faɗa da ita, amma saboda tsoron balain Mahreen yasa ta ja baki ta yi shiru, kada azo ayi bincike ya zamana ba Mahreen bane balai ya dawo sabo a tsakaninsu, wannan dalilin yasa da ya ce mata ko akwai wanda take zargi ta ce mashi babu kowa, ta rufawa wanka asiri, and tasan waye Obaid sai ya nemo koma wacece very soon shiyasa bata ce Mahreen take zargi ba. Ita kuwa Heleena tin da ta zo bata fita waje ba, tana part na Momma, bata saba da hayaniya da shiga jama'a ba, kun ga gidansu daga ita sai Smart and iyayensu suka taso, kuma shi ma Smart ba wai sun yi rayuwa kaman yaya da kanwa bane, kun dai ga irin rayuwarsu, kowa yana side ɗinsa, to haka suke har zuwa lokacin da suka rabu, so ta saba rayuwa ita kaɗai a ɗaki, yanzu ko abinci a ɗaki ake kai mata, tin dai da ta zo bata fito ba. Chuchu and Jawad suna can suna fama da jarabarsu, har yanzu kuma Chuchu dai shiru babu ciki, shiyasa yanzu Jawad ya fara shiga damuwa sosai, har yana shirin ɗaukarta su je Dubai su ga likita, dan ya san waye a cikinsu yake da matsala. A ɓangaren Mahnoor da Jaish ma dai har yanzu basu samu ciki ba, zargin Jaish ba gaskiya bane ba, bata da komai kawai kulawace take samu yasa ta kara kyau, ciki kam shiru babu, amma shi Jaish bai wani damu sosai ba, dan ya san ALLAH yake badawa a dik time da ya so, kuma yana son yara sosai, karfin tauhidi ne yasa baya nuna damuwa sosai. Aneesa da Yah Rizwan soyayyarsu ta yi karfi sosai ta yadda har King ya san da zancen, sai dai Mama bata sani ba, dan ba zata yarda ba, zata ce bata son Rizwan, kada ku manta a lokacin da za'a aurawa Aneesa Jawad ta ce ba zai yiwu ba, bata son haɗa jini da uncle Abbas, shiyasa King bai sanar da ita bama, dan yana fama da kansa bayan son ta kara mashi zafi a kan zafi. ------------------🔥 A yau Sharifat ta diro a Kingdom of Power cike da ɗaukin son ganin Ramish da kuma shukawa Leesharh rashin mutunci bayan bata san cewa yanzu Leesharh princess take ba, bata ma a kingdom ɗin. Tin da ta diro take tambayar kawarta Sareena ina Ramish, sai dai su ce mata ta duba side ɗinsa kila yana a ciki, shakkar zuwa wajen take yi yasa ta ce Sareena ta rakata, amma ita Sareena ta ce ba zata je ba, dan basa shiri ko kaɗan. Guyson tin da momma ta bashi wannan magani ya sake komawa yadda yake, shiru-shiru mai hakuri da kamala, ga sanyin hali, sun sake kashe mashi zuciyar again. Ya dawo jure dik iskancin da Mahreen take yi mashi, yana hakuri da ita, in short ma kome take yi burgesa take yi kamar da, sai ya yi ta kallonta yana murmushi kawai, sai dai daga wannan rana bata sake gigin ce mashi yaro ba, dan Jaish ya yi mata faɗa sosai, ya ce in ta sake ce mashi yaro sai ya zaneta, dan ya tambayeta me ta yi mashi ya ɓata rai har haka, babu kunya ta ce wai dan ta ce mashi yaro ne yake fushi. Sosai Jaish ya yi mamakin karfin halin Mahreen, hakan yasa ya ji a ransa dole ma a aura mata guyson dan ta gane shi ba yaro bane, in ba haka ba ba zata daina raina mashi wayau ba, sai ranar da ya koya mata hankali, sosai ya yi mata faɗa ya ce kada ta sake raina nagaba da ita, ta rinƙa ce mashi yaya, ba ya fita shekaru ba!. Shi ne fa take ce mashi yaya, amma fa tana fushi da shi, dan yau kwanaki uku da faruwan hakan bayan gaisuwa bata kula shi, ko ya yi mata magana bata amsawa, wai shi ne ya je ya sa Jaish ya yi mata faɗa, dan haka babu ita babu shi, sosai bawan ALLAH ya shiga damuwa, ya yi ya yi da ita a kan ta faɗa mashi me ya yi mata take fushi da shi ya bata hakuri. Amma taki kula shi, daga karshe ma taki bashi lokacinta, sai dai idan sun haɗu a hanya ta sauya hanya da sauri, taki bari su zauna ko na minti ɗaya bare ya ji damuwarta ya san ta in da zai ɓullo dan gyara alaƙarsu. Wlh yana tsananin son yarinyar nan da zai iya jure komai a kanta amma ban da fushinta. Yau ma tin da ya tashi da zafe da ɗan zazzaɓi ya tashi, kuma dik damuwar bata kula shi ne sila, hankalinsa ya tashi har ya shiga zazzaɓin firgici. Sanye yake da sleeping dress zubin pj's ya fito daga room ɗinsa, har ɗan rawan sanyi yake yi. Bedroom na momma ya wuce kai tsaye, sai dai ya yi mamakin ganin yadda ake ta abubuwa a gidan nasu, ana ta shirye-shirye da girke-girke. Zaune a saman sofa ya isko momma tana rike da waya, a kusa da ita ya zauna tare da kwantowa jikinta yana ɗan turo baki. "Shalelena yau kuma waye ya taɓoka?". Momma ta faɗa tana shafa wannan kyakkyawan arabs hair ɗin nasa mai matuƙar ɗaukan hankali. "Momma biki ake yi a gidan nan ne naga ana ta hidima?". Ya faɗa yana kallon fuskarta cike da tsananin kauna. "Yayanku ya kirani da safe ya ce muna da manyan baki a shirya masu tarba ta musamman, shiyasa ake shirya masu". Ɗan zaro ido ya yi. "Momma ko dai shi ne zai dawo?". Kai momma ta girgiza kafin ta ce. "A'a idan shi ne zai faɗa mun, ya dai ce bakinsa ne zasu zo". Ɗan kwaɓe fuska ya yi alamar bai ji daɗi ba da aka ce ba Smart ne zai dawo ba, yana kewan yaya nasa. "To momma shi yaushe zai dawo?". Hannu tasa ta ɗan shafi lallausan kumatunsa kafin ta amsa da. "Yanzu dai ban sani ba, amma ya ce soon zai dawo". Sam momma bata san sune suke hanya ba, a tinaninta baƙin Smart ne zasu zo daga Paris, yaki faɗa mata ya yi nasara ne, yana son yi mata bazata. Miƙewa guyson ya yi yana faɗin. "Dama na zo dubaki ne momma na, tin da kin wayi gari lafiya bari in yi wanka in zo mu yi hira". Ya kai karshen maganar tare da manna mata sumbata a kumatu. Cool smile ta sakar mashi kafin ta ce. "ALLAH ya yi maka albarka shalelena". Da amin ya amsa kafin ya wuce ya nufi waje, cike da kallon kauna Momma ta bishi tana jin tamkar dik cikin ƴaƴan nata ta fi sonsa, yana da tsananin shiga rai tamkar Big Bro, shi fa guyson da alama jininsa ma irin na Big Bro ne, idan ana maganar Big Bro kuma kun san ba'a banbanta shi da Smart, so ba sai na kama sunan Smart ba, kada ku rinƙa matawa they're identical!! Yana fita ya nufi bedroom na Mahreen cike da muradin ya fara kyakkyawar safiyarsa da kyakkyawar face ɗinta bayan na mommarsa. Bakinsa a ɗauke da sallama ya tura kofa kai tsaye ya shigo ciki. A miliyan ta juyo da kallonta a kansa, tana tsaye a tsakiyar ɗakin daga ita sai towel a kirji wanda bata ma ɗauresa ba, tana rike da shi ne, daga wanka ta fito, ta tsaya tana tinanin kalar kayan da zata sanya ne ya afko mata ciki. Ai juyowar da ta yi bata san time ɗin da ta saki towel ɗin ya yi kasa ba, dan ta tsorata jin mutum a ɗakin. Subhanallah ai suman tsaye guyson ya yi idanunsa a kanta, ya ga abin da ya juyar mashi da kai. A miliyan ta duka ta ɗauki towel ɗinta ta ɗaura daga kirjinta tana dalla mashi wata uwar harara kafin ta ce. "Me ka kalla?". Tambayar ma dariya ta so bashi, wai me ka kallah, to shi kam me zai ce mata ya kallah?. "Fita mun a ɗaki kuma kada ka kara shigowa in ba haka ba in faɗawa Yah Jaish kana shiga harkata, ɗan iska kawai, dama na jima da sanin ɗan iska ne kai". Shiru ya yi bai amsa mata ba, yana dai ta binta da wani irin mayen kallo from head to toe. "Ba zaka fita daga ɗakin nan ba?". A fusace ta faɗa. Slowly ya ɗan motsa lips ɗinsa wajen cewa. "Babu abin da na kalla face kayana, kuma ni ba zan fita daga ɗakin nan ba har sai kin faɗa mun me na yi maki kike shareni, ko na yi maki magana bakya amsawa". Muryarsa shar ya yi maganar, da alama abin da ya gani yasa ya wartsake daga kasala da yar zazzaɓin da yake ji. "Kayanka kuma a jikina?". Cikin tsiwa da masifa ta yi maganar tana dalla mashi harara. Shi kuwa cikin sanyin murya ya ce. "Ki rage hararana kada idanunki su faɗi kasa, kayana na gani mana, baki san ke kanki tawa bace ko?". Cikin zafi ta ce. "Saboda kai ka halicceni ai dole na zama taka, wlh ka fita mun a ɗaki in ba haka ba kome na yi maka kai ka nema, kaga bana shiga harkarka kai ma ka fita nawa!". Siririn smile ya saki kafin ya ce. "Ba zan fita ba har sai kin faɗa mun dalilinki na guduna, me na yi maki? Kina cutar da zuciyata sosai wlh". Wani irin kallo mai jefa mutum cikin shakku ta wurgesa da shi kafin ta ce. "Ra'ayina ne in yi maka magana ko kada na yi, dan haka dik wata alaƙa da kai na datseta, bani babu kai, dan haka zaka iya tafiya". On a serious note ta yi maganar, ita nan har ga ALLAH fushi take yi da shi, wai sun raba jaha!. Nisawa ya ɗan yi. "Ni kuma ba zan iya hakura in barki ki fita daga harkata ba, Please Mahreen, ki yafe mun idan ma wani laifi na yi maki, kin ga dai na baki hakuri ko?". Kallon up and down ta yi mashi kafin ta ce. "Bana alaƙa da ƴan iska, ko kaɗan baka ji komai ko ka bani hakuri ba na ganina tsirara da ka yi, hakan ya kara tabbar da sunanka a gareni na ɗan iska, dan haka kawai ka fita mun a ɗaki". Ta yi maganar cikin faɗa tana yi mashi pointing door da hannunta. "Mahreen ya za'ayi in ji babu daɗi dan na kalleki a haka? Kayana na gani, to menene kuma zan ce ban ji daɗin hakan ba, very soon fa zaki zama........" Bai idasa maganar ba ta katse shi cikin faɗa da zafa. "Wai uban me naka a jikina da tin ɗazun kake ta cewa kayanka a jikina ka gani?". Hannunsa har yana ɗan rawa ya ɗagosu ya nunata da yatsa kafin ya ce. "Ke kanki gabaɗaya, Please Mahreen ki saurareni kin ji? Zan yi dik abin da kike so"...... Ai wani irin ɗaure fuska tamau ta yi kafin ta ce. "Ni ɗin ce taka? To sannu ubana, wlh ka fita a ɗakin nan tin kafin in ɗauko wani abin in buga maka". Yana tsaye ko gezau bai yi ba, idanunsa a kan ɗan bakin masifar nan tata dake mugun bashi sha'awa yana ɗaukar hankalinsa. Ganin bai motsa ba yana karewa albarkatun jikinta kallo ne yasa ta kara fusata tare da rarumo kwalbar turare a fusace ta yi kansa da shi da nufin ta buga mashi. Sai dai tana zuwa ya riko hannun nata da hannunsa ɗaya, tare da juyar da ita ya mannata da jikinsa, ya zamana bayanta ya mannu da kirjinsa. Slowly ya kwanto da kansa a saman shoulder ɗinta, sai kokarin kwace hannunta da ya rike take yi amma ta gagara. "Mahreen don't you know that i love you ne da kike mun dik wannan abin? Meyasa kike wahalar da zuciyar da bata san komai ba face sonki ne wai?". Kam balai, ai wani irin ɗaure fuska da ta yi, da karfin tsiya ta juyo garesa tare da daddagewa ta ture shi baya, cikin faɗa ta ce. "Ni Mahreen kake so?". Kai ya gyaɗa mata almar yeah ita fa. Ai wani irin shegen dariyar da ga sheke da shi sai da ya saki baki yana kallonta, sai da ta yi mai isarta sannan ta tafa hannayenta biyu cikin juna kafin ta ce. "Ni Mahreen kake so? Haba dai yaro! Ai babban goro sai magogin karfe in faɗa maka, na fi karfin yaro kamar kai, to kai me zaka mun ma idan na aureka? Yaro da kai". Ta faɗa cikin rashin sanin ma'anar kalaman nata, shi kansa babban gore sai magogin karfe Chuchu ke faɗa mata hakan, ta ce ita babbar goro ce sai magogin karfe, bata san Chuchu na nufin ita sai ƴan gidan sarauta ko kuma masu muƙami a gwamnatance ba, ba'a ce mata girman shekaru ba, da yake kan nata ba natsuwa sai a hankali kun ji haukar da take zubawa, har da wani wai me zai yi mata idan ya aurenta yaro da shi, sai kace tasan me ake yi ma a gidan auren, kawai dai surutunta take zubawa cike da hauka da faɗa. Tin da ta fara magana bai katseta ba har ta dasa aya, sannan ne ya ce. "Mahreen kina nufin ni baki sona? Please kada ki ce hakan, zan yi dik abin da kike so kin ji?". "Kai yaro tsaya in faɗa maka, ni ba matar yara bace, mata manya ce irin masu shekaru 30 haka, kamar dai su Yah Jaish ɗin nan ko uncle Taheer nike so ba irinka karun yar..........". Ai bata karisar da maganar ba wani zazzafar mari ya wanke mata fuska wanda yasata dole ta haɗiyi sauran maganganun da ta yi niyar faɗa, lokaci guda ya shiga huci tamkar zai kama da wuta, ransa ta yi mugun ɓaci da ta ce mashi irinsu Uncle Taheer take so, sai ya ji tamkar ta watsa mashi wuta a zuciya, ai gani yake yi ma dama suna soyayya da uncle Taheer, take kishin nasu ta gado ta motsa tasa ya rasa control ɗinsa. Amma da yake yana da raunin zuciya sai kuma tausayinta ya yi gaggawar kama shi, take ya yi danasanin abin da ya yi mata, muryarsa na sarkafewa ya ce. "Please Mahreen kada ki ɗauki hakan matsayin cin mutunci, kiyi hakuri kin ji?". Haba ta ji hannun maza ba wanda ta saba ji a kauyensu ba, har ɗauke wuta ta ɗan yi na wucin gadin kafin kuma ta dawo, tana dawowa ta fasa mashi ihu mai rikita dodan kunne, da gudu ta raɓa gefensa zata wuce ta fita, wai zata kai karansa wajen momma da Jaish. Cikin zafa ya rikota tare da cewa. "Baki da hankali ne zaki fita a haka?". Ya faɗa yana ɗaure fuska kamar bashi bane mai rarrashinta a yanzu. Cikin kuka hawaye bibbiyu ta ce. "Ka sakeni mugu kawai azzalumi, jikinka ne ko nawa idan na fita a hakan?". In a cool voice sosai ya ce. "Jikinmu ne mu biyu, dan haka ba zan bari ki fita wani ya kalle mun ke ba". Ya kai karshen maganar tare da ɗagata cak sai saman bed ya direta. Tana ƙoƙarin tirjewa ta diro kasan bed ɗin ya yi gaggawar ce mata. "Wlh kina saukowa sai na faɗawa Obaid kece kika yi mashi aika-aika ranar". Ai tana jin haka ta sake zunduma mashi ihu mai sauti tare da komawa ta zauna kafin ta ce. "Ban yafe maka ba, ALLAH zai saka mun". Shi dai tin da ba zata sauko ta fita haka ba ai lafiya lou ne, koma me zata ce mashi tin da ba zata fita waje ba to ta daɗe bata ce ba, juyawa ya yi ya nufi waje, har sai da ya kai bakin door sannan ya ce. "Ki shirya ki tsara kwalliya ki zo garden ki nuna mun kwalliyar, idan ya yi kyau zan yaba, idan kuma bai yi kyau ba zan gyara maki". Cikin zolaya ya yi maganar, ya kai karshe yana kashe mata ido ɗaya. Haba ai sake zunduma ihu ta yi tana faɗin. "Mugu kawai, ba zanzo garden ɗin ba, kuma wlh sai na faɗawa Yah Jaish, sannan sonka ne na ce bana yi, bana son yaro sai manya". Har cikin ransa ya ji zafin furucinta, bare ma idan ta ce mashi yaro wannan abin yana kona mashi rai fiye da tinanin mutum, amma saboda yasan ya yi mata laifi, ya mareta, yanzu sulhu yake nema sai ya wuce ya fita bai sake cewa uppan ba, zuciyarsa tana yi mashi zogin ya sanyata kuka, sam bai so hakan ba, to amma ya zai yi? Basa iya controlling kishinsu ne su, abin a jininsu yake, da mata da mazansu dik haka suke, sai dai fatan ALLAH ya sassauta masu zafin kishi kawai. Yana fitowa ya nufi room ɗinsa, wanka ya je ya yi ya shirya ya nufi garden dan hutawa ya yi waya da Auta, dan ya yi kewarta daga jiya da yamma zuwa yau, a ransa yana tinanin irin tsokanar Mahreen da zai rinƙa yi yana sanyata farinciki, ya ci alwashin daga yau sun kullah kenan, ba zai barta ta sarara ba, ya rinƙa takura mata har sai ta so dolenta. ------------------------------🔥 SPECIAL TIME IN CROWN OF INJUSTICE. Karfe 4 na yamma daidai jiragen Black Tiger suka yi landing a international airport na Tunisia, already Smart ya ce da Jaish ya turo mashi motoci da misalin karfe huɗu airport zasu ɗauki bakinsa zuwa gida, so Jaish bai je ba sai ya tura motoci jibga-jibga guda shidda su tari baƙin. Kowacce mota tana ɗauke da tambarin Kingdom of power wato tambarin zaki kenan. Da wannan tambari Smart ya ganesu, dan dik motocin sabbi ne ba waɗan da ya sani bane, kun san Big Bro a zuwansa Kingdom of Power na farko ya yi ɓarnar da yasa aka sayi sabbin abubuwa, ciki har da motocin, bayan tafiyar Smart aka sayesu. Strange things never end in this world, Sweetie, Pretty, Ronnie suna saukowa daga jirginsu suka yi arba da kyakkyawan fuskar Big Bro a tsaye a gabansu yana fuskantarsu. Gabaɗaya sojijin yakinsa ne suka yi mashi zobe a wajen dan bashi cikakken tsaro, kasar Tunisia ta shaida da King of Black World ya zo cikinta a karo na farko, dan wancan zuwan tasa zuwan yaki ne da ya mamayesu, wannan kuma zuwan farinciki ne yasa suka san da zuwan. Airport ɗin nan ta cika dam da sojojin yakinsa kawai, kuma dikka mutane ne ba robot ba, bai zo da robot ba, ainahin ƴaƴan da yake kwata daga iyayensu ya horarsu a fagen yaki su suka yi mashi rakiya this time, abin da ya yi mugun tada hankalin jama'ar kasar yasa labarin ta yi gaggawar isa kunnen King Zuhair cewa sun yi bakon da basu taɓa ganin mai karfin mulki irinsa ba, dan tin daga kan jiragen da suka take ma jirginsa baya har izuwa kan kyakkyawan tsadadden jibgegen jirgin da ya ɗaukosu an san karfin iko da karfin mulki ta zo, ganinsa da ido yasa sun sha jinin jikinsu, domin kuwa sun ga yadda iko da izza suka yi mubaya'a a jininsa. Sai dai yadda suka ja mahaukan sojojin yakin da suka take mashi baya ya sha sun yi balain tsorata, mamaki sosai suke yi kan yadda dik waɗan nan jiga-jigan warriors wai ran mutum ɗaya suke karewa, basu taɓa ganin tsaro irin nasa ba gaskiya. ---------------------🔥 Kallon juna Sweetie da Smart suka yi, lokacin guda suka sauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya, da sauri suka karisa in da yake tsaye ya zura hannaye a cikin aljihun wandan tsaddaden three-piece suit ɗin jikinsa launin white color yana binsu da kallo da waɗan nan sharp eyes ɗin nasa masu sanya mutum shiga shakku idan ya wurga maka su, suma dai sun shiga shakku, dan kuwa sun tsargu sosai suna tinanin ko dai hukuntasu zai yi ne da yake binsu da wannan kallo. Sai da kuma suna karasowa in a cool way sosai ya ce. "Welcome to the home my blood brother". Ya faɗa yana canza kallon da yake bin Smart da shi izuwa kallon tsananin kauna. Amma kuma tamkar bai ga Sweetie ba, Smart kawai yake kallo. Hot hug Smart ya bashi cikin tsantsan farinciki over. Zaro hannayensa daga aljihunsa ya yi ya rungumi Smart da kyau yana bin Ronnie dake nufosu da kallo, shi kuma Ronnie sai kallon birnin yake yi, ya ga sabon waje. Shiru Sweetie ta yi tana tinanin me ta yi mashi da yake fushi da ita haka, bata san hankali yake son koya mata ba, ta ya za'ayi wani ya zo daga baya ya sameta a tare da shi har ya bata shawarar su bashi wahala kuma ta yarda? Ai wlh ban yi zatan haka daga gareta ba, tare fa Smart ya zo ya gasu, so yana son koya mata rikon amana ne, dik yadda yake son Ronnie kun san zai fi son Smart a kansa, amma dik da haka da yake Ronnie ya fara sani ai iya wuta bai rage ko mai kankantar son da yake yi mashi ba, sai ma karawa da ya yi, zai yi shawara da Ronnie bai yi da Smart ba, dik saboda me? Saboda kafin ya san Smart Ronnie ya fara sani, sam bai yi tinanin bata da hankali har haka ba, shiyasa ya shareta, dan hana ganin kenan za'a iya wasa da ƙwaƙwalwarta a bata shawara ta cutar da shi da gaske kuma ta yi accepting, wannan kuskure ne babba ta aikata wanda yakamata ta san zaman da suka yi ya fi karfin ayi saurin juya mata tinani a kansa. AMMA FA A NASA TINANIN NE YAKE GANIN HAKAN, KU FA ME KUKE TINANI? ABIN DA YA FAƊA GASKIYA CE KUWA? FUSHINSA A KANTA NA GASKE NE KUWA? YA YI DAIDAI DA YA YI MATA HAKAN KUWA?. TO NI MA DAI KADA KU CE INA BIN BAYANSA, AMMA BATA KYAUTA BA DA ZATA YI SAURIN KARƁAR SHAWARAR SMART KAMAR DAMA TANA JIN HAUSHINSA KO DAMA JIRAN WATA DAMA DA ZATA WAHALAR DA SHI TAKE YI, GASKIYA BIG BRO ZAMANSU YA WUCI RA YI HAKAN..🥱 Raba jikinsa da Smart ya yi ya riki hannunsa suka wuce cikin motocinsu, shi kuma Ronnie ya riki hannun Sweetie da idanunta suka ciko tab da kwallah, da kuma Pretty, suka shiga cikin motar kusa da na su Smart. KAI MY PEOPLE'S WLH BIG BRO YANA SON SWEETIE, DAN IN WATA CE WANNAN BAKAR ZUCIYAR TASA DA YA YI MATA ILLAH, AMMA ITA SAI DAI AYI FUSHI DA ITA A SHARETA, GASKIYA DAI YA BATA MATSAYI A ZUCIYARSA, AMMA FA A NAWA TINANIN NE!. -------------------🔥 Zaune take a saman sofa a parlon Mommah tana shan cappuccino, har wani lumshe idanu take yi, cappuccino momma ba dai daɗi ba, tana sanye da English wears, ta yafa fen karami a kanta. Daga bayanta aka zuro hannu aka karɓe cup ɗin cappuccinon, kai tsaye ya kai ɗan bakinsa ya yi sipping tare da ɗan lumshe ido. Ai miliyan ta juyo dan ganin wanene, tana ganin guyson ne ta wani uban ɗaure fuska tare da dalla mashi harara kafin ta ce. "Ba zaka fita rayuwata ba ko?". Gera guda ya ɗaga mata alamar e yana kara sipping cappuccino. "Wlh sai na faɗawa momma da Yah Jaish". "Iya karfinki kenan su ai dama na sani, wai ba da safe na ce idan kin yi kwalliya ni zaki fara zuwa ki nunawa ba? Meyasa baki zo ba?". Wani irin kufula da haushi ta yi. "Ba zanzo ba, dan ni kwalliyata yara basa gani". Ta faɗa tana cigaba da harararsa, ta fahimci cewa idan ta ce mashi yaro ransa na ɓaci shiyasa take yawan ce mashi hakan bayan ta yi wa Jaish alkawarin ba zata sake ce mashi yaro ba, to ga shi ta sake. Ya ji zafin kalmar sosai, amma sai ya shanye da cewa. "Ga shi kuma karshe dai saboda yaron ake wannan kwalliya kullum, dan yaro ya gani ya yaba, to na gani amma ban yaba ba, jeki saka abaya a kan kayan sai in yaba". Cikin zolaya ya yi maganar yana kara sipping abinsa, ga fuska a ɗauke da murmushi. Haba ta tsani ya ce mata zai yaba kwalliyarta, dan gani take ta wuci nan, cike da jin haushin kalamansa ta ce..... Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 -------------------------------------------🔥♥️ ZABUWAR DUNIYA STEP ONE!.🔥🔥🔥 Haba ta tsani ya ce mata zai yaba kwalliyarta, dan gani take ta wuci nan, cike da jin haushin kalamansa ta ce. "Kai har kasan abu mai kyau ne dama? Ai yaba kwalliya sai manya ban da yara irinka". Kashe mata ido ɗaya ya yi tare da sipping cappuccino, ya ɗan lumshe ido ya sake warosu a kanta. "To na ji dai, amma please jeki saka abaya sai ki zo mu yi magana". Ɗan bakinta ta murguɗa mashi tana yi mashi kallon up and down kafin ta ce. "Ban yi niyya ba, a haka na yi ra'ayin zama, dan haka ba zan saka abayar ba". Shiru ya ɗan yi yana tinanin me zai ce mata wanda zai tunzurata yasa ta je ta saka abaya dan ta rufe shape ɗinta, kayan jikinta sun bayyanar da surar da ALLAH ya yi mata, yana jin kishin wani ya ganta dik da a part na momma take, yasan ko Uncle Taheer baya shiga part na momma sai da kwakwarar dalili, iyakacinsa part na mama sister ɗinsa kenan, ƴaƴan king kawai ke shiga part na momma, suma manyan sai da izini, daga kan guyson ya yi kasa ne kawai basa neman izinin shi ga, amma su Jaish dik sai sun nemi izini, dokar king ce wannan, a haka kuma suke tafiya cikin tsari da bin doka ba kara zube suke abubuwa kamar marasa kan gando ba!. Dik da yasan brothers ɗinsa ne kawai ke shigowa, amma yana kishi sosai ta zauna cikin wannan shiga, sannan kuma yasan halinta sarai, yanzu zata iya dira waje, dan karamin aikinta ne ku ganta a garden ko a harabar kingdom ɗin yanzu!. Almost 2 mins for silent yana tinani kafin ya ce. "Yanzu dai a taƙaice dressing ɗin da yaro yake so zaki rinƙa yi kenan? Yanzu ni aka buɗewa jiki in gani in yaba? To na gani kuma na ji daɗi, my chocolatey tana da shape mai kyau, kuma naga balla ɗinta (tula-tula) sun kara girma yanzu ta fara zama ƴan'mata, suna kara girma kaɗan zasu iya kai shayar da baby, shiken sai in aure abata ta haifa mun.........". Ai bai karisa maganar ba saboda balai irin nata ta buge cup ɗin hannunsa, ya faɗi kasa cappuccinon ya zube kasa. A kufule ta ce. "Dama kai ɗan iska ne na sani, wlh ni ba zan aureka ba, kuma wlh na fi karfin in saka kaya domin kai, ALLAH ya kiyaye". Ta kai karshen maganar zata nufi room ɗinta da sauri tana dalla mashi harara. Da sauri yana sakin smile ya ce. "Haba mana, please kada ki canza kayan nan ki katse mun jin daɗina na kallon balls ɗina, ki bari saboda ina samun natsuwa ganinki a haka". Ai ko kula shi bata yi ba, ta yi gaggawar shigewa bedroom ɗinta tana huci, kara faɗaɗa murmushinsa ya yi kafin ya ce. "Jaira, har yanzu dai baki wuce ayi maki wayau ba, sai tsiwa da iya magana kamar wata babba, ai mun kulla kenan, sai kin dawo kan hanya". Ya kai karshen maganar tare da nufar side na kuyangun dake hidima a part ɗin. Magana ya yi masu a kan su zo su gyare in da ta zubar da cappuccino, sannan ya fito ya nufi part na su Mahnoor dan yana son yin magana da ita. Ita kuwa Mahreen tuni ta je ya cire kayan jikinta ta yi watsi da su, ta ɗauko abaya har da hijabi babba wanda ya kai mata har gwiwa ta sanya wai dan ma kada guyson ya sake gane mata ƴan tula-tulan ta da suka fara tasawa sosai yanzu, ta fara zama ammata. ----------------------🔥 Baki a ɗauke da sallama ya shiga parlon Jaish, Mahnoor na zaune a saman sofa tana kallon film a ɗayar wayan Jaish, ta ci kwalliya a yadda ta fito ainahin matar Prince, tamkar ka saceta ka gudu da ita, wasa-wasa tana ta kara sajewa da larabawan nan abinta, ga wani kyau da take karawa saboda Jaish ya iya bata murtuƙu. Tana ganinsa ta sakar mashi smile tana amsa sallamar tasa. A saman sofar dake fuskantarta ya zo ya zauna yana faɗin. "Barka da hutawa aunty Mahnoor". Kashe wutar screen ɗin ta yi game da ajiye wayar a gefe guda, sannan ta dawo da hankalinta kansa kafin ta ce. "Barka dai Yah Omar". Ɗan kasa da murya sosai ya yi kafin ya ce. "Yah Jaish yana ciki ne?". Kai ta girgiza mashi alamar a'a baya nan. Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa. "Yauwa Alhmdllh dama magana nike son mu yi kuma bana son ya jini". Tattare natsuwarta gabaɗaya a kansa ta yi kafin ta amsa da. "To ina jinka". Da alama jinin sarauta ya fara natsawa cikin jinin Mahnoor, domin kuwa yanzu very king and respect ga salo take magana, dama can akwaita da natsuwa sosai, sai ya haɗe, yanzu sometimes idan tana magana zaka zaci Jaish ne yake magana saboda yadda take bada word one after the other, ga class. Shiru ya ɗan yi, yana son faɗa mata abin dake a ransa amma yana jin kunya, yana jin kamar ba zai iya ba. Ta lura da hakan sai ta ce. "Yah Omar ni sister ɗinka ce, kada ka damu ka ɗaukeni kamar Zunaira ka ji?". Cool smile ya saki wanda ya kara fito da kyansa kafin ya ce. "Dama haka kike a raina, dikkanku bana banbantaku da Auta, sai dai ke da yake maganar ta shafi Mahreen ne sai nike jin nauyi". Yanzu ta gano abin da ya yi mashi nauyin faɗar, dan ta saukaka mashi sai ta ce. "Ka ɗaukeni a tsaginka ba tsaginta ba, kaddara bani da alaƙa da ita". Shi ma ya gano da cewa ta gano kasan harshensa, amma tana son tabbatarwa daga bakinsa, dan haka shi ma sai ya saukaka mata da cewa. "Dama aunty Mahnoor ba zan ɓoye maki ba, gaskiya har ga ALLAH ina son Mahreen, kuma aurenta nike son yi mu rayu a tare, amma ta ce wai bata sona.....". Ɗan dakatawa ya yi saboda ganin yadda Mahnoor ta zare mashi waɗan nan fararen idanun nata. Kura mata ido ya yi yana jiran jin dalilnta na zaro ido. "Bata sonka kuma? For what reason?". A ɗan dame ya ce. "Wai ta ce ita manyan mutane masu irin 30 years take so ba yaro kaman ni ba". Siririn tsaki ta ja kafin ta ce. "Na zaci ma wani dalili ne, wannan ai shirme ne, rabu da ita ta gama haukarta, tana da shekaru 12 to 13 ne take wani cewa mai shekaru 30 take so? To ta kaisa ina wai?". Kasa ya ɗan yi da kai yana tina kalaman Mahreen na ɗazun da take cewa yaro da shi me zai yi mata idan suka yi aure, a lokacin ya so gwada mata kaɗan daga abin da zai iya yi mata in suka yi aure, amma sai ya share ya rabu da ita tin da a lokacin sulhu ya je nema, amma ya ci alwashin yi mata abin da zai goge sunan yaron dake bakinta ɗin nan, gaba ko da kuɗi aka bata ba zata sake gaya mashi yaro ne shi ba!. Ya yi nisa cikin tinani sai faɗa Mahnoor take yi, unexpected ya ji ta ce. "Bari ta zo ta sameni, yarinya ne bata ji, ana ce mata ga annabi tana rintse ido". A sanyayye sosai ya ce. "Please aunty Mahnoor kada ki yi mata faɗa, ki bita a hankali, bana son in ga ta shiga damuwa bare kuka, kuma kin san in kika yi mata faɗa zata yi kuka ne". A raunace ya kai karshen maganar. To fa, Mahnoor ta ji zallar soyayyar gaskiya, wai kada ayi mata faɗa, ALLAH sarki bawan ALLAH, shi dai dik abin da zai ɓata mata rai baya son shi. Jinjina mashi kai kawai ta yi ba tare da dogon turanci ba, daga nan suka ɗauko hiran gari kawai suka cigaba da yi cike da mutunta juna, a nan Chuchu ta shigo ta samesu, sai suka ɗaura hirar a tare. Chuchu ta yi kiba yarinyar nan sosai, ta zama yar duma-duma abinta, ga haske da kyau da ta kara, Jawad ya iya kiwo sosai. --------------------------🔥 Zaune take a saman sofa a parlon King tana fuskantarsa, yana sanye da white arabs jallabi mai shegen kyau, sai tashin kamahi mai kwantar da hankali yake yi, a yayin da ita kuma take sanye da abaya mai balain kyau, ta ɗaura alkyabba a kan kayan, ta fito a yar sarkinta cas. Kanta a kasa tana ɗan murza ƴan yatsun hannunta, shi kuma kallansa a kanta gabaɗaya, kun san Yah Rizwan da iya love word, ga shi da natsuwa da sanyin murya, cike da kaunarta ya ce. "A waya dai akwai bakin magana, amma gani ga ki kuma kin yi shiru, ko dai a iya waya ne kawai aka iya hira?". Uhmmm yau ne karansu na farko da zasu yi hira face to face, dik sai take jin nauyin kallan cikin idonsa, and dik wasu kalamanta sai ta ji sun gudu. "Aneesa ba zaki mun magana ba? Amma kuma kika matsa mun kina son kallona face to face lallai yau a bayyane zamu yi hira ba a waya ba". Ɗan turo mashi baki ta yi. "Ni Yah Rizwan kyanka da kwarjininka ne yasa dik wasu kalamaina suka gudu ai". Cikin shagwaɓa tana kumbura kumatu ta yi maganar........ Nisawa ya yi tare da sakin smiling kafin ya ce. "ALLAH na gode maka da ka bani wanna kyakkyawar tauraruwar, Aneesa a gaskiya da na rasaki tabbas zan yi danasani". Kara turo mashi baki ta yi. "Ni Yah Rizwan na faɗa maka ka canza mun suna ko?"........ Hannu ya kai ya shafa kyakkyawan sajensa dake kwance luf. "Zan canza maki, but not now, akwai special day a cikin rayuwarmu dake dab da zuwa, a wannan rana zan baki abubuwa kala-kala ciki har da sabon suna wanda zai rinƙa kwantar maki da hankali". Siririn ƙayataccen murmushi ta saki kafin ta ce. "Zan kasance cikin dagon wannan rana ina adduar samun damar ganinta"......... "To yanzu dai ɗago kanki ki ganni bari in yi maki wasu ƴan tambayoyi". Cikin sigar soyayya mai tafiya da imani ya yi maganar. Slowly ta ɗago da kallonta a kansa, a fili ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce tabarakallah, sannan ya ɗan yi gyaran murya game da saita natsuwarsa. "Nasan baki san komai dangane dani ba Aneesa, amma ni nasan komai a kanki, yana da kyau ki sanni". Ya ɗan dakata yana kallonta. Ga mamakinsa sai ya ga ta ɗan yi murmushi, a natse ta ce. "Nasan komai dangane da mijina Yah Rizwan". "To me kika sani dangane dani?". Cike da muradin son samun amsa ya yi tambayar. Ɗan gyaran murya ta yi kafin ta ce. "Kai yayana ne kuma mijin da zan aura, dan haka babu kunya ko in tsaya yi maka wani ɓoye-ɓoye, hakan zai iya shafar zaman aurenmu ya kawo mana matsala, dan haka yana da kyau tin kan mu yi aure in san me kake so me baka so dan kiyaye su". Ta ɗan dakata tana kallonsa, ya tsareta da ido kawai yana saurarota. "Na farko dai kai mutum ne mai son mace mai natsuwa, mace yar wanka mai ɗaukar gayu kamar dai Chuchu". Yadda ta yi magana a nan ya ji tamkar ko tana kishi ne dan ya so Chuchu a baya, amma dai ta faɗi gaskiya yana son mace yar gayu mai ɗaukar wanka, sai dai zuciyarsa ta yi tambayar meyasa ta kafa misali da Chuchu?. Cigaba ta yi da cewa. "Mace mai saka kananan kaya a gida, macen da zata saki jiki da kai, baka son mace mai nuna kunya a gidan aurenku, kana son mace mai shagwaɓa sosai wacce ta iya magana tamkar zata yi kuka, kana son mace mai yin magana a sanyayye sosai, kana son macen da ta iya love sosai, wanda love word suka zauna a bakinta ya zamana kullum suke fita daga bakinta ba tsiwa da masifa ba, and kana son macen da zatana yawan kasancewa a kusa da kai, mace mai ibada da kuma fara'a, lastly kana son mace mai cikar welcome and good bye". Tana zuwa wannan point ɗin ta dakata cak tana ɗan kawar da kallonta daga kan. Ai bai san time ɗin da ya furta. "Wow!!". Ba, ya sha madarar mamakin jin yadda ta zayyano ra'ayinsa karkaf babu ko mistake ɗaya, amma ya jefi kansa da tambayar a ina ta san dikka wannan? NI KAM NA CE BAKA SAN ANEESA BA NE, YARINYAR DA UWARTA BATA DA LABARIN ABU MA A ZO WAJENTA ZA'A SAMU BARE LABARIN MUTUMIN DA TAKE SO, AI KA GODEWA ALLAH MA DA BATA ZAYYANO MAKA HAR GIRMA DA TSAWON BANANARKA BA, YO ANEESA AI SAI SHIRU KAWAI MALAM RIZWAN. Ya shagala a duniyar tinani muryarta ta daki dodan kunnensa da cewa. "Kana son soyayya sosai kuma ka yi matukar iyawa, ka iya sexy and romance love sosai, sannan a rayuwarka kana son kissing ɗin mace a.........". Dakatawa ta yi, ita da kanta ta tsinci kanta da kasa cigaba da zayyano mashi kalaman, dan ta yi crossing line ɗin waɗan da za'a iya faɗe, sauran ra'ayoyin nasa sun yi nauyi. Ai fa Rizwan yau bakinsa ya mutu, sai dai a ransa yana jin bayan Aneesa babu macen da fa cancanci ya aura, ita ce ta dace da irin ra'ayinsa a mata, ta san komai dangane da shi gata da fahimta sosai. A natse ya furzar da iska mai ɗan ɗumi daga bakinsa kafin ya yunkura zai yi magana kenan suka ji busa ya karaɗe ko'ina a cikin kingdom ɗin, sai dai busar bata yaki bace, ta alamar baki ce, kun san akwai take kala-kala na busa da kuma flag a kingdom ɗin. To a taken flag da zarar an ɗaga white flag nuni yake da wani shahararren sarki ya kawowa kingdom ɗin ziyara, shiyasa ake wannan busa ta tarban bakin, idan kuka ga sun ɗaga black flag to suna alhini ne ko an kawo masu hari sun gwabza yaki sun rasa wasu daga cikin mutanensu, dan jimami sai a ɗaga black flag dan hankalin ƴan uwan waɗan da aka kashe ya kwanta su ji sanyi a ransu su kuma san lallai kingdom tasan da su kuma tana tausaya masu tana jajanta masu. To idan suka ɗaga red flag kuma alamar zubar da jini kenan, zasu fita ɗaukar fansa, za'a mai da martani, so na faɗa maku tsagwaran sarauta mai dokoki suke bugawa a kingdom ɗin. Kallon juna suka yi kafin ya ce. "Wasu baki kuma yau muka yi haka? Da alama wani sarkin ne yazo, dan kin ji busar ba irin ta normal bakin da suka saba zuwa bane". Kai ta jinjina mashi zata yi magana kenan suka ji takun sahun mutane alamar ana dimfaro parlon, hakan yasa suka dakata suna sauraron waye zai ɓullo. Ga mamakinsu sai suka ga warrios guda biyu masu sanye da kayan yaki wanda ba irin na kingdom ɗin ba, kun san na kingdom ɗinsu mai tambarin zaki ne, na Big Bro kuma bakar damusa. Shiru suka zubawa warriors ɗin idanu suna kallansu, shigowa suka yi suka hau bincike cikin parlon tsab domin tabbatar da tsaro, basu ce dasu ko sannu ba, hasali ma basu bi ta kansu ba har sai da suka kammala bincike komai, sannan ne ɗaya daga cikin warriors ɗin wani mai fasasshen murya dakakken namiji ya ce. "Muna buƙatar kubawa king fili dan yana shigowa yanzu, ku fice". Wani irin kallon hadarin kaji Aneesa ta yi masu, ta buɗi baki da nufin ta faɗa masu ai ubanta ne king ɗin dan haka babu in da zata je, sai Rizwan ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu, dan ya fahimci waɗan nan ba warriors na kingdom ɗinsu bane, da alama basu da mutumci, tana yi masu rashin kunya zasu saɓa mata kamanni, hakan yasa ya dakatar da ita tare ce masu babu komai zasu fita. Dakatawa warriors ɗin suka yi har sai da Rizwan ya miƙe ya riko hannunta suka fita ta kofar part ɗin mummyn Chuchu. Sai da suka ga tafiyarsu sannan suka nufi kofar da suka bi suka shigo suka fita. Jim kaɗan da fitarsu sai ga Big Bro and Smart hannayensu sarkafe cikin na juna, daga bayansu Sweetie, pretty and Ronnie ne suka shigo. Smart ya ce su zauna a saman sofas bari ya kira family. Ba musu suka zauna, Sweetie ta zauna kusa da Ronnie, ta zuro hannunta cikin na Ronnie, slowly ta kwanto da kanta a saman shoulder ɗin Ronnien tana satar kallon Big Bro da ya yi kasa da kai tamkar mai tinanin wani abin. Uhm kun san me yake tinani kuwa? Zafin kishi ne tamkar ta kashe shi, to shi ne ya yi kasa da wai dan kada ya ga ta kwanta a jikin Ronnie, so yake ya danne zuciyarsa ya shareta, kome zata yi kada ya kulata, ALLAH ne kaɗai yasan irin tafasar da zuciyarsa take yi a lokacin da ya ga ta kwantar da kanta saman shoulder ɗin Ronnie, har wata yar karamar huci yake saki yana ɗan cicciza harshe kamar yadda guyson yake yi idan ransa ta ɓaci, to shi ma Big Bro haka yake ciza tongue ɗinsa yana ta faman sauke ajiyar zuciya ko zuciyar ta ɗan yi sanyi. NIKO NA CE ANYA BA ZAMU ZUGA SWEETIE TA SAMU WANI SAURAYI A KINGDOM ƊIN NAN KODA UNCLE TAHEER NE SU KULLA SOYAYYAR KARYA BA.....🤔 SAURA WATA TA CE SO NIKE AYI YAKI KO AYI KISAN KAI, NA LURA NE SHI BIG BRO TA ƁANGAREN KISHI KAWAI NE ZA'A CI GALABA A KANSA BA ƁANGAREN SHARIYA BA, KISHI NE KAWAI BATA IYA SHANYUWA A GARESA, DAN HAKA BA SAI MU HUKUNTASA DA NUNA SON WANI BA? KO YA KUKA JI SHAWARATA MY PEOPLE'S?.......🤔 Cikin sanyin murya ta ce. "Ronnie bana son zama a wannan gidan, please ka rakani zuwa gate zan tafi ne". Tamkar zata yi kuka ta yi maganar. Juyo da kallonsa a kanta ya yi kafin ya ce. "Meyasa baki son gidansu Big Bro? Sannan ki tafi zuwa ina?"......... Hawayen da take ɓoyewa ne suke ƙoƙarin zubowa ta amsa da. "Babu amfani ka zauna a wajen da ba'a sonka, sannan muma muna da gida ai, kuma nasan dik wanda na faɗawa sunan masarautarmu zai min kwatancen ta in da take, gara in koma can ya fi mun". Cikin raɗa take yi wa Ronnie magana wai dan ma kada Big Bro ya ji, bata san dik a kan kunnensa ake komai ba, tsab ya ji su, sai ta ɗan bashi tausayi kaɗa. JAMA'A BIG BRO YA FARA TAUSAYI. Amma bai ji kamar zai fasa hukuncin da ya yi niyar yi mata ba. Daidai wannan lokaci Smart ya shigo, momma na gaba yana bayanta ya rufe mata ido da hannu ya ce wani abin zai nuna mata. Jaish, guyson, Obaid and Omaid duk suna biye da shi a baya, a yaran momma Auta ce kawai ta rage bata nan, ayya ana yi babu ita. Miƙewa tsaye Big Bro ya yi da ganinsu, take su Ronnie ma suka mimmike tsaye suna kallanta. A tsakiyar parlon Smart ya kawota tare da tsaidata saitin face ɗin Big Bro dake binsa da kallon kauna, sannan ne ya ce. "Momma are you ready?". Kai kawai ta iya jinjina mashi, saboda jikinta ya rigada ya bata ga abin da zai nuna mata, ta ji cewa first love ɗinta ne ya aminta ya biyosa. Slowly ya zame hannunsa daga kan fuskarta, ai a hanzarce ta buɗe ido kai tsaye kallonta sai kan Big Bro wanda shi ma ya dawo da kallonsa a kanta. Ai bata san lokacin da ta matsa dab da shi tana ɗan blinking eyes ɗinta alamar tana son tabbatarwa da gaske ne ko mafarki?. Shi ma matsawa dab da ita ya yi ya bata hot hug sosai, lokaci guda ya ji wani irin tsananin kaunarta ya shigesa, bai taɓa sanin daɗin uwa ba, amma yau da ya rungume mahaifiyarsa ta ainahi sai yake jin tamkar a hannunta ya girma. Guyson da ya gama ruɗewa ne muryarsa na rawa ya ce. "Momma ya naga Yah Omerish ya zama mutum biyu?". Omaid and Obaid dik sun tsaya sai zazzare idanu suke yi suna raba kallonsu a kan Smart and Big Bro, sun ruɗe, sai suke ganin kamar kansu ne yake juyawa kawai ai mutum ɗaya ne. Jaish ma dai da ya gagara gane komai ne ya ce. "Yah Omerish wanene wannan?". Dawo da kallonsa a kansu Smart ya yi. "Our Big Bro". Ai har suna haɗe baki dikkansu wajen cewa Big Bro ɗinsu kuma?. Jinjina masu kai ya yi alamar kwarai kuwa. Ɗago kai daga jikin Big Bro momma ta yi tare da yi wa su Smart alamar da hannu a kan su zo. Da sauri suka karisa wajenta, nan fa ta haɗesu waje guda ta rungume sosai a jikinta, suma dikka rungumeta suka yi cike da kauna. Almost 5 mins suna a haka kafin momma ta sakesu ta ɗago da kallonta a kan Big Bro, idanunta sun cina tab da kwallah, suna haɗa ido kwallar nata ya zubo kan kunatunta. Hannu Big Bro yasa ya hau goge mata hawayen nata kafin ya ce ta daina kuka please. Daidai lokacin King ya shigo cikin rashin kwarin jiki, kana ganinsa kasan bashi da lafiya. Da mamaki yake ta faman binsu da kallo, wani irin farinciki mara misaltuwa ne ta bayyana a kan fuskar king, dik da ba'a faɗa mashi ba yasan cewa Smart ya yi nasarar dawo mashi da first love ɗinsa ne. Da kallo ɗaya Big Bro ya yi wa king ya ji wani irin azabbaben sonsa ya kama shi, hakan yasa ya matsa kusa da king ya rungumosa a jikinsa yana jin tamkar wani part na rayuwarsa ne king, tamkar kuma sun daɗe suna rayuwa ba yanzu ba. Smart ya ɗan yi mamakin ganin yadda Big Bro ya karɓi King, saboda yasan Big Bro da kaifin basirar iya gane mai laifi, a saninsa kuma King bai yi masu adalci ba, amma meyasa Big Bro tashi ɗaya ya yi na'am da shi?. Ya jefi kansa da tambayar da bashi da amsarta, hakan yasa ya matsa shi ma kusa da su, dan King sai yi mashi alama da hannu yake yi a kan ya zo ya haɗesu ya rungume please. Da sauri ya je ya faɗa jikin king yana sauke ajiyar zuciya, su Jaish dik suka tafi jikin King suka rurrugumesa suna murna. Nan ma almost 5 mins suna rungume da juna kafin Big Bro ya zare jikinsa, sai ɗaya bayan ɗaya suka zare jikinsu. Smart ne ya taimakawa king izuwa saman sofa ya zauna, sannan ya umarci kowa da ya zauna. Da sauri suka zazzauna, momma ta zauna a kusa da King, Smart and Big Bro suka zauna a sofa guda, Obaid and Omaid sofa guda, guyson zai tafi wata sofar Smart ya matsa mashi tsakaninsu shi da Big Bro ya ce ya zo ya zauna a nan. Sai a lokacin Big Bro ya ɗago ya kalli guyson, ai da kallon farko ya ji wani kaunar yaron nan a ransa. NI KUWA NA CE JININKU DA HALINSU IRI ƊAYA AI DOLE KA SO SHI. Hannu ya kai ya shafi kan guyson, can kasan maƙoshinsa ya ce. "Menene sunanka?". Har yanzu kallon mamaki guyson yake binsa da shi ya amsa da. "Sunana Omar". Omar Big Bro ya maimaita sunan, daga haka bai sake yin magana ba, ya ɗago kai da kallonsa unexpected sai kan fuskar Sweetie dake sharar kwallah. Kuma ita ma shi take kallo, a wannan karon dai sai ya gagara zare kallonsa daga cikin nata, yanayin yadda yake kallonta tamkar wanda ya ga bakuwa daga wata duniya, ita kuma kallo mai kama da harara take binsa da shi alamar haushinsa take ji. Sun jima suna kallon juna har King ya c bari a kira family dik su zo, shi Big Bro bai ji ba yana ta faman kallonta, dik hankalinsa ya tashi na ganin yadda damuwa sosai ke kwance a cikin idanunta, sai ya kara jin tausayinta ya kama shi. One by one family suka fara shigowa cikin parlon, kowa ya shigo sai ya gwada ruɗewarsa a fili na ganin Smart ya zama biyu, sai sun natsu daga baya sai suka banbancin hasken fatar Smart da Big Bro. Sai dai lokacin da uncle Abbas ya shigo cikin parlon sai da Big Bro ya ji kirjinsa ta buga da karfi da ya gansa, sai yake jin tamkar ya taɓa yin rayuwa da shi a wata duniyar, kun san da yake ya mance da komai na duniyar shaiɗanu, so ya mance da dad ɗin nasa ma. Shi kuma uncle Abbas sam bai nuna kamar ya san Big Bro bama, sai dai shi ma ya ruɗe sosai da ya gansu su biyu, sai tambayar King yake yi wai dama su biyu ne? A ina ɗayan ya girma to? Ko dai shi ma a Paris ne, dik ya damu sosai ya shiga ruɗani. Amma King bai ce da su komai ba har sai da family dikka suka gama haɗuwa exept irinsu Heleena, Zee da Mahreen waɗan da dai suka kasance ba ƴaƴan King ba, dan har Uncle Taheer babu shi a wajen. Sai dai suka gama haɗuwa dukkansu sannan ne King ya sanar da su waye Big Bro. Nan fa kallo ta koma kallon kallo a parlon, masu mamki suna yi masu murna suna yi, Maman Yah Ramish ta yi tsalle ta dire ta ce wlh ba zata yarda da cewa dik wanda aka kwaso sai ace mata ɗan King bane, ba zai yiwu ba, anyi na Smart sun yi shiru, yanzu kuma a sake kawo masu wani! Ba zasu yarda ba, tana masifar tana kallon Momma, ko kaɗan bata yarda ta kalli Big Bro ba, dan wlh dik cikin parlon bayan momma da King babu wanda ya kalli Big Bro sau biyu, da kallo ɗaya ba kari suke zare idanunsu. Ai dik rashin kunyar Sareena sa ɗaya ta kallesa bata sake ba, tana balain son kallonsa amma tsoro ya hanata, kun san idanun Big Bro ba daga nan ba a kaifi da razana mutum, wlh dik balain tsoro ya basu. Shi kuwa tin da ya zauna a wajen kallonsa a kan Sweetie da ta yi kasa da kai bayan ta ga bashi da niyar daina kallonta, kun san idan ya kafeta da ido zai iya ɗaukar mintoci masu yawa bai kyafta kallonsa ba. Jin sun fara surutu ne yasa kasa ta ɗan fara juya mashi, ita kanta Sweetie juya mata kanta ya fara yi, basu saba da hayaniya ba, sai suka ji ina na zasu iya zama a wajen ba. Momma ce ta ce. "To me kike nufi kenan da zaki ce ba ƴaƴansa bane?". Cikin tsananin takaici momma ta yi tambayar, da mama ta kure hakurinta, ta yi mata a kan Smart ta shanye, yanzu kuma so take ta sheganta Big Bro ne ko me?. "Kin fi kowa sanin me kika kullah, amma dai ke kanki kin san waɗan nan ba ƴan gidan nan bane, ke baki ga yanayin idanunsu bane? Wlh ba jinin gidan nan bane, kekika san in da kika kwasosu........". Tana magana tana hararar mommah. Sai dai bata kai karshen maganar ba ta wani ci uban birki sakamakon miƙewa da Big Bro ya yi da nufin ya bar parlon, bai san a kan me suke tattaunawa ba, dan baya jin larabci, sun dai cika mashi kunne kawai zasu ja mashi ciwon kai. A tinanin mama ya miƙe ne zai yi wata magana a kan maganarta, sai ta ga ya dubi Smart, in a cool way sosai ya ce. "Ba zan iya zama a nan ba, ina son waje so silent like gida, nan ya mun jama'a dayawa". ALLAH sarki bai iya zama a cikin mutane ba, ko da yake shi da ya girma cikin ɗaki yaushe zai iya zama da mutanen da suka wuci biyu zuwa uku, ai ba zai iya ba. Cikin harshen turanci ya yi maganar. Hakan yasa dik suka ji abin da ya faɗa. Wlh dik cikin parlon nan ba wanda bai so Big Bro ya cigaba da yin magana kada ya dakata ba, saboda yadda sexy voice ɗinsa take, ga natsuwa sosai. Smart da dama ya yunkura zai yi wa mama magana kenan Big Bro ya katse shi ne ya miƙe tsaye, cikin sanyin murya ya ce. "Momma baki da lokacinsu a yanzu, please muje part ɗinki". Smart ya faɗa yana maido da kallonsa a kan Big Bro. "Muje part na mommarmu babu hayaniya". Ya faɗawa Big Bro hakan. "Kai ni wajen da wuri". Cewar Big Bro. Shi dai king bai iya ce masu komai ba saboda rashin kwarin jiki ga jinya, yanzu baya son ɗaga murya. Hannu Big Bro ya miƙawa momma a kan ta zo su tafi dan ya ga ta miƙe. Ba musu ta yi gaggawar matsawa ta rike hannunsa. Dik cikin parlon babu wanda ya sake iya ɗaga ido ya kallesa har Smart ya yi gaba suka rufa mashi baya shi da momma. Har ya yi taku step biyu sai kuma ya dawo baya ya ce. "Omar let's go together". Ya faɗa tare da juyo da kallonsa a kan Ronnie and Sweetie, da hannu ya yi masu alamar da su zo. Miƙewa Ronnie ya yi yana riko hannun Sweetie, sai dai kuma ina, kwace hannunta ta yi tana faɗin. "Ni ba zan je ba, kai kaɗai ya kira". Da yarensu na Korea ta yi mashi magana, dan ta iya yaren ita ma a zamanta da su. WAI MA YA AKA YI BIG BRO DA RONNIE SUKA IYA YAREEN KOREANS NE? IN BAKU MANTA BA DA SUN FI YAWAN MAGANA DA KOREA FIYE DA TURANCI, UHM AMSAR ITA MA WATA DOGUWAR LABARI CE FA, KU DAI MU JE ZUWA. "Bani kaɗai ya kira na kin sani, please sis ki bari mana, ki tashi muje". Ba dan ta so na ta miƙe tsaye Ronnie ya riko hannunta suka nufi part na momma, King ya bisu da ido yana son kasancewa da su, amma ya miƙe ya koma room ɗinsa a zuwan cewa sai dare zai samesu a part na momma. Mama dai sai cika take yi tana batsewa, ranta ya sosu musamman da Smart ya ce wa momma wai ta wuce lokacin tsayawa yin magana da su, wani irin kululun bakinciki ne ya turnuketa, wato yanzu momma ta kara yin gaba ta barsu, ita ba sa'an yinsu bane, lallai dole ta ɗauki mataki, dan wlh momma bata isa ba. Su dai sun wuce sun barta da cika tana batsewa, miƙewa Obaid da Omaid suka yi suka nufi waje Omaid yana faɗin. "Kai Obaid yakamata a canzawa bududa wajen zamansa, nan sanyi ya yi mashi yawa". Obaid da ya gama gane karatun ne ya ce. "Gaskiya dai kam, dan na lura sanyin da ya bugasa na kwanaki biyun nan kamar ya bashi daman jin shi wani ne". Sun yi maganar a lokacin da suke ficewa daga parlon, UHM DA MAMA SUKE YI FA. Suna fita suka wuce part nasu, a hanya Obaid ya ce. "Kai Omaid bamu gama da balain Yah Omerish bama ga wani bakin mugun ya bayyana, wlh na gagara kallon cikin idanunsa, ya bani tsoro yadda ya ɗaure fuska tamkar ɓauna". Omaid ne ya ce. "Daga gani wlh wannan ya ci uban Yah Omerish a bakin mugunta da mugun hali, kana ganin fuskarsa, wlh nima na kasa ganinsa sau biyu, idanunsa suna da kaifin da lokacin da na kallesa a farko sai da na zaci na yi wani laifin, ya ruɗani yasa na shiga shakku da zargin kaina, kai gaskiya wannan guy ɗin shegen kwaro ne, dole mu yi kyakkyawan plan a kansa". Ya kai karshen maganar daidai lokacin da yake shiga bedroom ɗinsa. Wato Big Bro yaran nan za su shiryawa plan, my people's mu faɗa masu gaskiya ko mu bari Big Bro ya fara gwada masu waye shi?. ----------------------------🔥 Zaune Momma take a saman sofa, Smart yana zaune kusa da ita, su Sweetie dik sun zazzauna, while shi kuma Big Bro yana tsaye yana kallon room ɗin, yaga bata wuce toilet ɗinsa na kingdom ɗinsa ba. Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 -------------------------------------------🔥♥️ ZABUWAR DUNIYA STEP ONE!.🔥🔥🔥 Zaune Momma take a saman sofa, Smart yana zaune kusa da ita, su Sweetie dik sun zazzauna, while shi kuma Big Bro yana tsaye yana kallon room ɗin, yaga bata wuce toilet ɗinsa na kingdom ɗinsa ba, dik ya ji tamkar yana takure, a gaskiya bai sake ba, wannan bakon waje bata yi mashi ba. Yana cikin kalle-kallen nasa ne idanunsa suka sauka a kan Smart da ya masa ya riko shoulder ɗin momma tare da ɗan kwanto da kansa a gefen wuyanta yana yi mata raɗa a kunne. Ɗan kura masu idanu ya yi yana son fahimtar gulmarsa da Smart yake yi. Shi kuwa Smart cewa yake yi. "Momma kin ga wancan mai golden hair ɗin ita ce babbar surikarki, heartbeat ɗinsa ce, kuma wlh yana balain sonta tamkar ransa, yadda kika ji na ce heartbeat ɗinsa to hakan ce". Tin da ya fara magana momma take sakin murmushin da zan iya cewa bata taɓa smiling mai kayatarwa irinsa ba, ba karamin daɗi ta ji ba jin Big Bro yana da mata, kuma yana sonta over. NI KUMA NA CE WAYE YA BASHI MATA, SMART BAYA SON ZAMAN LAFIYA NA LURA. "Omerish kana shiga sabgata dayawa". In a cool way sosai Big Bro ya faɗa yana hararar Smart da yake cigaba da yi wa momma raɗa a kan Pretty da ta kwanto da kanta jikin Sweetie, cewa yake yi. "Kin ga second surikarki wannan da kika zaɓa mun, dan farincikinki ita nikeso". Ita kam momma in zata sanya ranta saboda farinciki, ai bata san lokacin da ta fara yi wa Pretty da Sweetie alama da hannu a kan su zo wajenta ba. Yau Big Bro ya ga ikon ALLAH, tamkar momma zata mayar da Sweetie da Pretty cikinta, ta rungumesu tana ta farinciki, ganin irin farincikin da momma take yi ne yasa Big Bro ya ji ba zai iya katse mata shi ya ce mata Sweetie ba matarsa bace kuma shi baya sonta ba, dole ya bar zancen yadda Smart ya faɗa masu saboda wannan farinciki na momma ya ɗaure. AKWAI CASE KENAN. Ita ma Sweetie saboda ganin yadda momma take wannan fariciki ta rungumesu, da sun yi motsi kaɗan zata tambayesu ko suna son wani abin ne yasa ta ji ba zata iya ce masu shi ba mijinta bane, sai ta daure ta shanye maganar tana satar kallonsa, sai ta ga shi ma ita yake kallo, dama so yake yi su haɗa idanu ya ce mata kada ta yi wani magana. Ya kuwa yi saa ta ɗago dan satar kallonsa, da hannu ya yi mata alamar ta yi shiru ta zauna a matsayin matarsa a gabansu. Wani irin harara ta dalla mashi wanda bata san ta yi ba kafin ta ɗauke kanta tana ɗan murguɗa baki, ya ɗan yi mamakin ganin ta murguɗa mashi baki, dan yasan ita bata yin wannan rashin kunya, Pretty ce mai murguɗawa Smart baki, to amma tin da yanzu shi yake nema ta farantawa mahaifiyarsa sai ya danne kawai. Cikin zolaya Smart ya ce. "My blood kawai fa ina faɗa mata yadda kake kaunar heartbeat ɗinka me fa". "To sai na ce maka bani da bakin faɗa mata ne?". Hmm yadda Big Bro yake magana sai ya tafi da mutum, wlh sai ya yi magana ba zaka taɓa zatan shi ya yi ta ba, a natse sosai. "Dik bama wannan ba, nasan wanka kake son yi zo muje ka yi wanka ka shirya ka huta sai ka zo mu ci abinci". Cewar Smart. Ɗan girgiza kai Big Bro ya yi, ya ɗan yi shiru na sakanni kafin ya ce. "Omerish this place is to small for me, and ban gama kallon momma ba, barni da ita". Ya kai karshen maganar tare da zama a kusa da ita ta ɓangaren Sweetie kenan, dan dik ta rungume su Sweetie a jikinta. Shi Smart yana ta ɓangaren Pretty. Jaish, guyson and Ronnie dai sun zauna a saman sofa sai kallonsu suke yi gwanin birgewa. "Momma dik su tafi ina son yin magana dake". Cewar Big Bro. Ganin yadda ya yi magana on a serious note ɗin ne yasa ta fahimci maganar tana da mahimmanci, dan haka sai ta ce. "Jaish ka kira mun Mahnoor ga sisters ɗinta ta ɗaukesu zuwa ɗakinsu Mahreen". Ta yi maganar tare da tsai da kallonta a kan Ronnie dake kusa da guyson, kansu ɗaya da guyson, a shekaruma kusan shekarunsu ɗaya, amma Ronnie ya ɗan fisa da kaɗan, sannan hasken fatar larabawa da koreans ba iri ɗaya bane, kuma renon Black World da Kingdom of power ba ɗaya bane, hakan yasa Ronnie ya fi guyson haske sosai. "Wannan kyakkyawa kamar Omar ɗin nawa fa?". Cewar Momma da ta kafe Ronnie da kallo. "My pleasure na ne momma, he's my brother from another mother". Ya faɗa yana riko hannunta, shi kuma Jaish ya miƙe ya tafi kiran Mahnoor. "Ka gansa kyakkyawa sosai, amma yana kama da matan naku fa"...... Slowly Big Bro ya juya ya kalli Ronnie, sai da momma ta yi magana ya lura hankalinsa ya kai kan kamanni, tin da yake da su bai taɓa lura ba. Shiru ya yi yana tinanin ko dai Ronnie yana da alaƙa dasu ne? Yakamata ya bincika gaskiya. Muryar momma ce ta katse mashi shirun da cewa. "Omar ɗaukesa ku je ɗakinka to". Miƙewa guyson ya yi tare da cewa Ronnie ya zo su tafi, sai dai da larabci ya yi maganar, shi kuma Ronnie baya ji, haka yasa Smart ya maimaitawa Ronnie da turanci. Miƙewa tsaye ya yi suka nufi waje, a daidai wannan lokacin Mahnoor and Jaish suka shigo. Nuna mata su Sweetie ya yi a kan ta ɗaukesu zuwa ɗakin Mahreen. Ai Mahnoor tana ɗaura idanunta a kan Sweetie ta ji wani irin kaunar yarinyar ya shigeta, barema yadda ta ga gashin kanta, wlh a kingdom ɗin nan dik wanda ya ga gashin kan Sweetie sai ya sake waigowa ya kalla, to abu ne da basu taɓa kallo a zahiri ba, gashin mai balain ɗaukar hankali, gata kyakkyawar gaske. Ai da sauri Mahnoor ta ce su zo su tafi. A natse suka miƙe suka bi bayanta, parlon ya rage daga Jaish, Smart sai Big Bro. Cikin zolaya Smart ya ce. "Ko dai nima ina baku waje ne shalelen momma?". Harara Big Bro ya watsa mashi yana rarraba yatsun hannun momma da ya rike. Zoben da Jaish ya sanya mata kwanaki Big Bro ya zare daga yatsunta, dan ya ga zoben ya ɗan kamata har ya zana mata shati a yatsun nata. Da ya cire zoben ma sai ya hau shafa in da zoben ta zana zanenta kaman yana son cewa momma sorry, amma bai yi magana ba. "Momma akwai tarin abubuwa sosai a wannan kingdom ɗin, daga zuwana na fahimci hakan, waɗan can yara guda biyu masu kama ɗaya kuma masu yanayi da mu ɗin nan ƴaƴan waye?". Cewar Big Bro da yake magana a kan su Omaid, wlh ba zaka taɓa zatah Big Bro ya kalli jama'ar da suka zo cikin parlon king ba, amma tsab ya kallesu ta idon da su basu sani ba, sannan dik ko yanzu ya gansu zai ganesu. Kun san fa idan magic da magic suka haɗu abin ya zama family issues ne ta bayan fage, kuma in har mai karfin tsafi kamar Big Bro ya bayyana a waje to dik kananan nan zai iya zaƙulosu. JAMA'A KU CE WA SU MAMMIE GA UBANSU YA ISO!. Smart ya yi mamakin jin yadda ya yi tambaya a kan su Omaid. Momma tana kallon dogayen yatsun Big Bro ta amsa mashi da. "Brothers ɗinku ne, daga su sai autarku mace wacce ke aure a Crown of Justice". Ta kai karshen maganar tare da kai ɗayan hannunta ta riko yatsun Big Bro tana kallo, shi harta yatsun hannunsa ya fita daban da na sauran yaranta, dogaye da su, ga shi kuma a babban yatsansa na hannu da karamin ya bar farce nails mai tsawo sosai, sauran yatsun nasa kuma ya yanke nails ɗin. Ta yi mamakin ganin yadda yatsun nasa suke, ga su da balain kyau, farare tas tamkar madara, suna wani kyalli suna glowing. "Shikenan tin kannena ne, ni zan gyara komai da kaina". Ya faɗa yana ɗago da kallonsa a kan Jaish da yake ta faman binsu da kallo. "Da wani abin ne? Ko sun aikata wani abin ne?". Smart ne ya tambaya. "Dama ai su kullum cikin aikata laifuka suke, dan dik mutum irinsu baya son zaman lafiya". Big Bro ya bada amsa. Da sauri Jaish ya ce. "Ai idan ka ce aikata laifuka ma ka faɗi kaɗa, waɗan nan yara sai addu'a". Momma dai sun saka ta a duhu, dan haka sai ta ce. "To ni dai ba zan shiga tsakaninku ba, yanzu dai kuje ku yi wanka kuzo ku ci abinci shi ne damuwata". Ko kaɗan bata damu ba, dan tana ji a jikinta Big Bro zai kula da kannen nasa matuƙa. "Momma bana son in bar part ɗinki, a nan nike son room". Cewar Big Bro. "Meyasa ba zaka je tare da ɗan uwanka ba?". Momma ta tambaya. Sake yatsun hannunta ya yi tare da gyara zama kafin ya ce. "Kingdom ɗin nan ya mun kaɗan, a takure nike, amma idan ina part ɗinki kina tare dani zan rinƙa jin tamkar a sarari in da babu ginin komai nike". Sosai momma ta ji mugu-mugun daɗin kalamansa, hakan yasa ta ce. "Akwai ɗakuna guda uku dake babu kowa a nan, ka ɗauki ɗaya.......". Katseta ya ɗan yi da cewa. "Ɗaya mafi kusa dake ba". Kyakkyawan murmushi ta saki kafin ta kai hannu ta shafi lallausan kumatunsa. "ALLAH ya yi maku albarka dikkanku". Smart and Jaish ne suka amsa da Amin ban da Big Bro, momma bata lura da bai amsa ba, ta ɗan kara shafan kumatunsa tana jin tamkar ta mai da shi cikinta dan tsantsar so da kauna. Miƙewa Smart ya yi tare da cewa. "Bari in duba mana ɗakin da ya fi kyau guda biyu, Jaish ka shigo da kayanmu, suna cikin bayan motocin da suka ɗaukomu". Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya nufi wani siririn corredor wacce ɗakunan suke ta wajen. A nan ya zaɓawa Big Bro guda ɗaya shi ma ya zaɓi guda ɗaya, dama baya son zama a part ɗin Jaish. Dawowa ya yi ya zo ya rike hannun Big Bro suka nufi room ɗin. Da kallon kauna momma ta bisu har suka kurewa ganinta, sannan ne ta miƙe ta nufi ɗakin Mahreen dan ta ga su Sweetie da kyau. Zaune ta iskosu a saman bed, Sweetie ta buga uban tagumi tana tinanin Big Bro, ita kuwa Pretty ta tada kai da cinyar Mahnoor suna ɗan hira, dama su kunga sun san juna, Sweetie ce bakuwa. Mahreen kuwa ta matsa sai shafa kyakkyawan gashin Sweetie take yi tana tambayarta me ta shafawa kan nata ya zama kala haka mai balain kyau? Wai ita ma zata shafawa nata ne. Kun san tin da Mahreen ta ga Sweetie ta rikice, taga madarar kyau, kuma babban abin da yasa Mahreen ɗin ta kaunaci Sweetie shi ne gashin kantan nan dai mai balain ɗaukar hankalin nan da kowa yake santinsa har Big Bro, sai taɓa mata kai take yi tana karawa. Da Sweetie ta ce mata babu abin da ta shafa gashin ne yake a haka, sai Mahreen ta ce to zasu zama kawaye? Kun san mutuniyar da son gayu, to ta ga Sweetie yar caras cas shi ne ta manne mata, tin ɗazun take ta faman shafa mata gashi tana watsawa, dik wani ɗauri da Sweetie ta yi wa gashinta sai da Mahreen ta warwaresa tsab ta hau watsa mata gashin. Ita kuwa ta buga tagumi tana jin zuciyarta na yi mata zafi saboda abin da Big Bro yake yi mata. Jin sallamar momma yasa dik suka kai kallonsu a kanta, har suna haɗe baki wajen amsa mata sallamar. A kusa da Sweetie ta zauna tana kallon fuskarta. "Ƴata lafiya kuwa? Naga kamar tin da kuka zo baki a cikin mood mai daɗi". Ƙaƙalo murmushi Sweetie ta yi. "Babu komai Momma, kawai kaina ne yake ɗan ciwo". Momma zata sake yin magana Pretty ta rigata da cewa. "Karya take yi maki momma, faɗa suka yi da mijin nata tin kafin muzo, Yah Omerish ne ya bata shawarar ta daina yi wa Big Bro magana, shi ne ta daina yi mashi magana, shi kuma abin ya ɓata mashi rai ya bar masu gidan gabaɗaya, daga baya suka yi ta nemansa har suka gaji, kwana uku baya tare da mu, da zamu zo nan ma ina ganinsa wani jirgi daban ya hau ba namu ba, kuma ya rigamu sauka a nan, to shi ne har yanzu basu shirya ba". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa zaune. Sosai momma ta ji daɗin yadda yakasance Sweetie tana da sirri da natsuwa, wato tana kokarin rufawa mijinta asiri, abin ya burge. Kallon tsab momma ɗin ta yi wa Sweetie kafin ta ce. "Ni mahaifiyarki ce, kada ki koyi ɓoye mun komai kin ji? Kada ki kalli mijinki matsayin ɗana kice zaki ɗaukeni a surkuwa, uwa nike a wajenku dikka, dik abin da ya yi maki ki faɗa mun kada ki sake ɓoyewa, yanzu faɗa mun abin da ya faru dallah dallah". Ƙasa ta yi da kanta, bata so faɗa ba amma sai ta ce. "Dama ranar ne ya shake mun wuya saboda na yi maganar wani namiji, to a ranar Yah Omerish ne ya rabamu faɗa, shi ne sai ya ce Big Bro bai san daidai da ba daidai ba a wani lokaci, kuma shi bai san ya yi kuskure ya bada hakuri ba, dan haka in nuna na yi fushi da shi in janye daga garesa har sai ya gane yana yin kuskure ya koyi bada hakuri, to shi ne shi kuma ya ji abin da muƙa faɗa sai ya yi fushi damu tin kan mu mu yi fushi da shi". Ta kai karshen maganar hawaye suna cika mata ido, ALLAH SARKI ITA BATA SAN ME SOYAYYA BA SAI A KANSA, ZUCIYARTA BA ZATA IYA JURAN HUKUNCINSA NA KIN YI MATA MAGANA BA!. Momma ta gama fahimtar komai, murmushi irin nasu na manya ta yi kafin ta ce. "Kin yi ganganci kuma shi ma Omerish ya yi gangancin shiga tsakanin mata da miji, meyasa zaki bi shawarar wani a kan mijinki? Koma me ya yi maki ai mijinki ne, kin fi kowa sanin halinsa, kin san yadda zaki bi da shi ya koyi gane kuskurensa, kin san yadda zaki yi mashi ya koyi bada hakuri ba sai kin yi fushi da shi ba, ke ba mace bace? Mu fa mata dik girman namiji a tafin hannunmu yake, kina da hanyoyi da dama na horasa ba sai ta fushi ba, fushi da miji yana rusa soyayya sosai, kada ki sake yin fushi da shi, zan koya maki hanyar horasa cikin ruwan sanyi, batu na karshe kuma shi ne kishi a jininmu take tin daga kan iyaye da kakanni, ko da sunan wasa kada ki sake yin maganar wani namiji a gabansa, in ba haka ba bana jin akwai mai iya karɓarki ta daɗi a hannunsa". Ta ɗan dakata tana kallon fuskokinsu yadda suka tsareta da ido. "Da na ce ku zo dining mu haɗu mu ci abinci, to tin da hakan ya faru kowacce ta kaiwa mijinta abincinsa ɗaki dan ku gyara alaƙarku, zuwa dare zan yi magana dake". Ta kai karshen maganar tana sanya hannu ta sharewa Sweetie hawaye. "Kada ki yi kuka, nan gidan farinciki kika zo, gida ne da suka san darajar ɗan Adam, gida ne na masu kima da sanin yakamata, ki saki jiki ni mahaifiyarku ce gabaɗaya". Tana kai karshen maganar ta jawota jikinta. A hankali ta hau rarrashinta tana shafa bayanta har sai da Sweetie ta sauke nannauyar ajiyar zuciya alamar ta huce kenan. "To tashi ku yi wanka bari in baki kayan Zunaira ki saka, dan zai yi maku daidai". Tamkar Sweetie zata ce mata sun zo da kayansu, amma sai ta yi shiru saboda tana son dik wani abin da zai fito daga hannun wannan golden heart ɗin, momma ta wuci mai golden heart ma ai. "Mahreen haɗa mata ruwan wanka ko". Momma ta sake faɗa tana rabata da jikinta. Da sauri Mahreen ta diro kasa ta nufi toilet, ai tinda Sweetie ce zata haɗa mata da gudu ma, yarinya mai golden white hair ai dole aji da ita. Miƙewa momma ta yi ta fita. Momma ma fita Sweetie ta ɗagawa Pretty duka a baya tana faɗin. "Idan kika sake faɗar abin da ya shafi rayuwata ba da izinina ba ALLAH sai kin sani ne". Cikin zafa Pretty ta miƙe zata kai mata dukan ita ma Sweetie ta yi gaggawar dirowa kasan bed ɗin ta nufi toilet. Pretty zata biyota Mahnoor ta riketa tana faɗin. "Haba dai aunty Pretty amarya a wajen babban yayanmu, rabu da ita ki ci girma". Tana huci ta ce. "Ni aunty Mahnoor ki kyaleni in gwadawa yarinyar nan ni ba sa'arta bace ba".......... "A'a ba za'ayi haka ba, rabu da ita kin ji hai". Ta faɗa tare da jawota ta koma jikinta. Sweetie da shegen neman tsokana ana ƙoƙarin tausan Pretty ta leƙo da kai daga cikin toilet ta ce. "Haba aunty lutiya ai ni na wuce ki dakeni yanzu, matar Big Bro nike fa". Tana faɗar hakan ta koma ciki da gudu ta rufo kofa, har da murza key dan Mahreen ta gama haɗa ruwan ta fito. Takaci tamkar Pretty zata yi kuka ta ce. "Aunty Mahnoor ina cewa kin jita ko?". "Na jita amma rabu da ita zamu rama wani lokaci, ni baki faɗa mun bama, yar uwarkice? Naga kuna kama ovar". Kai ta gyaɗa alamar e kafin ta ce. "Twin's sister ɗita ce"....... "ALLAH sarki amma kuna kama sosai da sosai". Tana turo baki ta ce. "Na fita kyau ai, ita kalar gashin kanta ne jarinta, shiyasa take shiga rai, kowa yake sonta, ba da ban gashin kanta ba na fita kyau sosai". Pretty gidan rigima Mahnoor ta faɗa a ranta, a fili kuma ta ce. "Sosaima kin fita kyau, ai ko gashin ma naki ya fi nata kyau". "Da gaske nawa ya fi kyau?". Kai Mahnoor ta jinjina mata alamar e, kawai tana son rabasu faɗa ne, amma ita kanta tasan kalar gashin Sweetie wane yaro, ya fita daban, kyansa ma na musamman ne. Haka suka cigaba da hira, Sweetie na fitowa daga toilet ɗaure da towel a kirjinta sai ga momma ta shigo wasu kuyangu biyu suna biye da ita a baya hannunsu ɗauke da da kayan sakawa masu balain kyau da kamshi. WAI KUN SAN DA CEWA HANKALIN SMART BAI TAƁA BASHI YA YI TINANIN BABU AURE A TSAKANIN SWEETIE AND BIG BRO BA, SHAP YA MANCE CEWA SWEETIE MUSULMACE, SHI KUMA BIG BRO BA MUSULMI BA NE, BABU AURE A TSAKANINSU HAR SAI YA MUSULUNTA, AMMA KWATA-KWATA HANKALIN SMART BAI TAƁA KAIWA NAN YA YI TINANI BA, KUN SAN HANKALI KE TINANI, BAI MAI DA LURA BA!. Wani irin kunya Sweetie ta ji ya kamata, saboda yadda taga Momma ta ganta babu kaya. Momma kuwa jawota jikinta ma ta yi tana faɗin bari ta shiryata da kanta, sannan ta ce Pretty ma ta je ta yi wanka. Miƙewa ta yi tana turo baki ta nufi toilet. Momma da kanta ta shirya Sweetie cikin dandatsetsen doguwar riga irin ta ƴaƴan sarauta ta larabawa watau na Auta kenan. Ta sanya mata wani haɗaɗɗen alkyabba mai balain kyau na fitina. Ya subhanallah, Sweetie ta yi fitina a cikin kayan nan, ga wasu irin turarukan larabawa da momma ta turara kayan nan da shi, kamshi mai kwantar da hankali, sai ta fito a princess ɗin da gaske, ita kanta momma ta shaida an yi wa kyau kyau a wannan waje, dik cikin surkanenta har ma wanda basu zo ba bata jin zata sake samun mai kyan Sweetie da Pretty. Ita kanta momma launin gashin kan Sweetie ya yi balain tafiya da imaninta, sai ma da ta tara mata shi ta ɗaure, ta yi mata irin yadda larabawa ke ɗaure gashinsu, haba ai sai ta hau santin gashin tana addu'ar ALLAH yasa jikanta na farko daga wajensu ya ɗauko irin wannan gashi, zasu samu sabon launi a zuri'arsu, abin ya balain burgeta. Mahnoor da Mahreen dik sai santin kyan da Sweetie ta yi suke yi, to kun fa san dokar kingdom of power ba kowa yake kaiwa Prince abinci ba zai matarsa ko amintaccensa, dan haka momma ta ce kowacce ta je ta kaiwa mijinta abinci ɗaki, ta riko hannun Sweetie suka fita, ita kuma Pretty dama tasan hanya ba bakuwa bace, so da ta kammala shiri sai ta wuce room na momma. Ta yi mamakin gani momma da Sweetie zaune a gefen mattress suna tattaunawa, cikin sanyin murya ta ce. "Momma na je ɗakin Yah Omerish baya nan". Miƙewa momma ta yi tare da riko hannun Sweetie tana faɗin. "Dik sun dawo nan ai". Ta yi maganar tana nufo Pretty dake tsaye. Gaba ta yi suka rufa mata baya har zuwa dining, nan ta nunawa kowacce abincin mijinta, dan da kanta ta raba masu abincin ta shirya komai. Ɗauka suka yi sannan momma ta wuce gaba suka rufa mata baya, kowacce ta nuna mata room da mijinta yake a ciki kafin ta juya ta koma nata room ɗin. Kallon juna Sweetie and Pretty suka yi, Pretty ta dallawa Sweetie harara tare da cewa. "Zan kamaki ne?". Murguɗa mata baki Sweetie ta yi kafin ta ce. "Ba zan kamu ba ai". Kwafa Pretty ta yi. "Haka kika ce?". Kai Sweetie ta gyaɗa alamar e. Yunkurawa Pretty ta yi zata ajiye kayan abincin hannunta ya capkota, Sweetie ta yi gaggawar shigewa ɗakin da Big Bro yake tana murmushi. Kwafa Pretty ta yi game da cewa. "ALLAH zaki zo hannu ne sai kin yi kuka". Ta faɗa tare da wucewa ciki ita ma. -----------------------🔥 Siririn sallama ta yi mashi cikin natsuwa, a natse ta tako ta nufi ciki. Yana tsaye a tsakiyar ɗakin yana jin kamar ba zai iya zama a kingdom ɗin nan ba, dan wajen ya yi mashi wani iri, yana ta bin ɗakin da kallo, yana son kwanciya amma ya raina bed ɗin nan, wai a haka fa momma ita ce sarauniyar da ake ji da ita, part ɗinta ya fi na dik saura kyau da tsaruwa, amma Big Bro ya gagara kwanciya a gadon saboda wai ta yi mashi local dayawa. Da kyar ya yi wanka a toilet ɗinsu ya fito, cikin pj's white color ya shirya sakamakon ya ji birnin akwai zafi, ga shi bai saba da zafi ba, dik sai ya yi mugu-mugun takura, abin dai sai a slow. Ta kasan ido ya saci kallonta, ai a wani irin slow ya ɗago da kallonsa gabaɗaya a kanta, ya subhanallah, kara waro idanunsa waje ya yi yana kallon haɗuwarta. Shi kansa ya shaida ta yi fitina cikin wannan shiga, a ransa ya ce tamkar moon cikin stars (tamkar wata cikin taurari). A fili kuma sai ya kara ɗaure fuska yana ta ƙoƙarin dakatar da kansa daga kallonta amma ya gagara iyawa, dan yau ta wuce a ganta a iya kau da kai. A saman carpet ta dire masa abincin, sannan ta karisa gaban bed ɗinsa, alkyabbar jikinta ta cire ta ɗaura a gefen bed ɗin dan bata saba da da shi ba, so sai ta ciresa kafin ta dawo wajen abincin zata zauna kenan sai kuma ta ga rashin dacewar hakan, koma dai menene ita ce karama a kansa. Dan haka sai ta fasa zama ta nufosa. Dik in da ta yi sai kwayar idanunsa sun bita, wlh wani irin yawu da ya haɗiye time da ta cire alkyabbarta sai da makogwaronsa ta yi wani irin harbawa, wannan ƙashin makoshin nasu sai da ta harba da karfi. A gabansa ta kariso ta tsaya, cikin sanyin murya ta ce. "Barka da yamma Big Bro". Shiru bai amsa mata ba, kallonsa ya koma kan matasan kyawawan tula-tulanta dake ɓul-ɓul da su gwanin ban sha'awa da ɗaukar hankali, yanayin doguwar rigar tata mai breast cuff ne, so yana iya kallan tudun tula-tulan nata. Take ya ji wani abu ya tokare mashi maƙoshi, har wani kishirwa ya ji, dik sai ya ji tamkar an takure shi waje guda. Ganin bai amsa mata ba ne yasa ta ce. "Ina mai baka hakuri a kan abin da ya faru a rannan, na gane kuskurena kuma ba zan sake ba". Ta yi maganar tare da ɗago da kallonta a kansa. Ai wani irin dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, ji yake yi tamkar ya sanya hannunsa ya shafi tula-tulanta, haka kawai suka tsole mashi idanu suka kuma tokare mashi maƙoshi. Jin alamar bashi da niyyar yi mata magana ne yasa ta hakura tana jin zuciyarta tamkar zata fashe, ta zo har wuya, gaskiya horon nan ya yi mata tsauri, ba zata iya jurewa ba ko kaɗan. Da sauri ta juya tana sanya hannun ta toshe bakinta saboda wani irin kuka da yake shirin kubce mata, waje ta nufa da gudu. Slowly ya kai hannu ya riko hannunta, da sauri ta juyo, tana jiyowa ya fisgota ta faɗa saman lion chest ɗinsa. Ɗan rainin wayau har da sauke cool ajiyar zuciya alamar shi ya ji daɗin wannan sabga, amma kuma da ya tsaya yi wa yar mutane iskanci. Tana shirin fashe mashi da kuka ya yi gaggawar ɗaura yatsansa a saman ɗan bakinta kafin ya hau girgiza mata kai alamar baya so kada ta yi. Ɗago kai ta yi suna kallon juna, wani irin fitinannen son junane yake kara shigarsu wanda basu shirya mashi ba. Hannu yasa cikin dabara ya ware jelar gashinta da momma ta ɗaure mata, ya zare pin ɗin take gashin ya watse har gadan bayanta, kun san gashin nata very silky haka yake. Can kasan makoshi ta tsinkayo sharp voice ɗinsa ya ce. "Kin yi kyau sosai". Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta mai da kanta saman kirjinsa ta kwanta, cikin sanyin murya ta ce. "Nagode ka zo mu ci abinci". Hannunsa ya tura cikin gashin nata, a hankali ya fara shafawa yana lumshe ido saboda daɗin kamshin tirarukan da momma ta turare mata kaya ya tafi da imaninsa. "Meyasa kika gujeni kwanaki dayawa?". Muryarsa ta ratsa dodan kunnenta. A miliyan ta ɗago kai, mamaki ne ya kamata, wai meyasa ta gujesa, lallaima bawan ALLAHN nan, to ita da shi waye ya guji ɗan uwa? ALLAH mai iko. Ganin ta kafesa da ido ne yasa ya ɗan hura mata iska daga bakinsa. Ɗan lumshe ido ta yi ta sake warosu a kansa. "Kai ne fa ka gujemu". A shagwaɓe sosai ta faɗa, ɗan matseta a jikinsa ya yi tare da rankwafo da kansa a kanta. "Kada ki faɗawa momma ke ba matata bace". Kamar mai raɗa ya yi maganar. "Amma kasan dik daren daɗewa zata san gaskiya ko? Kuma ai bama zai yiwu ba, dan a matsayina na matarka dole zan rinƙa kwana da kai a ɗakin nan a idanunsu, to ya zamu yi?". Cike da shakku ta yi maganar. Uhm shi da ba addini ne da shi ba sai ya ce. "E to me laifi a ciki dan mun kwana a tare ɗin?. Ba zasu taɓa sani ba sai in kece kika faɗa masu"......... Tab yanzu ta kara tabbatarwa Big Bro bai san addinin musulunci ba. Cikin natsuwa ta ce. "Haramune mace da namiji su zauna a ɗaki ɗaya haka in ba ma'aurata ba, addinina ya haramta hakan, dan haka ba zai yiwu ba"......... Yana kallon cikin idonta, ya yi shiru na ƴan mintuna, har ta fidda ran zai sake yin magana sai ta ji ya ce. "Zaki kwana a saman sofa ni zan kwana a saman bed, ya yi maki?". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Dik da haka watarana zasu gane fa". Kai ya ɗan girgiza mata. "Ba zasu gane ba, ba zamu jima a nan ba zamu koma, momma tana sonki, please kada kisa farincikin da take yi ya kau". Kai ta ɗan jinjina mashi. "In Sha ALLAH farincikinta ba zai tsaya ba, zan yi abin da ya dace"....... Murya kamar yana a cikin maye ya ce. "Promise?". Kai ta jinjina alamar e kafin ta ce. "Zan yi alkawari, amma kai ma ka yi alkawarin ba zaka rinƙa taɓa mun jiki ba?". Kai ya jinjina mata alamar ya yi alkawari babu wani abin da zai yi mata, kawai dai zasu shiga ɗaki matsayin mata da miji a kingdom ɗin wa idon kowa, amma da sun shiga sun rufe kofa kowa zai yi ta kansa babu ruwan kowa da kowa. MY PEOPLE'S ANYA WANNAN WASA ZATA YIWU KUWA? HMMM KOWA YANAI MASU KALLAN MATA DA MIJI FA, TAB AKWAI CASE, YANZU WASAN SABUWAR DUNIYA ZAI FARA!. "Muje mu ci abinci to". Ta faɗa tana kallonsa. Mai da kallonsa kan kayan abincin ya yi, sai yaga sun yi mashi local, shi da tsabar izza da kuɗi idan ya ci abinci a kayan abinci ba'a sake saka mashi abinci a ciki sai dai a rinƙa sanyawa kuyangu ko sojojin yakinsa a ciki, kullum cikin sabbin kayan zuba abinci yake cin abin, amma yanzu yake ganin wasu warmar wai a ciki zai ci abinci, to amma ya zai yi tin da momma ta zuba mashi? Ci yazama dole ai. Kwace jikinta daga nasa ta yi ta nufi wajen cin abincin. Bayanta ya bi da kallo yana jin wani irin tsananin sha'awarta na fusgarsa, ji yake tamkar kawai ya kai kansa gareta, ya sallama mata kansa, amma ina ba zai yiwu ba, ya ma yi alkawarin zai daina taɓata, kunga dole in yana so ta cigaba da aminta da shi ta nunawa Kingdom ita matarsa ce to dole ya yi ƙoƙarin danne kansa. Ya yi nisa cikin tinani ta yi mashi alama da hannu a kan ya zo mana. Ba musu ya karisa wajen, zama ya yi a saman carpet ɗin, sai ya ji tamkar a kan kasa ya zauna, wai carpet ɗin babu laushi, ba kamar na kingdom ɗinsa ba. Zuba mashi abinci ta yi ta turo mashi gabansa, wani irin kallo ya bi abincin da shi, to shi ko shinkafa bai taɓa ci ba a rayuwarsa, yaga su basmati yau, sai ma suka yi mashi maka da tsutsa da kayan miya, cimansu ya sha banban nesa ba kusa ba. Amma yana jin yunwa, daurewa ya yi ya ɗauki spoon yana kokarin toshe hanci saboda kamshin girkin bata yi mashi ba. Sam Sweetie bata lura da halin da yake ciki ba, ta ɗauki spoon tana ɗan jujjuya abincin ita ma, sam bai yi mata ba, amma saboda kada ya ga kamar ta walaƙanta mommarsu ta ce abincin bai yi mata bane yasa ta ce bari ta daure ta ci, bata san shi ma ɗin bai yi mashi ba. Ɗebowa ta yi zata kai baki kenan ta ga ya miƙe da zafa yana toshe baki saboda aman da ta kubce mashi, da sauri ta miƙe tsaye ita ma. Ina tuni ya isa toilet, daga in da take tana jiyo wani irin kakarin amai da yake yi, hankalinta ne ya yi mugun tashi har bata san lokacin da ta afka cikin toilet ɗin ta bi bayansa ba. TO FAH!. ---------------------🔥 A daidai wannan lokacin shi kuma goyson yana tsaye a tsakiyar room na Mahreen yana kare mata kallo, ya zo bata labarin Big Bro ɗinsu ya bayyana, kun san idan kana son mutum ko wani irin abin farinciki ya sameka zaka yi haba-haban sanar da wanda kakeso, shi ita ma ya ɗebo farincikin ya zo sanar da ita. Amma ina bata bari ya sanar da ita abin da ya kawo shi ba fa hau zazzaga mashi masifar ya fita mata a ɗaki, tana tsaye a gaban mirror tana ta kallon kanta, Chuchu ta yi mata make up, shi ne take karewa kanta kallo, sai faɗi take yi. "Mahreen wutar kyau, kyau iya kyau yarinya yar babanta, wannan kayan manyan kai ne, yar beautyn bappanta, kin fa yi kyau". Kamar wata zararriya ta tsaya tana yabon kai. Tin da ya shigo ya tsareta da ido, sai zazzaga faɗa take yi tana ya fita amma sam baya jinta, hankalinsa na kan kyanta, ga doguwar rigar tata ta zauna a jikinta tsam, sai yake jin tamkar zai iya karisa tsawon rayuwarsa yana kallonta ba tare da gajiyawa ba. "Ba zaka fita mun a ɗaki ba sai na je na faɗawa Yah Jaish kana shiga harkata?". Cikin tsiwa ta faɗa. Gera guda ya ɗaga mata kafin ya kwaikwayi yar muryarta ya ce. "Ni gaskiya ba zan fita ba har sai kin saurareni kin ji me na zo faɗa maki". "Ni babu abin da zan saurara, kawai ka fita". "To zo ki fitar da ni idan kina da karfi". Kwafa ta yi a kufule ta ce. "Haka ka ce?"........... Gera guda ya ɗaga mata alamar e. Fuuuuuu ta nufosa tana janye hannu riga sama ita a dole zata fitar da shi waje. Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 -------------------------------------------🔥♥️ ZABUWAR DUNIYA STEP ONE!.🔥🔥🔥 Ko kaɗan bata ji shakkarsa ba tazo harda kara gyara hannun riga, sannan tasa hannun ya cakumo cikinsa, ta daddage wai zata ɗaga shi sama ita ga mai karfi. Ko motsa shi bata iya yi ba, shi kuwa yasa hannunsa ɗaya ya riko waist ɗinta ta wajen cikinta, sama ya ɗagata, saboda tsabar neman magana shi ma irin nasa da rashin son a zauna lafiya, ko da yake dama ya ce ba zai barta ba, ya rinƙa shiga gonarta kenan. Daga in da yake ya yi jifa da ita sai saman bed ɗinta. Murmushi ya saki mai ƙayatarwa kafin ya ce. "Jita ko karfin ɗaga hannuna ɗaya bata da shi, da wani idanunta a wajen, gata ba nauyi kamar kwali". Yadda yake murmushi ita kanta ba zata so ya daina yi ba, dan wlh ba karamun kyau ya yi ba, ya haskaka ɗakin matuƙa, ga fararen hakwaransa tas suna ta kyalli tamkar babu abin da ya taɓa ratsa bakinsa ya wuce, dimples ɗinsa irin na yayansa Big Bro. A fusace ta ɗago daga gadan, amma ganin yadda murmushinsa ta yi balain haskaka ɗakin ne yasa ta ɗan tsaya a saman mattress ɗin tana satar kallon shi da wayau, dama ta taso ne da nufin ta sauko kasa ta kamashi da kokawa, ganin yana sakin cool murmushi yasa ta fake da ta tsaya tana huci tana harararsa sai kallan madarar kyan da ALLAH ya zuba mashi take yi. Lokaci guda a ranta ta ji cewa in banda ma soyayya da babu ruwanta da kyau ko kuɗi ai ita kanta tasan guyson ya fita komai da komai, ya fita kyau, haske, kuɗi, komai ma, amma a haka yake ta binta yana rokon soyayya daga gareta, ALLAH mai iko kenan, ALLAH mai adalci sosai, ba ruwansa da karfin mulkinka sai ya sanya maka son almajira ma, dan kawai kowa ya ji shi mai daraja ne. -------------------🔥 Mata da suke ganin su ba kyawawa bane ma ni kuna bani mamaki wlh, na taɓa jin wata da kanta tana zagin kanta wai ita mummuna ce, for what reason? Kina hauka ne? Angaya maki ALLAH ya taɓa yin abin da babu kyau ne, sannan dik cikin abin da ALLAH ya halitta babu abin da ya karrama sama da halittar ɗan adam, amma har kina da bakin da zakice baki da kyau ko ki ce wata bata da kyau? Billahillazi babu ɗan adam ɗin da bashi da kyau, domin kuwa dik abin da ALLAH ya halitta mai kyau ne, bari in baki misali, ALLAH ya yi ki da bakar fata, kice bari ki canza zuwa fara, wlh ba karamin muni masu canza halitta suke yi ba, to tin daga nan zaki gane dik abin da ALLAH ya ajiye a wajen bashi da muhallin da ya wuce wannan waje, uhm ALLAH yana bawa bayinsa abubuwa da dama a time da ya so, ya halicci fara, ya hanata sura da diri, dan basu dace da ita ba, ya halicci baka, ya bata kaifin ƙwaƙwalwa da ilimin da duniya zata yi alfahari da ita, zata taka in da farar bata taka ba. Amma mu duba me ALLAH ya ce. Allah ya bayyana cewa duk abin da ya halitta yana da kyau, yana da hikima, kuma babu rashin adalci ko kuskure cikin halittarsa. Wannan ya haɗa da kyawawan mutane da waɗanda ba su da kyau a bayyane, domin dukkanin su suna da wani sirri da amfani a cikin tsarin halitta. Cikin Suratul As-Sajdah sura ta 32 aya ta 7 zuwa ta 9. Wannan aya tana tabbatar da cewa kowane abu da ALLAH ya halitta yana da kyau cikin tsarin da ya so. Kazalika cikin Suratul At-Tin sura ta 95 ayata 4. Wannan ayar na nuna cewa a cikin asali da tsarin halitta, mutum yana da kyakkyawan sura da daraja. Suratul Ghafir sura ta 40 aya ta 64. Ayar nan na nuna cewa ALLAH ne ya halitta mu cikin sura mai kyau wanda yake bisa kyakkyawan nufi da tsarin hikima. Dan haka babu halittar da ba ta da amfani. Suratul Ali Imran sura ta 3 ayata 191. Rabbana ma khalaqta hadha batilan..............Abin da ke nuni da cewa kowane abu da ALLAH ya halitta yana da hikima da ma'ana ba kawai kyakkyawa a bayyane ba, akwai ta sirrance da ALLAH ya yita. Idan na ce zan tsaya zayyana maku ayoyi a kan halittar ɗan adam sai mu kare page ɗin nan, dan haka ku daina raina halittar ALLAH, babban kuskure ne. Dik yadda Manzon ALLAH ya kai ga son Nana A'isha sai da ranan ya tsawatar mata da ta ce wa wani yana da katon kai, iya abin da ta faɗa kenan, amma manzon ALLAH ya ce mata wannan magana da kika faɗa A'isha, muninta ya kai ta iya lalata ruwan teku, to ke waya aikeki ki ce da wata mummuna ko ki cewa kanki Mummuna?. Ki ji da kanki, ki ji a ranki kin fi kowa kyau, ki ce babu biyunki a kyau, kada ki kuskura ki taɓa haɗa kanki da wata, dan ke tadabance, na jima ina son yin magana a kan halittar nan wlh lokacin ab-ban samu, yau dai nace bari in daure in yi, kada karatun littafai ko kallon fina-finai yasa ki ji ke ba kyakkyawa bace, ina karya ne wlh, kyanki sirri ne, ki natsu zaki gano hakan. A dai hasken fata na Nigeria ni ba baka bace, ni fara ce, amma ina balain kaunar bakake sosai, shiyasa bana taɓa yin rubutu babu bakaken fata ko ban daraja fatar ba, saboda me? Saboda wasu Annabawa bakaken fata ne, sannan tushen kowani ɗan adam baki ne tin da Annabi Adam (As) baki ne!!. Kada ki raina halittarki ko na wata, baki san sirrin da ALLAH ya ɓoye a wajen ba!!!. ---------------------🔥 Ganin ta shagaltu da kallonsa ba tare da tasan tana kallon nasa bane yasa ya ɗage mata gera guda yana cigaba da ƙayataccen murmushinsa. "Yah how far? Nai maki kyau ne?". Ya faɗa yana kai hannun saman waist ɗinsa, ya riko kugun nasa yana ɗan jujjuyawa kaɗan-kaɗan. "Kai ɗin ne kyakkyawa? Tab ka cuci kyawawa, yo ai nina ma fika kyau". Ta faɗa tana harararsa. "For sure kin fini kyau, amma ke kaɗai ce kika fini, ni dai kawai cewa na yi shin nai maki kyau ne? Ban ce na fikiba chocolatyna mai ɗan karamin baki sai faɗa da masifa". Cikin zolaya ya yi maganar. Tana cigaba da harararsa ta ce. "To ai na fika baki nesa ba kusa ba, kai ba dan ALLAH ya ceceka bakin naka pink color sosai bane da ai bama za'a san kana da shi ba saboda ƙanƙanta"........... Shiru bai yi magana ba yana cigaba da murmushi. "Ni ka fita mun a ɗaki na ce". Ta faɗa tana dirowa kasan bed ɗin kamar wata renon Chinawa. Yana tsaye bai motsa ba har ta kariso gabansa, a karo na biyu tasa hannu zata cakumesa ta kaishi waje, sai dai a wannan karo hannayenta dikka biyu ya damko da hannunsa ɗaya, ya mai da hannayen nata ta bayanta. Ƙoƙarin kwacewa ta fara yi amma ta kasa, hakan yasa ta hakura ta fara faɗin. "Ni ka sakeni bana so". Gera guda ya ɗage mata. "Ki kwaci kanki tin da kina da karfi". Turo mashi baki ta yi. "In baka sakeni ba sai na ja maka ALLAH ya isa". Wani irin kallon kurilla yake binta da shi, showly ya ɗan rankwafo kanta kaɗan, hakan yasa ta yi gaggawar ja da baya, matsawa ya yi dab da ita, da sauri ta sake ja da baya. Haka suka yi har suka kurewa wall ɗin wajen. A hankali ta juya ta ga sun kure bango, da sauri ta juyo da kallonta a kansa, ai wani irin razana ta yi na ganin ya matso da face ɗinsa dab da tata. Zazzaro mashi idanu waje ta yi, da sauri ta sake cewa. "Ni ka sakeni bana so"...... Shiru bai yi magana ba, yana dai cigaba da kallonta. Cikin faɗa ta ce. "Na ce ka sakeni ko?". "Shiiiiiiiii, ki daina magana mana, ki tsaya shiru". Ya faɗa cikin wata iriyar murya tamkar yana a cikin maye. Kirjinta ne ya yi wani irin bugawa na jin yadda voice ɗinsa ta rikiɗe, shi kansa ya rikiɗe mata, idanunsa sun canza kala, yanayin fuskarsa gabaɗaya ta sauya, hannunsa da ya riketa sai kakkarwa yake yi tamkar yana jin sanyi. "Ba zan daina yin magana ba tin da ba bakinka bane nawa ne, ni ka sake ni, dama kullum ina faɗa cewa kai ɗan iska ne, to ni ina da mutumcina, ka sakeni"........ Kashe mata ido ɗaya ya yi, in a low voice sosai ya ce. "Ai ban ga mutumcin naki ba, kuma wlh in kika sake yin magana a nan zaki sha mamakina". Ya yi maganar kallonsa a kan ɗan siririn dogon wuyanta. "Magana fa saina yi tin da ba da bakinka nike yi ba, kuma sai ka sakeni in ba haka ba in gantsara maka cizo a hannun naka sai an kaika asibiti..........". Ai bata kai karshen maganar ba ta ɗauke wuta diff sakamakon matsawa da ya yi ya haɗe bakinsu waje guda. Da karfi ta fara kokarin kwace hannunta dan ta turesa, sai dai kuma ina, bazata iya ba, ta yi iya kokarinta ta kwaci bakinta daga nasa, nan ma ta gagara. Shi kuwa ai ɗayan hannunsa ma yasa ya mannata da jikinsa sosai, ya rikota ta baya, ga ɗayan hannun nasa kuma ya rike hannayenta da shi. Hot kiss ya bata mai rai da lafiya for almost 5 mins kafin slowly ya zame ɗan bakinsa daga nata yana lumshe idanunsa tamkar mai jin barci. To ɗazun da ya ce kada ta sake yin magana bata yarda ba da ta sake, yanzu kuma sai ga shi bai ce kada ta sake yin magana ba ta yi shiru diff tamkar an ɗauke wutar nepa, ta kafe shi da ido tamkar wacce ta sume mashi, ko motsi bata yi. Da kyar ya iya waro idanunsa gabaɗaya a kanta, saboda tsabar neman tsokana irin nasa shi ma sai cewa ya yi. "You're over, in kara kaɗan?". Yadda ya yi maganar tamkar irin wanda kwaya ta buga ɗin nan. Shiru bata amsa mashi ba, hakan yasa ya ɗan saki hannayenta tare da ɗaukarta cak sai saman bed ɗinta, yana jin tana breathing, hakan yasa ya fahimci ba suma ta yi ba, kawai ta tafi hutu ne na wuccin gadi, zata dawo daidai idan ta ɗan huta, yau dai babu bakin rashin kunya. NI KUWA NA CE AKWAI BALAI A KINGDOM YAU, AN SHAWA YAR BAPPA ƊAN BAKIN MASIFA. Gyarawa ya yi ya kwanta a kusa da ita kamar wata matarsa, har da juyowa ya ɗan yi rugingine yana kallon fuskarta, jira yake yi ta dawo daidai su buga diramarsu, dan yasan ALLAH ne kawai zai raba wanna faɗa yau, ya ɗebo da zafi, to amma ya zai yi? Sai da ya ce mata kada ta sake yin magana taki bin umarninsa, shi kuma ba zai iya shanye maganarta a kurkursa da shi haka ba, dan haka ya cika aiki, da alama ya shirya duk diramar da zata buga yau. ------------------------🔥 Sosai ya bata tausayi ganin yadda yake ta kwarara amai tamkar zai amayar da dik wasu ƴaƴan hanjinsa. Tsorata ta yi na ganin halin da yake a ciki, bata taɓa ganin mutum yana amai irin haka ba, sai ta zaci zai amayar da kayan cikinsa ne dikka. Da gudu ta fito ta nufi room na momma, jikinta har kerma yake yi saboda tsoron kada ya mutu. Zaune ta isko momma da Mahnoor, Mahnoor ta kwanto da kanta saman laps ɗib momma tana aikin matsa yatsun hannun momma ɗin, ita kuma momma tana ta shafa kanta suna hira tamkar uwa da ƴa. Ko sallama Sweetie bata yi masu ba ta afko cikin ɗakin, hakan ya razana Mahnoor sosai, ita kuwa momma a dake take ta bita da kallo. A gabansu ta kariso tana faɗin momma ta zo Big Bro yana ta amai. Da sauri Mahnoor ta miƙe zaune, hakan ya baiwa momma damar miƙewa ita ma, ba tare da ta yi masu magana ba ta nufi waje da sauri. Da gudu Sweetie ta rufa mata baya. Har lokacin yana cikin toilet ɗin yana tikar amai sosai, ciki momma ta shiga, ita kuma Sweetie ta tsaya a tsakiyar ɗakin tana kai komo tamkar wadda aka ce mata mom ɗinta ce a icu. Almost 5 mins da shigar momma cikin toilet ɗin sai gasu sun fito a tare tana rike da hannunsa, har fuskarsa ta yi jajir saboda wahala, da wuya idan ya taɓa yin amai irin haka a rayuwarsa. So mugun wasa, Sweetie bata san lokacin da ta isa gabansu tana faɗin. "Meyasaka yi amai? Meyafaru?". Momma mace mai fahimta, sai ta riko hannunta tana faɗin. "Babu komai, kada ki damu babu abin da ya same shi, abincin namu ne bai yi mashi ba, bari in yi wa mom Omerish magana tana nan zata girka maku irin abincinku, dan dik tafiyar abincin naku kusan iri ɗaya ne, zan sa a kwashi waɗan nan yanzu". Sai a lokacin Sweetie ta ji kunya ya kamata, da sauri ta ɗan ja baya ta basu hanya tana wani yin kasa da kai. Nan ma momma ta fahimta sai ta ce. "Kadaki damu, na kara tabbatarwa da ɗana ya samu wacce ta dace shi, kuma wacce zata kula da shi sosai, ba shakka kina sonsa sosai". Ƙasa ta yi da kai sosai, momma kuma ta saketa ta wuce gaba, a bakin bed ɗin ta zaunar da shi kafin ta ce mashi tana zuwa. Kai ya jinjina mata kallonsa a kan Sweetie, ya yi mamakin ganin yadda ta birkice sosai ta tashi hankalinta dan ya shiga wannan hali, ya kuma ji mugun daɗi over. Momma na fita ta ɗago kai da kallonta ta sauke a kansa, sai ta ga ai ita yake kallo. A hankali ta motsa bakinta wajen cewa. "Sannu ya jiki?". Shiru bai amsa ba kuma bai daina kallonta ba. Ganin hakan yasa ta wuce izuwa saman sofa zata zauna kenan muryarsa ya daki dodan kunnenta. "Momma fa tana dawowa". Ya faɗa tamkar ba shi ya yi maganar ba. Ɗan turo mashi baki ta yi. "To me zan yi kenan?". Tana kallonsa ta yi maganar. Da hannu ta nuna mata gefensa a kan ta dawo wajen ta zauna. Bata musa ba ta nufesa, zama ta yi tare da ɗan juyo da kallonta a kansa. Haba take idanunsu ya sarkafe cikin na juna, har momma ta yi sallama ta shigo basu jita ba, sun lula wata duniyar da su kansu basu tantance a takamaiman wace duniya suke na, Mercury ne ko Jupiter, sun dai lula duniyar sama. Ba karamin daɗi momma ta ji ba na ganin yadda suke balain son juna a tinaninta, sai ta ce ba zata katse masu jin daɗi ba, dan haka bata yi masu magana ba tasa kuyangun da suka biyota suka kwashe kayan abincin suka yi waje da su, ita ma ta rufa masu baya. Ajiyar zuciya dikkansu suka sauke a lokacin da suka fuskanci mutum ya fita daga ɗakin, da sauri suka kai kallonsu kan hanyar fita, nan suka ga an kwashe kayan abincin, a hanzarce suka dawo da kallonsu a kan juna, mamakin kansu suka shiga yi ta yadda har aka shiga ɗakin aka fita basu sani ba, lokaci guda Sweetie ta saki murmishi tare da miƙewa tsaye ta nufi saman sofa. Shi ma kiƙewa ya yi ya nufi hanyar fita, bata ce mashi ko uppan ba shi ma haka ya fice daga ɗakin. Bai zame ko'ina ba face room ɗin Smart dake kusa da shi, to shi da ba addini ba ina ruwansa da sallama, kawai ya tura masu kofa ya shiga. Manne da juna ya samesu, Pretty sai zuba mashi shagwaɓa take yi, sun ci sun ƙoshi abinsu, Smart na kwance saman bed daga shi sai doguwar wandon pj's, ya cire rigar, ita kuma Pretty ta kwanta a saman lion chest ɗinsa tana kuka wai sai ya yi mata kwalliya, bafa a fuskarta zai yi kwalliyar ba. A'a a fuskarsa zai yi ta ga ya zai zama, wai yana da kyau a haka ma, amma idan ya yi kwalliya sai ya fi kyau, rigimar da take ta yi mashi kenan yaki kulata, shi ne take ta faman jan mashi dogon hanci. A karo na farko yau sai da gaban Big Bro ya faɗi da ya gansu haka, a ransa ya shaida shi ma yana buƙatar irin wannan rayuwa, sannan yana son mace mai balain shagwaɓa da son jiki irin Pretty, ita Pretty idan Smart yana waje bata taɓa zama bata manne mashi a jiki ba, kun tuna ita da Kamran a Forest saboda shegen son jiki ba haka take lafe mashi a jiki ba? To haka take ita, Big Bro yana son hakan sosai, shiyasa Pretty take burgesa, ba dan haka ba ma ranar da ta daki Sweetie da wlh ba zai barta ba, sai ya hukuntata, amma saboda yana fatan ta koyawa Sweetie waɗan nan ɗabi'un nata yasa ya ɗaga mata kafa ya yafe. Hannu Smart ya ɗaura a saman bayan Pretty kafin ya ce. "Big Bro akwai wani abin ne?"......... Harara ya dalla mashi kafin ya ce. "Zo ka rakani waje"....... Cike da mamaki Smart ya ce. "Waje kuma?". Shiru bai amsa ba, bashi ma da niyar sake yin magana, dawo da kallonsa a kanta Pretty ya yi kafin ya ce. "To tashi mun a jiki bari in rakasa waje". Baki ta ɗan turo. "Idan ka dawo zaka yi kwalliyar?". Kai kawai ya gyaɗa mata, ɗan bakinta ta kai ta manna mashi sumbata a kumatu kafin ta mirgita ta sauka daga kirjin nasa ta koma saman gadan. Dik abin da suke yi Big Bro yana kallonsu, shi ma dai yana ta kara kwaɗayin irin wannan rayuwa tasu. Bargo Smart ya ja ya rufa mata har zuwa wuya, sannan ya sumbaci forehead ɗinta kafin ya sauko kasa. Rigarsa ya ɗauka ya sanya, dik Big Bro yana tsaye tamkar wanda aka sassaƙa. Smart na zuwa gabansa ya ɗan kai mashi dukan wasa a kirji kafin ya ce. "Sistermu ta yi barci ne?". Kai Big Bro ya ɗan girgiza alamar a'a kafin ya juya suka nufi waje. "Mezaka je yi a waje?". Smart ya tambaya. Shiru bai amsa ba har suka hau elevator suka sauka kasa. Ainahin harabar kingdom ɗin suka fito ba harabar family part ba. Tafiya suka fara yi suna ɗan hira jefi-jefi Smart yana ta yi mashi bayanin dik wasu abubuwan da suka dace, dik in suka wuce waje sai ya yi mashi bayanin wajen. Shi dai shiru bai cewa komai ba. Ai jin Big Bro ya fito yasa dikka su Sareena suka fito kallonsa, sai dai kuma fa har yanzu dik wanda ya kallesa sau ɗaya baya iya maimaita na biyu a lokacin, Sharifat da ta kallesa ta ce to wlh ita yanzu shi take so ba Ramish ba, ta hakura ta barwa Leesharh Ramish. Ita ƙuwa Sareena ta ce zata yi faɗa domin samun soyayyan ɗaya daga cikinsu, a ranta ta san Big Bro ko gawarsa ta fi karfinta, shiyasa bata ɗaurawa kanta azaba ba, bata fara abin da ta san ba zata iya ba, commond kallon sa sau biyu a lokacin guda basa iya yi to ina ita ina iya neman soyayyarsa? Ai ta ce da shi da Smart dik abu ɗaya ne, dan haka gara ta tsaya wajen Smart ɗin sai ya fi mata sauki. AI BAKIN RIJIYA BA WAJEN WASAN MAKAHO BANE SAREENA, WAYA CE MAKI BORNO GABAS TAKE? BIG BRO AI SAI DAI IYAYEN YARA, WANE KAN YARO. Ita dai Sharifat ta ɗebo da zafi, ta ce yanzu Big Bro take so. Dik cikin ƴaƴan King har da waɗan da suke uba ɗaya da Big Bro babu wanda bai ji sonsa a ransa ba, dan shi ɗin na daban ne, sai dai kuma babu wanda ya sawa kansa zai samu, sun dai bar son a ransu. -------------------🔥 Sun sha kewaye sosai har aka fara kiraye-kirayen sallar mangariba, a nan ne suka nufo family part. Suna tafiya ne Big Bro ya hango side na uncle Abbas, murya a sanyayye sosai ya ce. "Wannan part na waye?". "For our uncle". Smart ya bashi amsa yana kallon Smart ɗin. Shiru Big Bro ya ɗan yi idanunsa suna ganin masa abubuwan tsafi dayawa a cikin wannan part ɗin, a ransa ya ce kenan suma a nan suna yin amfani da magic ne ko yaya?. Smart ne ya katse mashi zancen zucin nasa da cewa. "Meyasa ka yi magana a kan su Omaid ɗazun?". Shiru ya yi har sai da suka hau elevator sannan ya ce. "Akwai dalili, but not now zaka sani, yanzu dai ina Omar?"........... Shiru Smart ya ɗan yi kafin ya ce. "I think yana room ɗinsa, da wani abin ne?"....... Kai ya ɗan jinjina alamar e. Dawo da kallonsa a kansa Smart ya yi kafin ya ce. "Zan iya sani yanzu ko shi ma sai gaba?". "E to kusan hakan, sai na san waye ya haɗa shi da wannan ciwo tukun nan, yanzu dai mu je ka bani wayarka na nan bari in yi magana". Smart ya so tambayar wani ciwo kenan?. Sai kuma ya yi shiru, dan yasan ko ya tambaya ba samun amsa zai yi ba. Shiru suka yi har suka isa bedroom na Smart, ya ɗauko waya ya baiwa Big Bro, a wajen Big Bro ya tsaya ya shigar da numbar da yake son kira. Ana ɗagawa ya hau yin magana a natse cikin bada umarni. Shiru Smart ya tsaya yana mamakin jin kalaman ɗan uwan nasa. Umarni ya bada da a kwaso kayan aiki a cikin jiragensa, a zo a ginawa mahaifinsa palace ɗin da babu wani sarki a wannan zamani da ya taɓa mallakan makamancinsa, fitan da ya yi yanzu suka yi kewaye fili ya duba, dan haka ya samu ishasshen filin da yake ganin zasu isa a gida har da katafaren airport a cikin palace ɗin wanda jirage zasu iya sauka ko tashi, kun ga idan wani zai yi tafiya a family no need na zuwa airport. Kun tuna wani katafaren waje da na taɓa magana a kai wanda dik jumma'a ake tsere da dawakai a wajen? Kun tuna filin? To wannan fili Big Bro yasa a baje komai a fitar da tsarin palace irin nasa a wajen, ya buƙaci da a kawo masu gold, da su za'ayi kwalliyar ginin ma, yadda dai ya narka dukiya a nasa ginin haka zai yi wa mahaifinsa. Abin da ya yi mugun ɗaurewa Smart kai shi ne hadda Big Bro ya ce nan da kwana talatin ya bada su kammala wanna ginin, mamaki Smart yake yi a kan ta yaya za'a gama ginin nan a 30 days, bayan ba gini na wasa ya ce ayi ba, hawa goma daidai kamar sabon palace ɗinsa na Black World, yaushe aka fara bare a gama?. To amma nasa dai ido shi kam. Bayan ya kammala wayar ne ya miƙawa Smart wayansa ya nufi waje. Da kallo Smart ya bisa har ya fice sannan ya dawo da kallonsa a kan Pretty da barci ya yi awon gaba da ita. Toilet Smart ya wuce dan ya ɗauro alwala lokacin yin sallah ta yi. Zaune a zaman dadduma Big Bro ya isko Sweetie, tana sanye da dogon hijabi har kasa, ta idar da sallar mangariba. Sai kallon hijabin nata yake yi, bai taɓa kallo hijabi a zahiri ba, sai a media, kun san yadda birnin nasa take, do yasan hijabi, a zahiri ne bai taɓa gani ba. Saman bed ya wuce ya kwanta yana cigaba da kallonta, while ita kuma bata tashi a wajen ba har sai da lokacin sallar ishai ya yi, ta yi sallah sanan ta miƙe bayan tayi addu'ointa. Cire hijabin ta yi, ta naɗesa da kyau, hijabin Auta ta je ta ɗauko dama, sai yau ta san ta yi sallah mai kyau da natsuwa ga cikken sutura. Waje ta nufa ba tare da ta yi mashi magana ba, har zata buɗe door ta fita muryarsa ya katseta da cewa. "Ina zaki je?". A natse ta juyo. "Momma ce tace idan na yi sallah in zo in ɗauka maka abinci".......... Shiru bai sake yin magana ba, kai tasa ta fice waje. Ajiyar zuciya ya sauke yana tinano irin yadda Pretty ke kashe Smart da shagwaɓa, wannan abin ya tsaya mashi a rai, ita dai Sweetie a sanyayye take magana babu wani shagwaɓa. Jim kaɗan ta dawo ɗauke da kayan abincin, yana jin yunwa sosai hakan yasa bai ɓata lokaci wajen saukowa kasa dan su ci ba. Ko da ta buɗe abincin, irin cimarsu ne, su texmari spagh da su kali-jeera, amma sam bai yi mashi ba, dan yana da zaɓen abinci sosai shi, a kowani rana yana da ra'ayin abin da yake ci, amma tin da yana jin yunwa, sai ya daure ya ce ta zuba mashi su ci. A natse ta zuba masu suka hau ci tana ta aikin satar kallonsa. Wlh ba ƙaramin tafiya da imaninta yake yi ba a lokacin da yake motsa kyawawan lips ɗinsa, sai ta ji tamkar ta mashi sumbata a wajen. Shi ma nasa ɓangaren satar kallonta kawai yake yi, ji yake yi tamkar ya jawota jikinsa. A ɗayan ɓangare kuwa, shi ma dai Ronnie bai iya cin abincin kingdom ɗin ba, domin kuwa amai ya rinƙa zabgawa tamkar babu gobe, guyson ne ya taimaka mashi da kyar, kuma ya faɗawa momma shi ma Safras bai iya cin abincinsu ba, momma tasa aka kwashi kayan abincin aka fitar da shi waje, da mom Smart ta girkawa su Big Bro sai momma ta sanya aka sakawa Ronnie. Kun fahimci dalilin da yasa shi Smart da Pretty basu yi korafi kan cimar Black World ba? Saboda shi yasaba cin irinsu a Paris, kunga Pretty ma ta saba ci a tare da shi a can, sannan abin da ya sa Smart ya iya cin abincin larabawa time da ya zo kingdom ɗin shi ne daddynsa na Paris balarabe ne in baku manta ba, yayan momma ne, so ya taso ana girka ciman larabawa time to time, dan haka ya iya cin ciman dikka biyu shi kam. ----------------------------🔥 Bayan sun kammala Sweeeti ta ce bari ta kira kuyangu su tattare wajen, shi kuma ya miƙe ya koma saman bed ya kwanta. A haka ta dawo tare da kuyangu suka zo suka gyare wajen tsab suka fita. Zama ta yi a saman sofa tana tinanin irin rayuwar da zasu yi a tare a wannan ɗakin kenan sai suka ji knocking na door. Kallon juna suka yi kafin su mayar da kallonsu a kan kofar. Zata yi magana ya ɗan yi mata gyaran murya alamar bai yarda ta yi magana ba, (wai irin kada wani ya ji mashi voice ɗinta, amma fa in jini😸) hakan yasa ta yi shiru. Miƙewa ya yi ya nufi door ɗin da kansa. Yana buɗewa sai ya ga Smart ne tsaye cikin sleeping dress masu balain kyau, mamaki ne ya kama shi na ganin Smart na knocking, wai meyasa zai yi knocking ba zai shigo kai tsaye ba?. Wato addinin musulunci duniya ne jama'a, ya za'ayi ka shiga ɗakin mutumin da kake ikirarin yana da mata kai tsaye ya shige masu ciki without their're permission? Wannan ai sai rayuwar dabbobi. Kallon tsab Smart ya yi mashi kafin ya ce. "ALLAH yasa ban katse wani abin ba, dan naga yanayinka sai a slow"......... Shiru Big Bro bai amsa mashi ba, yana dai kallonsa. "Yanagaka haka ne wai? Naga kamar kana cikin maye ne? Ko dai kana kan network ne?". Smart da neman tsokana ya sake tambaya. Sai yanzu Big Bro ya gane nufinsa, dan haka sai ya kai mashi duka a shoulder, in a cool way sosai ya ce. "Ai ni ba irinka bane". Ɗan leƙowa cikin ɗakin Smart ya yi wai dan ya tabbatar Sweetie bata jinsu kafin ya ce. "Shiyasa ranar na tarar kana mafarkin sisterta har da cewa ta cigaba da maka wasa da shi kada ta daina ko? To kai wani irin ne kenan?". Shi ma Big Bro satar kallon cikin ɗakin ta wutsiyar ido ya yi kafin ya ce. "Fita mana a ɗaki". Ya faɗi hakan ne saboda ya ga Sweetie tana kallonsu, ita ma da gulma so take yi wai ta ga wanene ya yi knocking. "Dama ai ni ba zama zan yi ba, ina zan zauna in ga abin da zai hanani barci bayan yar tsana ba iya mun komai zata yi ba, ni dai yanzu abin da ya kawoni shi ne ka zo mu je wajen daddy kafin mu yi barci". Sosai Big Bro ya ji daɗin cewa zasu je wajen King, dan yana son sake ganin daddyn nasa. "One minute". Big Bro ya faɗa ba tare da ya jira amsarsa ba ya saki kofar ya koma ciki. Smart da tsona ya ce. "Zaka iya ɗaukar five mins ma dan naga alamar sai ka huce". Ɗan jinjina kai Big Bro ya yi irin zan kamaka ɗin nan, jan kofar Smart ya yi ya rufe masu ya tsaya a gefe yana jiransa. Kusa da Sweetie Big Bro ya tsaya, in a cool way sosai ya ce. "Kada ki fita ko nan da door, ko knocking aka yi kada ki buɗe". Cikin bada umarni ya yi maganar yadda kuka san shi ya ajiyeta. Ita kuwa da yake soyayyarsa ya rufe mata ido farincikinsa kawai take so sai ta ce. "Okey In Sha ALLAH". Kamar zai rungumeta ya bata kiss yadda ta motsa lips ɗin nan nata, amma sai ya daure tare da juyawa ya nufi waje. Smart na tsaye yana jiransa, yana zuwa suka wuce part na king. Suna tafiya sai tsokanar Big Bro Smart yake yi, wai har yanzu bananarsa a tsaye take, dan haka dan ALLAH ya rinƙa sassautawa sister ɗinsu dan yarinya ce, kada ya je ya kasheta. Sarai Smart ya san Sweetie bata yi kama da wadda aka yi dis virgin ɗinta ba, amma saboda neman tsokana ne yasa yake yi mashi wannan tsiya. Shi dai Big Bro bai yi magana ba, har suka isa bedroom na King. Kwance saman bed suka isko King Ramish yana zaune a gefensa suna ɗan hira. Hayewa saman bed ɗin suka yi suma, cikin girmamawa Ramish ya ɗagawa Big Bro gaisuwa da turanci. Da kalma ɗaya ya amsawa Ramish, wannan ma sai da ya ɗauki one minute kafin ta amsa. Haka ya sake ɗagawa Smart ma gaisuwa, nan ma Smart ya amsa cike da kauna. Da kallo ɗaya Big Bro ya yi wa Ramish ya ji ya kwanta mashi a rai, haka kawai ya tsinci kansa da kaunarsa, shi ma Ramish ya ji yana kaunar yayan nasa sosai. "ALLAH ya yi maku albarka ƴaƴana". King ya faɗa cikin raunin murya. Smart da Ramish ne suka amsa da amin, shi kuma Big Bro sai ya ce. "Daddy meyasa ruhanan tsafi suka sanya ka kwanta jinya haka? Meyasa suka rike maka dikkan gaɓɓan jiki? Shin ka ci wani bashinsu ne baka biya ba?". DUM!! DUM. Haka kirjin King ya bada bugu, while Ramish da Smart kuma suka kalli juna. Shi kuwa Big Bro ya kai hannu ya ɗan riko hannayen King cikin nasa, lokaci guda King ya ji tamkar an kwashe mashi dik wata ciwon dake a jikinsa, saboda waɗan nan yatsun Big Bro da ya bar dogayen nails ɗin sun taɓa mashi tafin hannu, dik wasu ruhanan sun gudu, a miliyan suka saki King suka watse. Da karfi King ya yunkura ya miƙe tamkar wanda aka karawa karfi. Ai cike da mamaki Smart ya ce. "Big Bro me yake faruwa? Mekake son cewa?".......... Shiru bai amsawa Smart ba, kallonsa a kan dad da ya miƙe zaune ya ce. "Daddy menene yasa suka yi maka wannan mummunar riko haka? Akwai wani dill da ya haɗaku ne?". Kai King ya jinjina mashi kafin ya ce. "E akwai abin da ya haɗamu na alkawari, amma dogon labari ne, dama na yi wa Omerish alkawarin zan faɗa mashi gaskiyar komai tin kafin ka zo, ina tsoron sake rasa ƴaƴana a karo na biyu ne yasa na gagara faɗawa Omerish, amma yazama dole zan faɗa maku". Ya kai karshen maganar dik dakiya irin nasa da jarumta sai ga idanunsa sun ciko da kwallah, tin daga nan Smart da Ramish suka san ba karamin abu bane King ya ɓoye, abin da zai sanya shi hawaye ai babban balai ne. "Babu ƴaƴan da zaka sake rasawa daddy, faɗa mana meyakefaruwa? Wani alkawari ka yi masu da baka cikaba wanda ya sa suke shan jininka haka?". Cewar Big Bro. "Zan faɗa maku amma ba a daren nan ba, sai zuwa gobe da safe, amma ina ji a jikina da zarar na faɗa maku komai zai zo karshe"...... Smart ne ya yi sauri cewa. "Tabbas komai zai zo karshe In Sha ALLAH". Shi kuma Big Bro da ya san yaren tsafi sai ya ce. "Babu abin da zai zo karshe dad, ko kusa ko alama kana tare da mu, ka kwarara kanka ka ji?". Jinjina masu kai King ya yi, daga nan suka shiga hira King yana basu labarin ɗan uwansa mahaifin su Bobo. Har wajen karfe 10 na dare, sannan ne ya tambayesu sun je wajen Akka sun duba lafiyarta?. Kai suka girgiza alamar a'a, sam King bai ji daɗi ba, dan haka ya ce da safe kafin su zo wajensa su fara zuwa wajenta. Da okey suka amsa mashi kafin su miƙe su sauko kasa suna yi mashi good night. One by one suka bisa suka bashi sumbata a kumatu kafin su nufi waje. Sai dai suna kaiwa daidai kofa zasu fita muryarsa ya katse su da cewa. "Ina da tabbacin na haifi waɗan da zasu tsaya a kan komai nawa!". Dik cikinsu babu wanda ya fahimci maganarsa sai Big Bro, amma da yake yana da kwarin gwiwa a kansa sai bai ɗauki hakan da muhimmanci ba. Smart da Ramish suka amsa da. "In Sha ALLAH a koma ina ne zamu tsaya maka dad". Shi kuma Big Bro ya ce. "Zaka tsaya da kafafunka a gaban ginunnukan dake kwance daddy". Jinjina kai king ya yi yana sakin murmushin da ya jima bai yi kwatankwacin irinta ba. Har zasu fita again Big Bro ya sake dakatawa ya juya yana kallon King wanda shi ma su yake kallo. A karo na biyu ya sake cewa. "Zaka tsaya da kafafunka a gaban ruguzazzun palace daddy". Cikin alamar karfafawa ya faɗa mashi. Sam King bai amsa masu ba har suka fice, kuma bai cire idanunsa daga kafesu da kallo da ya yi ba, sannan bai daina murmushin da ya fara ba. Suna fita suka yi hugging juna su ukun dikka, sannan Ramish ya wuce part ɗinsa yana yi masu good night cike da kauna. Su ma wucewa nasu part ɗin suka yi. A daidai tsakiyar kofofinsu suka tsaya suka rungumi juna kafin su yi sallama, basu je ganin momma ba. Room ɗinsa Big Bro ya shiga, toilet ya wuce, a gurguje ya yi wanka ya fito. Cikin sexy sleeping dress ya shirya kafin ya tako ya nufi in da Sweetie take kwance, sai tashin wani fitinannen kamshi yake yi. A gaban sofar da take kwance ya tsugunna, ta lulluɓa da katan bargo tana zuba barci cikin farinciki. Tsautsayi da kaddara tasa ya kai hannunsa ya ɗan yaye bargon wai dan ya ganta da kyau. Shirye take cikin wasu kyawawan sleeping dress wanda suka zauna ɗas a jikinta, ga shi rigar tana da irin breast cuff ɗin nan, gata da siririn hannu, yadda ta kwanta kana iya ganin tula-tulanta sosai, sannan yaye bargon da ya yi yasa rigar ta kara yin ƙasa sosai, hakan ya basu damar fitowa sasai. Ɗan lumshe idanunsa ya yi ya sake warosu a kanta, lokaci guda ya wani irin ɗauke wuta, sai ya ji tamkar an shakesa nunfashinsa bata fita da kyau, hannunsa har tana ɗan kerma ya kai zai taɓa mata tula-tula............. Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 -------------------------------------------🔥♥️ ZABUWAR DUNIYA STEP ONE!.🔥🔥🔥 23 Tunawa da alkawarin da suka yi wa juna na bazai taɓata bane yasa ya yi gaggawar fasawa, ya janye hannunsa dan baya karya alkawari ta daɗi, sai in abu ta fi karfinsa, kaman da yake mai magana ɗaya haka yake, dan haka sai ya kara jan barkon ya mayar ya rufeta da kyau ba dan ya so ba, ya yi shiru yana kallon face ɗinta for almost 10 mins kafin ya miƙe ya nufi bed ɗinsa. Har zai kwanta sai ya tina bai ga momma da guyson ba, kuma yana son ganinsu. Dan haka sai ya nufi waje dan ya duba. Room ɗin momma ya fara shiga kai tsaye babu ruwansa da ya tsaya tura kuyangu su nemo mashi izini. Momma ta yi mamakin ganin yadda ya shigo mata babu neman izini, bata san shi nan babu ruwansa da wata sarautarsu ba, shi ma sarki ne a fadarsa, dan yana son ganin mahaifiyarsa sai ya nemi izini, a ta daidai ina aka ce hakan? To koma a ina ne ban da shi Black Tiger ato. Momma na zaune gefen gado tana magana da daddyn Smart a waya, ya ce su mom Smart su dawo ne suka ce wlh kafansu kafan Smart idan ba haka ba su ba zasu dawo ba, shi ne ya kira momma wa ta sakar mashi mata da ɗansa su dawo in ba haka ba shi ma su jira dirowansa. Kun san mom Smart and daddy akwai love, to haka kawai ta biyo ɗanta ta gudu ta barshi ya zama tuzuru, shi ne nan ya ce biyosu zai yi. Sai hakuri momma take bashi yaki yarda sam, to shi ne ta zauna tana faɗa mashi abin da ya tsayar da Smart ɗin yasa bai ɗawo. Big Bro yana shigowa ya zauna a kusa da ita shiru yana sauraron abin da take faɗe dik da baya jin larabci, yana ta kallonta tamkar ya ga wata bakuwar halitta daga wata duniya. Ganin kallon ya yi mata yawa ne yasa ta kai hannunta ta ɗan rufe mashi idanu tana murmushi. Nisawa ya ɗan yi kafin yasa hannun ya zame hannunta dake kan fuskar tasa, sannan ya rike hannun nata yana ɗan jujjuya yatsunta kaman yana duba wani abin. A haka suka kasance har ta kammala waya, tana katse kiran ta ce. "Baka yi barci ba?". Kai ya ɗan jinjina mata yana kallon yatsunta. "Ko dai wajen namu bai yi maka bane yasa baka yi barci ba?". Nan ma kai ya jinjina kawai wanda kuma Momma bata fahimci me yake nufi ba, ta dai gane baya son magana kuma baya son hayaniya sam-sam. Shiru suka yi for almost 10 mins, a tinanin ta zai yi magana sai ta ga shi fa ko shekara zasu yi shiru ba zai damu ba, dan haka sai ta ce. "Kana son wani abin ne?". Kai ya gyaɗa mata sama kafin ya ce. "Ina son ki kira Auta a kawota nan gobe". Cike da mamaki ta ce meyasa. Shiru ya yi for almost 2 mins, har ta fidda rai zai yi magana sai kuma ya ce. "Ina son ganinta". Ajiyar zuciya momma ta sauke, da ta zaci wani abin ne. Kamar yana son yin wata magana again, sai kuma ya yi shiru tare da miƙewa tsaye, ita ma ta fahimci akwai abin da yake son faɗa mata, amma harshensa tai mashi nauyi, bai saba yawan magana ba, dan haka sai ya gagara jan dogon hira da ita. "Good night". Shi ne kawai abin da ya iya sake faɗa kafin ya miƙe ya nufi door. Da kallo ta bi bayansa, a ranta tana jin akwai abin da ya saɓa a rayuwarsa sosai, ba haka kawai yake da mugun bawa mutum tsoro ba, ita kanta shakkar ganin cikin idanunsa take yi, idan ta kallesa a lokacin ta sake kallonsa gabanta har faɗuwa yake yi, kun tuna a birninsa ma babu mai iya ganin cikin idonsa? To kunga ai mutanan Crown Of Power sun yi kokari da suke iya ganin idonsa, dan suna sallah ne yasa suke da jarunta da kwarin gwiwar iya kallonsa. Big Bro fa shi ba wai bashi tsafi aka yi tamkar yadda ake bawa wasu misali kamar zarina dasu Mammie ba. Magic ɗinsa a zuciya ta ƙwaƙwalwarsa take, tin yana ɗan shekara biyar yake koyan magic, karantarta ya yi tamkar yadda ake karatu a makaranta, ba wani ne ya bashi ba bare ya iya kwacewa, shi sai dai ya baiwa mutum. To uban su Mammie ne shi, su nasu tsafin tsammasu aka yi, shiyasa kuka ga dik in yaga ruhanan tsafi a waje yana iya ganewa, dan shi Master ɗinsu ne, yana iya raba irinsu ga wasu, shiyasa na jikin king suka gudu da suka gansa, dan shi nashi ruhanan idan zai bawa wasu ma ai sun fi karfin waɗan nan, baya da kananan ruhanan tsafi, jiga-jigan bakaken shaiɗanu yake da su, ai wlh mai iya raba Big Bro da magic sai ALLAH, ku ji fa, koya ya yi, shi master ɗinsu ne, ba bashi aka yi ba bare a kwace ko ace za'ayi mashi controlling ɗinta, kayansa ne, kunga kuwa daga nan har abada tana cikin kwakwalwarsa sai in cire kwakwalwar za'ayi a wanke mashi ta dawo sabuwa wanda kuma hakan ba zai yiwu ba, shi sai idan shi ya yi ra'ayi ya jingineta gefe. To kun ji dalilin da yasa yake iya ganin abubuwan kingdom ɗin, da kuma dalilin da yasa babu mai iya sarrafa mashi magic ɗinsa, da abin da yasa Duniyar Shaiɗanu suka sakesa magic bai barsa ba, kayansa ne! Ku bar mashi kayansa ya ɗauka!!........😸 Momma bata san sharp eyes ɗinsa bane, akwai kaifi da kwarjini, sai kuma ga magic, dole ya tashi hankalin dik wani mai kallonsa. KUN GA SWEETIE TA YI NAMIJIN KOKARI KUWA!. Ta shagala da kallonsa sai gani ta yi ya juyo da kallonsa a kanta har sai da kirjinta ta wani bada Dum!!! Dum!! Shi kuwa in a low voice sosai ya ce. "Ina ne ɗakin su Omar?". Ajiyar zuciya ta sauke a hankali. Kwatance ta yi mashi, kai ya ɗan jinjina zai juya kenan ta katse shi da cewa. "Idanunka suna bani tsoro, sannan sanyinka da rashin son maganarka ya yi over, Ina son yin magana da kai amma na gagara, ko sunanka ban sani ba". Cike da mamaki ya juyo gareta da ƙyau, da wanan yatsan hannunsa dake da dogon nail ɗin ya yi pointing kansa kafin ya ce. "Ni ɗin ne nike baki tsoro momma? How?". Yana ɗan blinking eyes ɗinsa ya yi maganar. Sai a lokacin ta san cewa ta yi magana, a tunaninta a cikin zuciya ta yi maganar, bata so ya ji ba har ga ALLAH, amma ya zata yi? Ya riga ya fita. Ganin ta yi shiru ne yasa ya tako ya dawo cikin ɗakin. A in da ya tashi ya koma ya zauna, hannayenta ya riko cikin nasa, in a cool way sosai ya ce. "Kada ki ji tsoron eyes ɗina, a haka suke, kuma babu komai a cikinsu, meyasa bakya tsoron na Omerish sai nawa? Dikkanmu ba abu iri ɗaya muke da shi bane? And bugu da kari ai irin eyes ɗinki muke da shi". Tin da ya fara magana ta rasa me zata ce mashi, saboda bata shirya amsar ba maganar ya yi mata fitar unexpected. Ganin ta yi shiru ne yasa ya ce. "Wani irin magana kike son yi dani? Ko magana dubu zaki yi zan amsa sau dubu ko da hakan zai ja mun ciwo ba zan gaji ba". Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Jeka kwanta da safe zamu yi magana". Jinjina mata kai ya yi tare da miƙewa ya nufo waje, tsaresa da ido ta yi har ya fita. --------------------------------🔥 Good 10 minutes Mahreen ta ɗauka a wannan yanayi kafin ta fara blinking eyes ɗinta, yana dai kwance yana kallonta yana jiran ta tashi su buga dirama. Yunkurawa ta yi ta miƙe zaune, bata ko kalli in da yake ba ta fara ƙoƙarin sauka daga gadon. Da sauri sauri ya rikota tare da cewe. "Ina zaki je?". Ai a wani irin zafa ta kwace hannunta, cikin faɗa ta ce. "Idan ka sake taɓani ALLAH ya isa ban yafe ba, ɗan iska kawai". Tana kai karshen maganar ta watsa da gudu sai waje, kafin ma ya yunkura ya miƙe ta yi waje abinta. Da sauri ya sauko ya rufa mata baya, kai tsaye bedroom na Jaish ta shiga, babu ko sallama ta afka ciki, shi kuwa yana ganin ta shiga part na Jaish ya sauke ajiyar zuciya, dama momma ce baya son a faɗawa, dik da yasan zai ji kunya idan ta faɗawa su Jaish, amma da sauki a kan su momma. Zaune ta isko Jaish a saman sofa a cikin bedroom ɗinsu, yana rike da waya yana latsawa, Mahnoor tana toilet. Tana zuwa da gudu ta faɗa jikin Jaish tana kuka. Da sauri ya ɗagota yana kallon face ɗinta, a natse ya ce. "Menene yafaru? Waye ya taɓoki?". Tana kuka sosai ta ce. "Yah Omar ne ya saka bakin shi cikin nawa, ka ce in rinƙa girmama shi, ina girmama shi kuma bana shiga harkarsa, amma shi yana shiga tawa, ina ɗaki ya zo ya kamani yasa bakinsa cikin nawa". Tin da ta fara magana Jaish ya bushe da kallonta har ta kai karshe, ko me ya tuna sai kuma a karo na biyu ya watse da dariya sosai mai sauti, yana yi yana girgiza kai. Ai tsayawa cak da kukan ta yi tana kallonsa, har da ɗan tashi daga jikinsa ta yi dan ta ji daɗin kallon nasa. Sai da ya yi mai isarsa sannan ya ce. "Zoki jini wata magana to". Ya faɗa yana jawota jikinsa. Shiru ta kwanta a kirjinsa bata yi magana ba. "Zan jawa Omar kunne ba zai kara yi maki abin da ya yi ba, amma kada ki faɗawa kowa abin da ya yi maki kin ji?". Kai ta gyaɗa sama kafin ta ce. "To ba zan faɗa ba, amma Yah Jaish ka ce ya daina yi mun magana ma bana so". Cikin sigar rarrashi Jaish ya ce. "Mahreen babu kyau musulmi ya ce kada ɗan uwansa musulmi ya yi mashi magana, haramun ne, ko bai yi maki magana ba ke kiyi mashi in kina son shiga aljanna kin ji ko?". Kai ta gyaɗa alamar to ba dan ta so ba, daidai lokacin Mahnoor ta fito ɗaure da towel a kirjinta, tana fitowa suka haɗa ido da guyson dake laɓe a bakin kofa yana sauraron Jaish da Mahreen, zata yi magana ya yi gaggawar ɗaura mata yatsarsa ɗaya a saman lipa ɗinsa, alamar ta yi shiru. Ai tana ganin haka tasan to sun bugata shi da mutuniyar, dan haka sai ta wuce zata nufi closet ɗinsu kenan muryan Jaish ya katseta da cewa. "Zo ki ji". Shi ne abin da ya faɗa. Ba musu ta nufesa, a natse ya ce da Mahreen. "Tashi ki je bari in duba matata nima". Tana turo baki ta miƙe daga jikinsa. Da sauri guyson ya juya ya yi waje, bata lura da shi ba ita ma ta yi waje. Tana fitowa ya sanya hannu ya toshe mata baki tare da ɗagata sama sai bedroom ɗinta. A saman bed ya direta, in a cool way sosai ya ce. "Please ki yi hakuri ba zan sake ba"........ Harara ta dalla mashi kafin ta ce. "Wannan kai ka sanshi, ni dai na faɗawa Yah Jaish kuma zai hukuntaka ne ya ce". Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Ina sonki". Ya faɗa tare da juyawa ya nufi waje. Kai tsaye ya koma bedroom ɗinsa dan ya duba Ronnie, yau zuciyarsa fes ya yi kissing abar kauna. ----------------------🔥 Mahreen na fita Jaish ya jawo Mahnoor jikinsa, hannu yasa ya ware towel ɗin jikinta kafin ya kwanto da kansa a saman shoulder ɗinta, ya fara shafa tula-tulanta dake tamkar an hura balo-balo. Kaman mai raɗa ya ce. "Gobe zan je Jimeta in ALLAH ya kaimu". Idanu ta zazzaro mashi tare da juyowa da kyau tana kallonsa. Ɗago kai ya yi a take idanunsa suka rikiɗe. "Kinga gwara in je in sanar da bappa Omar ɗina yana son Mahreen a bamu aurenta, dan na lura Omar ya fara zaucewa a kanta". Cike da zumuɗi ta ce. "Habibi zan bika".......... Wani irin sumbata ya kai mata a kumatu kafin ya ce. "Zuwana ne ni kaɗai wannan, amma na yi alkawarin zuwa dake next". Tamkar zata yi kuka ta ce. "Please habibi, na yi kewar bappana sosai". Tumurmusheta ya fara yi yana lallashinta a kan ta yi hakuri next zasu je, amma yau kam zuwansa ne shi kaɗai. Dan dole ba dan ta so ba ta amsa da ta hakura, farincikin yadda bata ja in ja da shi ne yasa ya miƙe tsaye da ita a jikinsa suka wuce saman bed, yarinya ta yi wankanta zata yi kwalliya zai sake sakata yin wani. Yana hayewa gado ya ja masu bargo asuba ta gari. ------------------------🔥 Kai tsaye in da momma ta kwantanta mashi ya nufa. Yana zuwa ya tura kofar ya shiga. Zaune a saman dadduma ya iskosu, suna sanye da jallabiyas, Ronnie Jallabiyan Omar ya saka. Sosai Big Bro ya ga wani irin kyau da Ronnie ya yi, sai da ya tsaya yana kallonsu. Kun san Big Bro yasan Ronnie ya musulunta ai, tin suna birninsa time da Smart ya je ya sani, so bai yi mamakin ganinsa da jallabiya ba, ya dai ga tai mashi mugun kyau ne. Ronnie na ganinsa ya miƙe, dama suna zaune ne Omar yana kara mashi karatun Alkur'ani. Ajiye Alkur'anin ya yi, da sauri ya nufi yayan nasa yana faɗin. "Ban san ina room ɗinku yake ba, na yi kewarka sosai". Ya kai karshen maganar yana faɗawa jikin Big Bro. Rungunesa Big Bro ya yi tare da yiwa Guyson alama da hannu a kan ya zo shi ma. Da sauri ya miƙe ya zo. Haɗesu ya yi ya rungume yana jin wani irin tsananin kaunarsu a ransa, yanzu ba zai iya banbance Omar ya fi so ko Ronnie ba, sun zama abu guda a ransa. Ya jima rungume da su kafin ya rabasu da jikinsa yana binsu da kallo. Almost 5 mins for silent sannan in a cool way sosai ya ce. "Ya jikinka Omar?". A natse guyson ya ce. "Alhmdllh, ya jima bai tashi ba ai ciwon". Jinjina kai Big Bro ya yi kafin ya ce. "Ya kusa daina tashi ma ai, ku yi barci zuwa da safe kazo mu yi magana ka ji?". Kai suka jinjina a tare kafin su koma ciki, dadduma da Alkur'ani suka ɗauka suka nufi wajen ajiyewa. Yana tsaye yana kallonsu har suka ajiye, sanna ne suka juya suka nufi saman bed. Sai da ya ga sun kwanta sannan ya juya ya rufo masu kofa. Yana tafiya Ronnie ya ce. "Omar kana da budurwa ne?"......... "Mata dai nike da". Ya bashi amsa yana jawo bargo. Cike da mamaki Ronnie ya ce. "Mata kuma Omar?". Kai ya jinjina yana ɗan lumshe ido. "To yakamata ka haɗamu mu gaisa, sannan kuma kana da mata zaka kwana dani a nan? Ita fa da waye zata kwana?". Kallonsa guyson ya yi kafin ya ce. "Ai ba'a ɗaura mana aure ba, kawai za'a ɗaura ne". Ajiyar zuciya Ronnie ya sauke. "Okey na fahimta, yanzu na gane, to ka haɗamu mu gaisa". Make mashi kafaɗa Omar ya ɗan yi kafin ya ce. "A'a ba yanzu ba, bari sai bayan aurenmu zaka ganta da nikaf". To shi Ronnie bai san me nikaf ba, dan haka sai ya ce to shikenan ALLAH ya kaisu lokacin. Da Amin guyson ya amsa, daga haka suka yi shiru kowa ya hau yin addu'ar barci. A ɓangaren Big Bro ma yana komawa room ɗinsu saman bed ya haye ya kwanta, ya juyo da face ɗinsa suna fuskantar juna da ita, sai kallonta yake yi, dik yadda ya kai da baya son haske a ɗaki in zai kwanta yau sai da ya bar haske saboda ya yi ta kallon face ɗinta har barci ta yi awon gaba da shi..............ASUBA TA GARI. -----------------------🔥 7:30AM. A hankali ta motsa kyawawan idanunta ta warosu waje, da kyar ta iya miƙewa, barci bai gama isarta ba, da kyar ma ta iya tashi ta yi sallar asuba ta mayar da barci. Yaye bargo da ta lulluɓa ta yi, sannan ta zuro kyawawan kafafunta kasa, ta saba da kwana a room ita kaɗai, so yanzu bata saba da su biyu ba, dan ko da Pretty ta je Black World kunga ai na koyaushe suke kwana a tare ba, da Smart take kwana, so ta saba ita kaɗai, mancewa ta yi yau su biyu ne a ciki shi da ita, miƙewa tsaye ta yi tare da rike waist ɗinta da hannu dikka biyu tana ɗan miƙa. Sai da ta gana sannan ta kai hannu ta danki kasar rigarta tare da yin sama da shi zata cire ta shiga toile unexpected idanunta suka sauka cikin nasa. Ai bata time da ta yi ihu ta saki rigar a miliyan ba, zazzaro mashi idanu ta yi tana kallonsa, shi kuma tamkar wanda ya suma idaunsa a kan kirjinta da wuyar rigar ta yi kasa. Ganin ba fuskarta yake kallo bane yasa ta yi gaggawar bin in da yake kallon da ido. Ai tana ganin tula-tulanta a waje bata san time da ta rarumo bargo ta kudunduna a ciki ba. Wata uwar harara ta dalla mashi a lokacin da ya ɗago da kallonsa kan fuskarta. "Me kake wani kallona?". Cikin tsiwa ta faɗa, bama ta san ta yi maganar ba fa. Shiru bai daina kallonta ba, da sanyin safiyar nan ta motsa mashi bar gadon, dik sai ya ji ya kasa motsawa, dama so yake yi ya je wajen King, amma ta kara jefasa cikin wani hali. Ganin bashi da niyar yin magana ne yasa ta nufi toilet da bargon a jikinta. Binta da kallo ya yi yana jin tamkar ya jawota jikinsa ya rungume ko zai ji sanyin abin da yake ji, amma babu hali. Haka ya zauna a wajen shiru har ta fito ɗaure da towel a kirjinta, a karo na biyu ta manta da mutum a ɗakin ta fito ɗaure da towel, kun san in baka saba abu ba sai a hankali, akwai wahala. Ai a wannan karon yana kallonta sai da ya ɗan yunkura kamar zai miƙe, dan yadda ya ga skin ɗinta yake wani glowing, kun san yadda skin na Koreans yake, abin ba'a magana. Yunkurwan da ya yi ne ma yasa ta farga akwai mutun a ɗakin, da sauri ta juyo da kallonta a kansa, yadda kuka san zai cinyeta da ido haka yake kare mata kallo. Harara ta dalla mashi kafin ta juya da sauri ta koma toilet, bargonta ta ɗauko ta fito, ta kudundune jikinta a ciki ta dawo cikin ɗakin. A gaban mirror ta tsaya, lotions ta fara shafawa, sai kuma ta ga dik in da ta yi sai ya bita da ido, hakan yasa ta fasa shafawar ta nufi closet ɗinsu. Kaya ta fitar riga da wando, rigar mai doguwar hannu ce, ita ma wandon haka doguwa ce, very silky haka, sai ta ɗauko headband na kayan. A cikinsu ta shirya, ta yi balain kyau sosai, sannan ta fito ta koma shafa lotions ɗinta. Dik wani motsinta a kan idaunsa. Dryer da ta gani a wajen ta jona zata busar da gashinta. Unexpected daga bayanta ta ji an karɓi dryer, tasan shi ne dan haka ba tare da ta juyo ba ta ce. "Ka manta ba zaka taɓani ba?" Shiru ya yi bai yi magana ba har ya karɓi dryer ɗin sannan ya ce. "Ban ce ba zai taimaka maki ba ai". Ya faɗa yana watsa gashin kanta da hannunsa, ya hau busar mata da shi. Har cikin ranta ta ji mugun daɗin hakan, sai dai bai kai ga karisar mata ba Smart ya yi masu knocking a kan ya zo su je wajen King su gaida shi. Ba dan ya so barinta ba ya bi Smart suka nufi part na King, sun manta jiya ya ce su fara duba Akka kafin shi. Yau dai zauna suka isko king a saman shinfiɗar dake a room ɗinsa, yana rike da cup of cappuccino yana sha, gefensa momma ce zaune, ɗayan gefensa Ramish ne a zaune. Suna shigowa King ya saki murmushi yana kallonsu kafin ya ce. "Omerish rufe kofar gabaɗaya dan ma kada wani ya sake shigowa". Da alama iya su da suke wajen King ya yarda da su, da momma, da Ramish and Big Bro da Smart. Datse kofar Smart ya yi suka kariso ciki. Dikkansu a gefe da gefen King suka zauna suna ɗaga mashi gaisuwa cike da tsantsar so da kauna. Big Bro ya zauna a kusa da Momma, shi kuma Smart ya zauna a gefen da Ramish yake. Fuska a ɗauke da fara'a King ya amsa. Abin ya yi mugun ɗaurewa momma da Ramish kai, su sun san King bashi da fara'a sosai wlh, ana jimawa kan ya yi murmushi, to meyasa tin daga daren jiya zuwa yau yake da faman murmushi ne?. Ta jefi kanta da tambayar da bata da amsarsa. Shiru ɗakin ya yi na ɗan lokaci, King ne ya katse masu shirun da cewa. "Na yi alkawarin faɗa maku abin da ya faru a baya jiya, amma fa ku sani zaku sake rasa kannenku guda biyu a karo na biyu". Ya ɗan yi shiru yana kallon fuskokinsu. "Tabbas zaku sake rasa Omar da Aneesa in har na buɗi baki na faɗa maku gaskiya". King ya sake faɗe. Dik cikinsu Big Bro ne kawai kirjinsa bata buga ba, saboda shi kalamai basa razana shi, amma Smart da Ramish and Momma sai da kirjinsu ya buga da karfin gaske. Ta maza Smart ya yi wajen cewa. "Dad mun yarda ka faɗa mana kawai"................ kallon king a kan momma ya ce. "Rahilarh ki yi hakuri da abin da zaku ji, na ɓoye maku sawon lokaci ba dan komai ba sai dan gudun ɓacin ranku, amma yau zan faɗi komai, zan yi fatan ku yafe mun". Shiru dikkansu suka yi, sai momma ce ta daure ta ce. "Babu komai, In Sha ALLAH zamu fahimceka". Gyaran murya king ya yi kafin ya ce. "Ramish ka yi hakuri da abin da zaka ji, dan nasan ba zai yi maka daɗi ba, sannan nasan ban kyauta maka ba, babu yadda zan yi ne yasa". Shiru suka ɗan yi, Ramish da zuciyarsa ke bugawa da karfi tamkar zai fasa kirjinsa ya fito ne ya ce. "Dad tin ma ban ji me ka yi mun ba na yafe maka wlh". Jinjina kai kawai King ya yi kafin ya tsaida kallonsa a kan Smart, sannan ya ce. "Omerish zan amsa maka buƙatar ka, wacece mahaifiyar Ramish, to hakikanin gaskiya ni kaina ban san wacece takamaiman mahaifiyarsa ba, abin da na sani kawai shi ne Ramish ɗana ne, kuma ba ɗan Aleezarh (Mama) ba ne". Dum!!! Dum Ramish da ya ji maganar tamkar saukar aradu ne ya yi gaggawar sanya hannu ya dafe kirjinsa dake barazanar tarwatsewa. Hannu Smart yasa ya dafa shoulder ɗinsa, dan dik sun lura da halin da ya shiga. A hankali Smart ya fara shafa gefen bayansa alamar rarrashi da kwarara mashi gwiwa. Kawar da kallonsa daga kan Ramish King ya yi sannan ya cigaba da cewa. "Da Rahilarh, da Aleezarh, da Umaiyya sun haihu ne a rana guda, wanda dama na yi wa Blood power alakawarin zan basu jinin ƴaƴana guda biyu su shanye sai in yi amfani da kashin bayan ƴaƴan nawa biyu in kera makullin spender dan rufe blood power, to shi ne a ranar da suka haihu sai na ɗauki biyu daga cikin yaran, na san dai na ɗauki ɗan Aleezarh, to cikin Rahilarh da Umaiyya su ne ban san ɗan waye na bada a ciki ba, Rahilarh ɗanki da kika haifa a tsakanin Omerish da Jaish a kansa nake magana, batu na gaskiya ba mutuwa yaran suka yi kamar yadda kuka zata ba, ni na bada su saboda in dakatar da ɓanar da su daddyna suka faro". "Da mahaifina, da kakansu Hoorain, da ɗan uwan mahaifina sarkin yammaci (Kakansu Bobo) da mahaifinsu Abdul Raof (Kakansu Leesharh) su ne suka hasasa blood power a cikin zuri'armu, a lokacin da suke manyan abokai kuma suke a kan mulki, yadda kuka ga masarautar su bobo wato Blood Crown take tafiya a kan tsafi har yau har gobe to haka dikka sauran kingdoms nan suke, ciki harda wannan masarauta, suna amfani da tsafi dan karfafa mulkinsu, shiyasa masarautu biyar ɗin suka yi karfin da ba'a iya yakansu a lokacin, sun kafa kasautunsu da karfin ikon jini, ni ban san yadda suke tsafi ba, kawai dai abin da nasani shi ne a lokacin da na hau mulki blood power ta buƙaci da na bada wanda na fi kauna domin a karawa rawanina karfi, shi ne ni kuma na ce ba zan yarda da tsafi ba, domin ni na samu wadataccen ilimin addini, nasan ba hanya mai ɓullewa suka bi, shi ne na tirge na bijirewa Blood Power, na ce masu ni mulki irin wanda ALLAH da manzonsa suka ce zan yi. (Kun tina labarin da na baku na Bobo time da zai hau mulki? Ba ance sai na bada wanda yake kauna ba? Kun tina ko? To haka tsarin Blood Power yake, su iyayen Bobo har yanzu sun ki saranda su cire kansu wannan, amma mu je zuwa bari King ya gama bamu labari)". "Sun yi juyin duniyar nan naki yarda da mulkin tsafi, to a lokacin bani da karfin da zan iya yakansu, sai na buƙaci sauran masarautun da mu haɗu mu yakesu dan mu kafa daula ta gaskiya ta musulinci, sai dai kash a wannan zama da muka yi dan haɗin gwiwa, Omranish (Mahaifin su Sweetie) shi ne ya fara miƙewa ya ce ba zai yarda ya bar tsafin mahaifinsa ba, dan haka zai cigaba da yi wa Blood Power biyayya suna bashi karfin mulki ya juya wanda yake so. Daga ya faɗi haka shi ma Herry (mahaifinsu Bobo) ya ce ba zai bar Blood Power ba dan suna bashi karfi dan haka zai iya juya duniya idan yana tare da su, da jin haka shi ma Abdul Raof ya ce ba zai bar Blood Power, suna son shi, na yi ƙoƙarin sanar da su illar da hakan zai haifar masu, amma suka yi burus da maganata, hakan yasa na ce to ni zan yaki Blood Power da karfin da ALLAH ya bani". "Tsawon sati na shafe ina tinanin mafita, daga karfe naga bani da karfin iya yakarsu, a wannan lokacin suka kashe mahaifina wai saboda naki yarda na basu jini, dik da haka ban sare ba kuma ban rusunar da kai a garesu ba, na sake tsananta tinani dan samun mafita, a wannan gaɓa Rahilarh ta zo tana da cikin Su Omerish, hankalina ya tashi dan nasan confirm zasu ce zasu ɗauki ɗana tin da naki yarda in zaɓi wanda nike so, sun san dole ina son ɗana ai, to ban sani ba ashe Umaiyya ma ta riga Rahilar samun cikin MieMie, na shiga damuwar da ko barci bana yi, to matsalata ma shi ne idan na basu ɗan nawa ba iya haka zasu tsaya ba, sun rinƙa karɓar ƴaƴana kenan a dik lokacin da suka tashi, shiyasa naki yarda tin farko". Dakatawa ya yi yana goge hawayen dake zubo mashi yana mayar da numfashi. A hankali ya ajiye cup na cappuccino dake hannunsa ya kalli Smart ya ce. "Omerish bani ruwan sha". Ya faɗa yana haki a hankali-hankali. Da sauri Smart ya miƙe ya ɗauko mashi ruwa, ya koma ya zauna tare da ɓalle mashi bakinta. Karɓa King ya yi ya kafa a bakinsa, sai da ya shanye kusan rabi sannan ya cire ya miƙawa Smart yana cigaba da sauke numfashi a hankali hankali. Dukkansu sai binsa suke da kallo, momma ma idanunta ya cika da kwallah tin ma bata ji karshen zancen ba. Ɗan hutawa for 5 mins King ya yi kafin ya cigaba da cewa. "Da naga ba zan iya dasu ni kaɗai ba sai na nemi mu yi zama da shuwagabannin Blood Power ɗin, a nan ne suka kafamun sharuɗan cewa in dai ina son tsame su Abdul Malik da zuriarsu daga Blood power dole fa sai na bada jini kamar yadda da suka buƙata tin farko, idan na yi hakan zasu yarda su zare sunan waɗan nan four kingdoms ɗin a list, daga nan suka tsara mun yadda zan bada jinin da suke so daga gareni. A lokacin na dawo gida sati babu cin abinci babu barci, ina ta tinanin yadda zan yi, daga karshe dai bani da mafitan da ya wuce in sake komawa in yarda da sharuɗansu, a nan ne na ce masu na aminta, amma ba zan iya basu ƴaƴana na farko ba, su mun afuwa in samu na biyu sai in basu, sun yarda da buƙatata, amma suka kafamun sharaɗin cewa dik ranar da na buɗi baki na sake yin maganarsu ko na faɗi wannan yarjejeniya da muka yi ga wasu to Blood Power zai dawo cikin zuri'ar Abdul Malik, dan Abdul Malik shi ne sarki a Blood power, ba da son ransu ma suka kashe shi ba, ba yadda suka iya ne, ruhanin tsafi na buƙatarsa shiyasa suka yi hakan, dan ya karya masu doka ya gagara sanya ɗansa ni kenan in bada jini, dan haka idan na kawo ƴaƴana biyu da suka buƙata zasu shanye jininsu, sai su keramin makullin da zan rufe black door da mahaifina ya gina da kansa domin zuwa blood power, suka kara gargaɗana a kan kada na kuskura na faɗi wannan magana ga kowa, da zarar na faɗa to shikenan alkawari ya karye har sai na sake basu wasu ƴaƴan nawa, wanda a lokacin tin ban san zan haifi Omar da Aneesa ba suka nuna mun su cikin ruwan tsafi, suka ce a cikin ƴaƴan da zan haifa akwai waɗan nan biyun, kuma sun kwaɗatu da jininsu, in har na buɗi baki na yi magana zasu ɗaukesu daga gareni ne, shiyasa da Omerish ya nemi jin gaskiya hankalina ya tashi, dan bana son sake rasa ƴaƴana, na yi kuka tamkar zan yi hauka a ranar da na ɗauki jariraina guda biyu da kaina na kai masu, ina ji ina gani, ina tsaye a gabana suka ɗauki jaririn nan suka caka mashi wuka a tsakiyar maɗigar kansa, suka ɗaga kafafunsa sama jininsa ya zazzaga a kan wani gunki da ban san na mecece bane, amma dai halittar macece, haka jinin ya rinƙa zuba a kanta yaron nan yana ta hargagin fitar rai har ya yi sanyi, sai da jininsa ya dakata da zuba cak, sannan suka jefomun gawarsa suka ce in rike bari a kashe ɗaya sai a zo a haɗa mun makullin rufe black door da kashin bayansu, kuma a dokarsu ne dole sai ina tsaye a gabana za'a kashe yaran". "Ba yadda na iya, dan na ceci zuri'ata na aminta da hakan, ina kuka tamkar karamin yaro haka suka kashe ɗayan jaririn a gabana suka sake jefa mun gawarsa, a can gida kuma na bari ana ta kukan yara biyu sun mutu, suka je suka binne gawar da Blood Power ta basu a matsayin yaransu, dan da na ɗauke yaran sun ajiye masu wata gawa ta karya ta yadda ba za'a gane ɗaukar yaran aka yi ba, dik wannan balain ina tsaye, haka ina ji ina gani wani kato mai kama da dodo ya zo ya karɓi gawan yarana da ko suna ban saka masu bama, a gabana yasa hannu ya ɓallo kasusuwan bayansu sannan ya yi jifa da gawarsu cikin wani rami mai zurfi dake wajen, ya wuce da kasusuwan izuwa wani ɗaki dan kera makullin Spender". Ya dakata yana wani irin kuka mai taɓa zuciya wanda ita ma momma kukan da take yi kenan, Big Bro ya rungumeta yana ɗan jijjigata, Smart da Ramish idanu sun yi jajir tamkar wuta, sun ji tashin hankali yau. King kuwa shi kaɗai yasan balain da ya gani a wancan rana, ya ga tsagwaran rashin imani, har yau idan ya tuna kuka yake yi tamkar ransa zai fita, a idanunsa yana ganin yadda jaririran nan ke magajin azaba suna wani irin jijjiga jininsu na zuba jajir da shi, kai wannan tashin hankali ba zai taɓa mantawa da shi ba a rayuwarsa, ba zai taɓa yafewa sarkin Blood Power ba, kuma har yanzu sarkin yana a raye shi ke rike da karagar wajen bayan mutuwar King Abdul Malik. Cikin tafasar zuciya King ya cigaba da cewa. "Suka kera Spender suka bani, na fito ta wajen na rufe wannan black door ta in da su Omranish suke bi dan zuwa can, to wannan shi ne farkon gabana da su Omranish, wai saboda me zan dakatar masu da jin daɗinsu? Su ba zasu daina tsafi ba dan haka in basu spender su buɗe black door su cigaba da zuwa Blood power suna salwatar da zuriarsu suna samun karfin iko, ni kuma na ce su da tsafi har abada, dan in na bada spender suka buɗe wannan kofa abin har zuri'ata zai dawo ba iya kansu kawai zai tsaya ba, shi ne fa suka ce zasu yake ni, ni kuma na ce shege kafasa, dan in dai yaki da takobi babu tsafi ne wane su, daga nan muka fara yakin da har yanzu muke gwabzawa, kuma har yau har gobe ba zan yarda in basu spender ba. Wannan dalilin yasa mahaifin Bobo ya je ya buɗe karamar blood power a kingdom ɗinsa, dan yana da ilimin tsafin, har yau har gobe shi yana tsafin, shiyasa shi baya kawo mun hari kan spender, ya rabu da zancen, sannan kuma akwai abin da ban faɗa maku ba, a jikin spender akwai wani abin da yakasance tamkar zobe ne na mahaifina wanda kuma sai daga baya na fahimci blood power suna balain tsoron wannan abin, da wannan abin zaka yi amfani ka juyasu kasa ruhanan wajen su yi maka biyya, a wani takardan tsafin mahafina na karanta, to abubuwan guda biyu ne, ɗayan ban san in da yake ba, da na gane ɗayan a dakin mahaifina ne sai na makalasa jikin spender dan kada ya ɓata, sarakuna da dama suna neman spender domin su buɗe black door su isa ga blood power su kuma yi amfani da wannan zobe na babana su saka blood power ta basu iko ta yi masu biyayya dan su mulki duniya, amma har yau ba su iya samun wannan dama ba". Lokacin da King ya zo wannan gaɓa sai da Big Bro ya ja dogon numfashi, saboda anzo ta kansa, shi ma abin da yake nemanwa kenan a jikin spender, ya buɗe blood power dan ya samu karin karfin iko ya mulki duniya. GASKIYA KING ABDUL MALIK YA KAI, HAR DA WANI ZOBEN DA BLOOD POWER KE TSORO YAKE DA SHI, YA JUYASU SON RANSA YASA SU BASHI POWER YA YI ABIN DA YAKE SO, ALLAH SARKI KING ZUHAIR, YA YARDA YA RASA ƳAƳANSA DAN KAWAI YA RABU DA MULKIN TSAFI, YA RUSHE GININ DA MAHAIFINSA YA YI, KAI GASKIYA AN CUCI KING ZUHAIR BA KAƊAN BA!!. "Wannan dalilin yasa kaga muke ta faɗa da sauran masarautun abu yaki ci yaki cinyewa, ba zan barsu su cigaba da tsafi ba, ba zan basu Spender, Blood Power waje ne da in kuka shiga zaku zaci ba a duniya kuke ba, waje ne da sai da na shafi sati biyu ina tafiya kafin na isa, wannan ma ɗan sun san da zuwana ne yasa suka gajarta mun hanya, abin babba ne, ƴaƴana a cikin alkawarinmu da blood power har da kashe ni suka ce zasu yi idan na sanar da yarjejeniyarmu, yau an wayi gari na sanar daku, ban san me makomana dana yarana Omar da Aneesa ba, sannan dan ALLAH kada ku faɗawa Akka na faɗa maku wannan sirrin, dan zata cutu, saboda tasan zata rasani, kuma tana tsoron bakin ruhin nan ya dawo zuriarmu, shiyasa hankalinta ya tashi da aka rasa spender, dan bata son tsafi ya dawo garemu!". Ya kai karshen maganar yana wani irin kuka mai mugun gaɓa zuciya. Da sauri Smart ya matsa ya rikosa yana cewa. "Daddy dakata da bamu labarin nan ka ɗan huta tukun nan, kada ka cutu........" Smart bai iya rufe bakinsa ba ya ga wani irin bakin jini ya fara fitowa daga hanci da kuma bakin King, take King ya fara wani irin numfashi mai karfi-karfi tare da fara jijjiga a hankali. WACECE MAHAIFIYAR RAMISH A TSAKANIN MUMMYN CHUCHU DA MOMMA? KING ZAI MUTU KO ZAI RAYU? IDAN YA MUTU WAYE ZAI KARISA MASU LABARIN? DAN BATA KARE BA! YA ZASU KARE DA BLOOD POWER? WAYE ZAI SAKE RASA RANSA? KENAN DAMAN DALILIN DA YASA KING DA AKKA SUKE TASAN HANKALINSU A KAN SPENDER? DAN SUN SAN IRIN AZABAN DA SUKA SHA KAFIN RABUWA DA ABUBUWAN TSAFI! YA MAKOMAN FOUR KINGDOMS? KAI YANZU FA CAKWAKIYAR ZATA FARA! KU SHIRYA DAN JIN WANNAN CAKWAKIYA. KENAN DAMAN ABIN DA YASA FOUR KINGDOMS BASA SHIRI? LALLAI KING ZUHAIR YANA DA GASKIYA, ASHE BAI YAKESU A BANZA BA, ASHE YA FISU GASKIYA. TO TA YA AKA YI SPENDER YA JE HANNUN PRETTY? NA CE MAKU YANZU WASAN YA FARA, MASU ZAGIN KING ZUHAIR SAI KU SHAFA MASHI LAFIYA!! SPECIAL GRO FAMILY A SHAFAWA KING LAFIYA.😌 GA MUNAFUKAI CAN SU MAHAIFIN SU SWEETIE, DA SU LEESHARH AND BOBO, GASKIYA KING YA YI NAMIJIN KOKARIN DA SAMUN IRINSA ZAI YI WUYA, IRIN WANNAN AZABAR DA BALAIN DA YA GANI KAFIN YA SAMU SPENDER YA RUFE BLOOD POWER ASHE DOLE HANKALINSU YA TASHI IN SUKA JI BABU SPENDER, DAN KADA BLOOD POWER SU DAWO FAMILYNSU, ASHE SHIYASA YAKE CIWO DA SMART YA BUƘACI SANIN GASKIYAR UWAR RAMISH, YASAN IN YA FAƊI GASKIYA NAN MA BLOOD POWER ZASU DAWO FAMILYNSA, ALLAH SARKI......😭 Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ------------------------------------------🔥♥️ ZABUWAR DUNIYA STEP ONE!.🔥🔥🔥 Hankalinsu ne ya yi wani irin mummunar tashi, a tsananin tsoro da tashin hankali momma ta kwace kanta daga rumgumeta da Big Bro ya yi ta yi kan King tana ambatar sunansa. Da sauri Smart ya tareta yana faɗin Ramish ya bashi ruwa. Riketa Big Bro ya yi ya sake rungumeta, a natse in a cool way sosai ya ce. "Omerish ku rabu da shi for some minutes, babu abin da zai faru, zai ɗan yi bleeding ne for some minutes daga nan shikenan zai wastsake". Tin da ya fara magana suka dakata da yunkurin yiwa King dik abin da suka faro, suka zuba ido suna kallan yadda wannan black blood ɗin yake zuba daga hancinsa and bakinsa, ga shi kwata-kwata baya numfashi, da za su bi umarnin Big Bro bama, amma ba yadda suka iya saboda lafiyar mahaifin nasu kawai suke buƙata a yanzu. Sosai Smart ya ji zafin abubuwan da suka rinƙa faruwa a tsakaninsa da King, dik fitinarsa ta jawo wannan matsala. Sai kuka momma take yi sosai, ALLAH sarki soyayya ba karya ba, tsananin so momma ke yi wa King, dik ta shiga tashin hankali ta firgice. Da suka ga kukan zai yi affecting ɗinta sosai sai Big Bro ya ce Smart ya ɗauketa su fita zuwa lokacin da King zai dawo daidai. Da sauri Smart ya miƙe ya cika maganar ɗan uwan nasa, shi kuma Big Bro ya matsa dab da King. "Ramish bani ruwa a bolw and towel". Big Bro ya faɗa yana kallon blood dake jikin King, ya ga jinin ta tsaya ne, shiyasa zai goge mashi. Sosai Ramish idanunsa suka yi jajir suka cicciko da kwallah, ganin haka yasa Big Bro ya ce. "Babu abin da zai faru kada ya damu, koma abu zata faru ba yanzu da saurin nan ba, sai sun samu labarin ya karya alkawarin zasu yi shirin ɗaukar mataki". Big Bro ba zai gane abin dake zuciyar Ramish bane dan shi bai san daɗin uwa ba sai yanzu ya fara sani, bai san me a zuciyarsa ba, raɗaɗinsa dayawa yake, ace wacce ka taso da ita, ta shayar da kai, kake ganin matsayin uwa sannan ace ba ita ce uwarka ta gaske ba, abin akwai ciwo, sannan babban abin takaicin ma wai ba'a san wacece takamaiman uwarsa a cikin matan ba, gaskiya wannan abu ya tsaya mashi a rai sosai, yana jin wani irin mugun nauyi a zuciya! Gabaɗaya tausayin mama ya rufesa!. Da kyar ya iya tashi ya ɗaukowa Big Bro abin da ya buƙata, ya kawo ya ajiye mashi a kusa da shi. A natse Big Bro ya jiga towel ya goge dik wani jini dake baki da hancin King, sannan ya sanya hannunsa ya tsaga jallabiyar jikin King daga wuya har wajen cikinsa. Sosai Ramish ya yi mamakin ganin yadda Big Bro ya tsaga sabuwar jallabiya cikin natsuwa ba tare da wani bubbuɗa hannu ko tada jijiyar wuya ba, sai dai ya fito da harshe waje ya datseta irin dai yadda suke yi idan zuciyarsu na kusa ko zasu zuba karfi a abu shi da guyson. Cirewa King rigar ya yi tare da kara goge mashi jiki, sannan ya miƙe ya cicciɓesa cak sai kan bed ya nufa da shi. Bayan ya kwantar da shi ya ja bargo ya rufesa, sannan ya tsaida kallonsa a kan Ramish. "Ku barshi ya samu good 5 hours yana barci komai zai yi daidai". Ya kai karshen maganar tare da juyawa ya nufi waje. Shiru Ramish ya ɗan yi yana tinanin ko dai babban yayan nasu likita ne? Amma kuma abubuwan da yake yi suna da al'ajabi da sanya mutum a ruɗani, ga shi da magana ɗaya, sannan yana jimawa kafin ya yi magana ɗayan, idan yana magana sai ka rantse da ALLAH saukar mashi da wahayinta ake yi, ba shakka akwai mugun ilimi a tattare da shi wanda kwakwalwar ɗan adam ba zata iya ɗauka a lokaci guda ba. TABBAS BAKA YI KARYA BA RAMISH, AKWAI ILIMI KAM, BIG BRO BA MUTANENEMA SUKA KARANTAR DA SHI BA, AMMA IDAN KUKA JI TARIHIN YADDA AKA YI YA BAR KINGDOM OF POWER ZAKU GANE ME NIKE FAƊE, DIK CIKIN KINGDOM ƊIN NAN A DAI BOKO BABU WANDA YA KAISA ILIMI, DOCTOR NE A ƁANGAREN KARATU BA AIKIN LIKITA BA, AMMA BA'A MAKARANTAR MUTANE YA YI KARATU BA, ABU ƊAYA NE BA'A TAƁA KOYA MASHI BA A RAYUWARSA SHI NE ILIMIN ADDINI, DAN ALJANNUN DA SUKA KARANTAR DA SHI DIKKA KIRISTOCI NE, HAKAN YASA YA TASHI DA SANI SOSAI A KAN ADDININ KIRISTIYANITI, YA SAN BIBLES ƊINSU DIKKA SOSAI, AMMA BASU BARI YASAN AINAHIN INJILA TA ANNABI ISA BA, DAN SUN SAN YANA DA BAIWA DA KAIFIN ƘWAƘWALWA TSAB ZAI GANE GASKIYA, DAN HAKA KO SU SMART BA ZASU GWADA MASHI ILIMIN BOKO BA, SAI DAI NA ADDINI, KUMA BIG BRO BA ZAI TAƁA YARDA YA MUSULUNTA BA SAI SUN RABASHI DA ABU ƊAYA ZUWA BIYU WANDA SU BA ZASU TAƁA ƊAUKAR ABIN DA MUHIMMANCI BA, SHIRI AKA SHIRYA MASHI A KAN HAKAN, SUN JUYA ZUCIYARSA TA YADDA ZASU YI AMFANI DA SHI DAN YAKAR ADDININ MUSULUNCI, DIK SABODA BAIWAR DA YAKE DASHI YASA SUKA ZAƁESA, ZAƁAƁƁE NE SHI. DAN HAKA IDAN ANA SON YA MUSULUNTA DOLE ZA'A RABASHI DA WASU ABUBUWA BIYU DA SUKA SANYA MASHI A JIKI BA TARE DA SANIN KOWA BA, DIK BA ZAKU GANE YANZU BA, SAI KING YA FARKA YA NEMI JIN A INA BIG BRO YA YI RAYUWA, IDAN AKA ZO MAI DA MAGANA MASU KAIFIN BASIRAR ZA SU IYA GANO MENENE AKA YI MASHI GUDA BIYU A JIKINSA DA ZAI HANA SHI MUSULUNTA HAR SAI AN RABASHI DA SU, DAN HAKA DIK ABIN DA BIG BRO ZAI YI A KAN ADDINI KADA KU GA LAIFINSA, BAI MA SAN YANAYI BA!. ----------------------🔥 Da sauri Ramish ya nufi saman bed ɗin, a natse ya fara tofawa king addu'oi yana fatan ya farka cikin koshin lafiyarsa. Bedroom na Momma Big Bro ya nufa, sai dai yana sanya kai zai shiga Smart na fitowa, karo suka ɗan yi Smart ya ja baya yana kallon fuskarsa, hankali a tashe ya ce. "Ya jikin daddy?". Ɗan lumshe idanu Big Bro ya yi alamar komai normal kafin ya ce. "What of mommah?". "Alhamdllh ta samu barci da kyar, tana buƙatar hutu sosai"........... Ɗan jinjina kai Big Bro ya yi, a tare suka juya suka nufi waje, a parlon momma suka zauna suna tattaunawa kan abin da yakamata su yi, da kuma me mafita. Sai yanzu Big Bro ya san cewa to ai blood power da yake neman mallakewa ma tasa ce tun da gadon King Zuhair, da King ya gaji kayansa kunga yanzu Big Bro ne zai gajeta, dan kowa sai ya bar magaji saboda wajen ta cigaba da kasancewa da rai kada ta mutu, shiru Big Bro ya yi yana tinani. Ni kuma na ce ya akayi matsafa dake blood power ba su suka reni Big Bro ba? Wanda ya renesa bashi da alaƙa da blood power, kuma a wajensa Big Bro ya fara ganin magic har ya ce zai koya kuma ya koya! Lokacin da King ya ki accepting blood power momma tana da cikin su Big Bro, tabbas a lokacin su sunga cikin, dama sun yi niyyar ko King bai aminta ba zasu ɗauke wannan cikin, yana daga cikin abin da yasa basu takurawa King ba, dan wajibi ne a kansa ya bada jini tamkar yadda da mahaifin su bobo yake yi in ba haka ba su sha jinin king ɗin, to basa dai son shan jinin King kai tsaye, saboda sun sha jinin ƴaƴan Abdul Malik ba sau ɗaya ba. (Kun ga which means King yana da borders kenan.) Bugu da kari sun kwallafa ransu a kan cikin momma lokacin, shiyasa ma cikin ya gagari kowa, dan an yi yunkurin zubar mata da shi ya fi sau goma, bana faɗa maku sai dai ta yi bleeding amma cikin yana nan ba, to sun so Smart and Big Bro kamar zasu yi hauka, saboda miƙa wuya da King ya yi ya nemi sulhu ne yasa suka hakura da su (kunga a nan ma ya tabbata akwai wasu azzaluman a cikin gida kenan dake son cikin momma ya zube, kai akwai fa case, akwai wasu sauran rina a gaba sosai, yanzu bamu yi komai ba, sai wasu daga cikin labarin nan sun bamu waje za'a fara ainahin wasa! Dama gidan sarauta gidan rikici da munafurci, ga cin amana, kai komai ma ya tara!.) Mai tsorata momma daban, kazalika wanda ya salwantar da rayuwar Big Bro ya bibiyi Smart dan kashesa shi ma daban ne, and wanda ya reni Big Bro shi ma daban ne, dik basu da alaƙa da Blood Power, shi blood power wani abin ne na daban, wanda kuma har yau har gobe a cikin ƴaƴan king suna balain son Big Bro and Smart, sannan suna son guyson and Aneesa, waɗan nan mutum huɗun sun gagara hakura da su, dannewa kawai suke yi dan kada su karya alkawarinsu da King Zuhair, sai dai kuma yau ga shi King da kansa ya karya alkawarin, kun sa kuwa akwai case, dan ba zasu hakura ba!!. -----------------------------🔥 A yayin da Big Bro da Smart ke zaune suna tattaunawar neman mafita, su kuma su Sareena suna can suna shirya plan yadda zasu tafiyar da aikinsu, yanzu tin da Sareena ta gano cewa ai ba aljanar gaske bace, yi masu aka yi dan basu tsoro, shikenan ta koma shaiɗancinta da ta saba, suna zaman meeting a side na Uncle Abba. Da ita, Omaid, Obaid and Sharifa. Suna zaune suna meeting ɗin yadda zasu tsara komai. Cikin nuna takaici Sareena ta ce. "Ni yanzu so nike mu fara wargaza soyayyar Yah Raj da wannan Zee ɗin, dan idan ina ganinsu a tare tamkar in kashe kaina nike ji, na tsani ganinsu a tare, idan muka wargaza soyayyar tasu sai mu wargaza ba Yah Smart ɗin". Jinjina kai dikkansu suka yi, Omaid ya ce. "Jiya ma na gansu a parlon Aunty MieMie tana kuka yana rarrashinta, tamkar in naɗa masu duka na ji!!!". Obaid ne ya capki zancen da cewa. "Haka ranar na gansu a garden ya rike mata hannu har da wani sunkuyowa kanta yana mata kalamai". Ya kai karshen maganar yana jan doguwar tsaki irin ransa bai so ba...... Sareena ce ta ce. "Dik ku bar faɗa mun kayan takaicin nan, yarinya kullum sanye da hijabi tamkar mai takaba, wlh na tsaneta, bata da sura mai kyau ne yasa kullum take sanya hijabi shegiya zata cuci yayanmu, sai an aura mashi ita ya yaye hijabin yaga bakomai..........". Da sauri Omaid ya katseta da cewa. "Ya ga gardi aka aura mashi matsayin mace ba". Kai suka jinjina a tare, Sareena ta ce. "Ta ya za'ayi mu rabasu ne wai?". Omaid ne ya ce. "Wannan ai mai sauki ne, kun sa kishi a jininmu yake, dik wanda ya sanmu ya shaida wannan, to da shi zamu yi amfani wajen sanya Yah Raj ya tsaneta, shirya mata soyayyar karya zamu yi, a hankali mu ja ra'ayinta, idan ta kama mu ɗauki hayan wani, mu biyasa makudan kuɗaɗe, mu bugar da ita mu kai mashi ɗaki sai ya yi mana video da ita ba kaya, zan sayi sabon sim card in yi amfani dashi wajen turawa Yah Raj videon, kinga daga nan ko yar gold ce wlh ya rabu da ita kenan har abada.......". BALAIN CAN, LALLAI OMAID DA OBAID SUN WUCI TINANI NA, KAI KUN JI WATA SHARRIN DA SUKA SHIRYA? WAƊAN NAN YARA FA HAR YANZU KO 20 YEARS BADU CIKA BA, GASKIYA DOLE BIG BRO YA YI SHIRI A KANKU, DAN GABA SHARRINKU MUTUM BA ZAI IYA ƊAUKA BA!!. "Irin wannan yakamata mu yi wa wancan shegiyar Pretty yar talakawa wacce ba'a san asalinta ba mu rabata da Yah Omerish". Cewar Sareena dake ta faman cika tana batsewa. Sharifa ce ta katsesu da cewa. "Wai dama ba'a san asalinta ba?". Kai Sareena ta jinjina. "Daga daji suka fito, a can Zunaira ta tsintota". Taɓe baki Sharifa ta yi kafin ta ce. "Tab lallai wannan bata cancanci familynmu ba gaskiya, dole kam a fidda ita". Ran Sareena ya yi sanyi da jin wannan magana, dan haka sai ta ce. "Shiyasa na ce zamu yi mata irin na Zee". Ta yi maganar tana kallon Omaid. Girgiza mata kai Omaid ta yi kafin ya ce. "Har yanzu Aunty Sareena baki san waye Yah Omerish ba shiyasa kike nufansa da kananan plan irin wannan, ai na rantse maki da ALLAH kina kuskura kika yi wa wannan Pretty ɗin irin wannan plan ɗin, idan bai kashe rabi da kwatan waɗan dake kingdom ɗin nan a kokarinsa na gani waye muka saka ya yi mata hakan ba, ke wlh dik wani iya duniyancinki ki kalli Yah Omerish ki barsa a nan, idan kuma so kike yi mu mutu a lokaci guda kuma to, dan wlh idan ya gane ko bai kashemu ba ba zamu sake moruwa ba, kuma kin dai san ganewa kwana ɗaya tai mashi yawa ya gano, tsab zai san plan ne tin da ita Pretty daga daji ta fito, so bata san kowa a duniyar mutane ba sai Auta, kinga kuwa yana gani zai san plan ne, Aunty Sareena kanki baya ja sosai shi ne matsalata dake!". Ya kai karshen maganar yana kaɗa kai irin bata san waye Smart ɗin nan ba. Shiru wajen ya yi, Obaid ne ya katse masu shirun da cewa. "Akwai wani abin da muka taɓa aikawa uncle ɗinmu a school, Yah Omerish yasa daga Paris aka zo aka ɗaukemu, bamu san ta ina ya samu labari ba, wlh horon da ya yi mana in faɗa maki ba'a taɓa yi mana kwatan wannan horo a air force school ba, dan ni sai da na gwammaci mutuwa, saboda haka shi Yah Omerish babban shiri yake buƙata, kuma mun shirya mashi plan A and plan B, idan ɗaya bai yi aiki ba dole ɗaya zai yi aiki". Omaid ne ya ce. "Kai ka daina tina mun wancan azaba, gaskiya Yah Omerish bakin mugu ne na bugawa ga jarida". Da sauri Obaid ya ce. "Amma gara shi sau dubu a kan wannan Big Bro ɗin, dan shi wannan daga gani renon shaiɗan ne, kuma ina da tabbacin bakaken aljanu ne suka shayar da shi, kana ganin idanunsa kamar bana mutane ba, fuska tamkar ɓaunar da aka sacewa yaro, babu alamar annuri ko imani a kan fuskarsa, ni har ban son ganinsa dan yana razana zuciyata". Omaid ya amsa da. "Hmmmm wannan ba'a maganarsa, bana fatan har ya gama rayuwarsa a duniya magana ta haɗani da shi, ni nama rasa wannan masifa dame ta yi kama, muna fama da balain Yah Ramish aka wani dawo da Yah Omerish, muna ƙoƙarin shaita Yah Omerish sai ga wani black evil ɗin wanda ganinsa ba alkhairi bane a garemu ya shigo ya rusa mana dik wasu plan, wlh ba zamu kyalesa haka kawai ba, mu tura kwari su bashi a jikinsa". YARA BASU SAN BIG BRO MA TWINS BANE WAI ZASU YI MASHI HORO DA KWARIN TWINS, MU JE ZUWA DAI DAN GANIN YADDA ZATA KAYA, A TINANINSU YAYANSU NE KAWAI BA TWIN NA SMART BA, YARA YARA NE, AI BAKIN RIJIYA BA WAJEN WASAN MAKAHO BANE!!.. "Gaskiya kada mu kyalesa, dole ya ɗanɗani azabanmu". Cewar Obaid, na'am da hakan suka yi, sannan suka cigaba da tattauna yadda zasu ɓullowa alamuransu cikin sirri. ----------------------------🔥 Yayin da dikka wannan abin yake faruwa, Zee tana side na Aunty MieMie suna hirar soyayyarsu da Dr Raj, yana balain son Zee sosai, ita ma kuma tana balain son shi, yanzu ta saki jiki sosai da shi tana bashi kulawa, soyayyarsu gwanin sha'awa da ɗaukar hankali, sai dai bai bari su mama sun sani ba, banda su Sareena da sa ido ma ai babu wanda ya sani sai Aunty MieMie, yana taka tsantsan, ita ma Zee tana kula sosai, ya tsaya tsayin daka wajen samar mata da farincini na musamman, ya rabata da damuwar rashin Khadija da rashin iyayenta, ya kyautata mata sosai sabida soyayyarsu. A can gefe ma Yah Rizwan and Aneesa ne suke kashe junansu da zallar kauna, da kalaman juna a kowacce rana suke fara wayewar gari, suna tsananin kaunar juna tamar Zee da Dr. Idan muka waiwaya side nasu Mahreen kuwa, kamar yadda Jaish ya faɗa haka ya wuce Jimeta yau, dan su dik basu san King bashi da lafiyar nan ba, su Big Bro sun ɓoye wannan ciwon nasa ya zama sirri tsakanin su huɗun da suka san labarin. Guyson bai san Jaish ya tafi nema mashi aure ba, yana can yana aiki da ya saba na tsokanar yar bappa, Mahnoor ma bata faɗa masu ba, ta bar abin matsayin sirri. -----------------------🔥 10:00AM. Bedroom ɗinsu Big Bro ya nufa dan komai ya saitun mashi yadda yake so, jirginsa ta sauka da kaya domin ginin new palace kamar yadda ya faɗa, ya wakilta Ramish kan ya kula da aikin, ya kuma sanya Jawad ya fitar mashi da zanen irin yadda palace ɗin zata kasance dan aikinsa ne. Ai sai da Jawad ya girgiza jik irin bayanin da Big Bro ya yi, tin da yake zanen gidaje bai taɓa kwatankwacin wannan gini ba, kai a kaf birnin wlh babu kwatan wannan gini. Haka suka fara aiki tukuru babu kama hannun yaro. A natse ya tura bedroom ɗin ya shigo ciki. Babu kowa a ciki hakan ya yi matukar bashi mamaki, dan dai shi ya ce Sweetie kada ta fita, to ina ta je? Ya jefi kansa da tambayar da babu amsa. A gaban bed ɗinsa ya tsaya tare da ɓalle botiran rigar jikinsa, sannan ya cire rigar, ya zame wandon ya rage daga shi sai short, wata farar towel mai ɗan girma da kyau da laushi ya ɗauko daga closet ɗinsu ya yafa a saman lion chest ɗinsa. Hanyar toilet ya nufa yana tunanin ko dai wajensu Pretty Sweetie ta tafi ne?. Tura kofar toilet ya yi zai shiga ita kuma tana fitowa tana ƙoƙarin ɗaura towel a kirjinta. Karo suka yi wanda ya ja ta yi baya-baya kamar zata faɗi sai kuma ta yi zafan rike kanta, take towel da ta rike ya yi ƙasa.......... Subhanallah! Wani irin ihu ta zunduma tare da sanya hannu zata mai da kofar ta rufe, dan ta gagara dukawa ta ɗauki towel ɗin. Hannu yasa ya rike kofar ta gagara iya rufewa, haba sai ta tsunguna ƙasa tana ɓoye jikinta, ta wani takure waje guda tana son laluɓar towel ɗinta, amma ta gagara, jikinta sai ɓari yake yi tamkar tsoronsa take ji! E hakikanin gaskiya kirar jikinsa ne ya tsoratata har jikinta ke kerma haka. Shi kuwa ɗauke wuta ya yi na ƴan mintuna, har wani irin harbawa makogwaronsa take yi saboda wani irin yawu da yake wani irin haɗiya da karfi, yau ya ga komai a filin ALLAH, sai da ya ji kansa ta buga, zuciyarsa ta harba da karfi, take abar gadon ta motsa. Wani irin nisawa da sauti ya yi, sai a lokacin ya farga da ashe kuka take yi. Rage tsawonsa ya yi wajen dukawa tare da ciro towel dake kan lion chest ɗinsa, sannan ya lulluɓa mata a saman bayanta kafin ya ɗagota, kin miƙewa ta yi tana tirgewa, sai da ya kara lulluɓeta da kyau kafin ta yarda ta miƙe, jan towel ɗin ya yi ya dawo da shi ta gaba da nufin zai ɗaura mata ta yi gaggawar sanya hannu ta damki kayanta, dan dai kowa yasan idan zai ɗaura mata abu a kirji dole hannunsa su taɓa mata tula-tulanta, shi ne yasa ta hanasa. Rage tsawonsa ya yi zuwa dab kunnenta, raɗa ya fara yi mata a kunne wanda bai bawa kowa daman ji ba. Ai bata san lokacin da ta saki towel ɗin ba, sai ji ta yi yana ƙoƙarin ɗaura mata, da sauri ta ɗago da ido ta sauke kallonta a kansa. Ta ɗan tsorata ganin yadda idanunsa suka yi jajir da su, kallonta kawai yake yi shi ma, yana jin tamkar a matse yake a takure. Kasa-kasa tamkar mai raɗa ya ce. "Ban ga komai ba ki ɗauka a haka". Harara ta dalla mashi kafin ta ce. "Ni Big Bro kana kwarata dayawa, ba zan yarda da zaman ɗaki ɗayan nan ba". DA ALAMA RAƊAN DA YA YI MATA YA WANKE LAIFIN GANINTA DA YA YI. "Ba zaki iya yin nisa dani ba ai, nasan sirrin dake ranki". Ya kai karshen maganar yana ƙoƙarin ɗaure mata towel ɗin da kyau. "Babu abin da ka sani na sirrin zuciyata, in kuma ka sani faɗi in ji". Shiru ya ɗan yi tamkar ya ɗan ɗauke wuta sakamakon lausasan tula-tulanta da ya taɓa garin ɗaura mata towel ɗin. Jin ya yi shiru ne yasa ta zaci bai ji me ta ce ba, sai ta sake cewa. "Babu abin da ka sani na sirrin zuciyata, in kuma ka sani faɗi in ji"........... Wani irin nisawa ya yi tare da sauke ajiyar zuciya a hankali kafin slowly ya kalli kirjin nata a sace, sannan ya dawo da kallonsa a kan face ɗinta, a ransa ya ce yar karama da ita sai tarin kaya, a fili kuma sai ya ce. "Sirrin dake ranki na barwa kaina tin da baki faɗa mun ba, kin fi yarda da Ronnie a kan ni, shi zaki iya faɗa mashi amma ni sai a ɓoye mun". Yadda ya yi maganar sai da ya ja ta tsaresa da kallo kawai, tamkar ba shi ya yi ta ba. "Ni ban yarda da ka barwa zuciyarka ba, kawai ka faɗa mun". Ta faɗa tamkar zata yi kuka........ A karo na biyu ya sake satar kallon kirjinta, dan baya son ta kamashi yana kalle mata kaya, shi kuma ya gagara hakura da kallonsu ne, ba zai iya jure cire kallonsa daga kansu ba, sun tafi da zuciyarsa sun gigita tinaninsa, idan kuma ya bari ta gane yana kalle mata sura to zata ja baya da shi ne wanda haka zai cutar da shi sosai, sakin jikin da take yi da shi yana ɗan rage mashi zafi. Yadda ta yi magana a ɗan shagwaɓe yasa ya ji ba zai iya tsallake wannan magiya ba, dan an tafi da zuciyarsa, kun san mutumin da shegen son mace mai shagwaɓa, dan haka sai ya ce. "Kuka zaki mun?".......... Kai ta gyaɗa tana ɗan turo mashi baki. Ba ƙaramin daɗi ya ji a ransa ba ganin yadda ya turo baki alamar shagwaɓa, take ya ji tamkar ya jawota jikinsa, amma sun yi alkawarin ba zai rinƙa taɓata ba idan har ba ya zama dole ba. "To ba sai kin yi kuka ba, zan faɗa"......... Ɗan jingina jikinta da jikin kofa ta yi tana binsa da wani irin kallon da shi kaɗai yasan ma'anarta, ita kanta bata san ma'anar wannan kallo da take yi mashi ba, kawai idanunta ke yi wanda zuciya ta ke ingiza idanun. "To ka faɗa mun ina jinka". Ta yi maganar tana sauko da kallonta izuwa kan zanen tattoo dake gefen kirjinsa ta sama wajen wuya haka, wanda tin da suka tsaya a wajen bata kalli surar jikinsa ba saboda tsoron abin da zata gani, surarsa na girgizata sosai wlh. Sai da ya ɗan nisa kafin ya ce. "So kike yi ki gwadani ko?"........ Kai ta ɗan jinjina alamar a'a. "Kai ka ce kasan abin dake raina, shi ne nace to ka faɗa mun in ji, wannan ba gwaji bane ai". Tin da ta fara magana ya tsare ɗan bakinta da kallo, tamkar ya jawota ya bata hot kiss, sai kuma ya basar tare da furzar da isa mai ɗumi daga bakinsa. "Sirrin dake ranki shi ne you love me over, and you don't want any distant between us right?". Mamaki ne ya yi matukar kamata na yadda aka yi yasan sirrin dake zuciyarta, like wow abin ya yi balain ƙayatar da ita, ai bata san lokacin da murmushin da ya kara fito da kyanta ya kubce mata ba. Zuba mata ido ya yi yana kallon yadda take murmushi, yarasa meyasa baya iya controlling kansa a gabanta, a waje zai yi dik abin da yaga dama, amma a gabanta ko magana ta yi ba zai iya ɗaukar lokaci mai tsawo bai amsa mata kamar yadda yake yi a waje ba, a waje ya kware da bada umarni, da zarar suna tare a ɗaki mai saukin kai yake zama. Yadda take wannan murmushi ya kara susuta zuciyarsa a kanta, ya kafeta da ido babu ko kyaftawa......... Hannu tasa ta ɗan rufe fuskanta kafin ta ce. "E haka ne, but kai ma ka faɗa mun abin dake naka zuciyar". Tamkar mai raɗa ya ce. "Ai kema ba ke kika faɗa mun abin dake ranki ba, ni na gane da kaina, dan haka sai ki gane nawa". Ya kai karshen maganar tare da raɓawa gefenta zai wuce yana satar kallon tsala-tsalan cinyoyinta dake ta wani glowing mai ɗaukar hankali. Ganin zai tafi yasa ta yi gaggawar riko hannunsa, tamkar zata yi kuka, ta marairace murya wajen cewa. "Ni ba zan iya gane komai kamar kai ba, kawai ka faɗa mun please"........ Jin yadda ta riko hannunsa ya sanya shi sauke nannauyar ajiyar zuciya, har cikin ransa ya ji rikosa da ta yi, yana jin tamkar ba zai iya sallake wannan ya cigaba da daurewa ba. Slowly ya juyo tare da kurawa eyes ɗinta idanu. "Babu abin dake a cikin raina wanda baki sani ba, sai dai in so kike ki ji wani sirrin da ni kaina ban san da shi ba".......... Ta fahimci me yake nufi, idan zata faɗa daidai yana nufin tamkar yadda yake son Ronnie haka yake sonta, matsayin sister kenan. Abin ko kaɗan bai yi mata daɗi ba, dan haka sai ta sake mashi hannu tare da juyawa da sauri ta nufi waje. Bayanta ya bi da kallo yana jin tamkar ya jawota jikinsa, amma babu dama, dik wani motsawa da mazaunanta suke yi a kan idanunsa ne har ta kurewa ganinsa. Siririn ajiyar zuciya ya sauke kafin ya tura kofar ya rufe sannan ya wuce ciki. Shiryawa ta yi cikin wasu shaggun kaya, wandon jeans ne mai bakain kyau da riga top navy blue, wandan kuma fari. Ta gyara wannan kyakkyawan gashin kan nata, dan har da shi ya lalace ta sake wankewa, karo suka yi da Heleena ta yi mata wanka da coffee shi ne ta dawo ta sake yin wanka, to har gashin kanta coffee ɗin ya ɓata, saboda Heleena ta fita tsawo nesa ba kusa ba. Tana gama shiri ta zuba turaruka zata nufi waje kenan ta ji motsin buɗe kofar toilet alamar ya fito. Ta wutsiyar ido ta saci kallonsa while shi kuma gabaɗaya kallonsa a kan waist ɗinta da mazaunanta da suke tamkar zasu fasa wandon jikinta. Sai da gabansa ya faɗi ganin hakan. Ta fahimci ita yake kallo, dan haka sai ta wuce zata nufi waje ba tare da ta gansa ba......... "Ina zaki je?". Ya faɗa a sanyayye sosai. Ba tare da ta juyo ba ta amsa da. "Wajen momma da su Mahnoor". "Dawo ki zauna". Ya faɗa on a serious note. Tamkar zata fasa ihu ta juyo da kallonta a kansa, take ta yi rau-rau da idanu zata fara yi mashi kuka. Ɗauke kansa ya yi daga kallonta ya wuce ya nufi closet ɗinsu. Juyowa ta yi tana kunkuni, ga haushin ya nuna baya yi mata son soyayya sai dai son yaya da kanwa, ga haushin ya hanata fita, sai ta kwanta a saman sofa tare da jawo bargo ta rufe har kanta, wani irin zafi ta ji zuciyarta na yi mata, take ta fara ruwan zafafan hawaye, har da wani shessheka take yi. -----------------------------🔥 Yana shiga bedroom ɗinsu ya isko Pretty sarkin son jiki kwance a saman bed, ta rungume pillows a kirjinta, ta yi ɗaiɗai a bed ɗin, ga uban bargo da ta lulluɓa da shi. Cike da damuwa sosai a ransa ya dawo, dan hankalinsa a tashe kada blood power su yi wa King wani abin, shi kuwa Big Bro da yasan ba zasu yi saurin ɗaukar mataki ba ai kunga hankalinsa a kwance, bawan ALLAH Smart bai da sani a ɓangaren tsafi, kunga dole hankalinsa ya tashi. Jin motsin shigowa ɗakin yasa ta ɗago kai tare da waro idanunta waje, ashe dama ba barci take yi ba. Ai tana ganin shi ne ta yaye bargon da gudu ta diro kasa, kai tsaye ta nufesa. Tana zuwa ta faɗa jikinsa, at the same time suka sauke cool ajiyar zuciya. Dik da yake a cikin damuwa sai da ya ji sanyi ta ratsa zuciyarsa na ganin irin kayan dake jikinta da kuma yadda ta yi hugging ɗintsa, rungumeta sosai ya yi yana sanya hannunsa ya riko santalelan cinyarta dake waje, dan short jeans ne zuwa cinyoyinta a jikinta, sai ɗan ƙaramin riga da bai gama rufe cibiya ba, ta saki gashi har baya, gari ya waye kowa ya fita ya gaggaisa da mutane amma ban da Pretty, tana ɗaki abinta, ko Sweetie bata nema ba. "Yah Omerish ina ka je tin da sassafe?". Tamkar zata yi kuka ta yi maganar. Ɗaukarta cak ya yi suka koma saman bed, ya kwanta da ita a jiƙinsa kafin ya sanya hannu ya tattare dark black curly hair ɗinta gefe, ya samu damar ganin face ɗinta da kyau, ta shagwaɓe fuska tana turo mashi ɗan baki. Sumbatar bakin nata ya yi kafin ya ce. "Rigimamma, yau ba zaki yi breakfast bane? Dan nasan baki yi ba"......... "Kai nike jira ai ka zo ka bani a baki". Ta faɗa ita ma tana sumbatarsa a kyawawan lips ɗinsa. "Da gaske yau ni ake jira?". Cikin zolaya ya yi maganar......... Kai ta jinjina mashi alamar e a shagwaɓe........ "Wai ni waye ya koya maki soyayya ne yanzu?". Ɗaure fuska ta yi tare da yunkurawa zata bar jikinsa tana faɗin. "Kome na yi maka sai ka ce koya mun aka yi, ni ba zan iya abu da kaina ba, ni mahaukaciya ce kenan ko jahila? Watau ni ba zan iya abu ba sai mutane ne zasu iya ko?". Ta faɗa tana wani irin huci, kun san akwai zafi a rinƙa cewa mutum bai iya abu ba, komai ya yi sai ace waye ya gaya mashi, shi ba zai koya ba zai tabbata ana faɗa mashi kenan? Dole ta ji haushi. Rikota ya yi da sauri yana faɗin. "Oh rigimammiyata kawai, sorry to, nasan ke kika koyi kayanki babu wanda ya faɗa maki, zolayarki nike yi". Da yake a kansa tana da saukin kai sai ta saki kyakkyawan murmushi tare da cewa. "To muje ka bani breakfast, yau kai zaka mun wanka". Ta yi maganar tana komawa jikinsa ta kwanta, sannan ta fito da dogon tongue ɗinta ta fara lasan lips ɗinsa tana kallon cikin idanunsa. Bakinsa ya ɗan buɗe ya capki lips ɗin nata, a natse ya fara tsotsa yana kai hannunsa saman mazaunanta. "I really love you my wife". Ya faɗa tare da capko lips ɗinta na kasa, ya fara bata hot kiss, take dik wata damuwa dake cikin ransa ta ragu, ya rungumi yar matarsa ya hau rage zafi. --------------------------🔥 CROWN OF JUSTICE. Yana fita kai tsaye side na su Ansar ya nufa, yana zuwa ya tura kofa ya shiga tare da yi masu sallama. Suna zazzaune saman sofa suna hira. Ai suna ganinsa suka mimmiƙe alamar girmamawa, ɗan ɗaure fuska ya yi, cikin wannan sanyi nasa ya ce. "Me hakan kuma?". Ansar ne ya ce. "Girma muke baiwa yarima mai jiran gado"....... Harara ya dalla masu kafin ya ce. "Bana son hakan fa, ni Hoorain da kuka sani ne abokinku, ba wani Prince". Anwar ne ya tari numfashinsa da cewa. "To dik da haka ai kai gaba kake damu a cikin warriors ɗin ma". Karisawa ya yi ya zauna yana cigaba da harararsu kafin ya ce. "Ya kuka tashi tuzurai?"....... Zama suka koma suka yi suna amsawa da. "Awww gori ake yi mana ma kenan". Kai ya jinjina masu. "E gori nike maku, dik wanda ya ji zafi cikin satin nan ya fito da mata ya yi aure".......... Anwar ne ya ce. "Dik ba wannan ba, yanaga kamar Lion namu yana cikin ɓacin rai ne?". Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ------------------------------------------🔥♥️ SABUWAR DUNIYA STEP ONE!.🔥🔥🔥 Anwar ne ya ce. "Dik ba wannan ba, yanaga kamar Lion namu yana cikin ɓacin rai ne?"........... Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Babu komai". Dafa shoulder ɗinsa Ansar ya yi. "Baka taɓa ɓoye mana komai naka ba, meyasa yanzu zaka fara ɓoye mana? Ka manta tare muke kuka kuma mu rarrashi juna?". Kai ya girgiza kafin ya ce. "Tare muke komai, amma ku yarda dani ba wani abin ke damuna ba, kawai na ji babu daɗi ne da nazama sanadiyar zuban hawayen Zunaira yau". Murmushi Ansar ya yi tare da cewa. "Awwww batu ake na ma'aurata, to shikenan a wannan gaɓa bamu nemi jin me yake damunka ba, je ka yi rarrashi, idan anki kulaka kuma sai ka dawo mu kwana a nan, mu ba zamu hanaka wajen kwana ba kuma ba zamu kiraka tuzuru ba". Cikin zolaya ya yi maganar. Anwar ne ya capki zancen da cewa. "Gaskiya ina fatan watarana nima in ga wannan rana, ace na yi faɗa da matata ina rarrashi tana ja mun rai da yanga, ina son yin aure our Lion". Ya faɗa fuskarsa da alamar damuwa..... Dafa shoulder ɗinsa Hoorain ya yi alamar karfafawa kafin ya ce. "Fito da mata zan yi maka aure ɗan uwana, for sure rayuwar aure akwai daɗi sosai musamman ka samu wanda kake so yake kuma sonka". Damuwa ce sosai ta kara bayyana kan fuskar Anwar, murya a rauna ce ya ce. "Ai ni kam bana jin zan samu wanda raina yake so ɗin nan, na sota ne tin tana karama amma ni kaina nasan na yi gangancin fara sonta saboda ba samu zan yi ba, amma ba laifina bane, laifin zuciyata ce da bata iya tantance abin da zata iya samu da wanda ya fi karfinta ba kawai ta fara so". Kallon juna Ansar da Hoorain suka yi kafin su matsa kusa da Anwar sosai dan tausan shi, har suna haɗe baki wajen cewa. "Wa kake so ɗan uwa". "Babu amfanin in faɗa maku ita, kawai ku bar zancen ALLAH ya bani mafi alkhairi a gareni". Girgiza kai Hoorain ya yi. "A'a please ka faɗa mana, zamu tayaka yakin nemanta har mu samu"....... "Ɗaya ne daga cikin ƴaƴan king Zuhair sister ɗin Zunaira". Ya faɗa a raunace sosai. Kallon juna a karo na biyu Ansar da Hoorain suka yi kafin Hoorain cikin tausasawa ya ce. "Wacece daga ciki?". Nisawa ya yi kafin ya ce. "Ban san sunanta ba, dan ita bata bada fuskar ko magana wani ya yi mata bare har yakama sunanta a cikin fili kowa ya ji, bata kula mutane, bama ta cika fitowa ba sai in ya zama wajibi". Fuskarsa ta kara tsananta nuna damuwa. "Kwatantamun yadda take zan gane wacece". Cewar Hoorain, dan shi dikkansu sanadiyyar Auta ya sansu....... Kwatance Anwar ya fara yi masu, tin da ya fara magana Hoorain ya gane wacece daga ciki, dan haka sai ya ce. "Da izinin ALLAH zaka mallaketa, amma dai yanzu ku tayani faɗa wajen ganin na dakatar da wannan gaba dake a tsakanin iyayen namu sai mu san abin yi". WA KUKE TINANIN ANWAR YAKE SO?. HOORAIN MAI KOKARIN DAKATAR DA GABAN NAN YA ZAI JI IDAN YA JI CEWA MAHAIFINSA NE BAI DA GASKIYA KUMA DA TSAFI YAKE AMFANI DOMIN KARA KARFAFA MULKINSA YA IYA YAKAR KOWACCE MASARAUTA, SANNAN YA SANYA SHAKKA DA TSORONSA A ZUƘATAN MUTANE? YA HOORAIN ZAI JI WAI? GARA SU BOBO ALREADY SUN SAN KOMAI TIN DA A KAN YA BADA JININ WANDA YAKE SO NE MA YA KI KARƁAR MULKIN YA GUDU YA BAR KINGDOM ƊIN MA, KUN GA KENAN ALREADY SHI YA SAN DA BLOOD CROWN NA AMFANI DA TSAFI, SU HOORAIN DA SU ZASH AND LEESHARH NE ZASU JI BABU DAƊI, SU DAI SU SMART ALLAH YA CECESU MAHAIFINSU MUTUMIN KWARAI NE TIN DA HAR YA YI ƘOƘARIN YAKAR WANNAN BLOOD POWER YA KUMA KI YARDA DA TAYIN DA AKA YI MASHI!. --------------------------🔥 Cike da murna suka amsa da. "In Sha ALLAH zasu daina wannan gaba very soon"........ "ALLAH yasa". Ya faɗa tare da miƙewa. "Zunaira na buƙatata, yanzu ma dai na ce bari in ga ya kuka kwana ne, sai da rana zan dawo". Ya faɗa yana kallonsu....... Fatan alkhairi suka hau yi mashi tare da fatan ALLAH yasa kada Zunaira ta sauko, ta bashi wahala sannan ta sauko, cikin zolaya suka yi maganar. Waje ya nufa yana faɗin. "Ai ita ba irinku bace, kyakkyawan zuciya take da shi, kuma tana tausayin mijinta sosai". Bai jira amsarsu ba ya wuce waje. Yana fita kai tsaye ya nufi part ɗin su Rishan dan su gaisa. Sai dai yana zuwa Rishan ya miƙo mashi waya wai ga shi ana nemansa. Ganin number Mommah ce yasa ya karɓi wayar da sauri tare da nufo waje. Yana fita ya nufi side ɗinsu yana kara wayar a kunne. Cikin girmamawa ya ce. "Momma ina kwana?". Daga ɗayan side ɗin ta amsa da. "Lafiya lou ɗana, ya gida da ƴan uwan naka?". Kara natsuwa sosai ya yi kafin ya amsa mata da. "Lafiya lou fatan kowa yana cikin koshin lafiya?". Ya yi maganar daidai time da yake shigowa bedroom ɗinsu. Da alhamdullilah mommah ta amsa mashi kafin ta ce. "Dama so nike ka kawo mun Zunaira cikin satin nan in ba damuwa, yayanta ke son ganinta". Dik da bai san a kan wani yayanta ake magana ba, sabida girmamawa da ladabi game da matsayin da momma keda shi a ransa sabida kyawawan halayenta yasa kawai ya amsa da. "Zan kawota In Sha ALLAH".......... Sosai mommah ta ji mugun daɗin irin yadda Hoorain yake mugun girmamata, baya ja da maganarta, idan ta yi magana ma baya neman karin bayani kawai yake amsawa da to cikim girmamawa, hakan ba karamin daɗi yake yi mata ba. Addu'a ta shiga kwaranyo masu tana zuba masu albarka, sai amsawa yake yi da amin amin yana bin Auta da kallo. Ta fito ta shirya cikin wasu haɗaɗɗun kaya, yau dressing na masarautar ta yi, wato shigar mutanen Korea, kuma ya yi mugun yi mata kyau, ta fito tamkar ka saceta ka gudu, sai dai kuma dik hawaye ya wanke mata fuska, idanunta sun yi jajir da su tamkar jini, alamar ba'a sauko ba kenan. Ai mommah na katse kiran nan ya yi zafan hayewa saman bed ɗin ya sameta. Tana ganin ya hauro ta yunkura zata sauka kasa, a hanzarce ya kwanto da kansata a saman laps ɗinta, idanunsa a kan face ɗinta. Ƙoƙarin tirgewa ta fara yi tana nuna bata son ya taɓata. Hannunta ya riko cikin nasa, murya a sanyaya sosai ya ce. "Haba my Hoonairata, ashe dama zaki iya yin fushi da heronki?". A tausashe ya yi maganar. Kai ta jinjina mashi alamar e, a kule ta ce. "In dai zaka rinƙa yi wa mata magana, to zan iya yin fiye da hakan ma. Hanunta ya kara matsewa cikin nasa, a natse ya ɗan sumbaci hannun kafin ya ce. "Shi kam Hoorain me zai yi da mata bayan yana da Hoonaira? Wlh ke kaɗai kin isheni, kuma kin fi kowa sanin ni bana magana da mata, ita ɗinma kuskure aka samu, amma na yi alkawarin ba zan sake ba". Harara ta dalla mashi kafin ta ɗan kwace hannunta. "Ba zan yi hakuri ba, dole sai ka karɓi hukunci". Yana kallon cikin idanunta ya ce. "Idan baki yi hakan ba ma ai sai in ce anya jinin modarawa ne yake yawo a jikinki kuwa? Saboda su ba'a taɓa taɓasu sun yafe ba, komai kankantar laifi sai ka biyashi, shiyasa har Manzon ALLAH (SAW) ya bar duniya babu waɗan da yake yi wa yawan faɗa a kan su rage zafin zuciya irin modarawa........". Hannu tasa ta buge ɗan bakinsa ba tare da ta bari ya idasa maganar ba, tana dalla mashi zazzafar harara ta ce. "Watau dama zagin modarawa kake yi ko?".......... "Yau dai dole dole sai an nemo laifi an ɗaura mun? To shikenan dai, amma dai kin san ke kanki sai dai in baki labarin su waye modarawa ko? A cikinsu kusan aka haifeni, aka raineni, jaruntarsu tasa na zama jarumai, ai rashin hakurinsu jarunta ce da zafin zuciya, idan mutum yana da tsoro in aka yi mashi ai tsoron yin magana zai yi ma bare har ya rama, amma su fa? Jininsu a tafashe yake, ni yabonsu na yi ba zagi ba, Hoonaira ki bari mana". Ya kai karshen maganar yana kifa kansa a saman laps ɗin nata. "Tin da ba zaki hakura ba nasan ko na yi kuka ba rarrashina zaki yi ba, bari in je Abbona ko ɗan uwana Kamran or Uncle Rishan ko dai su Ansar su rarrasheni". Ya faɗa yana tura hannunsa bayanta ya rikota da kyau. "Ba zan rarrasheka ba, kuma babu in da zaka je, a nan zaka yi kukan ka gama". "Da gaske?". Ya tambaya yana haurar da hannunsa sama izuwa tsakiyan bayanta.......... "Da gaske nike yi, ka tashi ka yi frog jump shi ne hukuncinka na kula wata". Kasa sosai ya yi da murya wajen cewa. "A kanki amma zan yi frog jump ɗin ko?". Bata ji me ya ce sosai ba sai kawai ta gyaɗa mashi kai alamar e. Aikuwa miƙewa ya yi tare da jawota gabaɗaya jikinsa. Ya rungumeta tare da fara kwance dik wasu maɗauri da doguwar rigar jikinta yake da shi. "My hero nifa frog jump na ce ka yi". Kamar zata yi kuka cikin shagwaɓa ta faɗa. A kunne ya raɗa mata. "Ai abin da zan yi yanzu kenan". Zata dake yin magana ya yi gaggawar haɗe bakinsu yana warware maɗaurin dake wajen shafaffen cikinta. Ai wani irin salon kiss da ya fara bata wanda bata san lokacin da ta rungumesa ta hau mayar mashi da martani ba, saboda yau ya yi abin da bai taɓa yi ba, kun san kiss na rarrashi daban yake, salonsa ma daban ne. Bata ankara ba sai ji ta yi ya zame rigar jikinta, a hankali ya sanya hannunsa ya riko waist ɗinta tare da ɗagota ya dawo da ita saman massive chest ɗinsa, ai tuni ta manta da fushi take yi suka shiga nunawa juba zallar kauna. Tsabar farinciki yau har ya so mantawa da ya ce sai ta girma ya wuce gona da iri, wani irin ihun da ta zunduma mashi ne yasa ya dawo cikin hayyacinsa, da sauri ya miƙe daga kanta yaka dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi. A gefenta ya kwanta tare da sanya mata yatsan hannunsa ɗaya a bakinta yana yi mata alamar rarrashi, dan ba zai iya yin magana ba a halin da ake ciki. Ganin hakan yasa ya yi mugun bata tausayi, sai ta matsa ta kwanto da kanta a saman faffaɗar bayansa tana ƙoƙarin shanye kukan da take yi. Shiru suka yi sai sautin kukanta dake tashi kaɗan-kaɗan, almost 30 mins a haka kafin sanyayyar muryarsa ya daki dodan kunnenta. "Am so so sorry my Hoonaira, ba zan sake ba". Ya faɗa tare da juyowa ya rungumeta ta gaba. Idanunta sun ƙanƙance sun yi ja alamar barci ta dage ta manna mashi sumbata a kumatu kafin ta ce. "I love you my hero". Har cikin ransa ya ji daɗi, a hankali ya kara matseta a jikinsa har sai da ta yi barci. Sannan ne ya lallaɓa ya kwantar da ita, ya ja mata bargo ya nufi toilet. A gurguje ya watsa ruwa ya fito, shiryawa ya yi da sauri-sauri ya sauko ya nufi wajen Kamran. Bakinsa a ɗauke da sallama ya shigo cikin ɗakin. Kamran da Abbo suna zaune a saman bed da Kamran yake jinya, ya warware sosai sauki nata samuwa, hukuncin King Zuhair da ukubarsa bata da daɗi ne, wani irin bahagon mutum ne da in a hukunta sojan yaki to fa za'a jima ana jinyarsa bai koma normal ba, wani mai karamar ƙwaƙwalwa da karamar zuciya ma a wajen yake mutuwa ko ya samu taɓin hankali. Ai Hoorain da Kamran sun yi namijin kokari da iya kwanciyar gadan asibiti kawai suka yi bayan fitowarsu daga horon King Zuhair. Kamran na ganinsa ya tsaresa da kallo, yana jin kaunarsa har cikin ransa, amma yaki yarda ya nuna, saboda balain zuciya, wai har yanzu yana fushi da su, dik da Abbo ya faɗa mashi matsayin Hoorain a wajensa, ya kuma faɗa mashi yadda tarihi ta wakana har ya bar kingdom ɗin, sannan ya nuna mashi wanene mahaifinsa (Udey) amma zuciyar ɗan mammarsa taki sauka, shi dai lallai sun yi mashi laifi, fushi yake yi da su, kun san dama in ya yi fushi sai Mamma ta yi rarrashi sosai, to su Abbo basu iya yadda ake rarrashin damisan mamma ba, sun tsaya sai hakuri suke bashi. A kusa da shi Hoorain ya zauna yana tambayarsa ya jiki. Banza ya yi da su tamkar bai ji ba, ya cigaba da tinaninsa na yadda zai yi ya kwato Pretty, dan shi wlh ba zai barta da wani be, dole ya ɗauko matarsa, ai shi aka baiwa ita. NI KUMA NA CE RASHIN SANI YA FI DARE DUHU!. Hannayensa Hoorain ya riko cikin nasa, a sanyayye ya ce. "Wai har yanzu fushi kake yi damu?". Wani irin kallo mai kama da harara ya dalla mashi kafin ya ɗan yunkura zai kwace hannunsa, tin da ya samu lafiya bai yi masu magana ba, bayan sunan Pretty bai iya kiran komai ba, Hoorain ya fahimci bashi da natsuwa a yanzu kuma shi irin mutanen nan ne wanda zuciyarsu a kusa take, shi ne yasa yaki faɗa mashi cewa ai Pretty sister ɗinsu ce, yasan a wannan hali idan ya faɗa mashi to fa tsab zasu iya rasa shi ne, dan ba karamin so yake yi mata ba, gara su barshi ya samu lafiya sosai ta yadda ko ya ji gaskiya sai dai ya sake kwanciya jinya kawai. Sosai Hoorain ya yi kokarin tausan shi, amma zuciyar ɗan mamma yaki sauka, da suka matsa mashi ma sai ya yunkura zai bar masu ɗakin. Riko hannunsa da sauri Hoorain ya yi kafin ya ce. "Ka yi hakuri kanina, a baya ban san alaƙata da kai bane yasa na dakeka kuma na hanaka ɗaukar abin da kake so, amma yanzu nasan wanene kai, na yi alkawarin tayaka yaki a kan abin da kake so, please ka yi mana magana ka ji?". Ya faɗa mashi hakan ne domi ya sanya ya yarda da su har ya sauko ya samu ya kaisu wajen Mamma, kun san shi Hoorain bai san cewa matar da ya taimaka a forest time da ya je ɗaukar su Auta ita ce mammarsu ba, dik yanzu Kamran suke jira. Da jin kalaman ɗan uwan nasa na zai tayashi faɗa su kwato Pretty yasa ya yi saurin juyowa, a sanyayye sosai da muryarsa irin na Mamma ya ce. "Da gaske zaku tayani kwato Pretty?". Kai Hoorain ya gyaɗa mashi tare da cewa. "Sosaima, zamu tayaka"......... Ɗan ɗaure fuska Kamran ya yi yana bin Hoorain da kallo kafin ya ce. "Amma kuwa in dai haka ne kai kam kai ka gaji Mamma a zafi, sannan in dai haka bil adama suke rayuwa ni ban yi farincikin kasancewata a cikin mutane ba, a tinanina zan ga mutane masu sauki da tausasawa game da kaunar juna shiyasa na matsu in fito daga forest ɗin nan, amma dik in da na je azzalumai kawai nike samu, tin shigowata duniyar mutane na fara yarda da zancen Mamma da take cewa mutane ba abin yarda bane, kuma ko mutun zai mutu kada ka taimaka mashi, dan in ka jawosa inuwa shi kuma rana zai turaka, tabbas Mamma tana da gaskiya a nan, jiya ka taimaki wancan da ya kwace mun Pretty sabida a lokacin baka san waye ni ba kafi kusanci da shi, baka damu ko na mutu ko na yi rai ba, baka damu da sanin wacece ita a gareni ba ka mun mugun duka a kan wancan, yau kuma da ka san waye ni zaka taimaka mun mu kwatota, zaka kwayewa wancan baya, kenan ku mutane ida ba naku ba baku taimakawa wasu? Ƴan uwanku sune kawai mutane masu daraja? Bayan su dik wanda zai shiga kunci babu ruwanku?". Tin da ya fara magana suka tsaresa da kallo har ya kai karshe, zallar kamannin magana da King Omranish da Commander ya sani yake gani a tattare da Kamran, sai a yanzu ya fara tinanin wasu abubuwa da ya sani dangane da King Omranish wanda yanzu sam babu su a tattare da Udey, tabbas King Omranish idan yana magana a bubbuɗe yake yinta babu tsoro ko shakka, magana kai tsaye babu shakkar abin da zata haifar, lallai maganar Kamran sak take da yadda babansa yake magana, ba ruwansa da wai Hoorain yayansa ne, ya kalli cikin idonsa ya faɗi sun iya zalunci, shi ba haka ya taso ya sani ba, kun san in baka taɓa rayuwa a cikin mutane ba ka shigo rayuwarsu daga baya sai ka rinƙa shan mamaki tamkar ka mutu, wani ma idan ya yi maka wani abin sai ka zaci dik mutanen duniya bakaken azzalumai ne. Su dai shiru suka bisa da shi, dan sun yi mashi uzuri bai saba zama da mutane bane, Abbo ne ma ya yi karfin halin cewa. "Haka ne zancenka, yanzu dai zoka zauna kada ka je ko'ina"........ Kun san shi babu ruwansa da sai mutum ya girma ne yake yin furfura ko kuma fifikon shekaru da sauransu, dan haka bai ɗauki Abbo a wata tsiya ba, yadda yake kallon su Pretty haka yake ɗaukar su Abbo, wato kowa ma a daidai shekarunsa yake gwadasa, ko da yake ba zaku yi mamaki ba tin da shi da ya ga su Sweeetie suna jaririrai ya rinƙa mamaki dan bai taɓa ganin kananan yara ba, shi da a tinaninsa kowa da girmansa ya zo duniya, bai san ma da uba ake haihuwa ba, kunga kuwa ai bakwa ji mamaki ba dan ya yi wa Abbo kallon girmansu da shekarunsu ɗaya. Dan haka yanai wa Abbo magana gatsau haka babu respect wanda hakan ya yi mugun hasala zuciyar Hoorain ya fusata zai ɗaukesa da mari kenan Abbo ya yi gaggawar rikesa yana faɗin. "Ka yi la'akari da yanayinsa, a nan ne zaka fahimci ba dan rani ya yi maganar ba face haka ya saba yin ta, dik yadda aka yi su biyu shi da gimbiya suka yi rayuwa, daga yanayinsa zaka san bai saba rayuwa da mutane ba, ka bisa a hankali zai saba kuma ka fahimcesa". Abbo ya yi maganar ne da larabcin Kingdom of Power, while shi kuma Kamran da yaren koreans yake yi masu magana tin da ya buɗi baki, kun tuna a farkon book ɗin nan na faɗa maku Mamma tana da yaren da suke yin magana da shi ita da Kamran ko? To wannan shi ne yaren watau Koreans language. (Ku fa akwai abubuwa da dama da zan tuna maku a book one, ciki har da mahaifin su Bobo watau sarkin yammaci, kun tuna a book 1 na yi magana a kansa lokacin da Auta ta je tambayar King zata je Dubai wajen Yah Omar sai sallama ya zo ya ce da King ga sarkin Yammaci ya zo? Ai a lokacin na ɓoye maku me King da sarkin yammaci suka tattauna ko? Na tsallake wajen, to dik batuce kan Blood Power da King ya rufe, zamu zo wajen zaku ji, wayyo ni, wasu abubuwan daga book 1 nike ajiye maku shi a dunkule baku ganewa har sai kusan karshen book. Uhm kun rike batu kan kauyensu Mahreen ko shi ma kun manta?🤔 Akwai case a can ma, akwai abin da nace ku rike zamu dawo labari a kansa, in kun manta ku tuno!!) Tausarsa Abbo ya yi har sai da ya hakura ya dawo ya zauna........ Cike da zaƙuwar son sanin in da mahaifiyarsu take Hoorain ya hau tambayarsa in Mamma take?......... "Tana forest tana jiran in samo babana in zo in ɗauketa". Ya basu amsa a taƙaice kuma a dake babu wani respect ko risinar da kai!. "Zaka iya yi mana jagoranci zuwa wajen?". Hoorain ya sake tambaya. "Me zai hana tin da nima ina son ta bar forest ɗin"........ Haba wani irin daɗi ne ya kama Hoorain, har bai san lokacin da ya rungume Kamran a jikinsa ba, Mammarsu zata dawo. UHM SUNA NASU HAUKAR, AI KO ZASU MUTU MAMMA BA ZATA DAWO KINGDOM ƊIN NAN BA A YADDA SUKE ZATA BA, DAN A TINANINTA MAHAIFIN HOORAIN NE YA ZALUNCETA, KUN GA BA ZATA SAKE YARDA DA SHI BA, AKWAI DAI CASE. Cike da zumuɗi Hoorain ya ce. "Zamu iya tafiya wajenta yanzu?"......... Commander ne ya tari numfashinsa da cewa. "Haba Hoorain, yi hakuri mana zuwa ya kara samun sauki, yanzu ai ba zai iya dogon tafiya ba". Ɗan rungumo Abbon Hoorain ya yi tare da ɓoye kansa jikin Abbon wai ya ji kunya. Muryar Kamran ce ta katsesu da cewa. "Ba fa irin forest da kuka sani bane, wajen yana da nisa da wancan masarauta da suka kwace Pretty, sannan kuma ragwaye basa iya zuwa wajen, mutuwa zaku yi da namun dawa, ko da yake kai naga kana da jarunta tin da ka iya faɗa dani". Ya yi maganar yana pointing Hoorain da hannunsa. BALAIN LALLAI KAMRAN YA RAINA SU ABBO, WAI JARUMAI NE SUKE ZUWA FOREST, SHI FA YANA GANIN BABU WANDA YA KAISA JARUMTA, SAI DAI KAI RENON LIONESS MAMMARSA. Babbar magana, zaro idanu Hoorain ya yi, dan kuwa yasan in kuwa haka ne wajen yana da mugun nisa, shi yanzu Kamran bai san a takamamman in da yake bane, amma wlh forest ɗin da nisa, in dai ta kingdom of power ne kuma to ai forest guda ɗaya ce a wajen wadda take a tsakanin masarautu biyun ta zame masu kamar border, kuma ita ce forest da ya tsinto Zunaira a ciki, idan zai iya tina komai daidai matar da ya taimaka har yake ganinta tamkar ya san fuskarta sabida kama ta jini da ta so yi da shi, to tabbas ita ce kenan? Ye jefi kansa da tambaya. A fili ya ce wlh ita ce, har sai da su Abbo suka ɗago suna kallonsa. Kamran ne ya ce. "Ita ce wa?". Hararar Hoorain ya wurga mashi. "Kai baka gajiya da faɗa da zafin zuciya ne?". Hoorain ya tambayi Kamran. Ɗaure fuska Kamran ya yi kafin ya ce. "A haka aka reneni na zama mafaɗaci". Ya faɗa a faɗace yana zarewa Hoorain idanu tamkar zai dakesa!. "To yakamata yanzu kasan ni yayanka ne, ka rinƙa tausasa harshe a kaina, ba zan juri komai daga gareka ba, ɗaga maka kafa kawai nike yi"........... Ɗan taɓe baki Kamran ya yi. "Me kuma yaya?". Ya tambaya on a serious note, dan har ga ALLAH shi bai sani ba. Ɗaure fuska tamau Hoorain ya yi alamar ransa ya ɓaci, dan yana ganin tamkar manna mashi hauka Kamran yake yi, bai san iya gaskiyarsa yake faɗe ba, zai yi magana Abbo ya rigasa da cewa. "Hoorain dole ka ajiye zafin zuciyarka gefe idan kana son ku shirya da ɗan uwanka, ka bisa a hankali saboda wlh iya gaskiya yake faɗa maka bai san komai ba"........ Shiru Hoorain ya yi yana ɗan jinjina kansa alamar haka ne. Shi kuma Kamran ya bisu da ido dan ba wani jin larabcin nan yake yi ba, suna ɓadda harshe suna magana su barshi a duhu, su kuma sun saba ne da magana da larabci shiyasa, take tinanin Rockey ɗinsa ta faɗo a ransa, ALLAH sarki ya yi wa Rockey wayau ya gudu ya barsa a forest, dan yana son ya je ya taimakawa Mammarsa kada a barta da kewa ita kaɗai. Haka suka cigaba da tattaunawa Hoorain na kokarin kai zuciyarsa nesa dan su sasanta da Kamran, Abbo na ta kara tausan zukatan zakunan dikka biyu dan a samu sasanci da fahimtar. --------------------------------🔥 CROWN OF POWER.🔥 Kuka sosai Sweetie take zubawa, dan takaicin hanata zuwa wajen su Mahnoor ɗin da ya yi, a dik mutanen da Sweetie take haɗuwa da su babu wacce ta so ta kaunata kamar Mahnoor, a tashin farko ta so Mahnoor matuƙa, saboda kyawawan halaye da saukin kanta, sannan tana jin daɗin yin hira da ita, amma kawai ya zo ya wani hanata fita, dole ta ji haushi. Slowly ya tsuggunna a gaban sofar da take, yana sanye da wandan Jeans irin rippet ɗin nan launin light ash, sai round neck polo shirt ita kuma fara tas, ya yi balain kyau sosai, ya fito a ainahin balarabensa, sai tashin fitinannen Kamshi yake yi. A hankali ya kai hannunsa ya yaye bargon da ta lulluɓa har kanta. Sai da ya ji kirjinsa ta buga ganin yadda take ruwan hawaye, dama ya zargi hakan shiyasa ya ce bari ya dubata. Ita kuwa wani irin mugun harara ta dalla mashi kafin a kufule ta ce. "Me ruwanka dani to?". Yadda ta yi maganar ba karamin narka zuciyar Big Bro ta yi ba, ya kurawa ɗan bakinta idanu, wasa-wasa ta fara koyan mahaifa yarinyar nan, har da su murguɗa baki. "Ni ka daina kallona kuma ka rufa mun bargona". Cikin faɗa da kuluwa da haushi ta yi maganar. Kun san halin mutumin, shiru ya yi bai yi magana ba har na tsawon mintuna 3, ranta ne ya kara ɓaci ta yunkura zata tashi kenan ya yi gaggawar rikota, in a cool way sosai ya ce. "Meyasa kike kuka?". Ai tsabar bakinciki da takaici bata san lokacin da ta ce mashi. "Ban sani ba, wai ina ruwanka da rayuwata ne?"....... "Akwai ruwana da rayuwarki sabida rayuwarki tawa ce". Ya faɗa a sanyayye sosai, wanda hakan ba karamun kara tunzura zuciyarta ya yi ba, sai ya rinƙa nuna kamar baya fahimtar abubuwa dan rainin wayau, yana nufin bai san meyasa take kuka bane da zai wani tambaya!. Zazzaro mashi idaunta da suka yi jajir ta yi, tamkar zata cinyesa da masifa ta ce. "Rayuwata ba zai taɓa zama naka ba, ni yanzu ma na fasa bana buƙatarka matsayin yaya, Ronnie kawai ya isheni, a gida ina da Kamran, bayan shi kila ina da wasu, bana bukatarka kuma!". Ta kai karshen maganar tana ƙoƙarin kwace rikon da ya yi mata, sai dai ta gagara, domin kuwa karfi ba ɗaya ba. Tin da ta yi wannan magana ya fahimci ranta ya kai kolokuwa wajen ɓaci, bata da raina manya, tana kuma tauna magana kafin ta faɗa, ya yi mata uzurin cewa bata cikin hayyacinta ne. Cikin sanyin murya ya ce. "Dik yadda kika ɗauki abin bai kai haka ba, amma ban san me zan ce maki ba, please stop talking about Kamran or some mens here in a front of me, dan bana son kara maki ɓacin rai kan wanda kike ciki, am trying to control my self, be patient please". Tin da ya fara magana ta natsu take sauraronsa, watau sorry ne ba zai taɓa ce mata ba bayan shi da kansa yasan ya yi mata ba daidai ba. A ranta ta kuduri niyyar sai ta santa wannan ɗan bakin nasa ya furta sorry a gareta, dan haka sai ta shammacesa sai da ta bari ya saki jiki ta kwace rikon da ya yi mata, da gudun gaske ta miƙe zata nufi waje. Aikuwa yana miƙewa taku ɗaya ya yi ya capko waist ɗinta, bata ankara na sai jinta ta yi a saman lion chest ɗinsa, wage baki ta yi zata zunduma mashi ihu ya yi zafin sanya hannunsa ya toshe mata baki da hannunsa ɗaya. Mutsu-mutsu ta fara yi tana son kwace kanta, sai dai ina ta kasa, shi kuwa shiru ya zuba mata ido har sai da ta gaji da kanta ta natsu tsit a jikinsa. Sai da ya ga ta natsu tana ruwan hawaye ne ya zame hannunsa daga bakinta, a sanyayye sosai ya ce. "Please Omaish, stop doing all this, kada ki bani wahala kisa in gagara controlling kaina a kanki". Ya kai karshen maganar tare da zame hannunsa daga bakinta gabaɗaya. Cikin kuka ta ce. "Ni ba zan zauna da kai a ɗakin nan ba, ALLAH komawa ɗakinsu Mahreen zan yi, tin da ni na sadaukar da farincikina don in faranta maka, na yarda zan zauna da kai a cikin ɗaki matsayin ma'auratan boge, amma shi ne kake ɓata mun rai, ka sanyani kuka ka kunsa mun bakinciki bayan ni farinciki kullum nike sakaka". Tin da ta fara magana ya yi shiru yana kallonta har ta kai karshe, sannan ne in a cool way sosai ya ce. "Menene na yi wanda bai yi maki ba zan gyara? But kada ki ce zaki rusa abin da muka shirya, kinga ina kokari cika dik promise dana ɗauka maki, kin ce kada na taɓaki and na yi hakan, komai kika ce am trying my best to force myself in yi hakan because of your happiness, ban san me kike so ba kuma". Yanzu ta gama fahimtar bafa zai ce mutum ya yi hakuri ba, sai dai ya ce zai daina yin abu, lallai ma shiɗin nan. Tana shessheƙa ta ce. "Ai na ce ka faɗa mun sirrin dake zuciyarka kaki faɗa mun, dan haka ina fushi da kai". Ɗan kura mata idanu ya yi, slowly ya matso da face ɗinsa dab da nata tamkar zai yi mata wani abin, can kasan makoshi ya ce. "Me kike son sani to?". Tana turo baki ta ce. "Ai kasan abin da nike son ji"......... Slowly ya sake kai ɗan bakinsa har kamar zai sumbace nata, suna iya jiyo numfashin juna suna kuma shaka. "Omaish kin san sirrin dake raina fa, but why kike wahalar da kanki?". Ganin lips ɗinsa zasu iya taɓa nata ne yasa ta yi gaggawar janye kanta baya kaɗan. "To na ji shikenan saukeni". "Kin huce? Baki fushi dani kuma?". A natse ya tambaya. A fili ta gyaɗa mashi kai, amma a cikin zuciyarta ita kaɗai tasan abin da ta shirya mashi, dan ta ce ba zata kyalesa ba. Sauketa kasa ya yi tare da ɗan janyota jikinsa, sai da ya goge mata hawaye tsab sannan ya saketa. Hannunta ya riko zuwa saman sofarta, ya saketa a wajen ya nufi saman bed ɗinsa, zai zauna kenan suka ji hayaniya mai karfi daga main parlo yana tashi, kallon juna suka yi kafin ta ce. "Hayaniyar me haka kuma?". Alama ya yi mata da hannu a kan bai sani ba ba tare da ya yi magana ba. "Mu je mu gani". Ta faɗa tana ɗan zare idanu. Kai ya girgiza mata alamar ba zai je ba, ya haye gado zai kwanta kenan ta ce mashi. "Big Bro voice ɗin Ronnie nike ji, tamkar da shi ake hayaniyar fa". Ai fasa kwanciya ya yi, bai ma san time da ya miƙe ya nufo waje ba. Da sauri ta rufa mashi baya, kai tsaye suka nufi in da suke jiyo hayaniyar. Ai suna karisawa main parlor bata san lokacin da ta wuce Big Bro da gudu ta faɗo tsakiyar parlon ba, daidai lokacin Smart ma ya fito, family dik suna wajen banda Mommah dake barci, King da bashi da lafiya, sai mummyn Chuchu dake barci ita ma, amma dik harda aunty MieMie tana wajen, ga Uncle Taheer baje a kasa baya numfashi, tamkar rai ya yi halinsa, gefe guda kuma Ronnie ne yake tsaye a kan kafafunsa yana wani irin huci, ya yage rigar jikinsa dikka, forehead ɗinsa sai dubar da jini yake yi, ga Bilal a tsaye suna fuskantar juna shima gaban goshinsa na zubar da jini, da alama kokawa suka yi. Guyson na tsaye kusa da su Sareena suna kallonsu, hankalin guyson dik ya yi mummunar tashi, faɗa ake yi da uncle Taheer Bilal ya shiga, guyson da Ronnie sun fito ne daga room ɗinsu za su je side na uncle Abban sai suka haɗu da uncle Taheer ya fito daga side na mama. Ronnie da uncle Taheer suma ci karo, to kun san ɗabiar mutanen Black World ne basa cewa mutum sorry, sai Ronni bai ce mashi sorry ba zai wuce, to kun san mutanen kingdom of power, sarauta da son girma da nuna isa a jininsu take, dan haka uncle Taheer bai yi wata-wata ba ya ɗauke fuskar Ronnie da marin da tin da ya zo duniya ba'a taɓa yi mashi ba. Aikuwa kun san Ronnie renon Big Bro kuma ɗan wrestling, zakarar Black World ba zai yafe ba, cikin fushi ya juyo ya ɗauke Uncle Taheer da gigitaccen marin da sai da ya sanya shi yin tangal-tangal zai faɗi, take kunnuwansa suka ɗauke ji na wucin gadin. Sai da ya ɗauki minti ɗaya kafin ya dawo daidai, shi ne har su Ronnie sun juya zasu tafi ya cakumo wuyar rigar Ronnie ɗin, daga nan suka kafa kokawa, daidai lokacin da Bilal ya iso wajen a time ɗin Ronnie ya yi wa Uncle Taheer one blow seven die da ya sanya shi suma. Kun san modarawa da haɗin kai, ka taɓa ɗaya ashirin zasu tarun maka, to shi ne Bilal ya shiganwa Uncle Taheer shi da bai san waye Ronnie ba. Dik da Bilal yake horarre kuma dakken jami'i karfinsu ya zo kusan ɗaya da Ronnie, amma Ronnie ma ya ɗan ɗarasa, hakan yasa suka gwabza faɗa suka jiwa juna ciwo, Bilal da ya ga Ronnie zai iya kashesa sai ya ɗauki wani kwalbar decoration ya bugawa Ronnie a gaban goshi, shi ne ta fashe take jini haka. Sai magiya guyson yake yi masu a kan su daina sun ki kula shi, da ya ga an fasawa Ronnie goshi ne ya zunduma ihu mai sautin da ya ja hankalin kowa, to tin da family suka zo su Dr Raj sun yi kokarin raba faɗar abin ya ci tura, dan Ronnie ba wasa ba, renon Big Bro ya gwada masu banbancin kwanji. ABIN DA YA FARU KENAN. Ai Sweetie tana ganin jini a jikin Ronnie ta nufesa da gudu tana ambatar sunansa. Daidai lokacin Bilal ya zo da gudu ya rarumi Ronnie sama zai buga shi da kasa, irin ɗaukar unexpected ɗin nan ya yi mashi. Gabaɗaya mutanen dake wajen babu wanda zai iya ce maka ya ga giftawar Big Bro a tsakaninsu sai suka gansa ya tari Ronnie da Bilal ya yi jifa da shi, yau ransa ya yi mummunar ɓaci, sabida ko shi bai taɓa kwanta hakan a kan Ronnie ba, yadda yake kaunar kanin nan nasa, wlh basu isa sun zubar mashi da jini a banza ba. Cikin fushi ya sauke Ronnie kasa, Bilal na tsaye bai san ya aka yi ba sai jinsa ya yi ya yi sama, kafin ya farga Big Bro ya bugasa da kasa har sai da kafarsa ta bada wata iriyar sauti alamar karaya. Da karfi Smart ya ce. "Subhanallahi komai kuma ya lalace". Ya kai karshen maganar tare da afkawa tsakiyar parlon da gudu dan in ya barsu ya karawa Bilal duka ɗaya sai mutuwa, yanzu ma haka Bilal kam ya fita a hayyacinsa. Gabaɗaya parlon salati suka saka, Pretty ta matsa ta rungume Mahnoor tana zazzare ido, sabida ita tasan kokawarsu bata kyau ne, ga ɗan banzan tsoro. Ita kuma Sweetie kan Ronnie ta yi da gudu tana ambatar sunansa. Big Bro yana shirin sanya kafa ya take wuyan Bilal a kasa Smart ya yi zafan rikosa ta baya yana faɗin. "Please Big Bro, for give him, nasan dik yadda aka yi su suka tsokani Safras, dan bashi da neman faɗa, amma please ka yafe masu". A cikin fushi ya hankaɗe Smart da karfi, sabida bai ga dalilin da zai sanya ya yafewa wanda zai dubar da jinin Ronnie yana a raye ba. Hannu yasa ya cicciɓo Bilal sama ya kara yin jifa da shi da karfi wanda hakan yasa Bilal numfashinsa ta ɗauke cak. Tsoro ne ya kama gabaɗaya mutanen parlon, Sharifa mai cewa tana son Big Bro ne jikinta ya hau kerma. Heleena kuwa ruɗewa ta yi, ta kalli Smart ta kalli Big Bro, ta ga kamannin har ya ɓaci. Da gudu Ramish ya fito daga room ɗin king, ganin abin dake faruwa ba karamin ɗaga mashi hankali ya yi ba, da sauri ya kariso cikin parlon dan sanin me yake faruwa?. Dr Raj dai baya ya ja yana salati yau za'ayi kisan kai a cikin family, Smart da baya gajiya da ƙoƙarin dannan ɗan uwan nasa ne ya sake nufar Big Bro da gudu yana ƙoƙarin rikesa, a karo na biyu ma sake hankaɗe Smart da karfi ya yi. Hakan yasa Smart ya miƙewa tsaye ya kalli Sweetie dake rungume da Ronnie tana bashi hakuri ya ce. "Sister dakatar mana da heartbeat ɗin nan naki kada ya yi kisan kai, karya kashe kaninsa da kansa". Shi fa Smart yanzu ya gano idan ba Sweetie ba babu wacce zata yi yin gaggawar tausar zuciyar Big Bro cikin ƙanƙanin lokacin, shiyasa ya ce bari ya daina wahalar da kansa yana shan azaba. Sai a lokacin daga ita har Ronnie ɗin dikka suka kai kallonsu a kan Big Bro, ganin yadda yake huci suka fahimci ransa ya ɓaci. Smart yana faɗin hakan gabaɗaya kallon family ya dawo kan Sweetie, har suka sanya ta ji kunya. Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki ta saki Ronnie ta nufi in da Big Bro yake, yana tinkarar Bilal dake kwance baya motsi ne tamkar wani zaki. Daidai zai sanya hannu ya shako wuyar Bilal ya ɗagasa sama ta yi gaggawar shiga tsakaninsu, tamkar zata yi kuka, ta ɗan tsuke fuska wajen cewa. "Please Big Bro, ka barsa haka, kaga baya motsi ko?". Hannu yasa zai tureta gefe guda ta yi gaggawar faɗawa jikinsa, dan in ba haka ta yi mashi ba ita ma jifa da ita zai yi. (Big Bro ɗan ikka mai rai ne asuway, yana yin abin da kwata-kwata isn't kamatable, to ni dai bari in haɗa kayana, zuwa gobe zamu ga zai iya tsalleke wannan runguma ya yi jifa da ita ne, ko kuma dai family zasu sha mamaki?🤔 Sweetie ta san ya kan tsiya, ta ce kada ya taɓata, amma yanzu da yake cutarsa zata yi har da rungumesa bawan ALLAH, ba komai zamu rama ne!.) Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ------------------------------------------🔥♥️ SABUWAR DUNIYA STEP ONE!.🔥🔥🔥 Anwar ne ya ce. "Dik ba wannan ba, yanaga kamar Lion namu yana cikin ɓacin rai ne?"........... Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Babu komai". Dafa shoulder ɗinsa Ansar ya yi. "Baka taɓa ɓoye mana komai naka ba, meyasa yanzu zaka fara ɓoye mana? Ka manta tare muke kuka kuma mu rarrashi juna?". Kai ya girgiza kafin ya ce. "Tare muke komai, amma ku yarda dani ba wani abin ke damuna ba, kawai na ji babu daɗi ne da nazama sanadiyar zuban hawayen Zunaira yau". Murmushi Ansar ya yi tare da cewa. "Awwww batu ake na ma'aurata, to shikenan a wannan gaɓa bamu nemi jin me yake damunka ba, je ka yi rarrashi, idan anki kulaka kuma sai ka dawo mu kwana a nan, mu ba zamu hanaka wajen kwana ba kuma ba zamu kiraka tuzuru ba". Cikin zolaya ya yi maganar. Anwar ne ya capki zancen da cewa. "Gaskiya ina fatan watarana nima in ga wannan rana, ace na yi faɗa da matata ina rarrashi tana ja mun rai da yanga, ina son yin aure our Lion". Ya faɗa fuskarsa da alamar damuwa..... Dafa shoulder ɗinsa Hoorain ya yi alamar karfafawa kafin ya ce. "Fito da mata zan yi maka aure ɗan uwana, for sure rayuwar aure akwai daɗi sosai musamman ka samu wanda kake so yake kuma sonka". Damuwa ce sosai ta kara bayyana kan fuskar Anwar, murya a rauna ce ya ce. "Ai ni kam bana jin zan samu wanda raina yake so ɗin nan, na sota ne tin tana karama amma ni kaina nasan na yi gangancin fara sonta saboda ba samu zan yi ba, amma ba laifina bane, laifin zuciyata ce da bata iya tantance abin da zata iya samu da wanda ya fi karfinta ba kawai ta fara so". Kallon juna Ansar da Hoorain suka yi kafin su matsa kusa da Anwar sosai dan tausan shi, har suna haɗe baki wajen cewa. "Wa kake so ɗan uwa". "Babu amfanin in faɗa maku ita, kawai ku bar zancen ALLAH ya bani mafi alkhairi a gareni". Girgiza kai Hoorain ya yi. "A'a please ka faɗa mana, zamu tayaka yakin nemanta har mu samu"....... "Ɗaya ne daga cikin ƴaƴan king Zuhair sister ɗin Zunaira". Ya faɗa a raunace sosai. Kallon juna a karo na biyu Ansar da Hoorain suka yi kafin Hoorain cikin tausasawa ya ce. "Wacece daga ciki?". Nisawa ya yi kafin ya ce. "Ban san sunanta ba, dan ita bata bada fuskar ko magana wani ya yi mata bare har yakama sunanta a cikin fili kowa ya ji, bata kula mutane, bama ta cika fitowa ba sai in ya zama wajibi". Fuskarsa ta kara tsananta nuna damuwa. "Kwatantamun yadda take zan gane wacece". Cewar Hoorain, dan shi dikkansu sanadiyyar Auta ya sansu....... Kwatance Anwar ya fara yi masu, tin da ya fara magana Hoorain ya gane wacece daga ciki, dan haka sai ya ce. "Da izinin ALLAH zaka mallaketa, amma dai yanzu ku tayani faɗa wajen ganin na dakatar da wannan gaba dake a tsakanin iyayen namu sai mu san abin yi". WA KUKE TINANIN ANWAR YAKE SO?. HOORAIN MAI KOKARIN DAKATAR DA GABAN NAN YA ZAI JI IDAN YA JI CEWA MAHAIFINSA NE BAI DA GASKIYA KUMA DA TSAFI YAKE AMFANI DOMIN KARA KARFAFA MULKINSA YA IYA YAKAR KOWACCE MASARAUTA, SANNAN YA SANYA SHAKKA DA TSORONSA A ZUƘATAN MUTANE? YA HOORAIN ZAI JI WAI? GARA SU BOBO ALREADY SUN SAN KOMAI TIN DA A KAN YA BADA JININ WANDA YAKE SO NE MA YA KI KARƁAR MULKIN YA GUDU YA BAR KINGDOM ƊIN MA, KUN GA KENAN ALREADY SHI YA SAN DA BLOOD CROWN NA AMFANI DA TSAFI, SU HOORAIN DA SU ZASH AND LEESHARH NE ZASU JI BABU DAƊI, SU DAI SU SMART ALLAH YA CECESU MAHAIFINSU MUTUMIN KWARAI NE TIN DA HAR YA YI ƘOƘARIN YAKAR WANNAN BLOOD POWER YA KUMA KI YARDA DA TAYIN DA AKA YI MASHI!. --------------------------🔥 Cike da murna suka amsa da. "In Sha ALLAH zasu daina wannan gaba very soon"........ "ALLAH yasa". Ya faɗa tare da miƙewa. "Zunaira na buƙatata, yanzu ma dai na ce bari in ga ya kuka kwana ne, sai da rana zan dawo". Ya faɗa yana kallonsu....... Fatan alkhairi suka hau yi mashi tare da fatan ALLAH yasa kada Zunaira ta sauko, ta bashi wahala sannan ta sauko, cikin zolaya suka yi maganar. Waje ya nufa yana faɗin. "Ai ita ba irinku bace, kyakkyawan zuciya take da shi, kuma tana tausayin mijinta sosai". Bai jira amsarsu ba ya wuce waje. Yana fita kai tsaye ya nufi part ɗin su Rishan dan su gaisa. Sai dai yana zuwa Rishan ya miƙo mashi waya wai ga shi ana nemansa. Ganin number Mommah ce yasa ya karɓi wayar da sauri tare da nufo waje. Yana fita ya nufi side ɗinsu yana kara wayar a kunne. Cikin girmamawa ya ce. "Momma ina kwana?". Daga ɗayan side ɗin ta amsa da. "Lafiya lou ɗana, ya gida da ƴan uwan naka?". Kara natsuwa sosai ya yi kafin ya amsa mata da. "Lafiya lou fatan kowa yana cikin koshin lafiya?". Ya yi maganar daidai time da yake shigowa bedroom ɗinsu. Da alhamdullilah mommah ta amsa mashi kafin ta ce. "Dama so nike ka kawo mun Zunaira cikin satin nan in ba damuwa, yayanta ke son ganinta". Dik da bai san a kan wani yayanta ake magana ba, sabida girmamawa da ladabi game da matsayin da momma keda shi a ransa sabida kyawawan halayenta yasa kawai ya amsa da. "Zan kawota In Sha ALLAH".......... Sosai mommah ta ji mugun daɗin irin yadda Hoorain yake mugun girmamata, baya ja da maganarta, idan ta yi magana ma baya neman karin bayani kawai yake amsawa da to cikim girmamawa, hakan ba karamin daɗi yake yi mata ba. Addu'a ta shiga kwaranyo masu tana zuba masu albarka, sai amsawa yake yi da amin amin yana bin Auta da kallo. Ta fito ta shirya cikin wasu haɗaɗɗun kaya, yau dressing na masarautar ta yi, wato shigar mutanen Korea, kuma ya yi mugun yi mata kyau, ta fito tamkar ka saceta ka gudu, sai dai kuma dik hawaye ya wanke mata fuska, idanunta sun yi jajir da su tamkar jini, alamar ba'a sauko ba kenan. Ai mommah na katse kiran nan ya yi zafan hayewa saman bed ɗin ya sameta. Tana ganin ya hauro ta yunkura zata sauka kasa, a hanzarce ya kwanto da kansata a saman laps ɗinta, idanunsa a kan face ɗinta. Ƙoƙarin tirgewa ta fara yi tana nuna bata son ya taɓata. Hannunta ya riko cikin nasa, murya a sanyaya sosai ya ce. "Haba my Hoonairata, ashe dama zaki iya yin fushi da heronki?". A tausashe ya yi maganar. Kai ta jinjina mashi alamar e, a kule ta ce. "In dai zaka rinƙa yi wa mata magana, to zan iya yin fiye da hakan ma. Hanunta ya kara matsewa cikin nasa, a natse ya ɗan sumbaci hannun kafin ya ce. "Shi kam Hoorain me zai yi da mata bayan yana da Hoonaira? Wlh ke kaɗai kin isheni, kuma kin fi kowa sanin ni bana magana da mata, ita ɗinma kuskure aka samu, amma na yi alkawarin ba zan sake ba". Harara ta dalla mashi kafin ta ɗan kwace hannunta. "Ba zan yi hakuri ba, dole sai ka karɓi hukunci". Yana kallon cikin idanunta ya ce. "Idan baki yi hakan ba ma ai sai in ce anya jinin modarawa ne yake yawo a jikinki kuwa? Saboda su ba'a taɓa taɓasu sun yafe ba, komai kankantar laifi sai ka biyashi, shiyasa har Manzon ALLAH (SAW) ya bar duniya babu waɗan da yake yi wa yawan faɗa a kan su rage zafin zuciya irin modarawa........". Hannu tasa ta buge ɗan bakinsa ba tare da ta bari ya idasa maganar ba, tana dalla mashi zazzafar harara ta ce. "Watau dama zagin modarawa kake yi ko?".......... "Yau dai dole dole sai an nemo laifi an ɗaura mun? To shikenan dai, amma dai kin san ke kanki sai dai in baki labarin su waye modarawa ko? A cikinsu kusan aka haifeni, aka raineni, jaruntarsu tasa na zama jarumai, ai rashin hakurinsu jarunta ce da zafin zuciya, idan mutum yana da tsoro in aka yi mashi ai tsoron yin magana zai yi ma bare har ya rama, amma su fa? Jininsu a tafashe yake, ni yabonsu na yi ba zagi ba, Hoonaira ki bari mana". Ya kai karshen maganar yana kifa kansa a saman laps ɗin nata. "Tin da ba zaki hakura ba nasan ko na yi kuka ba rarrashina zaki yi ba, bari in je Abbona ko ɗan uwana Kamran or Uncle Rishan ko dai su Ansar su rarrasheni". Ya faɗa yana tura hannunsa bayanta ya rikota da kyau. "Ba zan rarrasheka ba, kuma babu in da zaka je, a nan zaka yi kukan ka gama". "Da gaske?". Ya tambaya yana haurar da hannunsa sama izuwa tsakiyan bayanta.......... "Da gaske nike yi, ka tashi ka yi frog jump shi ne hukuncinka na kula wata". Kasa sosai ya yi da murya wajen cewa. "A kanki amma zan yi frog jump ɗin ko?". Bata ji me ya ce sosai ba sai kawai ta gyaɗa mashi kai alamar e. Aikuwa miƙewa ya yi tare da jawota gabaɗaya jikinsa. Ya rungumeta tare da fara kwance dik wasu maɗauri da doguwar rigar jikinta yake da shi. "My hero nifa frog jump na ce ka yi". Kamar zata yi kuka cikin shagwaɓa ta faɗa. A kunne ya raɗa mata. "Ai abin da zan yi yanzu kenan". Zata dake yin magana ya yi gaggawar haɗe bakinsu yana warware maɗaurin dake wajen shafaffen cikinta. Ai wani irin salon kiss da ya fara bata wanda bata san lokacin da ta rungumesa ta hau mayar mashi da martani ba, saboda yau ya yi abin da bai taɓa yi ba, kun san kiss na rarrashi daban yake, salonsa ma daban ne. Bata ankara ba sai ji ta yi ya zame rigar jikinta, a hankali ya sanya hannunsa ya riko waist ɗinta tare da ɗagota ya dawo da ita saman massive chest ɗinsa, ai tuni ta manta da fushi take yi suka shiga nunawa juba zallar kauna. Tsabar farinciki yau har ya so mantawa da ya ce sai ta girma ya wuce gona da iri, wani irin ihun da ta zunduma mashi ne yasa ya dawo cikin hayyacinsa, da sauri ya miƙe daga kanta yaka dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi. A gefenta ya kwanta tare da sanya mata yatsan hannunsa ɗaya a bakinta yana yi mata alamar rarrashi, dan ba zai iya yin magana ba a halin da ake ciki. Ganin hakan yasa ya yi mugun bata tausayi, sai ta matsa ta kwanto da kanta a saman faffaɗar bayansa tana ƙoƙarin shanye kukan da take yi. Shiru suka yi sai sautin kukanta dake tashi kaɗan-kaɗan, almost 30 mins a haka kafin sanyayyar muryarsa ya daki dodan kunnenta. "Am so so sorry my Hoonaira, ba zan sake ba". Ya faɗa tare da juyowa ya rungumeta ta gaba. Idanunta sun ƙanƙance sun yi ja alamar barci ta dage ta manna mashi sumbata a kumatu kafin ta ce. "I love you my hero". Har cikin ransa ya ji daɗi, a hankali ya kara matseta a jikinsa har sai da ta yi barci. Sannan ne ya lallaɓa ya kwantar da ita, ya ja mata bargo ya nufi toilet. A gurguje ya watsa ruwa ya fito, shiryawa ya yi da sauri-sauri ya sauko ya nufi wajen Kamran. Bakinsa a ɗauke da sallama ya shigo cikin ɗakin. Kamran da Abbo suna zaune a saman bed da Kamran yake jinya, ya warware sosai sauki nata samuwa, hukuncin King Zuhair da ukubarsa bata da daɗi ne, wani irin bahagon mutum ne da in a hukunta sojan yaki to fa za'a jima ana jinyarsa bai koma normal ba, wani mai karamar ƙwaƙwalwa da karamar zuciya ma a wajen yake mutuwa ko ya samu taɓin hankali. Ai Hoorain da Kamran sun yi namijin kokari da iya kwanciyar gadan asibiti kawai suka yi bayan fitowarsu daga horon King Zuhair. Kamran na ganinsa ya tsaresa da kallo, yana jin kaunarsa har cikin ransa, amma yaki yarda ya nuna, saboda balain zuciya, wai har yanzu yana fushi da su, dik da Abbo ya faɗa mashi matsayin Hoorain a wajensa, ya kuma faɗa mashi yadda tarihi ta wakana har ya bar kingdom ɗin, sannan ya nuna mashi wanene mahaifinsa (Udey) amma zuciyar ɗan mammarsa taki sauka, shi dai lallai sun yi mashi laifi, fushi yake yi da su, kun san dama in ya yi fushi sai Mamma ta yi rarrashi sosai, to su Abbo basu iya yadda ake rarrashin damisan mamma ba, sun tsaya sai hakuri suke bashi. A kusa da shi Hoorain ya zauna yana tambayarsa ya jiki. Banza ya yi da su tamkar bai ji ba, ya cigaba da tinaninsa na yadda zai yi ya kwato Pretty, dan shi wlh ba zai barta da wani be, dole ya ɗauko matarsa, ai shi aka baiwa ita. NI KUMA NA CE RASHIN SANI YA FI DARE DUHU!. Hannayensa Hoorain ya riko cikin nasa, a sanyayye ya ce. "Wai har yanzu fushi kake yi damu?". Wani irin kallo mai kama da harara ya dalla mashi kafin ya ɗan yunkura zai kwace hannunsa, tin da ya samu lafiya bai yi masu magana ba, bayan sunan Pretty bai iya kiran komai ba, Hoorain ya fahimci bashi da natsuwa a yanzu kuma shi irin mutanen nan ne wanda zuciyarsu a kusa take, shi ne yasa yaki faɗa mashi cewa ai Pretty sister ɗinsu ce, yasan a wannan hali idan ya faɗa mashi to fa tsab zasu iya rasa shi ne, dan ba karamin so yake yi mata ba, gara su barshi ya samu lafiya sosai ta yadda ko ya ji gaskiya sai dai ya sake kwanciya jinya kawai. Sosai Hoorain ya yi kokarin tausan shi, amma zuciyar ɗan mamma yaki sauka, da suka matsa mashi ma sai ya yunkura zai bar masu ɗakin. Riko hannunsa da sauri Hoorain ya yi kafin ya ce. "Ka yi hakuri kanina, a baya ban san alaƙata da kai bane yasa na dakeka kuma na hanaka ɗaukar abin da kake so, amma yanzu nasan wanene kai, na yi alkawarin tayaka yaki a kan abin da kake so, please ka yi mana magana ka ji?". Ya faɗa mashi hakan ne domi ya sanya ya yarda da su har ya sauko ya samu ya kaisu wajen Mamma, kun san shi Hoorain bai san cewa matar da ya taimaka a forest time da ya je ɗaukar su Auta ita ce mammarsu ba, dik yanzu Kamran suke jira. Da jin kalaman ɗan uwan nasa na zai tayashi faɗa su kwato Pretty yasa ya yi saurin juyowa, a sanyayye sosai da muryarsa irin na Mamma ya ce. "Da gaske zaku tayani kwato Pretty?". Kai Hoorain ya gyaɗa mashi tare da cewa. "Sosaima, zamu tayaka"......... Ɗan ɗaure fuska Kamran ya yi yana bin Hoorain da kallo kafin ya ce. "Amma kuwa in dai haka ne kai kam kai ka gaji Mamma a zafi, sannan in dai haka bil adama suke rayuwa ni ban yi farincikin kasancewata a cikin mutane ba, a tinanina zan ga mutane masu sauki da tausasawa game da kaunar juna shiyasa na matsu in fito daga forest ɗin nan, amma dik in da na je azzalumai kawai nike samu, tin shigowata duniyar mutane na fara yarda da zancen Mamma da take cewa mutane ba abin yarda bane, kuma ko mutun zai mutu kada ka taimaka mashi, dan in ka jawosa inuwa shi kuma rana zai turaka, tabbas Mamma tana da gaskiya a nan, jiya ka taimaki wancan da ya kwace mun Pretty sabida a lokacin baka san waye ni ba kafi kusanci da shi, baka damu ko na mutu ko na yi rai ba, baka damu da sanin wacece ita a gareni ba ka mun mugun duka a kan wancan, yau kuma da ka san waye ni zaka taimaka mun mu kwatota, zaka kwayewa wancan baya, kenan ku mutane ida ba naku ba baku taimakawa wasu? Ƴan uwanku sune kawai mutane masu daraja? Bayan su dik wanda zai shiga kunci babu ruwanku?". Tin da ya fara magana suka tsaresa da kallo har ya kai karshe, zallar kamannin magana da King Omranish da Commander ya sani yake gani a tattare da Kamran, sai a yanzu ya fara tinanin wasu abubuwa da ya sani dangane da King Omranish wanda yanzu sam babu su a tattare da Udey, tabbas King Omranish idan yana magana a bubbuɗe yake yinta babu tsoro ko shakka, magana kai tsaye babu shakkar abin da zata haifar, lallai maganar Kamran sak take da yadda babansa yake magana, ba ruwansa da wai Hoorain yayansa ne, ya kalli cikin idonsa ya faɗi sun iya zalunci, shi ba haka ya taso ya sani ba, kun san in baka taɓa rayuwa a cikin mutane ba ka shigo rayuwarsu daga baya sai ka rinƙa shan mamaki tamkar ka mutu, wani ma idan ya yi maka wani abin sai ka zaci dik mutanen duniya bakaken azzalumai ne. Su dai shiru suka bisa da shi, dan sun yi mashi uzuri bai saba zama da mutane bane, Abbo ne ma ya yi karfin halin cewa. "Haka ne zancenka, yanzu dai zoka zauna kada ka je ko'ina"........ Kun san shi babu ruwansa da sai mutum ya girma ne yake yin furfura ko kuma fifikon shekaru da sauransu, dan haka bai ɗauki Abbo a wata tsiya ba, yadda yake kallon su Pretty haka yake ɗaukar su Abbo, wato kowa ma a daidai shekarunsa yake gwadasa, ko da yake ba zaku yi mamaki ba tin da shi da ya ga su Sweeetie suna jaririrai ya rinƙa mamaki dan bai taɓa ganin kananan yara ba, shi da a tinaninsa kowa da girmansa ya zo duniya, bai san ma da uba ake haihuwa ba, kunga kuwa ai bakwa ji mamaki ba dan ya yi wa Abbo kallon girmansu da shekarunsu ɗaya. Dan haka yanai wa Abbo magana gatsau haka babu respect wanda hakan ya yi mugun hasala zuciyar Hoorain ya fusata zai ɗaukesa da mari kenan Abbo ya yi gaggawar rikesa yana faɗin. "Ka yi la'akari da yanayinsa, a nan ne zaka fahimci ba dan rani ya yi maganar ba face haka ya saba yin ta, dik yadda aka yi su biyu shi da gimbiya suka yi rayuwa, daga yanayinsa zaka san bai saba rayuwa da mutane ba, ka bisa a hankali zai saba kuma ka fahimcesa". Abbo ya yi maganar ne da larabcin Kingdom of Power, while shi kuma Kamran da yaren koreans yake yi masu magana tin da ya buɗi baki, kun tuna a farkon book ɗin nan na faɗa maku Mamma tana da yaren da suke yin magana da shi ita da Kamran ko? To wannan shi ne yaren watau Koreans language. (Ku fa akwai abubuwa da dama da zan tuna maku a book one, ciki har da mahaifin su Bobo watau sarkin yammaci, kun tuna a book 1 na yi magana a kansa lokacin da Auta ta je tambayar King zata je Dubai wajen Yah Omar sai sallama ya zo ya ce da King ga sarkin Yammaci ya zo? Ai a lokacin na ɓoye maku me King da sarkin yammaci suka tattauna ko? Na tsallake wajen, to dik batuce kan Blood Power da King ya rufe, zamu zo wajen zaku ji, wayyo ni, wasu abubuwan daga book 1 nike ajiye maku shi a dunkule baku ganewa har sai kusan karshen book. Uhm kun rike batu kan kauyensu Mahreen ko shi ma kun manta?🤔 Akwai case a can ma, akwai abin da nace ku rike zamu dawo labari a kansa, in kun manta ku tuno!!) Tausarsa Abbo ya yi har sai da ya hakura ya dawo ya zauna........ Cike da zaƙuwar son sanin in da mahaifiyarsu take Hoorain ya hau tambayarsa in Mamma take?......... "Tana forest tana jiran in samo babana in zo in ɗauketa". Ya basu amsa a taƙaice kuma a dake babu wani respect ko risinar da kai!. "Zaka iya yi mana jagoranci zuwa wajen?". Hoorain ya sake tambaya. "Me zai hana tin da nima ina son ta bar forest ɗin"........ Haba wani irin daɗi ne ya kama Hoorain, har bai san lokacin da ya rungume Kamran a jikinsa ba, Mammarsu zata dawo. UHM SUNA NASU HAUKAR, AI KO ZASU MUTU MAMMA BA ZATA DAWO KINGDOM ƊIN NAN BA A YADDA SUKE ZATA BA, DAN A TINANINTA MAHAIFIN HOORAIN NE YA ZALUNCETA, KUN GA BA ZATA SAKE YARDA DA SHI BA, AKWAI DAI CASE. Cike da zumuɗi Hoorain ya ce. "Zamu iya tafiya wajenta yanzu?"......... Commander ne ya tari numfashinsa da cewa. "Haba Hoorain, yi hakuri mana zuwa ya kara samun sauki, yanzu ai ba zai iya dogon tafiya ba". Ɗan rungumo Abbon Hoorain ya yi tare da ɓoye kansa jikin Abbon wai ya ji kunya. Muryar Kamran ce ta katsesu da cewa. "Ba fa irin forest da kuka sani bane, wajen yana da nisa da wancan masarauta da suka kwace Pretty, sannan kuma ragwaye basa iya zuwa wajen, mutuwa zaku yi da namun dawa, ko da yake kai naga kana da jarunta tin da ka iya faɗa dani". Ya yi maganar yana pointing Hoorain da hannunsa. BALAIN LALLAI KAMRAN YA RAINA SU ABBO, WAI JARUMAI NE SUKE ZUWA FOREST, SHI FA YANA GANIN BABU WANDA YA KAISA JARUMTA, SAI DAI KAI RENON LIONESS MAMMARSA. Babbar magana, zaro idanu Hoorain ya yi, dan kuwa yasan in kuwa haka ne wajen yana da mugun nisa, shi yanzu Kamran bai san a takamamman in da yake bane, amma wlh forest ɗin da nisa, in dai ta kingdom of power ne kuma to ai forest guda ɗaya ce a wajen wadda take a tsakanin masarautu biyun ta zame masu kamar border, kuma ita ce forest da ya tsinto Zunaira a ciki, idan zai iya tina komai daidai matar da ya taimaka har yake ganinta tamkar ya san fuskarta sabida kama ta jini da ta so yi da shi, to tabbas ita ce kenan? Ye jefi kansa da tambaya. A fili ya ce wlh ita ce, har sai da su Abbo suka ɗago suna kallonsa. Kamran ne ya ce. "Ita ce wa?". Hararar Hoorain ya wurga mashi. "Kai baka gajiya da faɗa da zafin zuciya ne?". Hoorain ya tambayi Kamran. Ɗaure fuska Kamran ya yi kafin ya ce. "A haka aka reneni na zama mafaɗaci". Ya faɗa a faɗace yana zarewa Hoorain idanu tamkar zai dakesa!. "To yakamata yanzu kasan ni yayanka ne, ka rinƙa tausasa harshe a kaina, ba zan juri komai daga gareka ba, ɗaga maka kafa kawai nike yi"........... Ɗan taɓe baki Kamran ya yi. "Me kuma yaya?". Ya tambaya on a serious note, dan har ga ALLAH shi bai sani ba. Ɗaure fuska tamau Hoorain ya yi alamar ransa ya ɓaci, dan yana ganin tamkar manna mashi hauka Kamran yake yi, bai san iya gaskiyarsa yake faɗe ba, zai yi magana Abbo ya rigasa da cewa. "Hoorain dole ka ajiye zafin zuciyarka gefe idan kana son ku shirya da ɗan uwanka, ka bisa a hankali saboda wlh iya gaskiya yake faɗa maka bai san komai ba"........ Shiru Hoorain ya yi yana ɗan jinjina kansa alamar haka ne. Shi kuma Kamran ya bisu da ido dan ba wani jin larabcin nan yake yi ba, suna ɓadda harshe suna magana su barshi a duhu, su kuma sun saba ne da magana da larabci shiyasa, take tinanin Rockey ɗinsa ta faɗo a ransa, ALLAH sarki ya yi wa Rockey wayau ya gudu ya barsa a forest, dan yana son ya je ya taimakawa Mammarsa kada a barta da kewa ita kaɗai. Haka suka cigaba da tattaunawa Hoorain na kokarin kai zuciyarsa nesa dan su sasanta da Kamran, Abbo na ta kara tausan zukatan zakunan dikka biyu dan a samu sasanci da fahimtar. --------------------------------🔥 CROWN OF POWER.🔥 Kuka sosai Sweetie take zubawa, dan takaicin hanata zuwa wajen su Mahnoor ɗin da ya yi, a dik mutanen da Sweetie take haɗuwa da su babu wacce ta so ta kaunata kamar Mahnoor, a tashin farko ta so Mahnoor matuƙa, saboda kyawawan halaye da saukin kanta, sannan tana jin daɗin yin hira da ita, amma kawai ya zo ya wani hanata fita, dole ta ji haushi. Slowly ya tsuggunna a gaban sofar da take, yana sanye da wandan Jeans irin rippet ɗin nan launin light ash, sai round neck polo shirt ita kuma fara tas, ya yi balain kyau sosai, ya fito a ainahin balarabensa, sai tashin fitinannen Kamshi yake yi. A hankali ya kai hannunsa ya yaye bargon da ta lulluɓa har kanta. Sai da ya ji kirjinsa ta buga ganin yadda take ruwan hawaye, dama ya zargi hakan shiyasa ya ce bari ya dubata. Ita kuwa wani irin mugun harara ta dalla mashi kafin a kufule ta ce. "Me ruwanka dani to?". Yadda ta yi maganar ba karamin narka zuciyar Big Bro ta yi ba, ya kurawa ɗan bakinta idanu, wasa-wasa ta fara koyan mahaifa yarinyar nan, har da su murguɗa baki. "Ni ka daina kallona kuma ka rufa mun bargona". Cikin faɗa da kuluwa da haushi ta yi maganar. Kun san halin mutumin, shiru ya yi bai yi magana ba har na tsawon mintuna 3, ranta ne ya kara ɓaci ta yunkura zata tashi kenan ya yi gaggawar rikota, in a cool way sosai ya ce. "Meyasa kike kuka?". Ai tsabar bakinciki da takaici bata san lokacin da ta ce mashi. "Ban sani ba, wai ina ruwanka da rayuwata ne?"....... "Akwai ruwana da rayuwarki sabida rayuwarki tawa ce". Ya faɗa a sanyayye sosai, wanda hakan ba karamun kara tunzura zuciyarta ya yi ba, sai ya rinƙa nuna kamar baya fahimtar abubuwa dan rainin wayau, yana nufin bai san meyasa take kuka bane da zai wani tambaya!. Zazzaro mashi idaunta da suka yi jajir ta yi, tamkar zata cinyesa da masifa ta ce. "Rayuwata ba zai taɓa zama naka ba, ni yanzu ma na fasa bana buƙatarka matsayin yaya, Ronnie kawai ya isheni, a gida ina da Kamran, bayan shi kila ina da wasu, bana bukatarka kuma!". Ta kai karshen maganar tana ƙoƙarin kwace rikon da ya yi mata, sai dai ta gagara, domin kuwa karfi ba ɗaya ba. Tin da ta yi wannan magana ya fahimci ranta ya kai kolokuwa wajen ɓaci, bata da raina manya, tana kuma tauna magana kafin ta faɗa, ya yi mata uzurin cewa bata cikin hayyacinta ne. Cikin sanyin murya ya ce. "Dik yadda kika ɗauki abin bai kai haka ba, amma ban san me zan ce maki ba, please stop talking about Kamran or some mens here in a front of me, dan bana son kara maki ɓacin rai kan wanda kike ciki, am trying to control my self, be patient please". Tin da ya fara magana ta natsu take sauraronsa, watau sorry ne ba zai taɓa ce mata ba bayan shi da kansa yasan ya yi mata ba daidai ba. A ranta ta kuduri niyyar sai ta santa wannan ɗan bakin nasa ya furta sorry a gareta, dan haka sai ta shammacesa sai da ta bari ya saki jiki ta kwace rikon da ya yi mata, da gudun gaske ta miƙe zata nufi waje. Aikuwa yana miƙewa taku ɗaya ya yi ya capko waist ɗinta, bata ankara na sai jinta ta yi a saman lion chest ɗinsa, wage baki ta yi zata zunduma mashi ihu ya yi zafin sanya hannunsa ya toshe mata baki da hannunsa ɗaya. Mutsu-mutsu ta fara yi tana son kwace kanta, sai dai ina ta kasa, shi kuwa shiru ya zuba mata ido har sai da ta gaji da kanta ta natsu tsit a jikinsa. Sai da ya ga ta natsu tana ruwan hawaye ne ya zame hannunsa daga bakinta, a sanyayye sosai ya ce. "Please Omaish, stop doing all this, kada ki bani wahala kisa in gagara controlling kaina a kanki". Ya kai karshen maganar tare da zame hannunsa daga bakinta gabaɗaya. Cikin kuka ta ce. "Ni ba zan zauna da kai a ɗakin nan ba, ALLAH komawa ɗakinsu Mahreen zan yi, tin da ni na sadaukar da farincikina don in faranta maka, na yarda zan zauna da kai a cikin ɗaki matsayin ma'auratan boge, amma shi ne kake ɓata mun rai, ka sanyani kuka ka kunsa mun bakinciki bayan ni farinciki kullum nike sakaka". Tin da ta fara magana ya yi shiru yana kallonta har ta kai karshe, sannan ne in a cool way sosai ya ce. "Menene na yi wanda bai yi maki ba zan gyara? But kada ki ce zaki rusa abin da muka shirya, kinga ina kokari cika dik promise dana ɗauka maki, kin ce kada na taɓaki and na yi hakan, komai kika ce am trying my best to force myself in yi hakan because of your happiness, ban san me kike so ba kuma". Yanzu ta gama fahimtar bafa zai ce mutum ya yi hakuri ba, sai dai ya ce zai daina yin abu, lallai ma shiɗin nan. Tana shessheƙa ta ce. "Ai na ce ka faɗa mun sirrin dake zuciyarka kaki faɗa mun, dan haka ina fushi da kai". Ɗan kura mata idanu ya yi, slowly ya matso da face ɗinsa dab da nata tamkar zai yi mata wani abin, can kasan makoshi ya ce. "Me kike son sani to?". Tana turo baki ta ce. "Ai kasan abin da nike son ji"......... Slowly ya sake kai ɗan bakinsa har kamar zai sumbace nata, suna iya jiyo numfashin juna suna kuma shaka. "Omaish kin san sirrin dake raina fa, but why kike wahalar da kanki?". Ganin lips ɗinsa zasu iya taɓa nata ne yasa ta yi gaggawar janye kanta baya kaɗan. "To na ji shikenan saukeni". "Kin huce? Baki fushi dani kuma?". A natse ya tambaya. A fili ta gyaɗa mashi kai, amma a cikin zuciyarta ita kaɗai tasan abin da ta shirya mashi, dan ta ce ba zata kyalesa ba. Sauketa kasa ya yi tare da ɗan janyota jikinsa, sai da ya goge mata hawaye tsab sannan ya saketa. Hannunta ya riko zuwa saman sofarta, ya saketa a wajen ya nufi saman bed ɗinsa, zai zauna kenan suka ji hayaniya mai karfi daga main parlo yana tashi, kallon juna suka yi kafin ta ce. "Hayaniyar me haka kuma?". Alama ya yi mata da hannu a kan bai sani ba ba tare da ya yi magana ba. "Mu je mu gani". Ta faɗa tana ɗan zare idanu. Kai ya girgiza mata alamar ba zai je ba, ya haye gado zai kwanta kenan ta ce mashi. "Big Bro voice ɗin Ronnie nike ji, tamkar da shi ake hayaniyar fa". Ai fasa kwanciya ya yi, bai ma san time da ya miƙe ya nufo waje ba. Da sauri ta rufa mashi baya, kai tsaye suka nufi in da suke jiyo hayaniyar. Ai suna karisawa main parlor bata san lokacin da ta wuce Big Bro da gudu ta faɗo tsakiyar parlon ba, daidai lokacin Smart ma ya fito, family dik suna wajen banda Mommah dake barci, King da bashi da lafiya, sai mummyn Chuchu dake barci ita ma, amma dik harda aunty MieMie tana wajen, ga Uncle Taheer baje a kasa baya numfashi, tamkar rai ya yi halinsa, gefe guda kuma Ronnie ne yake tsaye a kan kafafunsa yana wani irin huci, ya yage rigar jikinsa dikka, forehead ɗinsa sai dubar da jini yake yi, ga Bilal a tsaye suna fuskantar juna shima gaban goshinsa na zubar da jini, da alama kokawa suka yi. Guyson na tsaye kusa da su Sareena suna kallonsu, hankalin guyson dik ya yi mummunar tashi, faɗa ake yi da uncle Taheer Bilal ya shiga, guyson da Ronnie sun fito ne daga room ɗinsu za su je side na uncle Abban sai suka haɗu da uncle Taheer ya fito daga side na mama. Ronnie da uncle Taheer suma ci karo, to kun san ɗabiar mutanen Black World ne basa cewa mutum sorry, sai Ronni bai ce mashi sorry ba zai wuce, to kun san mutanen kingdom of power, sarauta da son girma da nuna isa a jininsu take, dan haka uncle Taheer bai yi wata-wata ba ya ɗauke fuskar Ronnie da marin da tin da ya zo duniya ba'a taɓa yi mashi ba. Aikuwa kun san Ronnie renon Big Bro kuma ɗan wrestling, zakarar Black World ba zai yafe ba, cikin fushi ya juyo ya ɗauke Uncle Taheer da gigitaccen marin da sai da ya sanya shi yin tangal-tangal zai faɗi, take kunnuwansa suka ɗauke ji na wucin gadin. Sai da ya ɗauki minti ɗaya kafin ya dawo daidai, shi ne har su Ronnie sun juya zasu tafi ya cakumo wuyar rigar Ronnie ɗin, daga nan suka kafa kokawa, daidai lokacin da Bilal ya iso wajen a time ɗin Ronnie ya yi wa Uncle Taheer one blow seven die da ya sanya shi suma. Kun san modarawa da haɗin kai, ka taɓa ɗaya ashirin zasu tarun maka, to shi ne Bilal ya shiganwa Uncle Taheer shi da bai san waye Ronnie ba. Dik da Bilal yake horarre kuma dakken jami'i karfinsu ya zo kusan ɗaya da Ronnie, amma Ronnie ma ya ɗan ɗarasa, hakan yasa suka gwabza faɗa suka jiwa juna ciwo, Bilal da ya ga Ronnie zai iya kashesa sai ya ɗauki wani kwalbar decoration ya bugawa Ronnie a gaban goshi, shi ne ta fashe take jini haka. Sai magiya guyson yake yi masu a kan su daina sun ki kula shi, da ya ga an fasawa Ronnie goshi ne ya zunduma ihu mai sautin da ya ja hankalin kowa, to tin da family suka zo su Dr Raj sun yi kokarin raba faɗar abin ya ci tura, dan Ronnie ba wasa ba, renon Big Bro ya gwada masu banbancin kwanji. ABIN DA YA FARU KENAN. Ai Sweetie tana ganin jini a jikin Ronnie ta nufesa da gudu tana ambatar sunansa. Daidai lokacin Bilal ya zo da gudu ya rarumi Ronnie sama zai buga shi da kasa, irin ɗaukar unexpected ɗin nan ya yi mashi. Gabaɗaya mutanen dake wajen babu wanda zai iya ce maka ya ga giftawar Big Bro a tsakaninsu sai suka gansa ya tari Ronnie da Bilal ya yi jifa da shi, yau ransa ya yi mummunar ɓaci, sabida ko shi bai taɓa kwanta hakan a kan Ronnie ba, yadda yake kaunar kanin nan nasa, wlh basu isa sun zubar mashi da jini a banza ba. Cikin fushi ya sauke Ronnie kasa, Bilal na tsaye bai san ya aka yi ba sai jinsa ya yi ya yi sama, kafin ya farga Big Bro ya bugasa da kasa har sai da kafarsa ta bada wata iriyar sauti alamar karaya. Da karfi Smart ya ce. "Subhanallahi komai kuma ya lalace". Ya kai karshen maganar tare da afkawa tsakiyar parlon da gudu dan in ya barsu ya karawa Bilal duka ɗaya sai mutuwa, yanzu ma haka Bilal kam ya fita a hayyacinsa. Gabaɗaya parlon salati suka saka, Pretty ta matsa ta rungume Mahnoor tana zazzare ido, sabida ita tasan kokawarsu bata kyau ne, ga ɗan banzan tsoro. Ita kuma Sweetie kan Ronnie ta yi da gudu tana ambatar sunansa. Big Bro yana shirin sanya kafa ya take wuyan Bilal a kasa Smart ya yi zafan rikosa ta baya yana faɗin. "Please Big Bro, for give him, nasan dik yadda aka yi su suka tsokani Safras, dan bashi da neman faɗa, amma please ka yafe masu". A cikin fushi ya hankaɗe Smart da karfi, sabida bai ga dalilin da zai sanya ya yafewa wanda zai dubar da jinin Ronnie yana a raye ba. Hannu yasa ya cicciɓo Bilal sama ya kara yin jifa da shi da karfi wanda hakan yasa Bilal numfashinsa ta ɗauke cak. Tsoro ne ya kama gabaɗaya mutanen parlon, Sharifa mai cewa tana son Big Bro ne jikinta ya hau kerma. Heleena kuwa ruɗewa ta yi, ta kalli Smart ta kalli Big Bro, ta ga kamannin har ya ɓaci. Da gudu Ramish ya fito daga room ɗin king, ganin abin dake faruwa ba karamin ɗaga mashi hankali ya yi ba, da sauri ya kariso cikin parlon dan sanin me yake faruwa?. Dr Raj dai baya ya ja yana salati yau za'ayi kisan kai a cikin family, Smart da baya gajiya da ƙoƙarin dannan ɗan uwan nasa ne ya sake nufar Big Bro da gudu yana ƙoƙarin rikesa, a karo na biyu ma sake hankaɗe Smart da karfi ya yi. Hakan yasa Smart ya miƙewa tsaye ya kalli Sweetie dake rungume da Ronnie tana bashi hakuri ya ce. "Sister dakatar mana da heartbeat ɗin nan naki kada ya yi kisan kai, karya kashe kaninsa da kansa". Shi fa Smart yanzu ya gano idan ba Sweetie ba babu wacce zata yi yin gaggawar tausar zuciyar Big Bro cikin ƙanƙanin lokacin, shiyasa ya ce bari ya daina wahalar da kansa yana shan azaba. Sai a lokacin daga ita har Ronnie ɗin dikka suka kai kallonsu a kan Big Bro, ganin yadda yake huci suka fahimci ransa ya ɓaci. Smart yana faɗin hakan gabaɗaya kallon family ya dawo kan Sweetie, har suka sanya ta ji kunya. Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki ta saki Ronnie ta nufi in da Big Bro yake, yana tinkarar Bilal dake kwance baya motsi ne tamkar wani zaki. Daidai zai sanya hannu ya shako wuyar Bilal ya ɗagasa sama ta yi gaggawar shiga tsakaninsu, tamkar zata yi kuka, ta ɗan tsuke fuska wajen cewa. "Please Big Bro, ka barsa haka, kaga baya motsi ko?". Hannu yasa zai tureta gefe guda ta yi gaggawar faɗawa jikinsa, dan in ba haka ta yi mashi ba ita ma jifa da ita zai yi. (Big Bro ɗan ikka mai rai ne asuway, yana yin abin da kwata-kwata isn't kamatable, to ni dai bari in haɗa kayana, zuwa gobe zamu ga zai iya tsalleke wannan runguma ya yi jifa da ita ne, ko kuma dai family zasu sha mamaki?🤔 Sweetie ta san ya kan tsiya, ta ce kada ya taɓata, amma yanzu da yake cutarsa zata yi har da rungumesa bawan ALLAH, ba komai zamu rama ne!.) Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 Hannu yasa zai tureta gefe guda ta yi gaggawar faɗawa jikinsa, dan in ba haka ta yi mashi ba ita ma jifa da ita zai yi. Zazzafar runguma ta yi mashi tare da rukunkume shi da karfi yadda ma ba zai iya zareta daga jikinsa ba!. Ai gabaɗaya kallon jama'ar parlon ne ya koma kansu, yau sun ga ikon God, gyara tsayuwarsa Smart ya yi yana kallonsu, dan shi ya rigada ya gano raunin ɗan uwan nasa, dan yanzu ransa fes sun samu wadda zasu rinƙa amfani da ita dan juya akalar Big Bro, abin ya yi mashi sugar. Sareena da Sharifa kallon juna sukayi, a tinanin Sareena Pretty ce, sai da ta lura da kalar gashin kan Sweetie sannan ta iya banbantawa, Omaid da Obaid dik iskancinsu sai da suka sha jinin jikinsu suka natsu tsit, dan ko da sunan wasa basu taɓa kallon duka irin wanda Big Bro ya yi wa Bilal ba, a ransu suka ce lallai ya tabbata da gaske wannan renon gunguma-gunguman bakaken aljanu ne, irin wannan zalinci da fusata haka? Basu taɓa sarawa mutum a wani ɓangare na mugunta ko iya horarwa ba, amma yau sun ma risinawa Big Bro ne bama sarawa ba!. Dik cikin parlon nan babu wanda ya taɓa kallon irin wannan duka da fusata na Big Bro, shiyasa dik suka ja gefe, har Ramish baya ya ja, dan shi ma mugun shakkar yayan nasu yake yi, Smart ɗin nan dai shi kaɗai ya iya gwada tinkararsa, shiyasa da suka ga Sweetie ta matsa ta rungumesa gabaɗaya suka saki baki sunana mamaki, gani suke yi kasheta zai yi yadda ya ɗauki zafi haka, baya ji baya gani, tamkar wani baby haka ya hankaɗe Smart dake matsayin jarumi ma bare kuma yar wannan abin, a cewarsu kenan. Dik da yake a cikin fushi sai da ya wani irin ɗauke wuta na ɗan lokaci, ji ya yi tamkar wanda aka watsawa ruwan kankara a zuciyarsa, dama kun san ya ɗan jibgi Bilal ɗin, so ya ɗan fara hucewa, shiyasa zuciyar ta yi sanyi daga runguma. A tinanin Smart zai zareta daga jikinsa ne, sai suka ga yasa hannu ya rungomota da kyau a jikinsa. Ai tin daga kan su Dr Raj har zuwa kan su Sareena, su Sharifa sai da kowannensu ya saki baki yana ganin ikon God, wasu daga cikinsu tambayar kansu suke yi dama yayan nasu yana da mata ne? Wasu kuma suna faɗin kai kaga wata iriyar soyayya, su Dr Raj kuwa faɗi suke yi lallai Sweetie ta cika mace, ko me take yi wa Big Bro ya yi mata irin wannan mahaukacin so haka? Amma koma dai menene wannan ta cika macen da kowani namiji zai yi burin samu, wacce zata iya tsai da miji a natse, ta san kuma yadda zata yi mashi ya sauko ko bai shirya ba, lallai irin wannan macen suke buƙata a rayuwarsu su sarakan zuciya. Jin ya rungumeta yasa ta fahimci ya ɗan sauko kenan, ɗago kanta daga kirjinsa ta yi, fuska dik ya yi jagaje-jagaje da gawaye, idanunta jajir ta sauke kan fuskarsa, while shi ma ita yake kallo babu ko kyaftawa. "Please king of my heart ka barshi haka ka ji?". Cikin kuka ta faɗa tana shessheƙa ga wani madaran shagwaɓa da ta zuba mashi dik dan ta taushi black heart ɗinsa. Aikuwa wani irin bugawa da zuciyarsa ta yi jin wannan shagwaɓa, kun san shi da shagwaɓa na 5&6, ga wani sunan da ta faɗa mashi wai king of my heart, oh God ai bai san lokacin da ya jinjina mata kai alamar to ya barshi ba. ALLAH MAI IKO, IDAN KA YI HAKURI A RAYUWA KOMAI MAI WUCEWA NE, WAI YAU SWEETIE KE CEWA BIG BRO YA BAR ABU KUMA YA CE YA BARI? KAI KU CE ALLAHU AKBAR. Hannun ta ɗaura saitin zuciyarsa ta fara shafawa a hankali-hankali, cikin natsuwa sosai, ga madarar shagwaɓa da ya fi na Pretty daɗi da ɗaukar hankali ta ce. "Cool down king of my heart!". Tana magana tana cigaba da shafa saitin kirjinsa tana kallon fuskarsa. One thing about Sweetie, sarai tasan Big Bro yana balain san shagwaɓa tin farkon zamansu, saboda tana ganin yadda yake biyewa Ronnie idan yana yi mashi, in Ronnie yana shagwaɓa zai iya ɓata awa yana sauraronsa, a jininsa son shagwaɓa take, and dik abin da Ronnie yake so da ya haɗa da shagwaɓa wajen tambaya zai aminta. Sannan tana da lura sosai, ta lura da shi matuƙa a lokacin zuwan Pretty empire ɗinsu, idan tana shagwaɓa har satar kallonta yake. Kun san meyasa bata yi mashi? Bawai bata iya bane, abin da ya yi Pretty shi ya yi ta, sai dai magana ake ta ilimi da basira a wajen, tin farkon haihuwarsu na faɗa maku Sweetie ta fi basira a lokacin da na yi bayani kan kalar gashin kanta, na faɗa maku masu irin wannan gashi baiwa da basirarsu daban take, tasan halin Big Bro fiye da Ronnie a yanzu, dan tana da ɗabiar karanta mutum sosai, dik wani motsinsa tana karantarsa fes, ranar da ta ce jikinta na mijinta ne da gangan ta yi wannan furuci dan ta tabbatar da abin da take zargi a kansa, tana karantar zuciyarsa a dik lokacin da ya yi motsi, tana sanin abin da yake so tin kan ya fahimci yana so. Amma dik da haka bata yi mashi abubuwan da yake so sosai, misali irinsu shagwaɓa, saboda gudun shaiɗan ya yi galaba a kansu, tasan tana son shi, kuma tasan bata iya controlling kanta a kansa, sannan tasan ko rantsuwa ta yi ba zata yi kaffara ba yana sonta shi ma, shiyasa take jan baya ta rufawa kanta asiri kada abin ya zarce kaifin kwakwalwarta da iliminta shaiɗan ya buga masu ganga, amma ta tara mashi shagwaɓa kala-kala a dik time da suka mallaki juna, dik wani abin da yake so dangane da mace ta sani kuma ta iya, kawai ba zata gwada yanzu bane sai gaba, abin da yasa yanzu ma ta yi mashi wannan shagwaɓa dan tasan hakan kawai zata yi ta ceci Bilal shi ma ta cecesa daga aikata kisan kai!!. Kawai tsareta da ido ya yi, da alama suman tsaye ya yi jin yadda take yi mashi magana cikin wani sigar da bata taɓa yi ba. Kallon Pretty Smart ya yi a ransa yana faɗin da ma ita ce ta iya irin wannan madarar soyayyan, ita kuwa Pretty dake kwance saman shoulder ɗin Mahnoor harara ta dalla mashi tana kwaɓe fuska irin shirmen banzan nan, ɗauke kansa ya yi dan shafawa kansa lafiya. Dik wanda yake a cikin parlon nan sai da ya gyara tsayuwa yana kallon wannan pure love mara mix ɗin. Take waɗan da suke ganin kansu matsayin cikakkun ƴan love irinsu Jaish and Mahnoor, Jawad and Chuchu, su Aneesa da dai sauransu dik sai suka ji ai bama su iya komai ba ashe. Su Sareena take suka yi mugun raina kansu a wannan ɓangaren, Omaid da Obaid tv suka mayar da Sweetie. Guyson ma dai fatan Mahreen ta iya wanna pure love ɗin yake yi. Dr Raj kallon Zee ya yi irin kallon nan na kinga madarar kauna ko?. Shi kam Ramish kara ja gefe ya yi ya zauna saman sofa yana kallonsu, yana jin shi ɗan love ne ashe shi ma ba komai bane a gaban su babban yayansu, ga in da ake love madararta. Mama dai taɓe baki ta yi tana kallon ikon God, ita kuma Heleena tinanin ranar da zata yi wa Smart irin haka ta shiga yi, dan Sweetie ta yi mugun burgeta. Take zuciyar Ronnie ta yi wani irin fes, yau burinsa ya cika yayansa ya faɗa tarkon kaunar sister ɗinsa, sai ya ji ai wanna faɗa da suka yi shi alkhairi ce a garesa tin da ya ga irin wannan lokaci da ya jima yake jira. Ɗan rankwafo da kansa saitin face ɗinta Big Bro ya yi, yana kallon cikin idanunta sosai, ya kara matsar da ita jikinsa da kyau. Tongue ɗinsa ya fitar, a natse ya hau lashe hawayen da gabaɗaya ya ɓata mata fuska. Ya ilahi ya lillahi, ai zuƙatan jama'ar parlon nan gabaɗaya narkewa ya yi, Smart ɗan neman rigima waje ya samu saman sofa ya zauna tare da ciro wayarsa daga aljihu ya fara yi masu video, har da cewa su Dr Raj su matsa kada su shigan mashi video. Sai da ya lashe hawayen nata fes, sannan in a cool way sosai ya ce. "Meyasa kike kuka bayan kuma kin san na hanaki yi?". Dik suna jin abin da ya faɗe, santin voice ɗinsa gabaɗaya suka hau yi, harta mazan ALLAH ALLAH suke yi ya sake yin magana mai tsawo, bare kuma matan da babu wanda bai kwaɗaitu da voice na Big Bro da kuma salonsa ba. Turo mashi baki gaba ta yi. "Ba kaine ka sakani kukan ba?". Cikin wani irin shagwaɓa mai jan hankali ta yi maganar. Ɗan zaro mata idanu ya yi. "Dana yi me?". Ya tambaya ta hanyar motsa lips kawai ba tare da wani sautin murya ya fita ba, da yake tana a kusa da shi dab sai ta gane me ya ce!. Zame hannunta daga saitin zuciyarsa ta yi tare da mayarwa bayansa, ta rukunkume shi da kyau, cikin sigar nuna cewa ita macece cikakkiya ta ce. "Muje ɗaki zan faɗa maka me ka yi ka sakani kuka". Ai malam Big Bro kara susucewa ya yi, dama wai ya lafiyar kura bare tai zawo, tuni komai ta motsa, ya zo har wuyan da baya jin zai iya jurewa, kun san shi ba kunya ke garesa ba, gara ma ita, dan haka sai ya ɗan rage tsawonsa ya ɗauketa cak sai saman lion chest ɗinsa, sai kuma a lokacin ya iya tuna wai mema yake yi ne?. Amma dik da ya tina bai sauketa ba, ya kalli Smart tare da ɗaure fuska sosai kafin ya ce. "Yanzun nan ka kai mun my pleasure hospital". Smart da shegen neman ɗan uwan nasa da tsokana ne ya miƙe tsaye, yana ɗaure fuska shi ma ya ce. "Ni ba zan iya kaisa hospital ba king of my heart........" Ai bai iya kai karshen maganar ba ya haɗiyeta saboda wani irin kallo da Big Bro ya danna mashi, abin like kada ka kuskura ka sake kiran wannan sunan, wato sunan Sweetie ce kawai, ita kaɗai zata kirasa da shi. Harara Smart ya dallah mashi kafin ya ce. "Mai da wukan king of our heart, zan kaisa hospital yanzu kuwa". Wlh parlon nan yadda kuka san babu kowa a cikinsa, dik sun yi tsit, saboda yau sunga abin da ya goge masu hadda gabaɗaya, Sareena, Heleena, Aneesa, Mahnoor and Chuchu dik maimaita sunan King of my heart suke yi a cikin ransu, sunan ya tafi da su, watau Big Bro shi ne sarki a zuciyar Sweetie. (SAI DAKE SWEETIE ƳA A GIDAN AISHA BAITA JIDDA MUMCY AND SECOND MUMCY AISHA SULAIMAN!. WATAU MUMCYS KUNA NAZA BAKACITY FA BAMA CAPACITY KAWAI BA HAR DA BAKACITY, NASAN KU KUKA YI WA SWEETIE WANNAN HUƊU BA TA CUTAR BAWAN ALLAH BIG BRO, TO BA ZAMU YARDA BA, MU ƳAN TEAM HANA RUWA GUDU MUN YI ALLAH WADARAI DA WANNAN ABU KUMA SAI MUN HANA RUWA GUDU, GA SHI TA JA ƊAN MUTANE ƊAKI ZATA LALATA MASHI TARBIYA.😑) Bai sake bi ta kan kowa ba ya wuce da ita ɗaki abinsa. Da kallo kowa ya bi bayansa, sai da ya kure masu sannan ji kake kowa na sauke ajiyar zuciya, yau sun ga balai sun kuma ga power of mace tagari!. Nan fa Smart ya kalli Ramish kafin ya ce. "Ita kaɗai ke iya dakatar da wannan yayan naku, ko suma ya yi da ya jita a kusa zai farka, sai ku yi taka tsantsan, yanzu tattari su Bilal zuwa hospital, kai kuma Ronnie zo mu je, dan da kaina zan kaika in kula da lafiyarka kada a mun ta su Bilal nima". Murmushi Ronnie ya yi kafin ya nufosa yana faɗin. "Ina ai ba zai yi maka ba kai kam". Girgiza kai Smart ya yi. "Kafi kowa sanin yadda muke kwashewa da shi, kai dai mu je". Yana magana yana kara ɗaure faska, ya kai karshen maganar tare da riko hannun Ronnie zasu nufi waje kenan muryar mama ta katsesu da cewa. "Kenan ya daki su Bilal a banza?". Ba tare da Smart ya juyo ba, yana cigaba da tafiya ya ce mata. "Ɗakinsa na part na momma zaki iya zuwa ki faɗa mashi ko ki ramawa Bilal ɗin". Ai tin daga nan ji kake gum ta datse bakinta da jiga-jigan makullai, sabida dik iskancinta mugun tsoronsa take yi, shi kansa Smart tsoronsa take yi, daurewa ta yi dan balai ta yi mashi magana. Shi dai Ramish bawan ALLAH shiru ya yi yana bin kowa da ido, da ka gansa kasan yana da dauriya ce kawai, amma bawan ALLAH'N nan yana cikin damuwa kam, idanunsa jajir da su. Sai bayan Smart ma ya fita ne Mama ta kalli Ramish kafin ta ce. "Ka sameni a ɗaki kaiku, and 5 mins kawai na baka". Tana gama faɗar hakan ta wuce ɗaki, so take ya zo ta yi mashi faɗa dan in baku manta ba tin bai san cewa ba mahaifiyarsa bace ya kaurace mata, wasan ɓuya ya koma yi da ita, in yasan zata je waje baya zuwa, dik dan kada ta tsaida shi da masifarta. Bayanta ya bi da kallo har ta kurewa ganinsa, a ransa ya ce. "Shiyasa bata damuwa dan ina cikin damuwa? Dik wata uwar duniya zata so ɗanta ya samu abin da yake so matuƙar ba cutarwa ce a garesa ba, amma ni tawa uwar ita take son rabani da abin da nikeso, tana kuntatawa rayuwata, ashe ba ita ta haifeni ba dole ba zata rinƙa jin wani tausayina ba, ba shakka naga aya". Ya kai karshen zancen zucin nasa tare da miƙewa da sauri ya nufi room na king alamar ba zai je kiranta ba kenan, dan shi yake jinyar daddyn nasu. WAI KUN SAN DA CEWA AKKA NA DA ƊIYA MACE? KING NA DA KANWA, UNCLE JAHIZ AUTA YANA DA SISTER, AMMA TA GIRMI UNCLE JAHIZ, DAN SHI KAM SHI NE AUTA, BARI DAI KING YA FARKA, LABARI BATA KARE BA, HAR YA SAMU LAFIYA ZAI FAƊA MAKU INA KANWAR TASU TAKE, SHI KAƊAI SAI AKKA NE SUKA SAN IN DA TAKE! LABARI ZAI BIYO TA KANTA!. MASU KOKARIN DOLE SAI SUN HAƊA DANGANTAKAR SU SWEETIE AND KINGDOM OF POWER KU KWANTAR DA HANKALINKU, TIN A BAYA NA FAƊA MAKU BASU DA ALAƘA, WAI KU BAKU GAJIYA DA KARANTA LITTAFI A KAN FAMILY GUDA NE? HABA MANA, KULLUM SAI A RINƘA WANI CEWA A'A IYAYENSU ƳAN UWA NE DA SAURANSU, AIKIN KENAN, TO NI DAI NA GAJI ATO, DAN HAKA STARS ƊINA BASU DA ALAƘA TA JINI SAI DAI TA SOYAYYA, KU KWANTAR DA HANKALINKU, KULLUM BURINA IN KAWO SABON SALO LABARINA YA BANBANTA DA KOWA AMMA KU BAKWA ZAMA WAYS😌 One by one mutanen cikin parlon suka fara watsewa, da kyar Sareena ta iya juyawa ta fita, saboda yau ta ga yadda ake soyayya da kirsa a in da ta dace, ta ga macen da ta cika mace mai iya juya zuciyar namiji kamar Big Bro, dik ƴanmatan king sun raina kansu yau wlh. Heleena na komawa bedroom ɗinta ta fara tambayar momma a ina ake ɗaukar small meals bari ta ɗauko, kwatance momma ta yi mata, da sauri ta fito dan ta je ta ɗauko, to kun san family part da wani mahaukacin girma, a garin dawowa ta ɓata hanya, sai shiga nan take yi ta sake fita, ga ginin iri guda ne, ruɗewa ta yi tana neman hanya har ALLAH ya faɗo da ita wani ɗan madaidaicin parlo. Ta sha madarar mamakin ganin su Sareena a wannan parlo suna hira, dik ƴan matan king suna wajen, harda su Mahnoor da Mahreen, ko sallama bata yi masu ba ta afko ciki, tana nan cikin wannan ɗan ikka shiga nasu, ta wani riko plate a hannu, daga shigowarta ta hau dalla masu harara tamkar zata cinyesu da ido. Aikuwa gidanta ta zo, dan kuwa harara suka fara dalla mata suma. Harta Aneesa dake rike da waya Yah Rizwan yana ta tsokanarta ta Whatsapp, wai dik basu iya soyayya ba, su je Sweetie ta koya masu yadda ake kula da miji, to dama a kule da haushi take kan kalamansa, sai ga Heleene ta zo tana banka masu harara, me kuke tinanin zai faru? Ai suma harara tamkar idanunsu zai faɗi kasa suka shiga dalla mata har sai da ta ɗan sha jinin jikinta, sai kuma ta kalli Sareena kallon tsab kafin ta ce. "Ke zoki wuce ki kaini part na Rahilarh"........... Kun san mom Smart haka take kiran momma da sunanta watau Rahilarh, to shi ne ita ma Heleena dan tabbatar rashin kunya da rashin hankali take kiranta haka, kunga gara mom Smart ai tinda matar yayanta ne, momma kanwar mijinta ne, ita kuma Heleena fa? Hmmmmm wai a haka kuma take son Smart ya aureta, tab ai Heleena kadama ki bari ya ji ga sunan da kike kiran mommarsa, dan jikinki ne zai faɗa maki. Ai suna jin ta faɗi haka suka wani bita da mugun kallon da sai da yasa ta ji kirjinta ya buga, wai ita nan zata gwada masu isa, bata san nan gidan isa da Izza ta zo ba. Sake pointing Sareena da hannu ta yi kafin ta ce. "I'm i not talking to you?!". Ai yadda kuka san da wall Heleena take yi, suka yi banza da ita. Ranta ne ya ɓaci, ji take tamkar ta matsa ta kama Sareena tai mata mugun duka, amma kuma ita kanta tasan ba zata iya ba, dan ba karfine da su ba, dan haka sai ta ce bari ta kira ɗaya daga cikin escort da suka rakota zuwa kingdom ɗin, securitynta kenan, bari ta kisa ya zane mata su. Sai kuma ta tuna ai kingdom ɗin nan ba irin kuci ku bamun masarauta bace, ba kowani yuyu ma yake shigowa family part ba, dan sun hana securitynta ma shigowa, ita kaɗai ta shigo, Kingdom of power suna da wani irin bahagon dokoki da tsare-tsare, basu ɗaukar raini ko wasa, babu wanda ya isa ya shigo family part ba tare da izinin king ba, sai kuma izinin momma, ko bako ɗan gida ya yi dole sai king yasan waye shi kuma daga ina yake, ba haka suke ba su, akwai dokokin da dolen uban mutum ya bi, in ma baka bi ba jikinka ne zai faɗa maka, so su basa ɗaukar wargi, ita kanta Heleena ɗin sai da aka nema mata alfarmar shigowa family part, dan sai da momma ta roki King sannan. Tina hakan ne yasa ta jefesu da harara ita ma, ji take tamkar ta je ta shake Sareena, wai ni kam na ce ba, anya kuwa Heleena bata san cewa Sareena abokiyar takararta bace kan Smart kuwa? Naga tin da ta zo ta tsani Sareena ne, kuma ba wanda ta rainawa wayau irinta, dik yadda aka yi tasan kishiyoyi suke, to ni dai zanga ya wasan nan zata kaya. Sai hararar su take yi, suma kuma harararta suke yi, yo su da kansu da kansu ma basu bari ba suna hararar juna bare wata bare, su kansu basu shirya ba, ga Aneesa nan tin ɗazun take faman harararsu dan Rizwan ya ce su koma su koyi soyayya, su Chuchu yau dik hararan juna ake ta faman yi. Daidai lokacin Omaid ya shigo cikin parlon dan ya faɗawa Sareena ga plan da suka shiryawa Pretty wanda ba za'a taɓa gane su suka yi ba. Yana shigowa ya bi Heleena da wani irin kallo kafin ya ce. "Wannan mai kama da snooker stick ɗin kuma daga ina?". Sareena na harararta ta amsa mashi da. "Wai part na momma take nema shi ne ta zo ta tasamu gaba zatai mana rashin kunya".......... Harara Omaid ya wurga mata kafin ya ce. "Yana da kyau ita ma a gyara mata zama, yanzu dai Aunty Sareena zo mu je akwai magana". My people anya kuna ganin lafiyar su Omaid kuwa? Dik tsoron da zasu ji baya hanasu sake yin abin da suka yi niyya, sam babu ja da baya a lamarinsh! Anya kuwa haka kalau suke kuwa? Gaskiya da alamar tambaya a lamarinsu, ku duba kuga yadda suka shiga tashin hankali da tsoro a lokacin da Big Bro ya daki Bilal, har suka natsu, amma yanzu har sun sake komawa ruwa, kai akwai matsala fa!. Miƙewa Sareena ta yi tabi bayansa tana hararar Heleena. Ita kuwa tsayawa ta yi shiru tana tinanin yadda zata yi, tin da dik sun ki kulata. Da dai ta gaji sai ta tausasa murya, ta dubi Mahnoor da cewa. "Please ki kaini part na Rahilarh". Taga Mahnoor ce kawai fuskanta ya nuna mai saukin kai a cikinsu, shi ne ta yi mata magana. Ba musu Mahnoor ta miƙe tare da wucewa gaba tana faɗin ta zo su je. Da sauri ta rufa mata baya suka wuce, da harara su Aneesa suka bita tamkar idanun zasu faɗo kasa suna jan dogon tsaki. After 10 minutes. Heleena ce ta fito rike plate of small meals daga room ɗinta, sannan ta nufi room ɗin da momma ta ce mata shi ne na Smart, dan kewarsa take yi, tin da ta zo basu haɗu ba sai ɗazun da ta gansa a parlo, tana san zuwa su ga juna. Excuse ta yi tare da tura door ta shiga. Yanzu ya dawo daga hospital, an gyarawa Ronnie wajen, ya fito daga wanka ɗaure da towel a waist ɗinsa, Pretty sarkin mulki tana kwance saman gado tana binsa da kallo. Gabansa Heleena ta zo tare da miƙo mashi plate ɗin tana faɗin. "Good afternoon brother". Bai amsa gaisuwar ba, amma ya kai hannun zai ɗauki meat roll guda ɗaya daga cikin plate ɗin dan tsokana. Sai dai kuma me? Yana kai hannu zai ɗauka suka ga an buge plate ɗin gabaɗaya ya faɗi kasa ya zube. A miliyan Heleena ta ɗago kanta, wani irin mugun kallo Pretty dake tsaye a gefe ta wurga mata kafin ta ce. "Yah Omerish wacece ita ɗin?". Ta faɗa tana wani mugun ɗaure fuska, irin babu wasa a tattare da ita ɗin nan. Ita kuma Heleena ruɗani ta shiga, ta gagara tantance wacce ta rungumi Big Bro ɗasun ne (Sweetie) ko kuma dai ba ita bace? Idan ita ce kenan maza biyu take tare dasu ko yaya? Kai kanta ya shiga duhu. Sosai Smart ya ji wani irin daɗi, dama so yake ya gwadata ya ga tana kishinsa ko bata yi shiyasa zai ci abin Heleena, in baku manta ba ai baya cin dik abin da Heleena ta kawo masu tin suna Paris, dan haka sabida gwada Pretty ya so ci. Kun san maza na mugun son su ga ana kishinsu, wani musulmin daɗi suke ji. Sabida ya kara gwada kishinta a kansa yasa ya ce. "Daga cikin family take". A hanzarce ta tari numfashinsa da cewa. "Kenan zaka iya aurenta? Akwai aure a tsakaninku?". Muryarta har rawa yake yi ta faɗa. Kai ya jinjina mata alamar e ba sister ta jini bace, dan haka zasu iya yin aure. Ai wani irin fusata Pretty ta yi, cikin fushi tana ɗaure fuska ta kalli Heleena, da yatsa ta nunata, cikin harshen turanci ta ce. "Ke mai kama da allon mayu, sa idonki cikin nawa, ni ba sa'an irinku bane, bani da mutunci a kan mijina, tin wuri ki ɓace daga ɗakin nan tin kan raina ya ɓaci in karya wannan kafar taki mai kama da burugalin burga miya, kuma idan kika bari ko bisa kuskure idanunki ya sake kallon mijina sai na ƙwaƙwale maki shi, fita waje yanzu!!!". Tana huci ta faɗa. Daɗi tamkar Smart ya zuba ruwa kasa ya lashe. Tsabar farinciki jawota jikinsa ya yi ya rungume yana jin zuciyarsa na wani irin sanyi, da hannu ya yi wa Heleena alamar ta wuce ta fita yana kara rungume yar tsanarsa. Idanunta sun cicciko da kwallah na jin Pretty ta kirasa da sunan husband ta juya da gudu ta nufi waje, wani irin kukan takaici ne ya kubce mata. Shi kuma Smart ya rungumi ƴar tsanarsa yana zuba mata ruwan albarka tare da rarrashi, rigima ta hau zuba mashi kan ita bata yarda yana kula wasu ba, rarrashinta ya fara yi cikin so da kauna game da alkawarin ba zai sake kula wata ba. -------------------------------🔥 Suna shiga room ɗinsu ta kai hannu ta saƙalo wuyansa, raɗa ta fara yi mashi a kunne, da sauri ya juyo da kallonsa a kanta, kaɗan ya motsa lips ɗinsa wajen cewa. "To faɗa in ji". Make mashi kafaɗa ta yi game da cewa. "Saukeni to tin da mun zo ɗakinmu". Ba musu ya sauketa ƙasa, saman bed ɗinsa ya nufa, zama ya yi yana binta da kallo from head to toe. Ganin hakan yasa ta koma saman sofa ta zauna shiru tana satar kallonsa, ɗan bakin da ya rinƙa zuba mashi shagwaɓa ɗazun kawai yake bi da kallo. Dik sai ta ji ta takura da kallon nan da yake yi mata, dan haka sai ta ce. "Big Bro in je wajensu Mahnoor?". Ta faɗa tana ɗago da kallonta a kansa.. Banza da ita ya yi tamkar bai ji ba, sau uku tana faɗa tana karawa, amma dik tamkar bai ji ba, da ta ga ba zai amsa ba sai ta miƙe ta dawo kusa da shi, a gefen bed ɗin ta zauna, cikin sanyin murya ta ce. "Please Big Bro ka yi magana mana, In je wajensu Aunty Mahnoor?". Wani irin kallo ya bita da shi wanda sai da yasata haɗiyar yawu mai wuyan wucewa, in a cool way sosai ya ce. "Kada ki sake kirana da Big Bro". On a serious note ya faɗa. Mamaki ne yakamata na jin abin da ya faɗa, ɗan zaro mashi idanu ta yi kafin ta ce. "To da wani suna zan rinƙa kiranka?". Banza da ita ya yi tare da gyarawa ya kwanta. Ganin hakan ya yi matukar tayar mata da hankali, sai ta matsa kusa da shi dab, tamkar mai raɗa cikin natsuwa ta ce. "Please ka faɗa mun ka ji?". Idanunsa a kan ɗan bakinta ya yi shiru bai yi magana ba, for almost good 5 mins, da ta ga bashi da niyar sake yin magana sai ta miƙe zata bar wajen idanunta na ciccikowa da kwallah. Tana miƙewa ya riko hannunta, da sauri ta juyo, ya bari sai da ta juyo sannan ya jawota jikinsa gabaɗaya ta tafi ta faɗa saman lion chest ɗinsa. Wani irin musulmin ajiyar zuciya ya sauke, hannunsa ya ɗaura a saman bayanta, face ɗinsu na fuskantar juya, ai take suka kashe juna da wani irin sanyanyayyen musulmin kallo mai narka zuciya. "Wani suna kika kirani da shi a parlo?". Ya faɗa ta hanyar motsa laɓɓansa kawai ba tare da wata sauti ba. Dama tin ɗazun ta gane me yake nufi, kawai so take ya furta da bakinsa ya ji daɗin sunan ne, shiyasa ta nuna tamkar bata gane nufinsa ba. Harararsa ta ɗan yi cikin wasa, muryarta a sanyayye ta ce. "Ni ba zan cigaba da faɗa maka wannan suna ba har sai ka faɗa mun gaskiyar yadda ka ɗaukeni". Da iya gaskiyarta ta yi maganar. Ta faɗi haka cike da tsammanin abin da zata ji daga bakinsa mai daɗi ne, sai dai kuwa da buɗar bakinsa sai ya ce. "Matsayin sister ɗita kike mana". Ajiyar zuciya ta sauke tare da yunkurawa ta bar jikinsa, bai dakatar da ita ba, ta koma saman sofa ta zauna, daga karshe ta kwanta tare da jawo bargo, tin daga wannan lokaci kalmar A bata sake haɗasu ba, ta daina kulashi, wunin ranar bata fita ko parlo ba, kuma bata ci abinci ba, ko da Momma ta tashi ta sanya aka kirata, ta zo ta ɗauka mashi abinci, ba musu ta je ta ɗauka ta kawo mashi room ɗin, ta wuce ta kwanta, ba yadda bai yi da ita ba a kan ta zo su ci abinci, amma tai mashi rantsuwa da ALLAH ba zata ci ba, dik da haka ya yi ƙoƙarin tursasata amma sai ta tirje, dole ya hakura ya kyaleta, yana ji yana gani ta wuni kwance saman sofa, sallah ɗai ke tada ita. Bawan ALLAH dik ya shiga damuwa, hankalinsa ya tashi, amma sai ya daure ya kawar da kansa har yamma, ya ga da gaske take zata iya cutuwa da yunwa fa, around 5 na yamma haka ya ji bafa zai iya jurewa ba, ko breakfast bata yi ba, bata ci lunch ba, ga yamma ta yi, fitowa ya yi ya nufi room na momma domin ya ɗauko mata abinci da kansa. Ai yana fita ta tashi ta rufe kofar ɗakin da key, da sauri ta afka toilet. A gurguje ta yi wanka, ta dawo ta tsala shirinta cikin wandon jeana baki da top fari, ta yi mugun kyau, ta gyara gashin kanta tare da zuba turarruka a jikinta. Sai da ta gama komai kafin ta koma ta buɗe door ɗin, sannan ta koma saman sofa ta kwanta hada jawo bargo ta lulluɓa tamkar bata motsa ba. Ta kuwa yi saa hatta kammala komai bai shigo ba, ya tsaya magana da momma, sannan ya sanya ne a girka mata sabon abinci, sai ya zauna zaman jira, sai rarrashin momma yake yi yana faɗa mata babu abin da zai faru, King zai wastsake, dan ma sun kara mashi da alluran barci ne sabida suna san ya samu cikakken natsuwa sosai, dan kwakwalwarsa ta taɓu sosai, hankalinsa ya tashi na tina baya, ace a gaban idanunka a yi wa ƴaƴanka biyu irin wannan kisa, ƴaƴan da ko suna baka raɗa masu ba, ya zakaji, ku kwatanta da kanku, idan kune a wannan lokaci ya zaku ji? Kunga dole king yana buƙatar hutu sosai ai, in ba haka ba sai a samu gagarumin matsala. Sai around 5:50PM suka kammala shirya mashi abincin, abin da bai taɓa yi ba a rayuwarsa wai ɗauko kayan abinci, sai ga shi da kansa ya ɗauko ya nufi room ɗinsu, kamar momma zata ce mashi ina Sweetie ta zo ta ɗauka mana, sai kuma ta yi shiru dan kada ta tambayo wani abin, a cewarta tin da yake neman abinci a yanzu ba lokacin cin abinci ba to da walakin goro a miya, kila wani abin ya yi wa Sweetie, tina hakan yasa ta ce. ALLAH ya bata jika daga ɓangarensu da wuri, dan zataso su su fara samun baby kafin kowa a gidan, dama King Zuhair bashi da jika ko ɗaya, to zata yi fatan Big Bro ya fara basu jika, daga karshe ta yi addu'ar ALLAH yasa yaron yazamana mai irin gashin Sweetie, dan ita kanta momma gashin ya tafi da ita!. Lokacin da ya turo kofar ya shigo sai da ya ji gabansa ta ɗan amsa, a hankali ya dakata ya ɗan shaki kamshin dake tashi a ɗaki har da lumahe idanu kafin ya wuce ya nufi in da suke ajiye abinci. Bayan ya ajiye ya nufo sofar da take kwance. Yana zuwa ya tsugguna a gaban sofar, a natse yasa hannu ya yaye bargon nata. Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kara shakar kamshinta yana ɗan lumshe ido. Sanyayyar voice ɗinta mai daɗin saurare ne ya daki dodan kunnensa, amma cikin masifa ta yi maganar. "Me zaka wani buɗe mun bargona? Ba nace babu ruwanka dani ba?". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa zaune. Hannunsa yasa ya riko nata, can kasan makoshi ya ce. "Zo kici abinci".................. Kwace hannunta ta yi. "Ai tin ɗazun nace maka ba zanci ba ko? Please ni ka rabu dani".......... "Wai meyasa kika zama rigimammiya ne yanzu? Meyasa kike fushi haka?". Da alamar damuwa a kan fuskarsa ya yi maganar....... Da hannu ta yi pointing ɗinsa kafin ta ce. "Kai ne sila ai, kome na zama kai ka ja". Pointing kansa ya yi shi ma kafin ya ce. "Ni kuma?". Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e. Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "To me na yi?"......... Harara ta dalla mashi kafin ta ce. "Nima ban sani ba". A kufule ta faɗa, ya fahimci ranta a ɓace yake, dan haka sai ya sake riko hannunta, yana shirin yin magana kenan ya ji muryarta ta katse shi da cewa. "Ni dai nasan a baya baka taɓa faɗar abin da ba gaskiya ba, baka iya faɗar kishiyar gaskiya ba, but yanzu dik ka canza".............. "Me na faɗa wanda ba gaskiya ba?". Yana ɗan matsa yatsunta ya yi maganar......... "Abin dake cikin zuciyarka, wlh kishiyar gaskiya ka faɗa". WATAU SWEETIE AKWAI HANKALI, BA ZATA CE YA YI KARYA BA, SABIDA HAR YANZU TANA BASHI GIRMA DIK FAƊAR DA ZASU YI!. "E gaskiya kika faɗa, ban faɗi sirrin dake raina ba, but ai na ce ki gano da kanki kamar yadda na gano naki, koma me ya faru ke kika matsa mun kika sakani faɗar ba daidai ɗin ba". Ya kai karshen maganar yana riko jelar gashinta da hannunsa ɗayar. "To ai ni na faɗa maka ba zan iya gane komai ba, kawai ka faɗa mun"....... "Omaish meyasa kike son jin sirrin dake zuciyata wai?"......... "Sabida ka ji nawa nima, shiyasa nike son jin naka". Ɗan kwanto da kansa a saman laps ɗinta ya yi, yana cigaba da ɗan murza jelar gashinta ya ce. "Kina son kureni Omaish"......... Shiru ta yi tana sauraronsa ba tare da ta ce komai ba, kallonta a kan dark black hair ɗinsa dake ta faman sheƙi. "To zan faɗi sirrin dake raina, but in na faɗa tukuicin me zaki bani?". Ya yi maganar yana ɗago kansa ya kalleta. Lallausan kumatunsa ta shafa kafin ta ce. "Mekakeso?"........ Shiru ya ɗan yi kan ya amsa da. "Zan faɗa maki, amma ba yanzu ba, kawai dai ki yi alkawarin zaki bani dik abin da na tambaya". Mancewa ta yi da zai iya tambayar komai sabida ba addini ne da shi ba, ga kuma zumuɗin son jin menene sirrin dake ransa ta amsa mashi da. "Na yi alkawarin bayarwa". Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya matsa dab da kunnenta, cikin raɗa ya ce. "Me kike tsammanin ji daga gareni?". Ɗan juyowa gefe ta yi tana kallonsa. "Banace ba, amma dai ina tsammanin jin abu mai daɗi". Kasa sosai ya sake yi da murya kafin ya ce. "Okey, Omaish is the queen of my heart, secret of my heart, happiness of my life and love of my heart". Ya faɗa yana mayar da ɗan bakinsa zuwa saman lallausan kumatunta, sumbata ya manna mata a wajen kafin ya sake cewa. "Wannan shi ne sirrin dake raina rigimammiya, kin tilastani sai da kika ji". Ai wani irin musulmin murmushi ne ya kubce mata, da sauri ta sanya hannayenta ta rufe fuska tana wani sakin uban murmushi. Hannunsa yasa ya riko hannayenta, ya buɗe face ɗinta yana ganin yadda take murmushi gwanin ban sha'awa. Zuba mata idanu ya yi na tsawon lokaci yana kallonta, bai ankara ba sai jin ɗan bakinta ya yi a saman kumatunsa ta manna mashi sumbata. "I really love you King of my heart". Lumshe idanu ya yi tare da sake warosu a kanta, bai iya sake cewa komai ba, sai dai ya matsa ya kwantar da kansa saman laps ɗinta da kyau yana cigaba da murza ƴan yatsunta da ya rike. Kwace hannunta ɗaya ta yi ta ɗaura a saman gashin kansa ta shiga shafawa a hankali-hankali. Wani irin daɗi da ya ɗebesa har barci ya ji tana ƙoƙarin yin awon gaba da shi!. (MU KUNGIYAR HANA RUWA GUDU MUN YI ALLAH WADARAI DA WANNA ABU DA YA FARU, SWEETIE TA CUCI BIG BRO.) Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 Shiru suka yi for some minutes, kowannensu da abin da yake tinawa a ransa, ita dai yau ya kure farincikinta, bakinta yaki rufuwa, ta shagala da tinanin yadda zata ɓullo mashi ya musulunta har su mallaki juna, bata san time da hannunta ya gangara zuwa saman kumatunsa daga shafan hair ɗinsa da take yi, sai ji ta yi ya buɗe ɗan bakinsa ya capki hannun nata. A hankali cikin shagwaɓa ta ce. "Wash, kai king of my heart, me na yi kuma zaka cizan mun hannu?". Yadda ta yi maganar ya sanya shi dole ya ɗago kansa, dik ta kashe mashi jiki, har barci ya ji tana ƙoƙarin kamarsa. "Maysh I'm feeling sleeping". Can kasan makoshinsa ya yi maganar, sai kuma ya ɗan nisa tare da sake cewa. "Smiling yana mugun yi maki kyau, da shi kika yi amfani wajen kafawa zuciyata tarko"............ Tana binsa da wani irin narkakken kallon kauna mai wuyar fassarawa ta ce. "Ga shi kai kuma baka taɓa yin murmushin na gani ba bare in san yanai maka kyau ko bayayi". A maimakon ya bata amsa sai ya ce. "Yanzu kin fasa fallasawa momma abin da muƙa ɓoye?"........ Kai ta jinjina alamar e tana murmushi. "Ba zan faɗa ba, saboda yanzu gaba kaɗan zaka zama mijina na gaske". Har cikin ransa ya ji wani musulmin sanyi ya lulluɓesa, tamkar ya jawota ya rungume, amma sai ya daure da cewa. "Go and eat your food yanzu kam tin da an tilastani an samu abin da ake so". "To ai na kai na tilastaka ɗin ne, ko ban kai ba?". Tana tsaresa da ido ta yi tambayar. Gera guda kawai ya ɗaga mata alamar ta kai, daga haka bai sake yin magana ba, ya dai nuna mata wajen da ya ajiye mata abinci, mikewa ta yi cike da farinciki ta nufi wajen, yanzu kam zata ci abinci lafiya lou. Miƙewa shi ma ya yi ya koma saman bed ya kwanta yana fuskantar. A natse ta zuba abinci ta hau ci tana satar kallonsa, bata son su haɗa idanu kai tsaye, tamkar ta san ya tsareta da kallo ne. Yayin da dik wannan abin yake faruwa a cikin gida kuma kowa yana nasa sabgar, su Chuchu dikka ALLAH ALLAH suke yi Sweetie ta fito su kulla kawance da ita, dan gaskiya suma suna son juya zuƙatan mazansu kamar haka. Ita kuma Mahreen ana harkar arziki tana can tana baiwa guyson wahala tanai mashi iskancin da ta saba, shi kuwa yana zaune saman bedside drawer ɗinta, yana fuskantar tana zaune saman bed, ta ce ya fitan mata a ɗaki ya ce babu in da zai je har sai ta faɗa mashi me ta cewa warrior da ya hangota daga sama tana magana da su. Daga view na room ɗinsa ya hangota a kasa tana magana da wani warrior, ransa ta yi mummunar ɓaci, ya sauko kasa da sauri, sai dai ko da ya sauko bai ganta ba, sai huci yake yi ya hau nemanta, amma dik in da ya duba bata ba labarinta. Ashe da ta bar wajen warrior ɗin side na aunty MieMie ta nufa, kuma ita ta tsai da warrior ɗin tana tambayarsa wai a ina ake sayar da irin amor ɗin jikinsa (kayan yaki) ɗin nan nasu, shi kuwa ya ce mata basu kawai ake yi daga fadar King. Tsabar albarka yai mata yawa sai ta ce waye King ɗin kuma a ina yake dan zata je ne ya bata ita ma, wai kayan ya yi mata kyau na jarumta, kun san mutuniyar da shegen son harkar jarumta. Da warrior ɗin ya fahimci yarinta ne a kanta sai ya ce ta shiga cikin gida ta tambayi King za'a faɗa mata har ma a nuna mata in da yake, sai dai saboda nema balai irin nata wai ya bata takobin dake waist ɗinsa bari ta taɓa taji ya nauyinsa yake. Da kyar ya samu ya lallaɓata ta wuce ciki ta hanyar ce mata ai takobin baya fita daga waist ɗinsa. Abin da ta tsaya take faɗe kenan goyson ya gansu, dik hankalinsa ya bi ya tashi, ya zo yana tambayarta kuma har da ce mashi wai ina ruwansa da rayuwarta. To kun san anrigada an kashe mashi zuciyar, sai kawai ya zauna yana ta rokonta game da rarrashi, amma yarinyar nan fir taki sanar da shi. Dik hankalinsa ya yi mugun tashi. "Ni ka fita mun a ɗaki". Ta faɗa tana dalla mashi harara........ "Idan baki faɗa mun abin da nike son ji ba babu in da zan je". Ya faɗa on a serious note. Harara ta shiga jifansa da shi kafin ta ce. "Bazan faɗa ba tin da kai ba ubana ko mijina ko yayana or addana bane....." Da sauri ya tari numfashinta da cewa. "ALLAH ni mijinki ne, dan haka ki faɗa mun yanzu"....... Kallon up and down ta dalla mashi tare da murguɗa baki. "ALLAH ya kiyayye ɗan yaro da kai ka zama mijina, wai kai me zaka iya ma idan ka zama mijina? Kalleka.........". Bata kai karshen maganar ba ta dakata sakamakon ganinsa da ta yi a dab da ita, ya matso sosai kamar zai haye bed ɗin. "Yaro kuma me zaka iya idan ka zama mijina". Ya maimaita cikin kunan rai, dik da yasan kalamai ne na yarinta kawai take yi mashi wanda bata san ma maanarsu ba, sannan dik da sun kashe mashi zuciya kalaman sun sosa mashi rai, yana jin zafin dik time da zata ce mashi yaro kuma me zaka iya idan muka yi aure. (Ai da yana Omar ɗinsa ta yi wannan magana da bata karaba ko da wasa, dan ina da tabbacin sai ya gwada mata abin da zai iya tin kan a shafa fatiha) Tsoronsa tamkar zai kasheta, amma hakan bai hanata dakewa ta ce. "Karya na faɗa ne kai ba yaro bane? Ai yaro ne kai wanda babu abin da ya iya sai kukan ci....." Wani irin shaka da ya kaiwa wuyanta ne ya sanyata dole ta haɗiyi zancen cip, da karfi ya shake mata wuya tare da haɗata da jikin headboard na bed ɗin, ya matseta kafin ya karisa hayewa saman bed ɗin, idanunsa sun rikiɗe lokaci guda alamar ya ji zafin kalaman. Har wani huci yake yi, da kyar muryarsa na rawa ya ce. "Zan gwada maki abin da yaro zai iya yi". Ya faɗa idanunsa kansu suna rawa a kan fuskarta, gabaɗaya ilahirin jikinsa rawa yake yi saboda ɓacin rai, ya sha faɗa mata ta daina ce mashi yaro kuma babu abin da zai iya, hakan yana bakanta mashi over amma bata ji. Guyson mutum ne mai halittar gashi a jiki har wajen hannunsa da kuma kafafunsa, hakan yasa da ransa ya ɓaci dik gashin suka wani mimmiƙe. Kara matse mata wuya da karfi ya yi kafin ya ce. "Mekika tsaya yi wajen wancan warrior ɗin?!". Still dai muryarsa na rawa ya yi maganar. Ganin yadda ya rikiɗe mata tamkar mayunwacin zaki ne yasa ta yi wani mahaukacin razana, take jikinta ya fara kerma, murya baya fita sosai ta bashi labarin abin da ya haɗata da warrior ɗin. Takaici ne ya kara kamashi na ta tsaya ta yi magana da wani, zame hannunsa daga wuyanta ya yi ganin yana ƙoƙarin yi mata illah, yasa hannu da karfi ya fisgo wuyar rigar jikinta, gabaɗaya ta tafi tamkar zata faɗo saman kirjinsa ya dakatar da ita ta hanyar sanya hannu a tsakaninsu. Sai da ya daidaitata sannan ya kai hannu saman kirjin nata, ƴan matasan tula-tulanta ya ɗan shafa tare da kewayesu da hannunsa tamkar yana zana round a wajen kafin ya ce. "Da waɗan nan ƴan abubuwan naki ma ni kin mun kaɗan, maleji zan yi dake, amma har kike da bakin tambayar me zan iya yi idan na zama mijinki ko? Zaki san me zan iya yi a ranar da zaki kasa gane a duniya kike ko a kahira". Ya nisa tare da matsar da face ɗinsa dab da tata. "Waɗan nan sun mun kanana, ke kanki kin mun kaɗan, ba zaki iya ɗaukata ba, amma ita soyayya babu ruwanta da girma ko kankanta, a lokacin da ta so kawai zata shigeka ne, ba dan haka ba ni nasan kin mun ƙankanta, sai na yi renonki kin girma in ba haka ba a ranar farko mutuwa zaki yi, in baki mutu ba kuma ba zaki sake moruwa ba, ni babbar mace nike buri, wacce zata iya ɗaukata ba ke yar karamar da sai na yi reno ba!". Tin da ya fara magana tsoronsa da shakkarsa ya shigeta, ta natsu tsit tana kallon ɗan bakinsa, amma da ta ga yana ce mata yar karama, kun san ta da son girma, and mara kunya baya sake hali ko kashe shi ake yi, dan haka sai ta ce. "Wlh ni ban yi maka ƙanƙanta ba saboda ni ba yarinya bace, a kanka ne zan mutu? Irinka goma ma zan iya ɗauka ba tare da na gaji ba". Murya na rawa ta yi maganar, and ta ce irinsa goma ma zata iya ɗauka ba wai tana nufin wancan kalmar ba, tana nufin nauyi, dan a haka ta fahimci zancensa, da ya ce ba zata iya ɗaukarsa ba ta zaci irin goyo haka ko ɗauka a kafaɗa irin wanda ake yi wa yara, shi ne dan ta gwada itama jaruma ce wai irinsa goma ma zata iya ɗauka, zata iya goyawa kenan. Watau kurici dangin hauka ne, bama fa tasan me miji yake nufi ba, bata san me ake a aure ba, sai rashin ji da rashin kunya ta iya. Ai da jin kalamanta sake fusata ya yi har bai san lokacin da ya matseta da jikin headboard na bed ɗin ba. "Irina goma zaki iya ɗauka? A ina kika san hakan? Ko kin taɓa ɗaukar wani ne?". A kule ta ce. "Sau nawa ma ina ɗauka". Ta faɗa tana ƙoƙarin kwace kanta, dikkan sun fahimci juna ne a baibai, ko da yake ita ta kwaɓe zancen, dan ita ce bata san ma'anar kalamanta ba. Haba take kishin maza ta motsa, har wani irin huci yake yi ya ce. "Ban yarda dake ba, dama wasu mutanen kauyen ba kula da kai suke yi ba, dole zan duba virgin ɗinki yanzu, dole zan duba ko kin taɓa baiwa wani damar shiga gonata, no wonder, shiyasa kike da rashin kunya har haka, shiyasa idanunki suka bushe, shiyasa har kika san ki ɗauki goma irina, ba banza ba, ashe kin taɓa ɗauka a baya". Kusan cikin fitar hayyaci ya yi maganar, zafin kishi na neman yi mashi illah a zuci. Ita dai da bakinta yaki mutuwa ne ta ce. "E na taɓa ɗauka ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, kuma rashin kunya ne na yi ɗin tin da ba ubana bane kai". Wani irin tukukin zafi ne ya turnuke zuciyarsa, ji yake tamkar kansa zai rabe gida biyu, idanunsa suka tsananta ja, jikinsa har yana wani irin tsuma tamkar ya dawo Omar ɗinsa na ainahi. "Ban yarda dake ba, dole zan duba virgin ɗinki, kuma wlh idan har na tabbatar da abin da kika faɗa, kin taɓa bawa wani dama ya shiga gonata, wlh ba zan yi kaffara ba sai na kasheki da hannuna!!". Cikin kakkausar murya ya yi maganar. Ita kuma da wauwata ya gama da kwakwalwarta sai ta ce. "Gona kam ba ɗaya ba ba biyu ba na sha shiga". Tana nufin ta sha shiga gonaki a kauyensu, dan ita a tinaninta faɗa yake yi a kan ta taɓa shiga gona, kun san har yanzu larabcinta da saura, shi ne take faɗa mashi ai ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba ta sha shiga gona, amma nufinta gonan bappanta. Datse idanunsa ya yi gam tamkar zai fashesu, da karfi ya daddage ya dalla mata wani gigitaccen marin da sai da ya turata hutun ɗan lokacin. Fisgota ya yi da karfin gaske ya kwantar a saman bed ɗin, Dr Omar zai yi bincike!. A farko bata san me yake shirin yi ba, dan ta ɗauka dukanta zai yi, sai da ta ga yasa hannu ya keta rigar jikinta ya jefar ne ta fahimci kaya yake son cire mata, a hakan ma bata fahimci abin da yake son dubawa ba, ta zaci zai cire mata kaya ne ya zaneta tin da ta ga a kauye malamarsu Inna Rabi sai ya cire masu zani ko sai ta ɗage shi sama take zane kafafunsu, to sai ta ɗauka kaya zai cire mata ya zaneta. Nan ta fara kuka tana faɗin kada ya cire mata kaya. Sai wani irin huci yake yi tamkar zai kama da wuta, cikin fushi ya ce. "Idan na sake jin bakinki sai na kashe ki!!". Yana gama faɗar hakan ya damki kafafun wandan jikinta baya ya cire botir ta sama ya kuma zuge zip kasa, ya damki kafafun wandan da karfi ya rabata da shi. Ya rage daga ita sai pant. Ai wani irin zabura ta yi zata sauka ta gudu, a miliyan ya danketa tare da kara kwantar da ita, ƙoƙarin kwace kanta ta yi domin ta rufe tsiraicinta, amma ina, ta gagara, nan ta fara ƙoƙarin yin ihu ko za'a kawo mata ɗauki, ai hayewa kanta ya yi tamkar wanda zai yi wancan abin, ya toshe mata baki da hannu ɗaya kafin ya jawo rigarta, ya daddaneta ya ɗaure hannunta da shi, sannan ya jawo veil ɗinta ya ɗaure mata baki da shi. Ai sai yau ta tabbatarwa da kanta yana da shegen karfin da yake cewa yana da shi, dan kuwa da ya danneta ko motsi bata iya yi ba har ya ɗaureta, ga shi kuma yadda ya yage mata kaya ya razanata, ta girgiza da shi. Baya ji baya gani haka ya cire mata pant, zafin kishi yasa gabaɗaya ya fita a hayyacinsa. Kuma cikin fushi yake komai, tana ji tana gani ya cire mata kaya dikka kafin yasa hannu ya buɗe kafafunta, tsabar yana cikin ɓacin rai ko sha'awarta ma bai ji ba, abin da yake son dubawa kawai ya kafa kai a wajen. Lokaci guda kuma ya ɗauke wuta, tamkar wanda aka bugawa guduma a tsakar kai, cikin zafa ya ɗago da kansa daga kallon da yake yi wa gaban nata ya kalli fuskarta, hawaye sun gama wanke mata fuska, da sauri ya diro kasan bed ɗin yana dafe kansa dake barazanar tarwatsewa. Waje ya nufa yana wani tangal-tangal tamkar zai faɗi, yadda kuka san yana cikin maye. Har ya kai wajen kofa kome ya tuna sai ya yi zafan juyowa ya dawo, da sauri ya haye saman bed ɗin. Yana ɗan kawar da kansa ya ɗauko pant ɗin nata, kamar yadda ya cire mata haka ya mayar mata da komai, har riga ya sanya mata, gagara ɗagowa ya kalli cikin idanunta ya yi, ita ma dai dik rashin kunyarta ta gagara kallonsa, ta yi kasa da kai tana kuka kuma ta natsu tsit babu hayaniya ko shirin guduwa. Shiru ya zauna a tsakiyar bed ɗin yana sauke huci a hankali-hankali, alamar yana hucewa kenan. "I'm so so sorry". Shi ne kawai abin da ya iya faɗe tare da yunkurawa da sauri ya diro kasa, bai sake waiwayota ba ya yi waje, zuciyarsa ce take bugawa da karfi-karfi, da sauri ya afka room ɗinsu, Ronnie na kwance a saman bed, ba ko sallama ya afko ciki, yana zuwa ya faɗa saman bed ɗin shi ma, Ronnie mai bandeji a goshi yana tambayarsa lafiya, amma ina babu amsa sai aikin sauke dogon ajiyar zuciya. (OMAR YA GOGE MUN HADDA. KO ME ZAI BIYO BAYA?🤔 ANYA MA WAI BIG BRO BAI KARYA MAGANIN DA SUKA BASHI YA KOMA AINAHIN OMAR ƊINSA BA KUWA? DAN DAMA KUNGA BIG BRO YA ZO HAR ƊAKI YA GANSA HMMMM.) -----------------------🔥 Bayan ta kammala cin abincin nata, miƙewa ta yi ta nufo wani sofa one seater dake kusa da bed ɗin, dik wani motsinta a kan idanunsa ne. Saman sofar ta zauna suna fuskantar juna, kuresa da kallon soyayya ta yi, shi ma kallonta yake babu ko kyaftawa. Almost 5 minutes for silent ta katse masu shirun da cewa. "King of heart wai kai baka gajiya da kallo ne? Ko kyafta idanunka fa baka yi". Cikin ɗan madaidaicin shagwaɓar da ba zai tada hankali ba ta yi maganar. Almost 2 mins ya ɗauka kafin ya bata amsa da. "Kin taɓa ganin inai wa wani wannan kallo bayan ke?"...... Kai ta girgiza alamar a'a tana sakin murmushi. Ɗan jinjina kai ya yi. "To kallon naki ne ke kaɗai". Haba ji ta yi tamkar an bata aljanna, ta ɗan kwantar da kanta jikin hannun sofar tana binsa da wani irin musulmin kallo kafin ta rungumo hannayenta a kirjinta. Gera ya ɗan ɗaga mata alamar ya ne?. Ɗan girgiza kai ta yi kafin ta ce. "Yadda na zauna haka ina jin tamkar na zauna a jikinka ne, yanda na rungumo hannayena a kirji ina jin tamkar kai na rungumo, ina fatan mu yi aure mu mallki juna dan in yi maka irin soyayyar da na tanada maka". Tin da ta fara magana yake kallon ɗan bakinta har ta kai aya, nisawa ya ɗan yi kafin tamkar mai raɗa ya ce. "Why sai mun yi aure? Yanzu ma ai kina da dama".......... Taso dakatar da murmushin dake kan fuskarta, amma sai ta daure ta cigaba da yi dan kada tasa ya ji babu daɗi, abin da yasa murmushin nata ya so dakatawa shi ne wannan magana da ya yi yasa ta tuna ashe fa ba musulmi bane, abin ya yi mata zafi, daɗin soyayya yasa ta manta ba musulmi bane. Bai san addini ba shiyasa zai ce yanzu ma tana da dama. Jin ta yi shiru ne yasa ya miƙo mata hannunsa a kan ta zo jikinsa. Ji ta yi jikinta ya kara yin sanyi, da kyar ta iya cewa. "King of my heart, ka bari sai mun yi aure ka ji? Zan zo jikinka har sai ka gaji". Cikin raunin murya ta yi maganar. Da hannu ya yi mata alamar meyasa sai sun yi aure? Tamkar zata yi kuka ta ce. "Saboda addinina bai lamunta ba har sai mun yi aure, idan muka yi aure muna da damar yin abin da muke so da juna". Ya ɗan ji mamakin maganganunta, amma sai ya kawar da mamakin da cewa. "Tin da haka kike so mu yi auren mana". Tamkar zata ce mashi ba zai yiwu ba har sai ya musulunta, sai kuma ta tina abin da ya faru ranar can da ta ce mashi ya musulunta, dan haka yanzu sai ta safawa kanta lafiya da cewa. "Zamu yi amma ai kasan ba'a nan ba, ka bari sai mun koma birninmu, kaga a nan su momma suna ganin dama already mu ma'aurata ne, to kaga babu halin kawo zancen aure a nan". Jinjina kai ya yi dan ya aminta da batunta, suka yi shiru tare da zuba juna ido suna zuba kallon love mai narka zuciya. Tsabar sun shagala sai jin babban masallacin king suka yi ana kiran sallar mangariba. Da sauri Sweetie ya miƙe ta nufi toilet.......... Da ido ya bi kyawawan mazaunanta da kallo yana haɗiyar yawu har ta kurewa ganinsa, hannu yasa ya ɗan shafi saitin zuciyarsa, a cikin ransa ya ce. "Kwantar da hankalinka wannan kaya dikka mallakinka ne, Omaish taka ce". A fili kuma nisawa ya yi tare da jawo bargo, har wani irin zafi yake jin gabansa tanai mashi saboda azaban sha'awarta da yake ji, ƙoƙarin danne kansa yake yi dan a cewarsa kada ya kashe Omaish ɗin tasa...... A haka ta fito ta same shi, dadduma da hijabi ta ɗauko ta shinfiɗa ya kalli gabas, har zata tada kabbara sai kuma ta juyo ta kallesa, cikin sanyin murya ta ce. "Ko zaka zo mu yi tare ka gwada?". Da sauri ya girgiza mata kai alamar a'a har da ɗan girgiza hannu irin totally bai yi mashi ba. Dama tasan za'ayi hakan shiyasa ma bata wani sanya abin a ranta ba, tambayar sama-sama take a ranta. So da ya nuna baya so murmushi ta yi tare da juyawa ta tada kabbararta, cikin natsuwa ta fara sallah, dik abin da take yi a kan idanunsa har ta idar, nan ta zauna tana addu'oi da tilawar Alqur'ani mai girma har lokacin sallar ishai ta yi, haka ta miƙe ta yi sallah, bayan ta idar ta zauna yin addu'oi, dik wani motsinta yana kallonta sosai, ko kusa ko alama addininta bai bashi sha'awa ba, sai ma gani da yake yi ɓata lokaci take yi, ta ja mashi lokaci, da yanzu wannan ibada ta zauna yi na awanni ai da suna tare yana kallonta tana zuba mashi romantic words, sai ya ji ya kara tsanar addinin nata. Big Bro ba zai taɓa yarda ya musulunta ba ko ya ji sha'awar addinin Musulunci ba har sai ranar da suka farga suka cire wannan cross dake wuyar tasa, wannan cross yana rike da kaso tamanin cikin ɗari na kiyayyarsa ga addinin musulunci, ba haka kawai cross ɗin ta kasance a wuyarsa ba, tsarata aka yi, tin yana karami ya taso da ita a wuyarsa, bai taɓa cireta ba dik me zai faru, ba kuma zai taɓa yarda a rabashi da ita ba, dan tamkar da ruhinsa aka haɗasa, an dasa mashi kaunar cross ɗin fiye da kansa, baku yi mamakin yadda cross ɗin take canza launin daga yanayinsa ba? Idan yana farinciki takan canza, kazalika in yana bakinciki ta bada launi daban, har wani wuta take yi idan ya ɗauki zafi, batu na gaskiya rabashi da wannan cross ɗin fa sai wani ikon ALLAH kawai, dan dik cikinsu babu wanda zai iya, bama zasu farga da shi ba bare har su yi kokarin cirewa, ba zasu taɓa yin tinani wata babbar illace garesa ba cross ɗin, zasu yi ta matsa mashi ne kawai ya musulunta, a dik time da suka yi mashi maganar musulunci kuma faɗa zasu yi dashi, dan baya son jin sunan addinin ko kaɗan, babu wanda zai kawo a ransa cewa shiri aka yi mashi, ba zasu farga ba! Ko mutuwa momma take da sunan in bai musulunta ba, wlh sai dai ta mutu, ba zai ragawa kowa a kan batun musulunta ba, zasu yi ta ganin laifinsa, su yi faɗa da shi, su juya mashi baya, amma dik a banza, dan ba zai sauya ba har sai ranar da ALLAH ya kawo wani sanadi wannan cross ta fita daga wuyar, idan sun samu suka rabashi da cross ɗin to sun ci kaso tamanin na yakin saura kaso ashiri wanda shi ma abu ne a jikinsa da zasu rabashi da shi, MENENE?.......... Akwai case fa. --------------------🔥 Ita kuwa bayan ta kammala addu'ar miƙewa ta yi, a mutunce ta tattare kayan ibadar tata, ta mayar da shi mazauninsa, ya fahimci ta ɗauki addinin nan nata da mugun mahimmanci, dan tin daga kan yadda take tarairayar dadduma da hijabin nan nata tamkar kwai ya fahimci hakan. Saman sofar da ta tashi ta koma ta zauna tana kallonsa. "In je in kawo maka abinci ne?". Ta faɗa tana mai da kallonta kan bargon da ya lulluɓa a ciki, ta ɗan yi mamakin ganin ya lulluɓa, saboda tasan yana cewa kingdom ɗin akwai zafi, kullum kure gudun Ac yake yi, amma wai yau ya lulluɓa. Hannu ya fito da shi daga cikin bargon ya miƙa mata, tamkar wanda yake a cikin maye ya ce. "Please Maysh come close to me". Wani irin harbawa zuciyarta ta yi jin irin sauyin da voice ɗinsa ta yi, amma sai ta dake da cewa. "Please king of heart, ka bari sai mun yi aure ka ji?". Tana shagwaɓe fuska dan ta ci galaba a kansa ta yi maganar. Can kasan makoshinsa cikin wata iriyar murya mai narka zuciya ya ce. "Please help me, ba zan yi maki abin da kike zato ba, just kawai in ji ɗumin jikinki a nawa ne, saboda sanyi nike ji over". Da ka ji muryarsa kasan yana jin azabar halin da yake a ciki. Mugun tausayi ya bata ganin yadda ya zama, jikinsa har tana ɗan kerma, dogayen yatsun hannun nan nasa har suna ɗan rawa, kuma abin da yasa ya kara bata tausayi shi ne yadda baya son yi mata abin da bata so, yana da damar yi mata dik abin da yake so ko taki ko ta so, shi kansa jawota jikinsa kun san idan ya yi niyya ai bata sanin tayaya ma take tsintar kanta a jikin nasa, amma yanzu tambayarta yake yi ta aminta da kanta dan kada ranta ya ɓaci, lallai ba zai yi mata wani abin da ba daidai ba, kuma ba ƙaramin so yake yi mata ba. Cike da tausayinsa ta ce. "Nasan baka taɓa yin magana biyu, tabbas na yarda da kai cewa ba zaka mun abin da banaso ba"....... Tin da ta fara magana kallonta kawai yake yi har ta kai karshe, sannan ne ya kara miko mata hannu dan a yanzu magana ma taki yiwuwar mashi. Slowly ta miƙa mashi nata hannun, cikin zafa ya jawota jikinsa, wani irin zazzafar runguma da ya yi mata har kamar zai ɓallata, ya matseta a jikinsa sosai tamkar zai mayar da ita cikinsa, ya gyara ya shigar da ita cikin bargon nasa, ya kai hannu yana shafa kyakkyawan gashin kanta, yana son yin kissing ɗinta amma ya rigada ya yi alkawarin ba zai yi mata komai ba har sai ranar da ita da kanta ta bashi dama, sai ya share batun kiss ɗin yana cigaba da shafe gashin kanta yana tinanin yakamata su koma birninsu, dan ya gaji da kingdom ɗin nan, dik a takure yake. BAI FA MANTA DA TUKUICIN DA YA CE ZATA BASHI BA, DA ALAMA SPECIAL ABU YAKE BUƘATA SHIYASA BAI TADO DA MAGAMAR BA, KAI BIG BRO ƊIN NE SAM BAKA GANE MASHI!!. Yayin da ita kuma take ta faman tinanin UBANGIJI ALLAH yasa ya yi gaggawar musulunta, dan tana burin su mallaki juna. Sun jima a haka shiru babu wanda ya ce da wani uppan har tsawon good 40 mins. Sannan ne ta ɗago da kanta da nufin ta yi mashi magana kawai sai suka ji ana knocking. Ai zabura ta yi zata bar jikinsa, ko kaɗan bai dakatar da ita ba, kasa ta diro, dik hankalinta a tashe ta ce. "Zan shiga toilet dan nasan waye ne". Ya fahimci so take ta ɓoyewa wanda yake knocking ɗin nan shi ne har da wani zata shiga toilet, amma sai ya jinjina mata kai kawai, da sauri ta gudu toilet dan tasan Smart ne ko Momma, su biyu suke zuwa room ɗin nan.. Gagara miƙewa shi kuma ya yi, daga in da yake kwance ya ce. "Omerish ka shigo ciki". Smart dake tsaye cikin sleeping dress masu shegen kyau ne ya yi mugun mamakin jin abin da ɗan uwan nasa ya ce na ya shigo ciki, dan haka sai ya turo kofar da sauri ya shigo, sabida a tinaninsa wani abin ne ya sami ɗan uwansa. Gaban bed ɗin ya karisa, tin da ta shigo idanunsa kan Big Bro, ya zaci zai gansa cikin ciwo, sai ya gansa ras. A gefen bed ɗin ya zauna yana kallonsa cikin ido ya ce. "Are you okey?". Shiru Big Bro bai amsa mashi ba, yana ta dai kallonsa. Smart bai lura ba ga shatin ɗan bakin Pretty da jan baki a kumatunsa, da zai fita ne ta bashi sumbata, ya manta bakinta akwai jan baki, to shi Big Bro yake kallo yana tinanin yadda Sweetie tai mashi ranar a birninsu. Ganin bai yi magana bane yasa Smart kai hannu ya yaye bargon da ya lulluɓa, ai zaro idanu ya yi kafin ya kai mashi dukan wasa a kirji yana faɗin. "Ka ce mun kana kan network ne mana in tafi in baka waje, shi ne zaka sa in shigo? Nasan saboda ni sister ta ɓuya ko? Dan ban ganta a nan ba, kai kaɗai kuma ba zaka hau network ba, dole kuna tare kafin in zo". Harara Big Bro ya wurga mashi bai dai yi magana ba. Sake kai mashi dukan wasa Smart ya yi yana faɗin. "ALLAH guy ɗin nan kana abin da kaso, kana more mana sister son ranka, amma bari in dubaka in gani ka bata samartakanka ne ko kuma dai dani da kai dik stage ɗaya muke, sai dai mu rage zafi". Ya kai karshen maganar dan neman tsokana yana kai hannunsa jikin wandon Big Bro, wai zai duba samartakansa. Ai wani irin damka Big Bro ya kai mashi a gashi da karfi. Tafiya Smart ya yi ya faɗa jikinsa yana faɗin. "Saboda zan duba ne zaka mun mugunta ko? To sai na gani, dan ban yarda da kai ba, muna nan muna jiran babys ku barmu a shanye a rana". "Omerish zafa ka daku, ina ruwanka da abin da ko mamallakiyarsa bata taɓa gani ba?". Can kasa kasa ya yi maganar. Ɗago kai daga kirjinsa Smart ya yi suna fuskantar juna. "Dubawa fa kawai zan yi, amma yanzu ai na samu amsa, watau sister ma bata taɓa gani ba ko? ALLAH sarki i pity you my love, sai dai ka rage zafi da kiss". Yadda ya faɗa ba har zuciyarsa bane, cike da iyashege da zolaya ya faɗa, hakan yasa Big Bro ya ce. "Kai anya ma kana da samartakan nan Omerish? Anya ba cutar sister ɗinmu zaka yi ba? Dan ga dikkan alamu kasan wannan harka". "Kai kai kai, daga magana zaka mun sharri, ni da nike malami ina ruwana da mata? Sisterku kawai zai baiwa kaina". Big Bro na binsa da wani irin kallon kauna da kuma kallon tuhuma na wasa ya ce. "Ban yarda da kai ba Omerish, sai na dubawa sister ɗinmu dan kada ka cutar mana da ita". Ya faɗa tare da yunkurawa, kafin Smart ya farga sai ganinsa ya yi gabaɗaya a saman bed ɗin Big Bro ya dannesa, watau tin da Smart bai duba samartakansa ba shi bari ya duba nasa. Ƙoƙarin kwatar kansa Smart ya fara yi yana faɗin. "Zaka kallanmun abin da shalelena mamallakiyar abin bata taɓa gani bako? To wlh baka isa ba, yadda ka killace naka sai mamalkiyarsa kawai zaka nunawa nima babu wanda zai kallewa yar tsana kayanta". Shi dai Big Bro ko uppan bai sake cewa ba, yasa hannu ɗaya ya riko hannayen Smart dikka biyu, sannan ya kai ɗayan hannunsa zai zame wandon Smart kasa. Ai da karfi Smart ya daddage ya yunkura ya miƙe, wani irin runguma ya yi wa Big Bro da karfi yana faɗin. "ALLAH ba zaka kallanwa yar tsanata kayanta ba, a kan me?"......... "Okey shi ne kai ka zo zaka kallanwa Maysh abarta ko? To baka isa ba". Cewar Big Bro. Da alama sun mance da Sweetie tana ɗakin, kuma dik abin da suke yi tana jinsu, farinciki ne ya kamata jin abin da Big Bro ya faɗa, watau ya sallama mata komai nasa bawan ALLAH. Ƙoƙarin kare kansa Smart ya fara yi, Big Bro kuma yana kokarin nuna mashi fifikon karfi, da kyar Smart ya sha, ya kwaci kansa ya sauko kasan bed ɗin, sai a lokacin ya samu damar hararar ɗan uwan nasa, sannan ya ce. "Haka kawai zaka kallewa beb ɗita kayanta, sai na faɗa mata, kuma idan ka gani ma idanunka ne zasu makance dan mallakin wata ka gani". Yunkurawa Big Bro ya yi zai kamasa, da gudu ya ja baya yana harararsa. "Zankamaka ne, sai nai maka sabon kaciya". Big Bro ya faɗa yana sake dalla mashi hararar wasa. "E to idan ka kamani ɗin sai a sake gwadawa, yanzu kam dai ALLAH ya kwaceni, ni dik bama wannan ba, saura 30 mins daddy ya farka, zo muje wajensa ya farka a idanunmu". Kai Big Bro ya jinjina. "Ka je zan sameka a can". Cikin zolaya Smart ya ce. "Watau dai ba zaka zo ba sai ka tumurmushe mun sister ɗita ko? Sai ka rage zafi....." Bai kai karshe ba Big Bro ya rarumi pillow ya jefesa da shi yana kallon kofar toilet. Smart ya gane karatun, watau Sweetie tana ciki tana jinsu, kashewa Big Bro ido ɗaya ya yi alamar ya gane tare da jefo mashi pillow ɗinsa a fuska ya nufi waje yana faɗin. "Kada ka ɓata lokaci please, nan da 30 mins zai farka". Kai kawai Big Bro ya jinjina tare da komawa ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya, shi kuma Smart ya yi waje. Yana fita Sweetie ta fito tana toshe baki saboda dariya da yake son kubce mata. Saman sofa ta wuce ta kwanta, ta ja bargo ta lulluɓa har kanta. Binta da kallo ya yi for almost 5 minutes, ta yi shiru cikin bargo tana murmushi, sam bata ji motsinsa ba sai gani ta yi an yaye bargon. Bai yi mata magana ba yasa hannu ya ɗauketa cak, ta ɗan tsorata amma sai ta dake tare da bin in da ya nufa da ita da kallo. Toilet suka shiga, bai sauketa a ko'ina ba sai wajen wash hand base, da kansa ya ciro masu brush, ya zuba dik wasu kayayyakin kamshi na goge baki, ya miƙa mata nata ya ɗauki nasa. Cike da farinciki ta karɓa, kusan a tare suka kai brush ɗin bakinsu suka fara gogewa a natse gwanin burgewa. Unexpected taga yasa hannu ya karɓi nata brush ɗin daga bakinta ya ajiye a gefe, ya ciro nasa daga bakinsa ya sanya mata a baki tare da riko haɓarta ya hau goge mata bakin a hankali-hankali. Ai suman tsaye ta yi, dan bata taɓa tsammanin hakan ba, ashe ya iya soyayya, sai dai dogon magana ne baya ya yi, watau baya tsayawa yin love words, a aikace yake nuna komai, ba zance a baki ba, ba zai taɓa cewa ga abin da zan yi maki ba, sai dai ki gansa a aikace. Ganin yadda ta kura mashi ido ta cikin mirror wajen ne yasa ya saki haɓarta ya kai hannun nasa ya ɗan rufe mata idanun. Murmushi ta yi kafin ta zame hannunsa, muryarta baya fita sosai saboda brush da yake yi mata ta ce. "Ina ruwanka dani ina kallon mijina?". In a cool way sosai ya ce. "Kina kallonsa ko kina mamakinsa?"............ "Dikka biyu, amma waye ya koya maka soyayya ne?". Zare brush ɗin daga bakinta ya yi yana mayarwa nasa bakin, sannan ya ɗan rankwafo kanta, a kunne ya fara yi mata raɗa kamar haka. "Maysh kina da dik abin da nikeso a tattare da mace......". Da sauri ta ɗago da kallonta ta cikin mirror ta sauke a kansa, zazzare mashi idanu ta yi, mamaki ne tamkar zai kasheta, har bata san lokacin da ta ce. "Dama kasan mace ne?". Shiru bai bata wannan amsa ba, amma tabbas ya sani mana, kada ku manta dik abin da mutanen birninsa suke yi a kan idonsa suke yi, harta fyaɗen da master devil ya yi wa Floris a kan idonsa ne, kuma ai shi ba jahili bane, ya yi karatun da dik Kingdom of Power ɗin babu wanda zai gwada mashi ilimi, aljanu fa suka karantar dashi, kun taɓa jin kiraar Alqur'ani daga bakin aljanu kuwa? Wlh mugun ilimi garesu, amma fa na kirkin cikinsu, wasu na banzan wlh da an fara yi masu rukia zaku ji suna karisarwa, kana ɗauko aya zasu karisar maka, haka ilimin boko na zamani, karatu ne a kansu fiye da ƴan adam, to su suka karantar da shi kunga kuwa bakwa haɗa iliminsa da na mutane ba, dan haka yasan komai, kawai dai feeling ne a lokacin bashi da shi, amma idan ya kalli mace mai cikar kirji da baya haka tana burgesa, ba wai dan ya biya buƙata da ita ba dan bashi da feeling, kawai dai zata burgesa, to ɗabiarsa na son mace mai irin wannan halitta shiyasa idan ya gani take burgesa, sai da ya fara jin feeling ya fahimci dalilin da yasa a baya mace mai irin wannan halitta take burgesa, kunga kuwa ai dan ya ce ga abin da yake so a jikin mace ba abin mamaki bane tin da yasan komai. Kunna tap na wash hand base ɗin ya yi, ya wanke brush ɗinsa da suka yi amfani da shi haɗe da nata da ya ajiye gefe, sannan ya tarbo ruwa a kyawawan fararen hannunsa ya kawo mata kusa da baki domin ta kuskure baki. Wurga eyesball ɗinta a kan cup na wanke baki dake wajen ta yi, a sanyaya ta ce. "Ga cup ai ko baka gani bane". Kallonsa a kanta ta cikin mirror ɗin ya ce. "Ba zaki yi amfani da ruwan hannuna bane?". Watau dai ya ga cup ɗin, da hannunsa ya yi niyyar bata ruwan. Da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a zata yi tare da buɗe ɗan bakinta ya ɗauraye mata, sannan ya ɗauraye nasa. Sake rankwafowa kanta ya yi tare da cewa. "Zomu yi wanka a tare". Da sauri ta ɗago ta kallesa, sai kuma ta ɗan turo mashi baki kafin ta ce. "Sai mun yi aure". Iska ya ɗan furzar kafin ya nufi wajen Jacuzzi ba tare da ya sake yin magana ba. Da ganin haka ta yi gaggawar fita ta bashi waje, dan ta san karamin aikinsa ne ya tuɓe a gabanta ya shige cikin ruwa. ALLAH sarki ya so su yi wanka tare, amma ba komai, WAI A HAKA MA FA BASU YI AURE BA YAKE BATA IRIN WANNAN KULAWA, IN ANYI AURE INA GA HAƊA KAYANA ZAN YI IN BAR MASU GIDANSU, DAN SAI SUN GUGE MUN HADDAR DA YA RAGE A KAINA! DA YAKE ALREADY SONTA NA RANSA KUNGA SUN MANNE DA JUNA!. Tana fitowa ta gyara mashi bed ɗinsa, dan taga yadda kuyangu jiya suka gyara, so bata son su rinƙa shigo mata ɗaki, shi ne ta ce bari ta gyara da kanta. Ta kuwa iya tsab, ta gyara komai sannan ta koma kan sofa ta kwanta, a haka ya fito ya sameta, a gurguje ya shirya cikin tsadaddun sleeping dress ɗinsa irin na jikin Smart, sannan ya nufi kofar fita. "King of heart zan je wajensu Mahnoor sai in ɗauko mana abinci". Ta faɗa tana miƙewa. Jinjina mata kai ya yi kafin ya ce. "Kada ki jima". Daga haka ya nufi waje. Daɗi sosai ta ji, sai ta miƙe ta shiga toilet dan ta yi wanka ta zo ta je wajensu Mahnoor, bata san suma jira fitowarta kawai suke yi ba. ---------------------------🔥 Kai tsaye bedroom na King ya nufa, zaune ya isko su Smart, King ya farka suna ta hira da shi, dama Big Bro suke jira ya shigo sai a cigaba da bada labari daga in da ya tsaya, dan da saura sosai. Gefen bed ɗin kusa da King ya zauna yana faɗin. "Good evening Dad"...... Hannu King ya kai ya shafi kansa kafin ya ce........ Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 28 Gefen bed ɗin kusa da King ya zauna yana faɗin. "Good evening Dad"...... Hannu King ya kai ya shafi kansa kafin ya ce. "Evening how was your day?". Shiru ya yi bai sake amsawa ba, sai ya mayar da kallonsa a kan Ramish dake ta binsa da kallo shi ma. Gera ya ɗagawa Ramish ɗin alamar kallon lafiya kuwa?. Nisawa Ramish ya yi tare da cewa. "Wlh mugun kyau kake yi mun, ban san meyasa bani gajiya da kallonka ba, good evening". ........... Ɗan kawar da kansa ya yi ba tare da ya amsa gaisuwar bama. Smart ne ya capki zancen Ramish da cewa. "Yanai maka kyau ko? To wlh ka kiyayyi heartbeat ɗinsa ta jika, kishin balai ne da ita, nan zata ce bata yarda ba, za fa ta iya kwakwale maka idanu a kan kallonsa king of heart". ........ Dik da Big Bro na harararsa sai da ya kai karshen maganar abinsa. Nisawa Ramish ya sake yi kafin ya ce. "A'a babban yaya, ba zan gansa a gabanta ba ai, sai in ni da shi ne kawai, kuma mu ai kannen miji ne zata kula damu"........ In a cool way sosai Big Bro ya ce. "Ramish kana biyewa Omerish ko? Dakuwa zaka yi, zai kaika ne ya baroka". Shi dai king sai murmushi yake yi yana kallonsu.......... "Ni kam ai dole in biyewa babban yaya, zan goyi bayanka amma a lokacin da babu babban yaya a wajen, tare ka zo ka ganmu, kaga dole in cigaba da goya mashi baya". Ramish ya faɗa cikin zolaya. Smart ne ya ce. "Yauwa ni kuma zan tsaya maka idan za a dakaka, zan tayaka faɗa". "Ai haɗeku zan yi in daka ɗin". Big Bro ya faɗa yana mai da kallonsa a kan king. Gera guda Smart ya ɗaga kafin ya ce. "Muna da sister fa! Kana tinanin zata bari ka dakemu ne? Ai mu a team ɗinta muke". Big Bro bai sake cewa komai ba, King ne ma ya katsesu da cewa. "To ni kuma ina team ɗinsa, zaku saka shi a gaba ko? Omerish Zunaira ta zo ne?". Cike da mamaki Smart ya kalli king kafin ya ce. "A'a Zunaira bata zo ba, meyafaru?"...,..... Dikkansu mai da kallonsu a kansa suka yi, a sanyayye ya ce. "To waye ya yi maka kiss a kumatu? Nasan Zunaira ce kawai ke yi maka hakan". Kallon Big Bro Smart ya yi, harara Big Bro ya dankara mashi kafin ya ce. "Dad matarsa tai mashi, haka ya zo mun ɗaki da shi a kumatu dan ya nuna mun shi ɗan duniya ne". Cewar Big Bro. Zazzaro idanu King ya yi kafin ya ce. "Mata kuma?". Kai Big Bro jinjina, dawo da kallonsa gabaɗaya a kan Smart King ya yi kafin ya ce. "Omerish yaushe ka yi aure bansani ba?". Wani dogon numfashi Smart ya ja ya sauke a hankali kafin ya zayyanawa king dik yadda aurensa ta kasance daga farko har karshe. Shiru King ya yi na a kallah mintuna uku kafin ya ce. "Amma kasan da cewa wannan yarinyar yar Omranish ce ko?". A karo na biyu Smart ya kalli Big Bro kafin ya ce a'a bai sani ba. Nisawa King ya yi kafin ya ce. "Waɗan nan ƴaƴa guda biyu ƴaƴa Omranish na karshe kenan, na amaryarsa da ya aura ne kafin ya mutu (king ma yana tinanin babansu Hoorain mutuwa kawai ya yi ba su Zarina suka yi mashi kullah kullah ba.) kuma su ne ƴaƴan da Omranish ya baiwa karagar tsafinsa a hannunsu, saboda rasa ɗansa na farko Hoorain da ya yi, ɗansa na biyu mahaifiyarsa ta mutu da shi a ciki (Kamran da Mamma kowa yana zatan mamma ta mutu da cikinsa ne.) to bashi da wasu ƴaƴa sai wannan ciki na amaryar tasa, shiyasa tin ƴaƴan suna ciki ya kudirta a ransa sune magadansa, su ne zasu tsaya ko bayansa, shiyasa ya basu karagar tsafinsa, amma abin da ban sani ba shi ne ya aka yi ƴaƴa suka rayu bayan ance mahaifiyarsu ta mutu a lokacin haihuwarsu? Dan tabbas nasan ƴaƴan biyu ne, kuma waɗan nan yara suna mugun kama da Omranish shiyasa na ce sune waɗan nan autars ɗinsa"............. Sarauta sai ɗan sarauta zai iya gane me a cikinsa, kuna ganin King kamar bashi da labarin sauran masarautu me suke ciki, ashe yasan komai, ba zaku tashi sanin masarauta ta san me yake gudana a wata masarautar ba sai magana ta haɗa, hmmmmm suna sane da komai da junansu ke yi fa, ashe shi yasan mom twis, tasan lokacin da daddyn su Hoorain ya aurenta, kai King ma ya iya sa ido ashe, sai ka gansa kamar shiru-shiru. King yana kai karshen maganar Smart ya cabke da cewa. "No wonder ƴar tsana take abin da take yi, ashe auta ce". Kallon tsab King ya yi wa Smart, ya fahimci lallai Smart bai san me ake cewa tsafi da sharrin sarauta bane shiyasa bai ɗauki maganarsa da muhimmanci ba har yake cewa wai saboda Pretty auta ce yasa take abin da take yi. Shi kuwa Big Bro amsawa King ya yi da cewa. "Amma Omranish yana a raye ko?". Kai King ya girgiza kafin ya ce. "Sun kasheshi nike zargi, amma cewa aka yi ya mutu ne".......... "Akwai matsala kenan" Big Bro ya faɗa..... King ne ya cabki zancen da cewa. "Matsala babba ma kuwa". Smart da bai gane me suke nufi bane ya ce. "Ku fahimtar dani". Shi ma Ramish dai bai gane komai ba, dan basu da ilimi kan yadda tsafi yake. King ne ya ce. "Matsalar da muka ambata a nan shi ne, da waɗan nan yara suna kai 18 years gabaɗaya akalar rayuwarsu zata canza, a yanzu babu abin da tsafin jikin nasu zai yi masu, sai sun kai 18 years zai fara aiki, zasu fara shan jini, zasu fara ɓarna yadda dai kaga mahaifinsu ya yi". (Dik wani addini da kuke ga Sweetie tana yi zata watsar da shi da zarar sun cika 18 years, sannan zasu koma irin mahaifinsu, su fita daga layin mutane, a yanzu babu abin da magic ɗinsu zai sauya masu, lafiya lou zasu rayu da shi sai gaba, kuma king Omranish da ya basu shi zai zo ya rabasu da shi, shiyasa kuka ji Big Bro yana tambayar yana raye ne ko ya mutu, ba kowani mutum ne yake iya kwace tsafin da wani ya baiwa wani ba, yana da mahaukacin wahala, muje dai zuwa, daɗin abin sai sun kai 18 years yake fara huda jininsu ya shiga.) Shiru room ɗin ya yi, can Big Bro ya katse masu shirun da cewa. "I will try my best in ga na rabasu da shi, dan tsafi ga ɗiya mace babban barazana ce ga al'umma". Kwarai Big Bro ya yi gaskiya, mace al'umma ce guda, ace mace tana da magic, zata iya bada jini, ta sha jini, haba abin ya munana over, saboda zata gurɓata al'umma guda, mace da jin kai da tausayi game da raunin zuciya aka santa, hakan babban barazana ne sosai!. Jinjina kai king ya yi kafin ya ce. "To kai ina kasan ilimin tsafi?". Sai da ya yi wannan magana ya tina cewa ai a ranar da Big Bro ya zo wajensa ma ai ya ce yaga ruhanan tsafi, kenan yana iya ganinsu? To dik wanda yake ganinsu ai yana cikinsu kenan. Da karfi king ya furta. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun". Sai kuma ya yi shiru. Shiru shi ma Big Bro ya yi yana ɗan mamakin yadda aka yi baban su Sweetie bashi da hankali da basira, ai ko shi da yake da magic ɗin da ya koya da kansa ba bashi aka yi ba ba zai taɓa baiwa mace magic ba, dik rashin imaninsa ba zai baiwa mace magic ba, dan shi kansa yasan mace al'umma ce guda, gurɓacewar mace babban abu ne. (Ai ba'a a banza ALLAH ya ce idan ka haifi ƴaƴa mata uku, ka yi masu tarbiya har zuwa ka aurar da su basu lalace ba, aljanna tatabbata a gareka ba) Abin babba ne wanda sai mai hankali ya natsu zai iya gane illar mace ta gurɓace, kada ku manta dik wani halin uwa a nono ƴaƴa suke shansa, sai ɗan da ALLAH ya cire zakka sannan, meyasa zaku ga kaso tamanin cikin ɗari na halin yara uwar suka ɗauko? A nono suke sha, dan ALLAH iyaye ku kula da tarbiyar ƴaƴanku mata, dan dik mace ɗaya al'umma ce guda a wajen, kurɓacewarta tamkar kurɓacewar al'umma ce, idan ta zo ta haifi yara bakwai, biyar daga ciki dik ita zasu yo, suma suka haifa haka abin zai cigaba da tafiya a gurɓace, to dan ALLAH mu kula!!. Gyaran murya king ya yi kafin ya canza masu topic na magana da cewa. "Bari in baku sauran labarin dana fara". Tsaida kallonsu dikka a kansa suka yi, shi kuma kallon Big Bro yake yi yana ƙoƙarin karyata zuciyarsa a kan ɗan nasa yana tsafi, yana son tilasta zuciyarsa ta yarda baya tsafi kawai dai ilimi ne. Cigaba ya yi da cewa. "Akka tana da yara guda bakwai ba mu uku da kuka sani ba, kafin ni akwai maza biyu, bayan Abbas akwai mace ɗaya, sannan bayan Jahiz ma akwai mace ɗaya wanda tin tana da shekaru 7 ALLAH ya karɓi abarsa, cikin brothers ɗina biyu da nike da su, ɗaya tin ranar da aka haifesa ya ɓata wanda nike zargin mahaifina ne ya sace ɗansa da kansa, na biyun kuma an haifesa da sati guda shi ma ya rasu, sai ni, daga ni sai Abbas sannan sister ɗinmu mace mai suna Zunaira wanda mahaifinmu ya aurawa King Abdul Raof ita (kakansu Leesharh) sai dai kuma ashe ba auren tsakani da ALLAH ya yi mata ba, domin kuwa kasheta suka yi, da ya yi mata aure dai sun nuna so da kauna, sun kula da ita sosai har ALLAH ya bata ciki, sun tarairayi cikin suka yi renonsa cikin kulawa har ya kai wata bakwai, to a nan ne suka ɗauketa zuwa blood power, suka cuccusa mata magungunar tsafinsu a baki, amma sai da suka yi mata asirin da ko motsi bata iyawa, idanunta dai biyu tana ganin komai sai dai bata da abin da zata iya yi, suka zuba mata magunguna a baki, babu imani babu tausayi suka ɗinke bakinta kafin su tona rami mai zurfi, da ranta suka sakata cikin ramin, ga bakinta sun ɗinke cike da magunguna, sannan suka binneta a wajen da tsohon cikinta, Blood Power suka ce mun wanna abin da suka yi ya zama gagarumin abin da yasa masarautun biyu suka kara karfin iko, dan babu jarumin da ya taɓa irin wannan sadaukarwa sai mahaifina, shiyasa a lokacin mulkinsa dik balainka Kingdom ɗin nan tafi karfin ka nunata da yatsa saboda karfin mulki, wane mutum, iyayenmu sun yi son ransu a lokacin da suke kan mulki, sisterta ta tafi ta barni da ciwon kewarta a zuciyata, na gagara mantawa da ita a rayuwata, lokacin da Blood Power suka bani wannan labari, ba dan karfin tauhidi ba, wlh da sai kwakwalwata ta taɓu, saboda dik cikinmu babu wanda ya kaini shakuwa da sisterta, a lokacin da ta samu ciki har cewa take yi zata yi mun takwara idan namiji ta haifa, ina ta murna, bana taɓa yin sati biyu ban je evil kingdom dubata ba, dik dan in ganta, mun shaku da ita sosai, rana ɗaya kawai aka ce wai ta rasu saboda ciwon ciki, hankalina ya yi mummunar tashi, har suma na yi a lokacin, da na fargaɗo na ce a cire mun ɗan dake cikinta kada abine ta da shi, sai aka ce ai anrigada an binneta, wlh haukane kawai ban yi ba a lokacin, na sha jinya, kullum na zauna sai na tinata, mace mai fara'a da son jama'a yadda kuka ga Zunaira, shiyasa na sanyawa Zunaira sunanta, halinsu iri ɗaya ne, suka kasheta suka ce mutuwa ta yi daga ciwon ciki, amma ina zuwa Blood Power suka ce mun ai ba mutuwa haka kawai ta yi ba, ga abin da babana da Abdul Raof suka yi, su suka kasheta, to ta ya kuke tinanin ba zan yaki waɗan nan masarautu ba? Meyasa ba zan tsani jinin waɗan nan masarautu ba? Dole tasa na ce Ramish ya rabu da matarsa, saboda na tsani jininsu, na yi masu tsana mafi muni a rayuwata, bana son haɗa jini da su! Omranish, Herry, Abdul Raof, Abdul Malik dik na tsanesu, kuma na yi bakincikin zuwana a jinin Abdul Malik, dole in yakesu, kuma muddin basu daina tsafi ba, billahil lazi ba zan ragawa kowa daga cikinsu ba sai dai in mutu, sun cuceni, sun zalunceni, sun binne mun sister mafi soyuwa a gareni da ranta, da ranta ma da tsohon ciki a jikinta, baya ga haka sun sanyani na salwantar da yarana guda biyu ina ji ina gani, sun mun tabon da bazan taɓa mantawa ba kuma ba zan taɓa yafewa ba, yaki yanzu aka fara, babu gudu babu ja da baya muddin ina raye! Alkawari na ɗauka! Jinin Zunaira ba zai tafi a banza ba, sai na karar da gabaɗaya zuriar Abdul Raof da kuma Omranish, wannan dalilin yasa na ce Zunaira ba zata shiga cikinsu ba, saboda nasan zasu yi amfani da ita dan su dakatar dani, kuma nasan zasu azabtar da ita, zata fanshi laifina da ba ita ta aikata ba kuma bata san na aikata ba, kuma kasancewarta a cikin kingdom ɗinsu zai sanya in ji jikina ya mutu a kai masu hari, dan zan ji tsoron kada harin ya shafeta, amma dik cikinku babu wanda ya iya fahimtar cewa ni uba ne na gari, kuma ba zan taɓa kin abin da ƴata take so ba matukar bai kaucewa faɗar ALLAH ba, kuka tsaya a kaina kuna faɗin ina san cutar da rayuwar ƴata da kaina, a lokacin bana son buɗe baki in faɗa maku gaskiya ne saboda alƙawarinmu da Blood Power". Ya ɗan dakata yana huci, idanunsa sun yi jajir suna zubar da kwallah masu zafi, ya tuna da sistersa Zunaira, ciwo mafi zafi a zuciya, kai King ya shanye abubuwa dayawa a rayuwarsa bawan ALLAH'N nan, kunga kuwa dole ayi ta gwabza yaki babu gudu babu ja da baya, dole king ya yaki family ɗin waɗan nan three kingdom ɗin, dole ya tsani jininsu, sun yi mashi mummunar tabo a cikin rayuwarsa da ba zata taɓa gogewa ba, wlh karfin tauhidi da yarda da ALLAH ne yasa har yanzu king yake tsaye a kan kafafunsa, da ya jima da mutuwa bawan ALLAH. Tsit cikin ɗakin ya yi, dik black heart na Big Bro sai da ya ji tausayin daddyn nasu yakama shi, saboda akwai tsananin zafi rasa wanda ka shaku da shi, sarashi ɗin ma ba ta hanyar ALLAH ba, kai dole king ya yi yaki, an zaluncesa over to over.......... Smart kam shiru ya yi yana tinanin lokacin da ya tsaya lallai sai Auta ta bi Hoorain, ashe King ya fi su gaskiya, shi yasan irin gabar dake tsakaninsu dole ya hana Auta zuwa in da suke, ALLAH sarki. Shi ma Ramish yanzu ya daina ganin laifin daddyn nasa na cewa da ya yi ya saki Leesharh, ashe ya fisu gaskiya, sai dai kuma ai su jikokin three kingdoms ɗin basu da laifi, su basu san komai ba, hasalima su basu rayu a kingdoms ɗin ba, Leesharh ta rayu a Dubai, Zash ya rayu a Paris, Hoorain a kingdom of Power, Kamran a Forest, su Sweetie suma a forest, sannan Sweetie Black World, Pretty kingdom of power, su Bobo a Paris, sadauki Rishan ne kawai ya rayu a kingdom ɗinsu, shi ma kuma yaro ne da bai san mafarin gabar ba, daga sama ya tsinci gabar. TO BABA KING A TAIMAKA A YI WA JIKOKI AFUWA, DAN BASU DA LAIFI, MUN SAN ANYI MAKA BA DAIDAI BA, AN KUNTATA MAKA, AMMA MU KUNGIYAR HANA RUWA GUDU NA BIG BRO MUNA NEMAN YAFIYA DA A YAFEWA JIKOKIN NAN, A BARSU DA MASOYANSU, IYAYEN KUMA MU MUN AMINTA A CIGABA DA GWABZA YAKI DA SU HAR SAI SUN ZUBDA MAKAMAI SUN AMINTA ZASU DAINA ABIN DA SUKE YI!!. "Dad ka daina tuna baya, dan zai iya affecting heart ɗinka, ka bar storyn nan haka ya isa, bama son jin saura, as from today, matsayina na first born ɗinka, ina cewa kada ka sake yin magana a kansu, ka koma gefe ka yi shiru, ka bar mana yakin, zamu karisa abin da ka fara, dan lokacin daina kukanka ya yi, lokacin da za'a ɗauka maka ainahin fansa ya yi". Cewar Big Bro da ya yi magana in a cool way sosai, ya kuma yita yana sharewa King kwallah. Cikin natsuwa ya sake cewa. "Dole zasu tako har cikin nan su durkushe a gabanka su baka hakuri, dole zasu zubda makaman yaki, dole zasu koma karkashin kingdom ɗinka, daga yau kai zaka rinƙa basu umarni kafin gudanar da mulkinsu, ka haifi zakuna masu tare maka faɗa kuma masu share maka kwallah". Matsawa King ya yi ya rungumi Big Bro yana zuba masu ruwan albarka. Matsawa su Smart suma suka yi suka rungumesu suna amsawa da Amin. After 5 mins suka raba jikinsu dana King suna kallonsa. Cikin sanyin murya king ya ce. "Inai maku addu'ar nasara a ko yaushe ƴaƴana, Omerish ɗauki wayata ka ce kowa na family ya zo yanzu". Jinjina kai Smart ya yi tare da ɗauko wayar, sannan ya shiga kiran numbers ɗin matan gidan kafin ya kira su Uncle Abbas dik ya ce su zo. Shi kuma Big Bro ya kalli Ramish, in a cool way sosai ya ce. "Ramish ina buƙatar wayoyi guda biyu da sim card ɗinku na nan yanzu a daren nan"...... Jinjina kai Ramish ya yi kafin ya ce. "To in kawo mai registar ya yi maka kenan?". Kai ya girgiza kafin ya ce. "A'a ka yi komai kamar nine a wajen, ai ba wani amfani da wayoyi zan yi ba, just kawai kafin in koma ne". Sosai Ramish ya ji daɗi yadda yayan nasa ya aminta da shi har yake cewa ya yi komai madadinsa, wannan abu ya mashi daɗi. Kafin 10 mins room na King ya cika da family, dik sun zo har da su Sareena. Gabaɗayansu a saman shinfiɗar king suka zazzauna, su momma a saman sofas dake wajen yaran kuma saman rug na gashin jimmina, iya Big Bro, Smart and Ramish ne kasai suka zauna a saman bed tare da King. Takaici tamkar zai kashe mama, sai dallawa Momma harara take yi, Mama fa idan ta ga su Big Bro ji take yi tamkar ta shake momma ta kasheta kowa ma ya huta, kuma daɗin abin dake bata haushi shi ne yadda momma take matsayin yar uwar king, ta kara jin hasada a wannan ɓangaren ma. Shiru suka zazzauna suna ta kallon King bayan gaishe-gaishe, shi ma King kallonsu one by one ya yi kafin ya ce. "Ina surkuwara? (Pretty kenan, dan shi King bai ma san Big Bro yana da aure da Sweetie ba, Momma kawai kunga suka faɗawa)"...... Kallon kallo aka fara yi a cikin parlon dan ba'a fahimta ba, momma ce kawai ta fahimta sai ta ce. "Sarakanai dai ba ɗaya ba. Suna ɗaki tare da su Mahnoor". Sai da momma ta yi magana suka gane matansu Smart ake magana. Nan fa mama kulu ta kawo har wuya, tana wani kumbura ta ce. "Awww dama su Omerish suna da mata ne?".......... Kai momma ta jinjina kafin ta ce mata. "Suna da shi". "To fah, ƴaƴan wani sarki suka aura kenan?". Mama ta sake tambaya tana wani yamutsa fuska......... Nan ma momma ta bata amsa da. "Su da suke ƴaƴan sarki ai basa buƙatar auren ƴaƴan sarki kuma, talakawa nike son su aura saboda babu amfani a karawa teku ruwa a bokiti". Taɓe baki Mama ta yi kafin ta dallamawa momma harara. "Awwww yanzu na gane ashe su Omerish ne kawai ƴaƴa a cikin gidan nan, Jaish ya auri ƴar talaka, kun yi accepting har da nuna mata tana da ƴanci, kuka nuna mata kauna daga ke har shi (King), suma yanzu sun auri ƴaƴan talakawa kun yi accepting, amma ni da nawa ɗan ya auri jinin sarauta ma kun ce baku yarda ba saboda mugunta da son zuciya ko?". Ta yi maganar tana kallon Momma. Kallonta momma ɗin ma ta yi kafin ta ce. "Ai shi yakamata ki kalla idan kina magana, saboda shi ne mai zartar da hukunci bani ba!". Ta yi maganar tana yi mata pointining king....... Siririn tsaki Mama ta ja kafin ta ce. "Ai shi bashi da wani zaɓi fache ra'ayinki, abin da kin rigada kin mallakesa sai abin da kike so zai yi, wlh Rahilarh ki ji tsoron ALLAH, ki sani zaki mutu". Momma ce ta ɗan nisa kafin ta ce. "Hmmmm Aleezar ban san meyasa ke bakya jin kunyar ci mana mutunci a gaban yara ba, ban san a wani irin makaranta kika yi karatu ba, a gaban yara fa"........ Haba tamkar kara ingiza mamah aka yi, cikin masifa ta nuna momma da yatsa tare da cewa. "Karki kuskura ki zageni Rahilarh, sannan kuma su waye yara a nan?..........". Ji kake tassssss. Bata rufe baki ba ta ji wani irin jiri ya ɗebeta, wasu irin taurari ta gani suna haskaka cikin idanunta, kafin ta yi ƙoƙarin gane a ina take ta sulale kasa sumammiya, haba ta ji marin maza, Big Bro ya wanke mata fuska da mari, baya jin larabci, baya jin me suke faɗe, amma ganin ta yi pointining momma da yatsa tana magana a kausashe ne yasa ya fahimci magana mara daɗi take faɗawa momma, shi kuma ba zai iya jurewa ba, dikkansu hankalinsu yana a kan mama ɗin basu ga saukowarsa daga gadon King ba, sai sautin saukar mari suka ji tasssss ya karaɗe kunnuwansu. Mama kenan sai dai muce ALLAH yasa kina da rabon sake ji kunnuwanki basu tashi aiki ba, dan mazama basa shanye marin Big Bro bare ke mace, ALLAH yasa iya suma kika tsaya ba wata matsala. My people ku ce Amin, dan marin Big Bro fa ba wasa ba. Ai wani irin zabura suka yi, da sauri dik waɗan da suke kusa da Mama duka ja baya. Momma ce ta ce. "Haba ai da ka kyaleta baka taɓata gaban yara ba". Ramish da haushi tamkar zuciyarsa zata buga ne ya ce. "Ita ba a gaban yaran take yin abin da ta ga dama ba". Bai ma san ya yi maganar ba, saboda haushin da ta turnuke zuciyarsa. Smart ne ya yi gagawar cewa. "Momma ki yi shiru, dan wannan Big Bro ɗin namu idan yana hukunci ba'a magana, kina ce mashi bai kyauta ba yanzu zai birkice maki abin ta yi tsamari, dan sai ya kara mata da abin da ya fi mari ma". Cikin harshen larabci ya yi maganar dan ma kada Big Bro ya jisa. Saukowa King ya yi daga saman bed ɗin, a hankali ya tako ya zo ya rike hannun Big Bro, ya jasa suka koma saman bed ɗin, bai ce komai ba, saboda dama shi ma Mama tana kona mashi rai abin da take yi ɗin nan, shiru kawai yake yi. Dr Raj dai ƙasa ya yi da kansa, dan shi kansa yasan mamar tasu bata kyautawa, amma ya ji zafin marin da Big Bro ya dalla mata. Momma mai fara zuciya ita da mummyn Chuchu suka yi kan mama ɗin suna faɗin a kawo masu ruwa. Da sauri Aneesa ta tashi ta ɗauko ruwa. Karɓa Mummyn Chuchu ta yi ta ɓalle bakin robar, a hannu ta tarbo ta shafawa mama a fuska. Shiru bata farka ba, sake tarbowa ta yi ta shafa mata, nan ma shiru, har sau uku tana yi amma shiru bata farfaɗo ba. Kallon Big Bro Momma ta yi kafin ta ce. "Please ka kyaleta ruwan nan ya taɓa jikinta".........Kai ya ɗan girgiza kafin ya ce. "Ni ban hana ba". Yana magana yana hararar Smart dake kallonsa dan ya kwantar da kansa a kirjin King. Da king ya rikesa suka dawo saman gado shi ne ya jawo Big Bro ɗin jikinsa ya kwantar da shi a kirjinsa yana shafa bayansa alamar rarrashi, shi ne Smart saboda tsokana kasa-kasa ya ce. "Iyeee yaro ɗan gata, shalelen momma da daddy, ya wani haye mana jikin daddy maza tashi".To shi ne yake harararsa. Kallon Obaid da Omaid momma ta yi kafin ta ce. "Ku sake ruwan nan ya taɓata"....... Watau momma tasan cikin twins ɗinta ne ɗaya suka rike ruwan suka hana ya taɓa jikin Mama. Ɗaure fuska Omaid ya yi kafin ya ce. "Ni bani bane sai dai in Obaid".(Wayyo ƴan biyu kannen aljani😂) Da sauri Obaid ya ce. "Sai dai kai ɗin"....... "Ni dai ban ce ku faɗamun waye bane, kawai dai ku sake ruwan". Momma ta faɗa. Kara ɗaure fuska suka yi irin da gaske suke yi ɗin nan kafin su ce. "Momma kema ALLAH ke kike kulata shiyasa ma take yi maki abin da taga dama"................."Yanzu dai ku sake ruwan, idan ta farfaɗo muka je ɗaki sai mu yi magana". Cewar Momma. Omaid ne ya ce. "Ni momma babu ruwana fa, da gaske bani bane"..... Ɗaure fuska guyson ya yi, Obaid zai yi magana ya rigasu, on a serious note ya ce. "Ba zaku sake ba anai maku magana kuna cewa babu ruwanku?". Da sauri Omaid ya ce. "Yah Omar bafa mu bane, amma Momma ku sake gwadawa mana ko zata farka". Kallon Mummy Momma ta yi kafin ta ce. "Sake zuba mata". Shi kuma guyson fuska a ɗaure tamau ya ce. "In mun gama zama ku sameni a ɗaki". Bada wasa yake ba, kwata-kwata babu alamar wasa ko murmushi a kan fuskarsa. Da okey duka amsa cikin girmamawa. Shi dai Big Bro bai san me suke cewa ba, dan baya jin yarensu. Ita dai Sareena kallonta a kan Smart ita kuma Sharifa a kan Big Bro shalelen King in ji Smart. Mummyn Chuchu na sake zubawa Mama ruwa sai gata ta farfaɗo a haukace tana ihu, rirriketa momma da mummy suka suna ƙoƙarin tausarta, faɗi take wani motane ya bugeta? Dan bata ɗauka hannun mutum bane ya dalla mata mari. Abin dariya ma. Miƙewa Dr Raj ya yi da sauri ya nufi waje, dan uwa ba wasa ba, ba zai iya jura ba, kuma bashi da karfin rama mata, and ita ce nan ta takalo abin da ya fi karfinta, dan taɓa momma a halin yanzu ai balai zaka jawa kanka wanda dik zuri'arka ba zasu iya ɗauka ba. Ita ma Aneesa abin ya yi mugun sosa mata rai, amma sai ta daure tin da mama ɗin ta ja, ganin haka yasa King ya ce su je kawai zuwa safe za'ayi zaman, dan yanzu ba za'a fahimci juna ba, amma zuwa da safe idan suka dawo yasan mama zata natsu ko kallon momma ba zata yi ba, dama kuma Mama ɗin ita ce fitinar familyn. Mimmikewa suka yi suka fita, momma da mummy suka rike mama suna ta bata hakuri amma bata ji faɗi kawai take yi wani mota ne ya bugeta, da alama bata cikin hayyacinta fa, haka dai suka nufi waje, ɗakin ya rage daga Big Bro, Smart sai kuma Momma, shi ma Ramish ya fita sawowa Big Bro waya and sim da ya buƙata. -----------------------------🔥 Bayan ta yi wanka ta shirya cikin nightschirt, irin kayan barcin nan ne tamar doguwar riga zuwa gwiwa haka, suna da jini irin t-shirt, and suna da gajerun hannu ga laushi da kyau. Ciki ta shirya ta fito sai tashin kamshi take yi ta nufo room ɗin su Mahreen. Nan ta isko ƴanmayan king dikka banda Sharifa and Sareena, har Pretty tana kwance a jikin Mahnoor, kai Pretty ba dai son jiki ba kam. Suna ganin Sweetie suka fara yi mata sannu da zuwa, fuska a ɗauke da fara'a ta amsa tare da hayewa gadon tana ɗan rungumo Mahnoor game da cewa. "Na yi kewarki Aunty Mahnoor, Big Bro ya hanani fitowa ne, dik na damu in ganki". Pretty ce ta ɗan ɗaka mata mari a baya tana faɗin. "Tashi a kaina, ki bari idan na tashi daga jikinta sai ki rungumeta ɗin, yarinya sai iyaye"..... Kamar zata rama dukan sai kuma ta basar ganin akwai mutane, ta koma kusa da Mahreen ta zauna tana faɗin. "Big girl yanaga kin zauna shiru ne yau?".......... "Babu komai". Ta faɗa tana juyawa ta kwanta, yau tin ɗazun suke yi mata magana taki amsa kowa sai yanzu da Sweetie ta shigo, abin da guyson ya yi mata ya haifar mata da tsoro da natsuwa na ɗan lokaci, shiyasa taki yin magana. Aneesa da shegen wayau sai ta ce. "Big Bro ya yi daidai da ya ce kada ki fito, dan in kin fito ɗin ma bakinciki zaki ci karo da shi". So take su saba da Sweetie shiyasa ta fara shisshige mata, tana son su zama kawaye. Ɗan zaro idanu Sweetie ta yi kafin ta ce. "Bakinciki kuma?". KADA KU MANTA SWEETIE TANA JIN LARABCI DAN MOM ƊINSU NA YI MASU KAFIN TA RABU DA SU. Jinjina kai Aneesa ta yi kafin ta ce. "E mana bakinciki". "Wani irin bakinciki to?". Sweetie ta tambaya. Gyara zama Aneesa ta yi kafin ta hau kora mata bayanin cewa Sharifa na son Big Bro, kuma suna can suna shirin yadda zasu samu soyayyarsa, daga karshe ta ce. "Amma kada ki damu ni zai taimaka maki wajen tayaki mu rushe dik shirin da suke shiryawa". Siririn murmushi Sweetie ta yi kafin ta ce. "Macen da bata cika mace bace take tsoron wata aba wai kishiya, ai ko mata ɗari ne zasu ce suna sonsa ba zan damu ba, dan nasan waye shi kuma na yarda da kaina, ba dik kai zasu iya kishi dani ba ai, dan in ina waje ma kallon namiji zai yi wa mata, dik mai sonsa ta zo zan yi mata hanyar zuwa wajensa, amma ta shirya likkafani, dan ciwon zuciya ce zai kasheta, ni ai bazasu iya dani ba, saboda soyayyar da na tanadawa mijina wlh ba ma zai iya kula kowace mace ba ko ance ya kula". With her full confidence take maganar, irin ita zata narka zuciyar Big Bro da kauna ba zata baiwa wata space na shiga ba. SAI DAKE SWEETIE MAI BAKACITY!. Tin da ta fara magana suka tsareta da ido har ta kai karshe, ajiyar zuciya dik suka sauke, Pretty ce ta ce. "Ke wlh ban san yaushe kika zama haka ba, daga yin aure kin zama yar iska, yanzu ko kunyata baki ji kike faɗin kashe zuciyar bawan ALLAH da soyayya ko?". Harara Sweetie ta dalla mata kafin ta ce. "Ni shiyasa bana son yin magana idan kina waje, bari ma in tafi, mom ta baki amanata amma yanzu kin daina kula dani sai faɗa". Ta kai karshen maganar tana ƙoƙarin sauka daga gadon. Da sauri du Aneesa and Chuchu har suna haɗe bakin cewa. "A'a zo ki bamu sirrin, irin wannan karfin hali da yarda da kai haka? Zoki bamu gaskiya". Kasa ta sauko kafin ta ce. "Idan wannan mai manya-manyan idon ta tafi zan zo mu sha hira da safe". Tana kai karshen maganar ta watsa da gudu dan tasan Pretty ba barinta zata yi ba. Aikuwa yunkurawa Pretty ta yi zata kamata ɗin ta ga ta gudu, kwafa ta yi da cewa. "Zaki zo hannu ne". Aneesa ce ta ce. "Za'a bamu sirri kin koran mana ita". Siririn tsaki Pretty ta ja kafin ta amsa da. "Ai sai ku bita"...... Da yake su suke son abu sai suka lallaɓa suka ja baki suka datse, daga nan suka miƙe suka fita, Chuchu ta nufi ɗakin mijinta, ita kuma Aneesa ɓangaren mama, to suna zuwa ne King ya yi kiran wannan gaggawa, suka tafi room ɗinsa, baya na ɗan dawo dan in faɗa maku zuwan Sweetie wajensu, yanzu mu cigaba!. Abinci ta je ta ɗauka masu ta nufi room ɗinsu da shi, tana zuwa ta ajiye abincin ta haye bed ɗinsa ta kwanta, dan ta gaji da kwanciya a saman sofa. Kunna tv ta yi tana kallon film ɗin larabawa har barci ya fara ɗaukarta. Sai around 10:30 ya dawo ɗakin. A lokacin ta kashe light na ɗakin ta kunne dim, haske kaɗan kaɗan ne. Shakar kamshin perfume ɗinta ya yi kafin ya kariso ciki, bai yi tinanin tana saman bed ɗinsa ba, sai da ya matso dab ya ganta. Da sauri ta sauko ƙasa tana ce mashi. "Ina ka je ka tsaya tun ɗazun yunwa nike ji?"........ Shiru ya yi har sai da ya zauna a gefen bed ɗin kafin ya amsa da. "Wajen daddy". Wucewa ta yi ta nufi wajen abincin tana faɗin. "Zo to mu yi dinner, cos I'm feeling hungry"........ Kai ya ɗan girgiza. "Ki yi kawai, I'm okey". Ai saka mashi shagwaɓa ta yi a kan lallai sai ya zo sun ci, bashi da zaɓi dole ya mike ya zo, zuba mashi kaɗan ta yi dan tasan da daddare baya cin abinci sosai, ta tura mashi a gabansa kafin ta zuba nata. Kafin ya ɗauki spoon sai da ya miƙo mata kwalin wayarta. Cike da zumuɗi ta karɓa, haba wani irin murna ne ya bayyana a kan fuskarta, fasa ɗaukar spoon ɗin ta yi, jikinta na rawa ta hau buɗe wayar, like wow wayar ta haɗu over to over. Ɗagowa ta yi ta kallesa sai taga ya ɗauki spoon yana cin abinci kuma yana kallonta. "Thank you so much King of my heart". Ta kai karshe tana sumbatar wayar. Ɗan lumshe idanunsa ya yi, dan ji ya yi tamkar shi ta sumbata. Da hannu ya yi mata nuni da ta ci abinci dare na kara yi, kada ta zo taci ta kwanta ya yi affecting ɗinta. Rungume wayar a kirjinta ta yi ta ɗauki spoon, ta ɗebo abinci zata kai baki kenan sai ta ga ya kai hannu ya zare wayar daga kirjinta ya ajiye a gefe. Kasa-kasa ya ce. "A kan me za'a ajiye shi a muhallina?". Ta gane nufinsa, watau ta rungume waya a kirjinta bayan muhallinsa ne wajen, ai ajiye spoon ɗin nata ta yi, tasa hannu bibbiyu ta rufe fuska tana murmushi. "Kai king of my heart, ka sakani na ji kunya fa"......... Hannu ya kai ya buɗe hannayen nata tare da ɗebo abinci a spoon ɗinsa ya sanya mata a baki, can kasan makoshinsa ya ce. "Ki ci abinci sosai ki kara girma dan iya jure mun". A yanzu ma ta fahimci me yake nufi, hararar wasa ta wurga mashi kafin ta ce. "Uhmmm ALLAH ya kaimu lokacin aurenmu, zan tina maka wani abin"............ Jinjina kai kawai ya yi tare da cewa. "Ɗauki wayar ki saka a chaji". Da sauri ta ɗauka ta je ta jona sannan ya dawo ta zauna. Sake ɗebo abincinsa ya yi ya kai mata baki yana satar kallon tula-tulanta da suke yi mashi kwalele, da ya zo kwace wayar ne ya ja mata wuyar riga tai ƙasa suka bayyana, ji yake tamkar ya kai hannu ya taɓasu saboda tsabar kyansu da ɗaukar ido, shi kaɗai yasan me yake ji a halin yanzu. Muryarta ce ta katse shi da cewa. "Ba zan yarda da wayanka ba, kana ta tura mun abincinka zaka sanya in kasa cin nawa, kai kuma kaki ci ko?"...... Shiru ya yi saboda ta ganosa, so ya yi dama yai mata wayau ta cinye abincin nasa dikka, dan baya son ci, shagwaɓar da ta zuba mashi ta narka zuciyarsa ne yasa ya zo ci. Kin sake karɓar abincinsa ta yi, ta ce kowa ya ci nasa. Dole ba dan ya so ba ya rufe idanu ya cinye, ita ma ta cinye nata, miƙewa ya yi ya ɗauketa cak sai toilet kamar ɗazun. A yanzu brush ɗaya ya ɗauka ya zuba kayan goge baki. A bakinsa ya fara sanyawa ya goge kafin ya ɗago haɓarta suna kallon juna ta cikin mirror ya sanya mata brush ɗin, a hankali ya goge mata baki tsab kafin ya ɗauraye masu da ruwa. Kamar yadda ya ɗaukota ya kawota haka ya ɗauketa ya fita da ita. A tsakar ɗakin ya sauketa ya wuce saman bed ɗinsa. Sai da ya kwanta ya jawo bargo sannan ya ce. "Idan zaki kwanta ki ɗauki wayarki mu yi chat". Ya faɗa tare da kara jan bargon sama. Kai ta jinjina mashi kafin ta wuce ta tattare kayan abincin dikka ta yi waje da su. Ta gyare wajen tsab sannan ta nufi saman sofa, har zata kwanta ta tuna da wayarta, da sauri ta ɗaukota ta dawo ta kwanta. Kunna wayar ta yi haɗe da jawo bargo, ga mamakinta sai ta ga wayar da sim card harma da su Whatsapp, bata yi magana ba sai ta ja bargo har kanta ta rufe, da yake in baku manta ba tana danne danne a wayar Ronnie so yasan abubuwa da dama, kai tsaye ta shige Whatsapp. Sai da ta shiga ta kunna data, aikuwa tana kunnawa sai ga sakonsa ya shigo, dik da bata da tabbacin shi ne ta yi farinciki, tasan da wuya idan wani yana da wannan number. Duba chajin wayar ta yi sai taga bata yi chaji sosai ba, dawo da kallonta kan sakonsa ta yi, dik da bata iya karatun turanci sosai ba ta karanta Queen of my heart da ya rubuta, murmushi ne ya kubce mata. Sai yau ta fahimci matsa mata da Ronnie yake yi a kan karatu, ga shi ya amfaneta, a cikin ranta ta ce ALLAH ya yi wa Ronnie albarka, ya dake sosai wajen ganin ta iya reading, ga shi kuma ta iya, dama shi karatun Arabic ta iya sosai. "King of my heart". Shi ta rubuta ta tura mashi. "Na yi zaton zaki bani hot kiss na barci amma baki bani ba". Abin da ya sake rubuta mata kenan. "Idan muka yi aure sai ka gaji da shi". Amsar da ta mayar mashi kenan. "Ina son mu koma birninmu domin mu yi wannan auren dai in huta". Murmushi sosai ta yi kafin ta ce. "Nima ina son hakan". Ta faɗa mashi ne dan ya yi farinciki kuma ya samu barci mai daɗi, amma ta kuduri niyyar faɗawa momma gaskiyar komai idan ta kara gina soyayyarsu kafin ya tada batun komawa, shiyasa yanzu kuka ga tana biye mashi, tana tsoron ya ce ba zai musulunta ba ko zai rabu da ita, dalilin da yasa take shiga jikinsa dan gina soyayyarsu da katangar karfe wanda ba zai taɓa iya rabuwa da ita ba ko da ance dole ya musulunta. "Smiling yana maki kyau over, zan samu ganinsa kafin in yi barci?". Abin da ya sake turo mata kenan. "Me zai hana kai da mallakinka, ni fa taka ce". Ta tura mashi....... "In dai da gaske kike yi ke tawa ce to zo mu kwanta a nan". Shi ne amsar da ya bata....... Jim ta ɗan yi tana tinanin amsar dayakamata basa, dan wlh ba zata je ba, tab ba wannan magana, kuma bata son ransa ya ɓaci, magana mai taushi take son faɗa mashi dan ya samu barci mai mugun daɗi, to meyakamata ta ce mashi kenan? Ta jefi kanta da tambaya. "Nasan ba zaki zo ba dama, because of your religion, i hate it more and more, ki daina yin addinin ma". Wani irin faɗuwar gaba ta ji ya dira mata a rai, ta daina yin addini kuma ya tsanesa, da matsala gaskiya. "Please ka daina cewa haka, zaka sakani kuka fa". Ta tura mashi har da alamar emoji. "Na daina to, amma kada ki sake yi mun maganar religion naki kin ji?"...... Kai ta jinjina tamkar tana a gabansa. "Ba zan sake ba, to ka ce kana sona"........ I love you. Ya turo mata har da emoji na heart. "Love you too King of my heart". "Give me a hot kiss before na yi barci, wayata ba chaji". Shi ne sakon da ya sake turo mata. Emojin kiss ta tura mashi alamar kiss. "Ba irin wannan ba, real kiss I need". Ya turo mata. Kirjinta ne ya sake bugawa da karfi, sai ta rasa me zata ce mashi. Tana tsaka da tinanin abin da zata ce sai ga voice note ɗinsa. Jikinta har yana rawa wajen buɗe voice ɗin dan ta ji me ya ce........ NI KAM SALON SOYAYYARSU NA SAKANI JAJJABI, ƊAKI ƊAYA SUKE KWANA AMMA KUNGA WATA SALO.🤔 Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 "Your balls are in my eyes, even when I close my eyes, I can see them, they are so beautiful, they are so captivating, I really like them, and I like your boobs too". Shi ne abin da ya faɗa a cikin voice ɗin cikin wata iriyar muryar da bai taɓa yin magana da ita ba, tamkar yana cikin maye. Sosai tausayinsa ya kamata, domin bai saba da irin wannan yanayi ba, dik ita ta koya mashi komai, tasa ya buɗe zuciyarsa, tasa ya zama haka. Tana tsaka da tinani wani sakon ya sake shigowa wayar. "Maysh, as the night wraps the world in its quiet embrace, I just want you to know that you're the last thing on my mind and the first in my heart. I hope your dreams are as beautiful as your smile, and your sleep as peaceful as your soul. I miss you more than words can say. Sleep well QUEEN OF BLACK WORLD. Good night, Queen of my heart". Tin da ta koya mashi love ya bi ya susuce a kanta. Wani irin madarar daɗi mai sahihin garɗi ta ji na jin kalamansa, ba abin da ya fi burgeta kamar Queen of Black World da ya ce, burinta zai cika ta gyara birnin ta cigaba da yin da'awarta. Dan haka jikinta na rawa ta hau yi mashi typing kamar haka. "King Of My heart, your words wrapped around my heart like a warm blanket on a cold night. Knowing that I live in your heart brings me so much peace and joy. You are my calm, my comfort, and my forever. Sleep peacefully, my king, and let your dreams carry you to me. I love you more than you’ll ever know. Good night, my everything". Da sauri ta tura mashi. Har wani ajiyar zuciya ya sauke na ganin abin da ta rubuta, karancewa tsab ya yi kafin ya yi switch off na wayar, ya miƙe ya mayar da ita chaji kafin ya dawo ya kwanta. Ita kuma shige-shige ta dinga yi a cikin wayarta har karfe 1 ya yi, sai da ta ga wayar ta ɗauke sannan ta miƙe ta nufi jikin chaja ta jona, sannan ta nufi toilet. Alwala ta ɗauro ta dawo, a gaban bed ɗinsa ta tsaya, kasa-kasa ta ambaci sunansa dan ta tabbatar da ya yi barci ne ko bai yi ba. Jin alamun ya yi barci ne yasa ta fara karanto addu'oi tana tofa mashi na ɗan lokaci, sannan ta nufi saman dadduma dan yin Sallah. --------------------------🔥 Sai around 8 na dare Jaish ya dawo, tafiyar da bai sanar da kowa ba sai Momma kunga ai babu damar kwana, part ɗinsa kawai ya wuce, yana shiga a gurguje ya yi wanka, time ɗin Mahnoor bata nan tana wajensu Chuchu, bama tasan ya dawo ba. Shirya ya yi cikin satin pjs launin light ash, ya yi matuƙa kyau over, kai tsaye fitowa ya yi ya nufi room na king, a lokacin karfe 9 na dare ta yi. Bayan sun gaisa da King da brothers ɗinsa Smart Tiger and Black Tiger ya fito ya je wajen momma. Ita kam ya ɗan jima suna hira har wajen 9:30, sannan ya yi mata sai da safe ya fito. Room na Mahreen ya shiga, nan ya iskota ita da Mahnoor a ɗakin, Mahreen na kwance ta bata baya, ita kuma sai faman lallaɓata take yi tana tambayarta me yake damunta. Suna jin sallamarsa Mahreen ta miƙe da sauri, tana sauke idanu a kansa ta fashe mashi da kuka, kallon juna suka yi shi da Mahnoor kafin su maida kallonsu a kanta. A kule Mahnoor ta ce. "Okey ni dama kima mannawa hauka kenan ko? Tin ɗazun nike tambayar meyake damunki kika ki faɗa mun, amma yanzu kina ganinsa kin saka kuka ko?". Takowa ya yi ya kariso ciki, da gudu Mahreen diro kasa ta nufesa, tana zuwa ta faɗa jikinsa tana kara sautin kukan nata. Ɗan rungumeta ya yi, cikin sigar rarrashi ya ce. "Waye yau kuma ya taɓaki?". Saukowa kasan bed ɗin Mahnoor ta yi ta nufosu ita ma. Mahreen kuwa cigaba da kukanta ta yi taki basu bayani, ba yadda Jaish bai yi da ita ba, amma taki bashi bayani, da ya ga hakan sai ya gane dik yadda akai abu ne mai matukar nauyi yasa bata faɗa mashi ba, dan tin da ta iya faɗa mashi guyson ya yi kissing ɗinta tofa sai dai in sama da wannan ya yi mata yasa ta gagara faɗa mashi. Dan ya tabbatar da zarginsa yasa ya ce mata. "Omar ne ya yi maki laifi ko?". Da sauri ta gyaɗa mashi kai sama alamar e tana kara tsanta kukan nata. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya rabata da jikinsa, rarrashinta ya fara yi, sai da ta yi shiru sannan ya ce. "Kada ki faɗawa kowa komai, idan ya yi maki laifi ni zaki rinƙa faɗawa dan in rama maki, yanzu ma zan rama maki ko da ban san me ya yi maki ba, kin ji ko?". Kai ta gyaɗa mashi tana turo baki. Shiru ya ɗan yi yana tinanin me guyson ya yi mata da zafi haka? Can wata ɓangare na zuciyarsa ta ce to ko dai ya nemeta ne? Da sauri ya girgiza kai, dan su basa zina, babu wannan, kuma shi yasan waye guyson, ba zai taɓa nemanta ba, wani abin dai mai zafi ya yi mata. Ganin ya yi shiru ne yasa Mahnoor ta ce. "Yaushe ka dawo?". Ta yi maganar tana kallan kayan jikinsa, a nan ta fahimci ya ɗan jima da dawowa. Sake Mahreen ya yi ya riko hannun Mahnoor yana faɗin. "Zo mu ke ɗaki, kajin bappa kwanta ki yi barci abinki, zan zane Omar". Jinjina kai ta yi tare da wucewa saman bed, fita suka yi suka ja mata door, sannan suka nufi room ɗinsu. Suna tafiya a hanya ne Jaish ya ce. "Mekike tinanin Omar ya yi mata da nauyinsa yasa ba zata iya faɗa mana ba?". Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta ce. "Ina tinanin ko dai ya yi kissing ɗinta ne". Kai ya girgiza. "Ba kiss bane, ranar da ya yi missing ɗinta ai ta faɗa mun, kina toilet ne yasa baki ji ba, amma ta faɗa mun". Mamaki ne ya rufe Mahnoor, bata san rashin wayo da shirmen Mahreen har ya kai ta iya faɗawa suruki yayan miji wai ya Omar ya yi kissing ɗinta ba, gaskiya dole ta yi mata faɗa, dik da shi Jaish matsayin kanwa ya ɗauketa, amma gaba idan ta san me miji yake nufi kunya da danasani zata yi, yazama dole ta yi mata faɗa sosai. Muryarsa ne ya katseta da cewa. "Ina zargin ko dai kirjinta ya taɓa ko wani abin makamancin hakan". Ya faɗa daidai lokacin da yake tura door room ɗinsu. Ciki suka shiga Mahnoor kunya ya hanata yin magana, sai ta canza topic ɗin hiran da cewa. "Baka bani labarin Jimeta ba, shin bappa ya bamu aurenta ne?". Kai ya girgiza a lokacin da yake zama a gefen bed, ya jawota jikinsa kafin ya ce. "Bappa ya rigada ya aura mata wani wai Faisal ita tin sati biyu da suka wuce, dama suna shirye-shiryen zasu zo su ɗauketa ne, na yi takaicin wannan abin, yanzu haka da bappan muka taho ya zo ɗaukarta".......... Ɗan zabura Mahnoor ta yi, har tana haɗe words wajen cewa. "Bappa ya zo? Kuma ya aurawa hamma Faisal Mahreen? Tab lallai akwai balai kuwa, ni dai yanzu kaini in da bappa yake in gansa kafin mu yi maganar aurenta". Cike da yanayi biyu a kan fuskarta ta yi maganar, farinciki da kunci, farincikin zata ga bappanta, da bakin cikin aurawa Faisal Mahreen da aka yi. Shiru ya ɗan zuba mata idanu na kamar 2 mins kafin ya ce. "Natsu ki ji wani labari". Tsai da kallonta a kansa ta yi, cikin natsuwa ya ce. "Da gaske ne bappa ya baiwa Faisal auren Mahreen, kuma last two weeks za'a ɗaura auren sai ALLAH ya yi wa gwaggo matar arɗo rasuwa a ranar (mahaifiyar Nenne) dalilin ɗaga bikin kenan, dama za'a ɗaura auren ne kafin a zo a ɗauketa". Zabura Mahnoor ta yi game da zunduma salati, wannan shi ne kana naka ALLAH na nashi, gwaggo dai ta koma ga ALLAH ta bar Nenne. Take idanun Mahnoor suka cicciko da kwallah tana salati. Rumgumeta da kyau ya yi, cikin sanyin murya ya ce. "Dik mai rai mamaci ne, addu'a kawai take buƙata a wajenku kin ji?". Ya faɗa yana ɗago haɓarta daga kirjinsa. Kai ya jinjina mashi tana ƙoƙarin shanye hawayenta. Cigaba ya yi da cewa. "Yanzu na roki alfarma a kan bappa ya baiwa Omar ita, amma ya ce mun yarigada ya baiwa Faisal, idan har ya canza magana to fa bai yi adalci ba, dan ya baiwa Faisal ke, aka rusa maganar, kusan hauka ya yi, yanzu aka dannesa da ita ba zai iya warware alkawarin nan ba, amma shi kansa ya so mata Omar ɗin dan ta samu rayuwa mai kyau, sai dai ina da damar zuwa in samu Faisal, idan ya janye shi kuma a shirye yake ya bamu ita". Shiru ta yi tana saurarensa, burinta kawai ta ji karshen zancen ya yakare. "Tin da Omar ya bayyana yana sonta to nasan da gaske yake yi, dan bai taɓa kwatanta hakan ba, kuma ni kaina ina san ya sameta ko dai ya yi farinciki irin wanda nike da na sameki". Ya faɗa tare da manna mata sumbata a kumatu, so yake ya mantar da ita batun mutuwar gwaggo da ta shiga damuwa a kai. "Na taka har kofar gidansu Faisal, na je mashi da batun ya rushe auren Mahreen kome yake so zan bashi, da farko ya nuna gardama dan yana ganin wasa nike ba zan iya bashi ba, amma da na ce ya faɗi abin da yake so zan bashi ya janye buƙatarsa, sai ya ce to a bashi shanu guda ashirin zai janye, ni kuwa nasa aka nemo mun shanu guda ɗari a rugar na saya mashi da dollars na basa, take a wajen yasa aka rushe batun auren nasu". Tsayawa ya yi yana kallon yadda ta fara sakin murmushi dan ta ji ba'a ɗaura auren da hamma Faisal ba. "A wajen bappa ya ce ya baiwa Omar ita, ni kuma bai ɓata lokaci ba na ce da bappa ba zan tafi a aura mata wani ba, sai dai a ɗaura aurenta a masallaci da anyi sallar azahar, dan ina tsaron Omar ɗina ya rasata, in takaice maki ban baro Jimeta ba sai da aka ɗaura wannan aure ta Omar da Mahreen, na biya sadaki, ko Momma bata sani ba sai yanzu da na dawo nike faɗa mata ai sun bamu auren, dama da zan tafi na faɗa mata auren zan je nema, tai mana fatan alkhairi sosai, ga shi addu'arta ta karɓu". Ai wani irin kara ta saki tare da sanya hannu bibbiyu ta rungumesa, ta mance da damuwar mutuwar gwaggo. Rungumeta shi ma ya yi tare da jawo wayarsa dake saman bed ɗin, number guyson ya dannawa kira. Yana ɗauka ya ce. "Zo ɗaki kasameni". Yana gama faɗin hakan y katse kiran ya mai da wayar gefe tare da gyarata a jikinsa sosai. "I really missed you sosai, me kina tanada mun". Ya faɗa mata cikin raɗa. "Special abubuwa na tanada maka". Haba wani irin daɗi da ya ji bai san lokacin da ya sake matseta a jikinsa ba, daidai lokacin suka ji sallamar guyson daga waje. Da sauri ta sakesa tana shirin barin jikinsa tamkar wadda aka ce mata momma ce ko king or su Smart ne zasu shigo. A gefen bed ɗin ta zauna tana satar kallonsa, while shi kuma ya yi wa Omar iso. Ciki guyson ya shigo bakinsa a ɗauke da sallama again. Da hannu Jaish ya nuna mashi saman sofa kan ya zauna zama ya yi yana faɗin. "Good evening Yah Jaish"......... "Evening how was your day?". Da Alhmdllh ya amsa kafin ya ɗagawa Mahnoor ita ma gaisuwa. Bayan nan shiru suka ɗan yi, a natse Jaish ya katse masu shirun ta hanyar fara yi mashi nasiha a kan ɓoye mashi yana son Mahreen da ya yi, ya ce kada ya sake ɓoye mashi dik abin da yake so, hakuri guyson ya bashi kansa a ƙasa. Jinjina kai Jaish ya yi kafin ya cigaba da magana, ya zayyane mashi yadda komai ya faru har aka bashi auren Mahreen ɗin, yanzu sun zama mata da miji. Cikin tsananin farinciki ya zamo daga saman kujera ya durkushe kasa, sai da ya fara yi wa ALLAH sujada, ya yi godiya da irin brothers da ALLAH ya bashi masu matuƙar kaunarsa da son farincikinsa, sannan ya yi godiya kan mallaka mashi Mahreen da ya yi, first love ɗinsa, har idanunsa sai da suka cicciko da kwallah. Murmushi Jaish ya yi kafin ya ce. "Babu komai, amma ni abin da nike so da kai yanzu kada ka nuna mata cewa kai mijinta ne, ka fara neman soyayyarta farko, hakan zai fi maka"....... Jinjina kai ya yi tare da kara yi wa Jaish godiya sosai. "Kana iya tafiya, kuma ba wai na baka lasisin ka je ka yi ta takurawa sister ɗita bane, in ka yi mata laifi nai mata alkawarin hukuntaka"......... Jinjina kai ya ɗan yi, a sanyayye ya ce. "Amma zan rinƙa tsokanarta kaɗan-kaɗan ta hakance kawai zai sa muyi sabo har ta fara sona". A kunyace ya yi maganar. Jaish dake murmushi ne ya amsa da. "E haka ne, amma dai kada ka rinƙa saka mun ita kuka, ɗazun ma ai ta kawo mun karanta". Ya faɗa yana binsa da kallo dan ya ga reaction ɗinsa, so yake ya tabbatar da abin da yake zargi a kan abin da ya yi mata, yana zargi breast ɗinta ya taɓa. NI KO NA CE BAKU SAN YA WUCI NAN BA MA, BABBAN SASHE YA TAƁA ƊAN ALBARKA, DAN MA DAI ABIN YA ZO DA SAUKI TIN DA A LOKACIN DA YA YI HAKAN MA AN RIGADA AN ƊAURA AURENSU TA ZAMA TASA, DAN HAKA KAYANSA YA GANI. A miliyan Omar ya ɗago kansa, suna haɗa ido da Jaish sai kuma ya yi gaggawar sunkuyar da kai kasa yana faɗin. "Ka yi hakuri Yah Jaish ba zan sake ba, amma ai ita ce ta tunzurani ta ce mun ta taɓa ɗaukar maza sun fi goma, shi ne ni kuma na ce ban yarda da ita ba sai na duba virging ɗinta". Ai saura kaɗan Jaish ya taune harshensa, saboda maganar ta fi karfinsa, har kamar zai ce ka duba ɗin? Sai kuma ya yi shiru, da sauri ya ce. "Tashi ka je sai da safe". Da alama Omar ya goge mashi hadda ne. Da sauri ya miƙe yana kallon Mahnoor dake ta yi mashi murmushi, dan ita bata gane kan hirarsa da Jaish ba. Waje ya fito ya nufi room ɗinsh cike da murna, zai shiga kenan suka ci karo da su Omaid zasu shiga room ɗin suma, in baku manta ba dama ya ce su zo su same shi a bedroom ɗinsa, to shi ne suka zo. Suna ganinsa cikin girmamawa suka ce. "Yah Omar gamu nan". Kallon tsab yai masu kafin ya ce. "Kuje kawai sai da safe".... Yanzu yana cikin farinciki ne over, ba zai iya hukuntasu ba shiyasa ya ce su je sai da safe. Juyawa suka yi suka tafi shi kuma ya wuce ciki farinciki tamkar ya zuba ruwa kasa ya lashe. AFTER SOME MINUTES. ----------------------------🔥 Sai da ya bari dare ta yi irin karfe 11 haka, ya fito daga room ɗinsu, already Ronnie ya yi barci abinsa, bedroom ɗinta ya nufa dan ya sake bata hakuri, tin da wannan abin ya faru bata sake yarda sun haɗu ba, in ta gansa gudu take yi, ashe dik wannan rashin kunya da tsiwar da take tsulawa akwai abin da take jin kunya, ya gane mata babban sashenta kunyarsa ya lulluɓeta over, ta so faɗawa Jaish ɗazun, amma ta rasa ta ya zata yi mashi bayani, tana jin kunya shiyasa ta danne abin a ranta, amma ta yi mashi ALLAH ya isa ya fi sau dubu a ranta. Murɗa handle na door ɗin ya yi ya shigo bakinsa a ɗauke sa siririn sallama ƙasa-kasa. Tana zaune a tsakiyar bed ɗin, ta kifa kai da gwiwowinta kamar kuka take yi, abin da ya yi mata babu karya ya yi mata mugun zafi, kada ku manta dik rashin kunyarta bata taɓa yarda gwaggo kakarta ta yi mata wanka tin tana yar karamarta ma, ku tuna rayuwarta a kauye mana? Dik abin da zai bayyanar da babban sashenta bata shiri da shi, a kan kakarta ta yi mata wanka ta ga tsiraicinta gwara ta kwana da datti, shiyasa ta yi takaicin abin da ya yi mata, shi kansa da ya dawo hayyacinsa yasan bai kyauta mata ba ko kaɗan, shiyasa ma ya zo bata hakuri. Ta yi nisa cikin kukan bata ji shigowarsa ba, hayewa saman bed ɗin ya yi a natse dan yasan ita ɗin yanzu mallakinsa ce. A kusa da ita ya zauna tare da kai hannu ya ɗan ɗago da fuskarta da ya gama yin jaga-jaga da hawaye. A tinaninta ma Sweetie ce ko Zee or Pretty, dan sune suke shigo mata ɗaki kai tsaye, sai dai tana ɗago kai ta ga shi ne. A miliyan ta ja da baya tana kallon fuskarsa kafin ta sauke kallonta izuwa kyakkyawan silky pj's dake jikinsa, ya yi balain kyau, gashin kansan nan ya kara kwanciya luf har gaban goshinsa, ga wani sheki da yake yi, sai tashin wani irin daddaɗar kamshi yake yi. Ɗan kura mata idanu ya yi kafin ya zare kallonsa daga kanta saboda wani irin kunyarta da yake ji, kayan jikinta ya bi da kallo, ganin abaya ne a jikinta yasa ya zargi anya ma ko abincin dare ta ci kuwa? Saboda yadda take yar gayu ya warhaka ba zaka sameta da wani kaya ba face na barci masu kyau tana tashin kamshi, amma wannan abaya tin da rana ita ce a jikinta bata canza ba. Wani irin zafi ya ji zuciyarsa na yi mashi na ganin yadda hawaye ke gudana a kan fuskarta, ya yi nadamar abin da ya yi mata sosai. Cikin sanyin murya ya ce. "Meyasa kike kuka haka? Baki da lafiya ne ko wani ne bashi da lafiya?". Ba wai dan bai fahimci kukan me take yi ba ne yasa ya yi wannan tambaya, so yake yi ko kaɗan ne ta yi magana dan ya karanci girman fushin dake ranta ya san ta in da zai fara rarrashi. Shiru bata amsa shi ba, sai ma kara ja da baya da ta yi, dan wani irin shakkarsa sosai take yi, ga tsoronsa da take ji. Sai da ta kurewa headboard na bed ɗin sannan ta dakata tana yin kasa da kai, dan bata son haɗa ido da shi. Ya fahimci yanzu kunyarsa da kuma shakkarsa take ji, dan haka sai bai matsa kusa da ita sosai ba. In a cool way sosai tamkar Big Bro ya ce. "Nasan abin da na yi maki ban kyauta ba, ni kaina naji babu daɗi, amma ki sani ba yin kaina bane, soyayyarki ta ja komai, ita ta rufe mun ido ta sanya bana jin komai sai ke, ina mai baki hakuri kan abin da ya faru, please kada ki ce zaki hukuntani a kan hakan, dan ba zan iya jura ba". Ya ɗan dakata yana ɗagowa ya saci kallonta. Har lokacin dai bata daina kuka ba, kuma bata ce uppan ba. "Please ki dakatar da kukan nan haka, yana sosa mun zuciya sosai, dan ALLAH ki faɗa mun me yake damunki kike kuka har haka". Cike da damuwa sosai ya yi maganar ga kuma sanyin murya dake nuna raunin zuciyarsa. Cikin kuka tana shassheka ta ce. "Shikenan yanzu zan samu ciki? Shikenan zan haifi ɗan shege?". Da kyar ta iya faɗin hakan...... Cikin rashin fahimta ya ce. "Ban gane zaki samu ciki ki haifi ɗan shege ba?". Tana wani irin shesheka mai taɓa zuciya ta ce. "Bappana ya ce mun dik ranar da na bari wata ko wani suka kalli tsiraicina shikenan zan samu ciki in haifi ɗan shege wanda kuma kowani numfashi yaron ya yi azaban wuta za'ayi mun in na mutu". Jim ya yi, yau ya ji sabon karatun da bai taɓa ji ba, wai zata samu ciki idan aka kalli tsiraicinta, kuma wai kowani numfashi yaron ya yi azabar wuta za'ayi mata, a lallai irin wannan fatawa na bappa dole ta wuni tana kuka, waye zai so azaba ana zaune kalau? Kai amma bappa ya iya tarbiya cikin ruwan sanyi, ga shi dik rashin kunyarta da rashin wayewa and ilimi tana tsayawa tsayin daka dan kare mutumcinta, bata san amfanin mutumcin nata ba a yanzu, amma zata kula da shi tamkar ranta dan gudu azaba. Wani irin sanyi ya ji ta lulluɓe mashi zuciya, wannan bayani nata ya kara tabbatar mashi da cewa lallai babu wanda ya taɓa kalle mashi babban sashensa, shi kaɗai ya fara kallan kayansa kuma halak ɗinsa, wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ɗan matsa kusa da ita, kalaman Jaish ne suka dawo mashi cikin kunnensa in da yake ce mashi kafin ya sanar da ita su ma'aurata ne ya fara neman soyayyarta tukun nan, ya sanya ta soshi sosai, hakan zai fi mashi. Tina wannan magana yasa ya ɗan yi wani jim, amma sai ya daure tare da kara matsawa kusa da ita, hannayenta ya riko cikin nasa, shakkarsa da take yi yasa bata kwace hannun nata ba, muryarsa a sanyayye sosai, cikin tausasawa ya ce. "Haka ne, bappa ya yi gaskiya, dik abin da ya faɗa maki haka ne, amma ai banda yayaki, ni yayanki ne, dan haka ko da na taɓaki ba zaki ɗauki komai ba". A miliyan ta ɗago da kallonta a kansa jin abinda ya faɗa, bata san lokacin da kukanta ya dakata ba, cikin sauri ta ce. "Yanzu kenan ba zan ɗauki ciki ba?". Cike da matsuwar son samun amsa ta yi tambayar tana zazzare mashi idanu. Kai ya jinjina mata kafin ya ce. "Ba zaki samu komai ba dan ni yayanki ne, in wani daban ne ya taɓaki zaki samu, dan haka sai ki kiyaye". Yana magana yana satar kallon kirjinta, kun san yadda wuyan abayoyin nan suke da ɗan girma, to sun bayyanar mashi da halaliyarsa yana kallesu. Bai ankara ba sai ji ya yi ta kwace hannunta daga rikon da ta yi mashi, da sauri ya ɗago da kallonsa a kan fuskarta, sai ya ga ta kai hannu tana goge hawayenta, matsawa ya yi dab ita sosai yana faɗin. "Bari in tayaki". Har zata yi mashi tsiwa sai kuma ta ga ya yi mata kwarjini, dan haka sai ta fasa tana binsa da kallo kawai. Goge mata hawaye ya yi yana cigaba da satar kallon kirjinta. Sai da ya goge tsab sannan ya ce. "Kin yi dinner kuwa?". Kai ta girgiza mashi alamar a'a kafin ta ta kai hannu tana ɗan jan wuyar rigar tata sama dan ta lura da in da yake kallo. "Muje parlo in baki dinner". Ya faɗa yana kawar da kallonsa daga kanta, saboda kunyar suga juna ido cikin ido yake ji. "Bari in yi wanka in zo tukun nan". Ta faɗa tana ƙoƙarin saukowa daga bed ɗin. Da kallo ya bita yana mamakin yadda ALLAH ya amsa mashi addu'arsa, kafin ya zo sai da ya yi addu'ar ALLAH ya ɗorasa a kanta ta hakura sai kuma ga shi ta hakura. Binta da kallo ya yi har ta shige cikin toilet ɗin, ajiyar zuciya ya sauke a bayyane. Sannan ya sauko ya nufi closet ɗinta. Da kansa ya zaɓa mata sleeping dress masu shegen kyau waɗan da suka ɗan yi shige dana jikinsa. A saman bed ya dawo ya ajiye mata su, sannan ya haye bed ɗin, ji yake yi yau tamkar ya mayar da ita cikin cikinsa saboda daɗi. Yana kwance ta fito ɗaure da towel a kirji, bata yi tsammanin yana nan ba, all her though ya tafi shiyasa ta fito, ko da ta fito kuma bata lura yana kan gadon ba, saboda ya shiga cikin bargo ya lulluɓa yana ɗan latsa waya. Waro idanu ta yi tana kallon kayan da ya ajiye mata a saman bed, sai kuma ta sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin ta karisa ta ɗauki kayan. Gaban mirror ta tsaya, sai da ta gama shafe-shafenta har ma da yin make up kafin ta ɗauki kayan ta yi dress room, a nan ta sanya a jikinta, ta yi kyau sosai, sai dai akwai alamar tana jin sanyi sosai. Fitowa daga room ɗin ta yi izuwa tsakiyar ɗakin, har lokacin bata san yana kan gadon ba saboda irin bargon nan ne da idan mutum ya lulluɓa baka iya gane yana a ciki. Hanyar fita ta nufa dan zuwa cin abinci kenan ta ji ya ambaci sunanta. A razane ta juyo har sai da ta bashi mamaki, dan shi bai zaci bata san da shi a ɗakin ba. Juyowa ta yi ta dawo kusa da shi, ba tare da ta kallesa ba ta ce. "Na'am"............ Cike da tsantsar kaunarta a ransa ya ce. "Kin yi kyau sosai, ban zaci zaki sanya kayan dana zaɓa maki ba"....... Kasa ta yi da kai tana ɗan murza hannunta, a cikin zuciyarta tana faɗin meyasa ta saka kayan nasa ne? Yanzu zai zaci ko wani abin ne ya burgeta haka. Can kasar zuciyarta kuma faɗi take ya iya zaɓe, zuciyarta ta narke mashi, kun san kowa yana son mai kyautata mashi. "Har yanzu kina jin haushina ne?". Ya tambaya jin bata yi magana ba. Kai ta jinjina mashi alamar e, kafin ta ce. "Ai har abada ma ba zan daina jin haushinka ba".......... Bai yi mamaki ba, dan idan da sabo ya saba da halinta, amma sai ya ce. "Meyasa ba zaki daina jin haushina ba?". Sabo da masifa yasa ta ɗago idanu ta dalla mashi harara tare da saukewa da sauri kafin ta ce. "Kai ne na farko da ka fara kallan tsiraicina bayan iyayena, ba zan taɓa yafewa ba, kuma ba zan manta ba!". Tana ɗaure fuska ta yi maganar. Shi kuwa sai ya mayar da abin wasa wajen cewa. "Kuma nine na karshen da zan ga kayana ba, babu wanda zai sake gani, kuma ni ai kayana na gani, ke ba matata bace? Ko kin manta ina sonki ne? Aure fa zamu yi". A sanyayye sosai ya faɗi hakan. Ɗagowa ta yi da nufin ta kalli cikin idanunsa ta yi magana, sai ta ji ta gagara yin hakan saboda kwarginin da ya yi mata ba zata iya kallon cikin idanun ba, dan haka ta yi kasa da kai tare da cewa. "ALLAH ya kiyaye in auri yaro kamar kai, ni bana son yara, matar manya ce ni irinsu Uncle Taheer masu shekaru 35 ya yi sa............". Ai haɗiye sauran maganar ta yi sakamakon wani irin shaka da ya kai mata a wuya, shi kansa bai san lokacin da ya diro kasan bed ɗin ya sameta ba, basa iya controlling kishi ne su, suna da zafi a kansa wada kuma wanna a jinin modarawa yake. Matse mata wuya ya yi, idanunsa sun yi jajir sosai, muryarsa har rawa yake yi wajen ce mata. "Idan kika sake danganta kanki da wani namijin bani ba, wlh daga ranar bakinki ba zai sake yin magana ba, kice mun yaro ba zan damu ba, dan dama ni babynki ne, amma kisa a ranki akwai ranar da ko kuɗi aka baki da ki kirani yaro a wancan nufin naki ba zaki kira ba, sai dai ki kirani da baby na nufin soyayya, tabbas zan banbance maki tsakanin baby da yaron da kike nufi very soon". Yana wani irin huci ya yi maganar. Jikinta ne ya hau kerma sosai, kuma har yau kwakwalwarta ya gagara iya tantance mata menene kishi? Bata san shi ba, dan haka ɗaukar abin da yake yi mata a matsayin zalunci take yi, a cewarta bata ga dalilinsa na hanata haɗa kanta da wani namiji ba da tsabar wauta da yarinta. Jin zata iya jin kamshin lahira ba tare da ya lura bane yasa da kyar ta buɗe baki, murya na sarkewa ta ce. "Ka yi hakuri ba zan sake haɗa kaina da wani ba". Take ya ji sanyi a ransa, dan bata taɓa bashi hakuri haka ba, kuma ita bata karya in baku manta ba, dan haka yasan tin da ta faɗi hakan to da wuya ta sake ɗin. Saketa ya yi tare da janye hannunsa baya yana wani irin nunfashi a hankali-hankali. "Muje ki ci abinci kizo ki kwanta dare ya yi". Ya faɗa yana kallon kyawawan dogayen yatsun kafafunta. Ita ma dai mai da numfashi take yi a hankali-hankali tana ƙoƙarin daidaita natsuwarta, jikanta kerma yake yi. "Ni na koshi da abinci". Ta faɗa a sanyaye. Ɗaure fuska sosai ya yi. "Ko kin koshi sai kin ci, dan haka wuce mu tafi". Cikin bada umarni ya yi maganar. Ɗago kai ta yi ta kallesa, take ta ji ta sha jinin jikinta ganin yadda fuskar nan tasa take matau babu alamar wasa, ya haɗe gerar sama da ƙasa. Kara jin shakkarsa ta yi ya mamayeta dikkan ilahirin jikinta, dole ba dan ta so ba ta wuce gaba ya rufa mata baya suka nufi waje. Kai tsaye dining suka nufa, umarni ya bata ta zauna sai ta faɗi abin da zata ci ya zuba mata. Mamakinsa ne ya kamata, yana dai nuna mata kulawa da soyayya, amma kuma yanzu ya zama masifaffen gaske, wai meya birkitasa haka ne kwana biyu? Ta jefi kanta da wannan tambaya. Zama ta yi tana turo baki. "Mezaki ci?". Ya faɗa fuska a ɗaure tamau, dik wannan kyakkyawar murmushin nasa mai ɗaukar hankali yau kwata-kwata babu shi a kan fuskarsa, sai ta ga ya koma mata kamar su Smart. Da kyar ta iya faɗa mashi me zata ci, buɗe kayan abincin ya yi, ya zuba mata daidai da ra'ayinsa ya tura gabanta. Ɗan ɗagowa ta yi ta saci kallonsa, sai taga ai ita yake kallo, jawo plate ɗin ta yi ta hau tura abincin tana turo baki, tsareta ya yi da kallo har sai da ce mashi ta koshi. Da buɗar bakinsa ya ce. "Bai mun ba wannan koshi, dole kicinye abin dake plate ɗinki dikka". Wani irin faɗuwar gaba ta ji da tsoro, tamkar zata yi kuka ta ɗago kai ta kallesa, yau ta tina da shagwaɓar da take yi wa bappa, ai bata san lokacin da ta turo baki game da shagwaɓe fuska ba. "Yah Omar wlh na koshi, cikina kamar zai fashe fa". Haba ai tana zuba wannan shagwaɓa ta narka iron heart ɗinsa, take ya jisa a wata duniya, bai ma san lokacin da ya ɗan shagwaɓe mata fuska ba shi ma ya ce. "A'a to ki kara kaɗan"....... DA ALAMA YARAN MOMMA AKWAI SON SHAGWAƁA. Ta yi mamakin jin yadda ya yi magana, a ranta ta ce kenan idan aka bisa a hankali ne yake da saukin kai? In aka nuna faɗa kuma shi ma sai yazama zaki? Ta jefi kanta da wannan tambaya. Hakika haka ne, komai zafin mutun in ka bishi da sauki dole ya sauko, abin da hankali da natsuwa bai kawo ba tashin hankali ba zai kawo ba, koda Omar ya koma asalin Omar ɗinsa da zarar ta bisa a hankali da shagwaɓa da tausasawa wlh zai sauko, dame Sweetie take cin riba a kan Big Bro? Ai saboda tana binsa a yadda yakeso da tausasawa ne shiyasa. Omar shagwaɓa a jininsa take saboda goyon kaka ne shi ɗin, dan haka in ta bisa a hankali har shagwaɓa ya dinga yi mata ko ya koma ainahin Omar ɗin nasa. Ita ma ta gane wannan karatu yanzu, sai take jin a ranta zata yi maganinsa ta wannan hanya tin da ta gano rauninsa. To ALLAH yasa kada a gari yin maganin nasa ki afka ramin........... Na dai yi shiru Kara turo mashi ɗan baki ta yi. "Cikina fa zai fashe ne, in kuma ya fashe kaga mutuwa zan yi"......... With the same voice da ta yi magana watau shagwaɓa shi ma ya ce. "Ga shi kuma banason ki mutu ba, to shikenan kara spoon ɗaya ina ganinki"........ Satar kallonsa ta yi a yadda ya yi maganar, still dai fuskar a ɗaure tamau. Spoon ta ɗauko ta yi cokali gudan da ya ce kafin ta ajiye tana sauke ajiyar zuciya. Ruwa ya zuba ya turo mata yana yaba mata ta yi kokari. Godiya ta yi mashi, ta karɓa ta sha tana ajiyar zuciya. "Mu je in rakaki ki kwanta dare ya yi". Tamkar zata ce ya bari zata tafi da kanta, amma sai ta tina yanzu ya zama masifaffe, dan haka sai kawai ta miƙe ta yi gaba. Bayanta ya bi yana kalle mata albarkatun jiki har suka kai room ɗinta. Sai da ya tabbatar ta kwanta, ya yi mata addu'ar barci, sannan ya manna mata sumbata a goshi, yana yi mata bye-bye ya fito daga ɗakin ya ja mata kofa. Harara ta dalla mashi tana turɓune fuska har ya fita, sannan ta ja barga tana faɗin masifaffe kawai, waye zai auri yaro irinka? Ni wlh manya nike so, ta kai karshe tare da jan tsaki ta juya baya ta kwanta shiru har barci ya yi awon gaba da ita. Shi ma a nasa ɓangaren yana komawa ɗakin barci ya je ya yi zuciyarsa fes yana ta farinciki yau beb Mahreen ta zama mallakinsa. ---------------------------🔥 Kwance ya iskota a saman bed sanye da camisole and short sleeping set, irin rigunan nan ne masu siraran hannu tamkar vest suna tsayawa a waist, sai kuma karamun short iya gwiwa, ta yi kyau sosai a cikin kayan, ga launinsu pink sai suka kara fito da kyanta. Barci ya yi awon gaba da ita wajen jiransa ya dawo, kusa da ita ya zo ya tsaya, a natse ya yaye bargon da ta lulluɓa. Sai da makogwaronsa ta yi sama ta sake yin ƙasa ganin irin kayan dake jikinta, santala-santalan cinyoyinta a waje. Wani irin yawu mai sauti ya haɗiya kafin ya ɗan rankwafo kanta kaɗan. Hannu bibbiyu ya sanya kamar zai ɗauketa sai kuma ya fasa, saboda a yanayin yadda ya ganta kamar already ta yi dinner, kun san Pretty bata wasa da abinci. Kashe wutar ɗakin ya yi tare da kunna dim, dare ya yi sosai baya jin shi ma zai iya cin wani abin. Zagawa ya yi ta ɗayan side ɗin ya kwanta tare da ja masu bargo. Tamkar jira take yi ya kwanta ta mirgino ta dawo jikinsa, wani irin ajiyar zuciya ya sauke, hannu bibbiyu yasa ya rungumeta, a hankali ya fara shafan bayanta har izuwa saman mazaunanta da suke ɗaukar hankali. Cikin barci ta ce. "Yah Omerish uhmm uhmm ka bari mana"......... Can kasan makoshinsa ya ce. "Baki son in rinƙa taɓaki ne?". Kai ta jinjina mashi alamar e. Ba musu ya zame hannunsa daga jikin nata, ya kwanta shiru yana jin wani irin azababben shaawarta dake neman yi mashi illah. Jin haka yasa ta tuna faɗar da Mahnoor ta yi mata a kan kula da miji, dik irin kular da kuke ga take bashi Mahnoor ta sakata, ita take koya mata komai, ta ja mata kunne sosai a kan hanashi taɓata da take yi, ta ce mata in dai tana hanasa to wlh kara aure zai yi, tina hakan yasa ta ce. "Yah Omeris". Can kasa-kasa ya ce. "Ma'am my wifey"............. "Fushi ka yi da ni?". "A'a meyasa zan yi fushi dake?". Kai ta ɗago ta manna mashi sumbata a kumatu tana murmushi. Shiru bai amsa mata ba, hakan yasa ta matsar da face ɗinta dab da nasa, slowly ta capko lips ɗinsa na kasa, kissing ɗinsa ta fara yi cikin wani irin salo mai jan hankali sosai. Shiru alamar ba zai biye mata ba tin da ta ce ya daina taɓata, hannunsa ta kama ta ɗaura a saman........... Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 Shiru alamar ba zai biye mata ba tin da ta ce ya daina taɓata, hannunsa ta kama ta ɗaura a saman mazaunanta tana shagwaɓe mashi fuska. Sarai ya fahimci so take ta gyara kuskurenta, tasan ta yi ba daidai ba, amma sai ya rabu da da ita kamar bai sani ba, ba wai baya son taɓata ɗin bane, so yake ya gwada mata ba a kan taɓata zai iya aikata komai ba, ma'ana ba zata iya buɗar baki ta bashi hakuri ba sai dai ta yi ƙoƙarin saukar da fushinsa ta hanyar surar jikinta, idan har ya biye mata yau to har abada ba zata koyi bada hakuri a kuskure ba, kullum ta yi mashi laifi zata yi amfani da surar jiƙinta ne dan ya sauko, yazama tamkar bai san ciwon kansa ba, hakan ba karamar rusa zamansu zai yi ba, yana da kaifin kwakwalwar hangen nesa shiyasa yaki biye mata har sai ta gane kuskuranta da kanta ta faɗi ga kuskuren nata ta bada hakuri. Lumshe idanunsa ya yi yana jin wani irin azababben sha'awarta dake neman yi mashi illah, ita kuma kissing ɗinsa ta rinƙa yi amma yaki biye mata, a ranta take jin kamar fushi ya yi da ita, shi kuma ya ce a'a bai yi ba. Zame bakinta daga nasa ta yi ta kwantar da kanta a saman kirjinsa shiru, idanunta ne suka cicciko da kwallah, ALLAH sarki bata saba da irin wannan yanayi na fushinsa ba, shiyasa idanunta suka ciko da kwallah, amma ko kaɗan bata ji kamar zata bashi hakuri ba, dan bata ɗauki abin da take yi mashi a matsayin laifi ba, kun san jinin sarauta na gudu a cikin jininta ita ma, sai izzar balai. Yana jinta ta fara ruwan hawaye, amma sai ya yi tamkar bai ji ba, daga karshe ma ya gyara ya ɗan juyar da ita suna fuskantar juna, idanunsa a datse tamkar mai yin barci. Kurawa kyakkyawar face ɗinsa idanu ta yi tana kallon yadda ya kara kyau sosai kwana biyun nan. Hannu tasa ta ɗan shafi kyakkyawar sajensa kaɗan kafin ta ce. "Yah Omerish". Ba tare da ya buɗe idanunsa ba ya amsa mata da na'am. "Fushi kake yi dani dan na ce kada ka taɓani?"........ Still bai buɗe idanunsa ba ya amsa mata da. "Meyasa zan yi fushi dake? Barci nike ji kawai, kwanta ki yi barci dare ya yi". Ɗan turo baki ta yi, a shagwaɓe sosai ta ce. "To ai kana bani hot kiss na barci kullum, yau baka bani bane kake tunanin zan yi barci?"......... Nisawa ya ɗan yi kafin ya matsar da face ɗinsa, a forehead ɗinta ya manna mata sumbata har lokacin bai buɗe idanu ba. Kukan shagwaɓa ta saka mashi tare da cewa. "Kullum a baki kake bani ai, amma shi ne yau zaka bani a goshi? To ni bana so"........ Tamkar mai raɗa ya ce. "Omnish ki barni mana, barci nike ji sosai, kwanta ki yi kema da safe kome kike so zan yi". Mamaki ne tamkar zai kasheta ta kara waro ido da kyau a kansa, dan ko da sunan wasa bata taɓa sanin cewa Smart yasan ainahin sunanta ba, bai taɓa kiranta da shi ba, lallai ta kara tabbatarwa ransa ya ɓaci. Shi kuwa saketa ya yi tare da juya mata baya ya kara jawo bargo, ya yi wa kansa alkawari in har bata gane kuskurenta har ta bashi hakuri ba ba zai sake taɓata ba, dan ma tasan ba dan jikinta ya aureta ba, kuma dik karfin sha'awar da suke da shi suna iya controlling kansu, ba wai haka suke kamar dabbobi ba!!. A maimakon ta bashi hakuri sai ita ma ta juya mashi baya tana hawaye, a shirme da yarinta irin tata, wai shiyakamata ya bata hakuri, dan haka ita ma ta yi fushi, yana jinta tana kuka amma ya danne kamar bai ji ba, da ta isheshi ma sai ya ja bargo har kansa ya rufe, ya toshe kunnensa daga ta ciki. KAI JININ SARAUTA DA JININ SARAUTA NE SUKA HAƊU, KOWA SAI JI DA IZZA, NI KAM ZAN GA YA ZA'AYI A SHIRYA TIN DA KOWANNE YANA JIRA A BASHI HAKURI, AMMA BATU NA GASKIYA PRETTY CE DA LAIFI, SMART YA FITA GASKIYA, GARA YA NUNA MATA KUSKURENTA, DAN TANA YI MASHI ABIN DA TAKE SO YANA YAWA, SO GARA YA FARA NUNA MATA KUSKURENTA!. Sai around 1:30 barci ɓarawo ya ɗauketa. Fahimtar ta yi barci ne yasa ya miƙe zaune tare da yaye bargon, gefe ya ajiye game da juyowa kanta. Ɗan kura mata idanu ya yi, a fili ya ce. "Rigimammiya kawai, ban taɓa tinanin akwai ranar da zaki yi kuka a gabana in iya shanyewa ban rarrasheki ba, amma yau kin sa na yi". Ya kai karshen maganar tare da kai hannunsa saman kumatunta ya goge mata ragowar hawayenta, a hankali ya gyara mata kwanciya, dan ta dunkule waje guda, ya gyarata tare da manna mata sumbata a saman ɗan lips ɗinta. Can kasan makoshinsa ya ce. "Kome kika mun sonki ba zai taɓa raguwa a raina ba, i really love you more than a word can say". Saukowa kasan bed ɗin ya yi ya nufi toilet ɗinsa. Wanka ya sake yi tare da ɗauro alwala ya fito, nafilfili ya fara yi, shi ne har karfe 4 bai kwanta ba, bayan ya idar da karatun Alqur'ani mai girma ya fito ya nufi bedroom na momma, a bakin door ya tsaya. A hankali ya fara knocking, a tinaninsa tana barci, ashe tana kan dadduma baiwar ALLAH, wai mace mai irin halin momma ta yaya ALLAH ba zai taimaketa ba a rayuwa, yaro irin Big Bro kawai ALLAH in ya baka ai an sallameka, bare ga su Smart, Jaish kawai ya fi su Bilal komai da komai, ga su guyson kwautar ALLAH, ance ku zama na kirki ku mori duniya da lahira kuna ganin kamar wasa ne, ai in kazama na kirki wlh ba zaka taɓa sanin ta in da ALLAH zai baka sakayya ba, kawai zaka yi ta ganin alkhairi ne palala ta ko'ina, hmmmm ALLAH ka sa mu zama irin momma completely. Da yake jaruma ce bata da tsoro tana daga kan dadduma ga Alqur'ani mai girma a gabanta tana karatu ta ce. "Shigo mana". Bafa ta san waye bane, amma saboda tana gaban UBANGIJINTA rike da Alqur'ani ta yarda babu wanda zai iya cutar da ita a wannan waje, shiyasa da confidant ɗinta ta ce a shigo. Turo kofar ya yi ya shigo, ta ɗan yi mamakin ganinsa, hakan yasa tana kai aya ta rufe Alqur'ani tare da juyo da kallonta a kansa. A saman sofa ya zauna yana faɗin. "Momma barka da dare"........ Cikin zolaya ta ce. "A gidanku ne daren ko?". Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "To barka da safiya". Still cikin zolaya ta ce. "Yaushe garin ya waye?". ....... Dafe kansa ya yi, tamkar karamin yaro ya ce. "Momma ki bari mana, ni to me zan ce? To barka da tsakiyar dare". Murmushi ta yi tana faɗin. "Ai sai ka faɗa, meyahanaka barci?". Ta yi maganar tana kallon face ɗinsa sosai, dayake akwai haske a ɗakin, ta ga alamar damuwa sosai a kan fuskarsa, kamar yana buƙatar wani abu kuma bai samu ba haka, har ta ganosa, tina yanayin Pretty and yanayin yaran nata ta yi, a take ta gane matsalar, dan ma ga idanunsa jajaye har yanzu basu washe ba. Katse mata tinani ya yi da cewa. "Momma cappuccino nike so, zan tashi da azumi ne"........ Da sauri ta katse shi da cewa. "Saboda meyasa zaka tashi da azumi?". Tambayarta da alamar tuhuma. Shiru ya ɗan yi, dan dalilin yin azuminsa ya ji ta ɗan yi mashi nauyin faɗa ne, dama zai yi azumin ne dan kaucewa shiga wani hali, Pretty tana caza mashi kai, and ya yi alkawarin sai ta gane kurenta zai sake taɓata, so gwara ya rinƙa yin azumi, da daddare ya kwana sallah dan gudun matsala. "Na gane, meyasa kake tinanin Omnish ba zata iya ɗaukarka ba? Meyasa zaka cutar da kanka har haka? A'a bana so, babu wani azumin da zaka ɗauka kana da mata". Ta faɗa tana kallon fuskarsa. Dik rashin kunyarsu yau ya tsinci kansa da jin nauyin yin maganar nan da ita, sai ya ɗan yi ƙasa da kai. "Da safe ka turo mun Omnish ɗin, ba zan yarda da shirmen nan naku ba, a tinanina Omnish zata kai 15 years a yanzu ko?"....... Kai ya ɗan girgiza kafin ya ce. "A'a sai dai 13 ko 14, kawai suna da cikar halitta ne amma basu da wani shekaru". Kai momma ta ɗan jinjina saboda ita kanta da jin shekaru sai ta ji tausayinsu ya kamata, dan tasan ba iyawa zasu yi ba. Amma sai ta ce. "Ka bita a hankali zata iya, a hankali zata saba"...... KAI UWA DABAN TAKE WLH, ALLAH YA KARA MASU LAFIYA, WAƊAN DA SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA ALLAH YA HASKAKA MAKWANCINSU, MU KUMA ALLAH YASA MU CIKA DA KYAU DA IMANI. Yau sai ga Malaman Smart da sunkuyar da kansa kasa irin kunyar nan. "ALLAH ya yi maku albarka, a dik lokacin da na ɗaga idanu na kalleku sai in ji tamkar na fi kowa sa'a a duniyar nan, ina alfahari da ku ƴaƴana". A tausashe ta faɗa, so take ta canza masu topic na hira, dan taga ya ɗan takura. Ajiyar zuciya ya sauke jin kalamanta, a natse ya sauko daga sofar, kusa da ita ya dawo, a saman shinfiɗar ya kwanta tare da kwanto da kansa a saman laps ɗinta, yana kallon fuskarta kafin ya ce. "Momma munfi ki alfahari, saboda ba kowa bane yake samun uwa irinki, sai an tona, dik kece kika zama silar zamanmu abin alfahari". Hannu ta kai tana shafa kansa. "Baka faɗa mun sunan ɗan uwanka ba! Ni ban san meyasa fuskarsa take bani tsoro ba, idan muka haɗa ido da shi ina jin faɗuwar gaba kamar akwai wani abin da yake damunsa ko yake faruwa da shi a ɓoye, na gagara zama in yi magana da shi, saboda in yana kusa dani ina fuskantar faɗuwar gaba sosai, ni nasan ba lafiya yake ba, a jikina ina jin hakan, amma ban san tayaya zan iya tambayarsa ba". Tin da ta fara magana ya tsareta da ido har ta kai karshe, sannan ya nisa sosai, dik abin da ta faɗa gaskiya ne, shi kansa yana zargin akwai abin da yake faruwa da ɗan uwan nasa, dan yana jin hakan a jikinsa, wai lokacin sai ya ji tamkar ana amfai da wani ɓangare na jikinsa, kun san su identical haka suke, dik lokacin da Big Bro yake magic Smart yana jin tamkar ana amfani da jikinsa, dan shi baya magic, sai ya ji zuciyarsa ta ɗau zafi, ransa ya ɓaci sosai ko da babu abin da aka yi mashi, to ɓacin ran daga zuciyar Big Bro take fitowa, dan in zai yi magic fa dik wani black heart sai ta motsa. "Momma ni kaina ban san zunansa ba, amma kada ki damu babu wani abin da yake faruwa da shi, ba dai kina addu'a ba?". Kai ta jinjina mashi. "To In Sha ALLAH babu wani abu na sharri da zai faru, ki cigaba da addu'a, batun sunansa anjuma zan tambayesa, dan ni da Big Bro nasan shi". Shafa kyakkyawar face ɗinsa ta yi. "ALLAH ya yi maku albarka". Da amin ya amsa kafin ya miƙe saboda an fara kiraye-kirayen sallar asuba. Sallama ya yi mata ya fito ya koma bedroom ɗinsu. Saman dadduma ya koma ya zauna yana tinanin gaskiyar momma lokaci ya yi da zai mai da Pretty cikakkiyar mace, saboda hakurinsa ya fara kai karshe. ------------------------------🔥 07:00AM. A hankali ya waro idanunsa da suka yi mashi nauyi tamkar barcin bata isheshi ba, yana waro idanun nasa ya wurga balleyes ɗinsa saman sofarta. Ɗan nisawa ya yi kafin ya yunkura ya miƙe zaune yana cigaba da kallon room ɗin, ga wani sanyayyar kamshin dake tashi mai kwantar da hankali. Lumshe idanunsa ya yi tare da sake warosu a kan sofa ɗin, bata nan shiyasa yake dubata ta hanyar wuwwurga eyesball ɗinsa. Yaye bargon ya yi, a hankali ya zuro kyawawan kafafunsa kasan bed ɗin kafin ya miƙe ya nufi toilet. Yana shiga ciki ita kuma tana shigowa cikin room ɗin cikin wani irin kyakkyawan shiga, ta yi wanka, yau Chuchu ta yi mata make up, wani irin fitinannen kyau na musamman ta yi, tana sanye da Dubai Abaya, Chuchu ta yi mata rolling gyalensa, tamkar ka saceta ka gudu, komai na Sweetie very unique ne, lipa ɗinta sun kasance dark purple wanda ba'a saba ganinsa a yau da kullum ba, ga launin hair ɗinta, anya kun taɓa karanta mai irin sifofinta a littatafai kuwa? Golden white hair, dark purple lips ya kuke hango kyanta cikin wanna abaya. Chuchu bata sanya mata janbaki ba, saboda yadda lips ɗinta kalarsu ya bayyana sosai, sai ta sanya mata lips balm dan su kara sheki da ɗaukar hankali. Gashin gerarta tamkar an zana. Abayar Auta ta sanya, da yake tana da tsawo sai ya yi nata daidai, ga high heel da ta saka a kafa, kyau iya kyau. Kayan abinci ne rike a hannunta, a saman carpet ta shiryasu, sannan ta juya ta fita. Bata sake dawowa room ɗin ba har ya fito daga wanka, ya shirya cikin silky pj's saboda yana son fita ya je wajen aikin da ake yi ya duba yanayin aiki, so no need for kaya mai nauyi. Ya yi balain kyau, sai tashin kamshi yake yi. Wayarsa ya ɗauko tare da komawa gefen bed ya zauna. Kunna wayar ya yi yana ƙoƙarin nemo number ɗinta ya ji ina ta tafi da sassafen nan kenan sai ya ji an turo door ɗin. Slowly ya ɗago idanunsa, ai bai san lokacin da ya waro idanun nasa gabaɗaya a kanta ba, irin like wow, buɗe idanunsa gabaɗaya a kanta ya yi, hannunta na rike da kwandon fruits masu balain kyau da ɗaukar hankali. Kusa da abincin ta karisa ta ajiye kwandon, sannan ta nufo saman sofa ta zauna tana kunna hasken screen ɗin wayarta. "Good morning King of my heart". Ta faɗa tana satar kallansa, dan ya yi kyau over. Bai amsa mata ba saboda ya mace a kallonta, sai da ta sake maimaita mashi, nisawa ya yi tare da sauke ajiyar zuciya. Wayarsa ya kunna tare da shiga Whatsapp. "You're over my Omaish, kin yi kyau over to over". Abin da ya yi mata typing ya tura kenan. Wani irin cool murmushi ta saki wanda tasa zuciyar Big Bro ya yi wani irin amsawa, har bai san lokacin da ya ɗan rintse idanu ya furta wash ba. Bayan ta kammala karanta sakonsa sai ta turo mashi. "Ko rabinka ban kai a kyau ba, kai makura ne nawan, komai naka daban yake da kowa". Tana ji ya sauke ajiyar zuciya da ya karanta sakonta. "Good morning, my sunshine, as the world slowly wakes up, my heart is already wide awake thinking of you, your love is the light that brightens even my darkest mornings, I hope your day begins with a smile and ends with peace, knowing you are deeply loved, may every breath you take today remind you how precious you are to me, have a gentle, beautiful day, my queen". Sakon da ya sake tura mata kenan na good morning da ta ce bai amsa ba. Ɗan ɗago idanu ta yi ta saci kallonsa, kallonsa na a kan screen ɗin, murmushi mai narka zuciya ta sake yi kafin ta hau yi mashi reply. "Morning my king. I hope you slept well and woke up with peace in your heart, just knowing you're out there makes my world brighter, may your day be filled with calm thoughts, easy moments, and quiet victories, always remember you're not alone, l believe in you, I'm proud of you, and I love you more with every sunrise my heart". Ta tura mashi ita ma. Lokacin da ya gama maranta sakonta sai da ya ɗago ya saci kallonta, a lokacin tana sake yi mashi typing na neman tsokana. "Ya naga lips ɗinka suna shining ne? Anya baka yi mafarki ba kuwa?". Abin da ta rubuta kenan ta sake tura mashi. Ya ɗauka da gaske take yi, dan bai saba da zolaya ba sai da Smart ya fara koya mashi, sai ya ce mata. "A'a ban yi mafarkin kowa ba". ......... Murmushi ta ɗan yi da ta gama karantawa. "Ban yarda ba, dik yadda aka yi ka yi mafarki, kaga yar mommarta ta yi kyau ka kyatsa har da magarkina ko? To asirinka ya tonu ne, sau nawa ka mun kiss a cikin mafarkin?". Amsar da ta rubuta mashi kenan. Tana turawa ta ɗago tana kallonsa. Lokaci guda ta miƙe a miliyan ta nufi waje da gudu saboda yunkurawa da ya yi da zafa zai capkota. Ai taku ɗaya ya yi ya rikota, da hannun ɗaya ya jawota jikinsa. Zazzare mashi idanu ta fara yi jikinta na kerma, saboda ta ɗan tsorata, numfashinta har ɗan sarkafewa yake yi. Slowly ya rankwafo kanta, tamkar mai raɗa ya ce. "Baki yi karya ba, na ganki na kyatsa, amma kiss fa ban yi na boge a mafarki ba, yanzu nike son yin na gaske dai"........ Da sauri ta hau girgiza mashi kai. "Please wlh wasa nike maka"..... "Zan maida wasan zuwa gaskiya". Ya yi maganar tare da kara jawo waist ɗinta ya mannata da jikinsa sosai. Da yake tasan rauninsa a yanzu, tasan me zata yi mashi ya bi layin da take so, sai ta kwanto da kanta a saman kirjinsa, a hankali ta kai hannu tana shafa lion chest ɗinsa daidai wannan cross ɗin nasa, a shagwaɓe ta ce. "Ni ba zan hanaka kayanka ba, ni ai taka ce, amma please ka girmama addinina tamkar yadda nike girmama naka, kaga dai ni ina balain son Yesu, kuma ina bin dikkan umarninsa, and kaima kasan Yesu ya yi hani da abin da zamu yi a yanzu ko?". Kai ya jinjina mata alamar haka ne. Jin haka yasa ta sake ce mashi. "Yesu ya haramta zina, idan ka yi kissing ɗina ka karya umarnin Yesu, please tin da ina girmama addininka kai ma ka girmama nawa ka ji?"......... Kai ya jinjina mata tare da ɗan saketa da sauri, saboda in baku manta ba ya ce yana balain kaunar Annabi Isa, kuma yana bin dokokinsa. Wani irin daɗi ta ji ya ratsa mata zuciya, ji ta yi tamkar ta rungumesa ta manna mashi sumbata, amma sai ta basar tare da cewa. "Zo mu yi breakfast". Kai ya ɗan girgiza mata kafin ya ce. "Bari in duba momma and dad in zo"....... Kai ta jinjina mashi alamar to, ta wuce ta koma sama sofa ta zauna tana binsa da kallon kauna mai narka zuciya. Cike da kaunarta a ransa ya fito shi ma ya nufi room ɗin momma. --------------------------------🔥 Hannunta a ɗauke da kayan abinci ta shigo room ɗin, Smart na zaune a gefen bed, kallo ɗaya ya yi mata ya yi gaggawar kawar da kallonsa, saboda wasu shaggun kaya ne a jikinta, wandan jeans ne da top, ta yi balain kyau a cikin kayan, shi ne yasa ya yi gaggawar kawar da kansa dan kada ta tada mashi wani abin. A saman carpet ta ajiye abincin tare da juyowa ta dawo in da yake zaune. "Yah Omerish good morning". Ya ji mamakin wanna gaisuwa sosai, tare suka tashi a ɗakin, tana kwance tana fushi da shi tana binsa da ido har ya yi wanka ya shirya ya fita ya je wajen king, dik bata yi mashi magana ba, yana fita ta tashi ta yi nata wankar ta shirya, lokacin da ya dawo ɗakin ma bata nan, dik fa bata kulasa ba, sai yanzu ta dawo masu da breakfast shi ne kuma wai ina kwana? A ransa ya ce to ko dai momma ta yi mata faɗa ne? Ko kuma dai wani abin take shirya mashi ne?. Jin ya yi mata shiru ne yasa ta ce. "Kazo mu yi breakfast"..... Kallonta na ƴan sakanni ya yi kafin a ransa ya ce okey hakuri ne ba zata bada ba kenan, lallai ma Pretty. Miƙewa ya yi ya karisa wajen abincin, bayansa ta bi da kallo tana mamakin kin yi mata magana da ya yi, sai ta fara harararsa, a ranta ta ce. "Zan yi maganinka ne, zaka gane Annabi Isa ba ɗan ALLAH bane manzon ALLAH ne". A fili kuma harararsa ta cigaba da yi. Sarai ya ganta, amma sai ya yi tamkar bai san tana yi ba, ya zuba abinci ya hau ci a natse abinsa. Good seven spoon ya ci sai ya ajiye spoon ɗin tare da kai hannunsa dikka biyu ya daddafe cikinsa, da sauri ya ɗago idanu ya kalleta, wani uwar harara ta dalla mashi dan ya bata haushi da bai kulata ba. "Omnish me kika saka mun a cikin abinci?". Ya tambaya da kyar muryarsa na sarkewa. Tana harararsa ta ce. "Maganin mutuwa"....... Zazzaro mata idanu ya yi, sai kuma ya yunkura zai miƙe, amma ya gagara, saboda wani irin azababben murɗa da cikinsa yake yi. Tongue ɗinsa ya fitar waje ya datse da hakwaransa gam tamkar zai tsinke tongue ɗin, kokarin sake yin magana ya yi, amma ya kasa, da hannu ɗaya ya yi pointining ɗinta yana son cewa. "Dama zaki iya kasheni?". Amma ya gagara iya yin magana. Take wani irin farin kumfa tas ya fara bulbulowa daga bakinsa, kafin ta farga sai gani ta yi ya sulale kasa ya kwanta yana wani irin murkusoso ya dafe cikinsa sosai, gefe-gefen idanunsa ruwan hawaye ne masu zafin gaske suke zuba alamar ba karamr azaba yake sha ba. Wani irin ihu ta zumduma tare da miƙewa da gudu ta yi kansa tana faɗin. "Yah Omerish me kake yi haka? Dan ALLAH ka tashi, ka bar irin wannan wasa bana so". Muryarta rawa yake yi sosai da take wannan magana. Ta yi maganar tana girgiza shi. Sai dai ina, bayan wannan murkusoso babu wani abin da yake iya yi, idanunsa ma yanzu rufewa suke yi tamkar wanda ake zarewa rai. Kuka ta fara yi hawaye sharɓa-sharɓa a kuncinta tana cigaba da girgiza kirjinsa tana kwala kiran sunansa. Yana son cewa ta bashi ruwa saboda wani irin azababben kishin da yake ji, makoshinsa tai balain ɗaukar zafi tamkar wuta ake hurawa a wajen, amma ya gagara ko yunkurin yin maganar. A daidai wannan lokaci shi kuma Big Bro yana zaune saman sofa, momma na zaune a saman bed suna fuskantar juna, lokaci guda ya ji kirjinsa ta buga makoshinsa ta ɗauki zafi sosai kamar yana son shan ruwan. Momma na yi mashi magana amma hankalinsa bayaa kanta, saboda ji yake yi tamkar a takure yake, tinawa da ya yi su identical ne yasa ya ce to ko dai Omerish yana cikin damuwa ne?. Ɗago kai ya yi ya kallon momma, a sanyayye sosai ya ce. "Ina Omerish ne momma?"........ "Ina ga yana barci, dan jiya bai yi barcin dare ba, nan ya zo muka yi hira, ina ga yana biyan barcin ne"...... "Shi ne ba'a kirani ba kuka yi hiran ku biyu". Murmushi momma ta yi kafin ta ce. "Ai ka yi barci ne lokacin".......... Shiru ya ɗan yi, shi dai a ransa yana jin wlh Smart baya lafiya, saboda zuciyar twins tana irin wannan bugawa ne kawai idan ɗayansu baya lafiya. Ɗago kallonsa a kan momma ya yi, sai ya ga ta yi gaggawar cire idanunta daga kansa, mamaki ne ya kama shi, kenan in baya kallonta tana kallonsa, in kuma ya kalleta sai ta cire ido? Ikon ALLAH, wai meyasa suke tsoronsa ne? Ya jefi zuciyarsa da wannan tambayar. "Momma zan je duba Omerish". Ya faɗa tare da yunkurawa zai miƙe ta katse shi da cewa. "Lafiya dai ko?"...... Kai ya gyaɗa mata kafin ya ce. "Babu komai, ina kewarsa ne"........ Kun santa da ƙwaƙwalwa ita ma, sai ta zargi ba lafiya ba, dole akwai abin da yake ji a ransa ko kuma akwai abin da suke shiryawa shi da Smart ɗin. Miƙewa ya yi, yana taka step biyu sai ga Pretty ta shigo da gudu tana kuka tana faɗin Yah Omerish ya mutu. Momma and Big Bro har suna rige-rigen tarota dan tambayar me yake faruwa?. Tana kuka tamkar ranta zai fita ta ce. "Yah Omerish yana cin abinci kawai ya faɗi kasa yana amai sai kuma ya daina motsi"......... Ai tin bata kai karshen maganar ba Big Bro ya yi zafan yin waje tin da ya ji Smart ɗin yana ɗakinsa. Da sauri momma ta rufa mashi baya rike da hannun Pretty ɗin. A lokacin da suka isa ɗakin Smart baya motsi. Da ace tin lokacin da ya fara murkusoson nan ta gudu ta sanar da su, kila su iya cetan rayuwarsa, amma a yanzu poison ɗin da ya ci ya yi affecting abubuwa da dama nasa, ta yi damage na cikinsa, ba zai rayu ba in ma yana da sauran nunfashi a yanzu kenan. Poison ya ci a cikin abincin nasa........ DAGA INA AKA SAMU POISON A CIKIN ABINCIN DA MOMMA KAWAI KE GIRKA MASU? SABODA TSARO DA LAFIYARSU BABU WANDA YAKE KAI MASU ABINCI SAI MATANSU NA SUNNA DA SUKA YARDA DA SU, TO HOW COMES AKA SAMU POISON?. AKWAI KURA WLH. A gabansa suka tsugunna, Big Bro ya kai hannu ya laƙaci kumfar dake bakin Smart, slowly ya juyo da kallonsa a kan Pretty dake ta faman kuka. "Kafin ya ci abinci bai ci komai ba?". Da sauri ta gyaɗa kai alamar e bai ci komai ba. Dawo da kallonsa a kan momma ya yi. "Poison ya ci, kuma ina ga daga cikin abincin nan ne, waye ya girka abincin?". Zazzaro idanu momma ta yi kafin ta ce. "Omerish baya cin abincin kowa idan ba ni na girka mashi ba, dan haka nina girka abincin nan da hannuna, kuma babu wanda ya taɓa abincin nan har Omnish ta zo ta ɗauka mashi"........ Pretty na girgiza kai tana kuka ta ce. "Wlh nima har na kawo mashi abincin nan babu wanda ya taɓa shi, yadda na ɗauko daga ɗakin momma babu wanda ya buɗe abincin har na kawo mashi". Kai tsaye Big Bro ya ce. "To kenan ke kika yi poisoning ɗinsa!!". Tashin hankali! Zazzaro mashi idanu ta yi tamkar kwayar zasu faɗo ƙasa, wani irin ruɗani da ta shiga bata san lokacin da ta fara girgiza kai tana sake gyaɗa kai sama alamar e da a'a ba. Miƙewa Big Bro ya yi ya cicciɓi Smart zuwa saman bed, hannu ya sanya a saitin zuciyarsa dan ya ji tana bugawa ko bata yi! Tsit ya ji babu wani motsi, gabaɗaya jikin Smart ta saki. Hankalin Big Bro idan ya kai miliyan to a yanzu ya tashi, har wani juya mashi ya ji kansa yana yi, da kyar ya iya cewa. "Me ya yi maki da zafi haka da har zaki yi poisoning ɗinsa?". Yadda ya yi magana sai da ya razana momma, bata taɓa jin murya mai firgitarwa da rikitarwa irin wannan ba, bata san in ransa ya ɓaci voice ɗinsa ma canzawa take yi ba. Muryarta na rawa ta hau girgiza kai tana faɗin. "Wlh bani bane"....... With harsh voice sosai ya ce. "Idan bake bace wacece?!! Meyasa a lokacin da ya fara ciwon baki kiramu ba sai bayan ya mutu?!! Meyasa ke baki ci abinin ba bayan a tare kuke breakfast kullum?!! Karya kike yi, ke kika yi poisoning ɗinsa!! Ko kuma da haɗin bakinki aka yi!!". Ya faɗa tare da miƙewa cikin zafa yana pointining ɗinta da hannu. Kuka mai sautin gaske ta fashe da shi kafin ta ce. "Wlh bani bace, fushi nike yi dashi shiyasa ban ci abinci da shi ba, dama ina son in ya gama ci ya fita ne sai nima in ci nawa, amma wlh bani bace.......". Bata karisar da maganar ba ta ɗauke diff sakamakon........... Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only please. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 BAN SAMU DAMAR YIN EDITING BA SABODA BANI JIN DAƊIN JIKINA!!.👏🏻 Kuka mai sautin gaske ta fashe da shi kafin ta ce. "Wlh bani bace, fushi nike yi dashi shiyasa ban ci abinci da shi ba, dama ina son in ya gama ci ya fita ne sai nima in ci nawa, amma wlh bani bace.......". Bata karisar da maganar ba ta ɗauke diff sakamakon ganinsa a gabanta da ta yi, har wani sama-sama ta ji numfashinta yana yi saboda razana. "Meyayi maki da kika yi mashi wannan hukunci?". Ya faɗa fuskar nan a ɗaure tamau. Gagara yin magana ta yi saboda tsoro da tashin hankali da ta shiga, ita damuwarta ma kawai shi ne su faɗa mata Smart ɗinta yana raye ko yaya? Shi take yi wa kuka yanzu, bata san ina zata sanya rayuwarta ba idan ya mutu, ba zata iya jura ba!. Ganin alamar yana son ɗaga hannu zai kai mata duka ne yasa Momma ta yi gaggawar matsawa ta shiga tsakaninsu, hannun nasa ta riko, muryarta a raunace cike da tashin hankali ta ce. "Gaskiya Omnish ba zata iya yin poisoning ɗin Omerish ba, dole dai akwai abin da ya saɓa, ko akwai wanda ya karɓi abincin lokacin da kika fito da shi?". Ta yi maganar tana juyo da kallonta a kan Pretty. Kai ta shiga girgizawa. "Wlh momma babu wanda ya karɓi abincin nan, tin da na ɗaukosa har na zo babu wanda ya taɓa shi". YAU FA AKE YINTA. Shiru momma ta ɗan yi tana tinanin, wlh ita ma tin da ta girka abincin nan ta kawo room ɗinta bata fita ba, kuma alamu sun nuna a iya abincin Smart aka sanya gubar ba a dikka abin da ta girka ba, da dikka ne to su Sweetie ma ba zasu tsira ba, dan tukunya ɗaya aka yi girki, zubawa kowa nasa kawai aka yi, a iya abincin Smart ɗin kawai aka sanya.......... Kansu ya ƙulle. "Momma ku je waje". Big Bro ya faɗa da kyar, dan sam baya son buɗe bakinsa saboda wani irin ɗaci dake ransa in ya buɗe baki za'a iya samun matsala!. Jin yadda ya yi magana yasa momma bata sami kwarin gwiwar iya ce mashi a'a ba, dole ta ja hannun Pretty suka nufi waje, sai kuka Pretty take yi tamkar ranta zai fita. Shi kuma dawowa ya yi wajen Smart, saman bed ɗin ya haye tare da matsawa dab da ɗan uwan nasa, zuciyarsa na tafarfasa ya haɗe fuskokinsu waje guda. A hankali ya zuro doguwar tongue ɗinsa waje, sai ya kai hannunsa ya ɗan matsa kumatun Smart, hakan ya bawa bakin nasa damar buɗewa kaɗan. Tongue ɗinsa ya zura cikin bakin Smart ɗin, take idanunsa suka canza launi, da tongue ɗinsa ya yi amfani wajen buɗe hanyar makogwaran Smart, kunga ai ba idanunsa biyu ba, so dole hanyar makogwaronsa tana datse, sai ya yi amfani da tongue ɗinsa ya buɗe hanyar. A hankali ya fara zubawa Smart yawunsa a cikin baki tana samun hanyar wucewa zuwa cikinsa, har lokacin huci yake yi. Kun san shi da yake master ne a magic, yawun bakinsa tana karya abubuwa dayawa ciki harda sihiri, yawun nasa zata sanya Smart ya yi aman poison ɗin kaf, sai dai kuma ko ya tashi zai sha jinya, dan abin ya yi affecting ɗinsa sosai. Ko da sunan wasa Big Bro baya taɓa tofar da yawunsa a waje, dan yasan me a cikinta, yanzu ma ba dan Smart bane bai ga dalilin da zai sanya ya bashi ba, saboda ba kowa yake samu ba, sai Sweetie mai facacity da ta lashe mashi zuciya. Yawunsa ba kamar na sauran mutane bane!. -----------------------------🔥 Cike da tashin hankali ta ja hannun Pretty suka nufi parlon King. Nan ta isko su mama, kusan dai dikka family suna a wajen, ga King yana zaune a saman sofa, kun tina zaman da jiya ya ce yau za'ayi? To shi ne ya fara haɗo kan family dan ayi wannan zama, ita ma Momma ɗin sau biyu yana kiran numbarta dan ya ce tazo tare da su Smart amma bata ɗaga ba. Kasancewar Pretty na kuka ne yasa dik suka kai kallonsu a kanta. Jaish ne ya miƙe yana tambayar momma ko lafiya. A tsananin ruɗe ta ce. "Ina fa lafiya. Ranka ya daɗe anyi poisoning Omerish". Ta faɗa tana kallon King. Ai yana daga zaune bai san time da ya miƙe a miliyan ba, har yana haɗe word wajen cewa. "Ban gane anyi poisoning Omerish ba?". Bayani momma ta shiga yi masu yadda komai ya wakana. Salati gabaɗaya parlon suka saka, guyson dake a zaune kusa da mummyn Chuchu, ya kwanto da kansa a saman shoulder ɗinta yana zuba mata shagwaɓar da ya saba ne, in baku manta ba dama ɗan ɗakin ta ne. A miliyan ya miƙe yana zaro ido cikin tashin hankali. Obaid and Omaid dik a razane suka mimmiƙe suna salati. Jaish, King, Mummyn Chuchu, guyson har suna haɗa baki wajen cewa ina Smart ɗin yake a kaisu wajensa.. Nan fa Momma ta sanar da su Big Bro ya rufe kofar suna cikin ɗaki da shi, dan haka dole a jira fitowarsa kawai. Mama ce ta ɗan ja siririn tsaki yadda kowa ba zai iya ji ba, a ranta ta ce in ya mutu sai na fi kowa murna, a fili kuma ta mike tsaye ita ma tana binsu one by one da kallo wai dan kada ace ita bata damu ba. Ciza laɓɓa King ya yi kafin ya ce. "Dama ni hankalina bai kwanta da waɗan nan ƴaƴan Omranish ɗin ba, kawai saboda bani san rigimar Omerish ne yasa na yi shiru, amma ni nasan barewa ba zata taɓa yin gudu ɗanta ya yi rareafe ba". Cikin rashin fahimtar in da kalamansa suka dosa momma ta ce. "Ban gane nufinka ba". Cike da manaki ta yi magamar. Nan fa kallon gabaɗaya jama'ar parlon ya koma kanta. Cikin kakkausar murya king ya ce. "Har kuna da bakin zuwa neman wacce ta yi poisoning ɗinsa bayan kuna tare da mugun iri a waje!!". Ya yi maganar yana kallon Pretty dake ta faman shessheka tamkar zata haɗiyi zuciya. Daidai lokacin Sweetie ta shigo parlon da gudu, dan ta ji hayaniya, to ta zaci faɗa ake sake yi da Ronnie shiyasa ta zo. Ai Pretty na ganinta ta kwace rikon da momma ta yi mata, da gudu ta tafi ta faɗa jikin Sweetie tana sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Rungumeta Sweetie ta yi, a ruɗe take faɗin. "Lafiya Pretty, meyake faruwa?". Cikin kuka tamkar ranta zai fita ta ce. "Sweetie ki ce Yah Omerish ya tashi, dan ALLAH ya tashi kada ya mutu"...... Cikin rashin fahimta Sweetie ta ce. "Ban gane ya tashi ba? Akwai abin da ya faru ne? Ina yake?". Kara rungumota Pretty ta yi, cikin kuka ta zayyano mata dik abin da yake faruwa. Salati Sweetie ta saka kafin ta kara rungumeta ita ma suka rushe da kuka a tare. Zuba masu ido dikka jama'ar parlon suka yi, wasu sun basu tausayi wasu kuma haushi, wasu na tayasu jimami wasu kuma suna tayasu kukan, wasu kuma suna ALLAH ya kara. "Jaish bana son ganin waɗan nan ƴaƴa a gabana ko a cikin gidana, suna kara mun bakiciki kan wanda nike ciki, ku fitar mun da su, kuma ba zan yafe kashe Omerish da suke son yi ba, dole su fuskanci hukunci!". Cewe King kenan. Idan hankalin Momma ya yi dubu to ya tashi, cike da damuwa ta ce. "ALLAH ya kara maka tsawon rai, amma dai kasan waɗan nan yara ba zasu iya aikata wannan laifi ba ko? Ina da tabbacin ko kaza ba zasu iya kashewa bare kuma mutum, mutum ɗinma mijinsu, kai a'a, akwai dai abin da ya saɓa.......". Hannu King ya ɗaga wanda ya sanyata dakatawa da yin maganar. "Rahilarh kina raina makiya, kin san jinin kiyayya kuwa? Ai idan mutum baya sonka baya sonka ne, na tabbata su suka shirya wannan abin". Kallon kallo ya koma faruwa a cikin parlon, su Sareena kansu ya shiga duhu suna son a warware masu shi, burinsu kawai su ji meyake faruwa dallah dallah. Su uncle Abbas wannan ya kalli wannan, wannan ma ya kalli wannan, Jaish and Jawad dik da basu san su Pretty ba sosai ba, amma sun ji a ransu ba zasu iya aikata wannan laifi da ake zarginsu da shi ba. Uncle Jahiz ne ya katse kallon-kallon nasu da cewa. "Yaya, ina da tabbacin abin da aunty Rahilarh ta faɗa gaskiya ne, waɗan nan yara ba zasu taɓa aikata wannan babban laifi ba, kada ka manta yanayin yadda tsarin tsaron abincin ƴaƴan gidan nan yake, a kicin kawai Cameras sun fi goma, kai ba karamin kwaro bane ya shirya wannan abin, waɗan nan yara wayansu ba zai taɓa kaiwa irin wanna plan ɗin ba". Uncle Abbas ne ya karɓi zancen da cewa. "Tabbas ba zasu iya aikata wannan laifi ba, sai dai kuma in shiryawar aka yi tare da su, ma'ana aka shirya masu, amma wannan laifi sun yi kakana wajen iya shiryasa". Mummyn Chuchu ce ta karɓi zancen da cewa. "Please ranka ya dade ka duba wannan magana, wlh ina da tabbacin waɗan nan yara basu yi wayon da zasu shirya wanna shiri ba, kada ka manta ita Omaish tare da babban yayansu ta zo, in tana da niyar kashe Omerish ai da tin kafin su zo nan zasu kashe shi, ko baka san labarin irin rayuwar da suka yi a masarautar baban yayan nasu bane?". Ta tambaya tana kallonsa. Kun san mummyn Chuchu da Momma kansu a haɗe yake, to momma ta bata labarin irin rayuwar da suka yi a Black World tamkar yadda Sweetie and Pretty suka bata labari, to shi King bai sani ba, dan bai zauna da momma a kansu ba. Jaish ne ya ce. "Dad ka duba please". Sun bawa Jaish tausayi ne yasa ya sanya baki, dan in baku manta ba shi Jaish baya shiga case na gidan, sannan yana ji tamkar Sweetie and Mahnoor suna da alaƙa saboda in ya ɗaga idanu ya kalli Sweetie a fusge wlh sai ya ga kamar Mahnoor, dikkansu suna da gurun wuya mai kyau da ɗaukar hankali. Ni Queen of surprise na ce baku yi mamakin yadda aka yi suke da kamanceceniyar wasu daga cikin suffa ba? Kada ku manta yanayin kirar jikin koreans, ba'a cika samu masu dirin halittar good bye and welcome yadda yakamata ba, saboda yanayin su sirara sai shape, to su Sweetie ya aka yi suke da shi? E ba yadda ALLAH baya halitta a dik sanda ya so, amma akwai na gado, siffofin Sweetie banbancinsa kaɗan ne da Mahnnoor, fuskar Sweetie and Pretty da skin ɗinsu ne da ka gansu ka ga koreans, amma tabbas akwai kama ta jini a tsakaninsu da Mahnoor. Wayyo ni cakwakiyar RAWANIN ZALINCI zai soma kuma, kwana biyu kaina ya ɗan huta, to dai ku karɓi wannan surprise ɗin, Sweetie, Pretty, Mahnoor, Mahreen suna da alaƙa mai karfin gaske ta jini, shiyasa dik iskancin Pretty batai wa Mahnoor, ba banza ba Sweetie take balain son Mahnoor, ba a banza Mahreen ta makalewa Sweetie ba, jini ba wasa ba! NI KAM PRINCESS TEEMA yaushe zan yi rubutu dama ban baiwa kasata Nigeria power ba? Mugun ji da Nigeria ɗin fa nike in faɗa maku gaskiya to. Amma ta ina kuke tinanin Sweetie, Pretty, Mahnoor and Mahreen suka haɗa alaƙa? Bari in haɗaku da tinani a nan kuma ku ɗanɗana bye sai wacce zata warware maku cakwakiyar nan ta bayyana, dan bata bayyana ba. Gyaran murya Jawad ma ya ɗan yi wajen cewa. "Dan ALLAH dad ka duba, wlh ba zasu iya wannan aiki ba, ka gansu mana, ko Zunaira zata fisu shekaru fa!". Ya faɗa yana kallonsu. Kun san shi kuma Jawad meyasa ya sanya baki a maganar? Saboda Sweetie tanai mashi yanayi da Chuchu, already ya jima yana ganin kamanceceniyar Chuchu da Mahnoor, magana ce kawai bai taɓa yi ba, ya ɗauka kawai kawancen da Chuchu and Mahnoor ɗin suka kulla mai karfi suka zama kamar hanta da jini ne yasa yake jinsu tamkar jini guda, kai bari in barku haka, gaba na sake warware maku hadda, ai surprise bata kare ba, masu zafi suna zuwa a gaba!!. Shiru King ya yi bai tankasu ba, saboda bai ga dalilin da zai sanya ya ɗagawa su Sweetie kafa ba. Wannan shiru da ya yi tafi komai ɗaga masu hankali, dan wannan shiru da ya yi yana nuna masu alamar tin da sun fishi sanin abin da ya dace sai su yanke hukuncu, shiyasa dik suka sha jinin jikinsu suka koma gefe suka yi shiru cike da shakka da tsoron buɗar bakinsa. Good 5 mins ya ɗauka yana binsu kallon kafin ya ce. "Jaish bana son in sake ganin waɗan nan yara a nan, ku zubamun su a kurkukun masarautar nan na ce!". Yana magana yana ɗan dafe saitin kirjinsa, saboda yana tina baya kirjinsa na zafi. Da sauri momma ta sake cewa. "Dan ALLAH ka yi hakuri, wlh ni na tabbata ba zasu iya aikata wanna laifi ba ko da wasa! Ka tsaya a yi bincike". "Rahilarh, waɗan nan jinin Omranish ne, babu abin da ba za su iya aikatawa ba, ni nasan waye ubansu, ni nasan bakin hali da zaluncin Omranish! Dole su yi gado dama, shiyasa na tsani jininsa da shi da Abdul Raof, dan haka yaki yanzu aka fara, kuma wlh ba zan ɗagawa kowa kafa ba! Ku jefa mun su a Prison tare da horo mai tsananin gaske da sai sun gwammaci mutuwa!!". With harsh voice ya yi maganar, ya yi ta kuma yana pointining ɗin su Pretty da suka rungumi juna suna kuka. Momma da karfin hali dik da ta san ransa a ɓace bai hana ta sake cewa. "Ko ba komai akwai aure a tsakanin Omerish da Omnish, dan ALLAH ka duba wanna lamari.......". Tsawar da ya daka mata ne ya sanyata haɗiye sauran maganar bata karisar ba. "Keeeee Rahilarh! Baki san komai dangane da gabarmu ba, kin ji abin da kika ji ne kawai, dan haka kada ki sake yin magana a kan jinin Omranish!!". Ya ilahi, gabaɗaya parlon ya koma kallon kallo, yau momma ake yi wa tsawa, lallai ba shakka dad ya kai kololuwa yau. Poitining momma da yatsa ya yi. "A kan Omerish babu abin da ba zan yi ba, dan haka ki iya bakinki!!"......... Tsit parlon ya yi kowa ya sha jinin jikinsa jin yau faɗar fa ta manyan kai ce. "Jaish ku tattare mun waɗan nan tsiya daga gabana tin kan in sanya takobi da kaina in sare masu wuya!!". Dad ya sake faɗa........... Cike da shakkarsa da tsoron faɗarsa momma ta sake cewa. "Meyasa za'a haɗa da Omaish bayan babu sa hannunta a ciki? Omnish kawai ake zargi.........". Hannun da ya ɗaga mata ne ya sanya ta dakatawa. "Komai kankantar jinin Omranish bazan barsa a gidan nan ba, dole dikkansu biyu za'a rataye!"...... Dum!! Dum kirjin momma ya buga saboda ta tina cewa ta kira Hoorain yana zuwa da Auta, ga shi shi ne first born na Omranish, dama ga kwantacciya a tsakaninsu da king ɗin, watau akwai balai sabuwa kenan. Daidai wannan lokacin Ronnie ya shigo cikin parlon shi ma, dan ya jiyo hayaniyar ne ya ce bari ya zo ya duba. Yana ɗaura idanunsa a kansu ya yi gaggawar nufarsu, abinku da jini ɗaya, take ya ji ransa ta yi mummunar ɓaci saboda kukan da yaga suke yi, tin ma bai ji laifin me suka yi aka sakasu kuka ba. Da gudu ya karisa wajen nasu tare da riko Sweetie yana tambayarta me yake faruwa kuma waye ya sakata kuka. A wannan lolaci Jaish ya iso wajen dan ya cika umarnin mahaifinsa, hannu yasa zai kama Sweetie Ronnie ya rike hannun nasa, fuska a ɗaure tamau ya ce. "Malam lafiya?!". Nan fa parlon ya koma kallon kallo, King gyara tsayuwa ya yi yana kallonsu, yau ga ikon ALLAH, wai basu san suma su Sweetie da gatansu bane? Kamar yadda suke taƙama da Big Bro and Smart su ma su Sweetie suna da zakunan brothers da suka fi nasu yawa ma, ga sadauki Rishan, Hoorain, Kamdan and Ronnie, bugu da kari in baku manta ba Zarina tana da wani dakakken mayaki commander daga cikin mayakanta mai kama da Hoorain sosai ko? Kun tuna shi ya taɓa kashe Auta? To yana nan labari zai zo ta kansa, shi ma dik jininsu ne, kunga kuwa ai suma suna da gata da masu tsaya masu, ai ina ga da Kamran ne ma a wannan waje suka sanya mashi su Pretty kuka da ya zubar da maza goma kafin ya ji me ya samesu!. Riko Ronnie Pretty ta yi tare da fasa mashi kuka mai sauti tana faɗin. "Wai cewa suka yi a kaimu prison, wlh ni bana son zuwa kada ka bari a tafi dani". "Me kuka yi da za'a kaiku can?". Ya yi tambayar yana kallon Sweetie da banda kuka babu abin da take yi. Kasa bashi amsa Pretty ta yi sai kuka take yi mai taɓa zuciya. Rikota ya yi yana ɗan shafa bayanta alamar rarrashi kafin ya ce. "Babu wani mahalukin da ya isa ya kaiku prison idan ina raye, ku yi shiru!". Ya faɗa yana jefa da hannun Jaish da ya rike, sanan ya tsaya a gaban Sweetie and Pretty tamkar wani zaki yana fuskantar jama'ar cikin parlon. Nan dai ran kowa ya ɓaci, wai kalaman Ronnie ya kona maru rai, tayaya zai ce bai ga mahalukin da ya isa ba, kenan ya raina har King?. Shi kuma ba wai raini bane, ransa ne ya ɓaci, kun san jini ba wasa ba, kuma yayansa Big Bro ya renesa ne ta hanyar da zai yi magana da kowa cikin jarumta ba tare da shakka ba, shiyasa ya faɗi hakan. Nan fa izzar sarautar ta motsa, King ya ce a haɗa har da Ronnin dikka a tattare mashi su zuwa prison. Haba aikuwa Ronni gyara tsayuwarsa ya yi, jinin sarautar nan dai shi ma ita take gudana a jikinsa, cikin nuna jarumta ya ce. "Babu wanda ya isa ya taɓa mun sisters, ni dai zaku iya kaini, amma su babu wanda ya isa ya taɓasu!". Uncle Abbas ne ya miƙe tsaye cikin fushi yana faɗin. "Kai yaro ka iya bakinka, hattara dai, yakamata kasan a in da kake!". Sweetie and Pretty laɓewa suka yi a bayansa, suka rirrike shoulder ɗinsa suna cigaba da kuka......... "Kai kuma waye karan kaɗa miya? A kansu ba zan yi hattara da komai ba, na faɗa babu wanda ya isa ya kui su prison Ina raye!". Ya faɗa yana kallon tsakiyar idanun uncle Abbas babu ko shakkarsa. Komawa gefe king ya yi yana jinjina kai, saboda yana ganin Ronnie yaga alamar jinin su Omranish a jikinsa shi ma. Nan fa su Jawad suka miƙe dan dakatar da Ronnie, kowani ɗa na halak ba zai taɓa bari yaga ana cin mutumci iyayensa ba. Sai dai kuma Ronnie ba kanwan lasa bane, shi a yanayin tarbiyar da Big Bro ya bashi ko ina ya je shi sarki ne mai ji da kansa, dan haka da Mummyn Chuchu ta ce mashi a gaban sarki yake ya iya bakinsa, sai ya ce mata. "Idan shi sarki ne a nan, to nima sarki ne a Daular mu, kuma yayana ya ce mun ko'ina na je ni sarki ne!!". Babu tsoro ko shakka a maganarsa, zallar jarumta da karfin hali. Su Dr Raj tsoron faɗa da Ronnie suke yi yanzu, dan suna tsoron ALLAH suna tsoron Big Bro, ga Bilal da uncle Taheer har yanzu suna asibiti basu san in da kansu yake ba, ina ai bazasu yarda su salwantar da tafiyarsu ba, dan haka sai suka ja baki suka yi shiru. King ya fahimci dikka ƴaƴansa dake cikin parlon suna shakkar Ronnie, bai san shakkar taɓasa suke saboda balain Big Bro ba, dan haka sai yasa a kira mashi warriors guda biyar kan su zo su tatattare mashi harda Ronnie su yi prison da su, ya umarci su Mama, Mummyn Chuchu, Momma da su shiga ciki kada warriors su samu ganinsu, kun san killacesu ake yi. Kallon King momma ta yi zata yi magana ya yi saurin ɗaga mata hannu alamar baya son jin komai daga gareta, dole ba dan ta so ba ta nufi cikin room ɗinsa tare da su mama tana addu'ar ALLAH ya yayyafawa wanna cakwakiya ruwan sanyi. Wasu dakakkun jaruman warriors guda biyar ne suka shigo cikin parlon, tamkar wasu bujuman zakuna. Kai tsaye king ya umarcesu da su fita mashi da Ronnie yanzu . Su Dr Raj dik baya suka ja suna kallon ikon god. Ronnie ya so gwabza faɗa da su, sai dai kuma ina ba zai iya ba, dama dai su uku ne ko su biyu zai iya kwatar kansa, amma su 5 ba zai iya ba, and mayakan Kingdom of Power ba wasa ba, sun samu horo iya horo, dan haka sai suka damke Ronnie, uku suka rikesa gam, ɗaya ya damki Pretty ɗaya ya danki Sweetie, suna wani irin taku ma jarumta suka nufi waje da su. Pretty da Sweetie sai kuka suke yi tamkar ba zasu rayu ba, sai ƙoƙarin miƙewa juna hannu suke yi, suna son rungume juna amma warriors ɗin nan sun hanasu. Suna ƙoƙarin buɗe door na parlon su fita unexpected sai ganin mutum suka yi a gabansu, dik jarunta irin na warriors ɗin Kingdom ɗin nan sai da suka razana ganin yadda face ɗin Big Bro take babu alamar taushi. Dik cikin parlon guyson ne kawai ya ga shigowar Big Bro daga part na momma, amma saura dik hankalinsu na'a kan su Pretty. Wani irin shaka ya kaiwa warrior da ya rike hannun Sweetie, ya shake mashi wuya da karfin gaske, hakan yasa dole ya saki Sweetie, da gudu ta tafi ta rumgume Pretty suna cigaba da kuka. Saura warriors dake wajen dik suka yi gaggawar sakin su Ronnie suka ja da baya. Shi kuwa Big Bro hannu yasa zai zari takobin dake waist na warrior da ya shake dan ya datse mashi hannun da ya taɓa Queen Of His Heart da shi, sai dai king ya yi gaggawar shiga tsakaninsu yana ƙoƙarin tausan Big Bro ɗin. Da kyar suka samu ya saki warrior ɗin, yana sakinsa warrior ɗin ya zube gwiwowinsa a kasa yana haki ya ji shakan manya. Shi kuma Big Bro cikin fushi ya ce. "Wani mai karan kwana ne ya sanya wani banza ya taɓa Omaish?". Dik da shakkarsa da suke ji bai hana uncle Abbas daurewa ya ce. "Yana da kyau ku rinƙa sanin in da kuke, gaban sarki kuke, dan haka wajibi ne a kanku ku rinƙa tauna kalamai.......". Wani irin kallo da Big Bro ya dannawa uncle Abbas ne ya sanya shi haɗiye bakinsa cif. "Babu wani sarki da zai kasance da sarauta idan ina waje, ni kaɗai ne sarki, dan haka ku bani amsata". With harsh voice sosai ya yi maganar. Uncle Abbas ya buɗe baki zai sake yin magana Jaish ya rigasa da cewa. "Big Bro uncle Abbas ne fa? Second dad ɗinmu ne shi"........ "Then so what? Koma wanene shi ya sani ni sarki ne a dik Daular dana kasance a ciki!!". Fusata iya fusata uncle Abbas ya yi, cikin ɗaga murya ya ce. "Ni fa tamkar uba nike a wajenku, kamar yadda zaka girmama mahaifinka haka zak.......". Katse shi Big Bro ya yi da cewa. "Tamkar Uba ka ce ba Uba ba ai, bana son na sake jin bakinka a cikin parlon nan, in kuma ka sake ina magana kana yi zaka rasa tongue ɗinka ne, dan sai na datse maka shi!". Yunkurawa Uncle Abbas ya yi zai yi magana kenan King ya ɗaga masu hannu wanda hakan yasa uncle Abbas ya yi shiru. Riko hannun Big Bro King ya yi suka nufi saman sofa, hakan ya kara fusata uncle Abbas, saboda a tarbiyya irin na masarautarsu da al'adarsu dole Big Bro ya fuskanci hukunci na sa in sa da ya yi da uncle Abbas matsayinsa na kanin mahaifinsa kuma babba a kansa. Amma king ya nuna ya fi son ɗansa sama da zumunci, wannan abin ya yi mugun konawa dayawa daga cikin parlon rai, ciki har da uncle Jahiz, bai ji daɗin yadda king bai dakatar da Big Bro ya gwada mashi cewa su uncle Abbas suna da mahimmanci a wajensa dan haka ya girmasu ba. Kwace rikon da king ya yi mashi Big Bro ya yi yana huci ya ce. "Dad ku faɗa mun wanda yasa a kama Omaish". Cikin tausasawa da sigar rarrashi king ya ce. "Calm down, nine na saka a fitar da su". A fusace ya juyo da kallonsa a kan King ɗin. "For what reason?". Uncle Abbas ne ya juya cikin fushi ya fita daga parlon, da sauri uncle Jahiz ya rufa mashi baya dan ya taushesa, saboda babu karya king ya baƙanta mashi rai, misali shi zai goyi bayan su Rizwan su faɗawa king magana ne da king zai rinƙa bin bayan yaransa? To ai ƴaƴa basu fi ƴaƴa ba. Jawad dafe kansa ya yi yana jin wani irin zafi a zuciyarsa, dan abin da bai taɓa faruwa a kingdom ɗin bane yake shirin faruwa, iyayensu suna faɗa, kai abin dai sai shiru. Ganin haka yasa Jaish ya yi gaggawar riko hannun Jawad ɗin, ya jasa dan su bar parlon, saboda sun ga abin is getting out of hand. Umarni king ya yi wa warriors dake wajen a kan su fita, sannan ya umarci su Sareena dik su fita. Cike da takaicin su Sareena suka miƙe. Sweetie and Pretty sun kara samun mugun bakin jini a cikin family, babu wanda bai tsanesu ba sai mazan gidan, a mazan ma Obaid and Omaid sun tsane su matuƙa. Kowa waje ya nufa saura Ronnie, Sweetie and Pretty, sai King and Big Bro, har lokacin su Pretty suna kuka basu dakata ba. Kallonsu King ya yi kafin ya ce su fita mashi a parlo. Da sauri Big Bro ya ce. "Babu in da zasu je dad, ka faɗa mun dalilin da yasa ka ce a fita da Omaish?". Ƙoƙarin tausarsa king ya yi, amma ina ya kafe har sai an faɗa mashi dalili, kai tsaye King ya ce mashi. "Saboda na tsani jinin Omranish".......... Kallon tsab Big Bro ya yi mashi kafin ya ce. "Su suka yi maka laifi ko ubansu?". A tsaitsaye yake maganar yana kallon king har cikin ido. "Amma kuma ai da sa hannunsu aka yi poisoning Omerish ko?". King ya faɗa cikin muryar dake nuna alamar ransa ta fara ɓaci. "Omnish ce take da sa hannu ba Omaish ba, dan haka Omnish zaka hukunta". Ya faɗa yana juyo da kallonsa kan su Sweetie da suke kankame da Ronnie. Da hannu ya yi masu alama a kan su zo. Da gudu Sweetie ta tafi ta faɗa jikinsa, shi ma Ronnie ya matsa ya faɗa jikinsa ta gefe, ita kuma Pretty tsoronsa da shakka ga tuhuman da yake yi mata ne yasa ta ja baya tana kallonsu tana kuka, bata nufosa ba. "Idan kana da matsala da mahaifinsu wanna bai shafesu ba, ina sonsu tamkar raina, in har zaka cigaba da korarsu to ni zan bar maka kingdom ɗinka, zan ɗaukesu ne mu tafi!". Ya faɗa cikin ɗan ɗaga muya yana shafa bayan Sweetie da hannunsa ɗaya alamar rarrashi. Durkushewa ƙasa saman gwiwowinta Pretty ta yi tana wani irin kuka mai taɓa zuciya. Unexpected daga bayanta ta ji an taɓa shoulder ɗinta. A gaggauce ta ɗago da kanta tare da juyowa. Wani irin zabura ta yi ta miƙe tsaye, muryarta har yana rawa waje ƙoƙarin kama sunasa amma ta kasa. Yana dafe da gefen cikinsa alamar ciwo yake yi mashi kenan, muryarsa can kasa-kasa a ɗan dashe ya ce. "Koda kowa zai yi yunkurin kasheni a cikin familyn dake gidan nan to banda Omnish Daddy, ba zata taɓa iya kasheni ba, nasanta sama da kowa, ko sauro ba zata iya kashewa ba, muguwar matsoraciya ce wadda ko waje bata iya fita a lokacin da muke Paris sai Zunaira ta rakata, ba zan taɓa yarda a ce ita ce ta saka mun guba a abinci ba, ta taka sahun ɓarawo ne". Da kyar ya iya kai karshen maganar tare da jawota jikinsa, ya rungumeta ta gefen lion chest ɗinsa yana ɗan bubbuga bayanta da hannu ɗaya alamar rarrashi. "Kada ka manta dad tun ina karami ake farautar rayuwata a gidan nan, to dan yanzu an yi poisoning ɗina ai ba wani abin mamaki bane ko abin da za'a tuhumi matata! Ka manta cewa tin kan asan za'a haifeta ake neman rayuwata ne? Meyasa zaka yi amfani da fushinka dake kan mahaifinsu ka ɗaurashi a kansu? Please dad ka nunawa su Omnish so tamkar ƴaƴa, saboda basu da laifi, hasalima zaluntarsu mahaifin nasu ya yi, kada ka manta fa a daji aka haifesu, suka girma a can, basu san komai ba face dabbobi, a hakan basu cancanci a tausaya masu ba?". Ya kai karshen maganar yana wani irin haki numfashinsa na yin sama-sama, ga idanunsa jajir tamkar wuta. Sake su Sweetie Big Bro ya yi ya matsa ya rike Smart ɗin da kyau. "Amma Omerish bana ce kada ka fito ba? So kake ciwon ya tsananta ko?". "Dik abin da yake faruwa ina ji ne ɗan uwana, ba zan iya jurar avoiding ɗin Omnish da daddy yake yi ba, bullying da ake yi masu tai yawa, shiyasa na fito dan in faɗawa daddy gaskiya"........ "Ya isa haka maganar, mu je ɗaki ka kwanta kuma kada ka sake tashi yanzu, kada ka jiƙa mana aiki". Big Bro ya faɗa tare da fara taimaka mashi suka nufi hanyar komawa room ɗinsu. "Daddy zan dawo mu yi magana". Big Bro ya faɗa. Da sauri su Ronnie suka rufa masu baya. Smart ya rike hannun Pretty gam har suka karisa cikin ɗakinsu. A nan Big Bro ya kwantar da shi suka fito shi da su Ronnie suka barsu tare da Pretty suka koma parlon King dan zancen bata kare ba, yanzu ne ma zata fara. Waye ya zuba poison a abincin? Ya king zai kare da kannensa da suka yi fushi saboda ya nuna fin son ƴaƴansa a kansu? Uhmmm muje zuwa. Har lokacin tana kuka sosai, hannunta Smart ya jawo ta zauna a gefen bed ɗin, da kyar ya iya cewa. "Ya isa haka kukan to"........... Ai kamar jira take yi ya yi magana, da sauri ta faɗa jikinsa tana ƙoƙarin shanye kukan nata. "Meyasa kika ce maganin mutuwa kika saka mun a abinci? Kenan kin san da an saka mun wani abin ne?". Muryarsa ya daki dodan kunnenta. Da sauri ta........ Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only please. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 "Meyasa kika ce maganin mutuwa kika saka mun a abinci? Kenan kin san da an saka mun wani abin ne?". Muryarsa ya daki dodan kunnenta. Da sauri ta ɗago da kanta daga kirjinsa, ga idanunta sun kumbura luhu-luhu, kai ta shiga girgizawa. "A'a ban sani ba, kawai dai ban san ya aka yi na faɗa ba, kuma kaga mun yi faɗa, da ka ce me na saka maka a abinci ne sai abin ya bani haushi tin da naga kasan bani nike girka abinci ba, kuma kasan ni me nike da shi da zan saka maka a abinci? Da farko ma na ɗauka wasa kake yi shiyasa ban kira su momma a lokacin ba, sai da naga ka daina motsi ne na gane da gaske ne". Zafafan hawaye suna biyowa kuncinta ta kai karshen maganar. Tin da ta fara ya zuba mata idanu yana kallonta har ta kai karshe, nisawa ya yi kafin ya ce. "To kinga illar dake cikin magana cikin fushi ko?". Kai ta jinjina mashi alamar e ta gani. "To daga yau ko wani irin fushi kike yi da mutum ki rinƙa tauna magana kafin ki furta shi garesa, saboda gudun faɗawa irin wannan matsala kin ji ko?". Ya kai karshen maganar tare da kai hannu saman fuskarta. A hankali ya fara goge mata hawayen nata. Kai ta jinjina. "Ba zan sake ba In Sha ALLAH"......... "Kin yi breakfast ne?". Da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a. "Okey bari in saka a kawo maki to". Nan ma kai ta girgiza da sauri tana faɗin. "Na koshi".. ........... Ya fahimci ta tsorata da abincin ne, tana tsoron cin gubar ita ma, dan haka sai ya ce. "Kada ki damu ba irin wanda na ci za'a baki ba, yanzu tsaron abincinmu zai tsananta fiye da na da, kafin mu ci abinci ma sai an dubata tsab dik da cewa a da ɗin ma ana dubawa, yanzu za'a tsananta". Mayar da kanta saman lion chest ɗinsa ta yi, ta kwanta shiru tana tinani bata iya cewa komai ba. A yayin da a can gefe kuma Big Bro yake ta fama da king a kan wannan gaba tasa da Omranish, cikin sanyin murya ya ce. "Dad already kun rigada kun zama ɗaya da Omranish ɗin nan, ban goyi bayan ka yafe ka kyalesu a kan cutar da suka yi maka ba, but ba zan goyi bayan ka hukunta waɗan da basu da hannu a cikin faɗar ba! Me laifinsu Hoorain? Kawai dan sun so ƴaƴanka? To ai kaima ƴaƴanka sun so nasu ko?". Shiru King ya yi yana kallon ɗan nasa, su momma dik suna zaune a saman bed ɗin suna kallon Big Bro dake zaune saman side sofa. Shi kansa king ya sani abin da Big Bro ya faɗa gaskiya ce, amma kun san zuciya bata da kashi ne!. A daidai wannan lokacin Ramish ya shigo ɗakin bakinsa a ɗauke da sallama. Ganin momma, mummyn Chuchu, mama, King and Big Bro ɗin ne yasa Ramish ya yunkura zai juya ya fita kenan Big Bro ya ce mashi ya zo nan. A natse ya karisa ciki yana tunani me ya tarasu haka? Dan shi baya gidan tin da sassafe, so bai san me ake ciki ba, ya lura yanzu gidansu ya zama sai rikici ake yi kullum. Cikin kaifaffar murya Big Bro ya ce. "Umarni nike baka Ramish, ka je ka ɗauko matarka, domin faɗuwa ce a garemu ace wai dan ka auri ƴar makiya har su yi galaba a kanka wajen kwaceta dan su kuntatawa kingdom ɗin nan, dan haka ka je har cikin gidansu ka ɗaukota!!". Ɗan zaro idanu king ya yi, sai kuma ya fahimci Big Bro yana da gaskiya, ai yakamata ne su gwada masu fa sun fi karfinsu, kuma zasu iya yin komai da suka ga dama, zuwa har cikin gidansu da Ramish zai yi ya ɗauki Leesharh ba karamar razanasu zai yi ba, zai sanya su shiga taitayinsu, lallai ba shakka wanna shawara ta yi, amma king ya yi mamakin yadda aka yi Big Bro ya fisa sanin ilimin mulki da dik wata tuggu sosai. Ni ko na ce ai dama baka haɗa ba King, Big Bro da tsawon rayuwarsa babu abin da yake yi face karance-karance da nazarin mutane, shi da mugunta ma karantarta ya yi ya koya, baya fita ko parlo, kai kuma King daga nan har birnin Sing zuwa kake yi, yaushe ma ka samu lokacin kanka bare wani kasance-karance da nazarin mutane, ai bama zaka haɗa kanka da shi ba, dik wani tsiya sanka-sanka Big Bro ya sani da kuke ganin san nan, wlh sai dai in bai yi niyyar yin abi ba!. "Na yarda zan so ƴaƴan Omranish, zan yi dik abin da kake so, amma nima ina da abin da nike so ka yi mun". King ya faɗa yana kallon ɗan nasa. Shi kuma Ramish wani irin ajiyar zuciya ya sauke tare da zama a saman ɗayan bed side sofa yana fuskantar su king, Amma ya gagara yin magana...... Shiru room ɗin ya yi suna kallon King suna jiran jin me yake so. Gyaran murya ya ɗan yi kafin ya ce. "Ina son ka rinƙa girmama Abbas da Jahiz tamkar yadda zaka girmamani, they're my brothers, and ba zan so ka rinƙa yi masu magana haka anyhow ba, ɗazu ban ji daɗi ba, it hot me more, kawai na danne ne". Shiru Big Bro bai amsa mashi ba for almost 2 mins sannan ya ce. "Dik wanda zai mun magana without respect to ba ɗauka ba, ni sarki ne mai san mulkar duniya! Bana tolerating nonsense!!". Kallon Momma King ya yi, ya ji sabon karatu wajen Big Bro, sarki mai son mulkar duniya kuma? Balain can, yau sun ji abin da ya sha gaban tinaninsu, ita kanta momma yanzu Big Bro ya fara kara ninka tsoronsa a ranta, kai lamarin ya sha gaban tinaninsu. Momma ce ta daure da cewa. "Ba zasu rinƙa yi maka magana da tsawa ba, amma kai ma ka rinƙa ƙoƙarin tausar zuciyarka a kansu ka ji ko? Su ɗin iyayenka ne"...... A takaice ya ce. "Iyaye biyu nike da shi, ke and dad". Alama king ya yi wa momma da hannu a kan ta yi shiru, dan sun lura a yanzu dai Big Bro ba zai taɓa fahimtarsu ba, shi girmamawa yake so, idan har za'a girmama shi to za'a zauna lafiya, akasin haka kuma zai iya hukunta kowa a duniyar nan banda mutum biyu, watau King and Momma, dan haka sai dai su rinƙa lallaɓasa har zuwa lokacin da ya daina zancen sarki mai mulkar duniyar nan, a lokacin zai rage izza da jiji da kansa, to a sannan za'a iya faɗa mashi suwaye Uncle Abbas kuma ya yarda. Jin sun yi shiru ne yasa Ramish ya ce. "Big Bro, daddy, mummy and momma please ku tayani rokar mama da ta yi hakuri ta yarje mun in je in ɗauko Aesh". Kallon Mama dikka suka yi banda Big Bro da yake kallon Ramish ɗin. "Sai ta ce ka je ka ɗaukota? Matarka ce ko matarta? Ko ita ta aura maka ita?". Big Bro ne ya jefa mashi waɗan nan tambayoyi. Cikin girmamawa Ramish ya ce. "Ko ɗaya, amma ta ce bata sonta ne, kuma ni ina son matata"......... Kai tsaye Big Bro ya ce. "To idan baka ɗaukota ba da ita take so ka rinƙa sex ne?". Balain can ai King da kansa sai da ya tauna harshensa saboda nauyin maganar da Big Bro ya faɗa kuma ko a jikinsa, bai yi mashi ma kamar ya yi magana ba, to dama shi ina ruwansa? Ai maganarsa babu ruwana da a kan waye ake yi, shi fa baya King and Momma baya ganin kowa da wata girma!. Momma Big Bro ya kara goge mata hadda yau, sai kuma ta ji zafin irin yanayin rayuwarsa, ta sake ALLAH ya isanta a kan wanda ya rabata da shi ya je ya kai shi wani waje, yanzu ta fara fahimtar babu addini a tattare da shi, domin kuwa in akwai addini ba shakka ko bai tashi da su ba abin zai yi sauki, amma sai abin suka haɗe mashi, ga rashin iyaye ga rahin addini, ai fin haka ma zai iya aikatawa. Ramish da shi ma zancen tafi karfin kwakwalwarsa ne ya yi kasa da kai kawai, lokaci guda ya ji kunya ta rufesa, ya ji ba zai iya ɗagowa ya kalli su momma ba, Mama ma dai haddar dake kanta ya goge, addu'a take yi a kan ALLAH yasa kada Big Bro ya sake buɗar baki ya yi magana a room ɗin nan, dan maganarsa ɗaya tana razana ƙwaƙwalwa, tana sanyawa mutun ya fi tsawon shekaru yana tinanin maganganunsa. King ne ya canza masu topic ɗin hiran da cewa. "Ina matar taka take?". Ya yi tambayar yana kallon Big Bro........ Shiru ya ɗan yi mashi for some minutes kafin ya ce. "Tana ɗaki". Ya bashi amsa a sanyaye....... "Okey Rahilarh ki gabatar mun da su in anjuma da yamma, zan gansu, kuma na aminta su kasance matan ƴaƴana". Cewar King. Ba karamin daɗi momma ta ji ba da jin kalaman King, cike da murna ta fara zuba mashi ruwan godiya. Miƙewa sumui sumui Mama ta yi ta nufi waje, dan bata son a sake sako zancenta a cikin Room ɗin, kada Big Bro ya sake caka mata magana, yanzu ma ya goge mata hadda. King da momma sun lura da fitarta, amma basu yi magana ba, dan suma ba zasu so Big Bro ya sake yin magana a kanta ba, saboda abin ba zai yi kyau ba ne. "Daddy take good care of yourself". Big Bro ya faɗa tare da miƙewa ya nufi wajen. Daga King har momma an rasa mai dakatar da shi, kuma suna son tambayarsa sunansa, amma sun gagara. Bedroom ɗinsa ya koma dan su yi breakfast. Slowly ya turo kofar ya shigo. Tana zaune a saman sofarta tana ta faman sauke ajiyar zuciya. Tana jin an turo kofa ta yi gaggawar kai kallonta wajen, ganin shi ne yasa ta miƙe tsaye da sauri, muryarta a ɗan dishashe ta ce. "King of heart ina Pretty ɗin? Ba'a sake yi mata komai ba ko?". Idanunsa a kan dogon hancinta da ya yi jajir saboda kuka, purple lips ɗinta har ɓari yake yi, dik tana firgice. Gentle ya tako izuwa in da take a tsaye. "Ya isa haka Maysh, babu abin da zai faru kuma, zo ki yi breakfast". Ya faɗa yana kai yatsansa ɗaya saman lips ɗinta dake ta faman kerma...... "Ni na koshi". Da kyar ta iya faɗa. Ya fahimci tsoron abincin take ji saboda abin da ya faru, sai ya ce mata. "Babu abin da zai faru, ko poison ɗin da kansa kika ci kina tare dani ai". Dik da ta yarda da maganarsa, amma zuciyarta na rawa a kan ta zo ta ci abincin nan gaskiya. Hannunta ya ja suka nufi wajen abinci. Dan dole ba dan ta so ba yau ta ci wanna abinci, zuciyarta na ta ɗari-ɗari har suka kammala. Sai da ta ga sun ci da kamar 30 mins babu abin da ya faru sannan ne hankalinta ya kwanta, ta samu natsuwa, ta kuma koma sama sofa ta kwanta, shi kuma Big Bro ya fita zuwa wajen aikin da ake ta faman yin. ------------------------------🔥 A yayin da dikka wannan abin yake faruwa Omaid ne tsaye a tsakiyar bedroom ɗinsu yana kai komo tamkar wanda ya yi wa yar sarkin aljanu cikin shege ake nemansa, dik da sanyin Ac dake cikin room ɗin bai hana zufa keto mashi ta ko'ina a sassan jikinsa ba. Sareena and Obaid suna zaune a saman bed, dik sun yi jugun-jugun, tamkar masu zaman makokin iyayensu. Hannu Omaid dunkule yana dukan ɗayar tafin hannunsa da shi, cikin sauri da kakkausan murya ya juyo tare da kallon su Sareena ya ce. "How comes wani ya canza mana plan? Kenan akwai mai bibiyarmu ne? Ta ya za'ayi mu shirya abu sai kuma a canza plan ɗin, waye ya canza poison ɗin nan zuwa wanda zai iya kashe Yah Omerish? Poison da muka shirya plan wanda zai wahalar da shi ne, to waye yake neman rayuwarsa da zai yi amfani da plan ɗinmu?". Obaid ne ya ce. "Wanna abin ya ɗaure mun kai, ta yaya wani ya bibiyi plan ɗinmu ya kuma yi amfani da hakan ya shigar da tsarinsa na son kashe Yah Omerish cikin namu? Waye kenan? Kuma ta yaya ya canza gubar?". Sake dunkule hannu Omaid ya yi ya daki ɗayar hannun tasa. "Koma wanenen na tabbata yana bibiyarmu ne, dik abin da muke shiryawa yana laɓe mana, amma zan ganosa ne, wlh sai ya ɗanɗani kuɗarsa tin da ya yi niyyar kashe mana ɗan uwa, mu da muke son poison ɗin ta wahalar da shi ta yadda kawai sunan Pretty ne zai ɓaci a gabansa, amma sai a nemi kaisa lahira? Mu cewa muka yi bamu sonsa ne? Wlh ba zan bar wanda ya yi niyyar kashesa ba". Sareena ce ta ce. "Wlh da Yah Omerish ya mutu da rayuwata ta zo karshe nima". ........ Siririn tsaki Omaid ya ja yana cigaba da kai kawo a tsakiyar ɗakin. "Gaskiya akwai bakaken shaiɗanu a gidan nan masu kaifin ƙwaƙwalwa da saurin aiki, ji yadda suka canza plan ɗinmu izuwa nasu cikin ƴan sakanni, wlh ba zan yafe ba, koma waye ne asirinsa zai tonu ne soon, kuma ga shi babban abin takaicin ma naga Yah Omerish bai tsani Pretty ɗin ba, ina ganinsa ya je parlon daddy ya ɗaukota, na laɓe ina jinsu ya ce wa daddy wai ya yarda da ita ba zata kashe shi ba, na ji raina ya yi mummunar ɓaci sosai Obaid". Miƙewa tsaye Obaid ya yi. "Yanzu yaki uku ne a gabanmu, gano wanda ya sanyawa Yah Omarish poison ya yi amfani da plan ɗin mu, da kuma gano aljanin da ya raina mana wayau, sai kuma farraƙa soyayyar Yah Omerish da Pretty". Sareena ce ta amsa da. "Gaskiya akwai sauran aiki a gabanmu, amma yanzu mu fara da Pretty, kawai mu sa a kasheta ne ko? Dan na tsani ganinta wlh". ....... Dogon tsaki Omaid ya ja. "Dallah ku yi mun shiru wawaye kawai, ke Aunty Sareena narasa wani irin ƙwaƙwalwa ne dake, Pretty ɗin zaki kashe ko? Kada ki manta yar uwar wanna matar Big Bro ɗin namu mai kama da aljanun tsakar daren nan ne fa, fuska kamar na ɓauna, ai kika kuskura wani abin ya samu Pretty, wannan matar Big Bro ɗin ne zata ta da hauka, tana tayarwa kuma kin san me zai biyo baya, dan wlh ina da tabbacin bakaken aljanu ne suka shayar da Big Bro tun da ance tin yana jariri ya ɓata, sam ba nonon momma ya sha ba, dan zalincinsa tai yawa, karamin aikinsa ne ya rataye mu, kina ga fa irin jibgar da ya yi wa Yah Bilal, duka biyu bai sake motsawa ba, ai dik abin da zamu yi babu ruwanmu da taɓa lafiyar Pretty, sai dai mu tunzura Yah Omerish shi ya yi mata laifi ta tsanesa tin da shi mun shirya tai mashi laifi ya tsaneta shirin bata yi ba". Ya kai karshen maganar yana harararsu, dan ya tsani wauta da shirmen Sareena, bata kawo shawari mai kyau, kullum kanta a toshe. Yana kai karshen maganar Obaid ya karɓe da cewa. "Kana da gaskiya, idan muka yi wa Pretty wani abin wanna mahaukaciyar matar Big Bro ɗin ne zata fara hauka tana kukan ƴar uwarta, kuma kun san a kanta wannan mugun babu abin da ba zai iya ba, kuna ji dai ya ce dik wanda ya sata kuka to kwanansa ya kare, shegiya mai kama da aljanu, kyanta har ya yi yawa, da idaunta kamar na mujiya, ni wlh nama fi tsanarta". Sareena ce ta ce. "Ba dole ka tsaneta ba tin da kaga ba zaka samu ba, ka ganta kyakkyawa".......... "Kai Aunty Sareena kina da gane abu wai lokaci, ALLAH badan Big Bro ya aureta ba hmmmmm, da ko zata mutu sai na aureta, wlh yarinyar ta haɗu, kina ganin gashin kanta kuwa? Ai ni a kallon gashin kanta kawai sai in ɓata wuni guda, kina ga lips ɗinta, kalarsu masu ɗaukar hankali, ALLAH Big Bro yana morewa shiyasa ba zai so ta yi kuka ba". Cewar Obaid Harara Omaid ya dalla mashi. "Dalla yi mana shiru, kai baka ce baka da lokacin mace ba? Yanzu kuma a kan wannan aljanar kake sanbatu? Ina kyan a wajen? Gashin nata kamar na ifiritu". Harara shi ma Obaid ya dallah mashi kafin ya ce. "Ka dai faɗi gaskiya, wlh kai ma nasan ka kyatsa, dan babu wanda ya ganta bai yi magana ba, har su Yah Raj na ji suna zancen gashi kanta, ko makiyi yasan ta haɗu yarinyar nan, gata yar caras, ni babu abin da yake kara ɗaukar hankalina a kanta ma irin kirjinta da gashin kanta". Ya kai karshen maganar yana dafe saitin zuciyarsa alamar ya tina abin da ta bugi zuciyar tasa. WATAU KO! AKWAI BALAI A TSAKANIN BIG BRO DA YARAN NAN AYSUWAY! KUN JI SWEETIE SUKE SO! KAI JAMA'A WASAN YANZU ZAI FARA FA. Omaid da yasan sun ganosa shi ma dan ba zai sameta bane yasa yake kusheta sai ya ce......... Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only please. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 Omaid da yasan sun ganosa shi ma dan ba zai sameta bane yasa yake kusheta sai ya ce. "Ku bar dik wannan zance mu koma kan abin dake gabanmu". Jinjina kai suka yi Obaid yana faɗin. "ALLAH ya bani irinta, ni kun san meyasa ma nike mara maku baya a kan plan ɗin nan?". Ya tambaya yana kallonsu. Kai suka girgiza mashi a tare alamar basu sani ba. "So nike idan Yah Omerish ya rabu da Pretty sai in aureta tin da tana kama da matar Big Bro". Siririn tsaki Omaid ya ja tare da cewa. "You're not serious, ai idan zuciyarka tana son abu kawai ka nemo ka bata babu ruwanka da madadi, ai tin da matar Big Bro ta shiga raina sai na sameta, ba wata madadi da zan yi mata, ita nike so! Kuma ita zan samu, wlh kome zan yi sai na yi ya rabu da ita na aureta!!". Ai wani irin dirowa kasan bed ɗin a miliyan Sareena ta yi, da gudu suka karisa gabansa ita da Obaid, suna zazzaro ido Obaid ya ce. "Omaid anya baka sha wani abin ba kuwa? Matar Big Bro fa? Kasan me kake cewa kuwa? Ita zaka aura? How to?". Dik a ruɗe suke magana, ga alamar tashin hankali a kan fuskokinsu. "To shi Big Bro ɗin malaika ne da ba za a shiga gonarsa ba? Wlh matarsa nike so, ta mun kuma sai na sameta dik balainsa, yanzu haka na gane ba matarsa ta gaske bace budurwarsa ce, basu kai ga yin aure ba, dan na ji suna magana, zan wuce ɗakinsu na ji yana cewa kada ta faɗawa momma basu da aure, dan haka tin da budurwarsa ce wlh takara zamu yi, ni da shi wanda ya iya allonsa ya wanke, wanda ya iya soyayya ai shi yake sace zuciyar mace, zai sha mamakina". Tashin hankali!!. With his full confidence ya yi maganar, babu alamar wasa a kan fuskarsa, dama can da yake kusheta so yake yasa Obaid ya cireta a ransa shi kuma ya ida nufinsa, amma tin da sun ganosa ya fito da zancen fili kowa ya ji, akwai kura kuwa!. Daga Obaid har Sareena an rasa mai bakin magana, Omaid ya goge masu hadda, balain can, wai takara zasu yi da Big Bro, e lallai akwai ta kam, lahira tana da manyan baki daga Kingdom of Power gaskiya!!. Anya Omaid lafiya yake kuwa? Anya bai sha wani abin ba?. Ganin sun daskare a tsaye suna kallonsa ne yasa ya ce. "Ku ai matsorata ne, wlh ko da wuta Big Bro yake yawo a bakinsa sai na kwace soyayyar budurwar nan tasa"....... Omaid bai san da gaske kusan da wuta Big Bro yake yawo a bakin nasa ba, saboda in dai ya juya magic eyes ɗinsa to fa yawun bakinsa tamkar acid take, tana lalata abu sosai, har karfe tana lalatawa, amma idan ya so tana zama mai taushi tamkar wanda ya zubawa Smart, shi fa Master ne da ya koya ya karanceta ba wani ya basa ba, shiyasa na ce maku baya tofar da yawunsa a wajen, wai kun lura dik abin da yaran nan zasu danganta Big Bro da shi hakan ce ko kusan hakan a kansa?. Obaid ne ya ce. "Omaid please kada ka ja Big Bro ya yi maka illa, ba zan iya jura ba". Murya a ɗan raunace ya yi maganar. Omaid zai yi magana Sareena ta rigasa da cewa. "Kai Obaid akwai saurin karaya ga sakawa mutane rauni a zuciya, ka bar jarumai suna magana". Shiru Obaid ya yi a ransa yana tinanin yadda zai sanya Omaid ya cire tunanin Sweetie a ransa shi kuma ya sameta, dikkansu dai suna so su kashewa ɗayansu kwarin gwiwa a kanta dan shi ya sameta. Kafewa Omaid ya yi a kan muradinsa cike da kwarin gwiwar zai iya cin nasara, Sareena na kara karfafa mashi gwiwa, dan ita ma kunga suna tsayawa tsayin daka su tayata yaki a kan abin sonta, bata taɓa kawo masu kukanta basu share mata hawaye ba, dan haka dole zata goyi bayansu ita ma, saboda team ɗinsu a tare suke babu juyawa kudurin ɗaya baya, wannan alkawari ne!. A daidai wannan lokacin Sweetie ta faɗo ɗakin bakinta a ɗauke da sallama, tana neman ɗakinsu Mahnoor ne, kun san bata san kan family part ba, so shiga ɗakuna take yi kawai tana duddubawa ko zata ga Mahnoor, iya ɗakin Mahreen da na Momma ta sani, ko parlon King sautin hayaniya ta bi ya kaita can. A tare suka juyo da kallonsu a kanta, a tare kirjin Omaid and Obaid suka buga, kallon juna suka yi kafin su sake mai da kallonsu a kanta. Sanin cewa da larabci suke magana a kingdom ɗin yasa ta ce. "Sannunku". Da larabci. Da sauri Obaid ya amsa mata da yauwa! Shi kuma Omaid sarki ji da kansa ga class na balai kai ya ɗan jinjina mata kawai. "Dan ALLAH ɗakin Aunty Mahnoor nike nema ban san in da yake ba". Ta faɗa tana bin Sareena da kallo, sai kuma ta kalli Omaid a sace ta sake kallon Obaid a sace, dan taga tamkar yadda Smart and Big Bro suke mugun kama haka Obaid and Omaid suke, sai kanta ya shiga ruɗani. Cikin salo da nuna class Omaid ya ce. "Kin baro part ɗinta a baya, kafin wannan kafin na mama na Yah Jaish ne a wajen, ma'ana da kin fito part na momma sai na su"........ Obaid and Sareena kallonta kawai suke yi suna sake satar kallon Omaid ɗin, basu yi zaton kwarin gwiwarsa ya kai har haka ba. Kai ta jinjina kafin ta ce. "Nagode sosai". Tana rufe baki Obaid ya ce. "Ko dai in rakaki ne kar baki gane ba?"...... Kai ta ɗan girgiza. "A'a zan gane In Sha ALLAH nagode". Ta faɗa tare da juyawa. "Baki ji ba". Omaid ya faɗa yana zura hannayensa cikin aljihun wandon jikinsa. Wani irin zazzaro idanu Sareena and Obaid suka yi suka kalli juna, shi kuwa Omaid ko a jikinsa, dan ya yarda da kansa, yana jin zai iya takara da yayansa. Juyowa Sweetie ta yi tana kallonsa. A natse ya tako zuwa gabanta, ya ɗaure fuskar nan tamau irin ba wasa nan, dan ma kada ta raina shi. A gabanta ya dakata, hannu ya miƙo mata yana ware tafukansa. "Omaid by name, what of you?". A natse ya faɗa.......... Mamaki ne tamkar su Obaid za su sume a tsaye, gani suke yi Sweetie bazata kula shi ba, dan sun ga bata kula kowa a gidan, hasalima bata fitowa sai dole!. Kasancewar daga ganin fuskarsa ta san ɗan momma ne yasa ta san kanin Big Bro ne, dan haka bata kawo komai a ranta ba, ta bashi hannun tana faɗin. "Omaish amma you can call me Sweetie". Ya ilahi, ai su Obaid kara zazzaro ido suka yi suna mamakin yadda aka yi Sweetie ta amsa Omaid? Kai abin da mamaki, basu san ita kallon kanne King Of her heart da take yi masu bane yasa ta kulasu, ba dan haka ba wlh ko hauka take ba zata kula wani namiji ba, dan tasan waye jarumin nata, a kan kishi babu abin da ba zai yi ba. Ɗan jinjiga hannunta a cikin nasa Omaid ya yi, sai kuma ya ɗan shafa skin ɗinta da babban yatsarsa yana jin wani irin sonta a ransa kafin ya ce. "Kina da kyau sosai, and kina da unique abubuwa masu matuƙar ɗaukar hankalin da ba'a saba gani ba, a zahiri ban taɓa ganin kalar gashin kanki ido da ido ba, sannan ban taɓa ganin kalar lips ɗin ba, ina dai gani a film sometimes, irinku basu da yawa a duniya gaskiya". Sosai ta ji daɗin kalamansa har sai da ta saki ƙayataccen murmushin da ya sanya kyawawan dimples ɗinta suka lotsa, sai ta ji ya burgeta, kun san zuciya tana mugun son yabo. Cigaba ya yi da cewa. "Harta wuyarki unique ne da bamu saba gani ba, and gurun wuyar ya yi balain yi maki kyau, sannan dimple ɗinki ba kamar namu bane, very unique and kyau ajin karshe, kin cancanci a baki sarauniyar kyau ta dik duniya". Har lokacin bai saki hannunta ba, ga shi cikin kwantar da murya yake maganar tana ratsa zuciya. Ko kusa ko alama bata kawo komai a ranta ba, ta ɗan saki jiki da shi tana kara cewa. "Nagode sosai brother, kuma kai ma ai kuna da kyau sosai, dik gidan nan daga Big Bro da Yah Omerish sai Yah Omar da ku, kuna da kyau......". Hannunsa dake cikin aljihu ya fitar tare da ɗaura yatsa ɗaya a saman lips ɗinsa yana faɗin. "Shiiiiiiii". Kura mashi ido ta yi tana jiran jin me zai ce, shi kuma kallonsa a kan purple lips ɗinta da suke wani sheki na musamman tamkar wacce akai wa kiss....... "Kada ki yi saɓo mana ƴan'mata, kuskure ne ki haɗa kyanki da na wani a gidan nan, ke ɗin karshe ce, zan iya cewa ni mai sa'a ne da kika kulani, dan naga baki kula kowa". Slowly ta ɗan zame hannunta daga rikon da ya yi mata, dan ta ji yana ɗan shafa mata skin sai ta tsinci kanta da jin tsikar jikinta na tashi......... "Ni nasan Big Bro ya fini kyau, abin da ya yi sa kuma shi ya yi ku, dan haka ni ba zan yarda na fiku ba". Jingina kai ya ɗan yi, har lokacin babu alamar murmushi a kan fuskarsa ya ce. "To shikenan tin da kin ce haka, amma dai kin yarda ke kyakkyawa ce ko?". Kai ta girgiza. "A'a ban yarda ba gaskiya, dan har yanzu ban ji daga bakin wanda in ya faɗa zan gamsu ba (Big Bro)"............. Nisawa ya ɗan yi kafin ya ce. "Zan gamsar dake in kika bani dama"......... Jinjina kai ta ɗan yi kafin ta ce. "Shikenan na baka dama, amma yanzu ni bari in je wajen Aunty Mahnoor". Kai shi ma ya ɗan jinjina. "Thank you for your time and I really appreciated yadda kika bani kulawa, idan ba damuwa anjuma mu haɗu a garden zan gamsar dake cewa ke ɗin kyakkyawa ce". Yana magana yana binta da wani irin kallo mai wuyar fassaruwa, ta kasan ido yana satar kallon surar jikinta. "Idan Big Bro ya barni zan zo". Ta faɗa tare da ɗan ja baya...... Ai su Sareena tv suka mayar da su, kallonsu kawai suke yi babu kakkautawa. Tamkar zai sake yin magana, sai kuma ya jinjina mata kai kawai, sallama tai mashi ta wuce ta nufi waje. Bayanta ya bi da kallo yana jin zuciyarsa na kara narkewa a kanta, har sai da ta kurewa ganinsa, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da juyo da kallonsa a kan su Obaid da kusan suman tsaye suka yi a wajen. "Why are you staring at me like that?". Ya faɗa yana dawowa cikin ɗakin.......... Da sauri Obaid ya ce. "Omaid sai yau na tabbatar da baka tsoron mutuwa, kana wasa da bomb yaro!". ....... Siririn tsaki ya ja yana zama a gefen bed. "Sai kuma ka yi ai matsoracin banza malalaci, ni ku zo mu cigaba da abin da yake gabanmu hai". Ya faɗa babu alamar tsoron Big Bro a ransa, tamkar an zare mashi tsoro ne, irin like ji yake yi babu wani shege sai shi. A gefe-gefensa suka zauna dan cigaba da yin magana, basu san shi ma Big Bro yana can yana ƙoƙarin bincikar wanda ya yi poisoning ɗin ɗan uwana ba, dan wlh kun san dai ba zai kyale ba ko?. Shiru suka yi suna jiran jin me zai ce, sai da ya ɗan yi gyaran murya kafin ya ce. "Zamu jefi tsuntsu biyu ne da dutse ɗaya gobe da daddare, zamu aiwatar da plan ɗinmu a kan Yah Raj, sannan zamu aiwatar da plan B a kan Pretty wanda bata isa ta shallake wanna ba wlh, dole aurensu zai rabu cikin ƙanƙanin lokacin". ME KUKE TUNANIN ZASU AIKATA?. Jinjina kai Sareena and Obaid suka yi alamar maganar tanai masu sugar. Shoulders ɗinsu ya riko yana faɗin. "Ku matso ku ji shirin". Matsawa suka yi suka haɗe kai, raɗa ya fara yi masu a kunne yadda babu wanda ya iya jin me suke faɗe. Wani irin makirin murmushi Sareena da Obaid suka saki suna faɗin. "Wlh wanna plan ɗin ya yi, komai ya yi daidai!". Jinjina kai ya yi tare da miƙewa ya nufi waje yana faɗin. "Sai ku shirya, zamu yi amfani ne da matar Yah Jaish tin da kunga suna shiri da ita, so kunga koda komai ya kwaɓe ita za'a tuhuma, ni bari in je duba yadda zamu yi amfani da ita cikin ruwan sanyi, naga kamar tana shiri da Yah Omar ma, bari dai in zo". Cike da murna Sareena da Obaid suka tafa hannu suna dariya, buƙata zata biya, Obaid zai samu Pretty idan suka rabu da Smart. Gidan sarauta gidan cakwakiyar gaske, kai nifa dan wlh ina ɗan taƙaita wasu abubuwa ne, dan kada book ɗin nan ya yi yawa over, in ba haka ba da zan ware dik wani tsarin da na tsarawa littafin nan cakwakiyar kai na zai ɗauka ta daɗi ba! Mu je dai zuwa ina ɗan taƙaitawar ma ba matsala!! AFTER SOME MINUTES. SWEETIE.🔥 Babu kowa a ɗakin da ya shigo, ya ɗan yi mamaki ya kuma duba time. 12:30. To ina ta je a wannan lokaci? Sai kuma ya yi tinanin ko dai wajen Pretty ta je ne? Dan ya lura hankalinta bai kwanta ba. Wucewa ya yi ya rage kayan dake jikinsa, ya je ya duba aikinsa komai ma tafiya yadda ya tsara da kyau. Ya rage daga shi sai bot short a jikinsa, ya nufi dressing room ɗinsu domin ya ɗauki towel da yake yawa a jikinsa. Yana sanya kai ita kuma tana sanyowa zata fito. Karo suka yi kanta ya bugi lion heart ɗinsa. Baya-baya ta yi tana tangal-tangal zata faɗi. A natse yasa hannu ya capko wuyar rigarta ya jawota gaba, tafiya gabaɗaya tai sai saman kirjinsa. Wani irin cool ajiyar zuciya ya sauke, ita ma dai shi ta sauke. Slowly ya fara bin kayan jikinta da kallon. Abaya ce ta Zunaira launin ash mai ɗan duhu, kasancewar tana da haske sai ya yi mugun yi mata kyau, ta yi rolling veil a kanta, sai tashin kamshi mai kwantar da hankali take yi. Har cikin ransa ya ji irin wannan shiga ta kwanta mashi a rai, dan ta yi daidai da maganin zafin kishinsa, kunga ta rufe jikinta kaf babu wani kayansa da wani zai gani, hakan ya mugu-mugun burgesa over. A garin ƙare mata kallo idanunsa suka sauka a kan kirjinta yadda wuyar abayar ta yi kasa. Ɗan limshe idanunsa ya yi ya sake warosu a kanta, a cikin ransa ya ce. "Ba zan iya cigaba da jurewa ba, buƙatata kawai in yi disvirgin ɗinki, ina son jina a jikinki sosai, I need this moment in my liand I wan to play with your balls da suke hanani natsuwa da barci yadda yakamata, I want you to give me beautiful bouncing baby's kamar ke ko guda 12 haka, I dream of having beautiful children with you, children that carry our love in their smiles". Kun san shi fa yana balain son yara, baku ga har gidan marayu yake da shi bane? Kun manta har renon marayu yake yi, baya son yaga rayuwar yara a tagayyare, saboda yana kaunarsu, wanna ne kawai aikin alkhairin da yake aikatawa a rayuwarsa watau kula da marayu da kuma kulawa da yara, ina da tabbacin saboda wanna aikin alkhairi ALLAH ya turo Sweetie cikin rayuwarsa dan ta nuna mashi haske ta fiddashi daga duhu, kun san in kana aikata alkhairi ALLAH ya nufeka da rahama, sai ya kawo maka mafita ta in da baka zata ba, bare shi da marayu da yara fa yake kula da rayuwarsu, ya renesu tamkar yaran sarakuna masu iko, ya basu dik wata gatar da zai sanya su ji suma ƴaƴa ne kamar kowa, su manta da rashin iyayensu, kai gaskiya a nan ɓangaren shi mutum ne da ya ci jinjina wlh!. Ya shagala da tinani sai gani ya yi ta yunkura zata bar jikinsa, da sauri ya rikota, can kasan makoshinsa ya ce. "Idan muka yi aure me zaki fara bani?". Ya faɗa yana kallon kyakkyawar face ɗinta dake ta faman sheƙi, wani irin narkakken kallo mai narka zuciya yake binta da shi. Cool murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. "Mekake so to?"........... Hannunsa ya ɗago kai tsaye ya ɗaura a saman tula-tulanta har sai da yasa gabanta ya yi wani irin faɗuwa, kirjinta ya buga da karfi. Rankwafowa kanta ya yi, a kunne ya fara yi mata raɗan hot sexy word kamar haka. "Your balls, zasu yi daɗin taɓawa, and ke kanki you're hot and sexy, zaki yi daɗi sosai, Maysh ba zan iya cigaba da jurewa ba please". Yadda ya yi magana na karshen nan sai da ya sanya numfashinta dakatawa da breating na wucin gadin, dan cikin wani irin murya ne mai kwantar da hankalin da dik wani masoyi zai zo masoyinsa yai mashi. Rasa me zata ce mashi ta yi, dan wlh kalamansa sun girmi shekarunta, hasalima bata san ma'anar hot and sexy da ya faɗa ba, bata san me yake nufi ba, amma kasancewar ya kira balls ɗinta yasa ta ce to dik yadda aka yi dikka batu ne na wancan sabgar, so sai ta rasa bakin yin magana. Muryarsa ne ya sake ratsa kunnenta. "Ina san karɓar vigin ɗinki, ina son wannan rana ta zo rayuwata". Ya yi maganar yana ɗaura hannunsa a saman shafaffen cikinta, ya shafa har izuwa mararta yana son yin ƙasa da hannunsa. Zabura ta yi ta kwace kanta tare da raba jikinsu, bai hanata ba, ya jingina da gefen door yana kallon face ɗinta yadda zallar tsoro ya bayyana. Da yar gudunta ta raɓa gefensa ta wuce. Waje ta yo, shi kuma ya yi shiru tare da ɗaga kansa sama tamkar mai tinanin wani abin, yana wani irin jan numfashi a hankali yana furzar da zafin gaske. Almost 5 mins yana tsaye a wajen kafin ya wuce da kyar ya nufi wajen towels ɗin. Ɗaya ya ɗauko ya fito. Ya ɗan yi mamakin ganin bata ɗakin, bai kawo komai a ransa ba ya wuce toilet. Ita kuwa tana fitowa bedroom na momma ta gudu, dan ya yi mugun bata tsoro, gabaɗaya ya canza mata tamkar ba shi ba, a ranta ta ce ita dai ba zata sake kwana da shi ba, tsoronsa take ji yanzu. Da gudu ta shiga bedroom na momma, kuma ta je ne da nufin ta faɗa mata gaskiyar abin da yake a tsakaninta da Big Bro, sai dai kuma momma bata nan, tana can part ɗin Ramish tana taya shi shirin tafiya wajen Aesh, saura 30 mins jirginsa ta ɗaga, momma na taimaka mashi wajen shiri ne, da ita da mummyn Chuchu, ita kuma mama tin da ta bar bedroom na King ba wanda ya sake ganinta, ta kule a cikin ɗakinta. Ganin momma bata nan ne yasa ta nufo waje, kai tsaye ta nufi room na Mahreen. Tura kofar ta yi ta shiga tana haɗawa da sallama. Ai wata uwar birki ta ja tare da zazzaro idanu tana kallonsu. Mahreen ce tsaye a tsakiyar ɗakin daga ita sai towel a kirji, guyson ya camki towel ɗin wai zai warware, ita kuma ta rike kayanta gam tana faɗin bata so ya rabu da ita. Sam basu lura da shigowarta ba, dan haka sai ta ja baya-baya a hankali ta yi waje abinta tana jin kirjinta na bugawa da karfi. Guyason kuwa ya kankame towel gam ya ce sai ya warware. Abin da ya faru shi ne, ya zo room ɗin ne da nufin ya ce mata ta shirya su je wani waje yawo, sai ya samu bata ciki, har zai juya ya fita ya ji saukar ruwa a toilet alamar tana wanka, da jin haka ya dawo ciki, saman bed ya haye ya kwanta yana fuskantar toilet door ɗin, zuciyarsa fes cike da muradin fara yin tozali da ita a yayin fitowarta. Ya kuwa yi sa'a, tana fitowa suka haɗa ido, nan fa ta ɗaure fuska, ta manta me ya haɗasu da kuma yanzu tana shakkarsa sai ta ce. "Meyakawoka ɗakina?". Tana magana tana faman ɗaure towel ɗin. Miƙewa zaune ya yi yana faɗin. "Wajen matata na zo". Ya faɗa tare da saukowa kasan bed ɗin. Harara ta dalla mashi kafin ta ce. "Ni ka fita mun a ɗaki ko in faɗawa Yah Jaish".......... Nufota ya yi yana faɗin. "Babu in da zance, tukun nan ma zo in ga property na, zo in duba sun kara girma ne?". Ya faɗa tare da kai hannu zai damki towel ɗinta. Da sauri ta janye baya tana faɗin. "ALLAH ya kiyayya jikina yazama propertyn yaro irinka"....... Da jin haka ransa ya sosu ya ce sai ya buɗe ya gani, shi ne ya damki towel ɗin ita ma ta damka suka tsaya cirko-cirko. Karfi yasa ya jawota jikinsa gabaɗaya, tafiya ta yi ta faɗa kirjinsa. Yunkurawa tai zata kwace kanta ya yi gaggawar mannata da jikinsa, yasa karfi ya ware towel ɗin tare da ɗauresu shi da ita a ciki gam. Kukan gaske ta saka mashi hawaye bibbiyu tana faɗin. "In Sha ALLAH ALLAH sai ya sakamun abin da kake yi mun, ni bana shiga harkarka sai ka rinƙa shiga nawa, ba zan yafe maka ba". Da jin waɗan nan kalaman nata sai ya taɓa zuciyarsa, tin da ta ce bata so baikata ya rinƙa yi mata hakan ba, ga shi kukan gaske take yi. Ƙasa da murya ya yi wajen cewa. "Ban yi dan na sakaki kuka ba, cikin wasa na yi, amma ba zan sake ba na yi alƙawari, yanzu ki daina kukan kuma ki faɗa kin yafe mun kin ji ko?". "Ka yi alkawarin ba zaka sake taɓani ba sai in yafe maka"........ Cikin sanyin murya ya ce. "Zan rinƙa kiyayewa ina yi abin da kike so, to kema zaki rinƙa yi abin da nike so?"....... Kamar wata ta ALLAH ta jinjina mashi kai alamar e, hakan yasa ya ji daɗi sosai, ya yi fatar ALLAH yasa ta kasance a hakan kada ta canza, nina dai na ce Amin. Ɗan raba jikinsu ya yi yana ware towel ɗinta, ya ɗaura mata kayanta kafin ya ce. "Idan kin gama shiri ina jiranki a parlo ki zo akwai in da zanu je kin ji?". Kai ta jinjina mashi, daga haka ya nufi waje. Ita kuma ta nufi closet ɗinsu. Yana fitowa ya ci karo da Ramish and momma da mummyn Chuchu suna rakosa. Cike da mamaki ya ce. "Yah Ramish Ina zaka je?"......... Ɗan rungumosa Ramish ya yi kafin ya ce. "Zan je ɗauko maka Aunty Aesh ɗinka ce".......... Cike da murna ya hau yi mashi fatan dawowa lafiya. Da amin ya rinƙa amsawa kafin shi ma ya yi sallama da su momma, bai je wajen Mama ba ya tafi, dan baya son ya je ta tayar mashi da hankali, har gobe kallon uwa yake yi mata tin da nononta ya sha. Dakakkun Guards guda goma King ya sanya su take mashi baya zuwa Kingdom ɗin, sai zaratan warrior guda biyar, da su za'ayi tafiyar. Shi kaɗai ya tafi, Rizwan ya so rakasa amma ya ce a'a zai je shi kaɗai, dan baya son wani mummunar abin ya faru. Suna zuwa airport ba tare da ɓata lokacin ba jirginsu ya ɗaga sai birninsu Leesharh, dik ya matsu ya ganta, har ayyanawa a ransa yake yi yadda zai ganta, yana imagine yadda zata yi idan ta gansa, har hasko hakan a ransa yake yi, bai sanar da ita yana zuwa ba, surprise yake son yi mata. Karfe 9 na dare jirginsu ya sauka a birnin su Leesharh, already Zash yasan da zuwansu, dan haka je da kansa da kuma motoci and securitys dan ɗaukosu. Hakan nema yasa Ramish ya shiga kingdom ɗin ba tare da mahaifin su Suhaima ya sani ba, wato uncle ɗinsu Leesharh dake kan kujerar da Zash ne yakamata ya haye tin da babansu ne sarki kuma baya raye. Da King Abdul Aziz yasan da zuwan Ramish ba karamin rikici za'ayi ba, dan ba zai barshi ba yadda ya tsani King Zuhair ɗin nan, amma kuma Zash ya yi amfani da cewa abokinsa ne zai zo dan basa son wannan faɗa ya cigaba da faruwa, su kansu dakatar da gaban suke so ayi, shiyasa suka yi haka. Zash yasan uncle ɗinsa ba zai bar Ramish ba, idan kuma ya kuskura ya taɓa Ramish sabon yaki ne zai sake ɓallewa wanda dakatawarsa abu ne mai matuƙar wahala, kuma ba zasu so haka ba tin da sun rigada sun auri kannen juna. Kai tsaye part na Zash Ramish suka wuce, sai da ya yi wanka ya shirya cikin wasu kayan, dik ya matsu ya ganta, har ya kasa hakuri ya cewa. "Bro wai ina matata ne?"........... Murmushi Zash ya yi kafin ya ce. "Ai dama na zuba maka ido ne in ga ko zaka iya hakura sai da safe". Pillow ya ɗauko ya jefi Zash da shi kafin ya ce. "Saboda kai baka san daɗin mata ba shi ne kake tunanin zan iya ko?"..... Capke pillow Zash ya yi yana faɗin. "Gori zaka mun ne?". Miƙewa Ramish ya yi. "Ai gara in yi maka gorin ko zaka samu ka shiga daga ciki". Yana murmushi ya ce. "To zo mu je, kada na shiga hakkinka, dan naga alamar kazo wuya". Ya faɗa tare da yin gama Ramish ya rufa mashi baya suka nufi room ɗin Leesharj dake part na mama Haulat. -------------------------🔥 Tsaye take a tsakiyar room ɗinta tana kokarin nufar gaban mirror. "Mama Yah Zash ya ɗauke mun sabbin towels da kika bani, wai sun yi mashi kyau, na ce ya saya wai naki yake so, ni ki ce ya bani kayana, dan nasan budurwarsa zai baiwa". Ta faɗa tana goge ruwan dake kanta da wani ɗan karamin towel da take rike da shi, daga wanka ta fito, tana ɗaure da towel a kirjinta ta fara takawa a hankali. A gaban mirror ta tsaya tana kallon kanta, ta kara wani irin sihirtaccen kyau mai ɗaukar hankali saboda balain gyaran da ta sha wajen Mama Haulat, kumatunta ya yi ɓul-ɓul, skin ɗinta sai wani irin sheki na musamman yake yi. Welcome and goodbye ɗinta nan tamkar ka kirasu su amsa, shape ɗinta ya kara fita sosai, da alama mama Haulat ta bata magungunar kara tula-tula, dan sun ciko bam, dama tana da goodbye sosai, sai suka kara cika. "Mama ko dai baki jini bane?". Ta faɗa tana ɗauko haɗin lotion ɗin da Mama ta haɗa mata na gyaran jiki........ Jin shiru Mama bata amsa bane yasa ta ce. "Anya Mama bata je wajen Yah Zash ba kuwa? Dik yadda aka yi ta bar parlon shiyasa bata amsa ba. Ta barni sai buɗe murya nike yi bayan kuma muryata ta Yah Ramish ɗina ne kawai, ina kewarka sosai mijina, ina burin ganinka". Nisawa ta ɗan yi, take yanayin face ɗinta ya canza, idanunta ne suka ɗan cicciko da kwallah, a hankali ta sake cewa. "Ina kwaɗayin kwanciya a kirjinka, ina kewar kiss ɗinka, Ina kewar muryarka, ina kewar komai naka, please ka dawo gareni kafin in zauce"..... Ta faɗa tare da juyowa ta jingina bayanta da jikin mirror drawer. Kanta ta ɗaga sama tamkar mai wani tinani, ta lumshe idanunta tana tinani. "Soyayyarka tana neman zautar dani, ALLAH ya gani hakurina ya fara karewa, ba zan iya cigaba da jurar rashinka ba, please ka zo ka ceci zuciyar da bata san komai ba face sonka"..... Tana kai karahen maganar slowly ta waro idanunta kai tsaye sai kan fuskarsa. Yana tsaye a bakin door, ya rungumo hannayensa a saman kirjinsa, tin da ta fito daga wanka ya shigo, dik abin da ta faɗa a kan kunnensa, ya ji komai, tsantsar kyan da ta kara ne yasa ya gagara yi mata sallama, ya mace da kallonta. Waro idanunta waje ta yi, sai kuma ta sake komawa normal tare da cewa. "Nasan gizon da ka saba yi mun ne, ni ka tafi in dai ba zaka zo a gaske ka ɗaukeni ba, na gaji da gizonka ko zuwanka a mafarkina". Tana magana tana harararsa. Blinking eyes ɗinta ta yi da sauri tare da sake warosu a kansa. "Ya naga ka rame sosai ba kamar yadda kake zuwanmin a mafarki da kibarka ba? Yau ka rame sosai me yake damunka?". A hankali ya motsa lips ɗinsa wajen ce mata. "Kawarki, shi ya ramar dani"............. Turo ɗan bakinta ta yi. "Sai yau ka yi ra'ayin amsa mun? Ba kullum in kazo mun baka amsa maganata ba, meyesa yau ka amsa?"........ "Saboda yau gaskiya ce ba gizo ba". Ya sake faɗa yana kallonta. Zazzare mashi idanu ta yi, muryarta har yana rawa wajen cewa. "Yah Ramish?". Ta faɗa tana pointining ɗinsa da hannu....... Kai ya jinjina mata alamar for sure shi ne....... Ai bata san time da ta saki ihu mai sauti ba, da gudu ta nufesa har ta manta me take yi. Buɗe mata hannunsa ya yi, tana zuwa ta faɗa saman chest ɗinsa, wani irin zazzafar rumguma ya yi mata tamkar zai mai da ita cikinsa, at the same time suka sauke ajiyar zuciya a jere-jere. Kankame shi ta yi da karfi ita ma tamkar yadda ya kankameta, sai ajiyar zuciya suke saukewa a jere-jere, tamkar zasu haɗiyi juna. Ruwan hawaye ta fara yi mashi, muryarta na rawa sosai ta soma cewa. "Yah Ramish dama zan sake ganinka? Dama zaka zo gareni? Ya ilahi ya lillahi, yau kam ina zan sanya kaina?". Ai shi kasa yin magana ma ya yi, dan wani irin azababben daɗin dake ratsa shi, jikinsa har yana ɗan rawa kaɗan-kaɗan........... Almost 10 mins suna manne da juna kafin ya ɗan sassauta rikon da ya yi mata, da sauri ya haɗe fuskokinsu, muryarsa tana ɗan dishashewa ya ce. "I really missed you my Aesh, na sha wahala a rashinki". Ya kai karshen maganar yana ɗaura lips ɗinsa a saman tata. Tana kuka hawaye bibbiyu ta kama lips ɗinsa na ƙasa, a hankali ta fara kissing ɗinsa tana kara kankamesa kamar wani ya ce zai sake rabasu. Haba kamar jira yake tini ya fara bata hot kiss, ya capki tongue ɗinta ya shiga sha irin shan huce hushin nan, ya kankameta a jikinsa yana aikin tura mata yawunsa, ya sanya hannunsa ta bayanta, ya kara matseta a jikinsa sosai. Ɗan zame bakinta ta yi tare da kai hannunta saman kyakkyawar sajensa, tana ɗan rawa da hannunta a wajen zuwa saman lips ɗinsa, ta kwanto da kansa a saman chest ɗinsa, wani irin kuka mai slow sound ta saki wanda da ka ji sa ka san farinciki ne ya yi mata over har ta rasa ina zata sanya ranta. Hannun nata da take yawo da shi daga kumatunsa zuwa lips ɗinsa ya riko ya ɗaura a saman bayansa, sannan ya ɗago haɓarta, tongue ɗinsa ya fitar ya hau lashe hawayen nata ya gagara yin magana, dan farincikin ma tafi karfinsa, ji yake yau in bai mayar da ita cikin cikinsa ba bai gamsu ba. Gabaɗaya hawayen nata sunki dakatawa, yana lashesu suna sake zubowa tamkar an buɗe tap, rage tsawonsa ya yi ya ɗauketa sai saman bed ɗinta, gabaɗaya ya tafi da ita suka afka saman bed ɗin, runfa ya yi mata da chest ɗinsa, cigaba da ƙoƙarin dakatar da hawayen nata ya yi amma ina sun ki dakatawa, ganin hakan yasa ya sake haɗe bakinsu waje guda. Zafafa ya shiga bata na huce haushin kewa, martani ta shiga mayar mashi na huce haushin kewa ita ma. Nan fa suka sake birkita juna, suka lula duniyar sama jannati. Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only please. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 34 CROWN OF POWER.🔥 Tsab suka kammala shirinsu cikin ƙanƙanin lokaci, sun shirya plan ta yadda za su yi amfani da Mahnoor kai tsaye ba tare da ta sani ba. A gefe guda kuwa sun shirya yadda zasu ɗauke Zee zuwa part na warriors, sun shirya da wani warrior zai yi amfani da ita su ɗauki video, dan haka sai Obaid ya shirya maganin barci cikin drinks ya nufi wajen Mahreen, da ita ya yi amfani ya yaudareta a kan zai saya mata amor, amma sai ta kaiwa Zee wanna drinks ɗin. Da ta tambayesa meyasa ba zai kai mata da kansa ba, sai ya ce. "Mun yi faɗa da ita ne, kuma ga shi Yah Raj ya matsa wai in kai mata ta sha, kin san abin nasu na masoya, to shi ne fa naga ke kina shiri da ita, ki kai mata, ki ce in ji Yah Raj please". Cike da kalaman yaudara a bakinsa ya miƙa mata. Karancin shekaru yasa bata fahimci ba'a sulhu da wanda ya ce baya sonka tin da safe ba, dan haka sai ta yarda da maganarsa ta karɓa ta fito parlo. A nan ta isko guyson, shi kuma Obaid ya fita ta ɓangaren Mama bai bari guyson ya gansa ba. Tana ganin guyson ta ce. "Bari in kaiwa Aunty Zee wanna drinks ɗin in zo". Kamar zai tambayeta ina ta samo shi, sai kuma ya jinjina mata kai kawai. Da sauri ta wuce part na Aunty MieMie. Sai dai bata samu Zee a can ba, dan haka sai ta nufi garden. Dan a nan ta san Zee na zama tare da Dr su sha hira. Obaid na ganin ta fito ya bi bayanta. A garden ta isko Zee zaune tana latsa wayar da Dr ya bata. Sallama ta yi mata tare da miƙa mata drinks ɗin tana faɗin. "Dr ne ya ce a baki". Ƙayataccen murmishi Zee ta saki kafin ta sanya hannu ta karɓa tana faɗin. "Kyautar masoya daɗi ne da shi". Ta faɗa tana kai cup ɗin bakinta ba tare da tinanin komai ba. Obaid na laɓe yana ganinsu, sai da ya ga Mahreen zata fito daga cikin garden ɗin ne ya yi gaggawar ɓuya. Fitowa ta yi ta koma cikin gida, shi kuma ya dawo ya tsaya yana kallon Zee har ta kammala shanye drinks ɗin, ba'a fi mintuna goma da shanta ba ta ɓingire a wajen sai barci hannunta rike da wayarta. Da sauri Obaid ya bar wajen yana jin wani irin farinciki na kara ratsa zuciyarsa. Yana tafiya ba'afi da mintuna biyu ba sai ga wasu warriors guda biyu sun shiga garden ɗin. A saman shoulder ɗinsa ɗaya ya saɓo Zee suka fita ta baya da ita. AIKI YA KAMMALA!. Murna sosai su Omaid suka rinƙa yi shikenan zasu raba Dr da Zee. Nan fa suka fara shiryawa Pretty nata shiri, sai dai nata ya ɗan basu wahala, dan sai karfe 8 na dare suka samu komai ya saitun masu yadda suke so, daga nan suka fito domin aiwatarwa. Cup irin na Zee mai shake da drinks Omaid ya fito da shi rike a hannunsa. Sun zuba Viagra da LowT a cikin drinks ɗin. Sareena suka baiwa ta nufi room nasu Mahnoor da shi, a wannan shiri Omaid bai faɗa masu menene bane, shi dai ya ce masu daga yau Pretty ba zata dake son Yah Omerish ba, zata tsanesa ta yadda dole ya rabu da ita, Sareena ta yi ƙoƙarin sanya wanna drinks ya je hannun Smart ita kam. Cike da murna ta fito da drinks ɗin zata nufi part na su Mahnoor. Nan dai Omaid ya bata drinks a wani cup daban, ya ce mata. "Idan kika baiwa Mahnoor kika ce ta baiwa Pretty ta bawa mijinta ita kaɗai dole zata zargi wani abin, amma ita ma ga nata, ki ce kowa na family an bashi ya baiwa mijinsa ne". Kai Omaid ba dai kwakwalwar iya tsara plan ba wlh. Karɓa ta yi ta wuce cike fa farinciki. Baki a ɗauke da sallama ta shigo parlon, Mahnoor na zaune a saman sofa a parlo rike da wayar Jaish. Ta sha mamakin ganin Sareena, miƙewa ta yi tsaye tana kallonta. Munafikin murmushi Sareena ta sake kafin ta ce. "Ya kike kallona haka? Lafiya?". Ajiyar zuciya ta sauke da sauri kafin ta ce. "Lafiya lou sannunki da shigowa". Da yauwa ta amsa tana karisowa gabanta. Cup nata ta fara miƙa mata kafin ta fara magana yadda Omaid ya tsara mata. "Daga part na momma nike, ta shirya wanna ne domin mazajenku, ta ce kowace mai miji ta baiwa mijinta, ga na Yah Jaish, wanna kuma na Yah Omerish ne, yanzu na kaiwa Chuchu ma nata". Bata kawo komai a ranta ba tin da an kira Momma, sai ta karɓ tare da ɗaurawa saman table tana godiya. Ɗan juyawa Sareena ta yi kamar zata tafi, sai kuma ta sake juyowa tare da cewa. "Ayya ko zaki taimakeni ki baiwa Pretty wanna ta baiwa Yah Omerish? Kinga bamu shiri da ita, tana fushi dani, so bani son yi mata magana, ke tinda kuna shiri ki taimaka ki bata kin ji?". Still dai bata kawo komai a ranta ba ta karɓa tare da cewa. "Ba damuwa bari in kai mata". Ta faɗa tana wucewa gaba, sai dai a ranta tana tinanin me momma ta shiryawa mazansu ne haka? Uwa ta gari kenan, ta sake faɗa a ranta. Bin bayanta Sareena ta yi suka fito a tare zuciyarta fes tamkar an yi mata kyautar aljanna. Suna fitowa Sareena ta koma wajen su Omaid dan jiran result na aikinsu. Ita kuma Mahnoor har bedroom na su Smart ta je ta yi knocking, yana kwance Pretty ta lafe a jikinsa tana zuba mashi shagwaɓa a lokacin. Da yake jikinsa ba kwari sosai sai ya ce ta duba wanene, dan a tinaninsa ma Sweetie ce. Ba musu ta sauko jikinta sanye da short zuwa gwiwa, da ɗan karamin vest, sai shafe mata tula-tula dama yake yi. Hijabin da take salla da shi ta ɗauko ta sanya a jikinta kafin ta nufi waje ɗin. Har cikin ransa ya ji daɗin ganin ta sanya wannan hijabi, har albarka ya sanya mata. Tana buɗe kofa taga Mahnoor a tsaye, ta sha mamaki amma da jin abin da ya kawo Mahnoor sai ta sauke ajiyar zuciya, kai tsaye Mahnoor ce mata ta yi momma ce ta ce a baki wanna drinks ɗin ki baiwa Yah Omerish. Karɓa ta yi suka yi sallama ta juya ita kuma ta dawo ciki bayan ta rufe kofar. Sai da ta cire hijabin sannan ta kariso in da yake, cup ɗin ta miƙo mashi tana faɗin. "Momma ta ce kasha wannan". Karɓa ya yi yana sauke ajiyar zuciya, ya ji daɗi sosai dan drinks da yake masifar so ne, sai da suka zaɓi abin da yake so wanda sun san ba zai iya tsalleke ta yi ba suka zuba mashi magani. Yunkurawa ya yi ya miƙe zaune. A hankali ya fara sipping drinks ɗin sanyin tana ratsa shi sosai. Zama ta yi a gefensa tana faɗin. "Yau ba zaka yi dinner bane?".......... "Zamu yi amma sai Big Bro ya zo, ya ce kada in ci abu mai nauyi sosai". Ya faɗa yana kawo mata cup ɗin saitin ɗan bakinta. Ba musu ta karɓa ta sha. Jawota jikinsa ya yi yana faɗin. "Momma ta san dik yadda zata yi ta faranta mun wlh, kamar tasan na kwana biyu ban sha su-de ba". Ya faɗa tare da kai mata bakinta. Sha ta sake yi tana faɗin. "Yana da daɗi sosai". Ta yi maganar tana shafa bayansa a hankali-hankali. Haka suka kasance har suka shanye drinks ɗik kaf. Nan fa labarin ya canza, dan dikkansu wani irin azababben canji suka ji a jikinsu, bare ma shi da ya fita sha, take ya ji wani irin karfi da azababben sha'awarta da ba zai iya dannewa ba ta kamashi, take wani irin zufa ta fara wanke masu fuskoki gabaɗayansu. Cikin ƙanƙanin lokaci dik suka birkicewa juna, kuka ta fara yi mashi tana faɗa mashi gabanta yana yi mata wani iri, saboda ita bata san sha'awa ba a rayuwarta. Kankameta ya yi, shi da bashi da kwarin jiki saboda ciwo sai ga shi Viagra da suka sha a cikin drinks ɗin ya kara mashi tsananin karfi na gasken-gaske. Ita ma ta samu karfi sosai, dan ta iya ɗaukar dik murjeta da ya fara yi cikin fitar hayyaci. Tana kuka tana kara kankamesa tana faɗa mashi ita dai gabanta na yi mata wani iri. Dik abin da take faɗe baya jinta saboda ya fita yin nisa sosai, gabaɗaya ya fita hayyacinsa, da zafa-zafa yake murjeta, kuma a wannan lokacin bata jin zafi ko kaɗan, saboda ita ma bata daidai, sai kokari kara kankame shi ma take yi tamkar zata mayar da shi cikin jikinta saboda karfin sha'awar dake addabanta. Ko kaɗan bata san lokacin da ya rabata da kayan jikinta ba, ya haɗe bakinsu yana bata kiss cikin zafa, ita ma tana mayar mashi da martani da zafa-zafa. Yadda yake murzan tula-tulanta da karfin gaske ɗin nan dik bata ji zafi ba, sai da ya shigeta da karfin gaske ne ta gane ALLAH ɗaya ne, a wannan lokacin ne ta dawo normal a miliyan. Da karfi ta fara bubbuga bayansa tana faɗin ya tashi a kanta zai kasheta. Sai dai ina, baya ji kuma baya gani sannan kuma bai ɗaga mata kafa ba har ya mayar da ita cikakkar mace. Ta yi kuka, ta yi ihu, ta yi magiya, dik karfin maganin nan sai da ta dawo normal saboda azaba, duka yakushi babu wanda bata yi mashi ba, tin tana iya kuka har ta daina motsawa, kuma ko kusa ko alama bai ji magiyarta ba, dan baya daidai. Ga maganin da shegen karfi, hakan yasa bata sake shi sha'awar ta kwanta ba har sai da ya yi sau uku a jere-jere. Sannan ne maganin ya lafa mashi, ya koma gefe ya kwanta yana mayar da numfashi, bai kai ga sanin aika-aika da ya yi ba ma tukun nan, shi dai ya samu saukin azabar da yake ji a gabansa. PRETTY SAI ALLAH, JIKOKIN AKKA LAFIYA MA YA AKA KARE DA SU BARE DA KARIN MAGANI? TAB I PITY YOU PRETTY, ALLAH YASA KINA DA SAURAN NUNFASHI. A yayin da wanna abin yake faruwa shi kuma Big Bro yana ɗakin Momma, yanzu ya je neman Sweetie, dan tin da ta baro room ɗinsa bata sake komawa ba, kuma ta sanar da momma gaskiyar abin da yake faruwa, ta ce yanzu tana jin tsoron kwana da shi ɗaki guda. Hankalin momma ya yi mummunar tashi, har waje ta samu ta miƙe na ƴan mintuna kafin ta dawo daidai, a haka ma Sweetie bata faɗa mata cewa yana magic ba, da ta faɗa mata ina ga suma momma zata yi, amma ta ɓoye ta faɗa mata basu da aure, hasalima shi ba musulmi bane. Momma ta ji zafi fiye da yadda ba'a zato, amma da yake tana da tawakkali sai ta daure, cikin sanyin murya ta ce. "Tin da yana sonki, yana son farincikinki, ki daure ki tayamu yakin dawo da shi kan hanya". Hakika ta tausayawa momma matuƙa, dan ta lura idanun momma sun ciko da kwallah, kawai ƙoƙarin shanye kukan take yi dan bata son Sweetie ɗin tasan da kukan. To maganar da suke yi kenan ya shigo nemanta. A kusa da momma ya zauna yana faɗin. "Momma kece kika rike Maysh ko? Tin ɗazun ina jiran ta zo shiru". Shiru momma ta yi ta gagara amsa mashi, dan gabaɗaya ta ji kanta na juyawa ne. Ganin haka yasa ya sanya hannunsa ya ɗan rungumo shoulders ɗin momma yana faɗin. "Momma lafiya?". Juyowa ta yi da nufin ta yi mashi magana, sai kuma ta gagara, dan idanunsa sun razanata, dik sai ta nemi natsuwarta ta rasa, ta ji tamkar an ɗaure tongue ɗinta. Meyasa wai Big Bro ya kasance haka ne? Meyasa suke shakar tinkararsa da magana? Da gaske nonon aljana ya sha? To yau dai bari ku ji yadda Big Bro ya sha nono aljana har ya girma. Shekaru 34 baya, wata kyakkyawar mace fara tas mai cikar sura da diri da dik wanda ya ganta sai ya sake waigawa ya kalleta, sanye take da fararen kaya har kasa, ta yi shiga irin na mutanen birnin Black World, watau doguwar riga mai maɗauri a tsakiya, ta ɗaure dogon gashin kanta gida biyu ta sako jelar a gefe-gefen shoulder ɗinta, tsawon gashin matar nan har ya kusa taɓa kasa, hakan yasa take nannaɗosa sak yadda Big Bro yake naɗe nasa gashin. Kyan wannan mata ya zarce kyan bil adama, yanayin hasken skin ɗinta banbancinsa kaɗan ne da na Big Bro, tana da dogayen yatsun da ta tara dogayen nails tamkar yadda Big Bro ya tara nasa, idanunta dara-dara gasu farare kal-kal da su tamkar audiga. Tafiya take yi a cikin dokar daji ta gefe-gefen ruwa, hannunta rike da wani ɗan sanda tana busa, abin mamakin shi ne ba tafiya take yi a kan kafunta ba, a kan iska take ta yi, tana busa tana juyo tamkar wacce ke yin rawa. Lokaci guda ta dakata da busar da take yi sakamakon jin alamar kukan jariri da ta yi, sai kuma ta sauko da fararen kafafunta kasa ta taka ƙasa, shiru ta ɗan kasa kunne tana wuwwurga eyesball ɗinta a wajen dan gano ta ina take jin wanna kuka. Tabbas kukan jariri ne, da sauri ta tashi sama dan ta gano daga in da kukan yake rashi, wasu korayen ganye ta keta ta wuce cikinsu, take ta bayyana a bakin wani tapkeken teku mai girma wanda kuma shi ne dai wannan teku da ya raba Kingdom of Power da Kingdom of Justice, watau tekun da su Kamran suka rayu a kusa da shi. Da sauri wanna mata ta karisa in da take hango farin towel tas a wajen. Tana zuwa ta kai hannu ta ɗauki towel ɗin, ashe jariri ne a kudundune a ciki yake ta kuka, ko cibiya ba'a yanke mashi ba, sannan jikinsa dik jini alamar yanzu ma aka haifesa. Juyawa wanna mata ta yi gabas da yamma kudu da arewa babu wani alamar mutum mai rai a wanna waje, hakan yasa ta rumgumi jaririn nan ta tashi sama da shi. Tafiya ta soma yi a yanayin da mutum ba zai iya kallonta ba. Ta yi tafiyar da in da mota ne sai an kwashi awa huɗu masu kyau ana yinta, sannan ta dira a wani daji mai cike da tsaunika masu girman gaske, ga dogayen bishiyoyi masu duhu, sam-sam babu alamar halittar ɗan adam a wannan waje, waje ne ma abin tsoro. Cikin tsaunikan ta fara kutsawa har ta karisa wajen wani babban tsauni har sama wanda daga ta bayansa yake aman ruwa yana kwaranya ta gaba. Wannan tsauni yana da katafaren kogo daga ta katsa. Wannan kogo ta shige ciki da wanna jariri, wani sabon duniya ne a wannan waje, wanda in baku manta ba a baya na faɗa maku yadda tsarin Duniyar Shaiɗanu yake, to nan ne. Kai tsaye fadar sarkinsu ta nufa, yana zaune a saman wani haɗaɗɗen kujerar da shi ma na gaya maku yanayin mulkinsu. So ba sai na tsaya dogon jawabi ba, mu je kawai. Yana ganinta ya miƙe tsaye, shi ma sanye yake da fararen kaya har suna jan kasa, yana da dogon gashi har gaba da gwiwowinsa, kuma gashin kan nasa fari ne tas babu ɗigon baki, idanunsa gwanin ban tsoro, dara-dara da su. Cikin matsuwa da son samun amsa ya ce. "Sarauniya Elvender ina kika shiga tun ɗazun nike ta nemanki". Murmushi ne kawai a kan fuskarta ta gagara rufe bakinta, gabansa ta kariso tana nuna mashi jaririn tana faɗa mashi yau ta yi tafiya mai dogon zango a nan ta samu wanna jariri. Da azama yasa hannu ya karɓi yaron yana kallonsa. Shi ma take murmushi ta bayyana a kan fuskarsa, ya nuna tsantsar kaunarsa ga wanna jariri, ya ce ta jira shi bari ya faɗawa sauran muƙarraban fada cewa ya samu karuwar yaro. King Lucian wato sarkin Duniyar Shaiɗanu mutum ne, while matarsa Elvender ta kasance aljana ce wacce suka yi soyayya mai tsanani, ta hana Lucian raɓar kowace mace, ta ɗaukesa zuwa duniyar aljanu suka yi aure a can, shiyasa kowa yake ta ce Lucian ya ki yin aure, idan ma aka yi mashi maganar aure a gida ɓatawa yake yi da kowa, dole aka rabu da shi. Ba wanda ya san da Elvender sai mukarrabansa na Duniyar Shaiɗanu, su kaɗai suka san da ita saboda kusan suna tare da ita ne, da sanya hannunta a wallafa Duniyar Shaiɗanu, da taimakonta, ba mutuniyar kirki yadda kuke zata bane, kawai dai tana son yara ne yasa ta zama mai sauki kan wannan jaririn da ta tsinta, ta kuma shayar da shi saboda son da take yi mashi, ta ɗaukesa tamkar ita ta haifesa, dik in da zata je yana jikinta, ta soshi fiya da kanta. Sai dai kuma da zuwansa Daular da kwanaki biyu suka fahimci wanna ba kamar sauran mutane bane, yana tattare da baiwa mai tarin yawan gaske, wanda a nan ne suka fitar da dokar killacesa kada ya yi mu'amala da kowa, tin daga wanna lokaci ta daina fita da shi, saboda dokace kada a sake bari ya ga hasken rana, daga nan rayuwarsa a cikin ɗaki ta fara, sun ce shi ne zai maye gurbin sarki, a yayin da Elvender ta bayyana shi a masarautar aljanu da cewa shi ne magajinta kuma shi zai hau kujerarta na sarauniya a wanna Daula, tin yana da kwanaki goma a duniya ya samu naɗin sarauta na masarautu har biyu, na aljanu da kuma Duniyar Shaiɗanu, har yau kuma dikka waɗan nan masarautu babu kowa a kan kujerarsa, suna jiran dawowarsa garesu ne kawai ya cigaba da mulkansu, aljanu na jiransa, Duniyar Shaiɗanu na jiransa, ba iya wanna ba, yana da muƙamai da dama, shi ɗin ba iya King Of Black World bane kawai, King Of Evil World, Kingdom of Ice Kingdom, masarautar iyayen king Lucian mahaifinsa kenan, suma suna da saurauta, sannan King Of Blue Kingdom (masarautar aljanu na su Elevender) kai muƙaman da yake da shi ba zasu kirgu ba, sai gaba, Blue Kingdom suna jiransa har yanzu, hakan ke haifar da tsananin kaifi a idanunsa da kallonsa yake razana mutane, su king dik suke shakkarsa, aljanun suna tare da shi, suna mashi kallon jikansu ɗa ga Elevender, kunga kuwa dole Big Bro ya kasance yadda yake, fin haka ma idan ya kasance ba abin mamaki bane, dole ko yawun bakinsa kawai ta zama wata abar, mu koma kan labari. In baku a taƙaice yadda zaku gane Elevender ita ta shayar da Big Bro har ya kai shekaru biyu ciff, a ranar da ta yayesa a ranar aka naɗa shi sarautar last born of Evil World, daga kansa aka datse aihuwa, ba'a yarda wata ta sake haihuwa ba, idan mace ta samu ciki ma binneta da ranta suke yi ko su soketa yadda na baku labari a farkon da na kawo maku labarin Evil World ɗin. Dan haka daga kansa ba'a sake haihuwa a Daular ba, sanna a wanna shekaru biyun nasa aka naɗa shi sarautar Ice Kingdom, suna mugun ji da shi, kuma har lokacin baya fita ko parlo. In takaice maku labari yana da shekaru huɗu Elevender ta kamu da ciwo, ta kwanta jinya sosai, amma ashe ciwon bana tashi bane, ta mutu, sai dai kafin ta mutu ta baiwa King Lucian wasiyar cewa ya ɗauke mata Big Bro daga Evil World, idan har yana sonta da gaske to ya je wani waje ya renan mata ɗanta, idan ya girma ya sanar da shi cewa mahaifiyarsa ta ce lallai ya mulki duniya, wanna ita ce wasiyarta a garesa, ko ta halin yaya ya zama sarkin da duniya dik zasu kasance masu yi mashi biyayya, wanna shi ne burinta, ta so ta renesa a kan haka amma mutuwa ya yi mata yankar kauna, dan haka lallai King Lucian ya bawa ɗanta saƙonta. Bayan ta gama rubuta wanna wasiya a takarda, tasa Lucian ya kaita ɗakin da Big Bro yake killace, sannan tasa aka kawo mata wuƙa. Ta yanka hannunta, wani irin farin ruwa ya fara zuba daga in da ta yanka, Big Bro yana kwance yana barci ta matse bakinsa ta zuba mashi wanna ruwan, sannan ta ce har ya mutu ba zai daina sonta ba, kuma zai cika mata umarninta, and ba zai taɓa daina son Blue Kingdom ba koda iyayensa na gaskiya sun bayyana. Ta yi mashi abubuwa da dama kafin mutuwa ya risketa, to fa daga nan ne King Lucian ya fara ƙoƙarin ɗaukar Big Bro su bar Evil World dan cika maganar masoyiyarsa, ya shirya komai da zai buƙata, ya bi dare ya bi rana ya ɗaukesa daga ɗakin da aka killacesa a ciki, ya raba Evil World da autansu, suka yi tafiya mai nisan gaske, sai da ya samu dajin da ta yi mashi kusa da wasu kauyoka, a nan kafa Daularsa, ya sassari bishiyoyin dake dajin, ya fara gina birninsa. Da ya fuskanci Evil World suna neman Big Bro ido a rufe ne sai ya yi magic ya girke fadarda na Birnin Black World ta yadda ba zasu taɓa ganin Big Bro ba. Haka ya renesa a ɗaki matsayin zaki, ya renesa yadda Elevender ta so ya kasance, ya rura mashi wutar son mulkar duniya a zuciyarsa, da yake ya sha nonon Elevender sai ya taso da sha'awar magic da mulki, hakan yasa ya fara koya, yana karanta daga littafan baban nasa, babu wanda ya taɓa koya mashi, a hankali ya koyi komai har ma ya zo ya fi baban nasa iyawa. TO KUN JI DAGA IN DA YA SAMO SHEGEN SON MULKAR DUNIYAR NAN TASA KO?. A TAKAICE NE WANNAN, ZAKU SAMU WANI BAYANI DAGA BAKIN WANI DA BAI BAYYANA BA!. AMMA ME KUKE TINANIN YA KAI JARIRI CIKIN WANNA DAJI HAR ALJANA TA TSINCESA? MU JE ZUWA, MATSALAR DAGA CIKIN GIDA TA SAMO ASALI!. Daga baya a hankali-hankali mutane suka fara cika birnin Black World wanda a hankali Big Bro zai baku labari da kansa ya aka yi suka mulki birnin. Dan haka mu koma kan labarinmu. Shiru momma ta yi bata iya yin magana ba. Daidai lokacin Obaid ya shigo cikin ɗakin da gudu yana ihun Yah Omerish zai kashesu. A zabure momma ta miƙe tana tambayarsa lafiya?. Cikin kuka ya ce. "Yah Omerish ne zai kashe Omaid". Cikin natsuwa momma ta ce. "Ina Omerish ɗin?". Jikinsa har kerma yake yi wajen cewa. "Suna parlon daddy". Da sauri momma ta riko hannunsa suka nufi waje, bata tsaya jin doguwar bayani ba, gara ta je ta ganewa idanunta. Suna shiga parlo suka isko gabaɗaya family kowa yana tsaye cirko-cirko, ga Sareena da Omaid suna zube a kasa saman gwiwowinsu, dik Smart ya farfashe masu jiki da dakakkiyar belt ɗin hannunsa. Sai huci Smart yake yi tamkar zai kama da wuta. Abin da ya faru shi ne, da ya dawo hayyacinsa ya ga aika-aikan da ya yi, bai bi ta kan Pretty ɗin ba ya maida kayan jikinsa ya nufo waje cikin zafa, saboda ya zargi ba lafiya ba. Har ya fita ya dawo ya duba cup ɗin da suka sha drinks, a nan ya ga diddigar magani a kasa, shi ne fa ya fusata ya nufi room na Jaish, a nan ya isko Mahnoor tsaye a gaban mirror. Tsabar fusata ko sallama bai yi mata ba ya ce. "Waye ya baki drinks ɗin can ki kawo mana?". Ta tsorata sosai da ganin yanayinsa, muryarta har yana rawa ta ce mashi Sareena, cikin fushi ya juya ya nufi part na uncle Abbas. Yana zuwa bai tsaya tambayar waye ya bata ba ya fara jibgarta tamkar an aikosa. Da ta ji kamshin mutuwa shi ne ta ce ai Omaid ne ya bata. Ya yi mamakin jin hakan, amma sai ya damkota suka koma family part. Ya wuce room ɗinsa ya ɗauki belt ɗinsu mai balain zafi. Omaid da Obaid suna ɗaki ya iskosu, ai yana shiga ya haɗesu da Sareena ya hau zanesu tamkar wanda aka yi wa wahayin duka, shi ne fa Obaid ya samu ya gudu ya je ya sanar da momma. Ko tambayarsu dalili Smart bai yi ba ya hau basu a jikinsu, ga shi shi kansa mugun zazzaɓi yake ji a jikinsa, in ya tina abin da ya yi wa Pretty sai ya taune tongue ɗinsa tamkar zai kashesa saboda haushi. Kansa na yi mashi balain ciwo, amma haka yake dukansu tamkar baya jin wani ciwo a jikinsa, ya ji haushi iya haushi, yasan yanzu ko Pretty ta rayu ba zata yarda da shi ba, dik da ita ta kawo mashi drinks ɗin, bai shirya dis virgin ɗinta ta wanna hanya ba, gaskiya yaran sun cutar da shi. Da ya tuna haka sai ya kara ɗaga belt ɗin ya hau sauke masu a jikinsu ta ko'ina. Da gudu momma ta shiga tsakaninsu ta rike belt ɗin tana ya isa haka. Ƙoƙarin kwace belt ɗin ya yi saboda yana cikin fushi idanunsa sun rufe. Sai da ta yi magana da karfi sannan ya gane ita ce. A hankali ya sake mata belt ɗin ya koma saman sofa ya zauna. Daidai lokacin king da Big Bro suka shigo kusan a tare, Big Bro da Sweetie suka shigo, shi kuma King shi kaɗai. Family ta gama haɗuwa, dama saura saboda jin ihun su Sareena yasa suka fito da gudu. Ganin abin dake faruwa yasa King ya umarci da kowa ya zauna dan su ji me yake faruwa ne da Smart ya yi masu irin wanna duka haka. Babu wanda ya ja da batun king, dik suka samu waje suka zazzauna. Kallon momma King ya yi ya tambayi me yake faruwa ne haka?. Cike da tashin hankali ta ce. "Wlh nima ban sani ba, ga dai Omerish ɗin ya yi mana bayanin me yake faruwa". Dawo da kallonsa a kan Smart King ya yi kafin ya ce. "Omerish me yake faruwa?". Shiru Smart ya yi for almost 5 mins, sai ajiyar zuciya yake saukewa, har sun fidda ran zai yi magana kafin ya ɗago kai, da kyar ya ɗan taƙaita abin da ya faru tare da ɓoye ɓarnar da ya aikatawa Pretty ya bayyana a matsayin magani suka saka mashi a drinks. Salati gabaɗaya parlon suka sa ban da Big Bro da ya ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya yana ciro wayarsa daga aljihunsa. Wani irin huci mai tada hankali Smart yake saki, a nan ne momma ta iya fahimtar lallai akwai abin da ya yi wa Pretty, ba iya maganin kawai bane, akwai abin da ya ɓoye. Gabaɗaya parlon kallonsu ya dawo a kan twis, Obaid ya makale a baya bayansu Omaid yaki sakin jiki, dan yana tsoron Smart. ALLAH ya cecesa bai sha jibga ba ya gudu wajen momma. Pointining Smart da hannu Omaid ya yi kafin ya ce. "Na yi ɗin, idan kana jin kana da karfi ba sai ka yi abin da zaka yi ba". Babbar magana!. Zazzaro idanu Momma ta yi a kan twins, idanunsu a bushe garau babu alamar tsoro ko shakka, Jaish har hannu ya kai yana mutsustsuke idanunsa dan ya tabbatar wai shin da gaske su Omaid ne kuwa?. Dik cikin parlon babu wanda bai zaro idanu a kansu ba sai Big Bro da yake zaune yana danna waya, tamkar babu shi a cikin parlon, kuma dik abin da suke yi a kan kunnensa, sai dai bai motsa ba. Hakan ya yi mugun ɗagawa Sweetie hankali, dan ita da Ronnie sun san shirunsa sau da dama baya zama alkhairi. Smart gagara yin magana ya yi, saboda bai san me zai ce ba, zuciyarsa tamkar zata yi bindiga yake ji, ga shi Momma ta ce kada ya taɓasu kuma, saboda tasan in ya ce zai cigaba da dukansu again ba zasu yi saura ba yadda ransa ya kai ƙololuwar ɓacin nan. Miƙewa guyson ya yi yana wani irin huci, kafin su momma su ankara sai suka ga guyson ya ɗauke Omaid da wani gigitaccen marin da ya sanya shi zabura ya miƙe tsaye. Unexpected guyson ya ga Omaid ya damko wuyar rigarsa da hannu ɗaya, ɗayan hannunsa kuma ya dafe kuncinsa da shi yana kallon guyson har cikin ido. "Sabome me zaka dakeni?". Omaid ya faɗa. Ai wani irin zabura su Jaish suka yi ganin abin da yake faruwa, a tarbiyansu ko da sunan wasa Omaid bai isa ɗagawa guyson murya ba. Gabaɗaya jama'ar parlon mimmikewa suka yi suna salati except King and Big Bro sai Smart da ya kifa kansa da gwiwowinsa saboda zafin da zuciyarsa take yi mashi, in ya tuna abin da ya aikata mata yana jin ɗaci over. "Omaid kana da hankali kuwa?!!". Momma ta faɗa cikin tsawa. Ɗagawa momma hannu ya yi yana faɗin. "Babu ruwanki a cikin wanna faɗar". Cikin fushi ya faɗa yana wani irin huci tamkar kububuwa, kamar zai rufe momma ɗin ma da duka. Haba ai yana faɗawa momma haka guyson ya rasa control ɗinsa, a fusace ya dalla mashi wani marin har sai da ya sake mashi wuyar riga, da karfi yasa kafa ya take Omaid ɗin a kirji har sai da ya faɗi kasa. Cikin fushi ya fisge belt dake hannun Smart ya hau jibgawa Omid tamkar ALLAH ne ya aikosa. Can dai ya ga duka da betl bata yi mashi ba, ya yi jifa da betl ɗin ya hau tattakasa da kafa, ta ko'ina duka yake kai mashi cikin fushi, idanunsa sun rufe. Kuka Obaid ya fara yi yana faɗin su dakatar da Yah Omar kada ya kashe mashi ɗan uwa. Sai dai dik parlon babu wanda ya sauraresa. Da ya ga haka sai ya nufi guyson da kansa, hannunsa ya riko yana bashi hakuri. Guyson ya rigada ya zuciya, baya ji baya gani, ai wani irin kakkarfar jifa ya yi da Obaid ɗin har sai da ya daki glass table na tsakiyar parlon, ya cigaba da tattaka Omaid da kafafunsa. Momma na kokarin yin magana sai gani ta yi Omaid ya miƙe tsaye ya cakumi wuyar guyson yana ƙoƙarin karawa da shi. Nan fa hankalinsu ya kara mummunar tashi, zuciya da zuciya ne suka haɗu. UHM YAU AKE YINTA FA, WAYE ZAI RABA WANNA FAƊA, MEYASA BIG BRO BAI SHIGA FAƊAR BA? ME ZAI BIYO BAYA? MEYASA KING MA YA YI SHIRU?. Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only please. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 Momma na kokarin yin magana sai gani ta yi Omaid ya miƙe tsaye ya cakumi wuyan guyson yana ƙoƙarin karawa da shi. Nan fa hankalinsu ya kara mummunar tashi, zuciya da zuciya ne suka haɗu. Zuciyar guyson ne ta kara fusata over, hakan yasa ya yi wa Omaid dukan da bai tsammaci zai yi mashi ba, dukan haushi, kuma dik cikin parlon babu wanda ya dakatar da guyson, Jaish ma ya so tashi ya karɓi Omaid ɗin ya yi mashi duka mai kyau, saboda yadda ya riki wuyar guyson ya ɓatawa kowa rai a cikin parlon, abin da ba'a taɓa yi ba a tarihinsu, wai kani ya ɗagawa yayansa murya, kai basu taɓa ganin wannan masifa ba, suna da tarbiya fiye da tinaninku. Yau dai Mahreen ta tsorata sosai ganin irin fusatar da Omar ya yi, a ranta ta ce kai wai dama haka yake shi ma? Dama balaƴaƴƴe ne. Ganin guyson zai iya kashe mashi ɗan uwa babu wanda ya sanya baki ko ya yi yunkurin dakatar da shi ne yasa Obaid ya kwalla kara tare da daka tsalle ya shako wuyan guyson ta baya yana wani irin huci. Kun fa san su twins zasu iya jibgar junansu, amma ba zasu iya bari wani daga can gefe ya daki ɗayansu ba, a kan hakan sai in da karfinsu ya kare, sai dai a kashesu tare. Ganin ya shake guyson ta sama yasa Omaid kuma ya kama kafafun guyson ɗin wai zasu kaisa kasa su ji daɗin jibgarsa yadda yakamata, dan ba zasu yafe jinin da ya zubarwa Omaid ba. Da sauri Dr Raj ya miƙe a nufin zai rabasu faɗa. Hannu king Zuhair ya ɗagawa Dr Raj alamar ya dakata, da mamaki yake bin king da kallo, ya dakata kuma? Ya jefi kansa da wannan tambayar. Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki haka ya koma ya zauna yana kallonsu. Daidai lokacin suka kai guyson kasa, sai ƙoƙarin kwace shakar da Obaid ya yi mashi yake yi, Omaid kuma ya hau kan cikinsa yadda kuka ga damisoshi suke faɗa a daji haka yaran nan twins suka zama. Da kyar guyson ya kwaci shakar nan. Nan fa ya miƙe suka fara karawa su biyu shi kaɗai, Obaid ya jajirce ba zai bari a halaka mashi ɗan uwa ba, shi kuma guyson jibgarsu yake yi da gasken-gaske kuwa. Alama ta nuna ba karfinsu bane a jikinsu yaran nan, sannan wani abin mamakin kuma shi ne, sun ki yarda su illata lafiyar guyson dik ya kasance kamar basa cikin hayyacinsu, idan suka ce zasu dakesa wlh guyson zai iya mutuwa a hannunsu, dan basu bane, amma sai dai su shakesa ko da wasa basu yi yunkurin dukansa ba, dik wanda yake parlon nan ya lura da hakan, hakan yasa ba ƙaramin mamaki abin ya basu ba, meyasa suke shakkar taɓa jikin Omar dik da suna da zararrar iya mayarwa Omerish martani?. Ganin abin is getting out of hand ne yasa Jaish ya miƙe dan ya rabasu. Hannu Big Bro ya ɗaga mashi alamar ya dakata, sai a lokacin ya kashe wutar creen na wayarsa ya ɗago da kallonsa a kan Jaish. Da hannu ya yi mashi pointining wajen zama a kan ya koma ya zauna. Ba musu ya koma ya zauna yana kallon yayan nasu. Gabaɗaya kallon jama'ar parlon ya koma suna satar kallon Big Bro, shi kuma hankalinsa yana a kan momma dake ta faman ƙoƙarin dannar zuciyarta tana kama sunan ALLAH a bakinta, dan gab zuciyarta take da bugawa, ta ga balain da bata taɓa gani ba, wai ƴaƴanta da suka samu tarbiya sama da kowa a gidan ne yau suke wannan abin? Ya za'ayi ba zata shiga damuwa ba? Dama ga matsalar da Sweetie ta faɗa mata. Shi kuma King ya dakatar da Dr Raj daga rabon faɗar ne ba dan komai ba sai idan ya shiga twins zasu yi mashi illah, dan a yanayin faɗar ƴaƴan momma ne ba zasu daka ba, dik wanda ya shiga tsakaninsu to fa komai ka iya faruwa ne. Shi kuma Big Bro abin da ya sanya ya dakatar da Jaish shi ne dik abin da yake faruwa so ake a haɗa kan ƴaƴan momma a gwara, su yi ta faɗa da junansu tamkar zakuna a dawa, har su illata kansu, kunga idan Jaish ya shiga an ci riba kenan, shiyasa ya dakatar da kowa daga rabon faɗar. Smart kuma tarasu yake yi, dan yana jin dik abin da yake faruwa, dannar zuciyarsa yake yi, saboda yana son tashi ya rabasu, amma baya son tashi a haka, zuciya zata iya ɗibarsa ya kashe ɗaya daga cikinsu, shiyasa ya yi shiru yana son dannar kansa, ya kifa kai da gwiwa. Jaish dai ya gagara hakura har sai da ya ce. "Omaid anya akwai hankali a cikin kanka kuwa? Ka san me kake yi kuwa?". Yana maganar ne cikin rauni, da alama tashin hankali ta kai makura a ransa, basu taɓa ganin irin wannan musifa ba. (Kun san dik faɗar da Big Bro and Smart suka yi kwanaki ba'a gabansu bane, a ɗakin Smart ne, na biyu kuma a Black World, so basu taɓa ganin irin haka ba.) Cikin tsawa Omaid ya ce. "Sai dai kai ne baka da hankali ba ni ba!!.......". Ya mayarwa Jaish amsa a tsawace cikin fushi. Ai yadda kuka san walkiya haka Smart ya miƙe, kafin ma Big Bro ya yunkura dan dakatar da shi har ya isa gabansu, a fusace ya damko wuyar Omaid, da karfi ya jijjiga shi ya yi jifa da shi gefe, zuciyarsa na tafarfasa ya nufesa, kafa yasa ya fara tattashi da shi irin dukan fitar hayyacin nan. Da gudu Obaid ya saki guyson ya yi kan Smart yana faɗin ya kyale mashi ɗan uwansa kada su kashe shi. Hawayen da momma ke ƙoƙarin ɓoyewa ne suka fara zubo mata a kan fuska, sun fi karfinta ne. Ai Obaid na zuwa Smart ya kwashe kafafunsa ya zube kasa shi ma, haɗesu ya yi ya hau ball da su babu tausayi babu tausayawa. Obaid na ihu shi kuma Omaid kokari ya yi ya miƙe, a maimakon ya badu hakuri sai ya ce. "Iya abin da zaku iya kenan duka! Baku isa ku gyara ɓarnar da muka yi ba ai, duka ce kuma ku yi iya yinku ku gaji ku barmu!". Ai wani irin zaro ido da jama'ar parlon nan suka yi kwace kwayar idanunsu zai faɗi kasa, innalillahi wa innailarhi rajiun, wannan musifa dame ta yi kama?. Miƙewa shi ma Obaid ya yi, da kyar ya iya cewa. "Azzalumai kawai, ALLAH sai ya yi mana sakayya tsakaninmu da ku!". Ai dakatawa cak Smart ya yi da dukan nasu da yake yi, ji ya yi tamkar an kwaɗa mashi guduma a tsakar ka, sai ya rasa ma me zai yi. Jifar Sweetie da wayarsa Big Bro ya yi tare da miƙewa ya nufo in da suke tsaye. A gefen Smart ya tsaya yana kallon twins, dik tsaurin idonsu da rashin kunyarsu sai ga shi sun yi kasa da kai, sun gagara kallon cikin idonsa, amma harshensu bai yi sanyi ba, domin kuwa a daidai wannan lokacin ma Omaid ya sake cewa. "Dik tsananinku da zaluncinku dai bai wuce ace ku kashemu ba ko? To kafin mu dayawa sun mutu! Bayan mu ma dayawa zasu mutu, amma ku ku zauna ku naɗe duniyar kada ku mutu!". With his full confidence yake magana. Hannu Big Bro ya ɗaura a saman shoulder ɗin Smart tamkar zai rarrashesa, sai kuma ja janyesa baya da karfin gaske har sai da Smart ya yi baya baya ya faɗa saman sofa. Kafin su Omaid su ɗago kai dan ganin me yake faruwa sai ji suka yi ya damko gashin kansu ta bayan wuya haka. Kafin su farga ya jawosu gabansa, yadda kuka san karfe da karfe haka Big Bro ya haɗe kan yaran nan da hannu ɗai ɗai ya dinga buga goshinsu da na juna. Ya ilahi ya lillahi, hankalin kowa ne ya yi mummunar tashin a parlon, harta king sai da ya miƙe daga saman sofarsa, ya san Big Bro zai ɗauki mataki, amma bai yi zaton irin wanna duka ba, wannan ai kashesu kawai zai yi, dama ga jibga da suka ci wanda tin da suka zo duniya ko rabina basu taɓa ci ba. Dafe saitin zuciyarta momma ta yi da karfin gaske, kafin a farga ta sulale saman sofar ta kwanta, take nunfashinta ya ɗauke ɗiff, ya ilahil alamina, baiwar ALLAH bata taɓa shiga musifa irin na yau ba, yadda Big Bro ya gwara kan yaran nan sai ta ji tamkar zuciyarta ya hau caccakawa mashi da karfi-karfi, matsayinta na uwa ba zata iya jura ba, ta zo har wuya da ba zata iya cigaba da jurewa ba. Babu wanda ya lura da momma ta faɗi, saboda dik kallonsu a kan Big Bro, sun ga sabuwar horon azabar da basu taɓa gani ba!. Da karfin gaske Big Bro ya cigaba da kwara kansu har sai da goshinsu dikkansu biyu ya fashe, jini ya wanke masu fuska gabaɗaya, amma dik da haka bai dakata ba, ihu suke yi tsakaninsu da ALLAH, amma bai kyalesu ba. Ƙasa jurewa Smart da Jaish suka yi, da sauri kusan a tare suka nufesa dan dakatar da shi. Da yake guyson yana ta gaban Big Bro ɗin yana kallon fuskarsa, su kuma bayansa suke kallo, sai guyson ya ce. "Yah Omerish kada ku matso". Ya faɗa yana ɗan ja da baya shi ma, saboda ya ga idanun Big Bro sun canza kala wanda suka yi mugun ɗaga mashi hankali. Da yake Smart ya san matsalar sai ya dakata daga wajen tare da rike hannun Jaish. Ai Sareena fitsari ta saki a wado a wajen ganin abin da Big Bro ya yi wa su Omaid, Chuchu ta kankame Yah Jawad gam, saboda ta tsorata over. Aneesa ma dai yau ta yi mugun tsorata, ta kankame Mama gam, Mahreen ta kankame Mahnoor gam, Sweetie ta rike Ronnie, a kunne ta raɗa mashi da su je dakatar da Big Bro. Ƙasa-kasa ya ce mata. "Ba Big Bro bane". Zazzaro mashi idanu ta yi kafin ta ce. "Bashi bane kuma?"....... Kai Ronnie ya jinjina kafin ya ce. "Yanzu ace maki Big Bro zai iya dukana kamar yadda yake dukansu zaki yarda?". Kai ta girgiza alamar a'a. Jinjina kai ya yi. "To kamar yadda in yana cikin hayyacinsa ba zai iya yi mun wannan duka ba haka su ma ba zai dakesu haka ba, yadda yake sona haka yake sonsu, ba shi bane, kuma dik yadda aka yi akwai dalilin da yasa yake yi masu wannan jibga". Shiru Sweetie ta yi kanta ya shiga duhu ne sosai, bata gane komai a zancen Ronnie ba. Sai kawai ta yi shiru tare da kwantar da kanta a saman kirjinsa ta datse idanu dan bata son kallon abin da yake faruwa. Sai da gaban goshinsu Omaid ya fara fitar da wani irin jini bakinkirin tamkar gawayi, sannan Big Bro ya sanya kafarsa ya daki kafarsu ta baya wajen gwiwowinsu, take suka zube gwiwowinsu a kasa, yana rike da gashin kan nasu bai saki ba, ya sunkuyar da kansu kasa wanna bakin jinin ya ringa kwaranya yana tsiyaya. Tsabar tsoratar da kowa ya yi har numfashi a hankali-hankali jamar parlon nan suke yi. Sai da wanna jini kaf ya gaba tsiyaya, sannan ne ya sakesu, yana sakesu suka sulale kasa basa numfashi. A tinanin jama'ar parlon sumar da su ya yi saboda wanna buga masu kai da ya rinƙa yi, sai dai ba haka bane, suma suka yi saboda sun samu lafiya, bakin jini na muguntar da aka saka masu ya gama barin jikinsu, yanzu sun koma ainahin yaran momma ɗinsu. Da gudu guyson ya kariso kansu, a gabansu ya taugunna yana tattaɓa kumatunsu, sun yi mugun bashi tausayi dik da sun ɓata mashi rai, jini ba wasa ba. Da alama guyson ya dawo Omar ɗinsa, domin kuwa ace irin wannan abu ya faru bai yi wa su Omaid kuka ba ai daga nan za ku san cewa Omar ne wannan. Slowly King ya koma saman sofarsa ya zauna yana cigaba da kallonsu, kowa komawa ya yi suka zazzauna cike da tsoro. Tamkar wani zaki haka Big Bro ya juya ya dinfari jikin tsakiyar parlon. Su mama nan kirjinsu ya fara bugawa da karfi-karfi haka. Kai tsaye mama ya nufa, faɗuwar gaba tamkar zai kashe mama, amma bata motsa ba. Yana zuwa ya kai hannu, da karfi ya damko Aneesa dake laɓe a bayan mama ɗin. Ihu ta fara yi tana faɗin Mama ta taimaketa, ita tsoron Big Bro take yi. Sai dai kuma ina, babu wanda ya iya dakatar da shi. In da su Omaid suke ya kawo Aneesa, sannan ya miƙa hannu ya damki gashin kan Sareena, ita ma haɗata da Aneesa ya yi ya hau buga kansu yadda ya yi wa Omaid da Obaid. Ai wani irin razana guyson ya yi ya miƙe tsaye yana kallon yayan nasa. A tsora ce mama ta kalli king da yake zaune hankalinsa a ɗan kwance ta ce. "Ka dakatar da ɗanka kada ya kashe mun yarinya, ban shiga harkarsa ba kada ya shiga tawa". Juyo da kallonsu a kanta su mummyn Chuchu suka yi, har lokacin basu lura momma ta suma ba, saboda tashin hankalin da suke ciki. Hannu King ya ɗaga mata alamar ta yi mashi shiru, zuciyarta ne ya kara harzuƙa, abinku da uwa da ƴa, da sauri ta miƙe da nufin ta je ta kwaci Aneesa dake ta faman ihu tamkar ranta zai fita, a cewar mama ɗin sai da ya kasheta ita, amma sai ta karɓi ƴarta. Zata wuce Smart ya daƙa mata tsawa a kan ta koma ta zauna kafin ya yi ball da ita, saboda tsoro da shakkarsa yasa ta koma ta zauna tana ruwan hawaye. Aneesa da Sareena suma sai da wannan bakin jini ya zuba daga kansu sannan ya sakesu, suka sulale kasa basa numfashi suma. Tsuru-tsuru jami'ar parlo suka yi da ido suna jiran su ga saura su waye kuma next za'a capko. Sai dai yanzu lamarin ya sha banban, dan kuwa unexpected suka ga Big Bro a gaban guyson dake tsaye yana kallon abin dake faruwa cike da mamaki. Wani irin razana guyson ya yi har ya ja baya, amma ganin Big Bro ne yasa ya sauke ajiyar zuciya dan shi yasan yayan nasa ba zai taɓa cutar da shi ba tin da bai aikata wani laifi ba. Ware dogayen yatsunsa Big Bro ya yi tamkar za su gaisa da guyson haka, a tsakiyar cikin guyson ɗin ya caka mashi waɗan nan yatsun nasa da karfi, take guyson ya durƙushe kasa a wajen ya fara kwaranyo wani bakin amai, bakinkirin sosai, tamkar laida, ga wani gashi-gashi a cikin aman nasa. Hannu Big Bro ya sake dunkulewa ya daki guyson a bayan wuya, take ya sake yin kasa da kai yana cigaba da kwarara aman nan. A daidai wannan lokacin daga bayansu suka ji wani irin kakkausar murya tamkar muryar kato ance. "Kai karamar halitta! Ka tabka babban kuskure na dukan ɗiyarmu da ka yi". Ai a miliyan gabaɗaya parlo suka kai kallonsu kan mammie da ta miƙe tsaye tana zazzaro ido, idanunta sun zama dark purple gwanin ban tsoro, ga wasu hakwara biyu tamkar na damusa da suka bayyana a bakinta ta sama, ta zama suffar horuwa kawai a taƙaici. Slowly Big Bro ya juyo da kallonsa a kanta, ɗan karkata kansa ya yi yana kallonta. Take ya ɗan mummuɗa wuyarsa yadda aljanu suke yi idan zasu yi rashin mutumci kenan, haka shi ma ya yi, yau faɗar irin na second mother ɗinsa Elevender za'ayi kenan, matar nan ta koyawa Big Bro aljananci ta mutu ta barmu da aiki. Haba dik waɗan da suke kusa da Mammie ne suka watse da gudu daga kusa da ita, sun tsorata sosai, su Smart ai a miliyan suka juyo da kallonsu a kanta. Uncle Abbas ma dai matsawa ya yi daga kusa da Mammie. Family sun shiga gagarumin ruɗani na wannan abin da ya faru, King kansa ya shiga ruɗani, abin ya kulle masu kai sosai. Mammie kuma dukan Sareen da Big Bro yake yi ne yasa ta motsa tsafin nata, dan ta hukuntasa, a haka ba tsafi tana tsoron tinkararsa. A hankali idanun guyson suka fara rufewa a lokacin da ya gama kwaranyo wanna aman, sulalewa kasa ya yi, shi ma ya sume a wajen. Da gudu Jaish ya yi kansa, Big Bro bai dakatar da shi ba sai ya bashi hanya ma. Da sauri shi ma Smart ya yi kan guyson ɗin dan duba lafiyarsa. Ita kuwa Mammie tamkar wata zakanya haka ta nufo Big Bro da nufin su kara, yana tsaye yana mamakin ne ma yadda aka yi ita mace take magic, dan shi fa dik balainsa yasan ba zai taɓa bawa mace magic ba, shiyasa kuka ji ranar ya zagi babansu Sweetie, dan yasan me illar hakan!. Aka ce rashin sani ya fi dare duhu, Mammie na zuwa tasa hannu wai zata shaki wuyarsa. Ihu Sweetie ta zunduma tare da datse idanunta gam ta kara kankame Ronnie, ta ji tsoron za'a shake mata king of heart ɗinta. Mammie na kai hannunta jikin fatan wuyansa hannun nata ya kone tamkar wacce aka zubawa acid, lamarin da ya kara tada hankalin family, king ya yi gigicewar da bai taɓa yi ba, yadda kuka san an zubawa Mammie acid haka hannayenta suka zama, har sama wajen shoulders ɗinta, harta naman jikinta sai da ya dahu, ya yi jajir da shi tamkar an ɗaye fatar waje, ga wani irin hayaki mai kama da tiriri da yake tashi a jikin hannun nata. Wani irin azababben ihu ta kurma wanda ya doɗe kunnuwan gabaɗaya jama'ar parlon, a nan take Mahnoor ta sume a wajen saboda razana, Chuchu ma dai ta fita a hayyacinta, sai wani irin azababben kerma da jikinta yake yi, ta kankame Jawad gam ta cusa kanta cikin kirjinsa, idanunta a datse gam bata ma ganin me yake faruwa. Uncle Abbas da Uncle Jahiz dik kallonsu a kan King alamar karin bayani suke nema, basu san shi kansa King ɗin yanzu karin bayani yake nema ba, dan bai taɓa tinanin lamarin ɗan nasa ya yi tsamari haka ba. Bai san ɗansa magajin kujerun mulki har guda biyar bane, ciki har da sarautar aljanu, yo me ba zai gani ba kuma? Ai su da Big Bro a Kingdom ɗin nan sai ta ALLAH kuma, masu karamar ƙwaƙwalwa hauka zasu yi wlh. Baya-baya Mammie ta fara ja tana ihun azaba. Takowa Big Bro ya fara yi yana nufar in da take, baya ta cigaba da yi har suka kurewa wall dake wajen, juye-juye ta fara yi tana neman hanyar sake gudawa, sai dai ina babu. Hannu Big Bro yasa ya damko gashin kanta dake cikin veil da ta yi rolling kanta, da karfi ya jijjigata kafin ya jefota tsakiyar parlon. Take su mama suka sake ja baya daga kusa da ita. A gabanta ya zo ya tsugunna yana kallon face ɗinta, ta yi ƙasa da kai sai wani irin wahalallen kukan azaba take saki. "Who are you?". Shi ne abin da Big Bro ya faɗa cikin natsuwa da sanyin murya wanda tin shigowarsa parlon bai yi magana ba. Big Bro ba'a yi mashi musu a magana ko a faɗa mashi karya idan abubuwan nasa sun motsa, ko kaki ko kaso in ya tambayeka sai ka bashi amsa, saboda daidai yake da kai, dik wani hau dake kanka nashi ya dame naka ya shanye, shi kansa bai san adadin abubuwan dake kansa ba, dan haka dole Mammie ta buɗi baki ta hau jawabin wacece ita da dik abin da ta aikata, sai a wanna lokaci suka iya tina Fanan da ta buɗe baki ta faɗa masu cewa ta baiwa Zarina ita. Ta fara faɗin dik irin tuggun da ta shiryawa Rizwan and Jawad dan kashesu, ta faɗi cewa ai mamarsu ma ba mutuwa ta yi ba, Zarina ta baiwa ita suka yi bakin tsafi, da ta baiwa Zarina maman su Jawad shi ne Zarina ta bata tsafi, da tsafin ta yi amfa wajen mallakar Uncle Abbas ta shigo gidan, hasali ita ta zo gidan ne bisa umarnin Zarina na cewa zata taimaka mata ta mallaki masarautar, dik wani tuggu da ta haɗa sai da ta warware masu tsaf. Daga karshe ta ce ita ta kwantar da Akka jinya, ita ce sanadi saboda Akka ta matsa ta tsananta tsaro a kan Spender, ta hanasu su mallake shi, shi ne nan suka haɗata da bakaken ruhanai suka kayar da ita jinya, shiyasa yanzu sai an ɗaga sai an kwantar. Wannan magana nata ya yi mugun ɗaga hankalin waɗan nan ahalali, take suka fara yi mata tofin alatsine. Jawad kam dai dafe kansa ya yi yana jin zuciyarsa tana yi mashi zogi, ashe bada mamarsu wannan azzaluma ta yi aka bata tsafi?. Ya ilahi ya lillahi. Rizwan kasa ya yi da kai yana wani irin huci mai ban tausayi da tsayawa a rai, dan in baku kanta ba shi ai ɗan ɗakin Mammie ɗin ne, kun manta tana nuna tana son shi sosai? Kuma shi ya riketa matsayin uwa da gaske, so hakan ya taɓa mashi zuciya, bai taɓa danasani kan wani abu ba sai a kan wannan mata, ya yi danasanin ɗaukarta matsayin uwa. Bayan ta kammala bada jawabinta kaff, shiru Big Bro ya ɗan yi for some second kafin ya ɗan juya eyesball ɗinsa. Yawun bakinsa ya tofa mata a fuska, take fuskarta ta fara konewa tamkar ya zuba mata acid. Ihun azaba ta shiga yi tamkar makoshinta zai fashe. Cikin azaba da fitar hayyaci tasa hannunta da ya ƙone over a kan fuskar tata da nufin ta ɗan kare ko zafin zai ragun mata, sai dai tana sanya hannunta wani irin fata ta fara kwayowa wanda ya gama dahuwa tamkar an ɗaura a wuta. Nan ma wani irin zababben ihu ta kara saki mai doɗe kunne wanda ya sanya numfashin Chuchu ɗaukewa ɗiff ta sumewa Jawad a jiki. Yanke jiki uncle Abbas ya yi ya faɗi a wajen sumamme, da gudu su Dr Raj suka yi kansa. Miƙewa Rizwan ya yi da sauri ya fice daga parlon dan zuciyarsa gab yake da yin bindiga. Jawad dai ya gagara motsawa, tamkar an sassaƙasa a wajen. Cigaba mammie ta yi da ƙoƙarin sosa azaban da take ji a kan fuskarta ko zata samu sassauci, tana kara kwaye namarta dake wajen. Sam babu alamar tausayi dede da kwayar zarra a kan fuskar Big Bro, hankalinsa a kwance ma ya dawo da kallonsa a kan King. "Daddy bana san sake ganinta a nan kuma". Ya faɗa tare da miƙewa daga kusa da ita. Ya juyo da nufin ya yi wa Momma magana sai gani ya yi ta sume, ɗan zaro idanunsa waje ya yi har sai da yasa hantar jama'ar parlon kaɗawa, da sauri ya nufi in da momma take, suma kaf kai kallonsu kanta suka yi, cikin zafa King ya riga Big Bro karisawa in da momma take. "Ku bani ruwa". Shi ne abin da King ya faɗa. Dikka family kan momma suka yi har su Jaish dake kan guyson yanzu sun koma kan momma. Ita kuwa Mammie sai kururuwar azaba take saki amma babu wanda ya bi ta kanta. Wannan azaba da Big Bro ya yi mata ba karamar azaba bace, ya dafar mata da namar jikinta, ga shi bata mutu ba, haka zata yi ta fama da wannan azaba, babu maganin da zai iya warkar mata da wannan konewa, a haka zata yi ta fama har rai ya yi halinsa, daga nan ko shekara goma zata kara kullun ciwon zai kasance sabo ne, namarta ya yi ta fitar da farin ruwan azaba mai yauki da wari, fuska da hannunta dik zasu yi ta tsutsa ne, haka illar yawunsa take idan ya juya black heart ɗinsa ya tofa maka, ita dai tata ta kare, kuma ta samu karshe mai bakar azaba da wahala, ta cuci kanta a banza!. IZINA CE A GAREMU, DIK WANI AZZALUMI KARSHENSA BATA KYAU, TO ME AMFANIN MA KA ZAMA AZZALUMI KANA CUTAN ƳAN UWANKA FISABILILLAHI? WAI KO KA MANTA DUNIYA TAMKAR CIN KASUWA MUKA ZO YI NE ZAMU KOMA GIDA NA GASKIYA GIDAN SAKAMAKO?. Wani irin dogon numfashi momma ta ja tare da saukewa a hankali, sannan ta waro idanunta da har ɗan kunbura suka yi waje. A natse ta miƙe zaune tana ta faman sauke ajiyar zuciya. Sannu suka hau yi mata kowannensu cike da damuwa a kan fuskarsa. Jinjina kai kawai momma ta yi ta gagara yin magana. Miƙewa Big Bro ya yi ya ɗauketa cak suka bar parlon, dan baya son ta ga abin da ta faru da Mammie bare hankalinta ya kara tashi. Warriors King ya kira suka fita da Mammie, ya ce su sanyata cikin kejin da suke sanya kananan masu laifi kafin a san irin hukuncin da za'ayi mata. Sannan yasa su Dr Raj suka ɗauki guyson da su twins dik suka kwantar da su a saman sofa, Dr Raj ya hau yi mashi treating forehead ɗinsu da ya farfashe. Mummyn Chucha and King ne suka rufawa Big Bro da momma baya, mama ta tsaya wajen Aneesa tana ta hawaye. Ronnie ya matso dan tasa Dr Raj aiki tin da dik aikinsu iri ɗaya. Sweetie kuwa da kyar ta iya miƙewa ta bi bayansu King, Smart da Jaish sai da suka tabbatar da guyson and twins sun samu kulawa hannun su Ronnie sannan suka bi bayan momma. Zaune suka iskosu a parlo Big Bro yana zaune a gefenta, ya riko hannunta cikin nasa yana ƙoƙarin tausarta. A gefenta suka zazzauna suma, King da Mummyn Chuchu suna zaune saman sofa guda suna kara tausan momma. Gagara hakura momma ɗin ta yi har sai da ta ce. "Meyasa ka yi wa ƴan uwanka irin wannan duka haka?". Ta faɗa tana kallon yatsun Big Bro ɗin yadda yake ɗan murza nata a hankali. Shiru ya ɗan yi for almost 2 mins kafin ya ce. "Ba dukansu na yi ba, bama su na daka ba, shaiɗanin dake jikinsu na daka, shi na fitar masu". Ai momma bata san lokacin da ta sauke wani irin musulmin ajiyar zuciya ba. Daidai lokacin Dr Raj ya shigo hannunsa rike da wayar king. "Daddy kira yafi kona ajere-ajere yake ta faman shigowa". Dr ya faɗa. Karɓar wayar King ya yi tare da duba call ɗin, da sauri ya miƙe tsaye yana ƙoƙarin bin number ya kira tare da nufar waje yana ce masu yana zuwa. Kira ne da Anti-Ballistic Missile Systems office ɗinsu na kasar. Wannan kira alamar babu lafiya ne, shiyasa ya fita waje. Mummyn Chuchu macece mai fahimta sosai, ta fahimci tamkar momma tana son ganawa da ƴaƴanta kawai, dan haka sai ta miƙe tana faɗin. "Ina zuwa bari in duba jikin su Omar". Da to momma ta amsa mata, waje ta nufa da sauri. Tana fita momma ta riko hannun Big Bro, idanunta a cike tab da kwallah ta ce. "Wai menayiwa mutane ne? Mena tare masu da basu son barina in zauna lafiya? Meyasa ƴaƴana ne kawai ake azabtarwa a cikin gidan nan? Kowani ciki na samu sai na sha azaba kafin ya zo duniya, ayi ta tsoratani ba'a son in haihu, idan ya zo duniya ba za'a barshi ba, na haifeku ku biyu, an rabaku tin ban san me na haifa ba, an ɗaukeka daga gareni, ban sani ba haka yasa na maida hankali kan renon Omerish, shi ma aka sakoshi a gaba, har aman jini jariri da shi yake yi, muggan mafarkai a kansa ta yi mun yawan da ba zan iya jurewa ba, yaron nan yana jariri sai in ga nunfashinsa ta ɗauke na ƴan mintuna sai kuma in ga ya dawo daidai, wani lokaci ya yi ta fafutuka yana bubbuga kafafunsa da hannunsa alamar an shake mashi wuya baya samun nunfashi, sai na rungume shi a jikina in yi tai mashi addu'oi, naga abin ba mai karewa bane, na shirya shirin cewa ya mutu, na kaurar da shi daga gidan nan. Haka na sha kukan rabuwa da ɗana na farko a duniya dik dan ya rayu, na zo na sake haifan wani yaron shi ma kun ji ya daddynku ya yi da shi, baya ga haka, na haifi Jaish, shi a Dubai na haifesa shiyasa abin yai mun sauki, Omar tin yana karami yake fama da ciwon cikin da bamu iya sanin na menene bane, mahaifiyata ta sha fama kansa, tamkar ba zai rayu ba. Haka dai ALLAH ya raya mun shi, Omaid da Obaid dama tin da suka taso a mugayen nan marasa jin magana da kiriniya nasan ba lafiya suke ba, na rinƙa yi masu addu'a wanda ina da tabbacin shi ne ma yasa abin nasu ya yi sauki, har Zunaira ba'a bari ba, an kasheta an jefar da gawarta a cikin ruwa, amma ALLAH yasa tana da rabon rayuwa, ta tashi, bansan meyasa ku kawai aka sakawa ido ba, wai menayi ne?". Ta kai karshen maganar da kyar hawaye sun gama wanke mata fuska. Da sauri su Smart har suna rige-rigen goge mata hawaye. Cikin sanyin murya Big Bro ya ce. "Komai ya kare, babu wanda zai sake taɓa mun ƴan uwa na barsa, su Omar dik yanzu zasu samu lafiya, sannan zan gano koma wanene ya saka mun ƴan uwa a gaba, zan yi mashi hukuncin da sai kun gamsu ya biya azabar da yasakaki a ciki, but ki mun alkawari ɗaya". Ya dakata yana kallonta. "Tin ban ji me kake so ba na yi maka". Ta faɗa yana riko hannun Smart da ɗayan hannunta. "Ki mun alkawarin ba zaki sake kuka ba kuma kome kike so zaki tinkareni kai tsaye ba ki ce kina tsorona ba". In a cool way sosai ya faɗi maganar. Da sauri ta jinjina mashi kai alamar ta yi alkawarin hakan. Shiru wajen ya ɗan yi na ƴan mintoci kowa da abin da yake tinani, can ta katse masu shirun da cewa. "Menene sunanka? Tin da kazo nike son tambaya amma na kasa". Ajiyar zuciya su Smart suka sauke saboda an taɓo in da yake yi masu kaikayi. Silent for almost 2 mins Big Bro ya yi kafin a natse ya kalleta sannan ya ce. "Tin da na tashi sunana Tiger, ban san wani suna ba, amma ki sakamun da kanki zan so hakan".......... Tabbas yana da suna, amma in baku manta ba da Duniyar Shaiɗanu suka sake shi ai komai da ya dangancesu ya shafe daga kansa, ya mance komai nasu, ciki har da sunan da suka saka mashi. Shiru momma ta ɗan yi, yana son tambayarsa waye ya renesa, amma tana shakka, dan haka sai ta ce. "Na baka suna Unays daga yau"........ Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ɗan jinjina kai yana maimaita sunan, shi kansa sunan ta yi mashi masifar daɗi, UNAYS WOW. Dawo da kallonta a kan Smart ta yi. "Ina ƴata?"....... Ɗan zaburs Smart yai tare da mikewa da sauri. Da kallo momma ta bisa, dama ta tambayesa ne dan ta tabbatar da zarginta, kuma ta tabbatar, dan haka sai ta ce. "Koma ka zauna bari in dubata". Wannan magana da tai yasa Jaish da Big Bro suka fahimci karatu. Miƙewa momma tai ta nufi waje tana faɗin. "Unays ka jirani bari in dawo ina da magana da kai". Ta faɗa mashi hakan ne dan bata son ya tilasta Sweetie ya ɗauketa su tafi, so take tai magana da shi kan wannan issue. Tana fita Big Bro ya dallawa Smart harara kafin ya ce. "Zo nan bari in bincikeka"......... Smart ya gane nufinsa sai ya ce. "A'a fa, yanzu ba ɗaya muke ba, ka bini a han........". Bai karisar da maganar ba sakamakon capka da Big Bro ya kai mashi a gashin kai, ya jawosa jikinsa yana faɗin. "Bari in fara tantancewa tukun nan". Jaish sarkin kunya da ya gane in da suka dosa sai ya miƙe sumui-sumui ya gudu waje abinsa, sun bashi kunya. Cike da zolaya Smart ya ce. "Za fa ka je ka tada abin da kasan kai ba samu zaka yi ba, sai dai ka rungumi pillow ka rungumi sorry, dan haka kada ka tono wanna lamari". Yana magana yana kara rike wandansa dan kada Big Bro yai mashi tsirara dik da yasan da wuya ya yi hakan, kawai dai tsantsar so da kauna dake tsakaninsu ne yasa Big Bro yake ɗan sakewa da shi har yana jansa da wasa. Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only please. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 Sumbata ya mannawa Smart a goshi, can kasan makoshinsa ya ce. "Ka yi babban laifi yau, kuma ba zamu yafe ba, amma ina fatan ka sama mana babys a wannan first karon kafin Maysh ta bamu nata"....... Kun san mutumin da son yara. Da sauri Smart ya ɗago da kallonsa a kansa kafin ya ce. "Waye ya faɗa maka abin da na yi? Ni fa ta bakin momma kana bani tsoro guy ɗin nan".......... Shafa fuskar Smart ya yi da tafin hannunsa, a natse ya ce. "I'm the successors to BLUE KINGDOM, then King of ICE KINGDOM, so ka daina mamakina". Yana magana yana shafa gashin kan Smart cike da tsantsar fresh kauna. Ɗan zazzare mashi idanu Smart ya yi. "Apart from Black World palace akwai Blue Kingdom and Ice Kingdom ne?". Sai da ya ja dogon hancin Smart ɗin kafin ya jinjina mashi kai alamar e. "To amma how comes? And a ina su kuma suke? Ni fa ka sake kulle mun kai, ka rikitani". Ya faɗa tare da miƙewa zaune ya bar jikin Big Bro ɗin. Kai Big Bro ya ɗan ɗaga sama tamkar mai tinanin wani abin, ba komai yake tinani ba face yana kallon hanyar Blue Kingdom, dan ita dai a sama take ba'a duniyar mutane ba, kada ku manta sune masarautarsu second mom ɗinsa watau Eleveder. Hmmm dik yaran momma kusan suna da second mom, Smart ma yana da ita matar daddynsa na Paris, Omaid and Obaid suna da ita suma, kuma ita ce nan take sanya masu kiriniya. Guyson Auta dik suna da ita. "Ba zaka gane ba ko na faɗa maka, so bar zancen". Big Bro ne ya bashi amsa da haka. Shiru Smart ya yi yana mamakin ɗan uwan nasa. Baki a ɗauke da sallama Sweetie ta shigo parlon tana sanye da hijabin Auta a jikinta, daga bedroom ɗinsu ta fito, ta gama shiri cikin sleeping dress ɗinta ne ta ce bari ta duba momma dan tasan wani matsaya momma ta bata a yanzu, me zata yi. Ganin su a zaune a parlon ne yasa ta kariso wajen, a saman sofa ta zauna tana faɗin. "Yah Omerish barka da dare"....... Kallo ɗaya yai mata ya ɗauke kai yana amsawa da yauwa. A maimakon ta ɗagawa Big Bro ma gaisuwa sai ta ce. "Yah Omerish ina Pretty? Tin ɗazun ban ganta ba, na yi knocking ɗakinku babu kowa dan ba'a buɗe mun ba"....... Tin da ta fara magana kirjin Smart ya fara bugawa da karfi-karfi har ta kai karshe. Ajiyar zuciya ya sauke, da kyar ya iya ce mata. "Tana barci ne, bata jin daɗi"............ Zazzaro mashi idanu tai. "Meyake damunta?". Tamkar zata yi kuka tai tambayar. "Zazzaɓi ne kawai, kada ki damu, ta ji sauki ma har ta samu barci". Ya faɗa yana satar kallon Big Bro da ya kafeta da ido tamkar zai cinyeta da kallo. Jinkina kai tai. "ALLAH ya bata lafiya". Kanta a ƙasa ta faɗa, amma tana satar kallon king of heart ɗin nata. Da Amin Smart ya amsa. Shiru parlon ya yi Smart yana jiran ya ji ta ɗagawa Big Bro gaisuwa, amma sai ya ga akasin haka, gagara hakura yai har sai da ya ce. "Sister meyake faruwa ne tsakaninki da ɗan uwana?"..... Da sauri ta ware idanunta a kansa alamar bata gane kan tambayar ba........ Ya gane nufinta dan haka sai ya ce. "Naga baki yi mashi magana ba tin da kika shigo". Wani musulmin ajiyar zuciya ta sauke kafin ta saci kallonsa, a sanyayye ta ce. "Babu komai Yah Omerish"....... "Ban yarda ba, ai baki taɓa samunmu a waje ki gaidani baki kula shi ba, menene yake going?"........ Ɗan turo baki tai. "Kai Yah Omerish, ni fa babu komai, kawai dai na daina yi mashi irin wannan gaisuwa da nike yi wa kowa ne, nasa special ne, kuma ina jin kunyarka ne yasa ban yi mashi ba". Ai a fili Big Bro ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, burin zuciyarsa kawai ya ji wani irin gaisuwa ta tanada mashi yanzu wanda ba irin na kowa ba. Shi kansa Smart ajiyar zuciyar ya sauke, da ya ji tsoron ace wani abin ne ya shiga tsakaninsu, to tin da ba komai ai shikenan. "Yah Omerish Ina momma?".... "Momma tana zuwa ki jirata a nan". Ya bata amsa yana gyarawa ya kwanta, ya tada kai da laps na Big Bro. Kurawa juna ido suka yi ita da Big Bro, slowly ya motsa ɗan bakinsa wajen cewa. "Wanna abin da kika sanya yai maki kyau sosai (Hijab)". Murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. "Nagode"........ "I missed more maysh". Ya faɗa ta hanyar motsa lips ɗinsa kawai ba tare da wani sauti ya fita ba bare Smart ya jisa....... Ɗan miƙewa ta yi ta miƙo mashi wayansa dake hannunta wanda ya jefeta da shi ɗazun da zai fara dukan su Omaid. Hannu ya miƙa ya karɓi wayar tare da ɗan shafa hannunta yana ɗan lumshe idanu. Komawa ta yi ta zauna tana kallonsa. Dik abin da suke yi Smart yana kallonsu, sai dai ya fi mayar da hankalinsa kan tinanin ya yar tsanarsa take a yanzu? Wani irin rauni ya ji mata? Ya damu sosai. Vibrate wayarta ta ɗan yi alamar shigowar sako, sai da ta saci kallonsa kafin ta kunna wutar screen light ɗin, dan tasan shi kaɗai zai turo mata sako. Tana buɗewa sai ga cool smiling ya bayyana a kan face ɗinta sosai. "Wanna kaya da kike sakawa suna da kyau, amma in zaki fita ne kawai suke maki kyau ɗin, yanzu sun takura mun ki ciresu"...... Shi ne abin da ya rubuta mata a sakon. Satar kallonsa ta sake yi kafin ta rubuta mashi amsa. "Dik yadda kake so in kasance fin haka zan yi a gidan aurenmu, a ɗakinka na aurenmu na sunnah sai yadda kakeso za'ayi"................ Sosai ya ji daɗin kalamanta, sai ya rubuta mata reply da. "I wish mu yi aure da wuri".......... "Why?". Ta tura mashi. "Because i love you, and bana son ratar da kike bani"......... Sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke a fili kafin ta ce. "Ni kaina bani son yin nisa da kai, kawai juriya ce nike yi, I love you too King of my Heart". Yana kokarin rubuta mata reply sai ji ya yi Smart ya kwace wayar yana faɗin. "Ya tabbata ku masoyan asali ne, watau gaka ga ta ma sai kun yi chat ko? To bari in ga me kuke cewa". Daidai lokacin ta turo mashi sakon. "Naga lips ɗinka sun bushe, kana jin yunwa ko?". Karance sakon Smart ya yi kafin ya ɗago ya kalli Big Bro, harara ya dalla mashi, da sauri Smart ya mai da kallonsa kan Sweetie, ƙasa da kai ta yi tana ƴan kame-kame. Kwace wayarsa Big Bro ya yi, a natse ya yi mata typing amsa da. "Yeah yunwa nike ji"........ Sake baki Smart ya yi yana kallonsu, dan sun goge mashi jadda ne. "Eyya sorry bari yanzu zan kawo maka abinci ka ji?". Ta tura mashi tana ɗan shagwaɓe fuska. A natse ta yunkura zata miƙe kenan sakonsa ya sake shigo wayar, tsayawa tai dan ta duba. "Babu wani abin da zai kawar da wannan yunwa da nike ji face ke, ke kaɗai ce abincin da zan iya...........in ƙoshi, babu buƙatar wani nau'in abinci".......... Ai sai da ta ji gabanta ya buga da karfi jin wanna kalaman nasa, da sauri ta ɗago da kallonta a kansa. Binta yake yi da wani irin mayen kallo, idanunsa suna ɗan lumshe tamkar mai jin barci, sun rage girma sun kuma ɗan sauya launi. A daidai wannan lokaci momma ta shigo bakinta a ɗauke da sallama, da sauri Smart ya miƙe tsaye yana son tambayarta, amma baya san Sweetie ta ji. Kallon Sweetie ɗin momma ta yi kafin ta ce. "Omaish je ki kai maku abinci ɗaki ki zo zan yi magana dake". Sannan ta dawo da kallonta a kan Big Bro, kallo ɗaya tai mashi ta ɗan kawar da kanta izuwa kan Smart da ya tsareta da ido. Miƙewa Sweetie ta yi ta nufi waje, abinci ta je ta ɗauka ta kai masu ɗaki, sai ta zauna a saman sofa, a ranta ta ce bari ta basu 30 ko 1h dan ta lura momma tana son yin magana da ƴaƴan nata ne. YARINYA MAI HANKALI. A saman sofa dake fuskantarsu momma ta zauna. Slowly Smart ya koma ya zauna shi ma yana kallonta. "Momma ya jikin Pretty ɗin?". Smart ne ya tambaya cike da matsuwar son jin amsa....... Kai momma ta ɗan girgiza kafin ta ce. "Ajiye wanna tambaya a gefe, dan in nace da sauki ma nai karya, amma musulmi ba zai gaji da cewa Alhamdulillah ba, dan godiya ga ALLAH wajibi ne a kan musulmi, yanzu ba wanna ba Unays magana nike son mu yi ka ji?". Tin da ta fara magana gabaɗaya Smart ya rasa farincikinsa, jikinsa ya yi mugun sanyi, shiru ya ɗan yi yana tinanin gaskiya sun Omaid sun cuceshi sosai wlh, addu'a ya fara yi mata ALLAH ya bata lafiya. Ɗago rinannun idanunsa Big Bro ya yi ya sauke kallonsa a kan momma alamar yana jinta kenan, bai dai yi magana ba. Cikin hikima da basira irin tata ta ce. "So nike in san waye kai ko da a taƙaice ne, sannan ina yin maka maganar da nike son mu yi"........... Dawo da kallonsa a kan Big Bro Smart ya yi shi ma yana jiran bayanai. Shiru Big Bro ya yi na ƴan mintuna da basu gaza biyu ba kafin ya ce. "I am the Crown Prince of four mighty empires, King of three sovereign kingdoms, the heir to four immortal thrones. I wield the most powerful golden seat and the sacred scepter no soul has ever held before". (Ya cire Duniyar Shaiɗanu a wannan lissafin nasa, bai sakasu ba, amma shi magajin masarautu biyar ne ba huɗu ba, sannan shi sarki masarautu huɗu ne ba uku ba, baya sanya Crown of Power a cikin masarautun da zai mulka, dan a cewarsa ga Smart nan, ya bar mashi wannan, shiyasa yake cewa sarkin masarautu huɗu ba biyar ba, amma magajin masarautu biyar ne.) Ya ɗan yi shiru yana kallon yadda momma ta zaro idanu tana mamakin jin kalamansa, like wow, ɗan baiwar da za'a jima ba'a samu irinsa ba in ma za'a samu kenan, shi sarki ne har aljanu yake mulka, sai dai kai Big Bro fakacity. "I don't know what to say about my lif, kawai dai ki ɗaukeni a yadda kika ganki". Ya sake faɗe a natse. Shiru momma ta ɗan yi tana jinjina wannan al'amari game da tunanin yadda zatai mashi maganar addini, tana son su zo wanna babi, dan shi ya fi komai tsaya mata a rai. Da kyar ta haɗo wasu ƴan dabaru dan jansa da hira ta ce mashi. "Meyasa ka tara gashi haka? Sannan meyasa kake mashi irin haka?". Ga mamakinta sai ta ji ya ce. "I'm a Christian, mabiyi Yesu, and mai koyi da shi, haka yake barin gashinsa shiyasa na bar nawa, don't stress your self momma, na ce komai kike so ki tambayeni kai tsaye ban da kwana-kwana". Sai da kirjinta ya yi wani irin bugawa da karfin gaske jin abin da ya faɗa, kuma ta ɗan tsorata na jin ya bata amsar abin da yake ranta ba tare da ta fitar da zancen fili ba. Zaro mashi idanu Smart ya yi kafin ya ce. "To taya kuka zama ma'aurata da sister? Ita ai musulma ce, ko bata san babu au...........". Da sauri momma ta ɗagawa Smart hannu, saboda ita tasan in suka kuskura suka ce mashi babu aure a tsakaninsa da Sweetie fa za'a samu babban matsala ne, dole a hankali zasu bishi. "Masha ALLAH, naji daɗin kasancewarka mai koyi da annabi Isa, wanna abin farinciki ne, amma zan so ka yi koyi dashi gabaɗaya fa". Cewar momma da da kyar ta tattaro waɗan nan kalamai saboda bugawa da kirjinta yake yi, hankalinta ya kara tashi. "Ban gane ba". Ya faɗa yana gyara zamansa, ya tattara mata nasuwarsa gabaɗaya. Sosai momma ta ji daɗin yadda ya nemi karin bayani, dan haka sai ta ce. "Kasan da cewa Yesu musulmi ne? Kasan cewa ALLAH yake bautawa?". Kai ya girgiza mata alamar a'a bai sani ba. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Yesu musulmi ne kuma addinin Musulunci ya yi wa hidima, sannan har ALLAH ya ɗaukesa zuwa sama ALLAH yake bautawa ba wani ba, idan har da gaske Kiristoci suna koyi da shi kuma suna sonsa meyasa ba zasu zama musulmai su bautawa abin da yake bautawa ba?". Ta jefesa da tambayar tana kallonsa a ba kai tsaye ba. Shiru ya ɗan yi, can kuma sai ya ce. "Yesu da kansa shi ne abin bauta ai momma"........... Smart dai ɗan kallo ya zama, dan ji yake yi ma tamkar kunnuwansa basa ji mashi abin da suke faɗe daidai ne, yana jin kamar ana formating brain ɗinsa ne dik bayan minti ɗaya. Nisawa momma ta yi kafin ta ɗaura da cewa. "Ba ALLAH bane kuma ba ɗan ALLAH bane kamar yadda suke faɗe, shi ɗin bawan ALLAH"........... Kai ya girgizawa momma. "No momma, shi ɗan ALLAH ne, in ba haka ba ina daddynsa?". Wannan tambaya nasa yasa momma faɗuwar gaba, yanzu ta gama gane Big Bro ya yi nisa, shiru ta yi ta rasa amsar da zata bashi. Daga bakin door muryar Sweetie ya daki dodan kunnensu da cewa. "Ba Yesu ne kawai UBANGIJI ya taɓa halitta babu uba ba ai, Annabi Adam, Nana Hauwa dik ALLAH ya yi su babu iyaye, ai idan mamaki zaka yi da rikar hujja to a kan halittar Annabi Adam zaka yi mamaki, saboda shi ne bashi da uwa kuma bashi da uba, then Nana Hauwa daga jinin Annabi Adam aka halicceta, kaga kenan bata da uwa, so bai kamata ku rike wannan hujja na cewa Annabi Isa bashi da uba ku ce hakan ne zai baku tabbacin ɗan ALLAH bane. Cikin suratul Iklas aya ta uku da ta huɗu ALLAH lamyalid wa lamyulat yake, bai haihu ba kuma ba'a haifesa ba, walamyakulla hukufuwan ahad, kuma wani bai zama tamka a garesa ba, ALLAH baya haihuwa, sai dai ya yi halitta, nakaso ne ka ce ALLAH yana da ɗa, dan haka baku da hujja a wannan ɓangare na cewa ɗan ALLAH ne shi, ku nemi wani dalili ba dai wannan ba!". With her full confidence tai maganar, kun san ita bata shakkarsa tamkar yadda su Momma suke yi, ta saba da kayanta. Daga momma har Smart waro idanu waje suka yi suna kallonta. Wlh da wani ne ya mayar mashi da martani irin haka da bakinsa bai sake yin magana ba a duniya, amma saboda ita ne sai ya kawar da kallonsa daga kanta yana ɗan lumshe idanunsa. A natse ya ce. "Maysh Yesu shi ne ALLAH that's all, in baku yarda dani ba dama ban tilastaku shiga addinina ba, kowa ya yi nasa (watau lakun dinikun waliyaddin, addininku na gareku addinina yana gareni kenan)". Da iya gaskiyarsa ya yi maganar. Rungume hannayenta a saman kirjinta ta yi kafin ta ce. "King of my heart, Yesu bashi ba ne ALLAH, kuma ba zamu taɓa barinƙa ba sai mun baka gamsuwa da hakan shi ne aikin da muka zo yi a duniya dama, yanzu ina da tambaya, idan ka amsa mun tabbas zan yarda Yesu ALLAH ne, kuma zan bi addininka". Ta faɗa tana binsa da wani irin kallo dake kara narkar da zuciyarsa, cikin ranta tsoro kamar zai kasheta, sai addu'a take yi ALLAH yasa kada black heart ɗin nasa ta motsa, kun tuna lokacin da tai mashi maganar addini abubuwan tasa suka motsa ko? To shi take tsoro. Gera ya ɗan ɗaga mata alamar yana jiran tambayar tata amma bai yi magana ba. Gyara tsayuwarta ta yi tare da cewa. "Idan har Yesu ALLAH ne waye ya halicci duniya? Dan dai kasan Yesu dai a duniya aka haifesa ko? Kuma ina da tabbacin kasan tarihin Noah (Annabi Nuhu) kana da tarihin shi kansa kakan Yesun watau Abraham kuke ce mashi ko? (Annabi Ibrahim) Idan har Yesu shi ne ALLAH waye ya halicci su Noah tin da bai zo duniya ba a lokacin No'ah! Ko dai sai da ya haliccesu kafin ya halicci kansa ne? Ya abin yake? Yi mun bayani!". Balain can, ai su kansu su momma kansu ya shiga ruɗani a waɗan nan tambayoyi na Sweetie, ai ba Big Bro kawai ba, idan za'a tara Kiristocin duniya dik babu mai iya bada wannan amsa. Shiru bai iya amsa mata ba, wlh shi kansa zuciyarsa ta san ga gaskiya, amma ba zai iya bi ba, dan tin lokacin da take yi wa Ronnie da'awa da lokacin zuwanta Church na farko ya fara karyata Yesu ALLAH ne a ransa, amma ba zai iya bin abin da suke so ba saboda wannan?. Cross ɗin. Ganin ya yi shiru ne ryasa ta sake cewa. "Wannan tambaya dik ba ita nike son yi bama, tambayar da nike son ka amsa mun ita ce, a cikin Ingila ta yaya na san ka karanta cewa ba halittun mutane bane suka fara zama a duniya ko? Nasan kun san da haka, ba mu bane farkon zama a wannan duniya, ALLAH ya taɓa wasu halittu da suka wanzar da ɓarna da zalunci a duniya wanda daga karshe ALLAH ya hallakar da su, to idan har kuka ce Yesu shi ne ALLAH ya aka yi tin bai zo duniya ba waɗan can halittu suka zo suka yi rayuwa har suka yi ɓarna aka hallakasu, aka kone duniyar gabaɗaya kafin daga baya a halicci Annabi Adam? Shi fa Yesu jikan jika ne na Abraham, ya fito kuma daga tsatson Annabi Ishaq wanda kafin shi kuma akwai Annabi Musa wanda shi ya fara aikin Yesu ya zo ya karisar, dan shi ya fara fafatawa da banu Isra'ila, ko baka san dikka da ku da yahudawa banu Isra'ila bane? Daga bayan Yesu wasu daga cikin banu Isra'ila suka ce shi ne ALLAH saboda ya yi magana yana jariri, suka karɓesa amma a matsayin ALLAH, saura da suka ƙi karɓarsa kuma su ne Yahudawa, nasan kana da tarihin Moses (Annabi Musa) kuma kasan a Taurat ya faɗi zuwan Yesun, dik kun san gaskiya amma saboda siyasa da kuma kin gaskiya manyanku suka ɓatar da ku, manyanku suna son zalunci da mulkin kama karya, annabawan ALLAH basu yarda da haka ba shiyasa suka canza Ingila ta gaskiya, suka ɓoye faɗar annabawa, suka shigar da siyasa da mulki acikin abin, dan su cigaba da cin karensu babu babbaka, suka durmuyar da kwakwalwarku a cikin duhu, to meyasa ALLAH ya baku rai da lafiya ba zaku fita ku yi bincike dan nemo addinin gaskiya ba? Ko dan kuma kuna jin daɗin ƴancin da suke baku na ku yi komai ba komai bane daga duniya sau Kaduna ko? Babu lahira, sun cusa maku cewa ai Yesu ya zo ne ya mutu dan zunubinku, ku yi abin da kuke so jinin Yesu ya goge dik zunubin da zaku aikata ko? Uhmmm kasan me Yesu zai ce a ranar lahira a lokacin da kafurai suka ji azaba suka je garesa suna ya cecesu ba zasu iya jure azabar tsayuwar hisabi ba?............". Hannun da ya ɗaga mata ne yasa ta dakata tana kallonsa. Idanunsa gabaɗaya sun canza launi zuwa jajir kamar wuta, dan ransa ya fara ɓaci............ "Saboda ina sonki ba shi zai baki damar ki tsaya a gabana kina faɗa mun abin da kika yi niyya ba, kada ki sake yin magana a kan addinina, bana son addinin naku kuma ba zan bishi ba, ko zaki tilasta mun ne?!". Ya faɗa yana miƙewa tsaye. Dik da tsoronsa da take ji bai hanata sake cewa. "Tabbas zan tilasta maka komawa musulunci, dan shi ne addininka na gaskiya, kowa naka musulmine, ya za'ayi ka ce kai ba zaka musulunta ba? Baka son gaskiya Big Bro........". Ai bata karisa maganar ba ta ji saukar wani irin gigitatcen marin da ya sanyata ganin taurari, take ta ji komai ya ɗauke mata cak, wani irin jummmmm ta ji, take wani irin jiri mai karfi ya kwasheta ta tafi gabaɗaya zata faɗi. Da hannu ɗaya ya rikota ta faɗo saman lion chest ɗinsa. A razane momma da Smart suka miƙe tsaye, da sauri suka karisa kusa da su. Take shatin hannunsa biyar ruɗu-ruɗu suka bayyana a kan fuskarta. Word ɗin momma har yana haɗe wajen cewa. "Haba Unays, meyasa zaka taɓa lafiyarta? Is she not your wife? Ko baka sonta ne?"........ Smart ne ya karɓi zancen da cewa. "Sorry my blood, amma idan ka cigaba da yi mata irin haka watarana zaka rasa ta ne". Ɗan rage tsawonsa ya yi ya ɗauketa cak sai saman sofa ya kwantar ba tare da ya amsa su momma ba. A gefenta ya zauna yana sauke huci a hankali-hankali. A tare momma da Smart suka dawo suka zazzauna....... "Momma bana son sake jin wanna addinin naku, ki faɗawa Maysh idan ta sake mun magana a kansa she will lose some pad of her body!". With harsh voice ya yi maganar. Cikin alamar tausasawa momma ta ce. "Ba zata sake ba, amma please kada ka sake yi mata irin wanna mari ka ji?"........... Jinjina kai kawai yai ba tare da ya sake yin magana. A daidai lokacin ta yunkura a hankali ta miƙe zaune tana sunkuyar da kai kasa, ba karya ta maru fa gaskiya. "I'm so sorry, ba zan sake yi maka haka ba, ni ma nasan na yi kuskuren yi maka magana a haka babu respect, ni ɗin ce bani da control a kan addinina, amma zan kasance mai tausasa kalamai a kanka"...... Ba wai dan bata ji zafin marin da yai mata bane, no ita ɗin yarinya ce mai hankali da hangen nesa, kuma tabbas tai kuskure a yadda tai mashi magana, tin da so kuke ya musulunta ai ba ja in ja da shi zaku yi ba har kuna ce mashi baya son gaskiya, wanna baku nemi ya musulunta ba, a hankali zaku bisa har ya fahimci abin da kuke son ya fahimta, kuma ta yi wani tinani ne, Big Bro ba mutum ne da wani zai iya tankwarasa ba, idan suna son ya bi abin da suke so dole ne su bisa a hankali, kuma ita da yake balain kauna zata iya juya zuciyarsa idan ta bisa a hankali, shiyasa ta bashi wanna hakuri, tana son shi over, tana son su rayu a tare, su haifi ƴaƴa su gina zuri'a mai cike da farinciki, to dole zata jure, fushi ba nata bane, idan ta daure ta yi nasara lokaci zai zo da in tai fushi da shi ba zai iya barci ko cin abinci ba, dan haka hakuri da juriya shi ne nata a yanzu. Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke na jin kalamanta, juyo da kallonsa a kanta ya yi, ɗan rintse idanunsa ya yi ganin shatin yatsunsa a kan fuskarta sun yi jajir, har cikin ransa ya ji hakan batai mashi daɗi ba. In a cool way sosai ya ce. "Tashi mu tafi ɗaki". Satar kallon momma tai, dan ɗazun ta faɗawa momma ba zata sake kwana da shi ba. Da sauri momma tai gyaran murya tare da cewa. "Unays ina son yau ka kyale mun ita mu kwana a nan". Da sauri ya juyo da kallonsa a kanta. Nisawa mai ɗan nauyi momma tai kafin ta ce. "Ta iya tausa sosai, so nike ta mun, kuma akwai abin da zamu yi da ita an juma, please ka barmun ita ka ji?". Dik da yasan ba gaskiya momma take faɗe ba duba da yadda tongue ɗinta yake rawa, amma sai ya riko hannunta, cikin sanyin murya ya ce. "Dik abin da kike so shi nike so, ta zauna dake". Yana kai karshen maganar ya miƙe tsaye, a natse ya fara tattakawa ya nufi waje. Da kallo suka bi bayansa har ya kai bakin kofa, zai fita kenan ya juyo da kallonsa a kansu. Da sauri suka zare idanunsu, ya gansu sarai, amma sai ya ce. "Kai zo mu tafi tin da yanzu dik ɗaya muke". Yai maganar yana kallon Smart da gabaɗaya yau an yi mashi formating brain, abin da bai zata ba yau ya gani. Miƙewa yai ya bi bayansa yana tinanin dole su haɗa kai da Sweetie dan ganin sun dawo da shi kan hanya, Smart bai taɓa zatan girman ilimi da hangen nesan Sweetie ya kai har nan ba, gaskiya ya jinjina mata sosai. Suna fita momma ta dawo da kallonta a kan Sweetie, cikin tausasawa ta ce. "Ki yi hakuri kin ji ƴata? Kada ki karaya, zamu yi nasara In Sha ALLAH, na fahimci kece rauninsa, kuma ba zai iya yi maki komai ba, sai dai na lura baya son raini, kuma wanna a jininsu take, dik basa ɗaukar raini, ki rinƙa tauna magana idan zaki faɗa mashi, saboda zuciyarsu makauniya ce, idan ransu ta ɓaci suna mancewa da suna son abu". Jinjina kai Sweetie tai, a sanyayye ta ce. "Babu komai momma, nasan halinsa sosai, nima ɗazun ɗin ban san ya aka yi nai mashi magana haka ba, amma ina fatan ALLAH yasa kada in sake yi mashi magana ba respect haka". Alama momma tai mata da hannu a kan ta zo kusa da ita, da sauri ta miƙe ta je. Rungumeta momma tai tana zuba mata ruwan albarka kafin ta ce. "Kin ci abinci ne?". Kai ta jinjina alamar e ta ci................ Karya take yi bata ci ba fa, kawai bata jin kamar zata iya ci ne, dan yau King Of Heart ya mareta bayan fara soyayyarsu, abin ya taɓa mata zuciya. "To jeki hau bed ɗina ki kwanta ko? Daga yau a ɗakina zaki rinƙa kwana, bari in duba daddynku in zo, gobe zaku je ku gaida shi, sai ki shirya, dan ya ce yana son ganin sabbin yaransa". Ta kai karshe cikin tausasawa tana ɗan murmushi. Murmushi Sweetie ta saki kafin ta ce. "Ina sonki sosai momma"....... "Nima Ina sonki sosai ƴata, ina jinki tamkar Zunairata". Wani irin daɗi Sweetie ta ji har da kara kwanta mata a jiki. Shafa bayanta momma ta yi, almost 3 mins suna a haka kafin Sweetie ta raba jikinsu. Miƙewa momna tai ta nufi waje tana faɗa mata ta je ta kwanta. Momma na fita ta sauke ajiyar zuciya, a ranta ta ce. "Ba zan iya kwanciya a gadanki ba momma, sai dai a saman sofa". Ta faɗa tare da miƙewa ta nufi cikin ɗakin, ita da an barta ma ɗakinsu Mahreen zata wuce, bata san cewa ta wuci nan ba, dole ne ita da Pretty a basu tsaro sama da kowa a gidan, tamkar yadda za'a baiwa su Smart tsaro, dan su ɗin bugun zuciyar zakunan gidan ne, in babu su babu su Smart, idan babu su Smart kuma ai a yanzu babu Kingdom of Power yadda makiya suka yi masu zobe ta ko'ina haka, Smart, Big Bro, Ramish su ne power ɗin Kingdom ɗin a halin yanzu!. Saman sofar dake ɗakin momma ta kwanta tare da fito da wayarta, har ta kunna wutar screen ɗin kuma sai ta mike ta ɗauko bargo da pillow daga wajen closet ɗin momma. Ta dawo ta kwanta ta lulluɓa. Tana kunna screen light ɗinta ta ci karo da sakonsa. "Na ji zafin ganin yatsun hannuna sun bayyyana a kan kyakkyawar fuskarki, ban ji daɗi ba, ya ragewa matata kyau". Shi ne abin da ya rubuta. A ranta ta ce watau dai hakuri ne ba zai taɓa badawa ba, kai Big Bro sai shirin ALLAH, ita ta gane kuskurenta ta bashi hakuri, amma shi dik da yasan bai kyauta ba ba zai bada hakuri ba. Kwafa tai yi ta share message ɗin taki reply, wai irin ta nuna mashi tana fushin nan sai ya bata hakuri. Fita tai ta fara yawonta a media. Jim kaɗan ya sake turo mata sako. "Maysh ba zan iya cin abinci ni kaɗai ba, ki zo mu yi dinner a tare please". Tana gama karanta sakon ta sake fita abinta taki reply, yana ganin ta gani kuma, hakan yasa ya ji babu daɗi, zuciyar maza ba zata iya fushi da abin da suke so ba, ya sake rubuta mata. "Fushi kike yi da ni my Maysh?". Yes ta tura mashi. Yana gama gani ya rubuto mata. "Please ki daina kin ji? You're hotting my heart". Cikin sigar tausasawa yai maganar. Wani irin tausayi ya bata, bai taɓa yin soyayya ba sai a kanta, kuma irinsu idan suna son abu da zuciyarsu gabaɗaya suke so, shiyasa idan aka yaudaresu zaku ga suna kashe kansu, dan ba zasu iya jura ba, sun rigada sun bada zuciyar. "Ba zan zake yin fushi da kai ba to". Ta rubuta ta tura mashi. Yana zaune a saman sofar da yake kwana, wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya tura mata. "A hot kiss Maysh". Kyakkyawar murmushi ta saki kafin ta kunna voice, a shagwaɓe sosai ta ce. "Uhmm uhmmm ni dai a'a, ka bari dai sai mun yi aure zan rinƙa yi maka mai sanyaka manta hanya". Tin da ya kunna voice ɗinta ya sanya hannu ya ɗan dafe saitin zuciyarsa yana sauke ajiyar zuciya, Maysh tai mashi shagwaɓa, gaskiya ta narka zuciyar Big Bro, har ya ji dik wata damuwa tasa ta gudu, shi fa idan zata kwana tanai mashi shagwaɓa zai iya kwana yana saurara. "Maysh barci kike son hanani ko?". Typing yai ya tura mata. Take sai ga voice ɗinta ya dawo mashi. "Uhm uhm ni in yi maka voice kai kuma sai ka mun typing ko? Bayan kuma kasan bana gajiya da son jin voice ɗinka, rowa kake mun ni da kayana ko? To ni dai ka mun voice in ba so kake yi in yi kuka ba". Ai Malam Big Bro tin da ya kunna voice ɗin ya lumshe ido yana jin wani irin azababben sonta yana kara huda zuciyarsa, neman natsuwarsa yai yana faman rasata. In a cool way a fili ya ce. "Maysh kina neman wuce lissafina ki kure hakurina"........ Voice ya danna ya hau bata reply cikin sanyin murya mai narka zuciya...... Lokacin da ya tura mata hannunta har yana kerma wajen ƙoƙarin buɗewa ta ji me ya ce. A daidai wannan lokaci momma da King suna tsaye a tsakiyar room ɗin king, sun yi cirko-cirko, da ka gansu kasan suna cikin tashin hankali. Sai kai komo King yake yi tamkar wanda ya zagi sarkin aljanu watau Big Bro ana nemansa ruwa a jallo a duniyar sama jannati , sai haɗa gumi yake yi, momma ma dai gumin nan take haɗawa. To wai me yake faruwa ne kuma?. Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only please. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 Abin dake faruwa a nan shi ne, zuwansu Zarina England ashe ba iya zaman meeting kawai suka yi dan haɗa kai da kawo karshen Crown Of Power ba, sun sayo muggan makamai ta karkashin kasa, sannan sun yi gagarumin shiri, dan sun ce Kingdom of Power ba zata yaku gaba da gaba kawai ba, dole sai sun haɗa da su Missiles ta sama dan taimaka masu, shi ne suka sayi muggan makamai irinsu. Cruise Missiles, FOAB watau Father of All Bombs, shi ne mafi girma a cikin makami nau'in bombs da ba su da sinadarin nukiliya, sai Mother of All Bombs watau MOAB, da irinsu Conventional Bombs, JDAMs, GBU, da sauransu. Waɗan nan makamai ana amfani da su sosai cikin yaƙe-yaƙe, kuma suna ɓarna sosai. Ba su da sinadarin nukiliya amma suna iya ruguje manya-manyan gine-gine da filayen sojojin yaki. To kiran da akai wa King daga Anti-Ballistic Missile Systems office ɗinsu shi ne tin daren jiya suke faman kakkaɓe makaman da su Udey suke harbo masu, da yake su suna da S-400 da S-500, waɗannan manyan makamai ne masu iya harbo missiles har da na nuclear daga nesa sosai, suna daga cikin jerin system mafiya ƙarfi a duniya masu iya tare makamai su hanasu sauka a cikin ƙasa. Sannan suna da THAAD watau Terminal High Altitude Area Defense, ana amfan da shi wajen harbo makaman ballistic kafin su isa ƙasa.Yana kare ƙasashe da manya-manyan birane. Sai Patriot Missile System, ana amfani da shi wajen harbo makaman da ke tafe a matsakaicin nisa, yana da radar da ke gano harin kafin ya karaso kusa. Shiyasa tin jiya suke ta kakkaɓe makaman basu barsu sun sauƙa a cikin birnin ba. Abin da ya fi ɗaga hankalin King shi ne su a halin yanzu ma basu da manyan makaman iya mayar da martanin hakan, sai karfin sojojin yake kawai suke da shi wanda za'a iya gwanzawaeda su gaba da gana, tin ainahi sun fi mayar da hankalinsu kan gina addininsu da yake-yake ta karfin sojojin yaki, ko kaɗan basu taɓa damuwa da su nemi makamai dan irin wannan rana ba, shiyasa suka shiga damuwa sosai. (To komai na rubuta a littafina ko daga book one ne ku ajiye shi a kanku dan yana da amfani, waye ya taɓa zatan aikin Smart zai shigo cikin labarina sosai?🤔 Kun ɗauka kawai haɗa makamai yake yi shi da daddynsa dan jin daɗinsu kuma su samu kuɗi ko? To dan yaki ne wait and see.) Amma dai yanzu mu faɗawa King cewa ɗansa yana da wannan ilimi ne ko dai mu barsa ya cigaba da shiga damuwa? Dan dai kun san Smart da daddynsa tun farko sun ɓoye wannan batu, a sirrance suke yin kayansu, haihuwa mai daɗi, shi fa King dik ta in da suka zo mashi yana da ɗan da zai tsaya mashi a wannan ɓangaren, shiyasa ni stars na labarina suke da siffa daban-daban, kowanne da kalar aikinsa, yanzu dai idan da tsafi da aljanu suke taƙama muna da Big Bro, idan makaman missiles ne muna da Smart, idan ta jirgin sama zasu yi yakin muna da Ramish air force ne, idan kuma da warriors ne shi ma muna da zaƙwakuran renon Commander Zafar, idan ma mata zasu aiko muna da su Aunty MieMie, idan karfi gwamnati zasu nuna mana muna da uncle Abbas, ɗan siyasa ne, idan taimakon wata ƙasa zasu nema to shi Big Bro ta ko'ina nemansa ake yi da ya haɗa kawance da su dan su zo su kwashe mashi tattalin arzikin kasa su bashi muggan makamai da tsaro, to a faɗa mana me ba mu tara ba? Shiyasa dik aikin da star na labarinan yake yi da amfaninta, ba kawai ina basu aiki dan suna bane, a'a kowa da amfaninsa, aikin da zan yi amfani da shi nike sakawa!!. ---------------------🔥 Sosai momma ta shiga damuwa dan tana tsoron kada makaman nan a samu akasi su faɗo cikin birninsu, zai yi ɓarna, za'a rasa rayuka da dukiya. Suna cikin wannan jimami da tashin hankali ga can uban nuclear yana tsaye a gaban mirror ɗin Big Bro yana kallon kansa, ya fito daga wanka, Big Bro ya ce ya zo su kwana a ɗaki ɗaya tin da momma ta ce ko kallon Pretty bata yarda ya je yi ba, shi ne Big Bro to su je ɗakinsa kawai su kwana tin da momma dik ta tattare masu mata ta rike. "Rahilarh menene mafita a wannan al'amari dake tinkaromu ko in ce ya tinkaromu?". King ne ya yi maganar a cike da damuwa. Momma da gabaɗaya ta fara karaya ne ta amsa mashi da. "To yanzu dai sai dai in ce ka tara yaranka ka ji me shawarar da zasu yanke maka ko?". Shiru King ya ɗan yi kafin ya ce. "E zan zauna da su, amma Ramish baya nan ai". Jinjina kai ta yi. "E haka ne baya nan, amma dama ina son yin magana a kan Ramish, yakamata a yi gwajin jini dan yasan mahaifiyarsa, abin da ciwo sosai a ce bai san mahaifiyarsa ba, wlh na san kawaici kawai yake yi maka yake dannewa, amma yana son saninta". Jinjina kai King ya yi. "Kin yi gaskiya, ai dole ma zai ji ciwo, dole zai so sanin wacce ta haifesa, bari ya dawo zan sa dik a yi gwaji mu gani"...... Sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke, har cikin ranta take son Ramish, saboda tin farko ya fi ɗaukarta tamkar uwa sama da Mama, baku ga baya ɓoye mata komai nasa ba, ita ya fara nunawa Leesharh, kuma ita ta yi mashi jinyar Aesh ɗin tasa a lokacin da ya yi mata aika-aika, ya fi shakuwa da momma sosai saboda kyan halinta, kun san kowa ya zo gidan ma ya fi shakuwa da ita sosai. "Idan ALLAH ya kaimu da safe ki haɗo mun kan ƴaƴana manyan zamu yi zama da su kafin Ramish ya dawo, shi ma ya ce yana nan tafe In Sha ALLAH". Da okey Momma ta amsa mashi kafin ta wuce ta haye saman bed ɗinsa ta kwanta, dan wani marayan jiri take ji, tana son faɗa mashi abin da yake gudana a kan Big Bro, amma gabanta har faɗuwa yake yi idan ta tina babban ɗanta ba musulmi bane, abin ya tsaya mata a rai over, kuma ga wani irin magana da yake yi wai shi ba zai yarda da addininsu ba su ma kada su yarda da nashi idan sun yi ra'ayi, ta shiga damuwa sosai. King ya lura da tana cikin damuwa, amma ya ɗauka a kan yakin da ya tinkarosu ne, dan haka sai ya hau gadon dan rarrashinta ya kwantar mata da hankali. A gefe guda kuwa Smart ya gama shirinsa cikin sleep kaftan ne ya zo ya samu Big Bro zaune a saman sofa yana chat da Queen of his heart. "Yakamata mu yi taking dinner blood". Smart ya faɗa yana kallonsa. Ɗan haɗe rai yai. "Ba zan iya ci ba sai Maysh ta zo, na saba ci da ita a tare".......... Cikin zolaya Smart ya ce. "To ɗaukeni a matsayinta". Harara Big Bro ya dallah mashi kafin ya ce. "Bata da madadi ai". "A'a nima ban ce ai mata madadi ba, kawai mu je zan baka a baki, dan nasan bai wuce haka take yi maka ba". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya ja hannun Big Bro, dan dole yasa shi ya miƙe suka nufi wajen abincin. Zama suka yi, Smart ya zuba masu a plate ɗaya, ya sanya masu two spoon, Big Bro yana ta faman dannar waya Smart ya ɗebo abinci a spoon ya kai mashi saitin ɗan bakinsa yana faɗin. "Bismillahir-rahmanir-rahim". Aikuwa Big Bro ya buɗe baki zai karɓa jin abin da Smart ya ce yasa ya fasa karɓa, ya ce. "Ba zan ci abincin ba". Ya faɗa tare da yunkurawa zai miƙe. Da sauri Smart ya rikesa yana faɗin. "Sorry na manta ka ce baka son addininmu, to zauna ba zan sake ba". Harara ya dallawa Smart kafin ya koma ya zauna. Cinye wannan spoon da ya ɗebo ya yi ya sake ɗebo mashi wani, a wannan karon sai yai bismillah a cikin ransa kafin ya kawo mashi saitin ɗan bakinsa. Karɓa ya yi ya fara tauna a hankali yana rubutawa Sweetie ta zo ya bata abinci a baki kamar yadda Smart yake bashi. Yau dai har ya koshi Smart ne ya rinƙa bashi a baki, ko sau ɗaya bai taɓa spoon ba, ya zama shalelen Smart ba iya shalelen King kawai ba. -------------------------🔥 "Maysh, Maysh, Maysh, barci kike son hanani ko? To in na kasa barci kema ba zan bari ki yi ba, dan sai na zo ɗakin momma na ɗaukeki, sai dai mu kwana a zaune a tare. Yanzu please a hot kiss". Shi ne abin da ya tura mata a voice na ɗazun. Jin alamar muryarsa ta sauya sosai kuma wlh tasan idan ya kasa barci tsab zai zo ya tadata ita ma, sai ta nemi canza topic na hirar tasu ta hanyar tambayarsa ina mom ɗinsu da ya ce zai kawo masu?. Shiru ya ɗan yi kafin yai mata reply da. "Very soon zaki haɗu da mom ɗinki".......... "Mekafi so a rayuwarka My King?". Ta sake turo mashi. Nan ma shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Akwai Yesu, wannan daban ne bana haɗa shi da kowa, sannan my cross, Momma and dad, Omerish, Omar, my second mom (Elevender) Ronnie, Maysh, Zunaira dik da ban ganta a kusani da ni ba amma ina sonta, Jaish and twins, abubuwan da nike so suna da yawa kam gaskiya, but waɗan nan su ne the most". Ta yi mamakin ganin abin da ya rubuta, dan haka sai ta ce mashi. "Wanne kafi kauna wanda ba zaka iya rabuwa da su ba?". Kai tsaye ya ce mata. "My cross, momma, Omerish and you, then Omar". Mugun mamaki ne ya kamata ganin zai iya rabuwa da mutane irinsu Jaish amma ba zai iya rabu da cross ba, a gefe guda kuma ta ji daɗin yadda yake faɗan abin da yake a ransa ba tare da shakka ba, sannan ta ji daɗin yadda yake son momma da Smart, watau su ne ba zai iya rabuwa da su ba. Gaskiya abin ya ƙayatar da ita. "Wani special gift zaka bani a ranar aurenmu?". Ta rubuta ta turo mashi. Shiru ya ɗan yi again kafin ya ce. "Dik abin da kike so". Cike da zolaya ta ce. "Cross ɗinka nike so, dan naga kana son shi fiye da komai, in har ina da mahimmanci a rayuwarka to zan so ka bani". Ba da wani manufa tai wannan magana ba, ta yi ne kawai saboda zolaya dan kuma ta ga irin karfin son da yake yi mata. Tin da ta yi mashi wannan message ɗin bai sake yin reply ba, saboda baya karya, kuma baya son ranta ya ɓaci shiyasa ba zai iya faɗa mata abin da yake shirin fita daga bakinsa a kan wannan Cross ɗin ba, is better ya yi shiru. A wannan shiru da ya yi ne Smart ya zo ya jasa suka wuce wajen cin abinci. Da ya zauna zasu ci abinci sai ya tura mata cewa Smart na bashi abinci a baki, ita ma ta zo ya bata. Ta ɗan yi mamakin ganin bai bata amsar abin da ta buƙata ba, amma sai ta kawar da zancen dan ita ma dama ba serious take yi ba, zolayarsa kawai take yi, ta biye mashi kawai suka canza topic. AFTER TWO DAYS.🔥 Acikin waɗan nan kwanaki biyu da suka wuce abubuwa sun faru, ciki har da farfaɗowarsu Omaid, goyson yanzu ya samu cikakkiyar lafiya, kuma ya koma ainahin Omar ɗinsa, sannan su Sareena dik sun farfaɗo, da ta ji cewa ga abin da ya faru da Mammie ɗinta sai hankalinta ya tashi sosai, ta rinƙa kuka momma tana rarrashinta. Aneesa dai ta rabu da aljannun dake kanta, yanzu ta koma ainahin Aneesa yar mama. A ɓangaren Big Bro kuwa, da kyar ya yarda yai kwana biyu a daddafe ba tare da ita ba, ya kai karshen hakurinsa, ya ce lallai sai dai momma ta bashi matarsa, sai dai kuma a kan hakan kusan ɓatawa suka yi da Smart, dan Smart ya ce idan yana sonta ya musulunta, shi kuma ya ce ba zai musulunta ba, a cikin waɗan nan kwanaki biyun sun sakosa a gaba a kan lallai ya musulunta, shi kuma ya ce ba zai musulunta ba, da Momma taga ba sarki sai ALLAH sai ta sanar da King ga abin da yake faruwa, shi kuwa King da ya kirasa ya ce ya musulunta kai tsaye ya ce shi fa ba zai musulunta ba, kuma su daina yi mashi maganar addininsu ko ya bar masu kingdom ɗinsu. Da ya faɗi haka sai ran King ya ɗan sosu, zuciya ta ɗebesa ya ce. "In dai ba zaka musulunta ba babu kai babu auren Omaish, dan musulma sai musulmi!". Wannan magana ta yi mugun ɓata mashi rai har ya kusa ɗauke King da mari, amma Momma ta dakatar da shi, cikin fushi ya ce. "Babu wanda ya isa ya rabani da ita, zan aureta a gaban idonku ne! Kuma ni ba zan shiga addininku ba! Zan bar maku kingdom ɗinku, Amma sai na auri Omaish a gaban idanunku ku tabbatar da zan iya". Sosai hankalin momma ya tashi, dan tasan tsab zai aikata, ita wannan lamari ya sake jagule mata, wlh sam ba haka ta so ba, ta so su bi komai ne a hankali, amma king yana neman ɓata komai. Da ya faɗi haka sai King kuma ya ce. "Bazata yarda ta aureka ba, tasan me take yi ai!". Cikin fushi ya ce. "To ka hanata yarda zata aureni in gani!". Dafe kai momma ta yi tana salati a cikin zuciyarta, shi ma dai Smart shiru ya yi yana salati game da damuwa, dan tin jiya Big Bro bai kula shi ba, tin da Smart ɗin ya ce mashi ya musulunta ko su ɓata, shikenan Big Bro ya ce sun ma ɓata kada ya sake kula shi, ya ɗauka wasa ne, sai ya ga akasin haka, domin kuwa tin jiyan ko ya yi mashi magana baya amsawa, ya bashi hakuri har ya gaji Big Bro yaki kulasa, ya ji babu daɗi, ya ce ya yi danasani, amma dik Big Bro yaki sauraransu. To rikicin da ake ta yi kenan, yau tin safe da wanna rikici suka tashi, King ya kafe Big Bro ba zai auri Sweetie ba, idan har yana sonta to ya musulunta, kuma ita ma ba zata yarda ta auresa ba. Tsaye suke a tsakiyar ɗakin King sun yi cirko-cirko, ga can su Zarina suna ta faman yi masu ɓarin wuta amma suna ta ƙoƙarin karewa, har yanzu ko missile ɗaya bai sauka a cikin kasan ba dai. Momma, King, Smart and Big Bro ne suke tsaitsayen nan. A fusace Big Bro ya juya ya fita, kallon juna su momma suka yi, Smart ne ya ce. "Momma kada fa ace tafiyar zai yi da gaske, dan ALLAH kada ku barshi ya koma birninsa, idan har ya koma wlh ba zai sake yarda ya zo in da muke ba, kuma ba zai taɓa musulunta ba, dan ALLAH momma ku dakatar da shi, dan cetansa ku yarda a aura mashi Sweetie ɗin a haka, zamu yi kokari ya musulunta sai ayi auren gaskiya!". Momma ta lura Smart ya rikice ne, burinsa kawai kada ɗan uwansa ya koma birninsa, shiyasa har ya ce a aura mashi Sweetie ɗin, ya manta haramcin abin da yake faɗe. "Momma ki yi magana, dan ALLAH ku dakatar da shi, ke kaɗai zaki iya dakatar da shi, ki taushesa, ki faɗa mashi zai auri Omaish, ki cecesa momma". A tsananin ruɗe Smart yake maganar. King ne ya ce. "Babu aura mashi ita da zamu yi har sai ya musulunta, ko zai koma birninsa sai dai ya tafi shi kaɗai, ita kuma zamu mayarwa iyayenta ita". "Hmmmm daddy baka san shi bane, wlh ka ji na rantse ba zan yi kaffara ba a kan Omaish idan bai shafe masarautarsu a doran duniya ba, su karɓeta su ce ba zasu bashi ita ba? Tab lallai daddy baka son zaman lafiya, ina son ka fahimci wani abu dad, shi fa Big Bro karfi baya tankwarasa wlh, dama ka bisa a hankali ne zai yi abin da kake so, kana tinanin ko iyayen Omaish suka tsaya a gabansa sun isa su hanasa aurenta da ya ce zai yi ne? Ba addini ne da shi ba, yana iya kashe iyayen Omaish kuma ya aureta muddin suka ce zasu shiga tsakaninsa da ita, kai kanka daddy wlh ba zai raga maka ba, saboda shi yanzu a juye yake, ba daidai yake da mu ba, momma ki faɗa mashi waye King Of five Empires! Kasan da cewa shi sarki ne a Daular aljanu? Kasan da cewa shi sarki ne na Dauloli har gida huɗu? Kasan kujerar mulkinsa dake black world babu wani sarkin da yake da kwatanta a yanzu? Kasan karfin mulkinsa kuwa? Fito na fito da shi babu riba, gara kawai ku rarrashesa shi zai fi maku". Cikin tashin hankali Smart yake kora masu wanna jawabi. Yana rufe baki sai ga Big Bro ya shigo damke da hannun Sweetie. Yana zuwa ya saketa a tsakiyar room ɗin, ido cikin ido ya kalleta kafin ya ce. "Faɗawa dad zaki aureni kamar yadda kika mun alkawari". Ya yi maganar yana pointining King da yatsarsa ɗaya. Kallonsu ta fara yi one by one kafin ta tsayar da kallonta a kansa. Da kyar ta iya cewa. "Zan aureka, amma sai ka musulunta tukun nan zamu yi aure...." Bata iya karisar da maganar ba sakamakon tsawar da ya daka mata. "No Omaish! Ni ba zan musulunta ba, kuma dole yau zamu yi aure!". Ya faɗa tare da sake damko hannunta da nufin su fita waje, a ransa yasa yau zasu yi aure kuma zasu bar kingdom ɗin. Fisge hannunta da karfi ta yi daga cikin nasa, idanunta sun cicciko da kwallah ta ce. "A'a! Hakan ba zai yiwu ba, ba zan taɓa aurenka ba har sai ka zama musulmi, in kuma ba zaka musulunta ba to gaskiya sai dai mu hakura da juna......"....... Zazzafan marin mai tiriri da ya sauke mata ne yasa ta dakatawa da yin maganar. With a harsh voice ya ce. "Idan kika sake cewa mu hakura da juna sai na kashe ki! Ke matata ce, nawa ni kaɗai! Momma ki faɗa mata hakan!". Ya yi maganar yana nunata da yatsa. Wasu zafafan hawaye ne suka wanke mata fuska, zuriyarta na tafarfasa ta daure cikin fushi ta ce. "Ka dakeni iya yadda zaka iya, ka dakeni ka kara, amma ba zan taɓa zama matarka ba har sai ka musulunta, in kuma ba haka ba wlh na faɗa sai dai mu hakura juna". Gabaɗaya hankalin su momma ya yi mummunar tashi, ga shi dikkansu suna tsoron tinkararsa, saboda yadda suka ga ya zama tamkar wani zaki, sai huci kawai yake yi. "Haka kika ce?!". Ya faɗa a gadarance. Kai ta jinjina mashi alamar e, ta dafe in da ya mareta ga hawayenta na zuba tamkar an buɗe tap, idanunta sun yi jajir ta ce. "Na soka son da ko kaina bana yi mashi, na yi abubuwa dayawa saboda kai, na sadaukar da abubuwa dayawa dik saboda kai, amma kai meyasa ba zaka iya hakura ka musulunta dan burinmu ya cika mu mallaki juna ba?!". Tana kallon cikin idonsa ta yi maganar, abin da babu wanda ya taɓa kwatantawa, wai a kalli cikin idonsa a faɗa mashi magana yadda ake so. "Omaish ba zan musulunta ba, kuma dole zaki aureni, ke tawace! Yau ba sai gobe ba dole zaki zama malakina, wait and see". Yana kai karshen maganar ya juya cikin fushi ya nufi waje. Sai dai yana kaiwa dab bakin kofa zai fita kenan tamkar wanda aka buge da karfe ya yi wani irin baya-baya ya faɗi ƙasa. Da gudu Smart ya yi kansa yana ambatar sunansa. Ina ko motsi bayani. Yunkurawa Momma and King da Sweetie suka yi zasu yi kansa da gudu suma, sai kuma suka dakata cak. Dakatawa Smart ma ya yi da ambatar sunan nasa sakamakon wani irin takun sahun da suka fara jiyowa na mutane, kuma takun sahun abin mamaki daga sama ake saukowa izuwa cikin ɗakin, and ba na mutun ɗaya ba, taku ne sosai na mutane da dama. Nan fa momma suka hau kallon juna da King, ita ma Sweetie kallon Momma ta fara yi, da sauri Smart ya ɗago yana kallonsu Momma shi ma. Take ɗakin King ya Kara wani irin hasken gaske, da alama baki suka yi. Kafin su ankara sai ganin bayyanar mutane suka yi a saman sofas dake cikin room ɗin wasu kuma suka zazzauna a saman shinfiɗar King, ga wasu manya-manyan jiga-jigan warrior tsaitsaye sun kewaye ɗakin gabaɗaya, suna tsaye tamkar waɗan da aka sassaƙasu. AI wani irin razana Sweetie ta yi, da gudu ta nufi bayan momma ta ɓuya, King and Momma dik kai kallonsu kan mutanen suka yi. A wani irin slow Smart ya miƙe tsaye yana kallon mutanen. Sanye suke cikin fararen kaya tas tas, harta warriors ɗinsu amor na yakinsu farare ne tas, wasu irin kyawawa da su tamkar rahanai, ga su da haske fata tamkar madara, wani dattijo ne mai farin gashin kai tas, da wasu ƴan mata guda uku da kansu yake ɗaya, sai wata yar yarinya karama da bata wuci Sweetie ba, sai kuma wani matashin namiji da ba zai wuci su Smart ɗin ba, ga kuma wata dake cikin farin mayafi sun rufeta tamkar amarya. Wannan dattijo ya tsufa tukuf, dan a shekaru zai iya kai shekaru 300 da wani abu kam, to kun san shekarun aljanu ba daidai da mutane ba. Manyan baki ne daga Blue Kingdom, wannan dattijo shi ne mahaifin Elevender, kuma ita kaɗai ce yarsa, shi yake kula da kujerar mulkin Big Bro kafin ya zo ya karɓi kayansa. Momma ce ta yi ta mazan cewa. "Bayin ALLAH lafiya? Daga ina ku kuma?". Dikkansu kallonsu a kan Big Bro, da wani golden scapter dake hannunsa wannan dattijon ya nuna Big Bro. Sai ga shi ya miƙe zaune, kai tsaye a kansu ya sauke kallonsa, yana ganinsu ya kara ɗaure fuska tamau. Wani irin kyakkyawan murmushi dattijon nan ya saki har sai da hakwaransa farare kal suka bayyana. Miƙewa tsaye Big Bro ya yi yana harararsu kafin in a cool way sosai ya ce. "Nahna meyakawoka nan kuma?". "Da na ce ka zo ka ɗauki matarka kaki shi ne muka kawo maka ita, ta matsa lallai tana son ganinka, tana son tarewa". Nahna ya faɗa yana nuna wacce suka lulluɓe da mayafi. Kara ɗaure fuska Big Bro ya yi. "Nahna na faɗa maka bana so, Maysh kawai nike so a rayuwata, kuma da ita kaɗai zan rayu, dan haka ku tafi yanzu". Ikon ALLAH ikon gaske, yau su momma sun ga babban lamari, wai aljanu ne suka kawowa ɗansu ziyara, basu taɓa zata ba, su fa basu ma san cewa ita kanta BLOOD POWER da suke magana a kanta gingima-gingiman bakaken aljanu ne suke juya ta ba, bafa mutane ke juya ta ba, wlh aljanu ne, to kun san aljanu akwai yadda ake control ɗinsu, sannan idan kana basu jini zasu shirya da kai, Big Bro yana tare da su Nahna tin yana karami shiyasa yake iya gane aljanu idan suna waje, Omaid and Obaid, Sareena and Aneesa dik da bakaken aljanu aka haɗasu shiyasa yana kallonsu ya gane akwai muƙarraban da yake mulka a jikinsu, shi ma guyson aljanunne suke sanya shi wannan ɗan banzan azababben ciwon cikin, dikkansu ture aka yi masu. Kallon Sweetie Nahna ya yi kafin ya ce. "Idan kuma bata raye fa? Zaka karɓi Zalzaliha a matsayin mata?". Da jin wanna magana hankalin momma da Smart ba karamin tashi ya yi ba, da sauri momma ta kara kankame Sweetie gam tana kallon dattijo Nahna. Ita ma Sweetie kankame momma gam ta yi tana ƙoƙarin kamo dik wani addu'a da zai zo bakinta. Shi dai King izuwa yanzu wlh ya gama sarewa da saddakarwa a lamarin Big Bro, yanzu ya yarda da batun Smart da yake ce mashi ja da Big Bro ba abu bane mai yiwuwa, su lallaɓa shi shi ne kawai abu mai yiwuwa. "Nahna, idan ka yarda wani abin ya samu Maysh mutum ɗaya daga zuriarku ba zan bari ya rayu ba!". In a harsh way Big Bro ya yi maganar. Wannan matashi da yake zaune ɗin ne ya miƙe tsaye yana faɗin. "Kai Zartar (Sunansa da duniyar Aljanu kenan) ka manta waye Nahna a wajenka ne da zaka faɗa mashi irin wannan magana, kakanka ne fa.......". Kallon Big Bro a kan Nahna ya ce. "A karo na biyu kana son sake rasa wani jikan kenan shiyasa ka kyalesa ya shiga gonata ko? Ka faɗa masu cewa sarkin Dauloli biyar ne a tsaye a gabansu, ko su yi biyayya, ko kuma kai kanka ba zaka koma da rai ba!". Yana yin wanna furuci take dik waɗan nan jiga-jigan warriors na Nahna dake tsaron ɗakin suka zube gwiwowinsu a kasa domin girmamawa ga Big Bro, da farko basu ganesa bane saboda a cewarsu ya ɗan yi hudu, kuma tabbas fatarsa ta sauya daga yadda yake da, yanzu yana fita rana kunga ko iskar waje dole ta sauya shi, sai da ya faɗa masu cewa da sarkin Dauloli biyar suke ne yasa suka gane shi, sai suka yi zafan zube gwiwowinsu kasa dan kwasan gaisuwa, amma shi wannan matashi yana tsaye, hakan yasa Big Bro ya yunkura tamkar zai nufesu. Da sauri Nahna yasa kafa ya daki kafafun matashin sai ga shi ya zube gwiwowinsa a kasa domin girmamawa. Magana one after the other Big Bro ya fara yi a natse wajen cewa. "Ku tafi yanzu, kuma kada ku sake zuwa sai na nemeku, sai dai ku sani muddin wani abin ya sami Maysh jininku ba zai yi saura a doran duniya ba!". Cikin bada umarni ya yi maganar. Ai yana rufe baki suka ɓata ɓat daga ganin su momma, da alama suna tsoronsa, ko da yake dole su bashi girma saboda sarkinsu ne shi, yana rike da zoben dake juyasu wanda kuma suka balain tsoro, shiyasa suke yi mashi biyayya, Elevender ce ta bashi wannan zobe da zai iya juyasu da shi. Dawo da kallonsa a kan Sweetie ya yi, ta wani kankame momma tana kuka. A tare momma da King suka sauke ajiyar zuciya, Smart kam dama tun ɗazun yake ta faman sauke nasa ajiyar zuciyar. Juyawa Big Bro ya yi zai fita King ya katse shi da cewa. "Na yarda zan aura maka Maysh ɗin taka"........ Da sauri ya juyo da kallonsa a kan daddyn nasu. Smart da momma ne suka kalli juna kafin Momma ta mai da kallonta a kan King. "Ko baka musulunta ba zan aura maka ita, kuma babu wanda zai sake rabaka da ita". King ya sake faɗa. Da wani irin kallo mai wuyar fassaruwa Big Bro ya bi King, a natse ya ce. "Yau za'a aura mun ita ba sai gobe ba!". Cike da bada umarni ya yi maganar. Tabbas a yau zan aura maka ita, a yanzu ma kuwa, amma sai dai irin aurenmu za'ayi maka, ma'ana irin al'adarmu, ka yarda?". "Koma wani iri ne ku yi, ni dai aure kawai zaku mana". Ya faɗa yana mai da kallonsa a kan Sweetie dake ta fama zuwa girgizawa Momma kai tana cigaba da ruwan hawayen dake kona mashi zuciya, idan tana kuka har wani jiri azaban zogi zuciyarsa take yi mashi. Smart da ɗazun yake cewa a ɗaura ko da Big Bro bai musulunta ba ma yanzu ya janye kalamansa, dan bai aminta da hukuncin King ba, saboda ɗazun baya cikin hayyacinsa ya faɗa, burinsa kawai su dakatar da Big Bro daga komawa Birninsa. "Okey to bani sadakinta yanzu, bari in kira su Jahiz and Abbas su zama shaida, Abbas zai zama waliyinka, ni kuma zan zama waliyinta". King ya faɗa. Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya Big Bro ya sauke kafin juya ya fita da nufin yana zuwa bari ya kawo sadakinta. Waya King ya ɗauko ya kira uncle Abbas and Uncle Jahiz dan su zo su zama shaidar wannan aure. Cike da tashin hankali momma ta ce. "Amma kasan hakan haramun ne ko?". Kai King ya jinjina alamar e ya sani, momma zata sake yin magana ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu kafin ya ce. "Please Rahilarh, nasan daidai da ba daidai ba, dan haka ki kyaleni kawai, aure kuma tamkar an ɗaura an gama yanzun nan In Sha ALLAH". TASHIN SENSE KENAN. Cike da tsananin tashin hankali Sweetie ta rushe da kuka mai sauti tana ƙoƙarin durkushewa kasa momma ta yi saurin rikota. Cikin sigar rarrashi ta ce. "Ki yi hakuri Omaish, na tabbata ALLAH zai kawo mana mafita". Gagara yin magana Smart ya yi, dan kansa ta kulle ne. Daidai lokacin sai ga Uncle Abbas and Uncle Jahiz. Uncle Abbas ya yi rama sosai saboda tashin hankalin abin da ya faru shekaran jiya, ya shiga damuwa. Suna shigowa sai ga Big Bro ma ya shigo hannunsa riƙe da wani white box mai shegen kyau yana kyalli sosai. A gaban King ya zo ya tsaya tare da miƙo mashi box ɗin ba tare da ya yi magana ba. Karɓa King ya yi, a sanyaye ya ce. "Wannan shi ne sadakin ƴata Omaish, Abbas ina son ka yi wa Unays walici a yanzu za'a ɗaura wannan aure". Cike da mamaki har suna haɗa baki wajen cewa. "Aure kuma yaya?". Kai King ya jinjina masu alamar e. Uncle Abbas ne ya ce. "To amma yaya meyasa ba za'a ɗaura a masallaci ba?"....... "A nan za'a ɗaura kuma yanzu". King ya faɗa. Matsawa Big Bro ya yi kusa da bed ɗin King ya zauna tare da yin ƙasa da kai yana jiransu kawai, baya son ya yi wa Sweetie magana, dan ta ɓata mashi rai fushi yake yi da ita, da zata ce su hakura da juna ta san how much he loves her ne? Kashe shi take son yi ne? Ya yi alkawarin ba zai sake kulata ba sai ta bashi hakuri, amma kuma tsabar ɗan duniya ne shi ya tsaya tsayin daka a ɗaura masu wannan aure, wannan kuka da take yi har cikin ransa yake jinsa, amma ya danne ya shareta yana jiran a ɗaura masu aure. Jinjina kai Uncle Abbas ya yi tare da cewa shikenan. Miƙa mashi box da Big Bro ya bashi King ya yi, karɓa Uncle Abbas ya yi yana jiran karin bayani. A natse king ya kora mashi bayanin cewa sadakin ne wannan. Uncle Jahiz kam baki ya saki yana ganin irin wannan aure yau. King ne ya ce. "Omerish and Abbas ku ne ta ɓangaren Umays, ni da Jahiz ta ɓangaren Omaish". Na'am suka yi da wannan zance. King ya sake cewa. "Mu zauna saman shinfiɗa". ....... A tare suka koma can suka zazzauna. Nan fa King ya sake cewa. "To mu fara". Uncle Abbas ne ya ce. "Ni Abbas Abdul Malik ina nemanwa ɗana auren ƴarka Omaish." Sai kuma ya yi shiru bai karisa ba, dan bai san sunan babansu Sweetie ba. King kuwa sai ya ce. "Ni uban Omaish Omranish Abdul Malik na bawa ɗanka Unays Zuhair Abdul Malik auren ƴanta kan sadakin da na aminta da shi!". Tashin hankali, yau fa ake yinta, zazzaro idanu momma ta yi, dan ita ta ɗauka wasa King yake yi, sai ta ga da gaske da suke aikawatarwa, aure ya kullu, MY PEOPLES AKWAI BALAI KUWA, YANZU WASAN ZAI FARA, THE CROWN PRINCE OF FIVE KINGDOMS WATAU KING UNAYS AND PRINCESS OMAISH OMRANISH, TAB MUJE ZUWA. Ai Sweetie na jin wannan furuci nasu ta yanke jiki zata zube kasa tamkar walkiya haka Big Bro ya miƙe ya tarota ta faɗa saman Lion chest ɗinsa, tamkar ba shi ne ya ce ba zai sake kulata ba, dik fa zafin sonta ne yake dukan zuciyarsa bawan ALLAH, dik a kanta ya yi wannan birkicewa. MEYASA KING ZAI HAƊA WANNAN AURE BAYAN YASAN HARAMUN NE? MEYASA WAI? HMMMM AKWAI CAKWAKIYA FA. Littafin RAWANIN ZALINCI na kuɗi ne, 1k kacal ne kuɗin karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuɗinsa book ɗin nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only please. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍